GIMBIYA NAFEESAH [6:58pm, 06/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ©ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Wata yarinya muka gani ta rugo dagudu tana kwala ma baba Rabi kira,baba Rabi dake kitchen tana ma kuyangu bayanin abinda sarki zaici da dare jin k’iran yayi yawa yasata fitowa. Yarinyar ta iso wajen baba Rabi tafara hak’i,alamun dai tasha gudu ta gaji,yarinyar tace “ba….ba….Rabbb….iii…na….bi…” baba Rabi tayi saurin tsaidata tace “Ni fah bana gane meh kike fada,ki nitsu saikimin bayani” yarinyar tayi shiru tana maida numfashi,sai bayan ‘yan seconds sannan tadawo daidai,baba Rabi tace “Inajinki Amina,biyoki akayi neh kikazo da irin wannan uban gudun?” yarinyar da aka k’ira da Amina tace “A’a wlh baba,Nabila ce take dukan Jamila achan wajen bishiyar da muke zama” baba Rabi ta dafe k’irji gamida yin salati tace “Ohh ni Rabi,wacce irin hasabibiyar yarinya neh wannan?,muje” cikin sauri suka nufi wajen bishiyar da Nabila ke zama tareda sauran sa’anninta suyi hira da yamma. Muma dai muna biye da ita don ganin ma idanunmu abinda ke faruwa Baba Rabi na isa wajen taga Nabila akan Jamila sai jibgarta takeyi kamar an aikota,bata ma san baba Rabi tazo wajen ba,cikin zafin nama da bacin rai baba Rabi ta buga mata wani uban dundu wanda saida yayi k’ara. Bashiri Nabilah ta bar jibgar Jamila ta duruma ashar tace “Kan ubanchan!!! Wani dan iskan neh yamin wannan dundu haka? Wlh saina rama” sannan ta tashi daga kan Jamila da bakinta yafara jini tafara karkade jikinta ta k’ara tamk’e damarar ta yanda zataji dadin dambe,tana juyowa tayi karo da baba Rabi wanda fuskarta yana murtuk’e ba alamar wasa a tare da ita. Cikin in’ina Nabila tace “Ba…ba…wlh….” baba Rabi ta wanketa da mari tace “Ke wace irin yarinya neh wai?ba ranar da gari zai waye har dare yayi bakiyi dambe ba” idon Nabilah suka ciko da kwallah amma ta danne don ta tsani aga hawayenta,acewarta wai in an gani za a rainata don ita batason raini. Tajuya wajen da Amina take rak’ube ta wurga mata harara tace “Toh munafuka algunguma,kinji dadi tunda kin kai gulma kuma anzo an mareni,wlh karki yarda muhadu don saina miki lis kuma…” baba Rabi ta gubje bakin tace “Yi min shiru,kuma ki wuce d’aki kizauna sanna karki kuskura kice zaki tab’a Amina in ba haka ba saina mugun sab’a miki” Nabila ta share hawayen da yafito daga idonta sakamakon bugun bakin da baba Rabi tamata yayi zafi sosai,batace komai ba tajuya tana guna guni tayi cikin gida Nan baba Rabi tadago Jamila da har yanzu ta kasa tashi daga inda Nabila ta barta sannan tace “Jamila meh ya hadaki fada da Nabila?” cikin kuka Jamila tace “Ba abinda namata wlh,muna wasa neh sai kawai tahau kaina ta fara naushi nah” baba Rabi ta girgiza kai tace “ki gayamin gaskiya,duk da nasan Nabila mafad’aciya ce na karshe amma nasan bata fada sai an nemi tsokanarta,share hawayenki” nan Jamila ta share hawayenta sai tace “Wai fah don kawai nace mata ‘yar duma-duma shine ta dakeni” baba Rabi ta jinjina kai tace “Yi hak’uri kinji Jamila,tunda kinsan batason sunan sai kibar kiranta dashi” Jamila ta k’ara share kwalla tace “Toh baba”. Baba Rabi tayita bata baki har ta hak’ura ta karkade jikinta tayi dakinsu. Haneefah Usman da Maman Khalil [7:15pm, 06/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ©ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Baba Rabi tajuya takoma kitchen don k’arasa ma mai martaba abincinshi. Abangaren Nabila kuwa tunda tabaro wajen damben nata tak’i tafiya d’akinsu,d’akin Nene ta nufa(Nene wata kuyanga ce wacce take aminiyar baba Rabi acikin gidan sarkin,tana sayar da kayan yara). Bayan maghriba baba Rabi tayi d’akin Nene don suyi hira kamar kullum,tana dosar d’akin taji muryar Nabila tana ta kyalkyala dariya,tayi sallama suka amsa mata sannan ta shiga. Tana zama akan taburma tajuya wajen Nabila ta mata wani kallo wanda yasa Nabila mik’ewa bashiri tayi hanyar dak’insu,tana fita Nene tace “Haba Rabi,mesa zakizo ki koranmin ‘yata bayan kinzo kin samemu muna hira cikeda nishadi?” baba Rabi ta furzar da iska tace “Nene,wlh al’amarin yarinyar nan ya isheni,ni sam bansan ma ya zanyi da ita ba,fad’an yau daban na gobe daban” Nene tace “Kiyi hak’uri Rabi,in ta girma zata bari,yanzu ma don yarinta neh yake damunta saisa” baba Rabi tace “Toh dai,Allah yasa hakan amma fah yanzu kamar abun nata k’ara gaba yakeyi” Nene ta danyi murmushi tace “Nabilah kenan,zata bari fah” nan dai suka cigaba da tattauna matsalolinsu har wajen tara na dare sannan tayima Nene sallama ta nufi d’akinta. Tana shiga d’akin taci karo da Nabila tana zaune akan sallaya tana karatun Qur’ani,saura kadan dariya ya kubce ma baba Rabi don kuwa tasan Nabilah tayi hakan neh gudun masifar da zata mata. Saida ta gama karanta surah din sannan tarufe Qur’anin ta maidashi mazauninshi sai ta tsugunna agaban baba Rabi tace “Umma,don Allah kiyi hak’uri kinji,bazan sake ba na rantse miki” baba Rabi tayi ma Nabila nasiha sosai,Nabila ta k’ara bata hak’uri sannan suka kwanta bacci. Wacece Nabilah??? Haneefah Usman da Maman K [7:33pm, 06/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ©ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Sunanta Nabeelah Musa,’yar Baba Rabi wacce take matsayin jakadiya a gidan sarki Mu’awiyah Abubakar,sarkin garin Yura dake Kaduna state. Sarki Mu’awiyah sarki neh meh matuk’ar adalci da son talakawanshi,yanada mata daya mai suna Sarauniya Hafsat wacce yaran gidan da ma duk ma’aikatan gidan ke kira da “Yabi”,macece saliha wacce bata muzgunawa wadanda ke aiki a k’ark’arshinta. Sarki Mu’awiyah yanada ‘ya’ya biyu kuma dukkansu maza neh,na farko sunanshi yareema Sultan sai na biyun kuma Saleem. Sultan bai cika zama a garin Yura ba sabida yanayin aikinshi,ahalin yanzu ma yatafi k’aro karatu neh while Saleem kuma yanzu yana University a China ,akwai tazaran shekaru kusan 8 tsakanin Sultan da saleem. Sultan fari neh kyakkyawa,miskili neh na karshe,saidai inya saba da mutum yana da fara’a. Saleem on the other hand kuma yanada surutu ba kadan ba,ko baisan mutum ba akwaishi da tsokana saisa yawancin mutane suka fi son maganar Saleem. Sultan yafi Saleem kyau nesa ba kusa ba Nabeelah yarinya ce wacce ta tashi a cikin gidan sarkin Yura,’yar kimanin shekaru 12,tanada d’an jiki sannan kuma batada tsayi shiyasa yawancin yara suke tsokananta da “‘yar duma duma”,tanada kyau wanda yananan daidai don kyaunta irin na boyen nan neh,batada haske sosai but tanada gashi irin na fulanin usul,mutane har mamakin rashin kamanninta da baba Rabi sukeyi,dayake mijin baba Rabi yarasu kuma yawanci basu sanshi ba saisa suke tunanin ko kamannin babanta na fulanin usul ta dauka don bata kama da baba Rabi ko kadan. Nabeelah tanada tsiwa ba kadan ba,batada tsoro,duk girman mutum da matsayinshi inhar ya takulo ta toh fah za aga rigima,yaran da ke zama agidan duk tsoronta sukeji don tana jibgarsu ba kadan ba,tanada surutu sosai. Aminanta guda biyu neh-Amina da Jamila,suma yaran masu aiki agidan sarki neh,dayake duk masu aiki sarki yana basu daki daddaya saisa yawanci sukazo da ‘ya’yansu mata. Amina,Jamila da Nabila tare suka taso tun suna ‘yan kanana suke tare saidai fah duk da sha’kuwar dake tsakaninsu da Nabila bai hanata jibgarsu,inka shiga fadarsu ma mutum zaiji kunya saisa iyayen ma basu magana ko sun dawo da ciwuwwuka,duk fadar da sukayi zuwa safiya suke ‘kara shiryawa su koma kamar basu ba. Wannan kenan Haneefah Usman da Maman Khalil [11:02pm, 06/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ©ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Washegari kamar kullum suka tashi sukayi sallah sannan suka zauna tilawar Qur’ani har rana ya fito. Baba Rabi ta tashi tsaye tace “Yauwa Nabila kije wajen Yabi ki tambayeta ko akwai abinda zaki kama mata kamin nazo,yanzu zanje na hada ma mai martaba karin kumallo neh” Nabila ta amsa da “Toh umma,barinje yanzu” sannan ta tashi tazo ta wuce ta gefen baba Rabi,tare suka jera har ‘kofar kitchen din sannan Nabila tace “Natafi umma” baba Rabi tayi murmushi tace “Don Allah yaukam karkiyi dambe da kowa kinji?bakiga kin girma bane? kuma ma ai manyan mata basu fada” Nabila tayi dariya tace “kai umma,shine harda wani cemin don Allah,In Sha Allahu bazanyi dambe ba” baba Rabi ta ‘kara murmushi tace “kije toh,Allah yamiki albarka” Nabila ta amsa da “Ameen” sannan tajuya tayi hanyar sashen Sarauniya Yabi Ta isa parlourn tayi sallama,kuyangu da suke ta kai komo neh suka amsa mata,ta gaishesu sannan tace “Yabi fah?” d’aya daga cikin kuyangun mai suna Zuhura tace “Tana daki”. Girgiza kai kawai tayi saita wucesu zuwa d’akin Yabi. Da sallamarta ta shiga,suka amsa mata,ta tsugunna cikeda girmamawa ta gaida Sarauniya Yabi,Yabi ta amsa mata cikin sakin fuska don ita harga Allah tanason Nabilah ba kadan ba,wata rana har tana cewa inama da ‘yarta neh. Bayan sun gama gaishe gaishen neh Nabila tace “Ranki ya dade ko da akwai abinda zan kama miki?baba Rabi tace kiyi ha’kuri yanzu tana had’ama mai martaba abin karyawa neh” Yabi tayi wani ‘kayataccen murmushi tace “bakomai Nabee,kawai dai kije kice mata ta sa a toya ‘kosai ayima yara sadaka awaje”. Nabila tace “Toh angama” sannan ta tashi ta isar da sa’kon Yabi zuwa ga baba Rabi Haneefah Usman da Maman Khalil GIMBIYA NAFEESAH [7:15pm, 16/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Baba Rabi tasa ‘kuyangi aikin ‘kosai kamar yadda suka saba wani lokacin sannan aka rabawa yara a waje. Da yamma Amina da Jamila suka gama shirin islamiyya tun da wuri sannan suka nufi dakinsu Nabila,sun isa lokacin ma ta fito daga wanka tana shafa mai a hankali. Jamila ce tafara magana tace “Laa!! Nabila dama baki gama shiri ba?kinga fah hudu ya kusa kuma ana dukan latti” charaf Amina ma ta ‘karba tace “Allah Nabila baki kyautawa,don ke baki tsoron bulala saisa kullum kike samu lattin amma ai mu muna tsoro” mtswww Nabilah taja wani dogon tsaki tace “Subhanallahi,kai ni fah kun cikamin kunne kun takuramin,d’aure ‘kafafunku nayi neh da dole saikun jirani mun tafi tare? In bazaku iya ba Bismillah ku kama hanya,saimun hadu a aji”. Jamila ta bude baki zata yi magana amma Amina ta girgiza mata kai akan tayi shiru gudun kar daga magana kadan cibi yazama ‘kari,asanyaye Amina tace “Allah yabaki ha’kuri,barimu jiraki a ta ‘kofar gida” batare da ta kallesu ba tace “Naji,saiku fita bari nasa kaya”. Jamila ta ‘kulu iya ‘kuluwa don itakam ta tsani hali irinna Nabilah,hali na gadara da ji da kai kamar ‘yar MULKI KO SARAUTA. Basu sake cewa komai ba suka juya suka fita daga dakin. Nabila bata fito ba har wajen 4:15,ta iso wajensu tana taku d’ad’d’aya,tace “Mutafi ko?”,suka kama hanya sai islamiyarsu da ke da d’an nisa da masarautar. Suna shiga gate na islamiyar sukaga an tara ‘yan lattin kuma malam Dawud neh yake duka,zo kuga su Amina da Jamila jikinsu sai rawa yakeyi,Nabila kuwa ko a jikinta tunda dai ita ba tsoron bulala takeyi ba. Malam Dawud yamusu bulala biyar- biyar,Amina da Jamcy sai kuka sukeyi harda ajiyar zuciya,nan duk suka kama hanyar ajinsu da yake aji uku suke dukkansu. Suna wucewa neh sai wata ‘yar aji biyar mai suna Aceey tafara musu dariya tana nunasu da hannu,Nabilah taja tsaki tace “Kutuma,kuna ganin yarinyar nan wai dariya take mana,kuzo muje muci ubanta” Amina tace “Nikam wlh bazanje ba” Jamila ma tace “Nabilah ki raba kanki da fada,ba sai tayita dariyan ba in tanaso” Nabilah tayi wani mahaukacin dariya tace “Ai wlh in na bari an sha da ni”. Dasauri ta nufi wajen da Aceey take zaune,Aceey ta sunkuya tana daukan pencil nata da ya fad’i a’kasa kawai saitaji an tureta,jikake ta fadi a’kasa tim,dama Aceey irin yarannan neh marasa ‘karfi amma sai tsokana. Nabilah dukanta takeyi ba ji ba gani har saida aka kira malamai da kyar suka raba fad’ar,fuskar Aceey duk yayi ja tsaba naushin da tasha,aka tattara su aka kaisu office na headmaster,nan aka ma Aceey bulala takwas tunda ita fara tsokanar sai akama Nabilah kuma guda uku. Haneefah Usman da Maman Khalil [7:15pm, 16/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Nabilah haushi bibbiyu ya hadun mata,ga haushin an rabata fad’a da Aceey ga kuma dukan da tasha. Har aka tashi daga islamiya ba wani walwalar kirki a tare da ita. Suna isa gida tawuce da’kin Nene don tasan bazata rasa rake ko aya awajenta ba,a ‘ka’idar ta inhar ranta ya’baci toh fah abu biyun nan neh kawai suke sata nishadi. Ta shiga ‘dakin Nene da sallamarta,cikin sakin fuska Nene ta amsa mata sannan suka gaisa,chan sai Nabilah tace “Nene rake nakeso” ko da Nene taji haka tasan dawar garin,ta tashi ta dauko mata rake sanda daya da aya ‘kulli daya. Nabila ta cire himar nata ta gyara zama tanashan rakenta suna hira da Nene,sun dad’e kad’an sannan ta tashi ta koma d’akinsu tacire uniform nata sannan tayi alwala tayi sallah da ‘yan nafiloli don Nabila ba baya ba wajen ibada duk da ‘karancin shekarunta. Wajen ‘karfe 8pm baba Rabi takai ma mai martaba abinci,Nabila tagaji da zama ita kadai kawai saita tashi ta nufi sashen Yabi. Sun dade suna hira,acikin hirar neh ma Yabi tace “Nabee,auta nah zai dawo gobe fah” Nabila tadanyi murmushi tace “Ayyah,ni bansanshi bama” Yabi tace “Ehh,lokacin da yatafi kina bakida wayo saisa”,Nabilah ya jinjina kai tace “Hakane kam,Allah ya kaimu”,Yabi tayi murmushi tace “Ameen Nabee” Haneefah Usman da maman Khalil [7:15pm, 16/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Da asubah bayan sun idar da sallah baba Rabi tace “Nabilah”,Nabilah ta amsa a nutse “Na’am ummu”,baba Rabi ta gyara zamanta tace “Yau d’ana zai dawo wato saleem,autar gidannan”,Nabila tayi murmushi tace “Eh jiya da dare Yabi ta gayamin”. Baba Rabi ta d’anyi jim sannan tace “Inaso ki nitsu,banda wawanci da sakarci,banda raini don shi ba sa’ar ki bane,duk abinda yace kiyi inhar bai sa’bama addini ba”,Nabila ta sunkuyar da kanta ‘kasa asanyaye tace “Toh umma,nagode kuma zanyi abinda kikace” baba Rabi tayi murmushi tace “Allah yasa miki albarka ‘yata” Nabila ta amsa da “Ameen”. Gida ya kachame da shirye shiryen dawowar Saleem,abinci kala-kala,ga wasu decorations da akayi an rubuta WELCOME HOME AUTA(dayake Auta iyayenshi ke kiranshi). Misalin ‘karfe biyar na yamma Saleem ya iso masarautar Yura,motocin da suka tarboshi ni kaina kasa ‘kirgasu nayi,jeeps neh masu numfashi ba’ka’ke sai she’ke sukeyi,aka shimfid’a red carpet daga ‘kofar motar da zai fito har zuwa sashen mai martaba sarki Mu’awiyah. Fuskokin ‘yan gidan cike yake da murna. Yadau lokaci kad’an sannan yafito,black jeans yasa da t-shirt fari,kyakkyawa neh irin chocolate in complexion haka. Taku yakeyi irin na ‘ya’yan sarauta masu ji da kudi da mulki,mutane sai kwasan gaisuwa sukeyi,bakinshi ya kasa rufuwa tsaba jindadin dawowarshi cikin familynshi. Yana shiga fada dagudu yaje ya rungume Yabi yace “Ummi,I missed u very badly,kullum ‘kara kyau kikeyi” Yabi sai murmushi takeyi tace “Auta,kai baka girma ko?” dariya yayi sannan yace “Inhar a wajenku neh kam toh bana girma” duk sukasa dariya sannan yaje ya rungume mai martaba. Aka gaggaisa sannan ‘yan fada suka watse suka barsu su ukun,chan sai saleem yami’ke,Yabi tace “Auta ina zuwa daga dawowarka?” murmushi yayi yace “Ummi banga baba Rabi ba shine zanje na dubota” girgiza kai kawai mai martaba yayi don shi har mamakin sha’kuwar da ke tsakanin baba Rabi da Saleem yakeyi Haneefah Usman da maman Khalil [7:15pm, 16/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Haka kuwa akayi,yana shiga d’akin Baba Rabi itakuma lokacin tana shirin fitowa,wangale baki tayi tana murmushi harda d’an kwallarta,rungumeta Saleem yayi sosai yace “Baba Rabi na sameku lafiya?ina kanwata?”,baba Rabi tace “Dazun nan ta tafi islamiya” saleem yayi murmushi yace “Ashe dai ta girma”. Suna hira suna tafiya har suka isa fadar sarki,nan aka jejjera abinci kala-kalar da juices,snacks,tarkace dai daban-daban. Akaci aka ‘koshi sannan aka tafi sallar maghrib. Da Nabilah tadawo fuskar baba Rabi cikeda annushuwa,Nabilah take tambayarta “Umma,yau dai naga farincikin ki daban neh” baba Rabi tace “Kwarai kuwa,auta yadawo”. Nabilah tace “Ohhhh kinga ni wlh na ma manta” baba Rabi ta d’an harareta tace “Amma shikuma yana isowa saida ya tambaye ni ina kike”,Nabila tayi murmushi tace “Allah sarki”. Itama sallar tayi sannan tayi isha anan bacci ya kwasheta,ba ita ta farka ba sai asubah. Washegari da yake thursday neh ba islamiyya kuma tunda ana hutun boko Nabila sai bacci takeyi har 9 ta tashi,tayi wanka sannan ta gyara da’kin,tunda ta tashi take jin kwadayin guava sai kawai ta yanke shawarar zuwa lambun gidan ta tsinko amma kuma bata iya ba. Ta gama komai nata sai ta nufi dakin su Amina,da yake ta wajen akwai kule saita ruga dagudu,tana d’aga labulen taci karo da Uwani (Maman Amina). Uwani taja tsaki tace “kai Nabilah,kekam bansan yaushe zakibar yarinta ba,kina abu kamar zararriya” maganar yama Nabilah ciwo, sai tace “Saidai in ‘yarki neh zararriya badai ni ba”. Ta juya dagudu tabar wajen,Uwani ta girgiza kai kawai ta bita da kallo tana mamakin irin rashin tsoron Nabila. Nabilah d’akin su Jamila tanufa,tare suka jera har lambun. Da yake dukkansu biyu basu iya hawa bishiya ba sai Amina kuma batanan sai kawai Nabila tace “Barin dauki manyan duwatsu na dinga jefawa a saitin guava din,zamu samu ko kad’an neh” Jamila tace “Ehh kin kawo point”. Hakan kuwa akayi,tayita jefawa kuma tasamu mai d’an yawa sun zubo ‘kasa,da taga duwatsu biyu neh kawai suka rage mata a hannu kawai saita dage iya ‘karfinta ta jefa nafarko,Saleem dake zaune acikin lambun dayake yana son zama awajen yaji sau’kar dutse daga sama,daga kan da zaiyi lokacin kuma Nabila ta ‘kara jefo wani dutsen,ai ba shiri ya mi’ke dasaurin shi ya nufi ta inda dutsen yafito. Yana isa yaga suna kwashe guava dinsu hankalinsu kwance,afusace ya nufi wajen,jamila na ganin haka ta arche da gudu,Nabila kuwa ko ajikinta. Yana isowa wajen ya cafkota ya ja gashinta yace “Hey!!!bakida hankali neh??” ta fara ‘ko’karin kwace kanta amma takasa saitace “Yadai malam,kai waye da kawai zakazo ka cakumoni” tsaki yaja ya saketa yana mamakin ‘karfi hali irin na yarinyar. Ta tsugunna ta kwashe sauran guava din,har tayi nisa sai kuma ta tsaya tajuyo ta gyara skirt nata sosai sannan tace “Sssssssss malam” yasan dashi takeyi amma sai ya basar,ita ba haka taso ba saita sake “Ko kana tsoro neh?kazo mana” abun haryaso bashi dariya wai tsoro,yana juyowa ta mishi gwalo,yabita da gudu itama kuwa daman da riga tayi ready ta kwasa da gudu. Da yaga ta gudu saiya tsaya yafara dariya azuciyarshi yace “Yarinyar nan batada kunya amma zanyi maganinta”. Tana isa daki taga Jamila azaune,nan itama ta zube tafara maida numfashi. Afuwan don Allah,wlh naje biki neh saisa banzauna ba kuma maman Khalil tana jinyar sistanta amma In Sha Allahu daga yau zamu dingayi kullum. Haneefah Usman da Maman GIMBIYA NAFEESAH [6:06pm, 15/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Ta dauki kusan minti daya sannan numfashinta ya dawo normal,Jamila tahau tambayarta “Yadai?ya dakeki neh?Biyoki yayi?” nan Nabila ta tanka mata tace “Iskanci,ke ba” sai ta kwashe da dariya. Tayi mai isarta sannan taci gaba “Ba kin gudu kin barni ba,ai na nuna mishi nima ba tayar baya bace sannan namishi gwalo nagudu shine fah yabiyoni kikaga na shigo nan a bai bai”,dukkansu biyu suka hau dariya,basu masan baba Rabi tashigo ba saida tace “Lafiyarku kam?wannan irin dariya haka saikace sabbin kamu”. Nabilah da Jamila suka tsaya kallon kallo ba wanda yayi magana har saida baba Rabi tagaji da jirar amsarsu sai kawai ta girgiza kai tace “Allah ya shiryeku,mutane neh ba abinda suka sa a gaba sai sha’kiyanci” sannan ta sa kai ta fice daga d’akin. Akazo cin guava nan fah rikici ya kachame,Nabilah ta mi’kama Jamila guda hudu itakuma ta ri’ke guda tara,Jamila tace “Haba Nabila,tare fah mukaje muka tsinko abunnan,ai ko guda shida neh saiki bani inyaso sai ke kici bakwai” Nabilah tace “Tabdi!! Kamar ya tare muka tsinko?ke fah ba abinda kika tsinana inba kallo ba,da wanchan mutumin yazo kuma gudu kikayi kika barni,kin ma ci sa’a neh ai da ko daya bazan baki ba” Jamila tayi ‘kwafa tace “Bazan yarda ba wlh”. Nan fada ya kaure tsakaninsu,Nene da tashigo wajen baba Rabi neh taga damben da sukeyi da kyar ta rabasu sannan ta sasanta su tabama Jamila guda biyar,Nabila kuma guda takwas. Da dare Nabilah na zaune a d’aki tana bitar haddarta baba Rabi tashigo tace “Yauwa Nabilah zo ki dauki madarar auta ki kai mishi dakinshi yanzun nan” saida ta kai aya sannan tace “Toh Umma” saita tashi ta ajiye Al- Qur’anin a kan drawer. Tayi sallama yakai sau uku amma bai amsa ba,kawai saita yanke shawarar shiga d’akin. Ta bud’e a hankali ta ‘kusa kanta,chan ta jiyo muryarshi yana waya a bedroom,tsaki taja a fili tace “Yana waya da ‘karfi kamar wani mahaukaci” ashe shikuma da yaji an bud’e ‘kofa saiya fito parlourn. Yana fitowa caraf maganar da ta fad’a a kunnenshi Haneefah Usman da Maman Khalil [6:56pm, 15/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Bata ji fitowarshi ba sai kawai taga mutum a gabanta,ta zaro ido tabude baki da niyar magana amma maganar ta’ki fita,buge bakinta yayi da hannunshi yace “Ke wato nagane bakida kunya ko?kin rainani,bakisan ni waye ba ko?” taji ras kam kuma gabanta sai dukan uku uku yakeyi amma tayi ‘karfin halin cewa “Ayyah ba fah dakai nakeyi ba amma shine harda buga min baki” juyawa yayi ya ‘kare ma d’akin kallo sannan ya juyo wajenta yace “Na dai ga ba kowa a d’akinnan,daga ke sai ni,da wa kike magana?ko da aljanun da suka haukataki kikeyi?” murguda mishi baki tayi tace “Ni ba mahaukaciya bane saidai in kaine mahaukacin,ni da ba don aikena akayi bama meh zai kawoni da’kinka?” har ya d’aga hannu zai wanka mata mari sai kuma ya fasa,furzar da iska yayi sannan yace “Ajiye abinda aka aikeki ki ‘kara mai kamin na ‘ballaki” Cikin rawar jiki ta ajiye jug din har takai ‘kofa ‘kasa-‘kasa tace “Allah ya isan min mugu” murmushin gefen baki yayi yace “Na jiki”,ai dagudu tayi waje. Tana cikin tafiya itakadai tana magana azuci “Duk yanda akayi wannan yanada cin zali,ashe dai jinshi yafi ganinshi tunda umma tacemin shi baida damuwa kuma yanada fara’a da son mutane,toh ko dai abokinshi neh wannan ya rainamin wayo?” afili tayi murmushi tace “Duk yanda akayi ma abokinshi neh bashi ba” haka dai tayita sa’ke- sa’ke har ta isa dakinsu. Abangaren Saleem kuwa kwanciya yayi akan kujera yafara tunani “Wace yarinya ce wannan? anya tasan ni kuwa?kodai tsaba rashin kunya neh yasa takemin haka?ko dai itace ‘yar baba Rabi?” wani zuciyar kuma yace mishi “Ina!! Ba yanda za ayi ‘yar baba Rabi ta zama haka”. Kwana biyu da faruwar hakan duk Nabila da Saleem basu sake haduwa ba. Yau yakama lahadi,Nabilah tadawo daga islamiya sai ta tafi da’kinsu Amina,anan ta tarar da ita tana wanki,dama Nabilah akwai son harka da ruwa sai kawai tace “Amina barin tayaki wankin”,Amina taji dadi har ranta sai tace “Ko kefa,dauko bokitin chan saiki zo kina daurayemin inna wanke” Haneefah Usman [7:32pm, 15/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Haka kuwa akayi,Nabilah taje ta ciko bucket ‘kato da ruwa tafara dauraye ma Amina kayan sannan ta shanya,ta dauraye mai d’an yawa saikuma ta tsaya. Amina ta tambayeta “Ya kika tsaya?ko kin gaji neh?” Nabila ta girgiza kai tace “Haba gajiya,kawai naga ruwan ya’baci neh,barinje ta chan gefen na watsar tunda dare neh kinga ba mai zuwa tanan” Duk da bokitin yana rinjiyarta amma haka ta dagashi,taje daidai bakin wani kwana haka saita watsar,watsarwar da zatayi gaba daya ajikin Saleem da yasha wankarshi sai ‘kamshi yakeyi zaije dinner na auren abokinshi. Wani ihu da Saleem yayi neh ya fargar da ita ajikin mutum ta watsa,arazane ta dago idanunta da niyar bashi ha’kuri amma ina!! Saleem ya harzu’ka iya harzu’ka,baima jira meh zatace ba ya iso wajenta ya wanwanketa da mari har uku,bashiri ta yar da bokitin dagudu tayi hanyar d’akinsu. Tana shiga tasaka key,hannunta dafe a kumatun da ya wanka mata mari sannan ta jingina da jikin ‘kofar d’akin,wasu hawaye neh suka zubo mata wanda batasan sun zubo ba don harga Allah marin ya shigeta kuma tunda taga yanda ranshi yabaci tasan in ba gudu tayi ba zai iya kaita lahira( ga tsoro ga rashin kunya) Amina ta gama wanki tanata jiran Nabila ta dawo amma shiru ba ita ba labarinta,daga ‘karshe ma kawai saita dauraye abunta ta shanya sannan taje ta kwankwasa ‘kofar d’akinsu Nabilah. Nabila da bacci yafara kwasarta ajikin ‘kofar taji ana knocking,a firgice ta farka ta fara karanto addu’o’in tsari,ita a tunaninta Saleem neh,da yake baba Rabi ta dade da yin bacci sai ta kwanta a bayanta tsaba tsoro. Da Amina taga ba abude ba sai kawai ta koma d’aki ta kwanta Washegari duk wanda yaga Saleem yasan ranshi a ‘bace yake,gaba daya yinin ranar da d’aki yayi shi,duk wanda ya tambayeshi meke damunshi sai yace kawai kanshi neh ke d’an ciwo. Mai martaba yatura baba Rabi ta tambayi Saleem watakila zai gayamata,da sallamarta ta shiga,suka gaisa sai ta gyara zama tace “Saleem,meke damunka?karkace min ba komai don ba tun yau ba nasanka” guntun tsaki Saleem yaja sannan ya labarta mata duk abinda ya faru akan wata yarinya ta watsa mishi ruwan dotti. Tayita bashi baki har dai ya d’an sake,suna cikin hira sai akayi sallama,dukkansu biyu suka amsa. Nabilah ce tashigo d’auke da tray na fruits da Yabi ta bata ta kawo ma auta. Saleem yana ganinta ya mi’ke,afusace ya nufeta yace “ke meh ya kawoki d’akina mara kunya,ko da yake gwanda da kika kawo kanki watakila na sassauta miki hukuncin ki”,cikin rawar murya Nabila tace “Kayi ha’kuri don Allah,wallahi ban san kana ta wajen bane saisa” baba Rabi da ta rasa gane meke faruwa tace “Auta meh ya hadaka da Nabila?ta maka rashin kunya ko?”. Daga Nabila har Auta a firgice suka juyo zuwa wajen baba Rabi,cikin rashin fahimta auta yace “Nabila ce wannan?” kusan lokaci daya Nabila ma tace “Umma dama wannan neh Auta????” Haneefah Usman da maman Khalil GIMBIYA NAFEESAH [8:37pm, 16/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Baba Rabi ta tsaya tana kallonsu sai chan tace “Meh ke faruwa neh?kumin bayani”. Jiki asanyaye Saleem ya zauna a kan kujera,ya furzar da iska da ya zama mishi kaman jiki,Nabilah kuwa tsugunawa tayi a wajen batace komai ba,saida baba Rabi ta sake maimaita tambayar sannan Saleem ya labarta mata daga farkon haduwarsu inda ta jefeshi da dutse kuma yace da gangan neh,caraf Nabilah ta kar’be “wlh umma karyanshi neh,banmasan yana wajen ba fah nikuma ina cire guava,inbanda shi ma mai yakaishi zama a lambu illah neman magana”,zaro ido Saleem yayi yace “Ke waye yayi karya?wlh zan pasa bakinki” cikeda tsiwa tace “Atoh,karya neh……” kiran sunanta da baba Rabi tayi neh yasa ta ja bakinta tayi shiru,nan baba Rabi tace “Yi ha’kuri auta,cigaba,ina jinka”. Saleem ya had’ama baba Rabi ‘karya da gaskiya yace “ko ranar da kika aikota da madara ma don nace ta zubamin a cup saita d’aga jug d’in ta juyemin madarar a jikina,Nabilah ta dafe ‘kirji tace “Lahh!!amma kai babba da kai kana ‘karya?” baba Rabi ta tashi da niyyar marinta amma dasauri Saleem ya tareta,cikin zafin rai baba Rabi tace “Kabarni na saita mata hankali,yarinya neh sam batasan girman na gaba da ita ba”,murmushi Saleem yayi sai yace “Yi ha’kuri,inhar ni neh toh wlh na yafe mata,abinda ya faru yariga da ya faru saidai a kiyaye na gaba”. Haka dai baba Rabi takoma ta zauna tashiga bama Saleem ha’kuri,shiko gogan sai wani murmushin mugunta yakema Nabila,daga ‘karshe yace “Bakomai,ni a matsayin ‘kanwata na d’auketa”,murmushi baba Rabi tayi sannan tamishi godiya,tasa Nabila ta bashi ha’kurin dole,ba don taso ba ciki ciki tace “Yi ha’kuri”. Murmushi dauke a fuskarshi ya matso kusa da inda take tsugunne sannan ya dagota ta tsaya,saiyace “I forgive u lil sis,amma daga yau karki ‘kara min rashin kunya kinji?”,murmushin ‘karfin hali Nabila tayi sai tace “In Sha Allahu bazan ‘kara ba” Hanee:mrgreen: da maman Khalil [8:54pm, 16/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Baba Rabi bakinta ya kasa rufuwa tsaba murna ganin Auta ya saki ranshi kuma ya nuna ya d’auki ‘yar tilor ‘yarta a matsayin kanwarshi,ji tayi kaman ta zuba ruwa a ‘kasa tasha. Jawo Nabilah yayi zuwa kan kujera dukkansu biyu suka zauna,nan yafara tambayarta wani makaranta take,wani aji da dai sauransu. Nabila uwar surutu haka ta zage ta bashi harda labarin da bai tambayeta ba,hira sukeyi kaman sun saba da juna. Sun dade suna hira sannan baba Rabi tace “Auta saika tashi kaje wajen Yabi ko?duk hankalinta a tashe yake da taga baka walwala” mi’kewa tsaye yayi sai yace “Kuma haka neh fah” sannan ya maida kallonsa zuwa ga Nabilah “Kanwata tashi muje” cike da zumudi Nabila ta mi’ke tace “Toh yaya Saleem”. Yabi taji mamaki sosai da taga Saleem ya saki fuskarshi,nan ta tambayi baba Rabi ya akayi,tiryan tiryan ta bata labari,dariya tayi sosai sannan tace “Auta zuciya,Nabilah neman magana” dariya sukayi gaba dayansu. Da aka gayama mai martaba ma girgiza kai yayi sannan yayi dariya yace “Allah ya kyauta” Abangaren Saleem tunani yakeyi a zuciyarshi “Ashe dai yarinyar bata da matsala,saidai daga jin magananta akwai yarinta a tattare da ita,matsalarta dai shine akwaita da tsiwa,nasamu ‘kanwa”,Nabila ma dai maganar takeyi da zuciyanta “Yanada fara’a,ashe shi ba mugu bane kaman yanda na tsamman,naji dadi nasamu yaya wanda zamu dinga hira mu fita yawo tare” Yinin ranar haka sukayi shi cike da nishadi,sukaje lambu suna ta hira sai Nabila tace “Ya Saleem wlh guava nakeso naci,barinje na tsinka” dasauri ya tashi tsaye yana dariya yace “wa?ke zan bari kije ki tsinka?saidai in inaso ki rusa min kai” dariya Nabila tayi sosai saitace “Kai haba,ai ranan ma bansan kana nan bane saisa” kama hannunta yayi yace “A’a,ki dai zo muje na tsinka miki”. Hanee da maman Khalil [9:14pm, 16/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Haka kuwa akayi,yaje ya dauki dogon sanda ya bubbuge musu guava dewa,dama akwai tap a wajen so sai kawai sukaje suka wawwanke suka baje sunaci. Gaskiya Saleem daban yake,yanda yake abu kaman ba d’an sarauta ba,sarautar ma mai ‘karfi na garin Yura,masarautar da ake ji dashi sosai a Kaduna state,bai da ji da kai da kuma nuna yafi wani,he is just living a simple life. Duk bidirin da Saleem da Nabila ke yi a lambu ashe dai Sumayya tana la’be tana ganinsu (Sumayya ‘yar mai yin goge-goge neh agidan,tafi su Nabila da kad’an). Mai martaba neh yakira Saleem awaya yace ya sameshi a ‘karamin parlour,ya gayama Nabilah sannan yace “ki jirani fah,ina dawowa yanzu” ta amsa mishi da “Toh”. Yana tafiya ba da dadewa ba Sumayya ta iso inda Nabila ke zaune,tsayawa tayi tana girgiza kwankwaso,Nabila ta kalleta ta watsar,a wula’kance tace “Ya da tsayamin akai?in ma neman fad’a kikeyi da ni toh a shirye nake”,tsaki Sumayya taja sannan tace “Uwar shishshigi,uwar kinibibi,uwar ‘kwazo,meh ya hadaki da Auta da har kike wani shishshige mishi haka?in ma sonshi kikeyi toh gwara ki cireshi daga ranki don shi nawa neh ni kad’ai” dariya Nabilah ta kwashe dashi,tayi mai isarta saitace “Wayyo Allah,an gayamiki ni bunsura ce kamar ke?ke wani abu wai so ya dama,ni banma sanshi ba balle na ma wani shi” Sumayya taji zafin maganar sosai tace “shegiya munafuka,kinsani kam” Tsaki Nabila taja tace “Wannan kuma sai ki tsaya in yazo saiki gayamishi,shi da bai masan da zamanki ba” nan fah fad’a ya kaure tsakaninsu,jibgar juna sukeyi ba kad’an ba,Saleem yadawo da kyar dai yasamu ya raba fad’ar,cikin kuka Nabila ta labarta mishi abinda ya faru. Wanka ma Sumayya mari yayi,yanuna ta da yatsa sannan yace “Sumayya kike ko meh?daga yau kika ‘kara kuskuren kama Nabila da fad’a wlh saina hukunta ki,wuce ki bani waje!!!” a firgice Sumayya ta tattara dankwalinta tabar wajen Hanee da maman Khalil [9:42pm, 16/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Saleem ya zauna ya dinga lallashin Nabila har dai tayi shiru suka ci gaba da hiransu. Akwana a tashi ba wuya wajen Allah,Nabilah ta zama cikakkiyar budurwa,ta ‘kara kyau,ga ta ‘bul-‘bul da ita gwanin ban sha’awa,ga uwa uba dirin da Allah yabata. Ayanzu shekarunta sunkai 18,tagama secondary school,mai martaba yace zai turata ‘kasar waje tayi karatu,ranar baba Rabi tayi kuka ta godema Allah da wannan sarki mai sonsu da son cigabansu. Saleem yanzu yana da shekaru 28,tsakanin shi da Nabila kuwa wani sha’kuwa neh wanda bazata misaltu ba yashiga tsakaninsu,wasu har tsammani suke ko suna soyayya amma ko d’aya,shi a matsayin ‘kanwa ya dauketa itama kuma a matsayin yaya ta daukeshi. Mai martaba yayi-yayi da Sultan ya fitar da mata don yanzu yakai 36 amma kullum maganarshi daya “Abba kayi ha’kuri,aure lokaci neh sannan ni har yau banga wacce ta kwantamin a rai ba” wani lokacin mai martaba har yayi tunanin “ko dai Sultan baida lafiya neh?” Ranar wani talata dangin Sarki Mu’awiya sukaje neman aure a garin yola,’yar sarkin garin Hamaz,sarkin Hamaz abokin Sarki Mu’awiyah neh na sosai da sosai,shine ya nema ma Sultan auren ‘yar sarkin Hamaz mai suna Amirah. Sunje garin Yola lafiya lau kuma an ‘kar’besu hannu bibbiyu sannan aka yanke ranar biki nan da wata biyu. Duk abinda akeyin nan uban gayyar wato Sultan bai sani ba,yana chan Qatar yana aikinshi hankali kwance. Yarima neh zaune a office shi da abokinshi,mai martaba ya kirashi,cikin girmamawa ya gaisheshi da tambayar lafiyar gida,mai martaba yayi gyaran murya yace “Yarima,tunda naga bakada niyan aure gashi shekarunka ‘kara gaba sukeyi shine na nema maka auren ‘yar abokina mai suna Amirah kuma Alhamdulillah sun baka,an sa ranar biki nan da wata biyu” da yake Sultan mai biyayya neh sai yace “Nagode,zan dawo kwanan nan don hidimar bikin,Allah ya ‘kara nisan kwana” mai martaba yayi murmushi yace “Ameen Yarima,Allah ya maka albarka”,yarima ya amsa da “Ameen” sannan sukayi sallama ya katse wayar. Abokinshi mai suna Abdul yace “Yadai mutumina?naji kana maganar hidiman biki,daman aure zakayi?” girgiza kai Sultan yayi yace “Unexpected aure ba don ni bansani ba sai yau”. Nan dai suka cigaba da tattaunawa Wacece Ameerah? Kudai biyomu ni Hanee da maman Khalil kusha labari;);) GIMBIYA NAFEESAH [10:36pm, 17/01/2016] Haneefah: GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Sarki Ibrahim Umar sarkine na babbar masarauta mai suna Hamaz dake jihar Adamawa,yanada mata biyu-Na farkon sunanta Sarauniya Fatima,na biyun kuma sunanta Maryam. Fatima tanada ‘ya’ya uku-Gimbiya Ameerah,Yarima Ukasha sai autar ta mai suna Gimbiya Nafeesah wacce tun tana ‘yar kankanuwar ta wata rana an kwantar da ita tana bacci a d’aki shikenan aka nemeta aka rasa,ba ‘karamin tashin hankali suka shiga ba musamman ma mai martaba da ya d’auki son duniya ya d’aura ma Nafeesah don sunan mahaifiyarshi taci,neman duniyar nan sunyi amma har yau ba ita ba labarinta.. Sarauniya Maryam kuma tanada ‘ya daya mai suna Hauwa wacce take sa’ar batacciya Gimbiya Nafisah. Ameerah tanada shekaru 24 dayake sarkin Hamaz bai samu haihuwa dawuri ba,tana karatu a AUD tana final year ayanzu haka,sarkin Yura da sarkin Hamaz abokai neh tun tashinsu,tare sukayi skul har suka gama sannan kowa ya koma garinsu daga baya kuma kowanne yazama sarki bayan iyayensu sun rasu. Awani meeting na sarakuna neh da suka hadu shine suke tattauna matsalolin familynsu,a hirar neh ma sarkin Hamaz ya tambayi sarkin Yura “Nikam ina Sultan neh?ya batun aure?ko har yanzu bai shirya bane?” sarkin Yura ya sauke wani ajiyar zuciya yace “Wani aure?mutumin da har yau yakasa fitar da mata,ni fah in gayama har nafara tunanin ko baida lafiya kokuma aljanu sun aureshi,ace mutum shekara 36 amma har yau shiru” sarkin Hamaz yayi dariya irin tasu ta manya yace “Allah sarki,inkaga haka toh fah lokacinshi neh baiyi ba,adai ta addu’a Allah ya za’ba ma ‘ya’yanmu abinda yafi zama alheri” sarkin Yura ya amsa “Ameen” sannan ya d’anyi jim na wani lokaci,sarkin Hamaz ya d’an ta’bashi yace “Lafiya kake dogon tunani haka?” murmushi sarkin Yura yayi saiyace “Nasamo mafita neh”,gyara zama sarkin Hamaz yayi yace “Inajinka,wani irin mafita kenan?”. Haneefah Usman OHW da maman Khalil [10:53pm, 17/01/2016] Haneefah: GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Sarkin Yura yayi gyaran murya yace “Ni in da zaka yarda da na had’a ‘yarka Ameerah da Sultan aure,yarinyar tanada nutsuwa ga hankali” Hade fuska sarkin Hamaz yayi yace “Banyi tsammanin zaka d’auka akwai bambanci tsakanin ‘ya’ya nah da naka ba,yanda kakeda iko dasu Sultan toh wlh nabaka iko akan ‘ya’yana gaba d’aya,nasan Ameerah bazata bani kunya ba kuma daman batada wani tsayayye” murmushi mai cike da farin ciki sarkin Yura yayi sannan yace “Nagode,amma dai zanturo ayi tambaya kaman yanda yake a al’ada”,fuska a sake sarkin Hamaz ya amsa “Ba komai,sai sun iso,in yaso sai asa date ma kawai” sarkin Yura ya jinjina kai yace “Hakan za ayi kuwa” Da sarkin Hamaz yakoma gida ya tara iyalanshi ya labarta musu yanda sukayi shi da sarkin Yura,Sarauniya Fatima tayi farinciki ba kad’an ba don tasan Sultan yaro neh mai hankali da sanin ya kamata,daga baya yace a kira mishi Ameerah,itama ya sanar da ita,cikeda kunya tace “Bakomai Daddy kuma in Allah ya yarda zaka sameni mai biyayya”. Sarauniya Maryam da Sarauniya Fatima neh zaune a babban parlour suna hira,bazaka ta’ba cewa kishiyoyi bane don suna shiri fiye da tunanin mai karatu,S.Maryam tace “Anty(da yake anty take kiran S.Fatima) ni dai na d’auki nauyin gyara ‘yata ciki da waje,ina fatan ba matsala?” murmushi S. Fatima tayi saitace “Ai dukkansu ‘ya’yanki neh,duk abinda ya dace kiyi” Da hakan neh sarkin Yura ma yakoma gida har akaje tambaya aka saka ranar biki nan da wata biyu shine yakira Sultee ya gayamishi Wannan kenan Haneefah OHW da Maman Khalil [11:09pm, 17/01/2016] Haneefah: GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Back to labari Bayan kwana biyu kuwa Sultee ya diro garin Kaduna,jallabiya yasaka designer irin dark coffee colour dinnan mai she’ki,gashi fari sai kyaunshi ya ‘kara fitowa wane balarabe(Su sadydy ma saida suka hadiye yawu,ni dai nace yafi ‘karfinku ehe:roll::roll:),yasaka agogo black shima daga gani kud’i yayi kuka a sayenshi. Motocin da suka dira a airport kamar masu tarar President,ga dogaraye neh,securities neh,duk dai gasunan anzo tarar Yarima Sultan mai jiran gado,da muka ganshi maman K ta taboni tace “Ke Hanee anya wannan mutum neh?” nace “Mesa kika ce haka?” atsorace tace “Kina ganin kyau kaman aljani fah,nikam nagudu wlh ina tsoro” nan take ta ari na kare,bironta ma yarwa tayi,nikam dariya nayita mata. Nan aka budemishi motar,nima dai neman motar nayi daga cikin convoy d’in na la’be tunda maman K tagudu tabarni. Ana isa masarautar akayi parking,red carpet aka shimfida a ‘kasa,akan carpet din an rubutu sunanshi in capital letters YARIMA SULTAN,ahankali ya fito da ‘kafafunshi daga motar,dogarai da mutanen gari sai kwasan gaisuwa sukeyi,murmushi kawai yakeyi gamida d’aga musu hannu alamun yagode yagode. Ya isa wajen iyayenshi ya rungumesu,mai martaba bakinnan ya kasa rufuwa don rabon da yasashi a ido yakusa shekaru 10,shi Sultan baison zama a 9ja wai don bayason surutu. Nabilah da Saleem neh suka fito atare,dagudu Saleem ya rungume yayan nashi wane ‘karamin yaro,Nabila acikin sanyayyen muryanta tace “Barka da isowa Ya Sultan”,sai lokacin ma shikam yalura da akwai mutum a wajen,”yauwa” kawai yace sai ya nufi cikin babban parlour. Anci ansha,anyi wasanni duk don tarbar Sultan amma shi tun da yagama cin abinci ya tafi d’aki bai sake fitowa ba sai da dare da mai martaba ya kirashi. Nabila tana zaune da Saleem tace “Ya Saleem,amma kafi Yarima fara’a da son mutane ba kad’an ba” murmushi Saleem yayi yace “Hakane kam,kinga shi baison surutu da yawan hayaniya,ko dani fah wani lokacin neh muke hira don yacika miskilanci”. Dariya Nabila tayi tace “Aikuwa sai na sashi surutun dole”. Washegari Nabila tasaka dogon riganta ba’ki mai ratsin ja,batayi ado ba amma tayi kyau sosai,ta hada fruits a tray saita kama hanyar side na Sultee,da sallamarta tashiga,ciki-ciki ya amsa,zaune yake a kan kujera yana danne danne da laptop. Kallo d’aya yamata saiya d’auke kanshi. Ta nemi guri ta zauna tace “Ya Sultan ina kwana?” batare da ya kalleta ba yace “Lafiya”,batayi ‘kasa a guiwa ba tace “Ni sunana Nabila,ni ‘yar baba Rabi ce” still idonshi yana kan laptop nashi yace “Okay yayi kyau”. Taji ba d’ad’i kam amma haka ta fara zuba mishi surutu,tun yana amsa mata sama-sama har ya daina. Nabilah ta d’anyi shiru,azuciyarta tace “Kyakkyawa amma sai uban miskilanci,ko don yaga yanada kyau neh oho”,chan tace “Ya Sultan,ni inason naje Qatar,kabani labarin garin”,cikeda ‘kosawa ya bar danna laptop din,ya d’ago ya kalleta yace “Don Allah tashi ki tafi,kin cikamin kunne da surutu har kaina yafara ciwo”, zata sake magana kenan ya d’aga mata hannu yace “Please go” GIMBIYA NAFEESAH [2:52pm, 18/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Duk zafin da zuciyarta yayi sai tayi ‘ko’karin dannewa,ta tashi a sanyaye tace “Kayi ha’kuri in na ‘bata ma rai,it wasn’t my intention”,ko ci kanki baice mata ba, itama dama bata sa ran zai bata amsa ba,juyawa tayi acikin tafiyarta mai fizgar hankali ta fita daga side din. Tana fita ya bi bayanta da kallo,azuciyarshi yace “Masha Allah,tana da kyau ba laifi gashi komai ya ji enough”,murmushi yayi afili, dasauri yayi Istighfari ya kawar da tunanin daga ranshi sannan ya ci gaba da aikin da yakeyi a laptop nashi. Abangaren Nabila kuwa tana fita daga side din lambu ta wuce,tana isa kuwa taga Auta zaune a wajen yana waya,samun wuri tayi ta zauna,kallonta da Auta yamata yasa yagane tana cikin damuwa duk da kuwa ta saka fake smile a fuskarta,katse wayar yayi. Arikice yafara tambayarta “‘kanwata wa ya ta’baki?” girgiza kai tayi,tayi ‘ko’karin maida hawayen da ke nema ya zubo mata,murmushin da akace yafi kuka ciwo tayi tace “Ba komai ya Saleem,kawai tunda na tashi bana jin dadin jikina neh”,kallon tuhuma yabita dashi yace “Yaushe muka fara wasar ‘boye-‘boye dake?”,kanta a sunkuye tace “Gaskiya na gayama”. Tashi tsaye yayi yace “Okay toh sai anjuma tunda bazaki iya gayamin matsalarki ba”,d’ago ido tayi taga fuskar nan tashi a had’e alamun ya ‘bata rai. Hanee OHW da maman Khalil [3:13pm, 18/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Dasauri ta mi’ke tsaye,ganin yajuya zaibar wajen yasa tayi saurin ri’ke hannunshi tace “Yi hakuri,zan gayama”,murmushi yayi sannan ya maida idonshi kan hannunshi da ta ri’ke,ai ba shiri ta sake hannun cike da kunya don ita bata ta’ba ko da wasa neh ta ri’ke mishi hannu ba saidai in mistakenly hannunsu ya gugi juna,rufe fuskarta tayi,Saleem ya gyara tsayuwarshi yace “Uhum,ina jinki”. Ahankali ta janye hannunta daga fuskarta tace “Ba yaya Sultee bane”,sanin halin Sultee yasa Saleem ya zaro ido yace “Meh yamiki?” Samun wuri tayi tazauna,tafara “kawai fah don naje na gaishe shi saina zauna nafara mishi hira shine yace wai nacika surutu kuma ina sa mishi ciwon kai sannan ya koreni daga d’akinshi” dariya Saleem yayi sosai har saida Nabila ta ‘kulu,saida yayi mai isarshi sannan yace “Meh ya kaiki?kema dai baki jin magana wlh,ba na gayamiki baison surutu ba?”,guntun tsaki Nabila taja tace “Yo ni ina ruwana,ba dai naje ba?” zama Saleem ma yayi sannan yace “da zaki bi shawara ta da kin bar shiga sabgar Ya Sultee don in kin kaishi bango wlh zai iya dakaki” zaro ido tayi ta dafe ‘kirji tace “Duka???” jinjina kai Saleem yayi yace “kwarai kuwa”. Nabilah ta d’anyi jim kamar mai tunani sai chan tayi murmushi tace “Ya Saleem kasan meh?” girgiza kai yayi alamun a’a saiyace “Sai kin fad’a”,wani murmushi Nabila ta sakeyi tace “Kasan bana rantsuwa akan banza ko?” kallonta yayi sannan yace “Eh”,Nabilah tace “toh wallahi tallahi kaji na rantse ko ya Sultee kasheni zaiyi saina je side nashi kullum don hira,kai ko baya tankani zanje na zauna nayita surutu,watarana shi da kanshi zai fara surutu”. Kallon Nabila yayi cike da mamaki yace “In dai haka neh kam toh wlh kin d’auka ma kanki aiki ja,zakije kita magana ke kadai in ya gaji kuma ya koraki,amma daga yau in ya sake koroki ko yamiki duka kuma kika gayamin Allah dariya zan miki tunda ke bakijin magana”. Murgud’a mishi baki tayi tace “Ehh naji d’in,meh ruwanka? ai ni nace zan yi kuma naga zan iya neh saisa,nidai kar wani ya sake gayamin maganar banza”,murmushi yayi ya tashi tsaye yace “Masifa kike ji kenan,bani na ta’boki ba amma zaki sauke haushi akaina,barin tafi kamin ki rufeni da duka” ya ‘karasa maganar yana dariya,itama dariyar tayi tace “Kai ya Saleem,wasa fah nakema,kayi ha’kuri don Allah”. Dawowa yayi ya zauna suka cigaba da hirarsu sunata kyakyala dariya gwanin ban sha’awa Haka dai kullum safe,rana da dare Nabilah tana zuwa side na Sultee tayita surutu shikuma ko sannu baya ce mata,in ya isheshi neh sai ya koreta Hanee da maman Khalil [3:41pm, 18/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Bayan Sultee yayi kwana biyu sai mai martaba ya ‘kirashi da dare. Sun d’an ta’ba hira irinta tsakanin d’a da mahaifinshi,chan sai mai martaba yace “Yarima,yaushe kake shirin zuwa ka dubo matarka?” cike da rashin fahimta Sultee yace “Bangane ba abba,mata kuma?”,murmushi yayi yace “Amirah nake nufi,wanda za ayi aurenku nan da wata daya and some weeks”,sosa ‘keya Sultee yayi yace “Eh toh,daman cikin satin nan nakeso naje”,mai martaba ya jinjina kai yace “Hakan yayi,amma da jirgi zaka je ai ko?don ni gaskiya ban cika son kuna dogon tafiya a motar ba” murmushi Sultee yayi yace “Duk yanda kace abba,bani da ja”. Har dare yayi nisa sannan Sultee yayima mahaifinshi sallama yakoma d’akinshi. Yau ya kama asabar kuma yau neh yarima Sultan zai tafi Adamawa wajen Gimbiya Amirah,duk da shi har cikin ranshi ba son auren nan yake ba amma sabida biyayya haka ya daure,fuskar nan tashi ba yabo ba fallasa da yake shi baicika dariya har chan ba saisa ba wanda zai gane ko farinciki yakeyi ko akasin haka. Abangaren Gimbiya Amira kuwa zaune take akan lumtsumemen gadonta acikin d’akinta wanda yaji kayan alatu,tana ri’ke da hoton wata yarinya ‘karama da bazata wuci 6 years ba tana shafawa,a hankali take magana “Lil sis,ina kika shiga? We so much miss u,ina matu’kar bu’katar ganinki,gashi yau zan hadu da wanda zan aura amma bakinan,dis place has never been same since u went missing” nan ta fara hawaye,S. Maryam ce tashigo wacce suke kira da ammi,ahankali ta tako har zuwa inda Amirah take zaune,saka hannunta tayi ta kar’be hoton,kar’be hoton da akayi neh yasa Amirah dago kanta,da sauri tashiga share hawayenta,ammi ta rungumeta tashiga bubbuga bayanta tace “Yi ha’kuri Amira,inaji a jikina Nafisa tana raye kuma In Sha Allahu zata dawo wajenmu ko ba jima ko ba dadewa,dukkanmu muna kewarta amma kuka ba shine mafita ba,addu’a ya kamata mu ci gaba dayi har Allah ya bayyana mana ita. Amirah ta tsagaita kukanta tace “Nagode ammi”. Nan dai ta dinga bata baki har tabar kukan sai ajiyar zuciyar da takeyi,da kyar ta lalla’bata tayi wanka sannan S. Maryam ta chanchara mata ado,dama ammi ba baya ba wajen iya kwalliya,Amira tafito fes da ita. Da azahar Sultee na airport don zuwa land of beauty,ni da maman K muma ba a barmu abaya ba don dukkanmu trolley d’ad’d’aya muka cika bem da kaya,Saleem da Nabee sune sukayi rakiya har airport din,a airport uwar surutu Nabila sai damun Sultee takeyi,shi duk haushinta neh ma ya cikashi,da abun ya isheshi saiya dubeta yace “Zo inason magana dake”,su Nabee sai zumudi akeyi ta tsamman wani maganar arziki neh,shiga motar yayi itakuma ta zagaya ta d’ayan ‘kofar tashiga,tana shiga shikuma ya fito da wayarshi kaman meh answering na call sai yayi murmushi yace “Inazuwa”,tayi fari da ido tace “Toh”. Yana fita daga motar ya danna car lock ajikin key din sannan ya juya ya koma inda yake tsaye kafin lokacin tashin jirgin. Hanee da maman Khalil [6:02pm, 18/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Saleem yaji wajen yayi shuru sai ya juya ya duba baiga Nabilah ba,nan ya hau tunanin ko ina taje don lokacin da Sultee yajata motar Saleem ya d’anyi gefe don amsa call. Nan Saleem yashiga trying na numbanta amma unfortunately ta ajiye shi acikin bag nata kuma bag din yana ajiye akan seat da ta zauna,a rikice ya taka zuwa wajen Sultee yace “Ya Sultee kaga Nabila neh?”,ko d’ago ido baiyi ba,ya fuske kawai abunshi sai chan yace “Wacece Nabilah kuma?”,kallonshi Saleem ya tsaya yi cike da mamaki sannan yace “‘yar baba Rabi”,nan neh Sultee ya d’ago idonshi yace “Saleem i have no idea gaskiya,kadai dubata maybe taje wani waje neh”. Sunkai minti goma sannan akayi announcing kowa yashiga jirgi,sannan neh ya mi’ka ma daya daga cikin drivers din key’n motar da ya kulle Nabila aciki, securities da zasuyi tafiyan da shi suka kinkimi trolleys nashi,muma dai muna biye dasu. Sun shiga jirgi kowa yasa belt,na juya wajen maman K dake zaune ta window nace “Maman K yau zakije kiga garinmu” murmushi tayi tace “ki bari kawai Hanee,duk na ‘kosa naga mun isa”,dariya nasa mata ganin irin d’okin da takeyi zata Yola. Nan jirgi ya d’aga cikin sararin samaniya,sai fatan Allah ya kaimu lafiya Abangaren Nabila kuwa tunda taji yasa key ba abinda takeyi sai kuka,gashi motar tinted ce ba wanda yaganta aciki,gaba daya tunaninta ya toshe,daga baya ta had’a kai da guiwa kawai tana hawaye da Allah wadai da mugun hali irin na Sultan,gaba daya basirarta ta toshe akan ta cire lock din ‘kofar daga ciki Bude motar da akayi neh yasata d’ago kanta,security neh ya bud’e ma Saleem ‘kofar motar,da yake baisan tana ciki ba,ji yayi an ‘kira sunanshi. Ya tsorata ya fara kiran sunayen Allah da addu’o’i,yafara ‘ko’karin balle murfin motar amma yakasa tsaba rikicewa,duk da takaicin da ya cika zuciyar Nabila bai hanata dariya ba,dariya takeyi ba kakkautawa. Jin dariyar da yayi neh yasashi saita hankalinshi waje daya,ya matso daf da ita ya taba jikinta,ya tabbatar mutum neh,d’aga kan da zaiyi saiyaga fuskar Nabila hawaye taf amma tana dariya. Wani uban tsaki yayi yace “Wai ke wace irin mutum neh?wlh kin bani tsoro,na zata ma aljana ce” Hanee da maman Khalil [6:42pm, 18/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Nabila ta kasa daina dariya,da farko ya ‘kulu amma daga baya shima dariyar ya soma. Yi sukeyi kaman zararru,saida sukayi suka gaji sannan sukayi shiru. Maida numfashi kowannensu yafara sai daga baya yake tambayarta ya akayi tazo nan,tsaki taja tace “Wlh ya Sultee mugu neh”,Saleem ya tambayeta “Meh yafaru?”,nan ta bashi labarin abinda yafaru. Ai tun kamin tagama meh Saleem zaiyi in ba dariya ba,dariyan mugunta harda hawaye,Nabila kuwa tacika tayi fam,tafara masifa “Wlh ya isheka,ya zaka sakani a gaba kana min dariyar ‘yan tasha?” dariya Saleem ya sakeyi sannan yace “Ko ma mene ki fada,ko dariyar ‘yan giya neh na yarda,ba ke bakiji ba?ai ya Sultee yamin daidai wlh”,murmushin takaici Nabila tayi sannan tayi ‘kwafa tace “Wlh bashi yaci don saina rama”,Saleem yayi murmushi yace “Ya za ayi ki rama?”,hararshi tayi sannan tace “Bazan gayama ba”. Nan ya kira driver awaya yace mishi yashigo ya kaisu gida,daman yace ya tsaya awaje neh don in yaga Nabila ya kirata. Har suka isa gida dariyar junansu sukeyi Masarautar Hamaz Shirye shirye ake tayi na tarar Yarima Sultan,abinci kala-kala dai gasunan barkatai,sun sauka lafiya akazo aka daukesu daga airport. Sarkin Hamaz mutum mai mutunci,ya tarbe Sultee hannu bibbiyu wane d’an cikinshi,akazo aka gaggaisa sannan su Ukasha da Hauwa ma suka shigo,sun gaisa a mutunce sannan suka tashi suka fita daga side din da aka ma Sultee masau’ki,suna fita Hauwa tace “Ya Ukasha kana ganin wannan guy din,kyakkyawa,inama da ni aka bashi” rankwashinta yayi yace “Ji iskanci,mijin addanki zaki wani ce inama da ke zai aura,kika sake maimaita hakan saina pasa miki bakin surutun kowa yahuta” tayi fuskar tausayi tace “Ni fah wasa nake maka shine zaka rankwashen,saina had’aka da Momy(S.Fatima),nan ya shiga rarrashinta tace ita atapir bata ha’kura ba saiya kaita yawo,ba yanda ya iya haka yace taje ta shirya don yasan halin momy in dai aka ta’ba Hauwa toh akwai rikici. Misalin ‘karfe biyar Ameerah ta shiga side na Sultee, ya amsa sallamarta ba tare da ya kalleta ba,sai danne danne da waya yakeyi abunshi hankalinshi kwance,samun kujera tayi d’an nesa dashi kad’an ta zauna sannan tace “Barka da isowa ya Sultee,ina yini?”,jin ta kirashi da “Ya Sultee” yasashi d’ago kanshi bashiri don ba wanda yake kiranshi da hakan sai Nabila,kallonta ya tsaya yi yaga tana mishi yanayi da wanda ya sani amma ya kasa tuna waye,saida ta sake maimaita gaisuwar sannan ya amsa,fuska a sake yace “Na sameku lafiya?” ta sunkuyar da kai tace “Lafiya lau”,nan fah duk sukayi shiru,da yaga dai miskilanci takeji itama sai kawai ya ajiye nashi yace “I believe kinsan dalilin zuwa na nan,inaso ki gayamin meh da meh kike shiryawa zakiyi” ta d’ago fararen idanunta ta sau’kar akanshi,azuciyarta tace “Guy din kyakkyawa fah na karshe,saidai ba yaro karami bane,Allah dai yasa yanda yakeda kyaun fuska haka zuciyarshi ma yake”,jin tayi shiru kuma ta zuba mishi ido yasa yace “Ke nake jira fah,kin zubamin ido kinkasa magana”,wani kunya neh yarufe Amira don bataso ya kama ta tana kallonshi ba,sunkuyar da kanta tayi tace “Ni ba abinda zanyi illa Walima”,jinjina kai yayi yace “Okay good”. Shiru suka ‘karayi,sun dad’e a hakan sannan ta mi’ke tsaye tace “Ni zan shiga ciki,sai anjuma,ahuta gajiya”,guntun murmushi yayi yace “Thank you,saida safe”. Ta kama hanya sai d’akinta ta fad’a kan gado sannan ta sauke wani ajiyar zuciya,abangaren Sultan kuwa kwanciya yayi akan dogon kujerar dake parlourn amma kuma meh? Tunanin surutun Nabila yakeyi,yana tuna in da yana gida da yanzu tazo ta dameshi da shegen surutun ta,nan take yaji shi so bored,murmushi neh ya subuce mishi wanda ya rasa gane na mene,chan kuma yayi tsaki afili yace “Na rasa meh zanyi missing akan gida sai yarinya mai shegen surutun tsiyar nan” Hanee da maman Khalil GIMBIYA NAFEESAH [1:38pm, 21/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Kiran sallar maghriba da akeyi neh ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula,d’aki ya shiga yayi alwala sannan yafito daga side nashi ya nufi masallacin da ke cikin masarautar,bai bar masallacin ba har akayi Isha don Sultee baya wasa da Sallah. Tare suka dawo shi da mai martaba sarkin Hamaz,dogaraye suka mara musu baya. Taku sukeyi mai burgewa,kuyi imagining sarki da yarima mai jiran gado suna tafiya a ‘kafa,kuma dai kunsan tafiya neh mai cike da charisma da ‘kasaita irin na jinin sarauta. Suna tafiya suna ta’ba hira kad’an- kad’an. Har ‘kofar side nashi mai martaba ya rakashi sannan sukayi sallama,Sultee ya shiga d’aki mai martaba kuma ya wuce sashenshi tare da mu’karrabanshi. Yana shiga parlournshi yaga kuyangi a tsattsaye awajen dinning,dukansu zubewa a’kasa sukayi suna kwasar gaisuwa gami da kirari,dinning area din yawuce,d’aya daga cikin securities nashi yaja mishi kujera ya zauna,yana zama ‘kuyangin da suka kawo mishi abincin suka zuzzuba mishi abinci kala-kala a plate daban- daban. Spoon ya d’auka ya dibi pepper soup na kayan ciki har zaikai baki wani security dinshi ya dakatar dashi yace “Sorry sir,just wait a minute” bai yi magana ba ya ajiye spoon din ya fitar da wayarshi ya fara danne-danne,securityn ya sa d’aya daga cikin ‘kuyangin tayi tasting kamin Sultee yaci don ya tabbatar ba a sa wani abu aciki ba Hakan kuwa akayi,d’aya ta zuba duk kalolin abincin a cikin ‘kananun plates,zama tayi a ‘kasa tacinye tas. Sai sannan securityn yace “It’s safe sir,zaka iya ci”,Sultee ci gaba da danna wayarshi yayi kaman baiji meh yace ba,sanin halinshi da securityn yayi yasa shi jan bakinshi yayi shiru Hanee da maman Khalil [1:38pm, 21/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Bayan mintuna kusan biyar Sultee ya d’auki spoon ya dibi pepper soup din ya kai bakinshi,wani dad’i neh ya ratsashi wanda har saida ya lumshe idonshi don dadi,azuciyar shi yana rayawa “Wow!Ashe ba ‘karya bane da ake yabon ‘yan yola da kwarewa a fagen girki”,bud’e cikinshi yayi da kyau ya shanye pepper soup din dama shi yana bala’in son abun,daga baya kuma ya d’anci yam balls,juice da aka sa mishi acikin cup neh ya d’auka ya kur’bi kad’an sannan ya goge bakinshi da soviet sheet,mi’kewa yayi ya kwashe wayoyinshi yayi hanyar d’aki. ‘Kuyangi suka tattara wajen suka goge suka saka turaren wuta mai ‘kamshi,nan take wajen ya d’auki wani sabon ‘kamshi yayi clean kaman ba yanzu aka gama cin abinci a wajen ba. Sultee yana shiga d’aki yawuce toilet yayi wanka sai yayi shirin kwanciya,gado ya hau ya d’auki wayarshi da ke ta faman ringing,yana dubawa yaga Saleem neh,picking yayi suka d’an ta’ba hira sai chan Saleem yace “Ya Sultee wallahi Nabila ta matsamin wai saina bata kunyi waya”,murmushi yayi yace “Okay,bata” Nabila ta ‘karba sai washe ha’kora takeyi kamar yana ganinta,tace “Hello ya Sultee,ina yini?ya gajiyar hanya?ya ka samu su Anty Amirah?Yola da dadi?ya garin yake?ya…..” katseta yayi yace “Tambayoyin da kike jeromin nan wa zai amsa su?kin dai san banason surutu ko?” lan’kwasa murya tayi tace “Yi ha’kuri ya Sultee,amma ka taimaka ka amsa min”,ata’kaice yace “Lafiya lau” zata ‘kara magana yayi sauri yace “Malama sai anjuma”. Bai jira meh zatace ba ya katse wayar sannan yayi murmushi,afili yace “Nabila uwar surutu kaman parrot”. Kashe wutar d’akin yayi ya tofa addu’a ya kwanta bacci Hanee da maman Khalil [1:38pm, 21/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Abangaren Nabila kuwa Sultee yana kashe wayar ta mi’ka ma Saleem wayarshi tace “Ga abunka” dariya yafara mata yace “Ya Saleem ya sallameki ko?ke din neh kin cika surutu wlh” hararshi tayi tace “Oho dai,ina ruwanka?sarkin gulma toh baza kaji ba”,da yake a kusa da d’akin su Nabila suke zaune sai ta mishi sai da safe ta wuce d’akinsu Washegari Sultee ya gama breakfast around 9 sai ya nemi amasa iso ya gaida su Sarauniya Maryam da Fatima,yashiga ya gaidasu suka amsa mishi fuska asake,s. Maryam sai janshi takeyi da hira da yake ita din gwana ce wajen hira,s. Fatima kuwa sai jifa-jifa take sa musu baki don a matsayin ta na surika bai kamata ace ta ‘bare baki tana hira da surikinta ba. Amirah ta fito cikin doguwar riga ‘ba’ki,tayi kyau sosai,zama tayi ta gaisheshi,asake ya amsa mata,s. Maryam kam ko a jikinta ta ci gaba da hiranta da Sultee wanda duk kunya ya cikashi,azuciyarshi yace “Surutu kaman Nabila”,s. Fatima da taga s. Maryam batada niyan tashi ta bar wajen sai ta mi’ke tace “Ammi’n yara ni nayi ciki,ko kuma ma muje don akwai abinda nakeso na nuna miki”,s. Maryam ba don taso ba ta mi’ke tabi bayan s. Fatima,aka bar Sultee da Amira kawai a parlourn Sama-sama sukayi hira saiya tashi tsaye yace “Ni zan fita ganin gari”,murmushi Amira tayi sannan ta mi’ke tace “Muje zan rakaka,tunda kai bakasan kan gari ba ai ba inda kasani”,guntun dariya Sultee yayi yace “Okay, muje”. Sun jera gwanin ban sha’awa don sunyi matching,suka isa wajen parking na motoci,nan securities suka tattaso,kowa sai cewa yakeyi zaiyi driving nasu,Sultee baice ko uffan ba,Amirah ne tace “Ba komai,mu biyu kawai zamu fita don ba nisa zamuyi ba” Hanee da maman Khalil [1:38pm, 21/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Wata shegiyar benz suka d’auka,Sultee neh yake driving. Ita ta dinga nuna mishi directions har sukaje San Hussain,Top 10,Tidbe,Oasis,Wetland da dai sauransu,duk inda sukaje sai sun kwashi tarkace kamar ba da kud’i suke siya ba. Sun gama yawo yawonsu sai yake tambayarta “Ba wasu shopping plazas neh?” zaro ido Amirah tayi tace “Akwai su sosai ma kuwa,naga time ya tafi neh saisa,kallonta yayi kad’an sai yace “muje ko da biyu neh saimu koma gida”,Amirah tace “Okay yalla’bai,bani da ja”. Dariya yayi ya girgiza kai,sunje Jalabu da kuma Yakubu shopping plaza ya d’ad’d’auki abubuwa dewa wai zaima su s. Fatima da s. Maryam tsaraba. Suna isa gida dogarai sukayi musu rututu,nan Sultee ya mi’ka musu leda guda uku yace d’aya na s. Fatima,d’aya na s. Maryam sai d’aya wanda shi ledan yafi girma yace su kai ma Amira d’aki. Jin yace Amira yasata juyowa tace “Wace Amira fah?” murmushi yayi yafara tafiya zuwa sashin shi yace “In akwai wata Amira a gidannan nan bayan ke sai ki min bayani”. Kasa ce mishi komai tayi sai kawai ita ma ta kama hanyar sashinta. Ammi da Mummy sun nuna jin dadinsu sosai kuma suka tura mishi da sa’kon godiyarsu. Hauwa tadawo gida daga skul tashigo parlourn sashin Amira taga Ukasha ma yana nan suna hira da Amira,idonta ya sauka kan ledan kayakin da Sultee ya bama Amirah,dasauri tace “Lahh! wa aka kai shopping ba aje dani ba?” Amira tace “Ya Sultee neh fah yakaini”,Hauwa iyayen rigima tace “Whatt?! Ai wallahi ba yanda za ayi yabar garin nan bai kaini ni da ya Ukashat ba” tasowa yayi ya rankwasheta yace “Ba na hanaki kirana Ukashat ba?in bazaki ce Ukasha ba karki kira sunana” dafe kanta tayi ta tsala ihu “Wayyo ya Ukasha,kayi ha’kuri,wlh rankwashinka da zafi”. Tsaki yaja yace “Ba zafi ba,Allah yasa rankwashin sumar da ke yayi”. Hanee da maman Khalil [1:38pm, 21/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS Dagudu Hauwa tabar parlourn taje tasamu mommy,nan ma taga leda cike da kaya,a shagwabe tace “Haba don Allah,wai ni mesa ba a sona a gidannan neh?” mummy bata gane meh take nufi ba saitace “Ana sonki mana,meh aka miki?”,cikin muryar kuka tace “Wai wai ya Sultee ya kai Ya Amira shopping kuma ya sassaya muku abubuwa amma ni ko tunawa dani ma baiyi ba” dariya mummy tayi tace “In banda abinki ai ko ke yanzu kika ce akaiki zakiyi shopping za a kaiki” d’aga kafad’a Hauwa tayi tace “Noo ni banaso,da ya Sultee nakeso naje”,nan Ammi tashigo tace “Meh kikace mara kunya?babba dake amma kina abu kaman yarinya ‘karama,in kin cika mara kunya sai kije ki sameshi ki gayamishi,fita daga d’akinnan”. Tura baki Hauwa tayi tabar d’akin. Akwana atashi yau Sultee yacika 1 week acikin masarautar Hamaz,kullum sai ‘kara missing na surutun Nabila yakeyi,da yake ta kar’bi numbanshi a hannun Saleem sai ta na kiranshi da wayarta,zasu gaisa lami lafiya amma inta soma surutu shiru zaiyi yana jinta har saiya gaji saiyace “Kingama?” in tace “Eh” sai yace “Toh sai da safe”. Ana gobe zai koma Hauwa tashigo side nashi,gaishe shi tayi saitace “Ya Sultee”,d’ago kanshi yayi yace “eh?ina jinki” tafara “Yau baza kaje shopping bane?” murmushi yayi don kuwa yagane tanaso ya kaita shopping neh don Amira tamishi hirar yanda sukayi. Yace “Zanje,je ki shirya kizo ki rakani” murmushi tayi tace “Ashirye nake,muje”. Tashi yayi,driver neh ya tu’kasu sai “San Hussain”,suna isa yace mata “Ki d’auki duk abinda kikeso,barin je ta chan ina zuwa,in kin gama ki jirani a counter”,cike da d’oki tace “Toh” Harta gama kwasan tarkacenta bata ganshi ba,bata jima da gamawa ba sai gashi yana turo troller wanda yake cike da kaya,lissafi akayi aka gayamishi kudin yabiya sannan suka juyo zuwa gida Hanee da maman Khalil [1:38pm, 21/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Motar yana tsayawa a harabar gidan ta bud’e ‘kofar motar tace “Nagode ya Sultee”,dagudu tafita daga motar tana jan ledojin ta. ‘dakin Amira ta nufa,nan ta tarar da Ukasha ma a zaune. Cike da mamaki Amirah tace “Hauwa,daga ina da wannan uban kayan?” rawa tayi sannan tace “Ya Sultee neh ya kaini shopping”,Ukasha yana kallonta yace “Yau na tabbatar baki da hankali Hauwa,yanzu ro’konshi kika je kikayi?” girgiza ‘kugu tayi tace “Ina ruwanka dani?in ma ro’ko neh sai meh?” binta yayi,ai da gudu tayi kan Amira tana ihu “Kayi ha’kuri karka ran’kwasheni,ba ro’konshi nayi ba” dariya yayi yakoma inda yake zaune yace “Mara kunya,da kin tsaya ai da sai kin daku”. Washegari Sultee ya sallami gaba daya ‘yan gidan,ya ba ma Ukasha bundle na 1000 yace “Kaine bankai shopping ba amma ga wannan”,girgiza kai Ukasha yayi yace “No ka barshi,nagode”,yayi-yayi ya kar’ba amma Ukasha ya’ki,mai martaba neh da yaga gardaman yayi yawa sai yace “Ukasha,kar’bi kud’in,ai shi yayan ka neh”. Kar’ban kudin yayi yace “Nagode ya Sultan”,murmushi yayi yace “Ba komai”. Nan aka tarkata aka kai Sultee airport,muma dai mun d’ad’d’aura seat belts namu,maman Khalil kaman zatayi kuka ta kalleni tace “Shikenan mun bar Adamawa”,nace mata “Kin manta zanu dawo d’aukan rahoton biki neh?” nan ta wangale baki sai murna takeyi tace “Na manta neh ai mutumiyar,Allah dai ya kaimu” murmushi nayi nace “Ameen”. Mun sauka lafiya,motoci dewa sukazo tarbar Yarima Sultan,cikin tawagar harda Nabila,tana hangoshi ta ta’ba Saleem tace “Ya Saleem ga Ya Sultee”,sai murna takeyi,kallonta ya d’an tsaya yi kaman mai karantar abu sai chan yace “Sai akayi yaya?Allah yasa yauma ki isheshi da surutu har ya disgaki a gaban mutane” Hanee da maman Khalil [1:38pm, 21/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Murgud’a masa baki tayi tace “Ya dizga din mana,ai ni ya dizga ba kai ba” murmushi kawai Saleem yayi bai ce mata komai ba. Sultee yana isowa inda suke tsaye a bakin motar ya mi’ka ma Saleem hannu suka gaisa,yayi kaman bai ga Nabila ba. Itakuma da taga haka sai kawai ta’ki mishi magana gudun disgel irin nashi,shiko Sultee yaso ta tare shi dda surutu sai yaga bata ce uffan ba,kamar zai mata magana sai kuma ya fasa kawai ya shiga motar sai gida. Mai martaba yayi murna kwarai da gaske da yaji Sultee da Amira sun daidaita kansu,saidai muyi fatan Allah yasa ayi biki a sa’a. Yabi murna ya cikata ganin babban d’anta ya dawo,baba Rabi,Nene,Amina da Jamila duk sunzo sun mishi barka da dawowa har d’aki amma ba Nabila ba alamunta. Har dare yana zuba ido amma bai ganta ba,sai chan ya ‘kira Saleem yace “Saleem kana ina?” Saleem ya amsa “Na d’an fita neh,da wani abu neh?” dasauri yace “No”(dama ya tambayeshi ko yana gida neh gudun kar suna tare da Nabila). Sultee yaci gaba “Ina Nabila neh?”,saleem yace “Gaskiya bansani ba amma dai inaga tana d’akinsu,in kira ma ita neh?” Sultee ya d’an yi jim sai kuma yace “No barshi kawai,ba komai”,Saleem yace “Okay toh bye”,kamin ya kashe Sultee yace “Umm,bance kuma ka gaya mata na kiraka ina tambayanta ba” dariya Saleem yayi yace “Ho ya Sultee,naji bazan gaya mata ba”,nan Sultee ya katse wayar Abangaren Nabila kuwa tunda taga Sultee yana wani ciccin magani a airport sai ta ji ba dadi,sai kawai ta yanke ma kanta baza ta sake shiga harkan shi ba illa gaisuwa da inta ganshi zai had’asu Kwana biyu shiru Sultee saidai ya hangi Nabila daga nesa,da ta ganshi take chanja hanya. Yau tana zaune a lambu ita kad’ai sai kawai taji mutum yayi sallama,d’ago kan da zatayi sai taga Sultee neh. Cikin in’ina tace “ya… Sul…tee… ina…yi…ni” murmushi yayi ganin ta wani rikice,zama yayi a gefenta sannan yace “Bazan amsa gaisuwar ba,are you avoiding me?” girgiza kai ta shiga yi tace “No ya Sultee wallahi ba haka bane,kawai dai…” saitayi shiru,kallonta yayi yace “Kawai dai meh?” ajiyar zuciya tayi tace “Naga kaman in ina ma magana ranka yana ‘baci bakaso neh saisa nabari”,”hmmm” kawai yace sannan ya mi’ke yace “Biyoni”. Nan ta fara binshi har side nashi,a parlour ya barta yashiga bedroom,kaman zata juya sai kuma ta fasa,don a tunaninta yace ta biyoshi kuma zai barta a tsaye shi ya wuce bedroom. Bai dade ba ya fito da wani ‘katon leather ya mi’ka mata,’kar’ba tayi tace “wa zan kai ma?” zama yayi akan kujera,ba tare da ya kalleta ba yace “Naki neh?”,cikin kidimewa tace “Nawa? nawa?nawa fah kace?” Gaisuwa zuwa gareki Amrah Auwal Muhd,nagode sosai. And to my sisi Faty Axland,Allah yabar zumunci,na rasa da wani baki zan nuna godiya ta,thanks alot kuma Allah ya baki lafiya. Sumayya Girei,Aseem,Milly my mamahh da Maryam miss purple kunfi kowa son book nan,i dey greet u all:D GIMBIYA NAFEESAH [11:21am, 24/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Kallonta yayi sannan ya d’aura ‘kafarshi d’aya kan d’aya akan centre table da ke parlourn. Nabilah azuciyarta tace “Wannan anyi d’an rainin wayo,baya magana sai kace bakinshi yana ciwo”,ashe dai maganar da tayi da zuciyarta ya fito fili,wani kallon da ya watsa mata yasa ta sha jinin jikinta,sai wani shan ‘kamshi yakeyi,da kyar ya bud’e baki yace “Ya da tsayamin akai?,ki d’auki leather bag d’in kiyi waje”. Ajiye leather din tayi a ‘kasa,cike da tsiwa tace “Meh zanyi da shi neh wai?kace nawa,yanzu kuma ina neman ‘karin bayani amma ka tsaya sai wani hahhad’amin fuska kakeyi”. Cike da mamaki ya maida dubanshi zuwa gareta,har zaiyi magana sai kuma ya fasa,d’aukar wayarshi yayi ya ‘kira Amirah. Ran Nabila yayi mugun ‘baci,afusace ta juya zata bar d’akin,har ta kai ‘kofa sai ya dakatar da ita yace “Umm zo ki d’auki kayan”,ba tare da ta juyo ba tace “Banaso,nagode”,ajiyar zuciya yayi sannan ya d’aga kafad’a alamun wannan kuma ya rage naki sannan yace “Okay ki d’auka kije ki kyautar amma dai karki kuskura ki bar min leather’n nan a d’akina”. Sanin halinshi yasa ta juyo ta d’auki leather din tana tuttura baki,Sultee kam bai ma san lokacin da dariya ya kubce mishi ba. Cike da mamaki da tsoro Nabila take kallonshi,tunani takeyi “Kai!!lafiyar ya Sultee kuwa?daman yana dariya har haka?ko dai hauka yayi?ko yasha wani abu da ya ta’ba mishi brain?” ta sa’ka wannan ta kunce haka ta dinga yi. Ganin ta tsaya kallonshi baki bud’e yasa yayi shiru,nan take ya ‘kara had’e fuskar nan kaman ba shi bane ya gama dariyar mahaukata yanzu. Kallonta yayi yace “Malama ya kike kallona haka?ko kina sona neh in taimaka miki?”. Zaro ido tayi,mamakin kalaman shi takeyi,sai girgiza kai takeyi,da ‘kyar ta iya furta “Ni??a’a,meh zanyi da mutumin da yakusa haifana ko ma ince ya haifen?ni banida ra’ayin auren sugar daddy balle ka nemi gayamin magana”. Murmushi yayi yace “Jeki”,murgud’a mishi baki tayi ta tattara leather din tayi hanyar d’akinsu Hanee da maman Khalil [1:25pm, 24/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Tana shiga d’aki baba Rabi da ke kwance ta tashi ta zauna,cike da tambayoyi ta ke kallonta sai chan tace “Nabilah,kayakin nan daga ina?”,Nabila ta ajiye leather din a ‘kasa saita zauna a kan gado tace “Hmm wlh umma ban ro’keshi ba,da ya bani ma nace mishi yabari ni banaso amma ya da ge saida na kar’ba,ki yarda dani wallahi ba ro’konshi nayi ba”,jikin baba Rabi yayi sanyi sai tace “Nasan bazaki ta’ba ro’ko ba amma dai waye ya baki?”. Nabila ta d’an yi jim sai tace “Ya Sultee neh”,cikin rashin fahimta baba Rabi tace “Ya Allahu,waye kuma ya Sultee?” Nabila tayi dariya tace “Lahh!umma dama baki sani ba?”. Baba Rabi ta ja tsaki tace “Ke ni banason shiririta,sunan mutum nakeso ba sunanku na ‘yan zamani ba”,nan Nabila tace “Ya Sultan fah nake nufi” Baba Rabi ta fad’ad’a murmushinta tace “Allah sarki,Allah ya sa ka da alheri,zo ki bud’e ledar mu gani”,turo baki Nabila tayi tace “Ni fah banason kayanshi,kawai zan mayar mishi” sai ta tashi ta suri ledar tayi hanyar ‘kofa,sunanta da baba Rabi ta kira shi ya sa ta tsaya cak,cikin ‘bacin rai tafara magana “Haba Nabila,yanzu har kyauta ya fito daga hannun Yarima kice zaki mayar mishi?a wani dalili?ai Yarima a matsayin ‘kanwa ya daukeki,yanzu in da Auta neh ya baki zaki ce bakiso neh?kul dama,karki sake wannan sakarcin” jiki ba ‘kwari Nabila ta dawo ta zauna ‘kusa da baba Rabi tace “Kiyi ha’kuri umma na sa ranki ya ‘baci,bazan sake ba” shafa fuskarta baba Rabi tayi tace “Ba komai,bude ledar mugani”. Su chocolates,biscuits,wafers,perfumes,jewelries da material guda biyar hade da gelensu da takalma,kaya kam tubarkallah. Baba Rabi dafe ‘kirji tayi tace “Yaron nan ai ba haka ake kyauta ba,kayan yayi yawa”,saita tashi ta d’auki mayafinta sai waje. Nabilah kam tazama speechless don kayan har tsoro suka bata,mamaki neh yacika ta,haka taketa bin kayan da kallo Hanee da maman Khalil [1:48pm, 24/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Tayi sallama a ‘kofar d’akin Sultee,amsawa yayi sannan yace ta shigo. Ta shiga tasamu waje ta zauna,ganin ita neh yasa Sultan sau’kar da ‘kafanshi daga kan centre table,a mutunce ya gaisheta,ta amsa sai murmushi takeyi tana mamakin sauyawar Sultan a lokaci d’aya. Sultan da baya magana,ko kallon kirki baya mata,gaisuwa ma da ‘kyar yake amsawa amma wai yanzu shine har da gaisheta a mutunce da girmamawa kamar uwarshi,taji dadi sosai. Bayan ‘yan gaishe gaishe sai tace “Yarima naga kayan da ka bama Nabila kuma mungode sai dai gaskiya bazata iya amfani dasu ba,kayakin sunyi yawa,ai da ko kad’an ka bata ya wadatar”,har ranshi bai ji dad’i ba amma bai nuna mata ba,sai ma murmushin ya’ke da yayi yace “Umma,agaskiya ni na bata kayakin nan neh a matsayin tsarabarta daga Yola,kuma ai kyauta yana da kyau and ni na dauke ta neh a matsayin ‘kanwata,kiyi ha’kuri ki d’aukeni kaman yanda kika d’auki Saleem”,kallonshi ta tsaya yi na d’an lokaci saitace “Ba komai,dama ni naga kayan sunyi yawa neh amma yanzu na fahimta,mungode sosai Allah ya ‘kara arziki”, murmushi yayi yace “Ameen”. Sallama baba Rabi ta mishi sannan tabar d’akin,tana fita Sultee ya sau’ke wani ajiyar zuciya,afili yace “Ya Allah,make my dreams come true”(Ya Allah,kasa mafarki nah yazama gaskiya),ni da maman K sai kallon-kallo mukeyi saitace “Hanee kingane?wani irin mafarki”,girgiza kai nayi nace “Wallahi bansani ba maman K,saidai nasan watarana zamu gane” Baba Rabi ta koma d’aki ta gayama Nabila yanda sukayi da Sultee. Haka ta tattara kayan ta kaishi cikin wardrobe ta rufe. Akwana atashi yau ya kama saura kwana shida d’aurin auren Amira da Sultee,suna waya sosai and sun saba da juna,har cikin jijiyon Amira Sultee neh,amma unfortunately a wajen Sultee ba haka abun yake ba,shi kawai don biyayya neh zai aureta ba don yana sonta ba saidai bai ta’ba bari angane ba. Hanee da maman Khalil [2:05pm, 24/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Saura kwana hudu bikin Sultee mai martaba yayi shatar jirgi na tafiya Yola zuwa masarautar Hamaz. Mutane dewa sunje ciki ko harda Nabila,muma dai muna biye da biros namu. Sun isa Hamaz lafiya,motoci da suka amsa sunansu aka kawo don kwasar mutane daga airport. Anci ansha an yi hira,abun gwanin sha’awa,sarauniya Maryam itace kan gaba akan komai kamar itane uwar amaryar(samun Kishiya irin S. Maryam sai an tona,ko da yake ba abun mamaki bane don sunada sanyin hali kamar frndy nah Ummitah). Tunda suka isa Nabila take ta son taga amarya,ta tambayi Hauwa “Sister don Allah ina neh d’akin Gimbiya Amira?”,Hauwa tayi murmushi ta kamo hannunta tace “Taso muje na kaiki”. Sun d’anyi tafiya kad’an sannan suka isa sashen gimbiya Amee,ba kowa a parlour,nan sukaji kamar ana kuka a d’aki. Dasauri suka shiga,turus sukayi ganin Amira ta rungume hoto tanata kuka kaman meh. Nabila ta taka zuwa bakin gadon ta kira sunanta a hankali sai tace “Kiyi ha’kuri anty,koma meh yake damunki kibar kuka kawai ki mi’ka lamarinki zuwa ga Allah”,d’agowa Amira tayi hawaye sai bin kumatunta sukeyi sannan tayi murmushi tace “Nagode sister”. Hauwa ta gayama Amira akan wannan neh Nabila,Amira ta rungumeta tace “Allah sarki,naji labarinki wajen ya Sultee”. Zaro.ido Nabila tayi tace “Nashiga uku,zagina yayi ko?ko yace na cika surutu?”. Amira ta share hawayenta tace “A’a ko d’aya”, saita chanja topic din. Hira sukeyi kaman dama sunsan juna,a d’akin Amira ma ta kwana. Washegari yakama thursday kuma yau neh akayi mothers’ day,iyaye sun je,duk kowa ‘ya’yan sarauta,abun ya ‘kayatar sosai. Washegari akayi Walima wanda malama Jamila Moh Ali da malama Shukurah suka gabatar,gaskiya malaman akwai ilimi. Hanee da maman Khalil [2:43pm, 24/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Washegari asabar da misalin ‘karfe goma aka d’aura auren Yarima Sultan Mu’awiya da Gimbiya Amira Ibrahim akan sadaki naira dubu hamsin,d’aurin auren da ya samu halartar sarakunan Nigeria da ma ‘kasashen da ke kewaye,shugaban ‘kasa ma yaje,’kusoshin gwamnati da dai sauransu. Sarki Mu’awiya baki ya kasa rufuwa,murna yakeyi da Allah ya nuna mishi auren Sultan,haka ma sarki Ibrahim. Da daddare wajen 9 aka tafi dinner a hall din AMA,anyi decoration pink and white,amarya tasaka pink material mai uban wal’kiya ango kuma yasaka Blue anmishi aiki a rigan sosai yayi bala’in kyau,hannun rigan irin meh lynx dinnan. Nabilah kuma wani material tasaka itama blue,coincidentally kuma Sultee blue yasaka,daga cikin wanda Sultee ya bata neh ta d’auki d’aya ta d’inka,a table d’aya ta zauna da Saleem sunata hira. Ana cikin program Saleem ya d’an fita answering call sai wani yazo ya zauna a ‘kusa da Nabila,mai da hankalinta tayi zuwa amarya da ake ma spray,Sultee kuwa gaba d’aya hankalinshi yana kanta. Mutumin ya gabatar da kanshi as Nafi’u amma Naf ake kiranshi,shi d’an sarkin Katsina neh,kyakkyawa neh ba laifi saidai bai kai Sultee ba,da farko ta shareshi amma daga baya saita fara amsa mishi,suna cikin hira sai dariya sukeyi sai wayarta ya fara ringing,tana dubawa taga Sultee neh,maida kanta wajen zamanshi tayi saita ga yananan amma ba ita yake kallo ba,atunaninta maybe mistake yayi ba ita yakeson kira ba. Mayar da wayar cikin purse tayi saita cigaba da hirarta,chan wani call ya sake shigowa still Sultee neh,tsaki taja azuciyarta tace “Ko meh matsalarshi dani oho,watakila ma yanaso ya dizgani a gaban mutane neh”. Saka wayar tayi a silent sai ta mayar cikin purse,bayan kaman minti goma sai wani waiter (masu raba abinci a wajen) yazo yace “Ma’am,yayanki yana kiranki a waje wai kije ta bayan hall” tace “Okay ina zuwa”. Tajuya wajen Naf tace “Ya Saleem yana ‘kirana awaje,bari naje”,tami’ke ta fita ta hall din tabi ta hanyar da zai sada ta da bayan hall din. Tun kafin ta isa ta fara kwala mishi ‘kira “Ya Saleem!ina kake neh?ni fah banganka ba”,gyaran murya taji ta bayanta,tana juyawa ta zaro ido ta dafe ‘kirji,cikin rikicewa tace “Ya……” Toh jama’a,ku dai cigaba da ha’kuri damu. We love you all GIMBIYA NAFEESAH [12:40pm, 25/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil A firgice tace “Ya…Sul…tee”,had’e fuska yayi kaman bai ta’ba dariya ba yace “Kina ganin kin girma shine kike raina mutane ko?”,cikin rashin fahimta tace “Kamar ya?bangane ba?wa na raina?”. Tsaki yaja sannan yace “Sau nawa na kiraki amma kikayi banza bakiyi picking ba saikace ni sa’anki ne”,bud’e baki tayi tace “Kayi ha’kuri wallahi….”,d’aura hannunshi yayi akan bakinshi yace “Shhh,bana neman bayani daga wajenki illa guda d’aya”,ganin yanda ranshi ya ‘baci yasa tasha jinin jikinta,asanyaye tace “Ina jinka”. Furzar da iska yayi yace “Kinzo bikin nan neh don kula samari ko meh?wayene wanda kuke zaune tare kuna hira kekuma tsaba rashin kamun kai kin ‘bare baki sai dariya kikeyi kaman wata sokuwa,dubi d’an iskan gyalen da kikasa,ke ko kunya bakyaji?”. Ran Nabila ya mugun ‘baci don ita dai tasan kayan da tasa ba wani transparent kaya bane,cikin masifa ta fara magana “Haba ya Sultee,mene aibu acikin shigar da nayi?da kake maganar wanda yazo muke hira kuma,yes yazo yace yana sona amma ni ba abinda zanyi dashi tunda dai inada wanda nakeso” tana gama fad’in haka tajuya afusace zata bar wajen,abangaren Sultee kuwa zuciyarshi neh yafara bugawa,da ‘kyar ya iya controlling na kanshi,jawo hannunta yayi da ‘karfi wanda yasa har ta saki ‘kara,cikeda ‘bacin rai da yafi nada yafara magana “Wallahi kinji na rantse,kika kuskura na sake ganinki da wani d’an iska asunan kuna hira sai namiki abinda baki ta’ba zato ba” Sakin hannunta yayi itakuma duk da taji tsoro amma cikeda tsiwa tace “And so?sabida meh bazan kula samari ba?kai zaka aureni neh balle ka tsaya kana kafamin dokoki marasa kan gado?”,huci yakeyi kaman zaki ya nufota,ai dagudu ta bar wajen don tasan indai ta bari ya kamata ba ‘karamin jibgarta zaiyi ba. Hanee da maman Khalil [12:58pm, 25/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil A bakin hall din ta tsaya tana maida numfashi,nan Saleem yazo ya sameta. Cikeda tuhuma yake kallonta yace “Yadai?gudu kikayi ko?waya biyoki?”,har zata gayamishi abinda ya Sultee ya fad’a mata amma sai wani zuciyan tace mata “a’a,wannan sirrinku neh,bai kamata wani yaji ba”,ajiyar zuciya tayi saitace “Na d’an fita ansa call ne tachan sai naga kule shine na gudu”,dariya Saleem yayi yace “Kai kanwata,Allah ya nunamin ranar da zaki bar tsoro,yanzu dai mushiga ciki” Su sadydy,shukee,milly da tulelen cikinta,fabee,bahirah duk mun hangosu sai cin abinci sukeyi dama sukam abinda ya kawosu kenan,daga chan wajen spray kuma mrs Adams,Faty axland,Benaxir sune suketa watsa ma amarya dubu daddaya. Nan aka fara neman ango ba aganshi ba,kiran wayarshi akayi yace ya d’an fita neh amma gashinan zuwa,bai jima ba kuwa yadawo fuskar nan tashi ba yabo ba fallasa har aka d’ad’d’auki hotona wanda George okoro neh cameraman sannan aka watse sai fatan Allah ya bama couples din zaman lafiya. Washegari da misalin 3:45 jirgin ‘yan biki ya iso Kaduna,motoci sukata d’aukan mutane suna kaisu masarautar Yura. Da dare mai martaba da matanshi su biyu suka saka Sultee da Amira agaba sukata musu wa’azi da kuma fatan Allah ya basu zuri’a d’ayyiba. Mai martaba yake tambayar Sultee “Yaushe zaku koma wajen aikinkan?”,Sultee ya ‘dan sosa ‘keya yace “Ehh dama inaso nan da 2 weeks zamu tafi don akwai abinda nakeso ingama before mutafi”,mai martaba ya jinjina kai yace “Okay amma dai zata koma side naka da zama”. Sunkuyar da kai Sultee yayi yace “Duk yanda kuka yanke yayi”. Nan taro ya watse akan washegari za a mayar da Amira side na Sultee Hanee da maman Khalil [1:16pm, 25/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Tun da sassafe akasa ‘kuyangi su gyara ma Amira side na Sultee sannan aka saka sabbin funitures tunda ita jerenta a Qatar akayi,dayake side na Sultee babba neh,2 bedroom flat,ga ‘katon parlour sai kitchen da store,an saka duk abinda zasu bu’kata aciki. Su Hauwa kam tuni Saleem ya kaisu yawo ita da Nabila don sun zama kaman friends duk da Nabila ta bata kusan 3 years. Achan masarauta kuwa Sultan neh zaune a lambu yatura akira mishi Nabila,’kuyanga’n da ya tura ta dawo tace mishi “Allah ya ja zamaninka Yarima d’an sarki,jikin sarki,baban sarki kuma kakan sarki da yardar Allah,takawarka lafiya Yarima mai jiran gado,ba wanda……” d’aga mata hannu da yayi ne yasa tayi shiru,cikin muryarshi na sarauta yace “Ya isa,ina take?”,sunkuyar da kai tayi cike da ladabi tace “Yarima naje naduba ta amma ance min tafita da Yarima Saleem”,afirgice yace “Whatt?!?!?!”,da hannu ya mata alama da ta tashi ta tafi. Dafe kanshi da yake sara mishi yayi yana “Innalillahi wa inna ilahi raji’un” azuciyarshi tunani iri iri yakeyi “Allah yasa tunani nah ba haka bane,kar dai Saleem da Nabila soyayya sukeyi?ina!!it can’t be possible,ba ma yadda zai yiwu,why?!!why?!!,I have to do something”. Har ya mi’ke saikuma yasake zama wata zuciyar tace “Take it easy,idan tunaninka ba haka bane kuma fah?”,shiru yayi na minti kad’an saiya mi’ke tsaye yabar wajen yana murmushi kaman dai ya samu mafita. Ankai amarya side nata sannan aka bata shawarwari masu amfani tukunna mutane suka watse. Chan dare Sultee yadawo da leather yashiga d’akin Amira,gaisheshi tayi ya amsa mata ba yabo ba fallasa sannan ya ajiye mata yafita daga d’akin Hanee da maman Khalil [1:32pm, 25/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Gobe da safen aka tattara ‘yan Hamaz aka maidasu. Kwana biyu dai haka zaman su ya kasance da Amira,komai ‘kuyangi ne sukeyi saidai girkin Sultee ne kawai takeyi tunda yace shi baya cin abincin masu aiki,zasu zauna suyi hira normal-normal amma dare yanayi zai mata sai da safe yashige d’akinshi itama tayi nata. Tsakaninshi da Nabila kuwa tun ranar dinner rabon da su had’u,ita harga Allah bata ma sha’awar ta sake ganinshi,har tana Allah-Allah ranar komawarshi yayi. Saura kwana tara su Sultee su tafi,yasamu mai martaba suna hira sai yake tambayarshi ” Nikam yarinyar nan ba makaranta zataje ba?ina ake nema mata?”,cikin rashin fahimta mai martaba yace “Wace yarinya kenan fah?”,Sultee yace “Nabila nake nufi”,murmushi mai martaba yayi yace “Daman Yale nake so na nema mata saidai admission nasu ba yanzu suke bayarwa ba” Murmushin da muka kasa gane ma’anarshi Sultee yayi sannan yace “Daman inada suggestion neh”,mai martaba ya gyara zama yace “Okay,go on”. Sultee yace “Naga yarinyar tanada rawan kai kuma in har ankaita inda ba tasan kowa ba inaga akwai matsala,kar taje ta jawo mana abun kunya abanza da wofi,why not a nema mata a Qatar tunda ina chan?” nazarinshi mai martaba yayi kaman yanason gane inda ya dosa amma sai ya basar yace “A iya sanina da Nabila batada rawan kai saidai tanada son mutane da surutu,’yanmata nawa ake kaiwa karatu inda basusan kowa ba kuma suke ri’ke mutuncinsu?ka kawo wani reason din ba dai wannan ba”. Sultee kanshi ya d’aure amma bai nuna ba sai yace “Daman ni shawara na bayar ba wai dole sai Qatar din ba”. Hanee da maman Khalil [2:08pm, 25/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Mai martaba ya d’anyi jim sannan yace “Ba wai na’ki gane point naka bane,yanzu in nace zan nema mata Qatar din ma wani sabon aiki neh tunda har nayi magana da ‘yan Yale din kuma sun bani tabbacin zasu bata admission,kaga Qatar din kuma wata ‘kila ma har sun gama bada admission kuma kasan ni bana son abu da cutarwa,kamar a hana wani wanda ya rigamu nema sannan mu abamu”,murmushin cin nasara Sultee yayi yace “Indai batun admission neh ba matsala don akwai wani school da zasu iya d’aukarta,ahalin yanzu ma suna kan bada admission neh”,jinjina kai mai martaba yayi yace “Ba damuwa,amma dai a hostel zata zauna” Zaro ido Sultee yayi yace “Hostel abba?kaga yanda suke rayuwa a hostel kuwa?yanda suke lokacin da kukayi karatu ba haka bane abun yanzu,komai ya lalace,fitsara yayi yawa sannan ina tsoro kar nan gaba suyi influencing nata ko da kuwa bata ra’ayi”,mai martaba baice komai ba sai kallonshi da yakeyi,chan sai Sultee yaci gaba “Indai inda zata zauna ne shima ba matsala don gidana akwai enough rooms”,girgiza kai mai martaba yayi yace “Bazai yiwu ba Sultan,shawarar nan bai ‘karbu ba,ko wata d’aya da aure bakayi ba amma zakace zaki d’auki budurwa babba ka ajiyeta a gidanka,ai ba aikin hankali aciki” Sultee yahau kawo ma mai martaba dalilanshi amma duk mai martaba yace bai amince ba. Da yaga abun ba na ‘karewa bane sai mai martaba yace “Zan yarda in har matarka ta amince da ku tafi da Nabila”. Godiya yayima mai martaba sannan yafice,yana isa side nashi ya samu Amira yace “Daman mai martaba neh yace yana neman alfarma a wajenki”,Amira tace “Toh Allah yasa baifi ‘karfina ba”,Sultee ya wani ‘bata rai alamun bayaso sai yace “Wai yanaso mutafi da Nabila kuma ta zauna damu agidanmu achan Qatar don achan ya nema mata admission,nidai na nuna ban amince ba amma yace shi bai nemi yarda na ba,indai kin amince toh shikenan”. Murmushi Amira tayi tace “Ayyah ai komai zan iya mishi,wallahi na amince mu zauna tare da ita dama ni banason zama ni kad’ai”,afili Sultee yanuna shi sam amincewar da tayi baimishi dad’i ba,tayita bashi ha’kuri sannan yace “Barinje na gayamishi”(hhhh su Sultee brainwork) Hakan kuwa akayi,yasamu mai martaba ya shaida mishi Amira ta amince,nan mai martaba yace “okay barin tura akira Nabila sai a gayamata ta shirya kayanta ko?”,dasauri Sultee yace “A’a abba,surprising nata nakeson yi,dama tace tanason garin saisa nayi hakan,amma dai kawai kace mata tasamu admission tashirya kayanta,next week zata tafi saidai karta san wani gari neh don Allah”,mai martaba yace “Allah ya taimaka”. Nabila tayi murna sosai da taji zata tafi school next week,saidai tanajin haushi zatabar Saleem,haka Saleem ma duk yabi ya rame kaman bashi ba,kai! Sabo bala’i neh wallahi. Sultee yayita cuku-cuku ta waya da taimakon abokanshi na chan hardai yasamar ma Nabila admission. Akwana atashi yau Sultee zasu bar gari tareda Nabila,Nabila sai mamaki takeyi “Ashe dai tare zamu tafi,maybe suna tashi nima jirginmu zai tashi,gashi basu gayamin a ina nasamu admission din ba”. An sassaka kayakinsu a booth sai mai martaba ya kirasu yana musu nasiha,yace “Ke Nabila karki yadda naji kinma yayanki ko matarshi rashin kunya,sannan ku kuma in tayi ba daidai ba ku hukuntata kuma kuta ha’kuri da ita tunda dai kunfita shekaru kunfita hangen nesa”,nan kwakwalwar Nabila ta dagule,a rikice take tambayar mai martaba “Tare dasu zan tafi neh?”,mai martaba yace “eh,agidansu ma zaki zauna tunda makarantar ba nisa da gidan”,kaman tasa ihu haka taji amma saita daure tafara a hankali “Wayyo Allah nah nashiga uku,tare da mai shegen takuramin nan zan zauna?”. Ashe dai maganar da tayi a hankali kowa yaji,nan kallo ya koma kanta,mai martaba yace “Yadai Nabila,bakiso ki bisu neh? idan bakyaso bazan saki dole ba,inyaso saina nema miki wani waje daban”,d’ago kai tayi tana bin ‘yan parlourn da kallo,nan ta kai kan Amira,dasauri ta juyo wajen mai martaba tace “Bazan b……..” GIMBIYA NAFEESAH [7:52pm, 27/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Nabilah tace “Bazan baka kunya ba in Allah ya yarda,kuma bazan ta’ba zubar da mutunci nah ba”,wani ajiyar zuciya Sultee ya sau’ke wanda sai da duk ‘yan parlourn suka dubeshi,fuskewa yayi ya tsare kaman ba shi ba. Mai martaba yayi gyaran murya yace “Alhamdulillah tunda kin amince zaki bisu,yanzu sai muyi addu’ar Allah ya kaiku lafiya tunda gashi lokacin tashin jirgin ya ‘kusa”,sarkin gida ne yayi addu’a sannan taro ya watse,duk aka dunguma zuwa inda aka parka motocin da zasuyi rakiya zuwa airport. Yabi,Baba Rabi,mai martaba,Saleem,Amina da Jamila duk anje airport,Amina da Jamila sai kuka sukeyi zasu rabu da bestfriend nasu,Nabilah ma dai kuka takeyi,ta bibbisu d’aya bayan d’aya ta rungumesu. Da tazo wajen Saleem saita kasa rungumeshi,tsayawa kawai tayi tana goge hawayen idonta,Saleem kasa jurewa yayi,bashiri ya jata jikinshi ya rungume yana bubbuga bayanta alamun rarrashi,sun d’au mintuna ahaka sai rarrashinta yakeyi,tayi shiru sai ajiyar zuciya. Sultee da ke gefe haushin Saleem ya cikashi,cikin masifa yafara “Ya zaka wani rungumeta saikace muharraminta?bawai ku yara ‘kanana ba, wannan ai d’abi’ar jahilai neh”,wani kallo Saleem ya bishi dashi sannan ya sake Nabila,ya bud’e baki zaiyi magana amma kallon da mai martaba yamishi alaman yayi shiru yasa yayi controlling temper dinshi,afusace ya juya ya koma motar. Mai martaba ya ‘kara ma Sultee nasiha akan ya dinga ‘ko’karin danne ‘bacin ranshi,ha’kuri yaba ma mai martaba sannan suka lula cikin jirgi zuwa Qatar,ko ya zaman zai kasance achan,kudai biyomu… Ni da maman K ma muna tare dasu don d’auko muku rahoto Hanee da maman Khalil [10:26pm, 27/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil QATAR Sun sau’ka a Doha dake cikin Qatar lafiya lau,driver’n Sultee da ke chan yazo ya d’aukesu zuwa Al Asmakh street,anguwa neh mai kyaun gaske. Wani gida driver yayi horn aka bud’e gate,gidan flat biyu ne aciki,Sultee ya bud’e d’aya daga ciki ya shiga sannan su Amira ma suka bi bayanshi,driver ya kwaso kayaki daga booth ya diresu a parlour sai ya musu sallama ya fice. Parlour neh ‘katon gaske,kujerun coffee colour neh,daga chan gefe kuma dinning area,ta hagu kitchen neh da store aciki,ta dama kuma wani ‘kofa neh. In an bud’e ‘kofar akwai toilet d’aya sai d’akuna guda biyu kowanne da toilet aciki,duka d’akunan royal beds neh aciki,d’aya coffee colour,d’ayan kuma pink. Ata’kaice dai gidan ya tsaru kuma ba acika kayaki dewa ba,just kad’an amma komai acikin tsari akayi. Sultee ya sallami Amira yace “Ni na tafi side nah,nan d’in saiku zauna ku biyu”,Amira tayi murmushi tace “Toh,daman ni nafiso mu zauna tare da ita”. Yana fita Amira ta maida kallonta wajen Nabila sai tace “‘kanwata tashi ki shiga d’aki mana ki huta,duk wanda yamiki ki saka kayanki aciki”,murmushi Nabilah ma tayi sannan tace “Nagode sosai Anty Amira,barin shiga ciki”. Da yake kujerun parlourn coffee colour neh kuma d’aki d’aya gadon shima coffee colour ne sai Nabilah ta saka kayanta a d’aki mai pink bed d’in. Da dare Sultee yamusu ordering na abinci daga restaurant,sunci sun ‘koshi sai suka zauna suna hira sama-sama,Nabila kam hankalinta yana kan wayanta ma sai chatting takeyi. Magana d’aya-biyu sai Sultee ya sakota aciki,chan sai ta tashi ta musu sai da safe. Har ta bud’e ‘kofar da zai sada ta da d’akinta sai Sultee ya tsaidata Hanee da maman Khalil [10:43pm, 27/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Yace “Aff! Kinga na manta”,juyowa tayi amma bata dawo ta zauna ba,da yaga bata da niyya sai yace “Zo ki zauna,magana nakeso muyi”. Taso ta mishi gardama amma kunyan idon Amira yasa ta koma ta zauna akan kujera,ciki- ciki tace “Gani” tana cigaba da danne-danne da wayarta. Sultee ya d’anyi jim sai yace “Ajiye wayar nan zakiyi fah don in ina magana da mutum banaso yana ta’ba waya”,tura baki Nabila tayi amma ba ta ajiye wayar ba sai tace “Ai ba wai kunne nah bane ya toshe da in ina danne danne bazan ji me kake fad’a ba”,tsaki yaja sannan yace “Tashi ki tafi in har bazaki iya ajiye wayar ba”. Jin yadda yayi maganar tasan ranshi ya ‘baci neh sai tayi saurin ajiyewa,dama abinda takeso kenan wato ranshi ya ‘baci. A hankali tace “Yi ha’kuri”,Amira kam dariya tayi tace “Ohh Nabila,ashe dai kema ba tayar baya bace”,murmushi Nabila tayi ta sunkuyar da kai. Saida ya gama jan ajinshi sannan ya dubeta yace “Rules na gidannan nakeso na gayamiki,na farko….”,da sauri Nabila ta d’ago kanta tana kallonshi,a razane ta katseshi tace “Ohh masifa!!wani rules kuma ya Allahu?,ni fah banason takura”,kallonta ya yi na ‘yan seconds sannan ya yi wani shu’umin smile sai yace “Ban nemi ji ta bakinki ba..and karki sake katse min magana,in ina magana shuru zakiyi sai na gama sannan ki d’ora da taki”. Nabila tace “Okay,Allah ya baka ha’kuri”,gyara zama Sultee yayi sannan yafara “Kaman yanda kika sani kinzo garin nan neh domin karatu,na samo miki admission a Carnegie Mellon University,zaki karanta Biological Science” murmushi Nabila tayi don taji dad’i,daman course da takeso kenan. Hanee da maman Khalil [11:08pm, 27/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Sultee yaci gaba “karki kuskura na ganki da saurayi,don kinzo ne kiyi karatu ba ki tsaya ‘bata lokacin ki akan samari ba,in har ba lectures kike dashi ba karki fita ko da bakin gate ne,bake ba fita ke kad’ai sai in da Amira ko kuma ni” “zan je na duba time table naki naga schedules na lectures naki don kar kimin ‘karya kice kin tafi lectures bayan ba haka bane,na samo miki driver domin kaiki school kawai,he’ll always be available,in time na cin abinci yayi dole ne ki fito mu had’u a dinning aci tare don bazan yarda da barin kanki da yunwa ba,nasan ki da baki…zaki iya cema abba bamu baki abinci saisa nayi ma tufkar hanci,a nan zan tsaya for today saidai ba iyakacin rules d’in ba kenan,a sannu zakisan sauran” Tun da yafara maganar nan Amira da Nabila suka sake baki suna kallonshi,Amira tunani kala-kala ya fara yawo a kanta “Anya ya Sultee ba son yarinyar nan yakeyi ba?irin wannan rules haka?”. Abangaren Nabila kuwa kasa ‘boye mamakin ta tayi,’kwafa tayi ta turo d’ankwalinta gaban goshi irin ture kaga tsiya dinnan,tana karkad’a ‘kafa,cike da rashin kunya tace “Ehh?meh kace??wai kar in kula samari?in ban kulasu ba kai zan kula?so kake nayi bunga a gida ko meh?batun fita yawo kuma wallahi saina fita,haka kawai ka hanani zagaya gari? tab!!ai wallahi sai dai sama da ‘kasa su had’u amma abinda naga dama zanyi”. Cike da mamakin irin rashin kunyanta yake kallonta,ranshi in yayi dubu toh ya ‘baci,tashi tsaye yayi yace “Okay fine,haka kikace ko?ban isa na kapa dokoki agidana kibi ba?that’s good,duk rawan da kanki yakeyin nan i promise u saina saita miki hankali,bana son reni”. Tsaki taja sannan ta tashi da niyyar tafiya d’aki,cafkota yayi,cikin wani loud voice yace “Wa kika ma tsaki?”. Hanee da maman Khalil [11:33pm, 27/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Hanjin cikinta suka kad’a ganin gaba d’aya yafita hayyacinshi,jikinta yana rawa tace “wayyo Allah ya Sultee zaka karya min hannuna,kayi ha’kuri bazan sake ba,wallahi na tuba,zan bi dokokin ka” tsaba azaban yanda ya ri’ke hannunta batasan time da ta fara hawaye ba,wurgata yayi tafad’i ‘kasa,bai yi mata magana ba ya juya ya fita daga parlourn. Yana fita Amira tazo inda Nabila take kuka,d’agota tayi ta taimaka mata ta tafi d’aki sannan ta fara mata nasiha “Nabila,kinga ya Sultee yana da mugun zuciya,kuma zuciyarshi bai da kyau,komai zai iya miki inhar kika kaishi bango,kinga nan ba 9ja bane,babu abba babu kowa sai mu kad’ai,rashin kunya ba naki bane,ajiyeshi a gefe zakiyi ki bishi a hankali kar watarana ya dakaki ko ma fiye da haka a gidannan”,tana hawaye ta rungume Amira tace “Toh anty Amira,zan yi iya ‘ko’kari nah na ganin na kauce ma hanyar da zaisa ya ta’ba lafiya nah”,Amira tayi murmushi tace “Yauwa,ko kefa? kiyi shiru toh”,sun dad’e suna hira sannan Amira ta koma d’akinta. Bayan sati daya Nabila tana taka-tsantsan da Sultee,gaishe shi takeyi kaman babanta,ga ladabi da takeyi kaman ba ita ba,yana cewa tayi abu cikin ‘barin jiki takeyi,wani lokacin har dariya ma abun yake bashi. Suna zaune a dinning suna lunch sai Nabila tace “Ya Sultee ayyah alfarma nake nema”,ba tare da ya kalleta ba yace “Uhum,na meh?”,a sanyaye tace “tunda mukazo ko gate banje ba,gashi jibi zan fara zuwa school kuma inaso naje nayi shopping abubuwan da zan bu’kata”. ‘dagowa yayi ya kalleta sai yaji tausayinta,chan sai yace “Bari mu gama sai muje”,godiya Nabila tashiga kwararowa,Amira kam sai dariya take mata. Sunje wani babban shopping mall,Sultee yace su za’bi abinda sukeso ita da Amira,kowa ya d’auki troller. Nabila taje ta wajen perfumes tana za’ba sai wani saurayi yazo yamata sallama,amsa mishi tayi sannan taci gaba da abinda takeyi. Nan ya mata introducing na kanshi as Yusuf sannan shima d’an 9ja neh amma yana aiki a nan Qatar,bata tanka mishi ba har ya ‘karaci flows nashi wai shi yana sonta. Ro’konshi tafara akan ya rufa mata asiri yatafi kar yayanta yazo ya sameshi amma Yusuf ya’ki,tura troller’nta tayi shima yana tura nashi a ‘kusa da ita. Dum!! Gabanta ya buga ganin Sultee a gabansu,kallonta yayi cike da ‘bacin rai,jikinta har rawa yakeyi don tsoro,Yusuf da baisan dawar garin ba ya mi’ka mishi hannu,Nabila ta fara kame-kame “Ya…Sul…tee…wallahi ban… sanshi ba” fincikarta yayi ya jata ita da troller dinta fuuuu suka bar wajen. Hanee da mama GIMBIYA NAFEESAH [8:36pm, 31/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ®OHW da © Khadijah maman Khalil Har counter sukaje amma still yana ri’ke da hannunta, ana cikin lissafi sai Amira ta iso wajen da nata troller din, ita duk bata lura da hannun Amira da Sultee ya ri’ke ba saidai taga yanayinshi ya chanja ba kamar yanda yake dazun ba. An gama lissafi aka kai musu kayakin cikin boot, janta ya ‘karayi yana sauri itakuma da yake high heel ta saka sai tana neman fad’uwa, Amira tayi saurin tarota tace “Yadai Nabee, kiyi tafiya a hankali mana”, Nabila kaman zatayi kuka tajuyo tana kallon Amira sai tace “Don Allah anty ki bashi ha’kuri,wallahi ba abinda yake tunani bane,ni anan ma na ganshi”, sai sannan neh ta lura Sultee ne ke jan Nabila, duk da bata san kan zancen ba tace “Ya Sultee ko ma meh tayi don…..” juyowa yayi ya d’aga mata hannu yace “Ban sa bakinki ba kuma ban nemi kisa bakinki ba,karki yadda ki had’ani da Allah”, ta bud’e baki zata sake magana amma Nabila ta girgiza mata kai alamun tayi shiru kawai kar ya Sultee ya mai da laifin kanta. Sultee ya cigaba da jan Nabilah har motar, yabud’e ‘kofar baya ya turata ciki, ran Amira sai tafasa yakeyi, tama rasa meh ke mata dad’i tsaba kishin da ke damunta. Ji tayi kaman numfashinta yana neman d’aukewa,karanto addu’o’i ta fara sai da taji sanyi sannan ta fara takawa kaman wanda ‘kwai ya fashewa a ciki, wata shegiyar horn da Sultee ya matsa neh yasa Amira ta firgita, ai tuni ta fara sauri. Ta shiga motar ko kallonta baiyi ba ya tada motarshi. Suna isa gida tun kafin Sultee ya gama parking Nabila ta fara kiciniyar bud’e ‘kofa, kallonta yayi ta rear view mirror yace “Karki kuskura ki fita daga motar nan”, ai bai ma gama maganar ba Nabila tayi unlocking na ‘kofar ta kwasa da gudu,parking yayi cikin zafin nama zuciyarshi sai ‘kara tafasa takeyi. © Hanee da maman K [8:54pm, 31/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Nabila batayi birki a ko ina ba sai d’akinta, tana shiga shikuma lokacin yake shigowa parlour, gwalo ta mishi sannan ta rufe ‘kofar sai tasa key, jingina tayi da jikin ‘kofar tana maida numfashi tana kuma neman tsari daga bala’in Sultee, azuciyarta tana cewa “Tab!! Ni wawiya ce da zan tsaya?, Yanda naga ranshi ya ‘bacin nan komai zai iya min, mtswww, ya takuramin ma wallahi, ni shikenan bazanyi aure ba yakeso ko meh? Dole ne ma na nemi shawara daga wajen Anty Jamcy ko ta whatsapp neh”, nan dai ta cigaba da ‘yan tunane-tunanenta. Sultee ranshi ya kai ‘kololuwar ‘baci,afili yace “Ni kika ma gwalo?wallahi ki bud’e ‘kofar nan tun kafin raina ya gama ‘baci in ba haka ba next had’uwar mu bazaiyi kyau ba”, Nabila tana jinshi sai ta murgud’a baki kaman yana ganinta, d’aga muryanta tayi yanda tasan zai jita “Ba sai mun sake had’uwa bane zaka min iskanci, ai wallahi kayi dama nayi hagu daga yau, mutum sai takuri ko ubana albarka, kai kayi aure nikuma kanaso namutu a gobruwa?”, girgiza kai yayi yana ‘kara jin zafin maganganunta,shi kad’ai yake magana “Ni yarinyar nan zata gaya ma magana?, no problem, in ta shiga hannuna sai na yi maganinta”. Ranshi a ‘bace ya juya fuu yabar wajen sai side nashi. Duk abinda akeyin nan a idon Amira, hawaye ne ya fara zuba daga idanunta, da gudu tashige d’akinta ta fashe da kuka. Kishi neh yake cinta ba kad’an ba, kukan neh kad’ai zai sa zuciyarta tayi sanyi, dama ance kuka rahma neh. Haka gidan ya kasance a ranar kaman gidan zaman makoki, shuru kakeji sai kukan tsuntsaye. Da dare ya shigo musu da kayakinsu, ajiye ma Nabila nata yayi a ‘kofar ta sannan yayi sallama ya shiga d’akin Amira. Ganinta yayi ta kifa kanta a guiwowinta tana kuka akan sallaya, da gani ta idar da sallah neh kukan yaci ‘karfinta. Ko kad’an baiji tausayinta da halin da take ciki ba, cikin ko in kula yace “Ga kayanki, sai da safe”, ya juya kenan ita kuma ta d’ago kanta, har zai fita daga d’akin asanyaye ta ‘kira sunanshi “Ya Sultee….” © Hanee da maman Khalil [9:59pm, 31/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Sultee ya tsaya chak amma bai juyo ba, share ‘kwallar da ya zubo mata tayi sannan tace “Ya Sultee inaso na tambaye ka ne”, juyowa yayi yana kallonta, ya saka hannayenshi duka biyu a cikin aljihu. Amira tace “Ya Sultee fisabilillahi abinda kakeyin nan ya dace? Nabila fah ta girma tazama cikakkiyar budurwa kuma yanzu university take, in ka hanata kula samari yanzu sai yaushe kake so ta kulasu? Shekaru ‘karuwa sukeyi fah ba raguwa ba, Life cycle na mace kad’an ne, Daga takai 25 dai toh wallahi samarukan gudu sukeyi, In ka hanata har sukazo suka watse kam ya zakayi da ita?”. Tuni Sultee ya had’e rai, a fusace yace “What do you mean?, Meh ruwanki?, ‘kanwata ce fah and duk yanda naso tayi dolenta hakan za tayi, And da ki ke maganar inta kai 25 samarin zasu watse, Mata nawa suke kaiwa 30+ amma still suna aure?, karki sake samuna da wannan banzan maganar, it’s none of your business”. Hawaye sharkaf a fuskan Amira, ta d’ago da jajayen idanunta ta d’aurasu a kanshi tace “Wai nikam ya Sultee ni kake aura ko kuma Nabila?, Takuran da kake mata ni bakamin irinshi, kulawan da kake bata, damuwar ka agareta, komai ma ita kake ma amma ni baka min, karka manta fah aure ba wasan yara bane, in sonta kake yi gwara ka aureta kawai, kaga in ka aureta ni na huta, kaima ka huta sannan itama ta huta”. A firgice yake kallonta, a razane yace “Kinsan meh kike fad’a kuwa?, ko ina da ra’ayin auren mata biyu you know definitely zan iya tunda ni ba rago bane kuma ina da kud’in, in zanyi ma sai na rasa wanda zan aura sai wannan fitsararriyar? jinjira wacce bata wuce a raineta ba?, mtswww please karki ‘kara ‘batamin rai da daren nan”. Bai jira meh zatace ba ya fita daga d’akin, Amira ta d’anji sanyi a ranta tunda dai Sultee ya ambaci bayason Nabila don ta mishi ‘karama, nafilfilu ta dinga yi sannan bacci ya kwasheta. ©Hanee da maman Khalil [10:12pm, 31/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ®OHW da ©Khadijah maman Khalil Washegari Nabila bata fito daga d’aki ba har saida taji Sultee yabar gidan, cikin sand’a da alamun rashin gaskiya ta nufi kitchen, nan ta tarar da Amira. Murmushi tayi sannan tace “Good morning anty Amira”, itama murmushin ta mayar mata sai tace “Morning sis,kin tashi lafiya”, Nabila ta d’anyi hamma tace “Wallahi yunwa nakeji,tun jiya da rana rabo na da abinci”, Amira ta d’anyi jim sai tace “Ba kin tsokani ya Sultee ba?, nikam meh kika mishi neh?”, guntun tsaki Nabila tayi sannan tace “Anty Amira mijinkin nan yanada matsala,wai fah don ya ganni da wani shine ya ‘bata rai ya fara ja ma sai kace kayan wanki, ni gaba d’aya ya takurani a gidannan”. Dafata Amira tayi tace “Yi ha’kuri, komai zai wuce in Allah ya yarda, kawai dai ki dinga kiyaye dokokinshi, gashi yanzu yana nemanki ruwa ajallo, hmm ina tsoron ranar da zakuyi karo a cikin gidannan”. Dariya Nabila tayi sannan tace “Ba saina yadda bane zai ganni? Dodging nashi zan dingayi, yana shigowa zan gudu d’aki, yana fita kuma zan sake na zauna a parlour abuna”, murmushi Amira tayi tace “Ke dai baki tsoro, ki bar neman magana dashi ni dai na gayamiki, yanzu ga breakfast naki nan ki d’auka kije kici”, Nabila ta d’auki plate tana d’iba tace “Barin je parlour naci”. Yinin ranar tayishi a sake tunda Sultee yana wajen aiki. Haka dai kwanaki suka ta ja har yanzu su Nabila sunyi mid-semester exams, tun da sukayi rikici bata sake bari sun had’u ba, tana jin alamun ya dawo gida take komawa d’aki, in zata tafi lectures na safe kuma tun 6 take fita a hankali tace driver ya kaita, in ta dawo kuma taga alamun yana side nasu toh bazata shiga ba, saidai ta la’be a ta wajen flowers in taga ya shiga side nashi sai ta ruga dagudu tayi d’akinta. ©Hanee da maman Khalil [11:11pm, 31/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Abinda Nabila bata sani ba shi ne duk ‘boye-‘boye da gudun shi da takeyi duk yana ganinta, da yake yanada time table nata so duk tym da yasan morning lectures take dashi zai zauna a ta wajen window yana le’kenta, har ta gama tafiyar sand’arta zuwa motar, shi kam tun abun yana bashi haushi har yazo yafara bashi dariya, zama yakeyi musamman yayita dariya shi kad’ai. Yau ya kama Thursday kuma yau ne Sultee zai tafi Switzerland don aikin office nashi, ya shirya tsaf sannan ya je ya samu Amira yace “Ni zanyi tafiya, duk abinda zaku bu’kata akwai a store kuma nasa miki kud’i a account haka ma Nabila ita ma nasa mata, karki yadda ki barta ta fita wai don bana gari in har ba school zataje ba, in kin barta ma za a gayamin”. Har ya kai ‘kofa sai ya juyo yace “Ba rakiya?”, murmushin ya’ke tayi sannan ta rakashi har bakin motar wanda driver zai tu’kashi zuwa airport, tana d’aga mishi hannu har motar yabar harabar gidan. Wani ajiyar zuciya ta sauke, a fili tace “Alhamdulillah, zamu huta da bala’i na kwana biyu”. Nabila tadawo daga karatu da yamma tazo ta tarar da wannan good news na tafiyar Sultee, har rawa saida tayi don murna, nan ta zauna take tambayar Amira “Anty, yaushe yace zai dawo? I hope dai ba kwanan nan ba?”, Amira tace “I have no idea don bai gayamin ba and ni kuma ban tambayeshi ba”. Murmushi Nabila tayi sai tace “Allah yasa ya dad’e”. Tana kwance da daddare kawai sai taga text message daga Sultee,yace “Salamu Alaikum, ki ‘kare guje gujenki, yanzu kam kin huta dani for some days amma in na dawo na samu kin tsallake rules nah kema kinsan sauran”, dariya Nabila tayi sosai sannan ta mishi reply “Don Allah karka dawo dawuri”. Sultee na karantawa yayi wani smile kawai ya ajiye wayar. Nabila ta zama free, komai yi takeyi, yau tana mall nan gobe tana chan, ita har ma ta manta da wani Sultee. Bayan kwana shida da tafiyarshi Nabila ta kunna music a parlour sai rawa takeyi, Amira kuma tana zaune tana viewing nata a waya, ihu sukeyi ba kad’an ba. Rawa ya d’au dadi kawai sai ga Sultee da friends nashi su biyu,da yake Nabila ta bama ‘kofa baya so bata san sun shigo ba, Amira kuwa sumar zaune tayi a wajen da take, tana ta ma Nabila nuni da ‘kofa amma ina!! Nabila tayi nisa sai crazy dance takeyi abunta. Sultee sake baki yayi yana kallonta, ba abinda yafi damunshi ma kaman wai ga frnds nashi har biyu a tsaye suna kallonta tana rawa da black three-quarter tare da white vest. Amira ganin kallon da Sultee ke watsa mata yasa ba shiri ta ruga d’aki dagudu, Nabila ta fara kiranta “Anty, ban gama rawar ba fah, ya kika tafi”. Amira bata juyo ba balle ta tanka mata, gyaran muryan da taji ne yasa ta juyawa. Zaro ido tayi ta dafe ‘kirji ta tsala ihu, ihu takeyi kaman mahaukaciya ganin Sultee a tsaye ranshi a dagule, fuskar nan ba alamun sassautawa. Cafkota yayi ya wanka mata mari yace cikin d’aga murya “Wani irin iskanci neh wannan? An gayamiki nan gidan ‘yan giya ne da zaki kunna wa’ka kina rawa sai kace arniya? Wannan dabi’ar kuma daga ina?”. GIMBIYA NAFEESAH [3:13pm, 02/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Tana ihu tana kuka ta fara magana “Wayyo ya Sultee kayi ha’kuri”, tsaki yaja yace “Wallahi in baki bar cikamin kunne da ihu ba sai na pasa bakin, ansa nake jira kibani ba ro’ko ba”, cikin kuka tace “Toh ka sake min kai na mana, akwai zafi”. Daya daga cikin abokanshi da sukazo ne yazo ya dafashi yace “Kayi ha’kuri ka saketa, bai kamata ka d’aga hannu ka mari mace ba, sam bai dace ba, ya kamata ka dinga controlling temper d’inka kar watarana ya saka da na sani”, ran Sultee sai tafarfasa yakeyi amma haka yayi ‘karfin halin sake gashin, tureta yayi har ta buga kanta a gini, yana huci yace “Bamu ‘kare magana ba, anjuma ki same ni a parlour”. Tana kuka tana matsa wajen da ta gara da bango bata tankamishi ba ta juya tayi hanyar d’aki, nan ya sake ‘kuluwa kuma, cike da masifa yace “Ba ki ji me nace bane?”, cikin murya mai nuna alamun taci kuka tace “Na…ji”. Kuka neh ya kusa ‘kwace mata, dagudu tayi d’aki ta fad’a kan gado tana cigaba da kuka, abun tausayi. A parlour kuwa friends nashi Abdul da Ahmad neh sukata bashi ha’kura tare da nuna mishi rashin dacewar marin da yayi ma Nabila, Abdul ya ‘kara da cewa “Duk da laifi tayi, kamata yayi ace ka zaunar da ita ka mata nasiha bawai duka ba, ta girme duka ai, don Allah ka gyara”, a sanyaye yace musu “Sorry dan Allah, I couldn’t control myself ne”, guntun tsaki Abdul yayi sannan yace “Ita ya kamata ka bama ha’kuri bamu ba, ni ka ‘bata min rai ma, kasa crush na kuka a banza”. ©Hanee da maman Khalil [3:27pm, 02/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil A firgice Sultee ya d’ago ya kalleshi, cikin wani yanayi yace “Whatttt??!!?!, an gayama ‘kanwata kaman ko wace mace ne?, bama haka ba, tayi ‘karama da kula samari”, dariya Abdul yayi ganin yanda Sultee yayi responding, sai da yayi mai isarshi sannan yace “Ko baka bani go ahead ba I promise you sai na bi ta bayan idonka mun daidaita da ita”, “mtswwww, kai d’an iska neh wallahi, ni kar ka sake ‘bata min rai, barin shiga na kira madam d’in sai ku gaisa”, sannan ya mi’ke ya nufi d’akinta. Tun d’aga ‘kofa yake jin kukan Nabila na tashi amma sai ya fuske kawai yashiga d’akin Amira, zaune take a kan gado kaman mara gaskiya sannan tana tsorace. Taka wa yayi zuwa cikin d’akin, d’agowa tayi ta kalleshi sannan ta sunkuyar da kanta, a hankali tace “Ina yini? Don Allah kayi ha’kuri, baza…..”, girgiza kai kawai yayi sannan yace “Ban nemi wani explanation daga wajenki ba, duk da kema kina da naki laifin tun da kin kasa aiwatar da abinda nace, it’s okay by me, nadawo ai, yanzu ki tashi friends nah sunaso ku gaisa”. Bai jira meh zata ce ba yafita daga d’akin, mi’kewa Amira tayi tabi bayanshi zuwa parlourn. Zama tayi akan kujera sannan suka gaisa da friends nashin, Ahmad sai ‘kare mata kallo yakeyi da yake riga da skirt neh tasaka kuma sun kama jikinta. (Don Allah mata a kula, in abokin miji yazo kuma zaki fita ku gaisa toh yazama dole ki saka hijabi a jikinki, haramun neh yaga jikinki, ko baida niyyan kallonki toh fah shaidan yana iya rinjiyarsa har ya fara tunanin wani abu daban, Allah yasa agyara). Sun d’anyi barkwanci sannan ta tashi ta d’auko musu drinks suka sha, ta ma kasa had’a ido da Sultee, zaman da tayi a parlourn ma ‘karfin hali neh kawai da kuma gudun kar su gane yanda zamansun yake. ©Hanee da maman Khalil [4:34pm, 02/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Sun d’an ta’ba hira kadan sannan suka mata sallama, Abdul yace “Madam mungode fah, ki kular min da ‘yar waje na”, murmushi Amira tayi sannan tace “Zan kula ma da ita In Sha Allahu”, kasake Sultee ya tsaya yana kallonsu, cike da ‘kosawa yace “Nikam muje na rakaku, nagaji inaso na huta”. Dariya dukkansu suka yi banda Sultee da ya wani had’e rai. Suna fita Amira tayi d’akin Nabila, tayita lallashinta da kyar dai tayi shiru sannan Amira taje fridge ta d’auko Ice ta saka a ‘karamin towel tana matsa ma Nabila goshinta da ya kumbura. Sai wash wash Nabila take tayi, daga baya suka je kitchen tare sukayi girki sannan kowa ya tafi d’akinshi. Sultee ne zaune a parlournshi da daddare yana zaune a kan kujera yana jujjuya tumbler da ke hannunshi, amma a zahirin gaskiya hankalinshi ba akan tumbler din yake ba. Tunani yakeyi ko wani hali Nabila take ciki yanzu, yayi nadamar marinta har cikin ranshi, da yaga tunanin ba mafita zai samo mishi ba sai kawai ya d’auki wayarshi ya ‘kira Nabila, lokacin ita kuma tana kwance a d’aki tana chatting kuma ba abinda tafi tsana kaman a kirata in tana chatting, tsaki taja afili tace “Ko meh mugun nan yake nema a wajena oho”, batayi picking ba har ya tsinke. Ya kirata yakai sau biyar amma batayi picking ba, a na shidan neh ta d’auka tana mai jin takaicin katse mata chatting da yayi. Batayi magana ba, shima kuma baiyi ba, sun dad’e a haka sai chan Sultee ya bud’e bakinshi da kyar yace “Where are you?”, cike da mamakin jin baiyi masifa ba tace a ta’kaice “My room”, ya d’anyi shiru sannan yace “Ba nace kizo ki sameni a parlour ba?”, ta’be baki tayi sannan tace “Na manta neh kuma ni kaina yana ciwo”. ©Hanee da maman Khalil [4:54pm, 02/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Ajiyar zuciya yayi sannan yace “So bazaki zo din ba kenan ko?”, Nabila tace “Bazan iya ba gaskiya”, baice komai ba ya katse wayar. Nabila tayi wani dariya, a fili tace “Zai maida ni jaka, inje daga ni sai shi achan ya jibgeni ba mai ‘kwata na”. Cigaba da chatting nata tayi hankali kwance, nan take labarta ma Anty jamcy wacce take kaman sistanta amma abun mamaki a groupchat suka had’u har suka saba, ta gayamata yanda sukayi da Sultee yau, anty Jamcy ta ‘kara bata shawarwari masu kyaun gaske. Ummitah neh ta tura mata wani comedy video, Nabila dariya takeyi har da hawaye, videon ya mugun bata dariya, jin kaman mutum a tsaye a kanta yasa ta d’ago da sauri. Wa zata gani?? Sultee neh. Ba shiri dariyan ya tsaya, tashi zaune tayi tana tsoron kar ya dakata. Zama yayi a kujeran da ke cikin bedroom din yana fuskantarta, a hankali ya soma magana “Dama ‘karya kikamin da kikace kanki yana ciwo?”, nan ne ta tuna da ta mishi ‘karyan kanta yana ciwo gashi yazo ya sameta garau sai dariya takeyi, murya na rawa tace “Eh, A’a, yana ciwo, nasha magani shine yatafi”, kallonta yayi irin kin rainamin wayon nan, murmushi yayi yace “Ki chanja ‘karyar, wannan baiyi ba, ko minti talatin baiyi ba kice ya tafi?”. Ta wani dafa kanta kaman tana jin ciwo sai tace “Kaga ya dawo ba?, inaga bacci yakeso, sai da safe”, kwanciya tayi a kan gadon, tana faman jan bargo yace “Ciwon kan naki ma mai ra’ayi ne, tunda ya iya barinki ki ‘bare baki kina dariya ai sai ya jira na gama maganar da ya kawoni”. Ahankali ta mi’ke zaune tace “Yi ha’kuri ya Sultee, kaga wallahi dazun kamin ka dawon nan neh kawai na kunna wa’ka, tunda ka tafi ko gate bana fita sai in skul zanje kuma ko……”. ©Hanee da maman Khalil [5:32pm, 02/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Hannunshi yasa a baki alamun tayi shiru, ai kuwa ta kama bakinta gum. Murmushi yayi yace “Hmmm, duk abinda kikayi da bananan nasani duk da bakisan waya gayamin ba”, ras! gabanta ya fad’i, a zuciyanta tace “Nashiga uku, anda wani munafukin ne ya gayamishi, ko da yake ina ganin driver neh ko gate man don su kad’ai ne zasu iya gayamishi tunda nasan Anty Amira kam bazata fad’a mishi ba”. Gudun kar ya ramfota yasa ta wayance tace “Amma mutane basu tsoron Allah, har da ‘kullamin sharri, Allah zai sakamin”. Kallonta ya tsaya yi cike da mamakin denying da tayi amma sai ya fuske yace “Ni ba wannan bane ma yasa nace kizo”, ya d’an yi jim sai yace “I’m really sorry about today, na mareki ba tare da nasani ba don raina ne yayi mugun ‘baci”, mamaki neh ya cika Nabila tana tunani “Anya ya Sultee lafiyarshi lau?, wai ni yau yake bama ha’kuri?” wani zuciyarta kuwa dad’i neh acike, ganin taji mamaki yasa yayi murmushi yace “Ki bar mamaki, kyaun d’an Adam daman in yayi kuskure toh ya nemi gafara, ko da kuwa ma wanda ya girma neh”. Murmushi tayi wanda bata san lokacin da ya fito ba, ga hawayen farinciki da ya zubo mata tayi saurin sharewa, cike da farin ciki tace “Ba komai ya Sultee, ni har ga Allah ban ri’keka ba, nasan duk abinda kayimin ni na jawo da na kauce ma umurninka, I’m so sorry, In Sha Allahu bazan sake ba”. Tashi tsaye yayi yamata wani smile sannan yace “Ba komai, sai da safe”, tanata murmushi tace “Allah ya tashemu”, har ya kai ‘kofa sannan yace “Ameen”. Yana fita ta kira Saleem ta gayamishi akan yau kam ta shirya da Sultee, shima d’in yaji dad’i don Nabila ta gayamishi duk takurata da yakeyi, sun dad’e suna hiransu sannan sukayi sallama. Da safe Amira taji mamaki ganin Nabila ta watsake sai fara’a takeyi kaman ba ita bane take kuka jiya tana cewa ta ha’kura da karatun zata koma 9ja. Bata ‘kara mamaki ba saida taga Sultee ma yafito yanata murmushi fuskar shin nan ya ‘kara kyau, Nabila ta gaisheshi ya amsa fuska asake har yana tsokanarta, abun dai gwanin sha’awa sunata hira har suka kammala breakfast sannan yace “Ni na tafi office, kaya na yana parlour ki bama driver ya kaimin laundry”, Amira ta amsa a sanyaye “Toh”. Su Nabila yau har da rakiya tayi mishi, da Amira taga haka sai ta ‘kara shiga duhu, gashi da ta tambayi Nabila sai tace mata “Kawai mun shirya ne”, bata yarda ba don tasan da wani abu a ‘kasa amma dai taja bakinta tayi shiru ta kama hanyar d’akin Sultee. Ta d’auki kayan ta juya zata fita sai idonta ya sauka akan wani takarda mai d’an girma, har ta share sai kuma wani abu yace mata ta duba taga mene aciki. Ajiye kayan tayi taje ta d’auki takardan sai ta zauna ta fara bud’ewa, first page taga anyi rubutu da capital letters “MY DIARY, MY BOOK OF SECRET THOUGHTS”, da sauri ta ajiye don tasan ba kyau le’ken asirin wani amma kuma kaman an mitsileta sai ta sake d’auka. Abun da tagani neh ya mugun tsorata ta, kuka ne ya kubce mata, tana dana sanin bud’ewar da tayi, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un ta fara karantowa, third page yafi komai d’aga mata hankali, da kyar ta karanta sannan ta bud’e next page, ganin in ta cigaba da karantawa zuciyarta zata iya bugawa yasa ta ajiye. Kuka takeyi kaman an aiko mata da sa’kon mutuwa. Anty Jamcy mun gaisheki sosai, Allah yabarmin ke. Amrah Allah ya ‘kara basira my dear, Allah yabar zumunci. Ummitah me luv u wujiga wujiga…. Sisi Faty Axland ke ta daban ce, Allah ya ‘kara soyayya tsakaninki da Lamido, Rabi’atu S K/mashi na jinjina miki sosai. Dukkanku masu son novel nan mungode kuma muna gaisheku, ku cigaba da ha’kuri damu akan rashin typing kullum, we’re both busy saisa but zamuyi ‘ko’karin kammalawa dawuri. ©Hanee da maman Khalil SHARE THIS: Twitter Facebook Google LIKE THIS: Like Be the first to like this.  RELATED GIMBIYA NAFEESAH GIMBIYA NAFEESAH GIMBIYA NAFEESAH FEBRUARY 3, 2016 ⁄ Advertisements GIMBIYA NAFEESAH [3:32pm, 06/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil 1st page ga abinda ke ciki “Abba ya kirani yace min nadawo gida yasamo min mata, duk da ba so nake yi ba amma sanin ladan yi ma iyaye biyayya yasa na amince”, 2nd page ya rubuta NABILAH, a ‘kasa kuma ya rubuta “It was love at first sight, ban ta’ba jin abu ya shiga min rai farat daya ba sai da na had’u da ita, she is loquacious, Ya Allah!! Kabani ikon aurenta”, 3rd page kuma “Nayi iya ‘ko’kari na na zuga abba har ya yarda Nabee zata zo Qatar tayi makaranta, nayi hakan ne don ina tsoron taje wani waje ta fara soyayya da wani, kuma na d’au ma kaina al’kawarin bazan ta’ba kusantar Amira ba har sai na auri Nabila”. ‘karfin hali Amira tayi ta bud’e next page din, ga abinda ke ciki “Ya Allah ka yafemin, nasan ina cutar Amira duk da bata ta’ba nunamin ba, watarana nasan zata iya tunani aranta ko banda lafiya ne saisa ban ta’ba nemanta ba, the truth is banaso na cuceta ne tunda nasan ba sonta nakeyi ba but ina matu’kar tausaya mata da take ha’kurin zama dani”. Tana gama page nan ta rufe takardar ta ajiye, kuka takeyi sosai, wannan shine son maso wani, azuciyarta tace “Ohh Allah!! Kabani ikon cinye jarabawar nan”, zuciyarta tafasa yakeyi ba kad’an ba, cikin zafin kishi ta kama hanyar fita daga parlourn, ta ma manta d’aukan kayan wanki ne ya kawota d’akin Sultee. Har ta kai ‘kofa sai kuma ta tsaya cak, ahankali ta fara karanta “Allahumma ajirni fi musibati wakhlifni khairan minha”, bayan ‘yan mintuna sai taji zuciyarta tayi sanyi. Gode ma Allah ta fara yi da ya halitto ta a musulma, dama ance wanda ya ri’ke Allah baya ta’bewa, gashi addu’an da tayi ya sau’ka’ka mata duk wani ‘bacin rai da takeji. Komawa d’akin tayi ta fito da kayan wankin sannan ta ‘kira driver yazo ya kai wajen laundry. ©Hanee da maman Khalil [3:46pm, 06/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Tana shiga side nata ta samu Nabila ta gama shirin tafiya school, fuskar nan d’auke da murmushi tace “Anty Amira na tafi school, bari naje driver ya kaini”, ‘karfin hali Amira tayi ta ‘kwa’kulo murmushin dole sai tace “Amma fah driver ya tafi kai kayan ya Sultee laundry, sai dai in zaki jirashi ko kuma ki tari taxi”, ba tare da damuwa ba Nabila tace “Ayyah ba komai, da ba don zanyi latti ba da na jirashi amma ina sauri, barin tafi kawai”. Asanyaye Amira tace “Okay, Allah ya bada sa’a”, Nabila ta amsa “Ameen” sannan ta kama hanya sai bakin gate. Tafita tana tafiya a hankali tanata Allah yasa ta samu taxi da wuri, in ta d’anyi tafiya kad’an sai ta duba agogon hannunta. Tsaki taja afili sannan tace “Da nasan bazan samu taxi ba da na zauna jiran driver wallahi”, ta tsaya tana ‘yan dube-dube sai wani motar da gani sabuwa ce yazo ya tsaya a gabanta, cike da takaici ta d’anyi gaba da motar kad’an, nan mai motar ya sake binta yana danna horn. Gashi motar tint ne so ba halin taga wayene aciki, sau’kar da glass din motar akayi aka ‘kwala mata kira “Nabila!!!”, a d’an tsorace ta juya tana kallon motar, ita tunaninta d’aya “Ni ba ‘yar gari ba balle asan sunana, ba wanda ma nasani a garin nan tunda ba inda nake zuwa daga gida sai school, toh wayene wannan kenan?”. Sake kiran sunanta akayi amma ta’ki zuwa, tana tsaye kaman ba ita ake kira ba. Mai motar ne da yaga batada niyan zuwa sai ya fito, jin an bud’e motar yasa Nabila juyowa. 4 eyes sukayi dashi, cike da mamaki tace “laaa!! Ya Sultee, ai bansan kai bane, kayi ha’kuri don Allah”. ©Hanee da maman Khalil [9:04pm, 06/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Murmushi yayi sannan ya had’e fuska yace “Zo nan”, sai ya koma cikin motar ya rufe. Ahankali ta isa wajen motar ta bude, wani sanyi ne had’e da ‘kamshi ya ziyarce ta, tada motar yayi suka bar wajen, makaranta ya wuce da ita sannan yayi parking a daidai lecture hall da zata shiga, ahankali ya juyo sai yace “Ban hanaki tsayuwa a waje ba? Mesa driver bai kawoki school din ba?”, Nabila ta amsa “Anty Amira tace ya kai kayanka laundry ne kuma bai dawo ba, in har zan jirashi zanyi latti”, ajiyar zuciya yayi sai yace “Muga wayarki”, mi’ka mishi tayi, nan ya hau danne-danne, chan sai ya ajiye shi a kan cinyarshi sai ya ce “Me kike jira?, ki tafi mana”. A rikice ta ke kallonshi sannan tace “Bangane ba, wayana nake jira ka bani”, wani kallo ya watsa mata sai yace “Nayi seizing, zan kawo miki sabo anjuma”, zata sake magana ya d’aga mata hannu yace “Don’t say anything, ba na son musu kema kin sani”, rai ‘bace ta bud’e ‘kofar ta fita. Sultee kuwa daga school nasu Nabila wajen siyan waya ya wuce, samsung galaxy edge ya sayamata sannan ya koma office. Abangaren Amira kuwa Nabila tana fita ta shige d’akinta ta zauna tana tunano abubuwan da ta karanta acikin 1-4 pages na diary d’in Sultee. A zuciyarta take magana “Amma fah kamar yasan me nake tunani, wallahi ni ina tsammanin lafiyarshi ba ‘kalau ba, ba namijin da za a aura mishi mata har tsawon wata hudu amma ba abinda ya shiga tsakaninsu, kai ko kallona ma fah bayayi mai kyau”. Chan sai ta tashi ta tsaya agaban mirror tana ‘kare ma kanta kallo, afili tace “Nafi Nabila kyau, diri, haske, hanci kawai tafini duk da nima inadashi, menene take dashi da ni bani dashi?”. ©Hanee da maman Khalil [9:19pm, 06/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Amira ta gama hasashenta gaba d’aya amma ba abinda Nabila ta fita dashi, ita ce ma ta ba ma Nabila tazara ba kad’an ba wajen fagen kyau. Sultee ne zaune a office nashi da wayar Nabila a hannunshi. Ranshi ‘bace yake karanta messages da suke exchanging ita da Saleem, tunani yakeyi “Allah yasa yaran nan ba soyayya sukeyi ba, Saleem is my only brother, zan iya ha’kura don shi”, chan kuma sai ya girgiza kai, wata zuciyar tace mishi “Ina!!! Soyayyar gaskiya fa kake mata, baza ka iya ha’kura da ita ba”. Bincike ya cigaba da yi har lokacin tashinshi yayi, ya d’auki phones nashi ya kulle office din ya sallami friends nashi da ke wajen sai ya nufi gida. Yana shiga gida lokacin driver ya sauke Nabila, har zata wuce ta’ki gaisheshi sai ya kirata, tana tuttura baki ta isa bakin motarshi tace “Gani”, bai amsa mata ba ya mi’ko mata wayar da ya sayamata. Kar’ba tayi nan take ta nemi haushin shi da take ji ta rasa, ihun dad’i tayi tana tsalle kaman zata rungumeshi ta fara kwararo godiya, bai ce mata komai ba illa murmushi da yayi ya kama hanya sai d’akinshi. Dagudu ta shiga side nasu ta fad’a kujeran da ke kusa da Amira, cike da murna Nabila tace “Anty kalli sabon wayana”, ta mi’ka mata wayar. Amira ta kalleta tace “Waiwai!! Sabuwar fitowa ce fah wannan, wa ya sayamiki haka?, ko dai mun kusa shan biki ne?” ta ‘karasa maganar tana dariya. Murmushi Nabila tayi sai tace “Haba aure, ni fah bazan yi aure ba sai naga ‘karshen biro”. Dariya Amira tayi tace “Kai Nabila, yanzu waya baki?”, tana murmushi tace “Ya Sultee ne ya kwace nawa dazu da ya kaini school, yanzu kuma muka had’u a parking space shine ya bani wannan”. A firgice Amira tace “Wani ya Sultee??, shi ya kaiki makaranta?, me ke tsakaninku?”, duk wad’annan tambayoyin kusan lokaci d’aya tayi su, bata ma san time da suka fito ba. ©Hanee da maman Khalil [10:12pm, 06/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil - Nabila baki bud’e take kallonta, da ‘kyar ta iya furta “A’uzubillahi, haba anty Amira, zargi na kikeyi ne? Wallahi ba abinda ke tsakaninmu illa zumunci da kuma dauka na da yayi a matsayin ‘kanwarshi nima kuwa a matsayin yaya na d’aukeshi, bai kamata ki yanke hukunci haka ba”, sai sannan Amira ta gane tayi su’bucewar baki, ‘ko’karin saita kanta tayi sannan ta kama hannun Nabila tace “I’m so sorry sis, ba wai ina zarginki bane, nasan ba abinda ke tsakaninku, amma ko akwai ma ni ban damu ba, dama shi mijin mace hud’u ne, sannan in har Allah ya ‘kaddara abu zai faru toh fah dole ne sai ya faru, amma kiyi ha’kuri in har na ‘bata miki rai”. Hawaye Nabila ta share sannan tace “Kiyi ha’kuri, in har baki yadda ba wallahi zan maida mishi da wayarshi ince nagode”, tana gama fad’in haka ta d’auki wayar tayi hanyar ‘kofar parlour. Da sauri Amira ta tsaidata tace “Noo karki mayar mishi, zai ga kaman kin raina ne, kiyi ha’kuri ki ri’ke wayar, na tayaki murna sosai wallahi, akashe lafiya”, tayi wani fake murmushi. Nabila ta juyo tana kallon Amira tace “ba kiyi fushi ba?”, Amira ta girgiza kai tace “Not at all sis, ba komai”. Murmushi Nabila tayi sai tace “Thank you, barin je nasa a chaji”, sai ta d’auki hand bag nata da ke kan kujera ta wuce d’akinta. Da Sultee yazo cin abinci sam bai nuna wani abu ba, sama sama dai yana hira da Nabila, Amira kuwa saidai tayi murmushi ta bisu da ido, jifa-jifa take sa musu baki. Kwanaki suna tafiya, rayuwa yana ‘karewa, abu buwa dewa suna faruwa masu dad’i da mara dad’i, tsakanin Nabila da Sultee kuwa sun sha’ku sosai, kullum Amira addu’a takeyi akan Allah ya rage mata zafin kishin da takeji akan Sultee, cikin ikon Allah kuwa ahankali ta bar damuwa, gaba d’aya ta bar jin wani abu in taga Sultee da Nabila suna zaune suna hira sunata dariya. Saleem da Nabila kuwa kullum suna waya, yana jira ne ma tazo hutu don ya amayar mata da abinda ke zuciyarshi. Nabila ta gama exams nata, ya Sultee ma yasamu hutu, duk suka shirya don zuwa hutu 9ja, Nabila sai d’oki takeyi zata je gida don rabonta da gida shekara d’aya kenan. Yau ya kama su Sultee zasu diro 9ja, tsaraba dewa Nabila ta siya ma ‘yan uwa da abokan arziki, ni da maman K ma mun siyo tsaraba ma duk masu son novel dinnan, kowa yazo ya kar’ba… lol. Da dare misalin 7:30pm jirgi ya sau’ka a airport din garin Kaduna. Motoci aka turo aka d’aukesu daga airport, Saleem yana ganin Nabila da gudu yaje ya rungume ta kaman za a kwace mishi ita, Sultee ya d’auko trolley’nshi ya fara neman Nabila, chan ya hangota rungume a jikin Saleem, nan take zuciyarshi ya shiga bugawa, bai ma jira Amira ba ya kama hanya sai wajensu Nabila. Yana isa ya fincike ta daga jikin Saleem, suna had’a ido dashi ta fara kame- kame “Ya Sultee kaga ya Saleem ashe tun dazu suka iso”, tsaki yaja sannan yace “Allah ya nunamin ranar da zaki san kin girma, wai ke bakisan kin balaga bane ko meh? Kina barin namijin da ba muharraminki ba ya rungumeki sai kace mara hankali, baki san zunubi kike kwasa ba ko?”, idanun Nabila ya ciko da ‘kwalla tace “Ya Sultee kaima kasan bana rungume maza wallahi, yanzun ma don ya Saleem ne kuma ina murnar ganinshi saisa”. Harararta yayi sai yace “Sai meh don kina murnar ganinshi? Sai akace idonki yarufe ki manta da haram da halal? Batun kina cewa don Saleem ne kuma, don yana matsayin yayanki ba shi ne ya sa ya zama yayanki ba, biological brother shi ne kad’ai aka halatta ku had’a jiki, Saleem fah ba komai naki bane karki manta”. Jinjina kai Nabila tayi tana nadamar abinda ta aikata, sannan tace “In Sha Allahu bazan sake ba”, murmushi yayi yace “Good girl”. Saleem da ranshi yayi matu’kar ‘baci yace “In tayi aure zanga iyakacin ikonka akanta”, maida dubanshi zuwa wajen Saleem yayi sai yace “hmmm, daman aure kam dole tayi ai”. Kallonta Saleem yayi sannan ya kalli Sultee saiyace “Aure kam kwanan nan ne ma don ni zata aura da yardar Allah, dama jira nakeyi ta dawo sai nayima mai martaba magana”. Daidai lokacin da Amira kuwa ta iso wajen da murmushi a fuskarta, cikin wani lion voice Sultee yace “Whattttt?!!!, Aure?, Nabila?, Da kai??” Saleem ya jinjina kai yace “Ofcourse, ni zan aureta, dama na dad’e ina DAKON SO”(Book by kausar). ©Hanee da maman Khalil [11:05pm, 06/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil - Wani wawan tsaki Sultee yayi, bai ta’ba shiga tashin hankali irin wannan ba, da kyar yayi ‘ko’karin controlling na temper dinshi. Bai ce komai ba ya ja trolley’nshi ya kama hannun Nabila sai motar, bai ma jira securities sun bud’e mishi ba ya saka hannunshi ya bud’e ya turata aciki sannan shima yashiga. Yana rufe ‘kofa Saleem da Amira suna isowa wajen, nan take Sultee yace ma driver ya tada motar su tafi gida, ba musu kuwa driver ya cika aiki. Trolleys d’insu ma dogaraye ne suka saka su a sauran motocin sannan suka bi bayansu. Da suka isa gida mai martaba yaji mamaki da yaga Nabila da Sultee a motar d’aya, amma da yaga su Amira sun iso kuma ba wani matsala sai kawai ya share akan daga baya zai nemi ‘karin bayani wajen Sultan. Duk anyi murna, Nabila harda hawayenta yau ta dawo gida, baba Rabi murna kaman ta zuba ruwa a ‘kasa tasha, dukkansu hudun ba wanda ya bari aka gane me ya faru a airport. Anci ansha anyi hira sannan kowa ya nufi d’aki don hutawa. Bayan Nabila ta rarraba ma kowa tsarabarshi sai ta je ta watsa ruwa, ta gama komai sai tayi sallolinta tabi lafiyar gado. Washegari bayan anyi breakfast sai baba Rabi ta jata suka koma d’aki, nan Nabila ta hau bata labarin school nasu da friends nata na chan, har da wayar da Sultee ya siya mata. Baba Rabi taji dad’i da taji Sultee da Nabila sun shirya, sun dad’e suna hira sai tace “Amma meke tsakaninki da Yarima?”, murmushi Nabila tayi sannan tace “Bakomai fah umma, me kika gani?”. Ajiyar zuciya baba Rabi tayi sannan tace “ke dashi a motar d’aya kuka dawo sannan matarshi tana motar daban, ana cin abinci ma ina lura dashi sosai, duk motsinki akan idonshi ne, inaga yama manta Amira ce matarshi ba ke ba, ya ta’ba gayamiki yana sonki ko makamancin haka?”, zaro ido Nabila tayi jin inda zancen baba Rabi ya dosa, a rikice ta ce “A’a wallahi, ni fah ba komai, kawai dai inaga baki lura bane, bani yake kallo ba wata’kila”, kallonta baba Rabi tayi sannan tace “Allah ya kyauta”, suka cigaba da hirarsu cike da nishad’i tana ‘kara jaddada ma Nabila akan karta kuskura ta butulce ma su Sultee don su suka mata gata a duniyar nan. Bayan kwana biyu da dawowarsu gaba d’aya Nabila a d’aki take yini, watarana ta zauna tayi tagumi tana tunanin ya Sultee da kuma maganganun baba Rabi na cewar yana sonta, haka zata yita dariya ita kad’ai tace ai wannan yafi ‘karfina, ina ma zai kalleni bayan yanada kamar anty Amira wacce ta fini da komai. Sun huta na sati d’aya sai mai martaba yace su shirya suje garin Hamaz, hakan kuwa akayi, Amira ta dage sai ta tafi da Nabila don tana bama su Ammi da mummy labarinta, da ‘kyar dai Nabila ta yarda zasuje tare. Sun sau’ka Hamaz lafiya lau, murna wajen familyn Amira ba kama hannun yaro, shekara d’aya ba wasa ba. Hauwa har ta gama secondary school yanzu tana jiran admission, Ukasha kuwa yana part 3 ya ‘kara girma yayi kyau abunshi, dama fulani ba dai kyau ba. Bayan maghriba aka zauna sai hira akeyi abun dai gwanin sha’awa, chan sai Amira ta fashe da kuka, duk parlourn sun rikice suka fara tambayarta “Lafiya?, me ya saki kuka?”, Nabila ta taso ta rungumeta tana bubbuga mata bayanta, da kyar dai Amira ta tsagaita kukan da takeyi, cikin muryar kuka tace “I miss her, da tananan da gidanmu ya zama full house, yanzu wayasan ko tana ina? Ko tana shan wahala?”, nan jikin kowa yayi sanyi jin ta ambaci Gimbiya Nafeesah, gaba d’aya parlourn rashin Nafeesah yadawo musu sabo fil, ‘karfin hali kawai sukeyi na ganin basuyi kuka ba amma duk sai da suka zubda hawaye. Nabila ta share hawayenta tace “Anty Amira kiyi ha’kuri, In Sha Allahu tana cikin ‘koshin lafiya, aci gaba da addu’a zata bayyana da yardar Allah”, girgiza kai kawai Amira tayi. Basu wani jima a parlourn ba kowa ya kama hanyar d’akinshi, Sultee ma dai ya musu fatan Allah yasa aganeta. Ana gobe zasu koma Yura Nabila ta fito daga wanka d’aure da towel sai Mummy tashigo d’akin don ta kirata suyi breakfast, turus ta tsaya ganin tabon da ke bayan wuyanta. Cikin hanzari ta nufi Nabila ta d’an ja towel d’in ‘kasa, kuka ta fashe dashi tana rungume da Nabila, Nabila da bata san meke faruwa ba ta hau tambayar me ya faru, Mummy ta kasa magana sai kuka takeyi. Da kyar ta samu tasa kaya sannan mummy tace “Don Allah ki kiramin ‘yan gidan gaba d’aya yanzun nan”, dasauri Nabila ta fita don sanar dasu sa’kon mummy, duk sunji mamaki da sukaga Nabila a birkice, jiki ba ‘kwari tace “Mummy tana kiranku gaba d’aya wai a sameta a d’akin da na sau’ka”, har rige-rigen zuwa d’akin suka shiga yi kowa da abinda yake sa’kawa a ranshi. Ammi ta rungumeta tace “Meh yasaki kuka anty?, in har akan Nafeesah ne In Sha Allahu zamu ganeta in har munada rabon sake ganinta”, nan mummy tafara dube-dube tace “Ina Nabila?, ku kiramin ita, karku barta ta sake barinmu don Allah”, nan aka tura akazo da Nabila. Tazauna a ‘kasa tana jiran ‘karin bayani, rungumeta mummy ta sakeyi sannan ta fashe da wani sabon kuka, acikin kukan take cewa “Yau Allah ya amsa addu’ar mu, wallahi Nafeesah ce wannan, wallahi itace, ga tabon da ke bayanta, Nafeesah nah ne”, ba ita kad’ai ba, dukkansu kuka sukasa in banda Sultee da yake tsaye yana ganin ikon Allah, Amira harda sheshsheka takeyi, awannan ranar sunyi kukan murna ba kad’an ba. Bayan kukan ya tsagaita ne Nabila tace “Noo bani bace Nafeesah, ni fah uwata jakadiya ce sunanta baba Rabi, kuma mu ‘yan Bauchi ne, ba abinda ya had’amu da Yola, kumin bayani, ni fah kaina yana neman fashewa, wallahi ina rikice, umma ce mamana, ni ba ‘yar sarauta bace, ni ba kowa bace illa yarinya talaka mai wadatar zuci har Allah ya kaini matsayin da nake ciki a yanzu”, nan ta fashe da kuka. Atake mai martaba ya ‘kira sarkin Yura ya shaidamishi abinda ke faruwa kuma yace suyi ‘kokarin zuwa da baba Rabi a ranar tunda akwai flight na yamma, sukayi sallama. Mai martaba ya ‘kira Yabi da baba Rabi ya musu bayani kaman yanda Sarkin Hamaz ya mishi, kuka baba Rabi tafara tana cewa “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, shikenan, dama nasan wannan ranar dole yazo”, duk suka bita da kallon tuhuma, Yabi tace “Bamu gane ba, yi mana bayani”, baba Rabi tana kuka ta ‘kara cewa “Tabbas Nabila ba ‘yata bace, labari ne mai tsawo amma muje Hamaz din zan warware muku komai”, tana kaiwa nan ta tashi tana kuka ta tafi had’a kayanta. Ba shiri mai martaba ya kira sarkin Hamaz ya gayamishi ai baba Rabi tace ba ita bace mahaifiyar Nabila. Fashewa da kuka Nabila tayi tana karanto “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”, dukkansu suna so suji ya abin ya kasance, Sultee da yaji abinda baba Rabi tace ba ‘karamin tashin hankali ya shiga ba, dafe kanshi da yaji yana sara mishi yayi, azuciyarshi yana cewa “Me ke shirin faruwa dani?, kar dai ‘kanwar matata uwa d’aya uba d’aya nake DAKON SO?, shikenan aure ya haramta a tsakaninmu?, nashiga uku, ya Allah gani gareka ka fitar dani daga wannan bala’i da na jefa kaina aciki, ina son ‘kanwar matata uwa d’aya uba d’aya acikin rashin sani, kai amma rashin sani YAFI DARE DUHU”. Sorry for the delay, yau dai munyi mai yawa. Sai kun sake jinmu ko gobe ko jibi, duk yanda Allah yayi dai kawai, we love you all, Allah yabar zumunci. ©Hanee da mama GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil - Hakan kuwa akayi, baba Rabi ta had’a kayanta tsaf ta saka a d’an ‘karamin jaka, tana kuka ta nufi parlourn sarki. Nan ta samesu suma sun gama shiri, shiga motar sukayi kowa da abinda yake sa’kawa a ranshi aka kama hanyar airport don sunci sa’a akwai flight na rana. Sun isa Hamaz, Ukasha ne da mai martaba suka je suka tarbesu. Nabila tana ganin baba Rabi dagudu ta rungumeta tanata kuka, baba Rabi ma ‘barkewa tayi da kuka sosai, mai martaba sarkin Hamaz da yaga kukan ba ‘karewa zaiyi ba sai yace “Kuyi ha’kuri, yanzu dai kuci abinci ku huta sai mu zauna muyi magana a nitse”. Nan fah aka bama baba Rabi d’aki ta shiga tayi Sallah aka kawo mata abinci, sam ta kasa cin abincin sabida halin da take ciki, a bangaren sarkin Yura da Yabi kuwa a daddafe suka watsa ruwa suka ci abinci don duk sun ‘kagu suji warwarewar wannan rikitaccen al’amari. Saida sukayi maghriba sannan sarkin Hamaz ya tura a kira kowannensu zuwa parlournshi don tattaunawa. Ba ‘bata lokaci kuwa Sultee, Nafisa, Amirah, Saleem, Ukasha, Hauwa, Yabi da sarkin Yura, sai mummy da ammi duk suka shigo aka zazzauna. Sarkin Yura ne yayi gyaran murya yace “Alhamdulillah yau an gane Nafisah, sai dai al’amarin akwai wani boyayyen abu a ciki wanda duk bamusan ya akayi hakan ya faru ba illa Rabi wacce yanzu zata mana bayanin abinda ta sani”. Nan fah kallo ya koma kan baba Rabi wacce take ta faman share hawaye. Murya a dishe tafara “Kaman yanda kuka sani, sunana Rabi kuma ni ‘yar Azare ce da ke jihar Bauchi, ina da ‘ya d’aya mai suna Nabilah, ita kad’ai Allah ya bani, ina matukar sonta da tausayinta wanda kuma kun san da hakan, tun da nakai ta yaye wajen mama na ban waiwayeta ba sai bayan wata shida don duk lokacin da nace zanje na dubota sai mamana tace min a’a nabari tukunna, banason mata musu sai kawai na bar maganar. Da naje gida d’aukota sai naga sun sha’ku sosai da mamana, hakan yasa na barta a Azare ni nadawo gidan sarki, bayan wata uku uku nake zuwa kuma Alhamdulillah lafiyarta lau, gata kyakkyawa abunta, sai dai duk da haka kullum kewarta nake yi, mijina yarasu lokacin tanada shekaru 2. Ahakan ne watarana lokacin tana da shekaru 4, na shirya da niyar zuwa na dubota ba tare da na sanarwa kowa a gida ba, da murna na na isa Azare, ina shiga d’akin mamana kawai sai naga abinda ya mugun firgita ni, Nabila ce kwance ba lafiya, numfashi ma da kyar take yi, aranar nayi kuka har na rasa me ke min dad’i, da dare nake tambayar mamana mesa bata gayamin Nabila batada lafiya ba, sai tacemin ai bataso ta tayarmin da hankali ne saisa kuma batayi sati da fara ciwon ba, ta ‘kara da cemin ai sunje asibiti ance wai hanjinta ne ya hahhad’u amma za’a koma nan da sati a mata operation. Tun da na isa gida ni nake jinyar ta, watarana na sata a gaba nayita kuka amma sai tacemin “Umma, kiyi ha’kuri ki bar kuka kinji?”, zan rungumeta har muyi bacci ahaka. Ana gobe zamu koma asibiti acikin dare Allah ya kar’bi rayuwarta, gashi na sata a raina sosai, bansan inda nake ba sai bayan kwana biyu. Muka cigaba da zaman makoki ‘yan uwana suna ‘kara ‘karfafamin guiwa har na samu na d’an watstsake, lokacin da Yabi ta kirani akan mesa ban dawo ba sai ban gayamata Nabila ce ta rasu ba, nace mata mamana ne batada lafiya amma dazaran ta warke zan dawo, tayimin Allah ya ‘kara sauki sannan mukayi sallama, kullum saita kirani mun gaisa kuma hakan yamin dad’i sosai. Ranar da ta cika wata d’aya da rasuwa mama na tacemin ya kamata na koma Yura, ba don naso ba haka na tattara kayana na kama hanya. Ahanyar mu ta zuwa ne mun tsaya a wani ‘kauye zamuyi Sallah, da yake mu dewa ne sai naje ta d’an bayan wani bishiya don na za ga, ina isa wajen naga yarinya sa’ar Nabila na ta had’a kai da guiwa tana kuka. Naji tausayinta sosai sai na isa wajenta nace “Yarinya me ya ajiyeki anan?, ki tashi ki tafi gida mana”. Baba Rabi ta ci gaba “Na jima ina mata magana kafin nan ta d’ago tana kallona, na tambayeta ina ne gidansu sai ta ce min cikin maganarta da bai gama fita ba “ni ban sani ba, kawai wata mata tazo ta ajiyeni tace min anjuma mama na zatazo ta tafi dani, kece mamana?”, na d’anyi jim kaman mai nazari sai namata murmushi nace eh, ni ce mamanki. Ta share hawayenta sai ta tambayeni me sunanta, ba tare da wani tunani ba nace Nabila, nan fah ta hau murna har mukayi sallah tare na siya mana abinci ma tare. Zamu shiga motar sai wasu mutane sukazo suna tambaya wai ko munga wata yarinya wacce take nuna alamun ta ‘bata, da yake babbar mota ne sai duk basusan ba da Nabila nashigo ba, masu nemantan har sukazo kaina, d’aya ya sunkuya yana tambayar Nabila ina mamarta, addu’a nafara yi Allah yasa kar tace bani bane. Da mamakina sai naga ta ‘kan’kame hannuna tace “umm umm, ni ga mamana”, murmushi suka mata sai suka ‘kara gaba, ba shiri na sauke wani ajiyar zuciya. Muka koma motar Nabila tana ma’kale da ni, ni ko dad’i ne ya cikani ganin na samu wanda zata zamarmin kaman ‘yata Nabila, nadawo Yura da yake basusan Nabila ta mutu ba sai na gabatar da sabuwar Nabila a matsayin ‘yata”. Shiru baba Rabi tayi tana kuka kad’an kad’an, gaba d’aya wajen mamaki ne ya cikasu, daga masu kuka sai masu hawaye kad’an, baba Rabi ta mai da kallonta wajen mummy sai ta sau’ko daga kan kujerar da take zaune tace “Don Allah kiyi ha’kuri, nasan ban kyauta ba da na ri’ke ‘yarki bayan agabana akazo ana nemanta amma da yake lokacin idona ya rufe akan nasamu gurbin Nabila, ban yi tunanin wani hali zaki shiga ba a matsayin uwa wanda ‘yarta ta ‘bata, wallahi ba da gayya nayi ba, dama na dad’e inama Nabila addu’ar Allah ya bayyana min iyayenta na nemi gafarar su don ni ce silar jinkirta komawarta garesu”, kuka ne yaci ‘karfinta sai tayi shiru, mummy tana hawaye ta taso ta ri’ko baba Rabi sai tace “Na yafe miki, har cikin zuciya na nayafe miki, Allah ya yafe mana baki d’aya”, kuka sukeyi dukkansu, Nabila tana kuka kaman mai neman shid’ewa, Amira ta rungumeta kaman za a ‘kwace musu ita. Bayan koke-koken ya d’an lafa ne sarkin Hamaz ya furzar da iska sai yace “Kinyi laifi babba da har lokacin da akazo nemanta kika’ki nunawa ba ‘yarki bace, wannan baida kyau, duk da nasan alokacin kina cikin zafin rashin ‘yarki”, baba Rabi ta jinjina kai tace “Kuyi ha’kuri, nasan nayi laifi babba kuma ashirye nake da na kar’bi duk hukuncin da zaku min”. Jikin kowa yayi sanyi a parlourn, Nabila ta fashe da wani sabon kuka tace “Haba haba haba umma, bai kamata hakan yafito daga bakinki ba, tun kamin nasan kaina kike kula dani, baki ta’ba nunamin ba kece uwata ba, duk abinda nake bu’kata kina bakin ‘ko’karinki kiga kin bani duk da kema kina da abubuwan yi da kud’in amma haka zaki ha’kura ki hana kanki don ni ki bani, kin bani tarbiya daidai gwargwado wanda ko da a gaban iyaye na neh iyakacin abinda zasumin kenan”, ta tashi ta rungumeta dukkansu biyu suna hawaye. Sarkin Hamaz ya sauke ajiyar zuciya sai yace “Tabbas kin kula min da ‘yata kuma mungode, yanzu abinda nake son na sani shine wayene ya zo har cikin gida ya d’auketa har ya kaita ‘kauye agaba da Bauchi sannan ya mantar da ita duk abinda tasani akan rayuwarta na baya?”. Nan fah kowa ‘kwa’kwalwarshi ta fara chaji, duk tunaninsu sun rasa wayene ya musu hakan tunda dai basu san wani ma’kiyinsu wanda yakeson ganin bayan d’aya daga cikinsu ba. Suna cikin tunanin abun sai wata tsohuwar baiwa tashigo tana share ‘kwalla, duk suka juyo suna kallonta, Ammi ne tayi magana tace “Dudu ya dai?, mesa kika shigo ba ko sallama?”, dudu tasa ihu ta zu’be a ‘kasa tace “Wallahi ni na saceta, wallahi ni ce, duk sharrin shaid’an ne”, afusace Ukasha ya nufeta zai wanketa da mari amma daddy(sarkin Hamaz) yayi saurin ri’keshi, idonshi a rufe ya fara magana “Daddy ka sakeni na daketa, tsohuwar banza tsohuwar wofi, mesa ta sacemin ‘kanwa?, yau sai kin san kin ta’bo ni”, da daddy yaga Ukasha yana neman fita daga hayyacinshi sai yayi magana a hankali “Ka nitsu banason zuciyarkan nan”, a hankali ya koma ya zauna a kan kujera yana bubbuga ‘kafa. Abba(sarkin Yura) ya watsa ma dudu wani shegen kallo yace “Gayamana, mesa kika saceta?, aikoki akayi?, wa ya saki?”, dudu ta tsorata sai zazzare ido takeyi, ba acikin hayyacinta ba ta fara surutu “Shi ne ai ya’ki ya aureni”, cike da mamaki daddy yace “wa?”. Dudu tayi wani dariyan hauka sai tace “Kai mana, nikuma shine na ‘kudiri aniyar sai na saka maka ba’kin cikin da har ka mutu bazaka daina ji ba, da yake na lura duk cikin ‘ya’yanka kafi son Nafisah saisa na kai sunanta wajen boka akan ya mata asiri ta tafi chan uwa duniya kuma ta manta komai akan rayuwarta na da kuma har abada karta dawo, boka ya kar’bi kud’ina yacemin aiki zaiyi kyau amma da sharad’in duk ranar da ta dawo nan har aka gane itace Nafisah toh fah ni fa hauka mun ‘kulla ‘kawance, banyi wata-wata ba nace naji na amince don ban ta’ba tsammanin zaku ganeta ba”. Cikin ‘bacin rai da daddy bai ta’ba shiga ba yatashi ya wanka mata mari lafiyayyu sannan ya fara dukanta yana ball da ita, da ‘kyar Sultee da Saleem suka rirri’keshi suna bashi ha’kuri, sai huci yakeyi kaman zaki, ‘kwala ma dogarin ‘kofa kira yayi, dagudu ya shigo ya rusuna kaman daman jira yakeyi a kirashi, cikin ‘bacin rai daddy yace “Ku dauki wannan tsohuwar banzar ku kullemin ita ku kuma azabtar da ita iya son ranku, banga amfaninta a nan ba, take her out!!!!!”, da sauri dogari ya nufi wajenta har yana neman fad’uwa tsaba sauri, dama dogari da cin zali balle an bashi order, tunkud’eta yayi yace “ke matsiyaciya, tashi ko na buga miki sandar nan na kaiki lahira”, bashiri ta mi’ke amma ko alamun nadama bata nuna ba, sai ma wani murmushin mugunta da tayi ta yi waje dogari yana ‘kara zungurar kanta yana dukanta da dorina. Duk parlourn jimamin abun sukeyi, ammi ta ja girgiza kai cike da takaici tace “Kai amma d’an Adam ba a mishi, ba abinda bamu mata- abinci, sutura, kud’in kashewa, amma tsohuwa da ita maimakon ta koma zuwaga Allah amma ina!! tana ‘kara loda ma kanta wasu zunubbai, Allah ya karemu daga sharrin zuciya”, gaba d’aya aka amsa da “Ameen”. Daddy ya kira Nafeesah (Nabilah) yace “zo ‘yata”, da sauri ta isa wajenshi, ka ma ta yayi ya rungumeta sosai, ita dad’i ne ya cikata yau gata a gaban iyayenta na asali duk da achan baya ma batayi maraicin rashin iyayenta ba tunda Baba Rabi ta zame mata uwa da uba. An yi hira cike da raha kaman ba abinda yafaru, yau gidansu yacika full house, dad’i kam ba za a fad’eta ba, gaba d’aya family sai da sukaji batun ganewar Nafeesah acikin daren nan, Saleem yayi murna sosai don yana ganin ta kwana gidan sau’ki tunda dai ‘kanwar Amira ce, Amira kuma matar Sultee ce. Har wajen biyun dare suna hira, Abba ne ya duba agogo, atake ya mi’ke tsaye yace “Hira yayi dad’i mun manta da time ya tafi, ya kamata a shiga bacci haka ai ko?”, daddy ya duba time yayi murmushi sai yace “Hakane fah, kaga Nafeesah ta dawo mana da farin cikin familynmu”, duk sukasa dariya sannan sukayi sallama da juna. Hauwa, Amira da Nabila a d’aki d’aya suka kwana, abun gwanin sha’awa, basuyi bacci ba sai bayan sunyi asubah. Abangaren Sultee kuwa yana komawa d’aki ya zube a kan gado, tunanin mafita yakeyi har baisan time d’in da hawaye ya soma zubo mishi ba, daren ranar shima dai baiyi bacci ba. Saleem kuwa yasha baccinshi hankalinshi kwance don a ganinshi ya samu Nabila ya gama. Washegari tun da sassafe ba ‘ki masu taya murnar dawowar Nafisah suka fara zuwa, da yamma aka had’a Walima akayi wa’azi sosai mai shiga jiki wanda malamar tayi magana akan son zuciya har ya kai mutum ga hala’ka, kaman yanda yazo a hadisi “Akwai wani ga’ba ajikin mutum in har ya gyaru toh dukkan jiki ya gyaru, in ya ‘baci kuma dukkan jiki ya ‘baci, wannan ga’ba itace ZUCIYA”, ta kuma yi addu’ar Allah ya karemu daga son zuciyar da zaisa mu sa’ba ma Allah, taro ya watse wajen maghriba, aranar kuma Abba da Yabi suka bi jirgin dare suka koma garin Yura, baba Rabi taso ta bisu amma Nafisah ta sa kuka wai ita abar ummarta anan, nan take Daddy ya ro’ki Abba akan ya bar baba Rabi tadawo Hamaz da zama tunda Nafisah tanaso, a wajen kuwa Abba ya amince. Baba Rabi tayi murna ta gode ma Allah da yasa ta had’u da mutane masu halacci. Bayan kwana uku Sultee ne kwance a d’akinshi, tunani yakeyi har baisan a fili yake magana ba “Ya Allah ka bani mafita, inason Nafisah sosai, in har ban sameta ba zan iya rasa rayuwa ta”, ya fashe da kuka kaman ‘karamin yaro “Gashi uwa d’aya uba d’aya suke da Amira, nasan na rasa Nafisah har abada”. Amira da tashigo d’akin don tanaso suyi magana akan diary da tagani sai ta tsaya tana sauraronshi, tunani ta shiga yi azuciyarta “Nasan ko da Nafisa bata son Sultee nan gaba zata soshi tunda dai shi yana sonta ahankali zai koya mata sonshi, kums yana da qualities da kowace mace zataso ta samu a matsayin miji”, chan sai tayi murmushi ta ‘karasa kan kujera ta zauna, har lokacin Sultee bai ma san ta shigo ba, ahankali ta kira sunanshi “Ya Sultee, Ya Sultee”, dasauri ya juyo, ganin ita ne yasa ya wayance ya share hawayen dake fuskarshi sai yace “Yaushe kika shigo?”, dariya tayi tace “Tun d’azu amma kai baka sani ba don ka tsunduma acikin kogin son Nafisah”. Kallonta yayi cike da mamakin abinda yafito daga bakinta, murmushi tayi tace “Don’t be surprised, nasan komai fah”, nan ta bashi labarin diary’nshi da ta karanta pages 1-4 da kuma abubuwan da taji yana fad’a yanzu sai ta ‘kara da cewa “Ya Sultee, ni mai iya giving up abinda nake so ne akanka tunda dai ita kakeso bazanso na kasance katangar da ya hanaka aurenta ba, kuma kaga bazanso rabo ya kasheni ba”, ta ‘karasar da maganar tana dariya, sai ta ‘kara “akwai shawarar da zan bayar inhar mukayi hakan toh i guarantee you inhar Nafisah neh ka aureta ka gama, ajiyar zuciya Sultee yayi sannan yayi murmushin ciwo yace “Hmmm, nasan kina fad’ar haka ne don ki kwantar min da hankali amma there’s no way da hakan zai faru”. Kallonshi tayi tace “Just listen to me”. Ku biyomu don jin wani shawara ne wannan, shin akwai wani hanyar da Amira da Sultee zasubi har Sultee ya auri Nafisa wacce suke uwa d’aya uba d’aya alhalin ita Amira tana raye?. Zamu baku amsoshin nan in har kuna tare damu. 07053072615 ©Hanee da maman Khalil SHARE THIS: Twitter Facebook Google LIKE THIS: Like Be the first to like this.  RELATED GIMBIYA NAFEESAH GIMBIYA NAFEESAH GIMBIYA NAFEESAH FEBRUARY 10, 2016 ⁄ Advertisements GIMBIYA NAFEESAH GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® NHW da © Khadijah maman Khalil - Amira ta nisa sannan tace “Zan je nasamu Daddy nace mishi banida lafiya ta fannin mu’amalar auratayya, bana jin sha’war komai, duk zaman da mukayin nan zaman ha’kuri kakeyi dani, ba abinda ya ta’ba shiga tsakaninmu don ko hannuna baka ta’ba ri’kewa ba sannan zance inaso ka sakeni ka auri Nafisah tunda aure tsakaninka da ita bai haramta ba, kuma exact thing da zan gayama Nafisah kenan, kaima in ya kiraka ka san abinda zaka gayamishi yanda zai yarda”, kallonta yakeyi baki bud’e yana jinjina irin son da take mishi da kuma Nafisah har zata iya hana kanta abinda takeso don ya samu farin ciki, hawaye ne ya sauko daga idanunshi, yace “Anya kina ganin hakan zaiyi?”, jinjina mishi kai tayi tace “Ofcourse, wait and see”, sai ta mi’ke ta nufi parlourn daddy. Ta sameshi yana zaune da Ammi da mummy suna hira, ta mishi sannu da rana sannan tace “Daddy inaso na ro’ki wani alfarma a wajenka, don Allah karka ‘ki amince min, ko da na mutu inaso wannan ya zama wasiyya na”, daddy ya dubeta a rikice yace “Whatt!!??, me kike fad’a ne haka?, me kike so na miki?, ki fad’i koma menene namiki al’kawarin zanyi in Allah ya yarda”. Sunkuyar da kai tayi sai tace “Daddy, inaso ya Sultee ya auri Gimbiya(Nafisah)”. A razane duk suke kallonta, mummy a birkice tace “Kinada hankali kuwa?, mijinki ne fah na tsawon shekara d’aya, kina a raye kuma kina cewa ya auri Gimbiya?, ‘kanwarki sakike ne fa”, share hawaye Amira tayi ta mai da dubanta zuwa ga daddy, cikin sanyin murya tace “Daddy karku tsamman banda hankali, wallahi babu abinda ya ta’ba shiga tsakanina da ya Sultee”. Ammi tace “Ehhh!??!, kamar ya?, kallonki ya tsaya yi har tsawon lokacin nan?”, Amira tayi ya’ke tace “Wallahi ku yarda da magana na, duk zamanmu ha’kuri yakeyi dani don ko hannuna bai ta’ba ri’kewa ba, ba wai don bana sonshi ko baya sona ba, matsalar daga waje na ne, nasan banida lafiya don har asibiti naje aka bani magunguna, na d’auki alha’kin shi da yawa duk da bai ta’ba nunamin ba, ta hanyar nan ne kawai zan iya saka mishi”, ta ‘karashe maganar tana kuka sosai. Gaba d’aya parlourn jikinsu yayi sanyi, nan take daddy ya tura akira mishi Sultee, batare da ‘bata lokaci ba kuwa ya zo parlourn. Nan daddy ya tambayeshi “Sultan, duk tsawon zamanku a matsayin ma’aurata kai da Amira kun ta’ba samun matsala ne?”, girgiza kai Sultee yayi yace “A’a daddy, wani abu ne ya faru?”, ajiyar zuciya daddy ya sauke sannan ya maida dubanshi wajen Amira, a hankali yace “Gayamishi abinda kika gayamana yanzu”, nan kuwa Amira ta koro ma Sultee bayani kaman yanda ta ma su daddy, sunkuyar da kai yayi ya kasa cewa komai, ganin haka yasa daddy yace “Gaskiya ta fad’a?, in har haka ne karka ‘boyemin komai, ka d’auke ni a matsayin mahaifinka ba mahaifin Amira ba”, cike da kunya Sultee yace “Haka ne daddy, ba abinda ya …..”, sai kuma yayi shiru ya kasa ‘karasarwa. Furzar da iska Daddy yayi sai yace “Amma all this while mesa duk cikinku ba wanda ya tinkare mu da maganar?, ba kasan cutar kanka kayi ba?, ka girma Amira kuma ka fita hankali da hangen nesa, in ita bata fad’a ba don ita ke da matsala ai kai zaka fad’a tunda lafiyarka kalau kuma shekaru sun ja”, ahankali Sultee yace “Ayi ha’kuri daddy”. Daddy ya mishi nasiha sosai sannan yace ya tashi ya tafi. Har ya fita daga parlourn sai Amira tace “Daddy, ya batun maganar aurenshi da Gimbiya?”, daddy afusace yace “Baki da hankali ne, don ke kin yarda ya auri ‘kanwarki an gayamiki shi zai yarda ne ko ita mamana (Gimbiya) zata yarda?, banason sake jin maganar nan daga bakinki, gobe zaki shirya Ammi’nku ta kaiki asibiti”, zaro ido Amira tayi sai ta fashe da kuka mai karya zuciya, cikin kuka tace “Yanzu daddy wannan abu d’ayan baza a iyamin a gidannan ba?, in da Gimbiya ce ai da ba abinda zatace tanaso ayi kuma a’kiyi, don Allah daddy ka taimaka ma rayuwa na ka yarda ya Sultee ya aureta, wallahi nasan ba za a samu matsala ba”, jikin daddy yamutu sosai, ya sauke ajiyar zuciya yace “Ba haka bane Amira, da ke da Nafisa duk d’aya kuke a wajenmu, na yarda amma bisa sharad’in in har d’ayan su bai amince ba toh fah maganar ta watse”. Nan take Amira ta share hawayen idonta sannan tayi murmushi ta rungume daddy tace “Nagode daddy, In Sha Allahu zasu yarda tunda suna sona kuma ai alfarma zasu min”, daddy ya d’an bubbuga bayanta yace “Ni dai na gayamiki, in d’aya bai yarda ba toh sai dai kiyi ha’kuri”, mi’kewa tsaye tayi ta ‘kara mishi godiya tana d’an hawaye, daddy yace anjuma da daddare duk su sameshi a parlour. Amira tana fita daga parlourn ta wuce d’akinta, fashewa tayi da kuka, zuciyarta yana mata zafi sosai, tana jin son Sultee har cikin ‘bargon jikinta saidai tasan dole ta ha’kura dashi tunda Nafisa yakeso, ta gwammaci ta rasashi gaba d’aya akan su zauna a ma’aurata amma baya sonta, tayi kuka sosai sannan ta tashi ta d’aura alwala ta hau nafila tana ro’kon Allah ya cire mata son Sultee daga zuciyarta. Sultee kuwa yana komawa d’aki tausayin Amira ya lullu’beshi, yasan ya zalunce ta duk da ba laifinshi bane. Yamma lis Amira ta sami gimbiya a garden tana zaune tana shan fruits, zama tayi a gefenta. Nafisa ta dubeta taga damuwa a tattare da ita, cike da kulawa ta hau tambayarta “Anty, me ke damunki?, baki da lafiya ne?, ko an ‘bata miki rai ne?”, girgiza kai Amira tayi tace “Ina neman alfarma a wajenki sis, ke kad’ai ce zaki iya taimakona, nasan bazaki ‘ki ba saisa na zo ro’karki”, Gimbiya ta d’anyi jim sai tace “Ba komai sis, duk abinda kike nema daga wajena ni mai baki ne, ke kad’ai fah gareni, ina jinki, gayamin”, murmushi Amira tamata sannan tace “Inaso in daddy ya kiraki akan kin yarda ya Sultee ya aureki kice mishi eh”, dafe ‘kirji Gimbiya tayi da sauri ta mi’ke tsaya tace “Anty ya Sultee fah kikace, mijinki”, Amira tace “Ehh shi dai”, Gimbiya tace “Ai ba aure tsakaninmu tunda ke yake aure”. Amira tace “Akwai!, nan ta mata bayani kaman yanda tayi ma su daddy, nan take kan Gimbiya yafara juyawa, zama tayi da’bas a cikin lallausan grass carpet da ya zagaye garden din, azuciyarta tace “Noo, ya Sultee?, he can’t be my husband, yamin girma, noooo!!!!”, nan wata zuciyar kuwa tace mata “Haba Nafisa, ita kad’ai ce addarki, ki tuna fa tun kamin tasan ke ‘kanwarta ce take kula dake kamar ‘yar uwarta, ai koma me ta ro’ka daga wajenki ya kamata ki mata”. Amira ta sau’ko daga kan kujerar da take zaune, ta zauna dab da Gimbiya, dafa kafad’arta tayi tace “Ba komai in har baza ki iya ba, karki damu, nagode”, tana kaiwa nan sai ta tashi tana share hawaye. Dasauri Gimbiya ta ri’ko hannunta, ba tare da ta juyo ba tace “Sis Allah ba komai, ba sai kin takura kanki ba”, hawaye Gimbiya takeyi sosai, cikin muryar kuka tace “Kinfi ‘karfin komai a wajena, wallahi na amince in har hakan zai faranta miki rai”, juyowa Amira tayi ta rungumeta suna kuka, sun dad’e ahaka sannan Amira ta zaunar da ita ta ‘kara mata ‘karfin guiwa akan don Allah ta amince in daddy ya tambayeta, ahaka suka rabu. Bayan Isha duk suka hallara a wajen daddy, sun d’an ta’ba hira sai daddy ya gyara zama yace “Yanzu dai inaso agama maganar nan kowa ya huta”, ya kalli Gimbiya yace “Mamana, Amira tazo min da wani magana wanda na’ki amincewa don nace sai in dukkanku biyu ke da Sultan kun yarda”. Atare zuciyarta da na Sultee ya buga, Saleem kuwa bai san dawar garin ba sai ya gyara zama don jin bayani, daddy ya gayamusu ‘kudirin Amira, Saleem mutuwa ne kawai baiyi a wajen ba amma idonshi yayi jawur, nan wani zuciyarshi yace mishi “Me na damuwa?, kai takeso ai tunda basu shiri da ya Sultee”, maganar daddy ne ya katse mishi tunani, daddy yace “muna sauraronku, Sultan ka amince?”. D’agowa yayi ya kalli Gimbiya wacce itama a lokacin shi take kallo, sau’kar da kanta ‘kasa tayi da sauri, ya maida dubanshi zuwa ga Amira wacce idonta yayi ja tsaba kuka, murmushi ta mishi alamun yayi magana, a hankali yace “Na amince daddy, in har hakan ne zai sa Amira farin ciki, ban ‘kullace ta ba kuma bazan ta’ba ‘kullatarta ba don tamin biyayya fiye da tunanin mutum”, jin Sultee ya amince yasa Saleem fara zufa. Daddy ya girgiza kai yace “Mamana ke fa?”, kallon Amira tayi sai taga bazata iya cewa a’a ba, cikin ‘karfin hali da muryar kuka tace “Na yarda daddy”. Nan take wasu zafafan hawaye suka gangaro daga idanun Saleem, yayi nadamar jinkirta gayama Nafisa sonta da yakeyi, daman ance “abari ya huce shi ke kawo rabon wani”. Gaba d’aya parlourn yayi shiru sai sautin kukan Nafisa da Amira ke tashi, a tunaninsu dad’in Nafisa ta amince ne yasa Amira kuka, basu san tana kukan ta rasa masoyinta har abada bane, Gimbiya kuwa kukanta tanayi ne don batasan wani irin zama zasuyi ita da Sultee ba. Daddy ya sau’ke ajiyar zuciya ya dubi Amira yace “Shikenan kuka ya ‘kare ai, sun amince, hankalinki ya kwanta”, murmushin dole Amira tayi sannan ta mi’ke ta d’auki paper da biro ta isa wajen Sultee, cikin ‘karfin hali tace “Sai ka cika aiki”, jiki ba ‘kwari Sultee ya ‘karbi papern ya rubuta mata saki uku cif sannan ya mi’ka mata, murmushi tamishi tace “Nagode ya Sultee”, Sultee baisan time da hawaye suka zubo mishi ba. Kowa da abinda yake sa’kawa, Amira ta kalli daddy tace “Daddy yaushe za asa date?”, daddy ya d’anyi jim sai yace “Sai nayi magana da abbanku(sarkin Yura) tukunna”. Daddy ya kira Abba washegari suka gama maganar date d’in bikin, da yake ya riga ya gayamishi abinda Amira ta ro’ka kuma shima yace in har sun amince ba matsala. Sun saka date nan da 1 month don hutun Nafisa ya kusa ‘karewa. Daddy ya kirasu ya gayamusu, Sultee dad’i yakeji sosai kaman an mishi albishir da Aljannah, Nafisa ma dai ta d’an sake kad’an but saidai ba kamar da ba don ita tana ganin abun bambara’kwai wai ace tayi soyayya da Sultee, Amira da Saleem kuwa duk sun maida lamuransu zuwaga mai dukka Allah. Bayan kwana uku Sultee da Saleem suka koma Yura, nan fah aka kama shirye shiryen biki, d’okin da Sultee yakeyi har ya bama Abba mamaki yasoma zargin ko dai tun dama wannan yaron yana son Nabila(Nafisa) ne? Amma dai ya barma zuciyarshi batun. Ahmed da Abdul da yake sun san komai game da son Nafisa da yakeyi sun tayashi murna sosai, da yamma yana waya da Ahmed sai yake ce mishi “Sultan ni fah gaskiya ina son Amira ba tun yau ba, ko zakamin hanya ne?”, Sultee cike da mamaki yace “Kamar ya ba tun yau ba?, kana nufin ka dad’e da kamuwa da sonta?”, murmushi Ahmed yayi yace “I’m serious, ina ranar da muka je gidanka muka samu tana viewing Nafisa tana rawa sannan daga baya tafito muka gaisa?, to wallahi tun time din na ganta ta mugun fizgata, na dai danne ne kawai don nasan haramun ne abinda zuciyata yake raya min”, tsaki Sultee yaja yace “Wato kai dama kallon matan mutane kakeyi ko?, Allah yasoka ma ba Nafisa ka kare ma kallo haka ba, but Amira matata ne before so na yafema kallonta da kayi”, dariya Ahmed yayi yace “Shege, kanason Nafisa har yayi yawa fah, ni dai yanzu ka bani number Amira inaso na mata magana”, Sultee ya amsa da “Okay ba matsala, zan turoma amma please kar ka ‘kara kallon matar mutane, ba kyau”, Ahmed yace “Toh nagode abokina, ina jiran number din”, sun d’an jima suna hira sannan sukayi sallama. (Tohh fah kunji, abokai ‘kare ma matan abokai kallo sukeyi, in ya zama dole afita agaisa toh a zumbula hijab babba wanda bazai nuna surarki ba, Allah yasa mudace). 2 weeks to biki aka kai kayan aure, size nata na bra da pant duk Amira ya tambaya ta gayamishi don ya tambayi Nafisa awaya amma tace mishi ita batasani ba, batason iskanci. Kayan aure yayi kyau sosai don ba ‘karamin kud’i Sultee ya kashe ba. Tun wednesday Sultee ya dira a Hamaz dashi da friends nashi da kuma ‘yan uwa da abokan arziki, tsakaninshi da amaryarshi kuwa ba wani hirar kirki sukeyi ba, kullum sai ya kirata amma in ta d’auka sai ta yi shiru, yayi ro’konta har ya gaji daga baya ya ha’kura tunda dai takusa zama mallakinsa zama ta sanine. Around 9 yana waya da wata childhood friend nashi(Safiya) yanata dariya sai kawai yaci karo da Gimbiya wacce ta biyo ta hanyar don zuwa wajen Ammi, tana d’aga kai taga Sultee ne sanye da farar shadda, yayi kyau sosai, bata mishi magana ba saita bi ta gefenshi da niyar wucewa, ri’ko hannunta yayi sannan yayi sallama da Safiya. Janta yayi zuwa wajen kujeru ata ‘kar’kashin bishiya suka zauna, sai tuttura baki takeyi ita adole bataso. ‘Kare mata kallo yayi sannan yaja tsaki yace “Yanzu da d’an iskan kayan nan kike yawo acikin gida?, karki manta fa akwai maza agidannan, ga dogarai ko ta ina, gaskiya ni ban yarda kina yawo ba hijabi a tsakar gidan nan ba”. A tsiwace tace “Ai a gidanmu nake ba gidanka ba, kayan da naga daman sawa zansa”, “haba sis, bazaki bar rashin kunya ba?, by saturday dai fah in an shafa fatiha shikenan”, maganar Amira ne ya katse mishi ansar da yayi niyan ba ma Gimbiya. Sultee ya furzar da iska mai cike da ‘bacin rai yace “Sis ki mata magana kam, gaba d’aya fa ta rainani, tana ganin kaman ni sa’anta ne, ko wayana fah bata d’agawa tsaba rashin kunya da ke yawo a kanta, amma barni da ita, zan sauke mata su, Allah ya kaimu saturday”, mi’kewa tsaye yayi, Amira ta tsaidashi tace “Please ya Sultee kayi ha’kuri, kasan yarinta yana damunta amma zan mata magana, kaji big bro?”, murmushi yayi sannan yace “Thanks lil sis”. Amira ta koma ta ja hannun Gimbiya, basu tsaya a ko ina ba sai d’akin baba Rabi, wasu magunguna ta bata wai tasha, ba don taso ba haka ta dinga shansu d’aya bayan d’aya. Chan sai Amira tace “Umma(baba Rabi), ‘yar kin nan bata jin magana wallahi, ya Sultee fah take ma rashin kunya, kuma agaba na yamata magana akan ta dinga saka hijab in zatayi yawo a tsakar gida tunda akwai maza sosai amma bud’ar bakinta sai tace mishi abinda taga daman sawa shi zata sa”, baba Rabi ta kama baki tace “Haka kika mishi Nafisa??, bakisan namiji ba a mishi haka ba ko?, shi ne fa zai aureki karki manta”, Gimbiya ta had’a fuska ita adole an ‘bata mata rai, baba Rabi ta dinga mata nasiha har dai ta sau’ka tace in Allah ya yarda bazata dinga renashi ba. Thursday akayi hawa, Sultee yasa kayan sarauta, yayi kyau na fitar hankali, friday kuwa Walima akayi don Gimbiya tace itakam batason bidi’a a biki, saturday misalin ‘karfe goma sha d’aya na safe dubbannin mutane suka shaida auren Gimbiya Nafisah da Yarima Sultan akan sadaki naira dubu hamsin, daga nan kuma aka wuce reception inda akayi awani babbar restaurant mai suna “Amrah’s Restaurant”. Suna dawowa daga reception Sultee ya dau wayarshi ya kira Gimbiya, a kira na farko ta d’auka, har yaji mamaki, muryarta a dishe tace “Hello”, murmushi yayi wanda sai da ta jiyo sautinshi sannan yace “Yakike?, yanzu kam an d’aura aure, kin zama mallaki na, ina fatan dai kinsan duk abinda nace kiyi zakiyi kam ko?”, jin batayi magana ba yasa ya cigaba “Na farko dai anjuma zan turo miki da kayan da zakisa a dinner, friends nah sun had’amana”, cikin masifa tace “Ni fah ba inda zanje, gwanda ma karka turo ehen”, ya d’anyi jim sannan yace “Good, in na turo Allah yasa karki sa, by 10 zamu tafi, ko baki shirya ba wallahi dole kije”, ‘kwafa tayi tace “Ohh dole ne abun?, bazanje ba!!!”, sai ta katse wayar. Ko minti biyar baiyi da gama wayar ba Amira ta shigo da kaya ta mi’ka mata tace “Ya Sultee yace na kawo miki, anjuma mai makeup zatazo sai ta miki na dinner d’in”. Batace ma Amirah komai ba illa jinjina kai da tayi alamun “Toh”. Tun 8 Sultee yagama shirinshi tsaf ya kira Amira wacce tazama kamar itace komai na bikin a waya, asanyaye take cemishi Nafisa fah ta’ki amata make up, wai ita bazataje dinner d’in ba, tsaki Sultee yaja sai yace “Okay ba matsala, ina zuwa”. Da saurinshi ya nufi d’akin Nafisa, yana shiga yaga tana kwance akan gado ta d’aura ‘kafa d’aya kan d’aya sai rigima akeyi da ita akan ta tashi ta shirya amma tace ita ba inda zataje. Sallamar Sultee yasa ta zare ido, ganin yashigo yasa gaba d’aya aka watse aka barsu su biyu, matsowa yayi kusa da ita ya zauna sannan yafara magana “Meh kikeyi da baki shirya ba?”, yasa hannu zai jawota kawai saitayi saurin mi’kewa tanufi toilet tana in-ina tace “Umm…emm..yanzu zan shiga wanka ne dama”, yanda ta tsorata dashi har ya bashi dariya, azuciyarshi yace “Ohh ashe dai duk rashin kunyarta don ba a d’aura auren bane”, cikin hanzari tayi wanka tafito, ya kira Amira akan tashigo da masu mata make up d’in, nan take kuwa suka shigo aka gyarata tsaf, duk sunji mamaki da ta yadda suka mata. 9:45 dai an shirya amarya tayi kyau abunta, Sultee kuwa yana zaune bai bar d’akin ba, da yaga ta fara gardama da ya kira sunanta sai ta nitsu. Motar d’aya suka shiga shi da ita, Amira kuwa tuni Ahmed ya ma’kale mata, shi ya d’auketa ya kaita dinner ma, Nafisa ta sake ta cashe kaman ba ita ba, bata nuna damuwa ba sam wanda hakan yayi ma Sultee dad’i, milly balalau na hango sai cin fried rice akeyi da cikinta, daga chan kuma futha da kdeey ansha wanka amma sunata yagar nama abunsu, mutane dai tirim sunje, su Jamila da Amina sune manyar ‘kawaye, sun kafa goggoro kaman masu tashi sama. Ba atashi ba sai wajen 12am, Nafisa ta ja Amina wai su shiga motar d’aya don ita yanzu mugun tsoron Sultee takeji, suna isowa bakin motar Sultee ya kalli Amina yamata murmushi yace “Umm, sorry please ki shiga wani motar daban, inaso nayi magana da amarya na”, jikin Nafisa yafara ‘bari, cikin sad’a’karwa tace “Ayyah ya Sultee kabarta, bestfriend dina ne, kaga komai tasani akaina ai”, juyowa yayi ya kalleta yace “Harda sirrinmu?”, cikin rashin fahimta Gimbiya tace “Wani irin sirri kuma?”, dariya yayi sannan ya ‘kara bama Amina ha’kuri sai yaja hannun amaryar sa suka shiga motar. A motar duk Gimbiya a takure take, gashi Sultee ya’ki sakin hannunta har suka isa gida, tun kamin driver yagama parking ta fara kiciniyar bud’e ‘kofar motar, murmushi Sultee yayi, driver ya fita ya barsu, Sultee ya ‘kara matsowa kusa da ita, kallon fuskarta yakeyi da d’an ‘karamin bakinta tanata kumbura baki, nan take yajishi cikin wani yanayi da bai ta’ba shiga ba sai ranar, ba shiri ya kama bakinta yafara kissing nata, tureshi takeyi amma ta kasa, har ya fara fita daga hayyacinshi, gashi babba kuma sabon shiga a harkar, kuma kun san ba sauki. Da kyar yayi ‘ko’karin saketa yana maida numfashi, gimbiya kuwa dagudu ta fita daga motar, ta isa d’akinta ta kwanta tafara jan tsaki “Allah ya isar min shan bakina da yayi, sai kace yasamu sweet, lallai ya Sultee ma ba ‘karamin d’an duniya bane, taci gaba da sa’ke-sa’ke har bacci ya kwasheta. Abangaren Sultee kuwa yana isa d’aki kan gado ya fad’a yana murmushi, Abdul yashigo suka gaisa sai chan Abdul yace “Abokina ya dai kaman baka daidai!,?”, murmushi Sultee yayi yace “bari kawai, yau na mallaki Nafisa, har ina Allah-Allah wednesday yayi mukoma don gaskiya ha’kuri na yakusa ‘karewa”. Kuyi ha’kuri da wannan d’in, zamuyi ‘ko’karin gamawa kwanan nan In Sha Allaaah © Hanee da maman Khalil Posted from WordPress for Androi GIMBIYA NAFEESAH GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® NWA da © Khadijah maman Khalil - Wasar ‘buya gimbiya keyi da Sultee, duk yanda yaso su had’u abun ya faskara don ta bar bin hanyar da tasan zata iya cin karo dashi. Ahmed da Amira kuwa soyayya sukesha abunsu, tuni Amira ta fitar da Sultee daga zuciyarta, sai fatan Allah yasa rabon Ahmed ne. Yau ya kama tuesday, an gama had’a ma gimbiya kayakinta, jere kuwa an riga da anyi tun kamin a d’aura auren a sabon gidan da Sultee ya siya. Sultee ba abinda yakeson gani irin Nafisa amma ta’ki bari su had’u, yau dai ya ‘kudiri aniyar ko ta yaya sai ya ganta. Yamma lis mai martaba ya kira Nafisa don mata nasiha, ya fara da cewa “Mama na inaso ki sani aure da kike ganin nan ba wai ha’kuri bane zalla kamar yadda ake fad’a, yes dole a saka da ha’kuri amma dai biyayya da kuma soyayya shi ke sa zaman aure yayi tsawo, duk da nasan ba soyayya kukayi dashi kamin a d’aura muku aure ba, nasan Sultan zai kula dake kuma bazai ta’ba bari ki cutu ba, kar ki mishi rashin kunya sannan duk lokacin da ya saki abu karki kuskura kice baza kiyi ba, duk abinda zakiyi a gidan aurenki ki dinga tunatar da kanki cewa Aljannarki yana ‘kar’kashin ‘kafar Sultan”, ya d’auki lokaci yana mata nasiha wanda ba abinda gimbiya ke yi sai kuka, maganar daddy ya ratsata ‘kwarai da gaske. Baba Rabi, Ammi da mummy ma sun taru sun mata wa’azi sun kuma bata shawarwari yanda zata dauwamar da zaman lafiya a gidan aurenta, idon Nafisa yayi luhu-luhu don kukan da tasha. Bayan anci dinner duk aka watse, Hauwa, Ukasha da Amira duk suka dunguma zuwa d’akin Nafisa, tana zaune tana ta tunani, ta amsa sallamarsu sai suka zazzauna. Hira sukeyi sosai sai dariya suke kwasa gwanin sha’awa, Sultee ya zo ‘kafarshi hud’u amma basu bar d’akin ba, tsaki yaja a zuciyarshi yace “Wad’annan akwai surutu, da ina zagin Nafisa akan tacika magana ashe dai surutun a jininsu yake tunda dukkansu sai zuba sukeyi”. Ammi da tazo wucewa taga Sultee ya fito daga hanyar d’akin Nafisa yasa ta doshi d’akin, tana zuwa tace “Ohh Allah, ‘karfe sha d’aya da rabi amma ku ko bacci baku da niyyar yi, oya tashi kowa ya wuce d’akinshi”, ta ‘karasa maganar tana nuna musu ‘kofa. Ukasha da Hauwa suka tashi ba don sunso ba suka musu sai da safe suka fita, Amira kuwa gyara kwanciya tayi, Ammi ta kalleta sannan tace “Ke baza kije kiyi baccin bane?”, Amira tace “A’a Ammi, anan zan kwana kawai”, Ammi ta ja guntun tsaki tace “Don Allah ki tashi tasamu tayi bacci, kinsan fah flight nasu 8 ne, zaki zauna ki cikata da surutu har ta rasa samun isashshen bacci”, Amira ta tura baki tace “Ni ba hanata bacci zanyi ba, tunda kin kore ni shikenan, sai da safe”. Tana fita Ammi ta matsa kusa da Nafisa tace “Kiyi bacci kinji?, kinga dare yayi”, “toh” Nafisa ta amsa mata, Ammi ta mata sai da safe sai ta fita ta ja mata ‘kofar. Tana fitowa ta wajen verendah na flat na Nafisa ta kusa cin karo da Sultan, ja da baya yayi da sauri yana sosa ‘keya, rusunawa yayi ya gaisheta, fuska d’auke da murmushi ta amsa mishi sai tace “Tana ciki ai, ka shiga mana”. Murmushin mara gaskiya yayi ya kasa magana, ganin kunya yacika shi ne yasa Ammi yin murmushi kawai ta wuce. Shiga d’akin yayi da sallamarshi, lokacin Nafisa ta d’aura towel zata shiga wanka, da yake ta bama ‘kofa baya shiyasa bata ganshi ba shikuma komai nashi ya tsaya cak, kallonta yakeyi kaman zai cinyeta. Rufe ‘kofar toilet da tayi ne ya dawor dashi hankalinshi, da ‘kyar ya kai kanshi kan kujera ya zauna yana jiran fitowarta, ta d’an dade kad’an sannan ta fito, bata ma lura da mutum a d’akin ba, ta bud’e wardrobe tafito da night gown wanda riga ne iya guiwa, ta gama shafe- shafe shafenta da feshe feshe sai ta saka night gown d’in, har ta hau kan gado duk bata lura da Sultee da ke neman mutuwa a zaune ba yana kallonta baki bud’e. Ta hau gado sai ta d’an mi’ka hannunta don ta kashe bulb d’in d’akin ne ta ga mutum zaune ya ‘kura mata ido, ihu ta tsala tayi hanyar parlour da gudu, ganin taji tsoro yasa ya tashi da sauri ya cafkota kar aji ihun a waje, rufe mata baki yayi asanyaye yace “Shhhh, ni ne fah”, sai sannan ta d’an nitsu amma still jikinta yana rawa. ‘kwace kanta tayi daga ri’kon da ya mata, tsaki taja tace “Shine zaka wani shigo min d’aki ka zauna ba ko sallama?, wai ma yaushe ka shigo ne?”, murmushi ya mata sannan yace “Tun kamin ki shiga wanka na shigo amma baki ganni ba sai yanzu”, murgud’a mishi baki tayi tace “Amma kuma kasan ba kyau kallon jikin mace kana namiji ko?”, kasake ya tsaya yana kallonta yana kuma jin mamakin abinda ta fad’a amma dai sai ya fuske, cikin ko-in-kula yace “And so?, macen da na ganin ai matata ce, fiye da haka ma an halarta min zan iya yi ba kallo kawai ba”, bata tanka mishi ba ta juya da niyyar komawa kan gado, ri’ko hannunta yayi, cike da tsiwa ta juyo, ta bud’e baki zatayi magana kawai taji yakai bakinshi kan nata, sai tuttureshi takeyi amma shi sai ‘kara mannata a jikinshi yakeyi, da taga yana neman wuce iyaka sai ta sa mishi kuka, ido a raunane ya saketa ya juya ya fita ba tare da yayi magana ba. Kan gado ta fad’a ta fashe da kuka tana cewa “Yanzu shikenan ni duk abinda yaga daman yi dani zaiyi?, wallahi bazan yarda ba, shi kuma da yake bai da kunya har cikin d’akina a cikin gidan ubana yazo yake neman gwadamin tantirancin shi”, tsaki taja ta koma toilet tayi brush tana ta goga harshenta tana d’an hawaye. Adaren ranar Sultee ya tsokano ma kanshi tsuliyar dodo, gaba d’aya ya kasa samun nitsuwa, tsaki ya dinga ja yana da-na-sanin romancing din Nafisa da yayi don yasan hakan ne ya jefashi a halin da yake ciki, juyi ya dinga yi da ‘kyar bacci ya d’aukeshi. Yau Wednesday ranar tafiyar Sultee da Gimbiya Nafee, tun asubah da suka tashi basu koma bacci ba, shiri akayi sosai, sunci sun ‘koshi sannan aka musu rakiya zuwa airport, ciki ko harda daddy da Ammi, mummy kam tace bazata iya zuwa ba tana a matsayin uwa, baba Rabi tayi kukan rabuwa da Nafisa sosai. A airport su daddy suka musu sallama zasu juya, da gudu taje ta ‘kan’kameshi da Amira tana kuka tace “Daddy don Allah mu tafi tare, Anty Amira kinga ai kinsaba da chan din, mutafi don Allah, bazan iya zama ni kad’ai ba”, ta ‘kara fashewa da wani kukan Amira na tayata, da ‘kyar daddy ya lallasheta yace “Yi ha’kuri mamana, kinga yanzu bamuyi shirin tafiya da ku ba amma ki bari in kin kwana biyu zamuzo dukkanmu kinji?”, girgiza kai tayi tana share hawaye “Daddy kayi al’kawari?”, asanyaye yace “Zan miki ‘karya ne?, in kin kwana biyu zamuzo mu dubaki, ai ba ke kad’ai bane achan, ga yayanki Sultan zai dinga kula da ke”. Cikin dishewar murya tace “Toh daddy, kuma…..”, announcement da akayi akan duk masu tafiya suyi boarding ne ya katse mata maganarta, daddy ya dafata yace “Yi ha’kuri kije, zamu dinga waya kullum”, kama hannunta Sultee yayi suka musu sallama, Nafisa sai waigowa takeyi tana hawaye har ta bar ganinsu, ji takeyi kaman a kunce auren ta huta tunda dai tasan ba sonshi takeyi ba. Acikin jirgi seat nashi ne ata window, asanyaye tace “Ayyah ya Sultee muyi exchanging seats kaji?”, cike da tausayinta yace “Okay ba damuwa”, sun lula a sararin samaniya, chan sai ya Sultee yace mata bari yaje toilet, yana tashi wani kyakkyawan saurayi bazai wuci 27-28 ba yazo ya zauna a inda ya tashi, sallama yayi mata ta amsa mishi, yace “sunana D…..”, katseshi tayi tace “Sorry please ni matar aure ce”, ya langa’bar da kai yace “Amma nayi rashin sa’a, wayene yamin shigan sauri haka?”, murmushi ta mishi tace “Yaya na ne shi”, ya d’anyi dariya sannan yace “Ohhh ko dai shine wanda ya tashi daga nan?”, wani murmushi ta sakeyi, zata bashi amsa kenan taji muryar Sultee cike da masifa yace “Excuse me, da matar mutum fah kake magana wanda hakan bai dace ba”, guy din ya tashi tsaye, ganin yanda Sultee ya wani had’e rai yasa yace “Sorry bro, wallahi bansan matar aure bace saida ta gayamin, I’m so sorry”, bai jira meh zaice ba ya koma seat nashi. Sultee iya ‘kuluwa ya ‘kulu, kishi ne yake cinshi, “wai matata tana ma wani murmushi har suna hira?, meh ma ya gayamata da ta ji dad’i haka?”, baisan sanda yayi tsaki a fili ba, Nafisa ta kalleshi sai taga sam bata kyauta ba, ahankali tace “Sorry ya Sultee, naga kaman ranka ya ‘baci”, afusace ya kalleta sannan yace “Wai ma meh had’inki dashi da zaki wage baki kina dariya dashi?”, kallonshi takeyi cike da mamaki, ita dai tasan ba tayi dariya da guy din ba. Shareshi tayi, haka yayita masifarshi har ya gaji yayi shiru, ita ba abinda takeyi sai dariya ‘kasa-‘kasa, da taga ya saka earpiece ya rufe ido sai ta tsamman yayi bacci, shafa fuskarshi tayi afili tace “In yana bacci zaka ganshi kaman wani silent guy amma masifar shi yafishi tsawo”, bud’e ido yayi ya harareta, da sauri ta cire hannunta daga fuskarshi, cike da kunya ta sunkuyar da kai, tsaki yaja yace “Ni ne masifaffe ko?, wai nikam mesa kika raina ni ne?, don kina ganin ina sassauta miki ko?, wallahi zan iya ajiye aure a gefe na yi maganinki, kema kinsan ‘karamin aiki na ne”, ‘kwafa tayi ta tura mishi ‘keya tace “Ahaka zaka ‘kare, mutum kullum cikin masifa sai kace a kanshi aka saukeshi”, juyo da kanta yayi yace “Da waye kikeyi?”, taji tsoro amma sai ta dake tace “Haa, na ‘kira suna ne?, mutum nace, ko kai sunanka mutum ne?, A’uzubillah!!, na tsani masifa wallahi”, ganin in ya biye mata zasu tara ‘yan kallo yasa ya tura kanta har ta kusa gara kanta, bai ce mata komai ba yaci gaba da jin ‘kira’ar Sudais da ke tashi a earpiece nashi. Kusan awa biyu Nafisa tanaso ta mishi magana amma tana tsoro, gaba d’aya sai taji tanason tayi magana, shirun ya isheta gashi ta kasa bacci, chan sai ta d’anyi innocent face, ta matso daf da Sultee ta kwanta a kan kafad’arshi, bai tanka mata ba yaci gaba da game nashi a waya, da taga baiyi magana ba sai ta sakala hannunta ta cikinshi, yaji yarrr amma dai ya fuske, chan sai Nafisa tace “Ya Sultee ayyah muyi surutu mana, wallahi na gaji da zama shiru, duk sainaji kaman baki na zaiyi ciwo don banyi magana ba, kaji?”, dariya ya kusa ‘kubce mishi amma sai ya gintse dariyar, a zuciyarshi yace “Ohh Nafisa akwai surutu, shi ne in batayi ba bakinta zaiyi ciwo” amma a fili sai yace “Ni banason surutunkin nan, nagaji”, shiru tayi na d’an seconds sai kuma tace “Ya Sultee, meh kakeji a earpiece din ne?”, ba tare da ya kalleta ba yace “Kira’a nakeji”, tashi daga jikinshi tayi tace “Laa!!, ya Sultee ayyah tsammin ear piece d’aya nima bari naji”, ajiyar zuciya yayi sannan yace “Don Allah ki ‘kyaleni, banson takura, ina wayarki da baza kiji dashi ba?” Fuskar tausayi tayi tace “Na manta dashi a gida, saidai in mun isa ka siyamin wani”, dariya yayi yace “Allah ya ‘kara, wazai saya miki wani?”, tayi murmushi tace “Kai mana”, Sultee yace “Lallai kam, ai kin ‘kare ri’ke waya kenan inaga don bazan saya miki wani ba”, kuka tasa mishi sosai hakan yasa ya jawota jikinshi ya fara lallashinta yace “Shhh, ni wasa nake miki, zan sayamiki kinji?”, tureshi tayi tace “Gwanda da ka gyara magana”, mi’ka mata earpiece d’aya yayi suka cigaba da jin ‘kira’ar suna d’an hira sama sama wanda rabi masifa ne. Sun sauka Qatar lami lafiya, driver yazo ya d’aukesu suka nufi gida. Agajiye suka shiga parlour, gidan upstairs ne, parlourn ‘katon gaske ne, Nafisa ko zama batayi ba tace a gajiye “Ya Sultee ina ne d’akina, inaso naje na huta”, bai mata magana ba ya fara hawa sama, ganin haka yasa tabi bayanshi, wani d’aki ya nuna mata yace “Nan ne naki”, sai ya juya ya tafi. Da yake da dare suka iso kuma duk sunci abinci so sai kawai kowa yabi lafiyar gado. Washegari bata tashi ba har wajen 10am, da wurwuri tashiga tayi wanka, tana ta Allah yasa Ya Sultee kar ya hauta da masifar tayi bacci dewa, doguwar riga tasaka sannan ta tsaya ‘kare ma d’akin kallo, d’aki ne had’ad’d’e da royal bed aciki, ga kujeru guda uku a ta gefe, da d’an ‘karamin carpet had’e da centre table, d’akin dai ya tsaru gaskiya. Takalmi flat shoe ta saka ta sauko ‘kasa, anan ta tarar dashi zaune a parlour yana kallon tv yana shan tea, tun da ta shigo yake binta da kallo kaman maye, zama tayi a kan kujera tace “Ina kwana ya Sultee?”, murmushi ya mata sannan yamata alamun tazo, cike da fargaba ta nufi kujerar da yake zaune, ajiye cup din yayi sai ya jawota ta fad’o jikinshi, acikin kunnenta ya rad’a mata “Haka ake gaisuwar?”, gyara zama tayi tana sunkuyar da kai tace “Eh mana”, kallonta yayi yaga ta mishi kyau, a hankali yace “Ni banason irin wannan gaskiya”, d’agowa tayi tace “irin wanne kakeso?”, murmushi ya mata ya ‘kura mata ido, yayi kissing nata na minti biyu sai ya saketa yace “Irin wannan”, cike da kunya ta fara ‘ko’karin tashi daga jikinshi, jawota ya ‘kara yi yace “Sarkin kunya, ina zakije?”, kanta a sunkuye tace “Breakfast zan d’aura mana”, tashi yayi cikin sauri yace “Sorry babyna, na saya ai tun dazu but kina bacci saisa ban tasheki ba”, wasa da yatsun hannunta tafara tana mamaki wai yau ya Sultee ne ke mata abubuwan nan, har yana kiranta “babyna”, dawowarshi ne ya katse mata tunaninta. Feeding nata yayi, tun tana tutturjewa har ta d’an saki jiki ya bata tayi nak, kwanto da ita yayi jikinsa suna kallon tv, Nafisa duk sai taji ta a takure, ahankali ta fara zamewa, ri’kota yayi yace “Yadai?”, a hankali tace “Girki zan mana”, girgiza kai yayi yace “Noo jiya fah muka iso, ki huta tukunna sai bayan 2days sai ki fara mana girkin, zan dinga siyo mana a restaurant”, ba don taso ba tace “Toh”, chan kuma kamar an mitsileta ta tashi tace “Ya Sultee ayyah kiramin su daddy muyi magana”, Sultee ya ‘kara janyota ya d’aurata akan cinyarshi yace “Okay” sannan ya ciro wayarshi daga aljihu. Kira d’aya biyu daddy ya d’aga, gaishe shi yayi tukunna yaba ma Nafisa, cike da d’oki ta kar’ba suka gaisa, sun d’anyi hira sannan sukayi sallama, saida tasa ya kira mata su Amira, Ammi, Mummy, Hauwa, Ukasha, sannan ta ‘kyaleshi. Sunacin abincin rana sai Saleem ya kirashi, sun gaisa normal, Nafisa ta fara jijjigashi “Ya Sultee zanyi magana dashi, ka bani”, Saleem daga d’ayan ‘bangaren yaji muryar Nafisa tana magiya kuma yasan ya Sultee ba bata zaiyi ba, dariya yayi yace “Ya Sultee bata don Allah muyi magana”, sawa a speaker yayi sannan ya mi’ka mata wayar yace “minti d’aya”, ta fara ‘ko’karin mi’kewa don ta haura sama amma ya Sultee ya dam’ke mata hannu, kallonshi tayi taga ya wani had’e rai, tuni tasha jinin jikinta, komawa tayi ta zauna suka shiga gaisawa da Saleem, basu wani dad’e ba ta kashe wayar. Ya Sultee ya watsa mata wani kallo ya fizge wayarshi yace “Bakida hankali ko?, na fasa saya miki wayar ma don naga har yanzu kanki yana mugun rawa”, idonta ya ciko da hawaye tace “Don Allah kayi ha’kuri, bazan sake ba”, ta dinga bashi ha’kuri da ‘kyar dai ya ha’kura. Da daddare tun suna gama dinner ta gudu d’aki don yinin ranar gaba d’aya a jikinshi tayi, ko motsi baya barinta tayi, sai wani shishshige mata yakeyi, ita yanzu tsoronshi ma takeji yanda yake nuna mata d’okinshi a fili. Around 9 ta fito daga wanka daga ita sai towel tana tsaye a gaban mirror tana goge kanta da ta wanke, ji tayi an rungumeta daga baya, zuciyarta ya buga dumm!!, jiki ba ‘kwari tace “Ya Sultee bari na saka kaya please”, girgiza kanshi yayi yace “umm umm” sannan ya juyota tana fuskantarshi, vest ne fari ‘kal ajikinshi sai three quarter, ahankali ya fara shafata, gaba d’aya yana neman dagula mata lissafi, tanaso ta tureshi amma ta kasa, kwance towel din yayi ya yar a ‘kasa, gaba d’ayansu suka zube akan gado, nan ya fara mata wasu abubuwa masu wuyan ganewa, in banda hawaye ba abinda takeyi, saida yayi iya son ranshi sannan ya ‘kyaleta ya kwanta a gefe yana maida numfashi, da sauri Nafisa taja bargo ta rufe jikinta tanata hawaye, bayan Sultee yaji ya d’an dawo daidai ne ya dauketa chak sai toilet, tare sukayi wanka suka fito, Nafisa ta kasa had’a ido dashi don wani kunyar shi takeji sosai, shikuwa gogan sai murmushi yakeyi yana ‘kara mannata a jikinshi. Daren ranar a d’akinta ya kwana, yana rungume da ita kaman za a ‘kwace mishi ita. Washegari haka sukayi sallah sannan yace ta tashi suyi nafila, sunyi sun idar sannan ya mata tambayoyi ta amsa, suka yi addu’o’insu sannan suka koma bacci. Da safe ta tashi a hankali da niyar shiga toilet tayi wanka, tana mi’kewa yana farkawa, cikin bacci yace “Ina zakije?”, kanta a ‘kasa tace “Wanka zanyi”, mi’kewa shima yayi yace “muje muyi”, ja da baya tayi tana rufe fuska tace “Allah ya Sultee ni bazan iya ba”, murmushi yayi ya kamo hannunta yace “Muje, zaki saba”, tare sukayi wankan bayan ya gama wasanninshi, mai ma shi ya shafa mata sannan ya shafa ma kanshi, da zatasa kaya ya zauna ya ‘kura mata ido, cike da kunya tace “Ya Sultee kaje kasa kaya mana, nima barinsa sai nazo na sameka a parlour’n ‘kasa”, murmushi yayi yace “Kunyar bai fita ba ko?, barinzo na ‘karasar dashi”, ahankali ya soma takowa zuwa inda take, damke towel d’in tayi tace “Yi ha’kuri, zansa”, dariya yayi ya koma kan kujera ya zauna, riga da skirt ta saka, sun kar’beta sosai. Ya Sultee ya tashi ya ja hannunta yace “Zo ki rakani nasa kaya na sai mu fita”, binshi kawai takeyi har suka isa d’akinshi, zama tayi a bakin gadonshi shima sai yazo ya zauna, a sanyaye tace “Ka fasa sa kayan ne?”, girgiza kai yayi kaman ‘karamin yaro yace “Ki fitar min da kayan da zansa mana toh”, cike da mamakin abubuwan da yake tsiro mata take kallonshi, chan sai tace “Da kam wa yake fitarma?”, murmushi yayi yace “Okay tunda baza ki iya wahala na ba, zanje na ‘karo aure kawai na samo mai sona”, ji tayi maganar ya daki zuciyarta, ta rasa gane meke damunta, mi’kewa tayi ta bud’e wardrobe nashi ta fitar mishi da black jeans da white shirt, sai vest da boxers da belt. Wajen sa kaya ma yace shi ina!! bai iya ba saidai ta sa mishi, ta juya bayanta tace “Toh amma kasa boxers din in yaso sai nasa maka sauran”, dariya yayi sannan ya saka ya matso daidai bayanta yace “Okay juyo ki sa sauran”, rufe ido tayi ta saka mishi vest da wando, ta samishi riga tana buttoning sai ya kama hannunta, d’ago kanta tayi tana kallonshi, cike da shagwa’ba tace “Ka bari na ‘karasa sa maka mana”, kamota yayi ya matseta a jikinshi yana sunsunar ta yace “I love you”, kalmar tazo mata a bazata don bata ta’ba tsammanin ya Sultee zai furta mata ba, jan hannunshi tayi tace “nidai muje muci abinci, inajin yunwa”, breakfast sukayi suna hira abunsu. Bayan la’asar ya d’auketa suka fita sha’katawa sannan ya kaita shopping duk da ba wani kayaki take bu’kata ba amma haka ya dinga jida mata kaya kaman ba da kud’i zai siye su ba, ya bata waya irin nashi i-phone 6+. Haka zamansu ya kasance, kullum tare suke yini da yake hutunshi bai ‘kare ba itama kuma saura kwanaki ya ‘kare, ya saba mata da jikinshi sosai, ya koya mata yanda zata soshi ba tare da saninta ba, ko wani dare sai yayi wasanshi da ita amma bai ta’ba mai gaba d’ayan ba don yasha alwashin sai in Nafisa ta furta mishi tana sonshi sannan zai yarda ya ta’bata. Yau ya kama monday, tanata sauri don kar tayi lattin gashi Sultee sai ‘bata mata lokaci yakeyi, komai ita take mishi kaman wani jinjiri wai sai yace shi bai iya ba, saka kaya kam yazama aikinta don har ta saba yanzu tabar kunyarshi, sai surutu take mishi don Allah yayi sauri ya sauketa a school. Cikin hanzari yafito ya rungumota jikinsa suka shiga motar, yana driving yana murza hannunta guda d’aya, sunata hira suna dariya, in ka ga Sultee baza kace shi bane, yayi kyau, yayi jiki, ya ‘kara haske, Nafisa kuma ta ‘kara cika tayi fresh, kana ganinsu kasan suna matu’kar kula da junansu. Yana parking yafito ya bud’e mata ‘kofar motar ta fito, light kiss ya mata sai yace “Take care of yourself for me, zan dawo anjuma, bari naje na duba abu a office tunda hutuna ya kusa ‘karewa”, murmushi ta mishi tace “Okay, bye”, yana tsaye yana kallonta har ta shiga hall din sannan ya koma motar ya tayar ya bar wajen. 10 mins to zata gama lectures d’in ya Sultee ya iso jiran Nafisa, wata yarinya da gani itama ‘yar 9ja ce ta iso inda yake jingine da motar, gaishe shi tayi ya amsa ba yabo ba fallasa sannan ya cigaba da danne dannenshi a waya, chan sai ta sake cewa “Umm, wa kake jira ne?”, cike da ‘kosawa yace “Mata na”, nan ta fara mishi zuba “Wow, she is so lucky, ta samu handsome guy irinka, how i wish nima zan samu irin haka”, maganar caraf a kunnen Nafisa da ta nufoshi. Tsayawa tayi cak tana kallonshi sai murmushi yakeyi, ita a tsammaninta da budurwar yakeyi, batasan da waya yake murmushi ba, tsaki taja ta juya zata bar wajen, juyowa yayi ya ga ita ne, da sauri ya sha gabanta yace “Babyna, waya ‘bata miki rai haka?”, kallon ka ma raina min wayo ta mishi sannan tace “Ka tafi wajen budurwar ka mana, ba kuna hira bane?”, cikin rashin fahimta yace “Budurwa na kuma?, a ina?”, girgiza kai tayi tace “Waccan wanda kake ma murmushi”, kallon wajen yayi yaga yarinyar d’azun nan ne kuma har yanzu tana tsaye tana kallonsu, tsaki yaja yace “wallahi bansanta ba, yanzu naganta nima a wajen, batun murmushi kuma ina chattin da ahmed ne yake gayamin ankusa sa date nashi da Amira”, ajiyar zuciya ta sauke tace “Allah yasa dai ba budurwar ka bace”, bayaso ya tsaya cacan baki da ita sai kawai ya jawo hannunta ta fad’o a jikinshi, kissin nata yashiga yi kaman mahaukaci, bata hanashi ba don ko ba komai tasan zata ‘kular da yarinyar chan, wani dogon tsaki sukaji anja, still Sultee bai bar abinda yakeyi ba saida ya lura ta bar wajen, murmushi ya ma Nafisa yace “Na kashe maganar, inda budurwa na ne ai bazanyi kissing naki a gabanta ba”, murmushi ta mishi tace “Yawuce”, hannunta ya kama suka shiga motar. Har suka isa gida zuciyar Nafisa bai bar zugin kishi ba, Sultee ya lura da haka, duk sai yaji ba dad’i amma a zuciyarshi ya gode ma Allah tunda dai tana kishinshi kenan tana sonshi. Sultee ya koma aikinshi, komai yana tafiyar musu normal, ko wani yamma sai sun fita yawo, Ahmed da Amira kuwa har ansa date nan da 5 months don tuni Amira ta gayamusu cewa ta samu magani kuma ta warke, ta bar sirrin ‘karyar da tayi tsakaninta da Sultee. Yau ya kama su Nafisa sun samu hutu na sati d’aya, ta dawo gida sai dad’i takeji zata huta, da daddare Sultee yashigo d’akinta yafara mata yanda yasaba amma na yau ya bambanta don har yana sauka ‘kasa, ganin hakan yasa taji tsoro sosai, iya ‘karfinta ta tureshi, ya kwanta yana numfashi sama-sama har bacci ya d’aukeshi. Washegari ya tashi da zazza’bi sosai, jikinshi har rawa yakeyi, Nafisa taji tausayinshi sosai, sai kuka takeyi tana mishi sannu, a ranar ne ta tabbatar ma kanta cewa lallai soyayyar Sultee ya mata mugun kamu, yinin ranar tayishi a wargaje don Sultee ba lafiya, ji tayi inama ciwon zai barshi ya dawo kanta, yayi kwana biyu sannan ya d’an samu sau’ki don ba ‘karamin kulawa Nafisa ke bashi ba. Ranar da ya warke Sultee bai nuna mata komai ba, suna hira ya rungumeta yace “I love you babyna amma ke bakisona ko?, kiyi ha’kuri ki soni, bazan ta’ba zaluntarki ba, i promise you”, idonta cike da hawaye ta rungumeshi itama tace “I love you too ya Sultee, wallahi ina sonka, banyi realizing bane saida ka kwanta zazza’bin nan, i’m so sorry”, wani farinciki ne ya lullu’beshi wanda bazai misaltu ba. A daren kam dai Sultee ya angonce, duk da ya bita a hankali amma kam tasha wahala, kuka tayishi kamar ba gobe don abun ya had’un mata da yawa; Sultee ya manyanta tunda saura kad’an ya cika 40 gashi tunda yake bai ta’ba kusantar na mace ba sai ayau din kuma akanta gashi su baba Rabi sun d’id’d’irka mata magunguna ba adadi. Da safe ya gyarata ya dinga sa mata albarka, jin kanshi yakeyi kaman wani sabon mutum, azuciyarshi yace “Aure rahma ne”, yayi ta jinyarta har ta warke suka cigaba da soye wansu. Kullum maganarshi d’aya- “Babyna inason yara, Allah yasa nayi ajiya a cikinki”, ita kuma sai dai tayi murmushi tace mishi “Allah ya kawo ya Sultee”, cikin ikon Allah kuwa ko 3 weeks basuyi da daidai tawa ba ta fara laulayin ciki, gwajin farko likita yace tana da ciki, Sultee yayi sujudul shukr ya dinga kwararo godiya ma Allah, aranar both families saida suka ji batun cikin, Nafisa kam abun ya soma bata kunya har ta dinga mishi complain “Haba ya Sultee yanzu shi ne zaka bi ka bazani a dangi cewa inada ciki?, kai ko kunya baka ji?”, had’e fuska yayi yace “Abun murna ne ai babyna, meh na kunya aciki tunda dai ni ne ubanshi?, lallai har yanzu yarinta yana damunki”, cike da kunyar maganarshi ta kai mishi dukan wasa tace “Ni don Allah kabari, Allah kana sa naji kunya”, dariya yayi ya dinga lallashinta yana gayamata yanda yakeson ta da kuma unborn babynsu. Sabuwar shafin kulawa ya bud’e mata, tare suke aikin gida sannan every evening su fita strolling ta arean anguwansu, kwana biyun su da fara fita har ta saba da neighbours nata su biyu amma ba ‘yan africa bane, da turanci suke hiransu kullum. Lokacin bikin Amira Nafisa tazo da ‘karamin cikinta mai 3 months and some weeks, bini-bini Sultee zai kirata ya tambayeta ya take da babynshi, mutane har dariya suka soma musu shikam ko a jikinshi. Anyi biki an watse, amarya a Manchester zata zauna da yake an ma Ahmed transfer daga Qatar, saidai mu musu fatan zuri’a d’ayyiba. Bayan biki da sati Sultee da Nafisa suka je Hamaz don Yabi ta damu tanaso taga Nafisa da jikanta da ke ciki, gaskiya Nafisa tayi sa’ar dangin miji don ba ‘karamin tarairaya suke nuna mata ba, Yabi tana matu’kar son cikin. Sunyi sati biyu sannan suka wuce, yana matu’kar kula da ita wane ‘kwai (Ya Allah kabamu masu sonmu tsakani da Allah), kullum baba Rabi, Amira, Ammi, mummy, Yabi duk sai sun kirata su tambayi lafiyarta, ita har tana mamakin su ganin yanda suka ‘kwallafa rai akan cikin nidai nace ba abin mamaki bane in akayi la’akari da shekarun Sultan don kuwa kowanne iyaye sunason ganin jikansu gashi yanzu sun samu ai dole suyi murna sosai. Cikinta ya cika wata tara suka dawo gida don haihuwa, Yabi taso suzo Hamaz amma Abba yace mata tayi ha’kuri tunda dai itama Nafisa za tafi so ta haihu a gidansu kuma anan ba zata sake sosai ba tunda gidan surukai ne, ba don taso ba haka ta ha’kura. Kwana uku da zuwarsu Nigeria cikin ikon Allah ta haifo ‘ya mace kamanninta sak Sultee, murna a wajenshi bazai fad’u ba, washe gari Yabi ta iso kallon jikanta don ta kasa ha’kuri, rungumeta tayi tana tuna lokacin da ta haifi Sultan don yarinyar tafi kama da babanta akan mamanta, baba Rabi ita tayi ungo zoma. Ana jibi suna Amira da Ahmed ma suka iso itama da d’an ‘karamin cikinta, tayi kyau abunta, da ta d’auki babyn har hawaye tayi a zuciyarta tace “Allah sarki, ashe rabon babyn nan ne yasa muka rabu da Sultan”, ranar suna yarinya taci sunan Amira don yace Amira ta cancanci fiye da haka daga wajenshi tunda ita ta sadashi da farin cikinshi, dama Amira tayi shopping na kayan suna akwati biyu, ai tuni tace tunda an mata takwara dole ta ‘kara kaya, sabon shopping ta shiga tayi ma little Amira har akwati biyar, baby ta tashi da akwati bakwai daga wajen takwararta, Sultee kam kaya kaman hauka yayi ma ‘yarshi da Gimbiya, bikin suna sai sam barka don naira yayi kuka, yarinya tayi farin jini. A daren ranar neh Amira ta gayama Nafisa cewa tasan Sultee yana sonta tun bayan aurensu da diary da tagani da dai sauransu har ‘karyar da ta shirya don su daddy su yarda ya saketa ba tare da sunga laifinshi ko nata ba, Nafisa mamaki ‘karara a fuskarta, ta ‘kara tabbatar da lallai Amira mai sonta ne na gaskiya wanda azamanin yanzun nan da ‘kyar asamu irinta, godiya bila adadin tayi ma Amira saka makon sadau’karwar da ta mata ta kuma yi al’kawarin bazata ta’ba nuna ma Sultee tasan maganar ba. Ranar da tayi arba’in akayi auren Saleem da wata ‘yar katsina mai suna Amrah, kowa sai yaba hankalinta yakeyi don yarinyar akwai nitsuwa. Bayan bikin ne suka koma ita da Sultee ta cigaba da zuwa school suna kula da Noor. Bayan 10 years Ba mu muka waiwaye su ba sai bayan shekaru goma, mun samu Sultee ya ‘kara zama babban mutum, naira ya ‘kara zaunuwa, soyayya tsakaninshi da Gimbiya kuwa kamar yau suka soma, ta gama makaranta amma ya hanata aiki wai yafiso ta dinga kula dashi da yaransu. Yanzu ‘ya’yansu bakwai, Amira wacce ake kira Noor, mai sunan Yabi wato Hafsat amma ana kiranta Mami, Ibrahim takwarar Daddy amma suna kiranshi Anas, Rabiya wacce suka yi ma baba Rabi takwara wacce suke kira da Futha, twins mata Fatima da Maryam takwarar Ammi da mummy ana kiransu Ilham da Ummitah, sai auta mai sunan Abba wato Mu’awiyah ana kiranshi Haneef. Yara kyawawa dasu sai Allah ya raya ya sa su girma akan turban addinin Musulunci. Anan muka ji labarin Amira yaranta hudu: Usman takwarar baban Ahmed suna kiranshi Zunnurayn, Abdullahi, Sultan ‘karami wanda ake kira Boy sai auta Fawziyyah ana kiranta Zeebly. Gidan Saleem da Amrah kuwa yaransu biyar: Nafisa ‘karama ana kiranta Feesha, Sabir, Sadiya, Abbakar Sadiq sai auta Aisha. Family ya ‘kara girma gashi kansu a had’e yake, every december gaba d’aya ake yin family re-union gwanin ban sha’awa. Ya Allah ka bamu zuri’a d’ayyiba mai albarka (Ameeeeen). Anan muka kawo ‘karshen littafin nan mai suna Gimbiya Nafeesah, duk kuran kuran da ke ciki Allah ya yafe mana. Gaisuwa zuwa ga: Aisha Naany(Allah ya saukeki lafiya), Sadydy gulgul, Shukurah, Amirah Maisikeli na Ahmed, Amrah Auwal Mashi, Bahiratu my crazy sis, Milly Balalau, Anty Muma, Hajju, Zainab Sifawa, Kdeey and duk sauran ‘yan Novels Novella da ban ambaci sunayenku ba, Allah ya bar zumunci. Godiya da jinjina zuwaga Fawziyyah maman Ilham, nagode ma Allah da yabani sister kamar ki, thank u for all the love and support, Jamila Moh Ali bansan ya zan gode miki ba, Allah ya saka da alkhairi, Khadijah body ke ta dabance. Excellent writers, Mu farka mata 1 & 2, House of novella na kdeey, Yau uwan juna na sisi axland, Zauren karatu na Sis Bena, M.Jabo munbarin hausa novels na Jabo our honourable admin, Be a lady with fashion na Futha, Sahaf’s Novels, Er lele hausa novel group, Maman Aleesha novels, Maman Haneep novels, matan kwarai na Serdeeyer, Hausa novels, Rookie Sadau novels, da ma duk sauran da ban ambata ba we luv you all da soyayyar da kuka nuna ma littafin nan. NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA), thanks for being here, duk members na ciki na gaisheku Allah ya ‘kara had’a kanmu ya kuma ‘kara basira. Dedicated to Faty Axland and Maryam Gidado (Ummieterh), love u loads and loads. Allah ya had’amu a aljannah baki d’aya (Ameen). Sai kun jini bayan exams a sabon littafina mai suna………. Www.haneefahusman.wordpress.com 07053072615.