*HAFSATU MANGA _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy Assalamu alaikum Habibaties, fatar duk kuna lafiya 😍 Na sake dowowa da labarin kauye kuma labarin sarauta mai suna HAFSATU MANGA 👌 Labari ne mai cike da kauyanci, ban dariya, sarauta da kuma makirci. Happy reading 😍 _____________________________________ 1⃣ A hakali ta sauko saman Motar fuskarta ɗauke da damuwa. "Na gode" Ta furta murya ƙasa-ƙasa kamar mai shirin yin kuka. Dattijon da ta yi ma godiyar ya ciro wata tsohuwar naira ɗari ya miƙa mata yana faɗin "Karɓi wannan ki siye abinci" Sai da ta share hawayen da suka zubo mata sannan tasa hannu biyu ta karɓa tana masa godiya "Na gode Allah ya saka maka da alheri" "Babu komai Allah yayi miki mafita" Cewar Dattijon, mutanen da ke cikin Motar suka amsa da "Amin" Sannan Dattijon ya tashi Motar suka hau titin unguwar Gada biyu, titin da zai sada su da tsakiyar birnin Gusau. Da kallo ta bi Motar itacen, hawaye na bin fuskarta, sai da ta daina hango Motar sannan ta maida dubanta gurin manyan gidajen da suke gabanta, wata irin ajiyar zuciya ta sauke mai haɗe da kuka mai ƙarfi, kukan da bata san ta ina yake fito mata ba, kukan da ba ta san ranar tsayawarsa ba, hawayen da babu mai share mata su, sai Ubangijin daya ƙaddaro mata rayuwar da ta tsinci kanta ciki. Ba ta damu da rashin takalminta ba, ta cira ƙafafunta cikin rashin kuzar tana ɗingishi ta nufi wata ƴar kwarkwaɗar data hango wadda ke tsakankanin gida da gida, cikin kwarkwaɗar ta shige ta zauna saman simintin dake gurin sai ta fashe ta sabon kuka muryar a daƙishe saboda majinar data kama maƙoshinta. Kuka take mai tsuma zuciyar mai sauraro, kuka mai ban tausayi, kukan rashin Uwa da Uba, kukan rashin ƴan'uwa da abokan rayuwa, kukan rayuwar da ta samu kanta da kuma wanda zata zo mata nan gaba, kukan rashin sanin makomarta, kukan baron duniyar jindaɗi, duniyar dake cike da masoyanta da abonkan rayuwarta, lokaci ɗaya komai ya tsarwatse mata ta rasa komai nata, yau gata cikin duniyar da bata san kowa ba. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, na shiga uku na bani na lalace, wayyo ni Allah na" Ta furta hakan yafi a ƙirga kamin kuka ya ci ƙarfinta, ta ɗauki tsawon lokaci a gurin tana kuka ba tare da kowa ya kula ba, kasancewar unguwar manyan mutane ce, ba kasafai za ka ga mutane a unguwar ba, sai Motacin dake kai da kawo suma kuma ba sosai ba, mutane dake tafiya da ƙafa kuma tsinta-tsinta ne kowa na sha'anin gabansa, ba kowa ba ne zai kula da gurin da take zaune balle har a iya gano da mutun a gurin kasancewar yamma tayi sosai. Hakan ya bata damar tausayawa kanta, ta ci kukanta har ta gode Allah ba tare da kowa yaji ba. Kiran Sallah Magariba ne ya saukar mata da natsuwa har ta samu damar jan numfashi ta lumshe ido tana sauraren Ladani tana girgiza kai. Yau Magariba tayi mata ba'a gida ba, wasu zazzafan hawaye ne suka fito daga idonta dake rufe suka gangaro zuwa kumatunta. A she kayi kuka a kula da kai a baka haƙuri gata ne, ji take kamar wani ya zo ya dafata ya rarrasheta kamar yadda mahaifiyarta take mata a duk lokacin da take kuka, amman ina! Yau ta rasa wannan gatan, lokaci ɗaya haske ya zame mata duhu, fari ya koma mata baƙi duniyarta ta barkace ta zo mata bai-bai, ji take kamar ita kaɗai ce ta rage a duniya, jikinta na bata wani yanayi na daban komai ganinsa take kamar mafarki. Sai daf da ƙare Sallah Magariba sannan ta fyace majinar data ɓata mata fuska, ba ta damu da share hawayen ba, ta fito daga kwarkwaɗar tana cigaba da ɗingishi. Hanyar dake damanta ta kallah kamin hagu, sai shawartar zuciyarta take gurin zuwa, ga kanta babu ko ɗankwali, zane da rigar dake jikinta ma ko wanne daban-daban ne kamar wata sabuwar haukaciya. Cikin unguwar ta kutsa kai, ba dan tasan inda za ta ba je ba, ita dai tafiya kawai take tana kalle-kallen manyan gidaje. Tafiya ta riƙayi har ta kusa kaiwa ƙarshen unguwar bata ga gidan da zata iya shiga roƙon mayafi ba balle abinci, a ƙofar wani ƙaton gida ta tsaya tana ƙare masa kallo, babban gida ne da aka ƙawata shi da ƙwayaƙwan lantarki, a gefen gidan kuma an yi masa kwalliya da fulawoyi masu kyau da ɗaukar hankali. A tunaninta babu mutane a gidan haka zuciyarta ta nasalta mata, gurin da fulawoyin suke ta nufa, kasancewarsu ba masu tsawo sosai ba, ya bata damar tsallakawa ta shiga ɗan filin dake tsakanin fulawoyin da kuma ginar gidan, zaunawa tayi a gurin zuciyarta cike da rauni da zullumin abunda zai same ta. Ɗaya bayan ɗaya tunanin ƴan gidansu ya soma dawo mata, nan take kanta ya fara sarawa tana son kuka amman ba hawaye, a haka ta gaji ta kwanta a gurin sauro na bin ƙafafunta da hannayenta, ba a ɗauki dogon lokaci ba bachi ya yi gaba da ita. Bachinta bai kai na mintuna ashirin ba, aka buɗe ƙofar gidan da ƙarfi, hakan yayi sanadin tashinta a firgice har tana ƙoƙarin yin ihu, a zatonta mutane da suka kawo musu wacan harin ne suka sake dawowa, ɗan bachin da ta yi yasa ta manta da inda take, da sauri ta fito daga cikin fulawoyin tana haƙi. Daga mai gadin har yaran gidan sakar mata ido suka yi, kowa kallon mahaukaciya yake mata, bama kamar mai gadin da ya haske ta da fitilar hannu. "Ke bar nan gurin" Mai gadin ya faɗa a tsawace. A maimakon tayi magana sai kawai ta fashe da kuka ta juya a firgice ta nufi sashen wasu gidajen, ba dan tasan inda zata ba sai dan kawai tayi nisa da gurin da mai gadin yake dan ta tsorata da yanayinsa sosai. A ƙofar wani gidan ta zauna tana cigaba da kukan, bata tuna ta jefar da naira ɗarin dake hannunta ba, har sai da cikinta ya fara kukan yunwa da ƙishin ruwa a lokaci ɗaya, wani irin murɗa cikin yake mata hanjinta na kukan yuwanwa, ji take idan bata ci abinci a yanzu ba za ta iya mutuwa, duƙawa ta yi a gurin ta matse cikinta ta rumtse ido. ______________________________ Labarin Masarautar Rishim da kuma Kauyen Kufawa. Labarine mai cike da sarkakiya, ban dariya, kauyanci, kurciyar Hafsat, tausayi, tashin hankali da dai sauransu [2/19, 9:46 PM] خديجة أبو بكر القلوي😍: *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 2⃣ Komawa tai can gefe ta zauna hawaye na bin fuskarta, kuka take son yi amman babu muryar kukan saboda rashin kuzari dake tattare da ita. Dama ta fara dubawa kamin ta duba hagu kamar mai tunanin inda zata je. Tana haka aka bude katon gate din take gefenta ta firgita sosai abun ka da bakauye sai kawai ta ranta cikin na kare ta koma can bayan kwarkwadar ta buya tana lekon mutumen daya fito daga cikin gidan ya doshi wata hanyar daban dan shi be ma kula da ita ba. Sai ta tabbatar yai nisa sannan ta fito tana tafiya a hankali sai waige waige take har ta isa bakin gate din, baki sake ta kai hannu ta tura kofar gate din sai ta jita a bude sai dai tai kara lokacin da ta turan din, hakan yasa ta sake arcewa kai kace ma biyota aka yi, babu komai a cikin zuciyarta sai tsoro da fargaba, cikinta kuma dauke da yunwa da kishin ruwa. Ganin babu sarki sai Allah yasa ta sake komawa duk kuwa da irin abunda zuciyarta take raya mata na cewar kille mata kai za'ayi a wannan gidan dan yai mata kama da na yan yankan kai, a hankali ta saka kanta ta leka harabar gidan, a yadda ta hango compound din sai yasa idanuwanta suka fiffito kamar wata zarrariya baki sake take kallon motocin dake harabar gurin. Tabbas gidan yan yankan kai ne, haka zuciyarta ke raya mata, sai dai hakan be sa ta zata iya komawa ba tare da ta nemi abunda zata jefa a cikinta ba duk da bata dan inda zata samoshi ba. Kamar ance ta juyo tana juyowa ta hango kofar Kitchen bude sai dai ita din bata iya banbance kitchen ne ko kuma wani abun na daban. Hango mutum na kallonta ta window yasa ta juyo har tana kokarin faduwa ta fita da gudu tana haki. “Na bani na lalace wacan aljanin nasu ya hango ne” Ta fashe da kuka sosai tana gudu iya karfinta duk da babu wani kuzari a tare da ita. Bayan wacan kwarkwadar ta sake komawa ta buya tana kuka babu hawaye, kwarkwada ce dake tsakanin gida da gida baka jin sautin komai sai iskar da ke kadawa, hakan ya bata damar tausayawa kanta da kanta tai kuka iya wanda take jin zai isheta amman ko kadan hawaye be zubo daga idonta ba. Lokaci lokaci tana shafa fuskarta wai ko zata ji saukar hawayen tun da bata ji sanyinshi ba, amman sai taji babu komai. “Hawayena ma har ya kare... ” Ta fada tana kara fashewa da kukan still babu hawaye. YARIMA ZAIN POV. Tana tsaye jikin fanfo yana wanke hannunsa ya jiyo karar taba gate, hakan yasa shi dagowa ya kalli gurin gate, kasancewar windows kitchen din da kuma dayar kofar duka suna fuskantar gate ne. Yasan Malam Adamu mai gadi be isa dawowa daga aiken da Anty Ummi tai masa ba, to waya turo gate din? Hakan yasa shi maida hankali sosai gurin gate din zuciyarsa cike da son sanin dalilin motsin kofar gate din. Bayan kamar mintuna uku sai aka sake turo gate din, karamin kai ya fara hangowa an ziro ana karewa gidan kallo, kai tsaye ya koma gurin windows yana son tantance abunda yake hangowa tana kallo inda yake sai ta juya ta zira da gudu, shi dai ba zai iya tantance abunda ya hango ba duk kuwa da kasancewar akwai wadataccen haske a ko ina na gidan, mutum ko aljan? Iyakar abunda zai iya tabbatarwa mace ya hango ba namiji ba saboda yawan gashin kanta, kuma karamar yarinyace sai dai idan mutum miyasa be hangota da tufafi complete a jikinta ba, ko dai mahaukaciyace ko kuma aljana haka zuciyarsa take raya masa sai sai tafi raja'a ga cewar aljanar ce ba mahaukaciya ba. Ji yai bashi da natuwar jiki da ta ruhi har sai ya tabbatar da abunda yake zargi ko ba komai ya kamata ya duba yaga ko minene saboda tsaro ba dan tsoro ba. Ta kofar kitchen din ya fita kai tsaye ya nufi gate din, yana isa ya kai hannu ya bude ya fita waje gaba daya ba tare da fargabar komai ba, cike da natsuwa yake kallon damansa kamin ya juyo zuwa hago, sai dai ko kadan be hango abunda zai sada idanuwansa ga kallon abunda ya gani dazu ba balle kuma har ya sake ganinsa, kamar zai juyo ya koma sai kuma yai gaba kadan ta inda kunnuwansa suke jiyo masa sautin kuka duk da bashi da tabbacin kukan ne. Ba'a iya jin sauwon takunsa balle kuma har mutum ya iya auna tafiyarsa, Yarima Zain irin mutanen nan ne da ba saka ta zuba zance baka saka suna kusa da kai ba har sai kamshin turarensa ya sanar maka da zuwansa, hannayensa duka biyu suna baya har ya karasa inda yake jiyo kukan. Wannan karon kallon Aljana yai mata dan ta bashi baya ne fuskarta tana kallon karshen kwararo, hakan ya bashi damar kallon bayan kanta da kuma sauraren kukanta, yasan babu abunda zai kawo mutum cikin daren nan kuma a irin wannan gurin ko da kuwa mahaukaciya ce, babu komai a cikin sautin kuka sai. “Yunwa wayyo yunwa zata kashe ni” Juyowa yai ya dawo zuciyarsa na raya masa abunda ya kasa natsuwa da shi, miyasa shi kadai ya ganta? Akan mi ya bibiyeta har ya ji tana jin yunwa? Idan be taimaketa da abinci ba mai zai faru da shi? Idan ma da gaske aljana ce mi zata masa? Har ya dawo cikin kitchen din wadannan tambahoyin ne a ransa, Anty Ummi ya tarar cikin kitchen din tana hada ma yaranta ginger tea. Kallo daya tai masa ta dauke idonta daman tasan yau kanenta baya cikin walwala saboda ta tabo masa inda baya son a tabo masa, bata bukatar tambayar damuwarsa domin hakan ya wuni a gidanta da abarsa. Tsaye yai yana kallon kofar gate din har ta gama hada tea ta mika masa nasa. “Kamar kana jiran wani” Ta fada tana kallon gate din ganin yadda ya tattara duka hankalinsa ya maida can. Hannu ya mika ya karbi kofin tea din. “Maybe...” Ya fada yana daga kafadunsa tare da tabe baki, sai ya kawar da idonsa daga kallon gate din. Aje kofin yai dan baya jin zai iya shan ginger a yanzu, yana son ya ce Amal ta kawo masa keys din motarsa dake falo kuma yana jin hauyin bude baki yai maganar hakan yasa ya nufi falon da kansa ya dauki keys dinsa ya fita ta kofar falon. Da sauri Anty Ummi ta fita ta kofar kitchen ta zagaya ta nufi inda yake kokarin bude motarsa tun kamin ta karasa ta fara masa fada saboda ranta a bace yake. “Au kayi fushi kenan ko? Saboda an fada maka gaskiya, kai ba dama a zaunar da kai ayi magana Allah da Annabi? Kanka farau mutuwa da zaka dauki abu ka saka a ranka? Ai ban san son da kake mata ya kai haka ba har sai ka hadiye zuciya ka mutu sai a binneka kusa da ita sannan hankalina zai kwanta” Tun da ta soma maganar be dago ya kalleta ba har ta gama ta juya ta koma, zaunawa yai cikin motar ya lumshe idonsa yana sauke numfashi a hankali. Ko kadan maganar Anty Ummi bata masa dadi ba, sai dai yasan ranta ne ya bace, kuma bata nufin komai a gareshi sai gyara domin ba zata so wani abun cutarwa ya same shi, ta fi kowa shiga damuwa da halin da yake ciki, shi kuma baya hango abunda take hangowa a matsayen mata a gareshi. Bayan kamar mintuna biyar zuwa shi da ya tashi motarsa, kamin ya karaso bakin gate din sai ga Malam Adamu ya dawo tare da Farhat Malam Adamu komawa yai gefe ya aje ledodin dake hannunsa ya bude masa gate Farhat kam yin tai yi kamar ba san da mutum a compound din ba ta wani dauke kai ta nufi cikin gidan. Da mugun gudu Zain ya bi ta kusa da ita kamar zai kadeta har sai da ta matsa gafe. Kwafa tai ta nufi kofar falon a fusace. Anty Ummi na zaune falo Farhat ta shigo kamar an jefota. “Wallahi Anty Ummi wannan kannen naki bashi da kirki kin ga yadda ya bi kaina da mota kamar zai takani, shiyasa bana son zuwa gidan nan idan yana nan” Murmushi Anty Ummi tai ta aje kofin ginger dake hannunta ta kama hannun Farhat ta zaunar da ita. “Kin riga kin san halin Zain amman kullum sai ki tai min complain akan matsalar, yanzu haka it wasn't intentionally amman kin wani fusata, kina da zagar min dan'uwa a gaban idona, kuma wasu abubuwan rayuwarsa ce amman idan baka saba ba sai ka dauka wulakanci yake maka” “Wallahi da gangan yai, shikenan dan yana dan sarauta sai ya dinga yi ma mutane wulakanci son sansa, haka ranar fa ina zuwan gidan nan ya dinga hararata” “No no no Zain amman baya harara haka dai kallonsa yake, maybe ya tsareki da idone ke kuma kika tsargu, amman ni nasan waye kanane” Anty Ummi ta fada tana dariya. “Ni dai gashi inji Anty Rukaiya tace wai idan na kawo miki ki kirata kayan mata ne...” Farhat ta fada tana dankama Anty Ummi bakar ledar dake hannunta. “Ba sai kin fada min ba, na sani marar kunya, tashi kije kar dare ya miki” Anty Ummi ta fada fuskarta babu alamun wasa, Sai ta ta dauki ragowar ginger da Anty Ummi take sha ta shanye sannan ta tashi ta fita tana mata sai da safe. Babu wani nisa sosai tsakanin gidansu da gidan Anty Ummi amman hakan be hanata gudu ba duk da kasancewar akwai haske a ko'ina. Ko da ta shiga gidansu har haki take saboda gudun data debo, da sanda ta shiga falon sanin cewar Ya Bashir na nan yana jiranta dawowar daman kamin ta fita ya fada mata zai yi magana da ita. Duk da hankalinsa yana gaban Plasma hakan be hanashi fahimtar shigowarwata ba. “Farhat bana nace ina son magana da ke ba?” Cak ta tsaya duk wani kuzari nata sai ya yanke, tsoro da fargaba tare da tunanin abunda zata fada masa suka cika mata zuciya lokaci daya. Zagayowa tai gabansa ta zauna tana mai nuna tsantsar ladabi da biyaya a gareshi ta risinar da kanta kasa tana jiran abunda zai fito daga bakinsa. “Ya kuka da Auwal?” “Ya na fada mishi sai ya ce dan Allah ka yi masa uzuri har ya dawo dan sunje Abuja gurin wani meeting da sun dawo zai zo ya sameka” Kai kawai ya daga mata, ta tashi jiki a sanyaye ta nufi dakinta, da shigar ta maida kofar dakin ta rufe ta fada saman katifarta tana sauke ajiyar zuciya, tana mai jin nauyin irin karyar da tai ma Ya Bashir sai dai idan ba karyar ta masa ba ya zata ce masa? Auwal din ne yaki ya fito a duk lokacin da tai masa maganar aure sai ya kawo mata wani uzurin, iya daga kafa tasan Yayanta yai mata kuma ya bata dukan danar data kamata amman ta kasa gane kan Auwal yadda yake ta mata yawo da hankali a duk lokacin da tai masa maganar aure har ta rasa gane kansa, a iya abunda ta sani zuciyarta tana son Auwal sosai kuma bata jin zata iya rayuwa da wani namijin bayan shi, wannan ne dalilin daya hana ta kula kowa a duk tsawon shekaru hudu da suka kwashe a tare, Auwal gwani ne kuma gwarzon da zai iya cinye ko wane irin kambu na masoya a fashen soyayyar irin tarairayar da kulawar da yake nuna mata a waje take fatan samun a gidansa, irin soyayyar da ake a cikin finafinai da littafai take son su yi ita da shi a gidan aurensu, saboda tana gani da tunanin babu namijin da zai iya bata wannan kulawar da soyayya kamar Auwal dinta. Farhat mace ce da idan tana son abu takan so shi duka, zata iya mutu da sake mutuwa ta kuma sake mutuwa akan Auwal, a shekara hudu nan da suka yi a tare babu wani a cikin familynta da be san da zancen Auwal ba, kama daga kawayenta har makota da yan'uwanta, tun tana makaranta gashi har ta gama tai service be taba maganar aikawa a gidansu ba, duk kuwa da sakancewar yana mata komai daya kamata saurayi yai ma budurwarsa babu abunda ya rage ta da shi, abu daya ne zai tabbatar wa da Farhat cewar Auwal yana da niyar aurenta saboda gabatarda ita da yai a gaban iyayensa shekaru biyu da suka wuce. Turo kofar da Anty Rukaiya tai ne ya katse mata tunanin da take. “Kin ce ta kirani?” A firgice ta kalli matar yayyan nata. “Ee tace zata kira ki” “Better” Tana fadar hakan ta juya ta bar jikin kofar. Farhat kuma ta busar da iskar bakinta tana lumshe ido. GIMBIYA HAMEEDA POV. Tsaye take jikin window dakinta, sanye take da dogowar riga mai ruwan zuma jikin rigar kamar na almiski anyi mata ado da stones masu haske da daukar Hankali, kanta babu dankwali, iskar hadarin dake kadawa yana watsar mata da gashinkai har ya baibaye mata fuska, bata damu da gyarawa ba da alama ma hankalinta kwatakwata baya gurin. Baka iya banbance abunda take kallo a tsakanin hadarin da soma haduwa tare da iska da kuma sauran taurarin da suke sararin samaniya. Jin motsin an taba kofar dakinta ne yasa ta sauke kanta kasa tare da kai hannunta ta share hawayen da suka zubo mata, juyowa tai a hankali ta kalli Abida irin kallon nan na neman dalilin shigowarta dakin. “Allah ya taimakeki naga garin akwai hadari ne shiyasa na shigo na rufe miki kofafin taga” Cewar Baiwar tana risinawa cike da tsantsan da kai. Ba ce mata komai ba ta taka a hankali ta isa bakin gadonta ta zauna, yatsun hannunta ta soma murzawa sai kuma ta fashe da kuka. Da sauri Abida ta karasa rufe windows da take ta karaso inda take ta risina har kasa tana kallon fuskarta cike da tashin hankali. “Allah ya taimaki uwargijiyata, mai zai kawo zubar hawaye a fuskarki a yanzu?” Bata ce mata uffan ba har sai da ta gama kukanta sannan ta share hawayenta ta nufi gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta. “Miyasa bani da sa ar rayuwa Abida? Miyasa komai na alheri yake tsallakeni ni na mana duniya take juya min baya? Miyasa nake ta rasa abubuwan da suke da muhimmanci a rayuwata?” “Duniya tai kadan ta juya miki baya Gimbiya Hameeda, komai a yanzu a hannunki yake” Abida ta amsa mata daga can inda take risine tana fuskarta Uwargijiyarta. “A cikin gidan nan da duniyar nan Hajiya Yalwa ta tsani kuka da kuma damuwarki data Yarima, zata jure komai amman ban da damuwarki data Yarima....” Hannu Gimbiya Hameeda ta daga mata daga can gaban madubin da take tsaye tai mata alama da ta fita. Cikin rawar jiki Abida ta tashi ta fice tare da jan kofar dakin. Zaunawa Gimbiya Hameeda tai tana cigaba da kallon kanta a gaban madubi, tasan babu abunda ta rasa na daga kyaun halitta da sura irin na ya mace, amman miyasa har yanzu Zain ya kasa yi mata irin kallon da take masa na son kasancewa da shi a matsayin miji kuma jagoranta? ‘Kina da gaskiya Abida na fi kowa gata a gidan nan, lokaci yai da ya kamata na daina kuka hakanan ni ma ai na cancanci farinciki kamar kowa, sakacinane yasa Zain ya tsallake ne ya auro yar'uwata, a yanzu kuma da bata raye ni ya kamata ace na maye gurbinta’ Shine abunda take sakawa a zuciyarta a fili kuma sai ta furta. “Mutuwarki tai min rana Haleema...” Ta furta tana wani shegen murmushin da ita kadai ta san manufarsa. #Sarauta #Baiwa #kuyanga #Comment #Vote #share [2/19, 9:46 PM] خديجة أبو بكر القلوي😍: *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 4⃣ FARHAT POV. Da tunani ta raya darenta hakan yasa bata samu bachi ba sai da bayan ta gama sallah asuba sannan bachi mai dade ya sace ta. Around 10:14am ta farka ta dade tana juyi saman gadon kamin ta sauko da kafafunta kanta sai jiri yake, duka mafarkinta akan Auwal ne ta rasa ta inda zata bullowa lamarin ba ta rasa yadda zata fahimtar da shi halin da take ciki. Daker ta unkura ta tashi ta shiga bathroom sai wata tafiya take jikinta duk yai mata nauyi, fitsari ta fara yi sannan ta wanke bakinta tana cikin wanke fuska taji an turo kofar toilet din an shigo. Saurin juyowa tai dan tasan mutum daya ke mata haka a duk fadin duniya. “Ya Bashir.... ” Ya furta muryarta har rawa take. Be amsa ta ba sai kallonta yake from head to toe, kayan bachi ne a jikinta wando da riga pink color. “Sai yanzu kika tashi?” “Ee.... Ya Bashir Anty Ruka...” “Bata nan taje aiki, su Ahmad ma an kaisu school. Kin yi breakfast?” “Aa daman yanzu nake son na yi” “Nima ban yi ba ke nake jira” Yana fadar hakan ya saki kofar toilet din ya juya. “Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un, ni dai na shiga uku” Ta furta tana fashewa da kuka, tafi karfin minti uku a tsaye cikin toilet din sannan ta fito hawaye na bin fuskarta. Saman gadonta ta ta same shi zaune yana jiran fitowarta, hakan yasa tai saurin share hawayenta. Tasowa yai ya karaso inda take tsaye yana kallonta da fuskarsa ba yabo ba fallasa. “Mi aka miki na kuka? Dukan yi nai?” “A'a” “To miye abun kuka a ciki? Haba Autar Mata miyasa kike haka ne? Sai ka ce ba wacce tai jami'a ba? Kina abu kamar ba wayayyiya ba?” Hawaye ya sake zubo mata sai yawo da ido take a kasa ta kasa daga kai ta kalleshi. Hannu yasa ya tallafo fuskarta yana shafawa. “Dan Allah ki daina zubar da hawayen nan, ni ya kamata ace ina zubarda su ba ke ba, Autar mata wa zai kalli fuskarnan taki da jikinki ya ce be kwadaitu da ke ba? Sai idan ba lafiyayye ba ne...” Ya karasa yana kai dayan hannunsa gurin kwankwasonta. “Ya Bashir kai fa dan uwana ne...” Ta furta cikin kuka. Hannu biyu yasa yana murza jikinta cikin wata irin siga tare da matsar da fuskarsa kusa da nata. “Farhat... Saboda kina yar'uwata na kawo kuka a gareki, ai kin san ban isa na tunkari kanwar wani ba ko? Wa zai min wannan idan ba yar'uwata ba, Farhat ki kwantar da hankalinki, zan miki duk abunda kike so zan baki kudi mai yawa sosai kuma ba wanda zai ji wannan sirrin kuma duk abunda kike so zan miki” Tai saurin ture masa hannu tare da matsawa baya. “Ni dai yunwa nake ji yanzu, ka bari na ci abinci” Yai murmushi kamar ba shi ba yana maida hannayensa cikin aljihu. “Je ki dauko mana breakfast a nan zamu ci” Kamar jira take sai tai saurin juyawa ta fita da sauri, tana fitowa bedroom din kai tsaye kofar fita daga falon ta nufa, taba kofar da tai yasa ya ji kara ya taso da sauri ya fito, tana hangoshi ta fice da gudu kanta babu dankwali ko takalmi bata tsaya sakawa ba. “Farhat.... ” Ya kwala mata kira, amman ina ko waigo ba tai ba, gudu take sosai kamar ance mata gashi nan bayanta. Fita babu mayafi ba sabon abu bane gurinta dan haka bata damu da rashin mayafin dake jikinta ba, balle kuma kayan bachin da take sanye da su, abu daya ya dame ta rashin takalmin da ke kafarta, ga kuma gudun da take kamar mahaukaciya. Sai da ta kai gate din su Anty Ummi sannan hankalinta ya kwanta ta soma tafiya har ta shiga ciki. YARIMA ZAIN POV. Komawa yai motarsa da sauri yana waige waige idan wani be ganshi ba, yana shiga yai mata key ya karasa gate din, horn daya yai mai gadin ya bude masa. A inda yai saba parking yai parking sannan ya fito ya nufi falon Anty Ummi yana kokarin budewa ta bude masa da kanta, sai wani dauke kai shi ala dole be huce daga fadan jiya ba. Ita kuma ta saka masa dariya. “Zain kenan kasan kana fushi da ni, miye na zuwa gidana kuma? ” “Dole ce tasa ai kinsan indai ba office ba bana gurin zuwa sai nan” Ya janye daga jikin kofar ya karasa shigowa. Sai ya nufi cushion ya zauna yana kallon wani gurin dabam. “Uncle....” Anty Ummi ta kirashi da sunan da yaranta suke kiranshi. Dagowa yai ya kalleta daga inda yake zaune. “Kamar akwai magana a bakinka” Shiru yai na wasu yan mintuna. “Wata yarinya na gani a kwarkwadar gidanku” “Mi tai?” Ta tambaya tana hade plates dinda suke kan dinning. “Ihun kwarto tai min wai zan taba mata nono, ni kuma i mean no no a a but ta dauka nononta nake nufi...” Ya karasa yana wani daga kafadunsa irin confusing din nan, shi kanshi abun ya tsaya masa a rai. Anty Ummi tasa dariya har da rufe baki. “Kai dai fada min gaskiya yadda kake gwaron kan nan zaka iya attacking wata fa shiyasa na matsa maka da maganar aure amman sai ka rika ganin laifina” Wata irin dariya ce ta subuce masa irin dariyar nan ta gaske, wacce ta bayyana fararen hakuransa da kuma dimples dinsa daya na gefen fuska, yasan Anty Ummi she's so friendly and funny. “Haba Anty Ummi mi zanji ajikin wannan yar mitsitsiyar yarinyar, ba komai fa a jikinta i just trying to help her, ina jin ma ruwan da aka yi jiyan nan duk a kanta ya kare” “Wai da gaske kake yi?” “I'm serious, tun jiya na anga da dare ta leko gidan nan tama ganina ta gudu, da na bi bayanta sai na ganta tana kukan yunwa” “A nan bayan gidan take” “Yeah” Anty Ummi ta nufi dakinta da sauri ta dauko mayafi, ko da ta fito Zain yana waje yana jiranta tana fito suka nufi gate tare. Anty Ummi ta rigashi isa gurin kasancewar ba irin tafiyarsa ta kasaita take ba, tsaye tai tana kallon ikon Allah, yarinya ce karama yai zaune sai sheka kuka take kamar ba gobe. “Zain kar fa kasa mu sace yar mutane na san ka da son yara” Ta fada tana kallon Yarima Zain daya karaso yanzu. “Idan sato ta zamu yi ai wani gidan zamu je mu sato ta ko wannan ita ta kawo kanta” Anty Ummi ya karasa kusa da ita cike ta tausayawa. Matsawa baya tai tana fadin “Dan Allah ni dai karki min komai, ni dai ba ni da kowa a nan” “Ba zan cutar da ke ba ki kwantar da hankalinki” “To” Ta furta cikin kuka. “Wacece ke?” “Ni ce ni” “Wa ce ce ke?” “Ni ce ni” Ta sake amsawa a karo na biyu, sai Anty Ummi ta waigo ta kalli Zain dake kokarin gimtse dariyarsa. “Ke wace ce ke?” Ta tambayi Anty Ummi. “Sunana Anty Ummi, nan gidana ne ina da yara hudu amman duk sun tafi makaranta” Ta karasa tana nuna mata gidan. Ta zaro ido waje. “Kai gidan yankan kai?” “Aa bama yankan Kai Allah ya tsare mu waya ce miki gidan yankan kai ne?” Tai Shiru tana ta kallon Zain, sai Anty Ummi ta nuna shi. “Wannan ne ya fada miki?” Ta gyada kai, alamar ee. Zain ya kara kallonta da mamaki, ita kuma ta wani daure fuska kamar da gaske shi yace mata haka. “Daga ina kike?” “Daga gidanmu” “Ina ne gidanku?” “Can garinmu” “Ina ne garinku?” “Kufawa?” Ta juyo ta kalli Zain. “Kasan garin?” “Aa shekaranjiya dai naji Mai Martaba yana maganar an kai musu hari...” Tayi karaf ta karbe. “Ee hari aka kai mana gayu suka kai mana hari da bindiga” “Su waye gayu?” “Barayi” Ya fadi kadan kadan dan kar aji, daga nan sai abun ya koma labari, kamar ba ita ce take kuka ba. “Idan aka ce musu barayi kashe mutum suke, da suka zo garinmu suna ta kashe mutane, sun kashe kakana da Baban abulle kuma ban san inda Inna larai take ba, ni kuma na gudu ina ta gudu har na hadu da mai mota ya kawo ni nan garin ya bani naira dari kuma darin ta fadi kuma yanxu yunwa nake ki kuma jiya ruwa duk akaina ya kare” Anty Ummi ta kalli Zain. “Yarinyar nan bata da hankali” Ta fada kadan kadan, ashe yarinya taji sai kawai ta fashe da kuka. “Wallahi ni ba mahaukaciya ba ce” Anty Ummi tai saurin daga mata hannu. “Tau ya isa, yanzu ki kwantar da hankalinki zan kira yan sanda na sanar da su saboda.... ” “Dan Allah karki kira yan sanda ni tsoronku nake Wallahi” Ta kara fashewa da kuka. Zain ya raso ya matso kusa da ita. “Kwantar da hankalinki, ba wani abun yan sanda zasu miki kawai za a sanar ne saboda tsaro” “Aa ni bana so” “Okay yanzu fada min miye sunanki?” “Sunana Hafsat Hafsatu manga” Daga Zain har Anty Ummi jikinsu sanyi yai jin sunan mahaifiyarsu. “Allah sarki...” Cewar Anty Ummi. Zain ya mika mata Hannu. “Sunana Zainudden amman ana kirana Uncle Zain wannan yayata ce” Ya nuna Anty Ummi. Sai ta saki baki. “Ko dai matarka ce?” “Aa yayata ce, baki ga mun yi kama ba” Ta kalli Anty Ummi ta kalleshi. “Ee zaka bani abinci na ci” “Eh mana zo muje ciki gida” Ya mika mata hannunshi. Sai ta lake kafada. “Aa ka taba min No-no” “Wallahi ba zan tana miki Nono ba, ba zan miki komai ba kinji na rantse” Ya fada da sauri. Har Anty Ummi na dariya. Ta dade tana kallon hannunshi kamin ta mika masa nata wani irin sanyi yaji a hannunta yasan wannan baya rasa nasaba da sanyin da ta sha jiya, ya rikota suka fita. A rayuwar Zain yana son yara fiye da kima, balle wannan da yaji ta da sunan mahaifiyarsa, ta kwanta masa sosai. Anty Ummi ce a gaba shi da ita suna baya, tasa duka hannayenta biyu ta rike hannunsa daya tana tafiya tana dingishi. “Miya samu kafanki” “Nima ban sani ba yanzu dai naji hana min ciwo” Ta amsa tana ta lekon gidan. “Ka rantse ba zaka min komai ba” Ya tsaya yana kallonta, ita dago kai tana kallonshi. “Idan baki yarda da ni ba, kiyi tafiyarki sai Anty Ummi ta kira miki yan sanda sai su kama ki” Tai saurin girgirza kai. “Aa na yarda da kai” A tare suka shiga mai gadi ya bude masa sai kallonta yake. Anty Ummi ta tsaya tana masa bayani. “Lallai tabbas naji an kai hari garin nan, dan garin bashi da nesa da damu a kauyen gindawa ne, dake karamar hukumar maru, I an ce an kashe mutane sosai Allah sarki nima na ganta jiya amman sai ta gudu” “Ashe dai da gaske ne” Cewar Anty Ummi tana kallon Hafsat cike da tausayawa. Hannunta Zain yaja suka karasa ciki bakin kofar falo ta tsaya tana kallon falon. “Ni dai tsoro nake ji... ” Ta fada kamar zata fashe da kuka. Risinawa yai ya rika duka hannayenta ya saka idonshi cikin nata. “Mama ba zan miki komai ba, ba kuma zan bari kowa ya cutar da ke ba, kin ga idan kika zauna can bbu kowa kuma akwai maciji zai iya cutar da ke” “Ai bana tsoron maciji...” Ta fada tana hade girar dama da hagu, murmushi yai ya dan ja mata kunne kadan. “Karya kike” Ta kyalekyale da dariya kamar ta saba da shi. “Amman ke daga ganinki baki jin magana ko?” “Haka nan ake cewa a garinmu amman ni nasan ina jin magana, kuma suna cewa ba ni da hankali a wai dan sun ga mamana mahaukaciya ce” Ta fada a shagwabe tana son yin kuka. “Aa kina da hankali mana, ina mamanki take” “Nima ban san inda take ba tayi hauka ta gudu, ta bar ni nan, maman bata da hankali, ita ta saka min wannan munduwar” Ta nuna masa abun hannun dake sanye a hannunta mai sunanta. A hankali ya taba munduwar hannunta cike da tausayinta. “Zo muje ki ci abinci” Anty Ummi ta fisge hannunta daga rikon da yai mata. Mikewa yai tsaye ya bi bayansu sai ya sameta falo tsaye tana ta kallon falon. Abinci Anty Ummi ta zuba mata ta kawo a plate ta mika mata. “Karki ce amman bari na kawo miki brush ki wanke bakinki kin ji?” “Zan iya ci ko ban wanke bakin ba” Tayi saurin zaunawa ta saka hannu a ciki ta fara ci, Zain ne yai saurin rike mata hannu sai Anty Ummi ta shiga dakin yara ta dauko mata sabon brush da toothpaste ta zuba mata ta mika mata tare da nuna mata bandakin dake falon. “Wannan ki wanke bakinki ga ban daki can” “Tau” Ta nufi inda aka nuna mata da sauri tana dingishi. Tana shiga bathroom din ta tsaya tana kallon abubuwan da suke gurin daya bayan daya take tabawa har tana gogawa suna kara. Tsalle tai ta leka kanta a mirro ganin bata cin masa yasa ta dauki bokitin ta kife ta taka akai tai tsaye tana kallon kanta. Yatsanta tasa ta taba toothpaste din ta lasa, tana jin zaki sai ta lashe duka, ta dauki shaving cream ta zuba a yatsanta ta goga a hakora, sai ta sauko saman bokitin ta fito daga bandakin. “Na wanke bakin amman ban ga ruwa ba” “To da me kika wanke?” “Wanda kika zuba min naji yana da zaki sai na shanye na zuba wani fari na wanke da shi, amman ban kuskure bakina ba” Tana karasa fadar hakan ta kai hannunta ta fara cin abincin. Daga Anty Ummi har Zain kallon junansu suke. Suna haka Farhat ta fado falon ba ko sallama, wani wawan kallo Zain ya watsa mata sai tai tsaye inda take tana kallon Anty Ummi. “Anty Rukaiya bata nan kuma...” Sai tai shiru bata karasa ba, Anty Ummi ta san me take nufi tunda tasan komai. “Shiga ciki” Ta wuce dakin da sauri har tana kokarin faduwa. “Idan nace miki yarinyar nan bata da hankali sai ki karyata ni ji yadda ta shigo ba dankwali kuma da kayan bachi, haka ta fito tun daga gidansu har nan” “Ina ruwanka da ita ko jiya ta fada min kayi kokarin kadeta, ba ruwanka da ita baka san damuwar da take ciki ba” Ya tabe baki tare da mai da kallonsa gun Hafsat take kallon Anty Ummi. “Mama ci abinci kinji bari na zo” Anty Ummi ta fada ganin yadda ta bar cin abinci ta sako mata ido. “Ni ba mama ne sunana ba Hafsat” Tana fadar hakan ta maida hankalinta gun cin abincinta. Anty Ummi ta ce “Na sani saboda kina da sunan Mamana nake ce miki ba zan iya fadar sunanki ba” Bedroom Anty Ummi ta nufa gurin Farhat. [2/19, 9:46 PM] خديجة أبو بكر القلوي😍: *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 3⃣ YARIMA ZAIN POV. A hankali ya kai dayan hannunsa ya cire tsadadden agogon dake hannunsa ya bude drawer ya dauko box din agogon ya saka shi ciki ya mayar, sai kuma yai tsaye a gurin kamar wanda aka dasa a gurin, baya iya tantance yanayin da yake ciki a yanzu shi dai yasan ba farinciki yake ba, kuma ba bakinciki yake ba, indan sabo ya saba da kakkausar lafazi daga bakin Anty Ummi dan haka ko kadan kalaman basu sashi damuwa ba, duk kuwa da kasancewar basu masa dadi ba. Amman yana jin kamar akwai abunda yake damunsa, yawun bakinsa ya hade ya nufi tagar dake bude yana kallon mutane da ke gudu suna fakewa daga ruwan saman daya fara sauka, hannayensa ya zuba cikin aljihu yana sauke ajiyar zuciya. Haleema ce ta fado masa a rai, irin rayuwar da suke da zamantakewar aurensu yake tunawa, hakika ta nuna masa so kamar yadda yake nuna mata, bata taba musa masa akan wani abun ba ko da kuwa shine mai laifi, ta kanyi kokarin ganin ta gusar masa da duk wani bacin rai, ko da wasa bata taba daukaka muryarta akan tasa ba, idan yana gida kullum tana manne da shi. “Ya Rabbi... ” Ya furta yana busarda iskar bakinsa. Mafita yake nema mafitar da ba zai taba samu ba har abada! ‘Taya zai rayu da wata maccen wacce ba Haleema ba? Taya zai sabu da ita?’ Shine abunda ya tsaya masa rai, ya rasa ta yadda zai fahimtar da Mai Martaba da kuma Anty Ummi su fahimci halin da yake ciki, shi dai be san so ba sai a Haleema ya zurfafa irin zurfafawar nan da har yanzu da bata raye yake jinta a kusa da shi saboda tasirantuwarta a zuciyarsa. Dada Yalwa ce kadai mace da har yanzu take tayashi jimamin rashin Haleema saboda ita kadai ce macen da take masa dukan gatan da yake so a duniyar har gobe, sam bata daukarsa Babban mutum kamar yadda sauran suke kallonsa ita a kullum kallon karamin yaro take masa saboda rayuwar maraici daya taso a cikinta. Shi kansa babu macen da take jin dadin sakewa da ita kamar ita da Anty Ummi, sai dai baya taba yardar yai sirri da ita saboda yasan Hameeda tana rabarta, kuma tana ma Hameeda kwatankwacin irin son da take masa kasancewarsu duka marayu, a zamanin yanzu babu wacce Yarima Zain ya tsana kamar Hameeda dan ko kallonta baya son yi. Wayarsa ce tai kara hakan yasa shi dauke dubansa daga waje ya maida gurin da wayar take, yai second uku yana kallonta tana da ringing sannan ya soma takawa a hankali ya karasa inda take, irin takun nan da zaka za ci wayar zata tsinke kamin ya karasa. Ganin mai kiran bashi da muhimmanci sosai a gurinsa yasa yaki daukar wayar har ta tsinke daman yau baya cikin yanayi mai dadi. Daukar wayar yai ya saka a aljihu ya nufi kofar fita da irin takunsa na da ba zaka zaci na dagawa ne da nuna isa ko kuma tausayin kasar yake ji. Bangaren Dada Yalwa ya nufa domin a can ne kadai yake samun ya sake a duk lokacin da yake cikin bacin rai da damuwa. Tunda ya doso sashenta hadimanta suke ta gaidashi sai dai ko daga kai be yi ya kallesu ba balle har ya amsa su. A falonta Babu kowa sai sayin ac da kuma kamshim turaren wuta dake tashi, kai tsaye ya nufi Bedroom dinta daman yasan irin lokacin nan bata zama falo da zarar anyi magariba take shigewa Bedroom dinta sai kuma gobe. Yana dora hannunsa a kofar dakin da zimmar turawa ya bude, sai gabansa ya fadi for no reason, hakan yasa shi janye hannunsa ya juya. “Yarima...” Cak ya tsaya jin an kirashi da muryar da yafi tsana fiye da komai a duniyar nan. Be juyo ba kuma be amsa ta ba, daman tasan ba zai amsata ba, dan amsawa tana masa wahala, a duk fadin gidan Mai Martaba ne sai Dada kawai zasu masa magana ya amsa musu ba tare da bata lokaci ba, sukan wani lokacin ko kallon basu ishe shi ba. “Dada tana ciki....” Ta fada kamar mai shirin yin kuka, zuciyarta cike da son ya dawo ya shiga dakin na Dada Yalwa, amman sai ya cigaba da tafiyarsa kamar ba dashi take ba. Tsaye tai tana kallonshi har sai da ya fice daga falon gaba daya sannan ta juya ta koma dakin na Dada. “Ya tafi...?” Dada Yalwa ta tambaya. “Ai daman ba zai shigo ba, tun da yaji muryata” “Dan yaji muryarki sai yaki shigowa?” “Amman Dada ai kin san yadda ya tsaneni ban san abunda na masa ba, ko kallon arziki baya min, yanzu ma dana masa magana ko kallona be yi ba” “Wai mi yake damun yaron nan ne? Jeki kira min shi” Har ta bude baki ta cewa Dada Yalwa ta aika wani sai kuma wata zuciyar ta hanata, juyawa tai ta fita tana ta tunanin irin yanayin da zata tararda shi, ba kasafai take son shiga part dinsa ba saboda hotunan da Haleema da take gani a falon wanda take tunanin a halin yanzu ya kamata ace ya manta da ita, tana ganin hotunanta ne suka dace a mazaumin na Yayarta wato margayiya Haleema. Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka take tafiya har ta isa part din Yarima, ajiyar zuciya ta sauke yafi a kirga kamin ta ta kai hannu ta tura kofar falon ta shiga, kamar ko yaushe yau ma akan hotunan Haleema da suke manne a falon ta sauke idonta, ba shiri ta hadiye yawu da karfi sannan ta karasa cikin falon tana rabon ido, Karaf ta sauke idonta akan Yarima dake tsaye jikin freezer yana kallonta. Daga inda take tsaye ta isar masa da sakon Dada Yalwa ba tare data karasa kusa da shi ba. “Dada na nemanka yanzu...” Bata jira tace abunda zai ce ba ta juya daman bata tsammaci zai ce wani abu ba, da kallon tsana ya bita tana daf da ficewa ya kirata kamar wanda be san sunanta ba. “Ke...” Da sauri ta juyo tana hade yawu. “Na'am” Shiru yai kamar ba shi yai kiran ba, kuma ta san bata isa ta juya fmta fice ba yace ta masa rashin kunya. “Kar Dada ta sake aikoki ki shigo part dina, bana son ganin abunda ya shafeki a part din nan...” Ya fada bayan wasu dakiku, ta gyada masa kai idonta na cika da hawaye, sannan ya juya ta fice daga falon. Da gudu ta karasa part din Dada Yalwa saboda kukan dake son subuce mata kuma bata son kowa ya ga kukan sai wacce take shaye mata hawayenta. A bakin kofar dakin Dada Yalwa sai ta tsaya ta hadiye kukanta hawayen ne kawai suke zirya a fuskarta, sannan ta kai hannu ta tura kofar dakin ta shiga. “Ke miyasa same ki?” “Yace ya tsanane baya son ganina karna sake zuwa part dinsa...” “Zain din ne ya fada miki da bakinsa?” Cewar Dada Yalwa cike da mamaki har tana gyara zamanta. “Dada da ace mahaifiyata tana da rai ko? Da ban rayu a gidanan ba, da Zain be isa ya wulakanta ni ba har ya fada min wa ennan maganganun, Dada saboda ina karkashin kulawar mahaifinsa ne shiyasa yake wulakanta ni, yana min kallon kankanci kallon daya yake min da bayin gida nan....!” Ta rushe da kuka tare da faduwa kasa jikinta na karkarwa kamar an mata mutuwa. Kibar Dada Yalwa be hanata saurin tashi ta nufi inda Hameeda take rusa kuka ba ta kamata, idan akwai abunda Dada tafi tsana a duniya be fi taga kukan Zain da Hameeda ba, ta tsana suyi kuka musamman akan maraici, hakan ba karamin kona mata rai yake ba. “Akwai wanda ya isa yai ikirarin ke ba yar nan gidan ba ce? Mi kika nema kika rasa a gidan nan da har maganar Zain zata tada miki hankali? Shi kansa be isa ya nuna ya fiki gata a nan gidan nan.....” Bata karasa ba sai gashi ya turo kofar dakin ya shigo, sai ta koma kansa da masifar kamar ba dan lelen jikanta ba. “Yaushe ka lalace har haka Zain? Taya zaka bude baki kayi mummuna furuci ga yar'uwarka? Idan baka sonta ai sai ka kasheta na gani ko? Wai mi yake damunka ne?” Be ce mata uffanba, duk fadan da take kallonta kawai yake kamin ya maida dubansa gurin Hameeda dake kuka a hankali ganin shigowarsa. “Ina jin gurin bakar matar nan da kake zuwa wannan Ummi ce take hure maka kunne saboda kazo ka tarwatsa gida nan dan nasan daman can ba son mu take ba, ai da ba haka kuke ba kuna shirinku amman tun da ta fahimci kana so Hameeda ta hure maka kunne tasa ka auro yar'uwarta yanzu kuma ya sake hure maka kunne ka dauki kiyayya ka dora maka ko? To baka isa ba” Kallon Dada Yalwa Yarima yake idonsa a sake cike da mamankin kalamanta, shi wa taba cewa yana son Hameeda da har Anty Ummi zata shiga tsakaninsu? Ko dai Hameeda ce ta kitsa mata wannan maganar.? Be ankaro ba yaji tana kara wani furuncin cike da bacin rai. “Wato iya gogaggiyar yar duniya ko? Sai ta koma can gefe ta rika zuga ka kana zuwa kana fada da yar uwarka ba gwaira ba dalili wato gata Professor gogaggiya” Rumtse ido yai cike da jin dacin kalamanta sannan ya bude ya kalleta idanuwansa har sun soma sauya kala. “Dada ki sassauta kalamanki akan Anty Ummi, bata wani buri a kan gidannan balle kuma har tai unkurin zige ni, Anty Ummi ba zata so abunda zai cutar da gidan nan ba ma balle kuma ni, Anty Ummi uwace a gareni kuma ita kadaice yar'uwata da na san zata fada min gaskiya komai dacinta kuma ba zata taba son na lalace ba ya kamata ki san da wannan Dada...” Ya juyo gurin Hameeda yana nunata da yatsa. “This is the best reason da zai sa na tsana abada, Dada ta aibanta min yar'uwa saboda ke, haka kike ma Haleema ko ki zo ki ce tayi abunda ba tai ba tana da kyaukawar mu'amala da kowa ban da ke...” Yana kaiwa nan ya juya ya fice cike da bacin rai. “Ee kasan ita wannan ba yar'uwanka ba ce daga sama ta fado, ko kuma tsintarta muka yi, kaji min yaro duk ita ce take hure masa kunne ita take kitsa masa komai annamimiya, ita ko damuwa bata yi da irin zaman da Zain yake yi tana nan ta kullafemu cikin ranta to Allah ya fita Wallahi, kinji har da kitsa masa wani munafurcin Haleema duk ita ce take hada ku...” Cewar Dada Yalwa cikin fushi daman can Dada ta tsani Anty Ummi saboda gani take komai da Zain ke yi ita take saka shi. *** *** *** Cike da bacin rai Yarima ya kwanta saboda abunda ya faru, daman duk abunda ya aikata Anty Ummi Dada Yalwa take blaming saboda be da gurin zuwa sai can kuma be da abokiyar shawara sai ita. Wannan dalilin ne yasa be farka cikin walwala ba, as usual Masallacin fadar yai sallah asuba, sannan ya dawo part dinsa yai azkar din safe. Around nine o'clock Abida ta kawo masa abincin safe wato breakfast, sai da ya shiga yai wanka ya shirya cikin kananan kaya ya shefe jikinsa da turare mai kamshin sannan ya nufi falon dan karyawa. Dinning room ya zauna yana bude abinci, it's his favorite indomie da kwai da kuma kifi sai ginger tea da. Spoon ya dauka ya soma cin indomie sai kawai yarinyar daya gani jiya ta fado masa a rai, ya tuna jiya gaba daya a mafarkinsa yarinyar nan ce har ruwa yana dukanta, kuma yasan jiyan anyi ruwa maybe bata samu gurin fakewa ba tun da yaga gurin da take zaune ba inda zata fake har tana kukan yunwa. Da sauri ya tashi daga cin abincin da yake ya koma bedroom ya dauki wayarsa da keys ya fice daga part din. A al'adarsa baya fita daga gidan har sai yaje ya gaishe da Mai Martaba da kuma Dada amman yau saboda hankalinsa ya dauko yana fitowa ya nufi parking space, motarsa ya shiga yai mata key tun kan ya karasa Babban Gate ya soma horn, cikin rawar jiki masu gadin suka bude masa suna gaisheshi. @360 ya hau titi, daga kan wurin sarkin zuwa gada biyu tafiyar 32 minute ce sai gashi ya isa cikin 18 minute saboda gudun da yai, a gurin ya fara tsayawa da motar ya bude ya fito hankalinsa duk a tashe sai a yanzu yake jin rashin kyautawar barinta a nan duk da be san ko wacece ba. Hangota kwance kamar matacciya yasa gabansa faduwa cike da sanyin jiki ya karasa kusa da ita. Ba a jin tafiyarsa dan haka bata san da mutum ba sai da ta ganshi tsaye a kanta, cikin rashin kuzari ta tashi zaune tana shirin fashewa da kuka jikinta sai rawa yake. Dukawa yai yana kallonta kamar yadda itama ta sako masa manyan idanuwanta tana masa kallon tsoro, a hankali ya kai hannu ya taba ta so yake ya tabbatar idan mutum dince da gaske. Sai akwai ta gantsara masa cizo, da sauri ya janye hannunsa yana dan bude ido tare da kare mata kallo, yarinya ce karama da ba zata wuce shakara takwas zuwa tara ba, gashin kanta yai bujibuji kamar mahaukaciya. Baya baya ta soma yi cike da tsoronsa. “Ke ke ke ba cutar da ke zan yi ba” “Ni ban yarda da kai ba...” Ta furta cikin shagwaba da son fashewa da kuka. “Ke listen....” “Ni ba lesa ne sunana ba, kai mugu ne...” “No no nono...” Be karasa ba ta zaro ido. “Kai dan iska ne ko? Ni bani da Nono” Ta dafe kirjinta tare da fasa wani uban ihu, aiko ba shiri ya tashi tsaye da sauri ya bar gurin har yana shirin faduwa... *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 6⃣ Zaunawa yai saman kujera ya dafe kansa, sam be jidadin tafiyar Hafsat ba, yasan bata da gurin zuwa kuma bata san ko ina ba a garin nan bayan haka kuma gata yarinya karama. “Uncle wacece ta tafi?” Amal ta tambaya tana kama hannunshi, dagowa yai ya kalleta kamin ya bata amsa Anty Ummi ta turo kofar falon ta shigo tare da sallama. Yaranta ne suka amsa mata suka je da sauri suna mata oyoyo ita kuma ta rumgume su fuskarta dauke da murmushi. “My headache an dawo ko?” Duk suka hada baki gurin cewa “Yes Anty Ummi” A hankali Zain ya juyo ya kalleta, sannan ya mike tsaye ya karasa bakin kofar inda take tsaye. “Wai mahaukaciyar yarinyar nan ta bude mata ta fita” “Farhat?” “Ita” Yana fadar hakan ya kai hannu ya bude kofar falon ya fice ba tare da ya kara cewa komai ba. “Zain kana son ganin laifin Farhat Wallahi to idan bata bude mata ta fita ba ya zata mata” Ta fada cikin yanayin damuwa, sannan ta nufi bedroom dinta Amal na biye da ita a baya, Ali da Muhammad kuma suka nufi kitchen dan neman abunda zasu ci. Ya samu kansa cikin yanayin damuwa sosai, yasan ko ya kansa a neman yarinyar nan be san inda zai ganta ba. Wani haushin Farhat yaji ya karu a ransa, duk ita ya dorawa laifi, kamar marar lafiya haka ya isa Kanwurin Sarki, tun daga bakin babban gate fadawa keta gaisheshi amman be kulasu ba har ya faka motarsa a babban kofar Mai Martaba, ya dade zaune cikin motar sannan ya bude ya fito ya nufi babar hanyar da zata sadashi da fadar mai martaba, a iya saninsa Mai martaba na fada yanzu dan yana shiga fada a duk Monday a daidai wannan lokacin gashi kuma dazu ya fita be gaishe ba da dada, dan haka ya kamata a yanzu ya shiga ya gaishe shi kamin ya karasa sashen Dada, tun da ya hango kofar fadar a kunne abun ya bashi mamaki, kawar da kwankwanto yasa ya kai hannu ya taba kofar fadar, sai ya samu kofar a kulle, hakan ya sashi fitowa gaba daya ya dawo ya zagaya ya mike doguwar hanyar da zata sadashi da cikin gidan. Duk gaisuwar da ake masa be ji ba saboda hankalinsa baya gurin, ko da ma yana gurin ba zai amsa ba dan be saba amsa gaisuwarsu ba. Tsakar gidan katon tsakar gidane mai cike da shuke shuken fulawoyi, an kawata jikin ginin da fanti fari sai aka kawatar tsakiyar da fenti golden mai haske da sheki, kowa da part dinsa gate ya raba su, daga gefen gate dinsu akwai wani gate na bayi da ma'aikatan gidan, daga bangaren hagu kuma akwai sashen da ake dafa abincin gidan na kowa da kowa, dama da kau kuma babban hanya ce da zata sadaka da sashen mai martaba. Bangare Hajiya Hadiza ya fara shiga katsancewar ita ce uwargidan mai Martaba, Sisters din ya tarar a cikin falon, cikin girmamawa da mutumci suka gaisheshi, be amsa musu ba kasancewar daya bayan daya suke gaisheshi, sai kawai ya ce “Ina Hajiya?” “Bata nan sun fita tare da Mama da kuma Dada Yalwa da Mai Martaba” Rafila ta amsa masa “Gurin me?” “Gurin gaisuwa, wani kauye wai Yayan Hajiya dake sarautar garin aka kashe” Juyawa kawai yai ya fice, hannayensa zube cikin aljihu, yana takawa a hankali har ya fita daga sashen gaba daya, part dinsa ya nufa kai tsaye yana ciro wayarsa dake ringing a aljihu, yai parking ya kara a kunne amman ya kasa magana kamar ba babban abokinsa ne ya kira shi ba. “Zain kasa muna da tiyata uku da rabi fa kuma ka fita yanzu” Sauke wayar yai a kunnesa ya katse kiran, a duniya ya tsani a tuna masa abu, ko da kuwa ya manta din ne balle kuma ba kasafai yake yawan mantawa da abubuwa. Keys yasa ya bude kofarsa, idan zai fita baya rufe janyowa kawai yake amman idan ya dawo sai ya bude da keys. Yana saka kafarsa cikin falon wani dadadden kamshi ya daki hancinsa, abun mamaki an gyara komai na falon an cire hotunan matarsa. Dada ce kawai take da keys din part dinsa, idan ma za a masa gyara a hannunta ake karbar keys a bude dakin, bacin ran dake cikin ransa ne ya karu, har ya soma jin numfashinsa na taushewa. Freezer ya nufa ya bude ya dauko gorar ruwa ya bude marfin ya kafa gorar a baki be sauke ba sai da ya shanye ruwan cikin gaba daya, sannan ya rufeta ya nufi kitchen ya jefata a kwandon shara. Miyasa Dada Yalwa zata masa haka? Saboda yai fada da Hameeda ko kuma saboda yau fita be gaisheta ba? Ko kuma tana nunanin ganin hoton Haleema ne ke sakashi yin fada da Hameeda. “Ban ga dalilin da zaisa ki dauke min hoton Mata ba Dada” Ya fada a haka kamar mai rada, kana ya sauke ajiyar zuciya kallon windows kitchen din. Ya dade a tsaye kamar sannan ya juyo ya nufo bedroom yana cire yellow T-shirt din dake jikinsa, sannan ya daurawa tawul ya shiga wanka. Be wani dade ba ya fito ya shirya cikin wasu kananan kayan ya fito da sauri dan lokacin shiga tiyarsu ya kusa. Be shiga wata motar ya shiga wacce ke part dinsa ba wacan ta dazu ba, a gagauce ya fita daga gidan, ko kadan baya son saba dokar aikinsa, yakan kiyayen duk abunda ya shafi aikinsa saboda yasan muhimmancinsa. 3:20 ya isa asibitin, a gurin sa aka tanada ma manyan likitoci su aje motocinsu ya faka motarsa. Sannan ya fito ya nufi cikin asibitin. “Allah ya taimaki Doctor” Wani mutun dake fitowa daga Emergency ya fada yana masa irin gaisuwar nan ta girmamawa. Sai a lokacin hankalin Zain ya kai gurinsa. “Sadiq me kake a nan?” Ya fada sanin mutumen da yai dan unguwarsu su Anty Ummi. “Wallahi wata karamar yarinya wani mutum ya kade shine muka raka biyo mutumen nan saboda ba a san kowa nata ba” “Ayyah Sorry Allah bata lafiya, zan shiga tiyata” Ya fada yana kokarin wuce, dan hankalinsa gaba daya yanzu yana gun tiyatar da zasu shiga. “Okay Allah yasa ayi a sa'a” Ya fada cike da girmamawa. FARHAT POV. “Marar mutunci bulutu, ai daman na san ba so na kike ba tunda uwarki ma ba sona take ba, yanxu duk hallacin da Bashir yai miki ki rasa da abunda zaki saka masa sai wannan? Idan ma da gaske ne miyasa baki zo kin same da maganae ba, sai kije xan wani guri kina fadar sirrin gidana, daman haka kuke da Ummi shiyasa baki da gurin zuwa sai can ko?” Faduwa tai zaune, idonta ya rufe ruf bata ganin komai saboda hawaye. Kalma daya ta Anty rukaiya bata shiga kunnenta bata ganin komai sai pre-wedding picture din Auwal da wannan yarinya. “Munafuka ai daman ya fada min, komai game da ke duk abunda kike masa yana sanar da ni na zuba miki ido ne kawai naga iya gudun ruwanki, yar iska kawai wato an kawo ki kin sha jar miya kin waye ko? Shine kike son hada ni da miji ni ki kashe min aure ki gina taki rayuwar, to Wallahi bari kiji na fada miki baki isa ba, kuma ki hada komai naki ki bar gidan nan tun kamin ma ya dawo, jaka kawai” Ta karasa tana jan wani mugun tsaki, ta juya a fusace ta fice. Hannu Farhat takai ta share hawayenta ta dauki wayarta ta saka password ta bude wayar, number Auwal ta lalubo har zata aika masa kira sai kuma ta kasa ta fashe da kuka. Ta kai minti talatin tana ta kuka sannan ta unkura ta tashi tsaye ta dauki Hijab din Anty Ummi da tazo da shi ta saka ta fito falo rike da wayar. “Gidan uban waye zaki? Ba nace ki hada kayanki ki bar min gida ba? O... Gidan Ummi zaki koma ta sake kullo munafurcin ta sake iskoni office ko? Koma ki hado kayanki koma” Ta turata da karfin ta koma dakin. Sai a lokacin hankalin Farhat ta fara dawowa jikinta har ta soma tuna maganganun dazu da tai mata, kayanta ta shiga hadawa sai kuma ta kasa, jin tai bata bukatar komai a yanzu , duniyar ma idan za a rabata da ita tana farinciki dan ita yanxu bata san wane irin hali take ciki ba. “Mama... ” Ta furta cikin kuka tana jin mugun son mahaifiyarta kusa da ita. Tashi tai da sauri ta dauki jakarta ta ratayawa ta fito daga dakin. “Ai kin san nan ba gidan ubanki ba ne ko?” “Tafiya zan yi Anka zanje yanzu Anty” Ta fada cikin kuka, bata tsaya jiran abunda Anty Rukaiya zata sake ce mata ba, ta nufi kofa hawaye na bin fuskarta kamar ba gobe. “Kara ma ki zo ki kwashe kayanki dan ni ko an dawo an bani hakuri ba zama zanyi da ke ba, makira kawai tsohuwar yar iska” Babu irin tambayar da mai gadi be mata ba, amman bata ma kula shi ba balle ta masa shi. Tayi sa'ar samun napep a bakin gate. “Babbar tasha zaka kai ni” Ta fada tana kokarin tsagaita hawayenta, sannan ta shiga Napep din. “Hajiya lafiya dai” “Ba komai” Tunda ya kama hanya be tsaya har sai da suka isa Babbar tashar gusau. “Ina zamu ki je Hajiya” “Anka” Ta furta tana hadeye kukanta. Da gudu masu tarbon mutane suka biyo Napep din suna tambayar inda zata je, mai Napep di ya amsa da Anka, sai suka nuna masa inda motar Anka take. Dari biyu ta mika masa bayan ya aje ta kusa da inda zata shiga motar anka din. Gabanta ne ya shiga faduwa tambayoyi nata zuwa mata a rai kala kala, ta samu damar yin kukanta ishasshen a cikin motar kasancewar ita ce ta farko kamin a samu wasu Passengers, sai biyar da rabi suka kama hanya Anka domin direbobin basa son tashi sai mota ta shiga, duk irin kiran da Jawahir take mata sai taki dagawa sai kuka take har passengers din suka fara tsarguwa wasu kuma suna tunanin ko mutuwa aka mata ne. Tunda suka kama hanyar garin kowa yake ta addu'a saboda sanin matsalar garin ta matsalar tsaro, Farhat kan bata komai sai kuka, har suka kai Mayanci, suna karawa gaba kadan suka ango wasu motocin an tsayar dasu a gefe sun danji tsoro sai dai ganin mutanen sanye da kakin soja yasa hankalinsu ya kwanta. Sai da suka karasa daf da su sannan suka gane cewar ba sojoji ne ba, fulanin nan ne na daji masu kashe mutane suka sanya kayan sojojin suna dauki da mugaye makamai. A take suka fitar da kowa dake cikin motar suka sa su kwanciya a gefen hanya, cikin har da Farhat dake kukan da zame mata na bakar rana. https://www.wattpad.com/story/179794212?utm_medium=link&utm_content=story_info&utm_source=android *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 7⃣ Anyi tiyata lafiya kuma cikin nasara kamar kullum, a Masallacin asibitin ya tsaya yai sallah la'asar sannan ya dauki hanyar gidan Anty Ummi.   A harabar gidan yai parking sannan ya fito ya nufi cikin gidan cikin rashin dadin rai, be samu kowa a falon ba, kasancewar yaran sun tafi islamiya, Anty Ummi kuma tana kitchen tana girki guri ya samu ya zauna ya maida hankalinsa kan wani film da ake a African magic channel. Yafi karfin minti talatin zaune a gurin sannan Anty Ummi ta fito daga kitchen sanye da abaya hannunta dauke da karamin roba, a hannun cushion ta zauna tana kallon dan'uwanta. “Kaga yarinya ne?” “Ban je namanta ba balle ma na ganta, nasan ba kusa zata tsaya ba” Ya fada ba tare daya dago ya kalli inda take ba. “Farhat din ma bata dawo ba har yanxu, na aika gidansu ance bata nan, na kuma kira wayarta a kashe Wallahi duk na damu” Tabe baki yai. Sai ya dauko wata magana. “Dada tasa an cire hotunan Haleema” Ko a yanzu ma be kalleta ba, sai dai sautin yadda muryarsa ya karantar da ita bacin ran dake zuciyarsa. Ajiyar zuciya ta sauke ya zauna daidai saman cushion din tana kallonsa. “Dada Yalwa tayi daidai kuma tayi abunda ya dace...” Sai a lokaci ya dago kansa ya sakar mata mayan idanuwansa yana kallonta, be yi mamakin furucinta ba, daman ya tsammaci hakan ita ce mace ta biyu bayan Dada da take kokarin saka shi ya manta da Haleema. “Lokaci yai daya kamata ace ka canja rayuwa Zain, a izuwa yanzu ya kamata ace ka yarda da kaddara kuma ka dauketa a yadda ta zo maka, shekara uku kenan da rasuwar Haleema a halin yanzu addu'a take nema ba tunani ba, mahaifinka ma baya jindadin rayuwar da kake kaine babba, amman kana maida kanka wani kalar mutum saboda mutuwa? Wacce tana kan kowa? Kai ma baka wuce ka mutum ba, balle kuma matarka da Allah be yi ta danka ba” Dauke kansa yai yana sauke numfashi a hankali. “Na kasa mantawa da ita ne Anty, tana yawan fada min tana tsoron kishiya, ina ganin kamar idan na auri wata ban kyautawa Haleema ba, musamman wacce suke son na aura din, uba daya suke da Hameeda amman kamar makiya suke saboda Hameeda bata son ta ko kadan, tana yawan min complain akan Hameeda, Hameeda ce kadai mace data hana Haleema zama lafiya da kwanciyar hankali a gidan nan, amman su kasa gane haka Mai Martaba da Dada suna son tsayawa akan sai na aureta, a ganinsu ita ta dace da ni saboda Haleema, a ranar da zata rasu ta rike hannuna, tana kuka tana cewa Zain karka barni ina jin tsoro, na tambayeta na ce tsoron me? Sai tace bata sani ba amman dai tana jin tsoro kuma bata son na tafi ashe tsoron mutuwa take, tsoron rabuwa da ni take, ina fita dakin da minti uku Allah ya karbi abarsa, i can't forget this” Ya cikama bakinsa iska tare da yin shiru na wasu yan mintuna sannan ya cigaba. “Anty bana jin akwai wata mace da zan iya zaunawa da ita naji dadin rayuwa da ita, itama kuma ta jidadin rayuwa da ni, Musamman wacce suke son hadani da ita, bana son Hameeda Anty kuma ni bana son bazawara, hankalina baya kwanciya da macen da bani na fara kusantarta ba, a kullum ina kallon Hameeda kamar ita ta kashe min Haleema saboda ita ta sakata a cikin halin da ta shiga wanda yai sanadiyar mutuwarta, taya za'ayi na zauna da ita? Taya zan ga farinta?” Anty Ummi ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, tasan yadda Zain yake son matarsa, tasan irin gwargwamaryar da matarsa tasha a gidan da irin kiyayyar da Hameeda ta nuna mata. “Wannan be isa ya zama dalilin da zaisa kayi ta zama ba aure ba, irin Haleema suna nan da yawa a duniyar nan, kuma nasan mai martaba yana kaunarka sosai xai so abunda kake so, dan haka duk yarinyar daka kawo xai sota matukar kana sonta, kayi kokarin neman kalar matar da kake so ka gabatar masu da ita tun gabanin su gabatar maka da Hameeda a matsayin matar aurenka, nasan ko Mai Martaba be yi haka ba, Dada Yalwa na daf da yin hakan” “Kin sani Anty, a dokar da kuma al'adar masarautar Rishim, yayan masarautar basa auren wacce ba jininsu ba, ko kuma ba jinin fulani ba, taya zan karya dokar da zata sa Mai Martaba ya cigaba da yi min kallon marar tarbiya, Dada kuma ta tsani matar da za a kawo a gidan?” “Ka bincika duk matar da kake so ni kuma zan tsaya maka kai da fata wajen ganin ka aureta, lokaci yayi da ya kamata ka rushe wannan dokar da al'ada ta gidanku, kana da hakki Zain kamar ko wane da, be kamata ka bar sarautar gidanku tana tauye maka hakki ba, kai ne Baban dan Mar Martaba idan ka lalace magauta dariya zasu masa kuma su maka, idan kuma ka gyaru shi kansa zai ji dadin hakan” Da sauri Zain ya mike tsaye fuskarta dauke da mamaki, maganar Sadiq ta dazun xe ta fado masa a rai na yarinyar da tai hadari kuma ba a san kowa nata ba, what if Hafsat ce. “Anty ina zuwa” Ya nufi kofar fita daga falon da sauri har yana kokarin tuntube. Anty Ummi kam da kallon mamaki ta bishi da shi har ya fice. Cikin a hanzarce ya shiga motarsa yai mata key, horn biyu mai gadi ya bude masa gate ya hau titi da gudu. Cikin yan mintuna ya isa ZAINUDDEN SPECIAL HOSPITAL, yana aje motarsa ya nufi Emergency da sauri, Nurses dake Emergency din sai gaisheshi suke amman be amsa ba, dakunan ya soma bi daya bayan daya yana dubawa har ya kai karshe be ganta ba, layin yan hadari ya nufi ya soma duba gadajen dama dana hagu, sai daf da zai kai karshen dakin ya hangota kwance saman gadon an daura mata drip fuskarta da bandeji da kuma kafafunta. Tsaye yai yana kallonta ya kasa karasawa inda take, tsigar jikinsa sai tashi take. Sai da ya hade yawun bakinsa sannan ya iya daga kafasar kamar marar lacca ya karasa kusa da gadonta, kallo daya yai ma fuskarta tausayinta ya kamashi yanayin yadda take numfashi kawai ya isa ya fahimtar da shi mawuyacin halin da take ciki. Yasha ganin hadari kala kala ya sha yin tiyata ko ya duba marasa lafiyar da ido baya iya daukar ganin ciwon, amman be taba cin karo da wacce ta bashi tausayi sosai kamar Hafsat ba, duk wani shiga da fitar numfashinta aunashi yake da nasa, yana jina jin zafin ciwon dake jikinsa kamar a jikinsa yake. Hannu ya kai ya taba jikinta, sai yaji temperature dinta very high. File din dake saman drawer ya dauka yana dubawa, sai ga wasu nurses uku mata sun iso gurin gabansu sai faduwa yake, a zatonsu wani abun ne akai a kuskure ko kuma ba daidai ba, domin sun san halin Zain matukar suka saba wata doka ko suka yi wani abu ba daidai ba, zai iya korarsu. “Waya dubata?” Daya daga cikinsu mai sanye da karamin hijab half sunna ta amsa masa. “Doctor Shukura, tace za a kara mata jini...” “Ban tambayi ki” “Sorry Sir” Ta fada da sauri. “Ina wadanda suka kawo ta?” “Ba musan inda suke ba Sir, amman na fada musu a kawo jinin sai suka ce wai wanda ya kawota yaje gurin meeting ya dawo, su kuma ba yan'uwanta ba ne” “A canja mata gado a kaita Mr Zain rooms” “Yes Sir” Yana fadar hakan ya juyo ya dawo gurin da nurses masu kula da gurin suke ya shiga can ciki ya dauko syringe tare da safar hannu da wata karamar robar dake daura drip, yana fitowa dakin nurses din na kawo gurin sun turota a gado. Tsayar da su hai ya saka safar ya daure dantsenta ya saka saka mata allura ya zuki jininta, Sannan ya cire sirinjin, Nurse din dake bayansa ta mika masa kada ta danne gurin sannan ya kwance robar da tsinin allurar ya jefar a kwandon shara. Da sauri suka wuce da ita, shi kuma ya nufi gurin gwajin jinin, in few minute aka gwada jinin aka bashi result kasancewar shi ya zo da kansa, yayi mamakin ganin jinin ya zo daya da nasa, be wani bata lokaci ba. Gaje gurin dibar jini aka dibi nasa leda biyu. Sannan ya dawo office dinsa ya bude freezer ya dauki madara da maltina ya shanye, sannan ya sake fitowa ya kama Ward din dakin Mr Zain, dakunan da aka tana da saboda masu hannu da shuni, tun daga yanayin gurin ma ya isa ya fahimtar da mutum haka, dakuna ne masu yawa aka jera kowanne da numbersa. Wayarsa ya fiddo daga aljihu ya nemo number Shukura, bugu biyu ta dauka. “Tambaya min Farida wane daki ta kai yarinyar” “Okay” Bayan an seconds ta amsa masa da “Mr Zain Room 37” Kashe wayar yai ya kara gaban dakunan dake kusa dasu yana duba numbers din dakunan har ya isa 37, hannu ya kai ya murda kofar ta bude, daya daga cikin Nurses din da suka kawota tana tsaye a kanta tana duba file dinta. Tana ganin Zain tasha jinin jikinta. “Zaki iya tafiya” Cikin sauri ta fice daga dakin, sai ya karasa inda Hafsat mutsu mutsu amman idonta a rufe tana son yin kuka. Zaunawa yai gefen gadon yana kallon fuskarta, har a yanzu tausayinta yake ji duk kuwa da kasancewar yasan ba a hayyacinta take ba. Yanayinta sai ya masa kamar na Haleema lokacin da bata da lafiya, hannu ya kai zai shafa fegen fuskarta sai kuma ya gimke hannun ya sosa lips dinsa. Wayarsa ce tai ringing kamar daman jiran kiran yake sai yai saurin daga tare da karawa a kunne ba tare da ua duba mai kiran ba. “Assalamu alaikum” Jin muryar Hajiya Hadiza uwargidan Mai Martaba kuma uwa a garesu yasa shi natsuwa sosai, tare da amsa sallamar. “Wa'alaikissalam Hajiya” “Zain Mai Martaba yana son magana da kai, magana ce mai muhimmanci, sai dai ina son duk abunda zai fada maka ka kasance mai biyayya agareshi” “Magana tana da nauyi ne sosai?” “Idan ka zo zaka ji” Daga haka ta kashe wayar, yasan idan har magana bata da muhimmanci ba zata kira tace yai ma Mai Martaba biyayyah ba, daman ta kanyi kokarin dorashi a hanya a duk lokacin da ta fahimci ana son hadashi da Mai Martaba ko Dada, domin ita kadaice take masa son gaskiya a cikin matan sarki. _Ibrahim ka zo anjima kadan ka sakawa patient din dake Mr Zain ward room 37 ka saka mata jini, Mai Martaba yana nema yanzu_ Sakon daya aikawa abokinsa kenan na karta kwana, sannan ya mike tsaye ya fice daga dakin, zuciyarsa cike da sake sake. FARHAT POV. Rayuwa tana zuwa ma ko wane bawa da abunda aka rubuta zai same shi ne, alkalamin kaddara baya barin kowa kuma baya manta kowa balle kuma har ya tsallake ka ya fada kan wani, iyakar abunda aka rubuta zai samu bawa a dole zai sameshi, ba mahana balle kuma matari. Ranar yau ta zame ma Farhat bakar rana, domin ta zo mata da abubuwan daban daban wadanda suke dara a rayuwar ko wane bawa. A yau bakin labari ya sameta na yaudarar da Auwal yai mata mutumen data shirya bada ranta a gareshi, wanda ta sadaukar masa da soyayyarta ta mallaka masa komai nata, a yau ya rumtse ido ya zabi kasancewa da wata wace ba ita ba, ya zabi wata a matsayin abokiyar rayuwarsa ta har abada. A yau Anty Rukaiya ta koreta mace data rike tamkar mahaifiyarta, macen da mijinta tsaya kai da fata wajen inganta rayuwarta, ya mayarda ita mutum ya bata ilmi ya wayar da ita, mace da take yi ma kallon uwa kuma uba a gurinta, A yau tai tafiyar da take hangen kanta kamar a mafarki, taya zata yarda ita dai din ce ta hadu da masu satar mutane domin biyan kudin fansa? A yau ita ce a zaune cikin kasurgun daji da babu kowa a gaban da yamma sai itace da ciyayi, a yau taji abunda mutane da aka dauke aka rabasu da danginsu suke ji, a yau ta fuskancin wulakancin da ake yi ma mutanen da aka yi garkuwa da su, idan zasu je fitsar namiji ake sakawa ya rakasu da bindigarsa, a gabansa suke komai, a yau ta ga matan da barayi suke takawa su keta musu haddi, a inda suke zaune babu fitila kuma babu abun rufa balle matashin kai, a zaune wasu suke kwana wasu kuma su kwanta hannayensu da kafafunsu a daure kamar dabbobi, idan suka yi kuskure kadan sai su zanesu da bulala, a yau din dai da aka kawota an kashe mutane uku a gabanta mutane da ba a biya kudin karbarsu ba. Da babura suka hauro da su cikin dajin bayan sun karbe komai masu, sai suka zabi wadanda suke ganin zasu iya samun wani dukiya a gurin iyayensu suka tafi dasu ciki har da Farhat, ranar yau ta zame ma Farhat bakar rana, daren kuma ya zame mata bakin dare. “Keee... ” Daya daga cikinsu ya tsaka mata tsawa, a firgice ta kalleshi, zuciyarta na mugun bugawa kamar zata fito fili. *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 8⃣ HAMEEDA POV. Kamar kullum yau ma gaban window take tsaye tana kallon harabar gidan da kuma masu kai da kawo a harabar.   A zahiri harabar gidan take kallo, amman a badini, hankalinta yana wani gurin ne daban, dalilin da ya sanya Zain ya juya mata baya take nema, irin rayuwar da suka yi a gidan take tunawa, ta yi marmarin irin kulawar da yake bata a baya, tana kaunar zaunawa da suke suna fira da juna.   Amman komai da canja mata? Mutumen da a duniya yafi kowa tsanar ganin hawayenta a yau shine yake kwadaituwa da saka ta kuka, mutumen dake kokarin yaye mata damuwarta a yau shine damuwarta take sashi farinciki.   Ta kasa yarda da komai, yau gobe burinta ya kasa ciki, ta kasa samun natsuwar aure kamar yadda ko wace mace take samun natsuwa a gidan mijinta, saboda ta hana kanta haihuwa, a yanzu kuma tada fito tana jiransa sai ya dauki kiyayya ya dora mata? Har gobe ganin take Anty Ummi ce ta shiga tsakaninta da shi, domin a da ba haka yake mata ba, gani take kamar itace ta saka ya auri Yayarta a maimakonta, bayan kuma ita tafi dacewa da shi, ta kasa yarda cewa Zain baya sonta.   Juyowa tai tana fuskarta cikin dakinta, but still jikinta na jingine da ginin gurin, a hankali ta sauke numfashi. “Wannan ce kadai damar da nake da ita a rayuwata, itace kawai hanyar da zan iya gusar da kiyayyata a zuciyar Zain, ina son mu koma kamar baya, ina kwadayin ka zama abokin rayuwata na har a bada Zain” Ta furta a hankali sannan ta tako cike da kasaita ta karaso gaban kujerarta dake gefen godonta, har zata zauna sai kuma tai tsaye tana ta tunani.   Yadda zata gyara alakarta da Zain take tunani, a ganinta har gobe Zain yana kaunarta kawai dai an shiga tsakaninsu ne.    Kwankwasa kofar dakin akai, hakan yasa ta dago kai ta kalli kofar, bayan wasu yan seconds Abida ta turo kofar dakin ta shigo bakinta kumshe da sallama, kanta a kasa karasawa tai gaban Hameeda ta risina. “Allah ya taimakeki Mai Martaba yana nemanki” Kallon rashin fahimta da mamaki tai mata. “Kin san dalilin kiran?” “Ban san komai akai ba ya shugabata” Yawun bakinta ta hade, ta soma takawa a hankali har ta isa gaban wardrobe dinta ta bude ta dauko mayafi ya rufe kanta sannan ta nufi kofar fita, zuciyarta na zillon rigan kafafunta. A iya saninta Mai Martaba baya fada a yanzu, kuma idan har wani hukunci zai yanke ko wata magana data shafi iyalinsa a falonsa na cikin gida yake zartarda komai. Kai tsaye part dinsa ta nufa tana kai hannu ta bude kofar falon farko sai gabanta ya soma faduwa. “Assalamu Alaikum” Tayi sallamar ne tana kokarin danne zuciyarta, yan matan Mai Martaba ne suka amsa mata, wato Sisters din Zain, cikin falon ta tana karewa duk wanda yakr cikin falon kallo kasa kasa, Hajiya Hadiza ce a kujerar dake kusa da ta Mai Martaba, sai Hajiya Maryam na binta, da Hajiya Zarah dukansu Matan Mai Martaba ne, Dada  Yalwa na zaune a kujerar data saba zama a duk lokacin da irin hakan ya samu.   Tun da ta zauna bata sake dago kai ta kalli kowa ba, wannan dabi'ar na daya daga cikin dabi'un da Mai Martaba yake so, yana cikin dabi'un da ake yabon Hameeda da su har ake ganin tafi duka yaran sarkin kunya.   Gyara muryar Mai Martaba yai, wannan yasa hankalin kowa ya koma kansa kenan, ciki har da Zain da zuciyarsa take can asibiti.   “Zain...” Mai Martaba ya kira sunansa, a natse ya dago ya kalli Mai Martaba. “Mi Hameeda tai maka?” Kallon Hameeda yai yaga kanta kasa, sai ya kalli Dada Yalwa kamin ya maida dubansa gurin Mai Martaba. “Allah ya taimaki Mai Martaba, bata min komai ba” Dada Yalwa ta tari numfashinsa. “Bata maka komai ba, zaka ce ta daina shiga sasshen ka? Ta daina bi inda zata ganka? Kace ka tsaneta? Ba wannan dalilin yasa tace zata bar gidan ba, saboda kana nuna mata banbance da sauran kannenka, kuma ba kowa ba ne sai wannan Ummi ita take zigashi a komai, har cewa yai ba zai kara kaunar Hameeda ba a rayuwarsa” Tunda ta fara maganar babu wanda ya saka mata baki sai da ta kai aya, babu wanda ya isa ya karyatata ko da kuwa karya take fadi babu kuma wanda ya isa ya fada ta fada, shi kansa Mai Martaba natsuwa yai yana sauraren Mahaifiyarsa. Bayan wasu yan dakiku ya sake gyaran murya a karo na biyu ya ce “Zain Hameeda da Ikram duka kanenka ne, a gurina duka daya kuke, Hameeda tsatson mu ce wannan kadai ya isa yasa ka girmamata, zan iya wakiltarta a komai na tsaya mata, kai ban tsaya maka ba, kai da ita duk a daki daya kuka taso wannan kadai ia isa ya yansa ka ganin kimarta, tafi kowa cancantar girmamawa a gurinka, kai ne Babba Zain be kamata ace wasu dabi'un marasa kyau suna tasowa daga gareka ba.   Komai na rayuwar duniya dan hakuri ne, idan har tai maka laifine sai ka sameta ku tattaunawa, idan kuma abun ya gagara sai ka samu Hajiya ko daya daga cikin uwayenka sai ka fada musu komai” Yayi shiru na wani lokacin, sannan ya cigaba. “Ko kadan bana son naji wata rigima ko rashin jituwa na tasowa tsakanin iyalaina, zuciyata tana sosuwa idan daya daga cikinku ya aikata wani abu marar dadi, idan laifi tai maka ka yafe mata kuma ku shirya tsakaninku bana son jin wani abu ya shiga tsakaninku daga yau” Tsit falon yai kamar ba kowa, zuwa can Hameeda ta dago fuskarta da hawaye shabe shabe. “Ka gafarce ni Mai Martaba, da nasan idan na fadawa Dada abunda Zain ya fada min zai zata fada maka ne da ban fada ba, Allah shine shaidata bana son abunda zai daga maka hankali a yanzu kuma na maka alkawari ba zaka sake jin wata yasassshiyar magana a tsakaninmu ba” Ta juyo ta kalli Zain da sai a lokacin ta lura da inda yake zaune. “Ka gafarta min Yarima, idan akwai abunda nai maka cikin rashin sani ko da gangace, ka taimaki ne ka rika fada min abunda nake maka da yake bata maka tai zan kiyaye, kuma na maka alkawari zan kasance mai biyaya a gareka har a bada” Ta karasa tana hade hannayenta hawaye na mata zuba kamar gaske. Kallonta Mai Martaba yai zuciyarsa cike da kaunarta, tarbiyarta da tsantsan da kanta da biyayarta suna burgeshi, tafi kowa gudun zuciyarsa a Masarautar. Zain kam be yi mamaki ba daman yasan yadda take narkewa a duk lokacin da irin hakan ta samu, ko a tsakaninta da Haleema ne sai Mai Martaba ya dora laifin akan Haleema ya ba Hameeda gaskiya. “Wata matsala ba zata sake tasowa daga gareni ba Insha-Allah” Ya fada yana maida kallonsa gurin Hajiya Hadiza dake gyada masa kai. Mai Martaba ya daga kai yana kallon sauran yan matan. “Na taraku ne gaba daya, saboda kar bayan wannan kuma wata maganar ta sake tasowa, kar abunda ya faru tsakanin Zain da Hameeda yasa ku rainata ko kui mata wani kallo dabe dace ba” “Insha-Allah zamu kasance masu biyayyah a gareka, kuma babu wani banbance da muke nunawa dukanmu, kanmu hade yake kuma za mu cigaba da kasancewa haka insha-Allah” Cewar Ikram on behalf of them, kasancewar ita ce Babba a cikin yan matan da suke cikin gidan a yanzu. Da hannu yai musu alama sai duk suka tashi tsaye ban da Matansa, bayan sisters dinsa sun fice Zain ya tashi tsaye da zimmar fice daga falon, sai kuma ya koma ya zauna sakamakon kallon da Mai yai masa. Natsuwa yai sosai dan yasan akwai sauran magana. A natse Hajiya Maryam ta fara magana, cike da isa daman haka take masa a gaban a duk lokacin da zatai masa magana. “Abu na biyu da yasa muka kiraka Zain zancen aurenka ne, wasa wasa muka kusan shiga shekara ta hudu da rasuwar Haleema amman shiru baka sake maganar aure ba” Ya dan dago kadan ya kalleta ya maida kansa. “Har yanzu ban samu wacce nake so ba ne shiyasa” “Har yaushe zaka ga wacce kake so, ai kin san halin Zain ko ta farko ai sai da aka matsa masa sannan yai, ni abunda na ga yafi dacewa kawai a hada shi da Hameeda” Da sauri ya Zain ya dago ya kalli Hajiya Zara wacce itace take maganar a yanzu. ‘Hameeda..?’ Ya maimaita a ransa, sai kuma ya kalli Hajiya Hadiza kai ta gyarda masa a hankali ta yadda shi kadai zai iya fahimtar abunda take nufi. Sai ya maida kansa kasa zuciyarsa na mugun bugawa da karfi. Hajiya Hadiza ta gyara zamanta tana magana a sanyaye. “Ba haka ya kamata kui masa ba idan har aure kuke son yai sai ku bashi damar nemo matar da yake so, idan har be samo ba zaku iya bashi duk wacce kuke ganin ta dace da shi, ita kanta Hameeda baku sani ba ko tana da wanda take so” “Yaushe zai zabo wacce yake so din, kun fi kowa sanin Zain, kuma tabbas yana son Hameeda ita kuma tana son shi ni na sani, Hameeda ita tafi kowa dacewa da ta maye gurbin Haleema” Wannan karon Dada Yalwa ce take maganar cike da bacin rai. “Da gangan nasa aka cire hotunan Haleema dan nasan idan ba haka akai masa ba, ba gyaruwa zai yi ba, kuma shi a halin yanzu ai be san wacce yake so ba, mace da matarsa ta mutu ba kamar sabon haihuwa ne komai sai an masa” Hajiya Hadiza ta ce “Kuma Hameeda tafi kowa dacewa da shi, saboda halin hakuri da Allah yai mata, da kuma kawaice zata iya jure duk wani abun da zai mata ta zauna da shi lafiya kalau, tunda suna son junansu” Shi dai be ce komai ba duk da zuciyarsa na cike da abubuwa, yasan ba son gaskiya suke masa kamar Hajiya Hadiza ba, su kullum a cikin neman laifinsa suke, dukan abunda zai kawo rashin jutuwa tsakanisa da Mai Martaba faranta musu rai yake. “Shi fa namiji ba a masa auren dole auren dole ma kuma na daya ba na biyu ba, haba abun ai ya zama wani kala, yanzu an daina wannan abun, mai zai hana Mai Martaba ya bashi damar da lokaci na zaben wacce yake so idan har be samo ba sai a yanke masa duk hukunci da ake so” Dada Yalwa ta tsire baki tana kallon Hajiya Hadiza cike da tsanar dan ita a ganinta bata son Zain ne kuma tana mata katsalandan a abunda ya shafi Zain, bayan kuma ita tana ganin tafi kowa dacewa da ta yanke masa duk hukunci da take ganin ya dace da shi domin tafi kowa son farincikisa. “Ke dai Allah be rabaki da shisshigi akan maganar Zain ya ba, ana ga gabas kina yamma sai kace baki san halin Zain ba, wani irin a bashi lokaci, shekara uku be ga wacce yake so ba sai cikin kankanen lokaci” Ta karasa da jan tsaki. Mai Martaba ya gyara zamansa bayan ya gama sauraren abunda yake fita daga bakinsu, ya san halin matansa ya kuma san irin zaman da ko waccensu take yi da Zain, hakan yasa a duk lokacin da zai yanke hukunci abunda ya shafi gidansa ko kuma Zain ya kan saurari abunda zai fito faga garesu. “Zain kana da wace kake so ko ta kwanta maka?” Kamar daga sama Zain yaji tambayar Mai Martaba, sai ya rasa ta inda zai amsa masa, kar yace babu suce zasu hada shi da Hameeda idan kuma ya ce akwai wa zai gabatar? “Mai Martaba a yanzu kam babu wacce nake so sai dai a bani damar zan nemo ko da a nan gidan ne” Maganarsa tai Mai Martaba dadi, daman baya son yanke masa hukuncin abunda baya so, haka ma Hajiya Hadiza, Hajiya Maryam da Dada Yalwa kam sun dauka Hameeda yake nufi ko kuma sauran yan matan da ake riko a gidan jin ya sako maganar gida a ciki. “Zaka iya tafiya Zain, Allah yai zaba maka abunda yafi zama alheri a rayuwarka” Cewar Mai Martaba yana kallonsa. “A tashi lafiya, Allah ya kara maka lafiya” Cewar Zain yana kokarin tashi tsaye. Sannan ya taka a natse ya fice daga falon yana ta mamakin yadda suke kokarin yi masa abunda aka daina yayi tun kaka da kakanni, kuma a aure na biyu bama na daya ba. “A shekarunan nawa” Ya furta yana duba jikinsa, sai kuma yai murmushi, kamin murmushin dake fuskarsa ya gushe tunawa da makircin Hameeda. And now yayi alkwarin wa Mai Martaba ba zasu sake yin wani abu makamancin wannan ba. After that baya tunanin zaibiya ganin wata mace da har zai iya aurenta. Tunani kala kala a ransa har ya iso part dinsa wanda can kusa da part din Dada Yalwa. Sai da ya duba agogon hannunsa kamin ya tura kofar falon ya shiga. Dare yayi yace zai fita a yanxu zuwa asibiti bayan ba aikin yake da shi ba, idan kuma har ya fita a yanxu be san yaushe zai dawo ba, beside yarinyar da zaije a akanta yasan yanxu ma bachi take, ya tabbatar Dr Ibrahim zai mata duk abunda ya bukata dan haka baya bukatar tada hankalinsa akai. FARHAT POV. Allahumma inni aj'aluka fee nuhurihim wa'a uzuu bika min shururihim. Ita ce addu'ar da take ta maimaitawa tunda suka kawo ta gurin, addu'ar mai muhimmanci da tasiri a halin yanxu, matukar ka karanta wannan addu'ar idan ka hadu da yan fashi ko masu satar mutane ko mai binka bashi ba zai tambaye ka insha-Allah sai dai ma ya kara maka, ko kuma wani mutum da kake tsoron sherinsa Allah xai kareka daga garesu, sai dai tun kana nesa da su ake karantawa. Kadan kadan take maimaitawa har ta isa gaban wanda ya kirata din jikinta sai rawa yake kamar mazari. Da yaren fulatanci yai mata magana ta sakar masa ido ta kasa amsawa balle ma har ta mayar masa da amsa, shikan a tunaninsa yaga yar'uwa ganinta fara kuma ga gashi har gadon baya, besan attachment ba ne. “Kai ba fulani ba?” “Fulani ce amman bana jin komai” Ya kalli dan'uwansa sai suka yi fulatancin sannan ya sake kallonta ya ce “Dige wane garee kake?” “Gusau” Ta amsa jiki na rawa sosai, a ranta kuma tana da maimaita addu'ar. “Kana gane hanyan geeda kouu?” “Ee ina ganewa” Cikin barkatacciyar hausa yake mata maganar, irin hausar nan ta fulanin daji bakinsa cike da goro, kayan jikinsa sun yi datti sosai kamar wanda ya shekara be yi wanka ba, hasken fatarsa ma dishe kamar an shafa masa laka, ban da hasken fitila da wutar karar da suka kunna na haskashi ba kai kace ma wani dodo a cikin duhu. “Amman kasan idan be ka san hanya ba zaka hadu da wani gungu kou? Dan haka in beka san hanya ba ka beri jauro shi kai ka, mun yi maka haka ne saboda hanyar fullanci” Ta duka kasa da sauri tana masa godiya har da kukanta. Daya daga cikinsu ne ya tashi dauko AK47 dinsa ya rataya, ya dauki rawani ya nade fuskarsa da shi sannan ya hau babur dinsa mai kama da dan 50 ta kuma ta hau baya ya soma keta dajin da ita, tayi zaton wani gurin za a kara kaita ganin kasurgumin dajin da suke fitowa cikinsa wani gurin ma kamar ba daji ba, wani gurin kai kace dan adam ba zai iya rayuwa a ciki ba, sam ba ta lura da hakan ba sai yau, shigar da suka yi da su dazu da rana bata lura da hakan ba saboda hankalinta kwata kwata baya jikinta balle har ta iya gane ta inda suka biyo sai a yanxu ne take ganin ikon Allah gaba daji baya daji, duhu kam ya yi musu kamar mutum na cikin daki. Be sauketa ko ina ba sai a bakin titi, a titi ma babu wasu motoci masu yawa, saboda dare ya yi sosai, gashi kuma kowa ya san hanyar ba mai binta a wannan lokacin sai wanda ya shirya saida ranshi. “Karka kuskura shigga kauye a yanzu, ka koma inda ka fito” “To na gode Allah ya saka da alheri Allah ya biyaku” Be amsa ta ba ya juya ya koma, ita kuma ta fara gudu tana kuka kamar mahaukaciya, kanta babu dankwali daman bata zo dashi ba, Hijab din Anty Ummi data saka kuma tun a can suka rabata da shi, gashi sun karbe mata waya balle ta kira. Haka ta rika sheka gudu kamar ance mata ga mutuwa nan bayanta, ba tai gudun minti arba'in ba ta hadu da wata motar data dauko katakai. Duka hannayenta biyu ta daga mai motar, amman yaki tsayawa, motoci kusan uku na wuce amman babu wanda ya tsaya sai wani mai motar haki, shima kuma dan an hasken safiya ya fara fitowa ne, har yayi kamar ba zai tsaya ba, sai kuma ya tsaya yana kare mata kallo. “Baiwar Allah lafiya” “Lafiya kalau, yan fashi ne suka tare mu suka shiga da mu daji, sai yanzu na samu dayan ya fitar ni, yace karna koma kauye, dan Allah ka taimaka min ka fitar da ni birni” “Subhanallahi, to ai yanzu Gusau zan je, ke daga ina kike?” “Daga gusau nake nima gada biyu” “Shiga shiga muje” Cikin sauri ta shiga bugubabbiyar motar a front seat. Bata daina addu'ar da take ba har suka isa cikin gusau, mai motar yai mata karanci ita take kwatanta masa ya kaita har kofar gida, dauke da hakinsa cikin mota. A lokacin bakwai saura na safe, tasan bata da inda yafi mata gidan Anty Rukaiya matukar tana cikin garin gusau, sai dai me zata ce mata bayan ta koreta? Anya ma zata karbeta kuwa? Idan ma ta karbeta Ya Bashir zai yarda ya zauna da ita? Cike da kwankwanto ta kai hannu ta buga gate din, bayan wasu yan mintuna mai gadin ya fito waje, ganin Farhat yasa shi sakin fuska da kuma mamaki. “Aisha lafiya dai” Bata amsa shi ya tsaya gaisawa da mai motar ita kuma ta tsaya a waje ta kasa shiga cikin gidan kamar bakonta, zuciyarta na raya mata taje gidan Anty Ummi kawai. “Bari na kira Alhaji” Cewar Mai gadin tare da komawa cikin gidan, Farhat kamar ta hana shi sai kuma wata zuciyarta ta dakatar da ita. Ba a dauki lokaci ba sai ga Ya Bashir da Ahmad a tare sun fito da sauri. “Farhat Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un miya same ki” Ya furta da cike da tashin hankali yana kallonta. Kasa amsawa tai ta noce kanta kasa sai ga Anty Rukaiya ta fito tana mata kallon uku saura kwata. “Rukaiya ya akai ta fita? Ba kince Ummi tace ta taya ta bachi ba?” “Korarta nai yi” Ta amsa kai tsaye. “Korarta kamar ya? Mi tai miki da zaki koreta? Wannan wace irin magana ce, yanzu baki san iya halin da kika sakata ba” Farhat kam kuka kawai take, ta kasa daga ido ta kalli hararar da Anty Rukaiya take mata. HAFSATU MANGA POV. Ana kiran sallah asuba Hafsat ta farka, sai taji kanta kamar an dora mata dutse, kafarta kuma da zogi, ga idonta bata ganin daidai dasu dishe dishi take gani, sai dai hakan be hanata karema dakin kallon ba, komai na dakin fari ne tun daga kan labulayen har zuwa fentin dakin ga ac da freezer duka farare kamar dai silin, tashi tai zaune tana kallon ko'ina, hannayenta biyu tasa ta dafe kanta saboda jirin da take ji, ji tai kamar ana ja mata hamnunta na hagu sakamakon robar dake hannun nata. Wani uban ihu ta fasa ta fisge robar hannunta da sauri ta jefar, a take jini ya fara zuba da wanda ake mata karin da kuma na hannunta data fisge. Sauka tai saman gadon ta shige karkashi ta dafe hannun nata tana fadin. “Na bani sun shanye min jini, wayyo.... wayyo...” Idonta duk ya cicciko kamar zai fito waje tsabar tsoro. *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 9⃣ HAMEEDA POV. Ta tashi cikin farinciki sakamakon aabunda ya faru jiya, komai ya xo mata kamar mafarki, tasan Zain ba zai taba tsallake maganar mai martaba ba, hakan zai bata dama ta gina sabuwar soyayyarta a zuciyar Zain, hakan na nufin mafarkin ya kama hanyar tabbatuwa. “Gimbiya kamar dai kina cikin fadinciki...” Abida ta fada tana kallonta, kamin ta cigaba da gyara gadon da take. Hameeda ta kawarda idonta daga wayar dake hannunta tana Murmushi. “Ba kiyi karya ba, a yau ina cikin farinciki da na dade ban samu kaina a ciki ba, kiran da Mai Martaba yai mana jiya, ya sasanta tsakanina da Zain” Abida ta yaye bedsheet din da yake kan gadon Hameeda tana fadin. “Ba ke kadai ba ce ake riko a gidan nan, amman mai martaba yafi baki muhimmanci fiye da komai, kin san dalili?” Kai Hameeda ta girgiza cike da kasaita tana wani lumshe ido. “Saboda ke marainiya ce, kuma ke kadaice kika tashi a gidan nan tun kina karama har girma a nan, bayan haka kuma kika yi aure kika sake dawowa, wannan kadai ya isa ya saka Mai Martaba ya rike ki da kima. Gimbiya kin fi ko wace mace ta gidan nan tarbiya da gudun bacin ran Mai Martaba, mi xai hana ba zaki yi amfani da wannan damar ki cimma burinki ba” “Ban gane ba” Ta fada fuskarta dauke da rashin ganewar karara. Karasowa abida tai kusa da ita ta risina har kasa ta dafa kafafunta. “Allah ya taimakeki ya kara miki lafiya, tun daga lokacin dana fahimci kina son Zain, sai na soma tausayinki saboda na fuskanci yanayinki da nasa ba daya ba ne” “Kina nufin Zain baya so na?” Da sauri ta hade hannayenta ta dukarda kanta kasa. “Idan har bakina zai furta hakan, to ko na cancanci a zubar da kaina kasa jinina ya zama fansa ga kalamin da ya fito daga bakina, wane lafiyayyen Namiji ne zai kalli mace mai kyau da kima ga cikar zati yace be kyasa ba? Sai dai idan be samu ba” “To me kike nufi?” “Shiga tsakanine Shugabata, ya kamara ki farka daga dogon bachin da kika dade kina yi, mutuwar Haleema ishara ne a gareki musamman dan ta da aka cire a mace, kece kadai mace data dace ta zama matar Zain a yanzu ke ce kadai kika dace ki haifa masa yayan da zasu milki garin nan a watan wata rana Shugabata komai a hannunki yake, Hajiya Yalwa tana son ki fiye da kowa, haka ma Mai Martaba to amman mi tasa Zain ya tsaneki? Bayan kuma a can baya yafi kowa kaunarki?” Fuskar mamaki da tunani tai. “Na dade ina neman wannan dalilin” “Daga ranar da kika bi shi zuwa gidan yar uwarsa, ya soma canja miki ko ba haka ba? Daga ranar ya kamata ki gane ba a banza ya barki ba, yanzu ma idan kika yi sake zai sake tsallakeki ya fada kan wata” A fusace Hameeda ta mike tsaye tana nuna mata kofar fita. “Abida fita ki bar min dakina...!” “Allah ya huci zuciyarki” Ta tashi da sauri jikinta har kyarma yake ta fice daga dakin kamar zata fadi. Kai Hameeda ta dafe yana busar da iskar bakinta. FARHAT POV. Bayan sun dawo cikin gida ne, Ya Bashir ya rufe Anty Rukaiya da fada, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, ransa ya bace sosai akan abunda ya faru da Farhat. “Ban taba ganin mahaukaciyar mace irinki ba, yarinyar nan amana aka bamu ita, bayan ta zo nan ta waye ta goge zaki turata kauye cikin dare? Akan wani dalili zaki turara gida? Da wani abun ya sameta me zaki fadawa mutane” “Bata min rai tai, na tarar bata yai girki ba kuma yara suna jin yunwa dana mata magana sai ta ce min ba zata girka ba, nai mata fada ta mayar min, wannan dalilin ne yasa na koreta” Daga shi har Farhat kallonta suke kallon mamaki, miyasa ta boye bata fada masa ba? Shine abunda ya tsaya a zuciyar Farhat, shi kuma yana mamakin wannan kankanen dalilin da yasa ta kori Farhat saboda shi. “Yanzu saboda wannan kika tura yarinyar kauye cikin dare? Rukaiya ina hankalinki yake ciki ne? Yanxu da wani abun ya sameta wa za a zarga?” “Kayi hakuri, an riga an rubuto haka shiyasa na aikata, amman ba zan sake ba insha-Allah. Ki yafe min Farhat kin ji?” Ta karasa tana kallon Farhat fuskarta a raunane, idanuwanta narau narau. Farhat dai bata ce komai ba ta tashi ta nufi dakinta idonta cike da kwalla. Ya Bashir ma dakinsa ya nufa cikin mugun bacin rai, daman tun jiya yake tambayar Farhat tace masa tana gurin Anty Ummi wai zata taya ta kwana.   Rasa tai abunda ke mata dadi, tasan fadin ba shine alheri ba idan ma ta fada ta ya zata bullowa lamari, sai a yanzu ne take yi lamarin kallon da harara, ta kasa fayyace mai gaskiya tsakanin mijinta da kuma kanwarta, amman taya Ya Bashir xai nemi Farhat? Me kuma xai sa Farhat tai mata karya? Wata kila dan suna Uba daya, ko kuma dan bata sonta kamar yadda take gani, idan kuma Farhat gaskiya ta fada mata fa? Bata ga dalilin da zaisa taje waje ta yada labarin gidan mijinta ba idan ma har gaskiya ne, miyasa bata same ta da zance ba? Miyasa ita bata taba ganin alamun hakan ba? Kai ta girgiza ta mike tsaye tana jin kamar an dora mata wani abu saman kan, bata san da isa bedroom dinta ba har sai da tai karo da kofar dakin. “Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un” Shine abunda take ta maimaitawa har ta isa gaban madubi ta dauki wayarta, contacts ta shiga neman Number Nawwara, har ta kai ga wacce aka rubutawa Mrs Jibril Makama babu bata lokaci tai dialing. In few minute Nawwara ta dauka tare da sallama. “Wa'alaikissalam, Nawwara good morning Nawwara” “How are you Ma'am?” “Ina lafiya, Mrs Jibril ina daya daga cikin masu bibiyar shafinki na Instagram da kuma facebook, sannan ina daya daga cikin members dinki na whatsapp” “I'm glad to hear that, akwai wani taimako da zan iya miki?” “Ina son ganinki inda hali” “Gani na ba shi da wahala, sai dai ni ina Sokoto ne, ki fada min matsalarki wata kila zan iya hadaki da wacce zata miki maganin abun a kusa da ke” A maimakon ta amsa ta, sai kawai ta kashe wayar fuskarta dauke da damuwa. “Anya zan iya tona sirrin gidana? Taya zan bar wani ya san sirrina?” Ta tambaye kanta ba dan ta san amsar ba, jin tashin motar Ya Bashir ya tabbatar mata da cewar ya fita. Da sauri ta fito falo sai ta samu yaranta sanye da uniform sun zauna saman kujera idonsu kan tv. HAFSATU MANGA POV. Sai bakwai da rabi Zain ya shigo asibitin, hankalinsa gaba daya yana gurin Hafsat, da ita ya kwana a ransa, hakan yasashi yin sammakon shigowa saboda ya dubata, kai tsaye Mr Zain rooms ya nufa, yana isa ya tura kofar dakin da take ciki. Yayi mamakin ganin gadon ba kowa ga robar jinin sai diga take kasa, sai dai hakan be hanashi karasawa cikin dakin ba, a zatonsa ko tana bandaki ne, dan yasan da fita tai daga asibitin gaba daya dole za a sanar da shi. Kunnensa ya kai jikin kofar toilet din, amman be ji motsin ruwa ba, hannu ya kai ya tura kofar bathroom din, sai yaga wayam babu kowa a cikin. Hakan yasa shi juyowa ya karaso gurin gadon yana dubawa, but still bata nan, har zai juya sai ya jiyo numsharin bachinta karkashin gadon. Dukawa yai ya leka. Bachin take a takure, tasa dayan hannunta ta dafe dayan da har yanzu be daina zubar da jini ba. Ya dade yana kallon fuskarta kamin ya mika hannunsa ya janyota. “Wayyo.... ” Ta saka ihu. “Shiiiiiiiiiiiiii” Ya fada yana dora yatsansa saman lebensa. Kokarin komawa ta rika yi har sai da ya ture gadon can gafe ya iya fitowa da ita gaba daya. “Jinina wayyo jinina” Tsayawa yai yana kallonta ba dan yasan abunda zai ce mata ba. “Bana so, ka kaini gida dan Allah, jinina suke diba” “Sa miki ake yi” Ya fada a hankali muryarsa kasakasa kamar mai tsoron magana. Bata saurareshi ba har yanzu kokarin kwatar kanta take daga rikon da yai mata, duka hannayenta biyu ya hada a hannunsa daya ya rike ya matse sosai har sai da taji zafi, a dole ta tsaya ta kalleshi har natsuwa ta shiga jikinta. Sai a yanzu take gene shi tabbas tasan shi, shine na gidan da ta gudo. “Kai ne wannan yaron ko?” Ta fada cikin muryar shagwaba tana kokarin yin kuka. Be amsa ta ba sai kawai ya sassauta rikon da yai mata. Ya tashi tsaye ya dorata saman gadon zaune, ta sauko tana kallon cikin idonsa, ya sake dorata ta sake saukowa. “Ni ba zan kwanta ba jinina suke sha ka kaini gida dan Allah” “Hadari kikai shiyasa aka kawo ki nan ake miki karin jini” “Kai ka kade ni ko?” Kai ya girgiza mata alamar a a. “Kai ne na sani, ka biyo bayana ya bi ta wata hanyar ka kade ni kaso na mutu ko?” Ya tsaya kallon dikin dake kanta da gefen idonta ba tare da yasan abunda zai fada mata ba. Ita kallonsa take da kyau irin kallin nan da ke nuna ba bana Allah da Annabi ba ne. “Kai da kanenka ka zo?” Be amsata ba, itama bata tsaya jiran ya amsa ta din ba ta cigaba. “Gashi nan kusa da kai, ku biyu ne masu kama” Kyakkyawan murmushi ne ya bayyana a fuskarsa wanda ya karawa fuskarsa kyau da annuri. “Jiri ne yake dibanki hau gado ki kwanta” Ta lake kafada. “Ni ba zan kwanta ba, dakin ma juyawa yake” Ta kai zaune tana rumtse ido tare da dafe kai, sai ta fashe da kuka. “Dan Allah ka kaini gida, bana son nan” “Kina son allura?” Tayi saurin bude ido. “Aa wayuo ni Allah, Dan Allah ka kaini gidan Sarki, a garinmu idan mutum ya bata gidan sarki ake kai shi” Ta fada tana wani abu da ido, sai lumshe suke mata, bakinta kuma a tabe kamar mai shirin yin kuka. Kallonta kawai yake fuskarsa da murmushi, haka kawai yake jin tana burgeshi, daga kukanta har dariyarta burgeshi suke. Ganin yana murmushin yasa ita ma tai dariya ta rausayar kai. “Dakin nan zai fado mana fa” Hannunsa ya mika mata, ta rika ta tako kusa da shi sai ya risina daidai ita ya dora kanta a kafadarsa. “Rumtse idonki” Ta rufe idon kamar yadda ya bukata. Yana kokarin tashi tsaye Ibrahim ya turo kofar dakin ya shigo. “Har ka shigo?” “Ee wannan yarinyar na zo dubawa” Ya amsa bayan ya tashi tsayen. Ido daya Hafsat ta bude ta kalli Ibrahim din, sannan ta rufe. “Miyasa nake ganin mutane biyu biyu?” Ta tambaya kadan kadan dar kar Ibrahim din yaji. Murmushi ya sake yi a karo na biyu yana kallon Ibrahim. “Wacece wai? Magana take ko?” Zain ya kada masa kai. “Ina ka samo wannan yarinyar ne?” “Daga sama ta fado” “Wallahi ba daga sama na fado ba ina da iyaye, amman duk sun mutu, an kashe kowa garinmu a kauyen kufawa nake, gayu suka je suka kashe kowa da kowa sai an kalilan suka tsira, nima wani mutum ne ya kawo nan garin, na boya bayan gidansu wannan yaron shine ya ganne da naje gidansu na saci abinci, har aka yi ruwa ya jika ni sai kuma ya dawo da safe shi da matarsa suka je dani gidansa sai suka ce zasu kaini gurin yan sanda ni kuma nai kuka sai wannan yaron ya cewa matarsa kar a kai ni a bari sai gobe, sai suka fita, ni kuma na dinga kuka sai wata yarinya mai kamada roba ta fito, nace ta bude min kofa tana bude min na fito, mai gadin ya tare ni nace masa yarinyar ce ta aikeni na dauko kayana haka nai sai na gudu ina tafiya sai wannan yaron yazo da wata motar da gudu ya kade ni....” Ta karasa tana kuka, tun da ta fara maganar bata tsaya ba, sai da ta kai aya, duk maganar da take bata bude ido ba, hannayenta kawai take motsawa. “Wow, wannan talkative din fa? Kuma da gaske haka akai?” Cewar Ibrahim yana kallon Zain dake Murmushi. “Amman ba ni na kade ta ba” “Kai ne... Kuma ka kawo nan kuke dibar min jini” Ta fada tana gyara daidaituwar hannayenta a wuyansa, da sukan karfinta ta makure masa wuya dan kar ta fado har ya soma jin zafin rikon da tai masa. “Saka miki akeyi, ni na saka miki shi” Ta dago ta bude ido kadan ta kalleshi. “Ba kai ba ne, wannan ne. Dan Allah kasan gidanmu ka kaini ko kuma gidan Sarki” “Mu a nan bamu da gidan Sarki sai gidan yan sanda” Zain ya amsa mata. Tayi shiru bata ce komai ba, Ibrahim zai yi magana wani mutum ya turo kofar dakin ya shigo sanye da uniform din police, daga Ibrahim har Zain kallonsa suke, ban da Hafsat da idonta yake rufe hannu ya mika musu suka gaisa sannan ya gabatar musu da kansa. “Sunana Auwal Muhammad, ni ce wanda ya kade wannan yarinyar akan kuskure...” “Kuma sai ka gudu ka barta ko?” “No ba guduwa nai ba nina kawo ta asibitin ai, lokacin da na kadeta muna da meeting ne shiyasa dana kawo ta ban tsaya kuma da naje ban samu dawowa ba sai cikin dare” “Amman abun kunya ne wannan maganar ta fito daga bakinka kana dan sanda, meeting yafi ran mutum kenan? A yanayin da ka barta tana bukatar jini amman ka taka kafa ka barta nan kai tafiyarka” Auwal ya rasa abunda zai kara cewa, a iya tunaninsa Zain dan'uwanta ne, ganin yadda yake dauke da ita kuma sai masifa yake masa. “Yanzu dai abunda ya faru ya faru, Zain ka yi hakuri” Hafsat ta bude idonta ta dago ta kallin Auwal, ba shiri ta maida idon ta rufe ta kara kankame Zain da dukanin karfinta. “Wayyo na bani wayyo Allah na dan Allah ka kaini gida ka ji...” Kuka ta soma yi na gasken har hawaye na zuba a idonta, ganinsa da tai da kayan yan sanda ya tsoratata sosai, gaba daya ta rude dakin da ihu kamar za a cire mata rai. “Zaka iya tafiya” Ibrahim ya fada, dan yasan Zain ba zai sake ce masa komai ba. “Amman ya jikinta?” “Da sauki” “An bada jinin ne? Kuma nawa aka kashe na magani” Wani wawan kallo Zain ya watsa masa, kamin ya dauke kansa ya fice tare da Hafsat a kafadarsa. Sai da ya fito harabar ward din sannan ta bude idonsa shima kuma dan taji ana masa wani yare da bata gane kansa ba. Lokaci daya ta daina kukan kamar ba ita ba, sai dai har yanxu bata daina ganin mutane biyu biyu ba. Hakan yasa ta maida idonta ta rufe bata sake budewa ba, sai da taji yana kokarin zaunar da ita cikin mota. Badan tana cikin ciwo ba da tafi kowa son murnar ta shiga mota, dan ko babur ta hau farinciki take balle kuma babbar mota kamar wannan. A front seat ya zaunar da ita sannan ya zagayo ya shiga yai mata key. “Amman kaji yadda mutanen can suke ce maka?” Be amsa ta ba, ita bata jira ya amsa din ba tace “Wai sa suna ta ce maka Sa, sun raina maka wayo suna nufi san saniya fa” Murmushi yai be ce mata komai ba, ya soma tukin. “Wannan motarka ce?” Nan ma be amsa mata ba. Hakan kuma be hana ta kara tambayarsa ba “Miyasa ka kade ne? Mi na maka?” Nan ma shiru. “Ina zaka kai ni?” Still shiru. “Kai miyasa kake yin shiru idan ina maka magana? Baka san ba kyau kyale mutum idan yana magana ba, mu a garinmu ba a kyale mutum idan yana magana, ba kyau har Sarki wai sarkin garinmu ba a kyale shi idan yana magana kuma har da dukan mutum ake, mu fa garinmu bayin sarki ne mu dukanmu ake idan muka yi laifi Inna Ladi kan kullum cikin aiki take bata ma gajiya kullum sai taje gidan sarki tayi aiki....” Ya tari numfashinta, dan ba zai iya da dagon magana irin nata ba. “Rufe idonki” Ta rufe. “Miyasa ka ce na rufe ido saboda ka sake kadeni ko? Ai na san kai na kade ni, kuma ka kira min yan sanda, kuma yanxu ban sna inda zaka kaini ba kila ma sai da ni zaka yi” “Yi shiru....” Ya furta ba tare daya kalleta ba, kamar umarninsa take jira sai ko tai shiru. Bata kuma bude idon ba har suka shiga gidan Anty Ummi. *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 1⃣1⃣ Kamar ta hadiye zuciya ta mutu haka take ji, bata tuna komai na rayuwarta, kokari taje ta manta da Auwal da Ya Bashir da kuma abunda ya faru da ita jiya amman ta kasa, abubuwa uku sun hade mata a lokaci daya. Idan tai unkurin kuka sai yaki zo mata, tana zaune dakinta har Anty Rukaiya ta fita ta dawo, bata motsa daga kwancen da take ruf da ciki ba har Anty Rukaiya tai shirin office ta fita. Sannan ta taso ta fito falo kamar marar lafiya haka take tafiya idanuwanta a sun yi ja sosai jiri na dibanta kadan. Saman cushion ta zauna tana matsar jiki kamar mai jin sanyi. Ji tai tana son waya da Auwal tana son ji daga gareshi tana son da tabbatar gaskiyar daga bakinsa, amman kuma a yanxu bata da waya a hannunta. Tashi tai ta koma dakin ta dauko hijab dinta ta saka ta fito cikin saurinta mai kamada zata fadi ta fita harabar gidan. Sai da ta kusa karasa gidan Anty Ummi sai kuma wani tunanin ya fado mata, zuciyarta ta soma ganin laifin Anty Ummi, da ace bata fadawa Anty Rukaiya ba da bata yi mata wulakancin daya sakata cikin halin data kasance a jiya ba. Ajiyar zuciya ta sauke yafi a kirga tana ta kwankwanton shiga. Can dai ta tura kofar gate din ta shiga cikin yanayin damuwa. Tunda ta hango motar Babansu Amal ta san yana nan, a ka'ida bata shiga idan Abban su Amal yana gida musamman da safe, saboda baya sake mata fuska ita kuma tana ganin kamar shigowarta gidan ne baya so. Da kanta ta tura kofar falon ta shiga, ba tare da ta tayi sallama ba. Anty Ummi dake tsaye gaban dinning ta juyo ta kalli kofa, ganin Farhat yasa ta sakin fuska tare da murmushi. “Yar halak tun jiya nake zancenki a raina” Shirun da taji Farhat tayi ne yasa ta aje kofin hannunta ya nufata tana kallonta cike da mamaki. “Ke miya sameki?” Farhat ta kalleta ido cikin ido ta ce “Yadda ce tasa na fada miki sirrina Anty Ummi, kallon uwa nake miki saboda tawa uwar bata kusa da ni, har abunda be kamata ki sani ba, kin sani a kaina, miyasa zaki je ki samu Anty Rukaiya da magabar bayan kuma na fada miki karki yi mata maganar?” “Ban yi mata maganar ba sai ta sigar da ta fahimta, idan har zan iya saka yata Amal a cikin matsala zan iya sakaki Farhat, kokarin cire ki nake a damuwa ina kokarin sama miki mafita ne, saboda bana son rayuwarki ta lalace” “Da baki fada mata ba, da bata mareni ba, da bata kore na bar gidan ba, har na hadu da barayi....” “Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un” Anty Ummi ta rikata ta zaunar. Farhat kuma ta fada mata komai daya faru ciki har da boye gaskiyar da Anty Rukaiya tayi ma Ya Bashir ba. “Anty ji nake kamar na sha wani abu na mutu, na shiga tsakanin yar'uwata da mijinta, yanxu rashin yarda zai shiga tsakaninsu, a kullum zata rika ganina da abun ne, a macuciya take kallona tana kallon na ci amanarta, tana min kallon wacce zata rabata da gidan aurenta. Da ace ban zo birni na waye ba da Ya Bashir be kwadaitu da ni ba har na shiga tsakaninsa da matarsa, da Auwal be ganni ba balle har ya yaudareni” Anty Ummi kallonta take cike da tausayawa ba dan ta fahimci inda furucin na karshe ya dosa ba. “Anty Ummi Auwal ya yaudareni wata zai aura, satin nan za a daura masa aure da wata macen ba ni ba, shekara hudu da muka yi a tare ya tashi a banza, soyayyar da yake nuna min ashe duk yaudara ce, yana yawan fadamin buri daya ya rage masa a duniya shine na aurena ashe karya yake, Anty naga iv aurensa da wata naga pre-wedding picture dinsa da wata, shiyasa a duk lokacin da nai masa zancen turowa sai ya canja min magana ko ya kawo min wani uzuri, shiyasa yake ta min yawo da hankali, ya san ba zai aureni ba ya bata min lokaci yasa na kori kowa nawa...” Maganar kawai take kanta na rawa kamar ba ita ba, sai a yanzu hawaye masu zafin gaske suka soma sauko mata. Anty Ummi ta kama hannayenta ta rike gam tana kallonta ta yadda zata tabbatar cikin hayyacinta take. “Da gaske kike Auwal ya yaudareki Farhat? Da gaske Auwal wata zai aura ba ke ba?” Ta daga mata kai. “Jawahir ta fara kirana ta fada min, na hau whatsapp naga hotunan da idona, Anty wannan shekarar ta zame min bakar shekara, bakin wata kuma bakar rana, ina ma ban zo duniya ba” “Amman Rukaiyah taji wannan abun?” “A lokacin data dawo da fushi ta dawo, ni kaina ban san mi nake ba a lokacin kamin na labarta mata komai ta sauke min mare biyu ta koreni, yanxu ma nasan ba zata barni ba korata zata yi, ni kaina ina son tafiya, ina son nayi nisa da mutane ina son na tafi duniyar da babu wanda ya san ni” “Farhat ba zaki iya rayuwar kauye ba, idan kuma kika je mi zaki fadawa Ummanki?” “Bana son kauyen wani gurin zanje inda zan manta kowa, ina jin kaina kamar babu komai a ciki, Anty ina son nai magana da Auwal ina son naji daga gareshi, yau zan bar garin tafiyata zan yi bana son kowa....” Magana take kamar tabbabiya, kana kallonta kasan kokarin fita hayyacinta take, sai lalaben hannun Anty Ummi take wai wayarta take nema, hawaye dake zuba a fuskarta kai kace fanfo aka bude. Hannunta Anty Ummi ta rika ta nufi dakinta da ita, saman gadonta ta zaunar da ita sannan ta cire mata Hijab din dake jikinsa ta kwantar da ita saman gadon. “Yi bachi Farhat kina da bukatar bachi” Anty Ummi ta fada idonta cike tab da kwalla. “Anty sanyi nake ji, kaina ciwo yake ko ina a jikina ina jinsa kamar ba nawa ba, zuciyana kamar zata tsage biyu nake ji” Bedsheet Anty Ummi ta dauka ta lullubeta hawayen na mata zuba. Juyawa tai ta fice daga dakin taja mata kofa, falo taxo ta xauna sai ta rasa abunda xata fara tunanin rashin kyautarwa Anty Ummi ko kuma cin amanar Auwal? Wani mugun tausayin Farhat ne ya lullube mata zuciya, abun ne mai wahala ace Farhat ta iya rayuwa a kauye a halin yanzu, idan kuma ta kara gaba bata san wane hali zata shiga ba, gata marainiya ga cin amanar da Auwal yayi mata, hawaye take sosai tana auna kanta a mazaunin Farhat idan har ita ce ya zata dauki kaddara uku a lokaci daya? Hankalinta ya dauku sosai har bata ji tsayawar motar Zain ba sai shigowarsa ta ji shima dan kofar falon tayi kara ne, sai tai saurin share hawayenta ta kalleshi, shima kallonta yake irin kallon nan na neman dalilin kukan yayar tashi dan yaga damuwa shimfide a fuskarta. Har ya zauna be dauke idonsa akanta ba, ba kasafai yake ganin kukan Anty Ummi ba, so that's duk abunda ya saka ta kuka yana da muhimmanci a rayuwarta ko kuma ta taba mata zuciya matuka. “Mutuwa aka yi?” Ta girgirza masa kai, daga haka be kara tambayarta ba, dan yasan ba zata bashi amsa a yanxu ba har sai ta samu natsuwa. “Ina Mama take?” Ta dago tana masa kallon rashin fahimta tare ta saka hannayenta ta share hawayenta. “Wace Mama?” Ta tambaya cikin muryata mai kama da mura. “Baba Asabe bata fada miki komai ba?” “Ban ma ganta ba, tana can ciki tana aiki” “Mai sunan Mama nake nufi yarinyar data gudu” “Ina ka sameta?” Ta tambaya tana gyara zamanta. “Wani mai mota ne ya kadeta sai ya kawota asibitin mu” “Subhanallahi tana ina yanzu?” “Tana cikin gidan nan” “Ban gane ba, daga asibitin ka kawo ta gidan nan?” “Kuka take wai bata son asibiti shiyasa na kawo ta” “Again? Zain miyasa baka bari shi da ya kadeta yaje da ita ba? Ai ba kadai kake son lada ba, baka san inda yarinyar nan ta fito ba dan me zaka rika shigar da ita jikinka ne?” Tsaya yai kallonta kamar ba hausa take masa ba, can kuma ya dauke kansa ya maida gurin plama. “Kawai yarinyar tana kwanta min ne” “Tana kwanta maka kamar ya?” “Kamar dai haka...” Ya daga kafadunsa biyu yana tabe baki, sannan ya tashi ya nufi dakin yara, Anty Ummi tashi tai ta bishi zuciyarta cike da rashin fahimtar yarin da ya mata. Ganin abincinta kawai babu ita yasa gabansa faduwa, juyowa yai ya kalli Anty Ummi ita ta kalleshi, sannan ya karasa cikin dakin yana dube dube. Kafafunta da basu karasa shigewa karkashin gado ba ya tsinyaka, sai ya isa gurin ya mika hannunsa ya jayowa. Bachinta take hankali kwance har da minshari, hannunsa yasa ya dauketa ya dora saman gadon Amal. Anty Ummi dai kallonsa kawai take har ya dorata saman gadon ya juyo ya fito, sai ita ta fito tana fadin “Miyasa ba zaka kaita gidanku ba sai gidana?” Tsayawa yai kana ya juyo ya kalleta. “Saboda nan din ma gidanmu ne, ki tausaya mata Anty baki ganin halin da take ciki? Ni na dauka ma ita kike yi ma kuka” Da shigar zolaya yai maganar amman fuskarsa babu dariya sai dan murmushin kadan. “Haka kawai zan zauna ina mata kuka, yarinyar da ban san ma da zuwanta gidana ba?” “Fada min abunda ya saki kuka? Kin sani jin babu dadi ina ganin kamar na miki laifi ko kuma wani ya bata miki rai?” Ajiyar zuciya ta sauke, ta gumde bakinta ta bude sannan tace “Ban san yadda zaka kalli abun ba, Farhat ce take bani tausayi, wai Auwal ya fasa aurenta... ” Tabe baki yai irin abun be dame shi ba, kuma be bashi mamaki ba, ya nufi dinning ya dauki kofin tea ta zuba ruwan zafi ya soma jefa sugar. “Ai daman ba zai aureta ba, duk wani namiji mai mutunci ai ba zai aure Farhat ba, wata kila ya gama da ita shiyasa ba zai aureta ba” Anty Ummi ta zaro ido. “Zain zato zunubi ne, Wallahi Farhat yarinyar kirki ce” Be dai ce komai ba, ya dauki tea sa da yanka uku na bread ya koma saman cushion din falo ya zauna yana sha. Ita kuma ta cigaba da hadama mijinta tea da take hada masa ta dauka ta nufi part dinsa cike da jin haushin Zain saboda furucin da ya yi akan Farhat. Sai goma saura ta fito daga part din mijinta zuwa harabar da ake aje motoci, suna tafw tana masa fira har ya shiga motarsa. Ba ta bar wajen ba sai da motarsa ta fita daga gidan gaba daya. Sannan ta biyo ta kofar falo ta shigo part dinta. Baba Asabe kawai ta tarar a falon tana fusa air freshener, dan shine last aikin da take bayan ta gama ko wane aiki. “Ina Zain?” “Yana gama karyawa ya fita” Baba Asabe ta amsa mata. “Tare da yarinyar ya fita?” “Aa shi kadai ya fita” Sai da ta leka dakin ta hango Hafsat kwance sannan ta nufi dakinta, a nan ma ta samu Farhat tana ta sharar bachi sai faman sauke ajiyar zuciya take. A gaggauce Anty Ummi ta shirya dan tayi latti zuwa aiki yau, gashi har goma da ashirin ta yi. Ko da ta fito Baba Asabe bata falon kuma bata kitchen da alama tana bq inda dakinta yake ita da yar jikanyarta. Tsabar sauri bata ma janyo kofar falon ba ta fito ta shiga motarta ta yi mata key, a bakin gate ta tsaya ta mikawa Malam Adamu dari biyar “Dan Allah ka karbo mana green beans da carrot ka bawa Baba Asabe jollof za ayi” Yasa hannu biyu ya karba yana fadin “To Hajiya a dawo lafiya” Bayan ta fice ya maida gate din ya rufe, sai ga Hafsat ta fito daga falon ta doso inda yake tana tafiya kadan kadan. “Ina zaki je?” Tayi shiru kamar mai tunanin abunda zata ce. “Koma can cikin gida” Kamar gaske sai ta juya ta koma, shi kuma ganin hakan tasa ya fita zuwa titi domin siyo kayan. Tana ganin ya fice ta dawo gurin gate din ta tsaya, a tunaninta yayi nisa hakan yasa ta bude gate din ta fito. Hango ta fito yasa shi dawowa, a maimakon ta koma sai ta kara sauri har da son hadawa da gudu dar kar ya tararda ita. Tafiya take tana waigensa, bata kallon gabanta ita dai burinta kar ya tararda ita sai kace wace tasan wani gurin zuwa. Kamar an dauketa an jefa haka ta fada cikin kwalbati dake gefen gidaje, hodin dake ciki ya daki bakinta har sai da hakuranta biyu suka datse halshenta ya fito waje....! https://my.w.tt/QM4r0PWFl3 *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 1⃣2⃣ YARIMA ZAIN POV. Tun da suka fito tiyata yake jin ba dadi, ba kuma na rashin lafiya ko na bacin rai ba, jikinsa na bashi kamar wani abu ya faru da shi ko kuma zai faru da shi ko wani nashi. Tafiya yake kamar mai tausayi kasa, a yadda ya sake fuskarsa zaka dauka murmushi yake maka saboda yadda ya samu kansa a yanzu shi ba farinciki ba kuma ba damuwa ba. Duk inda ya ratsa gaisheshi ake amman be daga kai ya amsa ba balle ya amsa musu, a kasaitaccen office dinsa ya shiga, wanda aka kawata da kayan ado na zamani irin wanda ake gyara manyan offices da su, sai da ya zauna saman kujerarsa mai juyawa sannan ya sauke ajiyar zuciya a hankali. Wayarsa ya dauko ya shiga contactlist dinsa neman Number Ikram, dialing yai in few minutes aka dauka muryar Hameeda yaji bakinta kumshe da sallama. “Assalamu Alaikum” Wani dip yai kamar ba zai amsa sallamar ba, yaji kamar kar ya amsa sallama. “Ina Ikram?” Ya tambaya yana wani hade rai kamar ance masa tana gabansa. “Bata kusa, kana da bukatar wani abun ne” Be jin zai iya kara amsa mata, sai kawai ya sauke wayar, daman yana son ya tambaya ne idam Mai Martaba yana gida kuma yana lafiya, duk da kasancewar yasan ya baroshi lafiya amman yana da bukatar jin lafiyarsa, saboda abunda yake ji, obviously jin muryar Hameeda ya hana shi tambayar hakan. Juyi ya soma yi saman kujerar yana lilo, bayan Mai Martaba Anty Ummi ce mutum ta biyu da suka fi kowa muhimmanci a rayuwarsa, it could be her wani abun ya sameta ko zai sameta, numberta yai dialing ringing biyu ta dauka. “Doctor” “Professor” “Ya aka yi?” “Kalau, kawai ina son ji daga gareki ne” Jimm tai, dan tasan ya saba kiranta a duk lokacin da yake tunanin wani abun ya sameta. “Lafiya ta kalau, sai dai ko Mai Martaba” “Na kira Ikram yanzu Hameeda ta dauka da akwai wani abun da zasu sanar da ni, kina gurin aiki ne?” “Yeah ban dade da zuwa ba na zo late ma” “To ina kika bar Mama?” “Wace Mama...?” Tuna Hafsat yasa ta ce “Oh tana can tana bachi” “Ita kadai?” “Baba Asabe ai tana nan, kuma Farhat ma tana dakina tana bachi” “Haba Anty kin san Farhat din nan ba wani hankali ya isheta ba, last time ma ba ita ta bude mata kofa ta fita ba, kuma ita ma Baba Asabe idan ba magana kika mata ba ai zata iya barinta ta fita...” “Hey hey hey... karka dame ni da zacen wata yarinyar kauye, aiki nake yi sai anjima” Ta katse wayar, tsaki yaja yana kokarin mikewa tsaye, lapcoat din take jikinsa ya cire ya rataya a hanger, ya fice office din da sauri. Tun kamin ya karasa gurin motar ya danna keys din hannunsa motar ta fita key yana isa budewa kawai yai ya shiga ya tashi motar. Daga saminaka area zuwa gada biyu area babu wani nisa sosai dan haka cikin kankanen lokacin ya iso. Tun da yai horn be ga an bude masa gidan ba zuciyarsa ta soma raya masa babu lafiya, sai dai yai horn kusan sau shida amman babu wanda ya leko balle ya bude masa, hakan yasa ya fita da mota ya taka kasa ya shiga cikin gidan, dakin dake kusa da gate ya fara leka dan ya gani idan Malam Adamu na ciki, amman sai ya tarar babu kowa ciki, yana nufar main house din sai ga Malam Adamu ya fito daga Bq da saurinsa, ganinsa yasa Zain tsaya yana kallonsa tare da jiran ya karaso. “Ranka ya dade dan Allah ka kira mana Hajiya yanzu yanzu” “Miya faru?” Ya tambaya da sauri. “Yarinyar nan ce ta fito ina cewa ta koma ta koma sai taje ta fada kwalbati ta buge kanta karfen ya shige mata a baki daker ma na cire halshenta sauran kadan ya kire....” Da gudu Zain ya nufi Bq kamar ance masa tana can, a balcony ya tararda ita kwance kamar gawa bakinta bude cike da jini, a firgice ya dauketa ya fito da ita, Malam Adamu na biye da shi. “Wallahi nayi ta mata magana sai ta gudu mi kuma na bita garin kamata ne ta fada a can, gashi ni da Asabe duk babu mai waya, balle mu kira, shine nace taje makota tasa a kira ta.... ” Tun da Zain ya daukota Malam Adamu yake biye da shi yana masa wannan bayanin har ya sakata backseat. “Ya isa haka Malam Adamu.....!” Zain ya katsa masa tsawa cikin wani irin tashin hankali. Sannan ya bude motar ya shiga, yadda ya fisgeta kai kace ma sama zai tashi, in few minutes ya isa ZAINUDDEN SPECIAL HOSPITAL, sai da ya dauki hanyar Emergency sannan ya ciro wayarsa ya kira aminisa Doctor Ibrahim, sai da yai masa kira biyu ana uku yai parking. “Ibrahim ka zo emergency yanzu nan za ayi ma wata dinki now please...” Be tsaya jiran abunda Ibrahim din yace ba ya kashe kiran ya kira wata Nurse. “Kiyi arranging gado yanzu nan ga patient nan zan kawo” Yana katse wayar, ya faka motarsa kofar Emergency, kamin ya bude motar ya daukota har an kawo gadon da za a dorata akai, sai da aka dorata akan gadon sannan ya kai hannunsa gefen wuyanta ya tabbatar tana da rai sannan ya bada umarnin a wuce da ita emergency room, a daidai lokacin Doctor Ibrahim ya iso a hanzarce ya tsayar da gadon ya dubata. “Ya aka yi taji wannan raunin...” “Ya akayi taji wannan raunin miya sameta.. Ba lokacin wannan ba ne, ka shiga da ita ka tsayarda zubar jinin sannan ka dinke mata halshenta that's all” Zain yayi magana a hasale yana nuna masa ita kuma as command cos shine boss. Kai kawai Doctor Ibrahim ya kada ya juya suka shiga da ita daya daga cikin dakunan da aka tanada idan irin hakan ya taso. Dadowa yai babbar kofar emergency din ya tsaya yana amsa wayar da Anty Ummi take masa. “Yanzu aka kirani wai Yarinyar nan ta buge bakinta...” “Ganin nan ma kawo ta har an shiga dubata” “On my way.... ” Ta katse wayar, shi kuma ya sauke ajiyar zuciya ya nufi motarsa ya shiga, daker ya janyo motar ya kaita gurin da aka tanadar masa dan faka motarsa saboda jikinsa da yaji jinsa kamar ba nashi ba. Be kula da rigar jikinsa ta lalace da jini ba sai da yaje zai bude kofar office dinsa ya shiga. Be yarda ya zauna ba sai da ya fara balle bamallan rigarsa ya cire farar rigar ya shefa a kwamdon shara sannan ya nufi closet ya dauko wata rigar ya saka sannan ya zauna saman kujearsa yana kallon hoton Haleema dake aje saman teburinsa yana fuskantarsa. Hotone daya fitarta kyauta tana sanye da jar abaya, fuskarta dauke da murmushin da suka bayyana hakorin maka dake gefen bakinta. Takwayin ajiyar zuciya ya sauke a lokaci daya sannan ya samu damar lumshe idosa yana lilo da kujerar. Lokaci daya ya bude idanuwan nasa duka biyu yana kallon Anty Ummi wacce ta turo kofar ta shigo yanzu. “Na dauka kai kake dubata naje aka ce Ibrahim ne ya shiga da ita” “Ba zan iya dubata ba” “Saboda mai?” Ta tambaya tana dora jakarta saman teburinsa. “Kawai dai” Ya daga kafadunsa sannan ya cigaba “Haleema ma ni na mata tiyata remember? Kuma i lose her, so wannan ma bana son na dubata at the end na rasa ta” Anty Ummi tai masa wani kallo kamin ta soma magana a hankali. “Haleema is your wife shiyasa daka rasata ka kasa mantawa da komai nata, har kake zargin kanka akan tiyatar da kai mata, amman wannan she's nothing but a foreigner, yarinyar kauye yarinyar da baka san inda ta fito ba” “She's helpless Aunt” “Yes you're right she's helpless amman akwai taimakon da ya kamata mu mata bayan wanda muka mata ne? Mun bata ci mun bata sha yarinyar nan har wanka kasa an mata a gidana, and what else ya rage? Sai ka dauketa ka kaita gidan marayu ko kuma gurin da kasan za a iya maida ita garinsu, ba wai kai ta ajiyanta ba, last time da ta fita babu abunda baka fadawa Farhat ba, ka dora laifi akanta, taje mota ta kade ka daukota ka dawo da ita gidana, and this time around ta sake fita bakinta ya bugu, next time gawarta zaka kawo min a gidana ka samu a matsifa, haka kawai mu yi ta wahala da yarinyar da ba musan inda ta fito ba, yarinyar kauye. Kayi taka tsantsan Zain, kai dan sarauta ne kuna da makiya ciki da wajen Masarautar Rishim, za a iya maka komai saboda Mai Martaba so think twice” Tana kaiwa nan ta fisgi tsadaddiyar jakarta ya juya ta fice a fusace, Zain dai sai kallonta yake da mamaki. Yatsunsa biyu ya dora saman goshinsa yayinda babban yatsan yake saiti da bakinsa. He was just thinking of Anty Ummi, zai iya rantsuwa bata taba matsa tsawa ba, but this time around tana son rikide masa zuwa wata kalar saboda Yarinyar kauye, ita tafi kowa fahimtar idan yazo da abu amman yanxu taki, tana goya masa baya akan komai da zai yi but why now? Amman miyasa yake son taimakonta? Ai ba shi kadai ya ganta ba, miyasa ba zai barta taje wani gurin ba? “I just can't...” Ya amsa masa kansa kamar wani ne yake a gabansa yana tambayarsa ba zuciyarsa ba. Ba kasaifa yake ganin mutum hakan nan kawai ya taimaka masa ba, but yana son taimakon Hafsat no matter what, yadda jikinsa ya bashi dazu ya tabbatar tana da muhimmanci a gareshi maybe saboda yana son taimakonta ne or something else. ANTY RUKAIYA POV. Daga gurin aikinta ta aje motarsa ta hau Napep ta dawo gida, even Mai gadinta was very surprise daya ganta tazo a napep. “Hajiya motar ta tsaya ne.?” Ya tambaya yana kokarin mai da kofar ya rufe. “Eh ta dan tsaya ne zan dauki abu na koma” Ta amsa masa ba tare da ta waigo shi ba, cikin gidan ta shiga da sanda kamar wacce zata yi sata, bata ji motsin kowa a falon ba, hakan ya bata damar shiga dakinta, sai kuma ta fito ta leka dakin Farhat bata ganta ba, she already know tana zuwa gidan Anty Ummi idan bata nan, so that's means tana can kenan domin bata ganta ba har toilet ta duba bata ciki. Dawowa tai dakinta tana kokarin zaunawa bakin gado sai taji tsayawar motar mijinta Bashir. Da sauri ya tashi ta shiga bathroom ta maida kofar ta kulle tare da saka mata key da can ciki, ya fiddo wayarta ta saka ta silent. Tun da ya shigo cikin falon take jin hayani sama sama bata jin abunda yake cewa amman da alama waya yake. Bayan ya kare ya shigo dakin sai kuma ya fita ya leka dakin Farhat be ganta ba, ya dawo falo ya kira mai gadinsa a waya. “Kaje nan gidan su Alhaji Hashim kace Rukaiyah na kira Farhat” “To Alhaji” Zaunawa yai saman kujera, sai kuma ya tashi ya nufi freezer ya bude ya dauko ruwa ya sha, ya kusan minti latatin a gurin sannan Farhat ta turo kofar falon ta shigo da tsoro, fuskarta duk ta fada saboda tashin hankali da kuma yunwa dan tun shekaranjiya rabonta da abinci. Tsaye tai kusa da kofar tana kallonsa. “Wuce ciki Rukaiya na kiranki” Tasan ya saba mata haka, wani lokacin da gaske ne, idan ta shiga zata ganta wani lokacin kuma ba da gaske ba ne, musamman yau da bata ga motarta a waje ba, but she's ready now ko da ba da gaske bane, zata shiga if ma zai yi raping dinta ne ba zata hana shi ba, saboda ta shirya tarwatsa rayuwarta komai ma zai sameta ya sameta din ita tana tunanin ta shiryama mutuwa. Takawa tai cikin tafiyarta ta masara karfi ta nufi bedroom din Anty Rukaiya. Tana shiga ya bi bayanta shi ma ya shigo ya maida kofar ya rufe. “Ina take?” “Tana gurin aikinta, Farhat na tura miki 300k a account kin gani?” “Bani da waya” Rikata yai ya yana kokarin zaunar da ita “Sai yaushe zan samu abunda nake so ne Farhat? Ki taimaka min mana, Wallahi babu wanda zai sani kuma ba zan bari ki yi ciki ba” Kallonshi tai idonta cike da kwalla. “Haba Ya Bashir? Kai yanxu baka jin kunyar tsayawa a gabana tsirara kasa zaka yi mu'alama da ni ta aure bayan wacce kake yi da Anty? Baka tsoron cin amanar matarka? Allah fa yana ganinmu fa” “Allah mai yawan gafara ne, ai tuba zamu yi, kuma Anty ki bata da matsala fa, wannan sirrinmu ne.... ” “Idan kai zaka iya cin amanarta ni ba zan iya cin amanar yar'uwata ba, Anty Rukaiya ta yi min komai a rayuwa be kamata na yi mata haka ba...” Kamin ta karasa ya shiga kokuwar cire mata Hijab. “Kin ga ina miki da lalama shiyasa kike min wannan abun ko? Ko dan kin ce naji bana son miki da karfi sai kin amince ne kike min wannan iskanci....” Wasa wasa wanki hula ya kusa kaisu rana, kokari yake yaga ya kai ga jikinta ita kuma ta kasa masa ihu saboda kar mai gadi yaji, tasan ba rufin asirinta bane da kuma na Anty Rukaiya, wani bangare na zuciyarta kuma yana son sakata ta amince. Jin hakan yasa Anty Rukaiya saurin bude kofar bathroom din ta fito fuskarta da hawaye shabe shabe kamar yadda ta Farhat take, zuciyarta kuma cike da kunci. Daga Ya Bashir har Farhat mutuwar tsaye suka yi dan basu san tana ciki ba, ba ma kamar Bashir da gumi ya soma keto masa duk da sanyin ac dake dakin. Jinginawa tai da gurin ta sulale kasa ta zauna tana kallon mijinta ido cikin ido. Jikinsa rawa yake har cikin antarsa ya kasa furta komai agareta kuma ya kasa dauke idonsa daga garin kallonta, kamar an tsikareta sai ta tashi da sauri ta bar jakarta a gurin ta nufi kofar fita ta bude da keys din dake makale jikin kofar ta fita, saurin fitowa yai shima he was just thinking of zata zuba musu wani abun ne ko kuma ta dauko wuka ta daba masa ko ta kullesu a dakin. Sai kawai yaga ta nufi kofar fita ta fice, a nan tunaninsa ya fara sauyawa zuciyarsa na raya masa ko zata tara musu mutane ne. Da sauri ya dauki keys dinsa dake kan freezer ya fita, motarsa ya shiga mai gadi ya bude masa ya fita amman ko kurar Rukaiya be gani ba, hakan yasa shi nufar cikin garin dan baya son kara ganinta yanzu. Tana fita tai sa'ar samun Napep sai kawai ta shige tace ya kaita Jibril Bala (JB) Secretaria gurin da take aiki, har suka isa hawaye ke mata zuba, sai da ta isa sai ta rasa kudin baya mai napep din sai da ta karba hannun daya daga cikin securities din da suke gadin gate din sannan ta taka da kafa ta karasa part din da office dinta yake. Duk yadda tai kokarin boye hawayenta sai haka ya gagara har ta isa office dinta hawaye zuba suke mata, kowa sai mamaki yake masu tambayar tafiya sun fi wadanda suka yi shiru yawa. Office dinta ta shiga ta zauna dip kamar an jefota, kawarta ce Samira ce ta shigo office din da sauri tana kallon yanayinta da kuma fuskarta. “Na san yau kin gani ko kinji abunda yafi karfin idanuwanki, amman ya kamata kiyi controlling kanki saboda kar kowa ya san sirrinki, keep yourself clam, and clean your tears do not let anyone know your secret, wannan sirrinki ne ke kadai, please stop crying” Ta karasa tana sa hannu ta share mata hawayenta. Anty Rukaiya ta dago kai ta kalleta. “I can't work right now, i don't know what to do” “Ki koma gida yanzu idan kuma ba zaki iya zama gidanki ba kije gidana, lemme handle the documents, just go and rest” Ta saka hannu ta kwashe duka takadardun da suke gabanta, ita kuma ta mike tsaye tana jin zuciyarta ta mata mugun nauyi har bata iya numfashi, saurin rike kujearsa tai saboda kokarin faduwa da take. “Samira i can't breathe” Ta fada tana wani irin shidewa. “Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un” Samira tayi saurin sakin documents din ta riketa da sauri. “Ina inhaler ki?” Bata iya amsawa balle har ta fada mata ta baro jakarta gida. “Please help us...” Samira ta fada tana fashewa da kuka saboda mawuyacin halin data ga kawarta tana ciki... _________________________________ What do you expect next? Anya Zain iya kyale Hafsat kamar yadda Anty Ummi ta bukata? Da gaske Hafsatu manga yar gudun Hijira ce ko kuma turota aka yi? Me zai faru da Anty Rukaiya? Ya Farhat zata kasance? One word for Ya Bashir One word for Anty Ummi. One word for Hameeda. What will happen next? #Share #Comment #Vote *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 1⃣3⃣ Tun da Anty Rukaiya da Ya Bashir suka fice Farhat take wani irin kuka, kukan data rasa dalilinsa, farincikin Anty Rukaiya taga gaskiya ko kuma bakinciki data kasance ita silar kuncin da zai tabbata a ran Anty Rukaiya? Da gumi da majina duka ta hada a gurin da take zaune, gashi bata da karfi ko na kwayar zarra, tana son ta tashi amman data unkura sai ta kasa, tun daga nan ta tabbatar da raunin daga zuciyarta yake, hakan yasa ta kara fashewa da kuka. Hankalinta ya tashi sosai lokacin da taji tsayarwa mota a harabar gidan, da fari tayi tunanin ko Anty Rukaiya ce ko kuma Ya Bashir, amman yanayin shigowa falon da kuma muryar da taji ya tabbatar mata da ba daya daga cikinsu ba ne. Iya kokarin da take na ta tashi ta fita daga dakin ne amman sai ta kasa, har Samira ta shigo dakin hankalinta tashe hawaye shabe shabe a fuskarta. “Farhat Farhat kira mana Bashir kirashi yanzu ki ce Rukaiya tana asibiti.... ” Kamar an sako mata karfi haka taji, sai ta zabura ta tashi tsaye jikinta da zuciyarta na mugun rawa kamar yadda bakinta yake karkarwa kamar mai jin sanyi. “Me.... Me.... Me.... ” Sai ta kasa tambaya. Samira ta matso kusa da ita ta rika hannunta. “Kin san inda Bashir yake yanxu? Kina da number sa?” Kai kawai ta iya daga mata, sai Samira ta mika mata wayarta, Farhat ta karba ta saka mata number, cikin sauri Samira ta karba ta danna kira, cikin kankanen lokaci aka dauka. “Hello Bashir Samira ce kawar Rukaiya kazo asibitin Yarima yanzu nan muka kai Rukaiya asmanta ya tashi..” “Sorry kin yi wrong number wannan Auwal ne” Cikin sauri Samira ta katse kiran jin abunda mai number yace mata, sai ta girgiza kafadar Farhat. “Ke number Bashir zaki bani ta Bashir” Sai da ta girgiza kusan sau uku sannan ta sake kai hannu ta karbi wayar ta saka mata number Bashir kasancewar tana da number shi a kanta. Bugu daya ya dauka sai Samira tai masa bayani sannan ta kama hannunta suka fice daga dakin, gurin shiga motar ma Samira ce ta sakata sannan ta zagaya ta shiga maxaunin direba ta tashi motar suka dauki hanyar asibitin Yariman Bakura dake Gusau babban birnin jihar Zamfara. Har suka isa Farhat bata fahimci inda suka dosa ba, ita dai kallon motoci da titin kawai take, bayan Samira tayi parking ta zagayo ta budewa Farhat ta fito da ita, bata iya banbance inda take balle har ta fahimci hanyar da Samira take bi tare da ita. Ko da suka isa Ya Bashir har ya isa gurin, Samira ce ta gane shi domin hankalin Farhat gaba daya baya jikinta balle ta iya gane shi din ne, sam bata iya gane fuskar mutane ma, ita dai taga mutum tsaye namiji ne mace ne wannan kam sai mai natsuwa ne zai banbance. Likitocin uku ne tsaye kan Anty Rukaiya maza biyu mace daya, dukansu kwararune kuma manyan likitoci, kokarinsu na neman numfashinta ne, gata a raye amman ta kasa breath hawaye sai zuba yake a idonta, duk wani taimako daya kamata likitocin su bata suna kanyi amman numfashinta ya tsaya cak! Likitan mace ta kalli kwayar idonta, bakin ya bace bat sai farin shima kuma kamar ba daidai take kallo da shi ba, jikinta ya yi mugun sanyi sai wani gurnanin majina take dake cikin kirjinta irin kakarin nan na mutuwa. Ciwo take ji sosai a kirjinta, kowa bawa yana son duniya da burinta yake barinta, sosai Anty Rukaiya take jin kamar ta fisgo wani daga cikin likitocin su taimaka mata ta tsaya, a yau zata tafi ta bar Yayanta da mahaifiyarta, a yau zata bar duniyarta da mijinta, a yau zata yi bankwana da abokai da yan'uwanta, a yau ta sha ruwanta na karshe ta ci abincin karshe, duk wani abun data mallaka a duniya a yau ba nata ba ne, sai wanda ta aje ma kanta na gobe kiyama, a yau zata dandani dacin mutuwa, kamar yadda ko wane bawa yake dandantarsa a duk lokacin da mutuwarsa ta gabata, a yau zata kwana cikin kabarinta, ta tafi gidanta na gaskiya kenan babu zance dawowa, katifa da gadonta da motarta ta gidanta da duk wani abu data mallaka a yau ba nata bane, ji take kamar a kara mata wani lokacin, tana jin inama za a bata damar fadin ko da kalma daya ce amman ba dama, tana kallo duniya zata barta, a yau ko ta shirya ko bata shirya ba dole ne ta sauka a masaukinta na gaskiya, domin ta cinma wa'adinta. Wani irin kakari take na fitar rai, irin kakarin nan da bashi da jin balle kallo, irin kakarin nan da idanuwanka suka soma bankwana da duniya, goshinta ya cika da zuba fatar jikinta ta canja sai sheki take tayi fari sosai saman da farin da take da shi, tayi tsawo. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke na fitar rai, sai idanuwanta suka kafe. Cikin sauri likitan ya kai hannunsa ya taba sauran ma suka shiga dubata amman ina mai kira yayi kira, mai rai ya karbi abunsa. Hannu likitan yasa ya shafe mata idonta, sannan suka warware zanen dake saman gadon suka rufe jikinta da shi. Daga Bashir har Farhat da wata gwaggonta da yan uwan Bashir da Samira da wasu abokan aikinta suna tsaye suna jiran fitowar likita. Yanayin yadda likitocin suka fito kadai ya isa ya karantar da su cewar Rukaiya ta rasu. Baya baya Ya Bashir yai har ya fadi kasa zaune sai ya cire hular kansa ya fashe da kuka kamar mace, a take kowa ya saka kuka a gurin ban da Farhat da take jin da ganin komai a mafarki, takawa tai ta karasa kofar dakin ta tura kofar tana kallon yadda aka lullube Anty Rukaiya, lallai mai rai ba komai ba ne, ta kasa yarda Anty Rukaiya ta rasu, gani take kamar zata tashi zata koma gida suka cigaba da rayuwa kamar da, tasan mutuwa bata da notice balle warning tana zuwa a da zarar lokaci yayi amman yanzu zuciyarta na raya mata dogon suma Anty Rukaiya tai bata mutu ba iyakar abunda ta sani alkawarin Allah baya tashi. Ji tai am dafata an kai hannu an rufe kofar dakin sai ta juyo ta kalli gwaggonsu wato Gwaggo Binta dake hawaye. Hakan ya kara tabbatar mata da Anty Rukaiya ta tafi kenan har abada, murmishi tai amaimakon kuka sai ta nuna kanta amman ta kasa magana, faduwa tai zaune tana son kuka amman ba hawaye..... ZAIN POV. Da yamma lis Zain ya shiga dakin da a kai Hafsat bayan anyi mata aikin a kunne kuma an sake mata bandeji gurin data jimu jiya, a sanyaye ya shiga dakin yana hango yadda take kwance zuciyarsa ta soma sosu, tsaye yai yana kallonta wani mugun tausayi ta bashi an saka wani karfe an bude bakinta sama da kasa, ga wani dinki da aka mata a halshe gwanin tausayi, zaunawa yai saman gadon idonsa da hankalinsa duka yana kanta, irin kallon da yake ma Haleema yake mata, duk abubuwan da suka faru lokacin daya fito da ita daga tiyata ne suka soma dawo masa daya bayan daya. Hannu ya kai ya shafa gefen fuskarta sai yaji tayi sanyi da yawa kamar wacce ke cikin kankara, wani tunanin ne ya zo masa sai yai saurin maido dubansa gurin bakinta yana kallon halshenta.... Manage 🙏🙏🙏 *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 1⃣4⃣ Ba ta gasgata gaskiyar mutuwar Anty Rukaiya ba har, sai da ta ga an fito da gawarta, hannu Farhat ta dora saman kai ta kurma wani uban uhu wanda ya tashi hankali duk wanda ke gurin. “Na shiga uku, na bani na lala ce Anty Rukaiya ta tafi ta barni La'ilaha illah Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un...” Gwaggonsu ce ta rikata tana kuka tana bata hakuri. Daker aka fito da ita daga asibiti saboda kukan da take, kamar sabuwar mahaukaciya haka aka isa da ita gida.    Suna fitowa mota sai yaranta suka fito daga cikin gidan da gudu sanye da uniform da alama basu dade da dawowa daga makaranta ba. Hankalinsu ya tashi duk kuwa da kasancewarsu kanana, ganin Farhat na kuka da Abbansu da kuma duk wanda yake tare da su. “Anty Farhat miyasa kike kuka?” Aliyu ya tambaya kasancewar shine babba ya fisu wayo, tausayin ne yaranne ya shiga zuciyar kowa, musamman ma Farhat data rasa abunda zata ce musu, taya zata fada musu mahaifiyarsu ta mutu macen data fita dazu lafiya kalau? Ya Bashir ne ya share hawayensa ya kama hannayensu ya nufi cikin gidan da su. “Abbah miyasa kake kuka? Ina Momi? Miyasa naga motar asibitin a nan gidan?” A take Aliyu ya jero masa tambayoyin amman ya kasa amsa masa ko daya hawaye sai sauka suke a idonsa. Dakinsu ya shiga da su ya janyo kofar ya rufe, sai kuma ya jingina jikin kofar ya fashe da kuka mai karfi kukan da be san ta ina yake fito masa ba. Ba a bari Farhat ta sake ganin gawar Anty Rukaiya har aka mata wanka aka mata sutura, daya daya aka hadeta da su Aliyu har lokacin kuka take kukan tausayin yayanta da kuma ita kanta. Su kansu yayan kuka suke domin a lokacin sun fahimci sun yi rashin mahaifiya ta tafi kenan har abada.   Mutuwa Anty Rukaiya ta taba, makota da yan'uwa da ma abokan aikin kowa sai al'ajab yake, daga wanda zai ce ya ganta jiya sai wanda zai ce satin daya wuce suna tare, gashi bata kwanta ciwo ba, mutuwarta kawai aka ji , mutane Anka ma da suka zo kowa kuka yake da kuma fadar alherinta.   A yadda Anty Ummi take kuka da alhinin mutuwarta sai ka dauka wata yar'uwarta ce ta jini, kuka take sosai saboda tana ganin komai daya faru laifinta ne, saboda Farhat ta labarta mata komai abunda ya faru, tayi dana sanin yin zancen da Anty Rukaiy da ace bata yi mata magana akan abun ba da duk haka be faru ba.    Anty Rukaiya ta samu mutane sosai ta kuma samu addu'ar da kyakkyawan yabo wanda ake son ko wane mamace ya samu, abokai da makota dukansu sun yi mata shaidar kwarai, dukansu babu wanda be zubar mata da kwalla ba. ***         ***        *** Misalin Bakwai da Rabi na yamma ta bude idonta, dizzy take ganin silin, hakan yas ta dade tana kallon sama kamin ta bi dakin da kallo sai wani lumshe ido take tana budewa.  “Mama... ” Ta juyo ta kalleshi da idanuwanta da suka yi rawaya, kokarin rufe baki take amman sai ta kasa sakamakon karfen da aka saka tsakanin lebenta na sama dana kasa, wani zafi taji halshenta nayi kamar an saka mata wuta. Duk iya kokarinta na yin kuka ne, amman sai ta kasa, hawaye kawai suke sauko mata babu kakkautawa. Tasowa yai daga inda yake zaune yazo gurin kanta ya tsaya yana kallon yadda hawaye ke sauko mata. Tausayinta ne ya rufe shi, as her age tana cikin mayuwacin hali ga kuma abunda ya sameta a yanzu, secondly ya tsani kuka  ko da haka kawai ne balle mai dalili irin wannan, musamman na mace domin yana ganin wanda aka cuta ko aka zalumta ne kawai yake kuka ko kuma wanda be shi da yadda zai yi. Risinawa yai bakin gadon yana saukar hawayenta har cikin ranshi. “Idan kina kuka ba zai yi saurin warkewa ba...” Yayi shiru yana cigaba da kallonta kamar yadda take kallonsa. “Kina son bakinki ya warke da wuri” “Na siya miki abun dadi?” Haka yake ta raba maganar yana tsayawa kamar mai jin wahalar maganar, alhalin babu gajiya ko wahala a tare dashi face kasaita da kuma sabo da yin maganar a haka. Tunda yake maganar kallonshi kawai take amman bata daga masa kai ba, bata daina hawayen ba. A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya busar da iskar bakinsa, kana ya kai hannunsa share mata hawayen. “Mamana daina kuka kinji? Zan siya miki nama da minti kina so?” Taji zancen abunda tafi so fiye da komai a duniya wato nama hakan yasa tai saurin daga masa kai. “To ki daina kukan...” Ya fada fuskarsa babu walwala. “Nan da kwana biyu zaki warke sai na siya miki kinji?” Ta gyada masa kai tana ta kokarin tsayarda hawayen, sai kuma ta nuna masa cikinta, shi kuma ya sakar mata ido yana kokarin gano abunda take nufi, bata isa jin yunwa yanzu ba, domin a drip din saka daura mata akwai abubuwan da aka saka a cikin wanda zai hanata jin yunwa da wuri, so ifa ba yunwa bace that's means fitsari ne kenan. “Fitsari?” Ta daga kai, sai ya kai hannu ya zai cire mata drip din tai saurin yaje hannun ta tashi tsaye tana lakame kafada, hannu ya sake mikawa zai kama hannunta sai ta sake gwacewa. “Robar zan cire miki kiyi fitsarin” Ta lake kafada tana hawaye. Ido ya sakar mata dan be san yadda zai yi da ita ba, zuwa can ya fiddo wayarsa ya shiga sashen message ya nemo number Doc Hafsat wato kwarirriyar likitar halshe, likitar data dinkewa Hafsat halshenta, ya aika mata da saka, sannan ya maida wayar aljihu ya cigaba da kallon Hafsatu data bata fuska tana kallonshi idonta cike da tsoro, gira daya ya daga mata sai ta kara lake kafadar ta juya masa baya.    Guntun murmushi ne ya bayyana a fuskarsa, kallonta kawai yake yadda take kiriniyar sauka saman gadon burgeshi yake, ita ala dole da karfin karin ruwan zata shiga bandaki tai fitsari, a ganinta idan aka cire zafi zata ji wata kila ma za a cire tare da fatarta ne gaba daya, yadda aka saka mata shi be dame ta ba cirewan ne yafi tsaya mata a rai, daman ko da aka saka mata shi bata cikin hayyacinta da ba zata bari a saka mata shi ba. Shi dai kallonta kawai yake har ta sauka saman gadon ta soma jan karfen ta nufi inda take zaton bandaki ne, lokacin data isa gaban kofar sai ta kao hannu ta murda amman ta kasa budewa juyowa tai ta kalleshi sai ya daga mata gira daya kamar dai dazu amman wannan karon ta gyada masa kai sai ya karasa gurin kofar ya dora hannunsa saman nata ya murda kofar ta bude. Sai kuma tai tsaye tana kallon toilet din komai dake ciki irin na gidan Anty Ummi ne ita kuma bata saba da irin wannan ba, abunda take masa kallon kula ko randa ita bata ga gurin fitsari a nan ba, hakan yasa ta bata fuska ta kalleshi. Shi kuma ya daga mata kafada, suna haka Doc Hafsat ta turo kofar ta shigo fuskarta shimfide da murmushi kamar kullum, har ta karaso inda suke tsaye Zain be tada kai ya kalleta ba kamar ma be san da shigowarta dakin ba, hakan be dame ta domin ta saba da dabi'unsa duk kuwa da irin kyakkywar fahimtar dake tsakaninsu. “Afternoon Doc” “Yarinyar nan ta farka fitsari take ji...” Bayan ya numfasa ya cigaba. “Kuma ba zata bari a cire mata drip ba” Murmushi Doc Hafsat tai ta karasa kusa da Hafsatu ta dafa kafadunta. “Wata kila ka mata wanin abun ne shiyasa taki yarda da kai, amman ni ai kawarta ce ko?” Hafsatu manga ta girgiza kai alamar a a, a ranta tana fadar. ‘Katuwa dake za ki ce kawata ce ke’ A fili kam babu bakin magana sai ido da lake kafada. “Yanzu dai fada min sunanta” “Sunanku daya” Zain ya fada yana saka hannayensa duka a aljihu. Sai Doc Hafsat ta wara ido. “Oh kai na tuna haka ne a jikin file dinta shiyasa take jin magana ai” Zain dai be ce komai ba ya nufi kofar fita. Daga asibitin gidan Anty Ummi ya nufo, yana yin parking ya fito ya nufi cikin falonta, tana zaune cikin falon amman fuskarta babu annuri idanuwanta duk sun kumbura kamar ba nata ba, sallamar da yai ma can kasan makoshinta ta amsa masa, hakan ne ya karantarda shi damuwarta tun gabanin ta gabatar masa da ita, ko da yake yasan dalilin damuwarta baya nasaba da mutuwar makociyarsu wato Anty Rukaiya yayar Farhat wacce yaga ana jana'iza dazu daya dawo da rana.   Yayi tsammanin zata tambayeshi Hafsatu manga ne, amman sai yaji shiru bata masa maganar ba, sai kawai ta bijiro masa da maganar Farhat. “Zain yarinyar nan tana cikin wani hali, kuma duk abunda ya faru nice, da ace ban yi maganar da Rukaiya ba da duk haka be faru ba” “Haka Allah yaso” Ya fada kamar be damu ba, sai wara ido yake dan bega Amal da yan'uwanta sun fito ba. “Na sani, amman kadai yasan halin da yarinyar nan zata shiga, yanzu kauye zata koma da zama, taya mace kamar Farhat wacce ta saba da zaman birni zata iya zama kauye? Ga rashin yar'uwarta ga cin amanar da wannan Auwal din yai mata da wanne zata ji?” Ta karasa idonta na cika da kwalla. Shi kuma ya bata amsa kai tsaye yana canja channel din tv. “Da wanda yafi mata ciwo...” Wata banzar harara Anty Ummi ta watsa masa, taya zai bata irin wannan amsar wato be ma damu ba, shi bata bashi tausayi. “Tashi ka bar min gidana” Juyowa yai ya kalleta yana kokarin tuna irin amsar daya bata, sai kawai yai murmushi. Sometimes Anty Ummi tana acting kamar wata karamar yarinya, da ace kyaleta yai sai kuma tasa complain tace tana ta magana ya shareta kamar ita ba yayarshi ba ce, tayi tai mitar cewar isar da kasaitar da yake a gidansu ko wani gurin har da ita zai yi ma, ko da yake wani lokacin duk irin maganar da zata yi ba zaice uffan ba indai ba yan maganar ke saman kai ba, idan kuma ya cilastawa kansa amsawa maganar ba zata mata dadi ba musamman idan akan Farhat ko familynsu take maganar, sai kawai ta sauke masa haushi, haka take masa ko da da mijinta ta samu tsabani shi da yayanta take saukewa haushi saboda shine a gidan kullum. “Wai ina maka magana kana watsomin wata amsar marar dadi ta dabam, mafita fa nake nemawa yarinyar nan...” Be kula zancen ba, sai ya dauko mata wata magana da daban. “Mama ta farka dazun nan, kuma abun ya zo mata da sauki sosai...” Tasan wa yake nufi da mama wato Hafsatu manga. “Dan Allah dan Annabi Zain ka rufe babin yarinyar nan bana son ka sake min magana akanta” Tana kaiwa nan ta tashi ta nufi dakinta cikin bacin rai, a tunaninta ga abunda ya kamata ya maida hankali suyi magana akai amman ya kasa sai wata banza can yake dauko mata zancenta.      Shi na tashi yai ya fice, a Masallacin unguwar yai sallah isha'i sannan ya isa Kanwurin, yayi mamakin ganin Hameeda a harabar aje motoci tsaye da wani magidanci suna fira, ba komai ke bashi mamaki ba but this one ya bashi mamaki sosai, ko da yake be san alakar dake tsakaninsu, amman be kama da mai neman wani abu a gurinta ba, amman idan har son ta yake ai da cikin gidan zata shiga a shi miyasa ta tsaya da shi inda ba a tsayuwa dan fira? Kuma gurin da kowa zai iya ganinta ciki har da shi? A zahiri ba yayi ma abu kallo biyu da sunan kwankwancewa ba halinsa ba ne, sai dai yana daya daga cikin dabi'unsa kurawa abu ido sau daya yai masa kallon tsab ya kawar kai ko minene kuwa, ba dan haka ba da sai ya sake kallon mutumen dan kara tantancewa. ‘To kai miye abunda ya dame ka?’ Wata zuciyar ta tambayeshi, sai kuma dayar ta bashi amsa. ‘So if ta fara kula wani hakan yana nufin tayi giving up akai na, zata barni na huta am happy for her’ Ya fada a ransa yana kunna kansa a sashen Mai Martaba. ***           ***          *** Ba karamin fama Doc Hafsat tai da takwararta Hafsatu manga ba, kamin ta sami ta yarda a cire mata drip din ta shiga tai fitsarin shi ma kuma da rigima, bayan ta fito Doc ta kara duba halshenta sannan ta dauke da kanta ta dorata saman gadon tana mata murmshi kasancewarta mai yawan far'a ga son mutane, abu ne mai wahala kaga fushinta.   Tana kokarin daura mata drip din ne wayarta tai ringing alamar kira, cikin sauri ta fiddo wayar ta cire safar hannunta tai picking. “Hello Ya Auwal...” Bayan wani lokaci sai ta amsa da. “Ban manta ba Wallahi akwai abunda nake, da zarar na gama zan bar asibitin gaba daya sai na kawo maka am sorry” Daga haka ta maida wayar aljihun Lapcoat dinta, ta kama hannun Hafsatu manga tana murmushi. “Rumtse idonki na nuna miki wani abu” Ba musu ta runtse dan a tunaninta wani abun ne da gaske, ko da ta bude har ta maida drip din a hannunta. Fita tai ta dawo dauke da allura har biyu a hannunta, Hafsatu manga na ganin allura ta zabura ta tashi zaune kamar zata sauka saman gadon sai kokarin kwalla take. “Ke ba allura zan miki ba, ai ke kawata ce ba zan miki komai ba” A cikin ruwan tai allurar, kamin tai ta biyu har bachi ya buge Hafsatu daga zaune, sai data gyara mata kwanciyarta, sannan ta fice daga dakin. GIMBIYA HAMEEDA POV. Burinta ya cika, abun nema ya samu daman son kawai take Zain ya ganta tsaye da wani tana zance, wannan dalilin ne yasa taki shiga da bakon can cikin duk kuwa da kasancewar ba girmansu ba ne, ko ba komai tasan Zain zai raya wani abu a zuciyarsa. Ta jidadi sosai da Allah yasa yau a nan ya faka motarsa ba a sashensa ba ko da yake ko a sashensa yai dole zai gani tunda zai ya wuce wannan hararar kamin ya isa part dinsa. Bata kara bata minti biyar a gurin ba ta sallami bakon ya wuce ita kuma ta dawo cikin gida ranta fari kal... ______________________________________ Al-hamdulillah am back... Kwana biyu bana online saboda matsalar wayata ne, da fatar ba kuyi fushi ba😍🥰 *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 1⃣5⃣ GIMBIYA HAMEEDA POV.    Cike da fadinciki ta dawo part dinsu, ta wuce dakinta fuskarta shimfide da murmushi, ji take kamar ta fara taka wani matakin nasara a yanzu, ba kamar da ba ne, yanzu kam ta shirya yin komai dan cinma burinta, tsoro fargaba tsaiko inda inda duk ba nata ba ne a yanzu.   Matukar abunda tai abaya tace zata sake yi a yanzu, zata iya rasa Zain har abada rasanwan na gaba daya ba wai karo na biyu ba. “Muna yawaita mafarkai, wani lokacin abunda yake nesa ake nuna mana wani sa'in kuma abunda yake kusa da mu ne, babu abunda zai iskeka a zaune har sai ka motsa...” Ita kadai take magana da kanta, tana tsaye bakin gadonta sai kallon bedsheet din take. “Shin ni ban cancanci jindadi ba ne a rayuwata? Dukan abunda yake nawa kokarin wuce ni yake sakaci yana sa na rasa abubuwan da yawa masu muhimmanci a gareni, shin laifine dan na nuna ina son Zain bayan kuma shi ya fara nuna min haka har ma ya bani dama...?” Ta nufi gaban madubi tana kallon kanta. “Me na rasa a jikina mi wata macen tafi ni da shi? Da har Zain zai gan ni kuma ya kawar da idonsa? Dole na gina sabuwar rayuwa da kai dole ne na tsara yadda komai zai tafi lokaci baya tsayawa kuma baya jiran kowa...!” Ta kusan kwashe awa daya tana ta magana da kanta kamar mahaukaciya, daga karshe ta dauki mayafin abayar dake jikinta ta saka akanta ta fito ta nufi sashen Dada Yalwa.   A natse ta tura kofar falon as usual yau ma Hajiya Yalwa tana dakinta dan haka ta nufi dakin kai tsaye, ba tai zaton akwai wani a cikin ba bayan Dada dan haka ta fada dakin tana fadin “Dada Yalwa Surukinki ya ce zai zo... ” Makale mata maganar tai ganin Zain zaune saman gadonta yana shan kankan, tufafin dake jikinsa dazu ba sune a yanzu ba hkan ya tabbatar mata da wanka yai ya canja kaya. Sai tai saurin juyawa zata koma. “Hameeda shigo mana” Dada Yalwa ta fada tana dago mata hannu. “Anjima zan dawo” “Zo nan Hameeda” Dada Yalwa ta sake kiranta, sai da ta kalli Zain dake shan kankanarsa sannan ta karaso cikin dakin fuskarta duk a fisgice, kusa da Dada ta zauna. “Dada bana son nai wani abun ya ce na bata masa rai” Ta fada muryarta na rawa kamar da gaske tsoronshi take. Dagowa yai ya kalleta sai tai saurin sadda kanta kasa ta mike tsaye. “Zamu maganar anjima Dada” Bata tsaya komai ba ta fice daga dakin da sauri. Daga shi har Dada da kallo suka bita har sai da ta fice sannan Dada ta maida dubanta gurin Yarima Zain. “Wani lokacin ina jin kamar saboda ku nake rayuwa kai da Hameeda, a dakin nan kuka tashi tare muke kwana da ku mu tashi daku wani lokacin ma abinci tare muke cinsa, na fi son ku fiye da ko wane jika nawa, saboda kawai kuna marayu a lokacin ina jin kamar idan baku kusa da ni zaku rasa wani abun ne, wannan yasa lokacin da mahaifiyarka ta rasu na zabi rikaka da hannu domin yi maka duk abunda ka kake so, a lokacin da Hameeda ta rasa mahaifiyarta ita sai nasa aka kawo min ita, haka na raineku ku biyu, a da kai da ita babu abunda yake raba ku sai bachi, akwai kyakkyawar alaka da fahimta a tsakaninku kamin Ummi ta shiga ciki...” “Ki daina zargin Anty Ummi Dada, babu ruwanta a cikin wannan” Ya fada ba tare da ya kalleta ba. “Na san yar'uwarka ce Muhammad, Hameeda ma yar'uwarka ce kamar dai ita, a gidan nan ta tashi da kai ta bude ido bata da uwa da uba a yanzu shim idan bata samu farinciki a cikin gidan nan ba ina kake tunanin zata samu? Bata da sakewa idan tana jin motsinka, bata iya walwala idan kana kusa da ita, bayan acan baya ba haka kake da ita ba, kai kanka baka iya zama sai ka nemeta, wannan rashin fahimtar dake tsakaninku yana taba min zuciyata sosai da ace kasan abunda nake ji da ko harara junanku ba zaku yi ba...” Dada Yalwa ta karasa idonta na cika da hawaye irin nasu na manya, gaskiya ta fada har cikin ranta take jin damuwa idan suka samu wani rashin jutuwa, duk kuwa da irin fadan da take masa tana dora masa laifi, idan ta gama fadan sai abun ya dawo mata a rai ya tsaya mata. Tashi yai tsaye yana sauke ajiyar zuciya, maganganunta sun taba shi, musamman ma kwalla da suka cika masa ido. “Zan je gurin aiki a can zan kwana saboda akwai aiki da yawa a asibitin.” “Allah ya tsare” “Amin” Ya nufi kofa bayan ya amsa mata da amin din. A falonta ya samu Hameeda kwance saman doguwar kujera idanuwanta a lumshe hawaye ya sauko mata ta gefen ido. Kamshin turarensa da taji ne yasa tai saurin bude idon ta tashi zaune ta share hawayen ta nufi dakin Dada Yalwa.   Ya dade tsaye jikin kofar falon kamin ya bude ya fice, jikinsa duk yayi sanyi da damuwar da ya gani a fuskar Dada da kuma hawayen Hameeda, hakan yana nufin tayi nadama kenan kuma ta daina son shi, domin idan har zai iya tunawa rabon daya ga hawaye a idon Hameeda da sunan damuwa kamar haka tun mutuwar Haleema.   Har ya shiga part din Mai Martaba tunanin yake ta yi, A falon ya samu Mai Martaba zaune yana kallon labarai, Hajiya Hadiza na zaune gafensa tana masa fira kasancewar ita ke da girki yau. Kasa Zain ya fadi ya kwashi gaisuwa sannan ya gaisheda Hajiya Hadiza, sai kuma yai shiru yana kallon tv.   Shirun da yai ne yasa Hajiya ta kalleshi ta ce “Kana da bukatar wani abun ne?” “Aa daman zan fadawa Mai Martaba ne cewar yau a asibiti zan kwana saboda aiki yayi min yawa” A hankali Mai Martaba ya juyo ya kalleshi shi kuma sai yai saurin sadda kansa kasa ya kasa hada ido da Mai Martaba, kallonsa sosai Mai Martaba keyi yana karantarsa, a iya saninsa Zain be saba masa karya ba, sai dai yau alamu ya nuna babu gaskiya a cikin maganarsa. “Tashi kaje kar dare ya maka...” Mai Martaba ya fada bayan ya dauke kansa daga kallon da yake masa. Cikin hanzari Zain ya tashi tsaye yana fadin “Na gode Mai Martaba Allah kara maka lafiya” Hajiya Hadiza ce ta amsa da Amin, shi kuma ya fice daga falon ba tare da ya sake kallon Mai Martaba.    Sai da ya busar da iskar bakinsa sannan ya bude motarsa ya shiga ya dauki hanyar asibitin. Sai da ya biya gurin masu kayan marmari ya siya sannan ya karasa asibitin, a gurin da aka tanada dan aje motarsa ya aje motar ya fito ya nufi sashen da zai sadashi da dakin da Hafsatu manga take ciki. A tunaninsa zai samuta a farke ne kuma tare da Doc Hafsat sai ya sameta tana bachi Doc Ibrahim yana tsaye jikin gadon. “Ina Hafsat taje...?” Ibrahim ya kalleshi ya ce “Aikin Hafsat kula da marar lafiya ba jinya ba, ya kamata ka san da wannan, amman duk da haka ta tsaya ta kula maka da ita, kiranta akai hakan yasa ta kirani ta fada min kuma ta bukaci na zauna da ita kar kazo baka tararda ita ba kace zaka koreta ko ka mata wani abun...” Hannunsa ya kai ya taba gefen fuskarta. “Yanzu yarinyar nan ta zame maka lalura Yarima wa zai kula maka da ita...?” Bayan kamar minti uku da yin tambayar sai Zain ya amsa masa. “Ni zan kwana a nan...” “Baka saba kwana a asibiti ba, komai dare sai ka koma gida, ko kuma ka taso tsakar daren kaxo nan kai aikinka, baka tunanin zasu zargi wani abu idan kace musu zaka kwana a nan, kasan yadda gidanku suke saka idonka akanka fa” “Na fadawa Mai Martaba aiki ya min yawa” “Be kamata ka masa karya ba Yarima” “Saboda...?” “Zata rushe wani percentage na aminci da yarda da kima da ke tsakaninka da Mai Martaba, kar kuskure yasa ka rushe wannan ginen da ke tsakaninku, ina ji maka tsoron abunda zai biyo baya” Sai a lokacin Yarima Zain ya dago ya kalleshi. “Baka tunanin na yi girman da zan rika yin gaban kaina? Am old enough to decide my future, a kullum Mai Martaba da Dada suna min kallon karamin yaro ne, su suke zartarmin da abunda zanyi, Mai Martaba yana samin ido sosai hakan yasa ya hanani zama a gidana bayan na yi aure ya cilasta min zama a masarautarsa” “Amman kuma sai ka masa karya?” Zain ya karaso ya dafa kafadar abokinsa. “Akwai inda karya ta halatta Ibrahim, na san ni kadai ne da namiji a gurin Mai Martaba amman bana jindadin yadda yake controlling dina kamar mace, kuma yarinyar tana bukatar wanda zai zauna da ita” “Amman ai yafi dacewa ka fada masa wata yarinya zaka kula da ita...” Zain ya yi murmushi irin wannan dake tsayawa a fatar baki. “Kai kadai ka kai haka Ibrahim, kai kadai ka isa na fada ka fada, kai ma kasan haka, a tarbiyar gidanmu idan Mai Martaba ko iyayenmu suna magana bama cewa uffan har sai sun gama, baya su kuma babu wanda ya isa ya mana fada sai dai mu yi masa, kuma dole ya sauraremu ba zai tanka ba har sai an masa izinin haka, balle kuma har ya yi sa'inda da mu ko ya gardanta min akan wani abu” Hannunsa yasa aljihu ya ciro keys din motarsa ya mika ma Ibrahim. “Ka ba wani ya shigo min da kayan Marmarin dake cikin mota ta” Kallonsa kawai Ibrahim yai ya karbi makullin ya dauke kai, a yadda ya fuskanta ran Zain ya soma baci matukar ya cigaba da maganar ba zasu kwashe lafiya ba, ko da yake sun saba fadansu kuma su shirya kansu idan ya fada masa wata magana da bata masa dadi ba, yana jin rashin kyautawa a abunda Zain yake kokarin yi ko ma yai, domin zai taba kamarsa a gurin Mai Martaba matukar ya gane gaskiya. AUWAL POV. Hannu biyu ya saka ya dafe kansa, idanuwansa sun kade sun yi masa ja sosai kansa sai sarawa yake, sai a yanzu zuciyarsa ke raya masa abunda yai ma Farhat be kyauta mata ba, tun daga lokacin daya samu labarin mutuwar Yayarta sai tausayinta ya rufe shi, ya kasa misalta irin halin da zata shiga idan babu shi babu yayarta a rayuwarta, ya san irin son da take masa yasan yadda ta dauke shi a rayuwarta, shi ma kansa karya yake ya ce baya son ta wata mace bata taba shiga ransa kamar yadda farhat ta samu guri a zuciyarsa ta zauna ba. “Auwal... ” Ya dago ya kalli Momy data kira sunansa. “Daman can kai kaso ka saka kanka ciki matsala tunda kasan mahaifinka ba zai taba canja alkawarinsa ba, amman kaje ka dinga soyayya da yarinyar nan ka yaudareta, haka ka zo ka cilasta mana zuwa gidansu kuma a dauko ta a kawo ta” “Nayi tunanin Abbah zai canja ra'ayinsa ne, ban dauka abun zai kai haka ba” “Taya zai canja ra'ayinsa bayan yasan kai da Sanaya kuna son junanku, kuma wannan alkawarin ya dade fa tun uban yarinyar nan yana da rai, yanzu kuma dan ya rasu sai mahaifinka ya canja alkawarin? Kai kanka ai mai taimaka masa ne ya cika ko” “Amman Momy nafi son Farhat Wallahi, tafi dacewa da ni mun gama tsara komai, kuma na ce ki nema min alfarma ki sake roka min shi ya yarda na auresu tare” “Yace ba zai yi ba, mi zaisa na cilasta masa? Ni bana da wani abun da zan iya ce maka bayan abu daya, kaje ka lallabata idan ta yarda zata jiraka nan da shekara daya sai ka aureta” Baki ya saki yana kallon Momynsa, sai kuma ya maida dubansa gurin Doc Hafsat data shigo yanzu. “Tsabar iskanci tun dazu nake jiranki shine kika samu guri kika zauna ni kika barni nan ko?” “Wallahi aa Dsp na tsaya wani dan aiki ne wata yarinya ce aka sa na kula da ita, amman ga takardun na kawo” Wani banzan tsaki yaja ya fisgi takardun a hannunta ya fice a fusace. Ita dai da kallo ta bishi tana ta mamakin wannan fushin nashi na yau. “Momy lafiya danki yake kuwa?” “Kyaleshi haushin tsohuwar budurwarsa ne yake son ya sauke a kanki” Ta tabe baki daman tana cikin mutanen da basa son ya auri Farhat. ANTY UMMI POV. Tun da safe Abban Amal ya bar gidan, daman ya kanyi fitar safe but ba kamar wannan karom ba, domin ya fita da bacin ran matarsa wato Anty Ummi sakamakon maganar dawowa da Farhat a gidanta ta tai masa, ita ma dai ta tashi cikin damuwa da tunanin yadda zata samawa Farhat mafita, har ga Allah abun ya dameta sosai domin tana yi ma Farhat daukar yar'uwarta ne ko kuma ma yar cikinta gaba daya. Hakan yasa yaranta ma gaba daya basu gane kanta ba, bata wani sake musu fuska ba har suka shirya motar makaranta ta wuce da su. Da taimakon Mai aikinta suka shirya abinci mai yawa aka bawa Malam Adamu ya kai, ita kuma ta shiga ciki tai wanka ta shirya cikin wata shudiyar atamfa. Zuwa tai falo ta zauna da zimmar karyawa amman ta kasa sai tunani take. Tana haka taji tsayawar motar Zain agogon falon ta kalla 10:38am ya nuna, dan haka ta san daga gida yake daman kamar kullum ko ya karya a gida sai ya zo gidan wani lokacin kuma sai ya baro gidansu ya xo nan ya karya. Da sallama ya shigo falon ta dago ta kalleshi tare da amsa masa cikin yanayin damuwa. “Yanzu nake tunaninka Zain” “Ni...?” “Ee da har zan kira ka sai kuma nai tunanin ko akwai abunda ya tsayarda kai a gidan ne” “A asibiti na kwana” Kallon Mamaki tai masa. “Jinyar yarinyar nan da kanka kake Zain? Anya...” Kamar wacce ta tuna da wani abu sai kawai ta fasa maganar ta tashi tsaye tana fadin. “Bari dai na kawo maka abinci ka karya, magana nake son mu yi da kai” Shi dai da ido ya bita, zuciyarsa nata ayyana masa abubuwa mabanbanta. Share Comments [2/19, 9:48 PM] خديجة أبو بكر القلوي😍: https://my.w.tt/E2nzUvfh93 *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 1⃣6⃣ Tun da yaga Anty Ummi tana jera masa abinci a center table ya san yau shi dan gata ne, abu ne mai wahala tai masa haka indai ba tea bane. Gyara zama yai ya fara karyawa da wainar fulawa cox tana cikin favorite dinsa, sai da yai nisa da cin abincin sannan Anty Ummi ta fara magana a hankali. “Zain ka san yadda nake da kai, ni yar uwarka ce kuma ba zan taba yi maka abunda zai cutar da kai ba, abu na biyu ban taba rokonka wani abu ba ban taba gabatar maka da wani abun ba, alfarma nake nema Zain ba zan cilasta maka ba, amman ina son kai nazari ka taimaki yarinyar nan dan girman Allah” Ya juyo ya kalli Anty Ummi dake ta magana kamar ba tasan abunda zata fada ba, dan tattaro maganar take ta ko ina ta kasa kasa hadata. “Wane taimako zan iya mata?” “Ka aureta Zain...” Ta fada kai tsaye, ba shiri ya furzar da dankalin dake bakinshi yana mata wani razanannen kallo. Sam be yarda Anty Ummi ta san abunda take fada ba.    “Zain yarinyar nan tana cikin matsala, kuma a bar tausayi ce Wallahi” “Amman dan tana abar tausayi sai ki zo min da maganar da hankali ba zai dauka ba? Wani irin na aureta? Kin san yadda na tsani yarinyar nan kuwa?” “Tsana mai wucewa ce Zain, kuma saboda na isa da kai yasa na nemi wannan alfarma a gurinka, kasan ban isa naje wani gurin na samu wani da wannan maganar, ban taba rokon kai min wani abun ba, kuma ban tsammaci haka daga gareka ba, nayi tunanin ni dima kamar mahaifiyarka ce Zain, na dauka girmamawa da mutumci da kake bani sun isa na roki abu kuma kai min, ka san dai ba zan taba yin abunda zai cutar da kai ba” “Mai Martaba ba zai bari na auri wata yarinya da ba yar sarauta ba, ko kuma jinsinsa ba kuma jininsa, beside ba zan taba zuwa masa da wata magana akan wata yarinya ba, yarinyar ma Farhat” “Ita Farhat din ba mutum ba ce? Ko kuma wata cuta ce a jikinta da zai hana namiji aurenta? Dole ne ka yi breaking rules din gidanku Zain kai namiji a gurin mahaifinka, ya kamata ka samawa yan'uwanka mata yanci kuma ka samawa kanka, lokaci yayi daya kamata ace kai kake saka musu rules ba wai su saka maka ba, ina son na taimaki yarinyar nan ko dan mu bawa tsohon saurayinta haushi” Tunda take maganar kallonta kawai yake yana ganin kamar ba ita ce ba. “Saboda kina son taimakonta sai kika babu wanda ya dace ya taimake ta sai ni ko? Yau dai kina son kanki da yawa Anty ke da kike tsoron abunda zai shafi gidanmu saboda dora miki laifi da suke amman yau ke da kanki kike cewa na karya dokokin gidan dan kawai na auri yarinyar nan?” Tashi yai tsaye saboda ransa yai kololuwar bachi, sai dai yayi kokarin taushe fushinsa gudun kar ya fadawa Anty Ummi wata maganar marar dadi. Da kallo ta bishi har ya fice sannan ta dafe kanta tana fadin. “Iyakar abunda zan iya kenan akanki Farhat, kuma bana nufin ki zama cuta a gareshi kai ne shaidata” ***      ***       *** Cikin bacin rai ya koma gida, wani bangaren kuma yana mamakin Anty Ummi, ko da ba Farhat ba baya jin ya shirya zaman aure da wata mace a yanzu balle kuma ita da yafi tsana da kowa, and taya Anty Ummi zata masa haka kamar wani karamin yaro?   Be yi awa daya a gidan ba, ya shirya cikin farar shadda ya fito part dinsa ya shiga part din Dada ya gaisheta sannan ya wuce part din Mai Martaba yai masa barka da tashi.   Bayan ya fito ya shiga motarsa ya nufi asibitin, yau kam ya dade be isa ba saboda yadda yake driving din. Rayuwarsa kawai yake tunani yadda zai gina wata sabowar rayuwar ba tare da Haleema ba, and now Anty Ummi ta dauko masa wata maganar marar dadin ji, a gida kuma Dada ta isheshi da zancen Hameeda da wanne zai ji? Ajiyar zuciya ya sauke yana tuna yadda ya baro Anty Ummi, kamar uwa take a gurinsa tayi masa hidimar da ko uwarsa ke da rai iya abunda zata masa kenan, and kullum yana neman hanyar da zai rama alherinta amman wannan ta masa nauyi, idan kuma be amince ba fa? Zata dinga ganin laifinsa ne? Let's assume ya amince din da wanne baki zai fadawa Mai Martaba cewar zai auro wata da ba zuri'arsa ba, da wanne ido zai kalli Dada? Hakan ba zai kara komai ba face fashim fahimta a tsakaninsu masarautar da kuma Anty Ummi. Ya dade cikin motar yana wannan tunanin sannan ya tasheta ya hau titi ya karasa asibitin. A zaune ya samu Hafsatu manga tana ta kallon tv dake dakin ko juyowa ba tai ta kalleshi ba. Zaunawa yai saman gadon kusa da ita yana kallonta, ji yai kamar an zare masa duka damuwarsa dake ransa, sai ya samu kansa da murmushi ya kai hannu ya shafa kanta. “Cutest...” Ture masa hannu tai ta watsa masa wata banzar harara kamar ba wani sa'anta. Dauke kansa yai daga kallonta ba dan ya daina murmushin da yake ba, dan har ga Allah fushinta burgeshi yake.   Knocked akai kamin a turo kofar dakin a shigo Ibrahim dauke da kulolin abinci, ko be fada ba Zain yasan daga gidan Anty Ummi kulolin nan suka fito domin nata ne. “Ga abinci inji Anty Ummi kuma tace tana gaida mai jiki sai ta shigo” Ibrahim ya fada bayan ya aje kulolin tsohon dake bayansa kuma ya aje babbar jaka da plate da hitar ruwan zafi, sannan ya gaishe da Zain ya juya ya fita. “Yaushe kaje can?” “Yanzu nan ta kirani tace na zo na karba, bedsheet da fillo suna cikin jakar nan, and Yarima ta shawarce mu da mu kai report din yarinyar nan gurin yan sanda saboda gaba kuma tana da gaskiya, saboda Doc Hafsat ta fada min akwai yiyuwar ta kasa magana da wuri...” Hafsatu manga na jin anyi maganar yan sanda tasa hannunta ta rike rigar Zain tana girgiza masa kai sai hawaye ya fara sauko mata. Zain ya kalleta ya kalli Ibrahim. “Miyasa ni bata fada min ba?” “Wata kila baka damu daka tambaya ba ne” “Dole sai na tambaya? What kind of nonsense is this?” Ibrahim ya dafa shi “Easy Prince nan fa ba masarautarku ba ne” Zain ya ture masa hannu. “Don't told me this, aikinta ne ta fada min duk wani hali da yarinyar nan take ciki amman tana abu kamar wacce bata san aikinta ba” “Kai kanka ka sani ma'aikatan nan suna shakkar fada maka abu kai tsaye idan ba kaj ka tambaya ba, shiyasa ta biyo ta wajena ta fada min, kuma ba maganar gaba daya take nufin zata dauke ba, tana nufin kamin ta warke zai dauketa tsawon sati daya ko kwana goma kamin da iya magana da shi saboda zai mata nauyi a yanzu” “Wannan ba hujja ba ce sai idan wani abun tai mata, taya daga an dinke halshe za a ce ba zata iya magana ba har natsawon kwana goma? Ibrahim nima fa likita ne” “Na sani, amman ai kai kwararren likitan zuciya ne, ita kuma na halshe so kowa da fanninsa, and ka daina dora mata laifi tunda ba ita tace yarinyar taje ta fasa bakinta ba, kuma ba ita tace ka kirata kasa tai mata aikin ba, kana magana kamar baka san wacece Doc Hafsat ba, har kake zargin tayi mata wani abun” Iskar bakinsa ya busar ya kalli Hafsatu manga dake ta hawaye tana kallonsu. “Ba gurin yan sanda za a kaiki ba, yi shiru” Yasa hannunsa yana share mata hawaye. Ibrahim kallonsa kawai yake yana mamakin yadda Zain ya dauki lamarin yarinyar nan ya maida shi akansa. FARHAT POV. tsakanin jiya da yau wanda ya san Farhat kuma ya wayanceta sosai ne kawai zai iya shaidarta, domin ta canja gaba daya kamar ba ita ba, bata iya cin komai sai kuka da ciwon zuciya da suka sakata gaba, ga fargaba da tsoron abunda zai biyo baya, domin zuciyarta na raya mata zasu cilasta mata abunda bata muradi ne, sakamakon maganganun da take jin suna tasowa da kuma yadda taga familysu suna tausayin yaran da Anty Rukaiya ta bari da kuma mijinta da duk yabi ya fita hayyacinsa. Ita kanta tana tausayin yaran, domin a kwana biyun nan kullum kusa da ita suke zama tare suke kwana abinci ma sai idan ta ci suke iya ci saboda suna ganinta kamar uwarsu ne, kuma tana rage musu kewar mahaifiyarsu, domin sun shaku da Farhat sosai. Ranar da aka yi sadakan ukun Anty Rukaiya kowa ya tsammaci Ya Bashir binta zai yi saboda kuka da yake, babu wanda be tausaya masa ba, duk ya yabi ya zama wani iri, yana jin kewar matarsa a kusa da shi balle kuma idan aka watse aka barshi da yaran be san iya halin da zai kara shiga ba, a dayan bangaren kuma yana nadama da danasanin abunda ya aikata wanda yai sanadiyar mutuwarta matarsa uwar yayansa. Sai a yanzu ne yake gane ya tafka babban kuskure kuma shaidan ya rudeshi har yai galaba akansa, da ace yasan hakan zai faru ta tun farko be fara ba. *** *** *** YARIMA ZAIN POV. Ya saka Hafsatu manga a gaba sai kallonta yake kamar yau ya fara ganinta, a kullum Hafsatu canja masa take, yanayinta yana masa kamar na Haleema duk da kasancewarta karama. Hannu ya kai saitin fuskarta ya shafa kumatunta da yatsansa, take yanayinsa ya canja bacin rai ya mamaye masa zuciya, kokarin kawarda abun yake tare da jan numfashi a hankali ya sauke yana jin babu dadi. Haka yake ji a duk lokacin daya tuna abunda ya sameta, gani yake kamar shine silar komai ya kasa yafewa kansa, kansa yake ta dorawa laifin, sosai yake tausayin halin da take ciki, idan ya tuna wanda zata shiga sai ya nemi sukunin dake tare da shi ya rasa, hakan yasa ya kasa cireta a ransa da kuma al'amurransa, duk kuwa da irin fada da kuma halin ko inkula da Anty Ummi take nuna masa akanta, duk abunda yake tana cikin ransa ba shi da  natsuwa idan baya kusa da ita, gani yake babu mai mata daidai sai shi, gani yake babu mai fahimtarta sai shi, idan dare ya raba kuma yana gadinta har garin Allah ya waye, saboda razana da take idan ta farka babu kowa a kusa da ita, gashi duk dare sai ya mata addu'a take iya bachi, ji yake kamar zata nemi wani abu ta rasa idan baya tare da ita.   Kallonta yake sosai irin kallon da ba zaka iya gane na minene ba, ji yake kamar ya cire maganar dake cikinsa ya maida mata, ina zai samu yan'uwata? Idan ma an samu ya zasu zauna da ita? Idan kuma sun mutu fa anya yan'uwanta za su yarda su rike ta yadda ya dace a yanayin da take ciki yanxu? Ya kasa dauke idonsa daga gareta kamar a fuskarta zai karanci amsar tambayoyinsa. Hafsatu manga kam bachinta take hankali kwance fuskarta sai sheki take sam ba zaka tsammaci akwai wata matsala ko damuwa a tattare da ita ba. Yana kula da duk wani motsi nata ciki har da shiga da fitar numfashinta, motsin da take lokaci zuwa lokaci ya tabbatar masa da bachin ya fara gimtsarta, a wata daya da yan kwanaki data kwashe asibitin tare da shi ya karanci komai nata yanzu ya fahimci abubuwa da dama game da ita, ya san yadda zai yi communication da ita duk kuwa da rashin maganar da take. Hankalinsa ya kara tattarawa gaba daya ya maida kanta, juyin da take ma burgeshi take domin izuwa yanzu ya dan saba da kiriniyarta ko da kuwa tana bachin ne balle kuma idan tana farke, ta shiga ransa sosai wannan yasa yake kyaleta tana masa yadda take so, da kuma tausayinta da yake hakan yasa yake mata daukar yar cikinsa. Hannayenta duka biyu ta saka saman idonta tana mitsitsikawa alamar ta farka kenan, zuwa can kuma ta bude idon tana hamma, karkato kanta tai kadan ta kalli gefen da yake, fuskarsa na nan kamar kullum babu dariya kuma babu daure fuska, ma'ana ba yabo ba fallasa. Tashi yai tsaye ya rikata yana kokarin sauko da ita saman gadon, sai ta bata fuska kamar zata fasa kuka har yau ha taki ta saba da wanki baki da brush saboda gani take kamar shine silar daya saka bata magana tunda kauyensu ba da shi suke wanke ba, gashi ita kullum zafi yake mata idan yana goga mata a hakora. Be kula yadda ta hade rai ba ya nufi bandakin da ita, dan indan sabo a yanzu ya saba da halinta na kin son brush shi kansa yasan dan kawai yana cilasta mata ne. Da kansa ya zuba mata toothpaste ya wanke mata bakin iya yadda yake jin zai fitarda dattin dake cikin hakoranta, sannan ya fita yaja mata kofar, sai da tai fitsari da alwala sannan ta fito. Ko da ta fito daga toilet din baya dakin, dan haka ta bude durowar dake gurin ta dauko katon hijab din da ya siyo mata yadi uku ta saka ta shimfida carpet ta soma sallah asuba, bayan ta gama ta kama gadon ta hau ta zauna tana ta bata fuska kamar an mata wani abun sai kokarin hawaye take, ba'a yi minti goma da zamanta ba Zain ya turo kofar dakin ya shigo Phone dinsa makkale a kunne sai amsa wayar yake kadan kadan kamar an masa dole, har ya gama wayar idonsa da hankalinsa na kan hawayen da suke mata tsiyaya. Bayan ya saka wayar aljihu ya zauna ykusa da ita ya zuba mata manyan idanuwansa kamar zai cinyeta. “Minene?” Ya tambaya kamar baya son magana.  Bakinta ta wangale masa ta nuna masa halshenta, sam taki ta saba da rashin maganarta lokuta da dama tana ganin abun magana amman ba bakin yi, ita gani take kamar wanin abun ne yai mata wanda yasa maganarta ta dauke. Kallon halshen yai kamin ya kalli cikin idonta, hannunsa ya kai ya share mata hawayen. “Ni kaina ban san abunda ya hanaki magana ba Mama, ban san ina matsalar nan take ba” Ta kara bata fuska tana ta kukanta marar sauti. Dauke kansa yai daga barin kallonta ya maida dubansa gurin wayar dake hannunsa duk da kasancewar hankalinsa gaba daya yana gunta, yana jin kukanta har cikin ransa saboda yasan dalilin kukan kuma ta cancanci tai kukan ko da babbace balle karamar yarinya kamar Hafsatu.    Sai da tai kukanta iya yadda take jin ya isheta sannan tai shiru dan kanta. Tashi yai tsaye ya hada mata tea ya mika mata, sai taki karba ta kwanta saman gadon ta rumgume hannayenta a kirjinta ta juya masa baya, ita ala dole tayi fushi.    Gira daya ya daga irin he can't believe it sai ya soma kurba tea yana kallon kofar da akayi knocking. Ya tsammaci daya daga cikin nurses ne ko Doc Hafsat ko kuma abokinsa Ibrahim, but abun mamaki Anty Ummi ce wace ta kwashe sati biyu bata leko asibitin ba, saboda fushin da take da shi.      Kallon mamaki yake mata da kuma kauna irin ta yan'uwa daman yasan Anty Ummi ba zata iya fushi da shi har na tsawon lokaci bata zo asibitin ta duba Hafsatu ba duk da kasancewar shi yana zuwa gidanta sai dai ba kamar yadda ya saba ba, cikin rashin kuzari dake bayyana damuwar dake fuskarta ta karaso cikin dakin ta aje kulolin dake hannunta daga bisani ta zauna saman kujerar dake gaban gadon Hafsatu Manga m. “Good morning Anty” Ya fada yana kallon yanayinta, ta dan kalleshi kadan ba tare da ta amsa ba ta maida dubanta gurin Hafsat da har yanzu bata juyo ba balle tasan wanda ya shigo dakin duk da kasancewar taji motsin shigowar mutum kuma tace ya ambace Anty dan haka tasan Anty Ummi ce duk kuwa da kasancewar ita ma kanta Hafsatu bata cika son Anty Ummi ba. “Ya mai jikin?” Sai da ya aje kofin tea dake hannunsa sannan sannan ya amsa. “Taji sauki” Hannu Anty Ummi ta kai ta taba kafarta hakan yasa Hafsatu juyowa ta kalleta sai kuma ta kalli Zain. “Gaisheta” Zain ya fada, sai ta hade hannayenta guri daya ta gaishe da Anty Ummi kamar yadda ya koya mata. Murmushi Anty Ummi tai tana kallonta cike da burgewa. “Har tsawon wane lokaci zaka cigaba da aje yarinyar a nan?” “Har zuwa lokacin da za a samu iyayenta, ko kuma nace zuwa lokacin da bakinta ya bude” Wani irin kallo Anty Ummi tai masa na rashin fahimta, da kuma jinjina nacinsa. “Zain kasan abunda kake fada kuwa? Taya iyayenta zasu tararda kai a nan suce sune iyayenta? Ina tsoron abunda zai taba martabar gidanku, dukan abunda ya same ka a yanzu ni za a dorawa laifi saboda yarinyar nan bangarena ta fito...” Ya tari numfashinta. “Yarinyar nan bata gane garinsu Anty, taya zan saketa taje ta fada wani hannun na dabam, secondly yanzu yarinyar nan bata iya magana idan wani abun take so wa zai mata” “Zuciyarka na yaudararka Zain kana dorawa kanka laifin abunda ya samu yarinyar nan, yau kusan wata daya kenan da wani abu baka kwana a gidanku, baka wuni a gidana, ka jingine komai naka hankalinka gaba ya koma gurin yarinyar nan... ” “Kamar yadda taki zuciyar take yaudararki game da Farhat ko?” “Farhat abar tausayi ce Zain ko baka gani ba? Yarinyar nan marainiyace kuma yanzu ta rasa yar uwarta, sanadin hakan takoma kauye da zama, sun kuma cilasta mata auren mijin yar'uwarta da wanne zata ji? Ni ce silar komai Zain da ban fadawa yayartaba da har yanzu sirrin yana nan a sirri be fito ba, amman yanzu fa komai ya bace saboda ni... ” A tsawace take maganar hawayen na sauko mata. Hannayensa yasa aljihu yana kallon Anty Ummi cike da mamaki. “Wannan yarinyar tafi Farhat zama abar tausayi, saboda bata magana a yanzu, kuma batayi boko ba balle ta iya rubuta abunda take so sai dai tai nuni...” Ta daki gadon da Hafsatu take zaune. “Fine ka cigaba da rikonta har karshen rayuwarka, amman karka kuskura ka kusanci gidana da ita kuma dole Mai Martaba yasan da zamanta...” Tana kaiwa nan ta tashi tsaye ta fice a fusace. Kansa ya daga sama ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kalli Hafsatu, sai a yanzu ya lura da hawaye take, daman a rayuwarta babu abunda ta tsana kamar taga babba yana fada, tana tsoron fada ko da ba da ita ake ba, balle wannan da tasan danta ake yinsa gashi kuma taji an ambaci Mai Martaba duk da bata san shi ba, tasan yadda nasu sarkin yake, dan haka tana tsoron sarakuna sosai. “Kina son allura?” Tayi saurin girgiza kai ta saka hannunta ta share hawayenta, dan tasan idan bata share ba zai iya cewa allura zai mata. Zaunawa yai a kujerar da Anty Ummi ta tashi ta bude kulolin ya zuba mata wainar kwai da dankali, ya sake hada mata wani tea ya mika mata. Duk irin son da take ma wainar kwai yau kadan ta ci tea ma kadan ta sha ta mika masa ya karba ya aje, sai kallonta yake shi dai kam be san dalili ba amma yana jin ba zai iya barinta ta tafi ba, idan ma ta tafi ina zata je? Da wa zata hadu? Ko da da gaske cutar da shi zata yi ba zai kyaleta ba, dan har ga Allah tausayinta yake ballema yanzu da bata iya furta komai, taya za ayi tadake magana? Shine abunda yafi tsaya masa a rai, ya san wani bangaren Anty Ummi tana da gaskiya, tunda ya kawota asibitin nan rabon da ya kwana a gida, kullum cewa Mai Martaba yake aiki ya masa yawa a asibiti can zai kwana, wunin da yake a gida Anty Ummi ma ya daina saboda kawai ya kula da yarinyar da be san ta inda zata amfaneshi ba, but wani bangaren yana duba maraicinta domin bata da kowa a yanzu dai shi. Hannu ya kai ya shafa gefen fuskarta yana dan murmushi kadan. Ita ma murmushin tai sai ta mika masa hannunta alamar ya bata, da girarsa ya tambaye ta minene? Sai ta dora hannunta saman kunnenta tayi masa alama da waya.    Hannu yasa aljihu ya fiddo wayar ya kunna mata bubble shooter ya mika mata. Tashi yai tsaye ya fiddo dayar wayarsa ya kira abokisa Ibrahim, ya fice yana kara wayar a kunnensa. Sai da ta kusa katsewa sannan Ibrahim ya dauka. “Hello...” “Bachi ma kake” “Hutu ai dole ne” “Bana iya tuna when last nayi bachin safe” “Ai kai ka so” “To ya zanyi? Abun ya zame min dole ne, yanzu ma Anty Ummi take min wata magana wai bazan kai mata ita gidanta ba, kuma dole Mai Martaba ya san da maganar” “To minene a ciki ni daman tuntuni ina tunanin ya kamata ace Mai Martaba ya sani Maybe ma zai iya taimaka wajen gane iyayenta” “No Ibrahim yarinyar nan tana cikin wani hali na bukatar taimako, abu ne mai wahala a iya gane iyayenta a yanzu saboda abunda ya afku wata kila an kashe su, gashi ba magana take ba ko wani abun ne ba fitowa zatayi tai magana ba, ba kowa zai iya kula da ita ba a yanzu” “Yanzu ya zaka yi da ita?” “Shiyasa na kira ka” “Ka kawo ta nan, Zubaida zata kula da ita” “Look Ibrahim ba ko wace mace bace zata iya daukar dawainiyar yarinyar nan, kasan halinta da rigima kuma abu kadan zata ce ba a mata daidai ba dai kuka, gashi bata iya bachi ita kadai” Ibrahim ya dan yi shiru na wani lokaci kamin ya ce! “Ko muyi ma Doc Hafsat magana? Naga tana da kirki kuma sun dan shaku da yarinya.. -” Be gama maganar ba, Zain ya katse wayar saboda haushi, taya zai kirashi neman shawara ya kawo masa zancen wata can daban macen da ba yar'uwarsa ba be hada komai da ita ba. Cikin jin haushin kiran da yai ma Ibrahim ya bude motarsa ya shiga. HAMEEDA POV. A hankali take cin dabinon dake cikin faranti tana wani shu'umin murmushi, murmushin dake kara fitar da muguntar dake zuciyarta, ranta fari kal a yau.   “Allah ya taimaki Shugabata ya tabbatar da wannan farinciki na ki” Cewar Abida cike da banbadanci tana gyara mata gado. Hameeda ta kara fadada fuskarta da murmushi. “Anfi wata daya rabon da Yarima ya kwana a gida ko kin lura da hakan?” “Na lura sosai ma Gimbiyata, a kwanakin baya mun taba wannan maganar da ke” “A kullum cewa Mai Martaba yake aiki ya masa yawa a asibiti, sanadin hakan yasa baya zama a gidan nan kuma baya kwana a ciki, amman kin san minene?” “Sai kin fada Gimbiyata” Tashi tsaye Hameeda tai ta nufi window tana kallon harabar gidan. “Wata yarinya yake jinya” “Yarinya kuma? Wacece ita kuma miye alakarsa da ita? Gimbiya ina tsoron kar wata ta dauke masa hankali fa hakarmu yaki cimma ruwa” “Hakarmu ta cimma ruwa Abida, kadan ya rage mu dibi ruwan mu sha, ba zan taba shukar dusa ba, kuskuren da na tafka a baya ba zan sake tafka irinsa ba, sakaci ne yasa yar'uwata ta auri mijina, a lokacin ina bachi yanzu kuwa na farka, mutuwar Haleema ya isheki ishara, dan haka daga yanzu babu wanda zai shiga gonata ya kwashe lafiya, na dade ina jiran wannan ranar taya zan sake sakarcin da zai sa na rasa Zain?” Juyowa tai ta kalli Abida dake tsaye a bayanta. “Ko kin san a can baya babu wacce Zain yake so sai ni? Amman Anty Ummi ta shiga tsakaninmu ita ta haddasa masa kiyayyata a zuciyarsa, dan haka alkawarina ne wannan sai nasata kuka da idanuwanta kamar yadda nima ta sakani” “Ta cancanci fiye da kukan ma Gimbiya, dukan wanda ya rabaka da masoyinka ya cancanci kisa ma domin shima kokarin kasheka yake...” Cije lips Hameeda tai tana mai jin tsanar Anty Ummi har cikin ranta. “Mai Martaba ba zai bar Zain ya auri wata bare ba, yanzu kuma sai naga da wacce bakar matar nan zata bullo...” “Ai idan baki yasan abunda zai fada be san wanda za a maida masa ba, daman can baya saka ci muka yi shiyasa har zai ya auri wata ba ke ba” Cewar Abida. Hameeda ta kalleta “Kaddara ce ta rubuta masa auren yayata kamin ni, yanzu kam kaddara bata rubuta masa auren kowa ba sai Hameeda....!” Ta karashe maganar cike da kasaita. Juyawa tai tana kallon Zain daya faka motarsa a parking space ya fito ya nufi part dinsa. “Ina abincinsa yake?” “Yana sashen Hajiya Yalwa” “Jeki dauko min ni zan kai masa” Cikin rawar jiki abida ta fita daga daki, bata dauki tsawon lokaci ba, sai gata ta dawo dauke da tray abincin ta aje gaban Gimbiya Hameeda. “Gashi ranki ya dade” Kai kawai ta daga mata sai ta juya ta fice. Ita kuma ta dauki abinci ta nufi sashensa da shi. Door bell ta danna sau daya dan tasan baya son ayi ta dannawa ko ayi ta knocked anyhow, bayan kamar minti goma ya bude kofar. “Ina Abida?” Ya tambayata dan ba kasafai yake son tana zuwa part dinsa ba, duk da kasancewar a yanzu suna dan samu fahimtar juna ba kamar baya ba, saboda fadan da Mai Martaba yai musu. “Na aiketa ne shiyasa na kawo maka da kaina” Ta fada bayan ta shigo falon ta dire masa abincin a dinning. “Muna da masu hidima da yawa a gidan nan, ko bayan Abida wata zata iya yi ba dole sai ke ba” “Bana jin kaskantar da kai a abunda na aikata, ko kuma wadanda zan aikata a nan gaba, ko ba komai kai mijin yayata ne kuma dan'uwana dan haka ka cancanci girmamawa daga gareni ta ko wanne fanni, besides a yanzu ba kasafai nake son shigowa part din da yar'uwata ta rayu ba, ko ba komai yana tuna min da ita, a halin yanzu nafi son Haleema ta fiye min komai aduniyar nan Zain na taka wani mataki da kai kanka idan na ganka raina baci yake saboda yana tuna min da ita... ” Sai kuma tai shiru ta nufi kofar fita, sai da ta kai hannu ta murda kofar ta bude sannan ta juyo ta kalleshi. “Kwana biyu baka kwana a gida...” Shiru yai kamar ba zai amsa mata ba, yana cire agogon hannunsa. “Aiki ne yake min yawa” “Ka tabbata?” Dagowa yai ya kalleta, ba shiri ta hadiye yawun dake bakinta ta sha jinin jikinta. “Ina nufin idan kana bukatar wani taimako zan iya taimaka maka...” Tayi shiru fuskarta narau-narau gwanin tausayi sai yawo take da idonta a falon kamar bakonta. “Kasan wani abu Yarima? Wani lokacin baka taba sanin muhimmanci abu har sai ranar da ya subuce maka, masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce duniya makaranta ce mai ajujuwa da yawa kuma mai darussa mabanbanta, rayuwa tana zuwa ma bawa ba a yadda ya tsammace ta ba, in seconds komai zai iya canjawa include rayuwa, tunani, buri, ra'ayi da ma wasu abubuwan da dama... Wani lokacin mutum yana da bukatar abokin tattauna musamman na kusa da kai, a misali ni! Bani da abokin fira wanda zan saurareni na fada masa damuwata ya fahimce ni har ya sama min mafita, na tashi ban san mahaifiyata ba, dan haka ban san dadi da rahamar dake jikin uwa ba, daga baya kuma sai na rasa mahaifina, yanzu kuma yar'uwata wace ita kadai ta rage min, na koma ni kadai sai cousins sai kuma waenda muke uba daya da su...” Ganin ya maida hankalinsa sosai akan maganar da take ya bata dama cigaba. “Duniya tana da daci a gareni Yarima, wata maganar ba zanyi ta da Dada Yalwa ba, ba komai ne zan fadawa Mai Martaba ba, ba kowace shawara zan yi da mutum ya fahimta ba, ba kuma kowa ne yake iya rike min sirrina ba..” Ya dauke kansa daga barin kallonta, hakan ya bata damar busar da iskar dake bakinta, ta lumshe idonta tana budewa ta saukesu cikin nasa. “Dukan abunda nake ina yi saboda Mai Martaba, bana son na sake yin abunda zaisa ya zargeni da laifi, zuciyata ba zata iya daukar komai da komai ba Zain, amman zan iya rushe tawa rayuwar saboda na gina ta wasu, ko ba komai nasan tawa rayuwar gajera ce mai cike da kunci...” Ta karashe maganar cikin tattausan lafazi hawaye na silalo daga idonta, juyawa tai kamar marar kuzari ta fice daga falon taja masa kofa. FARHAT POV.     ONE MONTH LATER.... Duniya ta juya mata baya, rayuwa ta zo mata ta inda bata tsammaceta ba, komai ya canja mata daya bayan daya ita kanta a yanzu bata iya gane halin da take ciki.     Sosai take jin kewar Anty Rukaiya da yayanta, wata daya kenan amman kullum jin take kamar jiya ta rasu, wani lokacin jin take kamar kanta empty ne saboda damuwa da tunanin dake ciki. Kowa ganin laifinta yake saboda ta ki amincewa da auren Ya Bashir, wanda a ganinta be ma dace ayi mata wannan maganar ba, taya zata iya rayuwa a gidan da yar'uwata ta rayu? Idan kuma ta zauna a nan anya zata iya rayuwa kuwa? Tun baya mutuwar Anty Rukaiya,Farhat ta dawo Anka local government da zama sai rayuwa tai mata kunci, kullum cikin kuka take na rashin yar'uwarta, a dayan bangaren kuma ta kan rasa wane tunani zata fara yi akan cin amanar da Auwal yai mata ko kuma Ya Bashir da yan'uwanta suke son ta aura? Kowa ya kasa fahimtarta ciki har da Mahaifiyarta. Juyi take tayi saman gadon karfi mai rumfa irin na da din nan, kamar yadda ta sabawa kanta da wuni a daki kullum. Jin motsin shigowar mahaifiyarta yasa tai hanzarin tashi zaune ta share hawayenta. “Amman dai kin ji kunya Aisha, Wallahi baki min adalci ba kuma baki yi ma kanki ba, kin tabbata butulu kuma dan kaza mai ci ya goge baki” Dagowa tai ta kalli Inna idonta cike da hawaye. “Inna taya zan rayu da mijin yar'uwarta? Taya zan aurin mijin da Anty Rukaiya ta aura? Ba kusan abunda bake ji ba, Wallahi zan iya kashe kaina idan na aureshi Inna” Inna ta jinjina kai tana hade hannayenta. “Lallai kuwa Aisha it bata ji zafin daukarki ta kaiki makaranta ba ta wayar da ke ki goge sai yanzu ke zaki ji kyamar auren mijinta da rike mata yayanta ko? Wato kin ci jar miya kin waye, kin bani mamai Aisha ba irin wannan tarbiyar nai miki ba, kuma ban tsammaci irin wannan sakamakon daga gareki, hakika da Rukaiya tana da rai data gwammace bata rika ki a gurinta ba” Fashewa tai da kuka mai tsanani, sai ina ta hau ta da masifa. “Ni ba kuka nace ki min ba munafuka, tashi kije dakin amo ga bakuwa can tana jiranki” Daga haka Inna ta fice, Farhat kuma ta kwanta a gurin tana ta kukanta kamar bata ji abunda Inna tace mata ba, bayan dan lokacin sai ga Anty Ummi ta shigo dakin da sallama. Amman kukan da Farhat take ya hana ta amsa mata, cikin tashin hankali Anty Ummi ta zauna bakin gadon kusa da ita ta rumgumota tana tambayar dalilin kukan nata. _________________________________________ Kun tuna waye Auwal kuwa? Anya Zain zai yarda Hafsatu ta zauna a gidansu Doc Hafsat kanwar Auwal? Da gaske Ya Bashir zai iya runtse ido ya auri Farhat? Ya Zain zai yi da Anty Ummi, mi zai biyo baya? Me Hameeda take shiryawa? Shin Farhat zata iya yima Anty Rukaiya halacci ta auri mijinta domin kawai ta rike mata yayanta? [2/19, 9:48 PM] خديجة أبو بكر القلوي😍: *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 1⃣8⃣ Dawowa tai ta zauna tana cigaba da masa kallon mamaki. “Amman miyasa?” “Saboda ke Anty, yau idan naje gida zan sanar da Dada da Mai Martaba cewar akwai wacce nake so” Hannayenta biyu ta daga sama tana yi ma Allah godiya. Shi kuma ya tashi ya fice zuwa gurin motarsa, idan ya tuna saboda Anty Ummi zai yi sai yaji kuzari da son yin haka, ta dayan bangaren kuma yana tunanin irin zamantakewar da zasu yi. Daga Gada biyu zuwa kan wurin sarki tafiyar awa daya yai har da wani abu, saboda yanayin driving din da yake, yana faka motarsa kansa yai mugun sarawa har cikin zuciyarsa, cikin rashin kuzari ya fito daga motar ya nufi part dinsa. Saman cushion ya zauna ya lumshe idonsa yana maida numfashi a hankali. “Saboda ke ne kawai” Ya fada yana bude idonsa. Sai kuma ya tashi ya shiga bedroom dinsa, kayan jikinsa ya cire ya bude drawer ya dauki tawul ya daura ya shiga bathroom, yana shiga ya raba jikinsa da tawul din ya kunna shower yai tsaye ruwan na dukan kansa, sai kuma ya juya ya jingina hannayensa jikin tile din ya rufe idonsa. Ya samu kusan minti talati a haka, sai da yaji kiran sallah la'asar a masallacin dake cikin fadar sannan yai wanka ya fito a gagauce ya shirya ya fita domin baya son ya rasa jam'i. Bayan ya sauke farilla ne ya shiga part din Dada dan ci abinci duk kuwa a kasancewar an kai masa nasa a part dinsa. A falo ya sameta zaune daya daga cikin bayin gidan tana matsa mata kafafunta, dayar kuma tana bare mata ayaba. Yana shigowa dakin duk suka sanda kansu kasa domin su kansu sun san kallo na daya daga cikin abunda Yarima Zain ya tsana, kusa hada baki su kai gurin gaisheshi muryarsu har rawa take, ba azabtar da su yake ba, amman yana musu kwarjin da ko motsi yai sai sunji kamar numfashinsu zai dauke. A kujerar dake facing dinta ya zauna yana gaishe fuskarsa cike da annashuwa kamar da gaske farincikin ne har cikin ransa. “Dada sannu da gida” “Wannan farincikin na minene? Da har tasa kai mana dawowar rana a yau?” Ya fadada fuskarsa da murmushi. “Na wani albishir ne mai girma wanda kuka dade kuna jira, ke kawo min abinci” Ya karasa yana kallon mai bare mata ayabar. Jiki na rawa ta tashi ta nufi inda dinning din Dada yake, Dada kuma tai dariyar daya bayyana hakoranta biyu na maka tace “Labarta min naji, indai mai dadin ji ne kana da babba goro...” Dagowa yai har zai yi magana sai Abida ta shigo fuskarta cike da damuwa sai da ta fara zubewa kasa ta gaishe da Zain sannan ta fadi gaban Dada ta kwashi gaisuwa, sai kuma ta zauna gaban Dada fuskarta kamar zata fasa kuka. “Akwai wata magana ne...” Dada ta tambaya tana kallon yanayinta. Murzar hannunta take kamin ta soma magana kamar da tsoro. “Allah ya taimakeki, Gimbiya Hameeda tana daki tun jiya bata fito ba, ta kuma min gargadi da kar na kuskura na shiga dakinta har sai ta bukaci hakan” “Bata da lafiya ne?” Dada ta tambaya cike da kulawa. “Allah ya kara miki nisan kwana, nima ban sani ba” “Jeko bude dakin” “Ta hanene ranki ya dade idan har na bude zata iya min mugun wulakanci...” Tashi Zain yai ya fice daga falon, kai tsaye part din sisters dinsa ya nufa wanda a cikin dakunan ne Hameeda take da nata. Yana isa ya tura kofar dakinta ya shiga. Tsaye yai cak sakamakon arba da idanuwansa suka yi da kayan mayen dake saman gadon Hameeda, ita kuma tana gefe daya ta makure guri daya ta hana ta sharar bachinta. Kallon kayan maye kawai yake yana mamakin inda ta samo su, yaushe ta fara shaye-shaye? Karasawa yai kusa da gadon ya dauki kwalbar yana dubawa, fuskarsa cike da damuwa da kuma mamaki. Kara matsawa yai ya kai hannunsa yana tashinta, firgigit ta bude ido ta tashi zaune tana kallonsa idonta a juye kwalli duk ya bata ido ya dararo har saman kumatunta. Zuwa can kuma ta zabura tana kokarin rufe bakinta, hakan ya tabbatar masa da cewar sai a yanzu ta gane shi kenan. “Waya baki wannan?” Tai shiru sai rabon ido take kamar munafuka. “Answer me....!” Tsawar daya daka mata ne yasa tai saurin sauka daga kan gadon ta koma can gefe, sai kuma ta nufo kofar ta kulle. “Doc.. Doc... Ne... Ya bani.. Shi.. ” Ta fada muryarta na gargada, ido Zain ya kura masa yana karantar gaskiyarta, ita kuma ta kasa daga kai ta kalleshi, sai wani munafukin numfashi take dan kawai ya jita. “I and Doc Hashim ne kawai Mai Martaba ya yarda su duba iyalansa? Shi ya rubuta miki wannan? I will call him” Yana juyawa, sai tai saurin faduwa kasa ta rike masa kafa tana kuka. “Dan Allah karka kira shi, ka rufa min asiri karka fadawa kowa” “Waya baki? Yaushe kika fara shaye-shaye?” Dago kanta tai ta kalleshi. “Ni na siya, bana samun bachi ne shine ya iya ina sha dan na riga bachi” “Mi kika rasa da har zai sa ki rika shayeshaye? Kin san halin da Dada zata shiga idan taji wannan labarin? Mai kike tunani zai faru idan na sanar da Mai Martaba?” Tashi tai tsaye ta nufin gurin window ta tana hawaye. “Na rasa komai, da fari Mahaifiyata ,mahaifina, sai kuma yayata, daman tuntuni na dade da rasaka, ba ni da wanda zai saurareni ya bani shawara akan wasu abubuwan, ba ni da kowa na rasa kowa, ada kana saurarena kana bani shawara akan wasu abubuwan ina maka kallon dan'uwa kuma abokin fira, yayata ma tana nan tana fada min gaskiya, amman bana gani sai a yanzu dana rasata nake gani nayi rashin da ba zan taba maye gurbinsa ba har a bada, Ba zan taba yafewa kaina ba, na musgunawa Haleema, tayi ta bani shawara amman ban dauka ba, yanzu na rasa ta na rasa kowa, Dada ba komai take fahimta ba, na koma ni kadai ba ni da kowa...” Ta zube masa tana wani irin kuka mai taba zuciyata tare da zubewa kasa ta rike lalulayen window da karfin gaske. Zain ya hade yawun dake bakinsa zuciyarsa na sosuwa da kalamanta. “Ki tattara duk wani abun maye nan ki dora saman gadon nan, otherwise na fadawa Mai Martaba... Lastly wash your face ki zo falo Dada na nemanki” Yana kawai nan ya juya ya fice. Part din Dada ya dawo ya zauna inda a gurin daya zauna dazu. “Lafiya take?” “Kanta ke dan ciwo sai kuma jiri, amman zata fito yanzu” Ya fada yana misalta irin yanayin da Dada zata shiga idan har taji Hameeda tana shaye-shaye. “Bari naje na dubata” Tana kokarin tashi tsaye sai yai saurin dakatarda ita. “No Dada gata nan fitowa” Sai kuma ya kalli Abida. “Abida akwai abu a kan gadon Hameeda jeki kwashe min komai kisa a leda ki kai min dakina” “An gama ranka ya dade” Ta tashi da sauri ta fice daga dakin. Hannu ya kai ya bude plate din da aka aje masa abinci sai kuma yaji ba zai iya ci ba, Hameeda ta tsaya masa a rai, zuciyarsa nata raya masa ita din abar tausayi dukan abunda ta fada gaskiya ne tana da bukatar wani kusa da ita, yasan yanayin gidansu sisters dinsa duk ji suke da kansu ko kuma ko wacce da mahaifiyarta a gidan, ita kadaice sai ragowar wadanda ake riko ne basa da iyaye a gidan, amman a waje suna da iyaye amman ita fa? Ba uwa ba uba, gashi ta tashi a hannun Dada bata saba da kowa ba sai shi da Dada da kuma Haleema duk da kasancewar ita Haleema ba a gidan take ba. Sallamarsa ce tasa ya dago ya kalli kofar, wata tafiya take daidai hijab din dake jikinta na kokarin tadeta ta fadi kanta a kasa ta zauna kusa da Dada. “Muhammad yace kanki na ciwo” Dada ta fada tana shafa kanta cike da tausayinta da kuma kulawa. “Ee ina son bachi ne” “Aa idan Muhammad ba zai dubaki ba, sai a kira Doc Hashimu ya dubaki” Sai Zain yai karaf yace. “Na bata magani.” Daga Dada har ita Hameeda din kallonsa suka yi, sai kuma Hameeda ta maida kanta kasa tana fadin “Ee ya bani magani, shiyasa nake son na kwanta” “To je ki kwanta Allah baki lafiya” Sai da ta amsa da amin sannan ta tashi ta fice, Zain ya bita da kallo zuciyarsa nata raya masa abubuwa. *** *** *** Around 4pm Doc Hafsat ta isa gida tare da takwararta Hafsatu manga, da fari Hafsatu tai kafuwar kin shiga gidan har sai da Doc ta lallabata sannan ta yarda ta shiga shima dan ta rike rigar da Doc Hafsat take sanye da ita. “Assalamu Alaikum ga bakuwa.... ” Doc Hafsat na saka kafarta cikin falon ta fadi haka cike da annashuwa, daman ta sanar da su tun lokacin da Ibrahim ya sanar da ita. Sai Momy ta amsa mata da far'ah tana taba hannayenta. “Lalle marhabun da bakuwar gidanmu.. Maraba da ke” Dukansu fuskarsu a sake take, daga Momy har Auwal da kuma Sapna. Kusa da Yayanta Auwal Doc Hafsat ta zauna tana fadin. “Amman fa bakuwar tsoron mutane take” Auwal ya kai hannu zai rikata sai tai saurin shigewa jikin Hafsat, amman hakan be hanashi fisgota ba. “Indai tsoron mutane kike kin shiga uku da ni, fada min inda na sanki dan ni nasan na taba ganin wannan fuskar” Ya fada yana lasa hancinsa, buge masa hannu tai tana murguda masa baki. “Really ashe dai kema yar duniya ce” Sai duk suka sa dariya har Momy, ita kuma tai saurin rufe fuskarta wai taji kunya. Hannunsa yasa ya janye mata nata hannun daga fuskarta yana kokawar rabata da katon Hijab din dake jikinta, a dayan bangaren kuma yana ta kokarin tuna inda ya san fuskarta. “I remember, ki ce na kade ranar nan, ga fuskarki nan, a lokacin ina sauri zanje aiki kuma na bi ta gidansu Farhat” “Au ita ce?” Cewar Momy. “Yeah amman yau ta min kyau sosai kamar ba ita ba” “Ai dole tai kyau Doc Zain fa yake kula da ita” Hafsat ta fada tana dariya. “Amman kin san shegen doctor nan ya sha da ni, assume as I'm ace kamarsa ya tsaya yana katsa min tsawa ban rama ba, i tot wani yayanta ne ko jininta that time i was very stupid da ban rama ba Wallahi” “Kai dan sarki ne fa, kuma asibitinsa ce” “Dan sarki? Like seriously? Ina ruwana da sarautarsa idan sarautar yake takama da ita mu kuma muna takama da kudi da kuma mulki, fada min akwai uban daya isa ya takani?” “No amman Dsp ai komai da muhallinsa” “Yeah amman ya shamace ni da yawa” Sapna ta kalleshi “Ni fa ban gane kan maganar ka ba” Sai ya labarta musu abunda ya faru bayan ya kadeta, domin acan farko ya fada musu cewar ya kade wata amman be fada musu yadda abun ya faru ba. “Wata kila kadewar da ka mata ne ya haddasa bata magana” “What” Ya fada yana kallon Doc Hafsat. “Yes aiki aka mata a halshenta be fada min dalilin jumuwanta ba, amman baya rasa nasaba sa wannan kuma har yanzu bata magana idan tana son abu sai dai ta nuna, gashi ba a san inda kowa nata yake ba” “Ayyah” Momy ta fada cikin tausayawa. Auwal kuma ya kalli Hafsatu manga cike da tausayi ya aje Hijab din dake hannunsa sama kujera ya daga ta ya zaunar saman kafafunsa. “Am sorry dear it wasn't intentionally” Har ga Allah tausayinta duk ya rufe shi, musamman da yaji shine dalilin rashin maganarta. FARHAT POV. Kana ganin yadda take tafiya kasan dole aka mata, fuskarta kamar bakin hadari babu annuri ko kadan a tare da ita. Tana zuwa ta juya masa baya. Shi kuma sai yai murmushi ya sauke hannayensa ya ce. “Ki kwantar da hankalinki Farhat ni ba zan miki dole ba, ko can baya ni ban nemi a hada aurena da ke ba, iyayenki ne suka ga dacewar hakan shiyasa suka gabatar min da ke ni kuma ba zan iya musa musu ba saboda yarana suma ina son su samu farinciki” Yayi Shiru tare da sauke ajiyar zuciya sai kuma ya cigaba. “Na zo ne kawai dan na fada miki, ko kuma na baki shawara, idan akwai wanda kike so ki fito da shi kamin lokacin da aka dibar miki ya cika, no ba zan cilasta miki zama da ni ba, amman karya nake na ce bana son ki Farhat, son ki ne ya jani na kasa hakura har na kusa fadawa halaka, abunda ban aikata a waje ba nai unkurin aikata shi a cikin gidana, da ace na san da zuwan wannan ranar da ban furta wata kalma a gareki ba, kuma da nasan hakan zai yi silar mutuwar Rukaiya da ban furtata ba ko da kuwa hakan na nufin ajalina ne... Nayi nadamar abunda nai....” Wani banza tsaki ta buga masa ta juyo ta dawo cikin gida ta barshi can waje. [2/19, 9:48 PM] خديجة أبو بكر القلوي😍: *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 1⃣7⃣ Kuka tai sosai har sai da Anty Ummi ta gaji da rarrashinta, sannan tai shiru idonta duk ya kumbura ya canja kala. “Ina ciki matsala Anty sun kasa fahimtata, nayi nadamar fallasa sirrin nan da nai da ace ban yi haka ba da Anty Rukaiya tana nan a raye da basu cilasta min aurensa, da yanxu ina cikin garin gusau da zama, sai dai naji d abunda Auwal yai min...” Cikin kuka take magabar, Anty Ummi jikinta duk yayi sanyi, ko Farhat bata fito fili ta fada mata ba, tasan da ita take da ace bata fadawa Anty Rukaiya ba da duk abun be kwabe kamar haka ba. Cikin rashin kuzari Anty Ummi ta kama hannunta ta rike. “Farhat ki kaddara haka Allah yaso a gareki, maganar Bashir kuma ba zaki taba shiga hannunsa da sunan aure ba matukar yan'uwanki zasu yarda ki auri wani” “Bani da wanda zan tsaida Anty, na kori kowa saboda Auwal shi kuma ya juya min baya ya canja min, bani da waya ma balle har na kira wani...” “Baki bukatar kiran kowa Farhat matukar zasu aminta ki auri wani to Zain zai aureki...” Cike da zarani da firgici ta kalli Anty Ummi baki sake. “Yes na san baku jutuwa, amman bamu da wata mafita bayan wannan” “Idan akwai wanda na tsana a duniyar nan kamar mutuwata Zain ne Anty kin sani, shima kuma ya tsaneni, wannan abun ba zai taba yiyuwa ba” “Ke dai kike tsanenshi, amman shi yana kaunarki, kawai dai halayinki ne baya so wanda nasan shi ma a yanzu ya daina, domin sai da ya zubar da kwalla akan abunda ya sameki, shi ma da kansa yake cewa da ace zaki amince da ya aureki...” Sanda kanta tai kasa ta hade yawun bakinta, ita kanta tasan wata karya da hankali zai dauka, wannan kam bata shiga ba. “Bayan shi ba muda wata mafita Farhat, kunma ina ganin ya cancanta ki auri Zain ko dan alakar dake tsakaninmu, sannan kuma Auwal ya gane kuskuren da yai ta hanyar ganin kin aure wanda ya fishi komai, mulki kudi kyau da komai ma” “Ba zan iya ba Anty ba zan iya auren dan'uwanki ba, nafi tsanarsa fiye da Ya Bashir, idan har na yarda na aureshi shima cutuwa zan yi” “Ba zaki cutu b Farhat na miki alkawari, kuma indai har na isa dake na kai na rokeke abu kiyi min to ki amince da auren nan saboda da ni!” Da sauri Farhat ta kalleta tana girgixa kai hawaye na cika idonta. “Idan har baki amince da auren nan ba Farhat, ba zan sake zuwa garin nan ba, ba zan taba mantawa da wannan butulcin da kika min ba har abada, kuma na rabu da ke kenan!” Anty Ummi na kaiwa nan ta tashi tsaye ta dauki jakarta tana fadin “Gobe ko jibi zai zo ganinki idan kin ga dama karki fito, ko kuma ki fada masa baki sonsa sai nasan kin cika yar halak” Juyawa tai ta fice Farhat ta bita da kallo baki sake tana hawaye. YARIMA ZAIN POV. Yana yin parking ya fito cikin bacin rai ya nufi Mr Zain rooms, sai da ya kai dakin da Hafsatu take sannan ya sauke ajiyar zuciya ya tura kofar ya shiga. Doc Hafsat ya samu tare da ita suna taba waya da alama game ta kunna mata ko kuma wani abun take nuna mata a ciki. “Ina kwana, Doc Ibrahim ne ya kirani yace na zo naje da Hafsat yayi min bayanin komai, amman sai zuwa anjima idan zan wuce zanje da ita” A tare ta jeru nasa bayanin, kai kawai ya daga mata ta karbi wayarta dake hannun Hafsatu manga ta fice. Kusa da ita ya zauna ba tare da ya kalleta ba ya fiddo wayarsa ya kira Ibrahim be yi picking ba ya shigo dakin hannunsa rike da wayar tana ringing. “Miyasa zaka fada mata komai? Ce maka nai ka turo min ita?” Ibrahim din be amsa masa ba be kuma daina murmushin da yake ba, sai da ya zauna. “Zain ka cika matsala Wallahi, matukar muna son Hafsat ta rike mana yarinyar nan dole ne mu fada mata gaskiya, beside baka da wani gurin kaita daya wuce can, kasan dai Anty Ummi tace ba zata karbeta ba, ba kuma zaka kaita gidanku ba, ina zaka kaita?” Iskar dake bakinsa ya busar ya kalli Hafsatu manga wacce ta kwanta saman hannayenta. “Zain, ina tunanin ya kamata ka amince da bukatar Anty Ummi” “Ko da hakan na nufin na cutu? Kai ma ka zabi bangareta” “This is not the right time to take anyone side, kawai ina baka shawara ne ga abunda nake ganin ya dace” “Auren Farhat kamar salwantar da rayuwata ne Ibrahim and you know it” “Ita bata salwantar da tata rayuwar akanka ba? Saboda kai aurenta a farin ya mutu? Saboda kai mijinta ya daketa har tai miscarriage, ka manta lokacin da Mai Martaba ya koreka ita ta dauki kaddarar zama da kai, a gabana ta furta cewar dan'uwanta yafi mata mijinta, ya fi mata yayanta kuma rayuwar dan'uwanta tafi mata rayuwar aurenta ko da hakan na nufin karshen rayuwarta ne, dukan abunda zai faranta maka rai Anty Ummi tana kokarin yinsa ko da kuwa ita zai bakanta mata maka rai ne, Anty Ummi da Hameeda su suka fi kowa baka gudummawa a lokacin da aka shiga takaninka da Mai Martaba ko ka manta hakan? Zain kai da kanka kake fada min kana neman ranar da Anty Ummi zata bukaci wani muhimmin abu kai mata saboda ta san tana da kane kuma dan'uwan da zai iya share mata hawayenta, amman yau kai da kanka kake son zubar hawayenta....? Am totally confused” Zain yayi saurin mikewa tsaye saboda hawayen da suka cika masa ido ya nufi window yana saka hannayensa aljihu. “Idan na amince da auren Farhat, nai yaya da Hameeda?” “Mai Martaba yafi son ka fiye da komai daya mallaka a duniyar nan, zai goya maka baya ka auri matar da kake so, kuma dole na Dada Yalwa da Hameeda su sakar maka marar yin fitsari, dole ne ka zama Namiji Zain, ko za a kada a raya karka yarda ya janye ra'ayinka akan aurenta matukar ka gabatar da ita a gurin Mai Martaba, aurenta saukeki ne a gareka Zain, zaka samu damar zama da Yarinyar nan a cikin gidanka...” Shiru ne ya biyo baya dakin yai tsif kamar babu kowa a ciki. Zuwa can Zain ya juyo ya kalli Ibrahim. “Ka tunatar da ni abunda be kamata na manta ba, zan yi komai saboda farincikin yar'uwata kuma uwata...” Ya karasa yana girgiza kai, sai Ibrahim yai murmushi ya tashi yaje ya dafashi. “Good, abu na biyu kuma ina son ka amince yarinyar nan ta zauna gurin Hafsat da zarar ka yi auren sai ka maidata hannunka” Zain ya kalli Hafsatu manga data bata fuska garin lake kafada har munduwar hannunta ta fadi, dan Murmushi ya sakar mata yaje ya dauki munduwar ya kama hannunta zai saka mata sai ya tsaya kallon sunanta dake rubuce. H A F S A T aka rubuta a rarrabe, wani abun mamaki munduwar ta azurfa ce mai tsada irin azurfar nan da sai wane da wane ke sakawa idan ma ba wanda ya sani ba babu wanda zai banbanceta da zinari. “Waya siya miki wannan abun hannun?” Ta nuna sama. “Babanki?” Ta girgirza kai alamar a a. “Mamanki?” Ta gyada masa kai, kama hannun nata yai ya saka mata, fuskarsa da mamaki. “Wannan azurfar mai tsada ce, anya yarinyar nan yar hudun hijira ce kuwa?” “Alamunta ya nuna haka, itama kuma haka tace” “Amman waya taba wannan zinarin haka mai sunanta?” “Azurfa ce” “Amman yayi kama da gold, mamanki mai kudi ce?” Ibrahim ya karasa yana tambayarta, sai ta girgiza masa kai idonta na cika da kwalla. “Tace mun mahaifiyarta mahaukaciya” “Amman.... ” Zain ya daga masa hannu. “Karka takura mata dan Allah, bata da bakin amsa tambayoyinka a yanzu” Sai ya kama duka hannayenta biyu ya hada guri daya ya rike yana mata murmushi. “Mama Doc zata tafi da ke gidansu ki zauna na wani lokaci kamin Anty Ummi ta yarda ki zauna gurinta” Ta lake kafada tana hawaye, alamar bata yarda ba ita ba zata zauna ba. “Zata kula da ke sosai kuma duk abunda kike so zata miki, kuma kullum zan dinga zuwa ina dubaki, zan siya miki duk abunda kike so” Ta kara bata fuska tana ta hawayen dole. Hakan yasa Zain jin babu dadi. “Kina son madara da nama?” Ta gyada kai da sauri. “To zan dinga siya miki kinji?” Ta sake gyada kai, sai yasa dayan hannunsa ya share mata hawayenta, sannan ya mike tsaye ya kalli Ibrahim. “Ka fada mata bata bachi ita kadai saboda tana tsoro, kuma idan zata kwanta ana mata addu'a, sannan k tambayeta nawa za a rika biyanta every month or week” “Wow...” Cewar Ibrahim yana dariya. Zain be kula shi ba ya fice hannayensa zube a aljihu. Misalin uku da rabi ya tashi aiki kai tsaye gidan Anty Ummi ya wuce, cikin kuzari ya tura kofar falonsa ya shiga zuciyarsa na mugun bugawa kamar zata fito. Yana shigowa ta juyo ta kalleshi fuskarta da murmushi tana kokarin cire hijabin da ke jikinta. “Yau kuma an tuna damu dirar rana aka mana” “Na dauka fushi kike da ni” Ya fada, bayan ya zauna saman kujera. Sai tai murmushi ta soma nade hijabin tana cewa. “Akwai wata rana da muka yi fada da kai saboda littafin makarantana da ka yaga, sai na dauki fushi da kai bana maka magana, da Mama ta lura da hakan sai ta kirani ta umarceni da na kama hannunka, sai na kama na rike cikin fushi, sai tace saki fuskarki Amina, karki sake fushi da dan'uwanki komai zai miki kiyi hakuri shi yaro ne, wata rana kuma ke uwarsa ce kinga uwa ai bata fushi da danta, ina son ki so dan'uwanki fiye da komai a duniyar nan, baki samu komai a ko wane lokaci amman ban da mahaifiya da mahaifi da kuma yan'uwa, kuma babu wani abu mai maye gurbinsu har abada! A lokacin ina da shekara goma, amman Allah ya bani hankalin da ban sake fushi da kai ba, komai zaka min zan kyaleka ko da raina ya bace, idan kuma naga wanda zai taba ka sai inda karfina ya kare, akan wannan turbar nake har yau, ban yi fushi da kai kana karaminka ba ba zan taba fushi da kai yanzu da girmanka ba, ko da nayi fushi da kai na dan lokaci ne idan shaidan ya ribance ni amman ba mai dorewa ba” Ta kai hannu ta share hawayen idonta, sannan ta tashi tsaye ta nufi hanyar bedroom dinta tana fadin. “Yau ban je aiki ba, kauye naje kuma ban samu na girka abinci ba, ka hada wani abun ka sha kamin na dora girki” Tashi Zain yai tsaye ya saka hannayensa aljihu ya ce. “Idan har auren Farhat na nufin farincikinki na shirya aurenta.... Zan kuma koyi hakurin zama da ita daga yanzu...” Da sauri Anty Ummi ta juyo ta kalleshi. [2/26, 10:39 AM] Ayusher P: *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 1⃣9⃣ Misalin goma na safe ya fito daga sasshensa, yau kam yayi bachin safe wanda a manta rabon da yayi irinsa saboda jinyar Hafsatu da yake. Part din Dada ya nufa, yau kam ya tararda Hameeda ita kadai na zaune falon Dada tana karyawa. “Ina kwana?” Ta gaisheshi muryarta na rawa, ba tare da ta bari sun hada ido ba. Be amsa ba be kuma fasa kallonta ba har ya zauna kusa da ita kasancewar ita tana kasa ne shi kuma yana saman cushion. “Akwai wani abun da kike son mu tattauna ne?” Ta dago idonta ta kalleshi sai kuma ta sauke. “Aa ba komai” “Feel free ki fada min abunda yake damunki, zan saurareki” “Kamar da?” Ta tambaya idonta narau-narau. Shiru yai kamar ba zai ce komai ba. “Fiye da da” Zata sake wata maganar sai ga Dada ta fito daga bedroom dinta sanye da wani tsadadden lace. “Kai Amaryata kin fito fes...” “Kasan fa kai dana ne ba jika ba” Ta fada tana murmushin kasaita. “Aa yau dai bangaren jika na dauka, ki bar da sai idan nayi laifi, ko da yake na kusa yinsa tun da kishiya zan miki kwanan” Dam gaban Hameeda ya fadi, zuciyarta nata raya mata ita ce. Dada ta bude baki. “Kai kai wace mai dajara ce wannan?” “Wata kyakkyawar yarinya ce kama da indiyawa” “Ciki ko wajen masarautar nan?” “Bata da alaka da masarautar nan, amman dai mai tarbiya ce” A take murmushi da annashuwar dake fuskar Dada ya gushe, ta murtuke fuska kamar an aiko mata da mutuwa. “Tarbiya bata burge mu, domin cikinta muke kuma munyi gadonta, ko da wasa be kamata ka tsallake marautar nan ka dauko wata ba, ba zaka burgemu ba, mai martaba da ni ba zamu lamunta ba, ba zamu yarda ka kawo mana bare ba...” Hameeda ta hade yawun bakinta da suka mata daci ta tari numfashin Dada. “Ko da baren nan ita ce silar farincikinsa? Kuma ita yake so kamar ransa? Haba Dada tun yaushe kuke jiran zuwan wannan ranar ranar da Yarima zai gabatar da wata mace a matsayin matar aurensa? Dada baki tunanin lokaci yayi daya kamata a bar kowa yabi zabin ransa? Kar kankancinta ya dameki ke dai abunda kika sani wanda zai aurota mai daraja ne a gurinki, dan Allah dan girman Allah ku bar mu mu auri wadanda muke so” Ta karasa tana hade hannayenta guri daya alamar roko. Zain was shocked irin yadda take defending dinsa. Dada was shocked too da abunda yake fitowa daga bakinta, ga kuma fuskarta na nuna gaskiyar rokon da take. “Yaushe tarbiyarki ta lalace haka da har zaki iya daga baki ki fadi wannan maganar?” “Auren biyu zan yi bana daya ba Dada, daga ni har ita muna da damar zaben abar da muke so ko da kuwa wajen masarautar nan ne, ke dai ce gatana a duniyar nan Dada idan kika tsaya min ko mai martaba ba zai musa ma bukatata ba, ke uwace a gareni shiyasa na kawo bukatata a gareni Dada ki taimaka ki zame min uwar da kike ikirari dan Allah” Ya marairaice mata sosai kamar zai yi kuka.. “Wato kunje kai da wacan bakar yar'uwar taka kun gada kai ko?” “Ba wani hadin kai Dada kema kin san idan bana son abu babu wanda ya isa ya saka nai yi, ni naga yarinya nanu ina sonta shiyasa kuma nayi tunanin zaki goya min baya shiyasa na gabatar da ita a gareki” Yana kaiwa nan ya tashi ya fice daga falon yana mai nuna bacin ransa a fili. Hameeda ta kalli Dada ta ce “Miyasa ba zaki amince masa ba Dada?” “Saboda ke nake son ya aura ba wata ba” “Ba zan taba yafewa kaina ba Dada matukar baki bar Zain ya auri matar da yake so ba, bana son Zain a yanzu Dada, son da nake masa na yan'uwanta ne kawai, amman ba zan iya zama da mijin yayata ba, Saif nake so kuma na gabatar miki da shi dan me zaki mana dole? Dada idan Zain be auri yarinyar nan ba kika san halin da zai shiga? Ke da kanki kike kewa ke uwarmu ce a gidan nan miyasa ba zaki mana abunda zai faranta mana rai ba” Ya karasa hawaye na sauko mata. Sai kuma ta tashi ta karasa gaban Dada ta kama hannunta ta rike. “Indai har dan ni neni dan Allah ki barshi ya auri wacce yake so, in yaso bayan aure sai ki gabatar masa da ni nasan ko dan kunyar ba zai iya musa miki ba, amman idan kika hana shi yanzu ba zai taba amincewa ya aureni ba, ganin wata yace yana sonta ma ai nasara shi yake nuna cewar ya fara zama mutum kenan dan Allah Dada ki amince dan Allah” “Idan har zan amince to sai dai ya hadaku ku biyu ya aureku...” “Aa Dada ki Kyaleshi ya aureta, in yaso daga baya sai ki gabatar masa da ni, idan kika masa haka yanzu zai iya kin amincewa nima ba zan ji dadin zama da shi ba a yanzu” Dada ta dauke kai ba dan ta gamsu ba. *** *** *** Daki daya suka kwana da Hafsat, da asuba Hafsat ta tasheta tai sallah sannan ta sake komawa bachi, bata tashi ba sai misalin goma na safe. Ta dade tana murza idonta kamin ta budesu kwarar biscuit daya ta gani an aje kusa da ita sai ta kai hannu ta dauka, a nan ta hango wani kasa tana kara dubawa sai ta hango an jera shi har kofar falo. Sauka tai saman gadon ta rika tsintar biscuits din da daidai har zuwa gurin kofa, hannu yasa ta kara bude kofar ta fito tana ta tsinta har ta kawo falo sam lura da kowa dake falonba har sai ta taji anyi gyara murya, sai tai saurin tashi tsaye zata waiga taga wanene sai kawai taji an dagata sama ana mata cakulkuli. Dariya take sosai har da kyalkyatawa kamar ba ita ba, da sauri Doc Hafsat ta fito daga Kitchen sanye da kayan bachi hannunta rike da knife tana kallonsu. “Ikon Allah yau Mama kece kike kyakyatawa haka” Auwal ya zaunar da ita saman kujera yana dariya. “Bata dariya ne?” “Tana yi amman bata kyakyatawa” Yayi murmushi yana kallonta cike da sha'awa, har yanzu bata daina dariyar ba sai dai ta daina kyakyatawa, sai da ta gaji da dariyar sannan ta kalli Doc Hafsat ta hade hannayenta tana gaisheta. Auwal ya mika hannun ya riko hannunta yana kallon munduwar dake hannunta. “Wai ya bincika iyayenta kuwa?” “Bana tunanin yayi hakan, kuma iyayenta a kauye suke kauyen kuma an kori kowa in ba yanxu su ka koma ba” “Ce miki yai daga kauye take? Look at this” Doc Hafsat ta rika hannunta tana dubawa. “I tot shi ya siya mata kamar zinari ko?” “Azurfa dai sinari ake mai suna sai a manyan birane, amman wannan azurfa ce mai tsada, baby shi ya siya miki?” Ya karasa yana tambayar Hafsatu manga, sai ta girgiza kai alamar a a. “Babanki ya baki ko Mama?” Ta gyada kai. Sai ya kalli Doc Hafsat ya ce “I don't think ya fada miki gaskiya akan yarinyar nan, idan har da gaske yar gudun hijirace miyasa be kaita sansanin yan gudun hijira ba, ko kuma ya kai ta gidansu, ai fadar sarki mai maraba da baki ce ko yaushe, actually yarinyar nan batai kama da yan kauye ba Hafsat, dubi abun hannun na nata duk iyayen da suka sakawa karamar yarinya kamar wannan azurfa mai tsada kuma mai sunanta ya nuna iyayen masu kudi ne, kuma ba yan kauye ba, abu na biyu kyawon yarinyar nan ya wuce ace daga kauye Kufawa take dube ta da kyau ki gani ba tai kama da hausawa ba...” Doc Hafsat ta kalleshi ta kalli Hafsatu manga. “Me kake nufi?” “I think satota yai” Ba shiri Hafsat ta saki baki sai kuma tai saurin rufewa tana girgirza kai. “No no Astagafurrullah, Doc Zain ba zai yi haka ba” “Ko...? Let's see...” Yasa hannayensa biyu ya rika kunnuwanta, yana kokarin tashi tsaye daga zaunen da yake a hannun cushion. “Cute baby, bye bye” Dariya tai amman ba mai sauti tana runtse ido. “Idan Momy ta fito ki ce mata naje kai Zainab airport” Kasa amsawa tai har ya wuce dan mamaki ya hana ta tace komai wani bangare na zuciyarta na son ya yarda wani bangaren kuma tana ganin kamar Zain ba zai iya haka ba, wayarta ce tai ringing, sai ta aje wukar saman center table ta nufi dakinta. Zain ne ya kirata ba karamin faduwa gabanta yai ba kamin ta dauka. “Hello ina kwana?” “Lafiya. Gani nan ganin Mama, ki sanarda iyayenki” “Okay sai ka iso” Tana aje wayar ta kwalama Hafsatu manga kira. *** ***** **** Sai ya shiga ya gaishe da Mai Martaba sannan ya fito daga cikin gidan gaba daya, a gaban wani katafaren Mall ya tsaya ya shiga ya zaba mata kala takwas masu kyau, dan be jin zata kai kwana takwas ma a gidan, sai kuma talkama, tsayawa yai yana kallon wasu talkami masu kyau dauka yai ya hada da wadanda cikin wani irin nishadi, har ga Allah yana jin son Hafsatu manga sosai yake jinta kamar yar da ya haifa, Allah ya sa masa son yara balle ita da take da shiga rai, and gata da sunan mahaifiyarsa sunan daya fi so fiye da ko wanne a duniya, yana da burin sakawa yarsa sunan idan Allah ya bashi, finally Hafsatu manga has it be ga dalili daya da zai hanata shiga ransa ba. Sai da ya biya kudin sannan ya koma dayan bangaren ya siya mata chocolate da wano sweet Candy mai dadi. A a mazaunin baya aka zuba masa kayansa sannan ya fito da wayarsa ya kira Doc Hafsat ya sanar mata da zuwansa sannan ya kama hanyar gidansu dake Millions quarters. Sai dai yai horn mai gadin ya bude masa sannan ya kunna kai harabar gidan, wayarsa ya sake daukowa ya aikawa Hafsat da sakon isowarsa, ko minti biyu ba ayi ba sai ga Hafsatu manga ta fito daga cikin gidan da gudu ta doso inda motarsa take fake, an gyara mata kai an saka mata ribbon tufafin jiya ne a jikinta amman tayi kyau sosai sakamakon kwalliyar da aka mata. Bude mata yai ta shiga front seat ta zauna sannan ya mika hannunsa ya rika hannunta yana murmushi. “Mama ya akayi?” Ta ware hannayenta alamar bata sani ba, tana murmushin daya fitarda dimples dinta. “An miki fada a nan ko an dakeki ko tsawa?” Ta girgirza. “Kina jindadin zama nan?” Ta gyada kai. “Good” Ya mika hannunsa a seat din baya ya dauko ledar dake da chocolate ya bude daya ya mika mata, cike da murna ta karba jikinta har rawa yake ta kai a bakinta. “Akwai dadi?” Ta daga masa kai, sai ta gutsiri wanda ke cikin bakinta ta mika masa, a maimakon ya karba sai ya mika mata bakinsa ta saka masa, kamar ba shi Zain din dake kyamar cin abun hannun mutane ba, balle kuma na baki da yake da tabbacin idan ya ci sai ya yi hararwa. Isowar Doc Hafsat ne yasa shi zuke gilashin motarsa ya gaisa da ita. “Ga tufafi nan a shigar mata da su, and duk abunda take bukata ki fada min, tayi kuka?” “Aa wani abun mamaki ma, yau tayi dariya har da kyalkyatawa lokacin da Auwal yake mata wasa” Ya danyi jimmm kamin ya ce “Wane Auwal?” “Yayana ne” “A nan gidan yake?” “Ee amman ba nan yake aure ba” A hankali ya sauke numfashi yana kallon Hafsatu manga, haka kawai sai yaji babu dadi, duk kuwa da kasancewar yana son farincikinta amman ya samu kansa da rashin jindadin hakan. “Ku shiga ciki akwai inda zamu je yanzu” Ya fada yanayinsa na canja. Fita Hafsatu manga tai rike da ledar tana masa bye bye, Doc kuma ta bude gidan baya ta dauki dayar ledar. Sai da suka shige cikin gidan sannan ya kunna motarsa ya fice, duk jin yai kamar bashi da lafiya damuwa ta rufewa wacce be san daga ina takeba. Kamin ya isa gidan su Anty Ummi ya dauki wayarsa ya kira Ibrahim, yana labarta masa abunda ya faru tsakaninsa da Dada da kuma Hameeda. “Amman ina tunanin akwai abunda Hameeda take hange” “She change fiye da tunaninka, yanzu ba ta nawa take ba, damuwa ya mata yawa ma, har shaye-shaye take” “Do you really think duk wannan gaskiya ne, baka tunanin plan ne?” “I don't think so, Hameeda ta bani gudumawa Ibrahim, tana bukatar taimako na a yanzu be kamata na kyaleta cikin wannan halin ba” “Ban zan hana ka ba, amman kayi taka tsantsan, mai son abunka ya fika dabara. Ina Mama?” “Tana Lafiya” Sai ya kashe wayar. Ya faka motarsa a harabar gidan Anty Ummi. Yana shiga tana shirin office, yau kam farinciki shimfide a fuskarta. “Yanzu nake shirin kiranka” “Gani na zo, amman ban karya ba” “Baka da matsala ga abinci nan a dinning, idan ka gama ka shiga dakina ka kara turare direba zai kaika Anka, abunda za aka bata yana bayan motar” ‘Really...? ’ Ya fada a ransa, a fili kuma sai ya ce “Okay” Ya zauna saman kujera, yana hade yawun bakinsa. Sai da ta dauki jakarta ta kai bakin kofa sannan ta kira shi. “Zain...” Juyowa yai ya kalleta. “Thank you so much” Kai ya gyada mata, sannan ta juya ta fice tana jan kofar. [2/26, 10:39 AM] Ayusher P: *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 2⃣0⃣ YARIMA ZAIN POV.   Sai da ya gama karyarwa ya bata lokaci sannan ya fito ya shiga motar, dereban Anty  Ummi ya kama hanyar Anka da shi, tafiya kawai suke yana mamakin kansa, but daya tuna saboda Anty Ummi zai yi sai ya kawarda komai a ransa.   Har suka isa be da natuwar jiki balle ta zuciyata, babu komai a cikin ransa sai tsanar Farhat, yadda zai iya daga ido ya kalleta yake tunani har suka isa garin.    Kusa da gidan direban ya faka motarsa,  sannan ya fita daga motar ya karasa da kafa kofar gidan yai musu sallama, sai da wani saurayi ya fito ya tambaya wanene direban ya amsa masa. “Daga Gusau muke, ita ai tasan da zuwanmu” Saurayin yana komawa cikin gida, sai gashi ya fito da kwanon fura da kuma tabarma. Direban ya karba ya karasa gurin motar ya shimfida, ya budewa Zain motar. “Ranka ya dade ka fito ga tabarma nan an shimfida” Wani banzan kallo Zain yai ma tabarma. “Bata da darajar da zanzo gidansu a shimfida min tabarma na zauna, kaje ce tai sauri ta fito ga mai siyenta ya fito” “An gama Allah ya taimakeka” Direban ya juya da sauri ya koma kofar gidan ya sake sallama da ita, yana mamakin furcin Zain. Bude motar Zain yai ya fito ya tsaya kan tabarma da takalminsa. Ba a kara minti biyu ba sai gata ta fito sanye da abaya green color, ta rame sosai kamar ba ita ba. Har ta karaso gurin Zain be kalli inda take ba sai kallon gonakin dake can yamma da su yake. Zuwa tai ta matsa ta rumgume hannayenta tana watsa masa harara kasa kasa. “Da ace kin min sallama, na nace kin baro wani hali daga tarbiyar gidanku” Ta kalleshi da kyau zuciyarta na sosuwa da kalaman. “Ban ga mutane ba, shiyasa ban yi sallama ba” “Haka ne, daman irinku marasa daraja basa kallonmu a mutane, saboda muna da matsayi na musamman” “Masara dajara suna a inda suke, mukan matakinmu ya wuce haka, tunda ka baro masarautarku ka baro aikinka ka kawo kanka gurina, ba tare da da fargaba ko tsoron abunda zai faru ba” Yayi murmushin takaici still be kalleta ba ya ce “Yana da kyau idan mutum zai siye abu yana da kyau kaje ka dubashi gudun cinikin kifi ruwa, fada min nawa ne farashinki domin ina jin nan da sati daya zan taimaka na siyeki” “Idan har siyena zaka yi, to abunda masarautarku take da shi, har ma a hada na masarautar kano da zazzau be siye ni ba, sai dai na taimaka na zama ya kamar kowa na yanka maka farashi mai sauki biyan, gudun saka masarautar Rishim a kunya” “Baiwar masarautar Rishim tafi karfin shiga kunya balle masarautar, ina ji miki tsoron ranar da bakinki zai ja miki a binneki da ranki, idan kin gama kallona ga abun sadaka nan a bayan mota ki shiga gidashi a kurkinku...” “Na fi karfin na shigar da abu da kai, sai dai a shigarmin dan nima surukar sarki ce a yanzu....” Tana kawai nan ta juya ta nufi kofar gidansu. Sai a lokacin Zain ya juyo ya kalli bayanta. “Kama damisa sa'a ne wasa da ita rashin kunya ne....” Komawa yai cikin motar ya zauna sai direban ya zo da sauri ya shiga gidan direba ya tashi motar. “Ranka ya dade ba a fitar da kayan da suke bayan motar ba” Zain be tanka masa ba, shi ma kuma be sake cewa komai ba, yaja motar suka kama hanyar gida. *** *** *** Bayan Zain ya wuce Doc ta dawo tare da Hafsatu manga cikin gida, daya daga cikin gowns din ta dauka ta saka mata. “Wow kin yi kyau Mama kin fito kamar balaraba” Murmushin jindadi Hafsatu manga tai tana shafa kayan, doc tai dariya tare da tashi tana amsa kiran da Sapna ke mata. “Ya akayi?” Sapna ta nuna mata hanyar kitchen tana cin soyayen dankalin turawa. “Abunda kika dora zai kone” “Amman shine ba zaki duba min sai kin kirani” “Ina laifi nama kiraki? Wai ku yan nigeria miyasa ba a muku daidai a rayuwar nan ne?” “Mtssw” Hafsat taja tsaki sannan ta nufi kitchen. Dariya Sapna tai mata tana kallon Momy data fito daga dakinta. “Momy ina kwana?” “Lafiya kalau yau ba zaki aiki ba?” “Sai na gama karyawa, kin san Abbah yace na daina zuwa da yunwa” “Hakan yana da kyau, daga nan sai a koreki ai” “Muke da gwannati ai waya isa ya koremu?” “Abun wani ai be taba zama naka ba, dan haka ba Alhaji Salis ne akan milkin ba, kanensa ya kamata ki san wannan” “Whatever ni dai nasan ina da alaka mai karfi da wani be isa ya koreni akan aikina ba” Momy ta tabe baki, kamin ta dauke kanta ta maida gurin tv. Doc ce ta fito rike da plate tana kwalama Hafsatu manga kira, da gudu ta fito. “Wow yarinya kin yi kyau kamar na sace ki” Sapna ta fada tana kallon yadda kalar rigar ta karbi fatar jikinta. Kallon rashin yadda Hafsatu manga tai mata jin tace ta sace ta. “Ungo zauna ki ci bari na hado miki tea” Hannu biyu tasa ta karbi plate din. Suna haka Auwal ya shigo sanye da kayansa na yan sanda hullar na rike a hannun. Wata uwar kara Hafsatu manga ta saki tare da sakin plate din dake hannunta ta nufi Doc Hafsat da sauri ta kankameta tana wani irin numfashi kamar zata shide. “Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un” Cewar Momy tana kallon Hafsatu manga kamar yadda duk suke kallonta. “Minene Mama minene?” Doc Hafsat ta tambaya. Bata iya amsawa sai kuka take ta rufe idonta gam, Sapna ta nuna Auwal. “Maybe uniform dinsa take tsoro kin san ba kowa ke son police ba” “Yan sanda kike tsoro?” Ta gyada kai da sauri jikinta sai rawa yake kamar mazari. “I told you” Cewar Sapna tana daga kafadunta sama, Auwal ya kallin uniform din yana murmushi. “Yanzu fa Mamata cewa tai na yi kyau, amman ina zuwa nan yarinya ta rika ihu kamar taga dodo?” “Miye marabinka da dodon? Ni dai dan Allah ka fita karka haukatata” Dariya yai ya juya ya fice. Babu irin lallabar da ba a mata ba amman taki yin shiru, haka Doc ta jata ta kaita dakinta ta kwanta ba dan tayi shirun ba sai dan ta gaji da rarrashinta. Ita kuma ta koma falo ta karya sannan ta dawo ta shirya ta wuce office. Around uku na yamma ta dawo daga aikin, ko da ta shigo Momy kawai ta samu a gidan, Sapna da Auwal duk suna gurin aiki. A gajiye ta shiga falon ta zauna saman kujera na wani dan lokaci sannan ta tashi ta shiga bedroom dinta. Can karshen gado ta hango Hafsatu manga na zaune har lokacin tana kuka idonta duk ya kumbura ga shi ko abincin safe bata ci ba, domin dazu kin kula komai tai. Zaunawa bakin gado Doc tai tana fadin “Wannan wace iri rayuwa ce haka Hafsa? Dan sanda kika gani a gabanki ko me? Tun kamin na fita babu kalar rarrashin da ban miki ba amman kin ki hakura, dubi yadda idonki ya kumbura kamar wacce aka yi ma wani abu haba dai... ” Wayarta ta fiddo ta dannawa Zain kira, sai da tai ta ringing kamar zata katse sannan ya dauka. “Hello Doc barka da wuni, Yarinyar nan ce tun dazu take kuka har yanzu taki ta daina” “Me aka mata?” “Ba'a mata komai ba, kawai saboda taga Auwal da uniform din police, tun safe take kuka har yanzu” “Gani nan zuwa” Ya katse kiran. Ita kuma ta kara matsawa kusa da Hafsatu manga tana mika mata hannu. “Zo nan dansanda bazai miki komai ba” Lake kafada Hafsatu manga tai alamar ba zata zo ba, har Doc ta gaji ta tashi dan canja tufafin dake jikinta. Cikin yan mintuna Zain ya iso gidan, ita kanta Doc tayi mamakin saurinsa sai kace wanda yake kusa da unguwar, text ya aika mata cewar gashi harabar gidan. Sai ta dauki Hijab dinta ta saka. “Zo muje ga Doc Zain can yazo” Sai a lokacin Hafsatu ta sauko daga kan gadon ta rika hannunta suka fita tare. Waige waige kawai take kamar ance mata dan sanda bullowa zaiyi ta wani wajen, daga cikin motar Zain ke kallonta har suka karaso, bude mata gidan gaba yai ta shiga tana ta shasshekar kuka. “Daman kuna da yan sanda gidanku?” Ya tambaya yana kallon yadda idon manga suka kumbura. “Ee Dsp Auwal Salis yayana ne” Jimmm Zain yai kamar mai tunani, ba zai ce be san dsp ba saboda yawan nunashi da ake a labarai idan wani abun ya faru, sai dai be taba sanin familynsu daya da Hafsat ba sai yau, impact be ma dauka dan garin nan ne ba. “Rufe mana motar” Haka kawai ya fada, ba musu ta matsa baya ta rufe masa ganbun motar, shi kuma yai ribas ya fice daga gidan, sai da ya kama hanya sannan ya kalli inda Manga take. “Mama fada min sun miki wani abun?” Ta girgirza kai. “Dan sanda kawai kike tsoro?” Ta daga kai. “Shikenan daga yau ba zaki sake ganinsa ba, zan kaiki gurin Anty Ummi kina so ko?” Ta lake kafada alamar bata yarda ba, sai sabbin hawaye take, yanzu kam hankalinta ya fara komawa gida. “Fine kina son chocolate na siya miki?” Ta daga kai. “Share hawayenki” Tasa hannu ta share. Hanyar da zata kaishi Jafatu ya kama zuciyarsa cike da tunani kala kala. A harabar gurin ya faka motarsa sannan ya bude mata ganbun motar “Ki tsaya nan bari na siyo miki na dawo” Ta daga masa kai. Sai ya bude gefensa ya fita ya shiga cikin Jafatu din. Tana zaune cikin motar tana jiransa ta hango wani magidanci sanye da narkakkiyar shadda ya fito daga Jafatu din makkale da waya a kunnensa hannunsa daya kuma rike da wasu papers, daya daga cikin papers din ne ta fadi, ganin hakan yasa Hafsatu manga fita da sauri ta nufi inda paper take duk kuwa da irin tazarar dake tsakani ta dauko ta falfalo da gudu ta kawo inda yake yana kokarin shiga mota ta mika masa. Kallonta ya tsaya yi sai ya katse wayar da yake da sauri ya karbi takardar bakinsa a sake kamar mai mamaki. Hannunta da Zain ya rika ne ya dawo da shi cikin hayyacinsa. Sai ya kalli Zain da sauri. “Yar ka ce?” Zain ya daga masa kai. “Allah sarki yarinya mai hankali” Mutumen ya fada yana shafa kanta, hannunsa yasa aljihu ya debo kudin da shi kansa be san ko nawa bane ya mika mata “Miye sunanki?” “Mama” Zain ya amsa masa a takaice, sai yaja hannun Hafsatu manga ba tare daya bari ta karbi kudin ba ya nufi gurin motarsa da ita. Da kallo mutumen ya bita har Zain ya sakata mota ya tada suka kama hanya. “Idan na sake barinki cikin mota kika fita sai na zaneki” Ya fada yana kallonta. Ita kuma sai ta bata fuska kamar zata fasa kuka. Hannayenta ya kalla “Ina abun hannunki?” Ta duba hannun, ita ma sai a yanzu ta tuna data bar shi kam mirror Doc Hafsat da tai mata wanka dazu da safe. “Yana gidansu Doc?” A nan ma kan ta gyada. Sai ya dauke kai ya cigaba da tukinsa har suka isa gidansu Anty Ummi, sannan ya fita daga motar ya zagayo ya bude mota ya fito da ita. Tana ganin gidan Anty Ummi sai ta bata fuska tana hawaye. Be kulata ba har suka shiga cikin falon hannunta na cikin nashi. Da kallo Anty Ummi ta bisu har ya zauna ita ma ta zauna kusa da shi tana hawaye. “Still...?” Ta fada. Kallonta yai. “Where else zan kaita bayan nan?” “Ba zamanta a nan ne matsala ba Zain, abunda zai biyo baya nake gudu” “Babu abunda zai biyo baya, just trust me” Ajiyar zuciya ta sauke. “Ina fatar hakan” Ledar ya bude ya dauko mata chocolate ya mika mata. “Please Aunt a mana one plate you know i can't speak louder” “One plate?” Ya daga kafadunsa. “Zan yi feeding dinta ne” Har zata ce wani abu sai kuma ta tashi ta nufi kitchen ta zubo masa abincin. Da kansa ya rika feeding din Hafsatu manga har ta koshi sannan ya cinye ragowar. Anty Ummi na zaune tana kallon ikon Allah. “You change Zain, kamar dai ba kai ba” “Akwai wani sabo a tare da ni?” “Babu, fada min dazu da kuka je gurin Farhat ya akayi?” Tabe baki yai yana jin sauraren yadda sunanta ke masa daci a makoshi. “Anty kin rage min girma da daraja da nake tare da ita, kin sa naje zance da yarinyar da tafi ko wace yarinya lalace a rashin kunya a duniyar nan” “Wani abun tai maka ne?” “No bata mon komai ba, amman dai kamar ita ma bata so” “Kar wannan ya dameka, ka tabbatar dai ka sanarwa mai martaba” Ya maida dubansa gurin Hafsatu manga data soma angaje bachin tana kwanto masa. Tasowa Anty Ummi tai tana kokarin rika hannunta. “Zo dakin zu Amal ki kwanta” Fisge hannunta tai ta rike na Zain. Haka ta wuni kusa da shi ko ina bata matsawa, dawoawar su Amal daga Islamiya ne yasa ta dan soma sakewa har ta sauko kasa ta zauna kusa da su tana kallon story book din da suke karantawa. Sai dare Zain ya baro gidan Anty Ummi a lokacin Hafsatu manga ta yi bachi kusan ma shi yai mata addu'a tare da Amal kasancewar gado daya suka kwanta. GIMBIYA HAMEEDA POV. “Farincikin ki ya fiye min komai a duniyar nan, zan miki duk wani abu da kike so Hameeda matukar ina raye.” “Kai nake so” “Gani ai kin samu ba zan taba barinki ba, tunda ni yayanki ne” Hoton da suka dauka tare take kallo tana shafawa hawaye na sauka daga idonta, kunnuwanta da Memory na taro mata wasu abubuwan daga rayuwarsu ta baya ita da Zain. “Ban san miyasa zuciyata ta kasa hakuri da kai ba! Ban san halin da zan shiga ba idan ka maye gurbin yar uwata da wata mace wacce ba ni ba, ina son ka Zain shin ko baka ganine?” Ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya. “Miyasa har yanzu na kasa daina kuka? Mi yasa zuciyata take wahalarda ni? Babu farinciki da kwanciyar hankali a matar da zaka aura Zain, kuma wallahi sai ka gane shayi ruwa ne” Ta share hawayenta sannan ta maida hoton cikin album ta maida cikin durowa ta tashi ta fita. Share your opinions. [2/26, 10:39 AM] Ayusher P: *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 2⃣1⃣ Be jin zai yi breakfast a gida yau, hakan yasa shi shiryawa da wuri ya fito part dinsa ba tare da jiran an kawo masa abun karin ba. Part din Dada Yalwa ya fara zuwa domin mata barka da kwana, sameta tsaye jikin kofa rumgume da hannayenta a baya fuskarta ba yabo ba fallasa. Tsayawa yai yana kallonta. “Dada lafiya dai?” Bata ce masa komai ba ta juyo ta dawo cikin falon ta zauna, shi ma zaman yai a kujerar dake facing dinta. “Dada ko dai ni na bata miki rai ne? Indai akan maganar aurena ne na janye ki saki ranki dan Allah” Wani dogon numfashi taja ta sauke. “Muhammad ni kamar mahaifiyarka nake, nasan da ace Hafsat ce a raye zata goya maka baya saboda abinda kake so ne, amman na kasa samu natsuwa da yarinyar nan da zaka auro, sai nake jin kamar babu alheri a auren nan da zaka yi” “Indai har dan na rashin natsuwa ne, kar hakan ya dame ki akwai alheri a ciki, sai dai idan har baki son auren zan iya fasawa” “Allah ya sanya alheri sai ka samu Mai Martaba ku yi maganar, amman ina son ka sani nan gaba kadan zan gabatar maka da wata bukatar, ko da wasa bana son ka musa min a kan haka” Yayi shiru yana kallonta kamar yadda itama take kallonsa irin kallon dake nuna babu wasa a kalamanta. “Zan miki duk abunda kike so” Kishingida tai jikin cushion din. “Ba zamu kashe kudi akan yar takala ba, ba za ayi dinner ko kamu a aurenta ba dauren aure ne kawai dole, saboda bana son duniya ta san waka aura har sai nan gaba, a sirrance za ayi auren dan bana son kowa yaji, auren nan ma a cikin fadar nan za ayi” Kai ya girgiza. “Haba Dada sai kace wanda zai auri karuwa?” “Idan dokokin basu maka ba, zaka iya fasa auren” Kansa ya shafa yana sauke ajiyar zuciya. “Shikenan as long as ba zaku wulakantata ba” “Wannan ya rage nata, tashi kaje Mai Martaba na nemanka” Tashi yai tsaye ya fice daga falon, Dada na binsa da kallon jin haushi. Sai ya bar part din Dada sannan ya kama part din Mai Martaba jikinsa a sanyaye yasan by this time Mai Martaba be isa fitowa falonsa na uku ba, wato falon daya ganawa da iyalansa kamar su Yaya da sauran wasu masu muhimmanci, babu tantama yasan Dada ta fada masa wata kila ma ransa ne ya bace. A falon na biyu ya samu Mai Martaba zaune shi kadai kamar daman shi yake jira, cikin ladabi yai sallama amman Mai Martaba be ko kalli inda yake ba balle ya amsa masa, guri ya samu nesa da shi ya zauna a kasa yana mika masa gaisuwa. A take Mai Martaba ya daga masa hannu. “Sanin kanka ne, Masarautar Rishim masarauta ce mai daraja da girma, a ko da yaushe ina fada muku kar kuyi abunda zai zubar da kima da darajar nasarautar nan. A yau ina son na fada maka wannan ya zama na farko kuma na karshe da zaka saka mahaifiyata ta nema maka alfarma mai girma irin wannan, ba zan iya musa mata ba” Har ya bude baki zai yi magana sai Mai Martaba ya sake daga masa hannu a karo na biyu. “Fada min wacece ita” Ya tambaya cikin Izzar dake nuna bacin ransa a fili. Wani daukewar wuta Zain yai na wani dan lokaci a rayuwarsa ya tsani bacin ran mahaifinsa domin yana ganin shi kadai ya rage masa a duniya, ko ba komai uba yana da muhimmanci a rayuwa babu ta yadda zai yi farinciki idan Mai Martaba baya yinsa, can kasa kasa ya tsinkayo muryarsa tana fitowa daga bakinsa. “Yar talakawa ce kuma a anka take zaune, amman tayi karatun boko da addini, gidansu mutane ne masu tarbiya...” Mai Martaba yayi shiru na dan wani lokaci kamin ya ce “Ba kai zaka fada mana tarbiyarta da rashinta ba, mu zamu binciko hakan da kanmu, ka taba zuwa kauye?” “Sau daya” Ya amsa da sauri. “Kar kafarka ta sake taka kauyen nan, zamu saka sarkin Anka ya nema maka aurenta a sirrance, idan sun baka za a daura auren a nan fada, zata so nasarautar nan a matsayin kuyangar da sarkin anka ya baka, kar wani daga wajen familyn nan yaji maganar auren nan, ba zamu dauki kuskure daga gareta ba karta kuskura ta aikata wani wawanci a cikin masarautar nan” “Duk yadda kake so haka za'ayi Mai Martaba” Ya fada cikin tsantsar ladabi da biyayya. Da hannu Mai Martaba yai masa alama daya tashi ya bashi guri, haka ya tashi jiki ba gwari zuciya ba dadi. Yana fitowa harabar gidan fadawa suka rika gaisheshi amman ko daga kai be yi ya kallesu ba balle har ya amsa musu, ba motar daya saba shiga ya shiga ba, wata ya shiga daban wacce take daya daga cikin motocinsa, yana fita daga masarautar kiran Ibrahim ya shigo wayarsa, a nan yake labarta masa komai abunda ya faru. Kamar yadda ya saba goya masa baya da shawarwari yau ma haka ne. “Kai ka kawo bukatar da ka san zata batawa kowa a gidanku rai, to miye abun damuwa dan mai martaba ya saka maka wadannan dokokin? Indai har kana son aurenta dole kai hakuri ka zura musu ido” “Amman kasan ni ba zan yarda su wulakanta min mata ba ko? Ko bana son ta idan na aureta hakokinta suna kaina kuma tana karkashin kulawata ba zan yarda ko maganar banza su fada mata ba” “Ni ma ban ce ka yarda a wulakantata ba, amman ka shirya fuskantar kalubale ta ko wane bangare, kai kana ganin ma Farhat din da iyayenta zasu yarda yarsu tazo gidan a matsayin kuyanga?” “Dole su aminta mana, a kowa talaka yaji yarsa zata shiga masarautar Rishim a matsayin baiwa ma zai yarda balle kuyanga, beside bana jin Mai Martaba zai nuna musu haka a fali nafi tunanin a cikin masarautar yake nufi ba da iyayenta ba” “In dai har haka ne, be tsaurara ba kamar Dada ba, ni na dauka ma ba zai amince ba shi da Dada, ganin Hameeda a gafe” “Hameeda yanzu ba ta nawa take ba, and ta bani goyon baya dari bisa dari, kusan ma ita ta cilasta Dada amincewa da kudirina, Ibrahim ta canja fa trust me” “Ba zan iya yarda da ita ba, amman zan iya yarda da kai ba zaka yi nasan ba zaka bata damar cin galaba akanka ba ko matarka” “Bari nai tunani daya mana, karka sa na raba hankalina biyu Hameeda ta canja wannan nake kokarin sakawa a zuciyata, so that na samu damar jinyar bangare daya” “Yayi kyau ina maka fatar alheri ango” Tsaki yaja ya kashe wayar. Kana ya danna horn Malam Adamu mai gadin Anty Ummi ya bude masa gate din. A dade a cikin motar bayan ya faka motarsa sannan ya fito ya nufi babbar kofar falonta. Hafsatu manga ya samu tsaye gaban Plasma remote a hannunta sai matsawa take ba dan tasan abunda take dannawar ba. “Mama” Ba shiri ta saki remote din ta juyo a firgice dan bata san da shigowarsa ba sai yanzu. Murmushi ya sakar mata ita ta mayar masa tare da fadin “Zat...” Yana kokarin zama sai ya fasa, mamaki karara a fuskarsa gurin da take tsaye ya nufa ya dafata. “Me kika ce Mama? Sake cewa naji” “Zat...” Ta fada tana saka hannu a baki. “Wow what a surprise, how how... ” “How...?” Anty Ummi ta amsa masa yayinda take fitowa daga wani bangare na falon wanda zai sadaka da tsakar gidanta dake can ciki. “Yes Anty magana tai fa, kuma tunda aka mata gyaran halshe bata magana” Anty Ummi tayi dariya. “Gashi nan dai tana magana, kuma tunda safe muke firarmu da ita” “Ya akayi kika sakata tai magana?” “Kai ba doctor bane miyasa baka saka ta tayi magana ba?” “I can't force her” “So you mean i force her?” “No i mean kinsan tana tsoronki” Dinning Anty Ummi ta nufa tana fadin “Ba wani tsoro, kawai dai baka san yadda zaka yi controlling dinta bane, ba maganar ce ta dauke ba tana tsoron magana ne saboda tana ganin kamar halshenta be gama warkewa ba, secondly tana son dadi so idan kai mata alkawarin zaka bata abu zata maka abunda kake so, na mata alkawarin indai zata cire tsoro tai magana zan rika bata ice cream da chocolate a kullum and i warning her idan batayi magana ba zan yi reporting dinta to police, amman idan tai magana zan siya mata kaya kuma zan kaita gurin Mamanta, shine kawai” Zaunawa yai kasa carpet din ya dauketa ya dora a saman cinyarsa cike da jindadi. “Cutest ni kike kin yi ma magana ko?” Sai tai dariya tasa hannayenta ta rufe idonta, shima dariyar yai zuciyarsa cike da jindadi ya shafa kanta ya sumbanci goshinta. “Zain miye haka?” Anty Ummi ta katsa masa tsawa. “Karamar yarinya ce, wannan da amin auren auri ai sai na haifeta” Ya fada yana ci gaba da shafa kanta ba tare daya kula da abunda yai ba. “Ko karamar yarinya ce bana do karka sake, a Muslim dubuwar da ta kai shekara tara ta isa balaga, kuma wannan yarinyar zata kai haka ko ma tafi so abunda kake yi ba shi da kyau” Kallon mamaki yai mata yana murmushi. “Ke da kike cewa yarinya bata balaga sai ta kai 18” Bata amsa masa ba, ta nufi hanyar kitchen cikin yanayin dake nuna bacin ranta. Bayan ta shige ya maido kallonsa gurin Hafsatu wacce ke ta kallonsa tun dazu ganin abunda ya mata wanda bata san sunansa, gira daya ya daga mata alamar why, sai ta sauka saman kafafunsa ta nufi kitchen sai waigensa take tana wani yatsina fuska. Tashi yai ya nufi dinning ya hada ma kansa breakfast, yana cikin karyawa ne Anty Ummi ta fito daga kitchen din ita kadai. “Ina Mama?” “Ina ruwanka da ita” “Like serious?” “Zain bana son shakuwar dake shiga tsakaninku da ita ne” “Why..?” Bata amsa shi ba, taja kujerar dinning din ta zauna. “Fada min ya kuka yi da Mai Martaba?” Be boye mata komai ba from a to z, bata jidadin yadda Mai Martaba da dada suka yi ba, amman bata da wani abun yi bayan amincewa kamar yadda kanen nata ya amince. “Zan je har can na fada mata ta sanar iyayenta so that su sani, kaga da an mata magana sai ta amince” Uffan be sake cewa ba, sai ya tashi tsaye yana kurba tea. “Na wuce office” “Allah ya tsare” “Amin” Ya amsa yana kallon Hafsatu manga data leko a kofar kitchen, hannu ya daga mata sai itama tai masa bye-bye da hannunta mai kumfa da alama wani abu take wankewa. Har ya juyo kamar zai cewa Anty Ummi wani abu sai kuma ya juya yayi ficewarsa. *** *** *** Tunda ya fita be dawo gidan ba sai washe gari, kasancewar jiya yayi dare so daga gurin aikin sai ya wuce gidansa. Tun daga yanayin fuskarsa Momy ta san akwai abunda yake faruwa, da kallo ta bishi har ya zauna saman kujera yana kallon Doc Hafsat dake sanya Hijab. “Momy ina kwana?” “Lafiya kalau, ya Zainab” “Tana lafiya, Momy na transfer to Kaduna” Duk kallonsa suka yi cikin rashin jindadi. “Yaushe?” “Jiya” Ya fada yana wara ido. “Ina yarinyar nan take?” “Ya dauketa tun jiya” “Saboda me kika bashi ita?” Ya tambaya a tsawace. “Ina da dalilin riketa ne na hana masa ita?” “Yes ai bashi da alaka da ita, sato yarinyar nan yai fa” Momy tayi saurin rufe bakinta. “Dan Allah Auwal ka rufa mana asiri, wani irin satowa kuma? Idan ma satota yai ina ruwanka Auwal?” “Haba Momy wane irin ina ruwana kuma? Ai aikina ne kula da lafiyar al'umma da dukiyoyinsu, dan haka dole ne na bincike shi” “Taya zaka tunkari babban mutum kamarsa kace zaka bincikesa?” “Ni ba ruwana da milkinsu ko mukaminsa ko sarautar gidansu, aikine ya biyo ta kansu idan ta kama ma har cikin masarautar zan shiga na bincika” “Dan Allah dan girman Allah Auwal ka rufa mana asiri, dan Allah ka Kyaleshi” Momy ta fada tana hade hannayenta alamar roko, Hafsat ma ta bata fuska kamar ta fasa kuka sam bata ji dadin abunda Yayanta yake magana a kai ba. Sai a lokacin ma ta tuna da abun hannunta da Doc ya aiko mata da sakon ta taho da shi ta kawo masa office. “Ina tunanin ma ya mayar da ita gurin iyayenta” “Inji uban wa? Ke ma da ke aka hada kai aka sato yar mutane you will be involved” Ya fada a tsawace, sannan ya mike tsaye ya fice daga falon cikin bacin rai. [3/4, 3:36 PM] Mrs Zainab Jega: *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 2⃣2⃣ Within a week Mai Martaba yasa aka yi komai kamar yadda ya fada, a sirarance aka daura auren bayan iyayen Farhat sun yarda da a daura a can saboda ta nace akan ita tana son Zain sai dai ba a fada musu cewar zata shiga fadar a matsayin kuyanga ba, wannan tsakanin Mai Martaba ne da iyalansa. Da farko sun nuna kin yarda sai dai jin wanda zai aureta ne ya suka bada goyon baya har ma suna murna. Ranar jumma'a aka saka za a daura auren kuma ranar aka yi walima domin sarkin anka ya aiko a fada musu za a wuce da amarya. A garin Anka aka yi walimar babu wani wakilin ango ko yan uwansa a gurin walimar duk kuwa da kasancewar ba a fadi ko waye ango ba, yan'uwansu na nesa ma babu wanda ya san da maganar aure. Daga ranar da aka tsayarda maganar sai kukan Farhat ya koma sabo, na daya mahaifiyarta bata farinciki da auren, ita kanta tasan makiyinta zata aura wanda aka cilasta masa aurenta, bata da wani zabi face na yarda da yadda kaddararta tazo mata, sai dai ta kudirta a ranta cewar ba zatayi zaman aure mai tsawo da Zain ba, ita burinta ta tsallake wannan siradin. Ranar aka yi walimar a ranar mahaifiyarta bata yi wunin biki ba abunda aka san ko wace uwa na yi idan za a aurarda yarta, a ranar Farhat ta sha kuka marar misaltuwa duk wanda yaga irin kukan da take ya san bata son auren ko kuma akwai wani abu daya faru. Misali karfe hudu na yamma aka aiko da manyan motoci masu kyau daga masarautar Rishim domin daukar Amarya, a lokacin ne aka shiga da amarya dakin gwaggonta danyi mata huduba, bayan an fito da ita daga can aka kaita gidan kawonta, sannan aka sake dawowa da ita dakin mahaifiyarta. Inna na ganinta ta kawar da kai kamar wacce bata son kallonta, hakan be hana Farhat karasa inda take zaune ba ta kama kafafunta. “Allah kadai yasan dalilin daya sa na amince da auren fiye da auren Ya Bashir, na san Ya Bashir dan uwana ne kuma mijin yaya, amman ba zan iya aurenta, ki yafe Inna dan Allah karki fushi da ni, ban sani ba wata kila ajalina na aura, akwai yiyuwar auren ya zame min silar samun aljanna ko wuta, ni kadai na san abunda nake ji Inna, dan Allah karki yi fushi da ni” Kallonta Inna tai tana tabe baki. “Da kina tsoron fushina da baki auri wani ba sai Auwal, miye yar'uwarki bata miki ba? Ku nawa na haifa? Ku biyar na haifa amman ke ta dauka ta rike ta sakaki boko kika waye bayan kuma ga yan'uwanta can wadanda suke uwa daya uba daya babu abunda basu ce ba lokacin da ta daukeki amman ta toshe kunnuwanta ta zauna da ke, sai ke yanzu dan ance ki auri mijinta ki rike mata yayanta sai kice ba zaki iya ba, ai gashi can yanzu sun dauki kanwarta wacce suke daki daya sun bashi sai ki zuba ruwa kasa ki sha, ba baki nake miki ba amman wannan auren ba zaki taba samun farinciki a cikinsa ba, ba auren kudi kikayi ba dan kinga dan sarki? Gaki ga shi ai basa ganin talaka da daraja” “Ba kisan yadda nake ji ba Inna, Wallahi idan na auri Ya Bashir mutuwa zan yi” “Ai da shi kika aura ana kaiki sai ki fadi ki mutu zai fi min kwanciyar hankali fiye da wannan da kika aura, tashi ki bani guri kuma karki kuskura ki shaida min duk abunda zai biyo baya....” Tashi tai tsaye sai kuma ta fadi zaune ta rike kafafun mahaifiyarta ta fashe da kuka, kuka tai sosai sannan ta tashi ta fita a lokacin ne idon Inna ya cika da kwalla. Kamar kwacce aka cirewa rai haka ta fito daga dakin Inna tana kuka, daya faga cikin dattijiwar da zasu rakata ta rika hannunta ta sakata cikin mota, sauran suka shiga a dayar motar dogaran suka kama hanyar Gusau da su. Har suka isa cikin birnin Gusau Farhat bata daina kuka ba, idonta duk ya kumbura fatar fuskarta tayi ja sosai saboda murjar da take. Tayi tunani gidan sarki za a wuce da ita sai aka nufi wata unguwar da ita wacce ba zata iya tantancewa ba, sakancewarta sabuwar unguwa dake can bypass hanyar kaduna. Babu kowa a cikin gidan sai dogarai da kuma bayi, domin su suka tarbesu dayar ta rika hannunta dayar ma ta kama hannunta suka nufi wani bangare na gidan da ita. Kato gidane plate mai girma da aka kawata ko ina da fulawoyi. Babban falo suka shiga da ita har lokacin hawaye be daina sauka a idon Farhat ba. Suna shigowa Abida ta zube kasa tana kausar gaisuwa. “Allah ya taimaki Gimbiya, Allah yaja kwanaki muna barka da zuwa a wannan masarauta mai dinbin albarka da alfarma, takawarki lafiya surukar mai martaba surukar da tafi ko wace suruka daraja da sa'a a duniya...” Bayan ta gama ta dauki wani carpet ta shimfida a saman carpet din dake falon. “Shimfidar nan taki ce Gimbiyata Allah ya taimakeki ya kara miki imani da nisan kwana” Karasa Farhat tai ta zauna sannan ta kai hannu ta share hawayenta. Hannu biyu Abida ta taba sai ga wasu bayin uku sun fito dauke da abinci suka dire gaban Farhat sannan suka kwashi gaisuwa. Da ido Abida tai musu magana dai duk suka tashi suka fice, sannan ta kalli gefen da Farhat take dan ba zata iya kallonta kai tsaye ba. “Idan Gimbiya ta min izini zan fita waje domin yin wani aikin” Kallonta Farhat tai tana tunani abunda zata ce mata, in her life wani be taba neman izininta dan yin wani abun daya shafi rayuwarsa. “Ranki ya dade ko akwai wani abun da kike so ne?” “Aa tashi ki tafiyarki” “Na gode Gimbiya, Allah ya taimakeki” Abida ta tashi ta fice daga falon cikin sauri, wani bangare na gidan ta nufa inda babu kowa sai shukeshuke, tsohuwar nokia ta dake cikin zane ta fito da ita ta saka number Hameeda ta kirata bugu daya ta dauka kamar mai jira. “Ta ci abinci?” “Aa yanzu suka iso, amman gashi can an kawo mata” “Ki tabbatar fa ita kadai zata ci shi ba tare da kowa ba, duk kika yi kuskure wani ya ci bayan ita kin shiga uku, kuma idan ta gama cin abinci ki dauke shi ki zubar inda babu wanda zai iya gani” “To ranki ya dade amman ina jin tsoro” “Kiyi ta sanyi jiki har tsoronki ya ja miki asirinki ya tonu, kiga yadda zan yi dake a cikin masarautar nan” Ta kashe wayar tare da yin kwafa. Abida ta dade rike da wayar kamin ta maidata a cikin zanenta ta nufi dayan bangaren inda aka sauke yan'uwanta, ko da ta shiga suna cin abinci da aka kai musu cikin girmamawa ta gaishesu, suma suka amsa mata da far'ah “Idan kun gama, direba zai maidaku ga kayayyaki can Mai Martaba ya ce a baku” Sai kuma ta tashi ta shiga wani dakin ta dauko wata farar takarda mai kamar ta sako ta mikawa gwaggonta. “Ga wannan daga Hajiya Hadiza uwargidan Mai Martaba sunce a gaisheku, akwai atamfa da shadda a dayan motar su kuma daga Hajiya Zarah da Hajiya Maryam ne sukansu matan Mai Martaba ne” Godiya sosai suka rika yi mata har suka rasa wani abun kara cewa, bayan sun gama ne Abida ta kaisu inda Farhat take suka mata sallama tare da yi mata addu'a sannan suka tafi, suna fita ta fashe da kuka kamar ance mata sun tafi sun bar ne kenan har a bada. Har gurin mota Abida ta raka su, sai ta ta shiga motar aka wuce da su sannan ta dawo gurin Farhat ta tarararda ita har yanzu tana aikin kuka. “Haba Gimbiya kuka be kama ci wannan fuskar taki ba, farinciki ya kamata ki yi domin Allah ya kawo ki inda hawayen bakinciki ba zasu sake ziyartar idanuwanki” “Rabuwa da yan'uwa babu dadi” Farhat ta fada tana share hawayenta. “Na sani Gimbiya amman wannan ai ba rabuwa ba ce ta har a bada, zaki sake ganinsu a duk lokacin da kika zo, yanzu dai ki share hawayenki ki ci abinci, Allah ya taimakeki” “Ki daina ce min Gimbiya ni sunana Farhat” “Ba zan iya kiranki haka ba ko da kuwa za a dora kaina saman dutse a dauki wani dutsen a fasashi, ni dai burina Gimbiyata ta ci wannan abinci” “Ba zan iya ci ba, bana jin yunwa” “Dan Allah dan Annabi ki ci abincin nan, ida aka bincika baki ci abinci nan ba ni za'ayiwa fada wata kila ma a koreni” “Saboda ban ci abinci za a koreki” “Kwarai kuwa kina da girma da martaba a gurin Mai Martaba, domin kin auri dan da yafi so cikin yayansa, kuma da namiji tilo a gurinsa, ai kekan yar gata ce gaba da baya” Jin abunda Abida ta fada na cewar za a koreta idan bata ci abincin ba, yasa ta dauki plate ta zuba sinasir din da miya ta soma ci, haka Abida ta tisata a gaba tana kallon har ta gama cin abinci sannan ta kwashe kayan. Farhat na zaune gidan har karfe takwas na dare, bayan ta gama sallah isha'i suna zaune tare da Abida sai knocked suka ji, cikin sauri Farhat taja gyalenta ta rufe kanta, abida kuma ta tashi ta fita daga bedroom din zuwa falon dan bude kofar. Ikram ce tare da kanwarta Sanaya, faduwa Abida tai ta kwashi gaisuwa, ko kula ta basu yi ba suka wuce cikin falon tare da barorin dake take musu baya, Ikram ce tai riga shiga dakin fuskarta dauke da murmushi, bakin gadon ta zauna tare kusa da Farhat. “Amaryar mu, ko kuma na ce yayarmu ina fatar kina lafiya” “Lafiya kalau” Hannu ta mika sai daya daga cikin barorin ta miko mata wani kwali da aka nade da farar leda ta aje mata. “Ga kyauta gada mahaifiyar mijinki, kuma sarakuwarki, tashi ki gyara zamu wuce masarauta yanzu” Ikram na gama fadar hakan ta tashi ta fito daga dakin tare da Sanaya da barori uku da suka rakosu, bayan sun fita ne Farhat ta bude kwali farin lace ne a cikin mai mugun kyau da tsada sai farar alkibba da fararen takalma da kuma turare mai shegen kamshi. Tashi tai ta shiga bathroom tai wanka tana fito ta shafa mai ta dauki tufafin ta saka tare da alkibbar sannan ta feshe jikinta da turare, sai ta nufi kofar ta tare da fadin. “Na gama” Dukan kallonta suka yi. “Masha-Allah ni daman nasan Yarima ba zai mana zaben tumun dare ba, duk abunda yasa Yaya ya kawarda fuskarsa ya auro wata bare to abun nan mai girma ne, sai dai kin manta da wani abu Yayan sarakuna basa kawo kansu idan ana nemansu sai dai aje inda suke a tararda su, fatar nan gaba ba zaki sake kuskuren kawo kanki da kanki ba” Ikram ta karasa fada tana rika hannunta. Ita kuma ta gyada kai sannan suka fice tare da ita. Ko da suka isa masarautar Rishim tayi tsif kamar babu kowa a cikinta, a kusa da kofar fada dogare ya faka motarsa suka fito tare da Farhat. Sai ga wasu barorin sun zo da gudu sun rika albbibarta dake jan kasa. Faduwa gaban Farhat yayi irin faduwar nan na bakunta da kuma tsoro a lokaci daya, a yau dai ta shigo masarautar Rishim a matsayin suruka, masarautar da bata taba ganinta da ido ba sai dai a waya shi ma kuma wani bangare na masarautar ake dauka. A duk yadda za a misaltawa mutum girma, fadin da kuma kyaun masarautar ya wuce misali, daga lokacin da mutum ya saka kafarsa a cikin masarautar sai duniya ta canja masa ta kaishe wata kasar ta larabawa saboda tsaruwarta, sai ka rantse da Allah ba a Nigeria kake ba, kofar fadar ma abar kallo ce balle kuma cikinta. Suna isa bakin kofar aka bude musu kofar, Farhat na saka kafatarta sai taji kamar tana cikin ruwa saboda sanyi da laushi da carpet din yake da shi, bata daga kanta ba har suka isa gaban wata katuwar kujera dake saman stairs. A tare da Ikram suka zauna Ikram ta gabatarwa Mai Martaba ita sannan ta juyo ta kalli bangaren iyayenta tana gabatar musu da ita, Hajiya Hadiza ce kawai ta amsa da far'a sauran duk shiru suka yi suka bata fuska. “Lale marhabun da sarakuwarmu, muna miki barka da zuwa masarautar Rishim, Allah ya sanyawa rayuwar aurenku albarka” “Godiya take ranki ya dade” Abida ta amsa a madadin Farhat datai shiru ta kasa cewa komai. Hannu Mai Martaba ya daga musu sai Hajiya Hadiza ta ce “Tashi ki shiga da ita sashenta” Ikram ta rika hannunta suka fito daga fadar ba tare da Farhat taji wata magana daga bakin Mai Martaba ko matansa biyun nan wato Hajiya Zara da Hajiya Maryam, tun daga nan zuciyarta ta soma sosuwa ta kuma dasa mata wani. Bata iya gane inda ake bi da ita iyar abunda ta sani dai suna tafiya, kuma tafiya mai dan tazara sannan suka iso wani bangare na masarautar mai part part ba dadi, daya daga cikin part din daya fi ko wane kyau suka nufa da ita. Tun daga gate din part din zaka tabbatar da sabon fenti ne aka yi na zamani mai kyau da daukar ido, ga katafariyar kofar an kawatata da shuke shuke, dare ne amman hasken lantarkin dake gurin ya maida gurin kamar rana, sai da suka zagowa suka hau madaidaicin stairs da ba zai wuce biyar ba zuwa shida sannan suka shiga cikin falon da kamshin turare ke tashi, kai tsaye upstairs suka nufa da ita daya daga cikin dakunan suka bude ta shiga sannan suma suka shigo. A tsakiyar gado Ikram ta zauna da ita, sannan suka fita daga dakin suka barta ita kadai. Ko minti latatin ba ayi ba sai ga Zain ya shigo ransa duk a bace, sai da ya rufe kofar falon sannan ya dawo saman cushion ya zauna yana karewa falon kallon fenti dai jiya aka yi shi, amman duk wani decorations da aka ma falon yau aka yi shi, ba aikin kowa ba ne face Hajiya Hadiza domin ita kadai ce a cikin iyalan Mai Martaba take son abunda yake so. Zain be tashi daga falon ba sai goma da rabi na dare, he was busy thinking of his life partner Haleema, irin daukin da yake na shiga dakinta da kuma yadda suka nunawa juna kauna, but this time around baya farinciki da wannan auren kwatakwata, and the most annoying thing an kai Farhat dakin da aka kai Haleema and that was his room. Ko da ya shiga tana kwance saman gado ta lullube fuskarta da gyalenta, sai dai hakan be hanashi ganin yadda fuskanta ta jike da ruwan hawaye ba, sai dai hakan be dame shi ba dan a tunaninsa shi yafi kowa cancantar yai kuka a yau. He is so different today kamar ba ango ba, babu annashuwa a fuskarsa, after that ko wane ango manyan kaya yake sakawa amman shi kananan kaya ne a jinsa, and what is more painful be halarci daurin aurensa ba, shi dai an kirashi an fada masa an daura aurensa, at that time yana gidan abokinsa Ibrahim cos this time around har Anty Ummi haushi take bashi, dan ta dame shi da maganar gashi kuma bata barinsa sakewa da Hafsatu manga. Yana shiga takalminsa ya fara cirewa, sannan ya shiga bathroom yai wanka tare da alwala ya fito ya dauki jallabiya ya saka. “Tashi ki yi alwala” Ya fada kamar an masa dole. “Bana sallah” Wani banzan tsaki yaja dan ta bashi haushi, abunda yake tunani Farhat tai zaton wani abu zai yi da ita shiyasa tace masa bata sallah. “Mtssssss” Farhat replied back. Kamar daga sama yaji tsaki. “Ke how dare you zan miki tsaki ki maida min?” A tsawace ya tambaya, ita kam ko motsi bata sake yi ba balle har ta amsa masa, seriously this time around taji tsoronshi sosai. Kwafa yai ya dauki carpet ya shimfida ya soma sallarsa. Bayan ya gama yai addu'a ya kashe wutar dakin ya hau gadon ya kwanta, sai ta matsa can nesa karshen gado tana cigaba da kukanta a hankali. Shi dai be kulata ba dan baya jin yana da lokacin hakan. Bachinsa yake peacefully till her crying wake him up, agogon dakin ya kalla it's 2.30am, wutar dakin a kunne ta koma can kusa da kofa tana rike da ciki sai kuka take. “What happen?” “Ina ruwanka...” Ta fada kamar ba ita ke kuka ba, sauka yai saman gadon ya sake kashe wutar dakin ya nufo gadonsa cos baya iya bachi da wuta a kunne, ko karasa be yi gurin gadon ba ta sake kunna wutar. “Ni tsoro nake ji karka kashe min wuta” Ba shiri ta bashi amsa sakamakon tarar daya watsa mata. Zuwa yai ya dauketa cak yaje gurin gadon ya jefar da ita saman gadon sannan ya sake komawa zai kashe wutar sai ta fara aman jini. Tsayawa yai kallonta she did what Haleema did on her first night too, yes he remember how he hug her tight tana ta aman jini har safe, and that the cause of her death after she giving birth, and all what he know Haleema told him Hameeda was the only person data dafa mata nama da daren da za kawota gidan. “Meke damunki?” Ya tambaya yana karasawa inda take. “Cikina ke ciwo” Ta fada a wahalce, hawa yai saman gadon ya rikota tana kokarin saukowa da ita sai ta buge masa hannu. “Stop touching me” “One word from your mouth i would beat the living day light out of you, mark my words” Da sauri ta janye hannnunta tana kakarin amai. Bathroom ya shiga da ita already ya cire mata alkibbar dake jikinta. MY REGARDS TO EVERYONE 🙌😍💋 BAN DA GHOST☠️💀 READERS 👿👿 Especially Wattpad ghosts 😡👹as soon as possible zaku fara reading empty pages 😂 am wicked too😎🤓👻. [3/4, 3:36 PM] Mrs Zainab Jega: *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 2⃣3⃣ Daga ita har shi a bathroom din suka kwana, shi yana zaune ita kuma ta jingina masa kamar matacciya. Sautin kiran sallah dake cikin fadar ne ya farka da su, shi ya fara bude idonsa dake cike da nauyin bachi, sannan itama ta soma motsawa tana jin jikinta babu karfi ko kadan. “Daga ni” Ta fada tana wani bata fuska ita ala dole ya taba ta, tana dukan shoulder dinsa, kallonta kawai yai be ce mata komai ba har sai da ta lura da ita ce tana kwance a kirjinsa sannan tai hanzarin tashi sai kuma ta kasa saboda babu karfi a jikinta. Da kansa ya daga sannan shi ma ya tashi tsaye, da kansa rika kokarin rabata da tufafin dake jikinta, amman ta hana sai kokarin kokuwa take da shi. “Ka bari bana bana so” “Fine idan na dawo baki yi wanka ba, barori zansa su miki” Be jira komai ba ya juya ta fita. Ta dade a zaune kamin ta samu karfin cire tufafin jikinta ta kunna shower.   Bayan ta gama tai alwala sai ta dauki tawul din dake gurin ta daura, ta saba fitowa a haka gida bata jin komai dan an ganta da kananan kaya ko kuma tawul kawai, but this time around tana jin nauyi sosai ta fita haka Zain ya ganta. Rasa tai yadda zata yi, ba zata iya maida kayan ba domin tana jin kyamarsu. “Ka kawo min kayana” Ta fada muryarta a dakishe, shiru be amsa mata ba, daman ta san ai ba zai amsa ba ko da wata dince ba ita ba balle ma ita ce, bude kofar tai a hankali ta leka dakin sai ta hango babu kowa, hakan yasa ta fito da sauri ta nufi wardrobe ta bude, gaba daya kayansa ne a ciki bubu nata ko daya, taya ma zata samu nata a ciki bayan ba a zo mata da komai daga gidansu ba. Jallabiyarsa ta dauka ta saka, duk kuwa da irin abunda zuciyarta ke raya mata matukar yaga ta saka kayansa sai ya kusa kasheta. A baki gado ta zauna tana kallon kofa kamar mai jiran shigowarsa. Thirty minutes later ya shigo dakin, tana ganinsa tai saurin tashi tsaye tana mursa yatsun hannunta. “Ban ga kayana ba, kuma ban yi sallah ba” Ta fada tun be tambayeta ba, and ta manta tace masa bata sallah, tsayawa yai kallonta from head to toe she's mad, haka zuciyarsa take raya masa, ita kuma ta kasa daga kai ta kalleshi sai hawaye ya sauko mata, all what her heart keep telling her zai fada mata wata maganar marar dadi ko ya mareta. “Ga dakinki can nan dakina ne” Dagowa tai ta kalleshi sai kuma tai saurin maida kanta kasa, kamar dai bata ji abunda yace ba ta cigaba da tsayuwa a gurin, har sai da ya karasa inda take ya dauki wayarsa ya fice.   Sannan ta fito daga dakin tana takawa a hankali kamar marar gaskiya, hagu ta fara dubawa sai ta hango dakuna biyu jere, mai bima nasa a bude yake yayinda dayan kuma yake a rufe, tana leka dakin sai ta dawo tayi tsammani ko yana ciki, sai ta nufin dayan dakin na uku tana tabawa taji kofar rufe da makulli, komawa tai dayan dakin data baro ta shiga. And the room is wow everything is perfect, duk da hankalinta baya jikinta a yanzu tasan an narka dukiya a dakin, kai tsaye wardrobe ta nufa tana bude taga an jera kaya daga sama har kasa. Bata tsaya choosing ba dan bata da damar wannan a yanzu, hannu kawai tasa ta janyo atamfar dake sama tana warwarewa tana gown. Sakawa tai sannan ta sake bude dayan bangaren babu komai sai veils. Mai dan kwauri ta dauka ta rufe kanta da shi, tsayawa tai tunanin gabas sai ta tuna inda taga yana kallon daya sallah nafila jiya. Tana kallon gurin ta hango Hijab da Carpet an aje mata saman kujerar dake gurin. Karasa tai ta dauka ta saka ta shimfida carpet din tai sallah sannan ta haye gado ta kwanta. “Farhat” Can cikin bachi taji kiran amman hakan be hanata amsawa ba, dan tasan mai kiran zai iya mata komai idan taki amsawa. Saukowa tai daga kan gadon ta fito, sai ta hango plasma kunne tana aikinta shi kuma yana zaune saman cushion ya saka tv a gaba kamar ba shi yai kiran ba hannunsa rike da kofin ruwa. Hakan yasa ta sauko downstairs ta zo har inda yake zaune ta risina a kasa. Da ido ya nuna mata tea dake gurin, sai ta dauka ta sauri ta shanye gaba daya, kamar yace dole sai ta shanye, sannan sake kallonsa. “Na shanye” Sai ya kalli maganin dake saman karamin plate kusan kala hudu, alamar ta dauka ta sha kenan. “Ni bana shan maga...” Bata karasa ta dauki ganin ta zuba a baki ta rika taunawa sakamakon kallonta da yai, ba tare da ta jira ya bata ruwa ba haka ta rika taunawa tana hadewa. Yanzu kam he believe Farhat is completely mad, ba zai iya mika mata kofin ruwan dake hannunsa ba, dan haka ya aje kofin saman center table dake kusa da shi, sai ta dauka ta sha idonta na cika da kwalla. “Me kika ci?” “Na sha tea sai na ci magani da ruwa” “You fool me kika ci nace?” “Ban ci komai ba, kayan suna nan dakinka” Ta dauka kazar amarci yake magana wacce ta tarar a dakin jiya. “In na sake tambayarki kika min shirme sai na buga kanki da wannan table din” Ya fada a tsawace yana nuna center table na gilas dake gefensa. “To ina ruwanka da abunda na ci, ka kyale ni mana” Itama ta fada a fusace hawaye na sauka a idonta, tashi tai tsaye da zimmar komawa dakinta sai ta riko hannunta da karfi ya fisgota ta fado saman cushion din sai ya matse mata baki, babu irin karfin da bata sa ba amman ta kasa banbanre hannunsa daga kumatunta sai kuka take. “Me kika ci jiya?” “Sinasir da miya” Ta fada a wahalce, sannan ya saketa ta zauna dai dai yana aika mata wata tambayar. “Shi kadai kika ci?” “Ee gidanmu ban ci komai ba, sai da na zo nan wata mai aikinku ta kawo min sinasir” “Zaki iya ganeta idan kin ganta?” “Ban sani ba, bakin mugu kawai, wai ina ruwanka da ni miyasa kake takura min ne? Ni ma mata ce ba baiwa ba but you treat me badly” “No i didn't but surely i will... And what did you just call me mugu ko? Zaki san mugu soon” Tashi tai ta nufi dakinta tana kuka. Wayarsa ya dauka ya aikawa Abida sako, in few minutes tai knocked kofar falon. Bayan wani dan lokaci ta turo kofar ta shigo tasan in zata daummawa a gurin ba zai ce mata ta shigoba, gabansa ta zube tana kwasar gaisuwa. “Kina tare da Farhat jiya ko?” Damm taji gabanta ya fadi, tasan wa yake nufi. “Ee mu muka tarbeta ranka ya dade” “Waya kawo abincin data ci?” “Falmo ce da Baba Laraba” “Je ki kirasu” Ta tashi ta sauri ta fice, gabata sai faduwa yake. Bata dade ba ta dawo tare da Falmo da kuma Baba Laraba duk suka zube kasa sua kwashi gaisuwa. “Waya kai abincin da Farhat ta ci jiya” “Mu muka kai Ranka ya dade” Hada baki suka yi gurin amsa masa “Gurin wa kuka karbo abincin?” “Gurin Gimbiya Hameeda...” Yayi shiru na dan wani lokaci. “Ita ta girka?” “Aa Allah ya taimakeka Hajiya Hadiza ce ta girka” “Taya aka yi kika sani?” “Ni zan girka sai tace a bari tai ma surukarta girki da kanta” “Shinkenan...” Sai suka tashi suka fice da sauri idon Abida har ya cika da kwalla. He hold his phone again ya turawa Hameeda sako cewar yana nemanta. Ba bata lokaci sai gata ta shigo falon, for the first time after mutuwar yar'uwarta Zain ya kirata da kansa part dinsa. “Me kika saka a abinci da Hajiya ta girka na Farhat...?” Ya fada be ko kalli inda take tahowarba, tsaya tai cak ta kasa karasawa a gurin tana kallonsa kamar an dasata a gurin, tambayar ta zo mata unexpected haka taji abun kamar sauka aradu kanta yai mugun tsawara, anya shine Zain din da yake fada mata zai zame mata fiye da da kuwa? “Answer me...!” Ya katsa mata tsawa har sai da ta razana. “Ban gane ba ban fahimci me kake magana akai ba?” Ta tambaya muryarta na rawa hawayena na sauko mata. Sai a lokacin ya juyo ya kalleta tare da tashi tsaye ya nufi inda ta tsaya din. “You hear me, abunda kika sawa Haleema shi kika sakawa Farhat ko?” “What do you mean?” “I mean you kill my wife and now Farhat right? Ke kadai kika girka ma Haleema nama ta ci a daren da za a kawo ta gidan nan she told me kuma ana kawota ta rika aman jini babu asibitin da ban kaita ba amman aka rasa gano ciwonta time to time take ciwon ciki tana wannan aman shi yai silar rasa jaririn cikinta at the end ita ma ta mutu, and yanzu kin karbo abinci daga hannu Hajiya kin saka wannan abun a abinci Farhat ta ci ta fara aman jini, so lemme tell you something idan Matata ta mutu Wallahi kema sai kin mutu....” Baya baya tai ta rufe bakinta tana hawaye, sai kuma ta juya da gudu ta fice daga falon, da kuka ta fito daga part dinsa ta nufi part din Dada Yalwa, tana shiga ta fadi kasa tana kuka kamar za a cire mata rai, cikin tashin hankali Dada ta fito daga dakinta ta nufo inda Hameeda take tana tambayar ba'asi. “Ke miya faru? Waya mutu?” “Nayi nadamar haihuwata da akayi Dada, na yi nadamar zaman da nai a cikin gidan nan, bani da sauran gata da ina da shi da Yarima be wulakanta ni ba” “Me ya miki?” Ta riko hannayen Dada tana wani irin kuka mai ban tausayi da taba zuciya. “Ya ce nina kashe Haleema yar uwata ta jini Dada Yarima ya ce ni na kasheta, yanzu kuma ina son na kashe masa Farhat” “Me? Muhammad yana cikin hayyacinsa kuwa? Wane irin hauka ne wannan” A nan Hameeda ta labarta mata komai daya faru, Dada ta kama hannun Hameeda suka nufi part din Zain da ita, tana shiga ta haushi da masifa. “Ai daman na san ba banza aka barka ba, idan ba asiriba taya zaka lakewa yarinya kamar wannan, abun be yi mata hakan ba sai ta kara maka da na kan gado wato ka bi ka haukace daga tashi da safe sai fara hatsaniya da Hameeda ko? An shigo cikin gida a rabaka da danginka ko” Hayaniyar Dada ce ta fito da Farhat daga dakinta sai ta tsaya downstairs tana kallonsu. “Ke kuma munafuka ke kika kitsa masa cewar Hameeda ta saka miki wani abu a abinci ko, wato ki hadashi da yar'uwarsa, ai daman na san Ummi ba zata bar masarautar nan ta zauna lafiya ba, ta dauko bakin halin ubanta” “Ya isa haka Dada ki daina fadar maganganun marasa kyau akan yar'uwata, abunda kuma na fada haka yake ita ce ta saka wani abu a abinci, so take ta kashe Farhat kamar yadda ta kashe Haleema and this around ba zaki tsalleke ba bana.... ” Tasss Dada ta sauke masa mari a fuska abunda bata taba ba, ta fashe da kuka. “Ba kai ba ne Zain, baka tsaba daga muryarka haka kai magana ba, tunda Haleema ta mutu baka dorawa kowa laifi amman yanzu zuwan wannan yarinyar Hameeda? Na san baka samun jutuwa da Hameeda amman taya Hameeda zata kashe yar'uwarta, idan har zargi zaka yi sai ka zargi Hajiya Hadiza tunda ita ta dafa abincin ko kuma ka zargi wasu dabam amman ba Hameeda ba...” “Ba laifin kowa bane...” Farhat ta fada daga upstairs din da take tsaye tana kallonsu, sai duk suka daga kai suna kallon yadda take saukowa tana magaba. “Amman jinin da nake ba laifin kowa bane, ina da Ulcer mai tsanani wacce take sakani aman jini idan na wuni ban ci abinci ba, jiya kuma haka na wuni ban ci komai ba sai da aka kawo min sinasir da miya miyar kuma tana da yaji, wannan ne ya haddasa min aman jinin dana kawana ina yi jiya da dare, amman babu abunda aka sakawa abinci, Be tambayani kuma hankalinsa ya tashi shiyasa yai zargin ko wani abu aka sawa abinci, da ace ya tambayi dalilin aman jinin nawa da duk haka be faru ba, dan Allah kuyi hakuri” Ta karasa maganar tana hade hannayenta yayinda ta tsaya daidai inda Zain yake tsaye yana kallonta. “Anki ayi hakuri munafuka, kai yanzu baka ji kunya ba? Gashi nan ta fada maka dalilin aman amman ka dauka ka ce Hameeda ce, to ka jira abunda zai biyo baya” Tana kaiwa nan ta sake jan hannun Hameeda dake kuka har lokacin suka fice. Zain couldn't talk, saboda Farhat tayi embarrassing dinsa gaban Dada bayan kuma yasan haka shine gaskiya, he is straight forward hakan yasa baya iya boye abubuwa, and what he told Hameeda he mean it from the bottom of his heart. But why Farhat tai haka? Saboda kawai ta kunyata shi? Oh yes tayi ne dan ta bashi kunya, haka zuciyarsa ke raya masa. Yana kallonta sai ta juya da sauri ta haye stairs. Zaunawa yai dai kuma ya tashi ji yai duk gidan ya fita ransa, hakan yasa ya koma dakinsa ya dauki keys dinsa ya fice daga gidan. Gidan Anty Ummi ya nufa cikin mugun bacin rai, be san gurin da zaije ba a yanzu kayan gidan Anty Ummi. In few minutes ya isa saboda gudun da yake. Yana taba kofar yaji ta rufe alamar basu tashi ba kenan kasancewar yau weekend, knocked yai bayan kamar minti biyu Anty Ummi ta bude kofar tana sanye da kayan bachin. “Zain... Lafiya dai” Be amsa ta ba har sai da ya zauna. “Lafiya kalau” “Aa ba lafiya ba, lafiya za a kai maka amarya jiya jiya ka fita da sassafen nan bayan kuma yau weekend?” “Anty me zan mata?” “Kamar ya me zaka mata what kind of rubbish is this” “Mama na zo gani, ko zuciyata ta yi sanyi” “Gata can” Ta fada tana nuna masa inda take cike da jin haushi. Hangota yai can rabe jikin kujera ta takure kanta tana ta bachi. “Haba Anty? Ji inda kika aje fa” “Ta aje kanta dai, daga dakin su Amal ta dawo nan saboda sunyi fada na mata magana, shine tai fushi” “Amman Anty idan Amal ce sai kinzo kin lallabata ta kwanta ko kuma ki dauko wani abun ki rufeta, miyasa ita kika kyaleta ta” “Amal ka ce Zain Amal is my biological daughter” “That's it that's it, Amal da wannan yarinyar duk daya suke a guna, idan yarki ce ake yi mta haka wani gurin ya zakaji? Farinciki? Sannan Amal ma bata wuce ta shiga halin da wannan yarinyar ta shiga ba, amman wannan abun da kike be dace ba, kuma ban jidadi ba” Ya karasa a fusace sannan ya tashi ya doshi inda take kwance kasan tile, ya kai hannu ya taba sai ta farka a firgice. Hawaye ya bushe mata a fuska zaunawa yai a gurin ya maida saman jikinsa. “Mama” “Uhmm ni bana son wacan matar ita da yarta, bana son su bana son zama nan” Ta fada tana nuna Anty Ummi dake kallonsu. “Miyasa” “Tana min fada idan na dukar mata ya, kuma ita Ammal din ita take tsokana na, ni na gaji da nan ka kaini garin mu gurin Inna Ladi da Mamana” Ta karasa tana fashewa da kuka. Wani irin tausayinta ne ya rufe shi, rumgumeta yai yana rarrashinta. “Shiiiiiiiii zan kaiki gida amman ba yanzu ba, kina son muje yawu dake anjima ko?” Ta gyada kai “Zanje da ke yawo na siya miki ice cream da madara da chocolate kinji” Ta gyada kai daga saman kafadarsa data kwantar da kanta. Anty Ummi ta tashi tsaye taba fadin “Kana bani mamaki Zain, ka baro matarka ka zo nan kana lallaba wata” “Karamar yarinyace wannan” “Haka ne, na gani ai” Daga haka ta shige dakinta. Shi kuma tashi tsaye ya kama hannun suka nufi kitchen, da kansa ya dafa mata indomie, sai surutu take masa labarin garinsu da kuma na Anty Ummi kamar be santa ba, wani gurin yai murmushi wani kuma har da yar dariya. Bayan sun gama suka dawo falo. Plate biyu ne nata daban nasa daban amman sai ta canja ta dauki nasa ganin nasa yafi nata yawa. “Sai kin cinye shi” He said with funny face. “Kai ma sai ka cinye shi” “Ai ni zan iya ai” Tayi dariya. “Uncle” Ta kirashi da sunan dasu Amal suke kiransa da shi kuma sunan da Anty Ummi ta fada mata ta kiranshi da shi. “Uhmm Mamana” “Miyasa kai baka kwana a nan gidan?” “Gidanmu nake kwana, nan ai gidan Antyna ne” “Ina ne gidanku?” “Wani guri ne can ciki gari” “Zaka tafi da ni yau ko?” Yayi shiru be ce mata komai ba, sai ta cire fork din dake cikin indomie dan har yau har gobe taki ta saba da cin da fork duk da irin kokarin da Anty Ummi take na koya mata. “Wannan na Mamana ne” Ta kai loma daya a bakinta. “Wannan na Babana ne, wannan na Inna Ladi ne, wannan na laure ne, wannan na Anty Ummi ne, wannan na Amal ne....” Haka tai ta jera lomomi har ta kai gareshi. “Wannan naka ne, na ci maka kai ma” Ta fada tana dariya, shi ma dariyar yai yana kallonta cike da burgewa. “Mama ina Babanki yake?” “Nima ban sani ba, ban taba ganinsa ba mamana kuma mahaukaciya ce” Indomie sa ya diba ya kai mata a baki ta karba ta cinye. Ido ya kura mata har ga Allah tana bashi tausayi. “Zain tashi ka koma gurin matarka” Kamar daga sama ya jiyo muryar Anty Ummi. Tana fadar hakan ya wuce kitchen. Tashi yai tsaye yana fadin. “Kije ki wanke hannunki anjima zan kaiki yawo” “Tau” Ta nufi kitchen din da sauri shi kuma ya juya ya fice. Tana aje plate din Anty Ummi ta kalleta ta ce “Je ki yi wanka fita zamu yi” “Ina zamu je? Uncle ma yace zai fita da ni” “Wani gurin zan kaiki inda za a kaiki garinku” Duk da son da Hafsatu manga na zuwa gida sai ta ji babu dadi, kamar zata fasa kuka ta fito daga kitchen din. A harabar gidan ya hadu da mijin Anty Ummi suka gaisa har yana zolayarsa wai ango. A maimakon ya wuce gidan kamar Anty Ummi ta bukata sai ya wuce gurin abokinsa Ibrahim. A wajen gidan ya tsaya ya kira shi a waya, ya sanar masa yana bikin gate “Ka shigo mana” “Dan Allah ka fito kawai” Ya kashe wayar. Ba a dauki lokaci ba sai ga Ibrahim ya fito fuskarta shimfide da murmushi. “Ango Ango Ango ka sha mai” “Ka fara ko? Kasan bana son haka ai” “Ko baka so ai dole muyi mana, miya fitar da kai da safen nan haka kana angon jiya jiya” Tsaki Zain yaja kamin ya bijiro masa da maganar abunda ya faru a yau. Ibrahim was shocked a yadda yake tunani Hameeda zata iya aikata haka, but baya son ya furta wani abu akan abunda ya shafi family Zain. “Amman kana da tabbacin Hameeda ce ta aikata haka?” “Ban sani ba, amman alamu ya nuna haka kuma a yadda Hameeda take zata iya” “It could be possible tunda ita ta girkawa Haleema abinci kuma abincin da Farhat ta ci ya kai hannunta, amman be kamata kai magana da ita hakan nan kai tsaye ba, wani lokacin kana abu kamar ba kai ba, a yadda kake fitowa kao tsaye kana fadawa mutane ko nuna abunda yake ranka wani amfani zai yi da wannan damar ya cutar kai, baka da tabbacin ita ta aikata hakan ko ba ita ba, and wannan abinci Hajiya ma ta girka you shouldn't talk to her” “Hakan da nai zai tsoratata idan ma akwai hannunta a ciki, but na gaji Ibrahim yarinyar nan tana cutarda ni ta karkashin kasa, duk wani fada da muke da Dada ko Mai Martaba akanta ne, a yadda ta tsani Haleema zata iya mata wani abun makamancin wannan, i tot ta canja shiyasa na saketa na sake jiki da ita” “Amman kai da baka son Farhat miye na damuwa idan ta mutu” Cewar Ibrahim yana dariya. “Rayuwa ake magana a nan ba so ba, and tana karkashin kulawata a yanzu dukan abunda Hameeda zata mata ko wani yai mata a cikin familyna zai yi mata ne saboda ni so dole ne nai wani abu akai, and Hameeda har shaye-shaye take yanzu kasan masu shan kayan maye basa cikin hankalin kansu” Ya karasa yana duba wayarsa dake ringing, number Ikram ce. “Mai Martaba yana nemanka yanzu, yace a duk inda kake ka zo ka sameshi yanzu kai da matarka” Yana picking ta fada masa. Sai ya sauke wayar ya bude motarsa. “Mai Martaba na nema sai mun hadu” “To Allah ya tsare zan kira ka” Yai ma motar key ya kama hanyar kan wurin sarki. [3/4, 3:37 PM] Mrs Zainab Jega: *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 2⃣4⃣ Yana isa fadar part dinsa ya fara wucewa. A lokacin Farhat na zaune gaban madubi tana saka sarka, da alama wanka tai sai dai fuskarta duk d kumbura kamar an daketa. Daga bakin kofar dakinta ya tsaya yana kallonta ta madubi kamar yadda ita ma take kallonsa. “Miyasa kika yi abunda kika yi dazu? Dan ki bani kunya? Ko dan ki sake sakani cikin wata matsalar?” Juyowa tai ta fuskanceshi. “Ba ko daya” “Tazo muje” Kamar dai zata tambaya sai kuma wata zuciyar ta hanata, wardrobe ta bude ta dauko mayafin da dake sa launin atamfar dake jikinta ta rufe kanta, sannan ta nufi kofa already shi har kai downstairs. A tare suka fita daga falon daga ita har shi babu wanda fuskarsa ke dauke da walwala, shi dai ya hade rai kamar an masa mutuwa ita kuma tayi fuskar tausayi. Duk inda suka bi sai an kai har kasa ake gaishesu shi din be kula su ba, itama bata damu da amsarwa ba. Kamar dai jiya ta kofar data shiga jiya yau ma ta nan ta bi, banbanci kadan ne jiya kawota aka yi a matsayin amarya yau kuma ita da kanta ta kai kanta dan amsa kiran Mai Martaba. Babu kowa a fadar sai masu aikin gyarashi, gaisheshi suka rikayi har ya isa gaban wata kofar wacce ta sadasu da wani falon na dabam mai cike da kayan alatu, nan ma babu kowa sai ac dake ta aikinsa, ita dai tana biye da shi har suka wuce falo hudu sannan ya dauke wata hanyar mai kama da corridor ta nan ta hango garden din Mai Martaba, hannusa na dama ya kai ya tura wata kofar sai gasu sun fado cikin wani babban falo, bata yi sallama ganin shi a be yi ba, karasa yai sai ya zauna kasa yana fuskantar Mai Martaba ita ta zauna kusa da shi, Dada na zaune saman kujera tare da Hajiya Hadiza, Hajiya Maryam da Zara kuma suna a kujera daya, sai Hameeda dake zaune gafen Dada. Gyaran murya Mai Martaba yai yana kallon Zain. “Na fada maka kuskure daya daga matarka ba zamu dauka ba anyi haka?” Zain yai shiru ya kasa amsawa ya kuma kasa daga kai ya kalli Mai Martaba. Hajiya Hadiza ta share kwalla da suka zubo mata ta ce “Mai Martaba karka hukuntashi da laifin da ba nashi ba, laifinane domin ni n girka abincin da yarinyar nan ta ci, kuma wannan laifin ba nata bane kuma bana mutum daya ba ne” “Sai dai idan kin so dorawa kanki laifi amman miye naki a ciki, ai yasan ke kika girka abinci amman daya tashi sai ya dora laifin akan Hameeda, kare da karau ma har da cewa yai wai ita ta kashe Haleema wannan magana ai ta girma” Cewar Dada cikin masifa. Hajiya Maryam ta tabe baki. “Daga zuwan yarinya jiya jiya har ta haddasa fitina, nan gaba abunda zata yi a gaba ai mai yawa ne” “Lallai kam kara asan abun yi tun kamin abun yafi haka” Cewar Hajiya Zara. Har Zain ya bude baki zai yi magana sai Farhat ta tari numfashinsa wacce suka ji muryarta kamar daga sama. “Allah ya taimakeka, dukan dan Adam ajizine, bana cikin daya daga cikin iyalanka amman wanda ya aje ni agidan nan yana da muhimmanci a gareka, dukan abunda Yarima ya aikata jiya laifinane domin ban fada masa cewar ina da ulcer ba, sai yai zato ko wani abun ne, hakan yasa ya kira ta ya tambaya ko akwai abunda ya faru, hakan yasa ta fasa kuka ta juye masa magana, amman bayan wannan babu abunda ya faru, Zain mai tsananin biyayya ne a gareka kuma mai jin nauyinka wannan ya hana shi yin musu maka abunda aka fada akansa, idan kuma Mai Martaba be yarda da magana ta ba, ina son ya bani alkur'ne na rantse masa da shi ko kuma ita Hameeda ta rantse akan anyi haka. Mai Martaba kai shugaba ne mai adalci da sanin ya kamata karka yanke hukunci bisa ga fushi, idan har zaka yanke hukuncin ka yanke min duk hukuncin daya dace da ni amman ban da na saki, karka cilastawa danka yin abunda Allah baya maraba da shi, na hadaka da girman Allah Mai Martaba ka tausaya mana.   Ina neman afuwarka akan abunda ya faru, ko wane adam ajizine dukanmu masu laifi ne, kai ubane a gareni sakancewar kao shugaba ne mai adalci da sanin ya kamata, kuma ina mai maka alkawari hakan ba zai sake faruwa ba” Idon kowa yana kanta, bama kamar Hameeda da bakinta ke sake tana kallon ikon Allah, Zain kuma yana kallon tana yin abunda ba zai iya ba, domin indai shi zai kare kansa sai dai Mai Martaba yai masa abunda duk zai masa amman ba zai iya ba, abu na biyu kuma kowa na mamakin yadda ta tsoma baki ba tare da Mai Martaba ya bata umarnin hakan ba. Kallonta Mai Martaba yake, tun da ta fara magana ya yaba da hankalinta, a natse take fitar da duk wani kalamin dake fita daga bakinta tana kokarin fahimtar da shi abunda sauran suka kasa, gata sai hawaye take gwanin tausayi. “Karya take wacan wacan yarinyar munafuka ce au laiye zaki yi ki karyatata” Cewar Dada tana jin kamar ta taso tazo ta daketa “Zai iya zama gaskiya mana, ai kin san Zain ba zai iya musa abunda aka cewa Mai Martaba ba, kuma kullum Hameeda ce take kawo kararsa akan ya mata abu, amman shi be taba kawo kararta ba, kuma be taba musa maka ba” Dada ta kalli Hajiya Hadiza wacce ta gama maganar yanzu. “Ee daman can son Hameeda kike ba ni na sani, duk da goyon bayanki ya auro wannan tsitattaciyar magen, to Wallahi ta Allah ba taku ba” . Mai Martaba yai gyaran murya a karo na biyu sannan ya ce “Dukan abunda zai tashi hankalin iyalaina bana sonsa, babu ta inda mata ta fi yar'uwa, dan haka bana son ka bar zuciyarka ta yaudare ka fifita matarka akan yar'uwarka, abu na biyu kuma ban jidadin abunda Hameeda tai ba, dan bana son auren ba shi ke nuna duk abunda kika yi ko kika ce na cilasta masa abunda ba zai kawo kwanciyar hankali ba, fushi gaba zargi zargi duk ina son a aje shi a cikin iyalin nan, Matar Muhammad Yayarki domin ta auri yayanki dan haka kar na kuskura na ji kin mata rashin kunya, ba ke ba kuma kowa a cikinku ya ce zai nuna rashin tarbiya a gareta zai tsaba masa, ita kuma ina son ta kama mutunci da girmanta karta kuskura shiga sha'anin da bana nata ba, kowa ya rike girmansa da matsayinsa. Zain ya girme ki Hameeda be kamata ki masa karya ba, karya tana daya daga cikin abunda na tsana, karya tana zubarda mutumcin mutum da kimarsa, karya kuma ba abu ne da akasan wanda ya girma a cikin gidan nan da yinsa ba, dan haka ki bashi hakuri da matarsa. Zain..” Mai Martaba ya kirashi a natse sai ya dago ya kalleshi tare da amsawa. “Kai mai yanke hukunci, ina fatar nan gaba idan haka ya faru kai zaka yi hukunci ba ni ba, ka kai matsayin da zaka yanke hukunci ko bana nan ko kuwa akan abunda ya shafi masarautar nan ne balle kuma abunda a shafi iyalina, Allah ya maka albarka” Wannan furuci da Mai Martaba yai ga Zain be yi ma Hajiya Maryam da Hajiya Zarah dadi ba, Dada kan kasa cewa komai tai ba dan komai ba sai dan hukuncin da Mai Martaba ya yanke be mata dadi ba, ba ta son cilasta masa ya cilasta ma Zain sakin Farhat nan, amman tana nan haushinta. Dan haka sai ta tashi ta bar falon.       Hameeda bata da damar musa masa tace ba haka bane, hakan kuma da Mai Martaba yai ya nuna ya aminta da kalaman Farhat saman da nata. Sai da tana jin kamar akwai kaskanci a tare da ita idan har ta bawa Farhat hakuri, amman ya zatayi umarnin mai martaba ba bata da wata dabara bace ta bi. “Dan Allah Yarima kai hakuri” Be amsa mata ba, sam be ma kalli inda take ba, sai ta kalli Farhat tana wani irin dauke numfashi kamar zata mutu, saboda bakincikin bawa Farhat hakuri. “Ki... Yi... Ki... Yi haku...ri...” Farhat ta dago ta kalleta. “Ba komai na yafe miki” Hajiya Hadiza tayi murmushi. “Mun gode Mai Martaba Allah ya kara girma da lafiya, daman ni nasan Zain ba zai ce haka ba, Allah ya tsare gaba” Da hannu Mai Martaba yai musu alama da su tashi su bashi guri sai kowa ya tashi ya fice, ban da Hajiya Hadiza wacce ta dauko masa sabuwar fira daman yau a dakinta ya wayi gari. Suna shigowa part dinsu Zain ya maida kofar falon ya rufe yana kallon Farhat data hade fuska kamar bata taba murmushi ba. “Da ya baki qur'an ki rantsen fa?” “Ai ba zai bani ba, domin manyan mutane basa daukar irin wannan hukunci sai ya zama dole, so kaga Mai Martaba ya yarda da ni sama da Hameeda” “Yarda da yai dake a yanzu ba shi yake nuna ki sake yin haka a gaba ba” Ya fada as he command her. “Shi kadai ka iya, ni kazo nan kana min fada amman yanzu kanwarka take kokarin cin zarafinka a gaban Mai Martaba” “Ban iya munafurci ba” “To ni na iya sa ido kai kallo” Ta fada tana harararsa, har tayi gaba sai ua rikota ya dawo da ita da karfi ya matse gashin kanta. “This will be the last time da zaki harareni” Wani irin kara tai tana kokarin kwatar kanta amman ta kasa, har sai da yaga dama ya jefar da ita saman kujera. ***      ***       *** Bayan ta gama hada breakfast su Amal suka ci suka wuce islamiya, ita kuma ta shiga ta shirya cikin bakar abaya ta dauko jakarta ta fito falo inda Hafsatu manga take zaune tana jiranta, duk ta bata fuska kamar ba ita ba. Zaunawa Anty Ummi tai saman kujera ta kama hannun Hafsatu manga tana sauke ajiyar zuciya. “Baki son zuwa gidanku ne? Zan kaiki ne saboda ki samu kwanciyar hankali, nima na samu Zain ma ya samu, bana son fadan da kike da Amal kuma bana jindadin yadda Zain yake shige miki komai zai iya faruwa, sannan na kasa natsuwa da ke a gidan nan, ke kanki nasan kina son iyayenki...” Ta tsayarda maganar sakamakon ringing din da wayarta ke yi, picking tai ta kara a kunne. “Hello Ummu, Subhanallahi gani nan zuwa” Tana aje wayar ta kama hannun Hafsatu manga suka fice, bata zame ko ina ba sai gidansu, wato family house dinsu, gabanta sai faduwa yake saboda tasan ciwon Abbansu a duk lokacin da asmarsa ta tashi bata masa da kyau. Sai dai a yadda ta tararda yan'uwata da kuma Abbansu yasa hankalinta ya kwanta, domin ta sameshi zaune har ana dan taba fira da shi, zubewa tai kasa tana gaisheshi Hafsatu manga kuma ta tada kai sama tana kallon falon da aka narkawa dukiya, da dai dai take kallon hotunan dake manne a falon har ta kai kan hoton mutumen data taba gani a Jafatu Mall har ta dauko masa takardarsa data fadi. Wayarsa Anty Ummi ce tai ringing sai ta dauka tai yar magana, sai kuma ta tashi ta kama hannun Hafsatu manga. “Waccece wannan?” Hajiyarsu ta tambaya. “Yar makociyarmu ce” “Allah sarki” Daga haka Anty Ummi taja hannunta suka fice, motarta ta shiga suka kama hanyar samaru suna isa ta fito mota wani saurayi ya fito, bayan sun gaisa ta mika masa Hafsatu manga. “Ka tabbatar a hannun sarkin garinsu ka kaita, idan kuma baka samu kowa ba ka dawo da ita, kar wani abu ya same ta” “Karki samu matsala, za'ayi yadda kika ce” Yana fadar hakan yaja hannunta sai ta fashe da kuka. “Anty na daina bana son zuwa ba zan sake biki miki Amal ba” Tsaye Anty Ummi tai tana kallonsu zuciyarta na sosuwa da tafiyar da Hafsatu manga zata yi, sai dai bata yi komai ba har ya sakata motar ya kama hanya. Sannan ta bude motarta ta shiga ta kamo hanyar gida. ****      *****    **** FLASH BACK... Tana jin motarsa ta yi saurin jera kulolin abinci a dinning, ta shiga bedroom da sauri ta dauko dankwalinta ta daura ta fito tana dariya ta daukin dawowar mijinta. A bakin kofar falo suka ci karo da shi yana kokarin shigowa ita kuma tana kokarin fita. "Sannu da zuwa" Ta furta tana dariya kamar yadda shima yake dariyar yana kallonta. "Yauwa ya gidan?" "Lafiya kalau" Ta karbi jakar kayan da ke hannunsa, tare suka karasa cikin falon, ya cire hular kansa ya mika mata ya bude aninin rigar shaddar da ke jikinsa ya zauna saman cushion yana sauke gajiya. "Kai Al-hamdulillah babu inda ya fi gida dadi, duk inda nake bana jin sakewa sai na dawo gida" "Al-hamdulillah dai an dawo lafiya ya ka baro Lagos?" "Lagos lafiya kalau" "Ka huta ka yi wanka ga abinci can yana jiranka" Ya kalleta zuciyarsa cike da so da kuma kaunar matarsa, sai ta mike tsaye tana murmushi ta nufi dakinsa dan aje kayan da ke hannunta. Bayan ya gama wankan ya zo falo suka ci abinci a tare, a yammacin ranar ta lahadi be labarta mata komai ba sai Lagos da abunda ke cikin Lagos, wani abun ya bata mamaki wani ya bata dariya a haka dai ta yi shawa'ar wata rana idan zai sake zuwa wani worship din zata bishi ta ga Lagos da kanta. Bayan sallah isha'i tana zaune daki a gaban madubi tana daura dankwalin atamfa ya shigo rike da wani dan karami abu mai kamar akwati fuskarsa dauke da murmushi kamar kullum, a gefen gado ya zauna yana kallonta itama sai ta kalleshi ta dauke ido. Hannunta ya kamo ta danka mata wani awarwaron azurfa mai dauki da sunanta wato Maman Hafsat. Tsalle ta yi ta dire tana ihu da murna. "Habib Ina ka samo?" "Na musamman ne ni nasa aka kera min shi a can Lagos din, kin san kin fada min idan Allah ya baki ya mace zaki saka mata Hafsat shiyasa na ce ya rubuta Maman Hafsat a jiki" "Na gode sosai Allah ya saka da alheri" "Amin, wannan kuma na yar mu ne Hafsat... " Ya karasa yana mika mata karamin na yara mai dauke da suna Hafsat. Karba tayi sai dai bata murna kamar yadda take a karban na farkon, shafa awarwaron ta yi idonta cike da kwalla. "Kin fara ko?" Ta share hawayen da suka zubo mata. "Kawai ina tunanin lokacin da zamu samu yar ne har mu saka mata awarwaron" "Kina tunanin Namiji zamu samu?" "Ina tunanin zuwan haihuwar ne Habib" Sauka ya yi daga inda yake ya gurfana kasan kuiwoyinsa ya dora hannayensa saman cinyarta. "Rufaida, komai fa na Allah ne, sau nawa zan fada miki ki daina saka kanki a irin wannan damuwar, kin san matsalar ba daga ni ba ne, kuma ba daga ke ba ne, kawai akwai lokacin da Allah ya diba mana ne wanda dole sai mun cin ma adadin kamin mu samu haihuwar, kuma na miki alkwari ba zan sawa dan kowa wannan sunan da kike so ba sai yarki" "Idan kuma Allah ya kaddara ba da ni zaka haihu ba fa?" "Kai Subhanallah Rufaida ana baki kina roko, wannan wace irin magana ce haka, yau ma daga dawowata bata min rai zaki yi?" "Ka yi hakuri Habib nasan haihuwa na Allah ne, amman abun yana damuna yadda yan'uwanka suke dora laifin a kaina yana damuna, kai kuma kaki ka yi musu abunda suke so, ni kake jawa kiyayyar ko jiya sai da Hajiya ta zo gidan nan tana rokona akan na barka ka yi aure, bata hana na mallakeka ba amman na barka ka yi aure tana son ganin jikokinta" "Itama ta yarda kin mallake ni kenan?" "Mi zai sa ba zata yarda ba? Dan me zata baka umarni kara aure kaki karawa? Kai kanka na tabbatar kana son ganin jininka Habib" Ta sauka kasa daga saman kujerar tana rokonsa hawaye na kwaranya a idanuwanta. "Na hada ka da girman Allah Habib na rokeka dan Allah dan Manzonsa, ka kara aure dan Allah ka yi aure kamar yadda Hajiya da yan'uwanka suke so, kai kanka kana son ganin jininka Habib, kuma idan kayi aure zaka wanke ni daga zargin da yan'uwanka suke min na cewar na mallakeka, wata kila ma ka samu haihuwa kamar yadda suke so" Mikewa ya yi tsaye ba tare da yace da ita komai ba ya fice ya bar mata dakin tana aikin kuka. Har ga Allah bata son mijinta ya kara aure, domin babu mace da take zaman lafiya da mijinta tana son shi yana sonta, ta so ya auro wata ko da kuwa yan uwansa suna sonta ne balle basa sonta, amman a yanzu ya zame mata cilas ta rokeshi ya yi auren saboda farincikin mahaifiyarsa ganin cewar shi kadai ta haifa kuma tana son ganin jikokinta. Ko wane gidan aure yana irin nashi kalubale da ma'aura suke samu kansu a cikin, wata ta kan zo da sauki wata kuma mai tsanani, wata akan samu mafita awarware wata kuma ta dauwama har a abada! Rayuwar auren Rufaida da Habib rayuwa ce mai kyau kuma abar burgewa ga kowa, irin yadda suke nunawa junansu so da kulawa kai kace a kwai daya suka fito, basa da matsala ta ko'ina, Habib baya son bacin ran Rufaida da ka bata mata rai kara ka bata masa kamar yadda itama take kokarin gujewa duk wani abu da tasan zai sosa nasa rai, hakan yasa mutane suke zargin cewa ta mallakeshi baya yi komai sai abunda ta ce, basu da matsala ta ko ina face rashin haihuwa da Allah ya jarrabi Rufaida da ita kamar yadda yake jarrabar wasu daga cikin bayinsa. Rashin samun haihuwa ita kadaice matsalar dake damun Rufaida da Habib, babu irin neman maganin da basu yi ba na gida da na asibiti, babu ranar da basa addu'a dare da rana akan Allah ya basu haihuwa, dukan asibitin da suka je ana fada musu cewar Habib bashi da wata matsala balle kuma Rufaida da mahaifarta take lafiya kalau kawai dai lokacin haihuwar ne beyi ba, wanda Allah ya riga ya rubuta adadin lokacin da hakan zai kasance, wanda bayi da yawa basu gane hakan ba, ciki kuwa har da yan'uwan Habiba da kuma mahaifiyarsa, sun kasa yarda cewar Rufaida bata da wata matsala, suna tunanin Habib yana fadar hakan ne kawai domin ya kareta, wasa wasa kiyayya ta fara shiga tsakamin Rufaida da yan'uwan Habib da kuma mahaifiyarsa, ganin an kwashe sharakara goma sha daya Rufaida bata taba batan wata ba balle bari (miscarriage), har ta kai Rufaida bata son shiga cikin yan'uwan Habib ko kuma ta kusanci Mahaifiyarsa saboda kori da habaici da ake mata. Mahaifiyar Habib ta yi iya hakuri da daga kafa wa Rufaida wanda take tunanin ya kamata ace Rufaida ta gano hakan da kanta amman kasa ganowa har sai da ta fito fili ta nuna mata tana son danta ya kara aure, da gangan Habib ya buga kafa da kasa ya ce shi ba zai kara aure ba, a tunaninsa idan har ya kara aure be kyautawa Rufaida ba, kuma zata shiga damuwa. Aka kida aka raya aka daka Habib ya tsaya kai da fata akan ba zai kara aure ba wai shi ya yarda daga Allah ne, wata kila lokacin haihuwar ne be yi ba. Lokuta da dama Mahaifiyar Habib takan sa Rufaida a gaba tana rokonta data bar danta ya yi aure saboda ya samu jikoki tana son ganin jikokinta saboda shi kadai ta haifa. Tun Rufaida na dauko abun wani iri har ta fahimce cewa Hajiya Larai wato mahaifiyar Habib ta yarda da zugar mutane da ke cewa ta mallake Habib baya ganin kowa sai ita kuma baya yin komai sai ta ce ayi. Wannan matsalar ce ta saka Rufaida a damuwa, ita da kanta ta zo tana neman ya kara aure amman ya ki wai shi bashi da ra'ayin kara mata biyu, idan ta matsa masa har kaurawace abincinta da shimfidarta yake amman hakan be dame ta ba, ita dai burinta ya kara auren kamar yadda mahaifiyarsa take so. *** *** *** Bayan ta gama kukan ta mike tsaye ta bi bayansa, a falo ta zame shi zaune saman cushion ya hada kai da guiwa ya noce kansa kana gani kasan damuwa ce tayi masa yawa. "Kana da son kanka Habib abunda yake faranta maka rai kawai kake, ko da kuwa hakan zai bakanta maka rai ne, kana kokarin ganin ka faranta min ko da kai naka ran zai bace sabo...." "Saboda na san hakan zai dawo min da bakincikina i zuwa farinciki, dukan abunda zai faranta miki rai shi zai faranta min rai, miyasa Hajiya ba zata fahimci cewar rashin haihuwar mu daga Allah ba ne?" Ya karasa mata tare da dagowa ya kalleta. "Miyasa kai ba zaka fahimci halin da Hajiya take ciki ka kara auren ba?" "Na fada miki bana da ra'ayin mata biyu" "To ka saki ni ka auro wata...!" Ba shiri ya tashi tsaye da sauri yana kallonta tare da mamakin kalamin da ya fito daga bakin matarsa, duk irin so da Rufaida take masa yau har ta iya bude baki ta ce ya saketa ya auro wata? "Da bakinki kike cewa na sakeki na auro wata? Kin san abunda kike fada kuwa?" Ta gyada masa kai hawaye na zuba a idonta. "Na sani, matukar hakan zan faranta ran mahaifiyarka da yan'uwanka da kuma kai kanka na yarda ka sakeni ka auro wata, kai kanka kana son haihuwa Habib ina karantar damuwar a fuskarka, ina ganin shaukin da ke fuskarka a duk lokacin da idanuwanka suka sauka akan yara, ina jin addu'o'in da kake yi cikin dare Habib, wata kila ni Allah be yi zan haihu da kai ba, miyasa ba zaka auri wacce zata haifa maka yaya ba?" Ta taso ya nufota yana fadin. "Ke kadai zaki haifa min Hafsat Rufaida..." Hannu ta daga masa tun kan ya karaso. "Karka sake shagaltarda ni da kalamanka, kar zuciyarka ta sake yaudaraka ka saba umarnin mahaifiyarka, ina jiye maka tsoron fushinta Habib ina jiye maka tsoron rana da zata fusata tayi mummunan furuci akanka Habib, ka ji tsoron Allah mahaifiyarka ita ta dauki cikinka tun kana kwana daya har ka kai wata tara ta haife ta raineka har ka girma ka hadu da ni na aureka, shin idan ban zame mata silar farinciki ba taya kai zaka zame mata silar bakinciki? Kai ma zaka zo dan da ka haifa ya tsabawa umarninka? Iyaye suna da muhimmanci Habib Annabimu sai da ya kira uwa sau uku sannan ya kira uba, ina son ka sani fushin Allah yana tare da fushin uwaye, kuma yardarsu tana tare da yardar Allah ina tsoron kar wata kai ma danka yai maka haka Habib-" Tunda ta fara maganar yake kallon hawayen da ke zuba a idonta har ta kai aya, yasan gaskiya take fada masa amman shi kuma ya rasa yadda zai fahimtar da Hajiya da ita kanta Rufaidar yadda ya yarda da abunda Allah ya rubuta zai same shi. "Shikenan, zan kara auren shine burinki da na Hajiya ko? Da yan'uwana, daga yau matsalar kara aure ta wuce zan kara aure sai ki nemo min matar da zan aura" Fashewa tai da kuka mai taba zuciyata ta nufi dakinta da gudu zuciyarta na mata mugun kuna saboda kalaminsa na karin aure abunda ko wace mace ta tsana. "Kin gani ko? Yanzu ma ba a tsira ba" Ya fada yana ware hannayensa tare da sauke ajiyar zuciya, komawa ya yi ya zauna ya dafe kansa sai ga hawaye masu zafi sun gangaro daga idanuwansa zuwa kuncinsa. ______________________________ Ya kuka ji wannan zubin? Akwai sugar kuwa? Comments. Share. Like. [3/4, 3:37 PM] Mrs Zainab Jega: *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 2⃣5⃣ Daidai gwargwadon dukiya Allah ya horewa Habib babu abunda ya nema ya rasa sai haihuwa, komai na duniyar nan Allah ya bashi ban da haihuwa. Hakan yasa Rufaida ta tsaya da kanta wajen ganin ya samu cikon burinsa domin shi ma yana son haihuwa, ita da kantata cilasta masa auren son auren a ranta domin kawai mahaifiyarsa ta samu kwanciyar hankali shima kuma ya samu. Kanwar makociyarsu ta nema masa wato Safiya, Safiya mace ce da kowa ke yabon halinta ana yaba tarbiyarta, aurenta daya kishiya ta hanata zama, mijin ya sakota da cikin ta haihu a gida dan be zo da rai ba. Rufaida bata tsira a gurin iyeyen mijinta ba, ganin ita ya saka ta nemo masa matar da kansa, zancen da suke cewa ta mallekeshi sai ya tabbata a garesu, duk wani abunda za a gudanar na bikin ita ce kan gaba sam ba zaka ganta kace tana kishi ba, sai dai idan ta shiga dakinta ta kanyi kukanta ita kadai, ko kuma a gaban kanenta kasancewar ita ce Babban a gidansu, babu irin magiyar da kannenta basu yi akan ta daina saka kanta a cikin lamarin auren amman ta ki. Duk abunda Habib yai ma Safiya na kayan lefe sai da yai Rufaida, ya canja mata kayan daki har spoon na cin abinci sai da ya canja mata shi. A dayan bangaren aka kawo Safiya, daidai gwargwadon ita ma iyayenta sun mata kaya kasancewarsu masu dan rufin asiri kuma sunsan wanda ta aura ba karamin mutum ba ne, rabar da aka kawo amarya Rufaida ta sha kuka kamar ta hadeye zuciyata ta mutu, hakika tana son mijinta kuma tana kishin ganinsa tare da wata, kanenta suna falo ita tana dakinta tare da Habib sai lallabata yake, be bar dakin ba sai kusan sha biyun dare, abunda ya tashi hankalin Safiya kuma ya bata mamakin ganin cewar ita amarya amman har tsowon lokacin yana tare da uwargidansa ita ya kyaleta. Be taba nuna musu banbanci ba, yana kokarin kwatanta adalci dai dai gwargwadon yadda zai iya, sai dai har ga Allah son Rufaida yafi na Safiya a zuciyarsa wanda yasa baya iya boyewa yana nunawa a gaban kowa. Babu abunda ya canja daga Rufaida sai ma abunda ya faru, daman can tana masa biyayya amman na yanzu yafi na ko yaushe. Tunda aka yi auren Rufaida bata da wata fargaba sai na gudun Safiya ta samu ciki, ita kanta tasan bata da matsala zata iya samun cikin a ko yaushe kamar yadda binciken likitoci ya tabbatar, amman ganin bata taba bari ba ya tashi hankali sosai tana ganin kamar ba zata taba haihuwa ba. Fargabarta ya koma damuwa tun daga lokacin da Safiya ta cika wata uku a gidan Habib, yanayinta da wasu abubuwan da take sai suka canja, saboda ta lura da cewar Safiya tana dauke da juna ba, Habib be fada mata ba ita kuma bata tambaya ba, amman taga alamun hakan a gurin Safiya saboda yawan amai da tashin zuciya da take, har ita da kanta take labarta mata cewar wannan shine wata na uku da bata ga al'adarta ba. A week later kanen Habib mata na bangaren uwarsa suka zo har cikin gidan suka fada mata wai Safiya nada ciki wata uku, duk wani kokari ta yi na karta nuna musu damuwar a fuskarta, sai ta nuna musu ta jidadi da farincikinta duk kuwa da kasancewar sun yi mata hakan ne dan su bakanta mata rai. A daren ranar ta samu Habib da maganar, sai ya rasa yadda zai kalli fuskarta kamar yai mata wani laifin. “Ba a boye farinciki Habib, ni nafi kowa dacewar naji labarin nan amman baka fada mim ba sai da kanenka suka zo suka fada min” “Na yi tunani abun ba zai miki dadi ba ne” “Haba Habib shekara goma sha daya muna neman haihuwa fa, yanzu kuma ka samu sai nace be min dadi ba? Na maka murna Allah ya sauke ta lafiya” Sai kawai ta fashe da kuka mai karfe. “Akwai ciwo Habib, akwai ciwo sosai ga mace mai auren da zata bude idonta a gidan mijinta bata ga yayanta ba, Allah be nufa ni zaka haihu da ni ba saman ni na san matsalar daga gareni ne” “Ban cire daga haihuwarki ba, ko Safiya zata haifi yaya ashiri ba zan sakawa daya daga cikinsu sunan yar da kike so ba, ke kadai zaki haifa min Hafsat, insha-Allah sai an kiraki da Maman Hafsat” Tun daga lokacin da cikin Safiya ya fara girma, kullum Rufaida cikin kuka take saboda abunda yan'uwan Habib suke mata, kai kace basu san Allah ba, kamar ita ta hanawa kanta haihuwa. A kullum Safiya sabon hali take kirkirowa domin kawai ta musgunawa Rufaida ita kuma tana kokarin hade damuwarta ta nuna abun be dame ta ba.. Lokacin da cikin Safiya ya cika wata tara edd ta ya cika ta haifowa Habib tawayen mata biyu masu kama da shi, a ranar Rufaida ta raina kanta a gurin ya'uwan Habib babu kalar wulakanci da gorin da basu mata ba, balle ma ranar suna sai kanenta ne suke kare mata fadan da kuma shi Habib din da kansa. A yadda yanayin ya canja saboda damuwar matarsa sai ka dauka baya farinciki da haihuwar. Wannan dalilin ne yasa Safiya ta fara shiga Malamai gudun kar nan ma Rufaida ta koreta ta hanata zaman aure kamar yadda wadancan kiyoshin suka mata, sai dai bata yi nasaraba, matukar Habib tai ma baya kamashi tayi kashin kudi har ta gaji. A haka suka kwashe shekara goma a tare, a lokacin twins sun yi wayo sai suka fi kaunar Rufaida fiye da mahaifiyar data haife su saboda kulawa da soyayya da take nuna musu, ta nan ma bata tsira ba sai suka ce ta shanye twins din suma magani tai musu. Ana cikin haka Allah ya bawa Rufaida ciki baya ta kwashe shekara ashiri da daya a gidan aure babu ko bari, farinciki gurin yan'uwanta da Habib da ita kanta ba a magana, Hajiyar Habib ce kawai sai yan'uwanta da Safiya ne basu jidadi ba. Hankalin Safiya ya tashi sosai ganin yadda Habib yake rawar jiki da Rufaida ko kasa baya son ta taba, sai ta sake shiga gurin malamai tasa aka taushe cikin Rufaida, ga ciki ya tsufa amman ba haihuwa tun ana kidayar kwanaki har lissafi ya bace musu, idan aka je asibiti sai su ce su basu ga komai ba babu ciki a jikinta bayan kuma gashi nan ya kumburo haihuwa ko yau ko gobe. Wannan damuwarce ta shiga zuciyar Rufaida ta hanata sukuni da walwala duk tabi ta rame ta lalace kamar ba ita ba, babu irin neman maganin da ayi amman ba a dace ba, a haka har ta kwashe shekara biyar dauke da cikin bata haihu ba. A lokacin duk wanda ya kalleta sai ya zubar mata da kwalla saboda mawuyacin halin da take ciki. Hakan be wadatar da Safiya ba, ganin har yanzu Habib yana sonta yana bata kulawa kusan kullum ma yana tare da ita, yasa ta koma gurin bokan da yai mata wacan aikin ya sake yi mata wani na a haukatarda Rufaida ta bar gidan ko mijinta ya daina nemanta. “Za'ayi miki aikin, amman fa duk ranar da ta tako kafarta cikin gidan nan, akanki zai koma” “Ai ni so nake ayi mata wanda zata bar garin gaba daya ta tafi can inda ba a santa ba, ta bar min mijina ni kadai” Sai da bokan ya jadda mata abubuwan da zata kawo da kuma ka'idar aikin, sannan ta zube masa kudi ta tashi. Kwana biyu da yin aikin ya kama Rufaida, ranar wata juma'a babu kowa sai ita kadai a part dinsa domin Kuwa Safiya ta saka yayanta a part dinta ta rufe saboda ta san mugun abun da tai, ji tai kamar an tsikareta sai ta tashi tsaye da sauri, a take kanta yai mugum sarawa sai da dafe kan a hannu biyu saboda taji yana juna mata, dakinta ta shiga ta bude durowa ya dauko awarwaron da Habib ya bata mai sunanta dana Hafsat ta riko ta fito daga dakin tana ta kukan da bata san inda yake fito mata ba. Kanta ta daga sama tana ta kallon falon kamar bakonta sai kuma ta nufi kofa da sauri tana ta dafe kanta ta fita daga gidan gaba daya. Bata yi tafiyar minti talatin ba amman da yake sihirine sai aljanun suka dauketa sai gata cikin kauyen Kufawa dake karkashin karamar hukumar Maru. A karkashin wani ice suka aje ta, a gurin ta zauna tana ta rusa kuka, duk wanda ya wuce sai ya tsaya ya mata magana amman bata iya cewa komai sai kuka take, a haka har Allah ya kawo wani dattijo, babu kalar tambayar da be mata ba, amman ta kasa ce masa komai sai kuka take shi ya rika hannunta ya tafi da ita gidansa, Matarsa Inna Ladi mace ce mai son mutane da kuma maraba da su, Inna ladi baiwa ce a gidan masarautar Kufawa hakan ya samo alsali ne tun daga kakarta kasancewa a wacan zamanin ana yayin sayen bayi masarautar kauyen Kufawa ta siyenta ita da kakanta, a haka aka haife iyayensu, har aka zo kansu kasancewar zamani a canja sai ya zama suna gidanjensu sai dai dukan wani aiki na gidan sarkin su suke yi su da duk bayin da aka siye tare kuma da yayansu, har yau har gobe idan Sarkin yaga dama zai iya daukar daya daga cikinsu ko yayasu ya bayar kyauta, sai dai walahar irin ta da da bauta d ake sha ya banbanta da na yanzu, daga gidanta take zuwa yin aiki a gidan Sarkin idan ta gama ta dawo tayi nata aikin, idan kuma bata samu zuwa ba sai ta tura yayanta. Ita kanta Inna Ladi tana kallon Rufaida ta san daga birni take kuma ba lafiya take ba. “Malam ina ka samo wannan matar?” A take ya labarta mata komai, ta tausaya mata domin ta san duk yadda aka yi wannan sihiri ne ga kuma tsohon cikin da take dauke da shi. A gidan Rufaida ta cigaba da zama wani lokacin ta kan fita ta tafi yawonta sai da yamma ta dawo wani lokacin kuma sai ta zauna a gidan tai ta kuka, a haka ta kwashe shekara daya bata haihu ba, daga nan Malam Sani bawa da Inna Ladi suka dingi yi mata addu'a da rubutu tana sha, wasa wasa ta kara kwashe shekara uku sannan ta haihuwa, ranar da tai nakudu babu inda ba a jita ba, saboda kuka da ihun da take, wani abun mamaki tana haihuwar yarinyar sai ta karbeta daga hannun Inna Ladi tana kallonta jikinta har rawa yake. “Hafsa Hafsa hafsa” Shine kawai abunda take ta fada, wannan dalilin yasa suka sakawa yar da haifa Hafsat amman Inna Ladi tana kiranta da manga kasancewar sunan mahaifiyarta ne. A hnnunsu Hafsatu manga ta girma duk wani abu da uwa take yi ma ya, Inna Ladi ce take yi ma Hafsatu manga, a haka har tai yi wayo. Ta bangaren Habib babu irin neman da basu mata ba, su da yan'uwanta amman basu sameta ba, wannan damuwar ce ta zame masa silar ciwon zuciyar da yake tasar masa lokaci zuwa lokaci. A duk lokacin daya tuna da Rufaida sai yaji kamar ya hade zuciya ya mutu dan bakinciki, a haka har aka kwashe shekara tara zuwa goma a lokacin twins din Safiya suna da shekara 28, tun gama karatun lauyan da suke ko wacce ta kama aiki sun zama manyan lauyoyi har ta aurar da su. Hafsatu manga kuma na da shekara tara zuwa goma. *** *** *** Suna rayuwarsu cikin jindadi da walwala, wata rana kwatsan barayin shano suka kawo musu hari daman sun dade suna aiko sakon cewar zasu kawo musu hari, sun kashe mutane da yawa garin kadan ne suka samu tsira wadanda suka kai gudu da kafa har suka kai wani garin, sai bayan an kashe rabin garin aka aiko musu da sojoji, a nan wasu suka samu tsayawa a makarantar bokon dake garin, aka kawo musu taimako gaggawa. Share your opinions. [3/4, 3:37 PM] Mrs Zainab Jega: *HAFSATU MANGA* _Yarinyar Kauye_ Wattpad @KhadeejaCandy 2⃣6⃣ Cikin rashin jindadi Anty Ummi ta dawo gidan mahaifinta bayan tasa an tafi da Hafsatu manga, jikinta ya soma bata babu dadi zuciyarta na raya kamar wani abun zai faru, and Zain ba zaijidadi ba, yes ta san ba zai ji dadi ba amman bata da wata mafita bayan wannan. A gidan ta wuni, tana ta jiran kiran daga mutumen amman shiru be kirata ba, hakan yasa trying numbersa sai taji ta kashe, sai da yamma ta koma gida, bayan taga jikin Abbansu da sauki sosai, sai dai har ta bar gidan mutumen be kirata ba, da tunani kala kala ta isa gida. Bata yi mamakin ganin Zain a falonta zaune ba, sai dai fargaba da tsoro sun cika mata zuciya na yadda zata tunkareshi da maganar. Da murmushi ta kalleshi “Ka kai yaushe kana jirana a nan?” Ya kalli agogon hannunsa. “Four hours, ina Mama” Ya tambaya yana kallon kofa dan har yanzu be ga ta shigo ba, sai tai kamar bata ji shi ba, ta rumgume yayanta dake mata oyoyo. “Anty tun dazu Uncle ke jiranki” Aliyu ya fada, sai tai murmushin yake. “Na gani ai...” “Anty ina mama?” Hankalinsa ya fara tashi daman tun dazu jikinsa ke bashi ba dadi. “Kids kuje ciki zamuyi magana” Bayan sun wace ta zauna a kujerar dake kusa da ta Zain. “Gida naje guba Abbah, ciwonsa ya tashi” Kallonta kawai yake be ce komai ba, be kuma nuna damuwa akan abunda ta fada ba, he care for her family amman a yanzu ba shi yake son ji ba, so he wouldn't talk har sai ta kai gabar da yake so. “Daga nan na bada ita ga wanda zai kaita gida...” Ta fada tana murza yatsun hannunta, nan ma be ce komai ba sai kallon yatsun hannunta yake, yana reading mind dinta. “Da safe ne, tun da mutum ya tafi be kirani ba and na kirashi wayarsa kashe... Amman na san idan ya isa zai kirani” Still shiru be ce komai ba. “Zain ban yi hakan dan musgunawa daya daga cikinku ba, nayi hakan ne dan samawa kowa mafita, abunda kake yi kamar kana son Mama ne, which is wrong, and she's too young for that ni kuma ina tsoron abunda zai faru...” Wani dukan hannun kujera yai wani irin fushi ya bayyana a fuskarsa. “Saboda kina iya controlling dina ba shi ke nuna kina iya controlling din wasu ba, ba ki da ikon zabawa Mama abunda ya dace da ita saboda ke ba uwarta ba ce, kuma ba kowan kowa ba ce a rayuwarta, ilminki be amfaneki ba tunda baki san ciwon kowa ba sai na ki, saboda tana nan gidan ne ya baki damar yanke mata wannan hukuncin ko? Ba zaki taba iya yanke alakar dake tsakanina da ita ba, and for your words abun kunya ne ace baki iya shaidun kanenki da alheri ba, baki yi karya ba ina son Hafsat sai dai ba irin son ta zuciyarki ke ayyana miki ba, har gobe ba zaki taba son abunda zai faranta min ba Anty Ummi, saboda baki taba zama uwata ba....!” Yana kaiwa nan ya tashi fuuu ya fice daga falon cikin wani irin bacin rai. Maganarsa ta daketa har kasan zuciyarta a take hawaye ya cika mata ido, sai tai saurin tashi ta daga kanta sama tana sauke numfashi. HAMEEDA POV. Safa da marwa kawai take acikin daki ita kadai, tana jinjina karfin hali da makirci irin na Farhat. “Wai har ni yarinyar nan zata daurawa sarka ta siyar a gaban Mai Martaba, lallai Zain ya auro yar bariki kuma tantiyar shedaniya, amman zan koya mata darasi zan bude mata sabon babin da bata taba karatu ba, tana ji tana gani zaman gidan nan zai gagareta, tunda na iya kawarda yar'uwata Wallahi kowa zan iya kawarwa saboda bukatata...!” Ta fada tana wani kashe ido, sai kuma ta karasa inda wayarta take ta dauka ta kira Abida, in few minutes Abida ta shigo dakin jikinta na rawa. “Allah ya taimakeki na amsa kiranki” Hameeda ta nufi jakarta ta dauka wani abu ta mikawa Abida. “Jeki dakin Farhat ki saka mata wannan abun a karkashin katifarta” Abida ta tsaya kallon abun cikin damuwa kamar ba zata karba ba. “Karbi na ce, kuma ki tabbatar kinyi yadda na ce miki, sauran ki bari wani ya ganki” “To ranki ya dade” Ta karba ta tashi ta fice da sauri, kai tsaye Part din Farhat ta nufa tana ta tunanin abunda zata ce mata ta yadda zata barta ta shiga har cikin dakinta. A hankali tai knocked kofar falonta gabata sai faduwa yake, bata isa tacewa Hameeda ba zata yi ba, haka kuma bata isa tayi mata kuskure ba domin tasan abun kanta zai dawo. Tana tsaye a gurin har Farhat ta bude kofar sai ta tsaya tana kallonta ita kuma tai kasa da idonta tare da risinawa ta gaisheta. “Allah ya taimakeki na ce ko kina bukatar wani aikin ne?” “Bana bukata” Taje zata maida kofar falon ta rufe Abida ta sake cewa. “Gyaran falo da daki fa nasan ba a gyara ba, saboda naji Hajiya Maryam tana cewa ba za a baki kuyangi ba gudun abunda zaije ya dawo, duk abunda kike so zaki fada min sai nai miki” “Idan akwai abunda ya zama dole na sanar miki zan sanar miki, amman gyaran gina ni zan yi abuna” Tana gama fadar hakan ta rufe kofar. A dole Abida ta tashi ta bar kofar falon ta dawo dakin Hameeda. “Ban samu sakawa ba, bata bar ni na shiga falon ba ma” “Saboda me?” “Tace bata bukatar komai ita zata yi da kanta” Hameeda ta mika mata hannu ita kuma ta danka mata abun a hannunsa, bata jira komai ba ta dauki mayafinta ta rufe kanta ta fice daga dakin, kai tsaye ta nufi part din Zain. A bakin kofa ta tsaya ta sauke ajiyar zuciya ta daidaita fuskarta ta yadda zata nuna babu abunda ke damunta, ta dade a tsaye tana knocked sannan Farhat ta bude kofar. “Lallai Antina, ke ba yar sarauta ba amman kin barni a tsaye ina ta knocked kamar wata baiwa” Hameeda ta fada tana murmushi, Farhat ta bar jikin kofar dan ta bawa Hameeda damar karasowa cikin falon. “A gurina darajarki tazara kadan ta bawa bayi, domin a yanzu ina sama da ke, ke da bayin dukanku a kasana kuke, so ko ba a kirani yar Sarki ba, za a kirani sarakuwar sarki domin dansa nake aure, kuma kin san ance matar Yarima ita ma gimbiya ce” Itama ta fada tana murmushi, ba karamin zafi maganarta tai ma Hameeda ba, amman sai ta nuna kamar bata ji komai ba. “Wow ashe haka aka gyara falon Yayata, Allah sarki yar'uwata, mutuwa tai mata gaggawa duk irin son da Zain yake mata yana fadar ba zai taba son wata mace kamar ba, yau gashi ya kawo wata a cikin gidanta” “Wacece yayarki?” “Macen da Zain yafi so fiye da kowa a duniyar nan, kuma macen da kike kokarin maye gurbinta” Farhat tasa dariya, sannan ta zauna kamar yadda Hameeda ta zauna a kujarar dake falon. “Ni bana kokarin maye gurbinta, sai dai na rufe gurbinta na gina nawa gurbin a zuciyar mijina” “Kinyi kokari gaskiya amman kin san komai lalacewar dan giwa yafi gawurtaccen bunsuru” “Wani dan girwar ba, amman idan ana maganar Zaki a dawo kin san ai shi ke da sarauta” “Haka ne, bari na tashi naga dakin Amaryarmu tunda taki gabatar ni ga dakin yayata” Ta fada tana murmushi, kana ta tashi ta nufi hanyar stairs, sai Farhat tai saurin cin mata tasa hannunta biyu ta juyo da ita ta rika fuskarta. “Ina tunanin kyakkyawar fuskarnan bata bukatar arba da dakin yayarta, wanda aka canja safur aka mallaka min shi a matsayin dakina, kamar yadda na mallake zuciyar mai gidan gaba daya” Hameeda tayi murmushi tare da ture hannun Farhat sai ta koma ta zauna. “Haka ne fa, yanzu dai fada min ina yayana yake” “Bana da tabbacin inda yayanke yake a yanzu, abu daya nake da tabbacinsa zuciyar yayanki tana nan tare da ni” Hameeda na kokarin soka abunda ke hannunta cikin hannun kujera ta ce. “Hakan yayi kyau Allah ya kara danko soyayyah” “Amin” Kamar kar Farhat ta rufe baki, sai ga Zain ya turo kofar falon ya shigo cikin wani irin bacin rai. “Dan Allah kin ganshi ya dawo” Ta tashi ta nufi inda yake tana murmushi. Tana shan gabansa ya kaice sai ta sake shan gabansa rikota yai ya jefar saman kujera, cikin wani irin bacin rai daya rufe masa ido har baya iya ganin Hameeda dake falon, haka yake idan ransa ya bace shi kansa baya iya controlling temper sa. “Wai baki da hankali ne ke? Useless” Yana fadar hakan ya nufi upstairs, wani kallon mamaki Hameeda tai ma Farhat, sai kuma ta tashi da sauri ta bar falon. Yana shiga dakinsa ya tararda dakin a yadda ya barshi ga aman da tai saman gadon bata cire bedsheet din ba, komawa yai falon ya riko kanta ta tuso keyarta har cikin dakinsa. “Wace irin mace ce ke? Baki san ki gyara daki ba, five minutes na baki ki gyara min dakin nan” Yana fadar hakan ya juya ya fice zuwa fadar Mai Martaba, faduwa Farhat tai a gurin ta fashe da kuka.. Ina aka kai Hafsatu manga? Anya Zain zai sake ganinta? Ya Anty Ummi zata kasance? Ya rayuwar Farhat zata kasance? Anya Hameeda zata rufe ido ta bar komai ya wuce kuwa? Wa za a kashe? Wa zai yi kisan kan? Ta wace hanya Dsp Auwal zai shiga rayuwar Hafsatu manga? Wane hali Zain zai kasance ce? Tsakanin Barrister Hassana da Barrister Husaina wa zai tsayawa Hafsatu manga a kotu? Ta ina zasu gane alakarsu da ita? Ina Hafsatu manga zata ga mahaifinta? Anya Rufaida Mahaifiyar Hafsatu manga tana nan raye? Sai yaushe asirin Safiya zai tonu? Wane hali take ciki kuma zata kasance? Miye alakar Zain da Hafsatu manga? Miye alakar Anty Ummi da Hafsatu manga? Shin Hameeda zata cin ma burinta na auren Zain? Wane irin hali Hafsatu manga zata shiga, mi zai faru da ita? Domin samun amsar wadannan tambayoyin turo 300 ta 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, sai ka turo da shaidar biyan kudin ta wannan number 08036126660. Ko kuma katin waya mtn 300 ta wannan number 08036126660. A nan na kawo karshen free pages din Hafsatu manga, kamar yadda na fada tun a Rai biyu cewar zan yi Hafsatu manga na kudi. Best regards 😍🌺 Khadeeja Candy ❤ [3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 27 Ko da ya shiga fadar ya tararda Mai Martaba na da baki wandanda suka kawo masa ziyara. Hakan yasa shi dawowa ya zagayo ta cikin gida, ya shiga bangarensa. A falonsa ya zauna ya natsu sosai kuma ya kagu mai martaba ya shigo ciki. Ya kwashe awa daya da rabi a falon sannan Mai Martaba ya shigo. Zain na ganinsa yai saurin saka daga kan kujerar ya zauna kasa, sai Mai Martaba ya kalleshi yana murmushi ya zauna. “Yarima lafiya dai?” “Lafiya kalau Mai Martaba, akwai wata magana da nake son mu yi da kai, na san kasan an kaiwa Kauyen Kufawa hari, shine nake ganin ya dace ya ashirya wani abu daga masarautar nan a kai musu, domin gaskiya ance sun yi hasarar dukiya da yawa ina ganin ya dace mu shirya wani abu sai na wakilceka” Mai Martaba yayi murmushi yana kallon Zain cike da burgewa. “Na jidadin da wannan maganar ta fito daga bakinka, hakan ya nuna ka fara maida hankali da yin abunda ya dace, amman ka makaro domin masarautar nan ta riga ta aikata musu da abunda zamu iya tun daga lokacin da abun ya faru” “Hakan yayi kyau, Allah ya kara maka lafiya” Ya fada hankalinsa na kokarin komawa wani gurin, wata mafita yake nema ta yadda zai sake ganin Hafsatu manga, ko da bata dawo gareshi ba yana son ya tabbatar da lafiyarta. “Allah ya taimakeka zan shiga cikin gida” Kai kawai Mai Martaba ya daga masa, sai ya tashi ya fice daga falon, wannan karon ta kofar waje ya fita, wato kofar fada ba kofar cikin gida ba kamar yadda ya shigo. A kofar fadar ya tsaya yana neman sarkin dogarai, sai gashi ya zo da gudu ya fadi gabansa yana kwasar gaisuwa. “Same ni a kofar gidana” Yana fadar hakan, ya nufi hanyar da zata sadashi da part dinsa. Sarkin dogarai na biye da shi sai fama saba rike yake har suka isa inda Zain yake son su tsaya. Sai da Zain ya duba yaga babu mai ganisu sannan ya kalleshi “Wani aiki nake son ka min, amman bana son kowa ya sani ko ya ji” “Allah ya taimake, babu sirrin da Yarima zai yi da ni wani ya jishi a bakina, idan har zan iya fadin sirrinka to zan iya kashe kaina da kaina” “Ina son ka nada wani amintaccenka yaje masarautar kufawa ya bincika mana wata karamar yarinya mai suna Hafsatu manga, a yau aka aika da ita masarautar gobe nake son samun labarin halin da yarinyar take ciki” “Yadda kace haka za'ayi Yarima, dan sarki jikan sarki, ba a musa maka ba dan zaki mai isa da takama, sarkin gobe sarkin jibi sarkin dake yanke hukunci ko da sarki na nan, matsayinka daban ne cika....” Zain ya daga masa tare da mika masa yan dubu dubu masu yawa. “Wannan ya zama sirri a tsakaninmu” “Ya zama Yarima, umarninka wajib ne” “Tashi ka tafi” Cikin sauri Sarkin dogarai ya tashi ya fice daga gurin. Shi kuma ya fito ya nufi masallaci a lokacin ana kiran sallah magariba ne, bayan ya gama ya fito ya nufo part dinsa, yana jin ransa babu dadi idan ya tuna abunda Anty Ummi tai sai ya rasa wane irin suna zai bata, a dayan bangaren kuma yana halin da Hafsatu manga take ciki. Yana taba kofar yaji ta rufe ba dan bashi da yadda zai yi da ba zai yi knocked. Sau biyu kawai yai knocked din sai gata ta bude masa kofar idonta a kasa kamar bata son kallonsa. “Sannu da zuwa” Ta fada murya can kasa kasa, yayi mamakin jin ta gaisheshi sai dai hakan be sashi ya amsa ba, sai ma cewa da yai “Karki sake rufe min kofa” “Tau insha-Allah ba za a sake ba” Kai tsaye upstairs ya nufa, a lokacin ta daga kai ta kalleshi. “Ga abincin ka nan” Har ya shige dakinsa be waigo ba balle har ya amsa ta, sai ta soma jin haushinta kanta miyasa ma tai masa magana? Yana shiga ya cire kayan jikinsa ya shiga bathroom yai wanka, sai da ya fito sannan ya lura da ta canja bedsheet din, gaban madubi yaje ya zauna yana kallon fadada kirjinsa, saitin zuciyarsa yake kallo gurbin da Hafsatu manga ta samu guri ta tsaya masa, ya nemi sukuninsa da walwalarsa ya rasa duk kokarin da yake na ganin ya yaki bacin ran abunda Anty Ummi tai masa sai ya kasa, ta ko'ina ganin laifinta yake baya jin zai iya yafe mata matukar wani abun ya samu Hafsatu manga. Wayarsa ce tai ringing sai yai saurin juyawa ya kalli inda wayar take kamar daman can jiran kiran yake. Tashi yai ya karasa ya dauki wayar ya duba brahim ne mai kira. Iskar bakinsa ya busar ya kamin yai picking. “Zain kana ina?” “Why?” “Anty Ummi ce tai min waya, ina son magana da kai” “Bana da bukata” Ya kashe wayar ya jefar saman gado, cikin kankane lokaci ya shirya ya fice daga gidan, domin yasan Ibrahim zai zo nemansa akan maganar wacce baya son jin komai daga gurin Anty Ummi a yanzu. Ciki ya gari ya shiga, gurin da yasan Ibrahim ba zai nemi shi a can ba, yana ganinsa kiransa yaki yai picking, har ya gaji da kiransa ya daina. Tun da ya bar gidan be dawo ba, sai karfe goma na dare, a dakinsa ya samu Farhat kwance tana bachi, wani irin haushi yaji kamar ya shaketa, cikin fushi ya fisge zanen da take lullube da shi ya tsaka mata tsawa. “Ke....!” A firgice ta tashi tana kallonsa tsoro shimfide a fuskarsa. “Tashi ki koma dakinta” Cikin sauri ta sauka daga kan gadon ta nufi kofar fita jikinta har rawa yake. A dakinta ta shiga sai taji ba zata jiya kwana a ciki ba saboda tsoro tsoron da bata san na minene ba, domin a gidan Anty Rukaiya ita kadai take kwana a dakinta. Bedsheet ta dauko tare da matashin kai sai ta shimfida a kofar dakin Zain ta kwanta. *** *** *** A hankali Alhaji Masa'ud ya saka spoon ya debi tuwon shimkafa ya tsoma cikin miyar allayahu kana ya kai bakinsa “Yau dai kamar baki cikin hayyacinki, duk rashin lafiyar Abbah ne?” “Da ita kadaice ai da sauki, wani abun na aikata abunda hankalina ya kasa kwanciya a shi” Ya dago ya kalleta da kyau. “Minene?” “Kasan yarinyar kauye nan da Zain ya kawo a gidan nan, na bata ita a kaita garinsu yau, kuma har yanzu mutumen be kirani ba, idan na kira kuma bata shiga” “Miyasa kika maida ita?” “Bata jutuwa da Amal, bana son nai mata abunda zai sa ranta ya bace saboda marainiyace, amman a duk lokacin da nai mata fada sai tai ta kuka wanda hakan yana daya daga cikin abunda yake sa Zain yake kallon ina musgunawa yarinyar, kuma Zain yana son yarinyar nan sosai ina tsoron abunda zai faru saboda karamar yarinya ce, beside bamu san daga ina take ba, yarinyar bata da yanayi da kauye, kawai dai akwai kauyanci ne a tare da ita, idan wani abu ya faru Abban Amal kasan ni zuri'ar Mai Martaba zasu dorawa laifi, amman shi Zain ya kasa ganewa” “Wa kika bawa ita ya kai ne? Ina kika samu mutumen kin sanshi ne?” “Ban sanshi ba, amman kawata ta sanshi Hajiya Juwairriya ce ta hada ni dashi, tace dan kauyen ne yana kawo musu sako daga kauye shi direba, shi ma ya bani labarin cewar komai ya koma daidai a garin” “Amman baki da hankali Aminatu, taya zaki hadata da mutumen da baki tabbatar da gaskiyarsa ba? Ita kanta Juwairriya ai ba wani dogon sani tai masa ba, yanzu idan wani abu ya samu yarinyar mutane fa? Mai zaki ce?” “Dan Allah ka tayani nemansa.” Ta fada idonta na cika da kwalla. “Babu ruwana a ciki, da kika tashi yanke hukuncinki kin nemi shawarata ne? Ko kin fada min abunda zaki yi sai bayan ki aiwatar ta kwabe miki zaki dawo neman dauki a gurina” Tashi tai ta fice daga dakin da zimmar komawa part dinta ta kira kawarta Hajiya Juwairriya. [3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 28 Har garin Allah ya waye Zain be rutsa ba ya nemi dalilin rashin bachi ya rasa, bacin rai ne ko kuma tunanin halin da Hafsatu manga take ciki? Bashi tabbacin dalilin rashin bachinsa amman yana da tabbacin a duk inda Hafsatu manga take a yanzu tana cikin wani hali domin jikinsa ya bashi haka. Kiran sallah farko ya sauka daga kan gadon ya shiga bathroom yai alwala ya fito rike da tawul yana goge ruwan fuskarsa, kofar fita ya nufa bayan ya jefar da tawul din saman gadonsa. Yana bude kofar ya ci karo da Farhat kwance a gurin ta dunkule cikin bedsheet tana sharar bachi, tsalaketa yai ya sauka downstairs. Motsin fitarsa ne ya tasheta daga bachin da take, kiran Sallah da take ji ne ya tabbatar mata da asuba ta yi, sai tai saurin leka dakinsa daga baya nan sannan ta tattara bedsheet din da filo ta koma dakinta, tana shiga tai alwala raka'atayil fajir ta fara yi sannan ta tai sallah asuba. Har ta gama addu'o inta ta fito ta shiga kitchen be dawo ba. Ruwa zafi ta fara dorawa sannan ta koma dakin, inda ta dauko acan zanen gadon ta sake budewa ta dauko wani ta shimfida, sannan ta gyara komai a muhallinsa, babu datti a dakin amman hakan be hanata sharewa ba ta goge ta saka air freshener, bayan ta rufe dakin ta dawo downstairs tana gyara. Daman can gyaran gida baya damunta ta saba da yinsa a gidan Anty Rukaiya, girki ne kawai zai wahalar da ita. Ko da goma tai ta gama komai cikin har da abun karyawa, bayan ta gama jerawa ta nufi dakinta tai wanka sai ta shirya cikin farar shadda, bayan ta gama ta sauko ta dauki breakfast din Zain ta shiga dakinsa ta aje, tna kokarin juyowa taji shigowarsa. “Breakfast na kawo maka” Ta fada tun kamin ya tambayi dalilin shigowarta dakin. “Karki sake shigo min daki” “Insha-Allah” Ta fada tana hade wani abu mai daci daya tsaya mata a makoshi, juyawa tai ta fita shi kuma ya shiga bathroom, zaune yai cikin bathtub bayan ya tube kayan jikinsa ya kunna shower ruwan yana sauka saman kansa, rayuwarsa ta baya ce ta dawo masa lokacin da suke tare da Haleema. _Wata rana zata zo Zain, ranar da zamu rayu ni da kai da wata mace a cikin gidan nan, ko kuma kai a rayu da ita a lokacin da bana raye, amman ina kishin wannan ranar Zain ina kishin macen da zata dafa maka abinci ka ci, ina kishin macen da zata tsaya daidai nan a zuciyarka_ Ta fada tana nuna saitin kirjinsa yayinda take zaune saman jikinsa yana rumgume da ita. Hannunta ya rika ya sumbance shi sannan yaja hancinta. _Babu zuwan wannan ranar Hamie babu kowa a duniyar mu sai mu kadai_ Ta dauke hannunsa daga saman fuskarta ta dora saman tsohon cikinta. _Very soon zaka zama uba kai ma, kamar dai mai martaba, amman Zain kai min wani alkawari mana? Zaka sakawa yar da na haifa sunana, idan kuma Namiji ne a saka masa sunan Mai Martaba_ _I will_ “I will” Ya furta yana lumshe ido, tare da busar da iskan dake cikin bakinsa, a Kasale yai wanka ya fito daure da tawul, a baki gado ya zauna zuciyarsa na raya masa abubuwan mabanbanta. Ya dade a zaune kamin ya tashi ya shirya cikin kananan kaya sannan ya feshe jikinsa da turare. Downstairs ya sauko ya nufi kitchen ya hada tea da kansa, hakan nan kawai yaji yana marmarin indomie he remember last indomie da suka ci tare da Hafsatu manga, da kansa ya dafa ya zuba a plate ya dawo falo har ya zauna zai ci sai kuma yaji ba zai iya ci ba, sai kawai ya dauki tea ya sha. Bayan ya gama ya tashi ya nufi kofar fita, yana bude kofar ya samu sarkin dogarai tsaye kamar daman can jiran fitowarsa yake. Sarkin dogarai na gani Yarima ya risina kasa ya gaisheshi. “Allah ya taimakeka, na sa an bincika an tabbatar da yarinyar nan bata je ba, sun ce ba a kawo wata yarinya daga birnin zuwa cikin kauye ba, Sarkin garin ma baya cikin garin wazirinsa ne ke rikon gari” “Na gode” Zain ya juyo ya dawo cikin falon, a kokarin da yake na ya danne zuciyarsa ne ya kira Anty Ummi amma sai ya kasa, dan haka ya kira abokinsa Ibrahim. “Please ka tambaya min Anty Ummi ina ta kai yarinyar nan an bincika bata cikin garin” “No Look Ibrahim ni ba zan iya kira Anty Ummi na fada mata haka ba, be kamata wannan yarinyar ta shiga tsakaninka da yar'uwarka ba abun....” Be gama fadin abunda zai fada a Zain ya kashe wayarsa. Zaunawa yai saman kujera ya dafe kansa ya runtse ido. *** *** *** Tun da suka barin garin gusau take bachi har suka shiga garin Kaduna, hayaniyar motoci dake layin go slow ne ya tasheta, mutumen na ganin ta farka ya sake mika mata lemun daya bata dazu ta sha, sai ta karba wannan karon bata sha ba sai ta rike tana ta kallon titi kamar tai kuka. “Sha” Ya katsa mata tsawa, sai ta lake kafada ta ki ta sha ta kasa masa kuka. “Duk baki sha shi ba sai nai miki dukan tsiya” A dole ta kafa baki ta sha tana kuka, nan da nan bachi yai gaba da ita. Bata sake farkawa ba har sai da ya farkar da ita da kansa. Cikin magagin bachi ta bude idonta sai yasa hannunsa ya daukota ya dora saman kafadarsa, wani dogon guri ya bi da ita ya dade yana tafiyar sannan ya iso wani babban gida mai cike da mutane, da alama manyan mutanen sun sanshi sai gaisheshi suke har ya isa wani babban falo. Saman kujera ya zaunar da ita ta dauko ruwa ya bata, kadan ta sha sai idanuwanta suka wartsake. “Ba nan ne gidan mu ba” Ta fada tana karewa falon kallo, be kula ta ba sai wata kofar yake kallo kamar mai jiran fitowar wani, ya kusan minti latatin a gurin sannan wata dattijor mace ta fito daga kofar da yake kallo tana sanye da doguwar rigar atamfa hannunta rike da waya, idanuwanta kuma sanye da farin gilashi. Sai da ta zauna saman cushion sannan ta kalli mutumen. “Rayyanu” “Na'am Hajiya ina wuni?” “Lafiya kalau, har ka zo da yarinyar” “Ee gata nan, ke gaishe ta” Ya fadawa Hafsatu manga, sai ta lake kafada “Ni ba nan aka ce a kawo ni ba” Hajiyar ta maida dubanta gurin Hafsatu manga, sai kuma ta soma taba katuwar wayar dake hannunta. “Ina fatar dai iyayenta sun san inda za a kawo ta?” “Ee da amincewar su aka kawota nan, sai dai sun ce mata ba nan za a kawota ba shiyasa kika ji tana fadin haka” “Yayi kyau, ta balaga kuwa?” “Aa bana jin haka Hajiya kin ga dan jikinta yadda yake ai, bana jin ta balaga” “To kasan ni bana son yaran kanana kamar wannan, saboda suna da wuyar sha'ani kuma ba ma aikasu ko ina aiki sai sun balaga sai an koya musu komai dan bana son a rika zuwa ana min complain, dan haka ka fadawa idan sun aminta sai musa Isa yai mata allura anjima” “Iyayenta basa da matsala Hajiya, na fada musu komai kuma sun aminta” “To ba matsala zan yi ma Isa waya sai ya zo yai mata allura, kaita ciki Siyama ta bata abinci” “Wallahi ni ba za a min allura ba wayyo Allah na” Shine kawai abunda Hafsatu manga take fada tana kuka iya karfinta, Hajiyar ko dagowa ba tai ta kalleta ba har ya shige da ita wani dakin. HAMEEDA POV. Tana tsaye jikin window tana tsinkar Sarkin dogarai tsayin da yai a kofar falon Zain da kuma fitowar da Zain yai suka yi magana. Tana ganin ya fito Zain ya koma ciki sai tai sauri juyowa ta baro jikin window ta dauki wayarta ta danna kira. “Hello Isma'il” “Gimbiya kina lafiya” “Lafiya kalau ya aiki?” “Ban ji ka ba har yanzu” “Yau nake da niyar kiranki, maganar ba zata yiyu ta waya ba ya kamata mu hadu gaskiya” “To ka zo gida anjima da dare” “Okay Allah ya kaimu” “Amin” Ta sauke wayar. “Rama cuta ga macuci ibada ne, cutarwar da kika min sai na ninka miki ita Anty Ummi sai nasa an wulakanta...” [3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *HAFSATU MANGA* 30 Yau kwanan Zain biyu be leka inda Anty Ummi ba, wanda a da baya iya zama sai yaje idan ma be wuni can ba da dare sai ya lekata. Ita kuma bata sake kiransa ba, duk wata magana da yai da Juwairriya akan mutumen da aka bawa Hafsatu manga ta gurin Ibrahim amman wai tsakaninsa da Anty Ummi kai tsaye ba. Be taba samman Hafsatu manga ta zauna a ransa sosai ba sai yanzu, duk wani motsi da zai yi tunaninta ne a ransa, ya kasa samun sukuni kamar yadda yake tunanin ita ma bata cikin walwala da jindadi, mafarkinta yake a duk dare mafarkin rayuwar da su kai a asibiti da kuma gidansu Anty Ummi, tunaninta yana tuna masa da Haleema, yana jin kamar ba zai iya rasa Hafsatu ba a yanzu, but wai Haleema matarsa ce kuma yar'uwarsa Hafsatu fa wace irin alakace a tsakaninsu da har yake jinta da muhimmanci a zuciyarsa. “Ga abinci can na gama” A can cikin duniyar tunaninsa ya jiyo muryar Farhat dake risine a gabansa. Idanuwan dake lumshe ya bude ya watsa mata wata muguwar harara, ita kanta yanzu ya tsaneta saboda Anty Ummi. “Sai yaushe za ki saba da daina taya min abincinki?” “Sai ranar daka fahimce minene aure ka dawo ma hanya” Ya sake kallonta da kyau, kamar zai ce wani abu sai kuma ya tashi ya nufi Upstairs, tashi tai ta shiga gabansa tana kallon cikin idonsa. “Kana min yadda kake so Zain, ni ba matarka ce ba baiwar ka ba, amman baka min magana kamar zaman gaba muke da kai a gidan nan, idan har ka bude baki kai min magana sai idan wata maganar ce marar dadi zaka fada min, baka cin abinci ka hana ni shiga dakinka kullum babu annuri a fuskarka kamar an maka mutuwa, dukan abunda nake ina yi ne saboda na samu aljannata kuma na faranta maka amman kai baka gani sai kokarin munana min kake” Ta karasa maganar muryarta na rawa hawaye na sauka a idonta. “Ki adana kukanki domin akwai ranar da zai taimakeki, be kamata ki fara kuka a yanzu ba, ba kin zabi zama da mijinta wata?mijin da soyayyar wata mace ta ginu a zuciyarsa, ta yadda wata mace mai kamala da tarbiya ba zata taba samu gurbi a zuciyarsa ba, balle ke da sai da kika yi aure kika san hanyar neman aljanna, dacan baki san da aljanna ba shiyasa kike barin wasu maza suna ganin surarki? Ba zan taba son ki Farhat duk abunda zaki yi ba zaki burgeni ba, babu abun burgewa gurin macen data yada mutumci a hanya tayi mu'alama da maza kala ciki har da mijin yayarta....!” Yana gama fadar hakan ya ratsa gefenta ya haye sama. Tsaye tai a gurin kamar an dasata, wasu tawayen hawaye suna sauko mata, maganarsa ta daki zuciyarsa ta huda har gadon bayanta, a take duniyarta ta rikice tunaninta ya fara yi mata gudun ruwa, kalaman mahaifiyarta na mata yawo a kwalwalwa. Cike da nauyin jiki ta daga kafarta tana takawa amman sai taji kamar ba takawa take ba, kamar wacce bata da lakka a jikinta haka ta zauna saman cushion ta saka dayan hannunta ta dafe kanta. Ba a taba fada mata magana mai daci marar dadin ji kamar yadda Zain ya fada mata a yanzu ba. Ta dade a gurin zaune tana jin zuciyarta tayi mata wani mugun nauyi har numfashinta na kokuwar subuce mata. Sai da taji ana kiran sallah la'asar sannan ta samu unkurawa ta tashi ta nufi dakinta. Tsayawa tai kallon dakin tana masa kallon kurrillah. “Indai har zan zauna da mijin wata ya fada min magana marar dadi akan matarsa, to ko nafi cancanta dana zauna da mijin yayata yafi dace na fuskanci wannan kalubalen a gurinsa, amman zan koya maka darasi Zain, sai na maka bitar karatun da baka manta” Ta fada tana hade wani abu mai daci daya tsaya mata a makoshi. Kayan dake jikinta ta cire ta shiga bathroom tai wanka, sai da ta zabi lace mai kyau ta saka ta chaba kwalliya, sannan ta sauko downstairs ta zauna saman cushion, ta gabanta Zain ya bi ya wuce hannusa da fuskarsa jike da ruwa da alama alwala yai, ko da wasa bata kalli inda yake ba har ya fice daga falon. Tana jin tashin motarsa ta tashi ta nufi kofar fita daga falon, gabanta ya fadi da farko saboda abunda take son aiwatarta ta ina zata fara? Tsaye tai a bakin kofar tana tunani kamin ta daga saket dinta ta nufi gate din gidan ta tsaya tana kalle kalle. Kamar an turo Abida sai gata da gudu ta zo ta risina gabanta. “Allah ya taimakeki da abunda kika bukata” She act like princess domin ta kusa minti daya zuwa biyu kamin ta amsawa Abida. “Yarima yace a shirya min mota zan fita yanzu” Abida ta dago ta kalleta sai kuma tai saurin maida kanta kasa. “To ranki ya dade” Juyowa tai ta dawo part din gabanta sai faduwa yake, ala ala take kar Zain ya dawota san zata samu damar aiwatar da bukatarta ba. Tana shiga ciki ta dauki mayafi ta rufe kanta sai kuma ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta, ta cikin madubin ta hango Hameeda wacce ta shigo dakin yanzu. “Ina zaki je?” “A iya sanina ke kanwar Zain ce ba yayarsa ba, baki da hurumin tambayar inda zanje balle idan na dawo ki tambayi daga ina nake” “Al'adar masarautar nan ce amarya bata fita sai nan da wata biyar, kuma ina tunanin kina daya daga cikin mutane da basu fahimci fada sosai ba” “Ba ke ya kamata ki min biyar sharudan gidanku ba, wanda ya dace yai miki tuni ya yi aikinsa, kuma da amincewarsa zan fita” Farhat na kaiwa nan ta juyo ta nufi kofar fita, ganin Hameeda na tsaye a gurin yasa ta juyo. “Idan kallon dakin dadi yake min, zan bar miki makulli sai ki rufe min” “Bana daya daga cikin talakawan garin Gusau balle kuma bayi, babu dalilin da zai sa na karbi makulli na rufe miki daki, ban ga abun kallon a dakin ba, ina ganin ke ce bakuwar naira shiyasa aka zuba miki su ki kalla iya kallonki” Tana gama fadar hakan ta fice daga dakin, Farhat ta rufa mata baya. A falo ta samu Abida risine tana fada mata ga motar can an shirya. Gurin da Zain yake aje keys din gidan ta nufa ta dauki ta mika Abida ba tare da tace mata komai ba. Tana gaba Abida na biya harta fita daga falon sannan Abida ta rufe kofar ta mika mata keys din. “Gada biyu” Ta fadawa mutumen dake gaban motar sanye da jajayen kaya na dogarai. “To Ranki ya dade” Tun da ya kama hanyar be tsaya ko ina ba sai gidansu Anty Ummi kamar yadda ta kwatanta masa, shi ya fitoya bude mata motar ta fita. “Ka koma anjima Yarima Zain koma da ni” “To ranki ya dade” Tura kofar gate din tai ta shiga, Malam Adamu yai mata maraba sama sama suka gaisa ta karasa cikin gidan. Bugu daya tai Baba Asabe ta bude mata kofar. “A maraba da Farhat” “Anty Ummi na nan?” “Eh tana ciki bata jindadi” Cikin saurin Farhat ta nufi dakinta, da sallama ta shiga Anty Ummi dake kwance saman gado ta dago ta amsa mata. “Farhat ke ce yanzu?” “Eh Anty bakida lafiya?” “Ee tare da Zain kuke? Aa ni kadai na ke” “Lafiya kalau Anty, wayar da kika min alkwari nake so” Anty Ummi ta tsaya kallonta. Sai ta zauna bakin gadon tana fadin “Anty kadai ce ya dame ni, ina bukatar waya ko dan chat kuma ina son waya da Mamana, i miss my friends” “Nasa an miki welcome back din sim dinki, amman ban siya miki waya ba sai Zain ya yarda” “Ina Sim din yake? Can I borrow your phone” Anty Ummi ta nuna mata inda wayar take, kamin ta sauka daga kan gadon ta bude drawer ta dauko layin ta mika mata. Cikin sauri Farhat ta dauki wayar ta tashi ta fice dga dakin ba tare data karbi layin ba. Ta kusan awa daya a harabar gidan sannan ta dawo ta mikawa Anty Ummi wayarta ta karbi layin. “Na gode Anty Ummi, amman ko karamin wayarki ba zaki bani ba na saka layina?” “Babu abunda zan baki har sai Zain ya amince, ina fatar da izininsa kika zo nan?” “E ya sani ya mace na gaisheki” Ta fada tana dariya kamar gaske. “Amman Anty yau ba zan koma gida ba har sai kin bani labarin alakar wannan Hameeda da Zain” Anty Ummi tayi murmushi tana kallon Baba Asabe wacce ta shigo cikin dakin hankalinta tashe jikinta har rawa yake. “Hajiya wasu...wasu na nemanki...” “Su wa?” Kamin Baba Asabe ta amsa mata sai ga police wajen hudu sun shigo cikin dakin kowanne fuskarsa babu annuri. “Ke ce Balkisu Salisu Fayau?” Anty Ummi ta tsaya kallon wanda ya nuna ta da yatsan cike da tsananin mamaki kamin ta amsa masa. “Ni ce” “You're under arrest, ana zarginki da sace yar mutane....!” Mikewa Anty Ummi tai tsaye cikin wani irin tashi hankali, Farhat kuma ta rufe baki ta zaro ido waje. HAFSATU MANGA POV. A kwana biyu da tai a gidan duk tabi ta rame sai kuka take faman musu komai aka bata sai ta ki ci sai taga dama. Yau ma daker tai wanka saboda kukan da take taki da saba da gidan balle har ta sake duk kuwa da kasancewar akwai yara a gidan. Kayan data zo da su sune a jikinta kullum, yau ma bayan ta yi wanka ta sake saka kayan ta zo falo ta zauna. “Ba zama zaki yi, tashi ku tafi” Ta lake kafada alamar ita bata son zuwa. “Tashi ko na saka a dakeki yanzu nan” Hajiyar ta daka mata tsawa, sai kawai ta fashe da kuka ta tashi taje gurin wata dattijiwar dake jiranta suje tare. Sai da suka taba yar fira da Hajiyar sannan ta tashi tare da kama hannun Hafsatu manga suka fice. Tana isa bakin titi ta tari Napep suka hau basu zame ko ina ba sai 88 estate. A bakin gate Mai napep din ya sauke su saboda ba a bari masu Napep ko a achaba su shiga ciki, da kafa suka taka har 54 block, a bakin kofar ta tsaya ta danna bell. Wata kyaukawar mace ce ta bude kofar gidan, fuskarta ba yabo ba fallasa ta shigarda idanuwanta can ciki kamar bata son kallon mutane. “Oh ke ce” Tana fadar hakan, sai matar dake rike da Hafsatu manga ta washe hakora. “Ee ni ce Hajiya ya gida?” “Lafiya kalau, shigo” Ta fada tana wangale mata kofar falon. Cikin falon suka shiga daga ita har Hafsatu manga kasa suka zauna, sama sama take amsa gaisuwar da Matar take mata kamin ta kalli Hafsatu manga. “Wannan ce yarinyar?” “Ee ita ce ke gaisheta” Hafsatu ta sakar mata ido kawai tana kallonta ba tare data gaisheta ba. “Dee ga yarinyar” Wanda matar ta kira da Dee ya dago kansa daga kan computersa jiyo ya kalli inda suke zaune, karaf idonsa suka sauka kan Hafsatu manga wacce itama kallonsa take. Kara dagowa yai da kyau dan tantance abunda idanuwansa suke gani, tasowa yai ya dawo kusa da matarsa ya zauna yana cigaba da kallon Hafsatu manga, awarwaron da ya gani a hannunta ne ya tabbatar masa da ita din ce. “Ita ce yarinyar da zata dan taya ni aiki” “Okay ai kun gama magana ko” “Ee 15000 per month” “Yayi kyau, Allah ya bamu ikon riketa da amana” “Amin amin Allah ya taimaka alhaji, ke kuma ban da rashin ji ban da shegen kukan nan da kike” Hafsatu manga ta lake kafada kamar ba data ita matar ke magana ba, Sai yai murmushi Hafsatu na kallonta ya kashe mata ido daya. [3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *HAFSATU MANGA* 29 Yana zaune a gurin a kai yi knocked kofa, be dago ba be kuma motsa daga inda yake ba mai knocked din kuma be fasa ba, har sai da Farhat dake dakinta ta fito ta nufi kofar ta bude. Ganin Anty Ummi yasa ta murmushi ta rumgume irin tayi missing dinta sosai din nan. “Sannu da zuwa Anty” “Yauwa Amarya” Zain be dago kansa ba har Anty Ummi ta shigo cikin falon ta zauna kusa da shi tana kallonsa zuciyarta cike da tsoro. “Zain” A maimakon ya amsa mata sai kawai ya tashi ya dauki wayarsa da keys dinsa ya fice daga falon. Da kallo ta bishi har ya fice sannan ta maida dubanta gurin Farhat tana sauke ajiyar zuciya. “Idonki ya kumbura Farhat kuka kika yi?” Farhat ta dan kawar da idonta. “Ina jin kamar ba zan iya zama a gida nan ba, baki da hankali, useless, karki sake shigo min daki, kalmomi ne masu daci da Zain ya fada min a tsakanin jiya da yau” Anty Ummi ta bar kujerar da take zaune ta koma kusa da Farhat ta zauna ta kama hannunta ta rike. “Haka naji lokaci da mahaifiyarmu ta tafi ta barmu, nauyin komai sai ya koma a kaina, you know aurena na farin ban taba son mijina ba, sai abun ya zame min biyu babu t inda zan jidadi” Farhat ta dago ta kalleta idonta cike da kwalla. “Amman wannan yana da banbanci Anty, bana son shi shima baya so na, amman ina kokarin danna nawa na masa biyaya, sai dai komai na masa kamar bana burgeshi, a dayan bangaren kuma ga wadannan yan'uwan nasa da basa so na, bana son kashe aurena a yanzu saboda za a min dariya, mahaifiyata kuma ba zata karbeni a yanzu ba” “I know how my brother is, amman mutum ne mai sauki kai da hakuri, be kamata ki fara complain tun yanzu, aure ba kika yi kin shiga wata sabuwar rayuwa kuma wata sabuwar ibada wacce sai kin yi da gaske tukuna zaki iya yakar zuciyarki akan abubuwa da dama” “I know Anty, zan yi kokari na danna zuciyata ko dan hakan na nufin na cutar da kai ne, gudun kar na baki kunya, amman Anty minene alakar Zain da Hameeda? Miyasa wannan tsohuwar Dada bata son Zain? A yadda na fahimta kamar dukansu basa son shi” Ta fada tana share hawayen idonta. “Na gode, zan sanar miki amman ba yanzu ba, yanzu ina son ki fada min abunda kike bukata” “Ina da bukatar jin muryar Mahaifiyata, ina son wayata a kusa da ni” “Akwai sim Pack a hannunki? Zan sa a miki welcome sai na siya miki sabuwar waya” “Eh yana hannuna, amman Anty miyasa Zain yake fushi da ke? Ko duk saboda aurena ne?” “Ba saboda ke ba ne, saboda wani abun ne na daban, zan koma tashi ki dauko min pack din” Ba musu ta tashi taje ta dauko ta dankawa Anty Ummi sannan Anty Ummi ta tashi ta fice cikin yanayin damuwa, daga part din Zain part din Hajiya Hadiza ta shiga suka gaisa, daman ta saba a lokacin da Haleema take cikin gidan idan ta zo sai ta biyo ta gaishe da Mai Martaba da Hajiya Hadiza sannan ta wuce. Fita yai daga gidan gaba daya, ba shi tabbacin tsanar Anty Ummi yai ko aa sai dai yana da tabbacin baya son ganinta ko magana da ita a yanzu. Tunani biyu yake zuwa masa a lokacin daya, taya zai bar wannan abun daya faru ya shiga tsakaninsa da Anty his own sister macen daya ke daukarta kamar mahaifiyarsa, what if mahaifiyarsa tana raye tai Hafsatu manga haka zai iya fushi da ita kuwa? Wannan abun yake ta tunani, while zuciyarsa already ta tsani Anty Ummi a yanzu? “To mi tazo ta fada min? Mi zata ce min? Dama na tsaya naji selfishness dinta” Ya fada dai dai lokacin daya faka motarsa a harabar asibitin, wayarsa tai ringing yana dubawa yaga Anty Ummi, sai ya maida wayar cikin aljihunsa. Ya fita ya nufi office dinsa, wayarsa ta sake ringing a karo na biyu bayan shigowarwa cikin asibitin sai dai wannan karon ba Anty Ummi ba ce Ibrahim ne. “What” “Kana ina” “Office” “Okay gani nan zuwa” Zain ya maida wayar aljihunsa sannan ya kai hannunsa ya tura kofar office din ya shiga, saman kujerarsa ya zauna ya lumshe ido yana juyawa a hankali. Kamar an tsikareta shi sai kuma ya tashi da sauri, tashinsa yayi daidai da shigowar Ibrahim a office din. “Ina zaka je?” “I was thinking of mu saka cigiyarta a gidan redio” “Matsayinka na wa?” Ya kasa amsa masa. “Baka da tabbacin inda yarinyar nan take Zain, maybe ma bata cikin garin nan abunda nake ganin yafi ka kawarda fushin dake cikin ranka ka fuskanci Anty Ummi kui magana ko zaka samu wani bayani ta yadda zaka ganota” Hannayensa ya zuba cikin aljihu ya nufi window office. “Duk inda yarinyar nan take Ibrahim tana cikin damuwa yanzu haka, jikina na bani yanzu tana can tana ihu wata kila wani abun ake mata” “No no bafa matarka ba ce, kuma ba yar'uwarka ba ce kana daukar abun nan da girma Zain, ni a ganina be kamata akan yarinyar da baka sani ba ka bata da Anty Ummi har kake kokarin jefa kanka cikin wani hali” “Ina son yarinyar nan Ibrahim fiye da tunaninka, ina jinta kamar wani bangare na jikina ta shiga cikin raina ta zauna irin zaman da ko nuninta akai raina ba ci yake, karamar yarinya ce wacce bata san komai ba, ina jin kamar ba zan taba samun sukuni ba idan har ban gano inda yarinyar nan take ba, duk halin da take ciki a yanzu saboda ni ne ta shiga” “Ba saboda kai bane, karka dorawa kanka laifi, yanzu zanje nai magana da Anty ko zamu samu wani abu daga gareta” “Thank you” Zain ya fada murya can kasa alamar mood dinsa ya canja. Suna tsaye Doc Hafsat ta shigo bayan ta yi knocked tana rike da wasu files. “Good morning Doc ga files din friday” “Aje kan tebur” Ya fada ba tare daya kalleta ba. “Wai Doc ta ina takwata ta a miss her” Wannan karon Doc Ibrahim take kallo. “Bata nan” “Bacewa tai?” Kasa amsa masa da Ibrahim yai ne yasa tace “Daman na san za a rina, Allah kadai yasan iya duniyar da yarinya zata tafi...” Zain ya juyo ya kalleta. “What do you mean?” Kasa cewa komai tai sai kallon tsoro take masa. “Talk” “I mean saboda bata jin magana” Doc Ibrahim ya daga mata hannu. “Okay just go” Bayan ta fice Zain ya kalli Ibrahim “Kasan wani abu ni fa ban yarda da yarinyar ba and...” “And what Zain? Sai kuma ya biyo ta gurin Anty Ummi? Ka manta ta hanyarta ne yarinyar ta bata” Ibrahim ya dafa shi. “Calm down Zain, haba dai kana kokarin wani hali da ban sanka da shi ba” Zain ya ture masa hannunsa ya nufi kofar fita, da kallo kawai Ibrahim ya bishi har ya fice sannan ya girgiza kai. HAFSATU MANGA POV. Bata cin abinci da aka bata ba, kuka tai ta yi har garin Allah ya waye, da safe aka tarasu tare da wasu yara wadanda suka darata girma aka raba musu abun kari mai kyau. Amman Hafsatu manga bata ci ba babu abunda take kira sai Mamanta, hankalinta be kara tashi ba sai da likitan da zai mata allura ya zo a gaban idonta akai ma wasu yaran allura, ana kawo gareta ta rika ihu kamar za a cire mata rai, sai da mutum biyu suka riketa sannan aka mata allurar. Hajiyar na tsaye tana kallon abunda yake faruwa, tun jiya ta soma tsarguwa da sha'anin Hafsatu manga saboda kuka da take tayi tun jiya. “Ina jin yarinyar nan kamar ba da son ranta aka kawo ta nan ba, kukan nan da take yayi yawa ni bana son kuka Wallahi” “Waya kawo miki ita Hajiya” “Wallahi wani daga cikin masu kawo mana yan aiki, shiyasa bana son amsar irin yaran nan a hannun namiji saboda ba a gane gaskiyarsu” “Haka ne, amman ai data saba Shinkenan” “Amman kamin ta saba din ai aiki ne, ina ganin replacement din ta za ayi da Hindatu, akai gurin wanda mu kai maganar da shi daman ya ce Hindatu tayi masa girma, sai a bashi wannan yarinyar mu huta” “Haka ya dace, amman kuma an mata allurar yanzu idan kika kaita, ai bata san komai ba” “Idan ta fara can suka ji ba zasu iya ba su dawo da ita, sai ta karasa a nan, ni bana son kuka so kadan” Likitan ya yi dariya. Haka yabi yara yana ta musu allura wasu ta biyu wasu kuma ta uku har ta hudu ma, bayan ya gama ta kirga kudinsa ta mika masa. HAMEEDA POV. Kamar yadda Isma'il yai mata alkawarin zuwa dare sai gashi ya zo, sai yau ba inda suka saba tsayuwa ta tsaya da shi ba, sai ta koma da shi can wani bangaren na gidan inda ba kasafai ake sauke baki a can ba. Bayan sun zauna ya mika mata wayarta. “Kin ga hoton yarinyar, Doc Hafsat ta fada min cewar ba a san inda iyayenta suke ba, rikon da Zain ya bata na yarinyar sai da ya roki karta fadawa kowa, daga lokacin da yaji labarin Yayanta Dsp ne sai ya dauke yarinyar daga gidan ya maida ita gidan yayarsa wacce daman can a bakin gida ya tsinta kamar yadda Doc Ibrahim ya fada mata” “Karamar yarinya ce balle na ce Zain son ta yake, amman har ga Allah ina kishin abunda Zain yake so” “So ba shi da kankanta Hameeda, zai iya yayuwa Zain sonta yake, idan har ba son ta yake ba, miyasa zai damu da ita har haka?” “Ka daina zigani da yawa Isma'il ka san ina son Zain sosai” “Gaskiya nake fada miki” “Ina tunanin yarinyar nan tana gidan Anty Ummi ko? So yanzu ina za a samu iyayenta?” “Samun iyayenta abu ne mai wahala gurin yarinyar da ba a san inda ta fito ba, ance yarinyar yar kauye ce kauyen Kufawa kuma ana zargin an kashe kowa nata, Hafsat ta fada min Yayanta yafi zargin sata to Zain yai yi” “Babu abunda zai sa Zain ya sato karamar yarinya kamar wannan, amman les assume wannan bakar Ummi ce ta sato ta” “Taya?” “Nima ban sani ba, amman ina son ka kara bincike ka tabbatar yarinyar nan bata iyaye a kusa sannan kuma ina son ka bincika idan tana gidan Anty Ummi yanzu haka” Ta mika masa atm din dake hannunta. “Akwai 500k a ciki, zasu isheka kudin transport” “Ki tabbatar wannan abun da zaki yi be shafe ni ba, kar ki sake ko sunana ya fito ciki” “Baka da matsala” Daga haka ya tashi ta zakoshi har gurin motarsa sai da ya shiga sannan ta dawo ciki gida, part din Dada ta nufa tana shiga ta samu Zain zaune sama kujera ya lumshe ido kansa a sama kamar mai bachi. “Sannu Yarima” Be amsa ta ba, be kuma bude idonsa ya kalleta ba har ta shige dakin Dada sannan ya tashi ya fice daga falon. [3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *HAFSATU MANGA* 31 HAMEEDA POV. Farhat na fita Hameeda ta koma dakinta, ta kira Abida waya ta sanar mata tana nan ciki tana jiranta, kamin abida ta shigo dakin ta bude handbag dinta ta dauko wani rubutu a gora rike a hannunta, fitarta ta mata dadi daman tana neman hanyar da zata saka zuba mata wannan rubutun. Abida na shigowa ta mika mata. “Je ki zuba mata a kofar shiga falonta, kuma ki tabbatar ko ina ya samu” Cikin yanayin damuwa Abida ta kalleta “Ranki ya dade idan kuma wani ya ganni fa?” “Babu wanda zai ganki, wai Abida mi yasa kika yi sanyi ne? Sai kace bake ba, a abaya fa ke kike nuna min wata hayar amman yanzu kina zame jiki kamar kina munafuntata, ko dai so kike na cigaba da zama a haka? Na bar mutane da suka cuceni  su ci bulus? Baki son farincikina ne?” “Allah ya taimaki Shugabata, nafi kowa farinciki da farincikiki, amman ina tsorona abunda zai biyo baya, kin ga ni bani da gata a masarautar matukar aka kamani da laifi Zain ba zai taba yafe min ba” “Ki kwantar da hankalinki babu abunda zai faru, idan har na rasa abu to ya kamata kowa ma ya rasa shi, tun har sun fara min wani kallo na daban, ya kamata na nuna musu ko wacece ni” Abida tasa hannu biyu ta karba. “To ranki ya dade” Tashi tai ta fice daga dakin bayan ta rufe rubutun cikin zanenta. Wata number Hameeda ta nemo ta aika mata sako. _Fauziya gani nan zuwa_ Hijabinta ta dauka ta saka sannan ta dauki makullin dakinta ta rufe dakin, ta sauka kasa ta nufi sashensa Dada kasancewar ita part dinta a kasa yake. “Assalamu Alaikum” “Amin Wa'alaikussalam, Hameeda” “Na'am Dada sannu da hutawa” “Yauwa fita zaki yi?” “Ee gidansu Fauziya zanje, na ce ko kina da masaniyar Farhat ta fita?” Dada ta kalleta da sauri. “Wace Farhat?” “Farhat dai, dazun nan ta fita ita kadai, babu yadda zan yi ba na tsayar da ita, amman sai ta rika fada min magana marar dadi” “Ita Farhat din?” “Ee ita fa” “Waya bata izinin fita?” “Nima ban sani ba, amman in ba Zain ba wa zai bata?  Yau dai anyi abunda ba a taba yi ba a gidan nan, ni dai na fita” Dada ta dauki wayarta ciki da bacin rai ta kira number Zain... “Saboda mai zaka bawa Matarka izinin fita bayan kasan mace bata fita a gidan nan sai tayi wata biyar, Haleema ma watan ta nawa kamin ta fita” Yana picking Call ta fada masa haka, shiru yai yana nazari, shi dai be san ya ce Farhat ta fita ba. “Ko baka jina?” “Wadannan dokokin Dada Farhat ba zata iya binsu ba, zamani ya canja babu amaryar da zata iya zama a wadannan watannin ba tare data fita ba” “O kai kai nata izinin fitar kenan” “Idan ban bata ba ai ba zata fita ba” “To yayi kyau bari Mai Martaba ya dawo” Sai Zain ya saka mata dariya. “Haba dai uwargida miyasa kike haka ne? Komai akai da wanda ya kai da wanda be kai ba ki dauka ki kaiwa Mai Martaba, gaskiya wannan kishin naki ya yi yawa” “Ba wani kishi yarinyar nan ta malleka mal, komai tai maka baka iya cewa komai” “Ba wani mallaka tsananin biyayyace kawai, ba fa nesa taje ba gidan Anty Ummi ta tafi” Taja tsaki ta kashe wayar, shi kuma yasa dariya. Ba shi tabbacin inda taje amman ya san ba zata wuce gidansu Anty Ummi ba, idan kuma har ba can taje ba to ina taje...? “Wannan yarinyar banza yarinyar ce” Ya sauka daga saman motar dake zaune ya bude ya shiga, ya dauki hanyar gidansu Anty Ummi. ANTY UMMI POV. Zain mutumen daya fara zuwa mata a rai, domin shine kadai mutumen da ta san zai iya komai akan Hafsatu manga, amman anya Zain zai iya ci mata mutunci har haka? Taya zai iya runtse ido ya yarda a wulakanta police ya shigo mata har cikin dakinta? Idan kuma yan uwan Hafsatu ne ko iyayenta taya aka yi suka san ta yi zama gida? Waya fada musu gidan? A take tambayoyin suka zo mata, bata samu amsar tambaya ko daya ba, daya daga cikin police din wacce ta kasance mace taje ta rika kafadarta. Tashi tai ta nufi inda Hijab dinta yake ta dauka ta saka, sannan suka sakota gaba kamar wacce tai kisan kai. Gurin motarsu suka nufa da ita sai ta tsaya ta ki shiga. “Ku min alfama mana na shiga motata tare da police biyu” “Ba za a miki wannan ba” “To bari na shiga motata” Bata gama rufe baki ba, daya daga cikinsu ya sauke mata mari a fuska, kana ganinsu kasan babu wasa a tare da su, da alama an fada musu karsu sassauta mata ne. “Akan me zaka daga hannunka ka mareni? Kasan abunda ka aikata kuwa? Kana da uniform amman baka san dokokin kasa ba? Babu dokar da tace a dake ni, ko da an tabbatar da laifin balle zargi kuke yi, i know my right no one can humiliate me” Ta fada cikin fada, tun da take a rayuwarta ba a taba wulakantata kamar haka ba, mutumen kamar jiranta yake sai ya tisa keyarta da karfi cikin motar, bata tsaya tirjiya ba, gudun kar su sake wulakantata. Farhat da Baba Asabe na tsaye jikin kofar falon suna kuka har suka wuce da Anty Ummi, Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un kawai Malam Adamu ke fadi, kamin ya dauko wayarsa ya kira Alhaji Masa'ud wato mijin Anty Ummi ya sanar masa. Sai da Farhat ta kama hanyar fita daga gidan Anty Ummi ta tuna da Zain be san da fitarta ba, ya zata tayi yanzu ta koma gida? A dayan bangaren kuma tana tsoron haduwa da Ya Bashir saboda unguwarsa ce ga shi kuma gidansa baya da tazara sosai tsakaninsa da na Anty Ummi. Cikinta ta soma jin yana murda mata kamar yadda yai mata a daren farko, a haka ta daure ta kama hanyar titi ba dan ta san abun yi ba, wasa wasa cikin ya fara motsa mata sosai har ta soma kasa magana, risinawa tai kasa ta rike cikin bakinta na cika da jini. Babu mutane sosai a gurin amman hakan be hana daidaikun motoci da kuma mutanen dake kai da kawo kallonta ba. Wani Mai napep ne ya faka kusa da ita “Malama lafiya” Tana dago kai tai ta kalleshi, sai da ta tofar da yawun bakinta sannan ta ce “Ba komai” “Ba komai naga jini a bakin ki?” Kokarin mikewa take tsaye, sai amai ya cika mata baki, a take ta fara kwarara aman jini a gurin tana wani numfashi kamar ranta zai fita. “Sannu” Ya fada yana yana fitowa daga Napep din, a nan mutane suka fara tsayawa ana kallonta. “Dan Allah kai ni gidan can” Cikin sauri ya koma cikin Napep din matar dake bayan Napep din ta matsa mata ta shiga ko ba komai Zain zai je ya dauketa a gidan kuma ba zata iya tsayawa a hanya ta na aman jini ba, impact bata san abunda ke damunta ba, this is the second time da tai aman jinin bayan wanda tai a darenta na farko, tana bukatar zuwa asibiti. Kamin su isa kofar gidan Anty Ummi Farhat duk ta bata masa Napep da jini ta wahala sosai kamar a darenta na farko, duk wanda ya ganta a haka sai ya tausaya mata, har cikin gidan ya shiga da ita bayan Malam Adamu ya bude masa gate ganin halin da take ciki, a harabar gidan ya tsaya da Napep, matar dake baya ta rika Farhat tana ta fito da Farhat da tufafin jikinta suka gama lalacewa, tafiyar take tana rangaji matar na rike da ita har ta zaunar da ita bakin kofar tana mata sannu. Malam Adamu yazo yana tambayar ba'asi sai mai Napep din ya fada masa, suna tsaye gurin motar Zain ta kunno kai cikin gidan. Kusa da inda suke tsaye ya faka motar ya fito yana kallonta, ita kuma taki ta daga kai ta kalleshi. “Miya faru” Mai napep din ya fada masa a halin daya sameta da kuma inda ya dauko ta, Malam Adamu ya kara da nasa yana fadar lafiya kalau ta bar gidan. Hannunsa yasa ya rikota “Taso muje” Cikin gidan ya shiga da ita, mai napep din ya wuce. Baba Asabe suka samu zaune a kasa tana kuka. “Lafiya Baba Assabe?” “Hajiya aka kama yanzu nan polisawa suka shigo suka kamashi” “Saboda mi?” “Naji dai suna cewa wai ana zarginta da satar yarinya” Hafsatu manga ce ta fado masa a rai, domin ita kadai ce yarinyar da Anty Ummi ta rika, amman su wa suka saka a kamata? Hannunsa daya yasa ya sake rikata ya shiga da ita bedroom din Anty Ummi har cikin toilet ya sakata. “Cire kayan jikinki” Yaja mata kofar toilet din, wardrobe Anty Ummi ya nufa ya bude ya dauko mata gown, ta kusan minti talati a bandaki har sai da ya unkura zai shiga sannan ta bude ta dauko leko kanta. “Bani riga” Dauka yai ya jefa mata, ta koma ciki ta saka sannan ya fito ta dauki mayafin Anty Ummi ta saka, sannan suka fito tare. Tun da suka kamo hanya be ce mata komai ba, itama bata kalli inda yake ba. A kofar gate din gidansu ya faka motarsa, sai ta bude ta fita sai gata ta zube kasa ba karfi. Bude gefensa yai ya fito ya rikata ya shiga da ita ciki falon ya zaunar da ita saman kujera. Tayi expecting zai yi mata nagabar dalilin fitarta ba tare da izininsa, sai taga kawai ya juya ya fita ba tare daya ce da ita komai ba. HAFSATU MANGA POV. “Miye alakarku da wannan yarinyar?” Ya tambayi matar dake tare da Hafsatu manga, “Ni ba kowa ba ce a gareta, amman kanwar mahaifinta ta bani ita akan a sama mata aiki, kwanaki na kawo Hindatu sai Hajiya ta ce ta mata girma shine aka ce bari a kawo mata wannan, amman tukuna bata balaga ba an dai mata allura?” “Allurar mai?” Wannan karon Zainab ce ta tambaya. “Idan an kawo mana wadanda basu balaga ba, Hajiya tana sa ayi musu allura da zaisa jikinsu ya inganta suyi saurin girma saboda Mutane suna fada cewar yara idan sun balaga a gidansu suna musu kazanta wasu ma basu san yadda zasu kula da kansu ba” “Amman baya cutar da su?” Tayi yar dariya. “Baya musu komai, ai likita ne ma yake musu alluran, sai dai ita Manga daya aka mata, sai an kwana biyu sai a kara mata wata” “Okay” Dsp Auwal ya fada sannan ya tashi yana amsa waya. Zainab kuma ta tashi ta shiga ciki ta dauko mata two thousand ta bata na hawan Napep matar ta karba tana da murna da godiya. Tana tashi tsaye Hafsatu manga ta tashi tsaye zata bita sai ta daka mata tsawa. “Ke zauna, ba aiki aka kawo ki ba, Hajiya nuna mata aikin da zata yi” Komawa tai ta zauna tana kuka. “Je ki gyara Kitchen kamin na tashi sai ki zo ki gyara falon” “Tashi aka ce” Matar ta sake daka mata tsawa, da sauri Hafsatu manga ta tashi da sauri ta nufi inda Zainab ta nuna mata tana kuka. Tana shiga ta zauna jikin freezer ta kara fashewa da kuka. Sai da matar ta wuce sannan Zainab ta tashi ta nufi dakinta ta bar Dsp a dayan bangaren yana amsa waya, bayan ya gama ya nufi kitchen domin ya lura da lokacin da aka wuce da Hafsatu manga. “Hafsat” Sai ta dago ta kalleshi cikin kukan. “Minene? Kin ganeni?” Ta gyada masa kai tana sharar kwalla. Zaunawa yai kasa kusa da ita ya dauketa ta dora saman kafafunsa. “Fada min ya aka yi kika zo nan?” “Wannan Anty Ummi ce ta dauke ni ta ba wani ni, ya saka ni cikin mota ya tafi da wani can wani gari ya bani wani abu na sha nai bachi, da na farka ya sake bani na sake bachi, sai ya kawo ni gurin wata mata katuwa mai gilashi tasa aka min allura, sai kuma suka kawo ni nan” Ta fada cikin muryar kuka tana murza idon, hannunsa yasa yana share mata hawaye. “Wannan matar kin santa?” “Aa ni ban santa ba, kuma karya take da tace kanwar Baba ta bada ni karya take, wannan Anty Ummi ce ta bata ni” “Wacece Anty Ummi?” “Wannan muguwar matar, yayar Uncle” “Wane Uncle?” “Zat” “Hafsat ba baki magana ba? Ya akai yanzu kike magana” Ya fada yana saka hannunsa cikin bakinta yana duba halshenta. “Nima dai kawai naga ina magana” A yadda take maganar yanzu kamar ba ita ce ke kukan ba. Yayi dariya yana jan kumatunta. “Zaki iya gane iyayen?” Ta gyada kai “Kin san garinku?” “Kufawa, amman bana ganewa amman garin an kashe kowa, kuma mutanen suna nan” “Sato ki Zain yai ko?” Tayi shiru kamar mai tunani. “Aa ni ina sonsa wannan matar ce bana so” Murmushi yai ya tasheta tsaye. “Tashi mu gyara kitchen” “Ni ban iya ba” “Zan koya miki” Ya fada with smile on his face. “Dauko ga tsinsiya can ki share sai nai mopping” “In mun gama zaka kai ni gida?” Yayi kamar be jita ba, ya fiddo wayarsa daga aljihu ya nemo number Hafsat tare da danna mata kira. “Hello Dsp” “Doc kina lafiya” “Kalau ya Anty Zee” “Lafiya kalau, kina da wani labari akan yarinyar nan da aka taba kawo miki wacce mata magana mai sunanki?” “Aa gaskiya tun da ya dauketa ban sake ganinta, kwanaki dai akwai wata cousin dinsa data zo gidan tana ta tambaya labarinta, kuma naji ance ta bata” “A gurin wa kika ji” “Gurin aminsa, kasan she's my fiance, to kwanaki da hankalinsa ba kwance ba na masa nagana sai ya fada min” “Amman miyasa cousin din take neman yarinyar?” “Nima ban sani ba, amman ta zo tana ta min bincike a nan naji yarinyar ma a hannun yayarsa take” “Sai da yarinyar nan suka yi” “Saidawa kuma? How do you know?” “Gata nan a tare da ni, an kawo ta ga aiki” “What” “Yes lokacin da na ce zan yi bincike akan maganar ai ke da Momy hana ni kuka yi” “Yeah kaga ai be dace ba, ni zai ga laifina kuma babban gida kamar wannan be kamata ace ka shiga ciki bincike ba” “Ya ci arziki bana garin gusau a yanzu, amman haka ba zai hana na bincike shi ba” “Amman dan Allah kar sunana ya fito ciki” “Idan babu hannunki a ciki ai sunanki ba zai fito ba” “Babu hannuna a ciki, amman Dps ka san Farhat tayi aure?” “What? How do you know” “Ni ma dazu naga tayi posting a fb, kasan tana cikin friendslist dina” Wani irin sarawa kansa yai, har ga Allah be ji dadin maganar ba. “Amman kin tabbata?” “Wallahi ita tai posting, bana tunanin kuma hacking din account dinta akai” “Wata aura?” “Allah ya mata sakamako, a yadda ta rubuta inda ba karya take ba, Doc Zain ne kasan kuma ya fika komai, kai baka ga post din ba?” “Ban hau fb ba yau, Doc Zain da muke magana akansa yanzu?” “Yes shi, amman ni kaina ban san da yayi wani auren ba bayan rasuwar matarsa, sai dai kuma bana tunanin ita zata yi karya da shi” “Bad news” Ya kashe wayar, zuwa yai ya dafa kitchen cabinet yana maida numfashi da karfi, sam sam sam maganar bata masa dadi ba, har ga Allah yana son Farhat kuma yana da kudirin aurenta, he was planning idan sun yi one year da Zainab zai gabatar da Farhat da mahaifinsa ya san a lokacin ba zai ki karba masa bukatarsa. But jin wannan labarin ya karyar masa da zuciya. A take ya kunna datarsa ya shiga Fb, sunanta yai searching ta shiga duba timeline dinta, post din ya fara yin karo da shi. _May the love we express to each other on 10th, always be the first thoughts during any trying times in the future. Finally I'm Mrs Zain Ibrahim Tukur Dan-maliki_ *Got married today* Haka facebook suka rubuta bayan dan guduntun rubutun da Farhat tai, he feel so hopeless, so shame, so disgrace. Sai a yanzu ya tabbatar da abunda yai mata rashin kyautawa ne, he remember all the good memories they spent together. “Na gama sharar” Kallon Hafsatu manga yai amman ba fuskarta yake gani ba, jinsa ne kawai a tare da shi amman tunanisa yana can wata uwa duniyar. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya sake kallonta da kyau. “Minene?” “Na gama sharar” “Okay je ki dauko mopper gata can” Zuwa tai ta dauko mopper ta mika masa. “Amman zaka maidani gurin Uncle ko?” “Baki son zama nan ne?” “Ka san kai dan sanda ne, kuma ni nafi son Uncle na ji yace zai kaini inda Mamana” “Karya yake miki, gashi ya siyar da ke an kai masa kudi” Sai ta bata fuska kamar zata yi kuka. “Ina mamana?” “Nima ban san inda take ba, amman zan bincika ta, karki yi kuka kinji?” Ta gyada kai hawaye nata sauka a idonta, duk yadda tai kokarin danna kukanta sai ta kasa har sai da ta fasashi, daukarta yai sama ya dorata saman kafadarsa yana jijjigata. “Shiiiiiiiiiiii” Saman karamin dinning da ke gurin ya zauna yana rumgume da ita, yana sauraren yadda zuciyarsa take mugun bugawa. [3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *HAFSATU MANGA* 32 Suna zuwa state cid sa ita saka sakata cell cikin wasu karuwan mata dake gurin.   Bata wuce awa daya a gurin ba, wani police ta zo ya fito da ita ya shiga da ita wani daki da babu kowa a ciki sai kujeru da tebura, gurin zama police din ya nuna mata, tana zaunawa sai ga wasu yan sanda biyu sun shigo dayan na rike da abun rubutu. Kujerar dake facing din nata ya zauna yana kallonta fuskarsa ba yabo ba fallasa. “Madam zamu dauki statement dinki, dukan abunda zaki fada zamu amfani da shi a gaban kotu” Anty Ummi bata ce komai ba, mutumen dake rike da littafin ya bude ya dora alkalaminsa saman littafin yana jiran ta fara magana ya fara rubutawa. “Section...... Under.... A karkashin dokar Nigeria ana zarginki da satar yarinyar mutane” “Ni ban sace yar kowa ba, taimakonta kawai nai, ita da kanta ta kawo kanka kofar gidana tana neman taimakona, I just help her bayan shi babu wani abu” “Amman mutum zai shigo gidanka haka nan kawai ka taimaka masa ba tare da kasan miye yake tafe da wannan mutumen ba? Ki fada mana gaskiya ko kuma nasa a wulakanta ki a gurin nan” “Babu dokar da tace a dake ni ko a wulakanta ni, zargina kuke yi dukan abunda zaku min nima zan nemi hakki a wani gurin” “Oh wato har kina da bakin magana ko? Sajan” Wanda aka kira da sajan din ya amsa da sauri “Sir” Kamin ya bashi umarnin da zai bashi sai ga Dcp Faruk ya shigo, da sauri suka tashi tsaye suka tsare masa. “A fito da matar nan ka kawo ta Office dina” “Yes Sir” Yana juyawa suka saka Anty Ummi a gaba zuwa office dinsa, fita suka yi suka barta daga ita sai Dcp sai kuma mijinta Alhaji Masa'ud. “Hajiya ayi hakuri da abunda ya faru, amman abunda ake zarginki da shi case ne mai girma, wanda dole ne mu yi bincike, wadanda suka shigar da karar suna zarginki da sace musu ya, kuma ina tunanin a matsayinki na mai aiki da kare hakkin dan adam ko da ba ke ake zargi ba, zaki iya tsaya musu wajen ganin komai ya tafi daidai” “Yanzu dai ba wannan ba, ni dai abunda nake so a bani belin matata in yaso duk abunda zai biyo baya sai ya biyo” “Gaskiya ba zai yiyu a bada belinta ba, a halin yanzu haka babu wani bincike da muka yi, yanzu ma saboda Alhaji Salisu Fayau ne yasa na fito maka da ita” “Amman kun bincika kun gane iyayen yarinyar ne? Domin yarinyar yar gudun hijirace an kashe iyayenta, wannan dalilin ne yasa na taimake ta” “Baki da wata hujja ta rike yarinya karama a hannunki kuma kice taimakonta kike son yi, miyasa lokacin da kika riketa baki zo hukumar yan sanda kin sanarba saboda gudun irin wannan? Yanzu ni abunda nake so ki fada min ina yarinyar take?” “Na bada yarinyar a kaita kauyensu, wa kika ba ya kaita? Tare da wa kuka je?” “Ban san mutumen ba, wata kawata ta hadani da shi, yace min shi dan kauyen Kufawa ne kuma ya san gidansu yarinyar, shiyasa na hadusu ya kaita” “Kin tabbata? Zamu bincika ina fatar dai gaskiya kike fada mana, domin wannan ba magana ceda hankali zai dauka ba, gurin wa kika ce a kai yarinyar?” “Gurin Sarkin gari” Telephone Dcp ya dauka ya danna kira. “Zo yanzu nan” Ko minti biyu be yi da aje wayar ba, sai ga wani police ya shigo tare da sare masa. “A saka kofur Illiyas yaje Kauye kufawa ya bincika mana idan an kawo yarinyar mai suna Hafsatu manga, kai kuma ka shigo mana da iyayenta yanzu” “Yes Sir” Yana fita sai ga wasu tsofin fulani mace da namiji sun shigo dakin macen jikinta sai rawa yake namijin ne kawai yake da juriya, shi ya zauna saman a Cushion dake can gefe, ita kuma mace ta zauna kasa jikinta na rawa kamar mazari. “Kune iyayen yarinyar nan Hafsatu manga” “Mune Ranka ya dade” “Ina hoton yarinyar yake?” Namijin ya mika masa hotun dake hannunsa. Anty Ummi ta mika hannu ta karbi hoton tana dubawa, Hafsatu manga ce zaune saman manyan kujera na alfarma, ba zata iya gane ina ne amman tana gani tasan ba a kauye ba, wani abun mamaki kuma tufafin dake jikinta tufafi ne masu tsada a jikinta. Phone din dake hannun Dsp din ce tai ringing sai yai picking yana murmushi. “Ranka ya dade babban likita” “Kana office?” “Ina nan, kujerar ce tamu ta Hajji ta fito” “Kai baka rabo da abun dariya, yayata ka kama ba dole na zo ba” Yana fadar hakan ya kashe wayar, sai gashi yayi knocked ya turo kofar office din ya shigo. “Bari mu tashi mu gaida saraku” Zain yayi murmushi yana mika masa hannu su gaisa. “Dcp ka yi babbab kamu, ka kama min uwa gaba daya” “Au haba, to ai kaga na ci ribar kamun ko mai komai ka kawo kanka da kanta har office dina” Zain ya yi dariya sannan ya zauna tare da kai hannu ya karbi hoton dake hannun Anty Ummi. “Wannan ai Mama ce” Sai kuma ya juya ya kalli mutanen dake bayansa. “Kune iyayenta?” “Ee ni mahaifinta ne ga mahaifiyarta nan” Namijin ya amsa. “Ina kuka samu wannan hoton?” “Wanda aka dauketa ne lokacin da muka je gidan wani baffan mu” “No wannan kayan ni na siya mata su, ta saka su ranar dana kaita gidansu Doc Hafsat, sannan kuma Hafsat ta fada min da bakinta cewar bata san inda mahaifinta yake ba, mahaifiyarta kuma mahaukaciya ce ita kuma wannan naga hankalinta na jikinta” Antar cikinsu ce ta kada, a take marar matar ta cika da fitsari. Dcp din yai saurin tarewa “Wannan ba hujja ba ce Zain, kuma wannan bincike mu zamu yi shi, yanzu dai abunda na ke ta so fada mana inda yarinyar take” “Bata san inda yarinya take ba, ni na dauka yarinyar daga wajen gidanta na kawo ta cikin gidan, kuma ni na hana a kaita gurin police saboda yarinyar tana tsoron police, yanzu haka kuma yarinyar ta gudu ba mu san inda take ba, so idan ma kamawa ne ni ya kamata ku kama ba ita ba” “No look Zain, ita muke zargi dan haka ita zamu kama” “Wannan wulakanci ne aka saka ku mata Dcp na sani, fada min inda iyeyen yarinyar nan suka fito zan saka Mai Martaba ya bincika garin” “Ba huruminka ba ne wannan, yanzu dai yarinyar muke nema” “Baku da hurumin aje Anty ta a nan dan ku wulankatata, ni zaku kama ba ita ba” Dcp yayi dariya. “Haba dai abokina ai kafi karfin a kama ka, ita ma din zan maka alfamar baka belinta amman case din yana nan dole a nemo inda yarinyar take” Zain ya juyo ya kalli mutane sai duk suka sadda kansu kasa macen na ta faman kuka. Babu ta inda suka yi kama da Hafsatu manga, duk wannan abun yasa plan ne , there's something behind it. “Zan a nemo yarinyar insha-Allah, amman duk aka gano yarinyar ta tabbatar da wadannan ba iyayenta ba ne, ni kuma sai na rufe su” “Wannan aikinmu ne ba naka ba” Cewar Dcp. Sai bayan magariba suka baron gurin tare da Anty Ummi, bayan an dauki statement dinta, sannan suka bada belinta. Daga cid office Zain ya wuce asibiti gurin Ibrahim, a tare suka yi sallah magariba, bayan sun fito daga masallaci Zain yake labarta masa abunda ya faru. “Duk yadda aka yi Doc Hafsat tasan komai akan case din nan, domin hoton da naga a hannunsu kayan da na saka mata ne lokacin da na kaita gidan” “Amman bana tunanin zata yi wani abun dan kama Anty Ummi, idan ma har haka ne nafi zargin yayanta, domin shi Dsp ne kamin a masa transfer, ta taba labarta min cewar ya nuna damuwarsa akan yarinyar” “Look yanzu muje gidansu yarinyar nan, ina son ganinta” “Ba sai muje ba, ta shigo asibiti dazun nan muka tabu da ita” A tare suka jera har sashen da Doc Hafsat take, a office ba ita kadai ba ce hakan yasa Ibrahim ya kira a waya, tana fitowa ta ganshi tare da Zain sai gabanta ya fadi. “Lafiya” Ta tambaya tana kallon Ibrahim. Zain be ce da ita komai ba ya wuce hanyar office dinsa, ita kuma ta jera tare da Ibrahim suka rufa masa baya. “Ibrahim mi nayi?” “Baki yi komai ba” “Ni ba zan iya da wannan abokin naka ba” “Tambayarki kawai zai yi” A tare suka shiga office din, a lokacin Zain na zaune saman kujerarsa mai juyawa. Zaunawa tai kamar yadda ta ga Ibrahim ya zauna. “Kin dauki Mama hoto lokacin da take gidanku ko baki dauke ta ba?” “Na dauke ta, amman ban mata komai ba” “Ke kika fadawa yan sanda cewar ta zauna gidansu Anty Ummi?” “Aa Wallahi ba ni ba ce, miya faru” “Komai be faru ba, amman nan gaba kadan wani abun zai faru, kuma idan har na bincika da hannu ciki sai na miki mugun wulakanci” Ta kalli Ibrahim idonta raurau. “Mi na masa” “Baki masa komai ba, amman yarinyar ta bata kuma yanzu yan sanda sun kama Antynsa da sunan ita ta sace yarinyar, wasu tsufo sun zo sun nuna sune iyayenta hoton da suka nuna kayan dake jikinta tufafin da Zain ya saka nata ne lokacin da xa a kaita gidanku, kuma saman kujerun ne” “Na shiga uku wallahi ban mata komai ba, kuma ban san yadda aka yi hoton ya fita ba” “Yanzu ke Hafsat baki san inda take ba, ko jin labarinta ba ko wani abun daya shafe ta” Tayi shiru kamar mai tunanin abunda zata ce, ta san inda take, kuma lallai ita ta turawa Hameeda hoton Hafsatu manga, amman bata yi hakan da wata manufa ba facen dan ita Hameedar ta bukaci haka, batan iya karfin alakar Hameeda da Zain ba dan haka ba zata iya fada masa cewar Hameeda ta zo gidan ita wata suna bincike akan maganar ba. “Idan na fada maka wani abu zaka yarda da ni?” Ta fada tana kallon Zain, shi kuma be ce mata komai ba, kallonta kawai yake fuskarsa babu annuri. “Wallahi ban bada Hafsat ga kowa ba, kuma ni da masaniyar komai akanta, amman jiya dazu ya kirani yana tambayata akan maganar yarinyar wai na bincika masa, ya fada min kai ka siyar da ita, wai gata nan an kawo masa gurin ga aiki” Zain ya kalleta da kyau sai kuma ya kalli Ibrahim ya sake kallonta. “Yayanki ne yake shirya wannan abun ko?” “Be na tunanin da sa hannunsa a ciki, domin yayi unkurin yin bincike da farko sai Momy ta hana shi, yanzu din ma ya bincika ne dan ya dauki wani mataki ya fada min cewar idan har ya bincika ya tarar da sa hannuna a ciki ni sai ya hukunta ni” “Ina Yayanki yake?” Wannan karon Ibrahim ne yake tambayarta. “Yana kaduna am masa transfer Dsp ne” “Yayi kyau, tashi ki tafiyarki” Tashi tai tana kallon Ibrahim tare da fadin. “Saboda kai nai dan Allah karka sani cikin matsala” “I can trust me” Juyawa tai ta fita ba tare da tace komai ba. Tana fita Zain ya dauki wayarsa ya sanar da Dcp cewar Hafsatu manga tana hannun Dsp dake kaduna, yayi saurin sanar da shi ne gudun kar wani abun ya biyo baya. “Amman da baka yi saurin fada ba, ka bari sai mun tabbatar mana” “Su zasu tabbatar ba mu ba” “Wai baka tunani da sa hannu Hameeda a wannan lamarin nan?” “Hameeda bata san na taba rikon Hafsatu manga ba, ina tunanin Dsp nan ne yake shirya duk wannan against me” Sai da yai sallah isha'i sannan ya baro asibitin ya nufo gida, sam ya manta halin da Farhat take ciki har sai da yayi wanka ya shirya ya sauko kasa, shi ma dan yaji motsinta a kitchen ne, saman kujera ya zauna ya dauki remote ya canja channel zuwa ta labarai, sai gata ta fito daga kitchen din dauke da plate tana dingishi kamar bata ita taka kafafun, kallonta yake har ta aje masa abinci, fuskarta ta rame sosai har idonta ya fito waje. Be ce mata komai ba har ta aje masa abinci ta nufi upstairs tana jin cikinta na murdawa ga kafafunta sun yi nauyi kamar ba zata iya taka su ba. Tashi yai ya bar abincin nan ya nufi hanyar dakinsa, sai ga wayarsa ta yi ringing, number Dada be tsaya komai ba yai picking. “Ka zo yanzu nan” Yayi tunanin akan fitar dazun ne zata sake masa fada, sai da yaje ya tararda wani labarin na daban, post din da Farhat tai ne a wayar Hameeda dake rike hannun Dada ta nuna masa. “Auren da ake cewa kar kowa ya sani shine ka saka matarka ta yai posting?” Karbar wayar yai ya duba, wannan karon be ce komai ba, har ta koro masa da complain dinta. “Daga yau cilas ne Farhat ta rika zuwa tana gaisheni, kuma karta sake fita daga gidan ka fada mata, kuma tayi gaggawar gage post din nan, kuma kar wani dan uwanta ya tako gidan nan, ko da dai rana kar ta yarda ta wuce bata shigo ta gaishe ni ba” Ta fada masa fuskarsa babu wasa kamar yadda yake a kalamanta. “An gama ranki ya dade shi kenan?” Ya jefawa Hameeda wayarta. “Kin cika sa min ido akan mata, ki barta ta sakata ta wala mana” Yana kaiwa nan ya juyo ya fito daga part din ya cikin bacin rai ya dawo part dinsa. [3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *HAFSATU MANGA* 33 A fusace ya shiga dakin Farhat, zaune ya sameta saman gado ta dora kafafunta tana dubasu, tana ganinsa tai saurin sauke kafafun tana kallonsa. “Da zaki fita wa kika fadawa? Ko an fada min nan ma kamar gidan yayarki ne da zaki fita a duk lokacin da kika ga dama, ki dawo a lokacin da kika ga dama? Irin rashin tarbiyar da kike a gidanku ita zaki zo nan ki mana?” “Tarbiya fita kawai iyayena ba su min, amman sun min tarbiyar da zan bawa mijina hakkinsa, ko da kuwa wanda na auran bana son sa, dan haka karka sake saka gidanmu idan kana maganarka” “Amman kin manta ba su miki tarbiyar iya bakinki ba ko? Shiyasa kuke fadin abunda kika ga dama har ma da zuwa ki yi post a facebook cewar kin yi kuma kin aureni ko?” “Kar hakan da nayi yasa kai tunanin ko alfahari nake da aurenka, ko kadan, aurenka yana rubuce cikin mummunar kaddarata, aurenka kaddara ce marar kyau” Matsowa yai cikin dakin ya kai hannunsa ya shake wuyanta. “Sai bakinciki ya kasheki zaki gane cewar aurena yana cikin mummanar kaddararki” Duk iya kakorin da tai na ta kwace fuskarta daga rikon da yai mata, sai ta kasa har sai da yaga dama ya jefar da ita saman gadon da kansa, sannan ya nuna ta da tsaya. “Wajibi ne kullum da safe kije ki gaida Dada, kar kuma ki sake fita ba tare d na ce ki fita ba” Juyawa yai ya nufi kofar fita. “Mutum baya mutuwa sau biyu Zain, tun ranar da aka daura min aure da kai na mutu...” Daf da zai fice tai masa furucin hawaye na bin idonta, be waigota ba yayi ficewarsa. Kuka ta dinga rusawa a gurin kamar zata hadiye zuciya ta mutu, ga wani dan banza zafi da kakafunta ke mata kamar ana gasa mata su a wuta. Dakinsa ya dawo ya zauna saman gado ya dafe kansa, be ji dadin shakar da yai mata ba, yasan wannan ba halinsa ba ne, amman kuma kiyayyar da yake ma Farhat zata iya juyar da shi zuwa wani mugun dabam. Cikin damuwa suka kwana daga ita har shi, sai dai hakan be hanata fitowa ta hada breakfast ba, shi kan yana dakinsa yana azkar har ta gama hada breakfast din ta tafe part din Dada. Tana taba kofar ta ji a rufe hakan yasa ta dawo part din a lokacin Zain ya sauko kasa sanye da short da bakar vest, wacce ta bayyana rabin kurjinsa, waya makkale a kunnensa, yana kallon yadda take tafiya har ta karaso tsakiyar falon ta tsaya dai dai shi, har sai da ya gama wayar. Ta duka har kasa “Ina kwana?” Be amsa ba yana ta kallon yadda ta rame idonta ya kumbura, ita ma bata tsaya jiran ya amsa din ba. “Naje Dada bata tashi ba, ga breakfast din ka can” Tana fadar haka ta tashi, sai ya kira sunanta. “Farhat” Ta juyo hawaye na sauka a idonsa, daman tun dazu kanta a kasa yake. “Mi ya samu kafanki?” “Ba ruwanka” Ta juya, sai ya mika hannunsa ya fisgota da karfi, sai gata a kirjinsa, ya saka dayan hannunsa wanda baya rike da wayar ya rike hannunta na dama ya matseta gam a kirjinsa. “Ki daina kokarin mayar min da magana, idan ba haka ba za ki sha wahala” Daukarta yai ya sauke saman doguwar cushion ya janye wandon bachinta yana duba kafar, kafafunta sun dan kumbura kuma sun yi ja. “Miya samu kafafunki?” “Ban sani ba” Ta amsa masa cikin mugun jin haushinsa. Har ya daga hannu zai mareta sai kuma ya lankwashe hannun ya dankwareta. “Tashi ki shirya muje asibiti” “Ina ruwanka da ni, ciwo na a jikina yake ba a jikinka ba, Kyaleni” “Jikinki ai nawa ne, ko bakinsan kudi na zuba na siye ki ba” Tasa hannunta ta ture masa fuska. “I hate you” Hannunsa yasa cikin bakinta zai janyo halshenta sai ta gantsa masa cizo, saurin sakinta yai ya tashi tsaye yana yarfar da hannun. Ita kuma ta tashi cikin dingishi ta nufi upstairs, sai kuma ta juyo tana tambayarsa. “Anty Ummi ta dawo?” “Ban sani ba” Ya fada fuskarsa babu annuri. “Karka sani hanyar daka sani ta bace maka” Tana ganin ya nufo inda take ta duke a gurin ta rufe kansa, ta yi zaton zai dake ta ne, sai kawai taga ya haye sama ya barta nan. Misalin tara da rabi ya fito dakinsa cikin shiri sai kamshin turare yake, keys a hannunsa ya nufi dakinta. Ko da ya shiga ita ma ta shirya har da su mayafi. “Taso muje” Ya fada kamar an masa dole, tasowa tai shi kuma ya sauko sai kawai tai tsayenta bata sauko ba. “Ni ba zan je asibiti ba, inda Anty zaka kai ni...” Kamar wata karamar yarinya haka take magana tana wani turo baki, juyowa yai ya kalleta sai ya hawo sama ya dauketa kamar wata jaririya sai mistinstika take tana son ya sauke ta amman ya ki sauketa sai cikin motarsa a front seat, ya zagaya ta dayan side din ya shiga ya tashi motar. Kamar ka runtse ido ka bude sai ga su cikin asibitin, he knows her well zata iya nasa tirjiya a gaban mutane dan haka ya shiga da kansa ya dauko Wheelchair, ya bude motar ya dauko ta ya dora sama ya turata har zuwa office dinsa. Fita yai sao gashi ya dawo da syringe da robar daurin hannun. Tana ganin syringe tai kokarin tashi amman yai azarbabin riketa ya saka kafafunta cikin nasa, yayinda yake a tsaye ita kuma tana zaune. “Ko ki tsaya ko na tsaka miki allurar da da karfi cikin kafafunki sai yayi jini” A dole ta tsaya ya daura mata robar ya dibi jinin, sannan ya fita da shi, bayan wani lokaci sai gashi ya dawo dauke da wani jinin leda biyu. Daukarta yai ya dora saman sofa dake office din ya fita ya dauko karfe ya daura mata jinin a hannun, sannan ya janyo kujera ya zauna gabanta. “Fada min ya kafar take miki” Ta kawarda fuskarsa ta masa banza. Ji yai kamar ya kamata yai ta dukanta har sai amsa masa, but baya son zama bad person all the time. Wayarsa ya dauko ya kira Ibrahim. “Ka shigo?” “Ee ya aka yi?” “Dan Allah same ni office” In few minutes Ibrahim ya shigo office din, ganin Farhat kwance a gurin ana sa mata jini ya bashi mamaki, miyasa ba zai kaita dakim jinya ba ya aje ta office dinsa. “Ta tambaye mi take ji a kafafunta” “As how?” “Just ask her” “Mi kike ji a kafafunki Farhat?” Juyowa tai ta kalli Ibrahim fuskarta dauke da murmushi. “Ina kwana?” “Lafiya kalau” “Tana min zafi, kuma bana iya takawa idan na taka sai na ji ciwo sosai amman idan ban taka ba bana jin komai, ta dan kumbura kadan kuma ta yi ja” Ta dan unkuro zata ta nuna masa gurin Zain ya bude nata hannu. “Wai miyasa baki da hankali, tun yaushe ya fara miki ciwo?” Ta ki amsa masa har sai da Ibrahim ya maimaita mata tambayar. “Tun jiya ya fara min” “Buguwa kikai da wani abun ko kuma haka kawai ya rika miki ciwon?” Zain ne yai mata tambayar, amman sai ta juya gurin Ibrahim tana bashi amsa. “Hakan nan akwai yake min ciwo” Zain ya kalli Ibrahim. “That's all” “Allah ya daidaita tsakaninku” Cewar Ibrahim sannan ya fice daga office din yana ta mamaki wane irin zama ne zasu yi haka ko ma suke yi. Sai da ya gama kara mata jinin sannan ya dauko mata magani bayan ko wanne ya rubuta mata yadda zata yi amfani da shi ya mika mata. Hannu biyu tasa ta karba. “Zain dan Allah kai hakuri kaji” Ya mata banza. “Dan Allah kai hakuri, idan ka yi hakuri ka kaini inda Anty Ummi ina son ganinta” Daukarta yai kamar dazu ya saka a Wheelchair ya fito da ita, sai magiyar ya kaita gurin Anty Ummi take masa ta marairaice masa kamar ba ita ba. Be ce mata komai har ya isa gidansu Anty Ummi, she was very happy da taga ya kawo ta gidan Anty Ummi, kamar dazu yanzu ma bude mota yai ya dauko ta, sai dai wannan karon fitowa kawai yai da ita ya barta nan ya shigarwa falon Anty Ummi. He feel uncomfortable, saboda ganin yan uwan Anty Ummi na gurin Ubanta dan haka yana zama ya taso ya zo waje. Jikinsa motarsa ya jingina yana jiran Farhat ta fito su tafi, sai ga Anty Ummi ta fito ta nufo inda yake tsaye. “Zain na sani ba abu ne mai sauki ka rayu da wanda kake so ba, ni kaina da nasan Farhat zata hada da irin matsalar da Haleema ta hadu da ita da ban cilasta mata aurenka ba, yarinyar nan marainiya ce mahaifiyarta bata son aurenta da kai, saboda ta tsaya kai da fata akan ita ba zata auri Alhaji Bashir ba, and na san matsalar gidanku Farhat ba zata iya daukar duka ba, ta fada min wannan ne karo na biyu da tai aman jini kuma tana jin cikinta na ciwo kamar yadda da Haleema take yi, ta fada min kafafunta na ciwo ba zata iya takawa, dan Allah Zain ka yi duk abunda za ka iya wajen ganin yarinyar nan ta samu lafiya, ka yi zaman lafiya da ita ba musan abuna gaba zata haifar ba, ta fada min irin zamantakewar da kuke, na mata magana na mata nasiha and she promise me ba zata sake wanin abun ba...” Ta karasa hawaye na sauko mata, sai Zain ya dauke fuskarsa. “Mama tana Kaduna gurin wani Dsp, na fadawa Dcp hka jiya” Hannu tasa ta share hawayen idonta. “Ee ya fadawa Abbah haka jiya da dare, yace yau za a zo da ita kuma idan an kawo ta zai kira, amman Zain baka tunanin kamar akwai sa hannun wani a lamarin nan?” “Yes ko wanene ma soon asirinsa zai tonu, mutane da suka gabatar da kara ba iyayenta na gaskiya ba ne” “Nima naga alamun haka, amman ba kake zargi?” “Dsp” A nan ya kwashe labarin komai ya bata. “Amman idan Dsp Auwal ne wanda akai ma transfer ai shine wanda ya yaudari Farhat” Zain yai shiru yana sauraren wani bakon al'amari, tare da kallon Farhat wacce ta fito daga falon Anty Ummi tana dingishi tana taka kafar a hankali alamar tana jin zafinta sosai. Tun kamin ta karaso ya bude mata front seat, ta shiga ta zauna shima ya zagaya ya shiga Anty Ummi tana masu bye bye. Tunda suka kamo hanya yake tunanin kalaman Anty Ummi, what if she's telling the truth? Yana iya tuna yadda ya rayu da Haleema cikin farinciki har mutuwa ta rabasu, what will happen idan har ciwon Haleema ne da Farhat? Driving yake yana kallonta har sai da jikinta ya bata ita yake kallo, ta juyo ta kalleshi ta murguda masa baki ta juyar fuskarsa, shi kuma ya dauke kansa ya cigaba da driving din yana jin dansa babu dadi. He needs to investigate, ya kamata ya gano abunda yake damunta, maybe ba irin cutar Haleema ba ce. HAFSATU MANGA POV. Tun ciki dare Zainab ta fada mata gobe ta tashi tun da wuri ta share mata ko ina ta goge, dan haka ta tashi tun da sallah asuba ta share falon da irin sharar da ta iya, taje ta kunna fanfo ta debo ruwa a bokiti tazo falon ta watsa a ko in sannan tasa tsumma tana gogewa, idan ta dibi ruwan da tsumma sai taje kofar falon ta matse ruwan ya sake dawowa, gashi ba tai removed center carpet ba. Duk abunda take Auwal na tsaye jikin kofa yana kallonta bata san yana kallonta ba shi ma kuma be mata magana. Har sai da taga tsumman ba zai yi ba taje ta dauko mopper ta saka tana gogewa gashi ruwan yayi yawa, sai kawai ta fashe da kuka. Takowa yai yaje inda take tsaye yaja hannunta zuwa gurin kujera ya dauketa ya dora saman kafafunsa. Ya rumgume a kirjinsa. “Hafsat zaki je gida yau” Ta daga kai ta kalleshi. “Gurin Uncle ko gurin Mama?” “Nima ban sani ba, but am sure zaki dawo nan, sai na nemo iyayenki ko a ina suke, daga Hafsat har Zain din sai sun yi regretting wannan” “Wa zai kai ni gidan?” “Yan samda zasu zo su tafi dake, umarni ne daga sama” “Aa bana son su, bana so” Around seven o'clock police suka kai knocked kofar suka karbeta, wani irin kuka Hafsatu manga take na fitar hankali, duk wanda ya ganta a lokacin xai yi zargin ko wani abin za a mata. A cikin mota wani police ya cilasata mata yin shiru, a haka tai bachin dole, misalin sha biyu na rana suka iso da ita Gusau. A maimakon a wuce da ita police station sai aka biya da ita wani gida, a wani madaidaicin falo suka shiga da ita, Hameeda na zaune saman kujera tare da Dcp da Fulanin mutanen nan da kuma wasu police biyu a tsaye. “Wallahi na so an daure matar nan” “Idan muka zafafa abun asirinki ne zai tonu, kin ga Zain classmate dina ne kuma zai iya yin bincike wajen ganin ya gane komai, and know Alhaji Salisu ma zai tsaya ma yarsa” “Amman ai tun farko baka fada min ka san Zain ba” “Nima ban san zai shigo cikin lamarin ba” Dcp ya kalli Hafsatu manga wacce ta sha jinin jikinta ta kame a guri daya ya nuna mata fulanin dake gurin tare da daka mata tsawa. “Kin ga wadannan sune iyayenki, idan aka tambaye iayyen ki nuna wannan ki ce shine mahaifinki, wacan kuma innarki, idan kika fadi wano abu wanda ba haka ba, sai nasa bindiga na harbe kanki kiji” Ta gyada kai hawaye ma mata zuba yana numfashi daker. “Wacece wannan?” Hameeda ta tambaya. “Ma... Ma... Mama...” “Good, wannan fa?” “Ba... Baba... ” Sai kuma ta juya gurin mutane. “Ana gama case din nan zaku bar kasar nan ku koma can garinku Nijar, ku tafi da ita ko da wasa karku yi saken barin ta dawo kasar nan” “To Hajiya, Allah ya saka da alheri” Kudi mai yawa ta diba ta basu, sannan Dcp yasa police din su tafi da ita office dinsa dake cid, ya kira Alhaji Masa'ud, da Alhaji Salisu da Zain ya sanar musu cewar an kawo yarinyar. A tare suka fito da Hameeda ita ta nufi unguwar Samaru shi kuma ya nufi Cid office. [3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 35 DOC HAFSAT POV. Kamar wata marar tafiya ta tashi a yau, tun shekaranjiya da abun ya faru ta kasa sake jiki ta dauki damuwa ta sakawa kanta. Tana son aikinta, ta san zata iya samun aikin a wani gurin, sai dai barinta gurin ne be mata dadi ba, domin tana jindadin gurin sosai, bata san iya maganganun da zasu biyo baya ba, domin kowa zai yi mamakin jin Zain ya koreta haka kawai. Bata dakinta ba har sai da Momy ta aika Sapna ta kira, sannan ta fito tana wani tafiya, kallonta Momy take har ta karaso ta zauna a kujerarta. “Wai Hafsat Lafiyarki kuwa?” Ta dan dago kadan ta kalli Momy. “Momy ina son aikina” “Kina son aikinki ko dai kina son Zain din?” Cewar Sapna tana zuwa kofin shayinta. “Aikina nake so, kin fi kowa sanin babu soyayya tsakanina da Zain, duka abunda na ke ina yi saboda Ibrahim shi nake so ba Zain ba, kawai dai ina jindadin gurin kuma ina jindadin mu'amala ta da kowa a gurin” “Amman ai zaki iya samun gurin da yafi wannan, miye abun damuwa a ciki? Ko wace asibiti kike so aiki a kasar nan zaki iya samu tunda kina da takardun masu kyau” “Amman Zain yana min kallo na ci amanarsa, kuma Ibrahim ya fada min mutanen da suka tafi da ita are not her real parents” “Ina ruwanki da yarinyar da aka koreki saboda ita zaki kanki a damuwa saboda ita? Ji rashin jutuwar dake kokarin shiga tsakaninki da yayanki haba Hafsat” “Momy har yanzu be kyale maganar ba, jiya ya kirani ya son na nemo masa number matar nan wacce ta zo tana tambaya akan yarinyar kauye” “Wacece” “Ina ganin yar'uwar Zain din ce” “Wato duk maganar da nai masa bata shiga kunnensa ba ko? Bari zan kira shi sai na bata masa rai” Momy na fadar haka ta tashi ta nufi dakinta, Hafsat ta yi shiru tana kallon tea dake gabanta. Sapna ta kalleta “Bloody please ki cire wannan tunanin a ranki, ni ban ga abun tada hankali ba, impact ni da za ki dauki shawarata ma ki fitar da wannan Ibrahim din ki yi aurenki, in yaso daga baya idan kina son aikin sai ya nema miki” Fashewa tai da kuka. “Shi ma fushi yake da ni” Sapna ta bato kujerarta ta zo ta dafa Hafsat. “Zai sauko kin san ai yadda yake son ki, so ki shareshi kawai ko bashi lokaci zai dauko dole ne yanzu yai fushi da ke saboda abunda ya faru yana ganin kamar da laifinki a ciki, kuma ina tunanin yarinyar tana da muhimmanci a gurinsu, waya sani ma ko yar daga cikinsu ne suke boye there's is something behind this issue” “Zai iya zama haka ko?” “Yes akwai abunda suke boyewa a tsakaninsu, kuma sun yarda da ke ke kuma kika kai failed dole zasu ji haushi” “Amman Ibrahim yana da yara, ba zai boye wata yarinyar ba, sai dai ko in Zain din” “It could be him ko kuma wanin abun dabam, dan haka ki bashi lokaci zai sauko” Ta gyada kai sannan ta dauki tea gaba daya ta shanye ta tashi ta nufi dakinta, wayarta ta dauka ta shiga massage tana aikawa da Zain sako. _Doc ka yarda da ni, Wallahi babu hannu a lamarin nan, amman akwai wata yar'uwarka tace min sunanta Hameeda ta zo nan tare da Doc Isma'il tana binciken yarinyar kamin hakan ya faru, ban san alakarka da ita ba, ba kuma ina nufin wani abun ba kawai dai na ga ya dace na fada maka ne_ Sai da ta gama tsara sakon kamar haka sannan ta tura masa. *** *** *** Babu irin cin mutunci da Momy ba tai ma Auwal ba, akan maganar har tana masa rantsuwa idan be fidda kansa cikin maganar ba, sai ta sanarwa Abbah kuma sai ta mugun tsaba masa. Tun da take masa fadan be ce uffan ba har ta gama sannan ya bata hakuri tare da alkawarin ba zai sake faruwa ba. “Ina ruwanka da yarinyar, uwa ka hada da ita ko uba? Akan me zaka tsaya kai da fata wai kai sai ka binciko abunda be shafe ka ba” “Momy na ce ayi hakuri ba zan sake ba, i promise” “Da ya fi maka” “Allah ya huci zuciyarki” Ta katse kiran, shi kuma ya sauke wayar yana jin mai haushin Hafsat. And ya ma kansa alkawari ba zai sake damun kansa da maganar ba. Amman ya tuna Zain yana jin zafinsa sosai, yana yawan auna yadda Zainab take tsaye a gabansa haka Farhat take tsaye a gaban Zain, yana morewa da ita dukan wani tanadi da buri da yake da shi akanta ya tafi a banza. “Zainab bata cikin tsarin matan da na ke so,amman look at me ina zaune da ita by force gaskiya abunda su Momy suke min ya yi yawa, yana da wahala a samu yaro mai biyayya irina, sun rabani da wacce nake so a duk lokacin da na unkuro zan yi wani abu sai sun shiga sun fita sunga sun hanani sannan hankalinsu zai kwanta” A fili yake zancen yana daga murya, kai kace ma ba a falo yake ba bayan kuma ya san Zainab tana cikin kitchen tana shirya musu abin karyawa. Lekowa tai daga kitchen din daman tun dazu tana jin hayaniyar yanayin wayar da yake da Momy. “Lafiya kamar kana magana” Be tanka ta ba, ya tashi ya wuce dakinsa cikin mugun jin haushi. Yana shiga ya wurgar da wayarsa saman gado. “With his dirty hands zai taba jikinta, wani kazami da shi malam, yarinyar da na dade ina raino wani banza ya zo kawai ya dauketa ta could you imagine?” Ya halbi wardrobe fa kafarsa. “Ni gaskiya an cuce ni, Wallahi ina son Farhat nan kawai Abbah ya zo ya hada ni da wannan yarinyar, and i was planning na aureta a my second wife wannan banza ya zo ya aureta. What if all those things a plan? Miyasa be kai yarinyar nan wani guri ba sai gidanmu? And now aka kawo ta aiki a cikin gidana?” Juyowa yai ya dawo falo, a lokacin Zainab na tsaye gurin dinning tana jera kayan abinci. “Zainab wace tsohuwa ce ta kawo miki yarinyar nan?” Juyowa tai ta kalleshi. “Miyasa ka tambaya?” “Just” “Wai mi yarinyar tai yi ne? Ni ban gane maka ba, an kawo yar mutane ka zo ka dauketa ka bada ita ga wasu police yanzu kuma kana ta tambayar lamarin yarinyar?” “Ba komai kawai ki amsa min” “Nima ban san matar ba, kawai dai ina son na tabbatar da wani abun ne, matar data kawo ta ai tace ita kanwar mahaifinta ce ko? Yanzu kuma Dcp ya aiko a ka dauki yarinyar wai wani case suke can iyayen yarinyar suna nemanta” “To ko wannan matar sato ta tai?” “Shine abunda nake tunani, amman da ta sato ta miyasa bata kaita ko'ina ba sai gidana? Ina kika hadu da matar ne?” “A nan kawai ta shigo ta tambaya wai ko ina son mai aiki, a lokacin tana tare da wata babbar yarinya nace mata ina so amman wannan ta mun girma sai ta za a kawo min karama, shine yanzu ta kawo ta” “Ki yi hankali da irin mutanen nan masu shiga gida gida neman masu son yar aiki wasu macuta ne, ida....” Tunawa da yai da magabar Momy yasa shi yin shiru be karasa ba. “Minene?” “Ba komai, abincin ya yi” “Ee” Ta fada ba dan ta gamsu babu komai din ba. *** *** *** He spent all night thinking of Yarinyar kauye, yana ta son hango wanda yai dalilin raba shi da ita, amman a duk inda ya duba sai Anty Ummi yake hangowa domin ita cw silar komai, but after ita fa? Waya san sirrin zaman Hafsatu manga a gidan? Just him and Ibrahim, Hafsat ta shiga ciki ne saboda Ibrahim ya sakata baya son kawowa zuciyarsa abunda ba shine ba, he started Suspecting something. Yayi saurin tashi tsaye yana dafa kansa. “No no no Ibrahim can't do this to me, i trust him?” ‘Amman kuma wa? He is the only one daya san sirrina duk wanda zai san wannan sirrin a inuwarsa ya fake, idan ma Hafsat din ce ai itama ta dalilinsa ta sani, but wait mai zai sa Hafsat tai masa haka? Ta san Anty Ummi ta ne? Amman ai da Anty Ummi bata bada yarinyar ba da duk haka be faru ba’ Sake sake yake ta yi a ransa, a duk inda ya zaga ya zagayo Anty Ummi ce matattarar faruwar komai. Lumshe idonsa yai y busar da iskar bakinsa a hankali. “Ban san tararar dake tsakanin ganina da na ki ba, kin yi kankanta na ce son ki nake, kin yi yawa na iya mantawa da ke, motsi kike da tafiyar numfashina, ko wace dakika tana kara azabtar da zuciyarta da nisan da kika yi da ita” Yaje gaban window ya tsaya yana cigaba da magana da kansa kamar sabon mahaukaci. “Ke kadai ce abu mai rai daya naji ya tsaya min a rai bayan tafiyar Haleema, ke kadai ce abu mai motsi dake sani nishadi da jindadi, ina jindadi kusanci na ke ina jin natsuwa da kwanciyar hankali idan ina kusa da ni, ban san kilo mita nawa ne a tsakanin mu ba, amman kusanci yana nan kusa da ni a gefen zuciyata, hoton fuskarki da rayuwar da muka yi yana nan a zuciyata, ba zan taba mantawa da ke ba har a bada, ina miki fatar samu natsuwa da kwanciyar hankali a duk inda kike...” Wayarsa ce dake kan gado yai kara alamar shigowar sako, juyo yai ya kalleta sai kuma ya dauke kansa ya jingina da gurin, it pain him idan ya tuna yadda ya bar bata, yadda take kallonsa da yadda hawaye suke zuba a idonta. Yana tsaye a gurin har rana ya hudo ya soma hasko dakin, sannan ya juya ya shiga bathroom yai wanka ya fito ya shirya cikin kananan kaya as usual ya feshe jikinsa da turare. Daf da zai wuce ya dauki wayar ya duba, yana ganin sunan Doc Hafsat a sms din yasa ransa ya bace, be bude sakon ba ya danna delete ya goge sakon, ya dawo contact dinsa ya goge number ya shiga block list yai blocking dinta sannan ya saka wayar aljihu ya fito, ya nufi dakin Farhat. Be sameta a dakin ki ba, hakan yasa shi daukowa kasa, sai ya samu tana kitchen tana hada musu breakfast. A bakin kofa ya tsaya yana kallon kafafunta ta tsaya tsaf da alama sun mata sauki ko kuma sun daina ciwon. Kamshin turaresa ne ya sanar mata da zuwansa amman saboda karfin hali taki ta juyo ta kalleshi, juyo yai ya fito ya shiga motarsa, sai kuma ya fito ya shiga cikin gidan ya dauko wani akwati ya fito ya bude bayan mota zai saka shi, tsaye yai cak yana kallon kayan Hafsatu manga wanda ya siya mata a lokacin da tai zama asibitin, ya sasu bayan motarsa da da zimar idan ya fito ya zubar amman ya manta sai a yanzu da zai saka box din yaga kayan, hannu yasa ya dauko wata riga ya rike yana ta kallo sai kuma ya kai hancinsa ya shinshina. Fasa saka box din yai ya rufe bayan motar ya dawo ya aje shi a front ya shiga gurin zamansa ya zauna yana rike da rigar, wayarsa ya dauko ya nemo number Dcp ya kirashi. “Ina ka ce iyayen yarinyar suke?” “Nijar, lafiya dai” “Nijar a ina?” “A damagaram” “Basu baka adireshinsu ba” “Mi zai sa su bani addireshinsu?” “Amman ai kai dan sanda ne dan sanda ma Dcp miyasa baka yi abunda aikinku ya tanada ba kamin ka mika yarinyar ga mutanen? A yadda muka ta so da kai Faruk ba haka kake a makaranta ba, kai mutum ne mai gaskiya da kokarin fitar da ita miyasa ka canja” “Har yanzu ina nan a yadda nake Zain, kai ne dai ka canja ka daina yarda da mutane, kana ganin kamar kowa kokarin cin amanarka yake” “Bana shakkar a ci amanata, kai ne dai bana son ka ci amanar wannan yarinyar, zan ninka maka abunda wadanda suka baka, har sai ninkin ya nimka sau dubu ka fada min da yarinyar nan take ko kuma ka nemo min ita” “Da biyana akai na yi wannan aiki, kai ai tun kamin ya kaimu haka zan fada maka farashin da zaka biya na warware maka komai, miyasa ka kasa ganewa ne? Kusanci na da kai yafi kusancin wanda zai hadu da ni da rana tsaka ya nemi na tozartaka ko iyalanka ya biyani” Zain ya katse kiran, tare da kunna motarsa yana fadin.. “Ba zan iya barin yarinyar nan a hannun mutane da bata sani ba, hankalina ba zai taba kwanciya ba” Cikin yan mintuna ya isa gidan Ibrahim, sai kace ba shekaranjiya ya gama fushi da shi ba, bashi da wani amini bayan shi wannan dalilin yasa ko sun samu tsabani sukana shirya kansu domin ko wanne baya iya gi sai da dan'uwansa. A harabar gidan ya tsaya ya kira Ibrahim a waya, ya sanar masa yana waje. “To ka shigo mana gidan bakonka ne” Yana sauke wayar ya fito cikin motar rike da rigar ya nufi kofar falon, knocked yai sannan ya tura ya shiga, a zaune ya samu Ibrahim Falmata na gefensa zaune sanye da Hijab tana gyara masa hannun rigarsa. “Yanzu bayan ka kore budurwata mai zaka zo nai maka?” Zain ya yi murmushi ya zauna saman kujera yana gaisawa da Falmata. “Ango ina amarya” “Tana lafiya ta ce a gaishe ki” “Ina amsawa nima ina gaisheta, kuma a fada mata angonta ya kori Abokiyar zamana a gurin aiki ba mu jidadi ba, gashi kuma Abban Siyama yaki ya fada mana laifin da tai” “To ai sa za ki yi ya aurota ya kawo cikin gida sai na san da gaske kina sonta” Falmata tai dariya, tare da tashi tana fadin. “Me kake ci na baka na zuba? Ba jimawa zai kawo min kanwata, Next week zan shigo na ga Amarya” “Allah ya kai mu” Sai ta shige daki sannan Ibrahim ya kalli rigar da ke hannun Zain ya kalleshi ya ce “Kamar rigar Mama” “Ita ce, Ibrahim ba zan boye maka ba, gaskiya na fara zarginka akan lamarin nan kai ma kana da sakaci, idan ma Hafsat ce sikar komai har da laifinka, tun farko sai da na ce karka sako yarinyar nan a ciki amman kace ka aminta da ita” “No i trust her, kawai dai kasan mata wani lokacin ba a sirri da su, kuma wani zai iya bugun cikinta ya ji wani abu, amman abunda na sani ba zatai unkurin cutar da kai ko yarinyar nan ba, na san dai garin dumi taje ta fadawa wani ko kuma wani abun, wannan dalili yasa nima nake fushi da ita” “Yanzu ni abunda na ke so, ka yi sanarwa ka zan saka naira millions uku ga duk wanda ya gano inda yarinyar take kuma ya kawo ta gurinka, kai zaka saka sanarwa kuma number za a bada” Ibrahim ya tsaya kallonsa yana mamakin lamarin Zain. [3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 34 Kamin ya isa cid din duk ya bi ya matsu, a hanyarsa ne ya kira Anty Ummi ya sanar mata duk da yasan Dcp zai kirata, sai ta sanar masa tana ma gurin. A harabar gurin ya faka motarsa ya fita ya shiga cikin office din. Anty Ummi da Alhaji Masa'ud na zaune a kujera daya, Yayinda Alhaji Salisu yake zaune a kujerar daje facing din ta Dcp, a dayar kujerar ya zauna ya zaune wacce ke gaban teburin Dcp. Bayan sun zauna Dcp ya shigo yana rike da hannun Hafsatu manga, mutanen da suka ce sune iyayenta suna biye da shi. Fuskarka ta jike shakaf da hawaye har idonta ya kumbura. Kin daga kai tai ta kalli kowa har Dcp ya zaunar da ita saman wata kujerar. Sai da ya gaisa da su sannan ya kalli Hafsatu manga ya ce “A jiya Zain yake fada mana cewar Hafsatu manga tana gurin wani Dsp dake kaduna, so na buga na bincike Dsp din yace aiki aka kawo masa ita ya fadwa kanwarsa ita kuma tana ganin hotonta sai ta gane taa fadawa Zain shi kuma ya sanar da ni, bana son muja abun da nisa ne shiyasa ban zafafa bincike ba, kamar yadda Alhaji Salisu ya bukaci a kashe maganar” “Amman aikinku ne Dcp, ya kamata ku yi bincike ko dan tabbatar da gaskiyar lamari” Cewar Zain. Sai Alhaji Salisu wato mahaifin Anty Ummi ya daga masa hannu. “A kashe maganar kawai zai fi, ka damka yarinya ga iyayenta, hankalin kowa ya kwanta” Ya karasa yana kallon Dcp. Sai Zain ya ce “Amman ka tabbatar iyayenta?” Dcp yayi dariya. “Zain ke nan, ga yarinyar nan zata tabbatar maka da bakinta” Ya kalli Hafsatu manga. “Ke daga kanki ki kalli can, wacece waccan matar....?” Ta daga kanta a maimakon ta kalli matar sai ta kalli Zain tana ta hawaye kamar an bude fanfo, ji take kamar ta fada masa gaskiya amman tana tuna maganar da Dcp yai mata cewar zai fasa kanta da bindiga matukar ta fadi gaskiya, ko yanzu ma da zasu shigo sai da ya jaddada mata. “Mama... Wacece wacan?” Ya kira sunanta a hankali sannan ya nuna mata matar. Sai a lokacin ta kalli matar, sai kuma tai shiru kamar ba zata ce komai ba. “Ma... Ma... Ma... Ma.. ” “Wacan fa?” “Baaba.. Baba... Baba...” Zain ya ji babu dadi, yasan duk yadda aka yi ba iyayenta na gaskiya ba ne. “Kin tabbata? Kin san kin fada min cewar mamaki mahaukaciya ce, kuma baki san inda Babanki yake ba, kin tuna?” Sai kawai ta fashe da kuka. “You see wadannan ba real parents dinta ba ne ya kamata kui arresting dinsu” Anty Ummi ta kira sunansa, ganin yadda yake tada jijiyon wuya, bata son ya nuna kulawarsa a kan yarinyar a gaban mahaifinta. “Zain dan Allah” Kallonta yai kamar zai yi magana sai kuma ya tashi ya fice daga office din. Su Anty Ummi kam basu bar asibitin ba sai da aka bawa fulanin Hafsatu manga, aka kashe case din sannan suka dawo gida. Cikin bacin rai Zain ya shigo office, yadda ya banki kofar office din ma ya isa ya karantar da kai haka, telephone dinsa ya dauka ya kira Ibrahim. Ba bata lokaci sai gashi ya shigo office din hankalinsa a tashe dan ya fahimci hali da abokinsa yake ciki. “Yarinyar ta san komai Ibrahim, da ita aka hada kai a cuci mama, wadancan banzaye mutanen ba iyayenta ba ne, na karanci hakan a idonta, kuka take sosai magana take son tai min amman ta kasa saboda tsoro” Ibrahim ya dafashi. “Ni ban gane kan maganar ka ba, zauna please” Ya zaunar fa shi, sai Zain yasa hannu biyu ya rufe fuskarsa, yana sauke numfashi a hankali, kokarin daidaita fushinsa yake, kokarin bawa zuciyarsa hakuri yake. Dagowa yai ya kalli Ibrahim yana ware yatsun hannunsa yana hadewa. “Ka rubuta mata takardar sallama, kuma ka fada mata idan wani abu ya samu yarinyar nan sai na rufeta, ko kuma nasa ai mata mugun wulakanci” “No no no Zain listen, babu hannun Hafsat a cikin matsalar nan, kawai tana kokarin taimako ne” “Wane irin taimako saboda tana budurwarka ai ba zaka ga laifinta ba, ka koreta karta sake shigo min asibiti da sunan aiki, idan kuma kai ba zaka iya ba ni zan iya zuwa nai mata wulakanci” “Zain duk kabi ka rikice akan yarinyar da baka san inda ta fito ba, sanadin yarinyar aka kama Anty Ummi yanzu kuma muna cikin wannan case din, wannan wane irin abu ne?” “Ibrahim fita ka bar min office dina” “Zain.... ” “Just go please, and make sure you fired her” Ibrahim yafi kowa sanin halinsa idan yai fushi baya jin rarrashi kuma baya saurarawa kowa. Dan haka ya fice shima cikin zafin rai. Zain be bar office din ba sai dare, ko da ya isa gida baya iya tantance halin da yake ciki, iyakar abunda ya sani yana jin jikinsa kamar marar lafiya, a bakin kofar falonsa ya tsaya ya kira Dcp a waya, sai da tai ringing kamar zata katse sannan ya dauka. “Yariman yarimawa” “Dcp ina yarinyar nan take?” “Na bada ita ga iyayenta yanzu haka sun kama hanyar Nijar, daman ta fada min ita kawai suke jira zasu koma gida” “Kai baka ga alamar ba iyeyenta ba ne na gaskiya? Miyasa ba kai bincike ba?” “Binciken mai ko?” Wani dogon tsaki Zain yaja ya jingina da kansa da kofar. Tun can farko be santa ba, daga lokacin data shigo rayuwarsa natsuwa da kwanciyar hankali suka barsa, he live a lokacin da be san da wanzuwarta a dogon kasa ba, yanzun ma zai iya rayuwa ko babu ita, even if ba iyayenta na gaskiya ba ne, zai runtse ido ya kyale komai domin samawa kansa salama. “Good bye...” Ya furta ciki murya marar dadi, idonsa na rikewa zuwa ja, saboda bacin rai da damuwa. A hankali ya tura kofar falon ya shiga, kukan Farhat ne ya fara masa marhaba da zuwa, daga kitchen take amman kuka take ta rairawa iya karfinta. Kai tsaye ya nufi kitchen din da fuskar nan tasa babu annuri. Zaune ya sameta ta rike kafa tana ta kuka sosai, ya risina yana duba kafar. “Minene?” “Ciwo take kamar zata cire” “Ai kinsan tana ciwo kika taso kika zo kitchen mi kika zo yi” “Na yi miya tuwon zan yi” Hannayensa yasa ya dauketa ya fito da ita falo ya kwantar saman kujera, sannan ya haye sama, kayan jikinsa ya cire ya sanya short and vest ya dauko kasa ya shiga kitchen din, tayi tunanin gas din zai kashe ya dawo, amman be fito ba har bachi ya dauketa, he use to cook tare da Haleema sometimes ma shi zai girka musu dinner, ko su yi tare, so he is very good when it comes to cook dukan wani kalar abinci da Haleema take so ya iya girkawa. Duk wani motsi da yake a kitchen din yana tuna masa da rayuwarsa ta baya ne, he can't remember when last ya girka wani abu mai nauyi sosai a kitchen dinsun bayan rasuwar Haleema. Tuwo ya dafa mata tuwon shimkafa, yadda ya dage yana murza tuwon sai ka rantse mace ce ba namiji ba, ko da ya gama ya kwashe ta yi bachi, yadda ya fito kitchen din ya hada gumi kamar wanda yai karamin yaki. Center table ya janyo ya dora mata tuwon sama sannan ya koma ciki ya dauki plate ya debo miyar ya kawo mata sannan ya shiga tashinta. “Farhat Farhat tashi ki ci abinci” Cikin maggin bachi ta ce “Ba zan ci ba, bachi zan yi” “Wallahi sai kin ci shi” Hannunsa yasa ya tasheta zaune ya zaunar da karfi ya bude mata ido. “Wake-up” Ta kalli tuwon da kyau ta ga tuwo ne, ba dan tasan miyar kubewa tai ba da tace siyo ta yai, agogon falon ta kalla. Goma da rabi ya nuna sai kuma ta kalli Zain da har yanzu gumi yake. “Waya girka?” Ya mata banza ya tashi yaje ya dauki wani plate ya zuba na shi ya dawo ya zauna. Komawa tai zata kwanta ya katsa mata tsawa. “Farhat, tashi ki tuwon nan Wallahi ko na mugun tsaba miki” “To kawo min roba na wanke hannuna” Kallonta yai da kyau sai kuma ya aje abincin ya tashi yaje ya dauko mata ruwa da ruwa ciki ta saka hannunta ta wanke sannan ya aje robar kasa. Har ta soma cin abinco ta gama be yi loma hudu ba, ya rike plate din kawi yana kallon tv ya kasa ci, ta yi mamakim yadda ya hada tuwo haka yai kyau kamar mace ta dafa, kamar ta tambaye shi sai kuma tai shiru ta mika hannu ta dauko robar ta wanke hannunta, da gangan ta karkarta robar ruwan suka zube. Juyo yai ya kalleta sai ya aje plate din ya tashi ya shiga dakinsa. Bathroom ya shiga ya wanke hannunsa sai ya tsaya gaban madubi yana kallonsa kansa, a zahiri kansa yake kallo zuciyarsa kuma Hafsatu manga take kallo, rayuwarta yake tunani ina mutane da suka dauke zasu kaita mi zasu mata? Su waye su kuma waya saka su? Kallon da tai masa dazun ya tsaya masa a rai, sai kuma Anty Ummi wacce ita ce silar komai, da ace bata kai Hafsatu manga wani gurin ba da duk haka be faru ba. Ya dade yana ta bautawa abunda ba zai bauta masa ba, sannan ya fito ya kunna shower yai wanka. Ko da ya sake dawowa falon karfe biyu da kwata, Farhat na kwance a inda ya aje ta tana ta sharar bachinta. Tsaye yayi bayan kujerarta yana kallon fuskarta, she looks so cute and so innocent, Hafsatu manga ce ta fado masa a rai yadda yake watching fita da shigar numfashinta rayuwar da yai da ita a asibiti yake ta gani. “Ya Rabb, ko wane numfashi yana tuna min da ke, hawayen da na gani a idonki sun hanani samun natsuwa” Ya furta yana shafa fuskarsa. Zuwa yai ya dauke kayan da ta ci abinci da su ya kai kitchen ya gyara gurin, sannan ya dauketa ya kaita dakinta ya kwantar da ita saman gadon yaja blanket ya lullube ya kashe mata wuta ya fito daga dakin ya dawo falo ya zauna. AUWAL POV. “Ni ban gane wannan abun ba, ka dauki yarinyar mutane ka bada ita wani guri, yanzu kuma ka zauna kana da fushi da ni kamar na maka wani abu” Ya daga mata hannu. “Karki dame ni, tunda kika ga ban fada miki komai ba ai sai ki kyale ni ko?” Ya tashi yaje gurin window falon ya tsaya yana danna wayarsa. Sai kuma ya kara ta a kunne. “Wai minene alakarsa da ita?” Hafsat ta amsa masa cikin kuka. “Basu da alakar komai, yaya yace sai ya kulleni idan wani abu ya samu yarinyar, kuma ya koreni daga aiki” “Ai kadan kika fara gani, nima sai na miki nawa wulakanci, uban waye ya aikeki fada masa tana hannuna?” Fashewa tai da kuka sai Momy ta karbi wayar. “Auwal dan Allah dan girman Allah ka kyale maganar nan, Hafsat zata iya samun aiki a wani gurin, babu ruwanka da alakarsa da ita” “To Momy ba zan sake ba” Daga haka ya kashe wayar, yaja juyowa yaga Zainab bayansa. “Wata kake so ne?” Ya dora hannayensa saman wuyanta yana murmushi. “Ni babu ruwana, da karin aure wani sha'anin ne da be shafe ki ba, karki wani tashi hankalinki kinji?” “Akan yarinyar ne?” “Yes” Ya mata kiss a goshi kamar ba shine yake fushi da ita ba. Sai kuma ya rumgume kankam a kirjinsa yana murmushi. ‘I will teach you a lesson Zain, indai akan yarinyar nan ne ka kori kanwata sai na koya maka hankali sai ka yi kuka da idonka’ A zuciyarsa yake wannan maganar a fili kuma kissing din matarsa yake suna kokarin lulawa wata duniyar. Washe gari bayan sun gama breakfast ya fito harabar gidan ya kira, Hafsat bugu daya ta dauka. “Doc ya kike” “Lafiya kalau” Ta amsa masa cikin rashin jindadi. “Fada min inda zan samu yarinyar nan wacce ta zo gurinki tana bincikar labarin yarinyar kauye” “Ni ban san inda zaka same ta ba, ba Momy ta ce ka daina maganar ba” “Wannan tsakanina da ke ne please, ki nemo min inda zan samu number karki bari Momy ta ji” “Ban san inda zaka samu ba” “Haba ki yi tunani mana, ya aka yi ta san yarinyar tana gidan? Ita da wa ta zo?” “Ita da Isma'il shi ya fada mata saboda shi kadai na taba firar da shi, sai kuma Ibrahim” “Ta hanyar Isma'il din zaki samo min number ta” “Amman Dsp...” “Please mana Sis...” “Okay” Daga haka ya sauke wayar, ya juyo ya dawo falon yana saka hannayensa aljihu. *** *** *** Tun jiya da suka baro garin gusau Hafsatu bata daina kuka ba, kukan hada ta da mutanen da bata sani ba kuma bata san inda zasu kaita ba, gashi ta kara nisa da garinsu, ga kuma wani dan banzan ciwo da mararta ke yi, bata san ciwon maraba dan haka sai ta dauka ko cikinta ne ke ciwo. Bata san garin da suka zo ba, iya kar abunda ta sani ana ta wuce garuruwa da yawa kamin su iso wannan kauyen da babu komai sai gidajen kara da shanu, ko ina fulani ne sun yi tunga tunga. Ciki dakin kara mutumen da suka zo tare ya sakata ya gargadeta akan ta daina masa kuka haka kar yan'uwansa fulani su gane cewar daukota yai ko kuma wani abun yai mata. Sai kai tas hannu a baki ta toshe bakinta amman bata daina kukan ba. “Wallahi in ba kai shiru ba sai na sa bulala na saneka da ita” A dole ta hade kukan ta zauna a gurin tana ta soshe soshe, nan da nan bachin wahala yai gaba da ita. 36 A hankali Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya, ya juyo ya fuskanci Zain da kyau ta yadda zai fahimci zancensa. “Look duk wannan abun be taso ba, at first daman can baka san da yarinyar a rayuwarka ba, so ka saka a ranka a yanzu ma baka santa ba, idan har Allah yana nufin sake haduwarku ba zaka sake haduwa da ita no matter ya shiga tsakaninku and no matter how far, ban sani ba ko zaka yarda da ni, amman Zain son yarinyar nan kake... ” “No no, karamar yarinya ce ba sonta nake so ma soyayya ba, bana tunanin haka” “Nima ban ce son soyayya kake mata ba, amman dai kana sonta, irin son nan da kan hana mutum samu natsuwa da kwanciyar hankali, a iya abunda zan maka a yanzu shawara zan baka a matsayena na amininka kuma dan'uwanka, ban sani ba ko zaka dauka” Maganar yake fuskarsa na nuna gaskiyarsa, sai da Zain ya busar da iskar bakinsa sannan ya cigaba da kallon Ibrahim. “Abunda na ke ganin ya fi ka fita waje na dan wani lokaci, Zain you need some spaces and fresh air, idan ka daga ma kasar nan a yanzu saka masu natuwa da kwanciyar hankali daka rasa, zaka yi nisa da Hameeda da kuma Dada, so kaga ka huta da matsalarsu dole zasu daga maka kafa, Anty Ummi ma da kake ganinta as wicked woman zaka kai nisa da ita, zaka samu natuwa idan har kai nisa kasan baka kusa da Mama and kasan she's nowhere to be found” “A a wannan ba shawara ba ce Ibrahim, ko kasar nan na bari ba zan taba samu kwanciyar hankali ba, taya ma za ayi na samu kwamciyar hankali bayan ba wacce nake so na aura ba” “Na san yadda kake ji Zain, but remember Allah ya baka Haleema a lokacin da kake sonta kuma kuke kaunar junanku, daya tashi dauke abarsa sai ya dauke ta ka isa ka hana faruwar haka? Yanzu kuma shi ya kaddara maka auren Farhat, da Hameeda Allah ya kaddara maka aure ya zaka yi da ita? Ita kanta Farhat din ba kai take so ba, amman Allah ya hada ku baka tunanin imaninka Allah yake gwadawa? Look at you cikin kankan lokaci Allah kawo Yarinyar nan ya gata karamar yarinya wacce zaka san inda ta fito ba, baka san iyayent ba, amman ya saka maka sonta, lokaci daya kuma wani abun ya shiga tsakani ya nisanta ka da ita, baka tunanin duk wannan yana rubuce a cikin kaddararka? Idan kai hakuri ka kawarda idonka kasan iya sakamakon da Allah zai maka a cikin lamarin nan? Trust me Zain zaka samu kwanciyar hankali a can, kuma zaka samu fahimtar matarka zaku nisanta da Hameeda saka samu damar nemawa matarka lafiya” Dafe kansa yai yana jin kamar ba zai iya ba, yasan Ibrahim yana da gaskiya, shi kanshi yana jin komai na duniyar nan ya isheshi ba shi tabbacin idan ya bar kasar zai samu kwanciyar hankali amman yana da tabbacin idan yai hakuri zama da Farhat Allah zai masa sakamako da wani abun, and yes idan ya bar kasar nan dole Hameeda ta shafa masa lafiya ita da Dada, amman anya Mai Martaba zai amince yai nisa da shi mutumen daya ki yarda ya barsa ya zauna wani gurin sai cikin masarauta zai yarda ya barshi yaje wata kasar ya dade...? “Kuje mana ko five years kui a waje, I promise you zaka dawo ka tararda farinciki” “Mai Martaba ba zai yarda nai nisa da shi ba” “Ba kai tsaye zaka nuna masa kana son tafiyar ba, ka nuna masa honeymoon zaku je, daga can zaka binciki matsalar lafiyar matarka, daga nan sai kai ta zamanka, idan har ya matsa maka sai ka rika zuwa kana dubashi har zuwa lokacin da zaka samu natsuwa da kwanciyar hankali sannan ka dawo, i promise you i will surprise you” Ya shi tsaye cikin rashin jindadi. “Zan yi tunani akai” Tare suka fito da Ibrahim yana ta jaddada masa irin alfanun dake tattare da barinsa kasar nan, da kuma irin illar da zamansa a nan zai masa. Bayan ta gama breakfast ta koma cikin dakinta tai wanka ta shirya cikin farar atamfa mai shudin ja, ba laifi ta yi kyau duk da kasancewar ba tai kwaliya ba, ta yi mamaki kuma taji dadin da kafafunta a yau ba su yi ciwo ba. Rike da mayafinta ta fito a falo ta tsaya ta sanya mayafin sannan ta nufi part din Dada, sai da tai sallama sannan ta shiga falon, Dada na hakimce saman kujera ta kasa daga kai ta kalleta har ta karaso inda take zaune ta kai kasa tana mata ina kwana.    “Lafiya” Ta amsa mata kamar wacce bata son magana, sannan ta dago tana mata wani kallon wulakanci. Har ga Allah Farhat ta ji babu dadi, ba tsararta ba ce balle ta ce zata rama abunda tai mata kuma ta san duk wulakancin da Dada da Hameeda suke mata suna mata ne saboda ita din ba kowa ba ce. Cikin rashin kuzari ta taso ta fito daga falon, ko da ta dawo part dinta hawaye ya cika mata ido. “Ba dai hawaye nake gani a idonki ba” Kamar daga sama taji maganar, sai tai saurin kallon kujerar Anty Ummi ce zaune fuskarta dauke da murmushin. Tayi saurin fadawa jikinta. “Laaa Anty yaushe kika shigo?” “Yanzu nan na shigo, naga kofar falon ma a bude kika barta, fada min me kika ma kuka?” “Ba komai, ya jikinki?” “Ke zan tambaya ya jiki ai daman ke na zo na gani saboda shekaranjiya na san baki da lafiya, amman yanzu fara fada min dalilin wannan hawayen na ki” Zaunawa yai saman kujera kusa da Anty Ummi ta maida dubansa gurin center carpet fuskarta abar tausayi ta ce “Anty ban san abunda yasa Dada da Hameeda basa so na ba, dukan abunda zan yi ba zan taba burgesu ba” Anty Ummi ta dafata tana murmushi. “Har a bada Dada da Hameeda ba zasu taba so naba balle ke su so ki” Ta dago ta kalli Anty Ummi. “Amman miyasa” “Je ki kawo min ruwa na sha” Tashi tayi tana dariya ta je ta dauko ruwan da kofi ta nufo inda Anty Ummi take. “Anty Amman naga kamar Zain ma baya samun jutuwa da Hameeda” Sai da Anty Ummi ta karbi ruwan ta sha sannan ta ce. “Ina mijinki?” “Baya nan ya fita tun dazu” “Je ki tura kofar falon ki dawo” Ba musu taje ta tura kofar falon ta saka mata keys sannan ta dawo ta zauna kusa da Anty Ummi. “Kuma Anty ita wannan Hameedar ba yar nan gidan ba ce ko?” “Juri'ar gidan nan ce. Mahaifin Zain da mahaifin Hameeda uwarsu daya ubansu daya, mahaifin Zain wato Mai Martaba shine babba, Hajiya Hafsat mahaifiyarsu ita ce uwargidan Mai Martaba, a lokacin ba a bashi sarauta ba, Allah ya jarrabi mahaifiyarmu da wabi, idan tana haihuwar yaya suna mutu wasu su kan tasa wasu kuma tun kuna kanana suke rasuwa, wannan dalilin yasa ya auro Hajiya Maryam tana zuwa ta fara haifa masa yaya mata, bakin kishi da kiyayya irinta ta Hajiya Maryam ya hana mahaifiyarmu zama a gidan Mai Martaba duk kuwa da irin son da take masa, a lokacin da Mai Martaba ya saketa sai taje ya auri Mahaifina wato Alhaji Salisu, ko da ta auri mahaifina yana mata biyu ita ce ta uku, Hajiya Binta ce uwargidansa tana da yaro daya a lokacin, sai kuma Hajiya Mariya, ita tana da yara hudu a wancan lokacin, Alhaji Habib shine babba a gidanmu, bayan auren mahaifiyarmu da wata shida Hajiya Binta ta fita gidan mahaifinmu ta koma garinsu Kaduna da zama ita da danta, wanda a yanzu haka a can take rayuwa ita da zuri'arta, Mahaifiyarmu bata shekara a gidan ba sai da ta haife ni, ina da shekara shida mahaifiya ta rika unkurin barin gidan mahaifinmu, iyakancin kulawa da kauna Mahaifina yana mata amman hankalinta yana gidan tsohon mijinta saboda shi take so, ba dan komai yafi mahaifinmu komai ba, domin a lokacin ba a bashi sarauta ba, a haka ta kashe aurenta ta koma gidan tsohon mijinta wato mahaifin Zain Alhaji Ibrahim Tukur dan maliki, Sarkin Rishim na yanzu. Mahaifina ba bari an tafi da ni ba, duk kuwa da kasancewar Mahaifiyarmu taso taje da ni a matsayin agola amman Mahaifina ya hana, a hannu Hajiya Mariya na zaune, ita ta rike ni kamar mahaifiya, wani lokacin tana kan hana yayanta abu ni ta bani, ta nuna min so da kulawa sosai wanda nake ganin ko da mahaifiyata a tare da ni iyakar abunda zata min kenan. Bayan Mahaifiyarmu ta koma a gidan Mai Martaba da shekara biyu sai Allah ya bata ciki ta haifi Muhammad Zainudden, ita kadai mace data haifawa Mai Martaba dana namiji, ta samu kulawa da soyayya a gurin Mai Martaba da Dada fiye da tunanin mai tunani, bayan Haihuwar Zain ne mahaifina yake bari na zo nan gidan idan mun samu hutu ko kuma idan ana wani abun. A lokacin na dauki Mai Martaba kamar wani makiyina ganin Mahaifiyata ta zabeshi ta bar Mahaifiya bayan kuma shima yana sonta, a lokacin da na fara girma ina zama matashiya Zain na tasowa bama samun jutuwa ko kadan, yadda kika san kare da mussa haka muka taso, idan yaje gidanmu na dakeshi, idan naje gidansu ma sai na dakeshi, hakan yasa tun ina karama bama samun jutuwa da Dada, domin idan na buge mata jika sai ta bugeni ita kuma mahaifiyata sai ta shigarmin. A haka dai wata rana Mahaifiyarmu ta tsareni tai ta min fada ta nuna min nice Babba kuma wata rana ni zai rike Zain, ina karama a lokacin amman sai Allah yasa min natsuwa da hankalin daukar maganar, daga lokacin ban sake fada da Zain ba ko da kuwa shine ya ja ni. Ba ta dade da yi mana wannan fadan ba, rashin lafiyar kwana biyu ta kamata ta sai ta tafi ta barmu. A wannan Ranar mun sha kuka ni da Zain, sai Dada ta dakeshi ta maida shi dakinta tana kula da shi, Mai Martaba kuma ya dauki son duniya ya dora masa, hakan ne yaja masa kiyayyah a gurin Hajiya Maryam tana ganin kamar ita ba a son yayanta kamar yadda ake son Zain. Shekara daya da rasuwar Mahifiyata sai iyayen Hameeda suka rasu, sanadiyar hadarin mota da suka a tare ciki har da Babban dansu Haleema ce kawai ta tsira ita da Hameeda a lokacin suna kamana amman Haleema ita ce babba, a tsakanin Ibrahim da Adamu wato Mai Martaba da Mahaifin Hameeda akwai shakuwa da soyayya da har ta wuce ta yan'uwan juna, suka zama kamar abu daya, rasuwarsa ce tasa ya dauko Hameeda a lokacin tana karama domin kawai ya rika ganinta tana rage masa kewa, Hameela kuma wata kanwar Mahifiyarta ta dauke ta tafi da ita bauchi, sai Dada ta karbe ta ta ajeta a dakinta sai ya zama Hameeda da Zain da Dada Yalwa, a kwana daya suke cin abinci, a tare da suke fita komai zasu yi a tare da Dada suke yi. A tsakanin yan Hajiya Maryam da Zain basa samun jutuwa, ga Zain Allah ya saka masa son yan'uwa da kuma yara kanana tun yana yaro, hakan yasa shakuwa da soyayya ta shiga tsakanin Zain da Hameeda, a lokacin Zain Humee yake kira Hameeda, a tare suke zuwa makaranta duk kuwa da kasancewar ba ajinsu daya ba, idan aka taba Hameeda sai inda karfin Zain ya kare, idan zai siyowa kowa abu to na Hameeda zai fi na kowa yawa. A lokacin nai aurena na farin, every week sai Zain da Hameeda sunje inda nake, a lokacin Zain yana University, Hameeda kuma tana Secondary school, ni kuma na gama NCE sai nai aure. Ana daf da nada Mai Martaba a sarauta ya auro Hajiya Zarah, a lokacin tana da yara uku da wani mijin, sai suka taru ita da Hajiya Maryam suka dorawa Zain kiyayya, hakan yasa Mai Martaba ya sakesu gaba daya, saboda baya son abunda zai taba masa yaro, ya auro Hajiya Hadiza, Hajiya Hadiza macece mai kirki da sanin ya kamata ta rike Zain kamar dan cikinta,m ta yadda har baka iya banbanta shi da yaranta wandanda ta zo da su gidan da kuma wandanda ta haifa a gidan, Bayan nada Mai Martaba a matsayin Sarkin Rishim sai ya dawo da matansa guda biyu daya saka,wato Hajiya Maryam da Hajiya Zarah, a maimakon su daina nuna masa kiyayyar sai suka koma a boye suna nuna masa kiyayyar. Suka shiga tsakaninsa da mahaifinsa da kuma Dada, wata rana Lahadi da rana tsaka Zain ya zo gidana ransa a mace, wai Mai Martaba ya koreshi kuma ya karbe komai nasa, shi kuma Zain be san abunda yai masa ba, Dada kuma ta kasa cewa komai. Muna da dangin uwa, Zain kuma yana da dangin uba amman ya barsu ya zabi zuwa gurina ya fada min damuwarsa kuma ya nemi zama tateyda ni. A gidan da nake aure Babban gida ne, dan haka na ware masa daki daya a cikin dakunan da suke waje. A dakin ya tare a nan yake komai nasa idan zai je makaranta sai ya zo na bashi kudi ko da yana da bukatar wani abun. Daman can Zain ba mutane mai yawan abokaiba, abokinsa daya ne Ibrahim wanda suka taso tare a makarantar jami'a, Ibrahim dan asalin jihar gobe ne, karatu ya kawo shi a makarantar har ya hadu da Zain. A inda yake zama a lokacin shi ma kamar a labe yake, domin wani dan karamin shago ne yake kwana, idan yai kwadagonsa sai ya zo su raba kudin da Zain, domin Zain baya iya aikin wahala a lokacin. A wannan lokacin ne Hajiya Maryam tasa aka dauki yayanta mata aka turasu waje karatu. Tun daga ranar da Zain ya dawo gidana, kullum sai mun fada da mai gidana, saboda yana ganin kamar ni kadai ya auro amman na kawo masa wani a gida yana ciyarda shi. Babu ranar da Hameeda bata zuwa gidan gurin Zain, wani lokacin daga makaranta take tserewa ta zo, wani lokacin kuma daga gida take zuwa, ko kuma ta same shi a makarantar, Hameeda ta siyar da duk wani abu data mallaka ta hada kudin tana yi ma Zain hidima, kamar an rufe bakin kowa babu wanda ya taba zuwa daga familyn Zain yace zai tambayi dalilin barin Zain gidan ko kuma ya shirya shi da Mai Martaba sai kowa ya saka mana ido, ni Hameeda Ibrahim muke dauke da nauyinsa. Rashin jutuwar ta cigaba da shiga tsakanina da mijina na wacan lokacin har ta kai ya bani zabi akan aurena ko kuma dan'uwana, ni kuma na zabi dan'uwana, sai ya sakeni a lokacin ina da ciki na farko na tattara na dawo gidan mahaifina, bakinciki yasa cikin ya zube, a lokacin Zain ya samu wani gidan haya na siyarda kayan dakina na biya masa, ba dan mahaifina ba shi da kudin da zai bani nai masa hidima ba, sai dan bana son kowa ya san halin da dan'uwana yake ciki, kuma bana son dorawa kowa nauyin dan'uwana. Muna ta karatu da addu'a akan lamarinsa, a lokacin ne na koma makaranta domin aure ya fita kaina bayan na cika idda, a lokacin ne na gane amfanin karatu a rayuwar mace, ko ba komai zai taimaki rayuwata na san yancina kuma zai taimakamin na daina tambayar kowa taro ko sisi, mace bata zama sai dan dayan abubuwa biyu, karatu ko kuma sana'a. Sannu sannu, abun ya fara karyewa, sai son da Mai Martaba yake ma Zain ya dawo sabo, ya aiko da kansa aka dauka masa Zain, ya maida shi cikin gidansa har ta kai ko daga nan zuwa can Zain bashi hali dagawa saboda Mai Martaba yana ganin kamar zai tafi ya barshi ne, a lokacin ne Mai Martaba ya fitar da Zain waje gurin karatun likita tare da Ibrahim, kamin ya dawo Mai Martaba ya gina masa private hospital mai sunansa, Zain ya fito kwararren likitan zuciya. kamin ya dawo kasar nan Hameeda duk ta shiga damuwa. A lokacin da Zain ya dawo sai ya fara sabuwar rayuwa mai cike da jindadi da walwala, ni kuma a lokacin nai aure na auri Abban Amal, ban haihu ba sai da nai digree na biyu, a shekara goma na haifi yara uku, I Aliyu, Muhammad da kuma Amal, bayan na haifi Amal na haifi Amal naje nai digree na na uku na samu aiki da Human Rights, haka rayuwarmu take ta tafiya, Zain bashi da yar'uwa ko kuma na ce uwa sai ni, nima bana da abokin shawara kamarsa... ” Anty Ummi ta kare tana share hawayen idonta fuskarta kuma dauke da murmushi. Farhat ta gyara zamanta. “Amman Anty miyasa Zain be aureta ba?” “A lokacin da Zain ya dawo kasar nan, akwati daya yai ma Hameeda ita kadai, Zain ya zo so Hameeda kamar ba gobe, sai dai ba so na soyayya ba, ita kuma ta so shi, ni kaina na dauka Zain son aure yake mata, hakan yasa wata rana da suka je gidana nake masa maganar tun da har ya gama karatu yana aiki ya kamata ya fito ai maganar aurensu sai yace min ba Hameeda yake so ba, shi sam bata cikin tsarin matan da yake so, a nan nai mamaki kuma na bashi shawarar ya rage shiga rayuwarta domin ita son aure take masa, daga lokacin sai ya fara canjawa yana ja da baya, a lokacin ne Dada Yalwa da ita Hameeda suke min kallon makiyiyarsu, suna ganin kamar ni na hana aurenta da Zain, ana haka kwatsan wata rana Haleema ta zo ganin gida ta ziyarci Fadar Mai Martaba gurin kanwarta, sai Zain ya ganta ya fara sonta, ita kuma tai na'am, suka kulla soyayyarsu gwanin sha'awa har ta kaisu ga aure, bayan sun yi aure Mai Martaba ya hada Hameeda da wani dan abokinsa, amman Hameeda ta ki zaman auren saboda tana son Zain, ta fito da ciki ta zubar da cikin, ta dawo gidan nan ta zauna tana ta hada Zain da matarsa, wani lokacin kuma da Dada ko Mai Martaba, sai ayi ma Haleema fada ita a bata gaskiya, ga kuma ciwon daya samu Haleema tun a darenta na farko wanda tun a lokacin Zain yake zargin Hameeda, domin babu asibitin da be nema mata magani ba ciki da wajen kasar nan amman ko ina sai ace lafiyarta kalau, amman idan ta tashu sai tai ta aman jini kamar zata mutu, sanadin hakan yasa ta wahala lokacin da take da ciki, Zain ne yai mata tiyata ya cire mata yaron cikinta, awa daya yaron ya koma ga Allah, kwana biyu ita ma koma ga Allah, Zain yana son matarsa sosai, ya kasa yafewa kansa yana ganin kamar shine silar mutuwarta saboda shi yayi mata tiyata, a lokacin Zain ya koma kamar mahaukaci ya shiga damuwa yana ganin kamar ba zai sake samun wata mata da zai so ta kamar Haleema ba. Zain mutumen da baya son a raina shi, yana son a bashi girma, a lokacin da yake zaune da Haleema suna zaune kamar kawaye, a tare suke komai suna nunawa kansu soyayya da kulawa” Anty Ummi ta kama hannun Farhat. “Ki taimaka min Farhat ki kula da Zain kamar mijin da kike so, ki koyawa kanki sonsa, ki manta da Auwal domin ya butulce miki, kuma ya nuna baya son zama da ke, ki dauki wannan auren a matsayin kaddararki, baki san sakamakon da Allah zai miki ba, kuma bana son ki bani kunya Farhat” Ta dora dayan hannunta saman na Anty Ummi tana murmushi. “Insha-Allah Anty Ummi ba zan baki kunya ba” “Na gode, bari na je Allah ya kara miki lafiya, na san nan gaba kadan Zain zai fara son ki idan kika haifa masa yara” Tayi murmushi a ranta tana ‘Wannan mutumen zai iya aje girman kai ya taba ma, nima gaskiya am not ready’ A fili kuma sai ta ce “Anty ba zaki tsaya na dora abinci ba” “Aa nima yarana yanzu na san sun dawo suna jirana” Har gurin motarta Farhat ta rakota, sannan ta koma ita kuma ta shiga motarta ta shiga Part din Hajiya Hadiza suka gaisa, ta mika gaisuwarta gurin Mai Martaba sannan ta kama hanyar gidanta. 37 Sai da ta fara shiga kitchen ta dora girki sannan ta shiga dakinsa ta gyara masa ko'ina ta canja masa bedsheet, wallet dinsa dake aje a kan aljihun gado ta dauka ta bude bedside drawer zata saka masa, sai ta tsaya kallon abubuwan data gani, dauko tai tana budewa gabanta ya fadi, kar dai ace Zain shaye-shaye yake. “Idan har baya yi miya kawo wadannan abubuwan a nan? Shiyasa yake abu kamar marar tausayi, haka suke basa sa tausayi a take zasu iya kashe mutu” Tayi saurin maidawa ta rufe, ta taso da sauri ta baro dakin, tana fitowa yana hawo stairs, tsaye tai tana kallonsa har ya karaso inda take tsaye kusa da kofar dakinsa. “Ba na ce karki sake shigar min daki ba?” “Saboda baka son naga abunda ke ciki ko?” Ta tsaya kallonta kamar be fahimci zancenta ba. “Do you know what the biggest mistake I have ever done is marrying you, mutumen da be yarda da kaddara ba, babu ruwansa da kowa, and the worst part of it dan shaye-shaye, na tsane ka Zain ban taba son ka ba kuma ba zan taba son ka ba” Uffan be ce mata ba, ya zagaye ta ya wuce dakinsa, sai kuma ta fashe da kukan da baya san na minene? na maganar data fada masa ko kuma kyaleta da yai. Bata san abunda a duk lokacin da tai unkurin kyautata masa sai ta kasa ba. A gurin ta ci kukanta har ta koshi sannan ta tashi ta shiga kitchen ta kashe gas din ta sauke girkin ta shige dakinta ta zauna. Be yi minti talatin dakin ba ya fito daga dakin, ya sauko kasa waya mallake a kunnensa, daga part dinsa part din Dada ya wuce kamar yadda Farhat ta sameta haka shi ma ya sameta fuskarta babu annuri tana hakimce saman kujera. “Dada ina kwana?” “Da ban kwana ba ai ba zaka ganni ba” Yayi murmushin daya tsaya iya bakin lebi ta zauna a kujerar dake kusa da ita. “Office zan je” “Da akwai wanda ya rike kafafunka ne” “Shawara na zo muyi da ke, amman kina min wulakanci” Tayi kamar ba taji ba. “Ina son naje Paris” “Gurin mai?” “Wata daya zan yi na dawo” “Wai gurin me zaja je? Kai da wannan yarinyar zaka je?” “Ko na bar miki ita?” Taja tsaki. Sai yai yar dariya kadan “Ba dadewa zamu yi ba, just one month darling” “Dole ne sai kaje? Aiki ne zai kaika ko kuma yawonka ne kawai” “Aiki ne zai kaini” “To kuma dole sai kaje da matarka? Tafiyar wata daya za ka ce sai kaje da ita?” “Ina son matata a kusa da ni, zan fi jindadi” Kallonsa tai da kyau kamar zata ce wani abu sai kuma tai shiru. Ganin hakan yasa shi tashi ya fice ya bar mata falon. Kai tsaye office ya wuce, wunin ranar be saka komai a cikinsa ba, kamar yadda yake jin zuciyarsa kamar babu komai a ciki, tunanin ya masa yawa har besan da wannen zai fara ba. He just decided ya bar kasar zai fi masa fiye da komai kamar yadda Ibrahim yake ce masa, amman kuma baya tunanin zai iya zuwa ya dade zaune a can tare da Farhat. Wani gurin gurin kuma yana ganin kamar bar kasar ba zai masa ba, shi namiji ne na dole ne a matsa masa auren Hameeda ba, idan har Mai Martaba ba zai masa dole ba to be kamata kowa yai masa dole ba, and yasan Mai Martaba ba zai yarda ya bar kasar ba, idan ma yaje wajen ba kwanciyar hankali zai samu ba tunda yana tare da Farhat. Ajiyar zuciya ya sauke ya kwanta saman kujera yana juyawa a hankali. Yana da bukatar Anty Ummi ita kadai ce abokiyar shawararsa bayan Ibrahim. Da la'asar ya bar asibitin ya dawo gida, sai kuma yaji gidan ya masa ba dadi, wanka yai ya canja kaya, on his way downstairs wayarsa yai ringing, Anty Ummi ce sai da yai kamar ba zai dauka ba sai kuma yai picking, fuska babu annuri kamar ance masa tana kusa da shi. “Zain kana ina?” “Gida” “Yara sun yi missing dinka suna ta tambayarka, kuma nima ina son magana da kai” Sai da ya aje numfashi sannan ya amsa mata da okay. Kitchen ya shiga ya dafa ma kansa indomie, bayan ya gama ya zuba a plate da zimmar ci sai kuma yaji abincin ya guntse shi, sai kawai ya aje plate din ya koma dakinsa ya dauki keys da wasu abubuwan ya fice. Kai tsaye gidan su Anty Ummi, ita kadai ya tarar a falon yara duka sun tafi islamaiya, tana kallon yanayinsa har ya zauna. “Zain duk ka rame?” “Mi nake da shi da zai sa hankalina ya kwanta ko nai kiba, yau kwata kwata ban saka komai a bakina ba” Ya karasa yana kallonta, tashi tai ta shiga Kitchen ta hada masa tea sannan ta zubo masa abinci a plate ta kawo masa. Tea kawai ya dauka ya sha. “Ban san abunda zan yi tunani ba Anty, ban san iya abunda yake damuna ba, na rasa Mamata, kin yi forcing dina na auri Farhat, gida kuma suna ta ganin laifina akan naki auren Hameeda da wanne zan ji?” “Kana manta wani abu Zain, kai fa Namiji ne komai zai iya tafiya a karkashinka, kaga wannan fushin da zafi zuciya babu inda zai kai ka, ka kwantar da hankalin ka fahimci komai...” Ya sake kai kofin tea a bakinsa, yana kallon Anty Ummi, a zahiri ita yake kallo amman zuciyarsa da tunaninsa suna can wani gurin. “Wannan Auwal din yace kai masa ita aikayi a matsayin mai aiki right? Waya kai masa ita? Ya akai aka kai masa ita?” Anty Ummi ta masa kallon Mamaki da rashin fahimta. “Mama again?” “Yes Anty, mu kadai muka san sirrin nan, ke ni Ibrahim Hafsat, Ibrahim ba zai fada ba, amman Hafsat ba zata iya rike mana sirrinmu ba, ina kika hadu da wannan mutumen da kika bawa Mama? Miyasa be kai ko ina ba sai gurin Yayan Hafsat, mutumen da already ya ganta a gidan? Ke kika nemo shi ko shi ya nemi ki bashi ita” “Aa ni na nema, amman ni ban ce ya kaita ga aiki ba, gidansu na ce ya kai” “An saka police sun kamaki saboda yarinyar, wai kin sace ta right? Talaka kamar irin wadannan mutanen police ba zasu iya tsayawa su wulakanta babban mutum kamar kiba, wacce sun san waye ubanki a garin nan, and ansan wanene mijinki a garin nan, wa zai miki wannan wulakanci?” Anty Ummi ta daga kafardarta alamar bata sani ba. “Hameeda ce kawai zata iya miki haka, amman ta ina Hameeda ta samu labarin? I have to find out maybe Hafsat kawarta ce, if not to Auwal ne, amman kuma me zai sa Auwal din yai haka? Bayan bashi da alaka da Mama kuma ba shi da ni? Hameeda zata iya yin komai wajen ganin ta wulakanta ki saboda yana ganin kamar ke kika hanani aurenta, amman kuma miya kai Mama gidan Auwal din?” “I dunno” “Hafsat ce kadai zata warware wannan” Ya yi saurin ciro wayarsa daga aljihu ya shiga blacklist ya nemo Number Hafsat ta cireta daga blocking ya danna mata kira, har tai har ta tsake ba a dauka ba, a haka ya jera mata kiran kusan uku ana hudu tai picking. “Hafsat kina ina?” “Ina gida” “Zaki iya zuwa nan gada biyu ki same ni House number 7” “Why” “Kawai ki zo, gidan Anty na ne ba sai kin fada a gidanku na san ba za a bari ki zo ba” “Okay” Ta amsa kasakasa, yana sauke wayar Anty Ummi ta kalleshi “Zain mi zaka yi karka saka yarinyar mutane ciki matsala” “Ku yanzu ai rayuwar wata yar kuka saka ciki matsala, duk abunda zai samu Mama ko ya sameta saboda ni ne, ya kuma bata fi ya ba, yadda Hafsat take yar wasu haka Mama take yar wasu, so idan zaki fadi wata magana akan Mama za ki kara bata min rai ne kawai” Hannu tasa tai zip up a bakinta. Suna zaune cikin falon suka ji tsayarwa mota, cikin sauri Zain ya tashi ya leka window Anty Ummi, motar Ibrahim ce yana hango yadda suka fito tare da Hafsat suka doso kofar shigowar. “Wato dana kirako shine kika kira Ibrahim ko?” Shine abunda Zain ya fada mata a lokacin da suka shigo falo, sai ta koma bayan Ibrahim ta tsaya kamar wata yarinya tana kallonsa kasakasa. “Yes, yadda kake da temper din nan ai sai ka faketa idan tai maka ba dai dai” Ibrahim ya fada bayan ya zauna kujera daya da Hafsat. “Ko kana nan zan daketa idan tai min shirme” “Aa kana wasa dai, a baka isa ka bugi Amaryata a gabana ba, yadda kasan idan An taba Mama sai inda karfin ka ya kare itama haka ne” Zain ya tabe baki. “Whatever, ke fada min bayan ni da Ibrahim baya san sirrin Hafsat tana karkashin kulawata?” Zain ya karasa yana kallonta, sai tai yi shiru kamar mai tunani. Duk suka zuba mata ido, zuwa can ta kalli Zain da mugun tsoro ta ce “Isma'il” “Wane Isma'il?” “Doc Isma'il, na asibitin ka likitan yara” Ibrahim da Zain sun kalli juna Zain ya ce “Ya aka yi ya sani?” “Lokacin da kake kwana asibiti ne, ya zo yana tambaya wai yaji labarin ka daina kwana gida saboda aiki ya maka yawa a asibiti, shine nace wata kake jinya, shine ya dinga bugun cikina yana ta tambaya a akan yarinyar, har zamanta gidanmu sai ya zo da wata mata itama tana ta bincike akan yarinyar” Tunda take maganar tana murza yatsun hannunta. “Wace mace kuma” Wannan karon Ibrahim yayi mata tambayar. “Sunanta Hameeda tace ita kanwarka ce, wai baka son kowa yaji maganar amman kace mata kana ajiyar yarinya a gidanmu ta zo ta ganta, daga baya kuma tace min karna fada maka” Zain ya zaburo kamar zai daketa sai Ibrahim yai saurin tashi ta tareshi. “Miyasa baki fada min ba tutuni? wace irin banzar macece ke?” “Ai na maka text daga baya” Ta fada tana shirin yin kuka. Zain ya dafe kansa ya juya baya yana dora hannunsa daya a baya. “that's it, daman nasan dole akwai wani abu a ciki” Sai kuma ya juyo. “Fada min Hameeda tana da alaka da Yayanki nan” “Bata da” Ta fada tana share hawayenta. “Make sure you are telling me the truth” Ya fada yana nunata da yatsa, idonsa na nuna tsananin bacin ransa har wani cizon baki yake. [3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *Karki karanta min novel idan baki biyaba, masu sharing Novel dina na barku da Allah. Idan kina son biya ki turo 300 ta 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, sai ku turo da shaidar biyan ta wannan number 08036126660, ko kuma katin MTN na 300 ta wannan number 08036126660* 38. Sai da yamma ta fito daga dakinta ta fito part Dada Yalwa. Bata falo dan hakata wuce dakinta zaune ta sameta saman carpet tana rike da carbi da alama sallah ta gama kusa da ita ta zauna, fuskarta gwanin tausayi Dada ta juyo ta kalleta. “Yau duk baki shigo ba” “Ina dakina bana jin fita ko'ina shiyasa” “Baki da lafiya ne?” “Lafiyata kalau, kawai dai...” Sai kuma tai shiru ta sadda kai kasa, Dada ta kai hannu ta shafa kanta. “Yi hakuri Hameeda komai zai wuce kinji?” “Sai yaushe Dada? Sai yaushe? Ina ganin ina bata kaina lokaci ne kawai, na hakura zan zauna da kowane irin miji zan fitar da wani na aura” “Aa wannan ma ai duk laifinki ne, sai da naso na hanashi auren nan amman kika ce a kyale shi, amman ko yanzu be sha ba nasan yadda zan bulla masa, tafiyar nan na ba zan bari ya yita ba, waya sani ko so yake ya gudu ya bar kasa” Hameeda ta mata kallon rashin fahimta. “Ina zai je?” “Wai Paris gurin honeymoon shi da matarsa” Rasss gabanta ya fadi, tashin hankalin da bata san daga ina ya fito ba a take ya sameta kamar wacce aka ce ma Zain ya mutu ya barta. ‘Honeymoon’ Ta maimaita a ranta tana kallon Dada, with so much confusion on her face, bata ankaro da inda take ba har sai da taji hannun Dada a fuskarta. “Ki kwantar da hankalinki, ba zan barshi yaje ba, kuma kwanan zan tirsasa Mai Martaba ya aureki” “Mai Martaba ba zai cilasta dansa ba Dada, yafi son dansa da kowa, da yana da niyar yin haka da ya aikata tuntuni” “Ki saka idonki kiyi kallon komai zai zo miki a yadda baki yi tsammani ba” ‘Ko kuma shi ya zo masa a yadda be yi tsammani ba, idan har ban samu farinciki da Zain ba, wata mace bata cancanci samun farinciki da shi ba’ Ta fada a ranta, a fili kuma sai ta sake kallon Dada tai murmushi. “Zan yi ta addu'a idan alheri ne Allah yayi, idan kuma ba alheri ba ne Allah ya kawo min mafita” “Amin Allah yai miki albarka, karkisa komai a ranki, nasan yadda zan yi” Ta gyada kai sannan ta tashi ta fito daga dakin cikin wani zafin rai da mamaki. “Shikenan ya manta da ni kenan? Ya manta irin rayuwar da nake da burin mu yi, da gaske baya so a yanzu? Idan har ta tabba gaskiya Anty Ummi kina ciki matsala domin ke kika lalata komai, ke kika shiga tsakaninada Zain...” Magana take a fili kamar ta manta da a cikin gidan take, wani zai iya jinta. Cikin hanzari ta koma dakinta ta banko kofar dakin da karfi “Daga kai har Farhat har Wannan bakar Ummi baku cancanci zama ciki kwanciyar hankali ba, bani da sauran amfani idan har ban saka ku kun fahimci babu farinciki a rayuwarku idan babu a rayuwar Hameeda ba, wannan wasa yanzu zamu fara Zain, sai na baka mamakin wannan karon Zain, duk halin da na shiga Kai ne sila, saboda haka ya kamata ka dandani dacin rashina a rayuwarka, idan har ban ragawa yar'uwata ba, to be kamata na ragawa kowa ba, hakurina ya kare babu wani sauran jira a yanzu kam” Wayarta ta dauko ya lalubo number kawarta Fauziya. Bugu daya ta daga tana zolayarta. “Amaryar Zain, Uwargidan Sarki gobe” “Uhmm Fauziya Zain honeymoon zaije da matarsa a Paris” “What? Ke kuma kina me?” “Nima, yanzu Dada take fada min” “Kina da matsala Hameeda, ke kika yi saka har ya auri yarinyar nan yanzu kuma duk kika sa ke sake ya bar kasar nan da ita ko da zasu dawo da ciki zata dawo kinga ta samu gida kenan” “Kema kin san babu yadda ban yin ba, amman komai yaki tafiya Zain shegen mutum ne Fauziya magani be kamashi, babu yadda ban yi ba amman be taba kamashi ba” “Dole sai ta hanyar magani? Kina abu kamar ba yar boko ba?” “Zan gwada wata hanyar, karki damu nima a yanzu ai be kamata na ragawa kowa ba, Farhat ba zata taba haihu da shi ba, ko ma ta haihu daga ita har shi ba zasu rayu ba, saboda Zain nawa ne ni kadai” “Haka nake son ji yar gari, yar'uwarki ma bata raga miki ba, baki raga mata ba balle kuma wata banza can, idan kin gwada hanyoyi ba su yi ba, ya kamata mu canja wata hanyar” “Zan shigo gidanku gobe insha-Allah. Ya kamata mu yi shawarar wasu abubuwan” “Okay sai kin zo” Daga haka ta aje wayar hannun, ta tashi ta bude bedside drawer ta dauko makulli ta ta bude wata karamar drawer ta dauko hotunan Haleema tana kallona, wani gurin sun yi tare wani gurin ita da Zain da Hameeda wani kuma ita da shi, dayan kuma ita kadai, hawayene ya fara sako mata. “Da ace na san ba zan taba samun Zain a matsayin miji ba, da ban raba ki da shi ba na yi nadamar abunda na aikata, Zain ne silar komai ki yafe min Yayata” Ta rumgume hotunan tana wani irin kuka mai ban tausayi. ZAIN POV. “She betrayed us, daman na fada maka ba zata iya aje mana sirrinmu ba, shiyasa tun farko ban yarda da ita ba, munafuka” Anty Ummi da tunda aka fara abun bata saka baki ba, ta tashi tsaye tana dagawa Zain hannu. “Yanzu dai ya isa, ba laifin kowa ba ne tun farko laifinka ne, babu yadda ban yi akan a sanar da police zaman yarinyar nan a gidan nan sai kan rika kareta akan tana jin tsoro, na san Mai Martaba ba zai taba hanaka ba idan ka dauketa ka shiga da ita Fada a matsayin yar gudun hijira amman kaki, sai kace yar da aka sato, wannan boye boyen da kake shi yaja har Hameeda ta samu damar yi maka haka” Ibrahim ya kalli Hafsat dake kuka ya ce “Hafsat tashi kije wajen mota ki jirani ina zuwa” Tashi tai sunsun ta fice hawaye na mata zuba. Sannan Ibrahim ya kalli Zain “Yanzu miye abun yi?” Anty Ummi ta ce “Ibrahim ina ganin be kamata mu shiga ciki ba, wannan tsakaninsu yan'uwan, dukan abunda Hameeda tai miki ko tai ma Mama saboda shi tai, be kamata mu shiga ciki ba” Sai kuma ta kalli Zain “Ya kamata ka san yadda zaka yi da ita, domin idan baka iya kama barawo ba sai barawo ya kama ka, karka je mata da wannan zafin ran, karka ce zaka mata da karfi domin wayonta ya girmi shekarunta, abu na biyu kuma kansan Mai Martaba be san da wannan maganar ba, sai kasan yadda zaka yi ta, ka kuma san yadda Dada bata son jin sunana a fadarku, dan haka kai taka tsantsan gudun karka sake saka rayuwar Mama a cikin matsala” “And please kar sunan Hafsat ya fito a ciki, kar ta sake shiga wata matsalar” Cewar Ibrahim, sai Zain yai masa wani kallo. “Really? Ita ba rayuwar wata ta saka a ciki matsala ba? Idan ma na gama da Hameeda sai na yi da Yyanta Allah kadai yasan abunda suka hada baki suka mata” Ibrahim ya kara matsowa kusa da shi. “Yadda kasan yana jin yarinyar kauyen nan haka nake jin Hafsat, ya kamata ka san haka they are all women” Yana gama fadar hakan ya juya ya fice daga falon zuciyarsa na mugun bugawa. He see no reason da Zain zai rika cin zarafin Hafsat akan abunda ko wane dan'adam be wuce aikata kuskure ba. Wayarsa ya dauka yai nemo number Hameeda ya aika mata kira, yayi mamakin da wayar tai ringing har ga katse bata dauka ba, yasan bata cika nisa da wayarta ba, kuma indai shi ya kira tana saurin dauka. But this time around sai da ya jera mata kira biyar ana shida ta dauka. “Hameeda kina ina?” “Miyasa ka tambaya?” “Ba amaida min tambaya da tambaya and you know me” Ya fada yana wani abu da fuska kamar ance masa tana gabansa. “Fada min inda kake na zo na sameka” Ya katse wayar, sai ya aika mata da text. Anty Ummi ta kalleshi “Ka tabbatar wannan hanyar zata bulle? Ina ganin kamar yafi dacewa ka bullo mata ta karkashin kasa, ina tsoron karta maka ZAGON KASA, yarinyar nan shu'uma ce” “Ba zan iya wannan ba Anty, kara na fuskance ayi ta ta kare” Yana gama fadar hakan ya maida wayar aljihu ya fice, Anty Ummi ta bishi da kallo. *** *** *** Kuka tai sosai har sai da ta gode Allah bata taba jin zafin rabuwa da yar'uwarta irin yau ba, tashi tai ta maida hotuna sannan ta shiga bandaki tai wanka ta fito ya shirya cikin wani koren yadi mai kyali, ta nufi freezer dake dakin ta bude ta dauko grapes ta zauna bakin gado tana ci, sai kuma ta jefar da plate din ta fashe da kuka. Tana jin wayarta na ringing taki ta duba har ta gaji da ringing ta katse a haka aka jera mata missed calls sai da taga dama sannan ta nufi inda wayar take ta dauka, ganin Zain ne yasa ta share hawayenta ta dauki wayar ta kara a kunnenta.... Yana katse kiran sai ga text ya shigo wayarta. *Ki same ni GRA Ali Gusau road yanzu* Ta gumde baki kamar mai tunani, sai kuma tai saurin waje wayar ta bude wardrobe ta dauko wasu kayan ta saka, sannan ta kira Fauziya. “Yanzu Zain yace na same shi a gidansa da ke gra” “To kije mana, amman miyasa ya nemeki?” “Nima ban sani ba, amman zan je da turaren nan, da na kiraki kawai ki zo please” “Amman kina ganin ya dace a yanzu?” “Yes shi kadai yake zama a gidan be cika zuwa ba ma, sai idan wani abun ne mai muhimmanci saboda yana kai takardunsa, can da wasu abubuwa, idan kuma naga ba shi kadai ba ne sai na fasa” “Eh to haka yayi Allah bamu sa'a, daman tuntuni ai sai nace ki gwada turaren kika ki” Bata kara ce mata komai ba, ta kashe wayar ta saka a jakarta ta dauki makullin dazu ta bude drawer ta dauko wani turaren kwalba mai tsananin kamshi, dake cikin kwalbar magani ta saka a jakarta sannan ta rufe gurin ta dauki mayafinta ta yafa ta fito rike da keys din mota, ta nufi part din Dada. Wannan karon a falo ta sameta zaune ana matsa mata kafafu, da far'a ta shiga tana gyara handbag din dake rataye a kafadarta. “Dada zan fita” Dada ta waigo ta kalleta “Ina zaki je?” “Zain ya kirani yanzu yace yana nemana, wai na sameshi a gidansa a Gra” “Lafiya?” “Nima ban sani ba, wai wata magana yake son mu yi” “Amman ba za ayi a gida ba sai kinje can?” “Ina ganin maganar tana da muhimmanci sosai dan ya fada min baya son kowa yaji, karna fadawa kowa idan zan fita, kema dan karki nemeni baki ganni ba ne” “To Allah ya tsare a kula kin ga ana kusan magariba” Dada ta yi murmushi tana jindadi a ranta duk da bata san dalilin kiran ba amman tana jindadin da har shi ya nemi Hameeda ta zo da kanta. Hameeda ta juyo ta fito tana Murmushi. Da kanta take driving tana jindadi kamar an mata kyauta, ba dadin kiran da Zain yai mata take ji ba, mission din da take da shi akansa take ganin kamar ta kama hanyar nasara. Tun da ta hango gate din gidan abude ta tabbatar da ya rigata isa kenan, gidane plate mai kyau, ko ina tsab kamar ana zaune a cikinsa babu inda yake da datti ko kazabta kasancewar ya dauki mai gyara masa gidan kullum, a gidan yai kudurin zama da Haleema amman Mai Martaba ya hana shi yin nisa da shi, a dole tasa ya zauna a cikin gidan sarautar. A kusa da inda ya aje motarsa ta aje tata, ganin motarsa dai ya tabbatar mata da shi kadai ya zo kenan, it can be possible ya zo tare da Ibrahim suka shigo mota daya, tissue box ta dauko ta ciri guda uku ta bude turaren ta zuba a jiki ta saka a jakarka. Sannan ta fito ta nufi main door. A falo ta same shi zaune yana jiranta, be dago ya kalleta ba, har ta gama kallon falon wanda hakan ya tabbatar mata da shi kadai din ne, daga inda take kokarin zaunawa ta fahimci bacin da ke fuskarsa, sai gabanta ya soma faduwa, wani nisan zango numfashinta yai ya dawo lokacin daya dago ya kalleta fuska kamar ance masa Mai Martaba ya mutu. “Hameeda ke kika shirya duk wannan ko?” Ta masa kallon rashin fahimta, tana saka hannunta a jaka. Sai ya taso ya nufo inda take. “Kika nemi Fake parents suka tsaya akan sune iyayen yarinyar kauye nan ko? Saboda kawai ki saka Anty Ummi cikin matsala” Kamar an zuba mata ruwan zafi haka taji saukar maganarsa a kunnenta, sai tai hanzarin cirs hannunta daga jaka ta tashi tsaye tana kallonsa. “Ban gane ba? Wace yarinya?” “Kin san komai don't you dare pay a game here, idan kina son kwanciyar hankali da zama lafiya ki fada min inda yarinyar nan take, idan kuma ba kiji ba duk abunda zai biyo baya ba zai miki dadi ba” Ta fara hawaye gumi na karye mata. “Ni ban san komai akai ba, ban san mi kake magana, mi aka ce na yi wannan karon?” “Ba cewa akai kin yi ba, kin aikata din ne wannan karon” Tayi baya baya shi kuma yana nufar inda take, sai tai saurin juyawa, ganin hakan yasashi hanzarin rikota ya juyo da ita, sai akwai ta dursuna masa tissue din a hannacin da gefen fuska, kwace fuskarta yai ya rokota da mugun karfi ya jefarda da ita jikin center table, kanta ya bugu da glass table din dake gurin nan take sai jini. Wani irin nauyi yaji kansa yayi hancinsa kuma da mugun yaji, girgiza kan yai sai yaji jiri na dibanshi, baya baya yai ya zauna saman kujera yana fashe hancinsa, sai kuma taji abu ya sauko masa har tsikar jikinsa sai da ta tashi, biyu biyu yake ganin duk abunda ke falo kamin wani irin desires mai karfi ya sauko masa wacce be taba jin irinta ba a rayuwarsa. Rumtse idonsa yai gam ya matse kafafunsa sosai, ji yai he can't control himself hakan yasa shi saurin tashi ya nufi bedroom dinsa ya turo kofar duhu na rufe masa ido. [3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *Masu karanta min novel basu biyaba da masu sharing Novel dina, Allah ya muku yadda kika min. Idan kina son biya ki turo 300 ta 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, sai ku turo da shaidar biyan ta wannan number 08036126660, ko kuma katin MTN na 300 ta wannan number 08036126660* 39 Tana jin lokacin da ya fita sannna ta sauko daga kan gadon ta shiga bathroom ta wanke fuskarta ta sauko kasa. Daidai inda ya aje indomie be ci ba, ta tsaya tana kallonta, kamin ta tabe baki ta dauke plate din ta nufi kitchen da shi, kayan data bata da wandanda ya bata ta hada guri daya ta wanke, bayan ta gama ta gyara kitchen ta fito ta sake gyara falon, ta saka air freshener. Sannan ta zauna a falon for a while sai kuma ta tashi ta koma dakinta, a ciki tai magariba da isha'i sannan ta saka kayan bachi ta kwanta saman gadon zuciyarta cike da kunci da kuma tunani kala kala. *** *** *** Can cikin bachinsa mai kama da suma ya rika jiyo kukan wayar da be tantance na wace wayar ba ne, yana kokarin bude idonsa yaji sun masa mugun nauyi, hakan yasa shi relaxing yaja numfashi ya sauke a hankali sannan ya bude ido. Yes dakinsa yake but he can't remember abunda ya kawo shi nan ba, yana kallon kansa ya ganshi naked. “Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un” Ya furta da sauri tare da tashi zaune, sai a yanzu ya lura da inda yake zaune, kasan carpet yake zaune, amman an turmuza komai na dakin kamar anyi fada, Especially ma bed din. Kukan da yake ji dazun na waya yaji ya karu, saurin tashi yai ya bude bathroom ya dauko bathrobe ya saka sannan ya nufo hanyar falon. A nan ma an bata wasu abubuwan, a lokacin ya tuna da abunda ya faru tun farkon shigarsa gidan. Dafe kansa yai ya ya jingina da kofar. “Hameeda, yarinyar nan duk yadda aka yi kuskuren haihuwa akai ba zuri'ar gidanmu ba ce” Ya fada a hankali yana mamakin yadda lamarinta keta ta azzara. “Me kike so kuma wannan karon? Saboda na gano gaskiyarki ne kika min haka ko kuma you up to something?” Ya kawar da kansa yana jin feeling din da be san na minenen ba, farinciki, bakinciki,damuwa, mamaki, haushi ko kuma me? And still har yanzu yana jin desires din be sake shi ba. Juyawa yai ya koma inda yaji waya na ringing, can karkashin gado ya janyota ashe ma wayarsa ce, number Dada ce ke kiran ta jera masa kira yafi talati. Be yi picking ba har wayar ta gaji da ringing ta katse, sai ya duba agogon wayar karfe goma sha daya saura ya gani na dare, sai a lokacin ya tuna da be yi magariba ba balle isha'i. Da sauri ya aje wayar ya shiga bathroom yai wanka sabulu sannan ya dora na sarki ya fito ya saka wasu tufafin ya gabatar da salla isha'i bayan ya rama magariba. Sannan ya dauki wayarsa dake ta ringing har yanzu ya kashe wayar gaba daya, da kallo ya bi dakin har ya hango wandosa dake can gefen wardrobe ya dauka ya cire keys da wasu abubuwan dake ciki, ya fito nufi motarsa sai da yakai hannu zai bude motar yaji abun a taso masa, jinginawa yai da motar ya rumtse ido yana wani numfashi. Ya kusan minti goma sha biyar a gurin yana kokarin controlling kansa sannan ya bude motar ya shiga ya dauki hanyar gida. Ba yi latti shiga fada ba, daman ba a rufe fada sai 12.00am, so babu wanda zai yi mamakin dawowar yanzu, bayan haka ma ansan yana zuwa asibiti wani lokacin har yankan wuce 11 ma. A part dinsa yai parking, ko kadan ba kawowa kansa zuwa part din Dada a yanzu ba duk kuwa da irin kiran da tai masa a waya, a kunne ya samu wutar falon, kayan kallo ne kawai a kashe. Sai da ya rufe kofar falon ya jingina da kofar for a few seconds, ya nufi kitchen ya bude freezer ya dauko gorar ruwa ya kafa kai be aje ba sai da ya shayensu duka, sannan ya jefar da gorar a kwandon shara ya kashe wutar kitchen likewise ya ka kashe ta falo ya nufi dakinsa. Saman kujera ya zauna, yanzu kam ya manta da zancen Hafsatu manga, dalilin yi masa haka da Hameeda tai yake nema, kwakwalwarsa na ta karanta masa abubuwan da basu gamsar da shi ba. Abun yaji ya koma motsa masa, sai yasa hannunsa cikin gashin kansa ya matse kansa sosai ya dantse bakinsa yana matse kafafunsa. “Ohhh Ya rabb” Ya furta yana rufe idonsa, sai kuma ya tashi ya nufi gadonsa ya kwanta ruf da ciki ya rumtse idonsa sosai yana murje murje a hankali kamar wanda cikinsa ke ciwo. Yadda yai kokarin daurewa sai yaji ya zai iya ba, rabon da yaji kansa a cikin irin wannan yanayin tun Haleema tana raye. Tashi yai ya tube kayan jikinsa ya shiga bathroom ya zauna karkashin shower ruwan na dukan kansa, he used to do this bayan rasuwar Haleema, duk lokacin da yaji abun ya motsa masa but this time around abun ma kamar karuwa yake. Ya kusan thirty minutes a haka sai da yaji abun a na masa yawo kamar kwaro a jiki, hankalinsa ya tashi jikinsa har wani rawa yake kamar mai jin sanyi, fatar fuskarsa ta ciko kamar zata yai kumburi, idanuwansa sun rikedw gaba daya farin ciki ya bace bat. Daker ya unkura ya dafa ginin gurin ya tashi ya fito daga bathroom, kayan bachinsa ya saka ya fito daga dakin, ya tattaro dukan kuzarinsa ya shiga kitchen ya hada ma kansa lemun tsami da ginger ya sha, sai kuma ya sake bude cabinet ya dauko kanwa ya zubaa cup mai yawa ya zuba ruwa be ma jira ta jika ba, ya kafa kai ya shaye yana bata baki, sai kuma ya rike cikin ya duke a gurin kamin ya sulale kasa zaune. Wani irin abu yaji kamar zai mutu, cikinsa yai mugun murdawa ba shiri ya baro kitchen ya shiga bathroom din dake falo ya amaye abunda ya sha, sannan ya wanke bakinsa ya fito ya nufi upstairs. Yana shiga dakinsa ya kwanta, kamar an tsikareshi sai kuma ya tashi da sauri ya fito dakinsa ya nufi dakin Farhat, a bakin kofar dakin ya tsaya ya jingina kansa kamin ya kai hannu ya tura kofar dakin. Wutar dakin na kashe yaji dadin hakan, yana shiga ya maida kofar ya kulle ya karasa a hankali gurin gadonta ya hau gefe daya ya kwanta a kife kamar barawo. Zabura tai ta tashi zaune sai kuma ta sauka saman gadon, ta nufi inda makunnin wutar yake ta kunna, sannan ta juyo tana kallonsa “Ba ka ce na daina shiga maka daki ba, kai me ka kawa ko dakina” Banza yai mata ya juyar da fuskarsa. “Ka tashi ka bar min dakina” Ya dan dago ya kalleta a tsawace ya ce “Ki kashe wutar nan bana son haske, kuma ki zo ki kwanta” “Ki kashe wutar nan bana son haske, kuma ki zo ki kwanta, like serious? Wato kai gaka boss ko? Nan fa dakina ne ba dakin ka ba, idan kana baka son haske sai ka tashi kaje dakinka” Ta fada cike da tsiwa. Tashi yai ya sauka saman gadon ya doso inda take, she thought idan ya zo marinta zai yi ko kuma ya rufeta da duka, sai ta dan juya baya ta rufe gefen fuskarta da tafin hannayenta. Sai kawai taji ya kashe wutar dakin ya dauketa sai saman bed. Sai uku da wani abu na dare ya bar dakin be samu fully satisfy ba, amman he feel relief saboda yanzu yasan abunda yai a cikin hayyacinsa yai komai. Dakinsa ya dawo ya shiga bathroom yai wanka ya fito ya saka kananan kaya sannan ya sake komawa dakinta. Kuka take har yanzu, wutar dakin ya kunna da kansa sannan ya karasa inda take ya kai hannu ya rikota, sai ta buge masa hannu. “Azzalumi wanda be san mutunci mace ba, ka maida mace kamar doll, duk yadda kaga dama haka kake wulakanta ni, baka kusance inda nake ba sai da kaje kayi shaye-shayenka, saboda ka maida ni yar iska, Wallahi ba zan taba yafe maka ba, ashe ma kiyayyar ka ta karyace tun da ka iya kawo kanka inda nake, kayi girman banza wlh kuma girman kanka na banza ne... ” Her last sentence make him smile kadan, before ya dauketa ya kaita toilet, yana ajeta tai saurin daukar bathrobe ta rufe jikinta, tana tsaye har ya gama hada mata ruwan zafi a boket, sai ta saka kafa ta ture bokitin ruwan suka zube gaba daya, kallonta kawai yai from head to toe sannan ya dauke kansa ya shiga hada mata wasu, sannan ya dago ya kalleta. “Zaki iya wanka ko nai miki” Ta watsa masa wata muguwar harara.ta murguda masa baki. “Ke dan Allah baki ji kunya ba? After seen your naked skin, kuma yanzu kina tsaye a gabana har kina murda min baki?” Taja wani irin dogon tsaki tare da sake murguda masa bakin, hannu ya kai ya riko fuskarta yasa dayan hannunsa ya matse mata baki har sai ta taji zafi ta bude bakin tama buge masa hannu, yawun bakinsa ya zuba mata cikin baki sai da ya tabbatar ta hade sannan ya sake ta ya fice daga bathroom din. Fashewa tai da kuka ta ta zauna cikin bathtub, kuka take sosai har cikin ranta taji zafin abunda ya faru, bata shirya ba da budurcinta a gareshi ba, duk da bata san wa zata ba bawa bayan shi ba, amman akwai zafi sosai mutumen da baka so ya kusance ko da shi yana son ka balle shi ma din baya sonka... ****** ****** 8am. Tana zaune cikin toilet dinta tana kuka, kukan abunda ya faru take, kukan farincikin Zain ya kusanceta, kukan bakincikin yau ta aikata Zina, kukan canja rayuwar data samu kanta a ciki a yanzu. Amman kuma bata da wani zabi bayan playing wicked games ga kowa, tana ganin kamar ba ita kadai ce ta cancanci zama cikin bakinciki ba. Tana zaune cikin toilet din taji shigowar Abida, cikin sauri ta tashi ta daura tawul ta fito. Abida na ganinta ta zube kasa tana kwasar gaisuwa, sai Hameeda ta daga mata hannu alamar ta tashi tsaye. Tasssss ta wanke mata fuska da mari bayan ta tashi tsayen kamar yadda Hameeda ta bukata, dafe kunci tai tana kallon Hameeda cike da tsananin mamaki, sai kuma ta fadi kasa ta kama kafafun Hameeda. “Ki gafarce ni shugabata, ban san abunda na aikata miki ba, amman lallai ko minene yana da girma da muhimmanci a gareki...” Hameeda ta tureta, cike da zafin rai ta ce “Munafuka algunguma, ashe duk sirrin da nake da ke, zuwa kike kina fadawa Zain kowa? ke kika fada masa na nemo iyayen karya na lakawa yarinyar kauyen nan ko? Kika fada masa ni nasa a kama Anty Ummi” “Wallahi bani bance Shugabata, baki da bakin Zain bamu yi wannan maganar ba, sai dai idan wani gurin ya jiyo” “Karya kike ke kadai kika san sirrina, sai Fauziya nasan kuma ba taba taba tona min asiriba, sai dai ke manyar kudi ja'ijar banza, yar cin amana, ai daman mutum ba abun yarda bane, balle ke da ba kowan kowa ba” “Wallahi ba ni bace shugabata, ki yarda da ni mi zaisa na fadawa wani sirrinki, ko za akasheni ba zan taba fadawa kowa ba” Abida ta fada tana kuka. Hameeda ta nufi wardrobe dinta ta dauko tsarkar zinarinta mai tsada ta mika mata. “Na ji ungo wannnan ki aje min, saura kuma ki fadawa wani na baki ajiya” Jiki na rawa Abida ta karba ta tashi ta fice har lokacin bata daina kuka ba. Hameeda ta bita da kallo. “Karshen zamanki yanzo gidan nan, ba zaki tona min asiri ba munafukar banza” Ta furta sannan ta dauke kanta ta nufi wardrobe dan daukar kayan da zata saka. [3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *Masu karanta min novel basu biyaba da masu sharing Novel dina, Allah ya muku yadda kika min. Idan kina son biya ki turo 300 ta 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, sai ku turo da shaidar biyan ta wannan number 08036126660, ko kuma katin MTN na 300 ta wannan number 08036126660* 39b Around takwas ya koma dakin dauke da cup din tea, saman mirror ya aje cup din ya kai hannu ya yaye zanen data rufa da shi, hannunsa ya dora saman kanta yaji yayi zafi sosai. Juya yai ya fita yaje ya dauko mata magani this time zauna nai bakin gadon sannan yasa duka hannayensa ya tallafota, cikin bachin ta bude idon tana ganin shi ne ta buge masa hannu. “Ka kyale ni mana” “Magani zaki sha da tea” “Bana so ba zan sha ba” Kallonta ya tsaya yi, nan da idonta ya kawo hawaye gashi kwayar idon ta kumbura. “Kanki na ciwo” “Babu ruwanka, ka kyale mana” Yaja zanen ta sake lullubewa. Be san abunda zai sake ce mata ba, akwai abunda ya sani a yanzu be kyauta mata ba, yasan ba wannan lokacin ya kamata ya zo mata ba kuma a wannan yanayin ba, impact shi be ma taba sakawa ransa irin wannan abun zai faru tsakaninsa da ita. Hannu ya sake kaiwa ya yaye zanen. Sai ta fashe masa da kuka. “Ka kyaleni mana” “Da kin sha tea zan kyaleki i promise” “Ba zan sha ba” Ji yai kamar ya kyale but he can't yana jin kamar be kamata ya barta bata ci komai ba bayan abunda yai mata, and he feel her tears dake ta sauka a idonta, tana masa wani irin kallona na tsana. “Me kike son ki ci?” “Ban sani ba, ka fita ka bar min dakina” “Zan fita idan kika sha, and stop crying” Ji yake kamar ya zalumce ta, and what is more shameful ya sameta ba a yadda yake zarginta, ba zai iya nuna mata ba amman tabbas yaji kunyar zargin da yai mata. Ta sake unkurin komawa ta kwanta sai ya rikota ya janyota ta matso kusa da shi ya mika dayan hannunsa ya dauko tea ya kafa mata a baki. Amaimakon ta sha tea sai ta dago kanta sama ta kalleshi hawaye na mata zuba. “Zain baka jin komai idan kana zalumtar mutum? Miyasa baka da tausayi?” “Just drink, ko na dura miki you know me well” Ya maida kanta bakinta ya saitu da kofin,a hankali yake bata tana kurbawa har ta shanye, sannan ya tashi ya sauka kasa ya dauko ruwa ya dawo ya mika mata tare da maganin. Ta kalleshi “Ba zan sha ba, ka kyale ni mana” “Dan Allah ki sha, bana son rigima da ke a yanzu” Bata amsa ba duk da ya hada ta da Allah, sai taja mayafin rufar ta lullube ta barshi nan tsaye rike da maganin. Juyawa yai ya fita da maganin dan har ga Allah baya son rigima da ita a yanzu, he know what he did tana da bukatar hutu a yanzu. A dinning ya aje maganin sannan ya fice daga part dinsa ya nufi part din Dada, as usual da safe Dada bata zama falo dan haka ya wuce dakinta direct, baya jin sallamar haka nan ta tura kofar dakin ya shiga, sai ya sameta zaune saman gado Hameeda na kwance saman cinyarta ita da Dada duk fuskokinsu na dauke da hawaye. “Tun jiya nake ta kiranka baka dauka ba kuma ba ka zo ba” Dada ta fada tana share hawayenta. Zauna yai saman kujerar dake dakin sannan ya amsa mata. “Ina office, kuma muna tiyata ko da kika kirani, na dawo gida late shiyasa ban shigo ba” “Hameeda ta fada min kana nemanta jiya” Ya kalli Hameeda ba tare da yace da Dada komai ba. “Wai kamin ta karasa inda zaku hadu ta hadu da wani mutum a hanya yana taronta ko da ta tsaya sai ya shaka mata wani abu, bata sake sanin inda take ba sai kusan magariba, ta ganta a ciki wani gida dake unguwar shine ta kira Fauziya da Ikram suka je suka taho da ita, motarta ma sai da aka aika direba ya dauko mata” Gaban Zain ya fadi, jin an ambaci Fauziya da Ikram, hakan na nufin sun ganshi kenan ko kuma wani plan din ne daban. Ganin yayi shiru be ce komai ba ya bawa Dada Yalwa damar cigaba tana kuka. “Fyade aka mata Zain kuma tace bata san ko wanene ba, ni Wallahi ba dan tace ayi shiru a rufa maganar ba da sai nasa an binciko ko wanene a kasar nan an wulankanta shi” Hameeda da idanuwanta suka gama kumbura saboda kuka ta dago kanta ta kalli Dada. “Dan Allah dan girman Allah ku rike min sirrina Dada, daga ke sai Ikram da Fauziya kawai kuka san wannan sai kuma Yarima, idan wannan maganar ta fita martabar masarautar nan zata fadi kuma za a yi ta kallona da abun ne, wata kila ma babu wanda zai aureni” Ta kara fashewa da kuka kamar yadda Dada ma take kukan. Har yanzu Zain be ce komai ba, he was busy thinking of something. Miyasa tai haka? Miyasa bata fada cewa shi ne ba? Ko dai komai be faru tsakaninsu ba? Shin Ikram da Fauziya sun ganshi Naked ko kuma aa? “Dada ba ni guri zan yi magana da ita” Sai a lokacin ta dago ta kalleshi suna hada ido tai sauri dauke nata idon ta daga daga jikin Dada, sai Dada ta tashi ta fice daga dakin tana share hawayenta. Kallonta yai da kyau kamin ya ce wani abu ta riga shi magana. “Na san abunda zaka tambaye Zain, matsalar Anty Ummi ce kawai a gabanka sai taka, to ba karya Abida ta fada maka ba, ni na shirya komai, iyayen karya kama Anty Ummi da siyar da yarinyar da aka yi ga masarautar Damagaram duk ni ce, na yi hakan ne saboda kai Zain, saboda ka kasa fahimtar komai, and wannan lokacin ba wasa nake ba, idan har ban samu cikar burina ba sai na watsa hotunan a cikin masarautar nan, sai na zubar da kimarka da kimar yayan da zaka haifa nan gaba, kuma kai duniya zata zaga saboda fyade kai min, Fauziya da Ikram zasu shaideni domin sun kararda ni Naked a falonka.... Na kirani mahaukaciya ko kuma duk sunan da kake ganin ya dace da ni, amman kai kaja komai....” Ta karasa hawaye masu zafi na sauko mata, OMG she exposed it, he just can't believe daga bakinta wadannan kalaman ke fito, ta bashi amsar tambayar da ba ita zai tambayeta ba, amman ita tafi komai muhimmanci a gareshi a yanzu. [3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *Masu karanta min novel basu biyaba da masu sharing Novel dina, Allah ya muku yadda kika min. Idan kina son biya ki turo 300 ta 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, sai ku turo da shaidar biyan ta wannan number 08036126660, ko kuma katin MTN na 300 ta wannan number 08036126660* 40 Ta dauka Abida ta Fadawa Zain komai shiyasa ta fallasa wannan sirrin har da fadin tasa an siyar da Hafsat a masarautar Damagaram, ta fada masa abunda yake son ji. Kallonta kawai Zain ke yi zuciyarsa na raya masa bata da hankali, taya zata yi duk wannan sannan kuma ta fito kai tsaye ta fada masa kudirinta. Shaye-shayen daya taba ganin tana yi ne ya fado masa a rai, hakan na nufin kwakwalta ta juye kenan ko kuma tana shirin juyewa. “Abida bata fada min komai ba, kuma ba abunda zan tambayeki kika ban amsa ba” “Ta fada maka komai Zain na sani, me zaka tambaya? Yadda za ayi yarinyar ta dawo? Ko kuma kana son ka tambaya na haukace ko ina cikin hayyacina? Ba haukacewa nai ba Zain, ina cikin hayyacina to be frank, kayan mayen daka tarar a dakina ba sha nake ba, na yi kamar ina shan ne a tunani zaka tausaya min ka so ni” Ta kai hannu ta share hawayen idonta, zuciyarta na mata mugun zafi. “Baki ji kunyar abunda kika yi ba? Me yake damun ki ne Hameeda ke wace irin shu'umar macece? Ke baki san rashi ba, baki san kiyayya ba? Kin dade baki yada wadannan hotunan ba, baki cika yar iskaba tun da baki fito kai tsaye kin fadawa duniya abun ba” Ya fada a tsawace zuciyarsa na mugun bugawa, yana mai jin kamar ya janyota da karfi ta buga kanta da gini. Murmushi tai irin murmishi nan da yafi kuka ciwo wasu hawayen bakinciki na fito daga idonta. “Na tambaye ka wani abu Zain? Lokacin daka rasa Haleema ya ka ji? Abunda kake ji a duk lokacin da ka tuna da ita shi nake ji idan na tuna da kai, kasan ba zaka aure ni ba miyasa ka saka na fara son ka tun farko? Ka tsalleke ni ka auri Yayata, ta mutu sai kaje ka dauko wata, na san kiyayya Zain saboda ka nuna min ita a fili, na kuma san rashin saboda na rasa yar uwata Babana, mamata sai kuma kai, bani da wani abu daya rage min a duniyar nan da zan yi alfahari da shi, ka yi min zalumci mafi girma a duniyar nan Zain, ka sana na dasa sonka a inda ba muhallinsa ba, na yi ta masa ban ruwa, a maimakon ya fito yai yado sai sayyunsa suka koma min ciki suna son su haukarta da ni, na bautu Zain na bautu da son ka, amman ladan sakamakona kiyayya ce, mi kake son nai ne Zain? Fada min mi zan yi ka dawo ka so ni kamar da?” “Ko a da ba son soyayya nake nuna miki ba, son yan'uwanta ne, wai ni kadai ne namiji a duniya ne? Ba akwai wasu mazan masu son ki ba? Ki auresu mana” Ya fada a tsawace yana zaburo mata. Hannu tasa ta dafe zuciyarta ta hade wani abu mai da ci. “Kai kadai ne Namiji a duniyar nan Zain, haka Hameeda take gani, idan na kalli idon wani namijin fuskarka nake gani, duk yadda nai kokarin dasa son wani a zuciyata sai na kasa saboda kai kadai nake so, kaji tsoron zuwan wata rana Zain wata rana da Allah zai jarrabeka kamar yadda ya jarrabeni, ba ni na sawa kaina son ka ba, jarrabawata ce ta zo a haka, miyasa ka kasa ganewa? Kaji tsoron addu'ar wanda aka zalumta...” Jikinsa yayi sanyi, sai ya kasa ce mata komai har ta tashi ta fice daga dakin hawaye shabe shabe a fuskarta, tafiya kawai take ba dan tasan abunda take takawa ba, hawaye na rufe mata ido bata ganin komai sa hudu, kamar wacce aka fisgo haka ta zame ta fadi jiri na dibanta. Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un da Zain yaji Dada na fadi ne yasa shi saurin tashi ya nufi falon, sai ya tararda ita kwance Dada na kokarin kamata. He was helpless sai kawai ya sa kai ya fice daga gidan gaba daya, ya saba zuwa gaishe da Mai Martaba da safe amman yau be tsaya gaishe shi ba ya fice. He was busy thinking of inda zai je, gurin Anty Ummi ko gurin Ibrahim, but seriously he don't know what to do now he needs someone da zai magana da shi. A harabar gidan Anty Ummi yai parking din motarsa bayab yabi shawarar zuciyarsa na son magana da yar'uwarsa fiye da abokinsa. Fito yai ya shiga cikin falon, Baba Asabe akwai ya tarar tana aikin gyara falon, tana ganinsa da risina ta gaishe shi, ya amsa mata tare da nufar dakin Anty Ummi, sai da yai knocked sannan ya tura ya shiga, tana tsaye gaban madubi tana fasa turare da alama yau da wuri zata fita, juyo yai ta kalleshi fuskarta dauke da murmushi. Sai dai yanayin yadda taga fuskarsa yasa ta zauna bakin gado tana cigaba da kallonsa. “Zain lafiya dai?” Hannayensa biyu yasa ya shafa fuskarsa ya cika bakinsa da iska ya busar sannan ya kalli Anty Ummi ya ce “Ya zaki ji idan na ce miki i raped Hameeda or Hameeda raped me, maybe we raped each other, zai kuma iya yiyuwa ba mu yi din ba” Anty Ummi ta tsaya kallonsa, at first dariya ta fara yi, sai kuma ta rike baki. “You're not a drunker, bari na ce ko wani abun kasha, na san kuma ka fada min zaka je kai magana da Hameeda jiya then what happen” Yayi shiru kamin ya ce “Maybe tana jiran ranar da zan kebe da ita ne dama, ni dai nasan ta zo na fara tambayarta kawai ta shafa min abu a hanci na buga kanta da table na shige daki, daga nan ban sake sanin inda nakeba, ina farkawa na ganni Naked, and yau da safe Dada na fada min wai wani yayi raping din Hameeda” Anty Ummi ta daga masa hannu. “Wait wait, ni fa ban gne kan wannan labarin ba” A nan ya kwashe abunda ya faru tun barinsa gidan ya fada mata. Anty Ummi ta tsaya tana mamaki. “Zain, Hameeda deserve you, idan har mace kamar Hameeda mai ji da kanta yar sarauta zata iya yi maka haka, to ta cancanta ka aureta, ina tsoron halin da zata shiga nan gaba, zata iya kashe wani akanka Zain ko kuma ta kashe kanta, kuma na tabbatar ba zaka taba son haka ya faru ba, ba kyau dan'uwanka yana cutuwa da abu kuma ka barshi ya cigaba da cutuwa da shi bayan kuma kana da yadda zaka yi a sama masa mafita” “Anty ko dai baki gane kan abunda tai ba ne? Shikenan kuma ni sai na cutar da kaina na aureta? Bana son ta ban taba mata son aure ba” “Wani lokacin so ya shigar mutum ne da inda be yi zato ba, kamar yadda yai ma Hameeda, wani lokacin kuma muna iya koya ma kanmu son, saboda muso yan'uwanmu, wani be iya so ba Zain, ka tausayawa yarinyar nan, kar ta fada hallaka, ji yadda Allah ya jarrabeka da son yarinyar kauye nan batanta duk yasa ka bi ka rude, yanzu idan wani abun ya same ta ya zaka ji?” “Nono Anty Allah ya tsare ni fa ba son aure nake mata ba, ba son soyayya ba kawai dai ina mata kallon yata ne” “Zain kai yi tunani, idan akwai yiyuwar hakan, ka daure ka aureta ko da na dan wani lokaci ne in yaso sai ka rabu da ita” “Ai dana aureta Dada ba zata bari na rabu da ita ba, ni ba wannan ba, yanzu so nake ki fadawa Farhat ta yarda ta bini zan cewa Mai Martaba zamu je Damagaram gurin honeymoon ni da ita, sai na dauko Mama” “Mama dai Mama dai yanzu kaji inda take hankalinka ya kwanta ko? Sai kuma me? Ai Farhat Matarka ce kai kafi dacewa ka sakata taje ba ni ba” “Bata jin magana ta Anty” “Baka mata da dadi ne shiyasa bata jin maganarka” “Amman ai ni mijin” “Shikenan dan kana miji sai kawai ka shigo cikin gida kai gaka boss kana mata yadda kake so” “Haka tace miki?” “Na san hakinka ne ai idan baka son abu, ita ma kuma na mata fada kuma na san ta gyara sai dai idan kaine baka gyara ba” “Kin gani ko? You always take her side” “This is not the right time to take anyone side, kawai ina fadar abunda yake shine kai da ita duk ya kamata ku gyara, zama aure ba haka ake yinsa ba, be kamata ace dayan na danne hakkin wani ba, yarinyar marainiya ce, gashi mahaifiyarta bata son auren nan, dukan abunda ya sameta a yanzu dariya zasu mata, da hakure a haka tana zaune da kai kuma ka zo kana gallaza mata” “Ita take hakuri zama da ni ko kuma ni nake hakurin zama da ita? Jin wata magana Anty kamar dai ita ce taki ni tsintoni kika kai” Ta tabe baki ta tashi. “Yanzu dai hankalinka ya kwanta ka gano inda yarinyar take, sai ka nemi gurin ajeta dan ni ba zaka ja min wani ballin ba, Abban Amal ma nasan ba zai yarda ta zauna a nan ba” “Ba zam ma zaunar da ita a nan ba, a cikin masarautar mu zan kaita, i feel like naje yau na daukota amman ba dama tun da Farhat bata da lafiya...” “Miya sameta” Anty Ummi ta tambaye shi da sauri. Sai ya daga kafadunsa. “I mean bata cikin far'a kin san yadda take ai, idan naje zan bata ki yi magana da ita” Ya tashi yana saka hannayensa aljihu. Bata sake ce masa komai ba har ya fice, tana tausayin Zain ta wani bangaren saboda halin daya shiga, zama da Farhat ga kuma Hameeda data taso shi a gaba yanzu, ga kuma Hafsatu manga da yake kokarin saka kansa cikin wata matsalar saboda ita. Bata tunanin kai Hafsatu manga a masarautar abu ne mai sauki a gareshi, sai dai tana ganin hakan shi yafi dacewa duk kuwa da kasancewar bata san abunda gaba zata haifar ba. Daga gidan Anty Ummi asibiti ya wuce, a can ya wuni, a can ne yake fadawa Ibrahim yadda suka yi da Hameeda yayi dariya sosai yana jinjina shu'umancin Hameeda Sai da yamma ya koma gida bayan ya biya a ten o seven ya tsaya yai musu takeaway, a falo ya samu Farhat tsaye, tana sanye da doguwar riga hannunta rike da cup. Tana ganinshi ta aje cup din ta nufi stairs. Da kallo ya bita har ta haye sannan ya aje ledodin a dinning ya hau sama ya watsa ruwa ya canja tufafi ya sake saukowa kasa, ya dauki takeaway ya nufi dakinta. Tana ganinsa ta juyar da fuskarta ta mikar da kafafunta ta kwanta, kasa ya aje ledodin ya zauna bakin gadon yana kallonta. Be san me zai ce mata ba, tashi ki ci abinci ko kuma ya jikinki yake? Hawayen daya fito ta gefen idonta ne yasa shi jin tausayinta for the first time, ya san be kyauta mata ba, ba kamata ya zo mata a cikin yanayin daya zo mata, but yayi farincikin daya sameta a mace, zargin da yake mata ya tafi, yanzun kan yasan ba duka mai shigar banza ce yar iska ba, wasu suna yi a tunaninsu wayene bayan kuma suna zubarwa da kansu mutunci ne kawai. Hannu ya kai ya shaye mata hawayenta sai ta buge masa hannun ta tashi zaune. “Ka daina taba ni bama” “Ga abinci ki ci? Fada min me kike ji yanzu?” “Ina ruwanka ba zan ci ba” Hannayensa biyu yasa ya rikota da dukan karfinsa sai gata ta dawo saman jikinsa, sai ya matse kanta a kirjinsa, dayan hannunta kuma ciki hannunsa yana murzawa. “Why are you so stubborn? Na san na yi kuskure amman ai sai kiyi hakuri komai ya wuce” “Kai a gareka ya wuce ni gurina be wuce ba, kuma ba zan taba mantawa da wannan ranar ba” Ya fada cikin kuka tana kokarin janye kanta daga jikinsa. A maimakon ya saketa sai ya juyo da ita ya zama bayanta ne ke gugar kirjinsa a yanzu, sai ya kai bakinsa saitin kunnenta ya rada mata. “Ban ce ai ki manta da wannan ranar ba, you know it's special, nima ba zan manta da ita” “Special day da miji yai raping din matarsa ba” “Bakinki ba zai daina fadar irin maganganun nan ba ko?” Yatsanshi ya saka cikin bakinta ya rika watsa da halshenta yana soka mata shi har can kasan halshenta. Cizo ta gatsa masa ba shiri ya saketa ya zare hannun yana yarfarwa. Ita kuma ta sauka saman gadon ta zimmar bar masa dakin, sai yai saurin fisgota ta fado kansa ya rumgumeta da dukan karfinsa, tana jin yadda zuciyarsa take mugun bugawa as well as yake jin yadda nata zuciyar ke bugawa. Dayan hannunsa ya kai ya ciro wayarsa daga aljihu ya kira Anty Ummi sai ya saka hands-free. “Anty Ummi zata yi magana da ke” Sakinta yai ya mika mata wayar, sai ta ki karba har Anty Ummi tai picking. “Anty fadi tana jinki” “Farhat” “Na'am” Ta amsa tana share hawaye. “Kina lafiya” Sai da ta kalli Zain sannan ta amsa. “Lafiya ta kalau” “Kin tabbata? Idan akwai wani abun ki fada min” “Ba komai, amman Anty kin san nace miki ina son waya” “Ban mata ba, Zain zai baki kamin ku tafi” “Ina zamuje?” “Raka shi zaki yi Damagaram ya dauko wata yarinya, na san ai ba zaki ki ba” Tayi shiru na wani lokaci, ba damar tace ba zata ba tunda Anty Ummi ce, sai dai kuma bata jin zuwan tunda hidimarsa ce ba tata ba. “Yaushe?” “Shi zai fada miki lokacin, kin yarda?” “Ee amman sai an fara bani wayar” “Ba matsala zai baki” “Na amince” “Allah ya miki albarka” One word Anty Ummi bata kara ba ta kashe wayar. “Me zaki yi da waya?” Ta shareshi tana tsaye a gurin har ya bude ledar ya fiddo kayan dake ciki. “Ba tambayarki nake ba?” “Wace yarinya ce za aje daukowa?” Ya dago kai ya kalleta “Ba a maida min tambaya da tambaya” Ta dauke idonta daga kallon da yake mata ta juya ta nufi bandaki. Sai a yanzu ya lura da tafiyar da take. “Kina jin ciwo ne har yanzu?” Daf da zata shiga bathroom din ya furta nata haka. Sai ta juyo ta tsaka matsa tsawa. “Ban sani ba” Taso yai da sauri ya doso inda take fuskarsa a hade.... [3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *Masu karanta min novel basu biyaba da masu sharing Novel dina, Allah ya muku yadda kika min. Idan kina son biya ki turo 300 ta 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, sai ku turo da shaidar biyan ta wannan number 08036126660, ko kuma katin MTN na 300 ta wannan number 08036126660* 41 Wunin ranar a part din Dada ta wuni, duk yadda Dada ta so ta kaita asibiti sai ta ki, ta ci kuka sosai kamar ba gobe. Tayi tunanin Zain zai tausaya mata ne, ga mamakinta sai ya tsallaketa yai tafiyarsa ga shi har dare yayi be sake lekowa ya ce ya jikinta ba. Duk irin tambayar da Dada Yalwa tai mata akan ta fada mata abunda suka tattauna da Zain lokacin da ta bar musu dakin Sai Hameeda tace babu komai, daga karshe ta taso ta baro mata dakin ta dawo dakinta. Bakin gado ta zauna tana kallon kofar bandakinta. “Wato duk irin hali da kalamin da nai masa be saduda ba ko? Bazarana ta ba zata yi aiki ba idan har banyi da gasken ba” A fili tau maganar sai kuma wata zuciyar ta jefa mata tambaya. ‘Anya baki yi gaggawa ba? Ai ya kamata ki bashi lokaci dazun fa aka yi haka, ai sai ki dan bashi lokaci kiga idan be yi komai ba tukuna’ “Kai Zain ne fa, abu na be cika daukarsa serious ba, yanzu na san zuwa zai yi ya fadawa Ummi wata kila ma su dauki matakin da zai wargasa nawa shirin?” Ta furta sai kuma ta tashi tsaye ta nufi karshen gadonta tana ta magana da kanta. “Zai iya zuwa ya dawo da yarinyar nan fa, amman ko da ya dawo da ita ai ba zai ga mutanen ba, balle su tona min asiri, nima ba zan yi sakacin da asirina zai tonu ba, amman nasan matukar ya dauko yarinyar asirina zai iya tunuwa domin zata iya nuna ni, amman ba lallai ne kowa ya yarda ba, idan kuma Zain yai wasa nuna tonan min asiri a cikin masarautar nan sai na tona nasa” Ta juyo. “Be kamata na dorawa Abida sata a yanzu ba, duk ta ta tona min asiri akwai aikin daya kamata ta min, yarda ce kawai ba zan sake yi da ita ba, idan ta san wata ai bata san wata ba” Ta nufi inda wayarta take ta dauka, missed calls ta tarar ciki har da na Fauziya da kuma na wata bakuwar number, contacts dinta ta shiga ta nemo wata number yan nijar da aka rubutawa Fulani mai +227 ta danna mata kira. Tayi mamakin da waya bata shiga har yanzu, rabon da tai waya da su tun lokacin da suka fada mata cewar sun siyarda Hafsatu manga a masarautar Damagaram. Komawa tai ga number Fauziya ta kira bugu daya ta daga. “Kawata ga hotunan an wanko, na yi ta kiran wayarki baki daga ba” “Bana kusa ina dakin Dada” A nan ta kwashe labarin abunda ya faru ta fadawa kawarta. “Kin san ni abunda na fi tunani? Ina ganin wannan bakar Yayar tasa ta shiga tsakaninku ne, saboda bata son ki ina ganin ta masa asirine ta dauke hankalinsa daga gareki shiyasa komai kika masa baya taba son ki” “Ina tunanin haka, amman kuma ni miyasa idan nai masa asirin baya kama shi?” “Wata kila har yanzu bamu dace da wanda zai kama shi din bane, amman kin fada masa Ikram da ni mun ganshi?” “Ee na fada masa, amman kamar be damu ba” “Anjima zan zo ma kawo miki hotunan ki nuna masa dan ya san da gaske muke” “Hakan za ayi, amman yanzu ina son ki fara tuntubar matar nan da ta hada ki da su ko Allah zai sa a samu layinsu ko kuma wani line da suke amfanin da shi” “Wallahi ko jiya na yi waya da ita tace itama bata samun layinsu a yanzu, amman ki kwantar da hankalinki babu yadda zai samesu domin su tuni suka bar garin, ko da yaje sai dai ya tararda yarinyar, kuma kin ga ita bata san inda zata zata samosu ba, dan haka babu wata hujja ta tona miki asiri” “Amman yarinyar idan ta ganni zata iya shaidani ai” “Ko ta shaideki Zain ne kawai zata fadawa shi kuma ya san komai, be kuma san inda zai same iyayen ba, abu na biyu bana jin zai kawo ta cikin fadar nan ma, ba ma lallaine yaje daukota ba tun da be san ta wace Siga zata shigo Masarautarku ba” “Haka ne, ina jiran hotunan zan ga abunda iya yi” Daga haka a kashe wayar ta nufi bandaki. ZAIN POV. Mai Martaba ya juyo ya kalleshi yana karantar abunda ke shimfide a fuskarsa. “Me zaka je yi a Damagaram?” “Lokacin da ina neman Farhat, na yi mata alkawarin idan na aureta zan dauke ta muje garin saboda wani kanen mahaifinta dake can, tun shekaranjiya take min maganar ni kuma bana son tafiya sai da amincewarka” Mai Martaba yayi murmushi. “Ka kyauta, na san kai ka matsayin da zaka iya tafiya duk kasar da kake so ba tare da ka tambaye ni ba, amman hakan da kake yana kara min sonka kuma ina jin na yi dacen da, duk da kasancewar kai kadai Allah ya bani namiji be sa ka lalace ce kamar sauran wasu yayanba, Allah ya maka albarka” “Amin Mai Martaba na gode sosai, ina jin ba zan wuce kwana biyu ba, shine nake rokon idan da hali Mai Martaba yai min alfarmar kiran sarkin Damagaram ya sanar masa zuwa na, ina ganin kamar yafi kyau da kuma kyautuwa na sauka a masarautar” “Ba dole ne, sai masarautar ta san da zuwanka ko saukarka ba, zaka iya shiga ka fito ba tare da sarkin ya sani ba” “Na san da wannan, amman ina ganin kamar zan fi jindadi idan na sauka a masarautar, ko ba komai matata zata samu kyakkyawar kulawa kamin mu dawo” “Mu da bama son a san da aurenka akan me zaka sauka masarautar, kuma tare da matarka” Zain yayi shiru na wani dan lokaci kamin ya ce. “Mai Martaba ina son matata, matata ba gurguwa bace ba musaka ba, tana kyau da duk wanda ya kalleta sai ya yaba da kyauta, kun yi mata suturar da zata iya shiga ko ina ta nuna kanta, bayayyiya ce kuma yar boko, talaucin gidan ne kawai matsalarta, kuna tsoron ace danku ya auro yar takalawa, bayan kuma talaucin da arzikin duk daya ne a gurin Allah, miye laifina dan na nunawa duniya matata? Yafi kyautuwa aji kunya kamin aure ba yan anyi ba, a gafarce idan maganganuna sun yi tsauri” Yanayin yadda yake maganar ne ya karantar da Mai Martaba cewar Zain be jindadin yadda suke masa akan matarsa. “Abunda baka gane ba, Masarautar Rishim masarautace mai kima da kwarjini, masarautace da babu irinta a fadin kasar nan, auren zumunci, kuma yayan fulani, ko yayan sarakuna abune da aka san masarautar nan da shi tun kaka da kakanni, kwatsan sai kuma aji kayi watsi da wadannan al'adun ka auro wata bare can dabam ba yar sarauta ba kuma ba tsatsonmu ba” “Irin wadannan abubuwan sun fi tasiri a zamanin baya Mai Martaba, ban taba fadawa kowa ba, amman nasan labarin auren nan ba iya familynmu kawai ya tsaya ba, idan aka boye lamarin yayan da zan haifa da ita suka taso ba zasu so ayi musu wani kallon ba, nima kuma ba zan so a kirasu da wani sunan ba, idan har aka aiyanta Farhat ina jin kamar ni aka yi ma, idan kuma aka min kai an taba masarautar nan ne, na kuma san Mai Martaba ba zai jure ana kiran jikokinsa da wani suna ko kuma ayi musu wani kallo wanda be kamata ba” “Lallai sarakuwarmu ta samu zama a zuciyar Yarima, yau shi da kansa yake mata kanfe” Zain yayi murmushin daya bayyana fararen hakoransa, yana mai jin nauyin maganar da Mai Martaba yai duk da murmushin dake kan fuskarsa. “A dawo lafiya, Masarautar Rishim zata sanarda zuwan Yarima da gimbiyarsa a gurin Sarkin Damagaram” Zain ya daga masa hannu cike da jindadi. “Godiya nake Mai Martaba Allah kara maka lafiya” Cike da farinciki ya baro part din Mai Martaba ya nufo part dinsa, ba dan komai ya zabi sauka masarautar ba sai dan ya samu damar yin bincikensa hankalinsa kwance, ko da wani abun ya biyo baya ba zai bashi matsala ba tunda Mai Martaba ya san da zuwansa Masarauta. Be shiga part dinsa ba, sai da ya bude motarsa ya dauko kwalin waya sannan ya rufe ya shiga falonsa. Yadda ya bar falon haka ya sameshi, inda ya ci abinci da ruwan da yasha ba a dauke ba, daman tun jiya bata sauko daga dakinta saboda kawai ya matsar mata baki sakamakon tsawar da tai masa, abinci ma sai da ya hau da safen ya kai mata haka ma da rana. Bayan sallah isha'i ne ya fita nufi part din Mai Martaba dan yi masa maganar. Saman center table ya aje kwalin wayar ya dauke plate din ya kai kitchen, sannan ya tsaya hada musu tea. Daga kwance taji motsin shigowarsa a tunaninta ya wuce dakinsa dan haka ta tashi ta fito daga dakin da samawa kanta abunda zata ci, tana saukowa downstairs Hameeda na turo kofar falon ta shigo. Sai tai tsaye tana kallon Hameeda, kamar yadda itama ta tsaya jikin kofar tana yi ma Farhat wani mugun kallo ta ita kadai ta san ko na minene, sai kuma tai murmushi ta mika mata takardar dake hannunta. “Ga sako ki ajema mijinki” Farhat sai da tai yi kamar ta tace ba zata karasa inda take ba, sai dai ita ta karaso sai kuma wata zuciyar ta hana ta, tana unkurawa zata taka Zain ya fito daga kitchen din dauke da cup din tea biyu hannunsa. Ganin Hameeda rike da abu a hannunta tana mikawa Farhat yasa yai saurin karasa inda Farhat take dan yafi kusa da iya ya sha gabanta ya mika mata cup din. Karba tai amman ta ki zuwa tana son tai masa tirjiya kamar yadda ta saba, sai ya saka dayan hannunsa ya riko kugunta ya juya da ita tare da rada mata. “Duk kika min tirjiya a gabanta, sai na murje ki yadda nake so yanzu nan kuma try me” Sakinta yai ya juyo ya nufo inda Hameeda take tsaye ya kai hannu zai karbi takardar, ashe kasan hutuna ne, sai akwai ta saki suka watse kasa. Wata muguwar Harara ya watsa mata. “Risina ki dauko su” Ba musu ta duka ta kwashe hotunan ta mika masa, sosai take son Farhat ta gani sai dai inda take tsaye bata iya hango abunda ke cikin hotuna iyakar abunda ta fahimta dai kawai hotuna ne. Fisgarsu yai da ido yai mata magana ta juya ta fice daga falon, sannan ya saka dayan hannunsa ya dauki takardar ya dora saman hotunan ya nufo inda ya aje wayar Farhat ya dauka daga inda yake tsaye ya mika mata. Kin zuwa tai takarba, ta tsaya daga gurin tana kallonsa. “Phone” “I know ka zo ka kawo min mana” Ya wara ido yana kallonta da kyau, sai kuma yai murmushi kadan. He can't believe Farhat ce take masa haka, ya gane yanzu dai bata tsoronsa ko kadan sai mai rashin kunya da take masa ce ta karu, karasa yai kamar yadda ta bukata ya mika mata wayar, sai ta mika masa teasa daya bata dazun sannan ta karbi wayar ta nufi upstairs ba gode bare na gode, ko alamar jindadi da murna ba tai ba. Da kallo ya bita sai da ta shige cikin dakinta sannan ya jiyo ihunta, ta wani bangaren yana daga mata kafa ne saboda fada mata da yai ba tare da yardarta ba, wannan babin kan yasan ya saba mata kuma ya yi abunda be kamata ba dan haka dole ya bita a yadda take masa ko dan su zaune lafiya. A yanzu so yake yaji da bangare daya, bangare Hameeda da kuma Na Hafsatu manga, abunda yake ganin idan ya samu Hafsatu manga ta dawo hannunsa ya tabbatar da lafiyata hankalinsa zai kwanta. Saman kujera ya zauna yana duba hutunan daya bayan daya. Shine a cikin hotunan wani gurin yana tare d Hameeda kwance saman gadonsa wani gurin kuma tana kan kirjisa, a dayan kuma babu kyau ganin sai dai kana ganinsa kasan baya cikin hayyacinsa. Kansa ya shafa yana furta “Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un” A take yaji babu dadi, a da bashi da tabbacin ya aikata amman yanzu yana da shi, tun da gashi a cikin hoton, jinginawa gai jikin kujera ya lumshe idonsa, sai ga hawaye ya zubo masa, be taba jin tsanar Hameeda ba a rayuwarsa kamar yau, shi kansa a yau ji yake ya tsani kansa, ba dan komai ba sai dan abunda ya aikata, tun yana sarauyinsa be taba kusantar wata macen da ba muharramarsa ba sai yanzu. Shi yai kana kyamar kansa a yau ya tabbatar da ya kusanci daya daga cikin manyan zunuban da Allah baya so, kuma ya yar'uwarsa. A guri ya zaune har dare ya raba sannan ya tashi ya shiga bedroom ya saka hotunan cikin wardrobesa ya shiga bathroom yai alwala. Har garin Allah ya waye zaune saman carpet yana istigifari da neman Allah ya yafe masa, ji yake kamar shine ya kai kansa da kansa. Sai takwas da rabi na safe ya fito daga dakinsa, yana sanye da short da white vest, ya nufi dakin Farhat, zaune ya sameta tana ta aikin taba waya kamar bata taba ganinta, tana ganinsa ta wani hade rai. A bakin kofa ya tsaya yana mata magana. “Ki shirya zamu je a dauki hotonki anjima, saboda za ayi miki passport” “Ina kwana?” Ta fada kasa kamar bata son magana. “Lafiya kalau” Ta dan dago ta kalleshi jin ya amsa ta, yana kokarim juyawa ya fice ta ce “Wayata ba kati kuma ina son magana da Mamana” Be juyo ba be kuma amsa ta ba, ya sauko kasa, breakfast ya hada ya zuba nata ya shiga har dakinta ya kai mata, ba tare da shi ya ci ba, he care about her tunda tana karkashinsa, daman kuma tun abunda yai mata ta daina dafa abinci sai dai yai order ko kuma ya dafa. A tare suka fita bayan sun shirya cikin manyan kaya daga ita har shi, har aka isa gurin passport aka yi musu abunda za ayi aka gama, Zain be kalli inda Farhat take ba. Shi ya dawo ya sauke ta, sannan ya karbi wayarta da zimmar saka mata layi sai ya tararda line ta ciki, be yi mamaki ba danan Anty told him ta mata welcome back na Sim dinta, dan haka ya dauko number ta yai mata transfer though bank ya mika mata wayar. “Thank you” Wannan karon ta gode amman bata nuna masa jindadinta ba, tana tunanin kamar idan ta nuna mata taji dadi zai raina mata da wayo ne, sai a yanzu ya kalleta sai kuma ya dauke kai, bayan ta fita daga cikin motar ya kama hanyar asibiti. [3/17, 2:09 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 42 Misalin biyar saura kwata na yamma jirginsu ya sauka Niger Republic. Sun samu kyakkyawar tarba daga gurin Sarkin Damagaram wato Sarki Idrissa Abdourahmane Idrissa II (Fake Name), tun daga airport Sultan of Damaragaram a aika da motoci aka dauko Yarima Zain. Mai Martaba Sarkin Damagaram wato Sarki Idrissa Abdourahmane Idrissa II yayi farinciki sosai da ganin Zain, a bakin kofar shiga fadar sarkin yasa dogaransa suka sakawa Yarima Zain wata kyakkyawar alkibba da raya masa wani kyakkyawan kambu aka aje masa takalmin fata, daya daga cikin kannan yayan sarki ta zo ta mika masa takobi, kamar yadda aka masa aka yi ma Farhat sai dai ita a maimakon takobi sai dayan yarinyar ta bata kwaryar nono. Da yarensu suke masa barka da zuwa ana nasa busa har ya ya iso cikin fadar. Sai wasu dogaran suka zo suka karbar masa takobin da kwaryar nonon dake hannun Farhat. Sun samu minti Talati a fadar Zain yana gaisawa da Sarkin Damagaram sannan aka kaisu masaukin da aka tanadar musu dake can yamma da fadar. Suna shiga Farhat tai saurin cire alkibbar da ke jikinsa ta aje ta shiga bathroom, kamar wacce ta shiga daki haka ta zauna a bandakin, har ya gaji ya jira ya tashi ya tura kofar bandakin, sai yai saurin saka hannayenta ta rufe jikinta. “Miye haka? Ya zaka shigo kuma ina ciki?” Kallon kawai yai ya dauke kai yai fitsarinsa ya fito ba tare da tunanin komai ba. “Wanka zan yi kiyi sauri ki fito” Ya furta sannan ya janyo mata kofar, yana jin lokacin daka sakawa kofar makulli shi kuma ya nufi gurin windows da suka kasance na glasss, hannyansa sanye a aljihu ya tsaya yana kallon wani bangare na harabar gidan cike da burgewa, domin kuwa masarautar Damagaram masarauta ce da aka ginata akan tsari da al'adun kasar Nijar, sai a yanzu tunanin abunda zai fadawa Sarki ya fado masa a rai, ya zai fuskance shi da maganar? Ta ina ma zai fara? An dai ce tana cikin masarautar gaske ne ko karya be sani ba, waya sani ma ko bata cikin garin faba daya, what if Hameeda kawai tana masa wasa da hankali ne kawa. Da wannan tunanin ya nufo sitting room yana ta sake sake a zuciyarsa, tunanin daya kamata ace tun gida yai shi sai a yanzu ya zo masa. Be tsara komai ba, shi dai iyakar abunda ya sani indai Hafsatu manga tana cikin masarautar nan da gaske ba zai koma ba sai da ita. Nan ma a jikin windows ya tsaya yana hango harabar masarautar. Wasu bayi ne manya da yara, a wannan bangaren suna ta aikin kada nonon da aka samar da shi a cikin masarautar. Kara matsawa yai jikin glass window din yana son kara tabbatar da abunda idonsa suke hango masa, be gansu ba har sai da ya kai hannu ya bude window, sai yai saurin barin jikin tagar ya nufo kofar fita, yana budewa ya samu dogarai har hudu tsaye suna gadin kofar. “Ku zagaya ta nan baya, gurin da ake tatsa nonon nan akwai wata karamar yarinya ku zo da ita sunanta Hafsatu Manga” Duk suka amsa da to suna mai bashi girma da nuna tsantsar biyayya, biyu suka tafi biyu suka tsaya suna cigaba da gadin kofar. Cikin ya dawo amman sai ya kasa zama zuciyarsa nata masa zillo kamar zata fito, gurin windows ya nufa ya tsaya, yana kallon yadda take kada gorar duman dake hannunta, be san lokacin da murmushi ya kubuce masa ba wanda ya bayyana fararen hakoransa, ba zai iya fadar dalili daya dake saka zuciyarsa son kasancewa da Hafsatu manga ba, baya iya auna yadda farinciki da annashuwa ke ziyartar zuciyarsa a duk lokacin daya ganta, be san dalilin dake hana shi sakewa da walwala idan bata kusa shi ba, sai dai yafi alakanta hakan da tausayinta da yake. Yana kallon yadda suka saka ta gaba sai kuma ya juyo yana kallon kofar ya gagara zama, kamin su shigo da ita duk yabi ya matsu. Ana taba kofar falon gabansa yai mugun faduwa, har ciki suka shigo da ita ya daga musu alamar sun gama nasu, sai suka juya da sauri suka fice. Ita kan kanta na kasa bata daga ta kalli kowa ba, sai dai taji kamshin turaren data sani wanda bata iya shaidar wanene mai shi, tsoro duk ya kamata tana ta sauraren a a karanta mata laifin da tai da kuma irin hukuncinta. Karasa yai kusa da ita ya risina ya leko fuskarta sai yasa hannunsa ya daga kanta ta fuskance shi, hawayene ke sauka a idonta, hawayen da yake jin saukarsu har cikin zuciyarsa. Ya kasa ce mata komai, yana ta jiran tai magana ko da nuna masa wata alama ta sannaya amman ba ko daya. Ta rame sosai kamar ba ita ba, amman kuma ta ciro ta bangaren hallittarta fuskarta ma ta nasa girma aai dai ba sosai ba. Hannu ta kai ta shafa rigarsa, hannun ya kama ya rika sai yaji wani irin sanyi ya ratsa nasa hannun, saurin fisge hannun tai tana yarfawa saboda zafin data ji sakamakon raunin dake hannunta. “Kin ganene Mama?” Ta gyada kai, sai kuma ta fashe da kuka ta rumgume masa kafafu. Jikinaa yai sanye yaji wani abu marar dadi yana zaga zuciyarsa. Dago kanta tai sai ya zauna a gurin ya zaunar da ita kusa da shi ya sake rika hannunta yana dubawa. “Miya samu hannun” “Bulal... La” Ta amsa cikin kuka. Kwanto da kanta yai jikinsa sai ka kara rushewa da kukan, shi kuma ya lumshe ido ya faga kansa sama yana daukar da aje Numfashi a hankali. “Daman ita ce wacce ka zo nema? Yarinyar da aka kama Anty Ummi saboda ita? Ita kanta Anty Ummi na san baka fada mata gaskiya ba da ba zata barka kazo neman wannan annobar ba” Hafsatu manga tayi saurin tashi, Zain kuma ya bude ido yana kallon Farhat dake tsaye kansa. Wata uwar harara Farhat ta watsawa Hafsatu manga sai ta juya da sauri zata fice Zain yai hanzarin rikota, jikinta har wani rawa yake kana ganinta kasan a firgice take. “Shiiiiiiiiiiiiiiiiii” Ya furta tare da saka hannunsa biyu ya rike fuskarta. “Rufe idonki” Ta rufe. “Ja Numfashi a hankali...” Taja “Sauke” Ta sauke. Haka yai ta fada mata tana yi har sai da ya tabbatar natsuwarta ta dawo jikinta sannan yace ta bude idon. A hankali ta bude babu Farhat a gurin daga ita sai shi ne. “Zat Zat kaje da ni can inda kake kaji, bana son nan dukana suke sosai basa da imani” Ya gyada mata kai. “Saboda ke na zo garin nan Mama, dake zan koma ba zaki sake nisa da ni ba” “Yanzu zamu tafi?” “Aa sai Sarki ya bani ke tukuna” “Ba zai bada ba, basa bari aje ko'ina” Ta fashe da kuka, sai ya kai hannu ya shafa fuskarta. “Zai bari, ni zan nemi haka, je ki cigaba da aikinki anjima za a kawo ki nan” Ta share hawayen idonta sannan ta nufi kofar har ta bude sai kuma ta juyo ta kalleshi idonta na cika sa kwalla. “Karka tafi ka barni” “Da ke zanje” Ba dan ta gamsu ba ta saka kai ta fice. Shi kuma ya sauke ajiyar zuciya yana jin babu dadin da be san dalili ba, dakinsu ya nufa sai ya samu Farhat zauna bakin gado tana sharar kwalla. A gabanta ya tsaya yana kallon fuskarta ita kuma ta gagara dagowa ta kalleshi sai wasa take da yatsunta, ba zata iya fadar abunda ta jike ji a yanzu ba, iyakar abunda ta sani taji babu dadin lokacin data ga Zain da Hafsatu Manga, rashin jindadin kuma bata san na minene ba, da gaske na bakincikin abunda ya faru da Anty Ummi ne ko kuma wani daban izuwa yanzu dai bata iya furta ko daya daga ciki, sai dai ranta ya sotsu da ganin yadda yake lallaba Hafsatu Manga abunda be taba mata ba tun da ta shigo gidansa. “Kuka kike yi?” Ta dago ta kalleshi da zimmar fada masa bakar magana sai kuma taji yai mata kwarjini sosai gashi ya tsareta da manyan idonsa. Dauke kai tai ta tashi tsaye ba dan tasan inda zata ba, sai ya riko hannunta ya janyota zuwa kirjinsa. “Minene na kuka fada min? Wata maganar nai marar dadi ko me?” Tana kokarin kwace kanta daga rumgumar da yai mata, sai duk taji kunyar kanta, kunyar hawayenta da ya gani hawayen da ita kanta bata san na minene ba. “Ni gida nake so gurin Mamana” “Idan na samu yadda nake so, zamu koma gida gobe inyaso idan kin hutu sai muje mu gansu haka ya miki?” Ta kasa cewa komai, ba karya tai ba tayi mamarin mahaifiyarta sai dai kuma a yanzu ta furta hakan ne kawai saboda ta kwaci kanta, sai dai har cikin ranta tana jin zaman gurin da suka soma yanzu yanzu ya fitar mata a rai. Duk irin kukuwar da take na fisge kanta daga gareshi be saketa ba sai ma kara rumgumeta da yai a kirjinsa, hakan yasa ta fashe da kuka. “Am sorry” Ya furta zuciyarsa kuma tana ta sosuwa da yanayin da ya ga Hafsatu manga........ Taya zai Zain zai fita da Hafsatu manga? Anya zai samu nasara kuwa? Zamu ji a cikon page din anjima domin wannan rabin page din ne. Ku rika hakuri da typing error. 🙏 [3/17, 8:36 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 42b Sun dade a gurin tsaye har sai da yaji ana kiran sallah magariba sannan ya saketa ya shiga bandakin yai wanka yai alwala. Cikin dakin yai sallah ita kuma ta fita falo ta yi nata sallah. Bayan ya gama ya fito cikin wasu kalar sufafin wadanda suka fito da kyauta da kuma kwarjin dake fuskarsa. Kusa da ita ya zauna yana kallonta. “Ga abinci nan ana jera me kike so ki ci” Sai kawai ta tashi ta nufi dakin daya fito ba tare da tace da shi komai ba. Be jin zai ci abincin shima dan haka ya tashi ya koma saman kujera ya zauna. Misalin tara saura Sarki Idrissa Abdourahmane Idrissa ya aiko kiran Zain, dole tasa Zain ya shiga ciki ya cire kananan tufafin dake jikinsa ya saka manya wato riga da wando na shadda sannan ya dauki hulla ya dora sama. Ko ba komai yasan zasu kara masa kalama Mai Martaba ma yana yawan fada masa ya rika saka manyan kaya saboda mutunsa da kuma na masarautarsa musamman idan wani gurin ya tafi. Tunda ya fito daga gurin dogaran da suke gadin kofar suka rika take masa baya har suka isa wani kebantattacen guri da sarkin ke zama yana hutawa. An gyara gurin ya kawata shi da kayan kawa na gargajiya masu ban sha'awa da matukar burgewa. Zain ne akwai ya shiga ciki yayinda dogarawan suka tsaya a waje. A kujerar dake fuskarsa ta Sarkin Zain ya zauna suna sake gaisawa a karo na biyu. Bayan sun gama gaisawar ne Sarki yake gabatar masa da Yarima Hamma wato dan sarkin wanda yake tare da shi a yanzu. Shi da Zain aka rasa wanda zai bude baki yai ma wani magana a cikinsu, shi yana ganin kamar Zain yafi dacewa ya gaishe tun da shi ya shigo masarautarsu shi kuma Zain yana ganin kamar kankanci ne ya gaishe da dan wani sarkin yana dan Sarki. Kallo daya Zain ya masa ya dauke idonsa, shi ma kuma tun shigowar Zain na farko be sake kallonsa ba. Suna haka Wata babban mace ta shigo dattijowa Hafsatu manga na biye da ita dauke da tray mai cike da kayan marmari. Tun da shigo idonta ya sauka akan Zain sai ta kasa dauke idonta shi ma kuka yaki ya kawarda idonsa daga kallon hawayen da suke zuba a idonta. Bata kula ba har ta tashi tuntube. “Ke mahaukaciyar ina ce? Baki ganine?” Yarima Hamma ya katsa mata tsawa, ganin tana kokarin fado masa. Abunka da wacce ke jira sai kawai ta fashe da kuka ta aje tray a gaban shi yayinda Dattijowar ta aje dayan a tray a gaban Sarki. Tsaki Hamma yaja ya tashi ya fice daga gurin. Dattijowar ta katsa mata tsawa. “Rufe baki” Zain ya kalli Dattojiwar ya ce “Tayi kankanta da aikin da kike sakata, gata kyakkyawa, da Mai Martaba zai min karamcin bani ita a matsayin Kuyanga da zan fi kowa farinciki” Sarkin ya kalleshi yana dariya. “Yarima kenan, wannan ai tayi maka kankanta da kuyanga, akwai su da yawa idan kana so, sai a dubo maka wacce tafi wannan gwari idan ma matasan kake so” “Wannan din dai nake so ranka ya dade, Masarautar Rishim bata marhabun da bayi saboda tana ganin kamar zamanin haka ya wuce, duk bawan da ka gani a gidan to am dauke shi aiki ne ko kuma dan gado ne tun kaka da kakannin, wannan yasa nake son idan har an bani ita na shiga da ita a matsayim Kunyanga nasan Mai Martaba ba zai zargeni ba musamman idan yaji kai ne kai min kyautar ta” Sarkin yayi murmushi irin nasu na manya, sannan ya kira sunan Dattijiwar dake jera masa kayan marmari a dan karamin tebur dake gurin. “Jekadiya” Ya fadi zauna tana daga nasa hannu. “Allah ya taimaki sarki” “A shiga da ita a anko masa ita a Kuyanga, zai yi kuzuri da ita a matsayin tsarabar mu” Wani irin dadi ne ya mamaye zuciyar Zain Annashuwarsa ta kasa boyuwa har sai da ta bayayyana a fuskarsa. Matar da aka kira da Jikadiya ta kama hannun Hafsatu manga suka wuce da sauri. “Godiya nake Mai Martaba Allah ya kara maka lafiya, tafiyar tamu ma ba mai dogon zango ba ce, gobe zamu kama hanya Insha-Allah” “Gobe goben nan?” “Ee daman akwai abunda zan yi a Niamey shiyasa na zo, dana kare kuma na ce ba zan wuce ba sai na kawo maka gaisuwa” Murmushin jindadi Sarkin yai. “Allah ya maka albarka, ka kyauta” Zain yayi murmushi sun dan taba fira kadan sai ya taso ya dawo gurin da aka tanadar masa, a nan din ma sai da Dogarai suka rakoshi har bakin kofar. Wannan karon ya samu Farhat zauna tana cin abinci, dakin ya shiga ya cire kayan jikinsa ya saka na bachi sannan ya fito falon ita kuma a lokacin ta tashi ta koma dakin. Yanzu ya natsu ya ci abincinsa sosai dan yasan yayi nasarar abunda ya kawo shi, har jin yake kamar ya rumtse ido ya bude yaga goben ta yi. A gado daya suka kwana sai dai kowa na bangarensa shi yana daga farkon gado ita kuma daga can karshe abun rufar ma ita nata daban ta dauka. Washe gari aka jera musu karin kummalo kala kala wani abun ya sanshi wani be sanshi ba, ko a abincin tarbarsu ma sai da aka shirya masu kalolin da basu sani ba, daga na gargajiya da kuma na waje. Daga Masarautar Damagaram aka aika da Hafsatu manga akai mata passport ita dai bata san abunda ake ba, sai dai hankalinta ya tashi lokacin da za a mata passport din ta dauka wani abun za'a mata. Sai da yamman lis Zain ya fito tare da rakiyar Sarkin har gurin motarsu, yana ta wara ido be ga Hafsatu manga, kamar yai magana sai kuma wata ziciyarta ta hana shi, A nan Sarkin yake fada masa Tsarabaraa ta kama hanyar sokoto tun safe idan tsun isa za aje har cikin gusau a kai masa, saboda akwai abunda ya san Yarima Zain ba zai iya zuwa da shi a yanzu ba. Suna sallama da Sarkin sai ga wasu matan biyu sun fito tare da Hafsatu manga an mata kwalliyar fulani tayi kyau sosai kamar ba ita ba. A Font seat aka saka Manga Zain da Farhat kuma suna gidan baya, sannan direba ya kama hanya. Ta natsu sosai gaban motar ko motsi bata yi kamar ba ita ba wacce ya sani da kiriniya da tabe tabe. Suna isa airport ya fito a nan ma sai aka mata izinin fita sannan ta fito. Sun yi zaman minti gom shabiyar sannan jirgin ya iso, Hafsatu manga na ganin Jirgi ta fasa kuka ka kankame Zain kamar ance mata ga mutuwa nan kusa da ita. Akwai sauran lokacin kamin jirgin ya tashi hakan ya bashi damar lallabta yasa ta rumtse idonta ko da suka shiga jirginsa tana kankame da shi ta kulle idonta gam. Daker ya zaunar da ita a kujerarta ya saka mata belt sannan ya kama hannunta ya rike sosai yadda zata daina jin tsoro, duk abunda yake Farhat na kallonsu amman sai tai kamar bata gani. Lokacin da jirgin ya motsa zai tashi sai da tai masa ihu da ya dago hankalin kowa izuwa garesu. Tasa dayan hannunta ta kankame hannun Zain.... [3/18, 2:00 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 43 Kowa yayi mamakin ganin Zain da Kuyanga (Sad'aka) ksancewar babu wanda ya san da zuwansa Nijar sai Mai Martaba da Hajiya Hadiza, ba mamakin kyautar suke ba, dan ba yau aka fara kyautar Kuyanga ko bayi a gidan sarauta ba, kawai suna mamakin yadda Zain ya yarda ya karbo ta ne abun mamaki. Kamin safe masarautar ta karade da maganar. Sun yi dawo late ko da suka shigo gidan Hafsatu manga na bachi, daman tun cikin jirgi tai bachi. Shi da kansa ya daukota ya shigo da ita cikin gidan, saman Cushion ya fara kwantar da ita, sannan ya wuce dakinsa, yana shiga ya cire kayan jikinsa yai wanka tare da alwala ya fito ya saka short da vest sannan ya dora jallabiya sama yai sallah. Shabiyu ta wuce ko da ya sauko kasa, har lokacin Hafsatu manga bachinta take hankali kwance, yana kallonta ya saki murmushi ya kai hannu ya shafa fuskarta a hankali, sannan ya nufi kitchen ruwa tea ya fara dorawa a electric kettle sannan ya kunna gas ya dora indomie. A falo ya dawo ya zauna ya kunna Tv yana kallo, a hankali ya juyo ya kalli Hafsatu manga, ya dade yana kallonta sannan ya dauke kansa ya tashi ya nufi kitchen din. Plate biyu yai na indomie dayan sanye da two two fork dayan kuma fork daya a cikin. Mai two fork ya aje saman Center table ya wuce da dayar dakin Farhat, yana tura kofar dakin ya tarar da wutar dakin a kunne ya san Farhat ba tai bachi ba. Sai dai kuma bata cikin dakin hakan yasa shi saurin aje plate din ya tura kofar bathroom inda yake jin motsi zaune ya ganta tana ta faman aman jini a galabaice, cikin hanzari ya karasa kusa da ita ya rikata shi ya dagota tai ta aman har ta gama sannan ya wanke mata bakinta ya cire mata kayan jikinta, bata da kuzurin hana shi cire mata tufafin a dole ta bishi da ido zuwa can ta lumshe idonta, sai da yai mata wanka sannan ya daukota ya fito da ita daga cikin bathroom din. Saman bed ya kwantar da ita ya bude wardrobe ya dauko mata wata doguwar riga, har ya saka mata rigar idonta a rufe suke kamar mai bachi. Fitowa yai daga dakin ya dawo kitchen ya hada mata normal tea mai cike da madara da milo sannan ya koma dakin, a yadda ya barta haka ya sameta tea ya fara ajewa ya dagota ta kwanta jikinsa sannan ya kai mata tea a baki, bata bude ido ba sai dai hakan be hanata shan tea ba, sai da tai rabin kofi sannan ta kawarda kanta. “Sannu” Ya furta yana aje cup din, sannan ya gyara mata kwaciyarta ya lullube, ya taso ya fito daga dakin. Zaune ya samu Hafsatu manga tana ta hawaye sai kallon gidan take. “Minene ba gani nan ba” Ya fada yana ware hannayensa, sai ta taso da sauri ta nufo inda yake. “Ni ban son wannan gidan” “Ina kike so? Ni a nan nake zaune ko baki son zama da ni?” “Nan din ina ne” “Gidana ne” Ta wara ido tana kallon katon falon. “Da gaske” “Eh” “Har da wacan abun tsakale tsakalen” Ta nuna Stairs, sai ya waiga ya kalli stairs din ya sake kallonta yai murmushi. “I miss you so much” Ya fada yana rika kumatunta, sai kuma ya kama hannunta. “Me kika yi aka dokeki a nan?” “Dan na yi jini” Ta bashi amsa kai tsaye. “Ina kika yi jinin” “A nan” Ya nuna gurin, tana waigawa inda take jiyo kanshin indomie. Ya tsareta da ido yana mamakin maganar. “Me ya gurin yai jini? Jimuwa kika kai ko me?” “Ban jimu ba nima haka nan dai kawai naga ya zuba ta kafafuna, shine idan na zauna sai na bata kayana har na bata gurin da wannan karamin sarkin Hamma yake zama sai wannan Jekadiyar ta dakeni” “Waya taba miki gurin har yai jini?” “Babu” “Fada min gaskiya mana, kin san ni ai baki boye min komai ko” “Ba wanda ya taba, nima haka nan kawai naga yana ji, amman cikina yayi ta ciwo kamin ya zubo” Yana tunanin it's too early ace ta fara menstruation yarinyar da ko nono bata fara ba, a musullunce yasan wace duk ta kai shekara tara ta isa ta fara haila, amman wasu sukan fara kidan dangi kamin haila why tai haila kai tsaye? No maybe dai wani yai mata wani abun yace karta fadi ko kuma bata sani ba. Shi kadai yake ta sake sakensa a zuciyarsa yana kallonta. “Muje ki ci indomie” Ya rika hannunta har gaban tuburin da indomie take aje, ya dauki spoon dinsa sannan ya mika mata nata. “Tunda aka kaini wacan gidan ban sake cin Indo ba” Ya wara ido tare da saurin rike hannunta “Shiyasa na dafa ai nasan kina so, bari ki fara wanke baki tukuna, na manta kin yi bachi” Ta turo baki “Mu a can ba a cilasta mana wanke baki, kuma da hannu muke wanke ba da abu mai karfi ba” Ta fada tunawa da brush din da yake bata ta wanke baki. Be ce mata komai ba yaja hannunta zuwa dakinsa ya bude sabon abun goge baki ya zuba mai ya wanke mata bakin da kansa tana da kuka musamman ganin jinin daya zuba a bakinta. Sannan suka dawo falon ta zauna kasa ta lankwashe kafafunta. Tana ta auna abinci a baki bata ce uffan ba har ta ci ta koshi shi kuma yana daga saman kujera zaune yana kallonta har ta gama cin abincin. “Sai wanka ko?” Tana jin yayi maganar wanka ta dora hannunta saman bakinta. “Shiiiiiii, dare ba a magana gidan wacan Sarki idan dare yai ba a magana, sai dai ayi kwana” Ta kwanta a gurin tare da yin matashin kai da hannayenta. Murmushi yai ya tashi ya dauke plate din ya kai kitchen, sannan ya koma dakinsa ya dauko mata bargo ya shinfida nata tare da matashin kai ya dauke ta ya kwantar a saman ya rufeta da wani zanen dabam. Ta bude ido daya “Ni kadai zan kwana a nan? Tsoro nake” “Aa yanzu zanje na dawo, rumtse idonki” “Tam” Ta rufe idon kamar yadda ya umarceta. Zauna yai sai da ya tabbatar bachi ya fara satarta sannan ya tashi ya nufi dakin Farhat, wutar dakin ya kashe ya kwanta bayanta ya dora hannunsa saman nata yaja blanket din da take rufe da shi ya rufe. A hankali ta bude idonta sakamakon kira sallah ta taji na asuba, ji tai kamar mutum a bayanta tana dubawa ta ga hannnunta cikin na Zain, sai tai saurin ture masa hannu ta tashi zaune. Hannu ta kai ta kunna bedside lamp sannan ta sauke kafafunta kasa. Sauka yai saman gado ya nufi inda makunnin wutar yake na dakin ya kunna. Sannan ya juyo ya kalleta. “Ya jikinki?” Uffan bata ce masa ba, sai ta tashi cikin rashi kuzuri ta shiga bathroom. Shi kuma ya juya ya fice daga dakin. Cikin karfi hali tai alwala ta fito tai sallah, sannan ta sake komawa saman gadon ta kwanta, bata farka ba sai takwas da rabi na safe, sai da ta shiga bandaki ta wanke bakinta da fuskarta sannan ta fito ta saka Hijab dinta ta sauko downstairs. Kofar fita ta nufa tana jin motsin Zain a kitchen tare da Hafsatu manga tana masa fira, har Part din Dada Yalwa taje ta gaisheta sannan ta dawo part din a lokacin Zain yana zaune saman dinning Hafsatu Manga kuma na zauna kasa tana karyawa. “Je ki ce Anty Farhat ina kwana” Zain ya fada yana mata Farhat wacce ta nufi upstairs. Sai ta lake kafada ita ba zata ba. “Je mana” “Uh aa” Ta sake lake kafadar tana aikin auna abinci a baki. Dauke kansa yai daga barin kallonta ya maida kan wayarsa dake kara alamar sako. Sunan Hameeda ne shimfide a jikin sakon, sai dai yai kamar zai goge sai kuma ya bude. _Akwai yiyuwar ina da ciki fa, ka yi wani abu kamin komai ya bayyana ni kadai bani tabbas akwai ko baba, amman idan har ya girma kaine a cikin matsala, domin zan yi amfani da wadannan hotunan na matsayin shaidar kan min fyade da gaske, kaga babu ta inda zaka iya wanke kanka, kuma san dole a yarda da ni._ Yana gama karanta sakon ya aje wayar, ya dauki abincin Farhat ya nufi dakinta, kwance ya sameta tana ta hawaye. Sai yanyo karamin tebur ya dora mata abincin a kai, sannan ya zauna kusa da ita. “Wai Minene na wannan kukan ne? Wani abun nake miki wanda baya miki dadi ko me?” “Bana jindadin zaman gidan ni kadai” Yayi shiru kamin ya ce “I can invite your friends here, ko kuma yan 'uwanki” “Amman Dada ba zata bari ba, na san bata so na ko gaisheta nai bata amsa min da kyau” “Ni kike aure ba Dada ba, zaki iya farincikin matukar hakan ne abunda kike so, Dada Yalwa Hameeda kawai take son na aura shiyasa ba zata taba maraba da duk wata mace da na aura ba, kuma ina tunanin Anty Ummi ta fada miki haka” Ta tashi zaune ta share hawayenta. “Da gaske zan iya kiran kawaye a nan” “Na taba miki karya?” Ya fada yana kallonta fuskarsa ba yabo ba fallasa. Har ya tashi tsaye sai kuma ya dawo ya zauna ya fuskanceta. “About this girl, karki daga hankalinki dan Allah, you know marainiyar ce bata da kowa a yanzu sai mu, ba san yadda zaki kalli abun ba, amman Hameeda ce ta shirya komai....” A nan ya kwashe abunda ya faru ya fada mata, ciki har da zancen abunda ya faru tsakaninsa da Hameeda. Ta rufe baki “So ka kusanci Hameeda kenan?” Ya kalleta “Im not sure, amman idan har na yi miyasa zaisa na kusance ki, na yi iya kokarin da zan yi na hana kaina zuwa gareki amman na kasa, hutunna data bani basu isa su zama shaida ba, zai iya yiyuwa ta kwanta ne a jikina kawai ta dauka ko kuma ta yi wani abun da zai sa ta a dauki hoto kamar ina kusantar ne, amman ina jin kamar na aikata” Ta sauko da kafafunta kasa tana fuskantarsa. “Amman Zain indai Hameeda zata iya aikata wannan, zamanta a tare da mu hadari ne domin zata iya unkurin kasheka wata rana” Ya kalleta. “Idan ta kasheni zaki ji wani abu?” Bata ce komai ba sai kallon kwayar idonsa take can kuma ta sauke idonta. “Maybe” Yayi murmushi tare da kamo hannunta ya rike. “Idan har ni zata kashe abu ne mai sauki, as long as ba zata cutar wandanda suke kusa da ni ba, like you as my wife, Anty Ummi as my sister, And Mama...” Sai kuma yai shiru. “Ban san matsayin a gareni ba yanzu, zata iya haduwa da iyayenta anjima ko gobe, but i promise myself this i will try my possible best to take good care of her ko da tana gurin iyayenta ne, ban san yadda zaki dauki maganar ba, but ina jin Mama kamar yar da na haifa da cikina ina sonta sosai” Ya yi shiru sai kuma ya kara matse hannunta cikin nasa. “I know kina kallona as wicked person, na san ban kyauta abunda nai miki ba from first place, amman ke kika bani damar hakan kin sani ko?” “Amman ai baka taba ganina da wani namijin ba, balle ka min shaidar iskanci” “Ido abunda yake gani yake iya yanke hukunci da shi, yanayin shigar da kike ba zata taba burge namiji mai mutumci ba, idan kuma dan iska ne idan ya ganki zai yi zaton ke ma haka kike. Yanzu na yarda ba ko wace mai shigar banza ba ce yar iska, wasu nayi ne just for fashion, and I'm sorry for that” Ya kai hannunsa saitin fuskarta. “It's very difficult for me na zauna da wata macen a matsayin matar aure, halayentar fuskarta yanayin mu'amalarta ba daya ba ne da naki, ba zan taba nadamar fadawa kowa ina son Haleema ba, saboda macece mai tsananin biyayya da gudun zuciyata, duk abunda ta san yana faranta min tana kokarin aikatawa, idan kuma na ce bana so ba zata sake yi ba, wannan ne dalilin daya kara min son a zuciyata, amman duk da haka ina kokarin ganin na zauna dake na baki hakkinki yadda ya kamata, kina karkashina a yanzu komai naki yana kaina, na yarda da hadin da Allah yai tsakanina da ke shiyasa na watsar komai....” Ya saketa ya tashi tsaye. “Amman zama da ni akwai wahala Zain” Juyowa ya kalleta. “Zan jure har zuwa lokacin da zaki fahimci minene aure, maybe a lokacin kin shirya zama da ni as your Husband, ki shirya jibi zamu je ki gai mahaifiyarki kuma ki yi mata bankwana na tafiya” “Gaskiya ni ba zan sake rakaka sha'anin wannan yarinyar kauyen ba” Ta fada tana dan turo baki. “Ni ne zan rakaki India a duba lafiyarki, and Mama zata bi mu” Yana fadar hakan ya fice daga dakin. Hannu ta kai ta dauki mug din dake cike da tea ta kai bakinta tana ta tunanin maganganunsa. Sai gata cikin wani kurbi a zuciyarta dake dauke da tusayinsa... Ko da ya sauko ya samu Hafsatu Manga ta gama cin abinci tana jera soyayen dankwalin turawa a dinning. Tana ganinsa sai tasa dariya. Zuwa yai ya tsaya a gurin fuskarsa da murmushi. “Me kike?” “Na gama cin abinci na cinye hadda naka, kaga na jera mutane” Ta shiga fada nasa. “Wannan Inna Ladi wannan Zat, wannan Mamana, wannan Yarima Hamma, nan ma wane gari ne? Can kuma ina ne?” “Gusau, can kuma Nijar” Ya fada yana zama kan kujerar dinning, sai ya dauketa ya dorata saman kafafunsa. “Kina son Hamman nan ko Mama?” “Shima yana zuba min abinci kuma idan za dakeni yana hanawa, shine ya siyeni a gurin mutanen nan” “Ba kince iyayenki ba ne?” “Aa wannan dan sanda yace idan na fadi gaskiya sai ya dakeni sosai sai ya halbeni shiyasa ban fada ba” “Amman Anty Ummi ina tace a kaiki?” “Nima ban sani ba, wani gurin kawai wannan mutumen ya kaini kuma yana ta min fada har da wani abu ya bani ina sha nai ta bachi, ya kaini gurin wata mata tasa aka min allura wai nai sauri na girma, sai suka kaini gurin wannan matar mai bakin rai sai ta min tsawa wai tashi ki yi shara” Ya kwatantata yadda Zainab ke mata Matar Auwal.. “Shi kuma sai yana tayani aikin, sai a daukoni aka bada ni gurin yan sanda suka zo da ni suka kaini gurin wani dan sanda da wata mata suka ce nace wadannan sune iyayena kuma ba sune ba, suka tafi dani can kauye had cikina yana ciwo suka rika sani ina bin wasu suna kiwon shanu, sai kuma suka saida ni ga Yarima Hamma...” Tun da ta fara bata tsaya ba, sai da ta kai aya. Shi kuma yai murmushi yana nazartar bayananta daya bayan daya. Sannan ya shafa kanta ya sauke ta ya tashi tsaye. “Bari naje nai wanka kema sai kiyi ko?” “Fita zamu yi?” “Yes zan kaiki gurin Anty Ummi ta ganki da idonta” “Aa ni bana sonta, ita da wacan matar” Ta fada tana nuna dakin da Farhat take. “Ba can zan baroki ba, tare zamu dawo kin yarda?” “Ee” “Good” “Minene gaud din?” Yayi murmushi ba tare daya fada mata ma'anarsa ba. HAMEEDA POV. Sun dade suna tattaunar maganar Kuyangar da Zain ya ce ambashi ita da Dada Yalwa, sai dai bata yarda ta nuna ma Dada cewar ta san wani abu a kai ba, Dada kuma tana ta mamakin zuwan nasa ne, ko da yake ta ji uzurinsa gurin Mai Martaba. “Yarinyar ta mallake shi mal, da ada ne ba zai iya tafiya ba tare daya fada min ba, amman yanzu Mai Martaba kawai ya fadawa gudun karya hana shi tafiya” “Uhm ai daga gani ba banza ta shigo gidan nan ba” Hameeda ta fada bayan ta turawa Zain sako. Sannan ta tashi tare da kofin shayinta da dawo part dinsu ta shige dinta, gurin window taje ta tsaya tana kallon harabar Part din Zain, so take ta ga fitowarsa akwai maganar da take son ta fada masa ta yadda zai tabbatar da gaskene tana kan bakanta. Ta kusan awa daya tsaye bata ga fitowarsa ba, sai ta dawo ta zauna tana kiranshi a wayarta, sai ta ta gaji da jera masa missed calls sannan ya daga wayar ba tare da yace da ita komai ba. “Ka dauka da wasa nake ko? Na baka sati biyu ka yi wani abu a kai, ko kuma na fito na fallasa sirrin gaba daya” “Kanki zaki fallasawa sirri Hameeda ba ni ba, ba yarinyar da kika siyar tana hannuna ba? Ki saurari hukuncinki gurin Mai Martaba” Yana fadar hakan ya kashe wayar. Sai tai saurin tashi tsaye. Mi yake nufi? Tona mata asiri zai yi? Lallai kuwa Mai Martaba zai fi yarda da shi fiye da ita. Safa da marya ta fara yi a cikin dakin, tana ta tunanin manufar maganarsa da kuma samawa kanta mafita. Sai da yaje ya gaishe da Mai Martaba tare da Hafsatu manga, ya nunawa Mai Martaba ita sannan suka dora da zancen garin, a nan yake sanar da Mai Martaba akwai maganar da ya kamata su yi amman ba yanzu ba sai nan da kwana biyu idan ya natsu. Mai Martaba yayi farinciki da kyautar da Masarautar Damagaram tai ma dansa, yaji dadi sosai ko ba komai yasan sun karrama shi. Daga gurin Mai Martaba ya shiga gurin su Hajiya Hadiza da Hajiya Maryam da Hajiya Zarah ya nuna musu ita kuma ya gaishesu sannan ya fito. A mota yai waya da Ibrahim ya fada masa komai da yadda abubuwan suka faru, har ma da zancen visa da zai nema musu zuwa kasar india, har da bashi Hafsatu manga suka yi magana sannan ya karbi wayar ya kashe, yana parking harabar gidan sakon Anty Ummi na shigowa wayarsa. _Gobe ne birthday Farhat ya kamata ka yi surprise dinta_ Kashe motar yai ya bude ya fita sannan ya zagayo ya budewa Hafsatu manga, sai ta rike masa hannu gangan kamar ance za a kwaceta. Wata haddaiyar bakar mota ya gani mai tsada da direba ciki, an faka ta kusa da kofar falon Anty Ummi. Zai ta ya zagayo sannan ya shiga cikin falo, tufafin jiya ne na fulani a jikin Hafsatu manga, wannan dalilin ne yasa ya shi kara son zuwa da ita gurin Anty Ummi dan a duba mata kayan Amal kamin ya shiga gari anjima ya siyo mata. Har suka shiga cikin falon Hafsatu manga na rike da hannunsa, a dayan bangare na falon ya nufa ya zauna ganin Anty Ummi da bako. Ganin hakan yasa Anty Ummi kiransa. “Zain baka ga Ya Habib ba ne?” Zain ya taso jin Anty Ummi ta ambaci Yaya sai ya karaso gurin ya zauna a dayar kujerar Hafsatu manga na rike da hannunsa. “Ai ban sanshi ba” “Yayana ne, wanda ke Kaduna be cika zuwa ba sai idan wani abun ya taso shiyasa baka sanshi ba, yanzu ma saboda rashin lafiyar Abbah ne da be samu damar zuwa ba a lokacin yana Dubai, shine yanzu ya zo” “Allah sarki” Zai ya fada tare da mika masa hannu suka gaisa, idon mutumen suna kan Hafsatu manga wani irin kallo yake mata kamar bana lafiya ba, ita kallonsa take tana kokarin tuna inda ta taba ganin fuskarsa, shine mutumen da takardunsa suka fadi ta dauko masa, yanzu ka tuna sai tai masa murmushi, a maimakon ya mayar mata da murmushi sai akwai yai fuskar tausayi da tashin hankali yai kiranta da kai, sai ta saki Zain ta tashi taje. Sai ya kama hannunta yana duba awarwaron dake hannunta yana duba awarwaron yai saurin kallonta yana mata wani irin rikonta daya firgitata. “Ina kika samu wannan Awarwaron?” Da karfi ta fisge jikinta ta juya da gudu ta koma gurin Zain kamar zata shige jikinsa. “Wallahi nawa ne ba satowa nai ba, Mamana ta bani shi” Ya mike tsaye da sauri zaije ya kamata hankalinsa ya tashi sosai. “Ina mahaifiyarki take” Zain ne ya tashi tsaye ya shiga tsakani yana tare mutumen. “Dakata Malam” Sai mutumen ya kalleshi kamar zai ce wani abu sai kuma ya koma ya zauna ya dafe kansa, sai ga hawaye sun sauko masa. Hafsatu manga ta kalli Zain kamar zata yi kuka. “Zat tashi mu tafi ni bana son wannan gidan” Haka Zain ya biye mata ya tashi tsaye rike da hannunta sai Anty Ummi ta dakatarda shi..... [3/20, 3:05 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 44 Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un. Kawai yake maimatawa yana dafe da kansa. “Ya Habib lafiya” Anty Ummi ta sake tambaya a karo na biyu, sai ya dago kansa ya kalli Hafsatu manga, fuskar mahaifiyarta ce ya gani shimfide a fuskarta, ya maida dubansa gurin awarwaron hannun da take kokarin boyewa a zatonta za a ce tayi masa sata ne. Sai kuma ya kalli Zain. “Waye mahaifin yarinyar nan?” “Nine yata ce” Zain ya fada kai tsaye. “Ka tabbatar da yarka ce malam?” Ya fada muryarsa na rawa alamar kuka na gab da kubuce masa daman tuni hawaye sun fara sauko masa. “Ba yarsa ba ce Yaya tsintarta muka yi...” Cewar Anty Ummi, Zain yayi kamar ya dakatar da ita amman bata tsaya ta saurareshi ba, sai da ta fayyacewa Ya Habib komai. Faduwa yai kasan gwuiyoyinsa yana hawaye kamar ba gobe, wasu na bin wasu ya kasa cewa komai. _Mahaifiyarta mahaukaciya ce_ abunda Anty Ummi ta fada masa yana ta masa yawo a cikin kai, ya kasa yarda ya gasgata cewar yarsa ce ba shi wani tabbaci akan hakan, sai dai kuma yana jin akasin haka wato na yarda cewar yarsa ce saboda abun hannun dake hannunta mai dauke da sunanta wanda yasa aka mata ita da mahaifiyar shekaru da dama da suka wuce, gashi kuma ance mahaifiyarta mahaukaciya ce zai iya yiyuwa mahaukaciyarce tunda ta bar gida ba tare da kowa ya sani ba. Kai ya sake dagawa ya kalli Hafsatu manga wacce ke buyo bayan Zain, fuskarta sak daya take da ta mahaifiyarta. “Babu tantama wannan yata ce....!” Ya fada cikin wani irin murya hawayen nata bin fuskarsa. Anty Ummi ta kalleshi ta kalli Hafsatu manga baki sake fuskarta dauke da tsantsar mamaki. “Ya wannan yarinyar kauye ce daga kauye ta fito” “Waye mahaifinta?” Ya tambaya yana tada kai ya kalli Anty Ummi wacce tai yi maganar. Anty Ummi tayi shiru kamar mai tunanin abunda zata ce. “Ni bani da Baba ban san babana ba, sai mamata kuma mahaukaciya ce, dan haka kai ba babana ba ne” Hafsatu manga ta fada tana turo baki har lokacin tana bayan Zain rike da rigarsa gani take irin na baya za a mata wato Anty Ummi tana son bada ita ne kawai ga wani kamar yadda tai mata a baya. Murmushi mutumen yai yaja wani dogon numfashi ya aje. “Ni ne mahaifinki, Indai Rufaida ce ta haifeki to nine Habib mahaifinki, ina siya miki wannan awarwaron tun baki zo duniya ba ke mahaifiyarki, uwarta ta bar gidana da cikinta ta shekara hudu da cikin bata haihu ba, kuma har yau bamu san inda take ba” Ya karasa yana fashewa da kuka tare da nunawa Anty Ummi Hafsatu manga, jikin Anty Ummi ne ya soma yin sanyi tabbas ta tuna lokacin da aka ce Uwar gidansa tana da ciki bayan shafe shekaru bata haihu ba, ta kuma san lokacin da take dauke da cikin na tsawon shekaru, hawaye ne ya zubo mata, sai ta kalli Hafsatu manga tabbas fuskar Rufaida ce a fuskarta ba zata taba manta kamanin matar babban yayanta ba. “Innalillahi Wa'inna Illahirraji'un” Ta furta tana rufe baki. Zain ya tabe baki yana zuba hannayensa a aljihu. “Ban yi tunanin idan na zo da ita zaki sake mata wani abun ba, shiyasa ban kawowa kaina komai akan tahowarta gidan nan ba, na san duka wannan tsarinki ne, ba anan zata zauna ba, dan haka ki rushe duk wani tsari da kika yi akanta” Anty Ummi ta hawaye ta kalleshi cikin muryar kuka ta ce “Ban shirya wannan ba Zain, ban san zaka zo da ita ba, Yaya ma be san da ita ba, kuma ba karamin mutun ba ne da za a ce an biyashi yai wannan abun, shin baka gani ne? Taya zai zubar da hawayensa akan karamar yarinya kamar wannan indai bashi da alaka da ita?” “Nima ban sani ba, iyakar abunda na sani duk wanda yai unkurin cutarda Mama zan iya cutar da shi nima, bani da tabbaci gaskiyarki akanta saboda kin taba unkurin hallakata, so ni duk ban yarda da wannan plan din na ki ba, idan har ita ce miyasa baki taba labarin ba? Miyasa lokacin da kika ganta baki gane ba?” “Saboda Mahaifiyarta ba nan take ba, ba kawowa raina cewar ita ce ba, saboda ban zata za ta iya zuwa har nan garin Gusau ba” “Oh sai Yanzu daya ganta da rana tsaka ya ce yarsa ce sai kika tuno? Haka kawai mutum zai ga yarinya yace yarsa ce ni na yarda” “Miye ribata idan yai maka karya?” Mutumen ya tambaya cikin muryar kuka. Zain ya daga kafunsa. “Ban sani ba” Hannun Hafsatu manga ya rika wacce ta fara hawaye zasu fita daga cikin falon sai mutumen ya kirashi. “Tsaya mana, fada min inda mahaifiyar yarinyar nan take ina son ganinta” “Ban sani inda take ba, itama kuma bata san inda take ba, and wannan ba zai na baka yar mutane ba so wannan plan din be yi ba” Ya karasa yana kallon Anty Ummi which means his last sentence is for her. “Ko da anyi gwaji?” “Wani abun kika taka idan munje gwajin ne?” “Kana magana kamar ba da ni ba Zain, Wallahi har ga Allah ban tsara komai ba akan wannan abun ba, ban san komai akai ba” “Idan ke baki tsara ba, maybe wani ya tsara someone like Hameeda Auwal ko kuma wani can daba mai wata manufar daban” Mutumen ya share hawayen idonsa ya tashi tsaye. “Zan nemo mahaifiyar yarinyar nan duk inda take, ko dan tabbatar da zargina, sannan ina hadaka da girma Allah ka bani damar gwajin DNA test dan tabbatar da hakan” “Miyasa tun farko baka nemi mahaifiyar ba, sai yanzu da ka gannin da ita zaka ce wani yarka ce?” “Ban san dalilin daya hana ni nemanta ba, tunda ta tafi babu wanda ya taba nemanta bamu sake neman ta, amman kullum da ita nake kwana na ke tashi tunaninta ne silar ciwona, amman yanzu zan nemeta koda hakan na nufin ajalina ne, dole na dawo da Raifaida indai tana duniyar nan” Ya furta yana ware hannayensa hawaye na sauka a idonsa. “Shekara nawa rabonka da ita?” In brief Ya Habib ya labartawa Zain tafiyar Rufaida har ma da cikin dake jikinta, shi kanshi sai a yanzu yake mamakin kansa na rashin zuwa nemanta, yana ta tambayar kansa yana ta neman dalilin daya hana shi hakan amman be gano ba. Akwai kamshin gaskiya a labarin sai dai hakan be isa ya saka Zain yarda da shi ba, domin za a iya shirya komai so he trust no one. “Ka min alfarma ko kan yarinyar nan ne na shafa” “Ba zan iya baka wannan damar ba, wata kila idan ka taba ta zaku bata ne tare, amman a yadda ka bani labarin matar da cikin zai iya yiyuwa ba wannan yarinyar ba ce, saboda shekarun sun yi tsayin da za a ce yarka tana nan karamar kamar wannan” “Nima ban tabbatar ba, amman jikina na bani cewar wannan jinina ce, amman ina son gwajin DNA, kuma zan nemi inda mahaifiyarta take” “Kamin nan zan yi reporting dinka gurin police dan ban yarda da kai ba” Sai yai murmushi takaici. “Kana da damar haka, nima zan fi jindadin haka” Zain be kara cewa komai ba, ya fito rike da hannun Hafsatu manga wacce tako ta daina hawayen har yanzu, a gaban motarsa ya nufa da ita ya risina ya share mata hawaye. “Ki daina kuka, ba zan bawa kowa ke ba, ba kuma zan yarda kowa ya sake cutar da ke ba kinji?” Ya gyada kai. Sannan ya bude mota motar ta shiga ya rufe, sai da ya zagoyo zai shiga side dinsa sannan ya kula da Mutumen wanda ya fito daga cikin falon ya zo waje ya tsaya tare da Anty Ummi suna kallonsu. Sai da suka wace sannan ya juyo ya kalli Anty Ummi “Miye alakarki da wannan yaron?” “Kanena ne uwarmu daya” Anty Ummi ta fada cike da damuwa. Sai kawai ya nufi motarsa tun kamin ya karasa direban ya fito da sauri ya bude masa yana shiga ya maida motar ya rufe ya koma mazaunin direaba yaja motar suka fice. Falo Anty Ummi ta dawo ta zauna saman kujera tana tunani. “Idan har hakan ta tabbata..... ” Sai kuma tai shiru hawaye suka sauko mata, sai ta lumshe ido ta fashe da kuka. HAMEEDA POV. “Ka gane ni?” “Ee ina da number ki ai” “Good ya aikin” “Da godiya” “Kasan kwanaki ka taba kirana akan maganar yarinyar Kauye nan ko?” Yayi shiru na dan wani lokaci. “Minene?” “Ga yarinyar nan na dawo da ita saboda kai” “Saboda ni ko kuma saboda wani kudirinki?” “Gaskiya saboda bana son zaman yarinyar nan a gidanmu ne, ban ce ka riketa har na tsawon lokaci ba, kawai na dan kankanen lokaci za ka rike min ita” “A kaina kika shirya game dinki wannan karon?” “Ba wani shiri, idan baka shirya ba, zan iya bawa wani ita daman saboda kawai naga ka damu da ita ne” “Bana so ki nemi wani” Daga haka Auwal ya kashe wayar, sai tai kwafa. “Idan kai baka min ba, ai wasu zasu iya min” Number Fauziya ta kira bugu daya ta daga. “Ke be karbeta ba” “Kar hakan ya dame ki, zamu samu wanda zai aje mana ita na dan lokaci” “Gobe da Safe dan Allah da zarar na kiraki zan aiko Abida da ita, make sure kin samo mutumen a yau” “Karki damu zan nema miki shi” “Ina son ki kawata” “Muna tare ai” Ta sauke wayar fuskarta dauke da damuwa. “Ba ni da wani Zabi sai wannan, idan ba haka ba yarinyar zata tona min asiri, kuma ban san abunda Zain ya shirya ba, ban san abunda yake da kudirin yi ba, amman na san wannan zai kawarda komai” Mikewa tai tsaye sai ga hawaye ya zubo mata. “Kai ne sila, na zama wata kalar mace wacce ban taba tunanin zama ba, sau nawa zan batar da yarinyar nan sau nawa zata dawo?” Sai kuma ta juyo. “Dole shi zan fara zubawa kamin na fita da ita, haka ya kamata sai fitinar ta koma tsakaninsu ta yadda hankalinsa zai koma can” Hannu ta kai ya dafe kanta ta rumtse ido tana jin yanayin jikinta babu dadi kamar yadda zuciyarta take. [3/20, 12:52 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 45 Daga gidansu Anty Ummi ya dawo gida tare da ita, har lokacin bata daina hawaye ba. Yana rike da hannunta ya shigo falon a lokacin Farhat na tsaye tana mopping. Kallo ta bishi da shi har ya zauna ya zaunar da Hafsatu manga gefensa. “Tafi kai da ita ka nunawa duniya an baka Kuyanga?” Ta fada tana tabe baki. Sai da ya kai hannu ya share ma Hafsatu manga hawaye sannan ya kalli Farhat yana mamakin kalamanta ya ce “Idan na nunawa duniya ita kina da damuwa da hakan ne?” “Ban dai g abun kallo ko burgewa a nan ba, shiyasa nake mamakin mutanen da zasu bata lokaci su kalli wannan yarinyar” “Mama zauna nan zanje na dawo sai na siyo miki kayan kinji...?” Ya fada ba tare da ya cewa Farhat komai ba, ta lake kafada alamar ba zata zauna ba. Farhat ta dauke kai ta kwashe kayan mopping din ta nufi kitchen. “Ni ban son wannan matar” Hafsatu manga ta fada. “Ba dadewa zan yi ba, yanzu zan dawo bana son na fita da ke ne wani abun ya faru....” Be karasa maganar ba wayarsa tai ringing kamar mai jiran kiran sai yai saurin ciro wayar daga aljihunsa yana kallon mai kiran. “Kana ina?” Yana picking Ibrahim yai masa tambayar. “Minene” “Akwai wata magana da nake son mu tattauna da kai” “Ina gida yanzu” “Hafsat ta fada min Yayanta ya kirata ya fada mata wai Hameeda ta kirashi zata bashi yarinyar nan” “What...?” “Ina ta hadu da shi?” “Shiyasa nake son mu hadu yanzu, Zain ya kamata a atakawa yarinyar nan burki ba zata zo ta zamar muku yar daba ba, nan gaba abun zai iya barin kanka ya koma gurin Mai Martaba baka san iya wanda zata cutar a cikin wannan halin ba” “Mu hadu office yanzu” Ya kashe wayar kana ya dubi Hafsatu manga, yana wani tunani na dabam. ‘Ko dai mutumen da ya gani a gurin Anty Ummi Hameeda ta hada kai da shi ne? Wata kila Anty Ummi bata sani ba amman shi mutumen ya sani, sai dai kuma be yi kama da irin mutumen da za a bashi kudi yai irin wannan shaidar ba, kamaminsa da yanayinsa be nuna hakan ba’ Hannunta ya rika. “Ta so muje ciki ki kwanta, yanzu nan zan dawo” “Aa ni kaje da ni” “Idan naje da ke, Anty Ummi karbeki zata yi ta bawa wannan mutumen kina son haka?” Ta yi saurin girgiza kai. “To mu shiga ciki ki kwanta yanzu nan zanje na dawo, ai nan gidanane babu wanda ya isa ya daukeki kinji?” Ta gyada kai, daukar yai ya hau da ita sama dakinsa ya shiga da ita ya kwantar da ita saman gadon, tana ta kuka a hankali. Sai fa kai kofa kamar zai fita sai kuma ya juyo ya kalleta sai ya dawo yaja blanket ya lullube ya share mata hawayenta ya sunbamci goshinta sannan ya fice. Ko da ya sauko kasa ya tarar tana saka turaren wuta, ko ina ya karade da kamshi sai zagaya falon take da shi, a gaggauce ya fita daga falon ya shiga motarsa ya dauki hanyar asibitin. Ta fiyar sauri yai ya riga Ibrahim isa a office din, sai da yai zaman mintuna goma sannan ya Ibrahim ya turo kofar ya shigo. “Duk yadda kake tunanin yarinyar nan ta wuce nan Zain ya kamata mu daukar mata mataki” Ya fada tun kamin ya zauna, sai kuma ya dora da. “Dazun Hafsat ta kirani ta fada min wai Hameeda ta kira Yayanta wai zata bashi yarinyar idan yana so, tana son ya aje mata ita na kwana biyu, yace mata ba zai karba yanzu zata iya samun wani ta bashi ita, ina tunanin tana tsoron yarinyar ta tona mata asiri ne” “Miye alakar shi da ita da har zata fada masa haka kai tsaye? Dole akwai wani abu kasa, wata kila ma wani shirin ne shiyasa ita Hafsat din ta fada maka” “No mahaifiyarsu ta gargade shi a kan ya cire bakinsa cikin lamarin, da yayi niyar sai ya maida yarinyar ne gurinsa saboda wulakancin da kai ma kanwarsa, sai kuma mahaifiyar ta shiga tsakani hakan yasa ya kyaleta, so ina ji kamin ya shiga ta hana shi din ne ya nemi numberta har yai mata magana, domin a yanzu haka abunda ya fada cewa yai Hafsat din ta fada maka yar'uwarka zata sake batar da yarinyar idan ba ayi wani abu ba, zata iya hallakata kuma baya son sunan yar'uwarsa ko wani nasa ya sake fitowa” “Ina ya samu number Hameeda? Abunda baka sani ba Ibrahim mutane yanzu ba abun yarda ba ne, kowa kokarin yin abunda ke gabansa yake, mutane da dama suna amfani ne da kai dan cimma wani buri da manufa ta su” “Ta hanyar Hafsat ya samu a wacan lokacin, ita kuma ta samu ne ta hanyar Doc Isma'il, gaskiya ya kamata kai wani abu indai ba so kake ta sake cutar da yarinyar nan ba” “Nima yau an so ayi wasa da hankalina, wani bangare ina ganin kamar gaskiya ne, sai dai kuma na kasa yarda da hakan dari bisa dari...” A nan ya kwashe labarin abunda ya faru ya fada ma Ibrahim. “Amman baka tunanin yana da gaskiya?” “Da ace ganinsa nai yana cigiyarta wata kila da zan yarda, amman haka kawai zan hadu da mutum a tsakar falo daga ganin yarinya ya ce yarsa ce sai kuma na yarda? Zan sa a bincika min a garin da yake shin da gaske yarsa ta bata ko kuma karya ne, zan gwada jininsa, kuma zan sa ya kawo hoton matar da yake ikiraren matarsa ai ita Mama ta sana mahaifiyarta dan haka za ta iya shaidar mahaifiyarta ko a hoto. About Hameeda kuma ina tunani lokaci yayi daya kamata ace na fallasawa Mai Martaba komai, dole ne yanzu kan na fada masa gaskiya, ta yadda ko na dauki mataki akanta ba zai zargeni ba” “Nima haka na ga ya dace gaskiya, zan sa abincika mana a kadunar amman ka sama mana addirensa ta yadda zamu san ta inda zamu fara” “Zan samo inshallah, kuma ina son a sallami Isma'il yau” “Na yi tunanin yin hakan tuntuni, kawai dai bana son maka katsa landan ne shiyasa na kyale” Ya tashi tsaye tare da nufar kofar fita yana fadin. “Ina da aiki a ciki” Kwantawa Zain yai jikin kujerar yana kallon air conditioner dake tsaye ta can farkon shigowa katon office din. *** *** *** Tana tsaye jikin windows ta hango shigowarsa, a gurin ta kasa ta tsare saboda mugun kudirin da take da shi har ya gama abunda zai yi ya fito ya shiga motarsa ya fita. Sai ta dawo kuryar dakin ta bude bedside drawer dinta ta dauko wani abu a gora mai kamar rubutu ta saka a kugunta sannan ta dauki Hijab dinta ta saka ta fito daga dakin ta sauko kasa cikin rashin natsuwa da faduwar gaba ta bar part dinsu ta nufi Part din Zain, wata zuciyar na raya mata ko dai ta koma ta ba Abida ta zuba mata? Sai kuma ta tuna shirmenta zata iya cewa tana jin tsoro ko kuma ta ce Farhat din ta hanata shiga. A waje ta tsaya tana kallon bakin kofar kamar ta zuba abun a nan, sai kuma taji tsoro wani ya ganta kasancewar duka dakunansu sama suke duk wanda ke sama zai iya hango na kasa ko da ba a part din yake ba. Musamman ma su da suke kusa sosai da part din Zain, idan ta watsa a nan wata kila daya daga cikin sisters dinsa su gani. Hakan yasa tai knocked din kofar sai waiga waige take kamar mai tsoro a tararda ita a gurin ta kusan minti goma tsaye a gurin har zata sake knocked sai kuma ta kai hannu ta tura kofar falon sai ta bude, ashe daman abude take, ganin falon babu kowa yasa ta jidadin hakan sai dai tana fargabar karta fito ta ganta wata kila ma tana kitchen ko dakinta. Ko da Hameeda ta shigo falon Farhat na ciki tana wanka, taji lokacin da akai knocked din hakan yasa tai saurin fitowa daga wankan, bata tsaya shafa komai ba ta zira zane da riga ta nufo kofar fita domin taji lokacin da aka turo kofar falon, a bakin kofar bedroom din ta tsaya tana kallon Hameeda wacce take ta aikin barbada wani abu a hanyar Kitchen tare dayan hannunta rike da gorar rubutu mamaki ne ya hana Farhat motsin kirki bare har tace wani abun. Juyawa tai ta koma dakinta ta dauki wayarta ta shiga message tana tsara sakon da zata aikatasa zan. _Ka yi sauri ka zo ga Hameeda nan tana zuba magani a kofar kitchen amman bata san na ganta ba_ Har zata tura sai kuma ta fasa ta saka sakon a draft, ta fito daga gurin message din ta shiga contacts sai ta tuna bata da number Zain daman can bata da number barre yanzu da aka mata welcome back na line wasu numbobin basu dawo ba. Hakan yasa ta yanke shawarar daukar ta a video da sauri ta shiga, camera ta danna video recording ta fito rike da wayar tana dauka har lokacin Hameeda na nan tana zubawa sai dai yanzu a dinning area take watsawa. Takun saukowar Farhat ne ya dago da ita tai saurin kallon stairs din. “Me kike aikatawa Hameeda? Magani kike zuba mana bayan sherin da kika ma Zain? Hakan be isheki ba sai kin kara da magani? Wai ana so dole ne? Yace baya ra'ayinki miyasa ba zaki kyaleshi ba?” Farhat ta fada tana kara sauta wayarta tana daukarta da kyau. Hameeda kam ta tsaya a gurin kamar an dasata. “Yanzu Kan komai ya kare, kowa sai yasan abunda kike aikawata, sai na fallasa komai tun daga kan siyar da yarinyar kauyen nan da kika yi? Da kuma sherin da kika bi Anty Ummi da shi na cewar ta sace yarinya, da kuma sherin da kika ma Zain kika zuba masa abu a fuska kika sumar da shi kika cw yayi raping dinki, sai na tona miki asiri a cikin gidan nan, sai Dada da Mai Martaba sun gane Wacece ke, kuma sai masarautar nan ta san zamanki a tare da su hatsari ne, kin ga wannan video da nake dauka sai na nuna kowa abunda kika aikata shi zai zama shaidata, kin ga dole ne Mai Martaba zai zama zaman lafiya da kwanciyar hankalin dansa ko kuma zama da mace makira irinki, Dada ma da kanta sai ta kyamace ki dan ba zata taba son abunda zai cutar da Zain ba, tana miki kallo mai kirki bata san ke makira ba ce” Muryar Farhat kamar tana fada da Hafsatu manga taji ne yasa tai saurin fito daga dakin ta zo bakin kofa ta tsaya tana kallon Farhat din wacce tuni ta kai kasa hannunta rike da waya tana dauka Hameeda, Hafsatu manga na hango Hameeda gabanta ya fadi sai kallon tsoro take mata duk kuwa da kasancewar ita Hameeda bata ganta ba, ba zata taba manta fuskarta ba, ita ce wanda ta tsareta tare da dan sanda nan a lokacin da suka laka mata iyayen karya. Baya baya Hameeda ke yi tana hawayen tashin hankali Farhat kuma na kara matsawa kusa da ita tana cigaba da daukarka, duk da irin sanyin ac da falon yake da shi hakan be hana Hameeda hada gumin tashin hankali ba, gaba daya ta rikice numfashinta har sarkewa yake. From head to toe Farhat ta sake daukarta sannan ta juyo tana fadin. “Yanzu kam asirinki ya tonu ba zan kyaleki ba wannan karon abunda kike yabisa haka” Hameeda ta bude baki ta saki abunda ke hannunta sai kuma ta daga hannun kamar zata kira Farhat sai ta kasa, ta hade yawun bakinta tana wani irin wahaltaccen numfashi wanda ya ki shiga sai dai ta fitar da wanda ke ciki, waiga tai bayanta ta kalli dinning din, idonta ya sauka kan wukar dake gurin da sauri ta kai hannu ta dauka ta yo kan Farhat. “Bayanki bayanki” Hafsatu manga ta fada tana ihu tare da rike kai. Farhat na juyowa Hameeda ta suka mata wukar iya karfinta ta jata, ba shiri Farhat ta saki wayarta ta fadi kasa ita tama ta fadi baki bude tana fada hannu saman dayan hannunta kuma na kan wukar. Hameeda ta yi saurin daukar wayar ta tsallaketa ta fice da gudu daga falon. Wani irin kara Hafsatu manga ta saka ta dafe kanta ta duke a gurin, sai kuma ta sauko da gudu ta yo kan Farhat, duk irin tsoron hawa da sauka stairs da take yau kam ta manta da shi, hawayen da taga suna zuba a idon Farhat ne yasa ta kai hannu tana kuka zata cire nata wukar.... Cikin rashin natsuwa da kwanciyar hankali ta dawo part dinta, bakin gadonta ta zauna tasa hannayentata rufe bakinta tana hawayen. “Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un, na shiga uku, na sake kashe rai na kashe *RAI BIYU* asirina zai tonu” Tayi saurin daukar wayar ashe har yanzu video kunne yake, cikin sauri ta danna red button wato stop ta video ya daina dauka sai ta shiga gallery da zimmar goge video but unfortunately suka nuna mata ta saka password. “Na shiga uku” Ta jefar da wayar, sai kuma tai saurin daukar wayar ta kashe ta daga katifarta ta aje wayar a gurin, sannan na nufi windows tana leken part din Zain, gumi sai zubar mata yake cikinta na mugun murdawa, jinginawa tai a gurin. “Mi na aikata na shiga uku, na bani na lalace wayyo Allah na” Ta fada tana kuka. Kamar an tsikareta sai kuma tai saurin tashi ta nufi inda wayarta take ta dauka ta kira Abida tana kokarin daidaita muryarta. “Ki shiga gurin Farhat tana son ganinki Yanzun nan” Bata jira abunda Abida zata ce mata ba ta kashe wayar, ta fashe fashewa da kuka.... [3/21, 8:54 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *Masu karanta min novel basu biyaba da masu sharing Novel dina, Allah ya muku yadda kika min. Idan kina son biya ki turo 300 ta 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, sai ku turo da shaidar biyan ta wannan number 08036126660, ko kuma katin MTN na 300 ta wannan number 08036126660* I repeat don't read my novel if you didn't pay. 46. Ganin ba za ta iya cire mata wukar ba, yasa ta tashi da gudu tana kuka ta nufi kofar fita, bata karasa ba Abida ta turo kofar falon ta shigo, sai Hafsatu manga ta kasa magana sai nuna mata Farhat take tana hade yawu da karfi numfashinta na tashi sama sama. Abida bata fahimci abunda Hafsatu manga take magana akai ba, har sai da ta karasa kusa da ita sai ta dora hannu saman kai ta kurma wani uban ihu. “Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un, na yi mugun gani, kasheta kikai?” Ta karasa tana kallon Hafsatu manga, kai Hafsatu ta girgiza mata tana kuka. Sai Abida ta fita da gudu tana ihu da kiran jama'a, can bayan kujeara Hafsatu manga ta koma ta rabe ta yadda ba za a ganta ba, ta fashe da kika. Kururuwan Abida ce ta fito da kowa dake cikin gidan fito waje ciki har da Hameeda wacce ta gama fita natsuwarta. Sai a aka dunguma aka nufo part din Zain. Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un kowa ke fadi, Hajiya Hadiza ce ta sa a dauki Farhat a kai asibiti, Sapna kuma ta kira Zain ta sanar da shi halin da ake ciki. “A kira police su tafi da ita, wannan yarinya annoba ce” Cewar Dada idonta na cika da hawaye, wasu na mamakin yadda Hafsatu manga za ta cakawa Farhat, yayinda wasu kuma suke mamakin ita din wace irin yarinya ce daga kawo ta jiya jiya yau tai wannan aika aikar, dukan wasu kananan maganganu a tsakanin yan gidan yake tashi. Mai Martaba ne ya aiko da kansa cewar kowa ya watse, a dole kowa ya kama gabansa, aka ja kofar part din aka rufe Hafsatu manga na ciki. Wani irin mahaukaci Faki Zain yai a lokacin da ya iso gurin, ya fito cike da tashin hankali ya tura kofar falon ya shigo, jini kawai ya tarar domin tuni an wuce da Farhat zuwa asibiti, kukan Hafsatu manga da yaji ne yasa shi kallon inda take labe tana lekensa. Kai ta girgiza masa. “Ba... Ba... Ba... Ba ni... Ni ba ce” Ta hannu yai mata alama da ta zo sai ta taso da gudu da nufo inda yake, kamin ta karaso police suka shigo falo Dada Yalwa na biye da su a baya, tare da wasu mayan dogaran Sarki. Juya tai da gudu ta koma gurin ta labe ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya. “Gata can ja'izar yarinya Annoba” Dada ta nunawa police din ita. Sai ya mike tsaye da idanuwansa da suka kada suka yi ja ya kallo police din ya ce “Ba ita ba ce karku taba” “Ka yi hakuri ranka ya dade babu abunda zai hanamu aikinmu” Biyu daga cikin police din suka nufi inda take suka daukota tana wani irin ihu kamar za'a cire mata rai. Zain rigansu fita yai ya koma cikin motar ya fisgeta kamar zai tashi sama, asibitinsa ya nufa dan yasan can za a kaita domin can ake kai familynsu idan basu da lafiya, ko parking din kirkir be yi ba ya fita ya shiga cikin asibiti tafiyar ce tai masa nisa har sai da ya hada da dan gudu ko da ya isa, Hajiya Hadiza da Hajiya Zarah da wasu kanensa suna tsaye bakin emergency room. “Tana da rai?” Ya tambaya tun kan ya karasa kusa da su, gabansa dai dukam uku uku yake. “Bamu sani ba, suna ciki suna dubata” Hajiya Hadiza ta amsa masa tana share kwalla dake mata zuba, har ya nufi gurin ya shiga sai kuma ya tsaka cak ya dafw kansa ya runtse ido, juyawa yai ya fice daga gurin gaba daya, gurin motarsa ya koma sai kuma ya rasa abunda zai yi, jinginawa yai jikin motar ya rumtse idon, zuwa can kuma ya bude ya ciro wayarsa dake aljihu ya kira Dcp, Dcp na picking Zain ya ce “Ka aiko min da yaranka biyu yanzu nan, masarautar mu an yi kisan kai” “Subhanallahi wa...” Be karasa tambayar ba, Zain ya kashe wayar ya bude motarsa ya shiga ya dauki hanyar fada. Ya riga su isa a cikin motar ya zauna har sai da suka iso, sannan ya fita daga motar yai musu magana suka rufa masa baya kasancewar shine a gaba, part din da su Hameeda suke ya nufa yana taba kofar dakin ya ji ta a rufe sai yai knocked, shiru bata bude ba, juyowa yai da su suka nufo part din Dada, yadda kasan an aikoshi haka ya banki kofar dakin ya shiga, tana falo zaune ita Dada Yalwa da alama maganar ce suke tattaunawa. Tana ganin Zain din da police sai ta mike tsaye da sauri tana kallonsa. “Ga nan” Ya nuna musu ita, sai tai baya baya idonta na cika da hawaye. “Mi nai?” “Ana zarginki da kisan kai” Dan sandan dake kokarin rika hannunta ya saka mata handcuffs ya fada mata, sai Dada ta saka salati tana tashi tsaye. “La'ilaha'illallah, Zain ko ka haukace ne, ga yarinyar da kanzo da ita jiya ita tai aika aikar fa, zaka lakawa Hameeda kamar wanda baya gani” “Idan ma da ke ta hada baki ake kokarin kashe min mata, zan ba ku mamaki, idan kuma yin kanta ne a karan kanta zata fuskanci hukunci” Ya furtawa Dada cikin bacin rai sannan ya kalli police din ya ce “Ku wuce da ita” Suna janta ta fara ihu tana kiran sunan Dada Yalwa. “Dada za su tafi da ni, wayyo Allah na Dada ko taimakeni....” Wani irin kuka take tana kiran Dada, gani take kamar idan sun tafi fa ita gidan prison za a kaita kai tsaye. Ihunta ne ya dago hankali duk wanda ke kusa da part din Dada kowa ya fito yana kallon ikon Allah, dan kowa mamakin ganin an kama Hameeda ya ke, Ikram ce tai saurin zuwa kusa da Zain tana fadin. “Yarima ba fa ita ta aikata ta....” Bata karasa ba ya wanke mata fuska da mari har sai da yai baya kamar za ta fadi. A bayan motar yan sanda aka saka ta tana ta kuka hannunta sanye da handcuffs. Kuka sosai Dada take cikin rashin karfi irin ana dattawa tsofi ta fita ta nufi part din Mai Martaba. Tsaye Zain yai a harabar gurin yana kallonta har sai da aka wuce da ita sannan ya nufi motarsa ya shiga gabansa na mugun faduwa. Asibiti ya koma wannan karon da yai parking kasa fita yai daga motar sai hawaye ke sauko masa daya bayan daya, wani dogon numfashi yaja ya sauke ya jingina kansa ga sitarin motar..... Ku yi manage please bana gida ne, rabin page ne gobe zan yi two page karashin cikon da kuma ma goben inshallah. [3/22, 11:51 AM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 46b Yafi karfi awa daya a cikin motar wayarsa sai ringing take amman ya kasa daga kansa ma daga sitarin balle har ya duba mai kiran wayar, wani iri yake jin kansa abubuwa mabanbanta yake tunani. Kama Hafsatu manga da kuma Farhat, Farhat din ce ta fi tsaya masa a rai rayuwarta da mutuwarta yake tunani. Knocked glass din motar akai hakan yasa shi dago kansa ya kalli Ibrahim sai ya kai hannu a zoke gilashin motar yana kallonsa da idanuwansa suka kade suka yi ja sosai. “Ya kamata ka kira iyayenta ka sanar musu” Sai ya dauke kansa daga barin kallon Ibrahim sannan ya ce “Ta musu ne?” Ibrahim be amsa masa ba, sai kawai ya ce “Bari na kira Anty Ummi” Wayarsa ya ciro ya nemi number Anty Ummi ya aika mata kira, tana picking ya fada mata abunda ya faru kuma ya sanar mata suna asibiti, Zain ya kasa kunne sosai yana son yaji ko zai fada mata tana raye ko mace amman ya be ji ya fadi ba. Har ya kai hannu ya bude motar ya fito, sai kuma yaji ba zai iya ba, jikinsa y mutu sosai ko lokacin da Haleema za ta rasu be ji irin wannan abun ba, be san takaimaiman abunda yake ji ba a yanzu, iyakar abunda ya sani akwai tsoro da fargaba a tare da shi, tsoron kar yaje ya ga gawar Farhat, fargabar kar ya ganta cikin mawuyacin halin da take ciki, taya raye ko a mace, bashi da amsar wannan tambayar a yanzu. Cikin rashin kuzuri ya kai hannu a karo na biyu ya bude motar ya fito ya nufi hanyar office din, domin baya son zuwa emergency din kar yaga Farhat. Cikin office dinsa ya shiga ya zauna ya dora hannayensa saman tebur din ya dafe kansa, haka kawai hawaye ke masa zuba, rabon da ya zubar da hawaye haka har ya manta. Shigowar Ibrahim ne yasa yai saurin tashi daga saman kujera ya nufi gurin windows ya tsaya dan bayan son Ibrahim din ya ga hawayensa. Cike da tausayinsa Ibrahim ya karasa inda yake tsaye ya kai hannu ya dafa kafadarsa. “I'm sorry Zain, she can't survive ita ma ka rasa ta...” Ibrahim ya fada yana kuka. Kamar daga sama Zain ya ji maganar, sai da numfashinsa yai nisan zango na yan seconds sannan ya dawo jikinsa. Wasu hawaye ne masu mugun za fi suka zubo masa, juyowa yai yana ture hannun Ibrahim dake kafadarsa. “Mata nawa zan rasa ne? Mace nawa zan aura su mutu? Miyasa bakinciki mutuwa yake ta daummawa a rayuwata ne? Ko yaushe sabon babi ake bude min, ko yaushe sabon tabon mutuwa na ke samu a zuciyarta....” Ya fada yana fashewa da kuka. Sai kuma ya dafe kansa yana fadin. “Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un” Ibrahim yayi saurin rikeshi, kamar an zame kafafunsa daga kasa haka ya tafi rifff ya fadi jiri na dibansa, ba suma yai ba sai dai har yanzu dakin juya masa yake hakan yasa shi saurin rumtse idonsa. Sai Ibrahim ya sake shi da sauri zai nufi kofa Zain ya kira shi. “Karka kira kowa, bana bukatar a amin komai” Cikin karfi hali ya tashi tsaye ya share hawayen idonsa ya nufi kofar fita tare da Ibrahim, Emergency din ya nufa har yanzu Hajiya Hadiza da kanensa biyu suna tsaye a gurin suna aikin kuka, a bakin kofar dakin Ibrahim ya tsaya, Zain kan kai tsaye ya tura kofar dakin da take ya shiga. Har gurin gadonta ya karasa an rufeta da farin zane tun daga kanta har zuwa kafafunta. Hannu ya kai ya yaye zanen yana ta kallon fuskarta gata wance kamar yai mata magana ta amsa amman idonta a lumshe, risinawa yai ya sumbanci goshinta sai ya rika hannunta ya fashe da kuka. Yana haka Anty Ummi ta shigo jakar hannunta ta saki ta dora hannu saman kai tana hawaye. “Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un” Ta maimaita hakan yafi sau ashiri sannan ta fashe da kuka, kamar wacce ta tuna wani abu sai tai saurin share hawayenta ta nufi inda Zain yake risine yana aikin kuka ta janye hannunsa daga na Farhat ta rufe ta dafa kafadunsa tana fadin “Ka yarda da kaddara Zain, haka Allah ya rubuta maka kuka ba zai dawo da ita ba, kuma ba kuke abunda take bukata a yanzu ba” Hakuri take bashi amman ita ma hawayen take. Mikewa yai tsaye sai ya juya ya fice daga, karaso tai ta dauki jakarta ta fito tana share hawayenta. “Ina Hafsatu manga take?” Abunda ta tambaya kenan daga fitowarta daga cikin dakin. Hajiya Hadiza ta ce “Ban sani ba ni dai ko da na fito gida mun baro Dada tana fadin a kira police su tafi da ita” Anty Ummi ta kalli Ibrahim. “Ibrahim a aje mana gawar Farhat, kar a bar kowa ya taba ba, kuma kar a fita da ita, na fadawa yan'uwanta suna nan zuwa, su kadai na yarda su dubata, kar ka bari a fita da ita, wukar tana gurinku ko gida?” “Tana nan” “Aje min ita please” Tana fadar hakan ya nufi kofar fita har yanzu hawaye take, amman bata karyaba saboda ta shirya wannan tana ganin lokaci yayi da wasar Hameeda zata kare. Cid police ta fara wuce ta fara wucewa domin duba Hafsatu manga sai ta samu bata nan an kaita gidan yarin yara, daga nan ta wuce gidan yarin kai tsaye amman suka hanata ganinta babu yadda ba tai ba amman suka hana, wai kaifin babbane tun da tayi kisan kai. Sabon dpo ta kira wanda aka kawo bayan dauke Auwal, sai da suka gaisa yake sanar mata cewar an sake dauke shi amman akwai sabon da aka kawo, bata jidadin hakan ba, saboda ta dan soma sabawa da shi sakamakon irin aikin da suke na kare hakkin dan'adam. Cikin rashin kuzari ta nufi station din, bata sha wahala gurin wuce ba, domin ta fada musu daga kunyar kare hakkin dan 'adam take kuma tana son magana da Dpo ne,sai da aja tambaya mata uzini a gurinsa sannan ya bata damar shiga. Jikinta ne ya kara mutuwa lokacin da tai arba Auwal, ta sanshi kamar yadda shi ma ya santa sanadiyar Farhat da ke hadasu a waya ko kuma ta kawo mata shi har gida ya gaisheta, amman matsala zata iya fin haka dan zai iya saka son kai a ciki. Gurin zama ya nuna mata sai ta zauna jiki a sanyaye. “Na kira wacan dpo ne sai ya ke fada min an canja shi” “Eh shekara jiya aka dawo da ni, kin san yanayin aikin na mu, daga nan kuma za a iya kaimu wani garin matata na ma na can ban dauko ta ba” “Daman na zo ne akan maganar yarinyar da aka kama Hafsatu manga, wacce ake zargi da kisan kai” Ta fada idonta na cika da hawaye. “Wacece yarinya ce?” Ta tambaya da sauri. “Yarinyar kauye wannan wacce kanene yake rikonta, wacce aka kai maka ita a matsayin mai aiki” Ya tashi tsaye da sauri. “Wata kashe?” “Farhat” Anty Ummi ta fada hawaye na zuba a idonta sosai. Koma yai ya zauna yana jin maganar tana masa yawo a kai. Wayar Anty Ummi ce tai ringing sai tai saurin dauka ganin number Ibrahim ta kara a kunne. “Okay tau” Shine kawai abunda ta fada ta kashe wayar. Sai ta kalli Auwal din ta ce “Ba ita ta kashe ta ba, bana jin Hafsatu manga zata iya kashe ta ba taya ma za ayi ta iya kasheta ba zata iya ba, tarko ne aka hada ma” Har ta gama wayar tai wannan maganar Auwal be ce komai ba, idonsa sun kada sun yi mugun ja. “Farhat... Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un” Ya furta, sai kuma ya kalli Anty Ummi ya ce “Kun tabbatar da ta mutu ne?” “Likitoci sun tabbatar da hakan, yanzu Ibrahim ya fada min wai Zain yasa an kama Hameeda saboda ita yake zargi” “Ba zan iya miki komai ba a yanzu, idan ballin yarinyar kike son a baki ba zan iya baki ita ba a yanzu, dole ne sai munje koto” Ya fada yana kokarin maida kwallah da suka cika masa ido. “Kotun nake son aje, shiyasa nai saurin zuwa nan, saboda na san Dada Yalwa da Mai Martaba zasu iya bukatar a kashe maganar saboda gudun zubewar mutuncin masarautarsu, iyayenta kuma na san zasu iya cewa sun yafe, amman idan kungiyarmu ta shigo ciki, kuma kai tsaye dole gaskiya zata fito kuma dole a gane mai laifi, ina son a wanke Hafsatu manga ne kuma a kama Hameeda ta dandani kudar abunda ta aikata” “Zamu komai, ba zaki iya ganinta ba, lauyanta ne kawai zai iya ganinta, kuma ba zamu shiga kotu ba doka ce under age ba a shiga kotu da su sai da lauyansu wanda sai yi magana a madadinsu” “Zamu shirya komai, kungiyarmu zata shigo ciki, na san lauyar da zata tsaya mata kwararriyar lauya ce, goyon bayanka kawai nake bukata dan Allah kar a hada baki da kai a kashe maganar nan” “Ba zan yi ba, Farhat kamar yar'uwa take a gurina ba jininta ba zai je a banza ba, ba kuma zan zuba ido Hameeda ta ci bulus akan Hafsatu Manga ba, zan yi duk abunda ya dace ina gawarta take?” “Tana Zainuddeen Special Hospital” Kai ya daga mata, sai ta tashi ta fice daga office din tana hawaye. “Da ban yaudareki ba, dan yanzu baki mutu ba, da yanzu kina can gidana cikin kwanciyar hankali, amman ba zan bar wannan ba... ” Ya fada yana share hawayen da suka zubo masa har cikin ransa yake jin mutuwar Farhat din. Telephone din dake gabansa ya dauka ya kira sai ga wani police ya shigo da sauri yana sare masa, fada yai masa sosai akan rashin sanar da shi kisan kan da basu yi, sai yace takardar ce yake cikewa shiyasa be kawo ba... [3/22, 2:22 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *Masu karanta min novel basu biyaba da masu sharing Novel dina, Allah ya muku yadda kika min. Idan kina son biya ki turo 300 ta 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, sai ku turo da shaidar biyan ta wannan number 08036126660, ko kuma katin MTN na 300 ta wannan number 08036126660* 47. Gaba daya masarauta Rishim tai tsit baka jin komai sai zancen kisan kan, a take maganar ta fara leka makota saboda yan aji a kara gaba. Mai Martaba na dakinsa yana sauraren korafin Dada dake kuka tan zayyana masa kama Hameeda da Zain yai, sai ga Hajiya Zarah ta shigo tana sanar masa cewar Farhat ta rasu, tun da ta fada masa maganar ya soke kansa kasa be dago ba har sai da Hajiya Maryam ta shigo ta zube a gabansa. “Allah ya taimake ka, ya kamata kai wani abu saboda gudun zubewar kima da mutuncin masarautar nan, an kama Hameeda a motar yan sanda, abunda be taba faruwa ga wani dan sarautarta ba yau ya faru a gidan nan, maganar nan fa yada ta za ayi, idan har ba kai wani abun ba, yanzu kuma ga dpo can ya zo ya shiga part din Zain yana bincike, anjima kadan nasan wata maganar ce zata sake tasowa saboda Ummi ba zata kyale ba, dole za atayi abunda zai zubarsa mutuncin masarautar nan daman can ba son mu take ba” “Shine abunda na gani, na san ai ita ce ta turo Zain din ya kamata saboda bata kaunar Hameeda in ba dan haka ba, mi zai sa Hameeda a cikin lamarin bayan kuma ga wacce tai abun an kama ta dumu dumu” “Ku bar hukuma tai aikinta, idan kotu suke son zuwa sai a tafi a can za a bayyana mai gaskiya da marar gaskiya, za a sako Hameeda domin Zain be da hurumin rufeta domin ba ita aka gani a gurin ba” Haka kawai abunda Mai Martaba ya fada. Sai kowa yai shiru, ita dai Dada an biyata tun da ya ce za a sako Hameeda. Tun daga baki kofa wani dan sandabke daukar hoto har aka isa gurin da jini ya zuba, wato inda aka caka ma Farhat wukar. Anan wani police din ya debi jinin ya zuba a wani gurin, Auwal kuma ya karasa gurin da gorar rubutu da kulli magani suke ya saka safar hannu sannan ya dauka yana dubawa, a cikin wata farar leda aka saka gorar, dayar kuma aka saka kullin magani, haka ya bi cikin gidan ya duba komai ya dauki abubuwan da yake son dauka sannan yasa aka kira Abida yai mata tambaboyi, sannan ya kulle part din gaba daya ya tafi da makullin. Daga gidan Asibiti suka nufo already an kai Farhat mutuware, da taimakon Doc Ibrahim aka bude musu gawar suka dauki hotonta ya basu wukar suka sakata a cikin wata ledar wacce aka rubutawa evidence, sannan suka fito, mahaifiyar Farhat ce da wasu tsofi biyu suka tare Auwal suna rokon a ba su ita wai su sun yafe. “Idan kun yafe, govnati ba zata yafe ba, dole ne sai na hukunta mai laifin” Shine kawai abunda dpo ya fada musu ya wuce ya barsu suna aikin kuka. Anty Ummi ce take bawa Mahaifiyarta hakuri ita tana kuka. “Ba a baku gawarta amman yanzu kin ga kotu za a shiga, dole ne sai hukunar yan sanda sun yi bincike kamin a rufeta gudun kar a rufeta kuma wani abun ya taso, case yanzu a hannun yan sanda yake” “Kaddarar rayuwace ta fada mata, daman can ban so auren nan ba, babu yadda ban yi ba akan ta auri mijin yar'uwarta amman ta ki, daman nasan wani abu sai ya faru tun da yayan manya basa daukar talaka da daraja, gashi yanxu sun kashe min ita sun huta” Ta kara fashewa da kuka, sai kuma ta juyo tana rokon Anty Ummi. “Na hada ki da girman Allah, ki taimaki ki sa baki a bamu yarinyar nan, saboda ayi mata sutura kamar yadda addinin musulumci ya tanada, wannan abun da kuke kokarin ne kamar kuna wulakanta gawarta ne, na bar banda ya kasheta da Allah lahira Allah yai masa hukunci ranar da komai baya boyuwa” “Za a baku ita Inshallah amman ba yau ba, ban kuma miki alkawari gobe ba, amman da zarar an gama bincike za a bada gawarta” Anty Ummi ta fada cikin wani irin kuka. Daga asibitin da taho da su gidanta, da yamma lis wasu yan 'uwanta suka ciko mata suka taho, tun da suka dawo gida Anty Ummi take ta zirga zirgar fadawa abokan aikinta abunda ya faru. Tun da ya shiga office dinsa be fito ba, ya zauna a ciki har dare, babu irin magana da hakurin da Ibrahim be bashi ba, amman uffan Zain be ce ba. Har sai da Mai Martaba ya aiko kasanensa waziri ya tafi da shi. Ana isa ya bude motar ya fita ya nufi part din Mai Martaba, ko da ya shiga shi kadai ya samu a karamin falonsa, be daga kai ya kalli Mai Martaba ba kuma be bude baki ya yi masa sallama ba. Mai Martaba na kallonsa ya san dansa yana cikin damuwa domin alamu sun nuna haka ga idonsa da yai mugu ja kamar an watsa masa barkono a ciki, kusa da Mai Martaba yaje ya zauna ya sadda kansa kasa yana sauraren abunda Mai Martaba zai fada masa, shiru shiru be ji Mai Martaba yace komai ba, hakan yasa ya dago kansa ya kalli Mai Martaba sai hawaye suka zo masa. “Dan Allah karka sa bakinka a cikin maganar nan Mai Martaba, ba sheri nake son yi ma Hameeda ba, ina da yakini da tabbacin cewar ita ta kashe Farhat, abubuwa da yawa suna faruwa ban tba sanar maka ba, saboda bana son tashin hankalinka, na san baka son Farhat, amman ni hakkinanne na kareta ko da bata da rai...” Mai Martaba ya kalleshi irin kallon nan na natsuwa dake tsakanin da da uba. “Ka ji abunda na ji a lokacin dana rasa mahaifiyarka, ka akwai ciwo sosai Zain karasa mutum mai muhimmanci a rayuwarka, ina tausayin rashin mata biyu da kai da kurciyarka, amman ina son ka kwantar da hankalinka, kuma kai hakuri, ba zan goyin bayan matarka a cima Hameeda mutunci ba, haka kuma ba zan goyi bayan Hameeda a cutar da kai da karamar yarinya ba, ba zan hana ka saka karar a kotuba, amman ina rokon ka janye zancen kama Hameeda a cell, a dawo da ita gida, ka taba mutuncin masarautar nan Zain kuma ka taba mutuncin Hameeda ma sawa a kamata a kaita cikin cell a kulleta” “Mai Martaba Hameeda shu'uma ce, ita ta kasheta” “Na san shu'umace tun daga lokacin da Hajiya Hadiza ta fada min abunda ta aikata maka, amman baka da tabbacin ita tai kisan Zain dan haka karka yanke hukunci a take, ka bar hukuma da kotu su yi aikinsu” “Mai Martaba Hameeda ta kashe Farhat ne saboda tana tsoron kar asirinta ya tonu, ita ta siyar da yarinyar nan a masarautar Damagaram....” Daga nan Zain ya tsakurawa Mai Martaba abunda ya faru from AtoZ. Mai Martaba ya jinjina kai yana mamakin karamar yarinya kamar Hameeda amman ta iya shirya wannan abun, ba zai karyata dansa ba dan yasan ba zai fada masa karya ba, dama ya yanke da lamarinta tun daga lokacin da Hajiya Hadiza ta labarta masa abunda Ikram ta fada mata wanda ita da Ikram din suke zargin ita ta shirya komai, domin Ikram din ta fada mata ko da suka je baya cikin hayyacinsa. “Hakan ba zai hanani saka baki a cikin lamarin ba, domin a karkashina take, tana zama ya a gurina, da hukuma ce zata yai aikinta ba zan hanata ba, amman kai ba zan zuba maka ido ka ci mutuncinta ba, dan haka ina umartarka da kasa a saketa, kotu zata bayyana komai, adalci daya zan maka Zain ba zan hanaka rawar gaban hantsi na kwatowa matarka hakkinta ba” Zain yaji dadin jin wannan maganar daga bakin Mai Martaba, hakan ya nuna yana goyon bayan aje kotun ba kamar yadda yake ganin kamar zai bari ba, daga nan Mai Martaba ya dora masa da nasiha da kuma nuna akan halin rayuwa. Hakan yasa Zain ya dan sake har ya tashi ya fita, da kansa yaje station din yasa aka saki Hameeda sai dai be yarda ko ido biyu sun yi ba ya dawowarshi, ita ta ari wayar wani a cikin gurin ta kira Dada ta sanar mata ansake ta, da Dada aka zo daukarta da Hajiya Maryam, tana ta kuka gwanin tausayi kuka kisan data aikata take gaba daya jin take ta tsani kanta, natsuwarta ta bar jikinta, bata jin abunda take ji a yanzu ba, ko a lokacin da Haleema ta mutu bata ji irin wannan ba wata kila saboda ita ba wukar ta soka mata kamar yadda tai ma Farhat ba. Hajiya Maryam da Dada hakuri kawai suke bata sun dauka ko tana kukan ne saboda kazafin da tozarcin da Zain yai mata. Sai dai har aka isa gida bata daina kukan ba, tana shiga dakinta ta kulle kanta cikin dakin ta fadi kasa ta fashe da kuka, Dada Ma kuka take a dakinta ganin Yar lelenta na kuka, wai ai dole Hameeda tai kuka saboda Zain ya tsaneta ya wulakantata. *** *** *** Cikin damuwa da bakinciki ya koma Kaduna, yana ta neman dalilin daya hanashi neman matar amman ya rasa, yana ta tunanin ya shiga ciki gari ya nemanta ko kuma ya dawo garin daya hadu da yarsa sai yaji ba zai iya ba, amman tabbas ya san wannan yarinyar yarsa ce, amman yana jin kamar ba zai iya komai a kai ba. Tunani yai masa yawa ta ina zai fara me zai yi yana cikin ransa amman shi da wani kuzarin aikatawar. Yana sauka jirgi direbansa ya zo daukarsa, sai yasa aka wuce dashi asibiti saboda yana jin kamar jininsa ya hau. Likitan daya saba duba shi ne ya duba shi wato likitansa, sai dai yai masa magana akan yawan tunani kamar yadda yake masa ko yaushe, sannan ya bashi kyakkyawar kulawa domin jininsa ya hau kusan 230, kwantar da shi akai asibiti, duk yadda ya so ya sha ruwan sanyi sai lokitan ya hana saboda lafiyarsa. Sam ya manta da ya kashe wayarsa sai yanzu da yake da zimmar kiran Hajiya Safiya ya fada mata cewar ya iso, kunna wayar yai ita ce wacce ya fara kira sai akai rashin sa'a Hajiya Halira ta dauka wato yayarta. Bayan sun gaisa take sanar masa cewa bata da lafiya. “Me ya same ta?” “Ciwon kai ne wai kan take jin kamar zai tsage” “Kuje asibiti mana, nima gani anan zan dan huta kamin anjima jinina ya hau” “Subhanallahi lafiya dai? Ko wani abun ya faru” “Ba komai” Ya kashe wayar, sai ya kira Number Ummi kamar yadda yake rubuce a number, ta dade tana ringing sannan ta daga ciki yanayin damuwa. “Ummi dan Allah yaron nan nake son magana da shi, ina son ki hadani da shi” “Ya Wallahi yanzu ba zan iya ba, muna cikin matsala yarinyar da ka ce yarka ce ita ake zargi da kisan kai ta kashe matar Zain yanzu yanzu haka tana hannun yan sanda” “What..?” Ya furta da karfi yana tashi daga kwancen da yake. “Garin ya haka ta faru” Nan ta zayyana masa abunda aka fada mata akan maganar da kuma matsayarsu. Yana sauke wayar ya kira direbansa ba tare da sanin likitan ba ya bar asibiti ya koma gida. Cikin tashin hankali ya shiga falon Hajiya dan labarta mata abunda ya gani, sai ya tararda yayarta da kanwarta suna zaune ita kuma tana bedroom tana shiryawa dan zuwa asibitin ganin ciwon kanya matsa mata. Da sallama ya shiga falon suka gaisheshi ya amsa musu suna masa ya jiki. “Al-hamdulillah” “Alhaji da ka rage yawan tunanin nan ance shine yake kara janyo maka hawan jini fa” “Wato wani abun ne na gani wanda ya tashi hankalina sosai, wata yarinya na gani mai kama da Rufaifa, kuma ina da tabbacin yarta ce” “Wace Rufaidar dai Alhaji?” “Rufaida Matata mana uwargidana” “Wallahi karya ne Alhaji ba yarka ba ce, duk wanda ya ce maka yarkance yana son ya yaudareka ne kawai” Cewar Hajiya Safiya wacce ta fito daga dakinta ba tare da ta karasa shirin da take ba, sakamakon zancen da taji Alhaji na yi. “Babu wanda ya ce min yata ce, ni na ganta da idona a gidan yar'uwata, domin naga awarwaron dana siyo mata a lokacin da ba haife ta ba, sai dai ita yarinyar dana gani yanzu karama ce” “Ka gani ko? Rufaida ta bar gidan nan da ciki yanzu sama da shekara ashiri da biyar ko zamanta gidan nan da cikin nan ai ta shekara biyar, sai kuma ace ta haifi karamar yarinya ace yarkance, wallahi ba yarka ba ce yaudararka kawai ake son yi karka yarda” “Sai na yi bincike sannan zan tabbatar da yata ce ko ba yata ba, amman alamu sun nuna cewar yata ce, dole ne na nemo Rufaida duk inda take a duniyar nan” “Na shiga uku, Wallahi karya suke maka Alhaji ba yarka ba ce, dan girman Allah karka kawo Rufaida gidan nan, wayyo Allah na...” Sai ta dafe kanta tana jin kamar zai rabe mata biyu..... _______________________________ Ku yi hakuri da rashin Editing, kuma ku yi hakuri da yadda nake rushing din rubutun, maybe ba zaku ji dadinsa yadda ya dace ba, amman ina son mu gama ne kamin azumi. Ga wadanda basa son mutuwar Farhat kuma kuyi hakuri, haka na tsara labarin tun farko, idan wasunku basu manta ba na fadi cewar Hassana da Husaina za su tsaya a gaban alkali domin shari'a that's means akwai kisan kai a ciki kenan. Ina fatar za ku fahimta. Thanks ♥️🖤 [3/24, 5:02 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 48. Da saurin ya karasa kusa da ita ganin yadda ta rike kan, Hajiya Halira ta mike tsaye tana fadin “Bari na dauko miki ma fi muje asibiti” A gurin ta zauna tana ta kuka saboda kanta da take jin kamar zai rabe gida biyu. A motar suka saka ta duk da irin nauyin zuciya da jiri dake diban Alhaji Habib be hana shi binsu zuwa asibitin ba, suna isa aka basu gado aka daura mata drip suka sa mata maganin a ciki nan da nan bachi yai gaba da ita, su Hajiya Halira da Maimunatu ne suka tsaya shi kuma ya juyo tare da direba ya nufi Family house din su Rufaida. Yana dosar gidan gabansa na faduwa, a harabar gidan direbansa yai parking, sannan ya fita ya nema masa uzini shiga cikin gidan, an fada masa Mai gidan baya nan amman jin shine yasa aka bashi izinin shiga. Da kansa ya bude motar ya fita a hankali yake takawa yana jin wani zafi da zuciyarsa ke masa numfashinsa na yin sama kamar zai fita. Dan Madaidacin falo ne ba a kawatashi sosai ba, amman an masa gyaran da babu wanda zai shigo ya raina gidan. Be yi zaman mintuna uku ba sai ga wata dattijiwar mace ta fito sanye da hijabi hannunta rike da sandar karfe ta dafawa a hankali dayan hannunta kuma rike da carbi, idonta na sanye da gilashi irin wannan na tsufi, mafara ce sosai kana ganinta ka ga ruwan fulani duk da kasancewar tana da jiki. Kallo daya zaka mata ka fahimci cewar mahaifiyar Rufaida ce domin babu abunda ta rage daga kammamin Rufaida. Cikin girmamawa Alhaji Habib ya gaisheta, ta amsa mishi tare da daga masa hannu. “Hajiya daman na zo ne akan maganar Rufaida” Daga kai tai ta kalleshi sai ta kai hannu ta cire gilashin idonta sai ga hawaye ya cika idonta. “Jiya duk a nan yan'uwanta suka taru suna kukan rashinta, shekaru kusan talati bata tare da mu amman babu wanda ya taba magana, kuma babu wanda ya taba nemanta, ashe tana cikin ran kowa furtawarne kawai ba a iya yi, kullum da ita nake kwana da ita na ke tashi, ban san hali da yata take ciki ba, ban san wace irin rayuwa take ba, tana a raye ko a mace ban sani ba” “Nima kaina ban san abunda ya hanani nemanta ba, ni dai na san na dawo daga jumma'a na shigo gida sai na samu bata cikin gidan, ban tambaya ba sai kawai na saka aka rufe part din ba tare dana nemeta ba, amman Wallahi Hajiya kullum da ita nake kwana da ita na ke tashi, a gusau naje gaisheda mahaifina sai..... ” Ya tsakura mata labarin Hafsatu manga wacce yake zargin yar Rufaida ce saboda awarwaron dake hannunta da kuma kammaninsu. Hajiya tasa hannu ta share hawayenta tana girgiza kai. “Wata kila yarta ce, tun ko da ta bar gidan nan ta tsoho ciki ta tafi, cikin data kasa haifewa shekara hudu, wata kil ta rayu a can ne ta haifi yar ta mutu” “Inshallah tana nan raye Hajiya, zan nemota a duk inda take, zan saka cigiya a gidajen redio nan da can kuma zan bada tsofin hotunanta da nake da su, zan kuma bincika gidanjen asibiti da mahaukata da yake can, saboda yarinyar tace mahaifiyarta mahaukaciyace” “Sai dai a sa a can, nan kam yan'uwanta sun saka tun jiya, har gidanka sunje basu sameka ba, Allah ya bayyanata mu dai mun rike Innahu ala raja'ihi lakadrin indai tana nan raye zata dawo garemu da yardar Allah, ko da ko kasar nan ta bari. Duk abunda ya bata ka karanta ta sai ya dawo gareka da yardar Allah, (Amman ta batan mutum ana karantata sau 300k sai salatin annabi 11, bayan ko wace carbi 100k bayan magariba ake yinsa)” “Nima zan cigaba da addu'a inshallah kuma zan yi duk abunda ya dace, gobe ma ke jin zan koma garin saboda na tabbatar, ina son a gwada jinina da na yarinyar dan tabbatarwa” “Haka ma yayi Allah ya bayyanata, kuma zan fadawa yan'uwanta idan sun zo” Daga haka yai mata sallama ya tashi ya fice. Sai da sallah isha'i sannan Hajiya Safiya ta farka, har kuma lokacin ciwon kan be saketa ba har bata iya bude idonta sosai. “Sannu...” Hajiya Halira tace mata cike da tausayawa, hannu ta daga mata tana maida idonta ta rufe. “Ina Alhaji...?” “Tun da muka kawo ki ya koma, kin san shima hankalinsa bakwance yake ba, gashi lafiyarma bata isheshi ba” “Be hakura ba ko neman Rufaida zai je?” Ta tambaya a wahalce. “Wallahi ban sani ba, amman dai ai kara ya nemeta duk da ina jin kamar bata raye” “Indai har ya nemota, to ni ce cikin matsala Ya Halira” Cike da tsananin mamaki Hajiya Halira ta ce “Saboda da me, ke kam ai jindadinki ne domin ko ba komai mijinki zai samu lafiya” “Samun lafiyarsa akan Rufaida ciwona ne, gashi tun yanzu na fara balle kuma idan ta dawo, asirina zai tonu sirrin dana shekara talatin ina rufewa zai tuno, haukar dake kanta kuma a kaina zata dawo indai har tana raye” Hajiya Halira taja baya da kujerarta tana ma kanwarta kallon tsoro. “Ban gane ba, kina nufin duk abunda ya faru da Rufaida laifinki ne?” Ta hade yawu a wahalce sannan ta sake bude idon ta kalli yar'uwata hawaye na zubo mata. “Ban taba fadawa kowa ba, babu wanda ya san wannan daga ni sai kawata sai kuma Allah, amman idan har aka dawo da ita ni ce zan haukace, domin haka bokan ya fada” “Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un, amman Safiya baki kyautawa kanki ba, kuma wannan halin ba halinmu ba ne, kin cutartarda ita kin cuci iyayenta kin cuci mijinta me tai miki?” “Bata min komai, ina tsoron kar sonta yasa Alhaji ya wulakantani ne, saboda na san wacan gidan da na fito hanani zama suka yi, ina ganin kamar idan ban yo haka ba, nan ma fita zan yi, kuma bana son aurena ya sake mutuwa, lura da irin son da Alhaji yke mata, ga son da Hajiyarsa take min ya koma kanta saboda ta samu ciki, sannan ina tsoron ta haifi Namiji, shiyasa nasa akai mata aiki aka danne ciki ta shekara hudu a gidan nan da shi, daga baya kuma nasa akai mata wanda zata bar gidan saboda ina kishin irin kulawar da Alhaji ke bata” Hajiya Halira ta fashe da kuka. “Haba Safiya, kin san irin mugun halin da kika saka baiwar Allah nan? Mace ko wata tara ta dauki ciki ya take ji balle shekara da shekaru, kila ma ta mutu baki sani ba, kin dauki hakkinta kin cutar da ita ba gwaira ba dalili, miye amfanin fada min wannan maganar ma? ” “Naje daga baya na ce a warware aikin, amman kaddara ta riga fata, ban samu bokan da yai min aikin ba, sai dai ya fada min tun farko cewar duk ranar data dawo cikin gidan ni ce zan haukace, kuma ina jin kamar hakan na dap da faruwa, saboda ciwon kan nan da nake bana lafiya ba ne, kuma yan'uwanta sun zo nan jiya suna tambayarta ,alamune dake nuna cewar aikin na daf da karewa, tun da kika ga shi ma yana nemanta” Hajiya Halira ta taba hannayenta tana salati. “Lallai Safiya duniya ta rude kuma ta yaudareke, gashi kin jama kanki yanzu ina amfanin wannan abun?” “Na dade ina jin nadamar abunda na aikata, sai dai ban san yadda zan yi ba, na rasa ta yadda zan tinkari Alhaji da wannan maganar, yanzu kam na san lokaci na ya kare ba zan iya hana shi neman matarsa ba” “Karki kuskura ki fada masa wannan maganar, kar kuma ki bari kowa ya ji wannan maganar, ki zubama sarautar Allah ido kawai, kuma ki karbi sakamakon abunda zai zo miki” “Amman yana da hakkin ya sani” “Idan har ya sani ba zai taba zama da ke ba” Hajiya Halira na rufe bakinta Alhaji na turo kofar dakin ya shigo, sai tai sauri share hawayenta tana amsa sallamarsa. “Ya mai jiki?” “Al-hamdulillah ya naka jikin” “Al-hamdulillah, Hajiya kuka kike yi?” Ya tambaya yana kallon Matarsa wato Hajiya Safiya wacce ke kallonsa tana hawaye, sai ya zauna bakin gadon kusa da ita cikin yanayin damuwa. “Kan be daina ciwo ba?” Hajiya Halira ta tashi ta fice daga dakin ta basu wuri. Rumtse ido Hajiya Safiya tai tana kokarin tsada kukan ta ce “Ya daina, ya naka jikin?” “Al-hamdulillah, na yi waya da twins na fada musu halin da kike ciki, gobe za su zo, da nima na so naje Gusau gobe amman saboda zuwansu zan hakura har jibi, ina son na kara bincikawa, yarinyar Ummi ke rikonta kamin shi yaron ya karbeta kuma ta fada min cewar wai yarinyar tana gidan yari ana zarginta da kisan kai” Zabura tai ta tashi zaune. “Wace Ummin?” “Kanwata wacce Gusau Ummi dai wacce kika sani” Tayi saurin rike kanta. “Lafiya dai?” Sai ta canja maganar dan kar ya gane halin da take ciki. “Ai da baka fada musu ba, kar hankalinsu ya tashi” “Hakkinsu ne su sani, nima ai nawa mahaifin na je zubawa har na ga wannan yarinyar ban samu na gaisa da su ba na dawo, kuma daman sun ji gurin Hajiya Halira dan Hassana ta fada min ta kira wayarki sai ta dauka ta fada musu kina bachi baki da lafiya, har na fada mata zancen yarinyar nan mai kama da Rufaida” Gabanta ya fadi, sai ta lumshe ido, ta kai hannu ta rika hannunsa. “Duk abunda nai saboda kai nai Alhaji, dan Allah karka juya min baya” “Ban gane ba...” Ya fada yana kama kallon rashin fahimta, sai ta bude idon ta saki hannunsa ta ce “Ya kamata ka huta saboda ciwonka yana bukatar hutu, ni na naji saukj ina ganin zuwa anjima ma go be likita zai sallameni, na damu lafiyarka sosai” Ya gyada mata kai. “Zan yi kokarin hakan inshallah” Sai goma da rabi na dare ya bar asibitin, bayan ya bata wayarsa tayi waya da yaranta kuma sun jadadda mata cewar gobe suna nan tafe ganinsa yasa ta daure ta nuna kamar taji sauki har ma da cin abinci dan kar ya damu. *** *** *** Washe gari da misalin takwas da rabi ya dawo asibiti tare da breakfast din da mai aikinsu ta girka. Nan ma ta ci ba laifi sai dai ta rame sosai kamar wacce ta shekara guda kwance tana ciwo. Misalin sha daya na safe twins suka iso gida, ko hutawa ba su yi ba suka dauki hanyar asibitin kowa wacce hankalinta a tashe ance mahaifiya babu lafiya gashi jiya sun ji muryarta ba a yadda suka saba ji ba. Sun tararda da ita fiye da yadda suke tsammaninta, ramar da tai ta daga musu hankali sosai ga kamaninta duk sun canja, a asibitin suka wuni da ita duk wani motsi nata yana idonsu abun uwa da yayanta, sai dai sun kasa gane dalilin hawayen da take tun da suka zo har yanzu. Bayan sallah magariba Husaina ta shigo da waya a kunnenta ta mikawa mahaifiyarta. “Mama ga Anty Ummi za ta miki ya jiki” Ta karba tana amsawa ahankali sannan ta mayar mata da wayar. “Okay shikenan zuwa jibi idan naga jikin Mama da sauki zan yi kokarin na dawo inshallah” Daga haka ta kashe wayar. Ta zauna kusa da Hassana wacce ke bare ayaba tana ba mahaifiyarta. Hassana ta kalleta. “Karbar case din za ki yi?” “To ya na iya Anty Ummi ce kin san ai ba zan ki ba” “Amman kin fada min Aliyu ya hana ki karbar criminal case irin wannan” Hussaina ta juyo ta fuskanceta da kyau. “Yarinyar nan is innocent, ba ita ta aikata laifin nan ba, dole na taimaka mata, ko Anty Ummi ce tai request wannan bukatar sai kuma naki karba, bayan bata taba nuna tana son wani abun ba. Kinga ai ba zata jidadi ba” “Yarinyar ta ba ni tausayi, taya za a ce ta iya kisa, duk da ban ganta ba amman a yadda kika fada min ta bani tausayi sosai, ya kamata ki taimaka mata kam, amman ki fara magana da mijinki tukuna” “Ee zan fada masa ai, rashin lafiyar nan ce ta Mama tasa ban yi masa maganar ba, kuma kinga yau ya kamata ace na karbi case din naje naga yarinyar amman bana gari, amman idan Hajiya ta samu sauki zuwa jibi zanje, dan karshen watan nan take son a shiga kotun, and the most painful part yarinyar bata da iyaye ba a san inda mahaifiyarta take ba, haka ma mahaifinta” “Amman ina Anty Ummi ina ta hadu da ita?” Hannu ta kai ta dauki abaya ta bare ta soma ci sannan ta ce. “Kanenta wanda suke the some mother, shi yaga yarinyar kofar gidanta ya shigo da ita, ita yarinyar daga kauye take, yanzu haka bata san inda kowa nata yake ba, ai kinsan shi ma Zain” “Oh na sanshi dan Sarkin nan ko? Amman waya laka mata kisan kan?” “Wata cousin dinsa ce, ita muke tunanin ta kashe ta, tare da shi ma suka zo da Anty Ummi, saboda yarinyar a gurin Anty Ummi take sai ta hada baki aka siyar da yarinyar a wata masarautar, shi yaje ya dawo da ita” “Kai amman Hussaina case irin wannan yana da hadari sosai, kin san ita kuma yarinyar zata yi kokarin ganin baki ci nasara ba” “Amman nima zan yi kokarin ganin na ci nasarar” Hawayen da suka ga suna zuba a idon mahaifiyarsu ne yasa suka daina firar da suke suka maida hankalin gunta. “Lafiya Mama?” Hassana ta tambaya. Sai tai murmushi dan ta fahimci inda zancensu ya dosa. “Hausawa sun yi gaskiya da suka ce sheri dan aike ne, kuma alhaki kwaikwayo ne, ta ko ina gaskiya kara bayyana take daman komai nisan dare dole ne gari zai waye...” Basu fahimci abunda take magana akai ba, san basu dauka akan maganar yarinyar ne ba. Hussaina ta tashi ta koma kusa da ita ta zauna. “Mama me kike nufi da wannan maganar?” Kallon Hussaina tai sai ta fashe da kuka. “Abunda n aikata ne zai dawo min, shekara talatin da suka wuce na binne wani sirri wanda yanzu yake bayyana kansa, ba zan iya cigaba da aje wannan maganar ba” “Ni ban gane abunda kike nufi ba” “Yarinyar da kuke zance a yanzu, ita ce yarinyar da mahaifinku ya zo yana min zancen cewar yarsa ce” “Taya...?” Duk su biyu suka hada baki gurin tambayarta. “Shekara goma sha biyar da suka wuce, lokacin kuna primary school, ai kun san Rufaida ko? Aboiyar zamana” “Yes yes yes yes” Cewar Hasana cike da son jin labarin. “Da ciki ta bar gidan mahaifinku, bayan ta shekara hudu da shi a gida, nice sila ni na mata asiri aka taushe ciki, kuma nai mata asiri aka haukata ta ta bar garin....” Ta fashe da kuka. Husaina ta rufe baki tana zaro ido, yayinda Hassana kuma ta jefar da ayabar dake hannunta ta dade kunnuwanta. “Aa Mama wannan ba gaskiya ba ne, ba ke ba ce” Ta kalli Husaina wacce tai maganar tana nuna kanta. “Ni ce nina aikata, kuma na san Allah ba zai barni ba, bokan ya fada min duk ranar da ta shigo cikin gidan nan, ni ce zan haukace kuma nasan ranar ta kusa zuwa indai tana raye” Husaina ta rumgumeta da sauri tana fashewa da kuka. Cikin kuka Hassana ta ce “Mama mi yasa kika aikata?” “Saboda kar Mahaifinku ya koreni, na yi aure na farko ina son mijina matar ta rabani da shi, babanku kuma saboda yana son haihuwa na aureshi, duk da cikin dana samu be taba nuna min so kamar yadda yake nunawa Uwargidansa ba, ina jin tsoron irin son da yake mata, musamman lokacin data samu ciki sai hankalin kowa ya koma kanta shiyasa na aikata saboda kar na rabu da mahaifinku” Ta kara fashewa da kuka. Husaina tai saurin sa hannu ta share mata hawayenta ba tare da ta tsayar da nata ba. “Ba laifinki ba ne Mama, laifin Abbah ne da be nuna banbanci ba, da duk haka be faru ba” “Wane irin laifin Abbah? Wannan son zuciya ne kawai, ta biye zuciya akan namiji ta aikata abunda zai iya kaita wuta, kuma at the end gashi zai dawo kanta” Husaina ta yi saurin kallon Hassana wacce ke maganar tana hawaye. “Ba zai dawo ba, indai har sai yarinyar ko mahaifiyarta ta dawo zai koma kan Mama, to ba zai taba dawowa kanta ba har abada” Hassana ta share hawayenta cikin muryar kuka ta ce “Me kike nufi?” “Ina nufin zan aikata duk abunda zan iya, wajen ganin ita da mahaifiyarta basu dawo ba, saboda ta mu mahaifiyarmu” “No wait don't tell me kema wani abun za ki aikata...? This is unfair” “Zan aikata komai akan mahaifiyata, saboda mu tai haka, ba zan bar wani abu ya cutar da ita ba ko baki gane ba?” Hassanata girgiza kai tana hawaye. “No no no ban gane ba, ita ba mahaifiyar wata ta cutar ba? Matar wani? Uwara wata? Kanwar wasu? Yar wasu? A maimakon ki taimaka mata wajen neman yafiyarsu sai ki ce zaki aikata wani laifin kuma? Wannan wane irin son zuciya ne? Sai yanzu na gane wahalar da na ke sha a gidan aure saboda ke ne Mama, mijina yana da abunda zai ciyarda ni ya tufafatar da ni amman baya yi, tun da na aureshi ban taba jin dadin rayuwar aureba, komai a cikin salary na nake yi na yi ma yara na, ya gwammace yaje ya bawa matan banza a waje mu ya barmu, idan nai magana ace nai hakuri auren zumunci ne, ashe duk laifinki ne Mama, yar wasu kika azabbatar shiyasa ke ma ake azzabtarda ni, ki nemi yafiyar wadanda kika cutar Mama, kuma ki sanar da Abbah dan nasan be sani ba” Husaina ta mike tsaye. “Wane irin a sanar da shi? Babu wanda zai san da wannan maganar sai mu kadai, zata nemi yafiyar Allah kawai, amman sirrin Mama ba zai taba fallasuwa ba, ba zan bari wani abun ya cutar da ita ba” “Ki kirga Husaina, dakika bayan dakika, minti bayan minti, awa bayan awa, yini bayan yini, dare bayan dare, wata bayan wata, shekara bayan shekara, shekara nawa baiwar Allah nan yai tana dauke da wahala? Yanzu kuma ga yarta nan tana wahala duk sanadin Mama, ciwon da Abbah yake saboda rashinta ne sai kuma ki ce ba za a sanar da ita ba, wannan game din da Mama take playing ta kare, shekara talatin tana cutar baiwar Allah, idan ke ce ya zaki ji? Dole ne Abbah ya san da wannan dole na fahimtar da shi komai, sannan na nema mata yafiyarsa” Hassana na gama fadin hakan ta kai hannu ta dauki veil dinta, sai Husaina ta rika ta juyo da ita. “Ki yi tunani kamin ki aikata abu Hassana, ko ki fadawa Abbah ko karki fada masa ba zan bar yarinyar da mahaufiyarta su dawo ba, tunda dawowarta na nufin tafiyar tawa mahaifiyar ne mark my words...” “Ki yi duk abunda zaki iya Husaina but trust me ramen karya kurarrene, kuma gaskiyar ta bayyana kenan...” Tana kaiwa nan ta dauki handbag dinta ta fice. [3/25, 9:04 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 49 “Ki yi shiru Mama ki kwantar da hankali, abunda ya faru kaddara ce baki isa ki kauce mata ba” Husaina ta fada tana share mata hawayenta. Ita kuma ta kasa daina kukan ga azabebben ciwo da kanta yake. Husaina ta nufi jakarta ta bude ta dauki wayarta ta kira yar'uwarta, ta dade tana ringing sannan ta dauka. “Hassana ki yi tunani kamin ki aikata abunda za ki aikata, wannan mahaifiyarmu ce tana da muhimmanci a garemu, yanzu kin fi son ki sakata a damuwa...?” Bata amsa mata ba, ta kashe wayar, ta jingina kanta jikin kujerar tana hawaye, fadin da rashin fadin su suka tsaya mata a rai, zuciyarta nata raya mata fadin shine alheri. Wayar da ke hannunta ta cire ma key ta kira Anty Ummi, sa da ta dauka sannan ta fara tambayar kan abunda zata ce mata. “Hello Hasana baki jina ne?” “Ina ji Anty Ummi, wata tambaya nake son nai miki, wai yarinyar da ke gurinki yar Abbah ce” Daga can cikin wayar Anty Ummi tai shiru kamar ba za ta amsa ba. “Miyasa kike tambaya?” “Ina son sani ne, Hajiya ce tai min wata maganar wacce ta daure min kai” “Ba ni da tabbaci, amman Abbanku ya ganta kuma ya ce yarsa ce, ba dan ma wannan abun da ya faru ba da gwajin jini zamu yi a tabbatar idan hakan ne ko a a” “Amman Anty ta fada miki sunan Mahaifiyarta?” “Ban taba tambayarta ba, amman ta fada min cewar mahaifiyarta mahaukaciya ce” “Na gode” Ta sauke wayar, sai ta unkura ta tashi daga falon tana share hawayenta. “Yan biyu lafiya dai? Ko jikin Hajiyar ne?” Adama ta tambaya ganin yadda tun dazu take zubar da hawaye. “Aa ba jikinta ba ne” Ta fada a takaice sannan ta fice daga falon ta nufi inda Falon Abbah yake, tana dosar gurin gabanta na kara faduwa tana misalta irin halin da zai shiga idan ta fada masa, zai yafe ma Mama kuwa? Me zai biyo baya idan ta fada masa? Babu abunda zuciyarta bata saka mata amman a haka ta danne komai ta shiga falon. “Assalamu Alaikum” Tayi sallama cikin muryar dake nuna alamun ta yi kuka, yana daga tsaye yana gyara hannun babbar rigarsa da alama ma can zai je gurinta. “Lafiya dai yan biyu?” “Wata maganar na ke son mu yi da kai” Ta fada ba tare da ta kalleshi ba. “Minene Hajiyar ce wani abun ya faru a ita?” Ganin yadda hankalinsa ya tashi yasa tai saurin ce “Aa akan maganar Yarinyar da kaga ni a gidan Anty Ummi ne” Ajiyar zuciya ya sauke ya zauna a kujerar da ke kusa da shi yana cigaba da kallonta tare da tattara hankalinsa guri daya ya mika mata. “Abbah....” Sai kuma tai shiru hawaye ya sauko mata, tana jin nauyi da kunyar kallonsa saboda abunda mahaifiyarta ta aikata, amman a haka ta daure ta daga ido ta kalleshi tare da kara kiran sunansa a karo na biyu. “Abbah. Shi dan'adam ajizine, wani lokaci shaidan da zuciya suna yaudararmu mu aikata abunda zai kai mu ga halaka, wasu suna aikata hakan saboda kishi wasu saboda so wasu saboda kiyayya, wasu saboda hassada, amman abunda zan fada maka a yanzu na fi alakanta shi da so, so kuma mai tsanani, irin son nan da a yau kake fargabar mutuwa da raba ka da ni ko Husaina” “Ba gane wannan karatun na ki na ke ba, idan ma mahaifiyarku mutuwa tai ki fada min kawai” “Ba mutuwa tai ba, yanzu haka na barota tana can tana kuka da nadamar abunda ta aikata, sai a yanzu ta gane ta yi kuskure babba, amman komai zai zo da sauki idan ka sassauta fushinka a akanta, ko ba dan ita ba, ni Husaina yayanka ne kuma ba zamu so ganin bacin ran mahaifiyarmu da wani balle kuma da kai” “Ke Hassana ki fada min ko minene bana son dogon sharhi” “Yarinyar da ka gani a gidan Anty Ummi yarka ce Abbah, yar Mama Rufaida ce kanwarmu ce...” Ya mata wani razanannen kallo. “Ta ya akai kika sani? Kin tabbatar da hakan?” Ta gyada kai tana cigaba da hawaye. “Tabbas yarka ce Abbah jininka ce” Yaja wani dogon numfashi na jindadi ya sauke tare da tashi tsaye yana takawa a hankali kamar zai fita kuma ba fitar zai yi ba, sai ya juyo ya kalli Hassana “Ya aka yi kika sani?” “Mama ce ta fada mana” “Ita ya aka yi ta sani?” “Saboda.... ” Nauyin furta maganar take ji sai dai bata da wani zabi. “Saboda ita ta aikata abunda ya sa ta bar gidan” “Ban gane ba” Ya tambaya cikin nuna rashin fahimtar zancenta. Ba karamin Jihadi tai na tsayawa ta tsara masa komai yadda zai fahimta ba. Ta tsammaci jin wata yasasshiyar magana daga bakinsa sai kawai taga yayi murmushi ya lumshe ido sai hawaye, zuwa can kuma ya dauki hannunsa ya dora a kirjinsa saitin zuciyarsa. Saurin tasowa tai ta matsa kusa da shi tana kiran sunansa. “Abbah, dan Allah ka kwantar da hankalinka, zan yi iya abunda zan iya na fiddo da ita daga gidan yari ta dawo gareka” “Taya taya tay?” Yanzu kam kuka yake yana nuna hannayensa. “Zata dawo Abbah ba ita ta aikata kisan kan ba, sheri aka mata na san Hassana ba za ta taimaketa ba, saboda tana tsoron kar abun ya dawo gurin Mama, amman ni zan karbi case din kuma zan tsaya mata, dan Allah Abbah karka tashi hankalinka” Ta furta ciki kuka hankalinta a tashe tana tsoron kar wani abun ya same shi. “A duk tsawon shekarun nan da nai ina tunani Rufaida amman na kasa yin komai ashe laifin Safiya ne? La'ilahaillah” Ya kwantar da kansa jikin kujerar yana kuka. “Haba Abbah dan Allah ka daina kukan nan, da wanne zan ji kai ko Mama? Karka jama kanka wani ciwon kuma” Sai yai saurin ciro handkerchief dinsa ya share hawayensa. “Gobe zan koma gida zan yi Anty Ummi bayani komai sai na karbi case din, inshallah zata fito” Kai kawai ya gyada mata ya tashi ya shige bedroom dinsa. *** *** *** *Two days later...* Gaba daya Zain kwaura yai daga cikin gidan, tun ranar da abun ya faru be sake kwana a cikinsa ba, sai ya koma gidansa dake can gra ya tare, baya zuwa office baya yin komai tun a ranar be sake zuwa masarautar ba, sai dai Mai Martaba ya aiko a dubashi, Ibrahim ne yake kawo masa abinci safe rana da kuma yamma, sai dai yadda ya kawo su haka yake daukarsu wani lokacin ya kan tirsasa masa ci, shi kanshi yana cikin damuwa ganin irin damuwar da abokinsa yake ciki. “Zain ka rage yawan tunanin nan, ba zai amfaneka da komai ba” Ya aje kofin shayin da ke hannunsa. “Ba tunani na ke ba Ibrahim, idan tunani na ke ban san wanne zan yi ba, rashin Haleema ko Farhat? Ko kuma zaman Hameeda a gidan nan, ko kuma rayuwata ta nan gaba? Mama da aka kai aka rufe ko kuma me? Kawai ina nisanta kaina ne da mutune saboda na fi jindadin hakan, bana son na cigaba da rayuwa a gidan da Hameeda take zaune, bani da wani buri yanzu wanda ya wuce na ganinta ta ta wulakanta” “Ba abu ne mai sauke mutum ya fuskanci kalubale kamar wannan ba, amman ka san sai special people Allah yake jarraba har haka ko?” Zain yayi dariyar data kara fito da ramar da ke fuskarsa. “Sa cina ne Ibrahim, na san yarinyar nan tana da hannu a mutuwar Haleema but still na yarda na zauna gida daya da ita da Farhat, wannan ai isgilanci ne na yi wasa da ran yar mutane, am such a bad guy na wahalar da yar mutane ban taba samun damar fada mata wata kalma mai dadi ba, ko da bata so na, ai aurena tai yi, na shirya yin rayuwa mai kyau da tsabta da ita amman Hameeda ta wargaza komai, duka wadannan kalubalen ta fuskance su ne saboda ni” Yayi saurin mikewa tsaye saboda hawayen da suka cika masa ido. Wayarsa ce tai ringing sai ya daga kansa sama yana kokarin maida hawayen and he can't pick the call. Dan haka Ibrahim ya kai hannu ya dauka yana karawa a kunne Anty Ummi ta ce masa. “Zain ga mu nan kan hanyar zuwa gurin Mama ka taho yanzu” “Okay” Ya amsa a madadin Zain sannan ya maida wayar muhallinta ya kalli Zain. “Anty Ummi ce tace tana hanyar zuwa gurin yarinyar nan ku hadu a can” Hannu Zain yasa ya matsi idanuwansa sannan ya dauki jacket dinsa dake kan kujera ya saka suka fito tare da Ibrahim. A mota daya suka shiga Ibrahim ke driving yana ta masa hira sama sama amman har aka isa Zain be ce uffan ba. A waje ya tsaya ya kira Anty Ummi ya sanar mata waje ta kwatanta masa inda take sannan suka shiga. Kato gidane mai kamar ma'aikata, daga wajen gate din sai ka dauka babu kowa haka a harabar gurin, sai dai reception dinsa kamar ko wane reception yake, a cikin ma'aikatan dake gurin akwai marar uniform wasu sam ba zaka dauka police ba ne. Da kwatanccen da Anty Ummi tai masa yai ta bi har ya iso inda suke. Tana zaune saman wani tebur tare da Barrister da be rike sunanta ba, ya san dai ita ce wacce Anty Ummi ta fada masa cewar yar yayarta ce kuma yai magana da ita a lokacin da suke kan mata bayanin yadda komai yake, sai kuma mutumen nan na ranar nan wand ya ce Hafsatu manga yarsa ce, Zain baya cikin mood din tambaya dan haka be ce masa komai bayan kallonsa da yai ya dauke kai ya kalli wani mutum daban dake tare da su. “Sunnanta Barrister Hassana, ba wacan ba ce amman twin sister dinta ce” Anty Ummi ta fada masa yana kokarin zama shi da Ibrahim. “Miya faru da waccan?” Ya tambaya yana kara kallon Barrister dan kara tantancewa, lallai wannan ta fi wacan haske ita kuma wacan ta fi wannan jiki. “Labari ne mai tsawo idan mun fita a nan zan maka bayani” Sai duk suka maida hankalinsu a gurin Hafsatu manga wacce aka fito da ita a yanzu, Alhaji Habib ne yai saurin mikewa tsaye ya doshi inda take tun kan ta karaso sai ta zo ta guje kamar za ta je gareshi ta gauce ta je ta rumgume Zain tana kuka. Tsaye Alhaji Habib yai yana hawaye, Anty Ummi kuma ta tashi ta karasa inda Hafsatu manga take ta shafa kanta tana kuka. “Mama...” Sai Hafsatu manga ta buge mata hannu ta kara lafewa a jikin Zain. “Ita ce Hafsat..?” Hassana ta tambaya tana nunata. Sai Zain ya dauketa ya dora saman kafafunsa yana mai jin kukanta har cikin rans. “Yi shiru Mama, fada min mi akai miki?” “Ba a min komai ba, bana son nan din ne” “Wahala suke baki?” “A'a suna samu shara dai da daukar kaya kuma suna cewa mu wanke bandaki” Wani irin tausayinta ne ya kamashi. “Ki yi hakuri zan dauke kinji? Nan da wani dan lokaci kadan za ki bar nan” “Ba yau ba?” Ta bata fuska. Sai ya rasa me zai ce mata har sai da Barrister Hassana ta matsa ta kama hannunta ta rike. “Idan kina son mu fitar da ke daga nan gurin dole ne sai kin ba mu hadin kai, ki fada mana komai yadda ya faru karki ji tsoro ko fargaba” “Ba ni ba ce wannan matar ce” Da kadan kadan Hassana take mata tambaboyi tana bata amsarsu har ta gama yi mata duk tambayar da zata mata, sannan ta kalli mutumen da suka zo tare da shi ta ce “Doctor Bismillah” Safar hannu likitan ya saka ya dauko wani karamin almakashi da yar roba ya nufo inda Hafsatu manga take. “Me za ku mata?” Zain ya tambaya a tsawace. “Gashin kanta zamu kira ina son ayi mata gwaji ne?” “Gwajin me?” “DNA TEST” Anty Ummi ta bashi amsa. “Why?” “Ta nan kadai zamu iya tabbatarwa da gaske Abbah mahaifinta ne ko kuma a a? Ta yadda kowa zai samu gamsuwa, ni, shi, Anty Ummi, kai, da kuma Hafsat din gab daya” Zain ya dauke kansa daga barin kallon Hassana ya kalli mutumen dake tsaye a gurin daya je tarbon Hafsatu manga kamar an dasashi. “Miye alakarki da wacan mutumen?” “Mahaifina ne, kuma mahaifin Hafsat” Zain be sake cewa komai ba, har likitan ya kiri gashin kanta. Sannan ya ce “Ibrahim zai yi gwajin shi ma likita ne” Har Anty Ummi ta bude baki zata yi magana sai Alhaji Habib ya rigata. “Ba shi ya yi” Sai likitan ya mikawa Ibrahim robar da ya zuba gashin, sannan ya je ya sake deban gashin Alhaji Habib ya saka a cikin wani kwankwan ya mika masa, ya cire fice yana kokarin cire hand gloves din da ke hannunsa. Lokacin da za a maida Hafsatu manga tayi kukan tana ta kiran sunan Zat. Cikin bacin rai duk suka fito ba ma kamar Zain da idanuwansa suka gama rinewa suka kai ja sosai. A mota daya Zain ya shigo da Anty Ummi, Alhaji Habib kuma yana cikin tashi motar tare da direbansa suka kama hanyar Family house din su Anty Ummi. Ita kuma ta dawo gidan Anty tare da Zain yayinda Barr Hasana ta nufi gidansu Zain dan yi wani binceken, Ibrahim kuma ya wuce asibitin. Da suka shigo gida ne Anty Ummi take masa bayanin komai ciki har da zancen Mahaifin Hafsat da yadda Rufaida ta bar gidan, kuma yadda aka yi case din ya dawo hannun Hassana yar'uwata saboda sun san Husaina ba zata yi abun kirki ba tun da ta zabi mahaifiyarta, kuma cigiyar Rufaida da Alhaji Habib ya bada a gidanje redio da tv, bayan kuma yasa a abincika masa a gidan mahaukata da asibitoci. “Ya fada min wai kannenta za su zo gobe suna son ganin Mama, kuma suna son au bincika mahaifiyarta da kansu” Zain yayi shiru yana nazari kamin ya kalli Anty Ummi ya ce. “Idan ta tabbata haka ne, ya za kiji da tsanar da kika nunawa yarinyar nan” Ta kawar da fuskarta dake hawaye sai ta dauko masa wani zancen. “Auwal ya fada min, gobe za a bada gawar Farhat, iyayenta za su zo gobe maybe ba za su yarda a yi mata sallah nan ba” Zain ya yi sauri Mikewa tsaye yana hade wani abu daya tsaya masa a wuya. [3/26, 6:28 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 50. Anty Ummi ta tashi tsaye tana kallonsa. “Zain ina zaka je?” “Ban sani ba, maybe gida zan koma amman ina jin kamar bana son zama a ko'ina” Ya fada hawaye na saukowa daga idonsa. “Dan Allah ka kwantar da hankalinka,kuma ya yarda da wannan kadarar” “Da ban yarda da wannan kaddararba, da Allah kadai yasan halin da zan shiga, kwanciyar hankali kan babu shi a tare da ni har abada, ba ni natsuwar ruhi balle kuma ta jiki, tunani ma ban san wanne zan yi ba, i lost Haleema three years ago, and now na rasa Farhat, i was just thinking of what would happen next” “Hameeda will go to jail akan abunda ta aikata babu abunda zai kara faruwa inshallah gaskiya zata fito komai zai bayyana” “Even if she go to jail bana tunanin damuwa ta zata wanke, domin na rasa su har abada ba zasu taba dawowa ba” “Ba zasu dawo ba, amman Allah zai iya musanya maka da mafi alheri, baka san abunda Allah ya tsara maka a gaba ba” Ya hade hawun bakinsa tare da saka hannu ya share hawayensa. “Bari naje gida ina bukatar hutu” “Ka zauna nan har zuwa dare, maybe zai kawo mana results din da wuri, maybe kuma sai gobe” Komawa yai ya zauna ya jingina kansada kujerar ya rumtse ido. Kitchen Anty Ummi ta shiga ta hada masa tea ta kawo masa, sai a karba ya aje be sha ba, ita kuma ta koma kitchen din ta dafa masa pepper soup, ta kawo masa har lokacin be sha tea ba. Karamin tebur ta janyo ta dora masa plate din tana kallonsa. “Ba za ka ci ba? Haba Zain damuwarka fa tana damuna, bayan wuya sai dadi idan ka yi hakuri komai zai wuce kamar ba ayi ba” “Haka ne, amman ba zan iya cin pepper soup din nan ba” Ya fada yana daidaita zamansa. “Ko kadan? Ba zan jidadi ba idan baka ci ba” “Dazu na tsammaci zaki je wa Mama da wani abun dadi, kin san ba abun dadi za su bata ba, and ta yi spending three days there she miss us kuma ya kamata mu kai mata wani abun dadi ko?” “Mantawa nai ban yi hakan ba, amman next time zan yi mata i promise” Ya kai hannu ya dauki plate din tare da spoon yana juya pepper soup din, sai yai murmushi. “Tana ta kirana tana ganin kamar zan iya yi mata wani abun? But I'm helpless” “You're not helpless ko yanzu zamu yi duk abunda za mu iya a tsaya mata” Ya gyara kai, ita kuma ta tashi ta nufi dayar kujerar inda wayarta ke ringing. Ganin number Auwal yasa tai saurin dauka ta kara a kunne tana amsa gaisuwar da yake mata. “Lafiya Kalau Al-hamdulillah” “Mashallah, daman na kiraki ne na sanar miki cewar Mun samu wata kwarriyar lauya mai zaman kanta zata tsayawa Farhat” “Kamar ya zata tsaya ma Farhat? Ban gane ba” “Ita zata shigarda da karar a madadina, ta fada min iyayenta suna da rauni kuma za a iya cin amana a cikin shari'ar” “Mu zamu ci amanar ko kuma wasu?” “Ban sani ba, amman dai hakan da zata yi yana da kyau domin za a kwatowa Farhat hakkinta, Hameeda zata iya komai na ganin ta fitar da kanta, ku kuma abunda kuke kokari ku fitar da Hafsat daga ciki, so na sanar miki ne kawai dan ki sani” “To yayi kyau Allah ya taimaka, amman wacece?” “Sunanta Barrister Husaina Habib Alhasan” “To ya yi kyau Allah ya ba mu sa'a” Daga haka ta aje wayar ta kalli Zain. “Kaji wani murdadden lamari, wai yar'uwar wannan lauyar zata tsayawa Farhat” Ya mata kallon rashin fahimta. Sai ta cigaba “Twins sis dinta ce fa wacce akakarbe case din daga hannunta aka bawa Hassana, abunda na gama fada maka dazun kenan, so take kar Mama ta fito saboda kar wani abu ya samu mahaifiyarsu” “Amman ba hadin kai bane kuwa? Idan har ta tabbata Mama yar wannan mutumen ce kin ga ai kanwarsu ce ko?” “Yes amman ita Husaina tana kokarin kare mahaifiyarta ne, saboda bokan ya fada musu duk lokacin da Rufaida ta dawo abun zai koma kanta, ita kuma Hassana tana ganin laifin mahaifiyarta ne shiyasa ta tsaya kai ta fata tana son ta wanke Mama saboda ta farantawa Mahaifinsu” Zain be kara cewa komai ba, farfesun ma kadan ya sha. Da yamma lis Ibrahim ya kawo masa gwajin DNA din. Daya karba sai ya kasa budewa yana gudun ganin sakamakon ba tare da wani dalili ba. Sai kawai ya aje takardar yana tambayar Ibrahim. “Ya zo daya” “Kama yai ka bude ka gani” “Ganin ba shi amfani, just tell me” Ya mike tsaye ya nufi gurin plasma ya tsaya ba dan xai yi komai ba, sai dan kuma baya son jin abunda Ibrahim din zai fada masa, Ibrahim ya kai hannu ya dauki takardar yana kiran Anty Ummi wacce ke ta dawainiya da yara da suka dawo daga makaranta yanzu. “Anty Ummi ki zo ga result din” A take ta baro dakin yaran ta fito falo ta karba gabanta na dan faduwa. “Ai na dauka sai gobe” “No ai daman gwaji ya danganta da kayan aikin da asibiti take da su, balle kuma asibitin kin san ta mu ce” “Allahu Akbar, Allah mai yadda ya so a sadda ya so, jinina ce Zain ashe Mama jinina ce Wallahi mahaifinta ne” Anty Ummi ta fada idonta cike da kwalla tana nufar inda Zain yake tsaye da takarda, shi kuma ya kasa juyowa ya kalleta balle kuma ya sake ce mata wani abu. Tsaya tai tana kallon bayan kansa tana auna yadda yake ji a zuciyarsa. “Na san baka farinciki sabo...” Sai yai saurin juyowa ya kalleta. “No you're wrong, na fi kowa farinciki, and i will be the first one da zai mata wannan albishir din” Yana kaiwa nan ya zagaya gefenta ya wuce. Sai Ibrahim ya tashi ya rufa masa. Dukan wani bincike da ya kamata Hassana tai sai da tai sannan ta baro fadar, a hanya Dpo Auwal ya kirata ya sanar mata cewar an samu lauyar da zata tsayawa Farhat, batai mamakin jin Husaina ba, daman tun ta tsammaci haka saboda ganin ba ta jidadin yadda aka karbe case din a hannunta ba, kuma ta fada mata zata yi duk abunda ya dace na ganin Hafsat bata fito ba, so wannan ba abun mamaki ba ne dan ta saka kanta akan case din. Tana gama waya da da Dpo ta kira Husaina bugu daya ta dauka. “Yar'uwarta” “Husaina abunda kike yi ba shi da kyau, akam me zaki karbi case din mu tsaya a gaban kotu akan mutun daya? Bayan kuma kin san gaskiyar komai” “Sanin gaskiya ba damuwata ba ce, mahaifiyata na ke karewa, ni kina ba ni mamaki wlh ke Yanzu kin fi son Yarinyar ta fito ita mahaifiyarmu wani abun ya sameta? Wace irin Ƴa ce ke?” “Mahaifiyar yarinyar aka ce ba ita ba” “It could be her, waya sani ko mahaifiyar bata raye? Idan Abbah ya dawo da ita sai mahaifiyarmu ta tafi? Haba dai Hassana ki yi tunani mana” Tsaki taja ta kashe wayar, a daidai lokacin da take parking a harabar gidan Alhaji Salisu Alhasan. Cike da bacin rai ta fito ta shiga cikin gidan, a tsakar gida ta tsaya tana gaisawa da kananinta sannan ta shiga cikin falon inda mahaifinta yake zaune tare da mahaifinsa da wasu kanensa. Yana ganinta sai ya tattaro dukan hankalinsa ya maida gurin har ta zauna tana gaishe da Alhaji Salisu. A nan ta soma yi musu bayanin kan case din har ma da fada musu cewar Husaina ta karbi case din, suna haka sai ga Anty Ummi shigo rike da takardar tana murmushi mai kamar kuka ta mikawa Alhaji Habib. “Ga result din” Kamim ya karba Hassana ta kai hannu ta karba ta bude tana karantawa, rufe baki tai idonta ya cika da hawaye sai ta mikawa mahaifinta. Cikin fargaba ya karba ya bude shi kam murmushi yai ya juya a gurin yai sujuda godiya ga Ubangijinsa. A ranar kasa hakuri yai har sai da ya saka yarsa a gaba suka koma gurin Hafsatu manga ba a hana su ganinta ba kasacewar Hassana ce lauyarta suna zaune a gurin da suka zauna da zu, suna gurin aka fito da ita. Ganin babu wanda ta sani a cikinsu yasa ta ki yarda ta karaso kusa da su, sai kawai tasa kuka. Alhaji Habib ya karasa inda take ta duka tana dafa kafadarta hawaye na zuba a idonsa. “Ya ta...” Ya furta yana murmushi mai cike da kunci. Ya shafa fuskarta sai kuma ya rumgumeta. “Ina Zat?” Shine abunda ta tambaya tana kokarin raba jikinta da na shi. Sai Hassana ta risino ta shafa bayanta tana kokarin yi mata bayani. “Hafsat wannan mutumen da kike gani....” Bata karasa ba ya daga mata hannu, yana share hawayensa. “Shi ya kamata yai mata wannan bayanin, da alama ta shaku da shi sosai, dazun ma da muka zo gurinsa taje yanzu kuma shi take tambaya, ina ganin idan yai mata bayani zata fi fahimta, ko mahafiyarta bata tambaya yadda take tambayarsa wata kila ma bata raye, Ƴa ta fada min ina mahaifiyarki?” Ya karasa yana tambayar Hafsatu Manga. Sai ta ɓata fuska. “Nima ban sani ba” “Yaushe rabon ki da ita?” “Tun muna kauyen nan kamin gayu su koremu” “Daman ta saɓa tafiya ta barki?” “Ee amman tana dawawa yanzu ko ta dawo ba zata ganni ba, saboda ba na can” Tasa hannu tana murza idonta. “Mahaifiyarki tana da awarwaro?” “Ee tana da shi” “Miye sunan Mahifiyarki? Kin san inda take zuwa?” Sai ta lake kafada. “Kai ma sace ni za ka yi?” “Aa zan nemo inda mahaifiyarki ta ke ne” Bata sake cewa komai ba, duk irin tambayar da yai mata bata amsa masa ba, Hassana ta dauketa hoto a wayarta sannan aka maida ita tana kuka kamar ɗazu. Washe garin ranar aka bada gawar Farhat kamar yadda Dpo Auwal ya alkawaranta, sosai iyayenta suka so su tafi da ita gida, amman Mai Martaba ya roki alfarma a yi mata wanka da sallah a nan, kuma aka rufe ta a nan, a ranar Zain ya sha kuka irin kukan da sam ba zaka za ci zai iya yinsa ba, a masarautar akai karbar gaisuwarta wadanda basu san da zamanta a gidan ba da wadanda basu san Zain ya aurota ba yanzu kan sun sani domin Mai Martaba ya bada sanarwar a fadawa kowa da kowa, a fadarsa akai zaman uku kamar yadda al'ada ta tanada, su kuma a can Anka Local Government suka yi na su, sai a yanzu Inna take nadamar abunda ta aikatawa Farhat irin furucin da tai mata da kuma nuna bata son auren, daman ba a son furuci ko fushin iyaye, ta yi nadamar da da bata da amfani dan ba zata dawo da ita ba, kuka take sosai kowa sai da tausaya mata. HAMEEDA POV. Tun daga ranar da aka dawo da ita gida, bata sake leka waje ko da part din Dada ne, ta kebe kanta a dakinta har aka yi karbar gaisuwar aka gama bata fito ba, Dada da kanta take shiga ta duba ta tana bata magana kamar dai sauran yan gidan, wandanda suke alakanta hakan da abunda Zain yai mata. Daga ita sai Fauziya suka san gaskiyar lamarin da ya hana ta sakewa da sukuni, ta rasa natsuwa saboda abunda ta aikata, ko a lokacin da ta aikata makamancin wannan ga yar'uwarta bata ji rashin natsuwa kamar haka ba, duk ta bi ta rame kamar ma ciwo, ko iska ya kada sai ta zabura gashi zuciyarta na raya mata cewar asirinta zai tonu idan aka shiga kutu domin Dada ta fada mata Monday nan mai zuwa za a shiga kotun. Yau ma Fauziya ta ziyarce ta bayan gama karbar gaisuwa da aka yi shekaran jiya, ta lura da yanayin da Hameeda take ciki ta tsammaci zata canja saboda fadan da tai mata jiya. “Haba Hameeda, idan fa baki sake kin zama kamar yadda kike a da ba, za ki iya tonawa kanki asiri, idan kika cigaba da wadannan dabi'un za a iya gane wani abu a tare da ke” Ta daga kai ta kalli Fauziya da idonta dake nuna tsantsar rashin natsuwa da kwanciyar hankali. “Fauziya kin taba kashe rai? Ta hanuna na daba mata wuka kuma ta mutu, yanzu idan anje kotu asirina tonuwa zai yi dole za a gane ni ce” “Taya za a gane ke ce? Fitowa za ki yi ki fadawa duniya abunda kika aikata? Haba dai ki daina yin abu kamar wata marar ilmi da wayewa mana, ki bani wayar zan jefar da ita a wani guri inda ba babu wanda zai gani ba” “Aa zan ajeta a gurina” Ta fada tana girgiza mata kai, dan bata yarda da kowa ba a yanzu, tana ganin tun da har Abida ta ci amanarta, to kowa zai iya cin amanarta. Duk juyin duniyar nan da Fauziya tai na ta karbi wayar dan ta taimaka mata sai Hameeda ta ki yarda. *** *** *** In all those days yan'uwan Rufaida da iyayenta sun saka cigiyarta a duk inda suke sa ran za su sameta kuma sun dukufa akan addu'a ba dare ba rana, Alhaji Habib kam har kudi ya saka ga duk wanda ya ganota ko ya san inda take ko inda za a sameta. Amman shiru babu ita babu labarinta. A haka Alhaji Habib yake yau yana Kaduna gobe yana Zamfara, be maida hankali kan ciwon Hajiya Safiya ba, tun daga lokacin da Hassana ta fada masa be sake leka asibitin da sunan ganinta ba, sai dai yana bada kudin kula da lafiyarta, ga ciwon kan ya ki sauka sai karuwa yake har ta fara fita hayyacinta saboda ya tsananta mata sosai. Babu irim rarrashin da Hassana da Husaina da yan'uwan Safiya ba su masa na ya hakura ba, amman yaki ya taka yaje dubata saboda baya kaunar sakata a idonsa. Gaba daya hankalinsa ya tattara ya koma gurin neman Rufaida. *** *** *** Yau dai kam yana jin komai yai masa tsauri, duniyar ta isheshi, kwakwalwarsa ta tushe yana jin kansa kamar babu komai a ciki, gidan duk ya fita ransa kuma be san wani gurinda zaije ya samu sakewa ba. Sai dai ya farka da tunanin Hafsatu manga kamar yadda yake a kullum, around nine o'clock ya kira Barrister Hassana yana son ta shige masa gaba dan ganin Hafsatu manga, he miss her so much, ya san yadda halinta yake bata da natsuwa idan bata ganshi ba, gashi maganar da yake son ya fada mata akan Alhaji Habib. A take ta amince duk kuwa da kasancewar yau assabar ce ba kasafai take son fita weekend ba. Kamar kullum yau ma sai da Ibrahim ya kawo masa breakfast din da matarsa ke hada masa kullum. Ko da ya shigo ya tararda Zain ya shirya cikin riga da wando na shadda sky blue sai kamshi yake. Ibrahim ya kalleshi yana jin kamar ya zolayesa sai dai kuma be dace da wannan wasar ba a yanzu. “Ina zaka je?” “Mama zan je gani, ka zo a daidai zan je mata da indomie nan dan tana son indomie, sai na biya na siyo mata chocolate” “Ai ka fada min da nasa Madam da girka mata wani abun dabam like nama na san ba zata ki so ba” “Karka damu wani lokacin za ayi” Suna maganar Barr ta kira Zain ta sanar masa tana gurin shi kawai take jira, a aggauce ya fita daga gidan ya bar Ibrahim nan, sai da ya biya ya siya mata kayan makulashe sannan ya isa gurin. Ciki ya shiga dauke da kwandon abincin da Ibrahim ya kawo masa, dayan hannunsa kuma rike da ledar da yai mata siyayya. Ko da ya shiga ya samu Barr Hassana a zaune tare da ita tana zuba mata farfesun kayan ciki a plate, tana ganin Zain tai saurin mikewa tsaye zata je inda yake sai yai saurin karaso kusa da ita yana fadin. “Zauna ni ma zaman zan yi” “Zat baka zo ba, kullum baka zo ba” Ta fada kamar tai kuka. “Gani na zo ai yi hakuri, aiki ne ya rikeni kina lafiya ko?” “Aa bana lafiya, jikina yana zafi kuma kaina na ciwo ina yin kuka kullum” Hannu ya kai ya dago kanta yana kallon yadda fuskarta ta rame kamar shi. “Zat yaushe zasu fitar da ni daga nan? Ka fada musu ba ni na kasheta ba” “Zan fada musu, dole ne sai munje kotu kotu zata wanke ki” Ta bude baki “Kotu? Aa bana so ina tsoro” “Babu wani abun tsoro ga yayarki nan zata tsaya miki a kotu har sai mun yi nasara” Ta kalli Barr Hasaana wacce ke mika mata plate da spoon. “Ba ni da Yaya” “Ba ni da Yaya” “Yayarki ce mana, wannan mutumen daya zo ai Babanki ki shine mahaifinki” “Aa ni bani da Baba ban taba ganin babana ba” “Babanki, ya shekara da yawa yana nemanki amman be ganki ba, yanzu mahaifiyarki ake nema idan an ganta zata fada miki gaskiya” “Mama ta bata magana Sunana kawai take kira” “Zata yi magana, zo mu ci farfesu sai kuma mu ci indomie” “Har da indo ka zo min? Amman zaka tafi da ni ko?” “Aa ba yau ba” “Zat bana son nan, dan Allah ka tafi da ni” “Mu ci abinci yanzu in yaso daga baya sai mu yi maganar tafiyar” A plate daya suka ci indomie, sannan suka dora da farfesun, shi kanshi ya manta when last ya ci abinci da yawa haka, duk abunda suke Brr na kallonsu suke da burgewa tana ayyana irin shakuwar da suka yi, tana jin son yar'uwarta Hafsatu manga har cikin ranta. Bayan sun gama Zain ya mika mata ledar chocolate din. “Kin ga Chocolate nan da biscuits na siyo miki da Milk Candy ki tafi da shi ki rika ci” Sai ta kalleshi tana bata fuska. “Ba za kaje da ni ba? Ko na shiga da shi sai su karbe ba zasu bari na ci ba” “Saboda me?” “Sun fini girma, hadda dukana suke” Idonta ya kawo kwallah, sai tausayinta ya kama shi. “Yi hakuri kinji zan daukeke daga nan ba za ki dade ba?” “Yaushe?” Sai Barr Hassana tai karaf ta ce “Shi ma be sani ba, Alkali kadai y sani dan shi zai yanke hukunci” “Amman ya kamata a duba lafiyarta tace tana jin zazzabi fa, kuma a fada musu a daina dukanta” “Karka damu da ciwonta tsoro ne yake tare da ita, ba wata wahala ake basu sosai ba, gidan yarin under age na kamar na manya yake ba, amman zan yi musu magana” Ganin ba tafiya za su yi da ita ba, yasa ta bude baki za tai kuk sai Zain ya rumgumeta. “Don't cry karki yi kuka, zan fitar da ke daga nan ba zaki dade ba, idan kika yi kuka ba zan sake dowowa ba” Jin hakan sai yasa tai saurin gintse kukan ta maida shi ciki tana kwalla. Ya dade yana rarrashinta sannan ya saketa aka koma da ita ciki yana jin babu dadi. [3/29, 12:20 AM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 51. Labarin abunda ya faru ka kadare ko'ina ciki da wajen garin Gusau, ko'ina zancen ake har da yan karawa miya gishiri mutane da yawa sun sa ido akan shari'ar domin magana ta zagaye ko'ina cewar za a shiga kotu, hankula kowa ya koma can kama daga Zain da Anty Ummi har Alhaji Habib da yan'uwan Rufaida da ma duk wanda ke da ruwa da tsaki a ciki. It's Monday morning as they said yau za a shiga kotun amman Zain yana jin wani irin ba farinciki yake ba, haka ma ba akasin hakan yake ba, baya iya fayyace yadda yake ji ba a halin yanzu. Around ten aka hallara a kotun kowa da kowa na nan ciki har da Hajiya Hadiza da Hajiya Zarah da kuma Kanen Zain da wasu daga cikin familynsu, sai dai babu Hameeda da Dada a gurin. Anty Ummi babu yadda ba tayi ba akan mahaifan Farhat su zo amma suka ki, wai ita ba za ta iya ganin bakinciki ba, Anty Ummi da wata Kanwar Rufaida mai suna Sumaiya suna zaune a guri daya, yayinda Zain da Ibrahim suke zaune a layin maza, tare da Alhaji Habib da kanensa Alhaji Nura da kuma babban abokinsa Alhaji Buhari, a layin dake kusa da mazaunin lauyoyi. Yan jarida da masu son gani da ido suna cikin kotu, wasu kuma na tsaye a window, hakan yasa kotun ta cika makil ciki da waje. Idon Hassana yana kan yar'uwarta tana kallonta, tana jin rashin kyautawa a abunda yar'uwarta zata aikata, zata bata son ta a gurin Abbah su, jaridu da yawa zasu ruwaito cewar yar'uwa da yar'uwa uwa daya uba daya suna shari'a daya, idan har yai winning za ta jidadin yadda hakan, sai dai ba zata so rashin nasarar yar'uwarta, domin ba a son lauya yana faduwa a shari'a. Ita da Husaina dukansu kwarararrin lauyoyi ne, ba zata yarda ta kada kanta dan'uwarta ba, haka ma Husaina ba zata ka da kanta dan ita ba, dukansu suna kokarin ganin sun yi nasara ne. Ko sau daya Hussaina bata dago ta kalli yar'uwarta ba sha'aninta kawai take tana duba takardun dake hannunta tana buge bugen waya. Mutane dake cikin kotu kuma na magana kadan kadan kowa na fadin albarkacin bakinsa. Ana haka muhuti ya shigo ya bada sanarwa cewar alkali zai shigo yanzu, sai kowa ya natsu, ba a kara minti biyar ba Alkalin ya shigo ta kofar dake kusa da mazaunin alkalin, hakan yasa kowa ya tashi tsaye daga lauyoyin har mutane dake cikin kotu. “Kotuuuuuuuu” Haka kowa ya amsa, har sai da alkalin ya zauna, bayansa wani dan sanda ne ya tsaya guri daya kamar an dasashi a gurin. Sai da alkali ya gama duba takardun da ke gaban teburin da aka aje masa, ya saka hannu a wasu sannan ya mikawa police din ya saka a jaka, sannan muhuti ya mike tsaye yana gabatar da katar farko. “Yau litani daya ga watan biyar shekara ta dubu biyu da biyu, a yau shari'ar farko wacce za a gabatar ita ce wacce Barrister Husaina da Dpo Auwal suka shigar akan zargin Hafsat Habib Salisu da kashe Farhat Muhammad ta hanyar soka mata wuka” Yana gama fadin hakan ya mika takardun ga alkali, alkalin ya shigo dubawa, sannan ya bada umarni aka shigo da Hafsatu manga yan sanda hudu na tare da ita daya mace sauran uku kuma duk maza, gaba daya sai hankali ya koma kanta, kana ganinta kasan tayi kuka har bata iya numfashi da kyau, ba idonta kadai ba har fuskarta ta kumbura, mutanen da ke cikin kotun kowa da abunda yake rayawa a zuciyarsa. Alkali ya tada kai ya kalli Hafsatu manga wacce kanta ke kasa tana zubar da kwalla. Sai da ya dauke kansa yai rubutu sannan ya ce. “Idan lauyoyin masu gabatar da kara sun shirya za su iya gabatar da kansu” A take Barr Husaina ta mike tsaye yana gyara rigarta ta ce “Sunana Barrister Husaina Habib Salisu lauya mai gabata da kara, a tare da ni akwai lauya mai taimakamin Barrister Bello Muhammad” Tana kaiwa wannan gabar sai lauyan ya tashi tsaye sannan ya zauna. Barrister Hassana ta mike tsaye with full confidence ta gabatar da kanta. “Sunana Barrister Hassana Habib Salisu, lauya mai kare wacce ake kara” Bayan ta koma ta zauna alkalin ya rubuta sunansu sannan ta wani bayani baya sannan ya sake dago kai ya kallesu ya ce “Idan lauya mai shigar da kara ta shirya zata iya gabatarwa” Barr Husaina ta mike tsaye tana dan risinawa alkalin. “Na gode” Sai ta fita daga gaban teburin ta karasa gurin Hafsatu manga tana fadin. “A ranar Alhamis 17 ga watan hudu shekara ta dubu biyu da biyu da misalin karfe karfe daya da minti arba'in da bakwai da rana, aka samu Hafsat Habib Salisu wacce ake kira da Hafsatu manga a falon Margayiya Farhat ta daba mata wuka wanda yai sanadiyar mutuwarta har lahira...” “Objection my lord, ya kamata lauya mai kara ta gyara kalamanta domin ba a samu yarinyar da ake tuhuma rike da wuka tana dabawa Margayiya Farhat ba, zargi kawai ake yi” Alkalin ya dauke idonsa daga barin kallon Barrister Hassana ya kalli Barrister Husaina ya ce “Ya kamata lauya mai kara ta gyara kalamanta” “Na gode ya mai shari'a, ina neman kotu ta bani dama na yi ma Hafsatu manga tambayoyi” “Kotu ta baki dama” Sai da ta risina tai masa godiya, sannan ta karasa gaban Hafsatu manga wacce ke hawaye har yanzu tana hadiyar kuka. “Shin zaki iya fadawa kotu kina ina a wannan ranar ta alhamis da misalin karfe daya da minti arba'in da bakwai” Kai kawai Hafsatu manga ta daga ta kalli Barrister Husaina sai ta kara fashewa da kuka. “Ba zaki iya fada ba? Amman miyasa kika kasheta? Me tai miki?” “Objection my lord, be kamata lauya mai kara ta tsare karamar yarinya kamar wannan tana mata irin wadannan tambaboyinba, domin ita kanta tana cikin rudu da tsoron abunda ya faru, kuma har yanzu zarginta ake ba a kamata dumu dumu ba” Barr Husaina ta juya ta kalli alkalin tana tarar numfashin yar'uwarta ta ce. “Ya mai girma mai shari'a dole ne Hafsatu manga ya bude baki ta amsa mana wasu tambayoyin, domin ita kadaice aka samu a falon a lokacin da Farhat take da sauran numfashi” “Korafinki be karbu ba Barrister Hassana, za ki iya cigaba” Ya karasa yana kallon Barrister Husaina. “Na gode Mai shari'a” Ya sake kallon Hafsatu manga ta maimaita mata tambayar, amman Hafsatu manga ta kasa cewa komai sai kuka take. Barrister Husaina ta kalli Alkalin ta ce. “Ya mai girma mai shari'a, a ranar Alhamis sha bakwai ga wata 4, da Misalin karfe daya daga cikin masu aikin gidan Sarki wacce ake kira da Abida Zakari ta shiga part din Zain inda ta samu Hafsatu manga a bakin koda tana kokarin guduwa, bayan ta dabawa Margayiya Farhat wuka a ciki, idan kotu ta bani dama ina son a kotu ta kira min Abida domin nai mata wasu yan tambayoyin” “Kotu na bukatar ganin Abida Zakari a gabanta” Ana fadar hakan Abida ta tashi tsaye tsumu tsumu taje gaban alkalin ta tsaya, sai da aka bata rantsuwar fadin gaskiya sannan Barrister Husaina ta kalleta ta ce. “Ko zaki iya fadawa Kotu a wane hali kika samu Farhat?” “Lokacin da na shiga falon na samu Hafsatu manga rike da wuka a hannunta a bakin kofa tana kokarin guduwa, Farhat kuma tana kwance kusa da dinning cikin jini tana daukar numfashi, Hafsatu manga na ganina sai ta fashe da kuka, ni kuma na fita ina ihu ta hakan mutane suka shigo sai ya buya bayan kujera ta fara kuka” “Na gode, za ki iya komawa ki zauna” Ta koma Barrister Husaina tasa kotu ta kira mata Zain, cikin takun kasaita ya taso ya zo ya tsaya gaban alkali. “Shin ko zaka iya fadawa kotu alakarka da Margayiya Farhat” “Matata ce” “Auren soyayya kuka yi?” Barrister Hassana ta mike tsaye tana dakar teburin dake gabanta. “Objection my lord, be kamata Barr Husaina ta rika tambayar abunda ya shafi rayuwar aure ko soyayya dake tsakanin Zain da Margayiya Farhat ba, akan kisanta ne ba akan soyayyarta ba” “Tambaya ta tana da fa'ida ya mai shari'a, dole ne za mu san wani irin zama take tsakaninta da mijinta, Wacece Farhat su waye kawayenta ya hallayarta take, dole ne zamu so mu so mu sani domin musan komai akanta abunda ne da zai taimake mu akan shari'ar nan” “Korafi be karbu ba, Barr Husaina zaki iya cigaba” “Na gode ya mai shari'a” Ta juya gurin Zain. “Shin auren soyayya kuka yi da ita” “Auren kiyayya kike tsammanin zamu yi?” “Tambayace kawai Malam Yarima ka amsa mana” “Auren soyayya muka yi” “Ya zamantakewar aurenku yake?” “Akwai kyakkyawar mu'alama kuma muna kaunar junanmu” “Shin ko zaka iya fadawa kotu kadan daga cikin halayen Farhat” “Macece Mai Hakuri da biyayya ga bin umarnin na gaba da ita ko da hakan be mata dadi ba” “Kotu zata so taji dalilin zaman karamar yarinya kamar Hafsatu manga a gidanka, bayan kuma akwai kyakkyawar alaka a tsakaninka da matarka, shin mai aiki ce ko kuma kanwarka ce” “Ita ma matata ce ita ma, masarautar Damagaram ta bani ita a matsayin kuyanga, a wani lokaci fa na ziyarce masarautar” “Akwai kishi da kiyayya a tsakaninsu ko? Kasancewar miji daya suke aure” “Babu, zaman wuni da kwana ne kawai Hafsat tai a gidan ta ya kishi zai iya shiga tsakaninsu” “Kishi zai iya shiga zuciyar mace cikin minti daya Zain, wata kila baka bawa Farhat kulawa yadda ya dace shiyasa baka fahimci kishi yana tare da ita ba ko babu, ko da yake ka fada mana tana da hakuri ko? Wata kila shiyasa ta danne zuciyarta ta kasa nuna ko da na minti daya ne a gabansa, shin ko akwai kyakkyawar alaka tsakanin Farhat da Hafsat na dan zaman da tai a gidan na wuni daya da rabi?” “Akwai” “Shin a lokacin da ka samu labarin cewar Hafsat ta dabawa Farhat wuka ya kaji” “Nayi mamaki domin na san fada be taba shiga tsakaninsu ba, kuma Hafsat ko cinnaka ba zata iya kashewa ba balle rai” “Na gode zaka iya komawa mazauninka” Ta fada tana murmushi. Sai ta nufi gurin da teburinta yake ta bude jakarta ta dauko wata farar leda mai wuka a ciki ta daga ta sama. “Ya mai shari'a wannan ita ce wukar da da Hafsat ta dabawa Margayiya Farhat ta kasheta, an samu sawon hannun Hafsat a jikin wukar, a bayanin da Abida ta bayar ta nuna cewa Hafsat ta kashe ta ne a lokacin da suke su kadai a cikin falon kuma tai kokarin guduwa, kyakkyawar fahimta dake tsakaninsu zai iya zama a gaban idon Zain ne kawai a bayan idonsa kuma wata kila suna samun rashin fahimtar juna, ba abun mamaki ba ne dan karamar yarinya kamar Hafsat ta dabawa babbar mace kamar Farhat wuka ba, domin ba sabon abu ne ba, kuma zai iyayuwa daman can Hafsat bata shigo gidan da kyakkyawar niya ba, domin a bincike da nai ya nuna cewar Hafsat tashi kauye ce kuma yarinya ce wacce ta tashi cikin maza da mata da basu san darajar kansu ba, hasalima har yanzu ba a san waye mahaifiyar Hafsat ba, a duk zaman da tai a kauye ta zauna ne a hannun wata mace wacce take baiwai ga sarkim kufawa, Hafsat zata iya kashe Farhat idan har tana ganin ta takura mata, ta hanyar fada da zata mata ko kuma ta sakata wani aikin da wannan nake rokon kotu mai adalci data yankewa Hafsat hukuncin abunda ta aikata, domin ya zama darasi a gareta, kuma izna ga yan baya na gode” Ya mikawa muhti wukar muhti ya mikawa alkali, sannan ta koma ta zauna. Bayan Alkali ya karbi wukar ya duba ya yi rubutu ya dago ya kalli Barrister Hassana ya ce “Ko Lauya mai kare wacce ake kara tana da wani abu da zata fada” “Ina da shi ya mai shari'a” Ta fita daga inda take ta nufi gurin da Hafsat ta ke. “Ki kwantar da hankali wannan kotu ce mai adalci, ina son ki bude baki ki amsawa kotu wannan tambayar, shi ke kika kashe Farhat?” Sai kasa dago kai ta kalli Hassana balle har ta ce wani abu. “Ya mai girma Mai shari'a, wannan kukan da Hafsat take yi kadai ya isa ya karantar da duk wani mai hankali cewar ba ita tai kisan kan nan ba, a tunani na mai hankali da hangen nesa zai yi mamaki ace Hafsat yar shekara tara zuwa goma ta dauki wuka da hannunta ta dabawa babbar mace kamar Farhat mai shekara ashiri da shida a duniya, a iya binciken da nai ya nuna cewar wani tsabani ko rashin jutuwa be taba shiga takanin Farhat da Hafsat ba, a bayanin da Zain ya bayar a gaban kotu ya fada ma kotu cewar zaman da Hafsat tai a gidan na wuni daya da rabi ne, shin taya wani rashin jituwa zai iya shiga tsakanin Farhat da Hafsat da har zai kai ga yin kisa? Barrister Husaina bata fadi karya ba, gaskiya ne Hafsat bata tashi gaban iyayenta ba, amman kuma bata tashi gurin mutane masu gurbatacciyar tarbiya ba, a kaddara ma ta tashi a cikinsu a karancin shekarunta anya za ta iya daukar wuka ta tabawa wani kamar Farhat wacce ta taba ganin ganin wuni daya da rabi kawai?” “Objection my lord, Barrister Hassana tana kokarin wasa da hankalin kotu ne kawai, domin ga zahiri ya nuna an ga sawun hannunta a jikin wukar” “Ganin tambarin yatsun be isa ya bada shaidar cewar ita ta kashe Farhat ba, ta wuni a gidan na tsawon kwana daya da rana ba abun mamaki ba ne dan an ga tambarin yatsunta a jikin wukar ba” “Korafi be karbu ba, za ki iya cigaba” “Na gode ya mai shari'a, ina bukatar kotu ta kora Abida Zakari domin amsa mana wasu tambayoyin” “Kotu na bukatar ganin Abida Zakaria gabanta” A karo na biyu Abida ta taso ta sake dawowa gurin data tsaya dazun ta sake tsayawa. “Shim ko zaki fadawa kotu abunda ya kai ki part din Zain?” “Gimbiya Hameeda ce ta kirani a waya tace Farhat tana son gani naje yanzu yanzun nan” “Da kika je a wane hali kika samu Hafsat da Farhat?” Ta sake maimaita abunda ta fada dazun, sai Barrister Hassana ta ce “Shin kin ga wukar ne a hannun Hafsat?” “Aa wukar tana jikin Farhat ne ita kuma Hafsat ta zo jikin kofa tana kokarin guduwa” “Shi kadai kike gani?” “Ee” “Shin daman idan Farhat zata kiraki tana kiran Hameeda ne ta ce ta fada miki” “Aa hasali ma bata taba kirana ba” “Shin miyasa ta kiraki a wannan karon?” “Nima ban sani ba” “Na gama ya mai shari'a” “Zaki iya zuwa ki zauna” Mai shari'a ya fada. Bayan ta koma ta zauna. Barrister Hassana ta nufi gurin zamanta ta dauko abu a lada gorar rubutu ne a ciki da kulli magani. “Ya Mai girma Mai Shari'a, an samu wannan ne a kusa da gawar Farhat, rubutu ne da kullin magani shi taya rubutun ya shiga gidan? Waya kawo shi? Shin Hafsat tayi girman da zata iya bibiyar malamai har ta shigo da rubutu a gidan? Wani abun mamaki har yanzu babu wanda ya san inda wayar Farhat take, bata gurin mijinta haka zalika bata wani guri a cikin gidan, kuma mijinta ya tabbatar min da cewar ya siya mata waya to amman ina wayar take?” “Objection my lord, zai iya yiyuwa Hafsat ta dauke wayar ne ta boye wani gurin” Hasaana ta juyo ta kalleta. “Haba Barrister Husaina, karki yaudari kanki mana, taya karamar yarinya kamar Hafsat zata shigo cikin gidan da rubutu da soketa da wuka kuma ta dauke wayarta? Shekara tara kadai ba goma sha takwas ba” “Korafi be karbu ba, Barrister Hassana zaki iya cigana” “Na gode ya mai shari'a, Ina rokon kotu data kira min Zain a gabanta domin ya amsa mana wasu tambayoyin” “Kotu na bukatar ganin Zain a gabanta” Ba bata lokaci Zain ya taso ta zo ya tsaya. “Ka fadawa kotu cewar matarka mai hakuri ce, kenan bata taba samun sabani da kowa ba?” “Bata taba fada da kowa ba, sai dai akwai takum saka a tsakaninta da wata yar'uwata Hameeda” “Takun saka kamar yaya? Basa jituwa ne suna yawan fada ne?” “Akwai dai rashin jituwa a tsakaninsu” “Miya kawa rashin jutuwar a tsakaninsu” “Saboda Kakata Hameeda take son na aura, saboda Hameeda tana so na, ni kuma Farhat na ke so, wani lokacin ta kan shigo sashen har su samu rashin jituwa” “Kenan akwai kiyayya mai tsanani tsakaninsu? Haka ne?” “Haka ne” “Na gode, iya kacin tambayoyina kenan a gareshi ya mai shari'a” “Zain zai iya komawa ya zauna” Alkalin ya fada. Sai Barrister Hassana ta sake requesting. Cewar alkali ya kira mata Ibrahim domin amsa mata tambayoyi. “Ibrahim kotuna na bukatar ka gabatar mata da kanta” “Sunana Ibrahim Abdullahi kwararren likitan ina aiki da Zainuddeen Special Hospital” “Mashallah, shi kai ne wanda ya tarbi Farhat kuma ya cire mata wukar da ke jikinta ko?” “Ee ni ne” “Shin ya ka samu gawar Farhat?” “Ko da aka iso da ita tana da sauran numfashi, sai dai kamin mu gama mata aikin rai yai halinsa” “Shin ya ka samu sukar da wukar tai mata?” “An daba mata ita ne daga saman cikinta sai kuma tai kasa, hakan yasa har wasu daga cikin hanjinta suka fashe, mun yi iya kokarin mu na ceton ranta amman Allah be nufa ba” “Shin karamin yarinya kamar Hafsat zata iya daba ma Farhat wukar har tai mata rauni haka?” “Zata iya idan tsawonta ya kai mita talatin zuwa talatin da bakwai” “Idan kuma be kai ba fa?” “Ba zata iya taba mata wuka kamar hakan ba, domin alamu sun nuna duk wanda ya taba mata wuka to ya saba ne ko kuma ya gwari ne akan abu” “Kai ne kai gwajin wukar da aka daba mata ko? Har ka samu safurin Hannun Hafsat” “Ee amman ba safurin hannunta kawai na samu ba, na samu samfarin hannun wasu mutanen biyu, sai dai na Hafsat ne ya fito saboda mun dauki tambarin yatsunta” “Kenan akwai tambarin yatsun wasu bayan nata” “Ee akwai” Barrister Hassana ta kalli Alkali ta ce. “Ya mai shari'a idan muka hada maganar Abida ta farko cewar Hameeda ta fada mata Farhat na kiranta, da kuma zancen Zain da ya fadi cewar babu jituwa a tsakaninsu, hakan na nuna ba Hafsatu manga kadai ya kamata mu zarga ba, da wannan na ke rokon wannan kotu mai alfarma da ta taimaka ta bada belin yarinyar nan kuma ta dage wannan zaman na dan lokaci domin ba mu damar bincike, sannan kuma ina rokon kotu data bawa aikawa Hameeda da takardar gayyata domin ta amsa mana wasu tambayoyin a zama na gaba, na gode” Alkali ya dade yana rubutu sannan ya dago ya ce “Kotu zata dage wannan zaman har zuwa ashirin da uku da watan shida, kotu ta bada umarnin a cigaba da tsare Hafsat a gidan kaso, sannan kotu tana umartar magatakarda da ya aikawa Hameeda da takardar gayyata” Ya buga abunda ke gabansa sannan duk suka tashi, suka fito waje tare da Hafsatu manga wacce yan gandireba ke tare da ita tana ta shekar kuka. Mahaifinta ma Hawaye yana jin kamar ya figota ta karfe ya dawo da ita, Zain kam tuni ya bar gaban kotu ya koma cikin motarsa ya zauna yana jiran abokinsa Ibrahim, Anty Ummi da Barrister Hassana tare suka fito ko wannensu rai babu dadi domin sun so a bada belin Hafsat amman hakan be samu ba, Husaina kam taa can ciki daman tana da wat shari'ar bayan wannan. [3/29, 10:17 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 52. Dada ta rike takardar sammacin neman zuwa Hameeda kotu tana girgiza kai. “Ina mamakin wannan kiyayyar ta Zain, wato yana kam bakansa cewar ita ta kashe masa mata ko? Lallai Zain ka bani mamaki” Hawaye kawai Hameeda ta kasa cewa komai. Sapna wacce ita ce wacce Mai Martaba ya aiko ta kawo ma Hameeda takardar, ta kalli Hameeda cike da tausayawa ta ce. “Ba fa wani abun ne, kawai dai an fadi cewar auna samun rashin jituwa ne tsakaninta da Farhat shine Barrister ta nemi kotu ta gayyatota ta amsa mata wasu tambayoyin, amman ba wai wani abun ba ne” Ta dago kanta ta kalli Dada tana share hawayen da suka ki su tsaya mata. “Zan je kotu, zan bada shaidar abunda na sani, kowa zai huta” Dada ta dafata cike da tausayawa. “Ki kwantar da hankalinki Hameeda, duk mai son ganinki a rana shi zai shiga cikin ranar nan da yardar Allah” “Hankalina zai kwanta, kaddarata ta canja wata kila a zamanin labarin harihim rayuwata ya shude, amman bana hangowa kaina kwanciyar hankali a gobe, jibi, sati mai zuwa ko kuma wani zamanin” Ta fada zuciyarta na ta raya mata wani abun da take jin ita din zata iya. Ta mike tsaye cikin rashin kuzari ta fice daga falon Dada ba tare da hawayen sun daina mata zuba ba. “Da nasan haka zamankewarku zata koma, da ban rika daya daga cikinku ba, da duk ban ga wannan bakincikin ba” Dada ta fada tana hawaye. Abunda yasa Sapna jin babu dadi, cox yana cikin abunda ta tsana ganin hawayen babba, saukowa tai daga inda take zaune ta zo gaban Dada ta zauna kasa ta kama hannayenta ta rike. “Dada dukan abunda ya ke faruwa Allah ya riga ya tsara haka zai faru, kuma shi yasan yadda zai daidaita al'amurransa,dan haka ki barwa Allah komai ki yi addu'a baki san abunda Allah yake nufi da wannan ba” “Haka ne, amman Sapna ni kadai na san abunda na ke ji akan abubuwan nan da suka faru” “Nima bana jindadi ba, Dada kusan ko wace jarida ta kasar nan sai da ta buga labarin abunda nan da yadda aka gudanar da shari'ar, mutane da yawa sun saka ido akan wannan shari'ar ba abun jindadi ba ne, ace irin wannan case din ya taso a gidan sarauta balle ma irin wannan masarautar mai kima da daraja, tsakanin shekaranjiya da a kai shari'ar nan da jiya na karbi kira yafi a kirga mutane sai neman jin abun suke, even on instagram ban huta ba kowa sai tambaya yake, ba ni kadai ba nasan duk wanda ke da alaka da masarautar nan sai ya sha irin wadannan tambayoyin” “Ai Mai Martaba be damu da zubewar kimar masarautar nan ba, a lokacin da nai masa maganar kar ya bari akai magabar nan kotu sai yaki daukar shawarata, ya goyawa dansa baya bayan kuma ya san abunda yake ba daidai bane, ai duk har da laifinsa gurin fadan nan da suka yi” “Karki ga laifin Mai Martaba Dada, maganar ce ta riga ta fita, idan ma be yarda anje kotun ba, ba za iya fayyace mai gaskiya tsakaninsu ba, idan har ya hana zuwa kotun Zain zai iya ganin laifinsa kuma ya ga an tauye masa hakki, amman zuwa kotun yana da amfani za a fayyace mai gaskiya a tsakaninsu, a yadda na ji wai an gano mahaifin Hafsat din kin ga shi ma ai ba zai kyale ba, zai ga kamar zaluntarta ne za'ayi amman idan kotu ce ta fayyace gaskiya kuma ta hanke hukunci dole kowa zai yarda” “Haka ne, Allah ya yanke mana wannan jarrabar hakan, ya kawo mana mafita da duk abunda zai fi zama alheri a rayuwarmu gaba daya” “Amin Dada shine kawai addu'ar daya kamata ki yi” Cikin hikima Sapna ta jata da wata hirar ta daban gudun kar ta saka abun a ranta. ***    ***     *** “Har yanzu baka ci abincin ba” “Anty na fada miki ba zan iya cin abinci mai nauyi ba” “Daurewa za kayi ka ci, Zain idan kana cewa ba zaka ci abincin ba zaka jawa kanka wata matsalar ne” Babu yadda zai yi da Anty Ummi ya san indai be ci ba, zata tai ta sha masa kai ne har sai ya ci. Dan haka ya dauka ya fara ci kadan yana wani tunanin. “Anty ina ganin kamar Mai Martaba zai ga cewar ban kyauta nasa ba ko? Labarin nan ya zaga ko'ina a garin nan, jaridu ni kaina tambayata ake ta yi balle kuma shi” “Babu wani rashin kyautawa a ciki, abunda kotu zata yanke shine daidai kuma na san inshallah zamu yi nasara, shi kanshi hakan zai fi kara masa girma da Martaba aga cewar a gidansa abun ya faru amman hakan be hanashi barin hukuma tai aikinta ba” “Haka ne, ina fatar zamu yi nasara” Ya fada sannan ya dauki ruwa ya sha. “Inshallah zamu yi, kawai ka cigaba da addu'a komai zai zo da sauki, amman kasan bana hangen nasararmu a yanzu, domin Hameeda shu'uma ce, zata yi kokarin duk yadda zata yi ta fidda kanta, gashi kuma wannan Barrister Husaina din tana son ganin bayan Hafsat” “Tana bani mamaki sosai taya zaka yi kokarin saka yar'uwarka cikin ukuba” “Ta dauki gefen mahaifiyarta ne, kuma daman kasan barewa bata gudu danta yai rarrafe, Allah dai ya kyauta” “Amin” Haka kawai ya fada ya mike tsaye. ***       ***          *** A duk lokacin da ya kwanta da sunan bachi sai bachin yai masa kwara daga idonsa, haka zai raya dare tana ta tunani kala kala, at first yana tunanin halin da Safiya take a yanzu, duk da kasancewarta ita ta saka kanta, amman abubuwan da ake bashi labarin tana yi suna bashi mamaki, a yadda ta fada sai idan Rufaida ta dawo sannan haukan zai koma kanta amman tana wasu dabi'u da halaye da ke nuna cewar kamar ba a hayyacinta take ba, idonta ya fada kuma yayi baki sosai kamar ana shafa mata kwalli har saman idon, ga wata uwar rama datai hallittarta na kokarin sauyawa zuwa wata kalar ta daban, duk bayan kwana biyu sai Hassana da Husaina sun zo dubanta, sai dai kowa tafiyarsa daban yake, domin Husaina ta dauki gaba da yar'uwarta, hankalinsu ya tashi sosai kullum Hassana cikin rokon mahaifinta take akan yaje ya dubata amman ya kasa zuwa ganinta saboda yana ganin kamar kallonta zai kara masa bakinciki ne kawai. Ta dayan bangaren kuma yana tunanin rayuwar Hafsatu manga, nasara da rashin nasarar duk suna ransa, sai yauahe zata fito zuwa yaushe zai kasancewa guri daya da yarsa yana ganin kamar lokaci ne mai tsawo ko ma ba zai zo ba gaba daya, ko da gaske Hafsat ita ce ta kashe Farhat zai yi duk abunda zai yi wajen ganin ya fito da ita, balle ma babu gaskiya a ciki, bashi da tabbacin komai a yanzu sai na fitowarta ta kowane hali, yana jin zai iya kashe dukiyarsa wajen kautar mata yancinta ko da hakan na nufin ya rasa komai na sa ne, a wani babin kuma yana jin babu dadin akan rashin jituwar da yayansa suke samu wato Barrister Hassana da Husaina, dukansu suna sukar junansu ne da abunda yafi wuka da bindiga, ko wance na kokarin ganin ta kifar da yar'uwarta ne, kuma akan mutum daya suke wannan abun, wato yarsa Hafsat, da wanne zai ji, ga Rufaida ta tsaya masa a rai addu'a ba dare ba rana nemanta kan har yanzu be daina ba, kamar yadda yan'uwanta ma basu taba nuna karaya ba. Haka kai spending one month kowa da abinda yake ta nuna a ransa, da kuma abunda yake hangowa a matsayin nasara da rashinta, da bangaren Hasana da Husaina ko wannensu ya damu da halin da mahaifiyarsu take ciki, wani lokacin Husaina har Tsoro take ji, ganin cewar sai Rufaida ta dawo abun zai koma kan mahaufiyarta amman tun yanzu tana abu kamar ya dawo kanta, ko dai hakan na nuna cewar Rufaida ta mutune abun ke dawo mata ko kuma tana can tana warkewa a duk inda take shiyasa mahaifiyarsu ke kara shiga cikin tashin hankali. Daga asibitin aka canja mata zuwa wata asibitin ta daban saboda halin da take ciki ba sauki abu sai karuwa yake. *23-06* Kotun ta yi tsit kamar babu wani abu mai rai ciki, kowa ya maida hankalinsa gurin alkali wanda ke ta rubuce rubuce, kamin ya dago ya kalli Hafsatu manga, sai kuma ya kallin sauran mutane ta saman farin gilashin da ke idonsa. “Idan lauyoyin sun shirya za su iya farawa” Barrister Husaina ce ta mike tsaye, hannunta rike da takardu ta kalli Alkalin ta ce. “Ya mai shari'a abunda abokiyar aikina take kokarin yi tana son wasa da hankalin kotu ne kawai dan ta batawa shari'a lokaci domin an riga an kama wacce tai kisa da hannu dumu dumu amman tana kokarin karkarta abun ga iyalan Mai Martaba” “Objection my lord, abunda na ke ba bata suna ba ne, tambayoyine kawai zata amsa mana, saboda tana diyar gidan sarki sai shari'a tace ba zata tuhumeta ba, ba zata amsa mana tambayoyin mu ba, saboda ita shafaffiya da mai ce sai a zuba mata ido bayan kuma tana cikin mutane da suke samun rashin jituwa da mamaciyar, sannan a jikin wukar anga tambarin yatsun mutane biyu bayan na Hafsat, dayan na Zain ne dayan kuma ba a san ko na wannene ba, dole ne kotu tai mata wasu tambayoyin kuma ta binciketa” “Tambarin hannun a jikin wuka be isa ya saka a kira yar babbar gida kamar Hameeda ba ana tuhumarta da abunda kowa ya san da hankali ne ya mai shari'a” “Kotu ta riga ta aika mata da sammaci dan haka dole ne ta tsaya gaban kotu ta bawa kotu amsa wasu abubuwan, ba alakan kisan kan da ita ba, tambayoyin kawai zan mata, kuma ya kamata lauya mai shigar da kara ta gyara kalamanta domin Hafsat zarginta kawai ake ba a ganta da laifin ba” Magana suke kamar masu fada da junansu kowa wacce ta cika tana jin kamar ta shako yar'uwarta. “Barrister Husaina ki gyara kalamanki” “Na gode ya mai shari'a, idan kotu ta ba ni dama ina son gabatar da shaidata a gabanta” “Kotu ta baki dama” “Bismillah” Ta fada sai aka shigo da Fauziya tana sanye da doguwar riga ta yadi tayi rolling kanta da jan mayafi. “Kotu zata son sunanki da kuma alakarki da wacce ake tuhuma” “Sunana Fauziya Hafis ni kawar Hameeda ce” “Shin ko akwai wani abu da zaki fadawa kotu” “Ee ina yawan zuwa gidan Mai Martaba kasancewar Hameeda kamar yar'uwa take a gareni, a zuwa na karshe Hameeda ta kai ni gurin Farhat mu gaisa na isko Hafsat tana ta aiki Farhat na mata fada, ita kuma tana mayar mata duk abunda tace mata daga kashe ta jefar da abun mopping din ta wuce dakin Zain tana harar Farhat shikenan abunda na sani” “Na gode zaki iya zuwa ki zauna” Fauziya ta sauka daga gurin ta nufi inda ta fito babu alamar karya ko Tsoro a tare da ita. “Ya mai shari'a wannan kadai ya isa ya nuna maka cewar Hafsat yarinya mai tsura ga raina na gaba da ita, a yadda take jin haushi Farhat zata iya aikata mata komai ya Allah ita Farhat din tana sane ko kuma bayan ta juya ko tana jikin dinning din tai tsalle ta daba mata wukar wanda hkan zai bata damar janta har kasan cikinta ta huda mata hanji, da wannan na ke rokon wannan kotu mai adalci data yankewa Hafsat hukuncin da ya dace da ita, kuma ina rokon alfamar kotu da dage wannan zaman dan bawa lauyoyinta damar bincike na gode mai shari'a” Daga haka ta koma ta zauna, sai Barrister Hassana ta mike tsaye ta fito daga gurin da take zaune ta tsaya gaban alkalin. “Ya mai shari'a, ina neman kotu ta kira Hameeda domin ta amsa mana wasu tambayoyin” “Kotu na bukatar ganin Hameeda a gabanta” Alkalin ya fada. Sai aka bude wata kofar dake can baya wata yar sanda na take mata baya aka shigo da ita yan sanda biyu kuma suna tsaye jikin kofar da aka shigo da ita. Sanye take da farin Hijab mai shudi da atamfar dake jikinta kanta a kasa har ta tsaya inda aka bukace bata daga ta kalli kowa ba. “Kotu zata so jin sunanki da kuma alakarki da mamaciyar” “Sunana Hameeda Farhat matar yayana ce” “Yayanki wanda kike so ko?” Barrister Husaina ta mike tsaye. “Objection my lord, Barrister Hassana tana kokarin juyar da maganar ne ta matda ita ta wata sigar daban wanda hakan be dace ba” Barrister Hassana ta kalli Mai shari'a. “Ya mai shari'a ina son kotu ta san alakar da ke tsakanin Hameeda da Zain ne, yan 'uwane amman na uwa daya uba daya ba, yan wa da yan kane ne su wanda akwai aure a tsakaninsu” “Korafi be karbu ba, Barrister Hassana zaki iya cigaba” “Na gode” Sai ta juya gurin Hameeda wacce ta dago kai a karon farko tana kallonta. “Ke kika fadawa Abida cewar Farhat tana nemanta kuma ta je da sauri, shin Farhat din bata da number Abida ne da zata kirata da kanta ta fada mata tana nemanta?” “Bata da ita” “Ke ya akayi tai number ki?” “Nima bata da numberta” “To taya akai kika fadawa Abida cewar Farhat tana nemanta? Taya kika san tana nemanta?” “Ba ita ta ce tana nemanta ba, nice kawai na kira Abida na fada mata cewar Farhat tana neman mata” “Ko miyasa kika yi hakan?” “Sabod ina son Abida ta shiga ta riske Hafsat a falon, akan gawar Farhat ko kuma ba akan gawarta ba, kawai dai ina son ta ga yarinyar nan a kusa da ita, ban san mi zan aikata a wannan lokacin ba, kuma ba lallai ne kowa ta amince da ni ba, idan ni na gani” “Amman taya aka yi kika san cewar Farhat ta mutu har Hafsat tana tsaye kan gawarta?” “Saboda ni na kasheta.....” Kai tsaye ta fada tana kallon Barrister Hassana. Chaaaa kotun tai da ihu kowa na fadin albakarcin bakinsa hankali sai ya kara komawa gurinta... [4/1, 1:53 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *53* Tsakanin Anty Ummi da Alhaji Habib da Zain ba zaka iya tantance irin al'ajabi da tsananin mamakin da ke fuskarsa ba, sakamakon jin furucin Hameeda, Barrister Husaina ma mutuwar zaune tayi daga inda take. Sai da Alkalin ya daki dan karamin abunda ke gabansa sannan kowa ya natsu kotun tai tsif kamar babu kowa a ciki. Wasu zafafan hawaye ne suka fara fitowa daga idon Hameeda ba tare da ta sani ba. Wanda hakan ya bawa Barrister Hassana damar sauke numfashi a hankali. Alkalin ya kalleta “Kin san abunda kike fada” “Na sani ya mai shari'a” “Amman mi yasa kika kasheta mi tai miki?” Barrister Hassana ta tambaya, sai Barrister Husaina ta mike tsaye. “Objection my lord, Barrister Hassana ta tirsasa Hameeda amsa laifin ne, saboda bata da wata amsa da zata bata a halin yanzu, ya kamata Brr Hassana ta sassauta tsararan tambayoyin da take mata domin gudun rikitata” “Tambayoyina a kan hanya suke ya mai shari'a, babu takurwa ko cilastawa a ciki” “Korafi be karbuba, Zaki iya cigaba da tambayarki Barrister Hassana” “Na gode ya Mai shari'a” Sai ta juya gurin Hameeda ta kalleta. “Mi yasa kika kasheta?” “Ba da gangan na kashe ta ba... ” Ta fada cikin muryar kuka. “Mi tai miki?” “Ta tare min abubuwa da yawa, ta karbe gurbin da nake tunanin Zain zai maye da ni, ita ce ta zubar min da kima gurin Mai Martaba, na dade ina aikata abunda zai sa Zain ya dawo ya so ni kamar, ita kuma ya bata da ita wannan yasa na shiga falonta ina zuba mata rubutun da niyar idan ta tsallaka zasu yi fada da Zain, ban sani ba ashe tana nan ta daukata a wayarta, sai kuma ta fada min zata yada video zata fadawa Mai Martaba kuma zata nunawa Dada, wannan yasa na dauko wukar da ke kan dinning na daba mata, na dauke wayar duk abunda ya faru akan idon Hafsat, na yi sammanin zata toma min asirina shiyasa na kira Abida na fada mata cewar Farhat tana nemantata yadda idan ta ganta zata dauka ita ta aikata kisan kan, tun daga ranar ba ni da natsuwa da kwanciyar hankali har yau” “Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un, yanzu saboda kawai ta dauki video abunda kike aikatawa marar kyau kika kashe ta. Anya kina da hankali da tunani irin na mutane” “Ina da hankali Barrister, a lokacin ba ni da yadda zan yi ne, ina tsoron ta fallasa ni kamar yadda ta fada, kuma ko ban kashe Farhat a yanzu ba, dole zata mutu nan da wasu watanni ko shekara ma su zuwa, saboda gubar da na ba Abida ta saka mata a abinci saboda na daukarwa kaina alkawarin duk matar da Zain zai aura sai na ga bayanta ciki har da yar'uwata” “Kina nufin ke kika kashe yayarki kenan” Ta gyada kai hawaye na mata zuba. “Daga ranar da Zain ya furta mata kalmar so har aka saka musu rana, sai zuciyata na kasheta kawai na huta shine magani, Fauziya ce ta karbo min maganin gurin wani bokanta domin ni ban taba ganinsa ba, yace na zuba mata maganin a abinci ta ci, za tai ta rashin lafiya tana aman jini har zuwa lokacin da zata mutu, ban ji komai ba lokacin da ta mutu bayan kewa irin ta yan'uwantaka, amman Farhat na kasa samun sukuni da walwala, na kasa aminta da kaina balle kuma wani kullum sai dai na kebe kaina nai ta kuka na kasa samun sukuni da natsuwa” Barrister Husaina ta mike tsaye hawaye na zuba a idonta ta ce “Ya Mai girma mai shari'a, ya kamata Barrister Hassana ta dakatar da tambayoyin da take yi ma Hameeda a haka har sai n binciki kwakwalwarta, domin babu wani abu da zai tabbatar da yarinyar nan cikin hankalinta take ko kuma gaskiyar abunda take fada, da alama bata cikin hayyacinta ne gaba daya” “Cikin Hankalina na ke Barrister” Ta fada sannan ta fiddo hannunta dake cikin Hijab sai ga wayar Farhat a hannunta, ta mikawa barrister Hassana. “Wannan wayar Farhat ce, na tabbatar akwai abunda na ke fada a ciki, na dauke wayar amman Allah be bani ikon jefarwa ba. Na san kowa zai yi mamakin abunda na fada, amman na gaji da rayuwar da na ke ciki shiyasa na fadi gaskiya, na cutar mutane da yawa, kuma saboda son Zain ne son da be amfanin min komai ba, duk kokarin da nai ban taba cin nasaraba, mafarkina be taba tabbatuwa ba, na yi damar zuwana a duniya yau, na yi nadamar sanin Zain a rayuwata, na bata sunan masarautar Rishim, na cutar da Yar'uwata, Farhat da Hafsat, ba ni da sa'a a rayuwata, da nasan haka rayuwata zata kasance da ban zauna da ku ba, na san Mai Martaba zai ji haushi na, Dada ma ba zata yafe min ba, ko ba dade ko ba jima nasan asirina zai tonu kuma Allah ba zai barni ba shiyasa na fadi gaskiya ta yadda za a yanke min hukunci daidai da abunda na aikata...” Ta fashe da wani iri kuka mai ban tausayi da sosa zuciya. Barrister Hassana ta nufi laptop dinta ta kunna ta bude wayar ta cire memory card din dake cikin wayar ta saka a laptop dinta ta nemo video ta bude video ta mikawa muhti muhtin ya mikawa Alkali ya kalla da kansa, sannan ya miko mata laptop din. “Ya mai shari'a, bisa ga amsa laifinta da Hameeda tai ba tare da batawa kotu lokaci ba, da kuma tabbacin abunda ta aikata a cikin daukar da margayiya Farhat tai wanda ya zame mana shaida, da kuma samunta da wayar da akai a gurinta, na ke rokon wannan kotu mai adalci da ta bada belin Hafsat kuma ta yankewa Hameeda hukuncin dai dai da laifin da ta aikata, ina rokon wannan kotun ta sa a kama Fauziya da Abida domin dukansu sun kashe rai kuma suna kokarin sake kashe wani ran ne, domin barin irin wadannan mutanen su cigaba da zama cikin mutane ba shi da wani amfani kuma barazana ce ga wasu rayukan, na gode ya mai shari'a, na gode ya mai shari'a” Ta dan risina masa tana hawaye, sannan ta zauna tana kallon Husaina wacce ita ma hawayen take daga inda take zaune. Sai da Alkalin yai rubutu sannan ya dago ya kalli Husaina. “Ko lauya mai kara na da wani abun da zata fada?” “Babu ya mai shari'a” Ta fada cikin muryar kuka. Sai ke maida kansa yai gurin takardun dake gabansa yana rubutu, dukansu abu daya suke yi ma kuka wato mahaifiyarsu, kowa yayi mamakin ganin Husaina tana hawayen a cikin kotu, ba yau aka fara shiga shari'a daya yai nasara daya kuma ya fadi ba, amman ganin dukansu suna hawaye shine abunda ya bawa kowa mamaki, meanwhile Anty Ummi hawaye take, duk wanda ke da alaka da Hameeda baya farinciki da abunda ya faru, Alhaji Habib da yan'uwansa sai yan'uwan Rufaida sune kawai suke farinciki. Ta bangaren Zain he feel Empty, ba farinciki kuma ba akasin hakan. A natse Alkalin ya dago ya ce. “Kotu zata dage wannan karar har zuwa shida ga watan bakwai, kuma ta aminta da bada belin Hafsat, kotu ta bada izinin kama Hameeda a kaita gidan kaso har zuwa lokacin da za a sake zama na uku kuma na zama na karshe, sannan kotu na umartar Dpo Auwal ya kama Fauziya da Abida ya gabatar da su a gaban kotu a ranar shida ga watan bakwai, kuma kotu ta bada umarnin a bincike kwakwalwar Hameeda domin tabbatar da lafiyarta kamin ranar shida ga watan bakwai” Yana gama fadar hakam sai ga police din dake tsaye jikin kofa sun zo da sauri mace ta tashi Hameeda tsaye aka saka mata handcuff, baka jin komai a kotun sai sautin kukanta. Yar gandireba dake bayan Hafsatu manga ta ja gefe tana fadin. “Jeka gurin mahaifinki” Sai ta daga kai ta kalleta sannan ta maida kanta kasa ta fara takawa a hankali kanta a kasa har yanzu kuka take, Alhaji Habib na hango ta fito ya taso fa sauri ya nufo inda Hafsatu manga take, ita kuma ta nufi inda Zain yake, tasowa Zain ya dosota cike da zafin nama har ya riga mahaifinta isa inda take ya dauketa ya rumgume, sai ta kara fashewa da kuka. Fitowa yai da ita daga cikin kotu zuwa harabar gurin inda motocinsu suke. “Shiii ya isa ai na fada miki za a fitar da ke daga nan, kin ga yanzu ba zaki sake komawa can ba” “Zat ina mamata?” “Nima ban sani ba, amman tana nan zuwa ita ta aiko wadannan mutane kanenta ne, kuma ga babanki can” Ya karasa tare da sauke ta kasa, tana kallon Alhaji Habib ta sake kallon Zain tana kokarin shigewa jikinsa “Ni ba babana ba ne” “Babanki ne mana, baki ga kunyi kama ba? Kuma yana tare da yan'uwan mamarki ita ce ta turo su” “Da gaske ita ce ta turosu? To ina su Inna Ladi” “Ban sani ba, idan ta zo zata fada miki, Mama ashe kina iya magana ko kika ki magana a kotu” “Tsoron Alkalin na ke ji” Yan'uwan Rufaida na isowa suka dauketa suna shafa kanta kamar zasu cinyeta kowane fuskarsa dauke da murmushi wasu kuma na hawaye, karba karba suka rika yi da ita suna jin kamar mahaifiyarta ce. Ibrahim ne ya karaso inda Zain yake tsaye yana kallon motar yan prison wacce aka saka Hameeda a ciki wacce aka zo da Hafsatu manga da ita sai a aka wuce da Hameeda aka wuce da ita ciki. Anty Ummi ce ta fito rike da kafadar Husaina wacce ke ta rusa kuka ta nufi gurin motarta ta saka ta sannan ta zagayo mazaunin direaba ta shiga tai ma motar key taja ta suka bar kotun. Sai barrister Hassana wacce ta fito rike da rigarta a hannu ,dayab hannunta kuma rike da madaidaiciyar jaka mai dauke da laptop da kuma wasu takardun a cikin. Gurin da Alhaji Habib yake tsaye ta nufo amman ta tsaya nesa da su tana kallonsu fuskarta dauke da murmushi Idanuwanta na zubar da kwalla. Alhaji Habib na hangota sai ya doso inda take cike da kaunarta. “Na gode sosai Hassana, karatunki ya yi min amfani Allah yai miki albarka” Tasa hannu ta share hawayen. “Amin Baba, nima ina rokon wata alfarma” “Name whatever you want zan miki shi” “Dan Allah ka yafewa Mama, na maka alkawarin zamu yi nasara, kuma nasan zama na karshe Alkali zai wanke ta ne kuma ya yankewa Hameeda hukuncin laifin da ta aikata” “Ai na yafe mata, na fada miki na fadawa yan'uwanta na yafe mata” “Ba irin wacan yafiyar Baba, tun da ta kamu da rashin lafiyar nan baka taka je ka dubata ba, saboda kana fushi da ita ko kace ka yafe mata hakam ba zai wadatar ba har sai kaje ka ganta, Baba ko ba dan tana matar ka ba, ni da Husaina muna tsakani ko dan ya kamata ka mutunta Mama, bana farinciki da abunda ta aikata, amman dukan dan'adam ajizine kowa be wuce fadawa cikin wannan halin ba, kuma ina tunanin a yanzu ma goge laifinta” “Kin goge Hassana, kuma yau yau din nan zan koma kaduna ba sai gobe ba, zan je na dubata indai hakan ne abunda kike bukata” “Na gode Baba” Ya gyada mata kai, sai ta juyar da fuskarta gurin su Zain tana kallonsu shi da Ibrahim. Su Hajiya Zarah da Maryam na isowa da labarin abunda ya faru gaba daya sai da masarautar ta girgiza, daman wasu sisters din Zain sun dawo da kuka. Babu wanda yaji dadin abunda ya faru musamman Mai Martaba wanda shine uba a gurinta a yanzu, yadda za a sanar da Dada Yalwa ne kowa ke tunanin, be shirya rabuwa da mahaifiyarsa a yanzu ba, sai dai yasan fada mata zai iya sanadiyar mutuwarta ko kuma faruwar wani abun saboda so da shakuwar da ke tsakaninsu da Hameeda. “Babu wanda zai fadawa Hajiya abunda ya faru, kuma zan karbe wayarta gudun kar wani ya kirata daga waje da sunan jaje ya fada mata” “Amman Mai Martaba baka tunanin zata tambayi Hameeda? Zata son jin halin da take ciki” Cewar Hajiya Hadiza cike da damuwa. “Za'a fada mata wani abun ne na dabam amman ba wannan ba, ko kuma a fada mata cewar ta ki ta bada shaidar ne a kotu shiyasa alkalin yasa a ka tsare ta” Hajiya Maryam ta ce “Sai dai zata dame ka da bukatar akayi wani abun a sakota, kasan yadda take jin Hameeda idan bata ganta a gidan nan ba, hankalinta ba zai taba kwanciya ba” “Damuwata da zata yi zai fi sauki fiye da a fada mata gaskiya” Ikram ta kalli Mai Martaba tana hawaye ta ce “Na san zama na gaba alkalin zai yanke mata hukuncin kisa ne, kuma ya wanke Hafsat, dan Allah ka yi wani abu Mai Martaba Wallahi son Ya Zain ne yaja mata shiga wannan halin, ko abunda ta aikata a kwanakin baya har ta kirani a waya ni da kawarta muka tararda ita sai ta fada mana wai Ya Zain ya mata fyade ban yarda ba, amman ban tona mata asiri ba saboda na san dukan abunda take saboda so take yi, tana kokarin aikata abunda zai sa Zain ya so ta ne” “Amman dukan abunda zai sa Zain ya so ta, be cancanci ta kashe yyarta ba, har ta kai ga Farhat, idan har aka barta ta cigana da zama a nan mu kanmu rayuwarmu tana cikin hadari, kuma ba zata taba barin Zain ba, bayan haka mutane da yawa sun sa ido akan shari'ar sai kuma aji Mai Martaba ya saka baki a ciki ko yayi wani unkurin? Sam hakan be dace ba a ganina” Cewar Hajiya Hadiza. Ikram ta kalleta tana kuka. “Tare muka tashi da Hameeda Hajiya, kin fi kowa sanin halinta ba haka yake ba, kuma ki misalta da ni ko Sapna idan dayan mu haka ta faru da shi ya zaki ji? Bata da uwa ba uba a yanzu bata da kowa sai Mai Martaba sai mu, ba a fili Mai Martaba zai dauki matakin ba, a sirrinsa zai yi, a biya diya ko kuma ayi wani abun a fito da ita dan Allah kar abari kotu ta kasheta” Mai Martaba ya kalleta a hankali. “Dukan abunda kike ji Ikram ba ki kai ni ba, amman Wallahi na rantse miki da Allah da yau ke ko Hajiya ko Zain wani zai kashe rai, to sai nasa kotu ta zarartar masa da hukuncin abunda ya aikata, itama wasu rayukan ta kashe kuma ba dan ba a son su ba, dokar Allah ce duka wanda ya kashe rai a kasheshi, domin rai be fi rai ba, itama kanta idan ba hukuncin aka yanke mata ba ba zata taba samun natsuwa da kwanciyar hankali ba, yana daya daga cikin dalilin daya sa ta fadi gaskiya ba tare da an matseta ba” “Amman Mai Martaba za a iya biyan diya...” Ikram na rufe baki sai ga Dada Yalwa ta turo kofar falon ta shigo, duk cirko cirko suka yi a zatonsu zata gane abunda ya faru ne, musamman Ikram da ke aikin sharar kwalla. Gurin da ta saba zama ta nufa ta zauna tana fadin. “Yanzu Zain ya kirani wai ya raka Hameeda airport zata tafi Kaduna gurin Alhaji Aminu (Yayan mahaifiyarta), wai ta bada shaidar da ake bukata shine ta koma can har a gama, ya ce wai idan ta fada min ba zan yarda ba shine tace kar a fada min zata kirani idan ta isa, kuma nata kira wayarta na kasa samu” Ta fada fuskarta na nuna tashin hankalin da ke zuciyarta,yanayin yadda tai yi maganar zaka fahimci cewar sam bata yarda da abunda Zain ya fada mata ba. Ikram ce take gyaran muryar tai karaf ta ce “Dukanmu nan mun san da tafiyarta Dada, daman tace kar a fada miki ne saboda ba zaki barta ba, ita kuma ta gaji da zama gidan nan wai tafi son ta tafi sai idan an gama shari'ar gaba daya sannan zata dawo, tun shekaranjiya ta fadawa Mai Martaba maganar tafiyar” Dada ta kalli Mai Martaba da idanunwata na tsofi dake nuna tana daf da yin kuka. “Ki kwantar da hankalinki Hajiya, ni kaina na fi son tai nisa da nan har sai komai ya lafa, domin bana jindadin rashin jituwar da suke samu da Zain” Mai Martaba ya fada mata. “Allah yasa gaskiya kuke fada min, daga zuwa bada shaida sai kuma ace ta tafi kaduna, ko dai wani abun ne?” “Babu komai Hajiya, idan ta isa ai zata kiraki ko kuma ke ki kirata domin tabbtarwa” “To Allah ya kaita lafiya” Ta tashi cikin rashin kuzari ta fice daga falon ba dan ta gamsu cewar hakan ne dalilin zuwanta Kaduna ba, zuciyarta na raya mata ba hakan ne gaskiyar ba akwai dai abunda suke boye mata. *** *** *** Ya sauke wayar daidai lokacin da Ibrahim yai parking a harabar gidan. A hankali Zain yaja numfashi ya sauke tare da kai hannu zai bude motar. “Are you happy now?” “No” “Sad?” Ibrahim ya tambaya. “No, idan na yi farincikin Mama ta fito, Hameeda tana gidan yari, Dada Yalwa fa? Akwai shakuwa sosai a tsakaninsu, kuma ba zata taba yarda ba ni da laifi ba, wannan abun ma zai iya sanadiyar mutuwarta” “Amman Hameeda ta cancanci dukan wani hali da zata shigo, ni wallahi na yi farinciki da ta fadi gaskiya tun shari'ar bata je nisa ba, kuma bata wahalar da kowa ba, da ace gaskiya bata bayyana ba, da Hameeda zata tai ta kashe maka mata ne har illa Mashallahu” “Yeah she deserve it amman bana son ganin mutuwar Dada, i won't forgive myself, tunda ta kashe yar'uwarta zata iya kashe kowa ma, amman ina jin da an gama shari'ar nan zan bar kasar nan zan koma paris na zauna” “Hakan ma zai fi, amman ban ce ka zauna kai kadai ba, you should engage yourself with something kar kaje kai ta tunani wani abun ya faru da kai, ka yi applying a cikin hospital dinsu na san zasu dauke ka tun da kana da takardu masu kyau, ka zauna a can ko da na shekara hudu me ko biyar” “Hudu biyar? No sai dai yadda hali yai, bana son zama kasarnan kwata kwata kuma ko na dawo ba zan zauna a nan ba” Yana gama fadar hakan ya bude motar ya fita. [4/1, 1:53 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *54* Daga kotun suka nufi gidan Alhaji Salisu wato mahaifinshi, a nan suka ci suka sha shi da wani kanen Rufaida dan sauran tuni suka kama hanyar komawa Kaduna. A nan ma Hafsat ta ga gata ba a barinta ta zauna ita kadai saman kafafun wani ko wata daga cikin kanen Alhaji Habib, ta sha hotuna a wayar kanenta sai yabon mahaifiyarta suke dan yanzu ne suke kara tabbatar da kamar da ke tsakaninsu. Da yamma ya kama hanyar Kaduna tare da Barrister Hassana da Hafsat wace ke ta kuka wai ita ba zata je ba sai anje da Zat tana ganin kamar wani abu za su mata. Da magariba suka sauka Kaduna, daga airport din Barrister Hassana ta nufi Asibiti gurin mahaifiyarta, Alhaji Habib da Hafsat manga kuma suka nufo gida, Jamil kuma ya nufi gidansu wato family house din su Rufaida, cike da farinciki Alhaji Habib ya shigo gidansa tare da Hafsatu manga yana jin kamar a mafarki ne, yau ga shi ya yar da yai shakara da shekaru yana memanta, gudan jininsa yar Rufaida yar da ya kwallafawa rai tun kamin ta zo duniyar ma. Direbansa na farki mai gadin ya zo da gudu tana daga masa hannu alamar gaisuwa. “Barka da zuwa Alhaji” “Yauwa Barka Sulaiman, mun same ku lafiya” “Lafiya kalau, Alhaji ka yi baki tun dazu suke suna jiranka” “Su waye?” Ya tambaya yana kokarin fitowa daga cikin motar. “Wallahi ban sansu ba, amman dai suna tare da wata mata marar lafiya, da suka zo sunce nan ne gidan Alhaji Habib Salisu na ce musu ce shine suka ce ga matar da kake nema am samu” “Wacece ina suke?” Ta tambaya da karfi. “Suna Bq a can na sauke su” Sulaiman be ma gama rufe baki ba, Alhaji Habib ya saki hannun Hafsatu manga ya nufi BQ din, kamin ya isa har da hadawa da dan gudu, a balcony ya same su zaune maza uku daya daga cikinsu dattijo ne, suna ganinsa suka tashi tsaye domin kallon daya zaka masa kasan cewar shine mai gidan, tun daga yanayin shigarsa da kuma siffarsa wacce ke kara fito da ainahin zatinsa. “Alhaji ina wuni” Duk suka hada baki gurin gaisheshi shi kuma ya amsa cikin yanayin da ke nuna ya kagu ya ga matar da suka zo da ita. “Lafiya kalau, ina matar yake?” “Tana can daki” Da sauri ya hau barandar ya shiga daya daga cikin dakunan da ya hango bude. Rufaida ce kwance kamar mai bachi sai dai shigowarsa yasa ta tashi zaune da sauri tana masa kallon tsoro. Idonsa ne ya cika da kwalla, sai ya fara takawa a hankali yana dosar inda take dakakkar shaddar dake jikinsa na amsa ko wane motsi nasa. Hannunsa ya daga ya nunata kamar zai fadi sunanta sai kuma ya kasa bakinsa sai rawa yake, hannu ta daga sama ta dora saman kai ta fasa ihu sai yai saurin komawa baya yana kallonta hawaye na zuba a idonsa. Hafsat ce ta shigo tare da Sulaiman Mai gadin gidan. “Mama” Hafsatu manga ta fada, ta nufi inda take da sauri, ita ma tana ganinta ta bar ihun ta ware hannayenta ta rumgume tana ta shafa irin abun nan na rashin hankali tana duba lafiyar yarta. Hafsatu manga kam rawa kawai take tana kara rumgumeta kamkam. “Mama da baki nan aka kaini gurin yan sanda aka kama ni wai na kashe wata ni kuma ban kashe ta ba, mama kin san wannan Zat din ko to shine ya karbo ni daga gurinsa, shi yana da kirki yana dafa min indo, kuma ya fada min ke kika aiko wadannan mutane nan wai kina nan tafe ke ma, ashe da gaske ne ko? Kuma mama wai wacan Babana ne?” Ta nuna Alhaji Habib da ke aikin zubar da hawaye har yanzu, ita dai Rufaida bata komai sai juye juye kai alamar bata cikin hayyacinta, daman can Hafsatu manga tasan ba magana take ba, idan har tai magana sai idan tana jin yunwa ko kuma zata kira Hafsatu manga shine kawai take bude baki tai magana. “Mama su Inna Ladi sun mutu ko? Ko suna nan? Aa basa nan an kashe su ma, amman Mama ke ina kika tafi? Wani guri kika boye ko? Na sani ai” Ta fada tana dariya. Alhaji Habib kam kallonsu kawai yake cike da tausayawa, matarsa ta fita daga haayyacinta ta koma kamar ba ita ba, har wata hurhurar wahala tai. Ya dade a haka sannan ya nufi inda take ita kuma ta fara masa ihu, sai Hafsatu manga ta tashi tsaye tana tareta. “Aa karka zo mamata tsoron mutane take” Komawa yai gurim mutane da suka zo da ita a nan suka tsaya suna masa bayanin inda suka sameta a kauyen kalgo, sun kira numbar da aka bayar basu samu ba, sai ta Mai maigadinsa shi ya fada musu inda gidan yake har suka iso, sai kuma sukai rashin sa'a baya gari, daya daga cikinsu dan sanda nw wanda ya rakosu tun daga garin kalgo har zuwa Kaduna, anan suka bashi labarin sun sha wahala kamin su zo da ita, dan ihu take musu har suka iso, Allah yasa ma motar gidace dan motar dayansu ce wanda ya kasance direbane mai zuwa gari gari. Tarba mai kyau Alhaji Habib yai musu ya aiki daya daga cikin masu aikin gidansa suka sawo musu abinci mai kyau a hotel. Ita kuma aka nufi main house da ita, amman a part dinsa, Hafsat manga na rike da hannunta, tana taka kafarta a kofar falonsa da zimmar shiga sai ta rafke ta fadi a gurin jikinta sai karkarwa yake kamar mai jin sanye idanuwanta kuma na rufewa tana dantsar baki. Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un, shi Alhaji Habib ke ta furtawa shi da Sulaiman da kuma Jabiru (Direbansa) Hafsatu manga kuma ta shiga girgiza ta tana kuka. Sai a lokacin yan'uwanta suka fado masa sam ya manta ma da wayarsa dayar a kashe take sai yanzu, da sauri ya nufi motar da suka shigo ya dauki wayar ya kunna ya kirasu ya sanar musu. Ko minti goma aha biyar ba a yi ba sai gasu sun iso ciki har da mahaifiyarta. Kowannensu kuka yake ganin irin halin da take ciki, kanwarta ta dauke Hafsatu manga dake kuka ta rumgume kamar ta cinyeta. Alhaji Habib da hankalinsa ke a tashe ya ce “Ina ganin kamar akai ta asibiti kawai zai fi” “Aa ai ba ciwon asibiti bane, ko an kaita wani abun daban zasu mata, kara ma ai mata rubutu kuma ayi mata addu'a, wata kila abun ne yake kokarin karewa” Cewar Hajiya Shafa wato gwaggonta. “Nima dai haka na gani Allah ya saka miki Rufaida” Cewar Mahaifiyarta, sai Hajiya Shafa ta ce “Ku kaita ciki, ni zan koma nasa a rubuta mata bismillah dubu na kawo mata, ko minene zai bar jikinta kuma zata samu lafiya da yardar Allah” Tana gama fadar hakan ta nufi kofar fita a lokacin ana kiran sallah isha'i, Bata dawo gidan ba sai goma da rabi na dare, har lokacin suna zaune tare da ita suna ta mata fifita, Hafsatu manga kuma na jikin Farida tana bachi, sai faman sauke ajiyar zuciya take, Daker suka dago kanta suka dora mata rubutun sauran suka shafa mata a kai da fuska, a take ta fara kwana kamar wacce ta shekara goma ba tai bachi ba, har yadda take jan numfashin tana saukewa ana ji. *** *** *** Kamar kullum yau ma ta samu mahaifiyarta babu wani sauki, ciwon kan da take tana nan da shi, ga wani abu da take da ido da kuma baki kamar mai magana da wani, Hawayen da Hassana ta zubar yau yafi ko wane hawaye da ta saba zubarwa domin a yau ta fi kowa tausayin halin da mhaifiyarta take ciki, bata bukatar a sake tunatar da ita, amman tasan karshen maihaifiyarta ya zo tunda Hafsatu manga ta tako gidan, abinda bata sani ba har Rufaida ma tana can gidan ba Hafsatu manga kadai ba. Misalin tara da tabi Hussaina ta shigo dakin tare da mijinta da kuma yarinyar ta daya. A lokacin Hassana na zaune saman gadon da Hajiya Safiya take kwance. “Me kike a nan?” Dagowa Hassana tai ta kalleta tana hawaye sai ta kasa ce mata komai. “Naga ai burinki ya cika ai ko? Za ayi zama na karshe zaman da za a wanke Hafsat a yankewa Hameeda hukuncin kisa, kin yi winning na yi losing, ba shikenan ba? Ina ganin be kamata ki zauna a nan ki tsareta har sai kin ga mutuwarta ko haukanta ba, da ace Mama tana cikin koshi lafiya a yanzu da zata fada miki a duniyar bata da makiyi irinki, kuma sai ta fi kowa tsanarki” “Husaina kin kasa fahimta” Ta fada cikin kuka. “In fahimta? In fahimce cewar Kina son wata bare fiye da mahaifiyarki, ko kuma kina son kashe mahaifiyarki da hannunki, wace uwace kamar tawa zata raini ya kamar ke ta bata tarbiya da kulawa amman ta girma ta tsaya defending wata a kotu saboda ita tai nasara mahaifiyar kuma ta kwanta ciwo? ” “Babu, hakika babu yar da ta kai kamar ni wacce ke son Mahaifiyarta ta samu rahamar Allah da gafararsa, Hussaina kin san irin azabar da aka tanadawar mace da ta mutu mijinta na fushi da ita? Duniya tana mata mummunar shaida? Kuma ta cutarta kishiryarta da yar kishiryar saboda wani bukatu nata ka kanta? Kin san Zafin wutar Allah da azabarsa anya kin yadda Allah baya yafe laifin wani kan wani? Abunda ya faru da Mama darasi ne a garemu da kowa, idan amman Allah be kamata duniya ba zai kamata ranar da babu mai iya daga ido ya kalleta balle har ya nema mata yafiya, ita kadai ta san halim da take ciki a yanzu, ita kadai ta san abunda take ji saboda abunda ta aikata, da ace tana cikin hankalinta a yanzu, da yafiyar Rufaida da Hafsat zata nema, kuma Allah ba zai yafe mata ba har sai idan su suka yafe mata” Hussaina ta durgushe a gurin ta fashe da kuka. “Bana son wani abu ya samu Mama, bana son ta tafi ta barmu, miyasa kika aikata Mama? Wayyo Allah Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un, na shiga uku ni Husaina ban jidadin ganin wannan bakar ranar ba... ” Kuka take sosai tana fadin haka, mijinta na yarta na lallasarta, Hassana ma kuka take daga can inda take zaune. *** *** *** *Washe gari...* A hankali take takowa hannayenta sanye da handcuffs, jikinta kuma sanye da kayan tufafin an gidan yari, fuskarta ba yabo ba fallasa, sai dai kana ganin idonta kasan ta sha kuka. Yar gandireba na bayan har suka iso harabar da ake ganawa da mutane, hango Anty Ummi da Zain yasa ta tsaya kamar ba zata zo ba, sai kuma ta tako a hankali ta karaso kusa da su, sai yar gandireban ta saka makulli ta bude mata handcuff din. “Minti goma sha biyar” Ta fada mata sannan ta juya ta koma can ciki inda ta fito. Tsaye tai tana kallon daidaikun mutane dake gurin dan bata son sauke idonta gurin Anty Ummi ko Zain, ganin hakan yasa Anty Ummi ta ce “Zauna Hameeda” “Na zauna kiji dadin kallona ko? Na san kin zo ne ki fada min kinji dadin abunda ya faru” Anty Ummi tayi murmushi irin murmushin da ke bayyana damuwar da ke cikin ranta. “Kin rasa abubuwa da yawa Hameeda, Mahaifinki, mahaifiyarki, yayarki, da kuma Zain, me zai sa nai farinciki da abunda ya sameki? Kin yi abunda ya dace da kika fadi gaskiya amman tun jiya kukan kama ki na kai, tsakanin ke da Farhat ban san waya fi wani rashin dacen rayuwa ba, ita ma ta tashi kamar ke, ba uba, sai uwa kawai, ta zauna a hannun yyarta irin zaman da bata jidadinsa ba, ta auri Zain ta hadu da kalubale daga gareki, har kika kasheta, tsakanin ke da ita sai na rasa wa zan tausayawa” Hameeda ta fashe da kuka tana jin rashin kyautawa a abunda ta aikata, zaunawa tai yana fadin. “Na san Dada da Mai Martaba ba za su taba yafe min ba” “Har yanzu Dada bata san abunda ya faru ba, shiyasa na zo nan zan baki ku gaisa, na fada mata cewar kin tafi Kaduna gurin Yayan Mahifiyarki har zuwa lokacin da za a gama shari'ar, ga wayar ki nan dazun na karbeta gurin Ikram dan makullin dakinki yana hannunta” Zain ya mika mata wayar, sai ta karba ta kunna ta cire password ta kira numbar Dada, ringing biyu ta dauka. “Assalamu Alaikum Hameeda” “Na'am Dada kina lafiya?” “Lafiya kalau, Zain ya fada min wai kin tafi kaduna gurin Alhaji Aminu har a gama case din da gaske ne” “Ee Dada ki kwantar da hankalinki ina nan lafiya kalau sai idan an gama case din zan dawo” “Na yi ta kiran wayarki ban samu ba” “Ee inda na ke ba network kowa sai yace min yana kirana bata shiga,amman ni idan na kira ina samu ai” “Amman dai zaki zo ki ganni ko?” Ta kalli Zain sai ya gyada mata kai alamar ee. “Ee zan zo idan an kwana biyu, Dada ina son ki sosai, ina kewarki ki kula da kanki dan Allah” “Inshallah nima na yi kewarki Hameeda, dama kin yi zaman ki a nan zan fi jidadi” Dada ta fada cikin kukan. Sai Hameeda ma ta amsa cikin kukan. “Na fi son nan Dada, sai anjima” Tana sauke wayar Zain ya mika mata hannu ta bashi wayar, sai ya kashe ya mike tsaye, itama ta mike tsaye tana kiran sunansa. “Zain I'm pregnant, ina son na fada maka tuntuni amman ban samu dama ba, ina ganin ya kamata na fada maka a yanzu...” Ta fada kai tsaye, ba shiri ya juyo ya kalleta, Anty Ummi ma ta mike tsaye tana kallon Zain... *** *** *** Tun da aka dora mata rubutun ta sha take ta aikin bachi har garin Allah ya waye, bata farka ba ko matsawa ba tai ba daga inda take, sai guraren karfe goma sha daya na safe sannan ta fara motsawa a lokacin har sun fara yanke shawarar kai ta asibiti dan sun fara tsorata, daman Hajiya Shafa ce take tausarsu itama izuwa yanzu ta fara tsorata da lamarin. Babu kalar addu'ar da ba a mata ba, har mai ruqya an kira da safen nan yai mata amman shiru. Kafafunta ta fara motsawa sannan ta tashi zaune dafe da kai tana ta maimaita. “Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un” Kan take ji kamar zai fashe mata, tana jin hayaniyar da suke kamar a mafarki, dan can kasa kasa take jin muryaoyinsu, daker ta bude idonta shima saboda kiran sunanta da Alhaji Habib ke ta yi ne dan ya karara ta bude idonta he just can't believe ita ce din. Tana budewa sai ta ga komai na juya mata tai saurin maidawa ta rufe. “Mama mama mama ke” Can sama sama take jin kiran bata da tabbacin da ita ake, amman tana son ta ga wake kiran da kuma wainar da ake toyawa take jin hayaniya sama sama. Daurewa tai ta bude idon tana kallon kowa dake falon hannunta saman kanta ta dafeshi gam dan tana jin kamar zai bare ne ya rabu gida biyu. Da dai dai ta bi kowa da kallo, tana son tantance fuskokinsu, bata gane au waye ba, amman tana jin a kwakwalwarta kamar ta sansu. Al-hamdulillah shine abunda kowa ke fada farinciki har zuci, wasu har da hawayensu. “Yanzu kam ya kamata a kaita asibiti, dan su zasu iya bata kulawa har ta koma normal” Cewar Farida. “Rufaida...?” Alhaji Habib ya kira sunanta. “Na'am” Sai ta amsa ba tare da ta sake dago kanta ba. Hafsatu manga ta cika da tsakanin mamaki har da sakin baki tana fadin. “Laaaa Mama ta yi magana laaaa, Rufaida...” Ta kirata da sunan da mahaifinta ya kirata ta amsa, ta nufota tana leken fuskarta tare da kara kiran ainahin sunanta. “Rufaida.. Ke Rufaida...” [4/2, 10:39 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *55* “Wato duk halin da kika shiga yanzu be wadatar da ke ki fahimce cewar Allah daya ne ba? Baki shiga hankali ba ko? Daman na san wannan din ma plan dinki ne, dan ba za ki taba bada kanki a take ba, And lemme tell you something indai dan a fitar da ke nan ne kika shirya wannan ba zaki taba fita ba, ki daina ganin cewar ni ne wanda ya fara zuwa ganinki ki dauka ko ina tausayinki ne, no duk abunda na ke saboda Dada na ke yinsa ya kamata ki sa wannan” Ya karasa a fusace yana nunata da yatsansa. Tun da ya soma maganar Hawaye ke zubar mata har ya kai aya. Dan murmushi tai irin murmushin nan da yafi kuka ciwo, ta saka dayan hannunta tana murza yatsunta. A hankali ta zauna tana wani jan numfashi. “Son ka be min amfanin ba Zain, yan'uwantakarmu bata amfana mana komai ba sai bakinciki da nadama, ban cin ci komai a rayuwarka ba sai kuka da bacin rai, lallai sai a yau na tabbatar da baka kaunata kuma ba zaka taba kaunata ba, amman ni har gobe ina kaunarka na kuma ba zan daina kaunarka ba har ranar da numfashi zai fita daga jikina, na tsammaci zaka tausaya min ne, ko kuma ka nuna min wata kulawa wacce zata bani damar zama na kai ko da na dan lokaci ne, amman sai ka rufeni da fada kana fada min maganganun da suka fi madaci daci a bakina” “Amman da gaske kina da cikin?” Anty Ummi ta tambaya, sai ta kalleta ta girgiza mata kai. “Babu...” Sai ta sake Mikewa tsaye a karo na biyu ta kalli Zain ta dauke kanta ta nufi hanyar da ta fito. Sai da ta shige sannan Anty Ummi ta kalli Zain ta ce “Abunda kai ma yarinyar nan be kamata ba Zain, maybe da gaske tana da cikin” “Karya take Anty bata da komai, kawai tana tunanin yadda zata bar gidan yarin nan ne, da ace tana da shi da gaske da ta tona tun kamin komai ya faru, ina tunanin wayar nan da tai da Dada da kuma kwana daya da tai a nan ya saka mata son ta zauna gida ne, so dat idan ta koma ai Dada ba zata barta ta dawo ba, and if har na kasance ta mi zai sa na yi raping Farhat at the same day? Tell me” “Maybe you're not satisfied...” “Oh Anty please stop talking rubbish, how could that happen? Idan ma gaskiya take za'a gani ai” Yana fadar hakan ya saki rikon da yai ma kansa ya nufi kofar fita. Anty Ummi ta rufe masa baya zuciyarta cike da tausayin Hameeda. *** *** *** Haka ka kwana aka wuni aka sake kwana likito suna bata kulawa ta musamman, domin tana bukatar cikakken hutu. All those days da tai a asibiti da Memory din haukar da tai ya zama mata kamar mafarki. Every hour sai ta shafa cikinta kawai tana mamakin yadda akai bata da ciki a yanzu, ita dai ta san kamin tai bachi tana da ciki bata san awa nawa tai tana bachin ba amman dai tana jin ta dade fiye da kima tana bachin, wata kila ma hakan na alaka da kawo ta da akai asibiti, tana son ganin wanda zai amsa mata tambayoyinta amman bata samu ba, domin likitan kawai take gani ba a barin kowa ya shiga inda take. Amman yau ta jidadi sosai da likitan ya fada mata cewar jikinta yayi kyau, kuma zata fara samum visitors. Hakan yasa ta tattaura hankalinta gaba daya ta maida gurin kofa idonta cike da son ganin wanda zai fara shigowa. Lokacin da akai knocked din kofar gabanta ya fadi soaai with no reason. Alhaji Habib ne ya fara shigowa rike da hannun Hafsatu manga sai kuma mahaifiyarta da kanenta, and Hassana na tare da su. Ko wanne fuskarsa dauke da murmushi, Hafsatu manga ta yi saurin sakin hannun Mahaifinta ta nufi inda Mamanta take. “Mama mama kin ji sauki yanzu” Hannu Rufaida ta kai ta shafa kanta ba dan ta fahimci wacece ita ba, sai dai ganin yadda ta jingina da ita tana tambayarta. Alhaji Habib ya zauna a kusa da ita tana kallonta with uncountable love idonsa cike da kwalla, kallonsa tai kamin ta bi kowa da kallo. Kowa ya canja a yadda ta sanshi shi din ba dan tasan mijinta sosai da sosai ba zata iya cewa ba shi ba ne, domin yayi looking old not yadda yake a da. Abunda bata sani ba ita kanta ta canja, sai dai bata iya gane hakan domin bata ga kanta ba har yanzu. Murmushinta sai ya soma komawa hawaye, har yanzu mutane take kallo tana ta son tantancewa amman ta kasa. “Ko dai mafarki nake yi ne? Komai ya canja Habib, Mama and duka yan'uwana, ban san wanda zai amsa min tambayata ba, amman ina ganin kamar ba ku ba, ina ciki?” Ta tambaya tana shafa cikin hawaye na bin fuskarta. Alhaji Habib ya yi dariya irin ta su ta manya kana ya ce. “Ga cikin nan, wannan yar kika haifa” Ta yi saurin sake kallon Hafsatu manga tare da dago kanta yadda zata kara tantancewa. “Taya? Me ya same ni? Ko dai mutuwa nai na dawo? Ban gane komai ba, na kasa fahimta” Ta rike kanta tana kuka. Alhaji Habib ya rika matarsa yana rarashinta, yana hawaye shi ma dan be san ta inda zai fara bata labari ba. Dagowa tai daga jikinsa tana kallon Hafsatu manga wacce fuskarta ke shimfide kan tata kamar an tsaga kara. “Ku fada mutuwa nai na dawo ko kuma suma nai na tsawon lokaci, domin ni ma kaina ina jin kamar akwai abunda ya faru da ni” Hassana ta rike hannunta ta risina tana kallonta da murmushi. “Abubuwa da yawa sun faru Mamana, a ciki akwai haihuwar Hafsat, girma na, tsufan Baba, dogon bachinki mai kama da suma da ma wasu abubuwan da dama” Ta mika hannu ta riko hannun Hafsatu manga ta hada da na Rufaida. “Wannan yarki ce, yar da kika haifa da kanki, ba zan iya fadin yadda kika haife ta ba, amman zan iya fada miki cewar a lokacin da kika haifeta baki cikin hayyacinki, shiyasa ba ki san kin haifeta ba, ke kanki ba zaki iya tuna daga yaushe ne hankalinki ya gushe ba, amman na san baki manta da mahaifiyata ba, kuma abokiyar zamanki wacce ita ce silar komai, sai dai duk da haka mahaifina da yan'uwanki basu watsar dake ba, sun yi ta shalarki har aka gano ki aka kawo ki nan dan ki hutu...” “Wacece ke?” Ta tambaya tana kokarin samun natsuwa. “Sunana Hassana, ina da yar'uwa Husaina ni da ita duka yyan mutum daya ne, Alhaji Habib da kuma Safiya” Kokarin tuna sunan take yayi mata kama da sunan da ta sani. Oh yes sunan Kishiryarta ne ta tuna, one after the other abubuwa suke dan dawo mata har tana banbance abubuwan da suka nan. Alhaji Habib ne ya labarta mata komai abunda ya faru wanda Hassana da Farida suke ganin kamar yayi sauri domin be kamata a fada mata haka a yanzu ba, shi ma dai ba shi da zabi ne saboda ta matsa ta san komai din dan fitar da kanta a cikin hudu. Ta zubar da hawaye sosai kamar yadda kowa da ke gurin ya zubar ban da Hafsatu manga, Hannu biyu ta sa ta dauki yarta ta dorata saman jikinta ta rumgume ta tana kuka. A iya abunda zata iya tunawa a zamantakewar da suka yi da Safiya bata taba cutarta ba ko da dai rana amman mi yasa tai mata haka? Hafsatu manga ta dago kai tana kallonta. “Mama ashe kina magana na jidadi” Kalmar Mama data kirata da shi taji sunan har cikin ranta. “Hafsat Hafsat yata” Ta furta ciki kuka sannan ta kara kankameta kirjinta.... The following day aka sallameta daga asibitin tare da maganinta da kuma sharudan yadda za a kula da ita, ba a gidan Alhaji Habib ta sauka, a family house dinsu ta sauka, tana samun kulawa ta ko'ina daga yan'uwanta da kuma mahaifiyarta, Alhaji Habib kam kusan kullum yana gida, yana jin kamar ya cinye ta ita kuma tana jin kamar ta mayar da Hafsatu manga a ciki ta sake haifota. A ranar data kwana shida a gidan Alhaji Habib ke labarta mata case din su Hafsatu manga, daman be labarta mata ba ne a wacan lokacin domin yana gudun abun yayi mata yawa, ta yi mamaki, al'ajab jimama na abunda ya faru, but she is happy jin cewar Hassana ce ta tsaya mata a kotun har akai nasara. A dayan bangaren kuma zuciyarta ta kwadaitun da son ganin Zain dan Hafsatu manga ta bata labarinshi ya fi a kirga, ba shi ba, ba Inna Ladi ba tana ta bata labarinsu da kuma zamantakewar da suka amman ita bata tuna komai ba. *** *** *** Tana yawan magana da kanta irin maganar nan da kai kanka kasan da aljanun da take gani take, ba tai ihu ba, sai dai wani lokacin tana yawan yin dariya har sai am mata allurar kwana, and each and every day Alhaji Habib na zuwa duba ta for sake of Hassana. Sai dai ita bata sanin ya zo ko be zo ba, tun asibiti na iya daukar lamarin har suka bada shawarar fita da ita waje dan a duba kwakwalwarta. Sai dai su sunsan ba matsalar asibitin ba ce, dan haka aka dawo da ita gida wato gidan mahaifan ta wanda babu kowa a ciki a yanzu sai wani kanenta daya dauki bangare faya ya zauna shi da matarsa, iyayen sun rasu su kuma kowa ya kama gabansa, yana ta iyalansa, a nan aka koma ana yin mata na hausa wai ko Allah zai sa ta samu sauki. Hassana da Husaina su suka fi kowa zama abun tausayi saboda halin rayuwar da suka shiga saboda halin da Mahaifiyarsu take ciki. Kusan ko da yaushe suna hanyar Kaduna. First weekend suna zaune gaban mahaifiyarsu, sun saka ta a gaba sai kallonta suke, ba son a kai gidan mahaukata saboda ba ta buge buge bata wani abu da zai illata mutum sai dai kallo daya zaka mata ka gane cewar bata da hankali, wani abun da ya kara bata musu rai kuma yake basu mamaki yadda yan'uwanta suka dauki ido suka dora musu kamar su din basa da alaka da ita duba ma ko yaushe suke zuwa ba. Wata kila suna ganin kamar Yayanta sun wadatar da ita ne ko kuma wani abun oho, Hajiya Halira ce kawai take ta dawainiya da ita. Suna cikin tattauna maganar ne ita da Husaina, sai ga sallamar Babansu which make them proud and Happy not just Hassana even Husaina tana farinciki da yadda yake yawan zuwa dubata. Duk welcoming dinsa suka kai Husaina ta kawo musu ruwa. Bayan ya sha ruwan ya aje ya kalli Hajiya Safiya wacce ke ta aikin bachi ya ce “Ya mai jikin?” “Al-hamdulillah Baba” Hassana ta amsa. Shiru yai na dan lokaci sannan ya ce. “Ina ganin ya kamata ko india ne a fitar da ita, itama tana da hakki akaina kamar yadda Rufaida ta fada min, be kamata a barta nan ita kadai tana ta fama ba” “Amman ina ganin kamar fitar ba zai haifar da da mai ido ba ne shiyasa ban taba unkurin yin haka ba, munata addu'a dai kuma mun saka ayi inda rabon ta warke zata warke” Hassana ta fada idonta cike da kwalla. “Amman dan Allah ka roka mana yafiyar Rufaida ko Allah zai sa abun ya saukaka mata” “Ya kamata mu bata dan lokaci Hassana idan aka kai wani lokacin ita da kanta zata iya yafe mata, be kamat mu cilasta mata ba” “Haka ne, Mama. Allah ya baki lafiya” Sai duk suka amsa da amin. *** *** *** Kusan every day sai wani yaje gurin Hameeda ya bata wayarta ta kira Dada Yalwa sun yi wata, da zimmar tana kaduna ita kuma tana Gusau. Sai dai hakan be hana Dada tambayar yaushe zata dawo ba, da kuma kewarta saboda tana tunanin kamar can din ma bata cikin dadin rai. Babu wanda matsalar bata dame shi ba, daga Mai Martaba har matansa da kuma yayansa, ban da Zain wanda tunanin halin da Dada zata kasancewa ne kawai ke damunshi, and ya maida hankalinsa gurin barin kasar dan baya son bayan shari'ar yaga yadda Dada zata shiga damuwa domin dole yau da gobe wata rana ta zata sani. A ranar da ta kama 6 ga watan bakwai kowa yaji dabam a masarautar Rishim domin ita ce rana ta karshe da za'a yanke hukunci, Even Hameeda feel so helpless, disgrace, she even felt like ta mutu kamin a isa kotun, ta raina kanta tun daga ranar da ta kwana daya a prison, har yanzu bata jin dana sanin fadin gaskiyar da tai sai dai tana bakinciki abunda ta aikata akan mutumen da be taba samu guri a zuciyarta ya kalleta da so ba ko sau daya... _____________________________ I feel her pain 😭💔 [4/3, 11:16 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *56* Kotun ta yi tsit kamar babu kowa a ciki, duk da kasancewar kotu ta fi ko yaushe cika, amman kowa ya natsu yana sauraren hukuncin da alkalin ke yankewa. Kowa yana nan daga familyn su Zain and duk wanda yake da alaka da Hameeda, Anty Ummi Rufaida, Alhaji Habib, even Alhaji Salisu was there with his family. Sai da alkalin ya karbi result din da aka bada na binciken kwakwalwarta da aka yi ya nuna cewar lafiya kalau take sannan ya soma karanto hujjojinsa, da dokar da aka tanadar da wanda ya aikata kisan kai da gangan, sannan ya yankewa Hameeda hukuncin zama gidan kaso har karshen rayuwarta, ya sassauta mata hukuncin ne duba da yadda ta fallasa kanta kai tsaye ba tare da ta wahalar da shari'a ba. Sai ta Alkali ya karatowa Fauziya da Abida laifin da ake tuhumarsu da shi suka amsa da cewar sun aikata har da ma da karin bayani akai sannan ya yanke musu hukuncin shakara ashirin da biyar a gidan kaso, bisa ga samunsu da sa hannu gurin taimakon Hameeda ga abunda ta aikata. Sannan kotu ta wanke Hafsatu manga bisa zargin da ake mata. Sai kuma alkali ya basu damar daukaka kara idan har basu yarda da hukuncin da aka yanke musu ba. Tsakanin Abida da Fauziya da kuma Hameeda sai aka rasa waya fi kukan nadama da bakincin hukuncin da aka yanke mata. Yan'uwan Zain ma kuka suke, kamar yadda yan'uwan Fauziya ma musu, Alhaji Habib da Rufaida and their families ne kawai suke farinciki sai kuma Zain and Ibrahim. Ikram kamar zata hadiye zuciya ta mutu saboda bakinciki, a tare suka tashi da Hameeda duk da kasancewar shakuwarsu da ita bata kai shakuwarsu da Zain ba amman an zama abu daya kuma tana jin kamar akwai rashin adalci ko rashin dacewa a abunda Zain yai mata tun farko. Kusan su suka rude kotun da kuka sai kuma yan'uwan Fauziya da ke ta tsalle suna faduwa kasa musamman mahaifiyarta. A harabar kotun Rufaida ta gaisa da Zain, he is happy yau dai ya ga maman Manga kuma cikin hankalinta, Ibrahim sai mamakin yadda kamarsu tai yawa ita da Hafsatu manga yake, Hafsatu manga kam baki har kunne ta sha kyau abunta, duk wani magana da ake tana rike da hannun Zain sai tsale take ita a gurinta kamar yau biki ake domin ganin Zain ga kuma mahaifiyarta ya faranta mata rai sosai. Hannunta Zain ya saki ya nufi gurin motarsa sai ta biyoshi tana saka hannun a baki. “Ina zaka je?” Juyowa yai ya kalleta sai ya rina daidai tsawonta ya cire mata hannun daga cikin baki yana murmushi. “Mama, I'm so happy for you, kin samu iyayenki both, an wankeki a kotu, yanzu hankali zai kwanta na san zaki samu kulawa ta musamman, hakan zai ba ni damar natsuwa a duk inda zan samu kaina, zan tafi wani gurin nesa da nan, maybe a can zan mutu, maybe na dawo, maybe kamin na dawo kin girma kin ginawa kanki wata rayuwar mai kyau, wani babun rayuwa ya bude miki sabon fegi...” Ya fada with tear in his eyes. Ita kanta bata fahimci inda zancen sa ya dosa ba, amman ta ji babu dadi. “Ina zaka je?” “Wata kasa can, inda babu ke babu Hameeda babu kowa sai na bude sabon rayuwa na manta da komai, maybe na sake farincikin kamin na mutu amman Maybe” “Miyasa zaka tafi?” Hi spend his time tell her the reason kamar wata babba wacce zata fahimta. “Kin ga idan na je can, zan manta da komai, kuma bana son na zauna nan Dada tana ganin laifina, bana son wani abun ya sameta tana kusa, and zamana a nan zai rika tunawa kowa abunda ya faru ne, wanda ni ma ba zan so hakan ba” “To Yaushe zaka dawo?” “Ban sani ba, maybe sai nan 20 years” “Minene titi yis din minene shi?” Yayi murmushi. Sai ya daga kansa yana kallon Ibrahim wanda ya karaso gurin. “Kamar tayi karama da irin wadanna maganganun sun girmi kunnenta ai” “Ina fada mata ne kawai as good bye, ka san ita ma kamar ya take a gareni” Mikewa tsaye Zain yai yana fadar hakan. Ita kuma sai kallonsa take jin zai yi tafiya duk ya daga mata hankali. “To zan bi ka ka ji?” “Na ji je gurin Mamanki idan na tashi tafiya zan kiraki” “Ka yi alkawari?” Sai yai murmushi ya shafa kanta. Sai ta saki hannunsa ta juya a guje ta nufi gurin iyayenta. A gaba daya masarautar Rishim babu wanda be yi kukan hukuncin da aka yankewa Hameeda ba, ciki kuwa har da masu ganin hakan ya ne ya dace, amman sai da suka tausaya mata, wadanda basa su kukan fili ba suka yi na zuciyata. Sai dai duk wannan wainar da ake toyawa Dada Yalwa bata sani ba. Domin tana can part dinta bata fito ba kuma Mai Martaba be bar kowa ya shiga can ba balle har ta ji. *** *** *** Kwanan Rufaida daya a Gusau gidan Anty Ummi ita da Hafsatu manga, irin kulawar da Anty Ummi ta rika basu har ta wuce misali, kamar za ta cinye ta ita da Hafsatu manga haka ta rika ji, a dayan bangaren kuma tana ta jijina lamarin Ubangiji ganin yadda yau Hafsatu manga ta juya ta koma yar dan uwanta. The following day suka koma Kaduna, a airport suka rabu ita ta dawo family house dinsu, shi kuma ya nufi gidansa tare da su Hassana da kuma Husaina. Sai da suka huta sannan suka wuce gurin da mahaifiyarsu take bayan sun yanke shawarar daukar mahaifyarsu su koma da ita can Gusau a tare da su domin bata kyakkyawar kulawa duba da yanayinta su ma kuma suna da yaya da miji, wanda idan suka matsa da yawan zuwa da dawowa shi ma aiki ne a gurinsu. Ba dan Alhaji Habib ya so ba ya amince sai dan babu yadda zai yi domin ya fada cewar zai samu mai kula da ita, sai suka nuna masa duk wata mai da ita ba zata kai su ba. Bayan fitarsu ne, ya shige dakinsa ya kishingida da zimmar yin bachi kamin ai yi la'asar sai ga kiran Rufaida ya shigo wayarsa ta number yar'uwarta, cike da farinciki da jindadi ya dauka ya kara a kunnesa tare da sallama, itama sallamar ta mayar masa sannan ta dora da ya gajiya. “Gajiya ta bi lafiya, Ina Hafsat” “Tana can tsakar gida tare da yara, ina Yan biyu?” “Sun fita sun tafi wajen mahaifiyarsu, na ji suna maganar dauke ta su maida ita gusau a tare da su” “Saboda me?” “Wai ba za su iya bata kulawa yadda ya kamata ba idan basa tare da ita” “Amman kai ka yarda?” “To ya zan yi, nima ai ba zan iya kula da ita yadda ya dace ba” “Amman ai matarka ce, hakkinka ne ka nema mata lafiya kuma hakkinka ne ka kula da ita” Ajiyar zuciya ya sauke a hankali sannan ya ce. “Wato wani abun da baki sani ba, Rufaida matar ta fita daga raina tun daga ranar tana gaskiyar komai, sam bana son zamanta a kusa da ni, bana son rabuwa da ita ne saboda yayanta..” “Ba zan cilas maka zama da ita ba, amman komai zaka yi ka yi dan Allah shi kadai, karka zalinci mutum bar shi ya zalince ka, komai daren dadewa sai kaga sakayya, kuma dukan abunda mutum ya shuka, shi zai girba, duniyarsa da lahira, Wallahi har ga Allah na yafewa Safiya abunda tai min, saboda nima ina son Allah ya saka ni cikin bayinsa na gari wadanda yake son, yake yi ma yafiya, abunda ya same ni kaddara ce daga Ubangijina daman can an rubuta hakan zai same ni dan haka ban isa na tsallake ba, ko da ita ko babu ita dole sai hakan ya sameni saboda an rubuta haka a agareni, bana son bakincikin abunda ta yi min ya shafi zamantakewar aurenku ko kuma ya hanaka yi mata adalci, zaka kone kanke kawai idan kai haka zaka tashi da baren jiki a ranar da ba zan iya amfana maka komai ba, wanda ya bika da shari sai ka bishi da alheri, abunda zaka aikata a yanzu shi zai raba kan yayanka ko kuma ya hada kansu shiyasa na ke son ka ji tsoron Allah a kan dukan abunda zaka yi” “Ban tsammaci yafiyar ki da wuri ba haka Rufaida, ban sammaci za ki iya bude baki ki yi magana mai dadi da ma'ana akan Safiya ba, Wallahi kin sa jikina yayi sanyi sosai” “Ba kowace kishiyace macuciya ba, ba ko wace abokiyar zama ce mai cutarwa ba, ban zauna da Safiya dan na cutarta da ita ba, ko kuma na yi amfani da kai ka cutar da ita, idana babu duniya akwai lahira inda Allah zai yi hukuncin akan zamankewarmu, wannan kawai na sakawa zuciyata kuma na zauna ita lafiya, ba dan bana kishin ba, sai dan na san akan abunda zan yi kishin kuma ina iya dawainiya da kishi na, ba shi ya ke dawainiya da ni ba” “Allah ya miki albarka, har ko yaushe ina godiya ga Allah da ya bani mace irinki duk kuwa da kasancewar baki tare da ni” “Amin izininka na ke nema ina son gobe idan Allah ya kai mu zanje a duba ta tare da yan gidanmu” “Na miki, Allah ya miki albarka.. ” Sai ta amsa da Amin suka taba yar fira kadan sannan suka yi sallama. Kamar yadda ta fada masa washe gari taje ita da wasu yan'uwanta masu sanyi hali suka duba ta, sauran kan sai ma zaginta da suke wai a ce duk abunda Kishiya tai mata amman zata zari kafa taje dubata dan bata da zuciya, Ummu Faisak wacce ta kasance kanwarta dake binta, sai masifa take ita da babbar yayarsu Asma'u Badamasi. Bata je mata hakan nan ba, sai da tai mata yar siyayyah, even Husaina da yar'uwarta sun yi mamakin ganinta, sai dai hakan be hanasu suna mata farinciki da jindadin zuwan nata ba, ransu be kara fari ba har sai da suka ji da bakinta ta furta cewar itata yafe duk abunda tai mata har ma da yi mata addu'ar samun lafiya. A week later, ta tare a gidan mijinta wato Alhaji Habib, Gidan sama ne mai kyau da daukar hankali ,kallo daya za masa ka san cewa an narka duniya a gidan, komai na gidan sabon ne, gida ne mai part biyu, dayan mata dayan kuma na shi, ko ina an kawatashi da kayan alatu dana more rayuwa. A part dinta aka warewa Hafsatu manga daki daya daga cikin dakunan da suke jera da dakinta, sosai aka kawata kayan dakin da gadon yara da kuma kayan ado suma na raya sai fenti pink da yar drawer wacce aka cika da littafai, an kawata gadon da teddys, kai ka rantse da Allah ka ce yar turawa ce da dakin ba Hafsatu manga ba. *** *** *** Within a week Zain ya shirya komai na sa na tafiya, dan shi kam ya kago ya bar kasar ma, duk wanda ya kamata ya san da tafiyarsa ya sanar da shi ciki kuwa har da Dada Yalwa wacce ke kwana tambayar Hameeda, babu yadda Anty Ummi batai ba akan ta hana shi zuwan amman sam ya ki yarda saboda yana jin garin ya isheshi gaba daya. Mai Martaba ma give him a total support na barin kasar, duk kuwa da kasancewar baya son yai nisa da shi amman yasan dansa yana bukatar hutu da kwanciyar hankali a yanzu. Be fadawa kowa shekarun da zai yi a can ba, in ba Ibrahim babu wanda yasan iya yaushe zai kai a can. A lokacin da ya zo yi ma Dada Yalwa sallama ta yi ta masa kuka tana fadar cewar shi ma tafiya zai yi ya barta kamar yadda Hameeda tai, sai da ya ji kamar ya fada mata gaskiya akan maganar Hameeda sai kuma wata zuciyar ta hana shi. Ce mata yai wata biyar kawai zai yi ya dawo shi kuma saboda ta natsa masa ta tambayar idan ya tafi ba zai dawo da wuri ba, sai yai mata alkwarin zai rika zuwa every end of the month ya dubata ita da Mai Martaba. Ranar Assabar ya bar kasar, Ibrahim and Anty Ummi da Hajiya Hadiza and Waziri (Kanen Mai Martaba) are the only people da suka raka shi airport saboda ya fadawa Mai Martaba cewar bayan son rakiya da yawa, iya kar kokarin da Anty Ummi zata yi na hana kanta kuka akan tafiyar Zain sai ta kasa, tana jin ya tafi a yanzu ya yi nisa da ita bayan kuma irin sabon da suka yi, even her kids that are along with her sai da suka yi kuka. Shi kuma be kulasu ba, yana ta aikin lasa waya kamar be damu ba, har Ibrahim da ke ta sharar kwalla lokaci zuwa lokacin be kalli inda yake ba, shi kansa Zain din kuka yake yi kukan rabuwa da su, da kuma kuka kewarsu da zai yi idan yaje can, yaushe zai saba da can din for how long zai manta da komai, anya komai zai gyaru har ya sake samun farinciki? He don't think so, sai dai kukan da yake ba a fili yake yinsa ba a zuciyarsa yake yinsa, duk wani bacin rai da dacin rabuwa yana nan kwance a kasan zuciyarsa. Sai da suka daina hango jirginsa sannan suka kama hanyar gida. A iya dauriya Zain ya yi amman hakan be hana shi sharar shawaye ba a lokacin da ya kadaice cikin girjin. *** *** *** Dan lokacin da tai spending a prison she learn a lot of lessons, ta tabbatar da ita din ba kowa ba ce, duk wani gata da isa da sarauta da take bugun gaba da shi a yau babu shi, kuma be amfaneta da komai ba, domin Mai Martaba be sa an daga shari'ar ba, ganin be yi din ba ya hana duk wani mai kuzari ya yunkuro ya yi. At first ta dauka ta ci banxa na kashe yar'uwarta da tai tana ganin kamar asirinta ba zai tonu ba, and ta kashe Farhat tana ganin kamar zata iya sai gashi hakkin RAI BIYU ya hana ta sukuni da zama lafiya, balle kuma kwanciyar hankali, duk da kasancewarta bata jindadin zaman da take a nan amman hakan ya fi mata fiye da zamanta a gidan hakkin kisa na binta. Babu ranar da bata kuka, babu ranar da bata jin kamar tai tsuntsuwa ta gudu daga gurin amman babu dama, she just wish cikin da ta fadawa Zain da gaske ne ba na testing son shi a gareta ba, da wata kila zai fitar da ita daga gurin idan ma be yi ba dole Mai Martaba zai yi. Amman komai ya chabe mata bata da wata mafita a yanzu.. FARHAT PARENTS. Sun jidadi sosai lokacin da Anty Ummi da Dpo Auwal suke fada musu irin hukuncin da aka yankewa Hameeda, hakkin Farhat da suka bi ya faranta ran mahaifiyarta sosai. Daman sun samu labari tun ranar da aka yanke hukunci domin akwai yan'uwanta da suke can wadanda suke halararta zaman kotun. Sai a lokacin ne Anty Ummi ta fadawa Mahifiyarta dalilin kin auren Ya Bashir da tai da kuma dalilin mutuwar Anty Rukaiya, Inna ta yi kuka sosai tare da nadamar da bata da amfani, a dayan bangaren kuma tana ganin laifin Farhat na kin fada mata gaskiya tun farko. Auwal dai tun sha biyu ya bar anka ya koma gida Anty Ummi kam sai da yamma lis ta dawo bayan sun yi mata dubin alheri na amfanin gona, da kuma fura da hoce abincin zamfara, sai kuma kuli da daddawa abubuwan da aka fi saffarasu a kauye... *AFTER 15 YEARS.... @2020* *Who's is already for their new life...?* [4/5, 6:31 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *57* *New life 2020* Yan mata ne guda hudu dukansu suna sanye da doguwar riga iri daya, uku daga cikinsu su yi rolling kansu da jan mayafi wacce ta kara fito da kyau gown din kasancewarta shudiya. Dayar kuma ta dora mayafin a kafadarta dayan hannunta rike da jar jaka, idanuwanta kuma sanye da katon gilashi kanta ya sha daurin first lady. Kallo daya zaka musu ka san cewa yayan manyan mutane ne, kama daga tufafinsu yanayinsa da kuma fatar jikinsu da ke amsa amon naira ta ko wane bangare. Ko wace da kalar kashim turaren da take, ba zaka iya bambance wanne ya fi dadi ko tsada ba, uku daga cikin yan matan fafaren yayinda da dayar kuma ta ke black beauty. Iska ne ya fara kadawa da dan karfi sakamakon hadarin dake haduwa a sararin samaniya. Lokaci daya suka dariya suka bushe da dariya su ukun, ban da dayar wacce ta saka hannayenta ta toshe kunnenta sakamakon cidar da aka soma yi, ta nufi mota da sauri ta bude front seat ta shiga ta zauna. Dariya suka ta mata har suka shiga motar sanin yadda take tsoron tsawa da cida. “Ohhhhh to yanzu mun ciro kudi me ya kamata mu fara ci, dan gaskiya yunwa na ke ji” Black beauty ta fada tana kallon yan'uwanta. “Vanilla ice cream...” Dayar ta fada sai dayar ta tari numfashinta. “No girl coffee²” “No Indomie” Wannan karon wacce ke front seat din ce tai maganar tana kallon wani gurin daban fuskarta dauke da murmushin da ya karawa fuskarta annuri. Beauty da ke driver side taja wani dogon tsaki. “Dan rufe mana baki, ke kullun indomie” Daya daga cikin wadanda suke zaune bayan ta leko kanta. “Beauty don't mind her she's indomie generation” Sai duk suka sa dariya har ita wacce tai maganar. Ta juyo ta kallesu. “Ai kara ni indomie ce, ke coffee, pearl ice cream, dukanku babu wacce take cin abincin gidansu, amman ni ina cin abincin gidanmu” Bauty ta kalleta. “Please zip up your mouth Pretty, idan ana maganar mutane ki daina kwatantawa da kanki, and i mean people, ke ma din da kike cin abinci gidanku ai mun fiki abun arziki” Wacce aka kira da Pretty ta kalleta. “To be frank indai ba indomie za mu siya a yanzu ba, ba zan biku ba” “Haba dai Pretty shikenan sai muje mu zauna a restaurant mu ci indomie?” Pearl ta fada. “Fine kuje ku ci abunda kuke so, ni daman gida na ke son zuwa saboda hadarin nan” Dayar da bata cika magana ba tunda suka fara magabar bata cika saka bakinta ba ta bude motar ta zagaya inda Pretty take zaune ta bude motar. “Fito malama ba dole” Ta kallesu da dai daya. “Are you guys for real?” Beauty ta daga mata kafadu. Pretty fita tai a motar tana kaiwa diamond duka cikin wasa. “And lemme remind you something, Abuja ba kamar Kaduna ba ne, kamin ki samu abun hawa a nan zaki sha wahala, sai idan kira za ki yi a zo a dauke ki” Beauty ta fada tana yi ma motar key. “Mind your business Malama tun ba a haifeki ba na san Abuja” Sai suka saka mata dariya, ita kuma ta nufi gurin titi. Wata farar motace ta sha gabanta wanda ke cikin motar ya sauke gilashin motar ya dan leko yana kallonta fuskarsa da murmushi. “Pretty ke ce haka” Fadada fuskarta tai da murmushin da ya fitar da dimple dinta dake gefen kumatunta. “MB” Ta fada kamar mai jin kunya. “To miye abun jin kunya ai na san ba laifinki ba ne laifin kawayenki ne, ina zaki je haka gari duk hadari” “Wallahi gida zanje, wannan Beauty din ce ta ce mu rakota Atm ta cire kudi kuma wai yanzu take min wulakanci wai na cika cin indomie... Imaging” “Gaskiya ta fada Pretty kin cika cin indomie ai” “Au kai ma haka zaka fada?” “Am sorry Friend, shigo na rage miki hanya” “Ai ban ce maka ta min tsawo ba” “Zan kaiki ki ci indomie” “Hubby ba zai ji dadi na ci abinci public ba, amman zan yi farinciki idan ka sauki ni gida” Ya dan tsaya kallonta for a seconds sannan ya mika hannu ya bude mota motar. “As you wish” Sai da ta shiga motar ta zauna sannan ta rufe ta maida hankalinta gurin titi. A hankali ya soma driving kamar baya son su isa da wuri. “Na fadawa Madam yau zaki zo ganin Babynmu” “Wallahi teams suka ki raka ni, amman gobe zanje ko da ni kadaice” “Da dai yafi, Allah ya kaimu” “Amin” Bata sake cewa komai ba, shi ma be sake yi mata magana ba, sai dai yana daga kansa lokaci zuwa lokaci ya kalleta. Ko da yai horn a bakin gate din gidansu har an fara yayyafi mai karfi, da gudu mai gadi ya bude masa gate. A harabar gidan ya faka motarsa ya juyo ya kalleta “Ke zaki zo ko zuwa zan yi na dauke ki” “Aa ni zan zo da kaina ai na san gida” “Okay” Ta kai hannu ta bude motar ta fita da sauri zuwa main door. Shi kuma yai ribas ya juya da motar ya bar gidan. Sai da ta kai gaban balcony da ke gurin sannan ta daina gudun tana tafiya a hankali, hannu ta kai zata bude main door din hakan yayi daidai da bude kofar falon da Raheem yai ya fito yana kallonta. “Waya saukeki yanzu?” Ya tambaya tare da janyo kofar ya rufe. “MB ne” Ta fada kai tsaye. “Ban ce kar na sake ganinki da shi ba?” Har ta bude baki za ta yi magana sai ga Hajiya Asma'u ta bude kofar falon tana kallonsu. “Fada kuke yi?” Sai da ta kalleshi sannan ta kalleta. “Aa” Sai ta ratsa gefenta ta wuce ciki. Hakan ya bawa Hajiya damar dakowa ta fito tana kallon dan ta. “Lafiya dai Raheem?” “Hajiya MB ne ya kawo ta fa” “Haba Raheem take it easy mana” Tana fadar hakan ta juya ta koma cikin falon, shi kuma ya zauna a daya daga cikin kujerun da ke jere kusa da kofar shiga falon. Cikin bacin rai ta shiga dakinta, dakin da aka kawata da komai na cikinsa pink. Gurin da take rataye jakunkuna ta nufa ta rayata jakar tare da dora wayarta saman madubi sannan ta cire tufafin jikinta ta daura tawul ta shiga bathroom. Gaban madubin da ke bandakin taje ta tsaya tana kallon kanta for a seconds sai ga hawaye ya sauko mata. “I can't tolerate this” Ta furta sannan tasa hannuta ta share hawayen ta cire tawul din ta kunna shower. Bata fi minti goma ba ta fito, bata damu ta shafa komai ba, ta nufi wardrobe ta dauko gown ta saka, har ta nufi kofar fita sai kuma ta tsaya tana kallon kanta, no ba zata iya fita da wannan kayan ba ya matse ta, dawowa tai ta dauki Hijab ta saka. “Hubby ba zai jidadi ba idan ina barin jikina sake” Ta fada tana kara gyara zaman hijab din a jikinta. Gaban madubi taje tana kallon kanta. “Da Hijabin ma kin fi kyau Pretty” Ta fadawa kansa tana mitsisika ido, sannan ta juyo ya nufo kofar fita. Tun ta fito daga dakinta ya daga kai yana kallonta har ta karasa cikin falon inda suke sannan ya dauke idonsa daga barin kallonta. As usual a kasa ta zauna dan ta fi jindadin zaman kasa fiye da zama saman Cushion. “Tashi kije ki ci abincin ki” “Me aka girka?” “Tuwo” “Tuwo? Indomie na ke so” Ta fada tana yamutsa fuska. “Ai gaki ga hanyar kitchen” Cewar Hajiya, sai ta mike tsaye tana dariya. “Macen da bata da ra'ayin kanta sai na wani tana cikin damuwa, ki koyawa kanki cin abunda ba abincin ki ba saboda wani selfish interest na ki ga wanda be san kina yi ba” Yanayin yadda yai maganar sam ba zaka ce shi ne ba, dan babu wata alama wacce ta nuna cewar shi yai magana ban ma aikin lasar wayarsa babu abunda yake. Juyowa tai ta kalli Hajiya sannan ta kalleshi. “Ina Mamakin mutumen da zai yi ta damuwa fa abunda be kamata ya dame shi ba, sai yaushe zaka fahimce kwakwalwata ta kasa haddace shiriritar da kake ta min mita a kunne? Miyasa ba zaka damu da abunda ya kamata ya dame ka ba?” Shi take fadawa maganar amman ita ke hawaye. Dagowa yai ya kalleta “Kin gani ko? Ba dama ayi magana sai ta ce da ita ake” “Da ni kake mana na san ai da ni kake, ba sai ka fada min ba” Ta fada da muryar kuka. “Amman Hafsat ai ya kamata ki bashi girman shi ko ba komai ya girme ki” Hajiya ta fada, sai Pretty ta nuna kanta ta nuna shi sai kuma ta kasa magana sai sakin baki da tai tana yi ma Hajiya kallon Mamaki. Sai kuma ta fashe da kuka ta nufi dakinta da sauri har tana hadewa da dan gudu. Sai da shige dakinta sannan Hajiya ta kalli Raheem. “Takurawar da kake mata Raheem ta yi yawa, ya kamata ka saka mata ido hakan nan yanzu kam” Kwantawa yai jikin kujerar da yake zaune ya lumshe ido yana sauke numfashi a hankali. Saman gadonta ta fada ta rushe da kuka mai karfi har jikinta yana jijjiga. Wayarta ce tai ringing sai tai saurin tashi ta nufi wayar ta dauka ba tare da ta share hawayen idonta ba, sai dai ta yi kokarin daidaita muryarta dan kar a gane kuka take. “Hello Amal” “Pretty ya kike?” “Lafiya kalau, ina Anty Ummi” “Tana lafiya, ki bude Instagram Uncle yana live” “Da gaske?” “Wallahi” Tayi saurin kashe wayar ya share hawayenta, sai ta nufi inda system dinta take da sauri ta dauka ta dawo saman gado ta zauna tare da cire hijab din jikinta. Ta dora laptop din saman jikinta ta kunna. Kai tsaye taje page dinta na instagram. Ji tai ba zata iya jira news feed ya kawo mata shi ba, dan haka ta shiga search side ta rubuta sunan da ake kiransa da shi. *Craftsman* a take aka nuna mata su, na shi na ainishi wanda a kai ma mark da kuma na fake da sai foundation dinsa da kuma support groups kala kala. Wanda aka yi ma mark da sky blue tai saurin budewa daman ta san shi ne na shi na ainahi domin tana following dinsa. Kamar yadda Amal ta fada mata tana live saboda wani program da suke a can kasar paris, ya saje ta turawa har baka iya gane shi din bahaushe a fata sai dai a fuska, turanci yake watsara kamar daga bakinsa ya fito, ya saka suit blue wanda ya kara fito da kyau da kuma annurin fuskarsa, beard dinsa ya kwanta sosai ya yi baki har wani shining yake, like always he look very beautiful and attractive, you can't call him young sai dai kuma he is not that kind he look very gentle. Bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba, zuciyarta na bugawa with each and every single word of his. bakinsa take kallo kamar wacce ke kirga fararen hakuransa. Idan yai dariya sai tai dariya idan kuma ya cigaba da magana sai ta maida hankali tana kallonsa, sai dai babu abunda ta haddace daga kalamansa, farincikinsa da walwalarsa kawai take lissafi, haka take a duk lokacin da take kallonsa, sai ta nemi bacin ranta ta rasa. Hannu ta kai ta shafa screen din laptop din hawaye na sauka daga idonta. “For how long zan yi ta jiranka Zain? For how long zaka san I am still alive? Sai zuwa yaushe za ka zo ka nemi ajiyarka? Na kasa sabawa da rashinka, kai na ke ta yi ma ajiyar kaina, sai yaushe za ka fahimci irin halin da na ke ciki? Ka manta da kana da mata ko? Zan jiraka Zain ko da jiranka na nufin karshen rayuwata ne, ko da hakan na nufin shiga wata duniyar ne, zan jiraka Zain dan jiranka shine kadai farincikina a rayuwa...” Tana gama fadar hakan ta daga kanta sama hawaye ya sauko ta gafen idonta... [4/6, 2:43 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *58* Wayarta ce ta sake ringing, sai ta bude idon ta kalli mai kiran. Ganin Amal yasa ta saurin dauka. “Kina kallonshi ko?” “Yeah, Amal ban san miyasa yake ta boye min kansa ba, ko maybe ya manta da ni ne ko kuma yana ganin matan turawa yana ganin kamar ni ban dace da shi ba?” Ta yi maganar cikin muryar kuka. “Bana tunanin haka pretty maybe dai akwai wani dalilin na dabam, amman ya gane ke ce da kika kira shi?” “Ya gane, daga lokacin da ya gane sai yai blocking dina, babu ind bana fallowing dinsa Facebook twitter instagram amman da ya fahimci ni ce sai ya blocking dina, ina son ganinsa Amal ina son na tambayi shi wani abu, da zarar mun gama exam zan je har paris inda yake” “Haba pretty ba ki bukatar yin hakan” “Amal ba ki tunanin nima na cancanci farinciki? Iyayena suna tare da ni amman ina jin uncompleted, Amal i love him so much” “I know, na ji Anty Ummi na fadin cewar jikin Hajiyarsu babu dadi sosai maybe ya zo dubata” “When? A satin nan? Ina ganin zan dawo Gusau na zauna a gurin Anty Ummi so that idan ya dawo na samu ganinsa” “No don't ba Exam zaku fara ba yanzu? Karki yi bar Exam dinki saboda ganin Uncle na miki alkawari idan ya zo duk yadda zan yi na hadaku zan hada ku” “Okay Thank you Sis” “Anything for Sis” Tana aje wayar ta kwanta samman gadonta ta cigana da kallonsa, wani lokacin take tunawa ten years back, lokacin da take secondary school, a duka hutun da suka samu Anty Ummi tana aikowa a tafi ta ita, ita ce take yawan bata labari a kan Zain, how he sacrifice for her, irin wahalar da ya sha na rayuwa, da kuma irin kalubalen da ya fuskanta, daman bata manta wasu abubuwa da suka faru ba, amman Anty Ummi ce take tuna mata da komai bit by bit, har komai ya dawo mata fresh, sai duk hutun da take zuwa da maganarsa da Anty Ummi take mata, ko sau daya bata taba bata waya su gaisa ba, bata taba hada da shi idan ya zo garin duba iyayensa ba. From that day Hafsatu manga ta sawa kanta son ganinsa daman ta girma ta kaunarsa, domin bata san a alakarta da shi ba bayan fitar da yai, amman ya zauna a kwakwalwarta har zuwa girmanta, Anty Ummi ce ta fayyace mata komai, bata san zafin sonsa ba sai a yanzu da ta mallaki hankalin kanta. Tun daga 17 years ta fara shiga yanar gizo saboda shi, ta yi ta samun fake account kamin Amal da Anty Ummi su banbance mata na kwaran na shi da kuma fake. Daga ranar da tai masa magana ta sanar da shi ita ce sai yai blocking dinta, a duk wanda take binsa abunda ya daure mata kai kenan har yanzu take mamaki. Bayan ta gama secondary school a Kaduna, sai Mahaifinta ya nema mata university Abuja, a gidan Hajiya Asma'u ta zauna wato yayar Rufaida Mahaifiyarta, daga lokacin da ta zo gidan dan Asma'u Raheem ya kwallafawa ransa sonta ita kuma tai ta nanata masa cewar ita matar Zain kamar yadda Anty Ummi take yawan fada mata. Ta nan maganar ta kai ga mahaifinta Alhaji Habib, already Hajiya Rufaida ta san komai domin ita ce best friend din yarta bata boye mata komai, Alhaji Habib yayi mamakin jin inda maganar ta fito domin ya dauka yarsa ta manta da Zain, ba shi da wani zabi bayan goyon bayan yarsa da kuma son abunda take so. Some people take it as a joke idan tana cewa shine mijinta domin bata boyewa kowa, more especially ma Raheem wanda ya kasance dan Hajiya Asma'u, yana tunanin tana yin haka ne kawai dan bata son sa, a yayinda mahaifiyarsa kuma take ganin kamar ta dasawa ranta sonsa ne saboda kawai ta ga he's billion, ga shi kyakkyawa kuma wanda duniya take ji da shi saboda kwariwar aikinsa da kuma irin taimakon da yake ma mutanen Africa especially Nigerians. Sai mahaliccinta ne kadai shaidar cewar son gaskiya take yi ma Zain, bata san dalilin son da take masa, saboda yayi sadaukarwa da yawa akanta ko kuma saboda yana daya daga cikin irin mazaje da take so ne? idan ta ga wasu suna crushing akansa a social media ko zahiri har ji take kamar ta hadiye zuciya ta mutu. On her First day a school ta hadu da kawayen kwarai yayan manyan mutane, wato Amina (Black bauty) Fatima (Diamond) Rabi'atu (Pearl) ita kuma suka saka mata Pretty da haka sunan ya bita har cikin familynsu, suka hada kansu komai za su yi a Scul din ko wajen scul a tare suke yinsa baka isa ka tana dayar ba sauran su kyaleka, idan dayan su ya samu abu kamar dukansu ne suka samu saboda hadin kai da kaunar junansu da suke. Ziyar farko da Anty Ummi ta kai mata da yarta Amal (That little girl yar Anty Ummi remember?) ta yi ta mata nasiha da tunatarwa. “Ki rika rufe jikinki, Zain mutum ne mai tsananin kishi akan abunda ya ke so, ba zai jidadi ba idan kina barin jikinki sake, karki kula kowa kin san ke matar aurece domin masarautar Damagaram ta mallaka masa ke a matsayin kuyanga (Saɗaka) shiyasa mahaifinki ko mahaifiyarki ba su taba miki maganar aure ba ko wani ba, sun maida hankali kan karatunki da kuma ingantacciyar rayuwar da za ki samu, duk wanda yai miki maganar aure ko so ki fada masa cewar ke matar aurece, ban ce ki yi ta tallata Zain ba amman ki tallata aurenki kuma ki kare mutumcin” Sune shawarwarin da Anty Ummi ta bada, da wadanan shawarwarin take amfani kuma take rayuwa har yau, sai dai tana cikin damuwa da rashin kulawar da Zain yake nuna mata, wani lokacin har ta kan tambayi kanta, anya baya manta da ita ba? Ko kuma ya cireta a zuciyarsa, sai dai kuma Anty Ummi ta fada mata cewar be da mata a can kuma be nema ba, amman miyasa har yanzu ya kasa nemanta? Kuma idan ta nuna masa cewar ita a waya ko social media sai yai blocking dinta? Wannan abun ne yake daure mata kai, a dukan account dinsa da tak following a facebook da twitter da instagram bada hafsat take using ba, saboda idan tai following dinsa da sunnan yana gane sai yai blocking dinta duk kuwa da tarin yawan followers da yake da su, Pretty_Nigerian take using, gurin Full name kuma Sai ta rubuta Mrs Zainudden, hakan yaba ta damar kallon duk wani abu da yake yi a media. Ta twitter ta hada da MB wato Muhammad Ballo one of those minister's son's yana da mata da ɗa ɗaya sai kuma babyn da matarsa ta haifa masa yanzu, he forced himself to her tun tana kin sake jiki har ta fara sake masa jiki domin yazo mata ne as friend, da sannu sannu yayita bincike a kanta da friends dinta har ya gano gaskiyar auren da take tutiya da shi, a haka ya bita yana avoiding duk wani abu da zai bata mata rai ko ya bata kawancensu. Ba shi matsala da ita sai dai da cousin brother dinta wato Raheem domin Raheem na kishinsa sosai, saboda kula shi da Hafsat take yi, da kuma shakuwar da ke tsakaninsu. Wanda shi ya kasa samun hakan daga gareta saboda kawai ya nuna yana sonta, yana ganin wautarta da kuma rashin hankali na son wanda be kula ta ba, ko da dai rana be taba kiranta ba. She face a lot of challenges a gidan saboda Raheem tun yana bibiyarta a natsake yana nuna mata so har ya fara gajiya da rarrashinta ta fara takura mata. Kullum Momy (Rufaida) cikin bata hakuri take na ta zauna gidan dan bata son zamanta a hostel, a haka tai ta hakuri har ta kawo shekararta ta karshe. *** *** *** Sai da aka dauke ruwan saman sannan ta tashi ta shiga bathroom ya wanke fuskarta. Bata sallah dan haka ta wuni dakin bata ci abincin rana ba har dare yayi, misalin takwas da rabi na dare, kiran Pearl ya shigo wayarta. Da sauri ta dauka daman she need some one to talk to. “Pretty ki turawa james style na siya mana sabon atamfa” “Okay” Ta amsa cikin yanyin damuwa. “Dear are you okay?” Sai ta fashe da kuka. “Pearl i was.... I'm thinking of myself am in so much pain” “About that Zain ko? Pretty ki kwantar da hankalinki komai zai zama daidai, kin ji? Ki kwantar da hankalinki we love you (on be half of them) ” “We love you too, thank you” Daga haka ta sauke wayar. Kofar dakinta aka turo hakan yasa tai saurin tashi zaune tana kallon wanda ya shigo sanye da jallabiya. Nuna fuskarta yai. “Share hawayenki” Sam ta manta da akwai hawaye a fuskarta sai yanzu da yai maganar, da sauri tasa hannu ta share hawayen. “Haka za ki yi ta zama kina zubar da hawaye ga wanda be san kina yi ba?” “Me yasa ba za ka min fatan ya sani ba?” Ya dan tabe baki sai ya saka hannayensa aljihu. “Ba ki ci abincin rana ba, yanzu kuma dare yayi baki fito cim abincin ba, haka zaki kwana da yunwa ne?” “Maybe” “You know i care for you, idan maganar da nai miki ce ta bata miki rai am sorry please, kije ki ci abinci ko kuma na debo miki a nan? Na sa Larai ta dafa miki indomie” “Ba amfanin ka yi ta bani hakuri indai za ka cigaba da bata min tai” “Ba kaunar bacin ranki na ke ba, domin nima nawa ran ba ci yake idan kika bata na ki, amman wani lokacin ina tunani anya ya damu da ke kamar yadda ke kika damu da shi? Ko sau daya be taba kiranki ba be nemi sanin kina raye ko a mace ba, yana can yana ta rayuwarsa ta jindadi, abun ma be yi kyau ba ace wai wata masarautar ce ta bashi kyautarki, ba za kiyi daraja a idonsa ba, maybe shiyasa ya kyaleki, amman in har yana son ki kamar yadda na ke son ki zai so kasancewa da ke kamar dai ni, one hour kika yi ba a gidan nan ba, ina cikin tunaninki,ke ma kuma da kike son sa ai gashi kina son kasancewa da shi ko?” Tun da ya soma maganar take hawaye, kai tsaye ta daka masa tsawa. “Be kamata ka shigo min daki kana fada min bakaken magana ba, ai Hajiya ta ce karka sake shiga dakina ko? Fita ka bani guri bana son ganinka” “Zan fita amman dan Allah ki sauko ki abinci” Yana fadar hakan ya juya ya fice. Sai ta fashe da kuka ta rumgume fillo ta kwanta zuciyarta na mata wani mugun suya. A week din haka tai ta zuwa scul kamar marar lafiya, bata sakewa bata walwala ta dauki abun ta saka a kanta gashi in ya dawo gida Raheem yai ta damunta. Sai dai friends dinta suna yi dukan kokarinsu wajen ganin ta sake jikinta ta yi walwala, amman bata kamar da ba, idan ma suna son ta sake sosai su dauko mata zancen Zain, more especially Bauty ta fi taba labarinsa har ma da wani abun na personal life dinsa wanda bata sani ba, sometimes har mamaki take yadda take. Sanin sirrinsa, sai ta ce mata ai a gurin friends ta ji. It's Saturday they are all at home daman haka suke every weekend za a je gidan daya daga cikinsu a zaune ana fira, on that day duk friend din da aka je gurinta ita ta tanadar musu komai, so today it's Pearl day. Fira suke sune ciye ciye a garden din gidan, ba laifi Hafsat ta dan sake jiki tana ta tsoma baki ana firar, sai dai duk firar da ake dauriya kawai Hafsat take, saboda cikinta da ke ciwo. “Pretty lafiyarki?” Beauty ta tambaya dan ta lura da yanyinta ga hannunta da ke dafe da cikinta. “Wallahi cikina ne ke ciwo” “Subhanallahi” Duk suka fada. Pearl ta ce. “Mun yi ciye ciye fa, kuma kamar ba a hada kifi da yogurt ko?” “Like serious? Mun ci farfesun kifi kuma kin sha yogurt ko? Ni dai ban sha ba” Cewar Fateema (Diamond girl). Pretty wacce ta gama razana ta ce “Na san ba a hadawa amman na dauka sai nono kawai ba da yogurt ba” “Gashi kuwa kina jin ciwon ciki, tashi muje asibiti kar abun ya taba ki” Sai duk suka tashi da sauri. Amman ita tana mikewa tsaye sai ta koma ta zauna saboda ciwon cikin. “Ba zan iya mikewa tsaye ba, it's so much pain” Tana rufe bakin sai amai. Sai duk suka saka salati hankalinsu ya tashi sosai. [4/7, 12:28 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *59* “Eh cikinta ne yake ciwo sosai har an bata gado ma” “Amman da sauki ko?” “Ee kifi ta ci da yogurt” Muryar wata macen ce ta amsa masa daga can cikin wayar. “Gobe zan Naija saboda Dada ba lafiya, amman ina son ganinta yanzu” “Okay bari na turo maka ita” Ya sauke wayar yana gyara tsayuwar gilashin idonsa, tsaye yake gaban wata katuwar glass door wanda hakan ya bashi damar hange dukan abunda ke wajen unguwar, yana sanye da short da vest dayan hannunsa rike da tea. A hankali ya kai kurba tea yana hadewa zuciyarsa ya bugawa da mugun karfi kamar zata fito. Lokaci daya wayarsa yai kara alamar sako, Multimedia message, ne mai dauke da video. Hafsat ce aka dauka tana kwance saman hospital bed tana bachi, ta takure kafafunta guri daya kamar yadda take bachi a lokacin da take karama. Dan murmushi yai sai yai baya baya ya zauna saman wata royal chair yana shafa screen din wayar. Rayuwarsu ta baya yake tunawa lokacin da yake jinyarta, haka take bachi sai ta takure kafafunta guri daya. Wani lokacin yana mamakin kansa da kuma ita, yadda rayuwata ta canja masa, be tsammaci zai iya sake sakewa da walwalah kamar da ba, amman da yai hakuri ga shi komai ya wuce, all those years da yai a paris kullum da tunanin Hafsat yake kwana da shi yake tashi ta shiga ransa fiye da komai. Be yi wata daya da baro kasar ba, ya kira Anty Ummi akan yana son ta sadashi da mahaifin Hafsat yana son magana da ita, number Alhaji Habib ta turo masa kasancewar ba guri daya suke ba, shi yana Kaduna ita kuma tana Gusau. Ta dade be kira numbar ba, yana ta tunanin abunda zai fadawa iyayenta idan ya kira, sai dai yana son waya da ita yana son ji daga gareta, ya san tana tare da iyayenta amman a yadda suka shaku abu ne mai wahala ace bata tambaye shi ba. Ranar da ya dialing number ya kira, ya ssmu kansa ciki wani yanayi marar misaltuwa, gaisawa suka fara yi da sannan ya gabatar masa ta kansa, Alhaji Habib yayi farinciki da yaji shi ne, sai Zain ya kasa tambayar Hafsat, yana ta saurare ko mahaifinta zai ce masa gata ku gaisa amman yaji shiru, har Zain ya masa sallama zai kashe wayar sai ya kira sunansa. “Zain na i know you have done a lot akan Hafsat, ta shaku da kai kusan ko da yaushe labarinka take, na san kai ma ka shaku da ita, amman Zain Hafsat karamar yarinya ce batai girman da zaka bata irin wannan kulawarba, idan har soyayya ta shige a yanzu da take karamar yarinya ba mu san me gaba zata haifar ba, ina son yata t samu ingantacciyar rayuwa mai kyau, kulawar da bata samu a gurinmu da iyayenta ba, a yanzu ina son na bata ita ni da mahaifiyarta, alfarma na ke nema a gurinka Zain, na san Hafsat tana matsayin kuyangar ka ne, amman ta yi kankanta da wannan idan ma na tuna abun yana bata min rai, domin a yanzu bata san komai ba, ina neman alfarmar ka fadi abunda zan baka na muƙataba, sai ka barranta ta daga kuyanga, idan har ta girma ta mallaki hankalin kanta, kuma ta ji tana kaunarka ita da kanta zata nemeka, ban yi hakan da wata manufa ba, sai dan inganta rayuwarta, domin akwai kalubane mai yawa a rayuwarta ta nan gaba matukar ka tayu a zuciyarta daga yanzu zuwa girmanta.” Shiru Zain yai kamar baya cikin wayar, ya rasa abunda zai fada tunaninsa ya tsaya cak har ya rasa abun tunani a kwakwalwarsa. “Zain kana jina Allah yasa ka fahimta” Jin shirun yayi yawa yasa Alhaji Habib cewa haka. Wani dogon numfashi yaja ya sauke sannan ya ce “Na fahimta, zan turo maka account dina ka saka min dubu talatin na muƙataba daga yau ƴarka ta tashi daga kuyanga na yanta ta kamar ko wace ya mai yanci da walwala” “Na jidadin hakan kuma na gode sosai, amman dubu talatin be yi kadan ba?” “Ba kudin ne abun dubawa ba, muhimmancin abun ne, abun dubawa” “Haka ne na gode sosai Allah ya saka maka da alheri” Alhaji Habib ya fada cike da jindadi. Zain kuma ya kashe wayar ba tare da sake cewa komai ba. A take ya tura masa sakon number account dinsa, in few minutes 30,000 suka shigo account din. Sai kuma ya ji babu dadi, ya san gaskiya mahaifinta ya fada, shi kanshi zai so ta samu rayuwa mai kyau fiye da kima, amman yana ganin kamar mahaifinta be fahimce ba ne da yake masa kallon sonta yake, shi har mamakin yadda mutane basa iya banbance so da soyayya yake, Ibrahim kawai ya fadawa abunda ya faru bayan ya gargade shi akan karya fadawa kowa dan yasan Anty Ummi ba zata jidadi ba idan ta ji. Amman yasan gaskiya mahaifinta ya fada idan tana kaunarsa wata rana ita da kanta zata nemeshi, sai dai be sa ran haka ba, dan a tunaninsa zata manta da komai ne. Daga lokacin ya rika kokarin cireta a ransa, a duk lokacin da Anty Ummi tai masa magana sai ya nuna baya so, shi yasa ko da dai rana be taba tambayarta a gurin Anty Ummi ba, har rokonta yai akan ta daina masa maganarta, abunda yayita bata mamaki amman be fada mata ba, babu wanda ya san da sirrin sai Ibrahim. After six months ya je gida ganin Mai Martaba da Dada Yalwa, be jidadin yadda ya samu Dada ba, duk ta rame kamar ba ita ba, kana ganinta ka san tana cikin damuwa, duk da yawan wayar da yake da ita a can be fahimci hakan ba sai da ya sakata a idonsa. A dakinta ya ci abinci a ranar yana kallon yadda ya kasa cin komai sai furau furau, da yai mata magana sai ta saka kuka irin na su na tsofi wai da wannen zata ji rashinsa ko na Hameeda, kara ma shi tana waya da shi kuma tana ganinsa, amman Hameeda tun da ya tafi bata sake waya da ita ba, idan kuma tai ma Mai Martaba maganar a kira mata ita a waya sai yace tana nan lafiya, idan ta kira numbar ta bata samu, a iya kokarin da tai ma zuwa kaduna kuma sai Mai Martaba ya hanata. Zain yayi mamaki da ba a fada mata gaskiya ba har yanzu, wata kila ma fada mata gaskiyar zai rage mata radadin rashin Hameeda da take ji, kuma a yanzu tana kallom an zalunci Hameeda ne. “Dada Hameeda tana wani gurin inda ba zai yi ta fito ba” “Kamar ya?” Ta tambaya tana tashi zaune, zuciyarsa nata raya masa karya fada mata gaskiya, sai dai yana jin fadin gaskiyar shine kawai mafita. “Dada Hameeda kisan kai ta aikata, ta amsa laifinta ne a lokacin da muka je kutu da sunan ta bada shaidar abunda ta sani akan Farhat, hakan yasa alkalin ya yanke mata hukuncin zama gidan kaso har na tsowon rayuwarta” Dada ta yi murmushi tare da hawaye. “Daman na sani, tun da ka dora mata kwaha za'ayi haka Zain” “Ba ni bane Wallahi Dada, ita da kanta ta fada ba tare da an matseta ba, kuma sai ta fitarta da wayar Farhat a hannunta wanda babu wanda yasan da wayar a hannunta, bayan haka kuma Dada ta fada mana cewar ita ta kashe Haleema ta hanyar sanya mata magani a cikin abinci, kamar yadda tai ma Farhat, daya daga cikin dalilin daya sa kika bar ganin Abida, domin ita ma tana can gidan yari alkalin ya yanke masu hukucin shekara ashiri da biyar a gidan kaso, ita da wata kawarta Fauziya” “Miyasa ba a fada min gaskiya ba? Taya zan gasgata ku ba zan yarda ba har sai na ga Hameeda na yi magana da ita da kaina” Ta fada cikin kuka. “Ban fada miki dan ki gasgata ni ba, sai dan ganin boyewar da ake miki bashi da amfani, dukan mu muna tsoron rasaki ne kawai shiyasa Mai Martaba ya hana kowa yai miki jaye ko ya fada miki gaskiya, ya canja miki layin waya ba tare da kin sani ba duk dan kar kiji hankalinki ya tashi, idan kina bukata zan kaiki gurin Hameeda yanzu kinyi magana da ita, duk wayar da kike da ita a baya tana gidan yarin ne, ita kanta ta bukaci a boye miki dan kar hankalinki ya tashi” Ta yi saurin sauka saman gadon. “Ina son na ganta ina son nai magana da ita, ita kadai ce zata fada min haka na yarda” Mayafinta ta dauko, Zain ya sakata a motarshi ya fita da ita ba tare da kowa ya sani ba a gidan, kamin su isa duk ta matsu babu kalar hawayen da bata yi ba, basu bata lokaci a zaune ba sai gata an fito da ita, cikin wani irin yanayi marar misaltuwa. Tana ganin Dada sai ta fashe da kuka, Dada Yalwa ma kukan take tai saurin tashi tsaye tana kallonta sai Hameeda ta zo da gudu ta rumgume Dada. “Dada ki taimaka min na fita daga nan, ba zan iya rayuwa a cikin nan ba, dana rayu a nan kara a kashe ni kawai na hutu, rayuwa a nan kunci Dada” Dada Yalwa ta dago kan Hameeda tana hawaye. “Da gaske ke kika kashe Farhat ko kazafi suke miki? Ke kika kashe Haleema da gaske” Jikinta ne yai sanyi, sai ta rasa abunda zata fadawa Dada Yalwa, ee ko aa. Kallon Zain tai sai kuma ta kalli Dada da wata kalar fuska tana tausayi da nadama. “Ba da gangan na kashe Farhat ba Dada, kurkure ne, Haleema kuma shairin shaidan ne, na yi tunanin kamar hakan mafita ne a gareni, dan Allah Dada ki yafe min” Lokaci daya Dada ta dauke hannayenta daga jikin Hameeda, hawayen da ke mata zuba suka tsaya, a take ta ji tsana da kuma mamakin yadda Hameeda zata iya kashe rai har biyu. “Da aka fada min ban yarda ba Hameeda, shiyasa na ce sai na zo naji da bakinki, ashe da gaske ne, a yadda na ke ganinki ban yi zaton ko a mafarki za ki iya kashe rai ba, ashe duk daukar da nake miki kin wuce nan, ina ta ganin Zain yana cin amanarki yana miki kage saboda baya son ki, ashe yana da gaskiya, a hannuna kika tashi amman ban miki irin wannan tarbiyar ba, wannan halin ba na ahlinmu ba ne, ba ki kyautawa rayuwarki ba, kuma ba ki burge ni ba, wannan ba so bane Hameeda hauka ne bakar zuciya marar lissafi irin ta kafirai marasa imani” Tana kaiwa nan ta juya da nufin barin gurin sai Hameeda ta rikota tana kuka. “Dada dan Allah karki barni, ba ni da kowa a yanzu sai ke...” Dada na ta tureta daga jikinta ta wanke mata fuska da mari. “Ban yi zaton rashin imaninki ya kai na ki kashe rai ba, ban san da irinki na ke zaune ba tuntuni, dacan baki san da ni ba kika aikata kisan kan, rai biyu? Kuma kika dawo kina nuna bake kika yi ba, kara Farhat baki hada komai da ita ba, amman Haleema fa yar'uwarki ce uwa daya uba daya, Allah ya waddaranki Hameeda...” Dada ta fada cikin kuka, sannan ta wuce Zain ya rufa mata baya, suka bar Hameeda a gurin tana kuka kamar na fitar rai. Tun daga lokacin Dada bata sake tanbayar Hameeda ba, duk wani bacin rai da tunani da suke tunanin zata shiga, sai abun ya zo mata da sauki, a duk lokacin da ta tuna da girma laifin data aikata sai ta ji ta fitar mata a rai, sai dai hakan be hanata tunani ko kuka wani lokacin. Sai da yai shekara daya da komawa paris sannan ta fara kaiwa Hameeda ziyara a gidan kaso, lokaci zuwa lokaci. Bayan shekara daya da dawowar, ya samu aiki a babban asibitin paris, kuma ya fara a sa'a domin kuwa sun yaba da kwarewarsa da kuma jajircewarsa, a dalilinsa na son manta da komai da kowa yasa ya maida hankali kam aikinsa, wanda hakan ya kara masa girma da farinjini a gurin turawan, har ta kai babu kamarsa a fadin asibitin, indai kwararen likitan zuciya ne to shine dai a fadin kasar wanda yafi kowa kwarewa da sanin aikinsa, duk abunda yake tarawa yana aiko da shi ne a naija ta hanyar Ibrahim ana taimakon mabukata da gajiyayyu, daga nan Ibrahim ya bude masa foundation. Ya sake zuwa naija ne bukin Ibrahim da Hafsat, wanda akai a a shekararsa ta hudu da kowa paris, bayan bikin ya kwashe wata daya a gida shi ma kuma daker suka bar shi yai su a naija, bayan ya koma ne kamar shekara biyu Hafsatu manga tai matsa tsaye a rai, sanadin hakan yasa abokinsa ibrahim ya bincika masa ita, sai aka kawo nasa labarin cewar tana cikin Koshin lafiya tana gudunarda rayuwarta yadda ya dace. Tun daga lokacin Ibrahim yake bibiyar rayuwarta, duk wani abu daya shafeta yana fadawa Zain ba tare da Anty Ummi ta san komai a kai ba. A ten years da yai a paris sunansa ya zaga ko'ina inda turawan da kansu suke masa lakani da *Craftsman*. Ya jidadi lokacin da ya samu labarin Hafsat bata manta da shi ba wanda hakan ya kara masa sonta fiye da da, ba tare da sanin cewar Anty Ummi ce take tuna mata komai ba, a tunaninsa ta haddace komai a kanta ne, a lokacin da tai masa request a facebook, yayi mamakin ganin girmanta, amman hakan be sa ya amsa mata ba dan a tunaninsa har yanzu tana da sauran lokacin domin yana ganin har yanzu bata san ciwon kanta ba, daga lokacin yai blocking dinta, sai ta koma instagram a can din ma haka yai mata kamar dai sauran account dinsa da take bibiya, ta hanyar Ibrahim ya samu labari lokacin da ta shiga university a Abuja. A lokacin ne ta bude sabon account ta canja sunanta, shi kuma ya kyaleta ba dan komai ba sai dan ya bata damar kallonsa wanda ya san zata so haka. Shi kuma ya bude wani account din yana following dinta, duk wani abu da take yana gani. Ta nan ya samu magana da daya daga cikin kawayenta wato Pearl, shi ya dauki kwangilarta tana fada masa komai akan Hafsat, lokuta da dama tana daukar hotonta ta tura masa ba tare da ita din ta sani ba, kusan dukansu sun sani dan ta fada musu amman ban da Hafsat dan ya bukaci a boye mata ne wanda hakan zai bata damar focusing akan karatunta. And he's happy tana final year babu abunda ya sameta, yaji kishi sosai lokacin daya samu labarin tana abota da MB, sai dai ba shi wani yan cin hana ta, kamar yadda be isa ya cire son ta a zuciyar Raheem ba, ya san tana da kyau da haiba irinta ya mace wacce ko wane namiji zai so ta kasance matarsa sai idan be samu ba. *** *** *** Tashi yai tsaye ya bayan ya gama tunane tunanensa ya shiga kitchen ya dafawa kansa Indomie, yana jin nishadi da kwanciyar hankali idan yana cin irin abincin da hafsat ta fi so fiye da komai, wani lokacin yana tuna lokacin da take jera indomie tana cewa gashi nan ga Mamanta ga wane da wane. He used to jerawa kamar yadda take yana fadin gata nan ga shi nan. He so much worry about her condition amman ya kasa nuna mata kansa duk da yana son ganinta a fili, sai dai kuma yana ganin kamar lokacin yin hakan be yi ba. As he said Misalin goma na safe ya baro kasar zuwa Nigeria, they spend hours a jirgi har yai bachi ya tashi sannan suka iso, at that time isha'i a ake a naija. A Abuja ya sauka, tun a airport ya kira one of her friends ya pearl ya tambayeta ko akwai yadda za'ayi ya Hafsat ba tare da kowa ya ganshi ba. “Akwai yadda za'ayi na ga PureHeart” “Gaskiya ba dama, saboda mahaifinta da Momy tun jiya suka zo, kuma Hajiya Asma'u ma tana tare da ita” “Okay, ki shafa min kanta dan Allah” “Inshallah” Sai da yai minti arba'in a garin Abuja yana hutawa, sannan ya hau jirgi zuwa garin Gusau. He feel Nigeria kamar ba ita ba, duk kuwa da kasancewar yana zuwa yana koma a duk lokacin da ya zo yana jin wani yanayi na dabam. Babu abunda ya karu a kasarsa sai ma raguwar cigaba da aka samu, ga zalinci irin na shugabani da karuwar cin hanci da rashawa. Sai dai hakan be taba sashi ya ji baya son kasarsa ba, domin mahaifarsa ce har gobe ba shi da kamarta tun da Familynsa da Sahibarsa suna ciki suna rayuwa. [4/8, 11:58 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *60* Yana farincikin zuwansa Gusau bayan tsawon lokacin da ya dauka baya garin, ba sa abunda yasa yake jin wannan zuwa kamar ya fi ko wanne muhimmanci ba. Kowa a masarautar yana farinciki da ganinsa kama daga Mai Martaba da iyalansa har Dada Yalwa wacce bata da ishasshiyar lafiya a yanzu. After spending the night with Hajiya Hadiza suna ta fira ya dawo part din Dada Yalwa. A dakinta ya sameta tana cin tuwo miyar yakuwa da manshanu, kusa da ita ya zauna yana murmushi ya nasa hannunsa cikin robar wanke hannu ya wanke hannunsa sannan ya kasa cikin tuwo. “Ya dai kamata na ci abincin kasata kuma tare da babbar mata” “Babbar matar da ka gudu ka bari?” “To ba gani nan yanzu na dawo ba” “Dawowarka tana da amfani Muhammad, ina son nai magana mai muhimmanci da kai” “Kamar ta me fa Dada?” Ya tambaya yana aikin auna loma a bakinsa. “Zain ni da mahaifinka duka muna son ganin aurenka, bamu san ta rai ba, musamman ni da tsufa ya ci ya cinye, Mai Martaba yana son ganin jikansa daga gareka, duba kaga gidan nan duk an kwashe yan mata an aurar da su sai jikoki da ita da kananan kannenka, amman kai ace har yanzu babu jika ko daya kuma babu mata, da kana da mata na san ai dole ka rika dawowa kana ganinmu, yanzu da wannan ciwon ya tafi da ni ai da yanzu sai dai kawai ka tararda gawa” “Rayuwa da mutuwa duka na Allah ne, ciwo baya nufin mutuwa Dada” Ya fada cikin rashin jindadin maganarta. “Na sani, amman indai idan kana kusa zai fi, na san na takura maka a zaman da kai a matanka na baya, a farko Hameeda tana yawan kawo min karar Haleema tana ce min tayi abu sai na dauka gaskiya ne, daga baya kuma sai nai tunanin ko makircin Ummi ne ta aura maka Farhat kuma nai tunanin Farhat din magani tai maka, ashe duk ba haka ba ne, Zain ina son kai aure na sake saka matarka a ido, na karanta mata ko sau daya ne, ina son farincikinka kai da Hameeda, sai dai yanzu na fitar da rai daga na Hameeda, sai dai na ka kawai bani da wani buri a yanzu wanda ya wuce na ga kaima ka kafa taka zuri'ar tlkana rayuwa mai kyau kamar kowa” Ya kalleta da irin kallon na tausayinsata, ya san gaskiya take fada shi kanshi yanzu yana bukatar auren, kamar yadda ya san Mai Martaba ma yana son yai aure, a tattaunarwa da Hajiya Hadiza a dazu ta fada masa a yanzu Mai Martaba ba shi da wani abu daya wuce na aurensa. “Dada zan yi aure, indai wannan ne kawai burinki da na Mai Martaba ku kwantar da hankalinku komai zai wuce, zan yi aure inshallah” Ta zare hannunta daga tuwo tana kallonsa da idonta na tsufi zuciyarta cike da farinciki. “Yaushe? Allah yasa nan kusa ne ba nesa ba” “Yarinyar da na ke so, nan da wata bakwai zata gama makaranta, so idan ta gama na ke tunanin zan fara wani motsi a kanta” “Har nan da wata bakwai Zain? Anya zan kai har lokacin kuwa? Tana ta jin kamar ina kusada kabarina” “Haba Dada kowama yana kusa da kabarinsa dan Allah ki bar wannan maganar” “To kan san ita mutuwa ba ka sani ba, ba a sanar maka ba, rayuwa bata da tabbas ko ga yaro balle babba irina” “Zaki ga aurena har yayana zaki gani da yardar Allah” “To Allah yasa” “Amin” Daga ranar ya saka kansa a tunanin yadda zai showa kan lamarin jikinsa yayi sanyi da maganar Dada, domin Mai Martabaa irinra ya nanata masa bayan kuma Ibrahim ya dade yana masa maganar kusan ya fi kowa matsa nasa shi da Anty Ummi. ga shi kuma baya son ya fitowa Hafsat a yanzu har sai ta kammala makarantarta, sai dai a maganar da Anty Ummi tai masa a yau ma ta kara sashi cikin wani, cox ta fada masa halin da Hafsat take ciki na damuwa da rashinsa. “Zain ina ganin kamar cutar yarinyar, duk ta bi ta haukace akanka, zuwan nan da kai sai na gargadi Amal akan karta fada mata, saboda bata da lafiya zata iya daga hankalinta” “Karatun kawai nake jiran ta karasa, i will Surprise her” “A yanzun ya kama ka bata mamakin, ta yadda zata kare karatunta cikin kwanciyar hankali da natsuwa ba a cikin tunani da damuwa ba” “Bana son wani abu ya samu karatunta ne” “Me zai samu karatunta bayan tana final year, kuma tana tare da kai, haba Zain ko dan maganar Dada da Mai Martaba ya kamata kai wani ai” “Zan yi tunani akai, you know somtimes ina mamakin yadda yarinyar nan ta aje ni cikin ranta na tsawon lokaci haka, ina jindadin hakan da ace a halin da ake yanzu Hafsat ta manta da ni ba san wane hali zan shiga ba” “Ai be kamata ta manta da kai ba, Zain indai har zaka sadaukarda farincikinka akan wasu to kai ma ka cancanci farincikin na har abada” Ya dan yi murmushi yana tuna wasu abubuwan da suka faru a baya. *ONE WEEK LATER...* Kwananta uku a asibitin suka sallameta, sosai Abbah ya so ta zauna tare da su a gidansa na abuja ta kara samun sauki sannan ta koma gidan Hajiya Asma'u amman Momy ta hana tana ganin kamar Yayarta zata ga ba a mata daidai ba, zata ga kamar sun raina kulawar da take bata ne. Ga Raheem da ke ta kai kawo tun da aka kawota asibitin Momy ta lura da rawar kansa, already ta san manufarsa tun da Hajiya Asma'u ta taba mata maganar. Sai dai har a sallamota ko gaisuwar kirki bata shiga tsakaninsu da Hafsat ba, tana kula MB sosai amman bata kula Raheem saboda ya nuna yana sonta. A gidan aka dawo da ita, sai kukan shagwaba take yi ma Momy. A gidansu da ke Abuja suka kara kwana sannan wuce Kaduna. On her first day a gidan bayan an sallameta daga asibitin, tana zaune dakinta ita kadai feeling so boring. Beauty ta kirata. “Dear kina gida ko?” “Ee” “Ki shirya gani nan zuwa, zan ki rakani wani gurin” “Okay but bana jin karfi sosai maybe ba zan iya tafiya mai nisa ba” “Karki damu ba nesa zanje da ke ba” Daga haka ta aje wayar tana tunanin ina zasu kaita kuma. Daman sun saba haka idan dayansu yana cikin damuwa sun kan fita da shi dan rage kewa da yin walwala, sai dai nata is different tun ciwo ne. Like by force taje tai wanka ta shirya cikin godon riga domin gown, abaya suna cikin tufafin da tafi kauna kuma ta fi jindadin sakawa. Shiru shiru basu zo ba har aka kira sallah azahar, ganin hakan yasa ta fito falo daman can ba son fitar take ba. Sai kuma fitowar ma tai mata babu dadin ganin Raheem zaune. Tana zaunawa sai ya tattara dukanin hankalinsa ya mika gurinta kamar wanda aka cewa wani abun zata ce masa, kallonta yake sosai yana ayyana irin dadin da zaiji idan yau ta aminta da shi ta so shi kamar yadda yake sonta. Tana da kyau sosai irin kyaun nan mai daukar hankalin maza ga dan karamin bakinta da manyan idanuwa, when she smile her right side dimple will appear abunda yake kara mata kyau a duk lokacin da tai dariya, she's so slim just the way da yake son matarsa ta takasance. Jikinta ne ya bata yana nan yana kallonta kamar yadda ya saba, har ta unkura zata tashi sai ga Beauty ta turo kofar falon ta shigo fuskarta da murmushi. “Assalamu Alaikum” Ita kadai ta amsa mata, yayinda Raheem ya jingina fa kujera kamar be ga shigowarta ba. “Dear let go” “Yanzu? I tot ma kin fasa” “Ya za'ayi na fasa kin ga duka suna can suna jirana fa, daga ni sai ke ne babu” “Ina ne zamu je?” “Yafa veil dinki za ki gani ai” A tare suka shiga dakin, Beauty na rike da hannunta ta dauko mayafin ta sake janyota suka fita dan taga jikinta da sanya. A bakin kofa ta tsaya tana kallon Beauty. “Ban fadawa Hajiya ba, kuma bata son ina fita bam fada mata ba” “Fine kirata a waya yanzu, tell her za ki raka ni wani gurin yanzu mu dawo” A gurin ta kira Hajiya Asma'u a waya ta fada mata sannan taje ta shiga motar, ta window dake bude ta hango yadda Raheem ke kallonsa abunda ya kara bata mata rai dan ta tsanai yadda yake tsareta da kallo. Beauty ce ke driving, while ita kuma tana front seat. Bata wani gurin da bata sani va Beauty ta nufa da ita, kamar ta tambaya sai kuma tambayar tai mata wahala haka ta zuba hanya ido har suka karaso gaban wata katafariyar Hotel, wacce bata taba zuwa ba, sai dai tana jin labarinta. “Beauty me za mu yi a nan?” “You know ba mu saba zuwa hotel ba sai da wani dalili, so ya kamata mu zaga cikin wannan mu bawa idonmu abinci, muna ta jin labarin hotel din nan yau dai na ce musu ya kamata mu zo” “Amman ba irin wannan lokacin ya dace ba beauty, bana cikin yanayin da zan sake sosai a yanzu” “Kar wannan ya dameki” “Amman idan wani ya gamsu fa” “To miye a ciki? Ba fa rooms kawai ke cikin hotel din nan ba, akwai guraren da yawa, like garden restaurant, suya spot and many more, ke dai fita muje” Ba dan ta so ba, ta fita daga cikin motar suka nufi wani bangare na hotel din, kama shiga ciki zaka rantse da Allah dare ne domin babu inda hasken rana yake shigowa sai dai na lantarki, da sanyin ac. Jere suke suna tafiya Beauty na mata hirar Hotel din, tafiya suka yi mai dan nisa, tun tana jurewa har ta soma jin gajiya, wani gurin suka iso mai kamar garden sai dai ba shi da fadi sosai and akwai irinsa kusan guda ashiri a gurin, she has no idea yadda akai saman yai hudu kamar dare bayan kuma ta san rana ce suka baro a can waje. A wanda suka nufa an kawata shi da blue wuta and flowers, kyallin da ke jikin fulawar sai blinking yake. Saman gurin an kawata shi da taurarin da zaka rantse da Allah na gaske ne. Yar dogowar hanya ce da zata sada su da inda suka nufa an kawata hanyar da kyandir. Sai ta rike Beauty tana dan jin tsoro dan babu hansken wuta sai na kyandir. “Beauty kin san inda kika kawo mu kuma” “Na sani mana, ke dai biyoni kawai” Beauty ta fada tana yar dariya, she trust her friend ta san ba zata cutar da ita ba, hakan yasa ta bita amman ba dan hankalinta ya kwanta ba. Lokacin da suka isa gurin sai kamshi turaren da take sakawa da sanyin ac ya fara musu marhabun. Wani kyakkyawan dinning table ne mai zanen heart a gurin da kujera biyu, tsakiyar table din an dora kyandir mai zanen heart, kasan gurin kuma an zagaye ko ina da kyandir din, and duk abunda yake gurin was decorated in red color. Flowers da ke gurin tana da tsawo sosai ta tare su basa ganin kowa kamar yadda kowa baya ganinsu. “Beauty I'm scared, kin ce min sauran suna nan amman ban ga kowa ba, and why all this?” “You shouldn't be, zauna a nan bari na je na kira su” Ta rika ta zaunar zaman kujerar da ke facing din kofar shigowa gurin. “Ko dai muje tare” “No ki zauna yanzu zan duba su, bari ma na kira su, aro min wayarki tawa ba kati” Ya mika mata wayar hankalinta ya dauko da tsoron da take ji a gurin dan haka bata kawowa ranta tunanin taya za'ace wayar Beauty babu cati ba. Tana kallon Beauty ta tafi da sunan kiran Pearl, ita dai tana ta mamakin kawo su irin gurin nan bayan they are not lovers, and gurin ma ya tsorata, dan tasan halin friends dinta zasu iya tsoratata da sunan sakata farinciki. Shiru shiru bata dawo ba yasa ta fara counting in ta kai goma bata dawo ba zata bita, so she decided to close her eyes kar ta ga wani abun marar kyau. “1...2...3...4...5...” After courting ten ta bude idonta, abunda ta gani ta dauka tsarawa take kamar yadda take yi idan tana tunanin Zain, tafowa take inda take da wani irin taku na kasaita da burgewa. Tana ta kallonaa har ya karaso sai tai murmushi ta runtse idonta tana murza su. “I'm such fool” After seconds ta bude, and he was still there wearing a beautiful smile. Saurin tashi tai tsaye baki sake ta kai hannu ta taba fuskarsa. Ta ji alamar mutum ta taba but bat yarda shi din ne ba. “Maybe I'm blind har na fara ganin mutane da fuskarsa” Ta fada with emotional tears in her eyes. “No you're not PureHeart” Maganar da yai ta maimaita kanta sau ba adadi a kwalwalarwa kamin ta sadata da tunaninta har ta maye ilahirin jikinta. His sound, his face, his smile, his everything was there near her. Jikinta ne ya fara rawa hawaye na sauko mata, sai ya kara matsowa ya rika hannunta ya dora saitin zuciyarsa. “Feel it” Wani irin bugawa zuciyarsa take kamar yadda take tata, a lokaci daya suke sauke numfashi da dauka, just like their hearts da suke bugawa a tare. “I feel it” Ta fada in a cool way, with her very calm voice. Sai ta fashe da kuka tasa dayan hannunta ta rufe bakinta ta rumtse ido gam... [4/10, 9:45 AM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *61* Jin tai kamar kafafunta ba zasu dauketa ta saboda rawar da suke, and her right hand was still on his chest har yanzu bugun zuciyarsa take ji. Ganin zata fadi din yasa yai saurin rikota ya zaunar da ita har lokacin idonta a rufe suke. Hannunsa ya kai ya rika tafin hannunta, wani irin sanyi suka ji tare da wani irin abu mai kamar shocking a lokaci daya. Tai saurin bude idonsa sai ta sauke su cikin nasa, sai kwalla ta biyo baya, shi ma kallonta yake ido cikin ido, wani boyayen sako idanuwansa suke aikawa nata idanuwan, daga inda yake zaune yana jin bugun zuciyarta yayinda ita kuma take ganin motsawar kirjinsa. “You... You... ” Magana take so tai amman ta kasa muryarta sai tawa take da alamar akwai kuka a tare da ita. “Ba za ki iya magana ba, har sai wannan kukan ya fita daga cikinki, so let's cry” Sai kawai ta fashe da kuka tana ta kuka yana kallonta zuciyarsa na sosuwa da hawayen da ke zuba daga idonta. Handkerchief ya ciro a alijihunsa ya mika mata, sai ta karba ta share hawayenta. “Zain...” Ta kira sunansa, sai ya katseta tare da dora hannunsa saman bakinsa. “Shiiiiiiiiii” Sai ta lumshe ido. Tashi yai daga inda yake zaune ya zaga ta bayan kujerarta ya dora hannayensa saman kan kujerar ya risino da bakinsa daidai kunnenta. “Zat za ki ce” Bude idon tai tana murmushi da hawaye at the same time. “I hate you i hate you so much” “I know” Ta mike tsaye sai ta juyo ta kalleshi. Zata yi magana ya rigata. “Tell me one good reason da yasa kike boye kan ki a gareni?” Kai ta girgiza. “No nice ya kamata na tambayi wannan, Zain da gaske kai ne? Ya aka yi ka zo nan? Miyasa ka boye kanka na tsawon wannan lokacin? Mi nai maka? Ka san halin da na shiga? Kasan dariya nawa na rasa saboda kai? Ka san kalar hawayen da na zubar? A ko da yaushe da kai na ke kwana na ke tashi da son na ke rayuwa, baka kusa da ni amman ka zabbatar da ni irin azzabtarwa da wani be isa yai min ita ba, ko wane namiji na kalla kai na ke gani, a ko da yaushe rayuwar da zamu yi na ke ginawa, na yi alkawarin jiranka Zain ko da jiranka na nufin ajalina ko kuma wata rayuwar da tabam, da zaka shekara dubu kana boye min kanka zan jekara dubu da daya ina jiran ranar da zaka dawo gareni, no matter how this thing we got turns out, i'll never regret one minute of it and I'll always love you, ina ganin kamai mafarki ne wasu sun kirani mahaukaciya akanka Zain, wasu kuma sun karyata ni, yayinda wasu suke ganin ina ga bata lokacina ne kawai, Zain you are the only one person I want to be with for the rest of my life and grow old with i love you...” Tun da ta soma maganar yake kallonta, and he didnt see just her, he saw his today, her tomorrow, and his future for the rest of their life... “Idan har zan iya ayyana yadda cika mamaye da cika a zuciyata, to ba son ki na ke ba kaunar ki na ke, ita ko kauna bata da abun kwatantawa a so ma balle har ya kai gareta, na rayu da ke a kusa da ni” Ya dafa zuciyarsa. “Komai a tare da ke nake, ina yawan jinki a kusa da ni, saboda kina cikin ruhina a zaune, ma so ki tun ban yarda son zai kara min amfani ba, na kaunatace ki a lokacin da bam yarda zata nemi haduwa da ke ba, ban za ci ruhuna zai cilastani neman gangan jikinki ba, Ruhin Zain da na ki a tare suke, shiyasa muka kasa samun natsuwa da sukuni har sai mun nemo junanmu, ban so ki na rayu da son ki ba, na so ki ne dan na kasa rayuwa idan babu shi all those years I'm in so much pain saboda ba ki a kusa da ni, i know everything about you in and out...” Ta hade kukan da ke cikin tana share hawayenta. “Amman miyasa kai haka? Na kasa yarda kai ne Zain ko dai wani aljanine yai min irin siffarka...” Kafarsa daya yasa ya taki kafarta har sai da tai kara. “Nine dai Pure Heart, zauna sai nai miki bayani” komawa tai ta zauna shi sai ya zauna a kujerar dazu, a hankali ya fara zayyana mata komai dalilinsa na boye kansa da kuma gaskiyar abunda ya faru tsakaninsa da mahaifinta. “All those years mun rayu a karkashin inuwar so daya, zuciyoyinmu sun rayu a tare, a lokacin da ni na ke rayuwa da ruhinka, kai kuma kana rayuwa da nawa, i wonder what kind of love is this” Ta fada cikin kuka. “Wani kalar so ne, wanda jarumin baya da wanda zai zo gaba ba zai yi irinsa ba, ba za a buga tahirin wata sarauniyar mace mai son wani namiji kamar yadda ke kike son Zain ba...” Hannunta tasa ta tare bakinta ta lumshe tana jan numfashi a hankali. Zuwa can kuma ta bude za ta yi magana sai ta hango friends dinta take ko wannensu fuskarsa dauke da murmushi, and dukansu sun yi boye hannayensu baya. Suna karasowa ta soma musu magana cikin muryar kuka. “Why all this? Miyasa ba ku fada min? Ashe kun san yana nan amman kuka boye min?” “I'm sorry” Beauty ta fada tana fiddo madaidacin kwali mai rubuce da sorry a jiki, sai kuma ta juyo da shi gurin red paint. *Will* ne rubuce a jiki, Pearl ta juyo nata *You* na Diamond ma *Marry* Sai ya nuna kansa dayan hannunsa rike da box din ring. Mikewa tai tsaye sai ta fashe da kuka ta juya musu baya duka ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta, yau kam komai kamar mafarki take ganinsa har yanzu ta kasa yarda ba mafarki take ba. “Yes yes yes...” Ta furta tana juyowa tare da mika masa hannunta ya saka mata ring din. Sai ta nufi gurin su Beauty da sauri tana kokarin rikasu. “Take me home, lemme wake up from this dream” Duk dariya suka saka mata, suna tayata murna ita kuma hawaye kawai take kanta na jikin Pearl, dake rike da ita kofar fita suka nufa da ita sai kuma ya waigo ta kalli Zain. “I love you” Ya furta by his lips not by voice. Ta yadda ita kadai za ta fahimci sakon da bakinsa ke isarwa. Har suka isa gida bata yarda ba mafarki take ba, babu yadda ba su yi ba a mota dan tabbatar mata da cewar gaske ne ba mafarki ba, amman sam ta kasa yarda. Har dakinta suka shiga da ita suka kwantar da ita saman gadonta. Sannan suka fito ba tare da sun fadawa Hajiya gaskiyar abunda ya faru ba, sai dai sun mata karyar zazzabinta ne ya tashi, abunda ya tashi hankalin Raheem sosai. “Daman ni ban so fitarta dazun ba, zuciyata nata raya min wani abun zai faru” Ya fada yana tashi ya nufi dakinta, kallon kallo suka yi sannan suka fice faga falon, Hajiya Asma'u ta tashi itama ta nufi dakin Hafsat, dunkule ta sameta da bargo tana ta rawar sanyi. “Subhanallahi ai ba mu ga ta zama ba tashi muje asibiti” Hajiya ta rikata sai ta ji jikinta ma da zafi sosai. Hajiya Asma'u ce ta rikata suka sauko kasa, sai ta zaunar da ita saman kujera take ta dauko Hijab dinta ta saka sannan rikata suka fita, ko da suka fita Raheem ya janyo mota har gaban kofar falon sai suka shiga gidan baya ita da Hajiya, har aka isa asibitin zoben hannunanta take ta murzawa daga Hajiya har Raheem babu wanda ya san da zaman zoben a hannunta har aka bata gado,  a take likitan yai mata allurar bachi tare da saka mata drip da maganin a ciki, sai bachi yai gaba da ita. Bata san iya awanin da ta dauka tana bachi ba, sai dai ta farka cike da jin gajiya kamar tayi wani aiki, hasken waje ya shigo ta cikin window wanda hakan ke nuna rana ta yi. Abunda ya faru ne ya fado mata a sai sai tai saurin duba hannunta zoben na nan har yanzu a hannunta, tashi tai zaune tana dariya ta shiga murza zoben, dafe kirjinta tai tana cigaba da dariya. Tana kokarin sauka saman gadon sai ga Hajiya Asma'u ta turo kofa ta shigo dauke da kayan abinci. “Mashallah Hafsat kin farka?” “Eh Hajiya, ban san idan na fada miki wani abu ko zaki yarda ba” Ta zauna kusa da ita cike da mamaki. “Fada min minene?” “Jiya Zain ya zo?” “Ya zo ina?” “Lokacin da kika fita din nan har ma kiraki na ce miki zamu fita da friends gurinsa suka kai ni, look at this shi ya saka min” Ta nuna mata zoben. “Anya Hafsat kin san abunda kike fada kowa?” “Na sani Hajiya, nima abun ya xo min kamar mafarkine, shiyasa ma zazzabi ya rufe ni” “Idan har da gaske shine miyasa ya boye kansa be fito ya ganki a inda kowa zan ganku ba? Anya mutumen yana son ki kamar yadda kike son sa kuwa? Mutumen daya shekara nawa ba tare da ya nema ki ba, rana daya ya dawo kuma ya samu wani guri daban inda ba gidanku ba ya gana da ke, a haka din kuma kike alfahari da yana son ki?” “Ya boye kansa ne saboda na samu nai karatu, kuma ashe Abbah ne ya nemi ya yantar da ni tun farko shiyasa baya zuwa gurina” “Me kike nufi?” A nan ta bayyana mata komai kamar yadda zai ya bayyana mata, Hajiya Asma'u ta yi farinciki sosai da jin hakan domin tana ganin ita ma danta zai iya samun Hafsat, kuma tana da tabbacin kanwarta Rufaida ba zata watsa mata kasa a ido ba, daman a can baya tana tunanin ko akwai alaka tsakanin Hafsat da Zain ne, amman tun da ta gada mata an yi mukatima ta san yadda zata bullowa kamarin. “Amman na jidadin wannan maganar, gaskiya mahaifinki yayi tunani mai kyau kuma yayi abunda ya da ce”  Ta fada tana kallonta fuskarsa dauke da murmushi. Hafsat ma murmushin take mai cike da farinciki da annashuwa. Ji tai tana son sake ganinsa wani irin shaukin kaunarsa ke ta karuwa a zuciyarta. “Mutumen da ke miki son gaskiya ba zai ta boye kansa har na tsawon wannan lokacin ba, wai dan kawai ki samu karatu, yanzu kuma daya tashi ganinki sai ya kebe da ke wani wajen daban inda ke da shi kawai za ku ga juna, da da gaske yake aurenki ya kamata yai kuma gurin iyayenki ya kamata ya fara zuwa, abu na karshe kuma ba zai boye kansa garemu” Hajiya Asma'u ta fada ta siffar da Hafsat zata fahimce ta. “Wata kila ya boye kansa ne saboda ba d gaske yake ba, tun da shi sannanen mutum ne, kin ga yana gudun a ganshi da ke as his wife, so wani abu ne da mutum baya iya rayuwa har sai ya saka wanda yake kauna a idon, bari na buga miki misali da ke kanki, tun yaushe kike bibiyarsa? Kina ta jin kamar idan ba ki ganshi ba za ki iya rasa ranki? Awa daya idan kika yi ba a gida ba, Raheem yana damuwa Hafsat, sai dai yana yin taka tsantsan saboda ni da shi duk a tunaninmu kina da karkashin Zain ne...” “A yanxu ma karkashinsa na ke Hajiya, saboda zuciyata tana can tare da shi, bana iya kallon wani namijin da sunan so, da ace Zain ya mutu kamin ya dawo gareni, da haka zan mutu ina ta zaman jiransa har mu riski juna a can, Hajiya so wani abu ne da baya iya bari ka ga laifin masoyinka, Zain ya so ne, tun kamin na san rana zata zo wacce zata kawo na zauna a gidanki har Raheem ya gan ni ya ce yana so na, mutumen nan yana nan raye kuma sai ki tsammaci zan so wani bayan shi? Wallahi ban ki Raheem dan wani abun ba, sai dan dalilin daya hana ni ganin ko wane namiji kyakkawa...” A hankali Hajiya ta sauke ajiyar zuciya. “Allah ya zaba miki abunda ya fi zama alheri, idan kin karya likita zai sallameki” “Na gode” Ta furta tana share hawayen idonta. Sai Hajiya ta tashi ta fita cikin yanayi marar dadi. Bandaki kawai ta shiga ta wanke fuskarta ta fito, bata iya cin komai ban banda aikin tunanin abunda ya faru har Hajiya ta dawo. Basu kara minti talatin ba likitan ya shigo ya basu sallama, kamin a isa gida duk ta bi ta matsu domin wayarta ce a ranta tana son ta dauki wayarta akwai abubuwan da take son tambaya gurin kawayenta. Ita da Hajiya Asma'u suna baya, Raheem kuma yana driver side yana jan motar. Ta madubin gaba yake kallonta yana jin wani irin abu a kirjinsa kamar zuciyarsa zata rabe. Wayar Hajiya Asma'u ce tai ringing, ganin number Rudaida yasa gabanta faduwa sai dai hakan be hanata daukar wayar ba. Sallama tai suka gaisa sannan ta tambayeta ko Hafsat tana kusa da ita. “Ee gata a nan lafiya dai?” “Lafiya kalau ina ta kiran wayarta bata daga ba, ina son na tambayeta wani abun ne” Sai Hajiya Asma'u ta mika mata wayar. “Ga mahaifiyarki” Karbar wayar tai ta kara a kunnenta da murmushi da kuma zumudin. “Hello Momy ina kwana” “Lafiya kalau yar Babanta da Zain” Hafsat ta yi murmushi kamar ta labartawa Momy abunda ya faru sai tana kunyar Hajiya Asma'u, sai ga shi Momy ta yi mata maganar da ta fi wacan dadi. “Abbahnki ya ce a tambayeki, ko kin san da zuwan magabatan Zain? Ke kika ce su turo?” Shiru tai gaba daya jikinta ya mutu, ba mutuwa irin na tsoro ko fargaba ba, mutuqa irin na wanda burinsa ya cika komai ya zo mata kamar mafarki. “Baby are you still there” “Momy you already killed me” “Congratulations, you will be engaged today” Momy ta fada tana dariya, sai ta kashe wayar a daidai lokacin da Raheem ya faka motar a harabar gidan, fita tai bayan ta mikawa Hajiya Asma'u wayarta tana hawayen da bata san na minene ba. A dakinta ta shiga ta kwanta saman gado tare da jan fillo ta rumgume ta lumshe ido, bata iya ayyana yadda take ji a yanzu loving someone and having them love you back is the most precious thing in the world. [4/12, 1:20 AM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *62* A baga dayan masarautar babu wanda baya murna da farincikin auren da Zain zai yi, Mai Martaba ya fi kowa farinciki shi da Dada daman sun dade suna jiran zuwan wannan ranar, duk kuwa da kasancewar sun so a saka bikin auren ne a kusa amman Abbah ya ki yarda saboda karatunta, ganin tana final year ne, ya fi son sai idan ta gama sannan ai auren wanda ya kama December 25th. A bangaren Anty Ummi ma farinciki ba a magana, domin abun ya zame mata biyu, dan'uwanta, da yar dan'uwanta, har ta kan kasa misalta wane bangaren zata zaba. ***      ***     *** Babu wanda baya mamaki da jin wanda Hafsat zata aura, masu daukar abun nata na hauka yanzu sun gasgata, kowa yana farinciki ban da mutum biyu. Raheem da mahaifiyarsa, tun daga lokacin da aka saka rana sai mahaifiyarsa ta tsanwace ta zaman gida ita da danta. Hakan yasa ta baro Abuja ta dawo Kaduna kusa da iyayenta inda take samun kyakkawar kulawa. Kawayenta ba su jidadin tafiyarta ba, amman a dole suka hakura tun da babu yadda za suyi duk wani abu da za ayi ta waya suke yinsa. But they both miss each other. Ba tai sati biyu a kaduna taje gusau gurin twins sisters nasa, wato Hassana da Husaina, rabon da taje gurinsu tun rasuwar Hajiya Safiya that was eight years ago kenan, they spend seven years suna jinyarta a gurinsu kamin ta Allah ta kasance, sai dai har ta bar duniya bata ji sauki amman Abbah yana bata dukan kulawar data dace, duk wani magani da aka yi siya mata a cikin aljihunsa ne, and every two weeks yana shiryawa shi da Momy da Hafsat suje duba har ta bar duniya, abunda ya kara hada kansu kenan suka kara kaunar junansu sam ba zaka ga yadda Husaina take son Hafsat ka ce ita ce tai ta challenging yar'uwarta a court dan a jefa rayuwar Hafsat cikin matsala ba. Ita kanta daga baya abunda tai ya dame ta kuma ta ji kunya, ganin yadda Rufaida ta rikesu kamar yayan cikinta kuma bata taba nunawa mahaifiyarsu kyama ba duk kuwa da irin halin data sakata, sai ta barta ta halinta tana ta girbar abunda ta shuka. Ba zuwan ziyara ga yan'uwanta kawai taje ba, zuwan nata mai babban dalili ne, domin Zain tai yi shi ya fada mata in the next three days zai yi birthday @43. A da be yi niyar yin birthday a nan ba, sai dai jin zata zo din yasa ya yanke shawarar yinsa a Nigeria. Bata fadawa kowa birthday sa ta zo ba, kamar yadda ta ji kunyar takawa taje saboda gidansu yai birthday din, kusan duka sisters dinsa na cousins da suke kusa sun zo birthday din. Duka abubuwan da aka yi a ranar sai a wayarsa ta gani lokacin da ya zo gidan da dare. Nata cake din ta hada masa mai sunansa sunan da take kiransa da shi a can baya wato Zat, yayi farinciki kuma yayi dariya sosai idan ya kalleta yana tuna baya, sun dade suna fira a kamin yai mata sallama ya wuce, tun da ta zo kullum sai ya zo fira wani lokacin da Ibrahim wani lokacin kuma shi kadai, amman duk zai tafi sai yaji kamar zai yi nisa da ita ne sosai. One week tai a sokoto ta koma Kaduna saboda exam din da zasu fara, bata dade Kaduna ba ta wuce Abuja, A gidansu Beauty ta zauna dan ba zai yiyu ta zauna a gidan Abbah da ke can ba saboda babu kowa gashi kuma bata jin dadin zama a gidansu Hajiya Asma'u. Hakan da Hafsat tai sai yasa ta jin babu dadi, ta san bata kyauta ba na kin sake mata fuska da kuma takurawar da take mata amman ita tafi ganin anfi yi mata rashin kyautawar na kin aura ma Raheem ita. Ita da kanta taje ta dawo da ita gidan ba dan komai ba sai dan kar zumuncinsu ya lalace kuma a zageta ace ta hana yar kanwarta zama gidanta.    Zaman wannan karo wanda ya kasance na dan kankanen lokaci yafi ko wane zama yi ma Hafsat dadi a gidan, kasancewar Raheem bata takura mata tunda yaji ta dawo gidan sai ya dauke kafarsa, har ta gama Exam da duk wani abu da zata yi ta dawo Kaduna sau hudu kawai ta saka shi a idonta, dan dauke kafarsa yai daga gidan baya zuwa a lokacin da yasan tana gidan sai idan tana makaranta ko wani wajen daban.   Kamar wadanda akai ma mutuwa haka suka rabu dukansu suna kukan rabuwa da juna, ba rabuwa suka yi na har abada ba, amman sun san kusancinsu ba zai yi kamar na da ba.   Batai wata daya da dawowa ba aka kawo lefenta cikin masu kawo lefen har da Anty Ummi, lefe na gani na fada you know abunda ya fito daga gidan sarauta ba sai na zayyana muku ba a kwai expensives abubuwan and lot. Su kansu gurin karbar lefen zaka dauka wani karamin bikine ake, ko kuma ace babban biki a gidajen talakawa. Ta bangaren taron jama'a ta bangaren abubuwan da aka ci aka sha kuwa ba za a iya lissafasu ba, not just lefe suka kawo har da kayan sa lalle da komai da komai domin bikin is near. ***   ***   *** Tun da Hafsat ta koma Kaduna saboda scul shi ma ya koma Paris saboda aikinsa, a ko da yaushe cikin waya suke, su yi chat amman be hanasu missing din suna ba, be dawo ba sai da ana saura one week ayi bikin sannan ya dawo, duk wani shirye shirye da ake na bikin Ibrahim ne yake yi a madadinsa, wanda kuma iyaye ne ya kamata su yi already sun yi nasu.    Ya dawo on Saturday aka yi sa lallebon Wednesday, Thurday akai friends evening, Walima akai Friday a ranar akai yi ma amarya lalle da kitso, Washe gari Saturday aka daura aure a garin Kaduna babban masallacin jumma'a da ke garin Kaduna, daurin auren daya samu halarta manyan mutane yan'siyasa yan kasuwa da kuma ma'aikatan gov... A ranar a kai mothers day da yamma akai wanki amarya lalle sannan aka kama hanyar Gusau da Amarya bayan iyayen da gwaggowani sun yi mata huduba, kuka sosai momy tai wanda zaka kasan gane na minene? Farinciki ko bakinciki rabuwa da yarta. Sun isa Zamfara late saboda jirgin be taso da wuri ba. A masarautar Rishim akai ma Amaryar kuma surukar fada tarba mai kyau, a fadar Mai Martaba aka fara shigowa da ita, sai gwaggonin Zain suka shigo da Dada Yalwa, suka budewa Amaryar kai suka saka mata turare kamar yadda al'adar masarautar ta tanada. A bangaren Hajiya Hadiza aka wuce da ita bayan an gama zaman fada, a nan Amarya ta ci abinci tare da yan rakiyarta sannan ta sake wanka ta shirya cikin wasu tufafin da alkyabba sannan aka zo da ita dakin Hajiya Zara, da Hajiya Maryam suka mata hudu, sai aka sake maida ita gurin Mai Martaba, yai mata huduba da nasiha akan zamantakewar aure. Sai kuma aka kaita gurin Dada Yalwa, tai mata nata huduwar, Dada har ta kukan tana tuna abubuwan da suka faru a baya, a dayan bangaren kuma kukan nata na farinciki ne yau ta sake ganin matar da Zain yake son kuma ya aura.    Bayan an fito da ita daga masarautar Rishim, aka dauki hanyar GRA ring road da ita. Haka aka jera motocin kaita kamar motocin saidawa babu shege a ciki balle yar'iska duka manyan motoci ne na alfarma. Har aka isa da ita gidanta kuka take abunda kowa be sa ran zata yi ba, tana kukan rabuwa da iyayenta ta san ba ta bar su bane har a bada amman ta nisanta da su, wata sabuwar rayuwa zata fara, duk irin daukin auren da take be hanata kewar iyayenta ba.    Babban gidane wanda idan za a kasa shi zai yi gidan hudu, amman aka hade akai yi gida daya, fentin gidan sky blue ne mai kyau, ko ina na gidan fulawoyi ne da shuke shuken itace ko'ina na gidan haske ne kamar rana.      Tsayawa fadin yadda aka tsara falon da kayan alatu bata lokaci ne, domin babu abunda aka siye shi a naija duk na abroad ne, har spoon din cin abincinta Abbah be yarda an siye shi a nan ba, sai waje. Balle kuma furniture da kayan kitchen, royal chairs aka saka mata like her dinning table. Ga wata uwar wallpaper da aka saka mata mai kyau da daukar hankali, an kawata falon da kayan kawai na zamani da mutum zai iya tsammanin a wata kasar yake idan yana ciki, kasancewar left and right side na falon an yisa ne da glass mai kamar fulawa, ga wani tattausasan Center carpet da aka saka mata a tsakiyar falon. A dakinta Turkish furniture aka saka mata and all the room was decorated with red curtain and red Center carpet just like her bed, everything was so perfect and beautiful.    A gefen gadon aka zaunar da ita her friends and relatives sa suka rakota suna tare da ita, da kuma wasu yan'uwan Zain, around eleven wasu suka fara watsewa, sannan aka shigo da Ango tare da abokansa. A bakin gadon ya zaune yayinda ita kuma take zaune a a tsakiyar gadon kanta a sukune ta rufe kanta da alkibbar da aka saka mata a fada.   Duk wani abu da akai na siyen baki da wasanin da kawayen amarya ke yi da abokan ango har akai aka gama bata dago ba, she's just smile tana wasa da yatsun hannunta. Bayan ya raka abokansa ya dawo dakin ya zauna bakin gadon kamar dazu fuskarsa dauke da murmushi, sai kuma ya leki fuskarta sai tai saurin saka hannayenta ta rufe fuskar. “Komai ya zamo mana kamar a mafarki, ban tsammaci zuwan wannan ranar ba, amman Allah ya tsara mana komai” Sai ta sauke hannayenta ta kalleshi. “Ni kan na tsammaci zuwanta, domin na san komai daren dadewa wata rana zata zo wanda zan kasance Amaryar a guri mijin da zan aura, kuma ina da yakinin Allah ba zai min zaben da be dace da ni ba” “Ko? Nikam kin ga ban dauka zan aureki ba, dukan abunda ya faru a yanzu ban kawowa raina zai faru ba” Ya fada yana kokarin saka hannayensa ya janye mata alkibar da ke jikinta. A tare suka yi sallah suka gode Allah tare da addu'ar neman tsari, sai da suka zauna suna cin ya kara ganin irin kyau da tai, hannayenta sun san kumshi ga kanta ya sha kitso jikinta har wani shining yake. He feed her just the way da ita tai feeding dinsa, bayan sun gama ya fita daga dakin yaje dakinsa ya canja tufafin jikinsa zuwa na bachi, wanda hakan ya bata damar canja nata ita da saka rigar bachi pink color. Ko da ya shigo ya tarar har ta kwanta saman gadon, sai kawai ya kashe wutar dakin ya kwanta bayanta. (Ban yi aure ba, so ban san yadda first night take ba 😜 beside kowa ya san idan akai aure abunda yake faruwa so no need to write 🤗) After sallah asuba suka sake komawa bachi, misalin takwas ta farka, bayan bayanta baya ma dakin gaba daya, cike da karfin hali ta sauko saman gadon da zimmar shiga bathroom amman jikinta ko ina yayi tsami, tana mikewa tsaye ya shigo dakin rike da kofin tea. Saurin aje tea yai ya nufota ta rikata. “Ina za ki je?” Ya tambaya bayan ya rikata ta Kwanto jikinsa. “Bathroom” Ta fada cike da shagwaba kamar za ta yi kuka. He kiss her forehead. “Bari na kai ki” Hannayensa ya saka ya dauke ta cak kamar ya baby ya kai ta toilet din ya aje kissing her neck, sannan ya fita daga bandakin. Ta kusan awa daya a toilet din tana gasa kanta sannan tai wanka ta fito daure da tawul, sai a yanzu take jin kunya, a idan tana tuna abunda ya faru sai tai murmushi wani abun kuma ya bata kunya, ji tai kamar ba zata iya kara hada ido da Zain ba, har ta shirya kanta be dawo dakin ba, ita kuma bata daina taro abunda ya faru ba a daren jiya ba, zuwa wayewar garin yau. Door bell aka danna tana jin lokacin da ya fita daga dakinsa yaje ya bude kofar, bata san me ba amman ta dan ji hayaniyar sisters dinsa, kamin wayarta tai ringing. Ganin number MB yasa tai saurin dauka tana murmushi, “Hello” “Amarya yar hutu, na san yanzu ma ba ku tashi ba ko?” “Mun tashi tun da asuba ma” “Aa ba zan yarda ba gaskiya, babu angon da za a kaiwa amarya kyakkyawa irinki, ace kun farka tun da safe ba zai yiyu ba” “Laaa baka yarda ba?” “Ya za'ayi na yarda? Ai ko qur'ane kika dafa min ba zan yarda ba, yanzu dai fada minnya gaji kuma ya angon na ki?” “Lafiya kalau muke, ina madam dinka?” “Tana nan lafiya ta ce a gaishe ki” “Ina amsawa na gode” Tana aje wayar Zain ya shigo dakin. “PureHeart ta so mu ci abinci, ga breakfast can an kawo” Ya fada yana dafa shoulder dinta yana kallon fuskarta ta madubi. Ita kuma ta kasa hada kasa hada ido da shi. “MB ya ce na gaishe ka” Ta fada tare da Mikewa tsaye. “MB” Ya nanata sunan yana tuna lokacin fa ta fada masa abotar da ke tsakaninsu. “Yeah wannan friend din nawa” “Na gane shi” Ya fada yana kokarin riko kwankwasonta. “Bana son ya kara kiranki dear, kin yi aure a yanzu so karki sake kulashi ni ban yarda da wani friendship ba tsakanin matar aure da mijin aure” “He just my friend” “It's not just.. Duk abunda musulunci ya ce mu bari ko mu gujeshi barinsa shi yafi, ni fa ina da kishi kuma ba zan so wani abun da zai kawo matsala a tsakaninmu ba” Ya fada yana goga mata hancinsa a gefen fuskarta tare da zagaye cikinta da hannayenta. “Fine, i will talk to him zan fada mishi kar ya sake kira mijina baya so, indai har hakan zai saka farinciki” Sai da yai mata kiss mai kara a kunne sannan ya ce. “Yes na fi son hakan, not just call har chat karku yi” “Yes Mi Omri” Hannu tasa ta ture masa fuska jin yadda yake cizon kunnenta. A tare suka karya da abinci da aka kawo musu, a gidan Mai Martaba da kuma na Anty Ummi. Bayan sun gama suka sake shiryawa cikin kayan alfarma, mai Martaba ya aiko da mota da dogarai aka je da su. Ko da suka je sun samu fadar makil da mutane, bayan sun gaisa da Mai Martaba ya sake yi musu nasiha da jan kunne sannan ta wuce sashen matansa. Sai da yamma akai hawan amaryar kamar yadda al'adar masarautar Rishim ta gada na yi ma sukukarta busa da wata wasar hawan dawakai wanda ake kira da hawan Amarya. Duk abunda akai aka gama Hafsat bata a cikin walwala saboda har yanzu bata daina jin zafi ba, tafiyarta ma idan ka kura mata ido zaka gane komai, dan bata tafiya kamar yadda ta saba, sai dai ba kowa ya kula ba kasancewar tafiyar yayan sarakuna take dai-dai da dai-dai. An gabatar mata da yan'uwa da kuma wadanda suke da muhimmanci a masarautar duk ta gaisa da su, wani iri ta ji lokacin da bayin masarautar da yan'uwan Zain suke ta bata girma, ko a nan kadai ta san ta yi sa'ar aure domin kuwa ta yi aure gidan da suka san muhimmancinta kuma suke son ta kamar yar gidan. Kusan kwana uku aka jera kullum da kalar abunda ake a fadar, a daren na uku ne akai liyafar cin abinci tare da addu'ar neman tsari da kuma albarkar aure. Bayan gama bikin fada, sai gaisuwar yan'uwan ta biyo baya, kusan kullum sai Mai Martaba ya aiko da mota da dogarai da bayi anje da ita gurin gaisuwar gwaggwanni da iyaye, bayan ta gama kuma kannensa suka biyo layi, daman haka al'adar take, surukar fada zata je ta gaishe da iyayen mijinta da gwaggwoninsa, su yi mata kyauta da alherai kala kala, kannensa kuma za su zo su gaisheta tai musu kyauta da tarba mai kyau. Bayin da aka aje mata ne suke fada mata irin abubuwan da zata yi, a gidansu ba a san da wannan al'adar ba, Zain kuma be fada mata ba, duk wani abu data dauka ta bawa yan'uwansa daga bangare Hajiya Hadiza ya fito da kuma Dada Yalwa. A month later suka bar kasar zuwa paris gurin da mijinta yake aiki daman can paris na daya daga cikin kasar fa Hafsat take da mafarkin zuwa, ta yi farinciki sosai lokacin da ta bude ido ta ganta a kasar with the love of her life. Hakan ya hanata bachin kirki cikin dare already ta gaji ga kuma Zain daya hanata sukuni, daukin zuwa paris ma be barta ba, she wake up early a lokacin da Zain yake ta sharar bachi, kamar like shi ya gaji ba ita ba. Dan karamim jean ne a jikinta wanda ya tsaya iya guiwarta, sai yellow vest mai siririn hannu, ta maida hankalinta sosai kan abunda take, amman tana jin kamshin turarenaa sai ta juyo da sauri ta kalleshi. Jingine yake jikin kofar kitchen din ya rumgume hannayensa yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi. Ita ma murmushin tai masa ta kanne masa ido daya. Cheek dinsa ya nuna mata. “Good morning kiss” Cup din hannunta ta aje ta karaso kusa da shi tai dage ta manna masa kiss din a kunci. “Good morning Mi Omri” Ta fada tana watsa da hancinsa. Sai yasa hannayensa ya zagaye kwankwasonta. “Morning how was your night” “It was so much fun” “Ohhh a kara kenan ko?” Ya dage gira daya with smile. “No i mean it was boring” “What?” Yayi fuskar shanu. Sai tai saurin rufe bakinta. “No i mean nice” Yar dariya yai ya juyar da ita ta bashi baya ya saka hannunsa cikin vest dinta. “Me kike dafa mana?” “Pizza” “Oh no Pizza at this early morning?” “To fada min abunda kake so bayan indomie” “Indomie kawai na ke so” “No ba za mu sake cin indomie ba” Ya dora kansa saman wuyanta still yana ta yawo da hannunsa a tsakanin cikinta zuwa kirjinta. “You know ina son indomie sosai tana tuna min da ke a duk lokacin da nake cinta it's my favorite” “It's my favorite too amman yanzu bana sonta” “Why” Ya tambaya yana lumshe ido tare da dan cije bakinsa. Sai ta juyo ta dora hannayenta saman wuyansa. “Saboda kai na ke cinta and now I'm with you, kai ma kuma saboda ni kake sonta kuma yanzu gani a kusa da kai, so we're each other favorites ,we don't need indomie anymore” “Really” Ya fada yana dora goshinsa saman nata. “Yes” Hancinsa yake goga mata kamin ya kai bakinsa ya tsotsi lebenta na sama. Tsalle tai ta lake kafafunta a kunkurunsa shi kuma ya kara dagota da kyau kamar wata baby. Jikin door din kitchen din ya jingina da ita yana romancing dinta sannan ya sauke yana shafa kitson da ke kanta. “I love you” Ya furta kamar mai rada, sai a lokacin ta bude idonta ta ta kalleshi. “I love you too” A gida suka wuni, kasancewar sai Monday zai koma aiki, washe gari kuma ya zaga da ita cikin garin ya nuna mata places da dama da bata sani ba. Wasa wasa ta fara sabawa da garin har guraren da bata je ba a da a yanzu duk taje domin week yana fita da ita ya kaita guraren bude ido da kuma shakatawa. Idan kuma suna gida suna a kujera daya a guri daya, every day a bayanta yake kwana ko kuma ya kwanta tana kirjinsa har garin Allah ya waye, wanda ya riga tashi a cikinsu shi zai hada breakfast. Bata da gurin zama sai saman kafafunsa a tare suke cin abinci har wanka tare suke, they spend two years together a paris suna ta rayuwarsu ta jindadi da farinciki. *** *** *** A duk yadda take daukin zuwa Nigeria ganin familynta, sai tafiyar ta fita a kanta ta kuma mata babu dadi, saboda damuwa da kuma kukan rashin Dada Yalwa da Zain yake ta yi, ita kanta bata farinciki da tafiyar ta zame mata ba dadi domin ta mutuwa ce ba ta ziyara ba kamar yadda take so. Irin taron da suka tarar a masarautar Rishim har tsoro ya bata kana gani kasan babban mutum ne ya rasu, duk yadda Zain yayi kokari danne zuciyarta sai ya kasa saboda yayi babban rashin da babu wanda zai maye masa gurbinsa har gaban abada. Da ita kadai ya rayu ita ta raine shi tun be san komai a duniya har ya kawo yanzu. Kukan da Zain yai kusan shi ya saka kowa kuka cikin har da wanda basu yi niyar kukan ba a kokarinsu na danne zuciyarsu. A masarautar akai mata sallah bayan anyi mata sutura, babu kalar addu'ar da Zain be mata ba, Mai Martaba ya nemi alfarmar aka zo da Hameeda daga prison ta ga gawar Dada tai mata addu'a da kuma bankwana sannan aka maida ita, a lokacin da aka dauki gawarta za a bar gidan ta ita sai yaji kamar ya rikota ya tasheta ya dawo da ita. Har akai amsar gaisuwar aka gama Zain baya cin wani abun kirki babu komai a zuciyarsa sai tunanin Dada Yalwa, idan har ya ci abu mai nauyi sai idan Hafsat ce ta tsare da abincin ta saka shi gaba tai feeding dinsa. Satinsu biyu a garin Gusau, har lokacin ba a daina zuwa musu gaisuwa ba, ana saura sati daya su koma Zain ya kai Hafsat Kaduna gurin iyayenta ta gansu, a ranar da ta dawo ta sha wahala sosai saboda aman da tai ta yi kamar zata amaye hanjin cikinta, sai da aka mata allura sannan ta samu bachi. Washe gari sai ta tashi da karfin jiki, daman Zain ya fada mata tun tana Kaduna cewar idan ta dawo zasu je gurin Hameeda, kasancewar Friday zasu koma. Daga ita sai shi ne a motar sai kuma direban da yake tukasu, ita dai kallonsa kawai take tana kwatanta irin bakinciki da damuwa na rashin da ke ransa, wani mugun tausayinsa ne ya kamata, a hankali ta kai hannu ta rika hannunsa, sai ya matse hannun nata gam ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya, ita kuma ta kwanto jikinsa tana kallon titi har suka isa. A dayan bangaren ta fito shi kuma ya fita a dayan bangaren sai ya zagayo gefenta suka jera suka nufi ciki, direbansu na a baya rike da manyan ledodi. Suna zaune a inda aka tanadar dan zama masu kawo ziyara aka fito da Hameeda. Kallo daya tai ma Hafsat ta dauke kai bata a fada wacece matar da Zain ya aura ba, iyajar abunda ta sani Zain ya yi aure domin yan'uwansa da suke kawo mata ziyara suna fada labarin abubuwan da ke faruwa, cikin kuwa har da Dada Yalwa wacce ke kawo mata ziyara every week. Sam bata gane Hafsat ba bata ma kawoma ranta Zain zai auri Hafsat ba. Har ta zauna bata kalli inda Zain yake ba kuma bata ce masa komai ba. “Hameeda” Ya kira sunanta yana kallon yadda ta lalace ta koma kamar ba ita ba, idonta har wani baki suka yi saboda kukan da take wanda ya zame mata jiki. Bata amsa ba tana ta kallon kasa kamar ba ta san da su a gurin ba. “We both lost her, kamar uwa take a garemu and now Mai Martaba kawai ya rage mana” “Har yanzu kana jin ni yar'uwarka ka ce?” “Yes no matter what kika yi you're still my blood, wacce Dada ta raina ta girmar da Ita” “Thank you Zain, amman ina rokon ka yafe min kamin nima tawa ta kasance” “Ni na riga na yafe miki” “Nima na yafe miki” Hafsat ta fada, sai a lokacin ta dago idonta dake zubar da hawaye ta kalleta. “Ke din wacece?” “Hafsatu manga, yarinyar kauye, yarinyar da kika dorawa kisan Farhat” Zain ya amsa mata, kallon ta sosai Hameeda take tana tunanon abubuwan da suka faru, yau gata a prison yarinyar kuma tana tare da Zain. “Na gode” Ta furta cikin muryar kuka. Sai ta mike tsaye hakan yasa suma suka tashi tsaye, Zain ya dauki daya daga cikin ledodin da yanzo da su ya mika mata. “Hijab Dada ne wanda take yawan sakawa idan zata yi sallah, akwai kur'anenta da carbi a ciki, sai kuma hotonta da namu lokacin da muke kanana, maybe zai rika tuna miki da ita” Hannu biyu ta saka ta karba sai ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi. Idanuwan Zain kuma suka cika da hawaye, daukar sauran ledodin Hafsat tai ta aje mata gaban, sannan ta rika hannun mijinta ba tare da kunyar komai ba suka fito daga gurin. The following day suka koma Paris, har lokacin Zain baya cikin dadin rai da natsuwa, duk kuwa da yawan kiran waya da Mai Martaba yake nasa da kuma Anty Ummi suna bashi hakuri akan rashinta. Tun daga lokacin Zain be sake wani farinciki ba domin mutuwarta ta suna masa da mutuwar Haleema da Farhat da kuma mahaifiyarsa, sai dai yana kokarin boyewa gudun kar ya shiga hakkin Hafsat. But when he truly findout tana da ciki sai ya nemi duka damuwarsa da bakincikin ya rasa, hankalinsa da tunaninsa sai ya koma kanta da kuma rainon cikinta. Abunka da kwararen likita har numfashinta kula yake da shi idan ya canja. Cikin so da kauna ta raini cikinta, bata kusa da iyayenta da kuma yan'uwan twins amman kusan kullum sai sun yi waya da ita, ta bangaren yan'uwan Zain ma haka, wani lokacin har kunya take a yadda suke tambayar idan taji wani abun. In a day idan baya gida wuni take da waya makkale a kunnenta especially lokacin da cikin ya tsufa sai yai ta jin kamar idan baya jinta a waya ko a kusa da shi wani abun zai iya samuwarta ne. Sosai ta so ya maida ita gida ta haihu amman ya ki wai can ba za'a kula da ita kamar yadda shi yake yi ba, and if wani abun ya sameta ko dan cikinta ba zai iya yafewa kansa ba. Hajiya Hadiza da Momy ma sai da suka masa magana akan ya dawo da ita Naija ta haihu sai yai musu karyar wai idan ta samu canjin iskar da take shaka cikinta zai iya samun matsala, ba dan sun aminta ba da zancensa suka kyaleta ba sai dan ganin yafi son tana kusa da shi din. Ranar da zata haihu bakin har kunne sabar raki, abu ya kai ga ma'iya 😂, you know abroad yadda suke barin mazaje aure su shiga dakin haihuwa tare da matan su, yana kusa da ita holding her hand duk wani motsi da take da numfashi yana ji kuma yana kallonta, haihuwa is not easy sai duk tausayinta ya kama shi, tana jin kamar abun ya dawo gareshi maybe shi zai daure da duk zafin da zaiji. She spend few hours tana nakuda kamin ta haiho masa twins. Namiji da mace, a take ya daga waya ya fada musu daman tun tana nakudar ya fada musu cewar tana asibiti. Daga Masarautar Rishim har Kaduna Family house dinsu sai aka rushe da murna da farinciki. Cikin Koshin lafiya ta haifi yaranta, sai dai ba su barta ta koma gida ba dai tai bachi ta huta suka bata kulawar data dace, basa wankan ruwan zafi irin namu na hausawa, magani kawai suka bata, a gida kuma Doc Zain na kokarin ganin ta ci abu mai kyau wanda ya dace. Hajiya Hadiza ce da wasu kanensa biyu dawacce zata kula da jarirai aka zo dasu paris. Ranar suna Namijin ya ci sunan Mai Martaba aka masa alkunya da Amir, macen kuma aka saka mata Sa'adatu wato sunan Dada, aka mai ta alkunya da Amira. Yan'uwa da ke naija sun yi sunansu su kan akan an yanka ragon kawai amman babu wani taron sunan saboda na kamar nan ba ne, abokansa yan naija ne akwai suka kawo matansu wasu kuma suka zo. Sai da Hajiya Hadiza tai sati biyu sannan ta koma Hajiya Zara ta zo ita ma tai two weeks ta koma, ko bayan arba'in sai da Hafsat tai wata biyu a can sannan ya yarda suka ta fo naija. Babu wanda baya farincikin da ganinsu ga twins dinsu kyawawa masu kama da su, wannan karon kin yarda tai ta bishi su koma a dole shi kadai ya koma, sai duk ya ji dabam, he really miss his wife and his twins. Shi da kansa ya nemi aje musu aikinsu ba dan sun so ba, ya hada komai na su ya baro kasar. Daya dawo sai ya kara gyara asibitinsa mai zaman kansa wacce Ibrahim ke kula da ita ya koma kan aikinsa. Hakan ya fi komai yi ma Mai Martaba dadi fa kuma hafsat ko ba komai tana kusa da gida duk abunda akai zata samu zuwa kuma zata ji. Twins na da shekara biyu da rabi ta sake samu ciki ta haifi wasu twins amman wannan karon duk maza, sai Zain ya saka musu Muhammad da Ahmad, a cikinta na uku na namiji ta sake haihuwa wato Mahmud, bayan shi ta haifi Namra ( Haleema) da Aisha (Farhat) sai dai da dai daya ta haifesu ba kamar twins dinta na farko da kuma na biyu ba. Dukan wata kulawa da ko fa kauna Hafsat tana samu daga gurin mijinta ,har take jin kamar ta fi ko wace mace sa'ar abokin rayuwa, ga yan'uwansa kamar su hadeta ita da yayanta, dukam wani abu daya faru a baya ya zame mata kamar tarihi, ta wani bangare kuma ya zame mata darasin rayuwa, wanda za a ciri mai amfani a ciki a watsar da sauran. Daga ita har shi Rayuwata ta zo musu da abunda ba su zata ba, gashi a yanzu tana zaune da matar da yafi kauna fiye da ko wacce, yana tare da iyalinsa kamar kowane mai aure kuma yana farinciki a gidansa, abunda be taba sawa rai ba. Yana yawaita godiya ga Ubangijinsa ta hanyar sallah azumi da kuma dakata, lokaci zuwa lokaci Al-hamdulillah shine akwai abunda yake fito a bakinsa.... Kamar yadda nima yake fitowa a bakin AL-HAMDULILLAH TSUMMA AL-HAMDULILLAH TSUMMA AL-HAMDULILLAH. Godiya ta tabbata ga Ubangijin Khadija, wanda ya halliceta tun babu ita ya rayata har ta kawo yanzu, kuma ya bata ikon rubuta HAFSATU MANGA, ya amince mata ta gamashi cikin jindadi da koshin lafiya. Al-hamdulillah Allah na gode maka. Tsira da aminci su kara tabbata ga Mijin Khadijatu (A. S) kuma angon Khadija (AS) wato Annabi Muhammad (S. A. W). Allah ina tawassali da sunayenka tsarkaka, ka yafe min inda nai kuskure ko tuntuben halshe, Allah ka sanya rubutuna ya zama mai amfanin ga al'ummar Annabinka, kuma ya zame min sanadin tsira. Godiya ta Musamman a gareku masoya na masoyan kwarai masoyan gaskiya, masu son na har cikin ransu wato members din Hafsatu manga Paid grp, baki yayi kadan ya gode muku, na irin goyon baya da kuka bani. Na gode na gode na gode sosai Allah ya bar zumunci mai dorewa har aljanna. Ummu Faisak Asma'u Badamasi Hajiya Zainab Kano (Mama) Maman Hafiz (Maman Candy) And Zubaida Malam You people are like family to me, ku kuke fara goyan min baya a dukan abunda zan yi ko ya shafe ni. Allah ya bar zumunci da so da kauna. Jinjina a gareki Mom Iman I'm in love with your comments every day. And all members of HAFSATU MANGA COMMENT GRP. Daga karshe ina neman yafiyar wanda na batawa cikin rashin sani ko ganganci, ina rokon addu'ar a duk lokacin da sakon mutuwata ya riskeku 🙏 i will surely miss you guys 💔😭 but don't worry ana tare we have each other numbers. Best regards 🌹😍♥️ Khadeeja Candy♥️🖤 Stay bless.😍 One heart♥️ One love♥️