DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in Godiya ta tabbata ga Ubangijinmu daya halicci alk'alami, yasanar da bawa abinda bai saniba. Salati da aminci da d'aukaka su k'ara tabbata ga farin jakada,babba d'an Abdullah Muhammadu-Sadiqul-amin,da alayenshi da sahabban shi da wad'anda ke kan tafarkinshi har zuwa ranar rarrabe tsak'anin k'arya da gaskiya (Alk'iyama). Godiya ta musamman ga Umar Dalha.Dakai muka kai ga gaci. Kima:- Kimarku muke gani Katsinawan Dukko d'ak'in kara,mun gaisheku gaisuwar kima, musamman Maskawan k'aramar hukumar Funtua da ahalin Muhammadu Me-ruwa dana Tankon Marka anan BCG,dana garin Gadagau. Dan tunawa da:- Gwanarmu a duniyar marubuta littafan Hausa. Marubuciyar 👇 {Dare ga mai rabo...} Halima Abdullahi (Amma). My One & Only Aminu A.Baba. Lovely Sister Badi'atu Ibrahim. Son Aliyu Yahya Namadi. Little peerless Ali Yahya Namadi (Malam Garga) Ubangijinmu ya kyautata makwancinku😭👏 Sadaukarwa:- Ga d'aukacin Hausawa da Fulani...musamman Ya'yan Ibrahim ako ina kuke a fad'in duniya...😊 ...GWAJIN DAFI 💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na d'aya. A kwance yake cikin damuwa, hawayen da suka cika idanunshi suka fara zubowa ta gefe da gefen fuskar shi suna gangarawa jikin matashin daya d'ora kai,a haka bacci ya d'aukeshi.Da sallama tashiga dak'in,kwanan abincin tabud'e, yananan yadda tazubashi, ALLAH ma yasa ya bud'e ya ga abinda yake ciki,da sanyin jiki tad'ago tana kallanshi,bacci 6arawo kamar yadda ake fad'a,to da alama saceshi yayi,tagirgiza kai cikin tsantsar k'aunarshi da tausayin halin da yake ciki,komai yana nan rad'am kamar yan awannin da suka shud'ene abin yafaru.Tausayin shi yadad'a mamayar zuciyar ta,dak'yar tamik'e daga tsugunan zuwa D'akin-girki tad'ora musu abincin rana.Bata koma dak'in ba sai da aka fara kiraye-kirayen sallar azahar daga mabambantan masallantan unguwa. "Julaib... Julaib... Julaib... Cikin natsuwa take kiranshi.Dak'yar yabud'e idanunshi da sukayi jawur saboda damuwa ga kuma bacci me nauyi daya kamasu.Tad'anyi murmushi"yi hak'uri na katse maka bacci lokacin sallah ne yayi.Yabita da kallo kamar bai fahimci abinda tafad'a ba.Tabud'e baki zata sake magana sai kuma tayi shiru tawuce dan sauke nata faralin. Yana dawowa daga masllaci takawo mishi abinci "Ta kalleshi,barka da dawowa" a zuba maka yanzu ne?"shiruma amsace. Yad'auke kai daga kallan da take mishi.Da sigar rarrashi tazauna agefenshi"Julaib... kayi hak'uri,zama da yunwa ba shine mafita ba,ba shine zai magance damuwar zuciyarka ba,zama da yunwa k'ara dagula maka lissafi kawai zaiyi, Dan ALLAH Julaib kadaure kaci kome k'ank'antar shi zai samar maka da natsuwa, natsuwarce kuma zata ba ka dama na tsayawa kai da fata wajan yawaita addu'a agaresu.Tazuba mishi faten waken dayaji kayan had'i k'amshinshi yagauraye d'akin."Dan ALLAH kadaure kaci, tamik'a mishi farantin amma yak'i kar6a, tabishi da kallo tana murmushi "To abaki zan ba ka? Tad'ibo a cokali indai hakan kake so ni a wajena abune me sauk'in gaske,takai cokalin tsakanin la66anshi na sama dana k'asa"Haaa bud'e bakin ka kaci kayan k'arin lafiya da gina jiki. Dakata haka malama! Yajuyo da 6acin rai me yawa a tashi fuskar yana mata wani irin kallo data kasa fassarawa"ni na ce miki inajin yunwane?Ko nasafe ban ciba amma kin sake dafo wani saboda almubazzaranci?Tabud'e baki zatayi magana yayi saurin katseta"Keee! kwashe kayanki ki fita bana san hayaniya.!Yahaye gado kanshi na mishi wani irin matsanancin ciwo kamar ana buga mishi guduma. Tabishi da kallo cikin mad'aukakin mamaki,tsawon zamansu da duk halin-ko-inkulan dayake mata tana mishi uzuri,akwai damuwa me yawa atare dashi,to amma yau itace rana ta farko daya 6ata mata rai,cikin raunin murya dake shirin fashewa da kuka tace"Julaib... hawaye masu d'umi suka zubo mata sharrr... Julaib...dama na san baka so na,to yau na dad'a tabbatar da hakan,na zama maka matsala ko?Adole kake zaune dani ko? Tasauke numfashi toh, ai ALLAH yanaji yana kuma gani na yi iya iyawata dan kawar da damuwar zuciyarka amma hak'ata bata tadda ruwaba,na sani za fi da rad'ad'in da kakeji bazai ta6a barin zuciyarkaba matuk'ar kana numfashi a doran k'asa, to amma ya kamata ka sassautama ranka,"Shekaru uku ba kwanaki uku bane"A shekara kwanaki d'ari uku da sittin muke dashi,to kwanakinnan sun ninka kansu har sau uku,kaga kwanaki dubu d'aya da tamin,kwanakin da sukayi a mace kenan"kukan mutuwa baya dawo da matacce"kasama ma zuciyar ka salama kayi rayuwa kamar yadda kowani d'an Adam me numfashi a doron k'asa yake yinta. Julaib...to wai me yasa baka jin tausayina na mace me raunine?Tasake binshi da kallo sai kuma ta gyad'a kai,saboda kawai baka so na?To shikenan amma ina so kasani ni har kwanan gobe ina k'aunarka duk da bana samun irin kulawar data dace,ni na yadda da abu daya,aure bautar Ubangijjne dan haka zan cigaba da dauriya dan nima kamar yadda Abbana yafad'a min"ina kwad'ayin babban rabo a gidan gaskiya(Darul-karamah)ni zan sauke nauyin dake kaina,amma tunda ba ka san ganina,ba ka san abincina,ba ka san hayaniya da duk wata kulawa tawa to ko Insha-ALLAH zan kiyaye, zan killace kaina a d'akina,amma fa k'ofata a bud'e take ina maraba dakai,a duk lokackin dakake da buk'atar tallafina kasanar dani kai tsaye,ni kuma zan baka tallafi irin wacce tadace da buk'atarka, karambani ne dai bazan kuma ba tunda kai ba a maka gwaninta... Tajuya da gudu zuwa d'akinta, gado tafad'a tana wani irin kuka, kukan data kasayi agabanshi hawayen sharrr...sharrr...suke zubowa, tad'aga hannayen ta sama"Ya ALLAH kataimaki mijinah...kayaye kunci da damuwar zuciyarshi, kamaye hakan da natsuwa...Ya ALLAH Ju..Jul.. Julaib..d'in...sauran kalaman suka mak'ale saboda kukan yaci k'arfinta,takifa fuskarta a jikin matashin hawayen nacigaba da zubowa. Kalamanta sun sanyaya mishi jiki, yarintse idanunshi da k'arfi yana jin kanshi kamar zai rabe gida biyu,"Wayyo ALLAH nah?!yafad'a a wahalce yasa tafukan hanneyen shi yak'ank'ame kan,jijiyoyin wajan sun fito rad'am kamar shatin bulala suna kuma harbawa da k'arfin gaske. "Wai...Wayyoh ALLAH...!Sai yafara fad'in "Babu tsimi babu dabara sai ta Ubangijjnmu.wucewar wasu dak'ik'u ciwon kan yad'an sarara mishi...sai kuma zuciyarshi tafara tunatar dashi. "Iyayanta sun maka halacci, sun maka karamci,sun taimakeka a lokacin da kake buk'atar taimakon,lokacin da ba ka da kowa ba ka da komai, lokacin da ba ka san a wace duniyar kakeba. Ruqayya matarka tana sanka tana k'aunarka,ka ga haka,ka kuma san da haka tun ganin farko daka mata bayan ka bud'e idanunka tsawan kwanaki,makonni da watanni a wata duniya daba zaka bada labarin wani abu guda d'aya na cikin taba,idanunka da ita suka fara yin tozali,haba Julaibib wannan ba halin girma bane,dan halal ai baya manta alheri,sai dai me halin kaji"Ci ka goge baki"abinda yake damunka bai shafe taba,ba ita takar zomo ba bai kamata ta d'auki rataya ba... Kai musulmi ne kayi imani da k'addara kuma yana daga cikin cikar musulunci, wannan al'amarik'addararrene tun daga lauhul-mahfus.. Zuciyar shi tacigaba da tunatar dashi. Yasauke numfashi da ajiyar zuciya, k'irjinshi ya mishi nauyi yana kuma mishi suya,yahad'iye wani zazzafan abu kamar garwashin wutan da aka bad'e shi da dakakken barkono d'an munci. Yamik'e zaune dak'yar sannan yaziraro k'afafunshi k'asa zaije ya rarrashi Ruqayya dan yana jiyo sautin kukanta, amma jirin dake shirin kaishi k'asa yasa yakoma yazauna ranshi ba dad'i...Yanzu ace mahaifin Ruqayya yashigo,ya zaiji idan yajiyo kukanta?Tabbasss ko bai nuna ba amma bazaiji dad'iba,gaskiya iyayanta sun maka karamci fa.Yajijjiga kai cikin gamsuwa,sai yamaida tafukan hannayenshi yarufe fuskarshi cikin tunanin rayuwarshi. ➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Zonkwa ne shalkwatar (Headquater) k'aramar hukumar Zangon-Kataf d'in kudancin Jahar Kaduna.Babban garine matattarar jama'ar sauran jahohin Nigeria da sauran yankunan nahiyarmu ta Africa,mutanan Zonkwa wayayyun mutane ne saboda masu ilmine,babban abun sha'awar,yadda ake zaune lafiya duk da tarin bambance bambance ta fuskar addini da al'adu,ga kuma k'asar noma me albarka.Manyan yaran wannan yanki guda biyu ne Kaje(Kajawa)amma bayan yak'in Zangon-Kataf sai suka zamanantar da sunan suka koma kiran kansu da Bajju. Baranzan da matarshi Zamburan sune asalin tushen Kaje,su d'in mafarautane da suka taso daga yankin Bauchi da Jos,ance saboda sunk'i kar6an jihadin D'anfodio.ance kafin su k'araso nan, matarshi Zamburan da wasu daga cikin tawagarshi sun mutu,amma ita Zamburan ta mutune a garin Forest sai sukazo suka kafa sansaninsu a saman dutse suna kiran wajan da Kufai(Kufayi) kamar yadda akasan maguzawa nayi a can bayan gari, amma yanzu gine gine ne masu ban sha'awa awajan na sarkinsu (Agwam Bajju) hausawa masu yawan fatauci suna zuwa harkar cinikayya irin ta da,ta bani gishiri in baka manda a tsakaninsu,ga zaman lafiya, zaman lafiyar da tasa idan sun shigo cikin gari talla sai da kayayyaki kamarsu citta,daddawa,zuma dasauran dangogin su,indai kuna shiri kukace kuna son yarsu ko d'ansu to ko Insha-ALLAH zasu baku sun kuma zama naku har abadan duniya,lokaci zuwa lokaci idan sun shigo cikin gari za suzo suganku, kuma zaku kaisu wajansu lokaci zuwa lokaci.ALLAH Alhakimu sunk'i musulunci,amma sun bama musulmai kyautar mutum sukutum da guda,sun kuma san musulunci da sallar za suyi,sai su taso su girma suna musulmai,d'aya daga cikin k'ananan yaran da suka taso a cikin musulunci yar asalin k'auyan Narom ce...Itace Khadijatul-kubra inda wasu bayin ALLAH mutanan Daura su suka nuna soyayyarsu gareta mahaifanta kuma suka yadda suka bar musu ita,Bintan Daura tazama uwa a wajanta,mijinta Garban K'aura yazama uba a wajanta, tagirma suka mata aure itama ta hayayyafa d'aya daga cikin ya'yan data haifa itace kakarsu Sudaida tawajan uwa,kuma shi Abubakar (Garban K'aura) aikin d'an sanda yakawo shi garin Zonkwa shekaru masu yawa,suka zauna a gidan Amasaye itace kakar,kakarsu Sudaida ta wajan uwa. Asalin wad'anda aka tarar a k'waryar cikin garin Zonkwa Fulanine masu kiwon shanu,da mutane suka fara yawaita sai suka tashi suka dad'a nausawa cikin daji kamar dai yadda al'adarsu take, dan shanunsu su samu wadatacciyar ciyawa da ruwan sha,ba tare da sun takurama wani ba,shima kuma bai takura musu dasu da shanun suba,Ance adai-dai wajan da aka tarar da Fulani makiyayannan anan wajan aka gina musu k'aton masallacinsu na Juma'a kuma masallaci na farko a garin,kusa dashi aka gina gida da Limamin da masarautar Zazzau ta turo musu dan yadinga musu limanci,yana kuma karantar dasu addini. Ibrahim Nabarandi asalin Bakatsine ne masu yawan fatauci,bayan tashin Fulanin nan shine yak'afa cikin garin Zonkwa,gidanshi babban gida ne kun dai san zamanin da daba siyan fili a ke yiba kai zaka shaci yadda yamaka kayi gininka, shine yazama Sarkin hausawa,duk wani bak'o a gidanshi yake sauka kafin a bashi muhallin zama.Manyan zauruka(soraye) irin nada sun kai goma anan duk wani bak'o indai namiji ne zaiyi zamanshi,mata kuma akwai d'akuna a cikin gida da aka gina musamman saboda irinsu,suna mishi kirari shi Ibrahim Nabarandi da: (Naladi bawan bak'o,yan gari kuma bayinka) Su kuma Kataf(Katafawa)suma bayan yak'in Zangon-Kataf d'in sai suka zamanantar da sunan suka koma kiran kansu da Atyap,Su kuma ana tunanin asalin maguzawan Kano ne suka fito suka kafa sansaninsu a wajan,Masu yawan fatauci musamman Kanawa kowa ai yasan mutanan Kano ba cima zaunan al'umma bane,harkar kasuwanci a jininsu yake tun tale-tale,idan suka zo a nan suke ya da Zango bi ma'ana suke hutawa daga doguwar tafiyar da sukayi,bayan sun huta sai su shiga k'auyuka da sauran garuruwa dan harkar fataucinsu, to dalilin hakan garin yasamu wannan suna na Zangon-Kataf...Shi kuma asalin ma'anar"Zango Ciwon kurkunune"da yake fito ma mutum a k'afa,ko ad'an yatsa sai yakasa tafiya saboda tafiyar k'asa da akeyi a da bana wasa bane,wani zarene yake fitowa a wajan sai yayi kamar zai tsinke yatsa ko k'afar,to a inda mutum yazauna zaman jinyan da zaiyi har sai ya warke zai iya tafiya,to sauran abokan tafiya ba jiran mutum za suyiba,to idan aka had'u da wasu,ko kuma suka koma gida sai afara tambaya"ina wane? Sai abokan tafiyarshi suce ai ya ya da zango. Akan kasuwa akayi wannan yak'in na Zangon-Kataf,su Katafawa sunce sai dai a tashi daga inda ake cin kasuwar a koma inda su suke so, tak'amarsu ai sune tushen wajan,kowa yazo a bayan sune,dan haka yadda suke so dole haka kowa zaibi,Su kuma Hausawa da Fulanin wajan sukaja tunga ALLAH yakashesu kasuwa baza ta tashi daganan ba...Kaya-kaya-kaya kowa yaja ya kafe nashi ra'ayin za abi... Atakaice kenan. Sarkin Zazzau na wancan lokacin adalin sarkine,daya samu labarin bayyanar wad'annan mutannan sai ya turo wakilanshi dan su musuluntar dasu, sai dai kash... Wakilan sarki sunci amanar sarki basuyi abinda yakamata ba,sai suka bi yarima suka sha kid'a,suka sasu a k'angin bauta,su kama mata da ya'yansu wacce duk tamusu sumata fyad'e,su kwashe musu katti majiya k'arfi su tafi dasu masarautar Zazzau a matsayin bayi dan haka akwaisu da yawa a masarautar Zazzau,d'aya daga cikin ire-irensu shine Yakowa wanda har gwamnan kaduna yayi kafin ya mutu,shi yasa suke wata wak'a wai (Ba zamu ramaba ALLAH ne zai rama mana🤔) Suka tafi suka bar baya da k'ura dan da yawan matan da suka ma fyad'e sun samu ciki kuma basu zubar ba sun haihu sun mayar da ya'yan irinsu kaico! kuma da yawansu an turasu Biafara Inda Ojuku shima ya jazama k'abilarshi ta Igbo haramcin yin shugabancin k'asar Nigeria har abadan duniya"garin neman gira an rasa idanu"Bayan yak'i suma sun kwaso ganimar yak'i,duk macen data musu suma sun taho da ita yankinsu dan suma anjaza musu salalan tsiya tunda basu da kowa duk sun mutu a wajan yak'i. Suna cikin k'unci da damuwar abinda aka musu kuma ba daman ramawa kasancewar su bayi sai ga bayyanar wakilan kiristanci(Missionaries)Su basuyi abinda wakilan Sarkin Zazzau suka yiba,suka taimakesu da duk irin taimak'on dasu kaga ya dace su basu, suka dinga musu wa'azi akan addinin kiristanci (Christianity) shine addinin gaskiya,su kuma sukayi na'am da hakan suka rik'e addinin da hannu biyu,nan da nan suka waye ga kuma bayyanar ilmin boko an gina musu makarantu,asibotoci da duk abinda ake buk'ata,shine sai suka bar zaman kan dutse suka kafa k'auyuka da garuruwa suka warwatsu tunda dama sunada mugun yawa, kamar irinsu:- Fadiya. Fadan Kaje Madauci. Madakiya. Katsit. Kamurun Kaje. Ladduga. Zonkwa. Da sauran su kuma ance wasu daga cikin sunayen Ya'yan uban Bajju d'inne Baranzan aka sama k'auyuka da garuruwan. Suma Katafawa suka kafa nasu k'auyuka da garuruwan kamar irinsu:- Asha a wuce. Bakin gogi. Dama kasuwa. Mashan. Unguwan wakili. Gora Bafai. Samarun Kataf. Zangon Kataf. Da sauransu da sauransu.Amma duk da haka Kajawa da Katafawa(Bajju da Atyap) masu yawan gaske sun zama musulmai iyaye da kakanni,suna kuma musuluncin da gasken-gaske,d'aya daga cikinsu Maryam Gid'ad'o Idris, inda tazo garinsu Samarun-Kataf tagina asibiti, masallacin juma'a da makarantar addini me suna (HAYATUDDEEN ISLAMIYYA SAMARUN-KATAF) Musulman wannan yanki Hausawa da Fulani sun amfana kwarai da gaske da wannan makaranta wanda ta sanadiyyarta suka fara halartar gasar Musabak'ar Alqur'ani me girma ta Jahar Kaduna,dan manyan malamai masu addini tad'auko daga Bauchi da Adamawa,sai wasu daga garin Samarun-Kataf,da Zangon-Kataf da Zonkwa, sune suke koyarwa. Shekaru masu yawa sun shud'e, an cigaba da mu'amala cikin kwanciyar hankali kowa yana neman kud'inshi lafiya lau.Wannan kenan atakaicen takaitawane. Doctor Julaibib Abdullahi D'ansarai asalinshi d'an D'ansarai ne,k'auyene dake k'aramar hukumar Malumfashi a Jahar Katsina,suma a wayansu suke saboda ilminsu,shi k'wararran likitan mata da k'ananan yarane,yayi aiki a jahohi biyar daga nan gwannati ta turoshi wannan gari a matsayin babban likitansu,garin yama Doctor Julaibib dad'in zama shida Iyalanshi,yayanshi guda uku suka cigaba da karatunsu,suma sauran yan'uwa na D'ansarai duk wanda yazo dan ziyara sai garin yamishi dad'in zama dan haka sai yanemi canji aiki yadawo nan da iyalanshi suyi zamansu,da haka danginsu na D'an sarai suka dawo Zonkwa gaba d'ayansu aka cigaba da hayayyafa. bayan ya gama aikin aikin gwannati (retired) Sai bai koma D'ansarai ba,yan'uwa da zai koma ko dansu to suna zaune anan,yagina k'atan gidanshi yacigaba da rayuwarshi a haka har Ya'yanshi suka girma sukayi aure,da matar d'anshi Bishir ta haihu sai Bishir yama Babashi kara yasa sunan mahaifin Doctor Julaibib wato Abdullahi.Ai ko Dr.Julaibib yaji dad'in wannan kara dan haka yad'auki san duniya yad'orama Abdullahi,kome nashi na Datti ne kamar yadda yake kiranshi,Abdullahi ya taso cikin gatan daya zarce na duk sa'anninshi. zai shiga aji d'aya a secondary ALLAH yama Doctor Julaibib rasuwa mutuwar data dakesu sosai,sannu ahankali kuma zafi da rad'ad'inta yanata raguwa,kafin matarshi tagama idda itama tace ga garinku nan. Mahaifansu suka cigaba da kula dasu.koda yagama Secondary sai yafad'ama mahaifinshi yafi sha'awar kasuwanci fiye da cigaba da karatun boko,mahaifinshi yayi na'am da hakan duk shi d'an boko ne ma'aikacin gwamnati, yace kowa da abinda yake sha'awa a rayuwarshi, idan aka hana mutum abinda ya keso to an shiga hakkinshi, sai dai idan abinda ya keso d'in shari'a bata yadda dashi bane.Yakawo kud'i masu tsoka yabashi tare da mishi addu'ar ALLAH ya sanyama kasuwancin na shi albarka.Haka rayuwa tacigaba da tafiya kamar yadda tasaba har suma mahaifan nasu suka kwanta dama. Alhaji Abdullahi dattijon arzik'ine, matarshi ta aure guda d'aya da albarkan ya'ya uku, Karima,Asma'u da kuma autansu Julaibib da suke kira D'ansarai,musamman mahaifinshi.Alhaji Abdullahi yanaji da Julaibib sosai dan bai manta gata da soyayyar da Dr. Julaibib ya mishi ba. Julaibib ya taso cikin tarbiyyar musulunci,ALLAH sai yatarfama garinsu nono yarone me jin magana,duk yadda iyayan nashi suka d'orashi a haka yataso.Yana gama secondary yasamu gurbin karatu a Kaduna State College Of Education(KSCOE)Gidan-Waya,shida abokinshi kuma d'an uwanshi Musaddiq.Duk wata d'awainiya ta karatun Alhaji Abdullahi ne yayita ba tare da mahaifin Musaddiq kuma Kawu a wajan Julaibib d'in ya bada ko sisin kwabo ba. Alhaji Ibrahim shine aminin Alhaji Abdullahi tun zamanin k'uruciya abin kuma bai rusheba har girma,Alhaji Abdullahi shi yaga kanwar abokinshi yace yanaso itama ta amince aka d'aura musu aure. ➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Ibrahim Me-Lambu shine tushensu Alhaji Ibrahim,dan haka Ya'ya da jikoki da Ya'yan jikokin gidan suna amfani da Me-Lambu a k'arshen sunayen su na makaranta,wasu ma da wane ko wance Me-Lambu suke amfani.Ibrahim Me-Lambu ya samu sunan Me-Lambu ne saboda sana'arshi ta saida kayan lambun kamarsu:-tumatur,tattasai, albasa, alaiyaho,yalo,latas, karas,lafsir da sauransu da sauransu. Asalinsu yan k'aramar hukumar Tsanyawa ne ta Jahar Kano.Cirani yakawosu garin Zonkwa Iyaye da kakanni,dad'in garin da kuma k'addarar ALLAH inda ya rubuta maka zama to ba makawa anan d'in zaka zauna kome dad'i ko rashin dad'in waje,da suna zuwa ganin gida daga baya suka daina sai kalilan daga cikinsu dan suna da yawan gaske a Zonkwa,wasuma basu da sauran dangi na jini a Tsanyawa,Unguwa gudace dasu k'atuwa ta musamman da ake kira"Lungun Kanawa.Sukayi zamansu a nan suka hayayyafa. Alhaji Ibrahim matanshi na aure guda biyune,Mama itace uwargida kuma mahaifiyarsu Musaddiq,Khausar,da sauran kanninsu maza da mata.Sai Umma mahaifiyarsu Aminu,Adnan,Sudaida da tarin kaninsu maza da mata.Kan ya'yansu a had'e yake saboda matan sunada fahimtar juna,mijinsu kuma yana musu adalci dai-dai iyawarshi. ➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Julaibib yana zaune atsak'ar gidansu yana nazarin wani littafi duk da wancan makon suka samu hutu.Musaddiq yashigo da sallama,yad'an daki kafad'ar Julaibib "Haba malam an samu hutu kaima ya kamata ka hutafa"Julaibib yayi kamar ba dashi yake maganaba.Musaddiq ya jijjiga kai"gaskiya na gaisheka"yawuce dak'in Inna, tana zaune a inda ta idar da sallar walha,sai yasaki labulan"to barinje na dawo anjima".Daga ciki ta amsa"shigo ai na idar.Yazauna suna gaisawa,sai yafara mata hirar Safiyya budurwarshi da sak'on data bashi yakawo mata. Aminu shima yashigo da sallama yana fad'in shi wai D'ansarai baya gajiya da karatune Inna?Yakama ha6arshi da hannun dama"Tabbb ina ruwan Alhuda-huda,koda yake bazai gajiba tunda yafi sha'awar zaman gida, gaskiyar magana wannan da macece da sai ince ALLAH ya kashe ya ba mijinta kakarshi ta yanke saka wallahi.Inna takalleshi"kamar yaya?Yawaiwaya inda Julaibib yake zaune"o Inna aishi ya huta da fitinar mata tayawan tambayar unguwa, zani gidan wance,anyi haihuwa zan shiga barka, zanje dubiya dan gidan wance an mishi shayi, muna da biki agabas,gobe suna a arewa,jibi tarewar yar gidan wance a yamma, zani, zani, zanin mata ai bata k'arewa.Inna tayi dariya. Julaibib yakalleshi ba laifinka bane, ka ci bashi zan kuma rama.Aminu yagyad'a kai"Nima zan so haka,ina nan ina jira,yashige D'akin-girki yad'auko kunun tsamiyarshi yafito"Inna yau naci aikine kamar ba gobe,tun daga sallar asubahi sai yanzu zan koma gida.Inna takalkeshi da tausayi "Wayyo sannu,a lallai ka aikatu neman kud'i makahon aiki, ALLAH dai yak'aro masu albarka.Amin Inna nagode barinje in kwanta.To ALLAH huta gajiya. Kasham...da yaransu na Bajju yana nufin abu me kyau.kuma a zahirin gaskiya wannan suna ya dace da ita dan me kyance, matsakaiciyace a tsawo,me k'irar kalangu,gata da yalwataccen gashi me tsawo da santsi,shi yasa ba kasafai take kitso ba, manyan idanunta masu maik'o(Oil eyes)da d'an k'aramin bakin ta su suka k'ara mata kyau na musamman,wankan tarwad'a ce a yanayin kalar fatar jiki,itama dalibace anan Kaduna State College Of Education(KSCOE) Gidan Waya.Aranar farko a kuma kallan farko data ma Julaibib so da k'aunarshi suka mamaye zuciyar ta ba tare data shirya hakan ba, duk tarin samarin dake mata nacin suyi soyayya sai taji ba wanda yamata nan duniya daya wuce Julaibib,ta so k'warai a ranar suyi magana amma hak'anta bata tadda ruwaba, saboda kwarjinin daya mata lokacin data tunkareshi,ashe gaba da gabanta aljani daya taka wuta.To amma me san d'an tsuntsu shi yake binshi da jifa"naci da shishshiginta yasa suka fara gaisawa duk da idan ba ita ta gaishe shiba ko zasu had'u sau dubu a rana bazai nuna yama ta6a ganin taba. Duk inda tasan zata ganshi to in dai ba tana da lecture ba to tana wajan,yau da gobe sai ya fahimci tana neman wuce makad'i da rawa sai yadad'a kamewa,amma da Musaddiq sun saba dan suna d'an ta6a hira dan shima yana da miskilanci idan baiga dama ba,amma gangaran d'in miskilai sai "Julaibib Abdullahi D'ansarai ". Musaddiq yana zaune a capteria yana cin abinci tazo tasa meshi tana fad'a mishi "Wallahi Musaddiq na ka sa danne zuciyata,na ka sa yin yak'i da ita,gaskiyar magana ina san Julaibib zan aureshi". Cikin tsoro da mamaki yace kina san Julaibib?Yagirgiza kai"to gaskiya ki cigaba dayin yak'in wajan ganin kin cireshi a zuciyarki,baza ki samu abinda kike so...ta tareshi da sauri"me yasa za kace haka? Saboda baki dace dashi ba"wai d'an dambe ya d'auki adda"ni nasan Julaibib farin sani wallahi,kinga kuma addininmu ba d'aya bane. Idanunta suka ciko da k'walla,"wai yau ita ake fad'ama namiji ba zai so taba a yadda take d'in nan me kyau... Tayi jimmm..na wucewar wasu dak'ik'u "Musaddiq kafad'a mishi "ni Kasham tanuna kanta ina sanshi,ina neman goyon bayan shi ya yadda muyi aure,na mishi alk'awari zanyi abinda yakeyi (Sallah)zanbi addininshi (Musulunci) Abincin da bai gama ciba kenan yamik'e dan zata dame shine kawai.Tabishi da kallo dan ALLAH kafad'a mishi.Ya amsa da To. Rannan tana zaune a d'akin karatu, nazari da bincike(Library) ta ka sa yin abinda yakaita tunanin Julaibib ne kawai yacika kanta,kamar ance ta d'ago kai sai kawai gashi yashigo dak'in,yaja kujera yazauna. Ganinshi yak'arasa kashe mata jiki, tanajin wani sabon yanayi daya tsirga ilahirin jiki da zuciyarta,gefe guda kuma tana jin takaicin k'in kar6an tayin soyayyar data keta mishi naci duk da kasancewarta k'wararriya data isa da kanta in dai a fagen hilatar d'a namiji yafad'o tarkon tane,ba wanda ta ta6a d'anama tarko bai fad'aba sai Julaibib,ta rasa me zatayi dan shawo kanshi,dan abinda takeji game dashi ba irin abinda takeji game da sauran maza bane,wani irin abune me sark'ak'iya,me zagaye ilahirin gangar jiki da zuciya,ita kanta bata san ya zata fassara shiba wallahi.Tasake kallanshi rubutu yakeyi cikin natsuwa,takad'a kai. "Julaibib...you're an enigma". Ahankali ta furta hakan,sannan tabi d'akin da kallo mutane dayawa sun gama abinda yakaisu sun fita,saita samu k'warin gwiwa koda zai wulak'anta ta bazai mata ciwo dayawa ba tunda mutane kad'anne. Tamatsa gaban kujerar dayake zaune,tasunkuyo tana kallan fuskarshi"Sannu da aiki Julaibib...tafurta hakan da wani salo irin na ta na yanga.Bai d'ago ya kalletaba kamar yadda take fa ta,bai kuma amsaba "shiruma amsace"rubutun shi kawai yakeyi. Tatsareshi da manyan idanunta masu maik'o,ya mata kyau cikin fararan kayan,yau kanshi ba hula,kwantaccen bak'in gashin kanshi yanata sheki da k'amshin irin mayukan gyaran gashi da yake amfani dasu,jikinta ya gama mutuwa murus,ga k'amshin arabian perfumes d'inshi yadad'a jefata a wani irin yanayi,ta lumshe idanunta wani murmushi ya su6uce mata "ALLAH dai yakai damo ga harawa ko baiciba yayi burgima"taja dogon numfashi tana zuk'e k'amshin,ahankali kuma tafara fesar da iskar tabaki ta hanci sannan tabud'e idanunta tacigaba da mishi kallan k'auna me cike da shauk'i har yagama rubutun,yatattara takaddun daya shigo dasu a gefe, yakwashi wad'anda yad'ibo a d'akin yamayar dasu mazauninsu. Magana take mishi amma yayi kamar ALLAH baiyi ruwan tsiran taba,ganin haka yasa tayi saurin k'arasawa bakin k'ofar da zai fita ta tare hanya sai yaja yatsaya. Please...Julaibib... Magana nake so muyi please...tahad'a tafukan hannayenta alamar magiya."please Julaibib, wallahi with all my heart ina sanka,kana burgeni, me zai hana ka aureni? Yagirgiza kai"Bazan iyaba.Idanun ta suka ciko da k'walla"wai kai wannan amsar ta "Bazan iyaba"bazata bar bakinka bane D'ansarai? Wai me zan yine da zaka so ni Julaibib?Yakalli agogon dake d'aure a hannunshi nadama tana 6ata mishi lokaci fa. Ki matsa zan wuce.Tasake kallanshi "Julaibib zanyi sallah fa...yad'ago yana mata rikitaccen kallanshi "Ki bani hanya nace ko? Yafurta hakan da 6acin rai a fuskarshi. Yamata wani irin kwarjini data kasa aiwatar da k'udurin zuciyarta.Sai tagyad'a kai ta kuma matsawa a kofar"shi kenan zo ka wuce.Ya ra6a ta gefenta kamar wanda akace idan ya ta6ata ya gama amfani a doron duniya. Tabi bayanshi da kallo har ya6ace ma ganinta...sai tayi d'an yak'e mak'alallun k'wallan cikin idanunta suka samu damar d'igowa a kyakkyawar fuskarta, sai kuma wani sanyi-sanyi data faraji, tsigar jikinta yana tashi alamar zazza7i yana so yakawo mata ziyara. Harshenka zakinka idan kasa keshi yacin yeka"... 11 Rabi'a Thani 1441 8 December 2019 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2 geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in. ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na biyu. Musaddiq yashigo da sallama, yad'auki ya zauna yasha,sannanya kalli Julaibib "sak'o aka bani wajanka...sai kuma yaja yayi shiru. Yad'an d'ago ya kalleshi"Uhun ina jinka sak'on me? Yaciro d'an k'aramin kati launin ruwan k'asa yanata kyal-kyali yamik'a mishi "karanta kagani.Kasham ce take gayyatar su party dan murnar zagayowar ranar da aka haifeta(Birthday) ranar talata a Bigard Hotel. Yad'ago yana mishi wani rikitaccen kallo "nasha fad'a maka yarinyar nan ta daina aiko ka wajena kana zuwa kana fad'amin ko?Ya jijjiga kai"to ba laifi ka cigaba amma abinda zan maka zaka sha mamakinshi wa...bai bari ya k'arasa ba shima yatareshi"ba laifinka bane nawane ainan d'in tace za tazo tasame ka da kanta, ni kuma sanin da nayi baka san hakan yasa nace mata ka tafi Matsirga amma takawo in ajiye maka da...shima Julaibib ya tare da sauri..."na tafi Matsirga,na tafi Matsirga fa kace?To saboda me zaka min k'arya?Ganin ranshi ya 6aci yace"kayi hak'uri D'ansarai.Baice komai ba yakoma yakwanta,duk sukayi shiru,zuwa can Musaddiq yasake kallanshi."Kasham da gaske tana sanka Julaibib, ko zamu d'an lek'a matane ko na rabin awa dan itama taji dad'i yaba kyauta tukwuici.Yagalla mishi harara"idan zakaje to ni ina ruwana?Musaddiq yayi murmushi"D'ansarai autan Inna me duniya.Inje kuma?To ni asuwa?Kare da gudun laiya?Da dai zakaje dana maka kara na rakaka. Yamik'e ni ga ka tafiya ta wajan Safiyya,yamik'a mishi hannu sukayi musafaha"Ka gaisheta.Musaddiq yad'an zaro idanu dan mamaki "Wuuu yau wace rana Julaibib yaji zanje wajan masoyiyata yace agaisheta? Julaibib yamik'e zaune da sauri,yana k'ok'arin kai mishi naushi yagoce yana dariya, ah ka ga mugu da 6allallan kafad'a kake so inji hirar"uu tambayata kakeyi?To tsaya yanzu zaka gani ya yunk'ura zai mik'e Musaddiq yafito daga d'akin da gudu yana fad'in "mu had'u a gidan Hajiya bayan sallar la'asar". Agajiye yashigo gidan,dawowar shi kenan daga Kaduna.Yaya Karima ta tareshi "oyoyo barka da dawowa.Yauwa Yaya Karima.Yacire takalman shi masu rufi,sannan ya zauna a tabarmar tsakar gidan suna gaisawa.Inna tafito daga D'akin-girki"lale D'ansarai autan Innar shi"sukayi dariya to gashi,ruwa tabashi a k'aramin kwanan sha. Yakar6a"nagode Inna.Da bismillah yafara shan ruwan,ruwan randan Inna me dad'in gaske ga wani irin sanyi,kowa kuma ya san ruwan randa sanyin shi baya cutarwa,ga k'amshin saiwoyin da take sawa a ciki da suke k'arama ruwan armashi wajan sha.Kad'an yarage sannan ya ajiye kwanan cikin hamdala ga ALLAH.Yakalle ta"Inna ruwan randarki gard'i da d'and'anonshi har yafi ruwan roba Swan.Sukayi dariya. Abdullahi babban d'an Yaya Karima yayi sallama ya shigo yana rik'e da hannun k'anwarshi Kamila da take kuka."Mama ga tanan tak'iyin shiru tunda ta dawo daga makaranta,wai me yasa baki bari an taso suba kikayi tahowarki.?Ya k'arasa wajan Kawunshi cikin murna "Kawu sannu da zuwa,sannan ya gaisheshi.Yarik'o hannunshi "Yauwa Abdul yakaratu?Ya d'ibo Inibi to ga tsarabar ka.Abdul yasa hannu biyu yakar6a"nagode Kawu ALLAH amfana. Karima takalleshi kwana biyu ka daina zumunci sai Musaddiq kad'ai yake sadar da ita."Baban Abdul dai yagaji shine yace in biyo sawu ko mun maka laifine"?Yayi murmushi yana shafa kai"Yaya Karima ba kumun laifi ba,bana samun lokacine amma Insha-ALLAH wannan Juma'ar zan shigo kin san tsarin karatunmu ba d'aya bane.Ta gyad'a kai"hakane Ubangiji yanuna mana Juma'ar.Ya amsa da amin. Wata magana zamuyi.Sai ya tattara hankalin shi ga sauraran abinda zata fad'a."Julaibib me zai hana kafito da yarinyar da kake so a had'a bikinka dana Musaddiq?Ina sha'awa k'warai ace yadda kuke kome tare to lokacin aure ma ku angwance tare.Yagirgiza kai"ni bani da budurwa ma, ki tayani addu'a ALLAH yakawo tagari.To amin. Amma duk yan matan Gidan-Waya ba wacce ka k'yasa?Yad'anyi tsaki'ni fa ba tsayawa kallansu nake yiba,abinda yarabani daku,yakaini can d'in shi nakeyi (karatu) Musaddiq yashigo yatarar da zancen, yace tab shi autan Inna sai a hankali kuma gashi da farin jini a wajan yan matan amma kowacce sai yace bata da kamun kai,bayan shi kanshi ya sani a shari'ance ba haramun bane dan mace ta yaba da kai tafurta maka kalmar k'auna.Musaddiq yaja dogon tsaki yana hararar Julaibib saboda tuno abinda yata 6ama yar course d'insu..... Atikah Aliyu Kagoro. Jikar Sarkin Kagoro ce tana da hankali da natsuwa kuma k'wak'walwannar dai Ubangiji ya hore mata shi na fahimtar karatu,Malamai ma ji da ita sukeyi bari d'alibai yan karankad'a miya.Tunda taga Julaibib tace nan duniya ba wanda yamata da aure kamarshi.sai dai kashhh...yawatsa mata k'asa a idanu.Atikah Aliyu Kagoro tayi kukan rashin shi. Rannan tazo wajan Julaibib d'in amma bata same shiba sai Musaddiq shine take fad'a mishi zata bar makarantar saboda ba zata iya cigaba da ganin Julaibib ba bayan yace baya ra'ayinta,ita tanaso yasota da zuciyarshi ne ba yaso ta dan an tursasa shi an mishi dole ba,amma badan haka ba tana kai maganar nan wajan Me Martaba to anyi angama maye ya auri ramammiya, Julaibib zai zama mijinta dan bai isa Sarki yabashi auren jikarshi yace baya so ba"ai wata fuskar ta fi gaban mari har abadan duniya"tad'ibo wasu damin sababbin kud'i tabashi,ya girgiza kai ki barshi kawai.Sai tad'an harereshi "kai karfa ka 6atamin rai dan ka san kai ba Julaibib bane,dogarai zansa su baka na jaki".Sukayi dariya.Yagyad'a kai"wannan gaskiya ne ranki yadad'e. Ta sake mik'a mishi"To d'an ALLAH ka kar6a.Yasa hannu biyu ya kar6a yamata godiya, sannan ya d'an kalleta"yanzu Atikah kin bar karatunki kenan?Tagirgiza kai"zan koma wajan Mahaifina a Saudi-arabia,dama tun daga yaye zamana ya d'ore anan,bayan na gama Secondary d'ina yaso k'warai in koma can in cigaba da karatu amma nace nafi san nan,ba dan ya so ba yahak'ura,saboda ni tagaban goshin Me Martaba ce,abinda nake so to dole kowa ma yahak'ura yasoshi indai yana neman zaman lafiya dashi. Da jami'ar Abuja zan tafi amma nace ni nan nake so,ni kaina kuma ban san dalilin dayasa na za6i nan d'in ba,ashe k'addarar had'uwa ta da wannan miskilin d'an uwan na kane zai zama silar koma wata wajan mahaifina wanda dama ba abinda yake so sama da ya ganni kusa dashi,saboda mahaifiyata lokacin da data haifi k'anina ko ganinshi batayi ba ta rasu,da yammacin ranar shima abinda ta haifa yace ga garinku nan,mutuwarta ta dakeshi sosai saboda suna san juna suna zaman lafiya. Yadad'e baiyi wani aure ba,auran da yasa ke ma Me Martaba ne yagaji da ganinshi haka ya aura mishi matar. Saboda ni duk lokacin daya samu sarari yake zuwa Nigeria kasarmu ta gado. Musaddiq ya kuma jan dogon tsaki fiye dana d'azu ALLAH yashiryeka.Julaibib yayi murmushi"amin shiriyar da ba ta ALLAH ba shirme da shiririta ce kuwa ,amin nagode". Shi da Inna suna zaune a tsakar gida,yana 6arar gyad'a Inna kuma tana gyaran tsakin masara, jefi -jefi suke magana, saboda shirin da suke sauraro a gidan rediyo. Assalamu alaikum. "Inna tana nan...? Daga zauren gidan suka jiyota.Cikin murmushi suka amsa sallamar.Inna tarage sautin rediyon "maraba da yar gidan Inna,to shigo mana kya tsaya a zaure kamar wata bak'uwa?Tashigo tana yar dariya"Inna na yi laifi na zaci kinyi fushi ne shi yasa naji tsoron shigowa kai tsaye"Dan ALLAH Inna kiyi hak'uri.Tazauna tana kallanshi"barka da warhaka Yaya Julaibib,Ina kwana.Yad'an shafa kai,tare da dauke kai daga kallan da take mishi. Sudaida...Lafiya lau, ya karatu'? Alhamdulillahi gashinan muna tayi ba kama hannun yaro. Tajuya wajan Inna tana gaisheta. ALLAH Inna jiya dakika aiko mantawa nayi da aka tashi daga makarantar allo ban shigo ba.Inna ta girgiza kai"ba kome nima nayi tunanin haka.Tasa hannu ta d'ibo gyad'ar tana tayashi 6arewa,yau za musha fate kenan?Inna tace wai da dambu zanyi. Tad'an k'aryar da kanta gefen dama"kai Inna gwamma dai faten,kin san Hajiya(Kakarsu)tafi san shi,zaifi armashi ma idan Yaya Julaibib yaje yasiyo mana tantak'washi.Yad'ago kai yana kallanta"ni zanje insiyo miki tantak'washi?Tace to ai da Hajiya da Inna za musha.Baice komai ba yamik'e yashiga dak'inshi, bai dad'e ba yafito yanasa hula,yama Inna sallama yafita... Sudaida tad'an d'aga murya karfa ka manta kaji?Yak'arasa ficewa.Shiruma amsace. Sai bayan sallar azahar suka shigo shida Musaddiq.Tace yauwa na ma huta dama yanzu nake shirin biyoku shago.Musaddiq yakalleta "ta samu kenan,idan kaji gangami da labari.Yabud'e kwanan data ajiye agabansu,tana murmushi"Yaya Musaddiq chips d'in gwaza namuku tunda baku cika san shan fateba"Yad'auki d'aya yakai baki,kai wannan yarinya da iyayi kike wai zuwa kashin rana da fitila.To Yaya Musaddiq chips lallai sai da dankalin turawa?Gobe ma da dankalin hausa zanyi. Julaibib yamik'e"kici lafiya...kai zo mutafi gidan Hajiya baza a rasa abincin arzik'i acan ba.Haushi yakamata"to wannan na tsiya ne?A ah sai dai shima chips d'in bazan ciba. Inna tasa baki"kai baza a maka gwaninta ba kenan?Ya waiwaya ya kalli Sudaida da wani irin kallo data kasa fassarawa"ni nasa ki? Tagalla mishi harara dan ba k'aramin haushi yaba taba,shiruma amsace ta shige D'akin-girki dan k'arasa abinda takeyi.Taja tsaki"shi wannan D'ansarai autan Innan ALLAH yasawwak'e mishi". Yana wankin kayanshi tashigo gidan, Asma'u ce ita yake bi.Takalleshi"manya ba a ganinku sai an cike foam,foam d'inma sai wanda ake buga mishi stamp.Yayi murmushi"Yaya Asma'u ban kai nan ba,wa ne kare da hantar kura?Barin dai k'arasa inzo mugaisa.Tawuce d'akin Inna suka gaisa,sai ta mik'e"barin lek'a d'akin autan na ki ko zan samu abun sawa a bakin salati.Tashige ciki tana mishi bincike. Yagama shanya kayan sannan yabita,baiji dad'in abinda ta mishi ba,gaba d'aya ta hargitsa mishi d'akin,har kayan sawanshi na cikin akwati sai da ta bincike.Yazauna yana kallanta cikin zancen zuci "Yaya Asma'u yar sa'ido ce ta gaban kwatance, da shiga sharo ba shanu,kamar wata yar C I D,kaza dai garin tone-tone wata rana zata tono wuk'ar yanka ta. Takalleshi"kai d'akin na ka ba wani abu da mutum zai kai bakinshi zuwa uwar hanji sai tarin littafai kala-kala?Yana tattara littafan data hargitsa yace"to dama me zaki samu a d'akin talaka kuma d'an makaranta?Aike zaki taimakamin koda da yar dubu goma in k'ara na Hand-out da 'yan wasu abubuwan,kinga kinyi halin girma,ladanki yana wajan ALLAH.Lallai yaran nan ka ci abinci sauranka ruwan sanyin randan Inna.Yanzu duk cikinmu akwai wanda ke cin kud'in Baba kai harma da Innan kamar ka? "Ni?yanuna kanshi da d'an yatsanshi"sharri dai ba kyau Yaya Asma'u.Tad'an harareshi tana dariya" za ka fad'i haka mana.Yagyad'akai"ALLAH Yaya Asma'u tunda ke hajiya ce kamata yayi ace kin d'auko ma Inna yar aiki,kina biyanta duk k'arshen wata,ni jarin nawa baiyi k'wari bane dani zanyi hakan. Tamishi wani kallo"ALLAH sarki, Inna ce za a d'auko ma yar aiki?To ina abun yake wai maye ya cinye jariri?Tabbb...kai akwai ka da san kashe kud'i na ba gaira ba dalili,amma fa harda dan baka san yadda ake wahala wajan nemo su bane.Na sani mana tunda nima ina sana'a.Ta tareshi da sauri "A ah ban yadda ba sana'ar taka har wata sana'ace da zaka fad'i wahalhalun cikinta?Kuna komawa Gidan-Waya Baba zai cigaba da kula muku da kome, kaga ai yafiku shan wahala daga kai har Musaddiq d'in,ko zirga-zirgan da yake yi tsakanin nan da Kaduna ai bakwayi.Hun Julaibib arzik'i gashin hancine rabuwa dashi ba dad'i,kabari sai ka gama karatun,ka fara sana'a ka'in da na'in sai muyi zancen. Yace to Ubangiji yanuna mana lokacin. Dama so yake yaji me za tace, amma ai ya riga yasan halinta na rowa,indai maganar kud'ine kuma itace zata bayar tofa sai anyi tata6urza,sa6anin idan itace zata kar6a yanzu mutum zai sha dogon lissafi da sharhi.Tamike" kai ni barinje wajan Inna baza a rasa abun kaiwa bakin salati ba.Yagirgizai kai"yanzu haka da abinda yakawota gidan,kuma abun tirrrr d'in tana da rufin asirinta dai-dai gwargwado dan tafi Yaya Karima ne sa ba kusa ba, amma Yaya Karima ta fita wadatar zuci. Da safe kafin Inna tafito ya gama had'a karin kumallo,yashare tsakar gidan,ya wanke bayi,tafito tana shi mishi albarka kamar yadda tasaba "Ubangiji yamaka albarka, yarufa maka asiri duniya da lahira. Yayi murmus"Amin Innar mu ALLAH yabar manake, yad'an kalleta"nifa yar aiki zan d'auko miki Insha-ALLAH kafin mukoma makaranta, ayyukan suna miki yawa,ni kuma a yanzu ina san ganinki cikin jin dad'i da hutu.Tayi yar dariya"to banda abinka Julaibib ina aikin yake da har za a d'auko maiyi?Dagani sai Alhaji,idan kana garine muke mu uku fa.Tagirgiza kai "ni kam nagode,da duk ya'ya haka suke jin tausayi da soyayyar mahaifansu to da al'umma ta kasance cikin tsabta da kwanciyar hankali mara yankewa,nagode maka gaya amma kabar zancen yar aiki,kai baka san 'yan aikace-aikacen ma motsa jiki bane?Na sani Inna"to kibari asamo miki koda wacce zata dinga miki hidimar tsakar gida,ke kuma kicigaba da yin abinci. Ga kayan motsa jikina nan ba sai ki dinga amfani dasuba.Inna takama ha6a🤔tana dariya"Wuuu rabani da wuyu"kashin k'ota"kayan motsa jiki na zamani ai sai ku,ni ina zan iya da wad'annan k'arafa da na'urori? ALLAH dai yamaka albarka autana.Yayi murmushi yana shafa kwantaccen bak'i gashin kanshi me shek'i da kyallin irin mayukan gyaran gashin da yake amfani dasu. Suna gama karyawa yamata sallama yatafi shagonsu dan neman na halali,dansu an d'orasu a kan dogara da kai a hakan kuma suka taso,ba dogara da kud'in mahaifa ba... Yana sanye da farar shadda,kanshi da farar hula zita,sai bak'in takalmi sau ciki,kafad'arshi ta dama rataye da dudduma,dawo warshi kenan daga sallar juma'a.A tsaye yake a k'ofar gidan yana tunanin kawun nashi jarumin mutum ne me kamanta adalci a komai nashi,ga shi yanaji da mahaifiyarshi da gasken-gaske,yana mata wata irin k'auna ta ban mamaki,kafin asamu me halinshi sai an tona,dan yafifitata sama da mata da ya'ayanshi,yar gatan tsohuwa kenan data kerema duk tsofaffin k'arninta, kai ita Hajiya ALLAH yamata gyad'ar dogo sama ya'ya,k'asa ya'ya tsakiya ma ya'ya,gaba d'aya ya'yanta takwas babu k'ashin yarwa. Kai Julaibib ka tsaya awaje kamar wani bak'o me jiran abashi izinin shiga?Hajiyace, yakalleta da murmushi"to ai dama ke nake jira "bismillah muje...Suna tafiya suna hira har suka shiga cikin gidan.Musaddiq yafito daga d'akinshi, kaga ban tsaya jiran kaba, wallahi a sahun makararru natsaya,idan su Baba suka fito suka hangoni a haraban masallaci kasan zan sha fadane.Kamar ba dashi yake magana ba yashige d'akin yad'ebi wasu takaddu zai fita,Musaddiq yakalleshi bari akawo mana abinci mana dama kai nake jira. "Bazanciba" Ah bazaka ciba kamar yaya? "Azumi nakeyi" yabashi amsa atakaice. Azumi yau juma'a? Yagyad'a kai "Eh azumin tsakiyan wata sha uku,sha hud'u,sha biyar,to yau sha uku ga wata.Yagyad'a kai"ALLAH yabada lada"yafara kiran Sudaida,Sudaida,shiru Khausar nan ma shiru sai yamik'e to ina jin basanan barin d'auko da kaina,suka fito tare shi yawuce wajan Hajiya, Musaddiq kuma yatafi D'akin-girki d'auko abincinshi. Sha d'aya da rabi a sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar asabar aka taso su daga makarantar allo, tana sanye da bak'ar abaya da farin hijab,da wasu littafan addini a jakar data rataya a kafad'a,allanta kuma ta rik'e a hannu.Suna zaune a dogon dakalin tazo tawuce kamar bata ganshi ba. Yamik'e da sauri yabita"haba ranki yadad'e Sudaida Sarauniyar Sinan,me yayi zafi haka idanu suke cin wuta?Takalleshi da 6acin rai"wai dan ALLAH kai baka da wajan zamane sai a cikin yan maro (Wiwi)? Zama da mad'aukin kanwa fa yana kawo farin kai. Yagirgiza kai cikin damuwa "Sudaida ba yadda zanyi da sune,ina zaune zaman jiranki suma sukazo suka zauna,wajene na kowa to ya zan musu?Khausar tazo tawucesu da takaicin Sudaida,ta rasa abinda yaja hankalinta wajan soyayyar Sinan. Bakice kome ba.Sinan yakatse shirun. Tad'an harareshi"ALLAH yaso ka na na huce.Yayi dariya tare da shafa k'irjinshi bangaren da zuciya take.Yauwa ko kefa,kinga yanzu hankalin masoyi ya kwanta.Sukayi hirarsu sannan yataka mata kad'an sukayi sallama,yaso yarakata har k'ofar gida amma tace nan ya isa, dan tasan su Yaya Musaddiq suna wajan da autan Inna,kuma ba tasan wannan rikitaccen kallannashi me ban haushi dan ba magana zai yiba..Taja tsaki"ALLAH yasauwak'e mishi wannan halin... Nagari ake so ba d'an gariba. 13 Rabi'a Thani 1441 10 December 2019 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD... 2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in. ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin 🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na uku. Kasham tabaro k'auyansu Madauci da yammacin ranar talata,bayan taji sauk'i daga jinyar da tayi na tsawon awanni ashirin da hud'u.Tashiga cikin makaranta da d'okin ganin Julaibib ta kuma hango shi a inda suke zama.Tak'arasa da saurinta "Barkanku da yammaci"Maimun abokin karatunshi ya amsa"Yauwa barka dai.Tatsare Julaibib da manyan idanunta masu maik'o cikin kallan k'auna me cike da shauk'i "kai bazaka amsaba kenan?Iskar data d'ibo tama bata isheshi kalloba.Tayi jimmm...na wucewar wasu dak'ik'u tana kissima wani abu a zuciyar ta,sai tad'an motsa kafad'a any way...sai anjima. Tajuya tayi tafiyarta tana murmushi. Julaibib my enigma man...Salonka yana k'ayatar dani wallahi"... Maimun yakalleshi"Kai nifa bangane ma wannan bita da kulli"dukan kabarin kishiyan ba"Meye had'inka da itane duk inda taganka sai tazo wajan?... Julaibib yafad'a mishi kome.Maimun Yagyad'a kai "to ka yadda mana tunda har ta amince za tayi sallah ba kuma wanine ya tilasta mataba,ai inaga ba wata matsala,kuma kayi jihadi ne,gata kuma Masha-ALLAH kyakkyawace.Yamik'e yana mishi wannan rikitaccen kallan nashi"bazan iyaba.Maimun zai sake magana yad'aga mishi hannu"dakata haka malam, taso mu tafi.Maimun yagirgiza kai "ba d'akin da zan tafi yanzu gwamma in d'anyi shawagina.Yajuya yayi tafiyarshi to shikenan. Yana shiga d'aki ya ajiye Hand-out, yasa hannu yana 6alle botiren gaban rigarshi tare da lumshe idanunshi a kasalance,yacireta rigar yajefa a saman kujera,ya gaji lik'is ga rashin bacci,dan baiyi wani baccin kirki a daren jiya ba saboda karatu da binciken wasu littafai da yake yi na tafsirin Alqur'ani me girma,idanunshi har wani yaji-yaji sukeyi,a a hankali yafurta"yau da wuri zan kwanta... "Zanzo tayaka kwana... Bazato yaji an mishi wata irin runguma ta baya,zuciyarshi tabuga dammm...dan wallahi yaji tsoro... "Zanzo tayaka kwana tunda Musaddiq baya nan.Tafad'a cikin rad'a Kasham...zuciyarshi taraya mishi, tabbasss ita d'ince danga k'amshin turaranta nan... Yayi k'ok'arin raba ta da jikinshi amma ya kasa,dan ruk'on kura taga nama ta mishi... Kanshi yayi wani irin sarawa. Tafara mishi wani salo da hannayen ta a cikin gargasarshi dake kwance lufff bak'ink'irin da sheki...kar...kar...kar...Jikinshi yad'auki rawa"baah...ba... bahh..banasooo!...dak'yar yafuzgo furucin.Tayi lallausan murmushi tad'ago kanta tana kallan kwantaccen bak'in gashin kanshi... Meye baka so din...??? Yayi shiru.Tagyad'a kai"tayaka kwannanne baka so ko wannan din?tacigaba da mishi wani salo da hannayenta a dai-dai saitin zuciya... Jikinshi ya mutu murusss... My enigma say something hun" Tasake fad'a cikin rad'a da wani irin salo na ta nayanga.Yadaddage ya hankad'eta...tafad'i tabaya akan katifarsu.Hanyar fita yayi sai dai abin mamaki "talaka da mata hud'u har da k'wark'wara me gari gwauro"ta kulle k'ofar dan dama baiji shigowarta ba. Daga kwancen take kallanshi, yasunkwui da kai,gaba d'aya ya jike sharkaf da zufa kamar wanda yad'auki awanni yana matso jiki.Wata jijiya tafito asaman goshin shi rad'am kamar shatin bulala ranshi in yayi dubu ya 6aci...Amma jikinshi ba k'arfi kona sisin kwabo kamar wanda aka zarema laka. Sai kuma jikinta yayi sanyi, tasan itace tasashi a damuwa tamik'e tsaye"Kayi hak'uri Julaibib "tahad'a tafukan hannayenta"Dan ALLAH kayi hak'uri ba naso ace ta dalilina kashiga damuwa,danni me k'aunar kace,farincikin ka shi nake so ba damuwa ba.k'walla yacika idanunta... muryarta tafara rawa Bazaka hak'ura bane D'ansarai? Yadda tayi furucin a hankali da wani irin salo,yasa yad'ago zai kalleta,itama shi take kallo caraf idanunsu yahad'u,yakauda kai dasauri yanajin wani irin abu yana zagaye ilahirin jiki da zuciyarshi,shi yasa baya san kallan wannan manyan idanun na ta masu maik'o.Kawai sai ta fashe da kuka,tsoro da mamaki suka baibayeshi to me aka mata wai??? "Kasham... Yafurta sunan dak'yar.Tad'ago da sauri tana kallanshi.Sai kuma yayi shiru kamar me koyan had'a kalmomi da yadda ake furtasu.Idanunshi sun kad'a jawur. Julaibib kayi hak'uri dan ALLAH". "Bakomai...Tayi murmushi yau wace rana ya mata wata magana ta daban ba amsar daya saba fad'aba na "Bazan iyaba"saita kalleshi "to za ka aureni?Yayi shiru kanshi ak'asa.Tad'an motsa kafad'a. Tana zuwa kusa da k'ofar ya matsa da sauri kamar zai hantsila.Tayi yar dariya"Matsoraci kawai "ni ba abinda zan maka yanzu amma duk ranar daka shigo nan tanuna tsakiyar tafin hannunta na maka kattt...kisan mummuk'e,sai tayi d'as d'as d'as da yan yatsunta wani murmushi ya su6uce mata. Tamishi wani kallan k'auna me cike da shauk'i...Tabud'e k'ofar tayi tafiyarta.Yasauke gwauran numfashi "wallahi da basu da lecture gobe da sassafe da yau yayi tafiyar shi gida kamar yadda Musaddiq yatafi.Yamaida k'ofar yarufe da sak'ata yasa mukulli sannan ya kwanta cikin wani irin yanayi. Tana zuwa d'aki tafasa ihu tafad'a gado.Lidiya da suke yan'uwa kuma d'akinsu d'aya sai dai kowa da abinda yake karanta kamar dai Julaibib da Musaddiq tabita da kallo sai juyi take cikin wani irin yanayi,tabar yanka ganyen Ogu da take yi na abincin darensu,tazauna agefen gadan. "Inzayadami Kasham?(Meyafaru Kasham) Kasham tacigaba da juye-juyenta cikin wani irin yanayi,zuwa can kuma tamik'e zaune, tajingina kanta ajikin gadan cikin sanyin murya tace " Julaibib ne" "Jesus Christ! Holy ghost fire!!! Lidiya tafad'a tare da dafe kirji da duka hannayenta,tabita da kallan takaici taja dogon tsaki, wallahi kinji kunya,wai dan ALLAH me kika ganine ajikinshi daya tafi da hankalinki haka? Dogone k'akk'arfa,kar kuma kimanta Baranzan wanda kukayi alkawarin aure dashi,shima haka yake,ke ya mafi Julaibib tunda shi Sojane training d'in da yakeyi shi ko rabin-rabinshi ba ya yi, sunansu kuma d'aya"Maza"ko akwai wani abu bayan haka?Tayi lallausan murmushi"taja dogon numfashi a hankali take fitar da iskar tabaki ta hanci.Sannan tace"Hummm...Lidiya kenan ai maza kama suka tara amma halinsu ya bambanta. Tagalla mata harara"kin gama asara,ni dai banga abin so a wajen me shegen girman kai ba,shi ba kowan kowa ba dillalin kashi.Sannu wannan dazai amsa miki da yauwa sai yaga dama amma ke kina neman haukacewa saboda shi...kai tirrr...wallahi tayi d'as da yan yantsunta takoma kan girkinta tana mita Rubbish girl... Kasham tazame takwanta"duk abinda zaki fad'a indai akan san D'ansarai ne bazai ta6a tasiri a zuciyata ba har abadan duniya, ina san shi koda shi aka tarama munanan halayen jama'ar duniya,ni na san ko waye Julaibib,ba shi da wani girman kai"so hana ganin laifi... Suna zaune a shago jadawalin bikin Musaddiq d'in suke dad'a dubawa,dan saura kwanaki goma sha biyu.Tayi sallama daga waje tana sanye da riga da zani da dankwali na atamfa ruwan goro da ratsin k'ananan filawoyi ruwan madara da Bak'i,tayafa bak'in mayafi takalmanta bak'ak'e abinci takawo musu. Wa alaikumussalam shigo.Tana shiga idanunsu yahad'u,yad'an saki fuska"yau Baba yayi tafiya sai zuwa yammaci zai dawo, ni kuma ban san irin garar da yake had'a muku ba idan kun kawo abinci"rake zan sha"sai Maths text book da Graph-book da za a sai mana ni da Yaya Khausar. Banza yar k'auye,tafi kibamu waje, ba dama a tambayeta me take so sai tace"rake"to ba za a sai rakenba.Julaibib yad'aga mishi hannu "a ah malam shan koko fa kwanciyar rai,to me yamaka zafi?Yamaida kallanshi wajanta"koda yakema idan fitsari abin banzane kaza ma tayi mana.Ta sunkwui da kai"kowa yayi zagi a kasuwa ya san da wanda yakeyi,shine ko nama a wasu lokutan baya iyaci duk san shi da nama kamar kura sai gani sai hange idan ciwon hak'orinshi ya motsa. Me kace? Musaddiq yatambaye shi fuska a yamutse.Abinda kaji na fad'a"ke Sudaida jeki ki...sai kuma yamik'e ina zuwa.Dakanshi yasiyo musu Maths da graph d'in yakuma kar6o musu gasassun kaji guda biyar,d'aya ki kaima Inna,biyu nasu Mama,ku kuma dukkanku kuyi hak'uri ku raba biyun.Tasa hannu biyu takar6i ledojin"mungode Yaya Julaibib".Yakauda kai daga kallan da take mishi.Jeki kinji karki daka ta wannan da hidimar aure tasa kanshi yake shirin yin gobara... mutum bai kar zomo ba sai kiga yana shirin ba shi rataya.Tawaiwaya inda Musaddiq d'in yake,shima su yake kallo.Sai ta toshe bakinta da sauri kar dariyar da take 6oyewa ta su6uce mata tashiga uku,idan yakoma gida da daddare zai iya bata na jaki...tajuya dasauri tabar shagon.Julaibib yabita da kallo fuskarshi da murmushi. Yauma Musaddiq ya rigashi komawa gida tun ranar laraba yatafi,Maimun ma an aiko mahaifiyarshi bata da lafiya shima yatafi.Yana fitowa daga masallaci yanufi d'akinsu dan yanajin yunwa shi kuma yafi gane yadafa abinda zaici fiye da yaje capteria,yana da miya dan haka yadora farar shinkafa yazauna yana yayyanka kabeji, tumatir albasa da gurji.Tana jingine da bishiyar barankaci tana hangoshi dan abaranda ya zauna saboda cikin akwai zafi kuma ba wuta,tana mishi kallan k'auna me cike da shauk'i,shi ko baima san tanayi ba kunu a mak'ota.Tasauke numfashi tana kiran sunan shi a saman la66anta wani murmushi yasu6uce mata ranar da duk ALLAH yabani sa a akanka?....Hummm tagyad'a kai"d'aurin gwarmai za kasha amma na k'auna... tajuya tafiyarta. Hajiya tashigo da sallama.Ya amsa cikin murmushi"Sannu da zuwa Hajiyarmu, yashimfid'a mata tabarma.Tace a ah mutanan Gidan-Waya saukar yaushe?Ai tun safe ina garin nan,wajejen k'arfe sha d'aya naje gida ba kyanan.Tagyada kai"Tabbas anyi haka,naje asibiti gaishe da Liman na masallacin juma'a ne.Yace "ALLAHU-AKBAR"ashe har yanzu ba a sallameshi ba?Ubangiji yabashi lafiya,zaman jinyar kuma yasa kaffarace. Ta amsa da amin,amin.Anjima ya kamata kuje kugaishe shi Yagyada kai "Insha-ALLAH. Kai kadaine agidan?A ah Inna tana wankane"Tamishi kallan nazari"ni wannan zuwan sam baka min kyan ganiba,duk kayi wani firgai-firgai sai kace angon da hidima tasha kanshi kud'ad'en aljihu sun k'are,ko dai bakaji dad'i kwana biyu bane?Cikin yar dariya yace "to da Musaddiq kike wannan gugar zanan.Kai tafi can Musaddiq d'in wa?Shi da za a mishi auran gata,dakai nake yi.Yagirgiza kai"Hajiya ni dai lafiya ta k'alau.Cikin kad'a kai tace"amma dai sanin hali ai yafi sanin kama,idan ta kumbura tafashe tayi wari zamuji. Bismillahi tamik'e"ni bazan zauna zaman jiran uwarka ba wannan halin nata tun na k'uruciya ashe bata barshi ba,taja tsaki haka takeyi idan tashiga bayi kamar tasamu gadon bacci da daddare,wani lokacin sai na bita da bulala take fitowa,shiga bayi ai lalurace da kake sauri ka kawar da ita kafito.Julaibib yad'an yamutsa fuska"Kai Hajiya"takalleshi saboda uwarkace sai ink'i fad'an halinta?Yagirgiza kai. Tace"to wooo ashe dai kowa yana san wawa haihuwarshi ce ba a so,dama wajanta nazo kwana biyu bangan taba"To kijirata mana.Wa?Ai tunda na mik'e sai dai kuma tabiyoni nawa gidan,tunda na ganka ai shi kenan ko baka gode bane? Aiko nagode miki ba kad'anba Hajiyarmu.Barin taka miki. Suna tafiya a hankali suna hirarsu,har gida yarakata sannan yawuce gidan Yaya Karima.Yaya Karima tadabance wallahi saboda halin dattakonta. Rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya,ranar juma'a aka d'aura auran Musaddiq da Safiyyah,abokan karatunsu sunzo d'aurin auran nan Motoci har hud'u cike tam da jama'a.Maimun yace gaskiya garin Zonkwa yamin ba zata yadda nake tunanin garin ashe yawuce haka.Aminu yagyad'a kai"k'warai kuwa muna yin addininmu da komai namu kamar yadda hausawa,musulmai sukeyi a k'asar Hausa tunda akwai malamai masana addini a fannoni mabambanta,ga makarantu sai wanda kaza6a. Maimun yakalli Julaibib cikin tsokana "Yah D'ansarai inane k'auyan mutuniyar takane?Na ta6a tambayarta tace min Mabushi ko Madakiya?Ko mene?Ni na manta.Shiruma amsace. Yagyad'a kai "To da alama yan miskilancin sun motsa kenan.Aminu yamik'e"Maimun zo muje muyi shawagi kaji,zama waje d'aya tsautsayi.Suka bar Julaibib a d'akin,sunyi yawo sosai har Fadar Sarkin hausawan garin saida yakai Maimun yakwashi gaisuwa,Sarki me kirki da karamci yayita sa musu albarka yamusu addu'ar sumu ALLAH yabasu mata nagari,sai bayan la'asar suka koma gida dan shirin tafiya wa'azin maza da za ayi agidan Bak'i,bayan sallar magriba aka rufe taro da addu'a abokansu suka dauki hanyar Gidan-Waya, Aminu dai yarik'e Maimun wai dole sai ya kwana.A kwana d'aya da sukayi sunyi sabo naban mamaki kasancewar duk su biyun baki abin magana ne, sukayi sallama da alk'awarin kaima juna ziyara a duk lokacin da suka samu sarari. Yafito daga cikin dalleliyar motarshi kirar Toyota bak'a wuluk sai walainiya takeyi a cikin hasken rana.Yana sanye da kakin soja,tafiya yakeyi cikin isa da gadara dajin cewa eh ya ne kayi hattara,ka kuma kiyaye ni ko kasha na jaki.Kwan kwan kwan...ahankali yake rank'washin k'ofar kwan kwan kwan...Just come in... yajiyo muryarta daga ciki.Yasa hannu a marik'in k'ofar yamurd'a yashiga. Yabita da kallo tana kwance ruf da ciki da kayan bacci,dasauri yak'arasa gadon ya d'agota...suka kalli juna na wucewar wasu dak'iku, sai ta kauda kai a maimakon tabashi sumba kamar yadda tasaba.Yajuyo da fuskarta yana k'ok'arin sumbantar ta amma ta fuzge da sauri. Takoma ta kwanta "Beauty...tashi muje asibiti me ke damunki ne haka? Nace maka bani da lafiya ne? Hey don't fool me,idan ba ciwo ba me zai ramar dake haka?Idanun ta suka ciko da kwallah sai kawai tafad'a kirjinshi tafashe da wani irin kuka. Lidiya tashigo da murnan ta sai kuma tayi saroro tana kallansu,Ya juya yana kallanta. Lidiya me yasamu Beauty haka?Tad'an motsa kafad'a"Ga kai ga k'afa ka tambayi me aka yanka? Ai ita zata fad'i meke damunta.Baranzan yayita rarrashinta dak'yar yasamu tayi shiru.Ya gewaye hannayenshi ajikinta,yana mata magana a hankali "na fa shirya mana party na Birthday d'inki da akayi bana nan.Lidiya tabashi hannu suka tafa. "Good Baranzan a ina za a yi?Yakalli Kasham yana murmushi"Kasham Hotel Kafanchan"Lidiya tayi d'an tsalke tana ihu "Hallelujah". Tad'an daki kafad'arshi ta hagu,suka kyalkyale da dariya.Tad'auki jakarta"to yah ne? Bani kud'i zanje inyi nail fixes da gyaran gashi.Ya zarosu da yawa baiko tsaya k'irgawa ba ya bata.Tak'arba tare da sara mishi"Yes Sir ta buga kafarta da dama a k'asa"Thank you Sir.Tafita da sauri.Yasaki Kasham ya kunna taba sigari, yamata kyakkyawan zuk'a sannan yafara fesar da hayak'in tabaki ta hanci cikin shakara yana mata wani kallo. I miss you deadly Beauty... Yamik'a mata karan taban,tagirgiza kai "No I'm not in the mood"yakalleta nifa gaskiya yunwa nakeji saboda d'okin ganinki ko karyawa ban tsaya na yiba dan nasan zaki dafamin abinci me rai da motsi amma gashi baki da lafiya "Tashi muje in nemi abinda zanci". Tacanja kayan baccin jikinta da wando legging ruwan zinare da wata shirt checker,tana sa ma6allan gaban rigar shi kuma ya d'auko katon ribbon ruwan zinare ya tattara gashinta daya hargitse yad'aure, yana kallan d'an k'aramin bakinta daya d'an bushe dan bata shafa mishi mai ba"ni fa da yunwan kome na zo, kema kuma kin sani,amma na ga kamar hak'ata bazata tadda ruwa yadda nake so ba ko?Tayi kamar bataji abinda yake fad'aba.Tarik'o hannunshi"dan ALLAH mutafi dan idan nakoma na kwanta wallahi ba inda zani". Yana sanye da fararan kaya, bak'ar hula da bak'in takalmi sau ciki yayi sharrr dashi,ya rataya bak'ar jaka a kafad'arshi.Daga bayanshi yaji k'arar mota, sai ya kauce gefe.Tasauke gilashin bangaran da take zaune. "Barka da safiya D'ansarai... Yayi kamar ba dashi take yiba, yacigaba da tafiyarshi har yasha kwanar lecture hall d'insu ya6ace ma ganinta.Baranzan yaja motar yana tambayarta"waye wannnan ana mishi magana yayi banza da mutane?Tamaida kanta jikin kujerar motar"Ina ga baiji bane dan naga da headphone a kunnuwanshi.Jikinta yayi sanyi bata so yaganta da Baranzan ba wallahi,duk maganar da yake mata tamishi shiru kamar me bacci. Wannnan party baiyi wani armashi kamar yadda suka saba yin chasu da rawar mak'osa ayi shaye-shaye yadda a kaga dama,dan gaba d'aya bata da walwala banda ma ya takura mata da ba inda zataje, kwananshi uku awajanta sannan yayi shirin komawa Jaji Barrack bakin aiki amma yayita rok'onta idan ta samu sarari tabiyoshi,ta amsa da to,amma tayi alk'awari ba wanda zata sake bi har ta kwana dashi indai ba Julaibib ba. Ranar talata Musaddiq baije ko ina ba yana zaune a D'akin-shak'atawa yaji ana k'wank'wasa k'ofar,yace shigo dan yasan kila Asma'u ce amma sai ta fad'a mishi dalilin ta na k'inyi sallama,amma me?Kasham yagani a tsaye. Kasham? Yafad'a da mamaki kece?Dama kinsan gidana ne?Takasheshi da lallausan murmushinta "Kabar mamaki,dan matambayi ai baya 6ata. Naji kayi aure shine nazo tayaka murna, I'm I not wellcome? Bata jira amsar shiba tama kanta mazauni a d'aya daga cikin kujerun d'akin,tad'anbi D'akin-shak'atawar da kallo, sannan takalleshi "To ina amaryar taka?Yamike bari akirata yashige d'aya d'akin sannan ya kullo k'ofa"Safiyya takalleshi lafiya?Yarungume hannayen shi a k'irji lafiya lau,tashi kije ku gaisa wata yar makarantar muce tazo mana ALLAH yasanya alheri.Tamishi kallan tuhuma"Oh wanda tamaka a makaranta bai gamsar da itaba har sai ta biyoka gida?Yayi murmushi"Haba amaryata yaushe akai daren da gari zai waye? Kasham...she mean nothing,ai kece komai na, yafara Istirja'i, shaid'anne yake so yasak'a miki mummuna,kinji amaryata?Tayi murmushi suka fito tare. Wani Ovation take dubawa tad'ago tana murmushi"Amarya barka da fitowa,tanuna Musaddiq kinga mijin kin nan kirkinshi ragaggene a wajena tunda har zaiyi aure amma bai fad'a minba,ni kuma ai naga abin farin cikine to meye na 6oyewa,?To koma dai yayane ba a gayyace niba amma danaji labari gashi na zo" Musaddiq ina tayaku murnar aure,kuyi hak'uri Ku zauna lafiya for better for worst.Suka mata godiya, tace haba ba komai fa,wata kilama mutumin nakane yace karka fad'amin. Kamar bai gane wanda take nufiba yace"Wa kenan? Tad'an kalleshi "Wa kake dashi a Gidan-Waya daya wuce D'ansarai?Yayi murmushi"au shi kike nufi?To ba ruwanshi,Julaibib bai ta6amin maganar kiba. ALLAH da gaske!??? Ta tambayeshi cikin mamaki zata cigaba yatari numfashinta"Indai maganar D'ansarai zakiyi tona rok'eki kiyi shiru kawai tunda bashi da wani amfani.Yafad'a miki gaskiya... Takatseshi da sauri "Karkasa jinina ya hau,danni nayi alk'awari ko ana ha maza ha mata sai na auri Julaibib dan ina sanshi,takalli Safiyya" Madam ku taimakeni dan na san za ku iya wallahi,sallah ne dai da banayi yasa kuke k'ok'arin nisantani daku ko?To nace zan iya, ai ko bai kamata a k'wacemin gatarin danace zan iya had'iyaba... Safiyya ta jijjiga kai kenan a yadda take magiyar nan ta dad'e tana yak'in neman soyayyarshi ALLAH ne kawai yatsare shi daga fad'awatarkonta,tasake kallanta masha-ALLAH tanada kyau najan hankali,d'an k'aramin bakin ta da manyan idanunta masu maik'o su suka k'ara mata kyau na musamman ga ta da yalwan gashin kai,gashi kuma da alama ma'abociyar kwaliyar jan hankalice,dabara tazo mata dan haka ta kalli Musaddiq cikin tashin hankali"Dama baka fad'a mataba?To bari kiji Kasham kike kowa?Ki bud'e kunnnuwanki ki saurareni dakyau"Julaibib yana da matar aure karatu ake jira tagama musha biki kuma kanwata ce,dan haka kitashi kibar min gida.Tamik'e rai a 6ace ta wuce cikin. Takalli Musaddiq shi kuma yayi saurin kau da kai"Shin da gaske ne abinda tafad'a? Yagyad'a kai "Aishi yasa tun farko nafad'a miki Julaibib bazai aureki ba danna sanshi farin sani.Tamik'e tana sa6a jakarta akafad'a" Shikenan amma ba hakan yana nufin na hak'ura da shi bane,ku ai musulmai mata hud'u kuke iya aura,dan haka ban damu ako tanawa zanzo ba,ni dai burina in mallaki Julaibib a kowani irin hali da yanayi,zanje inyi tunanin abinda zai fishsheni. Tana fita Safiyya tadawo.Yayi murmushi yana mik'o mata hannayenshi "Amma gaskiyar magana kin burgeni"bata mika nata hannayenba,tagalla mishi harara"Shi me gayyarma ba shiga shirginta yakeyiba sai kai,ba kamar kid'iba sai kayan ganguna? Yafuzgota da k'arfi" Haba Safiyyahhh... Kina ganin wani abu zai shiga tsakanin mune?Kasham bata gabana. Tashagwabe murya"ai ba anan takeba an danne bodari aka,ni dai kawai ko?Tad'ago tana kallanshi.Yagyad'a kai" Uhun ke me? Ni dai kawai maganin kar ayi to tun wuri kar a fara..Yayi yar dariya yana d'an jan karan hancinta"To ranki yadad'e zan kiyaye"Yakamata kuwa hakan.Sai yad'an bata marin soyayya suka k'yalk'yale da dariya. Kwanakin Julaibib uku a Kaduna sannan yadawo ranar laraba da yammaci,wata yar Seminar sukayi da k'ungiyar"Ansaruddeen"yana rataye da bak'ar jakar matafiya,godiya yakeyi ga ALLAH daya kaishi lafiya yadawo dashi lafiya sannan yashige gidan da sallama.Inna ta amsa sallamar da murnan ganinshi "Maraba da autana "Yazauna agefen tabarmar cikin murmushi,Iyaye dad'in ganine dasu,musamman idan kayi dace da masu ilmi da sanin yakamata. Fatanshi har kullum ALLAH yabashi ikon jiyar dasu dad'in rayuwa kamar yadda suka jiyar dashi,musamman ilmin addini dana boko da tarbiyar Al'Isamiyya da suka bashi. Yacire takalmanshi masu rufi da safa sannan yagaisheta"Inna ya zafi"?Tagyada kai "Zafi kam akwaishi,sai dai yakusa k'arewa tunda damuna nagab da sauka.Yadi6o ruwan randa yanasha yaji dad'i har ranshi saboda k'amshin saiwoyin datake zubawa aciki dan k'arama ruwan armashi wajan sha yana zancen zuci"Inna duk lokacin da bana gida ruwan randan nan naki nake fara kewa,ya ajiye kofin.To Ubangiji yabamu damuna me albarka.Inna ta amsa da Amin.Yaciro mata tsarabarta sannan yamik'e yasa takalmanshi"barinje gidan Hajiyar mu"To ka gaisheta. Daga gidan Hajiya yawuce gidan Kawunshi,yaran gidan suna zaune a D'akin-shak'atawa suna kallo,k'ananan suka taso aguje suna murnan ganinshi"oyoyo Yaya Julaibib,oyoyo Yaya Julaibib duk suka mak'alk'aleshi dan D'ansarai indai wajan kyautane to ba daganan ba,sam abin hannunshi baya rufe mishi idanuba, suna ganin ya bud'e jaka suka fara tsalle kowa yana fad'in "Yaya Julaibib bani, a ah ni zaka ba,nima ai na iya rabo Yaya Julaibib....yace a ah bari aba babba Sagir maza kaima Khausar taraba muku, yanunata da yatsa"banda ke a ciki,rabo irin na adalci kawai za kiyi a tsakaninsu.Tayi yar dariya"To shikenan Sagir kawo ledan."waisu Mama basa nan ne? Eh sunje gidan suna. Yajuya shikenan na dawo anjima. A zaure sukayi kaci6is,taja baya da sauri"Sannu da zuwa"ya amsa da yauwa.Daga ina kike? "Gidansu Nasmat.Ka siyo min tsaraba?Yad'an kalleta "Haba dai, babba dake acin tsaraba?Tayi yar dariya "Yanzu dan ALLAH Yaya D'ansarai wani girmane dani?Ina abin yake wai maye yacinye jariri?Ai duk girmana ban kai Hajiya ba,daga gidansu Nasmat naje gidanta na kuma tarar da ita tana cin tuffa kuma tace tsabarar dama kai matane. To dake da Hajiya dayane? Daga baya suka jiyo muryarshi.Tad'an karyar da kai gefen dama"Kai Yaya Aminu yanzu ni banfi Hajiya ba? Ke dalla tafi kabamu waje, irinki goma baza su kama k'afar Hajiyarmu ba bare su fita,to ke asuwa?Karankad'a miya dake. Julaibib yace"ah to kin daiji ko?Ya tambayi Aminu"akwai ragowar kunun tsamiya a d'akinka? Kaima ka san ba a rasa nono a riga sai dai idan rigar bata Fulani bace.Yace yauwa to kije ki d'auka kiyi farau-farau dashi.Tajuya zata shige gida"ai ni kunu koda d'uminshi ba d'ad'ani da k'asa yayi ba bare ragowa, zanzo har gida in kar6a,sai kaba Innarmu ta ajiyemin koda na zo baka nan... ...Kome na rayuwa naci dana sha an halicceshine dan d'an Adam,shakeru aru-aru tun kafuwar doron duniya,za kuma kaci har kagaji,basa k'arewa sai dai kagama rayuwarka katafi kabarsu... ...Rabo na me rabo ko kura tagani haramiyarta. 15Rabi'a Thani 1441 12 December 2019 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI 💔 Daga alk'alamin 🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na hud'u. Monday ranar aiki ko nasara na tsoronki.Ranar litini aka koma makarantun boko a zangon karatu na farko.Sudaida da Khausar sunfi kowa farin ciki saboda shigarsu aji d'aya a k'aramar Secondary,kuma a wannan lokacin aka turo yan TP(Teaching Practice) Julaibib na d'aya daga cikin wadanda aka turo makarantar su,to kamar yadda su Sudaida ke murna haka Kasham ma tayi murna dan makarantarsu d'aya. Dasafe yashiga gidan cikin shigarshi ta fararan kaya.Yagaishe da su Mama, sannan yakalli Sudaida da take karyawa"idan kika bari nafito daga d'akin Kawu baki gamaba to ni tafiyata zanyi.Tamik'e tsaye tana addu'ar gama cin abinci nama gama barin kira Yaya Khausar sai mujiraka a mota.Gaisawa kawai sukayi da Kawun nashi yafito suka tafi. Kasham tana zaune a farar kujerar roba a inuwar dalbejiya kullum tana ganin irin zirga-zirgan da Sudaida takeyi idan an tashi tara(break) tsak'anin wajan saida kayyakin da wajan da Julaibib yake yawan zama,da alama ita yake aika tasiyo mishi abinda yake buk'ata. Tasauke gwauran numfashi wato dai yana magana,kalli yadda Sudaida take dariya, duk yadda akayi shi yayi furucin daya sata darawa. Bayan an koma aji yamik'e yashiga d'akin malamai(Staff Room)sai ganinta yayi zaune a tebur d'inshi magana zamuyi tafad'a cikin murmushi.Ranshi a 6ace yama rasa abinda zai fad'a sai kawai yajuya dama alli(chalk)zai d'auka to gwamma yatafi Principal Office yad'auki wani acan.Tabiyoshi da sauri"ji mana Julaibib,ka tsaya kaji abinda zan fad'a maka,idan kuma kaki to ina biye da kai duk inda kasa kafafunka.Bai saurareta ba yayi tafiyar shi,sauri yake yi har yana tuntu6e, abin yabata dariya"To wai shi Julaibib tsoronta yakeji da bayaso ya tsaya kusa da ita ko me?Ta tuno ranar data mamayeshi ta rungumeshi a Gidan-Waya yadda ilahirin jikinshi yakama rawa.Toh ni dai bana gane ma wannan tsoron naka wallahi. Lidiya tak'araso wajan tana mata kallan takaici nama na jan kare"ai ke dai kin gama a sara Kasham,namiji yana gudunki amma ke kina ta shige mishi sai kace shine mahad'in numfashinki?Taja dogon tsaki"to kidai yi a hankali kafin dalibai su farga,dan kin san ba dad'i zaki jiba idan suka tasaki a gaba da wak'ok'in shak'iyanci.Tagyad'a kai"zan so hakan indai zasu danganta ni da Julaibib a cikin baitocinsu.Ke Lidiya bazaki gane kome ba dan baki fad'a tarkon so ba. Ai ko na fad'a tarkon so bazanyi hauka da wawanci da rashin aji a wajan da nasan ba a maraba dani ba.tawuce tabata waje."Iska dai na wahalar da me kayan kara. A sanda hantsi ya dubi ludayi na ranar a sabar,yana zaune a shagonsu yana lissafin mutanan da suke bi bashi kuma su kai shiru mak'atau balaguro a lahira"kamar sun sha nonon uwarsu,d'ago kan da zaiyi caraf idanunsu yahad'u.Yafara ambatan ALLAH a zuci. Tana tsaye a barandar shagon cikin shigar shadda me maik'o ruwan makuba riga da zani bata d'aura d'ankwalin shaddar ba sai ta yafa k'aramin mayafi ruwan madara a saman gyararren gashinta data d'aureshi da k'atan ribbon ruwan makuba jaka da takalmanta ruwan madara,fuskarta,ta d'auki kwalliya,ta rungume hannayenta a k'irji tana k'are mishi kallo,yana sanye cikin yadi ruwan madara kanshi ba hula saisayan dayayima gashin kanshi da k'asumbarshi sun mishi kyau,ya fito sharrr dashi k'amshin arabian perfume d'inshi ya mamaye har inda take tsaye. Yamaida kallanshi cikin littafin amma ya kasa cigaba da abinda yakeyi. A hankali tafara taku d'ai-d'ai har tashiga shagon.Hucin numfashinta kawai yaji a gefen fuskarshi"Dan Sarai barka da hutun k'arshe mako". Ke malama na fad'a miki kifita harkata ko ana soyayyah dole ne!?Tamishi fari da idanun ta sannan tafara magana da wani salo irin nata na yanga "Kana ganin ba a soyayyah dole?Tagyad'a kai "To ko ba ayi za a fara hakan akan mu,kaga zamu shiga kund'in tarihin duniya"Julaibib da Kasham"what a perfect match.. Wai kai sai dubu nawa kake so in fad'a maka ina sanka, zanyi sallah koda zan 6ata da kowa nawane sannan za ka yadda dani? Haba Julaibib lokaci fa yayi da zan tunkari iyayena da maganar ka,kabani goyon baya,kaga mun kusa gama karatunmu sai kawai muyi aure hankalin mu zai kwanta"kanwa ta kar tsami k'wannafi ya kwanta.Tayi taku biyu tad'auki ragowar ruwa da yasha,tafara kur6a tana kallan shi danjin abinda zai fad'a,amma har ta shanye baiyi wani motsi ba. "Jesus christ"! tafad'a cikin kad'a kai,miskilancin ka yawane dashi wallahi,wanda bai sanka ba zaiyi zatan kai kurma ne awasu lokutan fa. Bai kalletaba yace nima sau dubu nawa kike so in fad'a miki bazan iya auren kiba kafin ki yadda dani?! No No No tad'aga mishi hannu ni ba irin wannan banziyar amsar zaka bani ba. Musaddiq yashigo da fara'arshi ganinta yasa shi d'aure fuska.Suka gaisa a tak'aice tana tambayarshi ya d'aliban makarantar da yake TP?Ya amsa da lafiya lau a tak'aice.Yamik'ama Julaibib hannu sukayi musafaha. suka cigaba da maganganun su zuwa can Musaddiq ya kalleymta"Wai lafiya kuwa? Tamishi wani kallo"Kaima ai kasan tatsuniyar gizo bata wuce k'ok'i "Musaddiq ban sanka da irin wannan halin ba.Yadauke kai daga kallan datake mishi "Eh ai kinsan kamawa takeyi a d'aure me d'aurewa,Zama da mad'aukin kanwa kuma shi ke kawo farin kai. Musadd...yatareta da sauri "A ah kiyi hak'uri kawai matata tace bata yadda magana tadinga shiga tsakanin muba. Matarka?Ta tamabaye da mamaki Eh haka nace matata.Tad'an ta6e baki"to kenan tsoronta kakaji? A ah Ba tsoronta nake ji ba,sai dai bana san 6acin ranta kona sisin k'wabo.Ahaf,tawatsa hannaye "ba cinya ba k'afar baya.tama Julaibib lallausan murmushin ta"ni zan wuce sai mun had'u ranar litini a makaranta"tajuya tayi tafiyarta. Ranar litini itace da darasin farko a ajinsu Sudaida tana shiga ta tarar dasu a tsaitsaye suna caccar baki.Tabisu da kallo "Lafiya kuka cika ajin da hayagaga bud'ar kan karya?Linda tafara mata bayani "ranar juma'a Sudaida tana cikin yan weekend-sanitation na wancan makon, amma takama hanya tayi tafiyarta ba tare da tayi kome ba,shine yanzu muke fad'a mata wannan juma'ar dole ta tsaya suyi ita da Dinatu,shine tafara masifa wai ba wanda ya isa yasata tayi sai idan taga damar tsayawa tayine kawai zata tsaya,wancan makon ne take da aiki batayi ba kuma ai yariga ya wuce. Kasham tace"baki kyautaba maimakon ki bada hak'uri kome yawuce shine sai ki rufesu da masifa?Sudaida ta turo baki gaba"to ai bani kad'ai bace Dinatu ma tafito indai gaskiyane abun.Tatsareta da manyan idanunta masu maik'o"Idan kuma karya ne fa?Sudaida tad'an motsa kafad'a"shikenan sai tayi zamanta dama idan aka tsaneka ko ruwa ka fad'a sai ace ka ta da k'ura"tafara k'unk'uni. Kasham tajijjiga kai"ban ta6a dukan kowa ba tunda nazo makarantar nan,amma yau za kisha na jaki,jeki Staff-Room ki jirani.Yan ajin suka zaro idanu, wasu suka d'ora hannayensu aka"Yau Sudaida zata kad'e har ganyanta a wajan malamai.Har ta kusa fita daga ajin sai kuma takirata"Hey come back"Sudaida tadawo tana kumburi"Kneel down here"takai gwiwoyinta k'asa tana k'unk'uni.Kasham tanunata da yatsa ke"If you dare say something again...I will deal with you. Takira Dinatu tana tambayarta me yasa baki tsaya an gyara ko in dake ba? Cikin rawar murya"Tace bani da lafiya ina kwance a hostel ranarma ban shigo ajiba". Hakane? Ta tambayi sauran d'aliban suka amsa da eh.sai tadan dafa kafad'rta"Amma yanzu kinji sauk'i?Eh malama naji sauk'i.To jeki zauna ko.Tajuya gaban allo tafara rubutu,tagama rubutawa tajuyo tana fuskantar d'aliban tana musu bayanin sabon darasin da suka shiga. Sudaida tasake kallan siririn farin agogon fatar dake daure ahannunta na dama,lokacin tama ya kusa k'arewa amma dan wulak'anci ta barta a durk'ushe, gwiwoyinta har sunyi tsami dan rashin tausayi da imani,tabi k'eyarta har zuwan gashin kanta da harara, wannan uban gashin k'aryane ba na ta bane wig ne,ga wani d'inkin rashin mutunci da tayi da atamfar jikinta,koya tayi tasa oho?Taja dogon tsakin dayasa duk yan ajin suka kalleta da mad'aukak'nn mamaki. Kasham tasake jijjiga kai"ni keki jama tsaki ko?Wallahi yau sai nayi maganin bakin rashin kunya.Tashi kafad'a min abinda yasa kikaki tsayawa ranar juma'a.Taturo baki gaba"to ai Yaya D'ansarai ne yace shi bazai zauna jirana yarasa sallar juma'a ba,ni kuma shine na bishi. Wani lallausan murmushi yasu6uce mata har kyawawan fararan hak'oranta suka bayyana,jin ta ambaci D'ansarai wato dama k'anwarshice wannan? Kawai sai ta rik'o hannunta suka fita. Ajin yakaure da hayaniya,wasu suna mata ALLAH yak'ara gwamma ayi maganin bakin tsiwan, wasu masu raunin zuciya har idanunsu sun cika da kwalla na tausayin halin da zata tsinci kanta aciki indai tashiga dak'in malamai,musamman kuma da Kasham tayi wannan murmushin sai suke ganin lallai na tanadin wuyane da ALLAH ne kad'ai zai ceci Sudaida. Sun d'anyi nisa da ajin sannan suka tsaya.Kasham tadafa kafad'arta "Kidaina irin wannan halin bashi dakyau,masoya da mak'iya ba a guzurinsu halinka zai baka su a duk inda kaje"Next time karki sake binshi sai kinyi aikinki kingane ko? Tagyad'a kai.Nima kiyi hak'uri da abinda namiki.Tayi mirmishi "bakome jeki aji ga malamin lissafinku can zai shiga"Always be a good student. Takoma aji tana wata tafiya irin ta eh yane naci dubu sai ceto.D'aliban suka zaro idanuna suna binta da kallan sama da k'asa alamar"a ah abin mamaki wai Baturiya da suna manga.Dan ba hawaye ba wata alama ta an bata na jaki,amma ba damar tambayarta ya akayi aka haihu a ragaya?Danga Malamin lissafi nan yahad'e girar sama da k'asa,dan shima k'wallan shegene shi yasa ko d'an k'us k'us k'us d'in nan na d'alibai basuyiba sai an tashi tara za a baje kome a fai-fai.Sudaida tamusu fari tana wani lallausan murmushi sannan tazauna awajan zamanta,Suna had'a idanu dashi itama tashiga taitaiyinta. Suna ciye-ciyensu dasu A'isha a sanda aka buga tara,sauran yan ajin sun zagayesu ana tambayarta an daketa kuwa?ya akayi tabarta tadawo aji da sauri?Sun dauka har a buga tara basu gama horata ba,bulala nawa aka mata?Tawani hura hanci cikin kuri kamar gaske "tama isa ta dakeni ne?Ai wallahi ko kura ta san gidan me babban sanda.Suka kyalkyale da dariya suna ihu;shegiya yar gidan Ibrahim-Mai Lambu, tad'aga musu hannu"a ah kar wasa yayi wasa a tsikari uwar miji fa.Ni yar sunna ce dan haka kar wacce takuma shegan tani ehemmm. Kasham dasuke zaune a benci ita da wasu malaman suna hirarsu ta k'walamamata kira tayafito ta da hannu.Sudaida tadanja tsaki"nifa wannan malamar tana neman shigarmin hanci da k'udundune. Suka sake kyalkyale da dariya"kila yanzu ne zata hukunta ki a bainan-nasi.Dammm...zuciyarta tabuga tsoro ya baibaye ta, kuma kila hakane,ba mamaki tajuyo maganganun sune tunda dama ba a hankali sakayi taba.Bata kulasuba tamik'e tana Istirja'i. Ga ni tafad'a cikin ladabi "dole gyad'a tai mai idan tak'i tasha matsa"Kasham tabita da kallo,haka kawai taji tana santa,tunda k'anwar masoyin tane.Lidiya tace"meye haka kuma?Kin kira yarinya kin tasata a gaba da kallo kamar wata magiji.Tasauke gwauran numfashi, tasa hannu a jaka ta zaro kud'in dabata k'irgaba tamik'a mata"ungo kije kisai abinda kike so. Sudaida tabita da kallan tsoro da mamaki kamar yadda sauran malaman sukayi "to da wace hujjar nasara zaiyi hawan k'aho? "Kar6a mana Sudaida. Tajuya ba tare data kar6a ba"bar abinki nima ina da nawa.Lidiya tadaka mata tsawa"ke k'aramar mara kunya dawo.Sai kawai tasa gudu.Tayi kwafa zamu had'u dake gobe aji.Kasham tahad'a tafukan hannayenta"Dan ALLAH Lidiya karki daketa dan bata miki kome ba.How dare you Kasham kice bata min kome ba ni sa'ar wasan tace dazan kirata tak'i zuwa?Saboda ita kanwar wancan me shegen girman kan tsiyan?To niba ruwana abu kazan uban ta zanci.Haushi yakama Kasham sai kawai tace"ai ko abu kazan uban ta yafi k'arfinki har abadan duniya.Cikin tafasar zuciya Lidiya tanuna kanta da yatsanta"Kasham ni kikema wannan rashin mutuncin saboda wasu tsinannun hausawa?Ban miki wani rashin mutunci ba, magana kikayi ni kuma na baki amsa.Banda shiga sharo ba shanu ina ruwanki da ita?Ko ke kika kirata? Kome tamin ni naja,idan naga dama in mata hukunci,idan naga dama in k'yaleta bai shafeki ba"wannan sa kai a uku ne takaban siriki. Suka farar cacar baki malamai suka shiga tsakani daga nan taran yawatse dan an koma aji. Takoma Staff-Room dan bata da darasi a kowani aji har a tashi sai kuma gobe.Tabishi da kallo cikin harara dan kwana biyu taje yajin aiki akanshi, duk yadda takejin san shi ba ta kulashi sai dai tayita kallanshi.Tamaida kanta jikin kujera ta lumshe idanunta tana wata kisima a zuci "Julaibib kyakkyawane"Melanin beauty"tayi nazarin shi dakyau baya san hayani,wani abun ba wulak'anci yake mataba haka halinshi yake bashi da yawan magana,tana so ta aureshi tahaifi yarinya me irin kwantaccen gashinshi, tana san Julaibib ta rasa ya zatayi da rayuwarta"Ciwon so" data san inda zata nemo maganin shi tasha ta warke daga san D'an Sarai ne? "Oh my God!, ta dunk'ule hannu ta naushi iska" Dasauri tamik'e zuwa wajanshi D'ansarai takira sunanshi.Yad'ago yakalleta yacigaba da abinda yake yi,sai ta rasa me zatace...Dan ALLAH bani aran correction pen. Yaciroshi a aljihun gaban rigarshi daya soke yamik'a mata.Tashafi hannunshi sannan ta kar6a "nagode idan nagama zan kawo maka.Yagirgiza kai "Kirik'e kawai.To nagode,tasa ajaka dama neman magana ne itama tanada nata fa. Duk ranar alhamis suke House Assembly, wani ikon ALLAH sai akasa Kasham da Julaibib a house d'aya,Sudaida ma anan take. Kasham a matsayinta na sabuwar malama ita tafara musu bayanin kanta da yar nasiha,sai malamai biyu duk yan TP sai Julaibib cik'on na hud'unsu.Cikin natsuwa yake musu bayani sannan yad'ora da nasiha a kan su dage da karatu ba kawai sai lokacin jarabawa ko za ai wata kaci-kaci da muhawaraba, kullum Ku zama masu nazari da bincike da tambayar duk abinda baku ganeba, da wanda baku saniba da hakane ake samun ilmi me yawa,ita k'wak'walwa d'an Adam ne yake cikata da aiki,idan kuma baiyi hakan ba to ita zata cika mishi da abubuwa na shirme wanda bazai amfaneshi akaran kanshiba,bare har al'umma ta amfana,ina fata zaku dad'a sa k'wazo duk da nasan kunayi amma Ku k'ara, ina kuma fata zaku zama masu amana kamar yadda sunan gidan na ku yake "Amana House. D'alibai suka d'auki tafi.A'isha da take bayan Sudaida tace"Amma gaskiya ina san Yayanki Sudaida,yanayinshi me sanyine,sukayi murmushi.Mr Julius shugaban house d'in shima yatafa mishi,yau bani da abin fad'a.Yanuna Julaibib da yatsa"This great teacher of ours has said all".Yad'an bubbuga kafad'arshi sukayi murmushi,sannan yakalli d'aliban yad'an motsa kafad'arshi"shikenan you can go back to your classes" duk suka watse. Maimun yakawo musu ziyarar bazata ranar juma'a da yamma,sun kuma ji dad'in haka sunata ba juna labarin makarantun da aka turasu har Maimun yasako mishi maganar Kasham...Yayi kamar badashi yakeyi ba.Zuwacan kuma yagirgiza kai"ni fa ba zanyi abinda zai zama min matsala ba,aure ba abin wasa bane, ba kuma yin auran ne yadameni ba,a ah samun matar data dace dani me mutunci da mutunta kai.Kasan ALLAH Julaibib Kasham tana sanka,wannan soyayyar da take maka zaisa tamaka biyayya tabi umarninka.Yagirgiza kai"Kyaleta kawai Maimun. Maimun bai kuma maganarba suka cigaba da hirar data shafesu har Musaddiq yafito suka tafi k'wadago neman halali. Baranzan yajuya yana kallanta"Ke wai meye damuwarki ne?Wani haushin shi takeji gwamma tabar mishi d'akin dan batayi maraba da zuwan shiba,idan tazauna za ayi d'anyan aikine dan shima bashi da mutunci idan yana 6acin rai.A fusace tajuya zata fita,caraf taji yarik'o dantsen hannunta kamar zai k'aryata. Tarinse idanu dan azaba. Yasunkuya akan fuskarta"sai kin fad'a min da uban wa kika fara soyayya da har kike guduna? Sake min hannu.Yasake rik'eta tamau.Sai fa kin fad'amin da uban wa kika fara soyayyah? Haushinshi yadad'a ninkuwa a zuciyarta Kawai sai tace da"Ubanka...bata gama rufe baki ba taji saukan mari hagu da dama,idanunshi suka kad'a jawur"za kimin rashin mutuncine?Uba na sa'ankine?Yafad'a da karfi cikin tashin hankali da alama allurar soja ta motsa.Uba na ko? Tagyad'a kai duk da a zabar rik'on data keji.Kikace eh? Yashak'eta,manyan idanunta suka fir-firto numfashinta yazo wuya,yasake kifa mata mari hagu da dama,sai da taga wasu k'ananan taurari sun tarwatse, gefen bakinta ya fashe,ji da ganinta suka d'auke na wucin gadi.. Wannene abin so?... A tari fitsari a wanke zawo? 18 Rabi'a Thani 1441 15 December 2019 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin 🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na biyar. Dak'yar aka 6an6areta a hannunshi bayan tasha wahalar duniya.Yarafff... tafad'a gado tana wani irin tarin wahala tana fuzgo numfashin ta dayake k'ok'arin kufcewa.Shima ya fuzge daga rik'eshin da akayi ana ta bashi hak'uri,yayi kanta,aka sake rik'eshi Lidiya tashigo da gudunta dan bata san abinda ke faruwa ba yanzu aka kai mata rahoto"haba Baranzan kazama namiji mana, jarumin namiji me kwanan daji irinka me zai sa katsaya fad'a da mace?Kasham fa kwana biyu bata da lafiya ya kamata kamata uzuri.Anki a mata uzurin wa tafad'a ma bata da lafiya? Yabita da kallo tana kwance sambal,gashin kanta a hargitse kuma ta rame ba haka yasan Beauty d'inshi yar gayu ba.To kitashi muje asibiti. Shiruma amsace.Yad'ibo wasu damin kud'i yaba Lidiya wai tarakata asibiti ta tabbata an dubata ankuma bata magani me kyau.Tagyad'a kai tare da sara mishi "Yes sir tabuga k'afar damanta a k'asa. Tarakashi da adawo lafiya sannan ta rufo k'ofar ta zauna a bakin gadon,tasa hannu tashare mata jinin da yake gefen bakin ta,tabud'e idanunta suka kalli juna.Lidiya tad'an d'age gira"wallahi kashin kare baya taki" Baranzan shine yadace dake ba wancan tsinannan bahaushen ba,danni bazan fasa fad'a miki gaskiya ba,kome naku d'aya da Baranzan"Hun wai saboda wani bare da bai san ALLAH yayi ruwan tsiran kiba kike ga ba dani,indai bani namiki magana ba ke bazaki minba. Tamaida idanunta tarufesu"ita abinda yadami zuciyarta shi d'in ne yadameta"daga ita har Baranzan basu d'ad'ata da k'asaba"kowa da kiwon daya kar6e shi mak'ocin me akuya ya sai kura". A'isha tabiyo Sudaida dad'an gudunta da aka buga tara"Ke malama jirani"Tatsaya tana kalllanta har ta k'araso"Kefa kika ce ba inda zaki".Aisha tagyad'a kai"Eh nafa sane naga gaba d'aya ajin an watse an barni kamar mayya,me zaki siyane?Ta tambayi Sudaida"Ba abinda zan siya dan bana jin cin kome na makarantar nan yau.Wajan Nasmat zani.Tarik'o hannunta"Dalla shareta zo muje wajan Yayanku tad'an turo baki me zanje in mishi?Ke shifa Yaya D'ansarai ba yaso a dameshi.Ke dai zo muje mana ni wallahi ina sanshi.Sudaida tamata wani kallo sannan ta ta6e baki"Lallai kinji jiki, Yaya Julaibib d'in kike so?.Eh wallahi"Yanayin shi me sanyi ne,baya san hayaniya. Wa alaikumussalam.Ya amsa sallamar su. A'isha tamata nuni wai su zauna,ita kuma tana nok'e kafad'a.Yad'an d'ago yakalle su,sai yacigaba da nazarin d'aya daga cikin tarin littafan dake gefan shi,hannunshi rik'e da jan biro da alama hannu yake sawa akan aikin daya basu.Yasake d'agowa yakallesu ganin sun zauna sunata kallanshi"yaya wani Abu ne?Aisha tayi tsagal "Yaya Julaibib dama... da... sauran kalaman suka mak'ale saboda wani rikitaccen kallo da yake mata,sai ta mik'e "bakome Sudaida taso mutafi.Har sun jiya Sudaida taji kiranshi.Ta tsaya sannan tajuyo tana kallanshi ya yafitota da hannu.Tak'arasa wajan"Yaya Julaibib gani "Yad'anyi murmushi"hala kud'in taran na ku ba yawane yau?A ah wallahi muna da kud'inmu. Yamik'a mata wasu kud'in"duk da haka sai Ku k'ara,tasa hannu biyu takar6a"Mungode ALLAH yak'ara bud'i.Yad'an bita da kallo yana murmushi. A'isha taja tsaki kawai anzo wajanka amma saika wulakanta mutane. Sudaida tad'aga mata hannu"a ah wallahi Yaya D'an Sarai bashi da wulakanci, kuma baki ga abinda yakeyi bane?Ai dama nafad'a miki shi fa baya so adameshi...Nasmat tak'araso wajan tatarar da Aisha tana k'unk'uni "Ke da wa kuma?Da Yayanku d'an wulak'ancin can mana tanu mata Julaibib d'in da d'an yatsa.Nasmat ta kyalkyale da dariya miskili kafi mahaukaci ban haushi"to amma shi da baya shiga shirgin mutane to me yahad'o ki dashi? Tawatsa hannu"shareshi kawai suka cigaba da tafiyarsu suna hira. A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar lahadi suna hirarsu da Inna Khalifa d'an mak'otansu yashigo da gudunshi"Yaya Julaibib ana sallama dakai"To kace ina zuwa. Suka cigaba da hirarsu,ganin bashi da niyyar tashi Inna tace"Tashi katafi mana.Yamik'e To Inna yad'auki rigarshi daya cire yana sawa,a zaure yak'arasa sawa,yana fitowa caraf idanunsu yahad'u,yamata wani irin kallo data kasa fassarawa.Tayi yar dariya"Malam D'ansarai kenan wato ganina yasa ka canjawa kamar kaga me tagayyara rayuwarka har abadan duniya ko?To ni dai nazo gaisheka ne,wancan makon ko sau d'aya ban samu nazo makarantaba dan bani da lafiya kuma a dalilin sanka nashiga halin dana shiga amma ko katambaya"Lafiya kuwa Kasham bata zuwa makaranta?To koma dai yayane Thank God naji sauk'i,ina kuma so kamin jagora zan shiga gaishe da Mama."Bata nan"Yabata amsa a takaice. Takama ha6a🤔D'ansarai wallahi bakayi kama da masu zabga k'arya a kalaman suba,nafa tambayi yaran yacemin tananan,inaso muyi kome cikin mutunci da girmama junane shi yasa ban shigo kai tsaye ba,amma kai naga kamar ba hakama kake so ba,idan natsaya rarrashinka kuma raina ne kawai zai 6aci a banza,tunda har yanzu baka d'aukeni wata tsiya ba,ko albarkacin k'aunar da nake maka ban ta6a ciba. Koma inda kika fito,tunda ba gayyatoki nayi ba.Tagirgiza kai idan kamin haka tsakani da Allah baka min adalci ba,tanuna mishi Bible d'in hannunta daga majami'a (Church) nake,ana tashi nashigo cikin gari ko gida ban koma na ajiye Bible d'in ba,duk dan d'okin ganinka.Yau d'aya dai kamin adalci a matsayina na yar Adam bama masoyiyar kaba. Inna tafara jiyo hayaniya."Na rantse da girman ALLAH idan kika tako inda nake sai na 6allaki.Inna tajuyo furucinshi cikin fad'a.Kai dawaye Julaibib?Inna ta tambayeshi bayan tashigo zauren.Cikin tafasar zuciya yajuya yakalli Inna idanunshi jawur"ni da wancan mara kamun kance.Zuciyar ta tabuga Dammm...Kasham wato kwana biyu da bataji d'uriyar taba ta zaci ta hak'urane kamar yadda taita zuwar mata kwanakin baya. Inna dai hakuri take bata tunda maigayyar yace baya so, zuwan ta nak'arshe da Inna tafad'i haka yar dariya kawai tayi tamata sallama tatafi .To yau kuma kwatsam ba zato sai gashi tadawo. Kasham daga waje tace"Mama kice yabarni in shigo dan ba wajanshi shi kad'ai nazo ba har dake,idan kuma ba haka ba zan mishi abinda har abadan duniya bazai manta dani ba.Wata jijiya tafito rad'am agoshin shi kamar shatin bulala"ni kuma sai dai baki k'araso wajan nan ba amma wallahi sai na 6allaki"ke! yafad'a a tsawace idan kin fasamin abinda bazan mantaba har abadan duniya ke ba...Inna tatareshi"Kai Julaibib dakata! Inna wallahi...tad'aga mishi hannu na dai ce ya isako?Yasunkwui da kai.."haba Julaibib idan rai ya6aci bai kamata hankali ya gushe ba,wai kamanta da sharrin mace har yafi na shaid'an kaifi?.Bai sake magana yasa kai yafita. Kasham tashigo zauran suna gaisawa,Inna tabita da kallan tausayi"Iska na wahalar da me kayan kara.Takai gwiwoyinta k'asa tahad'a tafukan hannayenta alamar magiya idanunta sun ciko da k'wallah "Mama ki taimakeni mana". Inna tajijjiga kai"Zanso k'warai Julaibib ya aureki ko dan matsananciyar k'aunar dakike mishi,kuma ya tsamoki daga duhu zuwa haske amma hak'ata bata tadda ruwaba,to kema me zai sa bazaki hak'uraba? Sharrr...hawayen masu d'umi suka zubo a kyakkyawar fuskarta "saboda ina san shi Mama,Julaibib d'an kine na san zaiji maganarki,idan kikace dole ya aureni ai bazai k'i miki biyayya ba.Inna tadafa kafad'arta "Kasham kenan, kasancewar Julaibib d'a na ne ba yana nufin in tilas tashi yin abinda baya so bane,Julaibib yana da hakki akaina, kamar yadda nake da hakki akanshi,shi aure ba abin wasa bane,zaman aure kuma ana yin shine bana wucin gadi ba,a ah zaman din din din ne da ba a san rabuwa sai dai idan k'addarar hakan ta kasance ba yadda za ayi,kinga shi yasa ma ake so mutum yaza6i abokin rayuwar daya kwanta mishi arai, kowa yanajin k'auna da soyayyar d'an uwanshi da gasken-gaske,tayadda idan an samu sa6ani za ayi fad'a, idan an huce za ana juna uzuri,za a yafema juna, amma idan d'aya a dole yake zaune da d'aya to abu kad'an d'in da bai ta ka kara ya karya ba sai rigima ta 6alle wanda daga nan auran zai lalace an rabu, to ina amfanin 6ata goma biyar bata gyaruba? Suna cikin haka saiga Alhaji Abdullahi yashigo shima da nasiha yabita me ratsa jiki.Tagyad'a kai"Eh tabbas duk abinda suka fad'a gaskiyace wacce daga k'inta sai 6ata. To amma fa ita har kwannan gobe tana san D'an Sarai bata kuma cire rai da auran shiba. Bayan sun gama cin abincin dare.Alhaji Abdullahi yakalli Julaibib "D'ansarai na san ba abinda ke tsakaninka da wancan yarinyar amma duk da haka sai ka k'ara yin taka tsantsan,dan shaidan baya raina k'ofa,kai kace bazaka aure taba,ita kuma bata hak'ura ta daina bibiyarka ba.Kanemo mata kayi aure dan shine kwanciyar hankalinka damu kanmu,bana so kad'auki wani dogon lokaci ba tare da iyali ba.Yashafa kwantaccen bak'in gashin kanshi "Sannan ya amsa cikin ladabi.Amma cikin zuciyar shi inda kizo ke sak'ar wacece yake jin santa? Dammm...Zuciyar shi tabuga,yayi maza yakawar da tunaninta a,Yasauke gwauran numfashi " Yau ake yin ta wai anyi da mutum ya ji"... Hajiya takalli Sudaida da 6acin rai"Kai wannan yarinya da kafirin taurin kai take kamar mutanan farko,za ki d'auka kisha ko sai na sa6a miki? Ta turo baki gaba"ni fa wallahi na ji sauk'i"ke tafi can kinji sauk'i amma kwana biyu kina kwance?Ni na ta6a jin inda akayi haka? Baka da lafiya bazaka sha magani ba,baza a maka alluraba?To ko duk tsiyarki gobe sai kin tafi makaranta dan naga abun na ki "Tsiya ne d'inkin ludayi. Ya shigo da sallama.Tabishi da kallo "Yaya Julaibib ina atilan dana ce kasiyo min"?Yayi kamar ba dashi take magana ba, yazauna a kujera suna gaisawa da Hajiya.Tad'anyi tsaki"ALLAH yasauwak'e maka wannan halin... takauda kai daga kallan da take mishi tafara k'unk'uni saiga Sinan shima ya shigo"Tace yauwa Sinan kamar kasan ina mararin ganinka.Yagaishe da Hajiya tare da tambayar ya akaji da me jiki? A Alhamdulillahi ai taji sauk'i tunda har tana k'in shan magani, shekaran jiya da bata san inda kanta yake ba ai ina bata take kar6a tashanye ba musu ba gaddama.Sudaida ta turo baki gaba ni fa kaina ba inda yatafi yabarni muna tare har a k'abari. Sinan yamatsa kusa da gadan da take kwance ta lullu6e jikinta da bargon Hajiya fuskarta kawai ta bari a bud'e.Yamata wani kallo"Sannu sarauniyar Sinan" tagyad'a kai cikin murmushi.Yafara mata magana k'asa-k'asa. Takyalkyale da dariya tad'an zaro idanunta"Kaiiii Sinan wallahi ba ruwana.Sai yamik'e tsaye daga sunkuyan da yayi a kusa da ita"Me zan kawo miki anjima"?Tad'an harari Julaibib caraf idanunsu yahad'u tadauke kai,sannan tad'an marairaice "atile"dame kuma?Sai kuma yaba kanshi amsa"da masoyin sarauniyar Sinan rake.Tayi murmushi" Wallahi nagode maka ba kad'an ba Sinan.Tad'aga hannu tana mishi adabo"adawo lafiya. Filin wajan da malamai suke ajiye mashina da motoci taje,tad'are mashin d'in Shunkut dan yayi saiti da inda Julaibib yazauna a barandar d'akin malamai,tana kare mishi kallo...Tayi murmushi cikin sauke numfashi "Julaibib da ka san matsanan cin son danake maka wata kila daka ceci zuciya ta da take shirin yin gobara. Holy ghost fire! Lidiya tafad'a dan Kasham batama san tazo wajan ba.Akan wancan tsinannan bahaushen kina neman zama mahaukaciya"For Christ sake wai me yashiga k'wak'walwarkine? Lidiya kome zaki fad'a min indai akan son wancan bahaushen ne tamata nuni da inda yake zaune, to ina maraba dashi,kin sani tun ganin Julaibib a kuma kallanshi farko so da k'aunarshi suka mamaye zuciya ta,shi kanshi ya fad'a min uncountable times bazai aure niba and I don't know why har yanzu nake jin kaunar shi deep down my heart". Tadafa kafad'arta ki tayani addu'a duk ranar da ALLAH yabani sa'a yashiga nan ta nuna tsakiyar tafin hannunta,yad'and'ani zak'i da gardin zuma ta,to wallahi na mishi katttt...kisan mummuk'e.Lidiya ta kyalkyale da dariya"gaskiya iska tana wahalar da me kayan kara,malama dame kama ake yin k'ota.Wancan me shegen girman kanne kike tunanin za ki yaudare shi?To yaushe ma yatsayi kulaki bare har hilarki tayi aiki akanshi? Wallahi kinga dai bana san shi amma na jinjina mishi 👍zan kuma iya bada shaidarshi harkar mata baya yinta, dan da yanayi wallahi ko sau d'aya ne tun zuwanshi Gidan-Waya da mun sani,kema ai kin san mune idon gari a makarantar nan,wannan harkar sai sojanki Namamajo,ke dai kawai ALLAH yaganar dake,amma banda 6atan basira mutum yace baya sona to nima banga abinda zai sa ya kuma d'ad'ani da k'asaba tunda shi d'in ai ba mahad'in numfashi na bane,ko yaranmu d'aya dashi zan hak'ura in kyaleshi,bare wani hausawa me girman kan tsiya,shiba kowan kowaba dillalin kashi,kin sani ni nak'i jinin hausawa, ke ba hausawa kad'ai ba duk wani me sallah bana sanshi da inda k'arfin iko na rantse miki da ALLAH ba wasu tsinannun masu sallah dazasu zauna mana a gari.Taja tsaki fuskar nan tarine da 6acin rai ruwan kafircine zallah babu gauraye da haske da tausayi da Imani ko na sisin kwabo, jikar kajawace (Bajju) gaba da baya"bana san ma su sallah.Kuma ba yadda za kiyi dasu "sun zama kuturwar uwa dole a zauna dake.Kasham tabata amsa,sannan tasauko akan mashin d'in tawuce bayan aju-juwa da aka k'awata wajan da shuke-shuken filawowi masu ban sha'awa,tadinga bi tana tsinkosu kaloli mabambanta masu k'amshi tacika hannunta sannan tasa zaran ulu,ruwan hoda tadaure tawuce d'akin malamai zaman jiranshi.Dak'ik'a biyar da buga k'ararrawar canjin darasi sai ga shi yashigo,saida tabari ya zauna a kujerarshi yana hutawa ba ajin dazai kuma shiga sai gobe.Yakwantar da kanshi a jikin kujerar, idanunshi a rufe wani bacci me dad'i yafara shirin saceshi sai kawai yaji an shafa mishi wani abu a daidai hancinshi me wani irin k'amshin dad'i, yabud'e idanunshi da yanayin bacci har sun d'anyi ja. Tamishi lallausan murmushinta "perceive the natural fragrance of this bounch of flowers.Tafurta hakan da wani salo irin na ta nayanga sannan tacire daga hancinshi ta d'ora mishi a saman tebur.Yakauda kai daga kallan da take mishi kamar kura taga nama.Wallahi yama rasa abinda zai ce mata. Tayi k'asa da murya ganin wasu malaman sun fara sa musu na mujiya"ai nasan ban kyauta maka ba ko?Kai dai ba a maka gwaninta,d'an motsa kafada tayi "karka damu dani,kar kayi la'akari dacewa nice nakawo maka,tagirgiza kai kayi la'akari kawai da tarin amfanin da k'amshin furen filawa yake dashi ga d'an Adam.How I wish Jualiabib ka bani dama na nuna maka irin kaunar danake maka, tagirgiza kai cikin damuwa "How I wish ka tallafi zuciyata ka magance min damuwar cikinta...sai dai kash!Ban samu hakan ba,saboda baka san illar kaso a k'ikaba,tabbas daka san haka da baza kabari zuciyata tayi gobara ba.Tahad'a tafukan hannayenta alamar magiya "Don't let the love that I have for you to go in vain please...! Yad'ago yakalle ta,sai yaji wani abu ya tsirga ilahirin jiki da zuciyar shi,har ya bud'e baki zayi magana sai kuma yagirgiza kai"a ah Julaibib daure kawai, maganin kar ayi to tun farko kar a fara"kawai sai yamik'e yabar d'akin. Shunkut ya sunkuyo a fuskarta yana murmushi"Ke ki hak'ura dashi mana ai ba a soyayyah dole, yanuna kanshi da yatsarshi"ni d'in nan namiji ne duk abinda yake dashi namazan taka nima ina dashi,kiyadda kawai muyi soyayyah.A fusace ta tureshi"you fool! dawa za kayi soyayyah Shunkut?Tayi d'as da yan yatsunta over my dead body.Tagalla mishi harara sannan taja mummunan tsaki"ruwa ai ba sa'an kwando bane"sai yajuya yana tafiya "Amma kuwa za kiyi 6atan 6akatantan... A gajiye lik'is yashigo,gidan shiru dan Inna tana gidan Hajiya,yazauna yana hutawa, ya6alle botiren gaban farar rigarshi,yamaida kanshi jikin kujera tare da lumshe idanunshi sassanyar iskar bayan la'asar tana ratsashi. Mafarkan da kwana biyu nan yakeyi sun tsaya mishi a rai"Kasham yake gani cikin kyakkyawan kirar kalangunta,sanye da kayan fulani,gashinta yasha gyara ta tufkeshi a baya,amma kuma idan tayi magana muryar Sudaida yakeji"ya rasa kan wannan mafarki. Hayaniyar shigowarsu Kamila yasashi bud'e idanunshi,aiko suka shigo sunata zuba surutunsu, sunata mishi tambaye- tambaye.Shigowar Musaddiq yasa suka koma tsakar gida suna wasannin su,yadaki kafad'ar shi"kai malam tashi da ALLAH magana nazo muyi. Uhun ina jinka.Musaddiq yabishi da kallo"Julaibib ka nemi A'isha kawarsu Sudaida mana tunda dama ta nuna tana sanka kaine baka bada goyon baya,tana da hankali kuma ko su Baba idan sukaji ita kake so za suji da...yatari numfashinshi a hasale "bata min a matsayin matar aure ba,dan haka akai kasuwa".Yakalle shi da mad'aukakin mamaki"To me yayi zafi da har idanu za suci wuta haka? Tagyada kai "To yayi,indai har A'isha bata maka a matsayin matar aure ba to ashe gulmace da kai,kana kuma kallan mata za kuma ka iya za6a,amma da zarar magana ta tashi sai kace ba sa gabanka,to kuma harsu Baba sai sunji zancen nan. Yanunashi da yatsa"Idan kai zaka min zaman auran ai sai in aureta.Yamaida idanun shi ya rufe, shi wai ma wacece wata A'isha?Wasu lokutan dai Sudaida tana fad'a mishi"A'isha tace tana gaisuwa"ko kuma A'isha tace kaza da kaza game kai,sai dai bazai iya tuno me take fad'a d'inba, dan ba itace a gaban shiba,shi dai bai san tana sanshi ba,dan ko Sudaida bata ta6a fad'a mishi wai A'isha tana san shiba, kila Musaddiq d'inne kawai yake san had'awa. Sallar a zahar Julaibib yayi yagama azkar d'inshi sannan yafito daga masallacin makarantar,yau ba ayi wani karatun kirkiba saboda Inter-House ya kusa,ga dalibai nan sunyi rukuni rukuni na irin abinda suke so, suke dad'a yin gwaji (practice)yajingina da bishiyar giginya tare da rungume hannayanshi a kirji yana kallan Sudaida yadda take d'aga mulmulallan bak'in k'arfen discus da yadda take jefashi cikin k'warewa da nishad'i a bokan wasanta suna mata tafi wasu suna mata ihu dan tanayi yadda yakamata.Yayi murmushi yatuna lokacin da yake makaranta yayi wasannin kala kala,wasan kwallo ne bai ta6,a burgeshi ba wannan sai Musaddiq,saboda kwazanshi a fannin wasannin shine yarik'e shugaban wasanni na lokacinsu (Game Prefect) yakalli Khausar sune yan Javelin, Nasmat kuma ana bangaran Long jump. Yabar jikin bishiyar yana tafiyarshi cikin natsuwa har yaje Staff-Quater zai kar6i wasu littafai a wajan Mr Julius. K'arfe uku tanayi yasake komawa filin wasannin da Nasmat yafara cin karo yace"Ke idan ba zaku tafi gida bane ni kunga tafiyata.Dan ALLAH kajiramu barin kirasu tayi cikin filin da dan gudunta. A mota suka sameshi ya musu wannann rikitaccen kallan nashi Sudaida tabud'e baki za tayi magana yanu nata da yatsa"kul naji bakinki.Tad'an harareshi ta zauna tana turo baki gaba.Yaja tsaki"kunje kun shagala da wasanni ko sallar azahar ma baku yiba ga la'asar ta kusa,kufa kuna da ka'ida da bambanci tsakanin ku da wad'anda dama basu san kome ba sai duniyar, wallahi idan lokacin sallah yayi banga mutum a masallaci ba gobe...yayi kwafa, Nasmat tace"shi fa wannan Game Master muguntar shi har tafi ta Discipline Master.Ke tafi can shi ai ba makaho bane yana ganin k'atan masallaci ai a makarantar,na kuma tabbata da kun fad'a mishi sallah za kuyi bazai hana kuba,ai kowa ya san duk inda musulmi yake ba a rabashi da sallah,sai dai in sallarce bata dame shiba...Yaya D'ansarai... yatari numfashin ta"ke ba nace kar inji bakin kiba?Tasunkwui da kai"wannan mutumin wallahi yanada matsala,tafad'a a zuci,tad'anja tsaki. Nasmat takalleta"ke Sudaida tun d'azu kiketa k'unk'uni abin harda jan tsaki ke da wa? Shiru ma amsace. A k'ofar gidansu yatsaida motar bai k'arasa dasu gidansu kamar yadda yasaba ba,yakashe motar yafito yashige gida.Sudaida itama tabud'e bangarenta tafito tana masifa"aikin banza sammakon gaida makiyi,aiko ba a motarka zamu dawo gida. Aminu yana hangota yafara dariya"ke fa Sudaida naga alama raguwa za a yi.Ta turo baki gaba "Yaya Aminu me nayi to? Kinga fuskarki kuwa?Gaskiya yunwar makaranta ba ta dad'i har na tuna lokacin da mukayi makaranta a Bauchi.Yad'an kalleta kinsan yau me su Mama sukayi a gidan? Tagirgiza kai "Tuwon shinkafa miyar shuwaka"Sai kawai tad'ora hannayenta aka"Wayyo ALLAH! ni gaskiya yau ana ta 6ata min rai.Suwaye suketa 6ata miki rai?Takaryar da kai gefen dama ta marairaice "Yaya D'ansarai da su Mama,wallahi gidan Hajiya zan tafi ina canja kaya,dan bazan mutu da yunwaba.Yamik'a mata wasu nannad'ad'd'un carbon paper,Top-bond,babban pensir HB dawasu k'ananan tarkacen zane-zanenshi(Artistry Euipment) to tafi min dasu gida,yanzu haka Bakin Gogi zan tafi wani aikin signboard zanyi.Tasa hannu biyu takar6a "Yaya Aminu ALLAH yatsare.Amin Sudaida suka daga hannayensu suna ma juna adabo,sukayi murmushi sannan kowa yajuya yacigaba da tafiyarshi. ...Dare da rana suna aiki tuk'uru a kanmu,to muma kamata yayi mu zage dantse muyi aiki tuk'uru a cikinsu.Ubangijinmu kabamu rabo me amfani fid-dunya wal aakhirah. 21 Rabi'a Thani 1441 18 December 2019 We Ibrahim' Daughters 👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na shida. Da yammacin juma'a jikokin Hajiya sun cika gidan,tun daga zaure za ka fara jiyo hayaniyarsu sun tasata a gaba da shak'iyanci. Sudaida da Nasmat suma suka shigo,suna k'are mata kallo tasha had'ad'd'an leshin auduga ja da k'ananan fararan duwatsu,wuya,hannayenta, da d'an kunnanta na zinare sai d'aukar idanu sukeyi. Suka kalli juna suka k'yalk'yale da dariya"Hajiya manya wannan irin cakarewar k'uda a gefen gyambo?inji Nasmat. Sudaida tagyad'a kai "Gaskiya kin had'u saura had'uwarki da ALLAH, wannnan k'ure adaka haka?To dawalakin goro a miya,bazawarin tane zai iso da yammacin nan. Gaba d'ayansu suka kuma k'yalk'yalewa da dariya, abinda yahanasu jin abinda Hajiyar take fad'a. Aminu yashigo sai suka sa ihu da tafi "Yehhh... gashinan, gashinan shine bazawarin data k'urema adaka.Yakama ha6a🤔 wai wai wai, ai kowa ya san Hajiya ba dani take yiba,dan ta san ni bazan juri al'alarta na bani bani kamar mak'ogwaro kullum a bashi ba,bani da wannan hak'urin,kusa idanu anjima kad'an za ku ganshi. Khausar tace Alkasim ne.Aminu yace gajan hak'urine dake koma wanene za ku ganshi. Yamatsa wajan Hajiyar suna maganarsu. Sudaida tafara shak'o k'amshin turarenshi da iska takad'o mata kafin tayi magana yashigo yana musu wannnan rikitaccen kallan na shi"ku wallahi kun cika hayagaga bud'ar kan karya,sai kusama mutum ciwon kai.Sudaida da dama takejin haushinshi tace"sai dai dama can mutum da ciwon kanshi yashigo,kace kawai a baka magani za kasha. Suka k'yalk'yale da dariya. Nasmat tace"su autan Inna manya, kace kawai kazo tad'i wajan Hajiya kuma katarar mun tare inda za ka zauna.Sudaida tad'anja tsaki tana mishi kallan sama da k'asa yana cikin fararan kaya yayi shar dashi"Kuma wai haka zai zo hannu rabbana"Yatsareta da idanun shi"ke yarinyar nan wai meye damuwarki da ni ne? Yanunata da yatsa"za fa kisha na jaki,idan baki daina shiga harka ta ba.Ta turo baki gaba"Indai aka k'i jininka ko ruwa kafad'a sai a ce ka tada k'ura,ni kad'ai nayi magana?Ni kamayar marainiyar wayon ka ko?Tahaye gadan Hajiya tana k'unk'uni. Hajiya tace"kai Julaibib yi tafiyar ka anjima sai kadawo muyi hirar mu cikin dad'in rai,lokacin duk sun kama gabansu.Yayi murmushi yana kallan Sudaida data juya musu baya. Sudaida... yakirata.Sai tamishi kunnan uwar shegu.Ke Sudaida ba kiranki nake yiba? Hajiya tasa baki"yau na ji yarinya ba dake yake yiba?Shiruma amsace. Hajiya tashiga tafa hannaye da sallallami.Yad'aga mata hannu"kyaleta Hajiya na jaki kawai zata sha.Eh gwamma haka tunda abin nata tsiyane d'inkin ludayi.Yace"ke Asma'u d'auko min bulalan can.Tana jin haka tafara"Ihu sai tajawo k'atan bargon Hajiya ta duk'unk'une aciki.Yayi murmushi "k'aramar mara kunya kawai,fito a cikin bargon kika yadda zan miki walmukalifatu "wallahi bazan fito ba.Yama Hajiya sallama sai bayan sallar Isha'i zai dawo. Suna hirarsu da Inna tasako mishi maganar A'isha.Yasunkwui da kai tad'anyi murmushi dan ta san halinshi indai yayi haka to zaiyi wuya yayi magana.Kaga kwantar da hankalin ka niba dole zan maka ba,munyi magana ta fahimta da Musaddiq nima banga aibun taba shawara kawai nake ba ka, kanemi auran ta Insha-ALLAH ba kome sai alheri amma fa karka takura kanka idan ba ka so,dan aure ba abin wasa bane zamane da ake fatar yinshi har k'arshen numfashi.Yad'an shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi sannan yad'ago cikin natsuwa ya kalleta "nagode Inna ALLAH yak'ara girma na kar6i shawararki da hannu biyu.Tayi murmushin jin dad'i "Ubangiji yamaka albarka ya taimaki rayuwarka. Amin Innarmu. Wannan makon ya so zuwa wajan A'isha to amma bai samu sarari ba saboda sun gama TP(Teaching Practice)sun koma makaranta. Sai bayan makonni biyu sannan yasamu yashirya ranar juma'a cikin shigarshi ta fararan kaya kanshi da farar hula zita.Yana shiga lungun gidan yahango ya'yan gidan maza suna wasan Hockey. Nasir abokin Abdul yana hangoshi yak'arasa wajanshi yana dariya yace "Kawu" kamar yadda yaji Abdul yana fad'a "yau kaine a k'ofar gidanmu? Ko kazo gaishe da Mamanmu ne?Yagyad'a kai"eh nazo gaisheta ne amma ba shiga zanyi ba ka gaisheta zamuzo da Musaddiq na musamman mu gaisheta.Yayi tsallan murna"to zan fad'a mata.Aisha tana ciki? Julaibib ya tambayeshi.Eh tana ciki inkira maka itane?yagyad'a kai. Nasir yashige gida da gudunshi yana k'wala kiran sunanta. Tayi mamaki tare da k'aryata Nasir.Nasir yafara rantse-rantse da gaske ne yana k'ofar gida.Tarik'o hannunshi "To muje ai ba a k'arya kusa da gida,amma na rantse da ALLAH idan ba shi bane?tayi kwafa wallahi ka san sauran"Eh na yadda.Kanshi a k'asa kamar yana k'irga tsakuwan da suke yashe a wajan.Sai tasaki hannun Nasir da yake mata dariya ai dama na fad'a miki,yajuya wajan wasansu. Yaya Julaibib... Tafurta sunan kamar tana cikin shakkar shi d'inne ko wani me kama dashine?Yad'ago yad'an kalleta"na'am A'isha... Wani murmushi ya su6uce mata "ALLAH da gaske kaine a k'ofar gidanmu? Lallai yau farar rana ce me kyakkyawar suna "Juma'a.A mutunce ta gaishe shi,sai tayi shiru dan bata san abinda yakawo shiba.Shima shirun yayi na wucewar wasu dak'ik'u.Yad'an sake kallanta "na zo gaishe kine,inafatar banyi laifi ba?Tagirgiza kai"wani irin laifi? Gaskiya nagode da wannan ziyara ALLAH yabar zumunci. Ina Yaya Musaddiq? Ya tafi Kaduna.Hirar tasu jefi-jefi,bai wani dad'e ba yamata sallama yatafi. Tabi bayanshi da kallo har yasha kwanar lungunsu ya bace ma ganinta tana tsaye a wajan cikin mamakin ganinshi a k'ofar gidan su,kuma wai wajen ta yazo dan sada zumunci, tasake juya kwalban turaren arabian perfume d'in daya bata,tabud'e tashaki k'amshin me wani irin dad'i,bata zata za suyi magana irin na yau ba,dan sunsha had'uwa ta gaisheshi amma sama-sama yake amsawa.Ashe dai Sudaida gaskiya take fad'a mata,Yaya Julaibib fa yana da matuk'ar kirki,shi kawai baya san a dameshine,kuma baya san magana da yawa. Tajuya zuwa cikin gida ba tare data kawo kome a zuciyarta game da zuwan shiba. Bayan Musaddiq yadawo suka tattauna. Musaddiq yakad'a kai"gaskiya da ka sani kafad'a mata dalilin zuwanka"ai da zafi-zafi a kan daki k'arfe.Yagyad'a kai na fahimceka nagode yamik'a mishi hannu sukayi musafaha. Ranar juma'a data zagayo yaso kwarai yaje wajan A'isha d'an yafad'a mata kome,to amma hakan shi bai tadda ruwa ba" dan sun fara jarabawa me zafin gaske,ba wanda yakoma gida dan itace jarabawarsu tak'arshe a College Of Education Gidan-Waya,sai kuma a zauna zaman girbe abinda aka shuka.ALLAH yaba me rabo sa a. Lidiya tabita da kallo ita da d'akin, dan ta had'a k'aramin hazo ne da hayak'in taban da take ta zuk'a, takalli Ash-tray d'in da take karkad'e tokar guntayen taban data zuk'e,sai tazaro idanu da mad'aukakin mamaki,"Eh ta san Kasham tana shan taba amma sai ran ta yayi mugun 6aci,kuma bai wuce tasha kara uku ba,amma yau bata san ko kara nawa bane,tamatsa jikin taga tad'aga labulan tare da bud'e gilasan,hayak'in da gauraye d'akin yafara raguwa. Kasham... Lidiya takirata,tad'ago tana kallan ta manyan idanunta masu maik'o sun kad'a jawaur fuskarta har ta kumbura saboda kukan data sha bana wasa bane. "Inzayadami Kasham?(Kaham me yafaru) Shar...shar...wasu hawaye masu d'umi suka fara sintiri a kyakkyawar fuskarta"Kasham...dasauri ta d'aga ma Lidiya hannu "Don't dusturb me! Lidiya tagyad'a kai,tarungume hannayenta a k'irji tana kallanta,Tabud'e dirowa tana dube-dubenta "oh no dammed it"ta dunk'ule hannu ta naushi iska,da alama bata ga abinda take nema ba,takoma ta zauna tasake kunna taba, tabi taban da kallo da tunanin yadda karan zai kare a zuk'a d'aya,takai baki tamata wata irin zuk'a data kusa tafiya da numfashin ta,nan take kuma tari ya sark'afeta. Tari tadinga yi kamar na shika, abin har yaba Lidiya tsoro ta kamo ta suka fito waje dan tasha iska. K'irjinta yana mata wani irin suya,mak'ogwaranta ya bushe k'amas kamar miyau bai ta6a bi ta wajan ba. Tad'ago a galabaice takalli Lidiya" ruuwa.Lidiya tagyad'a kai"o barin siyo miki,tana k'ok'arin jinginar da ita ajikin bango dan ta fara wata irin shakuwa abinda yadad'a rikitar da Lidiya kenan. Hey...please come and help meee...!!! Yadda akayi furucin cikin yanayin tashin hankali da tsoro yasashi waiwayawa inda yajiyo sautin. Tasake yafito shi da hannu... Tabbasss ko su wanene wad'ancan taimako suke nema sai yatafi wajen.Bai gane Kasham da Lidiya bane sai da yakusa k'arasawa inda suke yaji Lidiya nafad'in ban san me yashiga kwakwalwarki da zaki karar da karan taba a zuk'a d"aya ba, gashi nan za kije ki kashe kanki abanza...wani irin abu yaji da yabi ilahirin jiki da zuciyarshi"Kasham kwance wanwar a k'asa,farin wandan legging d'inta yayi dabbare-dabbare da k'asa... Dan ALLAH ka taimake mu karta mutu,har lokacin tana dafe da k'irji tana wani irin numfashi,gefe da gefen fuskarta busassun hawayen wahala ne,idanunta suna rufewa da bud'ewa bak'i ciki yana 6acewa. K'amshin arabian perfume d'in data shak'a yasa tad'ago dak'yar takalleshi...sai tamik'a mishi hannunta na dama.Tausayinta yakamashi dan tana cikin wani irin mawuyacin hali,wallahi mutum ba a bakin kome yake ba"Ubangiji👏kamana kyakkyawan k'arshe.D'azu- d'azun nan yahango su,da yan course d'insu sunci kwalliya mazansu da matansu suna ta hotuna suna hayaniyarsu ta dandazon d'alibai. Sai da ya durk'usa sannan ya tabbatar lallai tabar tasha dan gaba d'aya warin ta takeyi"me zan baki ne?Dak'yar tayi furucin"ru.rr... ruwa...yabud'e ragowan ruwan swan d'in daya ke hannunshi.Ya waiwaya inda Lidiya take durk'ushe dan ta taimaka mata ta tashi, amma bai ganta ba.Sai kawai yad'agata ta jingina da bango, yamik'a mata ruwan.Saida tashanye shi duka sannan ta sauke gwauran numfash."Sannu...Yace mata da yana yinshi na natsuwa"Kwallah suka cika idanunta,inama inama ace sunyi aure ne yake bata wannan kulawar?Bata ta6a zatan D'ansarai zai taimaketa idan ya ganta a mawuyacin yanayi ba,saboda halin-ko-inkulan da yake nuna mata. "Kasham...yakira sunan ta.Tad'ago tana mishi kallan k'auna me cike da shauk'i,wallahi kasancewar su a tare,sai ta jita garas...kamar ba ita bace a mawuyacin hali d'azu ba. Haba Kasham kina mace me kima, amma ace kema kina k'arama sama hazo?(shan taba) abin nan ya bani mamaki fa,ga ki da ilmi kina kuma ganin abinda su masu yin tabar suke rubutawa ajikin kwalin"Mashaya taba suna iya mutuwa da k'uruciyarsu"haba Kasham meye amfanin shan taba sigari ne?Kina sane da "nicotine"gubar dake cikin taba ba karamin jazama hunhu matsala yakeyi ba.Dan ALLAH... yahad'a tafukan hannayen shi 🙏alamar magiya kamar yadda take mishi "Ki daina shan taba sigari dan babu kome a cikinshi sai illah. Wata irin k'auna da soyayyarshi ta dad'a mamaye zuciyarta"Oh God...ALLAH kamallaka min wannan bawa na ka.Tajijjiga kai "shikenan D'an Sarai nagode,na kuma maka alkawari ko muna tare ko bama tare, na sha taba na k'arshe a rayuwata,daga yau d'in nan na barta har abadan duniya.Yad'an saki fuska"yauwa Kasham.Ungwai bu gangan(Kasham nagode sosai) dakika kar6i nasiha ta.Tad'an zaro idanun ta"kaii dama kana jin yarenmu?Saita kyalkyale da dariya dai dai da dawowar Lidiya da roban ruwa swan.Sai kuma tayi saroro cikin mad'aukakin mamaki "wannan me shegen girman kan dama d'azu takira?Lallai hankali ke gani ba idanu gululuba.Shima mik'ewa yayi bai sake magana ba yajuya yayi tafiyarshi. Tadinga binshi da idanunta har sai da yayi nisa ya6ace ma ganinta sannan tamik'e tsaye itama tana yar dariya,wallahi wani irin nishadi ta tsinci kanta a ciki, takad'a kai" ALLAH dai yakai damo ga harawa ko bai ciba yayi burgima.Dama duk tunanin rabuwa dashi ne yajaza mata 6acin ran daya sa ta dinga k'arama sama hazo na rashin hayyaci. Lidiya taja dogon tsaki "mahaukaciya kawai, ya gama zaginki ke kuma kamar wata wawuya kina jin dad'i.Wani murmushin yasake su6uce mata"karki d'auki alhaki dan D'ansarai bai ta6a zagina ba,bare kuma yau da yamin nasiha,na kuma kar6eta da hannu biyu. Lidiya ta jefeta da ruwan swan d'in rubbish girl.Dasauri tacafe ruwan tana dariya"kanki akeji Lidiya... Haka nafi so an cema makaho je ka ka gani. 23 Rabi'a Thani 1441 20 December 2019 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na bakwai. Kasan mafarkin danayi daren jiya kuwa? Musaddiq yagirgiza kai.Wai Julaibib ne da Kasham suke kiwon shanu a wani k'aton fili iya ganinka me cike da koren ciyayi.Musaddiq yakyalkyale da dariya"D'ansarai fulani ka koma har matarka take taya ka kiwo saboda tsabar k'auna?Musaddiq da Maimun d'in da yayi mafarkin suka kalleshi yana zuba d'anyan na'a na'a, d'anyan citta da ya'yan algarib a ruwan shayin da yake dafa musu,zuman da suke shan shayi ya k'are,sai yazuba sikari d'an kad'an dan dukkansu basa san zak'i,yamaida murfin tukunyar yarufe,yayi kamar baiji abinda suke fad'a ba. "Julaibib. Maimun yakirashi.Yajuyo da saurinshi yana amsawa"na'am.Bakaji abinda nafad'a bane? Shiruma amsace.Yad'auki wasu kud'i a saman tebur yamik'a ma Musaddiq "Malam tashi ka kar6o mana biredi. Cikin natsuwa yake tafiya dawowar shi kenan daga gidansu A'isha amma cikin rashin sa a yatarar wai sunyi tafiya,ya dai barma Nasir sallahu idan ta dawo yazo yafad'a mishi.Sudaida tana hangoshi tafara murmushi dan ta kwana biyu bata ganshiba,jiya da akace ya zo, taje ta gaisheshi bata jeba. "Yaya D'ansarai sannu da zuwa... Iskar data d'ibo tama bai kalla ba bare yasan ALLAH yayi ruwan tsiranta.Ita da Sinan d'in daya ke shirin yimishi sallama suka bishi da kallo har yashige cikin gidan.Sinan yakad'a kai"Julaibib sai a hankali.Suka gama hirar su sukayi sallama. A D'akin-girki ta tarar da Mama.Mama tace yauwa d'auki abincin nan ki kaima D'ansarai.Haushinshi takeji ta turo baki gaba"Mama shi yace miki yana jin yunwa?Mama tabita da kallan mamaki,sannan tamata dak'uwa gidan ku"Sai yace yana jin yunwa za a bashi abinci a gidan nan?ke wace irin yarinyace?Jiyama danace kiji ki gaisheshi ashe ko bakije ba,saida zai tafi yake tambayar ki sai Sagir ne yace kina d'akinku kin kulle k'ofa.Sa an kine D'ansarai? Tad'auki abincin tabar Mama na mata addu'ar shiriya.Dak'yar tayi sallama dan tasan idan ma bata yiba,sai ya korata ta yishi.Ko kallanta bai yiba har ta ajiye abincin tajuya. Umma tashigo D'akin- shak'atawar dan lokacin da yashigo tana sallar.Yagaisheta cikin girmamawa.Tayi murmushi"D'an Sarai yaro ne me hankali, yasan ya kamata sosai"Karatu ya k'are sai jiran sakamako ko?To Ubangiji yabada abinda ake nema.Yad'an shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi."amin ya rabbi Umma". Tamik'e to bakaci abincin ba?Yakalli kwanon abincin"ai ni ban san ni takawo ma ba,dan a jiyewa tayi tafita.Kai kawai tagyad'a tafita. Tana cin na ta abincin Umma tasa meta batace kome ba hannunta kawai ta damk'o,rik'on data matane yasa tasan cewa lallai bana wasa bane"Umma me nayi?Bakiyi kome ba ko?Sai tafara tirjewa dan wallahi idan ta yadda Umma takaita d'akinta to na jaki zata sha ba kad'an ba dan Umma ba sauk'i,shi yasama ba ta wani wasa dasu akwaita da zafi,sam ba ta d'aukar rashin kunya shi yasa kowa yake shakkarta a gidan,yana yinsu ba d'aya bane da Mama,da wasu lokutan suke maida ita kamar wata kakarsu,sai tazo ta tsawatar musu suke daina wani abun. Umma dan girman ALLAH kiyi hak'uri na tuba nabi ALLAH na biki,kiyi ha...saukan marin yasa sauran kalaman suka mak'ale. Idanunta suka ciko da k'wallan wuya, dan marin ya ratsata yadda yakamata.Tasa ihu Mama dan girman ALLANMU zo ki ceceni,wayyo ALLAH! Ke...!Umma tace tana kallanta cikin zaro idanu "rufemin baki ke mara kunya ko?Ai ina jinku da Mama a D'akin-girki..Umma dan darajar Annabi Muhammadu kiyi hak'uri.... Mama wai kina inane?! Mama tak'araso wajan da saurinta"a ah to me tamiki kuma?Ni tama laifi dama jira nake Musaddiq yashigo in fad'a mishi.Sudaida kuka takeyi da gaskiyar ta ita dai aba Umma hak'uri dan idan ba itace da bakin ta,tace ta hak'ura ba to lallai sai tayi dukan nan ko kuma ta had'a ka da Adnan shima kwallan shege a wajan iya ba da na jaki.Mama takan cemishi "Sarki zalimu dan dai ba ya'yanka bane,baka san zafin suba shi yasa kake musu wannan dukan na rashin tausayi.Sai yayi dariya "ai ko su d'in ne haka zan musu indai sukace baza su bi abinda zan fad'a musu ba wallahi.Dak'yar takwace Sudaida a hannun Umma.Sudaida tace" nagode"to amma Mama kibata hak'uri.Tagyad'a kai"ai zata hak'ura ne.Umma tace"na rantse da girman ALLAH zan hak'ura ne kawai idan taje takaima D'ansarai ruwan sha,tamatsa da abincin gabanshi, takuma gaisheshi tabashi hak'urin dangwarar da abincin da akace takai mishi.Idan ba haka ba tayi d'as d'as d'as da yan yatsunta ta shige d'aki. Duk yadda taso dakewa idan zata shiga d'akin abin yaci tura.Cikin kuka tayi sallama.Yad'ago yana kallanta ta ajiye ruwan ta d'auko abincin,wani haushinshi yacika mata zuciya saboda shi aka so a bata na jaki,da Mama ba tanan a yadda ran Umma ya6aci ba k'aramar wahala zata shaba,shi ba a ganin abinda yakema mutane na halin-ko-inkula sai ita?Dak'yar tace"Ina wuni...wani sabon kuka ya kufce mata wai har hak'uri sai tabashi? Yaya...kayi hak'uri... tausayinta yaka mashi koma menene yasan Umma ce ta sata wannan ban hak'urin.Nayi hak'uri Sudaida ai dama baki min kome ba,to zuba min abincin kad'an, tadauki faranti tazuba ta mik'a mishi.Yayi bismillah yafara ci. Kafanchan ne garin dasu A'isha suka tafi. Babban gidane a Magiya Street me sassa guda bakwai sai dai a kulle suke da kwad'o saboda mutanan ciki ma'aikatane a garuruwa mabambanta,idan ana sha'ani ko sun samu hutun aikine za kaga gidan ya cika da jama'a. Sashin Kaka dana kusa da itane kawai koda yaushe a bud'e jama'a na kai kawo. Gidan yayi shiru saboda sauran yaran gidan sun tafi makaranta sai kukan tsuntsaye da suke ta shawaginsu."Hantsi ya dubi ludayi rana ta haska ko'ina. Hashim bacci yake so yayi amma wani nishad'd'd'an al'amari ya hanashi sak'at bare yabarshi yarintsa. "Aishahhh... Yafurta sunan a zuci sannan yabud'e idanunshi cikin agogon dake manne a bangon d'akin "goma da rabi na safiya. Sai yamik'e, sashin Kaka yanufa Alhamdulillahi"yafad'a daya fara jiyo dariyar ta, hira sukeyi da Kaka.Yayi sallama sannan yad'aga labulan dak'in,caraf idanunsu yahad'u tace"Hum manya gatan wasa,akwana a hantse... Kaka ta 6alli goronta tajefa a baki sannan ta d'an harareshi"to kar dai kanka yayi girma dan tace haka. Yak'arasa shiga yazauna a d'aya kujerar suna fuskantar juna da A'isha.Shi dai A'isha tana burgeshi baya gajiya da kallanta da duk wani abu data keyi.Yamaida kallanshi ga Kaka saboda me kikace kar kaina yayi girma?Tace naga dai wannan kirarin kyawawa akema. Aisha tasa baki "yanzu Hashim yana da makusa neKaka?Aiko makaho yashafa wannan k'ayatacciyar fuskar zaice me kyauce. Yad'an motsa kafad'a"Ah to gane min hanya...wai yaushane tafiyar taki?Tawatsa hannaye"ganinan dai, amma ba wani dad'ewa zanyi ba, tare dasu Mama zamu tafi,kasan har yanzu bamuyi hutu ba, amma da zamana zanyi wallahi garin bai ishe niba. Yagyara zama"Shikenan sai a miki babban gida kawai yadda zai dad'a burgeki,kidinga jin dad'in zama.Cikin rashin fahimta tayi yar dariya "Kaji Hashim fa babban gida sai kace wacce zata dawo da zamanta gaba d'aya? Yagyada kai"To menene A'isha dan kin dawo gaba d'aya? Ai kamar ba matsala bace garin da kike so ne,ga kuma mutanan da kike so. Yakalli Kaka da take ta cin goronta "Ke dai kamar mayya haka kike da goro.Eh koma dai mecece ni ba daina ci zanyi ba ko kai kake siyomin?Ya yamutsa fuska"To da wacce hujjar nasara zaiyi hawan k'aho? Tamishi dak'uwa idan baka siyo ba ai ubanka zai siyo.Shi da Aisha suka d'aure fuska wai su an ta6a musu Iyaye. Hashim yace"a ah Kaka wasa kar yayi wasa a tsikari uwar miji fa.A'isha tagyad'a kai"gaskiya ne dan uba baifi uba ba "Kaka tafara tafa hannaye cikin sallallami.Sai suka kyalkyale da dariya.Ba shakka wuyanku ya isa yanka. Tad'auko carbi zata shaud'ama A'isha ALLAH yabata sa a tayi tsalle gefe"Tabbb yanzu dan ALLAH sai ki shaud'amin wannan k'irgin carbin na ki me siffar rodi?To dawo ki gani mana.Tagirgiza kai"a ah wallahi ai sai in kwanta jinya, suka gama mata shak'iyanci san ransu sannan suka fara hirar arzik'i. Hashim yadad'a gyara zama sannan yakalli Kaka cikin natsuwa"Kaka gaskiyar magana nifa A'isha nake so ba wani 6oye-6oye dama karatune yahanani sak'at to yanzu kam sai dai godiyar Ubangiji an gama har kuma an samu abun yi basai maganar iyaliba? Kaka tad'aga hannayenta sama tanama ALLAH godiya"Ashe tuntuni dakake fad'in Aisha ce matarka na d'auka na k'uruciyane nan gaba idan aka maka zance za kayi tawaye?To masha-ALLAH,ALLAH yasanya alheri,naji dad'in wannan al'amari,dakan d'aka shik'an d'aka tankad'en bakin gado. Hashim yayi yar dariya"Aiko dai ba wani tawaye da zanyi yakalli Aisha ta sunkwui da kai amma labarin zuciya a tambayi fuska murmushi takeyi.Kaka tamik'e zata shaud'a mata carbin"Munafuka ana zance auranta ta nemi waje ta zauna saboda rashin kunya irin na ya'yan yau.Tashige d'akin baccin Kaka da gudu dan wallahi bata manta dukan carbin Kaka ba akwai mugun zafi. Hashim yayi murmushi Kakarmu ta kanmu ALLAH dai yabamu i taku.tsufa me amfani acikin hayyaci da tunani.To Amin Hashimu,amma ba abinda yake kawo tsufa me kyau me amfani sai aikin k'warai lokacin k'uruciya"tsohon banza daga yaran banza yafara"kurik'e karatun"Alqur'ani da sauran kyawawan dabi'u da halaye, kuyi gaskiya da adalci a kome,idan kuka d'ore a haka Insha-ALLAH babu ta6ewa a rayuwarku. IImi shine jigon rayuwa,shine abinda yake gyara d'an Adam,yagayara tunaninshi dan haka ku kara zage dantse da kwazo wajan nemanshi,Ilmi ko wani irine to yanada amfaninshi. ALLAH yama rayuwarku albarka. Amin Kaka. Hashim da A'sha sai rawar kai sukeyi kamar k'adangaran gobara,daga ranar yakoma cin abincin darenshi a d'akin Kaka abinda da ba yayi sai can nisan dare sannan yake tafiya na shi d'akin wani lokacinma Kaka ce take korarshi yatafi yabasu waje za su kwanta. Kafin su A'isha subar garin Kafanchan sai da aka tsaida magana tana gama makarantar secondary za ayi bikinsu ba wata matsala da aka samu kasancewar su Ya'ya mazane kuma duk Kakace ta haifi Iyayan nasu. Shi kuma nan da nan yafara aikin ginin gidanshi a Zaria Street. Kasham tana shafa ma faratanta jan farce (nail polish)ruwan k'asa,Baranzan yashigo cikin kakin soja. Suka kalli juna na wucewar wasu dak'ik'u."Beauty ina kikaje tun d'azu nake ta jiranki?Kamar ba da ita yake magana ba,zuwan can kuma bayan ta shak'i iska ta baki ta hanci sannan tace kasuwa naje siyo wannnan tanuna mishi nail polish d'in.Yazauna"anjima zani Jos amma kwanaki uku zanyi,to na baki time kafin indawo ki shirya kayanki zamu wuce barrack. Barrack kuma?Ta tambayeshi cikin mamaki"Eh barrack kin gama makaranta to zaman me za kiyi?Mutafi kafin lokacin auran mu yayi nafa gaji da zama ni kad'ai kingane ko?Bai jira amsawarta yajuya yayi tafiyarshi.Tabi bayanshi da harara lallai za ayita dan wallahi tayi rantsuwa ba wanda zata sake bi har takwana dashi indai ba D'ansarai ba,bata ga kuma wanda ya isa sata canja wannan ra'ayi na taba har abadan duniya.Ita ya ma sosa mata inda yake mata k'aik'ayine,cikin gari za taje wajan Julaibib ta kwana biyu bata ganshi azahiran ceba amma kullum dashi take kwana dashi take tashi a cikin zuciyarta. Tacanja kayan jikinta da dogon buje na velvet bak'i sai rigar shirt checker me d'amewa ta yafa siririn bak'in mayafi a gyararren gashinta data mishi ponytail style,jaka da takalmanta masu tudu bak'ak'e,tasa wasu manyan d'ankunne masu kama da awarwaro suma bakak'e sai siririyar sark'ar rosery a wuyanta. Kai tsaye tashiga shagon.Abdul yana zaune yana aikin gida da aka had'osu dashi daga makaranta a darasin tattali (Economics) tak'arema shagon kallo ya dad'a cika ba kamar kwanakin baya ba, za taso taga irin canjawar da D'ansarai yayi.Tadawo da kallanta ga Abdul "Kai d'an samari ina Julaibib d'in? Fuska a had'e ya amsa "Baya nan.Haushi take bashi ita ba wani abu za ta siyaba amma sai tazo tana damun mutane yad'anyi k'unk'uninshi. Taja kujera tazauna tana mishi kallan nazari,wani murmushi ya su6uce mata "wai shima k'arami dashi ya iya had'e girar sama data k'asa,tana so ta mishi wasu tambayoyi game da Julaibib amma ta san ko tayi a banza talaka ya girmi sarki bazai bata amsaba"Kai k'aninshine? Uhh yace batare daya bud'e bakiba. "Ina Sudaida?Ya yamutsa fuska shifa baya san adameshi, dak'yar kamar me ciwon baki yace "Ta tafi makarantar allo.Bata sake tambayar shi kome ba ta dai gane wannan halin nasu na rashin san magana a jinin sune.Itama sai ta bud'e Ovation d'in hannunta tana dubawa amma rabin tunaninta na ga Julaibib da inda yatafi. Da d'an hanzarin shi yashigo shagon tare da sallama dan ya san lokacin makarantar allo yayi ba ya so Abdul ya makara.Caraf idanunsu yahad'u"La'ila ha'illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin"tabbas da bata ganshi ba komawa zaiyi.Tamik'e tsaye tana mishi kallan k'auna me ciki da shauk'i " Yayi shar dashi cikin fararan kaya kanshi da bakar hula dara takalmanshi sau ciki farare,k'amshin arabi'an perfume d'inshi ya mamaye shagon,D'ansarai d'an gayu ne,me tsabta na gaban kwatance dan ba wanda zai juri sa fararan kaya sai ma'abocin tsabta.Idanunsu yakuma had'uwa...sai sukaji wani irin yanayi a ilahirin gangar jiki da zuciyarsu,da sauri yakauda kai yana Isti'aza. "My enigma ma You're wellcome.. Julaibib bazan gaji ba ga shi na sake biyo ka,wallahi ba saboda kowa nashigo cikin gari da safen nan ba sai dan kai.Abdul yad'auki allanshi "Kawu na tafi.To Abdul ALLAH yabada sa a. Yara6a ta gefensu yawuce yana amsawa da"amin ya rabbi. "Julai...yatari numfashinta"Kiyi hak'uri bazan ta6a miki k'arya wai dan kiji dad'i ba,bazan iya auran kiba, kiyi hak'uri dan girman...k''iris ya rage ta rungumeshi yayi taku biyu baya da sauri sai ta biyoshi har yafita a shagon yajuya da sauri yacigaba da tafiya.Tabishi da kallo har yasha kwana ya6ace ma ganinta. Damme what an enigma man.Tafurta tana furzar da hucin takaicin,ta rik'e k'ugu tana kallan shagon"Ya tafi yabar mata shagon duk da kayan mak'udan kud'in da suke dank'are a ciki amma ko a jikin shi, wai an yak'ushi bishiya"shi D'an Sarai ta rasa me yasa yakeyi kamar yana jin tsoronta a wasu lokutan? Ba saurayin data ta6a yi da baiyi kwad'ayinta ya nuna maitarshi a fili ba sai shi, To me yasa!!!??? Yanzu duk abinda yamata za ta iya d'auka ko? Sai kuma ta girgiza kai"Aiko ba kayan Julaibib bane baza ta iya d'aukaba tunda ba na ta bane,idan tayi haka ai tazama 6arauniya"which is forbiden".Taja kujera tazauna dan bazata tafi tabar mishi shago a bud'e ba tunda ita tasashi tafiya,da batayi yunk'urin rungume shiba ta san zai tsaya. Aminu ne yashawo kwanar yana rik'e da bokitin fenti da roller daga wajan neman halali yafito. Tamik'e da sauri tana fad'in"yauwa dan ALLAH Aminu ka taimakeni kajirama D'ansarai shago yaje gidane ni kuma sauri nake yi ban san abinda ya tsaya yiba.Ya ajiye kayan aikinshi aciki yajawo buta ba matsala.Sukayi sallama.Yayi alwala ya gabatar da sallar walha da aiki yanashi yi a dai-dai lokacin daya sabayi da zarar rana ta 6ullo.Shima gajiya yayi da jiran dawowarshi yaduba mukulli ya kulle shagon, a gajiye yake yaci aikine kamar ba gobe,yanzu zai je gida ya huta,gaskiya neman halali da wuya kowa kagani a inuwa to ba shakka ya sha rana. Tunda yakoma gida yarasa sukuni wani abu a can k'ark'ashi zuciyarshi yana damunshi,shi dai yasan Kasham tana san shi da gaske, to amma ya rasa gane fargabar da take mamaye zuciyarshi game da ita.Ga wasu irin rikitattun mafarkai da yakeyi,ya rasa gane ma'anarsu,sai dai shi har kullum yana mik'a al'amuranshi a wajan ALLAH,yana yawaita sadaka. Da daddare suna zaune a tsakar gida ita kanta Inna ta lura dashi, abincin ma k'adan yaci dan yasan Inna tana saurin gane yanayin shi da bazai ci ba dan cikinshi a cunkushe yake."Autana yau dai ko baka jin dad'ine?Yabud'e idanun shi daya rufesu kamar me bacci sun d'an canja kala"Inna kai nane naji yana d'an saramin.Tamishi kallan tausayi me cike da soyayya irin ta d'a da mahaifi"wayyo! Sannu...ai na ganka yau ba wata walwala,ya kamata kasha magani,ALLAH yasauwak'e. Yagyad'a kai "Amin Inna, ai nasha magani". Alhaji Abdullahi ne yashigo da sallama Julaibib yakar6i kayan hannunshi "Sannu da zuwa Baba" Yauwa D'ansarai mun wuni lafiya? Yau ka rigani dawowa. Yazauna yana hutawa.Inna tad'auko mishi abinci tana mishi nata sannu da zuwan.Ya amsa da kulawa.Yafito da kaya d'inkakku kala biyar dukkansu farare yana nuna ma Inna.To har anyi d'inkin ne? Amma sunyi kyau madalla Ubangiji yasa rai aka yiwa.Ya amsa da amin yana kallan Julaibib"Ina alfahari dakai D'an Sarai tunda kana san ganin tsohonka ya fi na kowa,amma ni gaskiya nan gaba kar a sake d'in kamin kaya duka kala d'aya yo wannan idan hira nake zuwa ai sai budurwar tawa tace min d'an anace,wanke kamayar,itafa bazata gane cewa kullum wani sabo nake sawaba.Julaibib Yad'an shafa kwantaccen bakin gashin kanshi "kai Baba wani irin zuwa hira kuma,yanzu sai kama Inna kishiya?A ah kaji D'ansarai da wata magana fa, ba a aurowa aka auro ta?Inna tana yunk'urawa za ta tashi yafara dariya"Dakata mana ina za ki?Ko sauraran shi bata yiba"kanka akeji...yad'an daga murya"zo mana Maimunatu...tashige d'aki.Alhaji Abdullahi yakad'a kai "Uh uh uh mata duk haka suke da kishi ba babba ba yarinya,ka ganta nan tunda k'uruciya indai zanyi maganar k'arin aure to zata tashi tabarmin wajen.Julaibib ya sunkwui da kai dan maganar ta mishi nauyi. Yasake kallan Julaibaib sannan yanuna shi da yatsa "Ita mace dad'in mu'amala ne da ita amma sai ka fahimci halinta,ka kuma sauke duk wani nauyi na ta daya ke kanka,to sai kaga ALLAH yahore maka ita kaji dad'in zama da ita,ai ka sani dai-dai da tsinken da zatayi sakacen naman da ka siyo mata idan tagama ci kai zaka kawoshi ko?Yagyada kai "Eh Baba na sani". Yace to mace yar gatace gaba da bayanta, kar kayi la'akari da kome yayin da zaka mata kome face cewa aure bautar Ubangijine, shid'in ne yace haka za a mata bad'an kome na taba.Kuma babban jigon zaman aure shine HAK'URI za kayi hak'uri da ita a wajan gazawar ta irinta yar Adam,kaima za tayi hak'uri dakai a wajan gazawar ka irin na d'an Adam,dan babu wani mutum a doron duniya da yake cikakken da bashi da nak'asu sai Annabinmu Muhammad sallallahu alaihi wa ahlihi wasallam.Dan haka sai ana kauda kai ana yafiya,dan wasu lokutan idan suka kwafsa maka sai kaji kamar ka karairayasu,kashafe su a doron duniya,to amma hakan bazai yiwuba dan namiji ne yake cika mace,macece take cika namiji,taimakeke niyace atsakanin juna. Kadinga tuna cewa tunaninka da nata ba d'aya bane,ko a gidan fiyayyan halitta za6abban za6abbuma sun nuna irin halin nasu,kuma hakan shine cikar macen taka,haka ALLAH yaga damar halittarsu. Yagyad'a kai cikin ladabi" To Baba nagode. Maza dangin gurjiya sai an fasa ake sanin me k'waya. 25 Rabi'a Thani 1441 22 December 2019 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na takwas. Baranzan yashigo gidan da d'okin ganinta, yanata k'wala mata kira amma shiru bata amsaba. Yashiga d'akin da niyyar tashinta dan ya san bacci ne kawai zai hanata amsa kiranshi da kuma fitowa ta mishi Oyoyo cikin d'okin ganinshi itama.Yaja yatsaya da mad'aukakin mamaki yana kallanta,tana zaune kwalliya take fuskarta,yanuna ta da yatsa"au dama kina jina amma kika ki amsawa?Wai lafiya kuwa?Yabita da kallan nazari cike da shakka. "Beauty wai lafiya kuwa? Tafurzar da hucin takaici sannan tace"da wannan kiran irin na yan farauta zan amsa maka?Tacigaba da zizara ma girarta jagira"ni gaskiya bana san rashin natsuwa.Yayi saroro kawai yana kallanta tagama kwalliyarta tajawo kayanta tana sawa bujen jeans ruwan bula da d'amammiyar riga mara hannu ruwan madara, yau tayi k'ananan kitson kalaba ta tubkeshi da ribbon ruwan madara sai d'an kunnan beads ruwan bula data sa,wallahi tayi kyau k'irar kalangunta ya fito rad'am,ta sunkuya tana sa takalmi ruwan madara sau ciki me tudu,tagama sawa tamik'e tsaye tana saba jakarta a kafad'a kalar takalmanta ruwan madara,tana shirin fita yakirata "Beauty...Taja ta tsaya sannan tajuyo fuska a yamutse take mishi wani kallan uku ahu"wani abune?Kamar yaya wani abune?Tad'aga misho hannu"kaga malam ya za muyi canjan tambaya ba amsa?Ni fa wallahi sauri nake yi idan ba ka da abin cewa...Yayi murmshi dan wannan kwalliyar ta tsumashi. "Kurum Ishshi Bazinzira(Akwai kud'i sosai, na rantse miki da ALLAH) Yanuna mata aljihunshi yaushe kike so muje Kasham Hotel muci ubansu?Da kud'i da maciji maganinsu kisa"sai yamik'a mata abinda ya nannad'e a warraping sheet.kallanshi tayi kamar bata gane abinda yake nufi.Yagyada kai "yes take it's yours...ta d'auke kai daga kallan da yake mata,ta san Champagne ne,to ita da ne zai bata Champagne taji ya burgeta ya mata gwaninta, cikin jin fushi tace" baa na so.Kamar ya bakya so? Mutumin na ki nefa?Tagalla mishi harara"so bloody what?To hell with it.Ba na sha,bazan k'ara sha ba,dan haka karka k'ara kawo min.Beauty... tad'auki agogonta na fata tana d'aurawa kana da lokacin 6atawa amma ba da Kasham ba,tayi tafiyarta.Yayi murmushi yakai d'aki ya ajiye mata, ya san za ta sha yanzu dai ranta a 6ace ne, ko me yasame ta haka oho yad'an motsa kafad'a shima yajuya. A waje suka had'u da Lidiya yake fad'a mata abubuwan da Beauty take mishi sunyi yawa fa,she bai gane me yashiga k'wak'walwar taba.Takad'a kai cikin takaici "Ranar wanka ba a 6oye cibi...dan haka ta k'yank'yasa mishi abinda ke faruwa. Yajijjiga kai "lallai biri yayi kama da mutum"To yanzu kina nufin cikin gari ta tafi wajan shi?Ko shakka babu,abin takaicin kuma nama na jan kare sai shishshigi da k'wala kai a faranti amma ba kwarjini. Oh damme.Yadunk'ule hannu ya naushi iska ran maza ya 6aci, allurar soja ta motsa.Ya kalli Lidiya za muyi magana anjima? Tagyad'a kai "shikenan. Yashiga mota ya zauna yana sauraran wakar"Who let the dogs out..ya kunna taba yana zuk'a, amma zuciyarshi k'ara tafarfasa take yi idan ya tuna duk abinda Beauty take mishi wai saboda wani filthy stupid bahaushe d'an cikin gari ne.Yadinga tuna beautiful life d'in da sukayi,suna matukar son juna,kuma Beauty kome na ta daban ne,musamman shi da take son shi tana bashi kome da yake so cikin dad'in rai,bayan alakoro har gyara take k'ara mishi.Wata soyayyarta ta dad'a tsumashi sai kawai yaja motar dama cikin gari za shi yabiya kud'in k'ofafin da yace a mishi na dank'areren gidan da yake gina ma Beauty ita da kids d'in da za ta haifa mishi. Yana tsaye a Mak'era suna magana da me aikin k'ofofin kawai ya hango ta goye a bayan wani me mashin sunata dariya. Ranshi in yayi dubi ya 6aci zuciyar shi ta raya mishi wannan ne tsinannan bahaushen da take bi cikin gari,sun gama abinda za suyi yanzu kuma zai maida ita gida.Lallai yau za a yi ta sai yashige mota yabi bayansu sai dai kash... Kafin yak'arasa har me mashin d'in ya sauketa ya k'ara gaba dan Samaru zai wuce shi yasa Baranzan bai ganshi ba. A tsakar gida yasame ta, ta d'ora k'afa d'aya akan d'aya tana cin k'osan rogo tana wata yatsina kamar dole a ka mata sai ta ci. Beauty daga ina kike?Yayi tambayar cikin d'aga murya da tashin hankali.Itafa Baranzan ko k'aunar ganinshi ba tayi dan haka tajuyo cikin jin haushin tambayar da wanda yayi ta"daga Inda ka aikeni mana. yanuna ta da yatsa"ke! kar ki min rashin kunya fa, manufuka kawai,ba daga wajan tsinannan bahaushen nan kike ba?Tayi lallausan murmushin tura haushi "Thank God tunda ma ka sani,wani abu ne? Tamishi tambayar cikin wani malalacin kallo sannan tacigaba da cin k'osan rogon ta hankali kwance tana wakar "Hail Mary mother of Jesus. Bazato taji saukan mari hagu da dama yafara zaginta ta uwa ta uba ya kaima k'osan kutifo ya tarwatse a tsakar gidan, hannayenta dafe da kuncinta idanunta sun kad'a jawur suna fitar da hawayen azaba. Hakan bai mishi ba kawai yasa hannu ya zaro belt d'in daya d'aure k'ugunshi yadinga labtarta har sai da ya tsistsinke ya jefar yana huci"ke dan abu kazan uban ki har kin isa kiyi soyayya da wani bayan munyi alk'awarin aure dake?Ina raye da raina da lafiya ta?Bazinzira (na rantse da ALLAH)idan kika kuma zuwa wajanshi abinda zan miki sai yafi wannan stupid,rubbish girl.Yagaji dan kanshi yayi shiru yajuya zai bar gidan.Dak'yar tamik'e dan ma zuciyarta ta bushene amma yadda tasha na jakin nan ai ko d'aga yatsa baza ta iyaba,tasha gabanshi"har ka gama kenan?Tagyada kai tare da had'e tafukan hannayenta. "Ungwai bu gan gang (Nagode sosai) Amma ka sani daga yau,yanzu d'in nan na gama soyayya da kai "I jilt"har abadan duniya.Wani kuka ya kufce mata amma bakinta bai mutuba, cikin kukan tanuna mishi d'akin ta shiga ka kwashe kayan sawanka da duk wani abu daka san na kane kabar mana gida. Jikinshi yayi sanyi"wai an jefi kaza da gishiri"bai ta6a tunanin haka ba"haba Beauty yayi d'an murmushi "It sound phony,to ma me yayi zafi ne da har idanu za suci wuta haka? Me yayi zafi? Ta tambayeshi cikin tashin Hankali. To meye ma bai tafasa har ya k'one ba bare wani zafi? Bana son ka Baranzan, kuma ko ban auri D'an Sarai ba kai dai na gama soyayyah dakai,tad'aga murya cikin kuka haka ake soyayyah?Haka ake nuna soyayyah? Kai baka iya kome ba sai duka? Julaibib ya nuna baya so na kai har yagaji yafad'a min inyi hak'uri shi dai bazai aure ni ba, yana nuna ina damunshi,duk abinda nake mishi baya so d'in amma dai-dai da rana d'aya bai ta6a d'aga hannun shi yace zai mareni ba sai kai,tanuna shi da yatsa sai kai me ik'irarin kana so na, kana so muyi aure in haifa maka Ya'ya,a haka ne zamu zauna zaman auran for better for worst till death due part us? Dukan da kamin ko Mamana da take da zafi bata ta6a min irin shiba tunda takawo ni doron duniya, tacire rigar ta,ta jefar tana nuna mishi wani k'aton tabo a kafad'arta"wannan ma tabon dukan kane wanda yariga ya zauna kenan har abadan duniya,kalli yadda ka farfasa min jiki?Tasake fashewa da kuka me cin rai,na rantse da ALLAH ta dankwali k'asa a d'an yatsanta ta la sa,na barka har abada kamar yadda na bar nonon uwata.Kai Baka da hankali baka san yadda zaka sace zuciyar mace ba, abinda ka iya shine ka kama mace ka yita duka kamar ka kama 6arawon da yayi fashi da makami da kakin soja a jikinshi da bindiga a hannunshi,wallahi ba ka iya kome ba,kaje ka koyo,sai kuma takoma sambatu Julaibib ya iya tafiya ta natsuwa,baya san hayaniya shi shigar shi kullum ta fararan kayane,ai kaima kasan ba me jure sa fararan kaya sai me tsabta na gaban kwatance"he is a gentle melanin beauty that I have never meet before. Yarik'o ta kiyi hak'uri Beauty raina ne ya6aci zuciyata tana ta tafarfasa abinda yakaini ga zagi da dukanki kenan, na ka sa danne temper na amma ai kinsan ina sanki, zai rugumeta tayi wani ihu ta k'wace da k'arfin bala'i"tamishi kallan uku ahu"ALLAH sarki ai ban san haka zuciyar ta ka tayi ba,da dai naga tiriri yana fitowa ta kirjin kane to da na yadda, taja dogon tsaki "kai koma menene da menene wallahi ba wajan kuka na bane mutuwar uwar kishiya,ai kome yazo k'arshe.The game is over. sunan wata wak'a. Yajuya yayi tafiyarshi ai yasan tashi da Beauty bata 6aci sau nawa suna fad'a kuma su dawo su d'inke kamar wani abu bai faruba.Ran tane kawai ya6aci amma da zarar ta huce za su daidaita.. Bai koma gidan ba sai kwanciyar bacci sunje Kasham Hotel Kafanchan sunyi holewarsu da yan mata,yayi tatil da uwar laifi(giya) tamik'e da sauri dan saura kad'an yafad'o a jikinta,Itama ta kasa bacci ne dan gaba d'aya jikinta ya mata tsami dan ma an mata allura tasha magunguna,dak'yar ta canja kayan baccin ta da wando jeans da bakar rigar sanyi me hula tazuba k'ananan abubuwan da zata buk'ata a jaka tabar d'akin tana surutai"ai kin banza talaka ya girmi sarki idan ma kayi aman ka kai zakata gyara d'akin gobe da safe. Yana tashi yaja doguwar hamma baki a bud'e yana mik'a tare da addu'ar"Our father who is in heaven,I love you thy name...bai k'arasa ba ganin ba Kasham kwance a gefe kamar yadda suka saba,yafito tsakar gida suka gaisawa da Babanta sannan ya tambaye shi " Ina Beauty ne? Baban yace wai ba ta d'akin? Eh bata cikin.To bata kwana a gida ba ko kuma yanzu tafita.Kai yaushe kashigo?Baranzan yasa ke yin hamma"ba a gidan ta kwana ba ke nan, dan a d'akin nakwana yanzu natashi daga bacci,Baba barinje gida in dawo.To Baranzan a dawo lafiya(Oh🤔 mu Ya'yan Ibrahim ALLAH d'aya gari bamban.Abin da mamaki wai talaka da mata hud'u harda k'wark'wara amma me gari gwauro) Sai yamma lik'is rana ta tafi tana shirin fad'uwa sannan Kasham ta koma gida,tafara masifa ganin bai d'auki ko tsinken sakacen shiba, a fusace tafara watso duk wani abu na shi tsakar gida ai na fad'a maka"I jilt.. Is over,Is totally over...na rantse da ALLAH zan mishi rashin mutuncin da har ya mutu bazai manta dani ba. Babanta yafito daga d'aki yana kallanta da kayan da take watsowa tsakar gida da mad'aukakin mammaki "Kasham me ya ta6a k'wak'walwarki haka?Ya za ki dinga watso mishi kaya tsakar gida?Cikin hayagaga...tad'aga mishi hannu"hey! ba ruwanka ai tun jiya nace ya kwashe kome na shi.Yarik'o hannayenta "Baranzan da za ki aura kayan shine fa kike watsowa? Tak'wace"Baba ka kyaleni a cikin hayyacina nake ban sha giya ba bare kace tafad'a min ba gaskiya ba,soyayyarce kawai bazanyi ba,na fasa auren nashi,kuma na yi alk'awari ko na rasa mijin aure to da in auri Baranzan gwamma in mutu ba aure.Baza ki auri Baranzan ba to saboda me?Wa zaki aura? Saboda bana son shi,kuma D'ansarai zan aura.Yakalleta da sauri yana maimaita sunan D'ansarai? Dansarai? Waye kuma haka? D'ansarai shine wanda nake so kuma a cikin gari yake,shi zan aura zan kuma yi abinda yake yi,shi musulmi ne,nima wallahi sai na musulunta na yi sallah. Yatafa hannaye cikin kad'a kai"Jesus Christ.Yabita da kallan nazari sai huci takeyi kamar ta ci babu.Yanunata da yatsa"to ban yadda ba.Tagyad'a kai"ni ai na fad'a maka ne dan ka sani,ba wai dan ka yadda ba,tunda dai ai ni zanyi zaman auren ba wani ne zai min b...saukan marin da aka mata yasa sauran kalaman suka mak'ale... Kasham ai ban san baki da hankali ba sai yau, a duk zuri'ar mu ba me salla sai ke ce za kice za kiyi? Tayi d'as d'as d'as da yan yatsunta"to baki isaba,ina tagirgiza kai wannan ba za ta sa6uba bindiga a cikin ruwa, dama abinda ki ka dinga yi kenan a makaranta bin mazan hausawa?Tama Maman na ta wani kallo me kama da harara"ni ina ruwa na da rashin sallar zuri'arku?Kuma aike ma kin san mazan hausawa ba k'ashin yarwa,sau dubu nawa ina kawo miki kayayyaki kinaci,kin kuma sani sarai su d'inne suke bani,baki ta6a k'in kar6a ko ki min fad'a akan in rabu dasu ba, sai yanzu dan nace ina san zama irinsu?Ashe kowa yana san wawa haihuwar shice ba a so? Tsamaninki banza kika dinga ci? Takai mata wani mari amma tagoce dasauri yabi iska, tamata dak'uwa kinci uwaki,dan abu kazan ubanki ba za kiyi sallah ba,abinda ba mayi dake sa'in'sa amma gashi daga fara cewa kina san wani tsinannen bahaushe har kina min rashin kunya kina fad'amin maganar dakika ga dama...Tabuga cinye na rantse da ALLAH baki isaba sai dai idan bana numfashi za kiyi sallah.Kasham tagyad'a kai"To maji ma gani ai...an binne tsohuwa da rai. Lidiya tashigo suka had'u suna ta zagin ta amma ko a jikinta wai anyak'ushi bishiya.Tad'an motsa kafad'a tare da ta6e baki "Kanku ake ji...ta d'auki jakarta"bazan iya wannan bud'ar kan karyan ba, kuci kanku kusha bak'in ruwa. "Kasham ani yake?(Kasham ina za ki?) Tajuyo muryar Maman a tsawace.Tayi taku biyu sannan taja ta tsaya"Ani yake?Tasake tambayar ta,ko a jikinta tace. "Ana kari Julaibib(wajan Julaibib zani) Dawo ki zauna karki kuskura ki bar gidannan.Tad'anja tsaki sannan tak'arasa ficewa da saurin ta"idan na dawo kar ki barni inshigo"kuma ko ku mutu ko ku rayu wallahi sai na yi sallah kuma ALLAH zai taimakeni in auri D'an Sarai...ALLAH dai yakai damo ga harawa... Tajuya kan mijinta cikin tafasar zuciya ni dai ka sani gaba d'aya zuri'armu babu wanda yake sallah,sai dai in wancan ne yake yaudare min yarinya,yake so tabi layin shi,to kaji na rantse da girman ALLAH bazan yadda ba, zanje har cikin gidanshi inci mutuncin shi, ba ki yamana ga shi nan yana shirin kama Kasham, dama ya dad'e yana fad'in idan munki sallah to Insha-ALLAH Ya'yanmu sai sunyi.Yagirgiza kai cikin damuwa yasan matarshi bata da mutunci, to shima dai dan uwan na shi Yayanshi uwa d'aya uba d'aya Shedrak,wanda a yanzu yake amsa sunan Alhaji Hafiz ba barin ta kwana yake yiba shima mafad'aci ne wallahi. Kiyi hak'uri Dinatu mu zauna musan abinyi,nima ba na goyon bayan abinda tazo dashi,kuma da kike fad'in Shedrak ne yake yaudare ta to yaushe rabonshi da zuwa garin Zonkwa bare har yashigo k'auyan Madauci?Tayi shiru.Yawatsa hannaye kingani ko?Ai shekarun da yawa ko Kasham baki haiifa ba a lokacin. Muje wajan Pastor ayi addu'a ko Baptismal idan yaka ma sai a sake mata.Tamik'e cikin gyad'a kai"eh to ka kawo shawara to tasu mutafi ai bamuga ta zama ba da zafi-zafi akan daki k'arfe. Kasham bata kwana a gidan ba,sai washe gari da hantsi.Lokacin kuma Mamanta ta dad'e da tafiya kasuwa,dama ita take fita ta nemo musu abinda za suci dama sauran buk'atunn rayuwa,yar kasuwa ce sosai da take cin kasuwancin ta gari da k'auyuka na nesa dana kusa,shi kuma mijin kullum yana gida yana aikacen-aikacen yau da kullum da akeyi a gida har girki ma a wasu lokutan idan ba kowa shi yake yi.Yad'ago yana kallanta "Kasham zo mana ganin tana shirin shigewa d'akin ta,tayi kamar ba ta ganshi ba kuma har had'a idanu sukayi lokacin da za ta shigo. Tazauna a d'aya farar kujerar robar,ko sannu bai samu arzk'in tace mishi ba bare in kwana (Oh mu Ya'yan Ibrahim🤔inda ranka ka sha kallo...sunan wani shiri a Freedom Radio)A ina ki ka kwana Kasham?Tazuba mishi manyan idanunta masu maik'o"wannan wace irin tambaya ce haka Baba? Yagirgiza kai "ai na ga ke a gida kikafi kwana shi yasa na tambayeki kuma Baranzan yazo nemanki na san ba a wajan shi kika kwana ba.Baba ba ruwanka da inda na kwana. Tad'ora k'afa d'aya akan d'aya tana karkad'a kafar dama,tana wata yatsina da hura hanci alamar bala'i takeji da gasken-gaske.Ta sauke gwauran numfashi Ka na ji ko Baba? Eh ina jinki.ALLAH sai na auri Julaibib,ka san yadda nake jin k'aunar shi a zuciya ta kuwa?Takad'a kai"no matter how zan kwatan ta maka ba za ka gane me nake jiba...sai tafashe da kuka duniyar ta cukurkud'e mata wallahi,rana zafi inuwa k'una,to a ina ake so tasamu sassauci ne?Julaibib,Iyayanta,Baranzan, Lidiya, da yan uwan ta kowa yana jin haushinta? To ita tace ma zuciyar ta ta k'aunaci D'ansarai ne??? Tausayi irin na d'a da mahaifi ya mamaye zucyarshi,saboda shi yana da san Ya'ya sai dai abinda tazo dashi me girma ne, amma ga dukkan alamu tana san wannan D'an...menene ma sunan na shi oho ya manta, tunda har ta yadda tabar Baranzan da suka shafe shekaru hud'u suna soyayyar su hankali kwance ba abinda ya ta6a shiga tsakanin su na tashin hankali amma akan shi wannan bahaushen sun fara fad'a,dama duk cikin Ya'yansu ai daga Kasham sai Rahab ne basa canja samari kamar yadda ake canjin kayan sawa,kuma su biyun ne suka maida hankali ka'in da na'in akan karatu, sauran maza da matan suna can suna cin karansu ba babbaka. Matanma sai su shafe watan ni takwas basu lek'o gida ba, suna can wasu garuruwa da jahohi suna zaman kansu suna kuma sheke ayarsu yadda yaka ma ta,galibi ma zuwan su gida sai da dalili me k'arfi kamar lokacin Christmast,New-Year, da Esther,su kanzo a Valentine amma ba kowane Valentine ba. Kiyi hak'uri Kasham dak'yar ya rarrashe ta tayi shiru,manyan idanunta masu maik'o sun kad'a jawur "Kiyi hak'uri Kasham ni kin san matsala ta ba babba bace,zan iya barin ki kiyi sallah tunda kina sanshi, za kuma cigaba da kasancewa 'ya ta,bazan tauye miki yanciba" you have human right"kuma shekarunki sun kai na duk wani d'an Adam me hankali,babbar matsalar "inda gizo ke sak'ar Dinatu baza ta ta6a amince miki ba,idan kinki ji to na san za ta yafe ki a cikin Ya'yanta, za ta barma hausawa ke forever kinga kuma baki mata a dalci ba, ta so ki ta kula dake ta miki kome na rayuwa...kema ba za kiji dad'i ba.Yakalleta yad'an motsa kafad'a ya cigaba da gyaran waken da yake yi na girkin rana.Itama tamik'e tana k'unk'uni.Yad'anyi murmushi k'uruci dangin hauka,Kasham baki san rayuwa ba.You know nothing but wannan soyayyar data rufe miki idanu." So makaho... Lidiya tabita da kallo "to wai ke da kike ta wannan hank'oran,kike k'ok'arin 6atawa da kowa akan wannan tsinannan kun dai-dai tane ya yadda zai aureki zai zama miki uwa da uba dasauran danginki da za ki rasa? Dan abu kazan ubanki ina ruwanki?Babbar manufuka kawai,bitch ai na san ke ki ka k'yank'yasa ma Baranzan! Lidiya ta k'yalk'yale da dariya dan abun bai ba ta haushi ba,ta kuma k'yalk'yakewa da dariya tana tafa hannaye Jesus Christ of Nazareth gaskiya kin fara cin kai (Hauka) Kasham ta fad'a gado ta rufe idanunta zuciyar ta tana wata irin bugawa,da bata d'auki alk'warin dai na shan taba ba to da yau ALLAH ne kad'ai yasan ko kwali nawa za ta sha,ba ma kara ba,ta dunk'ule hannu ta dinga naushin matashi idanunta na tsiyayar da hawaye masu d'umi " So babbar cuta... Lidiya ta dafa kafad'arta sai tamik'e da sauri kamar wacce kuna ta harba"get the hell out this house...ta fad'a a haukace.Lidiya tamik'e sai dai in bar miki d'aki amma ba gida ba,dan kema ba na ki bane. Wawuya kawai da har yanzu ta kasa gane san maso wani take yi... Sai kinyi 6atan 6akatatan za ki gane ashe shayi ma ruwa ne madara da bournvita ne ya canja mishi kala. Mamanta tana dawowa daga kasuwa ko hutawa batayi suka tasata a gaba sai gidan Pastor.Dama yasan da zuwansu dan haka suka zauna zaman jiran fitowarshi Yashigo D'akin-shak'atawar cikin bak'in suit, rigar ciki shirt, takalmanshi da mashak'in wuya (neck-tie)ruwan k'asa,wuyarshi da sark'a rosery. Yana rik'e da King James Bible.Da fara'arshi yake musu sannu da zuwa shi ma yazauna suka gaisa sannan ya nuna Kasham da kanta ke hayaki ta d'ora kafa d'aya akan d'aya"ke kina so ki bamu matsala me yahad'a ki da bahaushe ne?Tagalla mishi harara tana mishi wani kallan uku ahu "ah kaji k'arfin hali 6arawo da sallama,yanzu kurace za ta cema kare maye? Shi har yana da bakin da zai ma wani fad'a yaushe-yaushe aka gama rigima d'an shi na cikinshi yama wata yarinya yar Kurmin-Bi ciki,yanzu haka yarinyar tana cikin gidanshi sunyi auran leda (auren da ba Pastor ne ya d'aura shi a majami'a ba Church)wai sai ta haihu za a yi auran gaskiya dasa albarkan Iyaye.Yasake kallanta ba magana nake miki ba?To me ko zai had'ani dashi banda soyayyay.Ina son Julaibib zan kuma aureshi ko kamin addu'a bazai kama niba,ai wallahi gwamma ni ba ciki a kamin ba.Maman za ta mareta yahana kowa yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake yi, ki barni da ita kawai Dinatu. Pastor wannan abun yana cimin tuwo a k'warya,Ya'yanmu da zarar sun girma sun yi soyayyya da hausawa sai kaji suma suna san zama masu sallah, sai su gudu su aure su ko muna so ko bama so,to a kan me za su dinga yaudare mana Ya'ya suna mana d'auki dai-dai suna converting d'insu zuwa musulunci?Sannan su Ya'yan hausawa mata basa ta6a yadda suyi soyayya dana mu Ya'ya mazan,abun yana k'ok'rin shige makad'i da rawa fa,na rantse maka da girnan ALLAH Ya'yanmu mata da suke sallah a cikin gari sunyi yawan da ko mun fara k'irgasu lissafin zai k'wace mana,to gaskiyar magana sai kun k'arae zage dantse da k'wazo wajan preaching ta yadda za Ku dak'ile wannan al'amari suma suji suna k'yamar mazan hausawa kai ba su kad'ai ba da duk wani me sallah kawai(😊Up up up Diniyal-Islam👏). Yagyad'a kai"Ki kwantar da hankalin ki Dinatu wannan matsalar ita muke tattaunawa a taranmu na Christian Association Of Nigeria(CAN) har yanzu muna kan aikine,ai kowa yaci tuwo damu miya yasha, wannan makon ma a kawai babban taro a Jos har daga kasar waje za muyi bak'i.Wani murmushin mugunta ya su6uce mishi"wallahi za muma duk wasu masu sallah na Southern Kaduna(Kudancin Kaduna)wankin babban bargo a k'aramin k'oko'.Suka gyad'a kai cikin gamsuwa "yauwa Pastor ALLAH yataimake ku. Amin,amin. Pastor ya dad'e yana jero addu'o'in shi su kuma Iyayan sun durk'usa gwiwa bibbiyu sun rufe idanusu tare da had'e tafukan hannayansu idan yayi addui'ar sai yace In Jesus name we pray sukuma suna amsawa da Amen,amen,amen,ameeennn.... Ita dai kallansu kawai takeyi har zuciyarta ta lula tunanin Enigma man d'inta D'ansarai.Tayi murmushi "Julaibib idan ka aureni za kaji dad'in rayuwar ka,zan saka farin ciki na karanci"Catering & Hotels Management.Na san Food and Nutrition zan dinga shirya maka abinci me rai da motsi, ingantaccen abinci me gina jiki da k'ara kuzari,za kaci har sai ka ture..bata san Pastor ya gama 6aragadar shiba har sai da Babanta ya ta6ata"Kasham tashigo mu tafi gida an gama ganin idanunta a rufe sun zaci ko itama amsawa ta dingayi. "Gobe ma ku dawo". Tajuya tama Pastor d'in wani malalacin kallo sannan tajuya,wallahi ba inda zan dawo idan za a ma mutum addu'a lallai dole-dole sai yana wajan? ALLAN ai yana jin kome... Abinda yafi kome mahimmanci a rayuwar d'an Adam ya fi kome sauk'i,sai Ubangijinmu bai horema kowa mallakan shiba dan kar a k'unta ta ma bayinshi, sannan bai horeshi kaasatan (ake6e) ga bayinshi na gari ba, a ah yabarshi kowa yasamu,Ubangijinmu me rahama da tausayin bayine... Iskar da muke shaka ta ALLAH ce ba wani me iko da ita. Ruwa da kusan shine rayuwa duk rintsi duk wuya akwai shi. Rana kullum sai ta fito itama ta ALLAH ce babu wani me iko da ita.dasauransu... ALLAH mungode maka da kayi mu musulmai masu bin tafarkin Manzanka,ba dan mun fi wasu girma da daukaka ba a ah ganin da markace kawai. Ya Ubangijinmu!Kaine me jujjuya zukatan bayinka...ka tabbatar da zukatanmu a kan addinin da ko a wajanka ka kirashi da musulunci. 27 Rabi'a Thani 1441 24 December 2019 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na tara. A gida Nasir yasamu Julaibib yana fad'a mishi jiya da daddare su Aisha suka dawo.Yauwa Nasir nagode maka ba kad'an ba, yad'ibo dabino me yawa yabashi.Yasa hannu biyu yakar6a cikin murna.Nima nagode Kawu. Bayan sallar la'asar suna tsaye a k'ofar gidan tafito sanye da farin hijab tana murmushi.Tagaishe su a ladabce.Musaddiq yace to ya gajiyar hanya? Sai kawai kiyi tafiya ba sallama?Tad'anyi murmushi Yaya Musaddiq a min afuwa bazan sake ba.Yagyad'a kai to shikenan. Yayi gyaran murya karmu 6ata lokacin mu tunda lokaci jarin d'an Adam ne,Aisha magana ta gaskiya za muyi.Yad'an kalleta tana tsugune natsuwarta na ga sauraran abinda zai fad'a. Julaibib yana sanki, za ki iya auranshi? Shiru ya ratsa wajan, ta had'a kai da gwiwa dak'ik'u nata tafiya bata ce kome ba.Aisha yi magana mana. Yakalli Julaibib to wata kila ni take jin kunya barin ba ku waje"dama shirun budurwa yaddan ta... bawazara kuma sai ta tanka. Tad'ago da sauri kwallah sun cika idanunta"a ah ka tsaya kawai hawaye masu d'umi suka zubo mata sharrr...Lafiya kike kuka kuma? Tagirgiza kai inafa lafiya Yaya Musaddiq na shiga rud'ani,zuciya ta tana min zafi, tunani na yana shirin rikicewa.Saboda me? Musaddiq ya tambaya cikin mamakin kalaman ta.Saboda soyayyar mutane biyu"wa zan za6a?Takad'a kai cikin takaici"Kaiyah...Yaya Julaibib bakamin adalci ba,kaci amanar k'auna.Yakalli Julaibib sannan yakalleta"banga ne ba kamar yaya Aisha?Ta share hawayan da suke gudu a fuskar ta sannan tamik'e tsaye"Na so Julaibib amma dole tasa na hak'ura saboda banga fuska ba,kwatsam kuma sai ga ku da tayin soyayya a lokacin da yariga yak'ure. Musaddiq yad'an kalleta kin daina san na shine? Ko d'aya har yanzu ina san shi to amma ya zanyi?Akwai alk'awarin wani a kaina. Yaya julaibib ka ci amanar k'auna, kwarai na so ka,kai ka k'i bani goyon baya. Aisha ki taimake mu.Takalli Musaddiq da mammaki kamar yaya?Eh ni a ganina lokaci bai k'ureba tunda ba auran aka d'aura ba, gashi kin tabbatar da bakin ki kina san shi,amince mana kawai kome zaizo gidan sauk'i,su Baba zasu shiga cikin lamarin.Julaibib yana sanki,za kuyi zama cikin amana...ta tareshi da sauri"haba Yaya Musaddiq wannan san kai da yawa yake, me yasa kake aran bakinshi wajan cin albasa? Kai ni nama game ba wani so na da yake yi.A ah Aisha karki fad'i haka dan Julaibib ya zo wajanki ba sau d'aya ba ba sau biyu ba to a tunaninki zuwan me yake yi? Sada zumunci,ziyarace ta sada zumunci,kullum haka yake fad'a kuma haka na da'uki zuwan na shi.To Aisha.... Julaibib ya katse shi"kar muyaudari kanmu Musaddiq,neman aure akan neman aure haramun ne a musulunci,ni na yadda da hukuncin Ubangiji duk abinda ba ka samu ba to dama can rubutacce ne tun daga lauhul-mahfus ba na ka bane.Yad'an kalleta Aisha ina miki fatan alheri da dacewa a gidan aurenki.Yarik'o hannnun Musaddiq yamata sallama sukayi tafiyarsu.Tabisu da kallo har suka 6ace ma ganinta.wata sabuwar soyayyar shi ta dad'a mamayar zucyarta.Hashim ma yafad'o mata, shima tana kaunarshi da wata irin soyayya ta daban. Tagyad'a kai"lalalai wannan muk'addari ne"rabon kwad'o baya hawa sama... Tad'an cije le6enta na k'asa sannnan ta juya zuwa gida.. Da daddare bayan sun gama cin abincin dare ya fad'a ma Iyayanshi kome game da Aisha.Sukace ba kome sai a nemi wata.Ya amsa cikin ladabi Insha-ALLAH. Danbarwa me yawan gaske akayi tsakanin Kasham da Baranzan kafin ya yadda ya tattara kome na shi yabar gidansu tare da alk'awarin tunda tak'ishi saboda wani tsinanne to ko ba jima ko ba dad'e shine nan yanuna kanshi da yatsanshi shine zai zama ajalin Julaibib. Yanunata da yatsa"ni nake fad'a miki wannan maganar ki rubuta ki ajiye.Idan ka kashe shi ba tare da ya maka kome ba shari'a ai ba kyaleka za tayiba,kaima zakabi bayanshi ne. Tabi k'ofar da ake ta kwankwan sawa da wani malalacin tsaki tadad'a d'ora kanta ajikin matashin "Yes come in"suka shigo sama da k'asa take musu wani kallan uku ahu.Sisters ne su biyu "menene?Cikin d'oki me rik'e da madaidaicin kofin silver tabud'e murfin sannan ta mik'a mata"Shekaran jiya Reverend Father yadawo daga Jerussalam(Darussalam)to jiya Pastor yaje mishi ban gajiya shine yabashi Holy Water(Ruwan Zamzam)me yawa anba kowa ya sha,ke kuma bakije majami'a ba shine aka d'iban miki ta ajiye kofin a gaban ta.Tamik'e zaune da sauri daga kwanciyar da tayi,tasa k'afa ta ture kofin.Kafin suyi wani yunk'uri ruwan yabi carpert d'in d'akin.Suka bita da kallo cikin mad'aukakin mamaki"Kasham Holy Water ne fa?Tawatsa hannaye cikin halin-ko-in kula"dan Holy Water ne sai me?Suka 6ata fuska gaskiya baki kyauta ba.Tagyad'a kai "to sai a yanke min hukunci.Suka juya har sun kai k'ofa d'aya ta juyo"mun manta Pastor yace mu fad'a miki anjima ki shirya za ku tafi a miki baptismal. Taja dogon tsaki"Allah suturi bukwui inji kishirya k'onanniya" Ku fad'a mishi bana so dan haka ba inda zani wallahi.Takalleta na wasu dak'ik'u Kasham da kinyi hak'uri an miki kinga ran...Cikin hayagaga da tafasar zuciya tamik'e tsaye"na ce bana so,to a kyaleni ko ana dole a rayuwane? Daku dashi kuje kuyi baptismal d'in ko ba daku suke fornication d'in ba?"Get lost dan abu kazan ubanku,get the hell out of my room tanuna musu k'ofa yan iska kawai kuje kuji dana ku zunubin"dan nace ina san D'an Sarai shi kenan sai yazama zunubin da har sai anyi baptismal (wankan tsarki)?Ko wani abune yazama zunubi? Za su sake magana tayi wani ihu ta buga tebur d'in tsakar d'akin sai da littafin kai suka zubo k'asa"now get out dan abu kazan uban ko wace shegiya!.Suka fita ka me da ha6a🤔lallai Kasham ta ci kai(hauka)dole ko a mata wankan tsarki ko za ta samu lafiya. Tafad'o gado cikin takaici da damuwa da kuma matakin d'auka.Ba zato wani tunani yazo mata.Tamik'e da sauri har tana bugewa da katakon gefen gadan,tayi tsalle tana wani ihun jin dad'i"Halelujah...Diary d'inta ta d'auka tayi waje da gudu hurrayyy. Babanta tasamu yana zaune a inuwar barankaci yana sauraran rediyo a cikin shirin tambayoyin addinin kirista.Tazauna a gefen shi cikin walwala,yabita da kallo ba Pastor yana kiranki bane?Tayi yar dariya "Ba kirana yake yiba ya dai cene a fad'amin gobe da yamma inshirya za a min baptismal d'in.Yagyad'a kai Ohooo. Yacigaba da sauraran rediyonshi ita kuma tana bud'e diary d'inta tana karantawa.Wacewar wasu dak'ik'u tad'ago tana kallanshi"ni ko Baba in tambayeka mana. Uhun tambaye ni ina jinki.Tad'anyi rubutu a diary sannan ta kalleshi "wai brother d'inka daka ta6a bamu labarin shi har ka nuna mana hotonshi tun da dad'ewa yana nan kuwa?Yad'aure fuska"me yadameki da Shedrak? Ina ruwanki da jin labarinshi kuma?Yayi d'ad d'as d'as da yan yatsunshi ki karkad'e kunnuwanki ki jini da kyau "Shedrak is no more in our family,mun dad'e da yafeshi mun barma musulmai shi,kamar yadda shima yazabi zama musulmai da addininsu. Ta ta6e baki "Basakut Baba(Kayi hak'uri Baba) Dan na ga kamar ranka ya 6aci,ni abinda yasa na tambayeka a cikin wani littafi d'azu dana ke karantawa naci karo da sunanshi shine na tuno da wannan d'an uwan na ka,ai kaima ka san tunda muke dakai ban ta6a maka zancen shiba.Yakashe rediyon dan sun gama shirin.To woo na d'auka kina san jin labarin shine.Tad'an motsa kafad'a ko d'aya Baba dan labarinshi ba zai amfane ni da kome ba.Tamik'e Baba barinje unguwa amma ba dad'ewa zan yiba.Yad'aga mata hannnu yana mata adabo. "Sai aburak" ( Sai kin dawo). Sakamokon jarabawar su na fitowa Water Fall Hotel matsirg suka d'auke ta aiki amma k'ememe tace ba ta so duk da albashinta me tsokane.Mamanta takalleta cikin takaici to saboda me ba kya so?Saboda Baranzan yana da hannun jari a hotel d'in ni kuma na gama amfanuwa da duk wani abu indai a kwai Baranzan a ciki wallahi bazan yiba.Suka had'u suka dinga zagin ta amma tayi kunnan uwar shegu dasu ko a jikinta an yak'ushi bishiya. A sanda rana tatafi tana shirin fad'uwa Kasham tashigo gidan da kaya nik'i nik'i ta zauna tana hutawa.Rahab da Mamanta suka bita da kallo daga ina kike ne?Tabud'e manyan idanunta masu maik'o da suka d'an canja kala kamar me jin bacci"daga kasuwa nake tamik'a musu tsire da lemun kwali Don Simon tashige d'aki. Rahab tabiyota wai kashe-kashen kud'in nan da kikeyi ko dai kin yi sabon saurayine? Tamata wani malalacin kallo kamar za tayi magana sai kuma tayi shiru tad'auko diary d'inta tana rubutu.Tagama abinda takeyi takwanta da tunanin wanda zai zo yasiye aladunta gaba d'aya dan kud'i sosai take buk'ata,dama ita da Rahab kiwon aladu sukeyi da shi suke rufama kansu asiri shi yasama basa harkar tara samari barkatai,mazan ma ba sa, ba su na jaki kamar yadda suke ma yan matan bariki dan sun san ba da kud'insu suka dogara ba,a dating zata watse. Yauma aladu biyar takama tasiyar dan ba ta da kud'i. Dasafe tasamu Babanta a d'aki yana kallo tazauna tana tayashi suna hira. Baba ka san abinda yake bani mamaki?Yagirgiza kai"to wai shi Shedrak da aka yafeshi a cikin dangi yana jin dad'i?Yatsaida idanunshi a kanta tsawon lokaci, nazarin ta yake yi"Kin dameni da maganar Shedrak a yan kwanakin nan me ki ke so kiyi ne? Me ki ke shirya wane? Banza bata kai uwar akuya kasuwa,Meye a zuciyar kine Kasham?Cikin dariya tace kai Baba ALLAH ba abinda nake shiryawa,ni abinda yake bani mamaki ace mutum ba shi da yan uwa blood relatives saboda zai yi sallah kuma shi ya yadda da haka? Ni fa shi yasa nafara canja tunani a kan Julaibib saboda zo mu zauna zo mu sa6ane,to idan munyi fad'a wajan wa zani inji dad'i ku kun yafeni? Yagyad'a kai "Ehem yanzu kika zo inda muke so kizo, yanzu kin gane abinda muke k'ok'arin nuna miki kenan amma ki ka k'i sauraran mu gashi daga fara addu'a kin fara dawowa hayyacinki. Yayi yar dariya"God bless you my daughter. Wani murmushi ya su6uce mata amin Baba.Tagyara zama"gaskiya Baba ni yanzu na amince gobe muje a min baptismal.Yayi kyau Kasham,Yakad'a kai cikin damuwa "Hum Shedrak? Kar kiyi tunani irin na shi fa.Tagyad'a kai"haka fa.Ko yanzu yana ina ne oho mishi.Yace wa? Shedrak ai nasan inda yake da Dinatu ma tana zuwa gidanshi a shekarun baya...bai k'arasa ba tad'an ta6e baki tare da mik'ewa cikin halin-ko-in kula da maganar,Baba barinje inyi wanka dan yau zanje a min nail fixes.Tana shiga d'aki tayi tsalle tafad'o gado Hak'anta za ta tadda ruwa Halelujahhhhh... Ranar lahadi duk suna ta shirin tafiya majami'a(Church)ita kuma tana zaune tana shafama faratanta da taje aka sa mata na roba jan farce.Mamanta ta kalleta ke baza ki shirya ba sai kin makara? Ta yamutsa fuska"ni fa yau ba inda zani"baki da lafiya ne?Rahab data fito daga d'aki take tambayarta.Lafiya ta k'alau zuwan ne kawai bazan yiba.Shikenan sai ki mana abincin rana.Tagyad'a kai To Mama.Tad'aga hannu tana musu adabo sai kun dawo. Tamaida k'ofar gidan ta kulle sannan tashige d'akin Baban wajan daya ke ajiye muhimman takaddunshi tanufa,d'aya bayan d'aya take dubawa cikin tsanaki,wasu takardun ma tun na makarantar Primary suna nan saboda ya iya ajiya,anan taci karo da wani tsohon hoto Baban ne da Maman suna ganiyar k'uruciya, tamayar da hoton tana dariya,kakaf binciken ta bata ga abinda take nema ba.Rai a6ace taja dogon tsaki"Ohhh no damme,ta dunk'ule hannu ta naushi iska.Tayi jifa da wani tsohon wallet k'ananan katunan ciki suka tarwatse a tsakar d'akin.Tadafe kanta dake barazanar ciwo. Wucewar wasu dak'ik'u tana zaune cikin tafasar zuciya,ta tsuke bakinta kamar za ta rufeshi amma bata rufe ba tana zuk'ar iska, ta zuk'eshi da yawa sannan tafara fesar da iskar ta baki ta hanci ta sauke gwauran numfashi tamik'e ranta in yayi dubu ya baci ta tura hannunta acikin gashin kanta,tasake dunkule hannu ta naushi iska"Damme...a kasalance tamayar da takaddun, sannan ta tsuguna tana kwashe tarwatsastsun k'ananan katunan a cikin ma'ajiyarsu,idanunta suka kai wajan guda d'aya daya kusa shigewa k'ark'ashin kujera,tad'auko shi tana dubawa. Complementary card ne me d'auke da sunan Alhaji Hafiz Donatus,sunan unguwar da yakeyi,sai lambar waya na gida dana wajan aiki.Tayi tsalle cikin dariyar murna,ta k'ank'ame katin a kirji"Hallelujah...wallahi wani karfi da karsashi ne ya mamaye ilahirin gangar jiki da zuciyarta.Batayi niyyar yin abincin ba amma farin cikin data tsinci kanta a ciki yasa ta zauna ta shirya musu abinci da abun sha me rai da motsi(Yummy). A sanda hantsi ya dubi ludayi na safiyar talata tagama shirya kayanta a yar madaidaiciyar jaka trolley,tana zuge zip d'in Mamanta tashigo tana mata kallan nazari "Ani yake ?(Ina za ki) Kamar da gaske tajuyo cikin damuwa suna kallan juna,tad'an sosa kunnen ta na dama"Ramai zani wajan Tina tun jiya da rana nasamu labarin an mata Operation,tun ajiyan naso tafiya to bani da kud'ine.Wayyo! takad'a kai cikin damuwa ALLAH yabata lafiya, kigaishe ta,tasa hannu a mata sun gane(Lalita)taciro kud'i to kenan ko na mashin baki dashi? A ah ai na samu Mama ina da wanda zai kaini.To gashi kya kara wannan zai miki amfani, dan na san zaki tarar da ita da wata buk'atar,kin san majinyaci.Takar6a tana d'an murmushi "Nagode Mama. Maman tarakata har sai da ta hau mashin tana dad'a jadda dama me mashin d'in Ramai za ka kaita kayi tafiya da ita a hankali,dan jiya na hau mashin d'in wani wawan yaro saura kad'an yazubar damu.To Mama zan tafi a hankali kar in zubar miki da wannan kyakkyawar yarinyar ni da zaki bani ita wallahi ina so.Shi da Maman sukayi dariya ita kuma ta d'aure fuska"Kai malam ina da abinyi dallah ja mutafi. Mama sai na dawo.Yauwa Kasham ALLAH yakaiku lafiya. Suna zuwa kwanar da zata sadasu da cikin gari tace shiga nan yad'an juyo ya kalleta ba Ramai a kace zan kai kiba? Eh can ne amma na fasa mushiga cikin gari idan nagama abinda nake yi ka kaini tasha.Yaja mashin"to amma kin san kud'inki ya k'aru da yawa tunda har sai na jiraki kin gama abinda za kiyi a cikin garin ko? Tagyad'a kai "Indai kud'i ne to ka kwantar da hankalinka kamar ka mari uwar soja,wallahi abinda ka yanke da bakin ka shi zan ba ka.Yayi yar dariya "godiya nake yi me kyau, wallahi irinku nake so. Tanata mishi kwatance har suka zo gidansu Julaibib amma k'atan kwad'an da suka gani a k'ofar gidan yabata tabbacin mutan gidan ba sa nan tace su wuce shigon shi sai dai kash...nan d'in ma a kulle. Tasauko tana waige-waigenta ta hangota. "Hey Sudaida Ibrahim Me-Lambu... Sudaida tajuyo,idanusu yahad'u tak'araso wajan tana murmushi"Malama Kasham ke ce?Ina kwana. Takamo hannunta"Lafiya lau Sudaida,ya karatu? Alhamdulillah. Sukayi d'an shiru na wuce war wasu dak'ik'u.Kasham tasake kallanta"yanzu ajin ki nawa?Aji uku zamu shiga idan aka koma hutun nan.Tagyad'a kai"yayi kyau,kidage sosai kinji ko? Ina Ya'yanku na ga shagon a kulle? Sudaida tabi kofar shagon da kallo"Yaya D'ansarai ai baya gari,watanni biyar kenan har yanzu bai zo gida ba,Shida Yaya Musaddiq zuwan shi uku.Suna ina? Tad'an kalleta "Suna Zari'a k'aro karatu.Tad'anyi murmushi "Julaibib ya tafi Jami'a zai d'ora degree a Islamic Studies kenan,tun a Gidan-Waya taso canja course,da ace shima Special Education yake yi irin karatun Musaddiq wallahi da sai ta koma irin karatun,da yanzu itama ta nemi addmision ta bishi can. "Hummm my enigma man wish you all the best"... Takalli Sudaida to me zan bakine? Tazuge zip d'in jakarta taciro yar k'aramar "Damask rose-flower"ta rabo me kyan gaske tashak'i k'amshin sannan ta mik'a mata"gashi ba yawa.takar6a da godiya.Kasham ta sake ciro wani rufaffen envelop tamik'a mata"wannan ki ba Yayanki D'ansarai duk lokacin da ya dawo dan ALLAH ki adana shi dakyau,kar kuma kimanta, tahad'a tafukan hannayenta please... Sudaida tayi yar dariya ganin yadda tawani marairaice mata tagyad'a kai"Malama Kasham Insha-ALLAH I will do as you say"tadafa kafad'arta"Yauwa Sudaida thank you very much,I really appreciate sukayi dariya. Tabud'e wallet d'in hannunta kud'ine sababbi yan naira d'ari tad'ibo su dayawa bata tsaya k'irgawaba tamik'a mata, amma Sudaida bata kar6a ba. Tamata kallan nazari"Me yasa?Ba kome kawai ki barshi.Ba zato Sudaida taji ta rungumeta "Kar kimin haka Sudaida,ni kaina ban san dalilin da yasa nake k'aunar duk wanda yake da alak'a da Julaibib ba,ban san dalilin ba, hakanan nake jinku a jinina,tanannad'e kud'in tasa mata a tafin hannu, ai ni naba ki ba rok'ona kika yiba,sai ta sake ta a hankali. Kiyi karatu Sudaida,dan shine hasken rayuwa,shine abinda baya k'arewa kullum kina tare da abinki ba a fashin shi duk rintsi duk wuya yana cikin kwakwalwarki,Ina miki fatan alheri,ki gaishemin da D'an Sarai,Julaibib my enigma man dakyau da kyau.Me mashin d'in yatayar tahau,Sannan suka d'aga hannu suna ma juna adabo🙋Sudaida tad'an d'aga murya dan har sun kusa shan kwana"Malama Kasham kema ina miki fatan alheri nagode.Kasham tamata murmushi"Toh nagode suka sha kwana. Suka 6ace ma Sudaida. Cikin sa a suna zuwa tasha motar saura mutane biyu ta cika tabiya kud'in mutum biyun sannan ta sallami me mashin da kud'in da baiyi zatoba dan ta ninka mishi abinda yace tabayar,yatafi yana mata godiya.Tana shiga tazauna ta d'aura belt direba yaja motar sai... KADUNA garin gwamnahhh...cibiyar ilmi,wayewa da iya d'aukar wankan dake bin jiki.Oh yessss...mune the KD's mune nan,kowa kagani da wanka rainan mune,a wajan mu ya koya...😎 Me neman ruwa yatafi randa. Me neman jini yatafi kwata. Me neman labarin wuta ya tambayi tsire. Masu mura suke da majina. Masu ruwa suke da kifi. Masu abin fad'a ba sa fad'a. 3 Jumaada Awwal 1441 29 December 2019 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A. Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na goma. Motarsu na tsayawa a kawo tad'auki shatar taxi,dak'ik'u kad'an suka iso unguwar saboda ba cunkoson abubuwan hawa, tabi wajan da kallo bayan tasallami me taxi,tasake kallon wajan da tunanin ina za tabi dan hanyoyin sun karkasu. Yan makarantar Islamiyyar rana sun fara tafiya,wasu yara guda biyu maza za su wuce ta tsayar dasu "Sannunku yan makaranta. Suka amsa da yauwa sannu.Dan ALLAH tambaya nake yi gidan "Alhaji Hafiz Donatus" Tamik'ama babban katin hannunta, yad'an kalleta da mamaki bayan ya duba katin, sanin Alhaji Hafiz da yayi mutumin kirki me rik'o da addini,dan babban d'an Alhaji Hafiz abokin Kawun sune, to ita kuma wannnan me zak'o-zak'on faratan rumfar shaid'an fa?Kuma ko mayafi babu haka take tafiya kamar wata namiji,a gidan Alhaji Hafiz ma basa mu'amala da kome sai hijab,to kuma meye darin gamanka da ita? Tamabayarka tayi idan ka sani fad'a mata,idan baka sani ba fad'a mata.Zuciyarshi tafad'a mishi haka.sai yagyad'a kai. Yamik'a mata katin,gidan wanda nasani nake kuma kyautata zatan shine to kinga wancan titin yanuna mata titin da d'an yatsan shi tagyad'a kai tana kallan titin, to kimik'e shi,kwana tafarko zaki shiga,gida na hudu nan ne gidan ai zama kigani idan kika duba katin. Tahad'a tafukan hannayanta"nagode.A ah ba kome yarik'o hannun k'aninshi suka tafi. Tacigaba da tafiya har tazo gidan me k'atuwar k'ofa ruwan zinare,tayi tsai...na wucewar wasu dak'ik'u,ta kai hannu zata fara rank'washin k'ofar kenan sai gata a bud'e wata farar mota kirar marsandi tana fitowa, yabita da kallo ta cikin madubi,itama shi take kallo, yashiga tunanin a ina yasan wannnan fuskar ne? "Mahaifiyarshi"abinda yafad'omishi kenan daya ga manyan idanunta masu maik'o da yanayin k'irar jikinta,sai yayi ribas tabbas wannan yar'shice,yar d'an uwanshi Kantiok ga kamanni nan,yafito daga motar suna kallan juna,itama tagyad'a kai cikin gamsuwa tabbas wannan dan uwan Baban tane sai dai shi bak'i ne,Babanta kuma fari,yana sanye da dogayan fararan kaya,bak'ar hular dara akanshi da bak'in takalmi,yanata k'amshin turare me sanyin dad'i wajan shak'a. Tayi yar dariyar murna"Uncle.Yayi murmushi"na'am.Rahab ce ko Kasham ko Judith? Uncle Kasham ce.Masha-ALLAH sannu da zuwa, yakulle motar yazare makullin"to bismillah yanuna mata hanya mushiga ciki,yakar6i trolley d'in har suka shiga wani babban D'akin-shak'atawa me cike da ni'ima,wani sassanyar iska da k'amshin turaran d'aki ya mamaye ko'ina,kome agyara tsab a muhallinshi,tazauna a kujera tare da lumshe idanun ta tana zuk'e k'amshin tana zancen zuci "Lallai Uncle yana jin dad'in shi,tasauke numfashi sannan ta bud'e idanunta, suka kalli juna sai ta d'anji kunya ta kauda kanta gefe. Yayi murmushi kinsha hanya ai na san kin gaji,yad'auko abinci da ruwa da lemun kwali na biyar a raye (five alive) yamik'a mata kofi,tazuba ruwa tafara sha sannan taci abincin ya kuma mata dad'i taci to k'oshi dan bata wani tsaya bak'unta ba,kad'an tasha lemun ta godema Jesus Christ,Yesu almasihu me ce to. Saida da tagama suka fara hirar yaushe gamo?Shi dama bai san taba dan tun kafin a haife ta rabonshi da kauyansu Madauci.Ikon ALLAH banyi zaton wani a cikin ku zai zo inda nake ba,wai Kantiok ne da kanshi yafad'a miki inda nake?Tagirgiza kai"a ah ba shi bane,ni nayi ta bincike har naga complementary card d'inka, ni ba ma wanda yasan wajan ka na zo dan na fad'a ma Mama wajan k'awata Tina za ni. Yayi yar dariya"Dinatu kenan,wato me hali baya fasa halinshi,amma ba abinda yafaru ko?Eh Uncle ba abinda yafaru kowa lafiya.suka cigaba da hirar yan uwa ya tambayeta wannan,ya tambayeta wancan, wata amsar ta bashi dariya, wata kuma tabashi tausayi, wata tambayar kuma tace bata gane ko suwa yake nufi ba,dan tun kan a haife ta fa,har suka gangaro kan yan uwanta. Alhamdu Ya'yanshi nawa yanzu? Tad'an ta6e baki ita kanta tana dad'ewa bata ganshi ba"ai duk cikinsu Bitrus ne kawai yayi auran majami'a,amma Alhamdu ai gaba d'aya ya koma D one(D'orawa one)yana tsiran naman kare,baka ga yadda ya lalace ba saboda shaye-shayen miyagun k'wayoyi,amma watannin baya budurwar shi ta haihu ta kawo mana yarinyar data haifa mun gani.Yakad'a kai cikin damuwa,wannan irin rayuwa dame tayi kama? Yakalleta ke kuma na ki Y'ayan guda nawane?Bazaice kaso nawa bisa d'ari ba dan ba shi da k'ididdiga amma dai ya san samun cikakkun 'yan mata(Virgin)a cikinsu,ba masu yawa bane saboda wata irin rayuwar san zuciya,taci barkatai da suka za6a suke yinta cikin kwanciyar hankali.Tagirgiza kai"Uncle ban ta6a haihuwa ba,kuma duk abinda muka yi da Baranzan"I repent"Ya yadda da ita,yajijjiga kai"toh ya karatu kin gama secondary ko anan zaki k'arasa?Ta ajiye kofin lemun a saman tebur sannan ta bud'e jakar hannunta taciro wani babban envelop ruwan k'asa ta mik'a mishi. Yad'ago cikin mamaki da murmushin jin dad'in ganin sakamokon jarabawar ta na College of Education.Kinyi k'ok'ari kuma na yadda lallai baki tsaya shashanci ba"wai rok'o a gidan bebe"suka cigaba da tattauna al'amura mabambanta har Kasham tafad'a mishi gaba d'aya abinda yakawota. Yakalleta lallai kin yadda za ki musulunta Kasham?"Eh Uncle na yadda zan musulunta.Yagyad'a kai"To ki sani musulunci yana da sharud'd'a guda biyar duk wanda kika ganshi a cikin musulunci to tabbaci hak'ik'a sai da ya yadda da wad'annan sharud'd'an, Sharad'in farko kuma mafi girma a cikin su shine kalmar shahada. Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, bisa cancanta sai ALLAH,kuma Annabi Muhammad bawan shine kuma manzan shine. Ma'anar kalmar {لاإله} tana kore duk wani abin bauta ne koma bayan ALLAH{إلاالله}wannan kuma tana tabbatar da bauta ne ga ALLAH shi kad'ai ba tare da abokin tarayya ba. Sharud'd'an kalmar shahada kuma sune: 1.Ilimi wanda yake kawar da jahilci. 2.Yak'ini wanda yake kawar da kokwanto. 3.Ikhlasi wanda yake kawar da shirka. 4.Gaskiya wacce take kawar da k'arya. 5.Soyayya wacce take kawar da k'iyayya. 6.Janyuwa wajan yin aiki wacce ke kawar da k'in yin aiki. 7.Yadda wacce ke kawar da juyarwa. 8.Kafircewa da kin yadda da duk wani abin bauta koma bayan ALLAH. Tare da sanin cikakken bayani danga ne da"Shahdatu anna Muhammadan rasulullah. Ma'anar kuwa:Gasgata Manzon ALLAH a duk abinda yaba da labari,da yin biyayya ga abinda yayi umarni dashi,da nisantar abin da yaja kunne ko yayi hani dashi,da kuma bautawa ALLAH dai-dai da koyarwarshi. Bayan wannan sai sauran sharud'd'an musulunci sune Sallah,Azumin watan Ramadan, Zakka ga wanda yake da dukiyar data kai nisabin yin Zakkar,Aikin Hajji ga wanda yasamu iko. Kingane ko?Naga ne Uncle, kuma na yadda da duk abinda kafad'a to yanzun nan za ki kar6i musulunci. Ashhadu anla'ila ha'illallahu wahdahu laashari kalah...Wa ashhadu anna muhammadan abduhu wara suluhu.Yana fad'a tana fad'a har suka zo k'arshe. Yayi murmushi Alhamdulillahi yanzu kin zama musulma, ALLAH yamiki albarka. Acikin sunayan musulunci da kike ji wanne kike so a dinga kiranki dashi?Tad'anyi jimmm...na wucewar wasu dak'ik'u sannan tace"Uncle Sumayya nake so...Yayi murmushi ALLAHU-AKBAR kin za6i suna me daraja a tarihin addinin musulunci,Sumayya mace ta farko data kar6i addinin musulunci. Tunda kin zama musulma to akwai wankan shiga musulunci dan haka nake so ki natsu kiga yadda zan kwatanta miki.Yadinga mata bayani dalla-dalla sannan yace ta mishi bayanin yagani inda tayi kuskure ya gyara mata. "Dafarko tsarki zan fara sau uku,sai in wanke hannayena zuwa mad'aurin agogo sau uku,kurkure baki,shak'a ruwa a hanci da fyacewa sau uku,wanke fuska daga matsirar gashin kai zuwa k'arshen ha6a,daga gefen kunnan dama zuwa gefen kunnan hagu sau uku,wanke hannun dama zuwa gwiwar hannu sai uku,wanke hannun hagu zuwa gwiwar hannu sau uku,shafan kai daga matsirar gashin kai zuwa keya,a kuma dawo dashi da duka tafukan hannaye sau d'aya, sai shafan kunnuwa ciki da waje sau d'aya,wanke k'afar dama saman k'afa da tafin k'afar ko ina ya jike da ruwa zuwa k'wauri ko idan sawu sai an tabbatar ta wanku,ta hagu ma haka za a mata, wannan itace cikakkiyar alwala. Sannan sai in zuba ruwa a kaina da duka tafukan hannayena in cuccud'a in tabbatar gashin kaina ya jik'e da ruwa,zanyi hakan har sau uku,sai in wanke barin jikina na dama har zuwa tafin k'afar dama,sai in wanke 6arin hagu har zuwa tafin k'afa,sai ingame jikina da ruwan in tabbatar ko ina ya jik'e da ruwa,lungu da sak'on jikina. Idan kuma na so bayan nayi tsarki sai kawai ingame jikina tun daga kai har zuwa tafin k'afafuna da ruwa in cuccud'a ko ina nanma wanka yayi.Tad'an kalleshi amma Uncle wannan wanka zaifi dad'i a shower(shaya)ko?Yayi murmushi wannan sharhin kine amma ko ba shaya mutum idan yaso zaiyi abinshi.Kin burgeni yadda kika kowa kome dalla-dalla kamar yadda na fad'a miki,da alama zaki fahimci kome a d'an k'ank'anin lokaci. Wannan wankan shi za kiyi duk lokacin da jinin al'adarki tad'auke,shi za kiyi idan janaba tasa meki, shi za kiyi idan jinin biki yadauke,bambancin dake tsakaninsu kawai wajan niyya ne. Cikin d'an shakku takalleshi "to Uncle kana ganin Julaibib zai aure ni?Sumayya sanin gaibu sai ALLAH, tunda yafad'a miki ko zakiyi sallah shifa bazai iya auran kiba,amma babban abinda za ki fara yanzu shine addu'a"Allah ai maji rok'on bawane,ba kuma abinda ya gagara a wajan ubangiji". Yanzu kinga za kiyi wankan tsarki amma dole fa sai kin cire wannan faratan roban(nail fixes)dan a addinin musulunci sa shi haramun ne,tad'auki abin yanke farce tafara k'ok'arin ciresu,data gama yakaita wani d'aki, kishiga kiyi wanka,d'akin yar uwan kice,kome yana zaune a muhallinshi Dammm...Zuciyar ta tabuga saboda irin wannan k'amshin a d'akinsu Julaibib ta ta6a jinshi wallahi ranar data mamayeshi tashiga.Ta tsuke baki kamar zata rufeshi tana zuk'e sassanyar k'amshin tabaki ta hanci tare da lumshe idanunta,tana wata kissima a zuci,wani murmushi ya su6uce mata wucewar dak'ik'u masu yawa, tasauke gwauran numfashi sannan tarage kayan jikinta tashiga wanka. Yakoma D'akin-shakatawa yazauna, tunanin ya cika k'wak'walwarshi har baiji fitowar taba.Uncle na gama tafad'a lokacin da take k'ok'arin zama,ya kalli agogon dake d:aure a hannunshi lokacin sallar la'asar ya gabato.Yamik'e "zani masallaci,daga nan zan wuce in d'auko mutan gidan,ko kin jini shiru karki damu dan wata kila zamu had'u da cunkuson abubuwan hawa.Ta amsa da"to Uncle a dawo lafiya.Tad'auki wani littafi data gani a saman kujera"Islamic Perspectives On Reproduction, Health ChildBirth Spacing In Nigeria.Tafara karantawa. Miqdad ne yafara dawowa a sanda rana ta tafi za ta fad'i magriba na shirin kunno kai,ya san ba kowa a gidan shi yasama yatafi da mukulli amma yana ta6a kofar yajita a bud'e,yasa kai cikin murmushi tare da sallama bak'uwar fuskar yagani a kwance tana karanta littafin da ya ajiye a saman kujera jiya da daddare, tamik'e zaune daga kwanciyar da tayi,tajuya inda taji sallamar Dammmm...Zuciyarshi ta buga da suka had'a idanu,Hafsa yake gani a fuskar ta,hatta manyan idanunta masu maik'o irin na Hafsa ne. Tad'anyi murmushi"Sannu da zuwa. Yagyad'a kai"yauwa.Tanuna mishi kujera"kazauna mana, mutan gidan ba sa nann ne Uncle ya tafi d'auko su.Yasake kallanta jin tace Uncle wannan yar uwarsu ce ta Zonkwa yayi yar dariya sannnan ya zauna"kema sannunki da zuwa,daga Madauci ko?Tagyad'a kai. Fara kiraye-kirayen sallar magriba daga mabambantan masallatai na nesa dana kusa yasa shi mik'ewa barinje masallaci? Bai jira amsar taba yajuya yafita. Bayan sallar Isha'i suka shigo gaba d'ayansu dama Alhaji Hafiz ya fad'a musu kome tun a hanya.Hafsa ta rungumeta tana dariya "Yaya Sumayya ina tayaki murna da shiga addinin gaskiya.itama tasa hannayenta ta rungumeta tana murmushin jin dad'i suka saki juna suna kallan kallo. Alhaji Hafiz ya kalleta"Sumayya wad'annan sune iyalina.Yanuna ta wannan Maman Hasan kenan kasancewar haihuwarta uku duk yan biyu take haifa kuma maza amma ba sa dad'ewa suke komawa ga Ubangijinmu,akan wannan yanuna Miqdad haihuwar tafara tsayawa daga shi sai Hafsa, Zuhair da Khadija.Takalli Miqdad"Ashe babban Bros d'inmu ne shine baka fad'a min ba? Tamatsa wajan Maman Hasan tana gaishe ta"gaskiya Mama nima ina san yan biyu,kimin addu'a ALLAH yaba ni.Sukayi dariya dan bata wani nuna bak'unta ba kamar ta ta6a zama dasu.Maman Hasan ta jijjaga kai "ALLAH buwayi gagara koyo,duk wanda yakalli Sumayya ya kalli Hafsa yasan Yaya da kanwa ne,lallai jini abune me k'arfin gaske ko Khadija batayi kama da Hafsa ba kamar yadda Hafsa tayi kama da Sumayya. Hafsa ta d'auko abinci amma ba wanda yaci dan a k'oshe suke sai Miqdad kawai yaci,yana gama ci Maman Hasan takalleshi d'auki abincin nan ka kaima almajirai tun kafin ya lalace.Yad'an 6ata fuska dan baiso fitaba"Maman Hasan yanzu a ina za a ga almijiri?Dare fa yayi.Tad'an harareshi"kai malami ba kasan gidan almajiran kasan layin nan bane? Yad'an shafa kai"na sani. To can za ka kai musu suma suci da d'uminshi. Zuhair ya mik'e"Yaya Miqdad barin d'auka muje in rakaka.Yauwa Zuhair nagode.Suka fita Zuhair yana bashi labarin abinda yafaru d'azu a gidan Malam Muhammad Aminu (Kakansu). Sunyi hira sosai suna dad'a wayar mata da kai,ita kuma duk abinda bata gane ba kai tsaye zata tambaya karfe goma Alhaji Hafiz yakallesu to ya kamata kowa yaje yakwanta haka, Sumayya sai ALLAH ya kaimu gobe zamu fara karatu.Hafsa tamik'e"Baba Insha-ALLAH yanzu kafin muyi bacci zamu fara.Yagyad'a kai cikin gamsuwa"yauwa Hafsa ALLAH yamiki albarka.Su kayima juna saida safe. Hafsa matashiyar budurwa me ji da ilimin addini dana zamani,ajinta biyar Secondary a fanni kimiyya (Science)Suka shige d'akin baccinsu suna jin k'aunar junansu a zuciya.Taje tayi alwala tafito sannan takalleta "Yaya Sumayya kema kije kiyi alwala ganin tana shirin kwanciya.Alwala kuma Hafsa?Ba d'azu nayi alwala nayi sallar...tayi shiru sallar me ma?Ta tambayi Hafsa.Sallar Isha'i.Hafsa tabata amsa tana murmushi.Tagyad'a kai Yauwa shi.Hafsa ta zauna a gefen gadon "wannan alwalar idan za a kwanta bacci a keyin ta dan ita kariyace daga shaid'anu,shifa zama da alwala yana ba mutum kariya sosai a rayuwa amma ba kowa yake iya jure yiba,shi yasa Baba da Yaya Miqdad suke burgeni saboda sun rike wannan,wallahi basa zama ba alwala,nima dai wasu lukutan nakan kwatanta. Mako d'aya,biyu,uku shiru makatau balaguro a lahira,ba Kasham ba labarinta.Rahab taja dogon tsaki saboda gajiya dajin mitan da Maman take yi a kan rashin dawowar Kasham. Tadago takalleta"To wai menene abin damuwa dan har yanzu bata dawo ba? Kasham fa ba k'aramar yarinya bace.Yakike irin wannan maganar Rahab?Kasham ba 'ya ta bace, ya bazan damu ba.Yar kice amma kin san lafiya ita kesa aji mutum shiru, tad'anyi murmushi amma Mama kema sometimes bakya ganewa...ta tari numfashin ta kamar ya bana ganewa? Rahab tamik'e zaune daga kwanciyar da tayi ta d'an ta6e baki"ni wallahi na san ba yadda za ayi Kasham tayi wad'annan makonnin a Ramai,ni nafi kyautata zatan tana cikin gari wajan saurayin nan data nace tana so.Tadaki kirjinta da karfi"Jesus christ...ta jijjaga kai lallai biri yayi kama da mutum ni banyi wannan tunanin ba,yanzu barin shirya intafi Ramai d'in ga kai ga k'afa ai ba tambayar me aka yanka. Matina tana zaune a shagon kitson attachment d'inta ta hagonta Tamik'e dasauri ta tarota "oyoyo Mama sannu da zuwa"tabata wajen zama sannan ta kar6o mata ruwa da lemon mirinda da manyan cincin guda biyar a faranti. Tazauna suka gaisa.Mama kwana biyu ni da Kasham ba wanda yakawo ma wani ziyara,ni dama wannan Sunday d'in zanzo. Tafara girgiza kai tana tafa hannaye"Jesus Christ"Kina nufin Kasham bata wajanki makonni uku da suka wuce?Tace an miki Operation za tazo gaisheki? Matina ta kama ha6a"kaji muguwa zata jazamin masifa to ni Mama lafiya ta kalau ba abinda akamin.Takad'a kai"wato gaskiya ne abinda Rahab tafad'a Kasham tana cikin gari wajan wannan tsinannan bahaushen?Anya Mama Kasham tana wajan Julabib?Kin san yace bazai aureta ba...Ke tafi can idan takai mishi kanta yana ganin ta fad'i gasassa zai yi wani yunk'urin korarta ne?Matina tagirgiza kai"Kin san ALLAH Kasham bata wajan D'an Sarai dan bata ta6a 6oye min kome game dashi ba, kinga ko a makaranta bai tsaya kulata ba dan bata gabanshi,lokacin nema yake zaune zaman yanci da aikata abinda yake so dan ba idanun wani babba na shi,bare kuma yanzu dayake cikin iyaye da yan uwa? Tina nifa ban yadda ba idan kin san gidansu kawai ta shi mutafi ki rakani,tasan gidan har shagonshi sun ta6a zuwa da Kasham, to amma ta san halin Mama bata da kirki,yanzu zataje ta tada hayaniya bayan ta san wallahi Kasham bata wajanshi,to sai dai itama ta fara tunani ina Kasham za ta tafi tayi wannan dad'ewar?Bata saba haka ba dole kuwa Mama ta damu, amma dayake Judith da halin tane haka ai bata ma maganar ta sai ranar da aka ganta kawai. Shiru na nucewar wasu dak'ik'u zuwa can Tina ta numfasa"Mama na fi tunanin Kasham tana Kaduna?Cikin rashin fahimta tace Kaduna kuma?To wajan wa?Ko tayi sabon saurayine a can?Kasham bata da wani saurayi acan,sai dai kwanaki tafad'a min matuk'ar za ku takura mata,ku hanata auran Julaibub to lallai zata koma wajan Uncle d'inta dayake sallah.Tadafe kirjinta dan taji kamar ruguzowar wani abu a zuciyarta,ranta in yayi dubu ya 6aci.Takalli Tina "nagode,gobe dole zan tafi Kaduna na rantse da ALLAH ban haifi yarinyar da zatayi sallah ina numfashi a doron k'asa da raina da lafiya ta ba, Kasham taci k'arya ta kwana da yunwa ta tashi a rame.To maji magani an binne tsohuwa da rai. Cikin rashin sa a ta isa Kaduna,sai dai almajirai ta tarar agidan bayan sun gaisa da malamin take tambayarshi Alhaji Hafiz yad'an kama baki "Wai wai wai ai Alhaji Hafiz yafi shekara goma sha biyar da barin gidan nan,danshi yabani yace halak malak acigaba da koyarwa, kuma yanzu hakama basa k'asarnan shida Iyalinshi sun tafi aikin hajji.To ko kasan unguwar daya koma? Ban rik'e sunan ba,saboda shi lokaci zuwa lokaci yana zuwa mu gaisa,amma Lado ya sani. Kai Lado...Lado dayake biyama wasu almajirai karatu yad'ago yakalli Malam,Malam ya yafito shi da hannu zo mana.Yak'araso cikin ladabi.Ya sunan unguwar da Alhaji Hafiz yakoma? Ya amsa da ladabi unguwan Kanawa,amma Malam kafin tafiyarsu aikin hajjinnan mun had'u da Miqdad yace sun tashi sun koma Unguwan Rimi G.R.A inzo muje inga gidan,ni kuma ranar baka nan ni zanma yara darasu shi yasa ban bishi ba, amma na san idan sun dawo zaizo har nan ya daukeni muje.Malam yace"to kinji ko?Tayad'a kai tamusu godiya. Tadawo gida agajiye lik'is ga mugun 6acin rai,tadinga zagin Shedrak zagin tsamen nama tun mijinta yana tayata har abin ya isheshi yayi shiru dan abun na ta ya wuce makad'i da rawa,zagin shi takeyi kamar cin kwan makauniya, yadda take mishi tofin alatsine sai yaji ba dad'i "Lallai na ka na kane ko ya cinyeka bazai tauna k'ashin ba"ai koda suka yafeshi suka barma musulmai shi amma dai ai still blood brother d'in shine. Dakarfi yabuga sandar hannunshi a k'asa"Wannan zagin da kike ma Shedrak ya isa haka for what?Tanunashi da yatsa Shedrak d'inne baka so a zaga?To an zageshi matsiyaci kawai,ai dama yadad'e yana mana wannan mugun baki "Dinatu ya ishe kifa" yafad'a a tsawace dan banga abinda yamiki ba,shine yazo yatasa k'eyar Kasham sai sun tafi koko itace ta saci jiki tafi har inda yake? Ta tafa hannaye cikin bala'i"Holy Mary mother of christ yanzu saboda Shedrak kake min wannan hayagagar...Ashe kai munafiki ne, tunda har kake fad'a dani akan masu sallah?To kasani tayi d'as d'as d'as dayan yatsunta"as from today an daina dafa abinci a gidan nan kowa yazage yanemi kud'i yaciyar da kanshi,idan Kasham tadawo shikenan everything will be normal. Jikinshi yayi sanyi,fushin daya taso dashi yane mishi yarasa,sai yakoma rarrashi madadin shi da za a rarrasa"hun kud'i k'are magana.Yaro da kud'i abokin tafiyar manya.Hajiya naira Zainabu-Abu me maganin surukan zamani... Inji Sadi Sidi Sharifai.ALLAH ka azurtamu da arzik'i na halali.ALLAH muna niman tsarinka daga masifar talauci👏.Idan tahana shi abinci ai ya kad'e har ganyanshi, baya aikin kome,tunda aka sallameshi daga leburancin daya keyi na titin jirgin k'asa,to dama aikin ba wani na azo a gani bane,sai dai motsi yafi la6ewa indai ba niman ka a keyi ba... Dabara ba ta d'aure kaya dole sai da igiya. 6 Jumaada Awwal 1441 1 January 2020 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na goma sha d'aya. Hajiya Sumayya Kantiok Donatus... Ta canja tayi kyau na ban mamaki, kome na musulunci ya fara ratsa ta,sai dai ko a d'awafi baiwar ALLAN nan bata manta da Julaibib ba.Kullum addu'arta ALLAH yamallaka mata shi yazama mijinta,dan ita har kwanan gobe bata ga wani namiji kamar Julaibib ba. Makonsu biyu da dawowa tafara zuwa makaranta Sanawiyya kansancewar ta me k'wak'wa da san karatun kullum iliminta k'aruwa yake yi,dan addu'o'in cikin Hisnul-Muslim wallahi kad'an ne bata haddace ba,a kwaita da tambaya sai kuma akayi sa a mutan gidan suna da ilimi dai-dai gwargwado suna mata bayanin kome dalla-dalla ba jibge. Maman Hasan tabita da kallan tausayi"Iska na wahalar da me kayan kara"ta tsuniyar gizo ba ta wuce k'ok'i"Julaibib,D'an Sarai ko Enigma Man,wad'annan sunayan dai duk wayewar garin ALLAH sai ta kira d'aya daga cikin su,sun san labarin Julaibib a baki duk da basu ta6a ganin shiba. Rannan dai Miqdad ya galla mata harara"Ke malama kar ki damume da maganar wani D'ansarai mutumin da ko hoton shi baki dashi.Wani lallausan murmushi yasu6uce mata"na rantse maka da ALLAH inada hotunanshi,ni ban san yadda akayi da nazo nan ban gansuba ina tunanin Lidiya ce ta bincike min jaka ta kwashe su amma da hannuna na sakasu.Bros karka damu duk ranar danaje Zonkwa bazan dawoba sai da hotunan shi"za kaga kyakkyawan bak'in mutumi na,me tsabta,ma'abocin sa fararan kaya. Sumayya...a d'an firgice tad'ago sannan ta amsa"Na'am.Lafiya kika zabga wannan tagumin?Takad'a kai kwallah sun cika idanunta tamaida kanta jikin kujeran dan ba ta so su zubo "Maman Hasan Julaibib ne na kasa yin yak'i da zuciyata wajan cireshi a cikinta, kullum sai na yi mafarkin shi sai dai ban kwanta bacci ba me yasa?Saboda abinda kika sa a zuciyarki kenan tunanin shi,duk abinda ka kwallafa rai da shi to a mafi yawan lokaci sai kayi mafarkin shi"sa rai a ci shi ke kawo jin yunwa" Takamo hannayenta,Sumayya ki fahimci wani abu"D'an Adam da kike ganinshi to shi yake saima kanshi mutunci da daraja,shi zai kame kanshi sannan mutane su d'aukeshi da mutunci su girmama shi"Haja ita takema kanta kud'i.kin damu dashi da yawa,sannan abin takaicin bai san kina yi ba harara a duhu..kilama ya manta ya ta6a ganinki,shi yana can hankalin shi a kwance yana gudanar da al'amuran rayuwar shi,ke kina nan kin takure kanki cikin tunanin shi"wannan fa kamar aikin banza ne sammakon gaida mak'iyi. ...Julaibib yana da matar aure makaranta ake jira tagama musha biki,kuma k'anwata ce...kalaman matar Musaddiq kenan ranar dataje musu murnar aure... Tasauke numfashi"to amma ai banyi laifi ba ko a addinance.Maman Hasan tajijjiga kai"kwarai kuwa bakiyi laifi ba,hakan ya halatta sai dai a yadda muka saba a al'adance namijine yake furta hakan ga 'ya mace,saboda kawaici irin na Hausa-Fulani,sai dai ban san sauran al'ummatai ba,ba kasafai matan suke yin haka ba.Kiyita addu'a ALLAH alhakimune ba yadda ba ya shirya al'amura. Jikinta yayi sanyi ba wata gaskiya bayan wannan"a hankali tayi furucin nagode Maman Hasan da wannan tunatarwa. Miqdad yafito daga d'akinshi yana karya hula.Sumayya tabishi da kallo yanayi da d'abi'unshi suna mata shige dana D'ansarai shima ma'abocin sa fararan kayane.Yayi murmushi ganin kallan da take mishi"Sumayya ya akayi ne? Tayi yar dariya"wallahi Bros kayi kyau ba k'arya wannan shigar sunnan ta k'ayar dani fa. To nagode,yau ba Islamiyya ne?Akwai sai zuwa anjima. Hafsa tafito daga D'akin-girki tana kallanshi "Yaya Miqdad baza ka tsaya kaci abincin bane?Yad'an sosa kunne"fita zanyi.Tad'an marairaice"ALLAH sarki Yaya Miqdad inata sauri ne fa,wallahi na kusa gamawa. Yakalli agogon dake d'aure a hannun shi na dama"Ina bazan tsaya ci ba gaskiya.Ta turo baki gaba gaskiya ni dai banji dad'iba.Sai kawai tajuya tana k'unk'uni. Yarik'o hannunta"baba tawaje nah,kiyi hak'uri kiran gaggawa aka min a wajan aiki,yadafa kafad'arta yad'an d'age gira cikin murmushi"Yaya Miqdad ne fa?Tad'an harareshi tana dad'a turo baki ni dai...yatari numfashin ta"kinga kwantar da hankalin ki"bayan sallar azahar zan aiko a kar6a sai inci acan shikenan ko?Tad'anyi tsallan murna"yauwa Yayanmu to adawo lafiya"tabashi hannu sukayi musafaha suna dariya.ALLAH yasa tawaje nah...suka d'aga hannu suna ma juna adabo. Julaibib tunda yatafi sau d'aya yazo sai yanzu da suka samu hutun Semester, haka yadinga zaga gidajan yan'uwa yana gaishesu.Suna zaune shi da Musaddiq suna tattauna al'amuran daya shafesu Safiyya tayi sallama tashigo D'akin-shak'atawar sanye da dogon hijab suka gaisa cikin mutunta juna ta tashi tafita,bata sake shigowaba sai da tagama abincin rana tahad'a duk ahinda za su buk'ata a babban tire takai musu.Musaddiq yakar6eta da saurin shi"yauwa Safiyya,ALLAH dai yak'ara miki albarka da lafiya.Shida ita suka kalli juna suna murmushi,ta tsuguna da niyyar zuba musu yace"a ah wallahi amaryata ai kinyi me wuyar jeki kawai tuzuru zaiyi kome. Julaibib yayi kamar bai gane shagu6en ba,yad'auki kofi yazuba lemun kashu da abarba,yayi hismillah yafara kur6a.Musaddiq yace kai ni bangane bane anyi yamma da kare ni baza ka zuba min bane?Ya ajiye kofin yana nuna kanshi da yatsa"ni kace zanyi kome ko tuzuru? Ni sunana Julaibib ban san wani tuzuru kake nufi ba, ka san dama ni ban saba da sai anyi service d'ina ba, yazuba abincin a faranti yafara ci.Musaddiq yagalla mishi harara"wa za ka raina ma hankali? malam kayi aure kaji dad'in rayuwar ka,dawani tuzuru ne bayan kai?Yayi kamar ba dashi yake magana ba.Musaddiq yad'auki cokali to ajiye abincin muci mana. Yajanye farantin da sauri"a ah yau bazan ci abinci dakai ba,tashi katafi wajan matarka taba ka abincin abaki ma wannan ba damuwata bace.Au haka za kace?Yad'an d'age gira yana mishi wannan rikitaccen kallan nashi"Eh haka nace da magana ne?A ah ba ni da tacewa...wai ankama 6arawo da kayan sa ta. A sanda hantsi ya dubi ludayi na safiyar alhamis Sudaida da d'an d'okinta na san ganinshi ta tafi gidan Inna,amma irin amsa gaisuwar daya mata yasa jikinta yayi sanyi"wai an jefi kaza da gishiri,baiko d'ago kai ya kalleta daga tarin littafan daya barbaza a saman tebur ba,a dak'ile yake amsa gaisuwar da take mishi da lafiya...Tazuba mishi idanu na wucewar wasu dak'ik'u sannan ta d'ora envelop d'in hannunta a saman tebur d'in gabanshi.Yakalli envelop d'in a gajarce yacigaba da rubutun shi ba tare kuma daya d'ago kanshi ba yake tambayar ta"na meye? Haushinshi yakamata,ta galla mishi harara tajuya"nima ban sani ba.garammm tabugo k'ofar da k'arfi.Sai lokacin yad'ago yakalli k'ofar,yad'an motsa kafad'a yacigaba da abinda yakeyi har aka fara kiraye-kirayen sallar azahar bai gama ba, turesu kawai yayi gefe yayi alwala yatafi masallaci. Bai samu damar bud'e envelop d'in ba sai daya zo kwanciyar bacci"D'an k'aramin frame ne me hoton ayatul Qursiyu,a kasanshi wani tsibiri ne me ban sha'awa ruwa yana gudu...sai d'an takadda anyi rubutu sad'ara hud'u. ...Julaibib...na san kome zan ba ka a banza zaga ganshi,amma wannan na tabbatar ma kaina koda ba ka so na,na san za ka alkinta shi ko??? I dore you my Enigma... Kasham Kantiok Donatus. Yakaranta yasake karantawa,yakai hancinshi yana shinshina frame d'in daya ke k'amshin irin turaran ta.Yayi lallausan murmushi dan yaji dad'i har ranshi yajijjiga kai"Tabbas kin bani abinda zan alkin ta Kasham...na kuma gode. Sai ya d'orashi agefen gado yakwanta yana azkar d'in bacci, yanata kallan frame d'in yana tuna had'uwarsu da Kasham tun ranar farko da kallan farko da sukama juna a haka har bacci yayi awan gaba dashi. Azaure sukayi kaci6is taja baya da sauri jakar hannunta ta su6uce zata fad'i a k'asa,cikin zafi nama yacafe,yamik'a mata, takar6a tana gaishe shi. Idanunshi akanta"wa yabaki envelop d'in nan?Tamishi wani irin kallo fuska a d'an yamutse"Malama Kasham.Tun yaushe?Baku dad'e da tafiya Zaria ba.Yad'anyi murmushi cikin gyad'a kai"To nagode,Kawu yana ciki?Eh yana ciki.Yajuya zuwa cikin gidan tabishi da kallan mamaki D'ansarai kamar kuli-kuli yake da ba a gane gabanshi wallahi,Jiya fa shine yamata halin-ko-inkula amma yanzu har da wani murmushi taja dogon tsaki "Kai ALLAH yasauwake maka. Sumayya ta zage dantse tana kwankwad'ar madarar ilimi,gaba d'aya ta canja ta zama wata ta musamman"Unique charisma"fatar jikinta ma ta canja saboda canjin cima,a gidan Alhaji Hafiz za a ci abincin safe me kyau me gina jiki,da ranama haka a mafi yawan lokuta ba sa kasafai suke yin girki da daddare ba,sai dai asha su gwanda,Inibi,tuffa,dabino a kora da madara idan kuma abincin za ayi to mara nauyi za a dafa. Tana zaune a D'akin-shakatawa sanye cikin bak'ar doguwar riga kirar Saudiya,tayi rolling da mayafin tana nazarin"Dealing with Depression Islamically na Dr.Bilal Philips.Ta gaji lik'is a gangar jiki,amma zuciyar ta, tana k'ara k'arfafarta tad'aure ta k'arasa.Karo na uku kenan tana kallan d'an siririn bak'in agogon dake d'aure a hannunta ta k'osalokacin dawowar Hafsa yayi daga makaranta ta tambayeta wani abu.Tatsiyaya ruwa a k'aramin kofi daga babban tambulan takai bakinta da bismillah kad'an kad'an take kur6a tana jujjuya kofin kamar tana nazarin ruwan har ta shanye,ta ajiye kofin tana fad'in Alhamdulillah... Ahankali ta d'ora kanta ajikin kujerar tare da lumshe idanunta tana addu'a "Yahaiyu Yaqaiyumu birahmatika astagis,aslihli fi sha'ani kulluh,wala takilni ila nafsika d'arfata ainin" wato "Ya Rayayye dauwamamme,da rahamarka nake niman taimako ka gyara min al'amurana gaba d'aya,ALLAH karka barni da kaina koda da k'iftawar idanu ne". Miqdad daya shigo yatarar tana wannan addu'ar ya amsa da amin Sumayya. Tabud'e manyan idanunta masu maik'o da suka d'an canja kala saboda baccin da yake shirin kamasu. Abrugo? (Ka dawo) Yagyad'a kai dan shima yanajin yaran,Alhaji Hafiz ya koya musu kuma duk sun iya ko Maman Hasan tanaji. Umburak (Na dawo) Wannan addu'ar muhimmiyace daya kamata ace kowani musulmi yana yinta kullum ta ALLAH.Yad'auki littafi d'aya daga cikin tarin littafan data barbaza a saman tebur yana dubawa, yaciro biron daya soke a aljihun gaban rigarshi yana gyara mata wata kalma data rubuta ba dai-dai ba,yanuna mata kinga yadda ake rubutata, wancan wata ma'ana ta daban tabayar ba wacce aka tambaya ba.Tagyad'a kai "na gane,nagode Babban Yaya. Yamik'e zai shige d'akinshi, danshi ba ma'abocin zaman D'akin-shak'atawar bane. Tad'an kalleshi"afwan Yaya Miqdad ga wata tambaya,yakoma yazauna"Uhun ina jinki"Tace yau Malam nasiha yamana da muke rik'e sunanil rawatib kar muyi sakaci dasu,to ni kuma gaskiya ban san meye su d'in ba,to kuma dana tambaye shi shima bai fad'a min wai ya bani jinga (Assignment)in tambayo gobe yana jiran amsa. Yayi murmushi gaskiya Sumayya kina burgeni nan gaba da alama babbar malama za ki zama. Tajijjiga kai"Insha-ALLAH nima sai na ba al'umar manzon ALLAH gudummawa daga d'an abinda Ubangijinmu yanufeni da sani na ilimi,ka san fatana Yaya Miqdad?Yagirgiza kai.Fatana ALLAH yabani miji me ilimi wanda zai dad'a d'orani akan tafarkin dai-dai, wanda zai sa in zama productive akaran kaina,how I wish Julaibib ya aure ni... Yanunata da yatsa"ke dai da Julaibib d'in nan?Enigma man ko?Tayi yar dariya ai kuwa, yana da wuyar fahimta sai dai ni na fahimce shi, baya so adame shi,baya san hayaniya,baya shiga abinda ba da shi akeyi ba,amma ni har yanzu ina san shi"so gamon jini"yakad'a kai"ga shi kuma so ba samu ba,sai dai fatanmu har kullum ALLAH yaji6anci al'amuran mu.Amin big Bros.Sukayi murmushi. Mukoma kan tambayarki abinda ake nufi da sunanil rawatib sune sallolin da akeyi na nafila kafin sallar farilla ko bayan sallar farilla kamar :- Sallah raka'a hudu kafin sallar azahar da kuma rak'a biyu bayanta. Sallah raka'a biyu bayan la'asar. Sallah raka'a biyu bayan magriba. Sallah raka'a biyu kafin sallar asubahi. Babu wani musulmi dazaiyi wad'annan sallolin (Nafila) raka'a goma sha biyu(12) a kowace rana yana me d'a a da ganin girman ALLAH da k'ank'antar da kai a gareshi ba tare da ALLAH ya gina mishi gida a Darul-karamah (Aljannah) ba. Sumayya ba ki da burin samun gida a aljannah?Tayi dariya so kai.Yagyad'a kai "To ki d'auki sahawarar da annabin mu,annabin rahama daya bamu, kidinga yin wad'annan sallolin.Tad'an kalleshi"Bros bayan sallolin farilla dasu shafa'i da wutri,raka'atal fajri da sallar walha ne zan dinga yin wad'annan sunanil rawatib d'in.Eh Sumayya. Tagyad'a kai"na gane Bros I'm very glad, Godwilling daga yau zan fara ina kuma neman taimakon ALLAH da d'orewar shi har k'arshen numfashi na kataya ni addu'a. Ya amsa da To Sumayya Ubangiji yayi jagora. Suna kwance da Khadija tana duba Hadisin Annawawis Collection a cikin littafin Islamic Studies na B.A'isha Lemu(ALLAH Yajik'an ta.ALLAH yakyautata makwanci👏)baturiyar Ingila (England) data musulunta ta auri babban alkali d'an jahar Niger (Minna) Sheikh Ahmad Lemu tayi karatun addini me yasa take bada gudummawa da tarin iliminta ga al'umar manzan ALLAH shekaru masu yawa. Dawowar Alhaji Hafiz daga masallaci sallar la'asar yasa takalli Khadija data ke kwance a gefenta,ta gaji da wasanta tayi bacci,sai ta gyara mata kwanciya sannan ta tafi D'akin shak'atawa. "Yauwa Sumayya.ya amsa barka da dawowan data mishi.Takalleshi cikin natsuwa "Uncle na ji wa'azi sosai daga bakunan malamai mabambanta game da girman zumunci da irin matsayinshi a addinin musulunci da hukuncin me yanke shi dame sadar dashi, Uncle ni da kai a jinsi yaran Bajju ne,amma a addini mu musulmai ne, kuma addininmu na musulunci bai hana mu sadar da zumunci ga yan'uwanmu wad'anda ba musulmai ba, to amma kai me yasa ba ka sadar da zumuncin ka da sauran yan'uwanka na jinsi Bajju? Yakad'a kai"Sumayya ban k'i sadar da zumunci dasu ba har sai da naga suna niman kasheni... bari kiji abinda yafaru tun kafin a haifeki. "Wata rana hanya tabiyo dani ta Zonkwa sai kawai na k'arasa K'auyan mu Madauci dan mu gaisa tunda na kwana biyu ban jeba, wallahi kamar jira ta sukeyi sai ganin Kantiok, Dinatu da wasu daga cikin yan'uwanmu matasa a bayansu d'auke da kokara da adduna, nafito daga cikin motar ina kallansu da mamaki "Kantiok ina za kuje da tsakar rana haka?...ban gama rufe baki ba naji an sakar min adda a tsakar ka,aiko nan take jini ya 6alle,wani ne daga cikin yan'uwan mune da wannan aikin, danaga da gaske k'ara saramin yake shirin yi aida gudu nakoma motata amma kafin inyi wani yunk'urin tayar da ita sun fara dukar motar,gilasanta sun farfashe,banyi aune ba naga sun fincikoni wasu suna ba da umarnin a samin taya in babbake kawai kowa ya huta,wallahi na ci na jaki da gasken-gaske. Dak'yar Kantiok ya ceceni bayan ya samu nashi rabon,suka haushi da zagi ai ba haka suka shirya ba dan me zai 6ata musu shiri?Yana hawaye yake basu hak'uri,dak'yar suka hak'ura suna cigaba da zagina idan ban daina zuwa inda suke ba sai sun kasheni tunda sun riga sun yafeni,sun barma musulmai to inje in k'arata can dai gasu gada zomo ya ji kid'an farauta. Kantiok shi yakaini asibiti kwanana uku nad'anji sauk'i nace mishi ni zan tafi yadinga bani hak'uri wai ba laifinshi bane,ba yadda zaiyi ne "Naka na kane ko ya cinyeka bazai tauna k'ashin ba,nace mishi ba kome,nabashi complementary card d'ina,dama na zo in fad'a musu na yi sabon gida,wanda muka tashi a ciki na ba wani malami halak-malak acigaba da koyar da karatun alqur'ani da sauran littafan addini ina fatar ya zamar min sadakatul-jariya bayan numfashina ya k'are a doran duniya. Yakar6a yana tayani murna da kuma bani tabbacin duk lokacin daya samu dama zai kawo min ziyara bazai bari Dinatu tasan sabon gidan na ba,namishi ihsani kamar yadda nasaba mishi mukayi bankwana.Sai dai har yau d'in nan bai zoba,amma lokaci zuwa lokaci muna magana dashi tawaya daga baya kuma na daina jinshi ko na kira lambar ta shi ba ta shiga,amma yanzu Insha-ALLAH za muje gaba d'ayanmu. "Uncle to ya akayi ka musulunta? Yayi yar dariya"shekarun dayawa Sumayya,ina secondary aka kawo mana yan bautar k'asa (corpers) anan na had'u da Corper Muhammad Aminu,shi yake koya mana lissafi (Mathematics) kin san ko wani malami yana san d'alibin daya ke gane darasin shi,to haka abin yakasance tsakani na da shi,har mukayi sabo na ban mamaki har aikena yakeyi wasu lokutan in siyo mishi kayayyakin buk'ata na yau da kullum idan baya jin zuwa cikin gari,sai washe gari in taho mishi dasu. Har Staff-Quarter ina binshi idan yana da abun bani naci ko nasha yaba ni,idan babu muyi hira,wasu lokutan kuma yak'ara min haske akan lissafi.Yakan dafa kafad'ata yayi murmushi "Shedrak kwakwalwarka tana ja sosai akan lissafi,kaje ka karanci Accounting nan gaba kazama Accountant General Of The Federation. "Malam bani dame tsaya min inyi karatu iyayena sun mutu.Yayi murmushi dan Iyayenka sun mutu ba shine zai dakatar dakai daga san abinda kake san zama a rayuwa ba,kai namiji ne gwagwarmaya da rayuwar za kayi"babu maraya sai rago"zan taimake ka kayi karatu idan ka gama secondary ka kawo min takaddun ka zan samo maka addimision a jami'ar Ahmadu Bello(ABU)ga tallafin karatu da za a dinga ba ka,kuma ai sana'a zaka fara yi sai kaga kome yana tafiya. Corper Muhammad Aminu me sauk'in kaine da bai d'auki rayuwar duniya kayan gabas me k'amshin turaren d'an goma ba, a hankali dabi'un shi suka fara burgeni banyi aune ba sai kawai najini rannan ina karanta"Innas safa wal marwata min sha'a'irillah.Ni ban san kome ye ba amma nasan a irin karatun dayake yawan sawa ne,dama su bismillahi na iya saboda indai zaici abinci ko abinsha sai yafad'a dan wasu lokutan ma yana zubawa a faranti d'aya yace muci,tun ina jin nauyi da kunya har nasaba. Gab da zasu tafi sun gama hidimar k'asa nasame shi a d'aki yana karatun Qur'an sai da yakai aya,sannan nazauna ina gaisheshi dan ranar bai shigo makaranta ba"Malam yau baka shigo ba.Yagyad'a kai "Bana jin dad'i,ban dad'e da dawowa daga asibiti ba"Yadai? Yatambaye ni. Nad'anyi murmushi"ni dai malam ina sha'awar addininka sai dai baza a barni a gida ba.Yamik'e zaune daga kwanciyar da yayi yana fad'in Shedrak kai namiji ne,ka kuma fara mallakar hankalin kanka dan haka kanada damar yin musulunci tunda shi kake so.Da wannan nasamu k'warin gwiwa. Ranar da zasu yatafi nasha kuka shi ya rarrasheni"haba Accountant General Of The Federation wannan ba girman ka bane,share hawayenka maza basa kukan hawaye,wannan ai d'abi'ar yarane.Da haka mukayi bankwana. Direbansu yaja motar ni da sauran dalibai dawasu daga cikin Malamanmu muka d'aga hannu muna musu adabo🙋har motar tayi nisa ta 6acema ganinmu."We may or may not see each other again. Gaba d'aya sai makarantar ta gundireni kamar akan k'aya nake,a dadddafe nak'arasa.Muna gamawa nafara zuwa kasuwa, dako nake yi dan bani da kud'in da zan yi sana'a, nasha wahala amma na tara kud'i masu yawan danake ganin intayi ruwa rijiya idan bata yiba Masai,sannan natara yan uwanmu nafad'a musu k'udiri na nasan zama musulmi.Sai sukayi tsalle suka dire ALLAH yakashe su ban isaba, bazan yiba meye yata6i kwakwalwata haka?Nima naja tunga nakafe sai nayi sallah.Da suka rasa yadda za za suyi dani sai suka dinga zagina suna fad'in sun yafeni acikin zuri'a da jinsinsu na Bajju,har abadan duniya basu ba ni,ban bi takan suba na d'auki jakata sai cikin gari. Agidan Liman tsoho anan na zama cikakken musulmi na za6i sunan Hafiz nacigaba da harkokina da musulmai,ina kuma zuwa kasuwa ina yin dako dan incigaba da rufa ma kaina asiri duk da kome ana bani amma ban yadda na zama cima zaune ba. Rannan kamar wasa ina gwada lambar Corper Muhammad daya bani sai kawai naji ta shiga dan ban ta6a samun shiba sai ranar.Yad'aga da sallama nima ina murmushin jin dad'i dan nasan ma'anar sallamar dakuma muhimman cinta a musulunci"Malam ina wuni. Yad'anyi Jimmm...nawuce war wasu dak'ik'u cikin tunanin a ina yasan wannan muryar? Zuwa can naji ya amsa tare da fad'in "I'm I talking with the Accountant General of the Federation?Na kyalkyale da dariya ina gyada kai dan sunan fa yana sa ina jin kaina a duniyar wata"Yes Malam you're...mukayi dariya.Bayan mun gaisa nake fad'a mishi na gwada layin shi sau shurin masak'i ba ta shiga.Yace matsalar network d'in k'auyen kune,kuma ai laifin kane kadaure kawai Accountant kasamar muku na'urar sadarwa me k'arfin zango...nayi dariya kawai dan na san zolayata yake yi. Nafad'a mishi kome.Yaji dad'i sosai yadinga ambaton ALLAH cikin shauk'in murna,tundaga ranar sai muke yawan yin waya danma wasu lokutan ni ina samun tangard'an sadarwa sai dai shi yakirani,muna haka ALLAH yama Liman tsoho rasuwa.Iyalinshi basu kore niba amma sai naji gidan ba dad'i, rannan muna waya sai na fad'a mishi damuwa ta yace ba kome inzo Kaduna insa meshi,aiko washegari dasassafe nayi sallama da mutan gidan Liman tsoho nad'auki hanyar KD. Malam Muhammad yana aiki da ma'aikatar Ilimi ta jahar Kaduna(Ministry of Education)Ina zuwa yad'orani akan kasuwanci dan ya tambayeni zan tafi jami'a karatun ne? Nace mishi a ah nafi san kasuwanci d'an tunda nafara dako a Zonkwa naji dad'in kudi,yasani a makarantar addini,da daddare ma ba barni na zauna ba,ina makarantar Islamiyya ta maza,ina karatu ina sana'a, k'ank'anin lokaci kuma ALLAH yasama kasuwan cin nawa albarka,wallahi duk abinda nata6a sai yazama bud'i daga Indallahi. Shekaru na biyu a Kaduna muka had'u da wata Atika muna soyayya har an kai kud'in aure da sadaki amma Iyayanta suka dawo da shi wai su baza su ba tubabbe auran yar su da a ka haifeta musulma iyaye da kakannin kakanniba,Ina ai wannan ganganci ne zagin uba ranar sallah. Ran Malam Muhammad in yayi dubu ya 6aci yadinga fad'a wannan ma ai jahilcine to ko musuluncima ai da tubabbun yafara yacigaba da bunk'asa har zagaye ko ina lungu da sak'o nafad'in duniya gaba d'ayanta. A ranar bayan munyi sallar la'asar a masallacin unguwarmu yatsaida mutane dan su shaida.Yad'aura min aure da yarshi mace guda d'aya da ALLAH yabashi daga cikin Ya'ya maza guda bakwai Ummulkhair me kimanin shekara goma sha uku dan lokacin ajinta hud'u a secondary.Yakalli Sumayya yana murmushi kin san abinda yace min? Tagirgiza kai.Bayan an kaita gidana yadafa kafad'ata "Hafiz ga Ummulkhairi nan kaji tsoron ALLAH karik'e ta da amana,Idan tayi ba dai-dai ba ka nuna mata kuskurenta nan take,ka kuma muna mata yadda za tayi dai-dai,shi icce tun yana d'anye ake tank'warashi...Kome daza ka d'orata akai to a yau d'innan za ka fara k'ok'arin gina matashi a cikin zuciyarta,ko ba ta so to kai kajajirce karka karaya Insha-ALLAH sai kayi nasara.Ubangiji ya albarkaci auranku...abinda yafad'a min kenan yajuya yayi tafiyarshi. Sumayya tajijjiga kai"Malam Muhammad Aminu yacika jarumin maza Ubangijinmu kasa ka mishi da mafificin sakamakon ka.Amin,Amin Sumayya. Shigowar Maman Hasan yasa yanuna ta da yatsa"kin gan ta nan Sumayya har yanzu muna zaman lafiya.Tazauna a kujera tana kallansu"Eh gani nan,to me namaka kake ta nunani da yatsa?Tayi furucin da wani salo irin na shagwa6a.Sumayya tayi murmushi ganin wani irin kallon k'auna me cike da shauk'i datake mishi.Tsam tamik'e za ta shige d'aki "Sumayya dawo kiyi zamanki mana...dasauri tak'arasa shigewa ta rufo k'ofar tana girgiza kai "wanan kallan da abinda zai biyo bayan shi ba dani ba gaskiya"ga d'a da fatalwa. Bayan shekara d'aya Sumayya ta gama karatunta,har tasamu gurbin karatu a jami'ar Kaduna (KASU) tad'ora degree a Islamic Studies ta kuma k'ara zage dantse tana kwankwad'ar madarar ilimin addinin musulunci, dama can a goge take ga Ilminta na Catering &Hotel Managements,gashi kuma yanzu wani fannin na daban take karanta,yanzu larabci kamar dama can dashi ta taso sai dai me zurfi daya wane ba ta ganewa har sai ta duba k'amus d'in larabci... Sai dai weak point d'inta Julaibib musamman da sukaje taran Muslim Student Society Of Nigeria(MSSN)a jahar Katsina ta ganshi ganin idanun ta yayi kyau,yadad'a zama d'an gayu,shigarshi kamar ko yaushe ta fararan kaya.Shine shugaban kungiyarsu ta ABU,har tagaban shi tawuce suna tsaye shi da Maimun amma ba ta ga Musaddiq ba,wallahi daurewa kawai tayi ba ta musu magana ba amma ta dad'e a tsaye a gefensu tana k'are mishi kallo tana wata kissima a zuciya,har had'a idanu sunyi amma bai gane taba saboda tasa nik'abi ta kuma rufe k'wayar idanunta da gilas.Tunda taganshi d'aliban da suke k'ark'ashin kulawarta suka ka sa gane kan Amirarsu Sumayya...Da akace tazo zasu yi magana da yan Jami'ar Ahmadu Bello kasancewar su yan Jaha d'aya ne,kwanciya tayi wai bata jin dad'i,dan wallahi idan taga Julaibib har kuma sukayi magana to tsohon mikin k'auna ne zai 6alle gwamma daga nesa-nesa kallan kura... Yafito yana sa links d'in hannun riga Maman Hasan tanuna mishi Sumayya.Sai yazauna yana kallanta"Tatsuniyar gizo bata wuce k'ok'i,abu d'aya yahana shi zuwa yasamu Julaibib suyi magana akan Sumayya shine yace baya son ta,to ko dabara kad'ai bazata d'aure kaya ba dole sai da igiya.Yakira ta da kakkausar murya tunanin me kikeyi?Tun d'azu kin tasa kofi a gaba kin kasa san shayin.Yatsareta da idanu cikin d'aurewar fuska,ganin haka yasa ta sunkwui da kanta tayi shiru. Kina sane da maganar danace za muyi?Eh Uncle.Yanunata da yatsa"Ina sane da abinda ke faruwa, banyi niyyar magana ba,to sai dai naga abin yana k'ok'arin shige makad'i da rawa,mutane uku suna zuwa da niyyar auranki amma kina korarsu,wannan kuma ba dai-dai bane tunda ba haka zaki dauwama ba dole za kiyi aure,dan haka akwai abokin kasuwanci na dayace yana sanki to nayi na'am da shi dan mutumin kirki ne,kuma ban 6oye mishi kome game da keba, shima ya amince yana sanki a haka.To jiya yasame ni dan niman izini yana so zai zo ku gaisa. Sumayya karki 6oye min kome idan ya zo baku dai-dai ba,dan ba auran dole zan miki ba kin gane ko? Me zatace?Tagyad'a kai"Uncle zan zama me biyayya zan kar6i duk hukuncin daka zartai,dan haka ko wanene shi na yadda zan aureshi dan na san baza kamin za6en tumun dare ba.Yayi murmushi kin amince kenan?Tajijjjiga kai"eh Uncle na amince.To ALLAH yamiki albarka,yasa ki gama da duniya lafiya,ki kuma yi hak'uri da kome akan Julaibib, Sumayya wani hanin ga ALLAH baiwa ne.To Uncle nagode. Yamik'e shikenan ki daure kisha shayin.Takai kofin tsakanin la66anta kamar tana sha,suna fita shi da Maman Hasan da take mishi rakiya tadire kofin a k'asa tawuce d'akin baccin su takwanta tare da lumshe idanunta, kwallan da suka cika idanun suka samu damar zubowa sharrr...ranta ba dad'i sai ta fara karanta"ALLAHU-ALLAHU Rabbi laa'ushrika bihi shai'an.Tana ta maimaitawa har bacci yayi a won gaba da ita,sai da lokacin makarantar yakusa Maman Hasan tashiga ta tasheta. ...Aiki ke koran bak'o d'an gida ya dad'e da sabawa. ...Nagaji sai rago😊 10 Jumaada Awwal 1441 5 January 2020 We Ibrahim's Daughters 👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi nagoma sha biyu. Tana yankema Khadija faratan ta Hafsa tashigo da sallama,tazauna a hannun kujerar tana kallansu cikin murmushi sun sha wanka da kwalliya kayan su iri d'aya,doguwar riga k'irar Bahrain ruwan makuba, k'amshin turen ta ya mamaye d'akin. Tad'an kalli Hafsa"bakin ki da magana. Tayi yar dariya"Yaya Sumayya ba wata magana,amma fa kina da bak'o a waje.Tayi luuu da idanun ta kamar zata rufesu,sai kuma tabud'e su gaba d'aya a fuskar Hafsa "bak'o?Ta tambayi Hafsa itama."Eh bak'o ne a wajan ki amma wasu lokutan nakan ganshi tare da Baba.Tad'aga idanu takalli agogon da ke manne a jikin bangon d'akin k'arfe uku saura minti goma na yammacin. Tagyad'a kai "fad'a mishi ina zuwa.Ta amsa da to.Sumayya tabita da kallo da tunanin irin mutumin da idanun ta za su gane mata wani daban,ba D'ansarai ba.Tayi wani d'an huci cikin kad'a kai,sai da tagama yanke mata faratan duka sannan ta d'auki farin dogon hijab d'inta a saman kujera tasa. Miqdad yana zaune a D'akin-shak'atawar yana cin abincin rana yad'an kalleta ganin ta nemi waje ta zauna"Sumayya ba jiranki ake yiba?Tamishi nuni da Maman Hasan data basu baya tana kallan taga,waya takeyi.Ya watsa hannu"kije kawai ai ta san da zuwan shi ita ta aiki Tawaje nah(Hafsa)tafad'a miki,kema ai kin san gama wayar Maman Hasan ba yanzu ba,idan suka fara hira da tsoho me ran k'arfe Malam Muhammad Aminu sai kin sike ko kuma kud'in wayar ya kare an katse sadarwar tasu.Tarik'o hannun Khadija Miqdad ya girgiza kai "saketa kiyi tafiyar ki,ke Khadija zo nan ya yafito ta da hannu.Bata so ba sai dai ba yadda za tayi ne,yanuna mata kujera zauna anan kijira ta,ba dad'ewa za tayi ba kinji ko? Tagyad'a kai idanun ta sun cika da kwallah,yayi kamar bai gani ba yacigaba da cin abincin shi. Yana zaune a dakalin dake harabar gida yana duba wani d'an k'aramin littafi Dammm...taji ruguzowar wani abu me k'arfin gaske a k'ahon zuciyar ta, ta dafe kirji cikin Istirja'i dak'yar tak'arasa wajan da sallama.Yamayar da littafin aljihun gaban rigar shi yana amsa sallar. Yana d'ago kai zai kalleta caraf idanun su ya had'u,shi dama ya san ta,dan d'ai-d'ai kun ranane baya ganin ta lokacin da take zuwa Sanawiyya, itace dai yau tafara ganinshi. Takauda kai ba wani babba bane dan ita tayi zatan sa'an Uncle za ta gani tunda yace abokin kasuwanci shine,dogo ne kuma shima yana da nashi kyau da fasalin, yana sanye da shadda me maik'o ruwan siminti, hularshi k'ube ruwan siminti da ratsin bak'i, sai bak'in takalmi sawu waje.Yakatse shirun"ranki yadad'e barka da fitowa.Sai lokacin ta gaishe shi,yamik'e tsaye yana nuna mata wajan Bismillah ga waje ki zauna "tagirgiza kai "bak'on ka annabin ka"kai yafi cancanta daka zauna. Nagode amma ki barni a tsayen,ni namiji ne zan jure tsayuwar koda awanni biyu ne.Bata ce kome ba tazauna "Yad'anyi gyaran murya "Malama Sumayya kin san abinda yake tafe dani ko?Fuska a d'an yamutse ta amsa"Uhhh" ba tare data bud'e bakin taba.Yabita da kallan nazari dama Alhaji Hafiz ya sanar dashi kome shi yasa take amsa mishi a d'ad'd'age kenan,sai yayi murmushi cikin kad'a kai.Sai fa ya yi hak'uri dan ya san jin kan mata sarai bare kuma ga matsalar k'auna.Wayyo!Sumayya kema sai kinyi hak'uri,ni da shi ba d'aya bane koda kuwa uwar mu d'aya uban mu d'aya ne. "Sumayya kin san wani abu kuwa? Yadda yayi furucin kamar irin sun dad'e d'in nan ya zo da saurin shi yana so yabata labrin wani abu da d'umi-d'umin shi.Sai tayi saurin d'ago kai tad'an kalleshi amma bata ce kome ba.Idan mukayi aure,ALLAH yabamu haihuwa d'anmu na farko indai namiji ne to ni d'in nan yanuna kanshi da dan yatsa, na miki alk'awari ki rubuta ki ajiye,da bakinki me albarka zaki mishi hud'uba da sunan Julaibib... dan ki tabbatar ni masoyinkine na gaskiya me san abinda kike so.Cikin mamaki da dariyar data kasa dannewa na jin dad'i ta kalleshi kai tsaye ta d'an bud'e idanunta"to ya akayi kasan sunan shi? Yanunata da yatsa"an ta6o inda yake miki k'aik'ayi ko? Shi Salim wani irin mutum ne da duk abinda yake so yana yin k'ok'ari wajan sanin wasu muhimman abubuwa game dashi,ta yadda bazai sha wahala wajan mu'amala dashi ba.Ya gane soyayyar da take mishi wata jarabtace daga Ubangiji,tunda ya fad'a mata bazai aure taba,kuma ta yi hak'uri ta fauwalama ALLAH duk da yana ranta,to yanzu ga shi,shi ya zo zai maye gurbin shi da gyara harda alakoro Insha-ALLAH sai tayi alfahari dashi a matsayin mijin sunnah. Kayi alk'awarin sama d'anka sunan shi?Yajijjiga kai"Eh wallahil-azim na yi alk'awari. Tamishi wani lallausan murmushi sannan ta kauda kai daga kallan juna da sukayi nawasu dak'ik'u.Daga nan hira ta6alle... Zuhair ne yakatse musu hirar ta hanyar kawo ma Salim ruwan alwala a buta dan mukhtarin la'asar yayi.Tanata kallanshi yana alwalar cikin nutsuwa kuma cikakkiya har yagama yamaida hular shi kanshi sannan yamik'a mata butar,sukayi sallama dan an fara kiraye-kirayen sallah daga mabambantan masallatai,Miqdad ma yafito shi da Zuhair sun tafi masallaci dan sauke farali.Tabi bayanshi da kallo har yafita daga harabar gidan "Yanada saurin shiga rai. Fuska a sake tashiga gida. Maman Hasan tace"Yaya dai Sumayya?Sai ta zauna a kujera tana yar dariya wallahi haka kawai take jin nishad'i,rabon data tsinci kanta a irin wannan yanayin tun ranar da D'an Sarai yamata nasiha data daina k'arama sama hazo(shan taba) Maman Hasan ta tayata da murmushi"a Alhamdulilla labarin zuciya a tambayi fuska. Da safe tana shan shayin na'ana'a, kalla,kanumfari,da ya'yan algarib sai tiriri yake yi da k'amshi me dad'in dake k'ara mishi armashin da ko bakayi niyyar sha ba idan aka baka sai ka sha.Hafsa tashigo da waya d'akin baccin su dan yau bata fita D'akin-shak'atawa ba,anan ta zauna tana karyawa tana nazarce-nazarcenta. Tamik'a mata wayar"ga shi ana magana"takar6a takai kunnan ta da sallama,ya amsa sallamar yana tambayar ta ya gida ya karatu?A takaice ta amsa"Lafiya...Alhamdulillah. Sukayi shiru na wucewar wasu dak'ik'u"wake magana?Takatse shirun. "Salim ne. Salim... Salim... Tafad'a ta maimaita cikin tunanin ga no wa ye haka?Sai yatari numfashin ta,a d'an marairaice"Innalillahi...Ina zan sa kaina...? Mummuna ya ga mata.Kar dai ace baki gane Salim d'in ba?Haba Sumayya to Salim d'in kine fa. Ta d'an bud'e idanu"Oh...Ya Rahman afwan Salim ka san bani da lambar ka.Yayi yar dariya"na sani nima jiya ne na kar6i ta ki lambar a wajan Alhaji,yana nufin Alhaji Hafiz.Kin san ranar dana zo k'aunar ki ta mamaye k'wak'walwa ta har natafi ban baki ba,nima ban kar6i ta kiba.Suka gaisa a mutunce"Sumayya da yammacin yau nake san zuwa wajen ki shin kina da lokacina? Tad'anyi murmushi"haba Salim girman ka ya wuce haka,ai ko ba lokacin ka to dole a k'irk'iroshi bare ma a kwai,amma I'm really sorry to say...ka san yanayin karatu,yau k'arfe goma na safiyar nan zan tafi makaranta kuma gaskiya sai biyar da rabi za mu gama lectures sai dai gobe.Yagyada kai"ba damuwa da yau da goben duk d'aya ne.Kad'an suka ta6a hira sukayi sallama. Sumayya da Salim k'ank'anin lokaci suka aminta da juna.Sumayya har ranta take jin ta samu abokin rayuwa,saboda Salim mutum ne me sauk'in kai,bai cika d'aukar al'amura da zafi ba.Dariya takeyi saboda kalaman shi,yabita da kallo cikin zancan zuci,wallahi kome na ta akwai tsabta,hak'oranta farare tas kamar ba dasu take tauna duk abinda yake shiga cikin cikin taba. "Sumayya dawani man goge baki kike amfani ne?Takatse dariyar"man goge baki kuma?Yajijjiga kai eh dan na ga hak'oranki sun bambanta dana mutane da yawa cikinsu kuwa har da ni d'in nan yanuna kanshi,kamar bakya 6a tasu da abinci sai d'aukar idanu suke yi. Kana so kasan sirrin?Sosai kuwa.To ka zama me yawan aswaki ba sai lokacin alwala kad'ai ba, kuma musamman kasa mu aswakin al'araq,wannan shine sirrin ga shi kuma sunnane.Kuma ka san ko masana a harkar bincike na yanzu da suke ganin sune tushen ilimin kome,to sunyi bincike kuma sun ga no sun kuma tabbatar yin aswaki goge hak'ora da chewing-stick magogi,ba brush ba yana k'ara k'arfin dasashi. ALLAU-AKBAR tsarki ya tabbata ga ALLAH. Manzan ALLAH sai da yace ba dan kar ya takura ma al'umma ba da ya farlanta mana yin aswaki. Salim ya jijjiga kai gaskiya kin tunatar dani abinda na manta,nagode miki Sumayya lallai tunatarwa tana amfanar da mumini. Sumayya ki bani dama in tura Iyayena,ai mun d'an fahimci juna,yanzu mun san wasu daga cikin halayan junan mu ko? Duk da dai ba a sanin maci tuwo dole sai miya ta k'are. Takalleshi cikin natsuwa"Salim a da zuciya ta, tana rayamin inyi musulunci saboda Julaibib ne, kuma koda na kar6i musulunci na kar6a ne saboda shi,amma cikin k'udirar Ubangiji sai zuciya ta,tacanja daga wancan tunanani da niyar.A yanzu na yadda saboda zatin ALLAH nake musulunci,da taimakon su Uncle ta fuskar nasiha da zuwa Islamiyya da sauraran wa'azi daga bakunan manyan malamai mabambanta duk su suka cusa min yin abu saboda ALLAH,na san na rasa D'an Sarai amma zuciya ta bata aminta da barin musulunci ba,dan na gamsu addinin musulunci shine addinin gaskiya,ina zaune kwatsam sai Uncle yazo min da maganar ka,a lokacin na amsa mishi ne saboda kawai tsakani na da Uncle ba musu har abadan duniya,wallahi kome rashin jin dad'in abu in dai yabani umarni inyi ko in bari zan yi,dan na san soyayya ce a tsakanin mu,har fa zuciyata ta fara min sak'a da mugun zare amma ban biye mata ba,nayi ta addu'a ina neman rok'on Ubangijin mu yakawo min agaji kar in biye ma sharrin ta. Amma a ranar da idanuna suka fara yin tozali da kai,kalamanka da kome naka sai suka burgeni, zuciya ta tayi wasai...A ranar na kar6e ka kamaye gurbin Julaibib,tad'an sake kallanshi cikin natsuwa Salim har yanzu ina jin wani abu game da D'ansarai amma ba soyayya ba,saboda sanadiyar shi nabar kowa da kome, harkar da nake yi nabin maza da tara abinda duniya daga garesu yabar zuciya ta,fatana kawai in mallake shi,to sai nagane a yadda yake me natsuwa da kamewa hak'ata bazata tadda ruwa ba, sai na bijiro mishi da maganar aure, na sadak'ar zanyi sallah ba dan kome ba sai dan kawai na k'wallafa rai shi d'in kawai nake san mallaka,manyan idanunta masu maik'o suka cika da kwalla.Ubangijin mu alhakimu ne,sai gashi ya canja min da wani daban kuma zuciya ta ta aminta da shi,dan haka Salim kai nake so soyayyar da ba ka da abokin tarayya.Julaibib dai yana da lada a wajan ALlAH saboda halayan shi masu kyau da tsabta wanda addinin musuluncine yazo dasu da kuma karatun addinin da yayi shine ya siffantu da siffofin,nima sai yanzu nagane wasu halayanshi da, a da nake mugun mamakin me yasa shi baya kaza?Me yasa yake kaza? Tad'aga hannayen ta sama ALLAH kahad'ashi da macen albarka,kamilalliya me addini.ALLAH kasamu daga cikin wad'anda ta sanadiyyar mu wasu za su samu haske irin na addinin ka.Ubangiji ka kara mana lafiya ka kara inganta mana Imanin mu.Yanata kallanta cikin so da k'auna,sai yadad'a aminta da ita dan Alhaji Hafiz ya mishi bayanin kome dalla-dalla ba jibge. Sumayya... Bata amsa ba tad'ago a hankali suka kalli juna"Sumayya yau rana ce ta musamman a wajan mu ko?Tasunkwui da kai daga kallan da yake mata tana murmushi. Sai da a ka tsaida ranar auran Salim da Sumayya,Miqdad da budurwar shi Zainab sannan Alhaji Hafiz yatashi Miqdad d'in musamman dan zuwa k'auyan su Madauci wajan d'an uwanshi,bai ta6a zuwa garin ba amma da tambaya sai gashi a k'ofar gidan.Yanata sallama yaji shiru ba a amsaba,zuwa can sai yatuna to su ina ruwansu da wata sallama?Sai yakai hannu yafara rank'washin k'ofar.Yana gyangyad'i kamar a sama yaji ana buga k'ofar yamik'e dasauri yana fad'in"kai wanene haka daba zai shigo ba,bayan k'ofar ba kulle ta akayi ba amma yatsaya awaje?Sukayi kallan kallo na wucewar wasu dak'ik'u sannan ya matsa mishi yashigo,suka zauna a fararan kujerun robar tsakar gidan har yanzu kallan juna sukeyi "daga ina haka d'an Samari?Kantiok ya tambaye shi.Miqdad yayi murmushi daga Kaduna nake.Ai yana jin haka sai yamik'e ya rungumeshi yana dariyar murna"haba no wonder naji a jikina kamar na san ka to sai dai a ina? Kai yaran Shedrak ne ko?Ina Kasham? Ya baku zo tare ba?Su ma suna nan zuwa.Yasaki Miqdad yafita dasauri,lemun kwali Don Simon,ruwa da kofi yakawo mishi gashi nan kasha barin kar6o maka abinci... ya tareshi da saurin"a ah kabar shi kawai.Yaja yatsaya yana kallanshi"Kazo gidana amma baza ka ci abincin mu ba saboda me?Yad'an shafa fuskar shi"Kayi hak'uri Kawu ina azumi ne amma da ba abinda zai hana ni ci.Yadawo yazauna to kai saboda ALLAH za kayi tafiya ba sai kabar azumin ba?Ya amsa mishi cikin girmamawa"Kawu azumin yana da muhimmancine. Suna ta hira kamar sun saba. Miqdad yabashi sak'on da aka aiko shi wasik'a ce Alhaji Hafiz d'in yake sanar dashi"Kasham tana wajan shi tana kuma sallah,yanzu kuma ta samu mijin aure,dan haka zai aurar da ita,amma bayan bikinza suzo Insha-ALLAH,sai takardan kud'i (cheque)an rubuta mak'udan kaud'ad'e an sa hannu sai zuwa gidan kud'in(Bank)a Kar6a "Hallelujah..yafad'a saboda mamakin adadin kud'in daya gani a rubuce,gaskiya shi har yagama aiki bai ta6a kar6an rabin-rabin wannan ba,yana ta dariyar murna,shi kuma Miqdad tasbihi yakeyi a zuciyar shi"ALLAH buwayi gagara misali hatta wushiryar shi irin ta mahaifin shine,sunyi kama sosai sai dai wannan fari ne, mahaifanshi kuma baki ne. Kiran wayar ta tashigo yad'aga da sallama"Yaya Miqdad ya hanya ka sauka lafiya ko? Yagyad'a kai"na sauka lafiya Sumayya gani ga Kawu na ganshi ganin idanuna.Tayi yar dariya."to masha-ALLAH ba shi wayar.Yamik'a mishi.Yana jin muryarta yayi dariyar jin dad'i "Kasham sai kuma yajuya harshe zuwa yarensu na Bajju,sun dad'e suna hira sannan yafara gyad'a kai da alama wata magana me mahimmanci take fad'a mishi yake gyad'a kan cikin gamsuwa"amin Kasham nagode ALLAH yamiki albarka.Miqdad yakad'a kai"wato kowa dai ya san akwai ALLAH yadda da shine dai ba kowa yayi ba. Yana shirin tafiya yace ni har zan tafi banga Maman Sumayya baWai Kasham ce ta koma Sumayya?Eh kawu"Yayi murmushi kawai, Maman Kasham ta tafi kasuwa gashi kuma sai yamma za ta dawo,to ka kwana mana.Yayi yar dariya"Kawu ina da ayyukan da zanyi da yawa amma zan zo na musammma idan nasamu sarari zan kwana in ga sauran yan uwan mu.To shikenan ALLAH yakaimu"yarakoshi har inda ya ajiye motar shi yana bashin tabbacin zaizo ayi d'aurin auran su dashi.To Kawu aiko za muji dad'i ba kad'an ba,yad'auko rafar kud'i yan naira ashirin guda d'aya yabashi,sai yagirgiza kai,haba My Son ni ban ba ka kome ba ai kuma bazan kar6e na kaba, kabarshi kawai nagode,ga cheque na kud'i me yawa da zan kar6a.Miqdad yakalleshi cikin natsuwa"Kawu ai wancan d'an uwan kane yabaka,wannan kuma d'an kane yabaka,tashi kyautar daban,tawa ma daban,sai dai ban sani ba d'an uwa ya fi d'ane a wajanka?Yasake mik'a mishi sai yakar6a yanata mishi godiya,sukayi sallama cikin farin ciki.Yad'aga hannu yana mishi adabo tare da addu'ar ALLAH yatsare ya kiyaye mishi hanya,har motar tasha kwana ta6ace ma ganin shi, sannan ya juya,yak'are ma gidan kallo lallai gyara yazo tunda kud'i sun samu. Lokacin daya k'arasa cikin gari har an idar da sallar azahar dan haka yayi alwala yayi sallarshi raka'a biyu ta k'asaru yayi azkar d'inshi sannan yakoma mota yana bin shagunan bakin titin da kallo yana kuma tunano kalaman Sumayya "Idan kaje Rahama Store to ka tambayi shagon Julaibib za a kai ka,yana tambaya kuwa aka nuna shi shagon sai dai kash...Musaddiq ne a shagon, daya tambayi Julaibhib yace yana gida sai bayan sallar la'asar zai fito.Yamik'a mishi wata yar madaidaiciyar jaka ruwan k'asa"Idan ya fito abashi "Miqdad yasake mik'a mishi hannu sukayi musafaha yajuya ya fita daga shagon. Shima ya so ganin wannan D'ansarai d'in da Sumayya take bala'in so,yayi murmushi ganin yadda tayi da yace bazai kar6i sak'on wani Julaibib ba dan shi ba d'an aiken ta bane, wallahi idanunta har sun cika da kwallah ta sunkwui da kai k'asa bata kuma magana ba,sai tabashi tausayi.Sumayya yakira sunan ta,tana d'ago kai sharrr...hawayan masu d'umi suka zubo a kyakkyawar fuskar ta,tasa hannu ta share su sannan ta amsa a raunane"na'am...Yad'an harareta ke fa raguwa ce daga wasa sai hawaye? Tagirgiza kai"ni ma ban so hakan ba, ban kuma san ya akayi suka zubo ba,ni da Julaibib ai ba wata alak'a kuma sai ta yan uwan takan musulunci,sak'on dazan ba ka wallahi tun a Makka nasiyo mishi,da kuma na san zan had'u dashi a taron MSSN d'in nan na Katsina dana tafi dashi na bashi...ni a yanzu ina san D'ansarai ne saboda shi mutumin kirki ne me addini,amma karka manta ina da jan gwarzo na,dubu jiran mutum d'aya tad'an d'age gira tana wani lallausan murmushi sannan tafurta sunan Salim.Yayi yar dariya "Sumayya kenan so gamon jini.yashige mota yazauna ya d'aura belt sannnan yatayar cikin ambatan sunan ALLAH yad'auki hanyar Kaduna garin gwamna. Musaddiq yana lissafin wasu kud'ad'e bayan sallar la'asar Julaibib yashigo da sallama yazauna yana kallanshi har yagama yayi rubuce-rubucen shi a littafin da suke rubuta kome na kud'ad'en kasuwan cinsu yamayar cikin dirowa sannan ya ajiye mishi jakar a gaban shi "dazu aka kawo maka.Inji wa?Musaddiq ya dauki mukullin motar julaibib d'in zai fita sannan yabashi amsa "Wallahi ban san shiba bak'o ne"ni nafi. Yagyad'a kai " To Allah yatsare. Yabud'e jakar dabinon ajwa yagani, ruwan zamzam da farin miski sai envelop da sunan shi yake jiki 6aro-6aro da manyan bak'ak'e "JULAIBIB ABDULLAHI D'ANSARAI... Yabud'e da tunanin wa ya aiko mishi da wannan sak'on? Assalamu alaikum warahmatulla. Julaibib ina gaisheka gaisuwa irin ta addinin musulunci.Ya su Mama?Ya karatu?ALLAH yamaka jagora.Julaibib kasance wata yau raye a cikin musulunci ba wayau da dabara ta bace,a ah ganin damar Ubangijinmune"Alhamdulillahi bi ni'imatil Islam.Wallahi a duk inda naje babu rauni da tsoro zan bayyana identity d'ina saboda addini na yafi kowane addini tunda ALLAH mahaliccin muma yafad'i hakan a Alqur'ani cewa"Addinin musulunci shine addini ko awajan shi "Subhanallahi addinin mu kome anyi programming d'inshi an ba mu. "Julaibib na san kai mutumin kirkine me k'ok'arin bin dokokin ALLAH gwargwadan iko, dafatar baza ka canja daga yadda na sanka ba. Dan ALLAH kar kabari shaid'an ya rud'eka, rayuwar jami'a ta canja ka. Daga k'arshe nake mana barka da shigowa sabuwar shekarar musulunci.Me maka fatan alheri a rayuwa.Musha ruwa lafiya... Sumayya Kantiok Donatus(Kasham) Dammm...zuciyar shi tabuga da k'arfin gaske.Sumayya...Sumayya yafad'a ya maimaita cikin san tantance wai wace Sumayyar?Yad'auki wasik'ar yakaranta yasake karantawa,kenan ita ce Amira Sumayya da ta musu lecture akan"Media Influence?(Tasirin kafofin sadarwa)Kasham dai daya sani wacce sukayi College of Education ita ce ta musulun ta?ALLAH buwayi gagara misali,ko shekaran jiya sun samu sak'o ta k'ark'ashin k'ungiyar da take jagoran ta akan Islamic Vacation Conference(IVC)yayi zuru cikin tunano wasu kalamanta da suka ta6a had'uwa da ita a wata seminar da akayi a"National Teachers Institute Kaduna akan"Post Primary Institution Programmed"(PPIP)alokacin ta d'aga hannu aka bata damar yin magana"Tace a gajeran tunani na a kirashi da Propaganda zai fi armashi fiye da Program... bata gama rufe baki ba d'akin yad'auki kabbara kowa yayi na'am da hakan,wallahi shi yasha jin wannan sunan Sumayya Kantiok Donatus to sai dai ko sau d'aya bai ta6a tunanin wai Kasham ce ba...Yatuna ranar farko da daddare a wajan seminar abincin alfarma me rai da motsi aka aiko mishi dashi wai inji Amira Sumayya to ganin sauran ma an basu sai bai kawo kome ba"ashe albarkacin kaza k'adangare kan sha ruwan kasko "Amira... Sumayya Kantiok Donatus... Yafurta sunan a zuci...sai yaji wani irin yanayi ya ziyarci ilahirin gangar jiki da zuciyar shi game ita na farin ciki.Ashe shine bai gane taba saboda nikabin data sa,har da gilashin data rufe idanunta"Ina mana barka da shigowa sabuwar shekarar musulunci.Musha ruwa lafiya"abinda ta rubuta a k'arshen wasik'arta kenan.Yajijjiga kai "Tabbas yau goma ga watan"Muharram"yau kuma ga duk musulmin daya samu iko yana azumin "Ashura"Itama tana azumin kenan kamar yadda shima yake yi?Yakad'a kai cikin farin ciki. "Sumayya ina miki fatan alheri a rayuwa,ALLAH yadauwamar dake a musulunci har k'arshen numfashin ki,ALLAH yaba ki mijin da zai rik'eki da amana,mijin da zai ha6aka miki ki cigaba a rayuwa... Yad'auki jakar ya rataya a kafad'a yana kulle shagon sai ko ya hango wani d'an k'auyan su Kasham daya ke aikin share-share a Fajumali-Hotel yakira shi...yak'ara so da fara'ar shi"idan kaji gangami da labari,wallahi kamar ka san yunwa nake ji.Yakalleshi da natsuwa ai ba abinci na ce zan ba kaba,kuma ai yanzu lokacin cin abincin rana ya wuce k'arfe hud'u da rabi na yammaci fa?Yabuga k'atuwar hamma baki a bud'e kai da kake a k'oshe kenan wallahi rabo na da abinci tun daren jiya sai yan kame-kame dana yi da safe,ka taimaka min da abinda zan sai abinci dan ALLAH. Yagirgiza kai"K'wandala ta bazan ba kaba tunda na san mashayar D'one za ta tafi...zai fara mishi rantse-rantse yakatse shi da sauri"kaga in dai yunwar da gaske kake ji to jeka katako kace ma Umma tabaka tuwo na yadda zai isheka in jini...Yad'aga hannayen shi sama"Praise the Lord,Thank you God"yajuya da sauri yaje ya kar6o yazauna zai faraci Julaibib yasake kallanshi cikin natsuwa"Kasham tana ina ne yanzu? Kasham...Kasham... yakalli Julaibib wace Kasham d'in?Kasham kanwar su Alhamdu.Yata6e baki "Kasham ai ta dad'e da barin gida wai ta zama me sallah irin ku,ance wai tana Kaduna amma ni"I don't give a damme ko ma a ina take da me take yi fa.Hakane to idan ka gama ka mayar mata da kwanan.Yajuya yayi tafiyar shi... Sautu a kasuwar wauta jahilci. 14 Jumaada Awwal 1441 9 January 2020 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSICIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na goma sha uku. Rana ba ta k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya,ranar juma'ar d'aya ga watan Rabi'a Thani aka d'aura auran Salim da Sumayya,Miqdad da Zainab a ranar kuma ko wacce ta tare a gidan mijinta,sai dai mahaifin Kasham bai samu zuwa ba saboda zazzabin da yake yi. Sumayya sune zaune lafiya suna da fahimtar juna,suna ma juna uziri shi yasa suke da kwanciyar hankali,suna kuma fatan hakan yad'ore har k'arshen numfashin su. Yana karya hular k'uben dazai sa tashigo da sallama,ta kar6i hular tak'arasa karyawa tasa mishi. Yad'anyi gyaran murya"Ya dai Sumayya yau fa na ganki wata iri.Me ka gani? Shiru yayi yana mata kallan nazari "banga kome a fuskar kiba amma yana yinki ya nuna akwai wani abu,yadafa kafad'arta "kar kiji kome Sumayya ni mijin kine,ba ki da wanda za ki fad'ama damuwar ki sama dani. Yamata wani kallo"Sumayya mecece matsalar?Fad'a min in har akwai wannan amincin dake cikin zaman na mu. Tamayar da turaran data gama fesa mishi sannan tajuyo cikin d'an murmushi"Miji na nawa ni kad'ai ko?Yagirgiza kai"ai na fad'a miki Sumayya a yanzu bani da buk'atar sake aure,kuma in dai zaman na mu yad'ore a haka to ai ko kin isheni rayuwar duniya, yakalleta amma fa ba alk'awari na miki daga ke ba wata har abadan duniya ba.Tajijjiga kai"d'aya daga cikin abubuwan da suke k'aramin k'aunar ka a zuciya ta kenan fad'ar gaskiya kome d'acin ta. Sukayi murmushi. Tasake kallanshi cikin natsuwa"tun daren jiya nayi mafarkin Mama kuma har yanzu mafarkin ya tsaya min a rai sosai,dan haka nake neman alfarma kabarni in je in ganta,ka san Uncle ya hanani zuwa wai sai nayi aure idan miji na ya barni shikenan ban san dalilin shi na hakan ba.A yanzu na san kima da girman da uwa take dashi,lallai ta cancanci a mata kome dan a samu albarkar ta, rayuwa tayi kyau duk da rashin sallar da ba tayi, ina san ganinta kewar ta ta dameni,zan kuma yi k'ok'ari wajan ganin na shawo kanta mun dai-dai ta,wata kila tsawon shekarun da mukayi bamu sa juna a cikin idanu ba yasa idan taganni ta yafe min,ni dai ina ta addu'a ALLAH yasa sanyi a zuciyar ta,na san ba abinda yafi k'arfin Ubangijin mu.Yajijjiga kai"gaskiya ne Sumayya iyaye suna da girma da daraja a wajan Ya'yansu, a addinin mu na musulunci suna da mafificiyar daraja sama da kowa.To yaushe kike so mutafi? Bani da za6i,sa mana lokaci.Yad'auki agogon shi yana d'aurawa "Shikenan za muyi magana da Alhaji idan naje kasuwa.To nagode.Yayi murmushi kawai Tafiyar Dinatu Kaduna waja taransu na zumuntar mata a babban majami'ar su dake Sabon Tasha"Evangelical Church Winning All" (ECWA)na tsawon makonni biyu yabashi damar gyare-gyaran dayace zai yi, gidan yafito rasss har da sabon fenti ko'ina yanata kyalli.Ranar data dawo ta cika da mad'aukakin mamaki tana ka me da ha6a take tambayar shi"ni dai tun kafin in tafi Kaduna da ma na lura da wasu canje-canje saboda yawan kashe kud'in da kake yi,kai ko a ina ka samu mak'udan kud'ad'en da kayi wannan gyaran?Anya kuwa Baban Alhamdu ba ka daga cikin masu zuwa cikin gari suna fasa shagunan hausawa?Dama kwanakin nan abinda ake ta musu kenan. Yagalla mata harara"ai kema kin sani ko lokacin dana ke ganiyar k'uruciya banyi sata ba,bare yanzu da girmana da kome ALLAH yasauwake.To me kake siyarwa da bazan yi tunanin haka ba?Ba kome. Tazuba mishi idanu "gaskiyar magana bazan yadda dakai ba in dai ba fad'a min in da kasa mo kud'in nan kayi ba. Yamik'e"ai nima ba so nake yi ki yadda dani d'in ba. Tabishi da kallo har yafita. Da daddare har ya fara bacci ta tashe shi,fuska a yamutse yake kallan ta dan yanzu shima ya daina d'aukar raini tunda hatimin nasaran nan yana dashi"lafiya kin katsemin bacci kuma baki ce kome ba?"Baban Alhamdu please... kafad'a min in da kake samun kud'i,dan hankali na ya k'i kwanciya.Yasake d'aure fuska"Brother na Shedrak shi ya aiko min da cheque na mak'udan kud'ad'e,kuma ina so ki sani Kasham tabbas tana wajan shi,kuma tana sallah, bayan haka ma tayi auri wancan watan, na so zuwa ma to sai dai zazza6in dana yi yahana ni tafiya kuma suna nan zuwa, ina fata yanzu hankalin ki zai kwanta. Tadaki k'irji cikin ambaton Yesu alhamisu me ce to(Jesus Christ)tamik'e cikin tafasar zuciya"Kasham tana sallah bayan haka ma ta yi aure ni mahaifiyar ta ba tare da sani na ba?Tayi d'as da yan yatsunta ban ta6a sanin kai munafiki bane sai yau,wato ka tura Kasham taje tayi sallah dan adinga kawo maka kud'i ko?Haba no wonder baka wani nuna damuwar ka lokacin da muka neme ta muka rasa.Wallahi tirrr...da halin ka,kai munafikin addini ne tunda kana supporting masu sallah tacika gidan da hayagaga... Da abin ya ishe shi shima ya daka mata tsawa kin dameni fa,ki rufe ma mutane baki ke baki san dare bane?Tagirgiza kai, ai idan kaga na yi shiru to kafad'a min in da Shedrak yake a Kaduna gobe in buga sammako in d'auko yarinya ta dan bazan barma wasu tsinannun hausawa ba.Yayi shiru kamar ba dashi take magana ba,zuwan ca kuma ya d'ago ya kalleta"To tunda baza kiyi shiru ba, bari kiji kafin ki tafi Kaduna ni zan rigaki yin sammmakon tafiya,kuma na rantse miki da ALLAH tafiya ta bata dawowa bace,nima na bar gidan nan kenan har abadan duniya muje muci gaba da yin sallah sai in ga wanda zaki dinga wanke ma hannu a ka.Taja dogon tsaki "karka bari sai da safe yanzu ma kahad'a kayan ka dan ka tafi sai me?Mutuwa za a fasa ko hijabi? Tajuya garammm tabugo k'ofar,sai dai fa maimakon bacci yayi awon gaba da ita kamar yadda suka sa ba duk dare sai tane mishi tarasa sai kalaman mijin ta suka dinga dawo mata. Kusan mako d'aya kenan bataje kasuwa ba wai dan kar yatafi Kaduna bata sani ba,yayi dariya Dinatu kenan idan nayi niyyar tafiya Kaduna zaman ki acikin gidan nan bazai hanani tafiya ba...Dan ALLAH ba wannan nake san jiba,kace kawai ka fasa tafiya,kayi hak'uri da abinda na maka raina ne ya 6aci kayi hak'uri. Yakalleta ai dama kece za ki sani tafiya ba tare dana shirya hakan ba, amma idan muna zaune lafiya ai bazan yi tunanin tafiya wani waje ba tare dake ba"we're together for better for wost till death due part us. Yana waya tashigo D'akin-shak'atawar ta zauna a hannun kujerar daya ke zaune tana kallan shi, ganin wayar ta k'i k'arewa yasa tamik'e zuwa taga,tad'aga labulan tagar tana kallan mutane na kai kawo a cikin yamma cin.Bataji zuwan shi ba sai maganar shi taji cikin rad'a, tajuyo da sauri tana yar dariya"Kai Salim da girman ka da kome kake irin wannan furucin? Yagalla mata harara "Kaji yar rainin hankali ke kuma...sai ta sunkwui da kai tana murmushi.Toh shi kenan adai bar kaza cikin gashinta kawai.Ta girgiza kai"Uh uh gwamma kawai a yankata a dafata acinye ta kowa ma ya huta.Yamata wani kallo cikin d'an d'age gira,itama tarama irin kallan da manyan idanunta masu maik'o sai ko ya kyalkyale da dariya"Hun Sumayya me duniya...Za ko a yi yadda kika ce da kazar, tad'an motsa kafad'a, sukayi murmushi. Yakalleta cikin natsuwa"to ya jikin na ki? Abinda yadawo dani daga kasuwa kenan dan na kira wayarki ta ki shiga matsalar sadarwa"naji sauk'i sai dai bani da k'arfi kuma bakina ba d'and'ano.Yagayad'a kai"to Alhamdulillahi, k'arfin jikin sai a hankali za ki da wo dai-dai,ya6are vitamin c guda d'aya yasa mata a baki. Yakamo hannunta suka zauna a kujera "kuma na zo miki da wani albishir.Albishir?ta tambaye shi"eh albishir.Tayi murmushi fad'i albishir d'inka yanzun nan in wanke ka tasss...da ruwan tukwuici.Yakalleta da natsuwa yana murmushi"d'azu munyi magana da Alhaji akan tafiyar mu Zonkwa ya ce idan mun shirya shima a shirye yake musa rana, to nafad'a mishi jibi idan ALLAH yabamu a ran rai da lafiyar za mutafi,dan haka sai ki fara shiri yau,gobe da sassafe zan tafi kasuwa duk abinda kike so asiyo sai ki fara rubuta shi tun yanzu kin gane ko?Wani dad'i yamamayi zuciyar ta sai ta dad'a jinta garau ba sauran ciwo,ta k'ank'ame shi cikin murna"nagode mijina lallai ka cancanci tukwuici sai ta fara mishi wani irin salo na ta,da sauri ya k'waci kanshi yana dariya har hular shi tana fad'uwa"Ke wannan ne tukwuici?Ni na zaci wasu mak'udan kud'ad'e za ki sa min a asusun ajiya ta ta gidan kud'i?Tagirgiza kai"A ah wannan ai somin ta6i ne"tayi furucin da wani salo irin na shagwa6a. Yagayada kai"ah nima na aga alama to amma jama'a na jira na akasuwa amin afuwa sai na dawo anjima.Tam adawo lafiya suka d'aga hannu suna ma juna adabo🙋 Cikin nishadi suke tafiyar Alhaji Hafiz da Sumayya suna fad'a musu sunayan garuruwa da k'auyaukan da suke ta wucewa,sannu a hankali har suka shiga garin Zonkwa.Alhaji Hafiz yajuya yana kallan Maman Hasan"yanzu zamu shiga shalkwatar k'aramar hukumar Zongon-Kataf sai ku bud'e idanu ku fara kallo "tafiya mabud'in ilmi "Hafsa tace Zongon-Kataf d'in na gaba kenan?Eh Hafsa yana gaba ina gama idan zamu koma tacan zamu biya kuga garin sai mu bi ta Pambegua mu kuma gida. Jikin Sumayya yayi sanyi tunda matuk'in motar Miqdad yakusa shiga k'auyansu Madauci dan ta san halin Mamanta bata da mutunci "ALLAH kamin maganin abinda bazan iyaba...bani da kowa sai kai... Sumayya... A sama taji kiran Alhaji Hafiz"na'am Uncle me kace? Nace na ga an samu cigaba me yawan gaske,kinga wancan asibitin?Takalli asibitin"Eh Uncle.Da nanne wajan da muke buga k'wallon k'afa.Sukayi dariya, Zuhair yace dama Baba kayi wasan k'wallon k'afa?Eh Zuhair amma da ne.Yad'anyi tsallan murna"nima daga yau zan dage in koyi buga k'walan k'afa.Yakalleshi da kulawa "a ah Zuhair bana maka sha'awar k'wallan k'afa,na fiso kayi karatu sosai kazama"Cheif Judge"ko ka fasa zama alkali me adalcin ne? Yakyalkyale da dariya yana bud'e idanun shi"Wallahi ban bafasa ba.Yauwa Zuhair d'ina ALLAH yamaka albarka. A inuwar barankacin k'ofar gidan Miqdad ya tsaida motar,yabi gidan da kallo an gyara shi gwanin sha'awa,ba kamar zuwan da yayi watan nin baya ba,itama Sumayya abin ya mata dad'i tana rik'e da hannun matar Yaya Miqdad Zainab suka shiga gidan da sallama" Baban na ta kamar ko yaushe yana zaune shi kad'ai a tsakar gidan yayi tagumi da duka hannayen shi"labarin zuciya a tambayi fuska,ranshi a 6ace yake,yasa hannu ya share hawayan da ya zubo mishi sharrr...yana d'ago kai idanun su ya had'u yamik'e da sauri da sauri cikin mad'aukakin mamaki" Kasham...yanunata Kasham ke ce? A sanyaye ta amsa"na'am Baba... "Kasham kece nake gani haka? Halelujah suka rungume juna cikin murna"naji dad'in ganin ki Kasham... Hankalin ta yad'an kwanta ganin shima ya saki ranshi"Baba ai bamu kad'ai bane...bata gama rufe bakin taba sauran suka shigo.yasake ta ya rungume Miqdad yana shafa kanshi"My son sannnu ku da zuwa. Miqdad yanuna mishi Alhaji Hafiz"Here is your elder brother sai suka hau kallan kallo na wucewar wasu dak'ik'u aannan suka rungume juna suna ta kyalkyala dariya kamar wasu kananan yara Awunba wan Shedrak(Shedrak Dan'uwa na) Alhaji Hafiz ya janye jikin shi yana gabatar mishi da sauran,duk aga gaggaisa sai a k'arshe yasake nuna Salim wannan shine surukinmu mijjn Sumayya. Salim yak'arasa wajan shi cikin girmamawa dan ya gaishe shi,sai kawai ya rungumeshi cikin jin dad'i "Kaine karik'e mana yarinya da amana irin haka? Gaskiya naji dad'i nagode,ALLAH yama auran ku albarka,ALLAH yaba ku zuri'a masu amfani.Salim ya sunkwui da kai yana murmushi a ranshi yake amsawa da amin. Daga wani d'aki suka fara jin wani irin tari matsanan ci, bayan tarin yad'an lafa cikin galabaitacciyar murya aka fara magana"Baba dan ALLAH kazo kabani ruwa" duk suka bishi da kallo "Judith... Abinda zuciyar Sumayya ke fad'a mata kenan. Tasake kallan Baban ranshi a 6ace yakesai kawai tashige d'akin Dammm... zuciyar ta tayi wata rin bugawa da k'arfin gaske tayi mutuwar tsaye,numfashin ta yatafi wucin gadi na wasu yan dak'ik'u Judith ce a kwance marabanta da k'warangwal ya mushashshiyar fatar data rufe kasusuwan jikinta sai kuma numfashin da take yi. Da rawar murya ta furta Kasham...sai lokacin Sumayya tadawo hayyacin ta, tafara Istirja'i sai ta fashe da kuka ko ba a fad'a mata ba ta sani cutar k'anjamau ce, tunda dama ba abinda take yi sai yawan ta zubar... Judith ta tare ta"Kasham kar ki zubar da hawayen ki a banza ni ai tawa ta riga ta k'are, taimake ni kawai da ruwa yau ban san laifin dana ma Baba ba,gaba d'aya yaki shigowa d'akin nan.Takalleta wa yake jinyar ki? A hankali tace Baba.Tazuba mata idanu"Kin tafi yawan ta zubar d'inki kin manta da kowa a lokacin dakike cin duniyar ki da tsinki, ko gida bakya zuwa sai lokacin da kika bushi iska kizo zuwan asha ruwan tsuntsaye ki k'ara gaba,sai yanzu da kika ga mutuwa zaki dawo ki d'orama Baba abinda baiji ba bai gani ba?Tasake fashewa da kuka al'amurar rayuwar su ta taci barkatai da suke yi hankali kwance ya dawo mata, itama ba wayo da dabararta ne ya ku6ubtar da ita ba,ALLAH ne kawai yamata wannna gata da suturar da yanzu itama tana nan tana wannan kwamacalar. Kukan Sumayya daya tsanan ta ne yasa suka shiga d'akin dan gane ma idanun su abinda yake faruwa.Adai-dai lokacin kuma zawo ya 6alle ma Judit tana kwance kamar gawa sai k'arni da wari daya cika d'akin. Baban yabiyo su"dan ALLAH ku fito kubar wanna yar iskar yarinyar kar ku kwashi cuta,dan Sumaya tana jin k'arnin zuciyar ta ta tashi,tafara kelaya amai.Yakaisu D'akin- shak'atawar gidan kome atsare yake mayan kujeru da carpet ruwan k'asa sai kayan kallo a gefe da nu'urar sanyaya abubuwa(fridge) shima agefe duk sun zauna jungun-jungun saboda ganin Judith, kowa da kalar tunanin shi akan wani irin ciwo ne haka sannan me yasa ba a kaita asibiti ba? Me yasa Baban yake cemata yar iska a irin wannna hali na rai kwakwai mutu kwakwai? amma banda Sumayya da Alhaji Hafiz da suka riga suka san dawan garin. Baban me fara'a ne shi yadinga jan su da hira har dai suka saki jiki.Suna cin abincin da Hafsa ta girka musu yau an hutashshe da Kawunta.Dinatu tahigo gidan cikin kwala kiran sunan Kasham...Kasham... Kasham.. Sumayya ta cire hannunta a abincin tana Istirja'i kafin tashigo Sumayya ta mik'e, a k'ofar d'akin sukayi kaci6is,takalle ta sama da k'asa sai tayi murmushi"Hail Mary...tarungume ta.Sumayya ta rintse idanun ta tana jiran saukar dundu a gadan bayan ta amma bataji hakan ba, har suka saki juna tana dad'a k'are mata kallo, wani kyau da annuri na musamman tayi"Sannu Kasham tad'an dafa kafad'arta"na ji dad'in ganin ki suka shiga d'akin takalli Alhaji Hafiz"Sannu Shedrak shima ya canja mata gaba d'aya to yaushe raban data sa shi a idanun ta shekara da shekaru yayi kyau mijin ta kuma ya tsufa sai yaza kamar shine gaba da Shedrak.Suka shiga gaggaisawa.Ranar dai suna cikin farin ciki musamma Dinatu ganin duk wanda yazo musu sannu da zuwa sai ya yaba irin kyan da Kasham tayi kamar wacce take zaune a wata k'asa,kowa na so yaga na shi cikin wadata. "Lallai zaman Kaduna ya miki dad'i.Inji Lidiya.Sumayya tayi lallausan murmushi"kawai kishirya kayan ki mutafi.Tagalla mata harara"ai ko da kikayi wannan kyan banga abinda zai rud'eni in bar addinina ba.Itama ta galla mata harara"a ina kike da addinin?Kina da maraba da pagan ne? Kasham kar fa ki zageni.Sumayya tasake yin murmushi"come on Lidiya ni dake ai mun san gaskiya ko dan kawai d'aci gare ta?Ba fa yau na sanki ba,na sanki farin sani kamar yadda kika sanni farin sani,ranar Lahadi kina zuwa majami'a? Sai ta mik'e cikin borin kunya"bana zuwa kuna bazan je ba sai kiyi abinda za kiyi dani.Tafice fuuuu tana surutai rubbish girl...tabita da kallo haba yarinya ba abinda zanyi dake,za kuma ki dawo ne da k'afafunki. Sumayya tasa mu Maman a d'aki, ta tazauna akusa da ita sannan tafara rok'on ta "Mama dan ALLAH kiyi hak'uri kiya femin laifin dana yi, na san da ciwon haka azuciyar ki.Cikin fushi ta kauda kai"bazan yafe ba ki tashi ki bani waje.Haba Mama kiyi hak'uri kisa min albarka,ai har kwanan gobe ina sanki ina alfahari dake a matsayin mahaifiya,dan kinyi d'awainiya me yawa akaina tun ina cikin cikinki har kika haifeni, wallahi bani da abinda zan biya ki dashi.Tasake tuno girman hakkin Y'aya akan mahaifansu musamman uwa da addinin musulunci yazo dashi kaico! Wanda ba ya cikin musulunci wallahi yana cikin duhu me girma, inama-inama tana da wani iko!? Da ayau d'in nan kowa na ta sai ya zama musulmi. Takoma hannun ta Maman ta fizge da sauri"ke sakar min hannu mara jin magana kawai"kiyi hak'uri Mama na miki alk'awari bazan sake 6ata miki rai har kiji ciwon hakan ba Insha-ALLAH matuk'ar bai sa6a ma addinin musulunci ba.Tamata kallan uku ahu"Shari'a law" bata amsa ba tafara kuka haba Mama yanzu bazaki yafe min ba?Duk duniya bani da kamarki fa(In the whole wide world) Takalleta cikin fushi"kin san da haka amma nace kar kiyi sallah sai kika gudu wajan Shedrak har kina min k'arya wai an ma Tina Operation?Tagirgiza kai"gaskiya ban yadda ba kin nuna min Shedrak ya fini.Ba haka bane Mama. Tasake galla mata harara"to yaya ne? Tamarairai ce"Mama tafiya ta Kaduna wajan Uncle da duk abubuwan da suka biyo baya"It's a destiny (K'addara ce) suka kalli juna Sumayya tajijjiga kai "Ki yadda dani Mama wannan k'addara tace daban isa in kauce mata ba no matter how,kuma ai gwamma tawa tafiyar sau dubu tunda gashi na dawo a cikin hayyaci, koshin lafiya da kwanciyar hankali kuma kowa ya yaba,yayi sam barka to ai ko Alhamdulillah. To amma Mama Judith fa...? ran Maman yak'ara 6aci Sumayya tacigaba"Judith ta tafi amma bata dawo a cikin hayyaci, k'oshin lafiya da kwanciyar hankali ba, kuma kowa tirrr... da ALLAh wadarai yakeyi daganin ta, ba kuma wanda yakuma damuwa da ita sai ku.Ba aure tayi ba fornication shine sana'ar ta" which is forbiden"ba addinin daya yadda da hakan Islam ko Christianity sai dai san zuciya kawai,san zuciya kuwa 6acin ta yau ga Judit a ciki kuma Mama...ta tare ta dasauri ya isa haka Kasham jikinta yayi sanyi duk irin alwashin data d'auka ranar duk da sukayi ido hud'u da Kasham sai ta nemi shi tarasa,gaskiya Kasham tafad'a sai ta rungumeta"naya fe miki kome ALLAH ya albarkaci auran ki, wancan d'in shine Julaibib?Tagirgiza kai tana murmushi"ba shi bane.. taba ta labarin duk abinda yafaru da ita bayan barin ta gida. Tazuba mata idanu"to ni me zance miki Kasham? Sallah ne dai kin riga kin fara kuma ko na ce miki ki daina na san bazaki daina ba, kuma ma ban miki adalci ba,tunda duk a cikin Ya'yana dana haifa daga ke sai Rahab da Bitrus kune kawai masu jin magana, kune kuka maida hankali a karatu gashi nan kuma kune rayuwar ku tayi kyau,yanzu Bitrus shine personal manager a Bajju Community Bank(BCB) Rahab ta gama karatunta har ta fara aikin ta a asibiti, anjima kad'an za ta dawo gida tunda aikin rana wannan makon takeyi,ke kuma gashi kinyi aure hankalin ki akwance kuma kina cigaba da karatu.Rahab d'inma ta kusa yin aure.Sumayya tana ta godema Ubangiji daya sauk'ak'a kome fiye da zatan ta, tasaki jiki sunata hirar yaushe gamo suna kyalkyala dariya "Da da mahaifa sai ALLAH. A babban D'akin-shak'atawar gidan suka yi jam'in sallar su saboda k'auyan gaba d'aya ba masallaci tunda babu me sallah.Suna jam'in sallar Isha'i Rahab ta shigo da d'okin ganin Kasham dan tun a hanya tasamu labarin zuwan su, d'agowar su daga ruku'u Rahab ta tafi zata rungume ta Maman ta dakatar da ita"Ke Rahab karki ta6a ta baki ga sallah suke yiba?.Taja da baya da sauri"Oh Basakut"ta tuna idan suna sallah ko magana basa yi.Tajingina da bango tana kallansu"yadda suke tsayuwa,suyi ruku'u su d'ago, su tafi sujjada,su d'ago,su sake komawa sujjada suyi zaman tahiya har zuwa sallama kowa yafara karanta azkar d'in bayan kowace sallar farilla. Cikin murmushi tajuya wajan Rahab. Rahab takama ha6a cikin mad'aukakin mamaki tayi tsalle ta rungumeta tana ihun murna Jesust Christ Halelujah"Kasham kece kika zama wata big madam?What a suprise, ta daki kafad'arta"tell me the secret.Sumayya tashafa wajan"gaskiya fa akwai zafi"suka kyalkyale da dariya.Rahab ai kema kin canja kinyi kud'i fa"mint note"suna shiga asusun ajiyar ki duk k'arshen wata suka saki juna. Rahab tasake binta da kallo daga sama har k'asa gaskiya canjawar da nayi ba irin wacce kika yi bace"wonderful"tashafa kyakkyawar fuskar ta data ke ta hasken musulunci da Imani"wannan irin kumatu da kika fara ajiyewa ga fari, ni dai ko shafa man sa fari kika fara ne?(bleaching)Ba Sumayya ba hatta sauran sai da sukayi dariya dajin yadda Rahab taketa kod'a ta.Tazauna suka gaisa d'aya bayan d'aya take tamabayar Sumayya sunayan su.Salim yabisu da kallo ga dukkan alamu suna san junan su suna da kirki dama Sumayya tafad'a mishi Maman suce kawai sai a hankali to itama bata nuna kome ba banda farin ciki da ganinsu. Sumayya,Hafsa,Zainab da Rahab su suka gyarama Judith jiki da d'akin dayake ta k'arni kudaje sai budiri sukeyi,tana kwance cikin hawaye"wallahi da ace zan warke babu abinda zai hanani binku Kaduna in zama musulma.Hafsa ta amsa da sauri "ai ba dole sai a Kaduna ba, ko yanzu za ki iya k'ar6an musulunci.Wani dad'i yakama Sumayya.Ki yadda ki amince kina da rabo ne. Judith ko baki warke ba ALLAH zai kar6eki a haka Tagirgiza kai "uh uh ku kyaleni kawai dan bazan iya sallah ba tunda k'arfina ya riga ya k'are.Sumayya takalleta cikin natsuwa"ai addinin musulunci sauk'i gare shi Judit, ba dole sai a tsaye ko kina da k'arfi a gangar jiki za kiyi sallah ba matukar akwai lalura ko a yadda kike akwancen nan akwai yadda za kiyi sallah. Rahab tagalla musu harara sannnan taja dogon tsaki"addinin ta'addancin kike sha'awa Judith?Tamik'e a zuciye zata bar d'akin Sumayya tarik'o hannunta.Rai a 6ace tace "malama sakarmin hannu kishiga hankalin ki fa.Tagyad'a kai sannan tasake kallan ta ckin natsuwa"to kiyi hak'uri kizauna magana za muyi Takoma ta zauna fuska a yamutse.Shiru ya ratsa d'akin na wucewar wasu dak'ik'u. Tad'ago kai a zuciye"bana san wawanci fa, ke nake sauraro kin kuma yi shiru.To ai naga ranki a6ace yake shi yasa nayi shiru har sai kin d'an huce karr in k'ara miki zafi.Tamik'a mata lemon biyar a raye(five alive)d'an jik'a mak'oshin ki mana.Kasham I'm I your toy to play with?Tayi yar dariya "absolutely no kiyi hak'uri, amma ina so ki sani addinin musulunci ba addinin ta'addanci bane,addinin sauk'i da salama nw ga mabiyanshi.Tawatsa hannaye "ahab...ba cinya ba k'afar baya"ko d'azuma abinda wani musulmin ku Adam yagama fad'a min kenan awajan aiki.Nidai banga dalilin da zai sa inyi sallah ba,ina da yanci bazan koma inda bani da wani yanciba. Zainab ta tareta da sauri"ai ko addinin musulunci shine yabaki cikakken yanc me lasisi ma, musamman a matsayinki na 'ya mace,kina da yanci kamar yadda namiji yake da yanci,sai dai mu addinin mu, duk da yancin daya k'wato mana ya nuna mana namiji shine a sama da mace,idan banda addinin musulunci wa yake girmama 'ya mace ne? Rumawa da suke kiran mace"Devil" shaid'aniya? Wai mace shaid'aniyace ana neman tsari da ita kamar yadda ake neman tsari da shaid'an. Persia su kuma sun d'auki mace wulak'antacciya k'asa da duk wata halitta wulak'antacciya. Yahudawa su kuma sun d'auki mace kamar baiwa,da zatai tama namiji hidima, ita kuma ba ta da wani hakki akan namiji Zamanin jahiliyyar larabawa kuma idan aka haifi macen sai ma adinga zuwa maka jaje kai kuma kana 6uya,amata rik'on wulakanci,ko kuma tanaji tana gani da ranta da lafiyar ta a tona k'asa abinneta. Wanne daga cikin wad'annan suka ba mace yan cinta? To a duniyar musulunci da gidan musulunci ne kawai mace take yar ga ta,yar lele, sarauniya kome yi mata ake yi,kome kud'in ta k'wandala na ta na k'ashin kan ta sai ta ga dama za ta kashe.Duk masu yeekuwar yan cin mata indai ba wannan da addinin yabasu bane to wallahi k'arya ce,haushi suke ji, suna so ne ku fito ku sha wahala. Rahab ta ta6e baki"ni kalaman naki duk a matsayin tazo muji ta tawuce ta bayan kunne na d'aukesu. Sumayya tagirgiza kai"ai ko sun wuce tazo muji ta tawuce ta bayan kunne wallahi.A baya dana ke kamar ke ina fad'in haka, amma a yanzu dana san hak'ik'anin musulunci ai na san k'arya ce. Rahab kije kiyi bincike ki ga ne menene addinin musulunci na gaskiya da abinda ya k'unsa,ba abinda kike ganin gama-garin musulmai suke aikatawa ba, ba abinda kike karantawa a mujallu da jaridu ba,ba abinda d'ai-d'ai kun mutane suke fasara musuluncin ba,kije kiyi karatu da bincke a cikin littafan musulunci,ki saurari preaching da luctures d'in malamai,ba abinda wasu gur6atattun musulmai da rashin ilmi ko san zuciya yake musu jagoranci ba. Musulunci bai yadda da ta'addanci ba ko misqala zarratin,kuma duk wanda yake fakewa da musulunci to gaskiyar magana san zuciyar shi yabi... Rahab ta tari numfashin ta"za ki fad'i haka mana tunda kema kin zama musulma..."Eh zan fad'i haka dan na zama musulma na kuma san d'an abinda ALLAH yanufe ni da sani na daga ilmominshi. Rahab barin baki misali Christianity bai yadda da shan giya da karuwanci ba,hakane? Rahab tagyada kai.Takalleta cikin natsuwa"to yanzu abinda Alhamdu da Judith suke yi sai ace addinin Christianity ne yace suyi?Sai taki magana. Sumayya ta d'an motsa kafad'a kin gani ko? To kamar haka addinin musulunci yake.Ki yadda kawai Rahab ki kar6i musulunci wallahi sai kinfi jin dad'in rayuwar ki.Ta ta6e baki tana hararar ta. Sumayya tagyad'a kai tana murmushi "ALLAH kuwa gaskiya nake fad'a miki tabi hotunan d'akin da kallo kin gani,ko Jesus da Mary irin shigar musulunci suke yi a duk irin hotunan da zaki gani an za na su.Tajawo wata mujallar "Jehovah Witness"tana bud'e shafukan ciki Zainab da Hafsa kuzo kutaya ni gani a duk shafukan ciki kunga me"mini skirt da strap top kai ba d'ankwali? Suka kar6i mujallar suna dad'a gani,bayan sun gama dubawa Zainab tagirgiza kai"har shafin k'arshe ba bu,kowacce cikin mayalwacin kaya da lullu6i.Sumayya tace"to mazan fa"?Hafsa tace "suma suna cikin dogayan kaya ga gemu da k'asumba wasu ma har da rawani.Suka zuba ma Rahab idanu.Kingani ko?Wannnan shi yake nuna miki addinin gaskiya mukeyi"ai ko Annabi Isah Alaihissalam Jesus d'in musulmi ne. Judith cikin hawaye tace"wallahi na yadda daku.Zainab takalleta cikin natsuwa" to ki kar6i musulunci mana.Tagirgiza kai"I seek repent from God and I know he will forgive me.Hafsa takad'a kai cikin damuwa.Sumayya tadafa kafad'arta karki 6ata ranki"dan shiriya ba ta wajan kowa face mahaliccin mu,shi yake shiryar da wanda yaso a lokacin daya so.Tajijjiga kai "wannan gaskiya ne Yaya Sumayya.Haka suka kwanta zuciyoyin su ba dad'i kowacce da irin tunanin ta musamman ganin yadda Judit tazama "k'ashi da rai.Ubangiji kamana kyakkyawar k'arshe. A sanda hantsi yadubi ludayi tana zaune a inda tayi sallar walha kiran Salim yashigo tad'aga tana dariya"Humm mijina na wa nakai na.Yataya darawa "Sumayya ta tawa ni kad'ai fito waje muyi hira.Yazuba mata idanu har ta zauna a gefen shi,tabi wajan da kallo "wai kana nufin anan zamu zauna?Mushiga gida mana.A ah gwamma muyi zaman mu anan,mu shak'i natural air, ta tacciya me kamshi kinga turawa sun mana wayo sai su tafi "Bar beach"suje su shak'i iska tatacciya dan jikin d'an Adam yana buk'atar hakan,wajan da ba hayaniya kayi refreshing d'in gangar jiki, zuciyar ka da k'wak'walwarka. Nayi kewarki fa.Tabud'e idanun ta data rufesu tamishi wani kallan k'auna me cike da shauk'i"nima haka"sai sukayi dariya. Salim... Takira shi a hankali. Yakalleta... Tagyad'a kai"samun masoyi na gaskiya shine buk'atar kowani d'an Adam,masoyi me amana, masoyi me girmama abinda masoyin shi yake so matuk'ar ba sa6on ALLAH bane,masoyi me k'ok'ari da jikinshi,da kalaman shi, da aljihun shi, da lokacin shi wajan ganin masoyin shi ya samu abinda yake san samu"Godiya ta tabbata ga Ubangijin mu a kowani hali da yanayi. Wallahi ba ka da abokin tarayya a irin k'auna da soyayyar danake maka.Yayi Murmushin jin dad'i"Ina alfahari dake nagode Ubangijin mu daya mallaka min ke a matsayin mata"Sumayya ALLAH yamiki albarka ya lull6emin ke da rahamar shi.Kwanan su hud'u suka musu sallama suka koma Kaduna garin gwamna. Yau da gobe karyar ALLAH kome gudun ka sai ta ka mo ka. Tsufa labari...mutuwa k'arar kwana. 18 Jumaada Awwal 1441 13 January 2020 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na goma sha hud'u Zaman su lafiya cikin girmama juna. A yanzu fatansu bai wuce ganin Sumayya ta sauka lafiya ba.Tana kwance a doguwar kujera da yammacin tana ta nazarce-nazarcenta,tsohon cikin bai hana ta yin wasu abubuwan ba,taji muryar Mamanta.Wayyo!zama dak'yar ta shi da dabara kafin ma tayi yunk'urin ta shi ita ta shigo. "Oyoyo Mama sannu da zuwa... Da har na cire rai da zuwan ki. Taje ta d'auko ruwa da kanta tasha"Haba Kasham ya za ayi in k'i zuwa, bayan ni nace miki zan zo,kin san yanayin taran na mune yanzu haka ma sun tafi, ni a motar haya zan koma gida.Tabita da kallan tausayi"Sannu Kasham ALLAH yasauke ki lafiya, kwanaki ina ta mafarki wai kin haifi 'yan biyu. Tad'anyi murmushi kawai suka cigaba da hira. Wannan karan bazan bar Kaduna ba har sai kin kaini gidan Shedrak.Tagyad'a kai"to Mama"takira Salim a waya dan baya gari. "An ya Sumayya zan barki kifita kuwa? Ba likita ta ce banda yawan zirga-zirga ba?"Na sani kuma ban manta ba,dama Yaya Miqdad zan kira a waya yazo yad'auke mu.To idan baya kusa ko yana wani uzirin na shi baza ki takura mishi ba?"karka damu ai ta mu dashi bata 6aci,zan nemi alfarma na kuma san za a min.To shikenan ALLAH yatsare,kiyi zaman ki acan,nima Insha-ALLAH zuwa bayan Isha'i zan shigo sai inzo in d'auke ki.To nagode"ALLAH yak'ara tsare hanya yadawo mana da kai lafiya.Amin Sumayya nima nagode. Makonni biyu da tafiyar Maman ta haifi kyakkyawar 'yar ta sunyi murna sosai dan ba a samu tangard'an kome ba,ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar Salim d'in da tadad'e da rasuwa Ruqayya suna kiranta da Ummi.Gidan Alhaji Hafiz takoma Maman Hasan tana kula dasu yadda yakama ta,jegon ya kar6esu dan sunyi shar dasu saboda cimar abincin me amfani me gina jiki da k'ara kuzari ai shine jego "Abincin ka lafiyar ka... Cikin wani dare tana tsaka da bacci kiran Mama yashigo tad'aga cikin fargaban abinda kunnuwan ta za suji dan ta san tabbass ba lafiya ba.Kasham Judith ta mutu tafad'a tana kuka "lallai soyayyar d'a da mahaifa sai ALLAH"kalli irin wahalar data basu amma Maman take wannan kukan?Itama mutuwar tadake ta,duk da sun san k'arshen alewa k'asa.To amma ai ba yadda za suyi dan mutuwa dole ce ko mutum ya yadda ko bai yadda ba idan ajali yazo to fa silke baya tarewa, Kukan mutuwa kuma ba ya dawo da matacce. Babu addu'a tsakanin musulmi da kafiri dan haka sai tashiga rarrashinta da kalamai masu dad'i har tasa mu tayi shiru"nagode, ALLAH yamiki albarka bawanda yakwantar min da hankali sai ke"To za kuzo funeral service d'in ne?A ah Mama ba wanda zai zo kuyi abinku,amma Insha-ALLAH idan mukayi arba'in za muzo ai.Shikenan sai da safe takatse wayar.Tun daga nan har garin ALLAH j'arasa wayewa Sumayya bata kuma rintsawa ba,sai juye-juye take tayi da tunani barkatai daya cika k'wak'walwarta. Suna hirar su da Hafsa a D'akin-shak'atawa sukaji sallama tare da k'wank'wasa k'ofa.Hafsa tabud'e k'ofar tana amsa sallamar. Yana tsaye tad'anyi murmushi"au kaine tabashi hanya bismillah shigo "cikin ladabi yadurk'usa har k'asa yana gaishe da Sumayya.Tagirgiza kai" tana nuna mishi kujera"ta shi ka zauna meye na durk'usan? Bai zauna a kujeran ba sai yayi zaman shi a carpet d'in yana d'an murmushi"ai nan d'in ma yayi.Mamana bata nan ne?Hafsa tayi yar dariya "Aikuwa dai Maman Hasan yau tayi nisan kiwo tana can wajan tsoho me ran k'arfe Malam Muhammad Aminu. Alhassan d'aya daga cikin yaran da suke zama ma Salim a kasuwa ne, yaro ne me hankali da sanin ya kamata,tunda yaji sunan Maman Hassan shikenan yake ce mata Mamanshi, shi kuma Usainar shi ta rasu tun suna k'anana. Itama Maman Hassan tana yi dashi sosai indai yazo tana gida to sai ta san abinda tabashi kome k'ank'antar shi, tun yana jin nauyi baya kar6a har ya saba dan takance"Kai Alhassan anya wannan Mamana da kake kirana ba a fatar baki kawai ya tsaya ba? Uwa ta ta6a ba d'anta abu yaki kar6a? Tun daga nan yaba ta hak'uri idan tabashi sai yasa hannu biyu yakar6a yayi godiya. Ya ajiye ledar hannun shi a gaban Sumayya"Alhaji ne yace in kawo.Wai ya kira layinki ya k'i shiga,sai bayan la'asar zai shigo.Bakome Alhassan,nima ina ta kiran shi bata shiga akwai matsalar sadarwa yau"kace ina gaisuwa sai ya zo d'in"Yamik'"Zai ji"yad'an kalli Hafsa "idan Mamana ta dawo nima amik'a min sak'on gaisuwa zan dawo ranar Juma'a musamman dan in gaishe ta.Tagyad'a kai" tam za taji"sukayi sallama. Tana gama wanka suka tafi Zonkwa ita da Hafsa sun sauka lafiya kowa yayi murnan ganin su.Kwanan su biyar da tafiya da yammacin ranar sai kawai ganin Salim suka yi.Takalleshi cikin kulawa da mamaki"ba ranar Alhamis mukayi da kai za kazo ba?Yamayar da kanshi jikin kujerar"ranar alhamis ne amma na ka sa daurewa ne,amma yanzu ai hankali na ya d'an kwanta danazo na ganku"gobe kenan za ka koma? Yabud'e idanun shi daya fara rufewa yakalle ta da sauri"wai kina nufin tafiya zanyi in barku? Tagyad'a kai"haka nake nufi ga waya muna magana da juna.Yad'an harareta"kina wasa ne ko?Wani irin wasa kuma?Ai naga kwana goma kaba mu to yau munyi biyar ba saura biyar ba? "Sumayya... Yakirata...suka zubama juna idanu na wucewar wasu dak'ik'u yasauke numfashi yasa hannu yana yata6a kirjinshi dai-dai saitin zuciya "kina so na kuwa? Takalleshi baki a bud'e saboda mamakin furucin shi"haba Baban Ummi me yasa za kamin irin wannan tambayar?Yad'ora hannayan shi a saman tebur "saboda kince gobe zan tafi ma'ana ni kad'ai? Sumayya akwai ayyuka masu yawa agabana amma naturesu gefe duk da mahimman cinsu naza6i zuwa wajanki,sai dai kash...hak'ata baza ta tadda ruwa ba, dan na ga kina so ki watsamin k'asa a cikin idanu. Tad'an 6ata fuska ni dai gaskiya... Yatari numfashin ta"haba Sumayya ta tawa ni kad'ai yad'an d'age gira"bazan iya hakurin jure rashin ki bane,magana awaya kad'ai ni dai bata gamshe ni ba shi yasama kika ganni ganin idanunki yamata wani kallo"mhm me kika ce ne? Tasunkwui da kai"haba Sumayya yi magana mana,Salim mijiki ke kad'ai ne fa.Tad'an harareshi bayan kace ba alk'awari kad'auka ba,dan dai dole sai ka k'ara auren nan.Yagyad'a kai"gaskiya banyi wannan alk'awarin ba,kar baki yaci idanu su zo suna jin kunya.Tace"Uhhh madallah to yanzu kake so mutafi?A ah ai yamma ta yi kuma kinga Mama bata dawo daga kasuwa ba dole ai sai mun mata sallama, gobe da sassafe sai muwuce. Sumayya takoma makaranta dan hutun da aka basu ya k'are,karatu sosai sukeyi ba kama hannun yaro saboda wannan shekarar za su gama.Sumayya ba ta da wata gagarumar matsala a bangaran karatu duk abinda bata gane ba, to tana dawowa gida Salim zai warware mata shi,bata ta6a sanin me tarin ilmi bane sai bayan auransu data shiga wani d'an d'aki dayake yin nazari da bincike wallahi tasha mamakin irin tarin littafan addinin data gani.bai ta6a nuna mata ya san wani abu ba sai da zama yahad'asu. Salim jarumine me damuwa da damuwar iyalinshi. Suna hirarsu a D'akin-shak'atawa cikin nishad'i yajuyo kukan Ummi daga d'akin baccinsu ta tashi daga bacci kenan, yaje yad'auko ta,yabata ruwan zamzam d'in da suke bata tasha ya mik'a mata ita" ga ta ki bata abincin ta yunwa take ji.Tamarairaice Sumayya a wajan shayarwa ba ta da jarumta"kai ma ka san daga ta shinta a bacci baza tasha ba.Yagalla mata harara"ba yunwa take ji ba amma take ta k'ok'arin kai hannuna bakinta? Kar6eta mana.Tamika hannu ta kar6eta Tad'an 6ata fuska"ai ban san kana harara ba sai na ga idanun a k'asa.Yayi yar dariya"Hunn Sumayya ta ke dai bata abincin ta kawai ba na san neman magana. Sun gama karatu lafiya kuma sakomako yayi kyau Malam Muhammad Aminu shi yasamo mata gurbin karatu a Jami'ar Madina dan babban d'anshi a can yake da zama shi da iyalinshi Salim shi yanemi wannan alfarmar kuma aka mishi amma ba da san zuciya ba, a ah adadin makin da suke nema to na Sumayya ya kai...anata mata shirin tafiya inda zataje ta yi Masters a kan dai Islamic Studies.Kamar wasa tafara rashin lafiya yau ciwo gobe sauk'i,suka tafi asibiti aka mata gwaje-gwaje har aka gano abinda yake damunta ciwon siga(diabetes) amma sun d'ora ta akan magani da wasu sharud'd'ai da dole sai ta kiyayesu in dai tana san zaman lafiya,kuma sun bata kwanakin da zata sake komawa asibiti dan su tabbatar magungunan suna aikin da ake so ? Idan basa yi sai a canja wasu. Abokan karatunta kullum suna tafe, basa gajiya da zuwa gaisheta saboda halinta na karamci "masoya da mak'iya ba a guzurin su duk inda kaje halin ka zai ba kasu"abun hannu ta bai ta6a rufe mata idanu ba.Ranan Salim yakalleta "yaushe na baki kud'in da har za kice sun k'are Sumayya?Tad'an marairaice"Baban Ummi ni dai dan ALLAH kataimake ni kawai,akwai wacce mukama alk'awarin ba ta tallafi a k'ungiyarmu ni wallahi na manta,anjima za tazo k'ar6a ai da bazan kashe wadan can ba aciki zan bata" haba nijina duk abinda kaba wani shine na ka,wanda kaci kashi yake zama,wanda kake ajiyewa ba lallai kai d'in ne za kayi amfani dashi ba, wata kila sai dai magada su gada.Alheri dank'one da baya fad'uwa k'asa banza. Yak'irgo adadin data fad'a yabata"ina sanki Sumayya ta tawa ni kad'ai"Tasa hannu biyu takar6a nima haka mungode madallah Ubangiji yak'aro bud'i. Yad'an d'age gira yana mata wani kallo. Tagyad'a kai"Eh mana you're a good samaritan"Yad'an bata marin soyayya suka kyalkyale da dariya. Abu kamar wasa k'aramar magana ta zama babba,ciwo ya tasa Sumayya a gaba, kullum magani akeyi ciwo yana dad'a k'aruwa, watan ta d'aya cur tana kwance a gadan asibiti sannan tad'an dawo hayyacin ta,ita tamatsa aka sallame ta tare da k'arin wasu sharud'd'ai da zata kuma kiyayewa dan ta zauna lafiya. Yazuba mata idanu bacci take yi, tayi bak'i ta fita hayyacin ta,shima wallahi jinshi yake kamar mara lafiya.Yadad'a rungume Ummi da take bacci bayan ta gama rigimar a bata abincin ta kuma an yaye ta,ya had'a mata shayi amma tak'i sha,dak'yar dai ya rarrashe ta takoma bacci sai ajiyar zuciya take yi.Ya sauke gwauran numfashi "ALLAH yabaki lafiya Sumayya,ALLAH yasa kaffara ce". A hankali tabud'e idanun ta takai hannu tana d'an shafa kan Ummi sannan ta kalleshi "sannu Baban Ummi wai har yanzu baka fita ba?Yakad'a kai"Kayyah... Sumayya duk inda naje tunanin halin da na barki bazai barni inyi wani sukuni ba. Amma ai yau naga jikin na ki da sauk'i ko?To me za ta ce? Ita kad'ai tasan azabar ciwon da take ji,ba tasan yawan k'orafi tunda yana matuk'ar k'ok'ari da jikinshi,aljihunshi,kalamanshi da kuma lokacin shi, duk tsadar magana bai ta6a nuna gazawarshi wajan siyo mata shi ba, haka irin kalar abincin da akace shi zata dinga ci dayawa yasiyo mata ya ajiye. Tad'an yi yak'e dayafi kuka ciwo"Alhamdulillahi ala kulli halin". Ummi tasa hannu a baki tana tsotsa cikin dabara yazare hannu sannan ya kwantar da ita yana tambayar Sumayya abinda za taci da rana duk da a yanzu cin abincin na ta,ba wani na azo a gani bane,wasu lokutan ma sai yanuna 6acin rai sannan take d'an tsakura. Salim...tabishi da kallo yazauna a gefen gadan yana kallanta shima ya d'anji mamakin kiran sunan shi da tayi yanzu kai tsaye.Yarik'o hannayan ta yana kallan yadda tafin ciki ya d'ashe kamar mara jini amma ko d'azu da safe Doctor Zainab ta tabbatar mishi tana da jini dai-dai yadda ake so baiyi kad'an ba"Uhun me kike so kifad'a min ne?Sharrr...sharrr...wasu hawaye masu d'umi suke zubo mata"muryar ta tafara rawa"ni dai nagode ma Ubangijin mu daya min gata da samun ka a matsayin miji. Ina san ka Baban Ummi...tamishi wani irin kallo da yasa zuciyar shi bugawa da k'arfin gaske.Yakauda kai "Sumayya me za kici?Yasake tambayar ta.Kar ka damu zan sha shayi.Yasa hannu yana share mata hawayen"ki daina kuka ALLAH zai ba ki lafiya mukoma cin had'ad'd'an abincin ki me rai da motsi.Tabishi da kallo cikin kissima wani irin yanayi a zuciyarta.Hawayen suka sake zubo mata sharrr...idan tafad'a mishi yadda take ji a cikin jikinta tayar me da hankali za tayi zai rasa sukuni dan haka taja bakinta tayi shiru. Ranar da taje gidan Alhaji Hafiz suka wuni suna hira sai bayan isha'i yazo ya d'auke su.Sun kwanta lafiya lau cikin farin ciki sun dad'e suna hirar su kafin bacci yayi awan gaba dasu, amma cikin dare nishinta metsananin k'arfine yafarkar dashi daga bacci, yakunna wutar d'akin tana kwance cikin mawuyacin hali. Sumayya...!ko kallanshi ba tayiba, dan ba ta cikin hayyacin ta ne, idanunta sai rufewa da bud'ewa suke yi kamar wacce tasha kayan maye ta bugu sosai,bakin ta a bud'e ya bushe k'amas,ta rasa inda za ta tsoma ranta taji dad'i sai tafara wata irin shak'uwa,a gigice ya d'auko ruwa yana bata amma bata iya had'iya ba haka yake biyo gefen bakinta yana zubewa tana wata irin jijjiga... Sumayya...! Yafara girgiza ta Sumayya kalleni...!Ina hankalin ta baya jikinta tana gargara..."Laahaula wala quuwata illa billah "kome na ta ya saki a hankali tafara jan numfashi me tsawo sai ta sauke shi a hankali,sai takuma janshi sai yayi kamar ya tafi bazai dawo ba zuwa can sai ta sauke shi a hankali, haka tadingayi,yakwantar da ita yafara neman makullin motarshi amma tsabar rud'ewa wallahi sai yarasa a inda ya ajiyeshi,a fizge tafara kalmar shahada abinda yadad'a gigitashi kenan...zuwa can kuma kamar anyi ruwa an d'auke sai yaji d'ifff... Sumayya...!yakira sunanta da k'arfi yata6a kirjinta difff...Numfashi baya shiga da fita...Sumayya! Yad'aga hannun ta na dama yarafff...yafad'i a kan katifa.Abubuwa da yawa suka yamutsa k'wak'walwar shi bangaran tunani sai yaji ruguzowar wani abu a k'ahon zuciyar shi da k'arfin gaske Dammm...!!! Ta mutu...!Sumayya ta mutu...?!!! Sai yafara k'arya ta zuciyar shi dan idanun sun fara mishi gizo sun nuna mishi ga tanan tana numfashin ta"Sumayya au dama baki mutu ba? Yasake kallanta idanun ta a k'ak'k'afe ruwan ciki yak'ame k'amas suna kallan sama tayi tsawo da wani irin kyau na ban mamaki shi bai ta6a ganin wannan kyan ba ko lokacin da take ganiyar lafiyar ta take kwalliya da gayu...bai san awani yanayi yake ba har sai da aka kirashi a waya. Miqdad ne yake tambayar shi lafiya kuwa ban ganka a masallaci sallar asubahi ba,ko jikin Sumayyan ne?Asanyaye yace"Sumayya ta mutu.Cikin k'araji Miqdad ya sake tambayar shi"ta mutu? Yaushe?Wasu irin hawaye masu d'umi suka zubo mishi sharrr...sai kawai ya katse wayar yakifa kanshi a kusa da fuskar ta, ya rasa abinda yake mishi dad'i sai yafara Istirja'i...Miqdad shi yaje gida yad'auko su Alhaji Hafiz suka d'unguma gaba d'ayansu zuwa gidan hankali a tashe.Amma Salim yayi dauriya dan shi yamata wanka yashirya ta tsab aka mata sallah aka d'auketa a makara sai makwancinta na gaskiya kabari d'aki a cikin kasa"Uh uhun duniya rumfar kara...Wata rana zai fad'i.ALLAH yajikanki Sumayya yasa k'arshen wahalar kenan! Lokaci d'aya Salim yayi wata rin rama kamar wanda ya shekara yana jinya.A ranar Iyayanta suka zo.Maman tana kuka ta rungume Ummi tana sambatu "Holy Jesus why? Why? Me yasa Kasham za ta mutu yanzu? Me yasa za ka bari a kashe min yarinya...To wallahi bazan ta6a yafewa ba...me Kasham ta tare muku ne? Alhaji Hafiz ya k'araso wajan da sauri "haba Dinatu ya kike irin wannna kalaman ne? Mutane fa za suyi zatan kasheta akayi.To dama ba kasheta akayi ba? Kaima ai ka sani ko har ka manta tunda ba 'yar ka bace? Yakad'a kai cikin damuwa"ko na sani a yanzu dai na manta,mudai a addininmu na musulunci duk wanda yamutu to tabbaci hak'ik'a kwananshine kawai yak'are, amma ba mayune suka kashe shiba "ai sara da sassak'a basa hana gamji toho...a ah Shedrak wallahi Kasham dai kashe min ita akayi, ba ta zo sun ganta cikin rufin asiri ba?Takuma yin kururuwa cikin tafasar zuciya"Wai...Wayyoh...ALLAH!!! Kasham ta mutu...Judith ta mutu...oh Jesus Christ of Nazareth! Shedrak! Tazuba mishi jajayan idanun ta da suka rine da 6acin rai tadad'a rungume Ummi"bazan yafe ba. Yagyad'a kai"to naji amma dan ALLAH kiyi hak'uri da kukan nan muje ga abincin ku can kije ki k'arya.Bana ci, tasa gefen zaninta tana share hawaye da majina an kashe min Kasham an bar min grandchild cikin maraici... for God sake Shedrak Ummi guda nawa take da zata iya d'aukar wannan tashin hankalin? Yakalli Ummin"tabbass Ummi ba ta san kome ba,bata ma san me ake kira da mutuwa ba bare har yatashi hankalin ta,guda nawa take?Ko shekara uku batayi ba to amma ya za suyi da hukuncin ALLAH?Yadda duk yaso haka yake zartar da hukuncin shi"idan yaso yafitar da rayayye daga jikin matacce,idan yaso yafitar da matacce daga cikin rayayye"Qaadiran alaa manyasha'u.Dak'yar yasamu ta yi shiru da wannan sambatun da take tayi cikin kuka da d'aga murya. Makon su d'aya sukayi shirin komawa k'auyansu Madauci,Maman ta so k'warai abata Ummi ta tafi da ita amma Salim da Alhaji Hafiz suka bata hak'uri akan hakan bazai yiwuba kasancewar addini ba d'aya ba.Salim ma yasake ba ta hak'uri tare da alk'awarin kawo musu Ummi lokaci zuwa lokaci suna ganin juna. "Mutuwa ba ta zama masifa ga mumini,mutuwa hutuce ga wanda yadace da kyakkyawar makoma...ALLAH ba yana nufin 6atama bawa bane dan ya d'auki wani bangare najin dad'in shi Iyaye, mata, miji,Ya'ya da yan'uwa.. Alhaji Hafiz yadafa kafad'arshi "Salim...na san kai namiji jarumi ne,to na rok'eka da girman ALLAH kayi hak'uri kaga yadda kazama kuwa a yan kwana kin nan? Sumayya ta riga ta tafi rayuwarta ta doron duniya ta riga ta k'are,ba abinda take buk'ata awajan mu yanzu sama da addu'a...Addu'a itace abincin mumini...to mu yawaita aika mata dashi.Kaima ka natsuwa kacigaba da zuwa kasuwa ALLAH yabaka macen albarka.Yahad'iye wani abu me d'aci dak'yar yayi furucin" nagode Alhaji ALLAH yak'ara girma... Ummi tana gidan Alhaji Hafiz dan shi yanemi wannan alfarmar,amma Salim ya dai basu ita dan kawai sun cika mishi idanu ne,saboda yadda yake sintiri ba dare ba rana.Suna hira a D'akin-shak'atawa zuwan shi gidan a aranar karo na uku kenan.Alhaji Hafiz yakalleshi cikin natsuwa "Salim kayi aure mana.Yad'an yi murmushi kawai. Kayi shiru bakace kome ba?Alhaji ba auran ne bana so ba, tunani nakeyi anya zan samu mace kamar Sumayya?Wani irin zama mukayi me cike da amana, me cike da girmama juna,zan samu macen daza ta rik'e min Ummi da amana? Yagyad'a kai"me zai hana Salim?Kai da can abaya ka san za kuyi irin wannan zaman da Sumayya?To karka cire tsammani daga al'amarin Ubangiji mana.jikinshi yayi sanyi wannan gaskiya"nagode Alhaji ALLAH yak'ara girma. Ummi ta shigo da gudunta dan taji muryarshi"Abba na baka tafi ba?Uh ban tafi ba.Tayi dariya"to muje ka kaini Galaxy...in kira Yaya Zuhair mutafi tare?Yakalleta da kulawa "Ummi baza muje Galaxy ba, lokacin makaranta ya kusa,baza mu sake zuwaba sai an bada hutu kinji ko?Ta6ata fuska sai kawai tajuya tayi tafiyar ta, kwallah sun cika idanun ta.Suka bita da kallo har tafice. Me yasa kayi haka Salim?Dama taku da Ummi zata 6aci?Lallai yau na ganku a rana.Yad'an yi murmushi"ai ba duk abinda take so nake biye mata ba,wani lokacin ko akwai abin ina hanata saboda ta taso cikin sanin ba ko me da mutum yake so a rayuwa yake samu ba, ko da kuwa yana ganin abin baifi karfin shiba, kauna da soyayyar dana ke ma Ummi ba makauniya bace... Lokaci k'ank'ani Salim suka dai-daita da 'yar limamin unguwarsu aka daura musu aure,shima sai ya samu sauk'in zirga-zirga tsakanin gidanshi dana Alhaji Hafiz saboda Ummi.Mariya tana kula mishi da Ummi gwargwadan ikon ta, shima ya yaba da hakan sai suka samu kwanciyar hankali dan kowa yana yaba k'ok'arin dan'uwanshi,sai tak'ara bada himma tana mata rik'on tsakani da ALLAH kamar yadda zata rik'e Ya'yan cikinta"yaba kyauta tukwuici. Yana sanye da wandon chinos ruwan zinare sai riga me dogon hannu da ratsin ruwan zinari da bak'i,kwantaccen bak'in gashin kanshi yanata k'yallin hair fruits,k'amshin Arabian perfume d'inshi ya cika d'akin. Alk'asim da suke abokan wasa tawajan uba yashigo yana kallanshi "Lallai mutumin nan kana jin dad'in ka, kaga yadda kazama wani d'an matashin bak'in bature kuwa? Yabashi hannu suka yi musafaha.To ya karatun? Alhamdulillahi ai ya zo k'arshe tunda na gama rubuta Project d'ina.Ah lallai sai shirin tafiya bautar k'asa to Ubangiji yasa aje a sa a.Amin nagode. Yad'auki remote yana canja tasha baya san labaran CNN d'in nan,yan kanzagin Amurka (America)kanwa uwar gami ce,da yad'a propagandar k'arya akan addinin musulunci da musulmai.Yacire wayar shi da yasa a caji ta cika,suka fita zuwa gidan Hajiya sai dai gidan na ta da kwado sai sukayi zamansu a dakalin k'ofar gidan suna hira. Aminu yak'araso yana kallan Julaibib cikin raha yace"hey dude what's up?Yagalla mishi harara "Amincin ALAH zaka rok'amana ba wannan ba..yatare shi cikin dariya"kar ka wani harareni kai kayi shiga irin ta su ai dole in maka irin al'adarsu,shima yazauna sannan yamik'a musu hannu sukayi musafaha. Suna ta hira amma ya dai na jin abinda suka fad'a tunda ya hangota"indai yana gari to ranakun k'arshen mako irin haka yana ganinta.A natse take tafiya irin ta 'ya macen data san abinda take yi wato gefen hanya, yanata kallanta har tasha kwana.Wani murmushi yasu6uce mishi"Yarinyar can ya yaba da hankali da natsuwar ta.Aminu yayi yar dariya"Dan Sarai kenan biri yayi kama da mutum fa...na rantse maka ALLAH da zafi-zafi ake dukan k'arfe idan katsaya kallan ruwa...irin na Aisha to ko ba abinda zai hana kwad'o yamaka k'afa. Yajijjiga kai "tabbass zancen ka dutse... Washe gari lahadi yakafa ya tsare sha d'aya da rabi yabar Musaddiq a shago yaje dakalin wajan yazauna yana fatan ganinta,dai-dai lokacin aka ta shi daga Islamiyar su,wucewar wasu yan dak'ik'u sai ko gata ta zo zata wuce,yabita da kallo tana sanye da dogon hijab me hannu ruwan sararin samaniya kafad'arta rataye da bak'ar jaka. "Assalamu alaikum... Karo na biyu kenan yamata sallamar.Dafarko tayi tsammanin ba da ita yake yiba shi yasa tayi shiru, sai da yasake maimaitawa,a hankali tad'an juyo ta kalleshi sannan ta amsa.Da sauri yamik'e daga dakalin ganin ta juya taciga da tafiyarta... "am... Dan ALLAH...Jimana.Tatsaya ba tare data juyo ba tana jiran abinda zai fad'a.Yayi k'asa da murya "kinga yanzu sauran d'aliban za su firfito kuma kamar zamu takura musu idan muka tsaya anan, ko zamu d'an matsa daga can bakin Library? Batace kome ba suka k'arasa wajan yad'an jingina da k'arfen allan bayani(signboard)d'in yana kallanta ta sunkwui da kai. Ya Ilahi...sai yarasa abinda zai fad'a ta mishi arwa.Wucewar wasu dakk'ik'u tad'ago kai ta kalleshi cikin natsuwa dan shirun yayi yawa "Malam lafiya?Yad'an sosa kunne"Kiyi hak'uri da na san gidan da kike bazan tsaida ke a hanya ba,can d'in zan biyo ki dan kambamawar data dace dake kenan"Dan ALLAH ina ne gidan ku?Tagirgiza kai"ni ba yar garin nan bace karatu nake yi a Nursing School a cikin makaranta nake zama. Ayyah...to ya muka ji da shan geron Sunday?(garin kwaki/rogo)yadda yayi furucin cikin jimami yasa tad'anyi murmushi"har da kai? Yagyad'a kai"eh ai duk kanwar ja ce,nima d'alibi ne gobe war haka ai na tsufa a makaranta.Atakaice yamata bayanin kanshi itama haka da garin data fito. Adai-dai lokacin suka shawo kwana dawowar su daga makarantar allo kenan.Juyowar dazaiyi dan sunyi sallama da Bilkisu caraf idanun su yahad'u dana Sudaida"wani irin yanayi mara dad'i yatsirga ilahirin gangar jiki da zuciyar ta, tagalla mishi harara sannna takauda kai,cikin fushi tayi gaba su Khausar suka tsaya gaisawa suna d'an tsokanar shi"a k'ofar gidansu Nasmat tatsaya dan allanta yana hannun Nasmat d'inne kuma rubutu za tayi da wallahi bata tsaya ba"Khausar takalleta "to ke wai saurin meye haka kike yi?Sauri kuma ba wajan zuwa ba tunda gashi dole ta tsaya jiranmu.Tamusu wani malalacin kallo"shiru ma amsace.Nasmat tacigaba"anya waccan ba budurwar D'ansarai bace?Cikin tafasar zuciya ta fizge allanta"kya tambayi kaza hanyar rafi...?Fuuu tayi gaba tana k'unk'uni.Suka bita da kallan mamaki cikin tunanin abinda ya caza mata k'wak'walwa haka.Nasmat tad'an motsa kafad'a "wallahi can da yawarki yarinya. Tun daga ranar D'ansarai bai kuma yadda sun had'u da Bilkisu a kwanakin k'arshen mako ba. Ranar wata Juma'a yayi shigarshi ta fararan kaya yad'auki motarshi sai Matsirga anan yayi sallar Juma'a.Yana fitowa daga masallaci yadinga bin kwatancen Bilkisu kasancewar shi ba bak'o bane a garin sai ko gashi a k'ofar gidan.Wani dogon dattijo kyakkyawan farin Bafulani yahango, shi da wani da bai k'arasa shi a tsufa ba suna magana, sun dad'e suna maganganunsu sannan sukayi sallama. Julaibib yatare shi cikin sallama... Malam Lamid'o ya amsa sallamar yana mik'a ma Julaibib hannu dan suyi musafaha amma ya nok'e a haka ya gaishe shi cikin girmamawa.Malam Lamid'o sai ya yaba da natsuwarshi yayi murmushi"samari daga ina? Cikin ladabi ya amsa"Baba ni bak'on kune. Yagyad'a kai yana kara nazarinshi"af to,to madallah sannu da zuwa to bismillah shigo ciki,yabud'e mishi d'akin zauran suka shiga yanuna mishi wajan zama"zauna ina zuwa"yajuya zuwa cikin gidan sai gashi ya dawo da damammiyar fura da nono tasha zuma da ruwan sha "bismillah samari"to Baba nagode"yajuya yasake fita dan yabashi waje. wucewar dak'ik'u talatin yasake shigowa lokacin Julaibib yad'an sha fura dan baya wani jin yunwa. "Samari daga ina kake? Julaibib Abdullahi D'ansarai... Shine cikakken sunana daga Zonkwa nake. Yabashi labarin kome game da had'uwarsu da Bilkisu...Ita kanta ba ta san zanzo nan ba.Ni nazo wajan kane Baba indai bakama Bilkisu miji ba to idan ka amince zan turo maka manyana.Yamishi kallan nazari" yanzu misali idan na amince ita kuma Bilkisu bata amince dakai amatsayin miji ba fa?Yad'anyi jimmm...sannan yad'ago cikin natsuwa yakalleshi "bazanji dad'i ba amma bazan ji haushi ba ,dan na san kome na rayuwar bawa yana rubuce ne,yana kuma tafiya daki-dakine kamar yadda numfashi yake shiga da fita ajikin d'an Adam,zan mana addu'a ni da ita Ubangiji yahad'amu da abokan zama na arzik'i. Malam Lamid'o yabishi da kallo cikin zancen zuci"wannan d'an matashin tun yanzu yana da halin dattako to inaga ya dad'a girma,ilmi yadad'a cika k'wak'walwarshi? Julaibib idan har Bilkisu ta amince da kai to nima na amince dakai dan ni bazan ma Bilkisu auran dole ba sai wanda ta yadda tana so dan haka,kaje na yadda ka nemi soyayyar ta. Irinka nake ma Bilkisu sha'awa kasancewar ta me d'an ilmi duk da bai taka kara ya karya ba,to amma na san idan tazama matarka za ka ciyar da ita gaba,ta inda taka sa zaka taimaka mata har itama ta tsaya da kafafunta wata rana. Nayi karatun addini dana zamani dai-dai gwargwado,shi yasa na hana Jauro auran ta saboda ba abinda ya iya ba abinda yasani sai kiwon shanu,ni na san illar zama da jahili dan bazai amfanar da ita da kome ba,d'an abinda tasani d'in ma idan ba tsananin raboba a haka zai k'are.Katuro min manyanka za muyi magana gemu da gemu.Ubangiji yasa Bilkisu rabonka ce.Yasunkwui da kai yana murmushi labarin zuciya a tambayi fuska. Tana goge kayan sawanta abokiyar karatunta tazo mata da sak'on daya bata mamaki"Julaibib kikace yana nema na?Eh ai kibar wani mamaki dan ga kai ga k'afa ai ba tambayar me aka yanka, jeki wajan da ake ajiye abubuwan hawa za ki ganshi ganin idanunki. Dogon hijab me hannu ruwan k'asa tasa, yana hangota yafito daga cikin motar. "Bilkisu me gadon zinare... Tagaishe shi cikin natsuwa.Ya amsa yana murmushi"Yau dai gani ALLAH ya nufeni da zuwa a wannan yammacin,da zan bari sai gobe to amma dana tuna yaufa Juma'atu babbar rana ce sai kawai nace barin dai k'araso in k'ar6i goron juma'a ta kawai.Tad'anyi murmushi "goron juma'a kake so? Ai ko ka tara ka samu sai ta mik'a mishi lemon Schweppes d'in hannun ta.Yasa hannu biyu yakar6a "wannan kyautar goron juma'ar ta faranta min rai naji dad'i na kuma gode dashi zanci tuwon dawar Inna miyar kuka. "Bello yace a gaisheki" Takalleshi tabbass ya je Matsirga tunda basuyi maganar yan'uwan taba, Bello kuma shine autansu. Yaushe kaje?Duk suna nan lafiya? A lafiyarsu kalau,suma suna gaishe ki dakyau. Yad'auko bak'ar leda yaba ta "Malam ne yace in kawo miki.Tarungume ledar cikin farin ciki "nagode.Yad'an kalleta sannan yasanar da ita abinda yake tafe dashi.Tasunkwui da kai"bazance kome ba sai abinda Malam yace"fad'uwa ta zo dai-dai da zama kenan"Malam ai ya amince dani Bilkisu.A kunyace tace to ai shikenan.Sukayi sallama dan rana ta tafi za ta fad'i magriba na shirin kunno kai. Ana bikin duniya ake na k'iyama. Akwai lauje cikin nad'i... 20 Jumaada Awwal 1441 15 January 2020 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Masu k'orafin dan me Sumayya bata auri D'ansarai ba,da masu zaginmu wai labari ya d'auko dad'i sai kuma kawai a kashe Sumayya to duk mun ya fe muku bak'ak'en maganganunku, ALLAH ya yafe mana gaba d'aya.Sai dai ku sani shi Ubangijinmu baya ta6a barin wani dan wani, madamar wa'adin barin duniyar ka ya cika to fa ba tsimi ba dabara dole sai ka barta.Kuma ya kamata kufahimci wani abu,shi fa labarin nan idan kuna duba duk shafukan da suka gaba ta,ai muna rubuta"ALMOST TRUE STORY"ba k'irk'irar shi muka yiba,kaso casa'in na cikin shi ya farune,to sai ku gane ba dukkan abinda kake so ne kake samun shi a rayuwa ba,kuma dole ka kar6i rayuwar a yadda tazo maka,canja wani bangare na labarin to yana nufin canja labarin gaba d'ayan shine. ...GWAJIN DAFi💔Labarine me jigo kusan biyar d'unkule cikin d'aya,dan auna fahimtar makaranta. Your comments is beyond our expectation... Ibrahim's Daughters really appreciate. 1.Zainab Tijjani Ahmad (Ummu Bilqis) 2.Abdullahi Lawal Abdullahi (D'an Sarai). 3.Me Sunan Manya Khadija Kafanchan. Ya'yan Ibrahim suna godiya,dan kulawa yabawace. 1.Ummu Ammar. 2.Salima Uba D'an Zainab. 3.Maimunatu Ibrahim. 4.Bilkisu Muhammad (Darling) 5.Zaynerb bello 36 6.عيناء ابرهيم عبد المؤمن 7.Ummul Ameen. 8.Shamsiyya Sani 661 9.Ummee Umar Musa. 10.Samira Garba. 11.A'isha Rabi'u. 12.Zainab A.Sulaiman. 13.Hafsa A.Sulaiman. 14.Khadija Bashir(Ummu Hanan) 15.Ummu aimanal habashiyya(Maman Kinanata) 16.My Sau'ash( Asdilat💋 for real) 17.Nasiba Namadi 'Yar Zonkwa😀 18.Khadija A.Muh'd (Ummu A'isha) 19.+234 813 109 04..I don't really no your name,but you care. 20.A'isha Nura Sani (Dr.Maidiyam) 21.Saudat Ibrahim Yahya.Takwarata wannan sunayen na kifa sune rayuwata💋😀ni Asdilat KD...ina yinki fiye da shurin masaki. Shafi nagoma sha biyar. Soyayyarsu ta bazu a dangi,wasu sun yaba sunyi sam barka,yayin dawasu suka koma gefe suna k'unk'uni an rasa gane manufarsu. Suna hirarsu da Hajiya yake fad'a mata"Megado tace a gaishe ki,wannan k'arshen makon baza tazo Islamiyya ba suna jarabawa.Dan haka sai kisa ta a addu'a.Tagyad'a kai"Ubangiji yasa a fara a sa a, yasa asamu kuma abinda ake nema.Amin Hajiya. Sudaida tana share tsakar gidan tad'an ta6e baki"ni ana fad'in ban iya girki ba sai na iyayi,to su kuma Fulani kona iyayin ma ai basu iyaba,to su da abinda suka iyane banda tatsan nono da tallanshi gidaje da kasuwanni ne?Kai ALLAH yasauwake.Taja dogon tsakin dayasa Julaibib da Hajiya juyawa suna kallanta"lafiyar ki k'alau kuwa Sudaida? Ta'ajiye tsintsiyar bayan ta kwashe sharan ta zubar.Takauda kai daga kallan da suke mata"kalau d'ina Hajiya gida zan tafi... fuuu tawuce cikin fushi ko sallama bata musu ba.Hajiya tabita da kallo cikin nazari...sai kuma tayi yar dariya"dawalakin goro amiya. Julaibib yasauke numfashi "Hajiya kwana biyu yarinyar nan sai ta dinga cimin mad'aci,wallahi jiya data shigo wajan Inna tana kallona amma tad'auke kai ba ko gaisuwa kamar bata ganniba.Hajiya tace"yan wasan ne bata jin yi dakai,kaima ba sai ka share ta kaji da hayagagar...su Nasmat ba?Yayi d'an murmushi "Hajiyar mu ALLAH yaja nisan kwana me amfani. Amin Julaibibi amin. Malam Lamid'o dattijon arzikine yayi karatun addini dana zamani me zurfi a yanzu hakama likitan dabbobine(Veterinary Surgeon) abinda yatarfama garinsu nono kenan Ya'yanshi suke yin karatun boko me zurfi.Bilkisu itace 'yarshi ta biyar,ya barta ta cigaba da karatune kasancewar ta me san karatun,kuma tun data gama Secondary ba wani tsayayye sai Jauro shi kuma yace bazai ba Jauro auran taba,data ce ga abinda takeso ta karanta aikin jinya da unguwar zoma,yaji dad'i ya k'arfafeta dan karatun da za tayi zai amfani mata yan uwanta.Shi da matarshi sunyi tufka me kyau da k'wari wajan tarbiyyar Ya'yansu, sai Ubangiji yadubi niyyarsu sai suka ta so cikin tsoron ALLAH da ganin girmanshi ga kunya da sanin mutuncin mutane. Nurse Bilkisu Muhammad Lamid'o... Farace Kyakkyawar matashiyar budurwa,kyau irin na tsurar fulani da bashi da gauraye da kowace kabila dan gaba da bayanta, uwa da uba typical Fulani ne, kome na ta irin na mahaifin tane sai dai bambanci na ita macece shi kuma namiji ne,yanayin maganarta da muryar ta shine kawai irin na mahaifiyar ta. Bilkisu Megadon zinare...idan tayi murmushi ko dariya kai ko magana tayi sai kaga kamar da san a sanine...takeyi dan kawai tanuna yar lotsar(dimple)dake gefe da gefen fuskar ta da kuma yar siririyar wushiryar ta, abinda yak'ara mata kyau na musamman bak'in gashin kanta me yawa da tsantsi irin na asalin tsurar fulani,sai tattausan jajayan la66anta kamar ta turasu da jan jambaki... Bilkisu me kyauce ga sauk'in hali dan bata rud'u da kyawun halittar da Ubangiji yamata ko ilminta ba,kome na ta a natse take yinshi cikin mutunci da sanin kimar kai(a very meek damsel)Tun tana k'aramar Secondary ta sauke Alqur'ani me girma,har yanzu kuma tana karatun littafan addini. Sauri take yi tana kuma addu'a ALLAH yasa tasamu abin hawa dan gaba d'aya d'alibai sun gama watsewa a hanyar,Khausar ma ai ta tsufa a gida taimakon ta d'aya da Khausar ta tafi mata da jaka, da harda jakar da littafan ciki da ita kanta ruwan saman da yake shirin sauka zai k'are akansu. Takad'a kai cikin damuwa"gaskiya wanda duk baiji bari ba zaiji hoho,dama su Nasmat sun fad'a mata kar tasha maganin mura da tsakar ranan nan bacci zai sata,tamusu kunnan uwar shegu tawuce dispensary na makaranta takar6i maganin tasha aiko tun a masallaci suna sallar azahar bacci yafara kawo ma idanun ta ziyara,duk k'ok'arinta na korar baccin abin ya ci tura,ganin haka yasa tama Metron magana dan tasu da Sudaida ta zo d'aya sai ta bud'e mata Hostel"Clerkin's House"har kwanar Kakus d'inta, yar ajin suce amma sunan su d'aya da Hajiya dan haka suke kiranta da Kakus ta haye gadonta ta kwanta aiko bacci yayi awan gaba da ita har aka tashi bata sani ba,bata farka ba sai biyar saura na yammacin amma taji ta garau zazza6in da yake shirin rufe ta ya sauka,sallar la'asar tayi ta d'auki takalmanta tana sawa,lokacin Kakus ta takawo mata jik'ak'k'en k'anzon alkama da madara(corn flakes). Na ga kina sa takalmi badai tafiya za kiyi ba? Tagyad'a kai tana murmushi"yanzu kuwa"tazauna agefen ta"to amma ai kya tsaya kici abinci na san baza ki iya cin garau-garau d'in dining ba shi yasa na had'a miki wannan me d'an ruwa-ruwa tunda kina fama da mura,tamik'a mata kofin. Kakus...tasake dubu agogon dake d'aure a hannunta na dama.Uhun Jikalle me kike so kifad'a baza ki sha ba ko me?Tad'an marairaice"ALLAH Kakus...Sai kuma tayi shiru, tasa hannu biyu takar6a,cokali hud'u tasha ta'ajiye "nagode"taharareta"wannan dai dan kar ince baki sha bane kawai.Tadaki kafad'arta'ke yar rainin hankali, to ko akan me zan cika cikina da wanna bayan na san abinci na me rai da motsi yana jirana a gida.Ta tafa hannu cikin salati"Oh ni zamani! yanzu Jikalle ni kike dukar ma kafad'a saboda wuyanki ya isa yanka.Yadda tayi furucin kamar irin Kakar nan ta gaske yasa Sudaida ta kyalkyale da dariya,sai kuma tad'an marairaice itama"come on Kakus don't be upset"kema kin san bana miki haka,to yau d'aya dai ya kamata ki kar6i uzurina, Yaya Khausar ta dad'e da tafiya gida,kuma kinga hadari yana ta had'uwa sai cida akeyi bana so ruwa yatareni.Tadafa kafad'arta"na fahimce ki. Suka mik'e...muje in rakaki.Har gate d'in k'arshe nafita daga makarantar tarakata,dan ALLAH ni dai karki manta gobe ki taho min da soyayyiyar gyad'a,tad'an harareta"to anawa?A neman albarka tad'an zaro mata idanu ko bakya san albarkan manya?Sukayi dariya"so kai"sukayi sallama, sannan suka d'aga hannu suna ma juna adabo. Iska me k'arfi tafara ta sowa garin yahad'e yayi bak'i sai cida akeyi ba k'ak'k'autawa, abubuwan hawa suka dinga k'ara guda dan tsira daga dukan ruwan watan bakwai,tak'ara sauri akwai gidan yar ajinsu Zamburan agaba sai ta samu tafake,amma ina hak'anta bata tadda ruwa ba,kad'an-kad'an yayyafi yafara sauka tanad'e hannayanta a cikin hijab,sanyi yafara ratsata tarintse idanu"wayyo ALLAH na! Shikenan sabuwar mura zata dawo! Dagudu motar tazo tawuce ta,wacce yahango tacikin madubi yasa yayi ribas har yak'araso inda take,Caraf idanun su yahad'u yana bud'e motar,wani sanyin dad'i ya mamayeta. Yabud'e mata"to shigo mutafi mana kina ganin ruwan yana k'aruwa...tad'an harareshi sannan tashiga kamar wacce zata zauna a garwashin wuta. Yaja motar"me kika zauna yi a makaranta? Kamar ba da ita yake magana b.Ba tambayar nake yi ba? Dak'yar kamar me ciwon baki dan haushin shi takeji tace"baccine yad'aukeni a dormitry"bai sake magana ba yacigaba da tuk'inshi cikin natsuwa,sai dai ruwan daya cigaba da zuba kamar da bak'in k'warya yasa shi gangarawa gefen titi yatsaya har sai yad'an tsagaita. Yaya D'ansarai... Yad'an kalleta"na'am.Taturo baki gaba"nifa gaskiya in dai ba so kakeyi in k'arasa mutuwa ba to kashe wannan mukayyib d'in(Air Condition) ...kafin tagama rufe baki tafara atishawa,sai da tayi biyar ajere"Yar hamukallah "yace mata bayan ta godema ALLAH."Yahdi kumullahu wayuslih baalakum"tasa hannu tana jan hancin ta daya fara toshewa,k'wallah yacika idanun ta dan wallahi sanyi takeji bana wasa ba gashi kayan jikinta ajik'e suke.Sai da yamaida ita heater sannan tafara dawowa hayyacinta motar ta d'auki d'umi,ruwan yad'an tsaigaita motocin dasuka tsaya kowa yaja yacigaba da tafiya. Suna shiga gida Mama tace"Masha-ALLAH dama yanzu nake dad'a yima Adnan magana yad'auki mashin yabita makaranta yad'aukota"Yayi d'an murmushi"a hanya muka had'u dawowa ta daga Kaduna kenan.Adnan yafito daga d'akinshi yana mita"Mama banda kece da kanki kin cika min idanu kin shak'emin wuya da wallahi ba inda zani ruwa bai gama d'aukewa ba. Tagyad'a kai"to kayi zaman ka mana.Yak'arasa kulle k'ofar tashi"a haba dai Mama ai wata fuskar tafi gaban mari har abadan duniya.Yana shiga D'akin-shak'atawar yagansu...yauwa yayi yar dariya"kai madallah da autan Inna.Yamik'a mishi hannu sukayi musafaha,yajefama Sudaida mukullin"kai min d'aki". Khausar tashigo da lemu ta'ajiye agaban shi bismillah fa.Yagirgiza kai"bazan shaba,kirasa abinda za ki kawomin sai lemu me sanyi bayan yanzu aka gama tsuuga ruwan sama har da k'ank'ara?Yamik'e dai-dai da shigowar Mama."Mama na wuce.A ah ka tsaya yanzu nasa Sudaida takawo maka kayan bud'a baki.Yad'an shafa kai"Nagode Mama amma kiyi hak'uri sauri nake yi dan gidan Hajiya zani kafin in wuce gida" To ai ba kome musha ruwa lafiya.Amin Mama. Hey autan Inna... Zai shiga mota yaji kiranta yajuya yana kallanta ta canja kayan jikinta da riga da wando kirar Pakistan ruwan k'asa da yarfin k'anana filawoyi ruwan hoda me haske,tad'ora farar rigar sanyi tasak'a da farar hula me harafin M.Gashi inji Mama.Bai kar6i ledar ba yace me wannan harafin M d'in yake nufi?Takai hannu tashafa harafin"Masoyi na Sinan ko da wani masoyi ne bayan shi?Yamata wannan rikitaccen kallan nashi takauda kai "gashi ni sauri nake yi. Yashige mota ya zauna"ki kaimin gida yayi tafiyar shi.Tabi danjojin motar da kallo har ta 6ace ma ganin ta.Takalli ledar taja dogon tsaki"kawai dan kabani wahala,shi dai wannan halin na shi ALLAH yasauwak'e mishi...tashige gida tana k'unk'uni. A safiyar asabar suna hirarsu da Inna yana shan shayin na'a-na'a da ya'yan algarib tashigo da sallama, tagaishe da Inna sannan tazauna a kusa da ita tana fad'a mata sak'on Hajiya. Yamaida hankalin shi ga sauraran wak'ar wani balarabe yana wake Habibti d'in shi da irin soyayyar daya ke mata wai"ya kamu da yunwar son ta,kuma ita kad'ai take da irin nau'in abincin da za ta bashi idan yaci sai yadawo hayyacin shi,dan yanzu shi ya zama kamar gawane da rai"yad'auki remote yad'an rage k'ara yana cigaba da sauraran tsadaddun kalmomin da yaketa bayyana irin k'aunar shi gareta me sanya zuciya bugawa a cikin shauk'in so,har baitin k'arshe sannan ya canja tasha. Kiran daya shigo wayar shi yasa yamik'e yafita,Sudaida tabishi da kallo sai kuma tamik'e itama dan makarantar allo za ta wuce. Yana tsaye a k'ofar gida yana wayar cikin sakin fuska,yayi k'asa da murya yana gyad'a kai"na sani Megado amma na manta ne,ALLAH yamiki albarka da wannan tunatarwan.Yayi jimmm...yana sauraro"to shikenan karki damu kinji ko?...yauwa to nagode sai na shigo. Tawuce kamar bata ganshi ba. "Am Sudaida... Takalleshi fuska a had'e.Yayi yar dariyar data bata mamaki dan ba kasafai yake hakan ba.Yauma kin shigo gidan nan kin kuma ganni ganin idanun ki amma baki gaisheni ba,wai in tambayeki mana? Kallanshi tayi batace kome ba "Sudaida... wannan cin mad'acin da kike min bana jin dad'in shi kona miki wani laifi ne?Tad'an turo baki gaba sannan ta kauda kai"ni ba kome.Anya zan yadda dake kuwa?Takalli siririn agogon dake d'aure a hannunta sai kawai tajuya "gwamma da kai auran ka da gata kar inje insha dukan makara.Ki tsaya muyi sallama dan baza ki dawo makaranta ki same niba.Jikinta yayi sanyi amma bata tsaya ba tacigaba da tafiya"To ALLAH yakiyaye hanya ai zamuyi waya.Ki tsaya ki kar6i"tasa gudu nifa bana so.Yabita da kallo yana wata kissima a zuci. Jikokin Hajiya sun cika mata gida sunata sha'anin gabansu.Sudaida takallesu"kun san ALLAH cikin makaranta zan koma(hostel)na gaji da trekking sai randa aka ga dama za a zo a d'aukemu.Nasmat takama ha6a"to makarantar allon kiyi yaya da ita? Idan an ba da hutu na dawo gida sai in d'ora daga in da natsaya.Hajiya tasa musu baki"yanzu ke saboda makarantar boko za ki bar makarantar Mahammadiyya? Bayan shine a hakku akanki?Taturo baki"ai ba cewa nayi na daina ba,kuma ai nafad'a ma Baba ya kuma amince.Hajiya tamata dakuwa"to ni ban amince ba zai kuma zo yasameni bokon banza bokon wofi, bokoko a wuta. Nasmat ta kyalkyake da dariya"Ke Hajiya bokon kike ma wannan zagin kamar bakiyi ba?eh na zaga,dan kayi karatun boko indai ba karatun Muhammadiyy ai shirme kayi...ko ba ga sunan ba marasa addinin k'wararrune a fagage mabambanta na cigaban rayuwa amma sai kika mutum wai yasa abinda zai bautama sai saniya ko rana ko kwad'o...wannan ba 6atan basira bace da rashin sanin tauhidi?Ai ba abinda zai baku rayuwa me inganci sama da Alqur'ani da hadisan Manzon ALLAH dan ya tattara kome shak'undum kenan. Washe gari kuwa data je gaishe da Baba yake fad'a mata komawarta cikin makaranta an soke shi, Hajiya tazo da magana abar dubawa,yamik'a mata babban envelop foam ne guda biyar a ciki,ki kaima Nasmat na ta gida ko wacce tacike ranar Juma'a zaku fara zuwa makaranta,tasa hannu biyu takar6a"to Baba ta tashi tafita. "HAYATUDDEEN ISLAMIYYA SAMARUN-KATAF" yanzu har Samaru zamu dinga zuwa?Wallahi duk Hajiya ce da wannan aikin saboda kawai nace zan koma cikin makaranta shine har ranakun k'arshen makon ma bazata barmu mud'an sarara ba?Taja tsaki tana k'unk'uni,tad'auki biro tana ciccike inda ake so aciken. Maganar Julaibib da Bilkisu ta kan-kama sun kai kome da a ke kaiwa an kuma tsayar da lokacin biki watanni uku masu zuwa dai-dai da gama karatun ta. Julaibib ya tafi bautar k'asa,jahar Bauchi aka turashi angama basu horan sati biyu a sansaninsu(camp)yakoma inda zaiyi service d'inshi a k'aramar hukumar Azare. Sai da yayi wata d'aya sannan ya dira a Zonkwa dawani yammacin laraba rana ta tafi zata fad'i magriba na shirin kunno kai,yatsaya yayi sallar magriba sannan yatafi gida.Inna tayi murnar ganinshi dan bazata ya mata bai fad'a mata ko awaya ba.Baije ko ina ba sunata hirarasu ta yaushe gamo yana cin abinci ita kuma tanata kalan hotunan dasuka d'auka lokacin da a ke basu horo(training)tad'aga wani hoto tana murmushi ashe kunsha wahala?Yagyada kai"Eh Inna akwai wahala dan sojojine suka bamu horon cikin dare zasu kafa su tsare kowa sai yafito su fara bamu horo tayi yar dariya"lallai kun zama k'ananan sojoji.Amma ni ban wani sha wahala ba. Tagyada kai"ai baza kashaba tunda ka saba motsa jiki da manyan k'arafa yanzu har mata sai sunyi wannan?Eh har su sai sunyi masu tsohon ciki ne kawai naga an d'aga musu k'afa.Taja tsaki wannan tsarinne kawai bai min ba.Yad'anyi murmushi"To ya zamuyi Inna tsarin ne yazo da haka amma Insha-ALLAH bama cire rai da wata rana za a samu manya a harkar masu addini da zasu zamantar da abin dai-dai da shari'ar musulunci a raba mata musulmai da irin wannan shigar a bainan-nasi.Inna tad'aga hannu "Allahumma amin Julaibib. K'arfe shida na safiya sukayi kaci6is akwanar gidansu,dawowar shi kenan daga masallaci sallar asubahi,k'afafunta sanye cikin takalmi sneaker fari igiyoyin d'aurewa ruwan bula,wando ruwan bulu,farar riga sai hijab iya gwiwa ruwan bula sun sha guga tana goye da bakar jaka da Maths-set a hannunta.Tad'an bud'e idanu cikin mamakin ganin shi"Kai Yaya D'ansarai saukar yaushe? Yabita da kallo duk da garin bai gama wayewa ko ina yayi haske ba amma dai tayi kyau"Jiya gab da magriba.Excursion za kuje? Tasake kallan farin agogon dake d'aure a hannunta na dama"ba wani excursion Mr Goje malamin turanci(English)ne yabamu jinga (Assignment) kuma to be submitted before seven O'clock"to shine kike wannan saurin kamar za ki tashi sama?Tagyad'a kai"eh mana wallahi ji nake kamar inyi tsuntsuwa,wai dan ma ba acikin makaranta muke ba shine yad'aga mana k'afa,su yan cikin hostel ai k'arfe shida yabasu,duk wacce tawuce shida koda da dak'ik'a d'aya ne bazai k'ar6a ba,shikenan kuma fa a matsayn C.A test d'in mune,kuma nayita rok'on Yaya Adnan yakaini yace ba abinda zai fitar dashi awannan sanyin,ai dai ALLAH yajik'an Yaya Aminu ba dan yamutu ba dayana gida na san zai kai ni.Tayi gaba da sauri. A bayan ta taji horn yabud'e mata kofa"ke Sudaida zo ki shiga mutafi.Yad'an kalleta bayan sun hau titi"lallai baku raina Mr Goje ba.Yaya Julaibib wargi waje yake samu,shi wannnan Malamin mugune na gasken-gaske gashi kuma yanzu shine Labour Master,ya yanka ma mutum k'atan fili iya ganinka yace sai ka nome shi wallahi k'aramin abu ne a wajan shi. Hankalin Sudaida bai kwanta ba har sai da taganta a Staff-Room agaban tebur d'inshi ta'ajiye littafin ta kuma sa hannu,tafito tana sauke numfaahi"wai ALLAH na! nayadda k'wallan mangwaro na huta da kud'a.Takoma wajan Julaibib yanata kallanta ta gilashin motar yana kissima wani abu a zuci,tad'auki jakarta. Yad'ora hannun damar shi a saman sitiyarin motar"kin ko karya?A ah.Yakalli agogon motar ai da sauran lokaci kafin kuyi assebmbly ko muje Staff-Quater gidan abokina Aminu Idris ki karya a can?Tagoya jakar"barshi kawai Yaya Julaibib,ai Yaya Khausar zata kawomin.Sukayi sallama,yad'an lek'o da kai "kuyi hak'uri yau akwai inda zani dana dawo na d'auke ku"tad'aga hannu tana mishi adabo ba matsala nagode,tabi motar da kallo har yafita daga gate d'in farko sannan tajuya zuwa ajinsu tana murmushi. Kwanci ta tashi asarar me rai,biki saura wata d'aya,awannan lokacin Julaibib baya samun zama saboda zirga-zirga tsakanin Azare da Zonkwa,Yadad'a gyara bangaranshi dan anan zasu zauna tunda bai gama ginin shiba.Dasafe yaje gaishe da Kawunshi sunata hira musamman abinda yashafi kasuwancinsu,sai da zai tafi yamik'a mishi wasu mukallai na gidan kane,na baka d'aya daga cikin gidaje na na Unguwar-Rama daura da masallacin Yarbawa hakak malak. Julaibib yad'ago kai bayan ya duba takardar shaidar mallakar gidan sunan shinei ajiki"Kawu nagode ALLAH yasa da mafificin sakamakon shi, ALLAH yak'ara girma.Amin.wannan ai ba kome bane. Yad'auki Musaddiq sukaje suka ga gida,sabone dal sai k'ura dayayi tunda bakowa yasa yara suka wanke lungu da sak'o na gidan.Kafin yakoma Azare sun sa kome da ake buk'ata suka kulle sau ranar daza a kawo amarya. Yajingina da bishiyar mangwaran k'ofar gidan yana kur6an madarar shanun tatsar lokacin,hirarsu sukeyi cikin nishad'i irin ta masoyan juna.Bilkisu har naji kin fara k'amshin amarci fa.Tad'anyi murmushi.Yayi tsai da idanun shi yana kallanta"Megado baki ce kome ba? Takauda kai"Kazo ka tafi bana so kayi dare a hanya daga nan zuwa Azare tafiyace me tsayin gaske"Megadon bana san tafiya yau "Takalleshi cikin kulawa"saboda me?Yanunata da yatsa. Tad'anyi luuu da idanunta kamar zata rufesu sai kuma ta sunkwui da kai"Julaibib ai kai nawane,ni d'in nan ta kace Insha-ALLAH,amma bazan so ace nice silar ta6ar6arewar al'amuranka masu mahimmanci ba,bautama k'asa a matsayin ka na d'an bautar k'asar dole ne,kome kuma za kayi to kayishi yadda ake buk'ata,kazama me amana; tafiyarka ai ba itace rabuwar muba,koda munyi nesa da juna to amma ai zukatanmu suna tare,kuma ga waya muna gaisawa,muna chatting, har video call duk munayi,tad'ago cikin natsuwa da kulawa tad'an kalleshi"duk basu wadatar ba D'ansarai? Yanad'e hannayan shi a k'irji yana murmushi "sun wadatar Megado,ke macen alheri ce da bata taya 6era 6ari.Yamik'a mata kofin madarar yashiga mota yazauna yana d'aura belt "ALLAH yamiki albarka Bilkisu "tarufe mishi murfin"Amin D'ansarai nagode,sukayi sallama. Tabi bayan motar da kallo a hankali yake tuk'in har ya6acema ganinta.Tajuya zuwa cikin gida tana mishi addu'ar sauka lafiya. Inna tabita da kallo"har ya tafi?Sai lokacin tasan Inna tana tsakar gida,ta zauna a gefan tabarmar tana d'an murmushi,kumatun ta suka lotsa ciki"a kunyace tace ya tafi Inna"sai kuma tamik'e da sauri ta shige d'aki. Tana shan rake tana 'yan wak'ok'inta cikin nishad'i,Khausar kuma tana karanta wani littafi"The secret of occultics powers"su Nasmat suka shigo suna hayaniyarsu,A'isha tace ya naganku haka?Khausar takalle su "to da ya kike so ki ganmu? Tazauna a gefan gadon"banga kun shirya ba,za muje ganin d'akin amaryane. Khausar ta ajiye littafin"har kin tunamin ance da mahaukaci baya duka.Tabud'e wadrobe tad'auko hijab sannan takalli Sudaida"to mayyar rake badai za kice jiranki za muyi har sai kin gama shaba? Tamusu kallan uku ahu"kuyi tafiyarku dan ni bana zuwa gayyar sod'i.Suka bita da kallo cikin mad'aukakin mamaki"gayyar sod'i fa kikace? Zuwa gidan Yaya Julaibib d'in?Tayi kamar bataji suba...zuwa can bayan ta shaki iska ta baki ta hanci tafesar tana wani tsuke baki"Eh shi d'in fa wani abu ne?Ni dai wallahi banga abinda zanje gani wanda ban san shiba,ban ta6a ganin shi ba, taja dogon tsaki"gado ne fa da sauran tarkace, tad'ora hannun damar ta a katakon gadan su, wannan ai gadone ko?To gashi na gani akaima nake bacci,sauran tarkacenma muna dasu a D'akin-shak'atawa da D'akin-girki,kuma bama amaryace za tazo da suba,ta kuma jan dogon tsaki cikin tafasar zuciya"kai ALLAH yasauwak'e ma Fulani,wai ace kome mijine zaiyi,ga uban sadaki da suka yanke mai,dubu hamsin sai kace siyar da ita za suyi"ai dai k'arancin sadaki yawan albarkar aure wallahi. Khausar ta tareta da sauri"ke dakata haka malama ai a addinance dama mijine yakeyin kome na d'aki yakuma biya sadaki,dan hakkin akanshi yake ba akan iyayan taba,mu hausawa mune muka fifita al'ada sama da addini a wannan bangaran,kema ai kin sani sarai ban san abinda yasaki wannan furucin ba. A'isha ma takalleta"lallai ma yarinyar nan yanzu idan ma siyar da itan za suyi sai su siyar da ita a kud'i me mugun rangwame haka? Dan ALLAH nawa ne 50K? Kai Sudaida me yake damun kine naga alama bakya san Nurse Bilkisu Muhammad Lamid'o... Ni kuma wallahi tana burgeni saboda sauk'in halinta,wallahi sam bata d'auki duniya kayan gabas me k'amshin turaran d'an goma ba, haka fa ranan nan da muka had'u da ita a hanyar Islamiyyar su itafa tafara gaishemu amma kikayi banza da ita,bakyau irin wannan halin ko Yaya D'ansarai da baya san kula mutane amma idan kika mishi magana zai kulaki ko sama-sama ne. Nasmat tana ta nazarin kalaman Sudaida tayi yar dariya tana tafi tasake kallan Sudaida"kina kishi ne?Takusa k'warewa da raken da take sha Dammm... zuciyar ta tabuga tamata wani kallo"kishi kamar yaya,me zai sani yin haka?So...Nasmat ta bata amsa.Duk sai suka zubama Sudaida idanu"biri fa yaso yayi kama da mutum. Numfashinta yad'auke na wucin gadi... tamik'e cikin fushi tana kallan Nasmat "so fa kika ce?Tagyada kai"eh kwarai kuwa so.Sai tafara hayagaga..."eh so ne sai me?Suka kyalkyale da dariya ganin yadda take masifa"eh ina san nashi amma ba irin soyayyar da kike tunani bane, soyayyace irin ta yan uwan taka, karki manta ina da masoyi na da makaranta yake jira in gama sai in koma k'ark'ashin shi ta inuwar aure. Nasmat ta daki kafad'arta tana dariya "ahaf ba mage ba miyauuu...Takalli su A'isha"kuzo mutafi kunji tunda baza tajeba.Tabisu da kallo har suka gama fita a d'akin.Tad'auki hijab tasa gwamma kawai tabisu,sai wani irin abu mara dad'i ya tsirga ilahirin jiki da zuciyar ta,kawai sai ta koma ta kwanta,tad'ora tafin hannun damar ta a saman goshin ta dayake barazanar yin ciwo, ta yamutsa fuska tana hura iskar bakinta tana jin wani d'aci kamar tasha mad'aci. Mama uwargidan Alhaji Ibrahim macen albarka,macen k'warai dattijuwa me yakana da karamci, uwargidan cinta na dalci da amana takeyi,abinda yahaifar da kwanciyar hankali kenan,yasa zuri'ar gidan suka dunk'ule suka zama tsintsiya mad'aurinki d'aya.Duka Ya'yan gidan ta d'aukesu abu d'aya kamar ita ta haifesu.A d'aki tasamu Sudaida a kwance idanun ta a rufe,amma ba bacci takeyi ba.Ta zauna a gefan gadan,Sudaida tabud'e idanun ta da suka d'an canja kala.Mama takalleta da kulawa"wai mantawa kikayi da Sinan a waje?Tadad'a kwantar da kanta a saman matashi "Mama kaina ne yake min ciwo"sanin hali yafi sanin kama"sai tayi murmushi kawai"To ai ya kamata kije kifad'a mishi kar yayi jiran gawon shanu ko?A ciki ta amsa kamar ranta bai mata dad'i ba"to Mama na ji. Tana fitowa yatareta"Sudaida Sarauniyar Sinan"taturo baki gaba tana d'an harararshi"kai baka san kaina ne ya dameni da ciwo kuma Mama ta matsamin dole nafito"yayi murmushi wani lokaci haka take abu kamar wata 'yar k'aramar yarinya wai an matsamata dole tafito.Sai ya marairaice"Oh ALLAH! Wayyo! Sannu Sarauniyar Sinan taso muje ki kar6o magani? Tagirgiza kai'ai ma navfara jin sauk'i.Yasauke numfashi"kai nagode ma ALLAH,dama ni ne maganin ko?Sukayi dariya. Tana d'ago kai za tayi magana caraf idanun su yahad'u dana Julaibib,yana sanye da shadda ruwan k'asa yayi shar...shar dashi,magana yakeyi a waya yaja yatsaya nesa dasu.Tad'an ta6e baki"wayar tak'ici tak'i cinyewa,ba mamaki shi da wannna Bafulatanar ce.Yagama wayar sannan yamata wannan rikitaccen kallan da tadad'e bataga ya mataba,dama baya kulasu in dai yatarar suna hira ko magana tamishi sai yayi kamar ba dashi take yi ba"kunnan uwar shegu"tabishi da kallo har yashige cikin gidan.Takalli Sinan ni zan wuce"Shikenan anjima zan bada masoyin Sarauniyar Sinan akawo miki (rake) tayi d'an murmushi "nagode. Ranar Juma'a suna gidan Yaya Karima sunje mata ziyara sai gashi yashigo da sallama.Yazauna suna gaisawa da Yaya Karima tana tsokanar shi"Kai autan Inna har wani haske naga ka fara ko kaima kana gyaran angwancinne dasu halawa da dilka?Yakai hannu yana sosa k'asumbarshi yana yar dariya"Kai Yaya Karima duk sukayi dariya;banda Sudaida da ta tayi kamar bataji me aka fad'a ba,tacigaba da cin sinasir d'inta,Nasmat tace"wai ina masar Bauchin dana ce ka kawomin tsaraba?Haba ke kuwa Nasmat ai k'aton aiki za ki bani ace tun daga Bauchi har Zonkwa in rik'o masa?Gaskiya bazan iyaba,indai za kici kantu(rid'i)to kije wajan Inna ki kar6a. Ni masa nake so tunda baka kawo min ba ai shikenan nagode ALLAH kuma yabamu lafiya, amma da Bilkisu ce tace tana san masar ai baza ka d'auki hakan a matsayin k'aton aiki ba ko? To dake da Bilkisu Megadon Zinare...d'aya ne? Sudaida tamik'e"uh wannan Bilkisun dai ko gadon Mahogany ba ta dashi"tajuya za ta bar d'akin. Yarik'o gefen hijab d'inta..kafin yayi magana tajuyo cikin fushi"Yaya D'ansarai sake min hijab ka san dai bana wasa da maza.Su Nasmat suka kyalkyale da dariya kaji wata magana kuma? Yakalketa cikin natsuwa"idan kuma ban sake ba fa?Tayaye hijab d'in gaba d'aya daga jikinta tajefa mishi a fuska "kaje ka kai mata"fuuu...tafita mayafin Yaya Karima tajawo a igiya tayafa.Duk suka bita da kallo.Yaya Karima takama ha6a"to ana wata ga wata aure ya mutu ga gara.Takalli Julaibib ya sunkwui da kai"ranshi a 6ace yake,amma ta san bazai yi magana ba tunda yayi haka,wannan halin shine tun yana yaro indai ya sunkwui da kai. Yamik'e da hijab d'in a hannun shi "Yaya Karima ni zan wuce idan Baban Abdul yadawo kya mik'a min sak'on gaisuwa.To auta mungode kwarai kagaishe dasu Inna sai na shigo. Har yakoma Azare Sudaida bata yadda sun kuma had'uwa ba ko gidan Inna bata sake zuwa ba dan kar ma su had'u sai bayan data tabbatar ya tafi sannan taje.Yakirata sau d'aya a waya tak'i daga wa shima bai sake kira ba. Tana zaune a dakalin k'ofar gida da tunanin inasu Mama suka suka tafi haka harda kulle gidan gaba d'aya bayan sun san za su dawo daga makaranta?Sagir yazo da gudunshi zai kwashi kayan wasa a inda ya6oye can wani sak'o, tarik'o hannu"su Mama ina suka tafi?Matsirga su da Yaya Musaddiq da akwatuna,tasake shi yatafi. Lefe sukaje kaiwa kenan? Tad'an ta6e baki. Gidan Yaya Musaddiq tawuce. Safiyya tace"wata sabon gani.Tazauna a kujera tana yar dariya"ALLAH Yaya Safiyya ba lokacine kullum muna hanyar makaranta.Tagyad'a kai"na yadda,to shiga D'akin-girki kizubo abinci danna san kin kwaso yunwa,tak'arasa kwanciya a kujerar "ai azumi ma nake yi,ke me yahanaki zuwa garin Fulani kai lefen?Uhun ke dai bari har na shirya sai ga baki na yi ba zato ba tsammani basu dad'e da tafiya ba.Takuma ta6e baki tamaida idanun ta tarufe kamar tana bacci amma ranta in yayi dubu ya 6aci,taja tsaki tanata juye-juye,data gaji sai tamik'e tafito da littafin lissafinta tana nazarin Quadratic Equation. Julaibib da Bilkisu suna tsaye a wajan da ake ajiye motoci na cikin makarantarsu, tana tambayar shi "ya me jiki? Yagirgiza kai"ni fa ki daina tambaya ta ya me jiki, idan kina san sanin ya take ai zuwa za kiyi ki gaishe ta ko? Haba Megado wallahi kin bani kunya ace Yaya Asma'u takwanta a asibiti kwanaki goma kenan amma ki kasa zuwa gaisheta,aiko ba soyayya a tsakanin mu to akwai hakkin musulmi akan musulmi koda ba dangin Iya ba na Baba,gaishe da mutum idan ba shi da lafiya yana daya daga cikin hakkoki biyar akan musulmi da musulmi. Tasunkwui da kai"kayi hak'uri D'an Sarai Insha-ALLAH zan je.Yagyad'a kai"to muje in rakaki. Nagode zan je ni kad'ai suka d'an ta6a hira kad'an suka yi sallama. Abakin a sibitin ta tsaya ta sai kayan marmari sannan tashiga. Sudaida ce tabud'e k'ofar,suka kalli juna Bilkisu ba girman kai sai ta gaisheta,tatsuke baki cikin yamutsa fuska ta amsa mata dak'yar sannan tabata hanya.Tashiga da sallama ta durk'usa ckin natsuwa me had'e da kunya tagaishe da Hajiya tana tambayar ya me jiki?Dan ALLAH amin uzuri da banzo da wuri ba yanayin karatun mune sai a hankali,Tamatsa jikin gadan tana gaishe da Yaya Asma'u da tambayarta karfin jiki.Tayi murmushi"jiki Alhamdulillahi tunda gobe ma za a sallame ni. Hajiya ta kalli Sudaida"kawo mata ruwa mana.Tajuya tama Bilkisun wani kallo"Hajiya ita tace miki tana jin k'ishi?Mutanan d'akin suka bita da kallo in ka d'auke Bilkisu da Hajiya.Bilkisu ta sunkwui da kanta,Hajiya kuma tana nazarin Sudaida a karo na barkatai kenan tana nuna halin-ko-inkula da duk wani abu daya shafi Julaibibi tun lokacin da maganarsu da Bilkisu ta kan-kama, takad'a kai"lallai da magana karuwa ta ziyarci tuzuru. Yanzu sai ta ce tana jin k'ishi za a bata ruwa Sudaida?Bak'on ka annabin ka.Tamik'e tana k'unk'uni tad'auko ruwan ta dangwarar a gabanta.Hajiya tadafa kafad'ar Bilkisu da sigar rarrashi dan abinda Sudaida tayi bai kyautu ba sam"kiyi hakuri Bilkisu"Tad'anyi murmushi me had'e da kunya"ba kome Hajiya,dan kar suce taji haushin furucin Sudaida ne da baza ta shaba tunda ba ta jin k'ishi,kad'an ta tsiyaya a kofi tana kur6. Sudaida ta galla musu harara, tabud'e jakar ta tad'auko earphone tamak'ala a wayarta sannan ta toshe kunnuwan ta dashi, tashiga bin wak'ar, zaman d'akin ya gundireta sai tafita tabasu waje ganin hadari yana had'uwa yasa tawuce gida Feshin ruwan yafarkar da Khausar daga baccin data fara,ga littafan data barbaza a saman tebur har sun fara jik'ewa,tarufe taga tasuke labulan sannan takalli Sudaida "saboda ALLAH kina ganin ruwa zai jik'a min littafai amma kika ki rufe taga?Tayi kamar ba da ita take magana ba,sai ta fizge wayar"bakya jine ina miki magana?Tabita da kallo"ke wai kwana biyun nan lafiya kuwa?Eh ita takawo haka,tamik'a mata hannu bani waya ta.Tabata wayar tana gyad'a kai"lallai kam nima naga alama lafiyar ce takawo haka,tayi d'as da yan yatsunta"to amma fa karki manta duk kanwar ja ce,baki fini tsummaba bazan zauna kina 6ar6ad'eni da k'wark'wataba, wallahi ban kar zomo;tanunata da yatsa ke baki isa ki kisa ni d'aukar rataya ba.Sudaida tabita da wani malalacin kallo"ALLAH sarki. Suna tsaye kusa da rafin Matsirga D'ansarai yad'aga kai yana kallan Qudirar Ubangiji duk da ba ranar yafara gani ba,Tsawon tudun yayi gidan sama hawa uku tanan ruwan yake fitowa yana gangarawa wani rami a can k'asa me tsananin zurfi kuma a saman turawa sukayi titin jirgi k'asa kuma har yanzu tanan d'in yake wucewa,sa dai gaskiya duk wanda yafad'a ramin nan to ya gama numfashi a doron duniya wallahi. Bello yarik'o hannun Bilkisu "Adda zo mu tafi gida kinga hadari yafara had'uwa kar ruwa ya 6alle.Julaibib ya kalleshi"to mutafi suna tafiya suna d'an ta6a hira har suka zo k'ofar gidan.Julaibib yabud'e mota yad'auko wasu wara-warai (Awarwaro)masu kyan gaske a d'an gidan su"wannan kyautar soyayyace ta musamman ga wacce tayi nasarar mallake zuciyar Julaibib... Bilkisu Megadon Zinare...Bilkisu Zinariya kike kinfi azurfa.Yamik'a mata tasa hannu biyu ta kar6a "nagode k'warai Julaibib D'ansarai". Ke kad'ai nake so Megado... Tasunkwui da kai tana d'an murmushi cikin jin kunya kumatunta suka lotsa.Yad'an d'age gira"au baza kice kome bane?Tad'an d'ago takalli Bello ya ko zuba musu idanu kuriii yana kallansu. Yayi murmushi"Oh na fahimta,a dinga sara ana duba bakin gatari ko?Tagyad'a kai.Sukayi sallama a gaggauce dan an fara yayyafi. A sanda hantsi yadubi ludayi amma har lokacin garin da sanyi saboda ruwan saman da aka dinga tsuugawa kamar da bakin k'warya tun dare har wayewar gari sai wajan k'arfe bakwai da rabi ruwan yad'auke,Iska tana ta k'adawa. Tibishi yakalleshi amma jiya ka burgeni.Yakai mishi duka"wani burgewa ka sa inata tari kamar zan shid'e,sukayi dariya suka tafa"ai da haka za ka zama k'wararre.Tibishi yad'an ta6a shi"kai ga mutuniyar ta ka can,yajuyo da sauri "haba dai? Bai gan taba dan ta riga ta sha kwana" amma dai bata ganni bako? Yagalla mishi harara "kaji d'an iska to idan ma ta ganka sai me? Yamik'e"a ah wallahi da matsala,katafi kawai anjima anjima zan nemeka a waya. Tabishi yarik'o rigarshi ta baya "dakata malam ai ba haka mukayi dakai ba,sai ka bani kud'i indai kana so katafi,baiyi magana ba yaciro d'ari biyar yabashi yajuya da sauri dan kar tayi nisa.Tabishi yabishi da kallo yana kyalkyala dariya"Sinan shegen duniya,kura da fatar akuya yad'an yi tsaiii...nawucewar wasu dak'ik'u yana kissima wani abu a zuci sai kuma yad'an motsa kafad'a"any way akwai dai ranar k'in dillanci ranar da hajar me gari zai 6ata. Gudu-gudu sauri-sauri har ya cimmata yasha gabanta"haba Sudaida Sarauniyar Sinan ai ya dace ki tsaya ki saurareni ko?Tagirgiza kai"bai dace ba" Sinan katafi kabani waje karka 6ata min lokaci a banza a wofi.Yakwantar da murya yadinga mata kalaman rarrashi da bambaki har sai da yaga tana murmush"amma ai kai kafad'a min da bakin ka ka daina kulasu Tibishi amma ayyukanka suna k'aryata furrucin ka,jiya da yamma gab da za a fara ruwa tare naganku ka goyo shi a mashin kunyi hanyar D'One takalleshi cikin natsuwa wajan shan giyar koko ka kaishi da kanka Sinan?Yanzu kuma na sake ganinku tare kuna hirarku kuna ta dariya har da tafa hannaye; Sinan wai mantawa kake yi da d'abi'a tana na so? Zama da mad'aukin kanwa yana kawo farin kai fa. Haba Sinan me... Yatari numfashinta"Kiyi hak'uri Sudaida amma wallahi Tibishi shi ke bibiyata,ni kuma abinda yasa nakasa korarshi muyi baran-baran ina mishi kwad'ayin musulunci,wata kila ta dalilin Sinan masoyinki sai kiga ya samu dacewa zuwa addinin gaskiya kina wannan ai babban jihadi nevko?Tajijjiga kai"mutum d'aya yashiryu ta dalilin ka yafi abaka jajayan rak'uma guda dubu "Yad'an shafa k'irjinshi bangaren zuciya"Oh ALLAH nagode maka"sukayi dariya yad'an taka mata sannan sukayi sallama tawuce gidan Hajiya. Shi kuma yakoma wajan Tibishi yana fada mishi"abinda nake so dakai mudaina had'iwa a cikkn gari,ni idan inada buk'atar ganinka zan biyo ka har D'One.Yamishi wani malalacin kallo cikin fesar da hayak'in maro (wiwi) tabaki ta hanci "saboda wata Sudaida?To in tamabaye ka mana "haka zaka aure ta bata san kome a tare da kai ba sai halin waliyai?Ranar da duk tagano kana kanaga zata zauna dakai cikin aminci da amana? Yatareshi cikin hayaniya"kar kamin sanadin 6acin rai da sanyin safiyar nan dan zan gwada maka rashin mutum ci dan abu kazan uban ka,kafin Sudaida tasan kome ai na daina.Tibishi yagyad'a kai "wannan shine tazo muji ta tawuce ta bayan kunne.Yanuna shi da yatsa"indai muna tare da Sudaida to karka kuskura ka doshi wajan.Angama ranka yadad'e yajuya yayi tafiyar shi yana ma Sinan dariyar rainin wayo. Kafin tayi wani yunk'urin tashi dan ta jiyo muryar shi,har sun shigo D'akin-shak'awar. Musaddiq yakalle ta"d'auko kayan da Baba yabaki kiba Julaibib tamik'e "to. Musaddiq yamik'a mishi hannu sukayi musafaha"to ALLAH yatsare hanya shi Musaddiq a Kaduna yake bautar k'asa yanzu zai koma.Yazauna zaman jiran ta sama da dak'ik'u talatin bata kawo mishi ba ya kira wayar ta ta k'i d'agawa,sai yamik'e zuwa tsakar gidan ana yasame ta sunata hirar su dasu A'isha. Ke ina kayan ne? Tayi kamar bata ji ba. Khausar tabita da kallo tabbass wani abu ya samu k'wak'walwar Sudaida a yan kwanakin nan, d'azu ma haka sukayi da Yaya Aminu yace ta dama mishi custard;ta tafi d'aki tayi kwanciyar ta shima dagaji da jira yabiyo ta yana tambaya sai tace"Oh Yaya Aminu yi hak'uri na d'an mantane, barin je in dama maka.Yakalli agogo yagirgiza kai"idan natsaya gaskiya zan makara.Yad'aga mata hannu sai na dawo ko? Wallahi da sarki zalimu Yaya Adnan tama haka aida ta kwashi kashin ta a hannu. Ke Sudaida! Tamishi wani kallo bata amsa ba "d'auko min kayan mana sauri nake yi"Oh ga su can a kusa da d'akin Yaya Adnan.Yagyad'a kai "Khausar kawo min mota yajuya yana amsa kiran waya...tabi bayan shi da kallo tana wata kissima a zuci tad'anja tsaki tashige d'akinsu,tad'aga labulan taga yana jingine da motar shi har lokacin wayar yake yi,tad'an cije lebanta na k'asa sannan tasaki labulan takwanta a gado... Ruwa da dorina da kada shigar shi sai dai Kwarawan asali. 24 Jumaada Awwal 1441 19 January 2020 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in. ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi nagoma sha shida. Yafito daga mota yana kallan ta, tana sanye da shadda me maik'o ruwan makuba tayi kyau sosai a cikin yammacin"Bilkisu Megadon zinare...zinariya kike kinfi azurfa,na rasa yadda zanyi in fasalta miki irin kyan da kike k'arayi amaryar D'ansarai.Tasunkwui da kai ganin wani irin kallo dayake mata,abinda yake so tattausan jajayan labbanta kamar ta turasu da jan jambaki "wai yau saura kwana nawa yarage muzama abu d'aya?Tagirgiza kai"nima ban sani ba,dan bana lissafi.Sai yakama kai"Innalillahi Megado bakya lissafi?Lallai baki damu dani kamar yadda nadamu dake ba.Tayi murmushi me sauti, kumatunta suka lotsa"ai ba anan take ba Julaibib, abari agani mana an ba bature 'yar bak'ar fata. Yagyad'a kai"kema kince wani abu,ALLAH yabamu rai da lafiya yanuna mana lokacin. Sudaida takalleshi"Sinan jiya inata d'aga maka hannu.Fargaba taka ma shi, da d'an rawar murya yace"jiya da yaushe?Tayi shiru cikin nazarin shi kamar ya shiga rud'u"jiya da yamma, lafiya kuwa?Yasa hannu yashare zufan daya tsatstsafo mishi a goshi"jiya ya yi kato6ara amma da rana abin yafaru.Yad'anyi murmushi"a ah ba kome, kiyi hak'uri ban ganki bane. Nima ai na san da ka ganni baza ka shareni ba. Tibishi aka sauke akan mashin yak'araso wajan cikin tam6ele da sambatun da kamru uwar laifi take haifarwa,yamik'ama Sinan hannu"sai ka bani kud'in da zan sallami me mashin ko?Dasauri yaciro yabashi; yajuya cikin irin tafiyar bugaggun mashaya"ka rufa ma kanka asiri da wallahi yau allura sai ta tono garma,banza kawai,wawa.Suka bishi da kallo Sudaida toshe da hanci saboda wari da hamamin daya cika wajan,ta tsirtar da miyau"kai ALLAH ya sauwak'e...ya amsa da amin.Ya bud'e baki zai mata magana sai ga Tibishi yasake dunfaro su"kai d'an iska kura da fatar akuya.Sinan yamik'e da sauri"Sudaida shiga gida kawai anjima zan dawo,tajuya da sauri dan cikinta ya fara hautsinewa saboda warin Tibishi. Yaja shi suka bar k'ofar gidan. Danbarwa sosai sukayi da Tibishi bayan mayen uwar laifin ta sakeshi"Yahankad'e shi yafad'i tabaya,Sinan yafara nuna shi da yatsa"kar ka sake biyoni wajan Sudaida.Yamishi wani kallo"ALLAH ko?Na Sudaida ba da kanka asare idan kaje gida kace ya fad'i,haka kirarin na ku na hausawa yake ko?Eh hakane saura na Katafawa,yayi dariyar tura haushi"ai sama-sama kake jin yaran Kataf dan haka kona maka ba zaka fahimta ba,yamik'e yana kakka6e bayan wandan shi"ajuri zuwa rafi...wannan ma karin maganar ku ta hausawa ce ko?Sinan yakai mishi naushi cikin tafasar zuciya,shima da zafin nama yakauce yana fad'in"yau dai baka san gani na,to gwamma cikin girma da arziki in san inda dare yamin,yad'aga hannu yana mishi adabo sai mun had'u a D'One. Aminu yana aikin sticker na wani biki da aka bashi kwangila,Sudaida tashiga da sallama, yace yauwa dama ina neman d'an tayan aiki na leka d'akin ku banga kowa ba,tazauna tana tayashi suna hira har suka gama,sannan ta tambaye shi abinda take so ta tambayar shi "Yaya Aminu Sinan baya shaye-shaye kuwa? Yamata kallan nazari"me yasa kikayi wannan tambayar Sudaida?Saboda duk abokan dayake mu'amala dasu yan maro ne (wiwi)Tibishi kuma bayan maro har uwar laifi yana korawa,idan hali bai zo d'aya ba anya za'ayi abota?Ni kwanaki ya min bayani amma danayi d'an nazari sai nake ganin kamar akwai lauje cikin nad'i. Gaskiya a iya sani na dashi baya shan kome,to amma kinzo da magana abar dubawa,kibar kome a hannuna,zan bincika koma menene zamu gano Insha-ALLAH,yad'an d'age mata gira"kinga ne ko?Tayi yar dariya na gane, ALLAH yabarka da Siddika.Tazama sarauniyar Aminu kamar yadda kika zama sarauniyar Sinan ko?Sukayi dariya.Tana jin k'aunar Aminu fiye da duk sauran Yayyin su saboda sauk'in kan shi,yana jan su ajiki kamar ba babba ba,wasu lukutan har wajan budurwar shi Siddika tana raka shi hira,ko kuma yaba ta abu takai mata,shi Yaya Adnan shine me irin halin Umma baya san raini ko kad'an,da shine babban gidan nan ai da sun gama kad'ewa har ganyan su dan har yafi Yaya Musaddiq za fi. 'Yan lek'en asiri yasa amma basu gano mishi kome game da abotar Tibishi da Sinan ba.Yakalleta da kulawa,sun dai tabbar suna tare kuma sauran suna shaye-shayensu amma ko karan taba su dai da idanun su basu ga Sinan dashi ba,dan haka shawarar da zan ba ki tunda kin yadda dashi a matsayin mijin da za ki aura to karki tsananta binciken shi, babu wanda za'a tsananta ma bincike face sai an kama shi da laifi,su Baba sun amince dashi,kuma basuyi hakan ba sai da sukayi bincike,na kuma tabbatar da yana da babbar illar da zata shafi zaman takewar auran ku to baza su yadda dashi amatsayin surikiba,kiyita addu'a kina kuma nusarshe shi illar zama da irin wad'annan mutanan.To Yaya Aminu nagode. ALLAH yaba ka Siddika.Yayi murmushi. Tana gidan Hajiya taji sallamar Julaibib.Yanad'e hannayen shi ak'irji yana kallan ta"kina kwance anan gashi can anata karatu a makaranta.Tad'an harare shi"uh na gajine yau da gobe ai sai ALLAH,dan dai rana d'aya mutum ya huta sai afara binshi da k'orafi? Yatsuguna yana duba wasu tsofaffin littafai adirowan Hajiya"hutun jaki da kaya aka ba.Tad'auki man zafi asaman kujerar"kai baka san k'afafuna ciwo suke yiba "me zai hana su ciwo tunda jiya kinsha rawar samba" daga baya suka jiyo muryar shi, Musaddiq ne. Yagalla mata harara,sai ta sunkwui da kai"tashi ki wuce makaranta, tamarairaice"dan ALLAH Yaya Musaddiq...yatari numfashin ta shhh...yad'ora yatsan shi abaki,in dai ba so kike yi ki kwashi kashin ki a hannu ba to tashi kawai "tafara matso kwalla aranta tana addu'ar ALLAH yakawo Hajiya ita kad'aice zata ta ka mishi burki,itama d'in idan ta ga dama.Julaibib yasa musu baki"amata hak'uri mana tunda tana da lalura"wa zan ma hak'urin?Wannan yarinyar? Yanuna ta da yatsa"ai da lalurar arzikice da har pain-relief zan k'arama ta dashi,ai ka san jiya anyi Inter-School a Saint-Francis College to nan suka tafi tun safe har biyar da rabi ba makarantar da suka je ta allo data Islamiyya,ashe yauma basuje ba da safe suka kwanta bacci wai sun gaji,to d'azu ina gidan Umma takorasu kasan sun maida Mama kamar sa'ar wasan su koda tayi magana basu jiba,to su sauran sunji maganar Umma sun tafi ta yamma sai ita shafaffiya da mai tazo nan tayi kwanciyarta?Tafara kuka"ni dai ALLAH yanaji yana kuma gani banyi rawar samba ba.Yakalleta cikin fushi" karya zan miki ko?Me zai za k'afufunki suyi ciwo bayan wasan discuss kike yi indai ba rawan kika yiba? Hajiya tashigo"yayane Sudaida kike kuka kuma?Musaddiq yayi kwafa"kyale ni da ita kawai Hajiya samun waje ne kuturu da gad'a a rama.Julaibib yadafa kafad'arshi"ka kyaleta mana wata kila bayan ciwon k'afafun akwai hujjar datasa tak'i zuwa,ka san hali da dabi'ar mata Iyayanmu, yan'uwanmu,k'anninmu sai hak'uri, sai ana kawar dakai awasu lokutan idan ba haka ba,sai su maida kai wani iri,yazame hannun Julaibib daga kafad'ar shi, yajuya yayi tafiyar shi;tasauke numfashi sai a lokacin tashak'i iskar yanci"kai Yaya Musaadiq barkono ne,yanzu haka yakema Safiyya wannan halin?Hajiya tace"barin kira miki shi yaba ki amsa dan wak'a abakin me ita ta fi dad'i.Takama ha6a"wuuu...Tabbb Hajiya rufa min asiri kar k'ilu taja bauuu... Ya tashi sahur azumin nafila na ranar alhamis yana juya zuman dayasa a shayin na'a na'a da 'ya'yan algarib yayi tsai...cikin tunano mafarkin dayayi da daddare... "Kasham yake gani da kayan fulani tayi kyau k'irar kalangunta ya fito rad'am,amma idan tayi magana muryar Sudaida yake ji. Shekarun baya yayi wannan mafarkin to yanzu ma mafarkin ya dawo shi ya rasa gane kan wannan mafarkin.Yayi bismillah yafara kur6a amma ko kwata bai sha ba kome ya gundire shi,shayin yamishi wani irin d'and'ano mara dad'i,ya ajiye kofin a saman tebur.Yad'auki farar hular zita yasa yad'auki Alqur'ani me girma yana karantawa har aka kira assalatu daga mabambantan masallatai na unguwar,yayi raka'atal fajri sannan yafito suka tafi masallaci shi da Baba. Tana fitowa daga asibiti motar shi tana tsayawa,yabita da kallo tayi kyau a cikin fararan kayan riga da wando da d'an madaidaicin farin hijab,suka kalli juna sai yamik'a mata hannu ta san me yake so dan haka tamik'a mishi ragowan Schweppes d'in da yake hannun ta"ya ajiye a mota dashi zan yi bud'a baki "Megado kinga kyan da kike k'arawa kuwa tun bamu fara cin Shahrul-Asal (Honey Moon) ba?Ya d'aga kai sama alamar tunani"Bilkisu k'wak'walwata 6angaren nazari da tunani ta gaza gano yadda zan fasalta irin kyan da kike tayi,wai meye sirrin ne?Yazubama tattausan jajayan la66anta idanu;tayi dariyar da tun had'uwar su bata ta6a irinta agabanshi ba, kumatunta suka lotsa ciki sosai yar siririyar wushiryar ta,ta dad'a k'awata fuskar ta,Ya ilahi... shi da kanshi ya kauda kai yana jin wani irin yanayi a ilahirin gangar jiki da sararin zuciyar shi game da ita. Wai kai kwana biyun nan me yake damun kane sai kadinga wasu maganganu kamar lokacin kafara gani na?Yamata wani kallo"yunwar so ke damun zuciya ta. Matsirga zan tafi,takawar da wannan maganar.Yakalleta cikin makaki"wani irin Matsirga kuma da safen nan?Haba kibari kid'an samu bacci koda awa uku ne,kinga aikin dare kika yi na san baki yi bacci ba,idan kika d'an huta bayan azahar ba sai ki tafi ba?"ni dai dan ALLAH yanzu nake san tafiya kar inyi hutun jaki da kaya aka,agida sai in huta gaba d'aya.A ah Megado ban yadda ba,ba ranar lahadi da yamma kika dawo daga Matsirgan ba?Tagyad'a kai"Inna nake san gani, tayi yar dariya"wallahi gobe da safe zan dawo Insha-ALLAH.Ba ga waya ba kikara ta mana.Tad'an marairaice"ni dai nafi so inganta ganin idanu na.Yad'an harareta"shikenan tunda kin na ce sai kin tafi to muje in kaiki,idan muka kwana sai mubugo sammako da sassafe dan nima Zari'a zani a goben. Tad'an bud'e idanu dan mamaki"ka kwana a ina?Bai bata amsa ba yashiga mota yazauna sannan yakalle ta"shigo mutafi mun... kiran wayar Baba takatse shi yad'aga da sallama "kazo yanzu na yi baki suna jiran ka a shago.Ya amsa cikin ladabi"to Baba gani nan zuwa.Yad'anyi jimmm...D'ansarai lafiya kuwa?Kiyi hak'uri Megado na so kwarai mutafi tare to sai dai hak'ata bata tadda ruwa ba,akwai bak'in da suke jirana a shago.A ah ba kome" tashiga ta zauna yaja motar. Tasha yakaita yasata a motar haya, gidan gaba yabiya kud'in mutum biyun dan ta zauna ba takura,suna ta hirarsu yana fad'a mata wasu kalamai masu nauyi,tad'an harareshi sannan ta sunkwui da kai "ka san ALLAH idan baka daina fad'a min wad'annan kalaman ba zan daina sauraranka,kuma ko waya ka kira bazan d'aga ba, yayi yar dariya"ni kuma ban san inda kike bako? kaji yar rainin hankali kamar wata k'aramar yarinya, ba aikin asibiti kikeyi ba? Wancan makon ba d'akin yan hatsari kuma maza aka kaiku ku musu dressing ba?Wani dare ne jemage bai gani ba? Tasa hannun damar ta tashafa dogon karan hancin ta,tayi kamar bata gane me yake nufi ba.Akwai dararan da jemage bai gani ba fa.To wani dare ne kuwa?Shima yatambaye ta. Tamishi wani kallo daya sa zuciyar shi bugawa Dammm...bai kuma san dalili ba.Daren da aka haife shi da daran mutuwar shi ko ya gani? Yagirgiza kai.Kiran Adnan yashigo wayar shi, yad'aga da sallama.Adnan ya amsa sannan ya tambaye shi"kana ina ne D'ansaarai?Ina tashar mota.Tashar mota kuma?Me kakeyi a tasha? Bilkisu zan sa a motar Matsirga.Tam dama Hajiya zan kai unguwa Yaya Aminu yafita da motar gida. Shikenan zo ka kar6i mukullin.Suka cigaba da hirar su har Adnan d'in yak'araso suka gaisa da Bilkisu a mutunce yakar6i mukullin motar yatafi. Shafff...ya manta da kiran Baba sai da kiran shi yasake shigowa sannan ya tuna"Baba ayi hak'uri gani nan zuwa"yamayar da wayar aljihu "Bilkisu barin je in dawo.Takalleshi cikin natsuwa "bak'i fa kukayi kafin kugama abinda za kuyi ka dawo ai na tsufa a gida,sai dai munyi waya. Yagyad'a kai"shike nan nagode ALLAH yamiki albarka.Amin. "Sai munyi waya...suka fad'a atare. Sannan suka kalli juna sukayi murmushi yad'aga hannu yana mata adabo yajuya da d'an sauri dan kar Baba yasake kiran shi,tabi bayan shi da kallo har ya tsallaka titi ya6ace ma ganinta,tamaida kanta jikin kujera tana sake kiran lambar Inna dan ta kira sau shurin masak'i amma bata shigaba,saboda matsalar na'urar sadarwa. Motar su ta cika suna shirin tashi ta tura ma Julaibib sak'on murya(voice note). "Julaibib yanzu motar mu ta tashi... Ina sauka kai zan fara kira,ta mishi sautin sumba muahhh... 💋" Abinda yaketa rok'on ta ayan kwanakin nan tamishi kenan,amma k'ememe tace wai ita bata iya ba,rannan data bashi haushi yace"kar ALLAH yasa ki iya d'in za ki zo hannu duk sai kin biyani bashi dalla-dalla. Yadawo daga sallar azahar zai shiga d'aki kiran Bilkisu yashigo,yayi murmushi "haba Nurse Megado ko dak'ik'u talatin bakuyi da tashi bare kice har kin sauka, yad'aga da sallama "hayaniya da kururuwane ya cika kunnuwan shi "Bilkisu lafiya kuwa?Wata murya ta amsa"ba Bilkisu bace kazo Wadom yanzu-yanzu sunyi hatsari ne"Innalillahi Wa'inna'ilahi raji'un" Istirja'in shi Inna taji fito daga D'akin-girki da sauri. Yajingina kanshi da bango jikin shi a sanyaye "lafiya kuwa D'ansarai? Sai ga Musaddiq ya shigo duk suka zuba mishi idanu su. Musaddiq yace"me yafarune?Inna tawatsa hannu"abinda nake tambayar shi kenan kashigo.Yadafa kafad'arshi"yi magana mana Julaibaib..."Megado ce sukayi hatsari.Inna da Musaddiq suka yi Istirja'i suma, yaja hannunshi"to tsayuwar me muke yi?Inna sai mun dawo.Tabisu har zaure bakin ta d'auke da addu'ar Ubangiji yatsare musu hanya. Gudu sosai Musaddiq yayi.Wajan ya cika dank'am da mutane da jerin motoci,wani hukuncin Ubangiji kuma daga Bikkisu sai wani dake gidan baya sune sukaji mummunan ciwuka, sauran dai k'uk'k'urjewa kawai sukayi, shi dama d'an Wadom d'in ne yan'uwan shi sun zo sun d'auke shi zuwa asibiti. Ruguzowar wani abu yaji a k'ahon zuciyar shi lokacin daya ga Bilkisu a kwance sambal cikin jini fuj'atan, zuciyar shi tafara wata irin bugawa da k'arfin gaske kanshi yasara, yahad'iye wani abu me zafi,yasa hannayenshi biyu ya cicci6eta zai sa a mota sai kawai wajan ya kaure da salati, masu ihu na yi,masu fad'in Jesus Christ,Holy Mary nayi,masu d'ora hannaye aka suna sambatu da yarukan su na yi, bai fahimci kome ba sai da yaga Musaddiq ya d'auki farin hijab d'inta da yarine da jini ya koma ja,yad'aure mata kai,ashe kan tsagewa yayi ana hango ciki, yashimfid'eta a bayan mota. Jama'ar wajan na musu fatan su sauka lafiya, ita kuma ALLAH yata shi kafad'a yasa kaffarace.Shi kanshi Musaddiq ta maza yayi yake tuk'in saboda ya shiga rud'u da damuwa,a haka har suka koma Zonkwa. "Saint Louis Hospital 6angaren hatsari da taimakon agaji na gaggawa(Accident and Emergency) aka wuce da ita,Julaibib ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai-kawo yake yi a barandar wajan.Musaddiq yarik'o hannun shi suka zauna"kayi hak'uri Julaibib na kira Malam Lamid'o a waya yanzu haka suna hanya. Suna zaune jingum-jingum har su Baba da Malam Lamid'o da Yayyin Bilkisu Maude da Tukur sukazo, zaman awanni biyu sannan zugan likitocin da ma'aikatan jinya suka fito daga d'akin.Gaba d'aya suma suka mik'e kowanne hankali a tashe,Babban likitan yace ku biyoni office. Cikin natsuwa yad'ago yana kallansu bayan ya gama yan rubuce-rubucen shi a wani fallan takadda me sunan asibitin"kuyi hak'uri Insha-ALLAH kome zai zo da sauk'i,yanzu dai mun bata taimakon gaggawa wanda za mu iya amma gaskiya abin ya fi k'arfin mu dan ya shafi k'wak'walwarta sai dai kuwuce da ita Shika, Ahmadu Bello Teaching Hospital Ubangiji yaba ta lafiya,yanad'e takaddan yamik'a ma Malam Lamid'o"Idan kunje ku ne mi... "Doctor Garga Ibrahim Manogi... Maude yagyad'a kai"Alhamdulilahi Doctor Manogi k'wararren ne akan abinda yashafi k'wak'walwa (Neurology) kuma k'anwar Innar su yake aure, dan haka fad'uwa ce tazo dai-dai da zama.Suka koma d'akin da Bilkisi take kwance, jikinsu yayi mugun sanyi,wallahi mutum ba a bakin kome yake ba, Ubangiji kamana kyakkyawan k'arshe👏Tukur yace muna 6ata lokaci ai gwamma muyi harama. Malam Lamid'o da Tukur agaban motar sai Julaibib da Bilkisu a baya,su Baba dasu Musaddiq suka lek'o to Ubangiji yakaiku lafiya. Maude yace gobe sammako za muyi da Inna, Malam Lamid'o yagyad'a ka.Tukur yaja motar, suka bisu da kallo har suka fita daga asibitin suka hau kwalta. Julaibib yazuba mata idanu zuciyar shi na bugawa da k'arfin gaske d'ik d'ik d'ikkk...wuyan ta ya karye an sa mata stiffness collar,kanta yana cinyar shi har lokacin jini bai daina zuba ba,bandejin da aka nannad'e kanta dashi saura kad'an yajik'e,hannunta nadama akwai karaya guda biyu,idonta na dama ya zurma ciki sosai alamar ya fashe ruwan ciki ya gama tsiyayewa,idonta na hagu kuma ya kumbura suntum har wani kyalli yakeyi,gaba d'aya kamanninta ya canja saboda kumburin da fuskarta tayi. Idanun shi sun kad'a jawur kanshi yana wani irin sara mishi,yakad'a kai cikin maimaita Istirja'i yana tallafe da kanta... motar tsittt kowa da yadda abin yadake shi,wucewar wasu dak'ik'u hannun hagunta da yarik'e yaji ya saki tayi wata ajiyar zuciya Dammm...zuciyar shi tabuga!Yasake zuba mata idanu yana ta6a wuyan ta,harbawan da yake yi ya tsaya cakkk...Tukur yana kalkanshi ta madubi a hankali yagangara gefen titi yatsaya.Malam Lamid'o tun shigar shi motar kanshi ak'asa yad'ago"Tukur lafiya?duk suka juya baya,Tukur yabud'e motar yakoma baya yana tatta6a ta,da rawar murya yace"Malam kamar fa bata numfashi.Sukayi shiru nawasu yan dak'ik'u.Malam Lamid'o ya tabbatar Bilkisu ta mutu! "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!...KULLU NAFSIN ZAA'IK'ATIL MAUT!kowace rai sai ta d'and'ani mutuwa😭Ubangiji mun tuba,dama kowane d'an Adam me kuskure ne,sai dai mafi kyawun masu kuskure sune masu tuba.Ubangijin mu kamana gam da katar da kyakkyawan k'arshe,mu mutu cikin da'a da dokokin ka😭👏... "Julaibib yace Malam Bilkisu fa bata mutu ba,dogon suma tayi.Tukur ma yagyad'a kai"nima haka nake tunani yakoma gidan gaba yazauna yana k'ok'arin tayar da motar"Malam inaga jinin da take ta zubarwa ne yahaifar da haka.Juya da motar nan mukoma gida a mata wanka akaita d'akin ta na gaskiya Ubangiji yasa k'arshen wahalar kenan Bilkisu,kwallah suka cika idanun shi,yasa gefen babbar rigar shi yagoge. Julaibib da Tukur sukace "a ah Malam Bikkisu bata mutu ba,Insha-ALLAH kuma za ta warke. Malam Lamid'o yadafa kafad'ar Julaibib"kar muyi haka daku mana, ni tunda naga Bilkisu dama na san indai ba wani hukunci na Ubangiji ba to baza ta rayu ba,idan ma ta rayu to za ta samu tasgaro me yawa arayuwar ta,kuyi hak'uri Bikkisu ta riga ta tafi ni naga mutuwa ba d'aya ba ba biyu ba. A asibiti ma likita yabasu tabbacin ta rasu,dukkansu hawayene yake zubo musu sharrr... sharrr... Wayyo ALLAH!Duniya gidan ci rani,duniya gidan azo a wuce! kowa sai ya koma gidan shi na asali (Lahira) Gidansu Julaibib suka wuce da gawar Bilkisu dan Malam Lamid'o ya ce ba sai sun tafi Matsirga ba,duk inda musulmi yamutu ai za a iya yi mishi wanka a mishi sallah akwaishi makwancin shi. Inna da Musaddiq da Hajiya suna zaune cikin jimami sai ga Julaibib yashigo cikin tashin hankali "Lafiya kuwa Hajiya ta tare shi,me yadawo da kai? Ya zauna a kujera idanun shi sun kad'a jawur,wata jijiya ta fito rad'am a gefen goshin shi kamar shatin bulala, yabisu da kallo sai kuma yamik'e, jikinsu ya basu dan haka cikin zafin nama Musaddiq yarik'o shi"Hajiya tace kayi hak'uri... mutuwa ba ta jira ALLAH baya barin wani dan wani, ALLAH shi yayi Bilkisu, dama aran ta aka ba mu,to lokacin tafiyarta ta yi dan haka bamu isa mu hana ba,suka cigaba da rarrashin shi da kalamai masu taushi,Musaddiq yafita wajan su Malam Lamid'o dan har an shiga da ita D'akin-shak'atawar Inna. Maude ne yazo da Inna,tana ganin ta a kwance sambal fararan kayan aikinta sun rine da jini sun koma kalar ja,tayi fari fattt...ta d'ashe alamar babu sauran jini ajikinta.Inna ta zuba mata idanu cikin hawaye"Bilkisu ke ce kika zama haka? takad'a kai cikin sarewa da al'amarin rayuwa, kamanninta sun canja ta zama wata irin halitta,a fuskarta ba irin halittar d'an Adam ba amma wai hukuncin Ubangiji sauran gangar jikin ta lafiya lau ko k'warzone ba bu na ciwo,in banda hannun damar ta "Bilkisu kece mace d'aya acikin 'ya'yana na so ganin auran ki sai dai kash... Kana na ka ALLAH na na shi kuma na ALLAH shine dai-dai,ALLAH yamiki rahama yasa k'arshen wahalar kenan,Bilkisu kin dace Insha-ALLAH dan kin mutu a d'aya daga cikin ranakun da babu tambayar kabari akan mamaci,kin mutu ranar alhamis, tasa hannu tashare hawaya ta fuskanci su Innan Julaibib "mu mata abinda aka fiso ama mamaci da gaggawa,su uku suka mata wanka suka samata likkafani suka sata a makara Innan tad'auko fallan zani aka lullu6eta,Maude da Julaibib suka fita da ita aka mata sallah sai makabarta! Sun dad'e suna ne ma mata gafara musamman mahaifinta da masoyin ta Julaibib da Yayyinta su Maude da sauran yan'uwa da abokan arziki. "YA ALLAH!KA GAFARTA MATA!YA ALLAH KABA TA TABBATA! Suka juya zuwa cikin gari jikinsu a sanyaye,zuciyoyin su cike da alhini da d'acin mutuwa. Malama Lamid'o da iyalinshi suka fito za su tafi.Julaibib yana tsugune a gabansu ya sunkwui da kai,kukan shar6e yake yi hawayen suna ambaliya a fuskar shi, ganin haka yasa Tukur yarik'o hannun Inna da take matsar kwallah zuwa mota"Inna zauna.Cikin dauriya Malam Lamid'o shima yatsuguna yadafa kafad'arshi"kayi hak'uri Julaibib hak'ik'a wannan mutuwar babu wanda ta dake su kamarmu iyayanta da kai,to duk mu d'auki hak'uri kowa zaman jiranta yake yi,tabbasss da ina da wata 'yar bayan Bilkisu to dana ba ka, amma zan cigaba da maka addu'a"ALLAH yaba ka wacce tafi Bilkisu,yayita rarrashin shi sannan sukayi sallama dasu Baba.Tukur yaja mota suka tafi. Julaibib yabi bayan motar da kallo har tasha kwana ta6ace ma ganin shi sharrr...sharrr...wasu zafafan hawaye suka zubo mishi. Yakad'a kai cikin maimaita Istirja'i. Bayan sallar magriba Inna ta kawo mishi kunun tsamiya da kosai.Julaibib daga dawowa daga masallaci sai kuma ka kwanta? Tashi kayi bud'a baki mana.Yamik'e zaune dak'yar dan kanshi na wani sarawa "Inna bana jin yunwa cikina ya cunkushe kamar na ci abinci"Tajijjiga kai"na sani D'ansarai to amma dai ai ka san an umarce mu da gaggauta bud'a baki,azumi fa kayi daure kaci dabino kaji... yakar6i guda d'aya haka dai yaci amma wallahi baiji d'and'anon shi ba dakyar ya had'iye. Malam Abdullahi yashigo shima yazauna yadafa kafad'ar shi"Malam D'ansarai ai wannan lokacin yana d'aya daga cikin lokutan amsa addu'a,to ba sai kayi amfani da wannan damar wajan rok'ama Magado gafara dama kai kanka ba?Duk da yana cikin damuwa amma sai da yad'anyi yake ganin yadda suke ta rarrashin shi Inna wai ita sai ta bashi kunnun ma abaki wallahi kuma yau a d'akin baccin ta za su kwana tare "Karki damu Inna zan sha amma sai zuwa anjima kin san ba sosai nake cin abinci daga shan ruwa ba.Eh haka ne ,tamik'e ta barshi da Baba. Washe gari su Julaibib da iyayan su motoci guda uku sukayi dan zuwa Matsirga ta'aziyya sun tafi da manyan kololin shake tam da abinci ,kullum sai sunje har sai da akayi addu'ar uku. Yana rik'e da agogon da aka cire a hannun Bilkisu lokacin da za'a mata wanka sai jujjuya shi yakeyi,tunaninta da irin hirarra kinsu ya cika k'wak'walwar shi"Bilkisu a very meek damsel ta tafi ta barshi,burin su na zama ma'aurata bai cika ba. "Sai na kira... kalmar da suka fad'a ma juna ta k'arshe shi da ita kenan,sai sak'on muryar data turo mishi,yasake kunna sak'on muryar yana sauraro a karo na barkatai sau shurin masaki,ya kad'a kai"uh uhun mutuwa rigar kowa... Sudaida tashigo tana kallanshi cikin zancen zuci"shi ko wani irin so yakema wannan Bilkisun?Kullum taganshi sai taga ya dad'a ramewa,tausayinshi yamamayeta dan ba ta jin dadin ganin shi a haka,itama tayi nadamar abinda tadinga ma Bilkisu wanda ita Bilkisun ko a fuska bata ta6a nuna ta ji haushi ba"Yaya Julaibib dan Allah kayi hak'uri,kaga yadda kake ta ramewa? Yad'an kalleta"to nagode.Ta ajiye rediyon tafita. Inna tafio daga D'akin-girki tana kallanta tana sa takalmi"ba dai tafiya za kiyi ba?Tafiya zan yi Inna dan zanyi rubutun allo yau akwai darasu,amma idan nagama zan dawo in sha fate na.To shikenan, ALLAH yamuku albarka"Amin Innarmu. Malam Lamid'o yana zaune a d'akin zaure yajiyo sallamar Julaibib.Yafito da sauri kaine haka?To maraba yashiga suka gaisa.Malam Lamid'o yace ikon ALLAH dama Tukur nake jira yadawo anjima za muzo wajan na ku.Ya amsa cikin girmamawa"Malam shi yasa ma nazo dan Baba yafad'a min yadda kukayi ta waya"Indai za kuzo ne dan kawo wani abu game da kayan auran Megado to kubari. Malam Lamid'o yagirgiza kai"sam-sam baza ayi haka ba.Ya amsa cikin ladabi"wallahi Malam kome da aka kawo saboda Bilkisu na bar muku har abadan duniya arabama yan'uwa da abokan arziki bazan kar6a ba.Malam Lamid'o yayi shiru cikin jinjina wannan al'amari,sai kawai yad'auki wayar shi yakira Alhaji Abdullahi yafad'a mishi abinda Julaibib yace"Baba yayi murmushi "haba Malam dan D'ansarai ya ce haka har sai ka kira?Tunda yace ya bari to ya bari d'in ne,kutaya mu addu'a kawai Allah yabashi macen alheri.Ya ajiye wayar cikin sanyin jiki.Karka damu Malam Julaibib yafad'a."Julaibib ALLAH yamaka albarka,ALLAH yasa kagama da duniya lafiya, ALLAH yaba ka wacce tafi Bilkisu. Yamishi jagora zuwa cikin gidan. Innan Bilkisu tana ganin shi tafara kuka,ya sunkwui da kai cikin wani irin yanayi,ga tausayin ganin yadda Innar Bilkisu ta zabge,tayi bak'i, idanun ta sun k'ank'ance saboda yawan kuka"Inna kiyi hak'uri Bikkisu ba kuka take buk'ata a wajan muba,addu'a tafi buk'ata.Inna takad'a kai cikin hawaye "kaiya d'an nan ba kukan rabuwa da Bilkisu nake yi har yanzu ba,ina kuka ne saboda wata rana za a manta da Bilkisu wajan yi mata addu'a kaasatan(a ke6e) saboda bata bar baya ba,dama Ya'ya sune duk rintsi baza su gaji dama mahaifa addu'a ba,har sai ranar da suma suka koma ga Ubangiji.Yajijjiga kai haka ne,to amma Inna ya zamuyi da hukuncin Ubanguji?ALLAH bai k'addari za tayi aure ba, bare har ta haifi Ya'ya,Inna duk hukuncin Ubangiji akan bawan shi adalcine,duk da bata haihu ba to ai akwai sadakatul-jariya,sadaka me gudana kamar mutum yana raye adoron duniya ni zan je cikin k'auye inda duke wuyar ruwa zan gina mata rijiya...Malam Lamid'o yatari numfashin shi"a ah basai ka sake kashe kud'in kaba kabari kawai tunda kabar mana kome to zan gina mata da kud'in sadakinta...Inna tafashe da kuka ALLAH yabaka wacce tafi Bilkisu d'an nan, hakika kai masoyin Bilkisu na gaskene dan ka nuna mana haka duk da bata cikin doron duniya. Idanun shi suka kad'a jawur"ni gobe zan koma wajan bautar k'asa dama sallama nazo muyi sai an kwana biyu,suna sallama Bello yashigo da gudu yana haki yana dariya"Yaya D'ansarai ina dabinon ajwa na da inibi na?Suka zuba mishi idanu ba abinda yadame shi sai tsallan shi yakeyi"k'uruci dangin hauka.Yamik'a mishi ledar daya shigo da ita a hannunshi.Yakar6a cikin tsallan murna"Yaya D'ansarai nagode ya k'ank'ame ledar akirjin shi"to yaushe zaka dawo? Yakalleshi da kulawa"zan dad'e ban dawo ba. Bello yad'an zaro idanu"kaiii kaima irin tafiyar da Adda tayi za kayi?Inna fa tafad'a min wai ita baza ta sake dawo wa ba sai dai muje mu same ta,ni fa shi yasa baza ni ba,kai ai za ka dawo ko?Insha-ALLAH Bello... Idanun Julaibib suka sake kad'awa jawur ya tuno da Bilkisu da take cewa gobe fa zan dawo Insh-ALLAH... Cikin wani irin yanayi suka yi sallama yaja motar shi yatafi,ya dad'e a Water-fall d'in Matsirga yana kallan ruwan yadda yake gudu cikin Qudirar Ubangiji ba dare ba rana shekara aru-aru. Sagir yafito da gudu yana kiran shi" Yaya Julaibib wai katsaya.Inji wa?Yana hakin gudun da yayi yace"inji Yaya Sudaida.To ya shiga mota ya zauna yad'aura belt,k'afarshi d'aya tana waje.Tak'arsso wajan yana waya,wucewar wasu dak'ik'u sannan yagama wayar ya ajiye a gafenshi sannan yad'an kalleta kince in tsaya me zaki bani? Tabud'e gidan baya ta ajiye mishi wata madaidaiciyar leda ruwan hoda"Donut na maka, tarufe murfin tadawo wajanshi,wallahi tausayi yake ba ta duk yayi sanyi dama shi bame san hayani bane"sai yaushe zaka dawo?Ba rana sai dai kun ganni.Idanun ta suka cika da kwallah"dan ALLAH Yaya D'ansarai ka dinga cin abinci kaga yadda kazama kuwa?Ina cin abinci mana Sudaida ai d'an Adam bazai rayu ba abinci ba.Tad'an marariraice"to amma dai d'an tsakura ka keyi, kadinga ci dayawa,yamaida k'afarshi cikin motar tarufe murfin.Nagode Sudaida.kadinga cin abinci kaji?Tasake fad'a.To ya fad'a a tak'aice. Tasunkuyo"Allah ya kaika lafiya.amin Sudaida yaja motar tabi bayan motar da kallo har yayi nisa ya6ace ma ganinta,wani abu na mata kai-kawo a zuci,tasauke numfashi tabaki ta hanci sannan tajiya zuwa cikin gida ran ta ba dad'i. A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar alhamis suna cikin hutun makarantar boko na ranar yara(Children's day)kuma yau ba makarantar allo ba Islamiyya kowa yana abinda yake so ne, dan duk sun gama ayyukan gida.Tana kwance ranta ba dad'i tunda Julaibib yatafi sau uku kawai sukayi waya yauma takira shi sama-sama suka gaisa yakatse,tasake kira yad'aga da sallama"Yaya Julaibib na maka laifine? A ah baki min kome ba.To me yasa kike min wani iri? Yad'anyi murmushi"Sudaida kenan ni ban miki wani iri ba fa zan shiga aji ya katse wayar...Tayi lamooo a gadan,tunani barkatai ya cika k'wak'walwarta ta rasa na za6a tayi. Nasmat suka shigo suna hayaniyarsu kamar yadda suka sa ba,suka kalleta suka kwashe da dariya"Sudaida uwar tafakkuri (tunani)me kuma yafaru?Khausar ta ta6e baki tabud'e wadrobe ta d'auki kayan da zata goge a D'akin-shak'atawa tafita...Bata basu amsar tambayar su ba,takalli Zainab"ya maganar bikin saukar mu?Ta zauna a gefan gadan"ai Malam yayi tafiya sai ranar asabar zai dawo.A'isha tamik'e "barinje muk'arasa kallan mu dan yau bazan dad'e ba,angona Hashim anjima yana hanya.Nasmat tad'an daki kafad'arta"to gaggawa hannu hagu a romo mutumin da ko tasowa bai yiba.suka mik'e ita da Zainab.Nasmat tabi da Sudaida da kallo "dan ALLAH me yake damun kine?Tamaida kanta saman matashi"na fad'a miki ba abinda yake damuna to ki rabu dani mana.Sudaida na damu dake shi yasa nadamu da halin dakike ciki. Tamaida idanun ta tarufe...Nasmat ki kyaleni bana san hayaniya fa.Tamik'e ALLAH yabaki hak'uri, amma ina zargin wani abu koda yake...sai tad'an motsa kafad'a shikenan can da yawarki yarinya. Sai da aka cinye zangon karatu d'aya sannan Julaibib yazo gida.Yau alhamis ranar da ake bikin saukar Alqur'ani me girma nasu Sudaida,kome an shirya shi cikin mutunci, bangaran maza daban na mata daban Liman yabud'e taran da addu'a yama daliban addu'a Allah yasa suyi amfani da abinda aka koya musu a kowani irin hali da yanayi suka shiga na rayuwa...aka biyama d'aliban allunan su sannan aka cigaba da wa'azi da fad'akarwa akan neman ilmi dan shine yake sanya rayuwa tayi kyau tayi albarka. Bayan angama kome sannan aka shiga yin hotuna da rabama d'alibai kyaututtuka aka rufe taro da addu'a,Sudaida tasunkwui da kai abinda yaba mak'alallun k'wallan cikin idanun ta damar zubowa k'asa sharrr... wannan taran me tarin albarka mutane da yawa sun halacceshi amma banda Sinan,to me ya hanashi zuwa tunda ya sani?Tayi kwafa wallahi za mu had'u ne. Tana d'ago kai,caraf idanun su yahad'u, wani sanyi dad'i taji a ilahirin gangar jiki da sararin zuciyar ta. Alk'asim yak'araso wajan "gaskiya yan matan nan kun had'u,zai mik'a ma Sudaida rufaffen envelop A'isha takai hannu za ta kar6e,yajanye hannunshi da sauri"a ah ya haka? Tagyad'a kai"eh haka nake nufi,kai kaga hakan zata sa6u bindiga acikin ruwa? Wasa tare ci bamban?Khausar tace ko muma abamu ko itama tarasa. Yayi yar dariya "mata problem kunga fa ba wani abu bane a ciki,rubutune kawai akayi da biro bulu.Eh koma dai menene to abamu na mu. Nasmat ta katseshi"to wai ma yahaka?Ana zatan wuta a mak'era sai ga ta kuma a masak'a?Wallahi wanda nayi hasashen zai bata kyautar kaasatan bai yiba sai kai?Yamaida envelop d'in aljihu "shikenan karku samu damuwa za kuji a salansa, Sudaida sun hana in baki hannu da hannu zan aiko miki dashi gida,yajuya yayi tafiyarshi bai saurari hayagagar da suke mishi ba.Suka jera suna tafiya zuwa gidan Hajiya"Aisha tace wai me yahana Sinan zuwa wajan saukar mu,naga har Hashim daba d'an gari ba ya zo?Tawatsa hannu"nima ban sani ba amma ina ga kamar ba k'alau ba. Dayammacin ranar sai ga shi da kaya nik'i-nik'i lemukan gwangawani dana kwali, yana zaune a dakalin k'ofar gidan tafito cikin fushi Sagir na biye da ita da kayan,takar6a ta ajiye mishi "Sinan ba wad'annan nafi buk'ata ba,zuwanka wajan ya fi duk abinda za ka bani. Tajuya...Yasha gabanta da sauri yahad'a tafukan hannayen shi da sigar rarrashi"Sarauniyar Sinan kiyi hak'uri "Tagirgiza kai"ban hak'ura ba sai ka fad'a min abinda yahana ka zuwa.Yad'anyi jimmm... na wucewar wasu dak'ik'u"za ki yadda dani?Tayi shiru sai yacigaba"to ni dai na san na miki laifin da ban ta6a miki irin shi ba,Sudaida baccine yayi awan gaba dani,to ya zanyi?To wayar ka amfanin me takeyi na kira ka sau shurin masak'i baka d'aga ba,sai kace me baccin mutuwa? Yakad'a kai cikin damuwa"lallai na cancanci abani horo,itama fa wayar a yanayin shiru nasa ta,kiyi hak'uri Sudaida "ALLAH yana san masu hak'uri,masu had'iye fushi, suna da dama su rama abinda aka musu amma sai suke hak'ura su yafe,su maida kome ba kome ba saboda ganin girman ALLAH...yacika da dad'ad'an kalamai har sai da yashawo kanta. ALLAH da gaske ke nake so Sudaida alk'awari ba karyawa ni da ke sai mun zama abin kwatance mutu ka raba takalmin kaza. Da haka yaba Sagir kayan yamayar dasu cikin gida.. Kwana biyu da fara azumin watan ramadan yashirya shi da Musaddiq sai Matsirga. Inna tana zaune a d'aki taga ana shigo da kayayyaki tasa hijab tafito tsakar gida tana tambayarsu daga ina wad'annnan kayan? Sai ga Bello yashigo da murnar shi yana fad'a mata su Yaya Julaibib ne.Jikinta yayi sanyi tabi kayayyakin da kallo cikin zancen zuci"wato k'auna ta gaskiya tana d'orewa koda ba wanda ake k'aunar a doron duniya. Bello yarik'o hannunta "Inna na shigo dasu. Tayi murmushi"lale maraba,sannunku da zuwa bismillah tajuya zuwa cikin d'aki suka bita,cikin girmamawa suka gaisheta"Iyayan na ku k'alau ko? A lafiya k'alau Inna suna gaishe ku.To madalla ALLAH yamuku albarka,ku bakwa gajiya da hadima?Musaddiq yace"haba Inna ai bakome... yiwa kaine.To Ubangiji yasa ka muku da mafificin sakamakon shi;ALLAH yasa hakan amizaninku na kyawawan aiyuka. Amin,amin Inna. Inna su Malam basa nan ne?Eh d'azu shi da Maude suka tafi Zango wajan k'annin mahaifanshi,Tukur kuma jiya yakoma makaranta. Suka d'an ta6a hira sannan suka mata sallama taciko musu jarkoki da kindirmo da manshanu, Bello yasa kuka shi dole sai sun tafi dashi Inna tayi-tayi ya zauna amma ya kafe ya nata ihu shi dai zai bi su,duk yamak'alk'ale Julaibib ya 6ata mishi farar shaddar da yasa da majina da ruwan hawaye,yarik'o hannun shi. Inna bari muje waje muyi magana tabisu da kallo,a mota suka dinga rarrashin shi "kaga idan muka tafi dakai Malam bai sani ba idan ya dawo zaima Inna fad'a muma zai mana fad'a, yamak'ale kafad'a"uh uh ai idan tace kaine bazai yi fad'an ba,kuma kana da waya kafad'a mishi na san zai yadda,ni dai kawai ALLAH mutafi"to naji na kuma maka alk'awari idan aka samu hutu Insha-ALLAH zan zo in tafi dakai Zonkwa.Yad'ibo dabinon ajwa da yawa a aljihunshi idan ka yadda sai in bar maka wannan dabinon,yakalleshi sannan yakalli dabinon" to duka zaka barmin?Yayi murmushi"eh mana sa hannunka ka kwashe ma, yana ta d'auka da d'ai-d'ai da d'ai-d'ai yana sawa a aljihunshi har ya kwashe duka sannan yayi dariya aina kwashe, to sai ka zo d'in barinje in nuna ma Inna,yauwa Bello mutumin kirki barin rakaka,har ciki ya kaishi ya kuma fad'a mata yadda sukayi tayi murmushi kawai sannan suka sake yin sallama sunama juna asha ruwa lafiya. Rana ta tafi zata fad'i magriba na shirin kunno kai,an kusa shan ruwa takashe rediyon da take sauraran tafsirin Alqur'ani me girma a gidan rediyon jahar Kaduna(FRCN)farin gida kafin Sardauna.Tayi doguwar hamma tasa tafin hannun dama tarufe bakin ta, tana Isti'aza yau ba laifi tana jin azumin nan ajika dan ma yau Khausar ce da aiki da wallahi bata san yadda za tayi ba kanta har barazanar ciwo yake yi,daga can D'akin-girki tajiyo kiran Umma tamik'e da sauri tafita. Umma gani.Umma tamata wani kallo "ba tun d'azu nace ki d'auki dabgen Hajiya ki kai mata ba?Baki ji bane ko zuwan ne baza kiyi ba? Tad'an sosa kai Umma fa boss ce,bata d'aukar raini ko na sisin kwabo"Yi hak'uri Umma barin d'auko hijab,tasa hijab ta d'auki kwanan samiran sannan tad'an kalketa cikin shakka"Umma dan ALLAH daga nan zan biya gidan Inna.Tayi shiru kamar bata jiba sai da tagama zuba wani dabgen a wani samiran ta rufe sannan takalleta"adawo lafiya suma ki tafi musu da wannan.Wani murmushi yasu6uce mata dan ba k'aramin aikin Umma bane tahana"nagode Umma tarik'o hannun Hanifa'yar Musaddiq ta fari suka tafi. Tana shiga sai ga Nasmat itama takawo ma Inna hadaddan kunun aya kafin a kira sallar magriba sunyi alwala,ana kiran sallah sukaci dabino da lemun 6awo da ruwa me rangwamen sanyi sannan suka tada kabbarar sallah. Julaibib da Baba suka shigo da sallama sukama juna barka da shan ruwa sannan ya ajiye ledan hannunshi a gaban Inna.Nasmat tajawo ledan gabanta tafara shan abarban da yake ciki da kankana yankakku tana fadin"kyan rawa da makar6i.Sudaida ma tasa hannu ta d'auki kankana tana cema Hanifa sa hannu ki d'auka...Baba yayi murmushi ganin irin kallan da yake musu,yayi k'wafa yajuya zuwa d'akin shi Inna tana mishi dariya itama.Sudaida ta ka sa cigaba da sha, ranta ba dad'i har yanzu bai dawo yadda tasan shiba, ba wani kyan gani da yayi,yabar k'asumba ba wani gyara,kana mishi magana zai bika da wannan rikitaccen kallan,ya ya6a maka bak'ar maganar da ko barinje (mahauci) iya karta kenan. A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar laraba yana nazarin wani littafin tafsirin Alqur'ani me girma Hajiya tashigo da sallama,yamik'e da sauri yataro ta"maraba da zuwa Hajiyar mu,ta ture shi"kai tafi can matsa kabani waje,ta zauna a kujera tana murza k'afafunta,ya d'auko man zafi zai shafa mata tajanye k'afafunta da sauri"bana so.Yayi murmushi"haba Hajjaju makkatu wal madinatu gwiwata a k'asa,kaina bisa wuyana.Oho ashe kaima ka san kayi laifi,saboda ALLAH Julaibibi tunda kazo garin nan sau d'aya rakkin rak kazo gidana,ba fad'a to me yakawo wannan gabar? Kiyi hak'uri Hajiya bana jin dad'i ne.Tajijjiga kai tana mishi kallan nazari"kai Julaibibi tunanin Bilkisun ce yake susuta ka haka?Yagirgiza kai "haba dai Hajiya ba wannan bane. Yamik'e da sauri ya d'auko madara da maltina da kofi.Hajiya tabishi da kallo cikin mad'aukakin mamaki"ciwon har yakai ba ka iya yin azumi ne Julaibibi?Yadafe kai "Innalillahi.Ina yi, wai dama ke zan kawo ma na man tane.Tamik'e wa?Ni kaga tafiya ta.Yarufo gidan"barin taka miki suna tafiya suna hira"anjima da daddare zan zo miki hira sai ki tanadar min garwashi zan zo da d'anyan masara in gasa mana"To ALLAH ya kaimu har gidan Kawun shi yakaita. A D'akin-shak'atawa Sudaida ce kawai tana kwance a doguwar kujera tana waya,tamik'e zaune saboda shigowar su,kusan dak'ik'u goma sannan tagama wayar,tad'ago tana kallan Julaibib bayan ta d'ora ha6arta a kafad'ar Hajiya"Hajiyarmu you're welcome.Kin san abinda bature me jan kunne yake nufi da haka?Tajijjaga kai"tun kafin in haifi uban ki ya haifeki kuwa.Tad'an turo baki, Julaibib yayi murmushi yana shafa k'wantaccen bak'in gashin kanshi"Yo kya 6ata fuska ba tambaya kikayi nabaki amsa ba? Mu turancin mu ma gangariya masu abu da abun su kura da kallabin kitse, turanwan ne fa suka koya mana baki da baki,To me yasa bakya yi?Tad'an kalleta kaji wata magana to yaran turanci yarena ne?Ni yarene hausa idan takama ayi turan cin inayi mana"do you get me? Sudaida takyalkyale da dariya saboda yadda Hajiya tayi furucin tagyad'a kai"yes grandam.Su Mama suka shigo suna gaishe da surukar ta su cikin girma da mutuntawa. Da daddare yana gidan Hajiya suna hirarsu takalleshi"tunda katafi Azare kayi zaman ka shiru ba amo ba labari ko wata bafulatanarce takuma rik'e mana kai?Ya jujjjuya masarar sannan yad'ago yakalleta"ko d'aya Hajiya.To in dai haka ne ya kamata ka nemi wata,ga yan mata nan burjik a cikin dangi sai ka za6a ka darje,kana gani ganin idanun ka Musaddiq Ya'yan shi biyu ga cikin na uku nan.Cikin wasa yace"Hajiya banga wacce nake so ba ko za ki tayani nema?Tagyada kai"anyi an gama maye ya auri makauniya.Bai wani dad'e ba yamata sai da safe, saboda akwai tashi cikin dare domin yin munajaati ga ALLAH buwayi gagara koyo ga kuma tashi yin sahur. K'arfe-k'arfene sai dai a cikin k'arafan akwai zinare da azurfa. Idan baka san gari ba...saurari daka. Abdullahi Lawal Abdullahi (D'ansarai) Saudat Ibrahim Yahya (Takwara ta) Mungode da tunatarwan ku bisa wani kuskure da mukayi a shafi na goma sha biyar.. Falmata Maiduguri mungode da kulawa. 28 Jumaada Awwal 1441 23 January 2020 We Ibrahim's Daughters 👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASAOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'iba) Shafi nagoma sha bakwai. Bayan sallar asham Julaibib yawuce gidan Hajiya anan yatarar dawasu daga cikin jikokinta maza anata hira da ciye-ciye.Yajawo kaskon data cika da garwashi gaban shi, Musadduq yaja tsaki"Lillahi warasulihi yauma karasa abinda za ka kawo mana sai bushashshen masara?Kai ALLAH yasauwake.Ya amsa da amin "dan ka kawo mata bushasshen nama wai shi kilishi ba shi zai hanata cin gashashshiyar masara ba.Musaddiq yagirgiza kai"kai Malam ai yanzu ba lokacin cin kilishi bane,watan ramadan muke gasassun yan shila nakawo mata me ruwa-ruwa da yajin tafarnuwa ya ji kayan lambu.Yaturama Julaibib k'unshin duba kagani.Yayi kamar ba dashi yake magana ba yafara gasa masararshi yana tambayar Hajiya ta saurari tafsir na karfe uku da yammacin yau? Kwanci tashi har anyi azumi takwas, agida tasame shi yana shirin komawa Azare "tazauna tana kallan shi"Yaya D'an Sarai tafiya ba sallama?Yacigaba da shirya kayan shi a jaka ba tare daya d'ago ya kalle taba"ai naje gidan akace kin tafi Hayin-Dogo"haka ne to yaushe za ka dawo? Yarufe jakar yad'auki agogo yana d'aurawa a hannun damar shi"sai ALLAH ya kaimu sallah idan muna raye,ta taya shi kwashe kaya zuwa mota yayi sallama da Inna suka fito,tajingina da motar tana kallan shi cikin kissima wani abu a zuci yana zuba ruwa a lagireto har yagama yashiga mota yazauna yana d'aura belt. Yad'anyi murmushi"duk kinyi wata iri ko za ki bini ne?Ta turo baki gaba"da inada wannan damar ai da ba haka ba wallahi.Baiyi magana ba,yabata wasu kud'i"bayawa.Tasa hannu biyu takar6a"nagode Yaya D'ansarai ALLAH yak'ara bud'i,suka d'aga hannu suna ma juna adabo. Sun dawo makaranta suka tarar da Asma'u kanwar Sudaida ta ci kuka ta gode ALLAH idanun ta sun kumbura sun kad'a jawur"lafiya Asma'u? A tare suka tambaye ta,sai tasake jin wani sabon kukan ya kufce mata tafi minti goma sannan tafara rage sauti tana ta jera ajiyar zuciya"ke wai kukan me kike yi ana tambayar ki kin ma mutane shiru wacece sa'ar ki anan? Khausar ta tambaye ta.Taja majina tana hura iskar bakin ta"labarin zuciya a tamabayi fuska ranta in yayi dubu ya 6aci,cikin hawaye tafara magana"wai arasa wanda za a bani a matsayin mijin aure sai Yaya D'ansarai...wasu hawaye masu d'umi suka sake zubowa sharrr...sharrr...Sudaida tamik'e zaune da sauri kamar za ta hantsila,duk suka bita da kallo ganin yadda tayi sai kuma ta koma ta kwanta batayi magana ba dan ta ma rasa abinda za ta fad'a wallahi. Asma'u tacigaba bayan kowa ya san Alk'asim nake so amma ance a ah wai shi yaro ne ko Secondary bai gama ba,takad'a kai cikin takaici"saboda ALLAH wai Yaya D'ansarai. Khausar takalleta cikin natsuwa"bakya san shine? Dasauri tace"eh mana me zanyi dashi bak'ink'irin dashi kamar bak'in gashin kanshi...bata gama rufe baki ba taji saukar mari hagu da dama"Yaya D'ansarai kike za gi?To dame kwad'o yafi gaya?Ba gwamma shi bak'i kyakkyawa bane.Asma'u tamik'e cikin hawaye"amma wannan rashin 'yanci da yawa yake,ga mari ga tsinka jaka?Takalle ta "wallahi Yaya Sudaida bana san shi,tafita a d'akin da gudu cikin shashshekan kuka. Tadunk'ule hannu ta naushi iska"da kin tsaya k'aramar mara kunya da kinga yadda zan yi dake.Khausar takalle ta"ai baki isa ki kuma dukan taba akan me? Dan tace ba ta san shi shine ya zama laifi?Yaya Julaibib d'in?Kwarai kuwa shi wanene da kowa sai ya so shi so?Wa kika ta6a gani ko jin labari kowa na doron duniya ya so shi? Ko wanda yayi mu an samu wanda basa san shi ta hanyar k'in yadda da duk abinda yace ayi,da wanda yace abari,bare wani Julaibib ordinary human being,ai dama na dad'e ina zargin wani abu bani da tabbasss shiyasa naja bakina nayi shiru; to amma yau na samu yak'ini san Julaibib d'in nan ki keyi,to dake dashi d'in duk sai kuje kuji da manufurcin ku,ai shima ina lura da takunshi akanki.Yaya Khausar daza kice haka shi kuma Sinan d'in ina zan kai shi?Tawatsa hannu"ke kika sani... Cikin bugun zuciya tafara harhad'a littafan data barbaza a kan gado da niyyar yin nazarin su,ta tsuke baki tana yamutsa fuska Khausar tayi yar dariya tana rage kayan jikinta za ta shiga wanka Asma'u ta D'ansarai bak'ak'e biyu kila za su iya samar da wankan tarwad'a ko fari ko sarauniyar Sinan?Bata kula taba tamak'alama wayar ta earphone tana k'ok'arin toshe kunnuwan ta dashi. Khausar ta fizge"ke malama kirufa mana asiri karki zama kanwar kurma,so nawa ni da ke munajin bayanan da likitoci k'wararru a bangaran kunne,mak'ogwara da hanci(E N T) sukeyi,yawan amfani da earphone yana kawo matsala a bangaran ji"tagyad'a kai "naji bani wayata.Tamik'a mata, kita shi kisan abinda za ki d'ora tunda su Mama basa nan ko miyar shuwaka za ki mana mun kwana biyu bamu ciba wallahi,ta san Sudaida bata so dan tayi tsokana tafad'a. Yaya Khausar"ai bazan hana kiyi idan kina so ba"kuturu da kud'in shi alkaki ba sai na k'asan kwano ba?Gaskiya ne to d'anje kifara wanke min shuwakar kafin in fito wanka. Kwana biyu da maganar ranan Asma'u ce da aiki tasame ta a D'akin-girki tana kad'a miya sai ta kar6i maburgin barin taya ki,Asma'u tad'anyi murmushi "Yaya Sudaida saboda ALLAH ko kuma cin tuwon kishiya...?Duka biyun.Sukayi dariya, Asma'u tana zuba mata garin kuka tana cigaba da burgawa har suka gama, tad'an jefa kanwa kad'an wucewar wasu yan dak'ik'u tasauke to d'orama Yaya Aminu ruwan da zata dama mishi custard aranta tana mita"gaskiya Siddika ta shiga uku da shan kunu,ga fa kunun tsamiya can Inna ta aiko mai dashi amma duk da haka wai dole-dole sai ta dama mishi custard,ruwan yana tafasa ta dama tajuye mishi a flask. Tamatsa gefe tana cema Asma'u ai dai na taya ki,dan haka zo ki dora ruwan tuwon ki. Takalli Asma'u da natsuwa bayan tad'ora ruwan "waye yace za a ba ki Julaibib a matsayin mijin aure?Tayi d'an tsaki"na manta.Kin manta?Eh,to ban sa a ka ba inji 6arawon tagiya,sai kuma tayi kwafa"ba Hajiya ce da wannan neman maganar ba,haka kawai ga wanda zuciyata take marari... Tad'auki flask batace kome ba tajuya tafita. Asma'u tabita da kallo"yauma kinji haushi dan na ce ba shi nake so ba ko?Tad'an motsa kafad'a,sai dai kiyita jin haushin me zanyi dashi?Tad'auko garin dawa za tayi talge dan har ruwan ya tafasa. Littafan tane a saman tebur ta barbaza, nazarin su take so tayi d'aya bayan d'aya saboda ranar Litini za su fara jarabawa,tad'auki littafin lissafi tana dad'ayin nazari akan darasin da aka musu wancan makon Simultenous Equation sai dai ko dak'ik'u goma bata had'a ba taji ta gaji,ta kasa fahimtar kome duk da kuwa a wajan lissafi babbar k'waruwace,ita dai azumi yana ba ta wahala da mutum zai iya biya a mishi aikin ibada to ita dai azumi za ta dinga biya,kome a wahale takeyi,ta ture littafin gefe idan ba haka ba yanzun nan kanta zai fara ciwo kuma yau itace da aikin abin bud'a baki,a hankali taza me takwanta a doguwar kujera gwamma tad'an rintsa kafin lokacin aiki yayi,tad'anyi tsaki tun yanzu jikinta ya mutu murusss... ALLAH dai yasa Umma karta ba ta aiki me wahala. Kamar a mafarki tashak'o k'amshin arabi'an perfume tare da sallama.Dasauri tabud'e idanunta da suka canja kala dan bacci ya fara awon gaba da ita,yana jingine da k'ofar shigowa yayi sharrr...sharrr dashi cikin farin yadi me k'ananan huji-huji kana hango farar singilet d'inshi, bak'in gashin kanshi ya sha gyara yanata kyallin hair fruits,ba laifi yafara maida jikinshi sai taji dad'i a ranta. Tamik'e zaune cikin mamaki"Yaya D'ansarai?Yabar duba wayar hannun shi yad'ago yana kallanta "na'am,ina ta sallama baki amsa ba szumin tun yanzu ya fara duka kenan.Tayi murmushi"tad'anyi tsaki kai dai bari kawai, wai ba ka ce sai sallah za kazo ba?Yak'arasa shiga D'akin-shak'atawar"eh,yau da safe nazo anjima kad'an zan koma na manta wasu muhimman takaddune abinda yadawo dani kenan,yad'aga kiran daya shigo wayar shi, baiyi magana ba bayan sallamar da yayi,sauraro yakeyi... zuwa wasu yan dak'ik'u ya amsa da"nagode Maimun musha ruwa lafiya.Yasa wayar a aljihu,yana d'ago kai caraf idanunsu yahad'u yakauda kai...daga can tsakar gidan suka fara jiyo Asma'u cikin nishad'in ta,tana rera wasu baiti daga cikin baitocin wakar Sadi Sidi Sharifai da Maryam A.Baba(Sangandale)suka rera...tana tafe tana tafa hannaye. 🎶🎵Taho malam,taho gani nan da soyayya nafito daga gida🎵🎶 🎶🎵Ina shaidama a yau ne nasamu sak'onka, ina zaune a gida sai naji shi begen ka🎵🎶 🎶🎵Shine nafito in duba ko zan ganka🎵🎶 🎶🎵Amsar sak'onka na yarda in zam matar kazamo megidahhh...🎵🎶 Tana shigowa suka bita da kallo.Kunya da haushin shi suka rufe ta,tayi jimmm...fuska a yamutse tagaishe shi,bata jira amsawar shi ba ta d'auki abinda yashigo da ita"tin-opener"a saman tebur tajuya.Asma'u yakira ta.Sai tayi kunnan uwar shegu tak'ara sauri.A k'ofa sukayi kaci6is da Mama,takalleta da kulawa"saboda ALLAH Asma'u a wannnan gwalagwalan kwanakin nagoman k'arshe kika tsaya rera wak'a...?Tayarfe hannu "dan ALLAH Mama kiyi hak'uri kar Umma tajiyo ki, yanzu tashigo gidan daqowarta daga unguwa. Astagfirullah...Mama tayi murmushi"ALLAH yadad'a shirya ku. Sudaida tabishi da kallo bata ga wani yanayi a fuskar shi ba,yakalli agogon dake d'aure a hannunshi na dama,lokaci ya ja gashi har Matsirga yake so yaje kafin yawuce. Yad'an kalle ta"ke na wuce.Ta taka mishi har k'ofar gida inda ya ajiye mota"Yaya Julaibib ALLAH yatsare hanya, musha ruwa lafiya.Amin Sudaida nagode.Tajuya zuwa cikin gida tana zancen zuci"Yaya Julaibib bai san da maganar Hajiya akan an ba shi Asma'u ba. Asma'un kawai Hajiya tafad'a ma. Yau take sallah...kowa kagani yayi sharrr dashi dashiga ta burgewa ya kure adaka.Bayan an sakko daga sallar Idi Hajiya da wasu daga cikin jikokin ta suka mata rakiya zuwa gida.Me musu fid'an ragon sallah har yazo na Hajiya yake fara gyarawa kafin yawuce sauran gidajan, suna d'an hira da Sudaida tana kallan yadda yake yi cikin sauri da k'warewa. Julaibib yashigo da sallama,yana sanye da babbar riga,'yar ciki da wando na farin voil,takalminshi sau ciki da hular dara bak'a, k'amshin arabi'an perfume d'inshi ya cika tsakar gidan kamar lokacin yake fesawa, gyaran fuskar dayayi sai yak'ara mishi kyau"har ka cire kwalliyar sallar?Ba dole ba autan Inna,zanyi aikin fid'a da farar shadda ne?Zai shiga d'akin Hajiya yace "ka daiyi sauri kagama dan ga na Inna can yana jiranka.Tabi bayan shi zuwa d'akin. "Happy Eid-eel Fitr sarauniyar Sinan. D'an gajeran sak'on Sinan daya shigo wayar ta kenan,tayi murmushi.Tazauna tana kiran A'isha dan Kafanchan ta tafi wajan Kaka acan tayi sallah. Tad'aga da sallama,Sudaida ta amsa sannan tad'ora"zakara ya ja kaza kinyi sallah lafiya?Ta amsa"a ah mantawa kikayi takalmi ne yaja k'afa.Sudaida taja tsaki "ai wallahi sa a ma kika ci dana kira ki,keda za kiyi zaman ki shi Hashim d'in yazo nan yayi sallar wai sai kawai kika wani bishi...A'isha ta tari numfashi" ke dakata haka malama karki d'oramin jakar tsaba kisa kaji sudinga bina,wannan sallar nafara zuwa Kafanchan?Ni ba wajen shi naje ba wajan Kaka naje.Tasake jan tsaki"ba cinya ba k'afar baya. Itama ta amsa"a ah ALLAH yasa k'afar kafad'a ce, ke kika sani,ba Khausar wayar.Yaya Khausar gida tawuce ni ina gidan Hajiya.Tam barin kirata sukayi sallama. Asama taji Hajiya tana fadin"to na samo maka matar aure.Matar aure wace iri kamar yaya? Yatambayeta cikin rashin fahimta.Takalleshi"au ka manta yadda mukayi dakai cikin azumi?Ba ka ce in samo maka bane?Yakama kai"Innalillahi,Hajiya ni fa wasa nake miki.Tawatsa hannaye "kai kajiyo, amma dai aikin gama ya gama duk dai ban fad'a ma kowa ba sai yarinyar,to amma tunda kaima na fad'a maka to zan fad'a ma Iyayan na ku kowa yaji yakuma sani.Wacece ita?Tagirgiza kai"uh uh ba yanzuba ina so ne tad'an kara girma da hankali lokacin an kawar da Yayyinta. Shi da Sudaida suka kai juna.Yakauda kai cikin rashin sanin abun fad'a,yasauke numfashi,d'an madaidaicin kofin hannun shi ya ajiye a saman tebur."akara maka ne?Yakalli Hajiya kamar be ji abinda tafad'a ba na'am, a ah Alhamdulillah wannan d'inma ban shanye dukaba, yad'auki murfin yarufe kofin.Yad'an karkace kad'an yaciro rafar yan naira ashirin guda d'aya ya'ajiye agabanta"Hajiya ga nawa goron sallar ba yawa. Tayi murmushi"Julaibibi me yawan kenan ALLAH yayi albarka nagode madallah.Sai ga Nasmat ta shigo da babban foodflask cike tam da tuwon sallah"godiyar me wannan tsohuwar take yi? Idanun ta yasauka akan kud'in takama ha6a wai wai wai sai ta zauna"Hajiya lillahi warasulihi keda mutuwa tafara k'wank'wansa miki k'ofa me za kiyi da sababbin kud'i?Tamik'a mata hannu kawo su kawai,to ke me ma za ki siya ne? Hajiya ta d'auki kud'in ta"zancen ki dutse,zan kuma rasa ba ki, ki zauna jiran gawon shanu kinji ko?Takalli Julaibib"Autan Inna yau take sallah fa.Yamata wannan rikitaccen kallan na shi yayi-yayi tadaina kiranshi da wannan sunan amma tak'i "yan mata kyau da sallah idan tawuce sun zama jakai. Tagalla mishi harara"wallahi ALLAH yasauwak'e ai kaima ka san ba ma cikin irin wad'annan kucankan 'yan matan. Adai fad'ama wanda bai sani ba"ai kaima ka sani kana kuma gani ganin idanunka.Yad'an kalleta"uh ke dai abar tuna ba ya kawai wai gyartai ya ci sarauta,yajefa mata rafar 'yan naira biyar guda d'aya"ga shinan gaba d'aya 'yan matan dake zuri'ar Hajiya za ku raba,kowacce ki tabbata kin ba ta dan ba wacce zan kuma ba sisin kwabo na, yanuna Sudaida sai ki fara da ita.Tasa kud'in a jaka tabbb... Wannan shine tazo muji ta tawuce ta bayan kunni wannan nawane ni kad'ai kai dasu wallahi...bai saurare taba yama Hajiya sallama yatashi yatafi. Yaya Julaibib tabishi zaure.Yajuyo "na'am.Dan ALLAH rake za ka siyo min idan za ka dawo anjima.Yakalleta cikin natsuwa"Sudaida a ina zan samu rake yau sallah fa ai basa fitowa. Tad'an marairaice "ALLAH bayan sallar la'asar za a samu wanda yafito.Yad'an motsa kafad'a"idan an samu to.Nasmat da Sudaida su suka gyara naman suka soya ma Hajiya,dan dama sun iya kome an horasu da aiki. Yadda yake juyi a kan gadon cikin sulusin dare dan ba ya jin bacci,haka yake juya kalaman Hajiya"to na samo maka matar aure...amma dai aikin gama ya gama...yagyara rufa yana dad'a d'ora kanshi a saman matashin "hummm...wacece matar?Wacece ita? Yakad'a kai cikin sauke numfashi"ALLAH yajik'anki Megado... Wani tunani yad'arsu a zuciyar shi game da Sudaida,sai kuma yagirgiza kai"abun dakamar wuya...toh yanzu da Hajiya take wannan maganar "idan yarinyar bata mishi ba fa?Yana jinjina irin zaman da za ayi na har k'arshen numfashi ne fa, yagyad'a kai"abu mafi sauk'i suyi magana da Hajiya tafad'a mishi ko wacece,idan bata mishi ba toh a canja mishi da wata tun kafin Iyaye suji maganar. Daga masallaci sallar asubahi yaje yasa mu Hajiya da maganar amma fau-fau tak'i yadda suyi ta"wai ai yarinyar da d'an sauran ta,za ta fad'a mishi a lokacin daya da ce,kuma ba ta dawani makusa dole ma ya so ta tunda itama macece.Dole ya hak'ura yatattara yakoma inda yafi wayau...Ko hutunan da suka d'auka dasu Hajiya bai tsaya ya kar6a ba,dan Hajiya tace bata san wani hoto a waya,dole suka kira Misbahu me hoto ya d'auke su na kati,bai ma yi sallama da yan'uwa kamar yadda yasa ba ba. Tana wanke kayan makaranta Asma'u takawo mata waya"ga shi ya damemu da kira.Waye?Bata yi magana ba ta ajiye wayar a gefen ta,tajuya tayi tafiyarta. Aka sake kira tad'aga tana d'an turo baki kamar yana ganin ta"ni dai ALLAH na yi fushi.Shi yasa nake ta kira kika k'i d'agawa?A ah wayar tana d'aki na sa ta a caji,ni kuma ina tsakar gida ina wanki,ALLAH da gaske Yaya D'ansarai naji haushi dana je gida neman ka Inna tace wai asubanci kayi.To kiyi hak'uri. Nayi. Yauwa nagode ALLAH yamiki albarka. Amin. Sudaida...yakira ta. "Na'am.Baki fad'amin hotunan da mukayi a masallacin Idi sunyi kyau ko basu yi ba?Tayi yar dariya"sunyi kyau musamman wanda muka yi da Hajiya.To d'an turo min ta whatsapp"tabbb...ai kawai kayi hak'uri idan kadawo ka gani ganin idanun ka.Yayi murmushi "wato kin rama ko?To shikenan ki ajiye min,nima a makon nan zan shigo,kin ko ajiye min dambun naman ko duka kika ba wannan yaron?Ta gane wanda yake nufi amma sai tace"Yaya Julaibib wani yaro zan ba dambun nama har da na ka? Saurayin ki...yafad'a a dak'ile.Kai dan ALLAH Sinan d'in ne yaro?To dame kwad'o yafi gaya?Zak'i. Yabata amsa a tak'aice kafin tace wani abu ya katse wayar. Julaibib Abdullahi D'ansarai...Yana gama degree d'in shi na farko ya d'ora degree na biyu(masters) a dai Islamic Studies baya wani samun zama kullum cikin zirga-zirga tsakanin Zonkwa da Zari'a har ya kammala kome sai karatu da za a fara ba kama hannun yaro yazo gida yayi mako d'aya sannan ya tattara yakoma dan cigaba daka inda aka tsaya,shi dai Musaddiq bai cigaba ba sai harkar kasuwancin su ya keyi,yana kuma yin kome tsakani da ALLAH,kome a rubuce yake sai Julaibib ya zo ya nuna mishi. Sudaida tana zaune a tsakar gidan su Swachet wata yar ajin su ce ta je kar6o takaddun WAEC na shekara uku da suka wuce wanda Yayan ita Swachet d'in ya rubuta,tana so tad'anyi nazarin su,tana zaune zaman jiran Swachet takwaso matasu a d'aki.Tayi tsai...na wucewar wasu dak'ik'u da tunanin waye to da wannan aikin?Karo na uku kenan ana lek'owa ana komawa,to mutanan da suke shiga gida kai tsaye ko macece ko namijine indai ba mara gaskiya ba wazai yi haka? Tamik'e cikin sand'a dan san ganin ko waye.Caraf idanun su yahad'u,tabud'e idanu cikin mad'aukakin mamaki da tsoro, tanuna shi da yatsa"Sinan kaine kake lek'e?Me kazo yi anan unguwar? Ya sosa kai yana mata d'an murmushi" wai dama kece?me kika zo yi anan?Tayi jimmm... tana mishi kallan nazari kamar ba shi da gaskiya sai waige-waige yake yi"kar mu maimaita tambaya ba amsa mana. Yasake sosa kai yana murmushi "Sudaida sarauniya ta... wallahi na fito shan iskane kawai, sai kuma naga wata kamar ke shine nake lek'awa,yakalli agogon dake d:aure a hannunshi "kai jama'a lokaci fa ba wuya,kin san yau akwai wa'azin maza a gidan bak'i, muje mana,yad'ago yana kallanta har yanzu itama shi take kallo "lafiya kuwa Sudaida?Tagirgiza kai"ni mamaki kake bani wai duk girman cikin gari karasa inda za kaje kasha iska har sai ka shigo nan daba bahaushe ko musulmi me sallah ko d'aya? Ni fa wallahi Sinan ba na ga ne ma wasu al'amuran na kafa gaskiya.Anya Sinan...?Yatare da sauri cikin dad'in baki da rantsuwar ba abinda yakawo shi,har sukayi sallama yajuya da sauri yabar unguwar. Takama ha6a "Sinan fa kamar ba shi da gaskiya tajijjiga kai akwai lauje cikin nad'i. "Hey Ibrahim... Swachet ta dafa ta,me kika fito yi a waje? Sudaida tajuyo cikin sauke numfashi,sannan tasa hannu tazame hannun Swachet daga kafad'arta"na sha fad'a miki mu addinin mu na musulunci yaba Iyaye girma na alk'adari akan Ya'yan su, mu kome sunan mahaifin kane ba ka kiran sunan shi kai tsaye ba dan ya haife kaba sai dai dan yaci darajar sunan mahaifin ka ko mahaifiyar ka,ni sunana Sudaida to banga dalilin da zai sa ke kuma kidinga kirana da sunan mahaifi na ba,wannan al'adar turawar ba da Sudaida ba gad'a da fatalwa. Swachet tawatsa hannaye cikin halin-ko-inkula"ni banga wani abu ba fa.Takar6i takaddun tana gyad'a kai "tunda baki gane me nace miki ba ko?Tad'an ta6e baki tana yar dariya"Sudaida kin cika shagwaba tun muna JSS Class idan an miki abu sometimes sai kin turo d'an k'aramin bakin nan naki kamar gidan tsutsa gashi har yanzu as a matual baki bari ba haka zaki haifi Ya'ya idan sun baki haushi kidinga musu? Takai mata duka. Sukayi dariya.Muje in taka miki amma ba da yawa ba, dan akwai wanda nake jira.Sudaida takalleta da sauri"waye shi?Ko kema kin fara zuwa kwanan gidan ne.Tayi d'as da yan yatsunta"God forbid bad things ni da zan zama sister,ni bani da saurayi ma, sak'o kawai zai kawo min in kaima budurwar ta shi. Tibishi yatare shi"wai har ka dawo sai kace akan k'aya kake?Yafad'a kujera tare da lumshe idanun shi na wucewar wasu yan dak'ik'u sannan ya bud'e su"ai ban ma k'arasaba na had'u da Sudaida.Yacire kofin bommi(ruwan kwakwa) dayake shirin kaiwa bakin shi,yana mishi kallan uku ahu"to me kake nufi?Ya ajiye kofin a saman tebur yahad'a hannayan shi waje d'aya yad'ora ha6arshi akai"wai tsoron yarinyar nan kakeji?Har yanzu baice kome ba,ya daiyi tagumi yana zancen zuci"zan bar abinda nafara kawai tun kafin wankin hula yakaini ga dare,kwata-kwata bani da kwanciyar hankali.Tibishi yaja dogon tsaki sannnan yamik'e yabar d'akin yana zagin Sudaida, Sinan,hausawa dama duk wani wanda yake sallah harda Katafawa yan'uwanshi a jinsi da d'aukacin masu sallah na doron duniya gaba d'aya. Yatsaya a k'ofar D'akin-girkin yana kallanta tana kwasan tuwon dare,tayi kyau cikin riga da zani da d'ankwali na atamfa ruwan hoda da ratsin k'ananan filawoyi ruwan makuba,d'an k'aramin bakinta yanata kyalkyallin man le6e ruwan hoda"miyar me kikayi?Ta yamutsa fuska tana turo baki"labarin zuciya a tambayi fuska "miyar shuwaka.Yayi yar dariya"da kan ki? To Yaya Julaibib ya zanyi?Sarkin yawa ai ya fi sarkin k'arfi shi sukace suna so,na ce bazan yiba,Umma ta ce wai dole shi zanyi duk da itama fa ba wani so take yiba,ai wallahi gidan Hajiya zani bazan rasa abin sawa abakin salati ba.To yi sauri ki gama sai mutafi tare nima can zani barinje mu gaisa dasu Mama. A gidan Hajiya tana cin sinasir da miyar taushe,Julaibib da Hajiya suna hirar data shafe su,saiga Sinan yashigo da sallama.Hajiya ta amsa sallamar"wa alaikumussalam lale maraba da Sinan,bismillah.Yashiga yazauna cikin girmama yana gaisheta.D'ansarai yad'aure fuska ko kallan shi bai yiba yacigaba da duba wayar shi.Sinan yakalli sarauniyar ta shi kamar itama batayi maraba da zuwan shiba,yad'an sosa k'eya bayan ya ajiye ma Hajiya ledar d'aya shigo da ita,Maltina da madara ta ruwane a ciki "Hajiya ba yawa ni zan wuce."Hajiya tamishi godiya da sa albarka.Har yasa takalman shi Sudaida ba ta da niyyar ta shi.Hajiya takama ha6a tana kallanta ta"Oh ni 'yasu, Sudaida kar6i nan tamata dak'uwa.Tamik'e tana k'unk'uni. Shima Julaibib yamik'e"Hajiya magriba ta gabato.Tabishi da kallo "gaskiya ne gwamma ai harama dan a samu jam'i.Yazo yawuce su a k'ofar gidan kamar bai gansuba.Sinan yasauke numfashi "D'ansarai ALLAH yayi miskili,magana ta fatar baki bayan sallama rabon da muyi ta har na manta shekarar.Tad'an harareshi"ai dai ba ga ba yake yi dakai ba tunda zai maka sallama, rashin maganar ma ai kamawa takeyi a d'aure me d'aurewa.Yayi murmushi kawai"ba ta so ayi maganar Julaibib yanzu sai taji haushi,kad'an sukayi hira sukayi sallama dan anfara kiraye-kirayen sallah daga mabambantan masallatai. Tibishi yatari numfashin ta ta hanyar kyalkyalewa da dariya"mahak'urci mawadaci ne Zigwai, yabud'e hannunshi na dama, ya fa riga ya shigo tsakiyar tafin hannunki kin riga kin mishi kattt...kisan mummuk'e, bashi da wani kata6us sai yadda mukaja da akalar shi musamma ma ke; yad'auki kofi yazuba mata bommi"sha kijik'a mak'oshinki "tanasha suna dad'a tattauna yadda za su 6ulloma al'amarin,yanzu abinda za ayi ki kirashi a waya yazo yad'auke ki,idan kuma bazai samu zuwa ba to da yamma yazo Fajumali-Hotel. Tagalla mishi harara"kaima fa wasu lokutan shawarar ka ba ta d'auka bace.Kamar yaya ba ta d'auka bace?Tamik'e tana sa6a jakarta a kafad'a"to tayaya zan kama d'aki a Hotel d'in dake cikin gari tsakiyar hausawa?Sannan shi kuma kana ganin zai yadda ko hanyar yabiyo bare har aganmu tare?Yabata hannu suka tafa "shegiya yan mata wannan k'wak'walwar ta ki ba laifi tana ja,amma kafin ki wuce ya kamata kid'an bani na kashewa.Ta6alle jaka tawatsa mishi dubu biyu"kai kudin ka ba sa k'arewa a kome sai a burkutu(giyar k'ok'o) yanzu na san D'One zaka tafi.Suka fito yakulle d'akin yana bata amsa"kamar kin sani dan Alhamdu ma yana bina bashi. Cikin fushi yashiga d'akin tana zaune a kujera tana chatting,sai ta ajiye wayar tana mishi wani murmushi tare da gewaye hannayen ta ajikin shi tana mishi wani irin salon jan hankali"hey dude just chill up" abinda take mishi ya ka sa daurewa,dan haka yabiye ma yarima aka sha kid'a,wucewar wasu dak'ik'u sai ga shi yana kwasar dariya,yad'an shafa cikin shi"wallahi yunwa nake ji rabo na da abinci tun na safe.Tajawo abincin gaban shi "kaci ka k'oshi dakai na nadafa maka,dan ka fara zama na musamman a cikin zuciya ta,tasake kashe murya da wani irin salon na yan duniya"Sinan ALLAH ban had'a soyayyarka dana kowani namiji ba,saboda samun irin ka a cikin maza sai anyi da gaske,ina sanka Sinan.Yayi murmushin jin dad'i "ALLAH dagaske Zigwai? A yangance ta amsa"ga kai ga k'afa ai ba tambayar me aka yanka. Yakai loma bakin shi yana gyad'a kai"gaskiya na gani ganin idanu na, yagama cin abincin yamatsar da sauran gefe, wayar shi da aka kira ta katse musu hanzari, yad'aga cikin ladabi"a ah bana kusa amma dai yanzu zan zo,yakatse wayar yana kallanta "Babana ne yake son gani na yanzu.Tamotsa kafad'a"ba matsala,amma ai za ka dawo ko?Yamik'e"wannan dole ne bani mukulli idan nadawo ba sai nazo inata k'wank'wasawa ba koda kinyi bacci.tad'an taka mishi zuwa bakin k'ofa"kasiyo min balangu. Yagyad'a "kin samu balangu kin gama. Tibishi yak'araso yana dariya"akwai ranar kin dillanci...a ranar za ka gane da gero ake koko.Zigwai ta 6ata fuska"gaskiya ka daina zagin saurayi na.Yashige d'akin yana zagin ta"kaji yar duniya,saurayin ki ko dadironki? Tawatsa hannaye "what ever,idan ba haka ba zan fad'a mishi.Yaja tsaki"idan kin fad'a mishi sai me?A saran wa? Kafin me riga yarufa,me bargo yayi gumi. Yak'arasa cinye abincin da Sinan yarage,yana ta janta da hira tace"a ah zo kawai kayi tafiyar ka dan yace zai dawo.Yamik'e"to sai da safe,yakamota yana k'ok'arin ba ta sumba,ta ture shi"katafi mana indai ba kwa6armuce kake so tayi ruwa ba. Yak'ara matsawa kusa da ita"haba 'yan mata,dan dai d'an alakoran daza ki bani ai bazai sa ba bazai rage ba,tamu dake ba ta 6aci, yazuba mata idanu"anya banyi ihu da kirari na da6ama kaina wuk'a ba? Tagirgiza kai"bakayi haka ba Tibishi"marakiyi ai ba abokin tafiya bane" tamishi rad'a a kunni,ya bud'e idanu yana kallanta "ta jijjiga kai"na rantse da ALLAH da gaske nake yi,suka kyalkyale da dariya suka tafa"shegiyar duniya to mukwana lafiya,amma kirage min kayan dad'in daya kawo miki, tagalla mishi harara"ba zan ajiye ba d'an rainin hankali,kura da shan duka gardi da k'wace kud'i? Tibishi yana hango Zigwai ta sauka a kan mashin yatareta"me za kiyi a cikin gari?Tamishi wani kallo"ji wata banziyar tambaya kai me kazo yi?Ni cikin gari wajan zuwana ne.To nima haka zani wajan Sinan ne kwanaki hud'u kenan baya amsa wayata na tura mishi sak'onni sun fi guda goma nan ma ba amsa dan haka zani ingani ganin idanu na ko lafiya?Yad'aure fuska"ke Zigwai ina fata kina sane ke ba wata tsiya bace a wajan Sinan? Tayi shiru, yakalleta"to rashin jinshi a waya kuma ya samo asaline da irin zirga-zirgan bikin shi daya gaba to,kin san suna gama WAEC za ayi auran to saura kwanaki sugama zana jarabawar. Dammm...zuciyarcta buga. "Sinan zai auri Sudaida???!!! Tayi d'as da yan yatsun ta"incredible! Haka mukayi da kai Tibishi?To ko ba haka mukayi ba to ke kina ganin kai tsaye za kice Sinan yabar auran tane bai d'auki ke wacce taci kai ba? (hauka)Tarik'e k'ugu tana kallanta d'ai-d'ai kun mutanan da suke kai-kawo a cikin hantsin saboda sanyin da akeyi, suna tsaye sai ga su Sudaida sun zo sun wuce a mota,tabi motar da kallo har ta harba saman kwalta.Sudaida ma tagansu"wai a wannan mugun sanyin amma tayi irin wannan shigar me kama da tsirara,takada kai"ALLAH yasauwake.Tibishi yasauke numfashi"muzauna musan na kwatanci fa,kar k'aramar magana tazama babba, tagirgiza kai"ni fa yau sai na ga Sinan.Yad'aga murya dan tafara bashi haushi"wai ba na ce miki Sinan ba ya gari ba?To indai haka ne gwamma in koma gida dan ba saboda kai nafito a wannan sanyin Jauran ba.Yad'aga mata hannu "sauka lafiya. Sudaida tabishi da kallan tuhuma saboda karo na bakwai kenan ana kiran shi a waya yak'i yad'auko ta daga aljihu ma,bare yaga me kiran.Yad'an motsa kafad'a "share kawai.A share kamar yaya?Bai yi magana ba yaciro wayar a aljihu yana nu na mata kingani sunan Zigwai yafito 6aro-6aro a fuskar wayar sai yamayar aljihu yana mata bayani"wajan aikin mu d'aya dashi,to wasu takaddu yabani in cike,na kuma san tambaya ta zaiyi idan na cike su in kai office,ni kuma gaskiyar magana zuwa wajan ki yafi kai takaddun mahimmanci...ba zato sai ga Tibishi "jaba Sinan irin wannan abun da kakeyi ba kyau,ya kama ta aba duk me hakki hakkin shi. Cikin fushi Sinan yatare shi da hayagaga har abun yaba Sudaida tsoro da mamaki saboda irin zagin daya mishi"dan abu kazan uban ubanka baza a bayar ba ayi wacce za ayi dan dan iska kawai...idanun Sinan sun kad'a jawur saboda 6acin rai yanuna Tibishi da yatsa "ka6ace min da gani kafin in 6alle ka.Au haka kace? Yajijjiga kai"eh haka nace dan abu kazan ubunka.Yajuya yana kwafa"na rantse da ALLAH Sinan za ka gane da gero ake koko,za ayi walkiya kuma kowa zai gani ganin idanun shi;kura ce lullu6e da fatar akuya.Sudaida takalleshi"me kalaman Tibishi suke nufi ne?Yawatsa hannaye "Oho mishi ba mamaki yaje ya shata ne bata fad'a mishi gaskiya ba,zanbi shawararki kawai gwamma muyi hannu riga dan nagaji da rashin mutuncin shi.Tayi tsai tana kallanshi "rashin mutunci,to me yahad'aku da yake maka rashin mutunci?Bai bata amsa ba yasauke numfashi, yabata tsaraban Kaduna sukayi sallama. Tunda yakwanta yakasa bacci sai juyi yakeyi,zuwa can yamik'e yad'auki mukullin mashin yafita, gidan au Zigwai yatafi,tana tsaka da bacci yata sheta, tamik'e zaune akan gadan tana mitstsike idanu kamar gaske"na gaji da jiranka,tafara mishi abinda tasa ba, yarik'o hannayen ta,yakalle ta cikin natsuwa"Zigwai kiyi hak'uri da duk al'amuran da suka faru a tsakanin mu,kin sani aure zanyi,dan haka ba zan dinga barin matata ina zuwa wajan kiba,yaciro rafar d'ari biyar guda d'aya yad'ora mata a cinya "ga shinan ba yawa,amma a hakan idan kikayi maleji zai isheki kija jari, basai kin cigaba da sai da mutuncin ki a wajan sauran maza ba.Tafizge hannayen ta"me make nufi? Kana nufin mun rabu kenan? Incredible!rabuwa da kai ba abu me sauk'i bane,sai ta fashe da kuka,kuka me ta6a zuciyar duk wanda yaji bare kuma shi da ake kukan saboda ana son shi,ba a son rabuwa dashi.Idan yacigaba da zama za tasamu lagonshi dan haka yamik'e,dasauri tasha gaban shi"idan kamin haka kaci amanar kauna,wai duk irin sadaukarwar dana ba ka a soyayya?Yakalleta cikin tausayi da tafasar zuciya"ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yayi shiru,tagyad'a kai cikin hawaye"fad'i duk abinda za ka fad'a dan wanka da gari ba maganin yunwa yake yi ba"to kiyi hak'uri kawai ai ni da ke ba alk'awarin zama na har bada mukayi ba, bare kice na ci amana.Yajuya zai tafi. Tafara mishi wani salo daya sa shi tsayawa"Sinan na yadda za mu rabu amma ina fata baza ka sani a kwandon sharaba,idan mun had'u zamu dinga gaisawa.Yagyad'a kai"dan wannan karki damu.Takashe shi da murmushi "saura abu d'aya tsakani na da kai,kuma alk'awari kayi ranar birthday d'ina za kazo"you're the special quest of honour" idan ka halacci wajan to ka gama biya ta,kuma ka fita ko ba sabulu.Karki damu. Tasake shi yatafi. Tabishi yafito daga bayan labulen daya zagaye d'akin,nan yashige lokacin dayaji tsayuwar mashin yalek'a ta taga yaga Sinan ne, sukayi dariya suka tafa,yakai hannu zai d'auki kud'in a saman tebur tariga shi.Yakalleta "banga ne ba.Tagyad'a kai"ai nima zan fiso kaita zama cikin rashin ganewan,wallahi idan na ba ka dayawa dubu biyar.Yakarkace kai yana kallanta da mamaki"dubu biyar zan samu?Tazuba mishi idanu"to ina laifi dubu biyar a wannan marran,karanka ne yakama?Yakad'a kai"lallai kin cika yar duniya hayak'in taba.Takwanta tana dad'a jan bargo"maraina kad'an dai 6arawone,malam idan za ka kwanta kazo ka kwanta,idan ba ka jin bacci to ta shi kasan nakwatanci karka hanani bacci gobe sammako zan buga zuwa Zuturung. Yagalla mata harara"zuwa wajan wani dadiron na ki?Takyalkyale da dariya"ina da wani dadiro ne daya wuce kai?Hummm...bari dai mugama da wancan shegen bahaushen sai muzo mufara shirin aure. Suna cin dafaffiyar masara tashigo da sallama tazauna tana gaishe da Hajiya tare da fad'in "Hajiya gani ance kina kirana"Hajiya tabita da kallanta nazari, tarame tayi wata iri ba ta cikin wal-wala gidan na tama yau kwanki biyar kenan bata zo ba,shine ta aika akira ta"kwana biyu ban gan kiba ko lafiya?Lafiya lau"ta amsa a tak'aice.Hajiya ta gyad'a kai"to d'auki masaran kici mana,ni fa gaskiyar magana yarinyar nan ba ta da lafiya,Julaibibi wai ko kuna ganin yadda take k'arewa kamar kud'in guzuri? Dammm...zuciyar shi tabuga daya d'ago Yakalle ta, yacigaba da kallan ta ba tare daya ce kome ba.Hajiya tagyad'a kai"ah to kaima ka gani ko? To tunanin auran ne yamaida ke haka kome? Shima Sinan d'in kwana biyu shiru ko dai kunyi fad'a ne? Zuciyar ta tayi rauni,ba abinda take son yi sai kuka,bata 6ata lokaci ba tafara sharar kwallah a hankali sautin kukan kefitowa hawaye sharrr...sharrr...masu d'umi suka fara sintiri a fuskarta,tacigaba da kukan ta har da sheshshek'a;ba wanda yahana ta sai da taci tak'oshi sannan dan kanta tayi shiru,tahaye gadon Hajiya ta kwanta.Julaibib yayi shiru ran shi ba dad'i"mecece matsalar Sudaida ne?Kira yashigo wayar ta tad'aga da dishashshiyar murya"ina gidan Hajiya ne,tad'anyi sauraro...kayi hak'uri Sinan bana jin dad'i ne kabari sai gobe ko kuma kaba Yaya Khausar za ta ajiyemin...Cikin shashshek'ar kuka tace"to Sinan nagode... Hajiya tata fa hannaye cikin sallallami "Oh ni jikar mutum hud'u,amma wannan yarinya ALLAH yashirye ki,ba yanzu nagama tambayar ki ko ba ki da lafiya ne kikace ke kalan ki ba?To ai shi kenan kowa rai yama dad'i barin me shine. Tamik'e tana sa hijab.Sai ina? Julaibib ya tambayeta.Tad'auki mukulli tana kallanta Sudaida "idan kin gama kwanciyar jin dad'in za ki tafi gida ban dawo ba to dama karki kuskura kibar min k'ofa a bud'e,tamaida kallanta ga Julaibib"gidan Sahura za ni.Hajiyarmu adawo lafiya,nima dana gama cin masarar hannuna zan tafi. D'akin yayi shiru wucewar wasu dak'ik'u har yagama cin masarar ya ajiye totuwar yamik'e yana kallanta"tabbasss duk wanda yayi ihu to taimako yake nema"Sudaida ALLAH yadafa miki akan damuwar ki.A raunane ta amsa"amin Yaya Julaibib nagode.Yaja numfashi yafitar da iskar tabaki ta hanci"ni gobe zan koma makaranta, inaga sai ranar d'aurin aure Insha-ALLAH da sassafe zan taso,na san zan samu d'aura aure,su Nasmat duk sun fad'amin abinda suke so in sai musu,ke ma me kike so in sai miki?Tamik'e zauna da sauri cikin rawar muryar data rasa dalili"sai ranar d'aurin aure?Kana nufin bazan sake ganin kaba sai ranar da ALLAH yayi?Kwallah yacika idanun ta.Cikin rashin fahimta yakalleta"kamar yaya sai ranar da ALLAH yayi? Yaya Julaibib ranar d'aura aure to a ina zan ganka? Kuma ranar za a kaimu gidan aure,washe gari za ka koma makaranta to yaushe zan ganka? Kana nufin sai ranar danazo gida idan kana gari sai mu had'u?Ko zaka dinga zuwa gida na?Yagirgiza kai"me kike so Sudaida? Yayi tambayar da wata irin murya data sa Sudaida d'ago kai da sauri tana kallan shi cikin dukan zuciya. Yadafa k'irjinshi dai-dai saitin da zuciya take"zuciyata ayan kwanakin nan tana min wata irin bugawa da ban san abinda zan kwatanta miki ba Sudaida, na kuma rasa gane dalilin haka,ni fa tun bayan rasuwar marigayiya(Bilkisu)har yanzu ban samu kwanciyar hankali ba,bana yin ishashshen baccin da masana a harkar binciken lafiyar d'an Adam suke bada shawarar a kalla duk dare kayi baccin a wanni takwas. Yasake kallan ta cikin natsuwa "Sudaida kome da kika ga ina yi dauriya ce kawai; amma ciwon yana nan a zuciya ta kamar yan awannin da suka shud'ene,yad'an yi yake"koda yake baza ki fahimci radad'in rabuwa da masoyi ba!!!toh ina miki fatan alheri a gidan auran ki dafatan zama na har abada,mutu ka raba takalmin kaza,ina miki fatan samun babban rabo a alk'iyama Darul-karamah dake da zuri'arki...Yaya D'ansarai...yakauda da kai,yakuma riga ta magana"tunda baki fad'i abinda kike so ba,toh zan ba Asma'u gudummawa ta, zata kawo miki har gida.Bai jira amsawar taba yajuya da sauri yatafi.Tabi bayan shi da kallo dan ya mata susa a inda yake mata k'aik'ayi. "Rad'ad'in rabuwa da masoyi!... Tafad'a tasake maimaitawa,rad'ad'in rabuwa da masoyi!!! Sai tasa kuka wasu zafafan hawaye suka zubo mata sharrr...sharrr...wallahi Yaya D'ansarai nima ina jin rad'ad'in... wai...! wayyoh...! ALLAH na!!!! Nasmat data shigo tayi tsai...tana kallan ta cikin nazari,tarik'e ha6a"ikon ALLAH nazaune ya fad'i,a zaure sukayi kaci6is da Julaibib yana cikin damuwa tana mishi godiyar gudummawar daya ba yar a ba ta,sai yamata wannan rikitaccen kallan na shi yayi kamar baiji abinda take fad'a ba yayi tafiyar shi,tana tunanin me yasa meshi tashigo, toh ga Sudaida itama a wani irin yanayi. Tazauna a gefen gadon sannan tadafa kafad'ar ta"jimamin rabuwa da Yaya D'ansarai ne yasa kike wannan kukan ko me? Tarungumo ta"ni fa na shiga rud'ani, Nasmat ban san abinda yake damun zuciyata ba wallahi,amma ko a yanayin bugawarta ta canja,tsoro nake ji... tasaki Nasmat tana tsaida kukan"Nasmat bana san auran nan...Dama kawai a kyale ni. Takad'a kai"lallai ma Sudaida na ki wasa ne;kema kin san baza ta sa6uba... Idanun ta suka cika da kwallah"to ni wai ya zanyi ne? Ya za kiyi dame? Har ta bud'e baki za tayi magana sai kuma tayi shiru.Nasmat tayi yar dariya"Sudaida sarauniyar Sinan,kin san me? Kuka bai ta6a zama mafita a cikin matsala ba"ALLAH mahaliccin me kowa da kome za ki kaima kukan ki,zai taimake ki ta inda ba kya zato,nima na yadda ciki ba dan aci tuwo kawai akayi shiba,tabbasss a kwai abubuwan daya kamata yazama sirrin kane,sirri ne kawai tsakanin ka da zuciya.Tamik'e tana rik'o hannayan Sudaida"kin san a kwai makarantar Islamiyya lokaci kuma ya kusa,gwamma muje mu shirya dan ina tsoron ALLAH ina kuma tsoron dukan makaran Malam Jama'are da wannan shar6e6iyar dorinar,tamik'e suka kulle ma Hajiya k'ofa... Ana dara ga dare ya yi... Da sauran kuka anci gumba an hana maye. 2 Jumaada Thani 1441 27 January 2020 We Ibrahim's Daughters 👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi nagoma sha takwas. Julaibib yana gidan Yaya Karima yana mata sallama Baban Abdul yashigo,yamik'a mishi hannu sukayi musafaha"Malam D'ansarai ya karatu? Yayar ka ta fad'amin wai gobe za ka koma nace haba-haba dai ba shekaran jiya kazo garin ba?Yad'an sosa k'asumbar shi"ai yanayin karatun ne sai a hankali.Baban Abdul yagyad'a kai "maganar iyali kuma shiru mak'atau bulaguro a k'iyama tun bayan rasuwar marigayiya,ga shinan kana kallo k'annin ka mata shida za a aurar.Yayi murmushi"ALLAH yaba su zaman lafiya,amma gaskiya ni yanzu ba aure agaba na.Baban Abdul yanu na shi da yatsa"kai Malam D'an Sarai kar kayi butulci fa...yatare shi da sauri"ba haka bane Baban Abdul,shi aure d'an lokaci ne idan lokaci yayi mutum ko bai shirya ba dole sai yayi.Haka ne kuma"To Ubangiji yaba ka macen albarka,amma idan a kasa himma abun zaifi tafiya yadda yakama ta,a kawo k'arshen zaman tuzuran cin nan.Yayi yar dariya kawai sukayi sallama. Ango ka sha k'amshi.Yayi murmushi. To ya shirye-shirye ance aski idan yazo gaban goshi ya fi zafi ko?...Tacika shi da surutu yatare ta"Zigwai nagode da gaisuwa yakatse wayar. Tasake kira yad'aga,cikin dariya tace"haba na Sudaida ba da kan ka asare idan kaje gida kace ya fad'i,ai ban gama ba.Baki gama me ba?Kamar Yaya,me ye tsakani na dake? Babu,sai dai abu d'aya yarage a tsakanin mu,idan kuma kacika alk'awari to ba kare bin damo maganar birthday party na.Na sani ban kuma manta ba,zan cika miki wannan alk'awarin.Yauwa very good.Ita tariga shi katse kiran. Umma tashiga d'akin tasame ta a kwance"ke Sudaida me yasa kin cika kafiya ne kamar mutanan farko?A raunane takalle ta"Umma kaina ciwo yake yi matsananci kamar zai rabe gida biyu.Umma tad'aga murya"ki shirya kutafi makaranta kin nok'e ba kya jin dad'i, kici abinci kin kafe ba kya jin yunwa,kisha magani kin bud'e taga kin watsasu waje,to me kike so a miki?Tayi shiru idanun ta sun ciko da kwalla.To ki tashi maza-maza kifita yana jiran ki a waje.Tamarairaice Umma...Umma ta tari numfashin ta,tanu na ta dayatsa"ke kul...tashi nace.Jiki a sanyaye tamik'e tana goge hawayen da suka zubo mata da gefen farin hijab d'inta. Ba kowa a k'ofar gidan,sai kawai tayi zaman ta a d'an k'aramin dakalin dake tsakanin filawoyin wajen"Sinan gajiya yayi kenan yatafi?A hankali tsigar jikin ta yafara ta shi,sanyin yana ratsa ta, a takure tahad'a kai da gwiwa,tafara karkarwa hak'oranta suna dukan juna,tamik'e dak'yar zata koma gida.Yana tsaye ya nad'e hannayen shi a k'irji,yabi ta da kallo tana sanye da doguwar riga na atamfa me duhu da farin silifas, d'azu a gidan Hajiya riga da zani da dankwali na shadda ruwan toka ne a jikin ta,fuskar ta tayi fayau babu kwalliya,idanun ta sun kod'e dagani ba tambaya taci kuka ne fiye dana d'azu ta gode ALLAH. Luuu tatafi kamar za ta fad'i saboda jirin daya fara d'iban ta,a hankali takoma ta zauna,tasa duka tafukan hannayenta tarufe fuskarta tana k'ank'ame jiki dan bata daina jin sanyin ba."Sannu Sudaida jiri ko? Tagyad'a kai. Sudaida yakira ta.Tacire tafukan hannayenta a fuska sannan takalle shi,yamik'a mata Farm-pride yoghort d'in hannun shi"ki daure kisha.Tawani marairaice"Yaya Julaibib bazan iya sha ba,amai zanyi.Yazauna a gefen ta sannan yayi k'asa da murya cikin rarrashi"haba Sudaida kiyi hak'uri kisha zai miki magani,rashin cin abincin ki ya dame ni,Sagir ya fad'amin kinfi mako d'aya a haka,kullum sai Umma ta tasa ki a gaba kike cin d'an kad'an,yabud'e mata "d'an daure kisha kinji ko? Yaya Julaibib amai zanyi zuciyata tana ta tashi fa.Yagirgiza kai"uh uh kar6i kisha baza kiyi amai ba rashin cin abincin ne yasa miki ta shin zuciyar.Tasa hannu biyu takar6a,kad'an ta kur6a tamik'a mishi, yagirgiza kai"d'an kara...da haka har sai da tasha rabi,yakar6a yarufe yamik'a mata anjima kidaure kishanye zai miki amfani,kinga yadda kika zama kuwa Sudaida?Takaryar da kai gefen dama"kai baza ka shaba? Uh kisha kawai. Tamik'a mishi hannu"d'an ban dabino... baya rasa dabino a aljihu yasa hannu ya d'ibosu"guda uku suka rage.Tasa hannu biyu takar6a tana ci. A mashayar"Beer Parlour"suka had'u da Zigwai.Yaja kujera ya zauna yana kallan ta tana shafama faratanta jan farce ja,tad'ago takalle shi"daga ina kake tun d'azu ka shanya ni?Daga cikin gari mana,na je samo kud'in kashewa ne tunda ke muguwa ce fiance d'inki ba shi da kud'i amma baza ki iya taimaka mishi ba.Tagalla mishi harara"in taimaka maka fa kace?Kai bakaji kunya ba kura da shan duka gardi da kar6e kud'i? Yamotsa kafad'a"a very stingy woman,ba wata kunya dana ji,kin san da ina dashi bazan tambaye kiba,tare ma zamu kashe su. Tagama shafe faratan ta sannan tasa nailpolish d'in a jaka,tabi wajan da kallo ya cika dank'am da mutane maza da mata ga hasken disco light kore,ruwan bula da ja,wasu na shaye-shaye,wasu suna bin wakar da aka kunna a k'atuwar rediyon,tamaida kallan ta ga Tibishi "birthday party na bazai yiwu a ranar lahadi ba,na maida shi ranar juma'a.To saboda me?Tad'ora duka hannayen ta a saman tebur d'in"dole ranar juma'a zan yi shi saboda ranar juma'ace d'aurin auran Sinan ka gane manufa ta?Yajijjiga kai"na ga ne,kinyi tunani me kyau,amma fa a tsorace nake kar kwa6armu tayi ruwa.Yaba ta k'warin gwiwa "hey just chill up"kwa6armu baza tayi ruwa ba,duk abinda zai faru indai munci gari ba damuwa,ai ranar biyan buk'ata rai ba a bakin kome yake ba inji k'uda. Da yammacin ranar laraba,rana tayi sanyi Hajiya takira layin Julaibib yad'aga da sallama yana yar dariya"Oh Hajiyar mu na yi kewar kifa"taja tsaki"kai tafi can kaba ni waje,ka yi kewa ta amma tunda kasa k'afa kabar garin nan kaka sa kirana?Ayya Hajiya ta ke kad'ai,kin san d'an makaranta yana fama da geron Sunday(garin kwaki\rogo)ba ta siyan katin waya nake yi ba.Yadda yayi maganar cikin jimami da tausayin kai yasa Hajiya tayi dariya"Julaibibi kana dani amma katsaya fatarar katin waya?To bari yanzu za kaji alert..Yauwa Hajiya ta nagode miki ba kad'an ba Ubangiji yak'ara girma.Amin Julaibibi. Hajiya ina cikin damuwa,na ka sa samun natsuwa.Ashsha me yake damun ka Julaibibi?Tun ranar dakika fad'amin kin samo min matar aure,Dan ALLAH Hajiya ba wai butulci zan yi da za6in ki ba,dan na san baza kimin za6en tumun dare ba,to amma alfarma d'aya nake nema kifad'amin wacece ita?Taja tsaki"na d'auka wata lalura ce ke damun ka?To yar gidan Kawun kace.Wane Kawun nawa?A ah to kuma nan d'aya ni dai nafad'a maka sai ta k'ara girma,yo data isa aure tare za a had'a dana su Sudaida ta k'arasa karatun a gidan ka.Yar karama ce kenan,ajin ta nawa?A ji d'aya take a ka'aramar Secondary idan kuma kana so ayi bikin ta girma a d'akinta to,kayi rainon ta yadda kake so.Yayi shiru kamar baiji abinda tafad'a.Hajiya tayi dariya"Julaibibi na to sai anjima ta katse wayar.Yahura iskar bakin shi bayan ya maida wayar shi aljihu,yayi tsai...cikin tunani Kawun nan na shi ai suna da yawa,kuma kowanne yana da tarin ya'ya mata,yayi iya tunanin shi amma bai canko ko wacece ba, yarik'e kugu yana bin d'akin na shi da kallo... Sinan yana tsaye da mahaifin shi yana ba shi sak'on wasu kayayyaki da zai siyo mishi a Kaduna,Zigwai tak'araso wajan,tana sanye da matsatstsun riga da buje na material ruwan d'orawa an mishi d'inkin rashin mutunci da rashin sanin kimar kai,tantirancinta ya bayyana, tana rataye da bakar jaka,takalmanta masu rufi da tsinin diddige bak'ak'e"Sannu Alhaji tad'an rusuna tana gaishe da mahaifin shi,wani abu yadaki zuciyar Sinan, yad'auke kai daga kallan k'urullan da take mishi.Alhaji yakalle shi sai ya sunkwui da kai.Zigwai tayi wata yar dariya irin ta yan duniya"Malam Sinan angon Sudaida.Yad'ago yana murmushin yak'e,sai ta mik'a mishi envelop "sak'o nakawo maka.Yak'ar6a yana mata kallan tuhuma. Tajuya tayi tafiyarta tana murmushi"za ka gane da gero ake koko, Sinan ai sai dai muyi biyu babu. Suka kalli juna shi da mahaifinshi "yadafa kafad'arshi,Sinan ba girma a ganka kana mu'amala da irin wad'annan k'adangarun barikin, ka san shaid'an baya raina k'ofa.Yagyad'a kai "Baba baka yadda dani bane?Sinan ba rashin yadda ce tasa na fad'a maka haka ba,illah gyara kayan ka...ai kai ba k'aramin yaro bane,sai dai tunatarwa tana amfanar da mumini,ai mun ba ka tarbiyya gwargwadon iyawarmu,idan kaje kayi wani abu sa6anin wanda muka d'oraka a kai,to ai ALLAH yana ji yana kuma gani wannan tsakanin ka dashi ne,bazai kama mu da sakaci ba,ni dai idan za kayi sara to kadinga duba bakin gatarin ka, kasan da irin mutanan da za ka dinga mu'amala, ina jiye maka kaidin irin wad'annan da suke ji kamar su juwo mutum ta k'arfin tsiya ya dilmiya. Jikin shi yayi sanyi,yayi nadamar abinda yafara "nagode Baba.Alhaji Kamal yashige motar shi yatafi. Yazauna a wajan cikin damuwa"to wai ma me yakai shi k'ulla mu'amala da Zigwai? Sun gama jarabawa anyi speech and prize giving day anyi angama lafiya,kowa ya koma gida zaman jiran sakamakon girbe abinda aka shuka.Maganar biki ya dad'a kankama anata shirye-shirye,amare ana shan gyara Umma ce a wannan harkar dan kunsan ita bata d'aukar raini kona sisin kwabo ko ba dan ALLAH ba kowa sai ya bi. Jajibarin auren su Sinan kai ya d'auki zafi baya samun zama,yana sa takalmi Tibishi yashigo yana kallan shi"maganar birthday party na Zigwai zan tuna maka fa.Yakalle shi rai a 6ace"Tibishi karabu dani,dan ba wannan ne a gabana ba.Yajijjiga kai"nima na sani to amma karka manta alk'awari kad'auka.Yagama sa takalmi yamik'e "Tibishi ta shi katafi akwai inda za ni,suka fito Sinan yakulle d'aki kowa yayi hanyar shi. Bai dawo ba sai kwanciyar bacci a na ta dad'a gyara gidan amarya,sai da ya tabbatar kome ya kammala sannan hankalin shi ya kwanta, sai lokacin yasamu damar kiran Sudaida.Tana ganin kiran shi tad'an harari wayar tana k'unk'uni, sai da yakira sau uku sannan tad'aga"Sudaida sarauniyata...tatari numfashin shi"ni ba wata sarauniyar ka tunda tun safe baka nemi ni ba,na kira ka na jita a kashe,ni fa kana 6ata min rai. Wayyo ni Sinan to kiyi hak'uri ina can ina hidimta ma muhalllin kine,amma ko ina naje to tabbaci hak'ik'a kina cikin zuciya ta, ina son ki Sudaida... Tace hum...yacigaba'irin soyayyar da baza ta fad'uba,yayi yar dariya ALLAH dai yakai damo ga harawa ko baici ba yayi burgima,gobe war haka kin zama sarauniyar Sinan ta hak'ik'a,farin cikina zai fara daga gobe ne...yayita maganganun shi batace kome,basu wani dad'e yamata sallama dan zai kwanta ya gaji lik'is. Farar rana me kyakkyawar suna, wato juma'a.Yan'uwa da abokan arziki cike da gidajan biki an karkasa ayyukan shi yasa nan da nan akayi aka gama.K'arfe sha biyu da rabi Julaibib yasamu isowa garin.Yashiga D'akin-shak'atawar Inna ana gaisawa.Yaya Karima takalle shi"ai na d'auka baza kazo ba.Yad'an shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi"Yaya Karima yanayin karatun ne sai a hankali. To ALLAH yataimaka.Amin.Yawuce d'akin shi dan shirin masallaci.Yana sanye da babbar riga,'yar ciki da wando na farar shadda getzner,hular shi k'ube da aikin babbar rigar shi ruwan toka da ratsin fari da bak'i, takalmishi sau ciki fari,agogo da zoben shi na farin azurfa sai d'aukar idanu sukeyi saboda hasken su, k'amshin arabian perfume d'inshi me dad'in shaka,ya cika wajan.Duk suka bishi da kallo.Yaya Karima tace "gaskiya autan Inna kayi sharrr...dakai kamar wani ango,Yayi murmushi kawai"kice ma Inna na tafi masallaci. Yau gaba d'aya hud'ubar akan aure da ma'aurata akayi,bayan an idar da sallah anyi addu'o'i an shafa,auran Hashim da Aisha aka fara daurawa,sai Muhammad da Zainab,Abdullahi da Maryam,Abdulkarim da Nasmat,Huzaifa da Khausar...sai na Sinan da Sudaida da ake shirin d'aurawa,to amma wani wawan burki da aka taka sai da yatshi hankali jama'a,wasu suka fito daga masallacin dan ganin abinda yake faruwa. Sinan ne yafito daga cikin motar yana sambatu da tam6elen mashayar...Su...Sud... Sudai...damata...ta..taceba...wanda...zai...raba ni da ita... alk'...wari...ba karyawa mutu ka raba takal...min kaza. Ciki da wajan masallaci kowa yayi d'ifff...ya cika da mad'aukakin mamaki na ganin Sinan a wannan yanayin, a hankali k'ananan surutai yafara ta shi. Alhaji Kamal sai da numfashin shi yad'auke na wucin gadi yayi mutuwar zaune,dan abun ya kad'a shi"Innalillahi Wa'inna Ilaihi raji'un yake maimaitawa, Liman yakalle shi"dama ka san d'an ka yana shan giya? Yakad'a kai cikin damuwa "Liman bazan maka k'arya ba wallahil-azim ban sani ba,ban san kome game da Sinan ba sai halaye masu kyau. Sinan d'in aka fitar daga masallacin dan yafara kakarin amai.Liman yakalli mahaifin Sudaida meye abin yi? Kafin yayi magana Alhaji Kamal ya amsa"ba za a d'aura ma Sudaida d'an giya ba,irin wannnan hukuncin zan zartar ko 'ya tace wallahi,dan haka ina rok'on alfarma a d'aura auran nan da k'anin Sinan,yanuna Hamidan dake zaune a gefen shi cikin 6acin ran abinda Sinan yayi.Liman yabi sauran jama'ar da kallo,yasauke numfashi"k'warai zan so haka,to amma wani hanzari ba gudu ba idan aka had'asu aure Sinan bazai barsu suyi zaman lafiya ba, zumuncin dake tsakanin su na shak'ik'an juna zai samu tasgaro, indai ba tsananin sa a a kaci Sinan d'in me hange nesa da maida al'amura ga ALLAH bane.Alhaji Kamalu kayi hak'uri,ni na san da wanda zan had'a auran nan yanzu da izinin ALLAH gida bai k'oshi ba ai baza a ba dawaba. Yaciro dubu ashirin d'in da kaba bashi zakkarsu dazai taho masallaci "yanzun nan zan d'aura auran Julaibib da Sudaida akan sadaki naira dubu ashirin lak'anan(lakadan) Masallaci yad'auki kabbara. Alhaji Kamalu mutumin kirki me karamci shi yakar6ama Julaibib auran Sudaida, dubban nin jama'a sun shaida wannan aure. Hamidan yasauke numfashi,sai yanzu yashak'i iskar yanci dayaji ba dashi aka d'aura ba, yama Julaibib da Sudaida fatan alheri da sauran angwaye da amaren,yamik'e yayi tafiyar shi yana rok'ama Sinan shiriya...ALLAH kenan buwayi gagara misali,namiji baya auran macen da ba ta shiba,hakama mace bata auran mijin da bana ta ba...al'amarin aure,al'amarine daga Indallahi,shi yake had'awa sai dai wani yazama silar faruwar shi. Baban Abdul dake gefen shi yayi murmushi"ango ka sha k'amshi,aure d'an lokaci ne,idan lokaci yayi ko ba a shirya ba haka dole za ayi...ka tuno hirar mu ta kwanaki?Wannan gaskiya ne shirye-shiryen a yi daga baya,yamik'a mishi hannu sukayi musafaha suna murmushi, wallahi shima haka yake ganin abun kamar almara,har suka fito yan'uwa da abokan arziki sun baibaye shi suna taya shi murna da fatan alheri"Dare ga mai rabo...hantsi.Sunan wani littafi na gwanarmu (Halima Abdullahi Amma)Ubangiji ya kyautata makwanci👏 D'ansarai...yaji an kira shi.Yad'ago kai bakin shi d'auke da addu'ar"Alhamdulillahil-lazi bi ni'ima tihi ta tummussalihat"jin an daki kafad'arshi.Aminu ne yazare mishi idanu"toh daga yau sai yau na zama surukin ka,dan haka ba sauran raini,idan ba haka ba in k'wace k'anwata ka gane ko?Kome girma-girma kamar tusar jaki. Julaibib yamishi wani kallo "ai aikin gama ya gama,wuk'a da nama yanzu a hannu na suke da dai kafin a d'aura ne to danaji kurarin ka,nagaba yayi gaba Alhaji...Su Musaddiq suka yi dariya. Yara kowa yafara noman kare(gudu) dan yaje kai rahoto kuma kowa so yakeyi ace shine na farko, tun daga zaure Abdul yake k'walama Inna kira iya k'arfin shi har yashiga tsakar gidan,duk suna tsaye cirko-cirko cikin tararrabin abinda Abdul din zai shigo dashi na tashin hankali"lafiya kuwa Abdul?Sai numfarfashin gudun dayasha yake yi,yana haki da dariya yace"Inna Kawu D'ansarai aka d'aura ma aure. Asma'u dake tsaye kusa dashi batayi k'asa a gwuiwaba ta d'auke shi da wani bahagon mari,ji da ganin shi sai da ya d'auke na wucin gadi"wato wasan da takeyi da kai har yakai haka? Ka dinga mata kiran yan farauta tun daga waje duk ka tashi hankalin mu sannan kashigo mana da maganar banza"wa D'ansarai ya aura?K'anwar ubanka? Yadafe wajen dan ya maru idanun shi suka kawo ruwa,ya kasa magana sai kawai yajuya zai fita. Inna tarik'o rigar shi "Zo mana Abdul d'ina mai gida ran gida,me gida takobi...tayi furucin da sigar rarrashi,tasa hannu tashare mishi hawayen da suke zubo sharrr..."fad'amin gaskiya Abdul,me yafaru a masallaci... bata gama rufe baki ba sai ga Adnan yashigo da sallama,suka bishi da kallo, yaja kujera yazauna.Cikin jimami yafad'a musu kome. Masu murna na yi masu komawa gefe suna k'unk'uni na yi.Asma'u tajuya zata ba Abdul hak'uri taga ya fita. Asma'u tana jin abinda Sagir ya gama fad'a takai goshinta k'asa cikin sujudush-shukuri "yanzu ne za suyi rawar gaban hantsi ita da Alk'asim,tad'auki jakar da Sudaida tace tashiga d'akin Yaya Aminu tad'auko takai mata gidan Hajiya.Tana dire jakar a k'asa tayi tsalle cikin ihun murna ta rungume Sudaida"albishirinku?Duk amaren da suka sha wanka da kwalliya suka bita da kallo.Ta lumshe idanun ta cikin jan numfashi "wai me yafi dad'ine an tambayi na d'aure? Saki...tayi lallausan murmushi sannan tabud'e idanun ta"toh an d'aure lafiya an kuma gama lafiya, sai dai an samu akasi Yaya Sudaida dai da autan Inna aka d'aura... "Da Julaibib??? Suka had'a baki wajan tambayar ta cikin mad'aukakin mamaki.Nasmat ta san halin Asma'u ba mamaki tace da wasa take yi.A'isha ta d'aure fuska"ke Asma'u wacece sa ar wasanki a cikin mu?Tafara rantse-rantse gaskiya take fad'a...Daga tsakar gida suka fara jiyo tafa hannaye cikin sallallami.Nasmat talek'a Yaya Aminu ta hango suna masu Hajiya bayanin abinda yafara, a hankali tasaki labulan tana jijjiga kai"ga kai ga kafa ai ba tambayar me aka yanka.Maryam takada kai cikin damuwa "amma dai Sinan bai kyauta ba,ya 6ata rawar shi da tsalle.Zainab ta ta6e baki"wannan kuma ai can gasu gada kura ta ji kid'an farauta... kowacce ta tofa albarkacin bakinta. Sheshshekan kukan Sudaida sukaji, gaba d'aya suka juya suna kallanta.Aisha tace kiyi hak'uri Sudaida ALLAH yaso ki da rahama yato na asirin shi,da an d'aura auran ne bayan kin zama matar shi fa? Ai ko za a raba auren ku a yadda yake son ki ai ba k'aramar tata6urza za ayi ba. Takalli A'usha"wai da D'ansarai fa wannan me miskilancin tsiyan?Khausar tagalla mata harara sannan taja dogon tsaki"rainin hankalin ki yana da yawa wallahi.Su Aisha suka kyalkyale da dariya"duk miskilancin shi ai taku dashi ta zo d'aya,har hira fa kunayi.Takoma ta kwanta a ranta tana mita"maganar da sai ya ga dama yake yi.Aisha tasake kallanta"a shekarun baya dana fara k'orafi a kan halin shi kece fa me k'alubalantar kalamaina,bayani sosai kike min har nima daga baya nagane,tadafa kafad'arta haba ta D'ansarai ki daina asarar hawayen ki dan Julaibib mijin nuna ma sa a ne wallahi...tayi shiru kamar bataji me suke ta fad'a ba...tacigaba da zancen zuci"tabbass tana son Yaya Julaibib,to amma yanzu da fad'uwar tazo dai-dai da zama, kayan suka tsinke a gaban kaba sai ranta bai so ba. Tarintse idanu hawayen suka sake zubowa a kyakkyawar fuskar ta me d'auke da hasken amarci.Sinan baka kyauta ba, ka ci amanar k'auna, wato ranar da aka kira wayar shi a bai-bai yarufe ta,saboda sunan Zigwai suna sa ma maza suna sa ma mata,ashe kalaman Tibishi duk gugar zana ne,tadafe kanta daya fara barazanar ciwo,ai ko ba ta san Sinan to dad'ewar su tasa sun yi sabo na ban mamaki. Biki sai yadad'a komawa gidan Inn,bayan sallar Isha'i kowace amarya aka sadata da d'akin miji gidan aure, aure yak'in mata inji hausawa...Su angwayan da tawagar abokan su,su suka yanke shawarar a fara raka Julaibib gidan shi.Aminu dake cikin tawagar abokai yarik'o hannun shi"dare fa na dad'a yi zo muje kama Innarmu sai da safe,dan ka san bazan lamunta kadinga share waje kana barin k'anwata a gida ba,yanuna shi da yatsa"sai fa ka kula da kyau idan ba haka ba har gidan zani in tasa k'eyarta zuwa gida.Julaibib yakai mishi naushi a kafad'a amma bai same shiba dan ya goce da sauri"kar ka 6alla min kafad'a kasa gobe in shiga uku,aikin billboards ne dani guda wajan takwas.To ni ai bata shafeni ba.Yagyad'a kai"gaskiya ne ba ka da asara ko na miyan bacci. Inna tayi murmushin jin dad'i yau ALLAH ya nuna mata auran autan ta.Ta musu nasiha gaba d'ayan su sosai akan su zauna lafiya da matayan su.Alhaji Abdullahi shima ya d'ora"Ku kyautata musu Manzon ALLAH yace mafifici a cikin ku,mafifici a kyautatama Iyalin shi,ni na fiku kyautatama Iyalina,kuji tausayin su,kuyi hak'uri da dabi'unsu dan da k'ashin hak'ark'arin hagu aka halicce su.Yakalli Julaibib"Malam D'ansarai ai ka san ina yawan fad'a maka shi zaman aure gaba d'ayan shi hak'uri ne ko? Toh yau ka shiga daga ciki,yanzu za ka fara aiwatar da wannan nasihar a aikace,aure hak'uri ne,d'awainiyace me tarin yawa, shi yasa ake buk'atar juriya da jajircewa. Yarufe nasihar ta shi da wannan addu'ar ga wanda yayi sabon aure... "Barakallahu lakum,wabaraka alaikum, wajama'a bayyana kuma fi khair. Duk suka had'a baki wajan amsawa da amin,amin,amin. Inna da Baba suka bisu da kallo bayan sunma juna sai da safe suna fita d'aya bayan d'aya daga D'akin shak'atawar,kowanne yayi sharrr... dashi cikin farar shadda. Garin yayi tarwai da hasken farin wata, sassayar iska tana kad'awa a cikin daren,ga k'amshin furen filawar sarauniyar dare(Queen of the night) d'in k'ofar gidan yamamaye ilahirin ciki da wajen gidan. D'akin- shak'atawar a gyare yake, sai dai yau gyaran na musamman ne,k'amshin amarci ya cika ko ina.Suka zazzauna,aka d'an ta6a hira kamar yadda akan yi idan an rako ango sannan suka mik'e.Aminu yad'an daga murya "toh amarya mukwana lafiya, mun sai bakin ki akan kud'i masu tarin yawa,mun kuma damk'asu a hannun angon ki, dan haka yana shigowa mik'a hannu yaba ki yan kud'ad'enki,idan kuma kinci girma kin bar mishi to kinyi mafi kyawun karamci, duk ke d'in ce dai za ki amfana...Huzaifa yature shi"saboda ALLAH meye haka?Yad'aga mishi hannu"muje na ka gidan kaji abinda zan fad'a ma ta ka amaryar, suka fita suna mishi mita. Julaibib yarakasu k'ofar gida yadawo bayan ya kulle ko ina.Yarike k'ugu a tsakiyar D'akin shak'atawar cikin karatun wasikar jaki na wucewar wasu dak'ik'u,yasauke numfashi sannan yasa hannu yad'auki ledar da Musaddiq yaba shi yanufi d'akin da sallama.Yashak'i wani k'amshin turarenta dana turaren d'akin,k'amshin ne me sanyin dad'i,ya lumshe idanu yana dad'a shak'ar k'amshin cikin jan numfashi... Oh Ya Salam...dausayin ni'imahhh... A hankali yabud'e idanun shi yana bin d'akin da kallo,kome an tsara shi,ya zauna a muhallin shi,abun ya burge,ya k'ayatar duk da anyi shi a k'urarren lokaci,yau d"in nan fa. Shauk'in k'aunar daya mamaye ilahirin gangar jiki da sararin zuciyar shi tun bayan d'aurin auren sai yadad'a ninkuwa sau shurin masak'i,yaja stool yazauna yana k'are mata kallo tun daga k'afafunta da suka sha jan lalle da yarfin baki,har zuwa polish lace d'in data sa,zani da riga ruwan k'waiduwar kwai(beig)da mayafi ruwan kwai me shara-shara,k'ananan sabon kitson ta yar-yar-yar yadad'a fito da kyan fuskar ta,hannayen ta suma sunsha jan lalle da yarfin baki,d'an kunne, sark'a,zobe da siraran warawaranta na zinare sai d'aukar idanu sukeyi,ga kuma hasken amarci, yana kallan fuskar ta kome ya tarwatse mishi,murna ta koma ciki,saboda damuwa da tashin hankali dasu ke tattare da ita ruwan hawaye ne suka ta sinsitiri a kyakkyawar fuskar me d'auke da hasken amarci, yahad'e hannayen shi yad'ora ha6arshi akai"kar dai tsugune bata k'are ba...an sai da kare an sai biri?ALLAH dai yasa ba shi kad'ai yake kid'a da rawar shi ba! 'Sudaida..Yakira sunan ta cikin natsuwa. Tayi shiru...sai yayi k'asa da murya "Sudaida ban san damuwar kiba,amma ina so ki sani daga yau,yanzu d'innan duk wata damuwa dakike ji da ita,to nima zanji kwatan-kwacinta,kiyi hak'uri ki bani goyon baya dan in samu k'warin gwuiwar faran ta miki,akowani irin hali da yanayi.Toh me zata cene?Wallahi wani iri take ganin shi, kamar wani bak'o,nauyin shi take ji,ga kuma kewa da rabuwa da gida dasu Nasmat da akayi shekara da shekaru ana gwagwarmayar rayuwa da makaranta, musamman Khausar da kullum suke kwana daki d'aya, gadon bacci ne kowacce da na ta,amma har wardrobe d'in su d'aya,suyi fad'a su shirya,toh wai yau kowa a wani muhalli na daban zai kwana,ga Aisha da ta musu nisa tana Kafanchan idan suna san ganin juna fuska da fuska to sai sunyi tafiyayyiya a mota, kewan kowa da kome yalull6eta sai kawai tasa kuka(Hummm Sudaida aure yak'in mata inji hausawa...toh yanzu kin shigo filin shukuwa... Sai ki had'iyi k'wayar hak'uri ki kora da ruwan jarumtaka da jajircewa dan aikin aikine wallahi"an ba kuturu tallan jakai) Tun shigowar shi d'akin sai yanzu tacire tagumin datayi tad'an saci kallan shi,Bai cire kome nadaga shigar shi ba sai takalmi,k'afafun shi cikin safa. Sudaida... Yasake kiran ta"tashi muyi sallah...Tasunkwui da kai tafara shashshekan kuka. Tagirgiza kai"uh uh Sudaida yau fa ba ranar kuka bace,rana ce da za ki k'ara godema Ubangiji dan kin shigo gidan aure, auran nan kuma hanyace da zata sadaki da Darul-karamah.. Yad'auko Kofi yazuba madara yamik'a mata"kar6i kisha.Itafa ya dame ta,kad'aici take buk'ata wallahi,dan haka tace bata sha. Sudaida..Ta tari numfashin shi"Yaya Julaibib nifa gaskiya bazan iya zaman auren nan ba...tacigaba da kuka. Yayi tsaiii...na wucewar wasu dak'ik'u yana kallanta"idan rai ya 6aci toh hankali yanemo shi,abinda yatuna kenan yamata uzuri dan shima yaji rad'ad'in rabuwa da Bilkisu fuj'atan. Yagyad'a kai"To naji, amma d'an daure muyi salla ko?Dak'yar tamik'e ita fa wani irin hali da yanayi ta tsinci kanta a ciki kamar almara. Bayan sun idar da sallar yayi wannan addu'ar ga wanda yayi sabon aure.. "Allahumma inni as'aluka khairaha wakhaira ma jabaltaha alaihi,wa'a'uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi" Duk sukayi shiru na wucewar wasu dak'ik'u, a hankali yad'ago yana kallanta,sai yaciro wayar shi yasaita ta yana d'aukarta hotuna,tana d'ago kai caraf idanun shi yahad'u,tasunkwui da kai da sauri tana dad'a rufe fuskar ta da mayafin, bazato taji ya cire mayafin yarik'o ta yana d'aukarsu tare"Yaya D'an... sauran kalaman suka mak'ale saboda wannan rikitaccen kallannan na shi daya mata,ta turo baki gaba idanun ta sun cika da kwallah. Sai da yagaji dan kanshi yabari. Hucin numfashin shi taji a gefen damanta,yayi k'asa da murya"ALLAH yabaki hak'urin zama dani...Yagewaye hannayen shi a jikinta"Kin gaji da yawa ya kamata kiyi wanka da ruwa me d'umi sai ki kwanta kiyi ishashshen bacci ko?Dak'yar tayi furucin"ni ba sai nayi wanka ba. Yagirgiza kai"uh uh sai kinyi wanka za ki kwanta... yasake ta"kije kiyi wanka,yajuya yafita. Har tayi wanka takwanta sannan ya shigo tana kwance irin kwanciyar mage.Har kin kwanta"uhhh tace.Yaja stool yazauna yana kallanta"gobe fa sammako zanyi in koma makaranta kilama baki tashi daga bacci ba.Sai taji ranta ba dad'i.Tayi shiru kawai...ko za ki bini mutafi tare?Tad'an dago suka kalli juna"yad'age gira yana mata wani kallo"in shirya miki kayanki yanzu?Tawani marairaice tana zancen zuci"sai kawai aji tabi shi makaranta?Yayi yar dariya yana mik'ewa"kiyi baccin ki kinji,ni akwai nazarin da zanyi"Lailatun sa'ida...fi amanil-lah.Ya tafi D'akin- shak'atawa yana had'a wasu littafai da zai tafi dasu. Sinan bai farka daga nannauyan baccin daya d'auke shi bayan ya gama aman giyar daya shaba sai cikin sulusin dare.Yafarka da wasu miyagun mafarkai daba su da tushe bare makama, yabi d'akin da kallo zuwa kayan jikinshi,yashiga rarraba idanu"me yakawo shi d'akin Hamidan kuma?K'wak'walwar shi tafara aika sak'onni zuwa bangaren tunanin shi"me yafaru dashi? Yaufa ranar d'aurin auren shine,rana ce ta musamman a gare su shi da sarauniyar ta shi,a kuma daren su nafarko cikin angwanci, yakad'a kai ai sam-sam baza ta sa6uba bindiga cikin ruwa, ruwa baya tsami banza,tar-tar yafara tuno abinda yafaru kafin gushewar hankalin shi.Dammm...Yaji rikitowar wani abu a k'ahon zuciyar shi,kafin kiftawar idanu yajik'e sharkaf da zufa kamar wanda yayi wanka da kayan jikin shi, da sauri ya sakko a gadon kamar zai hantsila yawuce D'akin-shak'atawa anan yaga Hamidan yana bacci a doguwar kujera,kuma d'akin wayammm ba kowa,ba kamar jiya da yan'uwa da abokan arziki suka cika ko ina ba.A rikice ya sunkuya dai-dai fuskar Hamidan yana kiran sunan shi,yasa hannu ya yarfe zufan dayake ta tsatstsafo mishi a goshi a karo na barkatai,yahadiye wani abu mezafi. Hamidan yayi juyi sannan yabud'e idanu, dan a sama yaji kiran"tashi Hamidan ka zauna.Hamida yatashi yazauna yana kallan shi cikin 6acin rai,wallahi da shine babba sai ya zabga mishi barin makauniya dama da hagu,yakad'a kai"labarin zuciya a tambayi fuska sai kawai yajuya mishi keya.Cikin tashin hankali Sinan yace"dan ALLAH an d'aura aure na da Sudaida? Yajuyo yamishi wani kallo"tabbasss an d'aura auren Sudaida amma da dan'uwanta D'ansarai dan Baba ma bai goyi bayan a d'aura mata aure da d'an giya ba,yanzu haka tana d'akin mijin ta...yatare shi cikin k'araji da tafasar zuciya"ya ishe ka! Yafad'a kujera yana Istirja'i k'urunk'usss...ta faru ta k'are an yima me dami d'aya sata. Idanun shi sun kad'a jawur Tibishi da Zigwai sun kai shi sun baro. Yau bak'ar rana ce a gare shi me bak'in muni...yafara tuno abinda yafaru wayewar garin juma'a, a sanda hantsi yadubi ludayi yadawo daga ciro kud'i a ATM dazaiyi hidimar abun sha na walimar dare da za ayi bayan an kai amarya,yasa mukulli zai bud'e d'akin shi kenan sai ganin Zigwai yayi ta shigo gidan na su tak'aramar k'ofa, me gadi yana d'akin shi yana sallar walha,lallai idan ya barta Baba zai iya fitowa kowani lokaci,ga kuma bak'in yan biki,da sauri yazare mukullin daga jikin kofar yamayar aljihu,yaja hannunta da sauri suka bar gidan,suna fita yasaki hannun ta ya wanka mata mari san ya angijeta tayi baya tafad'i,yafara yarfa mata ruwan bala'i"dan abu kazan uban ki meye darin gamata da ke dahar za ki biyo ni gida? Ba mun gama ba,ba kare bin damo?Tawani marairaice"dan ALLAH angon Sudaida kayi hak'uri,ban san ranka zai 6aci irin haka ba, amma nima ai daga yau ba k'ari wankan wuta,na kira lambar ka sau shurin masak'i kaj'i d'agawa, kaga ai dole tasa, dan wajen Party yayi cikar farin d'ango amma ba special quest of honour,tacigaba da marairaita har tasamu fushin daya taso mishi yafara lafawa"dan ALLAH kazo muje ana gama yanka cake sai kadawo. Yagalla mata harara"baza niba ko dole ne? Dasauri takai gwuiwoyinta k'asa tana mishi wani irin murmushi na yan duniya da jan hankali" haba Sinan dan darajar k'auna da soyayyar daka kema sarauniyar ta ka,yau d'aya dai karka watsa min k'asa a cikin idanu bayan na gama sakankan cewa,ai ka gani ko a jikin katin gayyata an buga kaine bak'o na musamman me girma.kuma na fad'a maka tuntuni ka kuma amince da haka,haba Sinan ai alkawari bai ce haka ba,da tun farko ka fad'amin baza kaje ba ai da na canja ka da wani,tamik'e cikin hawaye tana kallan shi"shine nan nagode...nagode tajuya tayi tafiyarta. Yabita da kallo,sai yaji ran shi ba dad'i yasake kallan agogon dake d'aure a hannun shi,har yanzu k'arfe goman safiya bata k'arasa ba, bari kawai yaje tunda alk'awari yamata,zuwa goma da rabi sai yamata sallama yazo yak'arasa abinda zai yi kafin lokacin masallaci yayi. Da wannan tunanin yabita,yasha gabanta da mota yabud'e mota gidan gaba tashigo ta zauna"kiyi hakuri Zigwai.Tagirgiza kai"na hakura angon Sudaida,ALLAH zan so ganin ka anjima dan na aan wankan da za kayi zai bambanta da duk wani wanka da kata6a yi,yayi murmushi kawai. Wajan party ya had'u da had'ad'd'un yan duniya hayak'in taba,dashi aka yanka cake,sai dai agurguje yake yin kome yana kuma yawan duba agogon dake d'aure a hannun shi dan kar lokaci ya shammace shi. Tabishi da kallo"wai wannan duba agogon na meye?Duba agogon me kuma?Sai ta share zancen"me zan kawo maka ne kad'an jik'a mak'oshi?Yaharareta.Tayi yar dariya "ka d'auka ba abinda zaka iya shane?Dan dai kak'i yadda ne amma bommi ba giya bane, ko a zuba maka d'an kad'an?Yagirgiza kai"a ah kusha abun ku,ni dai na san giya ne bommi,tunda idan mutum yasha yana gusar mishi da hankali.Tata6e baki "idan kai baka sha ba ai hausawa dayawa yan uwanka sun sha.Toh Ubangiji ya shirye su. Taje tad'auko katan d'in lemun bakwai a raye(seven alive)ta6arke ledan a gaban shi tazaro d'aya, tabud'e murfin sannan ta d'auko kofi ta tsiyaya kusan rabin kofin sannan takalle shi"ko a cika maka kofin? Yamik'a hannu yakar6a "wannan d'in ma ya isa nagode, yana kai kofin tsakanin la66an shi tayi murmushin mugunta,ta dunk'ule hannu ta naushi iska"k'aramin arne ka had'u da gawurtacciyar arniya.Sinan sai dai muyi biyu babu,baza ka auri Sudaida ba nima ban aure kaba kowa yaji idan da dad'i.Tayi wata irin dariya irin ta yan duniya ganin ya shanye lemun duka "ALLAH yakai damo ga harawa... Wucewar wasu yan dak'ik'u sai yafara gani garara-garara yanayin shi yana canjawa,d'aukacin jama'ar wajan yafara ganin su suna kasuwa kashi-kashi yana ganin Zigwai da Tibishi suna magana a gaban shi cikin dariya da tafa hannu amma bazaice ga abinda suke fad'a daga haka bai san abinda yakuma faruwa ba.Ashe maganin bacci da gusar da tunani,kuma wanda yawuce ka'ida(over dose) suka zuba acikin wannan lemun guda d'aya,sun kuma yi ma kwalin alamar dasu kad'ai za su gane. A gida kuma Alhaji Kamal da Hamidan sun tun sha biyun rana suke neman Sinan amma ko sama ko k'asa basu ganshiba, hakama lambar wayar shi sun kira sau shurin masak'i na'ura me k'wak'kwalwa tana fad'a musu a kashe take,haka suka gaji sukayi shirin masallaci suka tafi. Sinan sai da yayi bacin awanni biyu sannan suka tasheshi,har lokacin bai gama dawowa dai-dai ba,sai suka dura mishi giya nan fa yadad'a rikicewa.Wani abokin Tibishi yakalli Sinan"wannan ba yau za a d'aura mishi aure ba amma yazo nan yashare waje ko auran dole za a mishi? Dammm...zuciyar shi tabuga duk da yana cikin maye.Yata shi yana tangad'i da tam6ele yashiga mota.Yana tafe jama'a na kaucewa da ababan hawansu, yana kuma shan zagi da tsinuwa daga bakin wasu,saboda k'iris yarage yahad'a hatsari mummuna,a haka har ya isa masallacin juma'a wajan d'aurin auren...wasu zafafan hawaye suka zubo mishi"Zigwai tasa ya zubar da mutuncin shi dana gidan su abainan-nasi, kalaman Sudaida suka dawo mishi duk da k'anka'ntar shekarun ta amma tayi hagen nesan da san zuciya yahana shi hangowa... Zama da madaukin kanwa...wai kai ba ka da wajan zamane sai acikin yan maro(wiwi)?...yatuno da maganar mahaifin shi na wancan makon"Sinan ba girma aganka kana mu'amala da wad'annan k'adangarun barikin... mun baka tarbiya gwargwadon iyawarmu... tunatarwa ce kawai...Yamik'e cikin tafasar zuciya "lallai yau za ayi ta tak'are me raba shi da Tibishi da Zigwai sai ALLAH Hamidan yakalle shi ganin yana bud'e kofa"Ina za ka a wannan daren Yaya? Ko kallan shi baiyiba yasa kai yafita. Tana kwance hankali kwance iskar fanka tana kad'ata.Yadamk'o gashin dokin daya cika kanta tozon rak'umi guda.Zafi yaratsa ta tabud'e idanu cikin gigita,suka kalli juna,sai ta dad'a rikicewa.Yanemi abun duka bai samu ba dan haka yad'auki belt d'in daya gani a gefen gadon, yafara dukan ta ba ji ba gani sai da belt d'in yatsitstsinke amma duk da haka bai hak'ura ba,yafara tattaka sai da yaga ta daina motsi sannan yatsallaketa cikin jini yafita, amma har lokacin bai huce abinda suka mishi ba,wasu jijiyoyi sun fito a gefen kanshi kamar shatin bulala,ran maza ya 6aci iya 6aci. Adaren yakoma neman Tibishi sai dai duk inda yasan zai ganshi yaje amma cikin rashin sa a bai ganshiba...tabbasss da aun had'u sai wani ya rasa ranshi ko kuma suyi mutuwar kasko.Yakama hanyar gida zuciyar shi a cunkushe, kaci6is sukayi da mahaifin shi da Hamidan za su tafi masallaci sallar asubahi. Sinan yasunkwui da kai ya ga 6acin ran da bai ta6a gani a fuskar mahaifin na suba"yanzu duk abin kunyar dakayi jiya hakan baisa ka kwana a gidaba? Yanuna shi dayatsa" anya Sinan,anya rayuwar gaba za tayi kyauvda albarka idan ba a tsaya an inganta rayuwar da ake ciki a yanzu ba? Anya Sinan kana tuna tsohon banza daga yaron banza yafara? Sinan yayi shiru a ranshi yana nadamar sanin Tibishi da Zigwai a rayuwarshi..Alhaji Kamal yakad'a kai"shikenan sai kaje ka shirya kafito masallaci, yakalleshi "kama rama sallolin jiya daka kwanta wannan baccin asaran?Tsoro yakama shi" shi Sinan yashiga ukun shi wallahi sai yanzu yatuna.Asanyaye yagirgiza kai"yanzu zan rama. Yakalli Hamidan"kaji,Ubangiji yashirye shi. Hamidan ya amsa da sauri amin Baba. Suka tafi masallaci kowanne ranshi ba dad'i. Yana durk'ushe agaban mahaifiyar shi yana bata hak'urin abinda yafaru amma fau-fau tak'i sauraran shi, tanuna mishi k'ofa"ta shi kabani waje ganin ka yana k'ona min rai,Sinan ka bani kunya...tirrr da wannan halin na ka, albasa batayi halin ruwa ba wallahi. Yayi k'asa da murya "Mama bana shan giya,makirci kawai a ka kulla min...ta tare shi a zafafe" kai karka maidani sakarya,wa zai kulla maka makirci?Makirci da munafurci har yawuce wanda kadad'e kana aikatawa,ko kawai dan dubunka ta cika? Alhaji Kamal yashigo"haba Mamansu idan rai ya 6aci to bai kamata hankali yagusheba,d'an yau ne ka haifeshi baka haifi halin shiba.Takalleshi a rikice "yanzu kana goyon bayan shine,har kana ba shi lasisi?Tad'ora hannayenta aka"oh ni yar mutum biyu" na rantse da ALLAH Alhaji idan yaron nan bai tashi yafitaba to zan d'aga mishi nono...Tabud'e baki da niyar sake magana sai kalaman suka mak'ale saboda 6acin rai.Tasa hannu tashare hawayen daya zubo mata. Sinan yasake shiga wani tashin hankalin gobarar gemu fiye dana d'azu"lallai ka shiga uku, rayuwarka tana cikin garari tunda har za kasa mahaifiyar ka zubar hawaye saboda mummunan laifin ka. Yanzu wa zai yadda dashi akan baya shan giya? Abu d'aya yasan yana sha a 6oye shine taba sigari,itama ba koda yaushe ba,wazai yadda dashi?Yadafa goshi"ko Alqur'ani d'ungurungum zai had'iye bashi da mafita. Nadama,haushi da bak'in ciki suka baibayeshi, kome yaji yafice mishi a rai. Alhaji Kamal yadafa shi"tashi katafi d'akin ka.Gwiwa a sage yamik'e.Alhaji Kamal yakalli matar shi "abinda Sinan yayi tabbasss bai kyauta ba,kuma bana goyon bayan shi,to amma wani hanzari ba gudu ba, idan fa yatuba bai kuma aikata hakan ba har abadan duniya,to ALLAH me gafara ne,zai kar6i tuban shi ya yafe mishi tunda bamu yama laifi ba face mahaliccinmu gaba d'aya, dan haka karki tsananta,ke uwa ce addu'arki har kullum ita ake buk'ata, kullum addu'armu da fatanmu ace Ya'yanmu sunyi zarra fiye da duk wasu Ya'ya wajan natsuwa,sanin ya kamata, mutunci da tsantseni,to inga yanzu kin mishi baki? Bazai amfani kan shiba,bazai amfane muba,bazai amfanar da sauran al'umar manzon ALLAH ba,kin 6ata goma biyar bata samuba,baya ba zani kenan... Yana rik'e da marik'in k'ofar d'akin shi kafin yamurd'a tabud'e jiri yayi awon gaba gaba dashi yifff...yasha k'asa.K:arar fad'uwar tashi megadi yaji.Yayi cikin gidan da sauri yana kiran Alhaji da Hamidan,sun yayyafa mishi ruwa amma shiru kamar an shuka dusa,dan haka suka wuce dashi asibiti. Tsakanin d'a da uwa sai ALLAH, hankalin mahaifiyar tashi a tashe,takira Hamidan tana tambaya"ya jikin na shi?Yakalli roban k'arin ruwan da aka sa mishi a hankali yake d'iga a cikin siririyar robar yana shiga jijiyarshi zuwa cikin jikinshi"Mama ya samu bacci saboda allurar baccin da aka mishi,likita yace jininshi yayi mugun hawa.To Alhaji fa?Tasake tambayar shi cikin damuwa. Sun fita shi da likita.To Ubangiji yasa kaffarace nima anjima zan shigo. Yagyad'a kai"To Mama sai kin shigo a iso lafiya.Yauwa Hamidan ALLAH yamaka albarka.Amin Mama. Tibishi yad'ora hannayen shi aka yana zare idanu"Holy ghost fire!...Inzayadami?(Me yafaru)Tafashe da kuka tana kad'a kai"ina katafi kabarni acikin wannan mawuyacin halin? Na neme ka a waya banji kaba.Yakoma yazauna"sha kuruminki Zigwai wayata nasiyar nayi kud'in mota zuwa Kafanchan kasuwar aladu, na kuma je da k'afar dama and'aukeni lodi mutanan k'asar China sunzo siya, lodin tirela hud'u mukayi,ba k'aramin kud'i nasamu ba,dan haka murabu da Sinan dan naga hak'armu baza ta tadda ruwaba.Me kake nufi? Yazuba mata idanu jikinta duk a farfashe yake"gaskiyar magana tunda Sinan yamiki irin wannan dukan kawo wuk'an to babu wata rana dazaki kuma mishi koda kun rage daga ke sai shi a doron duniya bazai kuma sauraran kiba.Tunda na samu abin yi kishare shi kawai,d'an iska yadaije amma ai munci gari,nima kwana biyu zan kiyayi zuwa cikin gari da duk inda nasan zai ganni,dan na san zai nemeni ruwa a jallo. Takalleshi amma tunda bai auri Sudaida ba na san zai koma ruwa tsundum. Yamata wani kallon sauna"ke Sinan fa ba sin ki yakw yiba shishshigi da nacinki yasa kika samu kanshi,kuma koda kika samu kan shi ai ba wani d'ad'ashi da k'asa kikayiba,ak'arshe ma bazuwa yayi yaba ki hak'uri akan kuyi hannun rigaba? Yamik'e"nidai buri na ya cika,dama yarinyar ce bana so ta aure shi saboda girman kanta,kin san sannu wannan ta fatar baki bata ta6a cemin ba,duk da tasan nid'in abokin saurayin tane aibtasha ganin mu atare,idan nabari ya aureta to za ta rabamu tunda na san zaiji maganar ta dan yana son ta. Zigwai takwanta"ai dai munyi biyu babu. Tibishi yakalle ta kisa ranki a inuwa,barinje kasuwa in miki siyayya,yana fita ta kyalkyale da dariya"haba Tibishi ai linzami ya fi k'arfin bakin kaza,kai ka had'ani da Sinan dan yazama saniyar tatsarmu,to mun tatseshi yadda yakamata, yanzu idanu na a bud'e suke ina ganin kowa garauuu ba ka da kud'in dazan aure ka,bari dai mucinye wanda kasamo,za ka nemeni ko sama ko k'asa karasa,garin zan bari dan yamin zafi saboda rashin Sinan, zan tafi wata jahar in bud'e sabuwar rayuwa da sababbin alhazan birni masu aljihu da kud'i ba irin kaba tsami ragowar burkutu giyar k'ok'o da hayakin maro da taba dayaci yacinye ka,sai na sai gida da mota,sannnan zan yi aure...toh maji magani an binne tsohuwa da ranta... Haka ya yi an sai da gonar rago an sai mishi fura. Farar dabara shiga rijiya da fura. 10 Jumaada Thani 1441 4 February 2020 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na goma sha tara. Kwanaki biyu Sinan yayi a gadon asibiti yasamu sauk'i sai dai likita bai sallame shiba sai zuwa gobe.Yakar6i wayar Hamidan dan ta shi ko ta fad'i ko kuma su Tibishi sun sace ta,yadaddanna lambobin ta sannan ya d'ora lambar a kira.Tad'aga da sallama,wani abu yatsirga ilahirin jikinshi,ta kuma yin sallama jin ba ayi magana ba sai ta katse.Yacire wayar a kunnenshi yana jujjuya ta,idanun shi sun kad'a jawur,tabbasss kukan zuci yakeyi.Yaya Sinan ba a d'aga bane ko matsalar na'urar sadarwa?Yajuya yakalli Hamidan d'in,sai ya gyad'a kai"zan cigaba da gwadawa wata k'ila tashiga.Sai da ya danna kira sannan yace"Hamidan dan ALLAH kaje gida Mama tadama min kunun tamba.Yamik'e yana murmushi"a lallai yau jikin Alhamdulillahi,a had'o da abinci ko?Yagyad'a kai"amma me d'an ruwa-ruwa. Yana fita yakai wayar kunnenshi,tad'aga da sallama.Yasauke numfash sannan ya amsa sallamar,yakira sunan ta Sudaida...Zuciyoyinsu suka buga,sukayi shiru na wucewar wasu dak'ik'u.Da rawar murya take fad'in"Sinan ya jikin?Ance kana kwance a gadon asibiti,Sinan me yasa kabiye ma son zuciya bayan ka san son zuciya 6acin ta...dama da gaske kura ce lull6e dafatar akuya?Sinan kai masoyina ne, wallahi ban ji dad'in abinda yafaru ba ko kad'an...ALLAH yashirye ka dana... yatari numfashin ta"na rantse miki da girman ALLAH bana shan giya"ba ka shan giya to ya akayi kasha? Ba fa a wasan kwaikwayo kafito ba.Yakad'a kai, matsalar kenan ba wanda zai gasgata shi"Sudaida na san na rasa ki,to amma duk da haka bazan barki cikin duhu ba,ranar wanka ba a 6oye cibi... yafara ba ta labarin had'uwarsu da Zigwai wanda shi kanshi yasha mamakin sauk'in halin ta,saboda irin wulak'ancin dayake mata,amma tashanye kullum bata fushi kwantar da kai take mishi na gasken-gaske da haka har taja ra'ayin shi yafad'a tark'onta. Cikin kuka tace"ai na fad'a maka dabi'a tana na so,maganin kar ayi to tun farko kar a fara,dan shaid'an baya raina k'ofa.Sinan ina maka fatan alheri a rayuwa,dan ALLAH kacanja abokai da mutanan kirki.Nagode Sudaida,kema ina miki fatan alheri da samun natsuwa a gidan auren ki.Sudaida sarauniyar Julaibib.Yagoge lambar ta daga cikin wayar sannan ya ajiye,yana jin ranshi ba dad'i sunyi sabo na ban mamaki da Sudaida tun tana yar k'aramar yarinya...Lallai sabo turken wawa. Julaibib daya jingina da k'ofar D'akin-shak'atawar yak'arasa shiga yazauna,ganin shi baisa ta daina kukan ba.Yakalleta cikin kulawa"kukan na menene Sudaida?Ai k'addara ta riga fata"rayuwar mu ba a hannu take ba,ALLAH ne yake tafiyar mana da ita,ta duk yadda ya so,shiyasa so ba samu bane,haka kuma samu ba so bane a wasu lokutan;yasa hannayen shi yagewayeta yana mata wani salo a hankali,yana kuma fad'a mata wasu kalamai sai ga shi tasa hannu ta share hawayen ta kuma yi shiru,tana k'ar6an sak'onnin dayake bata a ilahirin gangar jiki da sararin zuciya,wucewar wasu dak'ik'u sannan yad'ago fuskar ta suka kalli juna tayi saurin kauda kai"idan kunne na sun jiyo min dai-dai a cikin kalamanki naji kince shaid'an baya raina k'ofa ko? Ba baka sai kunne...jikin ta ya mutu murusss kai kawai tagyad'a.Yamik'a mata hannun damar shi "bani wayar ki.Tasa mishi a tafin hannun,yasa ta aljihu... Sudaida...Yakira tatad'ago tad'an kalleshi. Kin san me yasa nakar6i wayarki?Uh uh.Yasauke numfashi"to na kar6i wayar ki saboda ba na so wata mu'amala tacigaba da kasancewa a tsakanin ku,yanzu ke matar aure ce,shi kuma wani k'ato ne daba muharraminki ba,ba dangin Iya bare na Baba;shi kuma shaid'an baya raina k'ofa.Yabata wata sabuwa galleliyar waya da layi sabo a ciki.Tasa hannu biyu ta kar6a"Yaya Julaibib nagode da da tunatarwanka. Bayan sallar isha'i yashigo"Ina amaryar? Ta shaida muryar ko da acikin magagin bacci take, tafito sanye da hijab d'in data idar da sallah "sannun ku da zuwa...Yayi murmushi"yauwa amarya sha gud'a.Ya ba ta kunya ba kad'an ba,ta kuma ji abun banbarak'wai namiji da suna kande, wai Yaya Musaddiq da tsokanar ta,dama shi da Yaya Adnan sam ba shak'uwa a tsakanin su, wannan sauk'in halin sai Yaya Aminu. Cikin girmamawa ta gaishe shi tare da tambayar ya Yaya Safiyya?Yagyara zama"ai itace ma ta ai ko ni,wai tana gaishe ki,kin san yanayin na ta,tafiyar wahala take mata amma dai za ta k'ok'arta tazo. Taje takawo musu abinci Musaddiq yamik'e"a ah wallahi kuci kayan ku.Julaibib yazuba mishi idanu saboda me? Yad'an daki kafad'ar shi"ni kuma nawa da yake jirana a gida inyi Yaya dashi?Yamik'a mishi hannu sukayi musafaha.Suna tsaye a bakin k'ofa sukayi k'us-k'us d'insu sukayi dariya suka tafa.Tabisu da kallo"maza ma sun iya tsegumi?Tayi yar dariya wai itace ba su so taji kenan"Yaya Musaddiq mukwana lafiya.To Sudaida ALLAH yatashe mu lafiya. Tana kwance cikin damuwa saboda fad'an da Julaibib yarufe ta dashi kamar zai ba ta na jaki,sannan ya hanata tofa albarkacin bakin ta, na ganin da yama k'anwar Sinan a gidan; kila zaton shi Sinan ne ya aiko ta tunda zai kira lambarta yajita a kashe,ita kuma Maman suce tabata turaran wuta da su humra kala-kala takawo mata,dama ta siya ta ajiye idan tazo gidan saita ba ta toh kuma ga yadda al'mura suka kasance. Yanuna ta da yatsa idanun shi sun kad'a jawur"idan na kuma ganin wata ko wani a cikin gidan nan daya danganci Sinan na rantse miki da ALLAH abinda zan miki har ki mutu baza ki manta shi ba...Idanun ta suka ciko da kwallah Yaya D'ans...ke! nace ki rufe min baki ko?Yayi d'as d'as d'as da yan yatsun shi"baki sanni bane,yaja dogon tsaki yawuce d'akin shi. Tasauke numfashi da ajiyar zuciya,tasa hannu tana share hawaye,tabi k'ofar da ake k'wank'wasawa da wani malalacin kallo,ta maida kanta jikin matashi tana dad'a gyara kwanciya.Aka cigaba da k'wank'wasa k'ofar,dole tamik'e cikin fushi tana jan tsaki a ranta tana mita"na ci dambun kuturu.Tasa hannu tabud'e k'ofar caraf idanun su yahad'u,ta gallama Sudaida harara. Sudaida tayi kamar ba ta gani ba,tayi d'an tsallen murna fuskar ta cike da d'okin ganin ta tafad'a jikinta"oyoyo Hajiyarmu sannu da zuwa...suka shige D'akin-shak'atawar,Hajiya ta ture ta"ke gafara can karki 6alla ni,tazauna a k'asa tana dafe k'afafu da alama ciwon k'afar yana son motsawa. Da sauri Sudaida tad'auko man zafi ta d'urk'usa a gabanta tana murza mata a k'afafun tana maimaita"sannu da zuwa Hajiyar mu gaskiyar magana naji dad'in ganinki ba kad'an ba. Hajiya tasake galla mata harara"amma shine kika barni a waje ina ta k'wank'wasa k'ofa?Tayi yar dariya"kai Hajiya gidan amarya fa kikazo ni k'wank'wasa k'ofar kine ma yatashe ni daga bacci.Hajiya takalli agogon bangon dake d'akin sha d'aya saura minti goma na safiya"Toh ALLAH ko yasauwak'e da wannan baccin asaran. Tagirgiza kai"ba amin ba,ai lokacin abu ayi shi, amarci ai ba k'arya bane,ba kuma abinda ba ya sawa.Hajiya tazuba mata idanu cikin kallan nazari"amarcin ne yadad'a k'arar dake kamar bushashshen takand'a?Ke ko cikar d'akin bakiyi ba.Takai hannu tashafa wuyanta"sharri dai ba kyau Hajiya ni ba bushewar danayi wallahi,toh so kike kiga na zama ta shi da nishi?Tamata dak'uwa"kar6i nan aiko Iyayan ki na fi k'arfin in musu sharri bare ke karankad'a miya.Tad'an turo baki gaba"ai baza ki musu sharri ba tunda Ya'yan kine kina son su,nice dai ba kyau so.Hajiya takad'a kai kawai. Ina Julaibibi ne rabona dashi tun shekaran jiya da daddare.Haushin shi yamamayi zuciyarta,to amma Hajiya babbace ko yaya tanuna wani yanayi za ta iya gano ta bare kuma yadda ta tsare ta da idanu.Tamik'e tana rufe man zafin"ke Hajiya ai yanzu ba da bane dazai dinga zuwa gidan ki yana share waje,ni kuma dawa zai barni? Hajiya ta tafa hannaye tana sallallami"ba shakka rasa kunya 6aren tanka...lallai wuyan ki ya isa yanka. Sudaida tawuce tana dariya,ta kwana biyu bata shiga d'akin ba,k'amshin arabi'an perfume da k'amshin turaren d'aki ya gauraye sai yaba da wani irin nau'in k'amshi me sanyin dad'i wajen shak'a,carpet d'in d'akin kore da ratsin ruwan madara dawasu kyalli-kyalli masu d'aukar idanu,hakama labulayen d'akin ruwan madara da ratsin filawar rose yan shara-shara,sassayar iskar da take shigowa d'akin ta tagogin da suke a bud'e suna kad'a labulayen suna rangaji saboda rashin nauyin su,ya canja gadon daga inda tasani zuwa d'aya bangaren, wardrobe ma yacanja daga zuwa bangaren yamma,shoe-rack(ma'ajiyar takalma) cike tam da takalma mafi yawansu farare ne,kuma masu rufi(sau ciki) Yad'ago yana mata wannan rikitaccen kallan nashi da yake ba ta haushi,yamaida kanshi ga tarin littafan daya barbaza a saman tebur,yana kuma yin rubutu a na'ura me k'wak'walwa da alama wasu abubuwan yake shigarwa"lafiya za kizo ki tsaya min akai bayan kingani ganin idanun ki aiki nakeyi.Wulak'ancin D'an Sarai har yakai haka?Ta tambayi kanta,zuciyar ta tayi rauni idanun ta suka kawo ruwa amma bata bari hawayen sun zubo ba,ta kad'a kai"ba kome dama saboda ka ma ake cin k'asa,tasaki marik'in k'ofar"Hajiya ce take magana.Suna had'a idanu yagalla mata harara "dama ai duk wanda kika ga ya ci kaza to shine da ita.Tayi kamar bataji abinda yafad'a ba. Yasauke numfashi zuciyar shi ba dad'i ganin damuwar data shiga,ko kukan d'azu datasha kuka har tak'oshi yaji ba dad'i,to amma dole yayima tufkar hanci,kar garin kallon ruwa k'wad'o yamishi k'afa,ita da Sinan ai sun so juna, yau da gobe kuma bata bar kome ba,shaid'an baya raina k'ofa, dama ba abinda yake so sama da 6ata tsakanin ma'aurata,toh dole sai ya toshe duk wata kafa da yasan alak'a zata had'ata da Sinan dan yatserar dasu da auransu daga fad'awa halaka.Wani lallausan murmushi yasu6uce mishi "humm Sudaida za tafahimce shi,shi masoyin tane da babu kamar shi a doron duniya,shi da ita mutu karaba takalmin kaza,har lokacin da gangar jiki zai daina numfashi, rai yatafiii... Yazauna suka gaisa da Hajiya.Tanuna shi da yatsa"kai Julaibibi kazama jarumi dan a haka nasan ka, karka biye ma wannan malalaciyar matar taka tamaida kai rago, ace kazauna kana sharar bacci har hantsi yadubi ludayi?Yashafa kwantaccen bak'in gashin kanshi yana d'an murmushi"Hajiya wane ni da wannan aikin;ai sai manya gatan wasa,amarya sha gud'a suka kalli juna shi da Sudaida tad'an harareshi tana turo ba ki gaba. Wasu muhimman bayanai nake ta shigarwa ashafin mu na yanar gizo.Tagyad'a kai "Toh Ubangiji yayi jagora.Sunata hira da Hajiya cikin jin dad'i a wanta d'aya a gidan sannan takalle su"to ai na gaishe ku,barin tashi inje gidan Musaddiq jiya Safiyya bataji dad'i ba,wannan girman ciki ko yan hud'une a ciki iya ka kenan, ALLAH dai yaraba lafiya,suka amsa da amin. Julaibib yafita k'ofar gida inda ake sallama dashi. Hajiya takalleta cikin natsuwa"wato kink'i tsayawa ki kwantar da hankalinki ki rungumi kaddarar Ubangiji ko?Tasunkwui da kai.Hajiya tacigaba shi aure dakike ganin shi ai ALLAH ne yake had'a shi ba mutum d'an Adam ba;ko shi Sinan ai ya dangana dan yazo har gida ya fed'emin biri har bindi, ban kuma kullace shi ba,na san shi mutumin kirkine,sharrin shaid'an dana zuciya ne suka rud'e shi,tanuna ta da yatsa"tun wuri ki saki ranki ki rungumi auren ki dan shine gatan ki na d'iya mace,ga sauran yan'uwanki can kowacce tayi sharrr gwanin ban sha'awa da kyan gani,ke kuma kinanan jiya i yau,ke da Julaibibi ai kun zama k'arfe da mayen k'arfe.Tayi shiru kawai a ranta tana mita"ai Yaya D'ansarai yakamata ajama kunne tunda shine baya son ta,auren dole aka mishi a tunanin ta"rashin sani karen gwauro yakori bazawara.Sukayi sallama tad'an ta ka mata zuwa harabar gidan.Tare suka koma ciki da Julaibib..Ke Sudaida zo nan...tayi kunnen uwar shegu tashige wanka.Yakad'a kai yana yar dariya"Sudaida k'uruci dangin hauka... A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar talata,tana had'a lemun abarba da kashu ta toshe kunnuwanta da earphone,tana sanye da riga da zani na atamfa ruwan makuba da ratsin filawoyi manya da k'anana masu ruwan hoda da baki tayi wani irin d'auri na burgewa gashin kanta ta tubke shi da k'aton ribbon ruwan makuba,ta juya za ta d'auki siga caraf idanun su yahad'u, yana tsaye a k'ofa yanad'e hannayen shi a kirji,tad'auke kai cikin basarwa kamar bata ganshi ba,dan har yanzu a wuya take dashi, ba Yaya Julaibib d'in da tasani a da to yanzu ba shi bane,gaba d'aya ya canja Hali,d'azu-d'azu yagama yarfa mata ruwan bala'i wai yaran Kawun su yazo,ita kuma ta manta bata sa hijab ba tazauna suna shan hira da dariya. Tagama aikinta tazo za ta wuce yatare hanyar yana kallanta cikin natsuwa kamar wani abu bai faruba,ko da yake shi tsakani da ALLAH yamata nasiha irin haka bai dace ba dan kayan sun kamata kome na ta ya bayyana,itace dai ta maida cibi yazama k'ari.Na yi sallama baki amsaba,na tambayeki abinci na nan ma kinyi shiru lafiya kuwa?Taturo baki gaba"shiruma amsace. Sudaida ba magana nake miki ba? Nan ma tayi shiru.Me yasa kike jamin zarene kin san halina fa. Tamishi wani kallo me kama da harara,cikin fushi tace"to sai me?Me tsoron ta mutu ai shi yake maho.Yayi jimmm...Yana cigaba da kallanta cikin nazari,wucewar wasu dak'ik'u sai yajuya...tabi bayan shi da harara"ALLAH raka ta ki gona...Yaja yatsaya zai juyo sai kuma yafasa yayi tafiyar shi kamar baiji abinda fafad'a ba. Tana azkar d'in yammaci bayan ta idar da sallar la'asar tana tunanin a ina Yaya D'ansarai yatsaya bai dawo gida yaci abincin rana kamar yadda yasaba ba,duk da ba wani d'asawa suke yi ba,...shiru-shiru har bayan sallar isha'i haushin shi yakamata ita kuma ta k'i kiran shi a waya taji me yatsaya yi taje tayi kwanciyarta tana zencen zuci"wato ko da, da take son shi take kukan rabuwa dashi,to shi dai ba ta ita yake yiba tunda gashi suna zaman aure yana mata yadda yaga dama, tadad'a gyara rufa tana k'wafa aikin banza kawai tura agwagwa cikin ruwa,jikinta yayi sanyi "lallai san maso wani k'oshin wahala, har bacci yayi awon gaba da ita bataji shigowar shiba. Da safe tana tsaye a jikin taga ta zubama motar Julaibib idanu,tun jiya bai fita da ita ba,sanda yadawo gidan tariga tayi bacci kuma bai tashe taba, anyama ya dawo gidan? dan yadda ta ajiye mishi abincin dare haka taba almajiri dasafe, bai ta6a ba,har d'akin shi taleka yanzu kuma ba ya nan,to ina yatafine?Wata kila tun daga sallar asubahi yawuce gidan Inna ko gidan Hajiya,ta lumshe idanun ta tana mamakin canjin halin Yaya D'an Sarai. A hankali ake k'wank'wasa k'ofar. Tasauke numfashi,ranta ya mata dad'i Julaibib ne dan haka yake buga k'ofa na natsuwa.Tabud'e cikin d'okin san ganin shi ta ma manta da rashin jituwar su.Suka kalli juna yamata murmushi, murna ta koma ciki,zuciyarta tayi rauni,kwallah yacika idanun ta,ta rasa hujjar hakan wallahi, yarage fara'ar fuskar shi,yagyad'a kai labarin zuciya a tambayi fuska"ba kya maraba dani ko?Sai kawai yajuya, dasauri taruk'o gefen rigarshi tabaya"wallahi ba haka bane,yajuyo fuskar shi ba walwala"toh yayane?Taja da baya tabashi hanya dan yashiga,yakad'a kai"bazan shiga ba. Tamarairaice"Yaya Aminu dan girman ALLAH kayi hak'uri kashigo,wallahi na yi kewarka ne,tunda aka kawo ni Lillahi warasulihi sai yau d'in nan kazo duk yadda muke da kai..tayi furucin da yanayin shagwa6a.Yashiga D'akin-shak'awar yazauna a kujera"to banda abinki Sudaida yaushe zan ta zirga-zirga a gidanki? Tashige D'akin-girki dasauri takawo mishi kunun tamba yasha madara "Yaya Aminu ga mutumin.Yabud'e kofin yagani"to nagode Sudaida,kad'an yasha saboda ya riga ya k'oshi,a gida ma yana da wanda bai shaba na wajan Innan D'ansarai. Sun d'an ta6a hira sannan yace mata kishiga d'akin mijinki ki d'auko min mukullin motarshi zan kai ta gyara, ba yadda banyi dashi akan yad'auki tawa yayi tafiyar ba amma yak'i,sai tasha naraka shi yashiga motar haya,kuma a ranar yanada jarabawa...har tabashi mukullin yatafi hankalinta yayi mugun tashi"yanzu D'ansarai zaiyi tafiya yabar garin amma ko sallama bazai mata ba? Itako wace irin kiyayya yake mata haka? Ai ko kafin suyi aure yana mata sallama bare yanzu da take cikin gidan shi a k'ark'ashin igiyar aure.Tayi k'wafa"ai ba lallai ba tilas,yaje yadawo tana sauraren shi da duk ma wacce zai zo. Kwanakinshi biyu da tafiya,shi bai kira ba, itama bata kira ba,a kwana na uku ne dai takasa daurewa dan abin tsoro yafara bata...sai taga bata kyau taba itace a k'asa dan haka tasauke ...rawanin tsiyar tanemeshi. "Lafiya? Tamabayar daya mata kenan daya d'aga wayar,bai kuma jira amsar taba yakasheTacire wayar daga kunnenta cike da mad'aukakin mamaki" wai me wannan mutumin yake nufi ne? haushi da damuwa suka kamata.. tajafa wayar a kujera ko tunanin taci screen bata yiba, tawuce D'akin-girki tasauke dafadukan taliyan data dafa, tazuba a faranti takoma D'akin-shak'ata dan taci, sai dai tanata kallan taliyar har yayi sanyi baza ta iya ciba,ai ko almajiri yana kwala barar"allazi wahidin"tabud'e k'ofa tajuye mishi duka a robar shi.Yakar6a da rawar hannu data murya. "Iya ALLAH yabi yaki,ya yaye miki matsalar rayuwa.Tabishi da kallo tana fad'in"amin d'an Malam.Sauri yakeyi kamar zai ta shi sama dan kada sauran almajirai su farga da abinci a kwanon shi su rufar mishi, gashi kuma wasu gardawa ne guda biyu suka sashi ya barato musu abinci,idan bai kai musu ba ba k'aramin na jaki zai shaba,kuma ba shi da mataimaki sai ALLAH. Abu kamar wasa k'aramar magana ta zama babba,yau makon Jukaibib d'aya kuma koda wasa bai kira taba...Abun yak'ara jefata a kokwanto da fargaba"to lafiya kuwa?Gashi ba wanda za ta tambaya,haba ai da kunya sai a mata tirrr...wasu kuma su mata dariya su d'auketa sakarya ita da mijin ta amma bata san a halin da yake ba?Taja tsaki"to shi d'in ya kira tane?Ko ko dai idan akak'i jininka ko ruwa kafad'a sai ace ka tada k'ura?Wucewar wasu dak'ik'u tana zaune tunani barkatai ya cika k'wak'walwarta ta rasa na za6a tayi shi da gasken-gaske,ta tsuke baki kamar za ta rufe shi tana fitar da iska,gaskiyar magana kawai ta kasa samun natsuwar zuciya dan haka tak'arya 6illenta tad'auki waya takira shi. Bugu d'aya yad'aga kamar dama jiran ta yakeyi.Yayi sallama muryar shi a dake.Ta amsa sallamar tana gaishe shi.Asik'e ya amsa"lafiya...Gwiwoyinta suka sage,sharrr... sharrr...hawaye yafara sintiri a fuskarta shashshek'ar kukan na ta na fitowa a hankali. Yatare ta muryar shi ba sassauci"ke! Dakata, dakata haka malama! ni na ta6a fad'a miki ina sha'awar jin sautin kukan ki,bare yanzu da kike jinyi ki kirani?Yaya Jul...Kittt...Yakatse wayar. Haushi da mamaki suka rufe ta,ranta in yayi dubu ya6aci "Lallai ma D'ansarai...To ko da aka ba ka ni, idan ban maka ba sai ka sallame ni...tacigaba da kuka. Julaibib yacire wayar a kunnen shi yana murmushi"kulawa yabawa ce,ya kamata yakoma gida haka dama kullum idan sunyi waya da Hajiya sai ta mishi ciwon bakin yaje ya share waje kamar mara Iyali.Baba ma jiya sai da yace"Malam D'ansarai ka k'ok'arta duk lokacin daka samu dama kazo gida wajan Iyalin ka kaji ko?Ya amsa da ladabi"eh Baba Insha-ALLAH. Yakulle k'ofar d'akin shi dan tafiya masallaci, masallatai mabambanta sunata kiraye-kirayen sallar azahar. Da yammacin ranar talata rana ta tafi tana shirin fad'uwa,magriba na kunno kai tana zaune a tana nazarin littafan Islamiyyarta,motsin shigowar Julaibib taji yana shiga da kayayyaji D'akin-girki,sai da yagama yashiga D'akin-shak'tawar da wata babbar leda,a gajiye ya zauna yana kallanta yasa hannayen shi yana 6alle botirin gaban rigar shi,bata wani nuna d'okin ganin shi ba,fuskar ta ba yabo ba fallasa tace mishi"sannu da zuwa.Yagyad'a kai"yauwa yana cigaba da nazarin ta. Sudaida...Yakira ta. Bata d'ago ta kalle shi ba ta amsa "na'am.Duk sukayi shiru,ta sunkwui da kai amma ta kasa cigaba da nazarin kallan littafin kawai takeyi amma baza tace ga abinda aka rubuta ba. Ana fara kiran sallar magriba yafita. Tana kwance bayan ta idar da sallar Isha'i,zuwa wannan lokacin zuciyar ta ta gama tafarfasa ruwan ciki ya k'one k'urmus har ya kama da wuta,zuciyarta tayi gobara saboda takaicin D'ansarai autan Inna;tayi kwafa taja dogon tsaki tun wajejen k'arfe goma sha d'aya da rabi na safiya Hanifa tazo tafad'a mata"Baba D'ansarai ya dawo,har ya bata Inibi da dabino me yawa, tashigo ma da Inibi tana ci,wani sanyin dad'i taji a ilahirin gangar jiki da sararin zuciyarta,duk da bawani d'asawa suke yiba,ta tambayeta to yana ina? Hanifa tace yana gidan su"Kawu Adnan shi da Babana(Musaddiq) Nan da nan ta dad'a gyara ko ina tayi wanka tayi kwalliya tafeshe jiki da turare,ta turara d'akunanan gidan da turarukan d'aki ko ina yad'auki k'amshi da kyalli;to amma saboda tsiya d'inkin ludayi wai sai gab da magriba yaga damar shigowa gidan,kuma ko dak'ik'a goma cikakku bai yiba yasake ficewa,bai kuma sake shigowa ba sai yanzu awa biyu da idar da sallar Isha'i. Tamaida idanun ta tarufe kamar me bacci. Yatsuguna yana tashin ta,dak'yar ta tashi tazauna tana turo baki gaba,yakoma kujera yazauna"zan samu abinci?Takauda kai"banyi girki ba,dan wanda tadafa mishi da rana,bayan la'asar tajuye ma almajiri.To ko shayi ne had'a min yunwa nake ji.Batayi magana ba dan dai ba yadda za tayine da baza ta had'a ba,tad'an ja tsaki"aikin banza harara a duhu,shi baya gajiya da shan shayi, shayin ma daba a sa madara sai kace jikan buzaye,tahad'a takawo mishi lokacin ya shiga wanka,yafito cikin fararen kaya na shan iska, botiran gaban rigar a bud'e suke gargasar shi akwance lufff...bak'ink'irin da shek'i. Yad'auki shayin da bismillah yad'an kur6a sai yakalleta"me yasa kika samin siga bayan ga zuma?Tad'an harare shi"ni siga nake sawa a shayi,ai ba mutuwa za kayi ba.Yayi murmushi yana kad'a kai"k'uruci dangin hauka ga abinda aka tambaya ga amsar da take bayarwa "Sudaida mutan Matsirga suna gaishe ki,suna nan zuwa.Shiru ma amsa ce.Yabita da kallo"ke wai lafiyar ki kuwa? Ko dawowar tawace baki so?Ni fa shi yasa bana san zuwa,tunda raina ne yake 6aci.Tamishi wani kallo me kama da harara"na rantse da girman ALLAH ni...sauran kalaman suka mak'ale saboda haushin daya mamaye ta,takaicin ta ace yazo garin tun farar safiya,bai shigo yaganta ba,amma ya tafi Matsirga ba dangin Iya bare na Baba,dangin-dangirere wata tsohuwar budurwar shi data dad'e a kushewa,itace 'yar gwal har yanzu itace a sararin zuciyarta shi.Cikin fushi ta kwashi littafai da daddumar data yi sallah fuuu... Tawuce d'akin baccin ta. Ya ajiye kofin shayin a saman tebur yayi shiru da yanayin damuwa"me yasa Sudaida take mishi haka?Ai itace k'arfin dawowar shi a yau,amma ta watsa mishi k'asa a cikin idanu;duk yadda ya d'okantu da ita a yau d'in amma da ta shi mazantakar tamotsa sai ya danne zuciyar shi bai bi ta d'aki kamar yadda zuciyar take raya mishi ba,ya kwaso wasu littafi yana nazarin su. Tacire wayar ta a caji tahaye gado sannan ta kunna data,sak'onni suka dinga shigowa bata ta6a wayar ba har sai da suka gama shigowa sannan ta fara duba Status d'in su Khausar,haushi yadad'a kamata,ganin kowacce tana cikin shauk'in k'auna ita da masoyin ta...A status d'in A'isha ne taga Hashim ya zage yana daka shakwara a turmi tana ce mishi baiyi laushi ba sai ya k'ara dakawa,shi kuma yana fad'in nagaji fa gaskiya..ga wanda suke cin sakwaran da miyar Ogu suna dariya. Ga na Khausar nan ita da Huzaifa sunyi wani irin kyau na ban mamaki gaba d'ayan su sun canja,ta d'ora ha6arta a kafad'arshi suna dariya, d'ayan kuma wasu irin kalamai ne na tsananin k'auna ta rubuta shi ga hoton zuciya an gewaye ta da adon filawar Damask rose-flower. Na maryam kuma hummm sallah ba a magana,ta yi mugun mamakin abinda ta d'ora a irin yanayin zaman da tayi da kuma kayan jikin ta,a k'asa ta rubuta"My Snuggle...I miss you deadly... tabbb...ai bata gama kallo ba tabari tana zagin ta "abinda yasa meki ALLAH yasa kar yasamu sauran dangi.Tayita kira layin ta a kashe, duk da ta san taza6i wad'anda za su ga Status d'in na tane,amma ita sai hakan bai gamshe taba gaskiya. "Nasmat tamata magana" Hummm...Amaryar autan Inna kuna shan sharafin ku fa.. Sudaida ta6ata fuska"a ah abinda yafi sharafi muke sha. Nasmat takyalkyale da dariya...nima naga alama shi yasa sai jefi-jefi a ke ganin ki online...har yanzu kanwa bata kar tsamin bane k'wannafin yakwanta? Sudaida taja dogon tsaki"ke dai kika sani da neman magana ni sai da safe...kawai ta kashe data ta kwanta;bata duba sak'o ko guda d'aya ba,tunani barkatai ya cika k'wak'walwarta "hummm yunwar ya tashi"taja dogon tsaki wallahi ai ba lallai ba tilas. Washe gari ma da sassafe yabar gidan wai suna da taro a Zango Urban kamar tace yasiyo mata d'anbagalaje amma ta shareshi,ta d'auki wayar ta takira Yaya Aminu tana tambayar shi"kaima kana Zangon ne?Eh Sudaida.Dan ALLAH Yaya Aminu d'anbagalaje nake so amma me taushi.Kai kai kai Sudaida ai gwamma me k'arfin kinga za ki motsa muk'amuk'inki da dasashi ko kuwa? Tad'an marairaice"Yaya Aminu ni dai me taushi.To zan siyo miki Insha-ALLAH. Yauwa Yaya Aminu wallahi, shi yasa nake son ka ALLAH yabarka da Sidddiqa tazama sarauniyar ka.Amin Sudaida. Sukayi dariya. Abubuwa suke ta maimaituwa na rashin fahimtar juna a tsakanin su,musamman Sudaida da take d'aukar fushi a abinda bai kamata ayi fushin ba,abun ya k'i ci ya k'i cinyewa kamar cin k'wan makauniya.Yauma tunda yatafi masallaci sallar asubahi bai dawo gidan ba.A hankali taji ana k'wank'wansa k'ofar gidan ta san shine, dan taji tsayuwar motar shi.Tatashi tabud'e takoma tayi kwanciyar ta.Yatsaya a tsakiyar d'akin hannayen shi nad'e a k'irji. "Sudaida bak'in Matsirga sun zo. Dammm...zuciyar ta tabuga da k'arfin gaske.Tafara zancen zuci"Kutumelesi wato zuwa yayi dakan shi yad'auko su?Su suna da mutunci da kima a idanun shi,ya kuma damu dasu amma ita ko oho ko? Tajijjiga kai wani...kumallon mata yata so mata har wuya,amma ba tayi ko kawa da zuciyar ta bata amayo shiba.Tad'ago takalleshi"Oh sun zo?Tagyad'a kai"toh sannun su da zuwa. Yabita da kallan nazari ganin tana dad'a gyara kwanciya har da jan bargo ta lullu6a"ke wai menene haka?Kitashi kije ku gaisa mana. Tayamutsa fuska sannan tajuya mishi k'eya "gaskiya ni har yanzu bacci ne a cikin idanu na kum...Yatari numfashin ta "Innar su Bilkisu ce fa? Furucin shi yamata sukar wuk'a a k'ahon zuciya wallahi ta kasa daurewa,idanun ta suka kawo ruwa"shikenan kuma dan kayi bak'i bazan yi bacci ba,bayan idanu na har wani zafi da yaji-yaji suke min saboda rashin baccin?Ni fa na rantse da girman ALLAH bazan iya wannan zaman ba,tunda baka d'auke ni wata tsiya ba,toh ba dani ba wannan takuran,ko dan kaga gidan kane? Tagalla mishi harara"an hak'ura ana shan kukar k'azama kuma dole sai tayi tsada?Wallahi sai a hak'ura tunda ba mutuwa za ayi ba ehemmm. Suka zubama juna idanu cikin kallan-kallo nawucewar wasu dak'ik'u kowa zuciyar shi ba dad'i. Sudaida tana jiran martani ne tayi abinda idan ta tafasa za ta k'one,sai shi kuma yamata shiru,dan yadda ta6ata mishi rai idan yatsaya toh aika-aika za ayi,sai kawai yagyad'a kai"ki cigaba da abinda kike yi,amma fa kowa yaci ladan kuturu sai ya mishi aski,wanda ya girmama iyayen wani to bana kowa ya girmama ba sai na shi.Yakai hannu yak'ara mata gudun fankar "shikenan kiyi baccin ki.Yajuya yafita fuskar shi ba walwala,labarin zuciya a tambayi fuska. Tad'aga murya"eh yanzu kuwa zanyi baccin.Sai kuma tamik'e jikin ta yayi sanyi gaskiyar magana bai kamata tayi haka ba"ai bak'on ka annabinka, wanda yadamu dakai shine zai zo inda kake to bai kamata kanuna mishi halin-ko-inkula ba"bak'in karen masoyinka ai yafi farin ragon mak'iyinka. Yayi jimmm...nawucewar wasu dak'ik'u a bak'in k'ofa,Sudaida ta k'i fitowa ta musu sannu da zuwa to me zai fad'ama Inna?Sai yajuya zuwa D'akin-girki yad'ibo musu kofuna da lemun biyar a raye da ruwa har zuwa lokacin bai samo amsar dazai ba Inna ba,yahura iskar bakin shi"lallai Sudaida zata gane da gero ake koko yacigaba da tafiya,zai fad'a mata Sudaida bata nan. Yamurd'a k'ofar D'akin-shak'atawar da sallama yashiga,sai dai abun mamaki Baturiya da suna manga Sudaida yagani durk'ushe a gaban Inna tana gaisheta cikin girmamawa"kun zo lafiya? Yasu Malam da sauran mutan gidan?A Alhamdulillahi lafiya lau,duk suna gaishe ki,sannu mungode.Daganin yadda Inna take amsawa itama taji dad'in shimfid'ar fuskar da Sudaida tamata wacce tafi ta tabarma.Tamik'ama Bello hannu sukayi musafaha "d'an kanina kaga dana iya yaren fulatanci toh da yau duk hirarmu da fillanci za muyi shi. Bello yad'an bud'e idanu"kai dama baki iya ba?To kisa Yaya D'ansarai ya dinga koya miki mana,kinga lokacin da Adda batayi wannan tafiya me nisan nan ba to idan yazo da fillanci suke magana suyi ta dariya,ranan nan ma yace mata wai...Kai Bello Inna ta tari numfashin shi'ba na hana ka fad'an abinda ba a tambaye kaba? Sai yayi shiru. Da sauri Sudaida tamik'e ta kar6i kayan ta zuzzuba musu lemon a kofuna sanna tashiga D'akin-girki ta d'auko musu abincin data dafa tajuye a food-flask tana mita a ranta"kai ALLAH yasuwake da halin D'ansarai yanzu da suna da yawa dole sai tayi wani sabon girkin. Inna tasha lemon amma tak'i cin abincin.Sudaida ta karyar da kai gefen dama"haba Innarmu idan baki ciba ai baza muji dad'i ba,ni 'ya ce awajen ki,uwa kuma ai bazata k'i cin abincin 'yar taba ko da tak'oshi za tasa albarka,Inna idan bakiciba sai inga kamar da wata a k'asa a yadda muka d'aukeki ni da Yaya D'ansarai ke ba haka kika d'auke muba...suna had'a idanu tad'an harare shi sannan ta kauda kai. Inna tace"ba haka babe Sudaida, karki kuma furta irin wad'annan kalaman,ni na d'aukeku kamar Ya'yan dana haifa,ALLAH yamuku albarka,yabaku zuri'a d'ayyiba. Dole ta d'auki cokali tayi bismillah sannan tad'an ci kad'an, Bello kuma yace shi baya shi dan bayajin yunwa yanata cin meatpie da su Inibin da Julaibib ya bashi.Da za su tafi Sudaida tabata turmin atamfa,taba da Shadda yadi goma da turare wai aba Malam tana kuma gaishe shi,tak'aro ma Bello meatpie dayawa dan jiya tayi kuma ba wanda yazo gidan shiyasa bai k'areba.Yakalleta yana ta murmushi "kince za ki Matsirga?Tagyad'a kai"eh Bello zamu zo Insha-ALLAH.Yamik'a mata hannu sukayi musafaha "Adda Sudaida sai kinzo zan tatso miki madarar saniyata da Malam yabani karsana guda biyu nawa ni kad'ai ina kaisu kiwo har rafin Matsirga nake kaisu susha ruwa sai mudawo gida,sukayi dariya.Sannan ta rakasu haraban gidan suka shiga mota.Sudaida tasunkuyo tana maimata" ALLAH yatsare Innarmu,ALLAH yakaiku gida lafiya.Amin Sudaida, Inna tadinga shi mata albarka,tasa gefen hijab d'inta tana share ruwan hawaye,yau mutuwar Bilkisu ta dawo mata sabuwa.Suka d'aga hannu suna ma juna adabo.Julaibib yaja motar cikin karsashi,yana murmushi jin dad'i abinda tama Innar Bilkisu ya kankare duk wani bak'in laifi data mishi dayake jin haushi...wata irin k'auna da kewar ta suka mamaye ilahirin gangar jiki da zuciyar shi. Yadawo yatar da jarkokin kindirmo dana manshanu da sauran tsarabar da Inna takawo a inda yatafi yabar su.Yatsaya a gabanta hannayen shi suna cikin aljihun doguwar farar rigar shi,yakalleta cikin natsuwa"Sudaida ya baki adana suba?Saboda bani da buk'atar sune. Tagama wanke-wanken da take yi tamik'e tana yarfar da ruwan hannayen ta,tawani tsuke baki kamar me shirin yin fito.Yagyad'a kai"toh bani abinci sauri nake yi zan tafi Samaru.Cikin fushi tace"na rantse da girman ALLAH tun kafin wankin hula yakaika ga dare kasan inda za kaje kaci abincin ka,danni ba baiwa bace. Yazuba mata idanu"ji wasu soki burutsu da yarinyar nan take fad'a,yakalleta cikin natsuwa"nine bawan ki kenan, tunda duk rintse zan fita in nemo in kawo miki ki ci ko? Taturo baki gaba"ko bani dolen-dole kafita ka nemo,to ni guda nawa nake cin abincin? Kinga ba wannan ba d'auko min abinci na fad'a miki sauri nake yi"na daina girki a gidan nan, tunda ko a tsarin shari'a ai cewa akayi miji yaciyar da matar shi bawai mace tayi girki ba.Yagyad'a kai"to amma dai yin girki a wajen mace dole ne,tunda kyautatawace idan miji yafita ya nemo muku,ke kuma sai ki dafa muku, a kuma al'adar duk mutanen dana sani galibi matane suke yin girki haka aka taso anayi Iyaye da kakanni tun tale-tale.Ba sai da so da k'auna za ayi hakan ba?Tafara k'unk'uni.Shima sai yanzu ya harbo jirginta...kumallon mata ke d'awainiya da ita,to amma me san d'an tsuntsu shi yake binshi da jifa. Yarik'o ta tana k'ok'arin fizgewa sai yamata rik'on kura ta samu nama,sai ta koma tayi lamooo "Sudaida a duniyar ALLAH me namiki da bakya so na?Yad'ago fuskar ta suka kalli juna"haba Zaujatiii...Dan girman ALLAH fad'amin abinda zan miki dan in samu k'auna da soyayyarki.. yagewaye hannayeshi a jikinta yana mata wani salo...yayi k'asa da murya yana mata wasu irin kalamai na rarrashi da bambaki me k'aryar da damuwar data mamaye sararin zuciya. Sak'onnin na shi yana shiga ilahirin gangar jiki da zuciyarta duk da bata so hakan ba amma zuciyar ta tak'i bujirema hakan,k'aunar shi da haushin shi yamamaye ta,sai kawai ta fashe da kuka ta k'wace tashige d'akin bacci tafad'a gado takifa fuskar ta a jikin matashi tana jin wani irin abu dabata san ko menene ba. A tsakiyar d'akin yaja yatsaya yana kallanta"to meye abun kuka?Kai sha'anin mata a wasu lukutan sai su wallahi,banda dabi'arsu ta rauni da kuma dai shagwa6a wai tarwad'a da kukan k'ishin ruwa.Agefen gadon yazauna,yarik'o hannunta"kinga kukan ya isa haka share hawayen ki dan yana ta6a min zuciya,zai hadda sa min rud'ani fa...ta tureshi"Kalaman ka baza suyi tasiri a zuciya ta.Yagyad'a kai"toh na nawa kuma? Yaya D'ansarai ba ka so na dan tunda aka kawo ni gidan nan nayi adabo da farin ciki,kazo garin nan tun farar safiya amma sai gab da magriba za ka shigo gidan, sannan sai kadinga nuna min wasu can sun fini mutunci tunda za kaje wajen su kasahare waje kuyi hira,ni kuma ko oho,idan nakira ka a waya sai kadinga min fad'a... kaza da kaza haka tadinga fad'in duk abinda yazo bakinta"ni gaskiyar magana na gaji da matsalolin ka,idan cuta tak'i ci tak'i cinyewa ai rai take nema. Yayi yar dariya"wato laifi tudune...ba nine sama da ke ba?Ko ba aure tsakaninmu ai bai kamata zan fita kice min"ALLAH raka taki gona ba.Kin San wannan kalmar ta min ciwo ta kuma bani mamaki wai daga bakin ki tafito?Dan na miki fad'a akan abinda yake dai-dai?Dama gyara kayanka yana zama sauke muraba Sudaida? Tasunkwui da kai,itama ta gane tayi kuskure"Yaya D'ansarai...ta kira shi,sai kuma taja tayi shiru. Yakalle ta"na'am ya aka yine?Da rawar murya tayi furucin kayi hak'uri na gane kuskure na...Idanun ta yaciko da kwallah. Tad'ora ha6arta a kafad'arshi ta dama" kayi hak'uri...Na yi Sudaida ni ai ina son ki a kowani hali da yanayi kece dai kika ce sai kina sona za kimin girki ko?Tayi shiru cikin alamar kunya.Yakalleta yanzu dan girman ALLAH babu soyayyata dank'are a taki zuciyar?Tad'an ta6e baki a zuwan furucin shi bai gamshe taba ko a kwalar rigarta.Tajanye ha6arta tana mishi wani kallo cikin turo baki gaba,da yanayin shagwa6a ta tambaye shi"me kake cewa?Shima yarama irin kallan data mishi"a ah bance kome ba.Takyalkyake da dariya. Yawatsa hannaye "magulmaciya kawai ana so ana kaiwa kasuwa;uhhh yakama ha6a"wato an hak'ura ana shan kukar k'azama...kafin yak'arasa tarufe mishi baki da tafin hannunta na dama"ai dai na ce kayi hak'uri... Yasauke numfashi"ni dake muna san auren nan ba na dole aka mana ba,fad'uwa ce tazo dai-dai da zama,sai dai fa Sudaida bani da lafiya.Tad'ago tana kallan shi.Yalangwa6e kai "bakiga yadda na rame bane Zaujatiii... tamishi kallan tsafff sai taga hakan har a kan fuskar shi, tabud'e idanu cikin tsoro"toh me yake damun ka! Kayi rashin lafiya ne ban sani ba lokacin kana makaranta?Yagyad'ai"eh ai kullum a cikin ciwon nake...Cikin fargaba tasake binshi da kallo"ciwon me?Toh me yasa baza kaje asibiti ba Yaya Julaibib?Ai ciwon son kine bana ganin likita ba,nayi fama da kewarki sau shurin masak'i Zaujatiii.. So ba k'arya bane,wani mikine a zuciya ta"Sudaida ki furta min kina so na,kina k'auna ta, za ki zauna dani,muyi hak'uri da juna tunda zo mu zauna zo mu sa6ane. Tajijjiga kai"ni na yadda na amince,ina son ka,ina k'aunar ka akowani irin hali da yanayi mun zama k'arfe da mayen k'arfe Zaujiii... Yagewayeta da hannayenshi"hankali na ya kwanta, bani da sauran shakku,ba abinda za kimin yasake bani tsoro.Tayi murmushi"uh uh fa Yaya D'ansarai karkamin kurifa?Yagirgiza kai"ai nagane logonki yarinya,ba kuri bane,duk abinda za kiyi a banza wai talaka ya girmi sarki.Tagyad'a kai"ALLAH dan dai na tuba ne...sukayi dariya zuciyoyin su fesss...Hummm...Fushin masoya hutuhhh.... Nurse A'isha Muhammad Jibril{Asdilat for real💋} Ubangiji ya kiyaye min ke da kiyayewar shi,yatsare hanya,yakaiki Nursing School Mak'arfi lafiya. Ubangiji kama karatun na su albarka.Kasa su amfani kansu su amfanar da d'aukacin al'ummar Manzon ALLAH,da ita da duk wata Nurse dake fad'in KD garin gwamma da sauraran Jahohin mu na arewa,dana sauran yan'uwa musulmai na duniya kaafatan👏 Bar ganin ka ta ra...kiyayi me nema. A sara a kasuwanci jari. 15 Jumaada Thani 1441 9 February 2020 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintikau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na ashirin. Yaciro sakamakon jarabawarta a cikin jaka ya bata tana gani,ta samu sakomako me kyau credits shida har da lissafi da turanci"toh tunda kince kina so na,za kicigaba da karatun ki kwanan na.ALLAH da gaske Yaya Julaibib? Yagyad'a kai Insha-ALLAH.Tak'ank'ame shi tana bashi sumba da godiya...gaskiya na k'ara son ka ninkin ba ninkin,malala gashin tinkiya.Suka kalli juna suna dariya. Safiyya ta haifi sankacecen yaron ta me girman ban mamaki.A gidan suka had'u dukan su suna ta hirar yaushe gamo ta baki da baki duk da kusan koda yaushe suna had'uwa a Whatsapp. Khausar tasake kallan yaron sannan tayi yar dariya"gaskiya Yaya Safiyya duk girman cikin nan ki ban zaci d'a d'aya za ki haifo mana ba. Tagalla mata harara"toh madallah ke idan kin ta shi sai ki haifo yan hud'u.Tagyad'a kai"za ko kisha mamaki. Zainab takama ha6a"ke Khausar yau she akayi daren da gari zai waye ne?Yi hak'uri Maman Hanifa.Safiyya tayi murmushin mugunta"ai akan tafe kan isa Khausar,ALLAH dai yabamu rai da lafiya za kiji jin jikinki,ki kuma gani ganin idanun ki... Sai bayan sallar azahar Sudaida tawuce gidan Inna,anan ta tarar da Nasmat taje gaishe da Inna da bata ji dad'i ba kwanaki biyu da suka wuce.Tazauna tana tayata ninke kayan wankin Inna suna ta hirar su suna shan dariya, basuji shigowar shi ba sai ganin shi sukayi tsaye a bakin k'ofar yanad'e hannayen shi a k'irji"hirar me kuke yi haka ina ta sallama ba wacce tajini bare ta amsa.Nasmat tace"au yi hak'uri autan Inna bamu ji bane.Yagyad'a kai yana kallan Sudaida"d'an zo mana. Tamatsa wajen shi suna k'us k'us k'us d'in su,Sudaida tana kyalkyala dariyar kalaman daya fad'a mata.Nasmat taja tsaki"ke tunda maganar taku ba tak'are bace,to nifa tafiya zan yi kina 6ata min lokaci sai kace ba gida d'aya kuka kwana ba.Yajuya jeki Zaujatiii wannan yar sa'idanu ce.Tad'an d'aga murya"Yaya D'ansarai karfa kamanta. Idan na manta ki tuna min tawaya kafin in dawo.To adawo lafiya. Nasmat tabita da kallo"wato ke da D'ansarai abun nema ne yasamu matar falke ta haifi jaki. Kamar yaya?Tayi mumushi"ke dashi d'in duk kuna matuk'ar k'aunar junan ku,sai yanzu k'wak'walwata take hasko min wasu yanayi da nake gani a tattare daku na tsananin kishin juna a kowani hali da yanayi,kishi kuma baya k'ayatarwa matuk'ar ba soyayya,toh ALLAH ya dauwamar da k'auna har Darul-karamah(Aljannah) Sudaida tayi lallausan murmushi"ai ba ja kare ya mutu a juji.Ina son Yaya Julaibib amma halin miskilancin shi wasu lokutan yana bani haushi.Nasmat ta kyalkyale da dariya"miskili ka fi mahaukaci ban haushi.Abdul yashigo da rake ferarre,atile,yalon Bello da d'anbagalaje yakaima Inna a D'akin-girki wai inji Kawu,tana dubawa tamik'a mishi ledar "wannan dai Sudaida zaka kaima,maza tana D'akin-shak'atawa. Nasmat ta tafi,amma ita har dare tana gidan.Bayan sallar Isha'i Alhaji Abdullahi yashigo. Tamik'e da sauri takar6i kayan hannunshi tana mishi sannu da zuwa,yasa6a babbar rigarshi fuskar shi cike da fara'a"a ah Sudaidan Malam D'ansarai ce?Ta sunkwui da kai.To sannu da zuwa,yashiga D'akin-shak'atawa ita kuma takai kayan D'akin-girki sannan taje ta gaisheshi cikin ladabi."Lafiya lau,kunanan lafiya ko?Tad'anyi murmushi tana murza zoben hannunta,itafa har yanzu nauyin Baba take ji tunda akayi auren nan. Yacigaba, "ALLAH yamuku albarka,ayita hak'uri rayuwar duniyar ma gaba d'ayan ta hak'uri ce,idan akayi hak'uri da yawa aka jajirce, agaba sai kiga anyi nasara a koma menene.Yasa hannu a aljihun rigarshi yar ciki yad'ibo kud'i yan d'ari biyar dabai san ko nawa bane yabata.Tasake sunkwui da kai "Baba kabarshi nagode.Yakad'a kai"Sudaida kinga...tad'an d'ago takalleshi"ai ba wanda yake k'in alheri sai shaid'an, ke ai ya tace,a kowani lokaci naga dama zan iya miki kyauta ko da baki zo ba,to zan iya aika miki dashi har gidanki.Tasa hannu biyu takar6a"nagode Baba ALLAH yak'ara girma.Amin Sudaida. Yamik'e yatafi d'akinshi. Har tafara bacci a gadon Inna yashigo gidan.Baba yarufe shi da fad'a"kai Malam D'ansarai ban sanka da yawo kamar wanda yaci k'afar kare ba ko da daba ka da Iyali bare yanzu, ina katafi ina ta kiran layinka bata shiga?Ya amsa da ladabi"amin afuwa Baba,wallahi Gidan-Waya natafi game da karatun Sudaida,sai kuma nayi rashin sa a sai mako me zuwa,ni kuma ba na nan, kuma na tsaya ganin Provost d'in makarantar ne. Wayata kuma mutuwa tayi saboda rashin caji. Yagyad'a kai"to ALLAH yataimaka,amma maganar karatunta ai ba damuwa ko da baka nan,zan sa Aminu yayi kome.Yakalle shi kwanaki nawa za kayi kadawo?Baba nima ban sani ba sai dai kawai anganni. Yanunashi da yaysa"to kadinga kiyayewa da da da yanzu bambancinsu na da yawa,bazan ji dad'i ba idan kana tafiya kana share waje kayi zaman ka iyalinka kuma ko oho ba,a zaman takewar iyali ba abinci da abun sha kad'ai ake buk'ataba a ah har da kai gundarinka,kuma kullum kadinga tunawa kai shugabane za kuma a tambaye ka game da hakkin shugabancin da aka baka kana ji ko?Cikin girmamawa ya amsa"eh Baba nagode ALLAH yak'ara girma. Inna takalkeshi"kai Julaibib dare na dad'ayi kashiga kaci abinci.To Inna,yashigo yazauna yana cin abincin,yana kallan labaran k'asa amma rabin tunaninshi na wajen Sudaida da take bacci,daya gama ci yakai kwanon D'akin-girki sannan yazo yatashe ta suka wuce na su gidan. Dasafe Aminu yaje gidan suka tattauna akan karatun Sudaida.Yakar6i k'ananan hotunan ta, Sudaida tashigo da sallama ta ajiye jug d'in hannunta a gaban Aminu"dama ina ta sauri dan karka tafi.Yad'ora duka hannayenshi a saman tebur d'in"ban tafi ba amma ba sha zanyi ba.Tacire murfin"kagani Yaya Aminu kunun tsamiya ne mutumin ka.Yayi murmushi"toh idan nasha na ki inyi yaya da Innarmu da yake jirana? Julaibib yace wannan za kasha tunda kullum na Inna kake sha,da rana sai kasha wancan.Yamik'e kai Malam damun manya ai yafi na yara gard'i kusha abunku,yabashi hannu sukayi musafaha "ALLAH yakiyaye hanya,sai munyi waya.Julaibib ya amsa da amin,nagode. Sudaida Ibrahim Me-Lambu ta fara karatun lissafi da kimiyyar na'ura me k'wak'walwa (Mathematics/Computer Science)sai dai tana shan zirga-zirga,lallai ilmi ba a samun shi da sauk'i, sai anyi gwagwarmaya kamar zuma yake ga zak'i ga d'ankaran harbi.Yau tana gidan Hajiya tana shan rake suna hirar Julaibib da suka gama magana dashi ta waya,shima yana can yana fafatawa da karatun. Gajiyace da samun waje wai kuturu da gad'a,bayan ta gama shan raken bacci yafara kawoma idanun ta ziyara.Hajiya tatashe ta,tamik'e zaune tana mitstsik'e idanu"Hajiya lafiya?Tagyad'a kai"lafiya k'alau,kishiga d'aki ki kwanta a gado mana.Takalli agogon dayake d'aure a hannunta nadama tad'an yi tsaki"lokaci ya ja sosai,sai tamik'e tanasa hijab,tad'auki jakarta tara taya "Hajiya gwamma in tafi gida yamma tayi sosai. Hajiya tace shikenan sauka lafiya,sukayi sallama tatafi. Bayan sallar Isha'i tana zaune tana nazarin littafan data barbaza akan daddumar datayi sallah, hankalinta yayi nisa akan karatun kamar a sama taji an maida k'ofar D'akin-shak'atawa an rufe,ba tare dataji motsin shigowa ba,tamik'e dasauri kamar za ta hantsila littafin hannunta yafad'i k'asa,tarintse idanun ta tana Istirja'i zuciyarta tana bugawa da k'arfi saboda tsoro, d'akin yayi tsit ba motsin kome sai karar agogon bango tik tik tik...Tasake kasa kunne,nan ma shiru bataji kome ba,sai tabud'e idanun ta wato kawai tsorata tayi?Takad'a kai"wallahi mutum rahama ne,yanzu ma dan dare yayi ne amma da gidan Inna za ta tafi,ALLAH yakaimu gobe na daina kwana ni kad'ai.Caraf idanun su yahad'u,yana tsaye nad'e da hannayenshi a k'irji, kafad'ar shi tadama rataye da jakar matafiya ruwan toka,yayi sharrr...dashi cikin farin yadi da farar hula zita.Tanunashi da yatsa"Yaya D'ansarai kaine da gaske ko kuma gizo ne?Yak'arasa kujera yazauna "matsoraciya kawai,to da gaske ni d'inne. Tasauke numfashi"wai ALLAH to sannu da zuwa,sai kuma tad'an turo baki gaba"amma gaskiya ka tsora tani,kuma d'azu munyi waya amma baka fad'amin yau zaka dawo ba?Nasamu sarari ne shi yasa nace yau kome dare sai nazo na ga Zaujatiii...Takawo mishi ruwa da lemu,yad'auki ruwan yanasha yana mata kallan nazari ta dad'a ramewa.Ya ajiye kofin yarik'ota"Zaujatiii...me yake damun kine? Tad'ago kai takalleshi kamar bata ji ba"na'am me kace?Sai kuma tagirgiza kai"ni ba abinda yake damuna,tamik'e barin maka abinci me sauk'i ko yar dafadukar taliyace... yabita da kallo bawai jikin na ta yake k'arema kallo ba,a ah tunanin irin ramar datayi kawai yakeyi,kuma acewarta wai ba kome? Yatashi yabita"ni fa bazanci wata taliya da daddaren nan ba gaskiya.To me zaka ci? Yakar6i albasar da take 6arewa ya mayar ma'ajiyarta"dafamin shayi kawai.Tayamutsa fuska "shayi dai shayi dai?Taturo baki gaba"nima gaskiya baza ka sha wani bak'in ruwa da daddaren nan ba,kai baka gajiya da shayi kamar wani d'an Niger?Yayi yar dariya"bari sujiki ba ruwa na,ke dan baki san sirrin da yake cikin wannan shayin nasu bane da neman shi zaki dingayi ruwa a jallo. Takyalkyale da dariya"ALLAH yasauwake in nemi shayin da ba madara.Hum yarinya baki san amfanin wad'annan ganyayyakin bane. Takalleshi"toh meye amfanin su?Yagirgiza kai"zan fad'a miki amma ba yanzu ba.Sai yaushe?Sai lokacin dana koya miki sha,idan nafad'a miki amfanin nasu zaki yadda dani d'ari bisa d'ari dan kinji a jikinki,amma yanzu idan nafad'a miki,ba lallai ne kiyadda ba"gani ya kori ji.Tashagwa6e ni dai tunda baza kaci taliya ba to kaima baka shan shayin sai dai muje kaci donut da yoghort.Yarik'o hannunta"na yadda muje. Dasafe tafito tsab cikin shigar kamala da mutunta kai"Tazauna a hannun kujerar da yake"Yaya D'ansarai taso ka kaini na kusa makara.Batare daya d'ago yakalle taba yanuna mata abinci"zauna ki karya kafin in gama abinda nake yi asibiti zamuje a miki General-check up. Tabishi da kallo cikin mad'aukakin mamaki"asibiti kuma? Tagirgiza kai ni dai gaskiya lafiya ta k'alau ba abinda yake damuna.Yad'ago yakalleta a gajerce yacigaba da danna na'ura me k'wak'walwa"kizauna kici abinci nace ko? Ni fa banajin yunwa kuma ai...sai yad'aga mata hannu ya isa.Duk sukayi shiru nawucewar wasu dak'ik'u,tasake kallanshi"Yaya D'ansarai zan makara fa.Yayi kamar baiji abinda take fad'a ba.Haushi yakamata tamik'e tsaye"ni na tafi.Nan ma shiru yayi.Tajuya tayi tafiyarta tana surutai"da baka sa min rai ba da tuntuni banyi tafiya taba?Dama ai na saba tafiya ni kad'ai, ALLAH yasauwak'e maka wannan halin. Da yamma tadawo daga makaranta a gajiye,ba abinda take buk'atar yi sai bacci danko jiya ba wani baccin kirki tayi ba Julaibib ya hanata sakattt...Tana shawo kwanar gidan su tahango wata mota me d'aukar hankali fara karrr...sai d'aukar idanu takeyi a cikin hasken rana,wata kyakkyawar macece me garin jiki wankan tarwad'a tabud'e motar tafito tanama Sudaida sallama. Sudaida ta amsa sannan suka gaisa a takaice... tacigaba da tafiyarta,matar tace"Dan ALLAH jimana "tajuyo tad'an kalleta sai ta matsa kusa da ita,matar tagyara farin medicated glass d'in data rufe idanun ta. Takalleta sama da k'asa wani murmushi yasu6uce mata,tanunata da yatsa "Sudaida ko?Sudaida tad'ago suka kalli juna,sai ta gyad'a kai kawai dan bata san a ina matar tasanta har tasan sunan taba. Toh kiyi hak'uri na tsayar dake ba tare da kin san koni wacece ba,ina fata mijinki D'ansarai yafad'a miki zuwa na?Tak'ara kallan matar"wallahi ba k'arya hutu ya gama ratsata,ido ba muduba amma ai yasan kima,kayan jikinta na alfarma,a inda Sudaida taji dama-dama wai kibiya a cikin idanu shine shigar sanin darajar kai tayi harda hijab d'inta tsawonshi yawuce gwiwa da kad'an,tarasa amsar da zata bata tunda Julaibib bai mata maganar wata za tazoba gaskiya,sai tayi murmushi tana gyad'a kai"sannu da zuwa,toh bismillah "suka jera suna tafiya har tabud'e D'akin-shak'awa tanuna mata wajen zama taje takawo mata abin motsa baki suka sake gaisawa sannan tamik'e"bari a mishi magana. Suka kalli juna yana mata wannan rikitaccen kallan nashi da bata so dan haushi yake bata,yafito daga wanka yana shafa mai.Yaya Julaibib wani irin mutum ne me tsatstsauran ra'ayi da baza ka ta6a gane inda yadosa kai tsaye ba a wasu lokutan."kayi bak'uwa. Fuskarshi ba walwala "wacece ita da baki san sunan taba? Tajuya"oho nima a ina nasan ta,kafito ka ganta mana ganin idanun ka.Sai da yagama shiryawa sannan yafito, yana ganinta yasaki fuskar shi yana mata barka da zuwa, yazauna suna gaisawa da tambayar me jiki."jiki Alhamdulillahi.Ni da Baban Humaima ne yana mota. Yafita yashigo dashi.. "Doctor Garga Ibrahim Manogi "babban likitane da ake ji dashi a Teaching Hospital na Zaria,k'wararre ne akan abinda yashafi k'wak'walwa(Neurology) likitan da akace sune ma idan sunje Shika lokacin da Bilkisu tayi hatsari, shine yake auren kanwar Innar Bilkisu. Sudaida takawo musu abinci.Doctor Manogi yanaci yad'ago yana kallansu"gaskiyar magana abincin nan yayi d'an karen d'and'anon daya burgeni,kai Ustazu haka yake kiran Julaibib dole za kayi tumbi kwanan nan,yakalli Sudaida"kin gane ko idan ya6ata miki rai karki hana shi kome da yake so sai wannan Palatable girkin na ki tunda shi baya san cin abincin waje kinga ai kin horashi duk da ya iya dafawa amma dai kafin yadafa ai ya d'and'ana ko?Sukayi dariya.Doctor Manogi haka ALLAH yayi shi da sauk'in hali da raha sai yanayin shi yamata shige dana Yaya Aminu.Yakalli matar shi"Bongel Ustazu da matar shi basu burge kiba?Tayi murmushi"sun burgeni musamman ita, kaga bata sanni ba amma har tabarni nashigo mata gida duk da taji na ambaci sunan mijin ta,ka san wasu matan da kishin rashin hankali. Yad'an harareta"toh waya fad'a miki bata kishin shi? Kawai ta hak'urane dan ta san itace kad'ai a zuciyar shi, kin san jiya muna tare dashi bayan sallar magriba sai kawai yace min wai gida za shi,nayi-nayi dashi yabari yau mu bugo sammako amma yanok'e"wai ai yau d'in da sassafe zai dawo,amma kinga d'an rainin hankali gashi nan a zaune har bayan la'asar.Julaibib yasa hannu yana shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi yana murmushi. Bongel tad'an kalli Julaibib"ina son ganin Adnan Ibrahim Me-Lambu inji abinda yahana shi dawowa makaranta yayi B.ed d'in shi. Ai Adnan ya san dad'in kud'i ya zama d'an kasuwa kwanaki na mishi magana yace wai shi bazai iyaba wanda yayi abaya ALLAH amfana.Tace kash...na mishi sha'awar karatun saboda yaron yanada k'ok'ari yana d'aya daga cikin d'alibaina yan gaban goshi. Da muna magana ta waya daga baya na daina samun shi. Eh wayar tashice tafad'i yanzu wani sabon layine dashi.Ai ko zaka bani zamu muyi magana... Sai yanzu Sudaida ta fahimci wacece ita.Bongel Lecturer ce,yaren turanci (English) take koyarwa a FCE Zaria,lokacin da Adnan yake karatu tasha jin sunan Malama Bongel a bakinshi da irin kirkinta,da taimakonta ga d'alibai,bata san d'alibai wad'anda basu da himma,tafi matsa ma irinsu da yawan tambayoyi dan zaburar dasu, masu san karatun suna zage dantse ko dan kar susha kunya a gaban d'umbun jama'a yan uwanshi d'alibai,yan abi yarima asha kid'a,yan kyalekyale suna adawa da irin halaiyarta musamman na zuwa musu aji a bazata ta na musu jarabawar gwaji,irin su Adnan a lokacin sune yan gaba gaba,baya yadda yarasa laccanta sai da dalili me k'arfi.Malama Bongel ALLAH yabata k'warewa da juriyar koyarwa,ga kuma ilmin tsurar shi Ubangiji me kyauta da k'ari ya ba ta,babban kuma abinda yak'ara mata farin jini shine bata kada d'alibai a jarabawarta (carry over) Sunyi sabo da Adnan,saboda wani ciwo da yayi taje gaishe shi anan take tambayar shi d'an wani gari ne?Yafad'a mata Zonkwa,tayi murmushi kace kai d'an gidane,shikenan dazarar anyi hutu zata ba shi sak'o yakaima Innar Bilkisu a garin Matsirga,kanwartace uwa d'aya uba d'aya.A wasu lokutan ma takan ai ko shi takanas da kud'in mota yakai mata sak'o yakoma Zari'a a ranar. Malama Bongel tana da sauk'in kai,ba ta d'agawa da ilmin da take dashi,sai dai tana fama da ciwon idanu,tasha wahala dan akwai lokacin data ajiye aikin koyarwa saboda kome sai da lafiya akeyi, cutar glaucoma tayi mugun kamata,sai da suka tashi tsaye sannan tasamu lafiya,suka kuma ba ta medicated glass da take amfani dashi. Sudaida tasake kallanta cikin zancen zuci"kowani d'an Adam tara yake bai cika goma ba,kowa da irin tashi matsalar.Wato wannan zuwan kuma Innarsu Bilkisu ce ba ta da lafiya kenan,dan dasafe taji Julaibib yana tambayar mai jiki tawaya lokacin datake shiryawa,sai dai bata tambayeshi waye ba lafiya ba,shima bai fad'a mata ba,dan idan bai ga damaba ko ta tambaye shi,shiru zai mata kamar baiji ba. Shi kuma Julaibib sun had'u da Doctor Manogi ne a wani taran MSSN da akayi a jahar Taraba,sun fito sallah dan Julaibib shi yamusu limanci,suna yar hira yake tambayar shi shi d'an wani gari ne?Yafad'a mishi Zonkwa amma a Zari'a yake zama a halin yanzu dan shi d'alibine a jami'ar Ahmadu Bello.Doctor Manogi yanuna shi da yatsa"kar dai kai ne D'ansarai sarauyin wata Bilkisu data rasu?Yajijjiga kai"eh ni ne.Yace ALLAHU-AKBAR yamishi ta'aziyya sannan shima yamishi bayanin ko shi waye...daga nan hira ta 6alle har suka dawo Zari'a suka cigaba da mutunci da zumunci. Sunyi hira sosai sannan suka shirin tafiya, Bongel tadafa kafad'ar Sudaida"naji kin fara karatu me tsada na masu k'wak'walwa,toh ina tayaki murna.Ki zage dantse kiyi ilmi kema kiba al'umma gudummawa da d'an abinda ALLAH yabaki,musulmin kwarai shine wanda zai amfanar da yan uwan shi da alherin shi.Sudaida kinyi sa ar kama zuciyar D'ansarai dan ba shi da wata magana sai taki,dan ALLAH kiyi hak'uri da shi, shima dole yayi hak'uri dake,zo mu zauna zo musa6ane,ALLAH yabaku zuri'a masu albarka. Sudaida tasunkwui da kai bata amsa ba tana d'an murmushi,ta bata wasu biscuit da alewa"gashi aba su Humaima"Bongel takar6a tana godiya"su Humaima sun gode.Doctor Manogi yamik'e yana kallan Julaibib"zaka d'auko jakar taka mutafine? Yayi yar dariya yana sosa k'asumbar shi"sai ranar jumma'a Insha-ALLAH. Yagyad'a kai'ALLAH ya kaimu,toh madam mu zamu wuce.Yaciro rafar kud'i yan ashirin guda d'aya ya ajiye mata a saman tebur,tamishi godiya.Sukayi sallama Julaibib yatafi rakasu. Bayan sallar Isha'i yashigo ta mishi sannu da zuwa.Ya amsa da yauwa fuskar shi ba walwala takalleshi na wasu dak'ik'u"Yaya Julaibib za muyi bak'i amma shine baka fad'a min ba?Yayi kamar ba dashi take magana ba.Haushi yakamata. Yaciro wayar shi a aljihu sai ta fizge. Yad'ago yana mata wannan kallan da yake bata haushi,bai yi magana ba sai hannunshi daya mik'a mata alamar tabashi wayar,itama tayi kamar bataga abinda yayi ba"me yafaru ne ina maka magana kayi shiru?Oh baki ma san abinda yafaru ba ko?Tagyad'a kai"ALLAH ban sani ba.Yayi shiru kamar bazai yi magana ba zuwa can kuma yace"Da safe bana ce miki asibiti zamu tafi ba amma ki kayi tafiyarki makaranta saboda kin raina ni ko? Tawani marairai"dan ALLAH kayi hak'uri, to amma Yaya Julaibib ni fa lafiya ta k'alau.To ramar me kike yine?Tashafa wuyanta"oh ni Sudaida kowa haka yake fad'a ni kuma ban gani ba.Yad'an harare ta"ni ai nagani bakya san abinci ne ai da safen ma bakici abincin ba kika tafi, yanuna mata ledar da yashigo da ita,tamik'e tad'auko faranti a D'akin-girki tajuye mishi balangun me koren tattasai,albasa,kabeji da cucumber ga yajin tafarnuwa,ta tura mishi gaban shi"ai na kine zauna ki cinye shi.Yaba kyauta tukwuici"sai ta mishi godiya dafatar k'arin bud'i amma har ga ALLAH ita ba ta wani jin balangu, yanka biyu taci,ta d'auki rakenta tafara sha.Shi kuma yana dad'a fad'a mata lallai ta dinga cin abinci kar cutar gyanbon ciki(ulcer)takama ta. Yaya D'ansarai ba fa rashin cin abinci yake kawo cutar gyambon ciki ba.Yabar rubutun da zai yi yakalleta"to me yake kawo shi? Ta6alli rake ta taune ta zuke ruwan tazubar da 6awon sannnan tace"rashin cin abinci akan ka'ida shi yake haifar da cutar gyambon ciki.Kamar yaya bangane ba. Yanzu misali ka saba cin abincin safe k"arfe takwas kullum haka kake yi sai kuma kazo ka daina ci a dai-dai lokacin...toh shi ruwan matsarmama da yake d'iga ya narkar da abincin shima ya saba saukowa ya d'iga karfe takwas to kullum haka zai dinga d'iga ko kaci abinci ko bakaci abinci ba,idan akai rashin sa a bakaci a dai-dai lokacin ba to sai yad'iga a cikin cikinka shikenan wajen ya zama ciwo...ciwon da mutum zai zo yashiga wani mawuyacin hali na ni ya su.. Yakalle ta cikin natsuwa"ahab ba cinyaba k'afar baya... Ni dai na fada'a miki ki dinga cin abinci"toh Yaya D'ansarai nahhh...tayi furucin da wani salo na yanga da shagwa6a.Suka kalli juna sukayi murmushi,bata gama shan raken ba ta ajiye dan yau tayi d'amarar hana karatun daren nan,shi dai kullum cikin bincike da nazari,a makaranta karatu a gida karatu?Rai ai dangin goro ne yana buk'atar ban iska...batayi magana ba kawai zama tayi a gefenshi ta gewayeshi,a hankali tafara mishi wani salo...salon daya tilas tashi ajiye littafin nazarin yafara bin yarima dan su sha kid'a. Hantsi yadubi ludayi na alhamis bataje makaranta dan basu da lacca,tana kwance a doguwar kujera Hajiya tashigo da sallama, tamik'e zaune"lale marhabun Hajiyar mu,sannu da zuwa.Tasa hannu tad'auki ledar da Hajiya tad'ora a saman tebur"me nasamu haka? Tabud'e talek'a sai tasa hannu tad'auki guda d'aya awarar madarar shanu ce,tagutsira sannan takalli Hajiya "nagode ALLAH amfana. Tanaci suna hira,Hajiya kuma tana ta kallanta cikin nazari dan yar shimice ruwan madara ajikinta,ta yi kyau sosai amma ta rame"ni wai ramar nan dakike dad'ayi to ko dai ciki ne dake?Sudaida takama ha6a"wuuu..ciki?Tad'an ta6e baki"uhun rufani ki saya.Hajiya takad'a kai"eh lallai ba shakka k'uruci dangin hauka,cikin ne kike neman tsari dashi?Ke ba a haihuwar aka haifoki? Ya'ya da kike ganin su ai rahamane jin dad'in rayuwa ne,su Khausar ba gashi har sun fara zuwa asibiti awon cikin ba.Tamaida bayanta jikin kujerar tana cin awararta"hu'un to ni dai Hajiya bani da wani ciki.Ai ban musaba"ALLAH na tuba shi ciki ai d'an dumane a hankali yake yad'o. Julaibib yashigo da sallama yazauna a d'aya kujerar suna fuskantar juna da Hajiya"Hajiyarmu kin shigo?Ta amsa da eh Julaibibi.Yakalli Sudaida"lallai yarinyar nan,wasa tare ci bamban ko?Zanga me siyo miki rake anjima.Tad'auki ledar ta zauna a k'asa kusa da k'afafunshi"duba kagani,kaifa kake fad'in awarar madara bata dameka ba.Yad'auki guda d'aya"ai ba cewa nayi kwata-kwata bana ci ba.Tamishi wani kallo a marairaice"to afwan Zaujiii...yayi murmushi koma dai toshiyar baki kika bani yau dai baza ki sha rake ba,kema muk'amuk'inki su huta.Haba Zaujiii...kaima kasan"I can't do without sugarcane" tayi furucin da salon shagwa6a.Yamata wani kallo "au bama ni ba?Tasake wani narkewa"na rantse da girman ALLAH har da kai Yaya D'ansarai nahhh...Hajiya tagalla musu harara"oh Ya'yan zamani.Sudaida takalleta"da mukayi me kuma? Hajiya wai kin manta gidan amare kika zone?Hala kin manta hud'ubar dakika dinga manane a gidanki? Takalleshi"Yaya D'ansarai kome tace mu muku indai bai sha6ama shari'a ba,ko menene shi bata togance ko abu d'aya ba.Hajiya tayunk'ura tamik'e"toh barin barku kuci karen ku ba babbaka.Shima yamik'e"Hajiya kiyi zaman ki,ni dama wayata dana sa a caji nashigo d'auka. Yacireta dan ta cika.Tagyara zaman hijab d'in ta"ai ba ganin ka yasani tafiya ba dama nayi niyya ne. Yasa wayar a aljihu"ALLAH huta gajiya Hajiyarmu sai nazo.Inji Sudaida.Tagyad'a kai"sai na ganki. Suka fita da Julaibib. Bai dawo gidan ba sai da yamma tana D'akin-girki yamik'a mata raken"karki isheni da mita anjima.Tasa hannu biyu takar6a"shukran jazilan Ustazu. Yakalleta da sauri"au har dake? Yagyad'a kai tana yar dariya"har dani.Toh bar d'aura girkin nan kizo muje unguwa.Yaya Julaibib da wannan yammacin?Yad'aure fuska"ko da sulusin dare ne bazaki bane?Ta tsame hannunta daga cikin kayan miyar da take gyarawa"ALLAH yabaka hak'uri"ya amsa da amin.Kiyi sauri ki shirya ina jiranki a waje.Tabi bayanshi da kallo "zuciyar ta na raya mata wasu al'amura game dashi, takad'a kai"ALLAH yakyauta maka wannan halin wallahi. Yana kallanta tafito amma sai da wasu dak'ik'u suka wuce sannan yabud'e mata motar tashiga tazauna tana d'aura belt.Ganin sun bar cikin gari yasa ta tambayeshi inda za su,amma yayi kamar bai ji taba.Itama sai taja bakin ta ta d'inke,tamaida bayanta jikin kujerar tare da lumshe idanun ta,tana sauraran wa'azin daya kunna na Ahmad Ibrahim(Bamba)sai da yatsai da motar sannan tabud'e idanun ta tana kallan wajen,nan kuma ina ne?Ta tambayi kanta"fito muje mana..taji maganar shi a sama,tafito suka jera zuwa gidan. Inna tayi murna da ganin su kwarai, irin kambamawar data musu yasa jikin Sudaida yayi sanyi, wato su wasu irin mutane ne masu karamci da girmama d'an Adam,suna da shiga ran da ciresu a sararin zuciya bazai zama abu me sauk'i ba wai cire wando taka,shi yasa Julaibib yakasa mantawa dasu duk da babu wacce tazama sanadin had'uwar ta su a doron duniya.Inna tad'an kalli Julaibib"ai munyi waya da Bongel take fad'amin gobe zaka koma lallai abaka madara katafi musu da ita wai wanda suka tafi da ita sun tsaya a Gama-gira wajen wata k'awarta shine tabata duka,dama Maude nake sauraron shigowar shi in bashi yakawo maka ikon ALLAH kuma sai ga Ku.Ya amsa da ladabi"eh Inna nima ta kirani ta fad'a min,sammako zanyi a goben shi yasa nace barin zo in k'ar6a daga nan kuma Sudaida ta gaishe ki.Ai kuwa naji dad'i ALLAH yamuku albarka.Suka sake sabuwar gaisuwa da Sudaida tamata sannu da jiki.Jiki ai Alhamdulillahi naji sauk'i sosai. Da zasu tafi Sudaida tace gashi ni dai nazo banga Bello ba.Inna tad'anyi murmushi"ai da ya san da zuwanki da bazai raka Malam Zango ba.To agaishe shi. Zai ji.Julaibib yamata alheri me yawa,ada tana damuwa da irin hidimar da yake musu har tazo ta daina,tun ranar daya kalleta cikin natsuwa da girmamawa"Inna ki d'auke ni matsayin d'a,idan kika d'auke ni a haka toh na san duk abinda zan baki zaki kar6ane da dad'in rai kina kuma shimin albarka tare da min addu'ar dacewa a doron duniya da lahira. Megado ita tahad'a mu,koda ba ta, bazamu rabu ba dan kuma baku k'ini ba.Inna tajijjiga kai tasa gefen hijab d'in ta tana share kwallah"gaskiya ne d'an nan,toh ALLAH yamaka albarka,ALLAH yabaka zuri'a d'ayyiba,ALLAH yasaka maka da mafificin sakamakon shi, yasa hakan a mizanin kyawawan ayyukanka.Yanzuma irin addu'o'in data dinga musu kenan shi da Sudaida.Suna ta amsawa da amin,amin. Gidansu Sudaida suka wuce...Sauran k'anninta suka dinga murnar ganinta,itama taji dad'i sosai dan basa wani zuwa gidan ta,to yaushe ma suke da lokacin yawo?Daga andawo makarantar boko za a tafi ta allo,ko ta Islamiyya da daddarene kawai suke da lokacin kansu,idan ma ranar ba a had'o mutum da aikin gida ba (home work)Tasaki hannnunsu,taje ta rungume Mama kawai sai tasa kuka,Umma,Julaibib dasu Asma'u suka bita da kallan mamaki yanzun nan fa tagama kyalkyala dariyar shirmen gwarancin da Nana take mata... Mama tace ashsha"to me yayi zafi haka da idanu za suci wuta?Tana k'ok'arin d'ago ta Sudaida tadad'a k'ank'ameta.Umma ta fusata"ke menene haka yau naji shashanci rok'o a gidan bebe.Mama tad'aga mata hannu"na ki idanu 6arin mai a yashi.Umma takyalesu suna magana da Julaibib. Mama tayi k'asa da murya"to d'agani tunda bazaki daina kukan ba.Tayi shiru tana share hawayen sannan tad'an marairaice "Dan ALLAH har yanzu baki zo na ganki ba,ai dama na san ke kad'aice za ki zo,ko Umma ce tazuga ki?Mama tayi murmushi"au dalilin kukan kenan?Eh mana Mama.To karki damu inanan zuwa ni ba wacce ta isa ta hanani zuwa inda kike.Yauwa Mama ALLAH yabar mana ke,suna ta hira sai da Baba yafito yace su tafi gida haka dare yayi gashi sammako Julaibib zai yi.Sudaida tabi Umma d'aki tafito daga bayi alwala tayi tanasa hijab Sudaida tashigo.Suka kalli juna sai Umma tad'anyi murmushi"za ku tafi ne?Ta amsa cikin ladabi"eh Umma.Kun san Umma Boss ce bata d'aukar raini.Tabata wasu humrah masu k'amshin fita hayyaci"gashi nan dama ke kad'aice ba a kai miki ba.Tasa hannu biyu takar6a tana godiya. Umma to yaushe za kizo? Ke! Umma tafad'a cikin d'an bud'e idanu.Sudaida tasunkwui da kai.Sai kuma ta sassauta murya"Sudaida me zanzo in miki ne?Duk abinda kike so kima Mama waya ko ni,ko ki turo mana ta sak'o a rubuce ba shikenan ba?A sanyaye tagyad'a kai sannan sukayi sallama. Tafiyar Julaibib da yammacin ranar tadawo makaranta tana so tayi girki tatafi gidan Inna sai ga Asma'u tashigo.Tataro ta cikin murna 'oyoyo Yaya Asma'u sannu da zuwa.Ta amsa da yauwa tashige D'akin-shak'atawa,ganin haka yasa Sudaida tayi sauri tagama markad'a kayan miya taje suka gaisa,kamar kullum yau ma haka ta amsa gaisuwar cikin halin-ko-inkula tun bayan auren ta da Julaibib Asma'u take mata wani gani-gani data kasa gane manufarta.Tabi d'akin da kallo sannan ta sauke idanun ta akan Sudaida, tana sanye da riga da zani da dankwali na kamfala, ta ta6e baki"ina D'ansarai?Baya nan yatafi.Yatafi fa kikace?Tajijjiga kai"eh ya tafi.Toh yayi kyau... bani sak'ona sauri nake yi.Sudaida tagirgiza kai "bai bani kome in ajiye miki ba.Bata sake magana ba wayar ta taciro ta kirashi.Yana d'agawa ko sallamar daya mata bata amsaba tafara hayagaga... kai D'ansarai haka mukayi dakai? Tayi shiru tana sauraranshi...wucewar wasu dak'ik'u sai kawai taja dogon tsaki"kai malami wallahi daga bayane sadaka da karuwa...eh to naji sai ta mik'a ma Sudaida wayar "Zaujatiii... kud'in dana baki kin kai gidan kud'in ne?(bank)A ah sai gobe Litini...Yauwa toh kiba Yaya Asma'u dubu goma a ciki,ki bar sauran idan nadawo nabaki duka sai ki kai kinji ko?To Yaya Julaibib, ALLAH yadawo dakai lafiya.Tamik'a mata wayar sannan take ta d'auko takawo mata,a wulak'ance takar6a kamar wacce aka bata najasa. Sudaida takawo mata meatpie da lemu dan bata gama abinci ba.Tagirgiza kai"bani dankalin turawa da kwai zanje in soya a gida, tamik'e bani leda,inda suke ajiyewa ta nufa, Sudaida tabiyo ta da ledar tana fad'a mata amma fa kwan ya k'are.Sai tabi d'akin da kallo gwangwanayen madarar Nido tagari guda biyu dana Ovaltine guda d'aya sai siga me y'aya na kwali(cube sugar)sai tasa hannu ta d'auki gwangwanin madara d'aya da siga kwali biyu a ranta tana mita"ni nasan D'ansarai baya shan shayi da madara,yanzu nan ita za taita shansu? To aiko bazata shanyesu ita kad'aiba dan nima wannan ai yafi min dankalin.Sudaida tabita da kallo itama tana jiinjina k'arfin hali fin me kora shafawa irin na Yaya Asma'u.Toh sata za a kira wannan abun kome?Tunda bata tambayi wanda yasiyo ba. Abinda Yaya Karima bata dashi kenan ganin gari da san na Bello-badin,ko wajen Inna taje haka take mata d'auki d'ai-d'ai d'in duk wani abu daya bata sha'awa,abin mamaki kuma Baturiya da suna manga,kamar ba Inna da Baba ne Iyayen taba dan su sun san mutumci da karamci wallahi.Idan an mata magana ta ta6e baki tana fad'in to menene a ciki? Sata a gida ai rance ne...bare ita ai bama sata tayi ba tunda a gaban idanu take d'aukar abu.To amma dai ai ba ace an ba taba kai ALLAH yasauwake. Takar6i ledar tasa a cikin sannan tajuya"sai anjima.To Yaya Asma'u ki gaida gida. Kwana biyar bayan nan da yammacin la'asar tadawo daga makaranta kawai tawuce gidan Inna. Asma'u tana zaune tana cin dafaffiyar masara takalli Sudaida sama da k'asa bata amsa gaisuwar da take mataba,sai tambayar ta tayi"hala daga awo kike? Fuska a d'an yamutse dan tafara gajiya da irin abubuwan da Asma'un take mata tace"awon me? Asma'u tamata wani kallo me kama da harara "awon me mata suke zuwa yi a asibiti? Tamotsa kafad'a tare da watsa hannu"oho nima ban sani ba tunda ba ta6a zuwa nayi ba.Tawuce randar Inna tad'ibo ruwan sanyi,tashiga D'akin-girki tazuba abinci, tayi bismillah ta faraci. Inna ta idar da sallar la'asar tajuyo tana shima Sudaida albarka"kin kyauta dakika bata wannan amsar.Ke Asma'u tanuna ta da yatsa"me yasa kike san zama babbar kwabo ne?Asma'u tamik'e"to yanzu Inna me nayi?Ni fa dama kullum a gidan nan a ban iyaba aka d'auke ni.Eh ai halinki yake ja miki.ALLAH yabaki hak'uri Inna ni tafiya ma zanyi,me zaki bani?Inna ta d'aure fuska"ba abinda zan ba ki sai dai in omon wanke-wanken da kika kawo min za ki koma dashi.Kai Inna haba-haba dai,tashige d'akin bacci tana fad'in"ni ai na ga abinda nake so,sink'in sabulu da man shafawa guda d'aya ta d'auko. Inna takalle ta"Asma'u na ba ki ne?Tayi yar dariya tana turawa a jaka"Inna kayan ALLAH ai na annabine,ba sid'i ba sad'ad'a ma kinyi kyauta ga wasu bare kuma ni?Tajuya na tafi Inna,idan Baba ya dawo a gaishe shi.Suka bita da kallo kowacce da abinda zuciyar ta ke rayawa. Kwanci tashi a sarar me rai...Shekara d'aya da auren su A'isha,Khausar da Nasmat ne suka fara haihuwa,A'isha da Nasmat rana d'aya,ranar suna Sudaida tarasa inda za tayi ga makaranta,ana tashi Kafanchan tawuce gidan A'isha aka sha suna,ba ita taje gidan Nasmat ba sai da akaci aka kusa cinyewa dan ma na ka na kane...a yadda tagaji lik'is d'in nan,gida za ta tabi lafiyar gado. Tak'arema jaririyar kallo tad'ago cikin murmushi "ALLAH na rasa da wanda tayi kama,ranar da aka haife ta sak babanta yau kuma ta canja batayi kama da ku ba, tamaida ita k'irji ta rungume ta lumshe idanun ta"ina son yarinyar nan ki bani ita mana.Nasmat tayi murmushi"ai dama ta kice na kuma bar miki.Tabud'e idanun ta suka kalli juna sukayi dariya.Nasmat ta kalle ta"d'azu dangin mijin ki bakiji irin habaicin da suke yi ba wai wasu sai dai suci su juye shi a masai,wani abin mamaki kuma Yaya Asma'u itace shugaba,sai da Hajiya ta musu wankin babban bargo sannan sukayi shiru.Sudaida ta d'auki kunun aya tana sha"kar ki wani ce abin mamaki,yau kika san Yaya Asma'u da halinta?A ah ai ni abinda yabani mamakin shin ke d'in ba matsayin kanwar ta kike ba? Tad'anyi murmushi"da ne nake kanwarta lokacin ina gidan mu,toh yanzu kuma ai k'aninta nake aure ina zaune a gidan shi,ita kuma dangin miji ce,wasu dangin mijin kuma ba mutunci suka sani ba. Asma'un ce tashigo ma da Nasmat farantai takalli Sudaida sama da k'asa cikin ta6e baki "hamshak'iya,maduga ke sai yanzu kika ga damar zuwa? Komu da muke tare da Iyali ai hidimar su bata hana mu zuwa anyi kome damu ba,bare kuma ke da kike zaune ke d'aya ba wata hidima a kanki.Sudaida tayi lallausan murmushi"toh Yaya Asma'u dan ALLAH ina ruwan maza da wankan jego?Abinda tafad'a mata kenan tajuya suka cigaba da hirarsu dasu Nasmat. Ta koma gida tayi wanka tana so tatafi gidan Inna,kiran Julaibib yashigo tad'aga da sallama"Zaujiii...afwan yanzu nake shirin kiranka "kasha ruwa lafiya?Yau banyi azumi ba Zaujatiii... bana jin dad'i.Wayyo! Sannu ai naji muryar ka wata iri,sannu kasha magani sai ka kwanta,dan ALLAH yau dai karka tsaya yin wani nazarin karatu,lafiya ai tafi kome.Toh nagode,kin tafi gidan Inna ne?A ah sai nayi sallar Isha'i.Kiyi zamanki ina hanya.ALLAH yatsare, yakawo ka lafiya.Amin,nagode Zaujatiii...Sai kuma tad'an turo baki kamar yana ganin ta"ni dai ALLAH na tsani dawowar cikin daren nan.Yayi murmushi"sai nazo kawai. Jakar Magori take ji a k'aramar rediyo taji kwankwasa k'ofa,talek'a ta taga sai tagan shi a tsaye. Tabud'e ta k'ar6i jakar shi"sannu da zuwa Yaya Julaibib ina motar?Bazan iya tuk'i ba shi yasa nashiga tahaya.Har ta ajiye jakar bai shigo ba tasake fita sai taga a hankali yake tafiya,yashigo D'akin-shak'atawa yazauna tare da maida kanshi saman kujerar ya rufe idanun shi.Tazauna a hannun kujerar"sannu...ALLAH yasauwake.Bai amsa ba yamik'e wani jiri yakwashe shi luuu...sai ya durk'usa a gaban ta,yadafa gwiwoyin ta dan saura k'iris yasha k'asa. Sannu Yaya Julaibib. Yagyad'a kai ya yamik'e da sauri yafita,tabi bayan shi"Yaya D'ansarai ina za ka? Abakin famfo yatsuguna yana amai,itama ta tsuguna tana ta jera mishi sannu, yagama aman yabud'e famfo yana taro ruwan da tafukan hannayen shi yana wanke kanshi zuwa fuskar shi.Yad'an kalleta yamik'e dakyar jikinshi a mace kamar yayi awanni yana aikin dabai huta ba,yasake kallanta...yayi magana amma bataji me yafad'a ba,tamatsa kusa dashi "me kake fad'a Yaya D'ansarai?Idanun shi sun k'ank'ance, luuu kawai taga ya tafi zai sha k'asa,a tsorace tarik'o shi wani abu mara dad'i ratsirga ilahirin gangar jiki da zuciyar ta,nauyin shi ya rinjaye na ta, gaba d'aya sukayi jikin bango,dakyar yasa hannunshi nadama yadafe bangon, kome yana hautsine mishi,kanshi na mishi matsanancin ciwo kamar zai rabe gida biyu,cikin dukan zuciya tafara kiran sunan shi"Yaya D'ansarai... Yaya D'ansarai... zuciyarta tayi rauni sharrr... sharrr...hawaye suka fara sintiri a fuskarta,jikinta yafara rawa"Yaya Julaibib ta fara jijjigashi sai tana Istirja'i dan wallahi a tsorace take,tana sake shi ko shakka babu zai zube mata a wajen,gashi baza ta iya rik'eshi gaba d'aya ba, k'arfin namiji da mace bambancin a bayyane yake. Dak'yar tazame suka zauna a k'asa ta jingina bayanta da bango...tazuba mishi idanu a cikin hasken farin watan tana zancen zuci"gashi bata fito da waya ba bare takira wani daga cikin Yayyinta su zo su taimaka mata,takai hannu tana d'an ta6ashi"Yaya D'ansarai kata shi,Yaya D'ansarai dan ALLAH kabud'e idanun ka ka ji?Bazan iya bane dana kaika d'aki,a hankali yabud'e idanu yad'an kalleta sai kuma yamayar rufe...Tanata kallanshi tana ayyane-ayyane a zuci tana kukan shar6e, wucewar wasu dak'ik'u masu yawa sannan taji hucin numfashin shi me zafin gaske "Sudaida ki daina kuka naji sauk'i.Tahad'iye kukan tana kallan shi ta san fad'a kawai yayi dan hankalin ta yakwanta amma ko wannan hucin numfashin me zafi ai bana lafiya bane"Yaya Julaibib to za ka iya tafiya mutafi d'aki?Yagyad'a kai tamik'e tarik'o hannayenshi duka biyun sannan shima yamik'e suka tafi yakwanta, dan yak'i cin abincin data kawo mishi,shayin ma bai shaba... Yi dai-dai dan dai-dai,dai-dai ne ba dan wasu sunyi dai-dai ba. Facebook:سودة ا.باب Facebook:Bilkisu Ibrahim Bilkisu Ibrahim Email:Saudatibrahim333@gmail.com 23 Jumaada Thani 1441 17 February 2020 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJI DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba ( Aadilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na ashirin da d'aya. Dasafe yayi wanka yana sanye da yadi ruwan madara mara nauyi,yayi lamooo a cikin kujera.Tashigo da sallama tabi kayan abincin da kallo yana nan yadda ta ajiye"Yaya Julaibib har yanzu baka karya ba? Yagyara zama"na d'an sha kunun gyad'an, ina jin bakina ba d'and'ano ne.Tad'ago tana mishi kallan tuhuma bayan ta bud'e kofin"na ce bakaji sauk'iba ka ce ba haka ba,yanzu wannan kunnun an sha shi kenan?Kur6a d'aya kayi ko? Yad'anyi murmushi"afwan Zaujatiii...zan sha anjima.A hankali yamik'e"barin je gidan Inna ko za kimin rakiya?Uh uh adawo lafiya.ALLAH yasa.Ta amsa da amin tabi bayanshi da kallo wata irin k'auna da tausayin shi suka tsirga ilahirin gangar jiki da zuciyarta,bata ta6a ganinshi a irin wannan yanayin na daren jiya ba.Tasauke gwauran numfashi"Ubangiji yasa kaffarace Yaya D'ansarai nah... Takoma D'akin-girki tak'arasa ayyukanta sannan taje tayi wanka ta shirya cikin shigar mutunci da sanin kimar kai kamar ko yaushe tatafi makaranta. Bayan sallar Isha'i yashigo yana kallanta, itama ta idar da sallah tana azkar,tagama ta mishi sannu da zuwa zata cire hijab yarik'o ta"bar hijab d'in ki muje kimin rakiya gidan Hajiya d'azu ban samu na shiga ba, muna ta hidimar jama'a a shago.Tad'an turo baki gaba"a hakan da ba ka da lafiya me makon kadawo gida kayi kwanciyar ka,kaima kahuta ma ranka?Ai naji sauk'i. Tazuba mishi idanu nawasu yan dak'ik'u sannan tace"tun safe har zuwa yanzu me kaci?Na sha shayi a gidan Inna. Tad'an harareshi"shayi dai shayi dai ai sai kaje kayi ta sha, toh yanzu ga abincin dare na jiranka muje kaci sai mutafi gidan Hajiyan.Yagirgiza kai"bari mu dawo sai in ci yanzu banajin yunwa. Hajiya tana shan dabgen bindin sa suka shigo da sallama.Sudaida tasa hannu wai wai wai gaskiya matar nan kina sha'aninki wallahi,tagalla mata harara"kema wa yahanaki na ki sha'anin? Sakarya kanki kawai kika sani,toh maza d'auki faranti ki zubama mijin naki mana.Yad'aga hannu"a ah barshi kawai Sudaida bazan iya ciba.Suka zuba mishi idanu"har yanzu jikin ne Julaibibi? Hajiya ta tambaye shi.A ah naji sauk'i Alhamdulillahi. Ganin ya sake anata hira yasa suka saki ransu.Hajiya ta ajiye tsinken data gama sakacen naman daya mak'ale mata a hak'ori"to ko wannan zirga-zirga da kukeyi ai dole yakarar daku daga kai har matar taka,duk da yanzu na ga tafara sabawa, tana maida jikinta a hankali.Yad'anyi murmushi yana kallan Sudaida"ai Insha-ALLAH zirga-zirgan zai ragu dan an d'aukeni koyarwa a Gidan-Waya, farkon wata me kamawa zan fara zuwa.Hajiya tafad'ad'a murmushinta zuwa dariya"kai Masha-ALLAH...Wow Congratulations. Suka kyalkyale da dariya"Hajjaju makkatan ashe dai baki manta karatun ba?Inji Sudaida.Tamata dakuwa"ungo nan,mu turancin muma gangariya turawa yan misionaries su suka koya mana baki da baki.Toh Hajiya kingama aji bakwai d'in danaji ance anayi a zamanin da amma bakiyi aikin gwamnati ba?Oh oh k'arya ciwo aji hud'u nayi Baba ALLAH yajik'anshi da rahama yamin aure.Sudaida takalleta cikin natsuwa"toh kema nan kunyi soyayya ke da mijin naki?Hajiya tafara tafa hannaye cikin salati da sallallami. Sudaida tad'an yamutsa fuska "daga tambaya sai ki fara salati.Hajiya tajawo carbi zata shaud'a mata tamik'e dasauri tafita da kwanan da tagama cin dabgen tawanko hannunta sannan tadawo tana kallan Julaibib daya tsaida gwiwoyinshi yasa duka hannayen shi ya rungumesu,tazauna kusa dashi tad'an marairaice" Yaya D'ansarai anya kaji dad'in zaman nan?Yakalleta me kika gani?Kamar kana jin sanyi...Tabbasss sanyin ne yafara ratsashi amma bai nuna ba,sai yamik'ar da k'afafun na shi yasa hannu yana shafa kwantaccen bakin gashin kanshi "ba kome fa.Tagyad'a kai.Hajiya kuma tagalla mata harara "to iyayin yace me?Julaibib yakalli Hajiya "Sudaida fa amaryace kin kuma san amarya bata laifi,idan kina matsa mata to abu me sauk'i ne tayi yajin zuwa gidan nan. Takad'a kai tana yar dariya ALLAH sarki wacece amaryar? A in da ba amarya dai a kira ta da hakan,to dan ta daina zuwa gidan nan sai me? Sudaida takalle shi"lallai naji da kunnene dan haka Yaya Julaibib tashi mu kama gabanmu wannan farin watan sai yamana illah gwamma dake Hajiya auren ki da gata.Hajiya tagyad'a kai"ba shakka ai wuyanki ya isa yanka.Suka mata sallama tarako su har zaure "ALLAH yamuku albarka nagode,nagode Ubangiji yabamu alheri, yatashe mu lafiya.Amin Hajiya. Suka jera suna tafiyarsu a hankali suna hira har suka zo gida.Takawo mishi abinci yabud'e yana gani tuwon alkama miyar ku6ewa d'anya,yad'an kalleta a marairaice"Zaujatiii...dare yayi fa...itama ta kalleshi"uhun me yafaru?Yamayar da murfin miyar ya rufe"bai kamata in ci abinci me nauyi da yawa ba tunda kwanciya zan yi.Tayi shiru kamar bataji abinda yafad'a ba.Zaujatiii...ba ki jine?Na ji...amma da kasan baza kaci ba tun farko ai da mun tafima da almajirai suma suci da d'uminshi,takalleshi cikin kulawa"toh yanzu me za kaci?Yasake wani marairaicewa yanata kallanta yak'i magana,ta kyalkyale da dariya dan abin dariya yabata"Yaya D'ansarai wai meye haka kake ta wani kallo na kamar wata bak'uwarka? Me za kacine?Za ki bani abinda nake so?Tana yar dariya tagayd'a kai"ALLAH zan ba ka.To ni dai shayi zaki had'a min kuma dan ALLAH kar kimin mugunta kisa min siga,dan haka take mishi wani lokacin idan ba taso yasha shayin shi kuma ya nace sai yasha. Angama autan Inna"ke zo nan dawa kikeyi ne? Tashige D'akin-girki da wanda ya tsargu nake yi.Taje tahad'o kofi biyu tamik'a mishi d'aya ta rik'e d'aya yabita da kallan k'arin bayani,tagyad'a kai "tayaka shan abinda kake so zanyi ko ban kyauta bane?Yayi murmushi"kin kyauta mana,tad'ibo donut tabashi amma baici ba haka yasha na shi,itace dai taci guda d'aya suka gama takai kayan D'akin-girki sukaje suka wanke baki sannan sukayi shirin bacci. Cikin sulusin daren yaketa juyi dan ya kasa bacci,yatashi yazauna,yakoma yakwanta yayi hakan kusan sau biyar,har bacci yafara d'aukeshi yasake tashi zaune yakama kanshi da duka tafukan hannayenshi abin ba sauk'i wai ciwon arna,wani zazzafan zazza6i yarufeshi sai kuma sanyi yafara ratsashi"Sudaida...a hankali yafara kiranta ita kuma baccinta yayi nisa,yakai hannu yana d'an bubbuga k'afarta Sudaida...kamar a mafarki taji kiran tayi juyi sai tasake jin kiran tabud'e idanun ta taganshi jingine da gadon yana cigaba da kiranta,dasauri tamik'e zaune kamar zata hantsila zuciyarta na bugawa da k'arfin gaske tayi Istirja'i"Yaya Julaibib wai meke faruwane? Wani irin ciwone haka sai cikin dare? Yadamke hannunta gangam Sudaida sanyi nake ji rufeni.Tagyad'a kai" tabbasss garin akwai sanyi ga sanyin farin wata daya haske doron duniya kaafatan, dole mara lafiya yaji sanyi,to amma jikinshi yayi mugun zafi kuma yana jin sanyi to bai kamata kuma a rufe shi da abu me nauyi ba dan ba a so zafin yakoma jikinshi.Yana karkarwa yace"Sudaida rufeni sanyi nake ji,dakyar yayi furucin,tamik'e ta d'auko zanin a tamfa ta rufeshi. Yagirgiza kai"ban daina jin sanyin ba d'auko bargon mana,ta lalla6ashi yakwanta"yanzu zan d'auko kaji?Tarik'o hannunshi"kayi hak'uri Yaya D'ansarai tajik'a k'aramin tawul a ruwa tana fara goge mishi jiki yarik'e tawul d'in tamauuu"kyaleni bana so,kwanta kiyi baccin ki.Takwanta tanata kallanshi har wani baccin wahala yad'aukeshi dan daga ganin yanayin fitar numfashin ka san baya jin dad'i. Yashigo da sallama yazauna a kujera yana kallanta har ta idar da sallar,ta sunkuyo tana mishi sannu da jiki tana ta6a jikinshi har yanzu da zafi, a ranta tana yaba k'ok'arinshi dakyar yayi alwala saboda ciwon kan bai sake shiba,amma a haka yagangand'a yatafi masallaci dan samun jam'in sallar asubahi"ALLAH gari na dad'a wayewa asibiti zamu tafi,ni ciwo cikin dare tsoro yake bani.Yayi yar dariya"tsoro kikeji kar in mace miki? Sudaida ai ko da rana idan lokaci yayi tafiya zan yi. Tamishi wani kallo dayaji tasirin shi har a zuciya"ni bana san irin wannnan kalaman fa gaskiya,cuta ai ba mutuwa bace, wata kilama ni zan rigaka macewa,ba dai wanda yasan gawar fari"ALLAH dai yasa mucika da kyau da imani.Amin Zaujatiii...yazame yakwanta yanata kallanta tana shige da ficenta har wani bacci yasake awon gaba dashi. Sai da tagama shiryawa sannan ta tasheshi yaje yayi wanka su tafi asibiti.Yamaida kanshi saman kujera yana kallanta cikin shigar doguwar rigar atamfa da dogon hijab me hannu"ba makaranta za ki tafi bane?Can ne amma sai mun gama da asibiti zan wuce.Yamik'a hannu yakar6i jakarta yasa mata kud'i a ciki yamik'a mata,tasa hannu biyu takar6a tana godiya "ALLAH yak'aro bud'i Yaya Julaibib.Yayi murmushi kawai sannan yamik'e muje in taka miki.Takalleshi kayi wanka dai mutafi ko? A ah naji sauk'i fa ni anjima kad'an ma Kafanchan zan tafi.Takalleshi wani iri kamar za tayi magana sai kuma tayi shiru. Yau da wuri tadawo sai kawai tawuce gidan Inna suka sha hirar su Inna tamusu faten tsaki sai bayan la'asar tamata sallama takoma gida,tana ganin kiran Julaibib tad'aga a kame sallama kawai tamishi tayi shiru"Zautajiii...kin dawo daga makaranta ko kina can in biya in d'auko ki.A takaice ta amsa"nadawo.Lafiya kuwa?Tasake amsawa da"Uh batare data bud'e baki ba.Baki da lafiya ne najiki wata iri"k'alau nake.Yasauke numfashi"toh shikenan ganinan zuwa.Ta amsa da uhun. Taje tayi wanka tana zaune a gaban madubi tana kwalliya ya shigo da sallama ta amsa sallamar tare da mishi sannu da zuwa tacigaba da abinda takeyi bata wani damu da ganin shiba,yanad'e hannayen shi a k'irji yana k'are mata kallo,yau ta mishi kyau fiye da kullum,yak'arasa wajen ta da karsashi "Zaujatiii...kinyi kyau fa.Ganin ya d'okantu da ita yasa tad'an tsuke baki kamar me shirin yin fito,kamar bataji abinda yafad'a ba tacigaba da shafama la66anta jambaki ruwan hoda. Sai yad'ora mata ledar raken a jikinta"ga mutumin ki.Tad'anyi tsaki. Yabita da kallon nazari"tun a waya nakiji wata iri yanzu kuma tsakin me kikeyi Sudaida?ALLAH dai yasa banine na 6ata miki rai ba.Tad'an harareshi tana k'unk'uni.Ke karki sani a uku fa kin san ina k'aunarki.Ganin ta mik'e zata bar d'akin yasa yarik'ota da sauri sannan yakalleta cikin natsuwa"fad'a min laifina zan baki hak'uri,durk'usama wada ba gajiyawa bane. Haushin shi yakamata"na rantse maka da girman ALLAH idan bakazo munje asibiti ba to ko ciwon ka yatashi cikin dare ni karka tasheni ina tsaka dajin dad'in bacci na eheee,yasan za a rina...wannan fushin,haba-haba dai ke kuwa ya zaki fad'i haka? Yanzu lalurata ba taki bace?Takwace hannayenta tana turo baki gaba"eh batawa bace,ta kace kai kad'ai dan haka kaje kaji da ita kai kad'ai tunda na baka shawara baka jiba...Yayi yar dariya"kinga to kisha kuruminki Sudaidan D'ansarai yajata suka zauna a kujera sannan yaciro ledar magani da d'an k'aramin katin shi na ganin likita"duba kigani"daga asibiti nake abinda yasa ban dawo da wuri ba kenan,likita yamin test,wai typhoid ke damuna ga magungunan daya bani da allurai"anjima bayan sallar Isha'i za ki rakani allurar,kin san bana son allura idan nak'i tsayawa sai ki d'an bud'e idanun ki nan da nan sai kiga na tsaya amin ba tare da ankai ruwa ranaba ko kuwa?Tayi dariya"lallai kuwa wannan shine ta6ara megida da kukan yunwa. Tad'auki rakenta tafara sha da bismillah"da fa yau har yajin shan raken nan zanyi da bakaje asibitin ba.Ke d'in kuwa?Ke mayyar rake ce kuma ban ta6a k'in siyo miki ba,amma ni idan nace ki had'a min shayi sai kawai ki kama fushi wai bazan sha bak'in ruwa ba to haka a ke rayuwa?Kowa ba da abinda yafi so ai ko kuwa? Tajijjiga kai"ka fini gaskiya, toh kayi hak'uri na dai fushi da shan bak'in ruwa... tawani shagwa6e"nima ai gashinan a hankali na fara koyan sha,shekaran jiya ba tare muka shaba? Yagyad'a kai"Yau me kike dafa mana be?Tad'an kalleshi"ni fa da bazanyi wani girki ba,idan zamuje allura muje gidan Inna kaci tuwo ni zan sha Yoghort dan bana jin yunwa.Yamik'e"to shikenan,yatafi d'auro alwala dan anfara kiraye-kirayen sallar magriba daga mabambantan masallatan unguwa. A hankali cigaban rayuwa take zuwa daki-daki har zuwa sanda bawa zai had'u da aljalinshi,alokacin numfashi da duk wani abinda ALLAH yarubuta zai samu ko zaiyi a doron duniya ya gamayin shi.Julaibib Abdullahi D'ansarai a yanzu yasake samun cigaba daga matakin lecturer zuwa senior lecturer. Yana zaune a D'akin-shak'atawa yana yan rubuce-rubucen shi a na'ura me kwakwalwa,yayi k'iba yak'ara kyau da wayewa,bak'ar fatarshi tanata shek'i dan ta jik'e da hutu da kwanciyar hankali,shigarshi kamar kullum ta fararen kaya,hularshi dara daratsin fari da ruwan k'asa, agefe kuma Ya'yanshine Ya'yan abokinshi amininshi,kuma d'an'uwan shi Musaddiq suna zaune tankwashe da k'afafunsu cikin ladabi suna cin abincin rana. Asma'u tayi sallama tashigo. Julaibib yad'ago yana amsa sallamar yana mata sannu da zuwa,tazauna suka gaisa sannan tabi d'akin da kallo"ina madugar baza ta fito mu gaisa bane? Yagirgiza kai"Sudaida baza tak'i fitowa ku gaisa ba matuk'ar tana cikin gidan nan ko da kuwa bata jin dad'ine.Tata6e baki"haka fa, toh madallah. Suka cigaba da hirarsu ta zumunci,a hankali har tasako mishi zancen k'arin aure"Lillahi warasulihi ka dinga zama kenan da mace juya? D'ansarai ai kowa yana son ganin d'a na kanshi. Yad'anyi murmushi"haihuwa ai d'an lokacine Yaya Asma'u.Tawatsa hannu" kai tafi can,tunda an maida kai hannun zani dole za ka fad'i haka mana,ka barta tana ta karatu to yaushe kuwa zata yadda da haihuwa, haihuwa yaja mata koma baya a wajen karatunta,na sha fad'a maka yarinyar nan tsarin Iyali takeyi,idan ba haka ba me zaisa har yanzu bata haihuba? Su sauran da akayi bikinsu rana d'aya ba ga shinan daga me haihuwa biyu sai me uku ba? Jiya kuma nake jin wani k'arin abin haushin,abin duka ba sanda wai Gidan-Waya sun fara degree program dan haka ka barta tacigaba,haba dan ALLAH D'ansarai ina hankalinka da tunaninka suke ne?Ganin yayi shiru yasa tacigaba da zugashi da k'ara tabbatar mishi lallai tabbasss Sudaida ita take hana kwanshi zuwa duniya. Zuciyarshi tafara mishi tubka da warwara game da kalaman Asma'u.Tasake kallanshi "D'ansarai wai kai har yanzu baka ga biri yaso yayi kama da mutum bane?Yazuba mata idanu yana zancen zuci"anya Sudaida za ta mishi haka?Yana lura da ita,ita kanta fa tana san Ya'ya dan duk lokacin da za suje siyayya a kasuwa taga unisex riga indai ya mata kyau to sai ta siya,ran nan yashiga d'akin baccin su yatarar da ita tana jera kayan a babban a kwati trolley;yazauna yana kallanta "Zaujatiii...wai wa kike sai ma wad'annan kayan ne?Tad'anyi murmushi idanun ta sun ciko da kwallah alamar zuciyarta tayi rauni "takauda kai sha'awa suke bani Yaya D'ansarai musamman wad'annan biri da wandon(over roll) duk lokacin da ALLAH ya bamu d'a toh na shine ko na tane...kawai sai ta fashe da kuka"d'azu A'isha takirani wai ta kuma haihuwa d'a na uku kenan ta haifa... Maryam ta kusa haihuwan na ukun...kowacce tana da Ya'ya mu kad'ai ne bamu dasu...yafara rarrashi"kiyi hak'uri Zaujatiii... ALLAH yana sane damu bai manta damu ba,kome d'an lokaci ne,wata rana sai labari yayi ta rarrashinta har yasamu tayi shiru sannan yakalleta cikin natsuwa "Zaujatiii... ki daina wahalar da kanki a kan tara kayan yara na sha'awa duk wannan me sauk'i ne in dai ALLAH ya azurtamu da samun d'an, dan kyale-kyalen kullum sabunta su akeyi"budurwar bana tafi ta bara... Bayan haka kuma kullum gidan nasu cike yake da Ya'yan yan'uwa in dai tana gida,kai ko bata gidan in dai shi yana nan kuma ba makaranta za suje ba toh zama sukeyi su jirata,saboda san su da takeyi da kuma irin garar da take had'a musu,duk abinda yaro yake so in dai tana dashi to anyi angama maye ya auri makauniya"in dai abin ta6akalashe ne. Toh Lillahi warasulihi me irin wannan halin ce,za a ce baza ta bar nata Ya'yan suzo duniya ba saboda karatu?Anya kuwa?Yariga yasan Yaya Asma'u kowa ma za ta iya kushewa tazaga in dai taku batazo d'aya ba.Yakad'a kai cikin sauke numfashi"ALLAH yakyauta. Tabishi da kallan mamaki"ALLAH yakyauta fa kace? Eh Yaya Asma'u to me zance daya wuce haka? Tadad'a gyara zama"kai ko kake da abin cewa,cene da ita aure za kayi...kayi auren ka amarya tazo taita haifa maka Ya'ya,toh idan taga Ya'yan kake so taga amaryar taka tafara cika maka gidan da sanyin idanu to ai zata daina abinda takeyi na tsarin iyali ko kuwa?Toh zanyi tunani.Tamik'e"ya dai kamata,ni me zan samune a gidan? Tana fad'in haka ta nufi d'akin da suke ajiye kayayyaki tagama dube-dubenta tafito"kome ma ya k'are.Yauwa gwamma da kika gani ganin idanunki,dana fad'a miki ba kome ba yadda za kiyiba,kin san ni d'an albashine ga shi kuma wata yakai tsakiya,abubuwan sai dai godiyar Ubangijinmu a kowani hali da yanayi. Taja dogon tsaki tana mishi kallon uku ahu"amma a hakan kake k'ok'arin biya mata wasu mak'udan kud'ad'e dan tacigaba da karatu, tamik'a mishi hannu"ni bani abinda kayi niyyar bani kawai in tafi.Zan ai ko miki dashi har gida,Yaya Asma'u kidinga tausaya min mana.Tanunashi da yatsa"kai d'in?Na rantse da girman ALLAH ba ka da matausaya.Yakalleta da mad'aukakin mamaki yana nuna kanshi"ni d'in ne bani da matausaya Yaya Asma'u?Ko shakka babu dan ni banga matausayan ba,ba d'a ba jika to ko hidimar me kakeyi da har za a tausaya maka saboda yawan buk'atu?Daga kai sai matarka kuke cin karanku ba babbaka,takalleshi"za ka bani ne ko sai madugar ta dawo in zo in kar6a? Baice kome ba yasa hannu a aljihun gabar rigarshi yaciro kud'ad'en ciki yana nuna mata"kingani yan canjine wallahi bani da kud'i.Tasa hannu takar6a"eh kawo da hanau gwamma mannau ni na wuce.Yabita da kallo har tafita a D'akin-shak'atawar, yagirgiza kai "Yaya Asma'u matsala,ALLAH yashirye ta da masu hali irin na ta. Sun dawo sallar la'asar da yammacin,shi da Musaddiq suka tsaya a k'ofar gidan suna tattauna al'amuran daya shafi kasuwancinsu ta dawo daga makaranta,ta tsaya suka gaisa da Musaddiq sannan tawuce ciki da mamakin kallan k'urillan da Julaibib yake binta dashi wanda ba halinshi bane yawan kallan da har sai kaga munin mutum.Tana kwance a tsakar d'akin yashigo,tamik'e zaune suna kallan-kallo na wucewar wasu dak'ik'u "Yaya D'ansarai lafiya kuwa? Me yafaru ne? Yasunkwui da kai,sai gwiwoyinta suka sage dan ta san wannan halin na shi tuntuni in dai yasunkwui da kai to bazaiyi magana ba ko da menene,tajingina bayanta da kujera tare da lumshe idanun ta,tunani barkatai ya cika k'wak'walwarta"ita dai tasan lafiyar ALLAH suka rabu har tana tsokanarshi "Zaujiii...kafin in dawo kamana faten tsaki mana.Yagalla mata harara"na rantse da ALLAH tun kafin wankin bargo yakaiki ga dare ki tsaya kiyi abinki, danni ba bawa bane.Takyalkyle da dariya wato ya rama abinda ta ta6a fad'a mishi shekarun baya,farkon auren su kenan.Tawani marairaice"haba mijin Sudaida tamu dakai fa ba ta 6aci,kar fa faten tsaki yasa a ganmu a rana,tarik'o hannayenshi"dan darajar k'auna da soyayyata da take dank'are anan tad'an daki k'irjinshi dai-dai saitin da zuciya take, kamana faten tsaki,sukayi dariya,yagyad'a kai"eh zanyi amma ba fate ba tunda nima a wancan lokacin ba a hanani ba sai dai an jamin zarene. Yamik'e,tabishi da kallo"Yaya D'ansarai... takira sunanshi.Yakalleta kawai"dan ALLAH kayi hak'uri idan na maka wani abu ne.Yayi kamar baiji abinda tafad'a ba,zuwa can kuma yasake kallanta sai yad'anyi murmushi yad'auki mukullin mota a saman tebur yafita.Ta lumshe idanun ta tanata ayyane-ayyabe a zuci. A sanda hantsi yadubi ludayi rana ta haske ko'ina na safiyar talata,tana zaune a in da ta idar da sallar walha Hauwa'u tashigo tana fad'in"ina wannnan mijin naki me bak'in idanu da ba ya san zuwa gaisheni? Abokan wasa suke da Julaibib Ya'ya maza amma tasu da Sudaida ta zo d'aya,suna mutunta juna.Sudaida takama ha6a"yanzu mijin nawane me bak'in idanu Hauwa'u? Tajijjiga kai 'tabbasss,to ni duk zuri'ar D'ansarai da wanda yafishi bak'i ne?Sudaida tad'an harareta"lallai daga yau na san in da zan ajiyeki tunda kike cima rabin raina fuska a gaban idanuna,to amma kuma kyau tsagwaron shi da wanda yakama k'afar Yaya D'ansarai nahhh a duk zuri'ar Doctor Julaibb D'ansarai? Bata bata masa ba taje tad'auko lemun peach. Sudaida tawatsa hannaye"ahab ni dama na san irin abin nan ne na na makaho da yace ido da wari.Hauwa'u tayi murmushi"mu ai gaba d'aya a zuri'ar Doctor Julaibib Abdullahi D'ansarai kyawawane.Sudaida tagyad'a kai"muma ai hakan take a zuri'ar Ibrahim Me-Lambu.Sukayi dariya sannan suka gaisa suna hirarsu ta yaushe gamo dan sun d'an kwana biyu basu ga juna ba saboda yanayin karatun Sudaida da baya barinta zama a gida musamma tada fara karatun degree. Hauwa'u tafara ba Sudaida shawara"ku k'ara komawa asibiti mana ko wannan karan ALLAH zai sa a dace.Takalleta cikin natsuwa"Hauwa'u a asibiti ake ba da haihuwa?Tagirgiza kai"ba a asibiti bane,amma idan kunje d'in ai zasu k'ara dubaku,idan har yanzu ba me matsala a cikin ku za su iya canja muku magunguna da k'arin yan shawarwari ko kuwa? Tagirgiza kai"uh uh ni dai bazan koma ba,sauran magungunan ma na daina sha shekaran jiya na zubar dasu nagaji da shan k'waya kullum kwanan duniya bayan an tabbatar mana lafiyar mu k'alau, na fauwalama ALLAH duk yadda yayi dai-dai ne. Duk san mu da haihuwa idan ALLAH bai k'addaro mana ita a rayuwarmu ta doron duniya ba, toh fa bawani magani da dabaru da likita zai bamu da za suyi amfani,tad'an yi murmushi"ki cigaba da tayamu da addu'a itace babbar makamin mu.Hauwa'u tarik'o hannayen Sudaida cikin k'auna da tausayi "wannan halin na ki na maida al'amura wajen ALLAH me kowa da kome yasa nake dad'a k'aunarki,addu'a ina tayaku da ita kuma zan k'ara,Ubangiji yamana jagora ya iya mana kar yabarmu da iyawarmu dai-dai da k'iftawar idanu.Amin Hauwa'u. Asma'u tashigo da sallama tana musu wani malalacin kallo ganin hannayen su a had'e"to fa wani sabon salo ne wannna zuwa karuwanci da uwa? Hauwa'u ta amsa"eh mana to ya san ranki Ma'u?Kafin tayi magana Habiba Yayar Hauwa'u tashigo,tafad'a kujera tana wata yatsina wai ta gaji daga shagon d'inki take.Asma'u takar6i ledar ta zazzage kayan"toh bari muga style,material ne da da leshi kuma d'inkunan sunyi kyau sosai,wai ankon sunan da za ayine idan ta haihu.Hauwa'u ta d'auki material d'in tana dad'a gani dan shine ya burgeta "gaskiya da ina da kud'i da sai na yi shi. Asma'u tace"tunda baki da kud'in wannan ai akwai atamfa ta yaku bayi,dama ai dai-dai ruwa dai-dai k'urji.Habiba ta cafe"ah to shi mutum ba zai tashi ya nemi na kai ba,kome an dogara da miji har abinda ba wajibinshi ba a gida yakamata Iyayenshi su mishi amma basuyi hakan ba,kai ni wannan rashin tausayi dame zan kwatantashine?Kome dai miji?Taja dogon tsaki,toh gwamma dai mutum yasani shi mijin nan ba dan mace d'aya aka halicceshiba,ko bajima ko ba dad'e dole wasu mata ukun da izinin ALLAH sai sun shigo an dama dasu suma. Sudaida tayi tsaiii...cikin nazarin kalaman Habiba,babu kome a cikin su daya wuce shagu6e. Hauwa'u da bata gano dawar garin ba tace kai"sharri dai ba kyau wallahi,kuma kun sani ai ina sana'a sai dai banyi k'arfi bane,yaro kuma ai da rarrafe yafara,ni kuma dan san a sani yaji da kwarin miji da banten suriki da d'an masu gida bazan kwashe jarin nawa dan yin ankon suna na rana d'aya in dawo in tsuguna ba,kuma da kuke maganar kome miji toh dan girman ALLAH wace macece a doron duniya da baza taso ace kome mijin na tane yake mata harma da wanda iyayen nata suka kasa mata ba?Kudinga adalci a kalamanku fa...Asma'u da Habiba suka kalli juna suka kyalkyale da dariya Asma'u tace"ballagaza bankaura, sakarai ba ta da wayau...inji Sa'adatu(Barmani Choge) Sun so wacce sukai hakan dan ita ta tanka amma sai batace kome ba tashige d'akin baccinsu tad'auko material da leshi launinsu d'aya dana Habiba sai dai zanen jiki ya bambanta,tana fitowa ta d'orama Hauwa'u a cinya"gashinan ki d'auki d'aya,wannan karan dai na ceceki,dan haka daga yau ki tashi haik'an da niman kud'i dan ki huce takaicin zamani,duk da dai na ga zafin nema ba shi yake kawo samu ba,haka kuma dare d'aya ALLAH kanyi bature, indai kina da wadatar zuci to abun kowa bazai tsone miki idanu ba.Hauwa'u Tajijjiga kai "tabbasss zancen ki dutse. Tabi kayan da kallo"kai ko wanne fa ya d'auku,sai dai kawai in rintse idanu in d'auki d'ayan. Sudaida ta koma ta zauna"toh barinyi maganin ruwan idanunki kawai,kirik'e su duka na bar miki.Hauwa'u tad'an zaro idanu cikin mamaki"duka na wa?Kin barmin? Sai tafad'ad'a murmushinta zuwa dariya"kai masha-ALLAH jazakillah khaira-khaira jaza'ih...ALLAH yabarki da Alhaji D'ansarai me bak'in idanu har gaban abada.Takallesu ku tayani godiya mana. Zuciyar Asma'u ta gama tafarfasa har ta k'one,ankon fa takema D'ansarai magiya yamata yace shi bashi da kud'i shine yanzu matarshi har take kyauta da kala biyu,itafa d'aya ma tace mishi tana so..Lallai wanna akwai shegiyar yarinya wato kome na shi ya tattara mata kenan?Taja tsaki"itama Inna tana da matsala(🤔kunji fa)wai idan an fad'a mata sai tace wannan dai sa'idanune a abinda bai shafe kaba, ita ba matar shi bace?Ai ko ba aure a tsakaninsu yan'uwan junane,kuma duk Ya'yantane,tanuna Asma'u da yatsa"wallahi kina tare da wahala idan baki bar wannan banzan halin na kiba,ke wayasan damfarar da kike ma mijin ki da wannna shegen wayan na ki?Tasake jan tsaki Inna bazaki gane irin bautar da yakema wannan yarinyar ba wallahi dan ba kyau zuwa gidan nan kina gani ganin idanunki ne. Habiba ce taja dogon tsaki"kina ta wani zuba godiya kamar wacce a kamata gafara,ba fa sai kin gode ba tunda kowa ya san ai k'oshin wake na ruwa ne,da kud'in d'an uwanki D'ansarai aka siyesu, kuma ko ke zai iya sai miki wanda suka fisu ma... Hauwa'u ta tari numfashinta"a ah wallahi k'arya da ciwo gyambo da wari. Sudaida tayi dariyar tura haushi"ah toh gwamma dai da kika tuna mata,takalli Habiba tana murmushi"wad'annan da kike ganinsu tanuna kayan data ba Hauwa'u ni na siyesu da kud'i na,ai idan zan siya da kud'in Yaya D'ansarai toh bazan sai wad'annan masu rangwamen farashin irin ta gama-gari yakubayi ba,tunda kud'in ni nake zamansu. kufa yan uwane ba dole ne ya mukuba,sai dai yayi dan kara yasamu ladan zumunci, idan kuma yak'iyin haka ba wanda zaice dan me?kuma ko a wajen ALLAH bashi da laifi ko na sisin kwabo tunda ku ba a hakk'unshi bane,ni ce nan tanuna k'irjinta da kwibinta ni ce k'ashin hak'ark'arinshi,kinga ni ce nazama dolenshi, wallahi idan ana san zaman lafiya dani toh fa sai na fad'i irin wanda nake so,idan an kawo naga kalar bai min ba dole yakoma yaza6o wani, ko kuma in ce yad'ibo su da yawa in za6i wanda suka kwanta min a rai...Habiba ta tari numfashinta"tabbb ai ko baki isa ba,tamata wani kallan uku ahu kai... ALLAH ko ya isa da wannan iko sai kace ke kika kawo shi duniya. Sudaida ta kalleta cikin kukawa"Habiba kenan kisa ranki a inuwa dan ko ba iko dama ALLAH ai ya isa da kome,shine dama me kowa da kome na doron duniyar nan. Asma'u tamik'e"ke fa yarinyar nan wato salan mulkin ki kenan ki hana mutum rawar gaban hantsi ko? Batayi niyyar maida martani ba to amma Yaya Asma'u ta dad'e tana shiga mata hanci da k'udundune ya kamata ta fyaceta,kuma kunyar mara kunya ai asarace,idan babba ya yadda girman shi to ai ba laifi bane dan an taka. Sai tagyad'a kai"ai kuwa dai Yaya Asma'u na zama kuturwar uwa zama dani dole,kuma duk wanda zai zauna dani d'in to d'aurin gwarmai nake mishi.Habiba da take ji kamar ta shak'e Sudaida dan haushi tace"to ai barewa baza tayi gudu yar ta tayi rarrafeba.Sudaida ta kyalkyale da dariya"ai dama kyan rawa da makar6i,kyan d'an yagaji ubanshi. Asma'u tafara tafiya "to Sudaida na yi gida amma dai kiyi a hankali dan ni bazan mulku ba, idan kuma kika matsa da yawa to abu ne me sauk'in gaske cire wando taka inyi waje dake.tak'arasa fita ba dan bata da sauran abin fad'a ba,a ah sai dan kar k'ilu taja bauuu...ga Hauwa'u nan itama munafuka ce idan anzo maida magana Sudaida za ta goya ma baya sai a d'ora mata sata da maitar,amma lallai sai tasa Dannarai ya k'ara aure, itama Sudaida ta so data tsaya ta ba ta amsa dan haka duk sunji ciwon kalaman juna. Tacire hannun Hauwa'u da tayi tagumi dashi tana kallan su kawai,ta kashe ta da lallausan murmushi tunda ance iya ruwa fidda kai."kiyi hak'uri ba kud'i a hannuna amma idan bafade na autan Inna yadawo ranar jumma'a to zan turo miki shi wallahi har gida yazo yabaki kud'in d'inki dana takalmi da hijab,dan kin san ni a gidan nan k'arfine dani na gaban shari'a kum...Hauwa'u tasa tafin hannun ta rufe mata baki"dan girman ALLAH ya isa haka Sudaida. D'akin-shak'atawar ya d'auki shiru na wucewar wasu yan dak'ik'u.Habiba tayunk'ura tamik'e cikin fushi bata musu magana ba tayi hanyar fita.Sudaida tad'an d'aga murya"toh uwar biyu sauka lafiya sai kin kiramu,ALLAH yaraba lafiya.A ciki ta amsa da"uhun.Tana fita Hauwa'u ta kyalkyale da dariya"matar D'an Sarai yau kin burgeni.Takad'a kai"ni har ga ALLAH banyi niyyar kula suba to amma naga abun na su yana neman wuce gona da iri ne,shiru-shiru kuma ai ba tsoro bane gudun magana ne"dodo d'aya akema tsafi,ba su suke aure na ba Yaya D'ansarai ne dan'uwan ku,duk fad'in mutanan doron duniya idan za suce yarabu dani idan yana so na,yana san zama dani to ba wanda ya isa ya rabamu,tunda ba wanda yake mishi auran nan,shi d'in da kanshi yake abinshi,haka kuma idan yace ba yayi ba wanda zai tilasta mishi zama dani.Hauwa'u tajijjiga kai "tabbsss zancen ki dutse"ALLAH yashirye su da sauran dangin miji masu mugun hali na mugunta "abun wani banza na su dukiya. Tana kallan shirin Akhbar-Al'an tana cin awarar madarar shanu Khadija yar Khausar tashigo da gudunta cikin d'oki tafad'a jikinta"Inna Mamace tace in zo in tambayeki wai anjima za tayi tuwon shinkafa miyar shuwaka,shine tace wai a k'aton kwano guda nawa za a zuba miki? Sudaida tayi murmushi ta san wayau aka mata, kafin tayi magana kiran Khausar yashigo"Nana Khadija ta k'araso kuwa?Eh gatanan ta kuma fad'a min sak'on,ina za ki?Asibiti zan kai Misbahu ta kuma na ce dole sai munje da ita.Wayyo! har yanzu jikin ne?Shine Sudaida daren jiya kusan kwana mukayi bamuyi bacci ba saboda kukan shi. Toh ALLAH yasauwake zan shigo anjima idan kun dawo. Sukayi sallama. Inna me zan fad'a mata?Takalleta da kulawa"bari sai anjima idan nayi wanka sai muje can muci ko?Toh Inna amma kamar kinyi wanka ga shi kina ta k'amshin irin turaren Baba D'an Sarai,ina son k'amshin. ALLAH Khadija?Khadija tayi d'an tsallan murna kamar yadda yara keyi"ALLAH Inna,to maza shiga d'aki ki d'auko kema in fesa miki,da gudunta ta d'auko Sudaida tafesa mata.Nagode Inna.Tad'an kama ha6arta"yauwa Khadija ga yoghort can kije ki d'auka,tad'an mak'ale kafad'a"Inna ni dai nafi son Caprisonne.Tamik'e shikenan muje in baki. Sudaida tazuba mata idanu cikin tasbihi ga Ubangiji,k'udurar ALLAH dayawa take,wai yaushe-yaushe akayi auren su amma gashi har an haifi yar da za a aikota daga wani gida zuwa wani gida da k'afafunta da bakinta"oh ALLAH kaine ALLAH.Sharrr...sharrr...hawaye masu d'umi suka zubo mata"anya za taga gudan jininta a doron duniya kuwa?Ta rungumeshi a k'irjinta yaji d'uminta na uwa itama taji d'uminshi na d'a?Ta tuno da bak'ar magana habaici da dangin Julaibib suke mata,wanda in dai da mutum shi yake da ikon ba kanshi haihuwa to kuwa da tayi zuciya ta haifo musu yan hud'u a haihuwar farko,to ina ALLAH ne,ba kuma a mishi dole...tasake tuno kalaman Inna,Mama,kai rannan har Umma sai da tadinga kwantar mata da hankali akan dai tayi hak'uri tayi hak'uri,kullum haka suke fad'a mata musamman idan sun ganta cikin damuwa ko da ba wannnan ne abinda yake damunta ba "kiyi hak'uri Sudaida hak'uri kan tadda rabo,wata rana sai labari.. Khadija tamatsa wajenta"kukan me kikeyi Inna?Waya dake ki?Tarungumeta kawai tacigaba da kuka Khadija na tayata,sai da sukaci suka k'oshi dan kansu sannan sukayi shiru a hankali kuma bacci yayi awon gaba dasu. Kiran wayar Julaibib yatashe ta daga bacci"wash ALLAH Zaujiii...yatare ta da sauri"me yafaru ne Sudaida?Tayo k'asa da murya"ba kai bane ina cikin baccina me dad'i ka tashe niba.Yayi murmushi"to fa tawa tasameni kenan malami da tallan jigida,kiyi hak'uri ki koma baccin anjima mayi magana.Uh uh ai kuma ko na koma baccin ba lallaine yazo ba sai dai in ta juyi"goben zaka dawo?Na so haka to amma bazai yiwuba dan gobe muna da serminar a jahar Katsina idan na dawo kuma akwai jarabawar da zan ma d'alibai,nima na so zuwa dan zan ba Inna wasu kud'i,amma barin miki transfer idan kika ciro sai ki kai mata,yanzu zan kira ta in mata bayani.Ranta bai mata dad'i ba amma ta daure ta amsa da to tare da addu'ar ALLAH yakiyaye hanya,sukayi hirarsu ta kewar juna sukayi sallama. A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar laraba tabawa ranar sa a,Nasmat tazo gidan,suka rungume juna"oyoyo Nasmat...Sudaida ta d'auki Ahmad tana mishi wasa shi kuma ya bud'e wawulan bakinshi yana kyalkyala dariya.Nasmat taje tad'auko lemun sprite tabud'e tana mita "Sudaida kin zama abinda kika zama wallahi,abinda yasa meki ALLAH yasa kar yasamu sauran dangi.Tamata kallan k'arin bayani...Nasmat tagyad'a kai"in dai na zo gidan nan ni zan ba kaina ruwa ko abinci?Haka ake ma bak'o?Taja tsaki"na d'auka wani laifin nayi to kar kisha ruwan mana cikin wa zai shiga? Takama ha6a"kar dai zama da mad'aukin kanwa Yaya Asma'u ya sa kema kin zama abinda kika zama? Haushi yasa Sudaida tak'i magana tanama Ahmad wasa yana cigaba da dariya.Itama tamik'e zuwa wajan taga tana amsa waya,tagama wayar tad'an kalli dai-dai kun mutanen da suke kai-kawo a safiyar sannan tacema Sudaida"na biyo miki ne muje duba yar gidan Yaya Asma'u da jiki.Hu'un tafad'a ba tare tadata bud'e bakintaba.Menene kuma hu'un?Nasmat ta tambayeta.Tamik'e zaune daga kwanciyar da tayi tad'ora Ahmad a cinya"ke ni fa bazani in da raina zai dinga 6aci a banza ba,dan na riga na k'una bana tsoron wuta.A ah Sudaida kiyi hak'uri kawai idan an miki kan kara karkice za kiyi na itace.Tayi wani huci cikin kad'ai"ai na rantse da girman ALLAH ni yanzu har na gungume zan iyayi yadda zai shekara yanaci,kawai sai tarufe idanu tana zazzaga fad'a,Nasmat bata kar zomo ba amma an bata rataya. Tazuba mata idanu har tayi tagaji dan kanta tayi shiru,sai kuma tayi kwafa"banda ina duba darajar yan'uwantaka da dangantaka kinaga zan bar Yaya Asma'u tacigaba da cin dunduniyata tana min hawan k'awara yadda taga dama?Nasmat tagirgiza kai sannan ta amsa cikin natsuwa"a ah baza kiyiba, to amma karki manta hak'uri kan tadda rabo...idan ka gaida wada da tsawonka zaka mik'e...Sudaida ALLAH yana son masu hak'uri masu had'iye fushi,da dama su rama abinda aka musu amma sai suyi hak'uri ba saboda kowa da kome ba sai saboda zatin ALLAH... tacigaba da rarrashinta har fushin daya mamaye zuciyarta yalafa,ta kuma yi nasarar janta suka tafi dubiyan... Da kunu da miya har abadan duniya ba za su had'uba sai dai a cikin ciki. 27 Jumaada Thani 1441 21 February 2020 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na ashirin da biyu. A wulak'ance da halin-ko-inkula kamar yadda tasaba haka yauma ta amsa gaisuwar Sudaida, amma tanata jan Nasmat da hira suna shirin tafiya sai ga Hauwa'u itama ta zo dubiya,suka tsaya ana gaisawa, Hauwa'u tamatsa kusa da Sudaida "yar'uwa yayane jikin ne ko garin ne,ko wannnan bak'in mijin na kine dayaje yashare waje a Gidan-Waya?Takai mata duka a kafad'a,tagoce da sauri yabi iska.Kin sama mijina rabin raina idanu fa,meye darin gamarki dashine wai?Asma'u da wata k'awarta yar duniya me irin halinta sukayi dariya suka tafa"haka fa kullum ana nuna ana k'aunar miji amma an k'i nuna mishi k'aunar a zahirance,ta hanyar barin Ya'yanshi suzo su shak'i iskar duniya,takad'a kai cikin ta6e baki"kullum ana ba mutum amma har yanzu ya kasa yin zuciya yak'ar6a ko da sau d'aya ne,sai dai ayi ta asara,a wanke abun yabi rariya. Hauwa'u takalleta"ke wai Asma'u kullum ba ki da abinyi sai gori?Sannan ma dake ake magana me ko ko ita tace miki ba tajin dad'i?!Nasmat ma ranta ba dad'i tace"haba Yaya Asma'u wannan ba girmanki bane wallahi,kin san duk me gori matuk'ar bai tuba ba to yana haramtama kanshi rabon alheri ne a lahira, sannan wannnan gorin ma d'an Adam d'in doron duniya ba shi da iko akanshi,wannan ba huruminki bane Yaya As...kafin tak'arasa sai ga Hajiya tashigo d'akin tana d'agama Nasmat hannu "dakata Nasmat in dai gori ne ta tara ta samu, Hajiya tanuna kanta"ni d'in nan yau har goruba zan mata, zanyi maganin iya shegen nan k'auri da kare. Tayi d'as d'as d'as da yan yatsunta"ki bud'e kunnuwanki da kyau ki saurareni,na rantse miki da girman ALLAH in har Sudaida bata haihuba to ba itace ba ta haihuwaba,k'aninkine Julaibibi,matan kakanku ai su biyune uwargidan shice mahaifiyar ubanki,su uku tahaifa,amma amaryar shi sai da ta haifa mishi Ya'ya goma shabiyu, ubanki gashinan shima Ya'ya uku yahaifa,d'aya kanin na shi yahaifi Ya'ya biyu, d'ayan kuma ai har yakoma ga ALLAH bai haihuba,matar shi data gama takaba tayi wani auren bagata can da Ya'ya bakwai ba? Karima Yayarki Ya'yanta biyu,ke kuma yarki d'aya jallin-jal kamar rai,sai 6ari da kika ta6a yi sau d'aya duk shekarun da kukayi a gidan miji,mata nawane ta dangin kakar ta ku ga sunan a gidajen miji ba haihuwa sai dai suci su k'oshi suje masai su juye kayansu?Ai suna da yawa saboda ku ba irin haihuwa bane,toh Sudaida fa?Su goma sha takwas ne a gidansu,kuma duk cikin Ya'yana ba uwarki ce kawai me Ya'ya uku ba?Tanuna ta da yatsa"to dan haka ahir d'inki hawainiyarki takiyayi ramar Sudaida, kuma ko yanzu da k'anin na ki zai rabu da ita,toh idan ma na rantse ba kaffara a kaina bazata rufe shekara a wani gidan auren dazata yiba za ta haifo gudan jininta takuma sa zani tagoye abunta,ai ga sa'o'in auren na ta nan kina ganinsu ganin idanunki kowaccensu ta fara kafa na ta Iyalin... Tambayar me jikin da batayiba kenan ta ajiye ledar ayaba da lemun tajuya cikin fushi"jahilar addini kawai wacce bata yadda kome muk'addari ne tun daga lauhul-mahfus ba,na rasa a ina kika d'auko wannan bak'in halin na ki,banda ma ke shimmeruwa uku ce(sha-sha-sha)Sudaida ba yar'uwarki bace da zaki iya tare mata fad'a a inda kikaga za a wukak'anta taba?Toh karki daina abinda kikeyi ai hassada ga me rabo ta kice...Nasmat da Hauwa'u sukayi lallausan murmushi suna shima Hajiya albarka"ALLAH yak'ara girma me amfani Hajjaju makkatan...kaza dai garin tuno-tone take tono wuk'ar yanka kanta...baki shi ke yanka wuya.Sai da Hajiya tabar gidan sannan Asma'u tafara nad'e tabarmar kunyarta da hauka. Da wannnan 6acin ran Sudaida tawuce ATM taciro kud'in da za ta kaima Inna,sukayi kaci6is da Aminu shima ya zo ciren kud'i yabud'e mata murfin motar"shigo ki jirani tunda yau na ga ba layi.Dak'ik'u basu wuce goma ba yadawo.Yaya Aminu gida za ka koma? Yana tayar da mortar yake amsawa "Jos zani,amma ke zan mayar gida wani abune?Tasa hannu ta share hawayen da suka zubo mata sharrr... "mutafi kawai sai ka saukeni a Gidan-Waya. Sun d'auki hanya sosai sannan yajuyo cikin kulawa yakalleta"wai yau waya ta6a kanwata rabin raina ne?Tad'anyi murmushi"share kawai Yaya Aminu ni da Yaya Asma'u ce.Yakama ha6a wuuu... Asma'u ciwon idanu sai hak'uri,ai ko jiya danaje dubiya nima sai da muka hau sama muka fad'o,wai nayi kud'i bana son zuwa gaisheta,kinji sai kace wata Yayata. Sudaida takawar da zancen ta hanyar tambayar Siddiqa nan da nan ko yayi lallausan murmushi suka shiga hirar arziki har suka iso Gidan-Waya,har k'ofar gidan da Julaibib yake yakaita anan rukunin gidajen malamai,yasake kallanta cikin kulawa"Sudaida kiyi hak'uri na san kinayi amma ki k'ara wata rana sai labari,ai duk abinda yayi farko to tabbasss yana da k'arshe,wallah-azim da ana siyan haihuwa da kud'i toh dana sai miki kome tsadarshi,toh ina abin na ALLAH ne "ance da kare me sunan maza.Tajijjiga kai"na sani Yaya Aminu na kuma gode, duk cikin Yayyina kaine taurarona"Ina sonka sosai.Sukayi murmishi"nima nagode kanwata rabin raina data za6eni sama da kowa a matsayin tauraronta,toh me kike so in siyo miki a matsayin tsaraban mutan Jasawa?Tagirgiza kai"bani da za6i kasiyo min ko menene nagode. Yayi yar dariya"tunda kin bani wuk'a da nama Insha-ALLAH za6in nawa zai burgeki,idan nadawo zan shigo in baki tsaraban,sai in kar6i kud'in da kikace zan kaima Inna,kiyi hak'uri ko?Nagode Yaya Aminu tabud'e motar tafito,tarufe mishi"adawo lafiya ALLAH yatsare,suka d'aga hannu suna ma juna adabo.Tabi danjojin motar da kallo har ya6ace ma ganinta.Tarik'e k'ugu tana fesar da iska ta baki ta hanci sannan tasa hannu a jaka ta d'auko mukullin gidan tabud'e tashiga. Wani k'amshin turaren d'aki da sassanyar iskar da take shigowa ta tagogin da suke bud'e yamamaye ilahirin gangar jiki da zuciyarta,sai taji ta samu natsuwa ta lumshe idanunta tana jan numfashi"Yaya D'ansarai wallahi me tsabtane,ji yadda yazauna yagyara gidan kamar mace. Tashige d'akin bacci,tazauna a gefen gadon tad'auki wani d'an k'aramin hotonta da ya ajiye a dirowar gefen gadon,ta d'auki hotonne a wani excursion da sukaje a Wadom akan harkar gona tun tana aji biyu a k'aramar secondary,tak'arema hoton kallo tana tuno irin kyan da Julaibib d'in yace wai tayi...Wanda ita dan haushin irin munin da tayi ta turo baki gaba zata yaga sai gashi ya shigo gidan shine yakar6a,tamaida hoton ta ajiye tana murmushi ita tama manta ta ta6ayin hoton. Taje tayi wanka tabud'e wardrobe tad'auko riga da zani na shadda ruwan makuba dan dama akwai kayanta a gidan,wasu lokutan idan tazo makaranta ba ta komawa Zonkwa sai tayi zamanta koda ba Julaibib a garin tunda baya samun zama yau yana Zari'a gobe yana Katsina, jibi yana Kaduna,haka dai haka dai ake ta gwagwarmaya da zirga-zirga a cikin rayuwar. Tana azkar d'in yammaci bayan ta idar da sallar la'asar Aminu yashigo ya ajiye mata injin d'in matse ruwan rake tagama azkar d'in sannan takalleshi cikin murna da shakka tanuna injin d'in tana kallanshi"Yaya Aminu da gaske?Yajijjaga kai "Sudaida ko da nake da raha ai na san irin rahan da nake yi da kowa,bazanji dad'i ni akaran kaina amin irin wannan kyautar bayan na sa hannu na k'ar6a,sai kuma a kar6e wai wasa akeyi,dan haka bazan ma wani ba, bare ke kanwata da nake ji da ita a cikin k'annina,yad'an kalleta a kwai rake a gidan nan? Tamik'e ai ba a rasa nono a riga sai dai idan rigar ba ta tsurar fulanin asali bane,a na'urar sanyaya abubuwa(fridge)tad'ibo ferarrun rake guda biyar takawo mishi,yauwa d'auko wuka kigani. Yakar6i wuk'ar yak'ara yankasu k'anana sannan yasa a ciki,yan dak'ik'u kad'an yad'auki Kofi yajuye mata tataccen tsurar ruwan rake, yamik'a mata tasa hannu biyu takar6a takai tsakanin la66anta da bismilla takur6a,sai kawai tacigaba da sha har sai da tashanye duka.Suka kalli juna,yad'an dage gira"toh ya?Takyalkyale da dariya tana jijjiga kai "Alqur'an yayi ba k'arya,nagode Yaya Aminu ALLAH yasaka maka da mafificin sakamakon shi.Amin Sudaida"ke ma muk'amuk'inki sa huta da tauna,to kai baka shaba?Yagirgiza kai"sanda za a nuna min sahihancin injin d'in an matsa min na sha. Yamik'e yana gyara zaman hular shi"to barin kama hanya,taje ta d'auko mishi kud'in da zai kaima Inna sukayi sallama. Tana wanke d'anyen na'ana'a yashigo D'akin-girkin a d'okance"Zaujatiii...saboda ALLAH dama kinzo garin amma baki fad'a min ba?Yazuba mata idanu"to yanzu dana wuce Zonkwa ne fa? Tad'an motsa kafad'a"duk d'aya 6arin manshanu a miya.Yarik'ota cikin kewa sai kuma yasake ta barinje in sallami d'aliban da suke jira a waje yawuce D'akin-shak'atawa yad'ibo wasu takaddu yafita. Sai da yayi sallar Isha'i sannan yashigo yazauna a kusa da ita yana ganin rubutun da takeyi a na'ura me kwakwalwa"barka da shigowa Yaya D'ansarai.Yagyad'a kai"barkanmu kema kinzo lafiya?Tayi shiru kamar bataji shiba,wucewar wasu dak'ik'u kuma tad'an kalleshi"yayi murmushi kina k'ok'ari fa ALLAH yak'ara basira.A tak'aice ta amsa da "amin.Sai kuma tarufe Laptop d'in tamayar ma'ajiyarta. Ta dawo tazauna a d'aya kujerar suna fuskantar juna,zama nesa dashi da tayi yabashi tabbacin akwai maganar da zata fad'a mishi me mahimmaci dan haka take yi,dan haka shima yadad'a gyara zama dan yaji yau kuma dame tazo? "Yaya D'ansarai kana k'aunata kuwa? Baiyi tunanin abinda za ta fad'a kenan ba,amma sai ya 6oye mamakinshi ya amsa mata kai tsaye"eh Sudaida ina k'aunarki.To na rok'eka da girman ALLAH karabani da damuwa,kome yanada iyaka to tsakani da ALLAH abinda zuciyata za ta iya d'auka kenan,idan ba haka ba to ba abinda zai hanata kumbura ta fashe k'arshen rayuwata a doron duniya ya zo kenan,tanuna kanta da yatsa,ni na san ba autar mata bace dan haka zan tayaka addu'a ALLAH yabaka wacce tafini, wacce zata haifa maka sanyin idanu tunda ni na kasa, nima ALLAH yabani dai-dai ni. Yakalleta cikin natsuwa"me aka miki da kike zancen rabuwa?Da mamaki takalleshi"au yanzu baka gani ba?Saboda bakai ake ma ba?Tayi wani huci cikin kad'a kai"toh madalla,amma Yaya Julaibib gaskiya ni dai bazan iya wannan zaman ba,duk lokacin daka shirya nima a shirye nake zan ba ka sarari.Tamik'e.Jinan Sudaida koma ki zauna. Bata zauna ba sai kawai ta durk'usa a gabanshi tafara kuka "Yaya D'ansarai kaji tausayina mana bazan iya jure wani wulak'anci da bak'ak'en maganganu ba dan kawai ban haihuba,bana so zumunci ya6aci ne amma na rantse maka da girman ALLAH da da kaina zan d'auki mataki.Tasake fashewa da matsanancin kuka,kukan abu biyu take yi,gana rashin haihuwar akaran kanshi,gana wulak'anci da tozarcin da ake mata akan dai rashin haihuwar me makon ma abarta taji da abinda yake damunta.Haka ta dinga fad'ar duk maganar data fito daga bakinta ba tare data tauna ba. Yad'ago ta fuskarta sharkaf da hawaye da majina yazuba mata idanu na wucewar wasu dak'ik'u saboda ya rasa abinda zai fad'a mata,sunyi waya da Hajiya kuma tafed'e mishi bire har bindi "tabbasss an dad'e ana mata wannan cin k'ashin, amma shi da ita bata ta6a fad'a mishi ba,ko ya ganta cikin damuwa idan ya tambaya za ta girgiza kai"tace ba kome ko tace wani abu kazane ba gorin rashin haihuwaba,yayi tsaiii...har yasamo bakin zaren,sai yayi murmushi"kinga Sudaida share hawayenki tabbasss ni D'ansarai ina k'aunarki dan haka zan rabaki da bak'in ciki da damuwa.Takalleshi kallan k'arin bayani"Yajijjiga kai"kiyi hak'uri kibani lokaci zanyi tunanin yadda al'amuran za su kasance ba tare da an 6ata zumunci kamar yadda kika hango haka ko? "Zaujatiii...ina so kimin alk'awari zaki bani lokacin ba tare da kin sake tambaya taba har sai na zo miki da zancen,lokacin na samu mafita...za tayi magana yatari numfashinta"dan ALLAH kar kice kome,ai kin san ba zanyi abinda zai cutar dake ba. Tayi shiru kawai tana share hawaye tamik'e zuwa d'akin bacci takwanta tare da d'ora kanta a saman matashi. Kad'an yaci abincin daren sannan yaje yayi wanka yasa kaya marasa nauyi na shan iska,yazauna a doguwar kujera ya barbaza wasu takaddu yana aikin cikesu d'aya bayan d'aya sai dai ya kasa jure rashin Sudaida,kewarta ta dame shi dan haka yamik'e zuwa d'akin.Suka kalli juna tana kwance da wani littafin lissafi tana nazarin shi,tamaida kanta cikin littafin amma ta gagara cigaba da nazarin,yazauna a gefen gadan sannan yasa hannu yakar6i littafin. Tawani 6ata fuska"Yaya D'ansarai gobe fa muna da jarabawa shi yasa nake nazarin nan.Yamata wannan kallan da yake ba ta haushi yagyad'a kai"uh na sani...ni ma gobe zan tafi Katsina yaya kenan? Tad'an turo baki gaba tana dad'a gyara bargon data rufa"toh kowa sai yakwanta yayi ishashshen baccin da ake so mutum yayi duk dare,gobe kowa sai ya tashi a watstsake katafi Katsina,ni kuma in shiga makaranta ba shikenan ba? Takauda kai daga kallan dayake mata, tafara jero azkar d'in kwanciya.Ai ko ba shikenan ba,ki sallameni.Tagyad'a kai"toh jeka na sallame ka, ALLAH ya lullu6eka da rahamarshi da albarkarshi, asubah tagari.Yayi murmushi sannan yasa hannu yana mata wani salo...salon data kasa daurewa tamik'e zauna tana dariya"Yaya D'ansar...sauran kalaman suka mak'ale sakamakon wani sak'o d'aya bata me girman ban mamaki me sa a fita a hayyaci. Da safe yagama shirin shi tsab natafiya cikin shigar farar shadda yana zaune a D'akin-shak'atawa, yayi shiru cikin nazarin kalaman Sudaida dan ko da asubahi sai da tadad'a tabbatar mishi tana nan akan bakanta,ta kuma bashi sarari tana zaman jiran shi.Yadda yake juya zuman da yasa a shayi haka yake juya kalaman;tafito daga d'akin baccin su cikin shigar mutunci da mutunta kai kamar ko yaushe za ta shiga makaranta.Tazauna a hannun kujerar "Yaya D'ansarai wai har yanzu shayin ne baka shaba?Tun kafin in shiga wanka fa nakawo maka.Yasunkwui da kai.Sai kawai tamik'e tad'an kalleshi nawucewar wasu dak'ik'u "Yaya D'ansarai ALLAH yakiyaye hanya... Tad'an sunkuya tabashi sumba sannan tayi furucin da wani salon shagwa6a"sai munyi waya ko?...tajuya tayi tafiyarta dan tasan ba magana zaiyi ba in dai yayi wannan sunkuyar da kan"sanin hali ai yafi sanin kama. Yabita da kallo yana lallausan murmushi yayi d'as da yan yatsunshi"hak'ata zata tadda ruwa Insha-ALLAH ai ni dake mutu karaba yarinya.Yakalli agogon dake d'aure a hannunshi na dama,lokaci yaja a gurguje yagama karyawa,yad'auki jakar shi ta matafiya ya rataya a kafad'a da mukullin mota yakulle gidan yana addu'ar fita daga gida"bismillah tawakkaltu alallahi walahaula walaquuwata illah billah.Yashiga mota ya zauna yana d'aura belt yana kuma amsa wayar wani abokinshi na koyarwa da za suyi tafiyar tare.Tun daga ranar Julaibib yacanja taku tunda abin iya ruwa ne... A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar litini (Monday)ranar aiki ko nasara na tsoron ki tana kwance cikin bargo tana baccinta na tofan gira dan yau sai yammaci zata shiga makaranta kiran wayar Inna yashigo tad'aga da fara'a"Innarmu Sudaida takirata tana yar dariya"na'am yar gidan Inna,suka gaisa Inna tace"na ji autana shiru ni da Alhaji har mun gaji min kira layinshi sau shurin masak'i,da tana shiga baya d'agawa amma daga baya kuma ta daina shiga kwata-kwata. Dasauri cikin d'an bud'e idanu dan mamaki tace"shi Yaya D'ansarai d'in Inna?Eh shi d'in,ko baya jin dad'i ne kuke 6oyewa?Fargaba takamata dan kwana biyun nan itama fa bata gane mishi wallahi"a ah Inna lafiyar shi k'alau,yanzu ma yana cikin makaranta bari ya shigo inji abinda yafaru.Toh ALLAH yadawo dashi lafiya,ALLAH ya jishshemu alheri sukayi sallama Sudaida tana amsa addu'ar Inna da amin,amin Inna. Tafito D'akin-shak'atawa kawai taganshi kwance a doguwar kujera.Yaya Julaibib takira sunan shi. A hankali yabud'e idanun shi yana kallanta"har ka dawo ne amma baka nemi ni ba? Ni banji shigowar kaba.Yauwa sai tajuya ta d'auko wayarta"munyi waya da Inna d'azu barin kirata,yafizge wayar ta bishi da kallo yakasheta gaba d'aya sannan yatura a aljihun gefen rigarshi ta dama"rabu da ita Sudaida.Tazauna a k'asa gefen k'afafunshi tana bud'e idanu da mad'aukakin mamakin furucinshi"Innarce za a rabu da ita? Bai bata amsa ba yamaida idanun shi yarufe. Tasake bin shi da kallo cikin tsoro da shakka"to ko dai Yayi Julaibib ya fara k'arama sama hazo ne?data isheshi da tambaya sai kawai yamik'e yashige d'akin baccin su har yanasa mukulli,bai fito ba sai da za shi masallaci sallar azahar.Tamik'e ta tare k'ofar.Yad'an yamutsa fuska "ke bani hanya yanzu za tada sallah.Tagyad'a kai"ba in da za ka har sai ka fad'amin abinda yake damunka da har za kace a rabu da Inna.. "Adai-daita sahu a had'a kafad'a... Suka fara jiyowa daga masallaci yad'an kalleta cikin natsuwa"barin dawo daga sallah sai muyi maganar ko? Daga masallaci makaranta yawuce bai koma gidan ba,tagaji da jiranshi,itama tatashi tabishi,yana jin an kwankwasa k'ofar ya amsa daga ciki"na'am bismillah shigo,bai zaci itace ba.Takulle k'ofar tazare mukullin"Yaya D'ansarai ni fa ka sani a rud'ani wallahi, wai me yake damunka ne Inna za tayi magana dakai kace wai a rabu da ita sannan ka k'wace waya ta ka kashe,ta kama ka kashe me yafarune?Ni ma kwana biyun nan kwata-kwata bana gane maka.Yamaida kanshi jikin kujerar"to Inna me za tamin?Inna bata da maganin damuwata fa. Da rawar murya tafara nuna shi da yatsa"Kai Yaya D'ansarai Innarce..ba..ta da maganin... damuwarka?To duk fad'in duniyar nan ma kana da kamar tane?Takalleshi cikin takaici"to wa yake da maganin damuwarka?! Yajanye kanshi daga jikin kujerar yad'ora duka hannayenshi a saman tebur d'in sannan yakalleta cikin natsuwa"Zaujatiii...ke ce maganin damuwata,ina k'aunar ki, ina jin takaicin ace wai ni Julaibib yanuna kanshi da yatsanshi wai ni zan rabu dake dan kawai ba kya haihuwa, ni ina son ki a kowani irin hali da yanayi na rayuwa,Sudaida ko baki haifa min Ya'ya ba ba na nadamar aurenki. Ni yanzu abinda yake damuna yahanani rawar gaban hantsi shine na kasa samo mana mafita ta yadda zamu rabu salin-alin ba tare da Inna ko Kawu ran wani daga cikin su ya sosuba, kema kuma na san kin k'osa amma kina min biyayyane kawai saboda na rok'i alfarma kar kice kome...Dammm... Zuciyarya tabuga...tanajin wani irin yanayi mara dad'i yana bin ilahirin gangar jiki da zuciyarta,gaskiya idan tarabu da Yaya Julaibib...kai anya? Sai tabar wannan ayyane-ayyanen na zuci. Yawani marairaice"ALLAH yamiki albarka Zaujatiii...yarik'ota da wani salo"ko ke zan d'aurama wannan aikin na lalubo mana mafita danni dai har yanzu na ka sa, amma ko bama tare Zaujatiii...ki rik'e wannan a zuciyarki "ke ce mace ta farko dana fara k'auna,k'auna irin wannan ta aure zan kuma cigaba da k'aunarki ko da bama taren.Jikinta yadad'a yin sanyi da jin kalmar nan ta rabuwa...ganin hakan da tayi sai yacigaba da zugata ta hanyar kambama halayenta na kwarai,da kuma mamakin da yakeyi wai ita da kanta take ikirarin saki bayan ta san hadisin Manzon ALLAH da yace duk macen data nemi mijinta yasake ta batare da wata hujja ta shari'aba toh k'amshin aljannah ma bazata shak'aba,kuma shi k'amshin aljannah ana fara shak'arshine tun daga tafiyar shekara d'ari biyar,haba Zaujatiii...da ilminki da wayonki da kome na ki,tayaya wasu dangin miji can za su rabamu,bayan basu suka had'amu ba,ni fa nake auren nan ba wani ne yakemin ba,ai nine zan miki gorin haihuwa kece kin d'anji haushi ko?Karki kuma d'aga hankalinki a kan duk maganar masu magana,sau nawa muna zuwa ganin likita akan rashin haihuwa ana kuma bamu tabbacin dukkanmu lafiyar mu k'alau lokacine kawai baiyi ba,ba da bakinki kikace ke kin daina shan wata k'waya dan neman haihuwa kin barma ALLAH ba?Me Yaya Asma'u za tayi ta6ata miki rai?Yau kika san halinta?Ai tun kafin mu zama ma'aurata kin sani dan ko gidanku taje sai tanuna wannan halin na ta,kin gani ganin idanunki ke ganauce kuma jiyau.. Rashin haihuwa ba k'ask'anci bane wallahi,Idan kika duba gidan Manzon ALLAH a duk matanshi ba wacce ya keso sama da Nana A'isha kuma har ta koma ga ALLAH bata haihu ba,bayan ita a kwai wash matayen na shi da basu haihu ba,to me garage darajarsu?Annabawan ALLAH nawane da basu haihuba? Ganin damar ALLAH me idan yaga dama yabaka Ya'ya maza zallah,ko yabaka mata zallah,ko yahad'a maka maza da mata,haka kuma ganin damarshice yabarka bakarare(Mara haihuwa) kinga da... Bai k'arasa furucin shiba ta k'ank'ameshi tana kuka,yayi lallausan murmushi dan hak'anshi ta tadda ruwa,yacigaba da rarrashinta"Zaujatiii...ni D'ansarai ni ne me auren nan kuma na ce mutu ka raba,ko kin haifa min Ya'ya ko baki haifa min Ya'ya ba,kuma na miki alk'awari zan yima tufkar hanci,ba me kuma samun ke a damuwa a dangina,su suje su rungumi mazajensu cikin annashuwa ni kuma su dagulama Zaujatiii...nah lissafi?Toh karki damu kinji ko?Tad'ago takalleshi"Ya'ya D'ansarai nagode maka da wannan tunatarwar ta ka"idan rai ya 6aci to bai kamata hankali ya gushe ba...kai mijin alheri ne;tasauke gwauran numfashi "Rayuwata idan babu kai a cikinta za a samu tasgaro me tarin yawa,tadad'a k'ank'ameshi tana shak'ar k'amshin deodorant da arabi'an perfume d'inshi,yad'ago fuskarta suka kalli juna yad'an dage kira yana mata wani kallan k'auna yana murmushi "mun zama k'arfe da mayen k'arfe ko? Tajijjaga kai"eh wallahi autan Inna,D'ansaran Baba,Zaujiii... Ustazun Sudaida yar Ibrahim,jikar Ibrahim Me-Lambu.Suka sumbanci juna yace kuma"mayyar rake abin ma yasamu shiga wai d'an wake a hotel har da injin d'in matse ruwan ko da ta zama tsohuwa ba hak'ora ko? Tad'an daki k'irjinshi,shi kuma yabata marin soyayya suna dariya.Tad'auki wayarta a saman tebur d'in ta kunna"toh kira Inna gaskiya dan ta damu da rashin jinka tunda har takirani.Yagirgiza kai "gwamma mutafi Zonkwa ayi kome idanu na ganin idanu"zan fad'a mata kece kika hanani.Tad'auki jakarshi taraya a kafad'a suka fito daga office d'in, suka jera suna tafiya zuwa inda ake ajiye motoci da mashinan malamai tana fad'a mishi"Inna baza ta ta6a yadda ni na hanaka kiran taba,tunda ni kullum sai mun gaisa ko ta kirani ko in kirata. Watannin Sudaida bakwai kenan da tafiyarta Gidan-Waya,duk wannan watannin zuwanta Zonkwa sau hud'u,yanzuma tanata mishi magiya yabarta taje tunda sun samu hutu amma ya hana,wai tayi zamanta a in da mijinta yake ai shine zai fi mata kwanciyar hankali,tagyad'a kai"ni ma na sani ai bawani dad'e wa zanyi ba mak'o d'aya dan ALLAH, amma ya hana,haka dole ta hak'ura,dangin Julaibib kuma sun barta tana rawar gaban hantsi bata san me yafaru ba,amma tabbasss...ta dad'a yadda da kalaman shi kamar yadda yace ba me sa mishi mata a cikin damuwa. Da safe tana kwance tak'i tashi tahad'a mishi shayin shi ko ruwan wanka,shi yamusu kome,yagama shiryawa sannan ya zauna a gefen gado"Sudaida yakira sunanta.Tad'ago tana kallanshi yana sanye da babbar riga yar ciki da wando na farin yadi yana karya hular zita"har yanzu baza ki tashi daga kwanciyar k'asan nan ba?Tasauke idanunta k'asa"ni dai nafi jin dad'in nan.Yagyad'a kai"sauri nake yi damunje asibiti.Tamik'e zaune dakyar"ba sai munje asibiti ba,naji sauk'i Yaya D'ansaarai.Yagirgiza kai"za dai kiji sauk'i,tun yaushe nakai miki ruwan wanka amma har yanzu baki tashi kinje kin yiba?Yamik'a mata hannayen shi"ta so muje in cud'a ki.Tayi yar dariya"bayan ka shirya?Ai zaka 6ata adon ka,yi tafiyarka yanzu zan yi.Yad'an motsa kafad'a"uh to menene a ciki,ba sai in canja wasu kayan ba? Tamik'e tana mishi rakiya,kad'an ta taka mishi ta dawo tayi kwanciyar ta dan dama bata so tayi wankan,idan tafad'a mishi to sai ya tilasta ta yin wankan ko ta so ko tak'i. Har yadawo tana kwance yayi tsaiii...yana kallanta yana bin d'akin da kallo,ba abinda tayi yakad'a kai cikin damuwa"wannan ba halin Zaujatiii...bane tabbasss bata da lafiya.Dakyar yatashe ta sai wani narkewa takeyi, amma tanayin wanka sai tajita garau...yana kallon tashar larabawa suna nuna yanayin al'adunsu yana cin gasashshiyar kaza me kayan lambu tashigo yabita da kallo tana sanye da material bak'i me yarfin filawoyi ruwan k'asa, d'an kunne,sarka da warawarenta na zinare sai d'aukar idanu sukeyi saboda kyallinsu,fuskarta shar da kwalliya, bakinta yana kyallin jambaki ja. Tazauna suna kallan juna "Zaujatiii...kinyi kyau dame kike son tukwuici?Tad'ora ha6arta a kafad'arshi tayi furucin da wani salon shagwa6a "agada(plantain) yajuyo yakalleta"kin cinye wannan agadan dana siyo miki ne?Ta amsa kai tsaye"wallahi tun jiya.Yabud'e baki dan mamaki saboda ada shi yake matsa mata tasoya musu dan ba wani dad'ata da k'asa yayi ba,amma a yan kwanakin nan cin agada takeyi kamar ta samu abincin gado,d'an kullum, ranshi yadad'e me martaba tuwo miyar kuka abincin hausawa.Kai shifa bai yadda ba sai da yaje yaduba in da suke ajiyewa yaga ba kome sannan yadawo yana cemata lallai kinyi k'ok'ari,yad'auki waya yana kiran wani mak'ocin shi da yau yatafi Jos kuma anjima zai dawo dan ALLAH yasiyo mishi agada. Yasake kallanta bayan yagama wayar amma fa na d'auka bakya jin dad'i danaga tun safe kina ta bacci har shabiyun rana.Ai na fad'a maka lafiyata k'alau kawai ni dai nafiso in kwanta in yi baccine.Ya mata nuni da kazar.Tagirgaza kai dan ko sha'awar ci batayi,tad'auko lemun peach tana sha suna hira jefi-jefi suna kallansu har suka gama shirin,sannan yamik'e zai koma makaranta "adawo lafiya.Takashe kallan tad'auki wayarta ta kunna data zuwa duniyar yanar gizo... Da daddare kafin yadawo daga sallar Isha'i Sudaida tayi baccinta a inda ta idar da nata sallar. Yatasheta"Zaujatiii...ga agadan an kawo.Dakyar tad'an bud'e idanunta da yanayin bacci takalleshi sai ta mayar ta rufe,tayi wani juyi tana dad'a shemewa a dadduma"barshi sai da safe ni bacci nake ji,tacigaba da baccinta sai kuma tamik'e zuwa d'akin bacci. Yabita da kallo har tashige.Shi kad'ai yayi zaman D'akin-shak'atawa yaci abinci kad'an, yaje yahad'a shayin shi da baya gajiya dasha.Yagama yan rubuce-rubucen shi har zuwa sanda bacci yafara kawoma idanun shi ziyara,yashiga d'akin ta kashe wuta,yakunna fitilar wayar shi yana hasketa" tana kwance a k'asa kuma yau tsabar jin bacci ko kayan bacci bata tsaya sawaba,yad'anyi murmushi yana cigaba da kallanta numfashi na shiga da fita cikin kwanciyar hankali,sai tamishi wani irin kyau na musamman, ya dad'a gyara mata rufa dan yasan ko ya maida ita gadon to sai ta sauko wai ita k'asa yafi mata dad'i,yakashe fitilar yakwanta yana musu azkar d'in bacci. Abinda yaketa maimaituwa kenan,kullum bata da kuzuri,bata san yin kome sai kwanciya,yau dai abin ya isheshi,dan haka yana dawowa daga Kaduna jakarshi kawai ajiye,yatasata agaba sai tashirya sun tafi asibiti dan daren jiya kusan kwana sukayi tana mishi wash...wash...mararta tana mata ciwo amma abin mamaki baturiya da suna manga gari na wayewa sai tamik'e wai ta warke,yanzu kuma yadawo ya ganta lamooo bata da wani kuzari sai bacci-dai bacci dai bata gajiya...Yabita d'akin tanata nuk'u-nuk'unta"Zaujatiii...hijab d'in ne baki gane ba kome?Tabud'e wardrobe tad'auko. A k'ofar gida sukayi kaci6is da motar Musaddiq tsayuwar shi kenan suka fito shi da Hajiya. Sudaida tarungume ta tana murna"oyoyo Hajiyarmu sannu da zuwa,suka koma ciki.Julaibib yayi murmushi"yau farar ranace agaremu me kyakkyawar suna.Hajiya ta ajiye kofin lemun"to ance ka gaida me gaisheka,kunzo nan kun share waje kun manta da kowa kuna sha'anin gabanku.Julaibib yasa hannu yana shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi "munata fama dai da ayyuka da d'alibai Hajiya. Ganin Hajiya yasa Sudaida ta nemi kasalar data rufeta tarasa,tashige D'akin-girki tana k'ok'arin shirya musu abincin data cema Julaibib ita yau baza tayi wani girki ba,yad'an motsa kafad'a" duk d'aya 6arin manshanu a miya, dan shima ba kullum yake cin abinci me nauyi da daddare ba.Musaddiq dai bai tsaya cin wani abinci ba Sudaida tafito suka gaisa yamusu sallama suka fita da Julaibib.Har suka gama cin abinci bai dawo ba, takwanta suna hirarsu me dad'i da Hajiya,bacci yafara d'aukanta sama-sama, sannan taji sallamarshi yashigo musu da gashashshiyar kaza,bata tsaya ciba tamusu sai da safe taje tayi kwanciyar ta tana jinsu sunata hirarsu, ita kuma baccinta rabi-da rabi tayishi saboda ciwon maran d'aya matsa mata daren jiya to yauma daren yayi shine yace bari ya motsa. Yadawo daga masallaci sallar asubahi yaganta tsugune a bakin famfo tana ta yunk'urin amai amma yak'i zuwa,Hajiya tana mata sannu,tarik'ota suka koma D'akin-shak'atawa takwanta a doguwar kujera jikinta a mace yake murusss"sannu ALLAH yasauwak'e"Hajiya ta zauna tana mata fifita ganin yadda tajik'e sharkaf da zufa kamar wacce tafita motsa jiki da sanyin safiya. Yazuba mata idanu zuciyarshi ba dad'i saboda yadda take dad'a rintse idanunta tana mirgina kai gefen hagu zuwa dama tana yarfe hannuwa,tana ta6a mararta da take mata wata irin d'aurewa tamauuu...ita kad'ai tasan azabar da take ji, wucewar wasu dak'ik'u cikin ta ya dad'a yamutsewa ciwon yana k'aruwa,mararta kamar zata 6alle,Hajiya itama ta shiga cikin damuwa"Sudaida wai meke damunkine?wai!Wash...wayyohALLAHnan...uhhh...washhh.. tasake yarfe hannun hagu na dama na saman mararta,da kyar tayi furucin"Wayyoh! Hajiya marata ce take ciwo. Julaibib yajuya dan tsayuwar ba amfani, motarshi kuma ba ishashshen mai"Hajiya barin samu mai yanzu mutafi asibiti.Tagyad'a kai"to hanzarta dan naga abun yana dad'a k'amari. Wayyo ALLAH! tafad'a a galabaice tayi nishin wahala...uhhh...Hajiya marata!"sannu Sudaida yanzun nan Julaibibi zai zo mutafi asibiti.Ta cije le6enta na kasa ta yunk'ura zata mik'e zaune amma ta kasa;Hajiya ta taimaka mata,tad'ora kanta a kafad'ar Hajiya idanunta na rufewa da bud'ewa cikin azabar ciwo,cikinta na cigaba da hautsinewa ciwo na k'aruwa,da marar tayi wata irin murd'ewa sai ta k'ank'ame Hajiya tana Istirja'i da salati, tasake k'ank'ame Hajiya iya k'arfinta tayi wani nishi sai kawai taji wani ruwa me d'umi ya 6alle mata da kyar taduba sai taga jinine,cikin yan dak'ik'u zanin jikinta ya jik'e sharkaf,zata tashi jiri luuu...yayi awon gaba da ita ta zube a jikin Hajiya cikin d'aukewar numfashi. Hajiya ta rikice tashiga jijjigata amma ko motsi ga jini na cigaba da zuba, saboda rikicewa sai tarasa me ma za ta matane?Tana cikin wannan halin Julaibib ya turo k'ofar yashigo.Cikin tsinkewar zuciya yake kallansu saboda ganin Sudaida da yayi kwance cikin jini male-male,k'wak'walwarshi bangaren tunani da adana bayanai yafara tariyo mishi shud'add'en abinda yafaru a shekarun baya lokacin da Bilkisu take kwance sam6al cikin jini fuj'atan.Dammm...yaji ruguzowar wani abu a k'ahon zuciyar shi"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...baiyi wata-wata ba yasa hannayenshi ya cicci6eta cikin tashin hankali yayi mota da ita,Hajiya tabiyo shi. Sun 6ata lokaci suna dubata sannan wata ma'aikaciyar jinya takirasu"kaine mijinta? Yajijjaga kai kawai.Tad'an kalli Hajiya sannan tamaida kallanta gareshi"yarinyar nan gaskiya tana mugun jin jiki kuma matsalar ta fi k'arfin mu,tunda sai an mata aiki kuma likita baya nan,to sai ku gaggauta kaita wani asibitin,irin wannnan zubar jinin idan yazo da k'arar kwana sai a rasa mutum."ALLAH yabata lafiya yasa kaffarace. Tajuya tayi tafiyarta.Hajiya ta kalli Sudaida bata san wanda yake kanta ba.Julaibibi mu san abinyi mana.Idanun shi sun kad'a jawur,yayi wani huci cikin tashin hankali sannan yaba motar wuta,a guje yafito daga harabar asibitin suka fad'a kwalta zuwa wani asibitin. Dasauri suka d'auketa zuwa d'akin agaji da taimakon gaggawa suma sun 6ata lokaci sannan likita tafito suka bi bayan ta zuwa office suna tambayarta me yafaru?Yajikin na ta?Ku kwantar da hankalinku.Tadanyi rubuce-rubucenta a katin data shigo dashi tagama taturashi a aljihun Labcoat d'in ta, sannan tad'ago cikin natsuwa ta kalli Julaibib"ka gane ko,matsalar matarka sai an mata aikin gaggawa, idan ba haka ba za ta iya rasa ranta,saboda ciki tasamu amma ya zauna a bayan mahaifa. Shi da Hajiya suka kalli juna sannan suka kalleta cikin murna da mad'aukakin mamaki.Yayi yar dariya"ciki likita?Tajijjiga kai"eh ciki.Suka shiga tasbihi ga buwayi gagara koya dan furucin likita ya zo musu a bazata."Julaibib yayi sujudush-shukri.Likitar ta cigaba to amma an samu matsala dan cikin har ya fashe, abinda yasa take wannan serious bleeding d'in kenan (rupture ectopic pregnancy)kuma wannan aikin dole sai Gynea Doctor(likitar dake mu'amala da abinda yashafi lalurorin mata)kana...Julaibib yatari numfashinta"to ke fa? Ni nan da dak'ik'u talatin zan shiga wani aikinne(operation) amma karku damu dan nayi waya da Doctor Kagarko itama kwararriyace yanzu haka tana kan hanya.Tabud'e dirowa tad'auki wani fallen littafi tayi rubuta sannan ta fad'a mishi adadin kud'in da zai biya,tamik'a mishi wannnan fallen littafin kaje kabiya kud'in sannnan kaje a d'auki sample d'in jininka idan yazo d'aya danata basai an siyaba. Yamik'e yaje yabiya kud'in,kuma yasa hannu sannnan yawuce aka d'auki jinin shi ana dubawa akaga yazo d'aya sai aka wuce dashi laboratory dan tantance sahihancinshi kafin ak'ara mata. Doctor Khadija Aminu Kagarko tak'araso, matar me hankali da natsuwa ga tarin ilmi da ya ratsata,ta gaishe da Hajiya cikin girmamawa"ki mana addu'a Ubangiji yasa a dace.Hajiya tagyad'a kai"ALLAH ya amsa yar nan.Hajiya da Julaibib sunata kai-kawo bakunansu d'auke da addu'o'i tunda aka shiga da ita d'akin theatre,har akayi aikin aka gama aka fito da ita agadon marasa lafiya ana turata a hankali dan zuwa d'akin hutu,idanunta a rufe bata san in da takeba,ta d'ashe saboda rashin ishashshen jini,yasauke gwauran numfashi"Alhamdulillahi an tsallake tsirad'i d'aya na yin aikin cikin nasara,saura na farfad'owarta,ALLAH yasa tafarfad'o cikin hayyaci da lafiya. A sanda rana tatafi zata fad'i magriba na shirin kunno kai Sudaida tad'an motsa da alama maganin da suka ba ta na anaesthetic ya fara sakinta...wucewar wasu dak'ik'u kuma tayi motsi da fatar idanunta sai kuma tad'an bud'e idanun tana bin Julaibib da Hajiya da suke rige-rigen yi mata sannu,a hankali bakinta yamotsa tana salati, sai kuma ta yunk'ura zata tashi,yarik'eta da sauri "Zaujatiii... kiyi hak'uri kinga aiki aka miki kar a samu matsala,takoma takwanta ta damk'i hannunshi tamau tafara kuka mara sauti saboda jikinta ba k'wari"ni dai ku yafemin mutuwa zanyi furucin a hankali yake fita muryar kamar bana taba, sai kuma tafara sambatu "Dan ban haihuba sai a dinga min cin kashi? Ni zan ba kaina haihuwa? Shima autan Inna ai ina jin haushin shi dan bai kawo min agada ba,har madidi nace yasiyo min amma yak'i...Hajiya cikina ciwo yakeyi marata... wai...wayyoh Zaujiii...ni fa ba na san wannnan kallan na ka dan haushi yake bani...kai fa ran...da sauri yasa tafin hannun damarshi yatoshe mata baki dan kartayi kato6arar da zai sa shi jin kunyar Hajiya tunda ba a hayyacinta take ba kome ya d'arsu a zuciyarta fad'arshi za tayi.Ganin tak'i sakin hannun Julaibib dan yakira likita yasa Hajiya ta tafi kiranta"to fa tashin hankali gobarar gemu... Magani a shaka badan yunwa ba. Kome tsawon giginya daga k'wallo tafara. 2 Rajab 1441 25 February 2020 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in. ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na ashirin da uku. Kwanakin su uku Doctor Khadija Aminu kagarko tabasu sallama dan Alhamdulillahi ta samu sauk'i, wata ma'aikaciyar jinya tana tsokanar Julaibib saboda yadda yadamu da Sudaida,lokacin ba da magani (medication)nayi idan basu zo ba da kanshi za shi yakira su"ALLAH dai yasa d'an daza'a haifa yamaka kara yayi kama da kai dan ba k'aramar hidima kayi ba.Yayi murmushi kawai yana shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi.Mutan Zonkwa ma d'ai-d'ai kune wad'anda basu zo dubiya ba a cikin yan'uwa da abokan arzik'i. Doctor Kagarko takalli Sudaida cikin kulawa"ki kula da kyau kinga aikine a jikinki,banda aiki bare d'aukar abu me nauyi okey?Sudaida tagyad'a.Tarakasu har wajen mota, Sudaida tashiga tazauna sannan ta rufe musu motar, tad'an sunkuyo ta taga"Hajiya ALLAH yakiyaye hanya. Madam adinga kula da dressing d'in wajen yadda yakamata, kidawo akan lokaci kar fa kiyi sakaci.Tad'aga hannu tana musu adabo,suma godiya sosai suke mata.Doctor Khadija Aminu Kagarko ta san ya kamata. Julaibib da Hajiya su suka cigaba da kula da ita da ayyukan gida.Watannin Hajiya hud'u tafara musu zancen tafiya.Sudaida tawani marairaice"Lillahi warasulihi Hajiya yanzu sai ki tafi kibarni?Tagalla mata harara"to da ni zan tayaki zaman auren?Taware yatsunta hud'u watannina haka a gidan nan,ai ko na yi iya abinda zan iya.Julaibib yagama abinci yazubo musu a faranti"sannu da aiki Zaujiii...Yayi murmushi kawai,yashige bayi yahad'a mata ruwan wanka "Sudaida ga ruwan can kije kiyi wanka.Hajiya takama fad'a"kai Julaibibi bana ce kadaina kai mata ruwan wanka ba?Ruwan kawai da za ta bud'e famfo ta tara sai an mata kai haba,tanuna shi da yatsa "kazama jarumi dan a haka nasanka.Sudaida tamik'e kaji matar nan da wata magana to ko wankan ma idan takama ba shi zai min ba?Tamata dakuwa"ungo nan,zancen banza kawai dan an miki aiki shikenan kuma ke bazaki dinga motsa jikin kiba? Sudaida tawuce batayi magana. Ita kuma Hajiya tana dad'a jaddada mishi gobe Insha-ALLAH zan koma in da nafi wayau Zonkwa.Yagyad'a kai sannan cikin girmamawa yace"ALLAH ya nuna mana goben da ran mu da lafiya...mungode kwarai Hajiya ALLAH yak'ara nisan kwana me amfani.To amin kaga ai kai ka san yakamata,ita wancan matar taka ai bata gode min, niko ba in da zan fara azumin watan ramadana sai a d'akina. Kiyi hak'uri Hajiya bari tafito ai dole kuwa tagode miki. Suka cigaba da hirar su har Sudaida tafito,yad'ago yana kallan surarta a cikin hasken farin watan daya haskesu"kinyi kyau Zaujatiii...Hajiya tagalla musu harara musamman Julaibib daya kasa daina kallanta,takad'a kai"ba shakka ai kinji sauk'i tunda kika iya zama kiyi wannan kwalliyar abin ma bai tsaya anan ba kikabi jiki kika shafeshi da wannnan shu'umin humran me k'amshin fita a hayyaci,to ni kuwa zaman me zan kumayi? Sudaida tayi lallausan murmushi"haba Hajiyarmu ban fa sanki da halin sa'idawa ba,yanzu har wani kwalliya nayi?Ko unguwa ai zan iya fita a haka.Eh to in dai kai kikaci(hauka)ai bazan musa ba.Suka kalli juna ita da Julaibib tamishi wani kallo ta kashe mishi ido...Yakai hannu yana shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi a hankali ya motsa la66anshi,Sudaida ta matsa kusa dashi"ni dai Yaya D'ansarai ban gane me kake fad'a da la66a ba gaskiya.Hajiya tamik'e"abin nayi ne to ALLAH ya tashemu lafiya.Sudaida tace kai Hajiyarmu yau da wuri haka zaki kwanta?Eh dan gobe sammako zanyi Julaibibi sai da safe.To Hajiya ALLAH ya tashemu lafiya. Washe gari tun daga sallar asubahi bai shigo gidan ba sai da hantsi yadubi ludayi da kaya nk'i-nik'i,duk suka bishi da kallo har yagama shigo dasu sannnan yazauna suka gaisa.Hajiya tace"ai na zaci guduwa kayi saboda kar in tafi dama nace anjima kad'an tafiya ta zan yi ko kadawo ko baka dawo ba tunda duk wayoyinka a guda kabarsu. Mantawa dasu nayi sai da nayi nisa da tafiya sannan na tuna.Jos natafi na miki siyayyan tsaraba dana azumi.Hajiya tabi manyan ledojin da kallo tana jinjina k'ok'arinshi tare dasa mishi albarka"Ubangiji yayi albarka, yabaku masu muku madallah nagode nagode Julaibibi. Yayi murmushi"ai ba kome Hajiya, yad'an kalleta cikin natsuwa "na so kwarai da dakaina zan kaiki to amma hakan bazai yiwuba saboda yanayin aiki,yanzu ma Kafanchan zan tafi amma na ma wani direba magana k'arfe d'aya na rana zai zo kutafi,yasake bata wasu kud'ade sannnan yamik'e dan shirin tafiya Kafanchan. Sabo turken wawa...kowa yayi fushi da bak'o ya ji kunya,da Hajiya tatafi sai taji gidan ya mata girma gashi shima Julaibib ba ya nan tagaji da nazarin da takeyi a cikin na'ura me k'wak'walwa ta rufe, tasa bayan tafin hannunta na hagu tana Isti'aza tare da rufe bakinta saboda hamman da tayi.Julaibib yashigo da sallama, yazauna a kujera a gajiye lik'is yacire riga yabar farar singlet. Sannu da zuwa Yaya D'ansarai.Ya aikin? Yafurzar da iska tabaki ta hanci"aiki ba dad'i kuma ba dama a bari.Wayyo! neman halali da wuya,kowa ga ganshi a inuwa tabbasss ya sha rana sannu Zaujiii...nah,tad'an shafa kwantacciyar gargasarshi"ubangiji yak'aro lafiya ta gangar jiki da natsuwar zuciya,tad'ora ha6arta a kafad'arshi,tagewaye hannayenta tana mishi tausa. Yasauke numfashi yana jin gajiyar data lullu6eshi tana tafiya a hankali a hankali"Shukran jazilan Zaujatiii...Yad'an bud'e idanun shi daya rufe yakalleta "kin cinye agadan?A ah ai yanzu kad'an nake ci dan yafara fita kaina.Yayi murmushi. Kafin tagama abinci takawo mishi bawan ALLAH har yafara bacci sai da ta tashe shi tana mishi dariya"yau baza ayi nazarin karatu anjima ba kenan?Yayi mik'a yana salati"gaskiya yau ba nazarin karatun dazanyi,kin san tun a office nake gyangyad'i saboda baccin da kika hanani daren jiya.Takama ha6a tana yar dariya"Kai Yaya D'ansarai nice na hanaka baccin?Yagyad'a kai.Tayi yar dariya"au to shikenan ta kwana gidan sauk'i daga yau bazan kuma hanaka bacci ba shikenan ko?Yamata wannan kallan da bata so yayi bismillah yafara cin abincin data zuba mishi.Takauda kai tana k'unk'uni dan wallahi haushi kallan yake bata. Ramadan wata me albarka,wata me alfarma.Tana kwance ta kifa fuskarta a cikin matashin,ya san ba bacci take yiba tsabar jin jikine kawai,tunda ko da da take ita kad'ai azumi wahala yake bata bare yanzu ga ciki,bataji shigowar shiba sai da yazauna a gefen gadon yadafa bayanta "Zaujatiii... Tamik'e zaune dakyar tana kallan shi bata da kuzari kona sisin kwabo. yakalli cikinta yayi girma yanayinta ya canja gaba d'aya,tausayinta da k'aunarta suka mamaye ilahirin gangar jiki da zuciyarshi "Zaujatiii... Ki hak'ura da azumin nan mana,kinga wahala kike sha,barin had'o miki shayi kawai.Tawani marairaice "haba Yaya D'ansarai kalli agogo kagani k'arfe uku saura kwata na rana sai in karya azumi? Uh to menene ai kina da lalurane.A ah kayi hak'uri ai azumin ma ya kusa k'arewa tunda nayi ashirin to ai ko tara ko goman dasuka rage bazasu gagara ba Insha-ALLAH za k'arasa dani,nima ina kwad'ayin dacewa da daren"lailatul qadri".Yagyad'a kai"Toh ALLAH yasa mudace da wannan dare daya bambanta da darare dubu a daraja,ALLAH yabaki nak'uda kafiifan(me sauki) Tayi murmushi"amin Yaya Julaibib. Yarik'o hannunta tamik'e suka fito waje suna d'an tattaki har zuwa bayan gidan in da sukayi yan shuke-shuken su kamar su alaiyahu,ganyan ogu, timatir,attarugu,zogale,d'ad'd'oya(scent leave)da sauran su, dakyar ta zauna a d'an k'aramin dakalin wajen tasa hannu tana tsinkar lemar kwad'i/naman k'asa(mushroom)ya tsuguna yana tayata tare da tambayar ta"yau kuma me za kiyi dashi? Tun safe natashi da sha'awar shan romon shi(mushroom sauce) yad'an kalleta"ni fa yau a tsarin abincin mu ba shinkafa.Toh Yaya Julaibib,ni ma ba da wani abu zan had'a ba haka kawai zanyi romonshi in sha. Suka gama tsinka sannan suka wuce D'akin-girki yakar6a yawanke ya yayyanka mata, yad'uko kaskon suya yazuba magyad'a kad'an yad'ora a wuta sannan yakalleta"to na miki me wuyan zo kibashi tsoro. Tad'an kalleshi a marairaice nagode,to amma Yaya D'ansarai...sai kuma tayi shiru"uhun menene kuma? Tanuna mishi abinda take so yayi.Yad'auki wuk'a da albasar yana mita"ni fa a duk aikin gida ba abinda yake bani haushi irin yankan albasa,tagyad'a amma kuma kafi kowa san albasa me yawa a girki,jiyama ai miyar albasar kasani nayi dayake ba kai kake yankawa bako? Eh mana...sukayi dariya yana fara yankawa idanun shi suka fara ruwa, yarintse su"Zaujiii...Karfa kayanke"eh ai kin san zan iya yankewa amma kika sani,da sauri yayi yagama yana fad'in"kai gaskiyar bahaushe da yace albasa batai halin ruwa ba, yawanke hannayen shi da omo,yanad'e hannu riga toh aikin dai aikine an ba kuturu tallan jakai"yad'auko abin markad'e(blender)ina karas d'in dana gyara d'azu?Ai na had'a maka lemun,yana cikin fridge.Yawarware hannun rigar"yauwa Zaujatiii...Kin kyauta nagode ALLAH yamiki albarka. Yanzu barinje in yi alwala lokacin tafsir ya kusa,kuma yau d'in nan Insha-ALLAH nake tunanin zamu rufe sai ALLAH ya kaimu ramadan me zuwa ga masu tsawon rai.Toh Yaya Julaibib adawo lafiya, kuma dan ALLAH ana idar da sallar magriba ka dawo gida da wuri kasha ruwa,tazuba mishi dabinon ajwa a aljihu daya manta bai d'iba ba kaji Yaya D'ansarai?Yad'an dafa kafad'arta"Insha-ALLAH nagode Sudaida.Tabi bayan shi da kallo cikin yaba k'ok'arinshi da wata irin k'aunarshi da take dad'a narkewa a sararin cikin zuciyarta. Safiyar sallah garin yayi lullumi a sanda hantsi yadubi ludayi ta yi k'ok'ari tagyara gidan da taimakon shi,ko ina yana k'amshin turaren d'aki, sassanyar iska tana kad'a fararen lubayen da ratsin ruwan hoda saboda rashin nauyin su.Tana sanye da voil-lace ruwan sararin samaniya(sky blue)doguwar riga dan d'aura zani wahala yake mata yanzu,d'an kunne,sark'a da warawaran hannayenta da zobe na zinare,suna ta d'aukar idanu saboda kyallinsu,ga jan lallanta me yarfin bak'i da tayi k'afafu da hannaye sun k'ara haskata,bata d'aura dankwalin kayan ba sai tayafa k'aramin mayafi ruwan sararin samaniya me shara-shara,gashin kanta yasha gyara daren jiya a wajen gyaran gashi da Julaibib yarakata. Takoma D'akin-shak'atawa tazauna tana kallan shirye-shiryen wasannin sallah a tashoshi mabambanta aranta kuma tana mita"Yaya D'ansarai ya hanata tafiya gida taje tayi sallah a cikin Iyaye, yan'uwa da abokan arziki,sannan tun d'azu aka sakko daga masallacin Idi ya aiko a kar6a musu tuwon sallah shi da abokanshi kusan awa d'aya kenan,taja tsaki ai ko danko sukeci yaci ace zuwa yamzu sun gama ya shigo,a hankali tazame takwanta a doguwar kujera tacigaba da kallan amma ranta sam ba dad'i. Taji ana sallama tare da k'wank'wasa k'ofa, taja malalacin tsaki a yadda taji dad'in kwanciyar nan data sani tabar k'ofar a bud'e koma waye tad'aga murya tace a shigo,tamik'e dakyar taje tabud'e, bakinta yak'i rufuwa saboda mamaki sai bin yaran takeyi da idanu,suma sunata tsallen murna sunzo gidan Inna Sudaida,za suci dad'i,yarik'o hannun wasu daga cikin yaran"kai kuzo kawai in maidaku wajen Iyayenku dama daga masallacin Idi natarkato miki su,ban tsaya tambayar kowa ba,yad'aure fuska ganin sunk'i motsawa"mitafi nace ko? Wasu suka mak'ale kafad'a, wasu har idanun su yaciko da kwallah. Tarik'o hannushi"haba Yaya Aminu talek'o ta koma kenan,yagyad'a kai" eh mana tunda baza ki bamu hanya mushiga ba basai mu koma in da mukafi wayau ba?Oh dan ALLAH kayi hak'uri murna da mamakin ganinku ne yamantar dani abinda zan yi tun farko,tamatsa yaran sunata rige-rigen shiga,suka zazzauna suna tsallan murna wasu suna fad'in su sun dawo nan gidan Inna baza su wani koma Zonkwa ba. Yaya Aminu naji dad'i wallahi,tazauna suna gaisawa tare yima juna barka da sallah ALLAH yamaimaita mana na bad'in bad'in bad'ad'a...tana tambayarshi mutan gida.Kowa lafiya k'alau Sudaida, mutuniyarki Nasmat ta bani sak'o yana mota,yakalli yaran sun baje suna cin abinci, hakanan zuciyata taraya min dama kaje wajen Sudaida, nace musu nan zanzo shine suka dinga rok'ona ALLAH annabi wai suma za suzo.Tayi yar dariya"ai kuwa nagode daka zo min dasu ALLAH yabar zumunci,dama kad'aici ya dameni.Yakalleta cikin tausayi dan cikinta ya girma"sai hak'uri kanwata,kafin mu shigo na ga Julaibib d'in mutane sun mishi yawa,na san haka kawai bazai kyaleki ke d'aya ba. To Yaya Aminu kaci abincin mana. Yad'auki wayarshi yana duba sak'on karta kwana da aka turo mishi"ke ni dama kunu kika kawo min. Takalleshi wani iri "kai dan ALLAH wani irin kunu yau take sallah fa.Yamaida wayar aljihu"uhun ba a shan kunu ranar sallah ne kome? Yayi bismilah loma biyar yayi a tuwon sannan yad'auki cinyar kaza yad'an gutsira yamayar ya ajiye dan baya wani jin yunwa,ai kin san halina ni nama ba d'ad'ani da k'asa yayi ba, wannan sai su autan Inna kura kyaci da gashi,tad'an yamutsa fuska"to ai bashi kad'ai bane har da Yaya Musaddiq, yakama ha6a wuuu...au haka ne?Babbar magana ance da mak'asau bawa,barin kama bakina.Tayi yar dariya. Julaibib yashigo aka cigaba da hirar dashi, ranar wunin farin ciki sukayi,sai bayan sallar la'asar Aminu ya kwashi yaran dayazo dasu cikin mota,Sudaida takawo musu cin-cin,nama da goron sallarsu,kowa ta bashi a hannunshi,sunata murna da rige-rigen fad'in" Inna Sudaida nagode,ALLAH amfana. Takalli Aminu"na rasa me zan baka rabin raina. Julaibib yadafa kafad'arta"juye mishi ragowar kunun safen nan yatafi yayi farau-farau dashi.Tagalla mishi harara,yad'an d'age gira yana mata wannan rikitaccen kallan na shi"eyehhh...ni kike harara?Kinga Sudaida Aminu yakirata,tabishi da kallo daina hararshi haka,yad'auko sak'on Nasmat data rufeshi da wrapping sheet me zanen zuciya da rafar kud'i yan naira ashirin guda d'aya"nawa goron sallar.Julaibib yasa hannu biyu yakar6a"toh Yaya Aminu mungode ALLAH yak'ara bud'i,ALLAH yabarka da Siddiqa tazama tauraruwarka har gaban abada.Yadda yayi furucin yasa sukayi dariya. Sudaida tarufe musu motar itama tana godiya,Julaibib yasunkuyo"toh kagaishe mana da Hajiyarmu kace mata munanan zuwa mata yawon sallah ta ajiyemin dambun nama,tasa amin kilishi me tsomen aya,yanzu ma zan kirata in fad'a mata. Yad'aura belt yana dariya"toh kura duk kai kad'ai? Yaran sunata tsalle daga cikin motar suna d'aga hannu sunama su Julaibib adabo,a hankali yaja motar suka bi danjojin motar da kallo har tayi nisa tasha kwana ta6acema ganinsu. K'arfe hud'u na yammacin asabar motar Julaibib ta tsaya a k'ofar gidan Hajiya.A D'akin-shak'atawa suka sameta tana waya,tagama tasauke wayar a kunnanta tana murmushi"lale marhabun,yau ina da manyan baki. Takalli Sudaida cikin tausayi dan ta kasa zama a kujera, zama tayi ak'asa tana matsa k'afafunta da suka fara kumbura alamar ciki ya tsufa wash...tafad'a tana yamutsa fuska"sannu Sudaida ALLAH yaraba lafiya. Kai Julaibibi Sudaida tadawo kenan sai ta haihu ko?A ah jibi zamu koma ni bazan tafi in bartaba. Hajiya tagyad'a kai"madallah,to idan haihuwar tazo sai kuyi yaya?Hala ka ta6a kar6an haihuwa ne? Yashafa kwantaccen bak'in gashin kanshi"wannan karan dai zanyi,Hajiya bar wannan maganar kinji,ai haihuwar ma da saura,yad'an kalleta kuma ni gaskiyar magana"I can't do without Zaujatiii... besides me. Bashakka Julaibibi zama da mad'aukin kanwa...ni dai na sanka me kawaici amma wannan matar taka me suffar takand'a ta fara koya maka rashin ta'ido ko?To kaji dakyau baza tabikaba,to me zata maka da wannan tsohon cikin?Sudaida tayi murmushi tana zancen zuci"lallaima Hajiya ni ce na koya ma Julaibib d'in rashin ta'ido?Yaya D'ansarai wallahi gwani na gwanaye ne bar ganinshi haka Ustazu-Ustazu baya san magana hummm... takyalkyale da dariya tuno abinda yagama fad'a mata daren jiya data keta wani sha mishi k'amshi dan ta karance tsabbb...da abinda yake so. Tad'an turo baki gaba"Hajiya ai gwamma in zauna a suffar takand'a da dai in zama tashi da nishi...bakiji kirarin muba?Bena bakya tsufa sai dai kiyi girgiza ki sake sabon gashi,kuma waya jazamin wannnan k'aramin jikin idan ba ke ba?Takalli Julaibib"Yaya D'ansarai...Kasha kuruminka k'afata k'afarka ai tare ta gammu. Yauwa Zaujatiii...tabashi hannu suka tafa, tad'an yafito shi zo kaji,yamatsa kusa da ita tasaita bakinta a kunnanshi tana rad'a mishi wata magana, suka kalli juna,yad'age gira yana nunata da yatsa cikin yar dariya"da gaske Zaujatiii...? Ta amsa kai tsaye"na rantse maka da girman ALLAH.Hajiya takama ha6a ba shakka"wato ana nuna miki ma'aiki kina rintse idanu,da wannan tsohon cikin kike wannan iya shegen k'auri da kare? Tawatsa hannu"to ai shikenan jiki magayi baki kuma mafad'i.Yamik'e barinje shago wajen su Baba"ke sai na dawo zamu tafi gidan Kawu ko? Toh adawo lafiya. Yana fita Sudaida tamatsa kusa da Hajiya takalleta cikin natsuwa"Hajiya na rantse miki da girman ALLAH nima na fiso in zauna a nan sai bayan na haihu,toh kin san halin Yaya D'ansarai da banyi haka ba ni zai rufe da fad'a,kilama yace nina kira a waya na fad'a miki,saboda ni ma ina ta damunshi ya dawo dani gida,shi kuma yana cemin a ah acan zan haihu,dana fara nak'uda wai asibiti za mutafi, mutumin da a wasu lokutanma har na fara bacci bai shigoba. Kin san halin miskilancinshi idan suka motsa, maganar duniyar nan za ki mishi,sai dai yamiki kunnan uwar shegu,yasunkwui da kai bazai yi magana ba ko da me za kiyi,yamaida mutum kamar wanda yaci kai(hauka)to Hajiya me zuwa fada ga banza bare kuma Sarki na kira?Hajiya tajijjiga kai"eh lallai kinyi hikima da siyasar rayuwa a nan, dama idan kasan mutum to sai kaci maganin zama dashi, barni dashi zai zo zamu sake tattaunawa. Suna cin abincin dare kiranshi yashigo tad'aga da sallama,ya amsa muryarshi a dake"har yanzu kina gidan Hajiya ne?Eh Zaujiii... dama yanzu zan kiraka dan na jika shiru...yatari numfashinta"kin jini shiru,ke makauniya ce dabaza ki iya tafiyaba dole sai da d'an jagora ko?Tad'anyi murmushi wannan fad'an dawalakin goro a miya,ba mamaki taran dangi aka mishi akan dole yabarta anan,sai ta fad'a a tausashe duk shi d'in yace ta zauna idan yadawo za suje gidansu"Esbeer Yaya D'ansarai nahhh...ganinan zuwa.Hajiya takalleta"karki nuna mishi kin fahimci abinda yasa shi a damuwa,tarataya jakarta"toh Hajiyarmu mukwana lafiya. ALLAH yasa Sudaida. Da sallama tashiga D'akin-shak'atawar, yakalleta a d'age yakauda kai.Bismillah,wash...ALLAH! tafad'a sanda ta zauna a k'asa dirshan tana maida numfashi kamar wacce gudun famfalak'i"Yaya D'ansarai na dawo. Yayi kamar ba dashi take magana ba,ganin haka tasama ma kanta lafiya ta hanyar kunna data tana turama A'isha sak'o,wucewar dak'ik'u kusan arba'in sannan yamik'e zaune daga kwanciyar da yayi yakira sunan ta. Takashe data tana amsawa da na'am.Kishirya gobe da sassafe zamu koma. Gobe kuma?To saboda me?Hummm...ki bari kawai wai har da Baba a fad'a min ya kamata a barki,ni kuma bazan iya ba, Sudaida ko baza kimin kome ba to ni dai ina san zamanki kusa dani,yabud'e idanun shi daya fara rufewa gaba d'aya a kanta"Zaujatiii... ina k'aunarki ba tare da wani dalili ba,zan cigaba da k'aunarki a kowani hali da yanayi na rayuwa kingane ko?Tajijjiha kai"na'am na gane Zaujiii...ALLAH yabarmu tare,mutu karaba takalmin kaza. Ta sauke numfashi to amma Yaya Dansarai... wani hanzari ba gudu ba,Baba da duk wanda yace kabarni anan umarni suka ba ka ko shawara?Yad'ago yakalleta"shawarace ba umarni ba.Tawani marairaice"to in ko hakane bai kamata kawatsa musu k'asa a cikin idanu ba "Yaya D'ansarai tsakani da ALLAH ba wanda zai so ya haifi d'a a cikinshi bayan fad'i tashin da yayi a rayuwar d'an nan har yazama abinda yazama a doron duniya,sannan wani abun yata so,su bashi shawara a matsayinsu na masoyin shi da suka fi kowa k'aunar shi bayan ALLAH da manzon ALLAH amma yawatsa musu k'asa a cikin idanu ta hanyar kin kar6an shawarar da suka ba shi ace ransu bazai sosu ba?Duk fad'in duniya duk wani me da'awar yana k'aunar mu toh daga bayane sadaka da karuwa,dan da Iyayen na mu basu maidamu mutane a sanda bamu da kome baza mu iya amfana ma kanmu kome ba to da bamu girman da duk wani me son mu ya so muba. Tasake tausasa murya"Zaujiii...gyara kayan ka baya ta6a zama sauke mu raba,nima yanzu d'an mune a cikin cikina,to ai baza muji dad'i mu bashi shawara bayan mun maida shi mutum yak'i kar6a,bayan kuma shawarar bawai ta sa6ama shari'a bane"Yaya D'ansarai kayi hak'uri kabarni anan d'in,na tabbatar dan haihuwar farice,amma da baza su d'aga idanu su kalli rayuwarmu da abinda yake gaban muba, in dai bamu muka fad'a musu dan neman shawara ko kuma addu'a ba.Zaujiii...Aljannarka a k'ark'ashin Iyayanka take sai ka bisu ka kyautata musu zaka sameta fa.Tayi murmushi kasha kuruminka mijin Sudaida ni zan dinga zuwa maka hutun k'arshen mako(weekend)a 6oye,wallahi ba wanda zai sani sai Yaya Aminu dan na san ba zai k'i kawo ni ba. Kalaman Sudaida gaskiyace wacce daga k'inta sai 6ata,zuciyarshi tayi wasai,d'aya daga cikin jin dad'in doron duniya samun mace tagari "Zaujatiii...Ke macen alheri ce,ALLAH yamiki albarka. Kiyi zamanki ba sai kin dinga zirga-zirga tsakanin Zonkwa da Gidan-Waya ba ni duk lokacin dana samu sarari zan zo ko a k'arshen mako ko a ranakun mako(weekdays)ALLAH yamiki albarka yabaki nak'uda kafiifan. Yana had'a kaya a jakar da zaiyi tafiya da ita yana dad'a jaddada mata"Zaujatiii...kullum fa kisha ruwan zamzam d'in nan,kici dabino,ki yawaita addu'a ba dare ba rana,gobe Insha-ALLAH zan ai ko miki da hulba ki fara tafasashi kina shiga,da kinji alamun nak'uda ki d'ibeshi ki had'a da zuma ki cakud'a kidaure kishanyeshi kinji ko?Jikinta yayi sanyi sai take ji kamar kar yatafi,ko kuma su tafi tare tana lumshe idanunta mak'alallun kwallan da suka cika su,suka samu damar zubowa sharrr...yayi kamar bai gani ba,yagama shirya kome a jakar ya rufe yatafi yayi wanka yashirya cikin shigarshi ta dogaye fararan kaya kanshi da hular dara bak'a. Yagama d'aure bak'in agogo a hannun damarshi,sannan yagewayeta yana magana cikin tausayi da k'auna"haba Zautajiii...kuka kuma! yafara share mata hawayen ai ke macen albarkace Sudaida,ban ta6a nadamar zama dake ba ko na sisin kwabo...haba Sudaidan D'ansarai...Ki k'arfafamin gwiwa kamar yadda ki kayi jiya mana,wannan hawayen na ki sai su sa autan Inna a uku fa...yacikata da kalaman k'auna da kambamawa... Itama ta gewaye shi tare da d'ora ha6arta a kafad'arshi "Zaujiii... na yi shiru...ALLAH yamaka albarka. Yayi murmushi"amin.ALLAH yatsare min kai, yakiyaye ka da kiyayewarshi,tasa hannu tad'an shafa k'asumbarshi...wucewar wasu dak'ik'u sunata kallan juna, a hankali suka saki juna yad'auki jakar shi sannan yad'aga hannu yana mata adabo...Yajuya yatafi sai ta d'aga labulan taga tana cigaba da kallan shi yashiga mota yad'aura belt yayi azkar yasa mukulli yatashi motar...har yabar haraban gidan tana cigaba da kallan danjojin motar yayi nisa ya6ace ma ganinta sai taji wasu zafafan hawaye suna zubo mata sharrr...shar...tasaki labulan takoma ta kwanta cikin kewar masoyiii... Shekaru goma sha uku kenan cifff...da auren Julaibib Abdullahi D'ansarai da Sudaida Ibrahim Me-Lambu. A wad'annan shekarun ALLAH ya zurta su da Ya'ya sanyin idanu da Bilkisu...kyakkyawar yarinya data d'auko kyan Iyayenta,bak'in gashi me yawa da tsantsi irin na mahaifinta, sannan ALLAH yabata farar fatar da bana Iyayenta bane ganin damar Ubangiji ne kawai.Bilkisu yarinyace data yi farin jini a zuri'arsu kaafatan,gata da natsuwa bata da yawan magana kamar mahaifinta,idan kaji dariyarta toh dashi suke magana, ga ta da k'wak'walwa duk abinda aka koya mata sau d'aya toh ya zauna kenan ba ta buk'atar maimaici,tana da kaifin basira. Bilkisu Julaibib D'andarai... Shekarunta biyar a yanzu haka tana primary one a makarantar boko,bangaren Islamiya kuma tana da haddar Izifi goma sha biyar daga Yasin zuwa nasi duk in da kaja mata Insha-ALLAH zata cigaba. Sai Maimunatu Julaibib D'ansarai... kanwarta takwarar Inna suna kiranta Walida me shekaru uku.Sai kuma wani cikin da take dashi. Julaibib ya d'auki son duniya ya d'orama Y'ayan nan musamman Bilkisu son ta yake kamar me, saboda dalilai masu yawa,na farko ya sameta a sanda baiyi zato da tsammani ba,na biyu tayi kama da Innarshi,na uku sunan marigayi daya so auren ta kamar me amma ALLAH bai k'addari za suyi aure ba,na hud'u Sudaidan da yake so yake k'auna ita ta haifa mishi,na biyar yarinyar akwai ta da k'wak'walwa da sauransu da sauran... A gajiye lik'is yashigo gidan da sallama,suka gewaye juna tana mishi tausa a hankali yalumshe idanunshi wata natsuwa ta mamaye ilahirin gangar jiki da zuciyar shi "Zaujatiii...ta iya biyar dashi da lak'antar abinda yafi kwantar mishi da hankali,yad'an shafa kanta"nagode Zaujatiii...Takawo mishi ruwa yasha,sannan yaje yayi wanka yasa kaya k'ananan wandon chinos ruwan k'asa da shirt mara nauyi fara, yazauna yana hutawa,Sudaida tabishi da kallo. "Zaujiii...kayi kyau,sai ka zama wani d'an matashin saurayi. Yayi yar dariya"wani saurayi kina ganin Zaujiii...gemu da k'asumbarshi duk furfura...Ni dai a ah ai bawani tsufa kayi ba gaskiya,kai dai girman kawai kake so.Sudaida ai ko girma ya zo gasu Baba ga ku ga sauran bataliyar daza ki haifamin...Yaran suka shigo da gudu dawowar su daga makaranta kenan,suka haye jikinshi suna mishi surutu.Tace"Oya to muje ku canja kaya...sai suka dad'a mak'alewa a jikin Julaibib "ku tashi mana.Julaibib yad'aga mata hannu"kyalesu sai sunyi wanka zasu canja kaya. Tagyad'a kai tatafi tacigaba da ayyukanta. Tana aikin abincin dare Bilkisu tashigo D'akin-girkin tasha kwalliya da wata yar rigar turawa mara nauyi ruwan hoda da dogon wando da d'an k'aramin hijab ruwan hoda,tanata k'amshin arabi'an perfume d'in Julaibib fuskarta shar da kwalliya,tayi murmushi kawai dan ta san aikin shine,haka yake zama yamata wannan kwalliyar musamman idan tamata laifi tace baza tayiba,shi kuma zai rarrasheta yamata. Tafara ta6e-ta6e irin na yara"Mama in dai tuwo za kiyi ni bazan ci ba na fad'ama Baba yace to ki mana doya da kwai da nama,kuma ki had'a mana lemun citta da karas,ni natsani tuwo tana wani yamutsa fuska.Sudaida tajuya takalleta"ALLAH Hajiya Bilkisu?Bilkisu tagyad'a kai tana sake fuska 6ata ALLAH kuwan Mama.Tayi yar dariya"Hummm wato ke dai kullum aci me dad'i ko?Kalleki kamar za ki fashe duk kin fi kowa na gidan nan ki6a,toh yau tuwon dawa miyar kuka nake yi,kuma ba lemu tuwo za a ci asha ruwa.Tad'an buga k'afa cikin shagwa6a "ni dai ALLAH bazanci wannan bak'in tuwon ba,gidan Inna zan ce Baba yakaini ai ita zata bani nama,Baba yace ni ce amaryar shi tana nufin Alhaji Abdullahi,shi kuma zai bani madara da yoghort da biscuit short cake.Tagyad'a kai"toh a sauka lafiya ni dai yau d'an gado nake yi. Tagama kome tagyara D'akin-girkin sannan tafito tasame su yana koya musu aikin gida da aka had'osu dashi daga makaranta amma Bilkisu tanata ta6ara shi kuma yana wani lalla6ata,suka bata haushi kamar ta dake su.Bata dai kula suba itama ta zauna tana nazarin wani project...Basu gama aikin ba amma da Bilkisu tamatsa a tafi sai kawai yabiye mata taje tad'auko mukullin mota yakalleta"Megado nan da gidan Inna sai munje a mota? Tawani shagwa6e"eh Baba.Yakar6i mukullin to shikenan. Zaujatiii...Za kije ne?Idanun ta na kan Laptop d'inta ta bashi amsa"uh uh adawo lafiya. Yakalleta na wucewar wasu yan dak'ik'u" Sudaida yakiraya.bata amsaba tad'ago suka kalli juna said yawani kashe mata ido d'aya,takauda da kai kamar bata gane me yake nufi da hakan ba.Yayi d'as da yan yatsunshi"kin ci bashi wallahi.Tagyad'a kai"eh ba kome bashi ai hanji ne yana cikin kowa,kafad'i ko nawane zan biya.Yajuya ba fashi kuwa ina dawowa za ki bani. Tana jin barar"Allazi wahidin...tabud'e k'ofa takar6i robar almajirin tajuye mishi tuwon tunda d'uminshi dan ta san ko sun dawo shima ba wani ci zaiyi ba,wanda za taci kawai tabari,yakar6a cikin rawar jiki data murya"Iya ALLAH yabiya buk'ata duniya da lahira. Har bayan sallar Isha'i shiru basu dawo ba, taja tsaki ranta ba dad'i abinda yake ma yaran nan yana neman wuce makad'i da rawa fa,haka Bilkisu take mata wannan iya shegen k'auri da kare in dai tayi tuwo kai bama tuwo ba ko menene in dai bata ga dama ba to baza taci ba,sai tace ita wani abu na daban take so,tana ganin ya dawo zata fara shagwa6a ita yunwa take ji Mama bata ba ta abinda take so ba... Shi kuma sarki me Bilkisu sai yafara fad'a shifa baya so ta dinga bar mishi Megado da yunwa tunda ba ta son wannan ba sai a bata wanda take so ba? Ai Bilkisu yarinyace sai da rarrashi wata rana za ta daina,wani lokacin su shiga D'akin-girki yadafa mata abinda take so baya wuce soyayyen kwai,ko taliyar yara(indomie)ko yoghort da donut, wasu lokutan kuma yaje yasiyo musu gasassun kaji ko nama,itama mayyar naman ce haka za su zauna suci su k'oshi,shi yasa kumatu a wajenta har da na sai dawa,to ganin haka itama Walida ta ara tayafa in dai tuwo ne to baza su ciba sai dai in baya gari ta musu jan idanu shine zasu d'an tsakura su bar mata.. Ita har ga ALLAH tana ganin wannan abun idan aka d'ore a haka to za a samu matsala fa,ace kome yaro yake so sai an bashi?Haka yake so su taso su basu san babu a rayuwa ba?Wasu lokutan ko fad'a take musu sai yawani 6ata rai alamar baya son hakan duk da bai ta6a furta wa ba to amma ai labarin zuciya a fuska ma ana ganin alama,shi yasa ita kuma in dai Bilkisu ce za tace ayi kaza to baza tayi shi ba,kamar yanzu da tace atafi gidan Inna, tana son zuwa amma tace baza taba,shi dai Bilkisu bata laifi a wajen shi kome tayi,idan tafara mata fad'a sai yayi murmushi"haba Zaujatiii...Bilkisuna guda nawa take ne? Ai za ta bari wata rana.Toh yaushe ne wata ranar bayan kullum k'ara wayau take yi,dad'a sabawa da hakan take yi?Itace dai tun yana d'anye ake tank'warashi idan ya girma bazai tank'waru ba sai dai ya karye. Dare ya farayi tayi tsayuwar motarshi, yashigo da Walida tayi bacci ya kwantar da ita ya koma yakulle gidan sannan yad'auko Bilkisu,ai yana kwantar da ita tafara mutstsuke idanu sai ta mik'e zaune"Baba ina sauran nama na?Naman ki yana nan kuje kuyi bacci dare yayi sai gobe za kici abinki ko? Tamak'ale kafad'a ni dai a d'akin baccinka yau zan kwana... Yayi kamar baiji abinda tafad'a ba.Sudaida tayi murmushi a ranta tana fad'in"yayi kyau... Tarik'o hannunshi"Baba a d'akin baccinka zan kwana dan ALLAH.Yagyad'a kai"yashafa kanta na ji Megadona,to maza aje a wanke baki, tatafi dagudu ta d'auko brush da maclean takawo mishi, yamatsa mata taje tayi tanata tsallan murna "yau tare da Baba zata kwana, yarik'e hannunta suka tafi. Sudaida taje takwantar da Walida ta tofeta da azkar d'in kwanciya tagama abinda za tayi tanufi d'akin. Suna kwance tamak'alk'aleshi tak'i yin bacci tana bashi labarin yan makarantarsu da Inna dasu Kawu Aminu,tabisu da kallo Bilkisu wai lallai sai ya mata tatsuniyar d'an fulani me kiwon shanu dayaje birni.Yayi hamma yasa tafin hannun dama yarufe baki yana Isti'aza"ni dai gaskiya ban iya wannan tatsuniyar ba Megadona,dan ban san abinda yayi a birni ba. Takyalkyale da dariya tana d'an bud'e idanu dan mamaki" Baba ba kace Innace Mamanka ba? Yakalleta da kulawa"eh Bilkisu itace Mamana.Yad'an yamutsa fuska"amma bata baka labari ba?To gobe zan rakaka wajenta sai tabaka labari ai muma ita take take bamu labari,har fa da tatsuniyar gizo da k'ok'i. Sudaida tace"Bilkisu surutun ya isa tashi kije ki kwanta...Julaibib yatari numfashinta"kyale ta bata jin bacci ko Megadona?Tagyad'a kai a shagwa6e"ai haka takeyi idan ba kanan wai muje mukwanta.Haushinsu yakamata kawai sai tajuya"dan ALLAH ku kwana kuna hira. Sak'onshi yashigo wayarta"Zaujatiii... Kar kiyi bacci fa...ina lalla6atane.Takashe wayar tayi kwanciyarta"kai ka sani.Sai da baccin Bilkisu yayi ni sa sannan yabita...yakunna fitilar wayarshi yana haske mata fuska,tasa hannu takare fuskarta sannan ta bud'e idanu"Zaujatiii baki ga sak'ona bane? Na gani. Tafad'a a taik'aice...Sudaida ta kin fahimce ni amma kika share ni kina ji Bilkisu ta tasani agaba.Tadad'a gyara rufa"uh ai duk a cikin lokacin tane, yaushe ko za a bar ranta ya6aci sarauniya me D'ansarai.Yad'an daki bayanta yana matsa mata hannu a hankali"yau haka kike jin fad'ar sunan nawa D'ansarai gatsau ba ko sakayawa?Tayi shiru kamar ba da ita yake magana ba. Yagewayeta"to gani na zo a bani bashi na... duk da ranta a 6ace yake amma bata hanashi abinda yake so ba...shima ya fahimci haka shi yasa yake jinta wata ta musamman a sararin zuciyarshi, Sudaida ba dama ne wallahi,ta gama lak'antar shi,a cikin ruwan sanyi take hukunta shi sai yazo yana bata hak'uri da bakin shi dan a zauna lafiya...Yawani narke kamar k'aramin yaro"Zaujatiii... Ina k'aunarki fa I can't do without you.Batace kome ba tacigaba da bashi wasu sak'onni sai shima ya biyema yarima su sha kid'a... A safiyar asabar yara sun sami hutun makaranta Sudaida tamatsa sai sun tafi Zonkwa dan watanninsu biyu basu je,tagama shirinta tsafff sannan tashiga d'akin...baki bud'e take kallansu da mad'aukakin mamaki baccinsu sukeyi hankali kwance ya lull6esu da bargo,tun d'azu fa tahad'a ruwan wanka za ta musu yace tabari zai musu taje tahad'a musu abinda za suci suna gamawa sai tafiya amma shine bayan fitarta suka koma su kayi kwanciyarsu,wato sune masu idanun jin bacci ko? Tayaye bargon tana tashinsu ya bud'e idanu,ta6ata fuska "haba dan ALLAH Yaya D'ansarai kai bakiyi wankan ba,su baka musu ba? Yaziro k'afafunshi k'asa"kin san akwai sanyi ban san sanda baccin yasake awon gaba dani ba barinje in yi...tunda yashiga wanka ta san ko ya fito bazai musu ba, dan haka tatashi Walida taje tamata sai da tagama shiryata sannan ta tashi Bilkisu tamata tad'auko shadda getzner ruwan makuba yasha aiki da zare ruwan zinare da wasu k'ananan duwatsu masu d'aukar idanu saboda kyallinsu riga da buje da d'an kwali,tana ganin kayan tawani shagwa6e fuska wai ita baza ta sa kaya irin na Walida ba wanda Baba yasiyo mata dayaje Umrah doguwar rigar larabawa shi za tasa. Sudaida ta dafa kafad'arta da sigar rarrashi"kisa wannan kinga anko fa za kiyi ke da k'anwarki, yanzu zan miki wannan kwalliyar sai kuyi Selfie da waya ta.Walida tayi tsallan murna"Yehhh...ni ma na iya tsayuwa da shan baki a selfie,Bilkisu ta ta6e baki ita yar gata haihuwar samu sai kawai tafashe da kuka tana bubbuga k'afa ita fa dole rigar larabawan nan za a d'auko mata.Sudaida ta tsare ta da idanu"idan ban d'auko ba fa?Kawai sai ta kwanta a k'asa tana burgima tana k'ara fashewa da kuka dan ta san Julaibib zai shigo...Haushi yakama Sudaida tagyad'a kai "lallai mugun gata asara,rashin shi kwata-kwata illah... Tanunata da yatsa"ke Bilkisu ki rufe min baki.Bilkisu tacigaba da ihu da burgima tana kiran Julaibib"Baba kazo ka d'auko min doguwar rigar larabawan daka siyo min,Mama wai bazan sa ba. Sudaida ta kifa mata mari ba za a d'auko ba... taduba yar k'aramar dorinar ta take musu barazana da ita tarasa kawai sai ta jawo wayar caja tanad'e ta a hannu"baza kiyi shirun ba ko?Ga mamakinta kawai sai tagyad'a mata kai alamar eh.Ai batayi wata-wata ba shaud'a mata iya k'arfinta caraf a kan idanunshi. Bilkisu tagigice dan taji dukan yadda yakamata tak'ara fashewa da kuka kamar zata shid'e, ya d'auketa ya zubama wajen data shaud'a mata idanu,cajar ta fito rad'am da kwanciyar jini a wajen toh jikin hutu ko ina lukwui-lukwui da tsoka ga kuma farar fata,yakalleta fuskar shi ba wal-wala"Sudaida baki da hankali kasheta kike so kiyi? Dan tace ga kayan da take so sai yazama laifin da har sai kin mata wannan dukan?An siyo kayan dan ayi meye dasu?Ya rufeta da fad'a kamar zai daketa,Sudaida tayi shiru tana zancen zuci"wai ita ce za ta kashe mishi 'ya saboda ta daketa sau d'aya. Tashi ki d'auko mata rigar.Takalleshi cikin idanu"na rantse da girman ALLAH ba zan d'auko ba!Yashare ma Bilkisu hawaye"to fad'a min in da take in d'auko...Cikin fushi tace"wannan rigar haramiyar ta har abadan duniya wallahi.Shima cikin fushi yajuya rungume da Bilkisu"kar ki d'auko ki dafa kici... Sharrr...sharrr wasu hawaye masu d'umi suka zubo mata akan Bilkisu suke wannan ja-in-jar da Yaya D'ansarai?Ranta in yayi dubu ya 6aci wai shi wani irin so yake ma wannna yarinyar da har zai ga laifin ta amma yakasa tsawatar mata?Wannan makauniyar soyayyace wacce daga k'arshe baza ta haifar da d'a me idanu ba wai Zaujiii...Shine yake mata wannan hayagagar...za ta kashe mishi 'ya... tadafa rigar taci tunda baza ta bata ba...taci kukan ta ta k'oshi tayi shiru tunani barkatai ya cika k'wak'walwarta...yawa-yawan Ya'yan da suke samun matsala a rayuwar su to hakan yana samo asaline daga irin mugun gatan da ake nuna musu tun zamanin k'uruciya. Sai da hantsi yadubi ludayi sannan Walida tashigo d'akin cikin wata shiga ta daban riga da wando da k'aramin hijab yan kanti...ran Sudaida ya kuma 6aci wato fitan da yayi sababbin kaya yayafi ya siyo musu kenan? Walida takalleta"kingani Baba ya siyo mana wasu kayan?Tagyad'a kai"na gani Walida. Mama kuma na ce mishi ALLAH amfana... tad'an shafa kanta"yauwa Innarmu ALLAH yamiki albarka haka ake so duk wanda yabaki abu kisa hannu biyu ki kar6a kuma kiyi godiya...tayi yar dariya"wanda yagode sai ALLAH yak'ara mishi haka kika fad'a min ko? Eh Innarmu ashe baki manta ba.To nagode da kike rik'e duk abinda nake fad'a miki. Tad'anyi jimmm...sannan ta kalli Sudaida"Mama ita Yaya Bilkisu fa da Baba yakawo sai tace wai basu da wani kyau sai da yahad'a mata lemun tuffa da karas sannan ta yadda tasa...wai ita dai na Umrah nan take so,shine yace sai ya koma wata Umrah,damu zai tafi muje can muza6a irin wanda muke so da kanmu... Walida... Suka jiyo muryar shi daga D'akin-shak'atawa yana kiranta,sai ta d'an bud'e idanu "Mama...Baba ne yace wai kizo mutafi na manta... tafita da gudu tana amsa kiran na shi.Takoma tayi kwanciyarta"da bata hak'ura ba baza suyi tafiyar ba kenan kome?Tayi k'wafa"wallahi abu d'aya zai sa tabisu dan tafad'a ma su Baba abinda yake yi, da ba in da za taje,gwamma ayi ma tufkar hanci,ai gabama da gabanta aljani ya taka wuta,ita baza ta iya cigaba da ganin kayan takaicin nan ba nama na jan kare. Ko kallanta bai yiba,to itama a cikin fushi take dan haka ba wanda yakula wani har suka isa Zonkwa. Inna taji dad'in ganinsu sai ina za a saka ina za a aje takeyi da jikokinta haka suka yi wunin farin ciki.Bayan sallar magriba Sagir k'aninta daya yazama matashin saurayi takira yaraka ta wajen gyaran gashi har Julaibib yadawo basu dawo ba shima yazauna ana ta hira,Bilkisu Megadon Zinare an samu abinda ake so dafadukar cus-cus me nama da kayan lambu take ci,ga Baba ya kawo mata yoghurt tana taci tana sha cikin jin dad'i da kwanciyar hankali. Sai wajen takwas da rabi suka shigo Sagir yasake gaishe dasu Baba sannan yamusu sai da safe,ita kuma taje tayi sallar Isha'i ta zubo abinci tanaci;yad'an saci kallanta tayi kyau sosai amma ko nahiyar da yake bata kallaba har tagama ci takai farantin D'akin-girki sannan ta dawo ta zauna tad'an kalli yaran"kutafi D'akin-shak'atawa ku kalli wannan shirin na Balarabe da bai iya gaza gurasa ba...Suka mik'e da Sauri"ehhh kuwan Mama... Tad'an sunkwui da kai cikin ladabi"Baba ina son magana da ku.Yagyad'a kai"to Sudaida... Julaibib yayi wani huci"me wannan yarinyar take nufi? K'arar shi za ta kawo wajen su Baba?Ina jinki Sudaida me yafaru?Muryar ta tafara rawa alamar zuciyarta ta karye"ni dai Dan ALLAH Bilkisu zata dawo gidan nan da zama zan had'o kayanta... Inna tace"ashsha to me yayi zafi idanu za suci wuta har haka Sudaida?Inna kusan kullum sai mun samu sa6ani da Yaya D'ansarai a kan ta,wai d'azu da safe har yana fad'a min zan kashe mishi 'ya saboda na daketa,kuma agaban idanunta ya rufeni da fad'a kamar zai dakeni,Lillahi warasulihi Inna ace kamar Bilkisu sai abinda take so za a dinga yi a cikin gidan nan?Sannan ita ba ta laifi, ba ta kuskure kome tayi dai-dai be a wajen shi, wannnan abinda yake yi ya dace da tsarin ingantacciyar tarbiyya!? Ni dai ta zauna a wajenku kawai.Inna ta numfasa to me yakawo dukan?Sudaida duka ai baya ba da tarbiyya sai dai yakangarar,ni ma ba na son duka.Wani haushi yamamaye ta wallahi mantawa tayi kuka takawo gidan mutuwa"ai kamar yadda Bilkisu take hantar Yaya D'ansarai to haka abun yake a wajen Inna son ta take kamar me,shi yasa ba gidan da take son zuwa kamar nan dan Inna tana biye mata ne,yanzu ma abincin daren ta daban tadafa mata. Tasa hannu ta share hawaye"shikenan Insha-ALLAH daga yau ba ruwana da duk abinda Bilkisu za tayi ai ALLAH yagani bani da wani k'arfi ne dan haka zan kyamaci kome a zuciyata.Auna had'a idanu ya gallamata harara"ai dukan yayi yawa ne har ciwo kika ji mata to me zaisa bazanyi fad'a ba. Baba yayi tsaiii...yana nazarin kalamansu d'aya bayan d'aya,yakad'a kai"Maimunatu wannan hukuncin na ki na adalci ne kuwa?Tsakani da ALLAH Sudaida ta fiku gaskiya;kar k'aunar yarinyar nan tarufe idanunku fa,idan an ciza to yakamata a hura...yanuna Julaibib"Malam D'ansarai da ilminka da girmanka amma kana irin wannan abun?Kiwo aka ba ka game da sha'anin Iyalinka fa,shi itace tun yana d'anye ake tank'warashi...kana nunama Bilkisu tsananin gata amma ba kwa6a to an yi ba ayiba kenan...an 6ata goma biyar bata samu ba,dan me za tayi laifi ba za a hukunta taba?Mahaifiyar tace fa idan ba a nuna mata abinda takeyi kuskure ne tun yanzu ba,to a gaba ma cigaba dayi za tayi,kuma duk fad'an da zaka ma Sudaida to na rok'eka da girman ALLAH kadaina yi a gaban Ya'yanku,hakan yana gur6ata tarbiyyarsu,dan ALLAH Malam D'ansarai idan rai ya 6aci to bai kamata hankali yagusheba kaji ko? Yanuna ta"ke kuma Sudaida ba ke za ki yanke hukunci na rad'in kan ki ba kome ya miki,tunda shine ubansu shine a hakku a kansu dan shine shugabanku ke da yaran gaba d'aya.Ubangiji ya muku albarka,sannan duk yadda ranki ya6aci kiyi hak'uri dasu kinga banji dad'in furucinki akan Bilkisu ba,ke uwace bakinki amsashshene akan ta,dan haka ki janye wad'annan kalaman na ba babu ruwanki da duk abinda za tayi,ai kece kuwa me ruwa da tsaki yaushe za ki biye ta wani D'ansarai Ya'yanki kadararki su shiga garari,duk abinda ya kumayi ki bugo waya ni dake ki fad'a min zai sha mamakin yadda zanyi wallahi ALLAH kinji na rantse ko? Kalaman Baba sun tausashi zuciyarta"to Baba nagode ALLAH ya k'ara girma.Inna ma tajijjiga kai toh na gano kuskure na kiyi hak'uri Sudaida ALLAH yamuku albarka,ku tashi kitafi gida dare yana dad'a yi,ta lek'a D'akin-shak'atawa duk sun yi bacci Inna tace suyi tafiyarsu kawai. Suna zuwa gida taje tayi wanka tayi kwanciyarta shi kuma yatafi D'akin-girki zai dafa shayin na shi na fama taja tsaki sai kaje kayita sha...takwanta cikin tunanin tsohuwar soyayyar su..ita dai ta san da son Julaibib ta girma kuma ba tajin da wani abu dazai rage k'aunarshi a sararin zuciyarta,to amma wannan yawan sa6anin da saka fara samu ita tata k'arfin k'aunar ta zuciyarshi ce ta koma kan Bilkisu da kuma kud'in da yakeji yayi?Ko kuma giyar Ilmi da dukiyace tafara bugar dashi...!? Tad'auki wayarta takira"Umma kiyi hak'uri na kiraki da daddaren nan wata magana nake so muyi.Ba kome me yafaru ne?Hawaye suka zubo mata"Umma ni da Yaya D'ansarai ne...sai kawai tafara kuka,Umma bata hanata kukan taba sai da taci ta k'oshi tabari dan kan ta...Umma tasauke numfashi "Sudaida kiyi hak'uri ni bazan shiga tsakanin ki da D'ansarai ba ai kunfi kusa,kuma ai ba a ta6a zaman tare ace wani bazai sa6a ma wani ba...fuskantar matsalolin aure irin wannan ai dole ne dan haka ki k'ara hak'uri kuma ki yawaita addu'a kome yayi farko yana da k'arshe...kuma in dai akan Bilkisu ne to fa dole sai kin kawar da kai...ba kome za ki nuna ya dame ki ba...ki dai kiyi k'ok'ari ki jata ajiki kinga ai tafi shak'uwa dashi ko? Eh Umma...to ko ni nan a yanzu nagano wasu kura-kurai danayi game da tarbiyyarku to amma har kwanan gobe ina godema ALLAH ina godema Mama wacce ba dan ita ba da kuma kun samu tasgaro dan haka ki natsu ki san abinda kike yi game da sha'anin tarbiyyarsu... haba Sudaidan D'ansarai kika juya shi yayi wasu abubuwan da bai so ba sai kuma wannan za ki fara raki? Ki bi dashi ta siyasar rayuwa ko bai daina wasu abubuwan ba to amma ai za ki samu sauk'in wasu,Umma tad'anyi murmushi"taurin kan Bilkisu da kafiya kema fa haka da kike k'arama kinyishi,shi yasa bana miki da wasa...ita kuma sai abun yahad'u mata da gata... Julaibib yashigo lokacin suna sallama da Umma.Yakar6e wayar"k'arata kika sake kaiwa,me kika fad'a mata?Abinda kunnuwanka sukaji.Yayi murmushi"ALLAH ko?Tajijiga kai"bawai...yashiga rarrashi"kiyi hak'uri Sudaidan D'ansarai ni ma na gane kuskure na,bai kamata ace Bilkisu ce zata shiga tsakanin muba,ai tare tazo ta ganmu,lallai ke macen albarka ce dakika jajirce dan ganin na dawo kan hanya nagode Zaujatiii...ALLAH yamiki albarka ya saukeki lafiya.Sai taji zuciyarta ta yi wasai"ta marairaice Zaujiii..to idan banyi hak'uri ba me zanyi bayan mun zama k'arfe da mayen k'arfe,mutu karaba takalmin kaza...?Hummm fushin masoya hutuhhh... Rawa da k'afa d'aya sai gwani. Da ba 'yan koyo da gwanaye sun k'are... 5 Rajab 1441 28 February 2020 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na ashirin da hud'u. Gobe zan tafi Sudan fa...takalleshi wani iri" haba dan ALLAH shine baka fad'amin ba sai da daddaren nan?Yagyad'a kai"ai dan ma mun shiryane da sai na tafi zan turo miki sak'o ni nawuce sai ALLAH yamin dawowa. Tad'an harareshi"gaskiya banji dad'i ba,ba fa abinda na shirya maka.Uh bakome kibani abinda yasauwak'a,kin san ni bana raina kad'an"da hanau ai gwamma mannau. Tare suka shirya kayan tafiyar.Washe gari jirginsu yad'aga. A wad'annan shekaru goma sha ukun Julaibib Abdullahi D'an Sarai ya taka matakai da yawa a bangaren ilmi har ya zama shehin malami ferfesa gangaran(Professor)Yasai k'aton fili yana gina had'ad'd'iyar makaranta ta zamani bangare biyu bangaren addini da bangaren boko,aiki tuk'uru ake yi k'asa tanata cin kud'i,makarantace tun daga matakin prenursery,nursery,primary da secondary,abubuwa k'alilan suka rage mishi a bud'e makarantar,yana kuma da buri nan gaba yad'ora makarantar zuwa Jami'a me zaman kanta, yana kuma fatan makarantar tacigaba har bayan rayuwarsu,Ya'yansu su cigaba har jikoki...ta shahara har zuwa sauran k'ananan hukumomi da jahar Kaduna da d'aukacin sauran jahohin dake tarayyar Nigeria. Abubuwan rashin jin dad'in da suka faru kuma shine tun bayan yak'in Zongon-Kataf da yak'in da akayi a k'waryar cikin Kaduna na k'addamar da shari'ar musulunci wani hargitsi da kisan rayuka bai kuma faruwa a k'aramar hukumar Zangon-Kataf ba,to amma a 'yan kwanakin nan manyan kabilun yankin Bajju da Atyap da sauran kabilu da basa sallah sun fara neman hana musulmai rawar gaban hantsi,takalan fad'a ba irin wanda ba sayi to amma bai damu hausawa ba,saboda duk fad'in doron duniya kowa ya shaida duk in da kaga musulmi kuma bahaushen mutum to ba wani abu yakai shiba face neman ilmi ta yadda zai bautama Ubangiji ba tare da jahilciba,sai kuma neman kud'i,kuma musulmi na da sauk'in halin da basa son tarzoma,wannan dalilin yasa suka d'an sararama hausawa amma ba hak'ura sukayi gaba d'aya ba,aka cigaba da zama cikin aminci da amana kamar yadda zuciyar bahaushe take a ko ina. Tana kwance a d'akin baccinsu lullu6e da bargo tana chat da Nasmat,video call d'inshi yashigo ta d'aga da sallama,ya amsa da wani salo irin nashi yana murmushi"eyehhh... kaga Hajiya baki da wata matsala.Tayi yar dariya"godiyar Ubangiji a kowani hali da yanayi Zaujiii...Yagyad'a kai"ina yaran?Suna gidan Inna wai a can zasu kwana,yad'auki kofin gabanshi ya kur6i abinda yake ciki yamayar ya ajiye. Me kake shane?Shayi tad'an yamutsa fuska"asha lafiya. Zaujatiii...Yakirata.Na'am.Nayi kewarki, bakya barina inyi ayyukan dake gabana,gangar jikina ne kawai a Sudan amma tunanina da zuciyata suna gida wajenki,gashi kwanakin basa sauri,anya ba visa za kiyi ki taho ba?Tawani marairaice"ni ma nayi kewarka,Yaya D'ansarai...Esbeer kaji?Kamai da hankali akan aikin da kaje yi,ai kamar yaune zaka dawo gida katarar da zuri'a da Iyalinka cikin k'oshin lafiya Insha-ALLAH,ka yi kwanaki goma sha shidda,saura kwana hud'u kacal ai... Zaujatiii...na rantse miki da ALLAH daga shi ba wani kece duniyata,ina k'aunarki fa.Tagyad'a kai cikin gamsuwa da kalamanshi bawai shaci fad'i bane"ni ma haka Zaujiii...Ina k'aunarka a kowani hali da yanayi, baka da abokin tarayya a irin k'auna da soyayyar da nake maka"in poor and in rich,in sickness and in health...till death due part us''Yaja numfashi yafesar da iskar ta baki ta hanci"oh ya rahman...wani shauk'i da d'okin ganinta yamamaye shi...sun dad'e suna musayar kalaman k'auna sannan suka fara magana akan kud'in daya turo aka sai wasu kayan aiki na ginin makaranta. Hantsi yadubi ludayi tashirya cikin doguwar riga kamfala,tatafi gidan Inna suna tattauna wasu al'amura daya shafesu,Abu me aikin da Julaibib ya d'auko ma Innar tashi tashigo da sallama ta ajiye farantin hannunta a gaban Sudaida tana tsokanarta "uwar biyu tashi kici kwad'on zogale na miki naga kwanaki biyu in dai kinzo abinda kike tambaya kenan, yau kuma naji baki tambaya"tamik'e zaune dakyar tana murmushi"nako gode miki Abu ba kad'an ba,sannu da aiki,tad'iba da bismillah takai bakinta, tafara taunawa cikin gyad'a kai "gaskiyar magana wannan k'uli-k'uli akwai d'ankaren dad'i da d'and'ano, tasa hannu a jaka taciro dubu biyu tabata"yaba kyauta tukwuici Abu.Abu takar6a tana godiya "madallah ALLAH yak'ara bud'i,yasaukeki lafiya... tad'anyi murmushi kawai,sai Innace ta amsa da" amin. Abu tajuya takoma D'akin-girki tana yaba halin kirkin zuri'ar Hajiya. Bilkisu tashigo cikin shagwa6a ta rungume Sudaida tabaya"Mama kince za ki kira min Baba mu gaisa.Tad'an harareta"kin fa dameni idan nace na fasa sai ayi yaya dani?Asma'u da shigowarta kenan ta amsa dama me hali baya fasawa"wallahi abu me sauk'ine muyi k'uli-k'ulin kubura dake.Bata kula Asma'u ba tafara kiranshi,cikin d'oki Bilkisu ta manna wayar a kunne"Baba afqadtuka(nayi kewarka) Yayi dariya ALLAH Megadona?ALLAH kuwan Baba jiya ma nayi mafarki wai ka dafa mana naman talo-talo naci nak'oshi...tanata mishi shirme yana dariya... toh ni dai gaskiya idan bazaka dawo ba zan sa Kawu Aminu yakawoni in da kake ai yasan wajen ko Baba?Eh yasani.Ina Walida?Tatafi da Kawu Aminu siyo kindirmo a riga ni dai nace baza niba,shine wai yace idan suka dawo suma bazasu sammin ba,Baba kace Mama yau ta soya min dankalin turawa da kwai. Yagyad'a kai"to Bilkisu na har da lemun kwakwa ko? Tajijjiga kai tana tsallan murna"zan rage maka har kadawo,yaushe zaka dawo d'in?Insha-ALLAH gadan bil-lail.Tawani fasa ihun murna Sudaida takwace wayar ta buge mata baki"ban hanaki wannan ihun murnan ba?Kawai ki cika mana dodon kunne.Inna tafara fad'a"nifa Sudaida ban san sanda kika 6aci da saurin hannu ba,tad'anja tsaki"haba ina amfanin irin wannan?Tayafito Bilkisu da hannu"zo nan muga bakin...yauwa kingani ko har ya fara kumbura.Sudaida tace"kiyi hak'uri Inna,Inna bata kulataba sai da tagama lalla6a Bilkisu ta daina kuka sannan ta kalli Sudaida"ya wuce amma a dinga kulawa... tayi murmushi"to Inna a ranta tana fad'in "wuuu na manta ashe hantar Inna nata6a a gaban idanunta. Dawowar shi da kwana biyu ya tasata a gaba wai dole sai ta raka shi wata seminar,sun gama abinda za suyi suka wuce kasuwa yasai kayan wuta na mak'udan kud'ad'e da za a sasu a makaranta.Sudaida tayi tsaiii...cikin tafakkurin abinda za ta sai ma Yaya Aminu wanda zai burgeshi har yayi amfani dashi,saboda abubuwa da yawa basu d'ad'ashi da k'asa ba.Zaujatiii...tunanin me kike yi haka?Takalleshi"Yaya Aminu na rasa me zan sai mishi bani shawara"yayi murmushi"turare da kayayyakin da yake ayyukanshi dasu(artistry equipment) sune kawai zai yaba ko?Yauwa Yaya Julaibib wannan shawara taka ta samu kar6uwa nagode. Bayan sallar Isha'i taje gida tasame shi a D'akin-shak'atawa yana shan fura da nono,ya maida ludayin cikin kofin yana amsa sallamarta"Sudaida kece haka da daddaren nan,ina autan Innan?Ta zauna a k'asa tana maida numfashi kamar wacce tayi gudun famfalak'i saboda nauyin da cikin ta yayi"su Bilkisu yatafi d'aukowa a gidan Inna,ni kuma nagaji da jiranshi shine nayi tahowata.Da sauri ya d'auko ruwa ya zuba a kofi ya mik'a mata,har ta kai tsakanin la66anta da bismillah yasa hannu yakar6i kofin"yi hak'uri ina zuwa,bulkodi(glucose D) yad'auko yazuba mata babban cokalin cin abinci d'aya a cikin ruwan yajujjuya sannan yabata,ta shanye duka,suka kalli juna suna murmushi"yaya a k'aro?A ah Yaya Aminu nagode kwarai taurarona. Yazauna"da kinyi zamanki, kina kirana a waya ai kin san bazank'i zuwa ba.Yaya Aminu ba kome ai nima ina motsa jiki ne.Ya kalli k'afafunta da suka kumbura,har ranshi yaji tausayin ta"mata suna shan wahala da ciki fa,duk mace me ciki ai kana ganin yanayin ta ka san abin ba a cewa kome"lallai biyayya ga mahaifa dolen-dole ne ga duk mai son gamawa a doron duniya lafiya".Sannu kanwata to baza kije asibiti su baki magani ba? Tayi yar dariya ganin yadda yadamu dama haka yake nuna mata tausayi duk sanda suka had'u,tasa hannu tana murza k'afafun"wannan ba kome bane,ba shi da wani magani wasu suna yi yayin da cikin su ya tsufa wasu kuma ba sayi,duk cikina bai wani girma amma gashi na fara wancan makon ma naje an dubani kome nawa lafiya lau. Yakad'a kai"toh Ubangiji yaraba lafiya.Amin Yaya Aminu nagode"ga wannan.Yakar6i ledan, yad'ago yana murmushin jin dad'i bayan yaga abubuwan da suke ciki "yanunata da yatsa duka na Aminu ne shi kad'ai?Tajijjga kai.Toh nagode ba kad'an ba"ALLAH yamiki albarka Sudaidan D'an Sarai. Sukayi dariya.Sun d'an ta6a hira har zuwa takwas da rabi sannan yace ta tashi yarakata gida dare ya farayi,suka jera suna tafiya a hankali suna magana har suka zo k'ofar gidan"shige gida kinji dare na dad'ayi ga hasken farin wata kar yasa miki mura.Sai da safe ko?Tagyad'a kai"ALLAH ya tashemu lafiya tabi bayanshi da kallo har yasha kwana ya6ace ma ganinta. Ranar wata laraba a watan Rabi'u Awwal kabilun garin suka tashi da neman rigima ba wanda yataka ko ya zubar musu suka fito suka dinga zage-zage da k'one-k'onan tayoyi nan da nan gari yafara rikicewa kowa yatashi a wajen sana'arshi sai gida hankali a tashe, basu suka daina wannan abun ba sai wajen k'arfe d'aya na dare. Sudaida ta sauke gwauron numfashi "Zaujiii...garin nan yafara bani tsoro,sallolin yau gaba d'aya kowa a gidanshi yayi bayan ga masallatai nan, amma saboda tsoron wasu marasa sallah an rasa wanda zai fita?To wai me aka musu? Yayi murmushi "kome zai wuce Insha-ALLAH gobe za a tattauna da Agwam Bajju (Sarkin Bajju) kin san shi mutumne me san zaman lafiya na san kuma zai ja musu kunne Kwanta muyi bacci kinji"gobe asubanci zanyi zuwa Gidan-Waya, har Sudaida tayi bacci amma shi idanun shi biyu yana tunanin al'umara mabambanta, lokuta da dama shima yanaji kamar yatattara yabar garin,to amma idan ya bar garin ai anyi gudu ba a tsira bane"gudun da ba a tsira ba kuwa kwanciya ta fishi". Gaba d'aya zuri'arsu a garin suke Iyaye da kakanni,ai duk in da za shi dole dai sai ya dinga zuwa duba Iyaye da yan'uwa dan ya san mahaifanshi ba yadda za suyi su bishi ba,yasauke numfashi "zaman su a garin Zonkwa cikin wad'annan kabilu muk'addari ne tun daga Lauhul-mahfuz, k'addara ta riga fata,sai dai ya kamata suyi ho66asa dan suna so su fara musu cin kashi, shekaru kusan goma da suka wuce haka suka zauna cikin fargaba saboda fad'an d'aya 6arke sakamak'on k'addamar da shari'ar musulunci da akayi a Kaduna, a cewar su wai an kashe musu mutane da yawa a Kaduna dan haka suma za su d'auka fansa a kan musulman da suke zaune anan,tsawon lokaci haka suka zauna cikin tashin hankali,har dai kuma Ubangiji ya kawo k'arshen abun ba tare da sunyi kome ba...da wannan tunane-tunanen bacci yayi a won gaba dashi. Sai dai cikin baccin na shi yayi mafarkin daya dinga na shud'ad'd'en shekaru"Kasham dai yau ma yasake gani cikin shigar Fulani kirar kalangunta ya fito rad'am kamar dai wancan lokacin amma idan tayi magana sai yaji muryar Sudaida...ya farka yanata nazarin wannan mafarki"toh me yak'un sane?...baccin da bai kuma komawa ba kenan har aka fara kiraye-kirayen sallar asubahin farko... Hausa/Fulani Community Development Association(HAFCODA)Taza6i manya daga cikin su, suka tafi fadar sarkin Bajju,ya kuma kar6esu cikin mutuntawa, sun gabatar da abinda yakawo su,nasan zaman lafiya,da hak'uri da juna,shima Agwam Bajju a zahirance dai ya nuna 6acin ranshi"dan sanin asirin ciki sai hanji,ya kuma tabbatar musu su kwantar da hankalinsu lallai zai tsawatar musu ta hanyar yin gargad'i a dukkan majami'u(churches)ga wad'annan samari yan zauna gari banza masu son tada hargitsi,idan kuma basuji ba to lallai zai buga musu sandar shi(a al'adarsu idan har agwam Bajju yace zai buga sandarshi to duk abinda mutum zaiyi to ba zaiyi nasara ba) Wad'anda ba son zaman lafiyar suke yiba suka had'a taron su.Shugaban nasu yabisu da kallo d'aya bayan d'aya"kunji abinda yake faruwa, dama hausawa masu san zaman lafiya ne tunda duk abinda muke musu basu ta6a mai da martani ba...toh ni dai kawai bana son ganinsu a garin mune,kome sune suke dashi sama damu sannan hakan bai wadatar dasu ba kullum aure mana Ya'ya suke k'arayi,wani abin takaicin ko da wasa baza kaga wata yarsu kace kana sonta zaka aureta ta yadda da kaiba,sai tace bata yadda ba tunda baka yadda da addinin taba,kunaji suna fad'a kakar za6e me zuwa zasu za6i mutum biyu daga cikinsu su tsaya takarar Chairman to kuna gani za su yadda su sake dangalama wani na mu k'uri'arsune?Yaja dogon tsaki"infact I'm sick and tired of seeing all those masu sallah bounch of idiot,we've to do something,something seriously againts them. Wani daga cikinsu me rangwamen kafircin yace"da munyi hak'uri kawai ai mun riga mun zama d'aya,ga Ya'yanmu a cikinsu idan munyi yak'i mun kashe mazaje to yaya zamuyi da tarin mata da Ya'yansu?Nifa Ya'yana guda uku ne masu sallah.Cikin fushi shugaban nasu ya daka mishi tsawa"enough of this stupidity,so bloody what da Ya'yanka uku ne a cikinsu? Ko akwai 'yata a cikinsu na rantse muku zan iya kasheta, ba sune shegu masu kwad'ayin abin hannun hausawa ba? To da irin suma zan fara kisa,so dubu nawa suna wulak'antasu? Yanuna mishi k'ofa yana mazurai"now get out! Kai baka cikinmu. Yasake bin sauran da kallo,suma shi suke kallo suna jijjiga kai alamar gamsuwa da matakin daya d'auka,fuskokin nan babu rahama da tausayi kona sisin kwabo,idanuwa jawur saboda shan burkutu da hayakin maro."nayi dai-dai?Suka had'a baki wajen amsawa"kayi dai-dai.Yakyalkyale da wata irin gur6atacciyar dariya da bata da dadin ji saboda giya da hayaki sun gama lalata hunhunshi"that's very good of you... Suka rufe k'ofa suna cigaba da k'usk'us d'insu na yadda zasu canja salon takunsu akan hausawa, d'akin ya kaure da dariyarsu dan sun gamsu d'ari bisa d'ari da matakin da suka d'auka... Hankulan jama'a ya kwanta an cigaba da harkoki kamar yadda aka saba,sai dai kuma watanni kad'an a hankali abubuwa suka fara rinca6ewa za a koma yar gidan jiya,aka sake komawa cikin zaman d'ar-d'ar,basu da wani kwanciyar hankali, harbin bindigogi daga daji haka yake shigowa cikin gari ba dare ba rana alamar suna koyan harbi amma abun duka ba sanda da yake kuma dama bahaushen me ban haushinne na tanko me kan bashi,hakan bai d'ad'asu da k'asa ba,su dai neman halalinsu kawai. Mtswww ALLAH yakyauta. Gidan shiru saboda yaran yanzu a gidan Inna suke kwana a duk ranakun k'arshen mako,Julaibib ya d'auko musu abinci,tamik'e zaune dakyar suka faraci da bismillah yana kuma mata bayanin aikin kafa ma'adanar littafai(bookshelves)da aka fara a d'akin nazari da bincike na makarantar (library)Tayi lallausan murmushi"Ubangiji yacigaba da rufa mana asiri duniya da lahira,gaskiya naji dad'i wallahi.Amin Zaujatiii... Cikin firgici ta farka daga bacci a sulusin daren,wasu irin munanan mafarkai takeyi duk dare,har fargaba duk lokacin da rana tatafi zata fad'i magriba ta kunno kai,saboda da zarar ta kwanta baccin dare zata fara wannan mafarkan masu tashin hankali da sanya damuwa a zuciya.Julaibib yana zaune yana cike wasu bayanai a na'ura me kwakwalwa yaji motsinta,yajuya yana kallanta,tana zaune a tsakiyar gadon ta kama kanta da duka hannayenta cikin maimaita Istirja'i,rigar shimin dake jikinta ta jik'e sharkaf da zufa"Sudaida lafiya?Zafi kikeji haka? Yamik'e barin kunna miki mukayyib. Takalleshi a rikice"Yaya D'ansarai ba zafi nake jiba,jikinta yakama rawa"kasan abinda nake gani kuwa?Wai...yatari numfashinta ta hanyar sa tafin hannun damarshi ya rufe mata baki sannan yakalleta cikin kulawa"ba wai bana so inji abinda zaki fad'a bane a ah ina miki kwad'ayin samun lada saboda bin umarnin Manzon ALLAH dan yayi hani da bayyana mummunan mafarki,duk abinda kike gani to ki nemi tsarin ALLAH akan abinda kike ganin,kiyi tofi a gefen hagunki sau uku"A'uzu billahi minashshaid'anir rajim "sai ki juya daga gefen da kika kwanta zuwa d'aya gefen.Wannan shine abinda yadace.Ta rungumeshi tana sauke numfashi"nagode da wannan tunatarwan. Ranar wata Litini aka bud'e makarantar Julaibib a zangon karatu na farko me suna... "Alfurqan Science Academy. Musulman Zonkwa sunyi murna da farin ciki da samuwar wannan makaranta,Ya'ya dayawa an ciresu daga wasu makarantu an dawo dasu nan.Julaibib ya so kwarai ya zauna da Iyalinshi dan bata jin dad'i,sai dai hakanshi bata tadda ruwa ba dan da yammacin ranar ya mata sallama yakama hanyar Gidan-Waya washe gari da sassafe zasu tafi Jos asibitin k'ashi na Bima abokin karatunsune yayi hatsari a hanyar shi takomawa garin na su na Jos yakakkarye. Sai k'arshen mako yazo,gidan Hajiya yafara zuwa kamar yadda yasaba,su Hajiya an dad'a tsufa sai dai Alhamdulillah tsufa me amfani tayi dan bata rikice ba,tana gane kome da kowa,sun dad'e suna hairarsu kamar yadda suka saba.Bilkisu kuma tagaji da jiranshi kamar yadda Sudaida tace mata ta zauna ta jirashi ba sai ta bishi ba ai zo.Tanata k'unk'uni tana turo baki gaba,Sudaida tana shiga D'akin-girki Bilkisu tasa dogon hijab d'inta har yana jan k'asa,wai haka sabuwar malamarsu ta Alfurqan take sawa,shine tace lallai itama haka zata dinga sawa Julaibib kuwa yad'inka musu ita da Walida kala-kala,tayi sand'a tafice da sauri. Hajiya tana ganinta tace kai wannan yarinya da gaggawa kike hannun hagu a romo"sarauniya me D'ansarai ai ban ce zan rik'e miki uba ba.Julaibib yayi yar dariya ya tuno da Sudaida itace me fad'a mata haka musamman idan tana jin haushin su.Bata kula Hajiya ba tarungumeshi tawani shagwa6e"Baba tun d'azu kazo kayi zamanka anan.Yashafa kanta "Esbeeer Megadona yanzu zamu tafi. Takalleshi cikin farin ciki"Baba yau Mama ta barni ni na had'a maka lemun karas,kashu da citta"kaji d'and'anon kuwa?Yagirgiza kai.Wallahi sooo luciousss...yadda tayi furucin yabasu dariya. Shima yace"thank you sooo very much my dear Bilkisu. Yarik'o hannunta suka mik'e"Hajiya barinje in sha lemun nan tunda sanyin shi. Bilkisu tad'an zaro idanu tana kallan Hajiya"ALLAH na mantane amma yanzu zan kawo miki naki dama Mama bata san nafito ba.Hajiya tace"tafi can sai yanzu kika tuna dani to bana sha.Tabi Julaibib da sauri da yasa takalmanshi yafara tafiya"ALLAH kuwan sai kin sha idan ba haka ba nima bazan kuma shan dabgenkiba. Da daddare Julaibib yatafi kai Bilkisu da Walida hutun k'arshen mako gidan Inna,Sudaida tana shan rake taji tauuu...tauuu...tauuu...!k'arar harbin bindiga har tana hango kyallinshi ta tagar da take bud'e,raken hannunta ya su6uce, tarintse idanunta cikin matsanancin tsoro duk da abin ya zame musu jiki to amma na yanzu ya firgitata wallahi, tana Istirja'i yashigo da sallama yazauna yana kallanta"lafiya kuwa?Tad'ago tana kallan shi cikin mad'aukakin mamaki"kai bakaji harbin bindigar da akayi yanzu a jere har sau uku ba? Yaya D'ansarai anya garin nan za a samu kwanciyar hankali a cikin shi? Yamaida kai da bayanshi jikin kujerar yana murmushi"matsoraciya kawai...Ta tsare shi da idanu. Yad'an kalleta" ke ba kome fa na...Ta girgiza kai"ba kome fa kace?Haka shekaran jiya danaje gida muna magana da Baba shima yace wai ba kome,to ni abinda bangane ba,a ba kome d'in me yakawo wannan harbe-harben ba dare ba rana?Anya ba koyan harbin suke yi ba? Baza kusa yan lek'en asiri su binciko muku me ake ciki ba Yaya Julaibib? Yaciro wata takadda daga aljihun gaban rigarshi da biro yafara lissafe-lissafenshi a ciki"to me kika ga anyi?Koma me sukeyi bata shafe muba...tayi shiru tana kallan shi aranta tanata maimaita Kalmar"kome sukeyi bata shafe muba... Yagama ya bud'e Laptop d'inshi yayi yan rubuce-rubuce a ciki ya rufe sannan ya kalleta"gobe Insha-ALLAH zani Kaduna mun tura kud'in kayayyaki amma har yanzu shiru tun wancan makon muke waya da manager na wajen amma sai wani hanya-hanya yake mana toh zani inga koma meye ganin idanuna. Takalleshi wani iri ranta ba dad'i"nifa tafiye-tafiyen nan naka ya fara shigar min hanci da k'udundune wallahi,yana hanani rawar gaban hantsi, jiya fa yakamata kazo garin nan baka zo ba,na kauda kai banyi magana ba,yau kazo sai kuma gobe kace Kaduna za ka tafi washe gari da sassafe ka koma Gidan-Waya?A k'arshen makon ma baka hutaba?Ni gaskiya ban yadda ba shi Yaya Musaddiq d'in yatafi mana.Yayi yar dariya"Zaujatiii...uwar gidata anan duniya har a aljannah;ai ko Musaddiq yaci ya huta ko da yaushe shi yake tafiya,rabona da inje Kaduna saro kaya na kusa shekara fa,ko wannan karon bashi yace inje ba nine naga dacewar hakan shima yad'an huta...Kyan rawa da makar6i,amma kisha kurumunki Sudaidan D'ansarai ai na kusa ajiye koyarwar da nakeyi in dawo kan wannan makarantar gaba d'aya, kinga tafi-tafiye ya k'are sai mu manne kamar k'arfe da mayen k'arfe kullum muna tare mutu ka raba takalmin kaza ko?Yad'age gira yana mata wani kallon k'auna.Tayi shiru ta kyaleshi,dan wannan tafiyar da zaiyi ta 6ata mata rai sosai wallahi. Shi kuma yacigaba da maganar shi duk da bata kulashiba,ai ya san tanaji tunda ba kurma bace,ranar litini d'inma bazan bar garin nan ba har sai munje an sake miki scanning ni wannan girman cikin yana bani mamaki a watanni biyar kacal.Hummm kawai tace tazame ta takwanta dakyar. Da safe suna karyawa yazuba mata idanu yana zancen zuci ganin ta tsame hannunta a abincin wai ta k'oshi kuma ba wani cin kirki tayiba "wannan cikin gaba d'aya ya canja mishi Sudaida,ga yawan laulayi,ga rashin samun ishashshen bacci saboda munanan mafarkai,ga wasu k'ananan k'uraje da suka fito mata a duka la66anta ba irin magungunan da bata shaba dan su warke amma abin yaci tura,tayi sanyi sosai.A hankali tajingina bayan ta da jikin kujera tana yamutsa fuska"wash ALLAH!... Zaujiii...bakaji bayana ba kamar zai 6alle.Yafara mata tausa "sannu Sudaida. Tad'an kalleshi kawai. Aminu yashigo da sallama shima yakalleta cikin tausayi"Sudaida ko asibiti zamu tafi ne? Tad'an yi luuu...da idanunta kamar zata rufe sai kuma takalleshi"Yaya Aminu sai gobe za muje.To ALLAH yaraba lafiya,yamik'a ma Julaibib hannu sukayi musafaha sannan yazauna suka gaisa da Sudaida. Suna hirarsu da Julaibib amma suna sakota,wani abun tayi magana wani kuma ta musu shiru. Aminu yamik'a mishi katin za6enshi(voters card)ni dai wannan karan bazan yi za6e ba,tunda ko ka za6a wanda kakeso to a k'arshen wanda su suke so shine sai lashe za6en da kuri'a mafi rinjaye,magud'i kiri da muzu haka ake yinshi.Bai wani dad'e ba yamusu sallama yatafi.Shima Julaibib yayi shirin tafiya Kaduna. Yazauna a hannun kujerar da take kwance suna kallan juna na wucewar wasu dak'ik'u, tarik'e hannunshi"ban so tafiyar nan ba har ga ALLAH, ina ji ajikina kamar ba zamu sake had'uwa ba, idanunta suka kawo ruwa.Haba Zaujatiii...me yasa kike wannan furucin? Insha-ALLAH kafin magriba ai na dawo,sharrr...hawayen suka zubo mata,yafara goge mata"kiyi hak'uri Sudaida kome ya kusa zuwa k'arshe,kullum muna tare har sai kin gaji da ganina,yazame hannushi daga cikin nata,yamik'e yana gyara kwalar farar rigarshi"zo muje kawai kiyi zamanki a gidan Inna ko gidan Kawu idan na dawo sai in tsaya in d'auke ki.Uh uh ba kome idan naji bazan iya zaman ba to sai in tafi,tawani marairaice" Tafiyar za kayi Yaya D'ansarai? Eh Sudaida ina 6ata lokaci gwamma inyi maza in tafi tunda ba kwana zanyi ba.Yasunkuya yabata sumba,tashafa k'asumbarshi sukama juna adabo.Har yakai k'ofa takirashi"Yaya D'ansarai...yatsaya cak sannu yajuyo "na'am Zaujatiii...suka sake zubama juna idanu na wucewar wasu dak'ik'u,tasauke gwauran numfashi a sanyaye tagyad'a kai "shikenan adawo lafiya. A gidan Inna ma Bilkisu kuka tasa mishi ita bazai tafiba,ta had'a kai da bango tana sheshshek'a,dakyar shi da Inna suka dinga lalla6ata sannan tayi shiru ita da Walida suka rakoshi k'ofar gida tana k'ananan hawaye,yashiga mota ya zauna yana d'aura belt tarufo mishi motar"Baba ALLAH yatsare a dawo lafiya...Walida ta koma Gidan-Waya da gudu ita bata wani damu sosai ba.Tad'aga hannu tana mishi adabo,yaja motar yatafi,zai sha kwana ya leko tana tsaye, tad'aga murya"Baba Qad uhibbbuka... shima yamata adabo sannan yasha kwana yana murmushi furucinta"My dear Bilkisu kenan nima ina k'aunarki. Tafiya yake yi amma yanaji kamar yajuya wajen Iyalinshi,ranshi ba dad'i har yashiga Kaduna garin gwamna,kiran Sudaida yashigo yad'aga da karsash"Zaujatiii...gani a garin gwamna.Nayi tunanin dama yanzu ka shiga.To ya jikin? Ya tambayeta cikin kulawa.Da sauk'i yanzu bana jin wani ciwo sai dai na yau da gobe kawai irin na mace me juna biyu,yanzu ma na idar da sallah walha,na kuma maka addu'a ALLAH yatsare min kai a duk in da za ka shiga,nima na rok'i ALLAH yarabani da cikin nan lafiya,yabani nak'uda sassauk'a,sannan nace barin kira D'ansarai mijin Sudaida inji muryarshi da kalamanshi su k'aramin nishad'i. Oh ya rahmanu rahim...nagode ma Ubangiji da yabani ke a matsayin mata,ke macen albarkace,kece uwargidata har a aljanah,yasake yin k'asa da murya yana fad'a mata wasu kalamai wanda sirrin sune,tako kyalkyale da dariya"kai Ustazu...? Shima dariyar yake yi"na rantse miki da girman ALLAH Zaujatiii...Ko baka rantse ba na yadda da kai,ba abinda yake fitowa daga bakin ka game da soyayyarmu sai gaskiya"ALLAH yamaka albarka Abu Bilqisss...sai ka dawo d'in.Ya amsa da to sannan sukayi sallama ya zubama tashi wayar daya cire a kunne idanu,yayi lallausan murmushi yana shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi"Ummu Bilqisss...ya fesar da iska ta baki ta hanci,sannan yasa wayar a aljihu. Duk yadda yaso ya koma gida a ranar hakanshi bata tadda ruwa ba, sai dai sun gama kome da Manager,ashe daga can Lagos aka samu matsala amma kome ya dai-daita.Washe gari kuma wayewar gari litini yana shirin barin garin gwamma gari yarikice anata k'one-k'onen tayoyi da kisan rayuka na babu dalili,cikin damuwa Sudaida takirashi"ka riga ka taso ne?A ah.Sukayi shiru na wucewar wasu dak'ik'u"to ALLAH ya sauwak'e wai meye musabbabin wannan fad'an?Sudaida ai kin san idan guguwar siyasa tafara kad'awa sai dai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Tagyad'a kai"hakane,muma nan d'in sai a hankali,wallahi mutane dayawa suna ta kwashe muhimman abubuwansu suna tafiya wai sai angama za6e kome ya dai-daita sannan zasu dawo,Abu me aikin Inna ma yanzu tazo tamin sallama zata tafi k'auyansu, hankalin jama'a da dama yak'i kwanciya tunda sukaji Kaduna ba lafiya,yanzu mu kuma sai yadda hali tayi kenan?Ta tambayeshi.Eh Sudaida amma nan in da nake ba a kome sai dai ansa matakan tsarone ba shiga ba fita, amma Manager yayi waya da babban d'an shi sojane yanzu zai zo yafitar dani tunda dama rigimar a cikin garine.Ta amsa a sanyaye"to ALLAH yasa. Tana zaune cikin tsananin tsoro da damuwa na rashin mafita Aminu yashigo"ke Sudaida ki d'auki abinda zaki iya d'auka me mahimmanci yanzu zamu bar garin barinje in dawo...ta tari numfashinshi "har dasu Baba?Yakoma ya zauna tun safe nake magiya da rok'onsu su shirya mubar garin"gudun hijira wajibi ne idan kaga ba dama ka tsere...inji Garba Super,sunk'i toh ni dai gaskiyar magana tafiya zanyi dan wuya ko da magani ba dad'i, sunce basu hana duk me tafiya tafiya ba su dai sunanan,barinje ATM ki zama cikin shiri kafin in dawo. A sanyaye ta gyad'a kai sannan tasake kiran Julaibib sai dai tak'i shiga tabi D'akin-shak'atawar da kallo"to me zata d'auka? To suma da suka ankare mutanan garin suna tafiya sai suka tare hanyoyi ba shiga ba fita dan suna da wani k'uduri a zukatansu amma a zahirance fad'i suke ba kome ba kome,dole Aminu ya hak'ura.Bayan sallar la'asar wata motar roka shak'e da abinci da mutane hanya tabiyo dasu ta garin suma da gani ba tambaya yan gudun hijirane ko da wani gari suka fito? ALLAH masani. Direban a rikice yake sunata tsayar dashi amma yak'i tsaya"wanda maciji ya sare shi idan yaga tsumma sai gudu...Kawai yayi k'undunbala zai bi takansu sai suka tarwatse daga tsakiyar titin ya wuce cikin tashin hankali suka rufa mishi baya, saboda rikicewa sai sitiyarin yakwace mishi,take ta daki sabon masallacin mak'era da ake kan aikin ginawa, kowa yayi ta kanshi dan sun kusa cin musu,suka fantsama cikin gari gidajen mutane a kid'ime,su kuma ganin wannan ya dad'a tayar ma da mutane hankali musamman mata.Sudaida tashiga D'akin-girki ta sauke abincin data d'aura dan bata da kwanciyar hankalin da zata iya k'arasawa dama tun karin safe bata kuma sa kome a bakin taba. Takira Julaibib amma yana ganin kiran yak'i d'agawa a k'arshema yasa wayar a yanayin shiru (silent)saboda d'azu ta sake kiranshi akan kar yadawo, yabari ko zuwa gobe ne dan suma garin ya fara rikicewa, sai yace mata bazai iya ba yau d'in zai dawo yana ma hanya ta kwantar da hankalinta ba kome fa,kuma ta dafata mishi shayi,tayi abinci me kyau yana azumi kome dare bazai yi bud'a baki da kome ba bayan dabino sai abincinta ko da bai shigo kafin magriba ba,bai jira amsawar taba yakatse kiran ya kira Musaddiq yana tambayar shi"wai meke faruwane Sudaida ta dameni kar in dawo? Yayi tsaki"kai rabu da ita,da da wata babbar matsala ai dana fad'a maka,sun d'anyi zage-zagen sune d'azu ko dak'ik'u talatin ba suyiba suka koma k'auyukan su,in dai wannan hatsaniyar ne yau suka fara?Ka san halin mata basa raina abin tsoro,watama cinnaka za kaga tanama ihu da kururuwa a zo a kashe mata kar ya cijeta.Uh uh Musaddiq sharri dai ba kyau...to suwaye suke ta guduwa?Julaibib yasake tambayarshi.Masu guduwa dama yan ciranine amma ni dai a ganin idanuna banga wani zaunanna gari daya tafi ko mutum d'ayaba.To ALLAH yakyauta.Musaddiq ya amsa"Amin D'ansarai ka iso lafiya.Da wannan dalilin yasa yak'i sake d'aga wayarta. Sai da yashigo cikin gari sannan ya d'auki wayarshi zai tsokani Sudaida,sai dai missed call d'ari da yagani yasa zuciyarshi bugawa da k'arfin gaske kira daga kowa na zuri'arsu lambar Inna yafara kira amma tak'i shiga,fargaba ta kamashi lallai ba lafiya... A bakin hanya kuma sunyi kaca-kaca da kayan dake cikin rokan sannan suka banka mata wuta.Me neman kuka ne aka jefe shi da kashin a waki,wai saboda yak'i tsayawa suka fara k'ona shagunan bakin hanya...ALLAH Sarki shagon Ashiru Chindo suka fara k'onawa...Mtswww bahaushe me ban haushi na tanko me kan bashi...wai sai a wannan lokacin suka san eh lallai wad'annan mutanan da gaske sukeyi,suka fara neman mafita a sanda lokaci yariga yak'ure musu, dan ba a fafe gora ranar tafiya...kumamar tsanyar da wuri take tila...Dana sani mara amfani...suka cigaba da k'ona tayoyi suna watsa borkonon tsohuwa(tear gas)wallahi abu kamar wasa k'aramar magana ta zama babba,garin yayi bak'ink'irin ga har6e-har6en bindigogi ta ko ina. Yana cikin wannan hali kiran Sudaida yashigo yad'aga da sauri,cikin rawar jiki data murya tafara magana"Yaya D'an Sarai na rok'eka da girman ALLAH karka k'araso garin nan...me yafaru ne?Yak'i a keyi ka koma dan wallahi sun fara kashe mazaje suna k'ona gidajeee...tak'arasa maganar cikin sarewa saboda harbin bindiga shima yaji hakan jin kunnuwan shi.Kina ji? Ta amsa da eh ina...in...inaji...yana d'ago kai yaga gungunsu sun mishi k'awanya...zufa tasake karyo mishi Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un yafad'a,a wayar kuma yana jiyo hayaniya da surutai barkatai... wasu suna ihu wasu suna kabbara,anan kuma suna jiran fitowar shi"gaba kura baya siyaki. Sudaida tafi gidan Inna Insha-ALLAH zan zo in sameku a can yayi jarumtar fad'a mata haka. Tarintse idanunta saboda a zaba wai...wash...uhhh... bazan iya tafiya ba wallahi!wai...ALLAH na!Tafara nishin azaba Zaujiii...nak'uda nake yi haihuwa zan yi...wai...Wayyo!Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un dan ALLAH ka yafe min Yaya Julaibib mutuwa zan yi!A ah Sudaida ba nak'uda bane cikin naki fa watanni biyar ne...wallahi shine bakaji marataba!Tayarfe hannu. Yasake d'ago kai yakalleshi basu k'araso in da yake ba dan sun san ba ta in da zai gudu,yaga abinda bai gani ba d'azu bindigogi AK47,pistol, shar6a-shar6an wuk'ak'e gayama jini na wuce,adduna,tayoyi da jarka wanda ya tabbatar fetur ne a ciki,ga nishin da Sudaida takeyi cikin tsananin ciwon daya had'u da tashin hankali,sai yaji wasu zafafan hawaye sharrr... sun zubo mishi"yanaji yana gani amma ba shi da damar da zaije ya taimaketa... Sudaida kiyi hak'uri kiyi addu'a ALLAH yana tare dake,bata amsaba nishin azaba kawai take yi tana kiran sunayen ALLAH wai...ALLAH ka taima... bata k'arasa wasu suka shigo gidan.Wayyo! Yaya D'ansarai ga sunan...wani yad'auki wayar dama a k'asa take ta bud'e maganar"me D'ansarai ya isa ya hanamu yi?Zuciyar Julaibib tafara lugude...malam karka ta6a min mata yafad'a cikin k'araji.Yakyalkyale da dariya "matsoracin banza matsoracin wofi kaje ka 6uya kana magana ta waya,to idan ka isa kazo gidan na ka muyi gaba da gaba mana,I swear a gabanka zan zamu mata yankan rago kai ma mu maka,wawa kawai"filthy bastard... "Wallahi ALLAH ya fiku...yasake kyalkyalewa da wata irin dariya"eh ALLAH ya fimu mu kuma munfiku kaga dai mune zamuci gari,kabimu a hankali dan zakara a rataye baya caara.Bazan biku ba wallahi.Yajijjiga kai"that's very good,mun shigo gidan ka dan muyi bincike ance kuma kunada bindigogi to amma tunda kace bazaka bimuba za muyi maganin taurin kanka, kuma duk inda ka6uya a fad'in garin nan sai an binciko ka an kawo min kai gabana na maka yankan rago kamar yadda muka fara yima sauran tsinannun yan'uwanka. Yakalli Sudaida da take durk'ushe tana matagugu dafe da ciki,yayi murmushin mugunta"sai nayi abinda naga dama da wannan banziyar matar taka, ya kyalkyale da dariya.Kalamanshi suka soke Julaibib da Sudaida suk'ar wuk'a a k'ahon zuciya. Ambaton ALLAH takeyi a galabaice dan zuwa wannan lokacin k'arfinta ya riga ya k'are,d'an cikinta ya dunk'ule waje d'aya,wucewar wasu dak'ik'u kawai sai jini ya 6alle mata,tana kwance ko motsin kirki ba tayi,idanunta sun fara canja kala kad'an kad'an bak'in ciki yake 6acewa. Yayi jimmm...yana kallanta,yayi d'as d'as d'as da yan yatsunshi sannan yagyad'a kai bayan ya kalli sauran da suma shi d'in suke kallo"tunda kin min buk'ulun abinda nayi niyya to kema baki da sauran amfani a doron duniya,yad'aga bindiga yana gyara kunamar jiki(trigger)zan fasa k'ok'on kan matarka D'ansarai...Julaibib yafara karaji karka kasheta dan girman ALLAH kabari in zo ni ka kasheni a madadinta... yakyalkyale da dariya wannan daga bayane sadaka da karuwa...shege d'an iska ai kowa ya tuba dan wuya ba lada"may her gentle soul rest in hell...suka had'a baki wajen amsawa da"amennn...Dai dai da har6e kanta da yayi tauuu...tauuu...sai biyu jini yayi kaca-kaca a jikin bango rai yayi halinshi,suka zuba fetur sannan suka sake harba bindiga wuuuhhh...wuta ta tashi suka fita da gudu wayar ta katse. Julaibib yashiga cikin tashin hankali,ya tabbatar sun kashe Sudaida.Yayi Istirja'i yana kiran sunanta,ihun kiran sunan yasa wad'anda suka mishi k'awanya suka bud'e motar suna mazurai suka jawoshi "da uban wa kake magana tun d'azu a waya? Ko kana fad'ama sauran yan'uwanku masu sallah su kawo muku taimakone?To su zo d'in ba abinda zasu iya mana dan munfi k'arfinku har abadan duniya, yabisu da kallo duk fentin da sukama fuskokin su bai hanashi gane suba, wasu mak'otan shine,wasu ma akwai kud'ad'en da suke binsu bashi,bazato yaji an buga mishi bakin bindiga"you're very stupid ka tsaremu da idanu ba tambayarka muke yiba?Yarintse idanunshi dan yaji bugun har k'wak'walwarshi,bai gama dawowa dai-dai ba suka rufeshi da duka, naushi da mangari baji ba gani. Wasu tarin matasan hausawa suka hango sun samu mafaka,abinda yasa suka bar dukan Julaibib kenan suka rufarma wad'ancan.Julaibib yamik'a hannu yajawo wayarshi data fad'i yasa a aljihu,dakyar yashiga motar yatashe ta yana gani dishi-dishi saboda jinin da yake zuba dan sun farfasa mishi jiki bana wasa ba,yana zuwa k'ofar gidansu yaci burki wani abu mara dad'i yatsirga ilahirin gangar jiki da zuciyarshi"ina Innarshi? Baba?Walida da Bilkisun shi!?Zuciyarshi tana bugawa da k'arfin gaske saboda ganin gidan ya gama k'onewa har ya rufta,ya tabbatar koma menene a gidan ya k'one bashi da sauran amfani a doron duniya. Yafito daga motar yana jiri yana bin bango har yak'arasa gidanshi,yana cikin tafiyar ya yanke jiki yafad'i,awanni nawa yayi a kwance a wajen bai sani ba,ya farkane yaji mutane nabi takanshi cikin neman ceton rai, yarik'o k'afar wani"dan ALLAH taimakeni in tashi,yafizge k'afarshi"wannan rana ce ta kowa yayi ta kanshi,kalleni da kyau harsasai guda takwas ne a cinyoyina amma ina tafiya sai kai kana kwance babu alamar rauni me tsanani a tare da kai?Yayi gaba dan ALLAH kayita kwanciya har su zo su same ka a wajen...ai bai san da gaske zai iya tashiba sai da yaji hucin wutar da suka banka ya ta6i jikinshi. Dakyar da sid'in goshi yak'arasa gidanshi nanma ya gama ci da wuta,wani wajen kuma da sauran hayak'i,yana shiga D'akin-shak'atawar yaji kamar an sa adda an sare mishi k'afafu saboda tashin hankalin abinda idanun shi suka gani. Wayyooo...!!! Sudaida ce ta k'one k'urmus,maik'on jikinta male-male a wajen kamar anyi 6arin mangyad'a,tabbasss da a waje yaga k'onannan gawar nan to ba zai gane Zaujatiii...ce ba! Kuka yak'wace mishi jikinshi da zuciyarshi suka d'auki rawa"yanzu irin kisan gillan da akama sauran zuri'arsu kenan!?da sauran yan'uwanshi al'ummar Manzon ALLAH? Yahad'iye wani abu me zafin gaske kamar garwashin wutan da aka barbad'eshi da dakakken barkono d'an munci wayyo! Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!!!Lahaula wala quuwata illah billahil aliyul azim!!! Idanunshi suka kad'a jawur sai yaji kome yafice mishi a rai... zafafan hawaye suna zubo mishi sharrr...! sharrr...! kira yashigo wayar daya manta da al'amarinta yacirota a aljihu Musaddiq...yad'aga da sauri yana fad'in Musaddiq sun kashe Sudaida sun k'onata ina sauran Iyayan mune? Suna ina?Kaima kana inane?Musaddiq ya amsa cikin tashin hankali "saurara kaji abinda zan fad'a maka dan tun d'azu nake gwada kiranka bata shiga sai yanzu.Sun kashe su Baba a masallaci, gidajanmu, Iyayanmu, matanmu da Ya'yanmu sun banka musu wuta kafin sufito su gudu!Musaddiq yafara kuka sai dai mu bisu da addu'a kafin wa'adinmu yacika,D'ansarai sunci k'arfinmu, sunyi galaba...!D'ansarai bamu da abinda zamu kare kanmu dan nima haka nafito daga gida hannu rabbana...dakyar furucin nashi yake fita... Musaddiq me yasame kane?Saurareni kawai Julaibib meye ma bai sameniba!?Menene ban gani ba?Yak'ara fashewa da kuka"a gaban idanuna akama Adnan da Sagir yankan rago...!!! Kaiii ALLAH yatsinema arna...Julaibib k'afafuna a karye suke ga sara ba adadi a jikina,ga harsashin da suka harbeni yana cikin cikina...dakyar yake furucin Julaibib yadad'a manna wayar a kunnanshi dan maganar tashi k'asa take dad'a yi,kaima sunata neman ka ruwa a jallo dan haka ni shawarar da zan baka idan kasamu ma6uya to wallahi ka6uya,tunda ba abinda zaka kare kanka dashi...yafara tari da nishi duk tarin da yayi jinine yake fita ta baki ta hanci,yafara numfarfashi sama-sama, numfashin yana san d'aukewa,yafara magana a fizge D'ansarai mu yafema juna...abinda duk yake tsakaninmu na kud'ad'e da sauran al'amuran rayuwa duk mu yafema junaaa...!rayuwata...ta...k'are ina ji ajikina bazan kuma rayuwa a doron duniya ba!Cikina kamar ana huramin wutahhh...!!! Wai...washhh,Yayi nishi me k'arfi...jini yana zubowa tabaki ta hanci.. Ju...l...lai...bib...kumaaa...ina!yayi iya yinshi furucin yak'i fitowa yana nishi cikin tsananin ciwo... Kaskon wuta me wuyar tallafa. Na gaban wuta shi yake jin d'umunshi. 9 Rajab 1441 3 March 2020 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim ( Ra'ibs) Shafi na ashirin da biyar. Cikin tsananin tashin hankali yake fad'in Musaddiq...Musaddiq kana inane!?Shiru ba amsa yacire wayar ya duba har yanzu a had'e suke,wucewar wasu dak'ik'u Julaibib yana cigaba da kiran sunan shi Musaddiq!Dakyar ya amsa.Kana inane? Musaddiq yamirgina kai cikin ciwo"bazaiyi amfanin kome ba,na san mutuwa zan yi tawa ta riga ta k'are,D'ansarai...kab... ka6uya... k...kak... kaw... wai.Zuciyar Julaibib tasake tsinkewa yafara kuka"na rok'eka da girman ALLAH kafad'a min inda kake zan zo in taimake ka...kai kad'ai karage min d'an uwa na jini a doron duniya!yacigaba da magiya har Musaddiq yabud'e baki dakyar yace"ina wajen masallaci.Wani masallacin? Wanne Musaddiq? Yayi tambayar a gaggauce jin wayar shi tayi k'ara alamar caji saura kad'an yak'are... Musaddiq ya kasa magana sai nishin azaba yakeyi... Wanne daga cikin masallacin Muss...kafin yak'arasa fad'in sunan difff wayar takashe kanta.Yafurzar da wani huci yana kallan k'onannun k'asusuwan Sudaida sai yaji kukan cakkk...Ya tsaya,yamik'e tsaye yana mata addu'ar dacewa da rahamar Ubangiji"Zaujatiii...ya fad'i sunan yana jijjiga kai"sai ALLAH yahad'a mu a lahira... uwargidata ta duniya da lahirahh!... Koma wani masallaci ne Insha-ALLAH sai ya gano Musaddiq ya bashi taimakon gaggawa iyakar iyawarshi,zuciyarshi tabushe,wallahil-azim shima sai yayi kisa sai dai idan bai had'u da arne ba;koda zasu kashe shi,yana fita kuwa yaga k'aramar bindiga an kashe wani arne ta fad'i a hannunshi, yad'auka ya lalube aljihunshi yakwashe sauran harsashin yaloda a ciki sannan yafara tafiya cikin sand'a yana bin bango,daga nesa yahango gungunsu sun dumfaro inda yake,a hankali yazame yakwanta a cikin gawarwaki kamar shima mataccen ne. Suka zo suka wuce suna surutai da yaren Bajju,a d'an abinda yake tsitssinta daga yaren ya fahimci harsashin sune yak'are zasu koma gida su k'ara sabon lodi,dan haka yad'aga bindiga yasaita su daga kwancen ALLAH ya taimakeshi ya harbe guda uku nan take suka zube a k'asa matattu,sauran suka fara gudun ceton rai suna zage-zage a cikin gawarwakin nan akwai wanda bai mutu ba, amma dan abu kazan uban mutum yabari muje muk'ara shiryawa wallahi zai gane da gero ake koko...Julaibib yasake harba bindiga yasamu wani a kai shima ya fad'i yana ihu da kururuwa,sai da yak'ara mishi harsashi biyu sannan ya tashi yabar wajen kafin su dawo,zuciyarshi tana tafarfasa da kalaman wanda ya harbe Sudaida"zan fasa k'ok'on kan matarka...bata sauran amfani a doron duniya"may her gentle soul rest in hell... Julaibib a gaban idanuna sukama Adnan da Sagir yankan rago...ank'ona su Inna a gidajansu... sun kashe su Baba a masallaci...kalaman da suka dinga mishi amsa kuuwa a k'wak'walwarshi kenan.Sai yaji wani k'arfi yasake zuwa mishi. Yana cikin tafiya yaci karo da gawar Abdul d'in Yaya Karima an daddatsashi abun ba kyan gani,bai tsaya ba dan tsayuwar bata da amfani tunda ya riga ya mutu,su da arnan kuma kowa k'ok'arin kashe kowa yakeyi haka yakeya cin karo da gawarwaki kisan wulak'anci!Julaibib yayi yawon bin masallatai amma baiga Musaddiq ba,a wajen masallacin Malam Murtala yaga wasu mutane guda biyu an sa musu taya sun k'one k'urmusss...ba ta yadda za ayi ka gane ko suwaye wallahi,yaciga da tafiya zuciyarshi na tafarfasa daga baya yaji an harbe shi a kafad'a ashe wasu daga cikin su sun hangoshi... yajuya yana harbinsu shima har sai da harsashi yak'are,yatura bindigar a aljihu yakwanta yana a k'asa cikin mawuyacin hali jini yana zuba. A wannan rana ta litini kwana akayi ana gumurzu tsakanin musulmai da arna,duk da musulmai masu kayan aiki k'alilan ne amma sunyi k'ok'ari da k'arfin zuciya suma sun kashe arna ba wanda yayi galaba akan wani,kare jini biri jini akayi"ragasss mutuwar kasko.Toh wayewar gari ranar talata kenan kowa ya galabaita ba sauran k'arfi ba kayan aiki,ba abinda mutum zai sa a bakin salati,irinsu Julaibib masu azumi ranar litini babu kome a cikinsu sai abinda sukayi sahur a daren lahadi, ga raunuka a jikin mutane da yake buk'atar taimakon gaggawa amma kayan agajin(first aidbox) tun dare yak'are.Su kuma wad'ancan anata dafa musu abinci da kayan sha na k'arin k'arfi suna zuwa suna cika cikinsu, bayan haka kuma wad'anda akayi gumurzun dare dasu, sai suka dinga komawa gida, wasu matasan na daban suna shiga cikin gari da sababbin kayan aiki. (Tabbasss ni 'yar Ibrahim Asdilat KD...ganauce, ALLAH yasa inga Annabinmu Muhammad Sallallahu alaihi wa'ahlihi wasallam...yadda naga wannan al'amari ganin idanuna) Kuma a wannan safiyar ta talata jirgin k'asa yashigo garin musulmai suka fara hamdala ga Ubangiji cewa an kawo musu d'auki...Tabbasss d'auki a kawo ta hanyar k'arama barno dawaki dan k'ungiyarsu (CAN) ce takawo musu k'arin makamai,to a wannan lokacin ne sukama musulmai ainihin kisan k'are dangi, suka tarwatse kome da kowa na garin...musulmai sai kabbara da addu'o'i sukeyi a duwatsu suna harbinsu... amma ko gezau basuyi ba...sarkin yawa ai yafi sarkin k'arfi...Zakara a rataye baya caara;wasu na shiga gidaje sai sunma gida k'ark'af da kayan ciki sannan su banka mishi wuta,haka shaguna da koma inane, shagunan bakin hanya kuma sun kwakkwashe kome amma basu k'ona suba saboda wai anan zasu fara sana'o'insu. A wannan mawuyacin halin sukayi a rangama da Julaibib yayi matuk'ar galabaita yana numfarfashi,wata Juli ce tanuna shi"yauwa ga shegen da muke ta nema tun jiya,yabisu da kallo idanunshi sun kad'a jawur,dan tsabar rainin wayo da samun waje "kuturu da gad'a a rama.Wai har da mata suna rik'e da wuk'ak'e gayama jini na wuce,wanda za su iya harbi da k'ananan bindigogi sun rik'e,wasu da kokara da gorori, Kauuu...bazato yaji an buga mishi kokara akai"dan abu kazan ubanka you've no respect muna tsaye kaima kana tsaye? Kaci sa a ba bindiga a hannuna dana fasa k'ok'on kanka,Juli tamik'a mishi na hannunta"ga wannan"yature hannunta"rabu dashi ba yanzu zamu kasheshi ba sai yaci naman ubanshi me dogon gemunnan gashashshe; Now just kneel down,rise up your hands and close your eyes"haka yakai gwiwoyinshi k'asa yayi yadda yace.Wani da yayi tatil da uwar laifi yafara tambayarshi da yanayinsu irin ta mashaya"kai ne D'ansarai Lecturer a Gidan-Waya da nace kasamo ma yata gurbin karatu kace bata da credits d'in da za a d'auketa ko? Yayi kamar baiji abinda yafad'a ba.Sai yabuga mishi gora a kafad'a"childish monger I'm I not talking to you?Zuciyarshi tak'ara bushewa wallahi shak'a d'aya zai wannan ragowar ruwan burkutun numfashinshi yad'auke har abadan duniya a doron k'asa,sai kawai yamik'e tsaye yana kallanshi cikin idanu"Yes Indeed,I'm D'an Sarai Lecturer in Kaduna State College of Education Gidan-Waya.Wani yazo gabanshi"how dare you baka da kome amma zaka nuna mana zafin kai?Ka san harda wancan tsinanniyar makarantar taka daka bud'e yasa mukayi yak'innan?Dan na san halinka sai kasa wasu daga cikinmu sun zama irinku masu sallah,dama yara nawa kasa suka zama irinku? To suma duk mun kashe shegu saura kai...bai gama rufe baki ba Julaibib yayi kukan kura ya cafki mak'ogwaranshi,idanunshi suka firfito yafara kakari dakyar suka 6am6areshi,yafad'i gefe yana tari da maida numfashi,sai kuma ya mik'e ya dunfaro shi, yana nunashi da yatsa"yau ka gama kad'ewa har ganyanka wallahi.Julaibib da zuciyarshi tariga ta bushe baiyi wata-wata ba yakai mishi wani irin naushi da k'arfin bala'i a muk'amuk'i ahhh...yayi ihu ya tsuguna kame da wajen dan yaji naushin yadda yakamata,yana zubar da jinin bakinshi sai ga hak'ori biyu a k'asa yasake fasa ihun takaici kaciremin hak'ora? Julaibib yajijjiga kai zai sake kai mishi wani naushin yaji an bank'areshi ta baya...yayi iya k'ok'arinshi yakwace amma ya kasa dan rik'on kura taga nama suka mishi tamauuu...Idanunshi suka k'ara kad'awa jawur gangar jiki da zuciyarshi mazari sukeyi,wata jijiya ta fito rad'am a gefen goshinshi kamar shatin bulala saboda rik'on da suka mishi me bala'in azaba. Wanda aka fasama bakin ya goge jinin sannan yamik'e tsaye suna kallan kallo da Julaibib zuciyoyinsu na tafarfasa,har ya kar6i bindigar ya saita kirjinshi dai-dai satin zuciya sai kuma yayi wurgi da ita kaiii...yafad'a cikin k'araji"idan na kasheka one time naji haushin kaina wallahi...yakallesu kuci buhun abu kazan ubanshi yadda zaku iya,yatattaro miyan bakinshi me had'e da jini da kakin majinan da yayi yatofama Julaibib a fuska"filthy bastard.Yatasa matan agaba sukayi tafiyarsu. Aka fara ba Julaibib na jaki ba ji ba gani suna jaddada mishi"ai ko ba makami da hannuma zamu iya kasheka har lahira. Wayyooo...ALLAH!!!!Julaibib ya daku iya dakuwa sun mishi walmukalifatu da jiki!har ya daina numfashi,suka dinga janshi har zuwa inda wasu tarin gawarwaki suke suka jefashi,anjima zamu gasaku gashin kan saniya ba irin gashin tsire ba,suma suka juya sunata haki da numfarfashi... Wani sanyine yafara ratsa har 6argonshi kamar wanda a ka ajiyeshi a sararin dusar k'ank'ara ba kaya ajikinshi,ko ina nashi na karkarwa har ya'yan hanji,abinda ya dawo dashi cikin hayyacinshi kenan, dakyar da sid'in goshi ya bud'e idonshi guda d'aya,dan d'ayan ya kumbura suntum fatar idon tayi bak'ink'irin alamar duka da kwanciyar gurbataccen jini,wajen wani irin wari,k'arnin jini da hamami ciwukan dake cikin gawarwakin yakeyi, k'udaje kuma sukace ga sunan yau take sallah a wajen su.Abubuwan da suka faru kafin ya suma suka dawo mishi tiryan-tiryan,wasu zafafan hawaye suka fara zuba daga idonshi me lafiya sharrr... sharrr... Yafara Istigfari wucewar wasu dak'ik'u kuma ya mirgina kai cikin ciwo"ALLAH kaine mahaliccina! ALLAH ka fini sanin halin k'uncin da nake ciki, kataimakeni.Yayi iyakar iyawarshi ya d'aga hannunshi ya kori mayatattun k'udajen da suka baibaye fuskarshi ga kuma hayaniyarsu amma abun yaci tura, k'afarshi d'aya a karye take hannayen shima haka,zuciyarshi tayi tsananin rauni yana buk'atar taimako, mak'ogwaranshi ya bushe k'amasss kamar ruwa bai ta6a wucewa ta wajen ba,miyau ma dakyar yake tsatstsafowa a bakinshi, yahad'iye wani abu me zafin gaske kamar garwashin wutan da aka barbad'eshi da dakakken barkono d'an munci,kanshi yasara,yafara mishi wani matsanancin ciwo kamar zai rabe gida biyu.A wannan tsananin ya hango gungunsu da jarka,suna zuwa suka bud'e fetur ne a ciki suka fara juyema gawarwakin har dashi sai da suka matsa daga wajen sannan suka harba bindinga tauuu... nan take wuta ta kama wuuuhhh...suma suka juya sukayi tafiyarsu suna wata irin dariya ta rashin hankali da imani. Wayyo wai ALLAH!Wato idan kaji k'i gudu to Alqur'an sa gudune bai zo ba...shi dai Julaibib bai san ya akayi ba sai gashi ya mik'e...yana barin wajen wuta tabi takan sauran.Yana dafe da bango yana d'ingisa k'afa d'aya me lafiyar dakyar...wani irin jiri ya wulwulashi ya buga da k'asa yadunk'ule yana matagugu,numfashinshi fita ya keyi wani baya shiga, zuciyarshi na mishi suya tana bugawa da k'arfin gaske kamar zata fasa k'irjinshi ta fito!Wucewar wasu yan dak'ik'u sai gashi ya zube a k'asa wanwarrr cikin d'aukewar numfashi difff! Bayan da k'urar ta lafa manya-manyan matasan arnan da akayi yak'in dasu irinsu Nuhun gidan Diryan,Julius,Shekari da sauransu da sauran su,sune suka dinga tasa k'eyar mata da k'ananan yara zuwa Police Station d'in garin suna musu zagin tsame nama da mugun alkaba'i,su kuma suna biye dasu wasu na kukan zuci,wasu na nasarari,wasu ba uh ba uh uh,haka suke tsallake gawarwaki abun ba kyan gani,kaga gawa ta kumbura ta fashe kayan ciki a waje,awani wajen kuma sun saki aladunsu suna danasha da gawarwakin...Kai ALLAH ka k'ara tsinema arna!dan wata shari'ar billahil-azim sai a lahira!. Zuwan sojoji da jiniyarsu (siren)da wasu masu kud'in suka hayo kuji fa?Daga wasu garuruwan dan su fitar da yan'uwansu tunda har lokacin basu bud'e hanya ba,haka ake ta zama a Police Station cikin mawuyacin hali,amma wasu daga cikin arnan suna ta kawoma yan uwansu masu sallah abinci da sauran kayan buk'ata.Yayin da wasu bak'in ciki kamar ya kashe su da suka ga maza da yawa na daga musulmai sun fito da ransu da lafiyarsu,sunata mamaki da takaici, to su wad'annan a ina suka 6oya ne a cikin garin da har basu gan suba? Sun manta cewa"zakaran da ALLAH ya nufa da caara toh fa ko ana muzuru ana shaho wallahi sai ya yi. (Alhaji Umar Millionaire Doka,Wallahil-azim baza mu manta k'ok'arin da kayi na fara turo da sojoji Zonkwa ba har abadan duniya,Ubangiji yasaka maka da mafificin sakamakon shi,yasanya hakan a mizanin kyawawan ayyukanka) Wannan jiniyar tasa duk wani wanda ALLAH yasa yana da sauran numfashi a doron duniya na daga maza musulmai daya 6uya yafito,nan da nan suka fara d'aukar wad'anda suke kwance cikin mawuyacin hali zuwa asibitocin garin dan a basu taimak'on gaggawa, masu gudun hijira suka fara d'aukar hanya,wasu daga su sai kayan jikinsu dan an k'one kome nasu,wasu kuma ba a k'one ba,masu sauran yan uwa a wasu garuruwan suka shiga kiransu su taimako da mota azo a d'auke su an bud'e hanya...kai rayuwa bata da tabbasss! idan ka san farkon ka,toh baka san k'arshenka,Ubangiji kamana gamdakatar da kyakkyawan k'arshe👏abinda aka tara shekara da shekaru rana d'aya da wuni d'aya an tarwatsashi har abadan duniya sai dai a fara sabon nema daga farko!. Julaibib yana cikin wad'anda aka kwasa magashiyan zuwa asibitin"Zonkwa Medical Center" Suna kwance a k'asa a d'akin da ake zama kafin aga likita (reception)sai dai tunda aka kawo su ba wanda yakallesu tsakanin likita da ma'aikatan jinya bare susa rai da wani taimakon gaggawa.Wata ma'aikaciyar jinya tashigo tana yarfa musu ruwan bala'i kamar su suka kawo kansu "gwamma ku bud'e kunnuwanku dakyau ku jini ba wanda zamu duba sai ya bamu kud'i,idan ba haka ba to sai dai ku dauwama a haka har ku k'arasa mutuwa,taja dogon tsaki" ku d'in nan kuna da taurin kan tsiya to amma hakan kuma ai yana dakyau tunda kunji a jikinku,sau nawa muna muku hannunka me sanda?bama k'aunarku, bama k'aunar zamanku a garinmu kona sisin kwabo amma naci dambun kuturu kun kafe kai da fata,sai kuma tayi lallausan murmushi"ai gashi mun muku kattt...Kisan mummuk'e. Tajuya tana cigaba da fad'an kalmomin wulak'anci da tozarci.Julaibib daya sake farfad'owa ya mirgina kai cikin tsananin ciwo da tausayin kai"banda rashin imani a ina mutum yake da wani kud'i a yadda yake d'innan da har zai basu sannan su dubashi!?Tsananin yayi tsanani a gareshi shi kad'ai yasan abinda yakeji a gangar jiki da zuciyarshi sai kuma wanda yashiga mawuyacin hali irin wanda yashiga,suna buk'atar taimako toh sai dai kuma baiga ta inda taimakon zai zoba...sai kuma yayi saurin fad'in. "ALLAH na tuba,k'udirarka tafi gaban tunanin duk me tunani! Ya Ubangajin sammai da k'assai!Ya Ubangijina na mik'a duk al'amurana gareka! Muryarshi tafara rawa alamar karyewar zuciya💔Ya Ubangijina bani da k'arfi bani da dabara sai abinda kazartai a kaina! Ubangiji ka iya mana! Yamaida idonshi me lafiyar ya rufe dan d'ayan kumburan daya dad'ayi yasa kanshi ya mishi wani irin nauyi kamar an d'ora mishi buhun duwatsu,a hankali yacigaba da maimaita addu'ar"Allahumma lasahla illah maaja'altahu sahlan wa'anta taj'alul hazna izaa shi'ita sahlan... Wallahi abu kamar wasa k'aramar magana ta zama babba kwana biyu sunanan a haka kamar yadda wannan ma'aikaciyar jinyar tafad'a mutanan d'akin sai mutuwa suke yi...wari da k'udaje kam ba a magana.Doctor Bode Davis mamallakin asibitin da wasu matasa suka shigo d'akin yana nuna musu"kun gansu sune nake so a fita dasu daga waje muna so a gyara wajen...wani a cikin majinyatan yafara zaginsu"kai Bode ALLAH yak'ara tsine maka albarka,kuma in ALLAH ya yadda kaima sai sun maka abinda suka mana,ka sanni farin sani har family card nake dashi a asibitin nan amma yanzu kace bazaka dubani ka ciremin harsashin dake cinyoyi naba har sai na baka kud'i! ALLAH yatsinema gamayyar da zaka nemi taimako a wajen wanda kuke gamayyar yak'i taimaka maka a sanda kake tsananin buk'atar haka, tirrr da irinka, wallahi nayi nadamar duk wata mu'amala data ta6a shiga tsakaninmu!Wani yakai mishi kutifo"how dare childish rat...Zai sake kai mishi kutifo Bode yace kyaleshi yaji da abinda yadameshi,in dai kanada kud'i to zamu cire maka,ko da ATM card d'inkane in dai yana aljihunka sai mu d'auka kafad'a mana pin-number mu ciro kud'in muzo mu cire maka. Yana daga kwancen ya d'ud'd'ura musu zagi sannan yace"gwamma in mutu da in baku ATM d'ina gidan kud'i su rik'e kud'in na bar musu har abadan duniya. Kai bakinka ba zaiyi mutu ba duk da kana kwance sai yadda a kayi da kai? Eh bazai mutu ba ALLAH ya fiku, mutuwata da rayuwata ba ta hannun ko wani kafiri,a hannun ALLAH take tunda gashi nan har yanzu da raina, ai ba a san ranku muke numfashi ba,kuma na rantse da girman ALLAH sai na d'auki fansa,sai na rama abinda kukama Babana da k'anina! ALLAH dai yabani lafiya zan tafi Maiduguri,na rantse da girman ALLAH duk wanda ya kwanta toh da safe sai dai ku d'auki gawarshi ku rubuta ku ajiye alk'awari ne wannan,idan ko mutum bai mutuba to ya daina baccin dare sai dai in zai dauwama a kwanan zaune dingirgir.Kai! suka daka mishi tsawa"kamana shiru komu k'arasaka.Idan kun fasa k'arasani kuba jikokin Baranzan da Zamburan bane,dan kun kashe ni ai a kwai sauran matasa irina da zasu maye gurbina insha-ALLAH. Basu sake magana ba suka tafi.Suna fita yafara kuka yana numfarfashi,yana cigaba da zagin su...Wucewar wasu dak'ik'u sai ga wasu matasa guda biyu sun zo sun d'auke shi. Julaibib yabi bayansu da kallo yana zancen zuci"kowace irin azaba zasu sake gana mishi oho!zuciyarshi tak'ara rauni hawaye yafara zubo mishi,ba zato yaji ansa hannu ana share mishi hawayen"kayi hauk'uri ni zan taimakeku,dan banji dad'in abinda aka muku ba sai dai"I have no power da zan hana.Yakalleta da idanshi me lafiyar"ma'aikaciyar jinyace tana sanye da riga da buje farare kanta da k'arin gashi tozon rak'umi guda,yakauda kai... tabbasss shima da yana da k'arfin da zai iya magana to da shima ya d'ud'd'ura mata zagi bayan ya mata dukan mutuwa wallahi. Tabisu da kallo cikin tausayi"casualties ne rututu all of them ramshackle.Tayi tsaiii...cikin tunani ta yaya zata taimakesu?Sai kuma ta jijjiga kai tana murmushi yes,tayi d'as da yan yatsunta "fad'uwace tazo dai-dai da zama,sai tajuya da sauri tafita. Julaibib yasake mirgina kai bangaren dama cikin matsanancin ciwo,ga yunwa ta ci ta cinye k'irjinshi ya mishi nauyi,yana tunanin ma ya gamu da gyanbon ciki,numfashinshi yafara fita sama-sama kamar zai d'auke,a cikin zuciyarshi yake fad'in "Qadarullaahi wama sha'a fa'al...a hankali yafara jin wani abu na sukarshi kamar allura a ilahiran jikinshi me zafin gaske wucewar wasu yan dak'ik'u sai numfashin shi ya d'auke yayi doguwar suma. Bobby!...takira sunan shi a rikice ganin wata shar6e6iyar wuk'a gayama jini na wuce daya fito yana karkad'ata sai walainiya take yi a hasken rana, yana wak'ar shi cikin nishad'i da karsashi: Into my heart...come into my heart love Jesus... Come in...to stay...come into my heart love Jesus... Tajijjiga kai tana amsa mishi da"amennn.Yayi yar dariya"amennnn,fa kikace are you kidding me? Tagirgiza kai"Absolutely no...duk da zuciyarta lugude take yi karfa ya da6a mata wuk'ar a ciki"eh haka nace amennn,mu musulmai ai mun yadda da Annabi Isah Alaihissalam a matsayin d'an aike daga ALLAH,kune dai baku yadda da Annabinmu Muhammad Sallallahu alaihi wa'ahlihi wasallam ba.Tajuya harshe zuwa yaren Bajju. "Ashyyeaggo(Ina kwana Yace oh basakut(yi hak'uri) ashe bamu gaisaba "Ashyllafiya(kin tashi lafiya) yafad'i hakan a gaggauce ya nufi k'ofar gidan zai fita. Bobby ani yake?(ina zaka)ya tsaya cak sannan yajuyo suna kallan kallo na wucewar wasu dak'ik'u,idanunshi sun kad'a jawur da 6acin rai,takauda kai,yasauke numfashi amma baice kome ba,ita kuma tacigaba da maimaita"ALLAHU-ALLAHU rabbi laa'ushrika bihi shai'a. Kira yashigo wayarshi yad'aga"kuyi gaba zan biyoku yanzun nan. Jikinta yak'ara yin sanyi dan ta tabbatar cikin gari zasu sake komawa dan an kawo mishi rahoto d'azu;hausawan daba a k'ona gidajen suba suna ta zuwa suna kwashe kayayyakinsu. Kwallah suka cika idanunta,ta had'a tafukan hannayenta alamar magiya "Bobby I beg you In the name of Almighty ALLAH karka sake komawa cikin gari.Yaja dogon tsaki yana harararta"ba abinda zai hanani komawa.Yasa hannu zai cire sak'atan k'ofar gidan tasha gabanshi,muryarta tana rawa"haba Bobby wannan wani irin rashin tausayi ne?Me mutanan nan suka muku ne?Haba Bobby kuma fa kuna da yan'uwa a garuruwan da musulmai sune majority while ku kuma minority,yanzu idan sukace suma sai sun rama abinda ku kama yan uwansu na nan yaya za kaji a cikin zuciyarka? Tacigaba da fad'a mishi kalaman da suka sa jikinshi yayi sanyi,haba Bobby nima bazan so ace an kashe ka batare da kayi laifin kome ba,addinina daban da addininka amma duk da haka you're my cousin,kuma ina son ka,wannan soyayyarce ma tasa nake zuwa in da kuke,hawaye suka zubo mata sharrr...sharrr...Bobby ka mantane "Kyan a ayyia ni anaatsi kpa shya?(Duk abinda ka shuka to a k'arshe shi zaka gir6e) " Da anyi wyi yet kasham(me munine ko kyau) Tafara kuka kasani sarai Bobby biblically ba ace kuma wani addini haka, toh abinda kukeyi kana ganin Kaza baa chat?(ALLAH yana so) A hankali ya girgiza kai.Tace to na rok'eka dan girman ALLAH kayi hak'uri kazauna a gida.Ya amsa kai tsaye sai dai idan tare zamu zauna muyita chatting for all day long.Eh na yadda.Yasake kallanta bayan haka za kimin pepper chicken,za kimin pepper soup,da irin wannan hamburger da kuka zi mana dashi da fruit salad yanunata da yatsa"concur?Tajijjiga kai"hundred percent"muje katayani ai wannan abu me sauk'ine k'wace goruba a hannun kuturu. Alhaji Salim yasaki labulan ganin sun tafi D'akin-girki,yasauke gwauran numfashi cikin dukan zuciya,al'amarin ya ritsa da sune bayan ya kawo Ummi kamar yadda yasaba idan sunyi hutu a makatanta,ko kuma ranakun k'arshen makon da ya samu damar yin hakan,amma baya tafiya yabarta,tare suke yin kwanaki biyu ko uku sannan su koma,jikinshi yayi sanyi sosai, anya zai kuma zuwa Zonkwa bare har yashigo k'auyen Madauci? Yagirgiza kai"shi dai yazo wannan yanki na k'arshe har abadan duniya,amma idan Ummi tayi aure ta ga za ta cigaba da zumunci da dangin mahaifiyarta toh shi dai bazai hana taba,tunda matar Mazon ALLAH Sallallahu alaihi wa'ahlihi wasallam Safiyya tana zumunci da yan'uwanta na jinsi Yahudawa,wannan bai zama haramun ba. Yana wannan zancen zucin Rahab tashigo"Baban Ummi.Yad'ago yakalleta ba tare daya amsa ba.Tayi k'asa da murya"Mama ta fitane? Yayad'a kai.Sai ta zauna sannan ta fad'a mishi abinda yake faruwa a asibitin da take aiki"na san zaka taimakesu, mu an hana mu musu kome da tun ranar da aka kawo su dana fara basu taimakon gaggawa. Jikinshi ya dad'a yin sanyi"nagode Rahab da kika fad'a min wannan maganar Insha-ALLAH zan taimakesu.To kazo muje ka gansu dan kasan ya azayi kafin goben.Yagirgiza kai"bazan fita in bar Ummi da Bobby kad'ai a cikin gidan nan ba.Tayi yar dariya"kana tsoro kar ya soke ya 6arke maka 'ya da wuk'a ne?Tad'an motsa kafad'a"na san ba abinda zai mata amma dan hankalin ka yakwanta barin kira Kuno da Yachat su tayasu zama kafin mu dawo ko? Yagyad'a kai"yauwa yanzu naji dama-dama wai kibiya a cikin idanu.Takama ha6a kuma dai? To anyi ba ayi ba kenan. Bayan sun idar da sallar magriba Ummi take tambayarshi"Abbana d'azu naga kun fita da Aunt Rahab ina kuka jene?Yakalleta da kulawa "ceton ran wasu bayin ALLAH yan'uwan mu musulmai naje,gobe dasu zamu wuce Kaduna.Bobby yad'aga labulan d'akin "ke Ummi baza kizo muyi hirar bankwana bane ko me? Tad'anyi murmushi"zuwa kai amma kabari muyi sallar Isha'i.Yasaki labulan yak'arasa shiga cikin d'akin yamik'a mata wata babbar waya samfurin Samsung"to ga wannan idan kun gama you shoud let me know zani Fadiyan Guga ne.Takar6i wayar ranta ba dad'i, a daren litini yashigo da manyan wayoyi sunfi hamsin,da su na'ura me kwakwalwa wai duk tsintar yayi a cikin gari da tarin kud'ad'e a cikin buhu"lallai wata shari'ar sai dai a lahira wallahi!. Washe gari da sassafe sukayi sallama da kowa suka d'auki hanyar garin gwamma,ko a hanya basu samu wata matsala da jami'an tsaro ba dan kowa ya san abinda yafaru a Zonkwa, idan musulmai ne su jajanta tarebda addu'ar"ALLAH yasa kaffarace,idan kuma arna ne suji dad'in ganin mutanan da suke kwance cikin mawuyacin hali,da da dama da sun k'arasa su da bindiga,wanima gallama Alhajin Salim harara yayi"to wad'annan dai ai kuna 6atama kanku lokaci me wajen kaisu asibiti"repetitive strain injury ne dasu fa ko baku gani bane?Mun gani sai yaya?Alhaji Salim ya tambayeshi.Yamotsa kafad'a yana ta6e baki"they are in coma I don't think they will survive. Alhaji Salim yaja motar ba yare da yace kome ba. Motarsu tana tsayawa a harabar gidan sauran yaran suka fito da gudu" oyoyo Abbanmu... oyoyo Yaya Umminmu,suka ringume juna cikin farin ciki.Hajiya Bara'atu farar mace,jaruma me k'ok'arin adalci da gaskiya a duk al'amuranta tak'arasa saukowa daga matattakalar benen,fuskarya d'auke da murmushi, Ummi tasaki k'annanta ta rungumeta "Mamanmu nayi kewarki,kullum sai na yi mafarkinki. Tarik'e hannunta suka zauna"nima haka,toh ya fargaba?Ummi takad'a kai"Mamanmu al'amarin ba kyan gani sai ma kinga wad'anda muka kai asibiti mutum a raye amma ya fara ru6ewa tsutsotsi suna fitowa a jikinshi!takama goshinta da hannun dama kwallah sun ciko idanunta "kai! Mamanmu arna basu da imani kona sisin kwabo kuma...sallamar Alhaji Salim daya tsaya gaisawa da mak'otanshi da katseta daga abinda zata fad'a. "Sannu da zuwa Alhaji.Ya zauna"yauwa sannu da gida ya akaji da yara?Tayi murmushi kawai wanna ta tambayi ya masu jikin?Toh godiyar Ubangiji a kowani hali da yanayi,yakad'a kai amma abin kam ba gyan gani. Hajiya Bara'atu tama mijin na ta wani kallo dasu biyun suka san ma'anarshi duk da yana cikin damuwa sai da yayi dariya,sauran k'annin Ummi suka shiga tayashi darawa duk da basu san abinda yasashi dariya ba,Ummi ce kawai taga abinda yafaru tace musu "to kiyi shiru Ku fa a wasu lokutan baku da wayau,dan kawai kunga ana dariya sai kuma ku fara?Yaran suka kalleshi"kaima Abbanmu ALLAH sai kayi shiru.Toh nayi shiru ya daina dariyar,sai suma sukayi shiru. Ummi tamik'e"Mamanmu barinje in watsa ruwa,kuma kuzo muje daga nan kowa yabani labarin abin dad'in da Mamanmu tabashi da bama nan.Suka mik'e Yehhh...wallahi munji dad'i,munje kasuwar baje koli,munje gidan dabbobin daji har munyi selfie da 6auna da giwa da d'awisu kuma hotunan suna wayar Mamanmu tace dama zata nuna muku.Suka bisu da kallo cikin so da k'auna irin ta Iyaye da babu kamarta a wajen kowa sai su d'in har suke shige d'akin Ummi,sai tasama k'ofar mukulli dan kar wani yafito"toh duk ku zauna sai na fito daga wanka zan baku tsarabar dana siyo muku ta d'auko wayarta ta kunna musu wak'ar"Adam wa Hauwa na Ihab Taufiq nan da nan suka fara bin wak'ar. Mutane goma Alhaji Salim yad'ibo daga Zonkwa tare da d'aukar nauyin kome nasu na magani har zuwa sanda zasu samu sauk'i,sai dai a cikin watanni biyu da zuwan su"44 Nigerian Army Hospital"mutum d'ayane"Julaibib Abdullahi D'ansarai shine ya zama ZAKARAN GWAJIN DAFI. Sai dai shima a watanni biyun nan sau d'aya rakkin-rak ya farfad'o daga dogon suman da yayi yana kuka da sambatun kiran Bilkisuna,Innarmu, Musaddiq, Zaujatiii... Walida,Sudaida,da sauran sunayen yan'uwa amma wad'annan su yafi kira ko a cikin baccin shi. Sai kuma yau da yasake farfad'owa sai dai Alhamdulillahi wannan karan cikin hankali yadawo hayyacinshi,a hankali ya bud'e idanunshi yana bin d'akin da kallo,ya gane a gadon asibiti yake kwance, duk in da yasamu karaya an gyara,na hannayen shima sun warke sai dai k'afarce har yanzu da saura, ya maida idanunshi kan Ummi da take zaune nesa dashi tana magana a waya. Wacece wannan?Ya tambayi kanshi yana kuma k'ok'arin tunano a in da yata6a ganinta sai dai bangaren tunani da adana bayanai na kwakwalwarshi sun bashi tabbacin bai san taba,bai kuma ta6a ganin taba sai yau d'in,abu d'aya da zai iya tunawa shine wata ma'aikaciyar jinya tace zata taimakesu bayan nan kuma k'irjinshi yafara mishi suya sai jin wani abu kamar allura yana tsikarin jikinshi daga nan kuma ya numfashin shi ya d'auke.Idanunshi suka sake kad'awa jawur,yanzu ne yake jin asalin ciwo a jikinshi ko ina yayi tsami. Kwanakinshi hud'u kenan da dawowa daga hayyacinshi,amma ba wanda yasani saboda yana jin alamar za a shigo zai maida idanunshi ya rufe, yauma jin za a shigo da yamaida idanunshi ya rufe a haka har baccin gaske ya d'auke shi.Sai farkawa yayi yafara jin sheshshek'an kuka ana magana a hankali"kiyi hak'uri Ummi ki bar kukan nan dan banga amfaninshi ba,kar yajawo miki matsala". Mamanmu ni tausayi yake bani,duk wanda muka zo dasu sun mutu sai shi kad'ai yarage, sannan yanzu duk azabar da yasha an sake karya k'afar wai bata zauna a saiti ba?Takalleta cikin natsuwa"ba kina wajen akayi hoton k'afar ba? Kuma ai kinji bayajin da likitan yayi dan haka ba kome Ummi, ai gwamma ayi abinda ya dace a lokacin da yadace tunda ko an bar k'afar haka to daga baya dolen-dole dai sai an dawo an gyara"ayi agama ai yafi gobe adawo. Da wannan yawan kukan da kike yi ai gwamma ki dinga mishi addu'a"ALLAH yatashi kafad'a, yasa kaffarace wannnan wahalhalun rayuwar da yake ciki ko?Tagyad'a kai"to amin Mamanmu. Hajiya Bara'atu tayi murmushi"barinje wajen A'isha mu gama maganar kayan danace takawo min sai in zo mu wuce gida yamma na yi.Julaibib yasake tambayar kanshi"su wad'annan su wanene?Sune dai suka kawo shi asibiti suna cigaba da kula dashi ko shakka babu,kullum addu'arshi a garesu"ALLAH yasaka musu da mafificin sakamakonshi ya sanya hakan a mizanin kyawawan ayyukanshi. "This is my hijab...I will never remove. Wak'ar Ahmad Bukhatir data sa a matsayin ringtone d'inta tafara tashi,abinda yasa Julaibib yazabura tare da bud'e idanunshi yana kallanta.Itama abin ya bata mamaki,tabbasss da k'afarshi ba a sagale take ba,ba abinda zai hanashi mik'ewa. Tad'aga wayar da sallama,jikin Julaibib ya dad'a yin sanyi saboda ringtone d'in Sudaida kenan tun saninshi da ita da waya bata ta6a canja waba, haka kuma idan tana cikin nishad'i wak'ar da zaiji tanayi kenan,wanda a wasu lokutan shima ba zato sai yaji yana wak'ar,har rannan yakalleta "Zaujatiii...bakya gajiya da wannan wak'ar,ta masa"eh Yaya D'ansarai ai kalmomin cikin wak'ar ne babu na yarwa,ni duk wak'ok'in Ahmad Bukhatir ina sansu tunda ba harigido, gaskiya da gaskiyace kawai. Yamaida idanunshi ga kallanta. Tagyad'a kai"na'am Insha-ALLAH,tayi jimmm...tana sauraron abinda ake fad'a daga d'ayan bangaren,wani d'an lallausan murmushi ya su6uce mata gefe da gefenta fuskarta suka lotsa ciki sosai(dimple)sannan tace"fi amanillah...Ilal-liqaa.Tacire wayar a kunnanta tana kallan d'an siririn farin agogon dake d'aure a hannun damarta,tayi rubutu a wayar sannan tasata a jaka. Tamatsa kusa da gadan da yake kwance tana farin ciki da farkawarshi,cikin muryarta ta natsuwa tace mishi"sannu...ya jikin?Sai kawai idanunta suka kawo ruwa saboda tuno ranar data fara d'ora k'wayar idanunta a kanshi"yana kwance magashiyan wasu sassan jikinshi inda akwai sara da suka naman wajen yayi kore yana fitar da wani ruwa me wari,tsutsotsi yammm...sunata fitowa ta wajen, sai dai yanzu Alhamdulillahi yanata samun sauk'i,ta sauke idanunta akan k'aton d'inkin da aka mishi a kai da kafad'unshi duk sun d'auko warkewa. Tasake kallan fuskarshi sai taji irin abinda taji a ranar farko ruguzowar wani abu kamar gini a k'ahon zuciyarta,ta kauda kai da sauri,shigowar wasu ma'aikatan jinya guda biyu sanye da kakin soja ya bata tabbacin lokacin bada magani yayi.Tad'an sara musu dan suna aikin su yadda yakamata"aikinku yana kyau"bravo.Sukayi murmushi"Thank you. Tagyad'a kai"you're well come,tajuya tafita a d'akin tare da rufo musu k'ofar a hankali. Makonni uku bayan nan Julaibib yayi kyan gani fiye da zato saboda yana samun kulawa ta musamman da kuma cimar abinci me inganci da gina jiki,k'afar da aka dad'a gyarawa itama yana d'anyi tattaki da ita amma da taimokon sandunan da yake dogara jikinshi(crotch)a gajiye yashigo d'akin ya had'a zufa kashirban saboda d'an tafiyar da yayi,ya yar da sandunar yana goge zufan fuskarshi,tunani barkatai sun cika k'wak'walwarshi na abubuwan da suka faru, yanajin d'acin mutuwar kamar yanzu yafaru. Aka turo k'ofar tare da yin sallama. Yad'ago idanunshi da suka kad'a jawur ya amsa sallamar,bai kuma cewa kome ba har Alhaji Salim ya zauna yanata kallan Julaibib d'in cikin tausayi yana ayyane-ayyane a zuci,yasauke numfashi"Qadarullahi wamasha'a fa'al. Julaibib sai hak'uri dan ALLAH mahaliccinmu ya fika sanin halin da kake ciki,idan ka dogara gareshi zai samar maka da mafita a ragowar rayuwar da zakayi ga kuma tarin lada na maida al'amura gareshi.Nagode Alhaji, kuma bani da bakin da zan gode muku sai dai Ubangiji yasaka muku da irin sakamakon shi,dama kuma ina son sanin kud'ad'en da ka kashe min a asibiti nan.Alhaji Salim yagirgiza kai"ni duk abinda na maka na yi shine dan girman zatin ALLAH a matsayinka na d'an uwana musulmi me buk'atar taimako,ba wai na yi shine idan ka warke ka biyani ba,ni a wajen ALLAH nake neman ladana. Yagyad'a na sani Alhaji ban kuma man taba,kuma har abadan duniya bazan ta6a mantawa da wannan karamcin na kaba,to amma ina da kud'ad'e da yawa a asusun ajiyata ta gidan kud'i... idanunshi suka sake kad'awa jawur bani da kowa... idan ban baka kud'in ba to me ma zanyi dasune?Wa zan ba?Iyaye da Iyali da sauran yan'uwa ko? Toh duk sun rigamu gidan gaskiya, yakad'a kai cikin alhini da tsananin tausayin kai. Zuri'ata tatafi abadan,babu me dawowa har a nad'e doron duniya!!!Yad'aga hannayenshi"Ya Ubangijina!ka jikansu, ka gafarta musu!kasasu a cikin shahidan bayinka wad'anda zasu tashi ranar alkiyama jinin jikinsu da aka zubar yana k'amshin turaren almiski.Alhaji Salim yana tayashi da amsawa da"amin amin ya rabbi. Wucewar wasu dak'ik'u d'akin yayi shiru,Alhaji Salim yakatse shirun ta hanyar kallan Julaibib cikin natsuwa sannan yace"ai ko kai kake da abinda za kayi da kud'i.Julaibib yakalleshi kallan k'arin bayani.Alhaji Salim yajijjiga kai"abinda nake nufi ka samu damar da zakayi sadaka me gudana ga Iyaye da Iyalanka da wad'annan kud'ad'e ladan hakan yacigaba da binsu kamar suna rayene suna aikata aikin alherin da kansu ko kuwa?Julaibib yajijjiga kai yana wani lallausan murmushin da yamanta rabon da yayi hakan, labarin zuciya a fuska ma ana ganin alama,sai yamik'a mishi hannu sukayi musafaba "nagode,nagode kwarai da gaske da wannan tunatarwa taka Alhaji"Jazakallahu khaira-khaira jazaa'ih. Haka rayuwar Professor Julaibib Abdullahi D'ansarai tacigaba da tafiya Alhaji Salim yana kan hanyar zuwa dubashi kullum ta ALLAH, wasu lokutan kuma har da Iyalanshi,basu ta6a k'osawa ba har zuwa lokacin da likita yaga dacewar ya sallame shi dan ya warke sai d'an abinda ba a rasaba,wanda yau da gobe kuma da bata bar kome ba zata k'arasa warkar dashi. Alhaji Salim yad'aukeshi suka tafi gidanshi, babban gida kwarai da aka k'awatashi da filawoyin hibiscus da Queen of the night.Wannan gidanane ina fata zaka iya zama a cikinshi,kasan abin talaka sai a hankali,suka fito daga motar sannan yaba Julaibib mukullin d'aki guda d'aya daga cikin d'akuna shida da suke harabar gidan,yasa hannu biyu yakar6a yana ta godiya har Alhaji Salim yad'an dafa kafad'arshi"ba kome wannan ai...yiwa kai ne,ka shiga ka huta, yamik'a mishi hannu sukayi musafaha.Alhaji Salim ya wuce cikin gida. Julaibib yasa mukulli yabud'e d'akin... wani sanyi da k'amshin turaren d'aki suka daki k'ofofin hancinshi,yad'an lumshe idanunshi,rabon da yaji k'amshi me saukar da natsuwa a ilahirin gangar jiki da sararin zuciya tun Sudaidanshi tana raye, yabud'e idanu yana bin d'akin da kallo kome a kwai baya buk'atar k'arin kome sai tufafin sawa,yakwanta a gadon rigingine yayi matashin kai da hannayenshi tunani barkatai ya cika k'wak'walwarshi a haka har bacci yayi nasarar yin awon gaba dashi. God'iyar liman ba gudu ba ka ye. Alamar shiga masallaci cire takalmi. 14 Rajab 1441 8 March 2020 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs. DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION {Da Inganci Mukayi Fintinkau} Bismillahi wabihi nasta'in ...GWAJIN DAFI💔 Almost true story Daga alk'alamin🖊 Ya'yan Ibrahim Saudat A.Baba (Asdilat KD) Da Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs) Shafi na ashirin da shida. A mando sansanin Alhazai(hajji camp)wasu yan gudun hijirar Zonkwa suka yada zango musamman wad'anda basu da takamaiman in da zasu zauna,tabbasss suna samun tallafi to amma kun san k'asar tamu kome kashin dankaline...sune sukayi sama da fad'i da mak'udan kud'ad'en sai d'an abinda ba a rasaba talakwa suka samu,zasu cinye hakkin jama'a su kuma je lahira su biya a in da ba a biyan bashi da tsurar kud'i sai aikin alherin da aka aikata a doron duniya, da tallafin gidauniyar "D'angote Foundation" ta naira dubu d'ari-d'ari da aka ba mutane dashi suke jalauta rayuwar,Julaibib bai samu ko sisin kwabo ba,kuma hakan bai dame shiba,dan kud'i ba matsalar shi bane,sai dai ma yaba wasu,lokaci zuwa lokaci ya kanje Mando a gaisa da abokan arziki harma yayi ihsani ga wad'anda tasu wahalar tafi ta wasu. Julaibib ya d'auko wayarshi yana jujjuya ta makonni biyu kenan da siyan wayar tare da yin swap d'in layinshi sai dai har yanzu ya kasa kunnata, sai yayi kamar zai kunna sai kuma ya mayar ya ajiye, yau ma har ya mayar sai ya dad'a d'auko ta yayi jimmm... Sannan ya kunna,tana gama sai tuwa kira ya dinga shigowa ba k'ak'k'autawa"Yad'aga da sallama... kirane daga malamai abokan koyarwa da d'alibai;ya amsa waya sunfi hamsin kai a k'arshe gajiya yayi yasata a jirgi sannan yasamu damar fara karanta sakwanni na ta'aziyya kala-kala,daga nan ya bud'e wata wak'a da aka turo mishi wai Karmataka Studio Kano suka yi wak'ar ta'aziyya shi irin wak'ok'in nan basu dad'ashi da k'asa ba,yafara sauraro sai yaji har da yan'uwanshi yagama jinta har k'arshe,sannan ya kunna d'aya wak'ar sai yaji tsohuwar wakar da Rabi'u Usman Baba kano yayi tun lokacin yak'in Zangon-Kataf bai gama sauraroba,yakashe ya kunna yak'in Zonkwa "Zonkwa Genocide"anan yake ganin abinda bai gani ba ganin idanun shi...sun maida makarantar daya kashe miliyoyin kud'i wajen ginata filin ALLAH,haka babban masallacin juma'ar garin da aketa kashe mata miliyoyin kud'i wajen zamanar dashi,sai dai basu rusashi gaba d'aya ba,sun rataye k'aton kan allade a gaban masallacin,tarin kwalaben giya kam ba a magana da alama mashaya suka mayar da wajen. Yajijjiga kai "Manzon ALLAH sallallahu alaihi wa'ahlihi wasallam yayi gaskiya da yace babu amana tsakanin kafirai da musulmai kona sisin kwabo,duk yadda kuke dasu kuwa,taci na ciki wallahi. Sai ya tuno da wata magana da wani ALLAH Magani yata6a fad'a lokacin da yaga anata gudun hijira da ake fad'a a Kaduna"Wai musulmai suna ta tafiya to dawa za suyi yak'i?Ai sai sun dawo sun saki jiki tukuna zasu k'addamar musu... Ilai kuwa gashinan sun gani ganin idanun su. Yacire wayar a jirgi yafara gwada wasu lambobi amma ba wacce ta shiga,zai sake kira,wani kiran yashigo,ya zubama lambobin idanu anya ban san me wannan layin ba?Har ya katse ya sake shigowa yana gab da katsewa ya d'aga da sallama aka amsa tare da tambayar"dan ALLAH D'ansarai ne me wannan layin?Ya amsa kai tsaye"eh shine.Tace cikin farin ciki ALLAHU AKBAR D'ansarai Bongel ce.Nan suka gaisa tanata mishi ta'aziyya muryarta tayi rauni"mun gwada lambar ka sau shurin masak'i bata ta6a shiga ba,Baban Humaima yaje Zonkwa amma bai samu kowa na kaba,har Mando ni dashi munje amma ba labarin kome"wayyo duniya!lallai wata shari'ar sai dai a lahira. Julaibib yace dan ALLAH ki turo min lambar Doctor dana Innan Matsirga,yasake famo mata wani miki,cikin kuka tace"baka san abinda yafaru a Matsirga ba D'ansarai?Duk sukayi shiru sai yaji ta katse wayar.Yatallafi kanshi da duka hannayen shi yanajin wani irin yanayi mara dad'i yana tsirga ilahirin gangar jiki da zuciyarshi kamar wanda zai yi zazza6i.To me yafaru a Matsirga?Tambayar daya kasa samo amsarta kenan a k'wak'walwarshi, yad'auki wayar da niyyar sake kiranta sai kuma yaga gwamma yaje ya samu Doctor Manogi ya maida wayar aljihu yasa farar hula zita yafita. A harabar gidan suka yi kaci6is da Alhaji Salim da Ummi.Ummi tad'ago ta kalli Julaibib wallahi sosai take jin tausayinshi,takad'ai kai cikin jimami"ALLAH sarki kowa da irin tashi k'addarar rubutacciya tun daga Lauhul-mahfus. Alhaji zani Zari'a ne.Yau d'in nan? Yagyad'a kai"Insha-ALLAH yanzun nan.To ALLAH yatsare,bai damu da sanin abimda zaije yi a Zaria ba. Yakalli Ummi shiga D'akin-shak'atawa ki d'auko min mukullin mota yana nan a hannun doguwar kujera, taje tad'auko Alhaji Salim yakar6a sannan ya mik'a ma Julaibib,sai ya girgiza kai Alhaji kabarshi kawai zan tafi tasha.Yasaka mishi mukullin a aljihun gaban farar rigarshi"motar haya ai lalurace Julaibib,kai kanka za ka fi jin dad'in tafiya a wannan. Suka yi tafiyarsu suka bar Julaibib, yayi tsayuwar a kawu yafurzar da wani huci, can cikin zuciyarshi yana jinjina halin karamci irin na Alhaji Salim,kullum abincin nan sau uku a rana,idan ma anyi wani abu bayan abinci na ta6akalashe to shima haka za a ciko mishi kwano,shi ko da me zai saka musu bayan addu'ar da yake musu kullum,wani irin tagomashi zai musu?Lallai yaba kyauta tukwuici ko??? Yajijjiga kai"toh shima zai musu abinda baza su manta dashi ba har abadan duniya. Da wannan tunanin yashiga mota yad'aura belt sannan yatasheta bakinshi na ambaton ALLAH,yana tafiya yana tunanin al'amuran rayuwa me hawa da sauka,me cike da sark'ak'iya,me d'acin da ya zarta na mad'aci a wasu lokutan,me zak'in daya zarta na zuma a wasu lokutan"Dawaamulhal minal mahal (no condition is permanent) ba wani yanayi da yake din din din abadan a doron duniya sai buwayi gagara goyo Ubangijinmu me kowa da kome. Ya isa Teaching Hospital ya ajiye motar a inda ake ajiye motoci sannnan ya nufi office d'in Doctor Manogi amma yatarar a rufe,wani Likita yafad'a mishi yana Emergency yazauna ya jirashi idan ba sauri yake yiba...Yaciro wayarshi yashiga yanar gizo a kafar sadarwa ta Facebook,sai dai yasha mamaki kwarai da gaske da yaga tarin arnan Zonkwa da suka turo mishi da rok'on gayyata dan su zama abokai,wasu yan gaggawa hannun hagu a romo har sun tura mishi da sak'o ta messenger sai dai bai karanta ko guda d'aya ba ya gogesu yana tsaki"suna da wayau amma in da hankali yake to su basuje wajen ba,basu mayi tunaninshi ba.Masu lambarshi suma sunata mishi magana ta Whatsapp amma bai bi takan suba. Doctor Garga Ibrahim Manogi yacire farin gilas d'in da yarufe idanunshi yana nuna Julaibib "wa nake gani haka?Sai lokacin Julaibib yad'ago kai yaga Doctor Manogi da yayi wasu yan dak'ik'u kawai yana kallanshi,yamik'e tsaye suka rungume juna "ALLAH me iko Ustazu dama kana raye? Suka saki juna yabud'e musu office suka shiga,nan fa hira ta 6arke na abubuwan da suka faru har Doctor Manogi yabashi labarin abinda yafaru a Matsirga nan d'in ma kisan wulak'anci sukama musulmai wad'anda kwanansu yake gaba sun sha dakyar,sun tasa shanunsu gaba d'aya sun tafi dasu k'auyan kansu,su dai abinda yake hannnun musulmai yana tsone musu idanu,yana hanasu rawar gaban hantsi,sai dai na gaba ya dad'e dayin gaba,kuturwar uwa tilas zama dake,su cinye dukiyar su dawo gidan jiya cin busar doya da magwaro a matsayin abinci,irinsu Innan Bilkisu da sauran yan'uwansu Bongel sun musu yankan rago;a cikinsu Bello ne kawai yasha dakyar,mun dad'e muna fama da k'wak'walwarshi kafin ta dai-daita saboda irin halin firgicin daya shiga. Amma yanzu Alhamdulillahi ya warke garas,na samo mishi gurbin karatu a Jami'ar Madina yana can,amma ko jiya da mukayi waya wallahi sai da ya tambayeni har yanzu ba a ga wani daya dangance kaba ko mutum d'aya?Julaibib yad'anyi murmushi "Bello kenan,yakar6i lambar wayar shi,sai ya koma gida zai kirashi.Doctor Manogi yakalleshi"ka san ALLAH kawai zagewa za muyi kamar yadda musulman Kafanchan sukayi,duk wanda yasan yana cikin irin wad'annan mutanen to shima yazama cikin shirin ko ta kwana da makaman kare kai"tunda ba kwanciya akafi kare ba,sai dai a fishi da abun rufa. Haka suka ma musulman Kamatan haka, haka,hakaaaa sai da suka tashi garuruwa goma sha uku,amma dan rashin mutumci da da rashin hankali wasu tsinannu suke iya bud'e baki suce wai musulmai yan ta'addane,kuma gwamnati tanaji tana gani ba a d'auki wani mataki a kan suba,toh gobe ma idan sukaji sha'awar hakan ai basu da fargabar kome dan sun san idan sun kashe musulmai suna jin kamar sun kashe kiyashi ne,kuma da yake bahaushen mutum shima wani k'aton sakarai ne har yasake yadda ya koma garin Zonkwa wai da sunan cin kasuwa...na rasa ina hankali da tunanin wasu daga cikin mu yake. Sai da sukayi sallar azahar sannan suka tafi gidan Doctor Manogi,shi da Bongel suka dad'a yima juna ta'aziyya,yaba su Humaima kud'i,ran Doctor Manogi da Bongel bai musu dad'i ba saboda kud'in da yawa.Julaibib yad'anyi murmushi"kusa ranku a inuwa yanzu D'ansarai bashi da zuri'a,toh idan ban ba sauran yan'uwa abokan arzik'i na musulmai ba wa zan ba?ALLAH dai yasa tamu k'arshen tayi kyau, jikinsu yayi sanyi,suka amsa da amin.Sukayi sallama yaja motar yatafi,suka bi danjojin motar da kallo har tayi nisa ta6ace ma ganinsu. Yana zaune a harabar gidan yana alwala Misbahu k'anin Ummi yakawo mishi k'aramin Identification card(ID Card) d'in shine na"Zonkwa Internally Displaced Person daya manta dashi jiya a motar.Nagode ko?Misbahu yayi murmushi sannan yajuya yana fad'in barin d'auko hulata mutafi masallacin. Shehin malami(Professor)a Jami'ar Usman D'anfodio Sokoto(UDUS)Maimun AbdulQadir ya kawo ma Julaibib ziyara,sun sha hira har sun gaji,tun safe suke tare har bayan sallar la'asar,lokacin ne yake haramar tafiya.Cheque ya rubutama Julaibib na miliyan biyar.Julaibib yagirgiza kai"Professor kar muyi haka dakai mana wannan kud'in to ai ka kwashe kud'in asusun ajiyar takene. Yagalla mishi harara"idan ma zagina kakeyi a kaikace toh nagode,kuma ka kirani da Maimun kawai.Bazan iya ba Professor;matsayi ai ALLAH yake bayarwa kuma ya baka dan haka dole in baka,bazan k'i kiranka farfesaba.Maimun yace "uhum... wa yaga farfesa ciki fal geron sunday.Sukayi dariya dan sun tuno lokacin.Julaibib yace ai dane,yanzu cikin farfesa cike yake da dajjaja da labanun.Ya ajiye mishi cheque d'in"ba fa zan kar6a ba,na ma gode kwarai da kayi takakkiya kazo in da nake,dan me san kane zai damu da kai har kuma yazo takanas inda kake dan yaganka kuyi zumunci duk da tazarar dake tsakanin mu. Maimun yakalleshi cikin natsuwa "D'ansarai kar muyi haka dakai mana,wallahi da ina da lambar asusun ajiyarka da sai dai kaji alert. Julaibib kai ai abokin aminci da amana ne,har abadan duniya bazan ta6a mantawa da karamcinku kai da marigayi Musaddiq ba,duk in da zan ba da tarihin rayuwata to tabbasss sai kun fito a ciki.A lokacin da muke karatu a Gidan-Waya na baka wannan labarin yanzu ma zan sake ba ka"tun ina ciki mahaifina yakwanta dama,a haka mahaifiyata ta haifeni tacigaba da kula dani da sauran Yayyina su hud'u duk dani mu biyar,bata samu wani tallafi daga dangin mahaifinmu ko na ta dangin ba,kasancewar suma babu ta musu katutu,duk da haka munfi wasu daga cikinsu duk da mahaifinmu shima ba shi dashi,to amma ALLAH yatarfama garinmu nono gidan da muke ciki na shine ba haya muke yiba,wasu da yawa daga cikinsu kuma haya sukeyi,wasu kuma suna zaune a gidan da aka musu alfarma su zauna har zuwa lokacin da ALLAH ya yassare musu sukayi na su. Mahaifiyar mu tunda jajayen sawunta take sana'o'i mabambanta ta ajiye maganar aure a gefe ta kuma toshe kunnuwanta ga duk abinda zaije ya dawo na zamanta a haka ga k'uruciya ga rashin aure ba irin sharrin da ba a mataba,ita dai kawai burinta ta inganta rayuwarmu,a haka da taimakon ALLAH dana yan'uwa d'an abinda ba a rasaba ta gangand'a ta aurar da Yayyina matan,muka cigaba da gara rayuwar a yadda tazo ba a yadda muka so tazo mana ba,rannan dai ganin wahalar tayi yawa nace mata ni kawai zan fara bin mota in zama kwandasta idan na iya in samu mota in zama direba.Idanunta suka kawo ruwa tana kallona cikin jarumtacciyar zuciyarta me k'arama mutum juriya da hangen wata rana sai labari. Maimun ni da mahaifinka ba irin rayuwar da muke so kayi ba kenan,kullum burinmu ace Ya'yanmu sunyi zarra wajen ilmin addini,dan haka kayi d'amara kabani goyon baya dan girman ALLAH karka watsa min k'asa a cikin idanuna,tanuna kanta da yatsanta"madamar ina numfashi a doron duniya to Insha-ALLAH sai ka zama abin kwatance sai anyi alfahari an mori tarin ilminka... Idanun Maimun suka kad'a yanajin kamar a lokacin ta zaunar dashi tana fad'ama mishi kalaman.Julaibib mun sha wahalar rayuwa,har k'anzon abincin gidajan mak'ota take kankaro mana muzo muci.Kullum kalamanta na k'arfafa gwiwane "Maimun kayi hak'uri wata rana sai labari ba wani yanayi da yake din din din a doron duniya,a haka dakyar da sid'in goshi muka gangand'a na gama secondary,sai da nayi k'wadagon shekara uku sannan na had'a kud'in registration nafara karatu a Gidan-Waya. wasu lokutan inji kamar in gudu dan bak'ar wuya amma idan natuno da kalaman mahaifiyata sai inji k'warin gwiwa dan na san tanacan tanata k'ok'arin tara min wasu kud'ad'e kafin buk'atarsu ta taso,har zuwa lokacin da kuka shigo makarantar,tamu tazo d'aya kuka fahimci halin da nake ciki kuka taimakeni tun kafin in furta hakan,kuka yadda na dawo d'akinku gaba d'aya da zama inci abincinku,in sa kayan sawanku...da sauransu da sauransu,kun d'auke min abubuwa masu yawa game da karatuna, kuma kuna bani girma a matsayina na d'an Adam bakuyi duba da cewa k'asa nake da kuba. Mun gama karatu lafiya har na samu koyarwa,D'ansarai kazo ka d'aukeni muka tafi Jami'ar Ahmadu Bello wai ka samo min gurbin karatu...Yakalli Julaibib ban ta6a ganin mutum me irin zuciyar kaba,kai ka biyamin kud'in registration.Da taimakon ALLAH dana mahaifiyata da kai nakai matsayin da nake,toh ta yaya zan manta wannan d'imbun alheran Malam D'ansarai? Ya share hawayen da yazubo mishi sai dai shi ALLAH baya barin wani dan wani...ina matakin Senior lecturer mahaifiyata itama takwanta dama an gama cin mad'aci za a fara cin zak'in....ALLAH ya jik'anki mahaifiyata da sauran Iyayenmu kaafatan. Yakalli Julaibib"to dan na baka d'an wannan kud'in da bai wuce kacika matorka da mai ba (full tank)kawanice bazaka kar6a ba?Julaibib yayi yar dariya"D'ansarai ko tayar keke bai dashi bare mota. Babu damuwa motar ma tananan tafe Insha-ALLAH,ka kuma fara shiri dan Umrah na bana da kai zamu tafi muyi azumin ramadana a can.Julaibib yayi godiya sosai sannan yarakoshi wajen mota,anan ma sun 6ata wasu dak'ik'u kafin sukayi musafaha yashiga motar ya zauna direban yaja motar,shi da Maimun suka d'aga hannu suna ma juna adabo. Miliyoyin kud'ad'e Julaibib ya samu daga abokan arziki da gwammati,dan haka yasai fili babba yasake gina makarantar da tafi ta garin Zonkwa kome da kome gefen makarantar ya gina d'an madaidaicin gida.Ya ajiye aikin koyarwa na duk makarantun da yake zuwa, yadawo makarantarshi daya gina,suna cigaba da koyarwa da wasu malaman daya d'auka. Alhaji Salim yakalleshi cikin natsuwa bayan sun dawo daga masallaci sallar Isha'i"Julaibib na so kwarai da da matarka ta aure ka tare a gidan ka. Yad'an bud'e idanu dan mamaki"Alhaji aure kuma?Sai yagirgiza kai"zanyi zamana a haka har zuwa lokacin da nima zan daina numfashi a doron duniya.Alhaji Salim yakad'a kai dan shima ya d'an d'and'ana irin abinda Julaibib yake d'and'ana amma ba kamar na Julaibib ba. Lallai zasu tattauna cikin tsanaki,ai yana da ilmi zai kuma fahimci zama da auren zai fi mishi fiye da yak'arasa rayuwar a haka,tsananin martaba aure irin na bahaushe yasa kome tsufan mutum sai kaga yayi auren koda kuwa irin na butane kamar yadda suke fad'a. Wata d'aya bayan nan Julaibib yana zaune a D'akin-shakatawar gidan shi yana kallan kwanukan abincin da Misbahu ya ajiye,duk da yabar gidan amma kullum ta ALLAH basa gajiya sau ukun nan sai an kawo mishi abinci, yanzu idan yace a daina kawo mishi bai san yadda zasu fassara al'amarin ba, abu d'aya zaisa a daina kawo mishi wannan abincin shine suga macen aure a gidan,shi kuma bayajin wani aure a ranshi,jiya ma abinda Maimun yagama fad'a mishi kenan wai da yana da 'ya mace da tuni ya aura mishi ita"Julaibib yayi murmushi"haba farfesa gwamma da ALLAH ma yasa baka da ita 'yar tawa zan aura?Ya jijjiga kai"ai hakan shine dai-dai taci karanta ba babbaka. Ranar Juma'a bayan an sakko daga masallaci Julaibib ya tsaya suna gaisawa da Alhaji Salim,yakalleshi maganar Iyali har yanzu dai shiru bakace kome ba,yad'an shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi"zan duba...ko kuma ma dai Alhaji kasamo min yar mutunci a unguwar nan tunda ka dad'e a unguwar ka san yar babban gida. Alhaji Salim yayi murmushi"fad'uwa tazo dai-dai da zama,yakalli Julaibib "ka bani wuk'a da nama nagode,amma wani hanzari ba guduba idan kuma kaga yarinyar kaji bata kwanta maka ba fa?Ya amsa kai tsaye"zata kwanta min ko yaya take dan na san baza kamin za6en tumin dare ba, zan aureta zan kuma girmamata. Alhaji Salim yasake kallanshi"yanzu me zakayi a gida?Yad'an motsa kafad'a"bakome.To zo muje gidana akwai maganar da zan fad'a maka suka shiga mota suka tafi. Sai da suka gama cin abincin rana sannan Alhaji Salim yakalleshi cikin natsuwa"Julaibib zan baka auren 'ya ta Ummi kana son ta?Julaibib yaji wani irin yanayi na girma da nauyin Alhaji Salim,ai wata fuskar ta fi gaban mari har abadan duniya wallahi,Ummi a yadda ya karanceta ai bata da wani aibu tana da natsuwa da hankali,gata da ilmi,kai ko da ace ballagazace a dai irin karamcin da Alhaji Salim yamishi to wallahi ba abinda zai hanashi auren ta "Insha-ALLAH kuma sai ya d'orata a kan hanyar dai-dai bare kuma a kauwamen ta take.Ya amsa cikin girmamawa"to Alhaji nagode ALLAH yasaka da alheri. Yagyad'a kai"Julaibib ya kamata kasan wacece Ummi da kuma mahaifiyarta.Yayi shiru yana sauraro...Alhaji Salim yabashi labarin aurenshi da Sumayya,'yar data haifa mishi da kuma rasuwarta...Ni tun ranar daka farfad'o na tambayi sunan ka kace min Julaibib na gane ko wanene kai,da irin k'aunar da marigayiya take maka,dan haka Ummi yar wajen Sumayya(Kasham) ce,ita zan baka idan kaga kana sonta.Julaibib yabud'e idanu dan mamaki...zuciya da k'wak'walwarshi bangaren adana bayanai ta koma baya da gudu tana tariyo mishi kome daki-daki tun had'uwarsu ta farko da Kasham a Gidan-Waya ranar da sukaje yin registration... har zuwa ranar data aiko mishi da wasik'a,ruwan zamzam,farin miski da dabinon ajwa da abinda tarubuta mishi"Musha ruwa lafiya...ranar azumin ashura tara ga watan farko na musulunci Muharram...Da abinda ta rubuta a k'arshen wasik'arta Sumayya Kantiok Donatus(Kasham) Yayi shiru yana tasbihi a cikin zuciyarshi"ALLAH Alhakimu gwanin iya hakima, ALLAH buwayi gagara misali...Qudirarka da yawa take"ni Julaibib Abdullahi D'ansarai ni zan auri 'yar da Sumayya ta haifa?Lallai ba wanda yasan abinda gobe zata haifar sai ALLAH,dan shi wallahi har ya manta da wata Kasham da Sumayya a rayuwarshi...A hankali mafarkan da ya dinga yi na shekara da shekaru suka dawo mishi wannan mafarki me ban mamaki da yarasa gane ma'anarshi "Kasham da yake gani cikin shigar kayan fulani idan tayi magana sai kuma yaji muryar Sudaida. Wannan yana nuna Sudaida matar shice,haka kuma zai auri wata kenan me alak'a da Kasham d'in?Gashi kuwa ya tabbata 'yar data haifa a cikinta...kayan fulanin kuma yana nufin kenan Bafulatana ce?Yajijjiga kai"ko shakka babu tunda Alhaji Salim Iyayenshi Fulanine amma girman birni dan ko Iyayensu basuyi kiwon shanu ba bare kuma su... La'ilaha'illallah. Sai yasake tuno ranar da Maimun yake fad'a ma Musaddiq mafarkin da yayi"Wai shi da Kasham ne suke kiwon shanu a wani k'aton fili iya ganinka me cike da koren ciyayi"Musaddiq yakyalkyale da dariya"D'ansarai fulani ka koma har matarka take tayaka kiwo saboda tsabar k'auna?A lokacin bai kula suba.Yayi ma Alhaji Salim godiya sosai,amma har yabar gidan bai daina mamakin wannan al'amarin ba. Bayan tafiyarshi Ummi tashigo d'akin da sallama,ta zauna tana kallanshi"Abbana kace za muyi wata magana idan ka dawo daga masallaci, yana murmushi yace ban manta ba Ummi,ya san yana da yak'ini zata amince,sai yafara mata nasiha akan biyayya ga Ya'ya a wajen Iyayensu wajibine matuk'ar abinda suka zo dashi bai sa6ama shari'ar musulunciba,a hankali kuma yafara kambama halayenta na k'warai, ganin tana ta murmushin jin dad'i,sai ya maida abun zuga"ai na san baza ki bani kunya ba;baza ki watsa min k'asa a cikin idanu ba,ni a duniyar nan ban ta6a ganin yarinya me tsananin biyayya ga mahaifanta ba irinki,nima kinga shi yasa nake miki wata irin k'auna mumaiyiza(ta musamman) Tagyad'a kai"tabbasss ta yadda Abbanta yana mata k'auna ta musamman d'in dan kome nata na musamman ne wallahi a wajen shi. Cikin d'oki tace"me kake so in maka ne Abbana? Yakalleta cikin kulawa"aure zan miki Ummi,kuma ni da kaina na za6ar miki mijin.Da sauri ta sunkwui da kai dan batayi tsammanin abinda zai fad'a kenan,tanajin wata irin kunya na lull6eta. Yacigaba da magana "shekaru da yawa da suka wuce ina da labarin shi, mutumin kirkine... kuma nima a yanzu nayi nazarin shi tsafff...naga hakan ganin idanuna,hasashena yana bani zai rik'eki da aminci da amana,burina kullum a kanki Ummi shine kiyi aure,kiyi bautar cikin aure tunda ibadane, ranar alk'iyama ki samu sakamako mafi kyau da daraja,kisamu shiga darul-karamah (aljannah) aljannarma ina miki kwad'ayin samun mad'aukakiya (firdausss) Yayi shiru yana kallanta"Ummi kiyi magana mana ai ba auren dole zan miki ba,idan kina da za6inki na kuma bincika naga shima mutumin kirkine,toh shi zan aura miki,zan kuma ba wancan hak'uri na san zai fahimceni,tayi k'asa da murya cikin jin nauyinshi"Abbana ina fata in biku in muku biyayya a duk abinda kuka umarceni ko da bana so,zan tilastama kaina so,dan na san baza ku cuceniba,dan nima inaso agaba a bini,na san kuma sai na biku na samu albarkanku,nima zanga da kyau a rayuwata ta gaba. Yayi lallausan murmushi yana yaba hangen nesan ta"toh kin yadda da za6in Abban naki koda mutumin me gemu da k'asumba cike da furfura kamar na Abbanki?Tasake sunkwui da kai"shi wallahi haka Abba yake magana wasu lokutan sai yaba ka kunya. Haka rannan yace ma Mamansu wai tana ta wani shashshare shi,to shi gaskiya ya gaji da wannan shariyar,aure zai k'ara kuma sa'ar Ummi zai auro.Ita kuma ta galla mishi harara"dan ALLAH ka auro wacce bata kai Ummi bama.Sai yafara dariya yakalleta"ke Ummi ki zama shaida ai kinji abinda tace ko?Batayi magana ba,sai guduwa d'aki tayi ta barsu,yanzu ma tashi tayi yana kiranta amma bata dawo ba.Alhaji Salim yana da shak'uwa sosai tsakanin shi da Ya'yanshi,dan haka zaiyi wuya yafad'a musu abinda yake so na ayi ko abari kaga basubi umarnin na shiba. Haiya Bara'atu tak'arasa shigowa"to ai Alhaji wannan al'amari yayi dan shirun budurwa yaddan ta,bazawara kuma sai ta tanka.Tamishi wannan kallan nata dasu biyu suka san ma'anar ta"ko kuwa?Yana dariya ya amsa"ai zancenki ba ja kare ya mutu a juji. Ranar wata alhamis ba makarantar Islamiyya kuma dama ta gama secondary ana zaman jiran sakamako kafin a d'ora zuwa Jami'a,suna D'akin-girki Alhaji Salim yabisu yana musu sannu da aiki.Suka amsa mishi cikin sakin fuska.Yakalli Ummi "bar kwa6in nan ana sallama dake a waje.Tad'anyi jimmm...Hajiya Bara'atu ta kalleta cikin kulawa"jeki mana Ummi. Tajuya jikinta a sanyaye tana sanye da riga da zani na atamfar classic,tasa bak'in silifas da hijab tafita,sai dai bata ga kowa ba sai Julaibib,tasha jinin jikinta,ta gaishe shi duk da d'azu tagan shi a hanya da take dawowa daga gidan Alhaji Hafiz kuma ta gaisheshi.Yak'araso in da take tsaye"ai ni nake sallama. Sai tasunkwui da kai k'asa batace kome ba tana wasa da gefen hijab d'inta"to yaya na miki?nan ma shiru tayi sai yacigaba kinga karfa kiga dan na kwana biyu gemu da k'asumba sun cika fuskata toh na iya soyayya sai na zama tauraronki.Sai kuma yayi shiru yana kallanta ganin har lokacin batace kome ba.Sai yakad'a kai cikim jimamai"Oh D'ansarai marayan ALLAH ba uwa da uba ba sauran dangi da alama baka samu kar6uwa ba dan haka sai ka d'au na Annabawa kawai.Yadda yayi furucin cikin tsananin tausayin kai yasa tad'an d'ago tana murmushi,amma ba shi take kallo kai tsaye ba"Yaya Julaib...ba haka bane ai tunda Abbana ya gamsu da kai bani da ja...shima kallan fuskarta yayi..ALLAH buwayi sai lokacin yake ganin kamanninta da Sumayya har jerarrun hak'oranta farare, da manyan idanunta masu maik'o,wad'annnan sune abinda ta d'auko na ta kai tsaye da kowa zai iya ganewa.Kad'an sukayi hira yamata sallama dan ya lura a takure take. Watanni uku bayan nan aka d'aura aurensu Alhaji Hafiz yatsaya a matsayin waliyinshi, aka kai amarya gidan mijinta ana musu fatan zaman lafiya. Ummi tashiga bautar gidan aure da duka k'arfi da kuma iyawarta,zaman nasu ba yabo ba fallasa, suna mutunta juna,tana bashi girma a matsayinshi na babba kuma mijinta sama yake da ita,shima yana jin tausayinta amatsayinta na k'arama kuma mace me rauni... Yasauke gwauron numfashi a sanda k'wak'walwarshi bangaren tunani da adana bayanai tagama tariyo mishi kakaf rayuwarshi daki-daki. Yauma abinda yasa yamata haka jiya yatafi Gidan-Waya yakwaso kayansu anan yaci karo da kayayyakin Iyalinshi...abinda ya famo mishi wani miki kenan haka ya kwana ranshi ba dad'i... Ummi bata kar zomo ba sai ya bata rataya...yayi huce haushin kaza a kan dami.Yajijjiga kai"gaskiya Ummi bata cancanci haka ba,ai idan d'an kaciya baici kazaba toh tsakani da ALLAH bai kamata kuma yayi baraba...Har lokacin yana jiyo sautin kukanta dan haka ya mik'e dakyar duk da har lokacin kan nashi bai daina ciwo ba. Ruqayya...tanaji amma tak'i amsawa "haba Ruqayya...sai ya zauna ya gewayeta"Ruqayya Esbeer...ni me laifi ne,laifina kuma babbane...amma na gane kuskurena gani a gabanki na zo ki yafemin...d'ago kanki ki gani na san ke macen albarka ce,baki furta kalamanki ba har sai da kika rasa hanyar bi wajen shawo kan matsalar gidanki,ni d'innan nina tunzira zuciyarki,amma Insha-ALLAH zan kiyaye furucina...ni dai ki taimakeni ki yafemin...ta tari numfashin shi tamik'e zaune tana kallanshi da idanunta da suka kad'a jawur"na yafe maka. sukayi shiru na wucewar wasu dak'ik'u sannan ta cigaba da magana"Julaib...ina tabbatar maka kana d'aya daga cikin bayin da ALLAH yake so Insha-ALLAH idan katuno da jarabawar Annabi Ayuba Alaihissalam"ya kamu da ciwo tsawon lokaci, Ya'yanshi suka dinga mutuwa,duk jama'a suka k'aurace mishi to amma da yayi hak'uri ya mik'a al'amura a wajen Ubangijin mufa?ALLAH mahaliccin mu yace mishi "madallah da wannann bawa nawa me yawan hak'uri da juriya. Julaib...karage tunanin nan,ka sani wanda duk ya mutu toh ya mutu kenan abadan,babu sauran soyayya da k'auna da zaka nuna mishi face ka yawaita aika mishi da abincin shi(addu'a)idan kana da hali ka mishi sadaka me gudana,toh Julaib...ka musu anata aika musu da ladan kullum ta ALLAH, kaima kullum kana musu addu'a,nima ina musu, Abbana...Mamanmu, kai da d'aukacin al'ummar Manzon ALLAH ga wad'anda suka ga kisan gillan da aka musu,da wad'anda sukaji labari da sauran yan'uwanmu musulmai na garin Jos da Maiduguri da sauran arewacin k'asarnan. Duk masu ta'addancin nan tun daga duniya zasu fara ganin sakamakonsu,da izinin ALLAH fashewar kwai a saman kwalta za suyi,mutuwar kare a saura.Tad'an kalleshi"dan ALLAH kayi hak'uri ka saki ranki muyi rayuwar aure kamar yadda sauran ma'aurata suke yi cikin nishad'i da karsashi.Yasauke numfashi"Ruqayya ke macen alherice...ALLAH yamiki albarka.Tagyad'a kai"amin,shukran jazilan...Qad uhibbuka...yatari numfashinta kafin ta k'arasa furucinta"hubban jammahhh...sukayi murmushi"to yanzu muje ki bani abincin yunwa nake ji cikina ba kome sai yan hanji. Bayan ya gama cin abincin yasha magani yad'an huta,sannan tafara mishi bayani a kan gidauniyar"D'ansarai da Me-Lambu Foundation"da suka kafa musamman dan taimakon marayu da zawarawa yan gudun hijirar Zonkwa da ta samar da kud'i me tarin yawa,d'azu bayan tafiyarka masallaci Maman Hasan ta kirani tafad'a min.Baba Alhaji ma (Alhaji Hafiz) ya sake bamu gudummawa kamar yadda yasaba,sai dai wannan karan kayan masarufi muka samu kasancewar watan ramadana yanata matsowa. Abbana ma zakkarshi ta bana daya fitar d'ungurungum yabamu kud'in,shi tun jiya bayan tafiyarka Gidan-Waya yakira yafad'a min idan ka samu lokaci kaje ka kar6o dan ya kira lambarka bata shiga.Jikinshi yai sanyi "Ruqayya Ubangijine kawai zai saka muku,ina kuma rok'onshi yasaka muku da mafificin sakamakon shi. Yaciro wasu kud'ad'e masu yawa yana mata bayani "wad'annan farfesa Maimun AbdulQadir ne ya aiko dasu.Tagyad'a kai"mungode kwarai ALLAH yasaka mishi.Amin.Bayan la'asar sai inji in kar6o na wajen Alhaji zuwa jibi sai mutafi Mando mu raba musu,tunda kowa kika gani a wajen yana cikin halin ha'ula'i ne. "Julaib...wai har yanzu gwamnatin jahar nan ba wani tallafi da zata bayar ne? A yanzu dai kam babu amma bamu san a gwamnatin gaba ba tunda wannan ai kinga saura shekara d'aya tak'are tenure,ke dai Ummi Ubangiji yacigaba da rufa mana asiri duniya da lahira wanda yasamu kud'i ko yaya sai yafara sana'a kome k'ank'antarta yacigaba da addu'a ALLAH yasa mishi albarka sai kiga kome ya wuce,ai da rarrafe yaro yake tashi. Rannan naji a labarai agwam Bajju yana dad'a ba musulman Zonkwa hak'uri akan abinda yafaru wai ba a san ranshi hakan yafaru ba.Julaibib yakad'a kai"rabu dashi ai bakinsu d'aya,in banda haka a ina suka samu wad'annan mugayen makaman? Kud'in baikon da suke bayarwa duk ranar lahadi a majami'unsu bai isa yasiye suba...Gari ne dai an bar musu,ai k'asar ALLAH fad'i gareta,masu murnar sunyi kud'i da kud'in hausawa to yanzu baki gansuba"garin banza dama a farau-farau d'in bamza yake k'arewa. Ringtone d'in Ummi"This is my hijab...I will never remove.yafara tashi.Rahab ce dan haka ba tare da tayi sallama ba tad'aga.Rahab ta fashe da kuka"Ummi Bobby ne...Me yasa meshi ne haka Aunt? Tayi tambayar da kulawa.Cikin kukan take mata bayani"wai sun tafi Fadan Karshi d'auko akwatin gawa (coffin)na wani abokin su daya mutu, to a hanyarsu ta dawowa motar takama da wuta sun k'one k'urmusss. Ummi tayi jimmm...to me zata cene? Idan batace kome ba tabbasss Aunt Rahab baza taji dad'i ba,Bobby shine babban d'anta,kuma tana son ta,dan ko bata kira taba to ita tana yawan kiranta kusan rabin yaren Bajju ita ta koya mata a cewarta dole ne tayi haka tunda da Kasham tana raye zata koya mata, toh tunda ta mutu ita meye amfanin ta idan bata koya mata ba? Sauran kuma ta koyeshi a gidan Alhaji Hafiz da take zuwa. Ta tausasa murya"Aunt basakut (kiyi hak'uri)Kuka bazai dawo da Bobby ba"I know it's hurt, but you've to bear it,since you already know that sooner or later each and every one we will go back to our creator...tacigaba da rarrashinta har tayi shiru amma bata yadda ta mishi addu'a ba dan musulunci ya haramta hakan ga duk wanda ya mutu bai yadda da manzancin Manzon ALLAH Sallallahu alaihi wa'ahlihi wasallam ba.Rahab taji dad'in kalaman Ummi sosai "Thank you very much my dear Ummi for this condolence.Sukayi sallama. Sunyi shirin tafiya Umrah a can zasuyi azumin ramadana,d'aya ga wata kuwa jirginsu ya d'aga zuwa k'asa me tsark'i,garin Manzon ALLAH me safa me marwa,garin dabino da ruwan zamzam... ruwan zamzam me tarin albarka da duk buk'atar da kashashi zata biya Insha-ALLAH. Dabinon ajwa sukaci da tataccen ruwan inibi da tuffa,bayan angama kiran sallar magriba, shi da Ummi suka kalli juna suna murmushi yad'aga hannayenshi sama dan wannan lokacin amsa addu'a ne kafin a tada sallah"Ya ALLAH bayinka da aka kashe bada hakkin suba a ko ina suke a doron duniya al'ummar Manzon ALLAH! Ubangijinmu albarka wannan rana,albarkan wannan d'aki na ka me alfarma ka yafe musu!Ya Ubangijinmu mahaliccin kowa da kome jinin nan nasu daya zuba a doron k'asa,kasa yazama sanadi na samun d'aukaka da darajarsu!Ya Ubangijinmu kasa hakan yazama sandin shigarsu darul-karamah (Aljannah) Jannatul firdausss al'a'ala. "Ya Ubangiji!Miyagun da suke ma al'ummar manzonka kisan gillan nan idan wad'anda za su shiryune to ALLAH na rok'ek'a kashiryar dasu, idan kuma 6atattune abadan Ila yaumil k'iyamah... ALLAH! Kai ka haliccemu gaba d'aya, kuma gareka zamu koma gaba d'aya mun bar kome a hannunka kamana maganinsu.Ya Ubangiji! Muda mukayi saura a raye da imani to ka k'ara inganta mana imanin,idan kuma ka tashi kar6an rayukanmu muna maka magiya da sunayenka mafiya kyau,daraja da d'aukaka to ka kar6i rayukan namu muna masu imani,ranar rarrabe tsakanin k'arya da gaskiya, ranar da kud'i da Ya'ya basu da tasiri sai dai wanda yazo da ayyuka nagari...!ALLAH kahad'a fuskokinmu a darul-karamahhh... Ya ALLAH!me saukar da littafi,me gaggawan sakamako!Ka karya k'ungiyoyin abokan gaba.Ya ALLAH!Ka karyasu,ka girgiza su...!!! Ummi dake gefenshi itama ta d'aga hannayenta sama tana amsawa da"amin Julaib... aminnn ya rabbi... aminnn... k'arshe. Kome yayi farko tabbasss yana da k'arshe.Mu Ya'yan Ibrahim Godiya muke ma ALLAH marashin k'arshe daya nufemu yau da kammala rubuta labarin Julaibib Abdullahi D'ansarai ZAKARAN GWAJIN DAFI. 19 Rajab 1441 13 March 2020 We Ibrahim's Daughters👇 Asdilat KD...2geda with Ra'ibs Saudat Ibrahim Yahaya😂kisa ranki a inuwa kamar kin mari uwar Soja...Mu Ya'yan Ibrahim zamu rakaki gidan D'ansarai har D'akin-shak'atawa ki zauna kisha bak'in shayi...sai ki tambayeshi baki da baki dan wanga batu🙊gaskiya ba damu ba gaad'a da fatalwa🏃 Muhad'u a sabon littafinmu👇 Dasabon gini... A Facebook: Ibrahim's Daughters Novels. Insha-ALLAH. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!!! Baba Aminu Inuwa Ibrahim(Wambai) Jiya Alhamis ALLAH yamishi rasuwa...yan uwa kutayamu rok'a mishi gafarar Ubangiji,jinyar da akayi yasa k'arshen wahalar kenan👏😭 ALLAH YAJIK'ANSHI! ALLAH YABASHI TABBATA!👏 YAU JUMA'A AKA KAISHI GIDANSHI NA GASKIYA... D'AKI A CIKIN K'ASA! SHIKENAN FA RAYUWAR😭 Alhamdulillahi alakullu halin Wa'a'uzu billahi min amali ahalin nar. Subhanakallahumma wabihamdika ashhadu anla'ila ha'illa'anta astaqfiruka wa'atubu ilaika.