[12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 100 Bayan shakara biyu. Hauwa tana da yara biyu Khalil da mai sunana domin tun ranar da ta haihu uban ya yi mata huduba da Amina sai muke kiranta da Minal. Lokacin Hassana da Husaina sun yi wayo sosai suna yawo ko'ina da 'kafafunsu. Na sake samun wani cikin ya samu matsala sakamakon wani mugun zazzabi da na yi mai zafin gaske lokacin duka Bai fi sati shida ba. amma cikin ikon Allah fitar cikin da wata daya na sake samun wani lokacin ina tare dashi a legos. Sai ya ce sai na koma abuja Hauwa ta zo. Dana tambayeshi dalili kawai sai ya ce a gidan Baby Nana ta rasu haka zalika ma a gidan na samu matsalar ciwo mai zafi har cikinsa ya zube hankalinsa bai kwanta ba. Maganar ma sai ta ba ni dariya amma na daure ban yi ba, saboda Ina gudun ya mayar da abin rigima ina dai ta nazari akan tunaninsa kamar akwai rashin tauhidi a ciki, baby Nana ga abinda ya assasa mutuwarta. Ciki kuma da na samu ya zube wannan kuma ni dashi ba zamu taba cewa ga musababi ba, iko ne na Allah, kuma a dai gidan ai na samu cikinsu Hassana da Husaina gashi duka watanmu hud'u da zuwa ya Hauwa za ta d'auki lamarin tunda gaskiya yanzu muna zama na fahimtar juna. Ya ce da kansa zai yi mata bayani dalilinsa. Jin haka ya sanya na ce masa ba azanci ba ne yin hakan, kenan ita ba mutum ba ce, idan har yana zargin gidansa da matsala sai ya canza ba zai yiwu a ce saboda na samu ciki har ya samu matsala ya ce daga gidan ne idan ba rikici da neman tashin hankali ba. Ya ce itama tana samun wani cikin sai ta dawo. Ganin ya'ki fahimtata ya sanya na k'yaleshi domin kuwa ko bayan hali akwai girma da nauyin shekaru da suka fara turawa, yanzu nan sai ya rikice mana. Aka yi sa'a, Hauwa ba ta yi gardama ba. kwananmu biyar da dawowa abuja suka juya tare dashi. Dama Khalil tuntuni ya bar hannunta da Minal kawai ta tafi tunda tana shan mama. *** Baba Tabawa ta cigaba da taimaka mini da ayyukan gidan da dawainiyar yara duk da cewa suma rabi da rabi suke yi suna nan suna can gidan Momi sai dare suke dawowa, wataran ma sukan kwana tunda samun cikin da ya zube na cire su daga mama sun fara cin abinci sosai. Nakan zauna na yi ta mamakin yadda baiwar Allan nan ta had'a kan yara wanda ta haifa da wanda bata haifa ba ta ri'ke duka. Irin rikon da take yi wa Yusi ko ni uwarsa albarka. Ga Kamalu ma ta kar'be shi, daga hannuna. Duk yadda zuciyata take raya mini mummunan nufi akan abinda take yi ba tsakani da Allah ba ne na'ki aminta, domin babu wata alama ta mugunta da ta ta'ba nunawa akan yaran wanda zan gazgata hasashen zuciyata. Na kan zauna na yi ta tunani akan hakan wataran har na share hawaye idan zuciyata na kissima mini zarginta. To me ta yi mini idan ba alheri ba, muddin na cika 'yar halak kuwa duk irin abinda zuciyata ke raya mini akanta na yi tsalle na dire na ce ba haka ba ne. Amma wani abin mamaki a wasu lukutan sai na dinga jin mugun haushinta da kishi mai tsanani mussaman idan na tuna yadda maigidan yake bada muhimmanci kwarai da gaske akan abinda ya shafeta. Ni dalilin alherinta a gare ni nakan kawar da kaina na mayar da komai ba komai ba ne, amma Hauwa kuwa ba ta iyawa sun sha yin fad'a akanta don bata iya jurewa ba. Wasu lukutan ni nake shiga tsakani na nuna masa cewa duk sanda zai yabi matarsa ya daina yi a gabanmu zuciya bata da kashi. Amma ya'ki dainawa. Hauwa ba ta fi ni jin takaicin abinda yake yi ba, kawai ina daurewa ne, kuma ba ta fini kishinsa ba. Idan har muka ce zamu hade mata kai mu biyu abin ba zai yi kyau ba, shiyasa dai nake ta jurewa. Amma na soma yarda da maganar da kullum take gaya mini cewa duk abinda take yi akan yaranmu ba tsakani da Allah ba ne. Shi kansa maigidan ta d'aure shi, kuma baya ta'ba zuwa ya gaya mana ta yi masa lefi duk kuwa da cewar suna samun matsala mussaman ta fannin auratayya ni ina ganewa. *** Dawowar Salim daga karatu abubuwa suka fara lalacewa. Shine yaronta na biyu bayan Nusaiba itace babba sau daya kacal ta ta'ba shigo wa ta gaishemu. Shekara daya da wani abu yanzu bata sake shigowa ba duk kuwa da cewa tana yawan ziyartar uwar akai-akai, sa'i da lokaci idan ta zo su Yusi sukan shigo da yaronta, amma dai ita kam ba ta da fuska da fara'a, irin na Mamanta. Kwana biyu da dawowar yaron muna zaune ni da Baba Tabawa a falo muna hira, gefe kuma muna d'an ta'ba kallo a tibi da yake Baba Tabawa ma'abociyar son kallo ce dalilin da ya sanya ma kenan wasan kwaikwayon dadin kowa baya shigeta. Yanzu ma shi tashar arewa24 din suke haskawa. Kamalu ya shigo tsaf dashi cikin Pakistani da yake ire iren kayan da uwar rikon nasu ke sayarwa kenan, duk rabi kayan ma da suke sanyawa irinsu ne da jallabiyoyi wattanin bayane ma na ga ta yi musu sabbin dinkunan shaddodi da yadika. Sune sanye a jikinsa kansa da farar hula mai raga. Tun da ya shigo nake nazartarsa. Yana zama a gefena k'amshin turaransa ya kama mini hanci. Na zuba masa ido Ina kallo ban ce komai ba. Ya dube ni a nutse kafin ya ce." Mama mun yini lafiya?" Na amsa da "Lafiya lau ina Momin?'' A takaice ya furta." Na bar ta a gida, lafiyarta lau." Ya dubi Baba Tabawa da take ta tsokanarsa da yake da sheik take kiransa irin yadda taji maigidan na kiransa. Itama momin hakan take ce masa. Ya yi 'yar dariya yana gaisheta ta amsa tana fad'in." Mai zaka ci anan din duk da nasan dai Momi ba za ta barka malami da yunwa ba." Ya ta'ba cikinsa yana dariya ya ce." Aikuwa kamar kin sani wallahi tare ma muka ci abincin rana a koshe nake. Amma da daddare dai zan ci kwadon zogale." Ta ce." Idan wannan ne ai mai sau'ki ne, zan yi maka in sha Allahu." Ya ce." Na gode Baba." Daga haka sai ya shiru bai sake magana ba, ya fito da sabuwar wayarsa Samsung da momin nasu ta saya masa ya fara dubawa fuskarsa babu walwala. Shiru falon ya yi. Daga ni sai shi domin Baba Tabawa ta shiga kicin domin dora sanyayar dare. Kamalu tun yana yaro yake da wani irin hali na bakar zuciya da fushi. Wannan dabi'unsa ne raunanarsu kuwa yana da ala'ka da tafiyarsa karatu da kuma shekarun girma. Amma ba haushe ya ce idan ka jima ba ka ga mutum ba, to duk ranar da kuka hadu ka tambayeshi halinsa. Ni na haifi abina nasan halinsa ciki da waje. Yana da mu'amula ga wanda ya so su yi mu'amular. Amma baya jurar wulakanci a ko'ina ne, akan hakan suka dinga fad'a da Turmizi a can baya. Duk da har yanzu bai fad'a mini abinda yake damunsa ba, ni da kaina na karanci damuwa mai yawa a tattare da shi. Amma ba zan ce masa uffan ba har sai ya magantu tukkuna." "Mama ina ta kiran Lambar wayar Baba Hamusu bata shiga tun safe fa." Ya fad'i maganar yayin da yake kallona da wani irin yanayi. Na ce." Wata'kila network ne, amma Hamusu ai baya kashe wayarsa, ko jiya da yamma mun gaisa." A sanyaye ya ce." Ina tsammanin hakan." "Neman me kake yi masa ne?'' Na fad'a idona a tsaye a kansa. Bai dube ni ba ya furta." Ina son zuwa kano din ne na kwana biyu a wurinsa" Na ce." To ka gayawa Baban?" Ina nufin maigidan. Ya gyada kansa a nutse ya ce." E jiya naso na sanar masa kuma sai na manta, kuma mun yi waya fa, amma dai zan gaya masa ina jin tsoron ya ce a a ne Mama." "Ka dai gaya masa mu ji mai zai ce, itafa Momin taku?'' ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce." Mun yi maganar dazu har ta fara had'a mini tsaraba." Shiru na yi kawai ina kallonsa. Har yanzu yanayinsa bai canza ba. Na ce." Ka ga ka gaya mini dalilin da zai sanya ka zuwa kano ina tsammanin ai baku wani jima da zuwa ba ko ba haka ba ne?" Shiru ya yi bai ce komai ba sai da na sake maimaita maganarta sannan ya ce." Eh kafin tafiyarku legos ke da Baba muka je wata shida kenan yanzu. Mama ba na tsammanin zan cigaba da zama anan, can wurin Baba Hamusu zan koma?" "Akan wane dalili?'' Na fad'a ina kallonsa. Wannan maganar za ta iya janyo rikici a gidan, ta kuma janyo mana b'acin rai ni dashi, abinda maigidan ya tsana kenan. Ya dai yarda dai ya sanya akai su su yi kwana biyu gidan Gwaggo kwana biyu gidan Hajja a dawo dasu wajan matarsa. Ni kuma ba ni da damar magana ko da ta maslaha ce sai ya juyata ya yi ta neman rigima yana fad'in don ba shi ya haifesu ba zan nuna masa iyaka, zan nuna masa bai iya ba, duk yadda zan yi masa misali ba zai gane ni ba, karshe ma sai ya ce zai kira Baban Saude dole nake jan bakina na yi shiru na kyaleshi. "Mama ba zan rufe miki ba, tunda Salim ya dawo daga karatu yake yi mini wasu abubuwa na rashin kyautawa da nuna k'yama. Ba zai ci abinci tare da ni ba, ba zai kwanta d'akin da nake ba, haka zalika a cikin kwana biyun nan baya bina jam'in sallah a massalaci, ina kallonsa ya ke tafiya wani massalacin na daban. Ban san menene dalili ba, Mama amma kuma baya nunawa Yusi k'yama, wannan dalilin ya sanya ni yanke shawarar barin gidan gabad'aya domin ba na so watarana na kasa jurewa muddin a haka zamu dinga tafiya dashi babu kyakykyawar ala'ka, babu musabaha da girmama juna sai k'yama, zuciyata ba zata iya jurewa ba, Ina jin tsoron mu yi fad'a hakan ya ta'ba zumuncinku da zamantakewarku. Kin ga Momi babu komai a tsakanina da ita sai alheri Ina sonta sosai wallahi irin yadda nake sonki Mama, amma ba na so mu yi abinda duka zai bata muku rai shine dalilana." Nasan dama ruwa baya tsami banza. Amma kuma sanin da na yi wa yaron a baya kafin ya tafi karatun ba haka yake ba. Yaro ne mai nutsuwa da son mutane irin d'an uwansa Adam ga barkwanci. Nusaiban dai ce mara fuska. Na daure ban nuna b'acin raina a fili ba na ce." Kenan ba ku taba magana ba tunda ya dawo?" Ya ce." Idan na mik'a masa hannu domin musabaha baya kar'ba. D'azu da safe a gaban Momi ya yi. Hakan ya 'bata mata rai sosai ta yi masa fad'a. Shine ya tashi ya fita bai dawo ba har na fito, wallahi mama kada ki so ki ga yadda hankalinta ya tashi, shine take cewa kada na gaya miki." Shiru na yi ina nazarin al'amarin. Kamalu bai yi lefi ba domin kuwa anan ya yi aiki da hankali da kuma iliminsa. Na kuma ji dad'in abinda ya yi da har ya iya danne zuciyarsa bai biye masa ba. Shawarar da ya yanke itace mafita muddin kuwa ana son zaman lafiya. Idan har Salim bai gane abinda yake yi kuskure ba ne, to babu mamaki wataran gagarimar matsala ta faru tunda ni nasan wanene Kamalu a fagen zuciya. Amma yadda zan yi na sanar da maigidan halin da ake ciki shine matsalata. Na riga nasan rikice ne akwance domin kuwa baya d'aukar abinda ya shafi matarsa da wasa. Maganarsa daya amanarsa ce 'ya'yanta ma amana ne, a wannan ga'bar kuwa ya zame masa dole ya bincika domin tabbatar da gaskiyar abinda yake faruwa ya kuma gyara matsalar kafin ta yi nisa. [12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 101 Na ce." Abinda za a yi yanzu shine ka d'an daure kad'an, ai ni ka burgeni sosai da har ka yi irin wannan tunanin wannan ya sake nuna mini cewa Kamaluna ya bambamta sosai da wanda na sani a baya. Ka cigaba da yi masa magana kada ka biye masa ni kuma zan yi magana da Baban nasan dai haka kawai ai ba zaka kirkiri karya don jin dadi ka gaya mini ba ko?'' "Wallahi Mama babu karya cikin maganata gaskiyar abinda yake faruwa na gaya miki, menene ribata idan na yi k'aryar kuma me ya yi mini da zan 'bata shi." Na ce." To kada nunawa Momi damuwarka a fuska ka daure ka ji ko." Ya ce." In sha Allah Mama. Daga haka sai muka bar maganar muka shiga wata ina d'an jansa da wasa duk domin ganin ya manta abinda yake damunsa. Amma zahiri ni a can 'kasan zuciyata cike nake da fargabar yadda zan tunkari maigidan da maganar. Wala'ala ya fahimceni, wala'ala kuma ya juya mini manufa, amma dai tun yanzu ya kamata a ce ayi wa tufkar hanci kafin lamarin ya yi tsamari rayuka su zo suna 'baci. Daf da magriba ya tashi ya fita da zummar shirin shiga massalaci. Bayan kwana biyu ina cikin nazari domin har yanzu na kasa tsayar da abinda nake ganin shine daidai. Ba na so na yi magana ne a ce na goyi da bayan yarona wata'kila shi kansa zai iya ganin haka shiyasa hankalina bai kwanta ba har yanzu sai dai na gaza daurewa na sanar da Baba Tabawa abinda yake faruwa domin kuwa macace mai tsinkaye da nisan tunani. Ta jima tana jimantawa kafin ta ce." Ai shurun ba shine mafita ba, gwara ki gaya masa tunda shine jagoran kowa a gidan ya yi wa tufkar hanci kada lamari ya yi k'wari hatsaniya ta tashi ya ce mai yasa ba a gaya masa ba. Ina ganin duk wanda zai ce kin so kanki da zummar kawo gyara to ya zalinceki domin kuwa abinda ki ka yi shine daidai, ai ba ki za'bi Kamalu kin fifita akan Salim ba, duka naki ne kamar yadda itama Momin take nunawa, to ya kamata a ce wannan 'barakar da take ko'karin kunnowa an yi maganinta. Ajiyar zuciya na sauke bayan duk na gama sauraran maganganunta. Na ce." Shikkenan Baba, in sha Allah zan sanar da shi halin da ake ciki duk kuma yadda muka yi aki ji." Ta ce." To shikkenan, Allah Ya maganta." To daddare ina d'aki a kwance misalin takwas da rabi ya shigo mini cikin tsananin b'acin rai. Na tashi zaune da sauri gabana na fad'uwa. Ya zauna samar kujerar madubi na ce." Kai lafiya Kamalu." "Mama barka da dare." Da abinda ya fara kenan. Na amsa a takaice na ce." Menene?" Duk dauriyarsa sai da muryarsa ta yi rawa ya ce." Mama ba zan iya ba, ba zan iya jurewa ba, zan tafi kano gobe domin kuwa Salim baya neman zaman lafiya da ni." "Mai ya yi maka kuma?" Na tambayeshi jikina sanyi kalau domin kuwa wani yanayi na shiga na tsananin tausayin yaron ba komai ne ya janyo hakan ba sai maraici da rashi domin kuwa duk abinda Salim yake yi yana yi ne domin ya ga a cikin rigar arziki sa yake. "Salim tare da abokansa suke yi mini dariya har na ji daya daga cikinsu yana kirana da 'kolo, dayan kuma yana cewa mini criminal." Sai hawaye suka fara kasa tsare a kumatunansa. Zuba masa ido na yi Ina kallo a yayin da hawayen ke ta zarya a dakalin fuskarsa bai goge ba, ni ma kuma ban ce masa ya yi shiru ba sanin da na yi cewar kukan shine zai sassauta masa takaicin abinda aka yi masa. Idan an kira shi da 'kolo ai ba damuwa ba ne, ni na ji dad'i ma da ya zama 'kolon mahaddaci kuma marubucin al'kur'ani. Kalmar criminal din ce ta hargitsa dukkanin lissafina, Salim abin har ya kai haka. Abinda ya faru shekaru kusan shida yaro ya samu nutsuwa ya zama mutum shine yanzu za a tayar da shi. Cikin jan ajiyar zuciya ya ce." Mama Salim na b'akinciki da yadda Allah ya yi mini jama'a a area nan, sannan yana kishi sosai ya ga na bude massalaci manya mutane na bina sallah suna gaisawa da ni. Wannan na ji da kunnena yana fad'in duk wanda ya bi b'arawo sallah shi ma bashi da maraba da 'barawo, Mama yaushe wannan sunan zai goge a tarihin kuruciyata." Na ji kwalla ta ciko mini ido. Na daure ban yadda ta zuba ba, na ce." To share hawayenka ka daina kuka ka ajiye abinda yake faruwa a matsayin cigaba, domin kuwa haka siddin ba zaka cimma wata nasara ba tare da kalubale ba. Ita hassadar ai itace matakin komai. Kada ma ka damu, kuma ina mai tabbatar maka da cewa watarana Salim zai bi ka salla, zai kuma nemi fatawa a wurinka, wannan ni ce na gaya maka, domin kuwa Ina nan ina roka maka d'aukaka da shura ta fanninin addini anan gidan duniya, Kamalu idan Allah Ya yarda duniya da mutanan dake cikinta za su amfana da kai." Hannu yasa ya goge hawayen dake zuba a kumatunsa. Na ce." Ka kyale mini komai a hannuna, ka ji ko ka cigaba da hakuri, ni kaina a wannan ga'bar ba zan ha'kura ba dole a yi wani abu kai, amma kada ka nunawa Momi komai, ka bar abin a zuciyarka." A sanyaye ya ce." Shikkenan Mama, zan yi yadda ki ka ce din, amma ni ina so na koma can kano zan fi samu nutsuwa cigaba da gudanar da neman ilimina." Na ce." Idan har hakan shine alheri za ka koma Kamalu, ka cigaba da addu'a ka kuma bar maganar tsakanina da kai." To a daran na nemi maigidan a waya duk da nasan ba sosai yake amsa waya da daddare ba amma yadda nake jin zuciyata ba zan iya bari sai gari ya waye ba. Wayar ta katse bai daga ba sai na yi masa text na cewa Ina son magana dashi yanzu. Wajan goma da rabi ya kira ni da kansa. Na daga muka gaisa a nutse. Na ce." Baba ina son magana da kai amma kada ka juya mini don girman Allah da Annabi ka dubeta ta fuskar hankali da maslaha." A nutse ya ce." To ina jinki ai ni mai hankali ne ba mahaukaci ba, kada dai ki ce mini kin yi 'bari domin kwana biyun nan mafarkai nake yi marasa kan gado, Ina ganin ma farkon watan nan za mu zo." Na ce." Ban yi 'bari ba, amma ka sani cewa ni da kai ba mu da ikon komai akan abinda Allah Ya zartar. Idan har kaddara ta gifta cikin ya samu matsala ba za ka d'auki kaddara ba kenan?" Ya ce." Zan d'auka mana, ai mafarkan da nake yi ne ya sanya ki ka ji na yi miki wannan maganar. Na tuba ga Allah duk yadda ya yi daidai ne." Shiru na yi Ina sauraransa har ya gama maganganunsa. Na ce dalili ne mai karfi ya sanya ni kiranka a daran nan, kuma ni kaina zan ji dadin zuwanka domin ka gyara abinda yake faruwa Kamalu ne da Salim....... Duk abinda yake faruwa na zayyane masa. Ya jima yana nanata maganar da mamaki mai yawa a tare dashi ya ce." Yaushe Salim ya lalace haka, kuma abu ya faru tunda kuruciya saboda rashin hankali ka tara abokai kana gaya musu criminal?" Ya sake maimaita kalmar tabbacin hakan ya bashi mamaki. Na ce." Kamalu ya ce zai koma kano da zama can wurin Hamusu." Gyaran murya ya yi tare da cewa." Wannan kuma abinda yake cikin ranki ne shekara da shekaru shine ki ka samu mafaka dalilin wannan matsalar. Na gaya miki Amina idan har Kamalu zamansa zai koma kano to Yusi ma zai bi shi. Nusaiba da Salim Adam amana ne a hannuna. Haka zalika tunda Ina auranki yaranki ma amana ne a hannuna koda ubansu yana raye to balle kuma baya raye. Idan har kina ganin za ki yi iko da abinki ni ban iya ba sai na ce Allah Ya taimaka." Na ce." To yanzu ya kake so a yi? Kasan dai cigaba da zaman Kamalu a gidan Momi akwai matsala watarana za su iya yin abinda bai da ce ba." "Babu abinda zai faru, ki kyaleni da yaran dukkaninsu tunda kin gaya mini kin gama aikinki." Jiki babu karsashi na ce." Shikkenan sai da safe." Sai kawai na kashe wayar domin kuwa jikina yana ba ni kamar ba zai d'auki tsatstsauran mataki ba. Da lamarin na kwana na kuma wayi gari dashi dalilin da sanya kenan na kasa barin abin iyakacinmu. Na kira anti Yagana na gaya mata halin da ake ciki. Sosai kuwa ranta ya 'baci ta dinga fad'a tana cewa babu lallai babu dole muddin da cin zarafi da cin mutuncin da kuma tozarci Kamal dole ya bar gidan. Arziki ai ba hauka ba ne. Na ce." Anti Yagana tun farko fa ni dama abinda na guda kenan, shiyasa da matar nan ta bukaci zaman Kamalu a wurinta na dinga gocewa. Karin abin kuma maigidan ya'ki ya fahimceni, wai muddin Kamalu zai bar gidan sai dai su tafi da Yusi wanda na tabbatar da cewar hakan matsala ce babba. Da ya zauna mun yi magana da fahimta tuntuni da tun farko wannan matsalar bata kunno kai ba. Abu na biyu kuma ga yanayin bayanin da Kamalu ya yi mini yadda na fahimta shine shi Salim yana adawa da yadda Allah ya d'aukaka Kamalu fiye dashi, ai nasan yaron yana da kirki tun kafin ya tafi karatu dawowarsa al'amura suka lalace kishi ne shi mai yasa Allah bai yi masa ba." Ta ce." Wannan kuma Ubangiji zai kalubalanta. Wace irin wahala da gwagwarmaya ce Kamalu bai sha ba. Yanzu kuma Ubangiji Allah Ya d'aukaka darajarsa wannan duka ba dabararmu ba ce ikonsa nd, gaskiya a wannan ga'bar ni ma bana goyan bayan mijinki Kamalu dole ya tafi ya bar musu gidansu idan sun ce ba haka ba sai ya dawo hannunki shine karshen magana. Na ce." Anti Yagana ni na fi so fa ya koma kanon ko ya dawo nan wurinku hankalina zai fi kwanciya gaskiya, domin ai ko yana gidana ba a kashe matsalar ba tunda duk lokacin da ya fita zai iya yin karo da Salim din kin ga matsalar ai bata mutu ba." "To ni da kaina zan kira Yallabai din a waya na bashi shawara yadda za a yi. Jin haka ya sanya na ce." Kada ki kira shi yanzu anti Yagana mu bari ya zo mu ga hukuncin da zai yanke idan babu adalci sai ki yi masa magana." Ta ce." Shikkenan haka za a yi in sha Allah, na manta ma ban gaya miki ba shekaran jiya amaryar Babandi matar da ya aura ta uku ta haihu." A takaice na ce.'' A yi masa barka Allah Ya raya, domin ni yanzu ko lambarsa ma ba ni da ita yadda maigidan ya tsaneshi haka ya tsani mutuwarsa shiyasa na goge lambarsa daga wayata a gabad'aya duk domin a zauna lafiya. ** Bayan sati biyu al'amura suna cigaba da tafiya da dad'i babu dad'i. Har zuwa lokacin Salim bai kyale Kamalu ba. Kusan kullum da b'acin rai yake shigo mini duk da yana ko'karin daurewa amma ina fahimta. Ha'kurina yana daf da k'arewa domin tun ranar da na kira maigidan a waya na gaya masa abinda yake faruwa bai sake nema na da maganarba duk kuwa da cewa kusan kullum sai mun yi bidiyon call. Ni ma ban sake tayar da maganar ba na bari ne kamar yadda ya ce mu jira zuwansa. Amma koyaushe idan na dubi Kamalu na ga yadda ya rage walwala da kuzari zuciyata takan yi zafi. Ina dalili haka kawai saboda gudun b'acin ran wani a 'kuntata zuciyar yaro. Babu lallai fa babu dole muddin ba zai d'auki mataki ba wallahi sai Kamalu ya tafi ya bar garin da gidan gabad'aya. Ranar litinin da yamma suka sauka shi da Hauwa. Baiwar Allah ta kuma samo wani cikin domin yanayinta kadai ya tabbatar mini da cewa laulayi take yi ta yi mugun haske dama idan tana da ciki d'ashewa take yi. Macace mai kwainika Minal na da wata goma sha takwas. Allah Ya sa tana da san girma, tana yawo da kafafunta da yake abincin gwangwani take ci a can ta zama rusheshiya kataf-kataf haka take yawo uban yana tsokanarta da 'yar sukuta. Wai na washeta har ta fi su Hassana girma jiki tunda su jikin irin nasa ne. Kwana biyu da zuwansu na fahimci rashin jituwa a tsakaninsu. Kamar ma basa magana da juna. Na yi dai shiru ina kallon ikon Allah. Ita yini ma take yi a d'aki sai yamma take fitowa falo shi kuma har ya yi kwana biyunsa a wajena bai ce mini komai ba. Na cika da mamaki sosai. Lallai ma wannan mutumin wato maganar tabi shanun sarki kenan Salim ya yi daidai babu kuskure akan abinda yake yi. Ba zan lamunta ba domin kuwa har yanzu a cikin matsalar ake sai abinda ma ya yi gaba. Kamalu bai rasa madogara ba hakama Yusi idan har ba zai gyara abinda yake faruwa ba to na yarda ya ba ni yarana su kuma can hannun Babansu Hamusu. Cikin wannan nazarin Hauwa ta shigo d'akina ta same ni. Ta zauna gefan gado tana fad'in." Ko jikin ne?" Na tashi zaune Ina fad'in." A, a ni kam ai na warware na bar miki Hauwa." Kwafa ta yi tare da cewa." Ban ji dad'in shigar cikin nan ba wallahi.'' Na dubeta a tsanake tare da cewa." Mai yasa Hauwa ki godewa Allah da fatan samun masu albarka." "Humm!" abinda ta ce kenan kafin ta ce." Ban shigo domin na tunzuraki ko tayar da husuma ba. Idan kin lura da yanayin yadda muka zo da ni maigidan babu dadi don wallahi mugun haushinsa nake ji." Na ce." Menene kuma ya kamata ki manta da matsalar matar nan Hauwa, ki yi ta kanki haihuwa ta uku za ki yi da mutumin nan duk abinda zai yi ya je ya yi haka ya ga zai iya." "Wallahi Amina ko kaffara ba zan yi ba matar nan ba haka ta bar mutumin nan ba." "Mai yasa ki ka ce haka Hauwa, zato zunubi ne fa Koda ya kasance gaskiya ne?" [12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 102 "Amina maganar gaskiya zan gaya miki na gaji da zaman nan da muke yi na rashin 'yanci da kaskanci wallahi tallahi ba zan jiya jure ba, wannan shine dalilin ma da ya sanya ki ka ji na ce ina b'akinciki da takaicin samuwar wannan cikin na jikina, in banda ina gudun sa'bawa Allah wallahi da sai na zubar da shi." Da mamaki mai yawa a tare da ni na ce." Hauwa mai ya yi zafi haka, ha'kuri fa ya zame miki dole na farko mutumin nan d'an uwanki ne kuma mijinki uban yaranki, idan kin rabu dashi ki auri wa kenan, ke ce ya kamata ki zauna dashi Hauwa saboda haduwar jini da kuma zuri'ar da take tsakaninku." Cike da takaici ta furta." Shi ai baya ganin yadda muke yin hakuri Amina, a ce mutum bashi da wani mutunci da daraja. Shikkenan sai ka ajiye mata uku ka za'bi daya ka fifita saboda wata banzar hujja." Dariya na yi na gane dama duk wannan hayaniyar da take yi akan Momi ne, har yanzu ita ta kasa d'auke kanta daga sha'aninsu. Na ce." Hauwa da za ki d'auki shawarata wallahi da kin daina girmama al'amarin nan kin sanya shi a ranki, ki yi abinda yake gabanki kawai ki rabu da duk abinda zai yi, ai duk wanda ya gyara ya sani kuma duk wanda ya 'bata ya sani." Shiru ta yi tana kallona kafin ta gyada kanta ta ce." Idan kuwa har ina da hakki to Allah Ya isa ban yafe ba wallahi, domin ni don ba yadda zan yi ne na ha'kura da wannan sintirin haka kawai sai ta toge da ri'ke mana yara ita tana kamile a waje daya saboda shafaffiyace da mai." Na ce." Ai kin fi ta samun ladan aure Hauwa, don Allah maganar nan ta mutu haka haba." "Magana ba za ta mutu ba Amina, ba ni na haifi Kamalu ba amma zahiri sai inda karfina ya kare a kan sharrin da yaron nan Salim ya yi masa." Na dubeta a nutse." Wane irin sharri kuma Hauwa?" Shiru ta yi tana kallona da yanayi na damuwa sai ta gyada kanta cike da b'acin rai ta ce." Abin da akwai daure kai Amina, nasan kuma ba zai gaya miki ba saboda yadda ya nuna kamar ya yarda da maganar yaron. Nuna masa hakan ba daidai ba ne ya yi aiki da maganar mutum d'aya sai ya janyo mana rikici shine fa muke ta yi har yanzu ba ma ga miciji" Jikina ya sake yin sanyi a nutse na ce." Ki gaya mini Salim din ya nemi wani abu nasa ya rasa ne, ko kuwa ita ma Momin ta nemi wani abu bata gani ba?" Ta ce." A a babu d'aya Amina, ni kaina ina jin nauyin gaya miki wallahi, Amma ya zama dole ki sani domin ki nemi mafita Salim din ne yake gayawa maigidan wai Kamalu yana lalubensa a cikin dare har yana cire masa gajeran wando!" Wani irin yamm! na ji tun daga tsakiyar kaina har zuwa kafafuna. Yawun bakina ya tsinke gabana yana fad'uwa na ce." Hauwa wace irin magana ce wannan don girman Allah!" Ta dafa cinyata a hankali ta ce." Maigidan ya kira Salim domin jin 'karin haske dangane da maganar da ki ka gaya masa a waya tsakaninsa da Kamalu bud'ar bakin yaron sai ya ce masa Kamulu yana nemansa wai har yana cire masa gajeran wando." Shiru kawai na yi kaina yana juyawa. Abubuwan da suka shud'e a shekarun baya suka dinga dawowa kaina. Yusi da Kamalu. Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! maraici maraici maraici! an ce Yusi ya lalata yarinyar mutane, yau kuma an ce Kamalu zai yi luwadi. Hannu nasa na tallafe ha'bata gabad'aya tunanina ya tsaya cak! Ta dafa kafadata a sanyaye ta ce." Nasan dole ne ki kadu da jin wannan mummunan labari Amina, ki yi hakuri ban gaya miki da zummar na daga miki hankali ba, wallahi tallahi wannan shine dalilin da ya assasa mana rikici mai zafi saboda na gaya masa cewa wannan sharri ne kawai, kuma bai kamata ya yarda da maganar ba." Na dube ta a hankali na ce." Kenan ya yarda da abinda Salim din ya gaya masa." "Ya saurare shi dai a waya bayan sun gama shine yake gaya mini. Na ce to ya sanar dake kuma ya nemi Kamalu shima ya ji daga gare shi ya ce babu daya da zai yi a ciki. Jin haka sai kawai raina ya b'aci na fara nuna masa kuskuran abinda yake shirin aikatawa daga lokacin zamanmu ya rikice wai ban isa na nuna masa yadda zai yi ba. Tunda babu wanda na haifa a cikinsu na ja bakina na yi shiru shi ya san hukuncin da zai yanke." Cikin alhini da zullumi mai radad'i na ce." Hauwa na gode sosai, ba ki munafurceni ba, kuma duk da ni na haifi Kamalu amma kai tsaye ba zan bada shada a kansa ba, ai d'an yau ne, kuma ba komai ne ya janyo wa yaran hakan ba sai maraici amma in sha Allahu zan d'auki mataki, na gode sosai Allah Ya kula miki da yaranki." A nutse ta ce." Amin, ki yi hakuri don Allah kada ki sanya damuwa a ranki Amina." Dariya na yi wadda babu nishadi na ce." Kamalu da Yusi za su bar gidan nan Hauwa koda kuwa hakan shine zai kawo k'arshen zamana daku." Ta yi shiru tana kallona. Na ce." Wannan itace shawarar da na yanke rigima ce a kwance sai dai Allah ya magantata." "Kin san Allah kina barin gidan nan zan bar bashi wallahi, ya zauna da ita da yaranta 'yan iska gabad'aya." Murmushi na yi ina dubanta ita tafi ni ma d'aukar lamarin da zafi. Tashi ta yi ta fita ranta a 'bace. Na jingina bayana jikin gado ina sake tariyo maganganunmu. Ni ban san ma ya zan yi ba. Wayata na d'auka domin kiran anti Yagana. Bugun farko ta daga. Jin muryarta sai na raunana kwarai kukan da nake ta han'koron dannewa ya k'wace mini Ina yinsa na ce." Anti Yagana Ina cikin masifa." Furta wannan maganar ya yi daidai da lokacin da ya shigo d'akin ya zauna kan kujerar mudubi yana kallona. Cikin kuka wiwi! Na cigaba da cewa ." Anti Yagana na yi rashin da har na mutu ba zan maye gurbinsa, na yi rashi anti Yagana ni da yarana muna cikin maraicin Yaya Aminu Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un" Fadi take yi ki yi shiru ki gaya mini menene abinda yake faruwa Amina kar ki manta fa ke matar wani ce, yanzu babu abinda yake tsakininki da Yaya Aminu sai addu'a. Cikin kuka na fitar hankali na ce." Anti Yagana ina cikin jarrabawar rayuwa duk inda yarana zasu ra'ba sai an ci zarafinsu, sai an tozartasu, sai an yi musu sharri, anti Yagana maraici akansu a ka fara ne?" "Kin ga malama kada ki yi mana sabo don Allah, duk mutumin da Ubangiji ya cika jarabtarsa shine mumini kada saboda kin shiga rintsi ki nemi ki kafurcewa Allah." Shiru na yi Ina jan hanci ina cigaba da sauraranta. Na ce." Na ji anti Yagana, na ji duk abinda ki ka ce mini, amma idan kin samu labarin mutuwata to don Allah Ina neman alfarma kada wani ya zo ya yi miki dadin baki ya ce ki bashi Kamalu da Yusi zai ri'ke, don Allah ko wanene kada ki bashi mutanan yanzu basu da amana mugwayene azzalumai." Tashi ya yi, ya nufo ni ya zo zai kwace wayar na mike tsaye da tsalle duk da nauyin jikina da wayar a kunnena na kai masa wani naushi a kirji da k'arfi ya yi baya tare da rike kirjinsa. Cikin raina na ce gwara na kashe ka kafin ka kashe ni. "Ki gaya mini abinda yake faruwa." Wannan maganar na ji tana fad'a. Na jingina jikin bango(garu) ina numfarfashi sakamakon filinkin din da na yi. Na ce." Yaron nan Salim da na gaya miki suna rikici da Kamalu shine ya ce wai Kamalu yana nemansa da daddare har yana cire masa wan.....Ban kàrasa ba ya buge wayar daga hannuna ta fad'i kasan wajan. Ya sunkuya ya d'auka tare da kasheta gabad'aya ya sanya cikin aljihunsa. Daf da ni ya tsaya muka zubawa juna ido. Wani irin kallo yake yi mini wanda na kasa fahimtar ko na menene. Ni kuma wanda nake yi masa na tsantsar tsana ne da takaici. "Wanene ya gaya miki wannan banzar maganar Amina?" Kai tsaye na ce." Hauwa ce, ai ita ba munafuka ba ce, kuma uwa ce ta san ciwon haihuwa, idan har kai ba kasan ciwonta ba." Ya gyada kansa da mamaki mai yawa a tare dashi ya ce." Ni ki ke zagi a fakaice Amina." Na ce." Idan hakane zagi na zaga." Murmushi ya yi na takaici ya cigaba da cewa." Ita Hauwa ai kafin mu tawo nan sai da na gargadeta akan kada ta kuskura ta gaya miki maganar nan saboda gudun tashin fitina amma saboda ta shirya shirya mini rikici a gida shine ta sanya kafa ta shure umarnina lallai ranta zai b'aci wallahi." Na ce." Ai ba ta yi lefi ba gaskiya ta fad'a domin shine zama na amana. Kuma wallahi a yanzu Hauwa ta fiye mini kai sau dubu tunda ka nuna mini zahirinka na gani, ni duk wanda baya k'aunar yarana ni ma bana kaunarsa." Na fad'i maganar cikin 'karaji da ihu! Ya zo zai ri'ke mini hannu na fizge tare da matsawa cikin babbar murya na ce.'' Kada ka ta'ba ni, domin kuwa babu abinda za ka gaya mini na yarda, ka nuna mini iyakata, na rantse da girman Allah da Annabi sai yaran nan sun bar hannunka tunda ka gaza ri'ke su tsakani da Allah ko da hakan zai yi sanadiyar rabuwarmu a shirye nake." Kallona kawai yake yi har na dire maganata ya ce." Ki fahimce ni Amina, ban za'bi bangare daya na ajiye daya ba. Ni kaina lamarin ya sanya ni a rud'ani ba kad'an ba. Shirun kuma da na yi ba ina nufin na goyi da bayan maganar Salim ba. Ina bincike ne da kuma hanyar da zan kawo gyara. Akwai nauyi mutuka da gaske na tunkareki da maganar nan. Akwai kunya na titsiye yaron nan Kamalu ina neman hujja akan maganar Salim. Kada ki zarge ni bayan ba ki san menene a zuciyata ba. "Na gaya maka wallahil-azim ba zan yarda da kanzon kurge ba. A wannan ga'bar ko ni ko kai, Kamalu da Yusi fa basu rasa madogara ba. Sannan Ubansu ba makwadaici ba ne, ba mazinaci ba ne, sannan ba b'arawo ba ne. Banga dalilin da zai sanya a dinga jingina musu manya manyan sharri ba. Ban nemi ka rike mini yara ba. Haka zalika ma ban nemi matarka ta ri'ke mini yarana ba. A ba ni kayana mana dole ne, zan iya rikesu, mu rayu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali." "To ni kuma muddin a karkashin ikona ki ke yaran nan babu inda za su je muna tare har abada." Na dube shi ina gyada kaina na ce." Haka ka ce ko?'' "Kwarai kuwa, haka na ce, sai ki yi duk abinda za ki yi tunda ke ba ki da fahimta." "Zan kuwa yi, ai ba kai ka haifar mini su, baka da wani ji'bi dasu don haka baka da hujjar da zakace dole sai ka rikesu anan zan nuna maka karfin ikona." Ya ce." Sai ki nuna din ina jiranki..'' Daga haka ya ja tsaki ya juya ya fita yana fad'in." Sakarai kawai kullum kina girma kina cin tasono." Silalewa na yi a kasan d'akin na yi zaman dirshan na dinga tikar kuka. An dake ni an hana ni kuka kuma an bi ni da bakar magana. Wace irin masifa ce wannan mutum bai haifi yara ba ya ce lallai sai ya rike su. Ina cikin wannan yanayin Hauwa ta shigo sanye da hijabi a jikinta idonta jawur! Na tashi tsaye da sauri Ina kallonta gabana na fad'uwa. Minal ta dire mini a gabana tana fad'in.'' Ga takwararki nan Amina ubanta ya ce na tafi gidanmu." Cikin kad'uwa da muguwar fargaba na ce." Ki tafi gidanku akan wane dalili Hauwa?" "Saboda na gaya miki magana." Ta fad'a tana juyawa da niyyar fita. Na bita da sauri yayin da Minal din ta tawo kataf katafi ta rike gefan hijabinta tana kuka. Na ce." Shine kuma ke sai ki tafi." "To dama ai kamar akan 'kaya nake wallahi na gaya miki a gajiye nake." Na ce." Ita Minal din mai tayi miki to?" "Cewa ya yi na ajiye masa yarinya." Wani takaici ya yun'kuro mini lallai Alhaji Amadu ya mutu ya bar baya da kura. Iyalinsa na nema su tarwatsawa aminin nasa rayuwa. Na tabbatar da cewa ba kowane ya janyo wannan hayaniyar ba sai Salim. Na ce." Yana ina maigidan?" "Shi ya sani.'' Ta fad'a a takaice tare da sake nufar hanyar fita. Na ri'ke hannunta ina fad'in." Babu fa inda za ki je Hauwa." Dariya ta yi irin ta takaici ta ce." Ai ba ke ki ke aurena ba Amina, maigida ya ce na fitar masa daga gida zaman me zan yi." Jan hannunta na yi muka zauna kan gado na sau'ki Minal na d'ora mata a cinyarta sannan na d'auki wayata. Kiransa na yi bugun farko ya d'aga kamar yana jira. Na ce." Yanzu kai don girman Allah ba ka ji kunya ba, tsofai tsofai da kai kake aikata irin abun yara?" "Mai na yi kuma? Ke ba kya jin nauyin furta mini maganar da duk ranki ya so ko Amina?'' Na ce." Hauwa dai ko babu aure tana da 'yancin zama na dindindin a gidanka, to balle bayan wannan alakar akwai ta aure da zuria a tsakaninku, da ka ce ta tafi gida kai ba ka ji nauyi ba?" "Bata da wani 'yancin zama a gidana sai na so, tunda ba ta ji nauyin shure maganata ba, ni ma babu wani nauyinta da zan ji, kuma ina ruwanki matarki ce?" 'Dan sassautawa na yi domin kuwa ba zan so a ce dalilina sun samu matsala ba. Na ce." Idan saboda ta gaya mini wannan maganar nan ya sanya har ka yanke mata wannan hukuncin ka yi hakuri ka ji." Shiru ya yi bai ce uffan ba. Na ce." Ka janye abinda ka kudirta akanta domin kuwa sam bai dace ba." "Kin yarda ta yi ba daidai ba yanzu?" Shiru na yi ban ce komai ba. Ya sake maimaita maganarsa nan ma ban ce masa komai ba. Ya ce." To tunda bakinku daya kin ga kuwa babu amfanin zama da macan da bata buk'atar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Hauwa kawai ta tafi gidansu kafin na gama yanke hukunci ta san matsayinta." Gwiwa a sanyaye na kashe wayar ina kallonta babu damuwa a tare da ita tace." Ai na gaya miki Amina mutumin nan kaf dabi'unsa sun canza muddin akan lamarin matarsa ne yakan iya cin mutuncin kowa." Na ce." Babu da inda za ki je." Ta yi shiru tana kallona ina laluban wayar Hajja bugu daya ta daga. Cikin rawar murya na gaisheta ta amsa tana fad'in duk kuna nan lafiya ko Amina." Na ce." Lafiya lau Hajja don Allah ki yi masa magana matsala suka samu da Hauwa shine ya ce wai ta tafi gida." cike da mamaki ta furta." Hauwa ta tafi gida akan wane dalili?" Shiru na yi ban ce komai ba. Cike da kulawa ta ce." Amina ki gaya mini menene yake faruwa kin ji ko kada ki rufe mini komai.'' Hawaye suka silalo mini na ce." Hajja Hauwa ba ta yi masa komai ba wallahi, asalima ma matsalar ni ta shafa saboda kawai ta gaya masa gaskiya shikkenan yake jin haushinta." Ta ce." To gaya mini wace matsala ce, ni zan yi maganinta, Hauwa kuma ki gaya mata kada ta fito." "In sha Allah, gata nan a kusa da ni, na hana ta fitowa." "To hakan ya yi ina sauraranki." Tafad'a cikin nuna damuwa. A nutse na fara gaya mata tun daga farko abinda yake faruwa har zuwa yanzu da ake wannan rikicin. [12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 103 Hajja ta jima cikin alhini da takaici kafin ta ce." Ki yi hakuri a matsayinki na babba kuma uwa. Amina tabbas ko ba ki fad'a ba nasan idan za a tona zuciyarki to tanan cikin kunci da b'acin ran wannan lamari. Ki jure lallai kuma ya zama dole a yi wa tufkar hanci saboda gudun abinda zai afku anan gaba na rashin dadi. Zan nemi shi zai kuma zo nan inda nake akan maganar nan domin ni kaina ban yarda da hakan ba. Sannan duk abinda zai yi muku kada ku saurareshi. Ki jadaddawa Hauwa cewa da yawuna ban amince ta fito ba. Ke kuma ki yi hakuri kin ji ko, nasan abinda da ciwo a zucci amma in sha Allahu gaskiya za ta bayyana halinta." Cikin ko'karin danne damuwata domin kada ta ga kamar ban ji nasiharta ba na ce." Shikkenan in sha Allahu Hajja za mu yi yadda ki ka ce din, Allah Ya saka da alheri." Ta amsa da "Amin." Cike da damuwa muka yi sallama. Na dubi Hauwa tare da cewa." Kin ji yadda muka yi da ita ko?" A sanyaye ta ce." Na ji, amma kin san Allah wallahi ba na so na bude ido na ga mutumin nan Amina, wani irin haushinsa nake ji." Na ce. Ki daure zuciyarki, kuma duk abinda zai yi miki kada ki kula shi." Shiru ta yi ba ta ce mini komai ba tana ta girgiza kafarta. Cikin raina na ce Hauwa ita ma ba lefi yar bala'i ce. Haka muka wanzu a d'aki muna tattauna matsalar da yadda za mu maganceta. Tun fitar nan da ya yi bayan mun yi musayar yawu bai sake shigo mana ba, dama girkin Momi ne, cikinmu babu wadda ta neme shi. Gabad'aya muna falo ni da Hauwa da Baba Tabawa muna kallo da hira jefe-jefi. Kamalu ya shigo tsaf dashi cikin jallabiya yana ta k'amshi turaransa wanda na tabbatar da cewa Momin ce ta bashi domin turaran gaskiya irin na manya ne mai dadin k'amshin. Muddin ya shiga waje sai kowa ya ji shi k'amshinsa. Cikin nutsuwa duka ya gaisa da kowa. A dan sanyaye ya ce." Momi ba lafiya fa." Hauwa dai ko kallonsa ba ta yi ba. A takaice na ce.'' Mai yake damunta?" "Ciwon kai ne mai tsanani ba su jima da dawowa daga asibiti ba tare da Baba." Na ce." Allah Ya sawwa'ke. Ya amsa da amin." Baba Tabawa ta ce." Allah Ya sawwa'ke idan ka koma ka yi mata sannu da jiki kafin na mu shigo." Ya ce." To.'' Falon ya yi shiru na 'yan mintina kafin ya ce." Mama za ku je dubata ko?" Shiru na yi ban ce masa komai ba. " Ya sake maimaita maganarsa Hauwa ta dube shi tana harararsa ta ce." Wai kai wane irin yaro ne Kamalu?'' Ya dubeta a hankali yana dan murmushin. Ta ja tsaki tare da juyar da kanta gefe guda.. Murmushi kawai ya yi ya sunkuyar da kansa kasa. Baba Tabawa ta dubi Hauwa da yanayi na damuwa na lura maganace a bakinta amma ganin yadda fuskar Hauwa take a cud'e ya sanya ta kasa cewa komai sai ma ta tashi ta nufi kicin tana cewa." Bari na kwa'danta maka zogale mutuminka." Tana shiga kicin Hauwa ta kalleshi fuska babu fara'a ta furta.'' Kamalu kalle ni nan." Ya dubeta da sauri. Ta ce." Ka gaya mini gaskiya tsakaninka da Salim mai kuke aikatawa?" Cike da zullumi da d'an tsoro ya furta." Anti ban fahimci maganarki ba." Ta sake zare masa ido a karo na biyu tana cewa." Baka fahimce ni ba menene tsakaninka da Salim.?" Ya ce." Rigima yake nema na dashi kullum da abinda zai yi mini na rashin kyautatawa." "Gaskiyar abinda yake faruwa kenan a?" Ta fad'a idonta tsaye a kansa. "Wallahi anti shine gaskiya bayan wannan babu wani abu, kuma duk abinda yake yi mini ba na kula shi." Ta ce." To yau d'aya don Allah ka je ka zage k'arfinka a kansa ka had'a masa jini da majina ba zai ka'ra ba. Nasan duk da ya girmeka amma ka fi shi san girma da 'barage, ka nuna masa bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne." Da mamaki nake kallonta kafin na ce." Mai yasa ki ke bashi wannan shawarar Hauwa. " Ta ce." Ita ce mafita kawai dole su gwada k'wanji muddin Kamalu ya kai Salim k'asa wallahi sai ya daina yi masa shegantaka." Na girgiza kaina a nutse na ce." A a Hauwa wannan ba dalili ba ne, idan kuma wata matsalar ta faru fa, masifa fa zamu shiga gabad'ayanmu. Ta ce Daga nan sai ayi fad'an k'arshe kawai." Girgiza kaina na yi na ce." A'a Hauwa." shi ma yaron lamarin ya bashi dariya yana yi ya ce." Anti mai yasa zan dake shi?" Ta ce." Saboda d'an-iska ne masharranci." Ya gyada kansa a nutse ya furta." Gidansu zan bar musu ai, wallahi rashin lafiyar Momi yana da ala'ka da abinda yake yi mini, wannan shine dalilin da ya sanya nake rangwanta masa tausayi take ba ni." Ni ma na tabbatar da hakan sanin halinsa na zuciyata da saurin kai duka tun yana yaro karami." Hauwa ta ce.'' Kasan mai ya ke gaya Baba akanka?" Ya girgiza kansa yana kallonta. "Wai kana nemansa da daddare?" Cike da rashin ganewa ya ce." Nema wane iri abinda ba a d'akinmu yake kwana ba." Ta ce." Sharri ya shirya maka wai kana cire masa gajeran wando." Ya zuba mata ido fuskarsa cike da zallan mamaki da al'ajabi. Ni dai zukud'un na yi ina kallonta. Na rasa azancinta na gaya masa akwai nauyi. Ta dube ni tana cewa." Ba za a munafurceshi ba domin kema na ga baki da niyyar sanar masa abinda aka shirya masa na k'azafi.'' Na ce." To fadar ai bata da amfani Hauwa." Ni kaina nauyin gaya masa nake yi ni da na haife shi. Kafin mu yi aune dukkaninmu muka ga ya mike zumbur! hanyar fita ya kama. Da sauri na tashi tsaye ina kiransa Bai juyo ba ya bud'e kofa ya fice a gaggauce! Na dubeta tare da cewa." Kin ga ni ko Hauwa!" A sanyaye ta tashi tsaye itama tana fad'in haka yake da zuciya da dama. Na gyada kaina ban ce komai ba na nufi daki. Hijab na sako na fito ta ce." Ina za ki je kuma?" Ina ko'karin fita na ce." Bayansa zan bi dalili nasan halinsa shiyasa Hauwa ban so ki ka gaya masa ba wallah..... Kafin na rufe baki Yusi ya shigo a guje. Cikin rud'u da tashin hankali ya ce." Mama gasu can suna fad'a a harabar gidan Momi sai kawai ya fara hawaye. Na fita da gaggawa ya rufo mini bayana ban san inda nake jefa kafata ba gate din gidan a bud'e hayaniya na ta tashi. Ina shiga na hango ana rirrike Kamalu yana ta han'koran kaiwa Salim naushi duk ya fasa masa hanci da baki masu gadin gidan sun ri'ke shi da kyau shi kuma maigidan yana ri'ke da Salim da yake ta tare jinin da yake fita daga hancinsa da tissue. Ina isa wurin na ri'ke hannunsa sai suka cika shi. Da kyau na ri'ke shi domin sai zillo yake yi yana kallon Salim jikinsa na karkwarwa jijiyar kansa ta tashi radau botiran jallabiyar jikinsa duk sun zube. Salim kam jikinsa ya yi 'kwatakes hanci da bakinsa sai fitar da jini suke. Jamilu direbansu yana ta ko'karin fito da mota da zummar tafiya asibiti. Kafin mu fita daga gidan Hauwa da Baba Tabawa suka shigo yadda na lura da fuskar Hauwa wasai! Baba Tabawa ce kawai take salallami tare da tambayar ba'asin abinda ya had'asu. Ban ce komai ba na ja shi muka fita. Hauwa ta rufo mini bayana ko kallon inda maigidan yake tsaye ba mu yi ba. Muna dai kallon lokacin da Baba Tabawa ta nufe shi da tsananin damuwa a tare da ita. Muna shiga gida Hauwa ta ce." Ka yi daidai Kamalu na rantse da girman Allah ka cika d'an halak, ka haifu kuma ni zan tsaya maka idan ma ya ce zai bi kadin jinin da ka zubar masa." Na zauna saman kujera kaina yana juyawa wannan wane irin bala'i ne. Gabad'aya ma na rasa abinda zan ce. Yana zaune a gefena ina jin yadda kirjinsa ke fitar da wani irin nishi na juya na kalleshi wallahi gumi yake yi sosai kamar babu Ac a falon. Kamalu ne fa ba'a ta'ba shi ba ma yana siyan fad'a ballantana an ta'ba shi. Wannan ya tabbatar mini da cewa lallai sharri Salim din ya yi masa bai aikata ba. Yusi ya shigo idonsa ya kada ya yi jajawur! Ya tsaya akan d'an'uwan yana fad'in." Mai yasa ka yi haka Yaya, mai yasa ka dake shi har sai da jini ya fita, Yaya Salim ne fa, duk abinda zai yi maka ka ai sai ka duba Momi, ita kanta fa ba ta goyon bayansa matsalarku ce fa ta haddasa mata mugun ciwon kai. Yaya ba ka duba hakan ba Momi tana kwance amma kuke yin fad'a abinda ba ta so.'' Hauwa ta buga masa tsawa tana fad'in." Rufe mana baki shashasha kana abu sai ka ce mace, ya dake shi din, ai haka ake son namiji ya kasance." Maganarta ta yi daidai da lokacin da maigidan ya shigo. Gabad'ayansa a ki'dime yake rigar jikinsa har da jinin Salim. Ido jawur yake duban Hauwa ya ce." Kin kyauta Hauwa, abinda ku ka yi mini shine daidai ko? Ni ban isa na yi iko da hukunci a gidana ba, ban isa ba, kun had'a kai kun sanya kafa kun shure umarnina." Ya nisa kafin ya cigaba da ce wa." Ke tun kafin mu zo nan na gargadeki akan maganar kada ta fita saboda gudun tashin masifa ba ki ji, ki ka samu uwar yaron nan ki ka gaya mata. Hakan bai isheki ba har sai dai ki ka cire nauyi da kunyar yaron nan ki ka gaya masa. Hauwa kin zama wake d'aya. Dake zan yi kuka duk abinda ya biyo bayan wannan masifar domin kuwa ke ce sanadi kuma wallahi sai na hukuntaki." Shiru ta yi uffan ba ta ce masa ba. Na ce." Jikinka ne yake kyarma ka rasa nutsuwa saboda an daki dangwal ko, kuma d'an matar so. Amma ai bacci ka ke yi har da munshari kuma ba ka fasa hurd'odinka ba a lokacin da yaron nan ya nannako sharri ya alakantashi da yarona. Kamalu mutum ne kamar Salim sai da ubansa talaka ne ba irin abokin Alhaji Amadu ba. Amma ni Amina ni ce gatansa. Idan har kun ce ba za ku yarda ba ku kaishi k'ara kotu, sai ku yi amfani da dukiya mu kuma za mu yi amfani da karfin addu'a. Wanda ya rike Allah shi yake dahir." Baba Tabawa ta zo da sauri ta rufe mini baki da hannunta tana fad'in." Kina da hankali kuwa Amina kin manta wanene a gabanki mijinki ne fa, wai mai yasa kuke nema ku 'bata rawarku da tsalle, ku dubi alheri matar nan, kada ku sanya zazzafan kishi akanta, idan har kuka had'e mata kai duniya za ta zage ku." Cikin kuka na ce." Baba Tabawa ke ce duk abinda yake faruwa ba ki sani ba, ranar wanka ba a boyon cibi. Duk wannan husumar da ta wanzu Salim ne sanadi ya sanya Kamalu a gaba da neman fitina ta yau daban da ta gobe. Ya kira shi b'arawo dan'ta'adda. Ya zo ya yi masa sharri mafi muni wai yana nemansa da daddare, dukkaninsu guda nawa suke idan ba lalacewar zamani ba. Na yi kawaici na yi hakuri duk don kada a ga kamar na za'bi nawa. Amma dashi da matarsa basa gani to mai yasa yanzu ba zan fito na kare kaina na kuma kare yaron nan ba." Cike da mutuwar jiki ta juya tana kallon wajan da maigidan yake a tsaye wanda shi tun lokacin ma da na fara magana ya haye samansa. Sai ta nemi wuri ta zauna jikinta a mace ta ce. Amma kuwa wannan yaro bai kyautawa kansa ba, wace irin magana ce wannan mara dad'in ji, mai Kamalu ya yi masa da zai yi masa wannan 'kagen, jama'a wace irin rayuwa muke ciki ne?" Hauwa ta ce." Babu abinda ya yi masa kawai Yana b'akinciki da k'yashin yadda Ubangijina ya daukakashi fiye dashi shikkenan fa, sai kuma gadarar yana cin arziki uwarsa. Yana nishi ya furta." Daga yau an daina cin arzikin banza arzikin wofi wa yasan ma ta yadda uban nasu ya nemi kudin da ya tafi ya bar musu. Mamansa kawai ita nake dubawa itace take ba ni tausayi" Babu wanda ya ce komai sakamakon saukowar maigidan daga sama ya canza kaya amma nasan duk ya ji maganganun Kamalu. Bai ce mana komai ba ya kama hanyar fita ransa a tsananin 'bace! Yusi ya bi bayansa shi ma ba tare da ya yi wa kowa sallama ba. Hauwa ta ja tsaki tana fad'in." Haba ai ni yau kwanan farinciki zan yi wallahi." Yusi ya sake dawowa daga bakin kofa ya tsaya yana fad'in." Ka zo in ji Momi." Hauwa ta kalleshi amma ba ta ce komai ba. Sai harara da ta ke wurga masa. Ya sake maimaita maganarsa "Momi ta ce ka zo." Ya ce." Ka je ka ce mata gani nan." Har ya juya zai fita na ce." Yusi zo nan." Ya juyo yana kallona na ce." Zo." Ya zo ya durkusa kusa da ni. Na ce."Ka za'bi Momi ko?" Ya yi shiru bai ce mini komai ba. Cikin tsawa na sake cewa." Momi ce uwarka ba ni ba ko Yusi?" Sai ya sa kuka yana cewa." Mama don Allah kada b'acin rai ya sanya ku yi abinda zai janyo muku nadama, Momi duk abin nan da yake faruwa wallahi ba ta da laifi, tana sonmu dukanmu na yarda Yaya Salim ya yi laifi amma kada abin ya shafeta itama cike take da takaici da b'acin rai." Hauwa ta ce." Idan abin ya dameta tunda farko mai yasa ba ta shigo an tattauna ba." Da sauri ya ce." Bata da lafiya wallahi." Yana rufe baki Nusaiba ta shigo ta ci kuka ta k'oshi domin kuwa fuskarta har ta d'an tasa idonta ya yi ja wata'kila d'an uwan ne ya kira ta a waya a gaya mata. Yaranmu kaf tun daga kan Khalil Hassana da Usaina Minal suna bayanta. Ba tare da ta gaishe da kowa ba tana daga tsaye take cewa." Mun gode bisa abinda aka yi mana, Allah Ya saka da alheri, mu ba mu gaji fitina ba, domin tarbiyar da iyayenmu suka yi mana kenan, koyaushe Mominmu cikin yi mana nasihar mu zauna lafiya da kowa take yi. Mahaifinmu kafin ya rasu karshen maganarsa shine mu ri'ke Babanmu Alhaji Tajo a matsayin uba. Wannan dalilin ya sanya ba za mu yi fad'a daku ba domin muna kallonsa a matsayin uba, kuma muna buk'atar kwanciyar hankalinsa." Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta cigaba da ce wa." Sannan yaranku gasu nan Momi ba ta da lafiya, dama kokari ne kawai irin nata na ce kowacce ta raini abinta." Da sauri Hauwa ta ce." Dama ai ba mu sanyata ba, ita taga zata iya, rashin lafiya kuwa kowa ma a cikinta yake mara kunyar k'arya, wannan tabarmar kunya ki ke nadewa da hauka. Wanene musababbi idan ba d'an'uwan naki ba. Shi za ki jawa kunne a matsayinki na wadda take gaba dashi, cikinmu dai babu sa'arki da za ki zo ki yi wa d'ibar albarka, sai mai dan yara sun dawo gidan ubansu dama ai ita ta nema ba wani ne ya ce mata ta d'auke su ba." Ba tare da ta sake cewa komai ba ta kama hanyar fita jikinta duk a sanyaye. Duk da abinda suka yi wa Kamalu sai da na d'an ji wani iri a zuciyata. Gabad'aya ma yaran ba su iya fad'a ba daga ita har Salim din domin kuwa da sun iya fad'a ina ga da wutar ba ta mutu ba. Shi Adam ma tunda ake hatsaniyar bai ce komai ba sai share hawaye yake yi gwara Yusi ya zo yana kalubalantar d'an uwan nasa. Da zai tafi kiran da Momin take yi masa ban hana shi ba, amma hukuncin da na yanke a zuciyata yana nan ban janye shi ba sai yaran sun bar gidan da garin ma gabad'aya domin kuwa ba zan iya ba. A shirye nake da tarar kalubalen da zan fuskanta. Washe gari da safe kalau ya shigo mini tsaf dashi cikin Pakistani ni. Muka gaisa da yake a d'aki ya same ni ban kai ga fita falo ba tukkuna na ce masa ya je ya gaishe da Hauwa da Baba Tabawa ya dawo. Ya fita minti biyar ya dawo ya zauna a gefena. Na dube shi a tsanake na ce." Jiya mun gama magana da Hamusu a waya zan sanyaku a motar haya zuwa kano sai ku dinga waya dashi kafin ku sauka. " Ya ce." Na ji dadin hakan Mama, kin ga kuma Baba bai jima da tafiya kanon ba don har d'akinmu ya same mu ni da Yusi yana tambayarmu zai je kano ko muna da sa'ko wurin Baba Hamusu." Shiru na yi Ina d'an nazari tafiyarsa kano da gaggawa irin haka tana da ala'ka da kiran Hajja dama ta ce zata kira shi babu tamtama kuwa wurinta ya tafi. Na ce. " Hakan ya yi daidai ni ma na ji dad'i, ka je ka kira mini Yusi Amma kada ka gaya masa komai." Ya ce." To shikkenan. Ya tashi ya fita da sauri. Ni kuma cikin gaggawa na shiga toilet domin yin wanka. Ina fitowa su Hassana suka shigo tsaf gabad'ayansu Baba Tabawa ta shiryasu. Na ce." Kun zo mu gaisa ne, ashe kun san ni?" Husaina dariya ta kama yi ta haye gado ta kwanta tare da sanya babban yatsanta a baki tana totsa. Na ce." Ke ba ki daina tsotsar hannun nan ba dama." Ta yi shiru ba ta ce mini komai ba sai ma ta janyo rigar baccina da na cire da yake mai laushi ce ta dinga shafa rigar da hannunta. Hassana ta je ta cire hannun daga bakinta cikin tsamin baki ta ce." Momi fa ta hana ki." Na dubesu Hassanar na cire hannun ita kuma Husainar na mayarwa bakinta. Na juya da niyyar bude wardrobe na d'auko kaya na ji kuka da k'arfi da sauri na dube su. Husaina ce ke kuka sosai ta cukume Hassana da kokawa Minal na gefe a tsaye tana kallonsu. Wajan na nufa ina fad'in." Mai ya had'aku." Cikin tsamin bakinta tana kuka ta ce." Dutana ta yi, ina luwanta da ni." Dariya nasa na ce." Ke Hassana mai yasa ki ke duteta?" "Momi ta hanata tsotsar hannu." Ta ba ni amsa tana zumbura baki. Kamulu ya shigo ya ce." Fad'a suke yi ko Mama." Na ce." E dama haka suke yi a gidan Momin" "Wallahi yini suke yi fad'a ai Taburni tana aiki kuma Hassana ce mai zalinci. Wataran Momi idan ta gaji dai sai ta cewa da Taburni ta goya Husaina don a samu mafita nan sai ta ce ba ta yarda ba dira kuka. Momin da kanta take cewa a d'auko mata zani sai ta goyata ake samun zaman lafiya." [12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 104 Na ce." Allah Ya kyauta ka ja su ku je falo kafin na shirya amma ina Yusi din yake ?'' "Gashinan zuwa, amma mama kin san ba lallai ne ya shigo shi kadai ba duk inda ya ajiye kafarsa anan Adam yake ajiye tasa. Shiru kawai na yi ina nazari. Babu fa wani dalili da a yanzu zai hana yaran nan barin garin nan. Na ce." Je ka falo, idan sun shigo tare ka turo mini shi." Ya amsa da "to shikkenan. Kafin ya sanya yaran a gaba suka fita. Gama sanya kayana ke da wuya Yusi ya shigo ya sha ado cikin yadin kufta d'inkin kansa abin kallo ne ballantana takalmin da yake kafarsa. Babu shakka matar nan ta na hidima da yaran nan kuma duk abinda za ta yi babu bambanci abinda Adamu zai sanya a jikinsa shi Yusi zai sanya duk tsadarsa kuwa. Ko turarukan da suke amfani da shi wallahi sai mai karfin jari. Jikina ya yi sanyi kalau a yayin da nake duban yaron cikin Kamala da nutsuwa tare da kwarjini fatarsa luwai alamar hutu da jin dad'i sun ratsa jikinsa. Kafin ya zauna a gefana sai da ya d'an risina tare da furta." Mama ina kwana, an tashi lafiya?" Na amsa a nutse ina sake nazartarsa har yanzu babu walwala da sukuni a tare dashi tabbacin abubuwan da suke faruwa na damunsa. Ya nisa kafin ya sake fad'in." Momi ta ce tana gaisheki ta ce na gaya miki za ta shigo idan an jima." Sai da nutsu sosai na dube shi babu fara'a a tare da ni na ce." Yusi ina so ka bud'e kunnuwanka da kyau ka ji abinda zan gaya maka, hukuncin na yanke kuma babu mahalukin da ya isa a wannan ga'bar da tura ta kai bango ya dakatar da ni." Na yi shiru Ina kallonsa yayin da gabad'aya ya shiga nutsuwarsa alamun fargaba da tashin hankali sun bayyana a fuskarsa. Na cigaba da ce wa." Hukunci na yanke akanka kai da d'an'uwanka Kamalu za ku bar garin nan gabad'aya rikonku zai koma hannun Hamusu za ku cigaba da ri'ke mini harkokina yanzu shirin da na yi kenan domin tun jiya na gayawa Hamusu halin da ake ciki saboda haka yanzu za mu je tasha tare na sanyaku a mota in sha Allahu. Matsananciyar damuwa ya shiga wadda baki ba zai iya misalta irinta ba. Ina kallonsa yana ta ko'karin mayar da hawayen da ya cika kwarmin idonsa amma duk dubararsa sai da ruwan hawayen ya kwaranyo kumatunsa. Murya na rawa ya ce." Mama mai yasa za ki yanke wannan hukuncin, ki dubi Allah da Annabi ki janye kada ki hukuntani akan laifin da ba nawa ba. Ki dubi k'auna da soyayyar da Momi take yi wa jininki kada ki sanya 'yan uwanta su yi mata dariya. Mama ni da Adam akwai k'auna da sha'kuwa sannan ba na so na rabu da Baba, ba zan ta'ba mantawa da hallacinsa a gare ni ba. Sannan Momi tana nan tana yi mana shirye shiryen tafiya karatu saudia makarantar da Yaya Salim ya yi karatu, ki yi hakuri Mama, kada ki hukunta Momi da laifin da itama ranta yake soyuwa." Ga'bo'bina ne suka yi sanyi ganin yadda hawaye suke zarya a dakalin fuskarsa. Ya kama hannuna ya ri'ke kamatau jikinsa har karkwarwa yake yi. Na ce." Yusi ba ka ji wani iri a cikin ranka ba a lokacin da Salim yake yi wa dan'uwanka sharri, abu mafi muni fa ya jingina masa. Da farko ban d'auka abin ya yi tsanani ba na danni zuciyata duk domin a zauna lafiya. Amma Yusi ba abu ne mai wahala ba a yanzu dai na tsaya da Momi da Salim a gaban alkali domin yin shari'a dasu akan wannan mummunan sharrin da Ubangiji ya halakar da wani gari kacokan akan aikatawa. Hawayen da nake dannewa suka goce da karfinsu duka dinga fafara gudu a kumatuna. Na ri'ke hannunsa da kyau na ce." Ka ture maganar sabo da hallaci da kyautatawa Yusi duka nasan mutanan nan biyu sun yi mini, ni ma ina rokon Allah ya ba ni ikon rama musu, amma ba na ji a zuciya za a samu zaman lafiya da juna muddin Kamalu da Salim suna zaune a makwanci d'aya. Kun girma da kai dashi ku tafi ku taimakawa kanin babanku ku nemi arziki ta hanyar halak, ina da shaguna da dukiya a hannun Hamusu sai mu 'bullo da hanyoyin nema domin mu gina kanmu da gobenmu, watarana za ku yi aure, za ku hayayyafa a wannan lokacin ya kamata ace kun dogara da kanku Yusi ba wai a ce koyaushe kuna ra'be-ra'be a gidajen mutane ba." Kuka kashir'ban yake yi yana fad'in." Mama na fahimci azancin ki, na gane abinda ki ke so na gane, amma don Allah Ina neman alfarma a wajanki duk rintsi kada ki yi rigima da Momi wallahi mutuniyar kirki ce, ina kaunarta kamar yadda nake kaunarki Mama, kuma duk abin nan da yake faruwa babu sanya hannunta ko da anti Nusaiba ta dawo muku da yaran nan wallahi bata sani ba lokacin tana bacci da ta tashi ta samu labari wallahi sai da ran anti Nusaiba ya 'baci da kuka ta bar gidan. Ita kanta Momi ta rasa yadda za ta yi da su. Adam ne kawai bai shiga rigimar ba, Yaya Salim da anti Nusaiba sun had'e kansu sun daina jin maganar Momi." Na ce." Sai ka ce mara hankali Yusi, ba zan yi rigima da ita ba, to akan me? ai ta yi mini alheri, abinda dai nake so da kai shine ka samu nutsuwa ka kuma kwantar da hankalinka, maganar cigaba da karatu kuma ko ba ku fita waje ba sai ku d'ora a bayaro university ku kai matakin da kuke buk'ata in sha Allahu Lokacin da muka fito falo Kamalu da Adam ne a zaune suna magana da sauri yaron ya zame daga kan kujerar da yake zauna yana fad'in."Mama ina kwana mun tashi lafiya?" A nutse na amsa da kulawa sai ya koma saman kujerar ya zauna jikinsa duk a sanyaye. Hauwa ta fito daga d'aki da tawagar yaran a bayanta tana fad'in." Kun shirya kenan?" Kafin na amsa Adam ya gaisheta ba tare da ta dube shi ba ta amsa kamar ba ta so. Na gyada kaina tare da kallon kamalu da kansa yake sunkuye na ce." Tashi mu tafi." Baba Tabawa ta fito daga kicin hannuntà ri'ke da madaidaicin baho da dabino a ciki. A nutse muka gaisa kafin na d'ora da fad'in." Baba zan kai yaran nan tasha zuwa kano yanzu zan dawo in sha Allahu." Ta ce." To shikkenan sai kin dawo Kamalu a gaishe da mini da Gwaggo da kyau sai kun dawo Yusuf." Yadda take magana shi ya sake tabbatar mini da cewa ba ta fahimci nufina ba domin kuwa da ta gane hukuncin da na yanke sai ta yi magana akan hakan. Adam da sanyi jiki ya dubi Yusi yana cewa." Za ku je kano amma babu labari Yusi babu neman rakiya, ni ma ina so na je na gaisa da Gwaggo da Baba Hamusu." Yusi ya riko hannunsa ya tashi tsaye muryarsa sanyi kalau ya ce." Wallahi ban san da tafiyar ba sai yanzu ka yi hakuri d'an uwa, idan har za ka je sai mu je ai babu damuwa." Da farinciki a fuskarsa ya furta " Zan je mana bari na sanar da Momi kai kun yi sallama ko?" Yusi ya girgiza kansa a hankali ya ce." Zan shigo yanzu na yi mata sallama. Adam na fita ni ma na kama hanyar fita zuciyata cike da zullumi da nazari nasan ba karamin gagarimin rikici ne zai 'balle a gidan ba dalilin wannan matakin da na d'auka. Amma a shirye nake da tarar dukkanin kalubalen da zan fuskanta daga maigidan koda kuwa ta rabuwa ce. Ai an yi abinda aka yi, Allah Ya shige mini gaba. Muna fita harabar gidan Masa'udu shine babban direbanmu da maigidan ya ajiye mana domin zurga-zurga dukda ba kasafai muke fita ba amma tun farko dama ya hana mu tu'ka mota a wasu lukutan ma ya gwammace shi da kansa ya ja akan wata daga cikinmu ta ja Ya taso da sauri tare da risinawa yana gaishe ni na amsa a gurguje domin ba na so Adam ya sake shigowa ya same mu ban san mai zan ce masa ba. Cike da girmamawa ya ce." Hajiya za fito da mota ne?" Kaina na girgiza a takaice na ce." A a.'' Ya biyo bayanmu da sauri Yana fad'in." Hajiya ki yi hakuri na kai ku don Allah" Ya k'arasa maganar a raunane. Na Dan dube shi sai ya ba ni tausayi sosai suke ko'karin ganin sun ri'ke aikinsu sam ba sa son abinda zai 'batawa ogonsu rai ko su sa'ba umarninsa. Na ce." Yi sauri to." Da dan gudu ya nufi wurin da motocin suke ya fito da daya da gaggawa har zuwa wurin da muke tsaye. Kamalu ya bude mini na shiga na zauna kafin ya dubi Yusi cike da tsare gira ya ce." Malam shiga mota.'' Ya shiga ba tare da ya ce masa komai ba sai da akwai damuwa Mai yawa a tattare dashi don sai waige-waige yake yi. Sai da muka hau titi sosai hankalina ya kwanta domin ni kaina ina jin nauyi da kunyar yaron ina kuma fargabar ya zo ya riskemu ba zan iya ce masa tafiyar ba zata yiwu dashi ba. "Hajiya Ina muka nufa." Muryar Masa'udu ta katse tunanin da nake yi. na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce." Kai mu jabi park." Cike da bin umarni ya ce." An gama. Motar ta yi shiru ni da yaran duka muna cike da zullumi mussaman Yusi da nake hankalce dashi yana goge hawaye a fakaice. Ban tsawatar masa ba domin kuwa ban san mai yake ji a zuciyarsa ba, amma zahiri wannan shine iya gatan da nake ganin zan yi musu a duniya. Ba zai yiwu a ce koyaushe rayuwarsu ta kasance cikin kyara da hantara ba. Sun fara kaiwa munzali na girma a wannan lokacin ya kamata ace mun had'u ni dasu mun gina gobe dalili watarana za su yi aure su tara iyali suma. Sannan zuciyata ba za ta iya cigaba da jurar ganinsu cikin kaskanci ba, arziki Allah ne yake bayarwa su fita su nema kowa ya tsaya da k'afafunsa. Cikin ikon Allah motar dana sanya su ta yi lodi saura bai fi mutum hud'u ba. Cike da dauriya da ko'karin kara musu kwarin gwiwa muka yi sallama na ce lallai idan sun sauka Kamalu ya kira ni. Ban gushe daga wurin ba har sai da na tabbatar da tashin motarsu sannan na sauke ajiyar zuciya na gyara zaman nikab din da yake fuskata kai tsaye na nufi wajan da Masa'udu ya ajiye mota. Yana ganina ya taso daga inda yake ya bud'e mini na shiga na zauna sai a lokacin na ji wasu gagariman hawaye masu radad'i sun k'wace mini. Wato ni kuma haka kaddarata take, ina ro'kon Allah Ya ba ni ikon cinyeta ya kuma saukakawa yaran nan rayuwa ya basu hakurin maraici. Ina komawa na samu Hajiya maryam da Hauwa a falo suna d'an hira jefe-jefi amma yanayin fuskokinsu kadai shi zai tabbatar maka da cewa zuciyoyinsu babu dadi. Kwarai da gaske na yi kokarin danne abinda nake ji a zuciyata game da al'amuran dake faruwa. Na zauna muka gaisa a tsanake fuskarta babu wannan murmushi da yake sake k'awata haibarta ta yi fiyau da ita dama abinka da mara jiki tabbacin da gaske ne bata da lafiya domin ga yanayin lalura da rashin kwarjin jiki nan a tattare da ita. Ta ce." Amina na shigo nan ne saboda ke domin mu tattauna abubuwan dake faruwa da yaranmu, Allah Ya ga zuciyata ban shigo cikin rayuwarku da wata niyya ta cutarwa ba. Yana da kyau a matsayinki na uwa mai hankali ki yi nazari mai kyau Amina idan hankali ya 'bata fa nutsuwa da dattako ake sanyawa domin nemansa bai kamata ace kin d'auki munanan shawarwarin da ba za su zama silar gyar........Hauwa ta katse ta cikin fusata." Ai dama ban ce ki shigo domin ni ba, ko kuma kin ji na ce miki kin shigo ne da mummunar niyya. Hajajju ki dube ni da kyau ki ga ni, a waye nake babu wata kinaya da za ki yi mana, kafin ki san Amina da yaranta ni na zauna da ita. Idan har mijinki ya gaya miki cewa da hannuna wurin matakin da Kamalu ya d'auka bai yi miki k'arya ba, ga ni a zaune ai ina jiran hukunci tunda ku kun iya take gaskiya da gangan." Cikin rashin sukuni na ce." Hauwa menene don Allah, duk cikinmu nan babu yaro karami tunda har ta shigo domin mu tattauna magana dan samun daidaito bai kamata wasu maganganu mara dad'i su biyo baya ba." "Kina jin irin jirwayen da take yi mini ai, ai mu 'yan iska ne marasa 'yanci tunda mijinta haka ya nuna mata ba mu da sirri komai muka yi a tambade ita nata sirri koyaushe cikin danda'be shi yake baya so kowa ya ji. Bazan jure d'aukar cin kashi daga 'bangaranta ba wallahi." A nutse ta ce." Ba halina ba ne raina mutum Hauwa, kuma kamar yadda ki ke hasashe hakane maigidan ya gaya mini komai ke ce ki ke ko'karin ganin lallai sai an yi 'batacciya domin kuwa abinda muke ta bunnewa dalilin gudun rikici mai muni ke ki ka gayawa mahafiyar yaron nan, kuma ki ka cire nauyi da kunya ki ka dubi tsabar idon yaron nan Kamalu ki ka gaya masa to kin fad'a kin ji dadi Kuma in sha Allahu abinda ki ke fata ba zai faru ba da izinin Allah." Hauwa ta mike tsaye tana huci ta ce." Kin yarda yaronki mahassadi ne, kuma sharri ya yi wa Kamalu ko ba ki yarda ba, ai ita karya fure take bata 'ya'ya wallahi ni dai Hauwa Maryam ba ki isa ki siye ni da kudi da abin duniya ba. Wannan gingimeman sharri da d'anki ya alak'anta marayan Allah saboda rashin adalci da son zuciyarku sai ku ja baki ku yi shiru babu wani mataki da ku ka d'auka. Kenan wannan ya nuna kun sake bawa yaron lasisin ci gaba da aikata abinda yake yi dalili kun nuna masa akan daidai yake, na fad'a din idan ta yi miki zafi ki kaini 'kara ko kisa tsinken tsire ki tsire ni!" Tsaye na tashi da sauri na tare ta tare da mayar da ita kan kujera sai huci take yi tabbacin a fusace take kuma a shirye take da duk abinda zai faru. Hayaniya ta fito da Baba Tabawa daga kicin tana fad'in." Mai yake faruwa ne don Allah ku yi aiki da hankali da girman shekarunku kada hayaniyarku ta d'auki hankalin yaranku k'ananu har su fahimci abinda yake faruwa, kun san dai yaro da ri'ke abu a zuciyarsa. [12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 105 Cikin numfasawa Hauwa ta koma ta zauna tana huci! ita kuma Momi ta yi 'kasa da kanta k'walla cike a kwarmin idonta. Alamu sun nuna cewa ba ta iya fad'a na cacar baki ba koda fad'ansu ya yi tsayi da Hauwa ita za ta kaita kasa. Har cikin zuciyata ban ji dad'in abinda ta yi mata ba duk da cewa duka su biyun ban san menene a cikin zuciyoyinsu ba don haka ba daidai ba ne abinda ta yi tsinka na k'asa da kai ma tozarci ne ballantana wanda yake sama da kai ashekaru. Ni da ita duka haihuwa ce ta janyo mana domin kuwa da yara ba su had'a ba ina ganin babu wani dalili da zai sanya na yi sa'insa da ita akan namijin da ba shi da wani tabbas. Tun farko itama Hauwan da ta d'auki shawarata abinda yake yi akan Momin ba zai dameta ba tunda ta san tafi amfanarshi fiye da ita ko a wurin tarayya ta aure ne. Kuma ita ce uwar mai sunan mahaifinsa Ibrahim Khalil, uwa uba kuma 'yar uwarsa ta jini. Hauwa ba ta fi ni kishi ba wallahi kawai na fita ha'kuri da juriya ne dalilin gwagwarmayar da na yi a rayuwa ita ba ta yi irinta ba. BabaTabawa ta koma kicin jikinta duk a sanyaye bayan cikin hikima irin ta manya ta yi mana nasiha aka ci sa'a kuma Hauwa bata k'alubalanceta ba. Falon ya yi shiru bayan gushewar baba Tabawa daga wurin babu wanda ya sake magana. Ita Momi din tunda ta sunkuyar da kanta kasa ba ta sake d'agowa ba tabbatacin ta ji ciwon irin tijarar da Hauwa ta yi mata. 'Dagowar da za ta yi kuwa sai ya yi daidai da kwaranyowar ruwan hawaye a dakalin fuskarta. Ba ta yi yun'kurin gogewa ba sai ta kalleni ta fara magana cikin karaya da zullumi." Amina ni na haifi Salim amma wallahi ba na goyon bayansa akan irin abubuwan da yake aikatawa na rashin kyautatawa. Kuma na nuna masa takaici da 'bacin raina na kuma gargade shi akan kada ya kuskura abu mafi muni ya sake faruwa irin haka. Ina kwance cikin ciwo jiya na samu labarin doki-in-doka da ya shiga tsakaninsu. Wannan shine abinda ya fi tayar mini da hankali na ce kina ina har hakan ta faru. Ban haifi Kamalu da Yusi ba, amma yau zan gaya miki wani abu da nake ji game da yaran a zuciyata wallahi ina sonsu fiye da yadda ki ke tsammani. Yadda nake jin yaranku gabad'aya a raina haka nake jin wanda na haifa. Ina rokonki da Allah da annabi kada ki yanke kyakykyawar ala'kar dake tsakaninmu. Kada ki yi yun'kurin datse k'akkarfan zumuncin da yake tsakanin Adamu da Yusuf domin kuwa d'azu Adam ya je mini cikin damuwa cewa kin tura yaran kano, ki yi hakuri yara su dawo mu cigaba da rayuwa cikin aminci na yi miki alkawari wani abu makamancin wannan ba zai sake faruwa ba. Kuma in sha Allahu Salim zai shigo ya baki ha'kuri komai ya shige da izinin Allah." Ta gama maganar tana sanya hannu domin share hawayen da yake ta tsiyaya a fuskarta. A nutse na ce." Ki yi hakuri ki daina kuka akan wannan lamari Momi wallahi ban k'ullaceki ba, kuma ni har abada akan yara ba zan yi rigima dake ba, amma ina so ki sani ce wa muddin Kamalu da Salim na tare a Inuwa daya to sa'bani ba zai daina giftawa a tsakaninsu ba. Abinda ba na fatan ya sake faruwa. Ba wai ba ki isa ba ne, kin fi karfin komai a wurina domin ban mance alheri ba, ki yi hakuri yara dai har abada sun bar nan in sha Allahu suna can hannun dangin Babansu sai dai su zo da ziyara. kuma ban isa na yanke zumuci da ala'ka ba tunda ai ba ni na had'a ba." Ta yi shiru tana gyad'a kanta kafin daga bisani ta yi wani murmushi da babu nishadi ta ce." Shikkenan ba zan karya miki rantsuwarki ba tunda har kin rantse amma ya za a yi da kayansu akwai takardun Yusi na makaranta shi ma Kamalu akwai wanda na sanya aka yi masa domin na gama shiri tsaf za su tafi saudiya domin cigaba da d'ora karatunsu a can makarantar da Salim ya kammala." A nutse na ce." Babu damuwa duk abinda ya danganci nasu ne za ki iya aiko mini dashi sai nasa a mota a kai musu in sha Allahu rabbi, na gode sosai Allah Ya saka miki da alheri." A sanyaye ta amsa da "Amin." Kafin ta yun'kura da kyar ta tashi tana gyara madaidaicin hijab din da yake wuyanta ta ce." Zan shiga gida, Allah Ya ba mu alheri." Ni kadai na amsa mata. Hauwa uffan ba ta ce mana ba har muka 'kare maganarmu. Gabad'aya muka bi ta da kallo tana tafiya a hankali da rashi kuzari. Sai bayan da ta fita ne Hauwa ta ja tsaki tana fad'in." Sai ta d'an ban tausayi wallahi." Na dubeta a hankali na ce." Hauwa zan gaya miki gaskiya abinda ki ka yi wa matar nan ba daidai ba ne, don Allah ko don gaba kada ki sake kwatantawa ko so kike ki kàrasa gawar da ba ta ki ba. Kina kallon fa a yanayin da take ciki amma sai tsalle ki ke kina han'karo kamar za ki kai mata duka. Takaici abinda ki ka yi mata ne fa ya sanyata kuka. Ki duba shekaru da kuma d'awainiyar da take yi da yara don Allah." Dan murmushi ta yi sai kuma ta ja tsaki a karon da babu adadi ta ce." Ta yi kukan jini ma, ni ina ruwana, sau nawa a sanadinta ana sanya ni kuka, munafukar banza kawai duk abinda take yi wallahi da niyya take yi ai sanin zuciyar mutum sai Allah." Na gyad'a kai Ina sake ce wa." Magana dai ta mutu Hauwa don Allah ni dai kada hakan ta sake faruwa kin ji." Ta'be baki ta yi tare da furta." Haba ko yanzu na buga na bada ruwa wallahi zuciyata wasai nake jin ta. Murmushi takaici kawai na yi na yun'kura na tashi cikin zuciyata nake fad'in ba za ki ta'ba canzawa ba Hauwa, ba ki takali rigimar kina jin dad'i ba abinda zai biyo baya shine damuwar domin kuwa nasan akwai rikici akwance a tsakaninmu da shi uban gayyar. Shiga ta d'aki da kamar minti ashirin na fara jin hayaniya na tashi. Murya Hauwa a sama da wata murya da na kasa tantance ko ta wacece. Cike da zullumi da fargaba na fito falon na same su a tsaye cirko cirko har da yaranmu k'ananu a tsaye kusa da baba Tabawa dake ko'karin shiga tsakani. Nabila ce 'kanwar Momi mutuniyata ce sosai kuma tun lokacin rasuwar Alhaji Amadu muke zumunci don har musayar lamba muka yi. Sai ta d'an ja baya da ni ta rage kiran wayata bayan auran 'yar uwarta da maigidan. Ni kuma ban ta'ba nuna mata komai ba don wasu lukutan har magana nake yi mata idan na ga ta d'ora status a Whasap amma dai duk da hakan ta kasa sakin jikinta kamar lukutan baya. "Ba ku isa ku kashe Momi ba Hauwa. Idan ba zata iya ba, ni zan kar'bi rigimar akan me? me ta yi muku da za ku tisa ta a gaba, mace tana sonku da zaman lafiya, tana d'awainiya da yaranku amma kuna cin dunduniyarta. Idan kun had'e mata kai sai me? Mijinta yana sonta fa kuma ita alheri a jininta yake, wallahi ba za mu lamunta ba, za mu iya d'aukar kowane irin mataki akan hakan." Ido na zuba mata kawai kaina ya gama d'aurewa da maganganunta amma ba zan ce mata komai ba Hauwa kadai ta isheta tunda dama mai neman kuka ce. Aikuwa ta bugi kirji har tana had'awa da tsalle tana fad'in." Karya banza da wofi an had'e mata kan don Allah ku d'auki mataki, matsafa masu kauce hanya domin neman duniya menene ba mu sani ba asalin dukiyar da uwar guzumar taku ta tara daga majiya mai tushe cewa kudin tsafi ne uwarta da ubanta ta bawa gumaka suka shanye jininsu. Har mu za a zo a yi wa wata burga, mun ce ta yi dawainiya da yaranmu ne? Ita taga zata iya. Mu dai in sha Allahu ba zamu rayu da kudin Haram ba. Ba zamu fake da Allah da addini mu ciyar mu tufatar da kudin jinin mutane ba." Nan da nan Nabila ta rikici sai ta fara rawa murya idanuwanta suka ciko da ruwan hawaye ta ce." Wallahi tallahi Hauwa sai mun yi shari'a dake sai kin tsaya a gaban alkali kin bada sheda abinda ki ka fad'a, ba za mu yarda da wannan kazafin ba. Ta ce." Ashe babu dadi kazafi ko. Mai yasa kuka take gaskiya da gangan, yanzu ke nabila har kina da bakin da za ki zo ki tsaya a gabanmu da wata banzar magana. Ki je ki tambayi 'yar uwar ki irin zaman da muke yi da ita a gidan. Ai ba a banza ta ri'ke mana yara ba. A shirye nake ki kalleni da kyau babu wata 'yar iska da ta isa na ji tsoronta wallahi." Nabila ta kasa cewa komai domin ta yi mutukar kaduwa da jin maganganun da suka fito daga bakin Hauwa. Duk yadda ta dinga kokarin hana kanta kuka hakan bai samu ba cikin gaggawa ta kama hanyar fita ba tare da ta iya mayar da martani ba. Cike da mutuwar jiki na dubi Hauwa da take ta numfarfashi na ce." Tsakani da Allah Hauwa idan rai ya baci yana da kyau a sanya hankali da tunani. Yanzu ke don Allah a Ina ki ka ji wannan maganar kada fa ki d'auri kanki Hauwa mai ya yi zafi ne, ni dai idan har a kaina ki ke wannan balo'kokon to don Allah ya isa haka, yaran da suka asassa wannan rikicin na d'auke su da gidan fakat mu zauna lafiya, babu ruwanki da matar nan da duk abinda zai shiga tsakaninta da mijinta a kan hakkin kawai ya kamata ki yi magana, amma ki yi kokarin kawar da kanki daga barin ji da ganin abinda yake yi a kanta." Baba Tabawa ta jijjiga kanta cikin alhini da damuwa ta furta." Don Allah ku zauna lafiya, wallahi ba na jin dad'in abubuwan nan da suke faruwa." Tsaki ta ja kafin ta ce." A shirye nake da abinda zai biyo baya Amina, wallahi yadda na tsani mutuwata haka na tsani matar nan, kuma abinda na fad'a ai ba k'aharu ba ne, ni ma ji na yi ana fad'a a duniya." Daga haka sai ta tashi ta shige dakinta fuskarta babu rahama ko kad'an. Ni da Baba Tabawa muka bi ta da kallo cike da tsantsar mamaki. mai ya yi zafi haka, a ganina abinda take yi ai ni ya kamata na yi amma ban yi ba, ita lamarin nata yana nema ya wuce gona da iri fa. To ita rigima dama akwance take shiyasa tashinta bashi da amfani domin kuwa muddin ta tashi akan sha mutukar wahala wajan samun ruwan da zai kashe. A wasu lukutan ma ana kashetan shaid'an da mukarrabansa suke shiga cikinta su yi kane-kane, su bugi wannan bangare su bugi wancan b'angare. Lokacin da na ga kiran wayarsa hankalina ya tashi sosai dalili ban san mai yake 'kunshe a cikin Kiran nasa ba, daga jiya zuwa yau abubuwa masu muni sun faru wanda na tabbatar da cewa muddin ba a kai zuciyoyi nesa ba to rayukan kowa zai 'baci har da wad'anda ma ba su ji ba, ba su ga ni ba. Na daidaita yanayi kwarai da aniya ban bari raunina ya bayyana ba na d'aga wayar a nutse gaisheshi na fara yi bai amsa mini ba ya ce." Kai ni 'kara wurin Mahaifiyata bai gamsar da ku ba har sai kun had'a ba ki kun cutar da baiwar Allah ko Amina?" Na ce." Ban fahimci maganarka ba." "Nabila ta kira ni yanzu ta cikin tsananin damuwa tana fad'in irin abinda kuka yi mata yanzu daidai kenan Amina, ko kina so ki nuna mini hassadarki a fili domin Allah Ya suturta Maryam ta fi ku kyau da ilimi da goge, ta fi ku dukiya da kyauta da tausayi, kana ta fi ku mutunci da karrama dan adam. Idan har za ku yi kishi akan soyayyar da nake yi mata wannan ba zai dame ni ba, tunda zuciyata ce ita ta za'ba a madadinku, amma ba zan lamunci cin zarafi da sharri ba, zan shige mata gaba domin ganin an hukuntaku bisa sharrin da ku ka yi mata." A nutse na ce." To muna sauraran sammanci, ita Maryam tana da kai Tajo, Amina da Hauwa kuma suna da Allah, maganar da ka ke yi akan cewa muna yi mata hassada wallahi tallahi ni ban ga abin kyashi da b'akinciki a tare da wannan matar ba. Kudi dai kasan daidai gwargwado ina dasu babu wata mummunar hanyar da na bi wurin nemansu gumina ne, halak dina ne, babu wani mahaluki da ya ta'ba ba ni kwabonsa da zummar na yi jari, don haka wallahi babu wata mace da zan yi hassada akan wata banzar dukiya. Sai abu na karsh wanda nake so ka sani cewa ni Amina Tajo ba a gabana yake ba balle har raina ya sosu domin hankalinsa ya karkarta can wani gefe, ai ita soyayya guda daya ce tuntuni na bada ita a wani wuri har abada kuma wani namiji ba zai ta'ba samunta ba a wajena." Tsaki ya ja kafin ya ce." kuna abu sai ka ce jahilan farko. Duk da wanda ya ji wannan dabbancin da kuka yi ba zai yi muku kallon girma." Bai bari na ce wani abu ba ya kashe wayarsa. Ban damu ba, ni ma na ajiye tawa wayar zuciyata kamar ta tsage saboda tsananin tashin hankali da fargaba kafafuna sai kyarma suke yi tun a falo lokacin da Hauwa da nabila suke musayar yawu nake jin marata na murda mini kad'an kad'an. Sai da na shiga bandaki na tsuguna da zummar fitsari jini ya biyo baya. Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! kalmar da na fara ambata kenan na tashi tare da mayar da pant dina na fito tsakiyar d'akin na tsaya Ina dawurwura alamun zubewar ciki ne ba wani abu ba. Tunda aka shiga wannan rintsi wallahi na manta wai ina da wani ciki sai yanzu da naga jini ciwon marar ya tsananta. Jikina na gyara na fito falo a kintse Hauwa tana d'aki sai Baba Tabawa a falo da yara sun zagayeta tana basu labari. Kai tsaye d'akin na bi Hauwa tana kwance saman gado da wayarta a hannunta har yanzu babu sukuni a tare da ita ta tashi zaune tana kallona kafin ta ce." Ina kuma za ki je na gan ki da hijabi." Na ce." Hauwa babu lafiya 'bari zan yi wallahi yanzu haka maganar nan da nake yi miki jini ne yake zuba asibiti zan je. Ta yun'kura ta tashi da gaggawa tana fad'in." Bari na sa hijab muje Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Da sauri na fita daga d'akin jin yadda wani abu mai nauyi ya fado cikin pant dina. D'akina ana shiga da gaggawa na zarce toilet na yi sauri na tsuguna abun ya fado kafin wani mashahurin jini ya biyo baya da tsananin ciwon k'wankwaso da gwiwa. Bangon bandakin na dafe tare da rintse idona da k'arfi na kira sunan Allah Ina jin shigowar Hauwa d'akin da yake ban rufe kofar toilet din sosai ba kawai sai ta shigo ta kamani itama sunan Allah kawai take kira tana fad'in." Shikkenan gashinan ma ya fita cikin sau'ki sannu bari yanzu na tura Masa'udu ya je pharmacy ya sayo miki wasu magunguña ba sai mun je asibiti ba in sha Allahu, Allah Ya takaita miki wahala duk abinda ya yi saura zai fito cikin salama idan an yi amfani da maganin." [12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 106 Ban damu da jin abinda ta ce ba tunda na san aikinta ne. Ita da Baba Tabawa suka gyara toilet din tsaf. Baba Tabawa dai sai jajantawa take yi har da 'yar k'wallarta tana fad'in." Namiji ne gashinan har Ubangiji ya fara yi masa hallita. Hauwa da suke aikin tare uffan ba ta ce mata ba ta yi mata shiru kawai. Ina zaune a gefan gadon Baban ta zo ta fita da wata leda a hannunta tana fad'in. "In banda abinki Hauwa ya za a yi ya jefa d'an mutum a masai ina gaya miki gashinan Ubangiji ya fara fitar masa da hallitarsa. Ido na bi ta da shi Hauwa ta fito daga toilet din tana fad'in." Magana ai ta mutu Baba ki je ki kai a bunne shi tunda haka aka koya miki a makarantar islamiyarku ta mutanan da." Na dube ta a tsanake na ce." Abinda ya fita za a binne?" Ta gyada kanta tana fad'in." Haka ta ce, shine ta tattare ta zuba a leda wai ita dai ba da hannunta za a zuba d'an mutum a masai ba." Murmushi kawai na yi na ce." Hauwa kin san mutanan da camfi, wasu fa har yanzu suna wanke mahaifa tsaf su shiryata da likkafani su bunne. Ko musulunci an ce bata da wani amfani Ta ja tsaki tare da furta." Mu a asibiti ma wallahi tattarasu muke yi a buhu a kai bola. Bata da wani amfani face zaman da ta yi da d'anka a ciki." Shiru ya biyo bayan maganarta kafin ta numfasa a hankali ta ce." Wallahi Amina sai na ji Ina ma ace ni ce na samu wannan matsalar kin san Allah ba na k'aunar cikin nan da yake jikina." Na dube ta domin ni lamarinta ma yanzu ya daina ba ni mamaki, yadda ta tsananta kiyayyarta akan mijinta kamar ba jininta ba shine abinda yake masifar daure mini. Ni zullumi da tunanina ma yadda zan sanar da mai cikin ya zube ya amince kai tsaye ba tare da ya juya lamarin ba shine kawai abinda ya fi damuwa ita kuwa na fahimci yanzu gabad'aya ta daina tsoronsa balle ta daga masa kafa. Sai da na ci abinci tukkuna ta gwada mini duk yadda zan sa magunguñan da ta bayar a rubutuce aka sayo mini sannan na kwanta ita kuma ta tashi ta fita. Bacci ne mai nauyin gaske ya d'auke ni wanda cikinsa na kasance cikin hargitsin mafarkai marasa ma'ana. Shigowar kira a wayata dake gefena shi ya tashe ni cikin firgici na tashi zaune wanda ya yi daidai da tsinkewar jini da k'arfinsa wanda nake da tabbacin ya huda zanin jikina kuma babu makawa sai ya shafi mashinfidin da yake kan gadona. Wayar na d'auka na duba Hamusu ne da sauri nasa a kunnena. Jin shi cikin nutsuwa ya sanya hankali ya dan kwanta kad'an na amshi gaisuwar da yake miki kafin na tambaye shi su Kamalu da fara'a mai yawa a tare da shi ya ce mini gamu a ciki tasha a tare dama kiran da na yi miki kenan yanzu za mu wuce gida." Na sauke ajiyar zuciya tare da furta." Alhamdulillahi, ka gaishe mini da Gwaggo idan an jima da daddare na d'an samu nutsuwa a lokacin zan kira ka sai mu kàrasa tattauna yadda za a yi." Ya ce." To shikkenan anti sai na jiki in sha Allahu." Kashe wayar na yi na ajiye saman bedlamp kafin na zuro kafafuna kasa a hankali. Baba Tabawa ta turo d'akin ta shigo. Sai na sauke ajiyar zuciya domin na ji dadin shigowartata. Ta nufo ni tana fad'in." Sannu ai na shigo ya kai sau biyar ba ki tashi ba ga la'asar ta yi babu kyau bacci a irin wannan lokacin. Na ce." Tunda nasha magunguñan jikina ya mutu amma dai ciwon marar da sauki alhmdullhi sai jinin da yake zuba shine abinda ya d'an ba ni tsoro. Ta ce." Ai wannan dole ne sai a hankali zai dinga janyewa." Ban ce komai ba na tashi a hankali na nufi bandaki ina fad'in." Baba ki dan fito mini da wasu kayan tare da audiga sai ki miko mini." Ta amsa cikin kulawa. Wanka na yi da ruwan d'umi na gasa jikina sosai na shirya a toilet din na fito. Lokacin har ta cire zanin gadon da ya baci ta shimfida mini wani tare da sanya turaran wuta. Ina fitowa ta shiga bandakin da bedsheet din a hannunta. Bata fito ba sai da ta wanke zanin gadon tare da kayan da na cire ta fito dasu a boket ta fita can haraba domin shanyawa. Sai bayan sallar magriba Hauwa ta sake shigowa ta duba ni, mun kai kimanin minti talatin a tare muna tattaunawa kafin ta fita. A lokacin na samu sararin kiran Hamusu a waya gaishe ni ya sake yi kafin cikin inda-inda ya ce dama yanzu nake cewa bari na kira ki a waya gani nan tare da Gwaggo ma." Na ce." Allah sarki ba ni ita to." Tana kar'bar wayar cikin kulawa na gaisheta tare da tambayar yanayin jikinta ta amsa itama da kulawa. Sai da na d'an nisa tukkuna na fara yi mata bayanin duk abinda yake faruwa. Bata katse ni ba har sai da na kammala maganata kafin daga bisani ta ce." Hamusu duk ya yi mini bayani Amina kuma ai maigidan naki ma bai jima da tafiya ba mun jima muna tattauna magana akan lamarin rayuwar nan hakuri ake yi da d'a da dukiya duka babu wanda ya san mai amfanarsu sai Allah." Kaina ya yi masifar daurewa jin abinda take ce wa, gabad'aya tunanina sai ya tsaya cak! ya aka yi ya san abinda na shirya ko dai Hamusu ne ya gaya masa. Ita kuma Gwaggo mai take nufi da wannan maganar wato ita ba ta kishin nata kenan, tun asali ban santa da son abin duniya ba balle na ce ya rud'eta da kudinsa. Na ji maganar Hamusu yana cewa anti abinda ya faru shine d'azu bayan na sauko yaran nan a tasha sai na zarce dasu kasuwa domin saya musu kaya da abubuwan buk'ata kamar yadda ki ka bada umarni. A hanyarmu ta dawowa wallahi Sukairaju ya d'auko Yallabai a mota zuwa airport ya hange mu don shi bai ma gan mu ba shi Sukairajun ne ya gaya masa shine fa ya sanya shi ya biyo bayanmu har gidan Gwaggo. Babu yadda zan yi anti dole ta sanya na gaya masa komai a gabansa Gwaggwo ta yi fad'a sosai domin kin san ni da ke ba mu gaya mata matakin da muka dauka ba, anan ta sake tabbatar masa da cewa ita ta bashi yaran tun lokacin kwanciyata a asibiti kuma kyautar tana nan ba ta janye ba. Wannan dalilin ya sanya shi d'aukarsu amma ya ce zai a jiye su a gidan Hajja tunda ba kya son zamansu a abujan. Kyauta kuma ya kar'ba har abada." Wani irin takaici marasa misaltuwa ya lullubeni. Mutumin nan ya zame mini bala'i ta kowace siga dole sai ya tan'kwarani. Ban san lokacin da wasu lafiyayyun hawaye masu zafi suka fara silalowa kumatuna ba. Kashe wayar kawai na yi na ajiye ina jan hanci zuciyata kamar ta buga. can kamar saukar tsawa na ji saurin muryarsa a falo. Gabana ya fadi sosai domin kuwa wannan sautin ba na sa ba ne aro shi ya yi. Asali muryarsa sanyi ne da ita ko fad'a yake yi asalin muryarsa ba zata gigitaka ba sai dai zafin ba'kaken maganganunsa. Ban yi yun'kurin fita falon fa saboda bala'in haushinsa da nake ji a raina nasan dai dole zai shigo d'akin ya same ni. Baba Tabawa ta a shigo a gaggauce tana fad'in." Idan za ki iya fitowa falon ki fito Amina, mijinku ya shigo yanzu amma abin babu dad'i tsakaninsa da Hauwa." Na ce." Ka kyale shi kawa Baba, fitowata ba zata amfanar da komai b.... Ban kai ga rufe bakina ba na ji kukanta da maganganunta 'kasa-''kasa Baba Tabawa ta ce." Marinta yake yi fa." Na diro daga gadon da gaggawa "Duka!" Na furta da mamaki mai yawa, ai ba halinsa ba ne. Bar shi da ba'kar gaba da bakaken maganganu amma baya dukan mace. Bai ta'ba kai hannunsa jikina ba. Daidai lokacin da ya ke ce wa." Ke kadai ki ka zo, kuma ke kadai za ki fi ce mini daga gida. Yara kuma ita na yi niyyar bawa Maryam zan bawa, ban yarda da tarbiyarku ba." Tana kuka ta ce." Ai gado muka yi da ni da kai. Tunda abinda ya yi Hauwa shi ya yi Tajo. Hajja ta saki nono ta bawa Uwani ni dai duka babu na za'ba, Allah Ya saka mini." Ya sake kai mata mari ta goce tana fadin." Ni ma rabon shan wahala ne ya sanya ni auranka, kuma in sha Allahu mun rabu kenan har abada, kuma sani cewa wannan masifar daka 'kunsa mini sai ya shiga masai." Ya ce." Mu zuba ni dake 'yar iska shege ka fasa zan ga karshen iyashenki." Daga haka bai sake cewa komai ba ya dubi Baba Tabawa tare da ce wa." Ki had'o mini kan yaran nan ki biyo bayana da su. Da sauri cikin bin umarni ta ce." In sha Allahu ranka ya dad'e. Ya juya ya fita da saurin gaske. Na dubi Hauwa da mataccen jiki sai kuka take yi gabad'aya ta fice daga hayyacinta. Kafadarta na dafa ina fad'in." Sakin ki ya yi ne Hauwa?" Sai ta daga mini kai hawaye na silalowa ta ce." Kuma har abada ni da shi in sha Allahu." Ta wuce dakinta da sauri. Cikin sagewar gwiwa na bi bayanta ta shiga bandaki sai na zauna gefan gado har ta fito wanka ta yi ta fara shiryawa tana yi tana kuka. Na ce babu fa inda za ki je wallahi ai saki daya ne ki zauna ku daidaita." Shiru ta yi mini ba ta ce komai ba kuma ba ta fasa shirya kayanta cikin akwati ba. Na yi jigum da mataccen jiki, wato dai mutumin nan indai akan sha'ani na Momi ne baya ji baya gani, ai ban ta'ba tsammanin zai iya sakin Hauwa ba, a iya tunanina je ki gida ki huta kawai zai yi mata idan har an yi duba da matsananciyar dangantakar da take tsakaninsu. Duk kuwa da abinda za ta yi masa karfin zumunci da albarkar zuri'ar da ta ratsa tsakaninsu ba ta cancanci hukuncin saki daga wajensa. Ina zaune zukud'un ina tunani lallai kamar maganar Hauwa da 'kamshin gaskiya ko dai matar nan ba a haka ta bar mutumin nan ba, yakan rufe ido ya yi cin mutunci ga kowa muddin aka ta'ba nasabarta ko wani abu da ya dangance ta . Don kyautawa tabbas Hauwa bata kyauta ba ni ma a wurin na nuna mata rashin goyan baya, kuskure ne mai karfi kazafi ko tabbatar da abinda ba ka da shaida akai. Iyayen baiwar Allah nan daga ni har ita ba mu da masaniyar abinda ya kashe su. Mijinmu ta aura kawai bayan haka duka ba mu da wata ala'ka da juna. Wata'kila ita Hauwa ta jima tana bin 'kwakkwafi akan Momi din idan ba haka ba ta ina take samun irin wad'annan labaran masu muni. Tabbas idan gaskiya ne to momi abar gudu da kyama ce, idan kuma kishi ne ya rufe idon Hauwa ta kirkiro maganar ta fad'a bata kyauta ba ta aikata abinda ba shikkenan ba, amma a ganina a matsayinsa na namiji jagora mai nisan tunani bai kamata ya zartar da wannan d'anyan hukuncin ba. Gabana ya buga da karfin gaske a lokacin da na tuna irin abinda yake kwance ciki ya zube na shure umarninsa nasa yara a mota ba tare da yawunsa ba. Idan ya sake ni akan hakan ba zan wani damu ba, ai na yi abinda na yi daidai gwargwado sai na ha'kura da auran ma gabad'aya idan na mutu na riski Yaya Aminu a matsayin matarsa ta aljanna tunda ban tafi da zargen igiyar auran wani ba. Sai dai tsorona da fargabata shine ina shakkun ya sanar da Baban Saude domin kuwa yanzu shine yake tsaye akan al'amarina tun bayan sasancin da ya yi mana a shekarun da suka gabata. Kuma ba tun yau ba na lura da k'akkarfan zumunci da abotar da ta 'kullu a tsakaninsu. 'Bacin ran Baban Saude da tijararsa ita kadai nake gudu amma don ta kalubalen wannan mutumin baya damuna. Jan kofar da Hauwa ta yi shine ya dawo da ni hayyacina na daga kaina da sauri na ga gilmar fitarta da akwati madaidaiciya. Da azama na tashi na bi bayanta Allah Ya sa falon babu kowa tunda ya kwashe yaransa Baba Tabawa Kuma tana dakinta. Na ri'ke akwatin ina fad'in." Baki da hankali Hauwa ina za ki je a wannan daran ki yi tunani fa a abuja ki ke." Ta ce." Sai me idan a Abuja nake zan iya kwana a tasha a halin yanzu domin na yi rantsuwa ba zan kara kwana a wannan gidan ba." Na ce." Ke ma fad'a kawai ki ke yi, an ji ya sake ki, amma ai gidan d'an uwanki ne kuma uban yaranki, sannan addini cewa ya yi idan an saki mace ta zauna a dakinta ta yi idda idan da sauran rabo mijin zai iya mayar da ita kafin kammaluwar iddar don haka babu inda za ki je." Shiru ta yi tana kallona can kuma sai ga hawaye shaa! Murya a sarke ta furta." Wai saki Amina, ni mutumin nan zai furtawa saki ai ina ganin ko zai saki kowa wallahi ni ban cancanci hakan ba. Murmushi na yi Ina nazarin maganarta, ashe shiyasa ta mike kafa take iyashege saboda tasan ta taka tudu biyu a iya wautarta duk iyashegen da za ta yi masa ba zai iya sakinta ko wani hukunci mai tsauri ba. Rauni da gajeran tunani shine abinda yake cutarmu mu mata amma duk inda muke tunanin akan sha'ani na maza wallahi mune a k'asa dalili Allah Ya hallicesu daban da hallitar mata. Kuma dai dole duk isa da kasaitar mace sai dai idan ba ta yi auran ba. Ta nemi wuri ta zauna tana share hawaye na zauna gefanta a sanyaye na ce." Ke ma fa kina da laifi Hauwa tunda naga irin abubuwan da ki ke yi nasan lallai akwai abinda zai faru wanda gabad'aya ba zai yi mana dadi ba. Na sha gaya miki ki fita daga sabgarsa da matarsa idan ma tsuguna mata zai dinga yi babu ruwanki da su amma kin 'ki ji, kin ga a cikin igiyoyin auranki uku daya ta girgiza ita nata suna nan daram! Sai ta rufe fuskarta da tafin hannunta tana kuka cikin jajantawa kanta ta ce." Sai na gayawa mahaifiyarsa wallahi." Da sauri na ce." Aikuwa da kin da'bawa kanki wuka Hauwa, kin san ya tsani fa a kai shi k'ara wannan yana masifar 'kona masa rai, kuma dole Hajja ta bi ba'asin komai idan har za a yi adalci a lamarin dole ke ma a nuna miki rashin gaskiyarki. Kuma da yawa mutane za su ce kin shigar mini fad'a mun taru mun had'e mata kai muna azabtar da ita fassarar da za a yi mana kenan." Ta bude fuskarta tana kallona ta ce." To yanzu ya ki ke ganin zan yi, ni da wallahi gabad'aya hankali yana gida na gama shirya tafiya Bauchi." Na ce." Ki yi zamanki ki kyaleshi kuma don Allah kada ki sanar da inna Uwani kada sanadiyar hakan zumuncinsu ya raunana kin san mas'ala ta auran zumunci tana da wuyar sha'ani. A sanyaye ta ce." Shikkenan ba zan gaya mata ba amma wallahi matar nan yadda ta sanya ya sake ni saboda ita sai na wulakantata." Da mamaki mai yawa na ce." Wane irin wulakanci kuma Hauwa, don Allah ki samu nutsuwa gabad'ayanmu fa babu yaro, yanzu ke za ki gyara auranki da zumuncin da yake tsakaninki da shi, na gaya miki idan kina so ki samu nutsuwar zuciya don girman Allah ki fita sha'aninsa da matarsa." Shiru ta yi ba ta sake cewa komai ba, ta dai sunkuyar da kanta kasa tana tauna lebanta tabbacin abin da ya yi mata ya yi mata ciwo a zuciyarta. Sai wajejan tara da wani abu tukkuna muka rabu ta shiga d'akinta da zummar shan maganin ciwon kai ta kwanta dalilin kukan da ta ti'ka, abinci ma ni na bi bayanta da shi kafin na fito falo na zauna na ci nawa muna hira jefi jefi da Baba Tabawa wajan goma da rabi ya shigo Baba Tabawa da saurin gaske ta yi masa barka da shigowa ya amsa babu wata kyakyawar kulawar da yake yi mata domin mutuniyarsa ce sosai a wasu lukutan har barkwanci suke yi ita dashi amma abin mamaki ko yau ni ma ban ji dadin abinda ya yi mata ba. Ta dube ni tana fad'in." Ni ma kuna nema ku shafa mini kashin kaji Amina, Yallabai kamar fa haushina yake ji duk yadda nake ko'karin ganin na gyara ku abin zai shafe ni. Yadda ta yi maganar da alhini da damuwa sai ta ba ni tausayi da dariya na d'an yi kad'an kafin na daidaita kaina na ce." To ke ina ruwanki Baba, kawai dai ransa ne a b'ace shiyasa ki ka ga bai amshi gaisuwarki da kulawa ba, kada ki wani damu ai ba ki da lefi." Ta yi shiru tana jijjiga kai har da tallafe ha'ba. Na yi dariya sosai Ina fad'in " Hajiya Baba Tabawa ta mu ta gargajiya." Ta dube ni da yanayi na zullumi amma ba ta ce komai ba. Daga can barandar samansa na ji maganarsa na juya da sauri yana tsaye hannunsa zube a cikin jallabiyar dake jikinsa ya ce." Zo." Na yun'kura na tashi da tahamidi da kuma addu'ar rinjiye wannan lokacin nake jira, na kuma ji dad'i da ba a ja dogon lokaci ba gwara a yi ta ta 'kare kawai. [12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 107 Na d'auka idan na shiga d'akin zan gan shi a rikice cikin matsananciyar damuwa, abinda ya ba ni mamaki bai wuce ganinshi a zaune a gefen gado da waya a kunnansa yana magana cikin rarrashi da wata kalar murya wadda tun tsayin zamana da shi ban san shi da ita ba. Jikina ya d'an shika kad'an amma lokaci d'aya ban bari ya fahimci raunina ba, na zauna gefansa hankali da jina yana kansa domin fahimtar da wa yake waya. Kasa gane kowacece na yi domin da da farko na d'auka Momi ce sai da na ji yana kiran Maman Hanif tukkuna na yi tsai ina tunanin wacece wannan kuma. Tunani ya katse lokacin da na ji sautin maganarta cikin reshin kuka ban dai ji mai take gaya masa ba, amma gabad'aya yanayin yadda take magana shi ya tabbatar mini da cewa cikin tsananin b'acin rai take. Na dinga nanata sunan a cikin raina Maman Hanif domin na kasa gane wacece can nazarina ya hasaso mini Nabila kanwar Momi tabbas ita ce babban yaronta sunansa Hanif hakane yakan zo wurinsu Adam a duk lokacin da aka yi hutun makaranta. Ajiyar zuciya na sauke na sake kai duba na gare shi ya tak'arkare yana ta rarrashi da ban ha'kuri na gyada kaina ina jimanta matsayin momi da alhalinta a zuciyarsa. Maganar abinda ya faru tsakaninta da Hauwa suke tattaunawa da 'kyar dai da jibin goshi da irin rausayar da kai da muryar da yake yi ya rarrasheta ta ha'kura tare da kudirin janye 'karar da suke ko'karin shigarwa akan Hauwa. Na ji dad'i dai da bai gaya mata irin hukuncin da ya yanke ba ba domin a yadda yake a zaburen nan abu ne mai sau'ki ya gaya mata cewa ai ya saki hauwa. Wasu lukutan kuma zurfin cikinsa yakan burge ni ya kuma yi masa amfani. Tabbas Hauwa bata kyauta ba, kuma ni ban ga laifinsu ba don sun ce za su kai ta 'kara matsalar kawai idan har aka bari hakan ta faru gabad'aya rayukan kowa ne zai b'aci shiyasa Annabi ya yi hani da tayar da masifa domin idan ta tashi kafin ta kwanta sai an d'auki wani lokaci. Ya kashe wayar ya dube ni fuskarsa kadaran kadahan. Kafin ya yi gyaran murya ya ce." Ina alkawarin da muka yi ni dake ranar da baban Saude ya yi mana sulhu." Kallonsa na yi kafin na ce." Wane alkawari muka yi?" Shiru ya yi yana kallona kafin daga bisani ya gyad'a kansa ya furta." Kun kyauta ke da Hauwa, idan an ce kuna yi wa matar nan ganin kyashi ku ce ba haka ba ne, yanzu tsakani da Allah Amina daidai ne ku sanyo iyayenta da suke kwance a kabari ku zage su har ku jingina mutuwarsu da abu mafi muni shin kishi hauka ne?" Shiru na yi ban tanka masa ba, zuciyata kuwa in banda tsalle babu abinda take yi. Ya cigaba da ce wa." Maryam ba ta cancanci wariya da k'askanci irin haka daga wurinku ba, ke Amina idan har Hauwa za ta yi d'amarar cin mutuncin Maryam ni a nawa tunanin ke ba za ki ba ta goyon bayan ba dalilin kyakykyawar alakar dake tsakanin yaranku da kuma alherin..... Bai kàrasa ba na katse shi domin ji na yi zuciyata ba za ta iya d'auka ba. "Ni 'yar sharri ce ko, kuma muguwace 'yar hassada da ganin k'yashi saboda ba ni da gata ko?" Bai ce mini komai ba. Sai na cigaba da ce wa." Ita Nabila ai sharri ta yi mini domin wallahi ban san menene yake tsakaninta da Hauwa ba hayaniyarsu kawai na ji Ina d'aki a kwance kuma babu yawuna duk abinda Hauwa take yi babu hannuna amma ban ce lallai ku yarda ba da kai da su ba, don girman Allah kada ku bari mu sha ruwa, ku turo mota mai cike da sojoji su tafi da mu." "Wace hujja ce za ta nuna mini ba had'a ba ki kuka yi domin ku ci zarafin matar nan ba. Shin mai ta tsare muku ne, ni ba zan goyi da bayan karya na take gaskiya ba, domin alherinta nake ga ni, kuma ta yi mini ta yi muku." Na ce" Saboda muna yi mata bakinciki dalilin dukiyar da ta tara shiyasa muka had'e mata kai. Uban wanene ya ce ta d'aukar mini yara. Idan ka mallaka mata twin's wannan naka ne, ban damu ba, nawa dai da baka da iko a kansu ban ce mata Maryam ga yarana ri'ke mini ba." "Har da zagi a cikin maganarki saboda baki da mutunci ko Amina? Ni ban kira ki domin ki yi mini rashin kunya ba matsaya nake so mu nema ni dake zan 'bata miki rai wallahi tallahi!" Ya kai karshen maganar cikin tsananin b'acin rai." Kuka na fashe da shi tare da furta." Ai gaskiya na fad'a ban fa nemi wani mahaluki ya rike mini yara ba, karfi a gwada mini, an yi kuma an biyo mu da sharri a ce ba zan yi magana ba.'' Ya ce." To yaran da ki ke ta ha'kilo a kansu ai an mallaka mini su ke ce ki ke haukanki kuma wallahi sai na so zaki gan su balle ki gwada gadara a kansu, kin haife su ne amma billahi ko kaffara ba zan yi ba sun fi ki hankali, dama tuntuni na gane karamin Yusi nake nufi ya fi ki nutsuwa da sanin ya kamata saboda ai ba tarbiyarki ba ne shi din." Bakina ne ya mutu murus! na kasa tanka masa saboda tsabar takaici da b'akinciki wace irin masifa ce wannan nake cikinta ne, ni Aminatu. Hawayen rashin yadda zan yi suka dinga gudana a kumatuna. Wato ita 'ya mace ta ko'ina rananniya ce Mutumin nan ya dabaibaye rayuwata ya d'aure ni ya hana ni motsi duk ta inda na b'ullo sai ya ci galaba a kaina. "Yanzu daidai ne a matsayinku na iyalina ku tsaya a gaban alkali domin shari'a?" Kaina a sunkuye na gagara ce masa komai saboda gabad'aya ma tunanina ya tsaya cak kwakwalwata hutu take buk'ata. Ya cigaba da ce wa." Ba ni da wata hujja mai k'arfi da zan dakatar da su akan abinda suka niyyata don cin zarafi da rashin kyautatawa kun yi musu, menene na sanyo iyaye a ciki Amina har da ala'kanta mutuwarsu da wani lamari mara dad'i, kun kyauta a hakan?" Ya kai k'arshen maganar a d'an raunane har ma da karyar da kansa domin ga dukkanin alamun kukan da nake yi ya fara ta'ba shi, kuma yanayinsa ya nuna gabad'aya masifar shi ma ta ishe shi. Bance masa komai ba har sai da ya sake maimaitawa kafin na daure na ce." Ni fa laifina kake gani da gangan, amma wallahi ba ni da hannu akan duk abinda Hauwa ta yi, na gaya mata ba daidai ba ne, ta daina ta'ki ji, to ya zan yi mata, kuma kai ma me yasa ba ka tambayi dalili ba kawai sai ka dinga d'aukar laifi ka d'ora mini." "Ya ba zan ga laifinki ba Amina, idan kin manta da alkawarinmu ni ban mance ba, mun yi dake cewa duk rintsi duk wahala za mu zama abu daya matsalata zata zama taki haka zalika matsalarki za ta zama tawa, amma lokaci guda kin karya alkawari har kina nuna mini iko da gadara akan yaran da ki ka haifa da wani namiji, ni za ki yi wa gori ko?" Wasu hawayen suka sake silalowa saman kuncinta na ce." Ni ban ga ta inda na yi lefi anan ba, idan har gaskiya za a bi, yaron nan Salim ya fito karara ya nuna rashin kaunarsa ga Kamalu ya yi masa abubuwa masu muni amma da kai da ita matar taka babu wanda ya ta'ba nuna masa hakan ba daidai ba ne. A cikinku kuma babu wanda ya neme ni da maganar domin a ba ni ha'kuri ai ku din ba yara ba ne, kun san daidai da rashin daidai ba a kyauta mini ba in dai gaskiya za a bi, yaron nan Kamalu ba a yi masa adalci ba tunda sharri aka yi masa." Shiru ya yi bai yi magana ba, d'akin ya cigaba da d'aukar sautin shashshekar kukana da sautin jan hancin da nake yi. Ya nisa kafin ya ce." To yanzu ha'kuri ki ke so a baki kenan? D'auke kaina na yi ban kalle shi ba don yadda zuciyata take tsalle ji nake yi kamar na rufe shi da bugu. Ya rungumo k'afadata a hankali ya sanya ni a jikinsa yana jijjigani. Cirewa na yi tare da matsawa gefe ya dube ni a nutse kafin ya ce." Allah Ya huci zuciyarki ba a kyauta ba gaskiya, kuma zan gaya miki ni ma ban yarda ba. Shirun da na yi ba yana nufin na yarda da maganar Salim ba ne, ina ta nazarin yadda zan yi na kawo sasanci a tsakaninsu, tabbas Kamalu yaro ne da nake kyautata masa zato, ina so ki cire duk wani wasiwasi a zuciyarki ba na nufin yaranki da sharri sai alheri." Shiru na yi jikina ya d'an yi sanyi kad'an domin na d'an hangi alamar nadama da neman sasanci a tare da shi. Ya cigaba da ce wa." Ku zauna lafiya don Allah, ni na gaji da wannan fitinar taku. Kin tura yara kano ba tare da yawuna ba, tunda ba kya son zamansu a tare da ni shikkenan na kai su wurin Hajja tunda Gwaggwo ta mallaka mini su. " Ya fad'a cike da kwarin gwiwa." Na ce." Ni ba damuwata ba ce wannan abinda ya fi tsaye mini a rai shine datse igiyar auranka da ka yi tsakaninka da Hauwa akan wannan matsalar kenan hakan yana nuna cewa a shiryeka kake duk lokacin da sa'ba ni ya gifta tsakaninmu da matarka ka yi saki tunda bashi da wahala a wurinka." "Ni ba saboda wannan matsalar na saketa ba, Hauwa ba ta jin maganata domin duka wannan hargitsin itace mussababi domin da ba ta gaya miki ba ina ganin da duk hakan bata faru ba muna zaune lafiya, tun kafin mu zo nan na gargad'eta ta take umarinina, ke a ganinki abinda ta yi daidai ne ko rashin daidai ne. "Ni ma ban ce ai ta yi daidai ba. Amma kai ma ai ba ka yi daidai ba, mai yasa za ka saketa. Kai tsaye ya ce." Saboda na gaji da halinta." Na zuba masa ido da mamakin maganarsa a tare da ni. Wato ita mace cikin kowane hali za ta iya jure zama da namiji amma shi kuskure karami sai ya nuna rashin ha'kurinsa. Hauwa dai duk a cikinmu ta fi kowa kusanci da shi amma gashi yau yana fad'in ya gaji da ita. Na ce." Ka mayar da ita tunda ciki ne da ita sanin kanka ne a musulunci babu kyau sakin mace da ciki, kuma idan Hajja ta ji hakan ranta ba zai yi mata dad'i ba." "Ai ita Hauwa ba ta duba haka ba Amina, kuma cikinku wallahi kada wadda ta kuskura ta gayawa Mahaifiyata akan hakan rai zai 'baci." "Ai kai zaka gyara matsalar gidanka kafin ta fita waje idan ba ka so Hajja ta ji abinda ka yi sai ka yi gaggawar gyara kwabar da ka yi." Ya 'bata rai yana fad'in." Kina so ki ba ni umarni kenan?" "Ba umarni ba ne ban isa ba, shawara ce nake ba." "To ba zan d'auka ba har sai kun je ke da ita kun bawa Maryam da 'yar uwarta ha'kuri akan abinda ku ka yi musu.'' Ido na zuba masa ina kallonsa da mugun takaici. Na gyada kaina tare da janye idona daga kansa ban ce komai ba.. Sai ya cigaba da ce wa." Wannan shine kawai, ki ja ta tunda tare kuke kulle-kullenku sai ku je ku ba su ha'kuri domin mun yi magana da Nabila ce wa gobe za ta koma jos, to kafin ta tafi din sai ku gyara kuskuranku" Na juyo fuskata a d'aure na ce." Wannan kuma shine ba zai yiwu ba, idan hakurin da ka ba su bai isa ba, shikkenan don Allah ka cikashewa Hauwa sauran igiyoyinta da suka rage, idan hakan ma bai yi maka ba sai ka had'a har da ni gabad'aya." Ya ce." To kada ki sake yi mini magana akan abinda ya shafi tsakanina da Hauwa, ba ke ki ke auranta ba, ni ne babu ruwanki wannan shine maganarmu dake ta k'arshe akanta." Na dinga kallonsa zuciyata na sake suyuwa da kutun takaici da b'akinciki. Wannan wani abu ne da zai yi masifar wahala a ce Hauwa ta je ta bawa momi da nabila ha'kuri saboda iya zaman da na yi da ita na gane cewa macace mai mugun girman kai da kifad'i, ga taurin kan tsiya, bai shirya kwantar da rikicin ba, domin da ya shirya mutuwar matsalar ba zai 'bullu da wannan abinda ya san lallai da wahala ya yiwu ba. Jin an kira shi a waya ya sanya na tashi na fita daga d'akin ba tare da na sake cewa komai ba, matsalarsu ce can ta family iyakacina shawara, kuma ni ban tura Hauwa cewa ta yi abinda take yi ba, akan kanta take yi saboda wata manufa tata da kuma masifar kishi, duk wanda zai zarge ni da hannu akai ya d'auki hakkina. Ba zan sake cewa masa komai ba. Bai kwana a gidan ba a ranar sai washe gari wajen daya da rabi ya shigo cikin kayan shan iska da cazbaha a hannunsa ga dukkanin alamu daga massalaci ya fito mabiyin sunnah ne sosai da zazzafar akida da rashin son bidi'a da yawa. Bai fad'a ba amma tuntuni na gane ce wa mugun dan izala ne tunda yawanci abokanshi larabawan nan na madina duka 'yan ahalissuna ne. Muna falo duka a zaune ya shigo ya d'an tsaya ana gaisawa ya amshi ta kowa a d'an sake. Ina kallon Hauwa bayan sun gaisa ta tashi ta shige daki. Sai na ji wani iri a raina, na yi shiru tare da yin k'asa da kaina ina jin suna ta labari da Baba Tabawa kamar yadda suka saba. Ya jima a tsaye a wurin suna magana ban tofa tawa ba. Kafin ya haura samansa. Baba Tabawa ta juyo tana kallona da wani yanayi na alhini da damuwa ta ce." Irin wannan matsalar nake ta guje muku faruwarta Amina, rayuwar nan gabad'ayanta 'yar ha'kuri ce, shi namiji yana fa da wani irin iko da damar da Allah bai bawa mace ba, yakan iya yin komai ya kwana lafiya amma ita mace za ta yi abin ya zame mata matsala gagarima, ita wadda kuke ta ha'kilon akanta tana can hankalinta kwance mijinta ya kar'bar mata rigimar tunda ai kun had'e mata kai, ai ta fi ku wayo ta kuma fi ku shekaru da gogewa ta yaya ko tana da laifi zai gani bayan koyaushe cikin nuna alherinta take. Ki duba ki gani cikinku babu wanda ya fi kusanci dashi sama da Hauwa amma yau an wayi gari tana wasan 'buya da shi. Shi kuma ko a jikinsa bai damu ba, ya kamata a ce ku nemi sulhu ita Hauwa ta kar'bi kuskuranta tunda a bayyane yake ta yi ba daidai ba." Murmushi na yi irin na rashin sukuni na ce." To Baba Tabawa ya za a yi ne, mun jima muna magana dashi jiya da daddare abinda ya tsiro dashi ne nake ganin da wahala ace ya yiwu nasan Hauwa sai dai a rabu akan ta je ta ba su ha'kuri abinda ya ce kenan muddin tana so su daidaita ta je ta bawa momi ha'kuri da kanwarta nabila akan zagi da 'kaharun da ta yi wa iyayensu, ni kuma nasan halin taurin kanta da mugun kifad'i." Ta gyada kanta cikin damuwa tana ce wa." To ke dai ki yi takatsantsan sosai, amma a shawarce Ina ganin ta bi umarinsa kawai domin zahiri mijinku ba irin wanda ake tursasawa ba ne ko kuma mace ta juya shi. Na ce." Mu dai ba za mu juya shi ba. Amma ai matarsa da yake tare mata fad'a juya shi take yi kamar waina a tanda idan ba haka ba menene dalilin da zai sanya ya saki matarsa a kanta uwar babban dansa namiji kuma yar uwarsa. Baba Tabawa ki dubi lamarin nan fa da kyau!" [12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 108 Baba Tabawa ba ta kai ga magana ba kiransa ya shigo wayata da take ajiye a gefana. Ina d'agawa ya ce." Ki zo yanzu." Bai bari na ce komai ba ya datse kiran. Na yun'kura na tashi da wayar a hannuna ina fad'in.'' Baba bari na sauko sai mu cigaba da tattauna maganar da muke yi." Ta ce." Shikkenan a sauko lafiya." Ina hawa saman gabana ya fadi ganinshi zaune daga shi sai karamin wando na ciki ya cire kayan dake jikinsa. Kallo daya na yi masa na d'auke idona domin lokaci guda na fahimci menene a cikin kwayar idanuwansa. Gabana bai daina bugawa ba har na isa inda yake zaune. Na zaune zuciyata cike da zullumi da damuwa. Ya ce." Za mu sake gaisawa ko?" Kallonsa na yi cikin nauyin baki na ce." Ai mun gaisa da ka shigo. Ya kamo hannuna yana duba yatsun kafin ya rintse da nasa ya hade yatsunmu wuri d'aya a hankali ya ce." Wata kalar gaisuwa na zo miki ta mussaman." Shiru na yi tare da yin k'asa da kaina. Na fara jin cikina yana murd'ewa domin ban san ta yadda zan sanar dashi cewa cikin nan fa ya sake ficewa ba. "Kuna da abinci ko, domin Ina so na cika cikina kafin na wani lamari ya faru a tsakaninmu." A hankali na ce." Da abinci Baba Tabawa ta yi sai dai ba irin wanda kake so ba ne jallop din taliya ne da kifi.'' Ya d'an sake rintse hannuna dake cikin nasa a karo na biyu kafin ya ce." Gaskiya kam ba irin nawa ba ne, amma in dai da zafi a ba ni zan ci.'' Na ce." Da zafi mana tuna a kula yake." Hannuna nake ko'karin cirewa daga cikin nasa ya rike yana fad'in." Wai ke ba kya yin irin 'kunshin nan ja da 'baki zai yi mini kyau domin kina da kyawun fata ina so a dinga yi mini." Shiru na yi. Ba tun yau ba na fahimci yana son lalle sosai, ni ce dai ban mayar da hankali ba, amma na lura matarsa momi tana yawan yi. Amma henna ake yi mata a kafafu da yatsun hannuwanta. Ya ce" Akwai wata yarinya dake yi wa Maryam zan sanyata ta turo muku ita sai ta yi muku." A takaice na ce." Sai ta zo. Ya bi bakina da kallo yana lumshe Ido. Wani irin yanayi na ji a jikina amma nan da nan na shiga taitayina domin na fi kowa sanin cewa matsala ce kwance-kwance. Cikin 'yar damuwa na ce." Na kawo maka abinci ne?" Ya girgiza kansa alamun a'a. Na ce." Saboda me?" "Ke kadai za ki iya gamsar da ni yunwar cikina." Na yi shiru dai. Ina jinsa ya matso sosai tare da janyo ni jikinsa yasa hannu a dokin wuyana yana tatta'ba wajan da ya zama guru-guru kafin yasa baki ya sumbata. Ya dora hannuwansa biyu duka a kirjinsa. Ajiyar zuciyarsa na ji a saitin kunnena. Ganin ya fara ki'dimewa sai na dan ja baya tare da jan hanci domin na ma kasa cewa komai sai zare ido nake yi. Ya sake matsowa yana fad'in." Menene haka, yaushe rabon ma da na nemi wani abu Hajiya." Na ce." Ba haka ba ne, kawai dai Ina so na gaya maka ne cewar ba ni da tsarki." Sai ya yi sakato yana kallona har ya so ya ba ni dariya domin wata kala ya zama kamar wani sakarai. Na yi kasa da kaina na ji yana cewa." Ina ce 24 ga kowane wata na bature kike yin al'ada ko ba haka ba ne, yau nawa ga wata?" Ya fad'i maganar yana tsatstsare ni da ido. Ban dube shi ba na ce." Yau shida ga watan aprilu." "To mai ya kawo jini kuma?" Shiru na yi domin kuwa zahiri ba na so na yi masa karya amma da sai na ce ai lokaci ya kan canza sa'i, da lokaci mussaman idan shekaru suka tura. Tambayarsa ya sake maimaitawa idonsa a kaina. Cike da shahada da kundubala na ce." Dama ina so na gaya maka ban san yadda za ka kar'bi lamarin ba, amma ni Allah ne shaidata, shine kuma zai tsaya mini a ko'ina, wallahi shekaran jiya cikin da nake d'auke da shi ya fita. Amma na alak'anta faruwar hakan da wannan rikicin da muke ciki, alhamdulillahi babu wata matsala domin Hauwa ta sanya Masa'udu ya sayo mini magunguña masu kyau sun taimaka mini kwarai wurin wanko mini mahaifa. Lokaci k'ankani yanayinsa ya daidaita babu wani rausaye-rausaye da lumshe-lumshen Ido irin na fitina, zahirinsa ne ya bayyana ya 'kura mini idonsa da wani irin yanayi na mussaman tattare da shi. Kasa jimirin kallonsa na yi sai kawai na yi 'kasa da nawa idon cikin zuciyata Ina fad'in 'Duk abinda za ka yi, ka yi wanda ya fi shi a baya kaddara ce. 'Dakin ya d'auki shiru na tsayin mintina bai tanka mini ba amma a jikina na ji cewar har yanzu bai cire kwayoyin idanuwansa daga kaina ba. Cike da ko'karin ture rauni da kasalar dake ko'karin dabaibayi ni na dago idona. Karaf idonsa ya shiga cikin nawa, gabana ya fadi ganin cikowar kwalla a dukkanin kwarmin idonsa don sauran kad'an ma ta fara tsiyaya. Gwiwa ta sage cikina ya sake murdawa. Cikin gaggawar na sake yin k'asa da kaina ban yadda na sake kallonsa ba domin ji na yi gabad'aya na sare lamarin har ya kai a ce za a zubar da kwalla. Na san a yanzu abinda ya fi buri da buk'ata bai wuce ganin gidansa cike da yara ba. To ni ba budurwa ya aure ni ba, balle ya ce, sannan kuma shekaruna sun yi nisa dukda dai ban wuce haihuwar ba, bayan haka kuma ni dashi muna da matsala wadda ya taketa da k'afafunsa na kuma yi hakuri na bi shi a yadda yake so. Ba ni da niyyar sake zubar masa da ciki tunda alkawari na d'auka tun lokacin sulhunmu da Baban Saude. Idan zan samu ciki ya kasance duk yaron da zan haifa yana da matsala zan jure dalili alkawari da rantsuwar da na yi wa Baban Saude Allah ne mai yin yadda ya so. Gyaran muryarsa ya dawo da ni daga dogon tunanin da na tafi. Dubansa na yi sai na ga babu kwallar gogeta ya yi ko mayar da ita ya yi Allah ne masani. "Ta shi ki ba ni wuri kawai Amina." Wannan maganar ya furta mini babu sukuni a tare da shi. Ban ce masa komai ba na tashi na kama hanyar fita daga d'akin kamar yadda ya buk'ata. Jikina gabad'aya duk a sanyaye ban san kuma mai ya taka ba tunda zahiri yanayin da ya shiga ya nuna mini cewa ya ji zafin abin. Bayan kwanaki biyu gidan na mu ya kasance kamar kufai. To babu motsin yara shiru. Hauwa kuma ta tsiri zaman d'aki sai na yi, na yi da ita ta fito falo ta'ki. Sai yamma muke zama ni da Baba Tabawa mu d'an yi hira. Shi kuma maigidan tun shekaran jiyan da ya fita bai sake leko mu ba. Baba Tabawa tana kicin domin dora sanwar dare na fito falon da waya a kunnena. Bikin Yusura ne ya tashi kuma abinda ya kawo tsaiko a wancan lokacin balagorun da saurayin ya yi libiya domin neman kudi dalilin da ya sanya iyaye suke ce a bari ya dawo sai a d'aura auran tunda duk gidana. Mun gama magana da ita akan kada na ga ta sayi ko cokali domin tun da aka kawo kudin nake jadadda mata. Wancan karon ma na sanyata ta yi amfani da maganin sanyi hakan ba zai 'ki ba tunda ai 'ya macace, ita kuma duk inda take 'yar gyara da kula ce. Kuma koyaushe ba'a rabata da maganin sanyi domin shine tushen gyara aure da lalatashi. Garkuwar mata itace mai magunguñan Islamic din da na aminta da ita, dukda ita Hauwan ce ta had'a ni da ita, amma dalilin yawan sayan kayanta da nake yi ya sanya muka yi sabo da ita sosai. Duk wani nau'in magani na gyaran mace tana sayarwa masu kyau da inganci. Na ce ta sake yi mata magana akan ta hadawa amaryar set din amare kamar dai wancan karon zata hada mata magangunan sanyi da na gyaran nono sannan ta kuma yi mata budurwar kaza da sauran maganin gyara idan sun gama zan tura mata kudin daga nan, in sha Allahu 08089965176 duk wata 'ya mace da take neman sahihan magunguña masu kyau marasa cutar da GARKUWAR jiki to ta nemi GARKUWAR MATA domin kuwa kayanta duka babu na kaico ana samun biyan buk'ata. Bayan mun gama maganar sai na kashe wayar na nufi kicin domin anan nake jin motsin Baba Tabawa na sameta tana ta buga sakawara a turmi. Na ce." Sannu da aiki Baba." Ta juyo da sauri tana amsawa. Na ce." Baba ko dai a samo miki wadda za ku dinga aikin nan tare, dukan sakawara na mai k'wari ne." Tana dariya ta ce." Ni ma da kwarina ai, kuma aikin duka duka guda nawa yake. Yara ba anan suke cin abinci ba, ku biyu ne fa sai ni ta uku sai Masa'udu sai masu gadi biyu shikkenan fa, to sai kuma mai gayya mai aiki idan ya shigo gidan shi ma kuma sa'i da lokaci ne. "Na ce." Hakane amma duk da haka za a cigita wadda za ta taimaka miki koda da wanke wanke da shara ne ke kuma sai ki ji da girkin ko.'' Ta gyada kanta tana fad'in." To hakan ya yi babu lefi, yau na ce bari na yi sakawara an kwana biyu ba a yi ba. Na ce." Hakane kin ga ma tana daya daga cikin abinda maigidan yake so bayan towon da kike masa." Tana bud'e leda ta ce." Ina kuwa fatan Allah Ya sa ya shigo gidan yau." Na amsa da amin a takaice kafin bar kicin din jin alamun motsi a falon. Khalil ne tare da Usaina sai wata matashiyar budurwa da bata haura shekaru ashirin da biyar ba. Rige-rigen gaishe ni suka fara yi har da tsugunawa "Mama ina yini." In ji Khalil na amsa ina dariya tare da nazartarsu yaran suna cike da walwalarsu da annushuwa gasu nan cikin suttura mai amince. Itama ta tsuguna "Mama ina yini." Usaina kenan. Dariya ta kama ni na ce." Ina yini Usai ina Hassana da Minal" Ta tashi tsaye tana ce wa." Suna can gida." Khalil ya ce. Momi ce ta ce wai ga mai lallan da take yi mata." Na ce." Aikuwa ka ce mata mun gode sosai." Suka juya za su fita sai na ce." Kai Khalil dawo ku shiga ku gaida Mamanka mana." Ya ce." To. D'akinta suka nufa tare da Usaina tana bin sa zugwi-zugwi a baya. Na sauke ajiyar zuciya bayan shigewarsu na juyo kan mai lallan cikin nutsuwa ta gaishe ni na amsa ina fad'in." Wane iri za a yi mana ja ne ko baki?" Tana fito da kayan aikinta daga cikin wata 'yar jaka ta ce." Duk biyun Ina yi wanda kuke so za a yi." Na ce." To a yi mini duka ja da bakin. Amma dai ba na son dogon zama. Ta ce." In sha Allah daga nan zuwa magriba komai ya kammala." Khalil ne ya zo ya gifta ni yana goge fuska. Da sauri na ce." Kai menene ." Bai ce mini komai ba ya wuce yana dafe idonsa. Kawai na ji fashewar kukan Usaina cikin gwarancinta tana ce wa." Mama ta dake shi a fuska." Da wani irin yanayi na ce ." Mai ka yi mata?" "Ba komai." Ya fad'a da sauri ya kama hanyar fita kamar ma a tsorace yake Usainar ta bi bayansa itama da sauri. D'akin na shiga na ji motsinta a bandaki tana ta kakarin amai. Can na bita sai da ta gama tukkuna ta wanko fuskarta ta fito koda ta gan ni a tsaye a bakin kofa ba ta ce mini komai ba ta nemi gefan gado ta zauna. Laulayin ne ya dawo mata sabo da kuma hatsaniyar nan da muke ciki gabad'aya duk yanayinta ya canza ga wani uban haske da ta yi fau sai wasu k'ananun kuraje da suka feso mata a fuska. Na ce." Wai ba ki da lafiya dama Hauwa." Tabe bakinta ta yi kafin ta girgiza kai ta ce." Amai ne ya takura mini wallahi cikin 'yan kwanakin nan, amma in banda shi babu abinda ya dame ni." Na gyad'a kaina a sanyaye na ce." Allah Ya bada lafiya." A takaice ta amsa da Amin. Na ce." Khalil ya fito yana kuka Hauwa ba kya neman zaman lafiya ko, kin fi kowa sanin abinda mutumin nan ya tsana a rayuwarsa a daki yaran nan mussaman shi Khalil din daga gaisuwa kuma sai duka fisabillahi , ai ba shi ya yi miki ba." "So na ke a yi ta take ai, shiyasa na dake shi. Ni ma ai iyayene suka haife ni. Ya dake ni a fuska kwanaki yanzu kuma yana dukan zuciyata da iyakacin karfinsa. Bai isa dai ya canzawa towo suna ba." Shiru na yi Ina nazarin maganarta kafin na ce." Duk wannan bai ta so ba, za ki dasawa yaron nan k'iyayyarki da jin tsoronki a cikin ransa. zai kara yin nesa dake tunda tsakaninku duka ne da kyara da hantara, don girman Allah ki daina." Hannu ta daga mini sai kuma hawaye suka k'wace mata ta ce." Kin san irin rad'adin da nake ji a zuciyata kuwa Amina ? wai Yaya Tajo shine yake fifita wata bare wadda ba su had'a dangantakar komai ba akaina. Na haihu dashi Bata haihu dashi ba. Jinina ne shakiki. Ita kuwa a duniya suka had'u, amma ya tozarta rayuwata a kanta. Wallahi har na mutu ba zan yafewa matar nan da alhalinta ba." "Kai! Innalillahi! don darajar Allah Hauwa maganar nan ta mutu haka na rantse da Allah ta ishe ni. Ki gyara tsakaninki da shi kawai ki daina duba wata dangantaka namiji ne za ki ga abinda ya fi haka fa." Shiru ta yi ba ta ce komai ba, na ce." Ga mai lalle ta zo za ta yi mana, ki fito falo." Ta dube "Kin ga na yi kama da wadda za ta yi wani lalle yanzu?" Na ce." Kwarai kuwa, ai ke ya kamata ma ki yi kitso da lalle domin jan hankalin mijinki ku daidaita har ya janye abinda ya ratsa tsakaninku." Ta ja tsaki tare da gyara kwanciyarta tana fad'in." Kada Allah Ya sa ya janye wallahi babu abinda zan yi, ai ke ce matar gida." [12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 109 Na gyad'a kaina ba tare da na sake yin wata magana ba na juya na fita daga d'akin gabad'aya zuciya sam babu dadi. Yarinyar ta iya lalle sosai tana da zane ganin kamar ta d'auki mai wahala da jinkiri ya sanya na ce ta takaita domin ba ni son zama shine dalilin ma da ya sanya ban fiye yin k'unshin ba. Baba Tabawa ta kammala aikinta ta fito ta zauna a falon muna hira jefi-jefi har yarinyar ta kammala tsaf ta had'a kan kayanta. Na ce." Ai kina da acct ko?" Ta ce." E, ina dashi amma momi ta ce da ni kada na kar'bi komai." Cike da mamaki na ce." Saboda me?" Tana murmushi ta furta." Da farko antina ce take mata lalle sai ta yi aure ni ma dama tana koya mini shine na kar'bi sana'ar duk karshen wata nake shigowa cikin estate din nan naku akwai wad'anda nake yi wa bayan momi din. Mun saba k'warai da ita ta yi wa antina komai haka zalika ta samawa babban yayanmu gurbi a daya daga cikin shagunanta dake garin nan, gashi nan har ya yi aure shekara daya kenan matarshi ta haifi mace ya sanya mata sunan momi din wato Maryam muna kiranta da Sahiba." Da murmushi a fuskata na ce." Duk da haka dai ai ni ma alheri zan yi miki ganin irin yadda ki ka b'ata lokaci wurin yi mini ado da zananan henna mai kyau, shin ko ba kya so mu saba ne?" Dariya ta yi kafin ta ce." Kai anti wannan ba komai ba ne akan wanda nake yi don na ji kin ce na takaita ne shiyasa amma da wanda zan yi miki sai ya fi wannan tsaruwa." Na ce." Wannan din ma ya burge ni sosai na gode miki, amma ai ko turare kya kar'ba ko." Ta yi kasa da kanta tana murmushi. Ni ma murmushi nake yi can kasan zuciyata kuma ina tunanin idan har mutane za su dinga yabonka tun kana raye tabbas babu abinda zai hana ka sha'kar rahamar Allah idan ka gushe! wato ita dai Momi ko'ina alherinta zagayawa yake yi duk wanda ala'ka ta had'aka dashi muddin ya santa to alherinta zai fara gaya maka. Muna nan zaune muna hira da ita budurwar wadda take gaya mini sunanta Lad'ifa iyayenta yan asalin jalingo ne aiki ya kawo mahaifinsu nan abuja amma k'aramin ma'aikaci ne.. Ta duba agogon da yake tsintsinyar hannunta na dama wanda nake hasashen tana d'aura shi ne domin duba lokaci a sa'in da ta d'aurawa mutam lalle da kwance shi. Ta ce." Yanzu sai a cire tunda ya samu awa biyu cikakku. Dama dalilin da ya sanya ban tafi ba kenan.. ta d'auko wata leda babba da cokali mai dan fadi daga sama cikin nutsuwa ta fara cire lallen kafin ta d'aye salatif din zanen ya fito d'au ya yi bala'in kyau da kamawa. Baba Tabawa fadi take yi "Ashe haka kike da cin lalle Amina amma ba kya damuwa da yi." Na ce." Duk da haka dai ai lallensu daban yake suna yi masa hadi na mussaman." Da kaina na cire na hannun ya tafi da ni sosai nan da nan na ga ba dawo mace har ina jin dadin duba hannuna. Na ji tana ce wa." Sai gobe zai sake fitowa sosai." Tsaf ta goge mini kaf ta shafe duk inda lallen yake da wani abu sannan ta sake had'a kayanta a karo na biyu. Baba Tabawa da kanta ta d'auko mini takalmin da da nake amfani da shi a d'akina ta kawo mini na sanya na tashi ina fad'in.'' Ladifa alwala ai ta zama dole da fatan babu matsala ko." Tana murmushi ta ce." Babu matsala anti." Kai tsaye d'aki ba wuce na had'o mata Turaruka da sabulai. Fitowa ta yi daidai da lokacin da ya shigo yana daga bakin kofa suna magana da yarinyar kamar sun d'an saba da juna ko da yake shi din ba ma'abocin shariya ba ne idan yau kuka hadu to zai mu'amulanceka kamar kun yi shekara da sanin juna, mutum mai sau'ki hali da nuna shi ba wani ba ne a rayuwa. Ledar hannuna na mik'a mata ina cewa "Ki gaishe da mutan gidan, tunda kin ki kar'bar kudi ga wannan sai ki yi amfani da su, na gode kwarai." Ta kar'ba tana godiya sosai kafin ta kama hanya ta fita cike da nutsuwa. Baba Tabawa ta wuce dakinta itama. Sai mu biyu a falon na daure na ce." Barka da shigowa." A takaice ya amsa kafin ya nemi hanyar matattakalar samansa. Ban yi kasa a gwiwa ba na bi bayansa. Ya shiga bandaki nasan alwala zai yi ya fito yana gyara hannun rigarsa dake tattare. Kallo daya ya yi mini ya kama hanya zai fita na ce." Idan babu damuwa Ina son magana da kai." Bai juyo ya dube ni ba ya furta." To, bari na dawo daga massalaci." Ya fice a gaggauce. Na samu gefan gado na zauna babu wani karsashi a tattare da ni, nasan da ban yi masa magana ba, ba zama lallai idan ya fita ya dawo ba, shigowar nan ma nasan ya yi ta ne akan dole domin sanin halin da muke ciki. Idan yana irin wannan nukufurcin da d'aukewar kai wani irin damuwa nake shiga mara dad'i. To ban yi tsammanin amsa min din da ya yi ta bogi ba ce sai da naga har an yi Isha'i ta shige bai dawo gidan ba ya barni zaune a inda ya bar ni ina dakon shigowarsa. Bakwai saura ya fita yanzu gashi takwas har da minti ashirin na samu kimanin awa d'aya da wani abu zaune zuru a dakinsa. Na tashi na sauka kasa raina a dagule haka kawai nake kasa jimirin jure shariyarsa akaina duk dauriyata gazawa nake yi, kuma da na ce ina son magana da shi zahiri ko ya dawo din wallahi ban san abinda zan ce masa ba. Waya na d'auka na kira shi, bai yi jinkiri ba kuwa ya daga yana tambayata menene. Daburcewa na yi kafin daga bisani na daure na ce." Ka zo." Ya ce." Akan wane dalili." Shiru na yi Ina dan tunani sannan na ce." A lissafin da kake yi yau kwanan wanene a cikinmu?" Kai tsaye ya ce." Kwana kamar yaya." Na ce." Kwanan girki mana, wacece take da kai?" Ya ce." Momi ce take da ni ma, saboda itace nagartacciya matar da take gudun fushina ita nake ganin zan iya kwanan aure da ita, domin zahiri da bad'ininta babu mugunta ko zagon kasa balle zalinci a tare da ita." Shiru na yi maganarsa na dukan kaina. Na daure na furta." To mai kake nufi?" "Ba na nufin komai, kawai dai ya kamata a ce na yi nesa daku dalili ban san menene a zukatanku ba ke da ita Hauwan mai aikawa a sayo miki maganin wankin mahaifa." Maganar ta yi mini nauyi sosai, dama nasan abinda yake ta sa'barsa kenan. Na ce." Ai ba haka kawai ta aika a ka sayo mini maganin wankin mahaifa ba sai da dalili, idan ma kana ganin da hannunta a wannan case din to ka d'auki hakkinta wallahi." "Ita din mutuniyar arziki ce kenan?" Ya fad'a da izgili." Na yi shiru ban bashi amsa ba domin yadda ya fadi maganar ya nuna mini cewar a fusace yake. Jan tsakinsa na ji kafin ya datse kiran. Na cire wayar daga kunnena raina a kuntacce na tashi na shiga bandaki domin gyara jikina. Da kyar na iya cin abinci duk kuwa da dokin sakawarar da na yi amma takaici bai barni na ci da yawa ba. Hauwa kam ko dand'ane ba ta ce ba a daran sai da Baba Tabawa ta yi mata fatan wake da manja da kifi ga uban attaruwun da ta ce a zabga mata saboda yanayin bakinta. Sai bayan goma na dare tukkuna muka yi sallama kowa ya shiga domin ya kwanta. Lokacin kiran Hajja ya shigo wayata can saman dirowa romat na d'auka na rage murya domin koda na shiga d'akin kallo na kunna domin idanuwana gabad'aya a soye suke da zallan b'acin rai da damuwa Na shiga zullumi da nazari sosai a lokacin da na ga kiran Hajja domin sai nake tunanin ko ya sanar mata da wata magana ne. Yanayin yadda muka gaisa da wasa da dariya ya sanya na dan ji sanyi a raina sosai ta yi mini tambayoyi masu cike da hikima irin ta manya ni na na bata amsa cikin hikima ban yarda na sanar da ita akwai matsala ba tunda bai gaya mata ba, to fadarta daga bangarena takan iya janyo mini matsala babba. Ta ce." Ga Yusi dai muna tare dashi anan falo duk ba mu kwanta ba, Kamulu kuma ya ce mini zai shiga cikin gari can gaba da gidanku rijiyar zaki ya ce mini idan ban manta ba an gayyace shi bude wata sabuwar makarantar islamiyya ya ce mini zai kwana a gidan Gwaggo da safe sai ya wuce can din." Murmushi na yi a tsanake na ce." To shikkenan Hajja, Allah dai Ya saka da alheri na gode sosai, Allah Ya kara lafiya da nisan kwana." Ta amsa da Amin Ya Allah. Kafin ta bawa yaron wayar na ji maganarsa yana fad'in." Mama barkanmu da dare. Na ce." Barkanmu dai Yusi ya kuke?" Ya amsa da "Alhamdulillahi Mama." Shiru ya biyo bayan maganarsa. Gabad'aya tunda abin nan ya faru yaron baya sakewa da ni. Kamalu ne ma ya kira ni a waya shi ma sau daya sai ka ce wad'anda aka yi wa wata huduba akaina. Kai na girgiza a hankali na ce." To tunda ba ka da abin cewa sai an jima ko.". Yana 'yar dariya ya ce." Mama kenan, na yi shiru ne ai Ina sauraranki ko da abinda za ki ce mini." Na ce." Da yake ni ce sarkin korafi ko?" Shiru ya yi bai ce komai ba, amma ina jin sautin murmushinsa. Na ce." Malam kashe waya ka bawa mai ita." Da sauri ya amsa da "To mama." Amma ban ji ya kashe din ba, nasan jira yake yi ni na fara kashe tawa. Murmushi kawai na yi na ajiye wayar a gefena tare da sauke ajiyar zuciya. Washe gari kiran wayar Baban Saude ne ya tashe ni da yake jiya na jima ban yi bacci ba idona ya soye da tsabar tunani tare da neman mafita. Wannan shine dalilin da ya sanya da baccin ya kwashe ni bai ajiyeni a kusa ba domin ni kaina tunda nasan ba ni da tsarki sakin jikina na yi sosai motsin kirki ba na so na yi. Hannu na kyarma na daga wayar lokaci guda idona ya yi tarmazai wani irin yanayi na shiga ba fargaba kiran wayar Baban Saude a irin wannan lokacin yana da ala'ka da abubuwa da yawa. Walau mutuwa ko wata mas'alar domin kuwa nasan a cikinta muke Muryarsa radau ya amshi gaisuwata ya Dora da fad'in gani nan kan hanya domin kuwa daf nake da shigowa garin abuja. Na ce." Baban Saude ziyara za ka kawo mana kenan, ka gaya mini abinda ka ke so ka ci yanzu da kaina ma zan shiga kicin din na yi maka. Ya ce." Ai ba abincin gidanki na zo ci ba Amina, ni ko da me ki ka sauke ni a wajena daidai ne." A hankali na ce." To shikkenan Baban Saude Allah Ya sauke ka lafiya." Ya amsa da Amin a takaice kafin ya kashe waya. Na jima cikin nazari da tunanin dalilin zuwan Baban Saude a wannan safiya haka sai kace wanda ya kwana a hanya. Ashe ni da mutumin nan ba mu isa mu kashe matsala mu binne ta ba har sai ya dangatata da iyayena. Gaza ha'kuri na yi na daga waya na kira shi. Matarsa ce ta daga har tana kiran sunana. Da sauri na daidaita yanayina muka gaisa a tsanake kafin ta ce." Yallabai din bacci yake yi ko a tashe shi ne?" Na ce. "A'a kada ki tashe bari idan ya tashi sai ki gaya masa na kira." Na ji tana fad'in." Yawwa gashi nan ma ya tashi can sama sama na ji maganarsa ban fahimci mai yake cewa ba na ji tana ce wa dashi Maman Yusuf ce." Na ji shi sosai yana fad'in.'' Amina." Ta ba shi amsa da e, ita ce ya ce ta bashi wayar. Na ji dad'i da bai nuna mata a cikin rikici muke ba. Maganarsa na ji ta daki kunnena." "Ya aka yi?" Zuciyata ta yi wani zullo kamar za ta faso kirjina ta fito. Kalmar ''Ya aka ayi din nan tana yi mini ciwo kwarai da aniya, bayan yasan a cikin yin muke ni da shi. Na daure na furta." Yanzu don girman Allah Baba menene amfanin kiran Baban Saude da ka yi ashe ni da kai ba mu isa mu warware matsalarmu ba, mai ya sa har yanzu ka kasa yarda da ni." "Ya za a yi na yarda dake Amina? ba ki d'auki hanyar ba domin kuwa duk yadda na so ganin cewa da ni dake mun zama abu daya kin ki ba ni goyon baya, 'kiri-'kiri ki ke nuna mini gadara da ikon akan yaran da ki ka haifa da namijin da ki ka fi so a duniyar nan. Na ha'kura na kyaleki duk da cewar nasan har yanzu zuciyarki na kewar wannan mutumin da ya riga ya gushe a doran duniya bayan da igiyoyin aurena a wuyanki. Yanzu kina gwada fifiko da soyayya akan yaransa. Ni na yi ha'kilo na raba dare wataran ma da rana idan abin ya ciyo ni, na yi ta ko'karin ganin na samar da k'wayayyaina a mahaifarki kina zubarwa saboda ni din kare na bai kai tsaiko ba. Mai yasa zan yarda dake kuwa Amina. Na tabbatar da cewa Hassana da Usaina ma Ubangiji Allah ne ya nuna miki ikonsa a kansu ke kam ai tunda suka diro duniya ba ki isa ki shafe babinsu ba. Za su rayu ko da babu soyayyarki." Kaina ne ya dinga juyawa maganganunsa na ta amsa mini kunnuwana. Na rasa wadda zan d'auka a ciki na yi nazari. Wane irin zargi ne wannan da mugun bala'in kishi. Yaya Aminu ma da ba kowan kowa ba a duniyar nan musaki mai lalura har shi za a dinga yi wa wannan mugun kishi na bala'i. Zuciyata ta ce da ni wannan shi ake kira da "Kishin kushewa." Ban ankara ba kawai na ji kittt! ya kashe wayarsa. Na ajiye tawa a saman cinyata kana na tallafe ha'bata tare da nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Da gaske shi din ya kira Baban Saude saboda yana zargin na sake zubar masa da ciki. Hawaye ne ya silalo saman kuncina, ni kam mutumin nan Ina ganin ni kadai ya tsana a cikinmu, gabad'aya ya ki bari na na huta a rayuwata. [12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 110 Cikin kasala na yi wanka ina ta nazarin hanyar da zan 'bullo da ita domin ko'karin ganin na kare kaina tunda ban san irin maganganun da ya tsarawa Baban Sauden ba, kuma ban san shi din da me yake tafe ba. Ban yi wata kwalliyar kirki ba saboda babu nutsuwar yin hakan a tare da ni. Na gama shafa mai ina duba lallen jiya ya sake fitowa sosai ya bi fatar 'kafafu da hannuna ya kwanta abin ban sha'awa. Zuciyata babu sukuni na fita falo muka gaisa da Baba Tabawa lokacin tara da minti takwas na safe ta kammala shirya abin kari tsaf har ta yi wanka. Na tambayeta Hauwa ta ce mini ba ta fito ba tukkuna. D'akinta na nufa sai na sameta nad'e a cikin bargo tana bacci. Ban yi yun'kurin tashinta ba saboda nasan illar hakan na janyo kofar a hankali. Na dawo falon na zauna ina kallon Baba Tabawa daka can wurin daning tana gyarawa na ce." Baba mai aka yi ne yau." Sai da ta d'ago ta dube ni kafin a tsanake ta ce." Kunun gyada ne sai kosai da fanke, sai na yi wa Hauwa Indomee kuma kamar yadda ta buk'ata." Na ce " To kawai tsiyayo mini kunun da k'osan amma ba mai yawa ba. Ta amsa da kulawa. Na janye idona daga wurin da take zuciyata na can tunani na tsinkayi maganarta ina d'aga kaina na ganta a tsaye ta miko mini madaidaicin kofin da ta tsiyayo mini kunun kosai kuma ta ajiye mini shi a saman hannun kujerar da nake zaune . Ban ce komai ba na sanya hannu na kar'ba sai ta zauna gefana jikinta a sanyaye. "Na gama alamar akwai abinda yake damunki hajiya tun fitowarki na lura da hakan, ina yi muku addu'a tare da fatan Allah Ya iyakance muku wannan rikicin." Haka kawai sai maganarta ta karya mini zuciya na ji hawaye sun cika idanuwana. Tunda nake shiga matsaltsalu na rayuwa da rikicin duniya ban ta'ba jin kewar mahaifiyata ba sai wannan karon da nake ganin karfi da dabarata sun yi rauni. Komai ya cakude mini na rasa yadda zan yi da rayuwata. A irin wannan yanayin ne ya kamata a ce na je kafadarta na d'ora kaina a kai, na yi kuka ta share mini hawaye ta kuma fahimce ni ba tare da ta kyare ni ba.. Hawaye suka tsinke mini dalili na kasa jimirin jure hana su gudana. Ina ganin kamar kukan ma zai sanya ni na ji sasaauci a cikin zuciyata. Duk da ban rayu da uwata na tsayin lokaci mai yawa ban shaku da ita ba, amma ina shiga tsananin tashin hankali da kewa a duk lokacin da na tuna cewa ba tare raye na tuna irin wahala da gwagwarmayar rayuwar da na fuskata gani a cikinta sau'ki sai daga Allahu rabbi. Anti Yagana uwa ce a makwafin Mamanmu amma bai zama tilas ta fahimce ni ba kamar yadda uwa take mayar da damuwa da kukan d'anta nata. Uwa ta kan kar'bi wahala da fad'i tashi akan dai duk rayuwar abinda ta haifa. Idan tawa tana raye a 'kalla ni ma zan ji sasaauci ta wani gefen zan je na gaya mata damuwata ta fahimci ni kuma ta ba ni shawarwari. Cikin nashihun da Baba Tabawa take yi mini babu wadda na fahimta gabad'aya rauni ya yi mini 'kawanya na ma gagara tsayar da hawayen dake karakaina a dakalin fuskata. Daga karshe ta shi na yi ma na nufi daki rigif haka na fadi saman gado na fashe da kuka mai gunji ina kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Baba Tabawa hankalinta ya tashi ainun! domin biyo bayana ta yi da abin karin tana cigaba da rarrashina. Ganin halin da nake ciki ya sanya ta ajiye duk abinda yake hannunta ta tararrayoni jikina itama murya na rawa take fad'in." Amina komai ya yi tsanani maganinsa Allah don Allah kada ki karya mini zuciya da wannan kukan na ki, kowane bawa yana tattare da jarabawa, sai dai ta wannan ta fi wannan haka lamarin yake, amma ni a ganina matsalarku karama ce wadda za ku hadu ku maganceta ba tare da kowa ya ji ba, ban san ba ko bayan wadda na sani akwai wata matsalar da take damunki, don Allah ki yi shiru ki yi mini bayani ko Ina da shawarar da zan iya ba ki." Rungumeta na yi sosai ina kuka na ce." Baba Tabawa na sare zuciyata ta yi rauni ta yi sanyin da ba za ta iya jimirin jure matsaltsalun da ta jure a can baya ba. Ni marainiya yarana ma marayu Baba Tabawa ga damuwa iri daban-daban wanda nake tare da shi shine mussababbi Baba Tabawa mutumin nan ya tsane ni, wallahi ya hana zuciyata ta huta, bala'in yau daban dana gobe, na gaji! na gaji da auransa ya zame mini karfen kafa a rayuwata." Ta dinga girgiza kanta tana jimantawa kafin na ji saukar hannunta a kumatuna tana share mini hawaye take ce wa." Ki daina ce wa kin ga ji da ibadar Allah Amina, ba ki sani ba ko wannan itace hanyar shiga aljannarki. Ni kam sai nake ganin kamar kukan dad'i kuke yi, domin kuwa a kaso dari Ubangiji ya yi ba ku kashi tamanin, idan har an samu wani tasgaro da kalubale a cikin kashi darin nan a shawarce godiyar Allah ce za ta biyo baya. Kuna rayuwa ne anan a lullube amma Amina duniyar nan a rikice take wallahi talauci da k'akanakayi ya yi wa al'umma yawa. Matan aure zina zawarawa zina 'yan mata k'ananun yaranmu zina duk domin su ci abinci. A yanzu duk wata mata da Allah ya rufa mata asiri ta samu miji mai kula da iyali da d'aukar nauyin ci da sha da kula da lafiya, to wallahi tallahi ta yi hakuri ta zauna domin idan ta fito rayuwar da za ta fuskanta bayan auran gagarima ce. Amina mace yanzu ko tana da kudi tana kasuwanci muddin ba ta da miji abin zargi ce a wurin mutane koda kuwa tsarkakkiya ce, yanzu nan za ki ji wasu daga cikin marasa fahimta marasa hankali suna kiranta da sunan karuwa. Wannan rayuwar kin yi ta a baya Amina a lokacin duniya ta dan kwance gari bai lalace irin haka ba. Ki yi hakuri ki jure kalubalen gidan auranki in sha Allahu watarana sai labari." Sosai maganganun Baba Tabawa suka sanyayyar mini da jiki. Duk abinda ta fad'a babu k'arya. Na yi gwagwarmaya na san komai. Amma ni a irin fargabar da nake ci a yanzu sai nake ganin gwara mini zaman babu laluran miji hankalina zai fi kwanciya shin mai ake nema a cikin aure ne haihuwa to na samu. Ina da dukiyar da zan iya ri'ke kaina da yarana marayu. Allah da kansa ya ce a rabu idan abin ya ci tura, ai gabad'aya lamarin aure da maslaha ya zo domin kuwa abu ne na mutum biyu tare da yarjejeniya kafin tabbatuwarsa. Fuskata na goge a lokacin na ji idanuwana sun tasa sosai, ba komai ne dalili ba sai irin kukan da na yi wanda na shafe tsayin shekaru rabona da yin irinsa. Wayata dake saman madubi ta fara kara alamun shigowar kira. Da kanta da sauri ta tafi ta je ta d'auko mini ta ba ni na kar'ba ina dubawa A kunnena kawai na sa wayar kafin ba bud'e baki da kyar cikin alamun cushewar murya da dashewa na ce." Na'am.'' Muryarsa babu amo ya furta." Baban Saude ya sauka tun d'azu yanzu haka muna tare da shi sashena da nake saukar ba ki." Shiru na yi ban ce masa komai ba. Na ji yana fad'in." Ko ba kya ji ne?" A takaice na ce." Ina ji ya za a yi yanzu to?" "Ke muke jira?" Ban bashi amsa ba na kashe wayata jin yadda zuciyata take wani irin harbawa, ina ganin sai mutumin nan ya kaini kasa tukkuna hankalinsa zai kwanta. Baba Tabawa ta kwashe kayan karin kummalon tana fad'in." Sai dai a had'o miki wani don wannan ya yi sanyi. Cike da sarkewar murya da numfashi na ce." Ki bari na dawo tukkuna na yi ba'ko daga Maiduguri d'an uwan mamana ne ya zo." A sanyaye ta furta." Amma lafiya dai ko?" Ne ce." Baba Tabawa akan maganar 'barin cikin da na yi ne, shine ya kira shi ya gaya masa don yana zargin zubarwa na yi da gangan. Sai ta shiga girgiza kanta gabad'aya yanayinta ya nuna alamun damuwa da fargaba ta ce." Haka kawai kuma sai ki zubar da ciki Amina, ai kuna da ilimin addini daidai gwargwado wad'anda ma suke yin sakarcinsu a waje su samu ciki ba su zubar ba sai na sunnah, amma ban ji dadin wannan zargin ba. Ban ce mata komai ba domin duk bayanin da zan yi mata akan mutumin nan ba zata gane ba. Idan na ce mata shekarun baya na ta'ba yun'kurin zubarwa za ta fara wasu tunanuka marasa kyau akaina kuma bai zama lallai ta fahimci nufina ba tunda ita ai mutuniyar da ce. Akwai tauhidi tare da k'adaita Allah. Shi kam ai ko zan kwana ina rantsuwa ce wa zubewa ya yi babu wata hujja da rantsuwar da zan yi masa ya yarda kan cewa ba hada ba ki muka yi da Hauwa ba. Hijab na zura a jikina mai fuska har kasa muka fito tare da ita tana ta jadadda maganar har zuwa lokacin Hauwa ba ta fito ba.. Kai tsaye hanyar fita na nufa ita kuma ta nufi kicin babu karsashi da kuzari a tare da ita. Wuri ne k'ebantace ya ware a gidan domin ganawa da manyan bakinsa na mussaman. Gabad'aya wajen ya fi ko'ina kyau da tsaruwa a gidan. Masu hidima da aikin wajan su kansu na daban ne. Yadda ya sau'ki Baban Saude a sashen ya tabbatar mini da ce wa bai ajiye shi a nesa ba, suna tare domin tun bayan sulhunmu na farko na fara fahimtar abota mai karfi ta shiga tsakaninsu. Ina dosa kofar da zan shiga falon escort dinshi Sukajiru da Emanuel sune dai amintattun nasa da basa rabo dashi mussaman ma Sukairaju da duk inda zai tafi tare suke tafiya, bayan wasu jami'ai guda uku da naga ba sa rabo da shi. ina isa suka fara gaisheni na amsa sama-sama kafin da sauri Sukairaju ya bud'e mini k'ofar na shiga a nutse. Suna zaune a kujera d'aya hira suke yi cikin fara da barkwanci tsakiyarsu Loptop ce ta maigidan da alama akwai abinda yake nuna masa a ciki. Center tablet din da yake tsakiyarsu kuwa sha'ke yake da manyan kuloli akwai tazara sosai tsakanina da inda suke tunda girman falon ya shahara sosai. Kafin na kàrasa gabad'aya gwiwata ta sage saboda ban san irin tozarcin da Baban Saude zai yi mini a gaban mutumin nan ba Cikin nutsuwa na isa wajan da suke zaune na d'an rangwafa kusa dashi kafin na bude baki a nutse na ce." Baban Saude sannu da hanya, fatan duk mutan gidan suna nan lafiya ya su Dada da sauran 'yan uwa." Ya fuskanceni sosai yana dubana da wani irin yanayin da na kasa tantance shi. Ya ce." Kowa lafiya lau Amina, Dada tana gaisheki ai dana gaya mata cewa zan zo nan wurinki har ta sanya mini rigima wai sai ta biyo ni da k'yar na zame na gudo ba ta sani ba. Murmushi na yi wanda babu nisha'di ko na miskala zarratin cikin dusheshiyar muryarta da ta ga ji da kuka na ce." Dada kenan ai ba ta ta'ba zuwa ta ga inda nake zaune ba." Ya sake fuskantata sosai yana fad'in." Tabbas hakane amma ai tana samun labarai a kanki masu dad'i da akasin haka." Shiru na yi tare da yin kasa da kaina gefe guda Ina ta nazarin manyan mazuban abinci masu daukawar hankali dake jere a saman center tablet din da yake daf da su. Cikin zuciya na dinga tunanin akan haka. Akwai masu yi masa hidima nau'i daban-daban domin sai na ce duk tsayin zama da shi wasu daga cikin yaransa ma ban san su sosai ba. Amma dai zuciyata ta fi aminta da cewa wannan aikin ba na kowa ba ne face na matarsa da ya rataya fulawar so da k'auna irin ta indiyawa. Momi ce ta yi masa wannan hidimar domin fitar da shi kunya. Ko kad'an hakan bai burge ni ba duk da cewa ta yi ne bisa bin umarinsa amma sai nake zargin babu abinda bai gaya mata ba na abinda ya shafi tsakaninmu da shi. Na sake jin wani irin nauyi da kunci a cikin raina, gabad'aya sabgar mutumin nan ta fice mini daga rai domin kuwa kansa kadai ya sani bai da adalci ko kad'an. "Ina ita abokiyar zaman naki ai tare nake so na zauna da ku domin tattauna masla'ar da ta kawo gidanki Amina." Wannan maganar ita ta datse tunanin da na lula na daga kaina cikin kasala da zullumi amma abin da ya ba ni mamaki bai wuce ganin idanuwansa a kaina ba gabad'aya ma hankalinshi na kan 'kafafuna. Har cikin raina kallon ya ta'ba ni domin irin na mutukar 'kurrula ne, nan da nan na fahimci abinda ya assasa hakan bai wuce lallen da ya fito ya zanu radau a kafafuna ba. Da sauri na gyara zaman da na yi na mayar dashi zaman rakuma kafafun suka koma can baya ganin haka ya sanya shi da sauri ya janye idonsa tunda ya fahimci na gan shi sai ya cigaba da duba Loptop din dake gabansa bai ce mana komai ba yana jin Baban Saude yana tambaya Hauwa na kasa ba shi amsa domin kuwa ba na so ko da wasa sunanta ya fito a cikin sha'anina. Hauwa ba ta da wani lefi magani ta ba ni a amtsayinta na ma'aikaciyar lafiya bai yiwuwa saboda yana jin haushinta ya jingina mata lefin da ba ta da hurumi a ciki. [12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 111 Ya sake maimaita tambayarsa. Sai kawai na rushe da kuka mai tafe da gunji na ce." Baban Saude ita Hauwa ina ruwanta, kowa rai ya yi dad'i ai barin mai shine kuma ai idan d'an adam yana rayuwa a duniyar nan dole sai ya hadu da jarrabawa iri-iri." Shiru ya yi kawai yana kallona cike da mamakin ganin irin kukan da nake sharba kuma mai tafe da jan majina da shashsheka. Yanayinsa ya d'an nuna sanyi da sasaauci, ganin haka ya sanya na cigaba da rerawa da babban sauti Ina yi ina jan hanci. Wajan in banda sautin kukana babu abinda yake tashi. Baban Saude kawai ya zuba mini ido, shi kuma wanda ya assasa zaman kansa yana dukufe a computr kanzil bai ce mana ba." "Ashe kenan ba ni da hurumi ko ban kai abokiyar zamanki ta taso ta gaishe ni ba kenan Amina, ai ni tambayarki ita kawai na yi na ce da ke ina take ai ita din ma 'yata ce kamar ke din ko ba haka ba ne." Na gyada kaina tare da sanya hannu na ja hanci cikin reshin kuka na ce." To Baban Saude ai ban san me ya gaya maka game da mu ba. Shine dalilin da ya sanya ka ji na ce haka, idan har ba zai iya yadda da kaddara da abinda Allah Ya shiryo ba ai bai kamata ya na hada ni dak.....Ban kàrasa ba ya buga hannun kujerar da yake zauna ya furta." Me ki ka ji na ce miki Amina, wato a gabana din ma kaifin harshe za ki yi, idan shi kin raina shi saboda kuna kwanciya a shimfida da d'aya ai ni ya wuce a ce ki yi mini jayayya bisa umarnina, shin wai ko kin manta wanene a gabanki ne." Shiru na yi gabana na bugawa da karfi da karfi, don sasasucin dana hanga a fuskarsa ya 'bace bat ya dawo asalin baban Saude mafada ci. "Idan na isa ki tashi ki je ki kira wo mini ita." Ya fad'a cikin sigar bada umarni. Ban ce komai ba na tashi na kama hanyar fita kafafuna kamar an doke mini da tabarya. Allah Ya yi wa Baban Saude wani irin kwarjina da haiba da wata baiwa wadda idan ya yi magana ko babu fad'a a ciki sai mutum ya nutsu. Yanayinsu daya da jarumin film din nan na Hausa (Tahir fagge) Ina shiga d'akin na sameta ta yi wanka tana cin indomin da Baba ta dafa mata Ganin yadda na shigo ya sanya ta tsira mini ido har na isa wurin da take zaune. Kafin na furta komai ta riga ni ta hanyar fad'in." Lafiya na ga idonki a kumbure ko mutuwa aka yi ne ban sani ba ina ta baccin asara.'' Na girgiza kaina tare da fad'in." Babu wanda ya mutu Hauwa mijinki ne ya kai kararmu wurin Baban Saude." Ta yi shiru tana maimata sunan baban Saude kafin ta furta." Oh Yayan mamanku na maiduri ko?" Na ce." Shi fa, bai jima da sauka ba, yana can sashensa na baki ya ce na kira wo ki muje tare. Karamin tsaki ta ja kafin ta ce." To akan me Amina ba ki gaya masa cewa zaman idda nake yi ba babu igiyar aure a tsakaninmu, akan me kuma zai sanya ni a cikin abinda ya shafe ku." "Saboda yana zargin mun had'a baki tare mun zubar masa da ciki. Hauwa musabbabi akan 'barin da na yi kwanaki bai yarda zubewa ya yi da tsautsayi ba. Ga ni yake yi zubar da shi na yi ina sane." Ta dube ni da mamaki kafin ta ce." To shine me, ai ina ganin ni ba ni da hurumi anan Amina, wallahi kwata-kwata ma ni fa ba na jin dad'in jikina don Allah kada ku sanya ni cikin wannan cakwakiyartaku." Na ce." Na sani Hauwa, ki ta so dai mu je don Allah idan ya so ni zan gayawa Baban Saude ba ki da lefi, kada ki ce ba za ki je ba, wannan zai sake tabbatar musu da cewa babu gaskiya a tare da mu." Jim ta yi na sakkoni kafin ta ce."shikkenan mu je to." Ta ajiye plate din indomin wanda dama saura karashe kad'an ta d'auki ruwa ta kurba sannan ta tashi ina tsaye ina kallonta ta d'auko hijabin dake ta salla ta zura sannan ta dube ni. Ban furta komai ba na juya da niyyar fita ta rufo mini baya. A ka ci sa'a kuwa baba Tabawa ba ta fito ba tana d'akinta. Yana cin abinci a lokacin da muka shiga. Cima ce iri iri da snakes tabbacin an shirya sune domin shi akwai wad'anda ma bai bud'e ba suna cikin wamars Wanda dai yake gabansa farfesu kayan cikin rago ne ya yi kyau sosai da katon biredi yana dankwala gefe kuma bakin tea ne babu madara tunda dama tun asali sanin da na yi masa ba ya shan nadara da zuma sai idan ya zama dole, amma ko zaman da na yi a gidansa haka yaransa suke sayo mana madara ta gwangwani duk ranar da suka yi shayi kowa da tasa amma shi haka wadda take da girki zata d'auki tsurar fulas dinsa daban da ba'kin shayinsa a ciki ta kai masa dakinsa. Cike da nutsuwa Hauwa ta gaishe shi ma ya amsa da kulawa. Wurin ya d'auki shiru tun bayan gaisuwar da suka yi. Sai da ya kammala tukkuna a nutse ya goge bakinsa da tissue ya dube mu gabad'aya kafin ya furta." Hauwa da gaske ke ce ki ka tura Masa'udu direbanku ya sayowa Amina maganin wankin mahaifa?" Ta dube shi a tsanake ta furta." E, ni ce Baban Saude." Da d'an mamaki a tare da shi ya ce." Kenan da gaske hade baki ku ka yi ba kwa tsoron Allah dama?" Murmushin takaici ta yi kafin ta furta.'' Ko daya Baban Saude kaddara ce ta gifta wani lamari mai rikitarwa ya faru a gidan nan gabad'aya muka shiga cikin gigita, to wannan ya assasawa Amina abortion bisa tsautsayi cikinta ya zube . Ganin yadda ya fice ba tare da an samu wata tangarda ba ya sanya na rubuta magani jikin takarda na sanya aka sayo mata domin ya kara taimaka mata wurin wanko abinda ya rage a mahaifarta? Ya ce." A lokacin mai yasa kafin ki yanke hukuncin yin hakan ba ki yi yun'kurin sanar da mijinku ba, ko ko cikin bashi da uba ne?" Shiru ta yi ta kasa cewa komai sai da ya sake maimaita maganarsa tukkuna ta ce." Wallahi ban san abinda yake tsakaninsu ba domin kuwa na d'auka ita Aminar ta gaya masa shine dalili kuma dai ni kaina ba magana yake yi mini ba a lokacin." "Shine dalilin da ya sanya ki kenan yin gaban kanki a matsayinki na ma'aikaciyar lafiya ai kin fi karfin ki yi masa magana dalili yana fushi dake, doka ce babba a kowane asibiti amincewa da sanya hannun mai ruwa da tsaki, ina nufin wanda yake da hurumi akan abu, akan wane dalili zai amince cewa da gaske kaddara ce ba shirya zubarwa kuka yi a tare ba." Ta fashe da kuka tana ce wa." To ni dai Allah ne shaidata Baban Saude ni ma cikin ne fa da ni, a ganina kafin na bada goyon bayan wata ta zubar da nata ai ni zan yi yun'kurin zubar da nawa dalilin abinda ya ratsa tsakanina da shi, ai gashinan a zaune yana ji ni ba matarsa ba ce yanzu." Baban Saude ya dube shi da saurin gaske domin maganar Hauwa ta karshe ta kidima shi. Bai ce komai ba still hankalina na kan computer dake gabansa kuma bai dago ya dubi Baban Sauden ba.. Sai ya juyo gare mu yana fad'in." Ban san da haka ba Hauwa, kuma ni nan ban titsiyeki domin naga iya gudun ruwanki ba. Abinda ya sanya ita Amina muke zarginta da aikatawaa saboda ta ta'ba yunkurin yin hakan a shekarun baya, abinda ku ka yi ba daidai ba ne, ko ni nan babu wata mace da za ta yi mini haka na amince da gaskiyarta. Sannan ya sanar da ni cewa kun had'a kai kun ware d'ayar mutuniyar kirkin cikinku, ai duk macen da mijinta zai zauna ya dinga yabo tare da fad'in kirkinta ita ta amsa sunan mace ba irinku 'yan amshin shata ba, to me ta yi muku, mutuwa ce fa ta raba tsakaninta da mijinta mai rasuwa Alhaji Amadu, kuma ya barwa Amininsa wasiyya akan ya aureta domin cigaba da kula da ita da yaranta. Ban ga matar nan ido da ido ba, amma zaman nan da na yi kaf alheri da kyautatawa mijinta yake gaya mini, ni ma gashi na ga ni yadda ta sauke ni da hidima daban daban tamkar wani basarake. Ba ku ji kunya ba Hauwa, ita fa macen da ta fi biyayya ga miji itace sauniyarsa wannan matar ta dame ku ta shanyeku a komai sannan kun yi sake wanda kuke jin haushinta dominsa ya fi sonta kun hade mata kai shi kuma ya hade kai da ita, ina kara gaya muku Kun cika shashasha!" Tsit! wurin ya dauka bayan yin shirunsa, zuciyata ban da dokawa babu abinda take yi wannan wane irin cin mutunci ne da cin fuska Baban Saude ya shirya yi mini. Menene lefin Hauwa anan da za a sanyata a gaba da cin zarafi haka. Shikkenan a rayuwa mutam ba zai yi kuskure ba. Wasu hawaye masu d'umi da yaji suka fara simiyowa suna bin kumatuna. Wannan karon hawayen ne kawai suke fita masu zafi da ciwo babu damar yin gunji sai dai ciwon zuciya. Ya d'auki kofin shayinsa ya kurba kafin ya cigaba da ce wa." Gaskiya ku gyara domin kuwa babu wata gadara da za ku yi a karkashin ikon namiji, mijinku gashi nan yana ji ko shine ya yi ba daidai babu ruwana zan titsiye shi na gaya masa gaskiya ko ta yi masa dadi ko ta yi masa zafi wannan shine zaman tare Alhaji Tajo ba surukina ba ne a yanzu abokina ne, mun yi sha'kuwa ta ban mamaki a sha'aninsa zan yi tsalle na dire a ciki koda kuwa bai shafi Amina ba. Kuma za ki koma dakinki Hauwa kin ji ko?" Tana kuka ta ce." A, a Baban Saude ni kam na ha'kura gaskiya wallahi zuciyata ba za ta iya d'auka ba." Baban Saude ya yi shiru yana kallonta da mamaki kafin ya ce."Zuciyarki ba za ta iya d'aukar me ba?" Kafin ta furta wani abu ya rigata ta hanyar fad'in." Ka ji abinda na ke gaya maka ko, gabad'ayansu fa Maryam ta tsone musu idan ba haka ba menene na fad'in wannan maganar, zuciyarta ba za ta iya d'aukar ganin Ina tare da Maryam ba, idan har ina son zama da ita amsar kawai na saki Maryam sai zuciyarta ta d'auka." Baban Saude ya sa dariya yana fad'in." Hauwa don Allah zuciyarki ta d'auka domin kuwa akwai sauran tazara maigidanki bai cikashe ba idan yana da rabo kafin ya bar duniya watarana za ku zama ku hud'u a karkashinsa, ki yi hakuri idan har abinda ya fad'a gaskiya ne, ki d'auka ki kawar da kanki, abinda ma ke tudu biyu ki ka ci, ga ki kuma uwar Khalilullahi." Ta shi shiru ba ta ce komai ba sai sauke ajiyar zuciya take yi har ta ba ni tausayi domin ita kadai tasan irin zafin da take ji a cikin zuciyarta. Ya sake furta ki yi hakuri kin ji salihan mata ba a san su da irin wannan sakarcin ba, suna d'aukar kishiyarsu 'yar uwarsu kamar yadda ki ka d'auki lamarin Amina to itama Maryam ki d'auki lamarinta ku zauna lafiya kada wadda ta cutar da 'yar uwarta maigidanku matsalarku kawai yake fad'a mini tunda na zauna ita yana ta yabonta har sai da na ji wani iri a raina mai yasa ba za ku yi koyi da ita ba?" Shiru muka yi gabad'ayanmu. Sai ya nisa kafin ya cigaba da ce wa." Ni ban zo gidanku domin na sanya ku koke-koke ba, ita Amina ta san wanene ni, ta kuma san halina ciki da waje babu yadda za a yi na goyi da bayan karya na take gaskiya ba na so a sake gaya mini kun aikata wani shashancin makamancin wannan, ku dinga sanar da maigidanku matsala idan ta taso tunda ai ba zaman kan ku kuke yi ba ko?" Babu wanda ta ba shi amsa. Ya cigaba da cewa." Na gode da nutsuwar da ku ka yi kuka saurare ni, ina fatan a ce kada na zama dattijon banza a idonku bayan na gusa ku cigaba daga inda ku ka tsaya, Amina hakan ba za ta yi muku kyau ba." Jin ya ambaci sunana na ce." In sha Allahu rabbi hakan na za ta sake faruwa ba." Ya saki fuskarsa kamar ba shi ba ne wanda ya gama dankara mana bakaken maganganu ba ya dubi Hauwa yana fad'in." Ke ma na ci arzikin furfurata ko ?" Ta gyada kanta tare da sanya gefan hijabin jikinta tana share hawayen da ya kasa tsayuwa daga idanuwanta. Ya furta." To na gode tafiya zan yi yanzu nan tunda na gama abinda ya kawo, na gode sosai da tarba da karramawar da ku ka yi mini." Ba mu ce masa komai ba sai maigidan ne ya amsa masa a lokacin da yake rufe Loptop din gabansa yana fad'in." Ba za dai ka bari ka bi jirgin yamma ba kenan." Ya ce." Motar ma za ta kai ni gida cikin koshin lafiya, abinda na saba da zamanta tunda ni ba mazauni ba ne. " Ya gyada kansa kafin ya furta.'' To babu damuwa idan mun tashi sai mu shiga can wajan Maryam din ku gaisa ko." Baban Saude ya furta." Ai ya zame mini dole ranka shi dad'e wannan alatun da aka shirya mini yana da kyau na je yin godiya." Ya kuwa fashe da dariya yana d'an dukan kafad'arsa." Takaicin abinda suke yi ya dinga nukurkusata don sai nake ganin kamar ma da gayya suke yin hakan. Abin mamaki da al'ajabi wai yau Baban Saude ne da mijina suke wasa da barkwanci irin na abokai. Na girgiza kaina a yayin da nake jin wani irin bala'in takaici na taso mini ban ankara ba na ji motsin Hauwa ta mike tsaye kafin ta d'an rankwafa tana fad'in." Baban Saude a sauka lafiya don Allah a gaishe da mutan nan gidan da kyau." Da sauri ya dawo da hankalinsa kanta yana fad'in." Za su ji in sha Allahu rabbi Hauwa." Tashi na yi ni ma ina dan d'auke kaina domin gabad'aya ba na son kallonsu saboda b'acin rai na furta." Baban Saude ina zuwa yanzu akwai sa'ko da za a kai wa Dada." Ya ce." To, amma ki hanzarta domin na himmatu." Ban ce komai ba na bi bayan Hauwa wadda na hange ta can bakin kofa tana daf da fita. [12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 112 Haka muka jera tafiya ni da Hauwa babu magana kamar wasu kurame. Abinda dai ya sanya na k'ara ganin mutuncinta bai wuce yadda ta jure cin fuskar da Baban Saude ya dinga yi mana a fakaice ba, kuma bata yi yun'kurin ta mayar masa da raddi ba, duk kuwa da cewa lefin ta bai kai a ce an yi mata wannan titsiyar ba, amma ta jure duk domin yi mini kawaici hakan ya sanya ni jin kunyarta kwarai da gaskiya wannan dalilin ne ma ya sanya muna shiga gidan na dube ta a nutse na ce." Hauwa ki yi hakuri don Allah bisa abinda Baban Saude ya yi. Na kuma gode sosai da karar da ki ka yi mini." Murmushi kawai ta yi kafin ta furta." Wallahi ko kadan ban ji haushinsa ba Amina, idan da wanda nake jin zafinsa a raina bai wuce mijinki ba shine ma'kiyana lamba daya." Tana gama fad'in haka ta shige dakinta ta barni a tsaye ina bin hanyar da ta bi da kallo. Na jima a tsaye a bakin kofar falon kafin na sauke wata zazzafar ajiyar zuciya na kama hanyar d'akina zuciyata cike da nazarin hanyoyin da zan bi wurin ganin mutumin nan ya yi kukan zucci. Idan da hali ma ya yi na zahiri zuciyarsa ta cika da damuwa tunda shi ya sayi hakan da kansa. Yadda ba ya so ana yawon tiritirin kai shi k'ara bayan yana aikata lefi, to ni ma abinda na tsana kenan a rayuwa kuma tun farko-farkon auranmu na gaya masa ba na so ya'ki dainawa. Zai gane idan kai ni kara shine zai daidaitani. Ranar dai gidan na mu tsit ya kasance kowacce tana d'akinta dama ni da baba ne muke zaman falo Hauwa ba sosai ba kullum tana d'aki a kwance. Ban fito ba sai bayan magariba Baba ta kammala komai tana zaune ita kadai a falon tana kallo da carbi a hannunta. Gaisawa muka sake yi dalili ita haka dabi'arta take duk bayan sallar farilla sai an yi gaisuwa. Ban fi minti goma da zama ba Hauwa ta fito da waya a kunnanta tana fad'in." E gata bari na bata sai ku gaisa ." Ta miko mini wayar tana fad'in." Inna ce take magana." Cike da fad'uwar gaba na amshi wayar ina kallonta taje ta zauna saman kujera Muka gaisa da inna Uwani cikin kulawa da sakin fuska har muka kare gaishe-gaishenmu ban ji ta yi wata magana ba wanda da farko na d'auka Hauwa ta gaza juriya ta sanar da ita abinda yake faruwa. Wayar ta kar'ba suka d'an yi magana kafin su yi sallama ta kashe tana kallon baba Tabawa ta ce." Indomin nan nake so baba duk dai tsugar mini da ciki take yi amma idan ba ita na ci ba na jin dadi. Amma ki hada mini da dankalin turawa ki sanya wadataccen kifi." Na ce." Hauwa Indomee fa basir ce da atini idan kin manta na tuna miki gashi sai ki ce a sanya mini attaruhu ya ba zata tsugar miki da ciki ba, ki rage cin ta don Allah." "To mai zan ci Amina, ita kadai nake jin sha'awa wallahi ban ta'ba ciki mai azabar laulayi irin wannan ba, da farko fa shiru kamar ba zan yi ba Amma cikin sati biyun nan ina jin ciki kwarai." Na dube ta sosai ta dashe lebanta duk ya bushe ta ba ni tausayi. Dama kuma can tana da laulayi wannan ne ya yi tsanani. Baba ta tashi ta kama hanyar kicin din na ce" don Allah Baba Tabawa kada ki biye mata ki sanya attaruhu kad'an kuma kada ta yi da roman nan." Tana yar dariya ta ce." Haka kuwa za a yi, Hauwa ni ma na daina biye miki gaskiya." Ta dube ni tana ce wa." Kin san roman shine abinda ma na fi so na dinga lasa dad'i yake yi mini." Na ce." Mu bar maganar nan Hauwa, ni fa jikina ya yi sanyi ina fatan dai ba ki sanar da inna Uwani wani lamari ba ko." Girgiza kanta ta yi a hankali ta ce." Babu abinda na gaya mata wallahi, mun yi waya ne mun gaisa ta ce na ba ki wayar ku gaisa." Ajiyar zuciya na sauke domin har cikin raina na yarda da maganarta. To maigidan bai sake shigo mana ba sai da garin Allah ya waye tukkuna ban kai ga fitowa falon ba ya shigo yaran kaf dinsu a tare dashi da yake asabar ce suna gida babu makaranta sai sha biyu na rana suke tafiya tahafiz su tashi shida na yamma. K'amshinsu ya cika mini d'aki da uban da yaran sun sha gayu.Ido kawai na zuba musu Khalil ya fara gaisheni kafin sauran suma su tsuguna kasa kamar yadda suka ga ya yi "Mama ina kwana." Suka dinga jerowa ina amsawa. Khalil din ya ja baya suma sai suka ja baya suka tsaya kusa da su. Na jima ina nazarin abinda suka yi kafin na furta." Khalil ja su ku tafi wurin Mamanka ku gaisa." Bai ce mini komai ba sai ya dubi baban nasu da yake tsaye a jikin kofa shi bai shigo ba shi bai fita. Ganin irin kallon da yake yi masa ya sanya na gane umarninsa yake jira. Na cika da mamaki sosai a raina ina fad'in lallai akwai rikici a kwance idan har bai farga da abinda yake yi cewa kuskure ba ne ya za a yi mace ta haifi d'anta ka d'auke mata shi saboda fin karfi ka kaiwa wata har da ko'karin shiga tsakani akwai matsala idan ni na jure hakan ina da tabbacin za a sha daga da Hauwa. Kasancewar na lula cikin tunani ya sanya ban fahimci mai yake ce musu ba na dai ji yana magana da yaran kafin su kama hanya su fita. Ya rage daga ni sai a d'akin. Ya shigo sosai ya tsaya a jikin mudubi. Ganin haka ya sanya ni da sauri na tashi na bar wurin, bandaki na shiga duk kuwa da cewa ba ni da wani uzuri, kawai ba ni son kallonsa ne.. Ban fito ba sai da na d'auki kusan mintina sha biyar tukkuna na fito na samu d'akin babu kowa. Tsaki na ja kawai na wuce na je na zauna zuciyata a cunkushe. Ban yi tunanin zai dawo da daddare ba tunda sau d'aya yake shigowa wataran ba bayan shigo mana, tunda matsalar nan ta faru ya rikita mana lissafin kwanan turaka domin ko ya shigo baya kwana a gidanmu can wurinta yake tafiya hakan ma yana yi mini ciwo sosai. Muna zaune a falo gabad'aya har da Hauwa wadda take ta fama garzar yalo da Masaudu ya sayo mata can cikin kasuwa. Kamar koyaushe ya tsaya suna gaisawa da Baba Tabawa kafin ya haura samansa. Hauwa ta tarkata shirginta ta nufi daki ba tare da ta cewa kowa komai ba. Girgiza kaina kawai na yi saboda takaici wannan abin da suke yi ita da shi. Ina zaune ban motsa ba Baba ta ce." Hajiya ko za a hadawa maigidan abinci ne?" Na ce." Ba na jin yana da bukata baba daga gidan matarsa yake." Ta yi shiru tana kallon wani waje kafin ta sake dubana tana fad'in." Ko za ki tambaye shi dai." Na ce." Baba kyale shi don Allah, idan yana da bukata daya shigo zai yi miki magana tunda kun dan jima kuna magana kafin ya haura samansa, kin san ba shi da 'koron baki." Ta jijjiga kanta ba ta sake cewa komai ba sai ta tsirawa tibi Ido nasan ba ta so hakan ba don babu yadda za ta yi ne. [Kashe wayata na yi don ba na so na ga kiransa. Bai sake saukowa ba har muka tashi daga zaman falon baba Tabawa dai babu wani karsashi a tattare da ita muka yi sallama. Sai da garin Allah ya waye tukkuna na kunna wayar haka na kwana babu sukuni. Ina bandaki ina wanka na ji motsi ban kawo cewa zai biyo ni bandakin ba kawai sai ganinshi na yi ina tsaye tumbur da ni. Hankalina ya tashi ainun wata kunya mashahuriya ta ritsa da ni. Gani na dinga yi kamar ya keta mini alfarma nan da nan na ji idona ya fara kawo ruwa. Duk da ruwan kumfar sabulun da ya yi wa jikina sansani hakan bai hana ni yin gaggawar raromo towel dina da take sakale ba. Na fara kici kicin daure jikina tsananin yadda hannuna yake rawa ya sanya towel din faduwa kasan wurin ruwan da yake zuba ta saman shayar da na kunna ya jike shi. Raina ya b'aci mutuka haka na sunkuya na dau'ko towel ya yi jagab jikina babu kuzari na kashe shayar kafin na ya'ba towel din a jikina a hakan a jike. Ya tsaya kusa da ni a nutse kawai ya zura mini idanuwansa . Na daure na furta." Amma dai kasan haramun ne abinda ka aikata ko?" Ya yi shiru bai tanka mini ba kawai dai ya zura mini idonsa kaf ilahirin jikina rawa yake. Can kasa-kasa na yi tsaki tare da d'an janye jikina. Ya sake biyoni har sai da kirjinmu ya hadu. Hannuna ya kamo kafin ya duba tafin hannun kamar mai neman wani abu. Ya cika ya kamo na hagun shi ma yana dubawa. Cike da mamaki nake dubansa Ina nazarin abinda yake yi. Yadda yake sauke ajiyar zuciya shine abinda ya fara d'aga mini hankali. Ko'karin sanya ni yake yi a jikinsa ina dojewa, na lura lallen da akayi mini shi yake ta bibiko. Kokawa muka fara yi a toilet din har sai da ya cire mini towel din ya yi jifa dashi can gefe, kuka ne mai karfi ya k'wace mini ganina a haka cikin hasken rana. Ko auratayya zai yi da ni da safe ko da rana yakan sha wuya kafin ya ribace ni na amince domin na tsani ya ga zahiri na a gaske duk da na tabbatar da ce wa babu wata makusa a jikina da za ta janyo mini 'kyama a wurinsa amma haka siddin nake gudun haka. Saman tumbina da ya dan tasa ya d'ora hannunsa bai ce mini komai ba ya fara wasa da hannunsa a wurin har ya so ya zarce can kasa. Na matse gefe cikin zafin nama kafafuna na wani irin rawa. Ya sake biyoni a karo na uku. Sai kawai na silale a kasan wurin na zauna tare da takure jikina. Babu wani lamari da zai wanzu a tsakanina da shi a halin yanzu tunda har yanzu ba ni da tsarki kawai dai zai daga mana hankali ne. Ganin yadda nake kuka tukuru ya sanya ya juya ya fita can kasa na ji shi yana fad'in." Ki fito zan yi magana dake." Bayan ya fita na yun'kura na tashi tsaye har yanzu kafafuna ba su daina rawa ba, sabon wanka na sake yi. Dana kammala na rasa yadda zan yi na fito tunda towel din da zan d'auro ya jike babu wani a toilet din sai kananu kuma babu wanda zai ratsa ni. Na rasa yadda zan yi haka na jure na bude kofar amma ban fito ba ina hangensa a gefan gadona a zauna yana duba k'aramar wayarsa. "Ka miko mini towel ko zani ka ji." Ya dago ya dube ni da sauri amma bai ce komai ba, na sake maimaitawa Ina janye idona daga kansa. A nutse ya ce." Lallai za ki shekara anan a tsaye idan ni zan miko miki towel Amina." Jin haka ya sanya ban k'ara cewa komai ba. Na yi kundubalar fitowa haka haihuwar uwata. Da kyar da hard'war kafafu na isa wardrobe dina. Ina jinsa yana ce wa." Ni da kayana a ce za a boye mini, to wane lungu da sa'ko ne ba ki kama kaina kin dora a wurin ba, da hannunki fa ki ke miko mini idan kin manta wannan kirjin naki cinyesu ne kawai ban yi na taune ba, kina ba ni ina sha fiye da yadda raina yake so." Ban ce masa komai ba har na gama kintsa jikina yana ta sakin maganganu masu tsananin nauyi wanda na tabbatar da cewa wasu na aikata da sani na, wasu kuma ban san lokacin da na aikata ba domin kuwa bayan ni da shi sai Ubangiji da ya hallicemu ne kadai ya san irin ta'barewa da haukan da muke yi idan muna auratayya." Na dube shi bayan na juyo da fuskata, gabad'aya yanayinsa ya canza duk ya shiririce idonsa sun risina sun kankance tare da wani irin yanayi. Yana ta ko'karin dannewa amma abin ya gagara. Koda na zauna a gefansa sai ya janyo ni da k'arfi jikinsa na karkwarwa ya fara fadin." Na zata zan iya dauriya Amina, mai zan samu ne, ina ta shirye-shiryen tafiya legos tunda na lura babu tsarki a tare da ke." Na cire hannunsa da yake cikin rigita a nutse na furta." Ai ba ni da abinda zan iya baka a halin yanzu." Ya mayar da hannunsa cikin rigar yana fad'in." Ke ce kuwa ki ke da abubuwan bayarwa my love ." Na yun'kura na tashi hannun nasa ya sa'bule ya fito daga cikin rigata shi ma ya tashi da sauri na matsa gefe can nesa da shi." Wallahi ba ni da abinda zan baka, ba za ka samu hadin kaina ba muddin ba ka daina had'a ni da iyayena ba, na ga ji da rashin adalcin nan da kake yi mini, ni ba baiwa ba ce, idan kai 'karata shine zai sanya na shiryu to lalacewa zan yi bari ma na gaya maka gaskiya." Ya zuba mini ido da wani irin b'acin rai a saman fuskarsa ya furta." Haka ki ka ce ko?" Na ce." 'Kwarai haka na ce, ni da kai, duka babu yaro karami, kamar yadda ba ka so ana tiririn kai ka 'kara wurin magabatanka ni ma haka, ka san halin Baban Saude haka siddin ya zo ya ci wa Hauwa mutunci ai ni ce mai laifi tunda ba ka yarda cikin zubewa ya yi ba, amma ita Hauwa ai taimako ta yi, mai ta yi maka ka saketa kana bin ta da mugun nufi." Ya jima yana kallona na lura takaici da b'acin rai ne suka taru suka yi masa dabaibayi bai sake ce wa da ni komai ba ya gyad'a kansa kafin ya kama hanya zai fita. Cikin zuciya na ce.'' Shikkenan ka ji idan da dad'i, ita matar da ka ratayawa fulawar soyayya ta iya da kai kawai, Amina karkatacciyar kuka, mu zuba gaba ce dai da k'ullaci ni ma na iya." [12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 113 Muka cigaba da tafiya a gidan babu annashuwa da jin dad'in da ma'aurata kan jiyar da junansu. Ya sauko sosai ya yi tubis da shi domin salon horon da na d'auka ba karami ba ne. Gashi sun yi fad'a da Hauwa ballantana ya tafi wurinta tunda tun dama can ita matar so ba wani kwanciyar aure yake yi da ita ka'in da na'in ba da bakinsa ya gaya mini hakan ba matsa shi na yi ba.Ashe ni da ya mayar towon tushe nice marufar asirinsa domin kuwa tuntuni ni nake iyawa da fitinarsa ko Hauwa ba za ta nuna mini komai ba. Lallai a wannan karon sai na nuna masa kuskuran abinda yake aikatawa a ganina duk hatsaniyar da za mu yi bai kamata ya d'auke mana kwanan aure ya kaiwa wata ba, wannan gadara ce da take hakki da kuma yi wa addini kutse, ba zan iya ba gaskiya idan abinda na yi a yanzu bai sanya ya daidaita nutsuwarsa ba hanya a bud'e take sai ya sake kiran Baban Sauden ya zo. Ni kuma sannan zan sanar da shi irin abinda yake yi mana na take hakki. Gabad'aya ya nune koyaushe ya shigo gidanmu ba shi da wani kuzari tafiyarsa Legos ta dinga tangal-tangal domin ya turza-turza da ni na'ki amincewa da na bi shi, na gaya masa har abada kafata ta sake taka garin nan, idan lallai sai na yi zaman auran da shi to Ina nan. Baya tunkarar Hauwa ni yake ta yi wa bibiko. Har yanzu ban san abinda yake tsakaninsu ba. Shi baya shi ba, itama baya ita ba, an rasa wanda zai sassauto a cikinsu. Tana dai gefe tana kallonmu kuma duk abinda yake faruwa bata ta'ba tambayata dalili ba. Saura kwana daya ya tafi Lagos din ya ritsa ni a d'aki. Da farko rarrashi ya fara yi da ban baki tare da alkawarin ba zai sake kai ni kara ba. Hakan bai sanya ni na sassauto ba domin kuwa a duk lokacin da zan daga kaina na kalleshi wallahi duhunsa nake gani, a ganina zamana a gidansa kamar takura kai ne tunda shi kam ai kansa ya sani. Bai wani ba ni tausayi ba duk kuwa yadda yake rausayar da kansa da muryarsa hakan bai burge ni ba. Da ya lura duk abinda yake yi ban saduda ba sai fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Har da cewa ba zai ka'ra nema ba har ya mutu na je za mu tsaya a gaban Allah ranar lahira. Ban damu ba Ina zaune ina kallonsa ya kama hanya ya fice cikin b'acin rai. Tabbas na ji wani iri a jikina a lokacin da yake had'a ni da Allah. To ban san yadda zan yi na kwaci mutuncina a hannun wannan mutumin ba, domin ba ni da k'arfi ta kowane bangare sai ta wannan hanyar itace damata kuma hanyar da za ta sadudur masa da jiki. Da zai tafi ko sallama bai yi mana ba, sai da ya kwana uku ma da tafiya tukkuna muka samu labari a bakin Masa'udu cewa ya tafi ban ji komai a jikina ba, dalili na riga nasan irin rabuwar da muka yi ta rashin arziki ba zata bari ya shigo ya yi mana sallama ba. *** To kwanaki suka cigaba da tafiya har aka fara lissafin watanni da tafiyarsa bai kira waya ba haka zalika mu ma ba mu kira ba. Sai na so tsokanar Hauwa tukkuna zan ce mata ta kira shi a waya ta ji yana lafiya. A lokacin zan ga b'acin ranta ta dinga fad'in mijinki dai Amina, ki daina danganta ni da wannan rikitaccen tsohon. Na yi ta dariya idan tana hayaniya a raina nakan ce jinin jikinku kuma yana yawo a junanku tunda duk rintsi a ba za a canzawa towo suna ba. Babu wata ala'ka da ta sake had'a mu da Momi, tun bayan rigimar Hauwa da Nabila kanwar ta itama ta kama kanta, farko farkon zaman takan shigo mana amma tun sanda Hauwa ta yi mata cin mutunci ba ta sake shigo mana ba yanzu kusan watanni biyar kenan. Sai dai duk ranar juma'a takan turo mana yara su gaishe mu wasu lukutan har da abin arzikinta. Duk sanda ta aiko mana da abu sai dai ni nayi d'auka amma Hauwa ko kallo abin bai isheta ba. Kiyayyar da take nunawa matar tana bala'in ba ni tsoro. Kyautar Momi mafiakasari perfumes ne masu dadin kamshi wasu lukutan ni nake amfani da su, ko kuma na yi kyautarsu. Ni dai har yanzu ban kulleceta ainun ba domin sai nake ganin kamar ba ni da wata hujjar da zan tsananta gaba da kiyayya a kanta tunda a zahiri ko mun ki ko mun so matar mutum ce har da rabin mutum. Ko ga yanayin yabo da k'aunar da mutane ke yi mata ya ci a ce sha'aninta ya daina daga mana hankali ko sanya mana zazzafan kishi. Makasudi dai mijinta shine yake ta yun'kurin dole sai ya 'batata a wurinmu ya dasa mana kiyayyarta dangane da abinda yake yi a kanta ba kowace macace za ta jure ba. Kadaran kadahan nake jin ta a zuciyata. Kuma ba na jin haushinta ainun sai dai irin kishin nan da ba za a rasa ba. A ko'ina zan fad'a alheri ta yi mini don yara sun shiga tsakaninmu hakan ba zai sanya ni na mance ba. Na dai nesanta yarana da ita shikkenan sai a zauna lafiya. Sosai Nusaiba da Salim suka d'auki gaba matsananciya da mu. Adam ne kawai yake iya daurewa idan tsautsayi ya sanya mun had'u ya gaishe ni, amma tun ranar da su Yusi suka bar garin gabad'aya ya gaina shigowa gidanmu. Salim da 'yar uwarsa Nusaiba kam abin na su ya yi nisa idan za mu had'u sau goma cikinsu babu wanda zai dubi inda nake balle na sanya a raina cewa za a gaishe ni. Yusi bai ta'ba gaya mini ce wa Adam ya ziyarce shi har sau biyu ba duk kuwa da cewa yakan kira ni a waya sa'i da lokaci mussaman a ranakun da ba su da makaranta tunda tuntuni sun cigaba da d'ora karatunsa a bayaro wasu lukutan ba su da isheshen lokaci mussaman Kamalu da ya ri'ke b'angare biyu. Karatu yake yi sosai irin na da'awa sosai yake bin Malam sunna domin samun ilimi kwanaki satinsa guda a bauchi wurin Sheikh Guruntum. sai bayan da ya dawo tukkuna yake gaya mini da na tambaye shi dalili ya ce mini yana zuwa neman sani ne. Yanzu dai yana tare da Shaikh Abdullahi gadon-k'aya yana daya daga cikin yaransa da suke take masa baya. To a bakin Hamusu nake samun labarin zuwan Adam din don har yake gaya mini irin kayan da Momi din ta aikowa da Gwaggo ta hanyar Adam din. Na yi mamaki sosai kuma jikina ya kara yin sanyi da lamarinta a yi alheri da kyauta hannun hagu bai sani ba. Duk yadda na nuna mata rashin 'kara da kawaici akan yaran nan k'okarinta zumuncin nan da take ta nanata mini ya cigaba da tabbatuwa. Ubangiji Allah Ya ba mu ikon yin abu dominsa. Haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya a hangunce ta fannin maigidan namu kam yadda ba mu neme shi ba shima bai neme mu ba. Tun abin baya damuna har ya fara damuna mussaman da bikin Fadila babbar diyar anti Yagana ya tashi. An yi bikin Yusura sati uku da suka gabata lokacin muna tsaka da rikici dalilin da ya sanya ma kenan ban tambayeshi ba domin kuwa nasan zai huce fushinsa akan hakan ya samu damar gasa mini maganar da ransa yake so kuma ya hana ni zuwa, saboda kada dukan ya zama biyu ya sanya na k'yale shi. Hajja da kanta ta kira ni a waya game da zuwa bikin Fadila da suke shirye-shiryen tafiya ita da Gwaggo tare da yaran wato su Kamalu ai anti Yagana mutuniyarta ce don haka ban yi mamakin nuna za'kuwarta akan sha'aninta ba. Rasa abinda zan ce mata na yi na kama inda-inda da kyar dai na ce mata ni ma ina nan ina shiri amma wata'kila za su riga ni yin gaba. Ba ta fahimci cewa da matsala ba muka yi sallama na ajiye waya cikin zullumi da tunanin yadda zan sanar da shi tafiya maiduri ya bar ni kai tsaye. Da kunya kusan wata hud'u da tafiyarsa ban kira shi ba bayan kuma nasan da tsananin fushina ya tafi yanzu kuma na kira shi nace masa me?" Haka kwana biyun nan na kasance cikin yanayi na tunani har sai da Hauwa ta fahimta ta tambayeni na gaya mata halin da ake ciki. A lokacin itama jikinta mutuwa ya yi ta dinga fad'in lallai a wannan ga'bar baki da bakin magana Amina. Bikin Fadila kuma ai ke ce kirjin biki, idan ba ki halarta ba akwai matsala gaskiya. To katsam ina cikin wannan halin ya zo ba tare da tsammanin zuwan nasa ba, tunda ka'ida wata shida muke yi a can legos din mu dawo, wai Ashe Momi ce babu lafiya hawan jini da sugar har sai da ta kwanta a asibiti tsayin kwanaki goma ba mu sani ba. A bakin Masa'udu muke jin wannan labarin domin kuwa shi din ma ya tabbatar mana da zuwansa kamar yadda ya tabbatar mana da tafiyarsa. Bai shigo mana a ranar ba sai washe gari da rana wajan daya da minti biyar lokacin ma daka gani daga massalaci ya fito. Muna falo gabad'aya muka yi masa barka da zuwa ya amsa kadaran kadahan babu fushi haka zalika babu cikakkiyar walwala. Ya tsaya suna magana da Baba Tabawa kamar yadda suka saba har yana ba ta labarin rashin lafiyar Momi din da yadda ta ji jiki. Sosai ta dinga jajantawa tana k'ara tabbatar masa da cewa gabad'ayanmu ba mu sani ba. Wannan karon Hauwa ba ta tashi ba ban sani ba ko nauyin da jikinta ya yi mata ne oho, tunda cikinta a cikin wata na takwas yake ya fito sosai idan ta jibge a wuri d'aya da kyar take tashi. Ya kama hanyar samansa babu wadda ya sake kalla a cikinmu. Amma yanayinsa kadai ya tabbatar mini da cewa lalurar da matarsa take ciki ta dame shi saboda ga yanayin yadda yake bawa Baba Tabawa labarin ciwon tabbas ya ci jikinta da k'arfi. Bayan shud'ewarsa daga wurin da kamar minti goma na tashi na bi bayansa zuciya cike da zullumi da fargaba. A kwance na same shi kawai ya tsirawa rufin d'akin ido. Gabad'aya sai gwiwa ta yi sanyi (wai shin me cece ma duniyar nan ne) tausayinsa ya d'an kamani, amma bari tasirin hakan ya raunarta da ni ba. Har yanzu da sauran takaicinsa a cikin zuciyata. A nutse na zauna gefan k'afafunsa. Ya dube ni bai ce komai ba sai ya janye idanuwansa. Na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce." Wallahi ba mu san ta yi ciwo ba, ashe har kwanciya ta yi a asibiti babu labari ai da mun shiga mun dubata." Ya yi shiru bai ce mini komai ba. Sai na janye idona daga kansa na yi kasa da kaina ina dan wasa da yatsun hannuna. Shiru d'akin ya yi na minti kusan goma kafin na sake dubansa yanzu idonsa a lumshe yake kamar mai shirin bacci ganin haka sai na tashi da niyyar fita. Ba tare da ya bud'e idon ba ya ce." Koma ki zauna ina son magana dake." Na zauna din kamar yadda ya buk'ata. Ya tashi zaune tare da sauke k'afafunsa kasa. Ya dube ni a nutse kafin ya furta." Akwai matan da annabin rahama ya fad'a cewa ya gan su a can karkashin wutar jahanama, kuma suffofinsu sukan bayyana tun a duniya. Akwai kuma matan da tun a duniya za a dinga yi musu ishara da nuni da cewar aljannar Firdausi madawamiya ce a gare su. Sune muminai wad'anda ayyukan alherinsu yake bayyana ga ko'ina." D'akin ya yi tsit bayan ya gama maganarsa. Na dube shi tare da furta." Ni ina a wane babi kenan, ai ba kai kake bada aljanna ba." "Tabbas ba ni nake bada ita ba, amma tana k'asan kafafuna haka annabin rahama ya fad'a." Sai da na d'aure sosai kafin na furta." Ayyukana ba su kai ka daga mini kafa ba kenan?" Ya gyada kansa yana ce wa." Gaskiya ba su kai ba har yanzu. Momi ce ko yau ta fad'i ta mutu wallahi na yafe mata ki shaida aljanna da izinin Allah zata tabbata a kanta." Na yi shiru zuciyata tana hantsilawa saboda tsabar bala'in b'acin rai. Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un na cigaba da nanatawa ban sake mayar masa da martani ba, kuma ban tashi daga wurin ba na ji gyaran muryarsa yana cewa." Kwanaki mun yi waya da Hajja take sanar da ni za su tafi maiduguri da yaran zuwa hidimar bikin 'yar Yagana hakane ko." Ban dube shi na ce." Hakane yau saura kwana tara, jiya dai Hajja take ce mini ranar alhamis za su tafi." Shiru ya d'an ratsa wurin kafin ya nisa ya sake ce wa." Yanzu nawa ki ke ganin zamu ba su gudumawa ni dake?" A takaice na furta." Duk abinda Allah Ya hore maka." "Ai shawara na tambayeki ni Allah Ya hore mini tuntuni. Kawai ki gaya mini abinda za a ba su ai auran fari za su yi." Na kalle shi babu sukuni na furta." Ya za a yi na yanke maka abinda za ka bayar, ai ba kudina ba ne, naka ne, kuma dai daidai gwargwado sun yi hidimarsu ni ma kuma tuntuni na tura mata da tawa gudumarwar abinda ka ga dama shi za ka ba su." Ya gyada kansa yana fad'in." Ok na ba su 5m ya yi ko?" "Idan haka ka yi niyya ni ina ruwana?" Na fad'a tare da d'auke kaina domin har ga Allah zuciyata zafi take yi mini game da irin mummunan fatan da ya gama yi mini yanzu. Ya ce." Kada ki gaya mini magana Amina, ba na son rashin kunya da fitsara ko kin ga na ta'ba jikinki ne, kin ga alamar sha'awarki a kwayar idona, Ina ce wannan shine yake kawo mini raini a wurinki to ki ri'ke kayanki ba na so." Na fashe da kuka tare da cewa." To ai dama ban ce ka nemi shawarata ba ni ma, kuma ban ce ka neme ni ba, abinda ka yi niyya shi za ka yi, ni ma abinda na yi niyya shi zan yi, aljanna dai kuma babu wani bawan da yake bada ita ta Allah ce, ta hanyoyin alheri ana samunta ba sai ta dalilin wani ba." "Na ji abinda ki ka ce ta shi ki tafi." Na tashi haka kawai na tsinci kaina da buga siket din da yake jikina na kama hanyar fita raina a masifar kuntacce. Ban sauka ba tukkuna sai da na daidaita yanayina na sauka na same su suna nan a wurin suna hira Hauwa hannunta ri'ke da apple tana ci babu abinda ya dame ta sai addu'a da ko'karin rabuwa da cikin jikinta lafiya. [12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: *114* Ban zauna falon ba kai tsaye d'akina na nufa na yi zaune zugum a gefan gado zuciyata na ta yi mini sa'ke-sa'ke masu kyau da marasa kyau! Lallai cikin wannan duniya babu komai face rikici da tarin kalubale. Babu yadda ban yi ba da Hauwa akan ta shirya bayan magriba mu shiga mu duba Momi amma fafur taki tace itama abar dubawa ce domin kuwa bata kaita jin jiki ba. Ganin taki fahimtata ya sanya na kyaleta kawai muka shirya da Baba Tabawa muka tafi dubanta. A harabar gidan muka riski Salim da Adam a tsaye suna magana. Da sauri shi babban ya d'auke kansa yayin da karamin ya sassauta a nutse ya dube mu da ladabi yake fad'in." Mama ku ne." Na ce." E, mune Adam mun shigo duba Momi ne. Sai ya yi yar dariya wadda babu annashuwa a cikinta ya furta." To shikkenan mu je na yi muku jagora." Gaba ya yi muka bi bayan shi yayin da Salim din yake ta ciccin magani har da jan tsaki. Murmushi kawai na yi a zuciyata gabad'aya yaron ma ni tausayi yake ba ni, domin kuwa ya d'auki lamarin da zafin gaske. Falo muka zauna ya nufi bedroom din ta yana fad'in ."Bari na sanar da ita." Ba mu kai minti biyar da zama ba daya daga cikin masu aikinta ta fito daga kicin da wata madaidaiciyar roba a hannunta Hassana da Minal suna biye da ita. Ganinmu a zaune ya sanya yaran suka tsaya. Ita kuma mai aikin ta karaso wurin da muke har sai da ta risina kafin ta gaishe mu gabad'aya. Ina kallon yadda Baba Tabawa take jan yaran da wasa da tsokana amma suna can nesa da mu sun tsaya suna ta kallonmu kamar sun ga dodanni. Raina ya 'baci nan take zuciyata ta dinga raya mini abubuwa marasa kyau to idan ba an zauna da yaran an fadi wata magana ba mai zai sanya k'ananun yara irin wad'annan su dinga yi mini wani irin kallo. Abin b'akinciki da takaici ma har da 'yar cikina 'kiri-'kiri saboda kin gaskiya. Idona na zare musu sosai na ce." Tsayuwar ta mecece idan ba za ku gaishemu ba to ku daina kallonmu, ko mun yi kama da tibi ne.'' Matashiyar mai aikin da take jigila da su tana dariya ta furta." Ke Hassana ku zo ku gaisa mama ce fa." Na ce." A'a rabu da ita kada ta zo mu gaisa ta tsaya." Usaina ta fito daga kicin da shafciciyar wuka a hannunta tana fad'in." Mairo ga wukar ki yanka mana." Shiru ta yi tana kallonmu yayin da mai aikin ta je ta da sauri ta kar'bi wukar tana fad'in." A can sama fa na d'orata yanzu Usai sai da ya d'aukota." Ba ta ce mata komai ba ta nufo wurin da muke zaune tana zuwa sai ta dora kanta a cinyata tare da zura yatsanta babba a baki tana tsotsa. Na yi shiru ina sauke ajiyar zuciya yayin da na d'ora hannuna a saman kanta. Ganin haka ya sanya Hassana da sauri itama ta zo ta yi yadda Usainar ta yi dama tuntuni Kamalu ya gaya mini kishi ne da su, duk abinda daya tayi to babu shakka yar uwata ma sai ta yi. Da hannu na yi wa Minal alama ta zo wurina. Ta kuwa taho kataf-kataf domin yanzu itace take tashen ki'ba a cikinsu. Na ri'keta sosai Ina fad'in." Ina Khalil yake?" Cikin yanayin maganarta ta furta." yana can gidan anti Nusaiba." Baba Tabawa sai murmushi take yi tana jan su da wasa. Hassana da Usaina iyayen miskilanci ne, Minal din ta fi su sakin fuska da son mutane. Tunda suka dora kawunansu saman cinyata babu wadda ta dago sai da suka ji muryar Babansu tukkuna. Tare suka fito da Momin kallo daya na yi mata gabobin jikina suka shika wata irin rama ta yi mai ban tsoro kanta yana nema ya rinjayi gangar jikinta abinka dama da siririya idanuwanta sun yi kuru-kuru ta d'ashe kwarai da gaske ta yi fau, babu shakka babu karya a cikin lalurarta yadda mijinta ya dinga jadadda ciwon ya ci karfinta yanzu na sake gazgata kammaninta duka sun canza ta hadu da ciwuka masu hatsarin gaske sugar da hawan jini. Ta zauna tare da taimakonsa suka zauna kujera d'aya yana dan gaya mata kafafunta ko daga inda nake zaune Ina kallon yadda jikinta yake rawa. Ban ji haushinsa ba ko kad'an domin a yanzu dai babu maganar kishi ga matar da take cikin irin wannan yanayin na halin ciwo mai tsanani. Ta dinga fara'a a zahiri tana nuna jin dadinta. Muka gaisa cikin kulawa da mutunci. Na yi mata sannu da jiki haka zalika ma baba Tabawa ta dubata sosai. Ta dinga dariya ganin yadda twin's suka yi mini farincikinta ya kasa 'boyuwa tun kafin mu yi sallama take yi mini godiya har sai da jikina ya mutu tsabar tausayin halin da take ciki. Mairo ita ta janye yaran ta tafi dasu tana yayyanka masu mangwaron da tun farkon shigowarmu suke rigima a kansa. Duk abinda muke yi bai ce mana komai ba, mun dai gaisa amma tun bayan gaisuwar bai sake magana ba, sa'i da lokaci dai yakan amsa waya idan an kira shi. Misalin takwas da wani abu muka fito daga gidan tun a hanya muke alhinin yanayin da muka risketa baba Tabawa dai kasa daurewa ta yi a hanyarmu ta shiga gida ta fashe da kuka da sauri tasa gefan jihabinta ta rufe fuskarta . To ni ma dai kukan zucci nake yi domin na shiga rud'ani ba karami ba ganin yadda Allah Ya mayar da baiwarsa. Idan kudi na sayan lafiya nasan da ba wannan maganar ake yi ba. Wannan da duniya ta yi mata sheda cewa mutuniyar kirki ce wadda tun a duniya mijinta ya ce ya yafe mata itace cikin irin wannan yanayi to ina ga wanda ya shure umarnin Ubangiji kuma, Ubangiji Allah kasa mu dace Amin. A haka muka shiga gidan Hauwa na kwance saman kujera 3str tana kallo abinta. Ganinmu sukuku ya sanya ta tashi zaune tana tambayar lafiya. A takaice na ce." Lafiya lau." Na shige d'aki domin yadda kafafuna ke rawa ba zan iya tsayuwa a wurin ba. Na zauna gefan gado tare da rafka tagumi wani abu ne ya zo ya tsaya mini a wuya na tsananin fargaba da tashin hankali mace ta koma sai kace mai cutar kanjamau! ko mai farfadiya sai an rirriketa. Hawaye suka fara sauka a kumatuna. Haka kawai na ji duniyar ta fice mini daga raina gabad'aya. Shigowarta ya sanya na daga kaina na dube ta. Ta zauna gefana babu babu fallasa ta ce." Ashe kema kukan ki ke yi Amina." Sai ta sa dariya kafin ta cigaba da cewa." Ga Baba Tabawa can ma tana yin nata, ni kam matar nan ko dame take yawo wallahil-azim kurwata tafi tata d'aci, wallahi ni zan yi maganinta." Na gyada kaina ina ko'karin ture kutittiran abinda ya tsaya mini a wuya na ce." Hauwa k'ullaci da tsananta gaba da kiyayya wallahi babu inda zai kai ki sai tashar dana sani. Matar nan dai duk rashin Imanin mutum yaga halin da take ciki sai ya tausayata mata don Allah mu dinga sassautawa kanmu Hauwa." Ta ja tsaki tare da furta."lalura fa kowa yin ta yake yi, wallahi na fita jin jiki, ni mai yasa ban lanjare ba, saboda ba ni da hakkin kowa a kaina, ita kuwa bari na gaya miki abinda ta shuka ne take girba tun a duniya hakkin mutane ne wallahi." Na jima ina kallonta tare da auna maganganunta. Yadda take tabbatar da abinda ba ta da tabbas akai shine abinda ya fi daga mini hankali da lamarinta. Wace irin kiyayyace wannan. A ganina wannan abin da take yi jahilci ne tsantsa da rashin sanin abinda ya dace. To ba ni da bakin magana domin kuwa yadda ta yi nisa irin haka babu wani kalami da zan yi mata ya sanya ta sassauto daga irin kiyayyar da take yi wa matar nan wadda alherenta suke dabaibaye damu bakidaya. Ganin ban ce mata komai ba ya sanya ta tashi tana fad'in." Matsantawa kai ne kawai kowa ya kashe wutar gabansa. Shi kuma ai hakkin rai tun a duniya Ubangiji yake fitar da shi wallahi tallahi yanzu ta fara gani. Sai kawai na saki bakina ina kallonta har ta fice daga d'akin ban d'auke idona ba. Na jima a zaune Ina tufkewa da warware kafin na tashi jiki a sabule na shiga bandaki domin watsa ruwa a jikina. Gabad'aya cikina ya cushe babu dandano a bakina ko kad'an yunwar ma sam ba na jin ta, daga zarar na tuna halin da muka riski matar nan a ciki sai hankalina ya tashi. A haka na shirya cikin kayan bacci ina tsaye gaban madubi ina busar da gashin kaina. Ya turo kofar d'akin ya shigo. Ban yi zaton shigowarsa ba. Muka had'a Ido ya nufo wurin da nake tsaye daf da ni ya tsaya na gama abinda nake yi yana ta kallona ta madubi na juyo kirjinmu ya hadu waje daya. Kusan a tare muka sauke ajiyar zuciya. Ya riko hannuna muka zauna gefan gado. Yanayin fuskarsa kadai shi ya nuna mini cewar ya ji dadin abinda na yi. Ya furta." Kin kyauta sosai kuma na ji dadin abinda ki ka yi, idan haka kuke yi mini kara akan abinda nake so mai zai sanya ni ma na 'bata muku ai babu abinda ya fi zaman lafiya dadi ko." Kanzil ban ce masa ba. amma maganarsa ta d'an dake ni wato shi baya jin nauyin gaya mana irin son da yake yi wa matar nan tasa. Ya d'ora hannunsa a tudun kirjina wanda tun zaman da muke yi a wurin hankalinsa yake kai. Ya nisa kafin a kasalance ya furta." Momi ba ta da lafiya Amina cikinta da wajenta wallahi." A nutse na furta." Allah Ya yaye mata, da sauran al'ummar musulmi." Ya amsa da Amin kafin ya dora da cewar." Kin san yanzu wani result din ya sake fitowa bayan gwajin da aka yi mata satin da ya wuce cancer mahaifa." Da saurin gaske na dube shi. Ya gyada kansa "Wallahi ni kaina na kadu Amina na tausaya mata k'warai da aniya yanzu haka za mu yi booking domin zuwa india akwai kwararrun likitoci a can da za su caje mini ita sosai." Jiki a masifar sanyaye na furta." Tabbas Ubangiji shi yake saukar da ciwo ya kuma saukar da maganinsa, ina yi mata fatan alheri tare da addu'ar samun lafiya madawamiya, kai kuma Allah Ya baka ladan jinya." Ya sake amsa da "Amin Ya Allah." D'akin ya d'auki shiru har yanzu hannunsa na saman kirjina yana dan tattabawa. Ban hana shi ba kawai dai ina mamakinsa ne a ganina yanayin alhinin da yake ciki da damuwa akan rashin lafiyar maidakinsa bai kamata a ce wani sbu na jin dad'in duniya yana bijiro masa ba, to mai ma zai fahimta bayan yana cikin tashin hankali a haukana fa kenan Na dube shi yana lumshe idonsa kamar wanda ya samu audiga na dan ture hannun nasa muka kalli juna a sarke na ce." Dama ina son magana da kai." Kai tsaye ya furta." Idan har akan zuwa maiduguri ne to kada ki bata bakinki babu inda zakije." Na ce." To saboda me, kafi kowa sanin matsayin anti Yagana a wurina ko?" Ya gyada kansa a tsanake ya ce." Da dai ban rantse ba ne sai na bari ki je, amma wallahi na riga na rantse ki yi hakuri bayan bikin sai ki je ki ga d'akin amarya." Zuciyata ta dinga tiriri na dinga danne abinda yake yun'kuro mini domin ba ni son na nuna masa damuwata a kan haka a gaba ya samu abinda zai kuntata mini idan wata matsalar ta faru a tsakaninmu. Na gyada kaina tare da furta." Shikkenan mu ajiye wannan maganar ina so ka gaya mini matsayin zamanka da Hauwa a gidan nan, domin ni har yanzu na kasa gane abinda kuke nufi da kai da ita." Ya dube ni sosai kafin ya ce." Ke ina ruwanki kuma?" Na ce." Ni ce kuwa nake da ruwa tunda duk wata mas'ala da kuka samu da kai da ita a kaina ne, yanzu a matsayinka na babba mai hankali da jagoranci abinda kuke aikatawa daidai ne." Ya ce." Ai taki ta amince da cewar ta yi lefi, sannan taki ta bi umarinina idan tana so magana ta shige mai yasa bata biyo ki zuwa duba Momi ba. Ta cigaba da zama a haka duk ranar da ta gaji sai ta nemawa kanta mafita." "Gaskiya hakan ba daidai ba." Ya 'bata rai yana fad'in." To nuna mini daidai Amina." Shiru na yi ban sake magana ba. Ya ja tsaki yana fad'in." Na yabe ki sallah za ki kasa alwala, Hauwa ai ba yarinya ba ce idan tana son zama da ni ta ba ni ha'kuri ta Kuma bi umarina." Na ce." To ai kaine babba ha'kurinka shine zai fi rinjaye." "Na yi iya wanda naga zan iya yi a kanta Amina, wannan ya zama na farko ya kuma zama na karshe, kada ki sake titsiyeni akan lamarin Hauwa ko ni din sa'anki ne?" Shiru kawai na yi Ina kallonsa. Ya cigaba da ce wa." Dangane da maganar kwanan aure kin ga Momi bata da lafiya ya kike ganin za a yi?" Na ce." Yadda muke yi mana." Sai ya yi shiru yana tunani kafin daga bisani ya furta." Shikkenan sai a cigaba da tafiya a hakan, zan kwana biyu ban koma legos ba, domin idan na kai ta asibitin na dawo zan dan jinyaceta." Uffan ban ce masa ba, ya tashi tsaye yana kallona cikin sigar kulawa ya furta." Ki same ni a sama zan shiga in yi wanka." Ban iya ce masa komai ba har ya fita daga d'akin Ina zaune zuciyata ta kasa tsayuwa wuri d'aya. A daran na gurzu a hannunsa kwarai da gaske kamar wata sabuwar amarya sai da na yi ruwan d'umi domin kusan sau uku ya yi mu'amula da ni. Farkon dare da asuba bayan ya dawo daga sallah. Still Yana gama breakfast nan ma ya sake yin wani haka na sauko daga saman a galabaice. Na yini ciye ciyen kayan da zasu saukar mini da ni'ima domin na tabbatar da cewar a wannan daran ma ba zai daga mini kafa ba. Bayan kwanaki shida mun d'an samu daidaito kad'an. A lokacin kuma sun gama shiryin tafiyar da za su yi. Har gida ya yi mata jagora domin ta yi masa sallama. Zamanta ke da wuya Hauwa ta yun'kura ta tashi ta shige dakinta. Hakan kuwa bai yi mata dad'i ba, amma dai ba ta ce komai ba, muka d'an ta'ba hira sama-sama kafin ya sauko daga saman suka fita tare. Sosai na yi mata addu'a da fatan alheri ta dinga godiya da murmushin nan nata wanda duk rintsi baya ta'ba d'aukewa daga saman fuskarta..... [12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: *115* Bayan tafiyarsu da kwana ashirin da shida Hauwa ta haihu. Cikin ikon Allah ta haifi d'anta namiji kama da ubanshi har ta 'baci duk abinda ya kamaci ta yi wa kanta ta yi tunda haihuwar gida ta yi kuma lafiya lau ita da yaron da ta haifa, a matsayinta na ma'aikaciyar lafiya taimakon da muka yi mata kad'an ne. Sai bayan da muka samu nutsuwa gabad'ayanmu ni da tukkuna na nemi maigidan da yake koda suka tafi ba kasafai yake kiran waya ba sai dai mu had'u ta whasap to baya jurar typing sai da vedio call. Sai na ajiye masa sa'ko ta whasap din tare da hoton yaron nasan daga zarar ya hau zai gani. Ina idar da sallar la'asar na bud'eta sakonshi ya shigo yana online din muka sake gaisawa na tambaye shi mai jiki ya ba ni amsa mai dadi jiki yayi kyau domin a karshen watan da muke ciki ma za su dawo domin an d'orata akan maganguna kuma alhamdulillahi an samu cigaba.Sai ya d'ora da fad'in na yi wa yaron hud'uba da sunan Ahmadu domin shine sunan da ya rad'a masa. Rashin abin cewa ya sanya ni yi masa shiru kawai domin tunda Hauwa ta haihu take kiran yaron da sunan mahaifinta wato Ishak, ban san kuma mai zan ce mata ba gaskiyar magana kenan. Ganin na yi shiru ban ce komai ba ya sanya shi kiran sunana na kalle shi tunda bidiyo call ne ya furta." Ko akwai wata matsala ne domin na karanci damuwa a cikin kwayar Idonki." Na girgiza kaina a nutse na ce." Babu matsala amma gaskiya ba zan iya gaya Hauwa ga abinda ka yanke ba, mai zai hana kai ka gaya mata naga tare kuka samar da yaron nan ku biyu mai zai sanya ni ka saka ni a tsakiya. Hauwa tunda ta haihu take kiran yaron nan da sunan babanta, to ni mai kake so na ce kuma." Ya yi shiru yana kallona kafin daga bisani ya ce." Shikkenan zan gaya mata hukuncin dana yanke hakan ya yi ko." Na gyada kaina ina fad'in." Ya yi shine daidai sai ku tsyar da matsaya a tsakaninku, Allah Ya raya mana shi." Ya amsa da "Amin. Yana mai zuba mini ido." Ni ma na zuba masa nawa idon nan na fahimci canzawar da ya yi har da wani kumatu fatar nan ta sake yin fresh duk da bidiyo call yana sanya mutum muni da duhu to shi ban ga hakan ba, kamar ba wanda ya tafi jinyya ba ya yi kama da ango wanda ya tafi yawan sha'katawa da amaryarsa. Ajiyar zuciya na sauke yayin da nake ko'karin kawar da abinda na ji yana yun'kuro mini a game dashi na ce." Na canza kammanni ne Allah Ya taimaka ka." Sai ya rausayar da kansa yana ce wa." Sosai kuwa, wata na gani anan asibitin da muke mai kama dake duk sanda na yi ido hud'u da ita sai hankalina ya tashi wallahi yanzu ina cikin tsananin damuwa na yi missing d'inki my wife." Na dan bata rai tare da cewa." Matar kuma idan tana da aure fa, kana raya abun da bai dace ba akan matar wani daidai kenan a wurinka." Kansa ya girgiza kamar karamin yaro ya furta." Ba daidai ba ne, amma ba na tsammanin ai tana da aure budurwa ce, wallahi ba zan munafurceki ba Amina ba na iya d'auke kaina daga kanta domin yanayin hallitar jikinku daya 'yar duma-duma ce mai yawaltaccen kirji da tudun mazaunai." Dariya maganar ta ba ni na danne ban yi ba domin ganin abin nasa yana nema ya wuce makadi da rawa na ce." To sai ka tuntubeta idan ba ta da aure ka aurota ko?" Ya girgiza kansa yana ce wa." A'a ai ba musluma ba ce addinin hindu ce." Na ce." To menene a ciki sai ka musuluntar da ita." Kansa ya girgiza tare da furta." A a, abinda ya sa ki ka ji Ina yi miki maganarta kamar da kuke yi da ita ne ya b'aci da gaske idan na ganta ina shiga yanayi na buk'atuwa sosai." Shiru na yi ban ce komai ba. Sai ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta." Ina nan dawowa my love za mu sha soyayya ko?" Na kashe idona tare da fad'in." Sosai ma irin wadda kake so za mu yi." Sai ya zuba mini idanuwansa babu kiftawa. Na kama dariya ina fad'in." Ka na ji kamar ka d'auko ni daga cikin wayar ko?" Ya gyada kansa yana lumshe Ido. Hakan ya sake jefa ni a damuwa da sha'awa na sauke ajiyar zuciya a kasalance na furta." Ni ma na yi missing din Baba Yallabai baban soyayya." Kafin ya ce wani abu kiran da aka yi masa a wayar ya katse video call din. Na kashe wayar tare da ajiyeta a gefe Ina sauke ajiyar zuciya gabad'aya hirar nan da muka yi ta tayar mini da hankali wani irin nake ji a jikina. Sai gefin magriba na fito falon daga cikin d'akin Hauwa na ji kukan yaron ya tsananta da saurin gaske na shiga d'akin na same shi kwance cikin net dinshi yana ta wutsil-wutsil towel ya toshe masa hanci. Da azama na zuge net din na d'auko shi fuskarsa ta yi jazur saboda da alama ya jima yana kukan. Na zauna gefan gadonta ina jijiigashi gabad'aya ya shid'e a tunanina tana bandaki na tashi tsaye dashi a kafad'ata na tsaya kofar bandakin Ina Kiran sunanta shiru bata amsa ba kuma babu motsin ruwa. Sai kawai na kutsa kaina ciki wayam babu alamunta. Da sauri na fito gabana na dan fad'uwa na tsaya ina rarraba idanuwana a d'akin ban ga alamun komai ba.. Na fita kai tsaye kicin na nufa Baba Tabawa ta kammala abinci dare tana gyara kicin din. Cikin kasala da sagewar gwiwa na furta." Baba ina Hauwa?" Sai kawai ta tsaya tana kallona kafin daga bisani ta furta." Ba ta dakinta ne Amina?" Na furta." Kwarai kuwa, fitowa daga d'aki kenan na ji kukan yaron nan koda na shiga d'akinta bata nan." Ta sanya hannunta ta kar'be shi a sanyaye ta biyo bayana muka tsaya a tsakiyar falon. Ina Hauwa za ta tafi to. Ni nake tambayar zuciyata dalili tunda ta haihu ban ga alamun fitina a tattare da ita ba asalima wani babin annashuwa da farinciki ta bud'e. Baba Tabawa ta sanya babban towel ta goya yaron ni kuma na d'auko hijabina na sanya na fita can harabar gidan. Daga nesa na tsaya Ina hangen securitys a bakin gate. Masa'udu ya shigo da mota ya ajiye a wurin da motocin suke ya fito daga motar ganina a tsaye ya sanya shi da sauri ya nufo ni. Ya risina yana gaishe ni na amsa tare da fad'in." Daga ina kake domin zuciyata ta fara hasashen wani abu. Kai tsaye ya furta." Daga airport nake na kai Hajiya k'arama ne za ta bi jirgi zuwa bauchi don haka na ji tana fad'a a waya kafin mu isa filin jirgin." Ba tare da na sake cewa komai ba na kada kaina na koma ciki gidan raina a masifar b'ace. Anya kuwa Hauwa tana da hankali ki haihu kwana biyu kacal saboda mugun abu ki gudu ki bar jaririn da ki ka sha dawainiya da wahala a kansa kafin ya zo duniya kici kwakwa. Da kuma d'aita irin ta haihuwa da rashin kwari a jiki Baba Tabawa ta dinga salallami tana fad'in." Wannan wane irin sakarci ne Hajiya Amina, to shi wannan din da ta tafi ta bar shi ai hakkinsa ba zai bar ta, ina ruwansa da abinda ya faru. Ban ce mata komai ba na shige na je na d'auko wayata layinta na dingi kira wayar a kashe na kira ya kai sau goma amma is switch off. Na zube saman kujera ina Kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!" Na jima cikin wannan yanayin kafin na d'auki wayata dake saman cinyata kai tsaye lambar dr Sailuba na nemo itace tsayayyiyar likitan da take duba ni a duk lokacin da na samu ciki mussaman cikin baby Nana ta taka muhimmiyar rawa kwarai da gaske. Abu na farko da zan yi shine samarwa da yaron abinci matsalar raino wannan mai sau'ki ne. Bayani na yi mata sosai amma ban sanar da ita cewa uwar yaron ce ta ajiye shi ba. Ba mu yi sallama da ita ba sai da ta tabbatar mini da cewa da kanta za ta shigo ta kawo mini duk abinda ya dace. Na kashe wayar tare da zubawa Baba Tabawa idanu tana ta faman safa da marwa a katafaran falon duk domin hillatar yaron da yake ta kusurkusur da alamun kuka. Sai da bacci ya d'auke shi tukkuna ta zo ta zauna a gefana tana fad'in." Ko a tarihi ban ta'ba ganin shashashar uwa irin Hauwa ba Hajiya Amina lallai ta gwadawa wannan yaro rashin Imani." Shiru na yi Ina nazari kafin daga bisani na furta." Tana so ta huce fushin abinda ubansa ya yi mata shine ta dire shi ta yi tafiyarta. Abin mamaki kuma ita da mijin nata jini guda ne mamansa ta cika nono ta bawa Mamanta wace irin zuciyace wannan." Kai tsaye ta ce." Zuciyar kafurai ce." Muka yi shiru cikin alhini kafin ta cigaba da cewa." Ita kanta na tabbatar da cewa wallahi hankalinta ba zai ta'ba kwanciya ba ciwon jiki da ciwon nono ma ya isheta. Murmushi na yi tare da cewa." Ciwon nono mai sau'ki ne a wurinta tunda likita ce tana da hanyoyin da zata magance abinta ciwon jiki kam zata sha ai haihuwa ba wasa ba ce." Haka muka kasance cikin zullumi da tararrabi har Dr Sailuba ta zo ta tafi muna zaune a falon cikin wani irin yanayi na mamaki da takaici. Ba ni da niyyar sanar da kowa wannan lamarin a ganina hakan kamar bai shafe ni ba, yaro da na d'auka tunda ta tafi ta bar shi zan yi iyakar bakin kokarina. Amma tabbas Hauwa rikici da gangami ta shiryawa kanta kuma a zahiri naga wautarta domin ta aikata abu irin na marasa sanin ya kamata. Cikin hukuncin Allah lafiya lau muka kwana da yaron bai yi kuka ba domin kuwa Baba Tabawa ta bada dukkanin kulawarta a kansa. Ni kaina cewa ta yi na tafi na kwanta za ta kula da shi. Ban kwanta ba kuwa sai da na nuna mata yadda za ta dama masa madararsa idan Allah ya sa ya farka ta ajiye komai a kusa da ita wanda za ta buk'ata. Da safe kuwa kafin na fito ta shirya shi tsaf yana goye a bayanta yana bacci lukwi hankalina ya kwanta sosai domin duk juyin da zan yi sai ya fado mini a rai tare da takaici da b'acin ran abinda uwarsa ta aikata. Sai bayan sallar azuhur tukkuna na samu Hauwa a waya. Ta daga hankalinta a kwance domin ban ji alamun nadama da danasani a muryarta ba. Jikina ya mutu sosai da kyar na furta." Kina ina Hauwa?" Kai tsaye ta ce." Ina nan Bauchi." Na danne takaicina tare da cewa." Ashe kin shirya hakan tuntuni to hakan da ki ka yi a ganinki daidai ne ko?" Da d'an murmushi ta ce." Shine daidai Amina, domin wa'adin zamana ya kare a gidan tunda na haihu yaro kuma ai gidan ubansa ne tunda ba dashi na zo ba, mai zai sanya na d'auko shi na kawo shi inda babu tarbiya Amina sunan Amadu fa ya fi sunan ubana an ce mini ubana ba komai ba ne a lokacin da na nuna shi din wani abu ne, tuntuni na gaya miki dama ba zan jure wannan rashin mutuncin ba." Cike da takaici na furta." Amadu fa aka ce shine Mahmudu Muhammadu. Ki tuna mai wannan sunan shine wanda aka yi duniya dominsa Annabi Muhammadu S.a.w a ganina wannan abin alfahari ne a wurinki." Ta yi murmushi tana cewa." A a ba da wannan niyyar ya sanya sunan Amadu ba. Abokinsa mai rasuwa fa shi yayi wa takwara na ce masa Ina son sunan mahaifina tunda na farko ya sanya sunan mahaifinsa daga fad'in haka ya fara gaya mini magana tabbacin dama haushina yake ji to menene saura a tsakaninmu na fita daga iddarsa da dama." Na gyada kaina ina danne abinda nake ji a raina na ce." To kina ganin Allah ba zai kama ki da hakkin yaron ba shine ina ruwansa." Ta yi Dariya tare da furta." Allah Ya yafe mini shi kuma idan rayayyene Allah Ya raya shi." Na yi shiru domin kamar kalaman bakina sun kare da kyar na ce." Yanzu mai ki ka gayawa inna Uwani." Da sauri ta furta." Tun daga farko a har karshe wallahi ban boye mata komai ba, Amina ai na yi hakuri na yi kuma biyayya, ke kan ki ban shure shawararki ba, na yi ta ha'kuri tsayin wattanin dana d'auka a matsayin sakakkiya mutumin nan baya kula ni kuma bai furta ya mayar da ni ba, duk wata dama ya samu bai yi magana ba yanzu kuma ai komai ya zo karshe na gaya mata komai haka zalika ma babu wanda bai sani na a family din Babanmu." "Kenan Hajja ta ji komai?" Na tambayata cikin zullumi. Ta furta." Kwarai kuwa d'azu nan suka gama waya da Inna." Na yi shiru Ina nazari kafin daga bisani na furta." Hauwa idan zu'kata sun huce a daidaita don Allah kuma yaron nan da kaina zan kawo miki shi gobe in sha Allahu rabbi, ki yi hakuri don girman Allah ki kar'bi d'anki kada ki wulakantashi domin bakisan baiwar da take tare dashi ba." "Na rantse da girman Allah a yanzu dai Amina ko kin zo da yaron nan sai dai ki koma dashi don wallahi tallahi ba zan karbe shi ba sai ubansa ya zo da k'afafunsa ya nuna nadama akan abinda ya yi mini, idan har ke za ki iya jure wulakancinsa ni kam ba zan iya ba. Ki ri'ke shi kawai na bar miki." Bakina ne ya mutu murus na rasa abin cewa tunda har ta riga ta rantse nasan abu ne mai mutukar wahala ko na kai mata yaron ta kar'ba. Zuwa yanzu kuwa na tabbatar da cewa tunda Hajja ta ji fasuwar maganar to babu shakka wanda ya asassa ma ya sani. Zan jira yi ji daga gare shi domin kuwa babu wani bangare da zan tuntunba Allah Ya ga zuciyata na yi iyakacin bakin k'okarinta. Kwana daya biyu har uku ban ji daga gare shi ba. Gabad'aya ma yau kusan kwanaki biyar kenan rabon da mu yi magana tun ranar da na sanar dashi haihuwar Hauwa ban sake ganinshi a online ba. Sai na fara trying din lambar da yake kirana da ita busy bata shiga hankalina ya d'an tashi domin tunda suka tafi bai ta'ba kwana biyu bai ta'bo ni ba. Na gaza ha'kuri har sai da na sanar da Baba Tabawa halin da ake ciki itama ta taya ni zullumi tana ta addu'a Allah Ya sa lafiya ina amsawa da Amin. Idar da sallar magribata kenan na d'auki wayata dake saman dirowa ba na iya minti ashirin yanzu ban bud'e data na duba ba. Cikin ikon Allah kamar iska sakonshi ya shigo. Amma kalmar Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un dana fara gani tun kafin na bud'e sakon shine abinda ya assasa mini 'barin jiki da kakkarwar hannu. Na bude gabana na bugawa da karfin gaske... _"Allah Ya yi wa Maryam rasuwa bayan sallar la'asar ki sanar da duk wanda ya kamata Amina."_ Abinda yake rubuce kenan Wani irin tsananin tashin hankali da d'imuwa na shiga Ina daga zaune na dinga jin tafin kafata na wani irin yammm! Hannuna da ke ri'ke da wayar ya sandare wayar ta fad'i saman cinyata. Ni kaina saukar hawaye na ji a saman dakalin fuskata suna kasa tsare da babban sauti na furta." INNALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJI'UN! Allah Ya jikanki Maryam, Ubangiji Ka yafe wa baiwarka, ashe ciwo ba na tashi ba ne." Wani mahaukacin kuka mai gunji ya taho mini a guje! Na sanya tafin hannuna na toshe bakina ina fad'in." Mun shiga uku a wannan duniyar da bata da tabbas Ya Allah!!" Wayar na laluba da saurin gaske tabbas wannan shi zai zama izna ga Hauwa ya nuna mata cewa babu abinda yake cikin wannan duniyar face rikici da firgici tashin hankali da rashin tabbas Bugu d'aya wayar ta yi ta daga cikin kukan da na kasa jimirin danne shi na ce." Hauwa Momi ta rasu d'azu da la'asar yanzu nan maigidan yake sanar da ni.... [12/17, 7:36 PM] bintaumarabbale: *116* Cike da rikicewar murya ta furta." Wac...wace Momin kike nufi Amina?" Yadda ta fad'i maganar shi ya tabbatar mini da cewar a ki'dime take... Na ce." Momi dai da kika sani matar mijinki Hajiya Maryam." Dif ta yi sai sautin shuhhh! ne yake tashi a kunnana. Na daga wayar na duba tana ta tafiya. Sunanta na kira ta amsa a sanyaye "Na'am. Na ce." Ki sanar da inna Uwani halin da ake ciki Hauwa kin ga dai duniyar ko ita kenan fa." Ta yi shiru dai bata tanka ba. Na ja ajiyar zuciya ina jin yadda wani kutittiran abu ya tokare mini a wuya ba komai ba ne face damuwa da tsananin kidima da tashin hankali. Jin ta yi shiru ba ta ce komai ba sai kawai na datse kiran na nemi lambar Hajja domin ba na tsammanin ta san da rasuwar tunda a sa'kon da ya rubuto mini ya ce na gayawa wanda ya dace. Sosai Hajja ta gigice da ta ji labarin rasuwar dan har sai da na yi dakacen sanar da ita tunda ita kanta ba ta da koshin lafiya. Kasa jimirin sauraran kukanta na yi na datse kiran hannuna na rawa na ajiyeta saman cinyata hawayen suka sake zubo mini a saman fuska. Hannu nasa na sharce na sake saukar waya a karo na uku anti Yagana na kira na sanar da ita domin ta gaya duk wanda ya dace a yi jana'iza da shi. Na kira Babanmu na sanar dashi shi ma ya tabbatar mini da cewar za su kamo hanya gobe da sassafe shi da Baba Sule. Jiki a sabule na fita falo baba Tabawa tana d'akinta sai na bita can. Na sameta ta ninke kayanta ganin yanayina ya sanya jikinta mutuwa. Rashin kwarin kafafuna ya sanya ni zubewa gabanta na furta." Baba Tabawa Momi ce ta rasu fa?" "Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Kalmar da ta fara furtawa kenan kafin ta tallafe ha'barta cikin alhini da tace." Baiwar Allah nan ashe ciwo ba na tashi ba ne." Hanci na ja tare da furta " Baba tunda ranar da muka je duba baiwar Allah nan wallahi hankalina ya kasa kwanciya haka kawai daga ta fad'o mini sai gabana ya yanke ya fad'i wallahi ciwon nan nata ya tsaya mini a rai na sosai." Ta girgiza kai cike da kasala ta ce." To a Amina abin ne da ban tsoro ga yanayin yadda hallittunta suka jirkice ba ke kad'ai ba ni kaina da ita nake kwana da ita nake tashi a rana wallahi Ubangiji Allah Ya gafarta mata ya yafe mata, halinta nagari ya bita don arzikin Annabi." Da "Amin na amsa tare da cigaba da nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un domin samun nutsuwa da k'adaita Allah da kuma tabbatar da cewa gare shi muke kuma gare shi za mu koma. Mun jima muna cikin alhini tare da tariyo kyawawan halinta kafin mu yi sallama babu batun cin abincin dare domin gabad'ayanmu babu wannan kuzarin a tattare da mu. Ban ta'ba tsoron mutuwa ba sai a kan matar nan ni kadai a d'aki ta dinga yi mini gizo. Dana rintse idona sai na ga suffarta mussaman karshen ganina da ita lokacin da ta shigo yi manna sallama da za su tafi. Na cigaba da kiran sunan na d'auki waya na kira Sahura ganin kiran bagatatan cikin dare sai ta tsorata ta fara tambayata a ki'dime! Da kyar na iya gaya mata halin da ake ciki. Ita kanta sai da ta rude tana fad'in." Amina ban ta'ba ganin matar nan ba Amma wallahi mutuwarta ta gigitani. Ubangiji Allah Ya gafarta mata ya sanya karshen wahalarta kenan, mu Kuma da muka d'auki zunubinta Allah Ya yafe mana, amma ni kaina na jima da sanin cewar matar nan baiwar Allah ce duk kazafin da wasu daga cikin mutane suke yi mata ba gaskiya ba ne, kin san haka siddan Ubangiji ba zai d'aukaka bawansa ba sai da jarrabawa. Allah Ya yi mata rahama. Babu kuzari na ce." Amin suma Amin Sahura ni kaina a gigice nake wallahi a yanzu a cikin raina sai nake tunanin mai yasa na yi abinda na yi a baya dana sani na ha'kura kawai tunda duniyar guda nawa take. Zahiri matar nan alherinta na sani ban san wani sharrinta ba, domin idan zan bude baki na furta ga abinda tayi mini na rashin kyautawa wallahi na yi mata sharri Sahura, ba ki ki yadda nake ji ba a raina na tsorata da wannan duniyar gabad'ayanta. Ita kanta Hauwa tana can cike da gigita domin kasa magana ta yi da na kira ta a waya na sanar da ita wallahi sai kashe wayata na yi domin bakinta ya mutu murus ta kasa furta komai." "Ai Amina mutuwa wa'azi ci ga duk wanda Allah Ya sa zai hankalta, duk d'aukaka da sharafin mutum a duniya ba iya tsallaketa. Mu 'yan adam ai muna da mantuwa shiyasa muke ganin kamar ba za ta zo kanmu ba, a yadda dai kike ba ni labarin irin abinda Hauwa take yi wa matar nan wallahi ita ya fi kamata mutuwar ta dake ta, ta kuma ji tsoron Allah har ta mutu bata nemi afuwarta ba Allah baya yafe hakkin wani akan wani har sai wanda aka zalinta ya ce ya ya yafe, aikin banza ai kishi ba hauka ba ne, ni kaina Hauwa ta ba ni mamaki kuma na raina wayo da iliminta domin jalihi ne kadai ba zai fahimci cewa ba hassada take yi wa baiwar Allah nan ba." Shiru na yi Ina ta auna maganganun da take yi. Ni kaina na kan zauna na yi ta nazari akan mai yasa Hauwa ta zafafawa matar nan da yawa. Kishi ne ko hassada mai yasa komai sai ta mayar da shi rigima da sa'insa lefi ni aka yi wa amma ban yi irin abubuwan da take yi ba, tabbas dole a dora ayar tambaya a kanta koda kuwa ba hakan ba ne a zuciyarta ni kaina ba zan fita daga zargi ba tunda yan uwanta da yawa suna ganin cutar da ita muke yi ta hanyar hade mata kai da yi mata tawaye tare da fito da kishi muraran. Idan zan kwana ina rantsuwa da Allah kan cewa ba ni yi mata hassada da b'akinciki babu wanda zai yarda. Haka na kwana cikin zullumi da nazari na tashi da ciwon kai irin na gefe damuwa da tunani da rashin bacci. Misalin tara saura Baban Saude ya kira ni yana tabbatar mini da cewa suna kan hanya suna da d'an yawa. Na kira Babanmu ya ce mini shi ma sun taso su uku har da Ummansu Hadiza. Wanka na yi na kintsa na fita falo cikin hijabi har kasa na samu Baba Tabawa itama cikin hijabin da carbi ta kammala abin kari da d'an dama. Da asuba na ce ta yi abinci da yawa saboda bakin da suke tafe. Muka gaisa tare da sake yi wa juna gaisuwa. Masa'udu tare da Sale suka shigo da akwati kafin shigowar Hajjan Kamalu ne ya fara shigowa tukkuna suka shigo Hajja da Gwaggo da Hamusu a biye a bayansu. Bakin kofar na isa da sauri ina yi musu barka da zuwa. Na kar'bi jakar dake hannun Hajja ina fad'in." Gwaggo sannunku da hanya Hajja kun yi sauri sosai fa kamar a hanya kuka kwana. Suka zauna a kujera tana fad'in." Da asuba muka taso ai, kuma dai Garba ya kure gudu sosai shiyasa Allah Ya kawo mu." Na nutsu sosai muka gaisa a tsanake Hamusu dake can saman kujera mai cin mutum d'aya ya gaishe ni na amsa tare da tambayar iyalinsa da yaronshi Arif da bai wuce shekara biyu ya ce mini duk suna lafiya. Baba Tabawa bayan sun gaisa da yi wa juna ta'aziyya na ce ta kawo musu abin kari. Na dubi Kamalu dake gefe a tsaye jikin labule ya sake girma da fad'i sosai suffa ta mazantaka ta bayyana a tattare dashi har da gemu ya fara ajiyewa. Yatsansa makale da carbi mai lamba yana ta rarraba Ido a kanmu yanayinsa gabad'aya kamar mai nazarin wani abu damuwa da tashin hankali sun gama bayyana a tattare dashi. Ganin mun had'a Ido dashi ya sanya ni janye nawa idon. Ina jin wani abu na taso mini da tashin hankali. Ya gurfana a gabana cikin kula da ladabi ya furta."Mama ina kwana ya muka ji da hakurin wannan rashi." Na amsa da "Alhamdulillahi mun gode Allah." Ya furta." Allah Ya jikan Momi Ya gafarta mata." Gabad'aya muka amsa a falon. Na dubi Hajja tare da fad'in." Yusi bai samu zuwa ba ne?' A tsanake ta ce." A a ai tare duk muke tafe tun a waje ya ce Garba ya ajiye shi yana can tare da Adamu." Na gyada kaina ba tare da na sake cewa komai ba. Baba Tabawa ta kawo tire uku masu girma cike da abin kari na taimaka mata wurin zubawa kowa Hajja ta ce ." Hajiya Saratu tana tafe in sha Allahu mun yi waya da Alhaji Haruna shi da d'an uwansa Alhaji Dahiru sun ce za su yi kokarin samun jana'iza." 'Yan uwan mahaifin maigidan ne Wanda a yanzu su kadai ne suka rage musu a family din. Na gyada kaina a sanyaye na ce." Allah Ya kawo su lafiya. Kai na jima ban shiga tashin hankali da nadamar rayuwa ba sai a rasuwar baiwar Allah nan. Tunda gawar ta iso gabad'aya estate din namu ya cika da motoci jama'a daga kowace kusurwa abokanan maigidan dama wasu daga ciki abokan tsohon mijinta ne. Cikin gidanta cike da 'yan uwanta da zuriarsu tare da abokanan arziki da yaranta masu yi mata hidima da shagunanta. Ana ta koke koke masu dauriyar daga ciki kad'ane. Babbar yarinyata Nusaiba sumanta biyu har yanzu ba ta gane wanda yake kanta ba. Nabila kuma tana ta iskokai a wani d'aki da 'yan uwansu sun kulle-kulle kofa don kada ta fito daga inda muke a zaune muna jin ihunta. Cikin masu yi wa Momi wankan gawa har da Baba Tabawa lallai na yaba kwarai da aniya wurin jajuecewarta da dauriyarta koda yake yadda take ba ni labari a gaban idonta mahaifiyarta ta rasu kuma itace ta wanke ta. Wannan ya kara tabbatar mini da cewa Baba Tabawa tana daya daga cikin salihan matan da Ubangiji ya ce lallai yana jin kunyarsu a gidan duniya da lahira dalilin rashin haihuwa. Ban tashi tabbatar da cewa d'an adam ba a bakin komai yake ba sai da aka gama had'a Momi tsaf cikin likkafani a mike cikin makara ana ta lallabata sunanta gabad'aya ya shafe daga jiya zuwa yau din wasu na kiran ta da gawa wasu na kiranta da marigayiya. Yaranta da mijinta tare da yan uwanta sun kewaye makarar yayin da masu aikinta mata da muke tare da su a gidan suke gefe sun cure kansu wuri d'aya sai sharbar kuka suke yi. Hajja da Gwaggo suka nufi bakin makarar. Na yi na yi na ja kafata domin bin bayansu na kasa domin wata irin juwa da Hajijiya nake ji idona na ganinsu garagara, hawaye masu d'umi suka silalo kumatuna wanda ya yi daidai da lokacin da na yi hu'bbasa wurin sarrafa kafafuna amma suka doje ban san yadda aka yi ba kawai na ji a kasa na zube a lokacin ne kuma naga kamar gilmawar wani abu daga sannan ban sake gane komai ba sai dana farka tukkuna na tabbatar da cewar suma na yi lokacin har an kaita makwancinta an dawo. Anti Yagana sun iso tare da Inna Uwani. Ban yi mamakin ganin yanayinsu ba domin akwai d'imuwa da tashin hankali na rasuwar da aka kwantsama. Ko baka da ji'bi da mumini fad'in Annabi ne mutuwarsa dole ta nasheka balle wannan matar da alherinta ya rinjayi lefinta mijinta kuma tun kafin ta mutu ya yafe mata jama'ar da suka sallaceta sun zarta wanda Annabi ya fad'a tabbacin samun rahama daga Allah buwayi. Hajja ta shigo d'akin da muke tana fad'in." To alhamdulillahi tunda ta tashi da ji da ganinta da kuma lafiya mun gode Allah Yagana taimaka mata sai mu koma can gidan nasu mu yi namu zaman domin nan din zaman zai zame mana fitina. Gwaggo da fitowarta daga bandaki kenan daure da alwala ta ce." Ni ma shawarar da na yanke kenan hakan zai fi alheri." Anti Yagana ta dube ni a d'an sanyaye kafin ta ce." Sannu ba dai kya jin komai a jikinki ko?" Kaina na gyada mata a nutse na ce." Ashe kun zo?" Ta ce." Mun zo mun tarar da gidan a kacame ana ta hayaniya ke kuma gaki a sheme sai da likitanku ta zo ta dubaki fa dogon suma ki ka yi." Shiru na yi Ina nazarin maganarta kafin na ce." Anti Yagana mai ya faru ne?" Tabe bakinta ta yi ba ce mini komai ba. Na daga kaina na kalli Hajja dake tsaye jikin bango rumgume da hannunta a kirji nan take na karanci damuwa da b'acin rai a saman fuskata. Ban sake wata magana ba na tashi zaune hijabi na da yake gefe anti Yagana ta miko mini na zura a jikina tana taimaka mini na yun'kura na tashi ta ri'ke ni. Na ce." Ki cika ni zan iya tafiya da kafafuna. Inna Uwani ta ce." Da dai kin bari ta rike ki jikin naki ai har yanzu bai gama daidaita ba. Hajja da Gwaggo suka yi gaba. Wani irin kallo dangin marigayiyar suke mini na tsana da kyama. Anti Yagana ta juyar da kanta ba ta ce komai ba. Ni ma ban ce musu komai ba na ji daya daga cikinsu fad'in." Kun kaita kasa kun ji dad'i, sai ku jirayi hakki domin wallahi ba mu yafe muku ba, duk abinda za ki nuna a banza a wofi Maryam dai karshenta ya yi kyau ku kam in sha Allahu mutuwar wulakanci za ku yi." Maganganunta ne suka dinga yi mini amsa kuwawa! a kunne gabana ya dinga bugawa da karfi da karfi. Wannan babban kalubalen ban shirya tararsa ba a yanzu domin ba ni da hujjar da zan kare kaina Allah shine shahidi. Muka fita tun daga haraba cike da jama'a har zuwa waje mutane cike cikin manya manyan rumfunan da aka kafa. Kafafuna suka dinga hardewa gabad'aya sai na tsargu domin maganganun da matar nan ta yi sun sake dakusar da duk wani karsashi da kwarin gwiwata. Shin wane irin kallo jama'a suke yi mini a yanzu dana fito cikinsu. Cikin dubara na janyo saman hijabina na rufe fuskata dashi dama rike nake a hannun anti Yagana. Ina jin sanda Hajja ta tsaya suna gaisawa da ire-iren abokanan Yallabai din na ce da anti Yagana ta yi sauri mu wuce domin ba ni da wani kumaji da nutsuwar da zan iya tsayuwa a gaban jama'a domin kar'bar ta'azziya. Muka yi gaba muka bar su ita da Gwaggo suna gaisawa. Kuryar d'akina anti Yagana ta dangane da ni na zauna kan gado kamar wata sabuwar amarya na yaye hijabin da ya katange fuskata. Muka had'a Ido nan take na rushe da kuka na ri'ke hannunta katamau! Jikina na kyarma na furta." Anti Yagana Momi ta mutu sanadiyar lalure-laluren da suka yi mata hijabi, ina tsoron kada 'yan uwanta da jama'a su jinginta rasuwarta da ni da Hauwa, ai kin ji abinda daya daga cikin 'yan uwanta take fad'a ko?" [12/17, 7:36 PM] bintaumarabbale: *117* " 'Karamin tsaki ta yi kafin ta ce."Amina duk wanda zai alak'anta rasuwar matar nan daku to dama can ba masoyinta ba ne. Su kansu 'yan uwan nata da suke ko'karin tashin husuma ba kaunarta suke yi ba tunda har suke jingina rasuwarta da wani abu daban. Kishi halak ne kuma duk gidan da aka had'a mace fiye da biyu ana samun irin wad'annan matsaltsalun. A ganina wannan ba wani abun damuwa ba ne, rigima ce suke nema kuma in sha Allah rabbi har a share makoki ba za mu tanka musu ba. Ni gidan ma ba zan sake shiga ba tunda na lura duk yawansu babu mai dattako a cikinsu. Rashi Kam ba su kadai suka yi ba mutane da yawa ne domin Hajiya Maryam bango ce majingina kuma uwar marayu har ma da masu uban. Don haka iyakacin k'aunar da za su nuna mata su bita da addu'a tare da rungumar abinda ta bari shine kawai sakamakon da za su yi mata bayan rayuwarta. Don haka ki samu nutsuwa ki kuma daina tunanin kina da hannu lokacinta ne kawai ya yi kuma babu wanda ya isa ya tsalle rana da sa'in komawarsa ga Allah." Maganganun anti Yagana sun d'an sanya ni mini nutsuwa kad'an amma har yanzu zuciyata ba ta daina yin tsalle akan abinda na ji yana fitowa daga bakin 'yar uwar marigayiyar ba. Wajen daya da wani Abu Babanmu suka iso tare da baba Sule da Ummansu Hadiza kamar yadda ya fad'a. Baban Saude ne har yanzu bai shigo inda nake ba, anti Yagana kuma ta gaya mini tare suke da Babansu Fadila har da Baba Madu wanda ya kasance babban yayansu Mamanmu, mahaifin Babandi. Sai bayan la'asar tukkuna suka shigo da d'an yawansu duk muna zaune a babban falo. Maigidan tare da iyayenshi biyu 'yan uwan mahaifinsa da kuma Baban Saude Baba Madu da Babansu Fadila. Falon ya cika da sabuwar gaisuwa tare da yi wa juna ta'aziya. Ta mussaman suka yi mini gaisuwar na amsa yayin da nake jin cikowar ruwan hawaye idona. Ina jin Hajja tana tambayar Alhaji Haruna Hajiya saratu ya ce tana can gidan mai rasuwar tunda koda suka sauka nan ta shiga ba ta fito kuma har yanzu. Suna ta tattauna hirar marigayiyar yayin da maigidan ke sake basu irin wahalar da ta sha na jinyya farkon zuwansu asibitin a yayin da aka dora ta akan magani an ga sauyi sosai anga sau'kin ashe na tafiya ne, yana sake jadadda musu cewa ko ranar da zata rasu yini lafiya lau suka tashi ta ci abinci sosai kuma shi da ita sun jima suna hira irin wadda suka jima ba su yi irinta ba tun kafin kwanciyarta ciwo. Ya ce ya fita da zummar yin sallah ya dawo ya tarar da likitoci ce sun rufe kafin wani dogon lokaci kuwa rai ya yi halinsa. Na daga kaina Ina kallonsa a yayin da yake basu labarin akwai alhini mai yawa a tattare da shi zahiri kuma yanayinsa ya nuna mutuwar ta dake shi kwarai da gaske kwarmin idonsa ya zurma fatar lebanshi ta bushe kamar wanda ya yi azimin shekara bai sha ruwa ba. Irin wannan yanayin ya shiga a lokacin rasuwar tsohon mijinta Alhaji Amadu da kyar ya dinga cin abinci. Yanzu ma ba na raba daya da biyu rabonsa da abinci tun da aka yi rasuwar kwana da yini kenan. Gabad'aya sun jajanta sosai kuma kafin tafiyarsu sai da Baban Saude ya jagorancemu gabad'aya muka yi mata doguwar addu'a wadda take d'auke da surorin da ake karantawa mamaci. Yamma likis suka yi mana sallama gabad'ayansu har da Hamusu da Babanmu domin cewa ya yi shi ma ba zai zauna ba tafiya za su yi tunda sun yi abinda ya kawo su. Shi kansa maigidan ya so su kwana ko daya ne amma gabad'aya suka ki har da kawunan nasa. Hajiya saratu ce kawai ta zauna ta ce sai an yi sadakar ukku tukkuna. Yallabai din ya bada umarnin mayar dasu Babanmu gida. su Baban Saude kuma dama a motarsa suke tafe. Sai bayan sun tafi tukkuna Hajja ta dinga fad'a wai mai yasa anti Yagana ba ta jagoranci Ummansu Hadiza zuwa gidan mai rasuwar ba. Anti Yagana ta ce mata mantawa ta yi shiyasa ni kuma nasan ba haka ba ne ita da kanta ta gaya mini k'afarta ba zata sake taka gidan ba. Gaisuwar da ta yi wa maigidan ma ta isa ba sai ta je ta yi wa 'yan uwanta ba tunda dukkaninsu taron tsintsinya ba share ne. Sai bayan magariba Hajiya Saratu ta shigo. Ina d'aki lokacin na idar da sallah ban ka ga tashi daga kan daddauma ba ta shigo. Na saki fuskata sosai Ina fad'in." Mai sunan mamana ina yini?" Ta zauna gefan gadona a nutse tana fad'in." Lafiya lau Yayata kuma diyata." Na yi murmushi a hankali na ce." Ai tun d'azu aka ce kina can gidan marigiyar ina nan ina ta zuba idon ganin Momi." Ta dafa kafadata tana fad'in." Ga ni na shigo ai Amina ya muka ji da hakurin Maryam lokaci ya yi Ubangiji Allah Ya gafarta." Na amsa da "Amin Ya Allah." Cikin wata iriyar murya. D'akin ya d'an yi shiru wanda ya yi daidai da lokacin da anti Yagana ta fito daga bandaki daure da alwala. Ta saki fuska tana fad'in." Hajiya kin shigo kenan?" Ta ce." E wallahi Yagana ya gida ya yaran, ya muka ji da hakuri?" Anti Yagana ta ce." Ha'kuri da godiya Hajiya Allah dai ya jikinta da rahama." Da Amin ta amsa yayin da take sake dora hannunta a kafad'ata. Anti Yagana ta d'auki daddauma da hijabi ta koma can gefe domin gabatar da sallar magriba. Ta ce." Ai ni ban fito ba daga gidan ba sai da na gabatar da sallata tukkun." Na yi murmushi kad'an ban ce komai ba. Sai ta ce." Amina akwai maganganun da nake so mu tattauna dake idan babu damuwa." Cikin nutsuwa na ce." Babu damuwa Hajiya Ina sauraranki." Ta sauke ajiyar zuciya a tsanake ta ce." Hajja ba ta jima da sanar da ni abubuwan da suke faruwa ba a gidan nan naku sai rasuwar Hajiya Maryam ta ratsa hakan sai ya kara ba ni kwarin gwiwar zuwa domin na ji komai daga gare ki, Amina da hankalinki za ki biyewa Hauwa da har yanzu ba ta san rayuwa ba, mai yasa kuka kasa bawa mijinku kwarin gwiwa da taimako wurin ganin ya rike amanar abokinsa. Jimawata gidan marigiya Maryam tana da dalili domin 'yan uwanta ne suka zaunar da ni suna wassafa mini irin zaman da kuka yi da ita da irin abubuwan da kuka dinga yi mata na rashin kyautatawa, idan har hakan gaskiya ne Amina ban tsammata daga wurinki ba domin kallon da nake yi miki kin wuce a ce a yanzu an zauna a nuna miki abinda ya dace idan Hauwa ta yi hakan ba zan musa ba dama na san halinta da na ji sunanki a ciki ne sai hakan bai yi mini dadi ba, mai ake gudu ne a zaman tare irin wannan fa, yanzu ina Maryam din take ta mutu ta bar duniya to mai zai sanya ba za mu yi hakuri da rayuwa ba. Ashe Hauwa har sai da ta yi sanadin da Tajo ya saketa saboda kuma bata da hankali ta tafi ta bar yaro jinjiri fisabillahi ina hankali da imaninta yake." A nutse na dubeta tare da cewa." Mamana abubuwan da yawa sun faru masu dadi da akasin haka. Amma zan gaya miki wani abu da ba kowa ya san shi ba sai ni sai Ubangijin da ya hallice ni wallahi tallahi ban ta'ba kin Momi a cikin raina ba. Tabbas akwai kishi kuma kowace mace tana da nata daidai gwargwado amma ni Amina ban zafafa shi akan matar nan ba duk sanda zuciyata za ta kitsa mini mummunan abu akan kanta nakan yi tirr da ita da take bijiro mini mugun nufi akan matar da alherinta ya fara riskata kafin wata mu'amula mai karfi ta ratsa tsakaninmu. Duk abubuwan da suka dinga faruwa yaranmu suka had'a Amma ni da ita sa'insa mai muni bata ta'ba hadamu ba, kuma lafiya lau muka yi sallama da juna har ta koma ga Ubangijin talikai. Har yau har gobe ban kulleceta ba ban kuma k'ullaci yaranta ba ina jin tausayinsu kuma ina yi musu kallo irin na uwa." D'akin ya shiru bayan ajiye maganata na ja numfashi cikin bushewar ma'kogwaro na cigaba da cewa." Magana akan Hauwa kuma ni ba zan iya ce miki komai ba, abinda dai na sani shine Hauwa ta yi mini kokari kwarai kuma babu kishi da ganin kyashin juna a tsakanina da ita. Duk hanyoyin na bi domin na nuna mata abubuwan da take ba su da kyau na bi, na yi bakin kokarina amma ba ta ji ba. Dalilin rigimarsu da maigidan tana da ala'ka da ni da ita mai rasuwar da yaranta. Mun daidaita a wattanin baya har na so ni da ita mu je mu dubata a lokacin da ta kwanta a asibiti Amma fafur ta'ki sai tare da Baba Tabawa na tafi. Wannan shine abinda zan iya gaya miki Mamana bayan hakan ban San abinda yake tsakanin Hauwa da mijinta ba tunda tun kafin ta aikata haka na yi iyakacin bakin kokarina a kansu ita dashi amma babu wanda ya saurareni a cikinsu." Ta jima sosai kafin ta yi magana cikin yanayi na damuwa ta ce." Dangin matar nan dai a ciki suke da ku Amina domin gani suke yi bakincikinku ne ya kashe musu 'yar uwarsu duk wanda ya zauna ya tashi sai sun amayar masa da abinda yake cikinsu. Anti Yagana ta ja tsaki tana fad'in." To, abinda ya fi sai kawai su d'auki lasifika su fara bi sa'ko da loko suna shela tunda ba su da hankali, wannan ba k'auna ba ce abinda suke nunawa tsantsar jahilci ne kuma za su hana yar uwarsu kwanciyar lafiya a kabarinta muddin suka ce za su tashi rigima abubuwa da yawa ne za su faru. Dama zaman tare ai ya gaji haka dole a samu matsaltsalu ma bambamta sai dai kawai Allah Ya kyauta." Ta girgiza kanta tana fad'in." Hakane amma Yagana daidai ne Hauwa ta ajiye jariri sabuwar haihuwa ta shilla wata duniya ko a waje Tajo ya je ya auri yarinyar nan ya kamata ta aikata mana wannan rashin mutuncin. Jininmu ce fa ciki daya fa ba wasa ba ne Yagana ya kamata Hauwa ta gane kuskuranta wallahi ni dai idan da yawuna da shawarata ba zan bawa Tajo umarnin mayar da ita dakinta ba, tunda ta za'bi ta tozartamu shikkenan sai dai zumuncin ya lalace ." Anti Yagana ta ce." A a ba za a yi haka ba Hajiya, ai ko babu dangantaka ta jini an riga an zama daya tunda har yara suka ratsa tsakani. Don kyautawa Hauwa ba ta kyauta ba. A dai nuna mata kuskuran abinda ta yi a gyara ta dawo dakinta a ganina shine abinda ya fi dacewa." Ta gyada kanta ba tace komai ba tabbacin maganar anti Yagana ba ta gamsar da ita ba. Na ce." Anti Yagana idan Hauwa tana da lefi shima yana da lefi fa. Domin ya yi abubuwa sosai wanda ya kamata a ce ya gane kuskure ne a zamantakewa amma bai gane ba, ni na yi kokarin dannewa dalili nasan babu wani abun da yake dawwama sai ikon Allah wanda shi muka gani yanzu. Na yi ta ko'karin bata shawara kan cewa ta kawar da kanta ta kasa jimirin yin hakan har sai da bacin rai ya ratsa tsakaninsu. Ya kamata gaskiya a tsage Mamana. Shi kansa maigidan akwai tashi matsalar sai dai ace ta Hauwa ta rinjayi tasa." Ta ce." Ni dai da yawuna ba zan bashi umarnin dawo da Hauwa ba duk hukuncin da ya yanke daidai ne." Tana fad'in haka ta tashi tana cewa." Zan je na watsa ruwa can wurin su Hajja jikina duk ciwo yake yi mini na samu nasa wani abu a cikina." Na ce." To shikkenan Mamamu dama na ce da Baba Tabawa ta tu'ka mana towo don zai fi manà dadin ci akan tsabar shinkafar nan." Ta ce."Aikuwa kin yi shawara mai kyau Amina don tunda aka sanar da ni rasuwar nan wallahi ko na sanya abinci a gabana sai dai na kalleshi ba na iya ci. Kai rasuwar baiwar Allah nan ta ta'ba ni wallahi." Anti Yagana ta ce." Ba ke kadai ba wallahi ni kaina na gigita kwarai da aniya Ubangiji Allah Ya yi mata rahama." Muka amsa da amin gabad'ayanmu kafin ta yi mana sallama ta fita daga d'akin, anti Yagana ta dube ni tana fad'in." Na so na tambayi Ummansu Hadiza labarinta amma na sha'afa wallahi, ina so mu sake samun lokoci mu je mu sake dubata ko ya ki ka ce." Na ce." Hakane anti Yagana ni kaina Hadiza tana raina wallahi, dalilin da ya sanya kenan na ce da Hamusu duk karshen wata ya dinga yi mata siyayya yana kai mata, zuwan namu yana da amfani ai hannunka baya rubewa ka yanke ka yar." Ta furta." Ni har fargabar ganinta nake yi wallahi saboda Ina tuna irin kukan da ta dinga shirga a ranar da muke je kin san da kyar aka tura ciki muka fito, na jima ina kukan zucci duk sanda na tuna da halin da take ciki nakan shiga yanayi na damuwa mace a irin wannan wurin a ajiye Amina duniyar nan ta baci duk da ba ita kadai ba ce, amma su kansu ma'aikatan wurin wallahi wasu daga ciki ba su tsoron Allah." Cike da damuwa na ce." Anti Yagana lefin Hadiza na kisa ne ta kuma tabbatarwa da kotu gaskiyarta ba mu da wani yun'kuri da zamu yi domin ceto ta. Hakkin rai ba abin banza ne. Idan Allah Ya kar'bi tubanta kuma tana da ragowar rayuwa sai ki ga ta fito ta hanyar da ba mu yi tsammani ba. Idan Kuma sun kasheta shikkenan sai ta riski Ubangijinta a wankakkiya. Ubangiji Allah Ya kare mu daga fadawa jarabawa da mummunar kaddara." Ta amsa da Amin Ya Allah da yanayi na damuwa da nadama. Misalin goma da rabi maigidan ya shigo tare suke da Kamalu ban yi mamakin ganinsu su biyu babu Yusi ba domin sai na ce ganina da Yusi daya kafin a d'auki gawar marigayiyar na hange shi tare da Adam a rakube a bayan kujera. Yanzu ma su Hajja da Gwaggo sai tambayarsa suke yi ina jin Kamalu na basu amsa da cewa yana can tare da Adam. Maigidan bai tsaya ba suna gaisawa ya haye sama hankalina gabad'aya yana kansa don haka ban yi jinkirin bin bayansa ba. Na same shi zai shiga wanka da babban towel a jikinsa. Muka zubawa juna ido. Na isa dab da shi na tsaye a sanyaye na ce." Ya karin hakuri tun d'azu nake ta so na yi maka gaisuwa ban samu dama ba, Ubangiji Allah Ya gafarta mata, kai kuma Allah Ya baka hakurin jure rashinta, Allah Ya albarkaci abinda ta bari." Ya dinga amsa da "Amin Ya Allah cikin jin dadi. Ya nufi bandakin na bi bayan shi na taimaka masa wurin had'a ruwan wanka. Kallo yake ta bi na dashi babu yabo babu fallasa, amma kallon ya fara sa'bata sai na tsargu na fara tunanin ko shima ya fara yarda da abinda 'yan uwanta suke fad'a akanmu. Da na tuna kallon nasa babu harara da kyama a ciki sai na d'an samu sassauci, na fito na bar shi a bandakin domin ya yi wankan. Na zauna jigum cikin zullumi. Ya fito yana tsane jikinsa na tashi da sauri na bude wardrobe dinshi jallabiya na fito masa da ita da gajeran wando. Na mika masa ya kar'ba na koma na zauna yana kintsa jikinsa ya ce." Ki kawo mini abinci Amina." Da sauri na mike ina fadin." Dama abinda zan tambayeka kenan, tun yamma na ce da Baba Tabawa ta yi towo zai fi dadin tafiya." A takaice ya ce." Kin kyauta kuwa." Ya d'auki turare yana fesawa a jikinsa. Na sauka kasa cikin nazarin abinda ya yi a ganina wane turare zai fesa a cikin wannan yanayin da matarsa ta rasu ko kwana daya ba ta yi a kabarinta ba Na koma saman da tire a hannuna mai d'auke da kwanonin abincin da duk abinda nasan zai buk'ata. Yana zaune gefan gado yana waya da Sukairaju na ajiye tiren hannuna a saman daddumar da yake zama domin cin abinci... [12/17, 7:36 PM] bintaumarabbale: 118* Sai da ya kammala wayar tsaf tukkuna ya zo ya zauna saman daddumar da abincin yake a shirye. Na zuba masa guda biyu madaidaita ina ko'karin zuba miya ya furta." Wanene zai cinye miki wannan towon Amina?" Na dube shi a tsanake kafin na ce." Kai ne za ka cinye?" Sai ya gyada kansa yana fad'in." A a d'aya ya ishe ni, kada ki zuba miya a kai a b'ata shi ki yi addu'a dayan ma na iya cinye shi." Ban ce komai ba na cire dayan na mayar cikin fulas na fara ko'karin zuba miyar ya ce ki zuba ta yau'kin kawai kada ki sanya mini jar miyar, ki sanya mini man shanu akai wadatacce." Na yi yadda ya umarta Ina fad'in." To naman fa." Ya ce." Ki tsamo sai ki sanya mini." Ban ce komai na dinga tsamo naman ina zuba masa a saman towon har ya so yayi yawa." A nutse ya ce." Naman nan ya isa haka Amina, kina so na ci abinci jikina ya mutu ko?" Na girgiza kai a hankali na ce." Kallo d'aya na yi maka d'azu na tabbatar da cewa akwai yunwa a tattare da kai wallahi." Ya furta." Ba ki yi karya ba rabona da abinci tun yammacin jiya kuma ban wani damu ba wallahi." A nutse na ce." To yanzu dai ka daure ka cinye wannan har naman duka." Hannunsa ya sanya tare da bismillahi kafin ya ce." To ke ma sanya hannunki mu ci tare zai fi albarka. Na sanya hannuna a hankali na gutsiro na kai daidai bakinsa. Kallona ya yi na 'yan sakkoni kafin ya bud'e bakin na sanya masa towon ya fara taunawa a tsanake D'akin ya d'auki shiru na wani lokaci kafin na ji maganarsa yana fad'in." Ina mai sunan abokina lokaci bai ba ni damar ganinshi ba ina fatan baya tare da matsala ko?" Jim na yi Ina nazarin maganarsa can kuma na fahimci abinda yake nufi. Na ce." Lafiyarsa lau yana can wurin Baba Tabawa itace take d'awainiya dashi, alhamdulillahi babu wata matsala yanzu idan ka kammala cin abincin sai na kar'bo maka shi." Ya ce." Na gode muku sosai na kuma yaba da ko'karinku Allah Ya saka da alheri." 'Dan tausayi ya ba ni domin yanayin yadda ya yi maganar ya nuna mini cewa ya ji ciwon abinda Hauwa ta yi kuma abin ya dame shi abubuwa ne da yawa suka yi masa dabaibayi. Ta bakin Hajiya Saratun Hauwa ko a waje ya aurota bai kamata ta yi wannan sakarcin ba. Yaro d'anyar haihuwa ta ajiye saboda wani banzan dalili. Na ce." Ni kam banga abin godiya ba duk abinda na yi maka ai kaina na yi wa." Ya yi shiru bai ce komai ba yana dai ta kar'bar towon da nake bashi a baki har guda ya kusa k'arewa ya ce." Ban ga kin ci ba." "Na ce." Sai ka koshi my love dina." Ya sa dariya wadda ban yi tsammani ba yana fad'in." Na ga sai wani ji ki ke da ni Amina." Da d'an murmushi na ce." Tausayi ka ba ni." Ya gyad'a kansa da wani irin murmushi kwantacce a a tare dashi ya cinye malmalar towo daya na kara cire wani daga leda ba cigaba da bashi bai hana ni ba. Jefi jefi muna d'an ta'ba hira mafi rinjaye kan marigayiyar ne. Da kyar na daure na soko maganar da take ta damuna na ce." Akan lamarinka da Hauwa dukda ba ni da hurumi akai amma a shawarce don Allah kada ku bawa shaidan damar da zai shiga ya dagula muku zumunci domin na lura abinda ta aikata ya b'atawa mai sunan Mamana rai, ku yi hakuri a dubi zumunci da zuri'ar da ta ratsa a daidaita." Ya gyada kansa yana fad'in." Ki yi mana alkalanci Amina tsakaninki da Allah abinda Hauwa ta aikata ta duba mini? Ko kuwa ta duba zumuncin da kike magana akai. Da ba ta samu sararin zubar da cikin ba sai ta haihu ta tsallake abinda ta haifa saboda tsabar rashin Imani da rashi mutuncin ta gudu ta bar shi, kin ga fassarar ai ba ta shirya rayuwarsa a tare da ita ba tunda ai abincinsa yana jikinta idan ya mutu bata da asara saboda ta gane ni abinda na fi buk'ata kenan a yanzu taruwar iyali to bari ta yi amfani da wannan damar wurin ganin ta b'ata mini rai, kada ki so zuciya Amina lefin da na yi wa Hauwa ai ban cancanci wannan rashin mutuncin ba." Ya kare maganar cikin wani irin yanayi na damuwa da b'acin rai." Na yi shiru ina jajantawa. Babu shakka ko kaffara ba zan yi ba Hauwa tana can bauchi ne amma ruhi da zuciyarta suña nan dalilin abinda ta bari. Soyayyar d'a da uwa sai Allah. Ita kanta tana can Amma hankali da tunaninta na nan, ita a iya tunaninta hakan da ta yi shine zai sanyayyar mata da zuciya ta kuma k'untatawa wanda ya 'bata mata. Ko yana da lefi abinda ta aikata a yanzu ya shafe lefinsa nata za a yi ta hange kenan ta 'bata daya goma ba ta gyaru ba. Shiyasa masu karin magana suke fad'in." Duk abinda namiji ya yi ado ne mace idan tace za ta yi zai zame mata damuwa. A sanyaye na ce." Ba ta kyauta ba gaskiya ni ma raina ya b:aci sosai kuma na kira ta a waya na gaya mata ta yi kuskure domin har cewa na yi zan kawo mata yaron ta yi tsalle ta dire ta ce ko na zo na yi a banza, dalilin da ya sanya ni yanke shawarar kiran Dr kan ta zo ta ga yaron domin ta dora shi akan abinda ya dace. Alhamdulillahi kuma yau kwanaki tara yana cikin koshin lafiya domin daidai gwargwado Baba Tabawa na kula dashi." Na yi shiru kafin na sauke ajiyar zuciya na cigaba da fad'in." Don Allah ka yi hakuri na ari bakinta na ci mata albasa wallahi ta yi kuskure amma kada ka dubi hakan ka ture ka dubi dangantaka da kuma yaranku, sannan kaima ka gyara wasu abubuwan da kake yi Wanda bata so." Ya ce." Me na ke yi Amina, ni fa Samira na ce inaso ba Hauwa ba, zan gaya miki wata magana wadda ba ki santa ba har yau na kasa mantawa da matata ta fari Allah Ya jikanta domin soyayyar gaskiya ce a tsakaninmu. Ban ta'ba kallon Hauwa a madadin da za ta share mini kukan rashin Samira ba, kuma ban ta'ba yi mata kwatankwancin son da nake yi wa Samira ba. Idan na rabu da ita babu wata tangarda da zan samu tunda ni nasan bata da wani gurbi mai girma a zuciyata don haka wannan maganar mu barta kawai Amina." Duk yadda na so ganin na daure zuciyata daga barin jin zafin yadda yake yabon matarsa ta fari data mutu kasawa na yi sai na manta ma da maganar da muke tattaunwaa akai zuciyata ta fara tsalle tana tukuki tsabar zafin kishin da ya taso mini na ce." To ai wannan maganar da kake furtawa kamar gugar zana kake yi mana ni da ita Hauwan kawai ka fito fili ka gaya mini cewa Amina har yanzu ban samu madadin Samira ba, ai ta riga ta mutu kuma duk wanda ya rike ya tafi baya dawowa sai kawai ka ro'ki Allah Ya takaita maka kwana ka je ka risketa." Ya zuba mini idonsa yana kallona. Na juyar da kaina gefe tare da sake had'e fuskata. Shiru d'akin ya d'auka bai ba ni amsa ba. Na tsame hannuna daga cikin abincin da nake bashi na Yagi tissue paper domin goge hannuna. A hankali ya ce." Ban k'oshi ba." Zumbura baki na yi na yun'kura na tashi tsaye sai ya riko hannuna tare da janyo ni jikinshi ya mike k'afafunsa na zauna saman cinyarsa. D'auke kaina na yi domin ji na yi ma sam bana son kallonsa saboda takaici wannan a cin fuska ne a takaice." Ya ce." Amina kalleni." Kallonsa na yi babu fara'a. Ya rintse idonsa a tsanake ya ce." Kin san jini a jikin d'an adam ko?" Na yi shiru ban tanka ba. Ya d'an matseni a jikinshi yana sakin ajiyar zuciya cikin kunnena ya furta." A jinin jikinkina kike yawo. Ina can wata uwa duniya kina yi mini gizo Amina ina alkawarin soyayyar da ki ka ce za mu yi idan na dawo gida?" Da mamaki mai yawa a tare da ni na kura masa Ido. Ya sake matse ni a jikinsa yana me sanya fuskarsa tsakankanin wuyana wurin da yake bala'in so kenan a jikina. Jikina ya shika k'warai da aniya daga sannan na sallamawa sha'anin rijalu na sake yin lakwas ina ayyanawa a raina ko ni ce na fadi na mutu mutumin nan damuwarsa kalilan za ta kasance babu wani abu na jin dad'in rayuwarsa da zai fasa. Saukar hannunsa da na ji a kirjina ya sanya ni zabura. Na cire hannun da sauri sai ya had'e yatsunmu wuri d'aya yana bina da wani irin kallo wanda yake ko'karin kassara ni. Nan take tausayin kaina ya rufe ni. Yanzu nan ya gama jadadda irin alhini da kewar tsohuwar matarsa jiya kuma matar da ni da Hauwa muke ganin ya fifitata a kanmu ta fad'i ta mutu yau aka binneta a kabari wai har ya gama alhinin da jimamin yana bijiro da wani shagali da jin dad'in da bai wuce na 'yan sa'anni ba. Cike da kasala ya sake mayar da hannunsa saman kirjina yana tatta'bawa ban yi nawar sake cire hannunsa ba muka kurawa juna ido da kyar na furta." Ba ka ji wani iri ba? Lumsassun idanuwansa ya bude a dabarbarce ya ce."Na ji sun 'kara girma ko dan na yi kewarsu ne." Raina ya baci da jin amsar da yake ba ni. Wato ma bai fahimci akan abinda nake magana ba sai kawai na yi yun'kurin sauka daga cinyarsa ya kuwa ri'ke ni da kyau irin rikon da baki isa ki k'wace ba. Sosai na bude idona a kansa na ce." Gaskiya ni ka ba ni mamaki wallahi mutuwa fa aka yi maka mai zafi har alhinin ya bar gangar jikinka kenan." Ya gyada kansa yana fad'in." To ai ta riga ta rasu Amina, ni na isa na dawo da ita ne? Mutuwar nan kowa zai mutu to me zai sanya a tauyi rayuwa a bawa gangar jiki da ruhi abinda yake muradi kada ki manta ke fa ki ka yi mini alkawari idan na dawo za mu sha soyayya." Shiru na yi kawai Ina kallonsa gabad'aya kaina ya kulle mutumin ya gama goge mini duka haddar da na yi a kansa, ai na d'auka na gama karantar halayensa gabad'aya ashe da sauran abinda ban gama sani ba. Ya d'ora bakinshi saman lebunana ya sumbata kafin ya cire a hankali da wani irin yanayi ya ce." Abin nan yana d'auke hankali Amina zai mantar da ni abubuwa da yawa, bayan kiran sunan Allah a cikin kunci da damuwa sai wannan lamarin domin ni a wurina ma gaba yake da cin abinci, a wannan dare babu abinda zan fasa ai a haka duniyar ta ginu tun kafin mu zo cikinta ake mutuwa ake muka sunnah irin wadda za mu yi yanzu, mu ji dad'i mu gamsu kuma Ubangijin da ya ce mu yi hakan ya ba mu lada mai yawa." Na yi kasa da kaina dalili ba ni da wani karsashin da zan kalubanci maganarsa ta kowace siga ya fi ni gaskiya amma ai ana barin halas da kunya wallahi har yanzu matar nan idan ta fado mini a raina sai gabana ya fadi. Ya cika ni na sauka kasa Yana bude fulas din abinci jikinsa har d'an rawa yake yi ya ce." Abiñci zan baki kici ki koshi kamar yadda ni ma ki ka ciyar da ni daga nan kuma sai mu sake ciyar da juna wani abincin na mussaman ko ba haka ba ne?" Na ce." Gaskiya ba zan munafurceka ba a yanzu wallahi ba ni da wani karsashin da zan tari wannan lamari daka bijiro da shi. Ka yi hakuri tukkuna dukkunimu hankalinmu ya daidaita sai irin wannan nishadin ya biyo baya." Ya gyara yanayinsa yana fad'in." Ni ina da karsashina, sannan kuma a cikin nutsuwa da hankalina nake, menene a ciki ne haramun ne, saboda kawai an yi mutuwa sai a ajiye ibadar Allah ba na son jayayya Amina a bukace nake ke daga ganin yanayina ma kin san da hakan to me zai sanya ba za ki sama mini da farinciki ba. Kuka na fara yi tsakani da Allah ni ban san yadda zan yi na tari abinda yake so ba har na taimaka masa ya nishadantu irin yadda ya saba, har yanzu jikina babu wani kuzari ni gabad'aya ma duniyar ta fice mini daga raina. Don dole na dinga kar'bar towon da yake ba ni a bakina ina ci ina goge kwallar da take fitowa daga idona. Da kyar na ci rabin malmala na turje na daina kar'ba muka shiga toilet a tare wai zai yi mini wanka nan ma sai da muka yi kokawa kamar sababbin amare ina share hawayen takaici haka na yi wankan yana tattabe mini jiki muka fito. Towel ne kawai a jikina a daure na d'auki kayana zan sanya ya kwace. Cike da takaici na ce." Yaron zan je na kar'bo maka wurin Baba Tabawa fa." Yana ko'karin kashe fitilar gefan gadon ya ce." A yanzu dare ya yi da safe na gan shi sai mu gaisa sosai, ke dai mu kwanta kawai." Ya tura ni na yi kwanciyar ringingine dogare kafafuna na yi da zummar tashi ya raba nasa kafafun a kaina ya dabaibayeni. Abubuwa na tashin hankali da gigita lissafi ya fara yi mini jikinsa na wani irin rawa. Na dinga matse jikina ina ya'ki da gangar jikina da zuciyata akan kin 'karbar abinda yake mini, amma ban yi nasara ba, cikin kankanin lokaci ya fitar da ni daga hayyacina na kasa gane shin a duniya nake ko ni din ma na shilla barzahu ne ban sani ba. Kidima kam da ficewa daga hayyaci mun yi tunda abin ai ba sabo ba ne a wurinmu ya riga ya gama zame mana jiki sosai ya gurje ni ya gamsu na gamsu babu 'karya.. [12/21, 7:01 PM] bintaumarabbale: *119* Da asuba na sauka kasa bayan fitarsa sallah. Wanka na yi sosai da ruwan d'umi na gasa jikina. Anti Yagana duk tana zaune saman dadduma tana kallona na fito daga bandakin na kintsa jikina sannan na gabatar da sallah. Na shafa a nutse na juyo ina kallonta lokacin ta zame ta kwanta saman dadduma amma ba bacci take yi ba carbin da yake makale a hannunta take ja. A tsanake na gaisheta ba tare da tashi ba ta amsa mini tana kallona kafin ta sauke ajiyar zuciya ta furta." Gobe da wuri zan kama hanya Amina, jiya da daddare Babansu Fadila ya kira yake gaya mini mijinta ya kira shi wai bata da lafiya har da su karin ruwa." 'Yar dariya na yi kafin na ce." Anti Yagana ta kusa goya jika kenan." Harara ta mako mini tana tabe bakinta." Na ce." E, mana anti ai idan ki ka ji an fara da haka to k'aruwa ce." Ta girgiza kanta tana fad'in. " Yaran yanzu ba sa saurarawa 'yayan mutane daka an kai maka yarinya wata d'aya ka had'ata da lalura wasu fa ko shekara ba sa yi suke haihuwa." Da murmushi a saman fuskarta na ce." Hakane anti Yagana ai gwara matasan su yi auran da wuri ya fi alheri akan su dinga zinace-zinace kuma bari na gaya miki wani abu ba fa samarin ne kadai suke da wannan kawazucin ba har da 'yan matan wallahi dukkaninsu son auran suke yi." Ta yi shiru tana ta'be bakinta. Na ce." Kawai ki yi mata addu'ar Allah ya raba su lafiya, domin tunda ki ka ji an fara da haka to an gamu." Ta ce." To Allah Ya raba su lafiya." Na amsa da "Amin ko ke fa." Muka dan yi shiru na dan wani lokaci kafin ta ce." Wallahi ina tausayawa jama'ar da suke karkashin matar nan, da yawa akwai wad'anda suke d'aukar dawainiya mai yawa ta iyali iyaye da yan'uwa duka a karkashinta yau gashi ta fad'i ta mutu dole za su shiga wani yanayi wanda ba zai yi musu dadi ba. Su kadai nake tausayawa sosai dalili yaranku da suke ri'ke a hannunta ai jajensu kalilan ne tunda kuna raye sai ku cigaba da kula da yaranku Amma jama'ar da suke ci da sha a kasanta Allah ne kad'ai ya san su." "Hakane anti Yagana to ya za a yi ne? Lokacin ta ya yi cikinmu gabad'aya babu wanda ya isa ya dakatar da komawarta ga wanda ya halliceta hakika ya fi mu sonta shiyasa ya kira ta zuwa gare shi." Ta girgiza kanta tana fad'in." Ubangiji Allah Ya sa mu dace amma mutuwa kadai wa'azi idan har za mu hankalta." Haka muka kasance a d'akin muna tattauna batutuwa da yawa har garin ya yi haske sosai takwas saura yaran suka shigo su biyu Kamalu da Yusi. Gabad'aya muka zuba musu ido ni da ita. Yusi ya fyade sosai jikinsa a sanyaye ya zauna a gefena. Ban zan yi mamakin ganinshi da rashin kuzari ba. Ni nasan wacece Momi a wurinsa yadda ya shaku da ita ina tsammanin bai shaku da ni hakan ba, iya so da k'auna da kulawa ta nuna masa kwarai kowa ya sheda hakan, shiyasa duk halin da zai shiga ba zai zama abin mamaki ba. Muka gaisa da su cikin kulawa. Na dube shi a hankali na ce." Yusi ban yi maka gaisuwa ba ko." Ya kalle ni sai kuma ya d'an yi murmushi wanda daga ganinsa 'kago shi yayi domin babu wani nishadi a tare dashi. Na ce." Ka yi hakuri, lokacin ta ne ya yi kuma kowa ita yake jira babu wanda zai zauna a duniya, ai ita ta samu sheda da yabo ta kowane fanni don haka muna yi mata kyakykyawan zato in sha Allahu aljanna madaukakiya zata kasance yanzu gatan da za ku yi mata shine addu'a. Kansa a sunkuye har na gama maganata bai iya cewa komai ba sai yatsunsa da na gani ya sanya yana goge kwallar da take ko'karin zuba a kumatunsa. Na d'auke kaina jin zuciyata na nema ta karye na mayar da hankalina kan Anti Yagana da Kamalu ina jinsu suna tattauna batutuwan da suka shafi karatun da yake yi na neman da'awa. Ban ce komai ba ina dai sauraransu tana ta bashi shawarwari akan ya kula sosai ya san irin Malaman dai zai dinga bi domin neman fatawa dalili akwai Malaman da suke a dilmiye kuma su dilmiyar da mabiyansu idan suna kan a'kidarsu to sune masu gaskiya babu wanda zai kawo wata fatawa ko sahihan hadisan da suka inganta su aminta da hakan, babu wanda ya iya ya sani sai su. Babu zagi babu k'ago abinda babu shi a cikin al'kur'ani mai girma da hadisai a tabbatar dashi. Tana sake jadadda masa lallai ne ya kula ya san abinda zai fad'a mai inganci ne ya karanta cikin sahihan hadisan Annabi. Na ji dadin shawarwarin da take ba shi sosai domin ni kaina ni ma ina da burin na zaunar dashi domin na sake jan kunansa dalili ba na so ya yi zurfi akan a'kidar da yake kai a zo ana samu matsala da shi ko ana rigima da shi akan addini. ranar dai Hajja da Gwaggo ne kadai suka koma gidan mutuwar anti Yagana ta kwanta a d'aki tare da fad'in jikinta ciwo yake yi mata. Ni kaina ban ji sha'awar sake shiga gidan ba domin Ina gudun abinda zai sanya wata matsalar ta tashi wadda ba fata ake yi ba, tunda dai su 'yan uwanta rashinta bai dame su ba. Haka muka yi namu zaman makokin a gida duk wanda ya kamata yana shigowa ya yi mana gaisuwa ni da Hajja mussaman abokansa da matayensu. Ranar da aka yi sadakar uku Anti Yagana ta tafi kamar yadda ta fad'a maigidan ya sanya direba na mussaman ya d'auketa a mota ya kai ta har maiduguri. Washe garin ranar da ta tafi ta kira ni take sanar mini ta sauka lafiya kuma a daran ranar taje duba yarinyar abinda muke hasashene cikine da ita da gaske. Addu'a sosai na yi mata tare da fatan Allah Ya sauke lafiya. Washe garin ranar da akayi addu'a bakwai din Hajiya Maryam da safe Hajja ta had'a taro. Ban fito ba saboda ina ganin kamar abin bai shafe ni ba, Hajiya saratu da kanta ta shigo har d'aki ina kwance ta ce da ni na fito zaman har da ni za a yi. Ba kuma ta bari na ce komai ba ta juya ta fita. Babu yadda na iya haka na sanya hijabi na bi bayanta. Maigidan yana zaune kasan kafafunta Ita da Gwaggo da inna Uwani suna saman kujera. Ganinshi a 'kasa ni ma sai na zauna kusa da shi. Gaisuwa muka 'kara yi bayan wadda na yi musu d'azu. Sai na yi k'asa da kaina falon ya d'auki shiru kafin ta fara magana. Abinda dai nake hasashe ne zaman akan lamarinsa da Hauwa ne. A ganina kamar ba ni da hurumi amma ya zame mini tilas na zauna na saurara. Tunda nake da Hajja ban ta'ba ganin b'acin ranta mai tsanani ba irin yau. Yadda take yi masa fad'a har sai da ya d'an ba ni tausayi. Kansa a kasa cike da ladabi kuma bai katseta ba. Fadanta take yi tare da ko'karin nuna masa bai isa ya lalata zumuncin da yake tsakaninta da 'yar uwarta ba. Yadda na fahimta ita bata ji ciwon abinda Hauwa ta yi masa ba sai ciwon sakin da ya yi mata shine abinda ya fi daga mata hankali. Tana sake gaya masa cewa duk inda aka tara mata a gida dole sai an yi hakuri an kuma kawar da kai ba a yankewa mace mai juna biyu hukuncin saki. Na yi kasa'ke jikina duk a mace ashe da na gaya mata ni ma ya ta'ba sakina abinda za ta yi masa sai ya fi haka. Ha'kuri kawai yake bata. Hajiya Saratu ta sanya baki tana fad'in." Hajja a duba abinda Hauwa ta aikata a kuma yi wa kowa adalci kada ki tauyi wani daga ciki. Ban ce bashi da lefi ba yana dashi rashin hakuri da abinda ya aikata na datse igiyar aure. Amma zahiri fa Hauwa ta aikata abinda ya zama lallai a nuna mata kuskuranta, ban Fadi haka don ina 'kinta ba, yadda Tajo yake a wurina haka itama take a wurina, abinda nake ta jadadda muku anan shine Yarinyar nan ko daga waje a ka aurota wallahi duk b'acin rài bai kamaci ta aikata mana wannan wulakancin ba." Hajja idan maganata ta bata miki rai ki yi ha'kuri. Inna Uwani a sanyaye ta furta." Kina da gaskiya Saratu kuma ni dai da bakina ba zan ce Tajo ya mayar da Hauwa ba, ai dama ni na ce masa ya aureta ya kuma bi umarnina tunda hakan take ganin ya yi mata shikkenan sai ta zauna mu yi goyayya a gida." Gwaggo ta ce." A a Uwani ai ba za a yi haka ba, menene amfanin zaman da aka yi kenan ai domin a samu maslaha ne tabbas Hauwa ta yi kuskure amma a yi hakuri duka a kuma yi mata nasiha sosai sannan tunda akwai sauran igiyoyi babu wanda ya ji ya gani sai a mayar da auran ta dawo ta rungumi yaranta." Falon ya d'auki shiru kafin ya yi gyaran murya a nutse ya ce." In sha Allahu rabbi Hauwa zata dawo dakinta kamar yadda Baban Saude ya zame mini sheda a wattanin baya tun kafin haihuwarta na mayar da ita furta mata ne kawai ban yi ba. Amma Hauwa tana nan a matsayin matata har yanzu, ba ni da matsala da ita a yanzu smma abinda nake so anan shine inna Uwani ki gaya mata cewa ta ajiye wad'annan halayen nata da take yi mini anan ta zo mini da sababbi. Idan har zamu cigaba da tafiya da ita a haka ba ta canza ba to matsala tabbas ba zata mutu ba. Na yi hakuri na yafe mata sannan Ina neman afuwarku akan hukuncin da na yanke idan na 'bata muku." Inna Uwani ta fashe da kuka tana fad'in." Ni ai da cewa na yi ka kyaleta ka nemi wata kawai ka aura ita kuma sai ta auri eanda ya fi ka. Wato idan Allah ya suturta mutum jin dadin hakan sai ya fara ko'karin butulce masa amma shekarar ta nawa a kasa ba ta yi auren ba ta samu da albarkar zuri'a tana hofintar dasu. Na gode sosai Alhaji Tajuden Allah Ya yi maka albarka. Irin kukan da take yi sai da ya sanyayyar da jikinmu gabad'aya. Sai itama Hajjan ta fara share hawaye tana fad'in." Ni ba zan ga wannan masifar da jama'a suke kiranta ba in sha Allahu zumunci ba zai b'aci ba za a yi danasani ba. Allah Ya jikan Samira." Gabad'aya sai suka ba ni tausayi na ji cikowar kwalla a kwarmin idona na sanya hannu a dabarance na goge ina yi musu fatan alheri a raina. Tabbas na ji dadin ganin yadda lamarin ya zo da sauki lallai shaidan bai yi tasiri ba don da ya samu galaba da ba a tsayar da matsaya ba ana dambarwa gashi cikin ikon Allah an daidaita komai sshe ma tuntuni ya mayar da ita mu ne ba mu sani ba, tunda lokacin da Baban Saude ya zo ta gaya masa ya saketa a ranar ya yi mata alkawarin zata koma dakinta. Baban Saude ya taka muhimmiyar rawa sosai domin zumunci da abotarsu na tsakani da Allah ne da nuna kuskure tare da tsage gaskiya duk d'acinta. Da wani ne ganinsa millionaire wanda ya fi arziki da manya mutane sai ya ji shakka nuna masa kusuransa. Amma Baban Saude ba haka yake ba tun fil-azal mutum ne mara tsoro da shakka. Na yaba masa sosai kuma na ji dadin hakan har zuciyata. Gida ya watse kowa ya tafi don a washe garin ranar su Hajja suka tafi har da yaran gabad'aya sai ya zamana gidan daga ni sai Baba Tabawa da Sultan (Baba Amadu) shine muke kiransa da sunan. A daran ya shigo mini da yaran gabad'ayansu Khalil twins Minal sai suka zama baki. Suka rakube a kujera sun kasa sakin jiki kamar ba gidan ubansu ba, abin ya ta'ba mini zuciyata kwarai da gaske sai da na shiga d'akin na ci kukana na koshi. Na fito na tarar da Baba Tabawa tana ta hidima dasu kayansu tsaf an shigo dashi ta gyara musu d'aki tunda akwai d'akina a falon na mu. Na tambayi Khalil Baban nasu ya ce mini yana saman bai sauko ba. Kai tsaye can na nufa na same shi cikin jallabiya Bai jima da yin wanka ba. Kusa dashi na zauna da yake hankalina ba a jikina yake sosai ba ban fahimci dawa yake waya ba sai dai katse kiran da ya yi yana fad'in zai sake kira zuwa an jima shine abinda ya d'an ja hankalina domin sau tari yakan yi wayoyi muhimmai a gabana na sirri wanda ya kamata ya boye mini ma a gabana yi yake yi. Na tsargu sosai da abinda ya yi a yanzu na dinga kallonsa domin karantar yanayinsa babu yabo babu fallasa a tare da shi. Na ce." Mai zai hana Mairo mai'aikin nan da take hidima da yaran nan ta dawo nan . Naga sun saba da ita sosai za ta taimakawa Baba Tabawa kada abin ya yi mata yawa." Ya gyad'a kansa yana fadin." Yadda ki ka ce a yi hakan za a yi, na kuwa ji dadin shawararki." Na ce." Sai magana ta biyu yaushe Hauwa za ta dawo?" A tak'aice ya ce." Wannan kuma ita za ki tambayata hajiya." Na yi shiru Ina kallonsa da mamaki a tare da ni na ce." Ai ka ce ka yafe mata ya kamata ku tattauna a tsakaninku ko?" Ya gyad'a kansa yana fad'in." Na yafe mata mana, amma tsakani da Allah ni zan dinga binbininta, kofa a bud'e take haka zalika ma dakinta yana nan ta dawo duk lokacin da ta shirya bai dame ni ba." Na ce." Wannan ba magana ba ce Allah Ya taimaka, wata'kila ai bata ga fuska a wurinka ba." Ya 'bata rai yana fad'in." Ki kyale ni da wannan maganar Amina kada ki bata mini rai ko abin ya shafe ki ne?" Na yi shiru ina kallonsa kawai kaina na sarawa. Zan kira Hauwan na ji ta bakinta. Ya ce." Ya kike ganin za a yi da yaran nan Salim da Adamu. Za ku ri'ke su tsakani da Allah ko kuwa na bari dangin Mamansu su d'auka tunda ita Nusaiba tana d'akin mijinta." Da tsananin takaici da b'acin rai na furta." Wace irin magana ce wannan don girman Allah, ka dinga tauna harshe kafin ka gaya mini magana, ni fa mutum ce mai zuciya a kirji, kada na gaya maka ba'kar magana ka ji haushi." Ya yi murmushi irin na saman lebe kafin ya ce." To ai na zuba Ido ne naga za ki yi mini magana akansu na ji baki ce komai ba bayan kin san amana suke a hannuna, me yasa zan kawo muku su ba tare da na nemi amincewarku ba, kin yi magana akan mai dauwaniya da yaranku sannan kin yi magana akan Hauwa shiyasa na ce to bari na tunasar da ke" Na danne abinda nake ji na ce." Amma dai kasan idan ka kawo su gidan nan zan kula da su ko? Ni ma ai ta ri'ke mini nawa, kai ko bata yi mini alheri ba, ro'kon maraya sai wanda Allah Ya so wallahi su zo su zauna zan yi iyakacin bakin kokarina." Ya sauke ajiyar zuciya Yana fad'in." Alhamdulillahi, ita Hauwan fa, tunda ai bakinku daya kina magana da yawunta." Ban biye masa ba tunda na fahimci neman magana yake yi na ce." In sha Allahu rabbi babu matsala itama." Sai ya saki fuskarsa yana fad'in." To na gode sosai, mu taru cikin ladan da ni daku gabad'aya mu tashi a gefan manzon rahama, domin fadinsa ne duk wanda ya rike maraya ya kula dashi sosai to a ranar 'kiyama za su tashi tare. [12/21, 7:01 PM] bintaumarabbale: 120 Na so na share sha'aninsa da Hauwa amma na kasa hakurin tsame kaina. Kad'aici ne ya yi mini yawa da tunani da zullumi. Ban gazgata maganar nan da ake ta yawaita fad'a ba wato kishiya abokiyar zama ce sai yanzu. Ko babu komai bibibiyu tana da dadi idan baba Tabawa ta shiga kicin babu motsin yaran suna makaranta ita kuma mairon taje garinsu tun bayan rasuwar Hajiya Maryam din bata dawo ba amma dai ni da kaina na yi waya da ita tace mini in sha Allahu tana kan hanya. Gani ni ba ma'abociyar kallon ba wasu lukutan nakan kira Sahura a waya mu yi hira ko anti Yagana amma dai duk da haka mutum ai rahama ne. Wani sa'in na kan bita kicin din na sanya mata hannu mu yi aikin tare muna hira irin ta yau da gobe hum rayuwa kenan. Ajiyar zuciya na sauke na d'auki wayata dake ajiye a kusa da ni na lalubi lambarta. Bugu d'aya ta yi ta d'aga gaisawa muka yi cikin kulawa kafin na daure na yi mata tambayar da take damuna a kasan raina. Irin murmushin nan na takaici ta yi. Duk da ba ni ganinta nasan a cikin kunci da takaici take. a dusashe babu wani kuzari ta ce." Amina ban ga fuska ba har yanzu, na yi lefi na kar'bi laifina kuma na bawa duk wanda ya cancanta hakuri amma mutumin nan na kira shi yafi sau ashirin bai daga mini waya ba. Yanzu da za ki duba duka wayoyinsa za ki ga text messages dina na ban ha'kuri da kar'bar kuskure amma bai ce komai ba. Ya zan yi, ina so kafin ace na dawo mun d'an sasanta junanmu duka sai mu yafi juna tunda shi ma yana da lefi har ta'aziyar matarsa na yi masa amma hakan duk bai sanya ya saurareni ba." Na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce." Ke ma dai da wata magana kike Hauwa, ai tunda iyaye sun shiga ciki kuma da bakinsa ya ce ya mayar dake tuntuni tun kafin ma ki haihu a ganina kawai ki dawo ki rungumi jaririn yaron nan da bai fi kwanaki talatin a duniya ba. Idan har sai kin tsaya kin ji ta bakinsa ko sai ya kula ki wallahi yana gane hakan zai fara gwara kanki a garu tunda dama shi kin san rarrashi da kwantar dakai baya yi masa. A shawarce kawai ki dawo idan ya so koma me zai faru a tsakaninku ki kawar da kanki har ya gama kullacinki ya sauko nasan dai zai yi ta takalarki zuwa yanzu ai ya ci ace kin gama gane halayensa." A sanyaye ta furta." Shawarar da muka yanke kenan ni da Inna, in sha Allahu cikin satin nan zan dawo, Amina na gode sosai da kulawa." Cikin jin dad'i na ce babu komai Hauwa Allah Ya kiyaye faruwar hakan anan gaba. Ta amsa da Amin." Kafin mu yi sallama. Ban gaya masa yadda muka yi da ita ba kawai na ja bakina na yi shiru sai dai Ina ta zuba Ido naga dawowar su Salim gidan kamar yadda ya gaya mini amma yau kusan kwanaki goma kenan da maganar ba su dawo ba. Da daddare bayan ya gama cin abinci a tsanake na fara tambayarsa. Sai da ya kashingida tukkuna ya ba ni amsa da ce wa. Sun sake yanke shawara da 'yan uwan Momi din akan cewa Nabila za ta dawo gidan ta zauna domin ta cigaba da kula da su tunda dama bata da aure sannan kusan ta fi kowa Ido da shakuwa da Momin, ta san abubuwa da yawa da suka shafeta mussaman harkokinta na yau da gobe, muhimi dai manyan kadarorinta an kasafcesu kamar yadda addiini ya tana da an raba gado nasa wanda ya gada a matsayin mijinta ya barwa yaran gabakiya dukiyarsu tana hannunsa gabad'aya shagunanta na nan ne aka cigaba da hada-hada kamar yadda yaran suka bukaci da a yi musu hakan. Dalilin dawowar Nabila gidan kenan domin ta taimakawa yaran wurin kula da harkokin kasuwancin tunda suna so su dora daga inda Maman nasu ta tsaya ne." Zuciyata daya na ji dad'in hakan a raina, domin a ganina dawowar Nabila kusa da su za su ji dad'i koyaushe idan sun juya za su ganta a makwafin mahafiyarsu tunda jini ai ya fi karfin wasa. Ko nan din suka dawo ba za su sake sosai ba tunda ga abubuwan da suka faru a baya amma idan suna ganinta a koyaushe a gidan za su ji dad'i. Addu'a sosai na yi wa yaran tare da yi musu fatan alheri akan abinda suka niyyata Ubangiji Allah Ya yi mana jagoranci bakidaya ita kuma Allah Ya yi mata gafara. Ranar lahadi Hauwa ta sauka bayan la'asar. Na yi farinciki sosai da ganinta domin ko waya ba ta gaya mini ba sai kawai ganin Masa'udu muka yi da akwati lokacin ni da Mairo muna falo a zaune muna kallo baba Tabawa na kicin domin shirin dora sanwar dare yaran kuma na tahafiz. Masa'udu ya dire akwati bayan ya gaishe ni yana fad'in." Hajiya k'arama ce ta dawo." Ya juya ya fita da sauri ya sake shigo da wata akwatin k'arama. Na dinga dariya ina fad'in." Hauwa wace irin bazata ce wannan?" Ta nemi kujera ta zauna tana ce wa." Dama ai na gaya miki cikin satin nan." Na gyada kaina ina cewa." To me yasa ba ki yi mini waya ba." Murmushi kawai ta yi tana duban Mairo na ce." mai aikin Momi ce ba ki gane ta ba itace uwar dakinsu Khalil." Mairo na dariya ta furta." A a Hajiya ina ni uban masu gida ne fa kuma uban d'akina. Ta d'an risina tana gaishe da Hauwa cike da ko'karin bata girma. Itama ta amsa da sakewa da murmushi a saman fuskarta. Baba Tabawa ta fito daga kicin bayanta goye da Sultan yana dan kusurkusur. Ganin mu tare da Hauwa a zaune sai ta d'an yi saroro kafin kuma ta saki fuskarta da azama ta k'araso tana ce wa." Hajiya Hauwa sannu da zuwa." Ta amsa da "Yawwa Baba Tabawa ina yininmu ya kokari?" Baba Tabawa ta amsa da "Lafiya lau alhmdullhi ya aka baro su inna Uwani." Ta ce." Duk suna nan lafiya suna gaisheku." Baba Tabawa ta kwanto yaron tana fad'in." Kar'be shi ya ji duminki." Ba tace komai ba ta sanya hannu ta kar'bi yaron ta rugume shi a kirjinta. Baba Tabawa da sauri ta juya ta nufi dakinta minti uku ta dawo da madararsa a dame a cikin fida ta mika mata lokacin ya sanya yatsunsa a baki yana tsotsa. Ta kar'ba a dan sanyaye kafin ta yun'kura ta tashi da yaron ta nufi dakinta. Na dubi Mairo da ta kurawa tibi ido, tun zuwanta na fahimci ma'abociyar son kallo ce kuma American film duk da ba jin abinda suke fad'a take yi ba amma tana ganewa har idan na tambayeta tana fahimta kuwa tiryan tiryan ta ba ni labari. Na ce." Mairo shigar mata da akwatin nan dakinta. Ta tashi da sauri ta yi yadda na umarcta. Bayan ta fito sai na tashi na shiga d'akin na sameta zaune a gefan gado rungume da yaron ta gama bashi madarar ya koma bacci idonta ya nuna alamun kuka. Ta zuba mini ido har na zo na zauna kusa da ita bata janye idonta daga kaina ba. A nutse na ce" Ya yi bacci kenan?" Ta gyad'a kanta tana fad'in." Amina sai dai Allah Ya sakawa yaron nan amma na zalince shi, zai rayu ba tare da ya d'and'ana nonon uwarsa ba, kin san dama ba ni da wani wadataccen ruwan nono wallahi ya fi sati biyu da d'aukewa. Dole a cigaba da ciyar da shi da madara kafin ya kai matakin cin abinci, idan na dube shi sai kunyarsa ta kama ni, ina fargabar ya girma a tashi maganar nan da duk abinda ya faru Ina ganin zai yi mini wani irin kallo wata'kila ba zai yi imanina ba kamar sauran." Da sauri na ce." Haba dai ki daina fad'in haka Hauwa, dama haka Allah Ya shirya kuma ai d'a bai isa ya biya iyayensa hakkin dawaniya ba, ki daina fad'in bai zai yi imaninki ba, ai tunda ki ka sha wannan gwagwarmayar kafin zuwansa duniya wata'kila ma shine wanda za a huta dashi. Ke dai kawai ki cigaba da yi musu addu'a sannan kuma ki kiyaye faruwar makamanciyar wannan matsalar anan gaba. A Dan sanyaye ta ce." In sha Allahu rabbi babu abinda zai sake faruwa Amina, zan kiyaye sosai ba ni kuma da bakin da zan yi miki godiya." A nutse na dafa kafadarta na ce." Har abada babu godiya a tsakaninmu Hauwa duk abinda na yi miki kamar kaina na yi wa." Na d'an jima a d'akin muna tattauna batutuwa mabambamta kafin na fito lokacin yaran sun dawo daga makaranta ina jin karadinsu a dakinsu. Kai tsaye can na nufa na same su tare da Mairo kamar koyaushe tana kiciniyar basu kayan da za su sanya bayan sun cire unform din. Na ce." Khalil Mama ta dawo tana d'aki maza ku je ku gaisa." Hassana ta buga tsalle tana fad'in." Don Allah da gaske ne, dama Babanmu ya ce za ta dawo tana Makka haka ya ce mana ko Usai." Ta yi maganar tana duban abokiyar tagwaitakartata. Na yi tsam Ina nazarin murnar da suka yi a zaman da suke yi momin bata rasu ba kenan ubansu ya ce musu tana makka jira suke yi ta dawo shiyasa kenan na ga sun saki jikinsu a kwanakin nan ba kamar sanda suka dawo gidan ba. Khalil din dai bai ce komai ba tunda ya fi su wayo shi din ma ba gama sanin mutuwa ya yi ba amma ga dukkanin alamu bai yarda da maganar da baban nasu ya yi ba, don ban ga alamun murna a fuskarsa ba. Ya fita daga d'akin yana gyara maballin rigar jikinshi. Bayansa na bi kai tsaye naga ya nufi d'akin uwar. Na sauke ajiyar zuciya cikin raina na furta Allah Ya sassauta mana bak'idaya. Tare suka fito da Mairo wai sai sun tafi can gidan Momin tunda ta dawo. Na dube ta ina tambayar kukan mai Minal take yi ta gaya mini yadda suka yi a d'aki bayan fitata. Hassana ta yi hanyar fita tana janyo hannun Minal din suka fadi a bakin kofa domin ita Minal jikin ne amma babu kwari. Tsawar dana bugawa yarinyar ta yi daidai da shigowarsa. Ya gan su a bakin kofa durshen Minal na ihu! Ya cicibeta ta tashi ya rike hannunta yana tambayata. Usai da take tsaye kusa da Mairo itace ta bashi amsa cikin yanayin maganarta tunda har yanzu hausar ba ta zauna a bakinta daidai ba tana gwaranci Hassana ta fi ta iya magana. Ya 'bata fuska yana dan hararata ya ce." Ke kuma maimakon ki rarrasheta sai tsawa Amina, yaushe za su sake dake kina yi musu irin wannan hantarar." Na ce." Yaushe na hantaresu?" Ya ce." Karya na yi kenan, abinda gashi idanuna ya nuna mini." Na yi shiru ban sake magana ba. Fitowar Hauwa daga d'akin kafad'arta sa'be da Sultan ta d'auke hankalinmu. Khalil ya biyo bayanta da fida a hannunsa. Da mamaki yake kallonta amma bai ce komai ba. Ga dukkanin alamu dawowarta shi din ma ta yi masa bazata. Ta mikawa Mairo yaron tana fad'in." Ki goya shi yamma ta yi. Da sauri kuwa ta kar'be shi da towel din ta fara ko'karin sa'ba shi a baya. Ta hillaci yaran suka shige d'aki tana fad'in." Za ta basu tatsuniyar bari wa biba, da ta duduwa mai kan 'bari. Jin haka ya sanya Usai sakin dariya tana tsalle suka bi ta a baya har da Khalil din. Amma ban da Minal domin ita kam tana ta k'ananun kuka. Ciccibarta ya yi ya daukota a hannu ya zo ya dire mana ita a gabanmu yana fad'in." Wacece uwarta a cikinku?" Babu wadda ta bashi amsa. Ya dubi Hauwa yana fad'in." Wannan idan ba ki sani ba bari na gaya mini rigimammiya ce da kafiya da taurin kai. Momi Allah Ya gafarta mata itace kawai take iyawa da ita a duk lokacin da ta fara irin wannan koke-koken. Ba ki san wannan ba tunda ba ta rayu a hannunki ba. Abinda nake so na gaya miki akanta shine kada ki ce za ki dakar mini yarinya domin ba mu yi mata rainon duka ba. Minal idan ba a ta'ba ta ba tana da hakuri kwarai da saurin sabo, muddin kuwa ta fara wannan kukan nata babu shakka akwai dalili. Za mu samu matsala gagarima na ji labarin wataran kin kai hannunki jikinta. Kin saba dukan Khalil ki kwana kalau ban da wannan idan ki ka yi ranki zai 'baci mutuka." Ta yi kasa'ke tana kallonsa har ya gama kafin ta ce." To yanzu ni ai ban san abinda aka yi mata ba. Idan har yaro ba zai yi kuskure a hukunta shi ba ai an d'auki ga'barar lalatashi ko ba haka ba ne Amina." Na ce." Hakane kuwa, ina ga kamar wannan ba soyayya ba ce Allah Ya ja zamaninka." Ya gyad'a kansa yana cewa." Ai na fad'a muku abinda yake raina ban munafurceku ba, ba ni son a ci zalin yarana amana ce a hannunku." Shiru muka yi muna ta kallonsa har ya gama maganarsa ba mu ce komai ba. Sai ya sunkuya ya sunkuci yarinyar ya sanyata a k'ugunsa kamar wata 'yar yaye sai sakin ajiyar zuciya take yi. Hauwa ta ce." Wai don Allah me aka yi mata ne?" Na gaya mata duk yadda aka yi. Sai ta duba shi yana nufi hanyar samansa ta ce." Kenan ba ta san ni na haifeta ba ko?" Ya juyo yana cewa." Ko ta sani to ta manta yanzu tunda babu sha'kuwa idan kin manta ai ni manta kyarar da hantarar da ki ka dinga yi musu ba a duk lokacin da suka kawo muku ziyara. Lefin wata ya shafe su, me yasa za su tuna dake." Ta gyad'a kanta ba sake cewa da shi komai ba. Muna kallonsa har ya haura saman da yarinyar a 'kugunsa. Ta zauna saman kujera kusa da ni jikinta duk a sanyaye.. Na ce." Kada ki wani damu neman na yi yake yi duk abinda zai yi ki kyale shi kada ki biye masa idan ya ga baki damu ba zai bari." Ta dube ni da dan murmushi tana fad'in." Ina ganin fa don yarinyar nan takwararki ce yake fifitata a cikin yaransa. Ni dai fahimtar da na yi kenan Amina." Na zuba mata Ido Ina nazarin maganarta ni duk irin abinda yake yi akan yaransa ban ta'ba tunanin yana fifita Minal saboda tana da sunana ba. Na fi tunanin soyayya ce kawai irin ta iyaye ai dole a cikin yara wani ya fi shiga cikin rai idan nuna fifiko da k'auna ne ai Khalil zai nunawa ko mai sunan Amininsa Amadu(Sultan) sai na gaza ce mata komai na dinga kallonta. Murmushi ta yi irin na saman leben nan tana fadin." Kin cancanci irin wannan soyayyar Amina domin ke din mutum ce har da rabi kuma da gaskiyarsa kina da hakuri da kawaici saurin sabo, Amma duk ranar da aka ta'bo ki to za a sha daga. Mafiakasari kuma haka duk mai d'auke da suna Amina yake. Dariya maganarta ta ba ni na ce." Lallai Hauwa abinda na za ki fada kenan to na gode shine abinda zan ce." Ta tashi tana fad'in." Bari na bi bayansa saman." Ban ce mata komai na bita da kallo mai tafe da murmushi. Lokacin sallar magriba ne ya tashe ni daga falon zuciyata cike da nazarin maganar Hauwa akan Minal. *** To alhamdulillahi cikin ikon Allah kwana daya da dawowar Hauwa na fahimci sun samu daidaito a tsakaninsu, na ji dad'in hakan sosai kuma na jinjina mata domin ta yi kokari kwarai da aniya wurin ganin ta sassauto da zuciyarsa a lokaci k'ankani ba tare da an jima suna kai ruwa rana ba. Sannu a hankali muka cigaba da gudanar da rayuwarmu cikin rufin asiri da kulawa. Mun ajiye wani abu wai shi kishi muna mutuntuna junanmu tare da bawa juna shawarwari masu kyau. Maganar maigidan kuwa duka mun fahimci halayensa dai tunda namiji ne wahainiya ne mai rikida a koyaushe wata'kila akwai wasu darrusan da bai gama fahimtar da mu ba. Yana dai ko'karin bawa kowacce hakkinta kwana bibbiyu muke yi abinda na sani shine a cikin kwanakina biyun nan yana bani hakkina na aure don bai ta'ba tsallake rana daya ba sai ya neme ni. To Ina kyautata zaton ta bangaran Hauwan ma hakane tunda gaskiya ban ta'ba ganin wani canji ko jin haushi a ranar girkinta ba. Yara kuma muna yin daidai gwargwado da kiyayewa don ma rabin zaman nasu a skull ne sai ranakun hutu tukkuna muke yini tare Kuma sun fi sakin jiki da Mairo. Minal ce mai nacin zuwa wurina tunda dama tun fil'azal mun saba kuma ba ta da rashin son mutane irin na su Hassana. Na kan tambaye shi su Salim a wasu lukutan ya ba ni amsa suna lafiya. Bai ta'ba cewa mu shiga mu duba su ba, kuma bai ta'ba turo mana su ba. Sai idan Khalil ya je can gidan nasu a wasu lukutan Adam yake ba shi sakon gaisuwa zuwa gare mu. Ya dai gaya mini idan zai koma legos tare da Salim za su tafi zai d'ora shi akan wasu harkokin nasa. Ya nuna masa yadda zai kafa kansa nan gaba. Na yi addu'a sosai da fatan alheri. *** Watarana ina duba status kamar almara naga nambar Nabila wadda sama da shekara da wattani ta yi blocking dina tun lokacin rigimarsu da Hauwa dama kuma can jefe jefi nake ganinta to tun daga sannan ban kara ganinta ba sai yau tunda dama ni already Ina da lambarta ban goge ba. Kamar wadda aka tankwabewa hannu na shiga status din ina dubawa. Tsala-tsala hotonanta ne ta yi kyau kwarai babu karya tunda suna da gadon haske da kuma boko da gayu sai da ita Nabila har ta fi Momi wayewa irin ta duniyanci kar take. Na duba kasan wani status din da ta yi ta rubuta (Mrs Tajo Dambatta to be in sha Allahu 💕) da manyan harafi. Gabana ya yi wata iriyar bugawa mai tsananin gaske. Hannuna na rawa na shiga next status din da ya zama na karshe shi kuma ta rubuta (Mun zama kujera. Ni kuma warki ce daidai 'kugun kowane shege. Zan shigo za mu zuba shege ka fasa dan halak sai yanka") [12/26, 7:56 PM] bintaumarabbale: 121 "Ni warki ce daidai da kugun kowane shege." Wannan magana ta Nabila itace ta fi tsaya mini a raina. Na kuma zauna a tsanake na fara yin nazari akanta. Idan har maigidan nan zai auri Nabila a yadda na d'auki duniya a yanzu ba komai ba ce ai a ganina ba abin damuwa ba ne. Matsalar anan shine yadda salon yake nema ya canza. Ni da Hauwa a yanzu babu wata 'baraka a tsakaninmu mun zamewa juna 'yan uwa domin duk wani kishi da jin haushin juna mun ajiye shi a gefe. Mun had'e kan yaranmu gabad'aya muna taimakon juna. Idan da gaske ne zai auri Nabila alwashi da irin shirin da take yi akan shigowarta zai haifar da d'a mai ido kuwa. Ya zama dole a wannan ga'bar na taunawa mutumin nan tsakuwa ba don komai ba sai don dakushe shi daga barin irin ibtila'in da yake ko'karin d'auko mana. Idan har babu mugun nufi ko mugunta a sha'anin Nabila babu wata damuwa fa ni dai a bangarena ya aureta ta maye gurbin 'yar uwarta. Amma wannan rubuce-rubucen nata ya sanya ni a cikin shakku tare da 'kyamatar lamarin. Idan har aure yake so ya kara ba zamu hana shi ba amma fa banda Nabila wannan shine magana ta gaskiya. Ko Hauwa ban gayawa ba na ja bakina na yi shiru har sai dai girki ya dawo hannuna tukkuna. Duk wasu sabgogi da nake masa ban fasa ba. Kwalliya ma na yi sosai irin wadda na jima ban yi masa irinta ba. Ya kuwa dinga washe baki yana nan nan da ni. Har da su zolaya wai na yi kama da sauraniya. Na ce masa ai itace amma ta birnin zuciyarka. Ya kamo ni ya makale a jikinsa yana abinda ya saba. Na tashi ina gyara daurin dankwalina da ya tuje ya sake cakumoni Yana fad'in." Benu ba kya tsufa sai dai ki yi girgiza ki dawo sabuwa dal. Da gaske fa kamar amarya." Maganarsa ta yi daidai akan ga'ba. Na gyada kaina da d'an murmushi ina dubansa gabad'aya duk ya burkice a bukace yake alamu duka sun nuna. Na ce." Haka ake amarya Allah Ya taimaka amaryarka dai tana nan tafe ko ka dauka ban samu labari ba." Ya yi kasa'ke yana kallona kafin ya ce." Ban gane abinda kike nufi ba. Babu yabo babu fallasa na ce." Nabila fa." Ya tsira mini ido yana kallo. Na yi murmushin takaici a hankali na ce." An kusa daura auran ne?" Tsaki ya ja kafin ya ce." Ba na son shirme ke ba kya son zaman lafiya Amina." Na furta." Ka fito fili ga gaya mini gaskiya domin rufewar ba ta da amfani. Ya ce." Akan me zan boye muku neman aure Amina, ke a Ina ki ka samu labarin ina zawarcin Nabila?" Kai tsaye na ce." A wurinta mana!" Ya maimaita maganata "A wurinta?" Da sigar mamaki a tare dashi." Na ce." Wallahi kam kasan ina da lambarta jiya naga ta yi status da hotonta ta rubuta matar Tajo mai zuwa har tana had'awa da zaginmu ni da Hauwa." Sosai ya shiga mamaki kafin ya ce." Ni kam babu soyayya a tsakanina da ita. Ai ba na tsammanin zan sake auran bazawara Amina kishina ba zai barni ba balle ita da bata da alkibula ta yi nan ta yi can da sunan neman kudi gari gari. Matata da ta rasu Hajiya Maryam ita daban take gaskiya kuma ita din rainon abokina ne shiyasa ban yi kokwanto wurin auranta ba. Na ce." Wannan cin fuska ne a fakaice fa menene illar zawarawa ai ba duka aka taru aka zama daya ba. Ni kenan kawai don ba yadda za ka yi dani ne ko?" "Ban fad'a ba, tunda ki ka ga Ina zaune dake ai kina da matsayi a zuciyata don haka mu rufe wannan maganar ba na neman tashin hankali." Na ce." Magana kam ba za ta rufu ba, don gaskiya ba zan yadda da cewa babu ala'ka ta soyayya a tsakaninka da Nabila ba, gaskiya kawai za ka gaya mini." Ya 'bata rai ainun yana fad'in." Makaryaci ne ni kenan, Amina kin yi bala'in raina ni wallahi ke yanzu ba ki ji kunya ba dattijo Irina da furfura biyabiya a fuskata ki dinga titsiyeni har ki na cewa karya nake yi. Ko ban haife ki ba na kusa da na yi aure da wuri." Na ce.'' Yaushe ka ji na kira ka da makaryaci ni ban fad'a ba, kawai na ce ka gaya mana gaskiya kada ka boye domin hakan ba zai haifar da d'a mai ido ba." Ya ce." To iya gaskiyar kenan na gaya miki babu komai a tsakanina da yarinyar nan ko aure zan yi ni budurwa zan aure matashiya mai jini a jika." Shiru na yi ban ce komai ba amma zahiri maganar ta ta'ba mini zuciya mu kenan mun tsufa ba mu da jini a jika komai ya dakushe. Ai sharrin rijalu kenan. Cikin takaici na ce." Ai gasu nan masu jini a jikan suna yawo a gari sai dai can wurin da kuke kwakwa bai zama lallai ku same shi a rufe ba. Domin su da kansu suke bud'e kayansu. Ko kuma gayu su bud'e muku hanya ku kuma dattijai makwadaita ku kwaso kuna rawar jiki." Ya ce." Ai muna da nagartattu a dambatta sai na sanya Hajja ta bincika mini mara waye wa." Na ce." To Allah Ya ba da sa'a." Daga haka na yun'kura domin tashi na fita.. sai ta riko hannuna na koma na zauna d'abas! Takaicin hakan ya sanya ni rushewa da kuka. Ya tallafo ni da saurin gaske yana rawar jiki. Na daddage da k'arfi na fizge. Na kama hanya na fice daga d'akin ina goge fuskata. Kwanakin girkina suka fita muna ta rigima domin zahirin gaskiya raina ya baci da maganganun da ya furta mini. Yanzu a yadda yake sai iya auro 'yar sha shida a ganina mai zai tsinta a jikinta. Wannan wulakanci ne kawai. Hauwa ta sake kar'bar girki ta fita na kar'ba duka raina babu dadi kuma ban gaya mata halin da ake ciki ba saboda ba na so na hada ta da mijinta duk haukan kishina ta fi ni. Nasan rigima ce za ta tashi idan ta ji cewar neman auran Nabila duk da babu tabbas amma ai har yanzu ba ta daina yin status tana dorawa da sunanta da nasa a hade ba. Ya dinga bina yana rarrashi na bashi kaina domin samun hadin kaina shine zai karawa lamarin armashi irin wannan sabgar idan ana jin haushin juna bata dadi. Da wannan hanyar kawai nake gasa shi kuma nan da nan yake saduda ya nuna rauni da damuwa. Ni kaina nasan na tsaye masa a zuciya domin bai yi fiye yin annashuwa ba muddin muka yi fad'a fara'arsa k'alilan ce. Amma idan muna shiri mussaman ranar girkina Yana kasancewa cikin nishadi da walwala. Mun fi sati biyu a haka ga dai Hauwa nan ai yana kwana da ita idan hakane ta d'auke masa duk fitinarsa mana. Kana amfanuwa da mace kana fito da sabbabin iskanci kala-kala. Ya rintsa ni a d'akina misalin sha biyu da wani abu. Girkina ne amma tunda na kai masa abinci na sauko ban kara hawa ba. Da rantsuwarsa da komai yake gaya mini babu maganar auran Nabila ya miko mini wayoyinsa yana fad'in." Ki bincike wayata tsaf idan kin ga lambarta ki hukuta ni." Na ta'be bakina ban ce komai ba, kuma ban kar'bi wayar ba. Ya nanike ni sosai yana nuna mini inda lambobin mutane suke yana fad'in." Kin gani ko ki duba ki ga ni, ni me zan yi da wannan yarinyar ne Amina." Na gyada kaina a tsanake na ce." Ita ai tana da abinda za ta yi da kai, ko baka sonta na tabbatar da cewa ita tana sonka." Na d'auki wayata dake saman dirowar gefan gado na lalabi status dinta na yau ina nuna masa hotonta wanda ta cakare ta yi gayu kwarai da gaske kasan hoton ta rubuta (Amaryar Tajuden I. Dambatta) Ya jima yana kallon hoton wayar a hannuna kafin ya ce." Wannan bata ta da tunani Amina Allah Ya kyauta amma zan ja mata kunne idan ma tana yin hakane domin ta hargitsa mini iyali." Ban ce komai ba na kashe wayar tare da ajiyeta Ina kallonsa gabad'aya yanayinsa ya canza ya yi zuru-zuru kamar b'arawo a masallaci. Dariyar zucci na yi kawai na kawar da kaina. Ya cigaba da binbini da kalamai sai kace maroki ina jinsa ban ce komai ba. Ya d'ora hannunsa saman cinyata tare da sake matsowa. Na sauke ajiyar zuciya kamshin jikinsa ya sake saukar mini da kasala. Ya d'an tura ni na kwanta saman gado sai ya hayo sosai ya yi mini rumfa tare da hade yatsunmu wuri d'aya ya d'ora bakinsa a saitin wuyana ya saki wani goron numfashi kamar irin na macen da take dabda haihuwa. Wannan ya wuce da wasu wattani Nabila dai ba ta daina d'ora hotonta a status tana habaice-habaice ba. Ni Kuma kamar wadda ta yi wa asiri idan na ga status din nata bana iya d'auke kaina sai na shiga na gani. Tun abinda take yi yana ba ni dariya har ya dawo ba ni mamaki. Ta dage dai wai dole sai ta ba ni haushi tun kafin ta shigo gidan idan da kaddarar kakan kenan domin idan duk jikina kunnene ba zan yarda da maganganunsa ba. Namiji ne akoyaushe yana iya canzawa. Duk wannan bidirin da ake yi Hauwa ba ta sani ba don ban gaya mata komai ba. Da yake ni ba ma'abociyar dora status ba ce don sai nafi wata biyu uku babu komai akan status dina tunda ya haramta mini harkokin social media farkon auranmu na kiyaye tunda ya ce baya son hotona ko guda ya kara fita ina kiyayewa sosai idan har na dora status to hoton yara ne ko addu'a akan wata mas'ala ko kuma tahamidi ka Allah. Yau dai na ce bari na gwada tsokanar Nabila na gani. Hoton ranar auranmu a saudiya na dora wanda aka yi mana ina rungume a jikinsa. Duk muhimman hotonana suna nan a memory na na adana. Guda daya kawai na dora tare da rubuta shukuran ya rabb" Kafin na kai ga sauka itace kusan ta hud'u daga cikin wad'anda suka duba. Ban yi mamaki ba, na yi murmushi tare da kashe wayar na ajiye cikin zuciyata ina fad'in za mu ga dai zuwan da dawowar." Na tashi na fita falo da yake yammace yaran duk suna makaranta babu kowa a falon sai tibi tana yi ita kadai. Baba Tabawa tana kicin na leka d'akin yaran na samu Mairo tana shirya musu kayansu da aka goge. Ta juyo da sauri tana fad'in." Hajiya akwai abinda za a yi ne?" Na girgiza kaina a hankali na ce." E, to idan kin gama a nutse don ba sauri nake yi ba sai ki soya mini wainar fulawa yajin tafarnuwa amma kada ki sanya masa kuli idan za ki ni'ka." Ta ce." In sha Allahu an gama Hajiya za a yi yadda kika buk'ata." Har na juya zan fita sai na dubeta tare da fad'in." Nafiso ta yi 'kanzo fa wainar Mairo." Da yar dariya ta ce." Zan yi fiye da yadda kike so in sha Allahu." Na juya na fita jikina babu wani kuzari na arziki ciki ne da ni, ni na tabbatar da hakan duk da lokacin al'adata bai yi ba balle na gazgata amma ni cikina a sati d'aya ma yake bayyana kansa. Na leke d'akin Hauwa tana band'aki tana wanka kasancewar itace da girki sultan kuma tunda ban gan shi a wurin Mairo ba nasan yana goye a bayan Baba Tabawa yaron ya shaku da ita sosai. Na ga hauka a daran ranar dana sanya hotona da maigidan a status wurin Nabila sai da ta jera status sama da arba'in cinkus. Ni kuwa saboda nasan saboda ni ta yi sai na'ki dubawa daga lokacin ma na goge lambarta daga wayata na yi dariyata na koshi ina mamakin al'amarin. Babu wanda na gayawa ina da juna biyu Hauwa ba ta sani ba haka ma anti Yagana da Sahura ballantana maigidan bai lura ba domin ina ta karfafa jikina. Shi kuma a lokacin abubuwa sun yi masa yawa kwarai yana ta hidimar bude gidajen mai a Legos har guda uku. Da babban kamfanin siminti da za a yi bikin bud'ewa duk a can Legos din. Harkokinsa da yawa sun fi a can, sai ko kano anan Abuja bai fiye yin hada-hadar kasuwanci ba. Nasan dai yana da manyan manyan hotels da gidajen da kwarori suke zaman haya akwai kuma shaguna ana hada-hadar sayar da spire pats. Amma babu lefi gaskiya yana da kadarori masu yawan gaske da arzikin da a kullum yake kara ninkuwa duk inda aka ga haka kuwa tabbas dukiyar tun fil'azal ba a cudanyata da haramun ba. Yawan fitina da binbini ma duk ya rage saboda yadda na lura idan bai kammala da wannan hurd'odin ba hankalinsa ba zai kwanta ba. Da ya shirya tafiya legos kuwa bai nemi tafiya da kowa ba. Ya dai gaya mana tare za su tafi da Salim. Hakan bai wani dame mu ba. Akan tafiyar da zai yi babu wata daga cikinmu. Na gaza dai ha'kuri na ce ban yarda ba zan bi shi, domin a lokacin sai shaidan ya fara raya mini wani abu." Wata'kila an daura auransa da Nabila ya boye mana shiyasa bai nemi wata ta daga cikinmu ba. Zai d'auketa su lula can nesa domin su ci amarcinsu hankali kwance. Na tubure lallai sai na bi shi fa. Abin ya dinga ba shi mamaki ganin yadda yake daga da ni a duk lokacin da zamu tafi na dinga zillezille kenan ina nokewa na ce wannan gobe na ce wannan. Yadda na tubure sai na bi shi haka Shima ya tubure ya ce bai shirya tafiya da kowa ba dalili aiki ne zai kai shi mu zauna kawai ya ma canza tsari ya daina tafia damu shi kadai zai dinga tafiya abinsa Wannan maganar tasa sai ta kara haska mini hanya a daran ranar muka dinga rigima tun Yana biye mini da ko'karin mayar da abin wasa har dai ya bud'e wuta tunda maganganu na dinga saki masu zafi. Har yana fad'in ban isa na hana shi auran nabila ba idan ya yi ra'ayi kuma Hakan ma da nake yi ya kwadaita masa sha'awar auranta. Na ci kuka na koshi yadda ban rintsa ba haka zalika shima bai rintsa ba. Da asuba na sauka kasa raina a dagule gari yana yin haske na kira Hajja a waya duk abinda yake faruwa na gaya mata da irin zargin da nake yi domin kuwa shi abin zargi ne tunda yana yin wasu abubuwan a dukunkune. Ya za a yi a ce zai tafi Legos tsayin watanni shida babu mace a sanin da na yi masa mabukaci ne kwarai idan ba da wata a kasa ba. Ta yi mamaki sosai ta dinga fad'in itama bata san komai ba amma lallai zata bincike shi kuma tilas ya gaya mata gaskiya idan ma da maganar auran to zata rushe tunda ba ma sonta amma ba zata hana shi ya nemo wata ba muddin ta kwanta mana. Maganganunta sun dan sanyi mini sasaauci a raina. Wallahi tallahi itace rantsuwar musulmi Nabila tana zama matarsa na bar gidansa har abada domin ba zan iya kunsar wani takaicin ba bayan wanda na kunsa a baya. Yanzu wanene yake irin wannan kishin jahilcin babu burin zaman lafiya a tattare da ita. Zan kuma nuna mata iko da k'arfina akan wanda take yi wa fafutuka karyar banza take yi. Ya nemo wata da ba mu sani ba kamar yadda hajjan ta fad'a amma ban da Nabila. [12/26, 7:56 PM] bintaumarabbale: *122* Da ya dawo da daddare duk da girkin Hauwa ne bai iya ha'kura ba ya kira ni a waya. Dama na yi shirin hakan, sai a lokacin ne ma Hauwa ta san abinda yake faruwa domin a saman na sameta tana had'a masa abinci. Na yi zaton zan same shi cikin b'acin rai domin nasan babban abinda ya tsana shine a kai kararsa wurin mahaifiyarsa. Sai naga akasin haka. Na gaishe shi ya amsa yana kallona kafin ya nisa ya fara da ce wa." Yanzu Amina duk irin titsiyar da ki ka yi mini anan ni dake bata gamshe ki ba har sai kin sanar da mahaifiyata saboda rigima na gaya miki babu wannan maganar amma kin 'ki aminta da maganata na gaya miki ba na sha'awar auran Nabila ko kad'an a cikin raina wallahi amma irin wannan iyashegen da kike yi mini ya sanya nake so na aurentan sai na ga iya gudun ruwanki." Hauwa ta dago a slow da tashin hankali tana dubanmu ni dashi domin daka gani maganar ta dake ta kwarai da gaske. A nutse na furta." To ai ga hanya nan Nabila ta shigo gidanka Amina kuma ta yi waje shikkenan karshen zance domin na riga na yi wa kaina alkawari babu wata mace da zan zauna ta dasa mini kunci da takaici akanka. Abinda nake nusashka anan shine itafa ba don komai take yun'kurin shigowa rayuwarka ba saboda mune abubuwa masu kyau da marasa kyau sun faru a baya kowa ya kar'bi kuskuransa ya kuma gyara wallahi idan da zummar son zaman lafiya take cuso kanta gare ka bai dame ni ba, yadda take nunawa tana so ta zo ta ramawa 'yar uwarta abinda aka yi mata shine abinda yasa na tsaneta." Dariya ya sanya kawai Bai ce komai ba ya fara cin abincinsa bayan ya yi Bismillah. Hauwa ta tsaya daf da ni tana fad'in." Wace Nabila wai?" A tak'aice na ce" Kanwar Momi mana abokiyar rigimarki.'' Ta yi jim tana kallona kafin ta juya kansa tana fad'in.'' Yanzu don Allah kai sai ka auri wannan karuwa ce fa babu wanda bai san tana bin maza ba, duk ga mata nan a gari." Ya dube ta da mamaki yana fad'in." A a Hauwa wannan kaifin bakin naki shine yake jefa ki a matsala, ke yanzu za ki iya rantsewa da Allah kin ta'ba ganinta tana zina, irin wannan kazafin fa yana da wahalar warwara Hauwa." Na ce." Ai ba ita ta fara fad'a ba kaima ka fadi hakan idan ka manta na tuna maka da bakinka ka ce ba zaka iya auranta ba saboda kana zarginta da biye biye." Hankalinsa a kwance ya ce." Ni ban ce ina zarginta ba, nasan dai na ce ba zan iya auran bazawara ba saboda Ina da kishi." Ban san lokacin da da maganar ta subce daga bakina ta fito ba na ce." Ai ka iya 'karya da lauya zance dama." Ya kalle ni da saurin gaske yana cud'e fuskarsa ya ce." Ni ne makaryacin." Share shi na yi tare da juyar da kaina. Hauwa ta furta." Allah Ya taimaka mu ajiye duk wata magana mu yi wadda take da amfani ya kamata fa dole ka so abinda muke so domin zaman lafiyarka, a gaskiya ba mu yarda ba." Ya kai lomar abinci bakinsa a tsanake ya ce." Ai ba ku biyo hanya ba, duba fa ki kun yi mini kerere a kai, kuna so ku tursasani ne, ai muddin ni nake auran mace tana kasan kafafuna ban yi lalacewar da za ta gindaya mini sharadi ba. Ba zan auri Nabila ba in dai a son raina ne wallahi babu soyayyarta ko kad'an cikin raina. Ku kwantar da hankalinku don Allah, mu rabu lafiya." Na ce." Idan gaskiya ne to zan shirya mu tafi Legos din tare." Ya girgiza kansa yana fad'in." Ki huta kawai a gida zan tafi ni kadai shawara na canza, Kuma zan kula muku da kaina sosai in sha Allah." Don dole muka ha'kura da abinda ya yanke amma har zuwa ranar da zai tafi zuciyata bata aminta da maganarsa ba. Ilai kuwa bayan tafiyarsa da kamar minti talatin tawagar yaransa da suka yi masa rakiya zuwa airport suka dawo amma banda Sukairaju da Dahuru wannan duk inda za shi tare suke tafiya mussaman Sukairaju. Cikin wad'anda suka bi shi har da direbanmu Masa'udu da ya shigo kawo kular dake zuba musu abinci abinci kamar wanda aka sanya wa batiri ya tsaya suna hira da Baba Tabawa da yake mutuniyarsa ce yake gaya mata a cikin masu rakiya har da Hajiya Nabila domin da motarta ta tsaya a kan hanya shine ma ya daukota ya dawo da ita gida. Mamaki ne mai yawa ya kamani. Har ya juya zai fita na dakatar dashi tare da tambayarsa abinda yake cikin raina. Ya ce." Eh kwarai kuwa ba tare suka tafi ba yanzu haka ban jima da sauke ta ba ta shiga gida, amma dai Yallabai din tare suka tafi da Salim." Na gyada kaina a nutse na ce." To shikkenan je ka kawai." Ya fita da sauri ita kuma baba Tabawa ta shiga kicin. Hauwa tana d'akinta Bata fito ba. Na yi yun'kurin tashi kenan Baba Tabawa ta fito daga kicin ta zauna kusa da ni tana fad'in." Hajiya Amina akwai abinda na fara fahimta da matar nan Nabila." Na dube ta amma ban ce komai ba zuciyata tana can tunani. Me yasa mu bai bari mun yi masa rakiya ba ita ya gayyaceta, wannan amsar kawai nake son sani. Ta furta." Ba na yi wa Yallabai sha'awarta ai ya yi rashin mata sai da mu ce Allah Ya gafarta mata, amma dai wannan tana tattare da matsaltsalu masu yawan gaske." Na gyada kaina a d'an sanyaye na furta." To yadda dai yake gaya mana duk abinda take yi bai sani ba domin dai babu sha'awar auranta a tare da shi, amma kin san makirci da dadin baki na maza Baba Tabawa za mu iya sakin jikinmu wataran katsam mu ji gud'a, ba mu da yadda za mu yi. Kin ga sai ya sake zuwa ya raina mana hankali ya ce. " Kaddara ce ko ya kawo mana wata hujja ya ce ga dalilin da ya sanya ya aureta " Ta girgiza kanta tana jimantawa domin ita da ta fi mu yawan shekaru ma abin ya tsaya mata a rai. Hauwa ta fito ta same mu muna tattauna maganar. Taja tsaki kafin ta dube ni a nutse tana fad'in." Amina don girman Allah ki kyale shi ki daina damun kanki wallahi nasan ko ya aureta da wuri gayyar za ta watse shiyasa ban damu ba. Ki daina damuwa haba Nabilan me bagidajiyar banza da wofi." Murmushin takaici kawai na yi cikin raina na ce magana kam na bar ta shima na daina nuna masa damuwata a fili amma ina nan na kudire abu a raina. Satinsa hud'u ya dawo a cikin kwanakin bai fi sau hud'u muka yi waya ba. Ya dawo a tsananin bukace lokacin ni kuma laulayi ya lafkar da ni domin abinda nake zargi ya tabbata ya kuma bayyana kansa domin mai azaba ne da son kad'aici na tsiri zaman d'aki da rashin son hayaniya da k'unci. Sai masifar son abinda ya danganci yaji da manja. Koda ya tabbatar da cewa ciki ne da ni ya yi murna sosai ya fito da farincikinsa kowa ya sheda hakan. Kuma ya rage takura mini a duk ranar girkina saboda ya fahimci ba ni son damu abin ma gabad'aya baya ba ni sha'awa. Sai ya zamana bai fi sau biyu yake kwanciya da ni a sati ba. Laulayi sosai ya tisa ni a gaba har da su karin ruwa kusan sau uku. Anti Yagana ta ce mini za ta zo dubani domin da muka yi bidiyo call ta tsorata da ganin yadda na zabge. Na ce ta yi zamanta ba sai ta zo ba tunda itama tana tare da mai juna biyun Fadila tunda watan haihuwar ya tsaya a ka dawo da ita gida tunda ta fari ce. Hatta da Sahura ba ta san ina da ciki ba, itama anti Yagana yawan yin bidiyon call din da muke yi ne ta fahimta shine babu yadda na iya na gaya mata. Wataran alhamis da yamma ina kwance a d'aki da busheshshiyar agwalima a bakina ina tsotsa wata masifa ta ciki gari na waye wa da bushshiyar agwalima nake farawa kafin nasa komai a cikina ina nan da su a bushe da yawa bata yanke mini tunda akai-akai nake aika Masa'udu ya sayo mini. Kamalu ya kira ni a waya muka gaisa sosai cikin Kamala da nutsuwa na ji ya ce." Mama amma dai za ki zo walimar bude makarantar da Baba ya gina mini ko." Da mamaki a tare da ni na ce." Makaranta kuma Kamalu yaushe aka yi hakan ai ban sani ba ." Ya d'an yi murmushi kafin ya ce." Ai dama tun da na ji ba ki yi magana ba na ce wata'kila ba ki sani ba. Mama Baba ne ya gina mini babbar makarantar islamiyya da massalaci a hade anan unguwar Kadawa gobe Juma'a in sha Allahu za a yi bikin bud'ewa." Na yi shiru ina mamaki ko da wasa bai ta'ba gaya mini ba, nasan dai da maganar tafiyarsa Kano gobe amma bai ce mini ga dalili ba Na ce " wallahi ban sani ba Kamalu don bai gaya mini ba, na ta ya ka murna sosai kuma na yi addu'a Ubangiji Allah Ya yi maka jagoranci Ya amsa cikin jin dadi ya cigaba da cewa." Ai yana jin dadin irin yadda yake ganin bidiyona yana yawo a kafafan sadarwa. Ya ce mini har wasu daga cikin abokanansa suna tura masa tare da taya shi murna. Da ya tambayeni menene burina a duniya na gaya masa makaranta islamiyya da massalacin da zan cigaba da yad'a da'awata da sauran koyarwar addinin musulunci." Na gyad'a kaina ina mamaki duk yadda aka yi hakan ban sani ba na ce." Da yake ni social media bata dame ni ba yanzu kuma dai ba'a ta'ba gaya mini ga wani bidiyonka ba. Kwanaki can dai Sahura ta ce mini Maigidanta ya ganka tare da wannan malamin shaik ma'kari a lokacin da ya zo gaisuwar ta'aziyya. Daga sannan dai ban sake jin wani labari ba." Ya ce." Mama ai adduarki ta kar'bu alhamdulillahi. Mutane sun fara kar'bar abinda muke yi kuma suna mubayaa sannu a hankali za mu fara shiga kauyika domin wattanin da suka shige mun yi wa shaik Abdullahi G kaya rakiya zuwa gombe can wani kauye da arna suka yawaita wallahi ni kaina mama na musuluntar da mutum sama da ashirin a kauyen." Cike da farinciki na ce." Alhamdulillahi! lallai kana tare da nasara da d'aukaka Kamalu ka dage ka yi aiki tukuru ka kuma kula sosai kada ka shiga rigar da ba taka ba. Kada na ji ana fad'a da kai akan addini. Ka yi iya yinka kamar yadda annabin rahama ya fad'a shiriya ta Allah ce." Ya ce." In sha Allahu rabbi Mama zan kula sosai kuma yanzu zan turo miki irin bidiyon da nake yi ina sanyawa a shafukana na social media YouTube fecebook TikTok Instagram Whasap." Na ce." To ka turo mini na k'alla, Ubangiji Allah Ya sanya albarka Kamalu Allah Ya sa kafi haka." Ya amsa da "Amin Ya Allah " Na tashi zaune sosai a lokacin da ya turo mini tarin bidiyos din ta whasap na dinga bud'ewa ina kalla. Na farko yana koya yadda ake yin alwala na biyu yana koya yadda ake yin temama ga matafiya. Na uku yana koya yadda ake wankan janaba dana haila. Na uku yana koya yadda ake yin sallah tun daga kabbara tsayuwa ruku'u sujjada zaman tahiyya. Na dinga maimaita kallon bidiyos din hawaye suna silalowa a kuncina. Ni kaina na rasa hawayen menene na farinciki ne. Kamalu na ya zama gwani ya zama alarama kur'ani izifi sittin akan shi da ka yake d'auko aya ya dire ta. Na daga hannu sama ina kuka ina fad'in."Allah na gode maka, lallai kai ne masananin abinda yake boye. Na gode maka da ba ka sanya ni kaucewa hanya akan wannan bawa naka ba. Allah Yadda ka shirya mini yarona Kamalu ina ro'konka ka shirya sauran yaran al'ummarka." Na so a ce a ranar girkina na yi wa maigidan godiya ta mussaman domin duk abinda nake ji a zuciyata game dashi ya yi abinda lallai dole a yaba masa. Ko bai fad'a ba duniya ta sheda hakan ba yayin kyautar fariya ko ta ganin ido. A baka hannun hagu bai san an bayar ba. Ka zo yau a yi maka gobe ma ka dawo a yi maka ba za a ce an baka jiya ba. Baya ta'ba alheri ya fad'a sai dai duniya ta fad'a. Washe gari da safe dana daidaici Hauwa ta sauko daga saman tunda dama koda ba ni da girki na kan hau mu gaisa Wani sa'in ko shi ya biyo ni d'aki. Sai da laulayin nan ya tsananta ne ya sanya ni b'akincikin hawa saman nasa domin idan na kalleshi haka kawai sai na ji haushinsa ya kamani. Duk kuwa da kokarin lallabani da yake yi gudun kada cikin ya samu matsala ya zube kamar na baya. Baya yi mini abinda zai ba ni haushi duk abinda na ce ba na so zai bari duk son sa da ya kusance ni idan na nuna a a sai kawai ya ha'kura ya shiga wata sabgar shiyasa ganina da sassafe ya ba shi mamaki ya shirya tsaf cikin manyan kaya har da nad'i a saman jar darar da take kansa ya yi kyau ainun cikin shadda wagambari mai kalar sararin samaniya babbar rigar tasha aiki kafafunshi sanye da ba'kar safa yayin da takalmansa sahu ciki suke gefe sai kyalli suke yi. Gabad'aya d'akin ya game da kamshin turaransa wanda ya riga ya gama zaunawa a jikinsa. Na kàrasa a nutse na zauna a gefansa. Ya dinga kallona kamar ya ga sabuwar hallita ya ma kasa d'aura agogon da yake hannunsa kawai ya 'kura mini idanuwansa da suke cike da tambayoyi. [12/26, 7:56 PM] bintaumarabbale: *123* Agogon da yake ri'ke a hannunsa na kar'ba na ri'ke tsintsinyar hannunsa na dama wanda anan na lura yake daura a gogo na fara daura masa a tsanake zuciyata na kara yin sanyi da lamarinsa. Tabbas na yarda d'an adam tara yake bai cika goma ba. Kuma ko na'ki ko na so wannan mutumin tarin alheransa sun rinjayi sharrinsa ya yawa. Domin da wahala na ji suka da zambu a kansa ta ko'ina sai yabo da fatan alheri. Bai ce mini komai ba har na gama daura masa agogon yana kallona na kai hannun bakina na sumbuta kafin na dube shi fuskata a sake na ce." Barka da asubahi Babanmu." Yana k'ayatattacen murmushi ya amsa da "Barkanmu dai Aminatu my princess." Na dariya kawai ina kallonsa kafin na gyada kaina na ce." Da gaske?" Ya ce." Kwarai kuwa ai babu wata sarauniya a birnin zuciyata sai ke." Ban ce komai ba kawai na ri'ke hannunsa tare da had'e yatsunmu wuri d'aya. Ya sauke sanyayyar ajiyar zuciya yana kallona ya ce." Amma ni ba babanki ba ne Amina, kin manta ni duniyarki ne fa, ni ne mai k'urewa jin dadinki lamba mai yasa za ki kira ni da baba." Na danne kunyar da ta taso mini na dube shi da 'yar dariya na ce." Na rasa da wane suna ka dace ina ganin kiranka da Baba shine karshen mutuntawa." Yana murmushi ya dubi agogon dana daura masa ya gyada kansa yana fad'in." Yau ni dake kamar wasu sabbin masoya, kina so ki shagaltar da ni, jirginmu ya kusa tashi bakwai da minti goma yanzu takwas daidai za mu tashi in sha Allahu kuma yau zan dawo sai mu kàrasa soyayyar don na ga alama addu'ata ce ta kar'bu a kanki." Na dube shi a hankali haka kawai sai wani tausayinsa ya rufe ni, wai aka ce sai da so ake kishi da tausayi to amma in ba haka ba ai wannan mutumin ba abin tausayi ba ne, mutumin da Allah ya wadata da suttura da jin dadi na gidan duniya. Hannuna na kai fuskarsa ina dan jan gemunsa da ya yi 2colors fari da baki ya kwanta sosai ya kuma k'awata masa fuskarsa. Na furta." Ka yi kyau sosai, kamar ango." Ya kanne idonsa yana fad'in." Shine ai ba ki ga na yi gayu ba." Murmushi na yi tare da fad'in." Haba da Nabilan kenan?" Ya daga kansa yana kallon yanayina. Na ce." Mai yasa ka boye mini abinda lallai kasan ba zai 'boyu ba." Ya yi jim yana kallona, sai na girgiza kaina ina ko'karin mayar da k'wallar da take ko'karin zubowa na furta." Jiya Kamalu ya kira ni a waya ya gaya mini abinda ka 'boye mini. Ba ni da bakin godiya Baba, Allah Ya saka da alheri, Ubangiji Allah yadda ka dubi marayun yaran nan ina ro'kon Allah Ya dubi naka abinda ka yi na alheri Allah Ya sanya maka a mizani, na gode na god....! Ban kàrasa ba kukan da nake dannewa ya kufce. Da saurin gaske ya janyo ni jikinsa ya rike ni sosai yana d'an dukan bayana a hankali cikin sigar rarrashi yake fad'in."Daina kuka Amina, ai bake na yi wa ba kaina na taimaka, bakin san da cewa hakkin yaranki a kaina yake ba ai a musulce ni ubansu ne tunda ina auranki, babu buk'atar godiya a tsakaninmu. Yaranki da wani namijin ki ajiye a ranki kamar da ni ne, ai Aminu Salihi da k'arfi da lafiyarsa muka hadu muka nemi dukiyar tare don haka don na sake yin wani abu akan yaran nan ki ce za ki yi mini godiya ko ki yi kuka ni ma na sauke hakki ne, na kuma gode da kyawawan addu'oinki, Allah Ya shirya mini ku bakidaya. Ri'ke shi na yi sosai a ajikina ina sauke ajiyar zuciya amma hawayen dake zuba daga idona sun kasa tsayuwa. Ya dago ni yana duban fuskata ya sanya tafin hannunsa yana goge mini a d'an sanyaye ya furta." Ya isa na ce, ki yi shiru humm!, yawwa ko kefa, ki yi mini murmushi nan kin ji tawan" Murmushi na yi irin mai tafe da kuka na sake rungume shi a jikina kam kukan da k'arfi ya k'wace mini. Ya diririce sosai yana ta jijjigani "Menene haka Amina na gaya miki akwai abinda yake gabana, kukan na menene haka?" Na dago kaina Ina kallonsa cikin kukan na ce." Don Allah ka yi hakuri da abinda na dinga yi maka ka ji." Ya ce." Ni ba ki yi mini komai ba kuma ban ta'ba rikonki ba, ai ni ne zan ce ku yafe mini." Na ce." Mune dai za ka yafe wa tunda aljannar mu tana kasan kafafunka don Allah ni ma koda na mutu ka dinga yabona kana fad'in alherina irin na Momi." Ya b'ata rai yana fad'in." Me ya kawo zancen mutuwa kuma?" Na yi shiru ban ce komai ba domin ni ma jin maganar kawai na yi ta fito daga bakina. Ya tashi yana gyara babbar rigarsa ni ma na tashi Ina kallonsa yanayinsa ya canza. Na ce." Ka na son ka auri Nabila ko?" Wani irin duba ya yi mini kafin ya gyada kansa ya mik'a hannu ya debi wayoyinsa dake zube a gadon ya kama hanya zai fita. Na bi shi da sauri Ina fad'in." Ka tsaya ka ji." Ya ja ya tsaya yana dan hararata kafin ya ce." Ke ba a fara magana dake a kare lafiya Amina, wanene ya sako Nabila a cikin maganar mu?" Na ce." Dama zan ce ne na amince idan kana sonta ka aureta wallahi." A hanzarce ya furta." Ai dama can ku ba ku isa ku hana ni auranta ba idan ina da ra'ayi. Nabila ta bi ta hanyoyi da yawa domin kamun kafa ta had'a kai da su Salim ta nemi Hajiya Ayya mahaifiyar abokina Alhaji Amadu duk akan tana so ta maye gurbin 'yar uwarta na ce a a saboda wasu dalilina. Ba wai tsoronku ne ya hana ni auranta ba." A sanyaye na ce." To shikkenan, Allah Ya bata wani." Ya amsa da "Amin yana ko'karin bud'e 'kofar d'akin Tare muka sauka kasa wanda ya yi daidai da fitowar Hauwa daga dakinta cikin shiri. Ganinsa a shirye da shirin tafiya ya sanya ta ce." Da gaske dai ba za ka yi breakfast din ba kenan?" Ya ce." Idan na je gidan Hajja sai na yi na gode da kokarinki." Daga haka sai ya nufi kofar fita a d'an gurguje. Muka had'a baki wurin fad'in." Allah Ya tsare hanya a gaishe da Hajja." Ba tare da ya juyo ba ya amsa da "Za ta ji in sha Allahu rabbi." Rayuwa kenan ko da na gayawa Hauwa makasudin zuwansa kano. Ta yi mamaki amma irin na farinciki ko kad'an ban ga alamun kyashi ko hassada a cikin kwayar idonta ba. Idan ma ta ji wani abu a ranta a zahiri ta daure bata nuna mini ba. Kamar yadda ya yi alkawari kuwa a ranar ya dawo bai kwana ba yana gaya mini Anti Yagana tana gaisheni da sauran 'yan uwan Babanmu domin duk sun halarci taron har Yaya Talatu Yayarsu Yaya Aminu dake aure a kamaru itama ta zo. Duka suka bada sakon gaisuwarsu. Na ce ina amsawa. Lallai taron ya tattara manyan malamai attajirai da alarammomi daban-daban. Hoton nan da aka yi a wurin ya dinga nuna mini a wayarsa Kamaluna cikin manya masu daraja da tsantsar ilimi. Lallai babu abinda ya gagari Ubangiji babu shakka har na koma ga Ubangijin talikai ba zan ta'ba daina godiya gare shi ba. Ga kuma wani farincikin da na kasa boye shi a cikin raina ganin har da Salim da Adamu wurin taron kuma suna cike da walwala tare da farinciki akwai wani hoto da ya d'auki hankalina duk a cikin hotonan da aka yi a wurin taron bayan wanda aka yi musu su biyar na farko Kamalun sai Saminu Turmuzi Yusi da Adam, gabad'aya yaran suna cikin manyan kaya sun zama samari masu nutsuwar da babu rawar kai a cikinta. Turmuzi ya nutsu sosai haka zalika ma Saminu da ya zama k'ato dama can yana da jikin girma a gidanmu. Na cigaba da godiya ga Allah Ina sake duba hoton da ya yi masifar kyau ya kuma d'auke mini hankali kwarai da gaske shine wanda aka yi musu su biyu Salim din da Kamalu suna ri'ke da hannun juna suna dariya a take a lokacin na d'ora shi a saman profile dina na kuma sanya shi a fuskar wayata. Sai hawayen da nake ta dannewa suka zo kumatuna tuna irin artabun da aka yi a baya na tuna babban burin Momi kenan tabbatuwar zumuncin yaran da wannan ta rasu a cikin ranta. Sai kawai na gagara kasa kàrasa kallon hoton nan na mik'a masa wayarsa tare da sanya duka tafikan hannayena na rufe fuskata ina kuka wanda fitarsa yake yi mini wahalar gaske.. Ya tallafo ni sosai a jikinsa yana d'an tatta'ba wuyana a lokacin shima bakinsa mutuwa ya yi don bai iya yin rarrashin ta hanyar kalamai ba sai ta sigar da ya tabbatar da cewar zan lallasu. Sosai naga zahirin k'auna da kulawa mai wahalar samu a daran. MURFI. Tabbas komai ya yi farko yana da k'arshe kamar yadda Ubangiji Allah Ya hallici rayuwa da mutuwa. Ya kuma hallici kuruciya da tsufa. Ya hallici talauci da arziki. Ya hallici namiji da mace ya hallici dabbobi da tsirai. Ba shakka a shekarun da na yi tun daga haihuwata zuwa yau na fuskanci kalubale na rayuwa ma bambamta na kuma kar'ba hannu bibbiyu. Idan har Ubangiji ya wanzar da kai a wannan duniyar tasa ya zama dole ka bi dukkinin dokokinsa kuma kayi biyayya ga umarninsa. Ni 'yar adam ce kuma ajiza. Nasan ina tattare da kuskure wanda yake kan kowane bawa har da annabawan Allah ba su tsallake ba. Cikin irin jarabawar da Allah ya yi mana ni da maigidana wanda a yanzu muka samu kyakykyawar fahimta shine haihuwar yara mata biyu masu d'auke da lalurar sikila tun bayan twin's wanda sune cikkaku mutane masu ingantaciyar lafiya a cikin yarana dashi. Allah Ya azurta ni da mai sunan Hajja Halimatu muna kiranta da Suhaila tana d'auke da lalurar. Allah Ya sake azurta ni da mai suna Saratu wadda ta ci tudu biyu sunan Mamana da kuma yayarsa Hajiya saratu Muna kiranta da Islam. Wad'annan yara guda biyu sai suka tsaye mana a rai ni da mahaifinsu wanda har soyayya da tausayin da yake nunawa a kansu ta d'an so ta shafi zamantakewarmu da Hauwa duk da tana iyakacin bakin k'okarinta wurin daurewa amma a wasu lukutan takan nuna rashin jin dadinta akan irin abubuwan da yake aikatawa akan yaran. Ba na ganin lefinta wani sa'in domin kuwa zuciya ba ta da kashi ita da take da lafiyayyun yaran hud'u maza uku daya mace daya. Khalil Minal Sultan Aslam mai sunan mahaifinta kenan sai Mahamud ba su samu kwatankwancin wannan soyayyar ba cikinsu gwara Minal ita tin dama 'yar gidansa ce tuntuni. Tana jurewa sosai kuma tana ta ya ni kula da yaran a duk lokacin da ciwon ya motsa musu yadda nake shiga damuwa itama haka take shiga mu dinga zurga-zurga asibiti tare har sai da Babansu ya samar musu da likita na mussaman domin kulawa da su a duk lokacin da abin ya motsa. Suna rayuwa irin yadda 'yan uwansu suke yi cikin jin dadi da kulawa kuma suna zuwa makaranta sai dai wasu al'amuran masu tsauri suna gagararsu ba don komai ba sai don yanayin lafiyarsu. Amma karshen kulawa da so ubansu yana yi musu abinda na gama fahimta tsabar tausayi ne na iyaye. A duk sanda wata daga ciki ta kama ciwo tare suke yi domin yakan fi ni shiga damuwa da tashin hankali. Ba komai ake yi wa ba ran nan guda daya shi ake tattali da kashewa dukiya. Akwai wata rana da ciwon ya motsawa Sulaita ta dinga suma ya gigice kwarai da gaske shi da kansa ya jinyace ta a asibiti tsayin sati biyu ta samu lafiya. Na riga na gama fahimtarsa mutuwa kawai yake tsoro kuma ko da ciwo ko babu za a tafi. Shiyasa idan ciwon ya motsa baaya garin ba na gaya masa domin zai daga hankalinsa har ya gagara yin wasu al'amuran na rayuwarsa. Da yake ma muna kula da su sosai da bin dokoki ba kasafai abin yake motsawa ba sai a shafe wattani har shekara ma wata daga ciki bata kwanta ba. 'yan uwansu duka suna son su tare da taya mu kula da su. Don dole muka ha'kura da haihuwa saboda shawarwarin da ake ba mu. Ni da shi muke yin dabaru wurin kwanciyar aure wanda har yanzu akan hakan muke saboda ya yi rantsuwa babu rabuwa kamar yadda wasu daga cikin likitocin ke bashi shawara ya kuma ce babu maganar juya mahaifa ko shan maganin hana d'aukar ciki. Sai dai mu yi dabaru idan har rabo ya rantse an samu karuwa zai kar'ba Allah ne mai ji'bantar al'amura. Bai sake shawa'ar k'ara wani auran ba tun bayan turka-turkar da aka sha da Nabila ta gaji ta ha'kura sai bayan da Salim ya koma legos da zama tukkuna muka fahimci dama ba da niyyar kula da su ta tare musu a gida ba da niyyar ta auri maigidanmu ne. Ta cigaba da business dinta sai ta fi wata biyu a Dubai bata dawo ba. Karshe maigidan ya dawo da Adam gidanmu ya damka mana amanarsa. Dama kuma can shi ba shi da matsala kusan duka ya fi su nutsuwa da sanin ya kamata. Dole tasa itama Nusaiba ta ajiye komai ta nemi shiri damu. Cikinmu babu wanda ya kyamaceta ni hakan ma dadi ya yi mini sosai domin babban burina mahaifiyarsu ta kasance cikin farinciki a kabarinta ni ma na samu irin ladan da ta samu na ri'kon maraya. Wataranar asabar da daddare bayan na kammala abinda nake yi a d'akina na shirya tsaf na nufi wurin maigidan haka kawai nake jin shau'ki a cikin raina. Ashe farincikin da zan yi ya na gaba. Na same shi yana ta cike wasu takardu bai dago ba ya amsa mini sallamata na zauna daf dashi Ina duba takardar da take gabanshi. Sunayen mutane ne a jere ban kawo komai ba sai da ya kammala tukkuna ya dube ni yana kashe ido ya furta." Tawan ya ake ciki ne?" Ni ma na kanne idon ina fad'in." Ya labari?" Sai ya sa dariya yana fad'in." Yana wajenki ai!" Ban ce komai ba sai kallonsa nake yi. Ya d'an sauke ajiyar zuciya kafin ya furta." Kina da wanda za ki kai umara ne?" Na daga kaina da saurin gaske." Sai ya ce." Fadi sunansu na shigar yanzu wanda Allah Ya sa yana da rabo." Na ce." Gwaggo." Ya rubuta Yana fad'in." Daya kenan." "Baba Tabawa, Baba Sule Ummansu Hadiza Anti Yagana Sahura Ummansu Saminu Hadiza Hamusu." Na yi shiru ina ta kallonsa yana rubutawa. Ina dariya na ce." Kana so ka ga haukana ko?" Ya girgiza kansa a nutse ya furta." Duk wanda ki ka kira sunansa da izinin Allah zai je d'akin Allah Amina." Na gyad'a kaina a hankali na ce." Dada ta tsufa da yawa Baban Saude kuma ka kai shi aikin hajji shekara biyu kenan." Ya ce." Ai aikin Hajji daban umara daban a sa sunansa ko?'' Na daga kaina ina kallonsa. Ya rubuta ya dago yana fad'in sai wa kuma." Na ce." Suke kenan?" Na Fadi hakane kawai ba don sun kare ba, akwai da yawa daga 'yan uwan Mamanmu da kuma bangaran Babanmu. Nasan kuma dole zai tambayi Hauwa duk da yake kusan babu wanda bai je umara ta bangaran mahaifiyarsa ba. Ya ajiye biron hannunsa Yana fad'in." Amma Hadiza ba ta na prison ba ne Amina?" Na sauke ajiyar zuciya Ina kallonsa na ce." Ashe ban gaya maka ba ta fito wata uku da suka wuce ta shiga cikin ayarin wad'anda governor ya yi musu afuwa. Tana gida yanzu haka." Ya gyad'a kansa yana fad'in." To, alhamdulillahi amma kun kaita asibiti ko?" Na ce." An kai ta lafiyarta lau sai dai ta rame kaf kamaninta ma duk ya canza." Cikin alhini da jimantawa ya ce." Sai a hankali zata dawo daidai sai ku cigaba da bata shawara ta dage da azkar istigifari da neman afuwa wurin Allah, abu na gaba kuma shine idan ta samu miji ta yi aure shine mutunci." Na ce." In sha Allahu, mun gode sosai Allah Ya saka da alheri." Murmushin ya yi kafin ya rike hannuna yana fad'in." Menene abin godiya Hajiya." Ban ce komai ba illa rausayar da kaina da na yi. Ya janyo ni na fad'a jikinsa ya sanya hannu ya rumgumeni sosai a kirjinsa yasa bakinsa a kunnena yana fad'in." Mu yi soyayya ko?" Lumshe idona na yi a hankali yayin da na ji yarrr a ilahirin jikina gabad'aya. Ya dan hura mini iskar bakinsa a kunnena cikin wani irin sauti ya furta." I love you kaddarata. Na yi alfahari dake jiya na yi alfahari dake yau na kuma yi alfahari dake gobe. Allah Ya inganta mana rayuwa. Ya albarkaci abinda muka haifa. Hannuwana duka biyun na sanya na matse shi sosai ina fad'in." Amin Ya Allah, Ubangiji Allah Ya sa mu mutu rana d'aya." Sai ya fashe da dariya yana ko'karin dago fuskata ina nokewa domin ni har ga Allah a lokacin da zuciya daya na fadi maganar domin sai nake rayawa a raina idan ya rigani mutuwa ya zan yi? idan babu shi a doran duniya babu ni abinda zuciya take raya mini kenan!" 😃 To ni ma da nake bibiyar labarin naku na ce Allah ya amshi adduarki Amina. Idan Kun mutu rana d'aya Ubangiji sai ya jibanci al'amuran yaranku domin shine mai rayawa da kashewa. ALHAMDULILLAHI. ALHAMDULILLAHI. ALHAMDULILLAHI. Cikin ikon Allah anan na kawo k'arshen wannan littafi mai suna GUDUN AURE ina ro'kon Allah Ya yafe mini zunubi na, abinda na rubuta daidai Kuma ina dai rokansa ya ba mu ladan tare daku masu karatu. Na gode na gode na gode. Ubangiji Allah Ya sada mu da alheri, Allah Ya had'a mu cikin aminci daku a cikin wani littafin nawa da izinin mai duka..🙏