GIDAN MIJINA. 🚨🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨🚨 Short story Story &written by MAMAN AFRAH Marubuciyar RAYUWAR MARYAMU AND NOW GIDAN MIJINA Alhamdulillah I am back again🤗 Page 1_2 Kwance take akan gadonta tana ta zubar da hawaye kuka take sosai amma ba mai fitowa ba,ji take gaba daya gidan ya mata Zafi,kai bama gdn ba jin duniyar take ta mata mugu mugun zafi,sbd irin kuncin da zuciyarta.wasu hawayen ne masu zafi suka kara kwaranyo mata,tunani take lokaci yayi da zata nemi saukakewar wannan kaddararren auren tunda abin ya fara zuwa da tozarci da kuma cin mutuncin iyaye.lallai anzo wajen da zuciyarta bazata taba dauka ba bare har ta jure,wannan zagin da kabeer ya mata tabbas yayi muni da yawa,shin mesa wasu mazan basu dauki mata a bakin komai ba? Shin mesa suka maida matansu kamar wata shara ko ma in ce bola gaba daya? Sake juyi tayi ta koma daya gefen hannunta dayan tayi filo da hannunta,tana cigaba saka a zuciyarta tana jin yadda hawayenta ke gangarowa akan hannun da tayi filo dashi.yau tsawon shekaru goma tana gidan nan amma bata taba yin dawwamammen farinciki ba,rabonta da farinciki mai dorewa tun tana amarya. sunyi hannun riga da farinciki in ma ta fara farincikin to tabbas ba dorarre bane,domin kwa bazata taba samun hakan ba daga wurin mai gidanta ba.dan dk yadda taso suyi zaman lpy irin na ma,aurata tokwa zai sanya kafa yayi fatali da hkn.ta kasa gane manufarsa ko dalili akan hkn,ko kadan baiso tayi walwala gashi dai auren soyayya sukayi,bare tace ko lika masa ita akayi shisa yake mata irin wannan wulakancin.tabbas zata dauki komai amma banda cin zarafin iyaye ta daure tare da wulakanci kala kala amma kuma bazata dauki zagin iyaye ba ,iyayenta ba wadanda sukayi wahala da ita ba tun tana yarinya, har kawo yanzu da mahaifinta ya koma ga Allah Sai mahaifiyarta.tabbas dole ta dauki mataki daya a Cikin biyu ,ko dai ta daina ragawa kabeer kamar yadda take masa,kawai tayi fito na fito dashi ,ko kuma ya sawwaqe mata taje gaba Allah ya bata wanda ya fishi. "Mama kukan me kike"fauzy ta fada itama tana hawayen. Saurin goge hawayen tayi dk da tasan fauzy din ta gani,tana juyowa tayi tana mika hannu ta kamo hannun yar tata yar kimanin shekaru tara a duniya. "My fauzy wa yace miki kuka nake idona ne yake ciwo shine yake ta zubar ruwa"aysha ta amsa mata cikin shakekkiyar muryarta da taci kuka ta koshi. "A ah mama tun dazu fa nake tsaye ina kallonki kina kuka kodai baki lpy?"fauzy ta fada tana tsare mahaifiyar tata ido. "Haba fauzy ba,aso yarinya ta gari mai son shiga aljanna bata musawa babba idan yayi mgn"aysha tace tana shafa kan fauzy" "Yi hkr mama nima inason shiga aljanna,kawai dai naga abbanmu yana miki fada,kuma har naji yayi zagi bayan kin hanamu zagi kuma a islamiya ma malam ya hana zagi amma shi abbanmu ya..... "Ya isa haka fauzy abbanku subutar baki yayi Amma ba zagi yayi ba,maza kije kuyi alwala keda yan uwanki yanzu za,a kira sallah,nima gani nan fitowa kinji yar albarka"aysha ta fada tana mikar da fauzy tsaye tare da shafa kanta. "Toh mama"fauzy ta fada tana fita daga dakin da gudu abinta. "Innalillahi wa inna ilaihir raji,un" aysha ta fada tana komawa ta kwanta akan gadon wani tsoro yana rufeta na yadda taji yarinyar ta rike cewa abbansu ya zageta ,ita da ko kadan bata yiwa yaranta tarbiyar zagi ba,sai dai ta cewa yaro "gidanku"amma yanzu kabeer yazo yana zaginta a gaban yayanta wannan wace irin rayuwa ce? Tabbas ba karamin bata tarbiya bane ace yaro mahaifinsa ya zagi mahaifiyarsa a gabansa ,kai ko ba mahaifiyarsa aka zaga ba lallai zagi na zubar da kima.yanzu meye mafita a gareta shin koda kabeer ya saketa dole dai zata bar masa yayansa a gidansa kenan tabbas tarbiyarsu na reto tunda shi bai damu da Ya basu tarbiya ba ,kullum itace mai kokarin basu tarbiya sanyasu suyi abu mai kyau ko hanasu suyi abu mummuna.amma shi ba ruwanshi da wannan kawai abinda ya Sani ya ciyar dasu shayar dasu da dauke dk wani nauyi da yake kansa amma bana tarbiya ba dan wannan ya sakarwa mahaifiyarsu, bayan kuma shima suna da hakkin ya tarbiyantar dasu. "Mama munyi alwala ina cayyayata?"ta jiyo muryar amira akanta tana tambayarta. "Mama nima ina cayyayata"amir shima da shigowarsa dakin kenan ya fada yana tsalle. "Ku bari auntynku tazo ta dakko muku ita ta linke muku dazu bansan inda ta aJiye ba"ta fada tana mikewa tsaye daga kan gadon domin shiga bayin dake cikin dakin,dan tasan yanzu ne yaran zasu dameta da tambaya. "Yawwa aunty fauziy ki dakko mana abin sallarmu inji mama"ta jiyo muryar yaran suna fada lokacin da take kokarin tura kofar bayin.domin gabatar da sallar magriba. Da daddare bayan ta yiwa yaran shimfida ta kwantar dasu,itama bayi ta shiga ta watsa ruwa ta fito ta dauki riga marar nauyi ta sanya,turare ta dauka body spray ta feffesa.fitowa tayi ta nufi kitchen domin dakko abinci taci sbd yunwa da take kwakular yayan hanjinta,amma kuma jin bakinta take kamar madaci domin gaba daya bata jin dadin jikinta.dan har ji take kamar zazzabi na neman rufeta ga wani ciwon kai da take ji kamar kan zai rabe biyu dk da tasan hakan bai rasa nasaba da kukan da tashayi. Bubbude food flask dn tayi amma kuma sai taji bazata iya cin abincin ba, kofi ta dakko da tea spoon ,dawowa falonta tayi ta dauki kayan shayi ta hada mai kauri tasha ,sannan ta dauki paracetamol guda biyu ta hadiya ,komawa dakin yaran tayi ta kara tottofa musu addu,a ,sannan ta leka dakin hinde mai aikinta ta fada mata take yawan leka yaran sbd zata je ta kwanta,amsa mata tayi da toh,sannan ta juyo ta koma,bedroom dinta ta nufa ta je ta kwanta.amma a maimakon barci yazo ya dauketa sai kawai maganganun kabeer suke ta mata amsa kuwwa take taji ranta ya baci wani kululun bakin ciki ya tokare mata makoshi,nan da nan wasu hawaye suka gangaro daga idanunta,tunowa da tayi da irin wahalar da tasha wajen nakudar yayanta tabbas haihuwa akwai ciwo nakuda nada wahala bai dace ba kuma bai ma kamata ba ace an wulakanta iyaye .dk wanda zai zagar maka iyaye ba masoyinka bane ,iyayenka dk rintsi iyayenka ne,dk kaskancin iyayenka sunansu iyaye,kuma matukar ka cika dan halak bazaka taba bari a wulakanta maka su ba.dk da wanda ya zageka kansa ya zaga amma tabbas yayi hkn ne dan ya nuna maka iyayenka basu da kima ko daraja a gunsa. "Yama zaki yarda kabeer yake ciwa iyayenki mutunci ta hanyar zagi bayan iyayenki su suka sha wahalarki ,sukayi dawainiya dake har kika isa abar sha,awa kabeer ya ganki yace yana sonki har kika aureshi?? Mutumin daya ganki da hakoranki talatin ya aureki,amma yazo ya wulakanta miki wacce tasha wahala wajen wankin kashin hakorinki?? Toh kema mesa kika ki ki rama zagin daya miki?tunda ay uwa batafi uwa ba kuma ubama bai fi uba ba kuma shima dole zai ji ciwon zagin idan kn mishi hkn zaisa ya shiga taitayinshi ya kuma fahimci menene zagin mahaifa....... "Bazan taba rama zagi ba,domin ni ba irin tarbiyar da aka min ba kenan,idan na rama mun zama daya kenan,sannan nima na zagi iyayen nawa kenan,kuma me zan cewa yaranmu idan nima na zageshi,kinga kenan zasu dauka zagi abu ne mai kyau suma sukeyi tunda ga iyayensu suna zagin juna a Gabansu,wlh ba tarbiyarmu daya ba ni Kabeer"ta fada da karfi tana kara fashewa da kukan takaicin abin daya mata tabطدbas idan ya dawo sai ya san yau ya mata abinda ta kasa jurewa, abinda bazata ma taba jurewa ba dan sai ko ya san zasu fara zaman bariki a gadn koma dai ya Sawwaqe mata baki a daya ta koma gdn iyayenta yaje ya auro wacce ya zageta a dalilinta. Ku biyoni domin jin yadda zata kaya,ina ftn littafin zai samu karbuwa domin zai zo muku da sabon salo.ngd MAMAN AFRAH♥️🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨 Short story Story & written by MAMAN AFRAH MARUBUCIYAR RAYUWAR MARYAMU AND NOW GIDAN MIJINA Alhamdulillah I am back again🤗 *SADAUKARWA GA BABANA UBANGIJI ALLAH BASHI LAFIYA👏👏* Page 3_4 Tana nan tana sake sake da maganganu ita kadai, ta zauce kamar dai wata marar hnkali,kallon agogon bangon dakin tayi wanda yake aiki babu jira ko kakkautawa.domin shi lokaci tafiya yake baya jira kwata kwata Kuma matukar lokaci ya wuce to kwa ya wuceni har abada bazai sake dawowa ba,sai dai wani makamancinsa mai irinsa ma,ana mai sunanshi Amma lokaci dayane tak kuma in ya wuce baya dawowa baya. 10:45 haka lokaci ya nuna wani bacin ran ne ya kara lullube wanda take ciki dk da ba yau bane karo na farko da kabeer ya kai wannan lokaci a waje ba,amma yau sai taga lokacin baya yin sauri hkn kuma baya rasa nasaba da jiran dawowarsa da takeyi dk da takan jira dawowarsa a dk sa,ilin da yayi dare dn kota kwanta ma barcin Bayard zuwa ,sai dai wani lokaci barcin yakan dauketa ba tare data sani ba,domin ance shi barci barawo ne.dan wani lokacin ma har yakan kai sha daya gashi dai tun dab da magriba ya dawo daga kasuwa,wanka kawai yayi yaci abinci wannan sabanin ya shiga tsakaninsu,shine ya kama hanya ya fice,itama wacce tazo ta hada mata sabanin ta tafi gashi ita sun barta da ciwon rai.kwafa tayi tana jijjiga manta alamar ay zaka dawo gida dk tsawon lokacin da zaka dauka a wajen.dk da ba yau bane ya fara dadewa. Tana nan a haka can sai taji karan bude get din gdn,saurin duba agogo tayi lokacin har sha daya tayi da minti biyar,maida idanunta tayi ta rufe sannan ta budesu dai dai nan taji tsayuwar motarshi.saurin kokarin tashi zaune tayi dan a lokacin ne zuciyarta ke kara azalzalarta akan aikata dk abubuwan data gama saka mata ,domin yau tabbas ba gudu babu ja da baya.kantane ya wani bala,in sara mata wanda hkn yasa tayi saurin komawa ta kwanta.tana jin lokacin daya shigo cikin gdn,domin tana iya jiyo maganarsu shi da mai gadi,tasan bai wuce kaya ne mai gadin ya dakko masa daga mota.dake bangarensa da nata a kusa da juna suke ,ba a jere suke da juna ba sai dai suna kallon juna. tana jin lokacin daya bude kofar falon nasa ya shiga,ita dai tana nan a yadda take. Bangaren kabeer kwa daya shiga Part dinsa mamaki ne fal ransa,daya ga bai ga aysha a cikin dakinsa ba ,da farko daya bude kofar falon bakinsa dauke da sallamq ganin bata falon sai bai kawo komai a ranshi ba.dn yasan yakan sameta a falo indai ya kai lokaci irin wannan koda kuwa ba kallo take ba haka zata zauna ta jirashi,idan kuma ta gaji da zaman falon takan koma can bedroom dinsa ta kwanta ,hr sai ya dawo,wataran barcin ya kan dauketa Amma hkn da wuya dan bata iya rintsawa idan bai dawo ba ,dk da kuwa ba wani tarba mai kyau zata samu daga gareshi ba.ganin bata kn bed dn kawai sai ya cire mamakin rashin ganinta a tunanisa ko ta shiga bayi,kayan jikinshi ya shiga ragewa da Tunanin in ta fito daga bayin ya dn watsa ruwa.bayan ya kammala cire kayan sai ya dauki tawul ya daura a kugunsa ya koma kn gadon ya dn kishigida,yana Jiran fitowarta dan shi kwata kwata yama manta da abinda ya faru tsakaninsu,bayan ya dawo kasuwa.jin shiru bata fito ba Kuma baya jin motsi ko karan ruwa yasa ya tashi domin dubawa,kwankwasawa yayi domin karya fara budewa ta tsorata Tunda batasan ya dawo ba dk da yasan mawuyaci ne ace bataji zuwan nashi ba,yana tura kofar yaga wayam babu alamarta,sororo yayi yana bin bayin da kallo kamar dai yana son gano rashin wanzuwarta a wurin,saurin banke kofar yayi ya maido kallonsa cikin dakin yanaso ya gano iya lokacin data dauka bata dakin shin sakanni ne ko kuma mintina ne kai kodai awanni ne ma? Yake yiwa kansa tambayar,ganin ya gagara gano amsar yasa ya baiwa kansa amsa da cewar tana dakin yara may be ko wani. cikinsu ba lpy.jallabiya yasa ya fito ya wuce dakin su Fauzy dan yasan babu abinda aysha zatayi a dakinta.ganin wutar dakin a kashe sai abin ja daure masa kai dk da hkn bai yi kasa a gwiwa ba ,sai d yaje ya bude dakin ya kunna kwan dakin yaga kowa akan katifar sa yana barci hnkali kwance,wai hausawa suka ce dare mahutar bawa. Part dn ayshan ya nufa yana ftn Allah yasa ba itace ba lpy ba, fitilun ko ina a kashe amma yaga na Dakin a Kunne dn haka can ya nufa ,yana tura kofar Dakin ita kuma tana mikewa tsaye kamar wacce aka tsikara d allura.wani Bala,in sara mata amma hkn ta daure ta mike sbd ynzu bata ciwon kan take ba,karasowa tayi gabansa tazo ta tsaya zekeke a gabanshi. "Me kike bakije dakina ba?" Itace tambayar daya jefo mata fuska daure. "Me zanje yi dakin naka ?"itama ta jefa masa tambayar tana rike kugu. Rintse idanu yayi jin irin amsar data bashi,yanajin yadda ranshi ya baci nan take dan ba halin aysha bane raini takanyi komai cikin girmamawa ,ladabi da kuma biyayya bata yin abinda zai sosa ranshi. "Ke wace irin mgn kike haka,kodai kinsha wani abun ne?" "Babu wani abu dana sha a cikin hankali na nake,ko kanaso in maimaita maka abinda na fada yanzu.... "Ke dakata dalla banason shirmen banza da wofi ,hr ni zaki tsaya a gabana kina fadan mgn "ya fada yana daga mata hannu alamar dakatarwa ya juya ranshi bace zai fita daga dakin. "Dakata kabeer"ta fada tana saurin shan gabansa.tsayawa yayi baki bude yana binta da kallon mamaki dn yanzu abin yaso bashi tsoro da yaji ta ambaci sunanshi a maimakon daddyn fauzy,anya ba aljannu bane suka shigi aysha. "Haba aysha meke damunki ne,zo muje ki kwanta"ja fada cikin taushin murya da mika hannu zai rike hannunta ya kaita ta kwanta a gadonta ya gudu dakinsa dn kar aljannun su nada masa na jaki. "Sakeni kabeer "ta fada tana warce hannunta. "Wai me kikeyi haka ne aysha "ya fada yana daga murya da karfi har dakin na amsa kuwwa. " bari kaji kabeer nifa ba sakarai bace da zaka zagar mn iyaye ka ficewarka daga gdn Kuma yanzu kazo kana mn wani zance daban kamar dai ba zuciya a Kirjina.kuma da kake Maganar mesa banje dakin kaba me zanje yi a dakinka,bayan ko naje ni ba kowan kowa bace a wurinka,inyi wanka in sanya kaya da dk wani namiji mai lpy inya gani zaiyi sha,awata in bi jikina da turaruka masu kamshi inje dakin naka amma kallo ma bn isheka ba,sai kana wani yatsina kamar dai kaga kashi ko wani abin ki.matsawar ba kai ne kake bukatata ba to babu abinda ya shafeka dani koda jikinka na kwanta sai kace meneneio so kake sai na bude Bakina nace ina bukatarka?ko an fada maka ni bani da hakki akanka? duk wasu hakkoki subi bayan auratayya wato kwanciyar aure, sbd jima,i shine aure ko so kake inke bin maza kamar yadda wasu matan Auge auren sukeyi? Kuma wasu Sunayin hakanne badan mazajensu sun gaza ba wajen biya musu bukatarsu ba ,sai dai dn Rashin tsoron Allah,sannan kuma basu dauki zina a bakin komai ba.Amma dk da bana Samun yadda nakeso haka nake hakuri tare da tsare kaina sbd tsoron Allah da Kuma kyamatar zina,sannan da tunanin makomar yayana. Domin nasan dole barewa ba zatayi gudu ba danta yayi rarrafe.sannan wulakanci kala kala kamar dai tsintoni kayi ba auroni kayi ba,amma dk da haka ,amma dk da haka(take fada muryarta na shakewa sbd tana maganar ne tana kuka,dan maganganun daga can cikin zuciyarta suke fitowa tana fada suna sukanta a ranta.) Amma dk da haka sai ka hada mn da zagin iyaye?iyayena su suka Haifan sukayi dawainiya dani har na isa abar moro na isa abar sha,awa ka ganni kace kanaso,suka baka ni ka aura,amma zagi shine tukuicinsu?nace zagi shine tukauicin su???? Yanzu kabeer wannan shine adalci da halacci?shine halaccin da zaka mn a rayuwa,ka zagen a gaban yayana ,a gaban ummulkairi,sbd kawai tazo ta fada maka mgn sai kahau ka zauna ba tare da bincike ba?kuma ay a iya zamana da kai yaci ace kasan abinda zan aykata da wanda bazan aikata......zaburowar da yayi kamar zai kai mata duka yasa tayi baya. "Dakata aysha wai daman kina cikin hayyacinki kenan,ashe ba aljannu suka tabaki ba ,har kike kiran sunana gatsal yadda aka yanka rago aka rada mn.wai daman dk akan abinda ya faru dana dawo daga kasuwa kike wannan tada jijiyoyin wuyan? kije har gidanmu ki yiwa hajiyata rashin kunya kiyi tunanin zan raga miki,sbd ga soko ko?wanda bai san abinda yake ba.hajiya ta aiko a fadi abinda kikaje har gida kika mata amma kice inyi bincike,kenan hajiyata zata miki karya kike nufi ko me?daman abinda kika shirya yi kenan shine da nace kuje ku gaisheta baki ce komai ba, to wlh ki sani ba,ayi macen da ta isa ta raina mn mahaifiya ba In kyaleta,dn akan hajiyata in rabu dake ba komai bane a wurina ba!" ya karasa yana nunata da yatsa kamar zai dungure mata goshi. "Idan hr gskia kake son sani ka tambayi fauzy mana ay a gabanta komai ya faru,sannan da kake cewa akan mahaifiyarka zaka iya yin komai kenan ni nawa iyayen ba komai bane na wani banza naka dukiya koh,to nima iyaye na suna da kima da daraja dan haka ba mai zagar mn su in kyale,ai kasan daman hajiyarka ba kaunata takeyi ba,burinta bai wuce na bar gdn nan ba bare ummulkairi dake Nunamin kiyayya kamar wata kishiyarta zata iya yin kom....... "Ke Aysha banason shirmen banza da wofi Idan ma zigoki akayi to ke kika sani,dan haka kiyi abinda zakiyi in ma kin kashe auranki kanki kika yiwa dan ni wata zan nemo na aura ga matanan bila adadin wasu ma neman Mazan auran suke sun rasa ,ke kn samu kina raina halayen mijin dan an zageki to wasu dukansu ake a gdn auren kuma su hakura su zauna ,bare wani zagi da ba fito miki zaiyi a jikinki ba. MAMAN AFRAH😚♥️ 🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨 Short story Story & written by MAMAN AFRAH MARUBUCIYAR RAYUWAR MARYAMU AND NOW GIDAN MIJINA Alhamdulillah I am back again🤗 *SADAUKARWA GA BABANA UBANGIJI ALLAH BASHI LAFIYA👏👏* Page 5_6 "Kabeer bari kaji in fada maka wlh wlh koda rama zagin nayi bazan huce ba,sbd na gwammace zagin ya fito mn a jiki da wannan radadin da yake mn a cikin zuciyata.wanda nasan kamin wani babban tabo a cikin zuciyata wanda a dk sanda na ganka zanke tunawa dashi,dk wani kima da kuma daraja da nake ganinka dasu tabbas wannan zagin da ka yiwa mahaifana zai ke gogesu,hkn bazai barni In bi umarninka ba ko Kuma in maka biyayya, kaga kenan samun Aljannata a karkashinki zai ke rawa, ni kuma zaman aure dn shiga aljanna nakeyi bawai dn dadin duniya ba. dan haka......wata azababbiyar tsawa daya daka mata ita ta dakatar da ita. " keeee ya isheki haka ,ko an fada miki ni tsaranki ne da har kike kallona kina fada mn son ranki, wato ke har sakaran Tunaninki yana fada miki ki zageni, lallai to tabbas kinyi kuskure idan har dakikiyar kwakwalwarki zata fada miki ni KABIRU ki zageni.tabbas dk laifina ne dana bari har raini ya shiga tsakaninmu,badan hkn ba ,banajin zakiyi koda mafarkin zageni ,bare har kiyi tunanin zagina.shiru yayi ya numfasa sbd yadda yake mgn da karfi har jijiyoyin wuyansa suna fitowa rado rado,ita Kuma aysha kawai kallonsa take ido cike da kwalla.cigaba yayi da mgn "To shikenan tunda kina ganin koda kn rama bazaki huce ba,bari a dakko madoki ki rike a hannunki sbd tsaro ,domin kuwa kina bude wannan bakin naki kika zageni wlh wlh wlh kinji na rantse da Allah hr sau uku,to duka zan sanya miki kinga sai ki rama da madokin naki.dukanki zanyi yadda gaba ko zagin na miki masu maiko bazaki tarki ramawa ba.in dakeki in ga wanda ya tsaye miki,da banda hauka da rashin tarbiya ya za,ayi mace da tarki zagin miji,wannan abinda kike ba komai bane illa rashin ilimi da kuma wayewa,shisa naso na auri mace wayayya mai matakin ilimin boko babba,ba irin naki ba karatu iya secondry scul ga irin ta......... "Kabeer cin fuskar ya isa haka da kasan da wayayyun matan ka barsu ka aureni?shin kasan da masu babban matakin karatun Bokon ka barsu ka aureni? Sannan ni nasan bani da wanda zai tsaye mn dan ka dukeni,sai dai Allah yana gani kuma shi zai mana hukunci ranar gobe ,kuma kome mutum ke takama dashi Allah ne ya bashi kuma muma Bai manta damu ba amma ka sani ni bazan zauna inayin zagi in zaga ba da miji da Kuma doki in duka ba,domin zaman ya tashi daga zaman aur Ya zama zaman bariki dan haka gobe gdn mu zan tafi yanzu ma dan dare yayi"ta fada ta cigaba da kuka. "zaman bariki?"ya fada yana binta da kallo.juyawa tayi zata fita daga cikin dakin,ta koma daya dakin nata domin dakuna ne guda hudu masu dauke da bayi akayi da tangamemen falo. "Hakan yayi tunda hakan kika zaba ,to kije na sakeki saki daya,kuma idan kn tashi tafiya goben karki sake ki daukarmin yaro ko daya ,kije gdn naku da kika dauka gida,zakisan ba kara Mn rufa miki asiri nayi ba,dana aureki,indai zaman gidane da Kuma zawarci ga fili ga .mai doki.ni Kuma zan samo wacce zata Maye mn fiye da gurbinki"ya fada yana doka wani uban tsaki tare da juyawa ya fice daga dakin gaba daya. Aysha dake tsaye ,tayi mutuwar tsaye tun lokacin daya furta kalmar saki a gareta ,ya datse alakar auratayya dake tsakaninsu,tun lokacin jinta da ganinta suka dauka na yan sakanni.kuma bata samu damar furta komai ba ,har sai da taji karan banko kofar falonta da yayi da mugu mugun karfi kamar zai karya kofar,durkushewa tayi a wurin tana sakin wani marayan kuka,mai bn tausayi,lallai kalmar saki bata da Dadin sauraro ga macen da mijinta ya furta mata duk da daman ta gaji da zaman gdn kuma zatayi Murna idan ya sawaqe mata kodan idan tana da rabon yin rayuwar farinciki a gaba,itama ta ji dadi da ni,imar aure,dk da tasan tabbas akwai kalubale a kowane gdn aure amma dai tasan ba kamar GIDAN MIJINTA BA dk da haka sai taji zuciyarta hr wani daci daci take,lallai sakin aure bashi da dadi shisa kenan al,arshin ubangiji yake girgiza idan aka yishi,shisa ubangiji baya son saki,gashi dai halal ne ,amma Kuma halal dn da ubangiji bayaso. Ummanta ce ta fado mata "yanzu umma Ya zataji idan taji kabeer ya sakeni?"ta yiwa kanta wannan tambayar. "Kiyi hkr umma wlh hakurina ya kare a gdn nan,tabbas idan naci gaba da hakuri wataran bakinciki ne zai kasheni,kuma shi ba damuwarsa bace,wata zai nemo yaci gaba da rayuwa,keda yarana kune da asara"ta fada tana kwantawa a wurin,wani tashin hnkalin na Baibayeta data tuna Rabuwa da yaranta bare ma yace karta tafi masa da yaro ko daya.juyawa tayi rubda ciki tana danne saitin zuciyarta da hannunta,yadda take jin tana bugawa d sauri da sauri ga wani ciwo da taji wurin nayi. "Lallai kabeer yau ni ka SAKA,ni din da kace bazaka iya rayuwa idan. Babu ni ba?nice fa kace bazaka taba rabuwa da ni ba,kai ne fa ka kasa hakuri in cigaba da karatu bayan nayi Candy,kana ganin kamar idan bamuyi aure ba wani zai iya zuwa ya rabamu da juna.haka na hkr mukayi aure sannan ka Hanani karatun a gidan naka,haka na hkr sbd farincikin ka sbd biyayyar aure,sbd na faranta maka.amma yau dk babu wannan alkawarurrukan na kafin muyi aure ashe dk ka manta da komai?"ta fada tana komawa rigingine ta maida tafukan hannayenta kan fuskarta, ta rufe idanunta tana jin yadda hawayenta ke kwaranyowa kamar an bude fanfo. *FARKON LABARI* Malam saleh dan asalin garin roni ne,dake jihar jigawa,iyayensu su biyu suka haifa Kuma Suka mutu suka barsu shida yayansa salisu.a lokacin saleh yana da shekaru goma sha biyar shi kuma salisu na da shekaru ashirin ,sun taso a Hannun kakarsu ta wajen uba wato iya a,i.ta nuna musu kulawa bayan rasuwar iyayensu hkn yasa suke ganin kamar ma basuyi maraicin iyaye ba. Tunda salisu ya kammala karatun secondary school bai cigaba da karatu ba,lokacin ma mahaifansu Nada rai sai kawai yake aiyukan karfi yana taimakawa iyayensa,sbd suma ba wani hali garesu ba ,Mutane ne masu karamin karfi.Bayan rasuwarsu ma bai sha wahala ba wajen taimakawa dan uwansa tare da kakarsu ba. A haka hr wani makocinsu ya masa mgn yace yayi shawara da kakarsa akan zai tafi dashi kano ,ya nuna masa sana,a yakeyi dn ya samu halin cigaba da rike Nauyin dake kansa.haka kwa akayi yake bn Makocinsu kano ya nuna masa sana,ar sai da kayan gwanjo,sannan ya bashi wurin zama a gdn shi sbd yana d gida a kn daman anan yake da zama kawai dai dan asalin garin roni ne.matarsa ma bata da matsala dan haka salisu ya yaso a hannunsu ,yana sana,ar sa,da Allah ya sanya albarka sai gashi har dila yakan karba ya bude Idan ya siyar ya dauke ribar ya hadawa masu kayan kudinsu,dan dama makocinsu Rabi,u shi ya hadashi da abokinsa mai bada dilar gwanjo bashi. Ana nan salisu idan ya kwashi sati biyu ko uku yake tafiya roni ya gano su iya a,i da saleh ,ya kai musu abubuwan bukata.a haka har yayi jarin kansa yake bude dila tashi ta kansa. Bayan shekara biyar Lokacin salisu har ya samu yarinya a makotan gdn m.rabi,u mai suna zainabu ,suka dai daita aka sanya musu rana aure ,a inda m.rabi,u ja shige masa gaba,ya kama musu hayar gida a yan kaba,daman shima a lokacin yana da shekaru 29 haka bayan tarewar zainabu yaje roni domin dawowa da iya a,i da saleh daman so yake idan yayi muhalli ya dawo dasu kusa dashi ,haka kwa ya dakkosu suka dawo gidansa da zama daman daki biyu ne sai iya a,i ta shiga daya su suna daya shi kuma saleh da zauren gdn da wani dan daki mai kamar shago ,ja shiga ciki. Tun daga lokacin salisu ya so ya nunawa dn uwansa harkar gwanjo amma yaki ,tunda shima dai iyakarshi sec din ,da suka dawo kano ma yace shi ba yanxu xaici gaba da karatu ba shi adai daita sahu yakeso yake ja,haka dn uwan ya kaishi aka bashi Adaidaita yake ja yana kai musu blance. Haka rayuwa taci gaba da tafiya hr zainabu ta haifi yarta,aka sanya mata suna hasiya,sunan mahaifiyarsu salisu ne.yarinyar ta taso cikin gata da kulawa,sosai saleh yake son yarinyar komai ya samu ihsan dake haka suke kiranta.Yarinyar tayi wayo tana yawonta ko ina. Wata rana da saleh bazai taba mantawa ba a rayuwarsa itace ranar wata Alhamis bayan ya tashi daga aikin adaidaita misalin karfe shida na yamma,daman shi bai fiya aikin dare ba ,bayan ya shigo gida da dare suka sha hira a dakin iya a,i sunayi suna cin naman daya siyo musu su kulli daya su salisu kulli daya,ihsan kuma ice cream,a lokacin da yake yiwa iya a,i sallama zaije ya kwanta,salisu ma ya shigo anan ya fasa tafiya suka zauna suna ta hirarsu,har iya a,i tana cewa shima saleh ya samo mata a masa aure suna da dariya.haka suka yiwa juna sallama kowa yaje ja kwanta.can cikin dare saleh yana barci yake jin kuka da ife ife,da sauri ja bude idanunsa,tasowa yayi da gudu ja fito daga dakinsa dake zaure ,yana fitowa yaga gaba daya cikin gdn naci da wuta ,wutar hr ta fara shigowa cikin zauren ,saurin bude kofar gdn yayi ya fita a rude kuma a gigice yana neman taimako. Gaisuwa gareku Queen fulani Hanoupa Mmn islam Mmn jidda B.jarda Mame yusuf 😍♥️♥️♥️ 🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨 Short story Story & written by MAMAN AFRAH MARUBUCIYAR RAYUWAR MARYAMU AND NOW GIDAN MIJINA Alhamdulillah I am back again🤗 *SADAUKARWA GA BABANA UBANGIJI ALLAH BASHI LAFIYA👏👏* Page 7_8 Kururuwa saleh Keta faman yi ,yana neman agaji da kuma dauki daga Jama,a,bubbuga gidajen dake makotaka dasu yake,ya buga nan ya dawo ya buga,can kan kace meye wannan mutane sun taru ana ta kokarin kashe wutar.wasu ruwa suke dakkowa daga gidajensu wasu kuma da ruwan kwata suke kashewa,kafin kace me an kusa kashe wutar,dan lokacin da yan fire Service suka zo kadan suka tarda wutar Bayan an kashe wutar aka shiga fito da gawarwakin,domin gdn yayi kurmus sai kaurin hayaki dake tashi,haka aka fito dasu gaba daya sun kone babu wani mai sauran rai a cikinsu🥲(UBANGIJI KA MANA TSARI DA WUTA,YA ALLAH KA HARAMTAWA WUTA CIN NAMAN JIKINMU DUNIYA DA LAHIRA AMIN).mutane kowa na fadin albarkacin bakinsa,wasu suce ko tsakace ta hada gobarar ,wasu kuma suce wutar nepa ce tayi spark,Allah ne masani .shi dai saleh yana kan gawarwakin a durkushe yana kallon ikon Allah.kuka yake dk ya zama kamar tabi tabi dn ma dai yana ambaton" innalillahi wa inna ilaihir raji,un"Gasu nan a laye akan babbar tabarma dake gdn makocinsu aka shiga dasu,yaya salisu,iya a,i zainabu,da kuma ihsan.tab lallai dan adam ba kowa bane shi ,shine ke daukan kanshi wani abu. Washe gari aka musu sutura aka kaisu makwancinsu,tun a ranar da daddare m.rabi,u ya ya tafi da saleh gdnshi dan daman kawai a kofar gida aka dn zauna ake karbar ta,aziyya.suma yan uwan zainabu a can gidansu zasuyi zaman makoki ,sbd gdn bashi da kyan gani ma.haka saleh ya dawo wani shiru shiru dashi dn sosai mutuwar ta tabashi,sai dai ya zauna yayi shiru sai da m.rabi,u ya dage sosai akanshi da Addu,a tare da nasiha sannan ya dn fara sakarwa yana dan walwala Bayan wata takwas da rasuwar su salisu, dole m.rabi,u ya matsa masa akan ya fara sana,a domin zama haka babu dadi,dk da m.rabi,u bai taba gajiya da daukan dawainiyar sa ba .daman akwai kudi 40k da mai gdn da salisu ke haya ya kawo masa ,kudin hayar da salisu ne ya bada na shekara 80k to kuma shekarar daya biya kudin nata bata kare ba,Allah ya masa rasuwa ,to shine ya kawo masa rabin kudin.dake mutumin dattijo ne mutumin kirki.wandan nan kudin sune m.Rabi,u ya bashi yaja jari dasu tunda yanzu baya son tukin napep dn. Saleh ya yanke shawarar fara sana,ar kayan miya sune yaga babu a anguwar,sai an je can bakin titi ake siyowa.runfa aka buga masa ta kwano da bencina,ya saro kayan miya dasu salad cabej d.s.nan kasuwa ta bude sosai ake ciniki dn dama mutanen anguwar sun gaji da zuwa bakin titi siyayya. Zaman saleh a gdn m.rabi,u shine sanadin kulluwar soyayya,tsakaninsa da atika,atika diya ce a wurin m.rabi,u sai kaninta habu.wannan soyayya itace takaisu ga aure .sunyi aure suna son junansu a inda wannan sana, a ta kayan miya itace take rike da saleh da matarsa atika cikin rufin.dan ci da sha zuwa sitira dk baya gagara da ma sauran abubuwan bukata na rayuwar yau da kullum,har ma ya kan taimakawa uba kuma sirikinsa m.rabi,u. Cikin zaman takewar auratayyarsu ce,Allah ya azurtasu da diya mace,saleh ya sanya mata sunan kakarsa iya a,i. wato aysha,suna kiranta da humaira. Yarinya ta taso cikin gata da kulawa dai dai karfinsu. Aysha yarinya kyakkyawa ajin farko a kyau,gata da shiga rai dan dk layinsu kowa yasan aysha.akwai natsuwa ,hankali uwa uba hakuri. Dan tun tana karama bata da yawan hayaniya,har dai ta isa shiga scul aka sanya ta Anan wata scul dake cikin anguwarsu, MUFTAHUL ILM dan daga gdnsu babu nisa dan haka a kafarta take zuwa tana dawowa,dan idan ta tafi da safe to takan dawo gida kafin karfe uku tayi ta koma islamiya dan duk hade suke boko da islamiya. Aysha tana da kokari sosai dan gaba daya malaman boko da islamiya,sun santa da kokari dn duk abinda aka koya tuni brain dinta ke nadewa ,komai ka koya mata zama yake daram akanta.sosai sauran students suke bakincikin kokarin da Allah ya bata,dn daga class dinsu na boko hr na islamiya bata taba haura first position.wannan yasa m.saleh da umma atika ke iya kokarinsu wajen ganin sun mata kyauta ta bajinta idan ta kawo report card din ta. "Ummana ina kika sanya min turaren wannan na duba bn ganshi ba"aysha ta fada kamar zatayi kuka sbd ganin ta kusan yin latti yau gashi itace da duty yau dole su zasu tare masu latti su da teacher dn dake da duty yau,idan kuma prefect tazo a makare to sai malamin ya mata hukunci fiye da sauran daliban da suka makara.yanzu aysha tana matakin jss2 ne kuma prefect ce dan dama iya jss3 senior scul dn tana can tsallaken kwalta. "yanzu kina ganin bakwai har da minti goma amma bazaki zo ki tafi ba ,kn tsaya neman turare,ace kullum mutum sai yayi wanki da guga indai yasa uniform bazai Maimaita ba gashi dai kayan ba wani datti suke ba,na fada miki babu kyau mace ta shafa turare in zata fita"Umma atika ta fada tana daga waje. "haba umma ynzu sai nayi latti, dn allah ki fada. min wlh banaso inke warin gumi,Kuma kinga turare bashi da karfin kamshi tunda Body spray ne"Ta fada yayin da take tsaye bakin kofar daki tana neman yin kuka. "Ay sai ki duba Cikin lokar wannan karama"umma atika ta fada tana juyawa domin cigaba da abinda take.juyawa tayi a guje taje ta fesa Turaren ta dakko scul bag dinta ta fito da sauri,dakin abbanta ta shiga ta gaishe dashi ya bata kudin makaranta ta fito ta yiwa ummanta sallama ta fito tana sauri dan lokacin har bakwai da ashirin da biyu. Misalin karfe biyu aka tashesu daga scul,su uku suke tafiya ita da kawayenta guda biyu,sun zo daidai inda zasuyi hanyar gdnsu sukayi sallama da juna ta kama hanyar layin da zai sadata da gidah. Tafiya take a nutse sanye take da uniform green din dogon wando da farar rigah iya gwiwa sai karamin farin hijabi da ko cikinta,kayan sun bala,in karbarta,yellow din dankwalinta na prefect ya bala,in fito da zallar kyanta,doguwar fuskarta tayi kamar jikin hijabin aka halicceta.ko daga nesa kake kana iya hango wata Tawadar allah a gefen kumatunta ,labbanta sun yiwa fuskarta ado dan idan ba wanda yasan aysha ba zaiyi zaton pink din janbaki take shafawa.alhalin matukar scul zataje bata shafa komai daya danganci kayan kwalliya daga kwalli sai ko perfume.gashi daga scul ta dawo amma in ka ganta sai kayi zaton yanzu zata tafi scul din sbd yadda kayan suke a goge dan tsabar sawun gugar dake, tsakaninsu.AYSHA SALEH RONI akwai tsafta sosai amma na fita tsafta😅😜 Dai dai kwanar gdnsu tana shirin tsallake wata yar karamar kwata ,irin makwaranyar wanke wanke ce aka mata hanyar wucewa zuwa babbar kwata,shine ta biyo ta kan hanya wani wawan hon taji an saki,dago kan da zatayi taga wata farar mota mai bakin glass dn ko na ciki baka iya gani.dakatawa tayi da tsallaka kwatar amma kuma kafin ta matsa,mai motar ya bi ta cikin kwatar gaba daya sai ruwan kwatar yayi jikin uniform dinta,dn hr fuskarta sai da ruwan kwatamin ya taba,gefen hijabin tasanya inda ruwan bai taba ba ta goge fuskarta,kallon kayanta take da gaba daya suka gama baci,juyawa tayi ta kalli motar kamar zatayi kuka dan tuni ma kwalla ta taru a idanunta,gani tayi motar ta tsaya. "Me hakan kb ya zaka tsaya akan wannan karamar yarinyar???"zuly ta fada tana tsareshi da ido. "Haba zuly ya zakice mesa zan tsaya byn kina ganin yadda na batawa yarinya jiki da kwatami"kabeer ya fada yana kokarin bude kofar zai fita. "To wai me kake kokarin yi ne hakuri zaka bata,kome kake nufi kamar kai dai kb hr ka tsaya baiwa wannan kazamar yarinyar hkr,kodan na ga tunda muka shawo kwanar nan idanunka akanta,daman garin kallon nata ka shiga kwatamin Allah ma yasa baka jefamu cikin katuwar kwatar can ba, dn kaga farar mace"Ta fada tana murguda masa baki tare da juyar da kai gefe" Kankance idanu yayi yana kallonta,dan shi kwata kwata bayason raini,dn bai yarda kowace yarinya rainashi ba,"An kalleta dn kiyi abinda zakiyi"ya fada yana Bude kofar ya fita daga cikin motar,saurayine baki dogo kyakkyawa dashi dan bakin nashi ma na kyau ne,sanye yake da wando dogo wanda aka yayyaga gwiwar sa,sai farar riga mai dogon hannu an yi rubutu a jikin rigar kamar haka LUV ME 🧡 sai kuma akayi hoton heart ,kafafunsa sanye cikin bakin sau ciki. Kallon wurin daya ganta tsaye ta cikin mirrow dn motar yayi,lokacin tana goge ruwan fuskarta da hijabinta.amma me kamar anyi ruwa an dauke babu ko alamarta a wurin bare ya sanya ran ganinta,Hangawa ya shiga yi wai ko zai ganta amma bai ganta ba. "Oh God ina yarinyar nan ta shigane"cewar kb yana dafe goshi.juyawa yayi jiki ba kwari ya koma motar,"to ko dai aljana ce?"wani sashen na zuciyarsa ya tambaya. "Wayyo Allah kuyi hkr ku kuke ganinmu bamu ke ganinku ba"ya fada a tsorace dn kb akwai tsoron aljannu Zuly kokarin danne dariyarta take, dan ta fahimci inda tunanin kb yaje sosai tayi farinciki dn tasan yanzu sai yace yanason yarinyar bazaiga kankantarta ba,dn shegen son matane dashi.ita kuma taga lokacin da yarinyar tayi tafiyarta. "Ayya sorry insha Allah ay kafi karfinsu ,bazasu maka komai ba tunda ba da gan gan ka mata ba"ta fada dn ta kwntar masa da hnkali.kallonta kawai yayi ya maida kanshi kan styarin ,dn bayaso ko kadan ta gane ya tsorata dan karta rainashi.zuciyarshi ce ta bashi gwara ya bar wurin kar wani abu ya faru dashi.key ya yiwa motar ya figeta a guje yana barin layin ma gaba daya. Aysha kwa ganin sun bata mata kayanta yasa tayi tafiyarta,dan tasan tsayawar da sukayi ma zasu iya dukanta tunda duniya ba gskia yanzu,sai a dannewa bawa hakkinsa matsawar bashi da karfi ma,ana idan shi ba kowan kowa bane.wato bai ajiye ba bai kuma baiwa wani ajiya ba. Tafiya take kanta a sunkuye dn gaba daya kunya take a ganta a haka dk da ba sabon aysha bane kalle kalle ahanya,dn ma dai ta kusa zuwa gida,ita daman bata da fada gata kuma da zallar hkr ,dk da taji ciwon bata mata kayanta da akayi Amma bazatace komai ba ,bare ma bataga na cikin motar ba.shiga gdnsu tayi bakinta dauke da sallama,umma ce ta amsa mata,tana shigowa tayi ido biyu da kawunta kanin ummanta kawu habibu ya kawo musu ziyara. "Oyoyo kawu"ta fada da murna.su kuma tsayawa sukayi baki suna ganin yadda kayqnta ya baci,itama kallon jikinta tayi inda taga suna kallo Dan tabe baki tayi tace "wata motace ta fallatso min da zata wuce"aysha ta amsa kafin a jefo mata tambayar. "Kawu bari inyi wanka inzo mu gaisa ka bani labarin tsoffin nan"cewar aysha tana juyawa ta shige daki. 🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨 Short story Story & written by MAMAN AFRAH MARUBUCIYAR RAYUWAR MARYAMU AND NOW GIDAN MIJINA Alhamdulillah I am back again🤗 *SADAUKARWA GA BABANA UBANGIJI ALLAH BASHI LAFIYA👏👏* Page 9_10 "Magana fa nake miki aysha kinyi shiru"kawu habibu ya fada yana saurarenta Tsayawa tayi da cin abincin take juya spoon din a cikin a bincin kawai ,dn ita bata san me zata ce masa ba. "Wai humaira mesa ke kullum idan mutum yana bukatar amsarki sai yasha fama. "Wlh umma kamar yanda na fada banma san waye ba a cikin motar ba,dan ni juyawa nayi kawai na tafi ba tare dana jira ganin mamallakin motar ba"cewar aysha taci gaba da cin abincinta dn so take tayi sauri ta tafi dan karfe uku saura yanzu,kar ta Makara islamiya. "Shikenan ni daman nasan ba a fada aka watsa mata kwatar nan ba,dan ba halin aysha bane fada"cewar umma atika tana cigaba da tankadan garin tuwo. "Hmm aunty ay kinsan mutane ne ynzu kansu kawai suka sani basa tunanin wani,indai mutum yasan yana da abin duniya to taka wanda bashi dashi ba komai bane.dan dai tace yayi attempting dn tsayawa,ta taho alamar zai bata hakuri yasan ya aikata ba daidai ba, Amma Wlh badan haka ba idan da zan yi ido hudu dashi sai na masa fiye da abinda ya mata.su masu kudi gani suke talaka bashi da gata shi ba kowa bane"kawu habibu ya fada yana cika yana batsewa. Murmushi aysha tayi tana tashi ta ajiye plate dn data ci abinci ta shiga daki domin dakko jakar islamiyarta. "Yanzu dai ay shikenan tunda wacce aka yiwa abin ita ta hakura,tunda kai bakada hakuri komai aka maka sai ka dau fansa,fisabilillahi rayuwa ta iyu a haka habibu,komai fa na duniya dan hakuri ne,duka ma duniyar nawa take"abba da fitowarsa kenan daga bayi ya fada yana ajiye butar hannunsa. "Wannan haka yake Allah dai yasa mufi karfin zukatanmu" cewar umma. "Amin"abba da kawu habibu suka fada a tare. Aysha ta fito ta musu sallama domin tafiya islamiya,sakon gaisuwa ta bada a fadawa kakaninta.fita tayi ta barsu suna dan tattaunawa,ita kuma ta kama hanyar makaranta. A Bangaren kabeer da zuky kwa bai zame ko ina ba sai a kofar gdnsu zuly,tun da suka baro Inda ya fallatsawa yarinyar kwata bai kuma cewa uffan ba.itama zuly ganin babu fuska yasa ta kama bakinta,sai dai lokaci zuwa lokaci takan juya ta kalleshi.tunda suka taho babu abinda yake sai cika baki da iska yana hurar da ita,sai kuma ya sauke ajiya zuciya.yana tsayar da motar ya koma ya jingina da kujera,Zuly ce ta juyo gaba daya ta kalleshi Kafin ta fara mgn. "Haba kb wai dn allah mesa ka damu kanka da abinda ya faru,kwata ce fa kawai ka watsa mata shima bawai da gangan ba,to amma kuma kazo kana damun kanka kamar wani wanda ya kade mutum ya mutu,kawai ka manta da ita ka dawo Normal ,yarinyar da ganinta kasan yar gdn talak..... "Stop it! Dalla malama fitar min a mota"ya mata rai bace yana hayayyako mata. Zuly data saki baki tana zuba kamar lalataccen fanfo,jin ya doko mata wata tsawa ya sanya ta tsorata.saurin bude kofar ta fita a hanzarce,ta rufo masa kofar jiki na rawa dn tasan halin kb ba mutuncci yanzu sai ya shuka mata tsiya. Ganin ta bar masa jakarta ya bude kofar ya iyo cilli da ita,rufe kofar yayi,reverse yayi ya figi motar a 360. Zuly da har ta kama karamat kofar get din gdnsu,taji faduwar wani abu dimm,dake ko karan bude kofar da kb dn yayi bataji ba sbd tana rufe masa kofar ta juya tayi tafiyarta,dn tasa ba karamin aikinsa bane ya bula mata kasa ya kara gaba abinsa.ganin jakarta ce ya jefo mai tarin buks da handout wadanda take siya take ajiyewa dan ba wanda take karantawa daga ciki kawai tana siyane dn ta yiwa iyayenta basaja.dan bata shiga ko shiga class iyakarta bn samari,suyi ta zuwa Shopping da zuwa wajejen shakatawa daga karshe a dawo da ita gida. Yanzu ma daga scul suke kb yaje ya dakkota dan dukunsu B.U.K suke karatu sai dai ba department daya suke ba. Yatsina fuska tayi tare da tabe bakinta , tace " mayen mata kawai kai dai ba damar kaga mace sai kace kana sonta ,banda shegen son mata ni banga abin so a wannan kwailar yarinyar ba" ta fada tana jan tsaki, juyawa tayi taje ta dakko Jakarta ta shigewarta gida. Zulaihat wacce ake kira zuly yar gdn alhaji abdulrazzaq ,mahaifinta yana da kudi sosai sai dai mutane ne wanda sukasan abinda sukeyi .domin kudin da suke dashi bai sanya sun kasa baiwa yayansu tarbiya ba,saidai zuly bata jin mgn dan cewa tayi indai ba kasar waje babanta zai kaita ba bazatayi karatu ba.shi kuma yace dole sai dai tayi karatu a nigeria,dn bazai kai mace karatu waje ba,ita kuma dk yayunta mazane kuma dk cikinsu ba wanda yayi karatu a nigeria,shisa take gani babanta yayi son kai,dn haka bayan ya samo mata admisson a B.U.K aikwa take yaudarar iyayen dan ba karatun take ba ,su kuma basu da masaniya akan abinda take aikatawa dan har bn maza takeyi ,tana iskancinta ba tare da sun sani ba.(Allah ka shirya mana zuri, a ka mana katangar karfe da zina ameen). Kabeer tunda ya bar kofar gdnsu zuly yake so ya danganta da gdnsu,shi dai yanaso ya gskata cewar wannan yarinyar ba mutum bace in ba haka ba ya za,ayi tunda ya hadu da ita ya rasa Sukuni a zuciyarsa, shi da bai fiya sanya damuwar kowa ba a zuciyarsa,amma gashi ynzu ya sanya damuwar yarinyar da bai ma santa ba to idan dai ba mutanen boyen bane suka ajiye masa damuwar a ransa ba mesa hkn zai dameshi?"gashi kwa da ranar nan tabb babu tantama ma aljanu ne"wani bangare na zuciyarsa ya fada,daram damm gabansa ya yanke ya fadi,wani gumi ya tsatstsafo masa,tissue ya cira ya goge gumin."kodai tausayinta ne ya kamaka ganin ka mata rashin kyautawa amma kuma ta hakura ba tare da ta tsaya bama bare tace uffan"wani sashen na zuciyarsa ya kara fada.wata boyayyar ajiyar zuciya ya sauke,dan yadda da batun da zuciyarsa ta fada masa yanzu. A dai dai wani tangamemen gida tsaya,tare da sakin wani uban horn,mai gadin ne ya dan leko domin ganin mai horn din ganin motar gdn yasa yayi saurin tura get dn ya bude.shigowa yayi ya samu wurin da aka tanada dn ajiye motoci yayi parking.kafin ya bude kofar ya fito yana maida kofar ya rufe,mai gadin ne ya karaso yana masa sannu da zuwa,hannu ya daga masa ba tare da yayi mgn ba.hanyar part dn sa ya nufa,Ko me ya tuna kuma ya juya ya nufi sashen hajiya lubabatu,kofar falon ya tura shigowa yayi ba kowa a falon sai tv dake ta faman aiki,zubewa yayi akan kujera ya dan kwantar da bayansa ajikin kijerar sanyin ac na ratsashi.zamansa keda wuya sai ga hajiyar tana sakkowa daga stairs,sanye take cikin lace da aka yiwa dinkin buba tayi daurin dankwali ture kaga tsiya,hannunta rike da waya.har ta sakko bata lura dashi ba sai data zo cikin falon. "Autana yaushe ka shigo gdn bn sani ba?"ta fada tana zama a kusa dashi . "Yanzu"ya fada a shagwabe yana maida kansa kan cinyarta ya kwantar. "Ya na ganka haka ko karatun ne ya maida kai haka,ko kuma yunwa kake ji"ta fada tana shafa kansa. "babu komai kawai na taho daga scul shine a wani layi na fasawa wata kwata shine abin ke damuna"ya fada Yana marairaicewa. "To banda abinka meye na damuwar baka bata kudi taje car wash a wanke mata motar,ay indai akwai kudi to babu damuwa dn kudi sukanyi komai,idan nace komai ina nufin komai"cewar hajiya tana kallon fuskar kb. "Bazaki gane ba hajiya yarinyar fa ba,a mota take ba" "A me take"tayi saurin katseshi. "A kafa" "Kafa fa kace?to meye dn ka watsawa mai tafiyar kafa kwata,ai daman dole mai tafiya a kafa ya rakabe mai mota ya wuce indai ba hasada ba,ko kuma anaso a samu na siyen garin kwaki shisa ake tarar mai mota ya fatsa tunda ai shi dai mai akwai bazai bada hakuri ba saidai ya bada abin duniya wato kudiiii" "Hajiya itafa wannan yar yarinya ce karama kuma ni ne da laifin ba ita ba tayi kokarin kauce mn amma na watsa mata kuma da kike maganar abin duniya wlh yarinyar ko tsayawa batayi ba tayi tafiyarta" "Bata tsaya ba"Ta tambaya fuskarta dauke da mamaki. "Eh"ya bata amsa a takaice. Amma autana anya kwa mutum ce,a wannan zamanin da mutane ke cikin babu,wasu kamar su kwata ace an watsawa mutum kwata ya tafi ba tare data maka tsiwa ba ko tace sai ka bata kudin sabulu? Saurin tashi zaune yayi daga kwanciyar da yayi,ya kama hannayen hajiya duka biyu ya rike "Wayyo hajiya nima nayi wannan tunanin ,wayyo Allah nah kar taje ta shiga jikina ta cutar dani"ya fada tsoro fal fuskarsa. "Kai ba lallai bane ba aljana ce kasan talaka ma akwai masu wadatar zuci watakil tana da hakuri ne,shisa ta tafi ko kuma taga mai mota ba Sa,an fadanta bane kar aje karamar mgn ta zama babba"hajiya ta Fada dn ta kwantar masa da hankali amma a ranta tayi mamaki kwarai dn ita dk tunaninta talaka babu abinda yake bukata a Hannnun wanda ke da wadata Sama da kudi. "Haba yauwa hr naji dadi,me za,ayi da mutanen boye"ya fada yana jin karfin gwiwa.ganin hajiyar ta zare ido ya gane yayi baranbarama. "A,ah ba me za,ayi daku ba nake nufi"ya canja maganar ,dn kar aljanun nan da ake ciwa na gida su jishi ,dariya suka sanya dukansu,suna mikewa suka tafi domin baiwa cikin haqqinsa.dan lakacin sun san Yaya abdullahi ya dawo da kuma daddy. 🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨 Story & written by MAMAN AFRAH *Ku* yi *hkr* *na* *jina* *shiru* k *wana* *biyu* *sbd* *wani* *dalili* *ngd*😍 Page 13 &14 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHM " Nace aikin me ta maka da zaka biyota da kaya har gida"abba ya fada yana bin kb da kallo. "Wlh abba babu aikin dana masa dan Allah ka yarda dani"aysha ta fada wasu hawaye na bin kumatunta. "Bake aka tambaya ba rufe mana baki mai arahar hawaye"umma tace tana harararta. "Da kai fa ake ka tsaya kana karewa Mutane kallo"cewar umma tana aikawa kb wata Uwar harara dn bataso ko kadan yaga fuska a Wurinta sbd gaba kar yayi gigin kara tare mata yarinya a Hanya. "ba dan wannan Babyn da kuka ajiye ba ku kun isa kpu ganni ma,bare har ku samu damar fada min magana.ya fadi hakan a zuciyarsa ,a zahiri kuma sai yace"Wlh abba babu wani aiki data min kaji ma da kanta furta haka da bakinta"kb yace yana Maida fuskarsa ta salahan Mutane dan su kara yarda dashi. "To Meye amfanin bayar da Kaya,tunda bata Maka wani aiki ba?ko ladan aikin ne ya fara zuwa a gaba kake so ta maka aikin ?"umma tace tana kama tsantsa tare da karkata kai. "Nifa kamar yadda na fada cewa babu aikin data mini,kuma haka ta fada da bakinta bata mini aiki ba.kuma babu wani aiki da zata min anan gaba kawai zan bata ne dan Kyautatawa kum.......... "Dk Mutanen dake da bukata baka gansu ba sai aysha kawai ka gani?"abba da tun dazu baiyi mgn ba ya katseshi da tambayar. "Ba haka bane" "Yaya ne?"cewar umma da ta matsu a sallami kb kosa koma cikin gida. "Wato na fallatsa mata ruwan kwata ne to a maimakon ta min rashi n kunya sai tamin saba nin haka to shi ne hkn ya Burgeni nakeso in Kyautata mata,ita Kuma ta dau ko cutar da ita zanyi shi ne take ta Gudu,amma Allah yana kallo bani da cutar da ita amma in haka ya bata mukru rai dan Allah ku gafarce ni"kb ya fada yana ajiye ledar ka yan a kasa ya hade han nu wuri 1 alamar roko. "Sauke Hannu wan babu komai amma ka tafi da ka yan ,kuma inaso daga yau ko a Ins ka ganta babu kai ba ita bare har kace zaka bata wani abu"abba ya fada yana mika Hannu ya kama Aysha,ya yi wa umma nuni da su koma Ciki.dai dai kofa aysha ta wai wayo ta kalli kb dake kallomsu kamar ya bisu. Shima leder ya dauka yana bai wa wannan yarinyar dake wasa karba ta yi tana tsalle tana cewa ta go de amma kb ko saurare baiyi ba ya tafi zuciyarsa na wani iri ga zafi da Ransa ke yi dn shi gani yake Sun wulaka n tashi,shi da yake da mata masu aji sai wacce dama zai kula amma Suna tsareshi da tambaya kan wannan figigi yar yarinyar tun bai ce yana SONTA ba.haka dai ya karasa gün motarsa ya shiga ya figeta ya tafi. Tun daga wannan ranar kb bai sake ko da kallo Hanyar da zata sa dashi da angu war su aysha ba.sai dai kuma tana nan Zaune dara ram a zuciyarsa,dn yanzu dk ya dai na kula Yanmatam nasa ma sai zulaihat dake nace masa taki rabua dashi.yanzu bama ya zuwa ko ina sai dai ya Zauna yana ta tuna ni gaba 1 ya shiga damu wa ko yaushe bashi da tina ni sai aysha so yake ya ganta ko ya Samu sassauci a zuciyarsa. Aysha kwa Tun daga wannan ranar bata sake tuno da kb ba,umma ce ma take tambayarta ko ya kuma tare ta a hanya amma sai tace bai sake tare yaba ko motarshi Bata Sake gani ba,bare shi tun ummar na tambayarta har dai daga karshe ta gane ya tafi bazai dawo ba.sai dai ita aysha tana tuna shi ne kawai in zata wuce ta Wurin da suka hadu dashi,tana sauri ta wuce Wurin dan tana gani kamar zai sake bi yota dan haka data iso wurin take kara wutar sauri kamar taci da ka.dan Kullum gani take yana Nan yana jira tazo ya bita da gudu.daga karshe dai kullum tazo wa Jen sai ta hau kira suna yen Allah. AFTER THREE WEEKS Kabeer ya shiga damu war da bai taba zato zai shigeta ba a iya rayu warsa ba, gaba daya yayi baki ya rame baya iya komai sai yana tuna aysha dk ya fita hayyaci nsa.hatta hajiya ta kasa gane meye damu warsa,sabo da yaki ya fada mata dan ya tabbatar matukar ya sa nar mata to kwa da gagarumar matsala dan zata je ta shuka musu rashi n Mutinci domin tana Iya cewa asiri suka masa suka dauke masa hankali. Wannan dalili yasa ya boye musu gaba daya damu warsa,dk da sun damu da damu war tashi.haka yake ta kar yar zazzabi yake,sun kaishi asibiti ba ada di amma kullum abu sai kara cigaba yake. Kb dai yaga abu yaki da dadi dan haka ya nuna musu ya samu sauki dan yana so ya fita dan ya je yaga abar so kuma mura din zuciyarsa.dan matukar bai nuna ya warke ba to baza,a barshi ya fita ba bare har ya je ga mura dinsa . 😍😍😍😍😍😍😍🚨GI DAN MIJI NA🚨 Story &written by MAMAN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION. Page15 & 16 Tunda ya dawo daga masallaci da asuba bai koma ya Kwanta ba,wanka ya sake shiga dama da zai tafi masallaci ya yi wanka.ya fito ya shir ya da wani farin lallausa yardi da aka yi masa dinkin Hannu sun yi matukar masa Kyau.hula da agogo yasa takalmi yasa ya dauki phone dinsa ya kira hajia ya fada mata zai je sutura kakar wani friend dinsa ta rasu ,hajia addu,a ta mata tace sai ya dawo dan dama damu war da yake bataso kuma sai take gani kamar ba zazzabi bane kadai ke damu warsa.key din mota ya dauka ya fita yana ta zuba kamshi.karfe 6:55 agogo ya nuna ,sauri yake yana so yau ya ganta before ta je scul dan bazai jure ba har a tashe su daga scul ba. A nesa da Inda yake parking ya faka motar ya fito time ya duba 7:19 dan yayi ta Yanke amma da go Slow bazai bari ya iso da wuri ba.tafia ya soma yi a kafa ya dan yi nisa da Wurin motar samu wuri yayi ya labe.dammm Zucker ta Bada da ya tuna ko ta dade da tafia sauri yayi ya duba agogo 7:39 ya salam yace yana jin wani zazzabi zazzabi na nema ya rufeshi runtse Ido yayi da karfi yana jin kamar ya kurma ihu ko ya samu sassauci daga rada din da yake ji a ransa ,bu de da Ido yayi da ya ji bugu na zuciyarsa na karu wa,kamar an ce ya dago ai kwa ya hango aysha na tafe a nitse kamar yan da ta saba tafia.ajiyar zuciya ya sauke mai nau yi yana kara bude ido sosai yan da zai ke hangota sosai harta zo ta kusa dashi ta wuce ba tare data ganshi ba,shi kuma kura mata Ido yayi tamkar zai fito da Ido.dad da dan kamshi turare data barshi dashi mai sun yin kamshi shi ya kara rura wutar so a zuciyarsa.daker ya lallaba ya koma motarsa ya tafi dan har karfe 8:10. Tun daga wannan ranar kb kullum sai yazo dad yaga Aysha dan har sau biu yake zua amma time din da aka tashe su daga boko yake zua,sai kuma ya dawo da yammaci In an tashi daga islamia ya daina zua da safe ne dan kar hajia tasa ake binsa aga Inda yake zua karshe azo a samu matsala.yayi sati biu yana zua ba tare da ya bari aysha ta ganshi ba ko sau daya ba kuma yayi haka ne dan kar ta fada a girda cewar yana zua.Amma kuma shima hakuri yake kawai Dan ya kosa su hadu da aysha ba wai yake gani ta shi kadai ba,so yake su harda Ido da ita dan haka yau ya yanke Shawara zai fito ta ganshi koma mai zai faru sai dai ya faru. Karfe 5:00 ya gama shiri tsaf ka na Nan kaya yasa,bakar riga mai kara Min Hannu an rubuta GUCCI a jiki da capital letters sai Jeans da takalmi mai yatsa,sai agogo da man yan zobe na azurfa yasa ya fesa turaruka masu kamshi.Phöne nashi ya dauka zai kira fried dnsa aliyu sai kuma ya fasa dn bai so ya kawo masa matsala dn aysha ba 1 take d بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *_______________________________________ 🚨🚨GI DAN MI JINA🚨🚨 Story & written by MAMAN AFRAH Page 17 &18 Hannu mika ya dago habarta,tasa hannu ta buge masa Hannu daga habar tata.hannu yasa ya rike duka hannun nata ya ha desu guri Guda ya rike da hannu 1 Sunku yar da Kanta ta yi tana cigaba da kokori ta kwaci hanna Yenta amma ina ya musu riko mai karfi da bazata kwace ba. hannu1 yasa ya kara dago fuskarta dake jike da hawaye dn kuka take sosai tana tuna fada da kkuma kashe da ummarta ke mata na kar ta kuskura ta bari nmj ya rike ko da hannunta ne bare har ya taba mata jiki.baki ta kai zata cijeshi ya yi sauri ya Jan ye Hannun. "Ka sake ni banaso"tace da murya mai Sanyi da Sanya yawa. "To me ye dn na rike ki?"ya tambayeta yana mai kallon kwa yar Idonta. "Ay ni ba yar iska bace,kuma naga su abba Sun mana tsakani da kai"tace tana bata rai alamar bataso. "To ay nima ba dan iska bane kuma wa yace miki an mana tsaka ni dama ba tsaka ni aka mana ba yanzu ma tambayarki zan yi Kina bani amsa zan tafi sai kuma gobe zan dawo. Saurin zaro fararen Idonta ta yi jin yace zai dawo gobe. "Tambaye ni amma kar ka kara dawo wa" "Ya Sunanki?"ya tambaya yana murmushi tare da kanne Ido. "Ka sake min Hannu in fada maka" Ajiyar zucia ya sauke mai karfi'Sannan ya sakar mata Hannu. "Suna na AYSHA HUMAIRA" "Ni kuma Suna na KABEER"'yace yana wani kasataccen murmushi. Tabe baki ta yi ta Juya zata tafi,hannu yasa ya riko hijabinta. "wannan ba irin tarbiyata bace kar ka kara "tace Ranta a mugun bace tana masa kallon up And Down. "Sorry"Yace yana jin dadi a ranshi ya samu mata ba kamar yan matansu ba da in ka taba mace ko a jikinta kai wani lokaci ma suke tabaka.Allah shirya mana amin. Juyawa ta yi a hanzarce ta fara tafia ba tare da ta kuma bi takanshi ba. "I LUV YOU AYSHA"yace da Dan karfi yan da zata ji yoshi.saurin tsayawa Tayi tare da juyowa yan da taga ya wani tsaya ya maida hankali yana kallonta kamar wani mai jiran tsammani sai ya tuno mata da wani malaminsu da ya musu TP mai Abin daria hakan data tuna sai yasa ta saki murmushi mai san yi kafin daga bisani ta juya taci gaba da tafia Abinta. Tabar kb da baki sake yana bin bayanta da kallo har sai data bacewa ganinsa,murmushin da ya gani kwance a fuskarta shi ya kara dulmiyar da zuciyarsa cikin kogin sonta.dn gani yake kalmar daya furta ce ta sata murmushi.hannu ya dunkule ya naushi iska tare da furta yessss,mota ya shiga ya kure music ya fita da gudu ranshi fari kal. Aysha haka ta karasa gi dansu tana ta bata rai akan tabata da kb ya yi.haka ta shiga gida da fargaba dn tasa a ranta matukar umma ta tamba yeta dalili na Kin dawo warta da wuri to bazata Boye mata komai ba,sai dai tana tsoro tace har Hannu ya rike mata.sallama ta yi umma dake Bayi ta mata gyaram mur ya.shiga daki ta yi take cire Uniform dn kamshi ta ji wanda bana ba tuno mutumin da ya rike mata hijabi v ta yi wan da ya kira kanshi da Suna kabeer Nan ta ji gabanta yay mummunan bugawa haka kuma yay dai dai da kiran da umma take kwala mata wanda haka ya kara sawa ta rude ta dauki uniform din ta turasu a Drower tana zare Ido.بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *_______________________________________ 🚨🚨GI DAN MI JINA🚨🚨 Story & Written by MAMAN AFRAH Page NINETEEN & TWENTY Wai humaira me kike ne a daki sai kira nake Amma baki fito ba"umma tace daga tana rike da buta. "Ki hkr umma na amsa Kaya nake linke wa Gani Nan zua."humaira tace tana fito wa daga Daki gabanta na doka wa da karfi. "Ki kula kizo ki yi alwala,ki yi sallah"umma tace tana fara tata alwalar. "To umma na"Tace tana sauke wani numfashi, ta dauki buta ta nufi bayi tana mai gode wa Allah da umma bata tamba yeta me yasa ta dade a hanyar islamia ba.dan bazata boye mata komai ba ita kuma bataso ran ummar ya baci tun da dai matukar zata fada mata dole ranta ya baci ita kuma haka ne bataso. Tun daga wannan rana kb kullum sai ya tare humaira sai dai kuma bai kara yinkurin taba mata Yatsa ba,bare Hannu ba ko kuma wani abu mai kama da wannan.sai dai ita bata mishi maga na sai dai ta yi murmushi idan yana mata maga na amma kuma bata wani bata lokaci take tafia. Yanzu ta saba dashi sosai in ma ba scul tana shiga damua in bata Ganshi ba.dk da ba gane ko kuma fahimtar Kalamai da yake gaya mata take ba.a haka har ta shiga s.s. two domin lokacin ta gane manufar kb ta saba da komai da yake gaya mata wani lokaci tana maida masa marta ni. domin sabo da soyay ya ne suka shiga zuka tansu.dk da har time din gaba daya bangaro rin biu basu gane meke farua ba.illa dai ummar humaira data gane yarta na tuna ni da kuma kadaice wa ita kadai,haka ne yasa ta fara zargi kota fara kula saura yine basu da masa niya.haka ne yasa ta kara sa ido Kan tarbi yarta domin ta kai wani mataki da maza zasu ke kai hari na nemam luv a gunta.ta girma sosai halittar ta,ta kara fitoa diri kira da dk wani abu da mace zatai takama dashi in ta kai baliga. Kb da yake so ya auri aysha sai ya mai da hankali domin yanaso ya samu wani abu da zai dogara dashi wanda in ya tashi aure za,ace yana da sa na,ar yi tun da ba wani karatu mai zurfi ya yi ba bare ya samu wani aiki da zai dogara dashi.haka ne yasa ya nutsu sosai dan yanaso dad ya dorashi kan kasu wanci dk da Hajia bazata Amince ya auri yar talaka ba amma yana da tabbaci dad zai mallaka masa komai yakeso bare ma dad bai Kin talaka.damuar da yake da ita itace ko iyayen aysha zasu Amince masa ya aureta?a yan da yakeso dan shi ko karatu baiso taci gaba daga na sec.kuma ya lura abum dunia bai damesu ba ya lura da haka a gani na farko da ya musu. So ya shiga Rai da zuciar aysha yay kane kane dan a yan da take ji yanzu zata iya amince wa kb da aure in ta kammala sec.yanzu ji take dk wani buri da take dashi na karatu ya kau, so take ta auri kb kalamai da yan da ya gina kanshi a günta Suna matukar tasiri a zuci yarta.kullum kalamansa "aysha ki amince da aure na bazaki taba danasa ni ba,aure ne da zaki yi alfahri dashi zaki rayu cikin farin ciki da kanciyar hankali,zaki zauna karkashin kula wata rayu war da babu bakinciki kunci ko takaici.Yayanmu zasu yi alfahri damu a matsa yin iyaye na gari tabbas zasu ce Sunyi dace.aure ne da babu yaji bare wani saki ni babu saki a tsari na,domin nima bazan taba iya rayu wa babu ke ba aysha ke kadai mata ta har karshen rayu wata,bani da buri na auren mace sama da daya🙊 Zana dauki iya yenki tamkar mahaifa na zan daraja su suma zasu yi alfahri da aurenmu"wannan kalami su suke sa aysha ta ji dk dunia babu wani namiji da ya dace da ita face kabeer wannan ne kalaman da suka yi tasiri akanta dan ko Bata yi niyyar tsaayawa ba In ya ya fara jero kalamai yanzu zata tsa ya tana murmushi.domin yanzu an rage musu lokacin tashi a islamia dn haka in ta taso suke shan hirar su Ita da kb dn ko a gida ba tace an rage musu lokaci ba sai dae kb ya tare kullum.so ya mata ga kuma yarinta dake dawaini ya da ita.domin kb ya fita shekaru da kuma bude war Ido. A haka Suna tare a boye har dai humaira ta shiga s .s tree lokacin sun kara shakuwa sosai da Juna.kullum maga nar kb bata wuce bazai taba dena sonta ba,itama kuma a nata bangare haka ne.sai dai har yau bata taba karbar wani abu a gunsa ba,komai ya bata kin karba take har waya ya bata suke waya a boye amma taki karba dk wani abu daya bata taki karba sai yace zai a dan a mata a gunsa har sai Ranar da sutka yi aure zai bata.ta Kanyi murmushi amma bata ce masa komai.a time dn ne dady ya bashi ku dade ya kuma hadashi da abokan kasu wanci tuni harka ta bude ya bude shago a kasuwar kwari ya cika da Atamfofi shand do di lesi na d.s Hajia ta yi murna sosai da natsu war da danta ya yi bata Sän aure yake so ya yi ba shisa ya natsu ya kama zuwa kasua😀 Baya n wata uku *********************** Hajia ta je kaduna gun kan warta zuminci da ta tashi taho wa ta taho da yar kan wartata ummul khairi ,dn bata da ya mace.ummul khairi bata Jim maga na ko kadam ga raina na gaba sam sam bata da tarbi ya.ta kammala karatu n ta na sec. Tun data dawo ta dora rai a son kb dama can tana son sa amma bata masa ba.ta shir ya gaya wa hajia kome zai faru ya faru. Yau ya kama alhamis babu islamia humaira ta shir ya tsaf domin zua gun kaka nimta ta gaishe dasu.fitar ta ke n n wata mota ta faka a kofar gi dansu,wasu yan mata ne su biu suka tsa ya suka kare wa gi dan kallo na wulakamci Suna wani yatsi na fuska.shiga suka yi ciki ba tare da Sun yi Koda sallama ba,umma atika dake Shan rake tana tara cito a plate ta dago tana bin su da kallo na mamaki. "haba yan mata ya kuka shigo mana ba sallama"umma tace tana murmurshi . "Nan bai mana kama da Inda mutane zasu rayu ba,bare har mu yi sallama yafi kama da Inda karnuka,ko dabobi zasu Zauna amma ba Mutane ba"1 daga ciki tace Tana cire glases dn dake Ido Tana wa ko ina kallo na banxa. "Bama wannan banzar yar taki da take min hira da saura yina kullum a lungu,yau nazo ko ni ko ita"dayar tace tana hararar umma. "Hira da saura yinki kuma a lungu"umma tace cike da mamaki tana tashi tai jifa da plate mai sosu war rake ,ji tai kanta na wani iri sauri ta yi ta rike bango dan kar ta fa di kasa............. 😍😍😍😍😍🥎 بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *_______________________________________ 🚨🚨GI DAN MI JINA🚨🚨 Story & Written by MAMAN AFRAH Page TWENTY ONE & TWENTY TWO "haba tsohuwa tsa ya mana sosai da kafarki karki yi Warwas mana,mene ne na mamaki in kika yi la,a kari da zamani da muke ciki"dayar tace tana yin wata dry ta rainin wayo. "wlh kawata maybe ma ya kunsa mata ciki"itama dayar tace tana dry. "Ya salaam wlh kar ya kuke humairata bazata taba aikata haka ba"umma tace tana goge Hawa yen takaici daya cika mata ido. "lallai ma matar Nan Kin raina mana Wayo mu muke miki kar ya? to wlh Kinci sa,a yau yan mitunci ne a kai na da sai kiبسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *_______________________________________ 🚨🚨GI DAN MI JINA🚨🚨 Story & Written by MAMAN AFRAH Page TWENTY TWO & TWENTY THREE. Sosai abba da umma suka yi Mata to fada a kan abin da Tayi,tai kuka sosai amma kuma bata sa a ranta ba zata rabu da kb domin Tayi Nissan da bazata iya rabu wa dashi ba.haka abba ya hanata fita ko ina ko scul bata fita.kullum tana gida dk ta shiga damu wa. Kb kullum yazo in da suka saba hadu wa sai ya ga Kowa yan islamia Sun wuce amma bai ga aysha ba,har dai ya tare su hafsa ya tamba yesu aysha suka shai da masa meke faru wa Kamar yan da humaira tace su fada masa da suka je dubata su ga ko lpia take kin zua islamia.kb ya yi matukar mamaki da ya ji su zuly sun je Sun yi Cin mutumci a gidan su humaira ,amma kuma sai ya dai na mamaki domin zata aikata fin haka ma.tabbas binsa suka yi suka gano in da yake zua ita ma humairar suka bita suka ga in da ta shiga.gida ya nufa yana ji zuciqr shi na zafi. Da dare Suna Zaune a falo daddy ya Abdullahi. Hajia,ummul khairi sai kabeer dake Zaune ya yi shiru dan shi ko ko baki bai Sanya wa a hirar da ake dama tun da ya dawo daga Gun zule ya je ya mata tatas akn Abim da tai.ya je daki yake ta tuna ni ko Abenci kin ci ya yi yace bai da lpia.yanzu ma ummul kairi aka aika ta kirashi da doctor yazo dubashi basu san rashin aysha ne damu warsa ba. Haka kb da humaira suka zauna cike da ke war juna,dn kb har kasu wa ya bar zuwa.a haka dai har yaga bazai jure ba ya samu daddy da maga Nar yanaso ya yi aure,ya yi mur na sosai yace zai je su daita da iya yen humaira sai a hada da bikin ya Abdullahi. Daddy ya tun kari hajia da zan can zua nema wa kb aure,amma taki fir take fada ba Inda za,a ga ummulkhairi Nan ita zai aura.daddy Kuwa yace tunda kabeer na da wacce yakeso bazai aura masa ummul khairi ba,sai dai ya aureta a gaba in yana bukata.rigima sosai daddy da hajia sukayi amma daddy yace wlh babu fashi! sai an je nemo wa kb aure. Haka daddy suka je nema wa kb aure shi da wasu friends nashi ,kamar yan da kb ya fada musu ungu War da kumar sunan mai GDAN.basu Sha wahala ba suka samu GDAN. Abba yayi mamaki da ya ji meke tafe dasu,domin bai zaci mai kudi kamar daddy zai nemi hada zuri,a dashi ba.dattako dasu daddy suka nuna da kuma yan da aysha ke cike da damu war rabata da kb yasa ya amince.a take aka sa ranar aure amma sai ta karasa karatu.kudi masu yawa daddy ya ba abba amma yaki karba sai da ker ya dauki 50k na i see i luv.haka suka rabu Suna girmama Juna. Haka umma da aysha suka ji maga nar kamar saukar a radu,aysha Tayi Myrna sosai a ranta amma kuma tana far gaba umma kuma addu,a tayi.tun daga ranar aysha taci gaba da zua scul.abba yace ta fada wa kb yake zua GD Suna hira. Hajia ta dai na sakar wa kb fuska har sai yasa daddy ya Jan ye zan can aure.bare ma data ji talaka wane sai ta ji bata kaunar kb ya aureta.ummul khairi tayi kuka sosai da ta ji kb wata zai aura ba ita ba,kuma taci alwashi sai ta Hanata zama lpia a GDAN kb.dk da hajia tayi ta bata baki tayi hkr dk runshi sai kb ya aureta,haka ta bar shiga sabgar kb kamar yan da bukata domin yana Gani itace silar kn aminta da hajia tayi. Haka kb yaci gaba da zua kasua da kuma hira wirin aysha Suna nuna wa Junq SO hatta abba umma yanzu Sun yaba da kb sosai da nutsu wa da kamalarsa.haka kb yaci gaba da fada mata wanda suka zo GDA bazasu kuma da wowa ba wai dama tsohu war Budur warsa ce🙊shi bashi da wata data fita kuma yake so kamar ita. An sa Ranar aure dai dai da kammala scul dn humaira.haka aka sha biki aka kai amare GD jensu.in da kb ya gina musu GD na gani na fada a ungu war na,iba wa.kb ya samu Aysha a yan da ya yi zato dn haka kula yake bata ta musam man.Aysha ta yi farinciki da kular da me GD nata ke bata hr ma ta fara tuna ni ba ko wane me GD bane yake baiwa matarsa kula war da kb yake bata ba.kullum kara shiga ranta yake har bataso ta ya tafi kasua tafi so ko yaushe kuma ko wane lokaci su zama Suna Manne da juna. Amarci ake sha mai Zauna wa a rai.ta yi kiba ta yi matukar Can jawa su hafsa ma da suka zo haka suka yi ta tsoka narta wai kamar wata Matar shigabam kasa ita ko tace maybe kular da take samu ko Matar shugabam kasar bata samu😜 a haka hr suka shafe wata biu amma bata taba gannon hajia ba.kb dai ya dauketa Sun je gaishe da su umma hr sau biu Sun kai musu abin arziki,yaba sosai da suka ga aysha ,Sun kuma yi Myrna da zama lpia da suke kamar yan da humaira ta ba umma labari,sai dai bata gaya mata ba hr yau kb bai kaita GDAN su ba kai ita bata ma taba ido biu da hajia ba. Yau ma kamar kullum kb ya dawo daga kasu wa karfe 5 danshi da wuri yake dawo wa ya bar yarnsa a shago.tunda me gadi ya bude masa get yake ji kamshi mai dadi na turaren wuta murmushi yay mai Kawata fuska yana alfahri da aysha a matsa yin mata.tahowa tayi da tafia mai Kayatar da mai kallo kamar wata dawisu riga da sket ne na atamfa baka mai Jan fula wowi dnki ya matukar amsar ta fuskarta dauke da light make up ,rike yake da. kofar motar Yana binta da kallo ta tafi da zuciarsa gaba 1. "barka da zua sarki nah"tace tana karaso wa günsa. "Barka dai isha nah"yace yana binta da kallo na kurilla lumshe Ido ya yi kamshi humrar ta nah shige masa hanci da yana kashe masa jiki.a haka ya kama mata Hannu suka nufi part dnsa. Wanka ta masa ta goge masa jiki tare da sa masa kana nan ka ya.sinasir ta shiga bashi da miyar hanta sai lemo da tai na pine apple & coconut sai da ya koshi sai suka koma suka zube a 3seater Suna ta wasa nah da daria .phöne dn kb ce ta hau kara gabensa ne ya Bada rass dn ya dauka Yan mata ne yana duba wa yaga dad dnsa numfashi ya sauke a Boye ya kara phöne dn a Kinne suka gama maga nah ya kalli humaira jiki ba karfi yace "Ki shir ya da magrib zamu je GD dad na kira"yace kamar Baya so. "yeee yau zamu je in gaishe da su dad dama ban taba zua ba"tace cike da mur na"kb yake yake yi dn bai so ya domin ko ya gaishe da hajia bata amsa masa.humaira da bata sam meke faru waba ta wuce daki ta Bude in da doga yen rigu nah ta na lefe ta dakko wata fara mai Stones tasa tai rolling ta fesa turare. A han ya sai hira take masa shi kuma sai um yake ce Mata har suka iso aka Bude musu get kusa da motar ya abdullqhi ya paka tasa motar.part dn hajia suka nufa domin ya Saba Can yake fara shiga.humaira sai murmushi take yi,kb Kuwa sai fargaba yake.da sallama suka shiga falo a.c ce ta fara musu maraba da kamshi na fresh ner kb ne kalli ummul khairi da ko sallama bata amsa musu ba sai Shan lemo take tana kar Kada kafa. "Ke dn Raini Kina ji ana sallama Kin yi banza da Mutane?"yace yana doka mata harara. "Sorry ya kb barka da zua"tace cike da izza da reni hankali. "Ina wüni anti"humaira tace tana murmushi "Ke yar kau ye ban wüni ba"tace tana tashi ta haura sama.daga kb har humaira binta suka yi da baki sake.Suna zaune ba wanda ya kara maga nah sai ga hajia ta sakko daga stairs tana Hango humaira Ranta ya kara baci. "Ke yr talaka wa wane shege yace ki shigo Min falo"tace da karfi hr falo yana amsa wa.karkar wa humaira ta fara cike da tsoro. "kai fitsarau mesa ka shigo Min da yr matsi yata falo????"tashi ya yi da sauri yana kokari bata hkr hannu ta daga masa tana musu kofa ........ My afrah Allah baki lpia😌🥲 بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *_______________________________________ 🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨 Story & Written by MAMAN AFRAH Page 24---25 Kabeer ka fice min da ita daga falo nace" "Toh"yace ya kalli humaira dake zub da Hawa ye. ''Dan Allah ki yi hkr in wani abu na miki ki yafe min"Aysha tace tana kuka. "Ke dalla malama rufe min baki ke kuma a wa har zaki min laifi,a inama kika isa ki ganni bare hr ki min wani lefi?in ban da kabeer ya shigo dake wlh ko mai aiki baki isa in dauke ki ba,bare kuma har ki samu damar fadi in fada dani kaunarki ne bana yi ko kadan.dn haka karki kara zuwa inda nake,bada yawu na aka aureki ba ko Kaya da aka Hada na lefe ba sa Hannu nah a ciki tun da kince sai mai arziki to aiko bazaki samu zama lpia ba"tace tana nuna mata kofa da Hannu. Aysha da gudu ta juya tana sa hannu ta rufe bakinta sabo da kuka da yaci karfinta Kb ne ya juya da sauri zai rufa mata baya. "Kar ka kuskura ka fita"hajia tace rai bace gannin kb dk ya wani rikice. "Hajia ki yi hkr bata da laifi wlh" "Wato bata da laifi wai kai mai mata to ka bini a hankali wlh"Tace ta samu 1seater ta zauna tana wani hade rai.kb kuwa a kasa ya zauna ya sunkuyar da kai kasa yana mamaki na can jawar hajia dan ya auri matar da bataso.dk da bata son talaka amma bai zaci Abin ya kai haka ba. "kaga matar da nake so ka aura in hr kanaso mu dai daita "tace tana nuna masa ummulkairi data sakko daga stairs tana wani murmurshi. "Toh"yace yana ji kamar ya je ya make ummul khairi domin haushi. "Ya kb yaushe zan zo muku hutu"ummulkhairi tace da izgilanci dan ta kara bata masa rai ta faki idon hajia ta kashe masa ido daya. "duk ranar da kika shirya "yace a takaice yana cije lebenshi na kasa . "ummulkhairi zo zauna za muyi magana"hajia tace tana nuna mata wurin zama. Dab da kb taje ta zauna a maimakon inda hajia ta nuna mata. aysha na fitowa ta kama hanyar da zata sadata da get din din gidan,tafiya take tana kuka har hawaye na neman hanata ganin gabanta.sosai taji maganganun hajia sun taba mata zuciya tabbas tozarci bashi da dadi ko kadan da ace tasan abinda zata tarar da ko karyar rashin lpia tayi dan kar tazo a ciwa iyayenta mutunci abinda ba,a taba mata ba a rayuwarta lallai yau da ace watace ba surukarta ba bazata taba kaleta ba wlh sai inda karfinta ya kare,dan duk hakurinta da rashin son fadanta bazata yarda a ciwa mahaifanta zarafi ba ko zuly da taje gidansu tayi rashin kyautawa dan bata nan ne amma koda bazataci riba ba sai iya inda karfinta ya kare.ita kawai so take taje taga shin hajia kamarsu daya da kabeer dinta ko kuma basa kama ita ko a mafarki bata taba kawo cewa surukar tata bata ko son ganinta,ashe daman shi yasa kb bai kaita ta gaisheta ba amma hakan bai sa tayi wani tunani marar kyau ba akanta ba.domin yana da kyau ka yiwa mutum kyakkyawan zato ,Allah sarki rayuwa kenan kowa da irin tashi kaddarar.ita kuma da kaddarar suruka aurenta yake domin bata hango sassauci ko na second daya ba a fuskar mahaifiyar mijin nata.wasu zafafan hawayen ne suka kwaranyo mata tunawa da tayi a haka zata rayu duk da ba tare zasu zauna ba kuma ba ita ke aurenta ba amma ai dole ita ke da iko akan danta.sannan ga wannan ummulkhairin itama kai abin sai dai addu,a. "kanwata" Aysha dake kokarin bude karamar kofar get din zata fita ta jiyo sautin kiran a bayanta,saurin sa hannu tayi ta goge hawayen dake fuskarta ta juyo tare da kakaro murmushi. "ya abdullahi"tace tana gyaran murya jin sautin maganarta bai fito sosai ba muryarta ta dan shaqe kadan. "ina zuwa kuma naga kina kikorin fita?"yace yana rufe murfin motar. "ina yini"tace lokacin data karaso inda yake tana kokarin kawar da tambayar daya mata. "lpia ina kabeer din ,kuma kuda ake jiran zuwanku naga zaki fita" "eh am dama"sai kuma tayi shiru "dama ba nisa zanyi ba ,shi kuma yana baangaren hajia"tace tana kirkirar murmushi. "ok ki bari idan daddy ya gama ganinmu kyaje wurin da zakije din,kinga yanzu ma yana falo ku kawai ake jira nima abu nazo dauka a mota, muje part din daddy jamila ma tana can dake mun rigaku zuwa da muka gaishe da hajia sai muka wuce part din daddy"cewar ya abdullahi daya fahimci akwai wani abu ,dan dama yaga aysha ba yadda ya saba ganinta ba ga kuma alamun kuka nan a fuskarta dan gidan ko ina haske tarr kamar rana.kuma yasan laifin bai wuce na hajia dan ya san batason auren. Jim ta danyi sai kuma tace"toh"suka jera suka nufi part din daddy. Da sallama suka shiga a loakcin daddy ya haura sama domin dakko wayarsa daya barta a can ,zai kira kb saboda yaga har yanzu shiru basu zo ba.jamila dake zaune kan kujera ta wani hakimce tana kallo a tv ta musu banza bata amsa sallamar ba ,kai ko kallon inda suke batayi ba. "bakya ji ana sallama ne"ya abdullahi yace dan kar ya badu a gaban aysha dake girmamashi da ganin mutuncinsa. Juyowa tayi ta kallesu tare da yatsina fuska,ta juya ta maida kallonta kan tv ba tare da tace koda uffan ba.kwata kwata ta raina ya abdullahi ga babu abinda ta iya sai dai tayi ta charting sai kuma barci ga shigiyar karya da dankaran kazanta,amma a haka hajia ke sonta saboda yar kawarta ce kuma ko hajiar ma ba ganin girmanta take ba amma kamar ta maida ita ciki sai dai tayi ta cewa ya abdullahi yayi ta lallabata bata saba da wahala ba sai hutu saboda yar gidan masu kudice.bata damu da halin da yake ciki na ko in kula da jamila ke nuna masa ba hatta auratayya bata yarda in yana bukatarta sai lokacin da ita tata jarabar ta motsa sannan zata yarda dashi. "aunty jamila barka da dare"aysha ta fada a darare ganin yadda aka yiwa mijin,bare kuma ita da ba komai ba. Banza ta mata kamar ma ba,ayi ruwanta a wurin ba dan dama ita bata kaunar talaka bare kuma ya rabeta.ko kwanaki ya abdullahi da yace suje gidan kb kin zuwa tayi sai shi kadai yaje duk da kb da aysha sun kai musu ziyara wanda ko kallo basu isheta ba gwarama kb ta masa magana amma koda aysha ta mata magana yatsina fuska kawai tayi sai ya abdullahi ne ya kawo yasa yar aiki ta kawo musu ruwa da lemo sai snacks da yake shigowa dashi saboda bata girki sai na yan aikinta shi kuma ba abincin da kowa ya girka yakeci ba.suma su kb babu wanda yasha ko ruwa haka suka yi sallama suka tafi tun daga wannan ranar basu sake komawa ba. "zauna aysha kafin daddy ya sakko"yace dan kawar da abinda jamilar ta yiwa ayshan.aysha murmushi tayi ta samu wuri a kasan capet din ta zauna itama ta maida hankalinta kan tvn duk da ba wai kallon take ba gaba daya zuciyarta ta tafi ne ga tunani . "auta ba komai yasa kaga na dauke maka wuta ba sai akan auren yarinyar nan daka yi,naso ace ka auri ummulkhairi amma hakan bai samu ba to inaso ka sani kuma kasa aranka cewa bazan taba karbar wannan yarinyar a matsayin saraukuwata ba! domin yarinyar ba ajinka bace kuma ma banda asirin da suka maka yayi tasiri a kanka babu yadda za,ayi ka yarda ka aureta.dan haka yanzu idan har kanaso kaci gaba da ganin walwalata sai ka auri ummulkhairi,dan wlh sai yarinyar nan ta yabawa aya zakinta sai ta gwammace kida da karatu sai ta banbace tsakanin aya da tsakuwa idan har ummulkhairi ta shiga gidanka.sai ta raina kanta kai karshe sai ta bar gidanka da kafafunta🦶🦶yanzu ma dan nasan daddynku bazai taba yarda ba bare ya bari da wlh sai ka dankara mata saki" kb ne yayi saurin dagowa ya kalleta,a inda kuma idanunsa suka sake sauka akan ummulkhairi dake da ta doka murmushi kamar wacce akace an yiwa albishir da shiga jannatul firdausi.kankance idanu yayi yanajin wani tarin takaici na taso masa a rai da zuciya. Bude baki yayi zai baiwa hajia amsa wayarsa tayi kara daddy ne ke kira wani sansanyan boyayyan numfashi ya sauke yana godewa Allah da yasa kiran daddy shigowa.dagawa yayi daddy ya tambayesa mesa basu zo ba ,shi kuma ya fada masa sun jima da zuwa ma yana part din hajia ,daddy ne yace masa su taho har su hajia dan ya yi ta kiran wayarta ba,a dauka ba.da toh ya amsa.yana gama wayar ya sanar da hajia sakon daddy.mikewa tayi suka fito gaba daya domin zuwa part din na daddy. Suna zuwa suka shiga bakinsu dauke da sallama ya abdullahi da aysha ne suka hada baki wurin amsa sallamar tasu.mamaki al,ajabi ne suka kama hajia da har ta kasa boyewa a ranta kuma tana ayyana lallai sai tayi da gaske yarinyar nan zata fita daga rayuwar danta,dan duk tunaninta aysha ta bar gidan kuma a yadda ta mata bata taba tunanin zata tafi ko gidan kabeer ba ta dauka gidan iyayenta zata nufa amma sai gata ko gidan ma bata bari ba .kb kwa wani dadi yaji yana shigarsa ganin aysha zaune a falon daddy take ya fara sakin murmushi yana bin aysha da kallo kamar dai yau ya fara ganinta.ita kwa aysha kanta ta sunkuyar kasa😔 ganin wani mugun kallo da hajia ke jifanta dashi kai hatta ummulkhairi ba,a barta a baya ba wajen aika mata da harara kamar idanunta zasu fado kasa.😳 Karasowa tsakiyar falon sukayi a inda hajia ta nemi wuri ta zauna ummulkhairi ma da kb suka nemi wuri suka zazzauna jamila da har lokacin bata nuna alamun tasan da zuwansu ba tana kan kujera ta hakimce kafarta daya akan daya ya abdullahi haushinta yakeji da take nuna halin ko in kula ga mahaifiyarsa,amma kuma idan ya tuna zabinta ne sai yace ai daman duk wanda ya sai rariya ya san zata zubda ruwa kuma duk tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa kan doka😇 A bangaren hajia ma haka abin yake duk da jamilar dana ba wani girmamata takeyi ba,amma kuma sai taji haushin abinda ta mata a gaban aysha da kuma yayanta sai taji ta muzanta amma kuma tunda so take ta cusgunawa aysha dole tayi hkr ta daure ta kuma danne abinda jamilar ta mata. "my daughter duk kallon ne ya dauke miki hankali baki ganni ba?"hajia ta fada tana kallon inda jamila ke zaune. Banza ta mata kamar ma bata ji ba. "my daughter na...... "kawai banson hayaniya ne"ta katsewa hajia maganar kafin ta karasa.wani haushine ya ziyarci zuciyar kb data ya abdullahi ummulkhairi kwa baki kawai ta tabe taci gaba da latsa wayarta.aysha kuwa jinjina al,amarin takeyi a zuciyarta. "taso mana ki dawo kusa dani"ta fada tana dariyar yake data fi kuka ciwo" murkisisi tayi taki yin ko motsi bare hajia tasa ran zata taso tazo gunta kamar yadda ta bukata.takaici ne yasa hajia tashi kamar dai ta kwada mata mari amma kuma sai ta wayance.. "haba daughter kefa miskilancinki yawane dashi to ni gani nazo tunda inaso naji dumin yata"ta fada tana zaunawa kan kujerar da jamila ke zaune ,ta mika hannu ta kwanto da kanta kan kafadarta.tana wani shafa kanta kowa na falon haushi suka bashi. "ba wai miskilanci bane kawai banson a dameni ne,sannan ma fitar ba sonta nake ba dan ma kiran daddy ne da naki ne ma ba fitowa zanyi ba wlh"tace tana zame kan nata daga kafadar hajia ta kwanta akan kujerar tare da dora kan nata akan cinyar hajiar🙄🙄 "gajiya ce ke sanya haka kiyi hkr kinji,nasan ma ba wani dadewa za,ayi a meeting din ba sai ya maidake gida kije ki huta........ 😍🥰😘😍🥰😘😍🥰😘 .بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share *_______________________________________* 🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨 Short story Story & written by MAMAN AFRAH Page 26--27 Ya abdullahi ne juya ya doka mata harara. "lefin me tayi kake harararta kar na sake gani"hajia ta fada da kashedi. "amma hajia bakya ganin........ Sakkowar daddy itace ta katse maganar da ya abdullahi ke kokarin yi. "Barka da sakkowa daddy"kb yace yana murmushi. "barka dai auta ko kuma auta ya girma yanzu"daddy yace da zolaya yana dariya irin tasu ta manya. "ay daddy yanzu ya girma ba shine autan ba"ya abdullahi shima ya fada yana dariyar "daddy ay gaba da baya nine auta"kb ya fada yana zumburo baki.gaba daya falon dariya aka saka banda jamila da tayi karamin tsaki da ba wanda ya jita sai hajia,itakwa aysha murmushi tayi kanta har lokacin a sunkuye. "a toh shikenan mun ji kai ne auta"cewar daddy yana samun wuri ya zauna. Bayan kb ya gaishe da daddy aysha ma mikewa tayi taje har gaban daddy ta tsugunna har kasa ta gaishe dashi cikin mutuntawa da kuma girmamawa.amsa mata yayi yana mai jin dadin tarbiyar yarinyar yana kuma godewa Allah daya bashi suruka kamar aysha lallai har gobe yana alfahri da ita a matsayin matar dansa kabeer.komawa tayi kasa wurin zamanta ta zauna ,a yayin da mutum uku suka bita da harara,hajia ummulkhairi,da kuma facalarta jamila suna jin haushi da yadda take.ita dama jamila ta gaishe da daddy tun sanda sukazo sai dai tana daga kan kujerar da take zaune ta gaishe dashi, A alhamdulillah nagode Allah daya bamu rai da lpia ,ina kuma kara gode masa daya bani iko da dama na taraku domin mu tattauna magana wacce nake fata ta kawo gyara akan gyaran da nakeso ,ta kuma zama sanadin gyaruwar komai kamar yadda nake son hakan ya kasance. gyaran murya yayi kafin yaci gaba da bayani. wato shi ubangiji shike iko da kowa da kuma komai,shike bayarwa kuma shike hanawa.yanayin yadda yaso a lokacin daya so,duk wanda kaga Allah ya bashi to shi yaga dama ya bashi bawai dubara ko wayon mutum din ne yasa ya samu.kuma kowa dana ne yadda kowace uwa ta dauki ciki tsawon wata tara ta kuma shayar tsawon watanni tara kamar yadda yazo a alqur,ani mai girma cewa (ciki da kuma shayarwa watanni talatinne)dan haka kowace uwa haka tasha wahar haifar danta ta kuma shayar dashi da kuma wahalta masa a rayuwa.kuma babu wata uwa da bata son danta kowace uwa ka gani akwai soyayyar danta dankare a zuciyarta,dan haka kowa da kaddararsa mai kyau ko marar kyawu.sannan kowane mutum an rubuta masa arzikinsa da ajalinsa da aikinsa sannan da makomarsa tun kan yazo duniya duk wanda ka gani da arziki Allah ne yayi nufin ya bashi,haka kuma duk wanda ka gani a talauci haka shima Allah yakeso ya ganshi dan haka wulakanta wanda kafi da wani abu ba naka bane wala ilimi daukaka,mulki ,ko dukiya .dan kaima duk wannan abubuwan daka mallaka anan duniya zaka barsu da zarar mala,ikan mutuwa ya ziyarceka shikenan daga kai sai farin llikkafaninka wanda dashi ake kai kowa kabari mai kudi ko kuma talaka.kai ko ba,aje ga mutuwa ba wata rana zaka wayi gari ka rasa koma menene kake takamar ka mallakeshi. Domin rayuwar nan ba tabbas ba gareta ,yanzu zaka ga mutum ana jimawa ace maka ya mutu🥲mutum ba komai bane wlh shi yake daukan kansa wani daga an zare maka rai shikenan ka zama gawa kuma a lokacin za,ayi jana,izaarka a kai ka makabarta a saka a rami a rufe shikenan daga kai sai halinka.dan haka nake jan hankalinku nake kuma ankarar daku a matsayinku na iyalaina daku bi duniya a sannu domin bata da tabbbas ko kankani! mu guji duniya Allah zai so mu ,sannan mu guji abin hannun mutane suma mutane zasu so mu.shiru yayi yana bin fuskokinsu da kallo yana kuma karantar yanayinsu gaba daya.duk sunyi shiru da alama kuma zancen na shigarsu domin gaba daya sun yi sanyi. Abu na gaba da nakeso na yi magana akansa shine akan zamantakewar auratayya ,ku mata kuyi biyayya ga mazanku ,kuma mazan kuyi adalci a zamantakewarku.sannan hajia inaso ki sani cewa aysha surukarki ce kuma yarinyace mai biyayya,sannan kuma dama Allah ya rubuta ta a matsayin matar kabeer tun kan tazo duniya.dan haka ki yiwa Allah ina rokonki ki da ki karbeta a matsayin suruka.sannan inaso ki sani ba komai da mutum keso ko kuma yake son kasancewarsa ba yake samu sai abinda Allah ya kaddara.yau kusan watanni kenan da aurensu amma ko sau daya baki taba sanyata a idonki ba karfa ki manta itama 'ya ce kuma uwa da ubame suka haifeta kuma suma suna sonta kamar yadda muke son namu yayan,dan haka ina rokonki daki sakar mata fuska ki kuma karbeta a matsayin suruka domin rayuwa bakasan mai gaba zata haifar ba.sannan baka san mai maka rana ba sai Allah."yana kaiwa nan ya koma ya jingina da jikin kujerar Hajia ce ta fara magana"insha Allahu za,a gyara kamar yadda ka bukata kuma naji dadin wannan nasiha daka mana. Allah ja da kwana"ta fada a zahiri a ranta kuma tana raya tabbas ya gama zubar mata da girma a idon aysha,kuma ita bazata taba karbarta a matsayin suruka ba. "insha Allah daddy zaka samemu masu aiki da abinda ka fada"cewar ya abdullahi a ladabce. "daddy tabbas nasiharka ta taba min zuciya lallai kafin a samu mahaifin da zai zaunar da iyalansa yana fadakar dasu domin gyara rayuwarsu,domin su dace duniya da lahira za,a tona,in Allah ya yarda zaka samemu masu aiki da maganarka.Kabeer ya fada yana kallon daddy. "daddy munji nasiharka kuma muna godiya sannan zaka samemu masu kiyayewa"cewar ummulkhairi. "daddy mun gode kwarai da nasiharka garemu"jamila tace a takaice.falon ne yayi tsit kamar ba kowa. "Yata ke bazaki ce komai ba"daddy ya fada yana mai kallon aysha da kanta ke duke har loakcin.dago kanta tayi tayi sannan ta fata bayani. "daddy hakika ina alfahri da kai a matsayin uba kuma suruki a wurina ,sannan kuma wannan nasiha da kuma fadakarwa sunyi tasiri sosai a zuciyata,babu abinda zance sai dai ina maka ftn alkairi a dukkan lamuran rayuwarka,ina kuma addu,a ubangiji ya maka jagoranci ya baka rai da lpia yasa kayi kyakkyawan karshe ya kuma maka sakamako da gidan aljanna"tana kaiwa nan tayi shiru.daddy kwa tunda ta fata magana yayi tsai yana kallonta yana kuma yaba kaifin basira da iya magana da kyawawan lafuzza da ayshan keyi wanda gaba daya cikinsu babu wani wanda yayi magana makamanciyar tata.har hajiyar ma.ita kuma hajia da jamila dama ummulkairi sai binta suke da harara a inda ya abdullahi da kb suke ta jijjiga kai suna murmushi alamar ayshan ta burgesu. "ah alal hakika nayi matukar farinciki da abubuwan da kuka fada Allah mana jagoranci gabaki daya"daddy yace tare da rufe taro da addu,a dan dama yayi hakane sbd aysha da bata taba koda zuwa gidan surukan nata ba ,da kuma hajia dake nuna batasonta dan kasancewarta ba yar kowa ba ma,ana basu da abin duniya.daga haka kowa ya musu sallama ya fito aka bar daddy da hajia suna tattaunawa.ummulkairi part din hajia ta wuce ranta bace ganin kb da aysha sun jera suna ta magana suna murmushi ,hakama ya abdullahi da jamila data wani manne masa kamar zata koma cikinsa wai ita a dole zata nunawa aysha ita wayayyiya ce.haka sukayi sallama kowa ya shiga motarsa mai gadi ya bude musu get suka fice kowa ya kama hanyar gidansa. A haka rayuwa taci gaba da kasancewa cikin farinciki da kwanciyar hankali a tsakanin kb da aysha a haka har suka shafa watanni shida da aure.a lokacin ne kuma aysha ta fara rashin lpia ana zuwa asibiti gwajin farko aka gano tana dauke da cikin wata guda sosai kb yayi murna da samun cikin,sai dai cikin yazo da laulayi sosai wanda haka yasa kulawar da aysha ke bawa kb ta ragu domin yawancin kullum bata da lpia wannan ne yasa kb ya koma soyayya da yan matansa dumu dumu wanda daman ya dai ragene amma koda sukayi aure da ayshan bai fasa ba yana boye matane kawai. soyayyar da yakeyi da yanmatansa tasa ya daina baiwa aysha kulawa ,idan ya dawo daga kasuwa yayi wanka yayi kwalliyarsa ya fice sai kuma kwanciya zai dawo dan abincinta ma bai fiye ciba ya gwammace idan ya fita ya dauki budurwarsa suje su ci abinci mai rai da lpia mai tsada.wannan halayen da kb ya fara fito dasu sune suka sanya aysha cikin tsananin damuwa domin ya daina kulata ta kowace fuska,idan ya dawo ta masa sannu da zuwa sai kawai ya daga mata hannu ya fice ya barta a wurin.in ta tambayeshi ko ta masa laifine sai yace shi ba wani abu data masa kawai ya gajine ta barshi ya huta,kai gaba daya rayuwar ta sauya har dai aysha ta fara tunanin ko dai cikinne bayaso,dan yanzu ko mu,amalar aure sai ya dau lokaci baiyi da ita ba.amma a haka ko zai kai karfe nawa bai dawo ba sai ta jira dawowarsa kuma koda ya dawo ba wani kulata yake ba,wani lokacin ma ita ke kwanciya a jikinsa domin suna hawa gado yake juya mata baya sai dai ita ta rungumoshi saboda sosai cikin ke sanyata jin shawa,a amma haka zaiyi biris da ita kamar bai jita ba haka zata hakura ta kwanta a jikinsa wai ko ta danji sanyi sanyi da saukin abinda take ji. Haka aysha ta kasance cikin damuwa kullum da abinda ke damunta kai hatta abinci sai daya fara fita ranta tayi baki ta rame ga laulayi ga damuwa duk sai duniyar ta mata kunci,ko gidansu taje mahaifiyarta tayi ta tambayarta damuwarta amma tace babu komai domin bataso ta sanyata a damuwa ita kuma mahaifiyarta sai take tunanin ko laulayin cikinne ke sakata damuwa sai tayi ta mata nasiha .to indai kaga aysha ta saki jiki tana hira to sai dai in gida taje dan yanzu kb ko loacin zama da ita bai dashi bare kuma har yayi hira da ita. Aysha ta fara tunanin kodai kb neman mata yake duk da zuciyarta taki aminta da haka ,amma yawan tunani da take da kuma halin ko in kula yasa ta fara sanya masa ido akan dan lokacin da yake zama a gidan idan ya dawo wato lokacin dawowarsa daga kasuwa da kuma lokacin kwanciya da yake dawowa da kuma da safe kafin ya fita.na farko ta faki ido ta kalleshi ta wutsiyar ido a lakacin da yake bude pin din wayarsa domin tanaso tasan me yake a wayar ta hakane zata fara gano bakin zaren,sai data tabbatar ta gama ganin pin din bude wayar sannan ta maida kanta ta kwanta shi kuma yaci gaba da daddanna wayar har tayi barcin karya.ya dade yana ta danne danne a wayar daga bisani ya ajiye wayar akan bedside drower ya kwanta,sai data tabbatar yayi barci dan har munshari ya fara sannan kuma ya bata bayane sannan ta lallaba ta tashi da dakko wayar hannunta har karkarwa yake zuciyarta tana bugawa da sauri da sauri,sanin da tayi ada wayar kb ko pin baya sanyawa sai dai yake dan kaffa kaffa amma yanzu ga pin sannan idan an kirashi yake ta wani wuri wuri da ido alamar kamar marar gskia.har ta cire pin din sai kuma wata zuciyar ta haneta da bincika wayar tana nuna mata kazantar da baka gani ba tsafta ce.har ta ajiye taji dai hankalinta bai kwanta ba aikwa ta dakko ta kuma cire pin din nan take ta fara shiga call long anan ta fara cin karo da sunaye baby1 babie luv,my heart sunaye dai barkatai wasu sun kira wasu an kirasu sosai zuciyarta keta lugude acan kasa taga kiran data mishi yana kasuwa zatace ya taho mata guiva amma ya katse kiran bai dauka ba sunan data gani a numberta shi ya bata mamaki ya kuma so ya bata dariya INDO ya rubuta da manyan harufa.fitowa tayi ta shiga gallary hutunan yan mata kala kala gasu nan ko mayafi babu duk dinkin jikinsu a matse kai wasu ma english wears ne jikinsu,wasu hotunan kb ne da yanmata gasu nan barkatai mace ba daya ba ba kuma biyu ba wani an rungumeshi wani an masa kiss gasu nan dai kamar jamfa a jos. fitowa tayi duk da hotunan ba karewa sukayi ba,ta shiga whatsapp nan ma ga sunayen mata nan anyi chart na soyayya bila adadin hira da kalamai wanda ita tunda take dashi ma bai taba gaya mata irinsu ba.ta shiga nan ta fito ta shiga can sai data gama duba wayar kakaf sanan ta ajiyeta inda ta dauka zuwa lokacin hawaye ya gama wanke mata fuska zuciyarya sai zafi take mata,komawa tayi tanaci gaba da zubar da hawayen bakinciki wanda har sai da tayi data sani da bata buda wayar ba amma kuma ko ba kamai taji dadin budewar domin kuwa yanzu tasan waye mijinta kuma dawa take zaune take rayuwar Aure. Haka ta kwana cikin damuwa bata samu wani barci ba,shikwa sai barcinsa yake hankali kwance.da asuba ta tashi sallah ta tasheshi shima data tafi dakinta bata sake waiwayar inda yake ba,domin haushinsa sosai takeji ko fuskarsa bata son gani ita da a iya tunaninta baza,a taba yin ranar da zata ji bataso taga fuskar kabeer ba sai gashi auren bai je ko ina ba amma an samu matsalar da ko hanyar dakinsa bataso ta kalla bare kuma aje ga kallon fuska. Karfe tara dai dai ya gama shirinsa tsaf cikin kananan kaya da suka karbeshi sosai,wayarsa ya dauka ya kira abokinsa Aliyu domin yau ba kasuwa zai je da wuri ba akwai inda zasuje da aliyu. "kai ya ka shirya ne"kb yace yana yar dariya . "na shirya kai kawai nake jira" "okay gani nan zuwa"yace tare da yanke kiran.fitowa yayi daga sashensa a ransa kuma yana mamakin rashin ganin aysha dan kullum tana nan yake shiryawa amma kuma yau gashi kimis.sashen nata ya nufa dan idan ya fita bai san lokacin da zai dawo ba kar kuma ko bata lpia.tarar da ita yayi kwance kan gado ko kayanta na barci bata cire ba,bayan kullum da sassafe take yin wanka tayi kwalliya sannan taje ta zauna ta jira har sai ya gama shirya.da sauri ya karasa bakin gadon ya mika hannu ya taba wuyanta ko zaiji zafi dan duk tunaninsa bata lpia ne,itakwa aysha tana jinsa amma bata ko motsa ba dan kanta ke mugun sara mata. "aysha meke damunki ne?" "ba komai"tace a takaice yayin da idanunta ke rufe dan batason ganinsa. "okay zamu je anguwa nida aliyu daga can zan wuce kasuwa" "Allah tsare" kafin ya kai ga amsawa wayarsa na ta kara ,yana duba mai kiran ya saki murmushi juyawa yayi yana mai daga mata hannu bai ma lura da idonta a rufe yake ba ,ya danna ok ya kara a kunne tana jiyo maganar shi "sorry baby ba girmanki bane yanzu zamu taho......."sauran maganan bataji ba saboda ya riga da ya fice a falon.juyawa tayi ta dauki filo ta rufe fuskarta ta ringa kuka dan ta samu sauki a ranta,daga karshe bacin da batayi jiya ba yayi awon gaba da ita.can cikin barci take jiyo muryan mace na magana daker ta bude idonta da suka mata nauyi agogo ta duba 11:40 saurin tashi zaune tayi tana mamakin barcin da tayi,sakkowa tayi daga gadon ta kamo hanya dan ta fito taga mai magana "wai ina mai tsaron gidanne"taji maganar ta doki kunnenta,tana fitowa idanunta suka sauka akan ummulkhairi sai direban hajia dake dauke da trolly da kit binsu tayi da sakakken baki😨😨 "nuna masa dakin da zan zauna ya ajiye min kayana" بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *_______________________________________ 🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨 Short story Story & Written by MAMAN AFRAH Page 28--29 " 'Dakin da zaki zauna kuma?". Aysha ta tambaya fuskarta cike da alamun fargaba da kuma mamaki. "E mana! Ko ba za ki nuna ba,in zabi d'akin da ya mini? dan ma kin samu har na kulaki na tambayeki,a matsayinki na mai jire gida" Ummulkairi ta fad'a ta na wani yatsine fuska tare da d'ad'daga kai. "Ba haka bane ". Aysha ta fad'a a sanyaye. "To yaya ne? Koma dai menene ke kika sani" Wucewa aysha ta yi ta nunawa direban wani daki mai dauke da toilet a ciki da komai na buk'ata,d'akin gyare yake tass kamar ma a kwai mutum a ciki.Bayan ta juyo ta ga Ummulkairi a inda ta barta tsaye,kallonta ta yi sanye ta ke da riga da wandon jeans gaba d'aya jikinta a d'ame sai karamin mayafi da tayi rolling dashi sai glases kwalba a idonta ,da hand back d'inta sak'ale a hannu d'aya hannun kuma wayarta ce. "Ya dai? Kin ga shiga wacce ba ki iya irinta ba ko?Hmmm! Ai duk laifin Ya Kb ne daya kasa tsayawa ya za'bi macen da ta dace da shi,banda rashin sanin ciwon kai ace har karfe sha biyun rana mace ta na kwance tana barci sanye da kayan barci,maimakon a dau wanka na fitar hankali kafin miji ya fita kasuwa shima ya gani ya san ya ajiye mace ta nunawa sa'a a cikin gidansa, hmmm!" ta ce tare da juyawa ta fara tafiya a yangance ta na wani yauk'i da kwarkwasa kamar tana gaban namiji. Ita kuwa Aysha kallon jikinta ta yi sannan ta girgiza kai ta cigaba da tafiya za ta shige dakinta ta jiyo maganar Ummulkairi. "Ki sama mun abin da zan saka a cikina domin yunwa na ke ji" "Ban jin dadi" Aysha ta fad'a. "Kamar ya ba kya jin dad'i? Ai aikin bariki tilas ne". Ta ce ta juyawa ta kama hanyar d'akin da a ka kai mata kayanta ciki.Itama Aysha juyawa ta yi ta shiga d'aki tana jin kamar zata fadi ga damuwa, ga rashin karfin jiki ,ga kuma zuciyarta dake tashi kamar za tayi amai dan k'amshin turaren ummulkairi sosai ya kara tasar mata da zuciya. Haka ta daure ta shiga ta watsa ruwa ta fito ta dauki doguwar riga marar nauyi ta sanya,dan yanzu duk tafi jin dadin sanya su.Sallar azzahar ta gabatar dan lokacin har d'aya da mintina, addu'a ta zauna tayi sosai sannan ta tashi ta linke hijabin da sallayar ta ajiye,wayarta ta dauka ta kira no Hafsa k'awarta jinta a kashe yasa ta kira ta Husna,ba a d'auka ba har ta katse sake kira tayi a karo na biyu sannan aka dauka bayan sun gaisa ta sanar da ita dan Allah idan ta samu lokaci ta iyo mata iloka da alewar madara,sannan ta siyo mata goruba sosai Husna tayi ta dariya tana tsokanarta wai d'an baba ya yi kira dole ne tazo, a yau da yamma ta kawo mata.Haka su ka yi sallama ta kashe wayar sannan ta dauki wani dankwali ta daure hancinta dashi ta shiga kicin ta dorawa Ummulkairi indomie mai attaruhu da albasa ,ta juye sannan ta fasa kwai guda uku ta sanya albasa da maggi da curry ta soya mata ta juye ta dakko su ta ajiye a falo ta zauna tana kallo a tv gyangyad'i ta ke yi dan wani barcin ta keji sosai kamar ma ba ta yi ba, dan cikin barci da kuma kasala yake sanyata ga kuma zazzabin dake gewayata jingina ta yi a kan kujerar har hular kanta ta zame daga kan nata gashin da ta sanya ribon ta daureshi ta kama karshen ta tufke jelar ta sauka har gadon bayanta sai wani sheki yake ya bayyana. Ummulkhairi da yunwa ta hana ta sakat ta d'akko tsummar k'afarta ta nufo sashen Aysha,ko sallama babu haka ta afko falon tana shigowa idanunta su ka sauka a kan farar kyakkyawar fuskar Aysha da ta yi fayau da ita ga hancin nan kamar wanda a ka kara masa tsawo,baka hango komai sai gashin idonta da su kaeyi zagar zagar suka kwanta kamar ma ba barci take ba,gashin girarta kwantacce da kuma sajenta ,da gashin dake gaban goshinta duk sun kwanta sun kawata fuskar sosai ganinta haka ya tada hankalin Ummulkhairi kamar dai yau ta fara ganinta,ai idonta na sauka a kan gashin daya mata kama dana larabawa ko kuma indiyawa sai da zuciyarta ta yi wani tsalle kamar zata fito daga k'irjinta,sosai tayi mamakin ganin gashin Ayshan yarinya kamar wata yar shugaban kasa gabadaya alamomin jin dadi ne a tare da ita sai kawai taji ta raina kanta, gaba daya ayshan ta fita komai da komai kyau ,diri da cikar kirji anya kuwa ya Kb zai yarda ya aureta dan wanda ya ajiye mace kamar wannan me zai yi da ita kuma? tunowa da ta yi Hajiya za ta saka shi dole ya aureta sai ta ji hankalin ta ya dan kwanta,dan yanzu ma Hajiya ta aiko ta tazo ta yak'i soyayyarta ta samu gurbin zama a zuciyar yayanta dan idan yana ganinta yau da gobe dole zai ji yana sonta dan hakane ma suvka yiwa Daddy karyar Kaduna zata je shine ta tattaro kayanta ta taho nan.Wani haushi ne ya turniketa ta yi kan Aysha a zafafe kamar zata hauta da duka "Ke malama ina abincina ai wallahi tunda a gidan yayana ki ke dole ki girka ki bani,in ba haka ba in sanar da Hajiya wallahi". Ta fad'a tana rike k'ugu da hannu biyu. Aysha da kanta ya wani sara da k'arfi jin wannan hayaniyar da Ummulkhairi ke tsaye a kanta tana mata kamar ta mata wani babban laifi yasa ta daga yatsan ta ta mata nuni da karamin foodflask d'in dake dauke da indomie sai kuma bowl mai k'wai a ciki ta rufe da wani bowl din.Ita dama ba za ta dauka bane ta kai mata har dakin da take kamar wata uwarta.'Daukar kwanukan tayi tare da doka tsaki ta juya ta bar falon. Da yamma wajajen karfe hudu da rabi sai ga Husna ita da Hafsa sun zo,suna shigowa su kayi ido hudu da ummulkhairi da taci ado kamar mai zuwa biki ansa riga da sket na material dinkin ya kamata ansha maje up ga daurin dankwali,sai dai fuskar duk tabon kuraje na man bilicin da ake kwanbalawa.Sallama suke amma ta musu banza ta juya ta shige dakinta tana wani juya mazaunai da gaba daya suke manne jikinta kamar cingam babu wani tudu duk da tana da jiki amma bata da hips sai fadi tayi wani himgimgim.Dariya ma taso basu sai dai mamaki ya hana su dariyar dan suna tunanin kar dai Kb aure ya kara,basu gama jimamin ba Aysha ta fito tana musu maraba.Falo su ka shiga tun kan a gaisa suke jero mata tambayar wacece suka gani ita kwa cewa ta ke dan Allah su bata ledar kayan kwalam din taci kafin aje ga fadin wa suka gani. "Ga shi nan, ke da komai na duniya kike daukansa ba komai ba" Hafsa ta fada rai bace, ta tura mata ledar karba tayi ba tare da tayi magana ba ta bude ta fid do alewar madarar ta fara ci kamar yar yunwa dama wuni guda babu abinda taci,sai da taci sosai kafin ta dauki goruba daya dan gaba daya gorubar ma an banbashe mata,gurgura ta farayi sannan ta sanar musu wacece suka gani.Sosai su ke bala'i wai a kan me za ta yarda ta zauna mata a gida bayan a kwai aure tsakaninta da Kb,kuma ko kwalliyar nan ai dan a burge Kb a ka yi ta,ita dai ba tace musu komai ba ta d'auki ledar kayan da suka kawo mata tace su biyo ta d'aki.Suna shiga bedroom din suka zube a kasan capet nan aysha ta shiga basu labarin canjin da ta samu daga Kb tunda ta fara laulayin ciki da kuma abubuwan da ta gani jiya a cikin wayarsa. "Subhanallah! Gaskiya kina cikin damuwa wannan wace irin rayuwace, wai wasu mazan su keyi ? Ka dauki matarka ba a bakin komai ba,sanna ka fifita matan waje a kanta bayan ita tafi cancanta da ta samu kowace kulawa daga mijinta.,sannan ma da dududu ma yaushe a ka yi auren da har matsaloli irin wannan za su kunno kai cikin zamantakewar auren?". Hafsa ta ce rai 'bace. "Hakane ,amma ni kuma ina ganin abubuwan da kika gani ba wai suna nufin kb na neman mata bane ,kin san yanzu zamani nan wasu mazan ba wai sai suna zina bane su ke hulda da mataye barkatai ba ,a'a wasu ma kawai dan suke soyayya dasu kawai suna jin dadi suke tara yan mata da yawa,kuma ma yanzu wasu matan marar sa kamun kai ba komai bane dan namiji ya rike musu hannu ko kuma ya rungumesu gaba daya abin yazo da zamani da kuma karshen duniya sai dai kawai mace ta dagewa mijinta da addu'ar nema masa tsari da matayen banza idan kuma d'iya mace gareta ta nema mata tsari da samarin banza". cewar Husna. "Ni wallahi abin ne ya bani mamaki ya kuma shallake tunanina ,ban taba zaton yadda Kabeer ke nunamin so da kauna har ya tara mata haka bila adadin nifa na san abinda na gani". Aysha ta fada kamar za tayi kuka tunawa da tayi har hotuna ta gani ya na rungume da mace,yanzu ace wanda ta za'ba abokin rayuwarta sannan ma yanzu tana dauke da cikinsa zai zama abokin rayuwarta shine yake irin wannan abu. "Aysha kenan! Shi fa namiji haka ya ke son mata a halittarsu yake ,sai dai na wani yafi na wani,kuma da kike bayanin yana sonki ya kuma tara mata,shifa namiji da kike gani da ace za a bashi matan duka duniya ace mallakinsa ne amma kuma a ware guda daya ace ba tashi bace wato banda ita a mallakinsa to wallahi da gabaki daya hankalinsa zai maida kan wannan guda dayar,ji zai yi duk duniya ita ya ke so, ita yake muradin ya san wacece to haka namiji yake amma kuma ana samun wanda zaki ga basu damu da kula kulan yan mata ba amma fa basu da yawa gskia" Cewar Hafsa tana kallon Aysha da idanta ya ciko da kwalla. "Humaira ki yi hak'ur ki cire damuwa a ranki ko dan abinda ke jikinki,ki nunawa kb kamar ma ba ki san me yake yi ba, Sannan uwa uba ki dage da addu,a Allah maji rokone " Husna tace tana dafa kafadarta. "Shikenan nagod aminai na gari kuma insha Allahu zaku sameni mai aiki da shawarwarinku" Aysha tace tana murmushi. Ummulkhairi dake jikin window din bedroom din Aysha ta gama jin duk abinda suka tattauna tayi saurin barin wurin ranta fari kal. Su kuma falo suka taso suka dawo jin dirin motar kb,sallama suka mata su kace zasu tafi leda ta dakko cike da kayayyakin kwalliya da turaruka sai 5k ta basu sa hau d'an sahu.Rakosu tayi anan suka hadu da kb suka gaisheshi ya amsa da sakin fuska anan ta dakata da rakiyar ta juyo su kuma suka tafi,tana juyowa tayi ido hudu da ummulkhairi ta tare gaban kb sai wani fari take da ido tana wani tsuke baki shi kuma sai washe baki yake kamar gonar auduga,hakan bai bata mamaki ba sbd yanzu ta gama sanin halinsa.Karasowa ta yi itama ta tsaya a gabansu. "Barka da dawowa sadaukina" Ta fada tana kashe masa ido daya dan taba ummulkhairi haushi.Sakin baki yayi ganin Ayshan tayi wani masifaffan kallo irin na yan bariki,harshe yasa ya lashi labbansa sannan yace "Barkanki dai ishana"wani kululun abune ya tokarewa ummulkhari a makoshi. "Mu je na watsa maka ruwa ko kwa yi bankwana da gajiya" Tace tana mika hannu ta kamo hannunsa ,tasa daya hannun ta ruko k'ugunsa shima nata kugun ya riko suka tafi suka bar ummulkhairi tsaye da baki sake,ita Aysha tayi hakane da gangan dan ta cusa mata haushi shi kuma KB yama manta da ita a wurin😜 ummulkhairi dakinta ta wuce ta fada kan gado ta fashe da kukan bakin ciki MAMAN AFRAH😍🥰😘 MAMAN AFRAH😍🥰😘 بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share *_______________________________________* 🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨 Short story Story & written by MAMAN AFRAH Page 30--31 Sai da tasha kukanta ta koshi,sannan ta kira Hajia a waya ta shaida mata duk abin da ke wakana.Hajia taji dadin labarin da Ummulkhairi ta bata,na samun matsala tsakanin Aysha da Kb amma kuma kwata kwata bata ji dadin yadda Ummulkhairi tace ya biya Ayshan har sun tafi sun barta tsaye ,amma kuma tasan tunda dai akwai matsala tsakaninsu to tabbas da yiwuwar Ummulkhairin zata samu gurbin zama a wurin Kb.Sai dai itama Ummulkhairi ba tayi gigin fadawa Hajia cewar yana tare da wasu matan ba kamar yadda ta ji Aysha na baiwa kawayenta labari domin matukar Hajia ta san yana mu,amala da yan mata barkatai har ma yana iya rungumarsu to tabbas akwai matsala dan zata tsawatar masa ne akan abinda yake.Hakane ma ya bata damar boyewa Hajia domin tayi amfani da wannan damar tashi ta son mata ta ringa shiga wacce zai ke daukan hankalinsa har dai ta kai ga cimma nasara kamar yadda ta yiwa kanta alkawari,shisa da ta tashi fadawa Hajia tace akwai gagarumar matsala a tsakaninsu,amma kuma bata san wace iri bace.Bayan sun gama waya da Hajia a nan ta kwanta tana ta sake sake akan abinda ya faru yanzu tsakanin Aysha da Ya Kb ,tana tunanin yadda zata bullowa al,amarin har dai ta samu mafita ta tashi tana wani murmushi da ita kadai ta san ma,anarsa. "Yaro man kaza lallai ma yarinyar nan ke har wata bariki kika iya hmmm! zaki san kin taboni"Ummulkhari ta fada tana mai tashi ta shiga bayi ta wanko fuskarta saboda kukan da tayi.tana fitowa ta bude akwatinta ta dauko wasu fitinannun riga da wando sabbi dal ,daman duk yawancin kayan sune takanas ta je ta siyo su ,sai data tako babbar akwati da kaya daker ta rufu saboda cika da tayi.Gaban madubi ta zauna ta sake sabon make up ,tana gamawa ta dauki kayan ta sanya ta fesa turare kala kala sannan ta dauko wani farin karamin mayafi tayi rolling dashi ta dauki wayoyinta ,fitowa tayi ta zauna gindin wasu bishiyoyi da aka jera kujeru a wurin domin shak'atawa,kujera d'aya ta ja ta zauna tana fuskantar inda part sin Kb yake yadda yana fitowa da ita zaiyi tozali. Aysha kwa daurewa kawai take da ta rike Kb suke tafiya ji take kamar ta rike wuta kuma gaba d'aya sai abin da ta gani a wayarsa yake dawo mata.Haka zalika tayi hakane daman saboda Ummulkhairi,ba wai dan Kb din ba amma ganin ya bata hadin kai bai bayar da ita ba a gaban Ummulkhairi yasa ta ji dan saukin abinda take ji haka ta taimaka masa yayi wanka ta fiddo masa kaya ya sanya.yana tsaka da fesa turare wayarsa ta fara ringing daukan wayar yayi sai kuma ya maida kallonsa ga Aysha ya ga bama inda yake take kallo ba,kara kallon sunan mai kiran ya yi Zuly baby ,daukan wayar yayi ya fara magana. "gskia ki bari sai zuwa gobe yau akwai abin da zan yi"Haka kawai yace ya kashe wayar.Maida hankalinsa yayi kan Aysha da ta sunkuyar da kanta kasa,karasawa yayi gabanta yasa hannu ya dago da kan nata abin mamaki sai ganin hawaye ya yi wani na bin wani "Eeshana me yake damunki ne?" Ya tambaya cike da kulawa.hannu tasa ta goge hawayen tare da jan hanci ba tare da tace dashi komai ba, a ranta tace "Hmmm! Lallai namiji wato shi bai dauki wayar da ya yi a gabanta da wata macen zai iya bata mata rai ba?wato har ma tambayar damuwarta yake tabb maza sai a barsu" "Ko bakya jin dadi ne?" ya tambayeta yana zaunawa akan gadon kusa da ita. "Ba komai"tace ganin ya zauna kusa da ita har yana tambayar damuwarta wannan yasa ta ji ranta ya dan yi sanyi.haka suka zauna a falo suna d'an tab'a hira yace yana son yaci kosai da kunun gyada sosai ta ji dadi ganin bai da niyyar fita kamar yadda yake yi idan ya dawo daga kasuwa ya dad'a ficewa sai kuma lokacin kwanciya zai dawo.haka ya kamo hannunta suka tafi kicin domin ya tayata aiki dama tana da wake a gyare jikashi kawai tayi ta markada gyada kwa markadata suke kamar ta yin k'uli a ajiye in za,ayi amfani sai a dauka.Tana aikin suna hira abinsu a cikin hirar ne yake tambayarta zuwan Ummulkhairi take bashi labarin har da kayanta,dariya kawai yayi dan ya san shirin Hajia ne ita dai bazata canja hali ba.Har ta kammala ya tayata rikon tea flask din me kunu a ciki suka nufi part dinsa suna hira da yar dariya abinsu.Ummulkhairi ganin sun wuceta ko kallo bata ishi Kb ba ranta ya yi matukar baci,dan ita da farko tayi tunanin Kb fita zai yi shine Aysha ta rakoshi tana hangosu ta fara gyaggyarawa dan niyarta ta san duk yadda za tayi su fita tare amma sai taga sunyi hanyar kicin tana nan zaune suka fito tare suka nufi part din Kb .Bin su da kallo kawai take kamar taje ta shak'osu gaba d'ayansu haka take ji.sukwa akwala suka yi Kb ya jasu sallar magrib sannan suka ci abincin tare itama Aysha taci k'osan da kunun sosai a nan suka zauna suka sha hirarsu amma kuma ba,a minti sha biyar cikakke sai wata ta kira wayar Kb daga karshe ma sai wayar ya kashe gabaki d'aya.Cikin hirar tasu take tambayarshi zuwa gida wuni gobe ya amince mata haka sukayi sallar isha,i sukayi wankansu tare suka kwanta barci tare da gabatar da sunna,sosai Aysha ta shiga farinciki saboda rabonta da ta samu kulawa haka tun kan ta samu ciki. Ummulkhairi kwa ana zaune anyi kwam akan kujera ana jiran fitowar Kb ,tunda ta ji Aysha na fadawa k'awayenta kullum ya dawo kasuwa yana sake fita.Anan ta zauna har magriba sannan ta tashi rai bace ta hankada duka kujerun suka watse a kasa ta bar wurin ta koma daki😜cike da takaicin wannan rana amma kuma hakan bai sanya ta karaya ba kwafa take tana fadin "Allah kaimu gobe🙃 Washe gari da safe sai da Ummulkhairi ta dai daici lokacin fitar Ya Kb ya yi ta shiryo tsaf tana zuba kamshi direct part dinsa ta nufa ganin tun da Aysha ta hada break fast ta bar mata nata a kicin sai can taje ta dauka,da taji yunwa ta dameta dama da dare ma lemo tasha ta kwanta.Ganin sunki fitowa yasa ta je take buga kofar da karfi,Aysha ce tazo ta bud'e mata,kallon Aysha ta tsaya sama da kasa ganinta kamar wata ba india sanye take da fakistan riga da wando bakake kanta ko hula babu tayi kwalliya a fuskarta sai shek'i take abinta kayan sun amsheta sosai.Harara Ummulkhairi ta gallawa Aysha dan duk haushinta take ji kafin ta budi baki tace "Ba wurinki na zo ba malama ,wurin d'an uwana na zo ko shima bazan samu damar ganinshi ba??" Ta tamabaya tana mata kallon up & dawn.Dariya ce ta so subucewa Aysha ganin shigar da Ummulkhairi ta yi sanye take da doguwar rigar atamfa atamfar green mai ratsin yellow sai ta yafa karamin mayafi yellow ansha kwalliyar nan,ba komai bane ya baiwa Aysha dariya sai yadda rigar ta yiwa Ummulkhairi kamar wanda aka dauki buhun hatsi aka sanyawa riga🤣. "In ki ka yi hak'uri ma yanzu zai fito"Aysha ta fada tare da juyawa ta rufo kofar dan kar dariya ta kwace mata ta ballo ruwa hallaw.Tsaki ta yi tare da komawa gefe guda ta kama k'ugu ta tsaya.Jim kadan sai gasu sun fito tare. "Barka da safiya Ya Kb"ta fada tana wani tsuke baki. "Barkanki dai"Ya Kb ya fada hankalinsa akan Aysha. "Yaya dama inaso ka sauke ni a gdn su wata friend dina" "Hakan ba zai samu ba "Ya fada tare da sanya hannu a aljihu ya dakko kudi ya mika mata. "Gashi ki hau napep "ya juya suka jera da Aysha da zata rakashi gun motarshi.itakwa Ummulkhairi kallon kud'in ta tsaya saroro haushi tare da tarin bakin ciki sun mamaye mata zuciya.Tana nan tsaye har motar Kb ta bar gidan Aysha ta dawo dai dai zata shiga daki Ummulkhairi tace "Duk jarabar mutum dai bai isa ya raban da dan uwana ba" murmushi kawai Aysha tayi ta shigewarta daki ba tare da ta tanka ta ba.itama dakinta ta shige tayi jifa da jakarta da kudin da Ya Kb ya bata. Aysha kwa shiri ta sake cikin less mai shegen kyau ta yafa mayafi ta dakko keys din part dinta dana Ya Kb ta rurrufe ta fito ta tari napep ta tafi gidansu.Ta tarar gidan babu lpia domin kwa Abbanta ne bashi da lpia wani abu ya fito masa a gadon baya dan ko fita ma baya yi.Amma idan suka yi waya Umma sai tace kowa lpia k'alaw kai ko Abban ma sukan yi waya amma bata taba fahimtar baya jin dadi ba. BANI CAJI🙄 MAMAN AFRAH🥰😘😍 بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share *_______________________________________* 🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨 Short story Story & written by MAMAN AFRAH Page 32--33 Haka Aysha tayi wunin gida a ranar ranta kwata kwata babu dadi domin ganin mahaifinta cikin ciwo mahaifiyarta cikin damuwa yasa taji gaba daya duniyar bata mata dadi. Haka ta bar gidan zuciyarta cike da damuwa domin gaba d'aya ma shi ciwon Abban nata an kasa tantance wane iri ne wani k'aton k'urji ne wanda girmansa ya yi mutum ya hada hannayensa wuri d'aya ya dunk'ule tauri k'igir dashi kamar dutsi😭 haka dai Ummarta tayi ta kwantar mata da hankali kafin ta musu sallama ta kama hanyar gida. A lokacin karfe shida ma tayi, sai bayan ta hau dan sahu ta tuna cewar lokacin dawowar Kb gida ma ya wuce. Tana sauka ta baiwa dan sahun kudinsa, karamar kofar get din ta tura ta shiga ta maida ta rufe mai gadi dake zaune kan bencinshi yana jin redio ya gaisheta ta amsa masa sama sama dan gaba daya jinta take kamar ba a duniyar mutane take ba, damuwar dake ranta ta hanata ta ji dadi a zuciyarta koda k'ankani ne. Har ga Allah tana son Abbanta tana kuma tausayin Ummarta gashi basu da wani d'a me debe musu kewa tunda ita kadai suka mallaka sai kawu Habibu dake zuwa lokaci zuwa lokaci domin taimaka Ummarta wajen jinyar Abban nata kamar yadda Ummar ta sanar da ita yau, a cewar Umma anki sanar da itane saboda kar ta shiga damuwa saboda abinda take dauke dashi tabbas! kwa Umma tayi gaskiya domin gashi yanzu tunda ta yi arba da halin da Abbanta ke ciki bata samu sukuni ba ko miskala zarratin. Tana tafiya tana zancen zuci bata anakara ba sai ganinta tayi har tazo sashinta, bude kofarta ta yi ta shiga ta je ta ajiye jakarta da mayafinta, ta fito domin zuwa sashen mijinta dan ta ga motarsa alamar yana nan kenan tunda tasan matsawar ya dawo to fita kwa ta zama dole, amma kuma tunawa da tayi jiya ma ba Inda ya je wannan yasa ta fara tunanin ya fara gyara halayensa. Sai dai kuma in ko Aliyu ne ya zo suka fita tare a motarsa. Tura kofar tayi ta shiga amma kuma bata ga Kb a ko ina ba hatta bayin ta duba baya ciki, hakan yasa ta fara tunanin ta tambayi me gadi ko ya fitane bayan ya dawo? To amma kuma me yasa be kulle part din nashi ba? Tunda ya san yanzu ba su kadai bane a gidan akwai Ummulkhairi. Fitowa tayi da niyyar zuwa tambayar me gadi, shaida mata yayi Alhajin yana ciki bai fita ba,garden ta nufa wai ko can ya je yake hutawa, tun daga nesa ta hango inda kujerun suke amma babu kowa a kansu. Cikin lambun tabi ta dan zagaya amma babu shi babu alamarsa,abun ne ya daure mata kai haka ta kamo hanya ta dawo har zata shiga daki sai wata zuciyar tace ta tambayi Ummulkhairi dan jim tayi tunda tasan ba wani shiri suke ba amma a haka ta doshi dakin Ummulkhairin tana fargabar kar ta mata rashin arziki. Tana zuwa kofar dakin ta fara jiyo tashin sautin dariya data kasa banbance mamallakan muryan, kwankwasa kofar tayi amma ba, a mata magana ba kuma tasan an ji, sake nocking din tayi a karo na biyu, jin ba, a mata magana ba yasa ta tora kofar, abinda idanunta suka gani👀 shi ya sanya ta razana Ummulkhairi ce da Kb zaune akan kujera daya kanta akan kafadarsa suna kallo a waya yayin da wayar take a hannun Kb suna ta dariya abinsu hankalinsu kwance, kamar ma basu san da shigowar Aysha dakin ba. Wani kululun bakin ciki da takaici ne suka taru suka mamayewa Aysha ranta take ta ji wani kishi ya hayayyako mata hawaye ne suke neman zubo mata amma kuma basu samu dama ba domin kwa tayi namijin kokari wajen ganin ta danne su, bude baki tayi da niyyar yin magana amma kuma maganar da Kb yayi ita ta hanata furta tata maganar. "Dalla malama ya zaki fadowa mutane daki ba sallama? ko irin tarbiyar gidanku kenan? " ya fada yana wani hade rai tare da zaro mata idanu. "A, a toh kai ma dai ka fada Ya Kb, tunda idonka ya nuna maka yanzu"Ummulkhairi tace tana dariyar shekiyanci. "Yanzu dan na shigo dakin nan kake kiran babu tarbiya a gdn mu? Kafin in shigo sau nawa na kwankwasa kuka kyaleni?bayan na shigo na ganku manne da juna bayan ku ba ma, aurata bane ba kuma muharraman juna bane, kai koda ku muharraman juna bai kamata kuyi irin zaman da kuka yi ba yanzu amm....... "Ke dakata ke har kin isa kizo har dakina kice zaki gaya min maganar banza nawa ma ilimin naki yake da har zaki yiwa mutane wa, azi ko nasiha"Ummulkhairi tace tana aika mata harara. "Yauwa! Sisina fada mata dan tun kan ta san hanyar makaranta muka sani"cewar Kb "wlh dan d'an iliminta da baifi cikin cokali ba"Kb yace tare da fashewa da dariya, Ummulkhairi ta mika masa hannu suka tafa🤝 "wannan haka yake Yayana"tace tana maida kanta kafadarsa. "Ki fice kiba mutane wuri wama yasan daga ina kike"yace yana maida hankalinsa kan wayar dake rike a hannunsa. "Wallahi kwa Ya Kb kana fita itama ta saka kafarta ta fice, sai yanzu ta dawo"Ummulkhairi tace tana fakar idon Kb ta yiwa Aysha gwalo. Hawayen takaici ne suka cika mata idanu gaba daya ta daina gane komai haka ta juyo ta baro musu dakin tana tafiya ba tare da ta san inda take saka kafarta ba har ta karasa kan gadonta ta kwanta tare da fashewa da kuka mai taba zuciyar mai sauraro. Salloli kawai t gabatar ta yiwa mahaifinta addu, ar samun lafiya tare da duk musulmi sannan ta rokawa kanta sauki da sassaucin halin data tsinci kanta a ciki. Abin da Aysha bata sani ba shi ne tun da ta saka kafarta ta fita, itama Ummulkhairi ta tafi gidan kawar Hajia da ta hadata da ita zasu je wurin wani malami domin a shawo kan Kb yake kula Ummulkhairin domin a cewarsu itama fitar da tayi wurin boka ko malam ta tafi.Haka suka bada kudade masu yawa aka basu magani wanda nan take zai fara aiki sannan magani ne na shiga tsakanin Kb da Aysha. Haka barci barci ya k'auracewa idanun Aysha har wajajen karfe biyu na dare da taga dai babu abinda zuciyarta keyi sai sake sake tashi tayi ta dauro alwala ta ringa nafiloli tana kai kukanta gurin wanda baya barci sannan gyangyadi bai kamashi,bayan ta idar da sallolin ta karanta sunayen Allah 99 sannan ta karanta Alqur, ani mai girma.daga hannayenta tayi ta ringa jero addu, o, i bayan ta gama ta like abin sallar ta maida Alqur,an din ma ajjinsa. Komawa tayi ta kwanta lokacin har karfe uku da arba, in, cikinta ne ya fara k'ugi alamar yunwa fresh milk ta dauko mai sanyi tasha ta koma ta nkwanta nan take barci ya yi awon gaba da ita. Washe gari Bayan ta yi wanka ta gama shiryawa ta shiga kicin ta hada breakfast doya ta soya sai tayi miyar kwai, sai ruwan shayi mai kayan kamshi, dakkowa tayi ya nufi sashen Kb dan lokacin karfe takwas da kwata jerasu tayi a kasan capet dan Kb bai fiya san cin abinci a dinning ba.bedroom dinsa ta nufa,lokacin har ya shirya yana taje gashin kansa, shigowa tayi bakinta dauke da sallama Kb dake tsaue gaban mirror yaji kamar ta doka masa guduma a kansa. "ke! me ya kawoki dakina? " "kayi hak'uri abinci na kawo maka" "banason cin abincin naki ki fice min a d'aki banason ganinki, kuma kar in sake ganinki kin shigo min daki"yace yana nuna mata kofa. "Ya Kb,Ya Kb"sukaji Ummulkhairi na k'wala masa kira a falo. "Gani nan k'anwata"ya fad'a tare da daukan wayarsa ya gota Aysha dake tsaye kamar gunki ya fice, itama bayansa tabi suka karaso falon tare Ummulkhairi na zaune ta dora kafa d'aya kan daya sanye take da doguwar riga yar kanti jikin rigar roba gaba daya ta kamata.sai k'aramin mayafi data yafa tana ganin Kb ya fito ta tashi ta nufoshi sukayi gaisuwar larabawa suna ta murmushi abin su, "Allah tun jiya daka taho wajen karfe goman nan ban samu sukuni ba sai yanzu dana ganka"Ummulkhairi tacw tana wani mak'ale kafada tare da zunburo bakinta mai kama dana sauro. "Sorry nima haka na kasance amma yanzu ai gani ko? "ya fada cikin lallashi. Aysha da ranta ya matukar b'aci ta rab'a su ta fice daga falon, haka ta koma falonta ta zauna tana jin lokaxin da mai gadi ya wangale musu get suka fice. "Innalillahi wa inna ilaihir raji, un "kawai take furtawa,har ta ji zuciyarta ta yi sanyi. Tun daga wannan ranar Aysha bata kara sumun wata dama ba a matsayinta na mata a wurin Kb. Haka suke fita tare da Ummulkhairi shi ya san inda yake kai ta ya wuce kasuwa idan zai dawo haka tare zasu dawo, su shigo da take away ba ruwansu da neman abinci haka kawai ma sai su tafi yawo tare a gida suna tare kamar dai mata da miji soyayya suke zubawa abin su, sai barci kawai ke rabasu duk wannan shak'uwar daje tsakaninsu baisa Aysha ta musu zargin zina ba. Haka rayuwa ta ci gaba da kasancewa amma koda wasa Aysha bata taba sanar da kowa abin da ke faruwa ba. To wama zata fad'awa mahaifiyarta dake cikin damuwar jinyar mahaifinta ko kuma Hajia da ba k'aunarta take ba kuma ma ai da saninta abin ke faruwa tunda tasan da zaman Ummulkhairin a gidan, sannan bataso ta fadawa su hafsa saboda kar su ma su dauki abin a bai bai dan duk wanda zata baiwa labarin zai dauki mijinta mazinaci ita kuma bataso sunan uban y'ay'anta ya baci ko ba komai su y'ay'a a wurinsu mahaifine duk lalacewarsa, sannan kuma shi yaro bashi da laifi ba shine ke da alhakin zabawa kansa mahaifi ba dan haka tana ganin koma menene laifinta ne,kuma bai kamata take sanar da wani abin da ya zama sirrinta ba. Tana cikin gidan amma Kb ko ta kanta baya ba, dan ita wani lokacin ma sai tayi kwana biyu bata ganshi ba, kuma koda ta ganshin ma sai dai daga nesa,kai koda suna zaune da Ummukhairi Ayshan ta zo wucewa yi yake kamar ma bai santa ba.Akwai wani lokaci da taje ta tambayeshi zata je duba mahaifinta da bai da lafiya cewa yayi kar ta kara zuwa tambayarshi duk inda takeso taje abinta. Tun daga wannan ranar idan taga an dan kwana biyu sai taje ta duba mahaifinta, amma ka duk da bata fadawa mahaifiyarta damuwarta ba Umma ta gane tana cikin damuwa, amma data tambayeta sai tace rashin lafiyar Abbanta ke damunta gashi kullum sai magani ake amma a banza kurjin na kara girma asibiti har sun gaji da basu magani sun sauya asibiti yafi goma gashi yanzu kudin maganin ma basu dashi duk jarin kayan miyar ya kare a jinya komai da suke dashi a kare a neman magani. Tabbas idan Allah ya baka RAI da LAFIYA ka gode masa dan duk dukiyar da kake tak'ama da ita da kadarorin da kake alfahri ka tara lokaci daya sai Allah ya jarabceka da jinyar da zata cinye gaba d'aya dukiyar da kake da ita🥲Allah ka kara mana lafiya wanda basu da lafiya na asibiti dana gida Allah basu lafiya👏👏Dama Daddy ke taimaka musu yana canja masu asubiti daga karshe ya yanke shawarar fitar dashi kasar India aikwa yana fadawa hajia ta shiga ta fita tasa aka mantar dashi suwaye iyayen Aysha ma gaba daya kai hatta Ayshan ma ya manta da ita kwata kwata. A haka dai ciwo ke cin Abba dan har ciwon yazo y fashe yake zubar da ruwa, amma duk tsawon lokacin daya dauka yana jinyar sau d'aya Kb yaje dubashi shima Ummulkhairi tace su je su dubashi da ta ji Aysha tace bai da lafiya dan tanaso tayi tsegumi na ganin gidan su Ayshan. Itakwa Umma bata kawo komai dan duk randa Aysha ta zo sai tace Kb yana yiwa Abba sannu yace zai zo ya dubashi insha Allah. Koda sukazo da Ummulkhairi Umma bata kawo komai ba tunda Kb yace yar kanwar hajia sai dai bataji dadin yadsa Ummulkhairi ke yatsina ba, tana wani tofar da yawu. Ko Hajia da batazo duba Abban ba Umma bata kawo komai ba kuma daman tasan ba kowane mai kud'i keson zuwa inda talaka je rayuwa ba kuma ma ta fahimci Hajia ba da son ranta aka auri Aysha ba. Dan sun taba zuwa gidan bisa jagorancin Daddy amma bata ga wata alamar karbuwa a wurin Hajia ba. Cikin Aysha ya tsufa tana zuwa awo ,wani lokacin ma daga asibiti take wucewa gidansu taga jikin mahaifinta. Saboda gaba d'aya ma batason zaman gidan nata domin idan namiji ya juya maka baya sai kaji gaba daya duniyar ta maka kunci dan ma dai tana hadawa da addu, a, ga cikinta da ya tsufa amma hakan bai damu Ummulkhairi ba dan tunda ta samu kan Kb ita Aysha bata gabanta, yanzu so take suyi aure amma yana cewa ta bari akwai abinda yake shiryawa. Itama Hajia yanzu ranta fari kal danta na son abinda take so. Wata ranar larabace da asuba Allah ya karbi ran abinsa wato Abba ya amsa kiran mahalicci. Mutuwar data girgiza Umma da mutanen anguwa, ba, a sanar da Aysha ba sai kawai kawu Habibu daya dauki mai taxi suka je gidan Aysha domin ya taho da ita. Ya sanar mata jikin Abba ya matsa ne amma tana ta tambayarsa ko dai Abba ya mutu amma bai amsa mata ba, domin shima ya yi kokari soasi wajen ganin danne kukansa dan kar hankalin Ayshan ya tashi. Haka tasa hijabi duk ta rikice dan dama gaba daya yadda ta baro Abban nata jiya hankalinta bai kwanta ba haka ta kwana suk'uk'u duk damuwar Abban bata barta ta runtsa ba. Ga wata irin fad'uwar gaba dake damunta. Haka suka zo unguwarsu suna shigowa layinsu ta hango mutane maza a kofar gidansu sai mata dake ta tururuwar shiga domin yin sutura. Sosai hawaye ke zubowa daga idanunta amma bata yarda tayi kokan da manzo (S. A. W) ya yi hani a yi ba wanda ake k'walawa ana kiran an mutu an lalace, gata ya kare🙄 haka ta bud'e kofar motar ta fita tana ganin jiri ta shiga gidan yayin da wata mata da zata shiga gidan ta kama hannunta tana bata hak'uri Allah sarki rai bak'on duniya😭 tabbas kowace rai sai ta dandani mutuwa😭 Duk wanda ka ga ya muti shima bai san a ranar zai mutu ba😭😭 Haka za, azare ransa yana ji yana gani bashi da tsumi bashi da dabara, haka kawai zaiga mala, ikan mutuwa ya zo domin tafiya da ransa😭😭😭 Haka za, a wankeshi a sanya masa likkafani a daddaureshi, a dora a makara a sallata a kai a sanya a cikin kabari daga ranar ya koma rayuwa cikin kasa😭😭😭😭 A sanyaka a rami asa itace ganyen maina ,tukwane, kasa jik'ak'k'iya sannan bushashshiya, shikenan an shafeka a doran kasa daga kai sai halinka In kairan khairan in sharran sharran. Allah kasa mu aikata alkhairi😭😭😭😭 👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏 Aysha an bude mata Abbanta ta ganshi ta masa addu, a da ban kwana, haka suna ji suna gani aka daukoshi aka fita dashi daga gidan fita ta har abada fitar da ba, a sake dawowa. Ana fita da gawar Abba ciwon nakuda ya tashi wa Aysha........ MAMAN AFRAH🥰😍😘 بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share *_______________________________________* 🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨 Short story Story & written by MAMAN AFRAH Page 34--35 Ciwo ne ya sarke Aysha sosai wanda har bata gane su waye akanta, ga ciwo ga kuma damuwa. Suna so a fito a kaita asibiti wasu matane guda biyu suka fito domin samo abin hawan da za, a tafi asibitin a lokacin har an sallaci gawar Abba an dauketa domin kaita makwancinta. wasu maza ne guda hudu akan tabarma matan suka aika wani saurayi daga cikinsu ya samo abin hawan. Acan cikin gida kwa nakuda ce ta taso gadan gadan kakar Ayshan ce mahaifiyar Ummanta da wata makociyarsu ingozoma suke tare da Aysha kafin me wannan faya ta fashe har kan da ya dungo. Haka akayi ta taimaka mata har dai Allah ya sauketa lafiya. Ta haifi diyarta mace Allah sarki ga abin murna da farinciki ga kuma damuwa ta danne farincikin. Dan haka motar da aka samo domin kaita asibitin sai tafiya mai motar ya yi domin babu wata matsala ko k'ari bata samu ba.Haka Aysha da Ummanta suka saka diyar gaba suna kuka, kukan rashin ganinta da Abba bai yi ba kullum maganarsa Allah yasa kar ya mutu bai ga tsatson Aysha ba sai gashi ko kwana daya babu tsakaninsu a ranar da Abban ya bar duniya ita kuma a ranar ta diro duniyar. (shi yasa ake cewa mutum ya aikata alkairi,, dan idan mutum bashi da aiki sai neman mata to a ranar daya mutu wata macen ma a ranar zata balaga. Wata kuma a ranar zata diro duniyar kenan mutuwarsa bazata sa a daina komai ba ). Ummulkhairi ce ta kira Hajia take sanar da ita Mutuwar mahaifin Aysha, dan ita Ummulkhairin akan idonta kawu Habibu ya tafi da Aysha tana kuka, sannan Kawu Habibun ya kira Kb a waya yana sanar masa rashin domin lokacin daya zo gidan kwata kwata ya manta da batun Kb domin a rikice yake. Kuma lokacin suna tare da Ummulkhairin aka kira shi, dan haka sai abin ya bata tausayi sosai ta ji tausayin Aysha.data kira Hajia ta shaida mata sai tace ita babu inda zata je, shi ne Ummulkhairin tace ta fadawa Daddy ya je wurin suturar tunda indai ba ita tace ya je ba to fa ba zuwa zaiyi ba tunda ba a hayyacinshi yake ba, sai abinda tace masa kuma indai bai je ba mutane zasu zagesu sannan duk ranar daya dawo hayyacinshi ya gane bai je wurin mutuwar ba rai ne zai baci. Da haka hajia ta fadawa Daddy ya je wirin mutuwar baban surukarsa kuma sai ta ga mutuwar ta dakeshi kamar dai yana cikin hayyacinshi. Haka direba ya daukeshi ya kaishi a lokacin ma ba, a dawo daga makabarta ba dan haka suka tafi makabartar. Itama Ummulkhairi data tisa Kb a gaba suka tafi suna zuwa ya wuce makabarta ita kuma ta shiga cikin gidan. Ummulkhairi wuri ta samu ta zauna da yake gidan a cike yake, bata ga Aysha ba dan haka sai tayi zaton tana daki tana nan a zaune ta ji wasu mata suna hira hmmm gidan makoki ma yanzu hira ake tun ma ba, a dawo daga kai gawa ba. "Kai Allah sarki kinga shi ana fita da gawarsa ita kuma nak'uda na tasar mata" "wallahi kinsan haka lamarin Ubangiji yake, kana naka Allah yana nasa, gashi ko dawo wa ba, a yi daga kaishi ba har ta haihu"dayar tace tana kad'a kai alamar jimami. "Wacece ta haihu? "Ummulkhairi dake kusa dasu akan kujera su kuma suna kan tabarma ta tambaya da mamaki a fuskarta. "Diyar marigayin mana humaira"daya daga cikinsu ta bata amsa. Kawai gani sukayi duk ta birkice, saurin daidaita natsuwarta tayi Tace"Allah dayyaba" "amin "suka amsa a tare. Itakwa Ummulkhairi gaba daya so take ta tashi ta fita tasan yadda zatayi ta janye Kb su tafi gida kar labarin haihuwar ya je masa. Bayan an dawo daga kai mamacin anyi addu, a kowa kokari yake ya yiwa wanda mutuwar ta shafa gaisuwa, wasu kuma suna ta fita a gidan domin tafiya gida saboda suturace ta safe ana so aje gida ayi yan aikace aikace a samu ayi karin kumallo. Wasu kuma suna ta shiga dakin da Aysha take domin ganin abinda ta haifa sai dai hakan bai samu ba saboda har lokacin ba, a gama kintsa ta ba ita da jaririyarta. Kb ne zaune a kan tabarma kusa da Daddy su duka sun rasa me yake musu dadi gaba daya suna so su gano dalilin kin maida hankali wajen duba Abba musamman Daddy ma da yake ganin rashin kyautawarsa amma kuma ya kasa tunano komai daya fara kokarin tunawa sai ya ji ya manta komai. Suna nan zaune suna karbar gaisuwa su da su kawu habibu, a lokacin kuma Ummulkhairi tana ta fan kiran wayar Kb amma bata shiga. Kakan Ayshan ne da aka kira aka sanar dashi saukar Aysha yazo ya zauna kusa da Daddy yake sanar dashi haihuwar Aysha. Sosai yayi addu, a da fatan alkahiri, Kb kwa sai wwni wani dadi yake ji a cikin ransa yayi y'a. Ana cikin haka Hajia ta dokowa Daddy waya akan ya dawo gida haka ya amsa mata ba dan yaso ba, har sun musu sallama zasu tafi sai kawu Habibu yace su shiga daga zaure a karbo yar su mata addu, a haka kwa akayi kawu Habibu ya kawo yarinyar Daddy ya karbeta ya mata addu, a ya mik'awa Kb hannunsa har karkarwa yake ya karbeta yarinya kyakkyawa sak Aysha kiran salla ya mata bayan sun ganta suka baiwa kawu Habibu ita ya maidata cikin gida. Ummulkhairi da ta ga wayar Kb taki shiga hakura tayi ta shiga ta yiwa Ummar Aysha gaisuwa ta shaida mata Hajia ba lafiya shi yasa bata zo ba, itakwa Umma cewa tayi ba komai Allah bata lafiya. Daddy motarsa ya shiga dirabansa ya jashi suka tafi a inda Kb ya kira Ummulkhairi a waya ta fito su ma suka shiga mota suka kama hanyar gida, dan yanzu Daddy ba,a hayyacinsa yake ba bare ya tambayi ba, asin zaman Ummulkhairin a gidan Kb. Daddy na komawa gida yake sanar da Hajia haihuwar Aysha, ranta ta ji ya mugun baci shikenan ta hada zuri, a da talakawa, banza tayi masa da ya gaji ya fita ya bata waje daman sashenta ya je domin mata albishir din samun jika. Rigima Ummulkhairi ta ringa yiwa Hajia wai ta ga Kb yana wani rawar kafa, akan haihuwar Aysha karfa asirin ya karye ya fasa aurenta aikwa Hajia tace aure babu fashi nan da sati biyu za, a yi komai a gama.murna gun Ummulkhairi ba, a magana.. Kb ya koma ya yiwa ya radawa yarsa suna (FAUZIYYA) a inda ya baiwa Aysha kudade masu yawa domin ko za, a buk'aci wani abu, duk da tana cikin damuwa sai taji sanyi a ranta ganin Kb yana zuwa yana kuma basu kulawa a tunaninta komai ya gyarune bata san bisa umarnin Ummulkhairi yake yi ba dan gudun maganar mutane yasa suka shirya hakan tapi ta da Hajia hatta kayan Baby babu abinda ba, a kai ba. Sai dai kakar yar batazo ta ganta ba suma kwa basu damu ba. BAYAN WATA BIYU Lokacin an yiwa Abba arba, in itama Aysha ta zubar da wanka har ma an shafi kwanaki, a mak'otansu aka sama mata wacce zata ke dan mata raino, suka tattara suka koma gidansu. Komowar da Aysha tayi gidanta ya tayar mata da hankali sosai domin kuwa tazo ta tara da Ummulkhairi a matsayin kishiyarta wanda kwata kwata bata san da hakan ba part guda aka gyarawa Ummulkhairi aka jera mata kaya na gani na fada. Tunda Aysha ta dawo gidan wannan Kb bai kulata daga ita har yar tata domin kuwa su Hajia sun kara tashi tsaye akan lamuran Kb sun kara shiga tsakaninsa sosai da Aysha da kuma yarsa FAUZIYYA. Tana ji tana gani komai ya gagareta a gidan sai dai ta ringa wasa da diyarta dan take dauke mata kewa.Yanzu sun hade kai da jamila nan take zuwa suyi ta yiwa Aysha habaice habaice dan ita jamila ko cikin ma babu dan tace ba yanzu ta shirya haihuwa ba, sai ta gama more rayuwarta domin bataso ta tsufa da wuri. Shi kuma Ya Abdullahi gashi da son y'ay'a amma babu yadda zaiyi saboda Hajia ta tsayawa Jamilan. Ko wucewa Ayshan tayi sai su kwashe da dariya, amma ita ko a jikinta bata kawosi aka, saboda komai ma mutum zaiyi yanayi ne dan miji to ita kuma mijin ba ta ita yake ba. Haka rayuwa tayi ta tafiya kullum da irin abinda Ummulkhairi zata bullo dashi wanda zai batawa Aysha rai, sannan duk wani abu da tasan zai k'untatawa zuciyar Aysha shi takeyi. Aysha kwa bata kulata iyakarta tayi ta danne zuciyarya tana yin hakuri da kyma juriya, sannan kullum bata da aiki sai karatun Alqur, ani mai girma da kuma nafilfili akan Allah ya zama gatanta ga kuma nasiha da Ummanta ke mata domin zuwa yanzu Umma ta gama gano Aysha na cikin matsala. Musamman ma da aka mata kishiya ya yin da take gidansu dan makokin mahaifinta da kuma wankan jego amma hakan baisa an jinkirta auran ba, koma baza, a jinkirta ba ai a sanar da ita. Yanzu ta kai har honeymoon Kb ya dauki Ummulkhairi suka tafi tsawon watanni uku ba tare da Aysha tasan ko da sunan kasar da suka tafi ba bare tasan Lokacin dawowarsu sai dai komai akwai a store babu abinda suka nema suka rasa sai walwala kulawa da kuma farinciki irin wanda kowacce mace ke fatan samu a gidan mijinta. Yanzu Fauzy ta warware sosai kuma kullum kyanta sai kara bayyana yake, gata da lafiya yarinyar kana ganinta kasa Aysha ce ta haifeta. A haka har su Kb suka dawo daga inda suka tafi honeymoon. Wanda suka kara dawowa da sabon salo sosai dan rayuwar turawa kawai suke a gidan, dan yanzu zaka ga Ummulkhairi da mini sket da have best tana yawa suna rungume rungume da kisa kisai a filin gida ba ruwansu da kowa. Abu daya ne ma Aysha take jin tsoronsa shine kar su bata yar mutane hannatu yarinyar dake mata renon Fauzy. Wani lokacin haka zaki ga Kb ya goyo Ummulkhairi a bayansa amma haka Aysha zata wucesu kamar ma bata gansu ba. Wannan abin shi yake baiwa Ummulkhairi haushi domin so take ta yiwa Aysha abinda zata bar gidan domin Kb za zamto nata ita kadai, duk yanzun ma menene igiyace kawai a tsakaninsu amma bayan haka babu wani abi da yake wakana sai dai abinda hausawa ke kira da zaman HAK'URI. BAYAN SHEKARA BIYU Har zuwa wannan lokacin bata sauya zani ba, din kuwa babu abinda ya canja tsakanin Aysha da Kb sai shi da Ummulkhairi dake cin karensu babu babbaka. Amma kuma wani abu da Ummulkhairi bata sani ba, shi ne har yanzu Kb yana nan da kule kulen yan matansa, ita kawai Aysha ce a gabanta shi yasa bata damu da tasan komai ba tunda tana ganin ta shiga tsakaninshi da Aysha ai babu ita babu kishi da wata mace🙄 wata ranar litinin Kb yace wa Ummulkhairi zai je ta, aziyya gidansu wani abokin kasuwancinsa, ta kafe akan zata bishi amma kuma yaki yace ta zauna yanzu zaije yabdawo ba dadewa zaiyi ba. Haka ya shirya shiri irin wanda Ummulkhairi bata yarda da gidan mutuwa zaije ba, yana fita itama ta shiga motarta daya sai mata ta mara masa baya. Kb da ya gama waya da Zuly zai je ya dauketa a gidansu bai san Ummulkhairi na biye dashi ba, domin ta iya takunta daga nesa take bin motat tashi yadda bazai gane ba tunda ya san motar tata idan ta bishi a kusa kusa zaiyi saurin ganota. Tana kallo ya faka motar wata ta fito daga wani gida ,abin da ya batawa Ummulkhairi rai bai wuce yadda Kb ya fito ya budewa budurwar kofa ba, tana shiga ya maida ya rufe ua koma ya shiga ta mazaunin direba. A nan take Ummulkhairi ta hau dokin zuciya, ta kuma dau kudirin kawo karshen alak'arsu a yau ba sai gobe ba. Ganin ba,a ja motar ba zuciyarta keta mata sak'e sak'en wani abun sukeyi a cikin motar wanda ya danganci soyayya, jin gaba d'aya ta fita hayyacinta yasa ta kunna motarta ta karasa wurinsu. A dai dai motar Kb ta faka motar tata ta bude ta fito afujajan tana fitowa ta bubbuga jikin motar da mugun karfi wanda hakan yasa Kb da Zuly saurin dagowa suka maida kallonsu wurin wacce ta buga kofar. "To karuwa! an rasa maahinshini shine aka b'uge da bin mazan mutane"Ummulkhairi tace tana kama k'ugu yayin da ta rike marfin motar da d'aya hannun. "Karuwa! Ni kike kira karuwa? "Zuly ta tambaya tana nuna kanta da hannunta. "Eh! An fad'a din in ba karuwa ba wane suna kike jiran na kiraki dashi? " D'aga hannu Zuly tayi ta wanke Ummulkhairi da wani gigitaccen mari wanda yasa Ummulkhairi ta ga wulgawar wasu taurari. Itama hannu ta d'aga zata rama ta ji an rike mata hannu kallon Kb tayi da rinannun idanunta da suka sauya kala tsabar marin da tasha da kuma bacin rai. Haushi yasa ta warce hannunta daga rikon da ya mata, batayi wata wata ba ta daukeshi da mari😨😨😨 domin gani tayi ma ai ya raina mata hankali a mareta bai rama mata ba kuma ya hanata ramawa 🙃🙊 tabb lallai Aysha tana k'ok'ari tana kuma hak'uri ji yanzu dan abin da ta gani yanda ya gigita mata tunani inaga Aysha da tun kafin Ummulkhairi ta zama matar Kb ta tare a gidanta take cusguna mata🥲ashe haka take jin babu dad'i kai kaishi masifane. "Ke kina da hankali kwa?? Ni zaki mara? "Kb ya fad'a yana koma mata kamar wani zaki. Bata ankara ba ta ji ya dauketa da wani gigitaccen mari wanda yafi na Zuly zafi da rad'ad'i a kumatu. Nan take maganar Boka ta dawo mata. "Karki kuskura ko da wasa kice zaki kai masa hannu ma, ana ki dukeshi, komin kankantar duka matsawar kikayi haka to tabbas aiki zai lalace a take komai zai wargaje babu bata lokaci zai dawo hayyacinsa sannan babu wani aure da zai sake wanzuwa tsakaninku! " Saurin dawowa hayyacinta tayi daga tunanin abinda boka ya fad'a mata. "Ya Kb ni matarka Ummulkhairi ka mara🥲" tace hawaye na zuba a idonta. "Wace matar tawa to indai nine mijinki na sakeki saki uku!!!" بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share *_______________________________________* 🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨 Short story Story & written by MAMAN AFRAH Page 36--37 A gigice Ummulkhairi take kallon fuskar Kb tana zazzare idanu, nan take hawaye ya fara zarya a kumatunta. "Ahayye to yanzu dai ba mijinki bane sai asan nayi umma ta gaida ashshe"Zuly tace tana fashewa da dariya. Juyawa Ummulkhairi tayi ta kalleta ga zafin mari ga na saki sannan itama tana kara mata da wani abin haushin. "Baby zo mu wuce uzurinmu tunda komai ya kare kuma"Zuly tace tana kama marfin motar ta shiga. Shima juyawa ya yi ya shiga ba tare da ya k'ara magana ba. Jan motar ya yi a 360 suka bar layin. Ummulkhairi jin jiri na d'ibanta yasa ta karasa jikin motar ta jingina, da taimakon dafa jikin motar ta karasa ta ciro makullin motar rufe motar ta yi, tasa kulle d'an sahu ta tsaida dan kwata kwata ba zata iya tuk'i ba. Tun da ta shiga d'an sahun take aikin kuka, kuka take sosai dan ta rasa dame zata kwatanta halin da ta shiga yanzu cikin lokaci k'ank'ani, mai napep d'in ke bata hak'uri akan koma me ya sameta ta fawwalawa Allah. "Dalla malam ka yi abin da ke gabanka"ta fad'a a zafafe. "Ikon Allah, Allah baki hak'uri"ya ce tare da maida hankali kan tuk'insa. Banza ta masa .dai dai k'ofar gidan data nuna masa ya tsaya a ransa yana kissima lallai dole tayi abin da take so indai a gidan nan take," to ko me yasa ba, a yawo da ita a mota? "ya tambayi kansa. Sauka tayi ta bude k'aramar kofar zata shiga, "Hajia baki sallame ni bafa" ko waigoya bata yi ba bare ya sa ran zata masa magana, bare har a kai ga bashi hak'k'insa da ya buk'ata. "Allah ya isa ki je na barki da Allah "ya ce tare da jan dan sahunsa ya bar wurin dan ua san ko shiga gidan ya yi yace a biyasa ba lallai hakan ya samu ba karshe ma ido ua juye da mujiya. Tana shiga gidan da wani uban ihu ta hau stairs domin cimma Hajia, d'akin Hajia ta shiga babu ko sallama. "Lafiya dai na ganki haka waye ya mutu?" "Hajia wallahi ya sake ni"ta ce tana fad'awa kan cinyar Hajia. "Ya sake ki garin yaya haka ta faru?" Nan Ummulkhairi ta kwashe komai ta fad'a mata. "Me ya kai ki, bayan kinsan sharadin da boka ya gindaya? " "Wallahi na manta Hajia"ta ce tana k'ara fashewa da kuka. Haka Hajia ta yi ta lallashinta ta ce zata san abin yi bayan tasan bokan ya ce duk wanda ya yi kokarin maida auren sunan shi gawa. ********* A can gida kwa lokacin da ake ta tafka wannan kitimir mira, ita kwa Aysha tana can ta baiwa Hanatu Fauzy tana zaune da littafin addu, o i a hannunta tana karanta azkar din yamma bayan ta gama ta dinga jero addu, o i akan Allah ya shiga lamarinta dan ta san ba mantawa ya yi da ita ba yana sane da halin da take ciki. Gamawarta ke da wuya ta aji ye littafin ta jiyo dirin mota amma ba tasan ko motar waye ba tsakanin Ummulkhairi da Kb dan tasan duk din su basa nan. Ta ji lokacin da ya fita, yana fita itama ta fita a tata motar. "Assalamu Alaikum " Kb ya ce wanda basu je ko ina da Zuly ba ya ji yana so ya ga Aysha shi ne ya ajiye Zulyn ya nufo gida. Jin muryar Kb cikin falonta, da mamaki kwarai a fuskarta take kallonshi mutumin da a shekara biyu bai shigo dakinta ba amma yau shi ne ya shigo har da sallama fuskarshi a washe kamar gonar audiga. "wa alaikumus salam"Ta amsa har lokacin bata bar mamaki ba. "Eesha nah "ya fada yana rungumota jikinsa difff ta yi kamar an dauke wuta jin ta jikin mijinta da rabon da ya rabeta tun kan Abbanta ya bar duniya, tun cikin Fauzy bai da girma, tun sanda ta je gidansu yini ta dawo ta tarar dashi a d'akin Ummulkhairi. Kokarin kwace kanta take daga gareshi jin hawaye na neman sakko mata, riketa ya yi da karfi yadda ba zata iya k'wacewa ba. "I miss you" Banza ta yi dashi bata masa magana. "Haba Humairana yanzu ba kiyi missing dina ba" jin abin da ya ce yasa wasu zafafan hawaye zubo mata Shin wace macece zata ce bata yi missing din mijinta ba tsawon shekara biyu da watanni??? Alhalin tana cikin gidansa kuma da igiyar aurensa a kanta Shin ko kwana biyu a kace mijinki zai a dakin kishiyarki ranar bakinta ya kike ji??? Bare kuma a dauki har kwananki a had'a mata tsawon shekaru🥲😭 dole zaki ji babu dad'i dole zaki shiga damuwa, dole zaki ji kunci da tashin hankali.in banda ma na rik'e Allah ina ta addu, ar samun sassauci da tuni na kamu da hawan jini ko ciwon zuciya irin tabargazar da ku ke a gabana!!! "Ki yi hak'uri matata kar ki rik'eni a kan hakan wlh bansan komai game da hakan ba"ya fad'a yana shinshinar turaren jikinta, wannan furucin nasa ne ya dawo da ita daga sak'ar zucin da ta ke. Kalamai ya ke masu taushi da sanyaya zuciya, masu tsaga b'argo da dukkan sassan jikin mutum, ba tasan ya akayi ba sai ji ta yi an yi sama da ita😕 kwantar da kanta tayi a kafadarsa bai zame da ita ko ina ba sai kan gadon bedroom d'inta,anan na juya dan ban so na shiga hurumin da ba nawa ba. Sun nunawa juna so da kuma k'auna sunyi kewar juna marar misali, sai dai muce Allah ka rabamu da wanda zasu shiga tsakaninmu da masoyanmu ameen. Sosai Kb ya kwashi gara😝sabo da Aysha irin matan nan ne da basu da budewa dan ko da ta haihu kamar ma bata haihu ba, dan ma da mutuwar mahaifi🥲 shi yasa ba, a mata gyara da wuri ba. Kakarta ke sakata shiga ruwan bagaruwa, bayan ta fito ta shiga na magarya, da wasu ruwan itatuwa dake gyara gaban mace ya hanashi lalacewa ko da haihuwa nawa za ta yi. Kuma lokacin ma an mata wasu hade hade masu kyau da daka mai kara ni, ima da gumba haka ta tafi da kayanta bayan wanda aka yi ta matsa mata tana sha sabo da tana cikin damuwa. Tun da ta dawo ta tarar da Ummulkhairi a matsayin matar Kb kuma Kb ba ta ita yake ba sai ta tattara kayan ta ajiye, amma da yake ma, abociyar shan markad'ad'd'iyar kankana da madara da zuma ce dan kawai ta kan sha hadin dan ta ji dad'i a ranta sannan yawancin kullum akwai kunun aya a friege dinta, gashi bata taba tsarki da ruwan sanyi wannan ya hana ni, imarta daskarewa. Sai ana kiran magrib komai ya lafa suka shiga wanka tare suka d'auro alwala, suka yi sallah.sai sannan Ayshan ta tuno da Fauzy ganin shiru shiru hannatu bata kawota ba. Itama hannatun ta ga lokacin da Kb ya shiga sashen Ayshan shi yasa ta yi ta jan fauzy da wasa har dai kuma ta ga fauzyn na jin barci ta goyata da ta yi barcin ta kaita d'akin da take ta kwantar da ita. Tun daga wannan ranar Kb ya dawo da kulawa ga Aysha soyayya babu kama hannun yaro, duk da ta lura har yanzu yana tare da yan matansa dama an ce mai hali baya fasa halinsa, sai dai itama kuma da tasan halinsa sai ta sha maganin zama dashi.ga wani had'i yar uwa matuk'ar ki ka yi zaki ga kyansa na san sai kin dinga yi tsabagen kyan da yake dashi. * Ki samu kankanarki mai kyau kwallo d'aya. ** Sai kwakwa kwallo d'aya. *** Dabino kamar na naira 100 ****kanamfari dai dai misali kamar dai na 50. Yadda za ki yi, ki samu wuk'a ki huda kankanar, kamar yadda masu sayarwa keyi idan suna so su ga ko kankana na da kyau, ma, ana a mata v shape. Amma ki yi mai dan girma sabo da kayan da zaki zuba a ciki. Ki cire k'wallon dabinonki, sai ki daka shi ya yi laushi, shima kanamfarin daka shi za ki yi, ya yi laushi, sai ki fasa kwakwar ki zuba ruwan kwakwar a cikin kankanar ta inda kika huda ta. Sai ki gurza kwakwar a magogin kub'ewa, bayan kin gurza ki juyeta cikin kankanar hakama kanamfarin da kika daka, sai dakakken dabinon shima ciki zaki antaya shi. Ki dannasu su shiga, sai kisa wannan wurin da kika yanke ki maidashi jikin kankanar ki rufe, ki sanya a friege ta yi kamar 30 minute, sai ki fitar ki yankata wannan kayayyakin su gauraya ko ina sai ki cinye abinki😋 Zaki ga kyau kamar me dan Allah y'an uwana mata a jarraba a gani sai an gwada akan san na kwarai🤝💃 ********* Bangaren Ummulkhairi da gyatumarta Hajia dan wahala bayan sun je wurin bokan ya ce aure ya kare, amma basu daddara ba, suka yi ta zuwa wurare da dama amma abin babu labari. Dan yanzu ko gidan Kb ya je ko kallo Ummulkhairi bata ishe shi ba, sannan bokan ya gargadesu akan kada su yarda Su fad'awa Daddy mutuwar auren domin hakan ne zai yi sanadiyyar karyewar asirin da ke jikin Daddy.Jin haka yasa Hajia kama bakinta tare da gargadar Ummulkhairi akan kar ta kuskura ta fad'awa Daddy, haka kuma Hajia ko Kb bata taba tuntuba da maganar ba, dan bata so sanadin hakan Daddy ya san maganar. Wannan k'in yiwa Kb maganar ne yasa Ummulkhairi jin haushin Hajia sannan tasha alwashin fad'awa Daddy dan yasa Kb ya maidata gidanshi. Wata ranar alhamis Hajia zata tafi bikin y'ar k'awarta da za, a yi a Abuja,dan bikin zai fara tun juma, a sai kuma lahdi za, a kammala. Ta yi ta yi Ummulkhairi ta shirya su tafi amma tace bata jin dad'i, ita kuma Hajia ganin ga yan aiki nan a gidan sannan Jamila ma yanzu nan gidan ta k'auro wai bata son zaman gidanta sabo da rainin wayau. Haka Hajia ta shirya direbanta ya wulwula da ita tare da wata kawarta suka tafi a mota daya wai basa son son tafiya a jirgi😕😜 bayan Hajia ta tafi da kwana daya ashe akwai abinda Ummulkhairi ke shiryawa domin ta kasa hak'urin rashin Kb. Part d'in Daddy ta nufa da sallamarta ta shiga, ta sameshi yana kallon news, zaunawa tayi. Gabanta na bada sautin rass sabo da fargabar abin da zai biyo baya. Amma haka ta danne zuciyarta ta fara kokarin sanar da Daddy dan tana gani ai tunda Hajia na Abuja ba wani zai sanar da ita ba. "Ummulkhairi kina buk'atar wani abu ne? "ya ce ya yin da yake rage volume din tv. "Daddy dama, am daman"sai kuma ta yi shiru tana sosa k'eya. "Dama me? Ki yi magana mana me ki ke so?? " "Daddy dama so nake na ce dan Allah kasa Ya Kb ya maidani d'akina, ya sakeni kwata kwata yanzu bai kula..... maganarta ta yanke ne ganin Daddy ya rike kanshi da hannu biyu yana jero salati......... MAMAN AFRAH😘🥰😻 بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share *_______________________________________* 🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨 Short story Story & written by MAMAN AFRAH Page 38--39 "Daddy lafiya?" Ummulkhairi taa fad'a hankali tashe dan gaba d'aya yanayun nashi ya bata matuk'ar tsoro. Daddy dai bai ma san tana yi ba sai sunayen Allah yake ta ambata, ji yake kamar kanshi zai rabe gida biyu can kuma sai ya ta ga ya fara bin jikin bango yana dafawa yana d'aga kafafunsa daker kamar wanda suke a d'aure. Gaba d'aya Ummulkhairi ta gama tsorata, sai binsa take da kallo har ya shiga bayin dake can karshen falon daga korido, sai jin k'aran amai ta ke yana ta kolon amai ji tayi daman bata fad'a masa maganar ba, gashi yanzu ta janyo ya shiga wani yanayi wanda dole Hajia ta san me ya faru. "Ummulkhairi "ta jiyo muryar Daddy kamar daga sama, dago idanunta tayi take kallonsa, abin mamaki da k'afafunsa yake tafiya ba tare da ya dafa bango ba. Ruwane a fuskarsa da alama wanke fuskar ya yi. "Ina Hajia?"ta ji ya tambayeta duk da bata amsa kiran da ya mata ba sai binsa kawai da take da kallo. "Ba ta tafi Abuja ba" ta bashi amsa jikinta a sanyaye dan tun da ta ji ya ambaci ina Hajia take to tabbas ya dawo hayyacinsa, tun da dai ai yasan Hajia ta tafi Abuja biki to mesa yake tambaya. "Abuja kuma lafiya tayi tafiya bata sanar min ba? " "Biki ta tafi kuma ta sanar maka" jim ya yi yana d'an nazari sai kuma ya ce "Okay bari na hau sama"ya juya ya hau matakalar benen a nutse kuma kana ganinshi kasan ya dawo Daddy na asali domin lokacin da baya hayyacinsa ko magana yake sai ka ga alama kamar dai wani zautacce.Binsa Ummulkhairi ta yi da kallo har ya b'acewa ganinta. "wayyo ni na b'allo ruwa na jik'awa Hajia aiki, kai hatta nawa aikin ma ya jik'e gashi Daddy ko ta kan maganar dana fad'a masa bai bi ba"ta ce tana mik'ewa ta fito daga part din daddy ta nufo na Hajia. Jamila ta tarar zaune tana shan ice cream tana kallo sai wani yatsina fuska take, kallo d'aya Ummulkhairi ta mata ta haye sama ba tare da ta kuma bi takanta ba. Bayan dawowar Hajia A lokacin da ta dawo Daddy ya fita dan haka wanka ta yi ta huta abinta hankali kwance. Shima Daddy da yake haushinta yake ji yana gani ta yi tafiya bata sanar dashi ba sai kawai bai bi takanta ba ya wuce sashensa ya watsa ruwa ya kwanta tunda lokacin har karfe tara na dare ya yi, ganin Daddy bai je inda take ba tunda tasan itace da gidan shi yake mata abinda takeso tun da ta gama dashi. Sannan ko da Jamila ta sanar da ita Ummulkhairin ta je kd bata kawo komai a kai ba tun da tasan tana xikin damuwar mutuwar aurenta, kuma tunda ita tayi tafiya bazata ji dad'in gidan ba tunda ba wani shiri suke da Jamila ba. Tashi tayi ta nufi part d'in Daddy, sama ta haura ganin duk fitilun a kashe yasa ranta k'ara b'aci, tana ganin kenan har ya kwanta ba tare da ya damu da ya ganta ba. Kunna fitilun ta yi, ta je ta tsaya a kansa k'ememe Daddy kwa ba barci yake ba yana jinta ya watsa yinta. Hannu ta mik'a ta janye bargon da ya rufa dashi. "Gaskia ne wato har ka samu damar kwanciya ba tare da ka je ka min sannu da zuwa ba? Ka kuma duba na dawo lafiya ko akasin haka" ta fad'a rai bace tana wani masa fad'a kamar wata gyatumarsa. Mamaki ne ya rufe Daddy wanda hakan yasa ya kasa ko da motsi. "wai ba magana nake maka ba? Ta zafice shi kamar mai k'ok'arin kai masa duka. Tashi zaune Daddy ya yi a nutse sannan ya dubi Hajia yace "Kin ci albarkacin y'ay'a kuma sa'arki d'aya bana k'aunar yin saki sabo da Allah bayaso kuma duk lokacin da aka yishi sai al, arshin Ubangiji ya girgiza amma wlh da a yau sai na datse igiyar da ke tsakani na da ke!!! "Daddy ya ce yana nunata da yatsa. Gaban Hajia ne ya bada rass, ta hadiye wani yawu dank'ararre a mak'oshinta, lokaci daya wata zufa ta fara jik'a mata jiki. Gani ta yi Daddy ya koma mata kamar wani zaki mutumin da sai yadda ta yi dashi amma yau yake mata ikirarin zai iya sakinta. "Banda rashiin sanin ciwon kai ki fice daga gidan nan ki tafi har Abuja ba tare da sani na ba, sannan ki dawo har ki ke maganar wai banje na miki ban gajiya ba, tabdi to yaushe na zama sallamamman miji yaushe na zama mijin ta ce?? " "Tabbas da alama wannan shegiyar yarinyar ta jik'a min aiki", tace a ranta a fili kuma tace "Dan Allah Daddyn yara ka yi hak'uri wlh nima ban san me ya hau kai na ba, kawai na tsinci kai na da fadin maganganun nan ne amma da yardar Allah bazan sake ba, kuma tafiyar da na yi kayi hak'uri nasan ban kyaut... "Ya isa haka"yace yana d'aga mata hannu ya ja bargo ya koma ya kwanta ya barta nan tsaye. Kashe fitilun tabl yi ta zo ta kwanta,idonta biyu har barci ya lula dashi, itakwa lallabawa ta yi ta baro part din nashi ta koma nata tana dana sanin k'in raba auren Aysha da Kb da ta sani ta sanya Kb ya saki Aysha tun baya hayyacinshi, ta rasa me yasa ta manta da hakan sai yanzu ta tuna. Hmmm Hajia kenan ai indai zaka rik'e addu a wane mutum. Waya ta dauka ta dannawa k'awarta kira bayan ta dauka take sanar da ita abin da ke faruwa nan tace mata tabbas aiki ya b'aci sosai ran Hajia ya baci. Suna gamawa ta dannawa Ummulkhairi kira wajen sau uku amma bata d'auka ba, Ummulkhairi kwa tana ganin kiran Hajia ta ki dauka.. ******* Aysha da diyarta fauzy kamar yadda suke kiranta, suna samun kulawa sosai daga wurin Kb dan yanzu basu da wata matsala ko kad'an, matsalar Aysha d'aya shi ne Zuly ita ce ta takura mata dan idan Kb yana gida tayi ta kiransa a waya idan kuma baya nan tayi ta kiran Aysha a waya tana gaya mata bak'ak'en maganganu wanda ita Aysha ta rasa a inda Zulyn ta samu numberta .sannan ko da ta sanar da Kb shiru ya mata kuma be d'auki mataki ba, dan da ya d'auka da Zuly d'in ta dena damunta a waya. K'arshe da ta ga abin nata ba na k'are bane sai ta sayata a black list, duk da haka bata daddara ba sai tayi ta turo mata da message na maganganu mararsa dad'i tana ce mata " y'ar matsiyata ta yi asiri ta rabata da masoyinta ita ta aureshi to wlh ba zata barta ta yi zaman lafiya ba indai tana numfashi sai ta rabata da Kb"Irin wannan maganganun su suke damun Aysha tana ganin ita shikenan GIDAN MIJINTA haka zai zama kullum da wacce zata tada mata hankali, tana ganin babu Ummulkhairi ashe akwai Zuly hallaw kuma bayan itama bata da masaniyar wata ba zata zo ba tunda dai shi MIJIN nata haka yake da shegen son matan tsiya🙄. Haka rayuwa ta ci gaba da kasancewa yau zuma gobe mad'aci dama hakane yau ka ji dad'i gobe kuma akasin haka. Yanzu fauzy ta warware sosai dan har ta shiga makaranta boko da islamiya akwai direban da yake kai ta ya koma ya dawo da ita. Dan haka yanzu itama hannatu ta koma gidansu sabo da zuwa makaranta dama dan renon fauzy aka kawota yanzu itama fauzy ta zama sai dai tayi renon😄 A lokacin fauzy na da shekara shida a lokacin ne kuma Allah ya k'ara azurta Aysha da wani cikin, cikin da yafi na fauzy girma duk da dama cikin fari bai fiya girma ba. Amma dai wannan girmansa sosai dan har sai da Umma ta samo mata wata mata mai suna hindu domin take taimaka mata sabo da zama dak'er tashi daker. Lokacin da cikin ya isa haihuwa sun je awo hindu ta rakata direba ya kaisu sai kawai nak'uda ta tashi nan take aka shiga da ita labour room bata dau dogon lokaci ba ta haifo y'ay'anta tagwaye mace da namiji. Sosai Aysha ta yi murna dan ko da akayi scanning d'aya aka gani Allah ya boye d'ayan,sai bayan ta sauka ta kira Kb da Umma ta sanar musu. Kb daga kasuwa asibitin ya taho direct murna kamar ya goyi Aysha Umma kwa sabo da kara bata zo asibitin ba, amma Kb da ya kira Daddy ya sanar masa sai gashi shi da Hajia itama ta ji twins ne sai washe baki take har da yiwa Aysha sannu. Bayan ta huta aka sallameta daman lafiya ta haihu dan haka suka tafi gida, suna zuwa bayan tayi wanka ta kira Hafsa da Husna ta sanar musu. Da yamma sai ga Umma da wasu makotansu guda biyu, sai kuma kakannin Aysha na wajen uwa kowa sai sam barka yake. Ranar suna yara suka ci sunan Hajia da Daddy ana kiransu Amir da Amira. BAYAN SHEKARA UKU A lokacin fauzy na da shekara tara twins kuma na da shekara uku, amma kuma maimakon abubuwa su sauya na daga halayyar Kb sai abubuwa suka kara cab'ewa domin yanzu sai ya koyo tsabagen wulak'anci da wata iriyar izza duk abinda Aysha tayi bata iya ba kuma wulakantata ba komai bane a wurinsa duk kuwa da bashi girma da take kuma bata tanka masa duk iya abin da zai mata sai dai gani da ido 👀 ji da kunne👂 in ma ta ga bata so yaran su ji abinda ke faruwa sai ta yi ta lallashinsa tana bashi hak'uri duk kuwa da ba ita ke da laifi ba. Gashi dai ba wani abu ta canja ba dan idan ka ga Aysha ba zaka taba cewa ita ta haifi su fauzy ba gashi kullum cikin ado da kwalliya take. Amma a hakan babu abin da Kb ya raga mata dan tana zaune ma sai yake waya da y'an matansa amma ko ci kanka bata ce masa abin da take yi kawai danne zuciyarta take domin ita yanzu ta fi mai da hankali ga tarbiyar yaranta domin shi Kb ba tarbiyar yaran bace a gabansa shi kawai duniya ce da matan da ke cikinta suke gabansa ,wanda hakan yasa yake ganin matarshi da ya ajiye a gida ba komai ba. Dan yanzu wasu ne matan sabbin zubi ya yi, dan hatta Zuly yanzu ta yi aure .Ni ba kulawar miji ba ta dangin miji kullum jiya i yau amma haka nake hak'uri tun ina b'oyewa Ummata har ta kai ta kawo ina gaya mata komai dan bani da wacce ta fita sai dai ta yi ta ban hak'uri akan in dage da addu, a komai ya yi farko yana da karshe. Ga yaran yanzu da shegen wayo komai kake hankalinsu akan ka shi yasa nake nusar da shi amma shi da je ba tarbiyar yaran ce a gabansa ba babu abin da ya dameshi da yin abu gaban yaro sannan baya tunanin yin abu gaban yaro yana sa yaro ya fahimci irin rayuwar da ake a gidansu. Bugu da k'ari kuma idan har mahaifi na yiwa mahaifiya abu gaban y'ay'anta tofa yaran sukan ji haushin uban nasu, haka zalika mahaifiyar.sai dai abin da mahaifiyar za ta yi shi ne ta yi k'ok'ari wajen ganin bata biyewa mijin gaban yara dan kar a taru a zama d'aya. Fad'a gaban yara ba k'aramar muhimmiyar rawa yake takawa ba wajen kawo rashin jituwa ga d'aya daga cikin mahaifa wanda yaran suka fihimci ana shiga hak'k'insa. Sannan uwa uba rashin ba da power ma na sanya a raina wanda aka hana power misali mahaifiya tana zartar da hukunci uba ya dakatar da ita a gaban yaran ya nuna bayaso ta yiwa yaran fad'a ko kuma duka, to wannan na sanya yaro ya raina uwa haka zalika kema uwar idan kina yi yaron zai raina mahaifinsa tunda yana gani idan ya miki abu ma babu abinda zaki masa tunda mahaifinsa zai hanaki zartar da komai. A wata ranar asabar ce muna zaune da yara ina koya musu karatu tun da yau ba makarantar boko, islamiya kuma sai karfe uku ,Abban su fauzy ne ya shigo falon nawa cikin shirinsa na fita kasuwa. Yaran ne suka ruga suna murna sun ganshi wuri ya samu ya zauna ya dora Amir a cinya d'aya Amira ita kuma fauzy dama rubutu take yi. Kallon fuskarsa na yi na ga babu alamar walwala ko kad'an dan haka nima ban ce komai ba dama tun da na kwaso kayan breakfast ban koma sashen nashi ba. "Tun da ba makarantar boko ki shirya su ku je ku gaishe da Hajia" Gaba na ne ya ba da rass jin abin da ya fada dan ya san dai Hajia ba k'aunar in je gidanta take ba, amma sabo da mahaifiya take a wurinsa sannan musu ba d'abi, a ta bace yasa na ce masa. "To insha Allah zamu je mu gaisheta" "Gaskia ni dai bazan je ba Hajia bata min dariya su Amir kawai take kulawa"Fauzy ta fad'a tana kumbura baki, domin itama k'iyayyata ce ta shafeta a wurin Hajia suma su Amira dan albarkacin sunan su da aka saka musu ne take k'aunarsu. "kar in k'ara jin maganar nan a bakinki"na ce ina bata rai yadda zata fahimci ta yi ba dai dai ba, duk da nasan tabbas yaro na son mai jan shi a jiki. "Ke ku duka zaku je" Abin da yace kawai ya mana sallama yaran suka rakashi bakin mota, nikwa daga nan inda nake zaune na masa Allah kiyaye ko amsawa bai yi ba nima na fafa ne kawai dan na san ba amsawar zai yi ba. Misalin karfe sha d'aya muka gama shiryawa ,napep muka hau dan yau direba baya nan. A bakin get aka sauke mu muka tura kofar muka shiga tun da muka shigo gabana ke fad'uwa. Part din Hajia muka wuce nocking muka yi aka bamu izinin shiga, shiga muka yi d'auke da sallama babu wanda ya amsa sallamar sai Hajia da take ta yiwa Amir da Amira oyoyo Ummulkhairi kwa kallo d'aya ta mana ta d'auke kai dan tun lokacin da ta dawo daga kd daga baya ta samu wani Alhaji mai bala, in kud'i ta aura matarsa d'aya ta taka Ummulkhairi a rashin mutunci dan daga k'arshema sai da ta mata dukan mutuwa sannan tasa Alhajin ya saketa daman shima irin masu auri saki ne, to shi ne fa ta dawo gida da zama sai kuma ta mayar dani kishiyarta duk da daman kishiyarce tun da ta tab'a auren mijina. Wuri muka samu muka zauna ni da Fauzy. "Hajia barka da hutawa ina kwana" na ce xike da girmamawa. "Hajia ina kwana"Fauzy ma ta gaisheta. Banza ta mana tana ta yiwa su Amir magana. "Kin gani Mama shi yasa na ce bazan zo ba kin ga ko magana bata min ba kuma na gaisheta ta kyaleni kema ta kyaleki" "Yimin shiru"Nace ina harararta. Hajia kwa tsayawa ta yi da wasan da take yiwa su Amira ta ce "To da wa ya gayyaceku? Ni na ce ku zo mun gida da sassafen nan ko karyawa baku yi ba? Ban da shishshigi da neman gindin zama, ai na fad'a miki bana k'aunarki kuma bazan tab'a kaunarki ba! "Hajia ta ce tana nuna Aysha da yatsa. "Mama tashi mu tafi"Fauzy ta ce tana kama hannu na. "Ke fitsararriya me suffar uwarta, daman kema bance ki doso in da nake ba ai gadan talauci gadon tsiya"Hajia ta fad'a tana zazzarewa Fauzy ido. "Haba Hajia ki yi hak'uri shi yaro me ya sani, kawai dai itama tana so ki ke janta a jiki kamar yadda ki ke yiwa sauran y'an uwanta" "A ah lalle kin yi baki, har ni ki ke gayawa magana ina fad'a kina fad'a? Ku tashi ku fice min daga gida"ta ce tana nuna mana kofa da hannu. Haka muka fito ni da Fauzy dan su Amir basu biyomu ba raina sai kuna yake bana jure ka yiwa d'ana abu musamman da Fauzy ke ta kuka. Motar Kb na shigowa ta Ummulkhairi ta biyo bayanta, fitowa ya yi suma suka fito Ummulkhairi Amir sai Amira. "Ya Kb barka da dawo wa" Ummulkhairi ta ce tana aika masa murmushi. "Ya na ganki da su Amir halan su kad'ai aka kai wurin Hajia? " بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share *_______________________________________* 🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨 Short story Story & written by MAMAN AFRAH Page 40 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 "Ba su kad'ai aka kai ba gyatumarsu ta je dasu shi ne ta shuka rashin arzik'i ta taho ta baro su a can"Ummulkairi ta ce tana kanne ido d'aya. "Bangane ba ita Aysha ce ta je ta yi rashin mutunci" Kb ya ce da mamaki. Aysha kwa da ke tsaye sakin baki ta yi galala tana kallonsu. "Eh mana har fa zagin Hajia ta yi" "Zagi "ya fad'a a zafafe. "Wlh kwa dan Hajia har da hawaye ta yi na takaicin zagin da Aysha ta mata... Ai kafin Ummulkhairi ta kai aya ya yi kan Aysha kamar zai kai mata duka, ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba, Aysha tana so ta masa bayani ya k'i saurarenta, Fauzy ma da zata yi magana ya dakatar da ita kai a tak'aice sai da Kb ya zagi Aysha ta uwa ta uba .Aysha kawai hawaye ke zuba a idonta itama Fauzy ba, a barta ba a baya dan tana da wayo sosai kuma tasan ba,a kyautawa mahaifiyarta ba, ta kuma san Mamanta bata zagi Hajia ba tana so ta yiwa Abban bayanin yadda aka yi amma yaki ya saurareta. Ummulkhairi kwa ranta fari kal ta had'a ta ji dad'i dan da sanin Hajia ma ta taho ta yi had'in wannan. Wannan shi ne abin da ya janyo Kb ya sakeni lallai namiji duk hak'urin da nake k'unsa a cikin gidansa amma bai gani ba sai da ya ci wa iyayena mutunci! Da asuba bayan na yi sallah na yi azkar, karamar trolly na d'akko na sanya kayana a ciki tare da abubuwan da zan buk'ata, fitowa na yi na je d'akin hindu mai kula min da yara na sanar mata zan tafi ta kulamin da yara na, na dauki kud'i masu yawa sosai ta ji babu dad'i jin sakin da na ce mata yaa shiga tsakaninmu. Haka na shiga d'akin yaran na gansu suna ta barci abinsu, na fito jin hawaye na neman kufce min ni kuma bana buk'atar yin kukan yanzu. Sashe na na dawo na dauki jakata da akwatin sai wayana, fitowa na yi na bude kofar na fita mai gadi na ta bani hak'uri domin ya san ba lafiya bace za tasa na fita da akwati da sassafen nan kuma ba tare da yaro ko d'aya ba. Ina fitowa bakin titi na samu napep dan lokacin gari ya yi haske sosai akwatin na sanya a xiki nima na shiga na zauna na fad'a masa in da zai kai ni. A dede kofar gidan mu nasa ya tsaya na biyashi kudinshi na kinkimi akwatina na shiga buga kofar gidanmu, wata iya salame da suke zaune tare da Umma a gidan kanwar maman Ummance ita ta bude min kofar gani na da akwati yasa jikinta yin sanyi, jakata ta karba ni kuma na shigo da akwatin Umma dake shara ta yarda tsintsiya ta tsaya fuskarta da tsahin hankali tana kallona, jikina ne ya k'ara yin sanyi ganin damuwa k'arara a fuskar Ummana. D'aki na shiga da akwatin na ajiye, haka muka zauna jugum jugum na fad'a musu duk abin da ya faru ina fad'a ina kukan takaici dan gaba d'aya sai nake jin kamar ma yanzu ake min duk abin da aka mini. BAYAN WATA UKU Lokacin har Aysha ta yi iddah, dan haka kawu habibu yasa ta yi jamb kuma Allah ya taimaketa ta ci aka nema mata admission a B. U. K nan take Aysha ta fara karatu babu kama hannun yaro, dan dama tana son karatu gata da bala, in k'ok'ari sannan kuma ta hadu da k'awaye wayayyu suke koya mata komai na rayuwa dan idan ka ga Aysha ba zaka ganeta ba. Kamar ma ba ita ta haifi yaranta ba ba wanda zai ganta yace ba budurwa bace. Ta kwantar da hankalinta tana yiwa y'ay'anta addu, a tana karatun ta hankali kwance. Sai dai samari da manyan Alhazai da ke mata tururuwa ita kuma tana sallamarsu dan babu sha, awar aure a ranta yanzu dan kayan d'akinta ma tuni aka kwaso ta sai da wasu wasu ta jerawa Ummarta .Sannan ta kan sari takalma da pad ta mata da kayan shafa tana tafiya dasu makaranta tana siyarwa abinta. ********* Bangaren Kb kwa tun da ya saki Aysha sai ya ji kamar ya yadda k'wallon mangwaro ya huta da k'uda. Dan yanzu ne yake cin karensa babu babbaka, sai ya kwana yana waya da y'an mata yara kwa ga hindu nan ita take musu komai dan ko gidan Hajiya aka kai su bata wani iya rikesu dak'er take bari su wuni, ta dai ce ya nemi mata ya yi aure dan murna fal cikinta da ya saki Aysha Daddy ne ma ya masa fushi ya kuma nuna masa bai kyauta ba. Amma abin da ya sa Daddy bai tsaurara ba sabo da yana so Kb ya gane muhimmancin Aysha ne. Kb sai da ya zab'a ya darje domin kuwa wata kilalliya ya samu ana kiranta Hajara bai dai yar masu kud'i bace amma kuma iya daukan wanka da kuma kyau da take dashi shi ya ja hankalin Kb ya aureta. Bayan aure ansha amarci sosai dan Kb gani yake yanzu ya yi aure, ya samu mace dede da tsarinsa sai dai me😕 ashe amarya kwata kwata bata san in da mutunci ya dosa ba, bata ragawa Kb bare Hajiya bare kuma wata karan kad'a miya Ummulkhairi, sai ta taka har gida ta je ta yiwa Hajiya rashin mutunci kuma daga Hajiyar har Kb din babu wanda ya isa ya d'auki mataki dan gaba d'ayansu tsoronta suke. Abu d'aya ne bata yi shi ne tab'a masa y'ay'a, ba ruwanta da su Fauzy, dan tun da aka bata labarin irin zaman da Aysha ta yi ita kuwa ta ce wallahi duk sai ta gyara musu zama👍 A kwana a tashi sai ga Kb ya dawo yana da ya sanin auren Hajara,dan yanzu ta zame masa alak'ak'ai ko fita bai isa ya yi ba sai da izininta kuma ba boka ba malam kawai tsabar rashin mutunci ne. Gashi ko wane wuri zata je sai tare da Kb zasu je, sannan ya bud'e mata mota ta shiga ya bude'e mata idan zata fita🙄 Yan mata kuwa sai da ta sanya kowacce a black list ta sanya ya goge gaba d'aya numbers d'insu. Idan ya shigo gida wayarsa a hannun Hajara zata kasance bai isa ya danna waya ba kai ko kiransa aka yi sai ta fara d'auka ta tabbatar da mai kiran sannan zata bashi wayar. Gaba da gabanta aljani ya taka wuta🙃 Yanzu ne Kb ya fara ganin muhimmancin Aysha yanzu ne yake jin inama ya mai da hannun agogo baya, kai ba Kb ba hatta Hajiya yanzu tana dana sani akan abin da ta yi ta yiwa Aysha, yanzu sosai take jan jikokinta a jiki dan hajara bata basu dad'i ba daga ita har Ummulkhairi, Daddy kad'ai take ragawa dan gaskia sosai take girmamashi, dan bata kwana uku bata je gidan Hajiya ba idan kuwa ta je bata baro gidan sai ta sanya Hajiya damuwa,.Dan ita yanzu Ummulkhairi ta samu wani me mata uku zata aura sabo da ta gujewa rashin mutuncin Hajara da kuma gorin aure da take mata kuma dan Hajara ta d'aga hannu ta zabgawa Ummulkhairi mari ba komai bane a wurinta gata da tsawo da k'iba🤣. BAYAN SHEKARA BIYAR Aysha ta samu kammala karatun ta, ta karb'i result d'inta kuma alhamdulillah ya yi kyau sosai. Yanzu ta kara zama babbar mace ta yi k'iba abinta farinta ya dawo ha online bussiness da take yi shaddodi lesina atamfofi da sauransu, babu abinda bata siyarwa tana samun kudinta alhamdulillah babu abin da suka nema suka rasa dan dai Daddy ma yana taimaka musu. Yanzu kawu Habibu ne Umma ta sanya shi ya sa Aysha ta fitar da miji ta yi aure, dan dama shi ya matsawa Umma ta barta ta yi karatu dan haka yanzu kuma Aysha ta kammala kuma ga manemanta nan masu mutunci shi yasa take so ta fidda wanda take gani ya dace ta aura. Duk da yau kusan shekara biyu Kb na zuwa wurinta yana bata hak'uri akan ta taimaka masa ta dawo dak'inta su cigaba da rayuwa🙄😕 amma ta ce babu ita babu gidansa amma duk da haka bai daddara ba kullum sai ya zo ko da kuwa ba zata kulashi ba. Dan wataran yana jikin motarsa zai ganta ta fito tana tare da wani wanda ya fishi komai da komai, duk da daman yanzu kud'in nashi ba kamar na da ba, dan Hajara ta gama tatik'eshi ta kuma rabu dashi👎 ba ciki ba goyo💃 ta karawa rigarta iska😄 Umma ce zaune da kawu Habibu Aysha sai kuma Daddy da shi ne sanadin had'uwar. "Aysha inaso ki fidda mijin aure dan ni kamar y'ar da na haifa haka na d'auke ki"cewar Daddy. Sunkuyar da kai Aysha ta yi dan kunyar Daddy take ji. "Ba magana ake miki ba"Umma ta fad'a tana hararta dan tun jiya da Daddy ya cewa Umma a waya zai zo akan maganar ta gargad'i Aysha akan ta zab'i tsohon mijinta🤨 sabo da yanzu gaba d'aya Kb ya canja kuma ta lura har yau yana son Aysha ga nacin zuwa da yake kullum, sannan ta san Aysha ma taa son sa kuma idan ma wani ta zab'a ba tasan wayeshi ba sai ta je gidansa dan haka ta gaya mata ta zab'i wanda ta tab'a zama dashi ko dan y'ay'anta dan halin maza sai su gwara wanda ta san halinsa, zai fi wanda bata sani ba. Ta yi hak'uri da abin da ya mata a baya ta manta da komai. "Ki yi magana mana kin yiwa mutane shiru"Kawu Habibu ya ce yana kallonta. "Ku mata a hankali mana kun san... "Assalamu Alaikum" sallamar da aka rangad'a ta hana Daddy k'arasa maganar, Hajiya ce ke sallama ita da Kb amsa musu aka yi tare da basu izinin shigowa. Mamaki ne ya kama Aysha da Umma na ganin Hajiya a gidansu abin da bata tab'a yi ba. ban da Daddy da daman ya san komai ka iya faruwa tun da Hajara ta koya musu hankali. Gaisawa aka yi a inda Kb da Hajiya suja shiga baiwa Aysha hak'uri musamman Hajiya da har da yafiya take nema a wurin Aysha. Aysha kunya ta ji anan take ta yafe musu, sannan Kb ya roketa alfarmar komawa d'akinsa har da durk'usawa da rok'onta yafe masa ta yi tare da fatan Allah yafe mana baki d'aya. Daddy ya ji dad'i da Aysha ta amince zata koma, daman yafi so ta koma amma dan kar ya nuna san kai shi yasa amma babu wanda zai yarda mace mai nagarta kamar Aysha ta kufcewa ahlinsa.An maida auren Aysha da Kb akan sadaki mai tsoka, a in da Aysha ta tare a gidanta ta ci gaba da kasuwancinta ba tare da takura ba. Sosai Aysha ta ga canji daha Kb gaba d'aya kamar sauya mata shi akayi yake wani nan nan da ita kulawa da soyayya ita da yaranta sai sam barka sun koma rayuwa mai tsafta a inda Kb ya sauya gaba d'aya halayensa. Yanzu ko kule kulen matan baya yi 😄 Ummulkhairi har gida ta zo ta rok'i yafiyar Aysha ita kuwa ta ce dama bata rik'eta ba. Su Hafsa da Husna sunyi aure Alhamdulillah suna zaune da mazajensu lafiya.Lallai wani abun alkairi ne yanzu barin Aysha gidan Kb ya zama alkairi gashi ta karo karatu ta zama wayayya tana huld'a da wayayyo gashi ta iya kasuwanci sannan ta dawo ta samu kwanciyar hankali daga gareshi ba takura kai har ma da mahaifiyarsa sai dai sam barka. BAYAN WASU SHEKARU Yanzu Alhamdulillah Kb ya k'ara samun bud'i sosai dan yanzu arzik'insa ya k'ara hab'aka gashi ya samu kwanciyara hankali ,a yanzu y'ay'ansu biyar fauzy, Amir, Amira, sai kuma Atika mai sunan Umma da kuma Saleh mai sunan Abba Allah raya ya musu albarka amin. Alhamdulillah anan na kawo k'arshen littafin nan mai suna GIDAN MIJINA, abin da na fad'a dai dai Allah yasa ya mutane su amfana dashi wanda na yi kuskure Allah yafe mini amin. Masoyana ina alfahri daku a duk in da ku ke, musamman wanda suka jure suka tsaya tsayin daka wajen min sharshi ina godiya marar adadi👎✊ Nagode sosai da sosai sai kun sake ji na a wani sabon littafi na mai suna 😄😄😄😄😄😄😄😄😄😄 Y' K' PAGE 41➡️42 "Ke wai dama ke ce?" Manal ta tambaya cikin kankance idanu. "Ni ce Aunty" Mimi ta amsa tana murmushi. Bala,i yanzu yarinyar nan ce ta zama haka,sai kace wata budurwar kirki,tabbas sai yanzu na gane kamanninta sak gyatumarta dan na dade bn ganta ba sannan kuma mahaifiyarta ta ta dade da rasuwa shi yasa na manta inda nasan me kamanninta sai dai farin data yi sosai har wani yellow take,tabdi lallai ba karamin dibara mukayi ba da muka raba tsakaninta da wan mamanta dan da yanzu tana samun kulawarsa Allah ne kadai ya san irin ruwan kyan da za ta yi... "Bari idan na je ,in zan dawo sai na kiraka ka dakkoni tun da dai ka kafa sai na shiga motar taka" Mimi ta ce tana zolayar direban cikin barkwanci.maganar da mimin ta yi ita ta katsewa Manal tunanin da ta ke yi.Itama Mimin kuma ganin Aunty Manal din tana mata wani kallo yasa ta wayance za ta kama gabanta. "Haba Hajiya karama ,ai mota taki ce ,ni na isa mallakar mota kamar wannan,ai ni aikina kawai in tuka ki" Shi ma yace yana washe baki dan ba karamin birgesa Mimi ke yi ba sbd bata da girman kai ko kadan. "Hmmm ni dai na tafi" Mimin ta ce tana juyawa tayi tafiyarta cikin nutsuwa da yanga da suka zama jinin jikinta dan ita tsakani da Allah haka tafiyarta take ba wai da gan gan take yi ba. " A dawo lpia Allah tsare gabanki da bayanki,ya rabaki da makiya,makiyanki fadawanki m..... "Kai dalla rufewa mutane baki" Manal ta katse direban cikin daka masa tsawa jin yadda yake ta jerowa Mimi addu,o i Dakatawa ya yi yana zazzare idanu sbd tsoron da Manal din ta bashi. "Ayi hakuri Hajiya Allah huci zuciyarki" Yace yana jinjina mata hannu irin yadda akewa jinin sarauta. "Ka ji dashi gulmamme kawai" Ta ce tana doka wani uban tsaki ta juya ta tayi tafiyarta. "Kai ikon Allah wannan mata da jaraba take,wato addu,a ce bakya so na yiwa Hajiya karama to kwa wlh ba zan dena ba" direban ya ce yana waiwayen bayansa dan ganin ko akwai wanda ya jishi amma ganin bai ga kowa ba ya juya yaci gabq da abinda yake. Manal kwa na komawa sashenta ta dauki waya ta dokawa Hajiyarta dan ita bata zance da kaw irin wannan da kawaye gudun gori.Hajiya na daukan wayar Manal ta shiga zayyane mata dk abin da ya faru na ganin Mimi da ta yi dan ita gaba daya ta manta da wata mimi,sai yau da ta ganta.Sosai Hajiya ta cika da mamaki jin wai yarinyar har ta fara zama yan mata wato ta fara zama wacce za ta iya ja da su wata rana! Amma dai Hajiya tace babu wurin bokan da za aje,tunda dai yarinya daya ce,kuma burinsu dai bai wuce Kalil ya manta da ita ba ya daina bata kulawa ,kuma gashi an ci riba dan haka kar su je garin neman gira su rasa ido.Jin abinda Hajiya ta ce yasa Manal din hakura da kudurinta tunda ance abin da babba ya hango yaro ko ya hau kan rimi ba zai hango ba. Bayan sallar isha,i Kalil ne suke zaune a falonsa shi da Manal tana shan fruit shi kuma yana ta danne danne a laptop dinsa, jifa jifa suna dan taba hira amma Manal din ce kan masa mgn yana bata amsa dan shi gaba daya hankalinsa ya maida kan abin da ya ke.Tsayawa Manal ta yi da shan fruit din tun da ta tuno da Mimi da ta gani yau kawai sai take jin babu dadi a ranta ,haka kawai take jin kamar dai wani abu na shirin faruwa dk da maganar da Hajiya ta fada mata amma sai kawai ta ke ganin kamar akwai wani abun.Dan matukar dai ana kwana ana tashi tasan dole wataran Kalil zai iya tunawa da Mimi dk da boka yace asirin ba zai karye ba har sai in Kalil din ne ya hadu da wani wanda ya sani a baya,kenan kwa hkn ba zai taba faruwa ba tunda Kalil din ba su da wani dangi ko dan uwa koma wani wanda suka sani daga Baba me gadi bata jin akwai wani da zasu sake haduwa. Amma fa dk da hkn da take da tabbaci sai take jin a ranta dole sai ta tambayi Kalil din game da Mimi sannan hnklinta zai kwanta. "My dear,inaso tambayarka wani abu" Ta fada tana kafeshi da ido dan son gane gaskiyar abin da zai bata amsa da shi, a gefe guda kuma gabanta na tsananta faduwa na fargabar abin da Kalil din zai ce. "Ina sauraronki ,kinsan dai aiki nake yanzu amma dai hkn ba zai hana ni sauraronki ba sbd matsayinki gareni ya wuce haka" Cewar Kalil din yana ture laptop din gefe guda domin sauraron abin da Manal din ke son tambayarsa domin ya lura abin me muhimmanci ne.Sbd tun da suke zaune a falon suke dan hira tana masa yan tambayoyi yana biye mata amma bata ce tana son mgn dashi ba sai yanzu hkn yana nuna maganar me muhimmanci ce. " Dama ...umm, maganar yarinyar nan ce ta wajen karime(inna karime) kwana biyu bana ganinta ko taje wani wurin ne?" Ta tambaya idanunta tsai akansa ko kiftawa bata yi ,ga kirjinta da yake bugawa da sauri sannan a gefe daya tana tunanin makomarta matukar ya tuna da yarinyar ciki kwa harda dena zama a hadadden gdn nan dn tasan wlh dn Kalil bai cikin hayyacinsa shi yasa ya yarda suka dawo gdn,suke kuma hawa motocin Mimi da kuma wasu abubuwan da ba za su fadu ba. "Wace yarinya kenan?" Ya tambayeta cikin nuna rashin fahimtar wacce take tambaya. Wani dadi ne me bala,in armashi ya baibaye Manal jin yana tambayar wace ce ,ji take kamar ta tashi ta taka rawa dn murna. " Yarinyar nan Mimi yar gdn kanwarka marigayi ya" Ta fada hnkali kwance ganin bai ma san wacce take tambaya ba. "Ni nake da kanwa? Kuma har take da y'a? Nifa bansan kowa ba sai ke kuma bani da kowa na dangi sai ke kadai abar kaunata" Ya fada yana kasheta da wani shegen murmushi da kallon soyayya irin na masoya. "Allah sarki masoyina nima hakan take,bani da kowa sai kai" Ta ce tana matsawa kusa dashi ta masa kiss a gefen kumatu,hannu ya mika ya shafo kanta yana murmushi,sannan ya dakko laptop din ya ci gaba da abinda ya ke yi. "Kai rayuwa akwai dadi gskia, tabbas in kana so ka ga deden na miji sai ka tashi tsaye😒 nan ne zaka juyashi yanda ranka ke so sai yadda ka yi dashi ,anan ne za ka yi kidanka da rawarka hnkli kwance hhhhh ka baiwa boka kudi shi kuma ya maka aiki" Dk wannan maganganun a zuciyarta take yinsu(nikwa nace Manal ai kn kauce hanya,dan zuwa wurin boka batane babba ,dan mutum ko wurin boka yaje sallarsa ta kwana arba,in bata karbuwa.Haka zalika akwai ranar kn dillanci domin kuwa dk abin da aka yi shi ba ta hanyar Allah ba to karshensa ba zai yi kyau ba,sannan komai abin da akayi shi ta hanyar Allah kamar halin da mutum ya samu kansa,a gdn miji da kuma irin mijin da ya aura dk kaddara ne daga Allah kuma dama aure hanya ce ta shiga aljanna ba za a samu aljanna ba sai ta hanyar yiwa miji biyayya da kare hakkokinsa da kuma iyakokin Ubangiji)