[11/19, 10:00 AM] INDO: https://chat.whatsapp.com/Ghq9lsJzlnsD0d4jlde7rQ *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 1 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *GORGEOUS WRITER'S FORUM* Alhamdulillah!!, Ina Ƙara Miƙa Godiyata ga Allah Maɗaukakin Sarki. Yadda na fara rubuta wannan sabon Littafi Lafiya, ina roƙon Allah ya bani ikon kammala shi Lafiya. Bayan *SAWUN KEKE* Ga wani Sabon Salo, Sabon Tsari, Ina Fatan za ku bi ni a sannu domin jin Abinda ke Ƙunshe a cikin wannan Littafi Me Suna *HAƊIYAR GATARI* Kai tsaye Ba lallai ku fahimci me Sunan yake nufi ba, amma indai kun yi haƙurin Bibiya Za ku Fahimta. Ina Gaisuwa🫶🏽 Takun nan ce dai *INDO*...... Marubuciyar WATA HANYA DOGON YARO IDO HUƊU SAWUN KEKE TAJMAHAAL A JINI ƊAYA SIRRIN ƘETA AAMINAT (Bazawara) Da sauransu....................... 10/11/2023 Bismillahirrahmanirrahim. Sassanyar waƙa gami da hayaniya da iface-ifacen Ƴan Matasan Samari gami da Shewar Ƴan Mata ga kuma Surutan MC ke tashi ta ko'ina a cikin Ɗan Madaidaicin Hall ɗin, wanda ya sha Ado da kwalliya da ƙawa ta ko'ina. Duk da ƙarami ne amma sai Masu abin ne kaɗai ke iya yin shagali a cikinsa. Kai tsaye dai za a iya sanya shi cikin Jerin Abubuwan da ake kira SAI KA KAI SHEGE....... Casu gami da shaye-shayen Lemuka da ciye-ciye iri daban-daban ake yi. Kusan kowane Saurayi da Budurwarsa a wajen, in ma bai zo da tashi ba zai samu Abokiya. Cikin farin ciki da kwanciyar hankali Kowa ke gudanar da shagalinsa. Ihun MC ne ya karaɗe Kunnuwan duk ilahirin Mutanen dake wajen, cike da karaɗi da ƙarawa al'amari Ƙawa yake cewa "Don Allah duk wanda ya san ya zo Taya Irfan Mohammad Murna ne ya yi shiru kuma ya zubawa Ƙofar shigowa wannan haɗaɗɗen wuri ido, domin ganin Da wane Salo Babban Abokin Birthday Boy zai shigo!!!!!, sannan Duk wanda yake son jin kowanene Wannan Babban Aboki da muke ta jiran Shigowarsa ya ɗaga hannu." Cikin sauri gami da shauki mafi rinjaye Mutanen wurin suka ɗaga hannu. MC ya sa dariya yana cewa "Wallahi Sai kun biya wani abu zan gaya muku!!, in ba haka ba kuma zan hana Abokin Birthday Boy ɗin shigowa, Ina son a kece raini tsakanin Mata da Maza don haka ga inda Mata za su juye Jakarsu ga Inda Maza za su juye tasu." ya faɗa yana nuna masa wasu Ƴan ƙananun Tebura dake kusa da inda yake tsaye yana zubo maganar. Shiru ba wanda ya fara zuwa hakan ya sa MC ƙara cewa "Yau dai za mu gani Mata ne Jaruman ko Maza; Maza kar ku bari Mata su kayar da ku don wallahi suna fara fitowa kun faɗi warwas!!!!" ya ƙarasa maganar yana dariyar shakiyanci da Yaudara. Jin haka ya sa aka fara tsere tare da gudun wuce tsara a tsakankaninsu, cikin Lokaci kaɗan suka tara masa kuɗaɗe Mazan kuwa sabida Burga har da masu ajiye watch ɗinsu kuma suka ce in Matan sun isa su saka, Su ma Matan da yake sun ƙagara su ga shigowarsa wasu tuni suka cire layukansu suka ajiye wayoyinsu. Kasancewar Mafi yawancinsu Ƴaƴan Masu Kuɗi ne ko damuwa akan hakan ba su yi ba. Sai da MC ya ce ya dakatar sannan suka dena Wasan kece raini.... "Dariya ya saka yana cewa ba shakka wannan Babban baƙo namu me farin jini ne domin kuwa Mata sun yi da gaske sun kayar da Maza sabida son ganinsa!!!" Tafi akasa gami da shewa tuni wurin ya ƙara karaɗewa, Wasu daga cikin Mazan suna cewa an yi musu maguɗi, shi kuwa MC hakan ƙara ziga shi ya yi, sabida Magana Tamkar zai tashi sama. "To!!! to!!!! DJ yana Godiya yana ƙarawa!!; yanzu dai kowa ya saurara domin jin sunan haɗaɗɗen Abokin wannan Chocolate ɗin Birthday Boy namu!!" sai da surutan nasu ya lafa sannan ya ci gaba da cewa "1 - 2 - 3 ALIYU ALMUSTAPA NAIRA!!!!! Muna yi maka Barka da zuwa wannan waje!!!!" Tafi suka sake sanyawa gami da ihu, lokaci guda Salon wajen ya ƙara canjawa, da yawa daga cikin Ƴan Mata iyayi da kwainanensu sai da ya canja, duk suka zubawa Hanya ido cike da Ƙaguwa, kowacce ta ƙwallafa rai akan jan ra'ayinsa. Sanye take cikin wata fitinanniyar Gown wadda ta kama jikinta tsam-tsam, ta sha Make-up kamar ba gobe, ta yi bala'in kyau, duk wanda ya kalleta sai ya ƙara, ga eyelashes ɗinnan zaya-zaya sun ƙara mata kyau da armashi, ta baya kuwa haɗaɗɗen kitson Ƙarinta ya bazu akan bayanta zuwa kafaɗunta. Waige-waige take yi tamkar me neman wani abun, karaf idanunta suka sauka akan wani da ke tsugunne gaban wata Haɗaɗɗiyar Mota me Numfashi yana ɗan tattaɓa tayoyinta. Da sauri ta ƙarasa wajen gami da yi masa sallama tare da Addu'ar Allah ya sa Direba ne, da sauri ya juyo yana tsitstsilla ido kamar Munafuki, cikin yanayinta na jijji da kai da ɗagawa ta ƙare masa kallo sama da ƙasa sannan ta ce "Daga ina do Allah??, wannan Motar Me gidanka ce??" Jin tambayar tata ta sa shi washe baki sannan ya bata amsa, "A'a Hajjaju, daga wata Unguwa nake wai ita Ɗorayi." "To gayyatarka aka yi wajen Birthday ɗin??" da sauri ya girgiza kai yana cewa "Wace ni??, a'a kawai dai na ga an yi posting ne a Facebook ana gayyatar kowa shine na garzayo in sha 5 alive in tafi, Allah ya sa ma sun yi mana Ƴar garau-garau ɗin da zamu afa." dogon tsaki ta ja gami da binsa da wani kallo wanda ya fi kama da na ƙyama sannan ta ce "Menene garau-garau kuma??" tuntsirewa ya yi da dariya yana cewa "Ai Hajjaju ku manya ne ba lallai ku santa ba, wani Abinci ne namu na Hausawa." Tsaki ta ƙara yi a karo na ba adadi sannan ta ce "Kai nan har wani Bahaushe ne?? ni ai kama kake yi mini da irin Fataken nan, yaya ake kiran Yarensu ma??, irin waɗanda za ka ga suna aikin Gadi a Manyan Gidaje" cikin sauri ya ce "Buzaye?? yo ai Ranki-yadaɗe baki faɗi ba, na ji an ce Kakan Kakana asalinsa Buzu ne, amma dai tinda ban iya kowane Yare ba barni a Bahaushen kawai." ɗan numfashi ta ja kafin ta ce "Za ka yi min aiki in biyaka??" Da sauri ya ce "Haba Hajiya indai za ki bani na cin Taliyar Yara ai ba matsala zan yi." Murmushin samun nasara ta yi kafin ta ce "Dama PA ɗina ne na aikeshi wani wajen, to ba na son Yawo ni kaɗai shine nake so ka tsaya a matsayin PA ɗina a wannan wajen, Bayan Mun fito zan biyaka, amma fa za ka dinga yi mini ladabi sosai sannan kai za ka riƙe mini jakata." leƙewa ya yi ya ƙara gano Jakar tata, ba laifi da ɗan girmanta, jinjina kai ya yi yana ƙara faɗaɗa fara'arsa ya ce "Na Amince Ranki-yadaɗe, Muje kawai kina tafiya ina take miki baya, ba ki da matsala." ta yi wani yauƙi gami da cewa "Okay, amma in ba ka yi abinda ya kamata ba ba zan biya da yawa ba ko kuma ka rasa ko ficika." "Me zai hana yin aiki tuƙuru ma Hajiya ai kin wuce nan a wajena, ni a kullum ma in za ki mayar da ni Ɗan Aikinki indai za ki biya na Amince." Murmusawa ta yi kana ta miƙa masa jakar tana cewa "Yaya sunanka ne??" "Ali Haidara" ya faɗa yana ƙara washe haƙora kamar me tallan makilin, yana karɓa ta yi gaba ba tare da ta ce komai akan sunan nashi ba; da sauri ya dakatar da ita da cewa "Hajjaju don Allah jirani, kin san mu Buzaye sai da rawani." gaba ta yi tana cewa "Ina ɗan can wurin maza ka zo ka sameni." Zazzafar iska ya furzar yana bin bayanta da kallo. Sai da ya naɗe fuskarsa da kansa ya rage sai idanunsa kaɗai a waje sannan ya bi bayanta. A tare suka shiga ɗagwas-ɗagwas tana tafe yana binta a baya kamar wani Mijin Ta ce. Sai suka zama abin kallo kuma abin sha'awa ga Mutane, shi kansa MC sai da ya bata yabo da jinjina da girmamawa, hakan ya sa kanta ya ƙara huruwa Kamar Balo. Tinda suka shigo Irfan Mohammad ya zuba musu, ba kowa yake kalla ba face na bayan nata ita kuwa sam bai ganeta ba ma. Sai da ta ƙaraso inda yake suka gaisa sannan ta yi masa bayanin itace Leelah Facebook Friend ɗinsa, na bayanta kuma Body guard ɗinta ne. Tarbar Mutunci da Mutuntawa ya yi mata gami da yi mata godiya a bisa kyautar da ta bashi, sannan ya sa a rakata waje na Musamman a kula da ita. Har zuwa lokacin hankalinsa ya fi karkata kan Body gourd Ɗin nata, hakan kuwa ya sosa mata rai don so take ta ja ra'ayinsa akan Soyayyarta amma shi yana can yana kallon wani Gardin Namiji Ɗan Uwansa. Duk wanda ta haɗu da shi bayan gabatar da kai sai ta gabatar da Body Guard ɗinta. Bayan sun zauna Ya dubeta kafin ya ce "Amma Hajjaju za ki ƙara min Kuɗi ko??, na ga da farko PA kika ce mini yanzu kuma kin mayar da ni Body Guard!" tattaɓe baki ta yi a yanƙwane ta ce "Ka fiye azarɓaɓi, na gaya maka indai kuɗi ne ba ka da matsalarsu." Laƙwas ya yi yana zazzare ƴan idanunsa a cikin Naɗi. Shagali aka ci gaba da yi yayin da MC ke ta ɓaɓatun Kiran Abokin Birthday Boy amma shiru wasu har sun far tunanin ko raina Musu hankali yake yi. Kallo ne ya koma sama lokacin da wata Ƴar Budurwa me Halittun Indiawa ta doso ciki, sanye take cikin wata Shegiyar Doguwar riga blous fara tass!!, daga ƙasan rigar a buɗe yake buzur!! sai sharar ƙasa take yi daga baya, duk da Ɗan Mayafin da ta naɗe kanta da shi sai da Dogon gashinta dake ta sheƙi da walwali ya bayyana. Cikin nutsuwa da kamala gami da jin kai take takawa, tana yi tana sama da ƙasa da dara-daran idanunta wanda Allah ya ƙawata mata su da dogayen gargasa. A bayanta Kuwa wasu daka-daka Ƙartai ne hannayensu riƙe da award wanda ya sha ado irin na Indiawa. Duk wanda ya kalleta sai ya ƙara ba ma kamar Maza, Manyan Abokan Irfan ne kawai suka Ganeta ciki kuwa har da shi. MC Kuwa tuni ya ƙara ruɗa wajen da surutai kamar wanda aka yiwa allurar hauka. Tattausar ajiyar Zuciya ya sauke wadda ta kusa tawowa da hawayensa, shi dai ya san Ba dai Abokinsa ya ba shi Kunya ba. Kai tsaye wajen Irfan wanda yake binta da ido ta nufa, sai da ta isa gabansa sannan ta saki murmushin da ya ƙara bayyanar da ainahin kyaunta, cikin zazzaƙar muryarta ta ce "Ka yi haƙuri Yayana yana Uzuri ba zai samu zuwa ba." "Ba komai, iya ganinki da na yi ma ai ya biyani, ki temaka mini ki yiwa kowa bayanin abinda ke faruwa don kuwa duk wurin nan shi ake jiran gani." nisawa ta yi kafin ta yi magana cikin yanayin shagwaɓa "Ka san ba na son sa idon Mutane Irfan Bhai" "Na sani temaka mini za ki yi Chotti Bahen" ya yi maganar yana kwaikwayon tata maganar har da shagwaɓar, dariya ta yi kafin ta ce "To ka rakani sai ka fara gabatar da ni." amsawa ya yi sannan suka nufi wajen da MC yake. Leelah da ke tsaye ta riƙe Ƙugu wani baƙin ciki ya tokare mata Zuciya, ita da take shirin cusawa Irfan Soyayyarta ya ƙi saurararta sai wata me jan kunne. Ali ne ya dubeta kafin ya ce "Hajjaju a zauna mana" "Kai ba zan zauna ba" ta faɗa a masife, ya yi dariyar Yaro ba Mutum ba sai ya girma kafin ya ci gaba da sa hankali akan Irfan da Ƴar Indiyarsa. Bayan ta gabatar da Uzurin Yayanta ta bayar da kyauta tana shirin miƙawa MC Microphone Azaan ya dakatar da ita ta hanyar tare mata hanya yana binta da wani shegen kallo da babu komai a cikinsa sai zallar ƙwalama gami da iskanci. "Me ya sa za ki fito a irin wannan daren??, 11:37PM fa ai na ɗauka Mamarki ba ta barinki gantali yadda kike da tsaurin halin nan." Dakakkun idanunta ta watsa masa kafin ta ce "Ba ruwan wani da lokacin fita da shigata, bani hanya." "Ba za ki wuce ba har sai kin bani amsar tambayoyina, ko kuma daga nan in wuce da ke guest house ɗina mu kwana tare.... Tasss!!!! ta wanke shi da wani kyakkyawan Mari me ratsawa har cikin ƙwaƙwalwa. tuni wurin ya ɗau ihu da shewa don kuwa abin ya burge Mutane tamkar a film suke kallonsu. Azaan kuwa jin ana yi masa dariya ya ƙara fusata shi, sauke hannunsa ya yi daga kan kumatun yana cewa "Ni kika mara???" cikin ɗaga murya ta yadda har Microphone ɗin yana amsawa ta ce "Na Mareka How dare you!!!!" shu'umin murmushinsa ya saki ba tare da ta ankare ba sai jinta ta yi a cikin ƙirjinsa ya yi mata wata muguwar matsa, ta buɗe baki za ta yi magana ya rufe bakin nata da nasa, sai da ya kai a ƙalla 3 minute yana kissing ɗinta sannan ya saketa yana ƙara wararo mata tsayayyun idanunsa.... ita ma kallonsa take yi ya yinda Zuciyarta ke wata muguwar tafarfasa...... gefen mayafinta ta sa ta goge bakinta hakan bai wadatar da ita ba don haka ta taƙarƙare ta ƙwalla ihun cewa "Rochaaaan!!!!!!!!!" Sai da kowa na wajen ya firgita, aka ƙara zazzaro ido ana kallonsu, Azaan kuwa sai da numfashinsa ya tsaya na ɗan lokaci kafin ya ci gaba da gudana, Idan ya tsaya jayayya da kansa ma akan cewar bai tsorata ba ya ɓatawa kansa lokaci, tuni zuciyarsa ta fara bada Darrr!! darr!!!!! tana tsalle. Ba ihunta ne kawai ya tsorata shi ba jin sunan da ta ambata............. *PAID BOOK, 300 ONLY* *INDO* [11/19, 10:00 AM] INDO: https://chat.whatsapp.com/Ghq9lsJzlnsD0d4jlde7rQ *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 2 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *GORGEOUS WRITER'S FORUM* .........Zuwa yanzu ya gane dole akwai wata ƙullalliya. Cilak!! ya ɗauketa gami da rungumeta tsam a cikin faffaɗan ƙirjinsa, cikin gaggawa ya nufi hanyar fita. Da ido Azaan har ma da Irfan suka raka shi Zukatansu cike da saƙe-saƙe da mamaki iri-iri. Leelah ɗoki da son ganin abinda ke faruwa a gabanta ya sa ta yi saurin juyawa don ta karɓe ƴar jakarta daga hannun Bodyguard ɗin nata ta turmutsa gaba. Turus! ta tsaya ganin babu shi babu alamunsa sai Jakarta tata a kan Kujera. Ɗan ƙaramin tsaki ta yi kafin ta ɗauku jakar ta shiga cikin jama'a wanda suka yi cako-cako suna kallon lamarin me kama da wasan kwaikwayo. Sai da ta yi Free sannan ta ji wasu na cewa ai ya ɗauketa sun fita, wasu kuma suna mamakin ashe Aliyu Naira Yazo to me yasa ya ɓoye kansa?. Takaici da baƙin ciki duk ya isheta, gashi ba ta ga dramar da aka yi ba ba ta ga Aliyun da ake ta faɗe ba, gashi Bodyguard ɗinta ya tsallake ya barta. Sai da suka dangana da Tsadaddiyar Motarsu sannan ya direta. Dama jira take yana direta ta tirji ƙasa ta juyo kansa a masife ta ce "Dama abinda ka ɗaukoni a yi min kenan??, ka ɗaukoni ne don a tozartani a ci zarafina a idon Duniya?? ; wallahi sai na ɗauki mummunan mataki akan Azan ɗin nan! har shi Irfan ɗin" "Ki yi haƙuri Khushi! da na san Azaan zai zo wajen nan kin san ko ni ba zan zo ba bare na kawok....." katse shi ta yi cikin tsawa "Ka sani mana!!!! babban me laifi kai ne!!, in da ba ka ɗaukoni ba babu wanda zai wulaƙantani, kuma kana kallo amma ko ka yi magana, sai da ya tuntsirar min da madarar Mutuncina!!!." kamar zai yi kuka ya ce "Ba haka ba ne, ki dena ganin laifina..." "Kai ne fa ka haɗa Taron nan! kuma akan me za ka ce ba ka san wanda zai zo ba??" zuwa yanzu ɓacin ransa ya ƙara ninkuwa fiye da Da, tabbas da me saurin hannu ne ba abinda zai hana shi sharara mata maruka ko za ta dawo hayyacin. Sai da ta gama figeshi tsaf sannan ta zumɓuri baki ta shige Mota, ƙaratan Mazan da suke taka mata baya ma suka shiga. Ɗaya a mazaunin Direba ɗaya a wajen ɗan zaman banza. Jiki a sanyaye ya ja ƙafafunsa da suka fara nauyi ya shiga Motar. Cikin mutsuwa Direban ya fara ja suka hau Titi. Ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya dubeta cikin Muryarsa me matuƙar sanyi da sanyawa me sauraro nutsuwa ya ce "Sai Faɗa kike yi min akan laifin da ban aikata ba Kuchi!!, ko Irfan bai cancanci wannan hukuncin ba, na baki haƙuri kin ƙi haƙura, na gaya miki ba ni da laifi kin ƙi yadda, Kaise!?" faɗawa ta yi jikinsa gami da fashewa da matsanancin kuka tana cewa "Meine vah nahi pyaar karthi hoon wallahi!" Bubbugar bayanta ya shiga yi cikin sigar rarrashi ya ce "Mujhe bahoot khed hai Kushi!" banza ta yi masa ta ci gaba da rera baitin kukanta wanda yake ƙara soya masa Zuciya. Waya ya ɗauka ya tura kira cike da sa ran wanda ya kira ɗin ya ɗauka......... "Gaskiya ba ka kyauta min ba Azaan, me yasa indai aka haɗa lamari da kai sai ka tarwatsashi sabida Allah?" Irfan ya faɗa cikin rauni tamkar zai fashe da kuka. A gadarance Azaan ya ce "Ina ruwanka? kai na yiwa??" "Amma ai tarona ne ko??, ni na tara Mutane kuma ka zo ka tozartani, wallahi Allah kar ka ƙara yi min irin wannan; in banda Akuyanci irin naka a bainar nasi za ka dinga haiƙewa Yarin......." a tsawace ya ce "Dalla ina ruwanka ne Ɗan Iya!!!?, she's my sister and my wife, to meye naka a ciki? Faɗan cikin gida ne idan na ƙara jin bakinka a ciki wallalhi sai na saɓawa Tunaninka; Idiot!!!!!!!" yana kaiwa nan ya doka wani lafiyayyen tsaki ya nufi hanyar fita, tawagarsa suka rufa Masa baya. Da ido Irfan ya bi shi Zuciyarsa na wani irin tsalle gami da turiri. Sai a lokacin ya ji ihun da wayarsa take ta zurmawa, jiki a saɓule ya ɗauki kiran tare da yin shiru don bai san da wace kalma zai fara yi masa magana ba........ "Ban zaci haka ba Irfan!, ka san ko hanya ba na haɗawa da Azaan don me za ka gayyace shi Taron da ka san zan zo??, ka ga yadda ya tsinka igiyar Mutuncin gidanmu akan idon Duniya; ni wallahi yanzu damuwata ma idan Umma ta sani komai akanmu ni da kai zai ƙare, Yanzu ga wannan ita ma sai jaraba take yi min ga kukan Masifa, haka za ta dinga tijara har sai ta sa wanda bai sani ba ya sani; ka dena irin wannan, gwara kawai ka ce min kar na zo zai fi sauƙi akan wannan tozarcin da ka yi min!." sai da ya kai matsaya sannan Irfan ya numfasa, a sanyaye ya ce "Wallahi da ka san irin suyar da Zuciyata ke yi da ba ka zargeni a kai ba, ni ma fa Kushi Ƙanwata ce , in aka tozartata tamkar ni aka tozarta bare kuma a ce a Taron da ni na haɗa shi; na yi masa magana kuma ya ce kar na ƙara shiga zancenku na cikin gida ne, to yaya zan yi??" "Amma ai ka san zan zo me yasa za ka nemeshi??" "Na rantse da Allahn da raina ke hannunsa ba ni bane Roshan!, Ari ne ya gayyatoshi wallahi." tsaki ya ja kafin ya ce "Ta tabbata sai na ci Uwar Arin nan kenan!, Yanzu indai Umma ta sani duk wata ƙura akanmu za ta ƙare wallahi" jikinsa ne ya ƙara yin sanyi luɓis, cikin karyewar Zuciya ya ce "Roshan ba zan yi haka da gangan ba wallahi, Ina matuƙar Sonta kuma ina Matuƙar Kishinta na fika jin zafin abinda ya yi mata wallahi Roshan!!" "Me??? Irfan wai Kuchi ɗin?!!" cikin kaɗuwa ya jefa masa tambayar, kasa magana ya yi sai gyaɗa kai kawai da ya yi, da zarar ya yi magana zai iya rushewa da kuka don haka ya kashe wayar ya mayar da ita muhallinta. Haka Taro ya watse kowa na tofa albarkacin bakinsa, da yawansu cewa suke yi dama abin bai tsaya iya nan ba, don kuwa su burgesu aka yi. "Rookh jao Qadri!!!!" ya faɗa a tsawace, cikin sauri Qadri ya yi gefe da Motar saaaa!!!! ya caketa. Tureta ya yi daga jikinsa yana cewa "Matsa min!! ni kaɗai zan tafi na gaji da jin Mitar nan, kuma wallahi ki sani in raina ya ɓaci sai naki ya ɓaci, jarababbiya!!" Cikin sauri Qadri ya yi magana cikin harshen Hindi "Ka yi haƙuri Yallaɓai, komawarmu daban-daban gidan nan akwai haɗari, aikinmu ne kula da ku, ka temaka mana kar ka sa a koremu daga aiki." "Ba abinda ya shafeni da aikinku, in an koreku ma za ku samu wani amma yau dai ko zan je gida to fa ba a Motar nan ba." da sauri ta riƙe hannunsa tama cewa "Don Allah kar ka tafi ka barni, ka zauna mu tafi tare na dena ba zan kuma ba." "Af! da dai ban san halinki ba, kin dage sai kin yiwa Azaan kaza sai kin yi masa kaza, ina ke ina shi? ko kuma ni ne Azaan ɗin da za ki cika min kunne da surutunsa?!" "Ai ba zan kuma ba, don Allah ka zauna" ta yi maganar tana ƙoƙarin tsayar da kukan nata. Sai da suka yi da gaske Sannan ya haƙura bayan ya kori su Qadri daga driven ɗin ya watsa su baya su duka sannan ya karɓi kan Motar. Gudu kawai yake fafarawa tamkar wanda jiya ta wuceshi zai kamo gobe. Sai da ya dangana da parking space sannan ya yi wani kyakkyawan burki, bai tsaya gyarata ba ya buɗe ya fice cikin gudu-gudu sauri-sauri. Kai tsaye Toilet ya wuce ya sakarwa kansa shower ko zai ɗan ji daɗi a ransa. Abubuwan sun haɗe masa da yawa, Irfan ya kamu da son Kushi ga baƙin Halin Azaan, Gidan boss ɗin kuma shi ne wajen Mommynshi Ya jima kafin ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa, kai tsaye wajen wayarsa da ke ta famar ihu ita kaɗai ya nufa Zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri. Kasa ɗagawa ya yi har kiran ya katse. Sai da idanunsa suka ƙara girma ganin adadin kiran da tayi masa har guda goma sha ɗaya, rintse idanunsa ya yi da ƙarfi cike da son ƙwararawa kansa gwiwa. Wani kiran ne ya ƙara shigowa ya yi saurin ɗagawa ya kara a kunne bakinsa ɗauke da Sallama....... *PAID BOOK, 300 ONLY 09079885632* *©️INDO* [11/19, 10:02 AM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 3 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *GORGEOUS WRITER'S FORUM* "Kya hua Roshan?!" ta faɗa ba tare da ta bi ta kan sallamar tashi ba, cikin sauri ya ce "Kuch nahi hai Maa" "Jhoot batao tum!, ka lura da irin gudun da ka shigo Gidan kuwa?, Mujhe batao sach Roshan!" ajiyar Zuciyar wahala ya sauke kamar zai yi kuka ya ce "Main Sach Batao Maa!!" "Achcha!, main aajaoonga!" cikin zaro ido ya ce "Me yasa???" shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Ba buƙatar ka sani, ka kula da kanka" daga haka ta katse wayar. Zaman ƴan bori yayi a bakin gado yana bin wayar da kallo cike da rashin sanin abin yi. Message ya turawa Kushi kamar haka, "Na ba ki haƙuri kin ƙi ji yanzu Mama ta ce za ta dawo sai ki san abinda za ki faɗa mata, kuma kar ki sake sunan Irfan ya fito a ciki." Yana turawa yayi wurgi da wayar ya nufi wajen wardrobe domin yin shirin Bacci. Tana ganin Message ɗin ta zabura daga kwance ta zauna tana maimaita karatunsa, da sauri ta mayar masa da amsa "Kai ne za ka san abinda zaka faɗa mata." Tana turawa ta zame ta kwanta gami da ture wayar gefe ta shige cikin Bargo sabida gudun yin wani ƙwaƙƙwaran motsin da zai ƙara jefasu cikin tuhuma. Tana zaune akan ɗaya daga cikin duma-duman Kujerun da aka ƙawata tamfatsetsen Falon da su. Babbar Mace ce wadda za ta kai shekaru Hamsin da shida, ba siririya ba ce kuma ba za a sakata a sawun masu ƙiba ba. Ta haɗe cikin tsadadden Saree dark blue wanda yayi matuƙar karɓarta ya ƙara fito da kyawunta, hannunta da ƙafarta da wuyanta na sanye da ababen ado masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali. Gashinta wanda ya sha gyara ya yi kwance akan kafaɗunta sai sheƙi da walƙiya yake yi. Gefenta wata Budurwa ce a durƙushe kanta a ƙasa, hannunta riƙe da wani ɗan ƙaramin plate wanda ƙaramin kofi me murfi yake kai. Alamun Budurwar ba tun yanzu take a durƙushe ba kuma ta fara gajiya. Hakima kuwa ko kallon inda take ba ta yi ba idonta na kan tsuleliyar Iphone ɗinta. Kamar wanda aka jefo daga sama ya shigo yana ƙwala mata kira "Mammi!!!! Mammi!!!" ko gezau ba ta yi ba har sai da ya ƙaraso gabanta ya tsaya akanta kamar zai rufeta da duka sannan ta ɗago idanunta da suka sha Kohl ta zuba masa cike da son jin abinda zai faɗa. "Wallahi sai na kashe Aliyun nan Maa!!!." Murmusinta na shu'umanci ta saki kafin ta tsirawa kofin hannun Ƴar aikinta ido, ita kuwa kasancewar kanta na ƙasa ya sa ba ta san ana yi ba. Wata shegiyar tsawa Azaan ya doka mata, ta yi saurin zabura ta miƙe tana zazzaro ido. Ganin wani kallon tara ahu da take jifanta da shi yasa ta yi saurin komawa ta durƙusa sannan ta miƙa mata plate ɗin, sai da ta ja lokaci sannan ta ɗauki iya kofin. Cikin jin kai da izza ta ɗan kurɓa ta mayar ta ajiye akan plate ɗin wanda har yanzu yana hannun Ƴar aikin. Kallonsa ta yi tana ƙara sakin murmushi, cikin muryarta me cike da zallar jin kai da fariya ta ce "Wanene ya mareka??" "Wannan shegiyar Kushi ɗin ce, ai don tana ganin Aliyun ne shi yasa take mini duk rashin Mutuncin da ta ga dama, a tsakiyar Jama'a fa ta mareni kamar wani ɗanta har ta sa ana yi mini dariya; kuma wallahi da ba ta ganin Aliyun nan da ba za ta yi ba." Miƙewa ta yi ta fara wani taku me kamar sanɗa hannayenta goye a bayanta, "Kar ka damu kanka indai wannan ce, zan yi magana da ita ba za ta kuma ba, kuma ka sa a ranka ita ɗin Tamkar Baiwarka ce sai abinda ka yi niyya za ka yi mata, ni kuma zan yi maka komai!, ka je ka huta 12:18" a masife ya ce "To ni kaɗai ta yaya zan iya hutawa bayan an ci Mutuncina??, kin ga yadda ya ɗauketa daga gabana a Ƙirjinsa kuwa?? wallahi ji nake kamar na yi hauka!!" "Babu abinda za ka rasa a wajena Azaan!!" ta yi maganar tana kallon Ƴar aikinta wadda jikinta yake ta ɓari, ta riga ta kwana da sanin dole hakan za ta faru. Muryarta ce ta dawo da ita hayyacinta "Tashi ki bishi, bana buƙatar ya kwana da wata damuwa, idan kuma kika gaza yi masa komai sai na jefa duk danginki a cikin bala'in da sai kun gwammace Mutuwa da Rayuwa." Murmushi kawai Azaan ya saki ba tare da ya yi magana ba ya nufi ɓangarensa Ƴar aikin ta rufa masa baya. Mammi safa da marwa ta shiga yi a tsakar Falon Zuciyarta cike da raɗaɗi da zafin Marin da aka yiwa ɗanta a bainar Nasi, ya zama dole ta yiwa Mutanen nan abinda har abada za su dinga shakkarta, Dole ne sai ta nuna musu ita ma wuyanta ya riƙa. Da wannan tunanin ta dinga kaikawo a Falon ko niyyar kwanciya ba ta yi. Ko da ya kwanta mutsu-mutsu kawai ya dinga yi sai da kyar bacci me cike da mafarkai iri-iri ya kwasheshi. "Ayyiriri!!!!!!!!!!!!!!" sautin zazzaƙar buɗar da ta karaɗe Gidan ce ta tabbatarwa duk wani mahaluki da ke cikinsa Gari ya waye. Bai tsaya iya buɗar ba ya ci gaba da magana cikin zazzaƙar muryarsa me cike da iyayi da kwainane wanda ko wata Ƴa Macen Albarka "Kowa ya fito!! tsugunne ba ta ƙare ba an sayar da Biri an sayi Mage!!!, Ina Madara, ina Cakuleti, ina Bota, Ina kuma me wanki da Guga!!!, yau fa ranar ta Ƴan Mata ce wallahi a fito a bajeta a Faifai, ni ba Direban Mahaukata ba don haka ba na ɗaukar Hau ehe!!" Leelah ce ta juya kwanciya ta ƙara juyawa ta ji dai baccin ya tsere, tashi ta yi zaune ta cicciɓo wata ƙatuwar ashar ta danƙara, ta ci gaba da cewa "Shege da Ƙugu Kamar zaren-kaɗi, ina cikin Mafarkina me daɗi ya zo ya katse min, duk baƙin cikin Ɗan baƙin ciki fa sai na Mallaki ɗaya daga cikin Sugar Boys ɗinnan." Salma da ke zaune tana Karanta Alƙur'ani ta tuntsite da dariya sabida jin abinda Leelah ta faɗa. harara ta zuba mata tana cewa "Ke kuma dariyar me kike yi??" "A'ah!!!! gaba salamun baya salamun Matar Manya". ta faɗa tana ajiye Ƙur'anin. "Ni fa Mata nake kira ba Maza ba, kar na ga wani Gardi ya fito ya tsaya min a ka, ato!!, yau wallahi a shirye nake da tuɓe wandon Mutunci in zura na masifa, kowacce me koɗaɗɗiyar Fuska ta fito wallahi tin muna iya shaida juna!!!." Salim ya faɗa yana ƙara ɗaga murya. Ɗaya bayan ɗaya Ƴan Matan gidan suka fara bayyana a tsakar gidan kowacce tana tofa Albarkacin bakinta. Jarkar ruwa Salama ta janyo ta zauna a kusa da Salim, sannan ta ce "To gamu an tarkatomu min fito kuma sai binmu ake da ƙananun maganganu." "Hmm!! ke ai Hafiza dama baccinki kika je kika yi don na san ba kya shafawa; ku kuma wallahi Ɗan Man sa hasken nan nawa da kuka ɗauka ku fito min da shi; Sai ƙaryar banza da taƙamar fari bayan Ɗan Man ma ba kwa iya sayen na kanku sai na saya a sace min!!!; ni fa yau haƙurina ya ƙare gwara tin kafin Kano ta taru a gidan nan ku fito min da abina, ni yanzu a shirye nake da na tuɓe ki tuɓe Mu daku a tsakar gidan nan wallahi!!!" yana maganar ne gami da tafe-tafe da lanƙwasa hannunsa, da ya kai ƙarshe kuma ya bugi cinya sannan ya kame Ƙugu yana wani farr!!! da ido. A hasale Leelah ta ce "Kai ka san na fi ƙarfin Manka wallahi!!, kuma ka sani ni ban tsotsi Sata ba sai ka je ka nemi ɓarawo!!!." wata shegiyar harara Rabi'a ta doka mata gami da cewa ''To wa kike son cewa ɓarawon??" Leelah ta yarfa hannu tana cewa "Oho!! ba da kowa nake ba amma duk wanda ya tsargu ya shiga layi!!." Rabi'a za ta yi magana Salim ya katseta da cewa "Kun ga!! ba cecekuce na ce ko zo ku yi ba, a faka a fito mini da Mai wallahi ko kuma a ga yadda ake tsintsinar rashin Albarka a gidan nan." Salama ta zuba shewa gami da tafa hannuwa kafin ta ce "Ina bayanka daram! ni na ɗaure maka abin wallahi, Manka bai fi kwana uku ba sabida haka a fito da shi ko mu yiwa Mutum Alƙunut; don an ga muna da haƙuri sai a dinga takamu yadda rai ke so!!" Salim ya watsa hannu yana cewa "Gane min hanya fa!! ai haƙuri riga ce rashinsa ma haka, yau dai Rigar haƙurin na jingineta a gefe, ban ƙi a casu ba wallahi; daɗina da ke akwai faɗar gaskiya Me Wanki da Guga, ai wallahi da duk Matan Duniya irinki ne da ba a yi Yaƙi ba tin asali." Sumayya ce ta doka tsaki ta koma ɗaki tana cewa "Ai tinda ba ni na ɗauka ba ban ga dalilin zamana a wurin ba tinda ba haifata ka yi ba." Rabi'a ma tsakin ta yi sannan ta shige ɗaki. "Kan Doron Masifa!!!!? wato ina magana ma kuna kakkaɓe jiki kuna shigewa ɗaki??!!!, yadda kuke ji da rashin Mutunci fa ni ma haka nake ji da nawa, wallahi Ƙudrat daidai nake da Ƙugun kowace Ƴa a gidan nan!!!!" ya ƙarasa magana yana tafi gami da jijjiga jikinsa alamar a shirye yake. Rabi'a ce ta fito ta cillo masa Man tana cewa "Gashi nan jarababbe Ɗan kalan talauci, daga an ɗan ari abinka sai bala'i da masifa ai ni na fi ƙarfin ɗan man nan naka bare in sata, banza kawai!" a fusace take maganar sai ka ce ta fishi gaskiya. Shewa Salama da Salim suka sa suka tafa kafin Salim ya ce "Heeee!!!! ni Furangaɗi Ni Gallo!!!! Amma dai an faɗi ba nauyi, jeki mun ji, ni ne ƙarfamfana Ɗauɗar Aljihu ƙarewar Talauci, amma hakan bai sa na iya bizi ba." hararar sama da ƙasa ta zuba masa kafin ta buga wani dogon tsaki ta faɗa ɗaki cike da baƙin ciki da takaici. Juyawa ya yi kan Salma gami da cewa "Allah dai ya biyaki Uwar masu miƙa wuya, Barbela me Fari daga Allah!!, ke dai Allah ya hutashsheki shafe-shafe bare Talauci ya sa ki yi sata." Kafin Salma ta yi magana Mama ta fito daga ɗan ɗakinta tana kakkaɓe zanin ƙugunta gami da gyara masa ɗauri, "Wallahi ahir ɗinka Salim!! ka fita shirgin Ƴaƴana tin kafin na yi maka Rashin Mutuncin ƙare dangi!! da sanyin safiya ka kafa mambari kana kiran ƴata Ɓarauniya uban me ka ajiye da za ta satar maka??" Taɓe baki ya yi gami da sunkutar Bokitinsa yana cewa "Kowa dai ya gani ita ta fito da abin, Anty Salma kin ga tafiyata tinda Manya sun fara shiga lamarin, sa'a ma aka ci wannan me baki duk Goron ba ta fito ba." Salma ta yi ƙasa da kai ba tare da ta ce komai ba sabida nauyin Mama da take ji, duk fitsararta ba ta son yi a gaban Iyaye. "Uban me ka ce Salim???!! zan sa Isuhu ya yi maka bugun gangar jajiberi wallahi!" Mama ta faɗa a masife, "A'ahh!! me ya yi zafi ido zai ci wuta?! kwantar da hankalinki kamar kin yi baƙo ya mutu, cewa na yi Allah ya bawa Anty Rabi'a gida da Mota mu dinga kwasar arziki, ai abunta tamkar namu yake." Washe baki ta yi tana cewa "To ko kai fa! daɗina da kai ai akwai sauƙin kai, Allah ya amsa zazzaƙan harshen nan naka Salim na Salima!!, ai za a ci Uwar sabada lokacin." Dariya me haɗe da shewa ya saka ba tare da ya yi magana ba ya ci gaba da tafiya yana kakkaryewa tamkar Zabiyar Mata. Salma ma da sauri ta gudu ɗakinsu tana dariya ciki-ciki. *PAID BOOK, 300 ONLY 09079885632* *©️INDO*[11/19, 10:03 AM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 4 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *GORGEOUS WRITER'S FORUM* FREE PAGE........... Dukkansu alla-alla suke gari ya waye su fece daga gidan don za su fi samun damar sararawa. Tare suka fita Bayan sun dire Kushi a Makarantar da take karatu suka wuce da Roshan Kamfanin Bhaba wanda yake ƙarƙashin kulawarsa kasancewar Bhaban ba ya Ƙasar. Tana zaune a Garden hannunta riƙe da chocolate tana ci. Jefi-jefi takan tankawa Suhailat dake famar zuba mata surutu akan abinda ke damunta. Suhailat tana ɗagowa idonta ya sauka akan Mammi wadda ke tsaye a kansu tana binsu da wani shu'umin kallo, sai da gabanta ya yanke ya faɗi, har ga Allah ta ɗan tsorata amma sai ta maze ta ce "Mama lafiya kuwa??" jin ta faɗi haka ya sa Kushi ta ɗago don ganin da wa take maganar, haɗa ido suka yi Kushi ta yi saurin ɗauke nata gami da doka tsaki ta gutsiri cakuletinta. Murmushi ta saki kafin ta yi magana a gadarance "Wurin Kushi na zo ki gaya mata ina magana." Suhailat ta zunguri Kushi tana cewa "Kin ji, ana yi miki magana." "Waye??" ta tambaya kamar ba ta san da kowa a wajen ba, "Wai ba kina kallo ba? ki kula mana ke ta zo nema fa!" "Ke ni fa ban ga Mutum ɗin da zan kula a nan ba, ko dai kin fara gane-gane ne??" Suhailat ta dafe goshi tana cewa "Oh my God!" ta gane sarai Kushi tana sane take raina musu hankali daga ita har Matar. Abin ya yiwa Mammi ciwo amma sai ta maze ta ƙara faɗaɗa fara'arta ta ce "Ba ki ganeni ba ne Kushi??, ni Uwarki ce fa, ko ba a gaya miki hakan ba ne???" Wani shegen kallo ta bita da shi kafin ta saki murmushin rainin hankali, miƙewa ta yi ta matso kusa da ita suna fuskantar juna duk da cewar Mammi ta fita tsayi, cikin ƙarfin hali gami da tsaurin ido ta ce "Sa idonki cikin nawa!!!!, ko da wasa karki ƙara kiran kanki da Uwa a wurina, ba ki haifeni ba wannan Ɗan Iskan Azaan ɗin kika haifa, kuma har Abada ko a mafarki ba za ki taɓa taka matsayin Uwa a wurina ba!! ina fatan kin fahimta!" ta ƙarasa maganar tana huci kamar za ta hau kanta da duka. Ido Mammi ta tsira mata Zuciyarta na cika tana tumbatsa tana fusata, "Hmm!! Ke yarinya ce ba ki san komai a Duniya ba, tinda ba zan taka matsayin Uwarki ba zan taka matsayin Uwar Mijinki!!!, kin ga ko ba kya so na zama Uwarki, kuma za ki san kin yi kuskuren cin Mutuncina da kuma Marin Ɗana!!, akwai ranar da Azaan zai mallakeki ki sa wannan a ranki." cikin tsawa Kushi ta ce "Ba dai ni ba!!! ba ki isa ba da ke da shi!!!" shu'umin Murmushin nata ta yi kafin ta yi taku uku ƙwarara cikin yanayinta na jin kai da izza, "Kamar yadda Uwarku take yin komai kuma take mallaka muku komai don ta faranta muku ni ma haka nake yin komai domin nawa Ɗan, zan mallaka masa ke ko ta wane hali; ko da babu Aure yake sonki zan mallaka masa ke a matsayin Ƙwarƙwara!!!!!" Ji take kamar ta fashe da ihu amma a nan ihun ba zai fishsheta ba don babu me rarrashinta, makarin kukanta kuwa bai Wuce Aliyu ba. Jikinta har karkarwa yake yi sabida ɓacin rai, ina ma za ta iya da ta tarwatsewa Matar nan kai ta huta da wannan baƙin cikin, a kausashe ta ce "Tinda kin san tana yi mana komai ai kuwa ki kuka da lokacin da za ta kamaki a bisa laifin takura mana, kuma wallahi sai kin yi baƙar nadama a Rayuwarki, mara Ƴanci Korarriya!!!!" tana gama faɗe ta yi gaba fuuu kamar za ta tashi sama, Zaratan Mazan da suke takewa Mammi baya ne suka sha gabanta dole ta fasa tafiyar ta tsaya tana binsu da wani shegen kallo, a ranta tana ji dama da Wuta a kusa ta watsa musu ko ranta zai yi haske. Murmushi me sauti Mammi ta yi kafin ta ce "Duk inda ta shiga ta fito ita ɗin jinin Murtala Mai Zafi ce!! Yanayinta ne ya nuna hakan!, zafin kanta da tsaurin hali da kuma Tsageranci sak! Uwarta, sai na ji ta ƙara burgeni Matuƙa!!, Ina da burika da yawa a kanki, kuma zan cikasu ba tare da na sha wahala ba; ku barta ta tafi!!" Suna buɗa mata hanya ta ci gaba da tafiya, da sauri Suhailat ta bi bayanta don ta lura ta gama sabaucewa za ta iya zuwa ta yi wani wurin. Mammi ma jan tawagarta ta yi suka ɗaware Zuciyarta cike taf da mugun Alwashi akan Kushi. Hannunta Suhailat ta riƙe tana cewa "Ina za ki je ne Kushi??, ki nutsu don Allah ta tafi fa!!, kuma yanzu lokacin fitarmu daga School bai yi ba" Da kyar ta fizgo muryarta da ta fara dashewa sabida tsabar fusata ta ce "Ki kaini wajen Roshan!!" "Haba Kushi! me ya yi zafi haka?? ni ina na san ma inda Roshan ɗin yake??" "In ba za ki kaini ba ba ni mukullin Motarki!" Suhailat za ta yi magana Qadri ya ƙaraso wajen yana tambayar abinda yake faruwa. "Kaini wajen Roshan!" ta faɗa tareda nufar inda ya ajiye Mota. Ganinta a burkice ya sa shi bin bayanta ba musu ya shiga aiwatar da abinda ta ce. A zaune kawai yake amma ya kasa yin komai, tunane-tunane sun yi masa yawa, Yarinyar da ya kwana mafarkinta ita kawai yake muradin gani, gashi bai san inda zai fara nufa ba. Ya daɗe cikin tsaka me wuya kafin ya tuno Irfan zai iya saninta. Da sauri ya turawa Irfan kira cikin ƙaguwa. Imran ne ya ɗaga kiran yana cewa " Yaya Irfan ɗin ba shi da lafiya zazzaɓi yake yi, yanzu ma Mommy ce ta ce na zo na kirashi ya yi breakfast, tinda safiya ta yi bai fita ba" rintse idanunsa ya yi yana furta "Ya Allah!!" "Ko in ba shi wayar?, ya ce kar a dameshi ne!" Imran ya faɗa cikin sanyin jiki. Da sauri ya ce "Yeah ina buƙatarsa Imran, ka ba shi haƙuri please" Miƙa masa wayar ya yi yana cewa "Ya ce ka yi haƙuri" "Waye ne?" "Yaya Aliyu ne" da sauri ya karɓa har murmushi na suɓuce masa, "Ya aka yi ne shege ka sa ni zazzaɓin wahala, ya Kushi ta kwana don Allah??, wallahi na kasa yafewa kaina hankalina ya ƙi kwanciya." Sassanyar ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya ce "Kushi tana lafiya tinda da ita kaɗai ka damu, amma fa Umma za ta dawo daga Singapore sai dai in ta dawo ma labarin canjawa zai yi, a kaina za ta samu labari ba a kan Kushi ba; amma ya kamata ka tambayeni lafiyata ni ma!!." ya ƙarasa maganar cikin salon shagwaɓa. Dariya Irfan ya yi kafin ya ce "To ya ka kwana Yayana!" ɗan tsaki ya yi kafin ya ce ''Ba fa ƙalau ba, ni ma da zazzaɓin na kwana; a cikin baƙinka na jiya na gamu da wadda ta yi zabarin Hankali da mutsuwata, a kanta na kiraka don Allah in ba damuwa ka zo mu haɗe sai mu tattauna, wallahi ina buƙatar ganinta Irfan!, ko a kan kaina na kasa yin tunani sai tunaninta, ka ganni nan ina Company amma na kasa aikin komai har an fara yi min ƙorafi." Dariya sosai Irfan ya ke ƙyaƙyatawa har sai da Roshan ya ce "Abin dariya na zama ko Irfan? kenan ba za ka iya temakona ba?" Tsagaitawa ya yi kafin ya ce "Abin ne wallahi ya yi min citta, kullum cikin tsinewa masu soyayya kake amma yau kai ne kake ce min wata ta yi zabarin hankalinka, ai kuwa dolenta ta dawo da shi; wai ni don Allah Ƴar waye ita a cikin baƙin nawa? gaskiya ba ƙaramar Ɓarauniya ba ce tinda ta iya ɗaukar Zuciyar Zinaren nan". "Irfan Please ka bari!!, na lura a Mahaukaci ka ɗaukeni da gaske fa nake yi wallahi, in ba za ka iya zuwa ba ka zauna ni zan zo in sameka." yunƙurawa ya yi ya miƙe yana cewa "Tinda fa na ji Kushi ba ta cikin damuwa na ji sauƙi, ga ni nan zuwa." Nannauyar ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya ce "Ina jira!" daga haka ya katse wayar. Ruwa kawai ya watsa ya zura Jallabiya ya zabari key ɗinsa ya fice ko mai bai tsaya shafawa ba. Leelah tana zaune tana jujjuya Wayarta, duk ta yi nisa a Duniyar tunanin Irfan. Haja ce ta dubeta kafin ta yi dariya tana cewa "Na ga duk kin rikice Leelah wai meye damuwar ne??" Ikilima ta taɓe baki tana cewa "Meye kuwa damuwar, da alama wani take son yiwa Askin Aljihu ya ƙi askuwa". Sumayya ta yi dariya tana cewa "Ai kuwa in haka ne sai dai ki rungumi sabran don wallahi wasu Mazan ba a cin gajiyarsu." Ikilima ta ce "Tab sai dai in ba ki iya abin ba, ai ni wallahi duk ɗan iskan da ya ce ba zai wanku ba ni ma ba zai wankeni ba, akan me zan zauna ina missing yawuna a kansa?" Rabi'a ta ce "Gane min hanya Lima! ai wallahi Leelah ki rufe ido ki yi masa wankin zanin Mahaukaciya ki rabu da shi". Sumayya ta murmusa ta ce "Wannan ai ba ta fita ba ce, ke!!, mace fa aka ce miki, kin san Kaidin Mace kuwa?? kawai dai Leelan ƙaramar Ƴar hannu ce shi yasa ta zauna yake shirin goge mata hadda". Dariya suka sa me haɗe da shewa, a ƙufule Leelah ta ce "Ba ku san meke faruwa ba ne shi ya sa kuke tunanin haka, ni fa ba wani wanda nake son yiwa Aski, ba ma sai in ya kamu sannan ake Askin ba?, wai jiya ba na je birthday ɗin wani facebook friend ɗina ba? kun ga abinda na gani a wurin nan kuwa?? wallahi sai jiya na gane duk inda nake takawa ma kaɗan ne, Gaskiya shi kanshi Gayen ya haɗu, kun ga yadda aka dinga ɓarnar kuɗi a wurin nan?" Haja ta gyara zama tana zubowa Leelah idanu gami da cewa "Ke don Allah!!, don Allah ba ni labari". Sumayya ta ce "Dama ni ma ina so in tambayeki wai ya aka ƙare na ga har shabiyu ta wuce ba ki dawo ba; ko dai kin samu Me ƴar Mota ne kin bi shi Shan Minti" Leelah ta taɓe baki gami da cewa "Allah ya sittira, ni kadarata ba arha gareta da zan dinga rabawa kowa ba; Kawai Mutanen da na gani masu arnan kuɗaɗe da kyawawan Samari Ƴan hutu su ne suka tafi da hankalina, kin ga wata Yarinya Ba'indiya da ta shigo wajen nan!!? wallahi ke kowa sai da ya girgiza, kin ga wata muguwar shiga a jikinta?!! ke da kin gani kin san Ƴar Naira ce ba Ƴar Tsaba ba, amma gaskiya ni haushi ta ba ni sabida ko kallona Irfan bai yi ba amma da ta shigo duk sai ya dinga nan-nan da ita; Hee!! ai jiya an yi film wallahi!" Rabi'a ta ce "Ni fa wallahi ina Mugun son masu kuɗi ko da a labari ne, ki ga kuɗi yanda ki san satowa suke yi". Ikilima ta ce "Rai da lafiya ai wallahi ni a jikina nake jin ni ba talaka ba ce, kuma sai na yiwa Talauci yankan Ƙauna." Leelah ta ce "Ke dai bari!, ni fa yanzu so nake na samu shiga a wajen Irfan wallahi in kika fara soyayya da wannan kin kere Talauci, don Allah ku ba ni shawara ta ina ya kamata in fara??" Sumayya ta ce "Ke soyayyar zamani fa sai kina bayarwa ake yawan ba ki, amma ba komai da rashin tayi akan bar arha, kina da lambarsa ko?? ai ni Namiji komai taurin kansa a matsayin ɗankwali yake a wajena sabida na san ta yadda zan bi da shi, ke ma sai ka ce ba Ƴar Gidanmu ba har sai kin zauna an ba ki shawara akan wani Ɗan Ƙaramin Yaro, Allah na tuba Maza masu shekaru Sittin ma ni na iya juyasu bare wani under 30 " cikin jin daɗi Leelah ta ce "Allah ya iya miki Anti Summiy shi yasa nake ƙaunarki!!!, ga lambar ta shi ya za a yi?" "Ki kirashi ki ce masa kira kika yi ki yi masa ya gajiyar taro, da haka sai ki fara janshi da hira". "To wace irin hira??, ku tsara min abinda zan faɗa don Allah wallahi kwarjini yake yi min, kaina ya kulle baki ɗaya na rasa me zan ce masa, tin ɗazu fa zaman da na yi so nake na kirashi amma na kasa." Ikilima ta ce "Abu ɗan sauƙi! dawo kusa da ni ki zauna" tashi ta yi ta koma kusa da Ikiliman ta zauna tana cewa "Don Allah duk ku matso ku faɗi naku, so nake sai na susuta shi yau ɗinnan" Da'ira suka yi suka shiga tsara mata yadda za ta yi har da irin karya muryar da za ta yi masa. "Irfan in ba ka manta ba akwai wadda ta ce maka facebook friend ɗinka ce ita, sunanta Leelah har da bodyguard ɗinta ta zo" ido a waje Irfan yake kallonsa cikin tsananin mamaki "Kar dai ka ce min wannan tsohuwar mahaukaciyar kake so!??, ni fa na ga kamar kai ne bodyguard ɗin nata amma sai na basar sabida na ga ba haɗi tsakanin biri da gada, ni fa Allah ya gani ba ta burgeni ba". "Idan Allah ya so sai haɗin ya samu mana, tinda na ganta da kuma yadda ta yi min magana na gane tana da son ƙarya da son burga, ga uwa uba son cewar ita wata ce ko Ƴar wasu, amma hakan bai dameni ba kawai sai na ji duk ta tafi da nutsuwata, hakan ne ma ya sa na yarda na zamo bodyguard ɗin nata sabida ina son gane asalinta kuma ina son alaƙanta kaina da ita. "Tirƙashi!! aiki ga me ƙareka, to wai a ina ma ka fara ganinta kai?? me yasa kuma duk Ƴan Matan wurin nan masu aji da kima sai ita kaɗai za ka zaɓa? gaskiya da alamu SO bai yi maka adalci ba Abokina. "Ka san in Allah ya ƙaddara abu ba yadda za a yi, tabbas na kamu da so irin wanda ake kira daga kallo Ɗaya; ka dena raina ajinta ko kimarta, Allah yana yiwa kowane ɗan Adam baiwa ba tare da shi kansa ma ya sani ba, kuma kowane Ɗan Adam yana da Daraja; ni kaina na lura ba cikakken kamun kai gareta ba amma hakan bai dameni ba, kuma tin a daren jiya na sa a raina zan koyar da ita Darasin rayuwa, tayuwu ta dalilina za ta zamo me nutsuwa da hankali kuma kamila; Jiya lokacin da muka iso wajen ta sameni......" labarin yadda suka yi da ita ya bashi tsaf.... bayan ya kammala Irfan ya sauke gwauron numfashi sannan ya ce "Kana da gaskiya hasashen da ka yi mata ni ma shi nake yi mata musamman yanzu da na ƙara ji, kuma da alamu ita ɗin fa Ƴar Malam Shehu ce amma take wannan Fasa kan; ɗazu Imran yake buɗe kyaututtukan da aka ba ni jiya, wai ka san me ta ba ni kuwa?? ashe takarda ce a ciki wadda aka shaƙareta da kalaman soyayya, ni sai ta ba ni dariya ma, ni wallahi ta yi min kaɗan Roshan amma kar ka ji haushina!" ya ƙarasa faɗe yana dariya. Da ƙarfi ta banko ƙofar Office ɗin ta shigo cikin sauri buzur-buzur...... zumbur Irfan ya miƙe yana binta da idanu ƙirjinsa na dukan shalugude, ganinta a burkice ya fi komai jefashi cikin firgici da tsoron abinda zai biyo baya. Roshan ma zuba mata idanun ya yi Zuciyarsa na wani mugun tsalle..... ba ta zame ko'ina ba sai............... *Samu Ƴancin Karantawa, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal,☺️ Domin Ƙarin bayani 👉🏽 09079885632* *©️INDO* [11/19, 10:03 AM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 5 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *GORGEOUS WRITER'S FORUM* FREE PAGE........... Ba ta zame ko'ina ba sai kansa, sai da ta jita a jikinsa sannan ta rushe da wani mugun kuka tana faɗin "Wallahi! wallahi!! wallahi!!" iya abinda take faɗe tana ƙarawa kenan, shi dai ya yi shiru yana sauraren Zuciyarsa wadda take rawar Ƴan bori. Cikin tashin hankali Irfan ya ƙaraso wajen ya durƙusa kan gwiwoyinsa, "Don Allah Kushi ki faɗa mana me yake faruwa?, wallahi Kukan nan naki yana cutar da Zuciyata gani nake kamar laifina ne." murmushin ƙarfin hali Aliyu ya yi gami da cewa "Shiru za ka yi mata Irfan!, indai tana rantse-rantsen nan ba ta iya magana har sai ta gama, haka take tin tana yarinya ko ita ta ɓatawa kanta rai a kaina take juye fushinta". Zamewa ya yi ya zauna dafa'an, kamar zai fashe da kuka ya ce "Ni wallahi duk a tsorace nake, tayuwu akan abinda ya faru jiya ne, kuma laifina ne, daga yanzu ni dai ba zan ƙara haɗa taro ba ko Aurena za a yi gwara kar kowa ya zo." dariya ce ta suɓucewa Roshan, ganin yadda Abokin nasa ya susuce lokaci ɗaya. Ƙarar wayarsa ce ta dawo da shi daga Duniyar tunanin da ya faɗa, bai yi niyar ɗauka ba sai da Roshan ya yi magana sannan ya ɗauka ba tar da ya duba kowaye ba. Shiru ne ya fara karakaina a tsakaninsu kowa da tunanin da yake yi, shi hankalinsa sam ba a kan me kiran yake ba, ita kuwa nauyinsa ne yake neman hanata magana. Sumayya ce ta danƙara mata hararar gargaɗi, numfashi ta ja ta sauke a hankali sannan ta ce "Assalamu alaikum!" amsawa ya yi a taƙaice gami da tambayar da wa yake magana, "Lallai ma Yaron nan, ashe bai yi ma save no ɗina ba" ta faɗa a cikin ranta, dannewa ta yi ta ci gaba da cewa "Leelah ce, jiya ai da na zo birth ɗinka ban samu mun yi sallama ba na tafi." "Ayya!! ina me baki haƙuri fa, wallahi na yi busy da yawa ne shi ya sa" murmushi me sauti ta yi tana cewa "A'a ba komai wallahi, ai dama taro ya gaji haka, kira na yi dama in yi maka ya gajiya." yadda take wani kashe masa murya tana lanƙwashewa ba ƙaramin takaici da baƙin ciki ta ba shi ba, ba yabo ba fallasa ya ce "Okay na gode, yanzu ina da uzuri ki yi haƙuri, a huta lafiya". katse wayar ya yi yana dokawa Roshan da yake ta aikin hurawa Kushi iska a kunnenta harara, "Ai duk kai ne ka jawo min, a bar ni da abinda yake damuna ba za a iya ba, wai ya gajiya ta kira ta yi min kamar na sa ta" "Ita wa kenan??" a hasale Irfan ya ce "Waccan me kama da ɗanyar awarar mana !, sai ka ma tsaya tambayata?" Dariya Roshan ya yi yana cewa '' Allah ka dena cin fuskarta a gabana, in ba haka ba babu Kotun da za ta iya rabamu da kai." taɓe baki ya yi yana shirin yin magana Kushi ta katse shi ta hanyar fara tata maganar "Sai na gayawa Abbi ya yi min tsakani da ita wallahi!" "Wacece??" Roshan ya tambaya yana tsirawa fuskarta ido. Labarin abinda ya faru tsakaninta da Mammi ta bashi tana yi tana kuka tare da shan Alwashih indai ta haɗu da Azaan sai ta ɓaɓɓalla shi. Cikin mugun ɓacin rai ta yi wurgi da wayar zuwa gefe, "Na lura Irfan ɗin nan mugun ɗan yarfi da wulaƙanci ne, kuma zan yi maganinsa." Ta faɗa tana huci. Rabi'a Da Haja suka yi shewa har da rangaɗa buɗa, abin haushi ya ƙara bata amma sai ta yi musu banza don ba ta shirya Tijara ba. "Nawa yake da zai ce zai ja da ke ƙanwata! kwantar da hankalinki, ai tinda Allah ya haɗa mana komai ban ga ɗan iskan da zai gagaremu ba, ki bar damuwa a kansa" Sumayya ta faɗa cike da son ƙwararawa Leelah gwiwa, kuma ta ji daɗin hakan sosai. Hira suka ci gaba da yi tare da cin buri akan duk lokacin da ya shigo hannunsu ba zai ga da kyau ba. "A rayuwar nan in an san farkon rigima ba a san ƙarshenta ba Kushi, ki yi haƙuri don Allah, ko Bhaba ba na so ya ji abinda ke faruwa bare Maa, bare kuma har ki ɗaukaka ƙara zuwa gaban Abbi, kin san ba ƙaramar Wuta za ki tasa ba in kika yi haka; kar wata barazana tata ta dameki don ta faɗa ba lallai ya faru ba, Ki ci gaba da Addu'a Allah zai yi mana tsari da sharrinta." "Kenan ƙyaleta zan yi ta dinga raina min hankali?" "Mammi fa Ba sa'ar yinki ba ce, haƙuri da ita shi ne mafi Alkairi ko a wurin Allah sabida ita ɗin Uwa ce, in kina so Allah ya so ki to fa karki muzgunawa Makusantanki musamman Manya; ko da a hanya kika haɗu da Mutum Allah ya yi mana wasiyya akan kar mu ɓata masa rai, ki yi haƙuri ki manta da zancen mu bar shi iya mu don kar mu ƙara dawo da bara sabuwa, kin san Faɗan Umma ba ya Mutuwa." "To na ƙyaleta sabida kai, amma indai suka ƙara ba zan haƙura ba!" ta faɗa tana sauke nannauyar ajiyar Zuciya. murmusawa ya yi yana cewa "Na gode da kika haƙura sabida ni ɗin, kuma nan gaba ma ina so ki ƙara haƙurin sabida ni da kuma gujewa ɓacin ran Iyayenmu; yanzu dai in Umma ta dawo in ta tambayeki akan wani abu ki gaya mata na haɗu da wadda nake so kuma zan Aureta". Da sauri ta ɗago tana kallonsa gami da cewa "Kohne vah?!" "Sauka ƙasa Irfan ya baki labari shi ya fi ni saninta". kafin ya rufe baki tuni ta zame ta zauna a ƙasa tana fuskantar Irfan wanda ya zauna dirshen yana aikin kallonta. "Ka ji abinda ya ce?" ta tambaya tana tsare shi da idanunta da suka kukkumbura fulu-fulu. ƙasa ya yi da idanunsa wanda ya kasa yi musu shamaki da kallonta, mamakin yadda ta murmure kamar ba ita ce me kuka yanzu ba ya cika masa Zuciya. Murmushin ƙarfi da yaji ya ƙwaƙulo tare da cewa "Wai har kin gama kukan? na ga kamar ba ki yi ba don dai idanunki sun nuna!". "To ina ruwanka ni dai ka ba ni labari". Roshan ya ce "Haka take, gwara da Allah ya sa ka gani da idonka, ko wuni ta yi tana kuka da zarar ta gama haka za ka ganta kamar ba ta yi ba." "To fa!! salon naki ya burgeni, da alamu kina da saurin hucewa." dariya Roshan ya yi tare da miƙewa yana cewa "Kai dai ba ta labari kawai, akan Mita wannan da kake gani ta cancanta zama Sarauniya, ni duk ta sagar min da ƙafafu wallahi!" Irfan ya ce "Allah ya ƙara!, kin ga Kushi wata Me kama da Ƙosan yamma ya gani ya kamu da sonta, kuma gaskiya ba ajinsa ba ce don dai ba yadda za mu yi da shi, da alama mugun kamu ta yi masa Mayyar!" Zaro ido ta yi tana cewa "Mayya wadda aka ce suna cinye Mutane??" "A'a! da wasa nake yi, Mutum ce kamar kowa, kuma da alamunta tana da hankali sai dai akwaita da son abin Duniya." "To in kuɗi take so ai Muna da su, yaushe za mu je mu ganota?" "Tambayeshi, kai Malam yaushe za mu je? ko in kirata in ce za ku yi magana?" duk suka zuba masa ido cike da son jin abinda zai ce "Ni ko na na tashi zuwa ban gayyaci kowa ba, ba na so ta san ko ni waye; kamar yadda ta ɗaukeni a Talaka a haka zan je mata kuma a haka zan bayyana mata soyayyata, ina so ta soni domin Allah ba don Kuɗina ko wani ƙyale-ƙyalen Duniya ba, tin daga yanzu har zuwa bayan mun yi Aure ba na so ta san asalina, kuma idan ta sani kai ne Malam Irfan. "A'a ni!!? ba dai ni ba wallahi!, ni bakina akwai sakata kuma ban iya kwancewa Mutum zani a kasuwa ba. "To idan ta ce ba za ta Auri Talaka ba fa?" Kushi ta faɗa cike da al'ajabin maganar ta shi,,, "Ba ruwanki da wannan, ko me za ta ce zan iya jura. "Ai kuwa to ni zan fara yiwa Maa Albishir, na san Bhaba ma har tukuici zai ba ni." Aliyu bai tanka mata ba sai murmushi da ya yi, Irfan kuwa tunzurata ya ƙara yi suka ci gaba da girmama lamarin. 10:00pm Leelah, tana kwance ta rungumi ɗan yamulmulin Filon Sumayya tana waya da Saurayinta Abbas. Nuna masa take yi tamkar in ba shi ba ba ta ga wani Namiji a Duniya ba, shi kuwa sai fasa kai yake yi yana jin daɗi tare da burin wata rana a Ɗaura musu Aure. A cikin ranta kuwa haushinsa take ji don yau a haka ta wuni tana jin haushin kowa sabida rashin Mutuncin da Irfan ya yi mata. Ƙarya ta zunduma masa akan kanta yana ciwo za ta yi bacci, duk ya tashi hankalinsa haka nan ta wangarar da shi ta katse wayar. Da sauri ta miƙe zaune ganin sabuwar lamba ce take ta famar kiranta, a tunaninta Habib ne shi yasa ba ta bi ta kansa ba ta ci gaba da magana da Abbas. "Allah ya sa ba wani matsiyacin ba ne" ta faɗa tana murmushi cike da jin kanta. Kiran ne ya ƙara shigowa ta yi saurin ɗauka ta kara a kunne ba tare da ta yi magana ba. Sallama ya yi mata ta amsa tana ƙara kashe murya, "Don Allah da wa nake magana?" sai da ya ɗan nisa kafin ya ce "Hajjaju ni ne Alin nan? wanda kika bawa aiki kuma ba ki biya shi kuɗinsa ba, Alƙawari bai ce haka ba Hajjaju". wani mashi me dafin baƙin ciki da takaici ne ya soke ƙahon Zuciyarta, sakin muryarta ta yi kamar ba ita ce ta gama karairaya yanzu ba, a hasale ta ce "Uban wa ya baka lambata??, an gaya maka zan ci maka kuɗi ne? aikin banza mutum sai nacin jaraba, ba zan biya ba ma ai guduwa ka yi ba tare da ka kammala aikin ba, da ka san ba za ka iya ba ka ce za ka yi?!" jin sautin murmushinsa ya sa ta zaro ido gabanta ya yanke ya faɗi, "Allah ya sa ba wani Aljanin na nemowa kaina ba" ta faɗa a cikin ranta, har ga Allah abin na shi ya bata mamaki. "Leelah!!" ya kira sunanta cikin wata irin murya ita ba ihu ba amma sai ratsa ƙwaƙwalwar wanda ya ji ta. Idanunta ne suka ƙara fitowa sarari tsigar jikinta ta tashi bugun Zuciyarta ya ƙara tsananta, "Ina yi da jikina na nemi kuɗi ko yaya ƙanƙantar aiki yake, amma ba zan karɓi kuɗinki ba ko da kin ba ni, ni Mutum ne me girmama na gaba musamman wanda Jininmu ya zo ɗaya!; Leelah na kasa bacci, tin da idona ya sauka akan kyakkyawar fuskarki na kasa samun nutsuwa har sai da na nemo inda zan sameki, amma ina cike da tsoro da firgici don na san Ƴaƴan Masu Kuɗi ba sa saurarar Talaka." "Kutumar uban nan kayyasa!!!!" ta faɗa a burkice, "Kai yanzu kana matsiyaci da kai wanda yake karɓar kuɗi ya yi Gadi shine kake tunanin soyayya da ni?, ka shiga taitayinka wallahi ruwa ba sa'an kwando ba ne! ni na fi ƙarfin Talaka faƙiri irinka ya ce yana sona, duk wanda ya baka lambata ma sai na sa an ɗaureshi!!!" ta ƙarasa maganar tana huci, har ga Allah kawai rufe ido ta yi take masifar nan ba a hayyacinta take ba don ya gama rikita mata lissafi, ita ko kamanninsa ba ta tuna ba kwata-kwata amma sabida shi maye ne wai sonta yake yi. Marairaicewa ya yi kamar zai yi kuka ya ce "Leelah meye aibuna?! Ina neman halak ɗina ne fa ba wai sata nake yi ba, ina nema don na inganta rayuwata da Matar da zan Aura har da ta Iyayena da Ƴar ƙaramar Ƙanwata" ya faɗa yana kashewa Kushi da ke kwance a gabansa ta yi matashin kai da damtsensa ido. Sai da shiru ya buga wasa na tsawon minti ɗaya ba wanda ya yi magana a cikinsu sannan Leelah ta tattaro duk nutsuwarta ta ce "Malami! ba na son wulaƙanta Mutum, tin muna iya shaida juna ka fita daga rayuwata, ba zan iya Auren wanda sai ya nemo ya kawo za'a ci ba, haba!! ka yi min Adalci mana, na san da Talaka da me kuɗi duk ɗaya suke amma ni ban saba da irin wannan rayuwar Fatara da Talaucin ba, ka nemi daidai da kai ni ma ka barni na Auri ɗan manya daidai da ni." "Leelah wallahi ba na jin zan iya raba kaina da soyaygarki, ki ji tausayina kar Talaucina ya sa ki jefani cikin mugun hali, Zan ci gaba da nema tuƙuru domin na kyautata miki, na yi Alƙawarin ba za ki rasa komai daga gareni ba, don Allah ki faɗa min Inda gidanku yake zan zo na ganki." "Na shiga uku na lalace!!" ta faɗa a cikin Zuciyarta tana kallon ɗakin nasu wanda yake fayau, sauran abokan shawarar tata duk sun fita wajen samarinsu bare su bata abin yi, yanzu dole Zuciyarta ita ce Abokiyar shawararta. "Kin yi shiru!, ko dai za ki ba ni wahala ne kan neman Gidanku kamar yadda kika wahalar da ni wajen samun Lambarki?" "Ina zuwa!" ta faɗa gami da kashe wayar. nannauyar ajiyar Zuciya ya sauke yana lumshe idanunsa, zuwa yanzu ya lura akwai ƙaton aiki a gabansa, tsakin da Kushi ta ja ne ya dawo da shi daga Duniyar tunanin da ya leƙa, ido ya zuba mata yana bin ta da kallon tuhuma. "Ko sayen Mace ake yi kana da Kuɗin da za ka saya amma ka zauna sai Magiya kake yiwa wata Ƴar Matalauta Maƙaryaciya!" "Kushi zan fasa miki baki fa!!, ki dinga ambatonta da girmamawa Yayarki ce ita ma, daga yau Aunty kar na ƙara jin kin faɗi wata banzar magana a kanta!" "Ni ba zan ce mata Aunty ba har sai in ta Darajaka, indai kuwa a ƙasƙance za ta dinga kallonka wallahi ko ka Aure ta ba zan taɓa girmamata ba" ta yi maganar a tsiwace, har cikin ranta haushin Leelah take ji musamman yadda ta ji ta ɗauko hanyar wahalar mata da Ɗan uwa. *(SADAUKAR!!!... Na Sadaukar da Wannan Littafi nawa ga Aunty HADIZA D AUTA. Ina miƙo gaisuwa da ban girma.* *Samu Ƴancin karantawa, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Domin Ƙarin bayani 👉🏽 09079885632* *©️INDO*[11/19, 10:02 PM] INDO: https://chat.whatsapp.com/Ghq9lsJzlnsD0d4jlde7rQ *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 6 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *GORGEOUS WRITER'S FORUM* FREE PAGE........... Cikin sauri ta fice daga ɗakin jikinta har rawa yake yi tsabar kaɗuwa, ta fara kasa gane inda kanta yake don kuwa tsaurin idon Aliyu ya yi matuƙar cakusa tunaninta. Wajen Bishiyar Ceɗiyar dake tsakar gidansu ta nufa, su Innayi na zaune suna zuba surutu kamar yadda suka saba, Salim, Salma, Baby, Nana, sai Momi. Tana zuwa ta fara basu labarin abinda ya faru tare da neman shawara, Salim ya tafa hannuwa yana rangaɗa shewa "Ahayyee!!!!, Hajiya Leelah tawa ni ko na Allah, don Allah ki sa Ɗan Buhun Uban nan ya zo Unguwar nan mu yi masa Figar Kazar Kuku, in banda shi sakarai ne ma ai a Matan ma Allah ya yiwa kowa ta shi, ke ai ba ajin Talaka ba ce Auntyna ta kaina!!!, ya ganki kalar Naira ya ƙwallafa rai akan ya zo ya yi soyayya da ke ya ci banza, ƙila ma so yake ya Aureki in kika mutu ya ci Gadon Dukiyarki, wallahi kira shi Ƙofar gidan nan ya gane ke ba ƴar masu Kuɗi ba ce, kuma mu nuna masa mu ba irin Talauci ba ne, kin san Allah ranar zani zan ɗaura in yi ɗamara sai mun yi masa Zagin Tsamar nama, mu shuka masa rashin Mutuncin da har ya Mutu yana girbarsa!!!!" sosai Abinda Salim ya faɗa ya kwanta linkif a Zuciyarta, ba ta ƙara gazgatawa ba sai da ta ji Innayi da Momi ma sun ce haka, daga baya sauran Mutan wajen ma suka goya wa Salim baya. Yarda ta yi akan za ta ce yazo ɗin don haka ta yi saurin komawa ta kira shi. Lif-lif ta yi da murya ta kwantar da kai kamar ba ita ba, sannan ta ce masa ya zo sai su yi magana, sai da ta bashi full address sannan suka yi sallama, ita kanta har ta ƙagara ranar ta zo yadda za su yi masa rashin Mutuncin kece raini wanda ba zai ƙara marmarin nemar inda take ba. "Tab gaskiya Shu'uma ce Antin nan taki Khushi, wai ta ce na je Gidansu kuma na san don ta ci Mutuncina ne ya sa ta gayyaceni, na riga na samu labarin yadda suke ketawa Talaka rigar rashin Mutunci, ni ma zan hau layi." "Ni fa ji nake kamar na shaƙeta ta Mutu; duk ta sa ka susuce!" Khushi ta yi maganar har cikin ranta, "Ke! wai ba na hanaki irin maganganun ba? ban hanaki cewar za ki yiwa Mutum abu ba?" "Ka yi haƙuri!" ta faɗa tana murmushi. ƙwafa ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Ni kuma dama ai haka nake buƙata, samun lambarta ba zai sa ta yi wani ƙwaƙƙwaran zargi a kaina ba, amma idan na nemo Address ɗinta da kaina dole za ta yi zargina, kin san haka nan Don kin haɗu da Mutum kina Taraba yana Lagos nemar Address ɗinsa zai yi miki wahala indai ba kina da halin yi ba, kin ga kuwa yanzu tinda ita ta kaini da kanta zan samu damar Takura mata hankalina kwance; yanzu za ta gane ni ba irin waɗanda suka saba yiwa rashin Mutunci su kora ba ne, wallahi sai na zamo musu Tamkar Rai shi ne wanda duk jarabar mutum ko'ina aka zagaya ana tare da shi". dariya kawai Kushi take yi don abin nasa dariyar yake ba ta, har ta fara Tausayin Leelah don ta san shi sarai akwai Juriya ta fitar hankali, Yana iya jure yin komai indai har yana son kaiwa gacci akan abinda yake son yi, hakan kuma yana da nasaba da Mugun haƙurin da yake da shi, mara haƙuri kuwa bai iya juriya ba ko yaya aka yi masa abu rashin haƙurin ba zai sa ya jure ba. Suna gama waya Bilal ya kirata suka ɗora daga inda suka tsaya, shi ne ya mantar da ita Ɓacin ranta akan Aliyu har ta samu ta yi baccin farin ciki, sai dai yana cike da wasu mafarkai wanda ta kasa gane samansu da ƙasansu. Yau ta kasance ranar Laraba...... Da Misalin ƙarfe 05:00pm suka ba shi ƴancin Zuwa. Shi kuwa a Unguwar ma yayi Sallar La'asar tare da Irfan da Muzaffar, su a wurinsu abu ne wanda hannu ya iya Ƙafa ta saba, sun saba shiga Unguwanni yawon buɗe ido har da Unguwar da Mota ba ta shiga. Yau ma gantalinsu suka sha har lokacinsa ya cika sannan suka rabu shi ya yi hanyar Gidansu Leelah su kuma suka ci gaba da baɗaɗi. Da yake sanannu ne duk inda ya yi tambaya a hanya ake ɗora shi har Allah ya kawoshi Ƙofar gidan nasu. Gidan Larabawan Asali... sunan ya samo asali ne daga Bleaching ɗin da suka ƙware da yi har Innayi Kakarsu duk girmanta ba ta fasa shafawa ba, da zarar ƴan jikokin nata sun samo tare ake shafewa da ita Allura da ƙwayoyi ne kawai ba ta yi. Waɗanda ba sa shafa mai a gidan daga iyayensu Maza... Ridwan wanda suke kira Baba, sai Ƙannensa, Baba Jamilu, Baba Usama, Baba Habu, sai Umma, sai Yayyensu Maza guda biyu Yusuf (Isuhu) da Bukar, sai Salma wadda Allah ya yota fara tass kamar ba Ƴar gidan nasu ba, hakan ne ya sa Salim yake kiranta Barbela Me Fari daga Allah; wasu daga cikinsu ma suna da nasu hasken daidai gwargwado amma ba su godewa Allah ba, Leelah ma Fara ce amma ta raina natan shi yasa ta shiga harkar Bleachin don ta fi so ta ganta jajir kamar baturiya, musamman yadda ake yi mata kirari da me halittar Larabawa, kuma ta shiga da ƙafar dama don ya yi matuƙar karɓarta, wanda bai gama gane bambancin hasken asali da na shafi ba sai ya rantse a haka Allah ya yo ta. Rabi'u shi ne ƙaraminsu kaf gidan kuma gashi namiji amma hakan bai hana shi shafawa ba, tin yana ɗan ƙaraminsa ake mulka masa har ya tasa ya fara shafawa da kansa, ko da kuwa yana shafawa ana binsa da duka da zagi ne sai ya shafa sai dai me Man ta Mutu. Cikin wani Koren Yadi Me muguwar Arha, wanda a jerin waɗanda ake kira yi shirunka maraya ma shi ƙarami ne Ya haɗe yake ta zazzare ido. Da kansa ya shiga Kasuwa ya sayo irinsu kusan kala Goma ya bayar aka ɗinka masa, duk cikinsu kuwa ba wani kala me kyau sai masu cika ido, daga fari sai Yalo sai Kore sai ruwan ƙasa, hakan bai isheshi ba sai da ya ƙara zuba su a washing machine ya gurjesu suka yi laushi sannan ya kwashe, ko guga babu ya ninke ya turmutsa abinsa a sif, sai yau da zai fito ya ƙurewa wanka gudu. Yana tsaye yana rarraba ido don samun wanda zai aika ciki Sumayya ta zo giftawa hannunta riƙe da babbar leda baƙa. Riga da wando ne a jikinta sun yi mugun ɗameta, gashi ba wani mayafin kirki sai ɗan siriri. Har ta wuce shi ta jiyo tana binsa da wani kallo tin daga sama har ƙasa. Ɗan risinawa ya yi gami da gaisheta, ba ta amsa ba sai wani taɓe fuska da take yi, "Me kake yi a nan? ina fatan dai ba Kajin Mutane kake fako ba?" ta tambaya a yatsine, faɗaɗa fara'arsa ya ƙara yi har fararen haƙoransa suka bayyana, "A'a na zo wajen Leelah ne!" "Kai ne Ali?" gyaɗa mata kai ya yi, ta zuba masa wata shegiyar harara kafin ta saki wani dogon tsaki ta ci gaba da tafiya. Sai da ya dena ganinta sannan ya bawa dariyar da take cinsa damar fitowa, yau ya ga ikon Allah. Fuskarta ɗauke da murmushi ta shiga gidan, tsabar sauri har tana haɗawa da gudu, tana shiga ta saki shewa tana cewa "Leelah!!! fito na karɓo miki kayan, Shegiya Ƴar wahala wai da ba za ta bayar da hayar ba sai an bata kuɗi, sai ka ce ta ga muna cinye mata." Da sauri Leelah ta taso tana cewa "Yawwa na gode, Ɗan iska so nake ya gane duk da ba gidan Masu Kuɗi garemu ba mu ba tsaransa ba ne!" "Hehehe!! tab, ai wallahi tallahi Ba don ba abinda za ka yi da talauci ba da ba ka tsallake Yaron nan ba". Sumayya ta faɗa cikin zaƙuwa akan bada labarin, Da sauri Haja ta ce "Me kika gani?" "Wallahi kyakkyawa ne na ajin farko ajin ƙarshe, ke kin ganshi kuwa? ni fa ina ga iyayensa ɓatan Dabo suka yi ba Ƴan Najeriya ba ne, Ɗan iskan Yaro yana talaka amma sai kyau, wallahi kalar Madara ne Yaron; gaskiya Talauci bai yi masa adalci ba". Zumbur Rabi'a da Haja suka miƙe tare da nufar ƙofa a tiriliyan. Rabi'a ta ce "Da a baka labari gwara ka bayar". Ikilima ta ce "Wai da gaske kike Anti?" "Wallahil'azimu da gaske nake, kuma ki leƙa ki gani, ba don talaka ba ne in kika Auri wannan ai kaf Kurna ba lallai a samu wadda ta Auri kyakkyawa kamar ki ba." gyale Ikilima ta zabara tana cewa "Wajibin ne in ganewa idona tin kafin mu fita yi masa rashin Mutunci." Guɗar da Momi ta rangaɗa ce ta sa suka mayar da hankali kanta, "Allahu Akhbar! Allah me baiwa da ƙari, Allah me cuta da magani, in ya baka tsiya sai ya baka arziki, ya baka Talauci kuma ya baka Kadara; ai wallahi ni na san na haifu, Leelah ki sha shagalinki ni nan na ɗaure miki Ƙarƙashi, Yarinya me Farin Jini daga Allah, ba Boka ba Malam amma duk namijin da ya ganki sai ya rikice!!!!, yau da a ce me kuɗi ne hmm! wallahi ba abinda zai hanani kafa DJ yau a layin nan, ai Tinda Sumayya ta yaba da kyawunsa wallahi Uban kowa ma sai ya Sara ko yana so ko ba ya so!!!". "Kin ga Dije ba ma son magana cikin magana!, Uban waye yake bin Bokaye sabida Farin jini? ai wallahi Ƙaryar Mutum ko Maye ne, kuma in kyawun nan kike taƙama da shi ni nawa Ƴaƴan me suka rasa?" Momi ta ce "A'a ni ban ce ba!, Ƴa ce dai ta zama Kainuwa Dashen Allah ba na Mutum ba" Inna ta yi wani murmushi me cike da ma'anoni daban-daban, "Ai Dije in Allah ya ce ka yi sai ka yi ko ta halin ƙaƙa ne, wannan Karon dai ba a Buga a daidai ba tinda Kyau gareshi ba Asali ba, kin san Kuɗi su ne asalin Mutum yanzu". Taɓe baki Momi ta yi ba tare da ta ƙara magana ba, tunda Inna ta shigo zancen kuma an fi ƙarfinta sai dai kallo. Innayi ce ta iso wajen tana tafi tana rawa tana ƴan waƙe-waƙe "Allah gwanin Baiwa gwanin Hikima!, me yin Ƴan Matan Mata Duma-duma!!, Ƴaƴan kirki masu ƙashin Alheri!" "Hajiya Innayi !!" Momi ta faɗa tana dariya da shewa, dariya Innayin ta yi tana cewa "A to gaskiya fa!, Yara ƴan dumurmur Masu abin alkairi, ni bari ki ga fita zan yi wurin Yaron nan, in ya zo da leda in karɓo ta, in bai zo da ita ba in yi masa irin wankin da nake yiwa Fatarina". ta ƙarasa maganar tana gyara wani faskeken baƙin glass dake kan fuskarta. Dariya suka zuba suna ƙara fasa mata kai, ta hura hanci ta yi gaba, a soro ta gamu da su Rabi'a sun taru sai leƙensa suke yi suna zancensa, kurmutsawa ta yi ta wuce tana cewa "Har da waɗannan ƴan ciri-cirin Yaran da ko abin da za a taɓa ba su da shi ake leƙen Saurayin?" Baby ta zuba mata wani shegen kallo kafin ta ce "Wallahi baralallah Innayi!!, ko yanzu ina da abinda zan bawa Namiji komai girmansa, don ko'ina a cik......." Salim ne ya katse ta ta hanyar kai mata duka yana cewa "Ke uwarki!! shegiya me ƙirar Babe sai rashin Kunyar tsiya, idan ita tsohuwar nan mara kara ba ta jin Kunya ai sai ke ki ji don ke yarinya ce Yanzu Kunya ita ce adonki, ko me gareki ma? shegiya ƙirji kamar farantin Silba!" "Allah ya isa wallahi azzalumin banza!!" ta faɗa tana murguɗa baki, takalminsa ya cire ya yi kanta zai fara jibga ta fice da gudu sai kan Innayi wadda take tsaye tana zarowa Aliyu magana. "Na shiga ukuna! dan Ubanki so kike ki karyani ki tsugunnar da ni?!" Da sauri Aliyu ya ce "Subhanallah! bi a hankali mana Ƙanwata!!, kai kuma fa babba ne ka dinga haƙuri Abokina!" Baby ta kalleshi a raine kafin ta ce "Allah ya sittira na zama ƙanwarka, ai Zaren ba kalar Yadin ba ne, kalli fa kayan jikinka wallahi ko tsumman gidanmu ya fishi Daraja." Marairaicewa ya yi kamar zai yi kuka ya ce "Haba Ƙanwata, wannan kayan fa sai Juma'a Juma'a nake saka su, sabida zan zo na ga Hasken Idaniyata ne ya sa na saka shi yau." tuntsirewa suka yi da dariya suka tafa ita da Salim, Salim ya ce "Sabon Salo Bleaching a ɗuwawu!, ka ce wanda kake sawa yau da gobe ma sun fi haka lalacewa!! hee!!!! tab!, lallai Anti Leelah ta ɗebowa kanta Ƙara'i, kai yanzu sabida Allah a hakan kake neman Yarinya me kamar Baturiya?? wai ba ka ji kunya ba??" Baby ta ce "Gaya masa dai!" Innayi ta ce "Kun ga! ku yi mana shiru magana muke yi ni da shi; ka miƙo Ƴar ledar nan ta hannunka sai mu ci gaba da tattaunawa" Daidai lokacin Leelah da Sumayya har da sauran tarkacen suka iso wajen sai huɗa hancika suke yi suna shaƙa suna busarwa gami da ɗibarsa suna watsarwa. Ido ya tsira Mata cikin ransa yana saƙa abubuwa iri-iri a kanta, duk da ranar da ya fara ganinta ta yi kwalliya amma sai ya ga kamar yau ta fi kyau. "Barka da fitowa kyakkyawar Sarauniya!, Ina fatan kina cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali!" harara ta zuba masa kafin ta ja tsaki ba tare da ta yi magana ba. Ci gaba ya yi da cewa "Gaskiya ni me sa'a ne da na sake ganinki a rayuwata, da farko na shiga wani hali na damuwa don na yi zaton shi kenan idanuna ba za su ƙara tozali da Kyakkyawar fuskarki ba, na gode da damar da kika ba ni Leelah!!" Sumayya ce ta ɗaga masa hannu tana cewa "Ya isa !, ba mun zo ne mu saurari Tatsuniyarka ba, Ni a matsayina na Yayar Leelah ya zama dole na tantance ka kafin na bari ka fara ganawa da ita, ƙoƙarinka na cinye Jarabawar shi ne zai sa ka yi nasara". "To Anti! in Allah ya yarda zan yi iya bakin ƙoƙarina domin tsallake wannan Jarabawar, ina Matuƙar son Leelah Anti! zan yi duk iya bakin ƙoƙarina domin na kyautata mata." tin da ya fara magana idanun Sumayya suna kansa, cikin ranta tana ƙara yabawa da irin baiwar da Allah ya ba shi, ga magana ta kamala daki-daki, duk da ta san Talakan ne amma a wani kuiɓin na Zuciyarta sai ta ji Kishinsa, ji take ina ma a ce ita yake so ko shakka babu ko ba za ta ci ko sisinsa ba za ta yi soyayya da shi ta ragin lokaci, iyakaci watarana ya buɗe ido ya ji an Ɗaureta da wani ta bar shi a nan ƙwadagwas!. Sirrintacciyar ajiyar Zuciya ta sauke kafin ta ce "Da farko ina son sanin cikakken sunanka da kuma sana'arka, a Sati ko Wata kana samun Kamar nawa?, Menene matakin Karatunka?, sannan me yasa kake son Ƙanwata?" Gyara tsayuwarsa ya yi gami da yin ƙasa da kai sannan ya fara da cewa "Sunana Aliyu Mahmud, ni ɗan Unguwar Ɗorayi ne, Babana yana Sayar da Atamfa a Kasuwar Rimi, Mamata kuma tana sayar da Goro a cikin Gida, ina da Ƙanwa guda Ɗaya, matakin karatu kuma...am.. abin nan... na dai yi Candy amma in sha Allahu zan ci gaba, sana'a kuma gaskiya ba abinda ba na yi, ina sayar da Rake, sannan ina wankin Mota, kuma idan na samu wani ɗan aiki da za a yi kamar na gini haka ko ɗibar ƙasa ina yi, kuma ba laifi ina samu gaskiya, kuma in Allah ya yarda na kusa fara aikin gyaran Mota ina sa ran shi ne tsayayyen aikina; abinda ya sa nake sonta kuma gaskiya ba zan iya cewa ga Hujja ba, kawai abinda na sani ita ɗin ta cancanta a so ta, Tin da na ɗora idona akanta hankalina ya bar jikina ba na iya ganin komai sai ita, na kasa tunanin komai sai nata, kun san shi So Sarki ne, yana iya riskar Mutum lokaci ɗaya koda ba a shirya ba." sai da ta ɗan sarata kafin ta kalleshi fuska ba yabo ba fallasa ta ce "Wace irin soyayya kake yi mata? shin kana so ka aureta ne?, idan na ce ka fito a yi Aure yanzu za ka iya??" murmushi ya saki kafin ya ce "Soyayyar gaskiya nake mata ba ta wasa ba, ina sonta da duk Rai da Zuciyata, idan kika ce na fito kin yi mini babbar Alfarma a rayuwata, Allah ne kaɗai zai biyaki Alkairin da kika yi min, Rashin kuɗi shi ne zai ɗan kawo tsaiko a Aurenmu shi ne zai hana a ɗaura shi koda a yau ne, don ni a shirye nake, amma ina da ƙoƙarin neman halak zan yi aiki tuƙuru don na haɗa kuɗin da zan yi komai na Auren a cikin ƙanƙanin lokaci." "Anti Summy ki bar saurarar wannan sakaran shashashan!!, ni wallahi ko Maza sun ƙare ba abinda zan yi da shi, ni ba zan Auri jinin Talauci ba, ka ɗebo wani Yadi ka saka kamar za ka tafi roron Wake a hakan kake tunanin yin soyayya da ni?" Sumayya ta ce "Relax ƙanwata!, kwantar da hankalinki!" tsaki Leelah ta yi gami da juyar da kanta gefe. Maganganunta sun doki Zuciyarsa matuƙa gaya, sai dai ba yadda zai yi dole ya jure don yana son goge mata duk wani banzan tunani da yake kanta, sai yanzu ya ƙara gane zuwar mata ma a matsayin me kuɗi har ya Aureta tamkar ya kashe Maciji ne bai sare kansa ba, duk ƴaƴan da za ta haifa masa haka za ta shuka musu irin banzan tunaninta, don haka dole ne ya goge mata tata haddar ya koyar da ita wani Darasin. "To Malam Aliyu gaskiya ko maki ɗaya ba ka da shi na yin soyayya da Ƙanwata bare kuma Aure!, ka yi haƙuri ka kama gabanka sannan kar ka ƙara waiwayo mu, a matsayina na babba nake baka wannan shawarar don ba na so a yi rabuwar da ba ta Mutunci ba, kar ka ƙara neman Leelah ba kai ba ita in ba haka ba duk matakin da muka ɗauka a kanka kai ka sani don mu ba a kawo mana raini." Ikilima ta ce "Ai wallahi ni ban so ki ce haka ba Anti Summy, so na yi ki bar mu da shi mu yi masa Bugun Dawa ta yadda ba zai ƙara marmarin tuna Leelah ba, kai in banda babu ƙwaƙwalwa a cikin kanka ka dubeta ka dube ka fa? me gareka? me za ka iya bata? ni wallahi gani nake kai ɗinnan ko kana da Kuɗi ba ka isheni komai ba ka yi min kaɗan, bare kuma ba ka da Abokan rayuwa." Haja ta ce "To ai shi ne fa, ƙarfin hali ne da tsaurin ido irin na Bunsurun Namiji, wallahi mu da kake ganin mu sai mu yi maka tsirara mu koraka gaban tsohuwarka!" Cikin sauri ya mayar da kallonsa kanta yana mamakin jin abinda ta faɗa, jinjina kai ya yi gami da sakin murmushin Yaro bai san wuta ba sai ya taka, ai kuwa indai haka ya faru sun jawowa kansu silar bajewar Rayuwarsu, tarihinsu ma da ba za a ƙara ji ba. "Meye ka tsatstsare Mutane da ido? ka samu ka salallaɓa ka gudu tin kafin na yi maka ihun kwarto!!" Salim ya faɗa cike da iyayi da kwainane. "Zan tafi amma ga wannan Leelah ki karɓa don Allah!" "Rabi'a ta ce wai kai Maye ne?? uban me za a ci da abin hannunka??" Ikilima ta ce "To ai shi ne fa, haka kawai ma Mutum ya ciyo wa kansa bala'i don irin waɗannan cin abin hannunsu ma masifa ne, sai su yo maka fatalwa a banza" Haja ta ce "Gane min! shi ma bai isheshi ba bare ya bawa wani." "Ku yi min kyakkyawar fahimta don Allah, kyauta na bayar ba wai don wani abu ba." ya faɗa cikin sanyin jiki, abin nasu yana yi masa ƙuna sosai amma ba yadda zai yi da su sai haƙuri. "Wallahi Allah zan zazzabga maka mari tinda kai Jaki ne ba ka gane Magana sai duka!!, banza irin matsiyata an gaya maka ba a sonka, kai ba ka isa ba in karɓi abin hannunka, wallahi ka yi kaɗan Ko Ubanka ma Albarka!!, ni ka yi min ƙanƙanta sai dai in da Baban naku za mu kara sai ka je ka turo shi. "Leelah me ya yi zafi haka? me yasa za ki sako Mahaifina a cikin zancen da ya shafemu??" ya faɗa yana zuba mata idanunsa da suka fara cikowa da ƙwalla, "An sako shi ɗin!! ka yi duk abinda kake ganin za ka iya, banza mara daraja, ni ko a Ɗan aiki ka yi min kaɗan bare Mijin Aure sai dai ka haɗani da Babanka!" Kafin ya ce wani abu suka yo masa caa!!!! kowa na tsatstsaga kamar tantabarun da suka shekara ba su ci komai ba, sai da suka fige shi tsaf! har da watsa masa ruwan wanki. Salim da Salma ne kawai ke ƙoƙarin tausarsu suna hanasu duk da shi ma Salim ɗin yakan tofa albarkacin bakinsa, sai dai shi ba zagi ba baƙar magana sai habaici. Har suka dawo gida Zuciyarsa a dunguzume, idan ya tuna munanan maganganun da suka faɗa masa har ɗan zabura yake yi, ji yake kamar ya fashe da kuka. A Parlour suka samu Khushi tana zaune tana Karatu tana ganinsu ta ajiye ta miƙe tana washe baki cikin ƙaguwa da son jin labarin abinda ya faru. Sai da suka zazzauna Irfan ya ce "Wallahi rashin Mutunci suka kwasa masa masaki-masaki, yanzun haka zazzaɓi ne a jikinsa". da sauri ta koma kusa da shi cikin ɓacin rai ta ce "Ai kuwa indai wani abu ya same shi wallahi duk sai ya same su" Muzaffar ya ce "Ai mun ce za mu ɗauki mataki ya ce a ƙyale su, shi ya sa ni kuma ba zan ƙara cewa komai ba; ni zan zauna wata Ƴar kwalta ta ƙare min zagi ne? ai wallahi ko a mafarki hakan ba za ta faru ba." Khushi za ta yi magana ta fasa sabida jin ƙarar Paayal ɗin dake ɗaure a ƙafafun Ummansu, cikin hanzari duk suka miƙe tsaye Roshan ya zuba mata idanu yana murmushin farin ciki. Irfan kuwa ƙasa ya yi da kai ya kasa ko motsawa sabida mugun nauyinta da yake ji. Baƙin saree ne a jikinta wanda ya sha adon golden, ya yi matuƙar yi mata kyau, hannunta na kan dogon gashinta tana ƙoƙarin ɗaureshi. Manyan idanunta take rarraba musu tana wani ɗan murmushi na gefen baki. *Samu Ƴancin Karantawa, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Domin Ƙarin bayani 👉🏽 09079885632* *©️INDO* [11/20, 8:03 PM] INDO: https://chat.whatsapp.com/Ghq9lsJzlnsD0d4jlde7rQ *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 7 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *GORGEOUS WRITER'S FORUM* "Yaushe kika dawo Umma?" "Hmm! kwana biyu na lura kana son titsiyeni; na daɗe da sauka har na je wajen Abbi" idanunsa ne suka ƙara girma, cikin kaɗuwa ya ce "Me kika yo a wajensa??" cikin ƙasaitaccen takunta ta ƙarasa kusa da inda yake tsaye ta zauna sannan ta ce "Irfan a zauna mana!" cikin sanyin jiki Irfan ya zauna a kan Carpet har lokacin kansa a ƙasa kamar tsohon munafuki, mayar da kallonta ta yi kan Aliyu sannan ta ce "Vah hai Meri Bhaba Roshan!, ka ga dole ne na je na gaisheshi". sirrintacciyar ajiyar Zuciya ya sauke, ya yi tunanin har abinda ya faru tsakanin Khushi da Mammi ya risketa shi ya sa ta je wajen Abbin. Wurin zama ya nema ya zauna yana cewa "Mommy kin yi mana bazata fa" "Eh dama hakan na yi niyar yi" Gaisheta Irfan da Muzaffar suka yi ta amsa cikin sakin fuska tare da tambayarsu iyayensu, Muzaffar ne kawai ya amsa. "Irfan da kai na fi yarda don haka ka gaya mini abinda ke faruwa, na lura Roshan kamar ba daidai yake ba." gyaɗa kai ya yi kafin ya ce "Haka ne Umma daga Unguwa muke." "Kenan fitar da kuka yi ce ta kawo sauyin?" Khushi ta zumɓuro baki ta ce "Ni zan faɗa miki gaskiya Maa, wallahi wa....." da sauri Muzaffar ya ce "Maa wannan ƴar Adawa ce ni zan faɗa miki." murmusawa ta yi gami da cewa "Ina saurara!" Gyara zama ya yi sannan ya shiga bata labarin duk abinda ya faru, Irfan da Aliyu ba su ce komai ba sai zare ido. Labarin ya taɓa ta har cikin rai amma sai ta yi kamar ba ta damu ba, "Abinda ba za ka iya faɗa min ba kenan Roshan?" ta tambaya tana tsare shi da idanu, murmusawa ya yi gami da cewa "A'a Maa, kawai dai na fi so sai komai ya daidaita ne sai in gaya miki, na yi zaton komai zai zo da sauƙi." "Achcha!, ni ma Ina Sonta, ka ƙoƙarta ka shawo kanta; sai dai ina so ka san ba zan iya jure ganin ana wulaƙantaka ba, ya zama dole ka kula, su ma su kula". "Ni Mommy kawai ki je ku yi maganar Auren, ko ba sa so ki sa a yi da kanki!". Khushi ta faɗa tana taɓe fuska. Yalwataccen murmushi ta yi gami da cewa "Ba komai ne Kuɗi ke iya saya ba Khushi, zan iya saya masa Yarinyar amma ba zan iya saya masa soyayyarta ba, duk da kuwa tana da son kuɗi kin ga za ta Auri kuɗin ne kawai ba Roshan ba, tunaninsa me kyau ne kuma abinda yake so shi nake so don haka zan saurara musu ba zan shiga lamarin ba sai dai in tura ta kai bango". miƙewa Roshan ya yi yana cewa "Ku tawo mu je sashina Muzaffar; gaskiya Mommy ya kamata Bhaba ya dawo, na gaji da aiyukan nan wallahi." murmushi kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba don ta san ya riga ya dawo ɗin. Da daddare..... Tafasa da zaɓalɓala kawai Zuciyarsa take yi, ture wayarsa ya yi zuwa gefe yana jin kamar ya buga ta da ƙasa, ya yiwa Leelah kira ya fi a ƙirga amma duk tana waya, wadda ya tabbata da banzayen samarinta take yi. "Wai me ya sa ta kasance haka ne?" ya jefawa kansa tambayar da ba shi da amsarta, kamar ya ɗora hannu a ka ya dinga ɓarza kuka haka yake ji, jikinsa ya ɗauki wani irin zafi kamar wanda aka raɓa a wuta. Har ya haƙura da sake kiran nata amma sai ya kasa jurewa, ƙara janyo wayar ya yi ya tura mata kira, cikin sa'a ta ɗauka gami da sallama cikin wata siririyar murya. Duk da ya san ba don shi ta yi ba amma sai ya tsinci kansa da jin daɗi, da a ce kullum haka take a nutse da ya more, "Yanzu kin kyauta kenan Leelata?" ya yi maganar kamar an yi masa dole. Sai da gabanta ya yanke ya faɗi har ƙasa, tabbas ba za ta manta da muryar nan ba duk da ba yadda ta saba jinta ta ji ta a yanzu ba, lallai in haka ne ta kwaso wa kanta Bala'i da Ƙara'i ta bakin Salim, "Waye kai??" ta tambaya cike da son tabbatarwa, "Bawan Allahn da Sonki ya yiwa Mugun harbi ne, Na kamu da ciwo wanda ke kaɗai ce maganinsa Leelah!, ki yi haƙuri za ki ga kamar na ƙi jin maganarku ne, na yi ƙoƙarin nesanta kaina da ke sai na ji ba zan iya ba, ba ni na ɗorawa kaina sonki ba don haka ba zan iya yayewa kaina ba; ki temaka min kar ki bari rayuwata ta salwanta!". ya ƙarasa maganar kamar zai fashe da kuka. Shiru ne ya ratsa tsakani na ɗan lokaci kafin Leelah ta katse shirun da cewa "Ka gama???" "Indai magana ce a kanki ban ga ranar da zan dena ba Leelah! indai za ki saurareni zan iya kwana ban gaji ba." murmusin rainin hankali ta yi kafin ta ce "Ba ka da darajar da zan iya zama ina saurarenka sai dai ka je ka nemi gajarabul irinka, ni ina da waɗanda zan yi magana da su masu kima da Daraja ba mara aji mara Zuciya irinka ba; Kar ka ƙara kiran wayata tinda ba ta sa'arka ba ce, Yaro ɗanye cakal da kai sai shegen naci da rashin Zuciya! mewtch!!" ta ja tsaki gami da kashe wayar. Rintse idanunsa ya yi da ƙarfi yana faɗin "Ya Salam!, Allah ga ni gareka!". wani irin zafi Zuciyarsa take yi, da zai iya da ya yi kuka ko zai samu sassauci. "Ki ji fa Haja wannan ɗan shegiyar ne ya kuma kirana, ni dai ina ga da Maye na yi gamo!" ashar Haja ta zunduma cike da mamaki ta ce "Shi wai duk abinda muka yi masa bai haƙura ba?? tab"! ai kuwa sai mun yi da gaske, Talakawa fa tsinannen naci garesu da taurin kai ga uwa uba rashin Zuciya". "Ke ma fa Talakar nan ce Ƴar Talakawa, wannan kalmar ba ta dace ba, a dinga sarrafa Baki, da ma cewa kika yi wasu Mutanen". Salim ne ya faɗa yana watsa mata harara, tsaki kawai ta ja ba tare da ta ƙara magana ba don ta san Salim ya fi ƙarfinta indai wajen tafiyar harshe ne. Yana fitowa ya yi tozali da Bhaba a Falo, yana zaune yana danne-danne a Laptop, a gefensa Khushi ce a rakuɓe sai surutu take zuba masa, suna yi suna dariya. Da sauri ya ƙarasa yana cewa "Bhaba kai ma surprise??" Dariya Bhaba ya yi gami da cewa "E mana, zo ka ba ni labari ya-ya ka kwana?" kusa da shi ya zauna gami da kwantar da kansa bisa kafaɗarsa, zazzafar iska ya furzar kafin ya ce "Bhaba kusan ba lau ba, na kwana ina tunani da mafarkai, amma dai kana Lafiya ko Bhaba?, ya kamata ku dinga sanar min kafin ku tawo fa, haka jiya kawai sai na dawo na tarar da Maa a gida." "Ina lafiya Aliyu, kar ka damu za mu dinga sanar da kai in sha Allah, ya kuma fama da ƙanwarka? na shiga Masana'antu na ga ko'ina komai yana tafiya daidai, ina ƙara yabawa da ƙoƙarinka Ɗana." Khushi ta ce "Wai Bhaba har wata ɗawainiya yake yi da ni?" Murmushi Roshan ya yi yana cewa "Share wannan Tsarabar Indian Bhaba, Na gode da yabawarka, dama fa ina da maganganu da yawa har zan biyoka inda kake sai na haƙura". "Yanzu ai ga ni, ina saurara." "Abin sirri ne ba na so wannan Ƴar Madabon ta ji." ya faɗa yana dariya, turo baki ta yi gaba tana cewa "Ai ko an yi a gefe sai Bhaba ya faɗa min, ka san dai tsakaninmu Amanatun Amana!" "Bari in kwanta ta wuce!" Roshan ya faɗa gami da sunkuyawa, "Wai kana nufin Ƙarya nake yi!!!" ta faɗa cikin ɗaga murya tana zaro masa gwala-gwalan idanunta. "Ni ban ce ba kawai dai na ji ta tawo ne da girmanta kamar za ta lamutseni. "Ka ci sa'a yanzu safiya ce da sai na yi gutsi-gutsi da harshenka" ta faɗa tana huci, "To a bari sai da rana mana?" "Ko kula ka ba zan yi ba!" ta yi maganar tana juya masa ƙeya. Shi dai Bhaba ci gaba ya yi da aikinsa tare da yi musu dariya. Mama, Rabi'a, Haja, suna zaune a ɗakin Maman sun haɗe kai suna tattaunawa....... "Dan Ubanku a gidan nan kowa yana abin arziki amma banda ku!, ke dama Rabi'a Ranar nan ina ji ina gani wancan Ɗan Daudun ya gama ce miki Ɓarauniya, Dan kan Ubanki kina mace amma kuɗin Ɗan Man Bulitin ɗin ya gagareki sai kin haɗa da sata!, kuna kallo Laila yadda take fantamawa da Samari iri-iri, ji wannan dai da ya zo Talakan nan, ko ni da na leƙa na ganshi sai da yawuna ya tsinke, kuma da yake Ɗan Halak ne har da Ƴar Ledarsa ya tawo, to ko irinsu kuke tarawa ai za a rage, ko ba komai za a ce kina da kyakkyawan Saurayi me zubin Larabawan Sudan, yanzu fa Rabi'a a matsayinki na Babba Samarinki Biyar fa kacal, kuma Ƴan iska duk ba sa sakin hannu ma kamar na Hajara" Mama ce ke maganar cikin ɓacin rai da takaici, su dai sun yi shiru suna saurarenta sai da ta gama sannan Rabi ta ce "To ba kya ga Leelah ta fi mu kyau? kuma ita fa tana shiga cikin Manyan masu kuɗi ba ta da Ƙawa ko Aboki Talaka, kin ga kuwa mu ina za mu samu irinsu?" "Ubanki na ce!" Mama ta faɗa tana watsa mata daƙuwa, ci gaba ta yi da cewa "In banda rashin godewa Allah me Laila za ta nuna muku??, kuna da gaba kuna da Baya, kawai don haskenta irin na Turai ne shi kenan?? ɗan hancin ma da take taƙama da shi kuna da shi sai dai kawai ta ɗan fi ku karan hancin, wallahi da Rabi'u mace ne da na huta, ku na ga ba abinda za ku iya yi min, gashi Rabi'un ma duk da shi ne Autana ya fi ku kyau". Haja ta ce "Gaskiya fa Mama kina kan hanya, ni ma abin nan yana damuna, ya kamata mu nemi mafita, kowa ya fi mu Samari da Kuɗaɗe a Gidan nan, ki duba ki ga su Anty Summy don Allah, su ci me kyau su sha me kyau su sa sittira me kyau, ita kanta Leelah wani lokacin a wajen Summy take aron kaya take sakawa ta fita tana burge Samari ". "Rabi'a ta ce ita fa Summy maganar gaskiya tana Karuwanci, ni kuma da in je in yi Zina in samu kuɗi wallahi gwara da an aje in sata." Mama ta ce "A'a ai ni da ɗan sauran haddata, gaskiya ba zan bari ku yi karuwanci ba, sai dai ɗan shan mintin nan indai za su baku kuɗi to ku yarda, ya kamata fa mu kori Talauci Ƴaƴan nan!!, hmm!! kuna ji har yada mana da magana ake yi??" Haja tace "To Mama yanzu yadda za a yi ki ƙara nemo mana maganin farin jinin nan mu ci gaba da yi, in ƴan Samarin suka zo sai mu sauya Salo mu dinga kame Zuciyoyinsu." Mama ta washe baki gami da cewa "Yawwa Ƴata ta kaina, ai na san ke kanki yana ja, gobe zan je wajen Malam Manu zan karɓo muku, zan je wajen Yayarku Hasiya na karɓi ko ƴar Dubu biyar ce in tana da su, in ya yi mana aikin a Dubu uku sai in sayo muku Man da ƴar hoda da janbaki na dubu biyun ku dinga shafawa, yanzu sai da kwalliya wallahi". Sosai hakan ya yi musu daɗi suka ci gaba da tattaunawa a kan lamarin. Aliyu, Bhaba, suna zaune a Office ɗin Bhaba suna tattaunawa Aliyu ya ce "Bhaba ni fa aiki nake so." da ɗan mamaki ya ce "Aiki dai? wane iri kenan bayan wanda kake da shi?" "Garage ɗin Abdussalamu me yi mana gyaran Mota za ka kaini, zan fara aikin gyaran Mota." ɗagowa Bhaba ya yi daga kallon Takardun hannunsa ya zubawa Roshan idanu yana nazartarsa, "Meye dalili? so kake ka jawo min zagi ne??" girgiza kai ya yi gami da cewa "Naa Bhaba!, duk me hankali ba zai zage ka ba sai dai ya jinjina maka, za a ga cewar duk kuɗinka bai sa ka lalata Ƴaƴanka ba, ni fa a tsarina Bhaba ina so na san zafi da daɗin kowace irin Rayuwa, na fi so ko me zan yi in yi shi da jikina ba wai in dinga shiga rigarku ba Bhaba!; amma dai gaskiya ina da dalilin koyon gyaran Mota a wannan lokacin." jinjina kai ya yi gami da cewa "To in ji dalilin!" ƙasa ya yi da kai tare da sassauta murya "Bhaba... am... gaskiya na kamu da tsananin son wata Baiwar Allah ne, don ita nake so na koyi gyaran Mota". ya faɗa yana tsirawa Bhaba idanunsa da suka kawo ruwa kamar da an ce ar!! zai fashe da kuka. "Ikon Allah, wacece ita? ƴar waye??" Bhaba ya jera masa rubdugun tambayoyin cike da mamaki. Girgiza kai ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Bhaba na san kuna son Farin Cikina kuma kuna yi min komai, Ina tsanin sonta, kar wani abu gareta ya sa ku yi ƙoƙarin nesanta ni da ita!" Numfashi Bhaba ya sauke kafin yace "Duk na ji wannan Aliyu, amsata ita nake buƙata!" "Na san masu kuɗi su ake kira Wasu, wane, wance!; Ita ɗin ba kowa ba ce, kuma ba ƴar kowa ba ce, iyayenta Talakawa ne ita ma haka, sai dai tana da son kuɗi kuma ba ta son Talaka kwata-kwata, tana da son ƙarya sannan ta sa a ranta ba za ta Auri Talaka ba; Sabida halinta na raina Mutane ne ya sa da ta dubeni don ta ga Yadi a jikina ba ta san adadin Kuɗin da aka sa aka saye shi ba, ta yi zaton ni Talaka ne shi yasa take yi min kallon ƙasƙanci, ni kuma ina son Aurenta a matsayin Talaka, ina son sauya tunaninta na gyara mata rayuwa, bugu da ƙari kuma ina so ta so ni ne, ba Kuɗina nake so ta so ba, kuma ta so ni domin Allah ba don ƙyale-ƙyalen Duniya ba, shi ya sa na yanke wannan hukunci; don Allah Bhaba kar ka ce min a'a ka daure ka Amince da ita ka so ta tamkar yadda kake Sona. hawayen da suka fara tsere a kan Kumatunsa ne suka dakatar da maganar ta shi ba don ya kai ƙarshe ba... Bhaba ya murmusa kafin ya ce "Lallai yau na ga yadda Kiyashi yake yin Nasara a kan Zaki; Aliyuna ne ya saka ni gaba yana yi min kuka akan Mace??" goge hawayen ya fara yi, murmushi ya suɓuce masa, cikin sassanyar muryarsa ya ce "Bhaba Zuciyata tana yin rauni a duk lokacin da na tuna halin da nake ciki; su ɗin Ƴan Gargajiya ne suna da tsauri sannan ka san ba sa shakkar Cin Mutuncin Mutum, sun ɗauka son ƙarya nake yi mata ba na gaske ba, ba su san cewa zan iya komai dominta ba, ina da babban aiki a gabana Bhaba!!." "Tunaninka me kyau ne don haka ba zan daƙile ka ba, duk wanda ya ga wani a cikin wani hali kuma ya yi silar shiryuwarsa Lada yake samu; Allah ya ida nufinka na Alkairi Jarumina!; Zan yi magana da Abdussalamun" Bhaba ya faɗa yana murmushi, sosai abinda Aliyu ya yi da kuma wanda yake shirin aikatawa ya yi masa daɗi, yana matuƙar farin ciki a duk lokacin da ya yi duba ko ya tuna irin kyakkyawar Zuciyar ɗan nasa. Godiya Roshan ya shiga zubo masa, Bhaba yana shirin yin magana suka ji an banko ƙofar Office ɗin da ƙarfi. Kansa tsaye ya shigo har kan Bhaban sannan ya tsaya yana bin Aliyu da wani banzan kallo. Kawar da kai Roshan ya yi gami da cewa ''Ya haka Haydar? me yasa zaka shigo ko sallama babu kuma ka tsayawa Bhaba a ka?" "Na sa da kai ne???" ya faɗa a masife, banza Roshan ya yi masa, ƙwafa ya yi tare da kallon Bhaba yana cewa "Dad ni kuɗi nake buƙata!" rai a ɓace Bhaba ya ce "Sai ka bugeni ka ɗiba Haydar!!" Masifa ya fara yi "Ni fa ba na son irin wannan rayuwar Daddy!, haba don Allah, ka na da kuɗin nan amma ka bar ni ina yawo da tsiya, komai naka na wannan Ɗan iskan da wannan Shegiyar Yarinyar ne, ni ka manta da ni baka ɗaukeni a matsayin komai ba." Cike da damuwa Aliyu ya ce "Haba Haydar! wai ka manta da Mahaifinka kake magana?, kana faɗen baƙaƙen maganganu kana ɗaga murya kamar za ka dokeshi, bai dace ba irin haka." ya ƙarasa maganar kamar zai yi kuka, yana matuƙar jin baƙin cikin irin munanan halayen Ɗan Uwan nasa. Ƙara hayayyaƙowa Haydar ya yi yana cewa "Don Uwarka ina ruwanka?? Daddy ka shiga tsakanina da Yaron nan ka ce masa kar ya ƙara yi min magana ko da shi nake bare in ba da shi nake yi ba!!". Bhaba ya cire hularsa ya ajiye a gefe sannan ya ce "Haydar!! ba zan taɓa dakatar da shi akan gaya maka gaskiya ba, watan wata rana in da rabonka sai ka gane ka shiryu ta dalilinsa, Kuɗin kuma ba zan bayar ba; na yi maka sittira na baka ci na baka sha, ina kula da kai ina kula da lafiyarka, duk wani haƙƙinka da ya rataya a wuyana ina saukewa, to na sallame ka, babu guminka a cikin Dukiyata, kuma ba ka yi aikin komai ba, don haka ba za ka samu ko Sisi nawa ba musamman a yanzu da ba ka bini ta maslaha ba; kuma in ka taɓa abuna ba tare da sanina ba kai ma ka san Sata ka yi, daidai kake da kowane Ɓarawo ka gane???, idan har kana da Zuciya ka tashi tsaye ka san zafin nema; Shashasha mara hankali!!!" yana kaiwa nan ya miƙe ya yi hanyar fita fuu!!!. Da sauri Aliyu ya miƙe yana kiransa amma ya yi masa banza, rai a ɓace ya ce "Ka ga irinta ko?? wai me yasa ba za ka gane ba Haydar? ka san nauyin Zunubin ɓatawa Iyaye rai kuwa??" "Wallahi sai na sabauta ka yanzu a wurin nan!, Ɗan iska Munafuki har ni za ka dinga gayawa zancen banzar nan?" "To ka yi haƙuri!" Roshan ya faɗa yana ƙoƙarin ficewa daga Office ɗin. Tare suka fito Haydar ya yi saurin bin bayan Bhaba yana ƙara maimaita masa buƙatarsa, banza ya yi masa ya shige Motarsa ya bar Companyn. Aliyu ma wajen ta shi Motar ya nufa yana shirin shiga Haydar ya ƙaraso wajen yana hayaƙi..... "Ba dai junin ka Munafurci ba? to wallahi za ka gane na fika iyawa, ka je ka zuga shi ka yi bakan-bakan akan komai na shi ba wanda yake kalla da Mutunci sai kai sai Uwarka, to wallahi sai na yi maganinku!!" Zuwa yanzu abin na shi ya fara tunzura Aliyu, bai taɓa biye masa sun yi sa'insa ba bare faɗa, ko da wani ma bai taɓa yi ba bare ɗan uwansa, a yanzu kuwa ji yake ko dakuwa ce zai iya buɗawa a yi. "Na baka haƙuri ka dena bi nan da sharri, ni tafiyata zan yi, sai ka je ka yi duk abinda za ka yi ina jiranka!. a fusace ya ce "Ni kake gayawa haka? ai kuwa za ka gani, wallahi wataran sai na hana ka rintsawa da sunan bacci, shege Ɗan gidan taƙi zama, Ɗan me jan kunne Juyayya me zubin Karuwai, ". idanunsa da suka canja launi sabida tsabar ɓacin rai ya zuba masa, jikinsa har karkarwa yake yi "To Alhamdulillahi tinda Ita juyayyar Biyu ta haifa ita kuma wadda ba a juye take ba ta samu ɗaya, ka ga ko a nan ta farke ta ƙara!!, kuma duk abinda za ka yi ka guji sako Mahaifiyata a ciki, haƙurina ya yi low wallahi yanzu daidai nake da cin Uwarka!, Shege Ɗan Amarya!!!!". SHARE FISABILILLAH *Samu Ƴancin Karantawa, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Domin Ƙarin bayani 👉🏽 09079885632* *©️INDO*[11/21, 8:48 PM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 8 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *G.W.F* "To Alhamdulillahi tinda Ita juyayyar Biyu ta haifa ita kuma wadda ba a juye take ba ta samu ɗaya, ka ga ko a nan ta farke ta ƙara!!, kuma duk abinda za ka yi ka guji sako Mahaifiyata a ciki, haƙurina ya yi low, wallahi yanzu daidai nake da cin Uwarka!, Shege Ɗan Amarya!!!!". Sosai maganar ta daki Zuciyar Haydar, ya yi kansa a fusace yana cewa "Ni kake cewa ɗan Amarya? wallahi zan canja maka kammani a wurin nan!!!!" "Na faɗa, in ka isa ka ce ba Amaryar ba ce ba mana!, banza Fasiƙi, Mazinaci, Ɗan Giya!!" Kukan kura Haydar ya yi yana shirin shaƙararsa MD ya doka masa tsawa, dakatawa ya yi yana huci gami da cewa "Ni wannan zai kira Mazinaci!!?? wai ni sa'an wasan shi ne Dan uwarsa?!!" "Na faɗa mazinaci !!!,,, in ka yi Zuciya ka dena!!; Kuma ka dena sawa a ranka ka girmeni, na tabbata da Haihuwar wuri ta yi sai dai ka kirani Ubanka don na zama Babban Yaya!!" sake haurowa ya yi yayo kansa zai haushi da duka MD ya yi saurin riƙeshi a tsawace ya ce "Wai ba haƙuri nake baka ba??, me ya sa ba ka jin magana ne??" Aliyu ya ce "Da ka barshi ya zo mu buɗa in nuna masa Ƙarfin Mutum me hankali daban na ɗan shaye-shaye daban, wallahi da sai na yi maka Shegen Dukan da ba za ka gane Gidanku ba!!!" A fusace MD ya ce "Ashe kai ma ban isa na faɗa ka ji ba Aliyu?? ka duba fa ka gani ko'ina Mutane ne suka taru suna kallonku!, ina ganin na isa da ku ashe ba haka ba ne??" Ƙwafa ya yi kafin ya ce "Na haƙura dai sabida kai, amma wallahi da ba ka wurin nan sai na yi masa dukan da ba zai ƙara marmarin yin faɗa da wani ba." MD ya ce "Na san ai kai za ka ji maganata dama, maza ka yi tafiyarka!" Fizgewa Haydar ya yi yana cewa "Ni kuma wallahi sai na cirewa Yaron nan raini!!, ba zan taɓa haƙura ba sai na ga na yi masa lahani wallahi!, kuma indai ka shiga Motar nan ba za ka je inda za ka je lafiya ba." Rai a ɓace MD ya ce "Kar ka shiga Aliyu, tsaya ni zan kai ka gidan da kaina sai in ga tsiyar da zai iya yi!!, kai Manager maza ka sa wannan shashashan a Mota a fitar da shi daga Companyn nan!!" ya faɗa yana kallon Manager wanda ke tsaye a gefe yana kallon Ikon Allah. Amsawa ya yi kafin su ƙaraso da shi da wasu daga cikin Mutanen wajen suka fara kiciniyar janyeshi. ko da suka kama hanya tsaki kawai Aliyu yake ja, ya so an barshi ya yi masa ɗan banza duka wataƙila zai dawo cikin hankalinsa. "Abin fa sai haƙuri Aliyu ka dena damun kan ka In sha Allah komai zai wuce" MD ya faɗa cike da damuwa, jinjina kai Aliyu ya yi gami da cewa "Ba komai, ta wuce!" ba haka Md ya so ji ba amma sai ya maze ya ƙara marairaice fuska ya ce "Na rasa me ya sa shi kwata-kwata ba shi da hankali, bai yi halin Mahaifinku ba, kuma na san duk asalin abun daga Mamarsa ne, ta bar yaro haka sakaka ba tarbiya bai san mutuncin kansa ba bai san mutuncin wani ba, gashi na lura ba ya ƙaunarka kwata-kwata, yanzu ka ji irin munanan kalaman da ya dinga faɗa a kanka da Mamarka." a ƙagauce Aliyu ya ce "Shi irin nasa tunanin kenan, amma wata rana in Allah ya yarda zai dena." "Anya kuwa zai shiryu?, ai ya riga ya yi nisa ba ya jin kira, kana ji fa cewa ya yi in ka shiga Motarka ba za ka je gida lafiya ba, in ba sa'a ba wani tuggun suka shirya maka, shi neman kashe ka ma yake yi, gaskiya ya kamata ka tashi tsaye." "Kawu don Allah saukeni a nan akwai inda zan je" Aliyu ya faɗa cike da takaicin surutan MD ɗin. Md ma takaici da baƙin ciki ne suka kama shi, ya rasa wane irin yaro Allah ya haɗa shi da shi wanda sam ba ya ɗaukar zuga ko tunzurawa, gashi ya lura shi bai ma fiye son a faɗi laifin ɗan Uwan nasa ba. Jin ya yi shiru ya sa ya ƙara cewa "Ina magana fa, akwai inda zan je a saukeni a nan." "Wai kai wane irin Mutum ne Aliyu? wai ba ka ga ko fita kai kaɗai ba a so ka dinga yi ba sai da Masu tsaronka?, kai yanzu a nan kuma ba motar da za ka hau gare ka ba" "Zan ƙarasa a Napep, ai Allah ne me tsare bawansa ba wasu ba. ''Yanzu kamar kai sai a gan ka a Napep? ka dinga nemawa Iyayenka Mutunci mana!" "Kawu Please Ka barni na yi abinda nake so, ni waye in ba Mutum ba? ko a kan iska ake so in dinga yawo?" Faaaa!!!!! MD ya yi gefen Titi da Motar ya tsaya, a fusace ya ce "Ana so a kare lafiyarka kai kuma kana zillewa har da faɗa min magana, to sai ka tafi ai." "Ka yi haƙuri" kawai ya ce gami da ɓalle Murfin Motar ya fita, shi a rayuwarsa indai za ka aibata wani sannan ka yabe shi to fa ba zai taɓa jin daɗi ba, shi kuma MD halinsa kenan. Yana yin gaba ya ɗauki waya ya turawa Hajiya Habiba kira. Ba tare da ɓata lokaci ba ta ɗauka da ta ga shi ne, ko sallama bai yi ba ya fara cewa "Gaskiya Hajiya Habiba kina da sakaci!, yanzu ki duba ki ga Yaron nan Ƙanin Haydar ne amma kar ki ga irin zagi da cin Mutuncin da ya yi masa, da har dukansa zai yi sai da ƙyar muka samu muka hana shi." Wani mashin baƙin ciki ne ya soki Zuciyarta, a fusace ta ce "Ina Almustafan? a gabansa yana kallo hakan ta faru ko? ai duk laifinsa ne wallahi ya fifita wannan Ɗan iskan a kan babban Ɗansa, ai Babba babba ne duk inda yake." Da sauri MD ya ce "Ina!!, ba ya wurin, amma dai duk shi ya assasa fitinar don yana fita daga Kamfanin sai ga Aliyun ya zo ya fara tayar da hayaniya, bai kamata a ce Haydar ne babba kuma ana yi masa irin wannan ba, ai sai Duniya ta zage mu, wallahi Hajiya Habiba kar ki ga irin Zagin cin Mutuncin da ya yi miki ke da Haydar ɗin." "Dole zan ɗauki Mataki MD na gode maka da kake tunatar da ni, don Allah ka ci gaba da sa min ido a kansu. Tana gama faɗen haka ta katse wayar tana huci, ya zama dole ta san yadda za ta yi ta fara yun Yaƙin gaba-da-gaba da wannan Matar tinda ta sheƙa na ƙarƙashin ƙasar ta ga ba tsaba. Cikin farin ciki da murna ya turawa Bhaba kira, cikin sa'a ya samu ya ɗauka. Abinda ya faru da wanda bai faru ba ya gaya masa, kamar yadda ya lintumawa Mami Ƙarya akan Aliyu haka ya muzanta Haydar ɗin a wajen Bhaba. Sosai ransa ya ɓaci, suna yin sallama ya kira Mami ya ƙare mata ƙalau, hakan ya ƙara tunzura Zuciyarta. Murmushin mugunta MD ya yi yana cewa "Ai sai na haɗa muku Wutar da ba zaku iya kashe ta ba, Almustafa yana tsaye za a ji ya faɗi daga haka sai Ƙiyama; dole sai na cimma Ƙudurina a kansa!!" Roshan kai tsaye Gidan su Irfan ya wuce don yanzu komawarsa gida haɗari ne babba, da zarar Ummansa ta gan shi a burkice shi kenan hankalin Gidan ya gama tashi. Ba ƙaramar Murna Leelah ta yi ba da ta ga Daren Jiya bai kirata ba har gari ya waye, sai murna take yi tana faɗawa Ƴan Uwanta sun yi maganinsa. Tana zaune a garden kan wata haɗaɗɗiyar Kujera ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya tana taunar cingam, Azaan yana zaune a gefenta yana yi mata sambatu a kan Khushi ta yi masa banza kamar ba da ita yake yi ba. Gajiya ya yi ya fara fusata yana cewa "Ni wallahi tinda ba za ka iya yi min komai ba zan yi da kaina, kuma kar wanda ya ce ban yi daidai ba." dariyar da ta fara yi ce ta dawo da shi cikin nutsuwarsa, ya zuba mata ido yana mamakin dariyar. "Ni fa na ce zan yi ba kai ka sa ni ba, don me za ka zo ka takura min??, na ce zan yi maka to ka jira lokaci kawai " "Ni fa Mammi ba na so ki yi abinda za ki cutar da ita don ni sonta nake yi." ido ta zuba masa na ɗan lokaci kafin ta kawar da kai ta ce "Ba na jin akwai wata rana da za ta yi maka bayan ka gama amfani da ita, bai kamata ka so ta ba don ita ma ba za ta taɓa ƙaunar ka ba; babu wani so da zai haɗamu da waɗannan Mutanen sun riga sun tarwatsa shi tin farko! don haka ina so ka cireta daga Zuciyarka, koda kun yi Aure to ba me tsawo ba ne ka dinga tuna hakan!". Jikinsa ne ya yi sanyi liƙis, duk da shi ma ba shi da burin Aurenta har ƙarshen rayuwarsa amma yana jinta har cikin ransa kuma ba ya son abinda zai cutar da ita, a wani gefen na Zuciyarsa kuwa yana jin kamar in ya kashe kwaɗayinsa da ita zai ji ta fice masa a ka lokacin ba shi da wani hurumi da ita zai iya zubawa Mammi ido ta yi duk abinda za ta yi. "Lokaci ya kusa wanda zan sa Moonath zubar da hawaye, sannan na lalata rayuwar wanda ya Lalata tawa rayuwar." cikin yanayin sanyin da jikinsa ya yi ya ce "Wai Mammi meye tsakaninku da su haka? waye ya Lalata rayuwarki??" murmushi me cike da manufofi ta saki gami da shafar kumatunsa sannan ta ce "Lokacin da za ka sani bai yi ba, ka tashi ka je ka yi sha'aninka" Ba don ya so ba ya tashi ya bata wuri Zuciyarsa cike fal da tambayoyi. Yau Roshan ya fara zuwa Aiki a garage tin Misalin ƙarfe biyu ya je sai Ƙarfe biyar ya nemi damar tafiya Oga kuwa ya Amince don girmama shi yake yi sosai, ko aiki kasa sa shi ya yi sai da ya takura a ba shi abin yi tukunna, kuma ya zage ya yi aikin da iya ƙarfinsa. Kuɗin Aikinsa ya bashi daidai da yadda ya yi sannan suka yi sallama ya ɗaware. Bai zame ko'ina ba sai Gidan su Leelah. Ya yi wani kicin-kicin da shi kamar an ƙwatoshi daga bakin Kura. Irin Yadin ranar ne ya saka amma yau fari ne, duk ya ɓaci da datti na aikin Mota, shi kansa ma ya yi duhu. Rabi'a, Haja, Ikilima, Baby, Nana, Leelah. Daidai lokacin suka fito daga Gida kowacce ta sha kwalliya, kamar ba gobe, Ikilima, Rabi'a, Haja, duk Riga da Wando ne a jikinsu wanda suka yi bala'in kama jikinsu, sai wani ɗan siririn mayafi da suka zagaye kai da shi, Leelah kuwa irin ɗan siririn siket ɗin nan ne a jikinta, ita ma ya ɗame ta sosai sai ɗan ƙaramin mayafi da ta yana a kai ita ma, Baby da Nana kuma Ƴar Atamfarsu suka sa sai dai su ma ɗinkin ba na kima ba ne. Wani mugun takaici ne ya tsire Zuciyarsa sa'in da ya ganta ta fito a haka ko Kunyar Allah ba ta ji bare ta jama'ar gari, gashi Unguwarsu ba a raba ta da Mutane ga Matasa ƴan zaman sa ido Ƙungiya-Ƙungiya. Turus suka tsaya suna kallonsa cikin mugun mamakin sake ganinsa. "Tirƙashi!! yau ga Maye!" Rabi ta faɗa tana riƙe haɓa, bai ma san tana yi ba don idanunsa na kan Leelah wadda kishinta yake neman tarwatsa masa Zuciya. Ita kuwa ta kasa ko ƙwaƙƙwaran Motsi sabida mamaki, ba ta taɓa haɗuwa da Saurayi me naci irinsa ba, kowa da ya zo ko bai san halinsu ba in suka yi masa sau ɗaya to zai samu masu faɗa masa gaskiya akan kar ya dawo don gaba sai ya fi haka, sai gashi shi gori da zagi da cin Mutunci ba su sa ya sauke bakarsa ba. Kallon kallo suke yiwa juna kowa da irin tunanin da yake a Zuciyarsa. Cikin nutsuwa ya taka zuwa daf da ita yana ƙara zuba mata narkakkun idanunsa, cikin muryar da take ƙara bayyanar da damuwarsa ya ce "Yanzu Leelah a haka za ki ratsa duk Mazan da suke taruwa a Unguwarku?, Don Allah ki koma ki sauya wasu kayan, wannan sam ba su dace da Mace me Daraja irin ki ba." Dogon tsaki ta ja cike da takaicin jin abinda ya faɗa, wai har wannan Kalan Hanjin ne zai zo yana nuna Kishinta sabida tsaurin Ido?. "Dakata Malam, nawa ka bayar na Sadaƙina?, kai idan Gobe ake shirin Ɗaura mana Aura in ka haifu ka ce ka fasa don na fita a haka, wai kai Shekararka nawa ne ma dududu da kake zaƙewa a kaina? na tabbata na girmeka don haka ban ga alamun zaka isheni rayuwa ba." "Ko ban bayar da Sadaƙinki ba ai ni me sonki ne, bare ina sa ran wataran zan bayar, kin ɗauki soyayya tamkar tatsuniya ko? hala ba ki taɓa tsintar kanki a cikin irin halin da nake a yanzu b...." katse shi ta yi da cewa "Ka ga! ka bar ƙofar gidan nan ko in sa a yi maka shegen Duka wallahi!" ta yi tsaki gami da ci gaba da tafiya tana cewa "Ku gama min da shi sai ku biyo ni" ai kuwa kamar jira suke yi suka yi masa caa!!! kowacce tana kwalɓa masa baƙar magana. Rabi'u ne ya shigo Gidan da gudu yana cewa "Salim!! zo ka gani, ga wannan Saurayin Leelan ya dawo yanzu su Rabi'a suna can suna yi masa Jaraba". Da ƙyar ya miƙe daga sunkuyon wankin da yake yi yana riƙe Ƙugunsa gami da cewa "O'o ni Sa'adatu Sa'ar Mata, yanzu shi wannan Ɗan sallamammiyar dawowa ya yi?, kai mu je in gansa, last warning zan yi masa." yana ƙoƙarin tafiya Salma ta riƙe masa hannu cike da takaici ta ce "Wallahi Salim in ka tafi ba zan ci gaba da tayaka wankin nan ba, don ka samu ma ina tayaka shi ne sai ka dinga tafiya kana barina da zarar ka ji Munafurci?" "Haba me wanki da guga!, don Allah ki ƙarasa min zan biya ki kuɗinki, ki haɗa har da wancan da kike bi na" "A'a ni ba na kuɗi nake yi maka ba don Allah nake taya ka, in na kuɗin zan yi maka ina za ka samu ka biya ni?, kawai ka zauna mu ƙarasa in ya so sai ka je ka yi duk abinda za ka yi." "Don Allah ki bar ni in je in yi Ido Huɗu da wannan taɓararren, yanzun nan zan dawo ki ɗan tsaya ki huta." Momi ce ta fito daga Madafa (Kitchen) tana cewa "Wai ba dai Talakan nan ba ne ya tare mini Ƴa?, GRA fa za ta tafi shine Munafuki ɗan baƙin ciki zai tare ta??" "Sa ranki a inuwa Momina ai yanzu zan fita in yi miki maganinsa" Salim ya faɗa yana tattafa hannaye. "A'a zuwa da kai ya fi Saƙo, bari in je da kaina" ta faɗa tana yafitar mayafinta akan igiya. Da sauri ya tare ta yana cewa "Haba Momi kar ki bayar da mu mana! ki bar dai masu halin fita su zage siriki su yi amma ke ban sanki da haka ba!". "Kai ubanka! na ce ubanka!, ko ba na yi yau zan fara don na lura Maye ne yaron nan ba zan bari ya lashe min kurwar Ƴa ba, ba abinda za ta yi da shi don haka dole sai ya bar ta ƙwalamamme!" Innayi ce ta ƙaraso wajen tana cewa "Ke Dije ba na son iskanci, ki bar Yara su yi mana, ke ina ganin ba kya fita ki yi faɗa da Sirikan shi ne yau za ki fara?, ai gwara ki bar ni ni da nake Kaka in fita in yi duk abinda zan yi, kin san dai ko Aure aka tashi yi in ban amince ba iyayen Ƴar ba za su Amince ba, don haka ki bi ni a hankali; kai Jikana tawo mu fita" ta ƙarasa maganar tana kallon Salim, ba don Momi ta so ba ta cire gyalen ta rataye ta fara zazzagar masifa tana zage Aliyu. Lokacin da suka fito tuni su Ikilima sun saita masa hanya ya ƙara gaba. Masifa Salim ya dinga yi yana cewa an ci da rabonsa. Nan fa suka kafa zancen kowacce tana faɗen abinda za a yi masa in ya ƙara dawowa.... SHARE FISABILILLAH *Samu ƴancin Karantawa, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Domin Ƙarin bayani 👉🏽 09079885632* *©️INDO* [11/25, 8:42 PM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 9 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *GORGEOUS WRITER'S FORUM* FREE PAGE........... Haka ya koma gida jeme-jeme ransa a dagule. Tinda Maa ta kalleshi sau ɗaya ba ta ƙara bi ta kansa ba, tamkar ba ta damu da halin da ta gan shi ba, a ranta kuwa ta gama Ɗaura niyar yi wa Leelah da danginta abinda har abada ba za su taɓa Mantawa ba, tana ji tana gani wai Ɗan da ta fi so da ƙauna fiye da komai a Duniya ya zo gabanta yana kuka akan wata Ƴar Matsiyata. Khushi ce take ta ƙoƙarin rarrashinsa duk hankalinta ya gama tashi, yana yin Sallar Magrib baccin wahala ya yi awon gaba da shi. "Ni fa wallahi ko ta halin yaya ne sai na ga bayan Aliyu tinda ke kin kasa yin komai!!, idan na ɓatar da shi sai Daddy ya dawo kaina tinda yanzu ba wanda yake gani sai shi!" Aliyu ya faɗa a fusace kamar zai daki Mamin ta shi, cike da masifa ta ce "To wai Uwar me kake so na yi Haydar?, na yi duk iya ƙoƙarina amma abin ya ci tira, tin wata rana da na taɓa Asirce Almustafa ya zamana ba wanda yake saurara sai ni ta shiga ta fita ta karya Asirin tin daga nan ban ƙara cin galaba a kanta ba, duk wani shiri nawa sai ta tarwatsa shi, ta riga ta zamo min ƙarfen ƙafa yanzu shawara nake yi akan ta inda zan fara Yaƙarta amma kai ka zo kana yi min hayaniya, na fi ka jin zafin abin fa!." "To ni ki zuba min ido zan yi mata halin ƴan zamani kuma za ki gani." "Kai dallah can!!" ta faɗa gami da kai masa hamɓara, "Kai ba ka san wacece wannan shu'umar Matar ba, duk wani abinda kake ji da shi a kan farcenta kake, wallahi ko loma ɗaya ba ka isheta ba, bare kai halin ƙuruciya kawai za ka nuna, ni kuwa a matsayina na uwarka zan yi nazari kafin na san abin yi." yana shirin yin magana wayar Mami ta fara ƙara, da sauri ta ɗauka tana cewa "Yawwa MD ne". bayan sun gaisa ya sanar Mata Aliyu ya fara aiki a garage bai kuma san dalilinsa na yin hakan ba, yana da kyau su bincika su gane. Godiya ta dinga zuba masa don ita a ganinta shi ne me ƙaunarta da yake kwaso zance yana gaya mata. "Shi ma fa MD ɗin nan sai na ci Uwar Babarsa!" Haydar ya faɗa yana huci, "Shi yasa na ce kai ƙuruciya gareka fa, to MD me ƙaunar mu ne, shi ne yake gaya min duk halin da Aliyun yake ciki har ma da Daddyn naka, in ba shi ɗin ba kuwa wa ka ga yana yi mana haka?, yanzu ma gaya min ya yi wai Aliyun ya fara aiki a garage wai gyaran Motoci, ka ga kuwa ai akwai wata ƙulalliya." "Me?! gyaran Mota fa ??" ya tambaya a kiɗime, tabbaci ta ba shi kafin ya ci gaba da cewa "Lallai wannan Yaron shaiɗani ne, to Uwar me zai yi da gyaran Mota??, ai kuwa wallahi sai na gane dalilin". "To ka ji dai, Ɗan Wahala wai gyaran Mota, yanzu sai ka ƙara tabbatar da shu'umancin uwarsa, ƙila ma ita ce ta sa shi don ta ƙulla mana wani sharrin." Shiru ne ya biyo baya kowa yana na shi tunanin, wata dubara ce ta faɗowa Mami ta saki murmushin farin ciki sannan ta ce "Ina wannan Abokin nasa Ari??, kai ma ai Abokinka ne ko?" a daƙile ya ce "E Abokinmu ne mana, kuma yana faɗa mana sirrinsu". "To da shi za mu yi amfani wajen gane dalilin, ka same shi ku yi magana, na ji an ce sun samu matsala kwanaki da ya gayyaci Azaan birth ɗin nan, to ka sa shi ya je ya bashi haƙuri har ya jiyo mana komai. Murmushi Haydar ya saki, sai yanzu ma ya tuna da yin hakan, ashe dai tana da gaskiya da ta ce ta fishi sanin makamar aiki. A daren ranar Haydar da Ari suka gama magana, kafin gari ya waye Ari ya bawa Aliyu haƙuri tare da nuna nadamarsa a sarari. Shi kuwa da yake ba shi da riƙo ga haƙuri tuni ya manta da komai. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya ana kwana ana tashi. Aliyu bai ƙara zuwa Gidan su Leelah ba sai dai yana takura mata da Kira da Message ba dare ba rana ba safiya ba yamma har Asbaha ma bai fasa ba. A ɓangarenta kuwa yawan nasiha da Tsadaddun kalaman da yake zuba mata tuni sun fara ratsa Zuciyarta kuma sun fara cin galaba a kanta, duk da tana fuskantar zuga daga wajen su Sumayya da iyayensu. Idan ta yi kamar ta yarda da shi sai su bushe mata kunnuwa. Tuni Ari ya samu duk abinda yake son samu ya faɗawa Haydar da Azaan kasancewar duk layinsu ɗaya. Azaan bai damu akan hakan ba don ba huruminsa ba ne, muradinsa dai kawai ya samu sa'a a kan Khushi. A ranar Mami ta sanarwa Bhaba cewar Haydar ya samu Matar Aure kuma cikin Sati Uku ko huɗu take so a yi Auren, har da ƙaryar Likita ya ce ayi masa Aure cikin gaggawa. Kasancewar DR ɗin Bhaba da su Roshan daban nata ita da Ɗanta daban Bhaba bai gane komai ba kuma bai sa a ransa zai yi bincike a kai ba, dama shi ma yana cike da ƙudurin yi masa Auren ko Allah zai sa ya rage rashin hankalin da yake yi. Washegari Irin wankan Yamman nan da suka saba yi su fita gantali Unguwar masu kuɗi yau ma sun yi sun fito kenan suka yi alaragab da Mota a Ƙofar gidansu. "Wow Anti Leelah kalli wata shegiyar Mota!, Allah ya sa wurinki aka zo" Nana ta faɗa tana washe baki. Ita ma Leelan Addu'ar da take yi kenan a ranta amma a zahiri ko gezau ba ta yi ba da sunan ta ga Motar sabida duk iya shegenta tana da aji da kamun kai. Dukkansu sun kasa tafiya sun yi cirko-cirko sai mokaɗe baki suke yi ana gyara salon tsayuwa don dukansu ransu ya biya. Ikilima ta kasa jurewa ta taka zuwa wajen Motar cikin wai irin taku na rangwaɗa da ƙwarewa ta fannin bariki. Tin kafin ta ƙarasa ya fito ya jingina a jikin Motar yana zubawa Leelah wani shegen kallo wanda ta kasa gane ma'anarsa, ita ma kallonsa take yi a Zuciyarta tana tsananta addu'a akan ta samu shiga a wajensa, lokaci guda ta ji ya fara tafiya da ɗan sauran lissafinta. Tinda Ikilima ta ga suna bin juna da kallo baƙin ciki ya kamata ta koma cikin gida tana mis-mis da baki.... Ƙarasowa ya yi inda take tsaye yana sakar mata wani malalacin murmushi wanda ya ƙara narkar da Zuciyarta, surutansa ne suka dawo da ita cikin hayyacinta "Ki yi haƙuri na ga kamar fita za ki yi ni kuma na dakatar da ke!" ɓoyayyar ajiyar Zuciya ta sauke kafin ta ce "Ba komai, Allah ya sa lafiya". shiru ya ɗan yi yana tunani, shi sam bai iya Soyayya ba bai san yadda ake yinta ba bare wasu ƴan kalamai nata, shi tsakaninsa da mace kawai ya yi sharholiyarsa da ita ya sallameta, gashi ko ƙanwa Mace ba shi da ita bare ma ya san ta yaya ake rarrashinta. "Da alamu ba ka da abin cewa" ta faɗa tana ƙoƙarin wucewa. Cikin sauri ya ce "Aliyu Almustafa Naira!, shi ne sunana na z....." katse shi ta yi ta hanyar zunduma ashar ɗin da ta kuɓuce mata, "Aliyu Mustafa Naira???, wai kuma da gaske kake?" farin ciki ne ya lulluɓe shi ganin ta ruɗe da jin hakan, murmushi ya yi gami da cewa "Ƙwarai kuwa, na san za ki yi mamakin ta yadda na sanki; tin da muka haɗu a Birthday ɗin Irfan Mohammad na ganki kuma na kamu da sonki, na kasa jurewa shi yasa na nemo address ɗin ki don ina so ki zamo Matata!" duk yadda ta kai ga iya jan aji yau sai da ya tsinke mata. Murmushi kawai take fafatawa ba ji ba gani, a ranta tana tunanin Da akwai irin wannan alkairin zai zo mata amma wannan Matsiyacin Talakan ya zo ya addabi rayuwarta? me ya sa ma ta yi garajen fara son Irfan? rashin sanin cewa Aliyun da ta daɗe tana son gani zai zo har ƙofar gidansu neman soyayyarta. Tufka da warwara kawai take yi yayin da murmushinta ya kasa ɓoyuwa. Haydar kuwa shi kansa ya jinjinawa ƙoƙarinsa duk da ya kwana da sanin ba wai iyawarsa ce ta sa ta cikin shaukin nan ba kawai jin daga inda ya fito ne, shi kuwa da yake ba son gaske yake mata ba bai damu a kan hakan ba, in banda ma yana son muzgunawa Aliyu ai wannan ko a Ƴar Aiki ba zai iya ɗaukarta ba yadda ta fito daga wannan gidan me kama da Dandalin almatsutsai. Taushe Zuciyarsa ya yi ya ce "Na ji kin yi shiru ko ba kya so na ne??" wani ɗan banza kallo irin na yaudara ta jefa masa gami da cewa "Wa ya isa ya ce ba ya sonka?" "Kin amince kenan?" farr! ta yi da ido tana ƙara yalwata murmushinta "Ƙwarai ma kuwa!" ta faɗa tana wani yauƙi da silɓi. Kamar ya mangareta haka yake ji amma sai ya danne ya ce "Yaushe za mu yi Aure Sweerheart?!" zaro ido ta yi gami da cewa "Aure?! ko gama fahimtar juna fa ba mu yi ba, ka bari zan sanarwa iyayena duk abinda suka ce zan gaya maka." Yanzu komai dai ya zo ƙarshe, ya faɗa a cikin ransa. Ƙarya ya shuka mata akan ana jiransa zai tafi, a zahiri kuwa gajiya ya yi da tsayuwar wajen. Ba don ranta ya so ba ta yarda suka yi sallama ta shige gida, da so samu ne ba za ta gaji da ganinsa ba har sai lokacin bacci ya yi. Tana shiga ya bawa yara jibgin ledojin da ya yi mata siyayya suka kai mata ciki shi kuma ya fece. Tuni Gidan ya hargitse masu murna na yi masu nuna hassadarsu a zahiri suna yi, wasu kuma dai suna taya murnar amma ta ciki na ciki. Isuhu ne ya shigo yana famar zuba faɗa akan halin nasu tare da barazanar duk ƴar da ya ƙara gani ta tafi gantaln yamma ko na dare sai ya ɓallata. Tuni Iyayen ƴaƴan suka hau shi da caccaka kamar ba za su bar shi da rai ba, har ita kanta Mahaifiyarsa don gani take tamkar zai kashe mata kasuwar Ƴaƴanta su da har kwana suna yi a waje, Momi ma har da cewa hassada yake mata kuma baƙin cikinta da ƴaƴanta shi zai kashe shi. Inna da Momi an ɓula musu sun ga jini nan, suka kafa tasu masifar akan Mazajensu sun tara musu ƴaƴa amma sai lalaci ba sa ma fita neman bare su samu sai zama a bakin bishiya sai iya shiga majalisa a zauna. Sai da ya yi nadamar tanka musu da ya yi, dama can wannan dalilin ne ya sa ya dena yi musu faɗan yanzun ma ƙara ƙureshi suka yi. Yau kowa sai da ya sha Habaici daga wajen Momi musamman Salma da ko saurayi ɗaya ba ta da shi duk da cewar ta girmi Leelah ma. Su kuwa Inna da Mama abinda suka saba yi ne ta jefa musu su jefa mata. Umman ce dai ba ta iya cewa komai duk da abin yana damunta. Tin goman dare tsakar gidan ya yi tsit kamar babu kowa a cikinsa, wanda ko Ƴan Matan ba sa nan akwai Salim da Salma da Innayi su ne masu haɗa camba sai masu tayasu su Momi da Mama, Inna ma ba ta fiye shiga ba don ita zubin Salihai gareta a sarari a ɓoye kuwa sam ba haka take ba. "To kun ga dai masu Ƙashin Arziki!, wai ɗan Alhaji Mustafa Naira shi ne ya zo gidan nan neman Aure kuma ba wajenku ba, wai Yaron ba jika ne kenan a wajen Alƙali Kabiru Mai Zafi ba?? ai asalinsu Ƴan Cikin gari ne, ni na san su sarai in gaya muku, waɗannan su ne asalin Kano Uwata da kuka sani ta yi aikatau a gidan Alhaji Mai Zafi; ku dai wallahi kun jawo wa kanku zagi da gori, ni wallahi dama ni na haifi Laila!!" Mama ce ta zage tana zubawa su Rabi masifa, shiru suka yi mata don abin ya sosa musu rai don dai ba yadda za su yi. Sai da ta gama ƙare musu tas sannan ta haƙura ta kwanta tana ci gaba da yi musu gori akan ubansu bai tashi ya nema ba su ma sun ƙi nemowa su kawo mata. Haka suka kwana tare da ƙudurin dole sai sun yi Auren kece raini su ma. A ɓangaren su Sumayya ma zancen da suke yi kenan har bacci ya kwashe Inna sannan suka koma ɗakinsu. Salma ma yau abin Duniya ya isheta a kan gori da goribar da suke yi mata na cewar ba ta da mashinshini, kuma ba samu ne ba ta yi ba ita ba za ta iya kula samarin banza ƴan jagaliya ba shi yasa duk wanda ya zo take taka masa burki, don kuwa yawancinsu samarin Unguwar ne Ƴan jagaliya ƴan zaman bati siddan wanda Saurararsu ma ba ta da amfani. Kuka ta dinga yiwa Umma tana cewa duk wadda ta ƙara ci mata Mutunci sai ta rama, Umma dai sai haƙuri take bata tana rarrashinta har ta samu ta nutsu. Su ma su Leelah suna ɗaki suna shewa suna taune-taunen abinda Haydar ya kawo. Duk abinda take yi hankalinta na kan wayar da ta gani a cikin kayan ko za ta ga kiransa amma shiru. Abin kamar wasa har dare ya yi ta koma ɗakinsu shiru, tafi-tafiya har wayewar gari. SHARE FISABILILLAH *Samu Ƴancin Karantawa, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Domin Ƙarin bayani 👉🏽 09079885632* *©️INDO*[11/26, 4:58 PM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 10 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *G. W. F* FREE PAGE........... Abu kamar wasa har yamma ba ta ƙara jin motsin Haydar ba, Zuciyarta duk ta tsinke ta shiga damuwa, kowa na sabgoginsa amma ita ta kasa sukuni gabaki ɗaya hankalinta na kansa. Salim ne ya kalli Salma murya ƙasa-ƙasa ya ce "Anti Salama kin san menene?" girgiza kai ta yi alamar a'a tana ƙoƙarin ɗaure kayan da ta gama Gogewa. "Haƙuri nake son ba ki akan abinda aka yi miki jiya a gidan nan, na san wallahi kin ji ba daɗi kawai dai kina haƙuri ne. murmusawa ta yi gami da cewa "Kai waye ya faɗa maka?, ni ban ji komai ba kwata-kwata, koda an yi min laifi farin cikin da Leelah take ciki ai ba zai bari na ji komai ba; wallahi na ji daɗi sosai Allah ya tabbatar da Alkairi, ni dai ina so in ga duk mun yi Aure ko don mu ragewa Iyayenmu nauyi." taɓe baki ya yi gami da yin farr! da ido sannan ya ce "Allah Sarki!, ai wallahi Na san kina farin ciki amma dole ne sai abinda aka yi miki ya yi miki ciwo, batun Aure kuma ku da kuke son yi Allah ya tabbatar waɗanda kuma Yaudara suka sa a gaba su ma Allah ya kai damo ga harawa, ko bai ci ba ya yi birgima!" Dariya ta yi tana cewa "Ni tashi ka rakani in kaiwa Hajiya Yalwa kayanta, tin jiya take yo mini aike to sai yau Allah ya sa na gama Gugar". tashin ya yi yana cewa "Ai wallahi ni kina burgeni Salama, ba kya bin Samari don samun kuɗi, kuma ba kya Sata, ba ki sawa kanki Son Duniya ba kin riƙe Ƴar Sana'ar wanki da Gugarki kina samu kina temakawa Iyayenki". ƙullin kayan ta jibga masa a kansa tana cewa "Maganar ce ba ta isheka ba!, ni karɓar min wannan". Ƙaramar ƙara ya saki kafin ya ce "So kike ki ɓalla min wuya ki sabauta ni? ke daram da ke yanzu za ki ga an yi wuf da ke ni kuwa in kika ɓalle min wani abu babu Ƙatuwar da za ta yarda ta Aureni." Dariya ta sa ba tare da ta bashi amsa ba ta yi hanyar fita. Bin bayanta ya yi yana ci gaba da ƙorafi har Matar da ta kawo wankin ba ta tsira ba. Salim yana fita ya yi turus!! ganin Aliyu a tsaye, ya haɗe cikin ɗan yamulmulin Yadinsa Yellow. Har ta yi gaba ta ji yana cewa "Kai yanzu sabida Allah dawowa ka ƙara yi??, wai kai Gori ma ba ya yi maka ciwo ne?" juyowa ta yi don ganin ko waye, suna haɗa ido da shi ta yi saurin kawar da kai tana cewa "Kai Salim ka tawo mu tafi dalla, magrib fa neman yi take yi". Muryar Aliyu ta ji yana cewa "Ina wuni Aunty!" dariya abin ya bata don haka ta dara sannan ta ce "Ina wuni!" shi ma dariyar kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba. Salim ya tafa hannuwa ya riƙe haɓa yana cewa "O'o Allah Gwani!!, ina gaya maka gaskiya kana gaisar da wata? shawara fa nake ba ka don wallahi yau in Leelah ta ganka a Gidan nan Allah ne kaɗai ya san Hukuncin da za ta yi maka". "Haba ƙanina! ni fa ba da rigima na zo ba kawai na ga yau Jumu'a ne shi ya sa na zo mu gaisa". Salma ce ta dubeshi a tsanake ta ce "Ba don Salim ba ya sonka yake gaya maka haka ba, gaskiya yake gaya maka, ka san ba a yiwa so dole, kuma da a ce Leelah ba ta samu wanda take so har sun yi maganar Aure ba sai ka ci gaba ƙila za ka iya dacewa." "A to! gaya masa dai!!" Salim ya faɗa yana murguɗe baki. Kamar Karon Ƙarfe da ƙarfe haka Aliyu ya ji saukar maganar kwaram-kwatsam!! Salma ya zubawa idanu cike da son samun tabbaci, "Maganar Auren Leelah fa?" ya faɗa a kiɗime. Kafin Salama ta yi magana Salim ya ce "Fes da aniya!, jiyan nan Aliyu Ɗan Almustafa Naira ya zo wurinta suka gana kuma har sun tsayar da maganar Aure, in gaya maka yanzu komai ya zauna kawai jiransa muke yi ya turo Walidansa". Gefen leɓensa ya kama ya cije da ƙarfi gami da rintse idanunsa, wani irin kururuwa da kuwwa gami da hanƙoro ƙwaƙwalwarsa take yi, Zuciyarsa kuwa jin ta yake yi tamkar za ta fita daga cikin ƙirjinsa, bayan shi da Ɗan uwansa wanene Aliyu Almustafa Naira? tabbas in haka ne Haydar ya yi masa lahani kamar yadda ya sha Alwashin yi masa. Sama-sama ya jiyo muryar Salma tana cewa "To ka ji iyakar gaskiyar, kuma maganar gaskiya ga Ɗan Masu kuɗi babu lallai Leelah ta Amince da kai, zai fi maka kyau ma ka yi tafiyarka tin kafin ta fito". Salim ya ce "Kin ga Aunty Salma mu tafi mu kaiwa wannan Lukutar Matar Kayanta kar ta dena kawo miki Wankau ɗin mu boni." Bayan sun yi gaba Salim ya ce "Wallahi Salama ban taɓa ganin Saurayin da yake son Ƴar gidanmu kuma na tausaya masa sama da wannan ba, ni fa na lura wallahi da gaske yake sonta, ƙila sai ta fi ma samun kwanciyar hankali in shi ta Aura." "To ai Salim komai nufin Allah ne, Allah ya zaɓa mata mafi Alkairi kawai. da Amin ya amsa sannan suka saki hirar suka kama wata. Kasa motsawa ya yi daga wajen bare ya san inda dare ya yi masa, yana nan tsaye har su Sumayya suka zo shiga Gidan suna ganinsa suka ja tinga, Nana ta yi saurin shiga ciki ta sanarwa Leelah, ba jimawa suka fito suka sa shi a tsakiya suka fara kwarkware masa har da cewa idan Haydar ya san yana zuwa wajenta ma ai Mutuncinta zubewa zai yi. Hakan duk bai burge Leelah ba don haka ta gayyato Yaran Layinsu ta ce su yi masa wanka da ruwan kwata su kore shi, in suka ƙara ganinsa a Unguwar ma su ƙara yi masa haka su haɗa masa har da duka. A ganinta hakan shi ne mafita in aka yi masa ba lallai ya ƙara dawowa ba. Cikin gida suka shige suka barshi da gayyar Yara waɗanda ke ji da fitina da kuma rashin Ɗabi'a. Ai kuwa gamo da kasawa tuni wasu suka fara dukansa, wasu kuma suna kawo gudunmawar ruwan kwata. Da ƙyar ya iya ɗaga ƙafafunsa da suka yi wani irin nauyi ya fara tafiya kamar zai kife ƙasa. Raka shi suka yi har bakin Titi suna yi masa ihu tuni Yaran suka ƙara yawa sun fi Talatin, haka suka yi masa wanka tsaf da kwata. Shi kuwa ko Uffan bai iya cewa ba. Sai da suka zo Titin ne suka gamu da Bukar ya dawo daga gantalinsa yana tafiya yana haɗa Hanya, ganin abinda suke yi ya sa shi fara yi musu magana yana danna musu ashar. Ɗaya daga cikin Yaran ne ya bashi labarin ce Ƙanwarsa Leelah ita ta saka su. jin haka ya sa shi rarumar dutse ya fara binsu yana Haɗa musu ashar "Don Abutakazar Ubanku don ta sa ku sai ku yi? Ku ma ba kwa so ta yi Aure mu huta ko dan Jatta abin ubanku??!, Shegu munafukai Ƴan hassada!!" Watsewa suka yi kowa ya fara gudun ceton Kansa, sun san tsohon Ɗan Ganja ne yanzu sai ya bugawa Mutum Ƙaton dutsen kuma bala'in Ƴan Gidansu ma kaɗai ba zai bari a ƙwatar maka Ƴancinka ba. Cikin Unguwar ya bisu suka ci gaba da raba Wuta, hakan ya bawa Aliyu Damar nufar inda Motarsa take, tin kafin ya ƙarasa Qadri ya matso da ita, shiga kawai ya yi ba tare da ya yi masa magana ba duk da Qadri ɗin yana ta tambayar dalilin faruwar hakan. Bhaba da Maa suna zaune a Katafaren Falon da ke tsakiyar Gidan suna hira. Bhaba ne ya ƙara faɗaɗa murmushinsa yana cewa "Na manta ban gaya miki ba Ɗanki fa ya kusa Aure". "Shi??" ta faɗa a taƙaice, amsa ya bata da cewa "Haydar, ya yi mini magana akan ya samu wadda yake so, na yi farin ciki da hakan don kuwa ni ma ina da shirin yi masa ko bai shirya ba." Murmushi ta saki har haƙoranta suka bayyana "Ma sha Allah!, na yi farin ciki ni ma, ka ga yanzu sai ya san ya girma ko?" ta faɗa tana tsirawa Bhaba ƙwala-ƙwalan idanunta. Sosai ya ji daɗin nuna farin cikin da ta yi a kai, Cikin fara'a ya ce "Sosai ma kuwa, kuma dai cikin ƙanƙanin lokaci za a yi, gobe ma in Allah ya yarda za su je nema masa Auren wajen Iyayenta." "Oh! za su je ko kuma za ku je??" "Ni fa ba zan je nemawa Haydar Aure ba, Ɗan Farko ne fa!!, kuma ai yana da iyaye da yawa, Alhaji Awwal, Alhaji Ibrahim, Alhaji Abdussalam, MD, Alhaji Yusuf, su na wakilta su yi komai. "Achcha!, na san za su yi komai fiye da yadda za ka yi da kanka, Allah ya sanya Alkairi" Kafin ya yi magana suka ga Aliyu ya shigo tsamo-tsamo. Ya zama Kurman Dole, ko sallama bai yi ba sai shashshekar kukansa dake tashi kaɗan-kaɗan, bai kula su ba ya wuce hanyar sashinsa. Da ido suka raka shi su duka Bhaba ya cika da mamakin ganinsa haka, ya miƙe zai bi bayansa Maa ta yi saurin tashi ta nufi Sama cikin gudu-gudu sauri-sauri. "Subhanallah!" kawai ya furta don ya san yau akwai artabu. Dole ya fasa zuwa wajen Aliyu ya bi bayanta. A baranda ya sameta tsaye ta riƙe ƙarfen dake gabanta tana kallon ƙasa, kusa da ita ya ƙarasa jiki a sanyaye ya ce "Moonath...." saurin ɗaga masa hannu ta yi cikin shashshekar kuka ta ce "Kya ƙyaleni ba na son jin komai!" "Ba zan iya ƙyaleki ba Moonath!, kuka fa kike yi! me yasa haka? ni ban ga abinda za ki zauna kina yiwa kuka a nan ba." Goge hawayen ta fara yi gami da yin murmushin takaici "Kai a wajenka ba abin Kuka ba ne ni kuma a wajena abinda ya fi hakan ma zan yi!, ko Mutuwa ya yi kai kana da wani Ɗan, a wurinka za su dawo biyu ne ni kuma zan tashi da guda Ɗaya, Shi ne kaɗai Ɗa Namiji da na Haifa kuma watan wata rana shi zai zamo min Uba; kafin na sameshi babu irin wahalar da ban sha ba, kai da kanka sai da ka Guje ni ka Auro wata, haka danginka duk suka Juya min baya na zama Abar Gori da cin Mutunci sabida ban haihu ba, yanzu kuma na haifa shi ne kake cewa kar na damu da damuwarsa?? anya ka yi min Adalci kuwa Jaan??" jinjina kai ya yi Zuciyarsa sam ba daɗi, a sanyaye ya ce "Ni ma damuwar Aliyu damuwata ce don ko a yanzu ba ni da wani tamkar shi tinda shi ne me tausaya min kuma me Mutunta ni, sannan ban ce kar ki damu da damuwarsa ba amma abin zai yi min yawa Moonath, Ke kina kuka shi yana yi za ku jefani cikin wani hali, don Allah ki yi haƙ......" katse shi ta yi da cewa "Kar ka ba ni haƙuri don ba zan haƙura ba; Ni ban taɓa sa Ɗana kuka ba, kuma ban haife shi don ya yi Kuka ba, duk wanda ya sa shi kuka sau ɗaya ni zan iya sa shi ya yi na har Ƙarshen Rayuwarsa; Jaan! Billahillazi huwar Rahman indai Yarinyar nan ta bari Roshan ya faɗa mugun hali ta Dalilinta sai na yi mata mummunar Ɗaukar da su kansu iyayenta sai sun gogeta daga cikin Tunaninsu, indai wani abu ya faru da shi babu shakka sai na Lalatawa duk danginta Farin cikinsu!!!" Cike da damuwa Bhaba ya ce "Komai fa da maslaha ake binsa, kar ki nuna Ƙarfin Ikonki akan wata Ƙaramar Yarinya, na san Ƙuruciya ce kawai take damunta, ki bari ni zan shiga lamarin, zan je in yi magana da iyayenta komai zai yi daidai in sha Allah". "Ba na buƙatar ka shiga lamarin, ka je ka yi maganar Auren Haydar kawai ni kuma zan samawa Ɗana farin cikinsa, kuma ka san da ba zan iya ba ba zan ce zan aikata ba". "Eh na san ke me faɗe da cikawa ce kuma kina da ikon yi mata komai, don haka ba zan fasa ba ki haƙuri ba, na san shi kansa Aliyu ba zai so abinda zai ɓata mata rai ba tinda yana sonta sosai, yanzu dai ki dena kukan nan ki kwantar da hankalinki, ina so na je wajensa...." kafin ya ƙarasa ta katse shi da cewa "Ka je kawai, ni ma daga baya zan yi magana da shi" "Okay" kawai ya ce sannan ya nufi sashin Aliyu. Sai da su Salma suka dawo suka tarar su Rabi na maimaita abinda ya faru cikin nishaɗi da jin daɗi. Takaici abin ya basu har Salim da yake ɗan cas da as, cike da takaici ya ce "Amma ku wallahi an yi ƴan Bala'i, in banda abinki ma Leelah ke da kika samu Masoyi wanda ake kira na a zo a gani ina ruwanki da tsayawa Tijara da wannan? ai kamata ya yi ki bi shi ta lallami da lumana ku rabu sabida ke yanzu Darajarki ta ninka ta Da, Allah ya sa zancen ya koma kunnen danginsa su ce ba ki da Tarbiya, kin san dai zancen Duniya ba ya ɓuya, musamman ga manya irin waɗannan kin san dole yanzu duk motsin da za ki yi idanunsu yana kanki." Tsaki ta yi gami da cewa "Ka ga! Na ci Mutuncinsa ƙarewa ma na sa an yi masa abinda ko maye ne ba zai dawo ba, idan goyon bayansa kake yi sai ka je ka Aureshi." cikin zaro ido Salim ya ce "A'uzubillah! ina Gardi yana Gardi kike ambata mana Aure sai ka ce kin zo a zamanin Jahiliyya?, Allah ya yi min tsari, wallahi bakinki ya sari ƙasa!". Salama da baƙin ciki ya isheta ta ce "Ki dinga abinda hankali zai ɗauka Leelah, me yasa wai Duniya ta rufe muku ido ne?, akan son Duniya har kike irin wannan furucin da ko Kafiri a wannan zamanin ba lallai ya yi ba; in da ba ki fita ba kika yi masa banza ai da ba zai ganki ba ma bare har ya sa ran za ki saurare shi". "To ke ma Ƴar Wankau ba na son yawan Munafurci da tsugudidi, shi in Namiji ne ai ke macece sai ki je ki Aureshi, dama na ga ko kare bai shinshina ba, kina cin arzikin Mutum kina yi masa hassada." Salama ta yi saurin cewa "Allah ya baki haƙuri Leelah, in sha Allahu ba zan ƙara cewa komai ba; hassadar ma sai ka kai matsayin da za ka yi sannan kake yinta, ai kin fi ƙarfina ban kai matsayin da zan yi miki hassada ba, bare ma ba halina ba ne, kuma in Allah ya yarda ba zan ƙara karɓar abin da za ki ba ni ba tinda abin ya zama na Gori!" Kuka ne ya kufce mata ta yi saurin miƙewa ta bar wajen da gudu. Shewa Mama ta zuba "Hee!!! yau dai mun ga wasu a rana, komai a ce Salama komai a ce Leelah to dai yau ga abinda muka gani!" Dariya sauran Mutanen wajen suka sa Innayi ta ce "Lailah ce Ƴar kunama ka gama rainonta ta ɗalla maka cizo!, ai kowa ya san kafin Salama ta moreta sau ɗaya ita ta moreta sau goma." Salim ma tsaki ya ja ya ce "To Allah ya kyauta miki Anti Leelah, wai me yi maka shi ne tsinanne a wajenka sabida abin Duniya." daga haka shi ma ya bar musu wajen. Sosai jikin Leelah ya yi sanyi ƙalau, tashi ta yi ta nufi Ɗakin Umma don ta bawa Salama haƙuri, ita kanta ta san ba ta kyauta ba, kawai don tana cike da jin haushin Ali ne shi yasa ta gaya mata magana. Daren yau dai Kwanan Farin ciki Leelah ta yi don Haydar ya sanar mata gobe Manyansa za su zo a yi maganar Aurensu. Tin a lokacin labari ya karaɗe ko'ina su ma iyayen nata aka sanar musu don su shirya. Kwana ta yi tana mafarkai sabida tsabar farin ciki har gani ta yi an Ɗaura Auren a Mafarki. SHARE FISABILILLAH *Samu ƴancin karantawa, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Domin Ƙarin bayani 👉🏽 09079885632* *©️INDO* [11/27, 1:02 PM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 11 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *GORGEOUS WRITER'S FORUM* Tin da gari ya waye Momi ta kasa zama sai fakam-fakam take yi wai a dole sai ta haɗa musu abin tarbar Baƙi, ita dai Leelah abin har kunya yake bata don ta san sun fi ƙarfin duk wani abinda Momin za ta yi musu, wai har da Lemon Roba za ta sayo musu kamar ba su taɓa sha ba. Salim duk wannan rawar jikin da ake yi shi banda shi yana gefe don kuwa fushi yake yi da Leelah akan rashin Mutuncin da ta yiwa Aminiyarsa. Momi ce ta fito daga Madafa tana karkaɗe zaninta gami da gyara masa zama ta ɗage shi sama, "Salim!!!! Salim!!!!! wai don Ubanka ka zuba min ido kana kallo in ba ka taya ni ba waye zai taya ni?, ka zagaya baya wajen Bishiyar nan ta Gado da Ubanku ya saba zama ka ce masa ya tashi ya je ya nemo Kuɗin da za a sayo Fulawa da mai don yau sai na fita kunya a Gidan nan, ba zan karɓi baƙi haka sakaka kamar Shanu ba dole sai na yi musu tanadi. Murya ciki- ciki ya ce "Uhm aikin banza jefa Agwaga a ruwa, wallahi Momi ban ga abinda za su yi da abinda za ki jagwalgwala ki yi musu ba." "Uban me ka ce???" ta faɗa cikin ɗaga murya, da sauri ya ce "A'a meye na tashin hankali? cewa na yi da sawwaƙewa kanki kika yi don wallahi na san sun fi ƙarfin ɗan abinda za ki yi musu." "To dan Ubanka sai na yi!, sai dai in na basu su ɗauka su zubar ai dai na fita, ba za ka tashi ka je aiken da na yi maka wajen Malalacin Uban naka ba ko?, ba ma dole a haifi Ɗan Daudu ba! Mutum sai lalaci a ce nema ma ba zai iya fita ba?!" Sosai Gorin da Momi take yi masa shi da Babansu yake ɓata masa rai, dan dai Uwa Uwa ce kawai banda haka ba abinda zai hana shi yi mata abinda ko da wasa ba za ta kuma ba, a gefe guda kuwa yana jin haushin Abinda Iyayen nasu Maza ke yi, gasu Talakawa gashi ba sa son nema da Baba Ridwan da Babansu haka suke, shi kuma Baba Jamilu zai nema ɗin sai dai ko ya samu ba zai bawa iyali ba haka zai barsu su yi ta fakam-fakam, Baba Habu ne dai yake tashi tsaye ya nema kuma duk abinda ya samu alla-alla yake ya sauke nauyin da ke kansa. Yana tafiya yana gunguni da mita, tin kafin ya ƙarasa ya gamu da Baban nasu yana shirin shigowa cikin Gida, isar masa da saƙon kira ya yi kana ya ci gaba da tafiya don ba ya so a yi Tijarar a gabansa. Shi kansa Baba Usama cike da fargaba ya shiga Gidan. Ai kuwa tana ganinsa ta yo kansa tana cewa "Gwara da Allah ya shigo da kai!, wai kai ba ka da Zuciya ne? Manyan Mutane ne fa za su zo gidan nan amma ko ruwa me kyau wanda za su sha ba ka ajiye musu ba, haka ake rayuwa?, wannan wace irin Masifa ce Usama? so kake ka jawo mata zagi da Gori a wurin Dangin Miji?" jiki a sanyaye ya ce "To me za mu yi? me muke da shi da za mu iya ba su?" "Ko ba ka da shi sai ka nema, Ɗan Sarkin kiran babu!, sai ka ce a kanka aka fara yin ta, kuma wallahi ka san da sani sai ka yi duk me yuwuwa ka yi wa Yarinyar nan Kayan Ɗaki da na Kicin na kece raini, na gaji da wannan abin naka, ba rance ba Allah ya sa sata za ka yo ka saya sai ka sayo su ba fashi, don haka yanzu ma ina jiran Kuɗin Mai da na Fulawa. Kamar zai fashe da kuka ya ce "Ni ba ni da su Dije!, ban san ina zan je in samo su ba, gashi rayuwar ta yi tsada....." katse shi ta yi da cewa "Ba ruwana da tsadar rayuwa!, ai ka iya kwantar da Murya ka cuci Mutum, to wallahi ba ka isa ba ka yi kaɗan." Leelah ce ta ƙaraso wajen tana kuka shaɓe-shaɓe, cike da damuwa ta ce "Don Allah Momi ki yi haƙuri, tinda ba mu da shi ba yadda za mu yi sai haƙuri, ni ina da ɗan sauran Kuɗi a wajena sai a Sayo iya ruwa kawai a bar wani soye-soye, don Allah ki bar zancen haka, Abba don Allah ka yi haƙuri." "Dole ki ce haka dama mana, ni da nake yin komai a kan ki wai kin fi son Ubanki a kaina." cikin matsanancin Kuka Leelah ta ce "Wallahi ba haka ba ne Momi, ni dai na haƙura koda Haydar zai fasa Aurena in ba a yi wannan soye-soyen ba na haƙura; da Dukiyar Halal Allah ya ce kowane Mutum ya ciyar da iyalinsa, in kina haka za ki sa ya fara neman na Haram!" "Ke Buhun Ubanki!! har wani wa'azin ƙarya za ki yi mini?, ai shi kansa ya san muna yi masa ƙoƙari, in banda ina da ke ma ai da yanzu na haukace ko na ɗimauce, shi bai san cin mu ba bai san shan mu ba, gashi na haifi wani Ɗan Daudu shi da yake Namijin wanda ya kamata ya nema to ya zo a Ɗan Daudu kuma ba na shakka kan cewar wannan lalacin na Usama shi ne ya jawo haka". Ganin Momi ba za ta dena zuba bala'in ba ya sa Leelah ta janye Abba ta fitar da shi waje gami da bashi haƙuri da roƙawa Momin yafiyarsa. Shi dai kawai cewa yake "Ba komai Laila, ai Ƙaddara ce kowa da irin ta shi, uhm! ba komai ai!, ba komai wataran sai labari, uhm! Allah Sarki, ai ba komai!". Sai da ta ji Momin tana shirin biyo su ƙofar gida ta yi saurin komawa ta ci gaba da rarrashinta sai dai tana yin gabas ita tana yin yamma, in tana ba ta haƙuri kamar ƙara iza wutar take yi. Haka Momi ta wuni tana bala'i da Masifa, su ma su Inna duk ta kunna su, abu ne wanda kowa yake damunsa su ma suka kafa tasu Masifar akan Mazajensu. Leelah da Salma har ma da Umma sai aikin Kuka suke yi. Nana kuwa da yake tana bayan Momi ɗare-ɗare har da ita a faɗen maganganu. Salim kuwa tinda ya fice bai dawo ba sai bayan Magrib. Sai bayan Isha'i Baƙin suka iso. A ƙofar gida aka yi musu shimfiɗar ƙatuwar tabarma sai dai duk ta yamutse ta fara zama ƙashi, ɗan ruwan da Leelah ta bayar a sayo aka zo aka dire musu. Su Momi da Nana har ma da wasu daga cikin Ƴan gidan suna daga bakin Zaure suna leƙensu. Momi tana ganin an miƙawa su Baba Kuɗi ta juya cikin gida tana rangaɗa wata muguwar Guɗa, Innayi ta karɓe ta tayata suka ci gaba da yi. Inna ma shiga ta yi aka fara shewa da ita, Mama kuwa kadaran kadahan, Umma kuwa sai fara'a take yi tana cewa "Alhamdulillahi" abinda dukkansu ba wadda ta yi hankalin faɗe har ita kanta Uwar Ƴar. Sai da baƙin suka tafi sannan su Baba suka shigo suka sanar da su iyayen Ɗa sun buƙaci a saka ranar Aure Sati uku su kuma sun yarda don ba su da ikon Ja da Manyan Mutane. Sam Momi ba ta yi tunanin komai ba face ta kusa Aurar da Ƴarta ga Ɗan Masu Kuɗi, ba ta yi tunanin ta ina za su samu Abin yin hidima ba, ita dai kawai ta ci gaba da Murna. Baba ne ya miƙawa Abba kuɗin da suka bayar yana cewa "To ga wannan, duk ku shaida Kuɗi ne suka kawo na Aure." Abba ya karɓa yana cewa "Ai adana su za a yi sai mu yi wata hidimar da su" "Kan bazawara ba gashi!!!, to dan Ubansu ina Sadaki kuma??, ko suna nufin kuɗi ɗaya za su bayar?, ai kuwa ƙaryarsu, tinda ɗansu ma ya ga Ƴata ya ƙyasa ai kowa ma ya san ba ta wasa ba ce, don haka kamar yadda ake yi wa kowace Ƴa me Daraja sai an yiwa tawa, a biya kuɗin Aure sannan a biya ni Sadaki" Momi ta faɗa a masife. A sanyaye Abba ya ce "Haba Dije, ai sun ce za su bayar da Sadaƙin in an zo ɗaura Aure, kuma ko ma iya Sadaƙin suka bayar ai ba matsala tinda shi kaɗai Allah ya ce a karɓa". "To ba da ni ba!!, amma tinda sun ce za su bayar shi kenan, na zata mugun halin za su nuna mana su ma, waɗannan kuɗi kuma tattaro su za ka yi ka miƙo min, ni ya kamata in ajiye ba kai ba, in ma so kake ka yi kayan ɗaki da su to ba ka isa ba, sai ka fita ka nemo ka yo kayan ɗakin nan. Baba Jamilu ya ce "Yo ai ba a ta kayan Ɗaki yanzu, sun ce ba abinda suke buƙata za su yi mana komai." Zazzaƙar Guɗar da Momi ta tsumbura sai da ta sa wasu toshe kunnuwansu, hakan bai wadatar da ita ba sai da ta tashi ta fara taka rawa. Yau dai an ga abin mamaki, sai da Momi ta ɗaurewa kowa kai. Haka aka watse kowa da abinda yake faɗe. Tana zaune kan ɗaya daga cikin Kujeru biyun da suka sa wani ɗan Table a tsakiya, hankalinta kwance take shan Ice cream tana yi tana lumshe ido, hankalinta sam ba a kusa yake ba ta yi nisa a Duniyar tunani. Ta yi matuƙar tsorata jin Azaan a kusa da ita ya kira sunanta cikin wata maraitacciyar murya, ta yi tunanin gizo muryarsa ta fara yi mata, da ta buɗe ido ta gan shi ƙwadagwas a gabanta sai razaninta ya ƙara ninkuwa, "Ba na son ganinka Azaan Ple...." saurin katseta ya yi da cewa "Kar ki fusata, magana nake so mu yi." miƙewa ta yi a fusace tana cewa "Aap mujhe kya bataane ja rahe hai?!!" ƙara yin ƙasa da murya ya yi ya marairaice kamar zai yi kuka ya ce "Tum baith jao please!" ido ta zuba masa ganin yadda ya zama wani abin tausayi kamar ba shi ba, lokaci guda jikinta ya yi sanyi, komawa ta yi ta zauna har lokacin idanunta na kansa kamar wani kayan gabas. Ya Lumshe idanunsa gami da haɗiye yawun wahala, a hankali ya buɗe idon gami da ɗorasu akan kyakkyawar fuskarta, ya rasa me zai ce mata, shin wane irin zaɓi zai bi a cikin zaɓukan da Zuciyarsa take ba shi? shin da wane ɓangare zai yarda?, "Azaan! tum...." katse mata maganar ya yi da cewa "Mainne tu...." kasa furtawa ya yi sabida nauyin da kalmar ta yi masa, anya in ya faɗa mata haka kuwa bai cuci kansa ba?, wai me ta yi masa ne a rayuwa da ba shi da burin da ya wuce muzguna mata??, to amma ya zai yi da Umarnin da Mammi ta ba shi??, tunanin da ya faɗa kenan, gabaki ɗaya jikinsa ya ƙara mutuwa, ya rasa wane irin al'ajabi yake ji a tare da ita. Ido ta zuba masa kawai tana kallon ikon Allah, za ta iya cewa tinda take ganinsa a Duniya ba ta taɓa ganinsa cikin irin wannan yanayin ba, wani sashin na Zuciyarta ya cika da son sanin damuwarsa, wani gefen kuwa wani ɗan guntun tausayinsa ne ya fara yi mata tsiro. Ganin tana shirin faɗawa wata Duniyar ya sa ta miƙe zumbur tana cewa "Na lura ba ka da abin cewa!" cikin wani irin zafin nama ya cafke hannunta gami da kiran sunanta cikin wata susutacciyar murya, cak! ta tsaya ba tare da ta juyo ba sai ma rintse idonta da ta yi da ƙarfi, gabanta ya shiga faɗuwa a jajjere, "Main... tumse bahoot... pyaar karthi hoon Khushi!!!," ya faɗa cikin rawar baki kamar me shirin rushewa da kuka. Bugun Zuciyarta ne ya ƙara tsananta tsoro da razani suka ƙara dirar mata, da sauri ta girgiza kai tana cewa "Naa!, ba zan iya ba!, ban yarda da kai ba Azaan, main tumse pyaar nahi kharta!!!!" wani irin surfe da sussuka Zuciyarsa take yi, tuni jikinsa ya ɗau karkawa idanunsa sun ciko da ƙwalla, cikin fitar hayyaci ya ce "Sabida me ba kya so na Kushi??! ko dai kina son Roshan ne??" sai a lokacin ta juyo tana zuba masa idanunta da suka burkice, wani shegen kallo ta kora masa wanda ya ƙara juya hantar cikinsa. "Kai fa dama Mahaifinka Kafiri ne Azaan!, kuma kai ma haka, to ko a Addininku haramun ne Yaya ya Auri ƙanwarsa bare kuma mu da muke Musulmi, wannan ashshar ma da kake yi ko a Addinin naku haramun ne; ni ka sakar min hannuna!!" Sakin hannun nata ya yi ya shiga yamutsa tarin Sumar kansa, wata zazzafar iska ya furzar kafin ya ce "Ni ma Musulmi ne Khushi!! Addinin Mahaifiyata nake bi ba na Bhabana ba". murmushin takaici ta yi gami da cewa "Jhoot batao tum, babu yadda za a yi Musulmi me hankali ya yi abinda kake yi, ita kanta Uwar taka yanzu Kafira ce don babu danshin Muslimci a tare da ita!!" "Me yasa kike min haka don Allah?? ina so ki sani a kanki idanuna sun rufe, na riga na haukace kuma zan iya aikata komai don na samu abinda nake so, kar ki bari mu taka matakin da za mu yi abu mara daɗi Khushi! ki yarda da ni tin kafin Imanina ya ƙarasa gushewa; ni ina sonki ne ba wai ina son cutar da ke ba, kyun Kushi! me yasa ba za ki amince da ni?" Tsaki ta yi kafin ta ce "Jao aur mujhe jagah do!, aur main tumse shaadie nahi karoonga!!" Ba ta jira abinda zai ce ba ta yi gaba cikin sauri, wajen Mota ta je ta tsaya don jiran Suhailat, baƙin ciki ya haɗe mata goma da ashirin, ga Suhailat ta zo ta shanya ta ga shi kuma ya zo mata da surutan banza, tunaninta ɗaya ma ko waye ya gaya masa ta zo wajen?. Tinda ya ji Abbi ya kira shi don su yi magana jikinsa ya ƙara yin sanyi salam. Gashi bincike ya tabbatar masa gaskiyar Haydar ne ya je wajen Leelah da zancen Aure. Haka nan yake yawo shi ba me lafiya ba shi ba mara lafiya ba. Abbi na zaune kan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun Kujerun da aka ƙawata Falon hannunsa ɗauke da takardu yana duddubawa. Ba tare da ya ɗago ba ya amsa Sallamar Roshan. Kusa da ƙafafunsa ya ƙarasa ya zauna yana cewa "Abbi ba a rabo da karance-karance". Murmushi kawai Abbi ya yi ba tare da ya ce komai ba, sai da ya kammala sannan ya ɗago yana zame siririn glass ɗin da ke kan idonsa, "Barka da dare Abokina" ya faɗa yana ƙara faɗaɗa murmushinsa, firgigit ya yi gami da cewa "Na'am!!" ganin haka ya sa Abbi ya ce "Tashi zauna kusa da ni." cikin sanyi ya tashi ya koma kan Kujerar ya zauna yana cewa "An gama kenan!" "Eh na gama har ina gaisheka kana ce min na'am" dariya Aliyu ya yi yana cewa "Abbi ka san Duniya sai da nazari, gabaki ɗaya ban san me ka ce ba ne." "Okay, shi kenan, dama na lalubo ka ne akan batun Auren Ɗan uwanka da ya taso." Rass!!!! gabansa ya faɗi, da kyar ya daidaita nutsuwarsa sannan ya ce "Ina saurara Abbi, Allah ya sa dai kai ma ba ƙara Auren za ka yi ba". dariya Abbi ya yi kafin ya ce "Ai in ƙarawa zan yi sai na ji wadda kake so tukunna sai na Aure ta, a wannan lokacin ba Haydar ne ya dace da yin Aure ba kai ne, kana buƙatar me kula da kai har ma da Ƙanwarka, maza faɗa min, wacece Abokiyar tamu?, ina so ne a haɗa Auren naku rana ɗaya da Ɗan Uwanka, ka ga shi jiya ma an je an gama magana, nan da Sati uku in sha Allah zai zama Ango." Kasa cewa komai Aliyu ya yi, ya zama kamar wanda aka dasa a wajen, yau fa ya ga ranar da ake kira Baƙar Rana!. Jin shirun ya yi yawa ya sa Abbi yin gyara murya gami da saɓule Tabarau ɗin nasa duka, kallonsa ya yi a tsanake kafin ya ce "Na lura kamar ba ka cikin yanayi me kyau, amma ina so ka sani ko da ba wadda kake so a yanzu ba zan iya jurar ganinka kai kaɗai ba, dole zan nema maka ko a cikin dangi ko a Abokan Ƙwarai, gwara ma ka faɗa min gaskiya". sai da ya haɗa da Addu'a sannan ya fara samun nutsuwa, da ƙyar ya tattaro duk jarumtarsa ya yi murmushi sannan ya ce "Abbi ni ma ina da wadda nake so!". "Anya kuwa??, ya akai na ga duk ka firgice ? wai shin me kake ɓoyewa Abokin nan naka?". Ƙara faɗaɗa murmushinsa ya yi a cikin ransa yana neman temakon Allah don samun tsira daga Tuhumar Abbi, shi ba yaro ba ne bare a yi masa ƴar burum-burum bayan haka kuma shi Alƙali ne, don haka in ya ritsa Mutum sai dai Allah ya ƙwace shi. "Abbi da gaske nake, kawai na ji abin ne ya zo min a baibai, ban shiryawa Aure ko nan da Shekaru bakwai ba ma bare Sati uku, Abbi idan na yi Aure wa zai dinga kula min da ƙanwata?" cikin sa'a kalamansa suka hau Zuciyar Abbi suka yi ɗaram!, murmusawa ya yi kafin ya ce "Ai yana ɗaya daga cikin dalilan da ya sa na ce ka yi Aure, kai fa Namiji ne wanda aka sani da Fita ba zaman Gida ba, yanzu duk lokacin da ba ka nan fa Bayi ne ke kula da Ƙanwar taka, kai ma babu me kula da kai indai Iyayenka ba sa nan sai dai ka kula da kanka ka kula da ita, amma da zarar ka yi Aure ka ga kun samu wata Uwar, ko da Maimunatu ba ta nan za ku dinga ganinta, za ta kula da Ƙanwarka sannan kai ma za ka samu kulawa daga gareta; ina nuna maka kana rintse ido sai an yi Auren kuma mu ga kana ɗan Tumbi ko??" ya ƙarasa maganar cikin sigar zolaya. Murmushi haɗe da ajiyar Zuciya ya yi a tare, "Kana da gaskiya Babba Sarkin nasara!" ya faɗa cikin salon zolaya kamar yadda ya saba faɗa masa. Murmusawa ya yi kana ya ce "To yanzu faɗa min Wacece???" Nan fa Ɗaya wai an cewa shege ina Ubanka, yanzu wa zai ce yana so?? tabbas da ya yi tsalle ya ce da wadda yake so ƙarya ya yi don gujewa Ɗan Uwansa ɓacin rai, sama da ƙasa ya tabbata ba wadda yake so sama da Leelah gashi yanzu tana neman yi masa nisa, to kenan wa zai ce??, Suhana? ko kuma ya faɗi gaskiya kawai???............ (Sai ku ba shi Shawara masu Karatu🚴🏼‍♀️) SHARE FISABILILLAH *Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Tuntuɓi Lambar Waya👉🏽 09079885632* *©️INDO*[11/28, 7:40 PM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 12 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *GORGEOUS WRITER'S FORUM* FREE PAGE........... Jin shiru ya sa Abbi cewa "Ka yi shiru kuma?" cikin sauri ya ce "Ita ma Gidansu ɗaya da wadda Haydar zai Aura sunanta Salma". "Haɗa baki kuka yi za ku Aure Ƴan Gida ɗaya kenan?, to Allah ya tabbatar da Alkairi; anya kuwa ba da kaina zan je nema maka Auren ba?" ya faɗa yana dariya, cikin sauri Aliyu ya ce "A'a! tab!! wallahi ban yarda ba, ba za ka je ba". "To sabida me?" sai lokacin ya ankara da kwakyarar da ya kusa yiwa kansa, sassauta murya ya yi ya ce "Abbi tana da kyau ne sosai, ba na so ka ganta ka ƙwace min, waɗanda za su je ɗin ma sai na zaɓa don ba na son harkar snatching." Abbi ya yi dariya yana cewa "Allah ya shiryeka Abokina!, ai idan ma ban ganta yanzu ba ko ka Aureta zan iya yi maka Alqunut ka saketa; to ba komai duk yadda ka tsara sai ka faɗawa Abban naku zan ji daga gare shi." dariya ya yi gami da cewa "Na fi yarda da hakan, sabida na san ba za ta soka ba indai na riga na Aureta, na gode Abbi, bari in gudu" ya faɗa tare da miƙewa tsaye, "To ba za ka tsaya ka ga Uwar Gidan ba?" "Oh! zan biya sashinta in mun gaisa sai na wuce. "To Allah ya tsare. lokacin da ya amsa har ya yi tazara a tafiyarsa. Ko zama bai yi ba a ɓangaren nata suna gaisawa ya fice cikin sauri-sauri, ya ƙagara ya koma gida ya ɗan samu nutsuwa tin kafin kansa ya yi juyewar da ba zai iya gane ko'ina ba. Yana shiga ya fara ƙwalawa Khushi kira "Farinciki!!! Farin ciki!! Farin ciki!!!!" A firfice ta farka daga baccin wahalar da ya ɗebeta tana zazzaro ido. Har zai wuceta ta ɗaga murya ta kira sunansa, juyowa ya yi yana kallonta, ganin yadda ta yi wani kozai-kozai ya sa gabansa ya sake faɗuwa. Kusa da ita ya ƙarasa ya zauna yana tsira mata ido, ita kuwa sai lumshe nata idon take yi tana langwaɓewa. Ya san tana cikin damuwa amma bai bi ta kanta ba ya fara da cewa "Khushi Abbi fa ya ce zai yi min Aure nan da sati uku, kuma kin san Haydar wadda nake so zai Aura, ban san ya zan yi ba, anya kuwa ba guduwa zan yi na bar Ƙasar nan ba?" wararo masa idanu ta yi kamar ba ita ce me nuna jin bacci ba, cikin kaɗuwa ta ce "Kya matlab?" ɗan ƙaramin tsaki ya ja kafin ya ce "Wai ba kin ji abinda na ce ba? Leelah ita ce wadda aka gama maganar Aurenta da Haydar jiya". "Amma shi Haydar ɗin ya san ita kake so ya yi haka? wallahi Allah sai na yi maganinsa, sai na yi masa abinda Auren ma zai fita daga kansa" ta faɗa tana huci. Cikin yanayinsa na sanyi ya ce "Ba na so!, inda zan yi hakan da na faɗawa Abbi gaskiya, ko kuma in faɗawa Bhaba, ki rabu da shi kawai, ko ya Aureta dolensa ya saketa indai ba ta shi ba ce." kwantar da kai ta yi kan kafaɗarsa gami da sauke wata marainiyar ajiyar Zuciya, a sanyaye ta ce "Roshan Bhai!, na kasa mantawa da Azaan sai tunaninsa nake yi". idanunsa ne suka ƙara girma ya zazzaro su a kanta, "Kina tunanin Azaan?, wai ma ina kika je yau? ina ta so in tambayeki sai na yi karo da abinda ya fi ƙarfina, wai ba na hanaki zuwa wani wurin ba tare da izinina ba? kuma ma ke kaɗai ba tare da kowa ba." "Ka yi haƙuri, na raka Suhailat ne za su haɗu da Saurayinta, ni ma a can na haɗu da Azaan, kuma wallahi ba ni na nemeshi ba, ina cikin shan ice cream sai na ji muryarsa, na ɗauka ma haukacewa na fara yi" ta faɗa kamar za ta yi kuka, "To me ya yi miki da kike tunaninsa?" jim!! ta ɗan yi kafin ta ce "Ya ce yana so na ne amma na ce masa ni ba na son shi; na kasa samun kwanciyar hankali na kasa tunanin komai sai shi". jinjina kai ya yi gami da cewa "Tab! to ki nemi tsari da shi tin kafin ya fara burkita tunaninki, kin san in Maa ta ji labarin nan sai ta datse miki harshe ko?" sharr!!!!! ƙwallar da ta cika idanunta ta samu damar silliɓowa, "Na san faɗa za ta yi shi ya sa na tsorata, ina ga Asiri ya yi min shi yasa ma na kasa mantawa da shi!!" duk da halin da yake ciki sai da ta bashi dariya, sai da ya yi me isar shi sannan ya miƙe yana cewa ''Ki wuce ki kwanta ki bar labarin nan, ni bari na je wajen Maa". da kai ta amsa masa tare da zamewa ta ƙara kwanciya. Tana tsaye kamar taɓarya, hannayenta goye a bayanta. Ƙarasawa ya yi kusa da ita yana cewa "Maa tsayuwar me kike yi haka? na ɗauka ma kin yi bacci?" "Kawai ina nazari ne." ta faɗa tare da komawa ta zauna kan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujerun falon. Hannu ta miƙa masa gami da cewa "Ajao Beta!" hannunsa ya ɗora kan nata sannan ya zauna kusa da ita. "Akwai wani abinda za ka faɗa min ne?" gyaɗa kai ya yi gami da cewa "E, Yanzu daga wurin Abbi nake, ya ce zai haɗa Auren mu da Haydar, amma ba wannan ce matsalar ba wadda nake so ɗin ashe ita Haydar zai Aura, kuma har an riga an gama magana". Wani shegen kallo ta zuba masa tamkar shi ne me laifin, "Ai kuwa koda ɗaura Auren aka yi sai an warware shi, ba zan lamunta ba!" "A'a Maa, ni dai ba na son duk abinda zai zamo ɓacin rai, ki barshi kawai amma fa koda ya aureta ba zan fitar da rai ba, don ba domin Allah ya Auretan ba, na cewa Abbi zan Auri wata ƴar gidansu, kawai shi kenan a wuce wajen, kuma har yau ina kan bakata sai na koyar da Leelah darasin rayuwa ta yadda ba ta zata ba, don Allah Umma ki yarda da ni, haka nake son yi yanzu". numfasawa ta yi kafin ta ce "Na yarda da hakan, amma a bisa sharruɗaina, muddin ita ma za ta wulaƙanta ka ne kamar yadda Ɗayar take yi maka to fa zan yi abinda ba a so ɗin, koda ka Aureta indai za ta ɓata maka rai ni ma zan ɓata nata." gyaɗa kai ya yi yana cewa "Ni ma na yarda, na san ma hakan ba za ta faru ba in sha Allah; Kawu Mahmud da Abban Irfan da Kawu Rabi'u su nake so su je a yi maganar, don ba na so su san ina da wata alaƙa da Bhaba ko Abbi ko shi kansa Haydar ɗin." mayar da duk mutsuwarta ta yi kansa tare da tambayarsa "To ta yaya kenan? ka san dai in Mutum me hankali ne da zarar ya gansu ya ga sitturunsu zai bawa kansa amsar suwaye ba sai ya tambaya ba." "Irin shigar da nake yi su ma ita za su yi, shi ya sa na zaɓi su Kawu Mahmud na san su kaɗai ne za su iya biyewa shiriritata" ya faɗa yana dariya. Ganin yana fara'a ya sa hankalinta ya ɗan kwanta, duk da wani gefen na Zuciyarta na ƙara tunasar mata irin rashin Albarkar da Leelah ta yi masa, ga kuma Hajiya Habiba da take shirin tarwatsa masa rayuwa. Shirya mata yadda komai zai tafi ya ci gaba da yi tana ƙara tunzura shi, tin ba ta saki jiki ba har ta saki ranta ta fara dariya don kuwa wani abin na shi sai ya sa Mutum dariya ko babu shiri. Kamar yadda Aliyu ya buƙaci a lulluɓewa Bhaba gaskiyar maganar hakance ta faru, ba wanda ya san abinda ke faruwa sai Roshan, Khushi, Maa, sai ɓangaren Haydar da waɗanda suka sa shi. Bhaba ya so tirjewa a kan sai an je da shi Neman Auren Maa ta yi fir ta ƙi amincewa, ya so fahimtar wani abu a ciki amma sai suka ƙara baibaita lamarin dolensa ya haƙura don ya san rigimar Maa. Zama ya yi ya tsara wa su Kawu Mahmud duk yadda za a yi kuma suka Amince masa. Irin yadinsa me matuƙar arha ya sayo ya ya sa aka ɗinka musu su saka ranar da za su je. Kawu Mahmud ne ke taya shi yin komai da tsatstsarawa har da irin jirgawar da za a yiwa iyayen Yarinya. Kwana huɗu kenan da tsayar da maganar Haydar da Leelah. Su Baba na zaune a ƙofar gida suna hira su Kawu Mahmud suka iso. Sallama suka yi musu, suka amsa a Mutunce gami da yi musu bismillah su zauna. Zama suka yi aka ƙara gaggaisawa kafin Abba ya ce "To! to! to! kuna tambaya ne bayin Allah?" Kawu Mahmud ya ce "A'a mun zo wajenku ne." "Allah ya sa dai lafiya" Baba ya faɗa yana gyara zamansa. Kawu Mahmud ya faɗaɗa murmushinsa kafin ya fara da cewa "Lafiya ƙalau sosai ma kuwa, ku yi haƙuri mun zo muku kai tsaye kuma mun zo da babbar magana, idan an bamu dama sai mu faɗa." "A'a ba komai, ku faɗa mana muna saurarenku" Baba Jamilu ya faɗa yana saita zamansa don jin me ke tafe da su ɗin. Bayanin abinda ke tafe da su suka yi musa, da cewa Kawu Mahmud shi ne Mahaifin Aliyu, lafiyayyen bayaninsu ya bayar kamar yadda suka tsara, daga baya ya kora musu da cewar sun zo nema wa Aliyu Auren Salma ne. Baba Habu yana shirin cewa sai sun yi tunani a kai Baba ya ga ba fa'idar hakan tinda Yaron an riga an san shi, don haka ya ce sun Amince, duk ranar da aka shirya kawai a zo a yi maganar Aure. Godiya sosai su Kawu Mahmud suka yi nan aka ƙara caccafkewa. Baba Usama ne ya kawo shawara akan a haɗa bikin rana ɗaya da na Leelah in har iyayen Aliyun sun shirya. Dama abinda suke nema kenan, nan kuwa suka yi caraf da zancen suka amsa. Haka aka ajiye magana an riga an haɗe Auren da na su Leelah, har su Baba sun faɗi Sadaƙin da suke so. Haka suka tashi daga zaman kowa abin ya yi masa daɗi. Ta ɓangaren su Baba ma ba ƙaramin farin ciki suka yi ba, addu'arsu ɗaya Allah ya tabbatar a yi su huta da Gore-goren Mutane na cewar sun tara Ƴaƴa sun ƙi Aurar da su. Koda maganar ta shiga cikin Gida babu wanda bai yi mamakin jin ta ba. Haka aka dinga cira zancen kamar sun samu nama. Wasu sun yi wa Salma murnar samun Miji, wasu kuwa baƙin ciki suke tayata don gani suke yi ita ba tsararsa ba ce, don dai ma ita ba halinta ba ne mugun son Duniyar nan. Hankalinta ya yi bala'in tashi, haka ta dinga kuka tana cewa ita fa ba ta son shi ba za ta aureshi ba tinda Ƙanwarta yake so. Sai da Baba Habu ya yi mata nasiha gami da nusar da ita ya kwantar mata da hankali sannan ta Amince kuma ta saduda ta manta da komai, ta ƙarɓi ƙaddararta da hannu bibbiyu. SHARE FISABILILLAH *Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Tuntuɓi Lambar Waya👉🏽 09079885632* *©️INDO* [11/30, 6:53 PM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 13 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *GORGEOUS WRITER'S FORUM* F-P.......... Tin daga ranar aka fara shirye-shirye ta ko'ina ba kama hannun Yaro. Maa ma ta tashi tsaye tana shiri tuni ta gama yaɗawa Danginta da Abokan Kasuwancinta. Ta ɓangaren Bhaba ma ba zama, yanzu ya fi mayar da hankali akan shirye-shiryen Auren fiye da Kasuwancinsa. A ɓangaren su Momi da su Baba Habu ma kowa ƙoƙarin yadda zai rufawa kansa Asiri yake yi, musamman Baba Habu shi da babu wanda zai yiwa Salma kayan Ɗaki sai shi. Roshan kuwa yana cikin tara ahu, sai dai ba ya nuna wa kowa damuwarsa, a zahiri fara'a yake yi sosai, amma idan ya keɓe har zazzaɓi yake yi. Khushi ce kawai ta san halin da yake ciki, duk ta bi ta rikice ba ta walwala ko kaɗan. Ana saura Sati ɗaya bikin Maa ta tafi India don ƙara yin wani shirin. Ba don Aliyu take yin wani abun ba sai don Salma wadda ta amince ta jingine farin cikinta ta karɓe shi, hakan ya sa ta samu kyakkyawan gurbi a Zuciyar Maa, kuma ta sha Alwashin yin komai domin ta faranta mata. A fannin su Leelah kuwa abin sai wanda ya gani. A memakon ta kame kanta sabida an riga an yi Baikonta sai ta ƙara tashi tsaye wajen Yaudarar Samari da aske musu Aljihu kamar yadda Momi ta tsara mata, a cewarsu a nan za su haɗa kuɗin da za su yi duk wata burga da bajinta. Shi ma Baba Usama gorin da Momi ke yi masa ya sa shi fafutukar neman kuɗi ta ko'ina, duk inda ya je neman bashi sai a hana shi sabida kowa ya san ba shi da sana'ar ma bare a sa ran zai samu wataran ya biya. Sai da kyar ya samu wani Alhaji ya ce zai dinga yi masa gadi sannan ya ba shi rancen kuɗin, in lokacin biyansa ya yi sai ya cira a kuɗinsa da haka har su fanshe. Haka nan ya amince duk da yana ganin kamar ba zai iya aikin ba amma a wannan karon ba yadda zai yi. A ɓangaren su Salma, kuɗin da take tarawa na Wanki da Gugar da take yi su Umma ta ciro ta yo mata ƴar sayayyar kayan Kicin, su kofi su robobi da ƴan filetai da sauransu, sai fannin ɗan turaren wuta da Humra. Sai Dilka da Leelah ta dage sai an yiwa Salma kamar yadda ita ma aka yi mata. Da farko Salman ta ce ba ta so sai da ƙyar suka shawo kanta ta yarda sannan aka fara ɗan mulka mata. Ba laifi abin ya karɓe ta fatarta ta canja sosai, sai dai ba wani can ba don kayan haɗin Dilkar ma ba wasu na kirki ba ne. Leelah kuwa ta ƙara zama kamar balarabiya ta ƙara ja ta yi sulɓi sai ƙyalli take yi, ita da yake abin nata ya shafi tsadaddun sabulai da mayukan bilitin. Su Sumayya da su Rabi'a ma an tashi tsaye ana shirin yadda za a samu samari a bikin, a cewarsu a wani wurin ma sun nema bare abu ya zo gidansu. Su Rabi'a har da Mama ake yin shirin, ta ciyo bashika su ma sun tara na samari an zo ana shirin abubuwan bajintar da za a yi. Kowa ya zuba ido ya ga yaya Baba Habu zai yi wajen yiwa Salma kayan ɗaki. Sai dai abinda ba su sani ba me Zuciyar yi Allah ba ya hana shi. Yau Biki ya rage saura kwana biyar. Gidan tuni ya fara zama gidan biki, waɗancan su shigo waɗannan su fita. maƙota sai gangankon zuwa ganin Leelah ake yi don labari ya zagaye ko ina Ɗan gidan Alhaji Mustafa Naira za ta Aura. Ita kuwa sai yauƙi, iyayi, kwainane, ƙafafa, fasa kai, fariya, duk ta haɗa wuri ɗaya. Salma kuwa wasu kiranta suke yi kyakkyawa Matar Talaka, ita ma labari ya zagaye ko'ina cewar wani faƙiri za ta Aura. Sam abin ba ya damunta don ta sa a ranta kwanciyar hankali kawai take buƙata ba kuɗi ba. Yau ana zaune sai ga Mata kici-kici da Akwatuna ba zato ba tsammani sai ganin su aka yi sun shigo. Momi ta yi matuƙar jin haushin bazatar da suka yi mata, don ta so ta yi musu abin da za ta burgesu, wani abin da ya ƙara dugunzuma Zuciyarta ganin shegen kallo na banza da wofi da raini da suke jifansu da shi daga gidan har Mutanen cikinsa. Kowa na gidan abin ya taɓa Zuciyarsa don ba sa son raini kwata-kwata. su Sumayya har sun fara shirin mayar da raddi suka fasa sabida akwatunan da aka gama shigo da su gabaki ɗaya suka canja musu lissafi. Saiti biyu ne masu guda huɗu sai ƴar ƙarama, in an haɗa duka Takwas kenan har ƴan ƙananun goma. Tuni kowa ya fara santi da sambatu akan lefen. Cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya cika da Mata ana ta shewa da guɗa gami da yiwa Momi da Ƴarta kirari. Ƴan kawo lefe kuwa ana gama shigo da su ko zama ba su yi ba suka juya suka bar musu gidan. Hakan bai dame su ba su dai kawai sun ci gaba da Shagalinsu. Salim ne ya lallaɓo ya janye Salama daga cikin tawagar ƴan ganin lefe ya jata gefe, cikin takaici ya ce "Wai ke Salma don Allah ba ki san ke ma Amarya ce ba? kamata ya yi ki dinga jan ajinki, amma kin je sai washe baki kike yi kina murna akan lefen da ba naki ba." Harara ta zuba masa tana cewa "Me kake nufi da hakan? wai kana nufin ba zan taya Leelah murna ba?" sassauta murya ya yi kafin ya ce "Shiga za ki yi ɗaki ki yi bulum! kamar ba kya gidan, in ya so sai ki yi ta tsalle a ɗakin ke kaɗai, ƙarewar murna kenan, ni fa na fi so ke ma ki dinga jan aji, ba ki ga yadda Leelah take yi ba? sai hura hanci take yi magana ma yanzu ba kowa take yiwa ba?" Salma ta rausayar da kai kafin ta ce "To! ni me zai kai ni in dinga hurawa Mutane hanci? ni ko me kuɗin zan Aura ba zan yi haka ba bare ina talaka wanda zan Aura ma haka, ni dai ka barni in yi murnata tinda Leelah burinta ya cika, ni dai Allah ya nuna mini ranar da za a ɗaura Auren, ka san fa tana matuƙar son ta Auri me kuɗi, ko a Littafi ta ji an yi lefe me yawa irin haka sai ta ji dama ita ce " ta ƙarasa maganar tana dashare baki, taɓe baki ya yi gami da yi mata wani kallon tara saura kwata, "Gaskiya ke dai kalarki daban Salama, wallahi duk gidan nan ba me yi miki farin ciki don kin samu irin wannan kayan, kowacce ji za ta yi dama ba ke aka kawo ba ita aka kawowa, kin ga daga haka dole sai hassada ta samu; ni ba ma haka ba yanzu, ni fa na shiga damuwa sabida ban ga an kawo naki lefen ba, kar fa mu je su ce ba za su yi ba, ai kuwa da an ga salawaitun bala'i don wallahi ba za mu ɗaukeki sukutum guda mu ba su ba tare da sun yi mana lefe ba!" ya ƙarasa maganar yana tattafa hannuwa gami da jujjuya idanu. Jikinta ne ya yi sanyi, tabbas ita ma tana wannan tunanin, indai kuwa ba za su yi mata ba sun jawo mata gori, amma ba yadda za ta yi haka nan za ta jure. Ganin Salim yana ta cika yana batsewa ya sa ta yi murmushi cikin son kwantar masa da hankali ta ce "Yo kai banda abinka saura kwana huɗu fa yau, ka ga wasu ma fa sai ranar ɗaurin Aure suke kawo lefe, to ƙila su ma haka ne, kuma ko ba su yi ba mu ina ruwanmu? ba ka ga Babana ya sayo min Atamfar da zan saka ranar ba? ka zo ka raka ni ma na karɓo ɗinkin in zo in gogeta tin yau, Kawuna ma ya ce zai ɗinko min leshi, ka ga ai ina da kayan sawa." "Wai ke don Allah Salama ba kya jin ba daɗi ne? kina ji fa har maƙota munafukai sai habaici ake yi miki, amma shi ne kike wani lissafin ko ba a yi lefe ba ina ruwanki?" zuwa yanzu Zuciyarta ta gama karyewa don ya tuna mata abinda yake ta cin Zuciyarta tana ƙoƙarin danne shi, kamar za ta yi kuka ta ce "To wai yaya zan yi Salim? tin fa ranar da Leelah ta sa aka kori Ali daga gidan nan ban ƙara ganinsa ba, gashi ni ko waya ba ni da ita bare ya kirani, bai ƙara bi ta kaina ba bare ya san halin da nake ciki, iyayen nasa ma tinda suka zo sau ɗaya ɗinnan ban ƙara jin ɗuriyarsu ba, sai dai na ji Babana ya ce wataran sun yi waya da su; ni dai ka manta da su kawai ai lefe bai zama dole ba Sadaƙi shi ne dole, shi ne in ba su bayar ba ba wanda zai yarda a ɗaura Auren". cikin sanyin jiki ya ce "Kin fi ni faskiya kuma, to Allah ya tabbatar da Alkairi". Hira suka ci gaba da yi akan abinda ya shafe su, a nan su Sumayya suka same su, zama suka yi suka fara zuga Salama akan kar ta karɓi lefe kaɗan bare ma har a ƙi yi mata. Ita dai jinsu take yi ba ta ba su amanna ba har suka gaji suka ba su wuri. Sai da suka watse Salim ya ce "Kin ga waɗannan masu buɗewa Mutane ido akan abin Duniyar? wallahi kawai so suke su cuci Mutum su sa masa son Duniya su jefa shi a wahala, ni dai na rasa me yasa ƴan gidanmu suke a haka." Murmusawa ta yi gami da cewa "Mu yi musu Addu'ar Allah ya shiryesu." Ya ce "Amin in masu shiryuwa ne." Washe gari....... ba iya Salim ba kowa ma ya sa ran ganin an kawo lefen Salama sai dai har aka kwana aka hantse shiru, haka aka ƙara kwana har yamma ta yi ba labari. Salma dai tuni ta fitar da rai ta fawwala wa Allah, Leshin da Kawunta ya ɗinka mata da Atamfar da Babanta ya yi mata su ta goge ta ajiye a matsayin wanda za ta saka ranar bikin. Salim kuwa sai zumɓure-zumɓure yake yi, gabaki ɗaya haushin kowa yake ji. Momi ta lura da hakan don haka ta zauna ta tuje masa ta yi masa zagin tsamar nama akan dalilinta na ya fi son wata a kan Ƴar Uwarsa, har da cewa baƙin ciki da hassada yake mata don Leelah ta samu me Kuɗi. Abin ya yi bala'in damunsa, ya yi kuka har ya godewa Allah, ya kasa gane me yasa Mominsa take abu tamkar na marasa hankali, ita kanta Leelah wai haushinsa take ji, shi dai har ga Allah ya san ba wai hassada yake musu ba, kuma ba ya fi son Salma ba ne, sai dai ya shaida akwai shaƙuwa da ƙauna a tsakaninsu, kuma duk da Salma ba ta da kuɗi kafin Ƴar Uwar ta shi ta kyautata masa sau ɗaya ita ta yi masa sau goma, don ko wankinsa wani lokacin ita take yi masa sai ta ci tira ne suke yi tare. Da daddare ba zato ba tsammani sai ga su Kawu Mahmuda da Akwatu uku. Su Baba suka yi ta murna suna sa Albarka. Suka rabu cikin Mutunci da Mutuntawa. Ana shigar da kayan cikin Gida kuwa su Mama suka fara cewa ai yanzu an dena yin Akwatu uku sai biyar ko shida, a tsiyace shi ne huɗu. Ita dai Umma ko iya haka an biyata don ita ma ta fitar da rai, da ga an kawo kuwa sai farin ciki ya rufeta amma duk da haka ko inda Akwatun suke ba ta kalla ba bare ta ce wani abin. Duk da dare ne sai da aka tara Maƙota da yake akwai Nepa lokacin sai abin ya fi armashi. Sai shewa suke yi suna guɗa sai dai mafi yawancinsu ba su yaba ba, daga na Gidan har Maƙotan, har da ƙanwar su Baba, sai cewa suke yi waccan Atamfar me arha ce, wancan leshin ba shi da ƙarko, ai Leelah ita ta mori kaya ta mori Miji. (Ku ji fa sakarci masu karatu.🤔 Wai ba a damu da Kyawawan Ɗabi'u ko Halayensa ba sabida yana da Kuɗi ake kiran an Mori Miji🥹) Yau ana i gobe ɗaurin Aure kenan..... tin safe baƙi suka fara sauka kuma tin safen aka fara shirin Party. Leelah sai rawar jiki take yi har ta ƙagara Daren ya yi. Su Umma Rakiya Ƙanwar su Baba da sauran dangi har da Ƴan Uwan Momi da Maƙota, suna shirin tafiya Gidan Leelah a cewar su za su je jere sai ga Baba Habu da Motar kayansa, ya zo neman waɗanda za su je yiwa Salama jere. Nan ma an sha tsalle don kuwa kowacce tirjewa ta yi, su fa ga Gidan da za su sha AC ba abinda zai kai su su sha wahala har da ƙarin cewa ƙila ko Abinci ba za a ba su ba. Baba Habu abin ya yi masa ciwo har ƙwalla sai da ya yi Musamman da ya ga wai har da Ƙanwarsa uwa ɗaya uba ɗaya a cikin masu cewa ba za su yi masa abu ba sabida ba shi da Kuɗi. Salim ne ya daki ƙirji ya fita ya lalubo Abokansa duk da ba su gareshi sosai ba, Mutum biyu ne ke kula shi sabida kasancewarsa Kamar ɗan daudu sai kowa ya dinga cewa ba ruwansa da Mace sai ya zama abin tsokana da ƙyama. Su biyun duka suka sanar da Iyayensu mata akan su temaka su je a yi da su, cikin sa'a suka Amince. Daga su sai Matar Kawu Ishaq Yayan Umma, sai Salim da Abokansa, suka tafi. Gida ne ɗan madaidaici me ɗaki Biyu sai Kicin da banɗaki, ya sha fenti fayau ya yi kyau sosai, duk da cewar fentin ma me arha ne amma ko'ina ya yi son kowa ƙin wanda ya rasa. Da yake kayan ba masu yawan gaske ba ne komai ya hau ya zauna, sai Gidan ya ƙara kyau. Su ma sun yi tunanin ba za su samu ko ruwan sha ba sai ga shi an kawo musu Abinci har da nama, ga ruwa da lemuka. Leelah tin Azahar suka tafi kwalliya Sumayya ce ƴar rakiyar ta. Kamar yadda Haydar ya cancare kuɗi ya zube haka suke son su yi fita ta fitar hankali. Salma dai ta tubure ta ce ko kwalli ba za ta saka ba, Aliyu ya ce ba ya son wani Party kuma dama ba ra'ayinta ba ne, ko ƴar Walimar da ake yi a Gida ma ta ce ba za ta yi ba don ba ta da Abin da za ta bawa waɗanda ta gayyata. SHARE FISABILILLAH *Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Tuntuɓi Lambar Waya👉🏽 09079885632* *©️INDO* [12/6, 11:28 AM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 14 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *GORGEOUS WRITER'S FORUM* FREE PAGE........... Sai da kyar aka lallaɓa ta ta zauna Mardiyya Yayar Abokin Salim ta yi mata kwalliyar Yaya Isuhu ya biya dubu biyu. Ɗan Leshinta ta ɗauka ta maƙala ta koma bakin Gadon Umma ta ƙyafe, nan ma ta ce ko ƙofar takashi ba za ta je ba. Ko da aka tashi tafiya Partyn Leelah ba yadda ba ta yi da ita ba a kan ta je ta ce ita fa ba ta san zancen ba, dole kowa ya haƙura ya bi ta da na Mujiya. Leelah an sha kyau kamar ba za a Mutu ba, Yau jinta take tamkar a Ƙofar shiga Aljannah. Kamar buɗar ido cikin ƙanƙanin Lokaci gidan ya zama ba kowa sai Umma da Momi, sai Salama, kowa ya ɗaware wajen Perty, har Inna da Mama cewa suka yi ba su ga ta zama ba. Lokacin da suka dawo tuni Salama ta yi sahu tara a baccinta, sai da ta ji hayaniyar masu bayar da labarai sannan ta farka. Wasu kusan kwanan zaune suka yi sabida tsabar surutu da mayar da yadda aka yi. Tin sassafe Leelah ta sola wanka ta shirya cikin haɗaɗɗen Lesi kalar fari sai adon fulawa golden, mayafi golden da takalmi golden ta ɗora a kai, ta sha make'up na garari. Ta yi mugun kyau ko ɗan hassada ya ganta sai ya yaba ko ya yi shiru. Taku take irin na ƙasaita da jin kanta, yau girman kan nata ya ƙara girma don kuwa ba kowa take saurara ba, wasu ko kallon arziki ba ta yi musu. Salma kuwa tinda ta tashi take jin gabanta na faɗuwa ba gaira ba dalili, gabaki ɗaya sai ta shiga damuwa ta nemi wuri ta tsakure ta fara sharɓa kuka. Sai da ƙyar Umman Nabila ta lallaɓa ta gami da kwantar mata da hankali sannan ta shirya ta. Cikin lefenta Umman Nabila ta duba ta ɗauko wata shadda ƴar madaidaiciya kalar blue black, ɗinkin doguwar riga ne ya sha kwalliya tin daga sama har ƙasa, duk da ba wata me mugun tsada ba ce amma ta yi bala'in kyau da ɗaukar hankalin me kallonta. Da rarrashi da lallaɓi ta saka ta don kuwa cewa ta yi Atamfar da Babanta ya ɗinka mata ita za ta saka, sai da kyar suka shawo kanta. Ko Hoda ƙin yarda ta shafa ta yi bare ta zauna a yi mata make up. Komawa ta yi can ƙuryar ɗan fulillikin Gadon Umma ta maƙale, sai ka leƙo ka koma ma indai ba ka mayar da hankali ba ba za ka san tana wajen ba. Wasu irin tunani masu kama da mafarkai ne suke yi mata yawo a cikin kai, yau ne karon farko da ta fara jin rashin yarda da Aliyu har cikin ranta, haka kawai take jin tamkar ba da Zuciya ɗaya zai Aure ta ba, ga wasu abubuwa da take gani da zarar ta rufe idanunta. Mayar da hankali ta yi kan Addu'a don ita ce maganin kowane irin rikici. Biki ya yi Biki!, ko ina ya cika maƙil da ƴan uwa da Abokar arziki da ƴan sa ido da ƴan gulma, ko'ina ka zagaya kayaniya ake yi kamar a tashi Gidan. Kowa farin ciki da murna yake yi, mafi yawanci kowa na maƙale a wajen Leelah da Mominta, tsoffi ne masu gudun hayaniya suke gangarowa wajen Umma su zauna sai danginta waɗanda suka zame mata dole, su kuwa dama ba yawa ne da su ba. Kayan Abincin da aka haɗo da su a Lefen Leelah su aka zauna aka tsara girki na ƴan Ɗaurin Aure. Abincin ƴan biki kuwa Baban Salma aka bari da ɗawainiya, shi ya shiga ya fita ya nemo ɗan Geronsa aka markaɗo aka dama kunun safe, sannan ya nemo ƴar shinkafarsa ta hausa ya ce a dafawa ƴan Ɗaurin Auren Salma. An sha turnuƙu a bakin Murhu, inda ɗaukar film za a yiwa abin sai dai Searise don ya fi ƙarfin a dunƙuleshi waje ɗaya. Maza ma ba a barsu a baya ba, da Matasa da Magidanta na Unguwar da Yara, duk sun taru a ƙofar gidan Alhaji Usama sunan da bai taɓa amsawa ba Alhaji, yau mafi yawanci da shi ake kiransa. Abu ɗaya ne bai yi musu ba ƙarancin abinci don cewa suke yi kamata ya yi sai sun ci sun ture tinda Bikin na Manya ne. Ƙarfe 10:00am Motar Gidan Abinci ta sauka a ƙofar gidan, nan fa aka ƙara tara ƴan kallo. Sai da ƙyar waɗanda suka kawo ɗin suka samu Baba Usama suka sanar da shi Alhaji Mustafa Naira ne ya yi order ya ce a kawo nan Gidan. Farin ciki a wajen Baba Usama kasa ɓoyuwa ya yi, haka ya dinga ɓanshare haƙora kamar an ba shi tallar Makilin. Sai da Momi da danginta suka yi da gaske sannan suka tseratar da Abincin daga farmakin Mutane. Momi ta yi guɗa ta ƙara ya fi gaban ƙirgawa, tinda ta yi tozali da rantsatstsen Abinci kala-kala har da wanda ba ta taɓa gani ba kuma duk na bikin ƴarta sai ta ƙara tirewa, ji take ina ma da turmin zani ta goye Leelah ta yi rawa. Haka aka ci gaba da hada-hada kamar ranar idi, sai dai a wajen majiɓanta Amare kallo ya fara komawa sama, Ɓangaren Haydar ƙarfe 10:00am daidai aka yi da su za a ɗaura Aure, a ɓangaren Aliyu kuma 11:00am, gashi yanzu an buɗi ido 01:00pm har ta wuce babu labarin kowane ɓangare. Haydar na kwance kan makeken gadonsa yana shaƙar bacci, Budurwarsa Alina tana zaune kusa da shi daga ita sai pant da bra, ta zuba masa idanunta wanda suke nuna alamar kukan da ta mazga, abubuwa da yawa take rayawa a Zuciyarta, tabbas don dai ya ce mata ba son Leelah yake yi ba bayan an yi Auren zai saketa da ba abinda zai hana ta tarwatsa Auren ko ta halin yaya ne ko da kuwa hakan na nufin za ta kashe Leelah ɗin. A hankali ya fara buɗe idanunsa wanda suka yi bala'in nauyi, yana buɗe su ya ɗora a kanta, bai san lokacin da murmushi ya suɓuce masa ba. Zazzaro ido ta yi a razane, sam ba ta yi zaton farkawarsa a wannan lokacin ba, ta so sai yamma liƙis ko dare zai farka ta yadda dole lokacin an fasa ɗaurin Auren, musamman da ta ga ya yi wannan murmushin me kama da na gayya ko mugunta sai jikinta ya ƙara yin sanyi. Yunƙurawa ya yi ya zauna kafin ya janyo towel ɗin da ke kusa da shi ya ɗaura a ƙugunsa, ido ya zuba mata kamar yadda ita ma ta zuba masa, wani irin kallo suke yiwa juna me cike da ma'anoni masu yawa. Anya kuwa zan iya bari ya je a ɗaura Auren nan?, gaskiya dole na samo mafita, dole ne na sa ya koma baccin nan, dole ne na san abin yi. Ita da Zuciyarta suke shawarwari. Shi kuwa tunani yake yi dole ne ya yakice ta ya fita don ba zai bari damarsa ta kufce masa ba, indai har bai halacci wurin Ɗaurin Auren ba Bhaba zai iya sauya akalar komai ta koma kan Aliyu, wani gefen kuwa dariyar mugunta yake yiwa Alina, duk ta bi ta susuce akan Kishinsa shi kuwa sam ba ya jin zai iya yin kishinta don ita ba komai ba ce gare shi face abar ƙore ƙishi. Miƙewa ya yi cikin rashin ƙwarin jiki ya nufi toilet domin watsa ruwa. Tana tabbatarwa ya shige ta tashi ta ɗauko ƴar jakarta tare da lemon da ta san yana sha da cup, tsiyayawa ta yi a cup ɗin sannan ta ciro wasu ƴan ƙwayoyi a Jakarta ta ɗauki guda uku ta watsa a ciki, komawa ta yi ta ƙyafe tana ƙissima irin kyakkyawar tarba me jan hankali da gusarwa da za ta yi masa in ya fito. Yana kwance ya yi bulum! cikin bargo yana ta muzurai, Khushi ta shigo cikin sauri jikinta har karkarwa yake yi, kai tsaye kan gadon ta haye tana kiran sunansa cikin muryarta da ta fara fita daga hayyacinta sabida kuka. Da ƙyar ya yunƙura ya zauna tare da jingina bayansa a jikin fuskar gado, rinannun idanunsa ya zuba mata yana jin wasu irin allurai na azaba suna sukar Zuciyarsa. Cikin faffaɗan ƙirjinsa ta faɗa tare da fashewa da wani sabon kukan tana cewa "Roshan Maa ta yi fushi da kai". hannayensa duka biyu ya sa ya rungumota gami da zubawa koɗaɗɗiyar fuskarta ido, Murya a cunkushe ya ce " Na san dole ta yi fushi, amma ba ni take yiwa ba da Haydar take yi; Khushi! Zuciyata tamkar ta ƙone nake ji, ina matuƙar son Leelah, me yasa ta kasa fahimta ta? me yasa ta kasa yarda da ni?, ji nake kamar ba zan iya rayuwa me daɗi ba indai ba tare da ita, ina tsoron na kasa yiwa Salma Adalci idan na aureta, domin Zuciyata da dukkan tunanina ba sa tare da ita." dogon numfashi Khushi ta ja, ta sauke shi tare da wata zazzafar ajiyar zuciya, cikin muryar kuka ta ce "Zan gayawa Bhaba gaskiya!!, ba zan iya jurar ganinka cikin wannan halin ba!, ko ni da kaina zan iya sama maka farin ciki don ba amfanin wanzuwata a Duniya indai ka rasa shi ina kallo". "Tinda na ce ba za a yi haka ba dole ba za a yi ba, a bakina Bhaba ba zai ji wannan maganar ba, kuma ba na so ya ji a wajenki koda soyayyar Leelah za ta kashe ni; zan iya haƙuri na jure rasata a wannan lokacin amma ina so ki sani ba zan taɓa haƙura da ita ba......." "Aliyu!!!!!!" Bhaba ya kira sunansa a fusace!!!, a tare zukatansu suka bada bum!!!! duk suka zarowa Bhaba da yake ta huci ido jikinsu na rawa. ƙarasowa ya yi fuska a murtuke, cikin ɓacin rai ya ce "Dama na san akwai abinda kake ɓoye min Aliyu!!, duk ina Abotar dake tsakaninmu da ka kasa faɗa min gaskiya?? ashe wadda ka ce min ita za ka Aura ba ita kake so ba?, to kana tunanin barinka a cikin uƙuba shi ne mafita??, ashe don haka ka ɓata mana lokaci ka yi zamanka ka ƙi fita ko'ina? ko ba ka san azhar ta kusa ba??, Me yasa kuke son mayar da mu ƙananun Mutane ne?" Gudun Zuciyarsa ne ya ƙara ninkuwa, girgiza kai yake yi alamar a'a bakinsa na karkarwa, yana son yin magana amma ya kasa. Khushi kuwa ƙara ɓarke baki ta yi don ta tabbata Bhaba ya ji komai, shi kenan ta faru ta ƙare.............. SHARE FISABILILLAH *Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Tuntuɓi Lambar Waya👉🏽 09079885632* *©️INDO*[12/6, 11:28 AM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 15 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *GORGEOUS WRITER'S FORUM* FREE PAGE........... Neman Duniya an yiwa Haydar babu shi babu labarinsa, ita kanta Maminsa sai da ta fara tsorata don kuwa abin ya wuce Misali. Tin jiya bai dawo Gida ba, duk da hakan ba baƙo ne a wurinta ba amma a yau sai da ta girgiza, har cikin ranta ta yi zaton Maa ce ta sace mata Ɗa, wayarsa an kira fiye da misali amma bai ɗauka ba. Bhaba ya yi faɗa ya yi faɗa har ya gaji, shi dai ya san duk inda ta je ta zo Haydar yana sane ya gudu, kuma ya san ba zai wuce wajen Abokansa na banza ba. Har ya gaji ya dena kiransa ya tafi wajen Aliyu sai kuma wata Zuciyar ta ce ka ƙara kira. Haydar yana fitowa daga toilet Alina ta yi saurin miƙewa tana wasu ƴan buntsi-buntsirenta gami da caɓe fuska kamar za ta yi kuka, cikin wata mayaudariyar murya wadda ta san dole sai ya saurareta ta ce "Haydar!! yanzu da gaske Aure za ka yi ka bar ni?, menene abinda ban yi maka ba da za ka gujeni!" ya ɗauka ma in ya juyo zai ga tana kuka sabida yadda ta marairaice murya sai ya gan ta ƙirmisisi. "Kin san ni ba na ɓoye-ɓoye Alina, na riga na gaya miki gaskiya ni ba son Leelah nake ba, hasalima kawai zan Aureta ne sabi da wani dalili; nema kike yi ki ɓata min rai sai ka ce ke kaɗai ce kika fi sona a cikin Ƴan Matana, kin sani dai jiya da daddare ma wadda ta tayani kwana daban, kin bi kin wani ɗaga min hankali sai kuka kike yi. kofin da ta gama yin ƴan jiƙe-jiƙenta a ciki ta ɗauka gami da nufar inda yake, miƙa masa ta yi gami da cewa "Dole hankalina ya tashi sabida ni sonka nake yi da dukkan rayuwata, soyayyar ce ma ta sa na banzatar da kowa na riƙe ka kuma na baka dukkan abinda na mallaka a matsayina na ƴa Mace, kar ka manta kai ne Namijin farko da na fara haɗa shimfiɗa da shi, kai ne ka buɗewa duk wani Namijin da nake mu'amala da shi hanya, soyayyarka ce ta jawo min, na san indai ka yi Aure dole za ka rage saurara ta, za ka iya mantawa da ni ma; kar ka za ta ban yarda da kai ba ne, na san rayuwar za ta iya canjawa". ɗan tsagaitawa ta yi kafin ta ci gaba da cewa " na ga kamar ranka ya ɓaci, karɓi wannan ka kora". karɓar kofin ya yi yana zuba mata ido, tausayinta ya ɗan kama shi kaɗan, sai dai ba zai iya yarda ya yi asarar damarsa ba. A hankali ya kafa kofin a bakinsa, zai fara sha kenan idonsa ya sauka akan wayarsa da ke kan drower tana kawo haske ita kaɗai. Sai da gabansa ya faɗi da ya tuno Daddynsa, miƙa mata kofin ya yi kafin ya nufi wajen wayar ta shi, cikin sauri ya ɗauki kiran gabansa na faɗuwa. Rai a ɓace Bhaba ya ce "Ka kyauta Haydar!, ka yi min abinda ka saba, ka muzguna min hankalinka ya kwanta". "Me na yi to Dad??!" "Ba abinda ka yi, na san ba a hayyacinka kake ba ba ka san ƙarfe nawa ba ma yanzu, maza duk inda kake ka kama hanya ka tafi wajen Ɗaurin Auren nan iya ƙaramtar da muka yi ta isa haka Aure kuma ba fashi sai an ɗaura shi ko kana so ko ba ka so". yana gama faɗen haka ya gimtse kiran, zazzafar iska ya furzar gami da lumshe ido, komai ya zo masa da sauƙi don har ga Allah ya ɗauka zai ce masa ya Aurawa Aliyu ita. Watsar da lamarin Alina ya yi duk da tana ta kai kora da matse lamba, cikin gaggawa ya shirya ya tankaɗo ƙeyarta suka fito tare sannan ya yi hanyar Gidansu. Ya sha faɗa wajen Mami duk wanda Bhaba ya yi mata sai da ta kusa juyewa a kansa, ransa ya ƙara jagulewa sai ya ji ma gaba ɗaya ya tsani Leelah don ita ya ɗorawa Alhakin komai. Wani matsanancin kuka ne ya kufce masa, ya shiga rusa abinsa kamar ƙaramin Yaro, sai a lokacin ya iya buɗe baki ya ce "Bhaba ba ita ba ce!, ita har yau ta ƙi karɓar soyayyata, ga shi lokaci ya ƙure Abbi ya ba ni zaɓi biyu, ba yadda na iya shi ya sa na ce zan Auri Salma" "Amma da ka faɗa mana gaskiya ai ka san za mu ara maka lokaci, wai me ya sa ma ba za ka gaya wa Yarinyar gaskiya ba?" "Bhaba ka ƙyaleta kawai, yanzu tayar da maganar nan ma ɓacin rai ne ga Abbi, don Allah kawai a yi komai yadda ya sawwaƙa. "Roshan yana da gaskiya!!, abinda ya zaɓa kenan kuma shi za mu yi masa!" muryar Maa ce ta karaɗe kunnuwansu, sosai Roshan ya ji daɗin zuwanta. Bhaba kuwa takaici ta ƙara masa, "Yanzu ɓacin rai shi ne abin so? ki duba ki ga halin da yake ciki fa!!" ya faɗa cike da takaici, murmusawa ta yi kafin ta ce "Ka shirya Roshan! lokaci yana ƙara ƙurewa; Jaan!! abu indai kana son shi koda yana yi maka ɗaci haka nan kake jurewa, a fannin soyayya ne wannan, tana buƙatar nutsuwa, don Allah ka dena damuwa akan komai, ka cika masa muradinsa kawai". jinjina kai ya yi kafin ya ce "Shi kenan, mu za mu yi gaba sai ya tawo daga baya". Har ya kusa ficewa daga ɗakin Maa ta tsayar da shi da cewa "Wani hanzari ba gudu ba!! kar da ka manta kai a ɓangaren Haydar kake, kuma ka sa a ranka ba ka haɗa zuri'a da Aliyu da Mutanensa ba!" Jinjina kai ya yi sannan ya fice. Sai da Maa ta yi da gaske sannan ta rarrashe su daga shi har Khushi ɗin. Sai da aka yi sallar Azhar sannan aka ɗora da Ɗaurin Auren, na Haydar aka fara yi sannan aka ɗora da na Aliyu. Ana kammalawa kowane ɓangare suka watse saniba gudun masu ƙyarto, a hakan ma wasu sun fara gano usulin kamar da ke tsakanin Alhaji Mustafa Naira da Aliyu, abin da ya sa ma waɗanda suka san Aliyu ba su yi saurin ganewa ba shi inkiyarsa daban, Me Sanyi aka fi kiransa, ba kamar Haydar da duk inda ya zagaya da Inkiyar Daddynsa yake amfani ba. Hankalin Leelah ya kwanta saɓanin Da da ya miƙe tsaye, sabida jinkirin zuwan Ango, da ta ji an ɗaura Auren kuwa sai farin ciki ya turnuƙeta ta kowanne fanni. Salma kuwa sai hankalinta ya ƙara tashi, gashi yamma ta doso lokacin da za a tsigeta daga gaban iyayenta yana ƙara kusanto ta. Tana zaune can ƙuryar Gadon Umma kamar dai ɗazu, Salim ya shigo yana ƙwala mata kira. Turmutsawa ya yi har ya dangana da ita sannan ya miƙa mata wata ƴar leda yana cewa "Gashi in ji Mijinki!" Rikicaaa!!!!! gabanta ya faɗi, jin ya ambaci Miji a kanta ba ƙaramin tarwatsa lissafinta ya yi ba, har cikin ƙoƙon ranta tsoro ya kama ta, baki na rawa ta ce "Menene?!" "Waya ce!" ya faɗa yana kici-kicin ciro ta daga kwalinta, Sharr!!!! hawayenta da suke ta tsere a kan fuskarta suka ci gaba da buga wasansu. Duk da Keypad ce ta yi matuƙar burge Salim, fuskarsa ɗauke da fara'a ya ce "Allah ya sa mu a danshinku Amaryar Ali, wallahi wayar nan ta yi kyau, inda kina gida ne kika same ta ai ni garwasai mihandigarau!!" kasa ce masa komai ta yi sai tsilla ido take yi tana hawaye kamar wadda yake shirin yanka ta. Sai da ya gama ƴan latse latsensa sannan ya miƙa mata yana cewa "Karɓi nan, sai ki riƙe da kyau sabida masu dogon hannu, wallahi yanzu sai ki ji hammatarki tana shan iska, bare dama Mama ta gayyato danginta, kin san a wajensu Rabi'a ta Gada". ita dai ba ta ce komai ba, shi ma bai tsaya sauraren amsarta ba don ya san ba lallai ta ce ba. Ci gaba ta yi da zamanta ba wanda yake bin ta kanta sai dai a shigo a fita ko a leƙo a koma, gajiya ta yi da zaman ta zame ta kwanta, kwanciyarta ke da wuya baccin wahala ya yi awon gaba da ita. gaf da la'asar wayar ta yi ƙara, Salma ta farka a mugun firgice, jikinta har wata irin tsuma yake yi tin daga sama har ƙasa, ga wayar da ƙara sosai tuni ta karaɗe ɗakin. Cikin rawar jiki Salma ta lalubo ta ta ɗauki kiran gami da karawa a kunne, shiru ba magana har ƴan mintuna suka shuɗe, "Assalamu alaiki Salamathh!!!" haɗaɗɗiyar muyarsa ce ta yi nasarar dawo da ita daga ɗan ƙaramin mafarkin da ta tafi, a memakon ta amsa sai ta fara kuka ƙasa-ƙasa, "Ki yi haƙuri ki dena kuka, na san ni me babban laifi ne a bisa hakan ina neman yafiyarki Salamath!, in sha Allah zan sanya ki matuƙar farin ciki, ba zan bari ki zubar da hawaye ba, ba zan barki cikin ƙunci ba, na yi miki wannan Alƙawarin Matatah!!" rintse idanunta ta yi da ƙarfi gami da riƙe kanta da yake sarawa da hannunta guda ɗaya, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" kawai take faɗe tana maimaitawa a cikin ranta, anya kuwa ba mayaudari ba ne?, shi da yake son Leelah me yasa zai Aure ta? kuma har yana nuna kamar dama ita yake so?. "Indai kin yi fushi da ni ki yi haƙuri ki yafe min kar fushinki ya ida tarwatsa Zuciyata, Salamath!! ki ce wani abu don Allah". shiru ne ya ƙara ratsa tsakani kafin ta fizgo muryarta da kyar, "Ban yi fushi da kai ba, ai ba a fushi da Ƙaddara, yin hakan kamar yi da hukuncin Allah ne, kuma kai ba me laifi ba ne a wajena, don haka ba ka buƙatar yafiyata". Sassanyar ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya ce "Na gode da kika ba ni matsayin zama Mijinki, kuma ba ki yi fushi da ni ba sannan ba ki gaza yafe min ba duk da na ɓata miki rai, na gode!, Bari na bar ki ki huta". wurgi ta yi da wayar zuwa gefe ta haɗe kai da gwiwa tana kuka gami da wasu sababbin tunanin. Ana idar da Sallar la'asar DJ ya fara tashi a ƙofar Gidan. Yau Momi ta cika burinta, kamar yadda ta tsara ranar Auren Leelarta sai ta ɗauko DJ. An haɗa mutane a wajen sosai, an sha rawa kamar ba mutuwa. Kan Leelah ya ƙara huruwa kamar balo. bayan Sallar Isha'i jerin gwanon Motocin ɗaukar Amarya suka iso. Amaryar kanta ta shirya bare kuma masu kaita, hakan ya sa ba tare da ɓata lokaci ba aka fara cika Motocin. Ana kan wannan ƙadamin Mota biyu daga ɓangaren Aliyu suka iso suka buƙaci a basu Amarya. Nan fa kallo ya koma sama, kowacce da an tare ta da batun sai ta ce ga fa inda za ta ga Daula ba abinda zai kaita gidan Talaka, musamman da suka san bayan an kai Leelah ɗin daga can za a wuce da su wajen Dinner. Haka Baban Salma da Umma da ita kanta suka dinga kuka, Su kansu ƴan ɗaukar Amaryar sai da suka yi alawadai. Umman Nabila da Salim da Yaya Rahina Yayar Nabila, sai Baba Zuwaira da Nabila su kaɗai aka samu suka Amince da raka Salma Ɗakinta. An sha fama da ita kafin ta yarda ta rabu da Umma Haka aka ɗebesu kwaraf-kwaraf aka nufi Gidan Amarya kowa ransa ba daɗi. Ɓangaren Leelah kuwa wajen zalamar hawa Mota suka ɓata lokacinsu har aka yi gaba da Salma, sai da aka sha fama kafin aka samu suka daidaita, a hakan ma wasu ba su shiga ba duk yawan Motocin sun yi musu kaɗan sai adaidaita sahu suka hau. Su Baba Zuwaira sun daɗe suna yiwa Salma nasihohi da nusarwa musamman akan abinda ya faru na wariya da aka nuna mata sabida Kuɗi, da kuma fannin zamantakewa, sannan suka tafi. Gidan ya rage sai ita kaɗai shiru, gashi ko hasken kirki babu sai ƴar wayarta suka kunna mata suka ajiye. Zuwa yanzu ko kukan ba ta iya yi sai zare ido, ga wani bala'in ciwo da kanta yake yi, tin tana iya gane inda kanta yake har ta dena ganewa sabida bacci ya sace ta. Ƙarfe Goma da Minti ashirin ta farka, cikin nutsuwa ta buɗe idanunta tana ƙarewa ɗakin kallo, hallau dai babu kowa daga ita sai halinta, Zuciyarta ce ta ƙara karyewa ta shiga tambayar kanta anya kuwa Mutanen nan suna da imani?, su sun kawo ta sun jefar kamar Mushe sun yi gaba, shi kuma wanda ya yi silar zuwanta ko alamunsa babu. Yunƙurawa ta yi ta gangaro bakin gado ta zauna gami da doka tagumi tana mayar da numfashi, ɗan baccin da ta yi kanta ya dena ciwo sai dai wata muguwar kasala da ta lulluɓeta. Tana nan zaune tana aikin tunani Khushi ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama, ita ba ma ta san an yi ba bare ta amsa kawai sai jin Mutum ta yi a kanta ana yi mata magana da wani irin yare wanda ba ta san da zamansa a Duniya ba bare ta iya. Hasken da ya karaɗe Ɗakin ne ya bata damar ganin me yin maganar. Khushi kuwa ta yi futu-futu da rai ta ƙi yin Hausa. Tsoro ne ya ƙara ɗarsuwa a Zuciyarta, ido take zarewa Khushi jikinta na rawa, iya kayan da Khushi ɗin ta zaro tana nuna mata kaɗai sun isa razanar da ita. Doguwar riga ce irin ta Amaren ƙasashen Turai, fara tas sai walƙiya da ɗaukar ido take yi, sai mayafi da takalmi da jaka masu irin jikin rigar, wasu mahaukatan Sarƙa Awarwaro da sauransu. Duk da ko a ido Salama ba ta taɓa yin tozali da gold ba ta gane ko ba na gold ba ne sun fi ƙarfin a saka su a jerin waɗanda ta sani. zuwa yanzu ta gama kaiwa maƙurar rashin Yarda da Aliyu, Zuciyarta ta raya mata anya kuwa ba sayar da ita ya yi ba?. Wasu Zafafan hawaye ne suka shiga jerangiya akan kumatunta, Addu'ar neman tsari da sharrin wannan Jar mace ta gabanta ta fara yi, Khushi dai ko gezau ba ta yi ba sai surutu take zubawa hankalinta a sume. Shawarar guduwa ce ta faɗowa Salma, don haka ta tattara hankalinta waje ɗaya ta faki idon Khushi ta miƙe ta zura da gudu. Kwatsam!!!! ta ji ta shige jikin Mutum, gabanta ne ya ƙara faɗuwa rawar jiki da bugun Zuciyarta suka ƙara tsanani. Sai da ta fara ƙoƙarin kufcewa sannan ta lura a rungume take katamau a jikinsa, rintse ido ta yi ta fara jera magiya "Don Allah ku ƙyaleni na tafi!, wallahi ban san me na yi muku ba, don Allah ku yi haƙuri, ni kaɗai Ummata da Babana suka haifa". Kyakkyawar fuskarta ya zubawa ido yana jin tausayinta na ƙara kassara shi, cikin wata irin murya me kama da raɗa ya kira sunanta "Salaamaath!!" cak!!! kukan ya tsaya, tabbas indai ba da aljanu ta yi gamo ba wannan Muryar Aliyu ce, kuma sunan ma shi ta fara jin ya kirata da shi kaf Duniya, wai Salaamaat, ɗago ido ta yi a hankali don tabbatarwa kanta, tana ɗagowa suka haɗa ido ta yi saurin sunkuyar da kanta, wani mugun kwarjini ya yi mata har sai da ta ji kamar ƙasa ta tsage ta shige, ko motsi kasa yi ta yi sai Zuciyarta da ke ta famar tsalle-tsalle. SHARE FISABILILLAH *Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Tuntuɓi Lambar Waya👉🏽 09079885632* *©️INDO* [12/6, 11:45 AM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 16 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *G. W. F* FREE PAGE........... Khushi ya kalla gami da cewa "Shi ne kika zo kika tsorata ta ko??" Dariya ta yi wadda iyakacinta gefen baki sannan ta ce "Don ban yi mata Hausa ba ne ta tsorata". "To ki yi mata Yaren tsohonki mana!!, in banda neman sababi ta ce miki tana ji ne?" "Dama ai tsokanarta nake yi" ta faɗa tana ƴar dariya. Hannunta ya riƙo suka dawo ciki, a bakin Gado ya zaunar da ita sannan shi ma ya zauna, cikin nutsuwa ya ce "Ki shirya mu tafi Gida Salamaath". Mamaki ya ƙara turmushe Salma, to wai nan ɗin Daji ne ba Gida ba?, ta yiwa kanta tambayar da ba ta da amsarta. Khushi ta ce "Ba ka gabatar da ni ba fa". "Okay Sorry" ya faɗa kafin ya mayar da kallonsa kan Salma, "Wannan ita ce Khushi, Ƙanwata ce ita kaɗai na Mallaka duk Duniya, kuma na fi shaƙuwa da ita fiye da kowa, haka kuma ina matuƙar Ƙaunarta, tana da tsokana sosai sai kin yi haƙuri da ita. Ƙasa ta yi da kai tana wasa da yatsun hannunta, kalaman nasa sai yawo suke yi mata a ƙwaƙwalwa, Ta yaya zai nuna mata Baturiya kuma ya ce Ƙanwarsa? ko dai ya ɗauka ta haukace ne??. Khushi ce ta katse mata tunanin, "Ki shirya kar dare ya yi sosai, ni bari na je wajen Irfan, ba zan iya zama a nan ba". Ba Aliyu kaɗai ba har Salma sai da ta raka ta da ido. Ganin jikinta ya ƙara yin sanyi ya sa shi cewa "Share waccan tsarabar Indian don Allah, maza shirya mu wuce jiranmu ake yi". ƙwal-ƙwal ta yi da ido za ta fara kuka, cikin rawar murya ta ce "Ban san ina za ka kai ni ba, don Allah ka ƙyaleni a nan". idanu ya zuba mata kawai ba tare fa ya mayar mata da martani ba. Gabaki ɗaya ta sakankance don har ta ɗauka ma ya ƙyaleta kawai sai ji ta yi ya rungumo ta yana ƙoƙarin zuge zif ɗin rigarta. Da iya ƙarfinta ta fizge jikinta na rawa, "Ka bari zan sa da kaina" ta faɗa tare da fashewa da kuka. "Okay zan je in dawo" ya faɗa tare da tashi ya nufi hanyar fita. Yana fita ta canja kayan cikin sauri don gudun kar ya dawo, iya rigar ta saka ta ture sauran ababen Adon don ta lura ma ba ta san ta ina za ta fara saka su ba, gashi tsoronsu ma take ji. Ba ta daɗe da komawa ta zauna ba ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, kasa amsawa ta yi sai ma ƙasa ta yi da kai tana ficincina idanu, ta rasa me yasa yake yi mata Mugun kwarjini, ko muryarsa ta ji sai ta ji wani iri a jikinta. Ƙarasawa ya yi kusa da ita ba tare da ya ce komai ba ya ɗauki danƙareriyar Sarƙar ya fara ƙoƙarin ɗaura mata, ba ta yi gardama ba don ko motsi kasa yi ta yi har sai da ya gama ɗaura sarƙar sannan ta samu yin ƙwaƙƙwaran numfashi, hannunta ya riƙe ya zura mata awarwaro sannan ya damƙa mata ƴan kunne ya ce ta saka, ba musu ta karɓa ta fara ƙoƙarin saka cikin sanyin jiki. Paayal ya ɗauka gami da durƙusawa ya ɗauki ƙafarta cilak ya ɗora kan cinyarsa ya fara ƙoƙarin ɗaura mata. Kasa saka ɗankunnen ta yi sabida jikinta da yake wata irin hajijiya gabaɗi ɗaya sai ta rasa nutsuwarta sai aikin binsa da ido take yi cikin wani irin yanayi me wuyar fassaruwa, har ya kammala ba ta iya saka ko guda ɗaya ba, ganin ba zai iya jira ba ya sa shi karɓa ya saka mata. Da kansa ya ƙarasa shirya ta sannan ya umarce ta da tashi su tafi, da ta fara gardama sai da ta ga ya ɓata rai tukunna ta saduda ta bi shi. Sai da hantar cikinta ta ƙara yin kuka ganin jerin Motoci sama da goma a layin wai kuma duk ita aka zo ɗauka, ta riga ta saduda an sayar da ita, don dai ba yadda za ta yi ta tsira shi ya sa kawai take bin sa sawu da ƙafa. Sai da ta fara shiga sannan ya rufe ya zagaya kusa da Khushi wadda take ta aikin kuka ya fara rarrashinta. Gabaki ɗaya ya kasa gane kanta, sai kuka take yi ba tare da cikakken dalili ba, tin yana tambayar abinda ke damunta har ya gaji ya fawwala wa Allah. Tin daga waje Gidan ya sha ado, ga haske ta ko'ina. Zare ido kawai take yi gabanta na faɗuwa, ji take kamar ta kurma ihu sai dai ko ta yi ma ba ta da matemaki sai Allah don haka ta ci gaba da jera addu'o'i. Sai da Motocin suka tsaya sannan Aliyu ya fito ya zagayo inda take, buɗe mata murfin ya yi yana cewa "Za ki iya shiga da ƙafarki ko kuma sai na kai ki da kaina??" da sauri ta ce "Zan iya!" gefe ya matsa gami da cewa "To Bismillah" fitowa ta yi cike da tsoro da fargaba, ido ta ci gaba da zazzarewa tana kallon ko'ina, hannunta ya riƙe tare da cewa "Mu je na raka ki!" bin sa ta yi kawai don gudun ta yi gardama ta ji an harbe ta ko a yanka. Abubuwan ado da take ta famar tozali da su tin a hanya suka ƙara rikita lissafinta. Ba ta ƙara ruɗewa ba sai da ta ji Saukar furanni a jikinta ga wata irin hayaniya gami da waƙa suna tashi a cakuɗe. Wani mugun kuka ta saki gami da ƙanƙame hannunsa jiki na rawa, "Don Allah ka mayar da ni wajen su Umma, don Allah kar k......" Katse ta yayi ta hanyar sungumarta ya rungumeta cikin ƙirjinsa, sai buɗe ido ta yi ta ganta a tsakiyar Mutane ya direta, su kuwa duk idanunsu na kanta, ita dai ta ga sai fara'a suke yi suna surutu amma ba ta san me suke cewa ba, shi kuwa Aliyu ta ga sai dariya yake yi. "Barka da zuwa Ƴata!" wata Mata ta faɗa cikin sakin fuska, ta ɗan ji daɗi don ko babu komai ta samu me irin Yarenta. Aliyu ya ce "Wannan ita ce Mama Aminatu, Ƙanwar Bhabana ce." Ta ji shi amma sam ba ta fahimci inda ya dosa ba, sai ƴan ƙusha-ƙushin kukanta take yi. Mama Aminatu ta kama hannunta tana cewa "Tawo Mu je ki ga Dangi". kam!! ta riƙe hannunsa tana binsa da kallo alamar dai ba za ta bar shi ta bi wata ba. Mama Aminatu ta yi dariya gami da cewa "Kai kaɗai ta sani Aliyu!, ka zo mu je tare". Amsawa ya yi sannan ya bi bayansu, Mama Aminatu tana jan ta ita kuma tana jan shi. Tin daga kan Mutanen da suke kurkusa har na lungu da saƙo sai da suka bi suka gaisar sannan Mama Aminatu ta zaunar da ita kan wata lafiyayyar sofa. Duk yadda ta kai ga maƙale masa sai da ya sulleɓe ya barta da Mutanen da take matuƙar tsoro, don ma ta ji wasu suna yin Hausa gashi sun ƙi ƙyale ta sai famar yi mata magana suke yi. Tana nan zaune suka dawo suka ƙara salgafarta wai za ta gaisar da Uwar Miji. Sai da suka fita babban Falo suka ci burki da ita tare da nuna mata jerin Mata sun kai su Goma ko fi duk fuskarsu a lulluɓe sai idanunsu kaɗai ake gani, suka ƙara mata da bayanin ta zaɓi Uwar Mijin nata a ciki, sannan duk wadda ta zaɓa za ta je ne ta durƙusa a gabanta. To fa!!!! ana dara ga dare ya yi.............. sai yanzu ta ƙara tabbatarwa ta ga rayuwa ganin idonta, to yanzu a cikin Mutanen nan kowacce fuskarta a rufe ta yaya za ta iya gane Uwar Mijin? ko ƴar canke-canke za ta yi?? Umma Aisha ce ta ƙwarara mata gwiwa gami da kwantar mata da hankali. Duk inda ta juya sai ta ga kowa ita yake kallo har shi kansa Gogan nata, yana tsaye cikin Abokansa wanda duk kusan kansu ɗaya sai dai akwai Hausawa Akwai Indiawa har da Turawa, da ya kalleta sai ya tuntsire da dariya don ba ƙaramin tsinka masa malejin daɗinsa take yi ba in ya ga tana firgicewar nan. Alamu sun gama nuna mata kowa ita yake jira ya ga gudun ruwanta. Umma Aisha ce ta yi mata jagoranci don ta fi samun ƙwarin gwiwa sai dai duk da hakan ba sauƙi sai ma ƙara burkicewa da ta yi. Ta lura indai ba ta yi abinda suke so ba yau fa ba lallai su bar ta ta yi bacci ba don haka ta yanke hukunci zaɓa ko a mutu ko a yi rai. Akan ta farko ta fara tare da Addu'ar Allah ya sa daga haka shi kenan. Ji ta yi an fara yi mata dariya har ita kanta Matar da take tsugunne a gabanta, dafe kai ta yi ta fashe da wani mugun kuka kamar ta yi karo da Mutuwa har shirin shiɗewa take yi. Umma Aisha ta fara rarrashinta gami da nuna mata hakan fa ba komai ba ne. Mama Aminatu ce ta ƙaraso wajen tana cewa "Ke bar min Ƴa ta huta, yanzu dare ya yi ma sai a raka wa gobe, ta gaji da yawa ta je ta yi bacci." Umma Aisha ta ce "Allah ya kaimu, ni ma hakan nake shirin cewa". Hannunta ta kama ta ja ta zuwa wajen da su Roshan suke tsaye, hannunsa ta kama ta damƙa masa na Salma tana cewa "Ga ta nan, maza ka je ka rarrashe ta, gobe in Allah ya kaimu sai a ci gaba". ƙasa ya yi da kai ba tare da ya ce komai ba. Su kuwa suka yi masa banza suka juya. Irfan ne ya talle masa ƙeya yana cewa "Ɗan iska da kana jin Kunyar kuma ka tattagi Auren?" kafin ya yi magana Muzaffar ya ce "Amarya gaskiya kin bayar da Mata wallahi, sai ka ce an kawo ki cikin Aljanu?" Mohseen ya yi magana cikin Hausarsa irin ta ƴan koyo, "Shi bai sani mu ba". Dariya suka sa har da Aliyu, kallonsa ya yi kafin ya yi magana cikin harshen Hindi "Meraa Patnee ladhki hai, ladhka nahi" Dariya ya yi yana cewa "Oh Achcha!" Irfan ya ce "Mutum ne da naci wai shi a dole sai ya iya Hausa." duk da Mohsin ba wani gama sanin abinda ya ce ya yi ba ya san da shi yake don haka ya zuba masa harara. Aliyu dai jan hannun Salma wadda ke ta famar ɓurari ya yi yana cewa "Tumhaarie raat achchee beete". "Roshan Bhae!!" Saima ta ƙwala masa kira, tsayawa ya yi kallonta ba tare da ya amsa ba, cikin yanayinta na rawar kai ta ce "Aapka patnee bahut sundhar hai". ya murmusa tare da cewa "Danyavaadh" za ta ƙara wani bayanin ya yi saurin yin gaba, ta bi bayansa da harara tana murguɗa baki. Sai da suka dangana da bedroom sannan ya saki hannunta yana cewa "Matsoraciya kawai, Sai iyayi kamar gaske ashe duk Damisar takarda ce". Cikin shashshekar kuka ta ce "Ai dai ni ba ka ce min za ka kawo ni nan ba, kuma ai ka ce mana kai ba me kuɗi ba ne, Ni dai don Allah kar ka sayar da ni ka ga ni nake temakawa su Umma" ta ƙarasa maganar cike da tausayin kanta. Tuntsirewa ya yi da dariya sai da ya yi me isarsa sannan ya ce "Ki kwanta ki yi bacci in Allah ya kaimu gobe sai in yi miki bayani". Gefe ta nema ta zauna ta ci gaba da kukanta don ba ta jin za ta iya yin bacci a wannan Gidan da ba ta da tabbacin na Mutane ne ko na Aljanu. Har ya watso ruwa ya fito tana nan zaune tana kuka, banza ya yi mata ya yi shirin bacci sannan ya kwanta ba tare da ya ƙara bi ta kanta ba. Sun ɗebi lokaci a haka ba tare da ta gaji da kukan ba, tashi ya yi ya zauna dafa'an don kuwa ta hana shi rintse ido ma bare ya yi baccin, "Ki yi min shiru don Allah, in ba za ki iya yin baccin ba ki bar ni na yi". banza ta yi masa kuma ba alamun za ta dena ɗin. "Kin san Allah na fi ki lalaci, idan na fara nawa kukan ba wanda zai iya rarrashina, gwara ma ki yi min shiru ". "Ni dai ka mayar da ni gida" ta faɗa tana ƙara ɓarke wani sabon kukan. Zazzafar iska ya furzar kafin ya ce "Ba dai Dangina kike tsoro ba??, ai kuwa indai ba za ki yi min shiru ba zan ɗauke ki na kai musu, kuma kin san Allah ba za ki ƙara ganina ba ma". Cikin sauri ta fara ƙoƙarin haɗiye kukan sabida jin abinda ya faɗa, da so samu ne ma kar idonta ya ƙara gane mata su bare har ya je ya jefar da ita a wajensu, gashi da alamu zai iya aikatawa ba tare da ya tausaya mata ba. Tini ta gimtse kukan ta kama kanta ta haɗe tsokar jikinta, sai rarraba idanu take yi tana sauke ajiyar Zuciya. "Na gode Allah" ya faɗa a cikin ransa, ƙara haɗe fuska ya yi murtuk! ya dubeta ba alamun wasa ya ce "Taso ki kwanta!'' sum-sum ta tashi ba tare da musu ba, a gefen gadon ta raɓe ta kwanta gami da takure jikinta tsam!!. "O'o !! Allah buwayi gagara misali!" ya faɗa tare da riƙe haɓa cike da mamakinta, inda bai sani ba tsaf zai rantse ba daga Gidan su Leelah ta fito ba don ɗabi'unta da yawa sun bambanta da nasu. Zamewa ya yi ya kwanta yana bin bayanta da ido Zuciyarsa cike da saƙe-saƙe kala daban-daban. Dukkansu ba su san lokacin da bacci ya yi awon gaba da su ba. Kiran Sallah da ake yi ne ya sa ta farka, tana buɗe idonta ta ganta a wani baƙon wuri gabanta ya yanke ya faɗi, a take abubuwan da suka faru suka shiga fawo mata, "Subhanallah" ta faɗa tana ƙara wararo idanu, "Ni kuwa yau wane irin bacci na yi haka ban san inda kaina yake ba?" ta jefawa kanta tambayar cike da mamaki. Tashi ta yi ta zauna tana tuna ashe fa wai ba ita kaɗai ce a ɗakin ba, dube-dube ta fara yi amma fayau ba kowa, mamaki ne ya ƙara kama ta ganinta a tsakiyar Gadon har da wani ƙaton bargo da aka jibga mata, takaici ya lulluɓeta kamar ta yi kuka. Zaman karanta wasiƙar Jakin ɓata lokaci ne don haka ta sauka ta nufi banɗaki. SHARE FISABILILLAH *Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Tuntuɓi Lambar Waya👉🏽 09079885632* *©️INDO*[12/7, 8:51 PM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 17 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *GORGEOUS WRITER'S FORUM* FREE PAGE........... Tinda ta idar da Sallah ta yi Addu'o'i ta koma ta kwanta bata ƙara sanin inda kanta yake ba har sai ƙarfe goma na safe. Da ƙyar ta iya tashi, gabaki ɗaya jikinta duk ya mutu. Ta zo sauka daga kan gadon ta ci karo da kaya, ɗauka ta yi ta fara warwarewa, Atamfa ce me matuƙar tsada ɗinkin riga da zani, rigar ta sha kwalliya kuma ta tsaya tsam!, sai mayafinta da takalmi. Ture su ta yi gefe ta nufi toilet Zuciyarta cike da tambayoyi. Leelah sai bayan ta fitar da ran za ta ga Haydar sai gashi kwatsam, lokacin har ta yi nisa a bacci. Sosai ta yi farin ciki da ganinsa ko ba komai ya goge duk wani zarginsa da Zuciyarta ta fara yi. Da yake gwani ne a Gado cikin sauƙi ya samu kanta tare da siye duk ilahirin Zuciyarta, sai yau ta ƙara jin wani mugun sahihin sonsa ya kamata. Kwana suka yi suna karkashe love har gaf da asbahi sannan suka samu rintsawa. Da yake dukkansu ba damuwa suka yi da Sallah a kan lokaci ba ba wanda ya farka har garin Allah ya waye. Tinda Haydar ya ɗaskwara wanka ya fice daga Gidan ba ta ƙara jin Ɗuriyarsa ba, ita kaɗai take ta zazzare ido sai Ƴan Aiki da suke temaka mata. Tin Safiyar Momi ke ta famar kiranta tana shaida mata su wance da wance ma za su zo, su Sumayya ma sun kira ta ya fi gaban a ƙirga. Tin tana ɗoki har suka fara bata haushi don ta lura gayya za su yo mata irin ta jiya, da masu aji da marasa aji kowa zuwa zai yi, ita kuwa hakan zubar mata da Mutunci ne a idon Dangin Miji, a cewarta. Zama ta yi dirshan tana tunanin irin Wankan kece rainin da za ta yi don ta nunawa kowa ta wuce tsara, wani dakakken Less baƙi me adon fulawoyi Orange ɗinkin doguwar riga Bubu an yi masa adon beads work tin daga sama har ƙasa, shi kaɗai hankalinta ya fi kwanciya da shi don haka ta ɗauka ta mafa ta cokara ɗaurin ture ka ga tsiya ta koma ta ƙyafe kan Sofa tana danna tafkekiyar wayarta. Ba ta daɗe da gama shiryawa ba Aliyu ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, ƙasa-ƙasa ta amsa tare da yin ƙasa da kai. sanye yake da shadda Fara ƙal! ɗinkin kayan ciki da babbar riga wadda ta sha aiki Aska Tara, ya ɗora hula Miyaram, sai zuba ƙamshi yake yi. A kusa da ita ya zauna yana ƙare mata kallo, "Kin yi kyau fa sosai Salamaath!" ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi, ɗan kallonsa ta yi ta mayar da kai ƙasa gami da cewa "Ina kwana!" "Lafiya lau, ina kwana!" ya faɗa cikin sigar zolaya, turo baki kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba. Shiru ne ya ɗan ratsa tsakani kafin Aliyu ya ce "Sai kika gan ki a baƙon wuri ko?" gyaɗa kai ta yi alamar "E" ya ci gaba da cewa "Nan shi ne Gidanmu, waɗanda kika gani kuma Dangina ne na India da kuma na Nigeria, sai kuma Abokan Kasuwancin Iyayena da suka halacci Bikinmu, dukkansu ba bare ba ne; Maganar gaskiya ni ne Aliyu Almustafa Naira, wasu kuma suna kirana Aliyu Me Sanyi". cikin mamaki ta waro ido tana kallonsa cike da son ƙarin bayani, "To idan kai ne Aliyu Almustafa Naira shi kuma wanda ya Auri Ƙanwata fa??, kuma me ya sa ba ka faɗa mana tin farko ba?, me yasa kuma ka aureni bayan Laila kake so?" Tiryan-tiryan ya bata labari tin daga haɗuwarsu da Leelah har burin da yake son cimmawa a kanta, bai tsaya iya nan ba sai da ya sanar mata asalin gaskiyar Aurensu me wa'adi ne, da zarar Haydar ya rabu da Leelah zai sake ta ya Auri Leelan. Hakan daɗi ya yi mata sosai don kuwa gani take kamar ta ci Amanar Leelah ne da ta Auri wanda yake sonta, bayan haka kuma sam Aliyun bai yi mata ba, ta tabbatar ta girme shi ko da ƴan watanni ne, a ganinta kamar faɗuwa ce ta Auri ƙaninta, da ta ji za su rabu kuwa sai ta yi murna tuni ta saki ranta ta dena jeranta shi da Mijinta har da cewa ya dinga kiranta Aunty. "Af! na manta fa ba ki ci komai ba, ke kuma ba ki yi magana ba, ki tashi mu je ki karya". noƙe kafaɗa ta yi gami da cewa "A'a" "Okay bari na sa a kawo miki" shiru ta yi masa ta ci gaba da zazzare ido tana sa ran t ɗa ga ya tashi, shi kuwa ko niyya bai yi ba sai ma danne-dannen waya da yake yi. Zaman kurame suka ci gaba da yi har shuɗewar ɗan lokaci Ƙwanƙwasa Ƙofa aka yi tare da yin sallama, Salama ta zazzaro ido tana kallon Ƙofar gabanta na faɗuwa, magana kawai ta ji ya yi sai dai ba ta san me ya ce ba sai gani ta yi an buɗe Ƙofar an shigo. Ƴan Mata ne guda biyu dukkansu suna ɗauke da tray wanda aka cika su da tarkace iri daban-daban, kallonsa ta yi a ranta tana ayyana anya kuwa wannan Aliyun bai haɗa iri da Aljanu ba?. Bayan sun dire tray ɗin ɗaya a ciki wadda take bahaushiya ta ce "Yallaɓai Maa tana nemanka, Aunty Khushi ce sai kuka take yi ta ƙi cin Abinci." ido ya zubawa Budurwar Zuciyarsa na wani mugun tsalle, da kyar ya daidaita nutsuwarsa ya ce "Shi kenan!" Ɗan rissinawa suka yi kafin su fice cikin sauri. "Wai da gaske Ƙanwarka ce??" Har ya yunƙura da nufin tashi ya koma ya zauna sabida jin abinda ta faɗa, tsira mata idanu ya yi cikin mamakin jin tambayar ta-ta, "Kenan ba ki yarda da ni ba?". idanunta ne suka ƙara girma ta yi saurin sa hannu ta rufe bakinta, sam ba ta san lokacin da maganar ta fito ba, a cikin ranta take ta jujjuya ta amma sabida ta damu da sani har tana yin suɓul da baka, girgiza kai ta yi a kunyace ta ce "A'a na yarda, gani na yi kai Kalar Hausawa ne". "Oh! ni da Bhaba nake kama ita kuma sai ta kwaso Dangin Umman mu na India, kuma don dai kallon tsoro kika yi mata amma muna kama sosai". gyaɗa kai ta yi ba tare da ta ce komai ba, miƙewa ya yi tare da cewa "Yanzu zan iya tafiya ko akwai wata Tambayar??" girgiza kai ta sake yi, ya ce "Okay" tare da nufar hanyar fita. Tana kammala Karyawa ta lalubo ƴar wayarta ta shiga Kiran Lambar Umma, sai da ta yi kira huɗu ba amsa sai a na Biyar ɗin Umma ta ɗauka bakinta ɗauke da sallama, ajiyar Zuciya ta sauke kafin ta ce "Wallahi duk na shiga damuwa Umma ina ta kira na ji shiru". Umma ta murmusa gami da cewa "Kin san sha'ani Salama Wayar tana cikin tarkace sai da ƙyar ma aka gano ta yanzun". "Yawwa to, ina kwana" "Lafiya lau, ya kuka kwana?" "Lafiya ƙalau, Am... Umma ina Salim da sauran Mutanen?" "Duk suna nan lafiya" "To wai ba wanda zai zo min ne? " "A'a ai ko kowa bai zo ba su Umman Nabila za su zo tinda ya zame musu dole" washe baki ta yi tana faɗin "Yawwa na ji daɗi, a gaishe min da su". "In sha Allahu" ta faɗa tare da kashe wayar. Ajiye wayar ta yi a gefe sai washe baki take yi, duk ta ɗauka babu wanda za ta gani yau don haka duk ta tashi hankalinta. Aliyu ne ya yi sallama ta amsa murya ƙasa-ƙasa, ƙarasowa ya yi yana cewa "Kin gama ko?" ta gyaɗa kai, "Okay tashi mu je ki Gaisa da Mutane" lokaci guda jikinta ya yi sanyi ta yi tsumu-tsumu tana rarraba ido kamar an jiƙa Ɓera, jin shiru ya sa shi cewa "Kina da matsalar Kunne ne?" Da sauri ta girgiza kai cikin rawar baki ta ce "Amm... dama....dama.... ina son ce maka su Umman Nabila za su zo". "Baƙi za ki yi??" ya faɗa yana zaro ido, gyaɗa kai ta yi tana cewa "Na kira Umma na tambaye ta shine ta ce za su zo". "Kenan fa dole ki koma inda suka ajiye ki Jiya, kuma gashi nan ma wani Bikin Muke yi, amma bari na tambayi Maa na ji ko za ta yarda a Ɗauke ki" marairaicewa ta yi kamar za ta fashe da kuka ta ce "Don Allah ka mayar da ni can, ina so in ga Ƴan Uwana". ƴar dariya ya yi kafin ya ce "Bayan na iya yau ne za ki gansu? gobe fa ba lallai ba." kasa cewa komai ta yi don ta san ya fi ta gaskiya, ta yi ƙasa da kai tana jiran ƙiris ta kama kuka. Sai da ya yi zama dafa'an ya rarrasheta sannan ta yarda ta bi shi don ta kwashi Gaisuwa. Suna kammala Gaisawa ya rakice ta suka koma Gidan Jiya. Salma murna kamar ta dinga tsalle tana faɗuwa ita kaɗai, suna zuwa ta fara aikin share-share da goge-goge kamar wadda aka sakawa batiri. Shi dai yana daga gefe ya zuba mata ido yana kallon ikon Allah, yadda take ta fara'a ita kaɗai ya yi matuƙar tafiya da hankalinsa, da farko danne-dannen waya yake yi daga baya sai ya mayar da ita abar kallonsa yana yi yana murmusawa. Sai da ta gama sannan ta dawo ta zauna ko hutawa ba ta yi ba ta ce "Yanzu Girki zan ɗora" dariya abin ya ba shi don haka ya yi kayarsa sannan ya ce "Ba kya gajiya ne?, ki bari za a kawo komai" "Ni dai na fi so in yi da kaina" "Af! kin fi ni gaskiya, ashe fa a nan ba a matsayin Aliyuna nake ba ko?, to yanzu menene me ɗan sauƙi-sauƙi?" "Ni kam ko meye ma zan iya yi" "Oh! ba haka ba, ina nufin menene wanda za a yi ba tare da kowa ya yi tunanin komai ba??" langaɓar da kai ta yi gami da cewa "A yi shinkafa da wake kawai" "Kai! haba dai gwara dai a yi shinkafa da Miya ko?" ya faɗa yana dariya, ɗan murmusawa ta yi ta ce "E" "To akan me za a yi Girkin ko sai an sayo Gas?" girgiza kai ta yi ta ce "A'a Umman Nabila ta sayo min Kurfeto na Alminiyam kawai da shi zan yi, yanzu dai Gawayi za ka sayo kawai, sai Kayan Miya da sauransu". "To, amma lissafa min duk abinda zan sayo kar in yi miki shirme" dariya ta yi gami da cewa ''Ko a rubuta maka ne?" "Ke! Duk girman kan nan nawa sai na kasa riƙe wasu ƴan tarkace?, faɗa min kawai". Lissafa masa ta yi sannan ya kama hanya. Sai da ya sha wuya kafin ya gama sayo komai don duk bai san inda zai dosa ya same su ba sai da ya haɗa da tambaya. Koda ya dawo sai ya yi ruwa ya yi tsaki akan shi zai yi Girkin wutar ma shi zai kunna, tinda ta ga ya nace ta sakar masa ta koma gefe ta zuba masa ababen ganinta. Waje ya fita ya tarkato ledoji ya jibga akan Gawayin, yana shirin ƙyasta Ashana Salma ta dakatar da shi da cewa "Ba fa haka ake yi ba ka bari in kunna" "Ke na fa fi ki iyawa, tashi ki tafi ɗaki ki kwanta, in ba haka ba hana ni aikina za ki yi." Ba musu ta tashi ta koma ɗaki ta mimmiƙe, da yake a gajiye take ba wahala kuwa bacci ya yi awon gaba da ita. Ya yi sa'ar gawayin irin na Ƙiryar nan ne me wuyar kamawa, Ledojin da ya ɗebo sai da suka ƙone tas! wutar ba ta kama ba. Fita ya yi ya ƙara tattaro kan wasu ya zuba ya cinna musu wuta su ma suka ƙone ba labarin kamawa. Haka ya ƙara fita ya lalubo sai da ƙyar ya samu ba yawa sabida duk ya gama kwashe su. su ɗin ma ba sa'a don gawayin baƙi ƙirin da shi sai zafi da ya ɗauka. Kamar zai fashe da kuka ya kuma fita ya tarkato Yayi da Kwalaye, kamar ɗan bolaji shi ne har Wasu layikan, sai da ya tattaro da yawa sannan ya dawo ya zauna ya ci gaba da basu wuta, nan fa tuƙuƙi da hayaƙi da ƙauri suka ce salama alekum. Haka nan ya daddaure yana hawaye yana sharcewa yana tari yana komai ya ci gaba da azalzala Wuta. https://chat.whatsapp.com/EOb68TVK8Ki2ybe4h3ncyx Assalamu alaikum. ina mai so ta ga tayi ƙiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 💃🏽💃🏽💃🏽😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau. ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakkiyar Mace ❤️ina maza da basa cin abinci, ina maza masuso suyi kiba ina yara da basu da kiba..... ina farin cikin sanar daku *ZUMAR ƘIBA*, zuma ce wadda zata saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam. Hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza.. WhatsApp no 07044450136 "Salama Alaikum, Farar Mace Alkyabbar Mata, Barbela me Fari daga Allah, Macen da ake kira Sa'a ba me neman Sa'a ba, duk wanda ya Aureki ya wuce raini!!!!" Salim ne ke maganar yayin da ya kutsa kai cikin Gidan. Turus!! ya tsaya yana kallon Aliyu wanda ya yi wujiga-wujiga idanunsa sun yi ƙulu-ƙulu, fashewa ya yi da dariya gami da cewa "Ikon Allah ba ya ƙarewa a Duniya, yau ga abin mamaki Me Gari Gwauro, Talaka da Mata Huɗu!!!, to kai in ba Karambani ba me ya kai Doki Mahauta??". Aliyu ya ce "Sannu da zuwa, wallahi Wutar ce ta ƙi kamawa". Salim ya ce "To wai kai tsaya!, ina kai ina shiga tsarar Mata?? ko an gaya maka a banza suke girkawa ka ci?, Mace fa ba sa'ar kwaikwayonka ba ce ehe!!!" "Aliyu ya ɗan yi dariya gami da cewa "Gaskiya dai kunna Wutar akwai wahala, na yi zaton zan iya ne, kuma fa na iya kunna wuta don har girki ina yi, kawai dai Gawayin ne ba shi da kyau". Salim ya sa dariya da shewa yana cewa "Ahahahayye!!!! aikin banza harara a duhu, to ai yanzu in kana tunanin da sauƙi sai ka dena, ƙila kai ta icce ka iya kunnawa ka san an ce kowane tsuntsu da Kalar Kukansa, yanzu sai ka tashi ka bawa Mata Filinsu don wannan ba huruminka ba ne kawai dai karambani ne irin na Ƙartai!!". Aliyu zai yi magana sallamar su Umman Nabila ta katse shi, sannu da zuwa ya shiga yi musu cike da girmamawa. Su kansu sun yi mamakin ganinsa a haka amma ba su ce komai ba, gaishe su ya yi suka amsa gami da shigewa ciki. Salim ya ce "To wai kai tana ina??" "Tana ɗaki tana bacci". "To wallahi durƙusa ka ci gaba da kunna Wutar nan a to!, Salama ba ta baccin Rana tinda Allah ya sa yau ta rintsa ba ka isa ka tasheta ba" "To ai inda zan tashe ta da tin kafin ka zo zan tashe ta Ƙanina!" Salim ya taɓe baki gami da cewa ''Hum-um!! wai kai na yi maka kama da Jarirai ne da za ka dinga kirana ƙaninka?, Aunty Salma fa na san ta girmeka kai dai akwai ka da tsaurin Ido, ni daga yau ma Yaya Salim za ka dinga Kirana a to!!" ya ƙarasa maganar tare da buga cinya yana yin fari da ido. Aliyu ya ce "In kana so sai in ce maka Yayan amma fa ka san dai ni Yayanka ne tinda har na zama Mijin Yayarka, ba ka ji ana cewa Kowa Iya ta Aura Baba ne ba?? to ai kamar haka ne". "Cab!! ai kuwa ni ban yarda da wannan izalar da ba Gemun ba" ya faɗa yana mummurguɗa baki. Sokanabe suka ci gaba da yi basu san ma wutar ta kama ba sai daga baya suka lura ta ruru kamar za ta ci babu. Aliyu ya washe baki yana cewa "Da ka ce ban iya ba! gashi yanzu idonka ya gani yadda na kunna ta ko Yayar taka ma albarka" "Hakacin!!!, haka na gani a Jarida, wallahi kawai Arashi ne, Allah dai ya dubi idanunka da suka sha hayaƙin nan suka yi luƙu-luƙu ya bawa Wutar izinin kamawa amma ba don ka iya ba." "Na dai rabaka!, yanzu bakin tsanya ya mutu, in ni ne kai ma ba zan ƙara cewa uffan ba sai bayan kwanaki" Aliyu ya faɗa tare da nufar Kicin don ɗauko Tukunya. https://chat.whatsapp.com/EOb68TVK8Ki2ybe4h3ncyx Assalamu alaikum. ina mai so ta ga tayi ƙiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 💃🏽💃🏽💃🏽😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau. ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakkiyar Mace ❤️ina maza da basa cin abinci, ina maza masuso suyi kiba ina yara da basu da kiba..... ina farin cikin sanar daku *ZUMAR ƘIBA*, zuma ce wadda zata saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam. Hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza.. WhatsApp no 07044450136 SHARE FISABILILLAH *Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Tuntuɓi Lambar Waya👉🏽 09079885632* *©️INDO* [12/10, 7:46 PM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 18 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *GORGEOUS WRITER'S FORUM* FREE PAGE........... "Ke haka ake yi kin bar ɗan Mutane sai azabtuwa yake yi da hayaƙi?? me ya jaza miki bacci yanzu da ranar Allah?" Baba Zuwaira ta faɗa fuska ba alamun wasa. tsilli-tsilli ta yi da ido ta rasa abin cewa, sai yanzu ma ta tuna wai ta bar Aliyu yana shirin kunna wuta. Umman Nabila ta ce "Allah Sarki bawan Allah, gaskiya da alamunsa yana da tausayin Mace, ai ba kowa ne zai zauna kunna miki wuta ke kuma ki yi bacci ba". Yaya Rahina ta ce "Wallahi fa ni ma haka na gani, ke dai da yardar Allah kin samu Miji mai hankali, don haka ki rungumi abinki hannu bibbiyu kar ki bari zigar Mutane ta yi tasiri a kanki, yanzu martabar Ƴa Mace ita ce Gidan Mijinta ba zaman sakarcin da Ake yi a Gudanku ba." Umman Nabila ta watsa mata daƙuwa tana cewa "Uwaki!, ina ruwanki da zamansu, Aure ai sai lokacin ya yi ko?" Baba Zuwaira ta ce "Ke barta ta faɗi gaskiya, ai hakan suke, ni dai na kasa yarda ma da imanin wannan Ƴa Sumayya, dukkansu ma Yaran nan Girarsu a tsaitsaye kamar nonon Namiji". Dariya suka sa Yaya Rahina ta ce "Kina da gaskiya Baba Zuwaira, daɗina da ke fa akwai iya zaro magana!" Ta taɓe baki tana cewa "A to!" Hira suka ci gaba da yi kowa na tofa albarkacin bakinsa, Salma tuni ta sallallaɓa ta fice don ganin Aliyu da Girkin nasa a halin da suke ciki. Suna zaune suna gyaran Kayan Miya shi da Salim ta fito tana ta muzurai, daga gefe ta durƙusa cikin sanyi ta ce "Ka yi haƙuri bacci ne ya kwashe ni". "To ai ni na ce zan yi ko?" "To amma yanzu ka bari in yi, ga Nabila can ma na san za ta taya ni". amsawa ya yi tare da zare jikinsa ya tashi, bayan gajiya dama so yake ya bar musu Gidan don su fi samun damar sararawa. Sallama ya yi mata sannan ya tafi. Salim ya gyara zama yana cewa "Yawwa, gwara da ya tafi ya bamu sarari don wallahi cikina cike yake taf da labarai ko wurin sa Abinci babu". Dariya ta yi tana cewa "Allah Mutumina!! ai gaskiya na ji daɗin ganin ka, ban zata za ka zo ba ai" "Haba dai ke ma kin san ai ni da ke tif da taya ne, Amana ai ta fi ƙarfin wasa, ni wallahi a kan Abin Duniya ba zan ƙi zuwa gidanki in je gidan Leelah ba, Uwar me za ta ba ni?" "Daɗina da kai bakinka ba sakata shi yasa kuke yawan faɗa da Momi" Ta faɗa tana harararsa, taɓe baki ya yi gami da cewa "Ai wallahi na fi ta gaskiya kuma; jiya fa sai ƙarfe ɗaya saura suka dawo Gidan nan, kin ga Inna da Mama yadda suka dawo zani a hannu?, Umma Rakiya sai fyace majina take tana ƙarawa wai AC ya sa ta mura, ni kuwa na ce Allah ya ƙara, wallahi duk haushi suke ba ni, shi ma Shegen Mijin nata mai kama da Guntun Man Kitso, ke ni ai jiya na ga tijara ganin Idona". da sauri Salma ta ce "Kai dena zaginsa don Allah" "To a na me??" ya faɗa yana zaro idanu, "Sabida Yayan Ali....." saurin cin burki ta yi tana zaro ido wuƙi-wuƙi kamar ta yiwa Sarki Ƙarya, "Ƙarasa mana, Ya-ya me??" waskewa ta yi ta ce "Sabida Yayanka ne, sannan kuma sunan su Ɗaya da Mijina". wani farrr!! ya yi da ido kamar wanda aka jonawa wutar lantarki, cike da iyayi da feleƙe ya ce "Wa?! Allah ya huwaɗe ya zama Yayana, ke ni fa wallahi ko Hasan da Usaini muka fito ni da shi ba abinda zai hana ni Zaginsa, Ɗan Butar Duma!!". "To ai sai ka ci gaba ɗan rainin hankali" ya ci gaba da cewa "Oho dai, ina ba ki labari ai burin Mama ya cika su Rabi'a sun yi samari sun fi kala ashirin in gaya miki, shi yasa dama ta shiga ta fita ta fito da su rass!! kar ki ga yadda idanunsu suka ƙara buɗewa wallahi" Salama ta ce "Kai haba!!, ni fa wallahi da ma Auren su suka yi su huta, wai su ba sa tunanin Zalumtar Samarin nan da suke yi Zunubi suke ɗauka?" watsa hannuwa ya yi gami "A to!!!!, ni ma dai abinda nake gani kenan, sai dai mu ce Allah ya kyauta, wai kin san yau ma suna can suna dodon zuwa Gidan Leelah? ai in gaya miki da aka ce za a zo nan yau ma cewa suka yi su fa Gidan Leelah suka nufa, na ce Ala raka taki gona mu dama ba nemansu muke yi ba". murmusawa kawai Salma ta yi ba tare da ta ce komai ba. Ci gaba ya yi da kawo mata labarai wasu ta kula wasu kuma ta yi dariya ko murmushi. Sai yamma Liƙis sai ga su Umma Rakiya tinjin-tinjin tare da Yaya Hasiya da Yaya Badi'a. Ba su wani daɗe ba su Umman Nabila suka tashi tafiya suka rankaya suka bi su. Ita kaɗai ta ci gaba da zazzare ido a Gidan har bayan Magrib sosai sannan Aliyu ya dawo yana zuwa suka wuce ba tare da jira ba. Ƴan Biki tinda suka dawo suke zuba Tijara a kan Leelah ta wulaƙanta su ta yi musu rashin Mutunci, waɗanda suka ƙara kwana a Gidan sai da suka raba dare suna yamaɗiɗi da zancen. Momi sai hura hancika take yi don ita ba ta ga laifin Leelah ba, a cewarta matsayi matsayi ne in aka fi ka an fi ka. Salim kuwa ya yi dariya har ya godewa Allah, duk inda ya zagaya jefar musu magana yake yi, sai da Suka ritsa shi da masifa suka kusa yi masa na jakkai sannan ya haƙura da maganar ya koma gefe ya dinga tuntsira dariya. Yau ma sai da aka raba dare ana kwasar Shagali. Salma tana samun sa'ar cafko Maa aka gama abinda za a yi ta samu ta gudu ta kwanta. Washegari lokacin da ta fito Gidan sai tsirarun Mutane kowa ya san inda dare ya yi masa, abin daɗi ya yi mata duk sai ta ji ta sakayau kamar an cire mata rigar ƙaya. Bayan Kwana Uku. Ko'ina biki ya tashi kowa ya dawo daga shi sai halinsa. Su Momi ma sun dawo isu-isu sai dai yanzu salo ya ƙara canjawa don kowacce jin kanta take yi, ita Momi tana taƙamar Ƴar ta ta Auri me Kuɗi, Mama kuma tana tinƙahon Ƴaƴanta sun yi sabon kamu na Ƴaƴan Masu da shi. Su Sumy kuwa dama abu ne wanda an riga an saba sai dai an ƙara samun ci gaba fiye da Da domin an samu sababbi hanyar nema ta ƙara faɗi. Leelah Duk in gari ya waye ba ta ƙara sanya Haydar a idanunta sai dare ya kuma yi zai dawo ya kalamance ta. Abin yana ɗan damunta amma ta riga ta sa a ranta kawai yana fita ne sabida jama'arsa da kuma Kasuwanci, don haka ba ta tunanin komai. Yau haka kawai ta ƙagu da son ganinsa, ta sha kwalliya kamar ba za a mutu ba, ta gama shirya irin tarbar da za ta yi masa. Tin farkon dare har dare ya miƙa shiru babu shi babu labarinsa, tin ana sha ɗaya shabiya har ɗaya ta yi. In ta kira lambarsa ba ya ɗauka daga baya ma sai ya fara katse kiran, daga ƙarshe sai ya kashe wayar muɗis. Abin ya yi mata ciwon da ta kasa jurewa sai da ta sha kuka sannan bacci ya kwasheta Zuciyarta cike da tunane-tunane masu yawan gaske. https://chat.whatsapp.com/EOb68TVK8Ki2ybe4h3ncyx Assalamu alaikum. ina mai so ta ga tayi ƙiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 💃🏽💃🏽💃🏽😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau. ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakkiyar Mace ❤️ina maza da basa cin abinci, ina maza masuso suyi kiba ina yara da basu da kiba..... ina farin cikin sanar daku *ZUMAR ƘIBA*, zuma ce wadda zata saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam. Hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza.. WhatsApp no 07044450136 Tana zaune a ɗan Madaidaicin Falon dake ɓangaren nasu, ƴar ƙaramar wayarta ce a hannunta tana lallatsawa, a zahiri danne-dannen take yi, a baɗini kuwa ta yi zurfi a tunani. Tinda ta haɗa Alaƙa da Aliyu take wasu irin mafarkai marasa kan gado a kansa da Kuma wasu Mutane wanda a mafarkin kawai ta san Danginsa ne amma ba ta samu damar sanin ko suwaye ba. Jin an tallafo hamarta ya sa ta zazzaro idanu tare da wangame baki za ta zunduma ihu, karon da aka samu tsakanin nasa idanun da nata ne ya sa ta fasa yin ihun suka shiga yiwa juna kallin ƙunta. "Rufe bakin mana ko cinye ni za ki yi??" da sauri ta rufe shi gami da kawar da kanta gefe a ɗan kunyace. "Me kike tunani har ya hana ki jin sallamata?" cikin sanyin murya ta ce "Ba komai!" "Faɗa min!, akwai wani abun gaskiya, ko akwai wani abin da bai yi miki ba a Gidan?, ko kuma zaman Gidan ne bai yi miki ba??" cike da rashin sanin abin yi ta gyaɗa kai sai kuma ta yi saurin cewa "A'a! babu komai fa". "Kin raba min hankali kuma, faɗa min gaskiya. Shiru ne ya ratsa tsakaninsu na ɗan lokaci sannan Salma ta ce "Am...da....dama.. Abbana ya ce....." kasa ƙarasa maganar ta yi don ba ta san ta inda za ta kamo ta ba. Zaman dafa'an ya yi a kan Kafet sannan ya kalleta a nutse ya ce "Ina ji! Abba ya ce menene?" bakinta na harɗewa ta ce "Wai..wai fa... Garar nan da ake yi ce, shi ne yace ku yi haƙuri bai samu damar yi ba amma nan gab....." katseta ya yi bayan ya murmusa ya ce "A kan haka ne kike ta gunguni? ko ma shi ya sa ki tunanin?, abu ne fa wanda bai zama dole ba, ki bar zancen kawai don Allah, ba na raina ba ne amma ki ce ba sai an yi komai ba, ai Maa ta yi duk wani abinda ake buƙata idan kuma akwai saura ki faɗa min ko ki faɗa mata". gyaɗa kai ta yi ba tare da ta ce komai ba. Zura hannu ya yi a Aljihunsa ya zaro wata tamfatsetsiyar Waya ya miƙa mata yana cewa "Karɓi wannan ki dena fama da wannan Burin Ɗan Ga ruwan. kasa karɓa ta yi don kuwa ba ta taɓa yin tozali da irinta ba ma bare har ta zamo mallakinta, girgiza kai ta yi alamar a'a, dariya ya yi yana cewa "Ni fa wallahi da na fara ganinki na zata Jaruma ce kamar Ƴan Uwanki, ke ashe ma komai tsoronsa kike ji!" Murmusawa ta yi gami da cewa "Wai ni ba Yayarka ba ce kake tsokana ta?" "To Yaya yi haƙuri, amma dai ki karɓa Please" "Ba na jin Turanci kuma ka haɗa da shi a cikin maganar" ta faɗa tare da juyo masa ƙeya, "Tinda kika zo Gidan nan kike sa ni dariya, kina so cikina ya yi bindiga ko?" "Ni ban ce ka yi dariya ba ai, kawai neman tsokana ne yake sa ka yi; Ni fa da gaske nake ba zan iya riƙe Wayar nan ba, wannan ta hannuna ta ishe ni". ya lura abin nata da gaske ne don haka ya tattaro duk nutsuwarsa ya ce "Ni kuma da gaske nake da wannan Wayar za ki yi amfani, tinda Allah ya sa kika zamo Matata fa sai kin jure wasu abubuwan don yanzu ma gani nake ba a yi komai ba akan nan gaba, don Allah ki karɓa kafin na fara yi miki kuka". Nazartar lamarin ta yi kafin ta ce "To ajiye a ƙasa" ba musu ya ajiye mata, ɗauka ta yi tana ƙare mata kallo, tsakaninta da babbar waya sai dai ta hanga a hannun su Leelah su Sumayya, tana da tabbacin wannan ba ma tsarar ta su ba ce, to ta yaya za ta iya amfani da ita?. Tunanin da take yi kenan tana jujjuya wayar. Ba ta ankara da ya ɗauke ƴar ƙaramar ba sai ta ga ya miƙo mata Layin ciki. Jiki a sanyaye ta karɓa cike da takaici, ta so ya bar mata ita sai ta dinga ajiye babbar tana amfani da ƙaramar. Zuwa yanzu lamarin Haydar ya gama ɗaure wa Leelah jijiyoyin kanta, cikin kwana Uku sau Ɗaya ta sanya shi a idonta, da ranar Allah ta ga sun fito shi da wata Budurwa sun yi waje, ta tabbata sun ganta su duka amma ko kallonta ba su yi ba. Ya gama kwankwaɗa mata Madarar Mamaki, gashi duk iya nazarinta ta kasa gane abinda yake faruwa, duk ta tsargu sai tufka da warwara take yi. Yau suna zaune a Babban Falo suna Hira Aliyu ya ce ''Bhaba ina son Gida za mu zauna na ɗan lokaci tare da Salma." Bhaba ya jinjina kai gami da cewa "Me ya sa?" "Kawai na ga kamar ba ta sakewa ne a nan" ya faɗa yana kallonta, da sauri ta ɗago kai tana zaro ido cike da mamaki sharrin da ya lafta mata, kashe mata ido ya yi gami da yi mata gwalo. Harara ta danƙara masa har da cije baki, ji take ina ma za ta iya ta shaƙe shi. "Ba gasiya ya faɗa ba ne Ƴata?" Maa ta jefa mata tambayar gami da tsare ta da ƙartan idanunta, ƙasa ta yi da kai tuni kunya ta yi mata Hijabi, ji take dama ƙasa zata tsage ta shige ciki, a ranta kuwa ayyana yadda za su kwaso ta da Aliyu take yi don ba ƙaramin takaici ya bata ba. Bhaba ya ce "me ya sa ba ka faɗa tin wuri ba?, yanzu sai ka zaɓi Gidan da kake so." "Gidanka da aka kammala na ƙarshe a Unguwar Sabon Gida shi nake buƙata" "To fa! ba ka san cewa Yayanka yana cikin Gidan ba?" Bhaba ya faɗa yana kafa masa idanu, Haɗe rai ya yi ya ce "Ni fa na tsara Gidan nan sabida ina son shi, me ya sa shi bai ɗauki wani ba sai shi?, ni kam gaskiya shi kaɗai nake so". "A'a fa Aliyu!! ba na son neman faɗa, ka yi haƙuri ka samu wani, ai akwai wasu Gidajen a Sabon Gidan sai ka ɗauka, ko kuma ka Ɗauka a Tudun Yola" Aliyu zai yi magana Maa ta tari numfashinsa da cewa ''Ka san Aliyu ba ya taɓa neman rigima da wani, hasalima shi Haydar ɗin ne yake nemansa da jaraba Jaan!, lallai ina so a samawa Aliyu abinda yake so". "Amma kin san da kamar wuya in ce masa ya tashi sabida Aliyu zai zauna ko?, dukansu fa Ƴaƴana ne ina buƙatar daidaita tsakaninsu, in na yi hakan tamkar na fifita wani ne na ware wani, kin ga na haddasa musu rigima. Wani ɗan murmushi ta saki kafin ta ce "Nawa ne Gidan naka?, idan na biya ka kuɗinsa ka ga ya dawo ƙarƙashin Ikona ko?" Da sauri Bhaba ya ce "A'ah! wai meke faruwa ne Aliyu?, ni fa na lura akwai wani abinda kuke son ɓoye min kai da Haydar da iyayenku, wata magana take yi me kama da ta Ɗaukar Fansa". Aliyu ya yi ƙasa da kai yana fiƙi-fiƙi da ido, Maa ta ce "Kenan don zan sayawa Ɗana Gida sai ya zama ɗaukar Fansa?, don me ba zan yi masa abinda yake so ba tinda ina da halin yi?" "Ni ma ba halin ne ba ni da shi ba, kawai ba na son tashin hankali, ki nemi wani ki Saya" Yana rufe baki wayarsa ta yi tsuwwa, da yake tana hannunsa bai sha wahalar ganin Alert ɗin ba. Da mamaki ya kalli Maa cikin son ƙarin bayani, "Kuɗin Gidan ne na turo maka, in akwai ƙarin bayani za ka iya yi, daga yau zuwa gobe ina buƙatar a kawo min Takardunsa" tana gama faɗe ta tashi ta basu waje. Bhaba ya ce "Allah ya shirye ki, ni dai sai a yau na taɓa ganin cinikin Dole". Khushi da ke lafe a can gefe tana taune-taune sai lokacin ta bushe da dariya tana faɗin "Bhaba duk gumurzunka a Kasuwanci sai yau ka taɓa Ganin an yi haka??" Dariya ya yi ya ce "Ƴata na ga Cinikayya iri-iri amma sai yau na taɓa ganin irin wannan, na lura ke ma kina goyon bayansu in banda haka da mun shigar da su Kotu". "Allah Sarki Bhaba, na fa san sirrin in gaya maka?" "Faɗi mana ina jin ki. Kusa da shi ta koma ta zauna sannan ta ce "Kawai ka yarda da abinda Roshan yake so ne shi yasa, in banda haka ai za ka iya mayar mata da kuɗinta tinda Takardun suna hannunka". Ba Bhaba kaɗai ba har Salma sai da dariya ta kufce mata, dama ba ta raina abin dariya, kuma ta ɗan kwana biyu ba ta ga an yi comedy ba. https://chat.whatsapp.com/EOb68TVK8Ki2ybe4h3ncyx Assalamu alaikum. ina mai so ta ga tayi ƙiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 💃🏽💃🏽💃🏽😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau. ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakkiyar Mace ❤️ina maza da basa cin abinci, ina maza masuso suyi kiba ina yara da basu da kiba..... ina farin cikin sanar daku *ZUMAR ƘIBA*, zuma ce wadda zata saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam. Hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza.. WhatsApp no 07044450136 *Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Tuntuɓi Lambar Waya👉🏽 09079885632* *©️INDO*[12/12, 11:04 PM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 19 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *GORGEOUS WRITER'S FORUM* FREE PAGE........... Aliyu yana dariya ya ce "Bhaba shi yasa na ce ka fita shirgin wannan Tsarabar Indian, ka ga yanzu nema take ta buɗe muku rufi!!" Bhaba ya ce "Ai gaskiya ta faɗa, shi ya sa nake ji da ita, Ƴar Baiwa ita har ta gane abinda kuka kasa ganewa". Khushi ta ce "Ai na faɗa masa na fi shi Basira ya ƙi yarda, wai cewa ma yake yi Basirata ta cin Chocolate ce". Aliyu ya ce "Molankar banza, in ba cin chocolate ɗin ba me kika iya yi?, kullum Mutum sai tauna kamar Kajin Turai". Bhaba ya ce "Ƴata Salma sai ki yi Alƙalanci ni dai na gaji da raba gardama." dariya ta yi gami da yin ƙasa da kai, murya can ƙasa ta ce "Khushi ta fi shi gaskiya Kuma". Khushi ta sa shewa ta tafa hannu gami da cewa "Ka ji magana dai ta fito!!." Bhaba ya miƙe yana cewa "Aliyu in kun gama Muhawarar ka zo zan yi magana da kai". Da sauri Khushi ta riƙe hannunsa tana cewa "Bhaba Baitho, meri baat suno please, ina da magana" Komawa ya yi ya zauna gami da cewa "Main tumhari baat sun rahi hoo Beti". Ido Aliyu ya zuba mata baki a buɗe, yadda ya ga tana mutsil-mutsil da ido ya sa ya sha jinin jikinsa, da alama wata katoɓarar za ta ɗirka. cikin ɗan rawar baki ta ce "Bhaba!... Mammi Ƙanwarka.... me ya sa ba kwa tar........" saurin katse ta ya yi fuska a murtuke ya ce "Kul!! kar na ƙara jin zancenta a bakinki in ba haka ba za ki fuskanci fushina". bai jira cewarta ba ya bar wurin faa!!!! cike da takaici da mamakin tambayar. https://chat.whatsapp.com/EOb68TVK8Ki2ybe4h3ncyx Idanunta da suka kawo ruwa ta zubawa Aliyu wanda ya zama kamar sassaƙaƙƙe sabida kallonta, "Rosha....." saurin katse ta ya yi da cewa "Kar ki gaya min komai; in da Maa kika yiwa wannan tambayar sai ta hamɓare miki fuska ma, wallahi ni dai kar ki sake ki jefa ni a Uku, na gaya miki". Zafafan hawayen da ke yawo saman ƙwayar idanunta suka fara sukuwar saukowa ƙasa, cike da tausayin kanta ta ce "To wai me ya sa haka?, Azaan fa....." Cike da takaici ya ce "Wai ban ce ki bar ambaton sunansa ba??, na ce ki bari zan yi maganin matsalar kin ƙi ji sai nemo mana wata kike yi." Tashi ta yi tare da cewa "To na dena ka yi haƙuri" tana gama faɗe ta fallatsa da gudu ta yi ciki, da ido ya raka ta Zuciyarsa cike taf! da tausayinta, ɗan ƙaramin tsaki ya yi gami da cewa "Sai afkin ba wa Mutum haƙuri". Salma ta ce "Kuma in ba ta bayar ba a ce ta yi laifi ko?". "Ke ma can da yawarki, ai bakinku ɗaya dole ki ce haka" ya faɗa tare da zamewa ya kwanta. Shiru ta yi masa sai ma Tashi ta yi ta koma ɓangarensu tana tunani akan lamarin nasu, ita dai jikinta yana ba ta akwai wani abu a ƙasa tsakanin dangatakarsu, da yake abin ba huruminta ba ne sai ta manta da su ta ci gaba da sabgoginta. Leelah na zaune kan Sofa ta harɗe ƙafa tana danne-dannen Waya, sam hankalinta ba ya jikinta ta yi nisa cikin Duniyar Tunanin Haydar. Ba ta ji motsin kowa ba bare Sallama sai ganin Mace ta yi a kanta tana takawa ɗaya bayan ɗaya gami da bin ta da wani kallo irin na raini. Cikin mamaki ta bi Alina da ido Zuciyarta na bugawa, kallo ɗaya ta yi mata ta fahimci akwai zallar ƙwarewar bariki a tare da ita. Alina ta katse mata tunanin da cewa "Ke ce Matar Haydar ɗin??" a wani yatsine ta yi maganar kamar wadda ta tauna Kashi. Leelah ta ɗan numfasa kafin ta ce "Ni ce me ya faru??" wata shegiyar dariya ta saka wadda ta sa Leelah ta fara raina kanta, "Ga ki kyakkyawa!, amma fa na yi tunanin zan ga wata Babbar Shegiya ashe ba haka ba ne, To ke me kike da shi da kike tunanin za ki iya jan ra'ayinsa bare har ki mallaki Zuciyarsa??" ta yi tambayar tana bin ta da kallon shaƙeƙe, mamaki da Al'ajabi sun cikawa Leelah ciki taf!!, ta lura ba ƙaramar ƴar rainin hankali ba ce kuma in ta sakar mata yanzu za ta tsinka ta don haka ta tattaro duk jarumtar ta ta ce "Abin da ya gani ya kamu da sona da shi zan ja hankalinsa, wai don Allah wacece ke ma?? na ganki wani yare-yare da ke ke ba kyau da kama ba amma sai wani mole baki kike yi kamar an taka Ayaba". Kalmar ta yiwa Alina ciwo matuƙa, har ita wannan ƴar talakawan ƴar matsiyata za ta gaya wa maganar banza?, numfasawa ta yi kafin ta ce "Ban ga alamar kina da wani abin burgewa ba tinda kika kasa rufe Satin Amarci da Mijinki ba tare da ya fita neman Mata ba, sunana Alina, wadda take samar wa Haydar farin ciki ba dare ba rana, wadda ta zamo masa inuwa kuma Ƙoramar duk abinda yake buƙata." dum!!! dum!!! dum!!!!! bugun Zuciyar Leelah,,,, tashin hankali faɗa da me gari ran sallah, baki ba zai iya furta irin razani da firgicin da ta faɗa ba, "Kar dai tunanin da nake yi a kan Haydar ya zama gaskiya, kar dai da gaske Haydar Mazinaci ne Fasiƙi" abinda Zuciyarta ke saƙawa kenan, firgicewar da ta yi ta haifar mata da rawar jiki gabaki ɗaya bakinta ya kulle ta rasa abin da za ta furta. Alina ta lura da kiɗimewar da ta yi don haka ta saki wata ƴar dariya ta shu'umanci ranta fes!!, wani ƙyal-ƙyal !! ta yi da ido gami da hura hanci ta shaƙi iska gami da ƙamshin da ke tashi a falon ta busar sannan ta ce "Bakin Rijiya ba wurin Wasan Makaho ba ne Ƴar matsiyata!!, a ganina kuskure kika yi na Auren Haydar, kuma har kina tunanin yana sonki, hmm! za ki gane Kurenki" Kamar wadda aka sassaƙa aka dasa a wajen haka Leelah ta zama, sai ido kawai take iya gwalalawa Alina Zuciyarta na tartsatsi tamkar ana kyakketa ta da Reza. Haydar ne ya shigo fakam-fakam yana tafiya kamar wanda ake hankaɗowa bai iya sallama ba don haka bai tsaya yin ta ba ya ƙaraso kan Leelah ya tsaya ƙerere ! sai huci yake yi tamkar garwashin da aka watsawa Ruwa. "Maza ki tattara kayanki zan aiko a ɗauke ki, barin Gidan nan za mu yi!!" ya faɗa a fusace tamkar ita ta yi masa laifin. Wani sabon tashin hankalin, indai ba gizo kunnenta ya yi mata ba ji ta yi ya ce barin gidan za su yi, wannan wace irin masifa ce??, idanunta da suka fara yaji da suya ta zuba masa cike da son ƙarin bayani, tana son tambayarsa amma ta kasa. Muguwar Kibiya me ɗauke da dafin Azaba gami da Kishi ta soki ƙahon Zuciyarta har sai da ta zabura, Zuciyarta ta dena harbawa na wucin gadi. Ba komai ne ya jawo mata ba face ganin Alina a cikin Ƙirjin Haydar tana wani irin kuka me tsuma Zuciya gami da rikita lissafin me sauraronsa. Hankali tashe ya fara tambayarta abinda ya faru, ƙara ƙanƙame shi ta yi cikin shashshekar kuka ta ba shi labarin Leelah ta yi mata Zagin tsamar nama, har da gori da goruba. https://chat.whatsapp.com/EOb68TVK8Ki2ybe4h3ncyx Assalamu alaikum. ina mai so ta ga tayi ƙiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 💃🏽💃🏽💃🏽😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau. ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakkiyar Mace ❤️ina maza da basa cin abinci, ina maza masuso suyi kiba ina yara da basu da kiba..... ina farin cikin sanar daku *ZUMAR ƘIBA*, zuma ce wadda zata saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam. Hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza.. WhatsApp no 07044450136 Tamkar Zakin da ya shekara Biyar bai ci komai ba sai yau ya yi Tozali da nama haka ya nufi kan Leelah jikinsa har rawa yake yi, cikin matsanancin tashin hankali ta miƙe tana yin baya-baya gami da girgiza masa kai, bakinta sai karkarwa yake yi sabida son furta kalami amma ko ɗaya ya kasa fitowa, cikin zafin nafa ya kwarfa mata wani azababben mari kafin ta gane inda kanta yake ya ƙara sakar mata mahangurɓa wato marin bayan hannu. Wani azzalumin duhu ne ya mamaye fitilun dake haska ganinta, kanta ya shiga wata irin hajijiya da taratsi tamkar wanda aka jona wa shocking, yayin da hawayen azaba suka gangaro kan kumatunta ba tare da ta sani ba, gefen bakinta kuwa tuni ya fashe jini ya fara bi-bango. Durƙushewa ta yi kan gwiwoyinta cikin wani irin mawuyacin halin da kimanta shi ma aiki ne. Rufe ido ya yi ya fara zazzago masifa ba ji ba gani Auren Kurma da Makaho, "Har ke kin isa ki ɗagawa wadda na kawo cikin Gidana murya??, har me akai aka yi ki?? uban me gareki da har kike tunanin yin Kishina??, a tunaninki wata tsiyar na gani ta burgeni a jikinki da ta sa na aureki? uban me kike da uban me za ki iya ba ni da har za ki ciwa wadda take min komai Mutunci??, wallahi tallahi akan Ƴan Matana sai na illata miki rayuwa don ban ga abinda zan so a jikinki ba bare har na yi maneji, yanzu sai in tattara ki in kora ki Gidanku Shegiya Ƴar matsiyata!!". Sai yanzu da masifar ta kai masifa ta tuno da ambaton sunan Allah, Innallillahi ta fara jerowa cikin ɗaga murya tamkar wadda ta Taka Mutanen Ɓoye. Tana kallo ya rungumi Alina suka yi ciki, zamewa ta yi ta ƙarasa zama daɓar!!! kamar an juye laka, "Me ya sa za ka yi min haka Haydar??, me ya sa ka yaudareni? me ya sa ka Aureni bayan ka san ba So na kake yi ba?, ina matsayin Matarka amma Karuwarka ta fi ni muhimmanci a wajenka?, ashe da gaske Haydar kai Mazinaci ne??, me ya sa ? ta yaya na Auri irin wannan Mijin da bai san kima da martaba ta ba?? , na shiga Uku na lalace shi kenan rayuwata ta gama yawo" sai a lokacin wani mugun kuka ya samu Ƴancin fara nasa aikin. Ta sha kuka kamar ranta zai fita, a wajen bacci me nauyi ya sace ta. Bayan wani ɗan lokaci ta fara jin sautin muryarsa a kanta, a bala'in firgice ta farka tana zazzare Kadarar Mujiya. Daga shi sai ɗan Gajeren wando Alina tana gefensa cikin wasu arnan kaya wanda ba su da maraba da tsirara. Wasu sabbin hawayen ne suka fara yin ambaliya akan kumatunta. Masifar da ya shiga surfa mata ta sa ba shiri ta miƙe ta nufi ɗaki ta fara haɗa kayan nata. Koda ta tafi ɗakin sai da ya bi ta ya ƙara zage ta tatas!!! ya bi ta da gori da cin Mutunci ba ita kaɗai ba har Danginta da iyayenta ba su tsira ba. A ranar suka tattare duk kayansu aka dinga fitar da su zuwa Gidan Mami. Tin da ya samu labarin Maa ta sayewa Aliyu Gidan ya hau Dokin Zuciya ya ce ba zai karɓi wani Gidan a Hannun Bhaba ba gwara ya zauna a ɓangarensa na Gidansu. A can aka yiwa Leelah sabon jere da Kayan ɗakinta, shi ma na shi aka jera masa a ɗakinsa. Haka Leelah ta kwana cikin mawuyacin hali, ga wasu mugayen mafarkai marasa daɗi da suka taso ta gaba, ga zazzaɓi da ciwon kai ga tunane-tunane. "Ahahahayye!!, Yaraye nanaye! ayyiriri !! yaraye nanaye Ƴan Mata!!!, Filin cashewa ayyiriri !! filin cashewa Ƴan mata!!, kina da shi juya ahayye!!! kina da shi juya Ƴar Mata!!!" Salim ne ke Waƙar a tsakar Gidansu cikin ɗaga murya yana yi yana karya ƙugunsa da ya ɗaurawa Ɗankwali ya yi ɗamara, ƙarawa ya yi da cewa "Ahayye!!!! ni Salim Ɗin Salama Ɗan Gidan Dije da Usama ikon Allah!!! Kainuwa dashen Allah ba dashen wani Ƙaton Ba!!!, Turmi sha daka!!! sha kwaramniya Gugan Ƙarfe!!!, a yi da kai yanzu a yi da kai Anjima!; Ni dai ina ganin Rayuwa a Gidan nan wallahi!!" Tuni Zazzaƙar muryarsa ta gama karaɗe Gidan waɗanda ke ɗaki ma saƙonsa ya isa gare su. Kasancewarsa Kamar me Busa Khusur ɗin fara Wasa da zarar ya dasa kowacce sai ta fito sai dai in ba ta Gidan. Mama ce ta kalle shi gami da cewa "Ɗan Tijara! yanzu za ka kafa dama ai kwana biyu ba ka yi ba". "E na ji, lokaci ne da ya wuce shi kenan" ya faɗa yana farrr!! da ido gami da lallanƙwasa hannuwa. "Me ke faruwa ne Ƙanina?" Ikilima ta faɗa tana ƴar dariya, Taɓe baki ya yi gami da cewa "Hmm!! mu Mazan Jiya Allah na tuba meye ba mu gani ba?, tinda Allah ya sa aka yi Bikin Leelah da Salama rayuwa ta yi min Tutsun Jaki, Ƙawayena na Gidan nan sun ƙara Kilewa kullum ba sa shan Kokon da ake Damawa sai dai a ci Buredi da Shayi har da Madara da Milo, ni kuma an bar ni da korawa Da markaɗaɗɗen Gero, haka wai da daddare ba a cin Tuwo sai dai a fita a kawo Pizza ko a yo Indomi, ga Samari Ƴaƴan masu Abin na lelewa a Unguwar nan don Ƴan Uwana amma babu wadda ta taɓa gabatar da ni a wurinsu, wataran sai dai na ji Ƙamshin Kaza ko na ga takardar tsire; alawadaran naka ya lalace wai Jakin Dawa ya ga Na Gida!!" Rabi'a ta yi dariya kafin ta ce "Kafin na kama damata a duk hannayena na sha Iya shege a wajenka Salim, amma yau sabida ka ga Kumatukana sun fara maiƙo shi ne za ka zo da naka ƙauli da ba'adin, dama ai haka Duniya take ɗan hakin da ka raina shi ke tsokane maka ido, amma ba komai tsakaninmu da kai ai akwai Amana!" Mama ta yi murmushi ta hura hanci kafin ta ce "Salim kenan!!, in banda abinka ai ba kai ka fita ka nema ba bare ka sa ran samu". Ikilima ta ce "To in banda abinka nema fa akwai wahala, kai ma faka za ka yi ka fita ka nemo". "Allah ya sawwaƙe!!, ku ma ku bi a hankali don wallahi Duniya ba gaskiya wai Ɓarawo ya rasa Shaida, yanzu sai ki je ba ki ci Kasuwa ba Rumfa ta faɗo miki, Allah Sarki Aunty Summi tana Garin KD in da tana nan na san ko ba ta ban komai ba za ta rarrashe ni, bare ma na san za ta ba ni". Haja ta ce "Aikin banza! kai wallahi ka fiye sababin tsiya ma malam!" "Ke tsaya!! sababi fa ya zama dole, kina kallo Leelah sabida ta Auri ɗan masu Kuɗi ko a waya ba ta ƙara cewa ina Salim yake ba, kin ga ai ni na ga sababi sababi ya gan ni!!" ya yi maganar yana murguɗe-murguɗe da tafe-tafe. Momi ta ce "Ubanka!! sau nawa tana cewa yaushe za ka je amma sai ka ƙi zuwa?, kai fa ba ka da hali wai uwar akuya a kasuwa, shege da kai kamar sauran Minsileta!" Dariya suka sa, Salim ma ya saki shewa yana cewa "Heee!! Allah Gatan Kowa, Momi Tawa ni ko na Allah, ni fa ba na son raini ne, gwara ma tin kafin wankin hula ya kai ta dare ki gaya mata Girman kai da Fariya Aikin Shaiɗan ne bayan Shaiɗan kuma sai magadansa, Shaiɗan da Magadansa kuwa kowa ya san Ƙarshen su Jahannama!!". Wata langa ta wawura a kusa da ita ta miƙe tana cewa "Bari in faskara maka wannan a ka dan Ubanka sai ka ba ni bayani, shege ɗan Hassada". Artawa ya yi da gudu ya fice daga Gidan yana dariya. Momi ta wurgar da Langar ta tunkuɗo kallabinta gaba ta kafa aradun Masifa. https://chat.whatsapp.com/EOb68TVK8Ki2ybe4h3ncyx Assalamu alaikum. ina mai so ta ga tayi ƙiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 💃🏽💃🏽💃🏽😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau. ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakkiyar Mace ❤️ina maza da basa cin abinci, ina maza masuso suyi kiba ina yara da basu da kiba..... ina farin cikin sanar daku *ZUMAR ƘIBA*, zuma ce wadda zata saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam. Hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza.. WhatsApp no 07044450136 *Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Tuntuɓi Lambar Waya👉🏽 09079885632* *©️INDO* [12/13, 11:53 AM] INDO: *🪻HAƊIYAR GATARI🪻* 20 ©️ Ayeesha Abdulkareem *INDO* *GORGEOUS WRITER'S FORUM* Azaan, yana zaune kusa da ƙafafun Mammi ya ɗora kai a kan cinyarta yana ɓarza kuka kamar wanda bincike ya tabbatar masa gobe zai Mutu. "Mammi wannan ne karon farko da kika kasa samar min farin cikina, Aliyu da Haydar kowa ya samu abinda yake so amma ni kin gaza yi min komai, yanzu fa Khushi ko ganinta ba na samun damar yi sabida Aliyu ya ƙara ninka tsaro a kanta". shu'umin murmushinta wanda ba a iya fassara shi ta saki kafin ta ɗora hannu kan kwantacciyar sumar kansa ta fara yamutsa ta gami da shafawa, cikin maganarta me cike da gadara ta ce "Kar ka ga kamar ban damu da kukan nan naka ba Arjun!, yana matuƙar taɓa Zuciyata kuma yana ƙara tunzura ni bisa cimma wani ƙuduri nawa wanda ke lulluɓe a cikin naka Ƙudurin; kai ma ka kusa mallakar naka farin cikin, kwanan nan zan kawo maka Khushi har Ɗakina a matsayin kyautar da zan yi maka ta Birthday, na yi jinkiri ne kawai sabida Uwar su ta wuce duk yadda kake tunani, amma lokacin kukanka ya zo ƙarshe". Kuka ya ci gaba da yi yana bayyana mata irin tunani barkatai da yake yi akan Khushi, sai dai ya kasa bayyana mata wani kuiɓin na Zuciyarsa yana shirin ɗarsa masa Dafin sonta. Sai da ta yi da gaske sannan ta rarrashe shi, tashi ya yi ya wuce sashinsa Zuciyarsa a dugunzume. Aditya Buddha Daddynsa da ke zaune a gefe yana jin su sai lokacin ya samu damar tambayar ta manufar ta ta yin haka, cikin harshensa wato Hindi, da Yaren ta mayar masa da amsa bayan ta murmusa "Ina son shuka wa Moonath baƙin cikin da suka shuka min a rayuwa, ina son muzguna musu kamar yadda suka muzguna min; na lura Arjun ya yi nisa a cikin sonta amma ni ba hakan nake so ba, da zarar ya idar min da nufi na zan nesanta shi da ganinta, zan yi masa iyaka da ita, iya abinda nake buƙata shi ne raba ta da martabarta ta ƴa mace ta hakan ne kawai zan iya samun damar tarwatsa maƙiyana". murmushi ya yi tare da ba ta jinjina ba tare da tsoro ko shakkar ɓarnar da take shirin yi ba. Mutsu-mutsu kawai yake yi a kan gadon, gabaki ɗaya ya kasa samun nutsuwa, suyar da Zuciyarsa take yi har ya shafi gangar jikinsa, shi ba zazzaɓi ba amma jikinsa ya ɗauki zafi raɗau!. damuwa da ƙunci sun zamo Abokan mu'amalarsa wai a hakan ma don yana ƙoƙarin kawar da su ta hanyar ci gaba da rayuwarsa faran-faran da mutane. Abubuwa da yawa sun yi haɗin gwiwa suna kawo masa sara da suka cikin fusata da son yaƙarsa, har yau bai dena jin zafin raba shi da Leelah da Haydar ya yi ba, haka zalika mugun furucin Mammi da ke yi masa sukuwa a Ƙwaƙwalwa da Zuciyarsa, ga baƙar ƙiyayya ta Zahiri da Haydar da Mahaifiyarsa ke nuna masa, ga Babban Amininsa wanda ya ɗauka tamkar ɗan Uwa ya kamu da son Ƙanwarsa wadda a yanzu hankalinta ya bar gangar jikinta sabida faɗawa tafkin son Azaan. https://chat.whatsapp.com/EOb68TVK8Ki2ybe4h3ncyx Assalamu alaikum. ina mai so ta ga tayi ƙiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 💃🏽💃🏽💃🏽😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau. ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakkiyar Mace ❤️ina maza da basa cin abinci, ina maza masuso suyi kiba ina yara da basu da kiba..... ina farin cikin sanar daku *ZUMAR ƘIBA*, zuma ce wadda zata saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam. Hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza.. WhatsApp no 07044450136 Nannauyar ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya ɗora idonsa akan Salma da ke zaune a bakin Gado, ba aikin fari ba na baƙi amma ta yi zaune kamar butum-butumi, da alamu ita ma ta tafi Duniyar tunani, "Salamaath!" numfashi ta fizga gami da zaro ido, ba ta yi tsammanin jin sunanta a bakinsa ba a daidai wannan lokacin, kasa amsawa ta yi bare har ta juyo ta kalle shi, "Me yasa kika kasa sakin jiki da ni har yanzu?? ko dan na ce miki wata ran za mu rabu?" da sauri ta girgiza kai alamar a'a, ɗan murmusawa ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Me ya sa to kina kallo na kasa bacci amma kin kasa tambayar lafiya ta??" sai a lokacin ta yi saurin juyawa ta zuba masa idanu don kuwa ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi, ta daɗe da lura yana cikin tsananin damuwa sai da ta ga kamar abinda ya shafi danginsa ne ba ta son matsanta bincike a kai, musamman da ta san ba wai ya Aure ta ba ne don su zamo tsintsiya maɗaurinki ɗaya, wata rana dole rabuwa za su yi. Kaifin idanunsa ya sa ta sunkuyar da nata idanun ƙasa, cikin sanyi ta ce "Ina shirin tambaya sai ka riga ni sabida karambani irin na Yarinta". dariya ya yi gami da cewa "Eh! lallai kin ga makwancina Salamaath, har yarinta kike jona min ko??" dariya ta yi gami da cewa "Ƙanwata fa kake so, ka ga dole ne ka ba ni girmana, kuma kai ma kanka na ba ka watanni Shida, don haka a matsayin Ƙanina na ɗaukeka". lumshe idanunsa da suke yi masa yaji ya yi, ɓoyayyar ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya buɗe idanun nasa ya zuba mata gami da cewa "Ni kuma ban ɗauka haka ba, matsayin Matata na ɗauke ki; yanzu dai ki ajiye wannan zolayar ta ki, labari nake so ki ba ni wanda zai sa na yi bacci ba tare da wata damuwa ba". "To fa labari kuma?, ni ban iya bayar da labari ba" "Ai kuwa za ki koya don ni bana bacci haka salin alin, Mamata da Ƙanwata sun riga sun sabar min sai ina jin motsin wani na fi samun nutsuwar yin bacci" abin dariya ma ya ba ta don haka ta dara tana cewa "Tab!, ai kuwa kana lukutin yanayi, ni kam ban iya wani labari ba sai dai in na ƴan Gidanmu kake so". "Ba komai, hakan ma na gode ai, dama ina son tambayarki wai ina Leelah take samun Manyan Kaya da waya da take amfani da su in za ta fita?" ƙara tuntsirewa ta yi da dariya tana cewa "To kai ina ruwanka?" "Babu ruwa na don na ma shanye shi, amma ina so ki ba ni naki. "Allah dai ya kyauta!!, wallahi wurin wata suke karɓo Haya, ita sana'arta kenan bayar da Hayar kaya tsala-tsala har da wayoyi da haka take samun kuɗi, haka za ka ga ƴan Matan Unguwarmu Ƴan Ƙarya suna ta zaryar zuwa Gidanta, wallahi abin dariya yake ba ni, lamarin Duniya sai Du'a'i !" ta ƙarasa maganar tana tuntsira dariya, shi ma dariyar yake yi yana jinjina lamarin na su Leelah, in Mutum bai sani ba in ya gansu sai ya rantse daga Gidan masu Ƙumbar Susa suka fito, "Gaskiya Mutanen nan Ƴan jirgi ne na asali, su kuma aikin su kenan bayin Allah, ke kuma ya aka yi kike wankau? ba kya yin Askin Aljihun ke?" Zaro ido ta yi tana cewa "Ina ni ina Haɗiyar Gatari Aliyu?!!, ai ni wallahi tsarin da na taso a kai ban yarda da yin rawa da Bazar wani ba, haka Mahaifina yake yana da ƙoƙarin neman halak ɗinsa, bai yarda da bibiyar wani don neman temako ko bashi ba, haka muke rayuwa ranar da ya samu a ci ranar da bai samu ba a haƙura, hakan ne ma ya sa ni da Umma muke wankau don mu dinga Temaka masa muna temakon kanmu, daga baya ma Umma take ɗan fama da ciwon Ƙafa sai kawai nake yi ni kaɗai, da kuɗin muke ɗan kashe matsaltsalun Gida har Umma take sayen ƴan Kayan Kicin tana tara min." tinda ta fara magana ya tsira mata ababen ganinsa yana murmushi, sai da ta gama sannan ya ce "Ashe ra'ayin mu ya zo ɗaya, shi yasa jinin mu ya haɗu sosai; ni ma kin ga Duk Kuɗin iyayena na fi son na tsaya da digadigaina, Mahaifiyata babbar ƴar kasuwa ce da ake damawa da ita a wasu daga cikin ƙasashen Afirka, sannan ana yi da ita a irin su China, India, Singapore, Australia, Pakistan, ke na manta sauran don ko ina ana iya jin ta, a ƙasar nan duk wani kwallin Roshan Kohl nata ne, haka irin lallen nan baƙi da Ja wanda ke da laƙabin Khushi duk nata ne, a ɓangaren Mahaifina ma Ɗan Kasuwa ne na ƙasa da ƙasa, amma hakan bai dame ni ba, ina kula da Dukiyarsa haka kuma ina neman nawa halal ɗin, na yi aiki tuƙuru kafin na fara kafuwa, yanzun haka na mallakin Kamfanin da ake sarrafa Robobi, sai dai ni na fi ganewa Kasuwancin haɗaka, wato wanda ake haɗa hannun jari, saɓanin Mahaifina wanda yake Taka rawarsa a Fage shi Kaɗai, ni ma ina son denawa amma na kasa sabida na riga na saba". baki buɗe take kallonsa har sai da ya dasa aya sannan ta sauke wani gwauron nishi, "Allah ya gani ga Cuci Leelata Aliyu, me ya sa ba ka faɗa mata gaskiya ba?, ka san Allah tana sonka kawai don dai tana da son ƙyale-ƙyalen Duniya ne ya sa ta ture ka ta zaɓi Yayanka, gaskiya ba ka kyauta ba wallahi, dole ne ma na yi ƙoƙarin samar muku da farin cikin ku gabaki ɗaya". Murmusawa ya yi kafin ya ce "Shi ya sa kullu yaumin ake yi mana wasiyya da cewar a dena raina Halittar Allah ko da ba Mutum ba ce halittar, bare kuma Ɗan Adam wanda Allah ya yi wa baiwa iri-iri kowa da kalar ta shi, kullum nasiha ake yi mana a kan raina Ɗan Adam da kuma ƙasƙantar da shi; Leelah ta sa ranta a wulaƙanta Ɗan Adam in banda haka da in ta ƙare min kallo za ta gane ni ba irin yadda take zato ba ne; ina so ne na koyar da ita darasin Rayuwar Duniya shi yasa na zaɓi ɓullo mata ta bayan Fage, hmm! da ta san waye ni da ba za ta taɓa Kallon Haydar a matsayin Namiji ba, ni kaina ina da arziki bare na shiga Rigar Iyayena, shi kuwa Haydar Mamarsa ta dogara ne da Arzikin Bhaba, asalinta kuma iyayenta ba masu ƙarfi ba ne, shi kuma Haydar ya kasa ɗaukar nasihar da muke yi masa ni da Bhaba a kan ya dena shiririta ya fara nema, shi ba shi da aiki sai shaye-shaye da biye-biyen Mata sai kashe kuɗi kawai don ya gansu kamar a banza, wai a hakan ma Bhaba yana taka masa burki, abin yana yi min ciwo na rasa yadda zan yi da shi, ni ina ƙaunarsa sosai, amma shi gani yake ba shi da Maƙiyi sama da ni sabida Bhaba ya fi jituwa da ni sannan kuma ina gaya masa gaskiya, irin halayensa yana ɗaya daga cikin abubuwan da suke damuna". Sosai jikinta ya yi sanyi tuɓis!!, kallo ɗaya ta yi masa ta gane asalin gaskiyarsa duba da yadda idanunsa suka kawo ruwa fuskarsa sam babu alamun walwala, a gefe guda kuwa tausayin Ƴar Uwarta ya kama ta, ashe ma Ɗan shaye-shaye Mazinaci ta je ta Aura sabida tsabar son abin Duniya. Numfasawa ta yi kafin ta yi ƙoƙarin danne ta ta damuwar ta kawar da zancen ta kawo Labarin yadda suke haɗa wasan kwaikwayon ban dariya a Gidan su. Sun sha surutu kafin suka sanyawa bakinsu sakata suka yi addu'a suka tinkari bacci. Bayan wani ɗan lokaci. Shaƙuwa me tsanani ta shiga tsakanin Salma da Aliyu. Zaman su a Gidan su biyu ya temaka wajen haɗe kansu da sanya musu tsananin shaƙuwa, da yake duk ɗinsu gwanayen rawar kai ne haka suke kacakinsu su ɓarar su kwashe, su lalata su gyara, su yanka su feɗe su soya, su kashe su rufe. Ɓuruntu iri-iri ba wanda ba sa yi. A ɓangaren Leelah da Haydar abin sai Innalillahi don tsiyatakun ƙara hauhawa suke yi Kamar ba shi da mafaɗi a Gidan, wai sunan Mahaifiyarsa tana nan. Tana zaune sai ya zo ya shige da Matan Banza Bedroom su gama Alfahasharsu su fito suna jefa mata magana gami da bin ta da kallon banza. Tin a satin su na Amarci bai ƙara haɗa Gado da ita ba amma kowane dare yana da Abokiyar kwana. Masifa da Gori kuwa ba kama hannun Yaro ahi ya yi Matan Banza da yake kawowa su yi Mahaifiyarsa ta yi, har ma baƙi in sun yi. Ga kuɗi ga Daula ga sutturu manya tsala-tsala, ga Abinci me kyau ba shamaki, ga AC ga Kushin-Kushin masu taushi da sanyawa wanda ya hau su nutsuwa, tabbas irin Gidan take buƙatar mallaka a matsayin Gidan Miji sai dai yau an wayi gari ta mallaka ɗin a memakon ta yi ƙiba sai uwar rama da take yi kamar wadda ake ɗiba ana Miya. Rashin kwanciyar hankali da tsananin Damuwa sun zamo abokan rayuwart, Kullum cikin kuka take, idan ta dasa kukan hawayenta har ƙafewa suke yi, tabbas da suna ƙarewa ƙaran-ƙaf da yanzu babu labarinsu, ba ta da wanda za ta raɓa ta ji sanyi, gashi ta kasa gayawa kowa maganar don gani take ana ji dariya za a yi mata, don haka ko Momi ba ta faɗawa ba. Mami koda Haydar ya raba Aliyu da Leelah hakan bai yi mata ba, don ba ta ganshi a cikin mawuyacin halin da ta tsammaci ganinsa ba, shi ma Haydar a nasa ɓangaren banda baƙin ciki da takaici ba abinda ya tsinta, har ya yi shiru da zancen Mami ta yi masa Albishir da wani kyakkyawan shiri da ta yi wanda zai kawo ƙarshen Alaƙarsa da Bhabansa sannan shi da mahaifiyarsa su shiga ƙunci da masifa. Jin Albishir ɗin nata ya yi mugun yi masa daɗi, a take ya ji ba shi da wata damuwa tinda don ya san kamar an yi an gama ne. Azaan, ya zama Abokin faɗan Mammi don kuwa kullum tijara yake zuba mata, ta safe daban ta rana daban ta yamma daban haka ta dare ma daban. Kullum faɗi yake yi ta gaza yi masa komai, abinda yake turnuƙe Zuciyarta kenan yake ƙara tsananta mata tsanar Khushi da Iyayenta, kuma ta ci mugun Alwashin sai ta aiwatar ƙudurinta ko da hakan zai yi sanadiyyar rasa rayuwarta, ta san dai ta yi musu tambari ɗaya wanda za su Mutu bai goge ba kuma har su mutun Kullum cikin haɗiyar ɗacinsa suke. https://chat.whatsapp.com/EOb68TVK8Ki2ybe4h3ncyx Assalamu alaikum. ina mai so ta ga tayi ƙiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 💃🏽💃🏽💃🏽😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau. ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakkiyar Mace ❤️ina maza da basa cin abinci, ina maza masuso suyi kiba ina yara da basu da kiba..... ina farin cikin sanar daku *ZUMAR ƘIBA*, zuma ce wadda zata saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam. Hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza.. WhatsApp no 07044450136 A fannin su Summi likafa ta ƙara ci gaba. Abincin Gidan ma ya canja, da yake kowane sashi nasu suke yi, haka kowacce ƴaƴanta ke kawo mata Gara ta kwasa hankali kwance. Umma ce dai ta Dogara da Abin da Mijinta ya ba ta, shi take ci ta sha kuma ta kwana lafiya, sai dai ta jiyo ƙamshi a madafa, ko sun sammata ma ba ta karɓa don a ganinta kuɗin haram ne cin su kuwa bala'i ne. haka ake cakusawa tsakaninsu da Salim ya faɗa musu su faɗa masa, ranar da suka yi faɗa ba zai ci Abin su ba, ranar da aka yi Mutunci da shi kuma a kwashi gara tare da shi. Gabaki ɗaya sun karaɗe ɗan madaidaicin Falon da surutu, idan ta yi musu daɗi sai a yi shewa a tafa, filolin kan Kujera ma ba su tsira ba gabaki ɗaya an ɗaiɗaita su sabida jefe-jefe da tsalle-tsalle. Yau ji suke yi da shiririta kamar sun haɗiyi ƙwayar hauka. Wayar Roshan ce ta sa su tsagaitawa da surutun bayan ta fara ƙara da iya ƙarfinta, sai da ya kai Aya sannan ya ɗauka tare da yin sallama. Bai daɗe yana wayar ba ya katse gami da kallon Salma ya ce "Maa za ta tafi India, ta ce mu koma Gida". tsalle ta doka tare fa ihun murna ta faɗa kan Sofa. Baki ya buɗe sokototo yana kallonta kafin ya ce "Meye hakan sai ka ce kin yi tuntuɓe da iskokai??" ''Wallahi na ji daɗi da za mu koma can Gidan, nan ba Mutane sosai can kuwa da jama'a sannan zan dinga ganin Khushi kullum ka ga na samu Abokiya". taɓe baki ya yi cikin ko in kula ya ce "Uhm! ke kaɗai kuma, sai ki tashi ki kintsa". kafin ya gama rufe baki ta tashi tana cewa ''Yanzu ma kuwa" Bai yi zaton abin nata azimun ba ne sai da ya ganta niƙi-niƙi da akwati ga uban Hijab ta zumbula, dariya ya yi gami da cewa "Kin fi ni Ƙuruciya fa Aunty Salma" "Ni dai don Allah ka tawo mu tafi ba na son tsokana" Ba don ya shirya ba ta tasa ƙeyarsa suka bar Gidan. Ita da Khushi kasa bambance wadda ta fi murna ya yi sai dai ya bi su da ido kawai. Yau tana tashi daga bacci tin sassafe kafin ƴan aiki su fito ta fito ta fara share-share da goge-goge ita kaɗai tilo kamar Jaki a tsakiyar sahara. Sai da ta ci ƙarfin aikin Maa ta fito, cikin sauri ta yi kanta tana faɗin "Subhanallah! ya haka Ƴata? me ya sa kike yin aiki da kanki?" fuskarta ɗauke da fara'a ta ce "Na tashi da wuri ne ai" "Haba ke kuwa, don kin tashi da wuri ai sai ki yi wani abin, wannan ai aikin Bayin Gidan ne" Maa ta faɗa cike da damuwa don kuwa abin bai yi mata daɗi ba sam!, Roshan da ya ƙaraso wajen ya ce "Maa wannan ta riga ta saba, ni ma babu yadda ban yi da ita ba a kan dena shiga hurumin Ƴan Aiki amma ta ƙi denawa". "Au yanzu haka kake barinta tana yi maka aikatau a can Gidan??, ka kyautawa kanka kenan?, ba fa baiwarka ba ce ina ita ina wannan aikin?" Da sauri ya ce "Wallahi Maa ba yadda ban yi da ita ba". Salma ta ce ''Ina son yin aiki ne sabida ba na son zama kawai". "Ke do Allah!, tawo mu je ki huta, kar na ƙara gani kin yi" ta faɗa tare da jan hannunta suka nufi sashinta. Kwanansu biyu da dawowa Gida Maa ta tafi, washegari shi ma Bhaba ya wuce. Gidan ya rage daga Salma da Khushi sai ƴan aiki, Roshan kuma sai in ya dawo ake ganinsa. Haka suka ci gaba da rayuwa cikin farin ciki da nishaɗi ba tare da wata damuwa ba. Yau Misalin ƙarfe 01:19am......... Salma ce ke ta famar kai kawo a babban Falon hankalinta a matuƙar tashe, ta kasa zaune ta kasa tsaye, wayarta ta sake dubawa a karo na ba adadi, kamar za ta yi kuka ta ƙara tura wa Lambarsa kira sai dai yanzun ma abinda na'urar kamfanin Layi take faɗa tin ɗazu shi ta ƙara maimaitawa, wato switch off. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!!" ta faɗa tare da faɗawa kan Kujera sabida wani baƙin duhu da ya mamaye ganinta yayin da kanta ke wata irin majaujawa. https://chat.whatsapp.com/EOb68TVK8Ki2ybe4h3ncyx Assalamu alaikum. ina mai so ta ga tayi ƙiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 💃🏽💃🏽💃🏽😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau. ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakkiyar Mace ❤️ina maza da basa cin abinci, ina maza masuso suyi kiba ina yara da basu da kiba..... ina farin cikin sanar daku *ZUMAR ƘIBA*, zuma ce wadda zata saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam. Hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza.. WhatsApp no 07044450136 Idanunta a runtse ta fara surutu kamar wadda ta fara zarewa "Tinda nake tare da kai Ba ka taɓa kai dare haka a waje ba, gashi ka ɗauki Yarinya ka fita da ita, kuma ko labarinku babu!, me ke faruwa da ku Aliyu?? ina kuka shiga? me ya sa wayarka ba ta shiga??, me ya sa kuka yi nisa haka?" Muryar ɗaya daga cikin ƴan aikin Gidan da suka yi tsaye curko-curko ta tsinkaya tana cewa "Aramse Maalik mahila!" ɗago kai ta yi ta kalleta cike da takaici, ta sha gaya mata ba ta jin Yarensu amma ta ƙi dena yi mata, tsaki ta ja tana shirin yin magana wayarta ta fara tsuwwa. Jiki na rawa ta ɗauka ko dubawa ba ta yi ba don ta gama sawa a ranta Aliyu ne, muryar Maa ce ta ziyarci kunnuwanta, "Namaste beti!, me yake faruwa ne? ina Roshan??" Guntayen hawayen da suka fara sauka kan kumatunta ta goge kafin ta ce "Ina wuni Maa" a taƙaice ta amsa gami da maimaita tambayarta cike da ƙaguwa, "Tin da suka fita da Misalin shabiyun rana ba su ƙara dawowa ba" ta faɗa cikinn raunin murya, Maa ta ja numfashi ta sauke kafin ta ce "Na ga lokacin da ya fita, ina nufin ina ya ce miki zai je, hankalina duk a tashe yake, tin da na tashi nake jin Zuciyata tana tsinkewa yanzu tsoro da fargaba sun ƙara yi min yawa, jikina yana ba ni ba lafiya suke ba, na kira wayarsa ba adadi amma ta ƙi shiga ita ma Khushi haka, ba sa kashe wayarsu kuma duk inda za su je ba sa ɓoye min, amma yau ba su gaya min ba, don Allah ki faɗa min ko ya gaya miki". kukan da ta daɗe tana dannewa ne ya samu nasarar kufce mata, cikin shashsheka ta ce "Ya ce min zai je Meeting na Kasuwanci, bayan haka bai gaya min komai ba; ni ma gabana sai faɗuwa yake yi, ina cikin tashin hankali sosai, Maa don Allah ku temaka ku sa a nemo su, kuma har da Khushi fa suka fita!!" Suman tsaye Maa ta yi ko motsi ta kasa yi sai Zuciyarta da ke famar bugawa da mugun gudu, lokaci guda wasu zafafa hawaye suka fara gangarowa kan Kumatunta, cikin rawar murya ta ce "Ba lafiya suke ba Beti, addu'arki yake buƙata, ki dena kuka" daga haka ta katse wayar, zaman daɓaro ta yi a gefen Gado Zuciyarta kamar za ta tarwatse. Wata Dattijuwar mata da ke kusa da ita ta dafa kafaɗarta cikin harshen hindi ta ce "Ki yi haƙuri, bai kamata ki zauna kina zubar da hawaye ba". "Mamee dole in shiga tashin hankali, shi kenan maƙiyana sun yi nasara a kaina?? shi kenan sun yi nasarar ƙuntata min?, me ya sa ba su da burin da ya wuce tarwatsa wa ƴaƴana rayuwa?, Ba zan iya yafe wa kowaye ya aikata min haka ba Mameeji!!" ta ƙarasa maganar tana kuka har da shashsheka. Rarrashinta Mamee ta shiga yi tana kwantar mata da hankali gami da faɗa mata tausasan kalamai. Jin halin da Maa ta shiga ya ƙara ɗaga hankalin Salma, ci gaba ta yi da rusa kuka ba ji ba gani, gabaki ɗaya ta rasa inda za ta saka kanta. Da ƙyar ta iya ɗaukar wayarta wadda ke ihun neman ɗauki, hankali a tashe Bhaba ya ke jero mata tambayoyi tana ba shi amsa daidai gwargwadon abinda ta sani. Ya yi mamaki sosai da ya ji ta ce wai meeting Aliyu ya tafi, indai zai yi meeting ɗin sai ya nemi shawararsa ba haka nan yake yi da ka ba, amma yau bai ma gaya masa zai fita ba bare har ya nemi shawararsa, hakan ya ƙara tabbatar masa ba lafiya ba. Kuka sosai Salma ta ci har zuwa Huɗun asbahi sannan ɓarawo ya sureta. Abu a nesa sai gashi a kusa daf!!!...... Duk tsawon dare sai da ya ya yi ƙaura, farin wata da taurari suka koma sansaninsu yayinda rana ta maye gurbinsu da nata hasken, amma shiru babu Khushi babu Roshan babu labarinsu, kuma hallau duk wayoyinsu ba sa shiga. Tin safiya Ƴan sanda suke sagaraftu a Gidan da sunan bincike.......................... (Waye ya sace su Aliyu??, , me ke shirin faruwa??, menene ya faru da su??, wane mataki Maa za ta ɗauka??, me ya sa bai faɗa wa kowa gaskiyar inda za su je ba??. Ku biyo ni domin jin dukkan amsoshin ku) *Wannan Shi ne Fejin ƙarshe na Bati.😂 Wato dai shi ne LAST FREE PAGE☺️* *Samu Ƴancin Karantawa!!, ta hanyar biyan Naira Ɗari Uku 300 kacal☺️ Tuntuɓi Lambar Waya👉🏽 09079885632* *©️INDO*