[9/14, 10:34 AM] Aunty B: 81 Ya ba ni tausayi sosai a wannan lokacin dalilin da ya sanya na kasance tare da shi har na riko hannunsa cikin taushin harshe na shiga kwantar masa da hankali, ita rayuwar duniya dama ai darashi ce walau maikudin ko talaka. Ba abin mamaki ba ne don wanda ka suturta ya karfin komai ta silarka ya nemi ganin karshenka hakan ba sabon abu ba ne shiyasa waliyyan bayin Allah irin na da ba su k'aunar wata d'aukaka ko mulki idan kuwa Allah ya ba su dukiyar suna kar'ba ne don ba yadda za su yi ammafa daga zarar sun lura mutuwa ta tunkaro su suke yin kasafin abinda suka tara a duniyar tun kafin su mutu ko su haka rami a wurin da babu idanun jama'a su binne kudi da gwalagwalansu ko sun mutu babu wata hatsaniya da za ta tashi bangaran 'ya'yansu da 'yan uwansu. Ganin yadda na dage ina yi masa nasiha kamar wata malamar islamiyya sai ya kara langwa'bewa ya dora kansa a saman kirjinta ina dan jin saukar numfashinsa kad'an kad'an. Har ga Allah a lokacin zuciyar Imani ce ta motsa mini domin ba k'aramin tausayi ya ba ni ba, da yawa sai a dinga ganin idan Allah ya azurta mutum ya gama samun jin dadin duniya da kwanciyar hankali kuma abin ba haka ba ne wani talakan ma ya fi mai kudin kwanciyar hankali tunda shi babu mai yi masa hassada babu mai farautarsa kuma zai kwanta ya ci baccinsa ya koshi bashi da wani lissafi na rayuwa. Daga rarrashi da nasiha sai lissafin malama ya kwancewa tun ina daurewa har dai jikina ya nuna na kwanta a gadon kansa a saman cinyata. Ganin haka ya sanya ya mik'a hannuna ya kashe fitilar dake gefan gado ya matso jikina sosai tare da rungumeni a kirjinsa a tare muka sauke ajiyar zuciya daga lokacin kuma fara gudanar da lamarin da zai sassauta mana damuwar da muka tsinci kanmu a ciki. Da safe kamar sabon aure muka tashi mussaman ta b'angaranshi garau dashi kamar bai yi fama da wani ciwo ba. Na ji dadin hakan sosai kuma na yi farincikin yabawar da ya yi mini jiya cikin raina na yi ta addu'ar Allah ya kawar da sake samun sa'bani a tsakaninmu. Kicin na nufa na bar shi a d'akin bayan ya yi wanka ya kimtsa yana ta aiki da kwamfiyuta a cewarsa ya tara ayyuka rashin sukuni bai sanya shi dubawa. Na shigo d'akin bayan na gama shirya mana abin kari na same shi yana waya da Hajja karshen maganar dai na tsinta yana ce mata da yamma zai shigo. Na ji muryata tana fad'in." Hauwa ta kira ni wai kun barta a gida ita kadai don haka itama za ta biyo bayanku na ce dama tare ku ka zo da Amina." Ya ce." A a ita Amina ta je can garinsu maiduguri kamar yadda na yi miki bayani sai ta zo nan ganin gida, yanzu haka tana nan gidana na sharad'a na sanya an gyara mata zata zauna anan ita kuma Hauwa ta zauna mini a can, idan na zo da yamma zan yi miki bayani sosai." Ta ce." To in banda abinka ai mai lalurar ya kamata ka kawo kusa ba wai ka ajiyeta a can ba, kun taho kun barta ita kadai bayan ba lafiya ce da ita ba." Jiki a sanyaye na ajiye tiran hannuna na fita ina mamakin maganar da Hajja take yi, ko da yake ni ma ta zauna mini a lokacin da nake laulayi, to shi kuma idan aka ce za a yi masa haka kamar ba a yi masa adalci ba tunda karfin zamansa ya fi a can din. Na dawo na same shi yana cigaba da aikinsa ammafa fuskarsa ta dan canza kad'an. Hankalinsa na kan abinda yake yi ya ce." Kina jin mu da Hajja ko?' Na nuna ban fahimci komai ba. Ya furta." Wai itama Hauwa ta dawo nan tunda tana da juna biyu, Hajja tunda ta samu labarin cikin nan ta hana kanta sukuni, na ce mata a a dai ai ba zama zan yi ba wata'kila ma jibi zan koma." Na ce." Me yasa kace mata a a, ta dawo nan din don Allah idan tare take so mu zauna ai da d'akuna idan kuma gidanta daban take so ai kana da iko, itama Hajja tana da dalili ai lokacin da nake rainon baby Khadija ta zauna mini." Ya ce." Idan har Hauwa za ta dawo nan to ke za ki koma domin ba zai yiwu a ce ku nan ni ina can ba, idan sha'awa ta motsa mini matan banza kuke so na bi." Shiru na yi kawai ban ce komai ba, ba na tsammanin zan sake komawa legos koda kuwa Hajjan ce ta bada umarnin haka. Na ce.'' Yanayin yadda Hajja take magana ya nuna kamar a cikin bacin rai take shiyasa tun farko naso na je na gaisheta ta san da zuwana domin sai ta ga kamar ana 'boye mata wani abu ne. Na tare a sabon gida baka gaya mata ba sai 'boye-boye kake yi baka so a san kana garin nan ban gane dalilin yin hakan ba har yanzu." "Dalilina na yin haka suna da yawa Amina, amma yanzu tunda mun sasanta ba kya jin haushina zan gaya miki ba farko duk wanda ya ga jerin motocina na gidanki zai zargi wani abu rabuwar auranmu da nake ta b'oyewa duniya zata sheda hakan har ita hajjan ta ji labari gani can ina zawarcinki ke kuma kin koma zaman kanki irin na baya wanda mutane suka shede ki da haka. Za a yi ta yawo damu a duniya kowa na tofa albarkacinsa bakinsa. Na gayawa Hajja cewa kin je can maiduguri biki ni kuma na ce mata zan zo nan domin duba Gwaggo wadda ta haifi mahaifin Yusi, ko da na sauka garin nan hakan na sake gaya mata. Amma wannan ba abin da za a tsaya ana ta magana ba ne, zan yi magana da Inna Uwani a samu wata dattijiwar sai a tura mana ita can su zauna tare har Allah ya sauketa lafiya." Na ce." Idan dai hakan zai janyo matsala don Allah Hauwa ta dawo nan itama ba na son abinda zai sa Hajja ta ga rashin kyautawata" Babu damuwa ya ce." Idan kin aminta hauwa ta dawo ai abu ne mai sau'ki sai ta dawo din ke kuma sai mu koma tare " Girgiza kai na yi na ce "A a ni kam ai na dawo kenan in sha Allahu." Ya ce." To sai ki ja bakinki ki yi shiru tunda ke kin yi nasara amma ba zai yiwu a ce duk ku tattara anan waje daya ba. Ya fita sallar azhar bai dawo ba ya bar wayoyinsa a d'akina ana ta kira na shiga d'akin a daidai lokacin da wani kiran ya sake shigowa na d'auki wayar na duba sunan Hadiza ne yake yawo cike da mamaki nake bin sunan da kallo. To kai tsaye dai ba zan yanke hukunci cewa Hadizar gidanmu ba ce tunda mutam ne na mutane akwai ma'aikata mata da suke yi masa aiki mabambamta har da k'warori. Ba yadda za a yi na daga wayar tunda akwai tsaro (security) sai na ajiye har ta katse wani kiran ya sake shigowa a k'alla akan idona sai da aka kira sau kusan shida kafin a hakura. Ya shigo a gurguje yana fad'in.'' Ban san me mutane suka zama ba a wannan duniyar ba ni da lokacin da zan 'bata akan yin jawabi dangane da Sammani abinda suka samu na shaci fad'i ya ishesu babu wata gidan jaridar da zan tsaya bata lokacina a kansa. Na ce." Wani abun ne ya faru kuma?" Ya zauna gaban abincin dana shirya masa yana cewa." Sun ankara da ni ne duk da na rufe fuskata da takunkumi yanzu bakin gate din gidan nan mutane ne cike manema labarai da mabukata." Gabana na dan bugawa na ce." Akan me suke neman labari kuma? "Dangane da abinda ya faru mana tsakanina da Alhaji Sammani suke neman jin ta bakina." Na ce." Ka ja bakinka kawai ka yi shiru don Allah kada ka ce komai bayanin da ka yi da farko ya wadatar wata'kila wasu sun samu labarin ko ya yi yun'kurin kashe ka ta hanyar sanyawa a kwance maka k'ososhin mota." Ya ce." Ba na tsammanin haka, lamarin dai da suka samu shine na salwantar mini da gidan gonata dake tiga da kuma sabon kamfanin da na fara ginawa a mariri wanda shi kadai ya san da ajandar hakan to akan hakan dai suke so su ji abinda zan ce." Na ce." Ai ka ce ka yafe masa ba shikkenan ba. Mutane ne ba su san zaman lafiya shi kansa nasan yanzu yana can cikin jin kunya da damuwa ga kuma fargabar irin kallon da mutane za su dinga yi masa. Ya ce." Ai idan har suna ganina ba za su daina bibiyata ba Amina, ba ki san dan jarida da na ci ba ko." Shiru na yi ina kallonsa ya janyo wayarsa dake saman gado yana fad'in." Zuba mini abinci ina so na fita zuwa gidan hajja ina fargaba wallahi." Na fara had'a masa abincin a tsanake na ce.' An kira ka a waya ka ga ni ko?" Ya na duba wayar ya ce." Hadiza ce yayarki." Na dube shi cikin nutsuwa." Hadiza kuma?" Ya d'aga kansa a hankali ya sanya wayar a kunnansa kiranta ya yi. Kaina ya kulle da mamakin lamarin dama tana kiransa ashe shiru na yi kawai domin na ji wannan karon kuma dame take tafe. Gaisuwa suka yi ita dashi cikin girmawa har tana tambayata da Yusi shi ma ya bata amsa da kulawa tunda na fahimci duk abinda ya shafe ni yana bashi girma. Magana take yi masa cikin rauni har da rawar murya amma sakamakon yadda muryarta ta yi kasa ban ji komai ba. Na ji yana fad'in." Allah Ya rufa asiri in sha Allahu za a duba yiwuwar yin hakan, Allah Ya shirye shi da sauran masu hali irin nasa. Ya kashe wayar yana dubana kafin ya ce." Kuna da wani d'an uwa wanda Allah Ya jarabta da rashin ji ?" Da mamaki mai yawa a tare da ni na ce." Ba mu dashi gaskiya anti Yagana ce babba a gidanmu a maza kuma Usani ne Hassan dinsa ya rasu. Ya gyad'a kansa tare da cewa." Tana gaya mini dan'uwanku hukuma ta kama da zargin damfarar wani mutum miliyan hud'u da rabi." Na ce." Shine me kuma? Ba zai wuce d'an'uwanta da na sani ba mamarta sai da ta yi aure a wani wurin har ta haihu sannan Babanmu ya aureta shine kawai abinda na sani. "Tunda har Mamanta tana auran mahaifinku ai idan da kara shi ma d'an uwanku ne ko ba haka ba ne." Na ce" Don girman Allah ka daina biyewa Hadiza bata da gaskiya fa, ba zan boye maka ba ko kwanaki nan karyar rashin lafiya suka shirya da Ummansu ita Fatin ma bata sani ba ka d'auki kudi ka basu har miliyan shida sannan kuma na ji labarin an ce ka bata jari har tana zuwa Dubai sarin kaya. kai baka gaya mini ba itama bata gaya mini ba, ko da yake ai ta san bata da gaskiya ba zata gaya mini ba, wannan ma ban yarda ba karya take yi wallahi." Jim ya yi yana nazari kafin ya ce." Ta bukaci na taimaka mata kasancewar bata da aure dana tambayi matakin karatunta ta ce mini ko sakandire bata gama ba a gidanku ke kadai ce ki ka danyi karatu to kin ji dalilin da ya sanya na d'auki kudi na bata da niyyar ta yi jari domin ta tsaya da kafafunta a matsayinta na bazawara rashin sanar dake ba shi da ala'ka da wani abu tunda ni ban iya alheri na fito ina shela ba." Da takaicinsa na ce." Don ka gaya mini sai ya zama wani abu to ta dalilin wa kasan Hadizan Ina ce 'yar'uwata ce." Ya dube ni a tsanake kafin ya ce." Ni ba 'yar uwata ba ce kenan?" Shiru na yi ina kallonsa. Ya girgiza kai bai sake cewa komai ba ya fara cin abincin dana hada masa. Bakincikin abinda Hadiza take yi mini ya hana ni sukuni sai da na bari ya fita zuwa gidan Hajja tukkuna na kira anti Yagana muka gaisa na gaya mata maganar tariyata a sabon gida sannan na sanar da ita irin rashin mutumcin da Hadiza take yi. Ta ce ai d'aurin gindin babarsu ta samu auran suke su gurgud'e miki Amina amma idan ba haka ba wannan ai zubarwa da kai mutunci ne tun mutumin nan yana yi musu kara da kawaici har sai sun kure ha'kurinsa ta zubar mana da mutunci wallahi " Na ce." Anti Yagana Ina ganin kawai zan je gidan ne mu yi duk wacce za mu yi da ita gaskiya na gaji da abinda take yi mini wallahi ba zan jura ba. Ta ce." Kada ki je yin hakan zai iya b'ata masa rai ai mai hankali ne shi ya san komai kawai yana biye mata na tabbata idan ya gaji ko sauraranta ba zai kara yi ba. Ki zuba mata Ido kawai saboda idan ki ka yi magana za a d'auka kece ki ke hana mijinki alheri shima kuma tunda bai gaji ba ai kudinsa ne ba na ki ba." [9/15, 9:26 AM] Aunty B: 82 Mafarin samun matsalata da Hajja kin amincewa da komawa legos kamar yadda ya zo yana gaya mini sun yanke shawara ita dashi akan ni na koma can din domin kula da Hauwa a matsayina na wadda ta yi haihuwa uku. A cewar Hajja duk da Hauwan nurse ce ai b'ata ta'ba haihuwa ba balle ta ce ga yadda take kuma koda ta zo haihuwar yana da kyau a ce da akwai wani a kusa da ita. Lokacin da ya zo yana gaya mini kawai jinsa nake yi da kunne domin na tabbatar da cewa zamana ne ba a buk'ata anan din saboda ya kafe kai da fata ba zamu tattaro mu dawo nan gabad'aya ba dole wata ta koma can tare dashi. Na farko dai Hauwa ba yarinya ba ce a lissafin ma shekaru ma ta d'ara ni da kusan shekaru hud'u sannan kuma wace irin haihuwa ce ba ta gani ba, idan ba a shigo da son zuciya ba ina ganin ita kanta ma za ta iya kar'bar haihuwarta idan ta kakare ai akwai asibiti sai su je can, zamana babu wani abinda zai amfana tunda ba wani shiri muke yi ba to kamar dai yadda ya nemi alfarma wurin inna Uwani Ina ganin shine maslaha kawai a kai mata dattijuwa daga cikin danginsu. Da har Hajja ta amince da da shawarar da ya yanke kafin ya bar gidan ta kira inna Uwani suka yi magana ita ta rusa shirin ta ce ita dai hankalinta sai ya fi kwanciya Hauwa ta dawo kusa har da yin kuka tana gayawa Hajja ai ta je ta taya ni rainon ciki har sai da na haihu tukkuna.. Wannan dalilin ya sanya Hajja ta ce ya gaya mini na shirya idan zai koma sai mu tafi a tare. Kuka sosai na dinga yi ina fad'in ba a yi mini adalci ba domin sai da na shekara daya a can kafin Hauwa ta tare me zai sanya kuma yanzu a ce mini na koma saboda wani dalilin da bai shafe ni ba, iyakacin gaskiyata na gaya masa ba wai ina b'akinciki da haihuwar da za su yi ba, ina ganin kamar akwai son zuciya a wannan hukuncin dukda Hajja ta wuce ta nemi wata alfarma a wurina na turje mata to amma na riga na gama tabbatarwa da kaina cewa wannan hukuncin itama ta yanke shine domin son rai da kuma farantawa 'yar'uwarta ai ya gaya mini tunda aka samu cikin ta rasa sukuni idan zai yiwu ita din sai ta sake komawa ta zauna mata kamar yadda ta zauna mini ai ba hujja ba ce a ce dole sai ni zan je na zauna tare da ita tunda suna da yadda za su yi. Rarrashin duniya babu irin wanda bai yi mini ba na ce ba fa zan bi shi ba domin da muna abun arziki da ita ne ma da sauki to kowa ta ciki na ciki me zai sanya na je na bautata mata daga baya wani sharrin ya b'ullo. Ya nuna ai saboda shi zan yi, idan ma bai isa ba to na bi umarnin Hajja kamar yadda ta buk'ata kada na bijire, na ce ai ba ra'ayinta ba ne itama ta yanke hakan ne domin ta farantawa 'yar'uwarta rai. Kwana da yini muna ta abu daya domin duk ta inda ya biyo nasan hanyar da zan zame kaina na nuna masa ba da hurumina ne ba, ni ma lokacin da na haihu 'yar uwata Hadiza ce ta zauna mini. Na kuma gaya masa ko da wasa kada ya sanar da mahaifina domin yin hakan zai janyo mana matsala mai girma saboda na riga na san halinsa sarai. Itama anti Yagana ban gaya mata ba duk da mun yi waya da ita a ranar muna tattauna matsalar da ta shafe mu amma har muka yi sallama ban fad'a mata maganar ba. Da yamma sai ga Hajiya Saratu na karbeta hannu biyu sosai muka gaisa dama can muna girmama junanmu akwai kuma kunya da kawaici shiyasa ko da ta fara yi mini maganar ban iya jayayya da ita ba kawai na yi shiru saboda Ina jin nauyin na ce mata ba zan koma ba yanayin dana shiga ya nuna mata cewa ban yi na'am da abinda suke so ba. Jiki ba kuzari muka yi sallama ta tafi.. Sai da ya shigo gidan yake tambayata Hajiya Saratu ta zo na ce masa eh daga haka ban sake wata magana ba. Ya dinga bibiyata yana so ya ji abinda muka tattauna da ita bance masa komai sai da daddare tukkuna ya kira ta a waya a gabana suka yi Ina jin sautin maganarta tana cewa dashi idan zai yiwu kawai ya ha'kura tunda abu ne na lokaci Hauwan ta dawo tunda haka suke so saboda itama tana ganin kamar idan aka ce dole sai na koma an shiga shakkina idan ta haihun anan an yi taron suna sai ya tsara yadda zaman zai kasance idan ma za mu dinga zuwa can muna yi masa wata shida shida mu dawo hakan zai yi alheri. Na fahimci azancin Hajiya Saratu kuma kamar ta zo da sasanci anan a wannan ga'bar zai iya ha'kuri tunda ta b'angaransu sun dage ya ha'kura ta dawo nan din har ta haihuwa abu ne na lokaci kad'an bayan ta haihu sai mu raba na je na yi wata shida idan na dawo sai itama ta je ta yi nata wattanin. Ya kar'bi shawarar ne saboda gajiya da ja'ina daka kowane bangare amma na fahimci dan ba yadda zai yi ne ya amince ya fara shirin komawa amma cike yake da jin haushina acewarsa ni ce ya kamata na dubi halin da zai shiga amma kishi da son rai ya hana ni yin abinda ya dace. Shiru kawai na yi masa ban tanka ba har ya kammala shirinsa babu cikakkiyar jituwa a tsakaninmu na yi ta so mu rabu cikin girma da mutunci yana bijirewa haka na zuba masa ido har ya kammala shirinsa ya tafi babu wadataciyyar sallama a tsakaninmu. Bayan tafiyarsa da kwanaki uku Hauwa ta dawo a gidan Hajja ta sauka na samu labari ne a wurin Hajiya Saratu a lokacin dana kira ta a waya da kuma sutturuna na can da aka kawo mini na kira Hajiya Saratu ne a waya domin na sake wanke kaina tunda ita ta fahimce ni. A ranar kuma na kira shi duk da bai ne me ni ba, amma nasan yanzu ya huce daga fushin da yake yi tunanina ne ma ya rabu kashi biyu ban sani ba da Yusi ya koma ko kuma ya bar shi a gidan Hajja nasan dai da wahala ya bar shi a can din saboda makaranta kuma akwai sabo mai yawa a tsakaninsu zamansu a tare zasu debewa juna kewa.'' Wallahi ban zaci abin ya kai haka ba a ganina ban cancanci haka ba a wurinsa idan fa da adalci shima ya so kansa ne idan kullum zai dinga zuwa nan yana komawa yana da ikon yin haka tunda jirgi ne kawai bashi dashi amma yana da kudi kuma yana da alfarma a ko'ina,idan ya so duka karshen wata zai iya zuwa ya yi mana sati daya ya koma. wasa wasa dai yau kwanaki goma kenan da komawarsa bai kira ni a waya ba kuma bai amsa kira na ba. Abin ya fara damuna wannan ai kin gaskiya ne da gangan! E mana son rai da gangan domin kowaye ya ji wannan batun ya san son zuciya ne. Sai kawai na rabu dashi dama sautari idan yana irin wannan fushin na bashi ha'kuri ya ki ji share shi nake yi domin daga zarar ya fahimci damuwata akan abinda yake yi sai ya sake tsanantawa daga na watsar dashi sai kuma ya fara neman shiri. Sabgarsa na fita saboda na tabbatar da cewa ban yi abinda ya kai ayi mini irin wannan wulakancin ba. Sati guda ban neme shi ba ranar litinin da misalin uku da rabi na rana ya kira waya lokacin ma tana hannun Yusura tana game ta kawo mini. Babu damuwar komai na gaishe shi cikin nutsuwa domin idan na nuna masa na ji ciwon abinda ya yi mini zai ji dad'i tunda haka yake so ashe daliline ya sanya shi kirana ba wai ya kira ni domin ya ji yaya nake ba. Kanin mahaifin Hauwa ne ya rasu shine za a yi ayari har da Hajja gobe zuwa can bauchi shine yake ba ni umarinin na shirya gobe da wuri direban gidan Hajja zai zo ya d'auke ni mu tafi tare tunda ni nan bai ajiye mini direba ba sai dai gidan cike yake da masu tsaro. Jin gaisuwar mutawa ce ya sanya ban yi jayayya ba na ce masa to kawai bai kuma jirayi komai daga gare ni ba ya datse wayarsa cikin raina na ce za ka yi ka gama. Ina zaune Ina zullumi yadda zan shiga cikin dangin Hauwa da wane irin Ido zan dube su domin dai Hauwa ce tasu ba ni ba, bai zama lallai su fahimci hakkina ba tunda itace 'yar uwarsu. Idan kuma na ce ba zan je ba zai iya zama gagarimin lefi ta yadda za a kama ni da hujja a ce ni ce ba ni son zaman lafiya da Hauwa. A daran na kira anti Yagana na gaya mata ta yi mini fatan alheri na sanar da Babarmu ma shima dai addu'ar zuwa lafiya da dawowa lafiya ya yi mana Da safe da wuri muka shirya don ba mu kai ga karyawa ba ma direban ya iso haka muka tafi da abin karin can gidan hajjan idan mun je sai mu karya kafin mu tafi. Ban samu wata tar'ba muhimmiya daga wurin Hajja ba, babu wannan k'aunar da nake ganinta a cikin idonta, babu dai k'yama kuma babu sakin fuska muka gaisa kadaran kadahan. B'angaran Hajiya Saratu babu wata matsala sai ma rashin jin dadin abinda Hajja ta yi ya bayyana a fuskarta. Ban nuna damuwata a sarari ba na danneta dama na riga nasan duk daran dadewa inna Uwani sai ta farraka tsakanina da Hajja tunda a zahiri ta fito ta nuna kishin hakan, amma ni a ganina abinda na yi bai kai ace kowa ya kasa yi mini uzuri ba sai dama idan da wata a kasa. Na ji dad'i da ban ajiye ba balle na yi fargabar wata matsala ta kutsu ta rabuwa na yi danasani zan kuma kiyaye faruwar hakan tunda dama da soyayyar Hajja nake gadara an shiga tsakani. Koda Hauwa ta fito a kintse cikin shiri har da yar k'aramar akwati ni kam ban yi guzurin komai ba sai a lokacin ma na tuna za mu iya kwana fa tunda gidansu ne bai zai yiwu ace mu je mu dawo a ranar ba. Babu yabo babu fallasa muka gaisa tana zauna kujerar da Hajja ta tashi tana duba wayarta na dinga nazarinta a fakaice ta kara haske ainun abinka dama da farar fata ya yi bul-bul irin na mace mai yaron ciki duk wannan ramar babu ita kirjinta ya ciko sosai kamar wadda take rayuwa a ketare. Na d'an janye idona a hankali na sauke ajiyar zuciya Ina nazarin yadda za ta kaya domin dai ni ba zan ce direba ya mayar da ni domin d'auko kaya ba idan kwanan ya zama dole na nemi shop na sayi koda abaya ce. Zaman mota ya sanya kafafun Hajja yin tsami da kyar ta fito daga motar tana kukan kafafunta na yi mata zugi. Ni na taimaka mata muka shiga gidan Hajiya Saratu da ita Hauwan suna bayanmu Yusura kuma tana gefena ri'ke da jakata a hannunta. To an ce duk inda mai kudi yake yana da wani irin kwarjini da haiba abinda ya faru kenan saukarmu a gidan rasuwar ke da wuya maza daga waje suka dinga shigowa suna gaishe da Hajja ni kaina wasu daga cikin dangin Hauwa sun mutuntani gaisuwa ta mutunci muka dinga yi da su. wad'anda na fahimci kuma ban ishe su kallo ba ni ma bana kallonsu amma na yi kokarin samun inna Uwani a gefe na gaisheta domin sai satar kallona take yi kuma ba ta ce mini komai ba. Ta amsa babu yabo babu fallasa sai na ja gefe guda na kame kaina Yusura na gefena don ma Allah Ya yi mini kwarjini da haiba da ban san abinda zai faru ba. Akwai wasu dana lura suna ta shige da fice a d'akin da aka sauke mu kuma na fahimci sa'anin Hauwa ne irin 'yan uwan nan da aka tashi tare daya dai daga cikinsu da ta gaza ha'kuri ta dube ni da dan murmushi irin na munafurci sai ta kalli Hauwa dake kwance lakadan tana lasar lemon tsami saboda yawun da yake cika mata baki tana tambayarta wai Yusura 'yata ce dan an ce dama ina da yara biyu. Sai ta bata amsa da cewa itama bata sani ba. Hajiya Saratu da ta fahimci kamar da cin fuska ta yi tambayar ta ce." Sadiya idan 'yarta sai me, ina ce kema kina da 'yan matan yaran nan don Allah ku dinga yin shiru dangane da abinda bai shafeku ba." Ta na dariya ta ce." Anti Saratu daga tambaya sai a yi mini fassara ayi ha'kuri to." Ta d'auki wani fulas da yake cike da funkaso ta fice daga dakin. Hajja ta dan dube ni a nutse ta ce." Wai ni Amina yarinyar wacece ne wannan?" Na ce." Yarinyar Sahura ce Hajja ai ta jima a hannuna tun tana kan'kanuwa." Ta ce." Ayya, ai shi Yusi ya'ki zaman nan fafur da Baban nasa zai tafi har da kuka sai ya bishi Shima ya daure masa gindi wai saboda makaranta." Murmushi na yi a hankali na ce." Ni kaina Hajja na manta yaushe rabon da naga Yusi ko gidan da na tare fa bai zo ba." Ta ce." Ai duk lefinku ne kun yi abu a 'kunshe waye zai san halin da kuke ciki, ina sane ni ma ban zo ba, da ya yi mini jagora na duba Gwaggo na yi dawowata gida.." Da mamaki a tare da ni na ce." Hajja Yusi ne ya yi mini jagora har gidan Gwaggo." '"Kwarai kuwa shi da direbana kafin su tafi shima baban nasa sai labari ya ji mun je mun dawo." Na yi kasa da kaina cikin jin nauyi na ce." Ki yi hakuri Hajja hakan ba zata sake faruwa ba in sha Allahu rabbi. Shiru ta yi ba tace komai ba. Hajiya Saratu kuwa sai murmushi take yi ta ji dadin yadda Hajjan ta saki fuska har muna hira wannan yana nuna mini ko da asirin har yanzu akwai sauran kaunta a cikin zuciyarta. [9/16, 10:20 AM] Aunty B: 83 Sai bayan Ishai tukkuna muka tafi gidan inna Uwani dalili gidan da akayi rasuwar a cike yake da jama'a kasancewar gobe ne za a yi addu'ar sadakar uku. Babu nisa a tsakanin gidan mutuwar da gidansu Hauwa gabad'aya muka nufi can din har da ita. Hajja ta ce gobe da wuri idan an yi addu'a sai mu kama hanya mu tafi gida sosai na ji dadin hakan don haka inna Uwani tana shigowa tana gaya mata abinda ta yanke ta nuna rashin jin dadinta akan hakan har dai ta gaza yin shiru tana gaya mata ita me yasa idan ta je mata take wata da watanni ina lefin ma mu yi sati daya sai mu tafi. Jin abinda ta ce ya sanya mini fargaba don gaskiya bana so ko kwana daya mu kara a garin bayan wanda Hajjan ta yanke. Yanayin yadda inna Uwani ta nuna b'acin ranta ya sanya hajjan ta ce idan an yi addu'ar gobe jibi sai mu tafi lokacin dai duk wanda ya kamata a gaisa dashi an gaisa. Dukda hakan dai inna uwani ba ta ji dad'i ba ta so a ce mun zauna mun yi sati guda kamar yadda ta buk'ata. Jin shawarar da suka yanke ya sanya na fara tunanin nemawa kaina mafita dole gobe ma mu shiga cikin mutane kuma ba zai yiwu na sake komawa da kayan jikina ba ba don komai ba sai don na siyawa kaina mutunci. Na gayawa hajiya Saratu abinda yake da akwai da buk'atar son ta yi mini jagora mu fita a daran tunda da sauran lokaci dare bai yi ba. Hajja ta kama fad'a sosai irin wanda bata taba yi mini ba gabad'aya taki kar'bar uzurina tana fad'in ai nasan ba yadda za a yi mu yi tafiya irin wannan mu je mu dawo a ranar na ce mata mantawa na yi sai da muka fito daga gidan tukkuna Allah ya tunasar da ni. Ina jin inna Uwani da tunda muke maganar ba ta ce komai sai da ta ji hajjan tana yi mini fada tukkuna ta sanyo bakinta wai ko dai ba na son zuwa aka tursasani. Takaici da b'acin rai bai barni na sake wata magana ba, na yi shiru kawai da bakina Ina mamakin yadda yanzu gabad'aya Hajja ta daina fahimtata ta kuma daina tausaya mini. Haka dai muka fita ni da Hajiya Saratu ran mu duka a b'ace domin ita kad'ai ce ta dubi uzurina ta kuma fahimce ni ita Hauwa ma bata iya cewa komai ba har aka yi maganar aka gama kuma tana kwance a wajan amma uffan ba ta ce ba. Direban da muka zo dashi ne ya fita da mu. Garin ba bak'on Hajiya Saratu ba ne ta san wurare da yawa don haka ma ba mu yi nisa da hawa titi ba muka ci karo da wani shop a d'aya hannun na cewa magaji direba ya shiga damu ciki. Dogwayen riguna na sayo mana ni da Yusura na had'o da hijabai biyu da takalmi flat ko rabin awa ba mu yi ba muka koma gidan Hajiya Saratu tana kara ta tausata don gaskiya yanayinta gabad'aya ya nuna takaicin abinda aka yi mini tana gaya mini ita kanta ta rasa abinda yake damun Hajja a tsukin nan don ta fahimci kamar tana shakkar Inna Uwani dalilin ma da ya sanya ta fara dora zarginta akanta Na nuna mata babu komai kawai amma can kasan zuciyata abin yayi mini ciwo kawai da gaske, zan yi kokarin ganin na taushi zuciyata har mu tafi wani abu bai faru ta b'angarena ba. Mussaman aka kunna genareto saboda mu. Gidansu Hauwa sai na ce da kadan ya dara namu gidan kwaryar sama ce take dukan ta kasa. Gidan kuma na had'aka ne mutum uku ne amma kowa da nasa bangaran wanda ya rasu ne kawai gidansa a waje. Mahaifinsu ya rasu kuma shine babbansu sai dai gabad'ayansu 'yan boko ne babu wani dan kasuwa a ciki suna ci da biro da takarda rufin asiri na abinci ne kawai kuma a cikin sa'aninta dai Ina ganin ita kad'ai ce take auran mawadaci sauran duk sai a hankali suna kula da kansu ne dalilin aikin gwamnati da suke yi sai dai yadda na lura suna da hadin kai da k'aunar junansu ba kamar na mu gidan ba. Wajan goma da rabi har mun kwanta ni da Hajiya Saratu da Yusura muna d'aki daya ita Hajja da 'yar uwarta suna tare Hauwa kuwa ba na ce ga inda take ba tunda ko lokacin da muka dawo ban ganta a falon ba. Muna d'an ta'ba hira kad'an kad'an Hauwa ta shigo da wayarta a hannunta tana fad'in." Har kun kwanta ne?" A tsanake na dubeta na ce." E wallahi." Sai ta miko mini waya tana cewa." Maigidanki ne yake so ya yi magana." Na yi sakare Ina kallonta yana so ya yi magana da ni bashi da lambata ne?" Abinda zuciyata take tambayata kenan. Ta sake maimaita maganarta tana cewa'' Wata'kila ya kira layinki bata shiga ba kin san matsalar network, ni dai yanzu ya kira ni ya ce na hada shi dake." Ban ce komai ba na amshi wayar sai ta juya ta fita ni da Hajiya Saratu muka bi ta da kallo. Ita dai girgiza kanta ta yi a hankali ta koma ta kwanta ni kuwa na tashi zaune da wayar a hannuna ina tsammanin kiran nasa. Minti biyar da fitarta ya kira. Na daga a nutse na ji yana cewa." Kin kai mata wayar?" "Eh ta kawo mini barka da dare?" Na fad'a tare da ko'karin danne damuwata." Ya d'an diririce ban san dalili ba can kuma na ji ya amsa yana cewa." Dazu na kira Hauwa a waya ta ce mini kun fita ke da Hajiya Saratu ina kuka je?" Babu mamaki a tare da ni saboda nasan zai iya yin abinda yafi haka na furta." Ta yi mini rakiya ne na sayo abu a shop saboda ban yi guzurin kaya ba don ban yi zaton zamu kwana ba." Ajiyar zuciyarsa na ji kafin ya ce." Kada ki kara shiga wani shago da zummar sayan kaya Amina hakan yana nufin abubuwa da yawa, kin san dai ba zai yiwu ace ku je Bauchi ko dawo a ranar daya ba, me yasa ba ki bawa maganata muhimmanci ba a lokacin dana kira ki na gaya miki ki shirya ki bi su." Na hasala da jin yadda yake ko'karin d'ora mini lefi shekkenan ni ba zan yi kuskure ba, kuma ai da ya gaya mini bai ce mini na hada kayana kwana za mu yi ba." Na ce." Shine me? ai lefin ba na kowa ba ne naka ne ko ka gaya mini na hada kaya zamu kwana? da ka kira ni ka sanar da ni na bijire maka ne, na ce to shikkenan ban yi maka jayayya ba saboda kuskure karami sai kuma a gaza fahimtata." "Ban kira ki don ki gaya mini magana ba Amina, na ce kada ki sake shiga shago ki ce za ki sayi abu ina da dalilina." Shiru na yi ban ce masa komai ba sakamakon yadda na ga Hajiya Saratu ta tashi zaune tana kallona da yanayi na damuwa. Sai kawai na datse kiran ban tsaya na saurari sauran maganarsa ba, wane irin dalili ne dashi wanda ya wuce na tozarci shikkenan don ina a matsayin na matarsa ba zan shiga shago na sayi abu ba ni din wacece. Itama Hauwa ta so faruwar hakan hakan ne amma menene na gaya masa ga inda muka tafi bai kira ni a waya don ya nuna ya ji dadin karar da na yi musu ba ya kira ni yana tuhumata akan wane dalili. Ban iya daure kukan da yake ta yun'kuro mini ba na fara share hawayen da yake gudana a kumatuna Yusura ta yi lamo akan katifa tana kallona kamar ta taya ni kuka. Hajiya Saratu ta dafa kafadata tana rarrashina a yanzu ita kadai ce take nuna damuwarta a kaina Hajja kam sai a hankali 'yar uwarta ta samu galaba akanta. Hauwa ta shigo domin ta kar'bi wayarta ta same ni Ina kuka muna tattauna abinda yake faruwa da Hajiya Saratu sai ta yi kasa'ke tana kallonmu a lokacin Hajiya Saratu ta rufe ta da fad'a tana cewa." Ki ji tsoron Allah Hauwa yadda ki ke ko'karin gyara auranki to na hore ki ki gyara na 'yar uwarki wadda ki ka zo ki ka sameta da mijinta, bayan abinda ku ke yi na karkashin kasa har sai kin yi mata bita da kulli kin san fa duk abinda ya faru me zai sanya don ya kira ki a waya sai ki gaya masa shikkenan mutum baya kuskure.. Babu wata damuwa a tare da ita ta ce." Sai na yi karya kenan ko anti Saratu na ce masa gata nan a kusa da ni ko me? Ya tambayeni ina take na ce masa kun fita tare zata sayo kaya ko ba haka na ji kuna maganar ba. A lokacin da na yi masa karya ya ce na bashi ita kuma na yi yaya kenan, kuma na ji kina cewa muna yin abu ta k'arkashin kasa, ita din da kike shedarta kina da tabbacin ba ta yi ne? ai alhaki koikoyone wata'kila abinda ta yi ne ya waiwaiyo mata, ni wannan ai sai dai na kalleta kawai 'kiri-'kiri tana nuna mini 'kyama ta kuma fito da hassada da kishinta muraran a kaina ciki dai da izinin Allah sai na haifehe ko ana so ko ba a so gwara ma mutum ya ha'kura ya barwa Allah ikonsa Maganganun Hauwa sun yi mini nuni da cewa tabbas ta ji ciwon abinda na yi wanda har hakan ya sanya suka hade mini kai ita da mijinta. Amma kuma sun yi tsauri ga hajiya Saratu wata'kila ko ta manta da cewa ita din yayar mijinta ce fa ba kanwarsa ba, a tunanina ko kanwarsa girma da shekarunta bai kai ace ta tsaya a kanta da fitsara. Ni idan ta yi mini kishiyarta ce ba abin damuwa ba ne tunda da kishi a tsakaninmu amma ni da ban had'a jini dasu ba ba zan ta'ba yi wa mai shekaru irin na Hajiya Saratu rashin kunya ba. Abinda ya haddasa musu rikici kenan a tsakaninsu sai ya zamana ni na shiga tsakiya kuma a ta dalilina komai ya faru Hajiya Saratu fadi take yi "Ba za ta je ta zauna miki ba din, ko ita ce ta yi miki cikin, ai ni Amina ta yi mini daidai duk abinda za ku ce akanta kun dade baku fad'a shegiya mara kunya ki dubi tsabar idona ki dinga nema ki zage ni saboda kin samu kanki ko, idan kin manta bari na tuna miki ni Yaya nake ga Tajo ba k'anwa ba balle ki ce za ki gaya mini magana son ranki Ubanki zan ci domin ba na ciki da iskancinki shashasha mara wayo kawai, ai iliminki bai amfana miki komai ba sai rashin dubara." Tana kuka sosai take fad'in." Ai ba sai kin zage ni kin aibata ni zai tabbatar mini da cewa' Ba kya kaunata ba, duk dai abinda za ki yi a kaina ba yadda za a yi ki ce ni ba jininki ba ce, aure kuma dole dake da wad'anda ba su k'auna ku yi hakuri gashinan har da rabo a tsakani, idan ba aikin asiri ba menene wannan an ce ta na yin surukulle irin nasu ba barebari kin k'aryata ni, duk yadda ki ke kaunarta ni ce dai taki ba kuma yadda za ki yi da ni." Hajiya Saratu ta fusata ainun ta fitar da hannu ta tsinka mata mari tana cewa." Babu ruwana da wai kina da ciki Hauwa ni ba Hajja ba ce ba kuma zan yarda da cin kashi ba, sau dubu wallahi a yanzu gwara Amina dake tunda ita tana ganin girma da mutuncina, ke kam kin yi asara ba kuma ki ji dadin halinki ba. Hauwa ta dinga kuka daga tsaye Hajiya Saratu na fesa mata kausasan maganganun har Hajja da inna Uwani suka shigo d'akin suna tambayar abinda yake faruwa. Ni dai sunkuyar da kaina kasa na yi domin ban san abinda zai kuma biyo baya ba, abinda dai na yanke a cikin raina shine ko kasa da sama za ta hade ba zan kara zuwa sabgarsu ba har abada sai dai duk abinda zai faru ya faru. Hajja tana gama jin abinda ya assasa rigimar ta juya ta fita amma fuskarta kadai zaka duba ka tabbatar da cewa ranta a b'ace yake. Shirun nata kuma sai ya yi ma'ana domin idan ta yi magana za a ga kamar ta goyi da bangare daya amma a zahiri kowa ya san Hauwa ita ce mai lefi Haka muka wayi gari rayukan kowa a b'ace da da kyar ma inna Uwani ta amshi gaisuwata haushina take ji sosai a ganinta ba kowane ya haddasa rigimar nan ba sai ni tunda ni ce bare a cikinsu kuma hajiya Saratu ta zabe ni akan 'yar uwarta. Da sassafe washe garin sadakar uku muka d'auko hanya amma banda Hauwa wai sai ta dan kwana biyu tukkuna kodai ba ta zauna ta haihu ba sai cikin ya yi k'wari tunda duk dambarwar da ake yi duka cikin bai fi wata uku ba. A gidan Hajja muka ya da zango ban kuma tafi a ranar ba tunda dare ya yi sai da gari ya waye tukkuna na shirya tafiya har yanzu da damuwar abinda ya faru a tare da ni dalilin ma da ya sanya kenan ban bar gidan ba sai da na tabbatar da cewa na wanke kaina a wurin Hajja na kuma kar'bi gyara da kuskuran da na yi, amma na nuna mata har abada Hauwa ba a matsayin kishiya na d'auketa ba 'yar uwarta ce kuma ni ma ban ji dadin rikicin da ya faru duk ta dalilina ba. Muka rabu ba k'ullatar juna yayin da muke ta bawa juna ha'kuri ni da Hajiya Saratu tana ganin ni akayi wa lefi ai ni ya kamata a tausa acewarta tijarar da Hauwa ta yi mata kuwa ai kanta ta tonawa asiri ba wani ba har yau har gobe kuma tana goyon bayana ko mata dari Tajo zai ajiye a gidansa ni ce dai wadda ta aure shi a lokacin da mata suke gudunsa. *** Kwanaki biyar da dawowarmu na fara mantawa da abinda ya faru amma dai duk da haka sai dana sanar da anti Yagana irin wulakancin da nasha na kuma tabbatar mata cewa ni da kara shiga danginsu har abada duk abinda zai yi sai dai ya yi amma ba ni ba kusantar abinda ya shafi Hauwa. Ban kira shi ba kamar yadda bai kira ni ba kuma nasan yana da tabbacin mun dawo indai gaba ce ya yi ga fili nan ga mai maidoki sai mu zuba. Sosai na mayar da hankalina wurin addu'a tunda na fahimci kamar zama da auransa ba mai karewa ba ne, ina addu'a sosai tare da kula da kaina na kuma yi kokarin cire damuwarsa a raina hankalina ya karkata wajan cigaba da hurdodina a cikin gidan dai tunda ba na fita amma Hamusu yakan zo sa'i da lokaci mu yi lissafi haka zalika ma Usaini yana zuwa don shi kusan kullum ma muna tare. Yanzu har kaya nake bawa Sahura cikin sau'kin farashi tana tafiya dasu wurin aiki itama ta d'ora nata akai ta samu. Haka zalika ma Usaini yana turawa Maman bokola kaya can garinsu akan sari yadda zata samu nata A cikin wannan yanayin lokacin zuwa ziyara makarantarsu Kamalu ya yi. A wancan karon ban samu zuwa ba sai Hamusu ne ya je tare da Baba Inuwa kanin mahaifinsu da yake can wani kauye da iyalinsa a k'aramar hukumar Sumaila can ya je ya d'aukeshi suka je na dai tura masa kudi a lokacin da za su tafi na ce ya yi masa sayayya sosai sannan ya bashi wasu ya rike a hannunsa ko zai bukaci wani abu. Wannan karon kam tare za mu tafi domin yaron yana raina sosai kawai ina dannewa ne don ganin yadda Allah ya canza masa rayuwa a duk lokacin dana kalli hotonsa ina jin dadin ganinsa cikin nutsuwa don hotonsa ne akan fuskar wayata yana ri'ke da al'kur'ani mai 'kirar warshu yana ta karatu wata'kila ma bai san lokacin da aka yi hoton ba. Wani malami ne daga cikin malaman makarantar ya turowa Hamusu hoton ta whasap a tun farkon kaishi makarantar yanzu kuwa nasan ya k'ara girma sosai tunda abincin da suke ci hatsi ne (datsa) kuma suna noma suna aikin karfi ana koya musu sana'oin da koda an sallamesu zasu dogara da kansu. [9/17, 9:38 AM] Aunty B: 84 Cikin rashin sanin yadda zan yi na sanar dashi maganar zuwa ziyarar Kamalu na kira Hamusu a waya na ce ya kira shi ya gaya masa tafiyar tunda dama farkon zuwanmu ya ce da Hamusu duk lokacin da za a je duba yaron a sanar da shi. Da wannan na samu mafaka Hamusu ya ce mini ai tun shekaran jiya suka yi waya ya sanar dashi ya kuma tura masa kudi har dubu dari wai ya yi kudin mota alheri kuma dama sa'i da lokaci yana taimakawa makarantar. Babu yadda zanyi dole na ajiye nawa girman kan na nemi izini muddin kuwa Ina son zaman lafiya ba zai yiwu ace na je ba tare da saninsa ba. Ga mamakina kiran farko ya daga kamar dama yana tsammanin kiran nawa. Na dan yi shiru Ina dawurwura kafin daga bisani na daure na fara gaishe ya amsa a nutse kafin ya furta." Ya aka yi?" Na ji wani iri da tambayar da ya yi mini ta ya akayi kawai sai na danne na ce." Lokacin ziyarar Kamalu ne ya yi kasan wancan karon ban samu damar zuwa ba to shine na ce yanzu bari na sanar da kai Hamusu ma ya ce kun yi waya shekaran jiya ko." "E, ya gaya mini zasu tafi tare da kanin mahaifinsu wanda suka je tare dashi a wancan lokacin don haka zuwanki bashi da wani amfani tunda za su je so ban baki izini ba gaskiya.'' Ya fadi maganar cike da kwarin gwiwa da kuma nuna isa da bada umarni. Na ce." To shikkenan." Kawai na kashe wayar na nemi waje na zauna kan kujera da mamaki a tare da ni, gabad'aya ma rasa wane irin tunani zan yi akan wannan zaman da muke yi ni da shi shikkenan saboda wani dalili sai ya 'kullace ni akan son rai. Rigima ce dai yake so mu yi domin ba yadda za a yi a ce ya dinga take mini hakki da gangan! na tabbata da shi ya haifi yaron ai ba zai hana ni zuwa ganinsa ba, dama yana nema hanyar da zai 'bata mini rai sai gashi ya samu dama. Yini na yi cikin takaici da b'akinciki ga Yusura bata nan ta je gida suna da biki can dangin babanta sai kad'aicin ya yi mini yawa sai da na yi kuka tukkuna na samu sasaauci kuncin da zuciyata take ciki. Na kira anti Yagana na gaya mata irin yankar k'aunar da mutumin nan yake yi mini a zahirance kowa ya ji abinda ya yi ya san bai kyauta mini ba. Ha'kuri dai ta bani ta ce mini na kyaleshi duk abinda zai yi akan yaran domin Ina iya yin magana ya juyata tunda kiris yake jira ya ce don bashi ya haifesu ba ne zan nuna masa iko kiri kiri ya raba ni da Yusi duk sha'kuwar da take tsakanina da yaron nan ko nema na baya yi a waya haka ina ji Ina gani na ha'kuri babu damar da zan yi magana. Kuma Bai zama lallai na gayawa Hajja ta goyi da bayana ba tunda yanzu bata yayina dole na ha'kura don babu yadda zan yi Hamusu sukaje suka dawo lafiya lau da albishirin Kamalu ya sauke al'kur'ani maigirma yanzu yana kan yin hadda ya kuma fara rubuta shi. Farincikin hakan ya matar da ni takaicin da nake ciki domin yadda Hamusu yake yi mini bayani Kamalu ya zama gwani sosai domin suna zaune a wurinsa ba tare da ya d'auki al'kur'ani ba ya karance musu izifi ashirin daga sama. Muka yi waya da Gwaggo a washe garin ranar wadda itama take cike da farinciki na ce mata ranar juma'a jibi kenan a yi abinci mai kyau a yi sadaka dashi duk abinda ake bukata na umarci Hamusu da ya fitar da kudin da za su wadata Allah Ya amsa mana addu'a ya kuma shiryi yaranmu. ** Bayan sati daya Yusura ta dawo amma tare suke da wata dattijiwar mata wadda na sanya Sahura ta nemo mini domin taya ni aiki dukda aikin gidan bashi da yawa ni kadai ma zan iya yin abina to amma nasan zaman matar tare da ni zai d'ebe mini kewa dalili ko ma'kota bai ba ni damar hurd'a dasu ba yadda ya sanya masu tsaro a gidan na tabbatar da cewa ya yi hakane domin su sanya masa Ido akan duk wani motsina shiyasa tun bayan dawowarmu daga Bauchi babu inda na je gashi yau kwanaki arba'in da biyu kenan da tarewata a gidan ina kuma lissafi kwanakin ya yi daidai da lokacin da ya k'ulla gaba da ni. Watanni uku kacal na d'iba masa idan bai ajiye gabar ba sai dai ya ji labarin na bar gidan domin ba yadda za a yi ace zama ya yi kyau ta irin wannan sigar manya za su shiga maganar a bawa mai lefi lefinsa mai gaskiya a bashi gaskiyarsa. Baba Tabawa sunan mai aikin da Sahura ta samo bata ta'ba haihuwa ba har ta fara manyanta mijinta ya rasu ya bar mata gadon gidan da take ciki a yanzu. Yadda Sahura take yi mini bayani tun bayan rasuwar mijinta take fadi tashi don wataran ma takan kwana da yunwa saboda rashin abinda zata ci da rashin haihuwa don da ta haihu ko daya ne zata samu mai tallafarta wataran har gefe titi take bi ta yi bara da daddare ankara da hakan ya sanyan a unguwar aka samu wani mutum ya sanya mata kwano yana bata abinci Baba tabawa ta kwanta mini a rai dalili kuwa shine macace mai nutsuwa addini da sanin ya kamata a d'an zaman da nayi da ita na 'yan kwanaki na karanceta tsaf tana da gudun duniya kuma tana da zuciyar neman na kanta dalilin ma da ya sanya kenan lokaci guda ta amince da bukatar Sahura a lokacin da ta je gidanta ta sameta da maganar. Sai zamanta ya rage mini kad'aici mussaman idan Yusura ta tafi islamiyyar dana sanyata anan bakin titi domin ta cigaba da dora haddarta kasancewar dama ta yi saukar al'kur'ani wattanin shida da suka wuce wanda ya yi daidai da lokacin da ta zana jarrabawar fita daga secondary da kaina na yi tunanin sanyata a makarantar saboda zaman a haka bashi da amfani zata sake d'aukar darrusa masu muhimmanci kafin lokacin auranta tunda makarantar ba wai al'kur'ani kawai suke koyarwa ba har da sauran littafain na addini za ta kara sanin tsarki da hukunce-hukuncensu. Ranar da Sahura ta zo yini muka yi muna magana daya har dai na gaji na yi mata shiru domin kuwa ba zan ta'ba yin abinda take so ba don ban ga abinda na yi ba ai na d'auka sai mutum ya yi lefi tukkuna zai ta bibiyar wanda ya yi wa domin ya yafe masa. Ita kanta tasan maganata akan daidai take ba zai yiwu ace sun mori juna sun jiyar da kansu dadi ciki ya samu ace ni kuma dake gefe na je na yi musu wahala ba, ai ba yarinya ba ce balle ace kuma ita din menene bata sani ba tunda malamar asibiti ce duk wanda zai zage ni ya dad'e bai yi ba abu ne mai mutukar wahala wata mace ta aminta da hakan. Ita Sahura wai kada mutane su yi mini wata fassara ko a juya maganar ace ina yi mata b'akinciki don ta samu cikin haihuwa wanda ni kuma wallahi babu wannan a cikin raina komawa ne kawai ba zan yi ba, ni ma a lokacin da na samu nawa haka nayi ta fama dalilin ma da ya sanya kenan nake d'agawa Hadiza kafa saboda wahalar da ta yi mini. Wai lallai sai na kira shi na bashi ha'kuri na gaya mata ha'kuri kuma na nawa lamarin da ba yau akayi shi ba an kusa wata biyu to me zai sanya na damu kaina. Ina nan dai da kudirina wata uku na cika idan bai zo ba to kuwa zan san inda dare ya yi mini ai ko addini wannan abin da yayi ba daidai ba ne kuma daf yake da ya lalata auransa. Duk hujjar da ta kawo mini zan soke ta dole sai ta ha'kura ta kyaleni ta tafi da b'acin rai dalilin da na ki na yi abinda take so. Babanmu da Baba Sule suka zo ranar wata jumaa bayan an sakko daga massalaci na ji dadin zuwansu sosai na shirya musu abinci mai kyau suka ci suka koshi suna ta yaba gidan da fatan alheri na dinga nazarin Baba Sule gabad'aya duk ya susuce tufafin ma dake jikinsa kamar ba wankakke ba takalmi irin soso shine a kafarsa. Babanmu ne kawai cikin sutturar arziki tsaf dashi, sai na ji kunyar hakan a cikin zuciyata ko babu komai Baba Sule uba ne duk lalacewsa kuwa, duk ranar da babu ran Babanmu dole shi din zamu k'alla a matsayin Ubanmu kuma idan da kara duk wata taguwa da zan dinkawa Babanmu shima ya kai ace na had'a dashi ganin da na yi masa babu kintsi ya sanya jikina yin sanyi domin yanayinsa ya nuna yana buk'atar agaji ilai kuwa ashe damuwa ce mai yawa a tattare dashi dalili ubangidan nasa Alhaji Muntari ya karye jinya ta cinye masa kudi ga tarin bashin mutane dake kansa komai ya karye masa wasu sun ha'kura wasu kuma sun ce sai an biya su, wannan dalilin ya sanya gidan da yake ciki aka sanya shi a kasuwa domin biyan bashin da yake kansa. Yadda Baba Sule yake mini bayani lamarin ya bani tsoro mutuka da gaske yanzu uwargidansa anti Maimuna ita kadai ce ke jinyarsa anti Jamila ta gudu garinsu Bichi bayan ta turasashi ya saketa wai ba zata iya zama ta lalata kuruciyarta a banza ba. Yana gaya mini baban yaronsa namiji wato Turmuzi yana nan yawo cikin tashar Kano line yana bin 'yan kamasho da samarwa da matafiya mota a sallameshi ya lalace da shaye-shaye tunda wasu lukutan a tashar yake kwana sai yayi sati bai je gida ba. Kuka sosai na dinga yi ina kiran sunan Allah amma anti Jamila ba ta yi wa kanta adalci ba, ni a tsarina duk wahala ba zan iya watsar da yarana akan jin dadin duniya ba, babu ma yadda za a yi na tafi na bar yarana a wurin da nasan ba zasu samu kulawa ba hankalina ma ba zai ta'ba kwanciya ba. Anti Maimuna ta ba ni tausayi sosai ita kuma tata jarabawar kenan rayuwa kenan. Ba ni da halin da zan iya biyawa Alhaji Muntari bashi har na kusan miliyan talatin gabad'aya ma abinda nake juyawa bai kai hamsin ba ribar da take fita yau da gobe da ita muke buk'ata ni da Hamusu da kuma biyan yaran shago hakkinsu. Alhaji Tajo shi yake da iko koda miliyan dari ne don ya fitar ya bayar ba na tsammanin dukiyarsa zata girgiza amma da nauyi sosai a ce na tunkare shi da wannan maganar har cikin raina nake jin wani iri dangane da ibtila'in rayuwar da ya faru da Alhaji Muntari domin ko banza ya taimaka mini ni ma a can baya a wannan ga'bar ya kamata ace na tagaza wani abu kafin akai ga kar'bar kudin gidan da yake ciki wannan duniyar ta zama abar tsoro. Haka na kwana na yini da tunanin hanyar da zan bi wurin ganin na nemi taimako daga wajan wannan wannan d'an tahalikin ba tare da ya fassara ni ba. Na kira anti Yagana na gaya mata domin ta ba ni shawara itama dai abinda Sahura ta ce shi ta fad'a na sauke abinda nake ji kawai na neme shi domin yin hakan babban taimako ne da zai sanya ni dashi mu tsinta a ranar lahira. Na yi na'am da shawararsu domin a raina na ji zan iya jure cin kashi da bakaken maganganunsa muddin zai taimaka ai me nema baya fushi ni ko bashin ne ma ya biya masa su dai zauna a gidan ni kuma zan yi kokarin ganin na d'auki nauyin kaishi babban asibiti domin a duba lafiyarsa sosai. Na samu lokaci ranar lahadi da la'asar domin a irin wannan lokacin ne yake free sosai na kira shi a waya daf da zata katse ya daga yana sallama. Na amsa a nutse kafin na gaishe ya amsa can kasa kamar wanda yake cikin mayen bacci. A sanyaye na ce." Dama na kira ka ne kawai na gaisheka na ji ya kuke ina Yusi." Ya ce." Ina nan lafiya muna nan Abuja tare dashi gidan babban abokina Alhaji Amadu na taba baki labarinsa ko?" Na ce." Eh kun dai ta'ba yin waya sau daya a gabana ina yawan jin sunansa a bakinka." A dan sanyaye ya furta." Yana nan rai a hannun Allah Amina yana jin jiki muna kan shirye shiryen tafiya asibitin jiddah nan da kwana uku" Jikina a mace na ce."inna lillahi me yake damunsa haka?" "Kin san yana da ciwon zuciya dama to wannan karon da ciwon ya motsa masa abin ba kyau ni har na fara fitar da raina a kansa Amina." A sanyaye na ce." In sha Allahu zai tashi zai samu lafiya." Ya ce." To Allah Ya sa, ina fatan dai lafiya kuke na yi mamakin kiran da ki ka yi mini a wannan lokacin da ban yi tsammani ba, ni da kika kullace ni kina gaba da mijinki ko Amina baki damuwa da halin da nake ciki ba, ai ina kallon yadda ake soyayya a wurin Hajiya Maryam mai d'akin abokina Alhaji Amadu amma ni da nake da mata biyu kun yi watsi da ni ko, ita waccan din idan an yi mata uzuri ke fa? son ranki kike bi, ba ki damu da abinda zai same mu ni da Yusuf ko ba haka ba ne?" Jiki babu kuzari na ce." Ban kyauta ba ka yi hakuri amma me yasa ka gaza fahimtata ya kamata ku yi mini adalci a wannan lamari sai ka tsiri gaba da ni, ban kullaceka ba kaine ma kake jin haushina dalilin da ya sanya ma kenan na ga rashin dacewar haka na kira ka yanzu domin mu sasanta gabar ta isheni haka. "To tunda kin nemi sulhu zuwa za ki yi inda nake ai ki lallaba ni domin ni ma ba ni da wata lafiya rashin lafiyar abokina ta dame ni a kwanakin nan Ina buk'atar mai kula da ni ta ba ni magani ta kuma kwantar mini da hankali da kalamai masu dad'i zuciyata ta daina yi mini tunanin kamar ban yi sa'ar iyali ba." Cike da mamaki na furta." Yallabai duk me ya kawo wannan maganganun don Allah." Ya nisa kafin ya sake cewa." Kulawar da abokina yake samun wurin iyalinsa shine ya sanya nake jina kamar maraya gashi dai babu abinda Allah ya rage ni na jin dadin duniya amma matata ta na yi mini wulakanci." Dariya maganarsa ta ba ni wai wulakanci wato shi baya duba abinda yake yi mini a matsayin wulakanci saboda namiji ne duk abinda ya yi daidai ne." Na yi dariya 'yar kad'an kafin na ce." To shi ba ka ganin bashi da lafiya ai dole a ninka bashi kulawa ko ka manta lokacin da ka yi mura a gidana yadda na dinga lalla'baka ina rarrashinka kamar jariri." Ya ce." Ni dai na gaya miki zan sanya a kawo miki ticket da za ki same ni anan abuja gobe kafin mu wuce saudiya ki ba ni magani kada na tafi da lalura. A dukunkune yake maganar amma na gama fahimtar inda ya dosa wannan ya nuna mini cewa a mutukar bukace yake dauriya ce kawai da son dole sai an nuna iko ba zai neme ni ba muddin ba ni na neme shi ba yanzu kuwa dana tsaga billena na kira shi kai tsaye yake neman abu a wurina. Ni ma saboda tawa biyan buk'atar yasa babu ja'inja na amshi gayyatarsa nasan ta wannan hanyar zan iya samun abinda nake so kai tsaye tunda Allah Ya riga ya ga zuciyata da munufaar da zanyi hakan. [9/18, 9:57 AM] Aunty B: 85 Direbansa ya turo da mota ya d'auke ni bayan saukata a garin abuja kai tsaye gidanshi da yake maitama ya nufa da ni kamar yadda ya umarci direban nasa mai suna Ade wani bayerabe mai gaggausan jiki da rashin fara'a. Sai dai da yake ya san matsayina duk cudewar fuskarsa bai hana shi risina mini ba. Gidan kwatankwacin na Legos me d'auke da bangarori da dama kuma cike da ma'aikata da masu tsaro da iyayen motacin da na tabbatar da cewa wasu ma sai a yi shekara ba a hau su ba. Wurin ajiye motoci ya nufa domin gyara parking yayin da nake hangen maigidan da Yusi can daga nesa bakin wata bukka irin ta hutawa. Yana kashe motar ya fito da sauri ya bude mini kofa har yana dan risinawa na fito a hankali Yusi ya tawo a guje ya rukunkume ni yana dariya mamaki mai yawa ya lullubeni ganin yadda yaron ya yi wata iriyar ki'ba kamar wanda aka hura ya zama kato Na dinga binsa da kallo irin na mamaki da al'ajabi wannan wace irin ki'ba ce. Maigidan ya k'araso wurin yana sanye da jallabiya fara mai karamin hannu kansa da fara hula irin ta larabawa as'usul idonsa da farin gilashinsa. Na dube shi na 'yan dakika na fahimci zurmawarsa ya kara tsukewa dama abinka da mai karamin jiki ko dai da gaske yake shima din bashi da lafiya. Ade ya fito da k'aramar akwatina da na zubo kayana kala uku a ciki ya tsaya suna magana ni da Yusi muna gefa ya rike hannuna gam a cikin nasa yana cike da tsananin farinciki ni kam kallonsa kawai nake yi har na gaza ha'kuri na ce." Kai me ka samu ka ke ci ka zama d'an lukuti kana duba mudubi kuwa?" Dariya ya kama yi yana cewa." Abinci kawai nake ci ai an yi hutu makaranta Mama amma ina hawa gym na tsinka jina na." Na dube shi a lokacin da ya zo ya tsaya gabanmu Yana cewa." Ke kuma daga zuwa sai tuhuma." Yar dariya na yi a hankali na ce." Abin ne ai da mamaki wallahi kibar ta yi yawa." Ya wuce ciki yana cewa." Ke ki ka gada masa ai ba kowa ba.'' Yusi ya kamo hannuna muka bi bayansa yana ta yi mini labari yaran Alhaji Amadu wanda suka zama abokansa jinsa kawai nake yi amma ban ce komai ba sai dai zuciyata cike take da farincikin ganinsa cikin walwala da kyawun yanayi tare da lafiya da suttura irin ta 'ya'yan manya a jikinsa. Ga gida har gida babu abinda babu a ciki ko 'diyar shugaban kasa za a iya ajiyeta a gidan amma kash babu mace a cikinsa asalima ya tanadi gidan ne kawai domin idan ya zo garin ya sauka a cikinsa tunda karfin zamansa ya fi legos. Ya d'an ba ni tausayi kad'an domin kamar yadda ya fad'a cewa Allah bai tauyeshi da komai ba na jin dad'in duniya sai ta bangaran iyali, Ina ganin da zamansa anan yake dindindin zan iya ha'kura da can na zauna tare dashi to karfin zamansa ba anan yake ba, ni kuma gabad'aya zaman legos din ne ya fice mini daga raina. Wajan cin abinci cike yake da cima kala kala da kayan marmarin dogon daning ne mai d'auke da kujeru takwas gaba da baya tsarin gidan gwanin ban sha'awa kuma a gare cikin tsabta kasancewar akwai masu aiki maza da suke yi hidima a gidan koda baya nan. Sama ya hau nan turarkarsa take Ade ya shigo da akwatina ya ajiye ya fita, Yusi ya tashi da sauri ya bi bayan shi yana kiran sunan shi na bi yaron da kallo da alama akwai sabo a tsakaninsu. Ajiyar zuciya na sauke a nutse nake bin falon da kallo ya tsaru ainun ya ji kujeru da labuleye na alfarma hotonsa dana iyayensa gasu nan birjik a falo can na hangi na baby Nana kato a wata kusurwa a jingine ba a kafe shi a bango ba. Na jima tsaye ina duba hoton na share kwallar da ta ciko a idona na d'auka a gidansa na legos kadai ya ajiye hotonta ashe yana dashi a nan d'in ma. Yana ba ni tausayi sosai a wasu lukutan domin shi din abun tausayi ne.... Sai da na d'an samu nutsuwa tukkuna na tashi na hau saman tunda nan naga ya nufa ai nasan wulakanci da shan kamshi zansha shi nasan sai dai na kai zuciyata nesa. D'akuna hud'u ne kowanne a rufe sai guda daya da naka key a jikinsa ta waje hakan ya tabbatar mini da cewa yana cike ina ta'ba kofar kuwa ta bude na shiga da sallama a bakina. Ya fito daga bandaki daidai lokacin da na shiga d'akin wanka ya yi ya ce." Shigo ciki sosai mana." Na kàrasa na zauna gefan gado ina dubansa da gaske fa ya rame yanzu na sake gazgatawa da babu riga a jikinsa sa towol da ya dauro. Ya dube ni yayin da yake ko'karin zama kusa da ni yana fad'in." Ya gajiya?" Na daure a hankali na ce." Alhamdulillahi ya jiki ashe da gaske dai ba ka da lafiya Baba." Ya ce." Lafiyata lau me ki ka gani?" Kai tsaye na ce." Ramewa na ga ka yi?'' "Fargaba ce kawai wallahi na jima ban ga ciwon da ya tayar mini da hankali kamar na Alhaji Amadu ba sam ya'ki jin magani, yana nan fa sai dai a kwantar a tayar na gaya miki yana asibiti a yanzu amma jibi za a yi masa transfer zuwa asibitin makka. Cike da alhini na ce." In sha Allahu zai samu lafiya kaima ya kamata ka cire damuwa daga ranka kada wani ciwo ya sameka ka rame fa sosai Baba dama kai ba jiki ba." Yana yi mini wani irin kallo ya ce."Abin har da zolaya Amina." Girgiza kaina na yi a hankali na ce." Ban isa ba, kawai dai ramar taka ce ta d'an tsorata ni Yusi kuwa kamar wanda ake hurawa." Ai irin jikinki ne dashi na gaya miki ke ce ki ka gada masa 'kiba. Ya tashi ya nufi wardrobe yana fito da kayan da zai sanya ya ce." Da daddare idan kin huta za mu je ki duba shi ko?" Na ce." In sha Allahu rabbi." D'akin ya yi shiru na mintina shi yana ta hidimar shirya jikinsa yayin da ni kuma nake bin d'akin da kallo karaf idona ya sauka kan dirowar dake gefan gadonsa karamin hoton Samira ne irin wanda ya ajiye a gidansa na legos wanda na sanya ya cire shi. Kishi na ji ya soke ni, ai ta riga ta mutu shekara da shekaru ya kamata ace yanzu ya cire ta a ransa amma ace kowane gidansa da hotonta a ajiye ban san menene amfanin hakan ba. Ya juyo yana kallona ni kuma na janye idona daga kan hotonta ina ko'karin danne abinda nake ji. Bai ce mini komai ba ya zauna gefan gadon tare da gyara zaman hoton dukda ba abinda ya yi ganin haka ya sanya na tashi tsaye sai ya yi saurin fad'in." Ki yi wanka sai mu sauka mu ci abinci ko?" Ban ce komai ba na nufi bandakin zuciyata babu dad'i hotonmu ya fi kamata a ce ya ajiye gefan gadonsa ba na wadda bata raye ba, na fahimci har yanzu akwai sonta a cikin zuciyarsa hirarta ne kawai ba ya yi mini tunda ya fahimci ba na so. Muna cin abinci yake gaya mini Yusi a gidan abokin nasa yake kwana tare da yaranshi da yake matarsa daya Hajiya Maryam auran saurayi da budurwa suka yi kuma da yake 'yan boko ne sun tsara rayuwarsu haihuwa uku sukayi suka dakata sun fara da mace mai suna Nusaiba wadda suka aurar da ita shekara biyu da ta wuce anan abujan tana auran babban ma'aikaci a central bank. Sai kuma Salim wanda yanzu yake matakin shekara ashirin Adam kuma sha bakwai. Hajiya Maryam yar boko ce kuma muguwar 'yar gayu ce irin matan nan ne masu kyawun jiki da ado da kwalliya shekarunta sun buya sosai idan ka kalleta sai ka d'auka bata fi talatin ba amma ba haka ba ne shekarunta arba'in da d'aya a yanzu tsabar gyaran jiki ya sanya komai nata yana nan cif mussaman kirjinta tana kula dasu sosai kuma Yar kasuwa ce domin manyan shop ne da ita garin abuja da kano da kuma reshenta a jos tunda asali nan ne mahaifarta amma dai harkokinta sun fi yawa a Abuja tana fita kasashen larabawa mussaman dubai da Qatar da India domin sarin kaya dogwayen riguna takalma sari irin ba indiya da kayan maza Pakistani da kuma bangaran sarkoki abin hannu agoguna da sauransu. Yar kasuwa ce sosai wadda arzikin mijinta bai sanya ta nemi wuri ta zauna ba. Da yana gaya mini Yusi ya sha'ku da yaranta dalilin gidajensu na ma'kotaka da juna ban yi mamaki ba domin na tabbatar da cewa Yusi zai iya zama da kowa saboda yana da hankali da kuma iya mu'amula shi ma kuma Allah ya sanya masa kwarjini da farinjini a duk inda ya shiga. Bayan Isha'i ya d'auke ni a mota da kansa ya yi direving din motar muka nufi asibiti a can muka samu Yusi tare da matasan yaran suna zaune kusa da gadon da mahaifin nasu yake kwance ko'ina na jikinsa sa'kale da na'ura yana ta kokawa da numfashi Gaskiya dan adam ba abakin komai yake ba idan ma kana d'aukar kanka kai wata tsiyane wallahi gwara ka yi karatun ta nutsu domin Allah ne mai sarrafa al'amura gashi dai da kudin wanda da yawa muke ganin kamar sune karshen jin dadi bayan ba haka ba ne mai lafiya shine d'an gata domin kuwa duk wanda Allah ya wadata da lafiya shi ya yi wa arziki.. Ita da yaranta sun ba ni tausayi kwarai da aniya kuma yanzu na sake gazgata maganar da ya yi mini jiya a waya cewa suna mugun tsananin son junansu shiyasa gabad'aya ta susuce! Ta kasance kullum cikin zubar da hawaye...Da kyar ta iya amsa gaisuwata hankalina gabad'aya na kan maigidan nata da ko yatsansa baya motsi shi kansa na lura da kid'imewarsa da likita ya shigo suna magana yake tambayarsa ya ga an sake sanya masa oxygen bayan jiya aka cire ta kuma numfashinsa ya daidaita likitan ya ce masa ciwon ne ya sake tashi d'azu da yamma amma kuma numfashin ya fara daidaita ba kamar d'azu ba. Ya sake duba shi ya fita shi ma da yake likita jikinsa a mace balle ga mu da muke zaune. Sai wajan goma da wani abin muka bar asibitin cikin damuwa da zullumi domin kukan da Hajiya maryam din take yi ya ta ba mu gabad'aya har dashi gabad'aya yanayinsa ya canza shi bai yi na hawaye ba yana na zucci irin mai mugun cin ran nan. Na d'auka damuwar da yake cike ba zata bari ya nemi wata buk'ata ba. A daran bai iya bacci ba sai da ya kwanta da ni irin kwanciyar da na ji jiki a hannunsa har abin ya fara ba ni tsoro ganin yadda ya 'kirkiro wani style wanda ba mu ta'ba yin irinsa ba. Ban fahimci komai ba sai wahala saboda bai jima yana yi mini wassanin soyayya ba ya fara gudanar da abinda ya kud'irce a cikin ransa wanda tun ina yi masa kawaici har dai na gaza ha'kuri na gaya masa fa bana gane komai sai zafi da ciwon cinya. Ya ce shi ta haka yake so ya yi don ya fi jin dadi. Haka nan na ha'kura na kyaleshi ya dingi yi tamkar wani sabon angon da jima yana shan sassa'ke. Wallahi kasa juriya na yi don duk fitinata wannan lamarin ya sha kaina kamar da zalinci a ciki. Ashe lumbu lumbu ya yi mini na zo hannu ya yi mini 'keta kuka kariris na dinga domin ya rabu da ni yana fad'in bai gama ba. Da ya gama kuwa sai da na yi ruwan d'umi sannan na ji sasaauci na nemi waje can nesa dashi na kwanta cinyoyina suna ta ciwo. Na jima kafin bacci ya kwashe ni ina ta kallonsa yana baccinsa hankalinsa a kwance. Can gefin asubahi kiran da ya shigo wayarsa ya tashe mu gabad'aya a zabure ya lalubi wayar yana dubawa da sauri yasa a kunnansa Yana fad'in." Alhaji Jamil....."Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! wannan kalmar ce ta fito daga bakinsa bayan ya gama sauraran maganar mai kiran wayar wanda na ji ya kira shi da Alhaji Jamil. [9/19, 10:21 AM] Aunty B: 86 Dama a wasu lukutan mutuwa takan nuna kama kafin wa'adin ya cika. Ni dai dama ganin da na yi wa Alhaji Amadu a wannan dare na sare domin gwiwata a sanyaye muka fito daga asibitin lokaci kawai yake jira amma alamun sallama da duniya ya gama bayyana a tattare dashi. Alhaji Jamil k'anine ga Alhaji Amadu tare suke ta tiriri dashi shi k'aninsa ne uwa daya uba daya shi kuma abokinsa ne tun na 'kuruciya abokin da akayi gwagwarmayar rayuwa. Mutuwar Alhaji Amadu ta dake shi mutuka gaya domin ni sai na ce tunda na tashi daga kuruciya da girma ban ta'ba ganin kukan babban mutum kariris irin haka ba. Na fahimci ya yi kokari sosai wurin ganin ya danne kukan amma hakan bai samu ba kuka ya dinga yi sosai amma ba mai gunji ba yana nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! lamarin ya tsoratani sosai wanda hakan ya sanya ni ni ma fashewa da kukan domin na rasa yadda zanyi na rarrashe shi. Shine akan gaba wajan shirya Alhaji Amadu har aka kaishi gidansa na gaskiya. Duk da babu sha'kuwa a tsakanina da Hajiya Maryam ban nuna bak'untata ba mijina abokin mijinta ne sannan yarona yana tare da nata yaran ta ri'ke gabad'aya dalilin da ya sanya kenan na shiga cikin 'yan uwanta na zauna tare dasu har dare muna kar'bar gaisuwa a tare. Na sake yin karatun duniya sosai domin mutuwa wa'azi ce ga duk wani mumini na kuma tausaya mata kwarai da aniya ganin yadda ta zabge ta ki'dime a lokaci d'aya babu shakka mutuwar miji wani babban rashi ne da har abada ba za a ta'ba maye gurbinsa ba. Sai wajan tara da arba'in tukkuna na shiga gida tunda muna kusa da juna amma ban tafi ba tukkuna sai da na tabbatar da cewa ta ci abinci domin yini guda babu abinda yake cikinta babu irin rarrashin da ban bakin da ba a yi mata ba tace ba zata iya cin komai ba. Itace babba a cikin 'yan uwanta shiyasa da suka gaji da rarrashinta suka ha'kura dalili duk ta girmesu iyayensu kuma basa raye itace ke ri'ke da ragamarsu gabad'aya ni ma na tabbata don tana jin kunyata ya sanya ta kar'bi abincin da na hada mata da hannuna ta dinga ci kamar magani tana goge hawayen da suka ki daina fita daga idonta. Bai shigo ba sai wajan sha biyu saura shi Yusi yana can dama lokacin da ya shigo din har na yi shirin kwanciya amma ban kwanta ba din tukkuna ina dakkon shigowarsa. Wanka ya fara yi tukkuna ya same ni a zaune a gefan gado ya zauna kusa da ni. A nutse nake dubansa gabad'aya bashi da kuzari na ce." Sannu baba ya karin ha'kuri?" Ya amsa da "Alhamdulillahi yana dan duba wayarsa ya ce." Gobe su Hajja suna tafe tare da Hajiya Saratu da sauran 'yan uwan mahaifina." Na ce." Ubangiji Allah ya kawo su lafiya Amma ka ci abinci kuwa?" A nutse ya ce" Na ci amma ba mai yawa ba." "Ko kana buk'atar wani abu yanzu wanda sai sanya cikinka ya dan yi nauyi." "Wannan towon naki nake sha'awar ci irin wanda ki ka yi mini a gidanki amma dare ya yi yanzu za mu bari da safe sai ki yi mini ko?" Cike da kulawa na ce." Muddin da akwai duk abun bu'kata yanzu ma sai na yi maka har da d'umame ai ba wani abu ba ne." Ya girgiza kansa yana yi mini wani irin kallo ya furta." Ba ni da Imani sai na sanya ki aiki da wannan dare duba lokaci fa sha biyu har ta gota." A nutse na ce." To ai aikin lada ne?" Ya d'an jima yana kallona kafin ya girgiza kansa da cewa." Ki huta kawai na gode." Jikina ya d'an mutu da yawan kallon da yake yi mini wanda na kasa tantance na menene na soyayya ne ko na wani abin ne. Wayarsa yake latsawa kafin yasa a kunnansa ban tsammaci da Hauwa yake waya ba sai da na ji yana fad'in." Kin fi kowa sanin matsalar hakan tunda ma'aikaciyar lafiya ce ke to me zai sanya kuma ki aikata, idan kika zubar da cikin ai mun huta gabad'aya tunda ke ba za ki yi aiki da abinda ki ka sani ba." Ban ji abinda take ce masa ba. Ya ce." Ina cikin jama'a ne sosai muna kar'bar gaisuwa abokin nan nawa Alhaji Amadu ne ya rasu nasan zuwa yanzu kin samu labari ko ta kafafan sadarwa ne dalilin da ya sanya kenan ban samu damar amsa kiranki ba gashi yanzu da na nutsu na kira ki da kaina." Shiru ya yi yana sauraranta har ta gama yi masa magana cikin kuka wanda nake jin sautinsa kad'an kad'an. Ya ce." To shikkenan a d'aure mahaifar idan hakan shine solution ai kin fi kowa sanin hakan tunda ajikinki take gobe ki je asibiti da wuri ayi miki aikin Allah Ya sawwa'ke." Ya kashe wayar da damuwa a tare dashi. Ni ma sai na ji hankalina ya tashi wato dai muddin kana raye a duniyar nan ba zaka huta ba. Bai gaya mini ba amma na fahimci kadan daga cikin abinda suka tattauna cikinta ne yake barazanar zubewa. Na gaza ha'kuri na tambaye shi ya ce." Wai fita suka yi suka yi tare da Sadiya tafiyar kasa mai tsayi saboda rashin hankali tasan tana da karamin ciki bayan sun dawo gida shine take ganin jini kad'an kad'an wai tana tunanin cikin zai iya zubewa dole sai an yi d'aurin mahaifa." Da damuwa a tare da ni na ce." Aikuwa dai yana da kyau ta yi gaggawa zuwa asibiti gobe wata'kila tana da matsalar mahaifa bata da k'wari shine dalili amma kuma itama ta yi ganganci yin doguwar tafiya a k'ara tana da karamin ciki kamar ba ma'aikaciyar lafiya ba. Ya ce." Abinda take zargi kenan idan cikin ya zube ai ta huta." Ya k'arasa maganar cikin takaici da jin haushin lamarin. Haka kawai na ji na damu da hakan domin har ga Allah bana so wani abu ya samu cikin Hauwa ba don komai ba sai don ganin tabbatuwar farinciki da walwala a fuskarsa. A yanzu dai zuria itace karshen abinda yake nema a wannan duniyar bayan Allah Ya wadatashi da komai a duk lokacin dana kalleshi na tuna har yanzu bai ajiye magaji ba hankalina yana tashi sosai kuma nakan zubar da hawaye masu yawa domin jarabawar da ta same mu ni dashi na riga nasan ko na saki zuciyata da gangar jikina na haihu za mu sanya rai ne akan abinda muka samu bayan kuma ba mai d'orewa ba ne. Astagfirullahi wannan shine babban dalilin da ya sanya nake ji a cikin raina ko cikin na samu zan iya zubar dashi ba tare da ya sani ba don gudun shiga damuwa matsananciya bayan na bari na haihu muna ji muna gani mu rasa abinda muka samu kamar yadda muka rasa babynmu ta farko. Abin mamaki da daure kai a wannan daran ma na jigatu kwarai da aniya a hannunsa don ban ta'ba tsammanin ma zai neme ni ba ganin irin jimawar da muka yi jiya muna abu daya. Abu na biyu kuma a tunanina gagarimin rashin da ya yi zai dakusar dashi kewar komai na jin dad'in duniya ashe ba haka abin yake ba fahimtata ma kamar idan yana cikin damuwa ya fi kulafucin lamarin washe gari na tashi da ciwon jiki matsananci domin irin sarrafuwar da na yi a hannunsa a daran jiya Ina ganin ko ko kwa'babbiyar fulawar borodi ba ta kaini buguwa ba. Ina kwance gado bayan na yi wanka na kasa tafiya gidan rasuwar Yusi ya shigo yana gaya mini wai anti Hamida kanwar Hajiya Maryam tana kira na zo ko zan iya rarrashin antin nasu ta karya kumallo. Na ce masa ya je ganin zuwa yanzu. Da kyar na rarrafa na tashi na sanya hijabi saukata kasa ta yi daidai da shigowarsa hannunsa da ri'ke da carbi da alama daga wurin kar'bar ta'aziyya ta taso ya ce mini na je maza wurin Hajiya Maryam na zauna tare da ita yanzu Adam yake sanar dashi an yi an yi da ita ta ci abinci taki ci. Na ce yanzu Yusi ya zo ya sanar da ni. Na fahimci tunda aka yi rasuwar yake bawa abinda ya danganci matar muhimmanci don jiya ma shine ya k'arfafa mini gwiwar zama a kusa da ita a cewarsa zan deba mata kewa bayan 'yan uwanta. Ban ta'ba kawo komai ba a cikin raina abinda dai na ajiye shine bai ajiye lamarin Alhaji Amadu a nesa ba domin kuwa Allah ne kadai yasan irin taimakekeniyar da suka yi wa juna ba a lokacin da suke neman rufin asiri na duniya. Hajja suka sauka kamar yadda ya fad'a Hajiya Saratu da kannan mahafinsa su biyu Maza a ciki akwai mahafin matashi ta biyu wato Aysha wadda ta rasu sakamakon zazzabin typhoid kafin ta tare a gidanshi. Ba sosai na sansu ba duk da kasancewar suna da yawa kad'an na sani daga cikinsu, hakan yana da ala'ka da rashin zamanmu a gari tun bayan aure dangin Hajja ma in banda rasuwar da aka yi ta kanin mahaifin Hauwa babu wanda nasani daga cikinsu. Wannan karon mun sake sosai da Hajja da alama sihirin da aka yi mata ya warware babu wani kallo na baibai a tsakanina da ita sai mutunci da girmama juna. Haka aka yi zaman makoki na kwanaki bakwai mutumin nan bai daga kafa ba. Kullum da safe zai fita cikin jama'a ya kar'bi gaisuwa da daddare kuma sai ya rikid'e ya koma jarababbe na bugawa a jarida. Wannan dalilin ya sanya na yanke shawarar guduwa ba zan iya ba don ban san abinda ya zama ba kuma idan zai jima anan din bai koma legos din ba Hauwa sai ta zo ta kar'bi lamarinsa domin dai sha'aninsa ya fara ba ni tsoro da mamaki. Ban sanar dashi maganar data assasa mini zuwa ba sai bayan an share makoki kwanaki tara da rasuwar tukkuna na gaya masa amma ta sigar da ba zai zarge ni ba ai taimako ne kuma duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi sosai na gaya masa yadda alhaji Muntari ya dinga fad'i tashin akan lamarin yarana kuma ya rike mini su ba tare da ya bambamtasu da wanda ya haifa ba, na kara jadadda masa cewa abinda ya asassa mutuwar aurena dashi akansa ne saboda rubutun da na yi a fece book akan abinda ya faru wanda ya danganci Kamalu dashi. Bayanin da na yi masa cikin nutsuwa ya sanya ya fahimce ni ya kuma tausaya mutuka da gaske koda yake dama shi mai tausayi dalilin da ya sanya mini fargabar gaya masa saboda tsohon mijina ne ban san fassarar da zai yi mini ba. A take a lokacin ya ce na yi waya da Baba Sule duk abinda muka tattauna sai na sanar dashi zai taimaka in sha Allahu. Ban yi kasa a gwiwa ba kuwa na kira Baba Sule a waya ya gaya mini har yanzu dai ba kai ga kar'bar kudin gidan ba domin duk wanda zai zo tayin wulakanci yake yi. Na ce masa to abar batun sayar da gidan za a biya masu hakki hakkinsu insha Allah rabbi duk wanda yasan yana bin Alhaji Muntari kudi ya yi mini list din sunansu a takarda tare da asusun ajiyarsu idan na dawo sai ya kawo mini ni kuma zan tura masa sunayensu ta whasap sai a biya su hakkinsu. Na sanar dashi yadda muka yi da ya ce hakan ya yi amma fa na ajiye maganar tafiya don su Hajja ne kadai za su tafi bi ba yanzu sai nan da kwana talatin lokacin Alhaji Amadu ya yi arba'in da rasuwa shi ma kuma a daidai lokacin zai koma bakin aiki can Legos. Hankalina ya tashi sosai ba ni da damar yin turjiya tunda ya gama rufe mini baki abinda ya yi a yanzu akan buk'atata ba tare da ya musanta mini ba kudi irin wannan a cikin masu kudin ma ba kowane zai iya bayar dasu ba koda kuwa akwai dangataka mai karfi. Na gaya masa gidana da Baba Tabawa da kuma Yusura da suke can na barsu tsayin kwana goma sha uku ya kamata a ce na koma. Ya ce shi bai sai wata Baba Tabawa ba domin kuwa ba hannunsa wurin ajiyeta gwara ma Yusura ya shedata na kira wayar Mamanta ta zo ta dauketa itama Baba tabawa ta tafi gida idan na koma sai su dawo tunda ina son zama dasu. Ina kallo su Hajja suka tafi ba ni da ikon bin su saboda bacin rai har kuka sai da na yi amma ba a gabansa ba sai da ya fita tukkuna na yi na share na ha'kura na bi abinda yake so. Tun bayan share makokin Alhaji Amadu yake yini a gida sai fitar ta kama tukkuna yake dan fita kuma baya wani jimawa zai dawo. Yakan taba ayyuka a laptop dinshi wasu lukutan kuma a wayarshi tunda yanzu kai ya waye sosai ta internet ya za ka iya gudanar da harkokika na yau da gobe mussaman shi da yake da harkalloli daban-daban. Babu jeka ka dawo haka zalika babu yaudara ko sa'ba alkawari a sha'aninsa wannan kadai ya isa a yi masa shadar arziki domin idan ya ce zai yi abu to kuwa zai yi, idan ya ce ba zai yi ba kuwa babu wanda ya isa ya tursashi. Mutane tara da suke bin Alhaji Muntari kudi sai da ya bi su daki bayan daki ya yi musu tambayoyi kafin ya kowanne daga ciki ya bashi kudinsa daga karshe shi ma Baba Sule ya samu rabonsa don dubu dari biyu ya bashi ya ce ya yi cefenan gida. Na ji dadin hakan sosai kuma har cikin zuciyata na yi masa addu'a samun karshe mai kyau tare da dorewar zaman lafiya a tsakaninmu. Haka nan na cigaba da hakuri da bashi hakkinsa har fargaba nake yi dare ya yi domin Ina gane kurena kwarai kuma idan ya so har da rana ma turkeni yake yi. Ganin haka ya sanya na dage da shan kayan marmari da ruwan kaninfari Ina kuma dan yin farfesu sa'i da lokaci na zuba kimmba da minannas da yawa nasan yin hakan zai taimaka mini sosai. Amma mutumin nan yana goge mini hadda don wadda ya ba ni jiya ba ita zai ba ni yau ba. Har dai na gaza ha'kuri na ce masa ya fara amfani da magunguña maza masu karfi tunda ai da ba haka yake ba na san yana da sha'awa da karfin buk'ata amma bai kai haka ba, babu rufi ya ce mini eh saboda ni yake sha domin rainin da ya lura ya fara ratsa tsakaninmu. Na dinga mamaki sosai da abinda ya ce tabbas kuwa don wallahi yanzu har wani tsoronsa nake ji da fargaba idan ya fadi abu ban yi ba sai na ji shakkar haduwarmu da daddare domin duk kumburin jikina bai hana shi malkwad'ani ta kowace siga ba. Idan kuwa ya rike ni a hannunsa wallahi har cikin k'ashina nake ji Ina ta ko'karin k'wacewa na kasa. Jikin ne dama ba wani kwari domin ba yadda za a yi a hada karfin namiji da mace waje daya gashi dai babu wani nama a jikinsa amma idan ya d'amke ni Allah ne kadai ya san yadda nake shan wahala. [9/20, 9:50 AM] Aunty B: 87 Ban san a Ina Hauwa ta samu labari ina abuja tare da maigida ba sai kawai itama ta tayar da hankalinta akan lallai sai ta zo ta same mu shi kuma yana dakusar da ita akan ta zauna a can Bauchin ta cigaba da rainon cikinta tunda alamu sun nuna tana da matsalar mahaifa duk da ba tafiyar mota ba ce amma yawan zurga-zurgar bashi da amfani dalilin d'aurin mahaifar da aka yi mata domin ita kanta tasan zamanta a wuri d'aya zai fiye mata kwanciyar hankali da nutsuwa. Ina jinsu suna ta bugawa a waya ban ce komai ba, ni zan fi so ma tazo taga uwar da nake ci tunda ita jurinta kishi da ni, na dawo kano itama ta d'aga hankali sai ta dawo yanzu kuma ta ji labarin ina Abuja hankalinta ya tashi sai ta zo taga me muke yi wahala ce dai nake kar'ba nasan kuwa shima da akwai hujjarsa ta cewa ta yi zamanta acan din har sai cikin ya yi k'wari yadda ake so domin kuwa idan ya amince da zuwanta a yadda yake jin karfin nan da fitina kwanciya daya za a samu matsala idan cikin bai zube ba ta ci wahala. Haka na kasance cikin lissafi kwanaki tunda ya ce sai anyi sadakar arba'in tukkuna tunda kuwa na zo garin babu ranar da zata waye dare ya yi bai kwanta da ni ba. Saura kwanaki uku addu'ar arba'in din Alhaji Amadu Baba Sule ya kira ni a waya yana sheda mini rasuwar Alhaji Muntari jiya da daddare yake gaya mini har an yi jana'izarsa. Na shiga rud'ani mai tsananin gaske wanda har na kasa jurewa hawayen na nadamar duniya suka dinga zarya a kumatuna. Da magidan ya shigo ina kukan nake gaya masa rasuwar ya jimanta amma ba sosai ba ya yi masa addu'a a takaice ya cigaba da abinda yake gabansa. Na yini cikin alhini da damuwa duk yadda na so na danne damuwata akan rasuwar Alhaji Muntari na kasa domin daga zarar na tuna dashi da irin zaman da muke yi da wahalar da yasha ta jinya da yadda zuriarsa ke fuskantar kalubale sai na ji hawaye ya zubo mini mutuwar Yaya Aminu sai ta dawo mini sabuwa na dinga goge hawaye a fakaice tunda muna tare dashi yana aikinsa a Lopton ashe duk wani motsina yana hankalce shiru kawai ya yi mini har sai da na ki ci abinci tukkuna ya tanka mini ya fara fad'a yana cewa mutuwa kowa dole sai ya mutu na duba babban rashin da yayi akwanakin nan haka ya ha'kura ya ci abinci kuma ya cigaba da sabgogin rayuwarsa wai na shirya ci masa fuska ne shiyasa na sa shi a gaba ina kuka saboda rasuwar tsohon mijin dana aura a baya. Na yi shiru ban ce masa komai ba domin a lokacin ma da yake mini fad'an kukan nake yi don shi kadai zan yi na ji dad'i akan kaina nake tunanin faruwar hakan ace mace mijinta ya rasu ya barta da yara haka na yi ta fama da nawa yaran dad'inta ma ba a zaune nake ba ita anti Maimuna ba mai wayo ba ce kamar doluwa haka take don ba na tunanin ma ta yi karatun boko gashi yanzu an mutu an bar mata yara ita anti Jamila ta watsar da nata ta gudu saboda rashin tunani. Irin wannan wahalhalun rayuwar kawai nake tunawa sai na ji hawaye na zubo mini ita duniyar nan duk yadda ka kai ga yi mata dabara ta fi ka wayo kuma sai ka tafi ka barta babbar mafita kawai ka ri'ke addu'a kuma kada ka cutar da kowa. Ganin na yi masa shiru ban tanka masa ba sai ya kara fusata wai na tashi na fita daga d'akin muddin abinda zan yi masa kenan yana aiki Ina raba masa hankali. Ni ban ga abin damuwa ga mutumin da ya riga ya rasu ba kuma bayan mutuwar tasa ma abin tausayi ne da taimako a ganina idan ya ce mini akan me nake zubar da hawaye kamar ya so kansa ne tunda shi ma ai ya yi kukan mutuwar abokinsa. Dole a wannan ga'bar ya yi mini uzuri domin kuwa koda ban zauna zaman aure da Alhaji Muntari ba iya hallacin da ya yi mini ya kyautu ace mutuwarsa ta gigita ni. Na san bala'in kishinsa ne ya motsa ba wani abu wannan dalilin ne ma ya sanya na tashi na bashi waje kamar yadda ya buk'ata din tunda ni dai ba ni nake sarrafa kaina ba kuma hawayen dake zuba daga idonna ba ni da kwanji hana su fita. Washe gari da safe sukuku na tashi da damuwa da tunaninka fal a cikin raina na yi mamaki da bai biyo ni ya neme ni ya kwanta da ni ba wannan ce kadai ranar da ya raba mana shimfid'a tun bayan zuwana garin. Da kyar ya amshi gaisuwata yana ta jin haushin koda ya lura da rashin kuzarina sai ya fara 'kirkira mini aiki duk kuwa da yaransa masu yi masa hidima a gidan ya ce na yi masa towo na yi na gama ya ce na hada masa wasu takardu da ya zube a gado nan ma na gama ban ce masa komai ba domin na fara gajiya da abinda yake yi mini. Ya gama abinda yake yi ya zo ya zauna zai ci abinci ina bud'e miyar yaga taushece ya ce ai ba ita ya ce na yi masa ba kuka yake so. Na fara kuka ina fad'in." Ka kyale ni na huta dan girma Allah jiya ban rintsa ba saboda tunanin rayuwar nan ka ce na yi maka towon shinkafa na yi maka kuma yanzu ka ce mini miyar kuka babu kuka a gidan nan sai ku'bewa d'anya ko kwanaki ma da ita na yi amfani jiri ne yake damuna a yanzu kwanciya zan yi." Na zame na kwanta kasan wajan hawaye na cigaba da fita ta gefan ido. Ya d'auki flat din towon da na zuba masa ya tallafe da hannunsa na hagu kamar dai yadda ya saba idan zai ci abinci yana yi masa ladabi sosai kuma ba kasafai yake ci da cokali ba hankalinsa a kwance ya furta." Shin ko dai ke ma bin bayan mutumin nan za ki yi ne Amina." Shiru na yi masa ban ce komai ba. "Da na yi niyyar zuwa gaisuwa amma abinda ki ke yi ya ba ni haushi ba zan je ba." Yafad'a yana kallona. Nan ma ban ce masa ci kanka ba. Ya d'auki ruwa ya sha ya ajiye ya dube ni ina kwance sai ya gyada kansa da takaici ya furta." Ina ganin mutuwar mahaifi ko miji ya kamata a ce an shiga irin wannan matsananciyar damuwar Amina, ni kam wane irin dadi Alhaji Muntari ya ji jiyar dake wanda ya sanya kike ta yi masa kuka tun jiya ko kina da ajandar komawa gidansa ne mu dai wahalar da junanmu ni dake." Zaune na tashi ina goge hawayen idonta na dube shi sosai kafin na ce." Ba ni da ajandar komawa gidan Alhaji Muntari domin kuwa da da niyyar hakan a cikin raina wallahi tallahi da baka aure ni ba." Na numfasa Ina kallonsa shi kuma ya sake hade fuska tare da zubo mini ido. "Abu daya zuwa biyu ya sanya ni kokawa da rasuwar bawan Allan nan ko ka yarda ko kada ka yarda bai dame ni ba na farko shine hallacin da ya yi mini a lokacin da nake buk'atar agaji ya yi mini da kudi da karfinsa daidai gwargwado. Na biyu yadda gidansa ya tarwatse tun yana raye yaranshi suke walagigi ina ga kuma bayan rasu. Maganar nan da muke yi da kai a yanzu hankalina nakan babban yaronshi Turmuzi wanda tun asali nasan da cewa fitinanne ne an ce mini yanzu lamarinsa ya sake ta'barbarewa, ba zan manta ba mahaifinsa ya sha kokawa akan sha'aninsa. Wad'annan abubuwa biyu dana lissafa maka sune suka fi tsaye mini a rai domin kuwa na riga nasan sha'anin zumunci a yanzu ya zama abinda ya zama tunda can ma danginsu ba masu zumunci ba ne balle yanzu da baya raye kuma dama shi kadai ne mai dan rufin asiri a cikinsu. Ni uwa ce kuma na yi gwagwarmayar rayuwa da yarana nasan zafin da ake ji idan aka rasa wani 'bangare dalilin da ya sanya kenan nake tausayawa Anti Maimuna uwargidanshi domin ita amaryar ta gudu ta watsar da yaran yanzu gabad'aya suna hannunta kusan su tara ka gaya mini ya za ta yi dasu wane hali za ta shiga domin ciyar dasu da basu tarbiya. Shiru ya yi bayan na kammala maganata ya nisa sosai kafin ya dube ni a nutse ya furta." Yanzu ya kike so a yi ai na zama rumfa sha shirgi muddin wannan hawayen zai tsaya ki fad'i yadda ki ke so a yi miki zan yi in sha Allahu." A hankali na dube shi Ina nazartarsa akwai sasaauci a fuskarsa da kuma alamun tausayi da nadama kuma tunda ya ce zai yi to babu shakka kuwa zai yi din." "Abinda nake so kawai wannan yaron nasa Turmizi akai shi makarantarsu Kamalu bayan haka kuma ka shirya mana zuwa gaisuwa ni kuma zan zauna da anti Maimuna mu tattauna idan ya kama sai a bata jarin da zata kama sana'a ko?" Idonsa a kaina ya ce." Hakan ya yi miki?" Kaina na daga. Sai ya ce." Ai ni mai aiwatarsa ne tunda haka ki ka tsara shikkenan za mu je amma sai bayan an yi addu'ar arba'in din Alhaji Amadu idan na yi musu ta'aziyya daga nan sai na wuce Legos abinda na manta ban gaya miki ba kuwa hajiya Maryam ta bukaci akan na bar mata Yusi dalilin sha'kuwar da take tsakaninsa da yaranta akaran kaina ban so hakan ba sai dai ba yadda zan yi ne a yanzu tana buk'atar rarrashi da kuma biye mata akan dukkanin abinda take so domin dakushe mata kewar maginanta, nasan macace mai kokari sosai za ta kula da yaron kamar nata sannan ta yi alkawarin mayar dashi makarantar da Adam yake zuwa sai ya cigaba da dora karatunsa ina fatan babu matsala ta b'angaranki ko?" Haka kawai na ji ban ji dadin saurin yanke hukuncin da ya yi ba. To amma ba yadda zan yi koda kuwa raina bai so ba haka zan kar'bi hukuncin da ya yanke na tabbatar da matar tana da wata matsala mai muni ba zai bar mata yaron ba. Washe garin ranar da aka yi addu'ar cikar kwanakin arba'in na rasuwar abokinsa kamar dai yadda ya fad'a muka nufi kano bayan ya jima a gidan abokin nashi wanda na tabbatar da cewa ya shiga ne domin yi masu sallama da kuma kara tausarta yadda yake nuna kulawa da iyalin marigayin nake ji kamar kafin rasuwar tasa ya bar masa wasiyayya ne Gidan Hajja muka sauke ta ce itama sai a yi tafiyar da ita don haka muna idar da sallar la'asar muka nufi gidan Alhaji Muntarin dake kawo jirga inda na zauna yau kwanaki hud'u kenan da rasuwar an tashi daga zaman makokin sai kad'an daga cikin 'yan uwanshi sai kuma Babanmu tare da Baba Sule da suke zaman jiran isowar isowarmu tunda mun yi waya dama. Kai tsaye cikin gidan muka nufa ni da Hajja Yallabai din ya tsaya daga waje tare da Babanmu da jama'ar da suka ankara dashi. Kasa juriya na yi ganin yadda anti Maimuna ta zabge ta zama kamar mashiriciya ba komai ne ya janyo hakan ba kuwa sai jinyya da fargaba da zullumi na rayuwa. Tana tare da kakarta wadda itace ke zaune tare da ita don ta d'eba mata kewar takaba sai kuma yaran gasunan sun kara girma Salimat ta zama cikakkiyar budurwa sai dai dukaninsu babu wata sutturar arziki. Sun gane ni gabad'ayansu suka dinga gaisheni na yi musu ta'aziyya na tambayi anti Maimuna Turmuzi ta ce mini tun washe garin ranar rasuwar uban basu kara ganinshi ba. Nan ta shiga warware mini halin da suke ciki da yadda wasu daga cikin ma'kotan da akayi zaman arziki suke dan taimaka musu ta ce mini ai tun kafin rashin lafiyar maigidan nasu ta yi tsanani Jamila ta gudu ta ce ba zata iya ba kuma duka yaranta ta bari ko bata fadi mini ba na gansu da idona. Muka ci kukanmu muka ko shi ni da ita don kasa ha'kuri na yi a lokacin da take ba ni labarin tana kuka ina yi ina kallon Hajja ma tana share hawaye domin kuwa kowanene dole ya tausaya rayuwar kuncin da suke ciki. Shigowarsu ita ta sanya muka yi shiru Yallabai din tare da Babanmu Baba Sule da 'yan uwan Alhaji Muntarin suka yi musu jagora. Sosai ya yi wa anti Maimuna ta'aziyya ya kuma jajanta mata kwarai tare da yi mata nasiha mai ratsa zuciya da kawo misalai mabambamta daga karshe kuma ya kare maganarsa da jadadda mata cewa zai taimaka mata iyakacin bakin kokarinsa. Godiya kakarta ta dinga yi har da kuka Hajja ta dinga bata baki akan ta daina kuka hakan ba komai ba ne face taimakon kai da kai idan har bai yi hakan da dukiyar da Allah Ya hore masa ba sai ta zame masa masifa. Mun tattauna sosai da anti Maimuna inda muka tsaya a matsaya guda daya cewa bayan ta fita daga takaba zata fara gudanar da kasuwancinta a cikin gida za ta duba abinda ya fi saurin tafiya a unguwar sai ta kafa kowa rabonsa zai samu. Muka nufi gidan Hajiya Dogara domin yi wa mahaifiyarsa ta'aziyya. Matar da kyar take iya kallona saboda nauyi da kunyar abinda ta yi mini akan Kamalu ta dinga godiya kamar ta yi kuka domin alherin da Yallabai din ya yi musu na saukewa mamacin tarin bashin da ake binsa tun kafin ya yi bankwana da duniyar. A ranar da daddare ya aiki Sukairaju da kayan abinci da masarufi masu yawa gidan Alhaji Muntari. A gidana muka sauka gabad'aya har Hajja domin ya fi kusa da Danbatta ga dare ya yi Hajja ta ce da safe ta tafi ba ta son tafiyar dare. Baba Tabawa da Yusura sunan lafiyar Allah kamar ina tare dasu domin abinci da kayan masarufin dake store dina ina tsammanin za su iya hauraa shekara basu kare ba. Bayan haka kuma akwai masu tsaro a gidan kuma mun yi waya da Sahura sati daya da tafiyata na ce ta dinga zuwa gidan tana duba su duk sa'i da lokaci. Baba Tabawa kuwa aka ci sa'a ta yi favorite dinsa towon dawa amma miyar ku'bewa bushashshiya sai dai ta wadatu da daddawa da nama sai kamshi take yi. Aikuwa ya ci sosai har yana tsokanarta wai ta fi ni iya abinci dama idan na yi towo ha'kuri kawai yake yi yana ci. Hajja itama ta yaba mata sosai ta ce mini a ajiye mata d'umame da safe kafin ta tafi sai a d'umama mata shi. Baba Tabawa tace ai kamar ta sani ta yi shi da yawa. [9/21, 10:22 AM] Aunty B: 88 Had'uwarmu ta daran yau sai ta zama ta daban domin kuwa lamarin da ya bijiro dashi bai samu kar'buwa ba a wajena yayin da shi kuma ya kafe kai da fata sai ka ce wanda aka yi wa wahayi lallai ta haka yake so ya biya bukatarsa to sai bijirewata ta wanzar mana musayar yawu domin kuwa ni dai ban ta'ba jin inda aka yi wata kwanciyar aure a tsaye ba. A ganina ma ta wannan sigar ta yaya mutum zai fahimci wani abu ya za a yi lamarin ya yi armashin da kowa zai gamsu. Ya dage shi fa ga ta yadda zai yi domin sai ya fi gamsuwa a cewarsa ko ya koma zai jima sha'awarsa ba ta motsa ba ni kuma na ce ba zan iya jurar tsayuwa ba na amince a yi akwance duk yadda yake so zan yi amma a tsaye ba zan fahimta ba. Ai lamarin na mutum biyu ne ba na mutum d'aya ba. Sai ya fara fad'in ai Ubangiji ya ce ku shiga gonakinku ta kowace siga amma ban da ta waje daya don haka shi yau zai gwada yi a tsaye. Tun abun yana ba ni dariya da mamaki har ya dawo ba ni haushi da ganin kamar yana so ya sauka daga koyarwa addinin musulunci ya bi turbar nasara domin kuwa sune shaidanu masu kirkiro abun da zai cutar da mutane. Ya ce idan ba zan amince ya yi ta haka ba kuwa sai da na yi sucking dinshi har ya biya bukatarsa. To dama dama wannan da sauki tunda wani sa'in ina yi masa amma ba sosai ba don baya ganewa muddin ba wajan nan ya shiga ba. Ya za a yi sucking ya iya gamsar dashi a yadda yake sai mu kwana ba mu rintsa ba. Amma dai na fi aminta da yin hakan akan ya yi a tsaye k'afafuna ma ba zasu iya jurewa ba. Sarewa na yi da sha'aninsa domin kuwa duk tsayin lokacin da na d'auka ina yi masa abinda ya buk'ata din ko gezau bai yi ba wai da sunan samun satisfying yana dai nishad'antuwa k'warai da gaske tabbacin yadda nake yi masa yana jin armashi ammafa babu wani shau'ki na kawowa. Gajiya na yi kawai na matsa gefe daya domin kuwa kafad'una sun k'age dalilin sunkuyo jikina ma gabad'aya ya yi tubis bacci ne yake mamayata. Ganin haka ya sanya ya janyo ni a ki'dime ya fara sarrafa ni akwancen dai ya biya bukatarsa amma ta siga daban daban. Ni kam duk wanda ya bashi shawarar yin amfani da maganin k'arfin maza ya cutar dashi domin kuwa abin nasa yana nema ya yi yawa. Da sassafe ya shirya yana ta zoyalata zai tafi amma zai dinga zuwa ta mafarki ina fad'in duk wanda ya baka shawarar yin amfani da maganin karfin maza ya d'ora ka a hanya mara b'ullewa ai ba a ce kada a yi jima'i ba amma daidai misali yanzu wane hali zaka shiga a can babu mace. Sai a lokacin ya ke gaya mini shi babu wani maganin karfin maza da yasha hana karya dai ya yi amfani da maganin sanyi watan uku da suka wuce lokacin da Falalu mai yi masa abinci ya je garinsu mahafiyarshi ta bashi ya kawo masa a matsayin tsaraba. Falalun ne ma da kanshi ya dafa masa maganin da yake sassa'ke ne da saiwowi ya had'a da citta kaninfari tafarnuwa ya dafa shi sosai ya zuba masa a babbar gora ya yi amfani dashi.....08089965176 Wallahi maganin sanyi ne sadidan har basir ma yana lalata tasirinsa a jikin dan adam. Kaikayin gaba zafin fitsari fitar iska rashin ni'ima zubar fitsari karancin sha'awa ciwon mara ciwon kafafu rashin haihuwa. Ciwon ga'bo'bi rashin gamsuwa maganin kuma maza da mata ne duk wani dattin da yake mara za a fitsarar dashi, ga masu buk'ata a yi mana magana kai tsaye ta lambarmu da muka d'ora za a yi wa Allah godiya kuma za a yi mana godiya. Na yi mamaki sosai da na ji ya fadi haka. Dama ai duk lalacewar namiji wajan saurin kawowa ko rashin dogon zango ko kuma daukewar sha'awar da kankancewar gaba gabad'aya sai dai idan bai yi katari da sahihin magani ba. Haka zalika ma duk lalacewar mace wurin rashin ni'ima bushewa da fitar iska, d'aukewar sha'awa da matsalar rashin gamsuwa daga maigidanta sai dai idan ba a yi katari da ingantaccen magani ba. Haka zalika ma 'yan mata da zawarawan da suke da niyyar shiga d'akin mazajensu yana da kyau su ma su magance sanyin da yake tattare dasu domin gujewa matsala...08089965176 a tuntub'e mu kai tsaye muna tura kayanmu kowane gari. Bayan kwanaki uku da tafiyarsa yanayin jikina ya fara canzawa lamarin ba sabon abu ba ne a wajena amma ban tabbatar ba dai tukkuna har sai da lokacin yin la'adata ya yi ya wuce ban yi ba yayin da ciwo-ciwon da nake ji yake 'kara tsananta. Kakarin amai da safe taruwar yawu kasala saurin bacci da k'yankyami. Ciki ne da ni ba shakka lamarin bai yi mini wani armashi ba domin kuwa ban shirya d'aukarsa ba kuma ba na tsammanin zan gaya masa har sai na yanke shawarar da nake ganin itace mafita ga rayuwata. Ko anti Yagana ba zan gayawa ba balle ta dakusar da ni domin kuwa yana da kyau komai mutum zai yi ya kiyaye faruwar abinda zai sanya shi shiga rud'ani a gaba. A takarda na rubutawa Yusura abin gwaji ta fita bakin titi akwai chamis ta je ta sayo mini da sassafe na yi sakamako mai kyau ya fito positive. Shiru na yi da bakina kuma na dinga kokarin ganin na karfafi jikina don kada Baba Tabawa ta fahimci halin da nake ciki. Ba Allah zan yi wa butulci ba amma ya fi ni sanin dalilina na yin hakan zan nemi maganin da cikin zai fita tun kafin ya kai matakin da za a busa masa rai a yanzu dai bai wuce kwanaki a arba'in ba na tabbatar da samuwarsa ne had'uwarmu ta farko dashi zuwana Abuja tunda lokacin da na je ban fi sati daya da yin wankan tsarki ba kuma ni ba ban yi amfani da wata kariya domin gujewa faruwar hakan ba. Mun had'u sosai tun kafin ma na tafi maiduri mun yi kwanciyar aure amma rabon bai rantse ba sai yanzu. Da kaina na fita da daddare bayan Isha'i cikin hijab har kasa da nikabi har da safar kafa domin yin b'adda kama na nemi maganina na dawo gida. Zuciyata tana dokawa a daran ina ta shawarwari nasha ko kada nasha domin sai nake ganin kamar Allah zai tuhume ni kuma ba zai kar'bi uzurina ba tunda tun farko ai ba a san da menene silar dake haifar da ciwon ba iyaye da kakanni haka suka yi auransu ba tare da sanin matsayin jini ba. Domin kuwa da yawa As da As suna yin aure ba su san alakar jininsu ba kuma su yi haihuwa fiye da goma ba tare da samun wani mai lalura ba. Da yawa kuma akwai masu S A da S A din da suke aurensu lami lafiya su gama haife haifensu ba su ci karo da komai ba kuma yaransu duk yawansu suna rayuwa. Kamar yadda anti Yagana tasha gaya mini turawa ne suka kawo wannan rikitarwar har aka kafa doka mai k'arfi akanta. Akwai ciwon ba wai babu ba to amma babu hujja mai karfi wadda za a guji auratayya domin raya sunnar Annabi Muhammadu S.A.W. Cike da cajin kai da zullumi tare da fargaba na sha maganin amma daya nasha sabida yana da k'arfi dayan kuma na yi flushing dinsa. Wajan karfe uku na tashi da matsanancin ciwon mara na dinga murkususu ni kadai don sallar asubahi ma sai da safe na yi ta. Abin karin kummalo d'akin Yusura ta kawo mini domin ban Kai ga fita falon ba ina kwance a gado murfin gwiwata sai ciwo yake yi mini da kafafuna kasan marata amma babu d'igon jini a pant dina sai da uban ciwon dai. Na dinga zurga zurgar zuwa bandaki ina dubawa babu wata alamar zubar wani abu. Jikina ya mutu murus na yi kwance a gado ina istigifari ga Allah lallai duk yadda na kai ga so cikin ya fita idan fa Allah bai kaddara ba sai dai na ci wahalar kuma na haifeshi. Idan kuwa aka yi rashin sa'a na shiga hadari sakamakon shan maganin da na yi cikin bai fita ba kuma ba ni da tabbacin cewa yana cikin 'koshin lafiya sakamakon yun'kurin zubar dashi da aka yi da ganganci. Hawaye ya shiga silalowa daga idona tausayin kaina ya kama ni. Na ha'kura kawai na barwa Allah lamarinsa muddin cikin nan bai fita ba kafin yamma to ba zan yi yun'kurin sake zubar dashi ba. Duk abinda Allah Ya yi daidai ne. Da k'yar na iya kur'bar shayi na ci dankali da 'kwai kad'an na sake kwanciya da wayata a hannuna zuciyata na tashi yayin da nake dan jin sasaauci daga kasan marata na rintse idona a hankali ina tasbihi ga Allah tare da sake jaddada istgifari domin neman afuwata. Bayan azahar sai ga Sahura da ma mun yi waya da ita ta ce mini za ta zo a cikin satin da muka shiga. Dole ta sanya ni k'arfafa jikina domin kada ta fahimci wani abu amma duk ko'karin da na yi gurin kwarara gwiwata sai da ta gane ba na jin dadi ta fara zolayata wai ko nayi tsaraba daga abuja ne domin wallahi alamun mai yaron ciki ya bayyana a tattare da ni. Bagarar da maganarta na dinga yi na ki ba bata muhimmanci har ta yi ta gama ta fara gaya mini an zo tambayar auran Yusura kuma za a kawo kudin auran ranar juma'a wannan din nan ne dai dan gidan Yayar babanta wanda na tambayeta ta ce mini shi take so kwanakin baya sosai na yi farinciki da jin haka domin duk wani bincike sun yi tana kuma jadadda mini cewa yaron mane mi ne mai zuciyar neman na kansa kuma yana can yana gini a sabuwar unguwar nan ta rimin auzinawa. Yadda ta dinga zolayata ni ma haka na dinga zolayata ina dariya ta tsufa don ana yi wa Yusura aure shekara daya za ta haihu dole ta sau'ki jika. Fad'i take ai tare muka tsufa domin kuwa 'yar ki ce ba tawa ba. Sai da ta yi sallar magriba tukkuna ta yi shirin tafiya na sanya sabon direban da aka ajiye mini ya dauketa a mota ya kai ta har gida. To mukan d'an yi waya da maigidan sa'i da lokaci amma mafi akasari shi yake kirana idan ya samu sukuni ba sosai ya fiye amsa waya ba sai mai mutukar muhimmancin gaske Amma fa shi yana kirana a duk lokacin da yake da isheshhen lokaci sai mu fi karfin awa daya muna hira ta waya sosai. Amma fa ko da wasa ban ta'ba kuskuran gaya masa wani abu ba tunda cikin bai fita ba na bar shi kawai duk lokacin da ya zo garin sai ya gani da idonsa. Bayan wata biyu da dawowo ta ina lissafin watannin cikin dake jikina wata uku da kwanaki kenan wannan karon laulayi nake yi sosai domin kuwa ba komai nake iya ci ba na fi kauri dai a b'angaran manja da yaji wainar fulawa ko d'anwake da manja ko d'anmalele. Sai ko kayan gona wannan kuma Hamusu nake sanyawa ya sayo mini duk bayan kwana uku ya kawo mini hidimar soya waina da danmalele kuwa Yusura ce ke yi mini. Duk cika da kasaitata a ko'ina sai da na rairaye saboda azabar laulayi ban fita na je ko'ina ba balle a gane halin da nake ciki itama Sahura tun zuwan da ta yi bata sake zuwa ba sai dai mu yi waya. Anti Yagana ma waya muke yi kuma ban gaya mata komai ba. Ta ce mini dai karshen shekaran nan za ta zo amma ita kad'ai ba tare da yaran ba saboda makaranta. Muka tsaya akan zuwanta a karshen shekaran nan da muke ciki to sai dai kana taka Allah Ya na tasa domin kuwa rikicin da ya ritsa da Hadiza shine abinda ya tilasta mata zuwa ba tare da shiri ba. Hadiza garin neman duniya da son lallai sai ta yi kudi bayan tafiye-tafiyen da take yi zuwa dubai sarin kaya ashe ta had'a kai da wata mata da suka hadu a can dubai din itama 'yar kasuwa ce mazauniyar Na'ibawa anan gidanta yake kuma bazawara ce babba da yaranta ta ribaci Hadiza tare da kwaid'ata mata kudin da zata samu idan ta shiga 'kungiyarsu ta shan jini. Ba tare da dogon nazari da tunani ba tunda dama babu wani sanin addini a tare da ita ta fantasma kanta a harkar da babu fita muddin an shigeta kuma sharad'in shine dole sai mutum ya bada jinin dan adam mutum guda. Suka had'a baki da ita Hajiya Alili suka saci wani almajiri suka mika shi ga kungiyar kamar yadda suka buk'ata da da farko cewa suka yi da ita sai ta bada d'anta na cikinta ta ce musu ai bata taba haihuwa ba shine suka buk'ace ta cikin kwanaki biyu kacal ta kawo musu matashin yaro wanda bai balaga ba. Matsanancin tashin hankali muka shiga gabad'ayanmu domin lamarin da ya faru sai yake nema ya shafi zuri'armu gabad'aya mutane suna ta ririta maganar tare da 'kir'kiro k'arya da gaskiya har da masu cewa dama sun jima suna zargin alhalinmu ko maita ko karuwanci ashe 'yan mafiya ne, wasu kuma na cewa gidan namu dama ai ya yi 'kaurin suna yara tun suna k'ananu suke sace sace. Hadiza ta zama kamar zautacciya domin kuwa ita da mahaukaciya marabarsu kalilan ne zafin addu'a da irin saukar karatun al'kur'ani da ake yi akan 'batan yaron ya sanya da bakinta ta fad'i ta yi kisan kai domin kuwa yaron tuntuni an shanye jininsa hakkin rai da rashin sabo ya sanya nutsuwa ta yi kaura daga jikinta. Yadda bincike ya nuna ita Hajiya Alili tunda ta ji maganar ta fasu a gari ta yi 'batan dabo aka nemata a ka rasa a garin. 'Yan unguwa suka cinnawa gidanta wuta ita kuma Hadiza muna ji muna gani mota guda da 'yansanda suka tafi da ita. Tashin hankalin da ya assasawa Babanmu fad'uwa kenan ranga ranga rai a hannun Allah muka kai shi asibitin nuna koke-koke don wallahi ni tsananin damuwa da fargaba ya sanya na manta halin da nake ciki duk wasu lalure laluran da nake yi a tsaitsaye nemansu na yi ba rasa muka dinga zurga da kai kawo daga gidanmu zuwa asibiti zuwa ofishin 'yansanda. Ni da anti Yagana mune manya kuma mune masu rufin asiri a ciki. Itama Ummansu Hadiza sun ri'ke dukiya a da can domin mahafinsu tsohon mai kudi to amma yanzu babu domin duk rabinsu sun karye babu abin sukan rasa ma abinda za su sarrafa a cikinsu. Ga masifar da take ciki bata fita ba wata ta kara kutsowa Alajiji d'anta na fari da ta haifa a wani gidan ya je ya damfari wani makudan kudi asirinsa ya tuno yana hannun hukuma suna bincike akansa domin dama tsohon mai lefi ne ya jima yana harkar yahoo 419 shine kiran da ta yi Alhaji Tajo a kwanakin baya ta ke gaya masa ya taimaka musu. Son zuciya ɓacinta kuma duk wanda ya sayi rariya tabbas ya san sai ta zubda ruwa idan da godiyar Allah iya jarin da Alhaji Tajo ya bata ya isheta ta juya ta kuma ri'ke kanta har ta kula da wasu to amma ta sanya son zuciya da son dole sai ta yi kudi ta kowace hanya ga abinda ya janyo mata nan. Anti Yagana a gidana ta sauka wannan dalilin ya sanya muke zurga zurgar tare domin ba zan ta'ba bari ta yi ita kadai ba. Hankalinmu bai kwanta ba har sai da muka ga jikin Babanmu ya dawo yadda yake tukkuna muka samu nutsuwar tattauna yadda za a kamo bakin zaran matsalar da Hadiza ta rikitowa kanta. Lamari ne gagarimi wanda duk wanda ya ji abinda ta aikata ya jajanta mata don gaskiya da wahala idan hukuncin kisa bai rataya a wuyanta ba gashi an yi an yi da ita ta fad'i wurin da mutanan da suka sanyata suke ta'ki fad'a duk kuwa da azabar wahalar da take sha a hannun hukuma. Ranar da muka je da dubata alfarma kawai suka yi mana dalilin ina auran Babban mutum amma da babu wani uzuri da zai sanya su bar mu shiga wajenta. Kuka wiwi na dinga yi ganinta a jigace ta dimauce jikinta duk shacin duka abinka da farar fata ta ki'dime sosai tana ta zantuka marasa tushe anti Yagana ce mai dauriya bata koka ba amma idonta kadai ya tabbatar mini da cewa kukan zucci take yi. Fati Kam fad'uwa ta yi a wurin aljanu suka bugeta Hassana da Usaina suka fita da ita can waje domin wurin da muke babu iska. Da muka fito anti Yagana ta gargadi su Hassana akan kada wadda ta kuskura ta gayawa Ummansu halin da muka tsinci Hadiza su nemi hanyar da zasu kwantar mata da hankali koda kuwa ta 'karya ce don za ta iya shiga mummunan yanayi muddin ta ji halin da Hadizan take ciki. A daran aka sallami Babanmu daga asibiti a waya na kira Ayuba sabon direba na ce dashi ya zo ya d'auke mu a mota gabad'aya domin a galabaice nake kwarai da gaske gajiya da jiri da ciwon mara da kafafu ban kuma kawo komai a raina face wahala da fargaba tare da kai da kawon da na yi. Muna komawa gida ni da anti Yagana na zube a tsakiyar d'akina domin wani mashahurin ciwon mara ne ya turnike na dinga murkususu ina ri'ke cikina anti Yagana hankalinta ya tashi sosai ta kira Baba Tabawa tana cewa mu je asibiti na girgiza mata cikin halin da nake ciki na fara yun'kurin amai amma bai fito ba kakari na ke yi ban amayar da komai ba sai can na ji kamar an fasa ruwan pure water a zanina jini mai yawa ya fara gudana har ya fara naso a kafet din daidai inda anti Yagana ta ajiye kafarta. Cikin fitar hayyaci na furta." Anti Yagana 'bari zan yi jini ne yake zuba." A ki'dime ta tsuguna gabana ta daga cinyata jini sharkaf ya jika mini zani sai ta fashe da kuka tana fad'in." Ciki ne dake dama Amina Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Ta kwalawa Yusura kira tare da ce mata ta gayawa Ayuba ya fito da mota za mu je asibiti. dishi dishi na fara gani domin kuwa kafin faruwar hakan na yi masifar tsorata da irin mahaukacin jinin da nake zubarwa wannan shine ya assasa d'aukewar ji da ganina na wucin gadi. [9/22, 9:50 AM] Aunty B: 89 To cikin dai ya zube a lokacin da ban yi tsammanin fitarsa ba. Wahala kuma na ci ba 'yar karama ba domin kuwa biyu ne ashe na farkon ya fita ba mu jima da zuwa asibitin ba. Na biyu sai da aka kai ga yin wankin ciki tukkuna aka yo waje dashi. Jini kam na zubar ba kad'an ba aka dibi na anti Yagana aka sanya mini aka nemo leda daya a waje a kara. Tun a daran anti Yagana suka yi waya da maigidan ta sanar dashi halin da ake ciki. Ina jinshi lokacin da yake gaya mata ai ban ta'ba sanar dashi ina da juna biyu ba har wata uku da sati uku. Ya ce mata in sha Allahu gobe mu tsammaci zuwansa. Da safe Baba Tabawa da Yusura suka tafi gida domin yin abinci. Anti Yagana tana tare da ni a asibitin motsi kad'an sai ta dube ni ta share kwalla. Jikina ya yi sanyi na fara zargin ko likitan da yake tsaye a kaina ya yi mata bayanin wani abu ne. Ni babbar fargabata ma zuwansa asibitin nan domin kuwa gabad'aya na yi sanyi da lamarin dalili na riga na san likitocin asibitin Malam Aminu suna da gogewa ta fannin aikinsu dole zasu yi binciken abinda ya asassa fitar cikin nawa. Jiki babu wani kuzari na yi wanka da ruwan da ta had'a mini a bandakin dake cikin d'akin da nake kwance da yake waje na mussaman suka ajiye ni a asibitin dalili tun shigowarmu security suka shaida fuskata duk kuwa da yanayin da nake ciki na ciwo. Na shirya cikin doguwar riga na kintsa jikina sosai cikin rashin kuzari da k'warin gwiwa gabad'aya rashin walwala da sukuninta ya fi damuna sosai akan fitar cikin daga jikina. Likitan da yake duba ni ya sake shigowa muka gaisa ya yi mini tambayoyi na ce masa jiri ne ya fi damuna sai rashin jin dadin jikina. Magunguña ya had'a mini tare da ba ni shawarwari da yadda zan yi amfani da maganin ya ce mini sun yi waya da Yallabai din ya ce ya iso garin amma yana danbatta wurin mamanshi zai jira zuwansa asibitin kafin ya tafi gida tunda dama aikin dare yake da shi. Shiru na yi ban iya ce masa komai ba anti Yagana ta yi masa godiya kafin ya fita. Ina kallonta ta je ta yi wanka ta kimtsa jikinta ta sake zama a gefana ba ta da niyyar cin wani abu bayan gashinan Baba Tabawa ta yi abinci mai kyau Ayuba ya kawo. Na daure na yi mata magana a hankali ta dube ni amma ba ta ce mini komai ba. Na ce." Ba ki ci abinci ba anti Yagana." Kanta ta girgiza a hankali ta furta." Ba na jin yunwa Amina har yanzu ban daidaita ba wallahi jiyan nan na shiga rud'ani ba kad'an ba sai nake ganin kamar za ki tafi ki barni ne." Hawaye ya sake silalo mata. Murmushi na yi cikin raina na ce dama abinda take yi wa kuka kenan. Anti Yagana kenan ai mutuwa kam ta zame mana dole ko na rigata ko ta riga ni babu wanda zai zauna a cikinmu.. Na daure na ce." Ni ma ban ta'ba jin ciwo mai azaba irin na jiya ba wallahi ni kadai nasan halin da nake shiga anti Yagana Allah dai ya takaita mini wahala." Ya gyada kanta da kulawa ta furta." Gashi ma ashe 'yan biyu ne amma me yasa ba ki taba gaya mini kina da ciki ba Amina, ai ko baki sanar da kowa ba kya gayawa wanda ya yi miki jiya da muka yi waya yana ta fad'a shi bai sani ba." A dan sanyaye na ce." Anti Yagana shurun da na yi masa shi ya fi alheri domin kuwa nasan halinsa idan ya samu labari zai hana kansa sukuni ne, ni a tawa fahimtar kawai na bari ne duk lokacin da ya zo garin sai ya gani da idonsa. Ta ce." Wannan ba hujja ba ce ko dan gaba kada ki kara haka ai abin alherine kuma yana da hakki ki gaya masa. Baki san hakan zai yi masa ciwo ba kenan ga yanayin yadda yake magana a wayar ya tabbatar mini da cewa ya ji haushin abinda ki ka yi." Na ce." Zan kiyaye in sha Allahu rabbi yanzu dai ki ci abinci ba na so na dinga ganin ki cikin damuwa da alhini duk abinda Allah Ya yi daidai ne." Ta girgiza kanta da damuwar dai ta furta." Tabbas yadda Ubangiji ya yi shine daidai amma na so a ce kin haife tagwayen nan Amina, amma Ubangiji Allah Ya ba ki wani." Sunkuyar da kaina kasa na yi ban ce komai ba yanzu idan ba dan'uwanka na jini ba wanene zai gwada maka wannan soyayya. Tare muka ci abincin amma ni kadan na iya ci nasha maltina tana ci muna taba hirar lamarin Hadiza. Hamusu ya kira ni a waya ya ce gashi nan asibitin ya shigo dubani domin yanzu daya can gidana yake Yusura ta gaya masa ba ni da lafiya. Anti Yagana da kanta ta fita ta yi masa jagora muka gaisa sosai dalili tunda na dawo daga abuja ba mu had'u ba sai a waya idan na kira shi ko ya kira ni dangane da harkokinmu ya ce zai tafi amma da yamma za su so tare da Gwaggo anti Yagana ta ce masa sai dai su je can gidana domin kuwa ta ji likitan yana fad'in ya rubuta takardar sallama yana jiran zuwan Yallabai din ne. Ya ce idan ba su zo da yamma ba to gobe da safe za su je can gidan muka yi sallama ya kama hanya ya tafi shago. To sai bayan sallar azhar tukkuna suka zo asibitin tare da Hajja da Hajiya Saratu. Haka kawai sai na tsinci kaina da kasa had'a ido dasu gabad'aya domin hausawa suka ce mara gaskiya ko a ruwa gumi yake yi. Gabad'aya na kasa nutsuwa domin sai nake ganin kamar za a gane na yi wani yun'kuri a baya. Hajja sai sannu take yi mini tana fad'in an auna arziki ai tunda cikin ya fita ba tare da wata matsalar ba. Hajiya Saratu ma ta jajanta mini sosai tana cewa idan da rabo a kusa sai a kara samun wani. Shi ogan yana tsaye a gefan kaina tunda muka gaisa ya yi mini sannu bai sake magana yanayinsa dai ya nuna jimami da damuwar abinda ya faru. Jikina ya kara yin sanyi sai na kasa daga kaina na dube shi a lokacin da likitan ya shigo d'akin yana tambaya ko da matsala na girgiza kaina alamun babu komai. Yallabai din ya dora hannunsa a saman goshina sai likitan ya dube shi yana cewa." Da zu da muka yi magana da ita ta ce mini jiri ne kadai yake damunta amma in sha Allahu shi ma zai gusa nan da kwanaki uku tunda an dubata sosai babu wata matsala sai ta rashin kwarin jiki, bayan haka kuma ga magunguñan nan masu kyau na hada mata." Hannu ya ba shi suka yi musabaha da juna yana yi masa godiya yayin da likitan yake jadadda masa cewa babu godiya domin kuwa aikinsa. Tare suka fita sai hakan ya haifar mini da damuwa don sai nake ganin kamar akwai wani bayani da likitan zai yi masa wanda yake b'oyewa. Hira suke yi a d'akin tsakanin Hajja da Anti Yagana dama akwai shak'uwa a tsakaninsu tun zuwan da anti Yagana ta yi wajena a lokacin da ina Legos. Ni kuma jikina duk ya yi la'asar hankalina na can tunanin abinda zai faru domin kuwa nasan ko likita bai gaya masa wata magana ba na tabbatar da cewa sai ya tuhume ni dalilin da ya sanya na yi shiru ban gaya masa samuwar cikin ba tsayin wattani uku da satika. La'asar a gidana ta yi mana tare gabad'aya muka dunguma har dasu Hajja a ka yi sa'a kuwa Baba Tabawa tana ta hidimar abinci koda ta fito suka gaisa cikin barkwanci take cewa da maigidan towo take yi saboda ta ji labarin zai zo kuma ta sanya an samo mata daddawa da kuka masu kyau tunda ta fahimci ya fi k'aunar miyar kuka fiye da sauran abin ka'di. Ya dinga godiya kuwa cikin kulawa da sakin fuska wannan dabi'ar tasa ta rashin 'kyama tana kara masa martaba. Hajja fadi take yi kin kyauta kuwa Tabawa sai ki tu'ka towon da yawa ni ma na tafi dashi na d'umama da safe. Tashi ya yi ya nufi d'akinsa dake saman bene wanda ya jima a rufe tunda ni duk dabdalata a kasa nake yi ban sake hawa saman ba tun washe garin ranar da na tare a gidan. Duk da rashin jin kwarin jikina hakan bai hana ni tashi na bi shi bayan shi ba. Waya yake yi da Sukairaju a lokacin da na shiga d'akin tare suke zo dama tunda shi ya d'auko mu a mota ma. Na nemi kusa dashi na zauna a hankali Ina nazarin d'akin bai yi wata 'kura ba tunda ko'ina rufe yake da tagogi irin na gilashi da narka narkan labuleye a kewaye babu ma wata kofa da kura za ta shigo sai dai idan an dan gyara wasu guraran hakan ba zai zama lefi ba. Ya kashe wayar yana dubana a tsanake ya furta." Ya gajiya da jikin kuma?" A hankali na furta." Na ji sauki kai ma ya gajiyar hanya." "Ban gaji ba." Yafada idonsa a tsaye a kaina. Sai na yi kasa da nawa idon ina dan jin fargaba kad'an zan yi kokarin ganin na kare kaina ta kowace siga domin kuwa na fahimci zallan rikici da fitina a cikin kwayoyin idonsa." "Ina so ki gaya mini abinda ki ka taka, kada ki rufe ni Amina domin kuwa babu abinda na tsana a rayuwata sai zamba cikin aminci. Na kan ji na tsani mutum tsana ta har abada muddin na fahimci cewa yana zaune da ni da wata zuciya ta daban. Ki fito fili ki gaya mini me kike nema a wajena? Menene a can kasan zuciyarki dangane da zama da ni." Cikin nutsuwa na furta." Ban gane inda maganganunsa suka dosa ba Baba." Ya tsira mini ido da b'acin rai a tare dashi kafin ya gyad'a kansa ya ce." Kin san idan wani likita zai b'oyewa kowa wani lamari da ya shafe shi tsakaninsa da mara lafiyarsa ni dai alfarmata da yadda Ubangijina ya karramani a nan gidan duniya ba za a rufe mini wani lamari da ya dangance ni ba. Likitan da ya yi tsaye a kanki a daran jiya ya yi mini bayanin da ke kanki bai yi miki shi ba, ya sanar da ni dalilin zubewar cikinki wanda ki ka boye mini samuwarsa bincike ya nuna cewa lallai an yi yun'kurin fitar dashi ta kar'fi da ya ji, hakan ya haddasa matsala babba cikin ya canza mazauni, shi bai fice ba haka zalika kuma shi ba zauna daidai yadda ake so a mahaifar ba. Ya gaya mini biyu ne na farko ya fita jim kad'an bayan zuwanku asibitin na biyun ne sai da aka kai ruwa rana kafin su fitar dashi ko kina da ja akan hakan, ni dai na san Dr Iliyas haka kawai ba zai 'kir'kiri 'karya domin ya 'bata ki a wajena ya gaya mini ba, ya sanar mini ne domin akan akinsa yake ni kuma na aminta da bayaninsa sanin da na yi miki za ki yi aikata fiye da abinda ya fi haka. Na ro'ke shi ya rufe maganar ba don Ina gudun tozarci da tiriri na jama'a ba, nasan ni dai babu wanda zai zage ni, sunana kuma ba zai 'baci ba, na yi hakan ne kawai saboda idan maganar ta fita dole idan an rubuta sunanki za a rubuta nawa a gaba. Kuma da sauran igiyoyin aurena a kanki ba ni da yadda zan yi na 'karyata domin sakamako ne daga wajen mahukuta wad'anda suka san abin. In banda ke dashi Dr Iliyas din da ni na uku babu wanda ya san yunkurinki na fitar da cikin ta k'arfi saboda haka mu yi magana ta tsakani da Allah da annabi dake anan, na san matsayata lullub'e mini gaskiya kuwa zai iya janyo miki miki b'acin rai da fushi mai tsanani daga wurina." Cikin dauriya da ko'karin aro jarumta na ce." Ni wannan maganar ban santa ba. Sharri ya yi mini domin neman suna a wurinka to wai akan me zan zubar da cikin da Allah Ya ba ni, me ka yi mini ko ma ka yi mini wani lefi shi cikin Ina ruwansa da zan zubar dashi, kawai Allah Ya k'addari fitarsa ne a wannan lokacin amma ni kam ban san da wannan maganar ba. Ya gyad'a kansa yana kallona ido cikin ido sai na kasa dubansa na yi k'asa da kaina gabana na bugawa da k'arfi. Ya sanya hannunsa ya dago fuskata yana cewa." Ki rantse da girman Allan da ya hallice ki a wannan duniyar ba ki yi yun'kurin zubar da cikin nan ba Amina." Shiru na yi ban ce komai ba zuwa wannan lokaci kuwa kafafuna sun fara rawa saboda fargaba da zullumi domin kuwa ban hangi kwanciyar hankali da yarda da kaddara daga gare shi ba. Ya tashi ya je ya dauro alwala duk Ina zaune Ina kallonsa ya bude drowa ya d'auko al'kur'ani izu sittin ya dawo ya zauna a kusa da ni yana fad'in." Zan iya rantse miki da Allah cewa baki da gaskiya Amina, kuma bayanin da likita ya yi shine gaskiya." Na ce." Me ya yi zafi da har sai an yi rantsuwa da al'kur'ani, kafi kowa sanin hakan babban hadari ne, kuma al'kur'ani ba abun wasa ba ne." "Ban d'auko al'kur'ani da zummar wasa ba Amina, wallahi Allah daya ne kin yi yun'kurin zubar mini da ciki, ina so ki tashi ki je ki d'auro alwala ki yi yadda na yi ki d'auki al'kur'ani ki dora a saman kanki ki rantse da Allah muddin ki ka yi haka wallahi zan aminta dake d'ari bisa d'ari." "Zan yi dai alwala amma ba ni da hurumin rungumar al'kur'ani domin ba ni da tsarki, ko ma ina dashi ni ba zan yi wannan gangancin ba gaskiya." Ya jima yana kallona kafin ya furta." To na ji ki ba ni amsa me yasa ki ka rufe mini samuwar cikin ba ki gaya mini ba." Shiru na yi ina d'an duban yatsun hannuna kafin na ce." Babu wani dalili mai k'arfi na bari ne kawai idan ka zo garin sai ka gani da idonka, kuma anti Yagana ta ce mini hakan kuskure ne don Allah ka yi ha'kuri." "Ba ha'kuri na ce ki ba ni ba Amina gaskiya na ce ki gaya mini, tun muna mu biyu dake a d'akin nan idan kin yi mini gardama zan sanar da 'yar uwarki sannan na gayawa Mahaifiyata abinda ki ka yi mini." Na zuba masa ido da yanayi na damuwa na ce." Na gaya maka gaskiya baka yarda ba to karya kake so na yi maka wai me zai sanya ni na zubar da cikin ne ai ba shege ba ne." Sai ya tashi tsaye a fusace! "Ai kin shegantashi tunda ki ka zubar mini da shi, Allah Ya isa ban yafe miki ba Amina." Ya fad'a jikinsa na karkwarwa idonsa ya yi jajawur. Tsaye na mike ni ma da yanayi na ko'karin kare kaina na ce." Menene abin Allah Ya isa, shikkenan 'kaddara ba za ta faru ba sai a jingina mini ita, ai musulma ce ni nasan abinda addini ya koyar ko cikin da ba a same shi ta hanyar mai kyau ba haramun ne zubar dashi balle wanda aka sameshi ta hanyar halak, ban ga dalilin da zai sanya ku dinga kokarin dora mini lefi b......Ban 'karasa ba ya kawo mini hari na 'barin makauniya a kuncina sai na yi kasa da mugun sauri lamarin da bai taba ratsa tsakaninmu ba ko da wasa bai tab'a yun'kurin kai hannunsa jikina da zummar duka ba. Jikinsa na rawa yake cewa." An jingina miki lefin, ai ba ki da imani kuma baki da kyawun zuciya Amina na jima da sanin za ki iya aikata abinda ya fi haka akaina tunda baki zaune da ni da zuciya daya. Ki bar ganin kina cikin hali na lalura hakan ba zai hana ni na huce takaicina ba. Abinda nake nema ruwa da iska rani da damuna na samu har guda biyu kin zubar mini Amina Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!" Ya kai 'karshen maganar da kiran sunan Allah kafin rigijib ya zube a kan gadon ya rufe fuskarsa da tafukan hannayensa gabad'aya yana nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! da baban sauti. [9/23, 9:23 AM] Aunty B: 90 Ganin halin da ya shiga ya sanya mini muguwar fargaba domin kuwa tunda nake dashi ban ta'ba ganinshi a cikin yanayi na rud'u da tashin hankali ba. Tabbas lokacin rasuwar baby Nana ya shiga damuwa sosai amma sai nake ganin wannan lamarin ya fi d'imauta shi fiye da wancan din. Jikina babu kuzari ko na gamin gafara na kama hanya domin fita daga d'akin saboda ban san wace irin fitina zamana zai haifar ba. Fargabata da tsananin damuwata kada ya fitar da maganar domin kuwa ya fi ni gaskiya da hujja mai karfi dalili ni tun farko na d'auri kaina da ban gaya masa ina da ciki ba. Idan kuwa zan kafa hujja da cewar ai na zubar da shine domin gudun haihuwar mai sikila ba kowa ne zai fahimce ni ba, da yawa ma wasu za su ga ai don ina da yaran ne ya sanya ni yun'kurin zubar da ciki ba tare da damuwata ba. Ammafa muddin an zauna an dubi lamarin ta fuskar adalci za a fahimci abinda nake nufi. Wannan kadai itace hujjata ko da kuwa maganar ta fasu na tabbatar da cewa ya fi ni hujja mai karfi domin masu k'adaita Allah da tauhidi ai za su ga gangancina domin kuwa tun fil'azal ai haka iyaye da kakanni suke yin auransu su haihu lafiya ba tare da wata rikitarwa irin ta yahudu da nasara ba. Kai tsaye d'akina na wuce na kwanta don ba zan iya zaman falon ba dalili kwata-kwata bana cikin hayyacina ga jikina babu k'wari don har yanzu jirin bai gama sakina ba. Anti Yagana ta shigo d'akin ta same ni a kudindine a cikin bargo lokacin ma kuka nake yi amma mara sauti sai na yi saurin rintse idona ina goge hawaye a fakaice bata fahimci komai ba tunda daga bakin kofa ta tsaya tana tambayata ko jikin ne na ce mata a a Ina hutawa ne sai ta juya ta zata fita tana fad'in bari ta kawo mini abinci na ci sai nasha magunguña. Da kyar na iya cin loma biyar shi ma sai da ta matsanta mini tukkuna na ci sai da ta tabbatar da nasha maganin kan ka'ida tukkuna ta fita daga d'akin. Sai bayan ishi'i su Hajja suka tafi bayan sun shigo sun yi mini sallama tare da fad'a mini cewa za su sake dawowa domin sake duba ni cikin satin da za mu shiga. Ina daga kwance muka yi sallama cikin kulawa yadda suka nuna damuwarsu a kaina hakan ya faranta mini sosai sai dai can kasan zuciyata ina jin fargaba kad'an idan har suka samu labarin abinda na yi shin da wace fuska za su dube ni. Tunda na fito daga dakinsa ba mu sake haduwa ba sai da garin Allah ya waye anti Yagana ta matsa mini lallai sai na rage kwanciya na fito falo na zauna kan kujera hakan zai k'arfafa mini gwiwa domin idan ina yawan kwanciya kasala da ciwon jiki ba za su barni ba. Saboda haka ina yin wanka na shirya na fito falon na same su suna kallo har da Baba Tabawa na nemi kujera na zauna hankali na saman ina tunanin ko ya sauko ko wane hali yake ciki. Yusura ta kawo mini abinda suka yi na karin kummalo na kasa cin komai saboda bakina har yanzu babu d'aki. Baba Tabawa ta d'umama mini ragowar towon jiya bashi dai da yawa tunda Hajja ta tafi da wani amma ya isheni kuma ni kaina na yi mamakin yadda na ci sosai a lokacin na ji karfin jikina ya k'aru... Cikin wani yanayi na tambayi anti Yagana maigidan ya sauko tunda tun safe suna falon ta ce mini ya sauko har sun gaisa ya fita amma bai jima ba ya sake hawa saman bai kara saukowa ba kuma. A gogon da yake falon na duba sha daya da rabi domin kada ta fahimci akwai 'baraka ya sanya na tashi ina fad'in bari na hau mu gaisa. Kai tsaye na nufi benen da zullumi mai yawa a kirjina. Kofar d'akin kawai na tura ta bude bai murza mukkuli ba, Yana zaune a gefan gado ya shirya sosai cikin milk din shadda tazarce da aiki mai kyau a gaban rigar hularsa tana ajiye a gefe amma as'usul gilashinsa na ka'ida yana idonsa. Magana yake yi a waya a lokacin da na shiga d'akin na samu wuri gefansa na zauna amma gabad'aya na gagara kallonsa saboda tsananin yadda nake cikin damuwa. Jin yana ambaton sunan Maryam ya sanya ni shiga tunani daga bisani Kuma na gane da Hajiya Maryam suke yin magana matar abokinsa da ya rasu kwanaki. Sun jima suna tattauna abinda ya danganci mamacin yanayin maganganunsu ya tabbatar mini da cewa suna tattauna yadda za a raba abinda ya bari tunda mahaifiyarsa ta na raye kuma yana da 'yan uwa. Dole Mamansa ta gaje shi koda kuwa 'yan uwansa ba su gaje shi ba dalili akwai maza biyu a cikin yaranshi. Bayan sun yi sallama ya dube ni babu yabo babu fallasa amma bai ce komai ba sai ya cigaba da latsa wayarsa yasa a kunnansa ina dai zaune Ina jin shi Hauwa ya kira a wayar cikin kulawa na ji suna magana don ba na jin abinda take cewa tunda kamar ya yi kasa da murya ne don shi ma idan ta fad'i magana sai ya sake tambayarta abinda ta ce saboda maganarta can kasa take fita. Sai na juyar da kaina gefe ganin kamar ba ya so na ji maganar da suke yi na ji yana gaya mata daga nan din kai tsaye bauchin zai taho zuwa yamma ta tsammaci zuwansa tunda tafiyar mota zai yi. Jikina ya d'an yi sanyi Jin yadda yake lalla'bata da rarrashi har da kalamai irin na tausayawa da sadaukarwa. Sai na tsargu da jin abinda yake yi wanda na tabbatar da cewa wanzuwata a wurin ya kawo hakan. Na ji haushi sosai amma sai na danne domin kuwa a yanzu fushi ba nawa ba ne dalilin abinda na tabbatar da cewa ni ce mafi rinyen lefi dole a wannan ga'bar ko ban fito na gaya masa na aikata ba na nemi hanyar shiri da kuma ko'karin kwantar da matsalar don gudun fasuwar maganar. Ya ajiye wayar a kusa dashi bayan sun kammala ya d'auki agogonshi dake saman drowar yana daurawa bai ce mini komai ba. Na daure na ce." Ina kwana Baba?" Hankalinsa na kan abinda yake yi ya amsa da "lafiya ya gajiya." Sai na yi shiru ina dan satar kallonshi a fakaice. Sukairaju ya dan buga kofar kafin ya bashi umarnin shigowa ya turo a hankali cikin ladabi ya tsaya daga can nesa yana fad'in." Sir ka kammala ne?" Ya mike tsaye da hularsa a hannunsa yana gyarawa ya ce." E, na kammala zo ka d'auki wad'annan." Ya fad'a yana nuna masa Loptop dinsa dake ajiye da 'yar jakarshi." Da sauri ya yi abinda aka sanya shi ya bude kofar ya fita daga d'akin. Yana ko'karin sanya hular a saman kan sa ya ce." Ni zan tafi Amina, Amma kafin nan zan je Bauchi wurin Hauwa domin dubata ina fatan ba ki da matsala ko?'' Na mike tsaye da rashin karsashi na ce." Ba ni da matsala Baba amma ina so mu yi magana dangane da abin nan da ya furu na ga kamar ba ka yarda da kaddara ba don Allah kada ka tafi da 'kullacina a cikin ranka." Ya dube ni sosai wanda tun shigowata d'akin bai yi mini irinsa ba. "Kin aikata hasashen Dr Iliyasu ko ba ki aikata ba, wannan amsar kawai nake so na ji daga gare ki." Shiru na yi ina kallonsa shi ma yana kallona ido cikin ido. Mun d'an jima a haka kafin daga bisani na janye nawa idon daga cikin nasa zuciyata na dan harbawa ko alama ban hangi sasaauci a cikin idanuwansa ba. "Shirunki da yanayin yadda alamun rashin gaskiya suka bayyana a tattare dake ya bayyana mini ce wa." Dr Iliyas ba karya ya yi miki ba saboda haka ni kawai sai dai na ce na barki da Allah." Daga haka sai ya kama hanyar fita daga d'akin. Da saurin gaske na cimmasa idona cike da hawaye masu radad'i na furta." Maganar bari da Allah ba adalci ba ne, ka yi duk hukuncin da kake ganin za ka yi mini tunda ka'ki kar'bar kaddara, amma kwata kwata ka daina had'ani da Allah "Shi kadai ne zai yi mini maganinki tunda ai kin gagara Amina kin nunawa duniya cewa baki da na gaba dake kin fi 'karfin kowa ciki har da mahaifinki ni dai muddin ina da hakki akanki to fa ba zan daina cewa Allah Ya saka mini ba." Ya sanya hannu zai bude kofar domin fita na sake tare hanyar a karo na biyu cikin jarumta na ce." Ubangiji ba mutum ba ne kamar kowa kuma akan yi masa lefi a tuba ya yafe duk sharri da bala'in da kake nema dashi da izinin Allah ba zai same ni ba domin kuwa wanda ya hallice ni ya fi ni sanin menene a zuciyata Ina ce dai idan na gaya maka gaskiya shikkenan ai ikon hukunci ko azabtarwa ko d'aukar rai duka ba a hannunka suke ba. Na yi kuskure tabbas a lokacin da na tabbatar da cikin a jikina na yi kokarin fitar dashi kamar yadda Dr Iliyas din ya gaya maka. Dana fahimci bai zube ba sai na ha'kura kawai na barwa Allah kuma na ro'ke shi gafara a sa'in da na kuskure masa kuma ina da tabbacin ya gafarta mini, abinda zan iya gaya maka kenan domin a duniyar nan babu wanda baya kuskure Ina me baka ha'kuri hakan ba zata sake faruwa ba." Ya jima yana kallona da yanayi na mamaki da al'ajabi ni kuwa ban ji komai ba domin kuwa na lura rufe maganar da nake yi bashi da wani amfani gwara kawai na sanar da shi gaskiyar lamari tunda ya fi ni sanin hujjata ta yin hakan. "Hakan ba zata sake faruwa ba." Wannan maganar ya fad'a kafin a gaggauce ya bud'e kofar d'akin ya fice da saurin gaske. Na jima ina nazarin maganar da ya furta sai na shiga zullumi da tunanin domin ya yi ta ne a d'ukunkune karshen dai hukunci shine saki a shirye nake da kar'bar gakan daga wajensa. Da yamma muna zaune a falo anti Yagana suka yi waya da Babanmu nan take sanar dashi kwana biyu ni ce ban ji dadi ba shine dalilin da ya sanya ba mu sake zuwa ba tun ranar da aka sallameshi daga asibiti. Na ce mata ta gaya masa na ji sau'ki don zai iya tashin hankalinsa jin ba ni da lafiya Duk da ta gaya masa haka kuwa washe garin ranar sai da suka zo duba ni tare da Baba Sule sun jima a gidan muna tattauna sha'anin Hadiza domin kuwa kowa ya riga ya mik'a wuya don a zaman kutu na farko da aka yi ba a hangi sasaauci a tare da alkalin ba. Yanzu tana can gidan kaso kafin shari'ar ta kammalu a yanke mata hukunci. Bayan sun tafi da kad'an sai ga Gwaggo Hamusu ya kawota to ita tare muka yini har dare sai bayan Isha'i, tukkuna ya taso daga shago ya zo ya d'auketa a babur ya kai ta gida. Sai da na warware sosai sannan na gayawa Sahura abinda ya faru da ni amma ban gaya mata cewa ni ce sila ba. Ta jajanta mini sosai tana fad'in Allah bai yi rayayyu ba ne itama haka tasha wannan wahalar lokacin da nata tagwayen suka zube ta ce mini za ta zo ta duba ni ranar da babu aiki. **** To tafiya ta mik'a sosai don yau sati uku kenan da abinda ya faru amma tsakanina da maigidan muguwar gaba ce ta 'kullu. A zahiri shi ya d'auki lamarin da zafi na sani kowaye aka yi wa haka ba zai ji dad'i ba amma ya kamata ace ya yi hakuri ya kar'bi tubana tunda na gane abinda na yi ba daidai ba ne. Na kira shi ya kai sau bakwai tun bayan tafiyarsa na tura text amma daga karshe ma sai ya sanya ni a black list idan na kira duka layinkansa busy. Ban damu ba da farko saboda a ganina duk fushin da zai yi na dan wani lokaci ne zai ha'kura ya sauko ya kar'bi tubana ni kuma na kiyaye a gabana. Na dai ji dad'i sosai da ya rufe maganar bai gayawa kowa ba dama kuma kusan haka halinshi yake yana da zurfin ciki mussaman akan mas'ala irin wannan. Duk da damuwar da ta fara yi mini 'kawanya ban yarda anti Yagana ta fahimci wani abu ba har dai ta tattara ta tafi bayan an yi zaman kotu daya da ita inda ake tsammanin zama na gaba za a yanke hukunci na karshe. Bayan tafiyar anti Yagana Ummansu Hadiza ta zo mini a ki'dime tana kuka sosai duk ta figale ta lalace wai na taimaka na daukarwa Hadiza lauya domin kuwa a cikin lauyoyin gwamnati an rasa wanda zai kar'bi case din ganin haka ya sanya kowa yake tunanin zama na gaba Hadiza za ta san matsayinta. Na rasa yadda zan yi da ita domin dai Ina ji Ina gani ba zan daurewa karya gindi ba. Hadiza ta fad'a da bakinta tana da hannu dumu-dumu shedu sun shaida to me zai sanya haka kawai na d'aukar mata lauya saboda son zuciya. Kuka take yi sosai tana gaya mini halin da Alhajiji yake ciki shi ma yana can hannun 'yansanda a jos suna azabtar dashi mahafinsa da 'yan uwansa da suka uba daya sun ce babu ruwansu ga Hadiza ma za a yanke mata d'aurin rai da rai." Na rasa kalmar da zan yi amfani da ita wurin rarrashinta domin kuwa Allah ne kadai ya san irin rad'adin da take ji a cikin zuciyarta. Ban yaudareta da zumar zan yi mata abinda take buk'ata ba. Na dai rarrasheta da tausasan kalamai na kuma jadadda mata ce wa ta mikawa Allah lamarin sannan kuma ta tsananta da addu'a Ubangiji zai kawo mata d'auki. Da zata tafi na bata dubu talatin na ce kuma Ayuba ya kaita har gida don abincin ma dana sanya a kawo mata bata ci ba sai juye mata na yi a leda ta tafi dashi. *** Yau wata biyu kenan da tafiyarsa wanda ya yi daidai da abinda ya faru da farko da na ce ba zan kara kiran shi ba amma yau tunda garin Allah ya waye na tashi da wata irin kewa da sha'awa. Na zauna ina tunanin abinda ya janyo mini shiga yanayin tunda na farko ni ina gujewa sha da cin duk abinda zai daga mini hankalina babu namiji a kusa da ni. Amma yau din nan na wayi gari da tsananin kewa kuma tasa da son jin wani abu daga gare shi. Duka na bi layinkansa ina busy har yanzu bai cire ni ba, na duba shi a ta whasap na ga ya sauka tun kwanaki uku da suka wuce. Sallama na yi masa cikakkiya da addu'ar Allah Ya sa ya amsa mini a duk lokacin da ya bud'e ya ga sa'kona. Na kasance koyaushe cikin duba shi ta whasap din tsayin kwanaki tara da tura sa'kona bai hau ba sai yau. Na ga alamun ya duba sallamata amma kuma bai ce komai ba ya ma sauka. Sai na sake tura masa wata sallamar again ina ta addu'a Allah Ya sa ya magantu. Bai duba ba sai da gari ya waye tukkuna nan ma dai bai amsa mini ba. A takaice dai sai da na yi masa sallama sama da biyar ya bud'e ya ga ni amma ko d'aya bai amsa ba. Raina ya 'baci ainun. wannan mummunan dabi'arsa tasa ta gaba tana mugun b'ata mini rai. Kuma na fahimci yana da rike abu a zuciyarsa ba kasafai ake bashi ha'kuri ya ha'kura a lokaci daya ba. Sai kawai na share shi gabad'aya ni ma na fita daga sabgarsa duk kuwa da cewa tunani da kewarsa na d'an damuna amma dai Ina yun'kurin dannewa domin tsira da sauran mutuncin da ya rage mini. *** Sannu a hankali kwanaki suka cigaba da tafiya wattani ma suka 'kara nisa babu jituwa a tsakaninmu domin kuwa ya'ki ha'kura da abinda ya faru ya k'ullace ni da gasken gasken yau wata biyar kenan ina lissafi ganin mun kusa rabin shekara ba ma magana babu wata kyakyatawar kulawa ta aure sai na fara tunanin nemawa kaina mafita domin kuwa yana da kyau na san matsayin idan auran ne to idan kuma ba ya yi sai ya sauwake mini akan dai ya shareni ban san a wace makoma nake ba. Wata ranar litinin tun wajejen tara na safe na fita na je gidanmu akan lamarin Hadiza domin hukuncin rataya aka yanke mata amma sai nan da shekaru uku tukkuna a cewar alkalin za ta zauna a gidan prison ta kar'bi horo mai tsanani kafin a zartar da hukuncin. Tun bayan yanke hukuncin aka rasa gane kan Ummantasu abinda take yi kamar na mai tabin kwakwalwa shine Babanmu ya ce na taimaka a kaita asibitin dawanau domin su binciki lafiyarta domin kuwa baya yi mata kallon mai hankalina. Bincike ya nuna bata da wata matsala sai damuwa da tunani shine ya haddasa mata zaucewa depression yake nema ya kamata. Suka bata magunguña amma ba irin na mahaukata ba muka dawo gidan na dinga tausarta da bata ha'kuri tare da kawo mata misalai na rayuwa. Ta dinga kuka tana ba ni ha'kuri wai hakkin abinda ta yi mana ne da Mamanmu yake bibiyarta don Allah mu yafe mata. Na ce mata babu hakki kawai ta d'auki hakan a matsayin jarabawarta. Sai bayan isha'i na koma gida. Na tarar Baba Tabawa da Yusura suna kallon tarihi Annabi Yusuf a Mbc drama a tsaitsaye na tsaya a falon muka dan yi magana kafin na shiga na yi wanka tare da sauri alwala na yi Ishai a d'akin na ce Yusura ta kawo mini abinci don tashin hankali bai barni na ci wani abincin arziki ba duk kuwa da cewa Ummansu Saminu ta ciko mini kwano da shinkafa da miya har da salak da nama. Amma halin da Ummansu Hadiza take ciki ya sanya mini fargaba da nadamar rayuwa ashe dai da gaske ne karin maganar nan da ake cewa alhaki koikoyone ne gashi dai da bakinta tana fad'in abinda ta aikata. Abinci na ci sosai na koshi Yusura ta zo ta kwashe kayan ta fita da su. Sai a lokacin na samu sukunin duba wayata cikin nutsuwa nake bin komai a hankali Ina dubawa na shiga Whatsapp bangaran status ina d'an dubawa a nutse can sai na ga ya yi status hannuna na rawa na shiga ina mamaki domin sai na ce tunda mukayi serving din lambar juna dashi ban ta'ba ganin ya d'ora status ba. Katin d'aure aure ne mai d'auke da sunansa. Alhaji Tajudden Ibrahimu 'Dambatta da Hajiya Maryam Abubakar Sabi'u Jos wanda za a d'aura ranar juma'a mai zuwa a babban massalacin Juma'a na garin jos din bayan saukowa daga sallar Juma'a. [9/23, 8:02 PM] Aunty B: 91 Wani irin yanayi na shiga na tsantsar tashin hankali da fargaba wanda ba zan iya misalta irinsa ba. Idan hasashena daidai ne Hajiya Maryam ce wadda na sani matar abokinsa Alhaji Amadu da ya rasu wattanin baya. Amma fa zahirin gaskiya al'marin ya ba ni mamaki ba kad'an ba. Katin d'aurin auran dai nake sake dubawa da tu'ajibi a tattare da ni wato yana hasashen samun abinda abokinsa yake samu daga wurinta kafin rasuwarsa kenan. To hakane mana tunda ai ya sha fad'a mini abokinsa ya yi sa'ar mace tana da gayu da kula da kuma tarairayar miji shine dalilin da ya sanya tana fita daga takaba ya yi wuf da ita. Sai wannan ya sake tabbatar mini da cewa wato shi dai namiji har mace ta mutu ba zata daina d'aukar darasi akansa ba. A hankali na jingina bayana jikin gado ina cigaba da nazarin yadda al'amura suke tafiya a wannan duniyar. Ai babu mamaki don ya manta da sha'anina tunda akwai babban lamarin da ya sha kansa wànda yake hasashen samun nutsuwa a cikinsa. Na dinga danne hawayen dake ko'karin k'wace mini amma sai da suka fara gudana kuma da 'karfinsu suke zuba a kumatuna. Wato duk irin juriya da ha'kuri da kulawar da nake yi da mutumin nan bai ga ni ba ta wannan hanyar zai saka mini. Hanci na ja tare da girgiza kaina domin duk yadda na so ganin na yi dauriya akan lamarin naka sa yi kukan ne kawai zai sanya mini jin sasaauci a cikin zuciyata. Yana da kyau a wannan ga'bar da muke ciki ni dashi na san menene matsayina domin kuwa a shari'a ma aure yana dab da 'baci idan muka cigaba da tafiya haka. Zai auri Hajiya Maryam babu wanda ya ji ya gani, cikin rufin asiri alhalin itama bazawara ce kamar ni kuma 'yar kasuwar da take 'ketarawa 'kasashe sarin kaya. Ya lullube sirrinta ya kuma rufe idonsa ga ganin aibunta tunda dama ai tun kafin aure yana 'kwarzanta nagartatta. Ni kuwa motsi kad'an zai kira ni da gagararriya fitinanniya mara kamun kai saboda kawai na dogara da kaina, ina sana'a ban nema a wurin wani ba. Kullum cikin zargi nake a wurinsa saboda wad'annan dalilai ita kuwa duk da ta girme ni kuma ta jima tana harkokinta ya aureta a haka saboda dama hausawa suna fad'in kowace kwarya da abokin burminta matar abokinsa ce, kuma macace mai dukiya da duniya ta shaida hakan. Bayan haka kuma 'yar gayu ce kuma 'yar boko domin kuwa gabad'aya ta yi mana zarra ta ko'ina da ni da Hauwa sai da mu take bayanta. Wad'annan zantukan zuciyata take ta zayyano mini tare da nuna mini lallai na tashi na kare mutuncina muddin na bari ya zube to don kowa ya hau ya taka ba wani abu ba ne. Cike da faduwar gaba da tunani nake nazarin ta Ina zan fara domin yanzu ina yin wani motsi daga 'bangaransa za su ga kamar kishi ne don ya yi aure ko da na fadi halin da nake ciki babu wanda zai fahimce ni tunda shi bai fito ya fadawa kowa ba. Idan na nufi Hajja da maganar dole za ta bukaci sanin dalilin da asassa mana rigima wanda fad'insa zai janyo mini zubewar 'kima da mutunci da mummunan zargi. Amma babu shakka Hajiya Maryam sai ta ba ni yarona domin babu yadda za a yi na zuba ido a dinga juya ni alhalin ni ma Allah Ya rufa mini asiri. Daf ake da sallamo su Kamalu daga makaranta ni ma zan hada kan yarana waje daya kamar yadda ta had'a kan yaranta waje guda. Kuka na ci na 'koshi na hak'urk'urtar da kaina tare da barin abin ya tura kad'an kafin na nemawa kaina mafita don na yi rantsuwa da Allah da annabi wata d'aya kawai na kara akan wad'anda suka gabata idan bai neme ni ba zan tattara na bar masa gidansa sai dai ya aiko mini da shedar saki domin kuwa ban amfanin zaman da nake yi ba. Da kyar na iya rintsawa a daran saboda tsananin damuwa na tashi da ciwon kai irin na gefe d'aya da kyar nayi wanka na karya kummalo Yusura ta kawo mini abin kari d'aki don ban iya fita falon ba saboda yanayin da nake ciki na rashin sukuni. Sahura ta kira ni a waya a lokacin da nake karyawa muka gaisa kad'an domin na gagara daurewa muryarta har rawa take yi ta fara fad'in." Amina da gaske ne oga zai auri Hajiya Maryam jos matar amininshi da ya rasu watannin baya, a wajan aiki ne na ji ana ta maganar wallahi shine na ce bari na kira ki na ji." Na ce." Eh da gaske ne ranar juma'a za a d'aura auran." Sai ta shiga jimami da zullumi kafin daga bisani ta furta." Ban yi maraba da auran nan ba 'kawata ina jin tsoron matar nan ta shigo ta tarwatsawa Yallabai gida domin kuwa muguwar 'yar duniya ce ga bin malamai na tsiya a wurinta." Na ajiye kofin hannuna a nutse na ce." Ke a Ina ki ka samu wannan labarin Sahura babu kyau fa zargi da zato akan abinda ba ki da tabbas a kai." "Amina da gaske ne wallahi muna tare da wata 'yar garinsu anan wurin aiki itama aure ne ya kawota nan garin itace take ba ni labarin gidansu da ita kanta Hajiya Maryam din sannan anan wajan aiki ma na ji ana ta maganarta wai bata da hali." Na ce." Ni dai ba zan gazgata maganarki ba Sahura tunda na zauna da ita na 'yan kwanaki ban hango wani aibu mai muni a tare da ita ba. Idan ma tana asiri da jefe-jefe ni dai na yi mata nisa wallahi Inna Uwani da Hauwa sun buga sun bari Sahura kin san duk wanda ya rike Allah Ya kama dahir don haka ki bar maganar nan kawai domin ni a halin yanzu ma ba itace a gabana ba wallahi. A sanyaye ta ce." To shikkenan na bari tunda kin ce haka amma fa kema ba zama za ki yi ba kawai ki zuba ido domin wallahi tallahi matar nan za ta iya raba ki da mijinki." Dariya na yi wadda babu nishadi na ce." Tun kafin ma maganar aure ta ratsa tsakaninta dashi ai ya sa waigi mai girma a tsakaninmu don haka ni ba zan zargeta ba Sahura." Shiru ta yi nasan tana nazarin maganata ne. Na ce." Kin ga idan kin taso daga aiki ki zo za mu yi magana akwai abubuwan da suke faruwa wanda dole sai kin ji amma ina so ya zama sirri a tsakaninmu." Jiki babu kuzari ta furta." To shikkenan in sha Allahu rabbi ki jiraye ni daga zarar na taso daga aikin zan shigo, Allah Ya rufa asiri." A takaice na amsa da 'Amin Ya Allah." Na kashe wayar na ajiye a kusa da ni. Wajen sha biyu na fita falon sai Yusra kadai a zaune tana duba Wani littafin. Na tambayeta baba Tabawa ta ce mini ta shiga kicin yanzu. Kai tsaye hanyar kicin din na nufa na sameta tana hidimar dora abincin rana na ce ta had'a kayan waina masa saboda zuwan Sahura tunda favorite dinta ne. Store din ta nufa da sauri tana fad'in." To bari na duba buhun shinkafar don ta d'auko hanyar k'arewa." Store din na bita tana daga buhun farar shinkafar bata fi sauka gwangwani shida ba. Na dubi kayan abincin da suke store din lallai bahaushe ya yi gaskiya da yake cewa zara bata barin dami. Ko da yake ai saura kad'an na shekara da tarewa a gidan kuma tun lokacin kayan abincin suke ake diba tunda har da masu gadin gidan ake yin abincin da Ayuba direba sun yi kasa sosai kayan abincin kuma ba na tsammanin zan kira shi domin na gaya masa ga halin da ake ciki. D'aki na koma na d'auko kudi na fito na ce Yusura ta kira mini Ayuba. Ina tsaye a bakin kicin Baba Tabawa tana ciki tana goge-goge muna d'an ta'ba hira ya shigo na bashi dubu goma na ce ya sayo mana farar shinkafa ta towo na sake bashi dubu biyar daban na ce ya yi cefane da ita. Da sauri ya kar'ba ya fita ya kama hanya ya tafi. Ni kuma na koma cikin d'aki na zauna ina cigaba da karanta wasi'kar jaki. Sai bayan da na tabbatar ta ci abinci ta samu nutsuwa tukkuna na fara gaya mata abubuwan da suka faru da kuma hukuncin da na yanke akan matakin da ya d'auka a kaina. Ta jima tana jimantawa kafin ta dube ni a sanyaye ta furta." Na rantse da Allah Amina kaina ya kulle gabad'aya ma na rasa yadda zan yi na auna lamarin nan, to wai shawarar me ki ke so na ba ki tunda lokacin da za ki aikata ba ki neme ni ba. Ya fa fi ki gaskiya wallahi sai dai idan ki take hakan dagangan! Amma yanzu ke kanki kin san fasuwar maganar ba karamin gagarimin abu ba ne a wurinki." Na zuba mata Ido da yanayi na 'bacin rai na ce." Sahura na lura ba za ki taba ganin kusuran mutumin nan ba, ban sani ba ko don kina aiki a 'karkashinsa ne oho, sau nawa ina gaya miki irin abubuwan da yake yi mini na rashin kyautawa amma ba ki taba goya mini baya ba, duk lamari idan ya faru sai ki ce lefina ne, shi kenan bayan kuskure duk abinda ya yi daidai ne saboda yana da kudi ko kina jin tsoron ki goyi da bayana ki samu matsala a wajen aiki ne." Ta dinga galla mini harara kafin ta ja tsaki ta furta." Tare muka tashi yarinta da girma na tabbatar da cewa ko anti Yagana ba za ta fi ni sanin halinki ba Amina, nasan abinda za ki yi da kuma wanda ba za ki yi ba. Abinda fa ki ka aikata kuskure ne babba wallahi domin kuwa hukuncin rayawa da kashewa ba a hannunki yake ba to me zai sanya ki shiga cikin lamarin Ubangiji." Shiru na yi ina kallonta jikina duk ya mutu da maganganunta. Sai ta cigaba da cewa." Dole ne na gaya miki gaskiya domin ni dake zama ne muke yin sa na gaskiya da amana babu yadda za a yi ki yi kuskure na biye miki zahirin gaskiya ba ki kyauta ba, kuma ni babu yawuna akan abinda ki ka kudirta abinda nake ganin shine alheri a tare dake ki cigaba da bibiyarsa kina bashi ha'kuri domin wallahi kin yi masa lefi mai ciwo amma da yake dan halak ne ya rufa miki asiri bai gayawa kowa ba. Duk irin shariyar da zai miki ki d'auka hakan hukunci ne yana sonki irin Wanda ke kanki ba ki yi tsammani ba na tabbata duk ranar da takaicin hakan ya sake shi zai neme ki ku sasanta, amma ba zan ta'ba baki shawarar cewa ki nuna masa daidai ki ke dashi ba alhalin ya yi miki zarra ta kowace siga kuma har yanzu dai tunda bai aiko miki da takardar saki ba kina nan a matsayin matarsa." Ajiyar zuciya na sauke bayan na gama sauraranta na ce." Na ji bayaninki sis, na amshi lefina kuma tun kafin ya bar garin nan na nemi afuwarsa na gaya masa na yi kuskure ba zan k'ara ba. Amma ina so ki sani cewa shi d'abiarsa ce haka muguwar gaba da ri'ko sannan kuma a lokacin da ake bashi ha'kuri a sa'in yake 'kara tunzura sai ya tsananta abinda yake yi. Watsar da shi tare da fita daga cikin sha'aninsa shine yake dawo dashi daidai. Na yi iyakacin abinda nake ganin zan yi, ai ba zina ya kama ni ina yi da wani ba, ba sata na yi masa ba, na uku ba madigo ya kama ni ina yi da wata mace ba. Abu ne ya faru wanda da ni dashi duka mun san haka, kuma mun shede a haihuwarmu ta farko. To me zai sanya haka kawai saboda kuskuran da na yi wanda nake da ya'kini Ubangiji ya gafarta mini sai shi a matsayinsa na adam ya ri'ke ni a cikin ransa da mummunan nufi. Wallahi na bashi ha'kuri Sahura na kwantar da kai na yi kuka da kalamai na gazawa da nadama ya'ki kula ni ya ki ke so na yi masa. Na gaji na yi rantsuwa da Allah da Annabi ba zan sake nemansa ba, kuma muddin ya k'ara wata d'aya akan watannin da ya d'auka bai zo inda nake ba zan bar masa gidansa idan ya so sai ya aiko mini da takarda ta inda nake a shirye nake da faruwar haka tunda ai ba wannan ne na farko ba." Ta yi shiru ranta duk babu dad'i da kyar ta ce." Yanzu dai kin barwa wasu shi kenan, ke girman kanki ba zai bari ki kwaci mijinki ba ko sisi." "Idan dole ta wannan sigar ya kamata ace na k'wace shi a hannuna wallahi na bar musu shi dama wahala yake ba ni a zamantakewar auran namu gabad'aya ya fi ni moriya domin irin galabaitar da ni da yake a shimfida ba kowace macace za ta jure ba. Ki bar maganar kawai Sahura za mu ga zuwan da dawowar kawai ki taya ni da addu'a." "Shikkenan ai tunda haka ki ke ganin ya yi miki amma ina so ki sa ni cewa wata k'addarar fa bawa ne yake janyowa kansa ita da kansa. Kada ki ce Allah ne a wannan ga'bar domin kuwa kin so a lissafa miki aure abinda kowa yake gudar mike kenan." "Ai da na haihu dashi ne zan damu ko na turasa zuciyata zama dashi saboda gudun kada a ce kowane d'a da ubansa Sahura to ban ajiye masa komai ba, kin ga kuwa lissafi aure ai ba komai ba ne tunda ba akaina a ka fara ba, idan har 'kaddara ta sanya ya sake ni to Ina mai tabbatar miki da cewa ni da aure har abada domin kuwa kin fi kowa sanin irin kalubalen da na fuskanta a rayuwata ta kowane fanni. Ai addinin musulunci addini ne mai sau'ki kuma auran nan ba fa farilla ba ne balle a ce dole kowane bawa sai ya yi shi. Idan na ce zan kare rayuwata a haka babu dalilin da zai sanya jama'a su zarge ni saboda na yi auran nan har biyu na ji dadinsa da rashin dadinsa wanda shi ya fi rinjaye muddin zan ri'ke kaina na iya sarrafa sha'awata a duk lokacin da ta motsa mini to yin hakan ba zunubi ba ne a wurin Allah." Shiru ta yi mini tana kallona har na kammala maganata ba ta ce komai ba, yanayinta dai ya nuna sam abinda nake shirin aiwatarwa bai kwanta mata a rai ba sai don babu yadda za ta yi ne ta ha'kura ta yi mini shiru. Sai daf da magriba ta tafi babu karsashi da sukuni a tare da ita cikin raina na ce ba zan ta'ba biyewa son zuciyarki ba Sahura saboda na riga nasan wanene Alhaji Tajo ciki da wajensa. Bayan Isha'i muna falo gabad'aya domin ni ma fitowa na yi na zauna muna kallon tare domin na fahimci zaman takurar da nake yi zai iya haifar mini da wata matsalar wanda kuma nake yi dominsa hakan ba damuwarsa ba ce....Ayuba Ya shigo ya tsaya daga bakin kofa yana cewa." Hajiya za a shigo da kayan abinci." A nutse na dube shi." Kayan abinci daga ina?" Ya ce." Maigidan ne ya sanya a kawo." Da mamaki mai yawa na ce." Gaya masa ka yi cewa na aike ka sayo shinkafa d'azu." Shiru ya yi tare da yin k'asa da kansa. Raina a 'bace na ce." Ashe duk abinda nake yi a gidan nan Ido ka sanya mini Ayuba ni ba ni da bakin gaya masa kenan sai kai ko?" A nutse ya ce." Ki yi hakuri Hajiya umarninsa yin hakan domin ya ce duk halin da ake ciki a gidan a dinga sanar dashi." Shiru na yi ina nazari wato duk shige da fice da zurga-zurgar da na dinga yi lokacin rikicin Hadiza sai da ya gaya masa kenan. Na dube shi babu fara'a a fuskata na ce." Shikkenan a shigo dasu." Ya juya ya fita da sauri. Baba Tabawa ta tashi ta nufi kicin din da sauri domin gyara store din. *** To kamar yadda yake a rubuce a katin d'aurin auran da ya d'ora a status d'insa ranar juma'ar dai aka daura auran bayan an yi sallah. Hajiya Maryam Abubakar Sabi'u jos tsohuwar matar amininshi Alhaji Amadu yau ta zama matarsa. Cikin kunci na 'karasa yinina cikin damuwa da ciwon kai wanda ya dabaibayeni a ranar na dinga k'okarin ganin na hana kaina kuka amma na kasa jimirin yin haka rufe kaina na yi a d'aki na ci kuka na 'koshi haka kawai nake jin wani irin mugun haushi da kishin matar a cikin zuciyata na tabbatar da cewa yana sonta yana kuma tausayinta tunda har ya iya auranta ba tare da kai da kawo ba. Itama kuma tana sonsa domin auransa zai zame mata rufin asiri domin cigaba da hurd'odinta kuma ina da tabbacin cewa babu abinda zai hanata aiwatarwa na abinda ya shafi abinda take yi tun kafin rasuwar tsohon mijinta. Hankalinsa zai fi kwanciya da ita tunda ai ita ya san wanda ta aura abokinsa ne kuma shi kad'ai ya yi tarayya da ita, ni kuwa fa maza biyu na aura a baya na haihu da d'aya. 'Dayan ban haihu dashi ba, ina ganin wannan dalilin shi ya sanya shi cire shakku a kanta har ya yi gaggawar auranta jim kad'an bayan fitarta daga takaba. Daddare status din ya k'ara d'orawa a karo na biyu na wannan lokacin hutonan d'aurin auran ne ya d'ora yana cike da walwala da annashuwa tare da manyan mutane abokanshi da suka samu damar halarta domin taya shi murna. Hotonan na dinga bi daya bayan daya ina dubawa sun kai kusan arba'in kowane kuma yana cike da annushuwa kamar wanda ya yi auren fari. Wasu hawaye masu zafi suka k'wace daga idanuwana duk ko'karin dannarsu da nake yi. Zuciyata ta dinga harbawa da k'arfi azababben kishin da nake yi a kansa ya motsa mini na dinga jin kirjiina yana toyewa. hawayen idanuwana na sake tsananta ai da farko na d'auka zan iya jurewa ashe ba haka ba ne soyayyarsa ta riga ta gama mamayata na tabbatar da duk wani yun'kuri da zan yi akan kwatar 'yancina idan lamarinsa ya bijiro mini sai na koka da hawaye domin kuwa abinda nake ji a can kasan zuciyata a halin yanzu Allah ne kadai ya san shi. Na ji radad'i da kishi ainun a lokacin da zai auri Hauwa haka zalika ma ina jin ciwo da b'akinciki a duk lokacin da ya furta Marigayiya Samira matarshi ta farko ita ce first love dinshi. A wasu lukutan na kwana na yini ban kula shi ba saboda haushi. Amma a yanzu sai na ganin abinda na ji na bakincikin auransa da Maryam ya shallake na baya. Gabad'aya ma na shiga dana sanin duba status din wanda na tabbatar da gayya ya d'ora domin ya cusa mini b'akinciki. Zamewa na yi na kwanta ina shar'bar kuka na tausayin kaina gefe guda kuma ina ta tunano irin muguwar soyayyar da yake gwada mini a baya kamar zautacce ashe akwai ranar da za ta zo da zan zama banza mara galihu a wurinsa. [9/24, 7:43 PM] Aunty B: 92 Wannan kukan da nake yi ya zama me mini dole ne na yi shi domin yinsa kad'ai zai sanya mini jin sasaauci a zuciyata. Amma kuma tilas ne fa na yi wani abu akan wannan lamarin namu domin sanin matsayin da nake. Haka dai na yi hakuri na danni zuciyata da 'karfin addu'ar da na dimanta na d'an ji sa'ida a cikin raina, amma dai duk da haka idan lamarin ya fado mini a raina na kan shiga wani yanayi mara dad'i. Na cigaba da kasancewa cikin tunani da nazarin yadda zan b'ullowa alm'arin. Kai tsaye shawarar da na yanke a raina itace zan nufi maiduguri gidan Baban Saude nasan shi kad'ai ne zai dube ni ya kuma fahimci halin da nake ciki. Nasan kuma zai ri'ke ni kamar 'yar cikinsa a wannan karon ba zan ce zan yi zaman kaina ba balle a canza mini manufa a iya tunanin da na yi shine gidan Baban Sauden dai shine marufar asirina babu wanda zai zarge ni da wata niyya na ke ko'karin kashe auran. Ba zan gayawa anti Yagana komai ba itama sai dai kawai ta ji labarin ina garin. Kuma na tabbatar da cewa babu wanda zai zo ya ce zai tursasani akan abinda ba na so muddin na ci sa'a Baban Saude ya kar'bi kukana ina da ya'kinin zai iya yin gaba da gaba da Alhaji Tajon sai dai duk abinda zai faru ya faru. Ina ta shirye-shiryen tafiya ban gayawa kowa ba shawarar da na yanke shine Yusura za ta koma hannun mamanta itama baba Tabawa zan sallameta da alheri mai yawa, masu gadin gidan da Ayuba dama ba ni na ajiyesu ba. Ina shakkar Babanmu ya samu labari abinda na tabbatar da cewa ranshi zai b'aci matu'ka da gaske. Hakan ba zai sanya ni na janye ba domin kuwa Babanmu zuciyarsa ba irin ta kowa ba ce ba zai iya ta'buka komai ba ko da kuwa an zube magana an tabbatar da cewa ni ma ina da gaskiya ta wani gefan ana cutar da ni. Sati uku da d'aurin auransa inda wa'adin rantsuwar da na yi akan rashin zuwansa ya kusa cika saura sati daya kenan wattanin bakwai da barinsa garin. Hajiya Saratu ta kira ni a waya tana gaya mini Hajja babu lafiya har sun je da ita Egypt sun yi sati daya sun dawo gida amma jikin da sau'ki yanzu. Na ce mata wallahi ban sani ba da tun wuri na zo na dubata. Mamaki ta dinga yi wai saboda na ce mata ban sani ba, ganin kamar tana so ta fahimci wani abu ya sanya na yi mata sallama tare da bata tabbacin in sha Allahu Ayuba zai kawo ni gobe na dubata. Kwana biyu a tsakani Ayuba ya kai ni gidan Hajja na dubata jiki da sauki alhamdulillahi ta warware don tana zaune ma ana ta hira, ni ma na saki jikina sosai domin ko da wasa ban nuna akwai wata matsala ba. Cikin hirar da muke yi ne na d'an fahimci wani abu ashe maigidan ya zo garin har ya yi kwanaki ya koma a cikin tsakankanin wannan lokacin bayan sun dawo daga Egypt . Shiru na yi da suna maganarsa ban iya cewa komai ba domin kuwa ni ban san ma ya zo har ya tafi ba, amma can 'kasan zuciyata abin ya tsorata ni sosai ya kuma sanya mini shakku anya maganar Sahura bata tabbata ba kuwa ko dai da gaske ne matar nan Maryam da ya aura tana asiri tunda mijinta har ya mutu da ita kadai ya rayu. Tunanina ne ya katse a lokacin da na ji Hajja tana maganar ai ya je can bauchi wurin Hauwa wadda take daf da haihuwa ko yau ko gobe domin kuwa sun yi waya da inna Uwani ta ce mata kwanansa biyu a can kafin ya tafi. Jikina ya 'kara yin sanyi kwarai da aniya tabbas mutumin nan ya sake ni furta mini ne kawai bai yi ba saboda mugunta ya jingine ni a gefe d'aya. Ina jin su suna ta hirar abinda ya shafe su, idan ta had'o da ni na sanya musu baki amma kuma zuciyata cike take da mamaki lamarin to sunce ya zo ya kwana amma me yasa basu fahimci cewar ba ma tare ba. Idan har ya zo din ai a gidana ya kamata ya sauka bayan ya duba mahaifiyartasa. Wani sashe na zuciyata ya ce mini tunda ki ka ga basu fahimci komai ba to wata'kila bai gaya musu wata matsala ba kuma ai yana da gidajen a garin da guesthouse bai zama lallai ya kwana a gidanki ba, idan ya yi musu sallama da zummar tafiya wurinki ai ba zasu fahimci komai ba." Wannan hasashen na zuciyata shi ya zauna daram a k'wa'kwalwata. Wato abinda ya yi kenan har ya yi kwanakinsa anan din ya tafi bauci wurin matarsa ba su gane komai ba. Ganin haka ya sanya ni ma na cigaba da nuna fara'a da annashuwata ban yarda yanayina yayi sauyarwar da za su gane akwai matsala ba. Da suna hirar Hajiya Maryam amaryarsa ni ma na sanya bakina Ina biye musu domin kuwa ga dukkanin alamu ta samu karbuwa a wurin Hajja tana sonta don sai fad'in alherinta take yi. Tabbas matar ta san takan zama tare da duniyanci domin kuwa koda bata asiri zai wahala duk wanda ya kusanceta ya ga laifinta domin ta iya mu'amula da kyautatawa. Gashi dai 'kiri-'kiri sun mayar da ni sauna ita da shi sun kar'be mini yarona duk tsananin sha'kuwar da take tsakanina da Yusi idan mun had'u sai na zama bak'uwa a wurinsa. Yadda ma za a yi ya dawo hannuna a yanzu shine abinda ya fi daga mini hankali da sanya mini fargaba domin kuwa yadda ya d'aukaki mutumin nan kamar shine wanda ya haife shi. Haka zalika ma ta b'angaransa shi Yallabai din ya sanya yaron a cikin ransa wanda yake nuna kamar ya ma fi ni iko da shi. Yini na yi sai yamma na yi shirin tafiya Allah sarki Hajja ta had'a mini Turaruka masu tsada da k'amshi na jiki da kuma na wuta dana tsinke. Zuciyata ta tsinke k'warai da gaske domin kuwa na tabbatar da cewa ta ji labarin bada'kalar da take faruwa hankalinta zai tashi wanda hakan ka iya yin barazana da lafiyarta. Na kuma gane dalilin da ya sanya shi kansa yake 'boyewa saboda tabbatuwar kwanciyar hankalinta tunda ni din ta gaban goshinta ce in banda yanzu da magauta suka yi yawa amma zahiri Hajja tana sona k'warai, kuma tana son zamana da d'anta. Ranar da na shirya tafiyar laraba ce wadda na tabbatar da cewa Sahura tana wajan aiki ba za ta yi yun'kurin zuwa ta dakusar da ni ba sai dai ta dawo gida ta samu Yusura da Baba Tabawa. Akwati biyu na yi ta kayana na hada komai dana tabbatar da cewa zan buk'ata. Muka yi waya da Hamusu na gaya masa zan je maiduguri ya cigaba da kula da komai wanda dama hakan aikinsa ne. Bai kawo komai a cikin ransa ba muka yi sallama. Na umarci Ayuba ya fito da mota kai tsaye gidan Sahura muka nufa aka yi sa'a Idiris yana gidan bai fita kasuwa ba tukkuna tunda lokacin da muka fito daga gida tara da rabi na safe. Tun a mota muka yi sallama da Baba Tabawa na bata dubu hamsin na ce ta ri'ke a hannunta amma tunda na sanya mata lambata a sabuwar wayar dana saya mata duk lokacin da take da wata matsala ta kira ni ta gaya mini zan tura mata da kudi. Ta kama hanya ta tafi gidanta kad'an da gidan Sahura. Ita Yusra sai da muka shiga gidan tare sauran yaran duk suna makaranta a gurguje na tsaya muka gaisa da maigidan yana tambayata lafiya dai na ce masa kalau zan je maiduguri shine dalili. Na mik'awa Yusra dubu biyar ta kar'ba jikinta duk a sa'bule na kama hanyar fita a gurguje ina cewa dashi ya gayawa Sahura zan kira ta a waya idan na isa. Tashar kasuwar kwari na ce da Ayuba ya kaini. Ya tsaya yana jayayya wai na fadi inda nake so na je zai kaini tunda akwai wadataccen mai a motar kuma aikinsa ne hakan idan oga ya ji labarin hakan zai yi sanadin rushewar hanyar abincinsa. ganin yana yi mini taurin kai ya sanya na rufe shi da fad'a sosai na ce ya sauke ni muddin ba zai yi abinda na ce dashi ba. Ganin yadda raina ya b'aci ya sanya shi jan motar bai sake magana ba kuma kai tsaye inda na umarceshi ya nufa da ni. Muna isa na bude motar na fito. Shi ma ya fito da sauri ya d'auko mini akwatinana. Mota guda na d'auka domin ba zan iya jira ba. Ban ma tsaya yin sallama da Ayuban ba na ce da direban ya shigo mu tafi. Ina kallonsa ya koma motar jikinsa a sanyaye kuma har direba da nake cikin motarsa ya ja muka tafi shi bai bar tashar ba. Tun a mota na kira Baban Saude dama kwanaki uku da suka wuce mun yi waya dashi na fara gaya masa halin da ake ciki ya ce mini maganar ba ta waya ba ce sai na zo tukkuna sai mu tattauna. Na sanar dashi cewa gani nan akan hanya ya yi mini fatan alheri da sauka lafiya. Sai daf da magriba muka isa maiduguri na sake d'aukar mota har kofar gidan Baban Saude yana tsaye a kofar gida fuskarsa kadaran kadahan har na fito daga motar direban yana sauke akwatinana. Ya k'araso wajen da muke tare da kiran yaronshi dake wasa a can tsallake ya rugo da gudu wajan ya umarce shi ya d'auki akwatin kayana ya shiga dashi gida. Yaron ya d'auki babbar akwatin da sauri ya nufi gida da ita. Shi kuma ya sunkuya zai d'auki k'aramar. Da sauri na ri'ke tare da cewa." Haba Baba bari zan shiga da ita." Ba tare da ya ce mini komai ya saki akwatin na d'auka muka jera muna tafiya yana fad'in. " Kin ci sa'a yau kwanana uku da dawowa kuma na kan d'auki sati ko kwana goma ban koma ba, Amina wannan lamarin naki ai abun a zauna ne domin kuwa ba karamin abu ba ne. Ni namiji ne amma ba na goyon bayan azzaluman maza." Murmushi na yi tare da furta." Wallahi Baban Saude tura ce ta kai bango ha'kurina ya kare akan lamarin nan, domin kuwa duk yadda na so ganin na zauna abin ya ci tura kamar yadda na gaya maka yau wata bakwai kenan rabona dashi kuma duk ya rufe hanyar da zata had'ani dashi to kaga zamana ai bashi da amfani yana da kyau ace a neme shi domin ya sanar da manyana abinda ya yanke akaina." Ya gyada kansa yana fad'in." Don kuskure kin yi, amma hakan ai ba zai sanya a d'auki wannan mummunan matakin ba. Idan ba yana so ya jefa ki a wata masifar ba me zai sanya ya k'aurace miki na irin wannan watannin akan hakan dole mu neme shi, sai maganar zargi da rashin daidaituwar jini gabad'aya ma auran naku a baibai yake babu dacewa ai ta wani gefan kema kina da hujja Amina, na kuma ji dad'in da ki ke neme ni domin sanya ni a cikin lamarinki zan yi kokarin ganin na samar miki da farinciki in sha Allahu. Gidan Baban Saude mai yalwa ne kuma daidai gwargwado yana da rufin asirinsa don har yanzu da rayuwa ta yi tsadar nan shinkafa 'yar gwamnati ake ci a gidansa. Taliya 'yar hausa kuwa sai dai idan suci ta da sha'awa yadda yake jingine musu buhun shinkafa ta gwamnati haka yake ajiye masu kwalin taliya da makaroni na waje. Mutum ne mai wadata iyali matsalar kawai fa'da da tsautsauran ra'ayin takura iyali domin kuwa kafin a fita unguwa a gidan Baban Saude akan jima sai da 'kwa'kkwaran dalili. Matansa biyu kowacce da yaranta da d'akunansu ciki da rumfa ne manya. Akwai shaguna biyu daga waje wanda ciki matasan yaransa maza suke kwana cikin gidan kuma bayan d'akunan iyalinsa akwai falle falle biyu masu grima sai kicin da bandaki biyu na fitsari da kuma na ba haya sai wadataccen tsakargida mai yalwa don har da bishiya a tsakiyar tsakar gidan. Sayyada ce kawai take zawarci dama lokacin da anti Yagana ta je mini take gaya mini ai an sasanta anti Saude da anti Zainab sun koma d'akin mazajensu amma kafin hakan sai da aka sha daru domin shi cewa ya yi raba auran zai yi. Sai da Dada ta yi masa jan Ido tukkuna ya janye matakin da ya d'auka domin idonsa ya rufe baya duba kowa dama ai hausawa suka ce kowa nasa ya sani, shi yana duban 'ya'yansa yayin da mazajen suma suke duba wahalar da nasu yaran za su shiga muddin aka raba su da iyayensu. Anti Saude itace babba don ta girmi ma anti Yagana amma da kad'an kuma yaranta bakwai, ita kuwa anti Zainab haihuwarta biyar daya ya rasu hud'u a raye amma duk da haka ya ce shi sai an sakar masa yaransa kuma ya tubure lallai babu d'an da zai d'auka ya yi wa wahala kowanne yaro ya koma gidan ubansa. Gabad'aya ma sai sanya dokar kada a kuskura a bari yaran su shigo masa gida. Wannan matakin da ya d'auka shi ya gigita anti Zainab tunda ita nata akwai k'ananu a ciki kuma ita kadaice bata da kishiya mijin nata ya d'auki yaran ya kaiwa yayarsa ita kuma kullum ficewa take yi kasuwa ta baza hajarta. Anti Saude ce mai kishiya kuma yaranta sun girma sannan kuma duk maza ne. Anti Zainab kuwa da mata a ciki. Tashin hankalinta ta yi sosai babu shiri a 'boye ta je gidan Dada ta fashe mata da kuka tana gaya mata yadda aka yi tare da neman alfarma kada ta gayawa Baban nasu itace ta gaya mata. Wannan shine dalilin da ya sanya Dada ta bud'e masa wuta akan lallai ya nemi mazajensu ya zauna dasu ya ja musu kunne amma banda maganar rabuwa a duba yaran domin kuwa hukuncin da ya yanke ba shine mafita ba tunda dole ai watarana za su sake yin aure kuma mazan ba 'kwan'kwasasu ake yi a ji ba. Ita kuwa Sayyada da yake itace auta a mata kuma sunan Dada ne da ita dama tun kafin a yi mata aure 'yar lele ce tunda ya fahimci mugun miji take aure mara ciyarwa da kula da lafiya sai kawai ya maka shi a kotu akan ya sakar masa 'yarsa ya kuma fadi ko nawa ya kashe a lokacin da zai aureta zai biya shi tunda shi ya nemi sakin dama kuma haihuwarsu d'aya saboda farincikin Sayyadar ya bar yaron nata a hannunta domin kuwa kuka ta dira a gidan bayan alkali ya raba auran ta ce ita ba zata bada yaro ba. To da yake dama 'yar lelensa ce sai ya kyaleta ya ce mata amma muddin ubansa ya zo nemansa za a bashi abinsa. D'aki guda ya sanya a ka gyara mini tsaf har da katifa da sabon mashinfid'i da labuleye masu kyau d'akin yana ta k'amshin turaran wuta. Mama uwarginshi da kanta ta shigo ta kawo mini abinci a jere a tire na silba muka sake gaisawa bayan wadda muka yi tunda kafin na shiga masaukina sai da na shiga duka d'akunansu muka gaisa. Ta dinga tambayata mutanan gidanmu da yaran na ce mata duk kowa lafiya lau. Sai da nayi wanka tukkuna na d'an warware na ji 'kwarin jikina na zauna a nutse na ci abinci na 'koshi na fita da tiran ina sake yi musu godiya na koma d'akin na zauna tare da fito da wayata daga cikin jaka domin tun a cikin mota ban sake dubata ba. A mace take ban san dalilin da ya kasheta ba. Minti biyar da kunna wayar kiran anti Yagana ya shigo. Cike da fad'uwar gaba da fargaba na d'aga nasa a kunnena cikin wani irin yanayi na yi sallama bata amsa mini ba na ji tana ce wa." Ya aka yi ki ka kashe wayarki Amina tun wajan la'asar nake kiranki sai a ce mini a kashe take." A hankali na ce." Bacci na yini ina yi kuma tunda na sanyata a caji ban sake waiwayenta ba sai yanzu ina fatan kuna lafiya ina Fadila." A takaice ta furta." Lafiya lau, mijinki ne ya kira ni yake tambayata wai kin zo gidana na ce a a wani abun ne ya faru a tsakaninku ne?" Cike da takaici na ce." Babu abinda ya faru anti Yagana don girman Allah idan ya sake kiranki kada ki daga wayarsa." "Akan wane dalili zai kira ni na'ki dagawa Amina, ki gaya mini menene yake faruwa domin yanayin da ya kira ni a d'azu ya tabbatar mini da cewa akwai abinda kuke b'oyewa ke da shi." "Saki na ya yi." Na tsinci kaina da gaya mata hakan. Cikin rud'u da tashin hankali ta furta." Saki akan wane dalili, kina ina yanzu domin ya tabbatar mini da cewa tun safe ki ka fito daga gidanki direbanki Ayuba ne ya kira shi a waya ya gaya masa shine ni kuma ya kira ni yake tambayata." Cikin dauriya na ce." Anti Yagana abinda nake so dake a wannan ga'bar da muke ci da mutumin nan don girman Allah ki cire kanki idan zai kira ki sau dubu ya tambayeki abinda ya shafe ni ki ce masa ba ki da k'arfi akan lamarin ya nemi manyana su yi magana." Ta ce." To na ji, ko zan iya sanin abinda ya faru, sannan kuma ki gaya yanzu kina ina domin hankalina ya kwanta Amina sha'aninki yana nema ya fi karfina, don girman Allah ki fahimci kin girma fa kina dai kallon abinda ya samu Hadiza ko, mune manya a gidanmu ba mu da namiji babba dole mu zamu tallafi 'kannanmu da suke tasowa don Allah ki yi hakuri ki jure kamar yadda kowace mace take ha'kuri a d'akin mijinta ki zauna wannan ya zama mutuwa ce zata raba tsakaninku ki yi mana wannan alfarmar." Ta kare maganar cikin rawar murya. Ina kuka na ce." Anti Yagana ya zan yi ne da rayuwata gabad'aya duniyar ta yi mini zafi a yanzu bana jin dad'inta. Duk yadda zan yi na yi kokarin ganin na zauna d'akina amma abin ya gagara, Allah Ya had'a ni da wani irin (Ba'aboren namiji) sunan littafin Binta Umar Abbale ku nema ku karanta ya yi mutukar dadi. Tana kuka irin mai tafe da tsananin damuwa da takaici ta cigaba da cewa." Abubuwan da suka faru tsakanina da shi suna da yawa anti Yagana na gaji da b'oye miki na kuma gaji da zama da mutumin nan so nake yi kawai ya sauwake mini na huta idan ba so yake yi zuciyata ta buga ba." A sanyaye ta ce." Dalili dame bakincikinsa zai kashe ki Amina, ai taura biyu bata taunuwa a lokaci daya babu yadda za a yi ace a shari'ar ma'aurata an saurari b'angare daya ni ba zan yarda da maganarki ba har sai ya zo tukkuna an zauna an zube magana sai a fahimci wanene mafi rijayen lefi." Cikin kukan na ce." Anti Yagana ke fa macace ya kamata a ce kin dubi halin da nake ciki, ki fahimce ni wallahi ina da matsala ba wai da gangan nake so auran nan ya mutu ba ina da hujja mai karfi." "Hujjarki ai bata wuce kina gudun haihuwar yara masu cutar sikila ba dalili kuwa shine rashin had'uwar jini. Wannan ce kad'ai hujjarki wadda na sani Amina, sai kuma kishin da yake damunki tunda na ji labarin an ce ya sake yin wani auran, in bayan hakan ban san wani abu da ki ka taka ba. Sannan kuma ai kai tsaye ban ce miki baki da gaskiya ba, cewa na yi a bari a ji ta bakinsa tukkuna kafin a yanke hukunci wannan shine adalci, ai duk yadda zan so shi bayanki ne, matsalar namiji kuwa muddin ki ka ce ba za ki iya d'aukarta ba to Amina kina tare da damuwa domin kuwa kusan gabad'ayansu haka suke. Na ce." Wallahi anti Yagana ban da Babansu Fadila a ciki, ai ya yadda ki ka kasa fahimtar damuwata tuntuni na tabbatar da cewa ba ki kai ajin da nake ba dangane da karatun namiji, maza uku fa na aura kuma kowa da halinshi wallahi ban ta'ba shan wahala a hannun Yaya Aminu da Alhaji Muntari irin wadda nake sha a hannun mutumin nan ba. Ku ne kawai kuke yi mini kallo hutu da jin dadin amma ni kadai nasan irin takaicin da nake 'kunsa." Murmushi ta yi har sai da na ji sautinsa ta furta." Ha'kuri dai kawai na fi ki shiyasa ki ke ganin kamar ba ni da wata matsala da mijina. Amma kai tsaye ba zan musanta miki ba domin kuwa mai-d'aki shi yasan inda yake yi masa yoyo abinda nake so dake anan shine ki gaya mini kina ina yanzu hankalina zai fi kwanciya." Kai tsaye na ce." Ina nan gidan Baban Saude yanzu haka." Cike da zullumi ta furta." Gidan Baban Saude fa ki ka ce Amina?" [9/25, 8:18 PM] Aunty B: 93 "Kina da hankali kuwa Amina, shin ko kin manta halin Baban Saude da d'aukar jidali akan abu 'kalilan zai mayar dashi babba. Mai yasa ba ki yi shawara da ni ba tukkuna kafin ki yanke wannan hukuncin sanin kanki ne Alhaji Tajudden ya yi nisan da wani mahalu'ki zai kai ya ta'ba mutuncinsa ko da babu dukiya kuwa to dattijanka da girma da mutuncinsa ya wuce a ce kina yawon kai shi a k'ara, kuma duk ki tsallake 'yan uwan Babanmu saboda raini ki taho wurin Baban Saude saboda dama kin tabbatar da cewa shi din ba mutum ne mai nisan tunani da tsinkaye akan lamari ba. Yanzu me ki ke tunanin zai faru idan har ya kashe miki aure wallahil-azim ba ni babu ke Amina." Ta kàrasa maganar cikin tsantsar tashin hankali da damuwa. Sosai kaina ya d'aure da jin maganarta. Wai yau anti Yagana itace take kiran Baban Saude da mutum mara tsinkaye saboda wani na daban, ta manta cewa Baban Saude ciki daya suka zauna da Mamanmu. uwa daya uba daya ba wasa ba ne, kuma wallahi duk tsayayyar da yake yi akan gaskiyarsa yake mutane ne suke ganinsa masifafe. Ba na shakka ko fargabar had'uwarsu da Alhaji Tajon ai mutunci da sanin ciwon kai ya fi komai a rayuwar wanda yasan kansa. Baban Saude ba makwadaici ba ne ballantana yana ganin gaskiya ya take da gangan. Ai da Babanmu zai d'auki wani mataki da tuni ya d'auka tun kafin lamarin ya yi tsanani irin haka to ballantana kuma baba Sule da yake da son abin duniya. Ni gabad'aya ma na rasa gane inda anti Yagana ta dosa wallahi da ban san halinta ba da sai nace itama kudinsa take kwad'ayi. To na san halinta da kawar da kai da kawaici akan abin mutum sam bata da wannan zulamar. Abin mamaki wai yau anti Yagana ce take cewa idan na rabu da wani namiji ita da ni har abada. Sai kawai na ji wasu zafafan hawaye sun k'wace mini suka fara kasa tsere a kumatuna. A hankali na ajiye wayar na silale na kwanta saman ledar dake tsakar d'akin Ina wani irin kuka mai ciwo lallai mutumin nan ya yi wa rayuwata illa ta kowane 'bangare. Wajejan sha biyu na dare na tashi na je na d'auro alwala nafila na yi raka biyu cikin sujjadar karshe na fashe da kuka tare da kai wa Allah kukana akan ya za'ba mini abinda ya fi alheri a rayuwata muddin rabuwata da Alhaji Tajon akwai alheri to Ubangiji Ya gaggauta kawo k'arshen lamarin. Idan kuma zamana dashi bai kare ba ina ro'konsa ya daidaitamu cikin ruwan sanyi ba tare da an kai ruwa rana ba rayuka sun 'baci ta dalilin hakan. Na kwanta bacci da jin sasaauci a zuciyata domun kuwa ina kammala addu'ar na ji nutsuwa ta shigeni tare da tawakkali da kar'bar duk irin abinda Allah Ya zartar a kaina. Da safe bayan na yi wanka Sayyada ta kawo mini kayan karin kummalo d'akin da nake ta zauna muna d'an ta'ba hira jefe-jefi kafin ta fita daga d'akin domin ba ni damar karyawa a nutse. Gama karin kummalona ke da wuya Babansu Fadila ya zo wato mijin anti Yagana lokacin Baban Saude ya fita zuwa babban gida wajan Dada domin su gaisa. A soro na same shi a tsaye da shirin fita wajan sana'arsa muka gaisa kafin ya fara yi mini maganar da ta kawo shi domin jiya duk wayar da muka yi da anti Yagana a gabansa ne kuma shi ma a jiyan da magriba ya ga gilmawarta a Tasha sai yake hasashen anya ni din ce domin bai gama tabbatarwa ba sai da ya dawo gida tukkuna ya tabbatar da cewa ni din ya gani bayan saukata a garin. Nasiha da ban ha'kuri tare da kawo misalai irin na matan magabata ya dinga yi mini har yana cewa ko don yadda 'yar uwata take shiga damuwa matsananciya akan matsalata yana da kyau na jure na yi hakuri na samar mata da nutsuwa domin kuwa jiya raba dare ta yi akan dadduma gaban Allah tana addu'a da hawaye akan lamarin. Wannan dalilin ya sanya shi ma ya kasa rintsawa har garin Allah ya waye kuma ya kudire a ransa cewa zai zo ya same ni akan abinda yake faruwa. Hakika sun ba ni tausayi sosai ita dashi kuma sun isa su ce mini na yi ko na bari ba tare da na yi musu jayayya ba. Amma a wannan karon Ina ganin ba zan iya bin umarinsu ba domin kuwa duk abun nan da ake yi shi wanda ake yi dominsa bai yi wata magana ba, bai zo ba tun bayan kiran da ya yi wa anti Yagana jiya ban sake ji daga gare ta ba. Hakan na gaya masa na ce ya bari tukkuna ya magantu ai yanzu dama a hannunsa take idan yana da ra'ayin cigaba da zama da ni zai zo ya nemi sulhu idan kuma bashi da ra'ayi to zai aiko mini da shedar da zata nuna mini lallai ya gama zama dani, Ina ganin kamar haka ya dace a yi. Sai ya nuna ai ba haka ya dace a yi ba tunda ai anti Yagana ta gaya masa har yanzu na'ki na fadi abinda ya yi mini kuma ba shine ya ce da ni na tafi gida ba yaji na yi na bar d'akina don haka kuwa tunda ba shine ya ce na tafi ba ai babu lallai a ce sai ya nemi inda nake domin ya ji dalilina. Na jima ina nazarin maganar kafin daga bisani na yanke shawarar gaya masa abinda yake faruwa tunda ai shi din ba bare ba ne, sannan kuma maganace da za a zauna a zube ta shi ma makusancina ne tunda yana auran sha'ki'kiyata. Duk bada'kalar da take faruwa na zayyana masa da irin ni ma abinda na aikata da tuban da na yi sannan kuma na tabbatar masa da cewa na gane kuskurena na kuma nemi afuwa da gafarar Allah da kuma neman sulhu da shi domin mu yafi juna amma hakan bai yi masa ba har sai da ya d'auki hukuncin kaurace mini na tsayin wattanin tare da shigowa garin ba tare da ta nemi inda nake ba . Sosai al'amarin ya dake shi ya jima yana nazari kafin daga bisani ya dube ni da alamun tausayi da sasaauci ya ce." Ni ai duk ba ta gaya mini haka ba Amina ta dai ce mini kawai tana zargin ke ce ba ki son auran ki ke so ki kasheshi amma ba ta gaya mini dalili ba A hankali na furta." Ai ba ta sani ba don ban gaya mata ba har yanzu saboda na san halinta da sanya abu a ranta kuma ba zama lallai ta fahimce ni ba, in banda kai da Baban Saude babu wanda na gayawa sai ko Sahura 'kawar nan tawa. Ya ce." Lamarin na ku ne da rikitarwa Amina, kina da kuskure shi ma yana da nasa kuskuren ai dama ba za a d'auki lefi a daurawa mutum d'aya ba. Kuma gaskiya abinda ya fi tsaya mini a raina dangane da lamarin nan yawan zargin da ki ka ce mutumin nan yana yi miki babban abu ne a ganina wannan ba soyayya ba ce domin kuwa zargi yana daya daga cikin manyan dalilan da suke saurin lalata ala'ka ta auratayya. Ba zai yiwu a ce don ya aureki a matsayin bazawara kuma 'yar kasuwa ya dinga zarginki ba sam ba da shi da hujja ko a wurin Allah domin kuwa bai ta'ba kama ki da wani mummunan abu ba. Sai maganar tsayin wattanin da ya d'auka ba tare da ya neme ki ba, wannan normal ne Amina akwai matan matafiya da suke shekara da biyu uku ba tare da mazajensu ba kuma aurensu bai lalace ba sai dai kin san shi addini kogi ne domin ni kaina na ji wasu malaman suna cewa idan namiji ya k'auracewa mace na tsayin wata uku hud'u biyar har zuwa shekara to aure ya haramta a tare dasu amma fa sai in dai suna kwana tare a gida daya ya aikata hakan. Idan sun yi nesa da juna kamar dai matafiyi wannan ba lefi ba ne haka daga shekara daya zuwa biyu aure yana nan. To anan za mu iya cewa auranku yana nan tunda baya garin da a ce kuna gida daya ne kuna kwana a daki daya ya k'aurace miki tabbas akwai alamun a tambayi malamai domin sanin menene gaskiyar lamari. Wannan shine iyakacin fahimtata. Ya nisa kafin ya cigaba da ce wa." Sannan ke ma zan gaya miki gaskiya abinda ki ka yi bai kyautu ba domin kuwa kin shiga hurumin Ubangiji dalili kuwa ai shine mai rayawa da kashewa kuma bai zama lallai don kin haifi d'aya da lalura ba ki ce duka yaran da za ki haifa haka suke ba. A lokacin da ki ka lura da samuwar cikin sai ki bar shi kawai ki ro'ki Allah ya ba ki masu albarka kuma masu lafiya. Abu na biyu kuma kin ga mutumin nan bashi da yara shi zai so ko masu lalurar ne wannan kadai ya isa ya sanya shi ya k'ullaceki kuma ya ga duhunki domin kuwa ai zai ga kamar kina yi masa b'akinciki ne saboda wata hujja taki wadda bata da tushe balle makama, sannan da yawan mutane ba zu fahimceki ba domin kuwa za a ga ai ke ko dan kina da yaran ne ya sanya ki ka zubar masa da nasa cikin. Lefi ne babba ko wurin Allah Amina amma kuma na ji dad'i da ki ka gane gaskiya kuma ki ka nemi gafara a wurin Allah lallai Ubangiji mai afuwa ne kuma mai yafiya ne, sannan kuma shi ma Yallabai din yana da kyau ya yafe miki ya d'auki 'kaddara domin ta riga fata bai kamaci ya d'auki wannan matakin ba domin a ganina da tun farko kun kashe matsalarku a cikin gida hakan zai fi alheri ba tare da kowa ya sani ba domin kuwa irin wannan lamari baya buk'atar a ce a zauna ayi ta nanata shi saboda kowa da irin fahimtarsa wasu suna gyarawa ne wasu kuma na 'batawa." Tun a 'karshen maganarsa na fahimci gugar zana yake yi mini akan Baban Saude wata'kila kafin zuwansa nan din anti Yagana ta gaya masa halinsa shiyasa yake yin shagu'be shi ma yana nuna rashin dacewar kawo maganar wajan Baban Saude ni kuma gabad'aya duka sun kasa gane dalilina. Ban kawo 'karar Alhaji Tajo wurin Baban Saude da zummar ya wulakantashi ba, ni kaina nasan wargi ma wuri shi ka samu. Baban Saude idan yana yi wa wasu ya zauna lafiya ina ganin kwarjini gami da haiba irin na Tajudden ya wuce a ce ya yi masa tijara mai muni. Ina dai da tabbacin cewa za su yi musayar yawu irin na fahimta domin a samu matsaya akan abinda yake faruwa. Wajejen sha biyu na rana Sahura ta kira ni a waya a nutse na d'auka muka gaisa amma babu cikakkiyar walwala a tare da ita fara da cewa." Yanzu sis ashe dai sai da ki ka sanya kafa ki ka shure shawarata ko? jiya na dawo daga aiki na tarar da Yusra a gida da yamma Baba Tabawa ta shigo tana gaya mini kin yi tafiya zuwa maiduguri gaskiya ba zan boye miki ba ban ji dad'in abinda ki ka yi ba domin kuwa yanzu nan muka gama waya da anti Yagana tana tambayata wai ko nasan wani abu da yake faruwa game dake." Ta nisa kafin ta cigaba da cewa." Na ce mata kin gaya mini amma kin ce sirri ne, shine ta ce to na bar shi ba sai na gaya mata ba tunda amana na kar'ba a wurinki. Sai ta kashawar a sanyaye Ni kuma gaskiya na ji rashin dadin hakan mai yasa ki ka boye mata abinda yake faruwa da rayuwarki sis bai kamata ace har sai ta fito duniya tana neman dalili ba." Murmushi na yi mara armashi na ce." Sahura hakan da na yi shine kwanciyar hankalina da kuma samun nutsuwata don Allah kada ki ka ga lefina kada ki 'kullace ni, addu'a kawai nake so ki taya ni da ita, sannan maganar anti Yagana kuma ni na fi kowa sanin halinta kwata-kwata ba ta kar'bar uzurina in dai akan mutumin nan ne to bata ta'ba fahimtata kamar yadda ke ma ba kya gane nufina. Wannan dalilin ya sanya ban gaya mata ba domin lefinsa za ta take da k'afarta ta rufe gabad'aya ta d'auka ta d'ora a kaina, to shiyasa ko da na yanke shawara ban nufe ta ba kai tsaye na yi tafiyata a gidan Baban Saude." Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce." To ke yanzu me ki ka yanke a zuciyarki rabuwar ki ke ganin itace mafita a gare ki ko kuwa?" "Ban yanke komai ba Sahura sai abinda Allah Ya zaba mini, idan har rabuwar itace alheri ina farinciki da hakan, idan kuma akwai sauran zama a tsakaninmu to gaskiya ba zan koma ba lallai sai ya fahimci cewa abin fa da yake aikatawa kuskure ne, sai ya dauki matakin gyara da alkawari tare da sharad'in hakan ba zata sake faruwa ba. Murmushi ta yi irin na takaici kafin ta ce." Amina wani lokacin ina mamakin tsaurin idonki wallahi to wai Baban Sauden ki ka wakilita da ya kira Yallabai din ya titsiye shi akan kuskuran da mafi rinye ke ce mai shi. Idan fa an bi ta 'barawo to a bi ta mabi sawu na gaya miki tun ranar da na zo gidanki wallahi ke ce mai lefi mai yasa za ki zubar masa da ciki saboda wani banzan dalili da bashi da tushe. Son zuciya ne fa wannan tsagwaronsa ki ka nuna masa a zahiri saboda ke ai kina da yaran shi kuwa fa. Ki bari ki haihu mana ki ga abinda za ki haifa da lafiya ko babu kawai sai ki yankewa Allah hukunci, ba zan gaji da gaya miki ba, baki da gaskiya." Cike da tsantsar takaici na ce." Ban kyauta ba din Sahura duk abinda za ku yi ku yi din, haba na gaji da magana daya wai ana aure dole ne ko kuma tilas aka ce sai na zauna da mutumin nan da za ku bi ku tsangwameni. uwata ce ke da za ki kira ni a waya kina gaya mini maganar da ranki ya so, ko kuma ke ce ki ke zaune da mutumin nan ne, kwata-kwata kun kasa fahimatata, na yi kuskure na nemi afuwar Allah amma gabad'aya kuna juya mini magana saboda kawai wani dalili naku. Shi din sahabi ko kuma Annabi ne da ba za a 'bata masa rai ba. Ko annabawan Allah suna kuskure balle wani bawa kuma Allah Ya yafe musu saboda haka a yanzu daga ke har anti Yaganar ba na buk'atar ku fahimce ni, duk abinda za ku yi akan lamarin kun jima ba ku yi ba." Ina gama maganata na kashe wayar raina a mafisar b'ace. Tunda muke da Sahura ba mu ta'ba musayar yawu mai zafi irin wannan ba. Haba na gaji da jan magana d'aya muddin ba za su gane hujjata ba to sai mu yi ta tafiya a haka ba zan sake yarda wata ta kira ni a waya ta 'bata mini rai ba. Da takaicin abinda yà faru tsakanina da Sahura na yini duk yadda na kai ga ko'karin ganin sun fahimceni ita da anti Yagana abin ya gagara har sai da sa'bani ya gifta a tsakanimu, to kuwa ta yaya za a yi kuwa na manta da mutumin nan tunda ta dalilinsa anti Yagana take furta maganar da ban ta'ba tsammanin fitowarta daga bakinta ba, wai za ta rabu da ni har abada saboda shi yau ga Sahura tana gaggaya mini ba'kaken maganganu. Ban ta'ba nadamar saninsa ba a rayuwata sai a wannan lokacin. Da daddare muna zaune a babban tsakar gidan gabad'aya har da maigidan Baban Saude an shimfida masa dadduma mu kuma muna zaune a 'katuwar tabarma ana ta hira cikin nisha'di cikin raina ina ta mamakin hakan wato duk wanda zai k'alubalanci Baban Saude akan wani lamari tabbas ba zai zauna dashi ba ne, sannan kuma bai gama karantar hali da d'abi'arsa ba. Dada da Anti Yagana suka yi sallama a lokaci daya suka shigo gidan. Ganinsu a tare ya sanyayar mini da jiki domin kuwa na tabbatar da cewa anti Yagana ce ta je ta gaya mata abinda yake faruwa. Suka zauna akan tabarma ana gaisawa Baban Saude yana cewa da Dada ba ta gaya masa za ta zo ba a d'azu da safe da ya je can gidanta domin su gaisa. Sai ta kuwa ta kada baki ta ce." Ni ma dole ce ta sanya ni zuwa ai domin kuwa abinda ka boye mini shi Yagana ta je ta gaya mini shine na ce bari na zo da kafafuna gidan naka na ji dalilin da ya sanya ka b'oye matar mutane a gidanka, idan har za ka yi iko da yaranka Haruna wannan dai baka da k'arfi a kanta kuma babu yawuna a cikin yun'kurin da ka ke ko'karin aikatawa." Cikin nutsuwa ya ce." Wato Yagana ce ta je ta taso ki da daddaran nan kenan, kin kyauta Yagana na ce kin kyauta." Ya fad'a yana kallonta da b'acin rai a tare dashi ita kuma sai ta yi kasa da kanta tana cike da damuwa ta furta." Baban Saude don Allah ka yi hakuri wallahi ba nufi na ba ne na bata maka rai, Amma ni nasan Amina bata da wata hujja gabad'aya ma majority lefin nata ne tunda d'azu Babansu Fadila da ya zo ta gaya masa duk abinda ya faru wanda ni ta rufe mini saboda ta san ba zan goyi da bayanta ba." Ya ce." Shiyasa ki ka je ki ka gayawa Dada kenan saboda ni ban isa na yi hukunci ba, ko kuma ni zan goyi da bayan k'arya ko?" Ta yi shiru tana girgiza kanta alamun ba haka ba ne. Ya gyada kansa da takaici ya dubi Dada tare da ce wa." Duk abinda Yagana ta je ta gaya miki akan Amina kada ki amince da cewa ita kadai ce take da laifi domin shi ma mijin nata da akwai tasa matsalar, kuma yana da kyau ace yarinyar nan an dubi matsalarta an kuma d'auki matakin gyara. Ba ni da burin kashe mata aure sai dai idan har hakan ya zama dole, sannan kuma ni babu ruwana da wanda take aure dukiya nasaba ko wata d'aukaka ta mutum. Ni namiji ne amma ba na goyon bayan mazajen da suke zalintar matansu ta kowane 'bangare. Wannan dalilin ne ya sanya da yawa mutane suke yi mini kallon mafad'aci saboda tsage gaskiya. Dada babu yadda za a yi yarinya ta kira ni a waya tana kuka akan wata matsalar da ta dameta na ce babu ruwana a ciki dalili wata hujja dan ban zo a b'angaran mahafinta ba to ban ga dalilin da zai sanya na ja baya akan lamarinta ba, idan na yi hakan kuwa tabbas ban dubi zumunci ba, kuma ban yi wa 'yar uwata kara ba. Ba dalili ba ne a ce wai dangin babanta ne lallai suke da hakkin kare mata mutunci ba, to idan kuma suka gaza fa, ma'ana suka kasa ta'buka wani abu akan lamarinta shikkenan sai ta zauna a hannun wanda bai san daraja da mutuncinta ba." Wajan ya yi tsit kowa ya yi shiru yana sauraransa. Ya nisa kafin ya cigaba da ce wa." Tun kafin ta zo nan ta gaya mini halin da take ciki a waya da kuma ta zo ta sake jadadda mini duk abinda ya shiga tsakaninta dashi da abinda ta aikata masa da matakin da ya d'auka akanta. Dan Kuskure ta yi kuskure kuma ban goyi da bayan ta sake aikata hakan ba ko bayan raina na gargad'eta domin hakan fasadi ne mai girma. Ta kar'bi lefinta ta yi nadama ta tuba ga Allah kuma ta nemi gafara to me zai sanya ba za a yafe mata ba. Wannan sune kadai matsaltsalun Amina, kuma na ja kunanta kwarai da gaske akan ta gyara ta kiyaye a gaba. Ba wai ina goyon bayanta ba ne a yanzu ta ce ba ta da ra'ayin zama dashi cikinmu babu wanda ya isa ya yi mata dole domin kuwa ita ba yarinya ba ce ta san abinda yake mata ciwo sannan kuma tana da hujja ko a gaban alkali za ta fad'a masa dalilinta na son rabuwa da auransu saboda matsalar rashin daidaituwar jini da za a samar da yara masu ingantaciyar lafiya. Abu ne ya zo a zamanance ba mu ce za mu yi wa Allah wayo ba, amma zahiri lalurar nan akwaita dalilin da ya sanya ma kenan aka fara d'aukar matakin kare kai daga riskar abinda zai faru bayan an yi aure. Amma fa wannan bayanin nawa baya na nufin cewa ina goyuwa da bayan yahudawa ba ne a a ko daya domin kuwa ni kaina a lokacin da na auri iyalina babu gwaji na jini kuma ga yara na nan duka mun haifa lafiyarsu lau babu wani mai lalura daga ciki. Saboda haka Dada ki fahimce ni anan wannan ga'bar kada a tilasta yarinyar nan a ce dole sai ta cigaba da zama da bawan Allan nan alhalin bai san girma da mutuncin ba." Dada jikinta ya yi sanyi sosai duk karsashin da ta shigo dashi gidan babu shi a tare da ita a sanyaye ta ce." To yanzu na ji abinda kace Haruna, amma ya za ka yi ka hadu da mijin nata kasan dai shi ba yaro ba ne idan ma ka girme shi ba yawa kuma sannan ba irin mazajen yaranka ba ne da kasa ba yi musu tsawa da gindaya musu sharad'ai." Dariya ya yi irin ta manya a tsanake ya furta." Ai na girme shi Dada, kuma yana auran 'yata duk kudi da wani abinda yake ji dashi ya zame masa dole ya ajiye a gefe guda kafin ya tunkaro inda nake muddin yana so mu daidaita. Ni wani kudinsa ba zai rud'a ni ba, ke kan ki kin san da wannan Dada." Wani irin sanyi na ji ya sauka a zuciyata ta yi fes lallai Baban Saude ya shirya kare mini mutuncina. Ya dubi anti Yagana babu fara'a ya ce." An ce yana kiranki a waya to na gargad'eki duk lokacin da ya sake kiranki akan lamarin ki ce masa ya nemi inda nake kuma ki sanar dashi daf nake da komawa wurin neman abincina domin ina sa ran a satin nan da za mu shiga asabar ko lahadi zan tafi muddin kuwa ya bari na tafi bai neme ni ba to sai na dawo kuma" Cike da damuwa da kar'bar umarni ta ce." To shikkenan in sha Allahu don d'azu ma mun yi waya da shi har yana sake jadadda mini cewa shi bai saketa ba bayan wanda ya yi mata a baya shi kad'ai ne ya san wànda ya yi har yanzu akwai sauran igiyoyin auransa biyu a kanta." Gyada kansa ya yi yana gyara zamansa ya ce." wannan kuma abinda ya shafe shi ne, ki yi dai yi kokarin bin umarina idan ya tuntubeki akan matsalarsa ki ce masa ya nemi inda nake domin kuwa matarsa tana hannuna." Ta ce." To in sha Allahu rabbi." Kwanan farinciki na yi a ranar saboda irin tsayuwar da Baban Saude ya yi akaina na ji dad'i kwarai da aniya kuma na yi masa addu'ar samun lada a wurin Allah. *** To kwana uku a tsakani zuwansu Anti Yagana da safe ina bacci Sayyada ta shigo tana tashina wai Baban Saude yana kirana. Da zullumi na tashi na fita na wanke bakina sannan na nufi d'akinsa da yake can gefe da tsakargidan na yi sallama a nutse na shiga yana zaune da tukunyar shayi da mangal a gabansa ya gama dafa shayin yana tsiyayawa a kofi. Na sake gaisheshi duk da cewar d'azu kafin na kwanta mun gaisa. Ya amsa yana d'an motsa shayin da cokali kafin ya dube ni a tsanake ya ce." Jiya Yagana ta kira ni a waya ta gaya mini mijinki ya bu'kaci da a bashi lambata shine take neman izini na ce ta bashi babu komai to shine yanzu nan ya kira ni a waya yake gaya mini cewa yana nan tafe gobe juma'a komai dare zai shigo akan maganarku shin ya kike gani. Ni ba zan yi miki dole ba fa Amina domin kuwa ba kowane yake zaune da mutumin nan ba sai ke, idan har kin ga da 'kwara da cutarwa a ciki to ni don na ce masa ya sawwa'ke miki ba abu ne mai wahala ba a wajena. Idan kuma kin ga kina so ki cigaba da zama dashi sai a ja masa kunne tare da gargadin wannan ya zama na farko ya kuma zama na 'karshe idan har bai daina ba a gaba sai a d'auki matakin rabuwa ko yana so ko baya so tunda akwai al'kalai." Shiru na yi Ina nazarin maganarsa. Babu shakka Baban Saude ya cika jarumin namiji domin kuwa abinda ya yi a yanzu ba kowanne zai iya yi ba dalili shi wanda za a titsiye din mutum ne wanda Allah Ya wadatashi da farcen susa ya kuma rataya masa taguwar arziki. Na ce." Baban Saude idan har na rabu da auran mutumin nan duniya za ta zage ni. Sannan anti Yagana za ta 'kullece ni tunda har yanzu ta kasa fahimta. Ga 'kawata aminiyata Sahura mun samu matsala da ita duk ta dalilin haka. Zan cigaba da hakurin zama dashi muddin an nuna masa cewa abinda ya ke yi mini ba daidai ba ne, idan har ya gyara kuskuransa ni kuma na yi maka al'kawarin in sha Allahu rabbi zan yi kokari wurin ganin mun zauna lafiya, kuma zan kiyaye abinda zai sake kawo sa'bani a tsakaninmu kamar yadda ka yi mini nasiha." Ya jima yana kallona kafin ya gyada kansa a nutse ya furta." To Allah Ya yi miki albarka, ya kuma kare faruwar hakan anan gaba, sannan kuma ki yi amfani da duk shawarwarin dana d'ora ki akai, kina kallon yadda iyalina suka karanci halina tsaf to sai mu jima wata matsala bata gifta mana ba suna bina a yadda nake so, ni kuma ba na zalintarsu daidai gwargwado ina sauke hakkin kowacce. Ina so ki yi koyi dasu a dan zaman da ki ka yi tare dasu, ki d'auki darasi na zamantakewa tunda kina da abokanan zama to sai ku zama 'yan uwan juna, ku taimaka juna, ku ha'de kan yaranku waje daya, kada ku yarda wata 'baraka ta raba zumuncin yaranku a gaba za ku yi alfahari da haka. Sannan kuma kada ki kara samun ciki ki zubar wannan maganar na nanata miki ki ri'keta da kyau domin ba ke ki ke rayawa ba, haka zalika ba ke kike kashewa ba, tunda har kin yarda za ki cigaba da zama dashi a hakan to Ina yi muku fatan alheri Ubangiji Allah Ya sa har karshen rayuwarku wata matsala ba zata sake faruwa ba." Hawaye na ji sun ciko idona saboda tsananin mutuwar jiki. Wato ana zaton wuta a ma'kera ashe Baban Saude mutumin kirki ne na gaske ban sani ba, lallai anti Yagana da mutanan da suke masa wani irin kallo sun d'auki alhakinsa domin kuwa mutum ne nagartacce mai mayar da d'an wani nasa, irin wad'annan mutanan masu tsage gaskiya da gudun abin duniya sun yi 'karanci a wannan duniyar. [9/26, 9:21 PM] Aunty B: 94 Ina komawa d'aki anti Yagana ta kira ni a waya na daga tare da jin d'an faduwar gaba domin kuwa ban san dame take tafe ba. Sama sama ta amshi gaisuwa kafin ta fara gaya mini dalilin da ya sanya ta kira ni a waya. Na ce mata ai yanzu ma Baban Saude yake sanar da ni komai. Sai ta ja tsaki da alama har yanzu ciki take da ni don dai na yi mata nisa ne babu yadda za a yi ta zo inda nake ta huce fushinta saboda sanin halin maigidan , shiyasa haushina da take ji ya sake ninkuwa. Shiru na yi Ina sauraran duk maganganun da take yi uffan ban ce mata ba domin Ina iya yin magana ta ce na yi mata rashin kunya domin mu rabu lafiya duk abinda ta ce mini sai na ce to, ta kashe wayarta bayan ta gama gaggaya mini maganganun da ranta yake so da sunan jan kunne da gargadi akan zuwan da zai yi har tana cewa tasan ba ni da mutunci za a iya had'a baki da ni a wulakantashi da tozarci saboda yin hakan a wurin Baban Saude abu ne mai sau'ki dalilin da ya sanya ta kira ni kenan ta gaya mini sun yi waya dashi tun jiya kuma ya tabbatar mata da cewa da zummar sulhu zai zo. Ajiyewar wayar na yi raina fes cikin zuciyata na ce da ke dashi dukkaninku ba kwa son gaskiya, ko yanzu ai na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, na d'auka ai girman kai ba zai bar shi ya tako kafarsa ya zo ba, ai na ji dad'i mutuka da gaske da yadda Baban Saude yake da kafiya da dagiya akan ra'ayinsa. Duk da kwarjini da haibar da yake da ita ina da tabbacin hakan ba zai firgita Baban Saude ba dalili shi ma mutum ne mai ra'ayin rik'au kuma mai tattare da wadatar zucci. Washe gari da safe bayan mun karya kummalo na koma na kwanta bacci mai nauyi ya d'aukeni ko kadan ba na tare da wata fargaba ko zullumin abinda zai faru idan ya zo garin shiyasa kwata-kwata ma ban sanya abin a raina ba don ni har so nake ma ya zo din naga yadda za ta kaya wannan shi zai nuna mini cewa yana sona da gaske ko kuwa duka karya ce da yaudara. Sai wajan daya na rana na tashi rana gatse-gatse ina fitowa tsakar gidan da zummar wanke bakina da burushi na sami matan gidan suna ta aiki na yau na daban ne domin Sayyada na hanga a can cikin kicin ta dasa kujera tana ta suyar kaji. Mama tana gyara alayyahu ita kuma anti amarya tana tace zo'bon da yake kan wuta. Ina gama wanke bakin na shiga cikinsu muna aikin tare cikin zuciyata Ina tunanin ko saboda zuwan mutumin nan ya sanya Baban Saude yin wannan hidimar. Shiru dai na yi ban tambayi komai ba har muka kammala aikin gabad'aya towon farar shinkafa tas da miyar taushe wadda ta ji gyada da alayyahu gefe guda ga soyayyan man shanu nan da ya ji albasa. Ga soyayyun kaji nan masu yawa wanda Sayyada ta yi aikinsu. Bayan mun gama komai tsaf na share gidan na wanke shi tas lokacin Baban Saude ya fito daga dakinsa da zummar wankan Juma'a. 'yan samarin gidan ma daya bayan daya duk suka shigo suka yi wanka suka yi shirin massalaci. Ana saukowa Baban Saude ya shigo da dadduma a kafad'arsa ya tsaya daga bakin kofar d'akin Mama lokacin muna ta aikin daura zobo a leda ya ce maza a fito da abincin nan akai wa almajiran massalaci kamar dai yadda aka saba. Salmanu shi ma yaronsa ne shi ya shigo ya rataye daddumar a kan taga kafin ya kinkimi kular towon ya fita da sauri Abahuraira shi ma ya shigo ya d'auki kular da aka zuba miyar a ciki ya fita da ita. Da yake girkin anti Amarya ne itace ta had'a masa abincinsa a babban tire ya ce ta kai d'akin dai ta ajiye zai sake fita domin yana da ba'ko. Umarninsa ta bi ta yi yadda ya ce mata. Muna cin abinci Ina nazarin yanayin yadda Baban Saude ya tsara gidansa da rayuwarsa komai a tsanake babu harido babu hauka kawunan iyalinsa a had'e babu ba'kar gaba balle kishi mai tsanani. Sayyada ce take gaya mini ai duk ranar juma'a akan yi abinci mai kyau a kai massalaci akalla ya fi shekara goma yana wannan aikin ladan amma a cewarta na yau na daban ne domin kajin da ya sayo sun ninka wanda yake saya duk Juma'a. Jin haka ya sanya na gazgata zargina saboda zuwan Alhaji Tajo ne domin karramashi. Wannan ya kara tabbatar mini da cewa Baban Saude yana da kyawun zuciya kuma ba shi da niyyar kashe mini sai dai idan har ni na bu'kaci hakan. Bayan la'asar hud'u da arba'in da shida Baban Saude ya da kansa ya fita domin zuwa airport ya taro shi. Kafin ya tafi sai da ya leko ya sanar da ni tukkuna sannan ya tafi. To sai a lokacin ne jikina ya d'anyi sanyi na dan dinga jin fargaba amma ba sosai ba. Wanka na yi na shirya cikin doguwar riga amma ban yi wata kwalliya ba turare kawai na fesa a jikina na zauna gefen katifa da wayata a hannuna ina dubata. Tun ranar da ya d'ora hutunan d'aurin auransa ban kara ganin status d'insa ba, dama kuma ban ta'ba gani din ba, hakan sai ya kara tabbatar mini da cewa don na gani yasa tunda a lokacin ina ta neman hanyar da zamu shirya. Koda na tuna irin wulakanci da rashin arzikin da ya dinga yi mini a lokacin sai raina ya 'baci na ja tsaki tare da gyara kwanciyata a katifar ina tunanin akan wannan tsohuwar matar ya ki'dime matar da ko wadataccen nono ba ta dashi k'aramin jiki ne da ita bata da wani tudu ta baya a tsuke take har gwara Hauwa da 'yar cikar 'kuruciya a tattare da ita. Ai na godewa Allah da ya sanya duk su biyun babu wadda za ta nuna mini kyawun jiki ta ko'ina har yanzu da komad'ata. Ina daga cikin d'akin a kwance na ji shigowarsu ina jin muryar Baban Saude sama sama amma ban ji abinda yake cewa ba. K'amshin turaransa har d'akin da nake kwance kamshin da hancina ya jima bai shak'a ba. Zaune na tashi ina laluban mayafin rigar da take sanye a jikina gefe guda kuma gabana na d'an bugawa kad'an kad'an yanayin jikina ya fara sauyawa da wani lamari na daban.. Sai da na yi namijin ko'karin wajan ganin na rinjayi zuciyata don gudun kada ta kunyatani a gabansa. Ba ni da halin cire son da nake masa a zuciyata domin da damar a hannunata take ni kuma nake sarrafa zuciyata to Ina ganin da ba wannan maganar ake yi ba. Ni kaina nasan Ubangijina ya jarrabe ni da kaunarsa inda Allah Ya taimakeni rauni na bai ta'ba barin na nuna masa mahaukaciyar soyayyar a fili ba, Ina ganin da ya fahimci haka wulakancin da zai yi mini sai ya fi wannan. Kusan minti talatin da zuwansa Ina zaune a d'aki ni kadai ina ta tunanin mai yake faruwa a d'akin Baban Saude kuma ban ji ya kira ni ba, can na ji maganar Dada da sauri na tashi na fita na tsaya a bakin kofa tana d'akin Mama suna gaisawa ina tsaye a hannuna ri'ke da labule hankalina na bakin kofar d'akin Baban Saude takalma na gani uku a bakin kofar d'akin a zube ina tsammanin har da Babansu Fadila za a yi zaman domin na ji muryarsa a dakin. Dada ta fito daga d'akin mama tana magana wadda ban fahimci me take cewa ba ta dube ni muka had'a ido sai ta ja tsaki kafin ta furta." Dube ta da ido a tsaye kamar an kama 'bera a massalaci, ashe abin naki duk karya ce." Na bita da kallo ina gyara yanayina da tunanin maganarta to mai ta hanga a tare da ni da har take fad'in wannan maganar. D'akin Baban Saude ta nufa tana cigaba da yin k'ananun maganganu wanda kad'an na tsinta daga ciki tana ce wa." Mu a lokacin mu ina muka san wani kai 'karar miji balle yin jayayya dashi da ganin daidai ake da juna, ai duk macan da tace ba zata yarda ta zauna a kasan mijinta ba tana tare da wahala shiyasa auran yanzu ai baya karko.'' Na dinga kallonta da buguwar zuciyata to me kuma ya kawo wannan maganar idan dama ba ta shirya tsinka ni a wurinsa ba, Ina ce ai tun kafin a yi wannan zaman Baban Saude ya gaya mata abinda ya faru. Shine kuma za ta zo ta canza magana. Gabana ya cigaba da fad'uwa na koma cikin d'akin na zauna jikina duk a sanyaye hakika ban ji dadin gayyatota da aka yi ba domin kuwa za ta iya fad'in wasu maganganun da zai sake bashi kwarin gwiwa, kuma da take cewa su a da ba haka suke yi ba to yaushe zata had'a mazan da dana yanzu, ai yanzu lamarin rijalu ya lalace domin kuwa da yawa daga cikinsu basa tsoron Allah wasu ma idan baka fito ka nuna musu cewa daidai ake ba to ba za a zauna lafiya dasu ba. Da yawa akwai mazan da sun fi so idan sun ce kule a ce musu cass! a hau sama a fad'o a tare a buga a goga hakan ya fi musu dad'i, Amma wallahi idan suka samu mace saliha mai bin su sau da kafa sun fi yi mata iyashege da shegantaka. Hankalina yana kan agogon da yake kafe a bangon d'akin biyar da rabi yanzu ina lissafi lokaci a k'alla yanzu ya yi awa daya da zuwa amma ba a neme ni ba, ai na d'auka ni ma za a zauna da ni domin idan ya fad'i abinda ban yi ba na kare kaina kuma a shirye nake da na amsa lefin da na yi na bashi ha'kuri. Har na cire tsammanin cewa za a yi zaman da ni na ji muryar Baban Saude daga cikin d'akinsa Yana kwala mini kira. Na amsa da sauri tare da tashi zumbur na d'auki mayafin rigar jikina na rataya a wuyana na zura takalmi na fita. A nutse na shiga d'akin tare da sallama gabad'aya suka amsa har da shi Yallabai din da yake zaune a gefan Baban Saude Dada da Babansu Fadila kuma suna zaune a waje daya. Gefe guda kuma kwanukan da suka ci abinci ne a ajiye. Gefan Dada na zauna ina 'kara daidaita yanayin da nake ciki. A nutse na dubi Babansu Fadila na gaida shi ya amsa da sakin fuska kamar yadda muka saba gaisuwarmu cikin mutunci. Sai da na sake daidaita yanayina tukkuna na dubi gefan da yake zaune muka had'a ido da juna domin dama tun shigowata na lura da cewa idanuwansa suna kaina. Na ce." Barka da yamma ya hanya?" Ya amsa babu yabo babu fallasa da "Barkanmu dai ya kike?'' Shiru na yi ban sake cewa komai ba, d'akin ya d'auki shiru na sakkoni kafin Baban Saude ya yi gyaran murya a nutse ya dube ni yana ce wa" Amina tun kafin na kira ki zuwa nan mun tattauna abinda ya had'a mu anan mijinki kafin ya fadi aibunki sai da ya gama fad'in alhenki sannan ya fad'i dalilin da ya sanya shi yi miki wannan hukuncin domin horone a gare ki. Ya nisa kafin ya cigaba da ce wa." Kamar yadda ki ka tuba ki ka kar'bi kuskuranki haka nan shi ma a yanzu kafin shigowarki na nuna masa illa da rashin dacewar abinda ya yi, kuma na tunasar dashi abinda annabin rahama ya hore mu da mu yi wa iyalinmu a duk lokacin da suka yi mana wani abu na kuskure. Annabi S.a.w Ya ce." Na hane ku da nesanta kanku ga iyalinku idan sun yi muku lefi ku k'aurace musu na kwana daya zuwa kwana uku a shimfida ko kuma ku buge su da gefan rigar jikinku. Tabbas gashi nan a zaune ya nuna mini ya yi nadamar abinda ya aikata amma ya fadi hujjarsa ta yin haka a cewarsa idan ya kasance a kusa dake a koyaushe zai iya d'aukar matakin da rayukan kowa zai 'baci wannan shine dalilin da ya sanya ya k'aurace miki na tsayin wannan watannin ammana tare da bin sha'aninki domin sanin halin da ki ke ciki. Ya yi shiru kafin ya sake numfasawa ya cigaba da ce wa." Kamar yadda ki ka yi mini alkawarin cewa za ki cigaba da zama dashi a haka to Ina horanki da cewar wani abu makamancin abinda ki ka aikata kada ya sake faruwa idan kin samu ciki irin na haihuwa ki barwa Allah domin dukkanin hukunci yana hannunsa. Mijinki ya tabbatar mini da ce wa shi ma har yanzu yana sha'awar cigaba da zama dake domin yana sonki wani dalili mara karfi ba zai sanya shi rabuwa dake ba ko da kuwa Allah bai kaddara masa haihuwa ba. Saboda haka Dada da Maigidan Yagana za su zama shaida a tsakanin zaman nan da muka yi wanda nake da burin Allah Ya sa ba za a kara maimaitama shi ba a tsakaninku, idan matsala ta fuskantoku za ku yi maganinta a junanku tunda dukkaninku ba yara ba ne." Ya juya ya dubi inda yake zaune cikin nutsuwa ya furta." Ranka ya dad'e kamar yadda dai na gaya maka da farko cewa wannan yarinyar marainiya ce mahaifiyarta 'kanwata ce ni kuma a matsayin uba nake a wurinta. Don Allah ka ri'ke ta amana domin babu wani dalilin da zai sanya ka aureta cikin sutturarta ka dinga dora ayar zargi a kanta. Koda a gidan karuwai ka auro mace yana da kyau a ce daraja ta aure ya sa ka mutuntata to ballantana Amina da tun tasowarta a nutse take duk da irin jarabawar rayuwar da ta fuskanta a baya hakan bai sanya ta sarayar da mutuncinta ba. Sanin da na yi mata ita din za'kwa'kwa'kura ce mai himma da zuciyar neman na kanta amma ba a ta'ba yi mata shedar banza ba. Matarka ce idan da rabo watarana za ta zama uwar 'ya'yanka don haka muna neman wannan alfarma a wurinka a matsayinka na mai nisan shekarun da suka fi nata a duk lokacin da ta yi maka lefi wanda ba ma fatan haka sai ka kira ni a waya ka gaya mini, ni kuma zaka ga yadda za mu kwashe da ita. Muna kuma sake baka ha'kuri bisa abinda ta yi maka wanda ko waye a ka yi wa hakan ba a kyauta masa ba, yadda ka ce ka yafe mata a gabanmu zan sanyata yanzu ta sake baka ha'kuri domin tabbas yin hakan shi ya dace da ita." Jikina ne ya yi sanyi jin abinda yake ce wa, na yi shiru tare da sake yin k'asa da kaina ina jin Dada tana ce wa." Kuma ka rufa mata asiri baka tona mata ba, Allah Ya yi maka albarka mun gode sosai ka ji ko, Allah Ya saka da alheri, don Allah kada ka sanar da iyayenka da 'yan uwanka saboda kada su tsaneta a zahiri kowa zai ga ta yi maka mugunta tunda ita ai tana da yaran." Sai ta fashe da kuka ta sa gefan mayafinta tana share hawaye cikin kukan take ce wa." Uwarki tana kwance a kabarinta amma nasan a dalilin wannan zaman sai an tasheta ta ji abinda ki ka aikata, ai ita biyayyar aure ce ta kasheta ba ta ta'ba sa'bawa Ubanki ba har ta koma ga Allah, ga Yagana nan tunda take da mijinta shekara da shekaru bai ta'ba kawo mana 'kararta ba, sai ke ko Amina, dama ai Yagana ta gaya mini kin ce badamuwarki ba ce don a lissafa miki aure, ai ba a kanki a kafara ba, to wallahi ba za mu yafe miki ba idan har ki ka sake kashe wannan auran. Baban Saude dariya ce ta kama shi jin irin zantukan da take yi ya ce ." Ai magana ta riga ta kare Dada menene na kuka kuma, babu wani dalili da zai sanya a tashi uwarta daga makwancinta, in sha Allahu ta nan lafiya lau kamar yadda muka je muka rufe ta, tana cikin rahamar Allah." Ji na yi zuciyata ta tsinke dalilin kukan da Dada take shar'ba wanda na tabbatar da ce wa mikin da ya jima da warkewa daga zuciyarta ne a ka fama mata, dama duk lokacin da ake yin wani taro a family dinsu sai sun yi kuka idan suka tuna da ita. Wannan lamarin da yake faruwa ne ya tayar mata da hankali ya sanya take ti'kar kuka kamar yanzu aka yi mata mutuwar. Kuka na dinga yi a hankali Ina jan hanci. Can kasa na ce." Baban Saude in sha Allahu babu abinda zai sake faruwa wannan al'kawari ne na yi maka zan yi iyakacin bakin kokarina akan abinda ka ce mini." Na yi shiru tare da sake jan majina na dubi wajan da yake zaune wanda kaf hankalinsa yana kanmu ni da Dada, da alama kukan da muke yi din ya fara sosa masa rai na ce." Don Allah ka yi hakuri in sha Allah ba zan sake aikatawa ba, sannan kuma ni ma don Allah ka yi mini adalci ka zauna da ni lafiya ka daina 'kullacina idan na yi maka wani abin yin hakan shi yake k'ara tunzura mini zuciyata." A nutse ya furta." Kada ki damu magana ta shige in sha Allahu rabbi, za ki shirya tare za mu koma kamar yadda na yi wa Baban Saude bayani ai babu amfanin zaman tunda an sasanta mu ko?" Baban Saude ya ce." 'Kwarai kuwa, ai ko ba ka furta hakan ba dama ni ma niyyata kenan na ce ka dauketa ku tafi, shine abinda ya dace." Ya gyada kansa a tsanake ya sake duban Dada da take ta faman yi masa godiya sai ka ce wadda ya yi wa gagarimar kyauta, ita godiyarta yadda ya sakaye sirrin bai tona ba, har ma mahaifiyarsa bai gayawa ba. Ashe godiyar da take yi zata sake ru'banyuwa domin kuwa kyautar kujarar umara ya yi musu ita da Baban Sauden. Shi kuma Babansu Fadila ya yi masa alkawarin bashi zungureriya mota domin fad'ad'a harkokinsa na sufari. Ashe kafin na shigo sun jima suna tattauna al'amura na rayuwa anan ya fahimci yana buk'atar tallafi domin cigaba da gudanar da sana'arsa. Dama wajan kyautar ban girma ai ba daga nan ba, mugun kirki ne da shi tare da yin irin kyautar bazata wadda Allah yake so. Shi kansa Baban Saude da yake abin ya zo masa a bazata kasa rufe bakinsa ya yi, ya yi masa godiya sosai tare da addu'oi masu yawa. Na ji dad'i kwarai da alherin da ya yi musu hakan ya kara goge takaicinsa dake cikin zuciyata kuma ba ni damar yin jayayya dole na bi umarni kamar yadda suka buk'ata bayan Isha'i na hada kayana tsaf Salmanu ya fita da akwatinan ni kuma na tsaya yi wa matan gidan sallama da godiya Sayyada tana fad'in in sha Allahu za ta zo mini ta yi mini kwanaki. Muka rabu cikin kewar juna da kuma mutunta juna. Ashe tare suke da Sukairaju yana jikin mota a tsaye yayin da shi Yallabai din da Baban Saude suke tsaye a bakin kofar gidan suna magana. Babansu Fadila ya tafi ina tsammanin. na dan tsaya a hankali na ce." Baban Saude shikkenan za mu tafi na gode sosai Ubangiji Allah Ya kara girma, Allah Ya saka da alheri." Ya ce." Amin suma Amin Amina, Allah Ya sauke ku lafiya, ki kula ki kuma ki kiyaye da kyau." A hankali na furta." In sha Allahu rabbi. Da sauri na yi gaba jin kuka na nema ya k'wace mini. Kafin na kàrasa bakin motar Sukairaju da saurin gaske ya bude mini na shiga na zauna ina goge hawayen da suka fara zuba a kumatuna. [9/27, 9:20 PM] Aunty B: 95 Kaina a kasa Sukairaju ya bude masa kofar motar ya shigo a tsanake yana tattare babbar rigar da take jikinsa. Ya zauna sosai kusa da ni yayin da 'kamshin da yake fita daga jikinsa ya game motar gabad'aya Lumshe idona na yi a hankali na bude tare da sauke ajiyar zuciya a hankali da jin fargaba da fad'uwar gaba kad'an kad'an. Wani iri yanayi na fara ji a tattare da ni, na tashin soyayya tare da kewa dalili kuwa shine dama tun fil'azal k'amshin da ya zauna a jikinsa yana daya daga cikin abinda yake saurin tayar mini da hankali. Jikina na d'an janye hankali na had'u da jikin motar domin ina ganin kusancin da yake tsakaninmu shi ma yana taka muhimmiyar rawa. Sukairaju ya d'an juyo a nutse ya ce." Sir za mu wuce hotel din da muka sauka ne?" Ya gyad'a kansa a yayin da yake d'an gyara zamansa a gefana ya ce ." 'Kwarai kuwa ai tafiyarmu sai gobe da misalin tukkuna dole nan d'in za mu kwana." Sai ya juya da sauri ya cigaba da jan motar cike da bin umarni. Shiru ya ratsa tsakaninmu babu wanda ya dubi juna. Kiran da ya shigo wayata shine ya ratsa shiru da ya ratsa. Ya dube ni a hankali wànda tun shigowarsa motar bai yi mini irinshi ba amma bai ce mini komai ba. Na d'auki wayar dake saman cinyata tare da duba mai kiran anti Yagana ce. Numfashi na sauke babu kuzari na sanya wayar a kunnane ban san kuma mai take tafe da shi ba, yanzu har fargaba nake yi naga kiranta. " Kina ina yanzu?" Abinda ya fito daga bakinta kenan, ko amsa sallamata ba ta yi ba. A takaice na ce." Ga ni a mota tare da Yallabai za mu tafi." Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce." Na so a ce kin zo nan domin akwai taimakon da na sanya a ka yi miki rubutu ne da tofi." Shiru na yi tare da d'an satar kallonsa sai na ga hankalinsa yana kan wayarsa Allah Ya sa ma ban bud'e handsfree ba amma dai duk da haka ina fargaba saboda yana da kaifin ji, itama anti Yagana tana da matsala wallahi. Na ji tana fad'in." Kun jima da tafiya ne, amma dai ba yanzu da daddaran nan za ku d'auki hanyar abuja ba ko." A takaice na ce." Sai gobe haka na ji yana cewa yanzu za mu nufi masauki." Ta ce." To shikkenan zan kira ki da safe za mu yi magana in sha Allahu rabbi. "To, kawai na iya ce mata na kashe wayar tare da d'ora ta a saman cinyata. Anti Yagana rigima kenan yanzu da ta tabbatar da cewa an sasanta zan koma ta daina hantarata. Shiru ya cigaba da wanzuwa a motar shi Sukairaju yana can yana abinda yake gabansa. Ni da shi kuma kowa girman kai ya hana ya yi wa d'an uwansa magana. Lokacin da aka kira wayarshi ban kalleshi ba amma gabad'aya hankalina yana kan saurarar maganar da yake yi a waya. Matarsa ce Hajiya Maryam ta kira shi. Na yi shiru mamaki da tsoro yana shigata. Yadda yake kashe murya da tausasa harshe wajan mayar mata da amsa shine abinda ya fi d'aukar hankalina. Jikina ya shika k'warai da aniya domin abinda yake yi ko saurayi dan shekara ashirin da biyar albarka. Idan ni na zama towon tushe ai ya ji nauyi da kunyar Sukairaju domin yaronsa ne a ganina bai kamaci ya saki baki yana fad'in wasu manyan kalmomi na soyayya da turanci ba. Duk yadda na yi wajan ganin na ji a hakan ba komai ba ne a cikin zuciyata kasawa na yi don sai nake ganin kamar ma da gayya da cin fuska yake yi mini hakan. Da ta kira shi sai ya gaya mata yana uzuri a ganina bai kamata ya biye mata ba tunda dai ta san muna tare sai dai idan bai gaya mata cewa bikona ya zo ba, tunda duk yawancinsu munafukai ne ba su ta'ba yarda su fito da ainihin abinda yake kasan zuciyarsu. Ban san lokacin da na ja tsaki mai tsayi ba na dan gyara zamana tare da cire gefan rigarsa da ya had'u da mayafin da yake jikina. Had'e fuska na yi sosai a karo na biyu na sake yin wurgi da gefan babbar rigarsa da ya sake sauka a cinyata a dalilin gyara zamansa da ya yi. Sai ya juyo yana kallona still da wayar a kunnansa bai katse ba. Ban yarda na hada ido dashi ba amma yanayina kad'ai shi ya nuna a kusa nake wata'kila kiris nake jira na fashe. Kuma haka din ne don abinda nake ji a can kasan zuciyata ni kaina ya shallake tunanina. Ya kashe wayar tare da ajiyeta a saman cinyarsa kamar dai yadda na ajiye tawa. Sai ya d'auki gefan babban rigarsa ya d'ora a cinyata yana d'an murmushi amma bai ce komai ba. Zumbura baki na yi tare da kawar da kaina nasa hannu na cire rigar daga jikina. Sai ya sake mayarwa yana sake matsowa jikina. A hankali murya can kasa ya furta." 'kyan'kyamina ki ke yi Amina." Shiru na yi ban tanka masa ba, kuma ban kalleshi shi ba. Sai ya d'auki hannuna da yake ajiye a saman cinyata ya had'e yatsunmu waje daya ya rintse can kasa da karamin sautin da ni kadai zan iya ji ya furta." Mu 'kulla alkawari." Hucin numfashin maganarsa ya sauka a gefan fuskata. Ya sake matse yatsun da k'arfi yana sauke ajiyar a zuciya ya furta." Kin ji Hajiyata." Cikin wani irin yanayi na dube shi. Duk da idanuwansa rufe suke da gilashi hakan bai hana ni fahimtar halin da yake ciki ba. Ban iya ce masa komai ba na janye idona daga kallonsa zuciyata na d'an yi mini zafi kad'an domin sai nake ganin kamar akwai raini a lamarinsa ai ya kamata a ce yanzu ba shi da lokacin kowa sai nawa tunda mun jima ba ma tare a ganina bai kamata ya tsaya wata mace ta kira shi koda matarsa ce din ya biye mata da zantukan soyayya ba. Ya sake furta." Mun yi al'kawari ko Amina." Da 'kyar na ce." Ai mun yi tun a gaban Baban Saude." "Wani nake so mu sake yi ni dake kawai, kin ji rabin rayuwata." Na dube shi da sauri jin abinda ya furta wai rabin rayuwarsa. Lallai ban yarda ba idan har ni din rabin rayuwarsa ce ai ba zai dinga yin nesa da ni ba duk tsaurin lefin da na yi masa. Ganin na'ki biye masa ne ya sanya ya rabu da ni, a haka muka isa kasaitaccen hotel din da sai wane da wane, yana ta tsokanata ya d'auki gefan rigarsa yasa a jikina ni kuma bana gajiya da cirewa Na ce da Sukajiru ya shigo mini da akwatinana dole akwai abinda zan buk'ata kafin na kwanta sai na yi burush da kuma kayan baccina a ciki. Idan ya so gobe idan za mu tafi din ya kuma kai su motar tunda na tabbatar da cewar tafiyar jirgi za mu yi sai dai har yanzu ban gama tabbatar da cewa ina zai kai ni ya ajiye ba legos din ne ko Abuja. Tunda na yi wanka na fito yake ta bina da kallo don da kyar ma ya iya tashi ya je ya yi nasa wankan ya fito babu riga a jikinsa sai dogon wandon kayan da ya cire ya zauna kusa da ni a gefan gado lokacin muna magana da Sahura ta Whasap ina gaya mata sai ta kwantar da hankalinta auran bai mutu ba ga ni ma yanzu a tare da shi a d'akin hotel. Ganin ya zauna kusa da ni ya sanya na kashe data tare da ajiye wayar a gefe, Ina kallonsa ya d'ebi nasa wayoyin duka ukun ya kashe su, ban ce masa komai ba a hankali dai nake nazarinsa yanayinsa kadai ya gama fahimtar da ni halin da yake ciki. Ai na d'auka har yanzu da dokin amarcin a tattare dashi to mutumin da yake da amarya irin haka, zan d'an jarraba shi na ga ni saboda nasan babu wani dalili da zai hana shi 'kin kwanciya da ni a irin yanayin da yake ciki. Abinci muka ci a tare hankalinsa duk rabi yana kaina don ma ni ce karfin cin abinci. Da ga karshe sai ma ya ajiye cokalin hannunsa yana fad'in shi dan gargajiya ne bai saba da wannan ciye ciyen ba. Na ce sai ka sanya a kawo maka abinda ka ke so ko?" Ya yi shiru bai ce komai ba can kuma sai ya ce." Amma na ji dadin towon nan da aka sauke ni da shi a gidan Kawunki Baban Saude mutumin kirki ne Amina. Murmushi na yi kad'an amma ban ce masa komai ba. Shiru ya dan ratsa d'akin a kafin a hankali na ji ya kira sunana. Na daga kaina na dube shi a tsanake ya furta. Da gaske fa nake da na ce miki mu d'aura alkawari." Ina tauna abincin da ya rage a bakina na ce." Ai ban fahimci alkawarin da ka ke nufi ba. Zamansa ya gyara babu alamun wasa a fuskarsa ya ce." Tsakanina dake babu cuta babu cutarwa duk rintsi duk wahala kada ki zauna da ni da wata zuciya ki amince da cewa ni mai kaunarki ne ba kuma zan cutar dake ba, wallahi tallahi Amina da wata ce ta aikata mini abinda ki ka yi mini da har yanzu tana d'aure don ba zan yarda ba zan saketa kuma na yi shari'a da ita, babu ruwana da terere da surutun mutane sai Allah Ya ragewa aya za'kinta ke ce Amina wadda zuciyata take yi wa mahaukacin so. Ina sonki wannan kowanene zai shaida haka, kuma ina da burin gama rayuwata dake, ina da burin tara zuria dake koda duka za su kasance miskinai. Kamar yadda Kawunki ya fad'a na sani a zaman aure dole akwai kuskure dole kuma a samu sa'bani amma ina so ki sani sonki da kaunarki ne ya sanya mini wani ciwo mai wahalar magani a zuciyata. Wannan zafin kishin da zargin da nake nunawa a kanki ba yin kaina ba ne, Amina zuciyatace, na sha gaya miki ni mutum ne mai kishi da tsantsami a duk lokacin da na tuna cewa ba ni ne namiji na farko da na fara saninki a matsayin 'ya mace ba zuciyata tana yi mini wani irin ciwo wannan shine dalilin da ya sanya nake kasa sarrafa kaina, amma in bacin haka ai nasan wacece ke tun kafin aure ya ratsa tsakaninmu had'uwarmu ta farko na bijiro miki da wani lamari wanda hakan ba dabi'ata ba ce, na yi da manufar samun dace da macen aure mai tsoron Allah da gudun abin duniya. Kin fi kowa sanin ibtila'in rayuwar dana fuskanta dangane da matayen dana aura wanda da yawa mutane suka fara dora ayar tambaya a kaina. Auranki shi ya korar da wannan rud'anin ki ka yi hakuri ki karbe ni a haka da wasiwasin za ki mutu ko kuma za ki rayu. Wannan sai ya bawa sauran mata damar kawo mini hari da sunan soyayya tunda ai kin rayu tsayin shekara ba ki mutu ba. Amina in bacin Hauwa 'yar uwata ce, kuma Ina gudun 'bacin zumunci da babu dalilin da zai sanya ni na aureta tunda a can baya ai guduna ta yi saboda kada ta rasa rayuwarta kamar yadda 'yar uwarta Samira ta rasa tata rayuwar. Aurena da Hajiya Maryam kuwa wannan cikasa wasiyyar abokina na yi domin a cikin abinda yake rubuce cikin wasiyyar da ya rubuta da hannunsa kafin rasuwarsa har da neman alfarmar na auri matarsa domin cigaba da kula da ita da yaransa. Alhaji Amadu ya wuce komai a wurina domin duk yadda zan fad'a miki kirkinsa sai na rage mutum ne na k'warai mai kaunata da son cigabana. Ko ni ne na riga shi tafiya ba abin mamaki ba ne don na bashi wasiyyar ya auri iyalina saboda rufin asirinmu bakid'aya. Mu zauna lafiya don Allah, ki yi hakuri da ni, zan yi hakuri dake. A yanzu ke ce uwargina da ni da sauran iyalina muna hannunki. Muddin ki ka bud'e wata kofa ta samun sa'bani a gare mu to kin kashe kanki. Sai maganata dake ta karshe kada ki sake kaini 'kara wurin kowa domin kuwa ni ba yaro ba ne, ke ba ki ji kunyar kai mutum kamata 'kara ba Amina ke ce fa ki ka yi mini lefi kuma na yi shiru ban gayawa kowa ba amma saboda k'in gaskiya sai ki tafi ki kai ni 'kara na ji ciwon hakan sosai, kuma kin ci sa'a, ina sonki da ba zan je ba wallahi zan ta barinki da igiyoyin aurena a kanki duk ranar da ki ka gaji kya dawo." Cikin kuka na ce." Ai kai kaso hakan, mai yasa ka'ki ha'kura, ai na gaya maka gaskiya ban 'boye maka ka dalilina ba, kuma da na fahimci na yi kuskure ba 'a yi wa Allah wayo na yi nadama na ro'ki gafararsa, kaima na ce ka yafe mini, sai ka k'ullece ni, ka dinga gaba da ni, ka rufe duk wata hanyar da kasan zan hadu da kai, ta ya ya ba zan nemawa kaina mafita ba, ai Allah ma muna yi masa lefi ya yafe mana, a lokacin ya kamata ka kar'bi tubana mu sasanta junamu ta inda babu wanda ya ji ya kuma ga ni, hakan bai yi maka ba sai kawai katin d'aurin aurenka na gani, ni ma shine dalilin da ya sanya kenan na nemi iyayena domin su kira ka su ji menene matsayin aurena." "To mai yasa ba ki sanar da mahaifinki ba har sai kin yi tafiyayyiya kin je kin gayawa wani mutum, a ganina ai mahaifinki shi ya kamata ki sanarwa da halin da ki ke ciki Amina ba wai ki d'auko maganar ki kawota har nan garin maiduguri ba." "Shi ma ai Baban Saude ba bare ba ne, kamar yadda ya yi maka bayani uba yake a wurina. Babanmu kuma yana da kawaici sosai bai zama lallai ya iya ce maka komai ba." Murmushi ya yi kad'an kafin ya ce." Shi wannan din da ki ka kawo masa k'ara ta shi bashi da kawaici kenan." Na dube shi da wani yanayi domin maganar tasa tana nema ta d'auki wata hanya. Sai kuma da sauri ya gyara maganar da ce wa." Yana da kirki Baban Saude amma d'an tattaunawarmu na fahimci yana da wasu 'yan matsaloli ammafa ba masu muni ba ne ainun. Na dai gaya miki kada ki sake kai ni 'kara koma wajen wanene." Na ce." To kai ma sai ka kiyaye abinda zai 'bata mini rai, ai ka dauki alkawari ni ma na d'auka. Kuma da kake cewa wasiyyar auran Hajiya Maryam aka bar maka ai ka jima kana yi mini maganarta tare da sha'awar abinda take yi wa mijinta." Sai ya zuba mini ido da yanayi na mamaki a fuskarsa ya furta." Kada shashanci ya sanya ki sauka daga kan abinda muke tattaunawa Amina, in banda rashin hankali daga kawai na tausaya musu ita da mijinta a lokacin da yake halin ciwo sai ki canza mini magana, wato idan na fahimceki kina so ki ce da ni tun abokina yana raye nake sha'awar auranta ko ba haka ba ne." 'Dauke kaina na yi tare da d'an zumbura baki na ce." Na ga ai itama bazawarar ce mai yasa ba ka wani shiga damuwa ba, tana fita daga takaba fa ka yi gaggawar auranta, ai ko ni ban fad'i ba haka duniya za ta sanya ayar tambaya a kanka." Fashewa ya yi da dariya yana kallona yana yi ya ce." Mijinta da ya rasu shine ya rubuta hakan a wasiyyar da ya bari, cewa daga zarar ta fita daga takaba kada na ja lokaci a daura auren. Idan ba ki yarda ba zan nuna miki takardar idan mun je gida. Sai magana ta gaba kuma Amina ai ba ni na ga Hajiya Maryam na ce ina so ba, sannan me zai sanya ni na tsananta kishi a kanta bayan nasan abokina ne ya aureta shi kadai ya yi tarayya da ita. Ba ki son sai da so ake kishi ba ne." "To ai duk da haka itama 'yar kasuwa ce har fita take yi kasashen waje ta yi kwana da kwanaki ta dawo mai yasa duk hakan bai dame ka ba, idan adalci ne itama sai ka hana ta fita waje sarin kaya." Sai ya shiga girgiza kansa yana fad'in." A, a, akan me zai hana ta neman kudinta bayan a haka ta ginu, kin san yawan mutanan da suke ci da sha'a a 'karkashinta kuwa, maganar fita zuwa wata kasa wannan dama dole ta bari tunda girma ya fara hawa kanta yaranta sun fara tasawa sai ta wakiltasu, shi ma abokina yarda da cewa ba zata ci amanarsa ba ya sanya ya bata goyon bayan fad'ada sana'arta, kuma ke ma da ki ke yin wannan maganar ai ban hana ki kasuwancinki ba ko ba haka ba ne?" "Ni kenan kana kokwanto a kaina shiyasa kake takura mini da zargi har da Hamusu ka dinga tuhuma har da su Allah Ya isa, ka dinga bin shafukana na intarnat kana yi mini binceka duk wani abu da na dora da zummar talla idan bai yi maka ba sai ka sanya a sauke mini, ta karfi sai da ka ruguza mini kasuwancina na media." Numfasawa ya yi kafin ya ce." Neman rigima ne kawai irin naki Amina, abu ne a zahiri gashinan kasuwancinki dana Hajiya Maryam ya sha bam-bam, ita bata fitowa ta tallata kanta da sunan kasuwanci tunda na aureta nake bin abubuwan da take gudanarwa sannu a hankali ban hangi wani abin assha ba wanda zai janyo mana zubewar mutunci. Ke kuma dake da kayan tallan ki ke tallatawa duniya ya ba zan d'auki mataki ba. Ko ba ni da ido da neman rahoto daga jaridu ai ina kishin kaina ba zan lamunci irin wannan business din ba, idan ba ki manta ba farko auranmu na gaya miki ki bi duk hanyoyi na halak da za su kawo miki kudi amma kada ki bi hanyar da zata janyo mini zubewar mutunci." Shiru kawai na yi masa domin har yanzu ban gamsu da bayaninsa ba sai nake ganin kawai yana tsara ni ne saboda ban kai karfin matarsa ba. Ita ai babbar yar kasuwace babu buk'atar da ta bi irin hanyar da sauran k'ananun 'yan kasuwa ke bi domin su kafu da kiran kostoma ta riga ta kafu ta tsaya da kafafunta. Ganin na yi shiru ban sake cewa komai ba sai ya ce." Ni da za ki bi shawarata ma ki ajiye komai ki kama ni ki ri'ke da kyau, ni kuma duk bayan shekara daya ko biyu idan Allah Ya tsawaita mana nisan kwana na dinga baki ajiya mai girma kina haife mini. Sai ni kuma na cigaba da nema muku dukiyar tare dake da abinda za mu haifa." Kallonsa kawai nake yi na rasa ma abinda zan ce. Wai duk shekara daya sai kace wata kaza yanzu da shekaru suka fara tura mini ai Allah na tuba ko zan k'ara wata haihuwar bai fi uku zuwa hud'u ba idan ma Allah Ya 'kaddara. Shiru na yi masa ban iya cewa dashi komai ba saboda Ina yin fad'in wata maganar akan maganarsa ya canza mini tawa. Ya kai hannunsa kirjina tare da fad'in." Wannan na ga ya k'ara girma, na shiga tsananin u'kuba na rashinsu Amina." Maganar ta ba ni dariya amma ban yi ba kawai na zuba masa ido yana matsa mini kirji dake cikin riga. Cikin zuciyata na ce dama ai dole ka shiga ukuba tunda ka saba lugudarsu yadda ranka yake so, gashi amaryartaka ba ta dasu. Hauwa da nata suka bunkasa dalilin ciki tana can wata uwa duniya ashe abin maleji ne. Ganin ban hana shi abinda yake yi ba ya sanya ya janyo kafafuna kusa da shi ya fara kicikicin kwantar da ni a kasan kafet din da muke zaune. Na cire hannunsa tare da saurin tashi tsaye. Sai shi ma ya tashi da wani irin yanayi na tsantsar fitina ya kashe hasken d'akin ya riko hannuna muka nufi katon gadon da yake girke a d'akin. Ban hana shi tattabani ba sai da lamarin ya yi nisa tukkuna na ce masa ba ni da tsarki. Nan na ga gigicewa har da su rawar murya wai ban yi masa adalci ba. Na yi shiru Ina kallonsa yana ta abubuwa kamar wanda ya rasa hankalinsa yana fad'in duk ma yadda zan yi sai na nemi hanyar da zan biya masa buk'ata lallai ba zai iya ha'kuri a wannan dare ba. Na'ki rungumarsa na kyaleshi kawai amma sa'kon ya fara shigata daurewa kawai nake yi ina ta mutsu-mutsu! Tabbas na so na daure zuciyata da zummar ja masa rai, amma ina lamarin ya fi 'karfina ban ma san lokacin da na talfeshi a ki'dime har na so na fi shi za'kewa da kansa ya gane abinda na fad'a ba haka ba ne. Sai jakan ya k'ara sanya shi sakankancewa yana buga sambatu da nishin kamar wanda ransa yake daf da barin gangar jikinsa. [9/28, 7:54 PM] Aunty B: 96 Yadda muka wayi gari cikin walwala da farinciki shine abinda ya kara tabbatar mini da cewa ba a shiga tsakanin mace da mijinta domin kuwa wanda ya shiga tabbas watarana shine zai ji kunya mussaman idan ya aikata abinda zai sanya jin kunyar gangan. Misali da ba dan Baban Saude ya yi amfani da ilimi da k'arewa wajan kawo sasanci da daidaito a tsakaninmu ba wata'kila da ya yi amfani da 'daya sigar to da ba wannan maganar ake yi ba. To shi ma sai a ka ci sa'a ya yi amfani da hikima wajan ganin ya isar da sa'kon da yake ya isar din wanda shi ma daga 'bangaran Yallabai din na fahimci abin ya yi masa ciwo sosai, kuma kamar yadda ya fad'a din na tabbatar da baya sona da buk'atar cigaba da zama da ni ba zai ta'ba bibiyata da nufin kome da sulhu ba, duk da Baban Saude bai yi amfani da tsautsauran kalamai ba, amma yadda na fahimta ya ji haushi kawai ya danne ne domin samun a zauna lafiya.Tabbas idan hakane kuwa Ina da ya'kinin zai gyara anan gaba tunda na lura ya tsani a kai shi k'ara don ko lokacin da na ta'ba Kai shi 'kararsa wurin Hajja akan lamarin Hamusu fushi ya yi da ni mai tsanani idan ban manta ba ya dinga gaba da ni sai da kyar ya sauko. Dama tun asubahi ya ce na yi duk shirye-shiryen da zan yi jirgin karfe takwas za mu bi zuwa abuja kafin lokacin ma ya cika mun fito ni dashi a kintse Sukairaju dama tuntuni ya sanya mana kayanmu a mota. Kafin mu isa airport din Anti Yagana ta kira ni a waya kamar yadda ta fada na ce mata ai mun riga ma mun fito muna mota zuwa filin jirgi. Sai ta ce na had'ata da shi. Ba tare da na ce komai ba na mik'a wayar tare da gaya masa anti Yagana ce take so ta yi magana dashi. Ya kar'ba a nutse suka gaisa sai kawai ta fara yi masa godiya har ina jin yadda muryarta take rawa godiya sosai na abin alherin da ya yi wa su Dada da Baban Saude. Sai kuma alkawarin kyautar motar da ya yi wa maigidanta. Da kulawa sosai ya nuna mata cewa ta daina yi masa godiya akan abinda ya yi, ai duka an riga an zama daya don haka ba abin mamaki da godiya ba ne akan duk irin abinda zai yi mana. Ta cigaba dai da godiya dai har tana cewa dashi ya kara da hakuri dangane da zamantakewa ta dashi in sha Allahu wani abu ba zai sake faruwa ba. Ya ce mata babu komai shi ma a b'angaransa magana ta wuce hakan ba zata sake faruwa ba. Suka yi sallama ya miko mini wayar muka dan yi magana kafin ta katse kiran. Ya dube ni a tsanake yana ce wa." Yagana mutuniyar kirki ce sosai Amina." Murmushi kawai na yi ban ce masa komai ba, tunanina yana can wani waje na daban. Ya gaya mini ni da Hauwa ne za mu sasanta kanmu abin nufi shine za mu raba zama. Wata shida a Legos wata shida a Abuja. Abinda yake damuna shine mai yasa ita Hajiya Maryam din ba za mu raba da ita ba, ai matarsa ce ita kamar yadda muke matayensa. Ban ga dalilin da zai sanya ya ce mu biyu ne za mu dinga wannan zurga-zurgar ba. Ba na so na yi wata magana ne ya ga kamar kishi ne ko neman fitina shiyasa kawai na yi shiru amma zahiri wannan hukuncin bai yi mini ba kuma sai na rusa shi domin kuwa ba zan ta'ba yarda ya kafa abinda nasan lallai anan gaba zai zama rikici ba. Muka isa abuja wajan sha daya na safe. Gidanshi yana nan tsaf tunda akwai hadimai tare muka shiga amma ko zama bai yi ba ya sake fita sai zuciyata ta shiga wasiwasin akan fitarsa da gaggawa irin haka. Tun d'azu a mota kafin zuwanmu airport na ji sun yi waya da ita sai nake zargin gidanta ya nufa. Zuciyata ta cika da takaici da b'akinciki irin yadda yake rasa sukuni akan sha'anin matar nan abinda yake yi yana nema ya wuce gona da iri ban hana shi kula da matarsa ba amma yana da kyau ya daina nuna muguwar damuwa da ita a gabana domin kuwa ba zan iya jura ba. Ina fitowa daga wanka Yusi ya shigo. Na zuba masa ido har ya k'araso wajan da nake gefan gadon yana dariya yaro ya zama wani lafiyayye ya yi haske da kyau sai kace wanda yake rayuwa a k'etare kayan jikinsa ma abin kallone. Ya zauna kusa da ni tare da ri'ko hannuna ni kam kallonsa kawai nake yi na kasa cewa dashi komai. Ya ce." Mama ina yini." "Lafiya lau Yusi kai ne kuwa?" Na fad'a ina d'ago fuskarsa. Sai yasa dariya yana cewa." Ni ne mama me ki ka ga ni?" Ajiyar zuciya na sauke a hankali na ce." Na ga abubuwa da yawa Yusi wanene ya gaya maka na zo?" Kai tsaye ya ce." Baba ne Yana gidan Momi shine yake gaya mini tare kuke wai na zo mu gaisa." Yana rufe bakinsa Adam ya shigo da sallama a nutse ya k'araso wajan da muke jikinsa sanye da irin kayan dake jikin Yusi. Bashi da jikin girma da alama ya d'auko jiki irin na Mamansa ya d'an risina yana gaishe ni na amsa da kulawa. Ina fad'in" Adam mai kuke bawa Yusi ya zama d'an lukuti haka?" Ai kuwa sai ya fashe da dariya yana kallonsa ya ce." Wallahi babu komai Mama jikinsa ne irin haka momi ma kullum da asuba sai ta sanya shi ya motsa jikinsa amma baya raguwa gashinan duk ya fi mu girma. 'Yar dariya na yi tare da cewa." Abinci zai rage ciki kawai idan ba so yake yi wataran ya kasa tashi ba." Ya ce." Haka ma Yaya Salim ya ce wai sau biyu zai dinga cin abinci a rana kuma daban da irin wanda muke ci, shine Momi ta ce a'a, a kyaleshi 'kibarsa ta kuruciya ce yana zama saurayi zai sa'be, ba zai daina cin abinci ba." Na gya'da kaina ina d'an murmushi zuciyata kuma cike take da nazarin irin rikon da matar take yi wa yaron ko ni dai da na haife shi albarka tunda ga zahiri nan na gani da Ido. Jikina ya sake yin sanyi sosai to ai da kunya da nauyi a ce na bijiro da wata fitinar wadda zata kawo rud'ani a tsakaninmu. Tare suka fita da zummar zuwa su yi shirin tafiya islamiyya sha biyu na rana suke shiga su tashi shida na yamma. Shi kam maigidan ai tunda ta fita din nan bai shigo ba sai bayan la'asar wajan hud'u da rabi Ina zaune a falo cikin daya daga cikin kujerun da suke jere. Gajiya na yi da jiranshi ga yunwa ina ji a gaban idona kukunsa ya gama shirya komai a teburin cin abinci. Na tashi na je na d'iba daidai cikina na dawo falon na zauna ina cin abincin zuciyata na tunanin abin. Shi kansa sai da ya ji nauyi da kunya a lokacin da ya shigo ya same ni, ni kadai a zaune sai tibin dana kunna. Ya zauna a gefana yana fad'in." Amina kin ji ni shiru ko, ina can wajan Momi ne tun jiya take fama da zazzabi da mura." A takaice na ce." Allah Ya sawwa'ke." Daga haka ban sake magana ba. Na cigaba da cin abincina cikin nutsuwa. Sai ya ce." Yusi ya shigo ko?" "Eh Ya shigo tare da Adam.'' Ya furta." Ni ne na gaya masa ya zo ku gaisa." Na ce." Ai kuwa ka Kyauta." Shiru ya yi yana dan kallona da wani yanayi kafin ya ce." Mai ya faru na ga yanayinki ya canza ko ni ne?" Ya fad'a yana matsowa kusa da ni. Cikin zuciyata na ce aiki ya same ka. Shiru na yi ban ce masa komai ba. Ya tsargu sosai don gabad'aya kin sakar masa fuska na yi. Ganin haka sai ya tashi ya haye sama. Na yi zamana ban bi shi ba domin wallahi har cikin zuciyata haushinsa nake ji. Ni ba zuwan da ya yi wajenta ne yake ba ni haushi ba yadda yake d'aukar lamarinta da muhimmanci shine abinda ya fi 'kona mini rai. Yanzu ga matarsa can a wata uwa duniya d'auke da cikinsa amma ban ji ya kira ta ba tun jiya ai muna tare maganarta ma bai yi mini ba. Amma kan wannan tsohuwar yanzu sai ya gigice. Bai sauko ba sai daf da magariba, Ina zaune a falon ina kallon wani movies da ya d'auke mini hankali Na hangi saukowarsa cikin jallabiya da hula tashi kafiye naci a saman kanshi cikin shirin shiga massalaci. Janye idona na yi daga kansa shi ma bai ce mini komai ba ya fice. Na sauke ajiyar zuciya a hankali na tashi na hau saman domin gabatar da tawa ibadar. Ana idar da sallar ya shigo. Na lura yana so ya gyara abinda ya yi a d'azu shiyasa ya dawo da wuri. A saman dadduma ya same ni a zaune na idar da sallar amma ban tashi ba. Ya zauna kan wata kujera mai kamar gado da take can wani gefe a d'akin. Yana fad'in." Idan kina idar miko mini Loptop dina ga ta nan a gefanki. Ba tare da na ce komai ba na tashi na je na d'auko masa ya kar'ba tare da nuna mini wajan zama a gefansa. Zama na yi da hijabin a jikina. Shiru ya ratsa wajan yana ta dube-dubensa bai ce komai ba. Sai da ya gama tsaf sannan ya rufe computer ya dube ni tare da cewa." Za mu je gidan Momi ki dubata ko?" A sakarce na ce." Wacece Momi?" Duk kuwa da cewar na gane wadda yake kira da sunan irin yadda na ji yaran na kiranta da shi. Ya ce." 'Yar uwarki mana, da gaske ba ta jin dad'i kin san zafin zazzabi da mura dai." A nutse na ce." Mai zai hana ni zuwa na dubata, to Allah Ya sawwa'ke." Ya amsa da "Amin." Shiru ya sake biyo baya kafin na ce." Ya Hauwa kuna waya ko? Da sauri ya ce." Sosai ma kuwa, d'azu nan kafin na shigo sai da na kira ta, wannan watan da ya mutu shine na haihuwar wani ya kama sakamakon scanning ya nuna bakwai ga wannan watan da muka shiga shine daidai lokacin haihuwar." Na ce." Idan hakane ana sa rai nan da kwana uku kenan?' '' 'Kwarai kuwa, to amma kin san irin wannan ai ba a yankewa Allah hukunci." Na ce." Hakane wata'kila ma ka ga gobe ta haihu don ba abin mamaki ba ne a wajan Allah." Ya ce." Allah Ya sauketa lafiya dan Annabi." Na amsa da "Amin Ya Allah." Sai da muka ci abinci tukkuna muka fita zuwa gidan nata. Adam da Yusi muka samu a falon suna kallo . Na tsaya muna magana yayin da shi kuma maigidan ya nufi sama ban bi shi ba saboda bai nemi hakan ba. Ina nan a tsaye ban kai ga zama ba ya sauko yana cewa ya ki ka tsaya anan Amina. Ban ce masa komai ba illah Ido da na zuba masa. Akan wanene dalili zan bi shi ai yana da kyau a ce ya fara shiga ya sanar mata tunda ba a san a halin da take ciki ba. Idan shi mijinta ne ni kuma fa, wata'kila hakan bai zai yi mata dad'i ba. Bayansa na bi muna hawa benan yana sake tisa maganar wai na tsaya Ina ta d'ari-d'ari na'ki sakin jikina. Na yi masa shiru ban tanka masa ba. Da dai naga ya'ki ya bar maganar daf da zamu shiga d'akin na tsaya Ina dubansa babu fara'a a tare da ni na ce ." Don Allah maganar nan ta isa haka fa, ina dalili sai maimaitawa ka ke yi, ai ba daidai ba ne kai tsaye kawai mu kutsa mata d'aki idan kai babu lefi hakan ni kuma fa, ai ba mu san halin da zamu same ta ba." Yadda na nuna 'bacin raina akan hakan ya sanya bai sake wata magana ba muka shiga d'akin. Na yi kokari sosai wajan ganin na daidaita yanayin da nake ciki. Tana zaune gefan gado sanya da kayan bacci a jikinta. Wata kujera dake can gefe ya nufa ya je ya zauna shi kadai nasan ya yi hakan ne domin mafitarsa yana tsoron ya zauna kusa da wata daga cikin hakan ya zama lefi shiyasa ya ke'be kansa waje daya. Sosai muka gaisa cikin sakewa tunda dama ita din macace mai fuska da iya hurd'a da mutane. Babu wani abu na kishi da ganin kyashi da na karanta a tattare da ita. Sai dai na hangi tsantsar soyayya a cikin idanunta. Domin kuwa motsi kad'an za ta juya ta kalleshi ta dinga kokarin janyo shi cikin maganar da muke yi a tsakaninmu ni da ita amma ya'ki ya sake ya dai 'kyalemu muna hirarmu. Daga karshe ma sai ya sauka kasa ya bar ni tare da ita. Anan na dinga nazarinta duk da dare ne na fahimci tana jin jiki kuma murar ta kama ta da k'arfi. A lokacin sai kawai zuciyata ta dinga raya mini wani abu wai ko ciki ta samu domin sai nake ganin yanayinta kamar na mai karamin ciki. Kirjinta ya ciko ita kanta ma gabad'aya ta murmure ta yi ki'ba amma ba sosai ba. Jikina ya k'ara yin sanyi da al'marin Ubangiji. Lallai ciki ne da ita kuma shine dalilin da ya sanya duk ya gigice tunda abinda yake nema ne ya samu. Duk da ban tabbatar da hasashena ba amma tun a lokacin na ji na fara tausayin kaina. Zuciyata ta dinga yi mini munanan tunane-tunane. Idan ma har na samu cikin na haihu yarana ne za su tashi daban a gidan masu d'auke da wata lalura idan da k'arar kwana kuma d'aya bayan daya duk su mutu. Da wannan tunanin na kasance har muka bar gidanta daurewa kawai nake yi amma gabad'aya zuciyata ta kasa juriya sai da na buya a toilet na ci kuka na 'koshi na dinga yin istigifari da rokon Allah ya sassauta mini abinda nake ji a cikin zuciyata. Washe gari da safe sukuku na tashi babu karsashi a tare da ni. Hakan kawai abinda ba ni da tabbas akai ya ke nema ya daga mini hankali. To menene ribar auran ne haihuwa ce, mai yasa nake jin b'akinciki dan matar ta samu ciki. A ganina ai abin murna da farinciki ne a gare mu bakidaya.. Shirun da ya yi mini bai gaya mini matarsa tana da juna biyu ba shine abinda ya yi mini ciwo a ganina menene abin boye mini, idan ba yana nufin wani abu ba. Ko yana gudun ya gaya mini na ji haushi ko na nuna b'akincikina. Duk da bai zama dole a ce ya gaya mini abinda ya shafe shi da matarsa ba, amma ai idan da fahimtar juna da zama na amana ba lefi ba ne don ya gaya mini sai mu had'u mu yi farincikin tare gabad'aya. Na yi ta ko'karin ganin na danne damuwar da nake ciki amma ina sai da ya fahimci wani abu yana damuna. Ya dinga bibiyata duk domin son ya ji abinda yake damuna kawai na ce masa babu komai. To ne zance masa ni ban iya 'karya ba balle na yi masa, babu kuma dad'i na fito fili na nuna jin haushina dan matarsa tana da ciki. Kwana biyu a tsakani ya gaji da tambayata ya kyaleni kawai ya zuba mini ido tunda ya lura da cewar ba na son doguwar hira sai ya daina nema da ita. Amma baya fashin kwanciya da ni duk ranar girki na. A haka ya yi kwana biyu a wajena ya koma gidanta a washe garin ranar ya shigo da safe lokacin ma ban ma tashi ba tunda na yi sallar asubahi bacci ya d'auke ni mai nauyi. Shine ya tashe ni da farinciki yana gaya mini yanzu nan Hauwa ta haihu. Ganin yadda yake cikin annashuwa da murna ya sanya ni dole ni ma na ara na yafa ina tambayarsa abinda aka samu namiji ne kuma gabad'aya suna cikin koshin lafiya. Fatan alheri na yi musu gabad'aya tare da addu'ar Allah ya raya abinda aka samu. Ya kuma bada lafiyar shayarwa. Ya ji dad'i kuwa ya dinga amsawa cikin jin nishadi. A ranar ya shirya tafiya bauchi da nufin zuwa ya je ya dawo duk a ranar tunda tafiyar jirgice. Ban damu ba tunda ba kwanana ba ne, na yi masa addu'a da fatan alheri ya tashi ya fita domin zuwa ya kintsa. Sai bayan ya tafi tukkuna na shiga tunanin da na sani na kar'bi lambar wayarta a wurinsa sai na kira ta na yi mata barka tunda rantsuwar nan da na yi tana nan ba zan sake taka kafata garin ba sai dai duk abinda za a ce an jima ba a fad'a ba, wannan duniyar idan har mutum ya ce sai ya farantawa wani rai yana tare da wahala domin kuwa wasu lukutan ma Wanda kake kokarin ganin ka bashi farinciki shine na gaba gaba wajan ganin ya jefaka a masifa. Baban Saude ba irin nasihar da bai yi mini ba akan zama lafiya da abokanan zamana, na kuma d'auki nasiha da shawararsa duk wadda ta shirya zaman lafiya da ni, to ni ma a shirye nake dana zauna lafiya da ita, amma wadda take ganin ta fi karfin ta ba ni girmana na babba a cikinsu sai ta yi rayuwarta ni ma na yi tawa. Wannan shawarar na yanke a zuciyata wani sashe yana gaya mini cewa da duniya zata zageni hakan zai sake tabbatarwa da masu zargina cewa Ina hassada da ciki da haihuwar. Tunda ai tun farkon samuwar cikin an sha rigima da ni akan wani dalili. Ni ba zuwan ne matsala ba a wajena ba, Ina gudun kallon banza da habaici shine kawai abinda nake tunani, ba na so a yi mini abinda sai hasalani na kasa jurewa na aikata abinda bai da ce ba. To daga cewa zai je ya dawo a yini sai gashi sai da ya share kwanaki uku tukkuna kafin ya dawo sauran kwana dayan Hajiya Maryam da kwana biyuna ya yi su ne a tare da Hauwa. Ban damu ba saboda nasan hakan da ya yi shine daidai yana da kyau itama ya zauna da ita sosai domin su tattauna abinda ya shafe su. Da daddare ya dawo wajan goma da rabi har na kwanta ya shigo yanayin dana gan shi ya nuna mini cewa ya d'an jima da dawowa domin jallabiya ce a jikinsa. A can gidanta ya sauka zai cike mata cikon kwana dayanta. Ya zauna gefena ni kuma na tashi zaune Ina laluben hulata data fadi na mayar kaina a nutse na gaishe shi ya amsa yana yi mini wani irin kallo. Hakan ba sabon abu ba ne a wajena domin ni kaina na kan rasa me yake kallo a jikina babu dai abinda bai sani ba, babu kuma sabon abu. Saukar hannunsa na ji saman kirjina. Da sauri na ture ina dan hararsa. Ya sake matsowa jikina na matsa da baya Sai ya tsaya yana kallona kafin ya gyad'a kansa kamar wadda ta yi masa mugun lefi. Na daure tare a ce wa." Ina Hauwa da jariri suna nan lafiya?" "Lafiyarsu." Ya fad'a yana duba wayarsa kafin ya miko mini wayar yana fad'in." Kin ga hoton jaririn." Na kar'ba da sauri ina dubawa. Kamarsu daya wallahi, ina dariya na ce." Kamarku daya fa Baba, wannan yaron hotonka ne." Da d'an murmushi a fuskarsa ya ce." Haka mutane suke ta fad'i Hajja tana gaisheki yaushe za ki je ne?" Shiru na yi ban bashi amsa ba, ina ta duba hotonan yaron da yake cikin wayarsa. Sai ya sake maimaita tambayarsa. Ba tare da na dago kai ba na ce." Gaskiya ba zan rufe maka ba babu inda zan je." Ya dube ni da wani irin yanayi kafin ya furta ." Akan wane dalili, mai aka yi miki?" "Ba a yi mini komai ba." Na fad'a cikin mamakin yadda aka yi ya manta irin wulakancin da suka hadu suka yi mini har dashi. Hauwa na je garinsu cikin gidansu amma bola ta fi ni daraja suka mayar da ni abar nunawa da yi wa dariya ita da 'yar uwarta. "Idan kuwa hakane babu wani dalilin da zai sanya ki ce ba za ki je ba Amina muddin zan bada umarni ki bi shi." Hawaye ya ciko idona na ce ." Don Allah kada ka takura mini, ka kyaleni na ji da abinda ya dame ni, ba zan je fa domin kuwa ina da dalilina, idan kai ka manta ni ban manta ba." Ya gyara zama yana kallona tare da cewa." Ni ban manta komai ba Amina, ki fito fili ki gaya mini abinda yake damunki ba ki zauna kina barin shi a cikin ranki ba, na lura kwana biyu nan tun kafin Haihuwar nan ba ki da walwala ina alkawarin da muka k'ulla dake?" Hawayen dake cikin kwarmin idona ya d'igo. Na sanya hannu na goge tare da ce wa." Ai ni ban k'ulla alkawari da kai ba saboda na san ba iya cikawa za ka yi ba, kawai mu yi ta zama a haka cikin munafurtar juna." Sai kawai ya yi sakare da baki yana kallona. Ni kuma ina ta kuka kamar wadda aka yi wa rasuwa. Gadon ya hayo sosai ya riko hannuna kafin ya ce." Munafurci na yi miki?" Shiru na yi ban tanka masa ba. Ya ce." Ki tona mini asiri kawai ba wai ki dinga b'oyewa ba, ki gaya mini hak'kinki dana take tun zuwanmu nan, ashe duk takatsantsan din da nake akan kada wadda ta zarge ni a cikinku wato hakan bai yi miki ba, kina yi mini wani irin kallo." Hanci na ja, na cire hannunsa da yake cikin nawa na ce." Idan zaman gaskiya da amana muke yi menene na 'boye mini matarka tana da juna biyu, ai na gane nufinka kada ka gaya mini, na ji haushi ko na yi mata hassada ko?" Da wani irin yanayi ya furta." Wace matar tawa ce take da ciki?" Kallonsa na yi, muka had'a ido, sai na d'auke kaina ban ce masa komai ba Yasa hannu ya dago kaina ido cikin ido ya ce." Ki gaya mini wacece take da ciki." Na ce."Amaryarka?" "Ita ta gaya miki tana da juna biyu?" Shiru na yi domin ba ni da amsar da zan bashi sai na ce masa alamar hakan na gani. Sai a lokacin ma na fara jin kunya da nauyin abinda nake yi wanda hakan zai sanya shi saurin gano cewa kawai zafin kishi ne yake damuna." [9/30, 9:08 AM] Aunty B: 97 Ya jima yana kallona jin ban bashi amsar da ya tambayeni ba sai ya gyad'a kansa a nutse ya ce." Ni ne dai mijinta Ina ganin kafin ta gayawa kowa tana da juna biyu ni za ta fara gayawa, amma tunda maganar ta fito daga bakinki tabbas nasan ba 'karya ba ne, zan je na tambayata na ji dalilin da ya sanya ta 'boye mini abina." Ri'ke hannunsa na yi a sanyaye na ce." Kada ka tambayeta don Allah." "Akan wane dalili?" Ya fad'a cikin wani irin yanayi. Shiru na yi ban iya ce masa komai ba. Sai ya sake maimaita tambayar da ya yi mini a karo na biyu. Na daure cikin daburcewa na ce." Ni ma fa ba gaya mini ta yi ba kawai ina hasashene." Ya zuba mini idonsa 'kuri yana kallo. Nauyi da kunya ya sanya na yi kasa da nawa idon. Sai ya yi murmushi. mai sauti kafin ya ce." Momi ba ta da ciki Amina, domin kuwa da tana da shi nasan ba zata rufe mini ba zata gaya mini tunda tasan abinda nake nema ne ido rufe, daga yau ki daina yanke hukunci akan abinda ba ki da tabbas akai." Na yi shiru ban tanka masa ba, domin kuwa ni kaina nasan ba ni da abin fad'a kuma ya fi ni gaskiya to idan ma cikin ne da ita menene abinda ya dame ni. Kamar yasan tunanin da nake yi kenan ya matso kusa da ni sosai yana cewa." Ni zan fi so ma ki fara samun cikin Amina." Kallonsa na yi. Sai ya daga mini kai da wani yanayi ya cigaba da cewa." Momi ta kwana biyu shakararta arba'in da uku fa, ina tsammanin idan ba tsananin rabo ba a wannan matakin za ta iya wuce haihuwa don dai tana da karamin jiki ne." "Humm." Kawai na ce masa ina nazartarsa sanin halin maza akwai wahala, sun iya dadin baki da yaudara amma in ba haka ba yaushe zai zo ya zauna yana tsara mini magana. Shekara arba'in da uku shine ta wuce haihuwa muddin tana yin jinin al'ada bai d'auke ba za ta iya d'aukar ciki. Fuskata ya dago da hannunsa muka kalli juna sai ya matso da bakinsa daf da nawa yana so ya sumbuta gabad'aya yanayinsa ya canza da sha'awa. Ban yarda na bashi damar da hakan ba, ya gama lalube mini jiki da hannusa ya tashi ya tafi da sanyi jiki domin ga dukkanin alamu yana cikin wani yanayi na buk'ata. Bai fito ya gaya mini ba amma ina zargin ba wata cikakkiyar gamsuwa yake samu daga wajenta ba, Ina gane hakan ne a duk lokacin da kwana ya dawo hannuna. Yakan nuna d'oki da murnarsa. Washe gari da safe ina nad'e a gado ya shigo mini. Yanayin yadda ya shigo a hargitse ya sanya na gane akwai matsala. Na tashi zaune da sauri ina gaishe shi. Ya amsa a gajarce kafin ya ce." Ki shirya zuwa bauchi gobe in Allah Ya kaimu." Kallonsa na yi naga babu nishadi a tare da shi. Sai na daidaita yanayin fuskata ni ma a nutse na furta." Na gaya maka fa ba na tsammanin zan je gaskiya saboda Ina gudun wulakanci, tunda a wancan karon ni na je, to mai zai hana wannan kuma ita ta je." "Ba na son jayayya da taurin kai fa, kada ki 'bata mini rai, baki da wata hujja anan" D'auke kaina na yi ban ce masa komai ba. Ya girgiza kansa yana fad'in." Bari na kira Baban Saude na sheda masa tunda ba za ki yi yadda nake so." Cikin kuka na ce." Na fa na gaya maka irin wulakancin da ta yi mini a wancan lokacin Hajiya Saratu ce kawai ta goyi da bayana, ya za a yi ka tursasani zuwa wurin da za a tozarta ni." Ya zauna kusa ni a hankali." Zuciyata ba dad'i Amina, ke ma kada ki 'bata mini rai, ki yi abinda na ce dake kin ji ko, kada ki duba kowa ki duba ni Amina." Yadda yake magana da yanayi na damuwa shine abinda ya sanya mini kasala. Na goge ragowar hawayen da yake idona na ce." Ba na gudun zargi da zagin mutane Baba, amma ina kishin kaina, kuma wasu lukutan ba ni da juriya idan aka nemi a ci zarafina sai inda karfina ya kare ba na so na je garin mutane a yi rigima da ni." "Na fahimceki tuntuni Amina, amma ina so ki sani wannan zai zama abin zargi da gutsiri tsoma, ba na so na ji ana zaginki, ko a fadi mummunar magana akanki, duk abinda za ki yi ki yi shi domin ni kin ji matata." Tausayi ya ba ni sosai gabad'aya a hargitse yake ga dukkanin alamu akwai abinda yake dannewa bai fito ya fad'a ba. Ni ma kuma ba zan so na ji ba tunda tsakaninsa ne da iyalinsa. Zan je dominsa kamar yadda ya nemi alfarma, amma ba na tunanin zan kwana don ban ga dalilin yin hakan ba. A wannan matsayar muka tsaya na ce masa ba zan kwana ba kuma sai dai mu je tare ya ce ya amince da hakan. To na d'auka shikkenan magana ta 'kare har ya juya zai fita sai kuma ya dawo ya sake zama a kusa da ni kawai ya zuba mini ido. Ni ma sai na zuba masa nawa mu jima muna kallonsa juna kafin a kasalance ya furta." Ba ki gane ina da matsala ba Amina?" Na ce." Ban gane ba, ai na d'auka matsalar muka warware yanzu." "Ke nake buk'ata." Ya fadi haka yana bin sassan jikina da wani irin kallo. Cikin zuciyata na ce ka gama zagaye-zagayen kenan, wata'kila ma ko karyawa bai yi ba ya tashi da fitina. A nutse na ce." Ai ba girki na ba ne?" "Na dawo hannuki tunda yau na gama yi mata kwana biyunta, kuma haka na wanzu cikin buk'ata domin ba ta da lafiya, sannan ba zan rufe ki ba, ta kasa sabawa da ni sam bata da juriya irin taki." A hankali na ce." Lallai to ai a haka za ta saba, ni ba zan yarda mu fara 'yar haka ba gaskiya ya kamata ta zama mai juriya, tunda ni ma da haka na horu." "Duk da haka dai ai hallitarku ba d'aya ba ce, Amina ni fa kina saurin tayar mini da hankali motsinki kadai yakan jefa ni a wani hali balle kuma na kasance a kusa dake giwar matana." Mamaki ya kama ni jin yau wanda ake yi banbadanci shine shi ma yau wani dalili ya sanya ya shi yana yi. Na yarda namiji a gaban mace yakan zama sahorami koda kuwa mai mulki ne mai dukiya ne ko gawurtaccen malami akwai wajan da izza da jin kai basa tasiri. Ya sa hannu ya janyo ni ya matse a jikinsa yana kyarma yake fad'in." Jiya na dauka mutuwa zan yi Amina, da tsananin bukata na kwana ki tallafeni. Na ce." Ni fa ka daina gaya mini sirrinka Baba, dan gaskiya ni ma ba zan ji dad'i ba idan na ji kana gayawa wata abinda yake tsakaninmu." Hannunsa a cikin rigata ya furta." Babu ma wanda zan gayawa, to me ki ka yi mini, ni kullum cikin sanya miki albarka nake saboda Ina tsananin gamsuwa dake gimbiyata, Allah Ya ja zamaninki." Murmushi na yi amma ba mai sauti ba na tashi daga jikinsa. Ya bi yo ni da kallo idonsa a kankance. Na ce.'" Na ji amma gaskiya ka bari sai zuwa dare a lokacin ne ka fita daga hannunta, amma har yanzu maganar nan da muke yi da kai a cikin hakkinta ne." Sai ya tur'bune fuska yana fad'in." Wallahi ba ki isa ba, ba zai yiwu na zauna cikin lalura saboda wani lissafi na banza ba, ita ban samu gamsuwa ba da ita ba, ke kuma kawai sai na zuba miki Ido saboda Ina jin tsoronki ko." Shiru na yi masa. Ganin haka sai ya cire jallabiyar dake jikinsa ya ajiye da sauri zan sauka daga gadon ya riko hannuna har yana murd'ewa. Cikin zafi na ce." Zaka targada mini hannu Baba." Bai ce komai ba ya kwantar da ni ta karfin tsiya ya danne tare da bankare mini hannu ya rirrike da hannuwansa yana fad'in." Ku ba yara k'ananu ba ayi ta fama da ku, ki 'kwace idan kin isa, ko kin d'auka na yi tsufan da ba zan iya yi mini irin wannan danniyar ba. Ina dariya na ce." To duk mai ya kawo haka, ka sassauta mini don Allah ka cika mini hannu sun fara ciwo." Sassautawa ya yi amma bai cika ni ba, ya ce." Yadda nake ji na garau ko saurayi matashi ba abinda zai nuna mini, ke kullum idan za a neme ki, ko kina so sai kin yi jayayya haka da'biarki take Amina. Cikin jin ciwo domin hannuna ya k'age wajan hammatata na ce." Na ji don Allah ka sakar mini hannu wannan a zabtar da ni kake yi da gangan wallahi." Ya sake ni ya zauna gefan gadon yana kallona." Cire kayanki." Yafad'a cike da bada umarni. Baki na zum'bura tare da juyar da kaina. Bai sake cewa komai ba sai ya sanya hannu a jikina da kansa ya tube riga da siket din material din dake jikina ya cire rigar maman ya jefar a ki'dime ya had'a ni da jikinsa ya matse yana sakin wani irin numfashi ya dinga bin ilahirin jikina da sumbata kamar zai cinyeni. **** To kamar yadda muka tsara tafiyar abinda ya faru kenan. Mun je bauci kuma cikin ikon Allah muka dawo a ranar da muka je din. Na kuma yi mamaki kwarai da gaske da naga canji mai yawa wurin Inna Uwani da ita kanta maijegon da 'yan uwanta, sun tar'be ni sosai cikin sakin fuska da kulawa ba kamar yadda na yi tsammani ba. Inna Uwani duk ta watsar da wannan kiyayyar da take yi mini yau har tana yi mana fad'a da nasiha ni da Hauwa akan mu zauna lafiya da juna, haka zalika kuma kada mu yi zaman gaba, mu had'e kai mu zama tsintsinya madaurinki d'aya irin abubuwan da aka yi a baya kada su sake faruwa. Sosai na yi mamakin hakan. Cikin zuciyata na ce dama ai karya fure take yi bata 'ya'ya kuma duk mai gaskiya zahiri shine a sama. Abinda nake ta gudu bai faru ba, wata'kila dana biyewa zuciyata dangane da abinda ta tsara mini na shiga bakin duniya kenan na kuma zama abar kallo da tofin alatsine. Yaro tubarkalla ma sha Allahu wanda tun ranar da aka haife shi babansa ya yi masa huduba da Ibrahim Khalil sunan kakansa kenan sai uban ya ce a dinga kiransa da suna Khalil. Ya sha gata kwarai da gaske daga wajan Babanshi da abokansa kuma ni ban ji haushin duk irin hidimar da zai yi akan haihuwarsa ba, komai yana da lokaci kuma amfanin dukiyar kenan. Ba su shirya wani gagarimin taron suna ba don maijegon tana d'an fama da ciwon kafafu da yake sun yi kumburi irin na ciki, amma suna sacewa a hankalina. Ma'aikaciyar lafiya ce ita dalilin da ya sanya ma kenan ta ce babu wani gagarimin taro da zata yi iya family dinsu ma kadai sun isa tunda suna da yawa. Hakan ma don ba yadda za ta yi ne domin wani ko ka ce masa babu suna to sai ya zo shiyasa inna Uwani ta ce dangi ba za a hana su zuwa ba, ita kuma yanayin jiki da lafiyarta baya buk'atar hayaniya saboda jininta ya d'an hau kad'an bayan haihuwar amma dai ya daidaita yadda ake bukata yanzu. Hidima sosai ya yi musu don gaskiya ya 'batar da kudi ko ga yanayin irin mahaukatan kayan da sayawa yaron ita kanta maijegon ya saya mata sutturu sannan ya bata kud'i. Haihuwar fari ce a wajensa itama haka babu lefi a cikin dukkanin abinda ya yi. *** Da gaske dai maleji yake yi da amaryarsa domin tun yana 'boyewa yanzu a fili yake nunawa. Ita dai macace wadda ta kware wajan iya kamalai romantic amma fa a shimfida sunanta sorry raguwa ce. Wata'kila hakan kuma yana da ala'ka da rashin sabo domin kuwa kowane namiji da irin hallitarsa zata iya kasancewa tsohon mijinta ba shi da karfin sha'awa da fitina irin nasa. Shekara da shekaru ta riga ta ginu a haka, ga shekaru sun tura tana sake yin rauni gefe guda kuma ga hidindimu na yau da gobe harkokinta na kasuwanci wannan kadai ya isa ya cire mata na ci da kulafucin d'a namiji. Shiyasa aka ce mata suna suka tara kowace mace akwai ta inda tafi kauri akwai kuma ta inda ta gaza, wasu matan kuma duka sai ka ga Allah Ya had'a musu mazajensu suna amfanuwa dasu ta kowane sashe. Tabbas ba yabon kai ba. Ni kaina na tabbatar da cewa Ubangiji ya yi mini baiwa da ba kowace mace yake yi wa irinta ba. Bai fito ya gaya mini ba a fili ba amma na tabbatar da cewa ni ce first lady a zuciyarsa da kuma cikin gidansa. *** Kwanan Hauwa arba'in da shida da Haihuwa ya zo yana gaya mini za ta dawo amma ya nake gani domin ya bari ne ta gama wanka sai ya koma legos bayan mun yanke shawara. Na ce kawai ya bari ta zo nan 'din sai mu yanke shawara a tare domin ni har yanzu ban gama aminta da tsarin da ya yi ba, tabbas idan za mu raba wata shida shida ni da Hauwa to kuwa ban ga amfanin auransa da Hajiya Maryam ba domin kuwa idan ya ce zai biye mata akan abinda take so saboda wani dalili to kuwa babu shakka akwai gyara a cikin auransu. Ba zai yiwu a ce saboda mu kad'ai ne za mu d'aukar lalurarsa ba. Itama ai matarsa ce tsakani da Allah kenan ni na yarda zan d'auki wata shida idan ya so su kuma su raba wata uku uku a tsakaninsu. [10/1, 9:08 AM] Aunty B: 98 Da kansa ya je bauchi domin ya d'auko Hauwa da yaronta. Tabbas idan a da can babu soyayyarta a zuciyarsa to yanzu kuwa ba za a rasa ba, ba don komai ba sai dalilin abinda ya ratsa tsakaninmu wato yaron da suke haifa a tare. Ban ji haushinsa ba dangane da duk rawar kan da yake nunawa akanta da yaronta domin kuwa na riga na tabbatar da cewa hakan sai ta faru to damuwa da bakincikin hakan zai iya haddasa mini ciwo ne don babu wani abu da zan iya hanawa, matarsa ce kuma uwar yaronsa. Babu dalili mai k'arfi zan ce masa abinda yake yi ba daidai ba ne. A wasu lukutan ma ni da kaina nake taya shi mu had'u gabad'aya mu yi ta kallon hoton yaron wanda kamaninsa ke k'ara fitowa sak kamar ya yi kaki ya tofar. Ranar da ta dawo tare da ita ya kasance domin gidane mai yalwa wadataccen zaman mace hud'u kuma cikin sakewa babu takura balle wata ta ce an matseta. Washe garin ranar da ta dawo da yamma muna tare falon Khalil yana hannuna muna hira da ita cikin kulawa kamar babu wata matsala da ta taba faruwa a tsakaninmu yadda na lura ma ba ta fiye so mu had'a ido ba ko magana take yi kanta a 'kasa ko tana kallon wani waje daban a haka muke yin hirar. Cikin zuciyata na godewa Allah da bai sa na cuceta a zamantakewarmu ba abinda suka yi a can baya shine yake damunta Towol din goyansa ta d'auko mini na goya shi a bayana, cikin kankanin lokaci bacci ya d'auke shi. Ina daga tsaye Ina dan jijjigashi tana gaya mini irin rigimar da ya dinga yi kafin su yi arba'in har yanzu bashin baccin da ta tara bai sake ta ba. Maigidan ya shigo amaryarsa a bayansa ta nade jikinta da wata lafiyayyar lifaya irin ta manya. Duk shigar da za ta yi da gayu ba abin mamaki ba ne domin ko bata auran mai dukiya ita kanta hajiyar kanta ce ga uwar dukiyar da aka mutu aka bar mata da yaranta. Fuskarta a sake ta zauna kan kujera tana dariya yayin da take kallon Hauwa tana cewa." Maijego ina fatan ba ki yi fushi da ni ba ko?" Hauwa ta dan yi murmushi a takaice ta furta." Ban yi ba Hajiya ai maigidan ya ce ba ki ji dad'i ba ya jikin naki?" Ta ce." Wallahi kam a lokacin na yi ta fama da zazzabi da mura har da ciwon kai, dalilin da ya sanya kenan ban samu zuwa ba." Ta ce." Allah Ya sawwa'ke abinda ake ta fama dashi kenan." Na kwanto yaron fuska a sake na mik'a mata shi ta kar'ba da walwala a fuskarta. Ko ba a fad'a ba ita din macace mai masifar son yara ko ba na bata ne wallahi irin rikon da take yi wa Yusi ko ni albarka duk abinda yaranta za su sanya a jikinsu za su ci babu bambanci wannan kad'ai ya kan sanya ni jin kunya da nauyin yin tutsu akan lamarinta. Kuma sam ba ta da fitina a haka dai tana zaune da kowa lafiya ban ta'ba ganin kishi a idonta ba. Dad'in ganinmu mun sake muna hira gabad'ayanmu ya sanya shi kashingida kan kujera yana ta murmushi tunda suka shigo bai ce komai ba sai kallonmu yake yi yanayinsa ya nuna ya ji dadin ganin yadda muka fara fahimtar juna. Sai bayan mun nutsu tukkuna ya gyara zamansa domin mu tattauna tare da samun matsaya akan yadda za mu shirya zama. Legos ne kowacce bata so a cikinmu amma kuma tilas ya kamamu duka saboda babu yadda za a yi ace mu bar shi a can shi kadai alhalin duka muna raye adalci shine a ce a raba. Ni ya bawa damar magana tunda ni ce gaba dasu gidan cikin nutsuwa na ce." Ni na amince zan dau'ki wattani shida idan ya so ku kuma sai ku raba kowacce wata uku ina ganin hakan zai fi." Hajiya Maryam tana murmushi cikin nutsuwa ta ce." Anya kuwa ni zan iya akwai abubuwa da yawa da suka sha kaina anan din wallahi ba na so na yi nesa yanzu ko kad'an shi Yallabai din ya sani da za ku yi mini alfarma sai na ce ku barni a nan babu damuwa ta b'angarena in sha Allahu." Falon shiru ya yi bayan maganarta. Yana zaune bai ce komai ba alamu sun nuna tun a gidanta sun gama maganarsu ya d'aukota ya kawota ne don ya wanke kansa kada mu zarge shi. Na dubi Hauwa da tun da muke maganar ba ta ce uffan ba na ce." To ke me ki ke ga ni Hauwa." A takaice ta ce." Duk yadda kuka tsara ya yi mini sister." Sai na dube shi a nutse na ce." To ka ji abinda kowa ya fad'a menene ra'ayinka?" "Ra'ayina shine naku Amina, ku tsara yadda kuke ganin za ku zauna babu takura idan kun yi mata alfarmar da ta nema ni a wajena daidaine amma kada wadda ta kalubalanceni anan gaba. 'Yar uwarku ce ta kuma fito ta gaya muku dalilanta nasan zamanta anan din cikinku duk kun sani, idan kun goya mata baya to duk 'karuwar ta mu ce bakidaya." Cike da takaicin maganganun da yake yi na ce." To wa ka ji ya ce bai amince ba, na d'auka ai zaman da muka yi gabad'aya don mu samu matsaya ne a junanmu, ni ta b'angarena babu damuwa tunda har na iya d'aukar rabi na basu rabin na ce su raba a tsakaninsu Yallabai duk wannan maganganun ba su taso ba." Hauwa ta zumburi baki tana fad'in." To ni ma dai haka na ga ni." Ita kam dariya ta yi tana fad'in." Na gode sosai, Allah Ya daidaita zamanmu ya kuma amfani zuriyarmu, na gode ni zan koma." Ta mike tsaye tana gyara yafen lifayar da take jikinta. Na ce." A haba Hajajju ai babu buk'atar godiya duka taimakon kai ne wallahi kada ki damu an zama daya gabad'aya Allah Ya shige mana gaba." Ta amsa da "Amin." Fuskarta yalwace da fara'a ta kama hanyar fita tana fad'in." Sai na sake zuwa mu gaisa da yarona yanzu bacci yake yi ba mu gaisa sosai ba." Hauwa ta ce." To shikkenan sai an jima. Tana fita Hauwa ta dube shi kamar za ta fashe ta ce." Gaskiya zan gaya maka irin yadda kake nunawa matar kamar itace take auranka ya yi yawa. Ina lefi akan kawaici da karar da muka yi mata har sai ka fad'i wasu maganganu, ai sai ta d'auka hassada muke yi mata, kuma macace mai mutunci da sanin ya kamata gatanan babu wata matsala a tare da ita." Ya ce." Mai na yi muku kuma, shikkenan daga na fad'i magana sai ku juya mini, halinta na fad'a tana da sau'kin kai gashi dai duk ta girmeku amma bata nuna muku gadarar hakan. Sannan duk da dukiyar da take da ita bata d'auki kanta a wata tsiya ba, ta sake daku sosai ta daukeku 'yan uwa daga fad'in haka sai ya zama lefi." Na ce." Mu ai dama ba muce maka wata tsiya ba ne, kuma duk abinda take yi ai ba a sanyata ba gani ta yi zata iya, abinda dai zan gaya maka idan zama ya sake hadamu irin wannan muddin kasan zaka goyu da bayan bangare daya to kawai ka yi shiru da bakinka domin kuwa yin hakan zai janyo maka bacin rai za ka rikita gidanka da kanka." Ya ce." Tunda kece Hajja sai ki ba ni umarni kin ji ko, ku abu kad'an mutum zai yi sai ku zargeshi Allah Ya sawwa'ke." Yana rufe baki Adam da Yusi suka shigo janye da wata madaidaiciyar akwati gaban Hauwa suka ajiye Adam ya ce." Momi ce ta ce wai gashi ba Khalil ne." Ta ce." Ku ce mata na gode sosai Allah Ya kara arziki." Suka juya za su fita muka had'a ido da Yusi sai yasa dariya ya rike hannun Adam na d'auke kaina ina fad'in." Taka zata kawo ka wurina ne yaro." Har za su fita sai ya kira su ya dubi Yusi yana fad'in." Mai ka yi mata take hararaka?" A hankali ya ce." Babu komai Baba, ai muna shigowa kullum mu gaisa da ita ko ?" Ya fad'a yana kallon Adam da yake murmushi. Ya amsa da "E Muna zuwa." Ya ce musu ku tafi abinku rigima take nema." Suka bud'e kofa suka fita kamar wasu 'yan tagwaye komai na jikinsu iri d'aya ne. Kaya ne na waje irin wad'anda take sayarwa cike da akwati kayan nan kudinsu zai haura dubu dari uku domin duka babu k'ananu har da takalma da tarkace dai kala kala. Tare muka duba kayan yana zaune bai ce mana komai ba, har muka gama dubawa muka rufe akwatin bai tanka ba daga karshe ma sai ya tashi ya haye ya sama ya barmu a falon mu biyu. To ganin yadda muka k'ulle muka zama tsintsinya madaurinki d'aya ya sanya shi shiga hankalinsa ssosai. Tun ranar da muka yi zaman nan bai sake yin wata magana da ta danganci matarsa ba saboda ganin yadda muka nuna masa ba mu yarda ba a tun farkon fari. Dama neman magana ne kawai tunda na farko ai bai ga mun ware ta ba, sannan bai ga muna neman fitina da ita ba, maganace a ka zauna ana tattaunawa wadda kowa yake da hakki akai to babu dalilin da zai sanya shi ya budi baki ya yabe ta a gabanmu bayan alfarmar da muka yi mata. Macace mai nagarta kuma wadda take amfani da ilminta a inda ya dace. Duk irin kushe da kiyayyar da mutum zai yi a kanta wallahi kyawun halinta sai ya sanya wataran mai kushiya akanta ya yaba mata. Ina jin kunya da nauyinta sosai, ba don komai ba sai don yadda take k'aunar abinda ya jib'anceni. Na jima ban ga mutum mai kara da kawaici irinta ba. Daf da zamu tafi Legos muka yi waya da Sahura take gaya mini an kawo kudin Yusra an kuma sanya rana shekara daya mai zuwa. Na ce har saurayin ya gama ginin kenan ta ce mini saura kad'an. Daga sanda muka yi waya da ita na ce ta nemi mai wannan lambar 08089965176 wato garkuwar mata itace wadda nake sayan magunguñan Islamic a wajenta na ce su yi magana tunda tana nan kano akan ta hadawa yarinyar maganin sanyi da wanda zai sanya kirjinta ya ciko kafin zuwan lokacin bikin ta kara cika tunda har ga Allah yarinyar bata da wani jiki na arziki yanzu kuma tana matakin shekaru goma sha bakwai a duniya. Idan sun gama magana da mai maganin ni kuma zan tura mata kudin sai ta aika mata dashi. Ta dinga godiya har sai da ta sanya ni na ji haushi na ce ta bari ba na so domin kuwa Yusura haihuwarta kawai ta yi amma na fi ta cin moriya kuma ban yafe mata ba muddin ta sayi ko cokali akan sha'aninta kawai ta bar mini hidimata ta ce. Ta dinga dariya tana fad'in Lallai abin har ya kai haka. Na ce ya wuce hakama a wajena domin kuwa abinda ya shafeni. Kafin mu tafi sai da na kira Babanmu duka na yi masa bayanin abinda yake faruwa amma ban sanar dashi matsalar da ta kaini wajan Baban Saude ba, sosai ya yi mini addu'a da fatan alheri. Ya kuma tabbatar mini da cewa ana samun cigaba ta bangaran Ummansu Hadiza domin yanzu hankalinta ya fara daidaita ta dawo hayyacinta ta ha'kura da kaddara ta barwa Allah komai. Amma har yanzu Hadiza na can gidan yari a ajiye ba a kai ga yanke mata hukunci ba ana ta neman ita wadda suka had'a kai suka yi aika-aikar wato Hajiya Alili." Mun yi waya da anti Yagana na gaya mata za mu wuce legos ban rufe mata komai ba duk na gaya mata irin yadda muka tsara zamantakewar gidan. Ta ce mini hakan da na yi shine daidai a matsayina na babba daga cikinsu dole ni zan dinga 'kokarin d'aukar girma saboda tabbatuwar zaman lafiya. Sati uku da komawa legos na fara laulaye-laulaye. Ciki fa ya samu abinda ake nema ban gaya masa ba da kansa ya fahimta ya dinga murna kamar me ni dai dariya kawai nake yi masa amma can 'kasan zuciya cike nake da zullumi da fargabar abinda zai kasance bayan na haihu. Shi kuma maganarsa daya Allah Ya sa tagwayene. Kullum abinda yake cewa kenan sai dai kawai na yi murmushi gefe guda kuma na tsananta addu'a akan Allah Ya ba ni d'orarre. Ban yi tsammanin zai gayawa kowa ba kawai watarana sai Hajja ta kira ni a waya muka gaisa dama kuma sa'i da lokaci takan kira ni, ko kuma ni na kira ta mu gaisa har ta tambayeni zamanmu na ce mata komai lafiya. Cike da farinciki take magana ai maigidan ya gaya mata na samu ciki. Ta dinga ba ni shawarwari akan na kula sosai kada a sake samun matsala irin ta baya. Idan ma ina so sai ta zo ta zauna mini irin na goyon cikin baby Nana. Na ce mata in sha Allahu zan kula sosai amma ta yi zamanta tunda bata da wadataciyyar lafiya bayan haka kuma abun zai zama wani iri muddin Hauwa ta ji labari ba zata ji dad'i ba, abinda haihuwa ba ta farko ba ce, babu wata matsala da za ta faru. Da wannan na rufe bakinta ta ce mini shikkenan amma dai za ta sanya a rubuce mini al'kur'ani maigirma. Godiya sosai na yi mata muka yi sallama. Hajja macace mai dattako kwarai da gaske tana k'aunata fiye da tunanina don ma an yi yun'kurin shiga tsakanina da ita a baya. *** Watanni shida ciki ya bayyana ya fito sosai duk wasu gwaje-gwaje da scanning an yi mini tagwayene duk mata. Ya rasa ina zai sanya rayuwarsa duk fitina irin tasa ha'kura ya yi a sati bai fi ya kwanta da ni sau biyu ba wai kada yaran dake cikina suga kamar an takura musu. Acewarsa yawan motsa ni da yake yi zai sanya su dinga shan wahala. Abin sai ya ba ni dariya da mamaki. Tun suna ciki basu fito ba yana nuna musu k'auna irin haka, ai ni ma 'yar wani ce mai yasa bai duba hakan ba, a lokacin da ban samu cikin ba yake galabaitar da ni, wato kenan kowa nasa ya sani. A haka na yi wata shida a tare dashi a legos babu wanda bai san ina da ciki ba domin kuwa duk ya sanar da iyalinsa Hauwa har bidiyon call muke yi da ita musha hira Khalil ya yi wayo sosai yana koyar zama. Wasu lukutan ma idan na tambayeta yana Ina sai ta ce yana can wajansu Yusi idan ba nono ya buk'ata ba a can yake yini idan ba makaranta. Idan kuma da akwai idan za su tafi sai su mayar mata dashi. Da kanta ba tambayarta na yi ba take gaya mini yadda suke zaune lafiya domin a wasu lukutan ma takan shiga wajanta su hira itama kuma takan shigo. Na ji dadin hakan sosai da sosai, yanzu dai hankalinmu ya kwanta babu wani kishi na jahilici bayan haka kuma dukanninmu ba yara ba ne iyayene masu yi wa na kasa dasu nasiha. Tare muka koma da shi abujan sai da ya yi sati biyu tukkuna suka juya shi da Hauwa da yaronta. Duk dauriyar da ya dinga nunawa sai da na gane hankalinsa gabad'aya yana kan abinda yake cikina kawai don ba yadda zai yi ne ya dawo da ni, ya d'auki Hauwa domin babu irin rarrashin da bai yi mini ba akan na zauna na haihu a can a gabansa a cewarsa sai hankalinsa ya fi kwanciya na ce masa a a, mun riga ai mun gama magana tuntuni babu dalilin da zai sanya yanzu a warware idan har za a yi mini adalci a lamarin wattani uku kacal za su yi a can shi da ita ta dawo a lokacin ma na haihu in sha Allahu rabbi ko da ban haihu ba to kad'an ya rage. Da haka ya ha'kura smma ba don ransa ya so ba. Bikin Hamusu ne ya tashi gadan-gadan domin kuwa yarinyar da ya jima yana nema burin mahafinta ya cika ta kammala karatunta wannan dalilin ya sanya uban ya ce a d'auki wata biyu kacal a yi a gama komai Ya kira ni yana gaya mini duk abinda yake faruwa. Na ce masa duk abinda yake bukata ya nemi Usaini domin shi yake kula mini da shagunana ya had'a lefe abinda babu ya fitar da kudi ya saya amma ya yi mata akwatina shida ya kuma sanya mata kaya masu quality. Godiya ya dinga yi mini sosai na ce babu buk'atar hakan domin kuwa duk abinda na yi masa babu fad'uwa hakkinsa ne tunda dukiyar tare muke nema. Gini kuwa dama ya kammala abinsa can unguwar maidile ya sayi fili ya gina irin na zamani tuntuni gidan ya kammalu har bidiyo ya yi ya turo mini. Na ce masa idan sun tare ya nemi solar mai girma ya saya sai a sanya masa a gidan tunda na lura unguwar kamar sabuwa ce bata gama cika ba babu wutar nepa. *** Bikin ya matso sosai daga can suna ta shirye-shiryen a lokacin cikina watanshi bakwai da satika. Da kyar nake gudanar da abubuwan da suka zame mini dole saboda nauyin da cikin ya yi mini ya yi girma sosai ya kara sanya ni na d'unkule. Amma ina da burin so na ga na samu halartar bikin Hamusu dalili kuwa anan shine yaron ya wuce komai a wurina ni ce uwa kuma uwar dakinsa. Daga tambayarsa akan ya barni na je tunda ai tafiyar jirgi ce ba mota ba kuma zan motsa jikina na shiga cikin jama'a. Sai abin ya zama rigima saboda ya san ma ba bari na zai yi ba ya mayar da abin tashin hankali ya dinga sakin maganganu har sai da ya fusata ni dama haka yake so na ji haushi mu yi fad'a na kashe wayar raina a b'ace cikin zuciyata Ina fad'in idan ba zaka bari na je ba menene kuma na yin tijara kawai a ce ba zan je ba shikkenan sai magana ta mutu. [10/1, 9:47 AM] Aunty B: 99 Haka aka ci aka cinye bikin Hamusu babu ni uwar biki, sai hotona da ya turo mini nan naga ashe har da su Dada da anti Yagana sun samu damar zuwa bikin. Na ji takaici sosai amma haka nan na ha'kura na yi masa addu'ar samu zaman lafiya madawwami. Amma na yi masa alkawari idan na haihu lafiya takanas zan zayarci kano saboda shi. *** Duk abinda Ubangiji Allah Ya hukunta walau mai dad'i ko mara dad'i yana da iyaka. Kuma cikar mumini kenan yarda da kaddara kowace iri ce wannan shine yake tabbatar da cewa Allah yana sane dakai kuma duk jarabtar da ya yi maka idan ka cinye ba ba tare da ka bi wata hanyar ka sa'ba masa ba to zai maka tagomashin wanda kai kanka ba ka yi tsammanin irinsa ba. Haihuwa na yi cikin koshin lafiya haihuwar da ta sake bud'e kofofin arziki da alherai masu yawa. Duk irin zullumi da fargabar da na kasance a ciki a lokacin da nake d'auke da cikin da haihuwar ta zo sai na yi cikin sauki da taimakon Allan da ya ba ni ajiyarsu a cikin cikina. Lafiyata lau hakan nan yaran ma da na haifa lafiyarsu lau duka ba su d'auke da kowace irin lalura daidai da irin murar nan da ake haifar jarirai da ita tagwayena ba su d'auke da ita.. Tubarkala ma sha Allah shine abinda kowa yake fad'a a kansu domin kuwa yadda Allah ya gina musu jiki da lafiya tun a ciki ba wanda zai d'auka cewa 'yan tagwayene dalili wasu akan haifesu da rashin lafiya irin ta jarirai ko yan'kwanewa da yamushewar fata, su kam kalau suka fito cikin mahaifa daya kamar kuma an tsaga kara babu ita inda suka yi bambanci. Tunda aka haifesu ake ta hasashen da wa suke kama wasu suce da ni, wasu kuma su ce da babansu. Ita Hajja ma cewa ta yi da inna Uwani suke kama mai gabad'aya kenan. Jin haka ya sanya ina Uwani kasa rufe bakinta daga zarar an yi magana sai ta ce ai da ita suke kama. Can dangin Hajja suka kwaso domin ni kaina basa kama da ni balle kuma Babansu Hajja ta ce suna kama da inna Uwani shi kuma ya ce da Samira suke kama matarsa ta farko. Ni dai dariya kawai nake yi musu domin ba ni da ta cewa ganin yaran daidai da yatsuna ba su d'auko ba. Umara ya tafi a tsakankanin haihuwar ya je ya nuna godiyarsa ga Allah subahanawu-wata'ala. Satinsa daya ya dawo ya ce zai shirya walima domin sake nuna godiyarsa ga kyautar da Allah ya yi masa. Ban so ba saboda ba na so abinda zai kawo rud'ani a zamanmu na ce masa lokacin da aka yi masa haihuwar fari ma bai yi ba sai yanzu ya kamata ya bar shi kawai umarar ma da ya yi ta isa. Fad'in haka ashe lefine a wurinsa yana fad'a na kyaleshi ya yi yadda yake so kudinsa ne kuma yaransa ne ba zan tsara masa abinda zai yi ba, Yana da kyau ya nunawa Ubangiji godiyarsa ta sigogi da yawa. Hajja da inna Uwani da ita kanta Hauwan suka shiga maganar domin kasa barinta ya yi a tsakaninmu sai da har suka fahimta. Nan suka had'a baki gabad'aya suka nuna goyan bayansa akan a yi walimar ko da na nesa ba su zo ba ya yi ai hadayace ga jama'a. Jin haka ya sanya na yi musu shiru ban kara cewa uffan ba na zuba musu idona. Amaryarsa akwati biyu ta yi da kaya kowacce shake wai Hassana daya usaina ma d'aya. Wallahi rasa bakin magana na yi a lokacin da na bude kayan Ina dubawa. Da yake duk a gabansu ne Hauwa har tana cewa kada matar nan ta rusa jarinta akan yi wa 'ya'yan miji gwaninta. Ina dariya na ce ko daya tunda ki ka ga tana irin wannan kyautar ta yi nisa ne wata'kila yadda kike d'aukarta ta wuce haka. Hajja ta ce kuma ma dai mai son yi ce domin wasu akan su bayar sun gwammace wuta ta cinye domin Ubangiji yana duba duk wanda ya azurta baya fitar da kazantar dake cikin dukiyarsa da kansa zai fita ta hanyar tashin gobara ko ta wata sigar ta daban. Ta nisa kafin ta cigaba da cewa mijinku shi yake gaya mini cewa har gidan marayu ne da ita a can garinsu jos din tana d'aukar nauyinsu bayan makarantu da massalatai da ta gina duka hobosi ga tsohon mijinta da ya rasu. Wannan dalilin ya sanya ni jin kaunarta a cikin raina domin kuwa macace ta gari, ina kara horarku ku zauna lafiya da ita, kuma kada ku dauketa a matsayin kishi sai yayarku domin ta girmeku ku muntata da kyau. Sosai jikina ya kara yin sanyi da sha'anin matar wato mutane suna daukarwar kansu zunubi a duk lokacin da suke munana zato akan mutum alhalin ba su da sheda kawai zargi suke yi da k'age. Sai na tuna irin maganganun da Sahura ta dinga fad'i a kanta a lokacin auransu da Yallabai ya zama dole kuwa Sahura ta yi nemi gafarar Allah domin kuwa ta yanke hukunci akan abinda ba ta ta'ba ga ni ba. To walima ta kyau sosai, kuma ta samu halartar manyar mutane malamai da ma'aikatan gwamnati har ma da 'yan siyasa. Sahura ta samu zuwa itama yan gidanmu kuwa Babanmu ya samu halarta tare da Baba Sule sai anti Sakina da Fati. Anti Yagana da Yafalmata sun zo Baban Saude kuma a lokacin baya gari sai da ya kira ni a waya ya yi mini barka ya kuma kira maigidan shima ya yi masa barka. Hamusu ma ba a bar shi a baya ba ya zo shi kadai Amma domin da ya gaya mini za su zo tare da Gwaggo na ce masa a a saboda tafiyar mota ce Kuma bata da lafiya sosai na yi alkawarin idan na yi arba'in da kaina zan kai mata yaran ta sanya musu albarka. An yi hidima sosai yara sun samu alheri irin wanda ba zai misaltuba hotonsu kuwa yana ta yawo a kafafen sadarwa tare da yayansu Khalil da ya yi wayo har yana gudu da kafafunshi. Gida ya watse ya rage mu kad'ai. Ni da Hauwa muka cigaba da rainon yaran a wasu lukutan kuma Hajiya Maryam tana aikowa a d'aukar mata su, har su d'an jima a wajenta kafin su dawo. Kwanana arba'in da takwas na shirya zuwa kano. Amma ina jimanta yadda zan yi dawaniyar yaran ni kadai dama burina idan na isa na samu Baba Tabawa mu yi magana idan ta amince mu tafi tare domin zamanta a tare da ni zai taimaka kwarai tunda kaf gidajensa daga na Legos din har na abujan babu mai aiki mace duk maza ne. Hajiya Maryam ce kawai naga tana da mai aiki dattijuwa mai suna Taburni, itace ma takan yi dawaniya da yaran idan an akaisu can wajenta. Ya ce Hauwa ta shirya sai mu tafi tare. Sosai na ji dadin hakan kuwa ban yi nauyin baki ba na yi masa godiya sosai ya ce kwana hud'u kawai ya ba mu dama za mu yi mu dawo. Kwanakin sun yi kadan amma ban iya gaya masa ba saboda Ina gudun ya ce ya fasa ma gabad'aya tunda ya nunawa kamar akan dole ya ha'kura da tafiyar. *** Alhamdulillahi lafiya lau muka sauka a kano. Gidana na sharad'a muka sauka inda muka iske shi tsaf Baba Tabawa da Yusura sun gyara ko'ina har an yi mana abinci. Na yi mamaki kwarai da gaske nasan wannan aikin ba na kowa ba ne sai Sahura domin mun yi waya da ita ana i gobe tafiyar har ta na yi mini tambayoyi ashe abinda ta shirya kenan. Hidimar tace yin cefane mai kyau ta kuma sanya a yi mana abinci mai rai da lafiya. Cikin zuciyata na sake kudire wani alheri da ya jima a cikin zuciyata. Dadaddare Ayuba ya shigo mana da kayan abinci ya kai a store bisa umarnin maigidan ne ya tsaya muka gaisa sosai kafin ya juya ya fita. Ko da na gayawa Baba Tabawa kudirina ba ta yi jayayya ba ta ce ta amince za ta bi ni duk inda zan je, yadda na nuna mata tausayi da kulawa a lokacin da take neman d'auki yanzu ne daidai lokacin da za ta biya ni. Ina dariya na ce mata ai ni don Allah na yi mata ba don ta biya ni ba. Daga ranar kuwa ta shiga hidima da yaran bakid'aya. To duk inda ya kamata na je a tsakankanin kwanakin da ya ba ni mun je ne tare da Hauwa domin duk inda na ajiye kafata itama nan take ajiye tata. Baba Tabawa na goye da Hassana ni ina goye da Usaina ita kuma Hauwa tana ri'ke da Khalil a hannuna. Ayuba ne ke jan mu a mota rana ta farko a gidan Gwaggo na yini sai yamma muka yi mata sallama muka nufi gidanmu anan muka yi magariba. Sannan muka nufi gidansu Sahura dake kusa damu muka gaisa sosai da mamansu ta d'auki yara ta sanya musu albarka. Washe gari a gidan Hamusu muka yini amarya ta zama 'yar gari Hamusu kuwa ya rasa Ina zai tsoma ransa ya kai ya kawo ya siyo wannan ya ajiye ya siyo wannan ya ajiye bayan uban girkin da ya sanya aka yi mana. Sai da na ga abin ya yi yawa tukkuna na yi masa magana sannan fa ya dan samu nutsuwa. Dubu ashirin na bawa amaryarsa na ce ta sayi janbaki ta kar'ba tana godiya ta rako mu har bakin gate. Da muka fito tare da shi nake tambayarsa ya ake ciki da karatun Turmizi tunda shine ya shige gaba wajan kai shi makaranta kamar yadda maigidanmu ya yi alkawari nan yake ba ni tabbacin alhamdulillahi an samu cigaba kwarai da gaske domin hankalin yaron ya fara dawowa jikinsa domin lokacin da aka kai shi makarantar ma baya hayyacinsa dalilin irin shaye shayen da ya fara yi ya hadu da wad'anda suka fi shi wayo suka bashi kwayoyi har hankalinsa ya gushe garkuwar jikinsa ta raunana. A Tasha aka je aka d'auko shi yana zagari da kai kawo tare da sururai. Ya ce ko wancan watan da ya je dubasu ya same shi garau kuma ya kama karatu ka'in da na'in domin malaman a tsaye suke a kansa kuma makarantar cike take da tsaro babu ta inda yaro zai haura ya gudu. Kamalu kuwa farkon watan da zamu shiga zasu sallameshi da izinin Allah dama kuma shi mun gama magana dashi zai zauna a hannunsa domin taimaka masa da cigaba da gudanar da harkokin da muke yi na kasuwanci. Rana ta uku uwa da wuri muka fita saboda gida biyu nake so mu je, gidan Sahura da gidan Alhaji Muntari can muka fara zuwa saboda nasan idan gidan Sahura muka je da farko bai zama lallai ta bari mu fito da wuri ba. Alhamdulillahi na ji dadin ganin yadda anti Maimuna ta samu nutsuwa ta kafa sana'a kala uku tana sayar da itace manyan d'auri sannan ga buhuhunan gawayi anan a jibge kusa da itacen sai manja da man kulli da take sayarwa galan-galan. Lokacin da muke je duka yaran suna makaranta tunda da safe ne. Na tambayeta Salima ta ce itama ta samu koyarwa a wata nursery dake bakin titi gaskiya ne a lokacin da Babansu yake raye ya yi kokarin sanya su a makaranta da wannan yarinyar ta tsira gashi har wasu suna amfana da iliminta kuma tana samun kwabo da dari. Na tambayeta Jamila ta ce mini ta ji dai kwanaki an ce ta yi aure amma kuma tana zaune aka zo aka gaya mata wai an ganta a wani hausa film da ta yi bincike sai ta tabbatar da itace din auran ne ya mutu ta shiga wasan hausa. Sai abin ya ba ni dariya da mamaki cikin zuciyata na ce to Allah Ya kyauta. ** Yini zur muka yi a gidan Sahura ta dinga yi mana soye-soye har da su wainar fulawa. Ta soya mama dubalan cikin bokiti wai mu tafi dashi. Da daddare kuma ta hana mu tafiya sai da gama awara nan ma ta cika mana fulas wai idan muje gida sai mu ci a madadin abincin dare. Sahura kenan sarakan kirki da kyauta. Washe gari ranar da za mu tafi kenan da wuri ya yi waya ya ce sha biyu ta yi mana a filin jirgi domin ya gama yi ma shiri, dama na gaya masa tare muke da Baba Tabawa ya ce babu damuwa don haka da wurwuri muka shirya na ce Ayuba ya kai ni gidan Baba Sule domin shi kadai ne ban je na gaishe ba, ita kanta Hadiza na so na kai mata ziyara amma lokaci bai ba da damar hakan ba, sai da na bawa Ummansu kudi na ce a yi mata siyayya a kai mata. A gurguje muka gaisa da Baba Sule da iyalinsa na yi musu alheri daidai Gwaggwo sannan muka nufi gidan Hajja wanda daga can din sai kuma mu wuce airport. Hajja bakinta kamar gonar audiga ganinmu a tare kanmu a had'e sannan ga 'yan jikokinta da take ta burin Allah ya nuna mata su. Ita kyautarta dama ta turarece domin idan ta je saudiya su take sayowa da dayawa duk wanda ya ziyarceta ta bashi, ta had'o mana da yawa na jiki dana wuta tana ta yi mana addu'a da fatan alheri cikin tsananin farinciki mara misaltuwa. Ganin da sauran lokaci da muka fito daga gidan Hajja na ce da Hauwa mu je gidan Hajiya Saratu don ni sai na ce zuwana gidanta d'aya tunda nake. Shiru ta yi mini ba ta ce komai ba yanayinta ya nuna dai kamar ba ta son zuwa. Nan na fahimci cewa har yanzu akwai rashin jituwa a tsakaninsu tun daga lokacin da suka samu sa'bani akaina basu daidaita ba. Zaman amana muke yi a yanzu dole a tsakaninmu duk wanda ya hangi kuskure daga bangaran dan uwansa idan har da amana bai kyautu ace ya yi shiru ba mussaman idan aka yi duba da cewa ta dalilina suka samu matsala gashi zumunci ne mai karfi a tsakaninsu. Tun kafin mu shiga mota na nuna mata fa yana da kyau ta gyara domin kuwa kaf Hajiya Saratu ba'asar yin ta ba ce, ta wuce matsayin Yaya a wurinta sai dai uwa, gashi kuma yayar mijinta ce dole ita za ta yi hakuri ta nemi hanyar daidato domin su gyara zumuncinsu tun kafin yaranta su fahimci halin da ake ciki. Jikinta ya mutu sosai a lokacin da nake yi mata maganar ba kuma ta yi mini jayayya ba ta ce mu je din, dama ai ita bata d'auka da zafi ba, ita Hajiya Saratun ce ta ga kamar har yanzu bata huce ba domin koda ta haifi Khalil ba ta je mata barka ba. Na ce mata kada ta duba wannan kawai ta yi 'ko'karin gyara kuskuran da ta yi a baya. Takuwa ji dad'i sosai da muka je gidan nata, kuma duk yadda Hauwa take d'ari-d'ari da ita sai ba ta nuna mata komai ba a fuska ba, ta sakar mata fuska kamar babu wani abu da ya ta'ba faruwa na saba'ni a tsakaninsu. Sosai na ji dad'in ganin yadda suka samu daidaito da fahimtar juna. Muka rabu cikin girma da mutunta juna ta yi mana alheri sosai tunda dama can a sanin da na yi mata itama hannunta a bud'e yake. *** Bayan komawarmu da kwanaki uku na kira Hamusu a waya na ce masa ya fitar da kudi ya kuma nemi kwararrun ma'aikatan da za su gyara gidana na kuntau sannan ya sayi set din kayan d'aki da kujeru da gado labuleye masu kyau ya sanya a shirya gidan. Idan komai ya kammala kawai ya kaiwa Sahura mukkulin na mallaka mata shi gabad'aya tunda dama takardun suna hannunsa sai ya bata. Shi kansa ya taya ta murna sosai ya kuma bani tabbacin zai kammala komai a cikin sati d'aya. To mun yanke shawara har da maigidan kan cewa tare za su sake komawa da Hauwa saboda yanayin garin koyaushe cikin ruwa ake yi duk da gidansa ya sha bam-bam da sauran gidajen da suke garin legos amma dai hankalinsa ya fi kwanciya da mu zauna anan abuja zuwa wattani shida lokacin yaran sun yi k'wari sosai.. Na ji dadin hakan sosai kuma na yaba da yadda suke nuna mini kulawa dashi da matarsa. Sai dai tunda muka yanke wannan shawarar nake cin 'kaniyata a hannunsa duk ranar girkina nakan ji jiki kwarai da gaske baya daga mini 'kafa, idan na yi magana sai ya ce abinda ma ya kusa tafiya. Haka na yi ta hakuri dai har ya kammala musu shiri suka tafi sannan na samu sa'ida. ** Cike da mamaki Sahura ta kira ni a waya tana tambayata wai Hamusu ya kai mata mukulli da takardun gida in ji ni, na ce mata 'kwarai kuwa gidana na kuntau na mallaka mata halak malak. Sai ta rasa bakin magana ta yi shiru ta kasa cewa komai ba. Sai da na sake yin magana tukkuna na ji sautin muryarta cikin rawa kamar za ta yi kuka tana yi mini godiya na ce kin wuce haka a wurina Sahura dukiyata taki ce kuma ki shirya zuwa umara in sha Allahu farkon Azimi maigidan ya baku kyautar kujera ke da Anti Yagana da Baba Sule. Sai ta fashe da kukan da take ta b'oyewa na kashe wayar ina dariya da mamakin kukan da take yi a ganina ai Sahura ta wuce duk wannan abin a wajena yadda nake jinta a raina kamar anti Yagana da muka fito ciki d'aya. *** Ubangijina ya jarabce ni da abubuwa da yawa a lukutan baya wanda har nake ganin kamar ni kadai ce nake cikin masifa da ibtila'in rayuwa. Na yi kuka kamar ruwan idona zai tsiyaye yadda na ji dad'i na kuma godewa Allah shine ban ta'ba had'a Allah da waninsa ba, shi kadai na k'adaita na kai kukuna wurinsa domin kuwa nasan shine mai iko da kowa. Allah na gode maka wannan kalmar ba zata ta'ba yankewa daga bakina ba har na koma ga mahallicina. Yadda Allah Ya kar'bi adduata a yau da Kamalu yake zaune a gabana cikin Kamala da suttura tare da tsantsar nutsuwa da wadataccen ilimin Islama a tattare da shi. Kamalu ya girma ya zama saurayi mai tattare da tsafta nutsuwa da ladabi. Ban iya daurewa ba rungumeshi na yi sosai a jikina ina kuka ina tuna mahaifinsu har shi ma ya kasa daurewa ya fara taya ni Baba Tabawa dake goye da Hassana a bayanta ta fito daga kicin da saurin domin sautin kukan namu har can ta tsaya tana ba ni baki wai na daina yin kuka Allah ya kamata na godewa domin duk abinda yake faruwa hukuncinsa ne. Da kyar na yi shiru shi ma ya rike hannuna gam ya kasa saki. Cikin wannan halin Yusi da Adam suka shigo domin lokacin da aka kawo mini Kamalun ba sa nan. Wani tsalle Yusi ya yi ya rungumeshi suka fadi a wajan Adam ya dinga yi musu dariya. Shi ma Kamalun dariya yake yi wa Yusi ganin yadda duk kwalla ta cika kwarmin idonsa. Ya dube ni yana tambayata wai wane irin abinci Yusi yake ci ya kumbura irin haka, ko bashi da lafiya ne. Na ce masa lafiyarsa lau hutu ya samu da jin dadi. Adam dai yana tsaye yana ta dariya da yake yaro ne mai sakakkiyar fuska kamar ta Mamansa. Kamalu ya gyara hannun rigarsa ya daga k'wajinsa na hannun dama duk a mur'de ya dubi Yusi yana cewa ka ga ni da nake cikin hatsi ina kuma aikin gona da motsa jikina dubi kwanjina malam haka ake son namiji ya kasance. Adam ya ce abinda ake gaya masa kenan amma kullum sai ya ci nama ya zuba suga da madara da vombita da yawa ya tea Momi na bashi goyan baya. Yana dariya yake cewa ku raka ni na je na gaishe da Momi ni ma." Ya mike tsaye ya shiga tsakiyarsu suka kama hanyar fita. Ni da Baba Tabawa muka bi su da kallo cike da wani irin farinciki a zukatanmu bakid'aya. Abin mamaki da d'aure kai. Tun ina tsammanin dawowar Kamalu har na cire rai domin kuwa sha daya na dare har ta gota. Zuciyata ta shiga yi mini nazari ko kallo suka yi ne, ko kuma dai yaran sun d'auke masa hankali sam ban kawo cewa matar gidan ce ta hana shi dawowa ba sai da na kira ta a waya na tambayeta tukkuna kai tsaye ta ce mini zai kwana cikin 'yan uwansa ne. Mamaki mai yawa ya lullube ni amma ban iya cewa da ita komai ba muka yi sallama har tana cewa a shafa mata kan twins. Da zullumin lamarin na kwana a cikin raina. Don haka gari yana wayewa ban yi kasa a gwiwa ba na kira maigidan a waya da muka gaisa na gaya masa fa makaranta sun sallamo Kamalu yanzu haka muna tare da shi anan abuja jiya Ayuba ya kawo mini shi. Sai ya ce ai Hamusu ya kira shi a waya ta gaya masa. Daga can makarantar ma sun sanar da shi. Na ce zai yi sati sati daya anan domin mun gama yanke magana da Hamusu zai zauna a can wurinsa domin dora shi akan harkokin da muke yi. Bud'ar bakinsa sai ya ce bai amince ba dama ai tuntuni ya gaya mini idan yaron ya dawo zai had'ashi da d'an uwansa su tashi tare . Idan kuma ina ganin hukuncin da ya yanke bai yi mini ba sai na yanke nawa tunda duka 'ya'yana ne. Na dinga kokarin nusar da shi hakkin da dangin ubansu suke da shi akan yaran, idan fa magana za a yi ta gaskiya yana da kyau a ce suma an basu damar yin abinda suke so da yaran. Ya fahimci dalilina amma sai ya mayar da abin rigima . Ganin haka ya sanya na kashe wayar raina a b'ace. Ni wannan 'karfa-'karfa da ake yi mini akan yarana ya fara isata wallahi duk na gane take-takensa shi da matarsa wata'kila ya yi mata kyautar yaron tuntuni ban sani ba, tunda haka ya bata Yusi ba tare da neman izinina ba. Wannan lamari ya janyo mana sa'insa sosai a tsakaninmu, wanda har sai da na gaza ha'kuri ina kuka na kira Hajja na gaya mata ta yi masa magana ta ba ni ha'kuri sosai ta ce za ta sanya a kira mata shi a waya. Ranar kuwa da suka yi waya Baban Saude ya kira ni tare da rufe ni da fad'a irin wanda ban ta'ba tsammani ba. Shiru kawai na yi Ina sauraransa wato tunda na kira mahaifiyarsa to shi ma bari ya had'a ni da nawa iyayen. Baban Saude ya gama nasa fadan. Anti Yagana ma ta kira ni tana yin nata tana ce wa Ba ni da wato har yanzu kuma har yanzu na kasa gane irin k'aunar da mijina yake yi. Idan duk zai d'auki yaran da zan haifa ya bawa matarsa ai ta cancanta ne tunda kowa ya shaida ita din uwar marayu ce. Har da Allah Ya isa ta yi mini idan na kuma tashin maganar da kanta zataje ta yi wa Gwaggo bayani tana da tabbacin samun goyon baya da amincewa daga wurinta. Kuka na ci na 'koshi na ha'kura na kyalesu kullum dai da safe suna shigowa mu gaisa. Shi ma kuma kamalun ya fi sakewa a can saboda yaran don ma shi Salim yana can saudiya yana 'dora karatunsa sai 'yan yaran Nusaiba Sahib da Yasmin da ake kawo su duk ranakun weakened. Kiran Hamusun na yi a waya na yi mas bayani duk yadda al'amirin ya juye. Sai ya dinga dariya cike da nuna rashin damuwarsa yake ce mini wannan ai ba wani abu ba ne hakan ma da aka yi daidai ne da kuma hujja mai k'arfi. Dole na ha'kura na zubawa sauratar Allah Ido, amma kuma ban ta'ba nunawa matar wani abu a fuska ba, dalili ta wuce na ya'keta akan komai ba, wanda ya riga ya ce yana son naka ai kai yake k'auna. **** Haka zamanmu ya cigaba da gudana ni da Hauwa muna safara daga abuja zuwa legos yayin da ita kuma Hajiya Maryam take zaune a waje daya tana d'auke mana lalura da hidimar yaranmu. Bayan mai aikinta ta burni ta 'karo guda biyu masu d'an jini a jika domin kuwa wannan dawowar da Hauwa ta yi da ciki ta dawo har ya yi k'wari gabad'aya sabga da dawainiyar Khalil ta kuma gidanta. Kamalu kuwa har ta kai shi makaranta boko a cewarta bayan ya samu na addinin yana da kyau shi ma ya samu na bokon domin babu wanda ya san abinda zai zama anan gaba. Abinda Kuma ya k'ara zaburar da ita game da sha'anin yaron yadda yake koyar da su Adam karatun addini tare da sake nuna musu hukunce hukuncen tsarki da abinda ya shafi gyaran ibada. Kafin mu tafi legos kuwa Kamalu ya fara limancin wani sabon massalaci da maigidan ya gina anan kusa da mu. Abin ya ba ni sha'awa sosai wai yau Kamaluna ne yake jan ragamar mutane da yawa zuwa gaishe da Ubangiji. Na yi kuka a zucci na yi na fili na kuma yi godiya ga Allah da ya nuna mini wannan rana da raina da lafiya, rayuwa kenan wataran asha zuma wataran asha mad'aci. Ubangiji Allah kasa mu d'ayantaka duk rintsi duk wahala ka barmu da imaninmu kada ka bari mu kauce daga bin tafarkin sunnar Annabi Muhammadu S.A.W.