[8/14, 10:39 AM] Aunty B: *61* Ganin yana waya da Sukairaju akan sha'anin matarsa ya sanya na tashi ba tare da na ce komai ba na nufi d'akina na bar su a wurin. Mintina goma sha biyar Yusi ya shigo lokacin ina gyara jeran madubina na dube shi a nutse na ce." Yusi idonka kenan baka nema na, ka manta da ni ko?" Ya rungume ni yana yana dariya yana cewa." Mama kece fa kika ce duk lokacin da na ganku a falo kuna zaune na daina zuwa wurin." Na gyad'a kai Ina cewa." E haka na ce, amma me yasa da kuka dawo baka neme ni ba, ai ka zo mu gaisa ko?" Ya rike hannuna yana fad'in ." To ki yi hakuri." Ban ce komai ba na cigaba da gyara kayan shafata sai yasa hannu yana taya ni. Ya ce." Mama nasan yanzu Yayana ya kara girma ko?" Na ce." Sosai ma, ai za mu sake komawa duba shi in sha Allah." Da murna a tare dashi ya ce." To shikkenan mama, amma yaushe zai gama karatun kuma idan an sallamo shi daga makarantar a ina zai zauna." Na dube shi a nutse na furta." A can wajan Gwaggwo mana, mun yi magana da Hamusu zai dinga tafiya dashi kasuwa." Wannan maganar na yi ta ne a daidai lokacin da maigidan ya turo kofar d'akin a bazata don ban yi tsammanin hakan ba ya shigo. Yana da kaifin ji dalilin da ya sanya ma kenan ban tsaya yin kokwanto akan ya ji ko bai ji ba. Kawai na zuba masa ido yayin da shima ya zuba mini nasa idon wanda suke cike da tuhuma da zargi. Na fahimci yanzu yadda ya tsani mutuwarsa haka ya tsani jin sunan Hamusu a bakina, ban san menene dalilin da ya sanya ya d'ora masa karan tsana ba, bayan ada ba haka yake ba. Yusi ya bashi hannu suka cafka dama sararsu kenan motsi kad'an sai su had'a hannu. Ya dafa kansa da cewa." Ka je d'akina na rage maka abinci." Sai ya sake bashi hannu a karo na biyu suka tafa. Ya kama hanya da sauri ya bude d'akin ya fita. Ya rage da gani sai shi a d'akin. Na nemi gefan gado na zauna ina kallonsa don ban san da mai ya shigo ba, na san dai tunda ya ji maganar Hamusu ba zai yi shiru ba. A cikin halayensa marasa kyau akwai zargi na gama fahimtarsa. Na gyara yanayin fuskata sosai domin tarar abinda yake bakinsa. Ya zauna a gefana yana fad'in.'' Wace magana na ji kuna tattaunawa da Yusuf yanzu dai shine abokin shawararki ko?" Murmushin takaici na yi na ce." A a kai ne abokin shawarata Baba, magana muke yi akan Kamalu yana tambayata idan ya dawo daga makaranta a Ina zai zauna na ce masa can wurin kakarsu Gwaggo mun yi magana da Hamusu zai dinga tafiya dashi kasuwa." Ya gyada kansa yana dubana ya furta." Ashe kina bibiyar sha'anin yaron." Cike da mamaki na ce sosai ma kuwa." Ya furta." Babu inda zai zauna sai nan tare da mu gabad'aya domin raba kan yaran zumuncinsu zai yi rauni, baya ga haka kuma, a can unguwar taku ya lalace ai, to me zai sanya kuma a sake mayar dashi, idan har kun yanke shawarar zamansa a can kano to sai ku had'a da d'an'uwansa gabad'aya ku ajiyesu a waje daya." Na yi shiru ina auna maganarsa. Gabad'aya kaina ya kulle na gaza fahimtar abinda yake nufi da wannan maganganun yanzu ina iya furta wata magana ya canza mini manufa, ni dashi duka ba mu da karfin iko kamar dangin Babansu. Hamusu kuma yana iyakacin bakin kokarinsa wajan ganin ya bashi girma kuma bashi da wata matsala, amma tunda sun nema kuma suna da hakki akan yaran nan ya kamata a ce wannan karon na yi kawaici da alkunya na ba su daya na rike d'aya, amma ina ganin ba zan samu goyon bayansa ba, nema ma yake ya mayar da abin rigima da 'bangaranci. Na share shi kawai ban ce masa komai ba domin ina danne zuciyata ne ba na son na biye masa na san idan muka fara ni dashi gabad'aya ba zata yi mana kyau ba." Ya tashi zai fita na ce." A game da maganarka ta d'azu ina da ja kai." Ya tsaya tare da juyowa yana kallona. "Wace magana kenan." "Dangane da amanar matarka da ka ce ka ba ni, ban kar'ba gaskiya domin ni ma nema nake yi ka ri'ke amanata don har yanzu ban san kaina ba." Ya ce." Ai hakkinki ne a matsayinki na uwargida ki ri'ke mini amanar gida da duk wanda na kawo na ajiye shiyasa na gaya miki." Na ce." Ban kar'ba ba gaskiya kuma zuciyata ba ta aminta da zamanta a samanka ba, idan adalci za ka yi kawai ka ce mata ta sauko kasa." A nutse ya furta." Ba ki ji uzurinta ba ne, tana da ciwon kirji ta ce ko a wajan aiki a kasa take ba ta iya zurga-zurgar hawa sama." D'auke kaina na yi ban ce masa komai ba. Ya ce." Idan kina ganin da damuwa to kema sai ki tattaro ki hawo saman ku tare bakidaya hakan zai fi." "Ina buk'atar tsinka jinina, da zan hau ai da tun kafin ta zo gidan na hau." Ya daga kafad'arsa ba tare da ya ce mini komai ba ya bud'e kofa ya fita. Na ja jiki ahankali na kwanta saman gado ina matse jikina kawai na ji hawaye na fita daga idona. Ajiyar zuciya na sauke tare da dan rintse ido yayin da damuwa ke sake sukar ilaihin jikina. Daurewa kawai nake yi ganinsa ya k'ara motsa mini sha'awar da ta dame ni. Haka na 'kàrasa yinina cikin damuwa da takura da daddare da kyar na fita falon shi ma don kada Hajja ta zargi wani abin ne, na same su kuwa gabad'aya har ita amaryar inda ta sheka ado da wani uban Les ta soka d'aurin dankwali wanda ya fito da k'arin gashin da ta yi. Kwaliyya ta yi sosai irin ta amare har dasu gashin ido ga sarka nan d'azu awarwaro da zubona a yatsun hannunta. Ban damu ba domin abin da ya dame ni daban shiyasa adonta bai d'auke mini hankali ba, abinda dai ya so ya bata mini rai bai wuce ganinsa zaune a saitinta ba suna magana da juna. Na yi 'kokari sosai wajan nuna ban san me suke yi ba, muka gaisa har shi din da yake dan satar kallona itama amaryar ta yi mini sannu da fitowa Hajja tana cewa" ai yanzu nake shirin aika Yusi ya kiraki." Na ce." Wallahi ina yin sallar magriba bacci ya kwashe ni sai yanzu na farka. Kafin tayi magana aka kira shi a waya maganarsa ta d'auki hankalinmu gabad'aya zance ne dai bai mutu ba domin iyalan wani mamacin ma sun sake yin magana a sahar nan ta fece book inda suma suke kalubalantarsa akan take hakkinsu da ya yi. Gidan jaridar da duniya ta aminta da rahotanninsu sune suka kira shi domin neman k'arin bayani da kuma neman alfarma samun lokaci daga wajensa don su tattauna ya kuma wanke kansa dangane da zargin da jama'a suke yi a kansa. Kafin ma ya kammala wayar Sukairaju ya shigo, ya d'an tsaya daga gefe bayan ya gaishe mu. Sai da ya bari ya gama wayar tukkuna ya risina tare da mika wayar hannunsa. Ya kar'ba kimanin minti biyar ya gama dubawa ya mika masa wayarsa a nutse ya ce." Kada ku damu in sha Allahu alheri ne, gobe za mu tattauna da gidan jarigar Amana daily trust zan wanke kaina bisa zargin da jama'a suke yi mini., Sukairaju ya sake risinawa yana fad'in." Ranka ya dad'e lamarin ne ya karad'a gari mussaman social media jama'a sai maganganu marasa dad'i suke yi akanka, dalilin da ya sanya hankalinmu ya tashi kenan" Ya furta." No kada ku damu zai wuce an riski kalubale iri iri, an cimma nasara kuma, wannan ba komai ba ne, zan dai yi bincike akai sosai." Hajja ta ce." Amma dai Alhaji Sammani bai kyautawa rayuwarsa ba wallahi, yanzu wanene ya san iya adadin mutanan da ya takewa hakki." Ya ce." Sai Allah Hajja domin wad'anda suka rasu a 'karkashin ayyukana suna da yawa wallahi, kuma duk wanda na tabbatar da mutuwarsa zan fitar da hakkinsa na bayar, shi Sammanin shine ya zalince ni." Sukairaju ya k'ara shigowa a karo na biyu da sauri ya nufo shi da waya, kafin ya k'arasa ya dakatar dashi yana cewa." Sukairaju na gaji da magana daya don Allah kada ka k'araso nan, na san inda matsalar take zan kuma yi maganinta." Ya tsaya bai kàrasa ba kamar yadda aka umarce shi amma bai fita ba ya sake sunkuyar da kansa da ladabi ya ce." Sir lamarin ne ya sake yin tsamari ne wannan yana da kyau ka duba domin daga gida abin ya sake fitowa." Shiru ya yi bai ce masa komai ba, sai hakan ya bashi damar isa wajensa ya mik'a masa wayar tare da nuna masa abinda yake zo ya gani. Da sauri na ga ya d'ago kansa yana kallona da mamaki mai yawa a tare dashi. Ban kawo komai ba balle na zargi abin ya shafe ni. Ko da ya gama karantawa bai ce komai ba ya bashi umarnin fita. Numfashi ya fesar kafin ya yun'kura ya tashi ya nufi samansa ba tare da ya sake wata magana ba. Gabad'aya hankalinmu ya tashi har mahaifiyartasa, ta ma manta wadda take dashi fadi take yi Amina tashi ki bi shi maza domin yana buk'atar wani a kusa dashi. Ni kaina sai bayan na tashi din ne naga kamar rashin dacewar hakan tunda ga amaryarsa a ganina ita ya kamata ta je kusa dashi. Sai na dan tsaya da tafiya. Ta sake fad'in." Maza ki je mana, kin san shekaru sun fara hawa kansa kada ya yanke jiki ya fad'i. Gabana ya buga da karfin gaske dana tuna rashin lafiyar da yayi kwanaki fad'uwa ya yi har sai da aka d'auke shi bai san inda kansa yake ba. Na nufi saman da sassarfa da fargabar abinda zai biyo baya. yana zaune a gefan gado ya d'an tallafe ha'barsa da hannu kamar mai nazari na nufe shi yayin da tausayinsa yake tsirga mini, kusa dashi na zauna a nutse na ce." Baba kada tunani ya haddasa maka ciwo, kaifa babba ne, kuma kayi gwagwarmaya menene baka gani ba don Allah kada ka damu akan wannan abin, muna cikin tsananin bukatarka a yanzu." Ya dube ni a nutse ya furta." Ke da yaranki Kuna buk'atar hakkin tsohon mijinki Aminu Salihi wanda na take bayan rasuwarsa ko?" Gabana ya wani buga da mugun karfi. Na zuba masa ido Ina kallo lebana yana rawa tsabar mamaki da tashin hankali. Ya d'auki wayarsa dake saman dirowa ya farara labule. Minti uku ya miko mini, babu gardama na kar'ba wani pege ne da ban san me shi ba, akayi tagging dina wanda ya yi rubutun yana magana akan yadda Alhaji Tajo yake amfani da matasa domin tara dukiya har yana bada labarin Yaya Aminu da irin bautar da ya yi masa yana kuma jadaddawa a rubutunsa cewa da yawuna ya fito yake magana akan hakkina dana yarana da aka take. Cikin wani irin yanayi na tsantsar damuwa da tashin hankali na shiga fece book din ina ta scrolling abinda yake ta trading kenan. 'Cewa jita jitar da ake ji dangane da Alhaji Tajo da ma'aikatansa gaskiya ne, domin kuwa matarsa wadda yake aure a yanzu tsohon mijinta Aminu Salihi kafin rasuwarsa ya yi aiki a karkashinsa wanda kowa shaida ne dangane da yadda ya bautata masa a wata majiyar ma ana cewa sanadiyar aikinsa ne ya kamu da lalura sa'i daya kuma ya kore shi daga aiki domin ya gane bashi da mamora karfinsa ya kare, bayan ya sallameshi daga aiki bai bashi komai ba, a haka Aminu Salihi ya yi ta jiyya har ya rasu da damuwar hakan. Rahoto ya tabbatar da cewa da yawun Aminu Salisu mai hula wannan 'yar kasuwar nan da ta yi shura wajan fashion designer a kafafan sadarwa da amincewarta wannan rahontan ya fita." Gidajen jaridu da wanda suka kai da wanda basu kai ba sai posta hoto na da nasa suke yi. Wasu ma harda hoton yaya Aminu da Kamalu da Yusi. Kuka ya k'wace mini da k'arfi na sanya hannu na toshe bakina Ina kallonsa hawaye na shatata. Ya kar'bi wayarsa ya ajiye ya matsa daga kusa da ni, ya ja jikinsa ya jingina da allon gadonsa. A hankali na matsa kusa dashi ina kuka na ce." Wallahi tallahi Baba ba da yawuna aka fitar da wannan maganar ba, asalima ban san me pege din ba idan ka lura sabon shafi ne ba a jima da bud'e shi ba, wata'kila an shirya mini hakane domin a 'bata ni a wurinka, ba zan ta'ba cin zarafinka a duniya ba Baba idan ban ya'da alherinka ba ai ba zan yad'a sharri a kanka ba, ka yarda da ni wallahi ba ni da masaniya abinda yake faruwa, babu hannuna." [8/16, 9:06 AM] Aunty B: *62* Ya dube ni a yayin da na gama firgicewa domin hankalina ya kai ma'kura wajan tashi jin yadda lamarin yake nema ya sauya salo, hakika duk wanda ya shirya wannan lamarin ya yi mini farin sani. Na san dai kafin k'addarar aure ta ratsa tsakanina dashi a ko'ina na kan saki bakina na soki sha'aninsa na kushe shi, na nuna ba na daya daga cikin mabiyansa idan aka tambaye ni hujja ba na rufewa fad'a nake yi. Ban ta'ba tunanin hakan zai janyo mini gagarimar matsala ba tunda ban ta'ba zaton aure zai ratsa tsakaninmu. Ganin yadda na kanainaiyeshi da ro'ko da magiya ya sanya ya sassauta fuskarsa ya gyara zamansa a tsanake ya dube ni yana ce wa." Me yasa tunda muka yi aure ba ki gaya mini cewa Aminu Salihi ne mahaifin Yusuf ba. Hannu na sanya na goge hawayen da suke zuba na ce." Ban san ta yadda zan gaya maka ba wallahi, ni dai abinda nake so ka fahimta shine wallahi ba ni da hannu wajan wannan rubutun. Abinda na yi Imani dashi shine duk wanda ya shirya hakan yana da masaniya akan sha'anina." Ya zuba mini ido kafin ya ce." To ke wa kike ganin zai hakan a cikin wad'anda ki ka sani ko kike tarayya dasu." Na hada hannuna da nasa na rintse a na ce." Wallahi ba zance ba Baba, ka yarda da dani har cikin zuciyata babu mugun nufi a tsakaninmu." Ya ce." Ai dama ni ma ban ce da mugun nufi ba, abinda dai ya fi damuna yadda ba ki sanar da ni cewa uban yaranki ya ta'ba aiki a k'arkashina ba, kin ga dole ne yanzu zuciyata ta d'ora zargi akan cewa da hannunki maganar nan ta fita, da kin sanar da ni tuntuni da Ina ga da duk haka ba ta faruwa." A sanyaye na ce." Ban san ya za a yi na gaya maka ba, to na ce maka me? ya fa riga ya mutu shekara da shekaru kuma maganarsa a tsakaninmu zata iya haifar da wata matsalar maigirma." Ya d'an jima yana kallona kafin ya ce." Ki gaya mini gaskiya shin bayan rasuwar Aminu Salihi Alhaji Sammani ya je ya yi muku ta'aziya ko bai je ba." Girgiza kaina na yi a hankali na ce." Bai je ba." Ya ce." Kin ga hakan yana nufin kudin dana fitar da sunan magada suna wajansa" Shiru na yi ban ce komai ba, ni dai burina kada ya zarge akan abinda yake ta yawo a kafafan sadarwa. Ya dan riko kafadata tare da sanya tafin hannunsa yana goge mini fuska ya ce." Daina kukan haka na aminta dake wata'kila ana bin ki ta karkashin kasa ne to sai aka samu wannan damar amma duk yadda akayi wanda ya fitar da maganar nan ya san ki ciki da waje, babu komai zai wuce in sha Allahu." Yana maganar yana dan bubbuga bayana. Zuciyata ta dan yi sanyi amma har yanzu damuwar bata sake ni ba, domin yadda ake ta sukarsa ana yad'a sharri akan harkokinsa ya tsaya mini a raina. Luwai na yi a jikinsa ina sauke ajiyar zuciya yayin da hannunsa yake dan dukan bayana a hankali a hankali d'akin ya yi shiru na tsayin mintina goma babu sautin komai sai na numfashinmu.... Daidai lokacin da nake yun'kurin zare jikina daga nasa ta turo d'akin ta shigo duk muka bita da kallo Cikin 'yar fargaba na cire jikina daga nasa na d'an ja gefa, ta k'araso a nutse babu fara'a a tare da ita ta ce.'' Kin san dai ba haka ake yi ba ko? kada ki bud'e kofar fitina a tsakaninmu lamarin ba zai yi mana kyau ba wallahi, wace macece za ta yarda ayi mata wannan iskacin, aka ce ki zo domin ki kula dashi me yasa ba ki gayyace ni ba, a matsayin matarsa nake kuma amaryarsa me ya sa za ki 'kebe dashi kusan mintina talatin, kin san dai ko ke aka yi wa haka ba za ki ki dadi ba." Shiru na yi ban ce mata komai ba, domin duk maganganunta akan hanya suke tana da gaskiya kuma ko ni ce ba zan yarda ba gaskiya dalilin ma da ya sanya kenan na ja bakina na yi mata shiru tana ta furzar da takaicinta. Jin tana sanyo Hajja a ciki ya sanya ya ce." Ba za ki yi mana shiru ba ko? ke wai me yasa ba kya aiki da iliminki ne, me ki ka shigo ki ka ina yi da ita da kike so ki zage ni." Sai ta rushe da kuka tana cewa." Ni ba da kai nake ba, ai ta san ba ta kyauta mini ba shiyasa ta yi shiru bata da gaskiya, kai kuma kana biye mata, har kana so ka kare ta." Yunkurawa na yi na tashi domin fita daga d'akin ta bi ni da harara tana jan tsaki ban kulata ba na kama hanya na fice zuciyata a cunkushe. Ban iya rintsawa ba a daran ranar raba dare na yi ina duba comments din mutane dangane da abinda yake faruwa wasu sai zagina suke yi suna fad'in dama ba ni da kunya sannan kuma butulu ci na yi masa ban kuma san alheri ba. Tsirarun wad'anda suke goyon bayansa sune suke fad'in wannan maganganun. Amma dai masu zaginsa sun fi rinjaye. A daran dai na shiga fege dina na fece book din a karo na biyu zan sake yin rubutu akansa wannan karon rubutuna yana d'auke da sa'kon godiya da yabawa, jinjinawa da sadaukarwa a gare shi, na kuma fito na gayawa duniya cewa babu yawuna dangane da rubutun da yake ta yawo a kafar sadarwa asalima ban san me pege din ba, na rufe da yi masa kyawawan addu'oi tare da samun cigaba da d'aukaka da kuma gamawa da duniya lafiya. Washe gari da safe ban fita da wuri ba sai wajan takwas da rabi. Hajja kawai na samu a falo ita kad'ai. A nutse na kàrasa wajan da take na tsuguna na gaisheta kamar koyaushe ta amsa tana d'an bina da kallo, matar tana da saurin fahimtar mutum ko yaya ta ga can ji a tare dani sai ta nemi ba'a si, a nutse ta ce." Zo zauna kusa da ni, na ji me yake faruwa Amina wannan kumburin na Idonki ba na lafiya ba ne." Na zauna gefanta ina dan murmushi wanda sam babu nishadi a cikinkisa. Ta ce." Menene yake faruwa? Cikin rauni da damuwa na ce." Wallahi Hajja wani abu ne ya faru wanda bai yi mini dadi ba ko kad'an, wani rubutu ne ya fita da sunana a ciki wai ina neman hakkin yarana a hannun maigidan nan, mai rubutun kuma yana jadaddawa duniya cewa da yawuna ya fito yake sanarwa mutane." Ta ce." Assha to shine ai me kuma? Idan ma kin fito kin yi magana ai ba lefi ba ne, abinda dai nake so na fahimta shine dama Babansu Yusi din ya yi aiki a karkashin Tajo ko kuwa?" Na goge hawayen da ya dan zubo mini na ce." E, ya yi aiki dashi kafin rasuwarsa." Sai ta girgiza kanta cikin alhini ta ce." Allah Ya gafarta masa, ki samu nutsuwa kuma ki daina damuwa da hakan in sha Allah babu abinda zai faru." Na ce." Na gode Hajja Allah ya kara girma." Ta dafa kafadata tana cewa." Ina ganin umarar nan tare zamuje ki d'an samu nutsuwa ki kuma yi addu'oi, Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu." Na kalleta hawayen da nake ta dannewa suka fara zuba, na rasa wane irin so da k'auna baiwar Allah nan take yi mini, tana gudun b'acin raina sosai, tana kuma so koyaushe ta gan ni, cikin farinciki da walwala. Na ce." To shikkenan Hajja sai mu tafi taren in sha Allahu." Hauwa ce take saukowa daga bene tana sanye da kanun kaya amma ta dora after dressing akai ta yi kwalliya sosai a fuskarta kuma ta yi kyau daidai gwargwado. Ta iso wajan da muke zaune ni da Hajja ta zauna saman kujera tana fad'in." Hajja Ina kwana an tashi lafiya?" Ta amsa da "Lafiya lau tana dan dubanta." Ta d'an kalleni kafin ta ce." Ina kwana." Na amsa babu yabo babu fallasa." Hajja ta ce." Tajo bai tashi ba ne?" Babu kunya balle tsoron Allah ta ce." Bai tashi ba jiya bai kwanta da wuri ba." Hajja ta yi shiru tare da kawar da kanta gefe. Ni kam maganar ta dan dake ni sai nake ganin kamar da gayya ta fad'eta." Tashi na yi na nufi wajan cin abinci ina fadin." Hajja kin karya ne?" Sai ta ce." Kin manta yau litinin ina Azimi." Na ce." Wallahi na manta, Ina gyara kujerun wajan na dubeta." Hauwa ki zo mu karya." Ta d'an yatsune baki tana cewa." Ina ga sai an jima ba na karyawa da wuri." "Okey kawai na ce na gyara kujera na zauna a nutse na dan d'ibi abinda zan iya ci na hada tea na fara sha domin ya d'umama mini cikina. Saukowarsa ta d'auki hankalinmu gabad'aya duk muka zuba masa ido yanayinsa kawai nake kallo kamar ba shi wanda ya shiga damuwa mai tsanani jiya ba. Ban d'auka zai wayi gari da karsashi irin haka ba. Kwalliya ma ya sheka sosai cikin wani irin yadi irin na manya babbar riga da yar ciki da uban aiki a gaban rigar. Tun kafin ya k'araso wajan da muke kuwa kamshinsa ya karad'e mu. Ya risina yana gaishe da Hajja ta amsa tana cewa." Ban jima da tambayar Hauwa ba ta ce wa ai baka tashi ba." Yana dan gyara agogon hannunsa ya furta." Eh yau na dan so na makara ne wallahi, ina da baki a waje zan fita wurinsu yanzu za mu interview." Ta ce." To babu damuwa." Ya nufi hanyar fita bai dube ni ba. Abin ya sosa mini rai 'kwarai da gaske amma ban kawo komai ba illa iyaka azijanci irin na d'an adam, domin yadda ya sauko a gurguje wata'kila bakin masu muhimmanci ne. Ni kadai nake wannan hasashen a cikin raina. Ko minti biyar bai yi da fita ba Hauwa ta tashi ta haye sama ta bar mu a wajan ni da Hajja. 'Danjaridar ya ce. "Da farko Allah ya taimake ka muna so mu ji daga bakinka dangane da jita jitar da take yawo a gari mussaman a kafafan sadarwa, inda kowa yake tofa albarkacin da yake bakinsa dangane da mutuwar wani ma'aikacinka da iyalinsa suka fito suna kuka akan cewa ka yi amfani da lafiya da kuruciyarsa a lokacin da yake raye domin neman dukiya karshe ajalinsa ya sauka a karkashin aikinka, ba ka je ka yi wa iyaye da iyalinsa ta'aziya ba, sannan kuma babu ihsani a tsakani, mutane da dama suna zarginka akan son zuciya da ko'karin tara dukiya domin ka gina kanka." 'Dan jaridar ya nisa kafin ya cigaba da cewa." To ana cikin wannan turka-turka a gari da sauran kafafan sadawarsa sai ga wata majiya mai toshe ta yi sanarwa kan cewa Matarka ta yanzu wadda a can baya ta ta'ba auran wani Aminu Salihi wanda ya kowa ya shaida cewa ya wahalta maka k'warai da gaske dalilin lalurarsa yana da ala'ka da abinda ya shafeka, ya kwanta jiyya ba ka duba shi ba, ba kuma ka aika wakili ba, ya fadi ya mutu ba ka je ta'aziya ba sannan ba ka yi ihsani ga iyalinsa ba. Wannan dalilin ya sanya itama matarka ta yanzu ta fito take nemawa yaranta hakkinsu a wurinka, Allah Ya k'ara lafiya ko za a yi mana karin bayani dangane da zargin da jama'a da masu hakki suke yi maka. A tsanake ya yi sallama da mika godiya ga Allah da salatin annabi sannan ya fara da ce wa." Ni dai Alhaji Tajudden Ibrahimu 'Danbatta a iya sanina da hasashena babu wani wanda yake karkashina da hakkinshi yake a wuyana. Tabbas wannan ka'idata ne kuma tsarina ne ba na d'aukar tsaffi aiki, matasa majiya karfi nake d'auka. A cikin matasan ma muddin na fahimcin gazawar wani nakan sallameshi na maye gurbinsa da wanda na tabbatar da cewa za mu taimaki juna. Ma'aikatu nake dasu ba gwamnati ba ce ni. Babu yarjejiyar fansho da garatuti a form dina. Duk wani ma'aikici na ya san da wannan ya kuma amince da hakan. Ra'ayina ne yin alheri ga duk wanda na sallama saboda wani dalili, ra'ayina ne yin alheri da ihsani ga iyalan wanda ya rasu a karkashina, amma abinda nake so mutane su fahimta anan shine ba dole ba ne, ba kuma tilas ba ne in d'auki kudi na bawa wanda ya mutu ko wanda na sallama daga aiki kamar dai yadda na fad'a da farko ni ba gwamnati ba ne. Kuma maganar da mutane suke yi akan ba na zuwa ta'aziya ko dubiya wannan sharri ne aka yi mini. A duk lokacin da wani lamari ya faru muddin ina gari na kan yi kokari na je, idan kuwa wani uzuri ya rike ni na kan tura Alhaji Sammani da 'yan tawagarsa wad'anda duk suke a k'arkashin ikona kuma da alheri mai yawa. A lokacin da Aminu Salihi ya rasu ba na gari, kuma Allah ne shedata na tura a je a yi musu ta'aziyya tare da miliyar biyar domin a bawa magada, wannan shine abinda na yi. Ina so na gayawa duniya cewa' duk wannan maganganun da suke ta yawo akaina ba ni da hakki ila iyaka wanda na d'auki Amana na d'amka masa shi ya zambace ni. Babu wanda bai san yadda nake da Alhaji Sammani ba. Yau na fito na gayawa duniya cewa Sammani ne ya haddasa wannan lamari kuma ban fadi hakan domin na 'bata shi don na wanke kaina ba. A duniya kana iya zama da mutum da zuciya daya har ka dinga ya'kini a zuciyarka ba zai ci amanarka ba amma daga baya a samu matsala. Abinda ya faru kenan a tsakanina da Alhaji Sammani sai gashi lokaci kan'kani yana nema ya kai ni 'kasa, to saboda haka masu zargina da zagina ku bari domin ba ku da hujjar yin 'batanci a gare ni, sai ma dorawa kanku zunubi mai girma da kuke yi." [8/17, 9:56 AM] Aunty B: 63 Cikin sanin makamar aiki d'anjaridar ya ce." To Allah Ya taimake ka za mu su mu ji karin bayani daga bakinka dangane da maganar da fita jiya da daddare wanda ake ta jita-jitar cewa da yawun Uwargidanka maganar ta fita, masu bibiyar sha'anin za su so su ji wani karin haske daga bakinka" Dariya ya yi kafin ya ce." Babu yawun matata dangane da maganar jiya. Ni asalima ban san cewa tsohon mijinta ya yi aiki da ni ba sai da maganar nan ta fita, idan ma da yawunta a maganar ban ga aibu ba domin ta fito ne a matsayinta na uwa tana nemawa yaranta hakkinsu kamar dai yadda sauran mutane suke fitowa. Da ita da sauran iyayen marayun da suka yi magana na yi alkawarin bawa kowaccensu miliyan biyar biyar domin dogo da kai, kuma su kula da yaransu. Wannan na yi ne saboda Allah, sannan kuma har yau hanya a bud'e take ga duk wanda yake da k'orafi akaina zai iya tunkarata kaitsaye idan kuma hakan zai yi masa wahala zai iya isar da sakonsa ta kafafan sadawarsa domin korafinsa ya isa gare ni, a shirye nake da bawa matasa gudumuwa muddin sun bu'kaci hakan daga wurina." Wannan maganar tasa ta k'arshe ita ta karya karsashin d'anjaridar duk k'wakwarsa sai ya rasa abinda zai fad'a domin kuwa an riga an dabaibayeshi da halin girma da dattako. To abinda ya dinga tashe kenan a kafafan sadarwa. Wasu na fad'in hirar a rubuce ya yin da wasu ke d'ora bidiyon hirar a shafikansu ana ta zuba sharhi da cacar baki da bawa hammata iska idan aka samu b'angaranci daga mabiya dake comment section. An nufe shi da sharri sai kuma Allah Ya juyar da lamarin mabiyansa suka kara ninkuwa sakamakon hirar da aka yi dashi kuma yawancinsu duk matasa ne majiya karfi wanda suka rasa abin yi. Ni kaina na ji dad'i sosai dana saurari hirar mussaman wurin da ya wanke ni daga zargin da jama'a suke yi mini, duk k'wakwar d'anjaridar bai yarda ya soke ni ya soki iyayena ba, yana ta ko'karin kare mini mutunci amma hakan bai hana shi azabtar da ni ta karkashin kasa ba, gigin sabon aure ne ko tasirin asiri na kasa gane wanda yake dawainiya dashi sai sha mini kamshi yake yi abinda na lura dashi shine tun ranar da Hauwa ta kwana a dakinsa wasu daga cikin al'amuransa suka canza. Mussaman daga 'bangarena. Bai iya tsayawa ya 'bata lokaci mu yi magana ba. Yau kwana uku kenan tare suke kwana na riga na san hakan dole zai faru tunda kwanaki bakwai musulunci ya tanadar mata shiyasa kwatansu bai daga mini hankali ba Yadda dai ya canza a lokaci kan'kani shine abinda ya fi damuna tun washe garin ranar da suka kwana lamarin ya sauya salo. Zuciyata ta dinga yi mini sa'ke-sake akanta domin dai Ina ganin akwai hanyoyin da tabi wajan janye masa hankali ko asiri ko amfani da maganin mata. Sau daya dana hau samansa da zummar gaisuwa na fuskanci fuskar gizako ban 'kara marmarin sha'awa hawa ba, domin ba na so ko yaya ne ya yi mini abinda zai sanya ta samu kofar yi mini kallon banza. ina tsammanin Hajja ce ta yi masa maganar tafiyarmu saudiya domin ni ban samu kofa ba tunda ban ga fuska. Kwanan Hauwa biyar da tarewa ya kira ni a waya, lokacin ina bandaki ina wanka, na ji ringing har sau biyu kwata kwata ban tsammaci shi din ba, domin kafin shigata bandakin na kira Anti Yagana a waya ba ta daga ba, sai nake tunanin ko itace ta kira. Ina fitowa na dauki wayar ina dubawa wanda ya yi daidai da lokacin da ya sake kira na dan ji faduwar gaba kad'an dalili na san ba kasafai yake kar'bar uzuri idan ya kira waya ba a daga ba. Cikin nutsuwa nasa a kunne kafin na ce komai a hasale ya furta." Kina ina ne Ina ta kiran waya." Na tausa harshena na ce." Wanka nake yi." Tsaki ya ja wanda ya ta'ba mini zuciya sosai, tunda nake dashi bai ta'ba yi mini tsaki ba, sai yau don kawai ban daga waya ba, a ganina tsaki yana daya daga cikin nau'ika na wulakanta mutum, kuma wata'kila tana zaune a kusa dashi ya yi mini haka. Raina ya 'baci sosai zafin zuciyata ya motsa na dinga ji kamar na kashe wayar ma domin ban san wane kalar wulakanci zai yi mini a gaba ba. Ya ce." Hajja ta yi mini magana akan tafiyarku jibi na ce ni ba ki gaya mini ba, ban sani ba ko kina da wani mijin bayan ni kin gaya masa." 'Kafafuna ne suka dinga kyarma jin maganar da ta fito daga bakinsa sai na ji wani gumi ya yanke mini kamar ba daga wanka na fito ba. Gabana na bugawa cikin kaduwa da furucinsa na ce" Ban gane abinda ka ke nufi?" "Kin ji abinda na fad'a ai ba sai na maimaitamana ba, ba ni da wani mutuncin a wurinki, da ni da banza duk daya." Na ce." Ka ga Baba, har yanzu ban fahimci inda maganarka ta dosa ba, in banda neman fitina kai ka ba ni kujerar nan ba tare dana roka ba, haka zalika kuma ka fini sanin yaushe ne tafiya, to me zai sanya haka kawai saboda kana jin haushinsa ka nemi daga mini hankali. Me nayi maka?ka jima kana zargina saboda kawai ka aureni bazawara baka tauna magana motsi kad'an zan yi sai ka mayar da abin wata manufa, idan ka gaji da ni kana da dama a hannuna fa." "Ki zage ni kin ji ko, ai fitsara da rashin kunya ba sabon abu ba ne a wajanki Amina, kowa yana shura ya gagara ta fannin alheri amma ke duk wanda zai bude bud'e baki aibunki zai fad'a. Ina so ki sani wallahi tallahi ba zan juri wannan sakarcin ba, ba zai yiwu da mutuncina da k'imata a gari ki zubar mini da ita ba." Na danne kukan da yake so ya kufce mini na ce." wani abun kuma aka ce maka na aikata? wannan cin mutuncin ya isa haka Baba, ko namiji ka kama ni dashi iyakacin abinda za ka yi mini kenan, idan ba ka sona yanzu don Allah kada mu 'batawa juna lokaci mu rabu cikin mutunci ba sai ka kayi mini 'kaharu ba." Kashe wayar ya yi ba tare da ya sake ce mini komai ba. Na ajiye wayar a gefena tare da rufe fuskata da tafukan hannayena kuka mai karfin gaske ya k'wace mini. Cikin rashin kuzari na dubi wayata da na ajiye a gefe lambar anti Yagana ce. Sai zuciyata ta sake karyewa hawaye ya cigaba da zuba. Cikin kuka na daya jin yanayin muryata ya sanya jikinta yin sanyi a hankali ta ce." Menene kuma? Ina ce magana ta mutu tunda maigidanki da kansa ya fito ya wanke ki a idon jama'a, kukan kuma na menene?" Na ce." Anti Yagana kisan mummuk'e yake yi mini wallahi na rasa gane inda ya dosa, ai kin ga dai ya fito ya nunawa duniya girma da matsayina, amma wallahi duk wannan k'aunar da kulawar a yanzu babu ita, a tsukin nan cikakkiyar gaisuwa bata wanzuwa a tsakaninmu abinda ya fi daga mini hankali yawan zargina da yake yi, motsi kad'an zai canza mini manufa, kin ga zargi a cikin aure haramun ne." A sanyaye ta ce." Sai fa kin yi hakuri a wannan lukutan kin kawar da kai gefe guda, kin ki ji, kin ki gani, tunda yana da sabuwar amarya, ke ma kuma kishi yana damunki Amina, Ina ganin shine abinda ya hana ki zaman lafiya da mijinki." "Wallahi anti Yagana ba wannan ba ne, nasan ina jin babu dadi a raina amma ya zan yi, bayan Hauwa zai iya auro wasu mu zauna, wulakancin da ya tsiro dashi ne ba zan iya jura ba." "Amina ki yi hakuri na gaya miki, matsalarki ba ta kai wadda za ki tayar da hankalinki ba, mijinki yana sonki yayin da ya gama d'okin amarya komai zai sake shi, ke dai ki cigaba da kyautata masa kuma ki godewa Allah mahaifiyarsa tana k'aunarki to duk abinda za ki ga ni a wannan lokacin ki daure ba zai dawwama ba." Shiru kawai na yi Ina jinta, na san ba don komai take kafe ni a gidan ba, sai dan gudun lissafin aure, yadda na san halinta hakan ta san nawa, ina da hakuri amma kuma duk ranar dana furje babu mai iya tankwarani, kuma idan na bar abu na bar shi kenan har abada. Ta ce. " Kina jina ko Amina." Na ce." Ina jinki Anti Yagana. Sai ta cigaba da cewa." Akwai bikin da za a yi na yar gidan Babanmu Auwalu 'dan autan su Dada zai aurar da yaranshi uku maza biyu mace daya, shine Dada ta ce a sanar miki sabon watan da zamu shiga in sha Allahu." Na ce." Zan gayawa maigidan, in sha Allah na san dai ba zai hana ba, dama kiran da na yi miki d'azu zan gaya miki za mu je umara ni da Hajja jibi in sha Allahu zamu tafi." Ta ce." To kin ga kin samu dama sai ki tsananta da addu'a akan komai, dama kuma ita rayuwar duniya haka ta gada yau dad'i gobe kuka, ki godewa Allah kaddararki mai kyau ce." Na ce." In sha Allah Anti Yagana a gaishe mini dasu Fadila da kyau. Tunda na yi waya da Anti Yagana na ji sasaauci a cikin raina, na kuma yi kokarin danne abin a cikin zuciyata, domin na tabbatar da cewa Hajja ta fahimci damuwata ran kowa sai ya 'baci har shi maigidan. Satinmu uku a saudiya ni da Hajja muka dawo. Tun ina can hankalina yake kan Yusi domin kuwa zuciyata gabad'aya bata aminta da matar gidan ba. Duk yadda nake zaton ganinsa a firgice sai kuma na ga akasin haka lafiya lau na same shi har da 'yar ki'ba ya kara. Nan na fahimci azancinta kishi da kisan mummuke akaina ne, amma bata ta'ba nunawa akan yaron ba, a wasu lukutan ma idan ya zo ya same mu a falo har jansa da wasa take yi shi ma da yake d'an gari ne anti ya kira kiranta. Ranar da muka dawo na fahimci ya zama d'an dakinta sosai domin magana daya zai ce mini anti ta yi mini kaza ko ta ba ni abu kaza. Ban tambaye shi maigidan ba, domin jiya da daddare kafin mu taso mun yi magana ta chart ya ce mini zamu dawo mu iske baya gida zai shiga Kano kuma zai kwana biyu. Ban nuna damuwata ba domin ban sanya a raina cewa lallai sai ya yi murna da dawowata ba, abinda nake bashi kafin tafiyata yana da wadda take bashi a yau na kuwa tabbatar da cewa baya cikin bu'katuwa. Dama tun kafin tafiyata na cirewa zuciyata da gangar jikina sha'awarsa shiyasa idan za mu had'u ban cika kallonshi ba, wanda a lokacin da muke shiri kallansa kadai kan iya jefa ni a wani yanayi balle hancina ya ji kamshin turaransa da wannan ma yana jan ra'ayina sosai. Raina na cire a kansa ba wai don ba na jin sha'awar ba, tana motsa mini sa'i da lokaci na kan danne ne kawai tunda na kudire wani abu a raina. Kwanansa biyu kamar yadda ya fad'a ya dawo. Kadaran kadahan muka gaisa da juna kamar wasu abokanan gaba, amma na ji dadi da Hajja bata fahimci akwai wani abu a tsakanina dashi ba. Yadda bai nemi ba haka ni ma ban neme shi ba duk da nasan dole ne girki ya dawo hannuna ranar kuma ni zan kwana dashi Kwana biyuna suka tafi a banza Hauwa ta kar'bi nata . Tsayin sati Hajja ta kara a gidan na mu kafin ta fara haramar tafiya gida, ban so tafiyarta ba amma ta kafe a cewarta dama ba ta yi mini alkawarin zama dindindin ba. To har dai Hajja ta tattara kayanta ta koma kano gidanta na Danbatta ba fahimci komai ba dalili a tsukin kwanakin ba kasafai yake zama a gida ba da daddare kuma kafin ya shigo ya shige d'aki ta kwanta. Yau saura kwana shiga bikin da anti Yagana ta gaya mini, kuma har ga Allah Ina son zuwa ko babu komai zan shiga cikin 'yan uwa na yi walwala ko zuciyata za ta yi sanyi. Ba magana muke yi ba don na lura 'kebe kaina da na yi ya sosa masa zuciya sosai, ya kuma ji ciwon rashin zuwana dakinsa shiru kawai ya yi mini. Na dinga tunanin hanyar da zan bi domin na gaya masa. Rashin lafiya 'karya na 'kirkira, na kwanta yini guda ban fito ba. Yusi ya dawo daga islamiyya ya gan ni a kwance ya fara tambayata sai na ce masa kaina ne yake ciwo. Jikinsa sai ya yi sanyi ya zauna gefena yana yi mini sannu yana ta tattaba wuyana wai na tashi nasha magani, don ya kyaleni na ce masa nasha d'azu da rana . Ya'ki ya matsa ko'ina ko massalaci bai je ba, tare muka yi magariba da Isha'i a d'aki. Misalin takwas da rabi aka murda kofar d'akin aka shigo. Hauwa ce cikin kwaliyya har yanzu dai tana cancarewarta irin na amare. Mamaki sosai ya kama ni, na tashi zaune Ina kallonta. Yusi kuwa fuskarsa ta fadada da fara'a tun kafin ta k'araso yake fad'in." Anti." Ta saki fuskarta tana amsawa ta d'an dafa kafad'arsa tana kallona da murmushi a fuskarta take cewa." Amina barka da dare." " Barka dai na furta a takaice domin ni ba yarinya ba ce balle ta ce zata nuna bariki kar nake kallonta, kuma ba wai ta samu dama ba ne, kawai na kyaleta ne saboda ni ma ina ji da tawa da mijinta ina so ya shiga gonata ne kawai. Ta ce." Yau tun safe ba ki fito ba, ban kuma ji motsin Yusi ba dukda yau asabar nasan yana tahfiz amma idan ya je sama wajan babansa ya kan leko wurina mu gaisa har musha hirar Kamalu." Na dubeta a tsanake na ce." Ba na jin dadi wallahi tun bayan dawowarmu zazzabi yake damuna." Da d'an alhini a tattare da ita ta ce." Amma Kuma sai ki yi shiru, ai da kin gaya mini sai na baki magani." A sakarce na kalleta ina jin kamar na bugeta da mari, saboda ba ni da lafiya sai na gaya mata tunda ita nake aure. [8/18, 10:38 AM] Aunty B: 64 Ta juya da karsashinta tana fad'in." Bari na gayawa maigidan b... Bata kàrasa ba na katse ta hanyar fad'in." Saki na yi?'' Sai ta juyo tana kallona. Na dubi tsabar idonta na ce." Ban sanya ki ba, don haka cire kanki daga wannan sabgar ki kalleni da kyau ba sakarai ba ce, balle ki ce za ki yi mini ta 'yan duniya kallonki kawai nake yi Hauwa." Murmushi ta yi sai kuma ta d'an ta'be bakinta ta ce. " Menene abin fusata ranki ya dad'e, ni menene nawa a ciki, ba ni na kar zomon ba, zaman tare ne fa ya sanya na shigo dakinki, hakki ne na musulunci, ni kuma ba zan yi gaba dake ba domin ba dabi'ata ba ce hakan, amma ki yi hakuri idan abinda na yi miki ya 'bata miki rai." Ban tanka mata ba har ta gama maganarta ta fita na ja tsaki mai karfi tare da kawar da kaina gefe. Yusi da kansa yake sunkuye tunda muka soma maganar ya dago cikin yanayi na sanyi jiki da rashin jin dadin abinda ya faru ya ce." Mama to kin ce kada ta baki magani, kuma kin ce kada ta gayawa Baba yanzu ya za a yi to." Shiru na yi ban ce masa komai ba domin har yanzu raina a b'ace yake dangane da rainin hankalin da Hauwa take ko'karin yi mini. Wato ta fahimci zaman doya da manjar da muke yi shine da 'kumaji da gwarin guiwarta take taka 'kasa da ko'karin mayar da ni wawiya. Yusi ya dame ni da magana na buga masa tsawa raina a b'ace na ce." Idan ba ka yi mini shiru ba wallahi sai ranka ya 'baci yanzu nan, idan na mutu ai lokacina ne ya cika, ba wanda zai jira duniyar kowa sai ya mutu. Sai ya fashe da kuka tare da sanya kansa a tsakiyar gwiwarsa. Na janye idona daga gare shi na cigaba da tunanin hanyar da zan bi wajan ganin na dafa mutumin nan cikin ruwan sanyi domin zuciyata na ga alama ba zata iya juriyar nan da anti Yagana take ta nanata mini ba, a yanzu da ni bana tsoro ko fargar a lissafa mini auran ai ba ni kadai ba ce. Wajan tara da kwata na dare ya shigo dakin. Hankalinsa yana kan Yusi dake can kan dadduma a kwance ya ci kuka ya koshi, na yi na yi dashi ya fita ya ci abinci ya'ki, biscuits din da nake ajiyewa a d'akin ya ci da lemo kawai ya ha'kura, ni kuwa dama damuwar da nake ciki bata barni sha'awar komai ba. Kallo d'aya na yi masa na janye idona daga kansa Ina dan hade jikina sakamakon jin yanayina na nema ya sauya. Ni na san wannan rikicin da nake ji baya rasa nasa da buk'ata irin ta gangar jiki. Tun kafin auransa da Hauwa sha'awa take damuna tun ranar da na banki magunguñ nan, ranar d'aurin auransa kenan, har muke je saudiya muka dawo abin na damuna kawai ina dannewa ne, abinda jiki ya riga ya saba dole idan ya buk'ata bai samu ba ya shiga wani yanayi. Ba zan ta'ba nemansa ba abinda na kudire kenan a raina. Ya je ya daga shi a rikice yana fad'in." Kai aboki menene haka? ba ka da lafiya ne?" Yana maganar yana tattaba wuyana. Yaron ya share hawayen dake zubo masa. Ai sai ya kara rikicewa ya dago shi sosai yana kallona ya furta." Bashi da lafiya ne?" Share shi na yi ban bashi amsa ba. Da gaya haka sai ya sake mayar da hankalinsa kan yaron yana tambayarsa. Da 'kyar muryarsa can kasa ya ce." Mama ce bata da lafiya shine take cewa mutuwa za ta yi?" Ya dago da sauri yana kallona, ban dube shi ba ina dai kallon duk wani motsinsa ta gefan Idona. Sai ya tashi yaron tsaye ya riko hannunsa suka nufo wajena, sai a lokacin na dubesu ina daga kwance ban motsa ba ya zauna kusa da ni shi kuma Yusi ya tsaya saitin kaina tare da dora hannunsa a saman goshina. "Me yake damunki?" Yafada da 'yar kulawa. A takaice na ce." Me ka ga ni?" Ya zuba mini ido da yanayi na jin haushin amsar dana bashi. Ya girgiza kansa kafin ya dubi Yusi ya ce." Ka je wurin Antinka tana da abu mai dadi ka ce in ji ni ta baka." Ya amsa da "To." Ya kama hanya ya fita. Ya juyo gare ni sosai yana cewa." Ki gaya mini abinda yake damunki domin ba ni so Allah Ya kama ni da hakkinki, ni dai nawa hakkin da ki ka take kullum ina gayawa Allah ya bi mini." Jin abinda ya ce sai na tashi zaune sosai na dube tare da cewa." Hakki kuma na nawa ka take mini, ba ni da buk'atar kasan abinda nake ciki a halin yanzu domin abinda ya shafe ni." Ya gyada kansa da fad'in." Okey to bari ba kira Antinki don na lura ita kadai zata gaya miki ki ji, yadda kike tsoranta ba kya tsoron mahaifin.....Kafin ya k'arasa na buga katifar gadon da k'arfin gaske na bude muryarta sosai na ce." Kada ka kuskura wallahi, na gaya maka duk abinda za mu yi ni da kai sunan mahaifina ya daina fitowa daga bakinka, idan babba ya zubar da girmansa sai karami ya hau ya taka, ba fa zan lamunta ba wallahi, ban raina naka iyaye ba ban ga dalilin da zai sanya ka raina nawa ba." A tsanake ya ce." Rashin kunya ba inda zata kai ki, burunki na sake ki kije ki cigaba da harkokin tallata sura a social media ni kuma ban zan sake ki ba wallahi, domin duk inda aka je aka dawo za a ce Tajo ya ta'ba auranta, kin ga kenan yadda ki ka 'bata sunanki ni ma kin 'bata mini nawa." Rashin abin fad'a ya sanya na ja masa wani irin tsaki mai tsayi. Na koma na kwanta yayin da wani malolon abu ya dabaibaye mini wuya. Ya biyo ni gadon ban ankara ba ya sanya yatsunsa akan le'bena ya murde da k'arfin gaske yana fad'in. " Wallahi hukuntaki zan yi kuma na kwana lafiya, mace tana girma amma tana cin kasa. Kuka ne ya kufce mini da k'arfi kamar zararriya na tunkud'eshi kawai sai na rufe shi da duka da hannayena duka biyun kuka nake yi haik'an takaicinsa ne zai halaka ni. Ya daddaneni ina haurinsa da kafafuna. Ya tashi da sauri ya je ya rufe kofar d'akin ya dawo. Hasken ya kashe d'akin ya yi duhu. Ganin haka sai na dawo hayyacina na tafi tunanin abinda zai yi. A dan hasashen da na yi na hangi yana cire rigarsa. Da sauri na dira daga gadon na je na kunna haske d'akin na ganshi gabad'aya ya cire kayan jikinsa haihuwar uwarsa. Gabana na fad'uwa na ce. " Ka zo ka fice mini daga d'akina. Ya nufo ni jale jale yana fad'in." Ni da gidana da d'akina da kuma matata a ce na fita lallai ma." Na juya zan bud'e kofa na ga babu mukulli. Lokacin ya isko inda nake na yi saurin dauke kaina saboda kallon yanayin da yake ciki. Lallai namiji bashi da kunya zir haihuwar uwarshi fa. Kirjinsa ya had'a da nawa ya manne a jikin bango. Ya zira hannu da k'arfi ya rike 'kunguna. Ha'bata ta sauka a kafad'arsa na ji yana cewa." Ki kore ni mana idan kin isa, gidana ne fa." Cikin kuka na ce." To me za ka yi mini. Bai tanka mini ba illa sansanar jikina da yake yi kamar karen da ya jima yana farautar nama. Zubewa muka yi a bakin kofar dalili ni kaina duk dauriyar da nake yi abun da yake yi mini ya fara sa'bata. Faduwarmu rigijif ya yi daidai da lokacin da Yusi ya zo yana buga kofar. Gabana na fad'uwa na ture shi na tashi da sauri na bar shi a wajan. Ya ta so ya nufo ni a ki'dime Yusi na cigaba da buga kofar d'akin. Na dube shi na ga duk ya wani rikice kuma ba shi da alamar bud'ewa sai ma ya rikito kan gadon yana janyo ni, na matsa da saurin gaske ba wai bukatarsa ne ba na yi ba, halin takaicin da nake ciki ne ya sanya nake ganin k'yashin bashi kaina. Jin shiru an daina buga kofar ya tabbatar mini da cewa yaron ya matsa daga wajan. Kokawa katitir muka dinga yi ni da shi, tun Ina ji da kuzari da karsashin yin kokawar har gab'obina suka sage saboda ya fi ni k'arfi kuma matsa yake yi mini ta rashin imani a haka duk ya ta'be mini kirji suka dinga zafi, sosai na galabaita na zauna kusurawar gado ina kuka shi kuma kamar tsohon maye ya haka ya zame mini, duk abin nan babu suttura ajikinsa sosai hakan ya dinga ba ni mamaki wato shi kunya gaba ya bata ba baya ba. Na juyar da kaina gefe don har na gaji da kallonsa a haka ya janyo k'afata cikin sigar so lallai sai mun cigaba da yi yana fad'in." Ta ji tsoro a bata ruwan mad'aci." Na yi shiru ban tanka masa ba, gwiwar hannuna ce kawai take ciwo kuma shine ya kwalmad'e mini ita. Ya tale mini k'afafuna ya tusa kansa a tsakiyata. Tsigar jikina ta yi tsananin tashi. Na sanya hannu da k'arfi na cire kansa yana sake mayarwa ina cirewa tare da ran'kwashinsa da gwiwar yatsuna. Cigaba ya yi da tura kanshi tsakiyar cinyoyina yana sa hannu Yana janyo kafata. Hankalina ya tashi ya riga ya san ta hanyar nan ne kadai zai iya cin galaba akaina. Idan ma na yi yun'kuri domin fita daga tsakiyarsa kamar taimaka masa na ke yi, dole na ha'kura na kyaleshi a lokacin ma jikina gabad'aya ya gama rikicewa tsantsar fitinata ta tashi, na lumshe idona numfashina na fita a hankali a hankali. Ina jin ya lura da hakan yana tunkuda kirjina na yi flat a gadon ya bini ya danne shikkenan kuma ban sake tuna komai ba. Abinda dai yatsa mini a k'wa'kwalwata sambatunsa na yau ya fi na koyaushe kuka kuwa sai kace sabon 'dan yaye yana yi, yana kuka kamar wanda aka aikowa da mutuwar iyayensa abin na yau ya shaddade kwarai da aniya ni kaina sai da na koka ganin yana nema ya kwana a kaina, da kyar ya ha'kura, gefen asubahi ya ce sai ya kuma yi. Na rushe da kuka dashi domin duk kwadayina akan abin ji na yi ba zan iya jura ba, saboda jiya nan ya gurje ni kamar sabuwar amarya, kawai dama ya tanadi wannan ranar nan ne don ya fanshe kwanakin da ya yi bai kwanta da ni ba. Kukana bai hana shi yi ba duk da bai samu hadin kai dari bisa dari ba, ya yi nishadinsa sosai, ni kam ya riga ya goge mini hadda jiya nan shiyasa ban fitar da komai ba. Ana kiran asubahi ya rabu da ni. Sai da ya yi wanka tukkuna ya fita daga d'akin. Mamaki mai yawa ya dabaibayeni. Shin auran da ya yi ne ya kara masa fitina, ko kuma kawai dama ya shirya yi mini haka. Yanayinsa gabad'aya ya canza har karfi da kuzari ba kamar farkon auranmu. [8/21, 8:21 PM] Aunty B: 65 Bai dawo mini d'aki ba tun bayan da ya fita da asubahi. Na san dama da wahala ya dawo din dalilin da ya sanya ni kenan na hau saman wanda na fi wata rabona da hawa. A bakin baranda na ji maganganunsu ita da shi kamar dai kowanne a fusace! Ganin hakan ya sanya na juya zan sauka daidai lokacin ta bude d'akin ta fito tana goge fuskarta. Kallon juna muka yi, ba ta ce mini komai ba, ta bude dakinta ta shiga wanda yake kusa da nasa. Cikin zuciyata na ce in dai namiji ba ki fara kuka ba Hajiya balle wannan mijin naki da rikicin tsufa ya fara ta'ba shi. Ganin ta fito daga d'akin ya sanya na shiga. Yana zaune saman sofa da Laptop a gabansa. Ya dago ya kalleni ba tare da ya ce komai ba ya mayar da kansa yana cigaba da abinda yake yi Hakan da ya yi ya sanya na kama kaina. Na zauna ina fuskantarsa babu sukuni na ce." Ina kwana." Ya amsa amma bai dago ba." Na d'an zuba masa ido Ina nazarinsa wato kamar ba shi ne mutumin nan na jiya da daddare ba, sai wani hade rai yake yi. Na gyada ina dan jin zafi abinda yake yi mini a cikin raina. Gabad'aya yanzu ya gama sare mini, kuma dama tun farkon auranmu ban manta ba ya ta'ba gaya mini Allah ya ba ni ha'kurin zama da halinsa. Ashe ya san yana da wahalar sha'ani. Wata'kila dama yana jira mahaifiyarsa ta tafi sai abin ya k'ara tsamari tunda tun tana nan yake d'an yi, yanzu kuwa babu wadda zata gaya masa ya ji. Itama Hauwan wanene ya san abinda ya guma mata. Na daure zuciyata na ce." Dama zan gaya maka ne jiya anti Yagana take gaya mini ana biki a can garinsu mamanmu maiduguri shine aka ce a gaya mini, to ina so zan shirya gobe ko jini sai na wuce." Ya yi shiru bai ce mini komai ba, kamar ma bai ji abinda na gaya masa ba. A da kufule na ce." Ka ji." Bai dube ni ba ya furta." Ban bari ba." Sai na ji wani 'kullutun abu ya tokare mini a wuya, duk irin suburbudar da ya yi mini jiya da abinda zai saka mini kenan, ai tsayin shekara da wani abu ban ta'ba tambayarsa zuwa wani wuri ba, ban yi tsammanin zai hana ni ba. Zuciyata na yi mini zafi na ce." Dada ce fa ta ce a sanar mini, 'yan uwa duk za a had'u kowa zai je, to ni me yasa zaka hana ni, tun fa da na zo garin nan shekara har da doriya ban je wani wajan ba." "Ni dai na ce ban bari ba." Ya fad'a hankalinsa a kwance. Kawai sai na ji hawaye sun fara gudana a kumatuna. Ina jin dai d'an tahalikin nan ciwo yake so ya haddasa mini. Ya dago kai yana kallona lokacin da kukana ya yi karfi. Sai ya mayar da kansa ya rufe laptop ya rufe ya dan gyara zamansa yana dubana amma bai ce komai ba. Naja hanci a shake na ce." Wannan zalincin ya yi yawa, kwata-kwata ka hana zuciyata nutsuwa kullum sai ka gumama mini b'akinciki, ban san me na yi maka a rayuwa ba." Ya ce." Me na yi na zalinci, ba yunwa ba ishirwa haka zalika ba tauye hakki a shimfida, don kawai na hana zuwa unguwa shine zalinci." Na ce." Zalinci ne mana, kana fita ka yi walwala ka hadu da 'yan uwanka ku gaisa, ni ma na gaya maka Ina so na ga dangina domin Ina kewarsu ina so kuma zuciyata ta samu sasaauci." "Ko da ke, ko babu ke, za su yi bikinsu, ba ni so iyalina su yi nisa da dai kusa ne sai na barki amma gaskiya maiduguri ya yi nisa, kuma kin ga sai kin yi kwanaki kafin ki ce zaki dawo." Jin ya fadi haka ya sanya na ce." Ai kai zaka fad'i kwanakin da zan yi." Ya yi shiru yana lumshe ido kamar me shirin bacci. Na dawo kusa dashi na zauna na ri'ke hannunsa a hankali na ce." Ka ji my love." Ya bude idonsa da suka dan canza yana kallona ya ce ." Yaushe rabon da na ji wannan sunan abakinki, yanzu ai kina bukatar zuwa biki ko?" Shiru na yi ban ce komai ba. Ya girgiza kansa tare da sake rufe idonsa. Jikinsa na sake matsawa sosai a hankali na ce." Ka ji sweet love." Bai tare da ya bud'e idonsa ba ya ce." Matsa kada ki sanya na yi abinda ban yi niyya ba." Ban matsa ba, sai ma hannuna dana sa Ina d'an jan gemunsa a hankali. Ya bude Ido muka tsirawa juna ido. Hauwa ta turo kofar d'akin ta shigo hannunta ri'ke da wani kwando cike da kayan abinci. Janye idonta ta yi ta wuce can wajan da yake zama domin cin abinci ta fara shirya wurin. A hankali na dan matsa daga kusa dashi ina fad'in." Ka amince ko?"' "Zan yi shawara tukkun zuwa yamma zan gaya miki abinda na yanke." Don kada ya tsinka ni a gabanta ya sa na tashi daga kusa dashi ba tare da na ce komai ba na kama hanya fita. Na ji ta ce." Amina tsaya kawai a yi ta ta kare, ba zan bari a ginu a haka ba domin dukkaninmu musulmai ne, ba maguzawa ba, idan shi mijinki yana jin tsoronki, ni gaskiya ba a haifi wata mace da zan ji tsoro ba, kuma ba zan yarda na yi zaman boranci ba, ba kuma zan yarda a tauye mini hakki ba." Na ce." Akan me kike wannan zantukan." Da mamaki da takaici ta ce.'' Au tambayata ki ke yi akan me nake yin magana." Na ce." 'Kwarai kuwa." Yana zaune yana jin mu bai ce komai ba. Ta ce." Jiya girkin waye?" Na ce." Oho!" Ta zo iya wuya kawai sai ji na yi ta lallayo ashar ta jefo mini tana huci." Ni za ki mayar sakarai, kina abu kamar mai tabin kwakwalwa, na rantse miki da Allah ba za mu wanye lafiya dake ba, tunda ni ban shiga huriminki ba, ba zai yiwu ranar girkina ki dinga yi mini kutse ba." Na dube shi shima yana cike da mamakin zagin da ta yi don sai hararta yake. Na ce." Ka ji tana zagina ko?" Ya ce." Je ki kawai, ki kyale ni da ita." Ta kara fusata tana cewa." A dake ni a hana ni kuka, kuma a ce ba zan yi magana ba, sai ta fashe da kuka mai karfi Ya ce." Idan zagi ne ni zaki ga domin ni na kwana da Amina a ranar girkinki, amma ita bata da lefi, Hauwa wannan ya zama na farko ya kuma zama na karshe kada ki kuskura na kara jin zagi a gidana, kin nuna mini rashin tarbiya da kuma rashin aiki da ilimi. Ni ba namijin da mace take d'agawa hankali ba ne, ni na yi miki ba daidai ba, a wurina zaki nemi hakkinki, ita Amina ai bata da lefi. Ta sake fusata tana cewa." Haka zaka ce ko? Ni me yasa ba ka nemana a ranar girkinta duk da bata zuwa dakinka ai baka taba zuwar mini da bukata ba." Ya ce." Ai shiyasa na ce miki a wajena za ki nemi hakkinki, domin itama dole na yi mata." Ina tsaye ina jinsu duk abinda ta fad'a a kaina sai ya tare maganar yaki bari sunana ya fito. Cikin raina na ce idan don na ji dad'i ne ban ji ba, domin kuwa wataran ni ma zai iya kware mini baya a gabanta, na bude d'akin ba fita na barsu suna ta turzawa, amma na yi mamakin sosai, domin ni a tunanina tunda ba na zuwa dakinsa ranar girkina ita da shi suna kwanciyar aure, ashe zargin hakan kawai nake, ashe shine dalilin da ya sanya jiya ya famshe kwanakinsa. Yini na yi cikin zullumi da tunanin zai barni ko ba zai barni ba. Har na yi shirin kwanciya sai gashi ya shigo shi ma da shirin kwanciyar na zuba masa ido har ya k'araso ya zauna a gefana, yadda nake kallonsa shima haka yake kallona. Na daure na ce." Da ka sani ka ce na fito falo sai mu yi magana, kada ta zargi wani abu." Ya ce." Ina jin tsoronta kenan?" Girgiza kaina na yi a hankali na ce." Ba haka nake nufi ba, kai zaka nemi zaman lafiya a gidanka." "Kada ku zauna lafiya don Allah kin ji ko." Jan bakina na yi na shiru na rabu dashi abinda dai na kudire a raina shine idan za ta ce zata yi mini hayaniya ko ta zage ni kaniyarta zan ci, tunda ga wanda ya yi mata nan Ya dube ni a tsanake kafin ya ce." Na kira Anti Yagana a waya kan maganarmu dake ta d'azu." Yanayin yadda ya yi maganar ya sanya ni jin sanyi a cikin raina, har ga Allah ina jin dadin yadda yake mutunta anti Yagana har ya sakaya sunanta. Na nutsu Ina kallonsa. Ya cigaba da cewa." Na amince za ki je amma da sharad'in kwana uku kacal za ku tafi a jirgi ke da Yusi da Sukairaju nasa a yi muku shirin hakan, kada ki sa'ba umarnina." Da sauri na ce." In sha Allahu na gode sosai Allah Ya kara girma." Ya amsa da "Amin." Kafin ya cigaba da cewa." Ni ma yana da kyau na bada gudumawa ko." Murmushi na yi ban ce komai ba. Ya ce." Nawa ki ke ganin zan basu." Na dube shi sai na dan ji tausayinsa, shi dai abin sa bai rufe masa ido ba. Na ce." Ko nawa ka basu sun gode." Ya ce." Ai shawara na tambayeki sai ki ce mini ka basu abu kaza." Na ce." Wallahi ban san abinda zan ce maka ba. Shiru ya yi yana lalube a wayarsa. Shigowar sa'ko na ji a wayata dake gefana na d'auka ina dubawa miliyan goma ne. Na dube shi cikin mamaki mai tsanani. A nutse ya ce." Ki cire miliyan biyar ki basu gudumawace ni dake. Miliyan biyar din kuma kudin yaranki ne wanda na yi muku alkawarin satikan da suka wuce ba ke kadai na bawa kuna da yawa. Na ce." To ai ni ban ce ina neman hakki ba." "Idan ba ki ce ba yaran fa?" Ya fad'a yana kallona. Na ce." Ni dai gaskiya dawo maka dasu zan yi wallahi. Ya mike yana fad'in." Ki dawo dasu ki ga 'bacin rai, ki ajiyewa yaran zasu amfana anan gaba in sha Allahu, kuma koda jita jita zata sake tashi a gari ba zasu zarge ni ba." Kawai sai na bi shi da Ido bakina ya yi nauyin da na kasa ce masa komai ya bud'e kofar d'akin ya fita. Gari yana wayewa na kira Anti Yagana a waya muka gaisa sosai na ce." Ashe kun yi waya da maigidan." Ta ce." Jiya ba ya kira ne domin karin bayani akan maganarku ai ya ce zaku taho gobe ma." Na ce." E in sha Allahu anti Yagana amma don Allah don Annabi duk abinda na zo muku dashi kuyi mini kyakykyawar fahimta." A sanyaye ta ce." Me Kuma ya faru?" Na ce." Sai na zo din kawai zan miki bayani." Ta ce." Ni wallahi kin kashe mini garkuwar jiki Amina, ba fa na san fitina yadda mijin nan naki yake sonki me zai miki." "Humm! Anti Yagana kenan akwai matsaltsalu sosai, ke ba za ki gane ba ne wani irin mutum ne." Ta bata rai tana cewa." Kamar yaya wani irin mutum duk mazan fa haka suke Amina daga manya har yara, kin san Allah akan mutumin nan zamu 'bata." A sanyaye na ce." Anti Yagana me ya yi zafi haka ni ce fa taki, Ina ganin yana da kyau ki dubi uzurina." "Ki gaya mini kawai yanzu ina jinki ba na so ki barni da damuwa a raina. Ajiyar zuciya na sauke na ce." Anti Yagana kin san babban abinda yake lalata aure shine zargi ko?" Ta ce." Kwarai kuwa." Na cigaba da cewa." To shi wannan mutumin halayarsa ce, domin kuwa bashi da ta'ada mai kyau, ba na so tafiyarmu a haka ta ginu har tayi kwari, kin ga ina da kishiya ita kuma budurwa ya aureta. Ni kuma daga zarar mun samu sa'ba ni ya dinga ya'ba mini magana kenan, na auri maza biyu na yi harkar social media, ba ni da kunya ba ni da tarbiya, ina tallata surata a duniya zan 'bata masa suna maganganu da makamantan wad'annan, shine nake so manya su shiga lamarin nan dan gaskiya akan wannan wallahi a shirye nake da na rabu dashi." A dan sanyaye ta ce." To me yasa ba ki gayawa Babanmu ba." "Anti Yagana mutumin nan baya ganin girman Babanmu kin san ba wani girmansa ya yi da yawa ba yana ganinsa haka, shi ma kuma Baban namu ba zai iya tararsa da maganar ba, balle kuma Baba Sule." Ta ce." To nan din idan ki ka zo wa za ki gayawa?" Na ce." Anti Yagana ko ke ba za ki iya yi masa magana ba." Ta ce." Na ce masa me? Amina ni kwarjini yake yi mini wallahi." Na girgiza kaina tare da cewa." Shikkenan anti Yagana sai na zo din sai mu sake tattauna maganar. Jikinta a sanyaye ta ce." To shikkenan Allah Ya kawo ku lafiya. [8/23, 11:00 AM] Aunty B: 66 Baban Saude shine na biyu a gidansu Mamanmu mutum ne mai zafi da rashin san wargi, a iya tunanina shi kad'ai zan iya gayawa matsalata ya yi mata duban tsanaki, kuma ya tsage gaskiya duk d'acinta. Yadda na fahimta kwata-kwata ba zan samu goyon bayan anti Yagana ba domin gabad'aya mutumin nan ya gama dabaibayeta da alherinsa. Ba ita kadai ba ma kusan da wahala na samu goyon bayan duk wanda zan gayawa korafina akansa shiyasa sam ban tunkari Babanmu ba saboda na san zai tankwarani ne kawai ya ce na yi hakuri ko da kuwa ya duba maganartawa da k'amshin gaskiya. Anti Yagana tafi sha'kuwa da dangin Mamanmu tunda ita a can ta girma har ta yi aure, ni kuwa ban shaku dasu sosai ba domin har yanzu wasu daga ciki ma ban gama saninsu ba tunda gaskiya suna da family mai girma, shi kansa Baban Saude sai a shekarun baya na waye dashi domin matafiyi ne duk zuwan da nake yi ba na ganinsa sai an yi katari ya zo gida tukkuna, bashi da wasa ko kad'an kuma mutum ne mai dattako da sanin ya kamata, sannan kuma da yana gaskiya dan ko hukunci za a yanke a family din akan ce a bari ya dawo. Kudirin dana yanke kenan a cikin raina idan na je na huta zan ke'be dashi na gaya masa sai na ji abinda zai ce akan hakan don gaskiya duk mutumin da yake da hankali ya kuma san menene aure da zamantakewa ba zai dinga zargin matarsa ba Koda kuwa a gidan karuwai ya aurota. Wannan maganar ita na sake jadaddawa anti Yagana bayan saukata a garin a kuma gidanta. Sai ta fusata ainun tana fad'in muddin za ta fad'a mini na ji to na janye tashin maganar nan a family domin abin zai zama abin gotsiri tsoma kowane aure akwai jarabawa a ciki, a cewarta muddin na ce zan dinga bankada sirrina kowa ya sani to a shirye wasu suke da su lalata mini aure, kuma don Baban Saude ya kashe mini aure ba abinda zai dame shi ba ne, tunda saboda tsaurinsa yaransa uku suna nan a zaune a gida suna zawarci saboda irin tijarar da yake yi wa mazajensu yau da gobe sun gaji sun koro su. Na so na fahimtar da anti Yagana bafa nufina a kashe auran ba, a dai yi masa magana ya gyara kawai, ba zai yiwu ace don yana da iko ya zamana kowa yana shakkarsa ba, duk abinda ya aikata daidai ne ko da kuwa kuskurene. Na san ta san gaskiya kawai tana takewa ne dalilin dabi'unsa na bayyane kafewarta akan hakan ta sake tsamari da na gaya mata adadin kudin da ya bada gudumuwa sai ta kara jajurcewa kan cewa ba da yawunta a tozartashi ba. Ni kuma na san baban Saude ba zai yi masa magana domin ya bata mini aure ba sai dan gyara ko da take fad'in yaransa suna zawarci ban yarda saboda halinsa aka yi masa haka ba face kaddara domin kuwa yana kishin nasa ne bai yarda a wulakantasu ba. Mazan na yanzu sun riga sun zama abinda suka zama don ita Allah ya taimaketa tana zaune da nata lafiya lau ba zai yiwu a ce kowa haka yake ba. Duk da na ha'kura na bi umarninta ba ta daina jin haushina ba motsi kad'an sai ta ja tsaki tana fad'in." Allah Ya rufa miki asiri kina so ki butulce masa ko Amina, ni ganau ce ba jiyau ba, mutumin kamar ya tsuguna miki saboda kulawa amma lallai sai kin kago masa lefi, to ya ni ma ba zan ce kin fi sha'awar rayuwar tallata surar jiki ba, idan wasu ne suke rudarki wallahi za su kai ki su baro." Na gaji dai na rushe da kuka domin tuntuni shi yake damuna, ta hana ni na yi magana kuma na hanu amma tana gasa mini bakaken maganganu. Na tashi na shige d'aki na kwanta ina kukan yadda zan yi. haka aka yi shagalin bikin da ni cikin kunci domin duk yadda na so da na danne abinda yake damuna na kasa. Ni kaina ba zan so lissafin aure ba, to amma idan kaddarata ce hakan ya zan yi. Akwai fa matsaltsalu masu yawa dangane da zamana da mutumin nan amma ba kowane zai fahimci hakan ba. Sai Babandi ya takura mini da tambaya domin shi ya yi mini farin sani bayan anti Yagana babu wanda yake saurin fahimtar damuwata sai su dalili ina da yawan wasa da barkwanci kuma koyaushe fuskata a sake take. Matsanta mini da ya yi da tambaya ya sanya na dan tsakura masa kad'an daga cikin abinda yake faruwa Ban ta'ba tsammanin zai fusata ba. Kawai ya dinga bala'i yana kumfar baki fadi yake yi Idan baya sonki ya sake ki mana akwai masu so da yawa shi bai san dami ya tsinta a kala ba. Wannan ai jahilci ne ka auri mace tana zaune a gidanka kuma kana zarginta dan kin auri maza biyu kafin shi shine me? Wallahi ko yau ya sake ki ni zan aureki, idan ma kin ce ba kya sona akwai wanda zan hada ki dashi saurayi kuma mai rufin asiri, dama sautari auran masu kudin nan ba tomo ba ne. Da kyar na sassauto dashi ya yi shiru sai huci yake yi abin ya dinga ba ni mamaki. A wurin kafin mu rabu na nuna masa cewa lallai dole ya boye mini sirrina ba na so kowa ya ji, shi ma na gaya masa ne domin ya ba ni shawara, dan idan ya fasa maganar kowa ya ji mai raba ni da anti Yagana sai Allah. Illai kuwa duk kaffa kaffan da nake yi sai da ta tsargu ganin mun fito daga storoom din gidan tare muna magana tana cikin jama'a amma kaf hankalinta yana kanmu.. Gabad'aya jikina ya yi sanyi na wuce na karbo abinci cikin fulas na nemi Yusi dake can cikin yara na bashi ya kaiwa Sukairaju can gidan anti Yagana tunda tare muke ya zame mini jela duk inda zan je yana bina a baya bisa bin umarnin ubangidansa. Gidan bikin ne na ce masa ba na so ya biyo ni kawai ya zauna zan aiko masa da abinci shi ma ba a son ransa ba sai da na hada da fad'a tukkuna. Muna komawa anti Yagana ko ta bari mu huta ta fara surutai. " Idan Babandi ya zugaki kike kashe auranki Amina bai wuce shi din ya aureki ba tunda na gane dama tuntuni yana sonki bai fad'a ba ne sai yanzu, to me na sama ya ci balle ya bawa na k'asa. A yadda kike Amina ai sai irin su Alhajin Tajon din, shi din ma sai dai Allah ya k'wace shi, amma muddin Babandi ya aureki sai ya gane shayi ruwa ne shege yana yawo da bakar fuska. Duk da kuncin da nake cikin sai da na yi dariya na ce." Anti Yagana ina da wani mugun hali ne da za ki ce haka, ni fa abinda kike zargi ba shi ba ne, kin san dai Babandi mutumina ne ko?" Ta share ni ba ta ce mini komai ba, amma motsi kad'an za ta yi kwafa ta girgiza kanta tabbacin abin yana damunta. Sai ta ba ni tausayi domin na gama fahimtarta ita dai kokarinta ta danne ni na zauna saboda kada duniya ta zage ni, a kuma yi mini lissafin aure shine kawai abinda take gudu. Da daddare misalin goma da wani abu ya kira ni a waya. Dama tunda na sauka a garin sau d'aya mukayi waya kuma shi ya kira ni. Ina sane na ki d'agawa har sai da ta katse ya sake kira ta katse a k'alla sai da ya kira sau hud'u na daga ina sallama. Ya ce." Wanene Babandi?" Gabana ya buga da karfin gaske! jin sunan Babandi a bakinsa. Da kyar na daure na ce." 'Dan uwana ne." "Shine kuka 'keba a wajan da babu gilmawar mutane? idan dan'uwanki ne me zai sanya ba za ku tsaya a bainar jama'a ba." Na daidaita nutsuwa sosai domin yin hakan shi kadai zai kwace ni daga mummunar zarginsa. Shin a ina ma ya san na yi hira da Babandi. "Anan din ma sai ka tuhume ni akan abinda baka da hujja wai dan girman Allah a gidan karuwai ka auro ni Baba, ko kuma dai ka fara tu'ammalli da muggan kwayoyi da suke fad'a maka karya." "Kina mamaki ne don na tuhume ki, ki ba ni amsar tambayata kawai idan har Babandi dan'uwanki ne na jini me zai sanya ki 'kebe dashi shi kadai." "Saboda akwai muhimiyar maganar da muka tattauna, Babandi Kuma d'an'uwana ne na jini tunda iyayenmu cikinsu d'aya, kuma tun kafin na sanka nake tare dashi wannan shine bayanin kawai da zan iya yi maka a kansa." Kashe wayarsa ya yi ba tare da ya sake yin wata magana ba. Jikina a mace na ajiye tawa wayar ina tunanin yadda aka yi ya san na ke'be da Babandi. Sukairaju anan gidan anti Yagana na bar shi. Na san kuma ko giyar wake anti Yagana tasha ba zata gaya masa ba tunda ita kokarinta ma na koma gidana na cigaba da zama. Yusi ya shigo d'akin da nake da yaran 'yan uwa dana anti Yagana na ce su je waje domin lokacin k'wa'kwalwata tana buk'atar hutu. Suka juya zasu fita na kira shi ya dawo shi kadai na ce." Kun yi waya da Baba ne a wayar Sukairaju?" Da sauri ya ce." Eh d'azu da na zo kawo masa abinci na same shi suna waya shine na ce ya ba ni shi mu gaisa." Gabana na dan bugawa ba ce." Kai ne kenan ka ce masa ka gan ni tare da Babandi ko?" Ya gyada kansa yana cewa." E tambayata ya yi kina Ina shine na gaya masa kina can tare da Babandi a storoom." Na zuba masa ido ina ji kamar na gaggaura masa mari saboda takaici! Ganin irin kallon da nake yi masa ne ya sanya jikinsa mutuwa sai ya sunkuyar da kansa da kyar na ce.'' Jeka ku kwanta dare ya yi."Ya kama hanya ya fita ba karsashi. Cikin baccin da ya fara fizgata na ji tana kirana na tashi zaune da sauri Ina kallonta Tana cikin kayan bacci don wata'kila ma daga turakar mijinta take ta kufto ta fito saboda rashin ha'kuri ganinta a hargitse ya tabbatar mini da cewa ta san abinda ya faru wata'kila ma shi ya kira ta ya gaya mata. "Kina ganin abinda kuka yanke da Babandi shine mafita a rayuwarki Amina." Na dube ta a tsanake na ce.'" Anti Yagana me muka yanke ban fahimci inda maganarki ta dosa ba." Ta gyada kanta cikin takaici da jin haushi ta furta." Yanzu Amina a ce kamar Babandi shi ki ka bawa lasisi da ragamar auranki saboda kin zama mara mafadi babu wanda ya isa ya gaya miki ki ji, a ce wai Babandi shine zai tsara miki yadda za ki yi, Kuma ki bashi kwarin guiwa da hadin kai ya kira mijinki mutum kamar wannan da yake da kima da dattako da shekaru ya gaya masa maganganu masu kaushi, ashe Amina ni ban isa na gaya miki magana ba ko?" Sai kawai naga kwalla ta ciko a kwarmin idonta. Hankalina ya tashi sosai na ce." Wallahi tallahi anti Yagana ban yi haka da Babandi ba, ya takura mini da tambaya ne shine na dan tsakura masa abinda yake damuna, kuma na gargadeshi akan kada ya gayawa kowa, ban taba tsammanin ma zai iya kiransa da wata magana ba, a Ina ma ya samu lambarsa mutumin da ba kowa ya san lambarsa ba. Hawaye suka keto kumatunta suka fara d'iga. Sai na ji duk gwiwata ta sanyi me ya yi zafi Anti Yagana take kuka irin haka. Hawaye suka silalo mini na ri'ke hannunta ina fad'in." Wallahi tallahi anti Yagana ban sa shi ba, ban san a inda ya samu lambar wayarsa ba, ki gaya mini abinda ya fad'a masa domin tunda naga kina kuka na san abin babba ne." Ta goge hawayen tana cewa." Ni babbar damuwata shine duk rintsi duk wahala ki yi hakuri ki zauna a dakinki Amina, ba wai na kafe akan don mutumin nan yana da wata suttura ba a a ke nake dubawa da kuma yaranki, matsalarsa ba mai muni ba ce a ganina tsananin so ne yake janyo kishi shi kuma na fahimci duk lokacin da zai tuna maza biyu sun taba ki kafin shi yakan kasa sarrafa kansa. Kishin maza fa daban yake dana mata wallahi maza sun fi mata kishi, mu hauka muka fi su. Kada wani ya rudaki akan ki fito ki yi hakuri ki zauna domin Babandi ba zai ta'ba iyawa da bukatunki da na yaranki ba. Karshe dai ki kara famtsama harkokin da ki ka bari a baya." Ina kuka na ce." Na ji batunki anti Yagana Kuma na fahimci duk abinda kike nufi, ni kaina ba na so ace na fito daga d'akina, amma abinda nake so ki fahimta shine, bayan wannan matsalarfa akwai wata a kwance nasan baki manta da cewa samun haihuwa zai yi mana mutukar wahala a tsakaninmu ba duba da sakamakon gwaji da abinda ya faru a baya na rasuwar abinda muka haifa. Akan iya samun matsalar haihuwar yara marasa lafiya tunda har jini ya nuna anti Yagana kuma kinga ni duka yarana biyu a duniya, shi kuma a yanzu ne yake da buk'atar tara zuria. Haihuwa da wahala tun daga samuwar cikin raino da nakud'a. Ba fata nake yi ba duk na gama shan wannan wahalar Kuma na zo na haifi da mai lalura daga karshe ya mutu, anti Yagana akwai ciwo da damuwa wata ta zo daga bayanka kana kallo ta yi ta haihuwa kai kana zaune." Ta girgiza kanta cikin damuwa ta furta." Na gaya miki tun farkon lamarin nan ki k'adaita Allah, domin su kansu turawan da suka kirkiro abin nan hasashe kawai suke yi, babu fa wani mahaluki da ya isa ya canzawa Allah manufa duk abinda ya wanzar shine daidai. Ki saki zuciyarki ki zauna a dakinki, idan za ki haifi yara goma su mutu dama haka Allah ya nufa, idan kuma zaki haifi yara goma su rayu haka Allah ya nufa. Ai Kinga da za ki auri Aminu ba a yi gwaji ba, kuma gashi kin haifi yara masu lafiya kwarai da gaske, to wannan ma kadai ya isa ki barwa Allah abinda ya tsara miki" [8/24, 9:26 AM] Aunty B: 67 Ni kukan da take yi shi ya fi daga mini hankali domin na jima ban ganta cikin yanayi na damuwa da tashin hankali ba, kukanta yana da ala'ka da abu biyu domin yau yini aka yi a gidan bikin nan ana hirar Mamanmu har wasu daga cikin 'yan uwanta suka dinga kuka, a ganina matsalata kadai ba za ta sanyata zubar da hawaye irin haka ba, tashin zancen Mamanmu da 'yan uwanta suka yi shi ya kara dagula mata lissafi sai ni ce na yi namijin ko'karin tsayar da nawa hawayen na dinga rarrashinta akan ta yi shiru ban samu hakan ba kuwa sai da na yi mata al'kawarin duk rintsi da wahala zan ha'kura na zauna a d'akin mijina Da wannan alkawarin ta tashi ta fita ta barni cikin tunani da zullumi. Ni dai nasan anti Yagana ba makwadaiciya ba ce balle na ce mutumin nan siyanta ya yi da kudi. Na fi zargin dai abin a jininsa yake domin na fahimta duk wanda zai yi mu'amula dashi da wahala ya hangi kuskuransa. Ni a karan kaina na san shi din mutum ne domin kuwa duk inda ake neman dattako da nagarta taimako da tausayi ya kai a jinjina masa. Amma a dabi'a da halayya irin ta dan adam dole a same shi da wani nakasu wanda sai mu da muke zaune dashi za mu tabbatar. Baya ga mummunan zarginsa babu komai a tsakanina dashi face alheri domin har yau har gobe ina kallonsa da hakan, amma ina ji a cikin raina zamanmu ba zai yi dad'i irin yadda anti Yagana take so ba muddin bai canza dabi'a ba, ni kaina ba wai so nake a ce mun rabu ba domin duk abinda take yi mini hange ni ma ina yin hagen haka, to amma ai zaman ba zai yi tasiri ba idan da cin zarafi a ciki. Kamar yadda ta ce mini na kira shi na bashi ha'kuri bayan wanda ta bashi ban ce to dan na yaudareta ba na yi aniyar kiran nasa sai dai fargabata ban san irin martanin da zai mayar mini ba tunda na gama fahimtarsa bai iya b'acin rai ba. Sha biyu da wani abu idona biyu na kasa rintsawa saboda fargaba da tunanin d'anyan kan da Babandi ya yi mini, kawai don ina jin nauyinsa ne ya sanya ni dannewa amma tabbas da wani ne ba zamu wanye lafiya ba. Wayata na d'auka wadda har na kashe na ajiye zuciyata ta kasa nutsuwar barin gari ya waye na kira shi, na san yanzu da wahala idan ya kwanta ya kan kai karfe daya yana aiki da computer kafin ya kwanta. Da fargaba na lalubi lambarsa na kira hannuna na dan karkarwa karon farko kenan da nake jin fargaba da tashin hankalin wani raddi daga wajansa. Sai dai kuma daga zarar wayar ta fara shiga sai ta katse. Na tashi na fita falo wai ko network ne nan ma ta dinga yankewa, ni ce dai har farfajiyar gidan amma ta'ki tafiya. Babu kuzari na koma daki na zauna da wayar a hannuna na rasa wane nazari zan yi. Kai tsaye dai ba zan yanke masa hukunci ba, amma ai ban ta'ba kiran layinsa ya yi mini haka ba. Ban ha'kura ba na jarraba kiran Sahura sai gashi ta shiga har ta fara ringing na katse da sauri na sake nemo lambartasa a karon da babu adadi ta sake katsewa. A lokacin na gazgata hasashena a busy ya sanya ni. Bai d'auki waya ba na san ko text na tura masa ba zai duba ba tunda dama can ya kan tara messages na mutane kafin ya samu damar dubawa. Na kwanta cikin zullumi da tunani lallai akwai maganganun da Babandi ya gaya masa dama ai mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awakai yanzu shawo kansa sai na kusa zama k'aramar mahaukaciya. Ban ta'ba kawowa zuciyata saki a cikin irin hukuncin da yake ganin zai yi mini ba, domin ni kallon da nake yi masa ma kome zan yi masa na takaici ba zai d'auki matakin sakina ba sai gashi na wayi gari da ganin text dinsa na saki d'aya Inda ya rubuta a takaice da kuma babban hafarai "NI ALHAJI TAJUDDEN IBRAHIMU NA SAKI MATATA AMINA SALISU SAKI DAYA." Na yi bala'in kad'uwa daganin sakon gabana ya dinga bugawa da mugun karfi yayin da wani irin yawu ya tsinke mini a bakina. Da kyar bakina ya kar'bi abinda zuciyata take amayowa na dinga nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Zuciyata na harbawa da mugun karfi. To da yake babu abinda ya fi ambaton Allah samun sasaauci a lokacin dadi da b'akinciki, cikin kan'kani lokaci na dan shiga nutsuwata na fara tunanin yadda zan yi na shawo kansa ya mayar da ni ba tare da kowa ya ji ba. Babbar damuwata Anti Yagana da alkawarin da na yi mata jiya kafin ta je ta kwanta, amma ni idan ta ni ce zan iya jurewa tunda ba shine karo na farko ba. Har yanzu zuciyata ta'ki aminta da cewar da sanin mahaifiyarsa ya sake ni. Ya yi mini hakan ne saboda ya nuna mini ni din ba komai ba ce. Kishi ba hauka ba ne yana da kyau ya ji ta bakina kafin ya d'auki d'amarar tozartani. Hawaye masu zafi suka kece mini suka fara kasa tsere a dakalin fuskata. Na yi kasa'ke da waya a hannuna gwiwata ta sage tamkar an buga mini guduma, komai ya dagule mini na rasa ma abinda zan yi. Shi din zan nema domin na ji ba'asi akan abinda ya yi mini, har yanzu ban yarda da cewa abinda na aikata na cancanci hukuncin saki ba, ai ba rufe kofa na yi da Babandi ba, sannan kuma duk abinda zuciyarsa zata kitsa masa a kaina bai gani da idonsa ba, ni ba mazinaciya ba ce, idan ma yana hasashen hakan a kaina. Na kira shi ya fi sau goma sha biyu bata shiga. Hawayen nadama da tausayin kaina suka dinga gudana a kumatuna. Ba zan kira mahaifiyarsa na na gaya mata ba, domin na tabbatar da cewa ba ta san abinda ya faru ba domin da yawunta ba zata bashi goyan bayan yi mini wannan tozarcin ba. Sannan bata da koshin lafiya Ina ganin jin wannan labarin zai iya daga mata hankali har ciwonta ya tashi. Garin Allah ya waye sosai haske ya fito ban fita ba asalima ban tashi daga kan daddumar da na yi sallar asubahi ba. A hakan anti Yagana ta shigo ta same ni ganina a rikice ya sanya ta zo ta tsaya a kaina tana tambayata. Koda na dubeta sai wani sabon hawayen ya k'wace mini. Na d'auki wayata dake ajiye a gefe na mik'a mata. Tana dubawa tana salati sai ta silale rigijib ta zauna a gefena. Na rufe fuskata da hannuna ina kuka na furta." Anti Yagana ko me na yi wa mutumin nan ban cancanci wannan cin zarafin ba. Wallahi tallahi ba da hannuna Babandi ya kira shi ba, kuma dana san abinda zai faru kenan dashi kansa Babandi ban gaya masa komai ba. Anti Yagana ki duba lamarin nan a tsanake akwai izza da iko da nuna kowa ba komai ba ne a cikin sha'anin wannan mutumin ya iya taku ne shiyasa ba kowane zai fahimci hakan ba, amma menene lefi don an ce gyara kayanka, abinda fa yake aikata mini kuskure ne, na tabbata ko giyar wake Babandi yasha ba zai zage shi ba karshen dai rashin kunya kenan, magana ce ake yi akan dabi'ar da yake yi ba mai kyau ba ce, kuma duk wanda ya san ciwon kansa ya kuma san illar zargi a sha'ani na aure ya san hakan ba daidai ba ne, menene abin saki a nan anti Yagana don yana da wata alfarma wallahi ba zan bari ya wulakanta ni ba." Anti Yagana ta ja hanci idonta da sauran hawayen da ta gama gogewa ta ce.''Wallahi tallahi sai da na ji haka a jikina Amina, shiyasa fa jiya kafin na fita na umarceki da ki kira shi ki bashi ha'kuri Kuma ki shanye duk b'acin ran da zai k'unsha miki, dan kyautawa ke da Babandi baku kyauta ba, kuma tun a jiyan na kira Babandi na tambayashi yadda suka yi dashi ya ce ya yi masa magana ne akan abinda ki ka fad'a masa har ya kara da cewa dashi bai auro ki a gidan karuwai balle ya yi togaciya da kiranki da wata kalma ya kara da ce masa harkar social media da ki ka yi kin yi ne domin rufawa kanki asiri da yaranki, ni dai iyakacin abinda ya fad'a mini kenan ban sani ba ko ya rufe wata maganar wadda ya gaya masa ta fusata shi ni bai gaya mini ba. Kuma ko jiyan da muka yi waya dashi wallahi ha'kuri na bashi akan hakan kuma ya nuna mini ya ha'kura magana ta wuce amma hukuncin da ya yanke ya yi tsauri bai kai ga a ce an yi saki ba. Na ce." Anti Yagana ki kyale shi kawai dan Allah dan annabi kada ki kira shi akan neman hujjar da ya sake ni. Na san bashi da ita zai bata miki lokaci ne kawai hujja dai ita shi mai kudi ne, kuma ni ba kowa ba ce a wajansa a yanzu." Ta dube ni jiki a sanyaye." Ni fa Amina na fara zargin lamarin nan naki anya babu sa hannu a ciki, mutumin nan fa wallahi yana sonki ba zai iya sakinki cikin hayyacinsa ba wata'kila ana dan birkita masa tunani shiyasa ke din ma ya kasa aminta dake yake tsiro da abubuwa daban daban. Shiru na yi ina nazarin maganarta. Zan iya gazgata maganarta tunda na gani da idona a lokacin da inna Uwani take yayyafin rubuta a wajan benansa. Amma idan ma da asirin to tabbas akwai hali da kuma dabi'a. Ta shi ta yi zata fita duk ta ki'dime tana daf da kofa na kira ta a nutse na ce." Anti Yagana don Allah kada ki kira mutumin nan a waya dan Allah ki yi mini wannan alfarmar." Ta ja ta tsaya tana dan kallo kafin a sanyaye ta ce." To ai yana da kyau a tambaye shi dalilinsa ko." Na ce." Dalili da ba zai wuce abinda na gaya miki da farko ba. Kishi zargi giyar kud'i." "Amma dole mahaifiyarsa ta san da abinda ya faru Amina, domin bahaushe yana cewa ta inda aka hau ta nan ake sauka." Na ce." Itama din ba za ta ji daga bakinmu ba shi ya fad'a mata. Ni dai tsorona ma kada wata magana ta fita duniya ta ji na shiga bakin duniya kin san shi sha'aninsa a waje yake motsi kad'an manema labarai za su fara watsawa shine babbar damuwata kuma kin san yadda da dama mutane suke yi wa macan da take gudanar da harkokinta a internet ko da bata aikata komai halalinta take nema sai a juya mata manufa a yi ta jifanta da bakaken magana." "Babu abinda zai faru in sha Allahu ma ina fatan kafin zuwa gobe ya mayar dake shikkenan babu wanda ya ji ya kuma ga ni." Tana gama maganarta ta fita daga d'akin a gaggauce. Ban fita ba tukkuna sai da na yi wanka da yake da bandaki a cikin d'akin na kimtsa jikina abin yana ta sasakata a zuciyata ina dannewa idan takaici ya yun'kuro mini sai na ambaci Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Da kyar na iya kurbar shayi ban iya hadawa da borodi ba saboda lami nake jin bakina. Anti Yagana ta fito cikin shiri zata fita na ce." Ina kuma za ki je" Tana gyara gilashin da yake idonta da yake tana da dan matsalar Ido wanda yasa asibiti suka yi mata gilashi take amfani dashi idan zata fita ta ce. " Ba zan ji ma zan dawo kafin azuhur." A cikin raina na ji cewa saboda matsalata zata fita. Na ce." Anti Yagana ban san ki da biye biyen malamai ba don Allah kada ki fara akan wannan karamin dalilin, kada ki yi wasa da tunaninki, ni dake mu zauna mu tattauna abinda zai taimake mu. Nasan akan duk abinda ki ka tashi hankalinki, amma ki sani kowane bawa yana tafiya ne da kaddarsa, kuma mutumin nan bashi kadai ba ne namiji akwai su da yawa, idan Allah Ya kaddara mini sake wani auran nan gaba sai ya had'a ni da wanda ya fishi. Jikinta a sa'bule ta ce." Da wai zuwa zan yi a yi mini istahara ta musulunci Amina, idan kuma da dan wani taimako ko rubutu ko hayakin da za a baki sai ki yi amfani dashi domin sake janyo hankalinsa tunda dai ni na tabbatar da cewa mijinki yana sonki." Murmushin takaici na yi na ce." Anti Yagana ai maganar so da k'auna ta kare tunda har ya sake ni, ni dai abinda nake so ki samu nutsuwa don Allah mu barwa Allah." Ta gyada tana dan nazari kamar ta d'auki maganata sai kuma a zabure ta daga labule zata fita take cewa." Bari dai na dawo ai na san irin malaman da zan je wurinsu. [8/27, 5:50 PM] Aunty B: 68 Ina nan zaune ina sa'kawa da kwancewa Sahura ta kira ni a waya tana bin ba'asin kiran da na yi mata cikin dare kawai sai na ce mata mistake ne ni ban san ma na kira t ba sai yanzu da ta yi magana. Muka dan ta'ba hira kad'an kafin mu yi sallama. Na kira Yusi na tambayeshi akan kaiwa Sukairaju abin kari ya ce mini tun d'azu. Na sauke ajiyar zuciya tare da bashi umarnin tafiya har ya juya kuma sai ya tsaya yana tambayata wai yaushe za mu tafi tunda yau kwananmu uku haka baba ya ce mu yi kwana uku. Rashin amsar da zan bashi ya sanya na ce ya fita ya ban waje. Ya kama hanya ya fita jikinsa ba kuzari. Ni yadda ma zuciyarsa zata manta da shi kawai nake ji, na lura da irin wannan sha'kuwar ce take sanya mutum ya kwanta ciwo idan an rabu. Wai saki ni abin ma mamaki yake ba ni, hakika lamarin ya kidima ni. Wajan shad'aya da rabi anti Yagana ta dawo a gajiye ta zauna a falo. Na zuba mata ido tausayinta na ji yana tsirga mini duk wannan fad'in tashin akaina take yi da kud'inta da ga'bobinta. K'walla ta ciko kwarmin idona amma ban yarda ta zuba ba na yi c 'kok'arin mayar da ita Ina kallonta tana fito da kayan dake cikin jakarta ta ce." Ina hanya sai ga wayar Babanmu wallahi lokacin da ya kira ba ki ga yadda hankalina ya tashi ba domin na yi tunanin mijinki ne ya gaya masa abinda yake faruwa, wai ashe Hadiza ce za ta tafi dubai saro kaya shine ya ce wai na kira ta na yi mata magana domin shi fa idan da yawunsa ne bai amince a bar 'kasa da zummar neman kudi ba." Cike da mamaki na ce." Dubai uban me zata saro a can din, a ina kuma ta ga jarin da har za ta yi visa ta d'unkule kudi ta tafi wata kasa." Girzgiza kanta ta yi da takaici mai yawa a tare da ita ta ce." Ni ma tambayar da na yi masa kenan ya ce shi ma bai sani ba amma ya fara zargin mijinki ne ya bata domin Ummansu Saminu ta ji su suna maganar watarana bayan ta dawo daga unguwa suna d'aki ba su san ta shigo gidan ba. Bayan miliyan shidan da ta yi k'arya da rashin lafiyar Fati ta kuma tambayarsa kudi." Takaici da b'akinciki ya hana ni cewa komai. Har da hadi'n gwiwar hadiza wajan ko'karin wulakani da mutumin nan yake yi. Anti Yagana ta cigaba da cewa." Kwanaki da na yi mata magana akan me yasa suka shirya karyar ciwo don su kar'bi kudi wallahi ba ki ga rashin kunyar da ta yi mini ba, shiyasa ai na cewa Baban namu ba zan iya cewa komai ba akan Hadiza ba domin tana samun d'aurin gindin uwarta ne." Zuciyata na zafi na ce." Anti Yagana yanzu dan Allah wannan shine daidai ne, Hadiza fa ta wulakanta ni a wurin mutumin nan, ta zubar mini da mutunci, me yasa ba zai nuna ni ba komai ba ce, ya san ba ma shiri har da sakamakon saki mai zai sanya ya tura mata kudi." "Ni kaina raina ya 'baci to babu wata dama ta gyarawa ya riga ya faru kuma kin ce mini shine ya bata damar yin hakan baki da hujjar yin wata magana kud'insa ne." Hawayen dai da nake dannewa suka zubo a kumatuna na ce." Amma dai ai bai dace ba, fad'a fa muke yi me yasa zai tura mata kudi, yadda yake jin haushina akan lefin da bashi da tabbas ya kamata ace ya k'yamaci duk abinda ya shafe ni." Murmushi ta yi tana cewa." Wani sa'in fa maza sun fi mata kaidi Amina, ba ta yadda za a yi fa ki fito a yanzu ki nuna wannan bawan Allah ba ya kyauta miki mutane su yarda da maganarki, yana amfani da dukiyarsa ne wajan sayan al'umma bisa la'akari da yadda rabin mutane suka zama makwadaita. Babanmu da sauran 'yan uwansa ba zasu ta'ba yarda da maganarki ba wallahi. Ban 'ki ba Baban Sauden ni kaina yanzu na fara hasashen halayensa marasa kyau da yake b'oyewa mu kuma yana bayyana mana masu kyawu amma idan ba haka ba me zai sanya ya san da wannan rikicin a tsakaninku ya d'auki kudi masu yawa ya bawa 'yar uwarki, ya shirya kai ki kasa ne koda maganar ta fasu babu wanda zai aminta dake " Hannu nasa na goge ragowar hawayen da yake fita daga idona yayin da nake jin wani irin zugi a kasan zuciyata. Mutumin nan karshen munafiki ne. Ta ce." Kin ga ba wai naki yarda da abinda Allah ya kaddara ba ne, amma kin san istahara gaskiya ce Amina, an bincika mini sosai lamarin nan akwai sa hannu tunda ai farkon auranku ba haka yake ba, tunaninsa a rikitar ana so ma adasa masa kiyayyarki da zarginki a cikin zuciyarsa. Yanzu haka ma malamin ya ce mini yana can hankalinsa a tashe domin lokacin da ya yi sakin a tunzure yake k'wa'kwalwarsa tana ta gaya masa karya da gaskiya yanzu kuma da ya dawo nutsuwarsa ya fara nadama." Murmushin takaici na yi na ce." Anti Yagana duk wata istahara ta bi bayan wadda kai za ka yi da kanka, idan kin ce akwai asiri ko farraku a tsakaninmu ba zan musanta miki ba, amma ban yarda da cewa yana can hankalinsa a tashe ba me yasa bai kira waya ba." Ta ce.'' Ai yanzu akwai turaran da za ki yi wanda dolensa ya neme ki kafin nan kafi faduwar rana haka malamin ya ce." Dariya ce ta k'wace mini duk da halin da nake ciki amma yadda anti Yagana ta hakikance tsakaninta da Allah sai ta ba ni tausayi da dariya na ce." Anti Yagana ki yi hakuri ba zan iya hayakin komai ba indai akan bawan Allan nan ne, mu yi addu'a kawai idan da alheri komawata gidansa sai na yi hakuri na koma, idan kuma babu alheri sai ki ga Allah ya kawo mini wani." Ta 'bata rai tana cewa." Matsalata dake taurin kai Amina, kishiyarki wallahi ba a zaune suke ba, babban burinsu ki fice ki bar gidan, kin ga idan ba ki ba ni goyon baya ba sai na yi asarar kudina dubu arba'in na fitar aka ba ni turaran nan da kuma wannan rubutun." Na cika da mamakin jin kudin da ta bayar har dubu arba'in lallai anti Yagana ta d'auki lamarin nan da girma, ai idan dan ta ni ce wallahi ba wani yawon neman taimako da zan yi a ci kudina a banza. Na tabbata anti Yagana bata ta'ba zuwa wurin wani malami ba sai akan matsalata hakan ne ya sanya na amince zan yi amfani da maganin amma da sharad'in ko da bai kira ba to ba zata kira shi ba domin ta ce mini malamin ya ce idan bai kira ba to sai a kira shi. Ta amince da abinda na ce ni kuma na kar'bi rubutun da turaran a take a lokacin na fasa daya nasha ba tare da yakini ba. Da kanta ta je ta hura wuta ta ruru sosai ta shigo da garwashin da yawa a cikin kasko irin na kasa ni dai kallonta kawai nake yi ina mamakin yadda ta d'auki al'amarin. D'aki ta nufa da rushin wutar kafin ta kwalo mini kira na tashi na je na sameta tana kwance ledar turaran, ta ce." Sai kin cire kayan jikinki tsaf sai ki rufa da wannan zanin, amma idan kin zuba turaran akan wutar sai ki dinga yi kina kiran sunansa. Fashewa na yi da dariya na fadi saman gado ina kyakyatawa domin duk yadda na kai ga son ganin na danne dariyar kasawa na yi. Ta yi kasa'ke da ledar maganin a hannunta tana hararata. Ni kuwa Ina dariyar na ce." Wallahi anti Yagana dariya kike ba ni, wani irin turare ne wannan da har sai na yi tum'bur haihuwar uwata, na rantse da Allah malaman nan suna nema su jefa mata a masifa." Ta sha kunu tana cewa." Kina d'auka abin nan da wasa ko Amina, nema ma ki ke yi ki mayar da ni mahaukaciya saboda baki da mutunci ko ina tsaye akanki amma ki sanya ni a gaba kina yi mini dariya ba za ki fahimci abinda nake nusasheki ba sai ranar da ma'kiya suka kai ki 'kasa tukkuna." Ganin yadda ranta ya 'baci ya sanya na tashi zaune sosai na kar'bi ledar da turaran yake daure Ina fad'in." Zan yi yadda ki ke so anti Yagana" Shiru ta yi mini tana cigaba da wurgo mini harara. Babu yadda na iya da ita haka na tashi na fara cire kayan jikina, ya rage daga ni sai rigar mama tana tsaye tana kallona na dubeta tare da cewa." Ko suma din na cire su?" Ta girgiza kai." Ki bar su kawai ai." Ban sake cewa komai ba na zuba turaran akan wutar lokaci guda hayakin mai kauri ya tashi na yi sauri na rufa zanin ajikina na dukufa kan wutar ita kuma da sauri ta kama hanyar fita tana fad'in." Kada ki manta ki dinga ambaton sunansa fa." Na ce." To shikkenan." Ina jin karar jan kofarta na cillar da zanin na tashi daga kan wutar na matsa gefe ina haki da tari ya sarke ni. Hayakin ya cigaba da bin iska ina gefe guda. Na ji motsin bude kofarta a guje na d'auki zanin na je na dukufa kan wutar ta leko tana cewa." To kin ga haka ai ya fi, kin shaki hayakin sosai, in sha Allahu da izinin Allah zai kira waya yau din nan sai a daidaita, malamin ma cewa ya yi hakuri zai bayar." A zuciyata na ce.'' Anti Yagana da tun farko kin k'adaita Allah ba za ki nufi wajan wani malami ba, suma duk hasashe suke yi. To haka muka yini muna tattauna sha'anin Hadiza da abinda ta aikata, ni ma yanzu na dawo daga rakiyar Ummansu domin ta zama bakin ganga na yarda itace take dorata a gwadabe mara kyau amma duk lokacin da zata kira ni a waya nuna mini take yi itama Hadizan tafi k'arfinta ha'kuri take da halinta a zahiri kenan amma a bad'ini bakinsu d'aya. Na riga na gama fahimtar cewa Hadiza da ni take gasa tun daga kan mutuwar aurena kawowa yanzu burinta itama ta tara arziki har ta kere mini. Tun bayan sallar Isha'i na lura da anti Yagana jikinta ya yi sanyi duk wani abu da take yi babu kuzari domin abincin dare ma ni na yi mana towon samovita miyar ku'bewa tun yamma take ce mini jikinta yana ciwo dalilin da ya sanya kenan tasha Panadol ta kwanta amma dai karin kasalarta yana da ala'ka da dakon kiran wayar Alhaji Tajo domin yadda na fahimta ta gama aminta da abinda malaminta ya gaya mata. Muna d'an ta'ba hira sama-sama Babandi ya zo, bai samu wata tar'ba ta arziki ba a wajan matar gidan anti Yagana kenan, ni kaina daurewa kawai na yi nake tanka masa amma duk da haka babu cikakkiyar sakewa kamar yadda muka saba, ina jin hakan da ya fahimta ne ya sanya shi yi mana sallama ba tare da ya shirya tafiyar ba domin idan dai za mu had'u muka shafe sama da awa biyar muna hira ba tare da gajiya ba, yanzu kam ko minti talatin bai yi ba ya kama hanya ya tafi ba karsashi a tare dashi. Anti Yagana ta rakashi da tsaki da harara duk ina kallonta ban ce mata komai ba. goma da wani abu Babansu Fadila ya shigo ita lokacin ta shiga d'aki tana kintsawa. Ya tsaya a falon muna dan ta'ba hira da yake akwai sabo a tsakanimu dukda wani sa'in idan na zo garin har na kare kwanakina bai fi sau biyu muke had'uwa dalili shi din babban direba ne kuma yana da muk'ami a tashar da suke ajiye motocinsu da asuba yake fita sai dare yake dawowa kamar i yanzu. Ya tsaya yana tsokanata da fad'in." Ranki ya dad'e ina kamun 'kafa fa, a cewa maigidan a irin wad'annan motocin nasa muna neman koda guda d'aya ce wadda za mu dinga lodi daga nan kudu, idan haya ake bayarwa a taimaka a ba mu, idan kuma za a ba mu ne sojan haya zuwa shekara biyu in sha Allahu sai mu mayar da kudin, dama tuntuni nake so na samu dama na bi ta karkashinki, kwanaki an ce mana ya rabawa direbobi biyar kuma uku daga ciki ma an ce kyauta ya basu ba mutum biyu ya kar'ba." Tsakaninsa da Allah yake gaya mini babu wasa a cikin maganar. Ganin haka ya sanya ni ma na shiga nutsuwata na ce." Aikuwa ban san kana buk'ata ba wallahi tabbas watannin baya na ji yana maganar da wad'anda Allah Ya sa suna da rabo, amma in sha Allahu kuwa zan yi masa maganar idan na koma duk yadda muka yi dashi sai na sanar da kai." Da farinciki mai yawa ya fara godiya har da kirari kamar wani maroki na dinga dariya ina zolayarsa da cewa sharad'in idan na yi masa hanya ya samu babu shi ba kara aure fad'i yake yi." Na yarda ai tuntuni na gaya mini Yagana ta rufe kofar kece ba ki yarda ba." [8/29, 5:24 PM] Aunty B: 69 Dariya kawai na yi domin nasan yana fad'a ne kawai amma ba har zuciya ba, babu wani namiji da zai so ya rayu ya mutu da mace daya yawancinsu suna ha'kura ne saboda wasu dalilai amma an riga an hallicesu da son mata wannan a jininsu yake akwai ma mazan da suke da tarangahuma sun yarda su tara matan duk abinda ma zai faru sai dai ya faru. To wad'annan sune za mu kira da masu rashin tsinkaye da hangen nesa. gajiya na yi da tunani na tashi na je na kwanta wanda bacci da k'yar ya d'auke ni. Misalin shida da rabi wayar Hamusu ta tashe ni daga b'ingirewar da na yi bayan sallar asubahi Muka gaisa sosai dalili mun kwana biyu ba mu gaisa ba kamar yasan maigidan yana adawa da hakan a tsukin ya rage kira na a waya sai dai ya turo mini da voice note ta whasap. Ni ma sai na fi jin dadin hakan. Nan yake gaya mini Gwaggo ce bata da lafiya dalilin da ya sanya ya kira ni domin jikin nata ya fara tsanani. Cikin kankanin lokaci na ji hawaye ya cika kwarmin idona. Gabad'aya sai na diririce hankalina ya tashi sosai, na ce." Hamusu ina nan maiduguri na zo bikin yaran d'an'uwan Dada, ita Gwaggwon za ta san shi tunda tare suka taso. Amma zan yi kokarin d'auko hanya gobe yadda kake fad'in jikin nata hankalina ya tashi sosai wallahi, ina fatan kun kai ta asibiti. Ya ce." Kiran da na yi miki kenan, domin babban asibiti nake so mu kaita su bata gado sugar ne da hawan jini, mun je asibitin murtala likita ya dubata ya rubuto magani an Siya kwana biyu an samu sau'ki wallahi jiya kuma sai ta tashi bata iya motsa komai a jikinta, kuma ba damar na yi amfani da kudinki ban gaya miki ba " Raina ne ya baci jin abinda yake fada. Na ce." Hamusu wannan wace irin magana ce, ashe akwai ranar da za ka iya nuna mini cewa Gwaggwo ba ta haife ni ba, kudin nawa wanene yake juya mini Ina ce kaine jigo har sai ka tambaye don za ka kai Gwaggwo asibiti wallahi baka taba ba ni haushi ba irin yau." Ya ce." Ki yi hakuri anti Amina ta wani gefan fa Ina da gaskiya, kudi suna iya shiga tsakanin kowa shiyasa sanarwar take da amfani." Na ce." Ka ga malam maganar ta isheni haka don Allah, ka je daga dubu daya zuwa dubu dari biyar har abinda ya yi sama na amince muddin akan gwaggo ne. Sai ya fara godiya ban jira na saurari sauran maganar ba na datse kiran na fita falo. Anti Yagana tana kicin tana aikin karin kummalo Fadila tana taimaka mata Yusi da sauran yaran sun fito bakin famfo suna ta burush da wasa da ruwa. Na dan jingina a jikin bango a sanyaye na ce." Anti Yagana mun tashi lafiya ya hidima?" Ta amsa hankalinta yana kan abinda take yi, na ce.'' Ina ganin gobe asubanci zan yi zuwa kano Gwaggo bata da lafiya yanzu nan Hamusu yake gaya mini jikin nata sai a hankali." Ina dire maganar da take bakina Yusi ya zo ya tsaya da burush dinsa a hannuna. Anti Yagana cikin alhini ta ce." Allah sarki Gwaggwo ciwon har ya kai ace bata san wanda yake kanta ba, kenan tana asibiti a kwance." Na ce." Ina fa, tana gida saboda shashancin Hamsu bai gaya mini ba har sai da ciwon ya ci k'arfinta wai ya kaita asibitin murtala da farko yanzu kuma abin yayi tsanani shine fa ya kira ni yake gaya mini da abin haushi wai yana neman izini zai yi amfani da kudina. Ta ja tsaki tana fad'in." Wauta da rashin hankali shikkenan don ya d'auki Gwaggwo ya kaita asibiti da kudinki sai ki ce masa don me, ya ba ni haushi wallahi." " Wallahi ni ma ba ki ji yadda raina ya baci ba wannan ai shiririta ce rashin lafiya ya wuce komai, kuma ko dukiyata zata kare akan nemawa Gwaggwo lafiya anti Yagana wallahi ba zan damu ba" Ya girgiza kai tana cewa." Kwarai kuwa ai Ido ba mudu ba ya san kima." "Mama wai Gwaggo ce bata da lafiya?" Na dube shi ya zuba mini ido da yanayi na damuwa a tare dashi. Na ce." E, itace amma jikin da sauki alhamdulillahi." A sanyaye ya ce." Mama idan za ki je zan biki don Allah." Ya fad'a muryarsa har tana rawa, sai ya ba ni tausayi ni ma na ji idona ya ciko da kwalla dama daurewa kawai nake yi. Haka muka karya a daddafe har yaran suma gabad'aya jikinsu ya yi sanyi ganin yadda muke cikin alhini da damuwa Yusi dai ya takure a kusurwar kujera har da kuka sai da anti Yagana ta rarrashi tukkuna ya yi shiru. Garba almajirin anti Yagana ya shigo ya ajiye robarsa a bakin kicin ya shigo falon muka gaisa anti Yagana ta ce ya yi maza ya zuba ruwa a diro amma kafin nan ya fara wanke shi. Har ya juya zai fita sai ya tsaya yana kallon Yusi ya ce." Ka je in ji wannan din nan yama sunansa?" Ya tsaya yana tunani. fadila ta ce." Bak'on da suka zo tare?" Da sauri ya daga kansa yana cigaba da cewa." E shi ya ce na kira shi yanzu ya je Babansa ya kira waya za su gaisa." Na dubi Yusi da mamaki a tare da ni, dama duk safiya Yana kiran waya don su gaisa, da farko da Garba ya ce ya je na d'auka Sukairajun yana buk'atar wani abu ne bayan karin kummalon da aka kai masa. Yaron ya tashi da saurinsa sai na dakatar dashi ina fad'in." Yusi dama Baban yana kiran waya ne ku gaisa kullum?" Ya ce." E wataran ma har ya ce na bawa su Arif da Sultan su gaisa, ko Arif?" Ya fad'a yana kallonsa. Ya ce." Eh hakane har ya ce a gaishe daku bakidaya.'' Na gyada da mamaki fal a tare da ni. To shin wai me mutumin nan yake nufi ne? Ni ban ma ga amfanin zaman Sukairaju a tare da ni ba, kuma yaro dai ni na haifi abina ba za a yi wannan munafurcin da ni ba, ka sake ni amma ka dinga bibiyar 'yan uwana har da yaron da na haifa da wani namijin. Na ce ." To koma ka zauna ba za ka je ba." Anti Yagana da sauri ta ce." Akan me?" Shiru na yi kawai Ina kallonta da mamakin neman dalilin da take yi wanda ta fi kowa sani. Tana kurbar kunun gyadar da ta tsiyaya kofi ta ce." Ki kyale shi kawai ya je, idan kuma ba so kike ki fito da komai fili ba, ta inda ya fi ki wayo kenan, yadda yake tafiyar da lamarin a siyasance sai ki zuba Ido ki ga iya gudun ruwansa." Na yi shiru Ina nazarin maganarta. Ni dai da ta barni zan datse alakar ne daga yau din, shi ma Sukairajun na sallameshi don ban ga amfanin zamansa a tare damu ba illa dorawa masu gidan nauyi da ya yi." Kimanin minti ashirin yaron ya yi da fita sai gashi ya shigo ya zauna yana kallon anti Yagana ya ce." Baba ya ce na gaya miki zai kira ki yanzu." Da sauri ta ce." To shikkenan Yusifa." Kawai na saki baki ina kallon ikon Allah. Gabad'aya abincin ma da nake ci sai ya fita daga raina na zuba mata ido a lokacin da ya kirata suna magana akan rashin lafiyar Gwaggwo. Anti Yagana ta saki jiki da baki tana ta jadadda masa yadda Gwaggwon take jin jiki har da ce masa tana kwance bata iya motsa komai na jikinta. Da yake handsfree ta sanya wayar ina jin muryarsa tar yana cewa." Ni muna gaisawa da Yusuf na ji ya fashe mini da kuka koda na tambayeshi shine yake gaya mini kakarsa ce babu lafiya kukan yaron ya daga mini hankali kwarai da gaske dalilin da ya sanya ma kenan na kira ki domin na tabbatar ya gaya mini duk yadda aka yi, zan yi waya asibitin Malam din duk abinda ake bukata game ba zai gagara ba idan ma gado za su bata hakan zai fi sauki Allah Ya bata lafiya." Anti Yagana tana ta amsawa da Amin Ya Allah, mun gode sosai da kulawa Allah ya kara arziki da wadata." Suka yi sallama ta juyo tana kallona raina a tsananin 'bace na mik'a hannu dukkunsu har shi Yusi din ba su ankara ba na kife shi da marin da ba tabbatar zai gigita shi . Illai kuwa a ki'dime ya tashi ya yi hanyar waje hannunsa dafa da kumatunsa hawaye suka fara kasa tsere a kuncinsa. Anti Yagana ta rufe ni da fad'a tana fad'in." Sai kin je kin tsiyayar masa da ruwan ido haka kawai saboda zalinci zaki kifa masa wannan mugun marin me ya yi miki? Lefin dai ba zai wuce ya gayawa mijinki magana ba, shikkenan fa sai ki lahanta shi.'' Shiru na yi ban tanka mata ba kawai na tashi da zumar barin wajan. Yaron da yake tsaye a bakin kofa ya d'auka dukansa zan sake yi ya fita a guje yana sheshsheka. D'aki na shiga na zauna a gefan katifa kaina a daure domin duk yadda na kai ga ganin na hasaso abinda mutumin nan yake nufi a kaina na kasa ganewa. Shin wai ko ya manta da cewar ya sake ni ne, wane irin munafurci ne wannan da neman lallai sai ya d'ora mini lefi. Ka sake ni ka fita daga sha'anina mana. Wayata na d'auka da sauri kiransa zan yi domin na ji shin me yake nufi da ni ne. Kamar yana jiran kiran nawa karaf ya daga. A kaurare babu gaisuwa balle girmamawa dalili duk ya zubar da mutuncinsa a idona bana son mutum munafiki. Na ce." Ban gane abinda kake nufi ba, ko ka manta cewa yanzu babu wata alaka da take tsakanina dakai? Ina ruwanka da bibiyar abinda ya shafe ni. Gwaggwo dai mahaifiyar mijina ce wanda mutuwa ta yi mana kutse ta shiga tsakani, na tabbata kuwa a duniyar nan ba zan sake katari da namiji mai nagartarsa ba. Kana ta bina da sharri, ka yi nan ka 'bata ni, ka bi nan ka 'bata ni, to ta Allah ba taka ba, ka ja tsumman rayuwarka, ba ma buk'atar ko kwabonka, ba na son munafurci ni." Cikin nutsuwa kamar bai ji zafin maganganuna ba ya ce.'' Ai na mayar dake dama na yi ne domin ya zama gargadi a gare ki. Kuma ba don ke nake tsaye akan abinda ya shafeki ba, saboda wasu dalilai ne, ke ki ka haifi Yusuf amma ya fi ki hankali, kuma saboda shi din na shiga lamarin, ai na san kakarsa ce ko ba itace ta haifi Aminu Salihi ba." Cikin takaici da b'akinciki na furta." Ban mayu ba, wallahi ban mayu ba na saku har abada ni dakai dama can ba a son raina aka yi ba, ba zaka tozartani ba wallahi ko maza sun kare a duniya ba zan zauna da kai ba, kuma ko mutuwa Gwaggwo ta yi menene abinda ya dame ka, babu ruwanka ba na son munafurci." Na sake maimaita kalmar munafurci domin na tunzurashi. Bai tunzuru ba a tsanake ya ce." Sai ki yi kuma ni dai na mayar dake shekaran jiya na yi sakin jiya da safe kuma na kudire a raina na mayar dake yanzu kuma na sanar miki, don haka har yanzu kina karkashin ikona." Da sauri ya yanke wayar kamar ya san abinda yake bakina mai muni ne tabbas da bai kashe wayarsa ba sai dai ya ji ruwan ashar a kunnansa saboda yadda zuciyata take a tunzure. Na kasa motsi daga inda nake gumi na yanko mini tsabar tashin hankali kamar yadda ya fad'a a musulunce na mayu tunda ko jini daya ban yi ba kuma ka'idar musulunci jini uku ne na fita daga idda. Hawaye masu zafi suka fara karakaina a kumatuna. Anti Yagana ta shigo d'akin da karsashinta ganin yanayin da nake ciki ya sanya ta d'an yi sanyi ta tsaya tana fuskantata..."Menene kuma?" Tambayar da ta yi mini kenan. Cikin k'unci da takaici na ce." Anti Yagana a wannan karon dole ki yi hakuri na d'auki mataki da kaina domin siyarwa kaina mutunci. Yadda na lura da mutumin nan bashi da mutunci ko kad'an kuma yana yi wa mata kallon wulakantattu idan ba haka ba me zai sanya ka saki mace haka kawai babu hujja mai karfi saboda kawai jin dadi gobe kuma ka ce ka mayar da ita addinin bai ce haka ba Anti Yagana ki zauna ke kanki ki dubi lamarin nan a tsanake kada soyayyar da kike masa ta sanya ki danne lefinsa ba fa daidai ba ne abinda ya aikata mini." Jiki a mace ta ce." Na sani wallahi Amina, kuma bayan ke wallahi tallahi babu wanda ya kai ni jin ciwon sakin da ya yi miki, ni yadda na fahimta kamar bashi da ilimin addini mai zurfi boko ce kawai take dawainiya dashi shiyasa yake ganin kamar abinda ya aikata ba wani lefi ba ne. Abu na gaba kuma kin san shi, abinda ba na sha'awar ya kasance da ni a rayuwata wallahi kema ba na sha'awar ya faru dake, ba na yi miki sha'awar zawarci da lissafin aure don ma Allah Ya takaita gidan alhji Muntari ba ki haihu ba, wannan dalilin ya sanya nake ta dannarki ki yi hakuri ki zauna kowace mace tana da kalubale." Na ce." Anti Yagana kada ki ce na ki jin maganarki wallahi ba fahimci abinda kike gudu, amma dai don girman Allah wannan karon ki kyale ni da mutumin nan kada ki shiga ciki ki ja bakinki ki yi shiru kawai ki zuba mini ido." "To wane shiri za ki yi akansa kin san dai shi namiji ne ke kuma mace tunda kuma ya ce ya mayar dake bafa yadda za ki yi dole ha'kuri ne naki." Na sani anti Yagana ba shirin da zan yi akansa amma ba zan koma ba kamar yadda yake tsammani wallahi sai ya tako kafarsa garin nan." Ta gyada tanà d'an murmushi ta ce." Abu me sau'ki ai tunda yana sonki za ki gan shi kuwa. Ban ce mata komai ba har ta kama hanya ta fice daga dakin. [8/31, 4:42 PM] Aunty B: 70 Tun cikin dare na kammala shirye shirye na don haka gari yana wayewa na fito a kintse da zummar d'aukar hanya tunda d'akin da nake yana da bandaki ban fito ba sai da na shirya tsaf tukkuna. Gabad'aya suna falon ana shirin karyawa hadda maigidan a zaune bai fita ba dama ba kasafai yake fita da wuri ba idan juma'a ce. Fitowata ta d'auki hankalinsu gabad'aya na gyara yanayina don ba na so ta dakatar da ni daga kudirin da na yi. A tsanake na ce." Anti Yagana na shirya fa zan tafi kamar yadda muka yi magana jiya wallahi da Gwaggwo na kwana a cikin raina." Tana kallona ta ce." To kin gayawa mijin naki ko dai ?" Eh kawai na ce mata a takaice. Yadda ta zuba mini ido shi ya tabbatar mini da cewa ba ta yarda da amsar dana bata bata Yusi yana gefe a zaune ya yi nairainarai da ido saura kiris ya fashe da kuka dan tun jiyan nan dana mare shi bai zo wajan da nake ba. Kallo d'aya na yi masa na kawar da kaina daga kansa domin Ina so na horar dashi akan abinda ya aikata ko don gaba ya kiyaye furta abinda ba shikkenan ba. Cikin sigar zolaya Babansu Fadila ya ce." Madam ba gaisuwa ne ko na yi wani lefin ne kuma." Cike da jin nauyi na ce." Yi hakuri wallahi na d'auka dana fito na gaisheka, gabad'aya hankalina ne baya jikina." Ya ce." Amma dai kya bari ki karya tukkuna sai ki tafi, da za ki bari ma akwai motar da zata tashi karfe goma sha daya na safe sai na kira direban yanzu." Na ce." Anya kuwa zan bari ai ka barshi kawai zan iya shatar motar ma gabad'aya babu damuwa. Cikin dai zolayar dai da ya saba da sigar wasa ya ce." Au na manta Hajiya ce fa uwargidan a wurin Yallabai." Murmushi kawai na yi na dubu anti Yagana tana tambayata yaushe zan dawo.' Na ce." Nan da sati guda in sha Allahu zan dai kira ki idan zan taho din." Ba ta ce komai ba ta fara tsiyaya kunun gyadar cikin wani madaidaicin fulas tana fad'in." Ki tafi dashi ko a mota sai ki kurba kina dai sauka ki kira ni." Na ce." To shikkenan in sha Allahu." Hanyar fita na kama na ji muryarsa har tana rawa yana cewa." Mama ki gaishe mini da Gwaggwon." A takaice na ce." Za ta ji in sha Allahu. Na yi saurin ficewa addu'a d'auke a bakina. Ina fita harabar gidan na ci karo da Sukairaju zaune a bakin kofar masaukinsa yana waya. dauke kaina na yi, na sake hade raina sosai. Ido ya zubo mini Ina kallonsa ta gefan idona. Ban tanka masa ba na kama hanyar fita sai ya taso da sauri ya biyo bayana da wayar a kunnansa da maigidansa yake waya saboda yadda yake yin kasa da murya cikin ladabi kamar yana kusa dashi. "Ranki ya dad'e barka da asuba." Muryarsa na ji a daf da ni, na juya ina dubansa yana biyo bayana da wayar a hannunsa.. A takaice na ce" Barka kadai Sukairaju ya kake?" Ya ce." Alhamdulillahi, idan ba matsala Ina iya yi miki rakiya don yanzu muka gama magana da oga ya ce na biyo bayanki." Cikin jin haushi na ce." Makauniyace ni, da za ka biyo bayana ko kuwa ban san gari ba." Ya girgiza kai cikin ladabi ya ce." Ko daya kulawa ce da kuma bin umarnin maigida." Na ce." To ka kira shi ka gaya masa na ce ba na son kulawar wannan wace irin masifa ce ne ." Sai ya tsaya ya yi sararo. Na ja tsaki na fara tsayar da abin hawa shi kuma ya fara laluban wayarsa da sauri ya kara a kunne yana cewa." E to ga mu nan ni da ita atare a bakin titi tana tsayar da mashing tana tare da k'aramar akwati." Ina jin sautin muryarsa amma ban ji abinda yake cewa ba. Daidai lokacin adaidaita sahun dana tsayar ta yi parking na yi saurin shiga. Shi ma da sauri ya zagaya ya zauna kusa da direban shi kuwa ya ja babur din ya hau titi. Takaici kamar ya kasheni, ni wulakata mutum ba dabi'ata ba ce, kuma ba na so na fara akan mutumin nan tunda na lura shi ma yana gyara hanyar abincinsa ne, kuma duk umarnin da aka bashi dole ya bi. Ban ce masa komai ba har muka isa tasha na fito, shima ya fito da kudi ya biya direban ya zo yana ko'karin kar'bar akwatin hannuna. Na ce." Kira mini ogan naka a wayarka." Da sauri kuwa ya fito da wayar daga gaban aljihunsa ya kira shi ya miko mini wayar kafin ya daga na matsa can gefe wajan da babu hayaniya sosai duk da safiya ce amma tashar cike take da jama'a. Yana d'agawa ya fara da cewa." Sukairaju ya aka yi, na gaya maka duk inda ta sanya kafarta ka ajiye taka anan ka kula sosai da ka ji ko?" Na ce." Bashi ba ne ni ce Amina." Ajiyar zuciya ya sauke ya furta a Ina ki ka ajiye wayarki ina kira baki daga ba." Lokacin da ya kira tana cikin handbag d'ina kuma na ji kiran ina sane ban daga ba. Na ce." Tana hannuna wayar ba ni da lokacin d'agawa ne." "Okey na ji, ina za ki je da sanyi safiya haka harda akwati kin san duk inda ki ka nufa ba ki tsira ba tunda da aurena a wuyanki." "Shiyasa kenan ka bada tsarona saboda kada na gudu yawon bin maza ko." Shiru ya yi bai tanka mini ba. Na ce." Idan kana kan layi to don Allah ka umarci wannan gardin da yake bina a baya ya koma, ko kuma ya tattaro ya dawo karkashin aikinka dan banga amfanin zamansa a gidan mutane ba face dora musu nauyi da ya yi, domin ni na gaya maka ban mayu ba har abada zama ya kare a tsakaninmu." Hankalinsa a kwance ya ce" mutan gidan ne suka ce miki sun gaji dashi saboda yana dora musu nauyi ko kuma sharri ki ka yi musu." Da sauri na tari numfashinsa ." Sai sun fad'a sannan za a gane yanayin rayuwa ya za a yi baligin mutum kamar wannan ka zo ka ajiye shi a gidan mutane da sunan bada tsaro akwai wani tsaro ne wanda ya wuce wanda Allah yake ba ni tun kafin a haife ni." "Zan kira anti Yaganar na ji shin cewa da yawunta ne ki ke fad'in hakan, na san halinta da karamci ba za ta ci zarafin bako ba." Jin abinda ya ce sai jikina ya d'an yi sanyi nasan halinsa tsaf zai iya kiranta ya tambayeta. Kashe wayar na yi ban tsaya saurarar abinda yake cewa ba. Kafin na mikawa masa abarsa ya kara kira na daga wannan karon cikin tsare gira da kaurarriyar muryar da babu wasa ya furta." Ki gaya mini Ina ki ka nufa yanzu domin na ji hayaniya da karar ababan hawa hala kina cikin tasha ko?" Na ce." Eh ina tasha zan nufi kano domin duba jikin Gwaggwo da izinin Allah, zan kuma biya na gaishe da Hajja." Ya sassauta yana fad'in." Na amince dai ki je ki duba Gwaggwon amma ban amince miki zuwa wurin Hajja ba, ke kwata kwata ma ba na so asan kin shiga garin, ki zauna a gidanku kawai kwanaki biyu zan gama yi muku shiri sai ku biyo jirgi ku dawo gida ga'badaya." Na ce." Gaskiya ba zan iya shiga garin kano ban je wajan Hajja ba sai da ka yi hakuri.'' Kai tsaye na fadi hakan domin a karon farko na fahimci akwai abinda yake b'oyewa dama na san duk abinda yake faruwa ba ta sani ba." Ya sake sassauta murya cikin sigar rarrashi ya ce." Na ji kije amma kada ki gaya mata duk abinda ya faru tsakaninmu sanin kan ki ne bata da lafiya." Na ce." Ai ta inda aka hau ta nan ake sauka Yallabai, ai ba auran 'yar tsana muka yi ba sai da waliyyai da shedu suka shaida to me zai sanya kuma a boye musu saki yana da kyau ta sani yanzu saura igiya biyu." Diriricewa ya yi ya fara fad'in." Ki saurare ni ki ji, na gaya miki wallahi muddin ki ka sanar da Hajja wani abu sai na sa'ba miki, kin ji na gay......Datse wayar na yi Ina jin wasai a cikin raina na tabbata ta wannan hanyar ma kadai zan hukunta abina. Ya yi ta kiran wayata ban daga ba, da ya gaji sai ya kira ta yaron nasa, kimanin minti goma suna magana kafin su gama wanda ni lokacin ma na gama da wani direba inda na d'auki shatar mota guda na biya.. Ya k'araso yana tambayar direban yadda muka yi duk ya gaya masa ai na riga na biya ba tare da ya dube ni ba yake gayawa direban tare za mu tafi. Na dubi direban ina fad'in.'' Ni da na biya ka kudin motar umarnina zaka bi ko nasa." Cikin ladabi ya d'an risinar da kansa ya ce." Ranki ya dad'e umarninki zan bi, amma yana da kyau mu tafi tare dashi tunda yana tsoronki ne kin san fuskarki da ta maigidanki ba 'boyayyiya ba ce, ni na yi mamakin ma ganinki cikin tashar nan. Jin haka ya sanya da sauri na bude motar na shiga domin sam ban yi wannan tunanin ba yanzu abin sai ya zama magana da yayatawa kafafen sadarwa. Na dubi Sukairaju da yake ta ko'karin sanya akwati a bayan mota na dan leka ta tagar motar a nutse na ce." Ka je ka taho da Yusi ina nan ina jiranka." Yadda ya amsa da sauri shi ya tabbatar mini da cewa bai kawo cewa dabara na shirya masa ba. Ina ganin ya shiga adaidaita sahu. Na dubi direban da yake jingine a jikin motarsa na ce." Ka shigo mu tafi na gama magana dashi ya koma gobe zai biyo bayana da yarona." Ya d'an yi jim yana kallona kamar bai yarda ba, na 'bata rai tare da cewa." Ka ga idan ba za ka je zan fito na nemi wata motar menene hakane?" Ya bude motar ya shiga ya zauna a mazauninsa jikinsa duk babu k'wari haka ya kunna motar wani abokinsa ya zo ya tsaya suka d'an yi magana kafin ya bar wajan shi kuma ya ja motar muka fita daga cikin tashar sai sannan hankalina ya kwanta. Bayan mun d'auki hanya sosai na kira Hamusu domin jin a ina aka kwana nasan tunda mutumin nan ya yi ruwa da tsaki akan lamarin nan da wahala gwaggo bata kwana asibiti ba. Illai kuwa muna gaisawa ya fara da cewa." Yanzu nan da na fito daga wanka nake shirin kiranki wallahi, jiya wajan goma da rabi na samu kira daga maigidanki ya ce mini mota tana zuwa daga asibitin Malam za ta d'auki Gwaggwo babban likita zai dubata sosai. In takaice miki dai Gwaggo tana can an bata gwado kuma jiki da sauki alhamdulillahi na dawo gida domin na yi wanka, anti Amina ki kara yi mana godiya a wajansa lallai yana abinda ya dace da dukiyarsa wallahi anti Amina d'akin da aka kwantar da Gwaggo daban yake da sauran ita kadai ce ba hayaniya kuma tun jiya da daddaren likitoci suka ta zaryar shigowa dubata." Jikina ya d'an shika kad'an jin yadda Hamusu yake yi mini bayani kamar ya fashe da kuka sai godiya yake yi. Cikin raina na ce.' Haushinka yake ji Hamusu amma saboda iya taku da neman suna ya dabaibayeka da alherinsa ta inda da wahala ka hangi kuskuransa. Na ce." Babu damuwa Hamusu ai Gwaggwo ta wuce komai, ni ma gani a kan hanya in sha Allahu daga zarar na sauka zan kira wayarka." Babanmu na kira na gaya masa ina kan hanya. Na kira Sahura itama na sanar da ita, daga nan sai na fara tunanin inda zan sauka, ba zan iya zuwa gidan Hajja ba gaskiya gidanmu kuma babu spece d'akin da na yi zawarci Ummansu Saminu tana kiwon kaji. Kawai sai na yanke shawarar sauka a gidana na kuntau. Yana kulle har yanzu shagon ne dai ake ta hada hada a cikinsa dama mun yi da Hamusu cewa idan auransa ya tashi zai zauna a ciki gidan to an samu tsaiko ne daga bangaran budurwar da yake nema babanta ya ce sai ta yi karatun likitanci shi kuma ya'ki ya canza wata ya dage sai ita yanzu dai an kai kudi an sa rana shakara uku mun ci shekara daya yanzu saura shekara biyu. Sake kiransa na yi a karo na biyu na umarce da cewa ya sanya yara su wanke gidan su gyara shi sosai, shekara kusan biyu dole a samu datti. Ya ba ni tabbacin cewa kafin na sauka za a kammala. Koda muka isa ban fito ba saboda Ina gudun idanun mutane can tsallaken titin da muke na hangi masu sayar da abaya da hijab da nikab na fito da kudi na ce wa direban ya je ya sayo mini nikab. Ya kawo mini na rufe fuskata sai kwayoyin idona kawai ake gani. Na kira Hamusu na sanar dashi. Minti talatin a tsakani ya k'araso kan sabon babur d'insa da ya saya. Na fito daga motar Ina yi wa direban sallama shi kuma sai risinawa yake yi. Har na hau babur din na ce da Hamusu ya dakata dubu biyar na sake bashi bayan kudin motarsa dana biya shi tun a tashar garinsu. Ya dinga godiya kamar ya ari baki, har dai Hamusu ya ja babur din ban daina jiyo sautin muryarsa ba. Mun hau titi sosai ya ce.' anti ina za mu je ne? Gida zan kai ki ki huta ko kuma asibitin zan wuce da ke." Na ce." Hamusu kai ni asibiti na fara duba jikin Gwaggo hankali ya fi kwanciya." Yana yar dariya ya furta." Ai fa Gwaggwo jiki alhamdulillahi wallahi yau ta ci abinci sosai, kuma ta d'an ta'ba hira amma dai yanzu da na fito daga asibitin bacci take yi." Na ce." Fara kaini dai na ga yanayin jikin nata Hamusu." Ya ce.'' To anti Yusi fa a Ina ki ka baro shi a can wajan su anti Yaganar." Na ce." Eh can na baro shi Hamusu." "Àmma na so kin taho dashi anti ko dan Gwaggwon." Na ce." Ai wata'kila wani satin Anti Yaganar za ta zo nasan kuma tare za ta zo da yaran. Ni kaina tafiyar ai bata shiri ba ce shine dalili." Na gaya masa haka dan maganar ta mutu. To alhamdulillahi yanayin yadda na ga jikin Gwaggon alhamdulillahi ya yi sau'ki sosai, mun d'an taba hira kad'an dukda ba sosai muryarta ke fita ba amma dai Ina fahimtar abinda take cewa. Bacci ya kara surarta. Likitan da yake kan duty a lokacin ya tabbatar mana da cewa hakan shine samun lafiya domin a hankali duk sai ta rama bashin baccin da ta ci. Kai tsaye gidana na kuntau Hamusu ya wuce da ni bayan mun fito daga asibitin kenan. Na ji dad'in yadda na ga ya sake k'awata shagonmu ga kawunan keke nan na surfani da kuma na dinkin zare daban daban yara suna ta aiki ko'ina haske tare da decoration masu kyau ga hotonan jaruman film nan wad'anda suke tashe irinsu Mommy gombe Aisha Najamu Ruky Alim Maryam Yahaya Asma'u Gwarwashi Maryam Labarina da sauransu sun an yi banner dinsu cikin styles na d'inki daban daban. Ga kuma na mutane nan kala kala an gama a rataye Akwai sabbi ido daga cikin yaran da suke aiki wad'anda na sani kad'an ne daga ciki. Na tsaya tare da cire nikab din fuskata domin mu gaisa. Gabad'aya suka mike wad'anda muka saba da su a can baya suka dinga dariya anti Amina ziyarar bazata." Ina dariya na ce." Eh mana kuma na ji dad'in ganinku lafiya da yadda aka samu cigaba na gode muku sosai." Kusan a tare suka ce." Mune da godiya anti Amina, Allah Ya sa a fi haka d'aukaka Ubangiji Allah Ya raya miki zuria." Na amsa da amin cikin jin dad'in addu'ar da suka yi mini na wuce ciki Hamusu ya biyo bayana da akwatin dana zubo kayana Yana sake jadadda mini irin yadda 'yan film ke kawo dinkunansu wurin. [9/1, 5:22 PM] Aunty B: 71 Na ce." Wallahi na gani Hamusu an samu cigaba sosai, kana mutukar kokari kwarai da gaske, ai kyau da ingancin aiki ne ya sanya suke turereniyar zuwa shagon tabbas ya kamata a wannan shekarar kai da Usaini na kira ku ga gwarazana, domin shi ma ta b'angaransa alhmdullhi komai yana tafiya gashi dai bai kai shekarunka ba amma yana da fasaha da nasibi." Ya ce." sosai kuwa anti Amina Usani yana k'okari don kwanaki ma dana je duba shagon na ga har da 'bangaran huluna da takalma bayan na atamfofi da leces wanda dasu aka 'bude shagon. Na ce." Ba a fi wata uku ba ya kira ni da shawarar hakan da yake ya san ta kan huluna ya ce mini za a samu alheri sosai, na ce to shikkenan sai mu jarraba mu gani, cikin ikon Allah kuma ana ganin cigaba kasan da kad'an ake kai wa matsayin babba." "Gaskiya ne anti, yanzu ki huta zan je bakin titi na sayo miki abinda za ki ci." Na ce." Da kuwa ka kyauta Hamusu don wallahi wata irin yunwa nake ji, ka ga kunun da anti Yagana ta had'o ni dashi ko kad'an ban kurba ba." Da sauri ya kama hanyar fita Yana fad'in." Ai dole anti ki ji yunwa bari yanzu zan dawo in sha Allahu Ya fice a gaggauce. A tsanake na dubi ko'ina na gidan tsaf kamar mutum yana rayuwa a ciki har da sabon kafet Hamusu ya shimfida a tsakiyar falon domin dai na san kalar wanda na fita na bari ba irinsa ba ne. Girgiza kaina na yi cikin zuciyata na furta abu ne mai mutukar wahala a wannan zamanin a samu mutane masu nagarta da kyawun zuciya kamar iyalin Gwaggwo. Yaya Aminu da d'an'uwansa Hamusu mutane masu hankali da sanin ya kamata. Jakata na ajiye domin jin ana kiran sallar magriba da so samu ne na fara yin wanka amma ba hali saboda duhun magariba ya shigo sai an yi Ishai tukkuna. Ko matsawa ban yi daga wajan ba kira ya shigo wayata dake cikin handbag dina. Ina duba wanda ya kira na ajiye ban daga ba na nufi bandaki ina jin tana ta ringing ta katse wani kiran ya sake shigowa, babban abinda ya tsana shine ya kira waya ba a d'auka ba, ina jin ma ni kad'ai ce nake masa wannan shegantakar shiyasa yake ganin abin banbarakwai yake kuma yi masa zafi. Ya kira ya fi sau shida ban dubi wayar ba. Sallolin da aka bini bashi na rama. Kafin na d'ora ta magriba da ta riske ni. Ina sallamewa ya sake kira idona akan wayar ta katse na cigaba da jan carbi mai lamba da yake cikin yatsana. Koda Hamusu ya dawo shima sai da ya jira na kammala tukkuna. Ina dubansa ya ce." Anti ko kin kar'bi darika ne kina wazifa kema?" Kai na girgiza na ce." Ko daya Hamusu ka'idata ce dama ina zama bayan magriba na yi wa Annabi salati dubu daya muddin kaga ban yi ba kuwa wani muhimmin abu ne ya rike ni." Ya gyada yana fad'in." Allah Ya ba mu ikon yin ko yi daku anti." Na amsa da Amin Ina duban uban ledojin da ya lodo. Na ce." Wannan duk abincin ne Hamusu." Ya ce." A a anti akwai kayan shayi da wasu abubuwan da na san lallai za ki bu'kace su." Na ce." Sannu na kuwa gode wallahi." Yana bud'e ledojin ya ce." Af anti kin ga zan manta ko ina kan hanya Yallabai ya kira ni a waya yake tambayata muna tare na ce masa e ba ki jima da sauka ba, na fito sayo miki abinci ne, shine ya ce idan na dawo na kira shi zai yi magana dake na ce ko wayarki ta mutu a cikin jakata baki sani ba." Na ce." A a ina da caji wata'kila kawai matsalar network ne." Ya fara laluban wayarsa wanda ya tabbatar mini da cewa shi din zai kira ban ce masa komai ba yana jin wayar ta fara shiga ya miko mini cikin nutsuwa kuma ya tashi ya fita. Yana d'agawa na ji sautin muryarsa ya fito sosai tunda handsfree wayar take. Tsigar jikina ce ta motsa jin maganarsa sautari dama hakan tana faruwa da ni muddin zan ji ko na kalli wani bangare na jikinsa sai jikina ya motsa ban san menene dalilin da ya sanya motsinsa ko maganarsa ko wani abu da ya danganci jikinsa ke tayar mini da hankali ba, kuma duk mazan dana aura akansa kawai nake jin hakan. Na d'an samu nutsuwa tukkuna a nutse na ce." Ba shi ba ne ni ce ina yini." Bai amsa mini ba ya furta." Abinda ki ka yi a ganinki shine daidai ko? Kin shirya wulakanta ni a idon mutane da abokaina, kina so ki nunawa duniya kin fi karfin kowa ciki har da ni mijinki da wad'anda suke gaba dake ko Amina." A nutse na ce." Me na yi maka yanzu?" 'Kwafa ya yi ya cigaba da cewa." Sukairaju ya gaya mini yadda kuka yi dashi, idan ba ki shirya wani abun ba me zai sanya ki guje masa harda yaron da ki ka haifa kin bar shi a can me hakan yake nufi?" Shiru na yi masa ban ce uffan ba. Yadda dai yake maganar a kufule shi ya tabbatar mini da cewa yana cike da b'acin raina wanda ni dama hakan nake so, na lura kuma zargi yana daya daga cikin d'abiunsa wanda kafin ya daina sai an yara. Jin ban ce masa komai ba sai ya kara hasala." Na gaya miki dai kaga ki kuskura ki gaya Hajja wata maganar da zata daga mata hankali kin fi kowa sanin yadda ta d'auki lamarinki jin wata magana ka iya janyowa ciwonta ya tashi." Na ce." Kasan da hakan me ya sanya ka aikata, ai kai ya kamata ka kiyaye abinda zai sanya har ciwon nata ya tashi ba ni ba, ba zan munafurceka ba na gaya maka ko ban gayawa kowa cewa ka sake ni ba ita da ta had'a auran dole ta sani yanzu babu aure a tsakaninmu." Cikin inda-inda tare da diriricewa ya furta." In ji uban waye ya ce miki babu aure a tsakanina dake, na gaya miki tun jiya na mayar dake kuma wallahi kin mayu, ko kin so ko kin ki." Na yi shiru ban ce masa komai ba. Ya sake sakin ajiyar zuciya duk Ina jinsa ya ce." Yanzu kina ina, a gidanku ki ka sauka dai ko. Babu wata damuwa na ce." Ina gidana na kuntau a can na sauka dan zan fi sakewa." Cikin tsananin tashin hankali ya ce."Ki ka sauka a gidanki hakan me yake nufi kenan, ba ki da gidan iyaye ne?" Na ce." Ni nasan kaina haka zalika ma wadda ta aura maka ni ta san wacece ni, mahaifina ya san wacece Amina, idan zan bar gari na tafi wajan da babu idon wanda na sani sai bare wallahi tallahi na tabbatar da cewa mahaifina ba zai zarge ni ba to balle kuma anti Yagana data saki nono ta ba ni, amma ina mamakin yadda aka yi kai kake yi mini mummunan zargi irin wannan, motsi kad'an zan yi a tuhuma yake kayi maza ka ya'ki zuciyar da take kawo maka illolina dan na rantse maka da Allah idan kana biye mata daf take da ta tarwatsa maka rayuwa." Shiru ya yi bai yi magana ba na ce." Zan bashi wayarsa idan baka da abin fad'i." Gyaran murya ya yi ya dan ayi amfani da sanyayyiyar muryar da ya arota a lokacin yana fad'in." Zan shigo kanon gobe ki zauna a shirye zamu koma tare." Na ce." Nan fa daya ai ko zan koma auranka to fa ba zan koma legos ba wallahi, zan zauna anan din ba ni da damuwa duk lokacin da ka yi ra'ayi ka zo kawai." Ya ce." Hakan da ki ke yi shi yake sanyawa zuciyata wasiwasi akanki. Nafi kowa sanin cewa ba ki da hakuri ta fannin jima'i, me yasa zan barki a wani wajan ni kuma ina can uwa duniya ki cire ranki ba ni da ra'ayin raba gidana. "Tunda ba ni da hakuri ta fannin jima'i shiyasa kake zargina da zan iya neman namiji idan buk'ata ta motsa mini baka kusa." "Ni ban fad'i haka ba Amina, wani abu ne nake ji game dake a can kasan zuciyata na rasa yadda zan cire shi kin san ranar da ki ka wayi gari a gidana ban rufe miki ba na gaya miki ni mutum ne mai kishi, a duk lokacin dana tuna wasu mazan sun sanki kafin ni wallahi ba na iya sarrafa kaina Ina shiga wani irin kunci da damuwa." Ban yarda da maganarsa ba dalili nasan zai iya amfani da mayaudaran kalamai a wannan lokacin da ya ga ina nema na yi masa tutsu domin ya shaho kaina. Ai shi mai hankaline kuma mai shekaru ne sannan kuma kishi ba hauka ba ne, mata nawa manzon Allah s.a.w ya aura a matsayin zawarawa kuma ya rayu dasu cikin aminci bai zargesu ba. "Kin ji ko, ki yi hakuri idan Allah Ya kaimu gobe zan shigo garin sai mu tafi jibi, hankalina sai ya fi kwanciya idan kuna kusa da ni." A nutse na ce." Ba zai yiwu ba na gaya maka ba na so mu yi ta jayayya akan hakan yadda nake ha'kuri da dabi'unka a wannan ga'bar ni ma sai ka yi hakuri da abinda nake so." Shiru ya yi bai ce mini komai ba, na dubi wayar na ga mun kai kimanin minti ashirin da wani abu muna magana ana ta janyewa Hamusu kudi. Na ce" Zan bashi wayarsa." Bai ce mini komai naga ya datse kiran. Na ja tsaki a fili na furta shekarunka da iliminka sam ba su amfana maka komai ba. Wai kishi idan dashi din akwai hali da d'abi'a, tunda har yanzu ya'ki aminta da ni, yau ya bijiro da wannan fitina gobe ya bijiro da wata a wannan karon kuwa zan nuna masa ikona babu ruwana da kudi da shekarunsa dole na mutunta kaina. Ban bashi wayar ba sai da na binciketa tsaf domin wata wayar takan ajiye recoding na goge komai sannan da ya shigo ya kar'ba tare da yi mini sallama ya tafi. Sai da na yi wanka tukkuna na zauna a nutse na ci abinci hankalina a kwance yanzu na dan fara samun sasaauci a cikin raina. Kiran anti Yagana ne ya shigo wayata a lokacin da muke magana da Sahura ta whasap tana ce mini gobe da wuri zata zo, na ce ta taho mini da Yusura ta d'an zauna mini tunda sun yi hutu. Cikin fargaba na daga kiran na san dai fad'a ne zan sha shi akan abinda na yi wa Sukairaju ilai kuwa da abinda ta fara kenan yayin da kunnena yake jiyo mini sautin kukan Yusi. "Ke da na ce miki daga zarar kin sauka ki kira ni shine don iskanci saboda kin san abinda ki ka yi baki kira ni ba, kin kyauta Amina, ke duk yadda aka yi dake sai kin b'atawa mutum rai, kin ce mutumin nan ya zo ya d'auki Yusi saboda tsabar rashin mutunci ashe yaudararsa ki ka yi yaro yana ta murna suka tafi tasha suka tarar bakya nan, to gashinan tun jiya yake kuka abincin kirki ya kasa ci. [9/2, 5:52 PM] Aunty B: 72 Cikin ko'karin danne dariyar da take so ta kwace mini na ce." Anti Yagana ki yi hakuri don Allah wannan fad'a haka ko hadiyar yawu fa ba kya yi, ki yi hakuri ni kaina rashin kyakyawan network ne yasa ban kira ki ba amma na sauka tun kafin magriba. Zan kira Sukairajun a waya yanzu gobe sai ya kawo yaron. Amma Yusi ya cika shakiyi wallahi kawai ya sanyanki a gaba yana kuka kamar bai sanki ba." Ta ja tsaki har yanzu da sauran b'acin ran a tare da ita ta ce." Ai duk ke ce ki ka janyo koma menene da farko ai da ki ka nuna ba za ki dashi ba ya ha'kura daga baya kuma ki ka ce a zo a d'aukeshi ya ba zai yi kuka ba." Na ce" Anti Yagana kaina bisa wuyana ki yi hakuri." 'Kwafa ta yi bata ce komai. Na ce." Alhaji Tajudden ya kira ki a waya ne?" Na tambayeta ne domin na san zai iya bi ta kanta wajan ganin ya tilastani." "Bai kira ni ba wani abun ne ya sake faruwa?" Na ce." A a, magana ce dai muke yi ni dashi, ya ce ya mayar da ni, to ba ni da yadda zan yi dole nayi hakurin cigaba da zama dashi kodan farincikinki amma fa ba zan koma legos ba anti na gaji da zaman can wallahi, na amince duk lokacin da ya ga dama ya zo ya same ni anan din sai ya ajiyeni a wani gidan.'' "Wannan kuma tsakaninku ne ke za ki janyo hankalinsa har ya amince da bukatarki, ni menene nawa a ciki." Na ce." Anti Yagana na san zai iya kiranki ya gaya miki ne, ni kuma ga abinda na yanke." "Ni dai hudubata ki bi mijinki Amina wannan ce a tsakaninmu, aure kuma ba inda ba ya kai mutum, da farko ni ma ban so zamanki a can ba amma daga baya dana je na ga wurin da kike zaune cike da tsaro sai hankalina ya kwanta, maslaha ce tsakaninku ni ban ga abin ja'in ja ba, tunda yana da wata matar a can ba lefi ba ne don ya bar ki anan din." "Ni ma abinda na gani kenan, kuma kin ga harkokina sun yi karfi sosai, zamana anan din zai sake kawo cigaba." "Kada dai ki gaya masa haka zai ga kamar da niyyar hakan a cikin ranki yasa ki ka ce za ki zauna, ina ce Hamusu yana tsaya miki akan komai Amina har yanzu zuciyarki tana yi miki sha'awar rayuwarki ta baya ko." "Wallahi ko daya anti Yagana kawai dai zuciyar ce a haka, ko kad'an ba na son zama ina so naga ina juya kudi suna shiga suna fita, kuma ba na so komai na rayuwa ya gagareni." Ta sauke ajiyar zuciya tana cewa.'' Abu ne mai kyau hakan, amma ke za ki yi kokarin shawo kansa ya aminta da buk'atarki don wallahi ni dai ko ya kira ni ya gaya mini ban san abinda zan ce masa ba." Na ce." Zan jajurce akan hakan anti in sha Allahu kuma zai kyaleni. Sallama muka yi, ban bukaci ta ba ni Yusin ba domin zuciyata tana iya karyewa kukan da yake yana ta'ba ni daurewa kawai nake yi. To koda na kira Sukairaju a waya akan maganar yadda za a yi ya kawo mini yaron gobe ya ce mini ai tuni ma sun yi magana da ogansa gobe da wuri za su taso. Na ce masa shikkenan idan sun sauka ya kira ni a waya Hamusu ya je ya d'aukosu tunda ba sanin inda nake ya yi ba. Bacci na yi sosai babu wata fargaba da tsoro tunda gidan ba bak'ona ba ne, bayan haka kuma yaran shago sukan kai karfe daya na dare suna aiki kafin su rufe shagon kuma a bakin titi muke duk dare idan ka farka ba zaka rasa jin motsi ba. Wajan shida da rabi Babanmu ya kira waya dan kiran ne ma ya tashe ni daga baccin da ya kwashe ni bayan sallar da na gabatar. Na daga da dan faduwar gaba domin wayar safe haka take da sanya fargaba ko alheri za a gaya maka idan kaga kira irin wannan dole ka ji wani iri. Sai da naga mun gaisa a tsanake babu tashin hankali a muryarsa sannan hankalina ya kwanta na saki ajiyar zuciya. Nutsuwa na yi ina sauraran maganar da yake gaya mini cikin rarrashi da ko'karin nuna mini cewa na bi mijina ga dukkan abinda ya umarce ni, sannan kuma na yi koyi da Mamanmu wadda ta har ta rasu bata ta'ba yi masa jayayya ba, ya kuma kawo mini misali da ita kan cewa itama haka ta ha'kura da iyayenta da 'yan uwanta ta biyo shi saboda samun ladan aure." Zuciyata ta d'an karye kad'an amma ban saduda ba, yana fara maganar na fahimci inda ya dosa mutumin nan ya kira shi ya gaya masa akan matsayar da na tsaya, saboda ba na son yin jayayya dashi ya sanya na ce masa shikkenan zan bi umarinsa idan hakan zai faranta masa rai. Aikuwa ya dinga yi mini addu'a da fatan alheri wadda har na fara nadamar hakan da na yi masa domin ba har zuciyata na aminta ba. Cikin damuwar hakan Sahura ta zo ta same ni domin goma na safe ma anan ta yi mata tunda ba aiki a ranar. Zuwanta da minti ashirin Hamusu ya zo da kayan abinci da duk abinda zan buk'ata kafin ya wuce asibiti wurin Gwaggwo na ce ya gaya mata da yamma za mu zo ni da Sahura in sha Allahu. Yusura na sanya ta shiga kicin domin ta yi mana abinda za mu ci na ce ta yi da d'an yawa sai mu tafi dashi asibiti amma kafin nan na umarceta da ta fara dafa mini shayi tukkuna na d'umama cikina dan a hautsine nake jin cikina. Ina lure da Sahura sai kallona take yi a fakaice da dai na gaji da kallon da take yi mini na ce." Wai ke don Allah kallon me ki ke yi mini ne? Ina fa kallonki tunda ki ka zauna ki ke bina da ido na canza ne?" Tana dariya ta ce." Sosai kuwa kin canza wallahi wannan kamar ba Aminar da na sani ba ce, wannan kamar an 'bareta daga leda." Na dubi jikina ina son ganin abinda ya sanya ta fadi hakan. Ta cigaba da cewa." Tunda na zauna kamshinki yake surnanowa hancina kamshin ma irin na manya ne wallahi irin kamshin Oga ki ke yi sis, kin ga yadda fatarki take sheki kuwa kin cika kin zama wata 'yar gayu dubu fa faratan yatsun hannunki dana kafafu ki tas dasu. Da sauri na fara duban yatsuna ina fad'in." Ke kam Sahura kin fiye zuzuta abu wallahi, ni dama can haka faratan yatsuna suke ai ba na lalle shiyasa suka yi haske." "Ba haka suke ba wallahi ke kaf fa kin canza launi komai naki ya sauya shekarunki ma sun 'buya." Murmushi kawai na yi domin na riga na san duk abinda zan fada tana da amsar da zata ba ni. Na ce." Ke ma ai kin sauya sosai Sahura kin yi ki'ba da haske." Ta ce." Hum! ciwo nasha fa ki ce kawai na rame sis, gaya miki ne kawai ban yi ba watanni uku da suka wuce na yi 'bari na 'yan tagwaye wallahi nasha wahala sosai har sai da aka yi mini wankin mahaifa. Cike da alhini da damuwa na furta." Amma ba ki kyauta mini ba wallahi, ki tsallaken rijiya da baya irin wannan amma ki kasa gaya mini to menene amfanin hakan." "In banda abinki ai abin alheri ake fad'awa mutum ba na tashin hankali ba, kawai kuma sai na kira ki na ce dake na yi 'bari." Tsaki na ja na furta." Ba ki kyauta mini ba dai." "Kin ga mu bar zancan nan tunda ya wuce, na gaya miki garin zirga zirgar asibiti na ga ana jigila da Alhaji Muntari a asibitin Murtala bashi da lafiya wallahi ba ki ga yadda ya rame ba da alama dai yana jin jiki domin kuwa bai san wanda yake kansa ba suna ta yawo dashi a kan keken nan babu gado, Maman Salimat din ce ma muka gaisa a tsaitsaye itama bata wani gane ni ba sai da na ce mata ni ce Sahura kawarki maman Yusura tukkuna ta gane ni, dana tambayeta ta ce mini za su yi kokarin kai shi asibitin Malam ko Nasarawa amma fa ga dukkanin alamu babu abin domin da da akwai yadda yake cikin tsananin ciwo ba za su kai shi asibitin gwamnati ba." Tunda ta fara maganar jikina ya shika fargaba da tsoron duniyar nan ya dabaibayeni. Na ce." Sahura ni wannan duniyar tsoro take ba ni wallahi, yau ka ji wannan masifa gobe ka ji wata. Ko yau kana tare da mutum amma gobe ace maka ya mutu, wallahi duk duniyar nan ta fice mini daga rai." "Ai mai hankali ne kawai zai yi irin tunanin da kike yi sis, amma wanda ya riga ya auri duniyar ai gani zai yi duk abinda ake fad'a karya ne, ke akwai ma wad'anda basu yarda da mutuwa da ranar tsayuwa ba." Na ce." To Allah Ya shiryesu masu irin wannan tunanin kuma ba ta gaya miki abinda yake damunsa ba." "Gaskiya bata fad'a mini ba, a rikice fa take domin ga dukkanin alamu tun a gida sun ci kuka sun koshi, yadda dai jikinsa ya shika wuya ya langwane hannu ma haka nake ganin kamar ya samu mutuwar b'arin jiki" Cike da tausayi na ce." kome ya janyo masa wannan mummunan ciwon oho, ga nauyi na iyali da yara, gashi shi kuma a iya zamana dashi na fahimci cewa bashi da plan in banda wannan gidan nasa fa ba na tsammanin yana da wata kadara, duk abinda ya samu ya yi bushasha haka tsarinsa yake wallahi ya ba ni tausayi Sahura." Ta ce." Ai don ma ba ki ganshi ba ne wallahi ba za ki ce shi ba ne, duk wannan jikin babu ya zaizaye ya yi duhu." "Allah Ya bashi lafiya in sha Allahu za ki raka ni na dubo shi." Ta dube ni da mamaki." Ki duba shi akan wace hujja da dai kin haihu dashi ne, amma sis yanzu da auran wani za ki je duba tsohon mijinki." "To menene Sahura ciwo fa aka ce, don na duba shi sai ya zama lefi, saboda kawai abin magana bashi da wahala, ke fa da bakinki ki ka ce yana buk'atar taimako, ni kuma ina so idona ya gane mini muddin akwai buk'atar taimako zan taimaka masa wallahi domin ni ma ya taimaka mini ya rike ni da yarana ko yaya ne dole na dubi alherin da ya yi mini a baya." A dan sanyaye ta ce." Ban'ki ta taki ba sisi, amma kin san ba kowane namiji ne zai yarda da uzurinki ba, kin san kowa da irin fahimtarsa." Tsaki na ja na ce." Sahura kyale ni don Allah, ba dai akan oganki kike magana ba, yanzu ma rigima muke yi sai mu d'ora da wannan." "Wace irin rigima kuma sis, ba na son fa sharri mutumin nan na ji labari fa an ce goyaki ne kawai baya yi kuma ba ke ki ke yi masa ladabi shine yake yi miki, har cewa aka yi kin mallaka shi da mahaifiyarsa sai abinda ki ka ce musu a gidan." Tana dariya ta kai k'arshen maganarta da zolaya. [9/4, 11:40 AM] Aunty B: 73 "Sahura duk wanda ya gaya miki haka ya zalince ni wallahi domin kuwa ni kadai nasan da wanda nake zaune, ba zan iya 'boye miki abinda yake faruwa ba sis, amma wallahi kallon kitse kuke yi rogo, da yawa mutane za su dinga ganin ai kakata ta yanke sa'ka saboda mafiakasari mutane sun amince da cewa kudi sune jin dad'i alhalin ba haka ba ne, na yarda da maganar nan da hausa ke fadi cewa ka auri mai zuciya ba mai dukiya ba, mutumin nan yana da tarin matsaloli wad'anda ya bi ya ninke abinsa ba wanda zai gansu sai wanda zama ya had'a mussaman ni dai da nake a matsayin matarsa. Akwai ci dasha kula da lafiya da biyan buk'ata ta aure duk akwai wannan to amma kin san wad'annan abubuwan da na zayyano miki idan babu kwanciyar hankali ba za su yi tasiri ba. Idan zan zaga kaf garin nan Ina sukar mutumin nan babu wanda zai yarda da maganata domin ya riga ya siye jama'a da alherinsa." "Sis ki gaya mini abinda yake faruwa don wallahi ni gabad'aya kin kashe mini jiki, don Allah ki yi hakuri ki zauna a d'akinki." Murmushi na yi Ina dubanta, itama magiya take yi mini na ha'kura na zauna ko bata fad'a ba na san dalilinta bai wuce irin na Anti Yagana ba. Na ce." Sahura zaman bashi ne a wahala ba, abokin zaman shine matsala, ni idan ta ni ne wallahi ba ni da matsala dashi amma fa zan gaya miki abinda ba ki sani ba ya sake ni akan wani abu da yake hasashe kuma bashi da hujja akai." Cikin kad'uwa da tashin hankali ta furta." Saki kamar yaya k'awata, yanzu kina so ki gaya mini cewa babu aure a tsakaninku?" "Ya sake ni shekaran jiya saboda yana zargina. Duk na kwashe abubuwan da suke faruwa na gaya mata. Jikinta ya yi bala'in mutuwa har da 'yar k'walla a kwarmin idonta ta ce." Wato ita dai 'ya mace rayuwarta ta kan kasance cikin 'kalubale akoyaushe duk abinda ta yi ba zata tsira ba, sis na ga dai harkar social media nan da ki ka yi neman na kanki ki ka yi baki taba aikata wani abin assha ba wanda zai zama tambari na zubewar mutuncinki. Kuma mutumin nan ba yaro ba ne a ganina bai kamata ace yana yi miki munanan zargi irin wannan ba, wallahi a wannan zamanin sis da wasu 'yan matan har gwara zawarawa ban ce duka 'yan matan lalatattu ba ne, amma wasu mazan na yanzu sun gane gwara su auri bazawarar sun san ita suka aura akan su kashe kudi wurin auran budurwa daga baya su gane ba kamila ba ce, kuma mata nawa manzon Allah s.a.w ya aura a matsayin bazawara, ko wannan ya kamata a ce wasu mazan na d'agawa mata kafa. Amma abinda na fi fahimta ga mutumin nan yana da zafin kishi wanda dama haka aka ce na maza ya fi na mata, kuma idan ya yun'kuro masa yakan iya kasa sarrafa kansa, amma ai kishi ba hauka ba ne, zai lalata auransa ne kawai bai sani ba, a wannan ga'bar gaskiya ba na tare dashi." Na ce." To kin fahimce ni ashe, Sahura a shirye nake akan wannan dalilin wallahi na tsinke auran nan, ban yi abu tunda kuruciya ba akan me yanzu zan yi, har wanda yake aurena ya gaza fahimtata, koyaushe addu'a nake yi Allah ya kare mu daga rudin zamani. Shekaran jiya ya yi sakin jiya da safe ya ce ya mayar da ni. Ai aure ba abin wasa ba ne, ko 'yar tsana ba za a yi mata wannan wulakancin ba, Sahura dole ne na nuna masa nasan abinda nake yi." " 'Kawata ina bayanki, amma don Allah kada ki zafafa da yawa nasan halinki, ki dubi shekaru da kuma matsayinsa da wad'anda suke k'asansa, dan fa kuskure ya yi kuskure gaskiya." Na ce." Shi me yasa bai duba shekaru da matsayinsa ba, ai gudun zubewar mutunci yake yi a gari to idan bai yi wasa ba sabuwar jarida zata fita a kansa." "A a 'kawata kada ki yi abinda duniya zata san me kuke ciki, ki sakaya auranku don Allah, shi dai sannu a hankali ki hukuntashi amma kada ki fitar da sirrinku, ai dan Adam tara yake bai cika goma ba, bai kyauta miki ba amma ki dubi abubuwan alherinsa a gareki ki rangwanta masa. 'Kwafa na yi tare da cewa." Mu bar maganar nan Sahura ta ishe ni wallahi, yanzu ashe yawo ake yi da ni a gari ana cewa juya shi nake yi, mutane basa tsoron Allah." 'Yar dariya ta yi tana fad'in." Wallahi cikin unguwarmu na ji maganar tana yawo, kuma daga gidanku ta fito Ummansu Hadiza ce take gayawa ma'kota ai kin shiga kin fita akansa da Mamansa sai yadda ki ka yi dasu, Hadiza da ta zauna a gidan ta ga irin zaman da ku ke yi. "Ita Ummansu Hadiza tana d'auka yadda take bin malamai kowa ma haka yake, kin san mai yin abu sai ya dinga zaton wani ma yana yi, ai na gaya miki Sahura wallahi ban ta'ba tsugunawa agaban wani da zummar ya taimaka mini akan mutumin nan ba, kin fi kowa sanin halina. Anti Yagana ce ma da taga abin ya rincabe ta fara biye biye na ce mata ba na so, duk abinda ya tunkaro bawa kawai ya nemi sau'ki a wajan Allah." "Wannan shine gaskiya 'kawata domin babu wani abu da wani mahaluki zai yi maka face ya kara jefaka a masifa, kuma na ji labarin ma an ce Hadizan bata kasar wai ta tafi dubai saro kaya." Ta kare maganar tana dariya. Na ce." Ni ma haka na ji Sahura na ce me Hadiza take so ta zama ne, ai mutumin nawa shi ta kira ya bata jarin kudi zaman da ta yi a wajena ta samu kofa a gabana ya ce mata duk lokacin da wata buk'ata ta tashi ta nemeshi. Wallahi Sahura ashe had'a baki suka yi da Ummansu suka shirya karya ciwo ga Fati wai tana da cancer za a yi mata aiki, duk suka daga mana hankali ni dashi a lokacin ya ba su miliyan shida ya kuma bata kofar tambayarsa duk abinda suke so shi ya d'auka da gaske ne sai da anti Yagana ta bincika ta tabbatar da cewa k'arya suke yi. Kuma maganar fa da nake yi miki lokacin da ya tura mata kudin zuwa Dubai din rikici muke yi don har ya yi sakin ma, bai gaya mini ba itama Hadizan ba ta gaya mini ba sai da Babanmu ya kira anti Yagana yana gaya mata. Girgiza kanta ta yi tare da cewa." Amina Hadiza 'yar uwarki ce, duk inda aka je aka dawo babu wanda ya isa ya raba tsakaninku tunda uba daya ba wasa ba ne, amma wallahi ki yi hankali da ita dan ta gurgud'e miki auren nan ba wani abu ba ne a wurinta, nasan ta fi ni kusanci dake amma kin san wani abu da ban gaya miki ba tun lokacin da abin nan ya faru da aka dinga yawo da sunanki a social media cewa kin ce ke ma a baki hakkin yaranki da Yallabai ya take, na dinga bibiyar lamarin wallahi har acct din da ya fitar da magana na dinga bibiya na kwafo lambar da aka bude acct din na ajiye, wallahi Koda na tsananta bincike akai sai na gano lambar Hadiza ce amma ba kowa ya san tana da ita ba, kuma yanzu ki shiga fece book ki yi sarcin din acct din za ki ga babu shi ta goge, dama ta bud'e ne domin ta 'bata ki." Da mamaki mai yawa a tare da ni na ce." Anya kuwa Sahura Hadiza fa bata da wani boko akanta ina ganin azancinta ba zai iya b'ata damar bude fece book ba har ta yi wannan rubutun." "Itace fa na gaya miki, idan ba ta iya ba zata iya biyan kudi a bude mata ta yi amfani dashi a lokacin wanda ya bude mata ya goge shi gabad'aya." Na ce." To idan na fahimta ta yi amfani da boyayyiyar lambata ne don kada a gane ita ce, tunda ai ina da lambata ko a fece book din ma ina ganin gilmarwarta." "Shine ai abinda na gaya miki da wata wayar ta yi amfani amma da an tabbatar mini da cewa layinta ne kuma tana amfani dashi sa'i da lokaci." Dariya na yi na ce." Lallai Hadiza abin har ya kai haka, to Allah Ya kyauta ke kuma Sahura sannuki da k'okari, na rantse miki da Allah ban ta'ba kawowa zuciyata ita ce ba." Ta ce." Ke dai Allah Ya kyauta a wannan zamanin duk mutumin da Allah Ya rufawa asiri ai yana ganin hassada da bita da kulli na mutane." Wayata na d'auka na duba lokaci sha biyu saura na ce." Sahura kinga sha biyu har ta kusa muna luguden lebe." Na kwalawa Salima kira dake can tana aiki, ta shigo na ce." Kawo mana shayin nasan kin gama dashi." Ta ce." E Mama abincin ma na kusa." Na ce." Sannunki diyar albarka ranar bikinki ban san wane shagali zamu sha ba." Uwar ta fashe da dariya tana kallonta ta ce." 'Kugu za ki daure da gyalenki ki shiga filin rawa kawai Hajiya." Ina dariya na ce." Sai kin fad'a ma, ai rawa zan yi hadda juyi." Gabad'aya muka fashe da dariya. Yarinyar ta yi saurin fita tana sinne kai. Ta dube ni tana cewa." Kin san fa wani yaro dan gidan yayar babanta yana nan yana naci a kanta wai ya kama don Allah kada a bawa kowa shine fa uban ya zo yana gaya mini na ce to guda nawa Yusuran take da har za a fara wannan maganar shekara sha hud'u fa kawai don an ganta da tsayi shi yasa ake bata girma." Na ce.'' Ai girman 'ya mace ba wahala Sahura Kuma ta isa fa, ai tana da san girma, amma dai da Idiris zai d'auki shawarata da na ce masa kada ya yi mata auran nan na gaggawa ya bari ta damu koda diploma ce." Ta ce." Ya bari kuwa, ai shi idan magana ta 'yan uwansa ce baya wasa da ita, ni ma nafiso ta dan yi karatu ko yaya ne zai taimaketa anan gaba." Na ce." Gaskiya hakan zai fi dacewa." Wayata na d'auka na kira Hamusu yana d'agawa na ce." Kana asibitin ne?" Ya ce." E, anti Amina jikin Gwaggon kam alhmdullhi." Na ce." To haka ake so, ko za ka zo ka d'aukar muku abinci gashi nan Yusura ta kusa kammalawa kafin mu zo din." Ya ce." Ai yanzu nan ma Baba Zulai kanwar Babanmu suka zo da abinci dama kullum tana zuwa sai dare take tafiya wani lokacin ma da safe kafin na je ta riga ni, tunda sun hana kwana." Na ce." To shikkenan Hamusu ka gaishe mini da Gwaggon da ita inna Zulai din kafin mu k'araso." "In sha Allahu rabbi anti." Yafad'a cikin kulawa da girmamawa. To sai wajejan biyar na yamma muka gama shiri nida Sahura muka fito da zummar tafiya asibitin. Yusura na gidan anan muka barta dama tunda suka zo na cewa uwar ta bar mini ita ba jayayya ta ce dama ai taki ce. Hijabi nasa har kasa na rufe fuskata da nikab saboda ba na so jama'a su gane ni. Tare muka shiga shago da ita na gayawa yaran zan fita amma ba zan jima ba zan dawo, ita Kuma Yusura na ce mata ta rufe gidan daga ciki. A daidaita sahu guda muka d'auka har asibitin Malam. Muna d'an ta'ba hira na ce." Sahura duk abin nan da nake yi wallahi idan na tuna halin da Alhaji Muntari yake ciki sai na ji kasala ta kama ni, haka kawai nake tausayawa masa ki ba ni kwarin gwiwar taimakonsa tunda ke ki ka gaya mini yadda yanayin jikin nasa yake." Ta ce." Sis kina da raguwar zuciya gaskiya, na taimaka miki ta wace siga kenan?" "Idan mun shiga sai mu binciki asibitin bangaran maza ko Allah zai sa mu samu d'akin da yake sai na dubo shi." "Kina da tabbacin yana asibitin har yanzu watanni uku fa na ce miki da suka wuce, wata'kila ma an sallameshi yanzu." Na ce." Sai mu sanya rana ki raka ni na duba shi a gidansa, wallahi har yanzu ina tuna irin alherinsa akan Kamalu ya yi mini kokari sosai akan Yusi lokacin da ya aureni bai bambamta tsakaninsa da yaransa ba." Ta ce." Kina cikin wannan rikicin sis, kada ki rikitowa kanki wani don Allah ki bar maganar nan, idan ki ka yi masa addu'a daga nan ma ya isa ai Allah ya ga zuciyarki." "Babu abinda zai faru Sahura Ubangiji da zuciya yake amfani." Shiru ta yi tana girgiza kanta kamar buk'atata bata damu karbuwa ba a wurinta. To muna shiga asibitin muka fara cin karo da motocinsa tunda komai nasa baya 'buya duk motocinsa akwai alama mai d'auke da ayyukansa na yau da gobe Cikin faduwar gaba na ce." Kada dai mutumin nan ya sauka." Na d'auka a zuciyata nake maganar sai da na ji maganar Sahura tana fad'in." Shine ma ai kin san komai nasa a bayyane yake duk inda yake sai an gane, kuma tunda naga wannan motacin na tabbatar yana cikin asibitin nan." Na ce." Sahura kin ga irin abinda nake gaya miki ko? Matar nan fa mahaifiyar tsohon mijina ce amma ya yi ruwa da tsaki akan lamarinta ni ya hana ni ma aiwatar da komai, don girman Allah ki gaya mini ta yaya za a yarda da abinda zan fada a kansa." Muna cigaba da tafiya ta ce.'' Kin san kuma Yana da tausayi da zuciyar Imani fa, shiyasa ake ta yi masa sha'awar mulki domin ana yi masa kyakykyawan zato da wahala ya samu labari ko ya ga mai neman taimako bai taimaka masa ba, ya yi da jiki da aljihunsa wannan yana daya daga cikin kyawawan halayensa. [9/6, 10:17 AM] Aunty B: 74 Shiru kawai na yi ban ce mata komai ba domin gabad'aya kaina ya kulle da al'amarin nan da yake faruwa. Kiran da ya shigo wayata ya katse nazarin da nake yi. Hamusu ne, cikin nutsuwa na daga wayar nasa a kunnena. Sai da ya fara gaishe ni tukkuna ya furta." Kun shigo asibitin ne anti?" A takaice na ce masa ." Eh, na dora da fadin wai kai baka gajiya da gaisuwa ne Hamusu Ina ce da safe mun gaisa haka ma d'azu dana kira ka sai da ka gaishe ni gaisuwa nawa za mu yi ne a rana." Dariya ya fara yi kafin ya ce." Ai babu lefi anti girmamawa ce, kin cancanci hakan ne." Humm kawai na ce Ina ko'karin kashe wayar ya ce.'' Yallabai ma bai jima da shigowa ba tare da su Yusi suka shigo." Ban yi mamakin jin cewa suna tare ba domin akwai Sukairaju a tsakani. A takaice na furta." To babu lefi muna daf da shigowa ni da Sahura.'' Ban jira amsarsa ba na datse kiran. Ni da Sahura babu wanda ya sake wata magana har muka isa d'akin da Gwaggo take kwance wanda 'yansanda biyu ke tsaye a bakin kofa. Ko ba a fad'a ba nasan masu tsaronsa ne. Muka kàrasa wurin suka nemi su hana mu shiga wai sai ya fito tukkuna. Kawai na tsaya Ina kallonsu dan ban iya furta komai ba Sahura ce take ko'karin nuna musu wani abu Hamusu ne ya fito tare da wani likita suna magana. Ganinmu da sauri ya ce." Yallabai ya haka kuma iyalinsa ce fa, ita kuma wannan kawarta ce." Da sauri wanda yake tsaye a bakin kofar ya gyara yana sunkuyar da kansa ya ce." Madam sorry ban gane ki ba kasancewar kin rufe fuskarki, a yi hakuri." A nutse na ce." Babu komai." Na juya ina sauraran tattaunawar da suka yi da likitan yana fad'in tunda jikin ya yi sau'ki za a iya sallamarta gobe ko jibi ya dube ni yana kara yi mini bayanin yanayin jikin nata, da kulawar da ya kamata a dinga bata da kuma canjin abinci da sauransu. Na ce." In sha Allahu za a kiyaye. Ya yi mana sallama cikin girmamawa da kulawa ba don mun kai ba sai don alfarmar wani wanda duniya ta d'aukaka shi. Hamusu shi ya shige gaba kafin mu bi bayan shi ni da Sahura haka kawai sai na fara jin faduwar gaba kamar wadda ta tunkari ajalinta. Gwaggo na zaune sosai a gefan gado Yusi yana kusa da ita da lemon zaki a hannunsa yana bare mata. Yayin da shi kuma yake hakimce a wata kujera dake d'akin wadda take kallon gadon da Gwaggo take zaune. Da alama hira suke yi yanayin da muka riskesu gabad'aya fuskokinsu sun nuna farinciki da murmushi. Sukairaju da abokin tagwaitakarshi 'Dahuru dama su biyu ne masu take masa baya escort d'insa kenan suna tsaye a kansa. Sai gwiwata ta yi sanyi ganin yadda kaf hankalin Gwaggo yake kansa cikin kulawa suna magana shi ma ya bada hankalinsa kacokan gareta. Muka yi sallama gabad'aya ina kallon Sahura ta nufi wurin da yake da azama. Ni kuwa da sauri na kawar da kaina na nufi Gwaggo da kulawa ina fad'in." Alhamdulillahi Gwaggo jiki ya yi sau'ki ma sha Allah." Yadda na rungumeta itama haka ta rungume ni ta dora hannunta wanda yake da wadatar lafiya a bayana tana fad'in.'' Na ji sauki sosai Amina, na gode muku kwarai da gaske, yadda kuka yi mana Allah Ya sa ku ma yaranku su yi muku, Allah Ya yi albarka." Na dan gyara na zauna gefanta har yanzu ina ri'ke da ita a jikina na ce."Babu komai Gwaggwo, ai na yi wa Hamusu fad'a a lokacin da yake gaya mini, na ce daka yanzu kada ya kara bari sai abu ya yi nisa tukkuna zai gaya mini, ban ji dad'in abinda ya yi ba ko kad'an." Murmushi kawai ta yi bata ce komai ba. Yusi da tun shigowarmu yake ta satar kallona Ina kallonsa yaron kamar yana shakkata a tsorace ya ce." Mama ina yini?" Na dubi shi a tsanake na amsa da "Lafiya lau ya kake?" Da dan murmushi ya ce." Ina nan lau Mama ." Na harareshi da fad'in." Ai na ji labarin shegantakar da ka yi, za mu had'u ne." Dariya ya yi yana sunkuyar da kainsa. Jikina ne gabad'aya ya mutu sakamakon idonsa da ya zuba mini, a jikina na jiki hakan a nutse na dubi wurin da yake muka had'a ido fuskarsa babu yabo babu fallasa yake ta kallona. Sahura ta iso wurin da muke da wani irin yanayi a tare da ita, ba ita kadai ba ma na lura duk wanda yake d'akin bai ji dadin abinda na yi ba, shi ma Hamusu duk ya yi tsumu-tsumu sai ya'ke ya ke yi. Cikin nutsuwa na dube tare da cewa." Yallabai barka da yamma." Bai yi nauwar amsawa ba ya ce." Barkanmu dai mun same ku lafiya." Na amsa da "Lafiya lau." Da wahala dama ya nuna akwai 'baraka a tsakaninmu bai iya nunawa a bainar jama'a ba zan yi masa wannan shedar ya iya taku. Bayan amsawarsa ma sai ya biyo ni da kyataccen murmushi. Na yi saurin dauke kaina gabana na cigaba da bugawa. Ni kaina na san Allah Ya jarrabe ni shi, domin ko Yaya Aminu karyar so nake yi masa. wannan mutumin ya riga da ya gama sace zuciyata. Inda Allah Ya taimaka ni ban ta'ba nuna masa tsananin so ballantana ya rike hakan a matsayin makamin da zai ya'ke ni. Gyaran murya ya yi gabad'aya muka dubi wurin da yake. Ya tashi tsaye a nutse ya nufo inda muke hakan ya ba ni damar kare masa kallo, sai na ga ma ya kara ki'ba a cikin 'yan kwanakin nan da ba mu yi a tare ba. Na janye idona daga kansa Ina tunanin wanda yake cikin matsala ne zai murmure irin haka, rayuwarsa kawai yake yi ta jin dad'i tunda ai ba ke kadai ba ce da wata kawai yana yaudarar mutane ne. Hasashen zuciyata ya zauna daram a cikin kwanyata na yarda fa wanda yake tattare da damuwa za a same shi a firgice shi kam ya murje ya kara haske abinsa. Kai na ya tsaya kamshin da yake fita daga jikinsa ya tsananta sakamakon kusantuwarmu sai jikina ya fara neman ya mutu lamarin da nake ta dankwafewa yana yunkoro mini. Kamshin da ya riga ya kama jikinsa shi ma yana taka muhimmiyar rawa wurin galabaitar da ni. Sunkuyar da kaina na yi tsigar jikina ta na motsawa. Ya fara magana da dattako kamar ya cika cikakken mara aibu. "Zan tafi Gwaggwo Ina addu'a da fatan Allah Ya k'ara miki lafiya, in sha Allahu kuma gobe da kaina zan yi wa Hajja jagora domin ta zo ta duba jikin naki." Cikin rawar murya Gwaggwo ta ce." To na gode sosai, Ubangiji Allah Ya saka maka da alheri, abinda ka yi mana Allah Ya ninka maka ranar lahira, Allah Ya sa wannan taimakon ya zama shine matakin shigarka aljanna, kamar dai yadda na gaya maka ga Amina nan ita da yaranta mun baka amana yadda ka dubi yaran nan kaima Allah Ya dubeka, ni dai idan ta ni ce na baka yaran nan gabad'aya Allah Ya tayaka ri'ko." Ya ce." Na kuwa gode gwaggo, dama ai Yusuf nawa ne, na kar'ba har dashi Kamalun kuma zan ri'ke kamar ni na haifesu, ai ni ne da godiya Gwaggo." Sai ta sanya hannu tana goge hawayen da ya fara zuba a kuncinta. Sahura na taya ta. Ni kuwa gabad'aya jikina ya gama mutuwa ashe bana nan gwaggo ta kasafce mini yara. To idan kuma muka rabu fa, dama an ta'ba kyautar d'an mutum, ni kuwa da wace irin kalma ya yi amfani wurin janyo hankalinta irin haka. Har ya fice da tawagarsa ban dawo hayyacina ba sai da na ji muryar Sahura tana cewa." Lallai baka da ta Ido Yusi bin sa za ka yi ba zaka zauna wurin Gwaggo ka yi mata kwana biyu ba." Da saurin gaske na dubi bakin kofa wanda ya yi daidai da lokacin da yaron ya bude ya fita da sauri yana dariya." Na dubeta da mamaki mai yawa a tare da ni. Duk sha'kuwata da Yusi yau ya nuna mini iyakata sam baya son ma had'a ido da ni. Sai kawai na ji 'kwalla ta ciko idona, amma ban bari ta zuba ba na dinga mayar da ita ina jin Gwaggo na ta fad'in nagarta da mutuncinsa Sahura dama haka take so ta biye mata suna ta binkito abubuwan da yake aikatawa na bayan fage. Na juya ina laluben Hamusu a d'akin shi ma baya nan, daga ni sai Sahura da Gwaggwo da alama tun lokacin da ya zo tafiya ya bi bayansa shi ma. Gaskiya masu kudi da mulki suna jin dad'i sai ka ga babba da yaro kowa ya yi mubaya'a shiyasa idan a ka yi katari da wanda bai san menene zamani ba sai ya fara d'agawa da izza daga lokacin da Allah ya kar'bi damar daga hannunsa sai ya gane Allah daya ne. Ban iya sakin jikina da Gwaggo ba tun bayan tafiyarsa bakina ya mutu domin kuwa ban ga abinda zan ce mata ba, mafi yawancin hirar ita da Sahura suke yin ta. Muna zaune inna Zulai ta shigo, mu gaisa cikin mutunci har aka d'an ta'ba wasa da dariya tunda macace mai barkwanci.. Sai bayan Isha'i Hamusu ya dawo yana fad'in can Danbattan ya bi su. Har yana gayawa Gwaggo sakon gaisuwar Hajja kafin ta zo. Murmushi kawai na ke yi ina kallonsa cikin raina ina tunanin irin dambarwar da muka sha akansa har da su Allah Ya isa. Allah sarki shi kuwa sai rawar jiki yake yi saboda kyawun zuciya. Muka yi sallama da Gwaggo da alkawarin zan sake shigowa gobe idan ba a sallameta ba amma ba da safe ba sai yamma, saboda ba na so na sake riskarsa tunda ya ce zai kawo Hajja kuma da safen. Bakin titi muka fita muna jiran abin hawa Hamusu yana fad'in." Anti mutanan nan suna da karamci wallahi ashe Yallabai gada ya yi wurin mahaifiyarsa wallahi ba ki yadda ta karamma ni ba jin cewar ni kanin mahaifin Yusi ne, ta sanya aka kawo abinci da abinsha har da kyautar kudi dubu talatin fa." Murmushi na yi na ce." Hamusu kenan." Ya ce." Wallahi anti Amina da gaske nake fa samun mutane masu dattako a irin wannan zamanin sai an tona, su dai Allah ya gama yi musu komai." Sahura ta cafe maganar tana cewa." Sai ma ka ga yadda yake wasa da dariya da ma'aikatansa abin zai baka mamaki wallahi, ai muna cikin alheri Hamusu na gaya maka idan zai shigo kano sau hamsin a shekara wallahi sai mun san ya shigo domin mu da muke aiki dashi a sassan reshen kamfanoninsanan yana yi mana alheri kwarai da gaske. Ya ce." Ni ma sheda ne anti Sahura na ga alherinsa yau ." Na ce." Sheda a ina Hamusu Yayanka Aminu mai ya tsira dashi?" Suka dube ni da wani irin yanayi. Na ce." Kwarai kuwa, ko za ka iya nuna mini abinda Yaya Aminu ya tsira dashi kafin ya mutu. Sai wahala fa, amma shine kake so ka bugi kirji kace kaima shaida ne ko akansa ko Hamusu.." [9/8, 11:00 AM] Aunty B: 75 A sanyaye da rashin karsashi Hamusu ya bi ni da kallo a lokacin dana gama maganata. Yadda na fahimta kawai ya yi shiru ne ba wai don bashi da abin fad'i ba. Sahura kam akan tun akan titin ta fara yi mini sababi, abu ne mai wahala kaga abinda zai tunzurata tana da mugun ha'kuri da d'auke kai, ko a makaranta ma bata da abokin fad'a kowa nata ne, ansha yin fad'a kace-kace da muguwar gaba a ajinmu amma sannu a hankali ita take shiga rigimar kuma ta sasanta. Na lura kuwa akan mutumin nan bata da hakuri tunda wannan shine karo na biyu da ta bud'e mini wuta kamar 'yar cikinta. Na farko lokacin da na yi dogon rubutu akansa a fece book, dukda a waya mukayi muyasar yawun na lura ranta ya yi mugun b'acin dalilin da ya sanya ma kenan na sauko har na nemeta da ta yi mini jagorar ganinsa. Sai wannan shine karo na biyu sam ta manta akan titi muke fad'i take yi a gaban kowa ma za ki iya fad'in haka Amina domin na lura hankalinki ragaggene, to bari ki ji wallahi kanki kike da'bawa wuka, karonku na farko ke dashi ba ki labari ba, ballantana yanzu da kike karkashinsa. ai duk mai hankali zai fahimci jawabin da ya yi cewa babu dole akan abinda yake yi ma'aikatansa ne, ihisani ne kawai a tsakani kuma ke da bakinki ki ka gaya mini akwai wanda ya ke shirya wannan zalinci, wallahi abin kunya ne a ji wannan maganar daga bakinki sis, domin duniya ce zata zageki, ni kan haka gaskiya zan iya yin nesa dake tunda ba kya d'aukar ke shawarata" Ta karaci bambaminta ban tanka mata ba. Hamusu ne dai yake ta tausarta na yi musu shiru ina ta ko'karin tsayar da abin hawa. Kawai na ga ta tsayar da wani ta yi shigewarta tana gaya masa ja'in zai kaita. Na saki baki ina bin babur din da kallo har ya 'bace daga wurin. Mamaki mai yawa ya rufe, ni dai a ganina ban ga abinda tayar da jijiyar wuya akan maganata ba. Murmushi kawai na yi ina gyada kai lallai lamari ya baci tunda Sahura ta yi irin wannan fushin mun tawo tare kuma mun rabu da takaicin juna. Hamusu ya tsayar mini da abin hawa. Na shiga na zauna ina dan nazarinsa shi kansa yanayinsa duk babu dadi ya nuna abinda ya faru ba yi masa sukari ba. Hannuna na daga masa ina fad'in sai ka shigo. Direban ya ja da k'arfi muka bar wurin. Tsaf na samu gidan Yusura ta gyara ko'ina, tana kwance a falo ita kadai shiru sai ta ba ni tausayi sosai ta kar'bi jakkar hannuna tana yi mini sannu da zuwa. Na zauna babu k'wari a jikina ta kawo mini ruwa na dan kurba kad'an sai da na d'an samu nutsuwa tukkuna na tashi na dauro alwala tunda magriba a hanya ta yi mana, gashi ana kiran Isha'i. Tare muka gabatar da sallar da ita bayan mun idar na ce ta zuba abinci ta ci, domin ni gabad'aya cikina a cushe yake. Saboda kada kad'aicin ya yi mata yawa na bata wayata na ce ta shiga ta yi kallo. Na shige d'aki na kwanta da tunani a cikin k'wanyata. Ina daga cikin d'akin a kwance na ji an kira ni a waya kafin ma na yun'kura ta shigo d'akin tana fad'in." mama ana kira." Wayar na kar'ba ta kama hanya ta fita. Hamusu ne na daga a nutse ina kiran sunansa ya gaishe ni kamar koyaushe na amsa sai ya dora da fadin ." Anti ba zan samu shigowa yanzu sai gobe in sha Allahu Ina fatan babu matsala ko?" Murmushi na yi na ce." Babu komai Hamusu ko kaima fushin kake yi da ni ne irin na Sahura?" "A a anti, ai duk abinda ki ke yi kina yi akan d'an'uwana ta yaya zan yi fushi dake amma kuma fa maganar anti Sahura akan hanya take anti Amina, Ina ganin zuwa yanzu ya kamata ace kin manta da abinda ya faru, idan an yi duba da irin tarin alheran mutumin nan, bai cancanci suka da zambo a wurinki ba." Dariya kawai na yi domin ni kaina na san ba ni da hujja mai karfi da zan ri'ke domin kare kaina. Na ce." To na ji ai ba zan ki amfani da shawararka ba Hamusu zan kiyaye." Sai ya saki muryarsa sosai yana fad'in." Na ji dadin hakan sosai Anti Allah Ya kara girma." A hankali na amsa Ina dan murmushi wato dai ni a ko'ina ba ni da sa'a, ba ni da magoya baya muddin akansa ne. Sahura na fara nema a waya domin ba na so ta kwana da takaicina. Kiran duniya ta'ki daga mini waya. Sai na tura mata text na ban ha'kuri har da yar zolaya. Amma ba ta yi maido mini da amsa ba. Ban ha'kura ba na sake kira nan bata daga ba sai na rabu da ita zuwa gobe da safe nasan ta dan sauka. Na kwalawa Yusura kira ta shigo na mik'a mata wayar tare da cewa." Je ki cigaba da kallonki." Tagogin d'akin na bud'e dalilin zafin da na ji yana nasata. Dama tun can ban sanya fanka a d'akin ba sai ta tsaye na saya nake amfani da ita to tana can shago yara na amfani da ita dalilin da ya assasawa uwardakin zafi abun ya hadu da tasowar hadari. Bude tagogin da na yi ya sanya sauro shigowa dole ta sanya ni barin d'akin bayan na yi wanka na samu riga ta shan iska mai hannun shimi na sanya amma ta sauko mini sosai sai dai ta matse mini jiki sai na sanya hijabi akai na fito falon na samu Yusura ta bingire bacci ya kwasheta ga waya tana yi da film din bahubali wanda Yusi ya matsa dole sai da aka tura mini a wayar anti Yagana yake wai yana son film din zai dinga gani. Dole bacci ya kwasheta ga iskar fanka ga ta hadari yake tasowa ba ina jin dalilin da ya sanya ma kenan d'akin ya d'ume da mashahurin zafi. Babban bargon da yake shimfid'e akan katifata na d'auko da matashin kai biyu na gyara mana shimfidar sosai sannan na tasheta ta je ta yi fitsari ta dawo ta kwanta . Yadda hadari ya had'o sosai na gabas da irin walkiyar da ake yi da wahala idan ba a yi ruwa ba domin hadarin gabas ba kokwanto yana zubar da ruwa. Na fita na gyara abinda zan gyara na leka shagon lokacin suna ta shirye shiryen tashi dan ma da yawa daga cikinsu gidajen iyayensu a unguwar suke wasu kuma a shagon suke kwana. Kofar ciki na rufe sannan na rufe ta falon na nemi waje na kwanta lokacin ruwan ya fara sauka kad'an kad'an. Sai Kuma na ji ana ta'ba kofar na tashi zaune da mamaki. Kira ya shigo wayata da take ajiye a gefena don ban kai ga kasheta ba tukkuna. Hamusu ne ya kira Cike da mamaki na daga wayar na ji shi yana fad'in." Anti har kin rufe gidan kenan Yallabai na yi wa jagora muna tare ki bud'e kofar.'' Da fargaba mai yawa a tare da ni na ce." Yallabai kuma?" Da sauri ya furta." Eh anti ki yi hanzarin bude kofar ruwan ya fara karfi." Na yun'kura na tashi tsaye gabana na dan bugawa na dubi lokaci a wayata goma da minti arba'in, ban san me ya kawo mutumin nan wajena ba a irin wannan lokacin ko zuciyarsa ce ta raya masa ya yi mini zuwan bazata domin ya kurewa 'karyata ko ya tsira ni. Idan na'ki bude kofar nan na d'auri kaina hasashensa zai tabbatar a kaina wannan dalilin ya sanya na fita cikin ruwan da ya fara karfi na bude kofar. Sune tsaye shi da Hamusu biyu kacal bai zo da kowa ba. Ruwan har ya fara jikasu. Hamusu ganin na bud'e kofar bai ce mini komai ba da sauri ya shige shago suka rufo kofa. Jikina babu kuzari na matsa masa hanya ya shiga na tsaya na rufe kofar kafin na biyo bayansa. A rumfa na iske shi yana bin wurin da kallo. Na tsaya kawai ina kallonsa jikinsa na dan d'igar da ruwa rigar jikinsa duk ta kwanta sakamakon ruwan da ya ta'ba shi. "Kin yi mamaki ko?" Maganar da ta fara fitowa daga bakinsa kenan. Na ce." Ban yi mamaki ba, ai hakan yana daya daga cikin halinka dana sani." "Wannan yarinyar fa?" Yafad'a yana duban wurin da Yusura take kwance. Na kalleta baccinta take yi sosai na ce." Yarinyar Sahura ce." Ya gyada kansa kafin ya furta." Ni a Ina za ki sauke ni, annabi ya ce ka girmama bakonka." "Ai ba ka gaya mini za ka zo ba, za ka iya zuwa shago ka kwana da yarana domin nan ne masaukin baki a gidana." Ya tsaya kawai yana kallona kafin ya yi dariya wadda har sautinta ya fita ya ce." Idan za su yarda na kwanta a cikinsu ni a wurina ba komai ba ne." Shiru na yi ban tanka masa ba. Sai ya dubi jikinsa da yake d'igar ruwa ya kalleni." Mu je d'akin naki, ki ba ni aron zani na d'aura." Na ce." Ai ban zo da wasu kaya da yawa ba gaskiya ba ni da zani sai siket." "Zan sanya siket din, ke da ki ke lukuta ma ki ka sanya balle ni." Ganin Yusura na motsi ya sanya da sauri na nufi dakin ya biyo bayana. Da sauri na tayar da katifar da take kwance na tsayar da ita sai kafet kawai a wurin. Muka yi cirko-cirko muna duban junanku kamar shekararrun zakarun da suke matsananciyar gaba da junansu." "Ba za ki girmama ni kamar yadda Annabi ya fad'a ba kenan." Ya fadi hakan kafatanin hankalinsa a kaina. Na ce." Ai ba ka kira ni ka sanar da ni zuwanka ba ballantana na baka masauki." "To ke din a karkashin wa ki ke, ko ni kin gaya mini za ki zo nan?" Shiru na yi ban tanka masa ba sai ya tunkaro wurin da nake tsaye ban ja da baya ba amma Ina cikin matsananciyar fargaba. Gabad'aya ya danneni da kirjinsa har sai da na fadi a kasan wajan. Ya tsuguna yana fad'in." Ki ba ni abinda zan sakaye jikina na cire wannan jikakkun idan na kwanta ciwo kuma ke ce sanadi domin zan iya rantse miki na fi karfin shekara talatin rabon da ruwan sama ya dake ni." Muryata na d'an rawa na ce." Wannan kuma abinda ya shafeka ne. Sai ya tsirawa fuskata ido yana kallo, na kawar da kaina domin yanayin kallon da yake yi mini ya fara sa'bata. Yun'kurin tashi na fara yi ya mayar da ni ya zaunar ." Ban zo gidanki domin ki wulakanta ni ba da zummar sasanci na zo, na yarda na yi lefi ki yi hakuri." Har cikin zuciyata na ji dad'in karayarsa wanda da wahala a irin wannan zamani namiji karabiti ya yi wa mace lefi ya bata ha'kuri ballantana irin nawa mijin. Àmma ban nuna masa hucewata ba, na sake daure fuska tamau na furta." Amma kasan abinda ka ke yi mini kuskure ne?" "Na sani, dalilin da ya sanya ma kenan na ji zan iya jure duk wani cin kashi da za ki yi mini, kuma ba na so kowa ya ji na sake ki, mussaman Hajja." "Ai na gaya maka tun farko yadda ita ta kulla auran yana da kyau da ta san abinda yake faruwa, ni a wurina babu lefi don ta ji cewa igiya daya ta samu tangard'a." "Ban amince ba, ba zai yiwu hakurin dana baki ya tafi a banza ba, na gaya mini wannan lamari ya zama sirri a tsakaninmu na yi miki alkawarin in sha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba." Na yi shiru ban ce komai ba. Sai ya riko hannuna a hankali." Kin yi alkawari ko?" Kai na girgiza na ce." Ni fa mutum ce mai zuciya ya ba zan ji zafi da takaici ba a duk lokacin da wanda nake aure ya gaza fahimtata. Saboda kawai bai samu budurcina ba, ya aureni ina sana'a domin rufawa kaina asiri sai kawai saboda son zuciya da rashin adalci ya dinga yi mini mummunan kazafi." D'akin ne ya yi shiru tun bayan ajiye maganata bai ce komai ba sai karar saukar ruwan sama da ake ta shekawa. Na dube shi a hankali sai na ga yana rawar d'ari alamun sanyi. Muka had'a ido. Ya ce." Ki ba ni abu na gaya miki ko so ki ke yi na cire na yi tsirara ne sanyi ya dame ni." Na tashi na zuga akwati na d'auko masa zani da wata irigar irin ta jikina na mik'a masa ya tashi ya fara kicikicin cire kayan da suke jikinsa har yanzu rawar sanyin yake yi. Ya miko mini zanina Yana fad'in." Ban san yadda zan yi na daura wannan ba, kar'bi abinki wannan ma ta isa. Na kar'ba ina me saurin dauke kaina gabana na bugawa ganin yadda girmansa ya fito sosai domin ba tare da kare jikinsa ba ya cire wandonsa akan idonsa sai na kauce daga wajan da sauri na matsa can gefe tare da sunkuyar da kaina k'asa fargabar wani abu na fara yi. Ya juyo yana kallona na dai sake kawar da kaina a karo na biyu rigar ta kwanta ajikinsa tunda me hade da cotton da robo ce har ilayau girman nasa yana nan a tsaye na san kuwa da wahala idan ba mu yi rigima ba. Kulle kofar d'akin kararaf alamun zura sakata shi ya dawo da ni hayyacina ya rufe ya nufo ni a hankali cikin karamin sauti ya ce." Rigar ta yi mini kyau ko?" Kawai na saki baki ina kallonsa, nasan bashi da alkunya da kawaici a wannan fagen kunya kuwa gaba ya bata ba baya ba, zai iya cewa zai neme ni ga yarinyar mutane akwance a rumfa, bayan haka kuma zahirin gaskiya ni dashi muna ficewa ne daga hayyacinmu Iran muna wannan lamari ihu da nishi da surutai samfur-samfur ba irin wanda ba ma yi. [9/9, 9:19 AM] Aunty B: 76 Wata wawar runguma ya yi mini wadda ban yi tsammaninta ba a lokacin da ya k'araso wajan da nake tsaye. Gabad'aya muka fad'i a wurin domin kafafuna sun yi sanyi kuma ban tsammaci hakan ba. Sosai ya makale ni a jikinsa yana fitar da wani irin numfashi tare da sansanar sassasan jikina. Ban yarda na kar'bi lamarin ba domin yin hakan a wurina kamar abin kunya ne, na farko har yanzu zuciyata ba ta gama aminta da nadamarsa ba, na biyu kuma ba zan ta'ba yarda wata mu'amula ta shiga tsakaninmu ba yarinyar mutane tana kwance a falo na tabbatar da cewa abinda za mu yi ni dashi sai ya tasheta har ta fahimci wani abu. Wata'kila ya yi amfani da wannan damar ne domin a ganinsa zan janye abinda na kudira domin sanin wacece ni ta wannan fanin babu kara balle kawaici ni dashi din duk kanwar ja ce ballantana yanzu da muke cike da tsananin buk'atar juna ko bai fad'a ba nasan hakurinsa ne ya kare shiyasa ya canza wata dubarar. Na tattara dukkanin karfina na 'ban'bare shi daga jikina, domin d'umin jikinsa da yadda yake ta 'bari bai dame ni ba don ban kawo cewa zazzabi ne ya kama shi ba. Na tashi tsaye ina numfashi gabana na cigaba da buguwa domin ban san kuma abinda zai sake biyo baya ba tunda na fi kowa sanin halinsa. Ganin ya silale ya kwanta a kasan kafet din ya yi male-male kamar matacce daga wajan da nake tsaye ina jin sautin nishinsa sai jikina ya dan yi sanyi fargaba ta dirar mini dama ya gaya mini ciwo zai iya kama shi dalilin dukan ruwan da ya jima jikinsa bai kar'ba ba. Na dan matsa kusa dashi a hankali na ce." Tunda ruwan ya tsagaita kuma sha biyu ba ta cika ba ni dai ka tashi ka tafi." Idonsa da suke lumshe ya bude ya dubeni a hankali ya furta." Ba ki da imani Amina, ban yi tunanin kiyayyar da ki ke yi mini takai haka ba na gode." Ya mayar da idonsa ya rufe yana sake janyo numfashi sama-sama. Har yanzu bai fara ba ni tausayi ba don sai nake ganin kamar karya yake yi don ya samu kaina ne. Na dan sunkuya kusa da kansa nasa hannuna a wuyansa sai na ji mugun zafi na cire da sauri na dora a saman kansa nan ma ya d'auki zafi kwarai da gaske. Daga nan na gazgata cewa ba karya yake yi ba. Na dube shi a kwance sanye da rigata kamar wani mara galihu, kamar ba wannan attajiri mutumin nan da duniya take yayin sa ba, kamar ba wannan dattijon mutumin nan da daruruwan jama'a ke ci da aha a karkashinsa ba, kamar ba shine wanda jami'an tsaro ke risina masa ba suke kuma tsaron lafiyarsa. Yau gashi a karamin gida takurarre kwance a kasan kafet a d'akin da babu fanka. Sai na fara dawowa nutsuwata domin zuciyata ta fara yi mini munana tunani akansa wai idan ya mutu daga ni sai a shi a cikin irin wannan yanayin wace amsa zan bawa jama'a da manema labarai. Na sake rud'ewa a lokacin da na ga yana kokawa da sauro don sai cizonsa suke yi yana bugewa da hannunsa. Da sauri na riko kansa na dora a cinyata na furta." Sannu ka ga zazzabi ne ya rufe ka, dan tashi na gyara maka katifar sai ka kwanta ka ji." Ya dan motsa kad'an kafin a hankali ya ce." Ba na so, ai ina ganin lokacin da ki ka tayar da katifar saboda kada na kwanta, na gaya mini ai ni nasan dole sai na yi mura da ciwon kai." Murya na rawa na ce." To ai ba ni nace ka zo ba balle kace na kira ka ruwan sama ya doke ka asalima ban san za ka zo ba, kuma da ka ga hadari ai sai ka ha'kura." Shiru ya yi bai ce mini komai ba sai jan hanci yake yi alamun ya toshe! Na buga na raya ya tashi na kwantar da katifar ya ki tashi. Gashi sauro sai cizonmu yake yi ni da shi dukda akwai haske a d'akin amma bai hana sauron tasiri ba ga sanyi irin na ruwan da aka shara yana ta surarowa. Na ji hawaye na nema ya k'wace mini domin hankali ya kara tashi a lokacin da na ga jikin nasa baya sau'ki sai gaba yake yi. Ya tattare waje daya yana ta rawar jiki. Na fara kuka cikin damuwa da zullumi na cigaba da rarrashin ya tashi na shimfida katifar ina da zannuwa a cikin akwatina na lullube shi. Ya ce ba zai tashi ba ai da farko ya nemi na bashi zanin na'ki na bashi." Na sauke kansa dake cinyata da sauri na bude akwati na d'auko zannuwana biyu na zo na rufa masa. Domin na tabbatar da cewa bayan ciwon kan da mura da yake yi a yanzu zai iya wayar gari da zazzabin cizon sauro mai tsanani tunda bai saba ba. Da kaina na dinga buge masa sauron da tafin hannuna wanda duk yasha jininsa. Ni ban damu ma da wanda yake cizona ba. Cikin hawaye da jan hanci na ce." Ko za ka je cikin motarka ka kwanta a ciki tunda nan da sauro." Cikin halin da yake ciki ya ce.'' Har yanzu dai ba ki yi maraba da ziyarar da na kawo miki ba ko, ki ka sani ma ko mutuwa zan yi sallama na zo yi miki." Na sake shiga tashin hankali jin abinda ya furta. Ba shakka a wannan lokacin ana tsaka da yin mutuwar fuj'an, don an ce maka mutum ya rasu babu jinya kada ka yi mamaki. Na karaya sosai da sosai cikin kukan da nake ta dannewa na ce." Ba zaka mutu a gidana ba, wane hali kake so na shiga wasu cewa za su ni ce na kashe ka." Ya yi shiru bai ce komai ba. Na cigaba da kuka a hankali don ba na so dalilin abinda yake faruwa Yusura ta tashi. Kansa da yake cinyata nake ta shafawa ina ta jijjigashi domin na rasa ma abinda zan yi, ba na ajiyar magani balle na bashi gashi an yi ruwa dare ya tsala ba na tsammanin za a samu masu chamis. Agogon da yake d'akin na duba sha biyu da arba'in, ruwan ya d'auke tsaf. A hankali na sauke kansa na janyo zannuwan na rufe shi gabad'aya har fuskarsa na tashi zan fita. Na ji ya ce." Ina za ki je?" Da sauri na ce." Zan duba shago ne idan ba su kwanta ba sai na ce Hamusu ya duba chamis mafi kusa a samo maka magani. Ya ce." Dawo a bari sai gari ya waye abu daya za ki yi mini na samu bacci." Na dawo na zauna ina fad'in." Menene? Ya tashi zaune yana kallona muka zubawa juna ido da gaske ciwo yake domin alamun hakan ya bayyana a fuskarsa. Ya furta." Ni ban iya mura fa ba, tana galabaitar da ni sosai, ki shimfidar da katifar." Ban ce komai ba na tashi na yi abinda ya bukata domin ni a wannan ga'bar kokarina kawai na samu bacci ya d'auke shi da safe koma menene sai ya faru. Ya dube ni a hankali ya ce." Cire hijabin ki kwanta." Wallahi sai a sannan na tuna da karamin hijabi a wuyana." Na cire na kwanta kamar dai yadda ya buk'ata, na zuba masa ido ina jiran ganin abinda zai yi a gaba. Ya hayo katifar da zannuwan dana rufe shi kawai naga ya kwanta a saman jikina ya fara gyara zannuwan domin lullube mu. Jikina ya d'auki zafi sakamakon zafin da jikinsa yake yi, shiru kawai na yi ban ce masa uffan amma shi kansa ya san ba zan iya daukarsa a haka har garin Allah ya waye ba kamar akwai zalinci a ciki. Cikin d'an karamin sauti a daidai fuskata na ji hucin numfashinsa Yana fad'in. " Zan d'an fi jin sau'kin sanyin da yake damuna, idan kin gaji sai ki maye gurbina." Cikin d'an jan numfashi na ce." Ban gane na maye gurbinka ba, amma kai ma kasan hakan ba zai yiwu ba ko kana fa da nauyi." "Duk nauyina ai ban kai ki ba, na ce idan kin gaji ki dawo samana shikkenan ko?" Shiru na yi. Muka cigaba da sakin numfashi jikinsa ya fara shikawa alamun bacci ya fara d'aukarsa. Daga na motsa zai motsa shi. Na furta." Gaskiya sai dai ni na maye gurbinka da kyar fa nake numfashi wallahi ka fi ni nauyi." Bai ce komai ba ya Birkita ya kwanta kan katifar yana fad'in." Hau shikkenan ko?' Na gyara zannuwan na hau yasa hannuwansa biyu ya tallefeni na lullube mana jiki da zannuwan amma basu ratsa mu duka ba. Cikin hukuncin Allah kuwa bacci mai nauyi ya kwashe shi. A hankali na zame jikina na dan kwanta a gefansa Ina kallonsa yana sauke numfashi mai tafe da sarkewa daga kirjinsa. Har yanzu ina jin d'umin jikinsa a jikina da gaske zazzabi da mura ne suka kama shi da gaske. Zannuwan na gyara sosai ya rufe har kafafunsa amma ban da fuskarsa saboda fitar numfashi. Na yi amfani da wani karamin mafici na roba Ina dan kore masa sauron da yake ta zarya a d'akin. idona biyu asuba ta yi. Masallatai ana ta kiraye kirayen sallah. Na tashi zaune a hankali ina dubansa lokacin ya motsa da wani irin tari wanda yake nuna alamun kirjinsa a cushe yake da majina. Cike da zullumi cikin zuciyata na kama salati domin ni a ganina wannan dan dukan ruwan bai kai ace ya lafke irin haka ba. Ya tashi zaune yana cigaba da tarin na zuba masa ido har ya lafa a hankali na furta."Sannu." Ya amsa can kasa kafin ya ce." Ya zan yi na yi sallah ne, ni kaina na fara nadamar zuwa gidan nan naki." Na dubi rijar jikinsa duk ya yi wata kala ya firgice na dan ji tausayinsa kad'an domin da gaske baya jin dadin jikinsa. Na ce." Ni ban san yadda za ka yi ba. Ga kayanka nan duk sun jike har gajeran wandon da singilitin." Ya yi shiru yana dubana kafin ya furta "Zan yi sallah a haka ai akwai uzuri ki zuba mini ruwa." Ban ce komai ba na tashi na shiga bandakin da yake jikin d'akin na zuba masa ruwa a buta Na fito lokacin har ya sauko daga katifar na bashi hanya ya shige bandakin. Dadduma na shimfida masa na jira shi ya fito tukkuna ni ma na shiga na dauro alwalar.... Koda ya idar da sallar katifar ya koma ya kwanta bai ce mini komai ba a wannan karon tarin shi yafi matsa masa. Ni ma ban ce dashi komai ba na kwashi kayansa na fita dasu. Na samu Yusura tana motsi na dan bubbigi kafarta ta tashi da sauri na ce." Taso ki yi alwala." Na fita tsakar gidan da kayan a hannuna wanke su na yi tas na shanya cikin ikon Allah rana ta fito mai haske sai na mayar da kayan idonta domin su yi saurin bushewa. Yusura ta fito tana fad'in." Mommy ina kwana mun yi baki ne?" A takaice na bata amsa da cewa." E jiya kina bacci ba." Ba ta sake cewa komai ba ta nufi kicin tana cewa." Dame zan fara mommy." Na ce." Ki dora ruwan shayi ki sanya kayan kamshi sosai ki dan sanya barkono a ciki ko uku ne." Ta amsa da sauri kafin ta bude kicin din ta shiga. Na sake komawa d'akin na kwashe takalmansa na shige masa dasu ciki. Na dube shi har yanzu bacci yake yi lakadan. Wayata na d'auka na fito falon na nemi Hamusu yana d'agawa na ce." Ka tafi asibitin ne baka shigo mun gaisa ba." Da sauri ya ce." Haba dai anti na ce bari na dan jira gari ya kara yin haske sai na shigo mu gaisa kafin na wuce ko kina bukatar wani abu ne. Na ce." Sosai kuwa wai d'an dukan da ruwa ya yi muku jiya fa Yallabai na kwance kashir'bar mura da zazzabi har da tari sun kwantar dashi." Cike da damuwa ya furta." Subahanallahi! ai anti shiyasa nake ta ce miki ki bude kofar kin san akwai yanayi na girma da shekaru bayan haka kuma jikin bai saba ba, ni kin ga lami lafiya na kwana kuma na tashi garau da ni, ba na jin wani sauyi. "Hakane yanzu nan babu wani chamis da suka bude tunda yanzu gari ya waye kana da abun hawa ka je can asibitin wurin masu sayar da magunguña ka samo masa maganin mura da tari amma mai kyau." Da sauri ya furta." Anti ba ma sai na je har zan ba Ina fita babban titi zan samu." Na ce." Shikkenan sai ka dawo.'' Shi ya riga ni kashe wayar kafin na ce me na ji tashin karar babur d'insa Hamusu kenan. D'akin na koma ina jin Yusura na ta aikace aikace sosai yarinyar ta horu da aiki gashi nan babu abinda ba ta iya ba na rayuwa. Ido a bud'e na same shi yana numfashi da baki. gabana ya bada wani irin sauti yadda ya tsayar da idanuwansa a saman rufin dakin sai naga kamar wanda ba a jima da zare masa rai ba. A sukwane na nufe shi kafafuna na kyarma. duban da ya yi mini shi ya dan sassauta fargabata. Na zauna kusa dashi ina fad'in ." Ka tashi ga tea na dafa maka mai kayan kamshi zai taimaka maka sosai muryarka ta bude yanzu Hamusu zai kawo magani sai kasha, amma ni ba na tsammanin wannan dukan ruwan ne ya haddasa maka wannan murar saboda ka fa yi tafiyar mota." "A jirgi na zo ni malama." Ya fad'a yana lumshe idonsa. Na ce.'' Na sani amma ai ka ninka dambatta sau biyu wannan iskar daka sha'ka ta isa sanya maka lalurara. "Ke a tunaninki a wace irin mota nake irin wannan tafiyar?" Shiru na yi ina nazari. Gaskiya ne a irin motocinsa babu wata kafa da iska zata shiga har ta janyo masa toshewar hanci manyan motoci ne masu tsaro. Ya furta." Ko kin so ko kin ki kece sila, ni ai ban zo da niyyar kwana ba ruwan da ya ritsa dani ne, kuma na gaya miki sulhu na zo wurinki ba wani abu ba." "Ai sulhu ya k'are tsakaninmu na gaya maka ba zan koma can ba gaskiya abinda yake zuciyata kenan." Na fad'a tare da kawar da kaina gefe. Ya nisa kafin ya ce." Na ji amma kin san kema ba ki da hujjar da za ki ce sai a nan za ki zauna ko ba zai yiwu ba, muddin na amince miki akan bukatarki dole ni ma ki bi ra'ayina ki zabi daya daga cikin gidajen da nake da su anan ki zauna." "Menene da nan din?" Bai kai ga magana ba attishawa ta tare shi ya dinga yi har sai da na tashi na nemo masa tissue ya dinga fyace majinar data tsinke. Ya tara tissue din a wuri d'aya na kwashe na je na zuba ashara na dawo na same shi har yanzu yana ta attishawar dai. [9/10, 9:27 AM] Aunty B: 77 Lallai a yau na sake tabbatar da cewa mura tana daya daga cikin manyan laluran da suke galabaitar da jikin dan adam, daga jiya zuwa yau gabad'aya kamminsa sun canza fuskarsa har ta dan kumbura ga dukkan alamu ma dai yana da matsalar sanyi a jikinsa shiyasa da aka motsa shi ya tashi gabad'aya. Fita na sake yi daga d'akin na samu Yusura tana soya indomi da kwai na ce ta miko mini fulas din shayin da yake gefanta ta had'o mini da kofuna biyu masu dan girma na gilas. Na sake komawa d'akin yana kashingide attishawar ta lafa. Ya bi ni da kallo a lokacin da na kàrasa wurin da yake har na tsiyaya masa shayin da yake ta tiriri da k'amshin kayan shayi bai d'auke idonsa daga kaina ba. Ni ma ban ce masa komai ba na fara motsa masa shayin har sai da ya yi daidai yadda zai yi dadi sha. Na mika masa babu jayayya ya kar'ba har da godiya. Gefe na zauna ina d'an sauke ajiyar zuciya. Na ji yana cewa." Har yanzu ban gayawa Hajja kina garin nan ba, haka zalika ma na gargadi Yusuf akan kada ya sanar mata Ina so ni dake mu gama magana yanzu da daddare na d'auke ki a mota domin ki duba gidan da za ki zauna." Ba tare da na kalleshi ba na ce.'' Wai me yasa ba ka so Hajja ta san abinda ya shafe mu ne, kada fa ka manta mahaifiyarka ce, baka da hurumin boye mata abinda yake faruwa da rayuwarka." "Wannan ai ba abin alheri ba ne shiyasa nake lullube mata." Na ce.'' Yanzu ka amince kana kuskure ko?" Ya d'aga mini kai alamar E. Girgiza kaina kawai na yi ban kuma yi mamakinsa ba domin duk abinda yake yi mini a yanzu yana yi domin ya samu kaina, shiyasa duk abinda na ce ya yi kai tsaye yake amsawa babu ja'inja, a ganina kuma hakan ba zai hana shi watarana idan na ha'kura ya sake kuntuka mini ba." "Na ji dadin shayin nan sosai na gode miki." Maganarsa ta dawo ni da hayyacina. Na dube shi sai na ga yana kallona shima kafin a hankali ya ce." Kin kasa samun nutsuwa ballantana ni ma na samu nutsuwar da zamu cigaba da gudanar da rayuwarmu, akwai abinda nake so na gaya miki wanda ya shafe mu ne gabad'aya da duk wani makusancina amma ina fargabar ki juya mini magana ko ki ji kamar da gayya na gaya miki." A tsanake na ce." Ni babu irin wannan gilin a zuciyata me zai sanya ka sanar da ni alheri kuma na ji b'akinciki idan ba ka sanya ni daya daga cikin masoyanka ba to na tabbatar zan zo a ta biyu don haka ina yi maka fatan alheri akan duk abinda ya sami rayuwarka." "Na gode sosai, Allah Ya yi miki albarka." D'akin ya yi shiru ni ina ta jiran na ji ya gaya mini abin alheri ya yi shiru yana ta kurbar shayin yana lumshe ido da gaske ya yi masa dadi. Na ce.'' Idan bai isheka ba akwai sai na tsiyaya maka." "A a, ya isa wannan din an jima dai kafin na tafi zan kara shan wani." Na kar'bi kofin daga hannunsa na ajiye sai na ji ya ce." Kin cire key din motata cikin aljihun rigata ko?" Ban ce komai na janyo handbag d'ita na d'auko masa mukkulin . "Ina Hamusu ba shi ya bude motar ya debo mini wayoyinsa. Rufe bakinsa ke da wuya Hamusu ya shigo gidan na tashi da sauri na fita na same shi suna magana da Yusura hannunsa ri'ke da ledar magungunan na kar'ba tare da mika masa key din motar na ce." Yallabai ya ce ka debo masa wayoyinsa a mota." Ya kar'ba ya fita da sauri Allah Ya sa jiya da ya yi mini sayayya ya sayo rowan roba swan na d'auki daya na sake komawa d'akin. Na ce." Ga magunguñan wayoyin kuma yanzu zai kawo." Ya kar'bi ruwan da maganin Ina daga tsaye duk Ina kallonsa ya 'balli maganin ya sha. Na ce." Ko na dan dafa maka wani abu mai dan nauyi kafin ka tashi nasan maganin mura da kashe jiki wata'kila ma bacci ya d'auke ka yanzu." Ya ce." Da kuwa kin kyauta amma towo na garin dawa, miyar kuka kuma." Na ji shigowar Hamusu a karo na biyu muryarsa a falo Yana fad'in." Anti ga wayoyin." Fita na yi da sauri na amso masa shi kuma ya juya zai fita na ce." Akwai abin kari Yusura ta yi Hamusu ka zauna ka karya zata had'a maka komai sannan don Allah idan ka shiga cikin gari ka hado mini kayan towon dawa." Ya ce." In sha Allahu anti." K'aramar wayar a kashe take babbar ce a kunne na mik'a masa ya kar'ba cikin nutsuwa ya fara dubawa, ganin haka sai na juya zan fita hankalinsa na kan wayar ya ce." Ina za ki je kuma ke da ki ke jinya." Dawowa na yi na zauna ban ce komai ba. Ya d'an duba abinda zai duba kafin ya dube ni a nutse ba tare da nuna nishad'i ba ban dai sani ba ko b'oyewa ya yi ya furta." Kin san da cewa Hauwa tana da juna biyu?" Gabana ne ya buga da karfi sakamakon jin maganar da ta yi tsalle ta fito daga bakinsa ban kuma tsammaceta anan kusa ba. Sai da na yi namijin ko'karin daidaita kaina don gudun kada ya gane kid'imewata na kar'bi maganar da ya dumfare ni da ita da annashuwar da ban shirya yinta ba na ce." Kai ma sha Allah ko shine dama abinda ka ke cewa za ka gaya mini?" Ya gyada kansa da kwarin gwiwa ya furta." Kwarai kuwa na so na gaya miki tun kwanakin da suka shige to ban san yadda za ki ji a ranki ba, sai kuma wannan rikicin ya b'alle a tsakanimu zan fi so ki samu nutsuwa mu daidaita a tsakaninmu ke ma ki samu na ki cikin zan ji dad'i na ga kuna yi mini jereran haihuwa." Na danne abinda yake yun'kuro mini na tsantsar kishi da tausayin kaina na furta." Na taya ku murna sosai, Ubangiji Allah Ya raba lafiya ya kuma raya abinda za a samu. Maganar na samu ciki na haihu ina ga abu ne mai wahala domin ba abin wasa ba ne d'aukar ciki da rainonsa balle a zo kan k'adami na haihuwa. Tunda har jininmu bai hadu ba ina ganin mu ha'kura kawai da haihuwar nan Yallabai ai kai baka da matsala ni ce ma abin tausayi." Na kare maganata idona a tsakiyar nasa idon. "Ina ce wannan maganar mun rufe babinta tun wattanin da suka gabata dalilin da ya sanya fa kenan nake jin shakkun gaya miki saboda na fi kowa sanin halin rigimarki." Na ce." Me ka mayar da ni mara son zaman lafiya ko me? ko duk wannan addu'ar da fatan alherin da na yi muku baka gamsu ba har sai ka jefe mini magana idan ka boye mini cikin matarka ai ba zaka 'boye mini haihuwar ba tunda ba zata ta'ba dawwama dashi a jikinta ba." Shiru ya yi mini bai tanka mini ba. Hakan ya kara dagula mini raina. Gabad'aya ma sai nake ganin yana so ne ya raina mini wayo ya muna tsaka da rikici ya wulakanta ni har da tukwicin saki ban yi masa komai ba kuma ya zo ya ce mini na taya shi murna akan wane dalili. Haushinsa da nake ji sai ya dawo sabo dal, na ji kamar na ce ya bar mini gidana amma babu halin hakan. Ya kwanta tare da rufe idonsa yana jina ina ta sakin maganganu bai tanka mini ba. Na goge hawayen da ya d'an zubo mini a kumatu na tashi na fita. Hauwa tana da ciki wannan ya nuna cewa daga zarar ta fara haihuwa zata kar'bi gidan. Ni kuma saboda son zuciyarsa na d'auki ciki na yi wahalar rainonsa da nakud'a na haihu daga baya abinda na haifa ya mutu. Ita Hauwa itace mai rayayyun 'ya'ya kenan. Kishi ya rufe mini ido gabad'aya tunanina ya kulle har sai da muka yi waya da Anti Yagana ta sake mayar da ni hanya tukkuna na dan samu sasaauci tabbas Allah ne mai yi kuma shi ne mai kashewa da rayawa. Idan ya so duka yaran da Hauwa zata haifa su zama rayayyu idan ya so kuma ya d'auki ransu ba kuma tare da wata lalura ba. Tabbas akwai wannan ciwon kuma kisa yake yi bayan ya gama galabaitarwa amma hakan ba zai zama hujjar da za a ce ba za a haihu ba domin yana iya canza komai hakan ba abu ne mai wahala ba a wurinsa. Da wannan tauhidin nata muka yi sallama jikina duka babu karsashi da sukuni na sake yin tubus a lokacin da na tuna irin rantsuwar da ta dinga yi akan yadda ta tabbatar da cewa yana sona domin idan babu soyayya ba zai ta'ba zama irin yadda nake so ba har ya kwana a k'ukutance gida irin wannan da babu tsaro a cikinsa. Haka na wanzu cikin nazari da tunanin rayuwar da zan fuskanta a gaba. Dutsan guga na ce Yusura ta kar'bo mini a shago, tunda ko babu wuta babban gen suke kunnawa da kaina na goge masa kayan tsaf na ajiye masa a gefansa bacci yake yi sosai wanda na tabbatar da cewa maganin da ya sha ne yake tasiri a jikinsa. Ni da yarinyar dai muka yi akin towon har da man shanu ya sayo na kuwa soya shi da albasa mai yawa. Na ce idan zai tafi asibiti sai ya zo ya tafi dana Gwaggo domin zai yi mata dad'i a baki. Na had'a masa komai cikin babban tire har zobo na yi masa wanda ya ji citta duk don saboda ya samu sau'kin kirjinsa. Biyu saura na koma d'akin har yanzu dai bai motsa ba ga lokacin sallah. A hankali na dan bubbigi gefan katifar bashi da nauyin bacci dama can ya bude ido yana kallona na ce." Lokacin sallah ya yi.". Ya yun'kura ya tashi zaune yana fad'in." Ina buk'atar ruwan zafi wanka zan yi tukkuna." Na ce." Da ka ha'kura da wankan nan tunda ba ka jin dadin jikinka." Girgiza kansa ya yi. "A a ki sama mini ruwan d'umi kawai. Na tashi na fita ban sake cewa komai ba. A babbar tunkuya na d'ora masa ruwan sai da ya tafasa tukkuna na juye a bokiti na surka da d'umi sosai na kai masa bandakin d'akin. Ya tashi jikinsa da kwari sosai ya shiga bandaki na bi shi da kallo jikina a d'an sanyaye ni kuma shine kaddarata jiyyarsa tsakanin jiya da daddare da yau jikina ya nuna ya na yi muguwar gajiya saboda kai kawo. Maganarsa na ji daga bandakin wai na mika masa kayansa. Ya zuro hannunsa na bashi kayan gabad'aya har singilitin da wandon ciki. Na je na d'auko tiren dana shirya masa abinci na ajiye masa a gefan daddumar dana shimfida masa. Bandakin tsakargida na yi wanka na koma cikin d'akin na same shi ya idar da sallah yana waya da Hajja har yana cewa da ita ta bashi Yusi. Ban ce komai na fara had'a masa abincin a maidaidaicin filat na ajiye a gabansa gefe da yajin daddawa da man shanu. Na tsiyaya masa zobon a kofi. Ga mamakina na ji ya fara dariya harda kyakyatawa ina jiyo muryar Yusi kad'an-kad'an ko me yake ce masa oho, na ji yana fad'in." Idan na kasa juyo da hankalinta kai ma sai ka zo ka gwada taka sa'ar don wannan Maman naka ta fini rigima." Na ji maganarsa Yana fad'in." Dukana za ta yi wallahi ni tsoronta nake ji Baba." Yana dai dariyar ya ce masa "idan ta dake ka sai na rama maka ai." Jin haka na san da ni suke lallai ma Yusi ashe na zama abin zolaya a wurinsa, ban yi tsammanin akwai ranar da za ta zo yaron nan ya manta da ni ba. Suna gama wayar ya dube ni yana fad'in." Kin ji ni da Yusuf ko? shi ya ba ni shawara na zo na baki hakuri, da na ce ya zo mu je tare ya ce a a dukansa ki ke yi.'' Murmushin takaici na yi na ce." Ai na ji abinda kuka shirya kai kuma ka rasa wanda zai baka shawara sai wannan mashiriricin." Ya d'an janyo filat din da nasa masa towon ya tallafe da hannunsa yana fad'in." To menene ai yaronki ne ya rayu dake zai fiye da ni zai fi kowa sanin halinki." Gyada kaina na yi a hankali na ce.'' Kun kyauta kai dashi ai." Ya yi bismillah yana cewa." Towon nan tun kafin na yi loma guda yawuna ya tsinke wallahi." Yadda ya tallafe filat din a hannunsa shine abinda ya ba ni dariya na tashi ina fad'in." Ka dai ci a nutse kada ka 'kware." Bai ce mini komai ba ya cigaba da cin abinsa na zauna gefan katifa a nutse na janyo akwatin kayana na shiga duba kayan da zan sanya na yi wankan tun d'azu amma ban samu sukunin canza kayan ba ballantana na yi sallah. Na ji dai dadin ganin yadda jikin nasa ya yi sau'ki gashi nan har ya zage yana cin abinci. [9/11, 9:26 AM] Aunty B: 78 Cikin rashin sukuni na gama shiryawa domin a jikina na ji cewa kallona yake yi. Ina juyowa kuwa muka yi ido hud'u da filat din towon a hannunsa yana ci yana kuma kallona kamar wanda ya samu tibi. Na d'an zumbura baki can k'asa-kasa na ce." Ni kam wane irin kallo ne wannan?" "Me ki ka ce?" Shiru na yi ban ce komai. Sai ya cigaba da cewa." Kin ce idan ni maye ne na ci kaina ko?" Da sauri na dube shi da mamaki a tare da ni." Haka na fad'a?" Na ce cikin sigar tuhumarsa. Sai kuwa ya daga kansa." Eh mana haka ki ka ce ai na ji, yanzu kuwa zan zo na cinye ki, ai kin ba ni magani na yi ragal da ni, sannan kin ba ni towo da tantakwashi me ki ke tsammanin zai faru?" Dariya maganarsa ta ba ni, na ce." Kana nufin ka warware kenan, muryarka fa har yanzu bata fita sosai." Yana sud'e yatsun hannunsa ya ce." Za ki tabbatar da haka idan ki ka ji ni a jikinki." Na ce." Ai ba ka fara ba, domin kuwa gidan nan bashi da wani tsaro kai ka san kanka ni ma nasan wanene kai ." Ya yi shiru bai tanka mini yana cigaba da sud'e hannunsa na ce." Wai miyar ce ta yi dadi ko towon?" "Duka sun yi dadi wallahi kin biya ni sosai yanzu abinda ya rage kawai ki cikashe ladanki ki ba ni kanki?" Girgiza kaina na yi kawai Ina dubansa. Wani irin mutum ne da bashi da ta ido sakaka yake sakin maganarsa babu kunya balle kawaici. Muka fara bugawa dashi domin akan sai ya kwanta da ni fa acewarsa towon da na bashi ne ya tayar masa sha'awa ni kuwa nasan ba haka ba ne kawai neman fitina yake yi tunda ya samu kansa mura da zazzafin sun yi sau'ki, na riga na san da wahala dama hakan bata faru ba sanin hali yafi sanin kama. Ya rufe d'aki gam! ni kuma ina jin tsoron yarinyar nan ta ji shiru ga d'aki a kulle ta gane wani abu muke yi. Ni kaina a cikin buk'atar nake nasan kuma yadda na tara sha'awa haduwarmu ba za ta yi kyau ba. Ganin yadda nake ta fargaba akan kada yarinyar ta fahimci wani abu da farko yana magana a hankali sai ya fara daga muryarsa tunda ya lura ba na son hakan yana cakumo ni da kokawa, takaici da b'acin rai suka dame ni, na rasa yadda zan yi dashi duk ya yamutsa ni gabad'aya rigar jikina ma ya cire mini. Hawayen takaici suka dan zubo mini a kumatu a mai hali baya fasawa. Muna tsaka da hakan aka kira wayarsa hakan ya ba ni damar kwacewa a gaggauce na d'auki rigata ina sanyawa a jikina. Hauwa ce ta kira wai bata da lafiya bayan haka kuma gidan ya yi mata girma. Ban jin amsar da zai bata ba na fita daga d'akin da saurin gaske tsakargidan na samu Yusura tana kwance kan tabarma tana kallo a wayata. Na sauke ajiyar zuciya cikin yakini da amincewa ba ta ji abinda ya faru ba tunda da alama kallon ya d'auke mata hankali. Na zauna gefanta muna kallon tare amma hankalina kaf yana kansa. Ina dan jin motsinsa da amsa kiran waya jefi jefi. To a takaice dai a ranar da yamma aka sallami Gwaggo daga asibiti Hamusu ya zo ya sanar da ni cewa yanzu tana gida kuma babbar yayarsu da take aure a kamaru ta zo yanzu haka suna tare da gwaggon. Na ji dadin zuwa Yaya Talatu da yake haka muke kiranta a can kamaru ta yi aure da yaranta hud'u shiyasa ba sosai a ake ganinta ba sai da gagarimin dalili tun bayan rasuwar Yaya Amina bata sake zuwa ba sai yanzu. Na tabbatar kuwa ba zata koma ba sai jikin Gwaggon ya kara kwari da izinin Allah. Hamusu kafin ya fita ya tambayeni Yallabai na ce masa Yana ciki Yana hutawa. Koda na koma d'akin sai na same shi akan dadduma ya idar da sallar la'asar muka had'a ido na yi saurin shigewa bandaki na d'auro alwala na fito fuskata a d'aure bai sake birjiro mini da wata fitinar fa ganin yadda na keta bata raina sosai ya ce na bashi ragowar shayin da na yi masa alkawari. Na hada masa da zafinsa rau na ajiye a gabansa sai bi na da ido yake yi Ina sake cin kunu. Ni kaina nasan abinda nake yi din bai kai a ce ya kyaleni dan shi ba sai don ya ga rashin dacewar hakan akaran kansa shiyasa ya janye fadi ma yake yi ya gaji da zaman gidan so yake dare ya yi yayi tafiyarsa. Uffan dai ban ce masa ba domin ba na so kuma wata magana ta yi tsayi a junanmu. A nan din ya yi sallar Isha'i, ya ce na d'umama masa ragowar towonsa na yi masa yadda ya buk'ata ya zauna ya ci sosai ya kira Sukairaju a waya suka yi magana duk Ina zaune minti talatin ya iso har kofar gidan. Nan na fahimci ya kira shi ne domin ya ja shi a mota. Da zai tafi bai sake tayar mini da wata magana ba, sai kuma jikina ya mutu na d'auka zai sake yi mini maganar zabar gidan da zan zauna kamar yadda ya bukata. Cikakkiyar sallama ba mu yi ba ya kama hanya zai fita, na bi shi a baya da agogonsa da ya manta a kan katifa. Ya kar'bi abinsa kawai ya yi gaba, hakan da ya yi sai ya tsaya mini a rai, ita gaskiya d'aci gare ta, ban ga abin jin haushi ba tunda iyakacin bakin kokarina na yi masa. Koda na idar da sallar Isha'i sai na kira Sahura na ci sa'a ta daga muka gaisa na ce." Kin daina jin haushina kenan?' Babu annashuwa ta ce." Ba zan daina jin haushinki ba sai kin gyara halinki." Ina dariya na ce." Wani hali ne da ni mai muni Sahura." Shiru ta yi mini ba ta ba ni amsa ba, na ce." Mutumin fa anan gidana ya kwana". Da mamaki ta furta." Da gaske ?" "Wallahi bai jima da tafiya ba ruwan jiya da daddare ya d'an same shi?" Tana jimantawa ta ce." Amina kin samu kan bawan Allan nan wallahi ki ji tsoron Allah, ban ga namijin da yake bibikon mace kamar na ki ba, ki zauna ki yi nazari ke kanki kin san idan baya tsananin sonki ba zai ta'ba yarda ya kwana a wannan gidan na ki ba. Ina dariya na ce." Haka ma Anti Yagana ta fad'a ni kuwa jinku nake yi ni nasan wanene shi, amma kin san wani abu ya ba ni tausayi ni kaina wallahi ba ki ga yadda ya sha wahala jiya ba saboda dukan da ruwa ya yi masa ya lafke zazzabi mura tari da ciwon kai da kyar muka rintsa ga uban sauro da zafi a d'akin." "Humm! ki bari dai ya k'wace miki za ki yi kuka wallahi." "Ba wani kuka da zan yi Sahura ha'kuri da juna muke yi ni dashi fa kuma kune kuke ganin kamar ni nake cutarsa, mu bar maganar nan haka sis tunda kin kasa fahimta amma ina so ki san da cewa amaryarsa na d'auke da juna biyu d'azu yake gaya mini." "To shine me? kema Allah Ya ba ki naki rabon ba shikkenan." "Sahura ba na jin fa zan yarda na sake haihuwa haka kawai ba zan yanki tikitin wahala da hannuna ba." A takaice ta ce." Shikkenan ai." Yadda ta fad'i maganar shi ya tabbatar mini da cewa cikin takaici take ta ce." Wanki fa nake yi ki ka kira waya zan kashe." Na ce." Da daddare wanki Sahura?' "Ina da me yi mini ne?'' Ta ba ni amsa a kufule?" Na ce." Ki had'a ki bayar zan biya." "A a, ni menene amfanin lafiyata." Na ce." Na ga alama rigima ki ke nema Sahura a ina zan samu mai kunshi ne?'' "Muna da su anan sosai." Na ce." To ko za ki turo mini ita ta zo ta yi mini." "Idan hakan ya yi miki sai na turo ta." Na ce." Duk abinki dai ba zan yarda na yi fad'a dake ba Sahura." Ta ce." Dama kin ji na ce miki mu yi fad'a, ai gaskiya d'aci ne da ita." Tafad'a tana d'an jan tsaki. Na ce." Ai na ji shawararki shiyasa ma na amince zan cigaba da zama dashi gashi har ina neman mai kunshi haihuwa ce dai na ce ba zan yi ba." "To kada Allah Ya sa ki yi, idan kin samu cikin ki zubar kawai." Ta datse kiran ba tare da na farga ba. Dariya na dinga yi mamakinta ya rufe ni wai lallai sai ta gaya mini bakar magana alhalin ba ita za ta yi mini zaman auran ba, mai d'aki shi ya san inda yake yi masa yoyo. To ashe da ya fita daga nan mutumin nan wurin Babanmu ya je. Ban san abinda ya gaya masa ba, ni wajejen tara da rabi gama wayarmu da Sahura da kadan Babanmu ya kira ni ya rufe ni da fad'a har muryarsa tana rawa yana fad'in idan na janyo masa zagi a gari sai ya yi mini Allah ya isa tunda hakki na uba ya sauke mini amma ina nema lallai sai na guji aure na yi zaman kaina, muddin wannan hanyar zan bi to zai zare hannunsa daga kaina. Ban yarda na yi jayayya dashi ba na dinga bashi ha'kuri har sai da ya huci na kuma yi masa alkawarin bin umarinsa. Na jima ina jajanta lamarin yadda babanmu ya hasala yana nema ya yi mini baki shine abinda ya fi daure mini kai, Ina ganin da ya tsaya mun gama magana a tsakanimu zai fi ba wai ya yi yun'kurin had'a ni mahaifina ba. Ba ni da lokacin tambayarsa akan dalilin da ya sanya ya yi mini haka hujjarsa kawai bukatarsa ta biya ta kowace hanya bai yarda da abinda ya aikata zai bata mini rai ba. Da takaicin hakan na kwana a raina don har na yanke shawarar kiransa a waya na tambayi jikinsa amma hakan da ya yi mini yasa na share shi ban neme shi ba. Da safe ya kira waya na d'auka muka gaisa ya fara tambaya ina maganarmu ta kwana. Na nuna masa ban san maganar da yake nufi ba. Ya ce." Maganar barin ki daga wannan gidan naki." Na ce." Yadda ka ce haka za a yi." Ina ji ya sauke ajiyar zuciya tabbacin maganata ta faranta masa ya furta." Zan zo da daddare saboda gudun idanun jama'a, kamar yadda na fad'a sai mu je ki za'bi gidan da za ki tare." A takaice na ce." Sai ka zo?" Ya ce." Na gayawa Hajja tare muke dake kina can gidanku idan na zo sai mu je can ku gaisa ko?" "To, kawai na ce masa. Na kasa daurewa dai na furta." Na gaya maka duk irin abinda za mu yi ni da kai ka daina had'a ni da mahaifina menene ribarka ta yin hakan, ai ni ba na gayawa mahaifiyarka abinda zai daga mata hankali." "Ni ma na gaya masa ne domin na rasa yadda zan yi dake, nasan shi kadai ne zai tursasaki ki bi umarina tunda ni kin raina ni, Amina ai ba zalinci a zamantakewar auranmu, to ni ma don Allah kada ki zalince ni, sakin da na yi miki kuskure ne da zafin kishi ba zan boye miki ba ina mutukar sonki wallahi akwai kuma wani bakin kishi da yake damuna akanki idan ya motsa mini ni kaina tsanar kaina nake yi balle wanda zai kusance ni. Maganar nan ta mutu haka kada wanda ya ji, in sha Allahu hakan ba zata sake faruwa muddin kin kiyaye faruwar hakan anan gaba. Maganganunsa suka kashe mini jiki, tabbas kowane dan adam yana da dabi'a, kuma yana kuskure babu wanda ya cika cif kuma ha'kuri a rayuwar duniya ya zama dole mussaman a zama na aure. Dukda namiji ba a cika yarda dashi dari bisa dari ba, amma a wannan karon na dan ji tausayinsa kad'an kuma kalamansa sun yi tasiri a gangar jikina ya gaji zaman lafiya yake nema. Sahura duk da ba mu rabu da annashuwa ba jiya sai da ta turo mini mai k'unshin da kwatance ta zo har gidan tunda bashi da wahala a bakin titi yake. Yarinyar ta iya kunshi sosai ta yi mini kafafu da hannuwa ja da baki wanda rabona da lallai tun na haihuwar baby Khadija. Sosai na fito kamar wata amarya na bata dubu goma Yusura ta je ta rakata bakin titi. Da ya zo bai shigo ba ya kira ni a waya ya ce na fito na same shi. Hijabi nasa har kasa na rufe fuskata da nikab da zan fita na ce Yusura ta kulle gidan ta ciki idan na dawo sai na buga. Can tsallake na hangi motar wata kala ce daban domin bata nuna alamun tasa ba ce wata'kila ya yi hakan ne domin kada jama'a su gane wanene tunda duk motacin da yake tu'ammalli suna da alama wannan babu wata alama sai ta lamba. Sukairaju na jingine a jikin motar shi ma fuskarsa rufe da fece mark. Ina karasawa ya risina mini muka gaisa kafin da sauri ya bud'e mini motar na fara ko'karin shiga yana hakimce cikin k'ananun kaya da rigar sanyi mai kauri a sama. Kansa sunfuke da hula irin ta sanyi har kunne ya rufe idanuwansa sakaye da gilashinsa na ka'ida. Na zauna sosai kafin Sukairajun ya shiga ya ja mota. A hankali na furta." Barka da dare, ya jikin?" Yana kallona ya amsa "Barkanmu dai ya gajiya?" Shiru na yi ban bashi amsa ba, shi ma bai sake magana ba wata'kila ya yi hakan ne saboda kusantuwar Sukairaju tunda kallon da ya yi mini da farko shi ya tabbatar mini da cewa akwai magana a bakinsa. [9/11, 6:25 PM] Aunty B: 79 Gidansa na unguwar sharada kwanar ganduje wajan gidan Hajiya Mariya shi ya fi kwanta mini a raina dalili akwai alkarya a wuraran kuma daf da titi ne, bayan haka kuma ya yi kusa da wajan gidan Sahura dukda akwai 'yar tazara amma dai ba sosai ba za mu dinga samun sau'kin ganin ganin juna mussaman daga bangaranta. Gidane iya gida wanda aka narka dukiya wurin gina shi, gini mai k'wari da nagarta da kuma ababen more rayuwa sabo ne ga dukkanin alamu ba a jima da gama aikinsa ba. A gyare yake ko'ina sai da ba a shirya shi da furnitures ba da sauran kyale-kyalen zamani gidan ya yi mini sosai domin bai kai girman na legos ba ya yi daidai da zama babu tsoro da fargaba. Ya ce tunda shi na zaba to shi ma ya yi masa gobe kuma zai sanya a shirya mini komai na ce to shikkenan. Muka shishiga ko'ina muka duba muka hau saman benan ya bud'e wani d'aki a saman wanda shi kadai ne a dan shirye shi ma ba komai ba ne sai babban kafet da tuntu manya manya irin na sarauta uku, da manyan labuleye da suka kewaye d'akin. Muka shiga d'akin yana gaya mini watani shida da suka gabata ya yi wani bako daga kasar senegal shine ya sauke shi a d'akin a dalilin tsaro da rashin yardar mutumin wai ya ji labarin najeriyar ta lalace da 'barayi masu satar mutane shine yake jin tsoron zuwa ya kwana a hotel. Anan ya sauka tsayin sati hud'u har ya kammala abinda ya kawo shi ya tafi. Dariya kawai na yi domin nasan mutumin yana da gaskiya najeriya ta lalace sai da ta katsan-tsanan. Ganin ya nemi wuri ya zauna har da kishingida a jikin tuntu na ce masa yana da kyau ya tashi mu tafi saboda dare ya fara yi goma har da minti biyar ga gari na damuna, ga kuma yarinyar mutane na bari a gida ita kadai. Bud'ar bakinsa sai kawai ya ce." Ai kin zo kenan Hajiya kayanki kawai zan tura Sukairaju yanzu ya d'auko miki." Ya fad'a babu alamun wasa. Da mamaki mai yawa a tare da ni na ce." Kai ma kasan hakan ba mai yiwuwa ba ne, ko ka manta da cewa na bar yarinyar mutane a gida, kuma me yasa Sukairaju zai je ya d'auko mini kaya ba ni da sirri ne, ai ba haka muka yi da kai ba. Ya tashi zaune sosai yana kallona ya ce." Ba mu yi haka ba, amma yanzu na yanke hukuncin yin hakan domin ban ga amfanin komawarki wannan gidan ba tunda babu wanda za ki yi wa sallama." Raina a b'ace na tsaya kawai ina dubansa gabad'aya ma bakina ya mutu da masifar takaicinsa na rasa ma wane nazari zan yi. ya yun'kura ya tashi yana ce wa. " Tunda ba ki aminta da Sukairaju ya d'auko miki kayanki ba ni ne ba kya so ba huta to zan koma tare dashi zan had'o miki kayan tare da yarinyar shikkenan ko ." Shiru na yi ban iya cewa dashi komai ba. Ya d'auki gilashinsa da ya ajiye ya sanya ya tashi yana sa takalminsa hanyar fita ya nufa na bi shi da ido ina jin wani bala'in takaicinsa, da gaske dai yake na zo kenan amma mutumin mugun dan rainin wayo ne, shiyasa wasu lokotan baya ba ni tausayi. Zamana na yi gabad'aya jikina babu k'wari na fito da wayata daga cikin jaka ina dubawa goma da minti ashirin a ganina yanzu kafin su dawo har sha daya na dare ta yi. Ni hankalina ma ya fi tashi akan yarinyar mutane da take amana a hannun Ina nan zaune tsit babu motsin komai sai uban hasken fitilu a ko'ina, tsoro ya dan shige ni na zame na kwanta a hankali ina kiran sunan Allah kad'aici ko kad'an bashi da dad'i Wajejen goma da minti arba'in kira ya shigo wayata na duba sai na ga lambar Sukairaju ban kawo komai ba na d'aga na ji shi cikin tashin hankali . A tsorace da kidima na tashi zaune." Hatsari Sukairaju Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! na tashi tsaye da wayar a kunnane yana fad'in." Ki d'an samu nutsuwa duk muna lafiya babu wanda ya samu mugun rauni Yallabai ne ma ya samu targad'e a 'kafa. Hawaye ya fara sauka a saman fuskata na ce.'' Ita yarinyar fa ina fatan lafiyarta lau, kuma ya aka yi hakan ta faru? kuuna Ina yanzu." Ya ce." Ga mu nan bakin titin rijiyar zaki wajan Musa iliyasu. Na ce." Garin Yaya haka ta faru Sukairaju ina Yallabai din bashi wayar ina so mu yi magana." Shiru na ji sai tashin iska gabana yana ta bugawa na ji gyaran muryarsa kafin ya ce." Babu wani ciwo mai muni fa ki kwantar da hankalinki." Na ce." Yanzu kuna Ina ku dawo gida don Allah dare ya yi ina Yusura tana nan lafiya ko." A nutse ya ce." Gata nan kusa da ni tana lafiya babu abinda ya sameta, ni ne ma na yi gocewar 'kashi a k'afata za mu zo yanzu." Ya kashe wayar bai jjra jin abinda zan sake fadi ba. A tsaye na wanzu har Allah Ya sa suka shigo gabad'aya Sukairaju da akwatin kayanmu ni da Yusura shi kuma yana dan jan kafarsa amma jikinsa kalau daidai da gilashinsa yana idonsa. Zuciyata ta dan yi sanyi na dubi Yusura sai zare Ido take yi kamar ma a tsorace take idonta da alamun kuka. Na kama hannunta muka shiga d'akin ta zauna jikinta a sanyaye. Shi kuma yana can nesa saman kafet tunda d'akin da girma sosai yana tattare kafar wadonsa da ya ji ciwo. Na tsaya kawai Ina dubansa ina jin wani iri a a jikina, na san akaina duk wannan abin ya same shi, ina ganin idan ban yi hakuri na zauna dashi cikin ko wane irin yanayi ba Allah zai iya saka masa. Sukairaju ne ya shigo ya ajiye kayan a gefe, shine kuma ya gyara masa targadan tunda ba yadda bai yi dashi ba tunda lamarin ya faru su wuce asibiti a duba shi wurin da ya goce asa magani ya ce a a baya son haniyar jama'a, za su dame shi da zuwa dubiya harda masu neman labari tunda abin ya faru cikin dare wajan da babu idananun jama'a sosai kuma ba a fahimci wanene ba kawai magana ta mutu motar ma a can suka barta bakin wajan da abun ya faru suka shigo babur din adaidaita sahu. Mamaki mai yawa ya kama ni. Lallai na yarda soyayya babu abinda bata sanyawa, tana k'askantar da mai mulki mai saurata attajiri mai ilimi da sauransu. A wannan ga'bar na jinjina masa sosai kuma na yaba masa har cikin raina. To shi dai Sukairaju ya san mota lafiyarta lau tunda sabuwa ce bata da wata matsalar komai amma bai san ya akayi har 'kososhin tayar baya suka kwance ba sai da lamarin ya faru wanda Allah ne kadai ya auna arziki da sai da a ji mummunan labari tunda sitiyarin motar da ya k'wace daga hannunsa kifawa motar ta yi da kyar suka fito. Kwana muka yi ba mu rintsa ba muna tattauna maganar ni da shi yana zargin dai akwai masu bibiyarsa tun bayan zuwansa zai dai tsananta bincike. Da gari ya waye muka tashi da gyara masu aiki suka zo domin su kintsa gidan. Sukairaju ya fita ya samo mana abinda za mu ci. Da muka yi waya da Hamusu na gaya masa yadda akayi amma ban fad'a masa tsautsayin da maigidan ya samu ba ya ce zai zo da yamma. Yusura kam yarinyar na da nutsuwa kasa zama ta yi tare damu a d'aki daya bacci ma jiya dan barawo ne ya sace ta kuma don ba yadda za ta yi ne ta kwana a d'akin wai sai ta fita sai da na yi mata jan ido tukkuna na nuna mata gidan sabo ne ko ta fita babu d'akin da za ta samu a kintse balle ta kwanta shine ta takure a wata kusurwa ta rufa da hijabinta. Da safe kuwa ta fice wai zata duba gidan . Jiya dai da abin ya faru jikinsa lafiya lau banda targadan da ya yi sai kujewa a daf da gwiwarsa bayan wannan kam babu wata matsala sai da garin ya waye kuma ya fara kuka da ciwon ga'bo'bi na ce masa asibiti ya kamata ya je a duba shi sosai ko da daddare ne tunda yana gudun idonanun mutane wata'kila akwai abinda ya bugu a jikinsa ya ce ba zai je ba na kyale shi kawai. Gabad'aya na rasa yadda zan yi da sha'aninsa jikinsa ya nuna alama yana buk'atar ganin likita. Ya d'auki wayarsa Ina zaune ya kira Sukairaju wallahi na zaci ya d'auki shawarata ne ashe ba haka ba ne, koda Sukairaju ya shigo sai ya rufe shi da fad'a irin wanda ban ta'ba ganin ya yi masa irinsa ba domin kuwa a cikin yaransa na tabbatar da cewa yana sonsa kuma tasu ta zo daya. Fadi yake yi da kai za a had'a ba ki a kashe ni ko Sukairaju me ya sa na d'auki amana ragamar kula da rayuwata shige da fice na da duk wani motsina amma za ka bada goyan bayan cutar da ni, ban aminta da kai ba a wannan ga'bar jiya na yi maka shiru ne domin ban gama nazari akan faruwar wannan lamarin ba, yanzu zuciyata ta amince mini da hadin bakinka wajan ganin kun kai ni kasa in banda kai babu wanda ya san na shigo garin nan ya aka yi har k'ososhin jikin sabuwar motata za su zube baka sani ba, ina kake ina ka ajiye motar ? Kai ne ka cire k'ososhin ko kuwa wani ka biya ya cire domin biyan buk'atarku wannan amsar nake so ka ba ni tun muna biyu ni dakai ka fito ka gaya mini asalin abinda ya faru. Ya zube a gabansa cikin tsananin damuwa da tashin hankali yana cewa." Wallahi Yallabai ban san yadda aka yi ba, kuma zargin da kake yi mini ba haka ba ne, ba ni da niyyar cutar dakai Yallabai shekara nawa muna tare menene ban samu ba ta dalilinka, babu abinda ba ka yi mini ba na rayuwa idan ma na cutar da kai nasan Allah ba zai barni ba, a ko'ina ne zan iya sadaukar da rayuwata akan taka rayuwar ni dai nasan lokacin da muka koma unguwar domin d'aukar kaya daka bar ni a bakin mota ka shiga gidan na dan zaga baya domin yin fitsari da na yi sai na fito sai na tsaya sayan lemon fata anan bakin titin dai shikkenan abinda na sani, ina kuma tunanin wannan damar aka samu har ka cire k'ososhin motar ni kaina ranka ya dad'e na fara zargin akwai hannun Alhaji Sammani a ciki dalili nasan tunda ka rubuta masa takardar sallama ba zai ta'ba ha'kura ba mutum ne ma'ketaci wata'kila yana bibiye da kai har ya gano kaine ake d'auka a motar dukda boyewar da ka yi, kuma ranka ya dad'e jama'a da yawa sun san kana garin nan tunda shekaran jiya mun shiga asibitin Malam Aminu cikin motocinka wanda kowa ya sanka dasu, to ka ga bibiyarka ba zai yi wa wanda yake burin cutar dakai wahala ba. Jin ya yi shiru kansa a kasa shi ya tabbatar mini da cewa maganganun Sukairaju sun kar'bu a wurinsa. Na ce." Kada ka yanke hukunci cikin fushi, ka yi bincike dukda abin akwai rikitarwa amma ba na tsammanin za a had'a ba ki da Sukairaju a cuce ka." Ya dube ni kafin ya ce." Za a had'a ba ki da Hamusu kenan?" Da tsananin faduwar gaba na ce." Hamusu kuma?" "Kwarai kuwa bayan shi wanene makusancinki?wanene ya kawo ni gidanki ta yaya za a kwance k'ososhin dake jikin tayar motata babu sanin Hamusu." Na gyad'a da zullumi mai yawa a tare da ni na furta." Ba na tsammanin haka ranka ya dad'e, dukda dai ba a shedar mutan amma Hamusu ba zai aikata hakan ba." "Me yasa kai tsaye ki ka fad'i haka umm?" Ya fad'a idonsa a tsaye akaina cike da zallar tuhuma da mugun zarginsa da ya motsa. Shiru na yi domin kuwa ba na so mu jayayya agaban Sukairaju. Ganin haka ya dube shi tare da ba shi umarnin fita. Ya tashi yana fad'in." Na gode Yallabai, amma ya kafar taka Ina fatan bata yi maka ciwo ko?" A takaice ya ce." Ta warke Sukairaju na gode, kada ka yi nisa zan iya nemanka a kowane lokaci." Ya d'an risina yana godiya kafin ya kama hanyar fita. D'akin ya yi shiru ni fargaba da damuwa sun ishe ni, zuciyata nata tsalle da k'in rashin amincewa Hamusu zai aikata mini haka. Wata zuciyar tana ce mini Amina makashinka fa yana gindinka, ba ki san menene a zuciyarsa ba zahirinsa kawai ki ka sani. Hawaye masu zafi suka fara kasa tsere a kumatuna idan kuwa hakan ya tabbata lallai Hamusu ya cutar da ni ya zalinci kansa ya zalince ni, ya 'bata mini nasabar yarana." Ya nisa kafin ya ce." Har yanzu ba ki yarda da maganata ba ko?" Girgiza kaina na yi a raunane na ce." Ba wai ban yarda ba ne, abun ne kawai yake ba ni mamaki da al'ajabi." Sai ya girgiza kansa yana fad'in." Ni ma zargi na ce Ina yi ba wai na ce shi din ba ne, amma dai kin san shine mafi kusa dake da ni, kuma shine ya yi mini jagora gidanki, kafin Sukairaju ya san inda nake wanene zai je ya kwance 'kososhin mota?" Ina kuka na ce." Yanzu ka gama fad'a zargi kawai kake yi baka tabbatar ba, to me zai sanya ka tsaye ba tare da ka tsananta bincike ba ka nuna shine, kenan zargin da kace ka na yi bashi da amfani kawai ka fito fili ka ce Hamusu ne yake yun'kurin raba ka da duniya shikkenan sai zambu da gugar zana su 'kare." [9/13, 10:30 AM] Aunty B: 80 Ganin yadda hankalina ya tashi da maganar da ya yi akan Hamusu ya sanya bai sake tashin maganar ba, amma nasan ba wai ya ha'kura ba ne ya yi shiru ne saboda bashi da tabbas akan abinda yake zargi. Ni kaina ba wai na ce Hamusu ba zai iya aikata hakan ba ne, ai da adam ne wanda yake tattare da ajizanci amma amincewa kai tsaye bashi ne adalci ba. Muna nan dai zaune ni dashi cikin rashin sukuni ya kira personal doctor dinshi a waya ya yi masa bayanin yadda yake ji a jikinsa gabad'aya ko'ina ciwo yake yi masa ga rashin test a bakinsa da zazzabi kad'an. Doctor din ya ce zai yi masa text na magunguñan da zai sa a sayo masa domin yanayin bayanin da ya yi masa yana tunanin zazzabin maleria ne ke so ya kama shi. Ban yi mamaki ba da farko kukan ciwon jikin da yake yi na d'auka tsautsayin da suka samu ne ya ce shi babu wani waje da ya bugu a jikinsa bayan 'kasan giwarsa da targad'an da ya yi. Tabbas zazza'bin kuwa zai iya kama shi sakamakon sauron da ya cije shi a gidana. Ya kira Sukairaju domin ya zuwa wajan sayar da magani ya sayo masa. Kafin shigowarsa na ce." Ni da za ka d'auki shawarata da ka je asibiti ba fa a wasa da lafiya." "Ba ina da ni ." Amsar da ya ba ni kenan babu walwala a fuskarsa. Sai na yi shiru kawai na zuba masa ido yana da wani irin hali muddin bai so yin abu ba to babu wanda ya isa ya tursashi, ni kuma a tunani na zuwa asibitin kamar zai fi muhimmanci ko da yake wannan din ma ga dukkanin alamu babban likita ne tunda ba zai d'auki likitan da bai san aikinsa ba domin duba lafiyarsa ba. Zuwa la'asar gidan ya shiryu ta ko'ina har kicin komai ya ji, da alama masu aikin sun jima suna murza zaransu domin ni na d'auka za su iya kaiwa dare basu gama ba. Suka tattara kayan aikinsu suka tafi lokacin ma shi maigidan yana bacci saboda ya sha magani. Ni da Yusura muka zagaye ko'ina dakuna ukun da suke falon dukkunnsu a shirye kowane da set din gado kewaye da labuleye masu kyau falon set din kujeru biyu ya ci masu kyau da tsada da labuleye wad'anda suka dace wurin tibi ma yasha ado mai d'aukar hankali ko'ina hasken fitilu irin na zamani sun shirya mini kicin dina tsaf duk abin buk'ata babu wanda babu da alama kamfanin sun jima suna yi masa aiki. Sukajiru ya dinga shigo da kayan abinci yana jibgewa a store din dake cikin kicin din da yake da yalwar gaske. Gidan ya ba ni sha'awa sosai kuma daidai misali domin bai cika girma na d'aukar hankali ba sai dai an tsara shi sosai daidai zaman da babu tsoro kuma babu takura. Da fargaba na tashe shi domin yin sallar la'asar ganin hud'u har da rabi ta yi nasan ba a yi masa gwaninta wani lokacin to amma ai babu biyewa son rai wurin take umarnin Ubangiji ina ganin idan har na bar shi ya cigaba da barcin lokacin sallar ya kure ina da lefi, bayan haka kuma shi kansa baccin gabanin la'asar ko bayanta Annabi ya yi hani dashi. Ya tashi kuwa da d'an sau'ki jikin nasa don har gumi yake yi yana gabatar da sallar ya nemi abinci don da alama cikin magunguñan akwai wanda ya ke bud'a ciki kuma wai towon dawa irin wanda na yi masa a gidana. Ban yi masa jayayya ba na fita na duba cikin store din duk kayan masarufin da Sukairaju ya zube babu na towo babu dawa balle alkama sai samovita sai shinkafar towo. Na fita na sanar masa Ina dasu a gidana zan kira Hamusu yanzu sai ya je ya kawo mini. Da yake yana buk'ata bai ce a a ba. Na kira Hamusu na yi masa bayani sosai yadda zai fahimta na kuma bashi kwatancen gidan, da yake dan halak ne awa daya da yan mintoci sai gashi a babur dinsa ya kawo mini komai. Sosai ya ba ni tausayi saboda hidimar da yake yi a kaina ko ciki daya muka fito iyakacin abinda zai yi mini kenan. Ya kuma ki tafiya wai lallai yana so ya gaisa da magidan kafin ya tafi. Sai na nufin saman zuciyata na dan bugawa na same shi yana waya da wani mutum na dan tsaya kimanin minti goma ya kammala kafin ya dube ni kadaran kadahan na ce." Hamusu ne yake so ku gaisa yana kasa na ce bari na nema masa izini." Ya d'anyi jim kafin daga bisani ya ce." Ya shigo mana." Na juya babu k'wari a jikinsa. Na same shi a falo suna dan hira da Yusura na ce .'Ka hau saman d'akin da yake kallonka yana ciki.." Ya tashi da sauri yana fadin." Bari na sauko yarinya sai kin gaya mini sunan saurayinki tunda ni ba kya sona." Na dube shi da mamaki yana hawa benan na dawo da kallona kanta sai sinne kanta take yi na ce." Cewa ya yi yana sonki ne?" Ta daga kanta tana dariya kafin ta ce." E, mana, ni kuwa na ce masa ai ina da saurayina." Murmushi na yi da cewa." A Ina saurayin naki yake ko shine dan gidan Yayar babanku wanda Sahura take gaya mini." Ta daga kanta da kunya mai yawa a tare da ita. Na ce." Hamusu kenan shi ma ai da alkawarin auran wata a wuyansa ko ta biyu zai yi dake ne?" Da sauri ta ce.'' A a mama ni fa ba na son kishiya." Ta fad'a har muryarta tana rawa nasa dariya ina fadin." To shi wanda kike so din kina da tabbacin ba zai yi miki kishiya ba." Shiru ta yi bata ce komai ba. Sai kawai na girgiza kaina na wuce kicin da tunanin halin kuruciya yarinyar. Cikin nutsuwa na fara gudanar da aikina gefe guda kuma ina cigaba da nazarin yanayin rayuwar nan ta duniya wato dai muddin kana raye ka dinga ganin abubuwan al'ajabi da ban mamaki kala kala. Muryar Hamusu na ji a kicin din yana fad'in." Anti ni zan tafi?'' Na juyo Ina dubansa yanayinsa ya nuna mini ba a nutse yake ba domin damuwa muraran ta bayyana a tattare dashi. Cikin nutsuwa na ce." Shigo ciki mu yi magana." Ya shigo yana sunkuyar da kansa kasa, tausayinsa ne ya kama ni har na ji kwalla ta cika idona tabbas mutumin nan akwai maganar da ya gaya masa wadda ta sosa masa rai da wahala ka ga Hamusu cikin irin wannan yanayin mutum ne mai ha'kuri da yawan fara'a ba ka taba gane yana cikin damuwa koda kuwa akwaita a tare dashi. Na ajiye rariyar da take hannuna na ce." Ko ba ka gaya mini ba nasan abinda yake da akwai amma ina so ka sani ban goyi da bayan wannan zargin da ake yi maka ba, kuma duk inda za mu je ina nan akan bakana ban goyi da bayan a tozartaka ba a shirye nake da barin auran akan a wulakantaka Hamusu na zauna dakai nasan halinka kiyashi ba zaka kashe da gangan ba balle har ka yi yun'kurin kashe mutum. Bincike dai ban hana shi ya yi ba, amma rashin sanin wanda ya aikata ba zai sanya a gazgata cewa kaine ba, ai alheri ba ya zama sharri Hamsu ka samu nutsuwa kuma kada kada damu gaskiya zata bayyana. "Wallahi anti gabad'aya a cikin fargaba nake ya za a yi na aikata wannan mummunan aikin me ya yi mini da zan yi yun'kurin kashe shi a yake gaya mini fa wai lallai da sanya hannuna wurin faruwar hakan, wallahi tallahi anti ban aikata ba, ai mutumin nan alheri ya kamata mu yi masa duba da abubuwan da yayi mana na sadaukarwa da taimaka ko k'aunar jininmu da yake yi ya cancanci sadaukarwa ta kowane fanni, shiyasa hidima idan tasa ce wallahi ba na gajiya koda kuwa zan kwana a tsaye. Na yi mamakin jin wannan furucin daga bakinsa anti duk da duniya ta lalace akan samu irin hakan amma wallahi ni ba na daya daga cikin butulayen mutane." Na ce." Kada da ka damu Hamusu ka shige ka je ka cigaba da sabogiginka hankalinka kuma ya kwanta barazana yake yi maka domin akan bincike yake har yanzu shi ma bai gama tabbatarwa ba." Ya girgiza kansa a sanyaye ya ce." Shikkenan anti ni ma kuwa ba zan bari ba wallahi zan tsananta bincike na kuma sanya ido domin tonuwar asirin wad'anda suka aikata hakan." Na ce." Shikkenan hakan ya yi amma don Allah kada ka gayawa kowa maganar nan Hamusu ka barta cikin ranka." Ya ce." Na yi alkawarin yin hakan in sha Allahu rabbi anti. To har na gama aikin zuciyata ba ta daina tsalle ba. Nasan idan na tunkare shi da maganar tutsiyar da ya yi wa Hamusu cibi ne zai zama 'kari dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki sai kawai na share shi ban nuna masa cewa nasan abinda ya yi ba. Sai da na hada masa komai tukkuna na sauko daga saman na samu Yusura ta yi wanka ta shirya tsaf na ce taje ta d'ebi abinci wanka zan yi tukkuna. Na shirya cikin doguwar riga ta atamfa duka kala shida na zo dasu hud'u sun yi datti saura biyu kacal itama Yusuran nata sun yi datti na ce da safe sai ta wanke mana tunda akwai na'uwarar wanki a gidan. Sai komawa na yi saman a karon da ba zai lissafu ban ji matsalar hawa tunda kamar ina motsa jikina ne shiyasa hakan baya damuna. Na sake samunsa yana waya amma cikin fushi da kuma kausasan maganganu da harshen nasara ya canza harshe sosai na yi tsam Ina kallonsa gabad'aya baya hayyacinsa gumi sai yanko masa yake yi na b'acin rai da kuma saukar zazzabin da yake damunsa Fankar da ya umarceni da na kashe a d'azu da safe ita na kunna masa domin ita kanta rigar da take jikinsa daga baya ta jike da gumi. Turanci yake yi tsantsa har yana hadawa da yaran chanis wanda ban ta'ba jinsa a bakinsa ba ashe komai dalili yake yi. Na d'an fahimci wasu abubuwan amma kasancewar ban ji farkon maganar sai na gaza fahimtar mai yake faruwa. Ba wai dukiyar ba irin wannan kalubalen da farautar rayuwar mutum shine abin damuwa. Ya kai karshen maganar da bada umarni a rufe kamfanin gabad'aya na fi tsammanin wata matsalar ce kuma take shirin kutso masa bayan ga wata ba a kashe ba. Wannan kadai sun isa su hargitsa masa lissafi.. Ya kira Sukairaju a waya minti biyar ya shigo ya ce masa maza ya je Danbatta gidan Hajja ya debo masa kayansa na sanyawa da ya zo da su da laptop d'insa ya bashi key din d'akin. Bayan fitarsa ya dube ni Yana fad'in." Ki sama mini ruwa na yi wanka na samu sau'ki." Na ce." Ai wanka ba naka ba ne yanzu koda kuwa da ruwan d'umi ne saboda kada kuma zazzabin ya dawo." Cike da tsawa ya furta." Sai na yi ta zama cikin zuffa ina tsami kenan malama ki yi abinda na ce ko na tashi na yi da kaina, ai Allah Ya hore mini hannu." Tashi na yi na sauka kasa ina mamakin abin daga shawara sai masifa da bakar magana. Sai dana sauka kasan sannan na tuna akwai bandaki a cikin d'akin da yake na sake komawa sai na same shi a toilet din yana kwance shaya wadda ni a tunanina ma kwata kwata bata aiki sai naga ruwa ya kashe ya fara ko'karin cire rigar jikinsa. Shiga na yi bandakin na bude shayar ruwan da yake zuba bai cika sanyi ba da yawa zai yi daidai wanka a yanayin tunda ba zafi ake yi ka'in da na'in ba kuma ba sanyi ake yi ba. Ban ce masa komai ba na fice daga bandakin domin zuciyata ta fara yin zafi akan abinda yake yi mini duk kuwa da ko'karin da nake yi akansa Ban sake hawa saman ba domin ina ganin yin nesa dashi din zai fi mini kwanciyar hankali muddin bashi ya neme ni ba. Yusura tana falo a kwance cikin kujera tana kallo a wayata ashe finafinan da Yusi ya uzzura a tura a wayar za su yi rana. Na kar'bi wayar domin Ina son kiran anti Yagana dalilin damuwar da take damuna. Komai na tibin dake falon a hade yake sai na kunna mata tunda na lura ma'abociyar son finafinan indiyace na kamo mata tashar da suke yin fassarar hausa. Ta kuwa gyara zamanta sai kace mai d'aukar darashi. Cike da mamaki da zullumi anti Yagana ta furta." Hamusu ba zai aikata wannan d'anyan aikin ba Amina, a dai kara bincike da kyau a jikina nake jin hakan akwai dai makarkashiya amma ki bi komai sannu a hankali kuma don Allah ki dinga tausar zuciyarki akan mutumin nan ki yi duba da yanayinsa da al'amuransa na yau da gobe wasu abubuwan dole a yi masa uzuri ki bari ya samu nutsuwa ta bangaranki koda ya yi miki abinda ranki bai so ba ki tuna alherinsa ki yafe masa, ki yi kokarin ri'ke auranki domin a yanzu dai samun makamancinsa zai yi wahala Amina kuma mazan duk haka suke wallahi kwaryaar sama ce take dukan ta kasa kusan duk haka halinsu yake." Maganganun anti Yagana sun sanya mini kwarin zuciya na aminta cewa babu wata nasara a rayuwa face ba a ci karo da kalubale ba. Sannan kuma babu yadda za a yi a ce zaman aure ba a samu wata tangard'a ba. Wannan dalilin ne ma ya sanya ban turje masa ba da ya nemi inda nake hakan da na yi sai ya siya mini mutunci tun bayan tsawar da ya yi mini dazu akan maganar wanka ban sake nemansa ba wata'kila ganin haka ya sanya ya gane rashin kyautuwar abinda ya yi. Ai kowa rai ya yi wa dadi barin me shine iyakacin bakin kokarina ina yi akansa Allah ya sani da don ta ni ce da tuni ba wannan zancen ake yi ba domin a ganina tunda auran ba farilla ba ne sai na yi kokarin ri'ke kaina da sha'awata na tsira daga takaicin d'anamiji. Ya shigo Yana gaya mini an bar tibi a kunne na je na tashi Yusura ta je ta kwanta bacci ya dauketa a kujera. Ban ce komai ba na tashi na fita falon na sameta tana bacci sosai na kashe tibin sannan na tashe domin ta shiga daya daga cikin dakunan dake cikin falon ta kwanta ta kafe itafa a falon zata kwanta kan kujera. Ba na son matsa mata sai na kyaleta ta koma ta kwanta kan kujerar tana layin bacci. Ban kashe mata fitila ba saboda kada ta farka taga duhu ta ji tsoro tunda na lura zabuwa ce itama ba lefi. Na same shi zaune a gefan gado bai kwanta ba amma ya cire jallabiyar jikinsa yana zaune da k'ananu na ciki. Jigum din da ya yi ya d'an ta'ba ni kadan ko zazzabin ne ya ji dare yake so ya dawo. Na daure na ce." Ya jikin fatan dai zazzabi ya gudu." Lumshe idonsa ya yi a hankali ya ce." Na ji sauki alhmdullhi Doctor Saleh ai ba karamin likita ba ne, Allah Ya hore masa, ke ma na gode da kokarinki." Na ce.'' Kokari akan me?" Yana kallona ya furta." akan dawainiya da jinyar da na sanya ki." Murmushi na yi na ce." Ba komai Baba." Ya tsira mini ido yana kallo na haye gado ina fad'in.'' Ka kwanta ka samu hutu sosai da safe na san za ka sake samun kwarjin jiki." Ya nisa kafin ya ce." Duniyar gabad'aya ta yi mini zafi Amina ina jin wani yanayi a jikina mara dad'i, d'aukaka ko wata rigar arziki sukan zamewa wanda Allah ya ratayawa matsala babba." Hankalina na mayar kansa a nutse na ce." Kuma haka Allah Ya tsameka daga cikin dubban mutane ya rataya maka, ai wata ni'ima ce babba muddin ka yi amfani da umarinsa yadda ya ce shi kuma zai kare ka daga kariyarsa amma ina so ka sani dole ba zaka yi ta zama ba tare da jarrabawa daga Ubangiji ba. Kuma ba zaka hana mutane yin abinda zuciyarsu ke so ba, kawai ka yi ta addu'a da neman kariya." Ajiyar zuciya ya sauke a nutse ya furta."Allah Ya kyauta na gode miki ina jin kunyar Hamusu bisa titsiyar da na yi masa d'azu a yanzu kunyar yaron nan nake ji wallahi ni kaina nasan ban kyauta ba yanzu da gaskiya ta bayyana Alhaji Sammani babban yarona da muka sha gwagwarmaya a baya shine ya shirya kashe ni dalilin tonuwar asininsa bayan take hakkin marayu she ya jima yana cutar da ni ta karkashin kasa ya kuma yi mini asarar wasu muhimman kadarorina gabad'aya ma ni ba wannan ne abinda ya dame ni ba sai mamakin halin d'an adam ban san me Sammani yake nema a wannan duniyar da ba madawwamiya ba.