💫❣️*GADAR TSAUTSAYI*💫❣️ ✍️Alƙalamin Nusaiba Ibrahim Rimi (Nusy bee) Marubuciyar; Matar khalees Barrister Hibba Siraɗin uƙuba Kaddararmu ce ta zo a haka Masarautar Kaizur And now GADAR TSAUTSAYI SANARWA! Littafin GADAR TSAUTSAYI ƙirƙirarren labari ne,ga duk wanda ya hali ko suna ko gari ya zo daidai da shi,to a rashin sani ne🙏 GARGAƊI! Littafin GADAR TSAUTSAYI mallakin Nusaiba Ibraheem Rimi (Nusy bee)ne,ban amince a chanja ko a juya min littafi na ta kowacce fuska ba Haka nan ban amince a karanta min shi a YouTube channel ba sai da izini na *BOOK ONE* Page 1 *DSS HEADQUARTERS,KANO STATE, NIGERIA* Ƙaton office ya yi shiru tamkar babu wani mahaluki a ciki,baka jin ƙarar komai sai na kaɗawar AC ɗin da sanyinta ya wadaci katafaren office ɗin,tamkar dai babu wani mahaluki a cikin office ɗin Sai dai mutane ne sun kai goma sha biyu a zaune a jere akan kujerunsu, waɗanda suka kasance manya manyan masu riƙe da muƙami kala-kala a fannin nasu na ƴan sanda,ɗaya daga cikinsu, wanda ya kasance shine shugabansu,wato S.D Ibrahim Haruna yalwa yana tsaye yana fuskantar su fuskarshi babu alamun walwala,da alamu shine cheif officer ɗinsu,kuma yana yin wani bayani ne suna saurara Sake jan numfashi ya yi, cikin ɓacin rai ya cigaba da magana "Wannan abun kunya ne a gare mu,a ce wai wannan ƴarinyar da da yawanmu mun haife ta amma ta gagare mu a cikin garin nan Gaba daya ta lalata mana gari,ta lalata mana matasa, lafiya ƙalau zata yi order na kayan maye ta shigo da shi Nigeria,ta rabawa distributors dinta ta koma inda ta fito,amma an rasa wanda zai iya kama ta a cikinmu? Me hakan yake nunawa kenan?ba mu da amfani ko yarinyar bayanmu ta fi ƙarfinmu? Na gaji da ji da ganin gazawarmu hukumarmu akan yarinyar nan, tabbas wannan gazawa da abin kunya ya yi mana yawa,kuma wannan abin kaico ne" Ɗaya daga cikinsu ne ya ɗaga hannu cikin girmamawa, chief officer ya ba shi izinin magana, cikin sanyin murya ya ce"sir! Yarinyar nan fa ina zargin akwai waɗanda suka tsaya mata a sama, shi yasa take cin karenta babu babbaka,har ta kasa kamuwa kuma ta cigaba da samun confidence na aikata abubuwan da take yi " Cikin ɓacin rai state director ya dube shi,kai tsaye ya ce"babu wanda ya tsaya mata,ita ta tsaya da ƙafarta,kuma ta hana mu tsayawa,kuma ba zan fasa faɗin cewa mun aikata abin kunya ba,da muka gagara samun nasara akan yarinya ƙarama irinta " Shiru office ɗin ya ɗauka kowa yana saƙa da warwara,don dai an san maganar state director gaskiya ce,shekaru biyu kenan ana chasing wannan matashiyar yarinyar amma an kasa yin komai akanta, dole su san abin yi ko hukumarsu ta zama abin dariya a wajen al'umma A hankali ya lumshe kyawawan idanunshi ya buɗe,ya ɗaga kanshi a hankali ya kalli hoton yarinyar da yake kafe a ƙaton majigin da yake office ɗin,fara ce tas, tamkar wadda bata da alaƙa da Africa,kanta an yi kitson attachment kalar blue da ya sauka har ƙugunta,sanye take da riga da wando da ya kama ta,kanta ɗore da hat fara kalar kayan jikinta,sai jaka da ta rataya ta daidaita zamanta a gefen cikinta, idanunta sanye da bakaken glasses,amma hakan bai ɓoye ɗan ƙaramin murmushi da yake kwance akan kyakykyawar fuskar tata ba A hankali ya ɗaga hannunsa,har yanzu idanunsa ƙyar akan hoton nata,har zuwa yanzu ya kasa gane dalilin da ya sa wannan ƙaramar alhakin ta saka hukumarsu ɗan ƙaramin hauka,kuma har yanzu sun kasa zuwa ko kusa da inda take ballantana su yi tunanin kama ta State director ya dube shi ya ce"C.S.O HAISAM ABDULMALIK MADAKA! Shin kana da wani hanzari ne?" Wanda aka kira da C.S.O Haisam Abdulmalik ya miƙe tsaye cikin izza da yanayi na rashin son hayaniya, kyakkyawa ne fari,amma ba tas ba,suit ɗin da yake sanye da ita ta yi matuƙar amsar farar fatarsa A hankali ya bi mutanen da suke zaune a office ɗinda idanu,da yawansu sun fi shi muƙami da matsayi a wajen aikinsu,a hankali ya kawar da kai, cikin yanayinsa na rashin son hayaniya ya fara magana "Good evening Sir! Good evening everyone!! Ita ɗin ba kamar sauran mutane ba ce,tana rayuwa tamkar a cikin iska, shiyasa kamunta zai bayar da wahala Ko da ace babu wanda ya tsaya mata a zahiri to tabbas tana tare da masu tsaya mata a baɗini, saboda yadda take zuwa duk ƙasar da ta so,ta dawo Nigeria kuma ta cigaba da harƙallarta yadda take so ba tare da wani ya dakatar da ita ba" S.D da ya zamo ɗaya daga cikin waɗanda suka zubawa Haisam idanu suna ji da saurarensa,ya jinjina kai kafin ya ce"menene hujjarka na cewa akwai wanda ya tsaya mata? Ka san kai jami'in tsaro ne, da tsayayyiyar hujja za kayi amfani don kar ka ruɗa kanka ka ruɗa mutane" Haisam ya jinjina kai ya ce"a saboda hakan ne ma ya sa na gaza isa inda take har kwanan yau, saboda bani da wata rikaƙƙiyar hujja,amma kuma in dai ni jami'in tsaro ne na gaske watan watarana zan gano abin da yake ɓoye,don na tabbatar da cewa akwai waɗanda take yi wa aiki" S.D ya sake jefa masa tambaya yana kallonsa"wa take yiwa aiki? Kuma menene hujjarka?" Kai tsaye ya ce"ba na ce ba dai yanzu,wa take yi wa aiki?zai iya zama kowa ma a ƙasar nan muddin babu Allah a ranshi,zai iya zama wani ma a cikin wannan hukumar tamu,zai iya zama a cikin ƴan siyasar ƙasarmu,kuma zai iya zama farar hula,amma kuma bincike ne zai nuna,kawai abin da na sani game da aikinmu shine,ka zargi kowa,amma kar ka ɗora laifi akan wani " Da yawan mahalarta taron suka fara jinjina kawunansu cike da gamsuwa da bayanin C.S.O Haisam, State director ya sake dubanshi ya ce"to yanzu menene kake ganin mafita? Me kake ganin za'a yi?" Haisam ya shafa kanshi ya ce"a bani lokaci,zan yi bincike,kuma zan tabbatar na gano inda take kuma na kama ta da hannu na !!!" Kusan gaba ɗaya mazauna office ɗin a zabure suka ɗago suna kallonsa, mamakin ƙarfin halinsa akan abin da 90% ɗinshi rashin yiyuwa ta fi yawa,amma C.S.O Haisam yana bayar da tabbaci akai, murmushi A.D Hamza Zubair ingawa ya yi yana girgiza kai yana kallon Haisam, cikin muryar dattako irin tashi ya ce "Yunƙurinka da ƙwarin gwiwarka yana matuƙar burge ni jarumina To amma wani hanzari ba gudu ba,ita wannan yarinyar dukkanmu nan a cikinmu babu wanda ya santa, ma'ana ya san wani abu akanta,babu wanda ya taɓa ganinta a zahiri,babu wanda ya san ko da sunanta,da abu ɗaya ake iya gane ta,shine haruffan N.O.C.C.M da take amfani da su, waɗanda har zuwa yanzu ba mu san cikakkiyar ma'anarsu ba, ballantana mu san yunƙuri na gaba,babu wanda ya san sunanta,babu wanda ya san inda take zaune, ballantana ya san inda zata je ko inda ta baro,a duk waɗannan,wacce alama gare ka wadda zata nuna maka wacece ita? Ta yaya za ka iya gane ta? Akwai aiki a gaba fa!" Kallonsa Haisam ya yi, cikin sanyin murya ya ce"I'm sorry sir! Ni jami'in tsaro ne,a matsayina kuma bai kamata a ce kafin na fara aiki a ce na karaya ba,kafin na shiga aikin jami'in sirri na yi rantsuwar cewa zan kare ƙasa ta,zan yi chasing mai laifi,duk wayo,duk fikirarsa don na kamo shi,don haka ina sake roƙon a ba ni lokaci,wata guda kacal,as I said,I promise,zan kamo ta na gurfanar da ita gaban hukuma " Shiru office ɗin ya ɗauka na ɗan lokaci, kafin S.D ya dubi Haisam,ya ce"Best of luck Haisam! Amma yanzu wanne taimako kake buƙatar a yi maka don kama ta?" Haisam ya rissina ya ce"godiya nake sir! Ina son a haɗa min team na mutum shida, wadanda suke ƙwararru kuma masana aikinsu, waɗanda ba sa wasa sam da aikinsu, wadanda suka samu kyakkyawan training sune za su taimaka min akan wannan aikin " S.D ya ce"best of luck! In Sha Allah za'a haɗa maka su,kuma an ba ka wata guda,za mu ga ƙwarewarka,fatan alkhairi "Haisam ya rissina yana faɗin"thank you sir! Ni kuma na yi alƙawarin zan yi duk mai yiwuwa na ga ban bayar da kunya ga hukumarmu ba"S.D ya jinjina kai cikin kulawa,sannan suka cigaba da tattaunawa,ba su juma sosai ba suka ƙarƙare taron *RED CHINA RESTAURANT, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA* Ƙarfe biyar ne na yammacin ranar talata,garin ya ɗauki sanyi da danshi sosai sakamakon ruwan da ya ɗauke ƴan mintuna kaɗan baya,har yanzu akwai yayyafi kaɗan kaɗan,ga iska mai daɗi da ke busawa tana ƙara sanyaya yanayin garin Motar ƙirar Lexus ce ta gama daidaita parking a bakin restaurant ɗin,sai dai na cikin motar babu alamun zai fito tsawon mintuna biyar da yin parking ɗin Lokaci ɗaya ƙofar motar ta buɗe,a hankali aka zuro ƙafafu don fitowa daga cikin motar Daga yanayin ƙafafun kawai za'a tantance na mace ne,duk da cewa dogon wando ne a sanye a jikin mamallakiyar ƙafar samfurin jeans,sai takalmi canvas,sai dai akwai sarƙar ƙafa a ƙafar hagu, wadda ta sake bayyanawa ƙarara cewa wannan ƙafar ta mace ce Lokaci ɗaya ta fito gaba ɗaya, matashiyar budurwa ce wadda baza ta wuce shekaru ashirin da biyar ba, kyakkyawa ce sosai,fara ce amma ba tas ba,tana da diri amma bata da ƙiba sosai Sanye take da riga mai ɗan kauri ta kamfanin puma,sai dogon wandon jeans,kanta ta ɗaura scarp da ya bayyana gashin goshinta da ya kwanta luf,ta sanya spec da ya cinye rabin fuskarta, hannunta riƙe da ƴar ƙaramar handbag fara,kalar rigarta da scarp ɗinta Tsayuwar kusan minti ɗaya ta yi a wajen tana kalle-kalle fuskarta babu yabo babu fallasa,kafin daga baya ta nufi cikin restaurant ɗin tana tafiya a hankali kamar mai tausayin ƙasa Kai tsaye wani table ta nufa ta zauna, waitress ɗin wajen ta ƙaraso, cikin rissinawa ta ce"good evening Ma'am!" Kallonta ta yi fuska babu yabo babu fallasa, kafin ta yi mata nuni da hannu, waitress ɗin ta gane me take nufi, tunda ba yau ne karo na farko da ta saba zuwa tana bayar da umarni a haka ba,ta rissina sannan ta wuce don ta kawo mata abin da take buƙata Tana tafiya ta zura hannunta a wata kusurwa ta kujerar da take zaune,a take ta fito da wata ƴar ƙaramar takarda kalar yellow,kuma ba tare da ɓata lokaci ba ta buɗe takardar tana kallon rubutun 'OLD VENUE,BY 3:AM' Haka kaɗai aka rubuta a jikin takardar ta ninke tare da cusa ta a aljihu ta ɗaga kai tana kallon waitress ɗin da take dawowa ɗauke da tray na abin da ta saba yin order duk sanda ta shigo restaurant ɗin Shawarma ce sai mint tea,ita mint tea ɗin ta sha sannan ta miƙe bayan ta biya Bill ta fice daga restaurant ɗin ba tare da ta sake kallon wani ba,da yawan ma'aikatan suka bi ta da kallo suna ƙusƙus na halin wannan matar mai jiji da kai, tunda suke da ita sai dai ta shigo ta yi order,a Kawo Mata ta ci ta tafi, bata yiwa kowa magana,bata amsa gaisuwar kowa, babu wanda zai iya shaida muryarta,hakan ya sa wasu suke tunani wataƙila kurma ce bata magana Ita kuwa tana fita ta faɗa motarta,sai da ta rufe baƙaƙen tinted glasses ɗin sannan ta ɗauko wayarta ƙirar lastest iphone ta daddanna sannan ta kara a kunnenta tana zare scarp ɗin kanta "Hello!"muryar mace ta amsa bayan an ɗaga wayar Hannu ta saka tana gyara zaman dogon gashin ta, cikin muryarta mai cike da izza da jan aji ta furta "old venue,by normal time"daga haka ta kashe wayarta ba tare da ta jira amsar ɗayan ɓangaren ba Daga nan ta tayar da motar, ba tare da ɓata lokaci ba ta bar bakin wajen, kamar walƙiya ta fice daga layin Bata yi tafiya mai nisa ba ta tsayar da motar a kusa da wani ƙaton gate, cikin wani irin yanayi akan fuskarta take kallon gate ɗin gidan, abubuwa da yawa suna dawo mata kai,ta girgiza kai tana ɗan murmushi wanda ya yi kama da mai ciwo sannan ta tayar da motarta ta yi gaba,a ranta tana jin duk abin da ta yi bata yi kuskure ba,akan daidai take,don haka bata nadama *ALHAJI YUSUF MALIYA RESIDENCE, MALIYA ESTATE,KANO STATE* Ƙaton parlour ne wanda ya wadatu da kayan ƙawa da ado na zamani, parlourn ya yi shiru tamkar babu wata halitta mai rai a cikin parlourn Sai dai kuma ɗauke yake da ilahirin jama'ar da ke cikin katafaren mansion ɗin, wanda ya kasance mallakin Alhaji Yusuf maliya,wato mai gidan Alhaji Yusuf maliya shahararren dan kasuwa ne,mamallakin MALIYA GROUPS OF COMPANIES da MALIYA MOTORS,duk wanda yake cikin Maliya family, waɗanda aka haɗa su a cikin Maliya estate to mai arziƙi ne,daga lokacin da aka haifi jariri za'a ware masa wani kaso a matsayin hannun jarinsa,yana kai wa wasu shekaru a damƙa masa Iyali ne masu cike da haɗin kai da ƙaunar juna,duk da cewa ko da akwai ɓarakar ba'a bari ta bayyana, saboda tsananin zafi da tsatstsauran hukunci da zai fuskanta daga wajen shugaban wannan family Alhaji Yusuf maliya shine babba a wannan family,yana da ƙanne biyar,uku maza,biyu mata, Hajiya Sa'adatu ita ce wadda take bin sa, wadda a wannan ƙaton family aka santa da Mummy,babbar ƴar kasuwa ce, sannan yar kasuwa,mammallakiyar Maliya plaza da Maliya shopping complex,tana importing da exporting na kaya sosai Mai bi mata shine Alhaji Rufa'i, wanda yaran family suke kira da abbeey,yana da Company na shigowar spare parts na motoci, sannan yana da manyan shaguna a kasuwanni a ciki da wajen Kano,sannan shi ɗin babban jami'in custom ne,sai na uku Alhaji Aliyu,shima kamar sauran ya kasance ma'aikaci ne,yana aiki da NNPC,sannan yana da babban Company na sarrafa abinci,sai na hudu, lieutenant colonel Habib, soldier ne,kuma ɗan kasuwa Sai autarsu Salma, wadda yara suke kira Aunty, yar jarida ce, sannan yar kasuwa ce kamar dai sauran yayyenta Gaba ɗaya su biyar ɗin, Sa'adatu, Rufa'i, Aliyu, Habib da Salma sun kasance suna tsananin biyayya ga dokar ƴaƴansu Alhaji Yusuf,ko kara ya saka ya ce baya so kowa ya tsallaka to babu mai iya ko da matsowa inda karan yake,duk da cewa wannan tsatstsauran ra'ayin ya janyo wa ahalin wata gagarumar matsala wadda ta jefa su a cikin wani hali na wasu shekaru,kuma har kwanan yau an kasa samun mafita ga wannan matsalar #Nusy_bee Page 2 Matan Alhaji Yusuf maliya uku, Hajiya Zainab ita ce uwar gida,wadda yara suke kira da Ummeey, haihuwarta ɗaya a gidan,ita ce babbar yar Alhaji Yusuf maliya, wato FATIMA SHAHEEDA,sai Hajiya Atika, ƴaƴanta biyar,Safwan shine babba,sai Malika,sai Amina,mukhtar sai auta Fauziyya Hajiya Ruƙayya ita ce matar Alhaji Yusuf Maliya ta ƙarshe, tana da yara uku, Zainab,mai sunan Ummeey, wadda ake kira da Iman,sai Nafisa, sai autanta Usman Hajiya Sa'adatu, wadda ake kira da Mummy yaranta huɗu a duniya,Muyassar ne babba,ya kammala karatunsa na masters a ƙasar Britain,inda ya karanci civil engineering a jami'ar Harvard,ya fita da kyakkyawan sakamako,sai ƙannensa Hassan da Hussaini, wadanda suke jami'ar cologne suna karantar fannoni dabam dabam na lafiya,sai autarsu Na'ima, wadda take nata karatun a NUN da ke Abuja Alhaji Rufa'i yaransa bakwai,uwar gidansa na da uku amaryarshi tana da huɗu,sai Alhaji Aliyu,shi kuma yaranshi tara, duka daga matarshi ɗaya da suke zaune tare,sai auta Salma,mai yara biyu tal a duniya yan maza sakwanni, wadanda zuwa wannan lokaci dukkansu suna matakin farko a jami'ar Massachusetts da ke US A bisa al'adar MALIYA family,a duk lokacin da za'a ƙaddamar da wani abu mai muhimmanci,ko wanda zai shafi al'ummar ahalin,ana haɗuwa a katafaren gidan Alhaji Yusuf Maliya, kasancewar shine shugaban ahalin,a matsayinsa na babba,kuma wanda yake gina ahalin a duk lokacin da aka samu wata ɓaraka, musamman da ya kasance mahaifiyarsu gaba ɗaya, Hajiya Zulayhat Maliya, wadda kafatanin ilahirin ahalin suke kiranta da hajiyya innayyo,ta kasance a gidansa,a sashe na dabam da aka ware mata Kamar yadda aka saba yau ma sun taru a katafaren parlourn gidan,gaba ɗaya iyaye da yaran,da alamu wani gagarumin abu mai muhimmanci za'a tattauna a kai Parlourn ya ɗauki shiru, Alhaji Yusuf Maliya ya ja numfashi a hankali, sannan ya cigaba da magana "Sanin kowa ne a gidan nan,kun san abin da ya faru shekaru huɗu da suka wuce,wani tabo ya samu ahalin nan,girma da mutuncinmu ya zuba a idanun duniya,maƙiya sun yi farin ciki, masoya sun yi baƙin ciki A wancan karon na ɗauki hakan a matsayin tsautsayi,amma wannan karon ina ganin duk abin da ya faru dole ne mu bar shi a matsayin ganganci,duba da cewa ba shine karo na farko ba,amma menene shawararku akan hakan?" Hajiya Sa'adatu, wadda ta kasance babba a cikin ƙannen Alhaji Yusuf Maliya ta gyara zama tana jan numfashi, sannan ta ce"Alhaji Ni ina ganin ba wata matsala ba ce hakan, musamman duba da nutsuwa da tarbiyyar yaran,abu ne mai wahala su manta da hakan idan suka samu kansu a baƙon waje Kuma bugu da ƙari ya dace a ce an saka musu idanu, saboda su mata ne,kuma ita mace sai da sanya idanu,amma ni dai daga gare ni ina yi musu kyakkyawan zato,amma me kika ce Ruƙayya?"ta mayar da tambayar ga matar Alhaji Yusuf Maliya da suka fi shiri,wato Hajiya Ruƙayya, wadda yara suke yiwa lakabi da Mommy Mommy gyara zama ta yi, sannan ta ce"to ni dai ba zan ce komai ba,amma kuma ga yaran nan za'a samu kyakkyawar amsa daga gare su " Alhaji Yusuf ya dubi yaran,da alamu sun zaƙu a tambaye su ɗin,amma maimakon ya tambaye su sai ya mayar da akalar tambayar ga Hajiya Zainab (Ummeey) A tausashe Ummeey ta dubi Alhaji Yusuf bayan ta gyara zama ta ce "Alhaji a dai duba sosai,ka ga yara mata ne,kuma inda za su tafi babu wani babba a can Idan da hali a nema musu makarantar a nan,babu laifi su koma gabanka a Abuja,ko su zauna a anan a gaban iyayensu,a ko'ina aka yi karatun ba wani abu ake nema ba sai albarkarshi Idan muka yi duba a baya an yi irin haka,an samu sakamako mara daɗi,to mu bar wancan a matsayin ƙaddara,a wannan karon sai mu kiyaye,idan muka yi hakan sai Allah ya taimake mu" Da sauri yaran suka kalle ta cikin wani irin baƙin ciki,don gani suke yi Ummeey hassada take yi musu tana son ta shiga tsakaninsu da burinsu,amma babu halin magana, musamman da ya kasance suna gaban Alhaji Yusuf Maliya, wanda ko manyan ba sa yin magana sai an nemi jin ta bakinsu Sai dai kafin wani yunƙuri cikin ɓacin rai Hajiya Atika ta dubi Ummeey ta ce "A'a Hajiya Zainab,wannan ba girmanki bane!wanne dalilin zai saka ki yiwa yara baki bayan ba sune suka yi miki laifi ba? Ya kamata a rinƙa yi ana saran bakin gatari,don wannan abu bai dace ba gaskiya " Tana rufe baki Hajiya Sa'adatu ta ɗora"kuma ban da haka ma Allah na tuba ai yaran sun samu tarbiyya sosai,ina su ina wannan abu saboda Allah? Kawai dai kin san wasu mutanen, musamman waɗanda ba sune suka haifi yaro ba" Ummeey ta girgiza kai ta ce"kayya! Allah ya kiyashe mu da aikin danasani da ruɗin shaiɗan Kun yiwa magana ta gurguwar fahimta, babu komai, Allah ya tsare su,ya kawo abin da aka je nema Hajiya Sa'adatu ɗa ai na kowa ne,da ɗa da dukiya ba'a yi musu mugunta, saboda Allah ne kaɗai ya san wanda zai more su" Ganin abin zai zama na magana ya sa Alhaji Yusuf cikin ɗaurewar fuska ya ce"ya isa haka! Bana son na sake jin maganar nan ta cewa babu tarbiyya a gidan nan,hakan yana nuna na gaza ne, Ni kuma na san iya ƙoƙarin da na yi,a cikin matana babu mara tarbiyya,don haka haifar mara tarbiyya ba dai a gidana ba,sai dai idan abin ya zo da tsautsayi Sannan ke kuma Hajiya Zainab,maganarki ta cewa a kula babu kowa da yake kallonsu ni na san me nake yi,ku dai ku yi musu addu'a kawai, Allah ya bada sa'a,ya kare su daga ruɗin zamani,ya sa a samo abin da aka je nema"kusan gaba ɗaya aka amsa da Ameen Iman da Amina,sai ƴar Alhaji Rufa'i Surayya,sune wadanda ake ta wannan tattaunawar akan tafiyarsu abroad karatu,amma iyalan sun kasance cikin shakku saboda tabon da suka samu a cikinsu wanda ba su san ranar da zai warke ba Farin ciki sosai ya bayyana a fuskokin yaran,amma babu wanda ya samu zarafin magana tunda har zuwa yanzu Abba(Alhaji Yusuf Maliya)bai ba su damar yin magana ba,kamar yadda tsarin family ɗin yake,wato yaro baya taɓa yin magana sai ya sami umarni daga wajen babba Alhaji Yusuf maliya ya mayar da hankalinsa ga yaran da za su tafi karatun,su huɗu ne,bayan Amina da Iman da Surayya akwai Salim da Mufeed yaran Alhaji Rufa'i,amma da yake su maza ne,kuma matsalar da aka samu a baya ba daga mazan aka samu ba shi yasa ba'a damu sosai da nasu ɓangaren ba Alhaji Yusuf ya dubi yaran,a nutse ya kira sunayensu ɗaya bayan ɗaya,suka amsa cikin girmamawa, cikin nutsuwa ya fara bayani "Ku ba ni hankalinku nan Kun san tsarin, musamman ku yan mata,a Maliya family ba'a barin mata su fita don zuwa wata ƙasar karatu, saboda kowa ya san abin da hakan ya janyo mana Sai dai wannan karon za mu dage mu bar ku ku fita waje don karatu,ba don komai ba,sai don muna kyautata muku zato Zainab da Surayya za su tashi zuwa ƙasar US nan da kwanaki takwas in sha Allah,inda Zainab za ta karanci medicine ita kuma Surayya zata karanci business administration, Saleem da Amina za su tafi Turkey inda Saleem zai karanci medicine, Amina zata karanci engineering, Mufeed kuma zai tafi Spain inda zai karanci SOFTWARE ENGINEERING!" Ambatar software engineering kawai da Abba (Alhaji Yusuf Maliya)ya yi ya sa ɗakin ya yi wani irin shiru,tuni wasu zuƙata suka tsinke,wasu kuma suka shiga kokwanto da fargabar kar a sake afkawa GADAR TSAUTSAYI makamanciyar ta baya,ta rufta da su a karo na biyu,a wannan karon kuwa sun san kafin su dawo daidai za'a ɗauki lokaci mai tsawo Alhaji Yusuf Maliya shi kanshi ya ji wani canji,amma ko a fuska bai nuna ba,ya cigaba da jawabinsa cikin nutsuwa "Don haka ina yi wa kowanne yaro fatan alkhairi,ina fatan Allah ya kai ku lafiya ya ba ku abin da kuka je nema Nasiha ta kuwa bata wuce ku ji tsoron Allah ba, ku kama mutunci da ƙimar kanku musamman ma ku mata,ku yi abin da ya dace,kar ku ga cewa ba ma kallonku,kar ku manta cewa mahaliccinku yana kallonku,kuma a kowanne lokaci za ku iya ganinmu mun kawo muku ziyara,da wasa muka ga wani abu wanda bai yi min ba zan ɗauki matakin dakatar da karatun ne kawai, wannan gargaɗin ba iya mata kawai nake yi wa ba, har da ku mazan!" Cikin girmamawa suke jinjina kai,s hankali kowa a cikinsu yake daukar alwashin kiyaye dokokin da aka kafa musu, Alhaji Yusuf Maliya ya cigaba da bayani "Duk wani abu da kuke buƙata an kawo,ku duba,idan akwai abin da ba ku gani ba to sai ku yi min magana a kawo"Mufeed ne ya fara rissinawa yana faɗin"to Abba mun gode, Allah ya saka da alkhairi "sauran ma suka rissina suka yi godiya, Alhaji Yusuf ya ce"Masha Allah! Kuna iya tafiya,na sallame ku"babu musu suka miƙe ɗaya bayan ɗaya suka fice daga katafaren parlourn Bayani Alhaji Yusuf ya cigaba da yi,da yadda za'a saka musu idanu,ya dubi Muyassar wanda ya kasance shine babba a cikin jikokin gidan ya ce "Muyassar ga ƙannenka nan,ka saka musu idanu,ka tabbatar da cewa ba su aikata wani abin ashsha ba,na san za ka iya in sha Allah"Muyassar ya rissina yana faɗin "in sha Allah Abba! Allah ya ƙara girma" Alhaji Yusuf ya ce"to alhamdulillahi, Allah ya yi muku albarka baki ɗaya,wani ya rufe mana taro da addu'a "Muyassar ya yi musu addu'a Kamar yadda aka saba,suka yi sallama,taron ya watse kowa ya kama gabansa *ROCKY ESTATE,KANO STATE, NIGERIA* A hankali motar ƙirar Audi A4 take shiga cikin estate ɗin bayan masu sojojin da suke gadin ƙaton gate ɗin estate ɗin sun ɗage shi,kuma kai tsaye ba tare da ɓata lokaci ba motar ta cigaba da tafiya a hankali don isa inda take nufa A daidai wani katafaren gate motar ta yi parking,kuma cikin nutsuwa mamallakin motar ya matsa horn sau ɗaya,jim kaɗan kuma aka ɗaga gate ɗin, motar ta shiga cikin harabar katafaren gidan a hankali A parking space ya yi parking motar,tsawon mintina kusan biyar babu alamun zai fito,kafin a hankali ya buɗe motar yana mayar da wayarsa aljihu,da alamu kira ya gama amsawa CSO Haisam Abdulmalik Madaka kenan,zaƙaƙuri,ƙwararre kuma nagartaccen jami'in tsaro na farin kaya (DSS) wanda Allah ya hore masa sanin makamar iko da zuciya,gami da dagiya a bakin aikinsa,mutum ne mai matuƙar ƙoƙari da ƙwazo Shi kaɗai iyayensa suka haifa Mahaifiyarsa Hajiya Rasheeda ta rasu,daga baya mahaifinsa ya auro Hajiya Malika, wadda ta haifi yara mata biyu, Hafsa da Haleema, Hafsa ta yi aure shekaru biyu baya,tana zaune da mijinta a Abuja,ita kuma Haleema tana Egypt inda take karantar pharmacy Shekaru bakwai baya Haisam ya yi aure,amma saboda wasu matsaloli da suka Kunno kai a rayuwar auren nasu sun rabu da matar, yanzu haka ƴarshi ɗaya tilo mai sunan mahaifiyarshi, wadda ake kira da Amna tana tare da shi,sai dai ya ɗaukar mata nanny,yar dattijuwa da take kula da ita Kai tsaye ya nufi entrance ɗin gidan yana tafiya a hankali,da sallama ya shiga katafaren parlourn wanda ya gaji da haduwa, Hajiya Malika, wadda suke kira da Mamie ta amsa tana ɗago kanta tana kallonsa, kafin ya yi wani yunkurin ko ya furta wata kalma Amna da take zaune a study table ɗinta tana zane zanenta ta taho da gudu ta ɗafe shi,yana murmushi ya rungume ta,a kunne ta raɗa masa "I miss you Papa!" "I miss you papa's baby!"ya faɗa yana murmushi Itama murmushin take yi,ya sauke ta ya kama hannunta suka nufi cikin parlourn Sai da ya fara shiga ɗakin Mamie ya gaishe ta,ta amsa fuska a sake sannan ya ja hannun ƴar tashi suka nufi part dinsa Tare suka ci abinci kamar yadda suka saba duk dare muddin yana gari,suna ci suna hira sosai,tana ta zuba masa shirme shi kuma yana biye mata, cikin dabaru kuma yana tambayarta game da darussanta na makaranta tana ba shi amsa Rasheeda Haisam makawa (Amna) yarinya ce mai kaifin ƙwaƙwalwa da basira,a kamanni na fuska ta ɗebo mahaifiyarta,amma a halaye da ɗabi'u babu inda ta baro Haisam,akwai soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin uban da ƴarshi, shiyasa ko tafiya ya yi in dai ba aiki bane ya sha masa kai baya rabuwa da kiranta a waya Bayan sun gama cin abincin babu jumawa bacci ya ɗauke ta,a hankali ya saɓa ta a kafaɗa,ya ɗauke ta ya fice zuwa part ɗin su Sai da ya fara yin sallama a bakin ɗakin nata, Nanny ɗinta,da take kira da Mama tana zaune tana lazimi tun bayan ta idar da Sallar isha'i,tana ganinsa ta rissina tana gaishe shi,ya amsa yana gaishe ta sannan ya kwantar da Amna, ya yi musu bankwana ya wuce sashenshi Kai tsaye bayan ya canja kaya zuwa na bacci ya wuce ɗakinsa da babu wanda yake shiga, ɗakin bincike ne,ko kuma ɗakin sirri,a wannan ɗakin shi da kanshi bai yarda da kanshi ba ballantana ya yarda da wani,kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya mayar da dakin ya rufe Kai tsaye computer ɗin shi ya buɗe, ba tare da bata lokaci ba ya kunna,kuma kai tsaye ya shiga zuwa inda hotunanta suke,a nutse yake nazartar komai #Nusy_bee Page 3 A kaf cikin hotunan babu wanda aka yi a Nigeria,gaba ɗayansu daga ƙasashe ne kala-kala,wasu a Columbia,wasu a Mexico,wasu a Peru, wasu a Bolivia,wasu kuma a US A nutse yake ƙare mata kallo cikin nutsuwa da nazari,har zuwa yanzu babu wanda ya san sunanta na gaskiya,a taƙaice ma, babu wanda ya san sunan nata, babu wanda ya san inda take, ballantana wani information game da rayuwarta To amma kuma ai an san fuskarta,kuma tana shigowa ƙasar,to ya aka yi ta gagara kamawa? Ko dai da gaske ne zarginsa ya tabbata akwai masu taimakonta a manyan ƙasar? To idan hakane,a shugabanni kenan? Kai a'a!ko da a ce a shugabanni ne dole watarana zata zo hannu,sai dai a ce bayan an kamo ta a sake ta To me yasa ba'a taɓa kama ta ba? wayo ta fi mutane ne?ko dabararta ta fi ta mutane,ko ma dai yayane dai ƙwaƙwalwarta ai guda ɗaya ce,kuma sauran mutane ma haka, yadda take yin tunani take tserewa su ma haka za su iya yin tunani su bi ta har su ƙure mata gudu don kamo ta Wani hotonta ya buɗe, wanda take santa da baƙaƙen kaya,ta juya baya,haruffan N.O.C.C.M. raɗau a bayanta, wannan hoton idan bai manta ba ta turo musu shi da kanta,inda ta tura musu da adireshin inda take,amma da suka je can ba su samu komai ba sai wata takarda da ta sake maimaita waɗannan haruffan,N.O.C.C.M, waɗanda har zuwa yanzu babu wanda ya san me suke nufi Ɗan murmushi ya yi,a hankali ya ce"smart girl! Ban taɓa ganin yarinyar da ta zubar da darajar jami'an tsaro ba sai ke,na jinjina miki,amma ina yi miki jajen lalacewar shirinki a duk lokacin da na waiwaye ki,kar ki bari na fara binki,don tabbas zan kama ki"ya mayar da computer ɗin ya rufe,ya miƙe a nutse ya fice daga ɗakin,kanshi q cushe,amma yana son ya yi tunanin ta inda zai fara cikin sauƙi *UNKNOWN LOCATION* Madaidaicin gida ne,flat mai 3 bedroom and parlour,sai dai haske bai wadace shi ba sosai Fitowa ta yi daga ɗaya daga cikin ɗakunan gidan,shirye take cif cikin baƙaƙen hoodie riga da wandonta,a'a usual ta sanya scarp ɗinta, duk da cewa bai rufe dogon gashinta ba da aka gauraya shi da attachment kalar ja Zama ta yi tana gyara takalminta samfurin sketchers,tana gamawa ta miƙe, maimakon ta nufi ƙofa sai ta daka tsalle ta kama garun gidan,babu ɓata lokaci ta haura, cikin nutsuwarta ta ƙarewa ko'ina kallo kafin ta dira,kai tsaye ta hau babur ɗinta samfurin bike,ta tayar ta bar wajen Da wani tsananin gudu tamkar ba mace ba take tafiya,akan babur ɗin,ta yi amfani da wani handkerchief ta ɗaure rabin fuskarta Da yan dabarunta ta kaucewa duk inda ta san da yan sanda har ta isa inda take son zuwa Wajen ya fara shiga cikin jeji, ba tare da fargabar komai ba ta sauka a babur ɗin ta wuce cikin wajen Ta yi ƴar doguwar tafiya kafin da ƙafa ta isa inda take fatan zuwa Wani tsohon gida ne wanda ya fara rushewa ma, sannan ya shiga surƙuƙi da yawa,amma hakan bai dame ta ba,ta zaro wata yar ƙaramar fitila ta haska har zuwa cikin gidan Sai dai kallo ya koma sama,a maimakon muni da zubin wahala da yake tattare da gidan ta waje,ta ciki abin ba haka yake ba,don ya yi matuƙar taruwa tamkar ba a ƙasar take ba,kau tsaye kuma ta nufi katafaren parlourn gidan A hankali ta buɗe kofa ta shiga, mutanen da suke zaune a parlourn suka ɗago suna kallonta Su uku ne,mace ɗaya, sai maza biyu, ƙatuwar tukunyar shisha ce a gabansu,da kwalaben giya kala-kala Kusan dukkansu suna riƙe da glass cups, wadda suka zuba tsadaddiyar giyar,suna ganinta yanayin fara'arsu ya karu,macen ta ce "ROXY! THE AMAZING BABY!!" Ɗaya daga cikin samarin ya ce"ROXY!The shinning star!!" Ɗayan kuwa cewa ya yi"Welcome HERMOSA!!!" Babu wanda ta kalla a cikinsu,sai waje da ta samu ta zauna bayan ta cire ƙyallen da ta rufe rabin fuskarta, kyakykyawar fuskarta ta bayyana babu yabo babu fallasa,pipe ɗin shishar ta kama ta cika bakinta da hayaƙin shishar,a hankali ta fara fitar da shi ta hanci da baki cikin ƙwarewa, kafin ta sake jan hayaƙin shishar Sai da ta gamsu don kanta, sannan ta ɗago tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, kafin ta tsayar da idanunta a kan ɗaya daga cikinsu Kato ne,kakkaura mai ƙirar ƙarfi, baƙi ne sosai,amma hakan bai ɓoye tattoo ɗin shi da yake gefen hannunsa na hagu ba, kasancewar rigar jikinsa armless ce,sai wando da ya saka three quarter A nutse, cikin izza ta ce"David what's up? Nabyi kewarku fa"ta ƙarashe magana tana yin wani murmushi,tare da ƙanne ido ɗaya Wanda ta kira da David ya yi murmushi yana kurɓar giyar da take cikin Glass cup ɗin gabansa, sannan ya sake faɗin "Roxy the amazing baby! Wannan karon kin daɗe ba ki waiwayo mu ba,ko dai kin tsorata ne?" Ta ɗaga kai tana kallonshi,ta ɗan yatsina fuska ta ce"da me kenan?" Waro idanu ya yi,ya ce"da jami'an tsaron ƙasar nan mana,masu bin ki dare da rana" Ƴar dariya Roxy ta yi, wadda ta yi kama da ta rainin hankali, sannan ta ce"ka manta kenan da Roxy kake magana? Ashe? Har wani jami'i yana da ƙwarin gwiwar iya farmaka ta?" David ya ce"of course! Don na samu majiya mai ƙarfi ta cewa an samu jami'i mai cikakken ƙwarin gwiwar da yake jin zai iya ja da ke,har ma ya kamo ki a cikin wata guda kacal!" Da sauri ta ɗago tana kallonsa jin abin da ya ce"kafin ta kece da wata iriyar dariya,shima dariyar ya fara yi, kafin ta tsagaita ta ce"matsala ta da jama'ar ƙasata rashin kunya! Har yanzu babu wanda ya samu wani hint na abin da ya shafe ni bayan hotunana da na tura musu,sama da shekara ɗaya kenan,na ba su damar su kama ni idan za su iya,shine don bashi da kunya yake tunanin zai iya nasara akai na?"ta miƙe tsaye tana cire hular kanta samfurin hat, wadda ta fi sakawa a yawancin lokuta, sannan ta dubi David da sauran mutum biyun da har zuwa yanzu babu wanda ya ce komai a cikinsu,sun zuba mata idanu,bata damu ba ta fara magana cikin yanayin jin ɓacin rai, saboda a ganinta an taɓa jikimarta Cikin izza ta fara faɗin "ina son samun wani abu da ya danganci jarumin, kamar Sunansa, ɗan wanene shi?yana da aure? yayansa nawa?ina yake yawan zuwa?me ya fi so? menene rauninsa na rayuwa? Sannan su Wanene na sama da shi a wajen aiki? Ina son sanin wadannan muhimman abubuwan a kwana uku kacal"David ya ce"done ma'am!" Bata damu ba ta cigaba da faɗin"ina son na fara tunatar da shi wanene shi kafin ya san wacece ni? Ina son ya fara sanin makomar manyansa da suka shiga gona ta kafin ni ya san tawa makomar! Ba kamar yadda ya yi tsammani bane,ba shine mai juya akalar wasan ba,nice, sannan kuma zan mayar da shi abin wasa na!! Wannan abu ma raini ne a gare ni, jami'i kamar wannan, wanda har zuwa yanzu bai gama wayewa da aikin nashi ba amma ya fara tunanin karawa da wadda ta gagari manyansa,mu je zuwa "sannan ta mayar da hankalinta kan ɗaya namijin da macen, wadanda suka kasance sun fita daban a zubin halitta da David,alamu sun nuna ba yan kasar bane "Da harshen Spanish ta dube su tana faɗin"Sofia! Alejandro! Barkanku da zuwa,amma da kun yi haƙuri ina nan zuwa,amma gashi kun yi gajen haƙuri kun jefo kanku cikin matsala"ta yatsina fuska tana gyara gashinta ta cigaba da magana cikin halin ko in kula "kun sani Roxy bata alƙawari ta saɓa,kayanku za su isa har Ibiza,to menene na biyo ni nan kuma?bayan kun san a yadda nake rayuwa a nan ɗin? Kuma kun san yadda ƙasar tamu take?"ta sake jan hayaƙin shisha,ta cigaba da magana, hayaƙin yana fita ba tare da ta sake kallon sashen da suke ba "Bana son wani ya shiga matsala saboda ni,amma idan hakan ta faru kaɗan daga aiki na ne na ƙyale ku,sai ku fitar da kanku " A fusace Alejandro ya dube ta ya ce"za ki ce haka mana saboda kin karɓi kudinmu a hannunki,amma ki sani,wajibi ne ki biya kaya,idan ma tunaninki za ki cinye mana kuɗi ne to kin yi kuskure,ko kuɗi ko kaya,ko kuma ranki " Dakatawa ta yi da jan hayaƙin shishar,ta dubi Sofia da ta zubo musu idanu tana kallonsu, cikin harshen Spanish ta ce"ke fa? Me kika ce akan hakan?" Kai tsaye Sofia ta mayar mata da amsa"ina tare da Master na!" Miƙewa Roxy ta yi tana yin wani murmushi,ta dubi David,tana murmushi ta mayar masa da batun da suka tattauna da su Alejandro kasancewar shi baya jin Yaren Spanish,take suka fara dariya kamar taɓaɓɓu, Roxy har kusan faɗuwa ta yi tana ƙyalƙyala dariya,hakan ne ya fusata Alejandro,ya miƙe a fusace da niyyar shaƙe ta,ta yi saurin kaucewa tana aika masa da wani mugun kallo "Cikin harshen Spanish ta dube shi tana kaɗa babban yatsanta da ɗan tsakiya a fuskar Alejandro, kafin ta fara magana a fusace"gwamnatin Spain gaba ɗaya ma kallo na take yi daga nesa, ballantana kai wani ƙaramin mara kunya wanda babu wanda ya sanka a duniyar tantirai Kana ganin babu wanda ya taɓa yunƙurin kashe ni ne?da har kake tunanin cewa za ka gwada? Ka tafka babban kuskure irin wanda baka taɓa yi ba!! Da alamu kana jin cewa kana da karfin da za ka iya ƙwatar wani abu mallakinka a hannun Roxy,to wannan shine kuskuren ka mafi girma Tunda ka nuna cewa za ka iya ƙwatar haƙƙinka mu je zuwa,zan gani ko za ka iya!"ta ja baya tana kallonsa da alamun cikakken shiri A fusace ya kai mata naushi,amma sai ta goce,hakan bai bawa Kowa mamaki ba, musamman ga wadanda suka san wacece Roxy,dambe da gwada ƙwanji ba baƙonta bane,cikin wata iriyar dabara ta sa ƙafa ta taɗiye shi,ya zube a gabanta Yana daga kwance yake bin ta da kallo yana ɗan murmushi, cikin kwanciyar hankali ta wuce inda tukunyar shishar nan take,ta cika bakinta da hayaƙi,sai da ta zo daidai saitinsa,ta tsugunna a gabansa tana kallonsa, kafin ta hura masa hayaƙin,ta yi ƙasa da murya tana faɗin"ROXY the shinning star! No one can harm Roxy"ta juya yare zuwa Spanish ta ce" ka ci Sa'a bana sata,don haka zan dawo maka da kuɗinka,da ace ina cinye haƙƙin wani,da ba za ka sake jin ɗuriyar kuɗaɗenka ba, ballantana ka yi tunanin samun kaya,na gama magana,sai haɗuwa ta gaba"ta miƙe tsaye tana kallon David ta ce"ku bar nan wajen nan da ƙasa da mintuna biyar, sannan kar ka manta aikin da na ba ka akan wannan tsageran jami'in,yana bukatar ya san wacece Roxy! Na ga har yanzu akwai iyayin sababbin jami'ai a tattare da shi, zuciyarsa ta rufe, ƙwaƙwalwarsa ta rufe ya kasa tuna cewa manyansa sun ja da Roxy sun kasa, ballantana shi ƙaramin alhaki"tana kai wa nan ta fice daga parlourn ba tare da ta sake kallon kowa a wajen ba Da wani murmushi Alejandro ya bi ta da kallo, kafin ya mayar da kallonsa ga David, cikin harshen turanci yana murmushi ya ce"kyakykyawa ce,kuma tana da kaifin basira,bata da tsoro,jaruma ce, tabbas tana burge ni,ko a haka ma na san na ci ribar kasuwanci da ita"David ya miƙe yana faɗin "Ko ma dai yaya ne! Ka tashi mu fita daga gidan nan,don tunda ka ji ta yi magana da gargaɗi akwai ƙaton dalili "babu musu Alejandro ya miƙe, David ya wuce,suka bi shi a baya don ficewa daga gidan ta ɓarauniyar hanya kamar yadda suka shigo, saboda ɓad da sawu *MALIYA ESTATE, KANO STATE, NIGERIA* "Kai jama'a!ikon Allah!! Aunty Arfa kin ji wannan matar! Tabɗijam!!!" Aunty Arfa, wadda ta kasance mata ce ga babban ɗan Hajiya Sa'adatu,wato Muyassar,kuma ƙanwa ce a wajen Hajiya Ruƙayya,ta ɗago kai ta tana kallon Iman da take wannan maganar a fusace,a hankali ta ce"to fa!ke dai ba iya gajiya da daru!! Menene yake faruwa ne?" Surayya ta kalli aunty Arfa ta ce"maganar gaskiya aunty! Kawai don abu ya samu mutum sai ya zama kowa ma sai ya same shi? Ki ji Ummeey da wata magana da,wai menene da menene,kar a kai mu karatu this and that,tarbiyyarmu zata lalace bla bla bla, imagine fa! Wallahi ya kamata wannan matar ta kama girmanta,don wallahi idan ta cigaba da yi mana irin wannan halin Allah da gaske zan iya yi mata duk abin da na ga dama,sai dai abba ya dandaƙa ni, daɗin ma su Mommy sun mayar mata da amsa" #Nusy_bee Page 4 Shiru aunty Arfa ta yi tana kallonsu, Amina ta ja tsaki tana gyara zaman hular kanta,ta ce"dama wannan matar tana da wani hali wallahi, yanzu don Allah me zai ragu a jikinta idan ta yi mana fatan alkhairi saboda Allah? Amma saboda wani hali sai ta kama wani fata?to ta Allah ba tata ba,za mu je abroad,za muyi karatu,za mu zama wasu,zamu zama manyan mutane in sha Allahu"ta ƙarasa maganar tana dariya,su ma suka hau dariya Kallonsu kawai Arfa take yi, kafin ta taɓe baki ba tare da ta tanka ba,ita fa wannan gaba ta kai ta,ba don wannan abu da ya faru ba ita ai da bata cika burinta ba, don haka can ta matse musu, ita dai tunda ta samu biyan buƙatarta ai shikenan,su yi karatu ko kar su yi wannan damuwarsu ce Surayya ce ta dube su ta ce"kuma fa ta ba ni tausayi "ta ƙyalƙyale da dariya,ta ce"maganar gaskiya,ita kenan yar,amma a dalilin karatu ta fanɗare " Amina ta taɓe baki, Iman ta ce"ni ban damu da komai ba,ko tausayi ba ta bani ba Abin takaicin shine lokacin da ƴar tata take cikin gidan nan ai fifita ta ake yi akan kowa na gidan Ba ƙaramin daɗi na ji ba da wannan abu ya faru Yaya Safwan fa ya ba mu labarin lokacin da suke yara kiri-kiri Abba yake nuna ya fi sonta,gata yar wulaƙanci ta yi ta rashin mutunci kala-kala wai ita babbar yaya Yanzu sai a je can,wa ya sani ma ko ta bar duniyar?" Arfa ta kalle ta, Iman ta ce"tabbas haka yaya ya ce,kuma dama kin ga sai wani izza suke nunawa kamar su ɗin wasu tsiya ce" Surayya ta ce"cheer up girls! Mu dai burin mu ya cika,in sha Allah sai mun je abroad,mun yi karatu da yawa, mun yi amfani, sannan mu dawo gida mu auri musulmi wanda Abba ya zaɓa mana "suka yi dariya suka tafa Arfa murmushi ta yi kawai,ta ɗauki ƴarta jaririya wadda bata wuce watanni uku ba ta fice daga ɗakin tana cigaba da murmushinta *ROXY* 4:00pm...... A nutse take ɗaure dogon gashinta wanda yake da tsananin tsawo da cika,a hankali kuma ta dakata tana ƙurawa kanta kallo a jikin madubin da yake gabanta Ƙirjinta ne ya doka,a hankali ta lumshe idanu ta buɗe, saboda fuskar da take kalla,a hankali wani abu da ya shuɗe ya dawo mata ƙwaƙwalwa 'Kalle ki sak gyatumarki,don haka wajenta za ki tafi ' 'Abba na ni dai kai nake so ka ɗauke ni ' 'Ba zan ɗauke ki ba, saboda mamanki ta yi son kai,ta kwashe kamanninta kaf ta liƙa miki don son kai!" "Ummeena wai haka? Dama ana iya ɗibar kamanni a zubawa mutum?' 'ke rabu da ni da wannan shirmen,wuce mu tafi' 'Aa fa Hajiya,babu wanda zai saka yarinya ta tafiya da ƙafa,ba ni hannunki,zo nan na ɗauke ki' Ƙasa ta yi da kanta tana ba wa ƙwallar da ta taru a idanunta damar zuba,bata da wani fata a duniya irin sake ganin mahaifiyarta kafin mutuwa ta ɗauki ɗayansu,bata da burin komai sama da hakan,komai na rayuwa yana tafiyar mata yadda take so amma banda wancan ɓangaren Motsin da ta ji ne ya sa ta goge hawayenta,ta dake, saboda ta san Amra ce mai shigowa,gashi a duniyar nan tata babu wanda ta taɓa yadda ya ga rauninta, wannan ma yana ɗaya daga cikin abun da ya kassara mutanen da suke son ganin bayanta "Hi Roxy!"ta ji muryar Amra tana yi mata magana "Hi!come in!"ta bata amsa idanunta akan madubin tana cigaba da gyara dogon gashinta Shigowa Amra ta yi tana kallon Roxy kamar zata haɗiye ta,ita dai wallahi tana tsananin son wannan classic lady ɗin,bata taɓa jin tsananin sha'awar wani ko wata a duniya ba kamar yadda take jin ta Roxy Kyakkyawar mace ce,dirarriya,mai tsarin kyau da ƙawatuwa,ta ko'ina ta cika mace har mace Amma duk da wannan kyan nata Amra sai dai ta kalla daga nesa, saboda ko da wasa bata ga fuskar da zata neme ta ba "Hey! madam!! Why are you staring at me?"muryar Roxy a tsawace ta katse ta daga dogon tunanin da ta lula Ajiyar zuciya mai nauyi Amra ta sauke tana ɗauke kanta, Roxy ta aika mata harara ta ce a fusace "ya zama na ƙarshe, kin sani tuntuni, Roxy bata san kallon ƙurilla,idan wani abu kike so ma a jikin Roxy to kin fi kowa sanin ba za ki samu ba" Murmushi Amra ta yi ta ce"meyasa kike da ƙwarin gwiwar sanin ba zan samu ba?" "Saboda wannan ita ce gaskiyar da za ki sani, da alamu har yanzu ba ki san wacece Roxy ba"ta ƙarashe magana tana shigewa cikin closet ɗinta don saka kaya Murmushi sosai Amra ta yi tana faɗin "kar ki cika ƙwarin gwiwa Hermosa! Nice Amra fa, wadda komai ta saka a gaba sai ta same shi Ba baƙuwa ba ce ni a bariki,a tsawon shekarun da na ɗauka ina bariki ban taɓa saɓa saiti ba" Kallonta Roxy take yi tana jefa mata wani murmushi da ita kaɗai ta san ma'anarshi, kafin ta ce"Goodluck ƴan matan bariki! With time za ki gane bariki tunani yake cinyewa,ba ƙwaƙwalwa yake buɗewa ba"bata bari amra ta sake magana ba ta jefa mata dogon hijabin da ta dauko,ta ce"tashi mu tafi, kar ki fita a haka " Galala ta bi hijabin da kallo,kafin ta mayar da kallonta ga Roxy, wadda take sanye da doguwar rigar abaya,ta ɗaure dogon gashinta sannan ta fara ƙoƙarin saka dogon hijabin da ta ɗaukowa kanta "Ina zamu je haka ne?"Amra ta jefa mata tambaya tana tsare ta da idanu Ba tare da ta kalle ta ba ta ce"tashi mu tafi" "Na ce ina za mu tafi?"ta sake tambaya tana tsare ta da idanu Bata ba ta amsa ba,sai kammala saka hijabin da ta yi ta nufi hanyar fita daga parlourn,kan dole Amra ta miƙe,ta bi bayanta tana kallon yadda jikinta yake rausaya a cikin hijabin, kamar wadda take yi da gayya, Amra ta yi murmushi tana lashe baki,a ranta kuwa tana ɗaukar alwashi iri-iri Abin na Roxy bai sake bawa Amra mamaki ba sai da ta ga ta zaro niƙab ta ɗaura a fuskarta, Amra ta dube ta da mamaki,cike da rainin wayo ta ce"ikon Allah? Roxy ina kika koyi shigarmu ta musulmai? Kuma fa kin yi kyau kamar ba ke ce mai shiga yadda ta ga dama ɗin nan ba"ta ƙarashe maganar tana wata ƴar dariya mau tarin ma'anoni Roxy ta ɗago ta kalle ta da wani yanayi a fuskarta,a karo na farko da ta ji ta muzanta irin wadda bata taɓa yi a rayuwarta ba,da wata iriyar murya ta ce"au? Ke yanzu kallon musulma kike yi wa kanki dama?" "Da mamaki Amra take duban Roxy ta ce"kamar ya kenan? Ban gane maganar taki ba Roxy! Ina kika san musulunci har da za ki san yaya musulmai suke gudanar da rayuwarsu " Roxy tana wata ƴar dariya ta ce"of course a TV, programs da suka danganci musulunci ba sa wuce ni sam" Amra ta ce"hakan bai amfane ki ba, tunda ba ki musulunta ba har yanzu " Roxy ta yi murmushi ta ce"to ke menene shaidar da za ki kare kanki a wajena na cewa ke musulma ce? Sallah?azumi?ko sauran ibada? Kin ga ki wuce mu tafi,ina da wani abu mai muhimmanci da zan yi kafin na bar ƙasar nan,ina so na bi jirgin 4:00pm,so nake within 24 hours na sada Alejandro d kayansa, saboda bana son ya sake yi min hauka,saka hijabin nan "ta ƙarasa maganar da sigar bayar da umarni Amra bata yi mata musu ba,ta saka hijabin,ita kuma Roxy ta ɗaura niƙab ɗin suka fice daga gidan Abin da ya ƙara ba wa Amra mamaki bai wuce ganin Roxy ta tsayar da daidaita sahu ba,duk da yawa da kuma ingancin motocinta da sauran ababen hawanta Amra bata samu damar yi mata wata tambaya ba,duk da yadda kanta ya cushe da tambayoyi saboda mamakin Roxy Kai tsaye wata unguwar talakawa suka nufa, unguwa ce ta masu ƙaramin ƙarfi,ƙananan gidaje,da ƙananan lunguna,ga kwatoci ko'ina, shara kuwa wajen kaca-kaca,ga tsamin kwata da yake tashi a kowacce kusurwa ta unguwar Ita dai Amra sai yatsine fuska take yi fuska a matuƙar ɗaure,a ranta tana jajen inda Roxy ta san wannan wajen,har ta iya kawo su Wani tsuekukin mataccen gida suna nufa,wanda rabin katangar gidan ma ta zaizaye ta zube,da alamu ma gidan da har ƙasa aka yi,aka yi masa plaster, Kai tsaye ba tare da damuwa ba Roxy ta kutsa kai cikin gidan, Amra ta bi ta da kallo tana cin birki a ƙofar gidan,sai da Roxy ta shiga soro sannan ta leƙo tana kallon Amra da ta ci birki tana bin ta da wani kallo Ba tare da damuwar komai ba ta ce"ki shigo mana,tsayuwar me kike yi a nan?" "Ina ne nan?"ta jefa wa Roxy tambayar Kai tsaye Roxy ta ce"wannan abin da ya shafe ni ne,idan za ki shigo kawai ki shigo" Kan dole Amra ta shiga gidan ba don ta so ba,tana kallon ko'ina a yatsine, gidanma ma ƙyanƙyami yake ba ta, saboda yanayin gidan,sai ya yi mata kana da ƙazanta,duk da cewa daidai gwargwado an gyara gidan Da sallama Roxy ta shiga gidan, Amra ta kalli Roxy da tsananin mamaki jin tana yin sallama,abin da bata taɓa jin ta yi ba,wata mata da take zaune a tsakar gidan mai kama da wajen kiwon dabbobi ta ɗago tana kallon Roxy tana amsa sallamar da murmushi a fuskarta, Roxy ta ƙaraso ta durƙusa tana faɗin "Barka da yamma Mama" Matar tana ɗan murmushi ta ce"Barka dai, barkanku da zuwa,sannunku da zuwa"ta miƙe jikinta yana tsuma ya ɗauko tabarma, wadda yara sun kusa lalata rabi,ta shimfiɗa musu,ta ce "bismillah,ga waje ku zauna Ke ma zauna"ta ƙarasa maganar tana duban Amra wadda take tsaye ƙiƙam tana kallon su ba tare da ta yi magana ba Still bata yi magana ba,sai na ɗan matsawa da ta yi baya tana ɗan yatsine fuska don kar matar ta taɓa ta,itama bata yi mata musu ba ta ja baya fara'ar fuskarta tana ɗan raguwa,alamun abin da Amra ta yi mata ya sosa mata rai,ita dai Roxy tuni ta hakimce akan tabarmar tana ɗage niƙab ɗinta "Mama ina yini!"ta gaida ita "Lafiya ƙalau,ya hanya?ya iyali?ya kuka zo?" Roxy ta yi murmushi ta ce"lafiya ƙalau, Mama na san ba ki gane ni ba ko?" Mama tana ɗan murmushi ta ce"ban shaida ku ba wallahi Ku yi haƙuri gidan babu ruwa ne, gashi yaran suna islamiyya ballantana su karɓo muku a shagon ilyasu" Murmushi sosai Roxy ta yi tana girgiza kai, ta ce"kar ki damu Mama,na san ba ki gane ni ba ko? Kin tuna wadda ta kawo miki ziyara kwanaki kaɗan bayan samun Habu?" Shiru Mama ta yi na some seconds, kafin ta ce"eh tabbas na tuna, Hajiya ya za'a yi na manta wadda ta yi min alkhairin da har yanzu nake mora? Ai ni babu abin da zan ce miki ni da Habu sai fatan Allah ya biya ki da alkhairi, Allah ya saka miki da mafificin alkhairi" Roxy ta yi murmushi tana faɗin "babu komai Mama,ina Habu da ƴan'uwan nashi suke?" Mama ta ce"ai da yake an saka shi a allo ne,suna makarantar allo,sai zuwa anjuma za su dawo" Roxy ta yi ɗan jimmm kafin ta ce"ba sa zuwa makarantar islamiyya ne Mama?" Mama ta yi ɗan murmushi ta ce "da dai suna zuwa,amma kin san abu na yau da gobe,sai abubuwan suka fara yawa, abinki da hannu ɗaya, tunda kin ga mahaifin nasu ya rasu babu jumawa da tsintar Habu,to shine dalilin da ya sa suka koma allo kawai" Roxy ta jinjina kai cike da jimami ta ce"Allah ya ji kan shi da rahama,to boko kuma fa?" Mama ta ce"suna zuwa,habu ma ya fara zuwa wannan zangon da suka koma makarantar " Roxy ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce "to Allah ya taimaka,zan samu ganinsa?" Mama ta ce"eh sun kusa shigowa ma,ba za su wuce mintina goma ba, ƙarfe biyar suke tashi" Roxy ta gyara zama ta ce"babu damuwa, bari na jira shi ya dawo,za mu gaisa" Amra da take ta kallonsu cikin takaici ta dubi Roxy fuska a daure tana faɗin"Malama idan bata min lokaci za ki yi Just tell me,kin kawo ni wajen da za'a kashe ni da ƙazanta,ga warin talauci ya ko'ina,kin san ban saba rayuwa a irin wannan wajen ba,idan ke kin saba fine,but idan ba za ki taho ba ni sai na tafi " #Nusy_bee Page 5 Jiki a sanyaye Mama ta ɗago tana kallon Amra wadda ta yi maganar fuskarta a ɗaure,da alamun ɓacin rai ƙarara a kan fuskarta,don har ga Allah wannan mummunan gidan ya fara isarta,ga wari ga tsantsani da ya ishe ta,ta rasa yadda aka yi Roxy da ba ta Rayuwa a Nigeria ma ta san da irin wannan wajen a ciki Kafin wani ya sake magana Roxy ta gyara zama tana murmushi ta ce"ba wani abu ai,komai ya yi gaba,amma idan aka koma baya za'a ga tushiyar dawa,ko na ce asalin ungulu,kusan kowacce mace a bariki musamman ƴar talaka za ki ga kuɗi ta zo nema ne, don bata sanshi ba,kuma tana son ɗanɗana daɗinsa,to ba kowa bane ba ya iya jurar talauci ya shiga duniya,kin ga dai kamar Mama,uwa ta gari"ta karasa magana tana murmushi " Kalaman Roxy kamar an watsa mata ruwan zafi a zuciya haka ta ji su,amma sanin halin Roxy na iya mayar da magana ya sa ta yi shiru,don sanin kanta ne Roxy sam bata da haƙuri,kuma bata da ɗaga ƙafa,muddin aka shiga gonarta,sannan ga tsananin wayo da hikima,ga basira, shiyasa take gudanar da rayuwarta yadda take so a ƙasashe zuwa garuruwa Bata sake bi ta kan Amra ba, wadda ta yi kasaƙe tana kallonta,ta koma satar kallon Mama wadda fuskarta ta nuna alamun jin daɗin amsar da aka mayar mata sakamakon tsangwama da cin mutuncin da ta nemi ta yi mata Hira suka cigaba da yi da Mama da Roxy, cikin hikima da wayon da Allah ya hore mata take jefa wa Mama tambayoyi game da Habu, bata yi mamakin jin cewa yana da larurar asthma ba,dama ta san da batun tun ba yanzu ba Cikin damuwa Mama ta ɗora da batun "yanzu lokaci ne na damuna,ga yanayin zafi,ga kuma iskar gari,ciwon nashi yana yawan tashi,don ma wani lokacin sai mun haɗa da neman taimako a wajen mutanen arziƙi,kuma alhamdulillah ana samu,kin ga ko shekaranjiya da ciwon nashi ya tashi Musa ɗan maƙocinmu Malam Lado ne ya kai shi kyamis aka duba shi,ba ki ga magungunan da ya siyo ba,har da sabon abin zuƙar" Roxy ta yi shiru na ɗan lokaci tana jinjina kai,tana shirin yin magana sallamar yara ta katse ta Mama ce ta amsa sallamar,suka shigo yaran Su biyar ne,biyu mata sai uku maza babban da me bi masa maza ne,sai mata biyu da suke bi musu,sai ɗan ƙaramin su da bai fi shekara uku ba, wanda duk da wahalar rayuwa da ƙangin talauci da suke ciki bai hana kyawunsa bayyana ba, wanda ya zarce ya yi fintinkau wa sauran Kallon kayan jikinsa take yi,rigar gwanjo ce,sai wando yadi,su ma dai ragowar yayyen nasa babu wani mai sutura mai kyan gani, duk da cewa tsaf tsaf suke,amma ƙangin talauci ya ɓoye kaso mai yawa na tsaftar ta su Da girmamawa suka gaida Roxy da Amra, Roxy ta amsa tana murmushi tana tambayarsu sunayensu ɗaya bayan ɗaya,duk da cewa ta gane Habu,suka gaya mata ɗaya bayan ɗaya Sannan suka wuce don ajiye allunansu A jikinta ta rungume Habu tana cigaba da yi masa wasa tana murmushi,shi kuwa sai bin ta da kallo yake yi, kasancewar ba shi da sabo,kuma bai santa ba, gashi kuma ba mai yawan magana ba Ta ɗan juma tana wasa da yaron,ji take yi kamar kar ta rabu da shi,ita dai Amra tana tsaye akanta kamar wata sanda tana kallon su cikin takaicin wannan ɓata lokacin da Roxy take yi musu Sun ɓata wajen awa guda a gidan,har hira Roxy ta yi da yaran matar kafin ta yi musu sallama,ta direwa matar 100k ta ce a mayar da yaran makaranta, godiya sosai suka yi mata,ta janyo hannun Habu tana murmushi ta ce "autan Mama in tafi da kai?" Bai yi mata kara ba ya girgiza mata kai yana komawa jikin Mama ya rungume ta,suka yi ƴar dariya, Mama ta ce "ai shi wannan ba'a bayar da aron shi,na Mamansa ne,daga shi sai ita" Roxy ta yi ƴar dariya tana faɗin "to yaran mamansa, Allah ya bar ƙauna tsakaninka da Mama,ga wannan ku sha Sweet kai da yan'uwanka"ta faɗa tana miƙa masa rafar ɗari biyar Tsayawa ya yi yana kallonta, Mama ta ce"a haba! Kin biya musu kuɗin makaranta yanzu kuma za ki ƙara wani kuɗin? Don Allah ki bar shi, wallahi mun gode Allah ya saka da alkhairi" Roxy tana murmushi ta ce"ayya Mama!abin da ba ki sani ba ni ƙawar Fauziyya ce kafin rasuwarta,mun haɗu da ita a secondary,a wancan lokacin Allah bai taɓa nufa na zo gidansu ba,amma bayan rasuwarta na ji ina sha'awar zuwa na ganku,sai na same ku a cikin jarrabawar ubangiji,kuma kin ga Fauziyya ta yi min babban taimako lokacin da tana makaranta,duk sanda na samu matsala a makaranta ita take taimako na ta fitar da ni daga ciki,ba zan manta halaccinta ba Ni dai yanzu roƙon da nake yi miki shine ki ɗauke ni a yadda kika ɗauke ta" Murmushi sosai Mama ta yi,tana tuna babbar ƴarta Fauziyya, wadda ta rasu shekaru bakwai baya yanzu,a hankali ta ce"to Allah ya saka miki da mafificin alkhairi" Roxy ta ce"Ameen Mama, Allah ya ji ƙan Fauziyya da baba, Allah ya albarkaci rayuwar ƙannenta Wannan jihadi da kika yi Allah ya saka miki da alkhairi " Mama ta yi ɗan murmushi ta ce"har zuwa yanzu ba ki sanar da ni sunanki ba" Roxy ta ce"kin manta sanda na zo wancan karon na gaya miki? Sunana Zainab, kuma a yanzu ina jihar Kaduna ne da zama" "Allah sarki! A wanne gari kike a Kadunan?ai mahaifinsu ma ɗan can ne" Roxy ta ce"a cikin garin Kaduna nake,a unguwar dosa,to Mama za mu tafi,sai idan na sake dawowa "Mama ta fara yi wa Roxy godiya sosai,ita dai Amra har yanzu tana tsaye tana kallon Roxy da tsananin mamakin yadda halayenta da dabi'unta suke canjawa kusan kowacce daƙiƙa a rayuwarta Babu abin da Roxy ta tsana a duniya sama da ƙarya, ƙarya ba ɗabi'arta ba ce ko kaɗan, kuma bata jituwa da mai yinta,amma sai gashi tana ta zubo bayanin da take da yaƙinin duka ƙarya ne,a gaban waɗannan mutanen da take kallon basu da maraba da bola a wajenta Ba su sake ɗaukar lokaci ba suka yi wa Mama da yaranta sallama suka fice daga gidan, zuciyar Amra fal da tambayoyi kala-kala Adaidaita sahu ɗaya suka shiga,sai dai ba su yi nisa ba Roxy ta sauka,ta shige wasu lunguna ta ɓacewa ganinsu, Amra ta bi ta da kallo tana taɓe baki *MALIYA ESTATE* "Hooo Hajiya innayyo tamu,ko kewarmu ba ki fara yi ba ne? Kar ki manta fa, tafiya za mu yi, Allah ne kaɗai ya san lokacin da za mu sake waiwayar Nigeria"a cewar Iman tana rausayar da kanta tana yiwa innayyo magana, mahaifiyar Alhaji Yusuf Maliya Wani kallo innayyo ta watsawa Iman, sannan ta sake jefawa su Surayya da suke dariya wani mugun kallo,ta ce"ko me za ki ce sai dai ki ce,duk wasu yan kayan da na siya saboda motsa baki kin sace kin cinye, to wannan ahir ɗinki" Zaro idanu Iman ta yi,su kuma su Surayya suka kwashe da dariya, Amina har da taɓawa iman kunne, Iman ta galla mata harara,sannan ta dubi innayyo ta marairaice tana faɗin "haba innayyo ta! Daga yau ne fa, gobe iwar haka ma mun bar ƙasar miki ƙasar ma" Innayyo ta taɓe baki tana girgiza kai,ta ce"Ni wannan karatu naku da sai an tafi wata uwa duniya ba wai ina son shi bane,kawai dai ban yi magana bane saboda na ga baban naku ya dage, sannan kuma akwai masu yi muku baƙin ciki da hakan,tabbacin alkhairi ne karatun kenan" Tuni suka mayar da hankalinsu gaba ɗaya kan innayyo, ba don sun yi mamaki da maganganun innayyo ba, dama sun saba da jin abin da ya fi haka daga bakin innayyo akan Ummeey, kasancewar kaf sirikanta babu wadda ta tsana kamar Ummeey,duk da biyayya da ladabin da take yi mata Wannan sanannen abu ne a wajen iyalan Maliya gaba ɗaya,wani abin ma da ƙarin ƙiyayyarta baiwar Allah Ummeey take samu, inda kawai take samun sa'ada shine soyayyar da mijinta yake yi mata,duk da matansa uku kuma ita ce uwar gida amma soyayyar da yake yi mata dabam take Surayya ta dubi innayyo sosai ta ce"wallahi fa innayyo,ki ji min mata da hassada, banda abin kunya ta rasa wanda zata yi wa hassada sai mu,to ta yi mana ma,ina ga iyayenmu mata kuma?su da suka haifi yara maza da mata?ba ita ba da ta tsaya akan guda ɗaya?ɗayar ma wadda ta lalace?" Iman ta ce"saboda abin takaici ana saka sunayen mutanen kirki amma ni wai sai a saka min sunanta "ta ja tsaki cikin takaici Amina ta yi ƴar dariya ta ce "ku yanzu kuka san halinta,mu mun daɗe da sanin halinta" Iman ta ce"seriously Meena,ta kasa gane mugun halinta ne ya janyo mata lalacewar rayuwar tilon ƴarta,kuma Allah ya hana ta wasu yaran har zuwa yau,har da wani wai za mu lalace,to alhamdulillahi, Allah yana tare da mu, babu wanda ya isa ya yi mana lahani,ko boka ko malam " Innayyo ta dube ta ta ce"in sha Allahu ma nan gani nan bari, shiyasa ma nake turara ku da maganin ƙaiƙayi koma kan masheƙiya amma ku rinka yi min surutu kuna cewa ina damunku da ƙauri,gashi nan kun ga amfaninsa yanzu ai" Surayya ta rike haɓa ta ce"wai! Ai kuwa dai mun gani innayyo, Allah ya sawwaƙe,ya tsare mu sharrin mahassada kawai" Sauran suka ce "Ameen!"Iman ta ɗora da faɗin"ya kamata a ce mun gama ɗaukar duk abin da za mu buƙata girls, let's go please "suka miƙe babu musu, Iman ta ce"to granny,zuwa gobe dai zan bar miki gidan,dama kin san min abin da kike ci,ai ba wani abu bane "innayyo ta ɗauki mafici ta jefe ta da shi,suka fice da gudu daga ɗakin suna dariya, innayyo ta ce"yan nema kai!" *HAISAM* Su biyar ne a zaune a cikin ɗakin sirrin, wanda ba'a shigarsa sai mamallakin ɗakin,wato CSO Haisam Abdulmalik Madaka ya buɗe shi da security ɗin idanunsa(eye Scan)ko na yatsansa(fingerprint scanner) Hatta da Amna, ƴarshi ɗaya tilo baya barinta tana zuwa wajen ko da wasa, saboda tsananin muhimmancin da yake da shi a wajensa Mutanensa ne na DSS su huɗu,dukansu yaransa ne da yake aiki tare da su,a gabansu computer ce wadda take taimaka musu don gudanar da binciken nasu Hoton Roxy ne akan computer ɗin, Haisam ya ɗago yana kallon abokan aikin nasa, kafin ya fara jawabi "Wannan ita ce wanted ɗin tamu,a halin yanzu babu abin da muka sani nata sai fuskarta Ba mu san sunanta ba, ballantana wajen zamanta,daga ina take? menene bayani akan wacece ita? A'a! Abu biyu kawai gare mu, fuskarta,sai kuma haruffan da take amfani da su,wato NOCCM, wadanda har zuwa wannan lokaci su ma ba mu san abin da suke nufi ba Ita ɗin ana zarginta da aikata manyan laifuka a ƙasa,babbar hacker ce,ta ƙware sosai a sana'ar Yahoo, Sannan kuma cikakkiyar dealer ce ta cocain da miyagun ƙwayoyi Manyan abin lura a tare da ita su ne,na farko ta raina hukuma,bata jin tsoron kowa, sannan ta goge akan wannan harkar tata Duk da haka a matsayin mu na yan sanda maau bincike ya kamata a ce mun kama ta tabbas Amma kafin nan kamata mu zama masu lura,ko da ya kasance ana zarginta da Laifuka dabam dabam amma babu kisan kai, hakan ba zai saka kai tsaye mu ce bata yi ba, don hatta da Safarar kwayoyi da Yahoo da take yi sai daga baya muka sani, wannan ɗin ma zata iya aikatawa Abin da nake so shine mu yi taka tsantsan, sanannen abu ne a wajenmu cewa wannan matashiyar bata da suna a wajenmu,amma ina fatan za'a dace wajen samo ta a duk inda take a fadin duniya A yanzu za mu duƙufa wajen nemo sunanta,da ma'anar haruffan NOCCM da take yawan amfani da shi,amma ku menene shawararku? Ko kuna da wani hanzari?" Ɗaya daga cikinsu mai suna Musa ya ɗago yana kallon Haisam,a hankali ya ɗaga hannu, Haisam ya ba shi damar magana,ya mike yana duban Haisam, kafin ya ce"sir! Ina ganin ya kamata a fara mayar da hankali wajen gano ma'anar wadannan haruffan NOCCM,don ina kyautata zaton ƙungiya ce, wadda take daukar nauyin ta'addancin da take yi a duniya Don har yanzu bana ji a raina cewa ƴarinyar nan tana aiwatar da duk abin da take so ba tare da tsayawar wani babba ba,a takaice ma,bata da ƙarfin ƙwaƙwalwar da zata iya yin hakan " #Nusy_bee Page 6 Shiru Haisam ya yi na yan sakwanni, kafin ya ce "nima ina wannan tunanin wasu lokutan,amma kuma wacce iriyar ƙungiya kake gani zata dauki nauyin shigo da miyagun ƙwayoyi zuwa ƙasar nan?ta daukar fansa ce ko ta ta'addanci zalla?" Musa ya ce "to yanzu ba na ce ba dai,amma mu cigaba,akwai lokaci, bincike zai nuna" Haisam ya yi murmushi yana faɗin "Weldon Musa!You tried,but you have to be careful,ya kamata ka iya takunka,don yarinyar nan tana da haɗari sosai Yanzu abin da za mu mayar da hankali akai shine, menene cikakken sunanta? A ina take da zama?ko na ce a ina take sauka idan ta shigo Nigeria? A wacce ƙasa take da zama?don da yiwuwar sai mun bi ta har ƙasar da take! A wannan wata gudan ina so na samo komai game da ita, saboda alƙawarin da na ɗauka, don haka mu zama ready, yanzu haka tana Nigeria,mu yi ƙoƙari mu san next move action ɗinta,da kuma inda take shirin zuwa nan gaba kaɗan, saboda mu daƙile ta" Ɗaya daga cikin abokan aikin nashi mai suna Awwal ya ce"Sir! Wannan lokacin sai mun yi da gaske, zata iya kamuwa, in dai har ba da tsafi take yi ba ,amma abin akwai mamaki yadda mace take dealing ɗinmu a ƙasar nan,macen ma yarinya ƙarama kamar wannan " Murmushi sosai Haisam ya yi yana kallonsa,a hankali ya ce"ka raina mace ne? Kana ganin ta gaza ta yi irin wannan aikin?" Awwal ya girgiza kai ya ce"ko ɗaya Sir!kawai dai na ga ba'a cika samun mai karfin zuciya a cikinsu ba, wadda zata iya aikata irin wannan aikin" Haisam ya ce"har wadda ta fi ta ma za'a samu Abin da ke akwai na case ɗinta shine safarar miyagun ƙwayoyi ne sai Yahoo,bata safarar yara ƙanana,bata safarar muggan makamai,bata safarar mata don ta lalata su,kuma har yanzu ba mu samu wani single rahoto da yake bayyana tana kisa ba Kuma duk waɗannan abubuwan da na lissafa akwai macen da ta haɗa su tana yi,don haka kar ka zauna kana mamakin abin da ta yi,ka yi focusing akan yadda zata shigo hannu kawai" Awwal ya jinjina kai kawai,tabbas maganar CSO Haisam gaskiya ce,akwai matan da suke aikata waɗancan abubuwan da ya lissafa duka,kuma su ma suna gudanar da rayuwarsu yadda suke so Sun ɗan juma suna tattauna yadda za su shawo kan matsalar, Haisam yana sake jaddada musu kowa ya kasance a ankare, sannan kuma ya kasance cikin shiri a kowanne lokaci *ROXY* Thursday,23rd October,4:00am Su bakwai ke a cikin ɗakin da ya kasance kamar parlour,haske ko'ina,ga hayaƙi na taba da na shisha da ya bule ɗakin har ba'a iya ganin abin da yake cikin dakin sosai,gefe kuma kiɗa ne yake tashi kaɗan kaɗan daga ƙatuwar home theater ɗin cikin waƙar Go down dey ta shaggy da spice Su uku ne mata, Roxy da take kan computer tana danne-dannenta,gefenta kuma ƙatuwar tukunyar shisha ce tana bulbulawa cikinta hayaƙi,sai Amra da take zaune a tsakiyar maza biyu, David da Salis Wise,sai Hannah da suke buga wasan karta ita da Jamilu da oga boss, wanda ainihin sunansa shine Rabi'u Shaye-shayensu kawai suke yi hankali kwance,ga kayan maye kala-kala,ciki har da giya da cocain, waɗanda suke taɓawa lokaci lokaci Banda Roxy da ta yi focusing akan abin da take yi da shishar da take sha,bayan wani lokaci ta daki table ɗin da yake gabanta tana faɗin "an gama da wannan harkar!"ta ture computer ɗin gabanta ta yi baya ta faɗi ta fashe Kallonta Jamilu ya yi yana murmushi,ya ce"ya dai our boss? I hope kin kwashe kuɗin?" Kaɗa yatsunta biyu ta yi,ƴar manuniya da na kusa da shi,tana yatsina fuska ta ce "ai ba masu yawa bane kuɗin, Just 70m" "Murmushi suka yi kusan dukkansu, Amra tana murmushi ta ce"wow! Congratulations!ya Kamata kuɗin nan ki haɗa mana shagali da su" Hanna ta ce"Yes ma! Idan da hali ma ba'a ƙasar nan ba,ki bari sai mun koma Ibiza " Yatsina fuska, wadda ta zamar mata kamar dabi'a ta yi tana kallon Hanna, kafin ta ce"No way! Ya kamata mu rinka tuna wasu abubuwa idan muna aikata wasu Ko ba komai za mu rage zunubi "ta mike tsaye tana gyara zaman jacket ɗin da take jikinta ta ce"wani orphanage na samo,ina son na yi donating kudin zuwa can" Gaba ɗayansu babu wanda fuskarsa ta washe sai Oga boss,ya ce"wow! Good idea my dear,hakan yana da kyau,i love the way you care for others in life Roxy, I will help you in sha Allah "hannu ta ba shi suka tafa, sannan ta samu waje ta zauna Wani kallo David ya bi ta da shi,haka zalika Hanna, saboda tsananin mamaki da takaicin maganarta,kafin su yi magana Amra da take watsa mata wani banzan kallo ta ce"okay! Na gane yanzu,wato orphanage ɗin da kika ja mu last week ita za ki kai kuɗin ko?" Roxy ta kalle ta cikin kwanciyar hankali ta ce"ina wannan tunanin" "Tabɗijam! to wallahi ba ki isa ba! Babu yadda za'a yi ki tsallake mu,mu da muke yi miki amfani dare da rana ki miƙawa wasu matsiyata ƙasƙantattu kuɗi Kina yin hakan ne don ki siya soyayya a wajen mutanen ƙasar nan? Ko kina so ki canja ne ki nuna cewa yanzu ke kin zama ta gari?to wallahi ba ki isa ba, I can't take this stupidity,dole dai ku arna sai kun nunawa mutane butulci irin wanda kuka saba Dama jiya ina ciki da ke,kin kai ni unguwar talakawa na shaƙi wari da ƙarnin talauci sannan kin gasa min maganganu,Ni ba zan biye miki ba, hankalinmu ba iri ɗaya bane shiyasa ban kula ki ba,na ƙyale ki kika yi ta abin da kika ga dama To shine yanzu za ki fifita waɗancan matsiyatan akan buƙatarmu?to wallahi ba ki isa ba,ba ki kai wannan ba!!! Wacece ke da za'a zuba miki idanu kina yin abin da kika ga dama?arniyar banza da wofi kawai" Gaba ɗaya ɗakin zubawa Amra idanu suke yi, wadda take ta masifa ko mayar da numfashi bata yi, banda Roxy da take zaune a kusa da shisha ɗinta tana cigaba da zuƙa tana fitar da hayaƙi, fuskarta babu alamun damuwa ko kaɗan, Oga boss ya dubi Amra cikin jin takaicin wannan abu da ta yi,rai a ɗan ɓace ya ce"wannan abu da kika yi sam bai yi ba Amra! Ita ce shugabarmu,kin ɗaga mata murya saboda kuɗinta, wanda ta nemo da wahalarta, tana biyan mu albashi wanda ya ishe mu shan sharafinmu,tana ɗaukar nauyin duk wani abu da muke buƙata,ina ganin wannan hayaniyar ba ki yi ta a inda ya dace da wanda ya dace a yiwa ba,hakan butulci ne Sannan kar ki sake yi mata gorin addini, saboda itama tana da nata addinin,kuma ta yarda da abin da take bautawa" A fusace Amra ta dube shi ta ce"malam ba da kai nake ba,da uwar ɗakin da kake neman gindin zama a wajenta nake"Oga boss zai sake magana Roxy ta ɗaga masa hannu, har yanzu bata kalli sashen da suke ba, asalima zuƙar hayaƙinta take yi hankali kwance Miƙewa ta yi tana tafiya kamar mai rangaji, har ta isa gaban Amra, wadda hantar cikinta ta kaɗa ganin yanayin Roxy, Roxy ta yi wani killer smile tana kallonta, kafin ta fara magana cikin izza yadda ta saba "Me kika ce ma? Wai.....na kai ki gidan talakawa na wukaƙanta ki na gaya miki magana bla bla bla! Ina son na tuna miki asali da tushenki ne! Yes!!!so nake na tuna miki ke ma ba kowan kowa ba ce,ba ƴar kowa ba, face yar gidan malam Namadi mai kayan miya a gefen kasuwa,kuma na san kin tuna da hakan, that's okay for me Sannan da kike maganar kin yi min aiki,aikin da waccan matar da kike kallo a matsayin ƙasƙantacciya ta yi min aikin da ko makamancinsa ba ki isa ki yi min ba, sannan wannan kuɗi nawa ne,Ni na yi wahala na samo shi,ke ma idan za ki iya go ahead and get yours, best of luck Madam monkey!"ta ƙarashe maganar tana bubbuga kafaɗarta ta dama Har ta juya ta sake juyowa tana kallon Amra wadda ta ƙame a waje ɗaya, ba tare da damuwa ba ta ce"yawwa sai Maganar addini,ke wanne addinin kike bi tukunna?" Ba Amra ba,hatta su Oga boss sai da suka razana suna kallonta cikin tsananin mamakin wannan tambayar,da ƙyar Oga boss ya dube ta ya ce"musulma ce mana" Kallonsa ta yi tana murmushi ta ce"really Oga boss? To menene shaidarka na addinin nata?sau nawa ka taɓa ganin ta yi Sallah?ka taɓa ganin ta tana azumi?" Shiru suka yi gaba ɗaya, Roxy ta ce"to bata da addini,kar ta sake yi min gorin addini, otherwise kuma wani abu mara daɗi ya biyo baya, I can't take that nonsense" Shiru wajen ya ɗauka,don da alamu ran Roxy ya ɓaci, sai da ta ɓata kusan mintuna biyar tana danna waya sannan ta kalli David ta ce"David ya batun aikin da na ba ka?" David ya numfasa ya ce"ma na gano kusan komai da ya danganci jami'in Sunansa HAISAM Abdulmalik Madaka,mai riƙe da muƙamin CSO a hukumar DSS,mutum ne mai matuƙar ƙwazo da ƙawazuci a aikinsa,idan ya saka abu a gaba to tabbas sai ya ga bayansa,sai ya yi nasara akansa Haka tarihinsa ya zo Ma'am " Jinjina kai ta yi ta ce"uhumm! Ina jin ka, cigaba mana" David ya gyara zama ya cigaba"sai batun iyalansa,ya yi aure shekarun baya,amma zaman shekaru uku kawai suka yi da matar sakamakon matsaloli irin na cikin gida,sun rabu yanzu haka, ƴarshi guda ɗaya Rasheeda Haisam makawa, wadda suke kira da Amna tana hannunsa" Ɗan murmushi ta yi ta ce"wow! that's is very interesting,ina jin ka, cigaba" "Ba shi da yaya ko ƙani,bashi da uwa,ta rasu,yana rayuwa tare da mahaifinsa Alhaji Abdulmalik Murtala Madaka, wanda ya kasance ɗan kwangila ne,kuma cikakken ɗan kasuwa,amma harkokin kasuwancin nashi sun fi yawa a Abuja da Lagos,da matar babansa hajiya Mariya Madaka,ita kuma babbar likita ce da take riƙe da asibiti nata na kanta" Roxy ta jinjina kai ta ce"good job David,a ina suke da zama?" "Suna zaune a Rocky estate ne"ya bata amsa"Roxy ta ɗaga kafaɗa tana taɓe baki tana murmushi ta ce "good,ina phone number ɗin tashi da na ce ka samo min?" David ya ce "na tura miki ta Whatsapp"babu musu ta miƙe ba tare da ta sake magana ba,ta fito zuwa compound ɗin gidan,tana kallon yadda gari ya fara wayewa,don an ɗan kwashi lokaci da gabatar da Sallar asuba Kamar mai nazari haka ta fara bin compound ɗin da kallo, kafin kuma ta ɗauke kai ta nufi backyard ɗin gidan kai tsaye *MALIYA ESTATE, KANO STATE, NIGERIA* A yau iyalan suna cike da farin ciki da kewa kuma duka a tare, saboda tafiyar su Iman izuwa ƙasashen da za su je karatu,ita dai Ummeey duk da yadda ta zama mujiya a cikin iyayen yaran hakan bai hana ta cigaba da kawo gudunmawa ta ko'ina ba Kasancewar ta san suna son kayan zaƙi tuni ta saka an shirya musu dubulan da alkaki,sai cake,aka yi packaging ɗinsu a bokitai masu kyau Da kanta ta yi sallama ɗakin Hajiya Ruƙayya, inda ake ta shirya kayan da za'a tafi da su, Hajiya Sa'adatu da take zaune ita da Saleem suna sake shirya kayan tafiyar ta su ta ɗago kai tana kallon Ummeey gami da amsawa Tana murmushi ta ajiye bucket ɗaya da take riƙe da shi,itama mai aikinta da ta riko sauran biyun ta ajiye,tana murmushin ta dubi Hajiya Sa'adatu ta ce "Hajiya ga su nan,na ga yaran namu akwai son kayan zaƙi,shine na saka aka yi musu, Allah ya taimaka ya bayar da abin da ake nema" Surayya da take fitowa daga ɗaki, kasancewar ta fi kowa raini a cikinsu ta dube ta ta ce"an gode Ummeey,amma da ba ki bayar an yi ba,mun riga mun karbo wanda aka yi mana already, Allah ya saka,amma da kin tafi da shi" Kallonta Ummeey ta yi, duk da cewa ranta ya sosu amma sai ta yi murmushi, kafin ta kai ga magana Hajiya Sa'adatu ta riga ta "Amma abin da mamaki Hajiya Zainab,na ga dai lokacin da Shaheeda zata tafi zuwa karatun nata kamar ba kiyi mata wannan hidimar ta kayan zaƙi ba, gashi na kasa yarda cewa kin fi son yaranmu akan yadda kike sonta,don dai babu munafunci mu dai mun fi son yaranmu akanta " Hajiya Ruƙayya da ta shigo ta dubi Hajiya Sa'adatu da sauri, wadda ta mayar da hankali kan Hajiya Zainab tana kallon reaction ɗinta tana fatan ta tanka, Hajiya Ruƙayya ta ce"kayya! Ai yadda ta faɗa ɗin ne,ɗa na kowa ne,itama ai ƴaƴanta ne,ita ɗin mai iko da su ce, Hajiya, Allah ya amfana,an gode sosai, Allah ya bayyana Shaheeda "Hajiya Zainab ta yi ɗan murmushin yaƙe ba tare da ta yi magana ba ta juya ta nufi hanyar barin parlourn, ba tare da ta kula da kallon rainin da suka bi ta da shi ba #Nusy_bee Page 7 Da kallon banza Surayya ta bi ta, sannan ta dubi Hajiya Ruƙayya tana faɗin "Mamie wannan matar makira ce fa Sai wani sumu-sumu take yi na munafurci Duk abin da take yi da sanin Abba,ko ma na ce shine ya sahale mata,amma wallahi ba zata rinƙa taɓa Ni ina ƙyale ta ba"ta kalli buckets ɗin da Ummeey ta kawo ta yi fatali da ɗaya,alkakin da yake ciki ya zube,ta cigaba da sababi "yanzu haka ma wani barbaɗen ta yi a cikin wannan tarkacen da ta kawo kamar ana yunwa,ni wallahi komai da ta kawo min ma mayar mata shi zan yi,ta je ta bawa ƴarta, wadda mugun abin da take yi wa ƴaƴan mutane ya koma mata" Hajiya Sa'adatu ta dube ta cikin kwantar da murya ta ce "kwantar da hankalinki Surayya,babu wanda ya isa ya yi muku wani mugun abu a duniya, yanzu ba sai anjuma zan mayar mata da kayanta,mu gaya mata ba ma bukata gaba ɗaya,ki kwantar da hankalin ki" Hajiya Ruƙayya ta dube ta ta ce"A'a Hajiya Sa'adatu! Kar ta haɗa mu da alhaji,a maimakon haka gwara mu zubar a shara,idan ma wani mugun abin ta yi Allah ya mayar mata kanta, kamar yadda ya mayar mata wancan karon" Iman da ta fito daga ɗakin ta taɓe baki tana cigaba da danna wayarta,ita yanzu lamarin matar nan ya daina ba ta mamaki ma Tsam Saleem da yake kallonsu ya miƙe, ba tare da ya yi magana ba ya fice daga ɗakin,sauran suka bi shi da kallo, Hajiya Ruƙayya ta ce"ji shashasha!" Iman ta ce"manta da shi Mamie,zai dawo hanya ne,na ga yana nuna cewa shi na Allah ne " "Mu kuma na shaiɗan ne kenan?"a cewar Surayya tana watsa mata wani kallo Dariya Iman ta yi ta ce"oh Allah! Ni fa ba da ke nake ba,amma kin ga abar maganar,mu je mu ƙarasa shiryawa, jirginmu ya kusa ɗagawa"babu musu suka miƙe suka shiga don ƙarasa shiryawa Bayan awa guda suka fito cikin shirinsu don tafiya, Ummeey ma ta fito lulluɓe da ƙaton mayafinta a kan tsadadden lace ɗinta,ta dube su tana murmushi, kafin ta ce"ƴan makaranta! To Allah ya kai ku lafiya,kun yiwa drivern magana?" Babu wanda ya kula ta,sai Saleem, ɗa ga Alhaji Rufa'i ya ɗago yana kallonta, cikin girmamawa ya ce"ba driver bane zai kai mu Ummeey, Mummy ce,sai Mamie da zata raka mu" Ummeey bata damu ba ta ce"to shikenan babu matsala,a wacce motar za mu tafi ne?" Kai tsaye Hajiya Atika da ta zo wajen ta ce"a'a Hajiya Zainab,ba waje"ta dube su fuska babu walwala ta ce "ku wuce mu je ko? Hajiya Zainab sai mun dawo mu kuma " Jikin Ummeey a sanyaye ta ce"to Allah ya kai ku lafiya ya ba da abin da aka je nema,takwara, Allah ya tsare ya taimaka,a yi ta dagewa ko? Allah ya kawo babban rabo na alkhairi"babu wanda ya sake kallon ta suka juya suka wuce suka bar ta a tsaye,har sun yi gaba Hajiya Sa'adatu ta dawo da baya,tana dubanta fuska a ɗaure ta ce"au! Sai hakuri fa Hajiya,kayan da kika aiko yaran sun ce ba sa ci,to kin san sha'anin yara,shine kawai na ce a zubar,amma an gode "daga haka ta juya ta bar wajen ba tare da ta sake saurarar Hajiya Zainab ba Da kallo sake da baki galala Ummeey ta bi ta da kallo, kafin ta ja ƙafarta jiki a sanyaye ta koma ɗakinta,sai da ta shiga sannan hawaye Masu zafi suka wanke mata fuska Daɓas ta zauna a kan kujera, hawaye Masu zafi wasu na korar wasu,bata damu da sharewa ba saboda yadda zuciyarta ke tafasa da raɗaɗi Ba tana jin zafin zuciyarta kawai don abin da aka yi mata ba, A'a har da tuna tata tilon ƴar da bata san inda take ba yanzu haka Bata da wani ɗa da zata kalla ta ji sanyi na cin mutunci da gori da take fuskanta daga wajen kishiyoyi da dangin miji,ya ɗaya ta tilo ta haifa a duniya,itama wata mummunar ƙaddara ta raba su da ita ta wata bahaguwar hanya, wadda hakan ya janyo mata kallon wulaƙanci da ƙyama tsakanin kishiyoyinta, kowacce da kalar yadda take bayyana zargin gazawa ta fuskar bawa ƴarta tarbiyya Bata da uwa babu uba,babu yaya babu ƙani,yayarta ɗaya gare ta, wadda tsawon shekaru goma sha biyar kenan da ta koma Egypt da zama,har yanzu ko sau ɗaya bata taɓa kawo ziyara na Hakan bai ba ta damar sanar da ita halin da take ciki ba,a maimakon haka ma sai ta zaɓi ta yi ta addu'a babu dare babu rana,da niyyar Allah ya dawo mata da farin cikinta da ta rasa,ko da ace Shaheeda bata raye Allah ya yi mata rahama, sannan ya kawo mata sauƙin wannan wulaƙancin da take fuskanta Ta so ta ja yaran kishiyoyinta da na dangin mijinta wadanda ƙaddara ta zaunar da su a waje ɗaya (maliya estate),amma hakan bai yiwu ba, sakamakon bambancin da iyayen suke nunawa kiri-kiri,yau da gobe tun yaran ba sa ɗauka har suka fara ɗauka,daga nan sai abubuwa masu kama da raini da wulaƙanci suka biyo baya Tana sane da cewa idan ta kai ƙorafi wajen Alhaji Yusuf Maliya za'a ɗauki mataki,amma hakan zai sake haifar da wutar ƙiyayyarta da baƙin cikin ganinta a gidan, sannan kuma duk da hakan wasu ba sa yin abin da ya dace ɗin duk da tsanani irin na Alhaji Yusuf, kamar Surayya,har shakkar shiga shirgin yarinyar take yi ko da tsautsayi,don ma watarana idan ta yi mata banza take yi da ita Lokacin da Shaheeda tana gidan babu wanda ya isa ya taka ta ya zauna lafiya, bata shiga sabgar kowa,daga karatunta sai na bincikenta,amma muddin aka samu wanda ya raina mata uwa lamarin ba zai yi daɗi ba, musamman da ya kasance ita ce ta gaban goshin Alhaji Yusuf,ko ɓoye soyayyarshi a gare ta baya iyawa sam Dalilin haka ya janyo mata ƙiyayya daga wajen sauran ƴan uwanta,na yadda mahaifin nasu yake tattalinta,babu yadda Ummeey bata yi ba ya daina nuna mata wannan soyayyar ƙuru-ƙuru amma ya ƙi,da ya gaji sai ya ce "Zainab na ga ke ma kina adawa da babbar ƴata magajiyata! Ko ke ma hassadar kike yi mata? Kishi kike yi da ita?"daga lokacin ta ja baya da su, saboda akan Shaheeda Alhaji Yusuf Maliya bai ƙi ya ɓata da kowa ba,har mahaifiyarsa, wadda ta ɗorawa Shaheeda tsana hakanan babu gaira babu dalili Har zuwa yanzu Ummeey tana kawar ƴarta,duk da maganganu masu zafi da muni da ta fuskanta daga wajen mutane hakan bai saka ta karaya ba,a kowanne lokaci tana fatan dawowar ƴarta,tana fatan ta sake waiwayarta,idan ma ta Allah ya kasance akanta tana fatan Allah ya ji ƙanta Rayuwa kenan!ko ina makomar cikin da ta zo da shi a ranarta ta ƙarshe a gidan?hawaye Masu zafi suka zubo mata, Allah sarki Shaheeda! A fili ta ce "ya Allah! Allah ka dawo min da Shaheeda Lafiya!idan kuma ta bar duniya Allah ka yi mata rahama!!! Allah na san kana sane da ni, Allah na bar komai na rayuwa ta a hannunka, Allah ka yi min sakamako na alkhairi!!!"ta sanya hannayenta ta rufe fuskarta tana cigaba da kuka a hankali *ROCKY ESTATE, KANO STATE, NIGERIA* *HAISAM* "Daddy! Daddy jiya fa baka kawo min chaculate ɗina,kuma ka yi min alƙawarin za ka zo min da ita" Kallon Amna ya yi, wadda kiri-kiri ta dasa masa rigima akan chaculate,ya ce"ho mamana! Babu excuse ne wai?ki koma wajen Nanny ɗinki yanzu,zan tafi aiki, I promise yau dai zan zo da ta jiya da ta yau,idan kuma kika ƙi sai na ƙi tahowa da ita" "Daddy you said promise ko?"ta faɗa tana kallonshi don son tabbatarwa "Yes my dear! I said promise,ki koma ciki,bana son ki rinƙa wasa da school,idan ba ki ci exams ba zan fasa siya miki new teddy fa" Shagwaɓe fuska ta yi tana faɗin "Please Daddy!"ya ce"to koma ciki, ki gayawa Nanny ta ƙarasa shirya ki ki tafi wajen driver ya kai ki school,Ni zan wuce aiki,sai na dawo ko?" Tana murmushi ta ɗaga masa hannu tana faɗin"Daddy Allah ya kiyaye hanya"yana murmushi ya ce"Ameen sweetheart! Ke ma Allah ya kiyaye hanya"ya ja motarshi ya nufi gate,yana hango ta ta jikin madubi tana ɗaga masa hannu tana murmushi Yana fita daga Rocky estate,ya hau titi kenan ya ji ƙarar wayarshi alamar shigowar saƙo,tashin farko bai yi tunanin komai ba,daga baya sai ya yi tunanin ko ɗaya daga cikin ƴan teams ɗin su ne waɗanda za suyi aikin kama Roxy,don haka sai ya yi tunanin ya buɗe idan ya samu wajen tsayawa Babu jumawa hold up ya riƙe su,ya tsayar da mota ya ciro wayarshi yana duba message ɗin da aka yi masa Sabuwar number ce,bai yi tunanin komai ba ya buɗe content ɗin message ɗin "Kafin ka yi tunanin shiga rayuwar wani ka fara tsare taka jami'i,fatan nasara NOCCM." Shiru ya yi yana kallon wayar na ɗan lokaci, kafin ya yi wani yunƙuri wani message ɗin ya shigo "Kada ka zauna kana nazari akan abin da ba shi da amfani,ka tuna cewa ba kai kaɗai kake rayuwa ba! NOCCM" Da gaggawa ya fara kiran layin,amma ya ji a kashe,yana ajiye wayar wani message ɗin ya shigo wayar,amma da wata number ɗin "Ƙoƙarin kira kake yi? Kar ma ka wahalar da kanka wajen kira,ba za ka samu ba,ka yi abin da aka saka ka NOCCM" Da sauri ya turawa Awwal number ɗin da aka kira shi kira na biyu,da gajeren message"Awwal yi min tracking wannan number ɗin" Amma message ɗin yana shiga wani ya shigo wayarsa"bibiyar number ɗin za kayi?kar ma ka wahalar da kanka ba za ka samu ba NOCCM!" Yana kammala karantawa ya ja tsaki,amma bai kai ga jan numfashi ba wani message ɗin ya shigo da wata number ɗin ta dabam"a maimakon wasarere da za ka yi da saƙona,ko yunƙurin bibiya ta,ina son ka tuna cewa akwai yarinya ƴar shekaru biyar da ta fita zuwa makaranta ita da drivernta mintuna kaɗan da suka wuce,ya kamata a ce ka yi tunani akanta NOCCM!" Cikin Wata iriyar gigita da razana ya daki stearing motar ta shi yana kallon wayar tashi cike da kaɗuwa, kafin ya yi azamar fara kiran layin drivern Amna Sai dai kuma wayar tana ta ruri amma ba'a ɗaga ba, hankalinsa ya tashi,take ya mayar da akalar kiransa ga Musa,Musa yana ɗagawa bai jira komai ba ya ce a gaggauce"Musa Please ka yi min tracking number ɗin Umar drivern Amna,yanzun nan" Musa ya ce"I'm sorry Sir! Amma ba ni da numbern " Haisam ya daidaita nutsuwarshi yana goge gumi,ya ce"bari na tura maka"ya kashe wayarshi Babu jumawa ya tura,yana turawa Musa numbern sai ga message ta wayar drivern Amna "Don't bother yourself,wayar tana hannu na,ka yi ta ran ƴarka shine mafitarka,idan ka gwada taurin kai kuma ta baƙunci lahira, kuma yanzu ka fara ganin hakan NOCCM!" Cikin wani irin tashin hankali ya fara sauke numfashi da ƙarfi "kafin da ƙyar harshensa ya fizgo kalmar 'Hasbunallahu wa ni'imal wakeel!"ba tare da tunanin komai ba ya juya akalar motarshi zuwa makarantar su Amna A bakin makarantar ya yi parking,ya fito kai tsaye ya nufi gate ɗin makarantar zuciyarsa cikin tsananin fargaba,a ranshi yana addu'ar Allah tsare masa ƴarshi ya yi masa maganin wannan azzalumar A office ɗin headmaster ɗin makarantar ya sauka,bayan sun gaisa ya buƙaci ganin ƴarshi, ba tare da headmaster ɗin ya kula da yanayinsa ba ya ce "Eh Rasheeda Haisam madaka tana cikin class ɗinsu yanzu haka,bari a kira ta"take ya aika a zo da ita Babu jumawa sai ga su sun dawo da ita, Amna ta taho da gudu ta ɗane shi tana faɗin"Daddy! Ka je aikin? Yanzu muka zo makaranta,a hanya wasu mugaye suka tsare mana mota,ina ta kuka, uncle Farouk ya ce na daina kuka,ɗaya har da ce min beautiful baby I love you,suka ƙwacewa uncle Farouk waya suka tafi,shine uncle Farouk ya ce na daina kuka,shine ya kawo ni makaranta Shiru ya yi yana jan ajiyar zuciya yana shafa kanta, kafin ya ce"to bari na koma ko? Ko wuce ki je ki cigaba da karatu,me ma kika ce kina so?" Ta ce"teddy da chaculate " Haisam ya ce"consider it done ranki ya daɗe!"malamin da ya kawo ta ya ja hannunta suka tafi,ya dubi headmaster ɗin ya ce"idan driver dinta ya zo a ce su jira ni,zan zo da kaina na dauke ya" Headmaster ya ce"okay Sir!"daga nan ya yi musu sallama ya tafi Wannan karon ko da yana driving da ya ji shigowar message bai yi wasa ba ya duba, sabuwar number ce dai,cewa aka yi "Na san yanzu hankalinka a kwance yake saboda ka tabbatar da cewa ƴarka tana cikin ƙoshin lafiya ko? Ka kwantar da hankalinka, saboda wannan ba hari bane, gargaɗi ne, gargaɗi ne na abin da zai iya faruwa idan baka daina bibiyata ba because...... NOCCM!" *Haisam zai daina bibiyar Roxy kuwa??* A cikinsu wanene zai yi nasara tsakanin doka da laifi?* #Nusy_bee Page 8 Shiru ya yi na ɗan lokaci yana nazarin saƙon, kafin ya kaɗa kai kawai,ya tayar da mota ya cigaba da tafiya don wucewa wajen aiki Yana shiga office ya zauna akan kujerar da ya saba zama,ya ɗauki shayin da aka kawo masa babu daɗewa ya fara sipping a hankali yana nazari Buɗe system ɗin sa ya yi ya lalubo ɗaya daga cikin hotunan Roxy da ta yi a ƙasashen waje,sanye take da sweater baƙa da dogon wando jeans,sai sketchers a ƙafarta,sai baƙin glasses da ta rufe ƙwayar idanunta,tana tsaye a cikin dusar ƙanƙara Ya kai mintuna biyu yana kurɓar tea ɗin yana nazartar hoton kamar mai son gano wani abu a hoton, kafin ya yi murmushi ya ce"smart girl! I like you!!!"ya ture laptop ɗin gabanshi ya janyo wayarshi ya fara ƙoƙarin aika kira Bayan ƴan seconds kaɗan sai ya fara magana "Awwal ka same ni a office ɗina"yana faɗin haka ya kashe wayar Babu jumawa Awwal ya shigo,bayan ya sara masa ya ja gefe ya tsaya yana faɗin "morning Sir!" "Awwal! Ya batun aikin da na saka ka?" Awwal ya sake sarawa Haisam Sannan ya ce"sir! Mun kasa samun location ɗin" Haisam bai yi mamakin jin hakan ba,don shima ya sani,a shirye take,abin da ya fi haka ma zai iya ji,a maimakon haka sai cewa ya yi "zauna mu yi magana Awwal" Babu musu Awwal ya sake sara masa, sannan ya samu kujera ya zauna, Haisam ya buɗo messages na NOCCM ya nuna masa ɗaya bayan ɗaya Mamaki sosai ya kama Awwal,ya ɗago yana kallon Haisam da neman ƙarin bayani, Haisam ya gyara zama sosai ya ce"yarinyar nan a shirye take Awwal Babu wanda ya san cewa mu jami'an DSS muna bibiyarta,yaya aka yi ta sani? Maybe akwai wani a cikinmu da yake kai mata rahoton komai,kuma zai iya zama ko ma wanene,amma ka san me na gano, kuma nake tunani a kai?" Awwal ya girgiza kai yana faɗin "sai ka faɗa" Haisam ya ce"tana da babban team da suke gudanar da aiki tare,waɗanda suke taimaka mata don cimma burinta,irinsu ne suka tare Amna da drivern ta suka ƙwace masa waya,a sigar gargaɗi" Awwal ya sauke ajiyar zuciya,duk yadda suke tunanin yarinyar nan ta wuce haka,amma sai ya ce"to Sir ya kake ganin za'a yi? Sannan kuma menene sabon shirinka?tunda abin ya fara haɗawa da ƴarinyar da bata san komai ba?" Kai tsaye Haisam ya ce"babu gudu babu ja da baya,asalima yanzu nake jin na ɗaura ɗamarar kamo ta, yadda take jin cewa tana da wayon da yake jagorantar ta ta aikata laifi haka nake jin ina da wayon da zan daƙile kuma na kama mai laifi "ya miƙe tsaye ya ce "mu je zuwa! yanzu aka fara wasan! I love the way you act!! smart girl!!!" *MALIYA ESTATE* Ringing ɗin wayarta ne ya tayar da ita daga baccin da ta kwanta bayan ta idar da sallar walha,ɗaga kanta ta yi tana duban wayar, kafin ta janyo ta a hankali ta ɗaga wayar ba tare da ta duba sunan ba "Ummu Shaheeda! Yau dai ga mu a Nigeria!" Tuni ta wartsake,ta nemi baccin da take ji ta rasa jin muryar gudan jininta, wadda ta rage mata a duniyar nan da zata kalla ta ji daɗi,ta tabbatar da a ce tana ƙasar da ba ta kasance cikin kuka da ciwon da take ciki yanzu ba "Yaya Saude! Ke ce!ke ce a garin? Allah sarki yaya Saude,ashe za ku dawo ƙasar "ta faɗa da muryar kuka Murmushi Hajiya Saudat ta yi,itama ta yi kewar ƙanwar tata sosai,ta ce"muna ƙasar,jiya muka sauka, lafiya dai ko?" Kamar wadda take jiran wannan tambayar sai ta fashe da kuka sosai, Hajiya Saudat ta yi murmushi tana lumshe idanu ta buɗe,ta ce"Zainab ba za ki girma ba dai da alamu Menene dalilin kukan kuma? haba autar Hajiya"Ummeey ta goge hawayenta ta ce"zan zo yaya,zan zo yanzu,kina gida ko? babu inda za ki je ko?" Hajiya Saudat ta ce"eh ina gida auta! Ai ko zan fita in dai kika ce za ki zo zan tabbata na haƙura da fitar ko don faranta ran autar Hajiya,sai kin zo"Hajiya Ummeey bata sake magana ba ta kashe wayar Daga nan kai tsaye Alhaji Yusuf ta kira, ta sanar masa da fitar ta zuwa gidan Hajiya Saudat, Alhaji Yusuf ya ce"Masha Allah! Ki ce ta dawo ƙasar kenan?" Ummeey ta ce"eh,ta ce jiya suka dawo "Alhaji Yusuf ya ce"to babu matsala,a ce ina miƙa sakon gaisuwa,sai mun zo"Hajiya Ummeey ta yi murmushi sannan ta kashe wayar A ƙasa da awa guda Hajiya Ummeey ta fito cikin shirinta na doguwar rigar lace,ta ɗora babban mayafinta yadda ya zama ɗabi'arta,ta faɗa mota,driver ya ja ta sai gidan Hajiya Saudat Hajiya Saudat ita ce ƴar'uwa ɗaya tilo ta Hajiya Zainab,wato Ummeey,su biyu kawai iyayensu suka haifa,sai da aka aurar da Hajiya Saudat sannan aka haifi Hajiya Zainab,tsakanin Hajiya Zainab da babban ɗan Hajiya Saudat wato Ishaq wata uku ne kawai,sai dai suna da shekaru biyu da haihuwa Allah ya yi masa rasuwa sakamakon ciwon ƙyanda Bayan shi Hajiya Saudat ta haifi yara uku amma duka ba su zo da rai ba,daga baya ma haihuwar ta tsaya gaba ɗaya Shekarar Zainab biyar Allah ya yi wa iyayen nasu rasuwa sakamakon haɗarin mota,a hanyar su ta dawowa daga tushensu,garin Duwala na ƙasar Kamaru,itama Zainab da suke tare a wannan lokaci ya ji ciwo sosai,amma da yake da sauran shan ruwanta a gaba sai ta samu lafiya Saude ta yi kuka sosai saboda rashin iyayenta,daga baya ta dangana, musamman da mijinta yake ba ta baki, ya nuna mata yanzu ba lokacin kuka bane, tunda Allah bai azurta su da nasu ɗan ba sai su rungumi Zainab,hakan kuwa aka yi Duk wani gata da soyayya babu wanda Zainab bata gani a wajen iyayen riƙonta ba,har ta kai shekaru goma sha biyar,inda suka aurar da ita ga Yusuf Maliya Yusuf matashin saurayi ne da karatun allo ya kawo shi Kano, yaro ne mai sauƙin kai da girmama manya,mai zafin nema da dogaro da Kai Ya kula da zainab sosai,sai dai itama shekaru sun ja har goma Allah bai ba suhaihuwa ba Hakan ya sa ya auri matarsa ta biyu wato Atika,itama kamar Zainab babu wani batun haihuwa,hakan ya sa ya haƙura ya cigaba da kula da matansa Duk da rikici da Atika ta so tayarwa bayan auren nasu sam bata samu fuska a wajen Yusuf ba, saboda mutum ne shi mai zafi,kuma baya taɓa ɗaukar raini Cikin hukuncin Allah lokaci ɗaya Zainab ta fara laulayi,sai ga ciki, Yusuf ya yi farin ciki irin wanda bai taɓa yi ba,hakan ya sa ya ƙara ba wa Zainab wata kulawa ta musamman Gashi kuma a lokacin harkokin kasuwanci suka buɗe masa sosai,kamar wanda ake jiran ɓullar ciki a jikin Zainab,haka ya yi ta kashe kuɗi wajen siyan kayan jarirai da sauran abubuwan buƙata kamar ba nemansu yake yi ba Hakan ya sake rura wutar rikici a cikin gidan,sai dai kuma shi Yusuf tsayayye ne,ba ya ɗaukar raini sam, dalilin haka Atika ta saurara Bayan Allah ya sauki Zainab lafiya ta samu ƴa mace,ya je garinsu ya ɗauko mahaifiyarsa da ƙannensa,har da bazawara da auren ya mutu,wato Sa'adatu Ƙaton gida ya gina, don lokacin daidai gwargwado akwai wadata sosai,kowa ya yi masa nashi ɓangaren,har jaririya wadda ta ci sunan mahaifiyar Zainab wato FATIMA ake kiranta da SHAHEEDA sai da aka yi mata nata sashen A lokacin ƙannensa maza, Rufa'i, Habib da Aliyu kowa ya yi aure ya ajiye iyali,shi Aliyu ma bai juma da yin nashi auren ba Zuwan innayyo, mahaifiyar Yusuf gidan ya sake tayar da sabon rikici,ba takaicin sunan da aka sakawa jikar tata ta wajen babban ɗanta,ba sunanta bane,don haka ta shiga tsakanin matan Yusuf don ta gwara kansu Sai dai ba ta samu damar hakan daga wajen Zainab ba,hakan ya sa ta koma suka haɗe da Atika, wadda ta fuskanci bayan kishin da take yi da Zainab har da hassada Cikin lokaci kaɗan arziƙi ya sake nunka na baya,an yi auren Salma autar innayyo,ta auri wani abokin Yusuf, itama Sa'adatu ta koma ɗakinta,inda Yusuf ya zama gatanta ya ba ta jari mai tsoka ya ba wa mijinta,a lokacin Shaheeda tana da shekaru biyu da haihuwa A lokacin ne Yusuf ya sake samun faraga ya buɗe kamfanoni har uku a kusan lokaci ɗaya, wadanda shahararsu a ɗan ƙaramin lokaci ya bayar da mamaki,hakan ya sa ya ƙara faɗaɗa kasuwancin sa,har ƙasashen waje yana fita don Kasuwancinsa A lokacin ne ya ƙara auren matarshi ta uku, Ruƙayya,an yi tashin hankali sosai,don Ruƙayya ƙanwar ƙawar Sa'adatu ce,asalima ita ta haɗa auren,kuma kai tsaye innayyo ta goyi bayan hakan,a dalilin wannan auren har saki ɗaya sai da aka yi wa Atika, saboda kalamai na rashin ɗa'a da ta rinƙa jifan innayyo da su,ya taka mata birki ta ƙi ta ji Ita dai Zainab ta zama ƴar kallo,bata tankawa,ko wani abu aka yi mata wanda ya dame ta tana zuwa ta samu yayarta Saude ta bata ta shawara,ita kuma ta kan ba ta haƙuri ta bata shawara A haka aka yi auren,tun sanda aka yi auren Ruƙayya ta so zuwa da fitina,sai dai laulayin da ya riske su kusan lokaci guda ne ya sa kowacce ta kama kanta Kusan lokaci ɗaya suka haihu da Atika,ita Atika ta haifi namiji,ita kuma Ruƙayya ta haifi mace Hakan ya saka Atika alfahari ganin ita ce ta haifi ɗa na namiji,duk da farin cikin haihuwar da Ruƙayya ta yi amma tana jin zafin wannan fifikon,amma sai ta saka a ranta ai yanzu aka fara Ranar suna namijin aka saka masa Safwan,macen kuma aka saka mata sunan Ummeey,wato Zainab Hakan ya sake tayar da bala'i na gaske,don Atika ta ce babu wata kishiya da ta isa ta haifa mata ya,har a saka sunanta,itama innayyo sai zuga ta take yi, saboda ta ga rashin dacewar saka sunanta Wannan issue akan yarinyar nan har yaji sai da Ruƙayya ta yi ta bar yarinyar a gidan ta tafi gidansu,amma Alhaji Yusuf ya ɗauki yarinyar ya danƙawa Zainab,ya ce ita kuma kar ta dawo,babu inda zai je Ko da ta dawo sai ta zo tare da yan'uwanta,babu kalar rashin mutunci da cin mutunci da ba su yiwa Zainab ba,amma bata ko kula su ba,sai dai ta ba su jaririyar Hakan ya sa Ruƙayya ta haƙura,aka cigaba da kiran ƴarinyar da Iman Wata sabuwa!duk da haihuwar da matan suka yi a kusan lokaci ɗaya hakan bai saka ya iya haɗa soyayyar Shaheeda da ta kowanne yaro ba,hakan ya tayar da rikici, musamman ma da matan gidan suka ƙara hayayyafa,amma ita Ummeey ko ɓatan wata bata sake yi ba tun bayan haihuwar Shaheeda Hakan yana damunta,amma ta miƙa lamarinta ga Allah,ta rungumi ƴarta tilo ta cigaba da kulawa da ita Shaheeda tana da shekaru bakwai yaya Saude, wadda ake kira da Hajiya Saudat a yanzu ta koma Egypt da zama, saboda wani ɗan ƙanin mijinta da ta riƙe, ya yi mata komai,ya mayar da ita uwa, kasancewar ya rasa iyayensa tun yana ƙarami Ba su cika gaisawa ba sosai, saboda a can baya babu waya sosai,sai dai bayan wasu shekaru masu yawa sun dawo, inda suka samu mummunan labarin abin da ya faru da Shaheeda, yanzu haka ma ba'a san inda take ba,yaya Saude ta yi kuka sosai,ta ci burin ina ma ana dawo da hannun agogo baya?da ta dawo da baya ta dawo a ƙasar don ta ɗauki Shaheeda, wadda har zuwa yanzu kukan da ta fita tana yi ya kasa barin tunanin mahaifiyarta To daga lokacin da Hajiya Saudat ta sake komawa Egypt bata sake waiwayar Nigeria ba sai yanzu, wannan kenan ✨💫 A daidai katafaren gidan da Alhaji Abubakar, ɗan rikon Hajiya Saudat ya gina mata Hajiya Zainab ta yi parking, ba tare da ta iya jiran mai gadi ya buɗe gate ba,ta ƙwanƙwasa ƙofa,yana buɗewa bata tsaya amsa gaisuwarshi ba ta wuce cikin gidan A ƙaton luxury parlourn ta iske dattijuwar tana shan kayan marmarin da mai aikinta ta yi mata blending,tana shiga bata yi wata-wata ba ta faɗa jikinta ta fashe da kuka Ɗan murmushi Hajiya Saudat ta yi,ta ɗago ta tana faɗin "za ki ƙarasa jikin tsufa autar Hajiya,zauna mu yi magana, wannan kukan ba shi da amfani,ya kamata ki san zuwa yanzu kin girmi kukan banza Zainab" #Nusy_bee Page 9 Hajiya Zainab ta gyara zamanta tana goge hawayenta, cikin karyewar murya ta ce"na rasa yadda zan yi miki bayani ne yaya Saude Abubuwan sai sake lalace min suke yi,ina kewar ƴata, aƙalla ko da a ce ina jin motsin ta zan ji sanyi A silar wannan abu da ya faru har yanzu ina fuskantar dariya da izgilanci da gori daga wajen kishiyoyi har ma da ƴaƴansu,ga ki ba kya nan yaya Saude,ina cikin wani hali"ta ƙarashe hawaye yana zubo mata sosai Abin ya taɓa Hajiya Saudat sosai,amma sai ta yi murmushi cikin dattako,ta kama hannunta ta miƙar da ita tsaye,kai tsaye suka nufi dinning area, Hajiya Saudat da kanta ta zuba mata abinci,dama ta saka an dafa abin da ta san ta fi so,sakwara da miyar egusi,ta tura mata gabanta tana faɗin "bismillah auta ta!" Kallon abincin Hajiya Zainab ta yi,tana shirin yin magana Hajiya Saudat ta ce"kin san bana san musu,na ce ki ci"bata sake yunkurin musantawa ba ta fara tura abincin da ƙyar,Hajiya Saudat ta fara ba ta labarin irin yadda ta yi rayuwa cikin farin ciki a Cairo Tuni ƙunci ya fara kwaranyewa daga zuciyar Hajiya Zainab,tana murmushi ta ce"ki ce daɗinki kawai kike sha Hajiya Gaba ɗaya kika manta da mu,kika bar mu da kujiba-kujiba"Hajiya Saudat tana murmushi ta ce"bari kawai auta,ai da an fita da Ni na zaga ƙasar zan fara tuna auta,sai na ji kamar na ce a zo a ɗauko min ke mu huta tare,mu ga gari,gari ya ganmu,abun sai wanda ya gani kawai" Murmushi Hajiya Zainab ta yi tana faɗin "gaskiya dai sai wanda ya gani Hajiya Lallai kin more,har wani jaja-jaja kika yi fa" Hajiya Saudat ta yi ƴar dariya ta ce"ke ma dai gashi nan ai,ba ki yi duhu ba,sai wani ƙara murjewa da kika yi kika yi kyau,da alamu dai Yusufa yana kula da autar Hajiya" Zainab ta yi yar dariya kawai,amma kallo ɗaya Hajiya Saudat ta yi mata ta gane dariyar ta yaƙe ce,sai dai ba ta tanka mata ba,suka cigaba da cin abincin tana ta tsokanarta Bayan sun kammala sai da suka yi sallar azahar da lokacinta ya yi, sannan Hajiya Saudat ta ja hannun Hajiya Zainab zuwa ɗakinta Zaunar da ita ta yi, sannan cikin kwantar da murya ta ce"Zainab! fuskance ni mu yi magana!! Haba Zainab! menene dalilin da ya sa a yanzu za ki nuna raki bayan hakan ba ɗabi'arki ba ce? Menene dalilin da ya sa za ki nuna rauni alhali ke ɗin ba mai rauni ba ce? Ganin hawaye a idanunki a yanzu a dalilin ƙaddarar da ta samu yarki ya sa jikina ya yi sanyi, nake jin kamar ba gaza akanki,kamar akwai abin da ban sauke ba,haka ne ko?" Kuka ya ƙwacewa Zainab,tana kukan ta ce"yaya Saude na kasa jurewa ne,ƴata ta ɓata,a yanzu tausayawa nake buƙata, sannan kuma......" "Kin iya addu'a? Kin dogara da Allah? Kin tabbatar shi zai iya yi Miki komai? Kin nemi ɗauki daga gare shi? To ki koma ki jira sakamako, Allah baya taɓa bai wa bawansa wanda ya dogara da shi kunya Ki zamo baiwar da ta dogara ga Allah,kuma ta tabbatar Allah zai yi mata komai,wallahil azeem babu wani bawa a duniya da zai iya yin galaba akanki ko da da magana ne Addu'ar uwa akan ɗanta karɓaɓɓiya ce,koma ga Allah,dage da addu'a,ki yi ta gayawa Ubangiji,da izninsa za ku ga kyakykyawan sakamako mafi alkhairi da amfani,wani kuka da damuwa da saka takaici a rai duk ba naki bane Zainab" Cikin rawar murya ta ce"amma Hajiya yadda suke nuna min fifikon ya'ya yana matuƙar damu na, kiri-kiri suke nuna min cewa ƴaƴansu ne,kuma tawa ƴar rashin tarbiyya ta yi aka kore ta, Sannan kuma ina yi musu hassada akan nasu yaran " Ƴar dariya Hajiya Saudat ta yi ta ce"to sai me? Ke dai har gobe ban ce ki cire hannu akan yaran ba, saboda ubansu bai taɓa nuna cewa ba naki bane, sannan a matsayin ki na babba dole sai kin ji kin kawar da kai,babu wanda ya rubuta ƙaddarar da zata same shi Sannan batun rashin tarbiyya kuma su ma sun san ƙarya suke yi,kamar yadda ba ki da iko akan halayya da ɗabiun Shaheeda su ma ba su da iko akan halaye da ɗabi'un yaransu Babu ruwanki da abin da aka ce, abin da za'a ce ko ake cewa,ki mayar da hankali akan me Allah zai ce? Allah ya yarda da hakan?wanne sakamakon zan samu a wajen Allah? Kina rayuwa da mijinki lafiya ƙalau, don Allah ki yi haƙuri ki cigaba da yi masa biyayya, Allah ya tsare Shaheeda ya dawo da ita cikin aminci "a raunane Hajiya Zainab ta ce"Ameen Hajiya A nan Hajiya Zainab ta kai yamma, kafin ta yiwa Hajiya Saudat sallama ta tafi gida, Hajiya Saudat ta rako ta tana cigaba da ba ta shawara, Kafin ta shiga mota *IBIZA,BALEARIC ISLAND,SPAIN* *PACHA IBIZA CLUB* Kamar yadda ta saba a kowane lokaci dogon wando ne baƙi a jikinta, sai dai rigar yau T-shirt ce fara,kan nan nata babu ɗankwali,sai p-cap ɗin da ta ɗora kalar rigar jikinta white Gabanta ƙatuwar tukunyar shisha ce ,irin wadda ta saba amfani da ita lokaci lokaci,tana ɗan jan hayaƙin shishar tana lumshe idanu tana buɗewa A hankali ta ɗaga kai tana ƙarewa mutanen da suke cikin club ɗin kallo, musamman matan da suke kan dandali suna taka rawa a waƙar Despacito ta su Justin Bieber,a hankali ta mayar da kai ta kwantar a kan kujerar da take zaune tana lumshe idanunta "Hi HERMOSA!"da a hankali ta buɗe idanunta da ya canja kala saboda hayaƙin shishar da ta bankawa cikinta,ta zuba su akan matashin baturen da yake tsaye akanta yana kallonta da murmushi a fuskarsa "Leonardo! welcome!!"ta faɗa tana gyara zama Waje ya samu ya zauna,ta miƙa masa hannu Kamar wanda za su gaisa,sai ya sa mata takarda a hannunta, sannan ya yi mata inkiya da idanu, ba tare da ta yi magana ba ta jinjina kai Sannan ta mayar da kanta ta kwantar a jikin kujerar da take zaune Duk abin da yake faruwa yana daga can gefe yana kallonsu,ya tabbatar akwai abin da suke shiryawa a nan ɗin,don haka sai ya zuba mata idanu ya ga gudun ruwanta Ba ta juma a wajen ba ta miƙe don tafiya,shima sai ya fara yunƙurin miƙewa don barin wajen,dama gaba ɗaya ya takura da hayaƙin taba da na shisha, ga warin giya Tana daf da shiga mota ta ji ya ce"hi!" Juyawa ta yi tana kallonshi,ya yi kyau sosai a cikin wasu designer t-shirt da wando, waɗanda suka amshi farar fatarshi,yana murmushi cikin harshen Hausa ya ce"Barka da wannan lokaci babbar yarinya" "Wanene kai?"ta jefa masa tambayar tana kallon cikin idanunshi Murmushi ya yi yana ɗan buɗe idanunsa,ya ce"Nima ɗan Nigeria ne kawai, I'm very happy da na haɗu da ƴar ƙasarmu a wata ƙasar, that's why Babe" "Wanene ya ce maka ni yar Nigeria ce?"ta jefa masa tambayar tana kallon cikin idanunshi Kai tsaye ya amsa mata da faɗin "haba Madam! Duk inda na ga ɗan'uwa ai zan gane shi Yanzu dai kaya nake buƙata,kuma ina da tabbacin zan samu a wajenki,ya za'a yi?" Kallonsa ta tsaya yi kamar mai nazari ,ya yi ɗan murmushi ya ce"kar ki damu babu mai jin me muke cewa,nan a Spain muke,ba Nigeria ba Still shiru har zuwa yanzu bata da niyyar magana,ya yi murmushi sosai ya ce"ba ki yarda ba? I'm MUBARAK!and you?"ya miƙa mata hannu don su gaisa Daga inda yake yana iya kallon yadda ta razana da jin sunan,duk da kallon tsanaki da take bin shi da shi, wanda yake da tabbacin akwai abin da take son ganowa Ɗan murmushin da yake yi ne ya sa ta ɗaure fuska ta ce"ka san ina siyar da kaya?amma ba ka san sunana ba?" "Simple thing madam! Na ga yadda kike naki business ɗin,kuma da yake mun saba da ƴan harƙalla a duk inda muka gansu muna gane su,ni dai sunana Mubarak,ke fa?" Kawar da kai ta yi ta ce"tunda ka san aikina sai ka nemi sunan,na san za ka samu"daga nan ta haye kan bike ɗinta ta tayar,a ƴan mintuna ta bula masa ƙura ta bar wajen Bin ta ya yi da kallo yana murmushi, kafin ya zaro wayarsa ya kira Awwal da suka zo ƙasar tare Mintuna kaɗan ya fara magana"Awwal!gata nan mun haɗu,mun yi magana,kuma da alamu ma ba zata yi turjiya mai yawa ba za mu samo kanta,be ready, kowanne lokaci daga yanzu zata iya shiga hannu"Awwal ya sara masa a cikin wayar ya ce"best of luck Sir" Bayan barazanar da ta yi masa na ƙwace wayar drivern Amna Haisam ya sauya taku na bincike akan ta,da kanshi, ba tare da sanin ƴan team ɗin nashi ba ya gano cewa tana shirin barin ƙasa zuwa Spain,sam bata san jirgi ɗaya suka hau da shi ba Sai dai shi a maimakon Ibiza kai tsaye Barcelona ya nufa,ya cigaba da bincike a sirrance ta hanyar wasu yaran Roxy ɗin da ya ba su wasu kuɗaɗe Tsawon kwanaki shida ya ɗauka yana tattara bayanai akan Roxy,sai dai har zuwa yanzu bai samu cikakken tabbacin daga inda Roxy ta fito ba,ya dai samu sunanta,da kuma tabbacin ita ɗin ƴar Nigeria ce Ya samu nasarar bincikar inda ya sauka a Ibiza,ya cigaba da bibiyarta,ta yi harƙalla da su Alejandro,asalima abin da ya kawo ta Spain kenan,inda ta damƙa kayan maye danginsu cocain waɗanda darajar su zata kai ta dala miliyan biyu a hannunsu Ya kwashi wasu kwanaki yana bibiyarta,har sai da ɗaya daga cikin yaranta, wadanda suke yi masa aiki a sirrance suka sanar masa kwanaki uku ya rage mata a Spain sannan ya tunkare ta bayan fitowarta daga Pacha Ibiza club Wannan kenan! 💫 Washe gari tun da safe Haisam yake ta cuku-cukun yadda zai yi ya samu kan Roxy, wadda zuwa yanzu ya san sunanta,sai dai ba shi da guarantee akan komai da ya sani daga gare ta,kuma yana fatan bata san shi ba, ballantana hakan ya ba shi matsala,don ya tabbatar sai ya kama ta da ikon Allah Da yamma ya gama shirinsa tsaf, yana jiran dare don tafiya club ɗin da suka haɗu da Roxy,ko a cikin boat ɗin da ya tsallakar da shi zuwa Balearic Island bincike da nazari yake yi, don ya san wacece wannan yarinyar wajen kaifin basira da iya taku, shekaru biyu ta ɗauka tana jijjiga hukumar tsaro,babu yadda za'a yi mutum mara basira da fikira ya iya yin hakan saboda ƙwarewa da sanin makamar aiki ta jami'an tsaron Nigeria A inda ya saba gano ta ya ganta,tana zaune tana busa hayaƙinta na shisha kamar yadda ya saba, gefenta yaronta David ne,sai Oga boss,sai ƴarinyarta Hanna da suke ta yin hira suna shewa,amma ita hankalinta yana kan shishar da take zuƙa,sai wayar da take dannawa lokaci lokaci Kai tsaye wajenta ya nufa yana faɗin "hi! Hermosa!" Dukkansu ɗagowa suka yi suna kallonsa kusan a tare,ban da ita,da ta ɗago daga baya hankalinta a kwance,ya yi murmushi yana faɗin "Barka! Sorry za ki ga ina yi miki magana da Hausa,na fi son na rinƙa jin daɗin mu'amala da ɗan ƙasarmu da yaren ƙasarmu" David da yake bin shi da kallon raini ya ce"wanene kai?" Kai tsaye Haisam ya ce"ka bari mu gana da uwar ɗakinka,ku ba mu waje" Kusan a tare suka kalli Roxy wadda ta ja hayaƙin shisha ta fesa shi a fuskar Haisam da take kalla kai tsaye, kafin ta ce "Ku ba mu waje,mu ji da me ya zo"babu musu suka miƙe suka bar wajen,shi kuma ya samu waje ya zauna yana fuskantar ta "Beunas tardes!"(Good evening in Spanish) Kallonshi ta yi, kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta yi murmushi ta ce "ka gaji da yin yaren naka ne?sai ka ari na wani?" Ɗan murmushi ya yi shima,ya ce"kin san bahaushe ya ce idan mutum ya je gari ya ga kowa da jela,shima sai ya samu ɗan zirin tsumma ya ɗaura"ta jinjina kai tana faɗin"kenan kai ma ɗaurawa ka yi dai ko?" Ya ɗan jinjina kai ya ce"kusan haka" Ta ce"well! Lafiya dai ko? menene dalilin da ya sa kake bi na?" Kai tsaye ya ce"kasuwanci nake so mu yi,ina son na shigar da kaya zuwa Nigeria amma na gagara, saboda wahalar da hakan yake ba ni Shine na zo na nemi alfarmar hakan daga gare ki,idan ma kina da wani connection ɗin ko dabarar hakan I'm ready ki ba ni,don bana jin daɗin yadda ake kama min kaya,gashi kuɗaɗe da yawa nake asara" #Nusy_bee Page 10 Da kallo ta bi shi har ya gama jawabinsa ba tare da ta ce uffan ba,sai hayaƙin shishar da take cigaba da zuƙa tana fesarwa,sun kwashi kusan mintuna biyu cikakku a haka,bata yi magana ba,ta zuba masa idanu kawai tana cigaba da shan hayaƙinta,shi kuma ya yi shiru yana jiran amsarta Zuwa can ta dube shi,kallon ƙasan idanu,ta ce"menene dalilin da ya sa ka fara business ba tare da kana da dabarun yin hakan ba?" Murmushi ya yi yana gyara zama,ya ce"ai da ni da ke bambancin ya kai tsawon sama da ƙasa ranki ya daɗe Ku ne manyan yan kasuwa,ku ne iyayen gidanmu a wannan harkar,why not ki yi min jagora,i bet za ki iya tsallakar min da kaya na" Ɗauke kai ta yi daga kallonsa tana jinjina kai,a hankali ta ce"yaushe ka shirya fita da kayan?" Kamar mai jira ya ba ta amsa a ɗokance"duk lokacin da kika tsara, yanzu feedback daga gare ki nake jira,ki gaya min maximum abin da za ki ɗaukar min da abin da zan biya" Miƙewa ta yi ba tare da ta kalle shi ba ta ce"mu yi magana next time, David zai karɓi phone number ɗinka,za ku yi magana da shi,akwai gidana na sirri da nake ganawa da baƙi, za'a kawo ka zuwa gobe, because I'm leaving this country in less than 48 hours " Murmushin fuskarsa ya faɗaɗa,ya ce"alright, thanks very much ma!"bata kula shi ba,ta yi hanyar ficewa daga club ɗin,ya bi ta da kallo yana murmushi, kafin ya fito da wayarsa David ne ya ƙaraso inda yake, ba tare da ya yi masa magana ba ya miƙa masa hannu yana galla masa harara, Haisam ya miƙa masa complementary card ɗinsa ba tare da ya kalle shi ba, sannan ya miƙe ya nufi hanyar fita daga club ɗin Washe gari tun da sassafe yake dakon kiran wayar Roxy,amma shiru babu wanda ya kira shi,har wajen sha ɗaya na safe,a lokacin ya gama magana da su Awwal,sun yi shiri cif Sai wajen ƙarfe biyu wayarshi ta yi ƙara,ya ɗaga yana duban wayar, unknown number ya gani,ba tare da damuwa ba ya ɗaga wayar David ne a daƙile ya ce"kana ina ne?" Kallon restaurant ɗin da yake ya yi,ya ce"ina wani restaurant ne" "Ya sunan restaurant ɗin?"Haisam ya gaya masa David ya ce "okay to yanzu ka fito zuwa bakin titi,ka bi hannunka na dama bayan ka tsallaka titi,ka yi doguwar tafiya,za ka same mu,sai mu karasa wajenta " "Okay babu damuwa "ya faɗa yana miƙewa don ficewa daga wajen Yana fita,ta cikin earbuds da suke kunnensa, ƙasa ƙasa ya furta"get ready Men!"suka amsa kusan a tare "yes sir!" Kamar yadda David ya gaya masa,babu ɓata lokaci ya bi hanyar da ya kwatanta masa ba tare da tunanin komai ba,yana tafiya yana bin hanyar da kallo,don babu mutane Daga can nesa ya hango David yana ɗaga masa hannu,kai tsaye ya miƙe don isa gare shi,amma me? Kafin ya ƙarasa wani mutum da fuskarsa take a rufe ya dira a gabansa,kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya hura masa wata powder a fuskarsa,babu ɓata lokaci ya sulale a wajen cikin fitar hayyaci, wanda shi kansa ba zai ce ga halin da ya shiga ba Ba zai iya tuna lokacin da ya ɗauka a wannan halin ba, kafin Allah ya nufe shi da farfaɗowa,sai dai tun kafin ya gama wartsakewa ya ji shi a ɗaure gam gam, yadda numfashi ma sai da ƙyar yake iya yi Dishi-dishi ya fara ganin mutane akansa,a hankali kuma ganinsa ya dawo tar-tar,ya ƙarewa kanshi kallo,inda yake ɗaure da wata ƙatuwar igiya, kafin ya kalli inda mutane suke Su shida ne, Roxy da yaranta biyar, cikin su har da David da Hanna,sai kuma waɗanda ya biya kuɗi don su fallasa masa sirrin Roxy Tasowa ta yi tana taku ɗaiɗai,tana murmushi,ta ƙaraso gabanshi ta durƙusa kusa da kanshi tana kallonsa tana sake waro kyawawan idanunta "Hi! Barka!! Sunana Roxy,shahararriyar ƴar safarar miyagun ƙwayoyi daga ƙasa zuwa ƙasa, sannan kuma babbar ƴar yahoo, wadda jami'an tsaro suke nemanta ruwa a jallo Yau dai gata ga jami'in tsaro, jami'in DSS"ta juya tana kallon su David tana murmushi,ya sunan nashi ma?"suka kusa haɗa baki"CSO Haisam Abdulmalik Madaka!"suka kwashe da dariya Haisam dai yana kwance a ɗaɗɗaure yana kallonsu,gaba ɗaya ji yake yi ya muzanta,don tun daga yanzu ya fara ƙyanƙyaso cewa matar nan ta raina masa hankali ne,bai gama tunani ba ta cigaba da magana bayan ta miƙe tsaye tana aika masa wani irin kallo "Na san jami'an tsaro suna nemana sama da shekaru,a tunaninka ni wawiya ce zan zuba idanu ina zuƙar shisha da fasa accounts ɗin mutane ina shagali?then you are mistaken dude!! Yadda kuke bibiya ta haka nake bibiyarku. Tun lokacin da ka amshi wannan case ɗin,ka ce a ba ka wata guda don ka kama ni nake bibiyarka,gashi watan yana so ya ƙare,amma har yanzu babu labarin kama ni, infact,don ma na sa ka ji ka kusa cimma burinka ya sa na haɗa maka wannan trap ɗin Na san kana cikin jirgin da na biyo zuwa Spain,amma da muka sauka a Barcelona kai sai ba ka biyo ni Ibiza ba, kafin ka ƙaraso izuwa Pacha Ibiza club ranar farko akwai yarana da suke kular min da shige da ficenka sun sanar da ni, lokacin da ka zo,muka haɗu a farko na saka an sake yi min bincike akanka,har yaran da ka zo da su, Finally, lokacin da kake waya kana communicating da naka yaran na yi hacking wayar, na ji komai,don haka na bari ka gama shirinka, sannan nima na zo da nawa shirin, wanda ya fi naka Yarana da suka ba ka hint akaina don ka kama ni ni na ba su umarnin su yi hakan,don ka haƙa ramin da zan jefa ka da kanka,kuma gashi a ƙarshe na yi nasara I repeated proudly N- O- C-C-M!!! Ka je ka cigaba da bincike akan waɗannan letters ɗin da ka fara before,ina ga da ka gano ma'anarsu da ba ka sake attempting shiga gona ta ba, David,yi masa allurar nan"babu ɓata lokaci David ya yi masa allurar,a take kuma jikinsa ya saki,wani bacci mai nauyi ya yi awon gaba da shi A ranar Roxy ta bar Spain zuwa Mexico,inda ta gama shirin sake order na wasu kayan,daga nan zata sake komawa Nigeria don ta rabawa distributors dinta Har ta bar Spain ranta yana a ɓace saboda ji kimarta da take jin Haisam ya taɓa,ta yi wasa da manyansa,shi wanene da yake jin zai iya biyo ta har inda take ya ce wai zai kama ta,ta ja tsaki ya fi sau a ƙirga *HAISAM* Yana zaune a garden ɗin da yake kusa da masaukinsu ya yi shiru yana kallon waje ɗaya,amma da alamu hankalinsa ba ya kan inda yake kalla, tunani yake akan wulaƙanci da tozarcin da Roxy ta yi masa,wanda tun da ya zo duniya ba'a taɓa yi masa makamancin irin wannan cin mutuncin ba Bayan Roxy ta gama yi masa bayanin da ya zauna masa akai,don tabbas zai yi amfani da su ya karya alkadarinta,ta sanya aka yi masa allura,ta saka aka cire masa kaya aka bar shi daga shi sai shortneakers,ko arzikin singlet babu, sannan aka kawo shi gefen gari aka ajiye shi cikin dare Sai da ya samu ya koma masaukinsa,ya sake lalubensu Awwal,Awwal ya shaida masa cewa lokacin da suke cikin magana da shi,ba su san abin da ya faru ba suka ji network ɗinsa ya katse, ƙarshe sun yi laluben duniya ba su same shi ba Tunda yake a wajen aiki ba'a taɓa yi masa illa an lalata masa aiki irin wannan karon ba,sai yanzu ya gane dalilin da ya sa Roxy take ba wa jami'an tsaro wahala, tamkar wadda aka yiwa training,tana aiki da lissafi sosai Amma kuma wannan abu da ta yi masa shine ya sa yake jin dole ma ya kai ta ƙasa ko ta wanne hali,zai san yadda zai yi da ita Miƙewa ya yi ya fice daga garden ɗin,a ranshi yana raya ta hanyar da zai bi ya rusa wannan yarinyar da ya kira annoba Da yamma ya kammala komai da shi da team ɗinshi,suka bar Spain zuwa Nigeria *KANO* "Arfa!ba Ni wayata!" "Wacece wannan da kake kallon hotonta? Malam ka gaya min ko ka ga bala'i a gidan nan wallahi!" "Arfa na ce ki bani wayata ko?"ya faɗa cikin ɗaga murya "Wacece wannan da kullum kake kallon hotonta? To wallahi ba zan bayar da wayar nan ba sai ka gaya min wacece! Okay!na gane!wato yanzu hotonta kake kalla ko?wato ina murnar na rabu da ƙaddara amma ashe tana liƙe da ni ko?ko tsine maka aka yi ne da har yanzu Kai kake sonta bayan kowa ya kama kanshi kanta?" "Oh seriously!ashe dai kin san wacece kike wahalar da kanki wajen tambaya?ba ni wayata dalla malama!" A maimakon ta ba shi wayar sai ta buga ta da ƙasa,sakin baki ya yi yana kallonta cikin mamaki da takaici,ta yi ta buga wayar da ƙasa har ta yi kwatsa-kwatsa da ita, sannan ta ɗaga jajayen idanunta ta ce"Muyassar! Na fi ƙarfin ka ci amanata saboda kilaki,ragowar arne!!!" Da wani irin ɓacin rai da hargowa ya ce"Arfa! Watch your tongue!ina yi miki gargaɗi da babbar murya kar na sake jin kin kira ta da kilaki,akwai kilaki da ta wuce ki ne? wadda ta gama tambaɗewa kafin a cuce ni a liƙa min?" "Muyassar!na za ka yiwa ƙazafi?don na kama ka kana kallon hotunan kilaki shine za kayi min ƙazafi!tsawon shekarun da muka ɗauka da kai baka taɓa tunanin ka yi min ƙazafi ba sai yanzu? Innalillahi wa inna ilayhi rajiun!! Allah ya yi min sakayya da kai,wa ya sani ma ko kaine ka fara nuna mata hanyar lalacewar shiyasa za ka......." "Arfa!"ya daka mata tsawar da ta kaɗa ƴan hanjinta,yana huci cikin tsananin ɓacin rai ya ce"do your worst Arfa,ki yi duk abin da ya zo ranki, lokacin ki ne,amma kar ki sake kiran Shaheeda da karuwa,ba ki sani ba,bari na sake nanata miki,I LOVE HER!I LOVE HER MORE THAN HOW I LOVE MYSELF! Kar ki sake haɗa wata ke da Shaheeda, Shaheeda ba sa'arki ba ce!!! Ki yi duk abin da za ki yi, lokacinki ne,amma idan kika sake aibata ta komai zai iya faruwa, ciki kuwa har da tafiyarki gidanku, diot!!!"yana gama magana ya ja tsaki ya juya ya fice daga ɗakin cikin tsananin ɓacin rai,yana jin zuciyarsa tana tafasa,ya rasa wanne irin zafi yake ji,ji yake ya yiwa Arfa dukan mutuwa ma,ko zai samu ya huce wannan abin baƙin cikin da ta cusa masa Ya sani soyayyar Shaheeda wani sashe ce ta rayuwarsa,da numfashinsa take bugawa,babu yadda za'a yi daidai da second ɗaya ya iya mantawa da ita,ko ta bar tunaninsa,a kowanne hali,a kowanne lokaci da ita yake kwana yake tashi,ya sani soyayyar Shaheeda da ita zai bar duniya, kuma har zuwa yanzu ba ya jin ya karaya,yana da kyakkyawan fatan ko ba daɗe ko ba juma zai mallake ta a matsayin matarsa Ita kuwa Arfa a wajen ta zube tana wani gunjin kuka mai motsa rai,ta daɗe tana zargin Muyassar yana tare da soyayyar Shaheeda,a da gani take yi ta haye,bata tare da kowacce matsala,amma sai ta tarfa Muyassar yana bacci yana sambatun kiran sunan Fatima Shaheeda,hakan ne ya tayar mata da hankali,ta so ta tuhume shi a wancan lokacin,amma ta san wanene Muyassar, mutum ne tsayayye wanda baya son wargi,hakan ne ya sa ta kasa fito masa gaba da gaba,ta fara bincikensa ta ƙarƙashin ƙasa A yau dai ta kama shi red handed tana kallon hoton Shaheeda,hakan ya sa ta fizge wayar,har suka yi rikici ya kai su ga haka Tana kuka sosai ta miƙe ta nufi inda wayarta take,tana ɗauka kai tsaye ta kira yayarta Hajiya Ruƙayya Hajiya Ruƙayya tana ɗagawa Arfa ta fashe da kuka sosai, Hajiya Ruƙayya da take zaune tana cin abinci sai da ta kusa ƙwarewa,a ɗan firgice ta ce"Arfa lafiya dai ko? Me aka yi miki kike irin wannan kukan?" Cikin hargowar kuka ta ce"Aunty na gaji!na gaji wallahi,na kasa gane ɗabiun da abban Zuhra ya ɓullo min da su kwanannan,ashe wai har yanzu yana son wannan matsiyaciyar ƙaruwar yarinyar,don Allah Aunty ki yi wani abu akai, wallahi ina tsananin kishin miji na,ba zan iya haɗa shi da wata mace ba,don Allah Aunty na!" #Nusy_bee Page 11 Hajiya Ruƙayya da ta kusa ƙwarewa da bayanin Arfa ta yi saurin kora ruwa tana zare idanu,a ɗan firgice ta ce"ban...ban fahimta ba Arfa,ki yi min bayani yadda zan fahimta,me kike nufi da abin da kike faɗa?" Cikin kuka sosai Arfa ta ce"na gaya miki Aunty kama shi na yi yana kallon hotunanta,dama tunda muka yi auren ba wani ba ni hankalinsa yake yi ba, gaskiya Aunty da sake,ya kamata a san yadda za'a yi,don ba zan iya zama yana wulaƙanta ni akan wata kilaki ba" Hajiya Ruƙayya ta numfasa ta ce"ki kwantar da hankalinki Arfa,da kin gaya min tun farko da tuni na yi wa tufkar hanci, yanzu ma dai bata ɓaci ba,sai na yi masa abin da ba zai sake sha'awar ko da kallon wata mace ba sai ke,ko da uwarsa ce kuwa,don ba zan ɗauki wargi irin haka ba" Arfa ta ja numfashi tana faɗin "to na gode aunty,sai na ji ki"suka yi sallama, Arfa ta miƙe tana goge hawayenta *TIJUANA, MEXICO* *CLUB SAFARI* A hankali take kwantar da kanta a bayan kujerar da take zaune tana sauke numfashi a hankali bayan ta gama zuƙar hayaƙinta na shisha, David da yake tsaye a bayanta ya sunkuyar da kanshi daidai saitin nata,murya ƙasa-ƙasa yana faɗin"Ma! Are you okay?" Shiru ta yi ba tare da ta yi magana ba,ba wannan ne karo na farko da David ya ganta a wannan hali, wanda har zuwa yanzu babu wanda ya san abin da yake jefa ta cikinsa Kafin ya sake yin wani yunƙuri ta buɗe idanunta da suka sauya kala tana miƙa masa hannu,ya san me take nufi,a take ya zaro ƙwayoyin da take sha idan tana cikin wannan halin ya miƙa mata, ba tare da tunanin komai ba ta afa su gaba ɗaya,ta mayar da kanta ta kwanta tana sake lumshe idanunta "Is everything alright ma?"ya tambaya a hankali Buɗe idanunta ta yi, waɗanda suka sake birkicewa tana lumshe su,da muryar maye ta ce"I want..... let's go home.....ppplease!" Ba tare da ɓata lokaci ba ya taimaka mata ta miƙe tsaye sannan suka fice daga club ɗin,bakinsa fal tambayoyi,ya san zuwa suka yi don su gudanar da irin kasuwancin su,amma ta shiga wannan halin, wanda ta saba shiga a duk lokacin da wani ƙunci ya mamaye zuciyarta, wanda har zuwa yanzu ba su san menene silar ƙuncin ba,don ko da wasa bata taɓa faɗawa wani ba Washe gari Roxy tana tsaye a bakin window ɗin ɗakinta tana kallon shuke-shuken da suke bayan ɗakin nata, sai dai kuma hankalinta ba ya tare da ita,asalima ya luluƙa can tunanin baya 💫 "Yaya! wallahi ina sonshi!don Allah ka yi haƙuri ka ƙyale ni,idan ban aure shi ba zan iya mutuwa Yaya saboda ni ya musulunta fa!yaya kar ka yi silar da za mu yaudare shi,bana son ya kalli musulmai a matsayin mayaudara,don Allah yaya ka yi mana addu'a, please yaya na!ta ƙarashe maganar tana haɗe hannayenta alamun roƙo "A'a baby girl! don Allah kar ki yi min haka! Na fara sonki tun ba ki san kanki ba,tun kina yar jaririya, wallahi sonki zai kashe ni,zai yi min illa,don Allah!don Allah baby girl!kar ki juya min baya ki auri wani, Please!!!" "Please yaya!zuciya ta tana wajen shi,idan na aure ka ba zan so ka ba,ba zan yi maka biyayya ba,Ni tashi ce, zuciya ta tana gare shi, Please! please yaya!!" "Baby girl! Are you telling me kina son wani?da shi kadai za ki rayu?all in before my eyes?what the heck!!! Baby girl wake up!nine fa yayanki,abin alfaharinki,abin sonki,amininki tun kina ƙarama,kin manta da haka?" "I'm sorry yaya!stay in your lane,but I will never marry you, I'm not in love with you!" 💫 "Roxy are you okay?"da sauri ta juyo tana kallon Hanna da ta zuba mata idanu tana yi mata kallon tuhuma Ɗaure fuska ta yi,ta ce"kin ga wata matsala ne, I'm okay mana"ta ƙarasa faɗa tana juyawa ta koma bakin window ɗin da take tsaye "But kukan me kike yi?"Hanna ta jefa mata tambaya, Roxy ta juyo ta kalle ta tana faɗin "kuka kuma?" Hanna ta ce ga hawaye nan a idanunki,kuka kike yi mana"Roxy ta yi ɗan murmushi,ta juya ta sake fuskantar windon tana goge hawayen da ke fuskar tata, kafin ta ce"I need space,can we discuss leter?" "But Carlos yana jiranki fa Roxy! Why na?me yake faruwa ne?kina da wasu aminai bayan mu ne da ba za ki iya gaya mana matsalarki ba? Please Roxy!"juyowa ta yi tana kallonta, kafin ta ce"kina da wata alaƙa da abin da ya dame ni ne?"Hanna ta girgiza kai,kai tsaye Roxy ta ce"so ba Ni waje! Maganar Carlos kuma ki ce ya dawo anjuma,idan ya wuce anjuma kuma shi ya rasa, I'm leaving this country first to thing tomorrow morning "Hanna ta kalle ta kawai, kafin ta juya ta fice daga ɗakin don isar da saƙonta, Roxy ta faɗa kan gadonta ta lumshe idanunta,tana jin da zata yi kuka ma da ta rage raɗaɗin da yake taso mata *DSS HEADQUARTERS, KANO STATE, NIGERIA* "CSO Haisam Abdulmalik Madaka! A last meeting da muka yi da kai mun yi magana,inda ka tabbatar mana za ka iya kama yarinyar nan ka dawo da ita,ta fuskanci doka,amma abin mamaki har yanzu shiru,babu wani feedback na a zo a gani,me yake faruwa ne?" Haisam ya ɗaga kai ya kalli state director jiki a sanyaye,bai taɓa jin ya muzanta irin na yau ba,amma ɓacin rai da shan alwashin da yake ciki sun haura muzantar da yake jin ya yi A hankali ya miƙe don bayar da ba'asi "Operation ɗina ya yi failing,amma zan sake trying in sha Allah " "Amma an ce ka bi ta har ƙasar Spain inda kuka saba harka da ita,me ya faru baka kamo ta ba?" Kai tsaye ya ce"wani slide mistake ne ya faru,amma very soon zan yi fixing ɗinsa" Shiru office ɗin ya yi,sauran abokan aikin nashi suna jifansa da wani kallo,kafin state director ya cigaba da faɗin"yanzu ka yarda yarinyar tana da kaifin basira fiye da tunanin ka?" Babu ko shakka Haisam ya jinjina kai SD ya yi murmushin takaici ya ce"to yanzu za ka bar mu mu yi aikinmu ko?tunda zuwa yanzu ka gane ba gazawa muka yi ba,da kake neman nuna mana ba mu iya komai ba" Haisam ya ce "I'm sorry sir!ko a baya ma ba raina iyawarku na yi ba,kawai dai ina da ƙwaƙwƙwaran sanin cewa zan iya kama ta,kuma...." "Sai kuma gashi ta rusa kwarin naka! Ko sai na gaya maka abin da ta yi maka,kowa ya ji sannan za ka bar cika mana baki?" Shiru Haisam ya yi ba tare da ya yi magana ba, kanshi a ƙasa, SD ya ja tsaki ya ce"wannan operation ɗin ya bar hannunka,zan mayar da shi hannun wanda ya dace,kuma zai iya abin da ya dace SO Shuaibu Ahmad musawa,kai za ka yi taking over na wannan aikin"Shuaibu ya dara yana faɗin "noted sir!" A Ranar dai haka taron ya watse zuciyar Haisam sam babu daɗi,kuma kai tsaye ya nufi gida ba tare da ɓata lokaci ba Yau bai nemi Amna ba,don ya san tana makarantar islamiyya,bai nemi mamynsa ba saboda ya san bata dawo daga aiki ba,bayan ya je masallaci ya yi sallar azahar ya koma gida ya kwanta akan gadonsa,yana cigaba da danne danne a wayarshi Kira ne ya shigo,ya ɗaga wayar yana faɗin "ya dai Saleem?" A buɗe yake a gare shi cewa bayan yaran Roxy da suka raina masa hankali akwai wanda ya ci amanarshi a cikin nashi yaran,a dalilin haka ya sa ya ji sam ba zai sake yarda da su ba, gashi kuma yana zargin a cikin hukumarsu akwai masu fitar musu da sirri A dalilin haka ya saka Saleem ya yi masa bincike akan Roxy, Saleem ba jami'i bane,mutumin gari ne, ko zurfin karatu bai yi ba, iyakar shi diploma a fannin political science,amma sama ta ka Allah ya ba shi ilmin computer da na sarrafa harshe,ga wayo da hikima da dabara, Haisam ya ja shi a jiki, kasancewar shi yana da alaƙa da shi ta wajen mahaifiyarsa,ya ba shi jari, sannan idan yana son yin bincike mai wahalar irin wannan Saleem yana taimaka masa su warware shin Daga ɗaya ɓangaren Saleem ya amsa yana faɗin "Barka da warhaka Oga!ya aiki?ya fama da mu kuma?" Haisam ya ce"alhamdulillah Saleem,ya batun aikin da na saka ka?" Saleem ya ce"Oga ai na jijjiga da abin da na gano game da yarinyar nan,a kaf abubuwan da ake zargi babu wanda yake a yadda ake kallonshi" "I don't get what you are saying Saleem?"Haisam ya tambaye shi "Da farko dai,na fara bincike akan wadannan letters ɗin da take amfani da su,kuma na gano ma'anarsu" Da sauri Haisam ya ce "I'm all ears Saleem,me suke nufi?" Saleem ya cigaba"wadannan letters ɗin ba ƙungiya ba ce,kuma ba wata alama ba ce,barazana ce kawai sai kuma yin wani abu da ta san zai ɗauke hankalin mutane Yawan amfani da su da take yi ga mutum a yayin da ya shiga gonarta shi zai saka mutum ya fara zargin wani abu a ƙarƙashin waɗannan letters,bayan kuma a zahiri babu komai a ciki,ta yi amfani da su ne don ta rainawa mutane hankali A taƙaice dai NOCCM full meaning ɗin shi shine NO ONE CAN CATCH ME! Kalmomin ba na wani abu bane sai na fariya kawai, shine abin da na samu game da kalmomin NOCCM Sai kuma abubuwa da yawa da na gano,amma kafin nan ita wannan yarinyar tana da wani tarihi da yake ɗauke da wani tabo, kusan dai na ce shine silar faɗawarta halin da take ciki Sannan kuma akwai sirri sosai a tare da ita wanda na yi nasarar ganowa, shine MUBARAK! MUBARAK kuma ya kasance........" "No Saleem,na san wannan cigaba da gaya min abubuwan da ka gano"babu musu Saleem ya saki batun Mubarak ya cigaba da bayanin abubuwan da ya gano game da Roxy, wanda har ya yi bayani ya gama Haisam yana ɗan murmushi Sai da ya gama tsaf Sannan Haisam ya ce"na gode Saleem,zan kira ka leter "bai jira amsar shi ba ya kashe wayar Gyara kwanciyarshi ya yi yana murmushi sosai,a hankali ya furta"Roxy!or whatever your name is, your end has began!"ya janyo laptop ɗinsa ya buɗo wasu hotuna yana kalla yana murmushi *NNAMDI AZIKWE AIRPORT,ABUJA, NIGERIA* Miƙewa ta yi don zuwa wajen da Bolt ɗin da ta tsare yake,kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗaga suka nufi suleja A can suleja bayan ta sauka kai tsaye ta kunna kai gidan da ta nufa, Amra da ke zaune tana shan kayan mayenta,gefenta wani saurayinta ne,ta ɗago tana kallonta cikin mamaki Waje ta samu ta zauna tana kallonta, kafin ta daga gira,alamun kallon fa? Amra ta yi dariya irin tasu ta yan maye ta ce"surprise! Yaushe kika sauka a ƙasar?"Roxy ta mayar da kanta ga wayarta da take cirewa a flight mode ta ce"yanzu na sauka,ina sauka kuma na yo nan,ko gida ban je ba" "Gaskiya ne tawan! To ina su David ɗin?" Roxy ta yatsina fuska ta ce"suna can" "Yaushe za su taho?"Amra ta sake jefa mata tambaya Banza Roxy ta yi mata, saurayin Amra ya cewa Roxy "Hi beauty!" Ɗagowa ta yi ya watsa masa wani kallon wulaƙanci sannan ta cigaba da danna wayar hannunta, kafin ta ɗago ta kalli Amra ta ce"ya ne? Ina buƙatar hayaƙi fa,kin san kai kogo ne" Amma ta ce"bari na ɗauko na haɗa miki welcome"ta mike ta fice daga parlourn tana faɗin "bad boy see you letter,ka ga ina da baƙuwa"bad boy ya miƙe yana faɗin "see you letter Hajiya ta,amma wannan baƙuwar taki zazzafa ce,ina son kayan idan babu damuwa " Dakatawa Amra ta yi daga fita,ta juyo ta kalle shi tana faɗin"hattara dai! wannan kayan ya fi ƙarfinka "sannan ta fice daga parlourn Shima bad boy ficewa ya yi daga parlourn yana faɗin"see you letter!" A ɗakin Amra kuwa,da sauri ta dauki waya ta danna kira,babu jumawa ta fara magana "Hassy! Tana nan fa "daga ɗaya ɓangaren Hassy ta ce"a haba!ki ce tana nan To kwana zata yi?" Amra tana leƙe ta ce"no ban tabbatar ba dai tukunna,amma kuma na san Roxy bata da alƙibla, yanzu zata iya chanjawa ko da ta yi niyyar kwana Ita kaɗai ta zo ba tare da mutanenta ba" Hassy ta ce"daidai kenan,ki tsare mana ita,ko da a ce kin ga alamun zata gudu ki jefa mata ƙwayar nan da na ba ki a lemon ki ba ta,kin san yadda za kiyi dai,amma dai na kwaɗaitu da jikin yarinyar nan over,kuma na rantse sai na kwanta da ita,ina tsananin sonta,amma ita sai jiji da kai da wulaƙanci" #Nusy_bee Page 12 Kai tsaye Amra ta ce"noted! Me za'a biya ni?"hassy cikin zaƙuwa ta ce"5m, yanzu ma zan tura miki ita ta account ɗinki"murmushi Amra ta yi ta ce"kuma bayan nan kafin ki yi komai ni zan fara gaskiya,don na juma sosai ina kwaɗayinta tana raina min hankali,don dai ƙarya take ta ce ita ba yar bariki ba ce" Hassy ta ce shikenan babu damuwa,ga ni nan zuwa,ki tabbatar da cewa komai ya hau kan saiti kafin na ƙaraso " Amra ta jinjina kai ta ce"babu matsala uwar ɗaki" Ƙwayar maganin da suka saba sakawa mutum a drink,su bugar da shi don biyan wata buƙata tasu,ko dai su yi masa sata,ko su aikata mugun ƙudurinsu ta ɗauko,ƙananan ƙwayoyi ne sosai,ta ɓoye su sannan ta fita zuwa ɗakin da shishar tata take Yadda ta bar Roxy haka ta koma ta same ta,kanta akan wayarta tana dannawa,ta yi murmushi ta ajiye mata shishar a gabanta ta kama haɗawa tana faɗin "Barka dai Madam! Ga mutuniyar tana yi miki sannu da zuwa"Roxy ta ɗago ba tare da ta yi magana ba ta kama pipe ɗin shishar ta fara zuƙa yadda ta saba tana cigaba da danna wayarta Amra ta fice daga parlourn tana leƙen Roxy, tunani take yi ta inda zata fara ɗauke mata hankali *MALIYA ESTATE, KANO STATE, NIGERIA* *MUYASSAR RESIDENT* Shiru Hajiya Ruƙayya ta yi tana duban Arfa da mamaki bayan ta gama tsara mata ƙarya da gaskiya,mamaki ƙarara ya bayyana a fuskarta,don ya rasa yadda aka yi aka samu matsala, saboda ƙarfin aikin nasu da aka yi musu bata yi tsammani zai salamce da wuri haka ba Zuwa can ta ja ajiyar zuciya ta sauke,ta ce"shikenan babu matsala,da Ni yake zancen,zan ɗauki tsatstsauran mataki akan shi, wannan alƙawarina ne" Daga nan suka fara tsare-tsaren yadda za su tafiyar da gidajensu ba tare da wata matsala ba, Arfa cikin ɓacin rai ta ce"ni abin da yake ba ni mamaki aunty me ya haɗa Abban Zuhra da son waccan kilakin? Sun rabu da!ya haƙura haka mana,da me na rage shi don Allah?" Murmushi Hajiya Ruƙayya ta yi ta ce"ke ba ki san halin namiji ba,ko me kike yi masa,ko yaya kike da kyau da kulawa sai ya leƙa ya ga wata,don haka ke dai ki san yadda za kiyi ki mallake shi kawai,amma shi namiji ɗan kunama ne,ba shi da halacci"ƙugin motar Muyassar da suka ji ne ya sa suka yi shiru suna kallon ƙofar da zai shigo Babu jumawa Muyassar ya shigo da sallama,babu wadda ta yi yunƙurin amsawa a cikinsu, bai damu ba,ya dubi Hajiya Ruƙayya, cikin girmamawa ya ce"sannu da zuwa Mamie!" "Sannu Muyassar!ai kai ne da sannu,kai ka fi cancanta da sannu" Shiru ya yi bai yi magana ba, Hajiya Ruƙayya ta ja tsaki ta ce"na ji abin da ka yi,ka tabbata butulu,wanda bai san halacci ba Amma ka sani ba ka isa ka zalunci ƙanwata ba wallahi,abin haushi ma,akan wata kucaka can,ko na ce karuwa! Ita uwar taka ita ce ta saka ka ka rinƙa kallon hotunan ta a gidan ƴaruwata har kana cewa kana sonta wa ya je wa ya dawo? To ka so ta ɗin!amma muddin ka auro ta wallahi sai dai ka zaɓa ita ko ƙanwata, mutumin banza kawai!"tana kai wa nan ta ja tsaki ta miƙe ta nufi hanyar fita,ta fice daga parlourn, ƙanwarta ta miƙe ta raka ta Muyassar ya bi su da kallo kawai,a duk maganganun da Hajiya Ruƙayya ta faffaɗa babu wadda ta fi yi masa zafi da ciwo kamar kiran Shaheeda da karuwa da Hajiya Ruƙayya ta yi,karuwa!karuwa dai!! Shaheeda bugun numfashinsa ita take kira karuwa,bata san ƙanwarta ce karuwar bane da har take da zarrar kiran wata da karuwa?ya yi ƙwafa yana girgiza kai,sai kuma ya yi murmushin takaici da ya tuna maganarta da take cewa sai dai ya zaɓa ko Arfa ko Shaheeda,shi kuwa Allah ya bayyana masa Shaheeda,ya aure ta ya ga ubanda za su yi Wacece Arfa ma? wadda tunda ya aure ta ba zai iya ɗorar da wani abu na jin daɗin aure a tare da ita ba? Bata san cinsa ba,bata san shanshi ba,komai sai dai ya nema da kanshi,bata girki,ko ta yi ma ba daɗin girkin yake ji ba,shara, wanke-wanke,da sauran ayyukan gida babu ruwanta da su,ya ɗauko mata ƴan aiki ba sau ɗaya ba,ba sau biyu ba,amma saboda mugun halinta da baƙin kishinta bata taɓa barinsu,a watanni kaɗan zata kore su Dama babu batun ruwan wanka, wannan sai dai ya haɗa da kanshi,batun hira kuwa babu wata kalma mai daɗi,ga masifar zargi A fili ya furta "Allah sarki Shaheeda na! Ko a ina kike Allah ya dawo min da ke lafiya,ina kewarki,na san da ke na aura da hakan ba ta kasance da ni ba"ya ƙarasa magana yana shigewa ɗakinsa, ranshi a matuƙar ɓace *HAISAM* A hankali motarshi take gangarawa zuwa tsukukun layin,wanda yake cike da kwatoci da shara,ga ƙananan gine-gine marasa fasali da kyan gani,don wasu ma sun fara zubewa Daidaita parking ɗin motarshi ya yi,yana ƙarewa wajen kallo,ya kai mintuna biyar yana kallon masu wucewa ta bakin glass ɗin motarshi,wasu yaran ma har hannu suke sakawa suna shafa motar,bai yi mamakin hakan ba,don ya san irin motarshi baƙuwa ce a irin wannan yankin Ya kai a ƙalla mintuna goma a cikin motar kafin ya buɗe murfin motar ya fita yana ƙarewa ko'ina kallo, tunani yake yi wa zai tambaya a wannan wajen don ya nuna masa gidan da yake nema? Da ƙyar dai ya yi shahada ya tambayi wani matashin yaro mai tahowa"Am.....abokina...don Allah tambaya nake yi" Yaron ya kalle shi ya ce"Allah ya sa na sani"Haisam ya ce "Don Allah gidan malam Tajo nake nema,marigayi malam Tajo"shiru matashin ya yi na ɗan lokaci, kafin ya ce"gida dai gashi can,ka ganshi can? wanda yake kulle da kwaɗo? To nan ne,amma yau kwana biyu sun tashi,kuma ba mu san inda suka koma ba Amma ka tambayi maƙwabtansu,za su iya sanin inda suke" Shiru Haisam ya yi,a ranshi yana jinjina makirci da taku irin na Roxy,wato ta san zai nemi iyalan shiyasa ta canja musu location ko? Ya yi ɗan murmushi ya dafa kafaɗarshi ya ce"babu damuwa,na gode,sai anjuma"bai sake sauraren saurayin ba ya faɗa motarshi,ya tayar ya yi reverse ya bar unguwar, fuskarshi a ɗaure cikin ɓacin rai,amma ko me zai faru sai ya kama yarinyar nan *SULEJA* Roxy tana zaune riƙe da shisha tana zuƙa Kamar yadda ya zamar mata jiki Amra ta shigo ɗakin riƙe da kofunan lemo mai sanyi a hannayenta Tana shiga parlourn ta miƙawa Roxy ɗaya Glass cup ɗin da ta riƙo,ta janye pipe ɗin shishar gabanta tana faɗin"aikin kenan Madam! Ko hutawa da bankawa cikinki hayaƙi ba kya yi! Let's chill girl!" Ba tare da Roxy ta kalle ta ba ta ce"but kin san i don't normally take alcoholic drinks " "Madam da hankalina fa! Ta yaya zan ba ki alcoholic, wallahi non alcoholic drink ne"ba tare da Roxy ta sake magana ba ta gyara zamanta tana kallon cup ɗin na ɗan lokaci,amra ta samu waje ta zauna tana kallonta Hannu Roxy ta miƙawa Amra, Amra ta zaro idanu tana faɗin "me zan ba ki?"kai tsaye Roxy ta ce"lemon hannunki za ki ba ni, I want to switch it" Ɗan murmushi Amra ta yi tana faɗin "Roxy kenan! Har ya zuwa ba yanzu ki yarda da ni ba?kina tunani zan iya cutar da ke? Haba Roxy!ko don halaccin da kika yi min ai ..."Roxy ta ɗaga mata hannu fuska a ɗaure tana sake miƙa mata hannu, alamun ta ba ta kofin Babu musu Amra ta miƙa mata,ta ɗauki na gabanta ta miƙawa Amra, Amra ta karɓa ta fara sha, itama ta mayar da kai ga na hannunta,tana sha tana danna wayarta Sai da ta sha kusan rabi sannan Amra ta miƙe tana murmushi,ta dubi Roxy tana faɗin "welcome to our world Madam Roxy! Hermosa!!!"tana kai wa nan ta fice daga parlourn tana ƴar dariya Roxy ta ɗan bi ta da kallo ba tare da ta yi magana ba, lokaci guda kuma ta fara jin kanta yana juyawa sosai,bata iya ganin komai sai duru-duru,hakan ya sa ta saki kofin ba tare da ta sani ba,ta dafa bango tana sauke numfashi Amra da hassy ne suka dawo ɗakin a tare,suka tsaya a kanta suna dariya Amra tana dariya ta ce"dama na san yadda kike akan rashin yarda,na san yadda kike da wulaƙanci, shiyasa na yi miki haka, kofin farko lafiyayyen drink ne,kika ce sai an yi switching,gashi nan ƙwayoyin da na zuba miki sun fara aiki,yau dole na more wannan jikin naki Roxy,ba ni kadai ba,har da ƙawata ma"ta karasa faɗin haka tana ƙokarin cire riga Kai tsaye ta nufo Roxy wadda take zaune kanta yana juyawa,tana zuwa bata yi wata-wata ba ta cafke ƙirjin Roxy,duk da cewa tana cikin hali na maye da gushewar hankali amma sai da ta ji zafi,ta runtse idanu tana tuno mutum na karshe da ya kama mata breast,take ta ji wani ƙarfi ya maye gurbin dukkan wasu gurabu da mayen nan ya cinye, cikin tsananin zafin nama ta hankaɗe Amra sannan ta kama buga kanta a jikin gini Kafin wani dogon lokaci kokawa ta sarƙe tsakanin su Amra da Roxy,ita dai Roxy Allah ne yake ba ta Sa'a take kare kanta kawai,amma taron su biyun ya wuce ƙarfinta,ga abin da ta sha da ya bugar da ita ya taimaka sosai wajen guduwar karfin nata Allah ya ba ta Sa'a ta janyo wata ƙaramar tukunyar shayi da Amra ta siya,ta bugawa kan hassy, wadda ta fi dagewa dole sai ta raba ta da kayan jikinta Ai kuwa ta yi sa'a,tuni jini ya wanke kan Hassy,ya zuba ya wanke fuskarta,cikin gigita da tashin hankali Amra ta ja baya tana kallon Roxy wadda har yanzu take tangaɗi,amma ta ƙi yarda ta faɗi,sai buga kanta da bango da take yi lokaci zuwa lokaci Amra ta yi kukan kura ta yi kan Roxy, cikin wata iriyar fusata ta hau dukanta ta ko'ina,don ta san babu abin da zata iya yi mata,ba ma zata iya gane ta ba a cikin wannan halin,sai da ta yi mata duka sannan ta jefar da ita, ta kama jan Hassy don ficewa daga ɗakin,don ta kai ta asibiti a duba lafiyarta,ta bar Roxy a kwance tana sauke numfashi Abin da ya sa ta yi haka kuwa shine,ta san Roxy bai zama lallai ta iya gane cewa ita ta yi mata wannan dukan ba, sannan kuma tana samun kuɗaɗe daga wajen Hassy,ya zama dole ta yi wani abu wanda Hassy ɗin zata ji cewar ba bakinsu ɗaya a wannan wulaƙancin da Roxy ta yi musu ba,suna fita Roxy ta dafa bango,ta ciro wata ƴar ƙaramar allura daga jikinta ta yiwa kanta, sannan ta koma kan kujerar yaraf ta zauna,ta kwashi a ƙalla mintuna biyar kafin ta buɗe idanunta da suka kaɗa suka yi ja,har yanzu bata gama dawowa daidai ba, ta miƙe tsaye tana gyara kayan jikinta, sannan ta ɗauki wayarta ta fice daga gidan *ROCKY ESTATE, KANO STATE, NIGERIA* "Daddy please ka zo mu yi game ɗin tare ka ji Daddy!" Muryar Amna ta katse masa hanzari, cikin shagwaɓarta da ta zamar mata jiki "Amna just do your work alone, nima kin ga aiki nake yi,don Allah ki daina interrupting ɗina" Shura ƙafa ta fara yi, Haisam ya lumshe idanu ya buɗe ya furzar da huci,ya ce"okay finally! Kawo mu yi game ɗin,amma idan na yi winning ɗin ki kar ki ce za ki yi min kuka" "Okay thanks Daddy"ta faɗa da murna, kafin ta ƙaraso wajen riƙe da tab ɗinta Ba'a juma da fara game ɗin ba Haisam ya cinye ta,ta kama kuka har da shura ƙafa tana faɗin sai an sake,ai bata shirya ba, Haisam yana murmushi ya ce"babu abin da za'a sake,ai ke kika ce a yi, leave me alone Madam!"ta faɗa jikinsa tana kukan shagwaɓa Nimra ce ta shigo sashen nashi da sallama,ya ɗaga kai yana kallonta gami da amsawa Nimra ƙanwar Hajiya Mariya ce,wato matar babansa,kamar yadda ta saba yau ma sanye take da kayan da suka ɗame ɗan siririn jikin nata,sai ƴar light make up da ta yi wa fuskarta,da mayafin da ta saƙala a kafaɗarta #Nusy_bee Page 13 Sau ɗaya ya kalle ta ya ɗauke kai yana ɗan taɓe baki, yarinyar sam bata burge shi saboda yadda bata da kamun kai sam,shi kuma a duniya ya tsani mace mara kamun kai "Hi!"ta faɗa tana murmushi sosai,ba ta ba shi damar magana ba ta cigaba da magana tana kallon Amna "Amna babu magana ko?"Amna ta kalle ta ta ce"good morning aunty!"tana murmushi ta ce"No I'm your Mummy,not aunty,kin ji?"ita dai Amna bata yi magana ba sai kallonta take yi Ɗan murmushi ta sake yi,ta dubi Amna da ta sake lafewa a jikin mahaifinta ta ce"ki je wajen Hajiya Mamie kin ji?ko wajen Nanny,za muyi hira da Daddy"babu musu Amna ta miƙe daga jikin mahaifinta ta fice daga sashen tana waigen ubanta "Good morning love!"ɗaga kai ya yi yana kallonta,tsawon shekaru biyu kenan,tunda suka rabu da mahaifiyar Amna take bin shi da sunan neman soyayyarshi,sai dai sam yarinyar bata burge shi ko kaɗan, saboda bata da kamun kai,bata da wadatacciyar tarbiyya "Aiki nake yi, can you please excuse me zuwa anjuma??" Kwaɓe fuska ta yi,a shagwaɓe ta ce"kai my baby boy! Aren't you happy of seeing me?" Ɗauke kai ya yi yanayin fuskarsa yana canjawa,ya ce"aiki nake yi ne,bana son a rinƙa interrupting ɗina " "Amma na ga kuna hira da Amna time ɗin da na shigo" Wani banzan kallo ya watsa mata ya ce"kishi kike yi da ita?"ɗan murmushi ta yi ta ce"no ba haka nake nufi ba,ya uwa zata yi kishi da ƴarta? Kawai dai ina son ka ba Ni time ne,ka ga don kai kawai na zo gidan nan"bai amsa ta ba,ya cigaba da danna system ɗin shi Ganin ya yi banza da ita ya ƙi saurarenta sai kawai ta fashe da kukan kissa,ya ɗaga kai yana kallonta gami da sassauta fuskarsa,a hankali ya ce "I'm sorry please,amma me ya faru da za ki yi kuka?me na yi miki?" Goge hawayenta ta yi ta ce"ba ka yi min ba,ka ƙi yi min dai" Ya sake dubanta sosai ya ce"me na ƙi yi miki?" Ta karyar da kai ta ce"ka ƙi ka kula ni,ka share ni,bayan na shafe tafiya na zo don na ganka kai kaɗai,amma ba za ka iya ba ni time ɗinka ba?even a little? Nima na ji ina da matsayi ko yaya ne a wajenka?" Cikin kwantar da murya ya ce"okay na fahimce ki Yanzu don Allah ki ba ni wasu ƴan mintuna na gama da wannan file ɗin da nake dubawa,idan ya so sai mu tattauna" Kwantar da kanta ta yi a jikin kujerar da take zaune ta ce"alright! I'm waiting"ya sake dubanta,ranshi ya fara ɓaci ya ce "I need space Nimra,idan kuma ba haka ba sai na bar miki gidan" Cikin sanyin murya ta ce"But na ce zan jira ka ai, ka gama sai mu yi magana "cikin ƙosawa ya ce"okay! To tunda ba za ki tafi ba ni bari na ba ki waje, I told you since bana son musu"ganin yana ƙoƙarin miƙewa ya sa ta miƙe ba a son ranta ba tana murmushi ta ce"I will wait sweetheart!bye!"ta fice daga sashen Tana fita ya miƙe da sauri,tuni ya ɗauki key din motarshi,ya fice daga gidan,don a rayuwarsa ya tsani a matsa masa *ROXY* A hankali take tafiya a gefen hanya,tana lumshe idanu tana buɗewa,da alamu har yanzu abin da ta sha bai gama sakinta ba, idanunta sun yi jawur, fuskarta a ɗaure tamau,alamun ranta a tsananin ɓace yake Wayarta ta zaro,ta fara yunƙurin aika kira,bayan ya sakanni ta fara magana yanayin muryarta tamkar wadda take cikin maye "Kana ina ne?"daga can ɓangaren Oga boss ya ce"ga ni a gida uwar ɗakina" Kai tsaye ta ce"ka zo bayan gidan Amra,ina buƙatar ganinka"tana kai wa nan ta kashe wayar Bata juma tana tafiya ba ta ji ana faɗin "wannan kamar wannan criminal ɗin da ake nema!" Ji ta yi ɗayan ya ce"a haba! Ta yaya zata yarda ta fito ita kaɗai a wannan lokacin?" Ɗayan ya yi shiru yana duba hotonta da yake wayarta, kafin ya ce"wallahi ita ce fa,ka ga hoton"ita dai ko kallon su bata yi ba,ta cigaba da tafiya abinta Ji ta yi sun biyo ta suna faɗin "ke!tsaya!tsaya!!bari mu tabbatar,kar ki motsa,tsaya a inda kike" Cigaba da tafiya ta yi a hankali har suka kusa cim mata,dayan ya ce "ki tsaya ko na yi harbi" Cak ta tsaya a inda take,suka nufo inda take da gudu,amma kafin su ƙaraso ta shammace su ta saka gudu da tsananin ƙarfinta,suka rufa mata baya Tsawon kusan awa guda tana ba wa yan sandan wahala,duk yadda za su kamo ta sun yi,amma ta ƙware wajen zilliya da rainawa yan sanda hankali,hakan ya fusata ɗaya daga cikinsu ya saita tsakiyar bayanta ya yi harbi,amma sai bai same ta sosai ba,ya same ta a kafaɗarta Sai dai a maimakon ta tsaya sai shigewa wani lungu ta yi ta ɓuya,duban duniya suka rasa ta, babu yadda suka iya haka suka juya suka tafi Ita kuwa Roxy bayan ta tabbatar sun tafi miƙewa ta yi ta cigaba da tafiya tana tangaɗi,ga mayen ɗazu har yanzu bai gama sakinta ba, saboda ƙwayoyin da su Amra suka zuba mata ba ƙaramin ƙarfi ne da su ba,ga jini da ya fara ɗibarta, saboda zubar jinin da take ta yi tunda aka harbe ta Tun tana ganin gari yadda ya kamata har ta fara gani dishi-dishi,ga ƙarfin jikinta da yake ta ƙarewa,a hankali duhu ya rufe ƙwayar idanunta,duk da haka bata karaya ta tsaya ba sai da ƙarfinta ya ƙare duka,ita dai bata san lokacin da ta yanke jiki ta faɗi ba ma *MALIYA ESTATE* *UMMEEY* Sauri sauri take yi don fita zata yi zuwa bikin ƴar ƙawarta Hajiya Jamila, Salma,amaryar ƙawa ce wajen ƴarta Shaheeda,sau tari idan ta ga yarinyar tana tunawa da ƴarta Shaheeda, saboda yadda halayyarsu ta zamo ɗaya,kuma manyan ƙawayen juna ne sosai Ko lokacin da aka aiko mata da katin gayyatar bikin Salma ta yi kuka sosai,don ta tuna Shaheeda, wadda a halin yanzu bata da tabbacin tana raye ko ta bar duniya Ƙoƙarin fitowa take yi daga ɗakinta sai ga Hajiya Sa'adatu ta danno kai cikin parlourn ta kamar wadda aka wurgo,sai huci take yi,da alamu ranta a ɓace yake, Ummeey ta kalle ta cikin faɗuwar gaba,ta ɗaure ta ƙaƙalo murmushi ta ɗora akan fuskarta tana faɗin "A'a! Hajiya Sa'adatu yau ke ce tafe? Maraba da zuwa"Hajiya Sa'adatu ta watsa mata wani mugun kallo ta ce "ai ke ce da sannu Hajiya Zainab! Wai me yake faruwa ne? meyasa ba za ki bar ni haka na huta bane? meyasa kika zamar min masifa da bala'i a rayuwata ne?"Ummeey da ke tsaye tana kallonta ta safe ƙirji tana faɗin "subhanallahi!me ya kawo wannan maganar kuma? Don Allah ki yi haƙuri ki zauna mu yi magana ta fahimta,me yake faruwa ne?" Kai tsaye Hajiya Sa'adatu ta ce"ba zama ne ya kawo ni ba,dama na zo ne na gaya miki ki yi wa yarki gargaɗi akan ɗana,ta hana shi zaman lafiya da matarshi,an kawo min ƙararta,bana son hakan ya kuma faruwa Haka kawai yanzu ta haddasa gaba tsakanin Muyassar da matarsa,ba zai yiwu na ɗauki ƴar mutane na ba shi sannan yarki ta hana su zaman aure ba,kar hakan ya kuma faruwa, bana buƙatar matsala a gidan ɗana Ba sai an faɗa ba kowa ya san yarki masifa ce,kuma annoba ce,to bana buƙatar wani tashin tashina a kusa da ni"ta juya da zummar ficewa daga parlourn Cikin karyewar murya Hajiya Zainab ta ce"Hajiya Sa'adatu ki fahimtar da ni,wacce ƴar tawa kike nufi? Dama ina da wata yar ne ban sani ba?" Kallon banza Hajiya Sa'adatu ta yi mata ta ce"wacce ya kuwa banda wadda ta janyo mana abin faɗa a family, ƴarki Shaheeda? Bana son abin nan ya kai mu gaban Alhaji, shiyasa na zo na gaya miki don ki ja mata kunne,ta fita harkar ɗana da gidansa, idan ba haka ba kuma komai zai iya faruwa,sai anjuma Hajiya "ta juya ta fice daga sashen zuciyarta cike da hassadar ganin Hajiya Zainab ta sake gogewa ta yi kyau kamar ba wadda take cikin damuwa ba Zama Hajiya Zainab ta yi a hankali a gefen kujera cikin wani irin yanayi da ta kasa fassarawa, Shaheeda?ina suka ga Shaheeda?tana a wanne halin? Ita a yanzu da zata ganta da bata san wanne irin farin ciki zata tsinci kanta ba,wai me yasa abubuwa suke ta faruwa da ita ne akan Shaheeda? Ta goge hawayenta tana faɗin "ya Allah ga yata nan, Allah idan da rabo ina roƙonka ka dawo da ita gare ni, ya Allah kaine masani kuma mafi hikima, Allah ka yi min daga taskarka" Kamar babu Abin da ya faru ta ƙarasa shiryawa ta fice don zuwa taron bikin yar su Salma,tana kallon su Hajiya Ruƙayya da Hajiya Atika suna magana,ta san mayar da yadda aka yi suke ya,bata ko yiwa sashen da suke tsaye kallo biyu ba ta shiga mota ta tayar ta fice daga gidan *HOSPITAL* "Amra wannan wacce mahaukaciyar yarinya ce kika haɗa ni da ita take neman rayuwa ta? Daga nuna mata hanyar daɗi kuma sai ta nemi kisa?" Amra ta kalli Hassy da take wannan maganar ranta a matuƙar ɓace ta ce"ai ƴarinyar nan ta yi min wulaƙanci,amma wallahi bata ci banza ba,sai na ganar da ita kuskurenta,kafirar banza ƙazama kawai " Hassy ta sauke ajiyar zuciya tana taɓa bandage ɗin da aka naɗe mata kai,a hankali ta ce"yanzu tana ina?" Amra ta taɓe baki ta ce"oho! Na dai bar ta a gida bayan na dake ta, gobe ta sake yi min wannan iskancin Itama karuwar ce fa,amma take nunawa duniya ita ba haka take ba Abin haushi, yarinyar da criminal ce, nemanta ake yi ruwa a jallo amma zata yi min haka, sai na tona mata asiri a wajen yan sanda wallahi"Hassy dai bata ce komai ba, Amra ta cigaba da faffaɗar maganganu, saboda ranta a tsananin ɓacin rai da take ciki *ROXY* A hankali take buɗe idanunta da take ganin dishi-dishi,ga jikinta ta ji ya yi sanyi babu ƙwari ko kaɗan,amma hakan bai hana ta yunƙurin tashi zaune ba tana sauke numfashi da ƙyar Ji ta yi an riƙe ta,an mayar da ita ta kwanta,ta dubi matar Oga boss da take riƙe da ita tana murmushi ta ce"sorry Ma'am! Jikinki babu ƙwari, ba'a juma da cire bullet ɗin da aka harbe ki ba, relax ma'am " Kallonta ta yi ta ce"ina Oga boss? A ina ya gan ni?" Matar Oga boss ta ce"a gefen hanya,da ƙyar muka gano ki,mun yi yawo sosai,sai kuma muka ganki a sume,shine muka dauko ki muka kawo ki nan,tun jiya da dare muka yi magana da likita ya zo ya duba ki ya cire miki bullet ɗin hannunki"Roxy ta kalli hannun nata ba tare da ta yi magana ba,ta sake dubanta ta ce"Azeema ina Oga boss?" Azeema ta ce"yana parlour" "Kira min shi"ta faɗa ba tare da ta kalle ta ba Babu musu Azeema ta juya ta fice daga ɗakin don kiran Oga boss, Roxy ta zauna sosai,ta lumshe idanunta, komai da ya faru yana dawo mata ƙwaƙwalwa tiryan-tiryan Ɗan murmushi ta yi tana tuna cin amanar da Amra ta yi mata,ta girgiza kai kawai,a ranta ita kadai ta san me ta shirya mata Tana nan zaune su Oga boss suka shigo ɗakin,da sauri ya ƙaraso yana faɗin"sannu ma'am! Ya jikin?" Kallonsa ta yi ta ce"Oga boss wani aiki nake so ka yi min,amma da Azeema za mu haɗa!" Waje ya samu ya zauna yana faɗin"okay ma! Wanne aiki ne?" Lumshe idanu ta yi ta buɗe, sannan ta fara yi masa bayani a nutse,a razane Oga boss yake kallonta, ba tare da shakka ko tsoro ba ta ce"eh haka nake so So nake na hukunta Amra,ina son a yau ta san wacece Roxy!" Jinjina kai ya yi,ya dubi Azeema ya ce"za ki iya?" Cikin bayar da tabbaci ta jinjina kai,ta ce"zan samu masu taya ni ma ranki ya daɗe Ke ce fa kika ba mu sutura, kika ba mu dukkan farin cikin rayuwa,raina ne kawai ba zan iya ba ki ba" Cikin kwantar da murya Oga boss ya ce"amma kuma akwai haɗari a cikin wannan aikin ranki ya daɗe,ga na nakasarwa idan an samu matsala Ba za'a chanja hukuncin da wani ba kuwa?" Kallonsa Roxy ta yi, cikin yanayin ɓacin rai ta ce "ka san wacece Roxy,babu wanda zai gaya maka halina ko da ace David da muke tare kusan koyaushe Ka san abin da na fi tsana,to me yasa Amra zata ci amanata? Na san Amra cikakkiyar karuwa ce kuma ƴar lesbian,amma a haka nake tare da ita duk da ni bana ra'ayin hakan,amma meyasa dole sai ta yi forcing ɗina na yi abin da ban yi niyya ba? Duk da cewa Amra bata cancanta ba amma ina girmama shekarunta,don na san ba ta kusa da sa'a ta ba ce,amma a ƙarshe ta zubar da ragowar girman da nake ganinta da shi ta ci amanata,amma kuma zan shayar da ita mamaki tabbas,na yi wannan alƙawarin!! #Nusy_bee Page 14 Shiru Oga boss da Azeema suka yi suna kallonta, Roxy bata damu ba,ta koma ta kwanta saboda nauyin da ta ji kanta yana yi mata,a hankali ta ce"Azeema ki nemi masu taya ki ɗin,zan tsara muku yadda za kuyi"Azeema ta rissina tana faɗin "noted ma'am!" Roxy ba ta sake magana ba ta koma ta kwanta,su kuma suka fice daga ɗakin Hannun Azeema Oga boss ya riƙo yana faɗin "ke wai ba ki da hankali ne? Ya za ki biye mata don tana cikin ɓacin rai da ciwo? Kin san girman kasadar da kika ɗauko kuwa? Ko ba ki yi tunanin abin da kan iya kai wa ya dawo ba bayan aiwatar da wannan ɗanyen aikin?" Azeema ta yi murmushi tana girgiza kai ta ce"sanin kanka ne Roxy bata yin abu ya kwaɓe mata,bayan haka ka san bata juyawa baya akan ra'ayinta, sannan kuma abin da ta yi mana ba zai ba ni dama na juya mata baya ba,tabbas sai na cika mata burinta,sai na hukunta mata wannan azzalumar matar da ta yaudare ta ta cuce ta, karuwar banza kawai" Oga boss ya jinina kai yana kallonta yana murmushi, kafin ya ce "to Allah ya bada Sa'a"Azeema ta shige ɗakin da Roxy take kwance tana faɗin "Ameen" *ROCKY ESTATE, KANO STATE* "Barka da dawowa Alhaji!"juyawa ya yi yana kallon mai aikin Hajiya Mariya da take gyara dinning area,ya ce"Barka dai,ina Amna? Ko ta koma wajen Nanny ɗinta?" Ta ce"Amna tana wajen Hajiya Nimra,suna sashenka"Haisam ya ji kamar ya ɗora hannu aka ya ƙwala ihu, ba tare da ya yi magana ba ya juya ya fice daga sashen A parlourn shi ya samu Nimra da Amna a zaune suna kallo,kallo ɗaya ya yiwa Nimra da ta tsuke cikin kayan bacci,ta saki gashin kanta gadon bayanta,ya ɗauke kanshi,ta miƙe tana kwantar da Amna da take bacci,ta nufi inda take tana taku ɗaiɗai tana girgiza jikinta, cikin karairaya ta ce"welcome sweetheart! Tun ɗazu ina ta jiranka " Kallonta ya yi ya ɗauke kai,ta ƙaraso tana daf da rungume shi ya kauce,ta tsaya tana kwaɓe fuska kamar zata yi kuka Bai sake kula ta ba ya ɗauki Amna ya wuce da ita wajen Nanny ɗinta, Nimra bata yi zuciya ba ta bi shi,har ya ƙarasa wajen Nanny ɗin Amna,tana fitowa Nimra ta sake biyo shi Tsayawa ya yi fuska a ɗaure ya ce"ya dai? I hope everything is fine" "So nake mu yi magana"ta faɗa a shagwaɓe "Sai da safe ma yi maganar"yana faɗa ya wuce don komawa sashenshi "But you promise me za mu yi magana idan ka dawo"ta faɗa tana biyo shi da sauri "Sai da safe" ya faɗa ba tare da ya kalle ta ba" "Ai gobe ma fita za kayi ba tare da na sani ba"bai saurare ta ba ya shige sashen shi, amma kafin ya shiga parlourn ta biyo shi Cikin ƙosawa ya kalle ta ya ce "ina haɗa ki da Allah ki yi haƙuri gobe za mu tattauna, yanzu kin ga akwai aikin da zan yi,idan kika zo kika yi interrupting ɗina za ki iya janyo min matsala,na yi Miki alƙawarin zan saurare ki mu yi maganar" Ba a son ranta ba ta juya ta fice daga sashen,ya shige parlourn shi ya rufe ƙofa yana jan tsaki Ya tsani naci,ita kuma wannan akwai ta da nacin tsiya Yana zama ya fara kiran Saleem,babu jumawa Saleem ya ɗaga kiran "I'm sorry Saleem! Ɗazu na ga kiranka,bana cikin yanayin da zan iya ɗagawa ne" Murmushi Saleem ya yi,ya ce"ba yawa yallaɓai,ai na san yanayin aikin Na samo address ɗin iyalan marigayi Malam tajo,dama shine abin da na kira na gaya maka kenan" "Good job Saleem!tura min" "Okay Sir "daga nan suka yi sallama Ko da Saleem ya tura address ɗin Haisam ya daɗe yana mamakin inda ta luluƙa ta kai su,ya yi murmushi yana girgiza kai,a hankali ya ce"Allah sarki yarinya! Ƙarshenki kuma ya zo kenan,sai dai na ce mu haɗu kawai nan gaba kaɗan " *MALIYA ESTATE* "Zan fita "ɗaga kai ya yi yana kallon Arfa da take a shirye tsaf, rungume da Zuhra, cikin kwanciyar hankali tana sanar masa zata fita" A fusace ya ce"a gidanku haka aka koya miki tarbiyyar tambayar miji idan za ki fita?sai da kika shirya kika gama komai sannan za ki wani tambaye ni za ki fita?" "Wanne mentality ɗin naka ne ya gaya maka tambayarka nake yi Muyassar? Ai ba Ni kaɗai ba ce aka yi missing koya min abubuwa da yawa a gidanmu,kai ma kamar ka samu lack of home training,tunda na ga baka san darajar aure ba,baka san darajar mace ba,asalima kai babu abin da ka sani sai tunanin karuwa da son kanka, don haka nima a bar ni na yi abin da na ga dama" Muyassar ya girgiza kai, yanzu ya daina mamaki idan Arfa tana yi masa rashin arziƙi, saboda yadda ta samu cikakken goyon baya daga wajen wadda take faɗawa maganganu duk sanda suka samu matsala,wato mahaifiyarsa Hajiya Sa'adatu Bai sake yi mata magana ba,yana kallo ta fice daga gidan,yana zaune bai tashi ba sai da ya ji ƙarar motarta, sannan ya miƙe jiki a mace ya ƙarasa jikin window yana leƙen waje Shi mutum ne mai son hutu da kwanciyar hankali,yana son soyayya da kulawa,amma babu wadda yake samu daga wajen Arfa zai tsabar kishi da zargi,bayan haka bata iya komai ba Ya rasa menene dalilin da ya sa mahaifiyarsa take matuƙar son su Arfa,don akan Arfa ba ƙaramin ci masa mutunci ta yi ba,sai da ya ji komai ya fice masa a rayuwa Ga masifar soyayyar Shaheeda da take taso masa tana hana shi sukuni,ko a yau da zai ganta da wallahi sai ya aure ta,sai dai duk abin da zai faru ya faru,ba damuwarsa ba ce Ya daɗe a wajen yana karanta wasiƙar jaki game da rayuwarshi da shaheedansa, kafin ya fice daga parlourn don barin gidan,a ranshi yana jin da yana da wani wajen da zai rinƙa zuwa yana yin zamansa ko ma ya kwana da ya je,ya huta da ganin Arfa, wadda har yanzu daidai da second ɗaya bai taɓa sonta ba *ROXY* Yau kwana biyu kenan da samun tsautsayin da ta yi, jikinta ya yi kyau sosai,har ma ta cigaba da yin kananan ayyukanta da system ɗin Oga boss Da kanta ta shiryawa Azeema yadda zata yi da zarar ta je gidan Amra,don tuni sun biya ta ƙungiyar su Amra ɗin,da ta tara manyan mata da yan mata,duk wadda kake so a kai maka,to an yi matuƙar Sa'a Amra ta buƙaci a kawo mata Azeema, wadda ta sauya suna zuwa star girl,dama tuni Roxy ta san irin matan da Amra take kwaɗayi irin su Azeema ne,don haka abin ya yi mata daidai ba tare da wata matsala ba Cikin wasu tsinannun kaya Azeema ta shirya, Roxy tana daga zaune tana kallonta tana ɗan murmushi, kafin ta ce"Good! Haka nake son gani!na tabbata idan ta ganki zata yi burin aiwatar da mummunan ƙudurinta"sai kuma ta yatsina fuska ta ce"na kasa gane abin da mata suke buƙata a jikin ƴan'uwansu mata,da har suke jin za su iya illata wani akan wannan mummunar ɗabi'ar tasu Daga yau ina buƙatar a cire mata sha'awar ya mace a rayuwarta har abada,ina buƙatar ta ji a duk duniya babu abin da ta tsana sama da wannan dabbancin,in other hand kuma ina buƙatar ta ji tabbas Roxy ta wuce tunaninta,tafi"babu musu Azeema ta ɗauki abayarta ta ɗagawa Roxy hannu,ta fice daga dakin tana ƙoƙarin saka abayar Itama Roxy miƙewa ta yi ta fice daga ɗakin, a ranta ita kaɗai ta san wutar fansar da take ruruwa a cikin zuciyarta *KANO STATE* *HAISAM* Da sauri-sauri yake fitowa daga sashensa,don a rayuwarsa ba ya son ɓata lokaci ko kaɗan, musamman a irin abin da ya shafi aiki Nimra ya gani a raɓe a jikin bangon parlourn,ta narke idanu ta langwaɓar da kanta,a cikin zuciyarsa ya furta "Kai!inna lillahi wa inna ilayhi rajiun! Wannan wacce iriyar masifa ce?" Katse masa tunani ta yi, cikin yauƙi take faɗin "Good morning sweetheart!" A taƙaice ya amsa da"morning!" Lumshe kyawawan idanunta ta fara yi tana buɗewa cikin sigar jan hankali, Haisam ya ɗauke kanshi, zuciyarsa tana zafi "Can we go now? Za mu iya magana?" Ba shi da zaɓin da ya wuce cewa"okay! bismillah "duk da cewa yana da abu mai muhimmanci da zai yi,ya juya ya koma cikin parlourn, ta biyo bayansa Yana zaune ya zuba mata idanu ganin bata da niyyar yi masa magana,gashi shi kuma yana da abu mai muhimmanci da zai yi, cikin ƙosawa ya dube ta ya ce "Nimra kin san yadda aikina yake, kuma a kowanne lokaci kusan na ce miki ina bakin aiki ne,idan kina da magana mai muhimmanci then let's talk,is not proper ki zuba min idanu kina kallona bayan kin ce min kina da magana,nima kuma ina da inda zan je, don akwai aikin da zan yi" Shagwaɓe fuska ta yi,ta ce"kenan yanzu baka da lokacin iyalinka sai na aikinka kenan?" Kanshi tsaye ya ce"kusan haka!" Ya faɗa ne don ta ƙyale shi, amma a maimakon haka sai ta kama murmushi tana faɗin "You must be joking my friend! Whatever,ko ma dai haka ne ni nan zan sauya yanayin aikin nan da yake cinye haƙƙin mutane,ka ba ni time, shima aikin ka ba shi,for now dai,a yi maganar a yanzu,anan, yaushe za ka tura magabatanka gidanmu?idan ba za ka iya magana ba ni zan yi wa daddynka magana,idan ya so sai su je can wajen abbana " Shi abin ma dariya ya ba shi,amma ya ɗaure fuska ya ce"ba sai kin gaya masa ba,idan na samu time zan yi masa magana, yanzu dai kina gani na da shiri aiki zan fita "juya ƙwayar idanunta ta yi ta ce"alright babu matsala,sai na ji ka,amma kar na ji shiru Please "ya jinjina kai kawai yana miƙewa,ta miƙe itama ta rufa masa baya suka fito har wajen motarshi Sunkuyar da kanta ta yi daidai windon motar tana kallonsa tana narkar da idanu yadda ta saba idan tana son ta ja hankali, ɗauke kanshi ya yi daga kallonta yana yunƙurin tayar da motar,da wata iriyar sexy voice ta ce"safe trip sweetheart! Allah ya dawo min da kai lafiya "ya jinjina kai sannan ya tayar ya fice daga gidan Kai tsaye address ɗin da Saleem ya tura masa ya nufa,sai gashi ya ya tsinci kanshi a gaban wani katafaren gida Bin gidan ya yi da kallo yana sake duba address ɗin da mamaki,amma da ya tuna wacece Roxy sai ya yi murmushi kawai,yana sake duba hotunan da aka tura masa Ya kai wajen mintuna talatin a ƙofar gidan kafin ya samu yaron da zai aika gidan ya yi masa sallama da matar gidan,babu jumawa sai gashi ta leƙo,sanye da hijabi har ƙasa,autanta Habu yana riƙe da hannunta Har ƙasa ya durƙusa yana gaishe ta,ta amsa da sakin fuska sannan ta ce"ka shigo ciki mana,sannu da zuwa"ya yi ɗan murmushi ya ce"a'a dama ba shiga zan yi ba, tallafin marayu ne aka ce na kawo muku"ya ciro kuɗi ɗaurin 100k guda biyu ya ce "gashi, Allah ya ji ƙan mahaifinsu ya albarkaci rayuwarsu"hannunta yana rawa ta karɓa tana faɗin "oh Allah! To an gode an gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, yadda kuke faranta mana Allah ya faranta muku, Allah ya kula da ahalinku kuma"ɗan murmushi Haisam ya yi,ya ce"babu komai Mama, in sha Allah ina nan dawowa nan kusa,hi boy!"yaron ya ɗaga kai a sanyaye yana kallonsa, tsananin kamar da suke yi da mahaifiyarshi ya sake tabbatar masa da zarginsa,kamar har ta yi yawa ma,ya kama hannun yaron yana yi masa wasa,duk da yadda ya nuna masa ba zai saki jiki da shi ba,amma saboda kayan biscuits da sweets ɗin da ya kawo masa ya saki jiki da shi,har ya ɗaga masa hannu da zai shiga motarshi Sai da suka shiga gida ya ɗaga waya ya kira Saleem, Saleem yana ɗagawa ya ce"komai ya yi daidai Saleem, thanks very much for your effort " Saleem ya rissina kamar yana gabansa ya ce"ka cancanci fiye da haka daga gare ni Oga, Allah ya ba da sa'a, Allah ya ba ku nasara akan maƙiya"Haisam ya kashe wayar yana murmushi #Nusy_bee Page 15 *ABUJA* "Hajiya Hassy girman kujerarki! Ga yaran na samo,ga su tsala-tsala,har sai sun fi Roxy garɗi ma"a cewar Amra a waya tana kallon su Azeema da ta saka suka cire after dress ɗinsu, kowacce ta zauna daga ita sai kayan banzan da ta saka Daga ɗaya ɓangaren Hajiya Hasana, wadda aka fi sani da Hassy ta ce"alright gani nan zuwa,kin san mai gidana yana gari,ga yaran miji da shegen sa ido,bana son a ɗago ni,dama gashi sun dame ni da tambayar ina na ji ciwo, matsiyatan yara kawai" Amra ta ce"maganinsu za ki yi kamar yadda kika yi maganin ubansu,ki kai su sama su ma a rufe bakin su daina saka miki idanu, suna uzzura miki da tambayoyi na babu gaira babu dalili,kamar waɗanda suke aurenki" Hassy ta ce"mhm! Gani nan zuwa dai,idan na zo sai mu ƙarasa maganar ko?"Amra ta ce"okay sai kin zo"suka kashe wayar Abinci da abin sha Amra ta kawo musu,ta shimfiɗa ƙatuwar darduma ta ce"bismillah,mu zauna girls"babu musu suka sauko,ta yi serving ɗin kowa,itama ta yi serving kanta Ba su juma da fara cin abincin ba kira ya shigo wayar Amra,wayar tana ɗakinta,don haka ta miƙe ta fice daga parlourn don ɗauko wayar Da sauri Azeema ta ciro ƴar ƙaramar ƙwayar da Roxy ta bata ta jefa a cikin kofin Amra,suka cigaba da cin abincin su a nutse Babu jumawa Amra ta shigo tana jan tsaki,don kiran da unknown number aka yi,kuma da ta ɗaga shiru ta ji,har ta gaji ta kashe wayar Kallo su ta yi tana murmushi,ta zauna tana faɗin"sorry ko? Na bar ku jira, kuma ƴar'uwar tawa tana hanya bata ƙaraso ba"suka kalle ta,sai da dariya ta kusa kama Azeema ganin yadda take magana tana wani karairaya kamar tana tare da namiji Ɗaya daga cikin ƙawayen Azeema, wadda ta fi ta iya bariki,ta yi fari da idanu ta ce"no babu komai baby,sai ta iso"Amra ta yi murmushi, Azeema da ɗaya ƙawar ta su suka kalle ta da mamaki jin ta kira ta da baby Ai kuwa babu jumawa bacci ya fara fizgar Amra,suka cigaba da cin abincinsu a nutse suna kallonta suna murmushi Mintuna biyar kyawawa ya ishi Amra faɗawa bacci mai nauyi,suka kalli juna suka yi shewa, Azeema ta miƙe ta fara laluben kitchen,su kuma sauran ƴan matan suka fara tuɓe mata kaya Babu jumawa Azeema ta dawo hannunta riƙe da tafasasshen ruwa, tana zuwa bata yi wata-wata ba ta sheƙawa Amra a daidai saitin gabanta,duk da nauyin baccin nan da ƙwayar ta saka ta sai da ta yi wani ihun azaba, ba tare da damuwar komai ba suka tattara komatsansu suka fice daga gidan Lokacin da za su fita daga layin a lokacin motar Hassy ta shigo layin,sai dai kasancewar babu wanda ya san wani a cikinsu ya sa suka wuce ba tare da sun tsaya ba ma,itama Hassy ta wuce gidan Amra zuciyarta cike da kwaɗayi da ɗokin haɗaɗɗun ƴan matan da ta gani Amra ta tura mata ta Whatsapp *MALIYA ESTATE, KANO STATE, NIGERIA* "Muyassar menene yake faruwa ne? A kwanaki biyun nan ƙararraki suna yin yawa akanka, mahaifiyarka ta kawo min ƙararka,haka zalika matarka,me yake faruwa ne?" Kan Muyassar a ƙasa yana sauraren yayan mahaifiyar tashi ya ce"ban san akan me kake magana ba Abba" Alhaji Yusuf ya ce"matarka ta tabbatar min da kana neman wata yarinya,har kana shiga lokacinta da sabgogin yarinyar , menene gaskiyar wannan maganar?" Shiru ya ɗan yi, kafin ya girgiza kai ya ce"a'a Abba,Ni ban san da wannan maganar ba gaskiya" "Abba wallahi ƙarya yake yi,har cewa ya yi wai ya fi sonta da ni,kuma akanta ni ba mace ba ce,ya rinƙa ci min mutunci saboda ita, tukunna ma,don ka ga ina rufa maka asiri, wallahi Abba tsohuwar budurwarsa ce,wato SHAHEEDA!!" Cikin wani Irin ɓacin rai Abba ya kalli Muyassar wanda ya yi ƙasa da kanshi kawai yana saurarensu, muryarshi tana tsaitsayawa ya ce"menene gaskiyar maganar matarka? Menene gaskiya game da halin da kake ciki na neman waccan yarinyar?" Kai tsaye Muyassar ya ce"ka gafarce ni Abba,na san dai har yanzu ina sonta,amma...."marin da Abba ya saukewa Muyassar ne ya sa ya yi shiru, cikin tsananin ɓacin rai ya ce"ko babu komai ka nuna min ni ba mahaifinka bane,ko da na ɗauki shekaru kana riƙe a hannuna,ka tashi ka ba Ni waje kafin na fusata na yi maka abin da ba za ka taɓa mantawa ba,tashi ka ba ni waje!'ya daka masa tsawa Babu musu Muyassar ya miƙe tsaye, fuskarsa babu alamun damuwa,duk da cewa shi kaɗai ya san yadda yake ji a ranshi,ya fice daga sashen Alhaji Yusuf Dubanshi ya mayar ga Hajiya Sa'adatu da ranta ya fi na Alhaji Yusuf ɓaci, cikin kakkausar murya ya ce"kina ina hakan take ta faruwa ne Sa'adatu? Yaushe ɗanki zai yi lalacewar bijirewa umarnina? Idan ban da shi wawa ne ko babu mata a duniya me zai yi da wannan fanɗararriyar yarinyar? wadda a yanzu ma babu tabbacin ko tana raye? To ki ja masa kunne, wallahi tallahi, muddin magana makamanciyar wannan ta sake zuwa inda nake akan yaron nan to tabbas sai na shayar da shi mamaki,sai na ɗauki mummunan mataki akansa Ku bani waje zan huta"babu musu suka miƙe ɗaya bayan ɗaya suka fice, zuciyar Hajiya Ruƙayya da ta Arfa fes Kai tsaye harabar gidan Hajiya Sa'adatu ta nufa,wajen parking space,anan ta iske Muyassar yana zaune,amma kallo ɗaya za'a yi masa ya bayyanar da damuwar da yake ciki, sai dai sam bata kula da hakan ba,tana zuwa ta sauke masa mari mai kyau, kafin ya ankarar ta sake sauke masa wani Dafe kuncinsa kawai ya yi ba tare da ya ɗago kanshi ba, Hajiya Sa'adatu ta cigaba da magana a fusace "Wallahi ba ka isa ba Muyassar! ba'a haifi yaron da zai bijire min haka ba, wallahi ko bayan raina ka auri yarinyar nan Allah ya isa ban yafe maka ba,kai ko labari na sake jin ka kalli hotonta sai na tsine maka!! Kai in banda abin namiji me za ka yi da Shaheeda ga Arfa kana da ita?asalima ga mata nan birjik a gari ko da kana sha'awar ƙari,amma idan na sake jin batun Shaheeda to lallai sai ka gane kuskurenka,tabbas sai na ba ka mamaki,dalla shiga mu tafi"babu musu ya buɗe motar jiki babu ƙwari,itama ta shiga baya,ya tayar suka bar wajen *ROXY* Yau kwana biyu kenan da tura Azeema gidan Amra da ta yi don rama abin da Amra ta yi mata,a ɗaya ɓangaren kuma tana samun sauƙi sosai,don zuwa yanzu hannun ya yi sauƙi sosai A yau ta shirya zuwa kano,amma kafin nan tana buƙatar ganawa da Amra tukunna,don haka ta shirya cikin wasu expensive track suit,irin wanda take yawan sakawa,ta sanya baƙin sketchers,ta ɗaura scarp akan dogon gashin ta sannan ta fice zuwa gidan Amra A hanya tana tuƙi tana kallon numbar David wadda tsawon kwanaki kenan yanzu idan ta kira ba ta shiga,ta rasa inda ya jefa wayar tashi A ƴan mintuna ta isa gidan Amra saboda gudun da take yi,ba tare da damuwar komai ba ta kutsa kai gidan tana gyara zaman baƙin spec da ta sanya ya rufe mata ƙwayar idanunta Murmushi ta yi ganin Amra a kwance an rufe mata ƙunar da wani yalolon mayani,tana sauke numfashi a hankali,ga wata ƴar'uwar cin mushenta da alamu ita ce take dawainiyar jinyarta,gefe kuma ga Hassy nan a zaune itama tana yin nata alhinin Da kallo suka bi Roxy gaba ɗayansu, ba tare da damuwa ba ta dubi Amra ta ce"ya jikin?" Cikin Muryar kuka ta ce"ke ce kika turo su ko? Dama wallahi ke nake zargi, tsinanniya kafira, Allah ya tsine miki albarka, shegiya arniya" Ɗan murmushi mai sauti Roxy ta yi,ta samu waje ta zauna ta ce"ashe kin gane kenan To ina fatan wannan jinyar ya zamar miki ishara ya hana ki aikata fasikanci har abada,dama na san ba za ki je asibiti ki zauna ba, saboda kin san me kika yi,ni lokacin bari na ƙasar ma ya yi,sai na ce Allah ya ƙara afuwa" Miƙewa tsaye ta yi,ta yi taku biyu sannan ta waigo tana kallon Amra fuska babu yabo babu fallasa ta ce"Gobe ki sake yunƙurin aikata hakan, musamman da wayo da dabara kamar yadda kika yi min,amma kuma kar ki manta,a duk lokacin da kika yi yunƙurin aikata fasikanci Roxy zata zamo a tare da ke,ta tarwatsa mummunan nufinki,sai anjuma ko?"tana kai wa nan ta fice daga parlourn,babu wadda ta iya sake yi mata magana a cikinsu,har Roxy ta fice *KANO STATE, NIGERIA* *HAISAM* A hankali yake fitowa daga office ɗinsa,a yau ne ya shirya aikata aikinsa gaba ɗaya,a yi ta ta ƙare kawai,don haka daga nan ma gidan malam Tajo zai wuce kawai Wayarshi ce ta yi ƙara, takaici ya kama shi ganin Nimra,ya ɗaga wayar ya kai kunne yana faɗin"I'm all ears Nimra " Cikin shagwaɓa ta ce"I'm going back to Abuja, Please ka zo ka kai ni airport, Please Love!" Cikin ƙosawa ya ce"Nimra meyasa kike son disturbing ɗina ne idan ina aiki?" Cikin shagwaɓa Nimra ta ce"amma ai baka da lokacina,kai kullum kana tare da aiki, yanzu haka za ka rinƙa yi kenan ko nan gaba?" "Okay wait, I'm coming "ya faɗa a gaggauce ya kashe wayar Yana ɓacin rai yana jan tsaki haka ya koma gida, lokacin Nimra ta gama shiryawa,tana ganinsa ta taso da farin ciki tana faɗin "Aunty Mariya sai mun yi waya,bye!"ta ja hannun Haisam suka yi waje yana bin ta da kallon mamaki, ita kuma Hajiya Mariya sai bin su da kallo take yi tana murmushi Har suka isa airport Nimra babu abin da take yi sai zuba surutu,shi dai jin ta kawai yake yi ba tare da yana gane abin da take cewa ba Kafin su yi sallama sai da ta yi ta ɗaukarsu hotuna,shi dai ya biye mata don su rabu lafiya,bayan ta gama ya yi mata sallama, sannan ya shiga motarsa,ya tayar ya bar airport ɗin kai tsaye a unguwar da iyalan marigayi malam Tajo yake ya yi parking,a bakin ƙofar gidan ya yi parking motarshi yana ƙarewa gidan kallo,da tunanin ta inda ya kamata ya fara Ganin zai ɓata lokaci ya sa ya yakice tunani ya ƙwanƙwasa kofar gidan,babban ɗan gidan ya leƙo,yana ganinsa ya rissina yana gaishe shi Haisam ya amsa da sakin fuska, sannan ya ce"maman naku tana nan kuwa?" Yaron ya ce"eh,bari na yi mata magana" Haisam ya ce"okay to yi maza,ina jiran ka"yaron ya koma cikin gidan don sanarwa mahaifiyar tasu Babu jumawa ta fito, Haisam ya rissina ya gaisheta yadda ya saba,ta amsa da sakin fuska sannan ta ce"bismillah! Ashe kaine,yau dai don Allah ka taimaka ka shigo mu gaisa sosai" Haisam yana murmushi ya ce"ai Mama yau maganar ma bata tsayuwa ba ce,mu shiga mu yi maganar,ina fatan dai yaran suna nan"Mama ta ce"eh duka suna nan, bismillah,shigo"babu musu Haisam ya bi bayanta,suka shiga cikin gidan *UNKNOWN LOCATION,KANO STATE, NIGERIA* *ROXY* Isowarta gidanta na sirri kenan ko minti biyar bata yi ba,ta shiga wanka,bayan ta fito sanye da bathrobe,kanta naɗe da ɗan ƙaramin towel ta ga wayarta da take ɓoye da number ɗinta ta sirri tana haske, kasancewar kowanne lokaci wayarta tana silent Bata kawo komai ba da farko, don ta ɗauka Oga boss ne,amma bayan ta shirya a cikin riga da wando hoodie tana duba wayar ta ga sabuwar number Tana kallo kiran ya katse wani ya shigo,ta dake ta ɗaga wayar ba tare da ta yi magana ba "Barka da wannan lokaci Madam Roxy!"ta ji muryar mutumin da ba zata taɓa mantawa ba ta doki dodon kunnenta Da ƙyar ta dake,ta saita nutsuwarta saboda yadda gabanta ya yi masifar faɗuwa,ta dake ta ce "Barka!wanene kai?kuma daga ina?" Ɗan murmushi ya yi mai sauti,sannan ya ce" na san ba za ki manta ni ba ai,amma kuma bari na sake yi miki tuni Sunana HAISAM ABDULMALIK MADAKA!kamar yadda kika sani, jami'in hukumar yan sanda na fararen kaya wato DSS, mai riƙe da muƙamin CSO Akwai rahotanni masu yawa akanki,na cewa ke ɗin ƴar safarar miyagun ƙwayoyi ce,kuma cikakkiyar ɓarauniyar yana,wato ƴar Yahoo,don haka hukumarmu tana nemanki,tana buƙatar ki kawo kanki,amma a shawarce kenan" Wani murmushi ta yi ta ce"okay! Kun gaji kenan?kun gaza da bibiyata ne?kun kasa?shine kuke nemana? To ku cigaba da jarrabawa, wataƙila a dace,amma kuma ka sani......." Ya cafke Maganar da faɗin "NO ONE CAN CATCH YOU ko? Mhm!anya kuwa?ko da ace an kama tilon ɗanki MUBARAK?" Cikin wani irin gigicewa da tashin hankali ta ce"what?what do you mean? Ɗana?why?why?me Mubarak ya yi muku? don't try to make that mistake,zan iya kisa akan shi,kar ka taɓa min ɗana,shine kaɗai ya rage min, shine rayuwata,don Allah!!!" "To malama FATIMA SHAHEEDA! If you are ready then sai ki kawo kanki ga hukuma,Ni kuma sai na sakar miki ɗanki,akasin haka kuma?"ya yi ɗan murmushi ya kashe wayar *To fa!dama Roxy ita ce SHAHEEDA?ita ce ƴar Ummeey wadda take kewa da bege a kowanne lokaci?wanne ɗa kuma ake magana akai?dama tana da ɗa?ya aka yi aka samu wannan kuskuren?to za mu ji dai,ku biyo Alkalamin Nusy bee a labarin GADAR TSAUTSAYI don jin yadda zata kaya* #Nusy_bee Page 16 Tashin hankali ba'a saka maka rana! faɗar irin halin da Roxy ta shiga ɓata baki ne,a haukace ta sake ɗaukar wayarta ta aikawa Haisam kira Sai dai ya ƙi ɗagawa,bata sare ba, cikin ficewar hayyaci ta cigaba da yunƙurin kira,sai da ta yi kira goma,a na sha ɗayan ya ɗaga Cikin tashin hankali ta ce"to ai ba ka gaya min inda zan same ka ba,ina zan kawo kaina ɗin?" Kai tsaye ya ce "ki yi tracking number na mana,ke ba software engineer ba ce?kuma a good tracker?try it mana" Cikin tsananin rauni ta ce"ba zan iya ba,don Allah ka taimaka min,ka gaya min address ɗinka na yi maka alƙawarin zan kawo kaina,amma ina roƙonka kar ka taɓa min ɗana,shi kaɗai ne farin cikin da ya rage min a duniya,idan ka cutar min da shi ban san yadda zan yi ba" Kai tsaye Haisam ya ce"to da kyau! Zan tura miki address yanzu,ina buƙatar na ganki a wajen nan da thirty minutes,ko kuma wannan yaron ba za ki sake ganinsa ba har abada" "Na yarda "ta yi saurin amsawa jikinta yana rawa Kashe wayar ya yi,babu jumawa message na address ɗin ya shigo ,tana gani ta miƙe tsaye,ko ganin gabanta bata yi sosai ta ɗauki hanya,a wannan lokaci ko ita ba zata iya misalta irin tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki ba Bata juma ba ta samu kanta a wani ƙaton fili da ba shi da nisa da gidanta, Haisam ta hango a kan motarshi a zaune yana murmushi game da tafa hannayensa,ta ƙarasa gabansa, cikin rawar murya ta ce"ina ɗana yake?" Yana murmushi ya ce"mu gaisa mana, Roxy zan ce ne ko Fatima Shaheeda?the most smartest girl I have ever seen in my life?" "I said where is my son Haisam? Kar ka yi min wasa da rayuwar yaro!i can't tolerate it anymore!"ta faɗa cikin fusata da tashin hankali Murmushi ya yi,ya nuna motar gabansu,ya ce"Men!"babu musu sai ga zaratan jami'ansu sun fito su biyar,hannun ɗaya riƙe yake da Habu,ɗan autan maman Fauziyya,matar marigayi malam Tajo Tana ganin Habu ta hau ihu ta nufi inda yake da gudu tana faɗin "ɗana!ku ba ni ɗana,shi kaɗai ne da Ni,don Allah ku ba ni,ku yi min duk abin da za ku yi min amma ku ƙyale min ɗana,shine rayuwata....." Sam bata ankara ba har suka buga mata ankwa suka ja ta zuwa motar Haisam,tana ihu tana fizge-fizge,tana ji tana gani aka tafi da Mubarak, wanda bata san inda za'a kai shi ba, tsabar tashin hankalin da ta riski kanta a ciki kafin a je station ɗin ma numfashinta ya ɗauke *BAYAN KWANAKI UKU* *MALIYA ESTATE* Izuwa yanzu gaba ɗaya ahalin Maliya sun samu labarin abin da yake faruwa a gari,wato dai yan jarida sun baza cewa wannan matashiyar yarinyar da ta addabi jami'an tsaro ta hana su saƙat take aikata abin da ta ga dama,ba kowa ba ce face ɗaya daga cikin ahalin a baya kafin ta hau GADAR TSAUTSAYI wadda ta kai ta halin da take ciki,wato Fatima Shaheeda,babbar ya a wajen uban wannan ahali wato Maliya family Yan jarida sun nemi Alhaji Yusuf Maliya don jin ta bakinsa akan bayyanar sunan ƴarshi a matsayin mai aikata babban laifi a ƙasa,duk da yadda ya kasance mutum mai mutunci da ƙima a idanun mutane Kai tsaye ya amsa da cewa tun kafin a zo wannan gaɓar ya daɗe da mantawa da ita a cikin ƴaƴanshi,ita ba ƴarshi ba ce, shiyasa ma ta daina amfani da sunan da ya saka mata,ta sakawa kanta wani A ɓangaren Hajiya Zainab kuwa yau kwananta biyu a asibiti,tun da ta samu labarin nan ta shiga tashin hankali sosai,amma hakan bai yi wa abokan zamanta ba,suka yi ta yaɗa maganar suna yar mata da habaici,hakan ne ya hauhawar da jininta,wanda ya tilasta mata kwanciya jinya Babbar yar Alhaji Ishaq, Maryam ce take kula da ita a asibitin,bayan ta samu sauƙi ta matsa a sallame ta,kai tsaye ta wuce gidan Hajiya Saudat Hajiya Saudat da bata juma da komawa ba don ta huta ta bi ta da kallo, ganin lokacin d aka shirya sallamarta bai yi ba, ba tare da tunanin komai ba Hajiya Zainab ta zube a gaban Hajiya Saudat tana kuka mai tsuma zuciya Kama hannunta ta yi, suka wuce zuwa bedroom ɗin Hajiya Saudat, Hajiya Saudat ta zaunar da ita a gefen gado tana kallonta, cikin kwantar da murya ta ce"a yi haƙuri,komai mai wucewa ne,komai idan aka koma ga Allah mai sauƙi ne, Zainab babu wanda ya isa ya ja da ƙaddara,idan kin yarda Allah ne mai yin komai ki gaya masa cikin dare da rana,yana kusa da ke,kuma yana ji kuma zai amsa kokenki Ke ɗin mai haƙuri ce, Allahn da ya jarabce ki shine zai kawo miki mafita, ba'a fushi da yi da iyawar Ubangiji Ki yi haƙuri Zainab,ki mayar da al'amuranki ga Allah" Zainab ta share hawayenta ta ce"Hajiya ni ba wannan ne yake damuna ba,sai yadda kishiyoyi suka saka ni a gaba, kowacce da kalar maganar da take yi saboda abin da ya faru,wasu a cikinsu ma faɗa suke yi wa ya sani ko abin da Shaheeda ta yi tarbiyyar gidanmu ne? Akwai ciwo sosai,duk wani haushin Alhaji da suka ji a baya a yanzu suna hucewa a kaina,ga maganar da ya je ya yi da yan jaridu, Hajiya,ba zan ɓoye miki ba,na ji ciwon wannan maganar,ya nunawa duniya ko babu Shaheeda zai rayu, Hajiya ba ni na ce akai Shaheeda makaranta ba, asalima wallahi ban goyi bayan hakan ba,ya zan yi? Hajiya ki ba ni shawara, zuciyata kamar zata fashe " "Haƙuri autar Hajiya, haƙuri, addu'a,istigfari,sallar dare,miƙa lamura kacokan ga Allah, sanyawa a zuciya cewa Allah ne mai yi,kuma shine mai jarabtar bawa, kazalika shine mai warware matsaloli,za ki ji zuciyarki fes zainabu Ki duba cewa,ban taɓa haihuwa ba,amma a yanzu ko wata mai ƴaƴa goman ba zata gwada min farin ciki da cin moriyar yara ba, akwai wadda ta haihun,amma kuma bata ci moriyar yaran ba,duk wanene mai yi? Allah Don haka yanzu ki tuna,akwai Allah,idan kika miƙa komai ga Allah,hakan ya isa" Hajiya Zainab ta goge hawayenta, cikin sanyin murya ta ce"in sha Allah Hajiya, Allah ya yi mana jagora " Hajiya Saudat ta dafa kanta ta ce"Ameen autar Hajiya! Allah ya albarkaci rayuwarki! Allah ya share miki hawaye, Allah ya zama gatanki auta " "Ameen hajiyata, Ameen, Hajiya yunwa nake ji" Hajiya ta yi murmushi ta ce"mu je ki ci ɗanwaken da na saka a yi min"babu musu suka miƙe suka fice zuwa dinning area Da kanta ta bawa Zainab abincin,tana ba ta tana janta da hira, wadda ta sa ta manta da damuwar da take ciki,suka sha hirarsu abin su Hajiya Zainab bata tafi gida ba sai da Alhaji Yusuf ya zo ya ɗauke ta da kanshi, Hajiya Saudat bata nuna masa damuwar komai ba,a mota ma suna tafiya yana ta kwantar mata da hankali cikin dabaru da hikima *MUYASSAR* Ɗaga kai ya yi yana kallon Arfa da take ta waƙa cikin farin ciki, cikin ƙosawa ya ce"Arfa na gaya miki kina damuna,ba ki bar ni na yi abin da yake gabana ba kin wani sako ni a gaba da waƙe-waƙen banza da na wofi,bana son sakarci fa!" "Sakarci?"ta faɗa tana fashewa da dariyar rainin hankali, ta ce "oh Allah! Wato sakarya ce ni,to ita kuma yar safarar cocain mecece ita?jan wuya?" Shiru ya yi bai ba ta amsa ba,ta ɗaure fuska gami da jan tsaki,ta ce"Allah wadaran naka ya lalace! Na godewa Allah da ya sa uwata ta gari ce da ta ba ni tarbiyya,gani nan a ɗakin aure ba a gari ina gantali kowa yana tsine min ba, lalacewar tawa bata kai jami'an tsaro su rinƙa bi na muna tsere da su ba, saboda ina yaɗa baɗala a bayan ƙasa,wa ya sani ma ko iya nan ɓarnar ta tsaya ko ta wuce haka?mu dai Allah ya tsare mu daga aikata irin wannan mugun aiki " Miƙewa Muyassar ya yi don ficewa daga ɗakin,don ya fara gajiya da irin wannan surutan na Arfa,don shi har yanzu bai ji soyayyar Shaheeda ta yi rawa a cikin zuciyarshi ba,ji yake yi waɗannan zantuttukan da Arfa take yi tamkar ana zuba masa ruwan dalma a cikin zuciyarsa,amma sai Arfa ta tare masa hanya Calmly ya dube ta ya ce"Arfa ba ni hanya,zan wuce " "Ba za ka wuce ba, saboda ina zargin waccan tsinanniyar tunda aka kama ta ka gigice,wa ya sani ma ko kana zagawa kuna haɗuwa? wataƙila ma ɗan da aka ce an yi mata tarko da shi naka ne,wanda kuka samu a rariya!" "Arfa!ko ki ba ni hanya na wuce ko na sauke miki mari!" "Idan ka fasa marina ba ka haifu cikin Umar da Sa'adatu ba!"bata rufe baki ba Muyassar ya sauke mata mari,bata gama gane kanta ba ya sake sauke mata wani sannan ya hankaɗe ta gefe ya nufi hanyar fita "Kan uban can kayyasa!ni ka mara? Muyassar Allah ya isa na,mugu azzalumi macuci,matsiyacin namiji, wallahi na yi nadamar aurenka,kuma kai ma na yi alƙawarin sai ka yi nadamar sanina,kuma ...." "Yadda kika yi nadamar aurena haka nima na yi nadamar aurenki, kin ga babu amfanin zaman nadama,don haka ki je na sake ki Arfa!!!"yana kai wa nan ya fice daga gidan da sauri,yana jin kururuwa da ihu da fizge-fizgen Arfa amma ko kallon hanyar bai yi ba,ya faɗa mota ya fice daga gidan *HAISAM* "Daddy yaushe za ka dawo?" Kallonta ya yi yana murmushi ya ce"ba zan juma ba in sha Allah,ki yi min addu'a sweetheart!" "Allah ya dawo da kai lafiya, Allah ya ba da Sa'a daddyna!" "Ameen mummyna! Much love"ta yi kissing ɗin shi a kumatu,shima ya yi kissing ɗinta ya ja mota ya fice daga gidan A bakin jail ɗin ya tsaya,ya nuna ID card ɗinsa,ba tare da ɓata lokaci ba aka ba shi hanya ya wuce da wayarsa a hannunsa Yana zuwa ya bayar da sunan criminal ɗin da yake son gani,babu ɓata lokaci ma'aikatan suka tafi don kiranta,shi kuma ya zauna a inda aka tanadar masa Babu jumawa aka gabato da Roxy,kanta a ƙasa, idanunta sun canja da alamun ta sha kuka sosai,sai dai babu alamun karaya a tare da ita,ta samu waje ta zauna,amma still kanta a ƙasa, idanunta a kan hannayenta da suke ɗaure da handcuff Murmushi ya yi sosai,ya ce"Barka dai! Sunana CSO Haisam Abdulmalik Madaka,Ni jami'in tsaro ne na farin kaya,wato DSS Tsarina ne muddin na saka abu a gaba tabbas sai na cimma shi, musamman idan ya zamana an wulaƙanta ni To!yau ga ni ga Roxy, wannan fitacciyar wanted ɗin, wadda take rayuwa cikin kwanciyar hankali tana gwara kan jami'an tsaro,amma sai ga ta a hannun waɗanda take rainawa hankali,malama Roxy Barka da zuwa komar Haisam!!" Kamar ba zata yi magana ba,sai kuma ƙasa-ƙasa ta ce"ina ɗana?" "Ban ji ba sosai, maimaita"ya faɗa yana aika mata wani kallon rainin hankali Ɗaga kai ta yi ta kalle shi,a hankali ta ce "cewa na yi ina ɗana mubarak? Wanne laifi ya yi maka ka kama shi?" Wata ƴar dariya ya yi ya ce "laifin da Amna ta yi kika saka aka yi musu barazana,ko ba ki san kukan ƴata yana tayar da bala'i bane?kuma muddin ta yi kuka sai na rama mata?" Hawaye suka zubo mata ta ce"to ba gani ba?ka rama akaina mana! Menene dalilin da ya sa zaka rama akan wanda bai takawa kowa komai ba?" Haisam ya ce"ita Amna me ta yi miki kika razana ta?" Tana goge hawayenta ta ce"ban yi da zummar na cutar da ita ba, ko da ban haihu ba na san zafin ɗa, ballantana ɗan da iyayensa da suke nuna masa soyayya ba sa raye" "Ban ga alamun kin san zafin ɗa ba Shaheeda,da ace kin san zafin ɗa da ba ki jefar da naki don wani ya tsinta ba,ba ki ji tsoron abin da zai same shi ba? Allah ya taimaka ya faɗa hannun na gari, alhamdulillah uwar riƙon nashi sai da ƙyar ta yarda da ni tunda na ambaci ɗaukar yaron na zo yi, sai da na yi mata bayanin wacece ke,da manufar da ta sa kika jefar da yaron ba ta kirki ba ce, sannan ta ba ni shi,a yanzu kuwa ba za ki sake ganinsa ba,zan ɗauke shi na mayar da shi inda zai yi rayuwa irin wadda kike yi,ko kina ganin za ki yiwa Allah wayo, shiyasa kika ɗauke ɗanki kika kai shi matsera wajen tarbiyya,ke kike lalata na wani?kina son shi har haka kika kasa tsayawa ki yi masa tarbiyya?a maimakon haka ma sai kika canja suna,kika canja addini don ki fi jin daɗin aikata ɓarnar da kike so? Ina jiran ba'asi Shaheeda!!"ya ƙarashe a ɗan tsawace, ranshi a ɓace, saboda ya ji zafin yadda ta wulaƙanta rayuwar yaronta fiye da komai #Nusy_bee Page 17 A hankali ta sunkuyar da kanta,hawayen da ya cika kwarmin idanunta suka zubo, cikin wata iriyar murya mai cike da raɗaɗi ta fara magana "Da ace kuskuren da na aikata a baya an same ni ne da irin wannan tambayoyin, ba'a watsar da rayuwata an ƙyamace ni ba,da wataƙila yanzu ina rayuwa a cikin farin ciki, wataƙila a gidan aurena, tare da ɗana,ko ma ƴaƴana,da rayuwata bata kasance cutarwa ga wani ba,da ta kasance mai amfani da alkhairi ga rayuwar mutane Amma ina!bakin alƙalami ya bushe,abin da alkalamin ƙaddara ya rubuta akaina babu makawa sai ya faru, wannan abu ne wanda ya kasance a rubuce tun kafin zuwana duniya Batun Mubarak kuwa,ban rabu da shi don bana son shi,ko don na fifita rayuwata ta duniya akanshi ba,asalima Mubarak shi kaɗai ne abin da nake da shi a duniya wanda nake tunawa ina da shi raɗaɗin da zuciyata take yi ya ragu,don haka wannan hanyar ita kaɗai ta rage min da zan tseratar da shi daga halaka Sannan maganar addini kuma,ban taɓa tunanin canja addini ba, don na canja suna hakan ba yana nufin na chanja addini ko ina wasa da nawa addinin ba Tabbas ina shaye-shaye,amma ba na wata alfasha bayan wannan,asalima na tsani aikatawa,shaye-shayen da nake yi ma ina yi ne don na gusar da damuwar da nake ciki ne,kuma a silar hakan na fara safarar miyagun ƙwayoyi " "Menene gaskiyar Maganar da ake faɗa na cewa kina yin Safarar muggan makamai? Ban ji kin yi batun ba" Kai tsaye ta ce"wannan ba gaskiya bane,amma idan ba ka yarda ba gani a hannunku,za ku iya bincike akaina " Haisam ya ja numfashi sannan ya sake faɗin"har yanzu ban ji wani dalili mai girman da zai iya sakawa ki aikata irin wannan mummunan aikin ba Shaheeda,ko ma me kika aikata ba za ki iya neman yafiyar iyayenki ki koma gare su ba" Ga mamakinsa sai ya ga ta yi ƴar dariya,ta dube shi sosai ta ce"na san mahaifiyarka ta rasu Allah ya ji ƙanta,amma mahaifinka yana raye,shi ɗin ya kasance yana zama ya yi shawara da kai,ya baka dama ka kare kanka idan ka yi masa kuskure ko ka zo da wani baƙon abu,to ka ƙaddara ba kowanne uba bane yake kasancewa irin mahaifinka " "Still I can't get you Madam! tukunna ma,duk me ya kawo wannan matsalar?" A hankali ta ce"ba komai bane ya yi silar tarwatsewar farin cikina sai faɗowar ARNOLD cikin rayuwata, wanda ya zama GADAR TSAUTSAYI da ta jefa ni ga tafkin ibtila'in da har yanzu nake ninƙaya a cikinsa" Kallonta yake yi sosai,ya ce "wanene kuma Arnold? Kuma menene ya haɗa rayuwarki da shi?" Lumshe idanu ta yi ya buɗe tana kallonsa, kafin ta ce"kana da lokaci?" Ya jinjina kai ba tare da ya yi magana ba,itama ta jinjina kai ta ce"good! To saurari labarin Shaheeda; *WAIWAYE.........* *WASU SHEKARU A CAN BAYA* Hausawa na cewa dare mahutar bawa,amma ga Shaheeda wannan maganar a yau dai ba haka take ba, wannan daren ya kasance dare ne mai cike da ɗimbin alkhari ga Shaheeda, daren farin ciki da annashuwa saboda alkhairin da zai same ta gobe Kasancewar ta yi nasara a jarrabawarta ta kammala secondary school,bayan an yi daga da Alhaji Yusuf da beloved yayanta Muyassar,a ƙarshe dai ya yarda zata je Belgium don cigaba da karatunta na tertiary inda zata karanci software engineering, course ɗin da take so kamar ranta Ummeey sam bata yi farin ciki da wannan zuwan ba,amma ko da ta yiwa Abba Magana faɗa ya hau ta da shi sosai,har sai da ta yi nadamar yi masa magana Ta shiga damuwa sosai, saboda bata da abokin hira a gidan sai yarta da mijinta da ba ita kaɗai ce da shi ba,to yanzu kuma ƴar tata ma zata sake yin nisa da ita Amma ita Shaheeda ko a jikinta,don dama akwai ƙuruciya sosai a kanta, kasancewar gobe ma zata yi birthday party ɗin da yayanta abin sonta Muyassar ya haɗa mata Tana nan zaune tana nazari,ganin nazarin ma ba zai yi ba sai ta miƙe tana murmushi ta nufi locker ɗinta,in da ta ajiye yar ƙaramar jotter ɗinta da ta yi list ɗin yadda shagalin nata na gobe zai kasance, bisa jagorancin yayanta abin sonta Muyassar, wanda duk abin da take so sai ya yi kokarin samar mata,ko da a ce kowa ba ya so a gidan kuwa Muyassar shi kaɗai ne sanyin idanunta a gidan, kasancewar sauran al'ummar gidan suna jin haushinta saboda bayyanannen bambancin da yake tsakaninta da yaran gidan a wajen mai gidan Kan gadonta ta koma ta kwanta,ta buɗe jotter ɗin tana kallon kyakykyawan rubutun nata tana murmushi "Ashe cake ɗin biyu ce ma,da babba da ƙarama,to zan gayawa yaya Muyassar ko ba'a siyo wata ba a siya min manya, don na san halin Ummeey na ba bari zata yi a kawo min cake ɗin nan ba,ba bari zata yi na yi birthday ɗin nan yadda nake so ya tafi ba Allah ya sa dai ta bari a yi casu,don wallahi tunda ta hana kama hall na san akwai abin da bata so a yi, uhm! Ummeeyna sai ita,ina sonki Ummeey na"ta ƙarashe maganar tana murmushi sosai "Wai Shaheeda dama har yanzu ba ki kwanta ba? Me kike yi haka da kika kai har yanzu idanunki biyu?" "A firgice Shaheeda ta kalli Ummeey da ta leƙo ɗakin ta same ta a zaune akan gadonta tana murmushi tana sambatu tana kallon jotter, Ummeey bata damu da yadda take da kame-kame ba ta ce"maza a kwanta,sai da safe"daga haka ta juya ta fice daga ɗakin Ita ma Shaheeda kwanciya ta yi tana murmushi,a hankali ta furta "zan yi kewarki Ummeeyna, Allah sarki ni,zan koma rayuwar wajen da ban san kowa ba,kuma babu wanda ya san ni,gashi kuma babu yayana Muyassar abin alfaharina,kuma uban gidan fita kunya"ta yi ƴar dariya tana rufe jotter ɗin Washe gari da safe Muyassar ya zo don ya kai ta super market don ta karasa siyayyar da ba'a yi ba ta birthday ɗin, Muyassar ya dube ta yana faɗin "a'a! Ka ga yar gatan Abba masoyiyar Ummeey,kuma ta hannun damar yaya Muyassar,ko na ce zuciyarshi" Murmushi ta yi tana faɗin "capacitated babban yaya! Jiya na yi kewarka fa, wayyo Allah yau za'a sha shagali" "Haba shagali ai abin sai wanda ya gani, yanzu dai da me da me kike buƙata?"ya faɗa yana kallonta cikin kulawa gami da buɗe mata ƙofar motarsa Shiga ta yi tana faɗin"mu je dai kawai,sai na ga wasu abubuwan zan tuna,amma dai new teddy mai kyau dai kar ka manta, sannan ka roƙi Ummeey ta ɗaga min ƙafa wannan karon na sha shagalina da teddyna,da ita ma zan tafi can Belgium in sha Allah "ta ƙarasa faɗa tana fari da idanunta Abin ya bawa Muyassar dariya,ya yi dariya sosai yana kallonta,ya ce"oh Allah! Wato dai duk inda ƙwaila take sai ta nuna hali,ina ke ina ɗaukar teddy bear har wata uwa duniya saboda Allah?" Kwaɓe fuska ta yi tana harararshi, ya yi ƴar dariya,ya sani ta tsani ya ce mata ƙwaila,a fusace ta ce"yau nake cika 16 years amma kana ce min ƙwaila,na kammala secondary school zan tafi University kai ma dai ka san na wuce ƙwaila ko?" Murmushi ya yi yana faɗin"au! Na manta fa,hakane ko?ashe an kusa shiga class, inyeeeee "murmushi Shaheeda ta yi tana fari,yadda ta yi farin ya ba shi dariya,amma sai ya yi fuska,don ya san idan ya yi dariyar zata iya saka masa rigima Sun yi sayayya sosai,wani abin ma shine yake cewa ta ɗauka, kamar yadda aka saba yau ma sai ya ja ta don biya,a raunane ta kalle shi ta ce"yayana ka ga kudin da yawa, kuma jiya Abba ya bani kuɗin amfani,why not ba za ka biya rabi ba nima na biya rabi?" Kallon banza ya watsa mata sannan ya wuce ya biya kuɗin ba tare da ya yi mata magana ba,aka fito musu da kayansu niƙi-niƙi Suna fitowa ta daka tsalle ta rungume shi tana murna tana faɗin"yayana na gode,na gode sosai, Allah ya biya ka"lumshe idanunshi ya yi ya buɗe,a hankali ya raba ta da jikinsa, saboda halin da ya ji tana ƙoƙarin ta jefa shi,a hankali ya ce"ke fa ba kya girma cutie,wuce mu tafi gida,kin ga lokaci yana ƙara ƙurewa" Bata yi musu ba ta faɗa mota,ya tayar suka wuce gida Taron ya ƙayatar sosai, don Muyassar ya tsaya mata,duk da a babban parlourn Alhaji Yusuf (Abba)aka yi, Muyassar ɗin ne kawai ya halarta sai ƙawayenta da ƴan makarantar su,amma babu wasu ƴan dangi ko ɗaya da suka halarta Ana daf da tashi daga taron ne Arfa ƙanwar Hajiya Ruƙayya ta zo,dama wani lokacin ta kan zauna a gidan,tana fakewa da wajen yayarta ta zo,amma a zahiri ba haka abin yake ba,wajen Muyassar take zuwa,don ta ganshi,don shi ko kallon banza ba ta ishe shi ba ballantana ya kula ta Kai tsaye kuma babban parlourn da ake gudanar da shagalin birthday ɗin Shaheeda ta nufa,tana shiga ta bi parlourn da kallo,gashi nan an yi decorating wajen,har da golden numbers 16 Taɓe baki ta yi,kai tsaye ta nufi wajen Muyassar da yake tsaye da Shaheeda suna yanka cake ta biyu suna murmushi,tana isa wajen hankalin kowa ya dawo kanta Ta ɗan yi ɗan murmushin yaƙe tana kallon Shaheeda da ta zuba mata idanu ta ce"happy birthday!" Shaheeda da ta yi tsammanin wani abu dabam, saboda sanin halin Arfa,ta yi fari yadda ta saba ta ce"thanks" Muyassar da yake kallonta yana murmushi ya raɗa mata a kunne"ƙwaila ƙanwar bera!" Diddira ƙafa ta fara yi na shagwaɓa, Muyassar ya riƙe hannunta yana murmushi,sauran ƙawayenta kuma suna dariya,ya ja hannunta suka koma kan yanka cake ɗin "Muyassar wajenka na zo fa!"s cewar Arfa tana danne ƙuncin da take ji a ranta game da wannan tsinanniyar yarinyar da ta addabi kowa,a cewarta Kafin ya yi magana Shaheeda uwar tsiwa ta kalle ta tana murguɗa fuska ta ce"sai dai fa ki yi haƙuri ki jira, yanzu yana cikin lokacin ƙanwarshi ne abin sonshi,amma idan mun gama zan bar miki shi"ta ƙarasa maganar tana murmushi Cikin ɓacin rai Arfa ta dube ta tana faɗin "ke ban yi miki magana,ko shi ba shi da baki ne? To bana son rashin kunya,dama an gaya min cewa ba ki da kunya,idan kika yi min sai na zane ki wallahi" Shaheeda ta gatsine fuska ta ce"tabɗijam! wallahi mai dukana a yanzu sai dai ruwan sama,gidan ubana fa kika zo kina son ki janye min yayana sannan kike maganar dukana, wallahi wuce nan,ki tafi,idan kina da muhimmanci a wajensa zai zo inda kike"Muyassar ya dubi Shaheeda wadda sam bai yi mamakin rashin kunyarta ba in dai ita ce, fuska a haɗe ya ce"Shaheeda kar na sake jin bakinki" Yana kai wa nan ta cafke da faɗin "sai in yi mata shiru ta yi ta gaya min son ranta?" Muyassar ya ce"amma ai ta girme ki ko?to bana son rashin kunya,idan ba haka ba kuma za mu raba hanya da ke"ya dubi Arfa ya ce "Madam a ɗan ba mu waje,ki zauna wajen su Mamie,idan na gama in sha Allah zan shigo "ta bi shi da kallo cikin ɓacin rai, Shaheeda ta faki idanun Muyassar ta yi mata gwalo Rai a ɓace Arfa ta koma sashen yayarta ta gidan,wato Hajiya Ruƙayya, wadda ta yi ɗaiɗai a parlounta tana ba wa cikinta haƙƙinsa,tana shiga ko sallama bata yi ba ta samu waje ta zauna idanunta yana tara ƙwalla Hajiya Ruƙayya ta ɗago tana kallonta da mamaki, kafin ta ce"ikon Allah! Arfa yaushe kika zo?" Ƙwallar idanunta ta goge ta ce"ban daɗe da zuwa ba aunty" "To kukan me kike yi daga zuwa?" Hawaye suka sake zubowa Arfa,ta dubi Hajiya Ruƙayya ta ce"aunty wallahi na tsani yarinyar nan,kin san ina tsananin son Muyassar,nema take yi ya shiga tsakanina da abin da nake so,amma wallahi zan sauke mata dattin da yake cikin kanta,gashi shima sai ya yi ta bin ƙaramar yarinya tana saka shi yin abubuwa kamar wani mara hankali,aunty wallahi ba zan iya zuba idanu ina kallonsu a haka ba, salon ta ƙara girma ma a ce za'a haɗa su aure" Hajiya Ruƙayya ta ce"don Allah daina wannan tunanin,idan shi mahaukaci ne uwarshi ai ta san me take yi,don haka ki kwantar da hankalinki,ki ci gaba da neman soyayyarshi,idan ma ya ƙi yiyuwa ni sai na yi wa uwar Magana, yadda na shigo gidan nan ke ma ta matsa miki hanya ki shiga gidan ɗanta,ba wani wayo gare ta ba" Arfa ta goge hawayenta ta ce"amma aunty wallahi bana ƙaunar yarinyar nan,sam bata da tarbiyya,ta raina mutane,ga haushin yadda take mannewa Muyassar kamar wani ubanta " Kar ki damu, za'a yiwa tufkar hanci,amma tabbas sai kin mallaki Muyassar Arfa" #Nusy_bee Page 18 Hankalin Arfa ya kwanta sosai,don ta san wacece yayar Tata Hajiya Ruƙayya,har ma ta saki jiki ta ci abincin da masu aiki suka jera mata Da daddare ta shirya cikin ƙananan kaya da suka bayyanar da surar jikinta ta tafi sashen Muyassar,wanda ya dawo nan tun bayan kammala karatunsa na tertiary da ya yi a abroad, Abba ya buɗe masa babban Company ya naɗa shi CEO Yana zaune yana duba wasu file yana shan green tea ɗin da ya sa a dafo masa ya ji knocking,da farko ya yi tsammanin Shaheeda ce, wadda ta ce zata kawo masa abincin da ta dafa masa,don haka ko kallon sashen bai yi ba ya ce"come in!" Shiga ta yi tana girgiza jikinta cikin salon jan hankalin ɗa namiji, yadda ta lafta turare da yadda ya ji ba'a yi sallama ba ya sa ya ɗaga kai da sauri yana kallonta,ya ɓoye mamaki da ɓacin ran da ya ji sun saukar masa a lokaci ɗaya ya bi ta da kallo, kafin ya dake ya ce"welcome!" Murmushi ta yi ta samu waje ta zauna,ta zare siririn mayafin da yake kanta, dogon gashin ta ya sauka har bayanta,a hankali ta cire rigar da take jikinta ta after dress tana kallonsa tana murmushi Fuska a ɗaure yake kallonta, kafin ya ce"lafiya dai ko?" Cikin narke murya ta ce "ziyara na kawo maka,na zo taya ka hira" Taɓe baki ya yi sannan ya ce"na gode,amma da kin ɗan koma, kin ga aiki nake yi,idan na gama zan zo na same ki" Tana shirin yin magana Shaheeda ta yi sallama,ya ɗaga kai yana kallonta yana amsawa da murmushi akan fuskarsa, ta ƙaraso tana gyara riƙon tray ɗin hannunta Tashi ya yi ya amshi tray ɗin yana murmushi yana faɗin "birthday girl! Ya taron?" Dariya ta yi ta ce "kai yaya! Wani ma ya ji fa sai ya ce ba da kai aka sha shagali ba,ka cinye min cake,don ma dai kai ka siya" Dariya ya yi ya ce"ba zan kula ki ba Fatsima,ya gajiya?" Harararshi ta yi tana tura baki ta ce"nice Fatsima?" "A'a ba ke ba,waccan"suka yi dariya a tare cike da nishaɗi Zama suka yi suka fara cin abincin da ta kawo a tare, Arfa da ta ƙule ta bi su da kallo ta kawo wuya,ta dube shi cikin fushi ta ce"amma Muyassar wannan wanne irin wulaƙanci ne? Na zo wajenka amma za ka bagarar da ni kana kula wannan yarinyar mara kunya mara tarbiyya!" Muyassar ya dube ta,amma kafin ya yi magana Shaheeda ta yi shewa ta ce"cassss! Wato ma nice mara tarbiyya ba ma ke ba ko? Ko don an ce gwano baya jin warin jikinsa?" Rai a ɓace Arfa ta kalli Shaheeda ta ce"ke yi min shiru kafin na ɗauke ki da mari,mara kunya mara tarbiyya kawai!" Muyassar ya riƙe hannun Shaheeda da sauri yana faɗin"enough Shaheeda,bana son sake jin wani abu daga bakinki idan har na isa da ke,kuma idan har kina amfani da tarbiyyar da Ummeey ta ba ki" Shaheeda ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce"kuma fa maganarka gaskiya ne babban yaya,idan ina da tarbiyya babu dalilin da zai saka na rinƙa kula karnuka suna yi min haushi,kai ma ya kamata ka san yadda za ka yi da su kar a gansu a tare da kai mutuncinka ya zube" Muyassar ya dafe kai ya bi Shaheeda da kallo cike da takaici,bai yi mamakin wannan ɗanyen aikin nata ba in dai ita ce, abin da ya fi haka ma zata yi, saboda sam bata taɓa barin bashin magana a rayuwarta,bata da haƙuri ko kaɗan idan aka taɓo ta,a hakan ma don Ummeey tana tanƙwarata ne A nutse ta juya zata fita, Arfa da ta je ƙarshe ta shaƙo mata wuya, ba tare da ɓata lokaci ba suka kacame da dambe,don duk da cewa Arfa ta girmi Shaheeda da wajen shekaru huɗu zuwa biyar hakan ba ya ba wa Shaheedan tsoro ko kaɗan Da ƙyar Muyassar ya raba damben, sannan ya ja Shaheeda gefe ya rufe ta da faɗa "Ba cewa na yi ki yi shiru ki wuce ba? Ke dole dai sai kin nemi magana hankalinki zai kwanta? wai meyasa ba ki da haƙuri ne ko kaɗan?a haka kike son ki tafi Belgium ɗin da wannan shiriritar? To su ba za su ɗauka ba,idan kika yi musu wannan rashin hankalin zane ki za su yi,silly girl kawai!!" Tana huci ta ce"amma yaya kana kallo ta rufe ni da duka ko?ko ni jaka ce irinta da zan rufe idanu ta rinƙa dukana? Wallahi ko yanzu ta sake dukana sai na rama!" Arfa da ke gefe tana mayar da numfashi,don bata saba dambe ba,ta ce"sai dai uwarki ce jaka,ba ni ba" Babu ɓata lokaci Shaheeda ta ce"uwarki ta fi kama da jaka wadda babu abin da ta iya sai sakin ki kamar tinkiya kina liƙewa maza" Muyassar ya buge mata baki ya ce "ba na ce ki yi shiru bane Shaheeda?" Ƙwalla tana taruwa a kwarmin idanunta,amma don masifa da ƙi-faɗi ta hana ta zuba ta dube shi tana kumbura fuska ta ce"to ba kana jinta tana zagin uwata ba sai na zuba mata idanu? To wallahi ta sake zagina sai na dake ta" Muyassar ya dafe kai ya ce"Shaheeda wuce cikin gida,bana son ɓacin rai "babu musu ta wuce tana waƙar"mai wasa da maza karya! tunda na ganta na raina ta" Girgiza kai kawai Muyassar ya yi, cikin ɓacin rai ya mayar da kallonsa ga Arfa wadda ta sake ƙanƙance idanu alamun Masifa, saboda waƙar da ta ji Shaheeda tana yi,amma kafin ta fara magana Muyassar ya daka mata tsawa "What's wrong with you Arfa? Kin zo kamar abin arziƙi kin kama dambe da Shaheeda?wannan wacce iriyar wauta ce?" Cikin ɓacin rai ya ce"oh duk zagi da maganganun da ta gaya min ba ka gani ba sai nawa da na so sauke mata dattin kanta?" Kai tsaye ya ce"na san me nake yi Arfa, lokacin da Shaheeda ta shigo parlourn nan ko kallonki ba tayi ba,amma sai da kika shiga sabgarta kika janyowa kanki magana" Kuka Arfa ta saka ta ce"lallai ma Muyassar! Wato goya mata baya za kayi ko? Na gode!"ta miƙe a fusace ta bar wajen,shima ya ja tsaki sannan ya zauna don fara abincinsa da ya fara sandarewa Ita dai Shaheeda bata sanar da Ummeey abin da ya faru ba,asalima ko a fuska bata bari wata alama ta bayyana ba, musamman ma da ta samu ta rama abin da Arfa ta yi mata, wannan ya fi komai yi mata daɗi Ita kuwa Arfa tana kuka ta shiga sashen Hajiya Ruƙayya, Hajiya Ruƙayya ta ɗago daga sakawa Usman diaper da take yi ta zuba mata idanu da mamaki, Arfa tana shiga ɗakin ta zube a gefen gado tana gursheƙen kuka "Me kuma ya faru?" "Aunty ba ki ga irin wulaƙancin da Muyassar ya yi min ba saboda waccan tsilar koɗaɗɗiyar yarinyar Har zagina fa ya yi ya hankaɗa ni waje, gaskiya ni ba zan iya lamuntar wannan rashin mutuncin ba" Hajiya Ruƙayya ta ce"a'a dole gaskiya a ɗauki mataki kam,kuma ke ma ai sai da na ce ki bar komai a hannuna,za mu tattauna da uwar amma kika ƙi,idan kuma kika cigaba da zuwa yana ci miki mutunci ni babu ruwana" "Amma aunty kin san irin son da nake yi masa,kuma shima ba ga alamu yana so na,kawai wani ƙulumboton waccan tsinanniyar yarinyar da uwarta suka yi ya guje ni" "Idan ma ƙulumboton ne ni na san yadda zan yi ai Yanzu ki kwantar da hankalinki,da kaina zan yi masa magana in sha Allah,idan kika ga bai aure ki ba to sai dai idan mutuwa ya yi,amma in sha Allah aure tsakaninku kamar an yi an gama ne Ki daina damuwa da wannan ƙwailar yarinyar, saboda ko da ace sonta yake yi kamar yadda kike zargi ni na san Mahaifiyarsa ba zata taɓa bari ya aure ta ba" Wata wawiyar ajiyar zuciya Arfa ta yi,ta ce"ko aunty? Amma menene dalilin?" Kai tsaye Hajiya Ruƙayya ta ce"babu jituwa tsakanin Hajiya Zainab da Hajiya Sa'adatu ne,shine dalilin Shekarun baya da Hajiya Sa'adatu ta zauna anan Alhaji ya fifita matarshi akanta, shine ya sa take jin haushinta "shiru Arfa ta yi tana taɓe baki Daga lokacin babu wanda ya sake shiga harkar wani tsakanin Shaheeda da Arfa, musamman da Muyassar ya samu Shaheeda ya yi mata faɗan duk abin da Arfa zata yi mata kar ta sake tayar da kai ta kalle ta, murmushi dai kawai Shaheedan ta yi masa a lokacin,amma ta gama ƙudurcewa a ranta duk lokacin da Arfa ta sake shiga harkarta sai ta ganar da ita kurenta, don wallahi sai ta yi mata duka a tsakiyar gidan,sai dai komai zai faru sai ya faru daga baya Sai kuma aka yi sa'a babu wanda ya sake shiga harkar juna a cikin su biyun,asalima kwanan Arfa biyu da zuwa ta koma gidansu Tafiya ta miƙa, lokaci ya yi ta ƙaratowa na tafiyar Shaheeda zuwa Belgium, murna da farin ciki kuwa a wajen Shaheeda ba'a magana,ji take yi babu ya ita a farin ciki,ga Muyassar mai sake zuga ta Sai dai a matan gidan babu wadda take farin ciki da wannan tafiyar,amma babu halin bayyanawa,duk da cewa Shaheeda ta san da cewa ummeey bata son tafiyar Tata amma ko a jikinta Kwana biyu ya rage jirgin su Aneesa ya ɗaga zuwa garin Ghent da ke ƙasar Belgium inda zata fara karatunta na course ɗin software engineering,idan Muyassar yana kiranta da software engineer har wani blushing take yi Yau zata koma kasuwa don siyan kayan tsarabarta kafin ta saba da Belgium,dangin su chaculate da biscuits da suka zama sune farin cikinta, Muyassar baya nan,yana gidansu,don haka ta kira shi a waya,kai tsaye ya ce ta biyo ta gidansu sai ya kai ta Driver ne ya kai ta har bakin gate ɗin,ta kalli drivern ta ce"baba Nuhu kawai ka tafi, babban yaya zai dawo da ni idan mun gama" Drivern ya ce "to babu matsala Hajiya"Shaheeda ta fice daga motar ta kutsa kai cikin gidan Hajiya Sa'adatu mahaifiyar Muyassar tana zaune a parlourn,tare da innayyo,kakarsu,ta daɗe da sanin su dukkansu babu mai ƙaunarta,amma ko a jikinta,tana ganin yadda mahaifiyarta take kuka saboda sun yi mata wani abin,amma ita gani take yi Ummeey bata yi niyyar ramawa bane,ta kan ce"gaskiya Ummeey wani lokacin gani suke yi kin cika yi musu shiru shiyasa suke yi miki abin da suka ga dama,amma wallahi da ni ce babu wadda ta isa ta taka ni ban murza ta ba,ko wacece kuwa, innayyo kawai zan iya ɗagawa ƙafa darajar auren ɗanta da nice ke" Ummeey ta kan ce"ke ƴarinya ce Shaheeda,da kin gane da kin ɗauka, haƙuri shine komai, shine maganin komai,da sannu komai zai wuce, duniyar ma nawa take?"Shaheeda ta kan taɓe baki, wannan azancin na Ummeey ba wani gane kansa take yi ba Sau uku tana yin sallama amma babu mai niyyar amsa mata,asalima cigaba da hira suka yi tamkar ba su san da Allah ya yi halittarta a wajen ba, Shaheeda ta taɓe baki ta ce"Allah ma ya gani na yi domin shi"ba tare da tunanin komai ba ta kutsa kai cikin falon ba tare da ta sake yin wata sallamar ba A fusace Mummy mahaifiyar Muyassar ta ɗago tana kallonta kafin ta ce"mara tarbiyya uban wanene ya ba ki izinin shigowa cikin falon nan?" Tana da abin faɗa,amma sai ta danne ta ce"yaya Muyassar ne ya ce na zo zai kai ni kasuwa,za mu ƙarasa siyayyar da za mu tafi Belgium "aunty Salma da ta shigo ta yi ƴar dariya tana faɗin "ai kuwa bakin naki ya iya faɗar Belgium ɗin! Ke dai ubanki ya dage sai kin bar ƙasa,bayan ga makarantu nan masu kyau a Nigeria,to Allah ya bada sa'a,don Allah kar ki ba su kunya Shaheeda, kin ga dai uban kuɗin da ya kashe wajen nemar miki gurbin nan"ta karasa magana tana zama akan ɗaya daga cikin kujerun falon Shaheeda ta yi murmushi,amma kafin ta yi magana a fusace Mummy ta ce"wannan tambaɗaɗɗiyar yarinyar dama kin daina bata bakinki Salma,amma ni ban ga alamun wani karatu da za'a yi anan wajen ba, sannan ki tashi ki fice daga gidan nan idan dai ba na ubanki bane" #Nusy_bee Page 19 Ƴar dariya Shaheeda ta yi tana faɗin "A'a fa Mummy,gida dai na ubana ne,kawai dai ba'a ciki yake ba ne,kuma ma,ni da na zo don na tafi?ai tafiya tawa ce" Bin ta suka yi da kallo cike mamaki da takaici,sanannen abu ne cewa Shaheeda bata da kunya,shine dalilin da ya sa kaf matan ubanta babu mai ɗaga mata yatsa,amma ba su yi tsammanin zata iya kallonsu ta yi musu wannan wulaƙancin ba "Ke Shaheeda!uwata da yayar tawa kike gayawa magana?ba ki da kunya?" Yatsina fuska ta yi ta ce"aunty yi haƙuri" Mummy cikin kufula ta ce"sai na yi maganinki mara mutunci matsiyaciya kawai! Shegiya mara amfani"miƙewa ta yi tsaye tana mayar da wayarta jaka tana faɗin "a'a fa Mummy!ina da amfani wallahi"daidai lokacin Muyassar ya shigo A kunnensa ta faɗa,don haka a kufule ya fara faɗin "Shaheeda mahaifiyata kike yi wa rashin kunya?" Babu tsoro ko shakka ta ce "cewa ta yi bani da amfani,ni kuma na san ina da amfani,ni gida ma zan tafi ba zan zauna a rinƙa tsine min ana kwashe min albarka ba,bayan uwata da ubana ba su kwashe min ba,sai anjumanku"ta wuce ta gaban Muyassar ta fice daga parlourn,suka bi ta da kallo Shima bin ta ya yi ganin ta ɗauki hanyar gate,ya ce"Shaheeda dakata anan,idan kika fice daga gidan nan sai na yi mugun saɓa miki"babu musu ta ja ta tsaya fuska a murtuke Mota ya koma ya ɗauko,yana zuwa daidai saitin da take ta buɗe ta shiga tana kumbure-kumbure Faɗa ya yi ta yi mata har suka isa super market ɗin da za su je,sai huci take yi amma bata yi magana ba,shima daga baya ya gaji ya yi banza da ita Duk da fushin da take yi hakan bai hana ta sakin jiki ta yi siyayyarta ba, Muyassar ya biya kuɗin suka kwashi kayan zuwa mota Har cikin gidan ya shigar da motarshi,har suka shiga babu wanda ya yiwa wani magana,sai da ya tsayar da motarshi ya juya yana dubanta,ko kallonshi bata yi ba ta fara yunƙurin buɗe motar ta fita Naɗe hannayensa ya yi a ƙirji yana kallon yadda take ta kokawa da mota, saboda bai cire lock ba,kuma ta san da hakan,amma saboda neman magana irin nata take ta kokawa da motar "Zan fita,ka buɗe min motar"ta faɗa tana sake ɗaure fuska "Ba zan buɗe ba, ba kina da hannu ba? buɗe da kanki" Tura baki ta yi,ya sauke numfashi sannan ya kira sunanta"Fatima!" Tana kumburi ta ce "na'am!" "Ba ni hankalinki my Teema" Bata yi magana ba ta juyo amma bata kalle shi ba,ya fara yi mata nasiha cikin nutsuwa da kwantar da kai,ta yi shiru tana jin shi, duk da cewa jin shi kawai take yi,amma gaba ɗaya nasihar iska take bi Sai da ya ga alamu kamar bata tare da shi sannan ya ce"Shaheeda anya kina ji na kuwa?" Gyara zama ta yi ta ce"ina jin ka mana,ka ce na daina faɗa manya suna faɗa ko?ko da ace sune suka yi min laifi na yi haƙuri"sai kuma dariya ta ƙwace mata, don maganar tashi gaba ɗaya a gwaranci ma take jin ta "Au dariya ma na ba ki Shaheeda? Ina magana kina yi min dariya?" Girgiza kai ta yi tana murmushi ta ce"a'a,wani abu na tuna,na gode yayana "kallonta kawai ya yi yana girgiza kai,ya san halinta abu ne mai wahala ta sauya Tana shiga part ɗin su kai tsaye ta wuce zuwa ɗakinta ta ajiye kayanta,ta fito tana ƙokarin kiran Ummeey, wadda ta san bata nan,tana gidan aminiyarta Hajiya jameela, wadda ta zama tamkar ƴar'uwarta uwa ɗaya uba ɗaya Bugu biyu ta ɗaga,ta shagwaɓe fuska tana faɗin"Ummeey har yanzu ba ki dawo ba?" "Ke bana son iskancin nan naki!ke ba yanzu kika dawo ba?kar ki ɓata min rai,ki ɗauki abinci ki ci, sannan ki ƙarasa gyara min kitchen ɗina,sai na dawo"ta kashe wayar Shaheeda ta miƙe tana murmushi ta ce"wai abinci,sai ka ce wata cus!ga chaculate da yaya ya siya min me zan yi da wani abinci?"ta ɗebo chaculate ta dawo parlourn ta kunna TV tana kallo tana cin abinta Da daddare bayan ta idar da sallar isha'i, tana zaune akan dardumar tana game a wayarta Ummeey ta leƙo,ta dube ta ta ce"Shaheeda sako hijabinki,ki zo abbanku yana son ganinki"babu musu ta miƙe,ta janyo hijabin da ta yi Sallah ta saka,suka fice zuwa sashen mahaifinta Alhaji Yusuf Da sallama suka shiga parlourn abban nata, Shaheeda ta bi mutanen parlourn da kallo,bata yi mamaki ba,don ta san hakan zai iya faruwa dabam Ummeey ce dai ta tsorata, saboda da ganin yanayin fuskokinsu ta san akwai abin da ya kawo su wanda ba mai daɗi ba, musamman da ya kasance Shaheeda ta je gidan nasu yau Har ƙasa ummeey ta kai ta gaida innayyo, wadda ta amsa ciki-ciki,ta dubi Hajiya Sa'adatu da fara'a tana faɗin "maraba da zuwa Hajiya! Sannunku da zuwa" "Yawwa sannu! yarki ce ta ɗago mu ai"ta bata amsa kai tsaye Hajiya Zainab ta samu kujera ta zauna tana kallon Shaheeda da ta zauna a kan carpet ɗin parlourn ta ce"kayya! Allah ya sa dai lafiya" "Duk wani abu da ya danganci wannan iblishiyar ƴar taki ai ba na lafiya bane Hajiya Zainab, Allah ya kyauta dai"da sauri Hajiya Zainab ta kalli Shaheeda, wadda ta yi tamkar bata ji abin da Hajiya Sa'adatu ta ce ba,itama ta ja bakinta ta yi shiru Alhaji Yusuf da ya gama amsa waya yanzu,ya dawo da hankalinsa kan mutanen parlourn yana kallon Shaheeda da ta takure waje ɗaya kanta a ƙasa,ya ce"ke Shaheeda ba ki iya gaisuwa bane?" Babu musu ta fara gaida innayyo, innayyo ta yi mata banza,bata damu ba ta gaida Hajiya Sa'adatu,caraf Hajiya Sa'adatu ta ce"Shaheeda ai ni yanzu ai ban isa komai ba,tunda ban wuce ki kalle ni ki zage ni ba" Ko a jikin Shaheeda, Abba ya dube ta cikin fushi ya ce"wato Shaheeda nunawa duniya kike yi mu mutanen banza ne ko? Mahaifiyar tawa da ƴar'uwata za ki je har gida ki zaga?" Hankali kwance ta riƙe haɓa ta ce"tooo! Abba yaushe aka yi haka kuma? Kowa fa ya san ba na zagin babba,kuma kai ma ka san haka Abba " "Au ƙarya aka yi miki tabbatacciya?"a cewar innayyo cikin fushi, Shaheeda ta yi kamar bata ji ta ba, innayyo ta cigaba da magana a fusace "Wato dai ba ki da ishashshiyar tarbiyya,na yarda da hakan tabbas,ke kuma jarrabawar da kika samu kenan,rashin tarbiyya,amma wallahi Zainab ba ki kyauta mana ba wallahi" "A'a fa innayyo!babu ruwan uwata,ya kamata ku rinƙa adalci,ba komai zai faru ku rinƙa ɗaukar alhakin baiwar Allah ba" "Ke Shaheeda! Shaheeda!!a gabana kike ƙaryata mahaifiyata? Irin rashin albarkar da kike yi kenan?" Kai tsaye ta ce"yi haƙuri Abba, Allah ya huci zuciyarka" Hajiya Sa'adatu ta ce"shegiya ƴar banza annoba!" "A'a fa Mummy,da ubana dai gashi kina gani, sannan kuma idan ni Annoba ce....."dukan da Abba ya kai mata ne ya sa ta yi shiru tana shafa fuskarta da ta sha mari, Abba cikin fusata ya ce"jaira kawai mara kunya,tashi ki bani waje "babu musu ta miƙe ta fice daga sashen hankalinta a kwance Tana fita gaba ɗaya parlourn aka mayar da akalar faɗan kan Hajiya Zainab da take zaune cikin fargaba,babu kalar maganar da innayyo bata faɗa mata ba, don ma dai Alhaji Yusuf yana tausarta, kuma ya hana Hajiya Sa'adatu magana Ranta a ɓace ta koma sashenta,kai tsaye ta nufi ɗakin Shaheeda wadda tuni ta manta abin da ya faru ma, chat ɗinta take yi da ƙawayenta tana sanar musu lokacin tafiyarta zuwa Belgium,sai ga ummeey ta banko kofar Tashi zaune ta yi tana kallonta, kafin ta nemi ba'asi Ummeey ta fara sauke mata mari a fusace,sai da ta yi mata biyu sannan ta fara masifa cikin fitar hayyaci "Shaheeda kashe ni kike son yi kenan? Ke yanzu ba za ki zame min sanyin idanu ba?ke kenan a cikin neman masifa,kawai burinki ki ganni ina ɓacin rai? da gaske annoba kike son zame min? To wallahi idan kika cigaba da yi min wannan halin sai kin fasa tafiyar, tunda da alamun ma idan kin je can abin da za ki rinƙa yi kenan, shashasha kawai!"ta fice cikin ɓacin rai Ƙwalla ta fara taruwa a idanun Shaheeda tana ƙoƙarin mayarwa, ɗabi'arta ce tun tana ƴar ƙaramar yarinya bata taɓa yarda ta yi faɗa ta yi kuka ko da ace an yi galaba akanta, yanzu kuma kuma bata kuka akan duk wani mutum da ta tabbatar ta fi shi gaskiya Wayarta ce ta yi ƙara, ganin Muyassar ne sai ta ɗaga ta kai kunne tana sauke numfashi, Muyassar yana jin yanayinta ya kwantar da murya ya ce"da wani abu ne Shaheeda?" "Ummeey ce ta mammare ni saboda su innayyo sun ce bani da tarbiyya na ce ina da ita" "Kayya!ke ma bakinki ba ya bari ki ci riba,kai mata wayar mu yi magana"a kufule ta ce"itama tana da waya" Ƴar dariya Muyassar ya yi,ya ce"haka ne,to bari na kira ta"kafin ma ya rufe baki Shaheeda ta kashe wayar ta Muyassar kuwa haƙuri ya yi ta bawa Ummeey yana gaya mata gaskiyar abin da ya faru lokacin da Shaheeda ta je gidan, Ummeey ta ce"ni ba wani abu nake jiyewa Shaheeda ba,mace ce, watarana zata yi aure,zata tafi gidan wani da wannan tsinin bakin ne? Ga taurin kai da gardama har ta yi mata yawa tun tana ƙaramarta, gashi sam bata da kunya ta yi ta ja min magana,ya kamata ka rinƙa yi mata faɗa "Muyassar ya rissina kamar wadda take gabanshi ya ce"in sha Allah Ummeey zata daina, yarinta ce kawai" "To Muyassar, Allah ya sa hakan" Muyassar yana ɗan murmushi ya ce"Ameen Ummeey " Washe gari da neman magana Shaheeda ta tashi, saboda baƙin cikin abin da aka yi mata jiya, shiyasa yau take neman wanda zata huce akanshi,don haka bayan ta gama karyawa ta koma wajen lambun gidan ta zauna A wajen lambun gidan sashen Hajiya Atika, wadda suke kira da Ammi yake,kaf gidan ta fi kowa yara,kuma ta fi son yara Tana zaune tana jin waƙar Alingo ta p-square tana bin waƙar Safwan ya zo zai wuce,yana ganinta ya yi murmushi ya ce "su yaya Shaheeda yan ƙasar Belgium" Yana direwa ta ɗora"su Safwan yan zaman gida Nigeria " Safwan ya ce"ai nima Ammi ta ce ina kammala karatun secondary za'a kai ni ƙasar waje na yi karatu " Shaheeda tana murmushi ta ce"ai dole ka je yaro tunda kishiyar gidanku ta je,kai dai ka buɗe ƙwakwalwar ko sau ɗaya ne don ka samu Sa'a ka tafi,ka san Abba ba ya biyawa daƙiƙi kuɗin makaranta har ƙasar waje,amma ni ka ga mahaifiyata na biyo"da kallo Safwan ya bi ta, kafin ya ce "ai nima ba daƙiƙi bane,kuma nima mahaifiyata na biyo" Ƴar dariya ta yi ta ce "kayya!yaro man kaza,kai dai je ka,kar allura ta tono garma"babu musu Safwan ya wuce zuwa sashensu Ƴan mintuna da shigarsu sai ga Ammi ta fito riƙe da hannun Safwan fuskarta a ɗaure, hankali a kwance Shaheeda ta ɗaga kai ta kalle ta, Ammi ta ƙaraso tana faɗin "ke Shaheeda! menene manufar tambayoyin da kika saka yaron nan a gaba kina yi masa? Wanne irin sakarci ne hakan?" Yatsine fuska ta yi tana yi mata kallon hadarin kaji ta ce"tambaya kuma? Ni?kuma a ina ma tambaya ta zama laifi?na tambaya an ba ni amsa, menene abin da ya kawo tuhuma kuma?" "Ke yarinya! Dama ana faɗin ba ki da kunya ba ki da tarbiyya,to ni na fi ƙarfin in yi da ke sai dai da uwarki,yar banza mara mutunci " "A'a ni ɗin dai,nice nake da lokacinki,amma dai ita waccan da kike ambata ki bar ta ta ji da abubuwan da suke gabanta, ƙasar waje ce dai sai na je,duk da zuga da busa da zungure da hankaɗe da ake yi wa malam Yusuf,babu mai shiga tsakanin hanta da jini,ni da ubana kenan"ta miƙe tana waƙar hanta da jini ba sa rabuwa ta wuce sashensu zuciyarta fes Hajiya Atika ta bi ta da kallo tana auna mata zagi,amma ita ko a jikinta, tunda dai ta samu inda ta juye nata ɓacin ran ai shikenan Yau ma dai tana zaune bayan isha'i tana game a laptop ɗinta da Muyassar ya siya mata sai ga Ummeey fuskarta a haɗe,ta ɗaga kai tana kallon Ummeey gabanta yana faɗuwa,a duniya babu mutumin da take tsoro,take shakkar ta ga sauyin fuska a tare da shi kamar Ummeenta,ko mahaifinta da ya kasance mafaɗaci bata damu da sauyawarsa ba kamar ta Ummeenta,don haka ta cigaba da bin ta da kallo gabanta yana faɗuwa #Nusy_bee Page 20 "Sannu da zuwa Ummeey"ta faɗa tana rarraba idanu "Yau kuma me kika je kika jangwalo? Dama ina ganin fitarki ta ɗazu na san ba banza ba,ina kika je Shaheeda?" "Ummeey lambu kawai na je,ce miki aka yi na yi wani abin ko?" "Ban sani ba,tashi ki tafi ubanki yana son ganinki"babu musu ta saka hijabi ta fice daga ɗakin, Ummeey ta bi ta a baya Da sallama ta shiga parlourn abban nasu,shi kaɗai ne ya amsa, Ummeenta ta yi sallama itama, Shaheeda ta samu waje ta zauna tana kallon Hajiya Atika da Safwan ta gefen ido,saura ƙiris ta fashe da dariya ganin yadda Hajiya Atika take ta cika tana batsewa Sai da ta gaishe su ɗaya bayan ɗaya, sannan Abba ya ce "Shaheeda wato iya shegenki ƙaruwa yake yi ko?" "To fa!su Fatima iyayen laifi!Abba me aka ce maka na yi yanzu ?" "Ƙaniyarki na ce! Wato dai ba za ki fasa halinki ba ko? Ɗazu me ya haɗa ki da Safwan har kika zagi mahaifiyarshi?" Kallon Safwan ta yi tana ƙwalalo idanu ta ce"innalillahi! Abba zagi kuma? Ka san dai bana zagin manya abba,zuwa ya yi fa yana gaya min magana akan zan fita ƙasar waje,kawai sai na ce masa ai ba'a kai daƙiƙai,ya ce ai shi ba daƙiƙi bane,na ce mu gani a ƙasa,shikenan fa! Oh Allah!Abba ka gani ko?dama fa na ce akwai mutanen da suke baƙin ciki da tafiyar nan tawa a gidan nan,ga alamu nan dai muna gani" Ummeey ta dubi Shaheeda cikin takaici,don ta tabbatar ba haka aka yi ba, saboda ba sabon abu bane a wajen Shaheeda cin zalin yara a gidan musamman Safwan,shi kuma kamar dole in dai ya ganta sai ya yi mata magana,amma kafin ta yi magana Abba ya yi abin da ya saba duk sanda aka yi case da Shaheeda a gidan "Shaheeda ni nake so ta tafi karatu ƙasar waje,da kuɗina na biya mata, babu wanda ya isa ya sa na janye sai Allah, don haka bana son sake jin an taɓo ta da maganar tafiyar nan Babyn abbanta!"ya faɗa yana mayar da hankalinsa ga Shaheeda,yana sakin fuska, Shaheeda ta yi murmushi tana faɗin"na'am abbana na kaina " "Allah ya yi miki albarka, Allah ya taimaka ya bayar da abin da aka je nema,na san ba ki da wasa a karatu, to ina son ki ƙara dagewa,banda kula abokan banza,banda shiririta duk da dai na san ba halayenki bane, Allah ya yi miki albarka "Shaheeda tana murmushi ta ce"Ameen Abbana " "Amma abban yara wannan ba yi bane!ya yarinya zata yi min rashin kunya kuma ka goya mata baya?" Kallonta ya yi fuska a ɗaure ya ce"Atika! Ba Shaheeda ba,duk ɗan da babba ya kasa jan girmansa a gabansa na ba shi umarni ya take,idan har kina son girmanki ki girmama kanki,sai Shaheeda ta girmama ki,ku tashi ku tafi,na sallame ku"kasancewar yau girkin Hajiya Zainab ya sa bata tashi ba,ta bi su da idanu kawai, Shaheeda tana murmushi ta rissina tana faɗin"sai da safe "sannan ta miƙe ta fice daga parlourn Ta san Hajiya Atika ba ƙyale ta ta yi ba, don haka ta tsaya kamar wadda take danna waya kawai, Hajiya Atika ta zo kusa da ita, cikin ɓacin rai ta ce"yarinya ƙanƙanuwa kamarki,wai kin iya haddasa husuma,wata ƴar tamilo da ke,Ni za ki haɗa da mijina?to......" "Tooooo! Ƴar tamilo kuma?"Shaheeda ta faɗa tana kama haɓa tana zare idanu" "Eh na faɗa! ƴar tamilo, ƴar tamilo ma da haka take da an shiga uku" Shaheeda ta gyara tsayuwarta ta ce"idan ni ƴar tamilo ce ke kuma sai yaya kenan? Tsaka ko?" "Shaheeda nice tsaka? Har fitsara da rashin mutuncin naki ya kai ki kira ni da sunan dabbar da Allah ya tsinewa?" "A'a to menene marabarki da ita? tunda dai Allah ya tsinewa mai hassada,kuma ga ki nan a cikinta dumu-dumu,kin ga kuwa babu laifi don na kira ki haka Kin ga ni mu bar wannan zancen, gobe zan tafi karatu Belgium,a saka mu a addu'a "tana kai wa nan ta sa kai da nufin wucewa A fusace Hajiya Atika ta ce"Allah ya tsare ni da yi miki addu'a,sai dai na roki Allah ya tsine miki albarka " Shaheeda ta ce"ko da yake bar shi ma, addu'a yawanci za ki ga ana neman malamai su taya mu da ita da manyan bayin Allah,don ta karɓu,amma ke kika yi addu'a da wannan bakin baki ai sai ki sa ma ta ƙi karɓuwa,sai anjuma "ta wuce tana ƴar dariya ranta fes, Hajiya Atika ta gama masifarta ta ja hannun Safwan da ya yi shiru yana kallon ikon Allah ta wuce sashenta ranta a ɓace Washe gari aka tashi da shirin tafiyar Shaheeda zuwa Belgium,tun safe Muyassar ya zo gidan, don shine zai kai su airport Suna zaune a ɗakinta suna haɗa kaya ya dube ta da kulawa ya ce"Shaheeda!ni dai roƙona a gare ki don Allah kar ki ce komai aka yi miki za ki rama,ki zama mai haƙuri mana,babu wanda ya kai mai haƙuri riba,amma rashin haƙurin nan babu abin da yake haifarwa sai dana sani " A kaikaice ta kalle shi ta ce"tunda na zo duniya nake ganin yadda ake ƙuntata ran Ummeey,mace mai haƙuri,sai dai ta ƙunshe baƙin ciki ta yi kuka,ka san da haka kai ma,ko da baka san wani ba ka san wani, tunda wani lokacin a gabanka ake ci mata mutunci,amma ni ko yaya aka taɓa ni ina tabbatar da cewa na sauke bashin wannan tsokanar da aka yi min,da na sauke sai na ji ni wasai, lafiya lau,to kuma sai ka ce min wani haƙuri yana bayar da abin da rashin shi bai bayar ba? Ka ga abar maganar,raina zai iya ɓaci"Muyassar ya girgiza kai cikin jinjina halin Shaheeda ya ce"an bar ta babyn Daddy "ta yi murmushi tana wani blushing Da kanshi ya kai su airport ita da Ummeey,don kaf cikin matan gidan babu wadda ta bi su,hakan bai dame ta ba,ta cigaba da sabgoginta har ta bar gidan Uncle Habib ne zai kai ta har Belgium,don haka suka same shi a airport,ta ɗagawa Alhaji Yusuf hannu,suka shiga cikin airport ɗin zuciyar Shaheeda cike da matsanancin farin ciki da ɗoki 💫 Roxy ta ɗago da idanunta da suka juye saboda damuwa da rashin samun kayan mayen da bata yi ba ta zuba su akan Haisam da ya yi shiru tun ɗazu yana kallonta,a sanyaye ta ce"Shaheeda ta bar Nigeria cike da farin cikin zuwa Belgium, ba tare da ta san cewa ta je ne don ta haɗu da hanyar tarwatsewar rayuwarta da farin cikinta ba na har abada, wannan tafiyar ta Shaheeda ita ce silar komai a yau, har zuwa samuwar Roxy, wadda a tsawon wanzuwarta babu wani abu mai suna farin ciki ko walwala,babu wani abu mai suna jin daɗin rayuwa,sai tarin ƙalubale,guje-gujen neman matsera daga nan zuwa can,kuka a ɓoye, saboda a wannan ƙadamin Roxy ta san babu mai lallashinta,sai dai rauninta ya zama makami ga mai harinta"Haisam da ya zuba mata idanu ya ce"ta yaya?kuma meyasa?" Roxy ta ɗan girgiza kai ta ce"ba na ce ba dai,amma bari na cigaba "ta cigaba ba tare da ta sake kallonsa ba 💫 Kwanan uncle Habib biyu a Ghent yana kammalawa Shaheeda komai,ya samar mata lafiyayyen ɗaki a hostel ɗin su,ya ba ta dukkan abin da take buƙata sannan ya yi mata sallama ya bar Belgium zuwa Nigeria Kwata kwata rayuwa bata ba wa Shaheeda wahala a sabon wajen da ta tsinci kanta ba,ta cigaba da rayuwarta cikin farin ciki, tana zama cikakkiyar yar gari sai gashi har ƙawaye gare ta Bata yi cikakken watanni huɗu ba a Belgium ta iya Yaren dutch na ƙasar Belgium, sannan ta yi manyan ƙawaye Alice da Olivia A ɓangaren karatu kuwa Masha Allah za'a ce,don a first semester ɗin su ita ce ta yi musu overall,dama fa Shaheeda ba baya ba ta fannin kai, kaf gidansu babu wanda ya kai ta kwanya,tun tana ƴar ƙaramarta bata taɓa faɗuwa a jarrabawa ba,gata da sauƙin kai,ita matsalarta a rayuwa rashin haƙuri,amma duk da hakan Abba ya fi sonta fiye da kowa a gidan,kuma a bayyane yake nunawa,hakan ne ma ya ƙara rura wutar ƙiyayyar da mutanen gidan suke yi mata Ummeey da ta san hakan zai iya faruwa kullum kokarinta ko da ace Abba ba zai iya daidaita soyayyar da yake yiwa yaran nashi baki ɗaya ba amma aƙalla ya ɓoye irin son da yake yi mata,sai dai inaaa!ko saurarenta ma baya yi,akan Shaheeda ba ya sauraren kowa Yau kwanansu biyu kenan da komawa Second semester, karatu ka'in da na'in ya ɗauki zafi ga Shaheeda, musamman da ya kasance wannan semester ɗin ita ce ta biyu,ko na ce ta ƙarshe a level one Yau ta tashi da menstrual cramps ɗin ta,kuma ya matsa mata sosai,gashi har jiri yake saka ta,ta samu da ƙyar ta sha magani sannan ta koma ta kwanta Ta juma tana bacci sannan ta farka,ganin har yanzu akwai sauran lecture ɗaya da lokacinta bai fita ba ya sa ta miƙe ta yi wanka,ta sauya kaya zuwa doguwar rigarta,ta ɗauki jakarta ta fita Sai dai ba ta yi nisa ba ta fara jin jiri, da alamu har yanzu jikin nata sai a hankali,amma haka ta dake ta cigaba da tafiya,don burinta ta samu ta yi attending lecture ɗin nan,don ta tsani fashin lecture Ba ta ankara ba ta ji jiri ya kwashe ta ya yi ƙasa da ita,har ta saddaƙar da ta faɗi ma,amma sai ta ji an riƙe ta,ta ɗago da sauri tana kallonsa Kyakkyawan guy ne sosai, waɗanda alamu suka nuna shi ba cikakken ɗan Belgium bane,amma ya fi kama da halfcast Da sauri ta ɗago daga jikinsa tana kallonsa,ƙatuwar sarƙar Cross ɗin da take wuyansa,da da tattoo ɗin da yake gefen wuyansa ta ɓangaren hagu ne ya alamtawa Shaheeda cewa shi ɗin ba musulmi bane,ta yi ɗan murmushin yaƙe tana faɗin "na gode"da Yaren dutch sannan ta wuce ta bar wajen Sai dai har aka yi lectures aka gama Shaheeda bata fahimci komai ba,asalima hankalinta yana wani wajen dabam,tunaninta ya tafi Da aka gama lecture suka fito ita da ƙawayenta Alice da Olivia, kasancewar su ma suna da rawar kai da surutu irin nata sai labarin yadda lecture ɗin ta kasance suke yi,amma shugabarsu a surutu da kauɗi ta yi shiru Olivia ce ta fara kula cewa kamar ƙawar ta su tana cikin damuwa,ta taɓo ta tana tambayarta,amma sai ta girgiza kai tana murmushi ta ce cikin Yaren dutch "babu komai,ko kin manta bana jin daɗi ne" Alice ta kalle ta ta ce"ai sai da na ce ki zauna kika ƙi,gashi nan duk kin yi wani iri"ita dai bata yi magana ba,suka cigaba da tafiya har suka isa hostel Kwana biyu da faruwar hakan Muyassar ya sauka a Belgium,kamar a mafarki su Shaheeda sun fito daga lecture suka ganshi,ai kuwa Shaheeda bata yi wata wata ba ta tafi da gudu ta ɗane shi tana murna, shine ya yi saurin riƙe ta don kar ta faɗa jikinsa yana faɗin "oh Shaheeda! Ke fa ba kya girma ko?"tana murmushi ta ce"na yi kewarku yaya,ina Ummeey?ina abbana?ya kowa da kowa?" Muyassar ya ce"babu tarba mai kyau,babu abinci, ballantana drinks,amma an fara yi min tambayoyi,sannu shugabar masu hankali" Zumɓura baki ta yi,ya yi murmushi,su Alice suka ƙarasa suka gaisa,sannan suka wuce wajen zaman ɗalibai a makarantar Gaban Shaheeda ya buga da ƙarfi sakamakon hango guy ɗin nan da ya riƙe ta sanda ta yanke jiki zata faɗi,ya yi kyau sosai,yana sanye cikin kayan da suka amshi jikinsa kalar blue black,ya mayar da hankali sosai akan littafin da yake gabansa,za alamu karatu yake yi Cikin ƙanƙanin lokaci Shaheeda ta nemi dirircewa,har sai da su Muyassar suka fara ganewa,amma sai ta wayance ta canja magana Sun juma a wajen suna hira cikin farin ciki ita da Muyassar,har sai da Guy ɗin nan ya tashi ya bar wajen sannan ta cewa Muyassar zata koma saboda ta duba darasinta na yau, Muyassar bai wani ja ba,ya ce "Allah ya yi jagora baby sister,ki dage da karatu,nima in sha Allah very soon zan koma na je na haɗa Masters ɗina" Waro idanu ta yi tana murmushi ta ce"like serious? Na bar Nigeria kai ma shine za ka bari? To amma da ba cewa ka yi tare za mu tafi ba?" Sosa kyakykyawar sumarsa ya yi ya ce"aure wai Mummy na ta ce zata yi min,ni kuma I'm not ready gaskiya, shiyasa zan koma, beside ina da wadda nake so,ita kuma zata ba ni wata" Murmushi Shaheeda ta yi ta ce"alright! All the best! Allah ya taimaka,ni zan shiga ciki to"suka yi sallama,ta nufi hostel shi kuma ya nufi komawa hotel ɗin da ya sauka #Nusy_bee Page 21 Washe gari Muyassar ya dawo,sun daɗe suna hira kafin ya yi mata sallama, Shaheeda tana murmushi ta ce"to yaya! Yanzu sai yaushe?" Muyassar ya ce"to kin ga dai yanzu karatu zan koma in sha Allah,ba zan ce kai tsaye ga lokacin da zan zo ba,amma kuma in sha Allah zan yi ƙoƙarin sake zuwa very soon,ke dai ki dage da karatu kawai, in sha Allah wannan little engineer ɗin sai ta zama hasken da zai haska Maliya family" Murmushi sosai ta yi,ta ce"yayana abin alfaharina, Allah ya tabbatar da bakinka,ina matuƙar son na ga na amsa sunan nan"tana murmushi tana juya kai ta ce"zan buɗe Company na kaina,zan zama shahararriyar yar sarrafen computer,zan ƙirƙiri apps da yawa waɗanda za su taimaka a harkar internet,kuma....." "To sarkin soki burutsu, Allah ya taimaka ya ba da sa'a kawai, I can't wait na ga wannan ranar "ya ƙarasa yana murmushi Ba su daɗe ba sosai suka yi sallama,ta koma hostel shi kuma ya tafi Kwana biyu zuciyarta ta kasa sukuni saboda wannan matashin Guy ɗin da ta gani, wanda tun ranar da Muyassar ya zo bata sake ganinsa ba Ta rasa yadda aka yi zuciyarta ta damu da tunaninsa,abin yana matuƙar damunta, har abin yake so ya shafi karatunta Kusan watanni uku kenan, karatunsu ya miƙa sosai,kuma suna daf da fara jarrabawar second semester, wadda daga ita ne zata tafi hutun session,zata koma Nigeria,gaba ɗaya yanzu bata da nutsuwa, kullum cikin karatu take da nazari,ita ce searching, practical, group discussion da sauransu Tana zaune a inda suke zama don karatu, hankalinta ya raja'a sosai,sai ga wasu samari sun zo sun zauna a kusa da ita suna kallonta cikin sigar rashin mutunci Sau ɗaya ta kalle su,ta cigaba da abin da take yi, ɗaya daga cikinsu ya ja mayafinta, ɗayan kuma ya ja handout ɗin hannunta ya yar a ƙasa, ganin abin nasu ba na ƙare bane sai ta miƙe,amma sai suka hana ta wucewa Kuka ta fashe da shi,suka kama dariyar izgilanci suna ta dungure mata kai,ta durƙusa a wajen tana kuka Ji ta yi sun yi shiru,tana ɗagowa ta ganshi yana miƙa mata hannu, ba tare da ya jira komai ba ya kama hannunta ya ɗaga ta suka bar wajen,bata yi masa musu ba ta bi shi tana kallonsa Wani waje dabam ya kai ta ya zaunar da ita,ya dube ta fuskarsa babu walwala, cikin yaren Dutch ya ce"ki rinƙa kiyayewa,ba su da kirki,za su iya yi miki wani abu da bai dace ba,ke mace ce,kar ki sake zuwa can" Jinjina kai ta yi a hankali, cikin sanyin murya ta ce"na ɗan kauracewa mutane ne saboda na samu damar karatu sosai" Shafa kanshi ya yi yana lumshe kyawawan idanunshi,ya ce"ya kamata ki kiyaye,ba a ko'ina za ki iya zama ba,sai anjuma"ya juya zai tafi,ta yi masa murmushi tana faɗin "na gode"ya ɗaga mata hannu ba tare da ya yi magana ba ya bar wajen Duk da yadda tunanin Guy ɗin da ko sunansa bata sani ba ya so ya hana ta sukuni amma ta dage da ƙarfin hali ta cigaba da karatunta,har ƴar rama ta yi,su Alice da Olivia har sun gaji da tambayarta me yake damunta Bayan sun kammala jarrabawa aka yi bikin fitar yan final year,an zaɓi wadanda za su yi speech a cikin ragowar ajujuwan,level one,two da three,a cikin waɗanda aka zaɓa a level one har da ita Speech ta yi mai kyau akan abin da ya shafi course ɗinsu na software engineering, kusan kowa da yake wajen sai da ya burge shi, gashi da turanci aka yi, English accent ɗinta ya burge kowa,ta sha tafi da hotuna kala kala Abin da ya bata mamaki a waɗanda suka yi speech na ƴan level three har da wannan matashin,wanda ta ji cikakken sunansa ARNOLD LIAM LAMBERT, wanda hakan ya ƙara tabbatar mata da cewa ɗan ƙasar Belgium ne,ko kuma mazaunin ƙasar Belgium,a takaice dai haifaffen ƙasar ne Shima ya yi speech mai kyau, yadda yake magana cike da jan aji da rashin son hayaniya ya yi matuƙar burge ta,don haka itama sai ta tsinci kanta a cikin masu tafa masa An yi biki mai kyau,an ci an sha,an tashi taro kowa yana cike da farin ciki Tana zaune a inda take zama sau tari, musamman idan tana karatu,yau ta buɗe wayarta tana chatting da yayanta Muyassar da Ummeenta,tana sanar musu da zata koma gida gobe,ta ji an ce "Hi!" Ɗagowa ta yi da sauri ta kalle shi,ya yi mata murmushinsa mai kyau,yana faɗin "good afternoon HERMOSA!" "HERMOSA?"ta maimaita tana kallonsa,ya sake yin murmushi ya ce"HERMOSA means beautiful in Spanish,can I have a seat?"bata yi musu ba ta nuna masa waje don ya zauna,ya zauna yana kallonta Cikin harshen dutch ta gaida shi,ya amsa yana murmushi,shima ya gaishe ta,ta yi murmushi tana kallonsa,ya ce"Good speech!" Da harshen dutch ta ce"kai ma ai ka yi magana mai kyau da ma'ana, tunda da alamu wata shekarar ku ne wadanda za'a shiryawa wannan bikin" Murmushi ya yi ya ce "na ji an ce ke ce mai overall a set ɗinku,ina taya ki murna" Kallonsa ta yi sosai ta ce"ya aka yi ka sani?" Ya ce"a set ɗinmu ni nake yin overall duk shekara,na kan bibiyi masu yin overall duk shekara, wannan karon kuma sai ta faɗo akanki,na yi mamaki kasancewar ki yar Africa,hakan ya faranta min sosai,daga wace ƙasa kika zo?" Kallonsa ta yi ta ce "kai ɗan africa ne?' Ya jinjina kai ya ce"mahaifina ɗan ƙasar South Africa ne, mahaifiyata ce ƴar Belgium,sai dai saboda domestic violence da ya faru da iyayen nawa tun ban san kaina ba mahaifiyata bata taɓa kai ni South Africa ba,a takaice ma,ban taɓa zuwa Africa ba" Shaheeda ta jinjina kai ta ce"Ni kuma haifaffiyar Nigeria ce,yar asalin ƙasar Nigeria " Ya jinjina kai yana murmushi ya ce"ya yi kyau Kenan ke ma za ki tafi ganin gida ne?" Shaheeda ta ce"gobe ma nake so na bar ƙasar nan zuwa Nigeria, na gama shirya komai" Ya jinjina kai ya ce"fatan alkhairi,zan iya samun numbernki?"tana murmushi ta saka masa,ji take yi kamar ta yi tsallen murna,kuma ta kasa gane dalilin hakan Washe gari jirgin su Shaheeda ya ɗaga zuwa Nigeria,farin ciki da ɗoki tamkar ta rufe idanu ta buɗe ta ganta a Nigeria,duk da bata so tafiya gaba ɗaya ba saboda sabon abokinta Arnold Tafiyar awanni bakwai ya kawo Shaheeda Nigeria daga Belgium, farin ciki kamar me don zata ga yan'uwanta,bata damu da yadda babu wanda ya zo daukarta ba,don Abba ba ya Nigeria,yana can harkokinsa na kasuwanci, Ummeey kuwa ba zuwa za ta yi ba ta sani, Muyassar ba ya ƙasar,a gidansu kuwa kaf babu wanda zai zo,don haka ko a jikinta ta hau taxi drop ta tafi gida Da ihun murna ta shiga gidan na su, Ummeey dai ta kasa ɓoye farin cikinta,ta tafi da gudu ta faɗa jikin Ummeey tana murna, Hajiya Jamila da ta zamewa Ummeey ƴar'uwa tana kallonsu tana murmushi,ta ce"ba'a ganmu bane ɗaliban turai?" Murmushi Shaheeda ta yi,ya durƙusa tana gaida su gaba ɗaya, Hajiya Jamila tana murmushi ta ce"ya karatun? Kin yi kyau abinki,kin murje kin yi jiki kamar ba ke ba, Belgium ta karɓe ki alhamdulillah" Cike da jin daɗi Shaheeda tana murmushi ta ce "alhamdulillah, Mummy ai karatun nasu da daɗi ba kamar a Nigeria ba" Hajiya Jamila ta ce "kar dai ki bari Salma ta ji ki,kullum a cikin complain take yi karatu yana ba ta wahala" Dariya Shaheeda ta yi ta ce"oh su Hajiya Salma manya, Ummeey bari na shiga ciki na yi wanka"daga nan ta miƙe ta shiga don yin wanka Bayan ta kammala hutawa Ummeey ta umarce ta ta je ta gaida matan gidan, babu damuwar komai a ranta ta sanya dogon hijabinta ta fice daga sashen Sashen Hajiya Atika ta fara zuwa,a matsayinta na babba a matan gidan,da sallama ta shiga,ta yi sallama ya kai uku amma babu amsa,duk da tana kallon Hajiya Atika a zaune tare da yaranta Safwan da Malika Kutsa kai ta yi ba tare da damuwa ba,tana zuwa ta samu kujera ta kame ta zauna tana murmushi, kafin ta ce "sannu Ammi,ina kwana?' "Wanene ya ba ki izinin zamar min a kan kujera? Malama tashi min akan kujera" Murmushi Shaheeda ta yi tana taɓe baki ta ce"Ni zuwa na yi mu gaisa,an daɗe ba'a haɗu ba To ya muka same ku?ya yaran?ya gida?" A kufule Hajiya Atika ta ce"ba'a gida ɗaya muke da uwarki Zainab ba? Je ki tambaye ta mana,ko kuwa mu uban naki ya sa ki raina?" Shaheeda ta girgiza kai ta ce"Ni yanzu na girmi faɗa,na bar wa marasa abin yi,kuma hankali dai daidai gwargwado na yi,na gaishe ki,bari na yi nan" Hajiya Atika ta ce"gwara dai ki tafi kafin na naɗa miki shegen duka anan" Shaheeda ta dakata daga yunƙurin fitar da take yi ta ce"a da ba'a daki Shaheeda ba sai yanzu da ta zama mutum? Ai mai dukan engineer Shaheeda a yanzu dai sai dai ruwan sama"ta sa kai ta fice tana waƙa Kai tsaye ta nufi part ɗin Hajiya Ruƙayya,tana zaune ita da ƙanwarta Arfa suna hira ƙasa-ƙasa,a ranta ta ce"munafurcin ya motsa kenan!"amma hakan bai hana ta kwarara sallama da ƙarfi ba Da sauri suka ɗago suna kallonta fuska a ɗaure,babu damuwa ta ƙaraso parlourn ta zauna tana kallonsu tana murmushi "Barkanku da dare,ya na same ku?ina wuninmu?" "Ke tsagera,iskancin da kike yi idan kin ga a baya na ƙyale ki wallahi a yanzu kika kuskura kika ce za ki yi mana wani rashin tarbiyya sai kin gane kurenki " Taɓe baki Shaheeda ta yi tana yi mata kallon banza, kafin ta ce"ke yanzu idan banda abinki wane ya ce miki idan kika ce za ki dake ni zan tsaya kamar itace ina kallonki? To kaf danginku babu wanda ya isa na yi masa wannan alfarmar don ki ji da wai Ni fa zuwa na yi don na gaishe ku na gaya muku na dawo,don kun san yanzu duba handout ma da tunanin assignment kawai ya isa ya sa na manta Allah ya halicce ku a duniya" Arfa tana yi mata kallon banza ta ce "karatu dai,ni wallahi ban yarda karatun ake yi ba,na fi zargin wata baɗalar ake yi da sunan karatu ana raina mana hankali " Dariya Shaheeda ta yi har tana kwarewa, kafin ta ce"to ai gwara ni,sai da na fake da karatun sannan ƴan iska irinki suke zargina,kar dai ki manta a gabana aka fito da ke daga ɗakin gardi,kar ki manta na san abubuwa da yawa,don haka ki yi rayuwarki nima na yi tawa,idan ba haka ba kuma allura ta tono garma"tana kai wa nan ta miƙe don ficewa daga ɗakin kafin ranta ya ɓaci a yi mara daɗi Arfa ce ta yi wuf ta shaƙo ta,bata yi wata-wata ba ta sauke mata mari, sannan ta hankaɗe ta,ta fice daga sashen Ko da ta koma sashen Ummeey ma bata sanar da ita yadda suka yi da matan uban nata ba,ta cigaba da harkar gabanta Ta ji daɗi sosai lokacin da ta buɗe Whatsapp ɗinta ta ga Arnold ya ajiye mata message,ta yi murmushi ta yi masa reply,bisa Sa'a yana online, suka cigaba da hira, wadda galibi ta karatunsu ce Washe gari ma Ummeey ta ce ta je ta gaida kakarta innayyo,bata yi musu ba ta je,amma baya sauya zani ba,don yadda suka saba wulakanta ta yau ma haka suka yi mata,ta ja tsaki ta fice daga parlourn Mummy ce ya finciko ta tana faɗin "ke! Wa kike ja wa tsaki?" Shaheeda ta yi murmushi ta ce"yi hakuri"sannan ta janye mayafinta ta fice daga parlourn Ko da ta koma gida ma bata yi wa mahaifiyarta batun komai ba, kamar dai jiya,ta cigaba da sabgoginta Tsawon kwanaki biyar da dawowarta kafin Alhaji Yusuf ya dawo,a tsakiyar gidan ta daka tsalle ta ɗane shi tana ihun murna,ya rungume ta cikin tsananin farin ciki da kewar ƴar tashi Hannunta ya kama suka nufi sashensa,matansa da sauran yaran suka rufa musu baya,matan kowacce da abin da take wassafawa a ranta Kamar yadda ya saba suka baje a babban parlourn shi da kuma yaranshi da matan ana hira,amma sai ya fi karkata akalar hirar ga ƴar gold ɗinsa Shaheeda, wadda ta taƙarƙare tana ta ba shi labarin karatunta da rayuwarta ta Belgium Ba su juma sosai ba suka amshi tsarabarsu kowa ya tafi,amma ban da Shaheeda da take sake buɗe sabon topic na hira Hajiya Ruƙayya da take da girki ranar ta dube su fuska a ɗaure ta ce"Alhaji ya kamata fa a ce ka sallami yarinyar nan, kowa ya tafi ita me take yi har yanzu?" Kai tsaye Alhaji Yusuf ya ce"hira da ubanta mana" Hajiya Ruƙayya ta ce"to sai ta tafi sai da safe ko? Don gaskiya saboda wannan ƙatuwar yarinyar ba za'a shigar min lokaci ba,dama dai ƙarama ce sai na yi uzuri" #Nusy_bee Page 22 A kaikaice Shaheeda ta kalle ta, sannan ta ɗauke kai, Abba ya dubi Hajiya Ruƙayya fuska a ɗaure ya ce "kishi kike yi da ita? Saboda ba ke kika haife ta ba?"tsam Shaheeda ta miƙe, Abba ya ce "dawo ki zauna Fatima" Shaheeda ta girgiza kai ta ce "Abba wani uzuri zan yi yanzu zan dawo"ta yi saurin ficewa daga parlourn don bata son rigima, kuma ta san halin Hajiya Ruƙayya,a kaf matan gidan ta fi kowa rigima Tana zuwa bayan ta yi wanka ta yi shirin kwanciya kan gadon ta ta haye ta cigaba da chat da Arnold, wanda har yanzu take mamakin sabo da shaƙuwar da suka yi,kuma take matuƙar jin sa a ranta Shaheeda ta cigaba da rayuwarta yadda ta saba a cikin gidan,ba ta shiga harkar kowa,amma duk wanda ya shiga tata ba'a rabuwa lafiya,kuma Abba ya goya mata baya sosai A ɗaya ɓangaren kuma shaƙuwarsu da ta ƙara ƙarfi tsakaninta da Arnold, wanda har zuwa wannan lokacin babu wanda ya san da zamansa, Ummeey dai ta kula ta sake liƙewa waya,amma bayan haka babu abin da aka sake ganowa Yawancin hirarrakin nasu akan abin da ya shafi course ɗin da suke karanta ne,na software engineering,ya koya mata abubuwa da yawan gaske,wasu kuma yana gaya mata yadda zata yi A haka ta cinye hutun session gaba ɗaya,sau uku Muyassar yana dawowa a wannan tsukin amma gaba ɗaya bata wani ba shi attention sosai Ta cinye hutunta lafiya,sannan kuma ta koma don ɗorawa daga inda ta tsaya Ranar da zata tafi kowa ya yi mamakin yadda ta kasance cikin farin ciki da ɗoki,amma babu wanda ya zargi wani abu, musamman yadda suka san Shaheeda take son karatun nan nata Muyassar ne ya mayar da ita makaranta,abin da ya ba shi mamaki ganin mutumin da ya zo zai ɗauke su ya kai su makaranta,ba kowa bane sai Arnold,kallo ɗaya Muyassar ya yi masa ya ɗauke kai,shima dai kallo ɗayan ya yiwa Muyassar ɗin sannan yake tambayarta hanya Tana murmushi ta ce"hanya lafiya ƙalau,mun dawo Arnold ga yayana Muyassar,yaya Muyassar ga babban abokina kuma malamina Arnold"ta yi maganar cikin harshen turanci Murmushi Arnold ya yi ya miƙawa Muyassar hannu suka yi musabaha, Muyassar ya daure ya miƙa masa,suka gaisa, sannan Muyassar ya dubi Shaheeda da take ta murmushi ya ce "to Shaheeda,ni dai zan wuce ko? tunda kin ga kin samu mai raka ki"ya karasa maganar yana murmushin yaƙe Shaheeda ta ce"kai yaya!don Allah ka raka ni mana,mu je tare Ka ƙarasa ladanka Please!"ta ƙarasa a shagwaɓe Ɗan murmushi ya yi kawai yana satar kallon Arnold da ya naɗe hannu yana kallon su yana lumshe kyawawan idanunshi,da hakan ya zamar masa kamar ɗabi'a, sannan ya kalli Shaheeda ya ce "wani uzuri zan ɗan yi ne,but I promise you zan zo nan da few hours" Babu yadda ta iya ta jinjina kai,ya ce "to yayana,sai ka zo, Allah ya tsare min kai a duk inda kake"ya yi murmushi sannan ya tari taxi ya shiga ya bar wajen Su ma motar Arnold suka faɗa suka wuce zuwa makaranta,suna zuwa Shaheeda ta sauka ta wuce hostel ɗin su,shima ya wuce nasu Da yamma Muyassar ya dawo kamar yadda ya yi alƙawari,suna zaune a wajen da ɗalibai suke zama karatu,suna ta kallon mutane da suke wucewa jefi-jefi Muyassar ya dubi Shaheeda ya jefo mata tambaya "Shaheeda menene alaƙarki da wannan arnen?" "Wanne arne?"ta faɗa tana kallonsa da fuskar mamaki Ya ce"yaron da ya ɗauko ki a airport ɗazu " "Oh!wai Arnold?shine arne? Kawai abokina ne fa,kuma yana koya min karatu, shikenan fa" "To amma ko ma dai yaya ne ya kamata ki san irin mu'amalar da za kuyi da shi,ko da a ce shi ɗin musulmi ne, bana son wannan mu'amalar da take tsakaninku ta wuce misali Please" Shaheeda ta ce "yaya na san me nake yi fa,babu abin da zai faru sai alkhairi in sha Allah" Muyassar ya ce"to Allah ya sa"ta amsa da "Ameen"sannan suka sauya hira Kwanan Muyassar biyu a Belgium ya koma UK, Shaheeda kuwa ta cigaba da karatunta cikin kwanciyar hankali A hankali rayuwa take gungurawa Shaheeda a makaranta,tana cigaba da karatunta cikin kwanciyar hankali,a gefe guda kuma ba tare da ta ankara ba, soyayya mai tsananin ƙarfi ta sarƙe tsakaninta da Arnold,wanda zuwa lokacin hatta mamanshi ta san Shaheeda,don tana yawan kawo musu ziyara har makarantar Muyassar yana iya bakin ƙoƙarin sa na ganin Shaheeda ta rabu da Arnold don tuni ya fara ƙyanƙyaso kamar akwai soyayya tsakaninsu,hankalinsa ya tashi sosai,amma kuma da ya tuna babu aure a tsakaninsu sai hankalinsa ya kwanta Inda tashin hankalin yake shine lokacin da Arnold ya kammala karatunsa, Shaheeda ta tabbatar da cewa tafiya zai yi,sai kawai ta fashe masa da kuka Da ƙyar ya lallashe ta, cikin karsashi ya ce"ki kwantar da hankalinki, yanzu lokaci ya yi da ya kamata iyayenmu su san halin da muke ciki,mu sanar da su, saboda kin ga lokacin karatunmu yana ta ƙarewa,ni na gama nawa ma, saura naki" Kallonsa ta yi da sauri,ta ce"ba zai yiwu ba,aure tsakanina da kai ba zai yiwu ba Arnold" Gabansa ya buga,ya zauna a kusa da ita a ɗan rikice yana kallonta, kafin a hankali ya ce"meyasa? menene dalilin da ya sa kika ce haka? Ko kin daina so na?" Kai tsaye ta ce"soyayyarka na tabbatar da ita zan bar duniya,sai dai aure tsakanina da kai ba zai yiwu ba, saboda bambancin addini da yake tsakaninmu da kai" Shiru Arnold ya yi yana kallonta, kafin ya lumshe idanu a hankali ya buɗe ya sake zuba mata su , cikin sanyin murya ya ce" "To me zai hana ni da ke kowa ya yi addininsa tsakaninmu? Ni ban damu ba ma,ko haifar yara muka yi su bi addininki babu matsala,ni dai ina sonki" Shaheeda ta girgiza ta mayar da kan nata jikin kujerar da take zaune tana sauke numfashi,a hankali ta ce"hakan ba mai yiyuwa bane Arnold,a addinina bai halatta na aure ka ba,alhali kai ba musulmi bane" Arnold ya ce"amma akwai wata ƙawar mahaifiyata da ƴarinyarta ta auri musulmi" Shaheeda ta ce"ai dama ga mu mata ne,ga maza kuma babu matsala sosai" Arnold ya girgiza kai cikin ƙunar zuciya ya ce"kenan a musulunci ana tauye mace kenan? Da gaske ne bata da ikon yin abin da take so sai namiji?" Shaheeda ta yi saurin girgiza kai,ta ce"aure a musulunci yana nufin namiji ne shugaba, shugabancin nashi bai tsaya iya bayar da Umarni ba,har ɗauke dawainiyar auren duka,don haka ya wajaba ga macen ta yi masa biyayya a abin da bai saɓawa Allah ba,to tun fari idan ta auri wanda ya kasance ba musulmi za'a iya samun gagarumar matsala, shine dalilin da ya sa" Arnold ya jinjina kai a sanyaye,ya ce"na fahimta Yanzu menene abin yi? Fatima kin san ina sonki sosai,kuma ba zan iya rasa ki ba,kuma bana fatan na ga wannan ranar a rayuwata,ki taimaka min Fatima,kar ki guje ni " Shaheeda ta girgiza kai tana goge hawayenta ta ce"ba zai yiwu ba na gaya maka, muddin ba ka musulunta ba na tabbatar ba zai yiwu na aure ka ba" Shiru ya yi na wasu seconds, kafin ya ce"to idan na musulunta zan iya?zai yiwu ki aure ni?" Da sauri ta kalle shi cikin tsananin mamaki,ya jinjina kai cike da ƙwarin gwiwa,ya ce"soyayyar da nake yi miki zan iya sadaukar miki da komai,ciki har da addinina ma" Ihun murna sosai ta yi tana godewa Allah, cikin tsananin farin ciki ta ce"na yi maka alƙawari,muddin ka musulunta ni kuma kai ne zaɓina,kaine komai nawa,ina sonka,ina matuƙar sonka Arnold"shima murmushi ya yi jikinsa a sanyaye,ta gyara zama ta ce"wanne suna za ka koma idan ka musulunta?" Kai tsaye ya ce"duk wanda kika zaɓa min a shirye nake na karɓe shi "Shaheeda ta miƙe tsaye tana murmushi ta ce"tukunna dai, akwai wani course mate ɗina,yana karantar da mu addini sosai,zan kai ka ya ba ka kalmar shahada zuwa anjuma in sha Allah, welcome to the religion of peace sweetheart!"ta karasa faɗa tana murmushi, sannan ta miƙe tsaye,ya raka ta har bakin hostel ɗin su,sai murmushi suke yi cikin tsananin farin ciki Muyassar ta fara sanarwa da cewa Arnold zai musulunta,bai nuna mata komai ba a wayar,ya yi masa fatan alkhairi kawai, sannan ya sanar mata da zuwansa zuwa gobe don ya mayar da ita gida Bayan magriba da kanta ta zo har garden ɗin makarantar inda ɗalibai masu nacin karatu suke yawan zuwa,inda Arnold ya saba zama,ta ja shi suka tafi wajen Sheikh Mukhtar,wani course mate ɗinta ɗan asalin ƙasar Oman don a laƙanawa Arnold kalmar shahada Da kanta ta yi wa Sheikh Mukhtar bayani, shi kanshi ya yi mamakin yadda Arnold ya yarda zai musulunta saboda Shaheeda farat ɗaya,don ya san su Arnold iri su ne waɗanda suke da tsananin tsauri a addinin kiristanci Hakan bai hana shi farin ciki ba, ba tare da ɓata lokaci ba ya karantowa Arnold kalmar shahada, Arnold ya maimaita, aka ɗauki kabbara cikin farin ciki Daga nan kuma aka tambaye shi sunan da yake so a saka masa,tana murmushi ya nuna Shaheeda, wadda take jin kamar an yi mata gafara saboda tsananin farin ciki, Shaheeda tana murmushi ta ce "a sanya masa suna MUBARAK!" Murmushi ya yi yana kallonta, Shaikh Mukhtar ya cigaba da yi masa bayanan abubuwan da suke Shari'a ne,bayan ya gama ya dubi Shaheeda ya ce"malama Fatima za ki iya ƙarasa yi masa sauran bayanin,don na san kin san abubuwa da yawa, Allah ya saka miki da alkhairi"Shaheeda ta yi murmushi, Sannan ta yi musu sallama suka tashi ita da Arnold suka tafi Har bakin hostel ɗin su ta kai shi tana murmushi,shi ma murmushi yake yi,ta ce"I'm proud of you Mubarak! Kuma ina tare da kai duk runtsi,na san tarihin soyayya ba zai manta da mu ba"Mubarak yana dariya ya ce"na san sai an sake updating Romeo da Juliet,kuma mu za mu zama updated ones ɗin"dariya ta yi sosai,suka yi sallama,ta tafi shi kuma ya shiga hostel ɗin su Washe gari tun safe suke a tare,tana sake wayar masa da kai akan abin da ya shafi addinin Musulunci, kasancewar ya saka kanshi sai gashi yana ganewa sosai Ko da Muyassar ya zo don tafiya da ita kiri-kiri ta shaida masa ita ta fasa tafiya,ba zata koma Nigeria yanzu ba,da ya tambaye ta dalili kai tsaye ta ce "yaya ka ga Mubarak jiya ya karɓi musulunci,yana buƙatar koyon al'amuran addini sosai,kuma ka ga ni ya sani,ya kamata na zauna na koya masa" A kufule Muyassar ya ce "Shaheeda yarinta tana damunki wallahi! Ina malamin da ya ba shi shahadar?ki kai shi wajensa mana,ko shi bai san yadda ake koyarwar bane?sai ke uwar iyayi da neman suna?" Tana kumbura baki ta ce"ni dai yaya gaskiya ba zan tafi na bar shi ba,ba gaya maka yana buƙatar kulawata, sannan yaya ka daina ce min yarinya, I'm matured enough, eighteen years nake don haka don Allah a daina ce min yarinya" Gaban Muyassar ya faɗi sosai, don ya fara hangen wani abu dabam,ya daure ya ƙaƙaro murmushi yana faɗin "da alamu dai baby sister ta kamu ko?" "Yaya kamuwa kamar yaya?"ta jefa masa tambaya Kai tsaye ya ce"kin kamu da soyayyar abokinki mana,gashi nan da yake ta karɓe ki har ƙiba kike yi abinki " Ga mamakinsa sai gani ya yi tana murmushi sosai, ta ce"yaya soyayya akwai daɗi,kai ma ya kamata ka samu wadda zata dace da kai, you Will enjoy it ina gaya maka" Tashin hankali! Muyassar ji ya yi kanshi yana juyawa,amma ya dake ya kalle ta ya ce"ai ni tuntuni na sami tawa sahibar zuciyar " Shaheeda tana murmushi ta ce"wow! A ina take yaya?tana da kirki?" Kai tsaye ya ce"anan take,kai tsaye ma zan ce gata nan, ƙanwata,abar so na da alfaharina,farin cikin raina FATIMA SHAHEEDA!!!" shiru ta yi na ɗan lokaci tana bin Muyassar da kallo idanu waje kamar ta ga wata sabuwar halitta, kafin ta yi ta maza, murya a dashe"yaya ka san me bakinka yake faɗa kuwa?" "Na sani sosai Shaheeda,ba ki sani ba ko? To da soyayyarki na rayu,tun daga lokacin da na fara riƙe ki a hannuna kina jaririya a raina nake jin na samu matar da nake so, kowacce daƙiƙa ta rayuwata tunda kika zo duniya da tsananin soyayyarki nake bugun numfashi Shaheeda,ke ce farin cikina,ke ce ruhina,don haka Please Fatima, don't break my heart Please, I love you so much my Queen!" #Nusy_bee Page 23 Kamar wadda ake controlling da remote ta fara girgiza kai cikin sauri hawaye yana zubo mata,da ƙyar cikin in ina ta fara faɗin "a'a! A'a yaya!yaya don Allah ka daina, yaya ta yaya za kace kana so na?yaya ka tuna,nice fa kanwarka wadda kake ji da ita,ka yi min alƙawarin za ka tsaya min a komai,yaya idan ka ce za ka aure ni ai ba za ka samu damar tsaya min ba,don Allah yaya kar ka yi min haka,yaya let's change this topic please,don Allah yaya!" Muyassar ya ƙarasa inda take da sauri, cikin tashin hankali ya riƙo hannunta,muryarsa tana rarrabewa ya ce "Please Shaheeda! Please!!don Allah kar ki yi min haka,ban san yadda zan yi ba idan kika rabu da ni"ta runtse idanu ta ce "ka tanadi yadda za kayi yaya,don wallahi bana sonka!bana son aurenka!! Mubarak shine abin da zuciyata take so kuma take muradi,yaya don Allah kar ka yi abin da zan tsane ka,yaya ina sonka,kai ɗin best friend ɗina ne,kar ka zama rival a gare ni, Please yaya!!!"tana kai wa nan ta fizge hannayenta daga na Muyassar ta ruga zuwa hostel ɗin su, wani irin tashin hankali da ɓacin rai kawai take ji,da gaske take jin sam abin babu tsari wai Muyassar yana sonta da aure, mutumin da ta ɗauke shi tamkar wanda suka fito ciki ɗaya Arnold da yake zaune a gefe yana kallonsu,yana jin abin da suke cewa,amma kasancewar da Hausa suke magana ba ya fahimta,sai dai kuma ya fahimci cewa ko ma akan me suke magana ba mai daɗi bane Muyassar ya bi Shaheeda da kallo cikin tashin hankali, kafin ya ɗauke kai,ya nufi inda Arnold yake zaune yana kallonsa, Arnold duk da ya fahimci Muyassar ba ya sonsa,amma ganin ya zo sai ya saki fara'a yana miƙewa don su gaisa,amma Muyassar yana zuwa ya nuna shi da yatsa, cikin harshen turanci ya fara magana "Bana son na ji dalilin da ya sa kake tare da ƙanwata,amma bana son na sake yi maka kashedi akan ka rabu da ita,idan ka kuskura ka lalata min ƙanwata za ka gane bani da kyau, muddin ka yaudare ta sai na yi maka abin da za kayi nadamar zuwa duniya, ka je ka nemi daidai kai,amma ƙanwata ta fi ƙarfinka!"ya karasa faɗa yana hankaɗa shi Hankalin Arnold ya tashi sosai,har Muyassar ya yi gaba ya zo ya sha gabansa kamar zai yi kuka yana faɗin "don Allah ka saurare ni,da gaske so nake na auri ƙanwarka,na musulunta ma ko ba ta gaya maka ba?" Muyassar ya tsaya ya kalle shi cikin idanu ya ce"ka musulunta saboda ka auri ƙanwata ko? To ka koma addininka na baya,amma ƙanwata ba zata taɓa aurenka ba"ya bangaje shi ya wuce, Arnold ya bi shi da kallo cikin tashin hankali Abu Kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba,don Muyassar kai tsaye da ya koma Nigeria ya sanar da Abba abin da yake faruwa, hankalin Abba da Ummeey ya tashi sosai, Hajiya Ruƙayya da labarin ya yi matuƙar yi mata daɗi tana murmushi ta ce "Ai dama matsalar da ake samu kenan idan mace ta ce zata tafi ƙasar waje ba wani nata don ta yi karatu,to Allah ya sa ma ba su yi watsewarsu ba" Abba ya kalle ta fuska a ɗaure ya ce"in sha Allah watsewa sai dai ki ganta akanki,ba akan Shaheeda ba"Hajiya Ruƙayya ta taɓe baki ba tare da ta sake magana ba Washe gari Abba da kanshi ya je Belgium,a lokacin har Shaheeda ta yi kukan ta gama,sun sake komawa da Arnold wanda ya koma Mubarak, tare suke karatu,su yi hira tare,sai dai bai taɓa zuwa inda take ba,itama haka Hankalin Daddy ya tashi sosai, saboda ya fuskanci soyayyar da take tsananinsu ta yi nisa sosai,kuma ta nuna masa kiri-kiri so take ta auri Arnold, wanda ya koma Mubarak yanzu Tana kuka take faɗin "Abba saboda ni ya musulunta,ina sonshi sosai Abba,don Allah Abba kar ka raba mu" Abba ya ja numfashi cikin damuwa ya ce "Fatima!na farko dai yaron nan ban yarda da tabbacin Musuluncinsa ba,don ya musulunta ne saboda ya aure ki,ba saboda Allah ba,na biyu ko da ace ya musulunta saboda Allah sai dai ya yi haƙuri, don na riga na yi alƙawarin aurenki ga Muyassar,don haka zan same shi mu yi magana,ba zan aura masa ke ba" Ihun kuka sosai Shaheeda take yi tana roƙon Abba kar ya hana ta auren Mubarak, Alhaji Yusuf da Alhaji Aliyu da suka tafi tare hankalinsu ya tashi sosai,a ranar suka tattara Shaheeda suka mayar da ita gida, Alhaji Yusuf ya yi rantsuwa akan ta gama karatun Kamar taɓaɓɓiya haka suka dawo da ita, Abba ya wuce da ita sashensa,tana kuka tana kiran don Allah a bar ta ta auri Mubarak Duk yadda ya so ya yi mata bayani ya yi,amma hakan ya ƙi aiki,dama Shaheeda akwai kafiya,akwai ta da gardama da tsayuwa akan ra'ayinta,hakan ne ya fusata Alhaji Yusuf,ya sa aka ƙwace wayarta,aka rufe ta a sashen Ummeey Duk abin da yake faruwa Ummeey tana kallo,amma bata magana,sai dai can ƙasan ranta ita kaɗai ta san me take ji saboda tashin hankali,amma ta miƙa lamuranta ga Allah kawai,kuma ta ja bakinta ta yi shiru Tsawon sati biyu babu wani canji,gaba ɗaya Shaheeda ta lalace ta fige ta fita hayyacinta,ba damuwarta karatun da Abba ya hana ta ba, damuwarta raba ta da Mubarak ɗinta da ya yi, wanda ya zama wani sashe na rayuwarta Sai da ta yi watanni uku da dawowa sannan ta koma hayyacinta,shima ta zama silent bata yawan magana, Muyassar kuwa tuni suka yi uwar watsi saboda haushinsa da take ji saboda shine silar rabuwarta da abin da take so,a cewarta Shima bai damu ba,ya koma don cigaban karatunsa ya ba ta waje don ta sake hutawa A lokacin ne Abba ya ba ta Sabuwar waya da sabon layi, sannan ya shaida mata zai mayar da ita makarantar BUK don ta cigaba da karatunta,amma ya yi mata gargaɗi akan kule-kulen maza,da kuma focusing akan karatunta Sannan ya ƙara da faɗin "maganar mijin aure kuma na riga na zaɓar miki, Muyassar shine mijinki,bana son na sake jin kin kula wani,tashi ki je, Allah ya yi miki albarka"ta miƙe jiki babu ƙwari ta tafi bayan ta yi masa godiya Tana komawa ɗaki ta yi murmushi tana kallon wayar hannunta, ba tare da ɓata lokaci ba ta hau jera numbern da take ta ajiya a ƙwaƙwalwarta tsawon watanni, lokaci guda kuma ta wuce zuwa banɗakinta da yake cikin ɗakin Tana rufe ƙofar daidai da fara ringing da wayar da ta kira ta yi,ƙirjinta ya tsananta bugu,duk da cewa banɗakin babu zafi amma haka take sharce gumi, lokaci guda kuma kamar an tsayar da jinin jikinta ta ji ya ɗaga wayar "Hello!" "Mubarak!"ta faɗa muryarta tana rawa,kuka yana kubce mata Sai da ya yi shiru na wasu sakwanni, kafin a hankali ya ce "Shaheeda! Shaheeda ke ce?"ya furta cikin harshen dutch Ƴar dariya ta yi tana goge hawaye ta ce"Mubarak a ina ka san sunana Shaheeda?" Murmushi ya yi sosai,ya ce"a wajen yayanki, yanzu dai ba wannan ba, kina ina ne? Me yasa kwana biyu na ji ki shiru?" Tana kuka ta tsara masa abin da ya faru, shiru ya yi na ɗan lokaci,a hankali ta ce"ba zan iya rayuwa babu kai ba Mubarak,ina sonka,kai ne rayuwata,kai ne farin cikina,kai ne komai nawa,ka taimake ni na same ka kar na rasa ka, Please Mubarak" Mubarak ya ja ajiyar zuciya mai nauyi ya ce "to yanzu menene abin yi? Ya kamata na zo na samu Daddy na yi masa magana,ya ba ni aurenki " Girgiza kai Shaheeda ta yi ta ce"ba zai yarda ba, Abbana ya ce ya ba wa yayana Muyassar ni,ya yanke ba zai taɓa komawa baya ba, in dai aka tafi a haka na tabbatar ba zan same ka ba" Mubarak ya ce"to yanzu ya ake ciki?" Shaheeda ta ce"ban sani ba nima, makaranta ma an dawo da ni Nigeria " Mubarak ya ce"zan zo Nigeria,zan zo har makarantar taku,za mu tattauna mu samo mafita " Shaheeda ta jinjina kai ta ce"ina jiranka, Allah ya kawo min kai lafiya " Ya jinjina kai yana faɗin"very soon " Daga lokacin kuma Shaheeda da Mubarak suka ɗinke suka koma zuba soyayya sosai,amma a ɓoye, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta mayar da jikinta,walwalarta ta dawo kamar baya Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci aka gama yi mata komai na komawa makaranta,inda zata cigaba da karatunta daga level two a maimakon level three,Sam hakan bai dame ta ba, musamman da ya kasance akwai wani gagarumin shiri da suka yi ita da Mubarak,duk da cewa duk sanda ta tuna da hakan jikinta yana yin sanyi Allah ya taimake ta ta cigaba da zuwa makaranta,sai dai a ɓoye duk ranar da ta je makaranta sai sun haɗu da Mubarak,kuma da yake a Nigeria ne babu wanda ya damu da ya saka mata idanu Game da Muyassar ma sun cigaba da zumunci,sai dai ba kamar baya ba,don da ya watsar da ita ma,daga baya ya dawo, kuma da ya ga ta sauko sai suka cigaba da zumunci, sai dai ya karance ta tsaf bata son batun aure ko soyayya ya gifta a tsakaninsu Yau ma tana makaranta,tun sassafe da ta je bata shiga lecture ba,suna tare da Mubarak,ya dube ta ya ce"ina fatan kin gama shirya komai Fatima" Ta girgiza kai, cikin sanyin jiki ta ce"ina sonka sosai Mubarak,amma ba zan ɓoye maka ba,ina son iyayena, mahaifiyata ni kaɗai ta haifa,ina tausayin ranar da zata buɗe idanu ta ga bana kusa da ita, kuma bata san inda na je ba,ji nake yi tamkar ban kyauta mata ba" Mubarak ya dube ta sosai ya ce "to yanzu ya kike so a yi?ko aikinmu kike son ki dawo mana da shi baya?" Da sauri ta girgiza kai ta ce "a'a ba ka fahimci me nake nufi ba,game da...." "Relax Fatima! Nima kar ki manta mahaifiyata ni kaɗai gare ta,kuma ba ta amince ba kamar dai mahaifanki,amma na bijire mata na taho nan,duk da so da kewata da take yi,kuma hakan ba yana nufin bana sonta bane,amma kuma ina sonki Ni ba zan raba ki da iyayenki ba,a madadin haka ma bayan auren za mu zo mu gaishe su mu nemi gafararsu,amma ya kika ce?" A sanyaye ta jinjina kai,ya yi murmushi yana kallonta,suka cigaba da tsare-tsaren yadda za su yi aurensu su rayu cikin farin ciki da juna A wannan halin ne Mubarak ya yi mata visa ta hanyar wani abokinsa Solomon ɗan ƙasar Nigeria,ya yi mata komai na ƙasar da suka zaɓa don tafiya,su cigaba da rayuwar su a can,wato ƙasar Spain A ranar da suka shirya auren tun da safe ta sauka a makaranta,sai dai babu alamu na niyyar shiga lecture a tare da ita,tana zaune hankalinta baya jikinta tana jiran shigowar Mubarak Can ta hango shi,ta miƙe cike da farin ciki,ya ƙaraso inda take yana kallonta yana murmushi,ya ce"ki zo mu tafi babu lokaci, Imam yana can yana jiranmu "babu musu ta bi shi,suka fice daga cikin makarantar Kai tsaye wajen wani limami suka nufa,anan aka ɗaura musu aure,bisa sadakin wani zobe na diamond da ya ba ta Ta yi tsananin murna sosai na samun mallakin zuciyarta Mubarak,shima dai farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha,ya ɗauke ta ya ya mayar da ita makaranta Sai dai kuma yana dire ta karaf! idanunta suka faɗa cikin na Muyassar! tashin hankali ba'a saka maka rana, tuni jikinta ya kama karkarwa,sai dai kafin Muyassar ya ƙaraso wajen Mubarak ya ja motarshi ya tafi, Muyassar ya bi motar da kallo ranshi a tsananin ɓace Ƙarasowa ta yi tana murmushin yaƙe,ya watsa mata wani kallo ya ce"ke da wanene a cikin motar nan?" "Am....dama....um.. wani course mate ɗina ne......" "Karya kike yi Shaheeda!"ya faɗa cikin ɓacin rai yana ɗaga murya Shiru ta yi tana haɗe rai, ranshi a ɓace ya ce "last question, Shaheeda da wa kike tare a cikin motar can?" "Yaya na faɗa maka kuma ka ƙi yarda,na ce maka course mate ɗina ne fa,kuma...." "Ƙarya kike yi Shaheeda!kar ki sake yi min ƙarya!! A bar shi ma gaskiya kika faɗa, me ya haɗa ki da course mate ɗin ki har haka?ana yi muku lecture amma ke kina cikin motarshi?"ya sauke numfashi cikin ɓacin rai,ya dube ta fuska a ɗaure ya ce "Bari na yi miki gwari-gwari don ki san cewa ni ba shashasha bane Wannan kafirin saurayin naki ne Arnold,na san yana shigowa makarantar nan lokaci zuwa lokaci,kuma don ke ya zo ƙasar nan, to zan gayawa Abba gaskiya,tunda a nan ɗin ma ba ki fasa ba,gwara ya ɗauki duk matakin da ya so akanki sakarya! wadda bata san ciwon kanta ba!!!" #Nusy_bee Page 24 Cikin tashin hankali ta faɗi a gabanshi tana faɗin "don girman Allah yaya ka rufa min asiri don Allah yaya,na yi maka alƙawarin wallahi na daina,ka yi haƙuri yaya, Please yaya" "Look!tashi Please,bana son wata magiya,bana son damuwa tashi mu tafi gida" Tana kuka sosai ta ce"to don Allah ka yi haƙuri kar ka gayawa Abba, idan ka gaya masa na shiga uku,don Allah kar ka gaya masa Please" Numfashi ya ja ya ce "to na ji,amma kuma da sharaɗi,kar na sake ganinki a wajen wannan ɗan iskan"ta ce"eh wallahi,na yarda" Ya ce"to wuce mu tafi"babu musu ta faɗa mota suka tafi A hanya suna tafe yana lallashinta da yi mata nasiha,amma hankalinta baya kanshi,yana kan Mubarak da ya zama angonta,ranta fes,har suka sauka a gida Da ta koma tunani ta rinƙa yi na yadda za su bi dabararsu ta yi aiki,su bar gari ba tare da wata matsala ba,amma sai ta turawa message na cewa zata neme shi,amma shi kar ya sake nemanta sai ta neme shi, saboda asirinsu zai iya tonuwa Tana ankare da yadda Muyassar yake yawan saka mata idanu,ko tana makaranta, ko tana gida,don haka kawai sai ya yi mata zuwan bazata,bata wani damu ba,take nuna masa bata gane me yake yi ba Ranar da suka shirya barin Nigeria gaba ɗaya jikin Shaheeda a sanyaye ta tashi, don sai da Ummeey ta kula da yanayinta, amma da ta tambaye ta sai ta ce babu komai,ta yi abubuwan da ta saba kafin ta tafi makaranta,amma kafin ta tafi sai da ta yagi takarda ta yi rubutu,tana goge hawaye ta ajiye akan dressing mirror sannan ta ɗan ɗebi wasu ƴan kayayyakin da take buƙata ta saka a jakarta sannan ta yiwa Ummeey sallama, ganinta da babbar jakar makaranta bai sa Ummeey ta kawo komai ba, saboda dama wasu lokutan tana ɗaukar babbar jaka Tana fita suka haɗu da Muyassar ya shigo,da murmushi ta gaishe shi,ya amsa yana faɗin "student! Ya karatun?" Ta ce"alhamdulillah yaya,kai ka gama naka ko?"ya ce"na kammala,kuma alhamdulillah komai normal, makaranta za ki tafi?"ta jinjina kai ba tare da ta yi magana ba Ya ce"okay bari na sauke ki ko?"babu musu ta shiga motar tashi suka fice daga gidan Bayan ya sauke ta ɗaga masa hannu ta yi ta shige aji,shi kuma ya tayar ya fice daga makarantar Tana tsaye daga venue ɗin nasu tana hangen motar Muyassar har ta daina ganinta,ta ba da wasu mintuna Sannan ta kira Mubarak ta sanar da shi Babu jumawa sai gashi ya zo,bata yi wata-wata ba ta faɗa motar,ya ja da gudu suka bar makarantar Kai tsaye daga nan airport suka nufa,komai ya zama ready,amma jirgin su da zai tashi zuwa Lagos,sai nan da awa ɗaya zai tashi,daga Lagos ne za su yi boarding jirgi na gaba zuwa Madrid,ita dai tana zaune ƙirjinta yana ta bugawa,gaba ɗaya ta ji ta sare tana jiran ko ma me zai faru ya faru Har jirginsu Shaheeda ya tashi cikin iska jikinta bai daina rawa ba, lokaci guda kuma hawaye ya wanke mata fuska,a ranta tana jin wai ita ce wannan Fatima Shaheedan dai, favourite ɗin abbanta,amma a yau an wayi gari saboda namiji ta bar abbanta da ya nunawa duniya bashi da kamarta,ta bar Ummeenta, wadda ita kaɗai Allah ya ba ta, wannan wanne irin abu ne?wacce iriyar makauniyar soyayya ce? Rushewa ta yi da kuka, Mubarak da yake gefenta ya yi maza ya riƙo ta cikin tashin hankali yana tambayarta abin da ya faru,ta girgiza masa kai tana faɗin "babu komai" Ya ce"ki gaya min,bana jin daɗi, zuciyata zafi take yi idan na ganki a cikin damuwa, please Fatima" Ta yi ɗan murmushi tana goge hawayenta ta ce"kewar iyayena na fara yi ne,ina son su sosai,kuma ina tausayin halin da za su shiga idan bana nan" Mubarak ya ce"very soon za mu dawo gare su mu nemi afuwar su,na san za su yafe mana ko?"ita dai ta yi shiru tana kwantar da kanta a gefen kafaɗarshi,ya rungume ta sosai yana sauke ajiyar zuciya Awa ɗaya da rabi ne ya ɗauke su daga Kano zuwa Lagos,kuma suna sauka kai tsaye ya kama musu hayar ɗaki a hotel ɗin da take kusa da airport ɗin A ranar Mubarak ya bincika babu jirgi mai zuwa Madrid,dole sai dai su bari zuwa washe gari,don haka dole suka haƙura da tafiyar yau ba don sun so ba Sai dai a wannan daren suka biya bashin soyayya na tsawon lokaci,suka fanshe tarin wahala da fargabar da suka sha,a wannan dare Mubarak da Shaheeda suka zama abu guda,suka kasance cikin shauƙin soyayya da ƙaunar juna Sosai ya yi ta tattalinta musamman da yakasance har yanzu Shaheeda yarinya ce ƙarama,don duka-duka shekarunta har yanzu sha takwas da ƴan watanni, sannan kuma ya same ta a cikakkiyar mace kamar yadda ya yi tsammani,dama ya sani Shaheeda bata da kule-kulen maza Washe gari Shaheeda ta tashi da zazzaɓi,ga kukan da take ta yi,hakan ya tilasta masa kai ta asibiti don a duba lafiyarta Shaheeda tana ganin likitan sai da gabanta ya faɗi,don ta gane shi,El-muaz Adam,class mate ɗin Muyassar ne a secondary school, saboda yadda Muyassar yake ji da ita ya sa su manyan abokansa ma suke ƙaunarta,amma yadda ta nuna bata gane shi ba shima haka, musamman da ya ganta tare da wanda yake da tabbacin mijinta ne,idan suka nuna sanayya a tsakaninsu bai san yadda zai ɗauki abin ba,don ma da gani ba bahaushe bane,kuma babu alamun yana jin Hausa,sai dai abin da ya ba shi mamaki yadda ya ganshi Sam bai yarda da tarbiyyarsa ba, musamman ganin tattoo ɗin da ya yi a wuyansa Amma ya yi mamakin yadda aka yi auren ƙanwar Muyassar amma bai sanar masa ba Hakan bai hana ya yi attending ɗinta ba,ya ba su magunguna suka wuce hotel ɗin da suka sauka A ranar sai da suka sake kwana saboda yanayin jikin nata,washe gari suka bi jirgin ƙarfe takwas zuwa Birnin Madrid 💫 Roxy tana zuwa daidai nan a labarinta ta yi shiru kanta a ƙasa sai sauke ajiyar zuciya take yi,da alamu ta zo wata gaɓa mai ciwo wadda ta kasa mantawa da ita a rayuwarta, ciwon har yanzu yana taɓa mata zuciya,a hankali Haisam ya ɗago yana kallonta, cikin sanyin murya ya ce"kin yi kuskure Shaheeda!kin tafka kuskure a rayuwarki,tun a wannan gaɓar na fuskanci yadda kika kassara rayuwarki,why? Why Shaheeda? meyasa kika zaɓi ki jefa kanki a cikin wannan mummunan halin? wanda har ki bar duniya tabon ba zai bar ki ba? Meyasa za ki yiwa kanki tabo irin haka?kai!!?"ya dafe kai yana murza goshinshi,da alamu abin ya taɓa shi sosai Ƴar dariya mai ciwo Roxy ta yi tana kallonsa, kafin ta ce "ka fara tausayawa halin da nake ciki right? To kar ka yi gaggawa,don har Shaheeda ta bar ƙasar a lokacin tana cike da farin cikin auren masoyinta,bata san illar da hakan ya ƙunsa ba,sai a gaba take gani A taƙaice ma dai,a yanzu babu wata Shaheeda a duniya,don himma, soyayya da hazaƙa,gami da mutuntakar da Shaheeda take da su duk sun mutu a yau, zafi da raɗaɗin da suka rage su kaɗai ne a tare da Shaheeda, babu abin da ya rage wanda take tunawa da shi a duniya ta samu nutsuwa sai ɗanta Mubarak " Haisam yana kallonta ya ce"to ina mijinta Mubarak?" Roxy ta jinjina kai ta cigaba da labarin; 💫 Tafiyar awanni goma ta kai su zuwa birnin Madrid,don sai da suka fara tsayawa a Casablanca babban birnin marocco,gaba ɗaya jikin Shaheeda a sanyaye, duk da yadda take farin ciki da auren masoyinta da yadda yake ta taraiyayarta,hakan ne ma ya rage mata raɗaɗin da zuciyarta take yi Kai tsaye gidan da ya kama musu haya suka nufa, gidan ya yiwa Shaheeda kyau sosai,don irin wanda take so ne ya kama Zamansu ya miƙa cikin matuƙar farin ciki da ƙaunar juna,cikin ɗan lokaci kaɗan Shaheeda ta sake,ta manta da wata kewar mahaifanta da kuma ƙasarta,batun karatu kuwa tuni ta daɗe da watsar da shi Kusan duk lokacin da yake gida ta kan taimaka masa da ayyukansa, kasancewar course iri ɗaya suka karanta,a dalilin haka ma ya yi mata alkawarin ware mata wani kaso a albashinsa, don tuntuni ya fara aiki a ƙasar, kasancewar yana da connection a ƙasar ya sa bai wani sha wahala ba,ga result ɗinsa ta yi kyau sosai Kusan duk weekend ya kan ɗauki Shaheeda su zaga birnin Madrid,su ne duk wasu manyan parks da ke cikin garin Madrid,har ma da wajensa, Shaheeda mai son yawace-yawace har Allah-Allah take yi weekend ya zo don su zaga gari A cikin watanni biyu da aurensu sun murje sun yi kyau hankalinsu ya kwanta, kuma a wannan tsukin ne Shaheeda ta fara laulayin ƙaramin ciki, wanda shi kansa Mubarak da kanshi ya gano da cikin,amma sai da suka je asibiti aka sake yi mata gwaji aka tabbatar da cikin Dukkansu sun yi farin ciki,duk da cewa Mubarak ya so su ɗan ƙara ɗaukar lokaci kafin samuwar cikin,amma sai ya bi ra'ayinta,suka yi farin ciki sosai,a ɓangare guda kuma ya sake zage dantse don ba ta kulawa da nuna mata soyayya 💫 A gida kuwa tun lokacin da Shaheeda ta saba dawowa daga makaranta ya wuce hankalin Ummeey ya tashi,ta fara kiranta a waya amma shiru,bata samunta, Shaheeda bata kashe waya, wannan abu ne wanda kowa ya sani a gidan, Sai dai idan wani dalili ne mai girma,don haka kai tsaye ta kira Muyassar ta sanar masa da cewa don Allah ya je makarantar su Shaheeda ya duba mata ko wani abin ne ya tsare ta, Muyassar yana jin haka sai da gabanshi ya faɗi,amma hakan bai hana shi zuwa makarantar ba Hankalinsa ya tashi sosai lokacin da ya samu tabbacin cewa ta fita a wata mota da ta saba fita,kuma dukkan alamu sun gwada cewa motar wannan matsiyacin yaron ce,a cewarsa,gumi ya shiga karyo masa da tunanin ina ya kai masa ƙanwa? Allah ya kiyaye kar ya lalata masa ƙanwa,don bai ga alamun mutumtaka a tare da wannan yaron ba,gashi kuma ba Musulmi ba Bai yi gaggawar sanar da Ummeey ba,don baya son ya ɗaga mata hankali,ya gwada kiran layin Shaheeda da numbers mabanbanta,wai ko blocking ɗin shi ta yi, amma amsar ɗaya ce,layinta baya amfani Hakan ya sa tilas ya koma gida,wani ƙarin tashin hankalin kuma a ranar Abba ya dawo daga Abuja,kuma yana zuwa kamar yadda ya saba ya buƙaci ganin sanyin idaniyarsa Shaheeda Ummeey ce ta sanar masa halin da ake ciki,don Muyassar ce mata ya yi ya bincika bai same ta ba,kuma an tabbatar bata shiga makaranta ba, gudun kar a je a sake jin abin da ya ji, hankalin Ummeey ya yi ƙololuwar tashi,ta san wacece Shaheeda,bata zuwa ko'ina idan bata tambaye ta ba,ita yawo ma bai dame ta ba, ballantana ma su ba su da ƴan'uwan da za su rinƙa zuwa wajensu Gaba ɗaya Alhaji Yusuf ya birkita gidan, faɗa kan mai uwa da wabi akan a fito masa da ƴarshi duk Inda aka kai ta, tamkar zai daki Hajiya Atika wadda suka fi samun matsala da Shaheeda,yana faɗin su ne suka ɓatar masa da ƴa, Hajiya Atika sai kuka take yi tana rantsuwar cewa ita babu ruwanta, Hajiya Ruƙayya ce mai cewa "haba Alhaji!ya za ka zarge mu da ɓatan ƴarka don ɗaukar alhaki? Allah shaida babu abin da ya shafe mu da ƴarka,amma idan ka cigaba da ɗaukar alhakinmu kai da Allah" Shi dai Muyassar bai yi magana ba,amma maganar gaskiya kowa a gidan ya ba shi tausayi, musamman ma Abba da Ummeey, wadda ita tun da ta fuskanci ƴarta ta shiga wani hali idanunta ba su huta da zubar da ƙwalla ba Washe gari Abba ya saka cigiyar neman Shaheeda a gidajen Radio da television ta ƙasa, lokaci guda gari ya ɗauki ɗumi na ɓatan Yar CEO na Maliya groups of companies, Fatima Yusuf Maliya,tuni gari ya ɗauka, saboda yadda Alhaji Yusuf ya kasance mai tausayi da sanin ciwon ƴaƴa mata,ya sa gaba ɗaya gari ya ɗauka da tausayin tashi ƴar El-muaz ne ya ga sanarwar,da yamma bayan ya koma gida ya huta,ya yi mamaki sosai,ya ɗaga waya ya kira Muyassar Bayan Muyassar ya ɗaga El-muaz ya ce "Man kwana biyu ko neman mutane ba kwa yi" Muyassar ya yi murmushin ƙarfin hali ya ce"ayyuka man,ya naka aikin?" El-muaz ya ce "alhamdulillah, yanzu na ga sanarwar ɓatan ƙanwarka Shaheeda, menene gaskiyar lamarin?" Muyassar ya yi ɗan shiru kafin ya dake ya ce"ta ɓata,amma ni na san ba ɓata ta yi ba,akwai wani saurayinta da ta bi,sai dai na kasa fitowa na sanar da iyayen nata" "What!"El-muaz ya faɗa yana zama a gigice,ya ce"ɗazun nan ta bar asibitina ita da wani Guy da nake tunanin cewa mijinta me, don da alamu ma ya je mata a yadda nata saba ba take zazzaɓi ya kawo ta na duba ta, don't tell me cewa wannan saurayinta ne Muyassar" Muyassar da wani irin tashin hankali ya lulluɓe shi,yana sharce gumi ya ce"ka gaya min gaskiya El-muaz,you know that girl is my life,my happiness,my everything,ka daina gaya min ta ba wa wani namiji kanta,na san ba za ta yi haka ba"El-muaz ya katse shi da faɗin"I'm sorry to say abin da na gani na gaya maka,sai kusan yadda za'a yi a ɗauki mataki, I'm sorry dude!"ya kashe wayarshi yana nadamar kiran Muyassar, zuciyarshi cike da tausayinsu Shi kuwa Muyassar yana sauke wayar ya hau sharce gumi yana faɗin"no!no it can't be possible, Shaheeda ta kasance da wani namiji ba ni ba a ƙarƙashin inuwar aure,nooooo! Why?why Shaheeda? please are you okay?" Dariyar da ya ji a bayansa ya sa ya waiga da sauri, Arfa da ya gani ya sa jikinsa ya fara rawa,don ya san ta ji komai, wayarshi da El-muaz ma babu mamaki ta ji, saboda wayar tana speaker Ƙasa magana ya yi sai rawa da jikinsa yake yi, Arfa ta kalle shi sheƙeƙe ta ce "ka ce ba ni da tarbiyya ko? To ga ma'asumiyar da kake so nan,ga halin da take ciki nan,sai anjuma ko"ta juya ta fice daga sashen #Nusy_bee Page 25 Da kallo ya bi ta har ta fice daga parlourn,a cikin ranshi yana jin wani irin tashin hankali,babu wanda yake tausayi kamar Ummeey,duk da irin soyayya da kulawar Abba a gare ta,yana nan a zaune sai ga Ummeey ta shigo cikin tsananin tashin hankali,ɗan kwalinta ma a hannu,a bayanta kuma Hajiya Ruƙayya, Hajiya Atika da Hajiya Sa'adatu ne da ba su juma da zuwa ba ita da aunty Salma da Hajiya Zaituna matar uncle Rufa'i A gigice Ummeey ta nufi inda Muyassar yake zaune kamar wanda aka dasa yana kallon komai, har yanzu ji yake komai kamar almara,sai Shaheeda ta bi wani sun gudu,har ma ta ba shi kanta,inaa! wannan ba mai yiyuwa bane, Shaheedansa ba haka take ba,kamilar yarinya ce mai riƙo da tarbiyyar da aka yi mata Yana cikin wannan tunanin ne su Ummeey suka shigo,kan Ummeey ko ɗan kwali babu,zaninta ma yana kwancewa tana gyarawa,ta shiga wani irin tashin hankali irin wanda bata taɓa tunani zata shiga ba a rayuwarta,tana zuwa ba tare da wata-wata ba ta fara jijjiga kafaɗarshi tana faɗin "me ka sani game da Shaheeda don Allah? Da gaske ne abin da Arfa ta faɗa na cewa Shaheeda saurayi ta bi?kuma ka sani?don Allah ka gaya min! Inna lillahi wa inna ilayhi rajiun!!!" Hawaye suka zubowa Muyassar babu shiri,ya dafe kanshi yana jin Ummeey tana cigaba da roƙonshi tana kuka mai tsuma zuciya, Hajiya Atika ce ta yi guɗa tana faɗin "Allah buwayi gagara misali! Allah ya ɗauke mana damuwar da ta addabe mu a gidan nan ta sigar da ta dace,an yi walƙiya dai a ƙarshe an ga kowa, Allah ya shirya mana zuri'a"ta ja hannun ƴarta Malika suka fice daga sashen Ita kuwa Ummeey a take ta yanke jiki ta faɗi,aunty Salma ce ta yi saurin ɗauko ruwa ta zuba mata,amma ina,ko alamun zata farfaɗo babu Tilas ta yiwa driver magana, Muyassar ya ɗaga ta da ƙyar ya fita da ita ya saka ta a mota,sauran mutanen dama tuni sun kama gabansu Gwajin farko da aka yiwa Ummeey aka gano jininta da ya yi mugun hawa, hankalin Muyassar ya tashi, tilas ya kira Abba ya shaida masa dukkan halin da ake ciki, dama tunda Shaheeda ta ɓata bai sake barin Kano ba Cikin tashin hankali ya iso zuwa asibitin,anan yake samun mummunan labari daga bakin ƙanwarshi Sa'adatu mahaifiyar Muyassar,a labarin nata ma har da ƙarin cewa dama Shaheeda ta daɗe tana lalacewarta da kafirin yaron da aka gansu tare,yanzun ma da alamu ciki ne da ita shiyasa suka gudu,har ya kai ta ta ga likita Shima dai a take Alhaji Yusuf ya yanke jiki ya faɗi,shima babu shiri aka shiga da shi, Hajiya Sa'adatu sai ihu take yi tana tsinewa Ummeey da yarta da ta kira annoba,tana iƙirarin idan ɗan'uwanta ya mutu sai ta yi Shari'a da Ummeey,tunda ita ta haifo musu bala'i a dangi Awanni shida Alhaji Yusuf ya ɗauka Kafin ya dawo hayyacinsa,shima dai jininsa ya yi mugun hawa Ita kuwa Hajiya Zainab sai da ta yi kwanaki uku kafin ta dawo hayyacinta,ta rame ta zabge ta lalace kamar ba ita ba Tsawon kwanaki biyar aka ɗauka a gidan Kafin abubuwa su fara daidaita,don a waɗannan kwanaki biyar ɗin gidan komawa ya yi tamkar na mutuwa A lokacin ne Alhaji Yusuf Maliya ya tara kaf ahalin Maliya family sannan ya tambayi Muyassar ya faɗi gaskiyar abin da ya sani game da Shaheeda Muyassar bai ɓoye komai ba ya sanar da Abba,sai da Abba ya nisa sannan ya saukewa Muyassar wani gigitaccen mari,rai a ɓace ya ce "ba ka cuce ni ba Muyassar!kanka ka cuta!! tunda har ka kasa sanar da ni halin da yarinyata ke ciki har sai da mai afkuwa ta afku Amma ku shaida,daga yau,Ni YUSUF AHMAD MALIYA,na cire Fatima daga cikin ƴaƴana,idan ta sake amfani da wani abu nawa,ko da sunana ne sai na yi Shari'a da ita!ku shaida hakan!ku tashi ku tafi na sallame ku"Ummeey ta kasa jurewa ta fashe da wani kuka mai gunji,babu wanda ya kula ta,sai Hajiya Sa'adatu da take yin wani murmushi na farin ciki ta ce "to sai mu ce Allah ya raka taki gona Sannan magana ta gaba, tunda ita ta zaɓi hanyar da take so nima na zaɓarwa ɗana mata,zan aura masa Arfa, ƙanwar Hajiya Ruƙayya " Hajiya Ruƙayya da Hajiya Atika tuni suka washe baki, Hajiya Atika faɗi take yi "Masha Allah! Amma na ji daɗin wannan abu,dama me za'a yi da mara tarbiyya, Allah ya sanya alkhairi ya sa a yi da mu" Shi kuwa Muyassar bakinsa ne ya kama rawa, hankalinsa idan ya yi dubu ya tashi,ba ya son wannan yarinyar Arfa,ya tsane ta ma,kuma har yanzu akwai soyayyar Shaheeda a cikin zuciyarsa, wadda yake jin har ya mutu da ita zai mutu, ko da a ce bai sake saka ta a idanunsa ba Runtse idanu ya yi yana jin yadda ake cigaba da tsare-tsaren yadda za'a yi bikinsu,shi dai bai sake fahimtar komai ba har Alhaji Yusuf ya ba su izinin tafiya Tsawon watanni biyu gidan ya kasance a haka, Ummeey bata da mai taya ta kuka,don ko da wasa ta yi wa Abba maganar Shaheeda sai ranta ya ɓaci,a ganinsa ai yaran kishiyoyinta ma ai nata ne,so shi bai ga abin damuwa da ɗorawa kai tension ba don Shaheeda ta gudu,haka ta zaɓarwa kanta,to ta je ta yi rayuwarta Hakan ya ƙarawa Ummeey tension,har ta shiga depression,ga jinya tana fama sosai,amma bata da wanda zai fahimce ta a gidan Hajiya jameela ce ta zo wajenta, wadda ta yi tafiya zuwa Canada na tsawon watanni shida,ta yi kuka sosai da jin abin da ya samu ƙawar tata,ta ba ta shawarwari sosai, waɗanda suka taimake ta har zuciyarta ta rage raɗaɗin da take ciki Ummeey ta cigaba da rayuwa a gidan tana zaman haƙuri,don bayan abin da yake damunta na ɓatan yarta mutanen gidan suka sako ta a gaba da gori da shaguɓe akan Shaheeda,sai dai ba ta tankawa, musamman da ta fuskanci ana shakkar a yi mata a gaban Alhaji Yusuf,don haka itama ta cire komai daga ranta 💫 A ɓangaren Shaheeda kuwa tana rayuwarta cikin kwanciyar hankali ita da mijinta Mubarak tsawon watanni biyu,a lokacin ne wasu irin matsaloli suka fara ɓullowa waɗanda ta kasa gane musu Da farko ankara da ta yi akan Mubarak bai damu da Sallah ba sam,idan za su wuni tare in dai bata ce masa ya tashi ya yi Sallah ba ba zai yi ba, maganar sallar asuba kuwa dama ba ya taɓa yi da asubar,kuma idan ba sharri zata yi masa ba zata iya cewa ba ya yi watarana ma,don sau tari ma cewa yake yi sai ya je wajen aiki zai yi Sai matsala ta biyu,ta fara gamo sunansa Arnold har yanzu shi yake amsawa,ba ya amsa Mubarak,ita kaɗai take kiransa da Mubarak, don ko abokansa na kusa da Arnold suka san shi Da ta yi masa magana sai ya nuna mata ai saboda sabon da suka yi ne ya sa sunan ya kasa fita daga bakinsu, faɗin hakan da ya yi ne ya sa ta ƙyale shi Duk wannan halin da suke ciki ya cigaba da koya mata abubuwa da yawa da bata iya ba wanda ya danganci computer, kama daga hacking security don gudun matsala, ɗora ƙaƙƙarfar security da sauran abubuwan da suka shafi software,kuma da yake tana da ra'ayi har yanzu ta mayar da kai tana ɗauka,don ma yanzu ciki ya saka ta a gaba da laulayi A cikin abokansa akwai wani Diego,sam Diego bai yi mata ba,ta tsane shi saboda yadda ya kasance mashayi ne,gashi ɗan maye saboda ta'ammali da miyagun kwayoyi,babu yadda bata yi ba don Mubarak ya rabu da shi amma ya ƙi,don haka ta cigaba da nuna masa tsana a fili,shi dai Mubarak bai damu ba Yau tana zauna tana shan lemon juice da take so saboda ciki, take yawan haɗawa yanzu ta sha,sai ga ƙarar intercom Da mamaki take kallon ƙofar,ta san lokacin dawowar mijinta bai yi ba,amma sai ta yi tunanin ko wani abu ya manta,don haka ta miƙe ta buɗe ƙofar tana kallon wanda yake taɓa intercom ɗin da mamaki Ba kowa bane sai Diego,ya yi mata wani murmushi ya gaisheta da harshen Spanish Wanda zuwa lokacin tuni sun bar Yaren dutch sun koma kanshi, saboda yanayin al'ummar da suke tare da su A fizge ta amsa fuskarta a ɗaure,yana murmushi ya ce"za mu iya zama mu tattauna?" Sai ta yi ɗan jumm sannan ta ba shi umurnin zama,suka zauna suna fuskantar juna Diego ya fuskance ta sosai ya ce"Arnold ya tabbatar min da cewa ke musulma ce ko?" Ba tare da ta yi magana ba ta jinjina kai tana kallonshi,ya ce "amma kuma kamar a addinin Musulunci mace bata auren wanda ba musulmi ba ko?" Kai tsaye ta ce "eh,nima ɗan'uwana musulmi na aura,don sai da na tabbatar da cewa Arnold ya musulunta sannan na aure shi" Kai tsaye Diego ya girgiza kai ya ce "Arnold bai musulunta ba,kuma ba zai taɓa musulunta ba,asalima babu abin da ya tsana kamar addinin Musulunci, lokacin da ya nuna mana yana sha'awar auren musulma dariya muka yi ta yi masa saboda mun san yadda ya tsani musulunci,sai ya ce mana so yake yi ya mayar da ke addininmu na Christianity,amma kuma sai na fuskanci ba haka bane daga gare ki,don kamar ke ce kika rinjaye shi Sai dai Arnold bai fasa bin addininsa na Christianity ba,don......" "Dakata! Diego dakata min!! Me kake cewa ne? Ƙarya kake yi, Mubarak ba zai yaudare ni ba,don......" "Kira shi da sunansa Arnold,kuma ko kin yarda ko ba ki yarda ba addinin iyayensa yake bi ba na matarsa ba,idan ba ki yarda ba kuma za ki iya yi masa dukkan gwajin da kike ganin za ki gamsu,na bar ki lafiya "ya miƙe ya fice ba tare da ya sake saurarenta ba Wani irin tashin hankali da firgici irin wanda bata taɓa samun kanta a ciki bane ya ziyarce ta,kai wannan maganar ma ƙarya ne, Mubarak ɗinta ba zai taɓa yi mata haka ba Gumi ne ya rinƙa karyo mata,ta miƙe ta kama safa da marwa,wani irin tashin hankali yana sake rufe ta Eh tabbas ba abin mamaki bane idan ya kasance Mubarak yaudararta ya yi da sunan ya karɓi musulunci don ya aure ta,na farko bai damu da duk irin shigar da ta yi ba idan zata fita,wani lokacin ma shine yake zaɓar mata kayan da za su nuna surar jikinta, Sai dai idan ita ce ta sauya,na biyu kuma sam bai damu da ibada ba,sallar asuba ma sam ba ya tashi,duk haƙurinsa da yadda yake sonta idan ta tashe shi faɗa suke yi,a dalilin haka ma ta daina tashinsa Share gumi ta yi tana samun waje ta zauna,ai yau azumi ya rage saura kwanaki biyar a fara shi,don haka zata gani idan zai yi ko ba zai yi ba Tana nan zaune har ya shigo gidan,ta ɗaga kai tana kallonsa,ya yi murmushi, cikin harshen Spanish ya ce"na yi kewar kyakkyawar matata,ya jikin,kuma ya ɗan jaririnmu?" Ɗaurewa ta yi ta ƙaƙaro murmushi ta ce"kewarka yake yi,ya karaso inda take ya rungume ta yana kissing goshinta,ya zauna a kusa da ita ya ce"ya dai? Na ga kin zama wani iri" Ta kwantar da kanta a jikin kujerar da take zaune ta ce"bana jin daɗi ne"janyo ta ya yi jikinsa ya rungume ta ya ce"ya kamata ki kwanta ki huta hakanan"bata yi masa magana ba ta miƙe ta shiga banɗaki Alwala ta ɗauro ta zo ta yi sallar maghriba da isha'i da ta kubce mata,yana zaune yana kallonta, sannan ta kwanta ta lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya Daga lokacin bata sake cewa ya yi sallah ba,tana kallonsa kawai,ba zai hana ta ba, Sai dai ya yi ta bin ta da kallo,duk da cewa zuwa yanzu ta fara gano wannan kallon ma yana da manufa Lokacin da azumi ya zo ta sanar da shi,amma sai ya birkice kan cewa ba zata yi ba, saboda cikin jikinta,ita kuma ta dage kan cewa sai ta yi,hakan ya haifar musu da gagarumar rigima, cikin fusata da rufewar idanu ya ce"haka addinin naku yake babu tausayi?da ciki ma sai kin yi azumi? To sai kin ajiye azumin!dole ma ki bar addinin nan,don tabbas ba zai yiwu ki illatar min da ciki saboda addini ba" Wani kallo Shaheeda take yi masa bakinta yana rawa,ta ce"Mubarak!no Arnold!!! Dama ba ka koma musulunci ba?da gaske yaudara ta ka yi don ka aure ni?" #Nusy_bee Page 26 Shiru ya yi ba tare da ya ba ta amsa ba, cikin ɗaga murya ta ce"tambayarka nake yi Arnold!dama yaudarata kake yi?ba musulunta ka yi ba dama? Har ka da na aure ka?ka bani amsa!" Kallonta ya yi ya watsar ba tare da ya yi magana ba,sai kuma ya miƙe zai bar wajen, cikin gushewar hankali Shaheeda ta shaƙo masa wuya tana faɗin "ka cuce ni,ka cutar da ni,ka halaka min rayuwata,ka mayar da ni inda ka ɗauko ni,ba zan sake kwana da kai a cikin gidan nan ba,na tsane ka,na tsane ka...."hankaɗe ta ya yi,ta yi baya taga-taga, amma kafin ta faɗi ya yi saurin riƙo ta, cikin idanunta yake kallo,a hankali ya furta "a tsawon watannin da muka ɗauka muna rayuwa tare da ke a cikin farin ciki a gidan nan kowa yana bin addininsa ne,don haka yanzun ma za mu iya cigaba,kowa ya cigaba da bin addininsa,amma tabbas na aure ki don ina sonki,kuma zaman aure yanzu muka fara da ke,ya rage naki ki karɓi addinina ko ki cigaba da bin naki,amma zama da ni yanzu kika fara"ya zaunar da ita a gefen gadon dake ɗakin sannan ya juya ya fice daga ɗakin Cikin tashin hankali mai tsanani ta bi shi da kallo,kukan ma da take yi tuni ya tsaya sai sauke ajihar zuciya da take yi,a hankali hawaye suka zubo mata,tana tuna maganar yayanta Muyassar "Ya musulunta ne don Allah ko ya musulunta ne don zai aure ki?" Ya yaudare ta kenan?in dai haka ne ai babu aure a tsakaninsu yanzu,tuni kuka ya kubce mata,take ta fara wata iriyar nadama,ta gudu ta bar abbanta da yake bala'in sonta,ta bar Ummeenta da ita kaɗai ta mallaka,ta bar masoyi na ƙwarai Muyassar ta biyo maƙaryaci, mayaudari, munafiki kuma azzalumi,to yanzu ya zata yi? Da wanne ido zata kalli iyayenta a lokacin da ta koma gare su? Da wanne idanu zata kalli Muyassar masoyinta, wanda ya so ta so na gaskiya,ya ƙaunace ta,ya zama gatanta? Take ta fashe da kuka sosai, ta jinginar da kanta jikin bango tana rera kuka zuciyarta cike da nadama da danasani Bata sake saka Arnold a idanunta ba,sai bayan kwana uku,a lokacin da aka ɗauki azumin farko,tana idar da sallar la'asar ya shigo yana bin ta da kallo Kallonsa take yi itama,bata yi mamakin kwanakin da ya ɗauka baya nan ba, dama wani lokacin idan aiki ya riƙe shi a company yana yin waɗannan kwanakin,amma su kan yi waya,sai dai wannan karon ba su yi wayar ba saboda ta kashe tata wayar Kallonta yake yi cikin kulawa yana murmushi,da alamu ma ya manta abin da ya faru kafin ya fice ya bar gidan Cikin kulawa ya ce"ba ki da lafiya ne?ko dai baby ne yake wahalar min da ke?"banza ta yi masa,bai yi fushi ba ya miƙe ya tafi kitchen,jum kaɗan sai ga shi ya dawo hannunsa riƙe da Plate mai ɗauke da wani nau'in wainar kwai da dankali,yana zuwa ya ajiye a gabanta,ya sa cokali ya ɗiba ya kai bakinta Kallon abincin ta yi ta ɗauke kai, murya ƙasa-ƙasa ya ce "ki ci abinci mana,kin san ya kamata ki rinƙa yawan cin abinci fa" Tana kwance kai tsaye ta ce"na gaya maka azumi nake yi" "Azumi? Azumi kika ce? Ba na gaya miki ba za kiyi azumin nan ba? To ko ki ci abinci ko ranki ya ɓaci" Kai tsaye ta dube shi ta ce"ɓacin rai kuma ai na gama tunda na aure ka,ka cuce ni ka yaudare ni kuma ka zalunce ni,ka tashi ka ba Ni waje kafin raina ya ɓaci na aikata duk abin da ya zo min kaina,tashi ka matsa nesa da ni" "Duk abin da za kiyi ban hana ki ba,amma ba ki isa ki cutar min da ɗana na zuba miki idanu ba Tunda kin nuna ba kya ra'ayina ba zan yi miki dole ba,amma za ki haihu ki ba ni ɗana sannan ki kama gabanki,a lokacin da kike ɗauke da cikina ya zama dole ki kular min da ɗana har ya zo duniya Don haka ki tashi ki ci abinci kar ki bar min ɗana da yunwa" Ko kallon banza ba ta yi masa ba, hankalinta ma yana wajen tunanin yadda zata yi da wannan ƙaddarrarriyar masifar da ta gayyatowa kanta ta auren Arnold,shi kuwa Arnold ganin ta yi masa banza ya sa zuciyarsa ta yunƙuro,tun ba yanzu ba ta karantar da shi abubuwa da yawa a addinin musulunci,har da wanda yake karya azumi,don haka bai yi wata-wata ba ya afka mata a lokacin Duk yadda ta so ta ƙwaci kanta hakan ya gagara,dama gashi ta galabaita,kuma ba ƙarfin su ɗaya ba,ya gama abin da zai yi ya ɗaga ta zaune,ya ce"ki ci abinci ki daina wannan kukan,amma na yi miki alkawarin duk lokacin da kika yi azumi sai na karya shi,sai anjuma "ya fice daga ɗakin ya koma parlour Tun daga ranar bai sake barin ta ɗauki azumi ba,da kanshi yake zaunar da ita da safe ta ci abinci,idan ta ƙi kuma ya mu'amalance ta ta ƙarfi,ya sake ba ta abinci sannan ya fice daga gidan Sai abu na gaba da ya ɓullo ganewa da Shaheeda ta yi yana shaye-shayen giya, ƙwayoyi da sauran kayan maye,shisha kuwa a parlourn yake baje ta ya yi ta zuƙar abinsa,bata taɓa damuwa ba,ko nuna masa ta damu da hakan Akwai abin da ta fuskanta game da ƙwayar da Arnold yake sha,tana saka masa bacci sosai a duk lokacin da ya sha ta,kuma ko da a ce yana cikin damuwa ya sha yana kwanciya bacci idan ya tashi zai tashi zuciyarsa wasai,ya yi ta harkokinsa cikin farin ciki Daga haka zuciyar Shaheeda ta kwaɗaita mata shan ƙwayar don ta samu ta yi baccin da damuwa take hana ta, sai ta kwashi kwanaki masu yawa damuwa bata bar ta ta yi bacci na cikakkun awa biyu ba,don haka kanta tsaye ta nufi inda yake ta ce "Wannan ƙwayar da kake sha take saka ka bacci nake so ka ba ni" Kallonta ya yi ya ce "ba kya samun bacci ne?" Bata yi magana ba sai jinjina kai,babu musu ya ɗauko ya miƙo mata Da farko ɗaya ta fara sha, ganin ta fara jin jiri ya sa ta kwanta, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci bacci mai nauyi ya ɗauke ta Daga lokacin Shaheeda duk lokacin da damuwa ta ishe ta sai ta ɗauki ƙwayar ta sha,tun ɗaya tana iya kwantar da ita har ta daina, ta koma shan biyu A wannan tsukin ne cikinta ya kai watanni shida,kuma a waɗannan watannin ko sau ɗaya bata taɓa yarda ta haɗa jiki da Arnold ba,shima kuma tunda ta haƙura da yin azumi ya daina karantar ta ta dole Tuntuni suka raba ɗakin kwana,yana ɗakinsa itama tana nata A wannan halin ne tana zaune a ɗakinta ta ji muryar Arnold da kamar muryar mace,da sauri ta leƙo tana kallonsu gabanta yana faɗuwa, yarinyar da ganinta baturiya ce yar asalin ƙasar Spain ɗin,kayan da suke sanye a jikinta ya tabbatar da wacece ita Da sauri kuma a firgice ta ƙarasa inda suke tana kallon yarinyar idanunta a rufe da kishin da har yanzu bai rabu da zuciyarta ba, dukkansu tsayawa suka yi suna kallon ta, cikin harshen dutch ta ce"Arnold wacece wannan?" Kai tsaye ya ce"ita ɗin budurwata ce,akwai wani abu ne?" Shaƙe shi ta yi ta ce "budurwarka?ko karuwarka? Ta fice min daga gida ko na illata ta,ta fice min ko na kashe ta!" Arnold ya ƙwace wuyan rigarsa yana aika mata da wani kallo ya ce"da gaske kike? Ta fice miki daga gida?ko kin manta ba wajenki ta zo ba?wajena ta zo? Ai ba don ke ta zo ba, don ni ta zo,ta zo ne don ta yi min abin da ke ba kya yi min,don haka ba ki isa ki hana ta shigowa ba"ya ture Shaheeda gefe ya kama hannun budurwarsa da sam bata ma san me suke cewa ba kasancewar ba da Spanish suke magana ba suka shige ɗakinsa Abubuwa suka sake taruwa suka yi wa Shaheeda yawa,ga damuwa da ta yi mata yawa amma bata da mutum ɗaya da zai ba ta shawara,kullum cikin kuka da tashin hankali,a yanzu Arnold ya daina damuwa da ta ci abincin ma ko ba ta ci ba, tuni shan ƙwayoyin saka baccinta suka ƙaru,ta zama kusan kowanne lokaci tana cikin shaye-shayen ƙwayoyin don ta hana kanta damuwa Cikinta yana da watanni bakwai yanzu, gaba ɗaya ta rame ta yi baƙi sosai, tamkar ba Shaheeda yar ƙwalisar Ummeey ba,sam fara'a da walwala sun kaurace mata, dama ita sam ba shiga sabgar mutane take yi ba, mijinta kawai ta sani,ko da yake saka ta interaction da abokansa dama can bata wani sakar musu fuska ballantana yanzu da ta san wanene ainihin wanda take kallo a matsayin mijin nata A yanzu ta sake tabbatarwa Arnold ba musulmi bane,kuma addinin nashi na Christianity ɗin ma ba damuwa ya yi da shi ba,don ita idan banda ya faɗa ma cewa zata yi bashi da addini A yanzu Arnold ya daina ɓoye mata shan giya ko neman matan da yake yi,dama tuntuni ya daina attempting ko da taɓa ta ne kamar yadda ta buƙata,amma idan ya ga dama zai kawo ko ma wacece ya so,su yi abin da suka ga dama ko da a parlournsu ne,ba a ɗaki ba, sai dai ita ta tashi ta ba su waje A baya Shaheeda tana cikin tashin hankali da taraddadin abin da zata je ta gayawa iyayenta game da wannan auren kasadar da ta yi wanda ya zame mata GADAR TSAUTSAYI da ya jefar da ita zuwa ga kwatamin dana sani,da wanne idanu zata kalli Ummeey da abbanta?akwai mutanen da suka so ta,suka nuna mata ƙauna,ta ba su kunya, irin su Muyassar,akwai mutanen da irin wannan faɗuwar tata suke jira,irin su mahaifiyar Muyassar, kakarta da sauran matan gidansu,ta san wadannan mutanen sun yi farin ciki sosai, Allah sarki!ko a wanne hali mahaifiyarta take ciki? Hawaye suka zubo mata,ita kaɗai Ummeey ta haifa,bata da wata sanyin idaniya sai ita,ta san ta yi kukan rashinta har hawaye sun ƙare mata,a fili, cikin harshen Hausa da ta daɗe bata yi ba,ta ce "Allah sarki Ummeeyna! Ki yafe min!ki yafe min Ummeey!!na san alhakinku ne yake ya bibiya ta har yanzu,na san alhakinku ne ya hana ni jin daɗin rayuwa,na bijire muku, kuma gashi a ƙarshe ina karɓar sakamako mafi muni da ciwo,ku yafe min"ta sake rushewa da kuka sosai tana dafe kanta,ita kaɗai ta san yadda take ji,da mummunan halin da take ciki Tana nan a zaune,bata san ma lokacin sallar maghriba ya yi ba, sai duba agogo ta yi ta ga lokacin sallar isha'i ne,ta miƙe jiki a mace ta nufi ɗakinta don ta yi alwala ta yi sallah Ko da ta idar da sallar ma kwantar da kanta ta yi a jikin gadonta tana cigaba da zubar da hawaye, idanunta sun kaɗa sun yi jajir,gaba ɗaya ji take yi ta rasa hope, tunaninta ya koma kan yadda zata bar Spain ta koma ga iyayenta ta nemi yafiyarsu Motsin da ɗan cikinta ya matsa mata sosai da shi ne ya sa ta miƙe cikin sanyin jiki ta nufi kitchen don samarwa kanta abin da zata ci ko babu yawa,don rabonta da cin abinci tun karin safe, shima kuma ɗan kaɗan ta iya ci Yanzun ma da ƙyar ta samu ta sha tea ta sake komawa parlourn ta zauna tana tunanin irin rayuwar da ta yi a baya,da yadda ta jefa kanta a kogin danasani Tana nan zaune Arnold ya shigo yana tangaɗi,da alamu giya ya sha ya yi mankas,ita mamaki ma abin yake ba ta,zai ƙaraci shaye-shayensa sannan ya hau titi ya ce zai yi driving Tana ta kallonsa yana ta tamɓelensa a tsakar parlourn kafin ya tunkare ta,kamar ba mai ciki watanni bakwai ba ta yi wuf ta matsa,ya sake tunkaro inda take,ta sake matsawa tana watsa masa wani mugun kallo,kafin ta ce "wai menene haka? Me giyar ta gaya maka yau ne da kake zuwar min haka? Bana so!" Yana tangaɗi ya ce "na gaji!na gaji da hana ni kanki da kike yi, Fatima bana buƙatar wata mace a duniya idan ba ke ba,don haka yau dole ki ba ni haɗin kai" Tsaki ta yi ya juya zata shiga cikin ɗakinta,ya damƙo ta, tuni ta manta da wata kasala da nauyin jiki ta fara yunƙurin ƙwatar kanta, ganin ba zata iya ƙwatar kanta ba ya sa ta ɗaga flower vase ta rotsa masa a kai,tuni jini ya wanke masa kai,ita kuma ta samu ta gudu zuwa ɗakinta Sai da ta rufe ɗakin sannan tsoro ya ɗarsu a ranta,ganin jini yana gudana akan Arnold, jikinta ya fara rawa,ta samu waje ta takure,ta zauna tana tunani A haka bacci mai nauyi ya ɗauke ta,mai cike da mafarki iri-iri marasa daɗi Can cikin baccinta ta ji ana buga ƙofar,a firgice ta tashi zaune,da gaske ne bugu ne,kuma muryar mutane take ji,da alamu ma ba iya Arnold kaɗai bane, tsoro ya ɗarsu a ranta,ta leƙa ta window a hankali Gabanta ya faɗi ganin ƴan sanda,ta yi saurin saka hijabinta ta fita a tsorace tana kallonsu Ɗaya daga cikinsu ne ya gaishe ta cikin harshen Spanish, sannan ya ce "Madam mijinki ne ya yi hatsari a mota yanzu,mun yi gaggawar kai shi asibiti,a can yana ta kiran sunanki,a takaice dai yanzu, mijinki Arnold Liam Lambert yanzu ya riga mu gidan gaskiya,amma kafin ya rasu mun ga ciwo a kanshi,kuma ya tabbatar da cewa ke kika ji masa, don haka yanzu za ki bi mu zuwa office ɗinmu,za mu tsare ki har sai an gama bincike,sannan sai mu ga abin da ya dace" #Nusy_bee Page 27 Kallonsa ɗan sandan da yake yi mata bayani kawai take yi numfashinta yana ɗagawa sama-sama, dishi-dishi ta hango ɗaya daga cikinsu yana ƙoƙarin buga mata handcuff,daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba A hankali ta fara buɗe idanunta,tana rufewa tana buɗewa, lokaci guda kuma komai da ya faru ya dawo mata fes Labari aka kawo mata na cewa mijinta Arnold ya mutu,kuma ana zargin da saka hannunta a mutuwarsa,a firgice ta yunƙura zata diro daga kan gadon, ƴar sandan da take tare da ita ta dakatar da ita gudun kar ta illata kanta, ga cikin da yake jikinta Kuka sosai ta fashe da shi mai ban tausayi, duk yadda likitocin suka so ta kwantar da hankalinta ta daina kukan hakan ya gagara,ba wai mutuwar Arnold ce kawai ta taɓa ta ba, sai tonuwar asirinta, ina ma a yanke mata hukuncin kisa a ce ita ta kashe shi,ina ma ta zo haihuwa ta mutu,ina ma zuciyarta ta buga ta bar duniya,irin tunanin da ta rinƙa yi Kenan tana rera kuka cikin tashin hankali da gigita Kwananta biyu aka sallame ta,kuma kai tsaye aka nufi station da ita,a can ta wuni,duk irin tambayoyin da aka yi mata ta kasa ba da amsa Diego shine ya tabbatar da cewa Arnold giya ya sha,a buge yake lokacin da ya yi hatsari,kuma tabbas hayaniya ta haɗa su da matarshi Fatima shiyasa ma ta gudu ɗaki,sai dai ba ita ba ce ta ji masa ciwo,kamar yadda suke tunani, sunanta kuma da yake ambata yana da alaƙa da kewarta da yake yi ne Da wannan bayanin Diego ya samu ƴan sandan suka saki Shaheeda,gashi kuma dama ba a son ransu suke riƙe da ita ba saboda cikin jikinta da kuma kukan da take yi, wanda duk wanda zai ganta zai tabbarwa kanshi na baƙin ciki ne Diego shine ya cigaba da kulawa da Shaheeda har ta samu sauƙi,da farko ya kan zauna ma ya yi ta ɗebe mata kewa,ya kawo mata abinci,ya hana ta shan ƙwayoyin da take sha cikin dabara da hikima, don sun fara illata ta da ɗan cikinta,daga baya ma sai ya kawo mata ƙanwarshi Martina don ta rinƙa ɗebe mata kewa Shaheeda ta yaba da karamcin da ya yi mata sosai,har hakan ma ya rage mata raɗaɗi mai yawa daga zuciyarta,ta yi iya ƙoƙarinta ganin ta rabu da damuwa kamar yadda Diego yake so Kwanan Arnold tara da rasuwa mahaifiyar Mrs. Andrea Lambert ta iso ƙasar Spain,a ranar Shaheeda ta ga wulaƙanci ta ga tozarci, Arnold shi kaɗai ne ɗa a wajen Mrs. Andrea Lambert,kuma a saboda Shaheeda ya gudu ya bar gida,babban abin da ya fi yi mata ciwo ma shine kasancewar Shaheeda musulma,hakan ne ya sa ta sake zargin eh tabbas ita ce ta kashe mata ɗa A ranar ta kore ta daga gidan,duk da halin jinya da kuma nauyin ciki bai saka ta tausayawa Shaheedan ba,haka tana kuka ta ɗauki iya abubuwa masu muhimmanci da zata buƙata ta bar gidan, zuciyarta cike da tunanin inda zata je,don lokacin Martina tana makaranta,gashi bata san gidansu ba Haka ta yi ta gararamba daga wannan titin zuwa wancan,gaba ɗaya hankalinta ba ya jikinta, tunani kawai take yi yadda zata bar Spain, don ko kuɗin abin da zata ci bata da shi ballantana na jirgi Tana tafiya tana bin gefen titi sai jin wani mahaukacin horn ta yi,tsabar gigita ma sai ta rasa yadda zata yi,a wajen ta durƙushe jikinta ko'ina yana karkarwa, wadanda suke cikin motar suka fito da sauri suka nufo inda take suna dubawa ko ta ji ciwo Sai dai kafin su ƙaraso juriyarta ta ƙare,tuni ta silale a wajen ta kwanta,suna zuwa suka ɗauke ta suka sanya ta a mota suka nufi asibiti Ita dai Shaheeda bata samu kanta ba sai washe gari,da matar da ta kusa kaɗe ta ta fara haɗa ido bayan ta dawo hayyacinta,ta ga kulawa sosai,suka ba ta labarin sun je ɗauko yaransu daga makaranta ne a hanya suka ganta Suka tambaye ta labarinta,daga ina take?bat gaya musu komai ba,kawai ta ce musu tana son komawa Nigeria ne,amma bata da kuɗin Flight,hakan ya sa suka ba ta shawarar ta zauna tare da su kafin mijin ya samu yadda zai yi ya saka ta a jirgin Nigeria Ta ji daɗin zama tare da su na tsawon kwanaki biyu,yaransu masu suna Ana da Mia suna ɗebe mata kewa sosai,sai dai bayan kwanaki biyun ta buƙaci zata koma inda ta fito kawai,don hankalinta ya koma ga iyayenta Tilas ba don sun so ba suka bar ta ta tafi,don duk shawarar da suka ba ta bata saurarensu, hankalinta da tunaninta kacokam suna gida wajen iyayenta Kai tsaye ta koma unguwar da suke zaune ita da Arnold, abin baƙin ciki ta samu gidan a kulle,haka ta zauna a ƙofar gidan tana rera kuka mai ban tausayi Sai dai kuma ta yi ƙatuwar Sa'a, saboda ɓullowar Martina da ta gani,babu shiri Martina ta taho da gudu ta rungume ta tana tambayarta "Muka neme ki muka rasa,yayana yana ta so ya mayar da ke Nigeria amma ba mu same ki ba"Shaheeda ta yi saurin cewa "to yanzu ki gaya masa,zan koma Nigeria Please"babu musu Martina ta ciro wayarta ta danna masa kira,bugu biyu ya ɗauka, kuma ba tare da ɓata lokaci ba ta sanar masa abin da yake faruwa Kai tsaye ta ce su jira shi,a nan suka zauna suka yi jugum-jugum bayan ta kashe wayar,ita dai Shaheeda fargaba da razani ba su bar ta ta fahimci komai ba Babu jumawa Diego ya zo, cikin kuka Shaheeda ta kora masa bayanin komai na yadda mahaifiyar Arnold ta tozarta ta,kuma ta kore ta daga gidan saboda tana zargin ita ta kashe mata ɗa,ya ɗan yi shiru, kafin cikin ƙunar rai ya ce "babu komai,dama ai tun farko bata so auren bane shiyasa ta yi haka,amma babu komai,na bincika yanzu,akwai jirgi mai tashi zuwa Nigeria,sai na yi miki boarding ɗin sa"babu musu ta yiwa Martina sallama,suka rabu cike da kewa,Diego ya ɗauki Shaheeda a motarsa suka nufi airport Ya yi mata komai na jirgin, sannan ya ba ta yan kuɗin da zata rike hannunta,ya dube ta cikin tausayawa ya ce "to shikenan tafiyar ko? Ina yi miki fatan alkhairi,sai watarana idan da rabon za'a sake haɗuwa,kuma kar a manta da mu please"ya juya ya tafi,ita kuma tana ta yi masa godiya amma sam bai juyo ba ballantana ya ba ta amsa Har Shaheeda ta shiga jirgi jikinta a sanyaye tana ta kuka,a wannan lokacin ji take yi inama Allah ya ɗauki ranta ta huta da wannan bala'in,don ta gama fitar da rai da rayuwa,ga taraddadin tashin hankalin da zata je ta riska a Nigeria sakamakon guduwar da ta yi ta bi Arnold,ga cikin da zata koma da shi,da baƙaken labarin kasancewar Arnold bai musulunta ba,da kuma mutuwarsa,da korar da uwarsa ta yi mata 💫 Roxy tana zuwa nan a labarinta ta kasa cigaba da labarin kukanta yana tsananta,ita kaɗai ta san irin ciwon da take ji da baƙin ciki na rayuwarta ta baya,a hankali ta yi ƙasa da kanta tana shashsheƙar kuka mai tsanani,shi dai Haisam kallonta kawai yake yi,ya kasa iya ce mata komai,kai a ƙasa tana girgiza kai ta ce "ba zan iya ba,watarana kawai na cigaba"daidai lokacin maasu kula da prison ɗin yake tabbatar musu da cewa tun ɗazu lokaci ya wuce, Haisam dai yana zaune kamar an dasa shi yana bin kowa da kallo kamar mutum-mutumi aka shigar da Roxy zuwa inda aka fito da ita Da kallo kawai ya bi su, gaba ɗaya jikinsa a sanyaye yake,shima ji yake yi kamar ya fashe da kukan kamar yadda take yi,a hankali ya miƙe tsaye jiki a sanyaye ya fice daga wajen yana tafiya kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki,tausayin Shaheeda ya kasa barinsa, tabbas laifinta ne,amma kuma ɗaukar irin wannan hukunci a gare ta da ƙananan shekaru ba abu ne mai sauƙi a gare ta ba Daga nan orphanage ya wuce inda ya kai Mubarak,don ya san abu ne mai wahala Roxy ta samu fitowa saboda laifukan da ake tuhumarta da su,amma zuwa yanzu ya fara nazarin yadda zai yi ya fito da ita ko ta halin yaya ne Signing ya yi na karɓar Mubarak gaba ɗaya,ya samu ya karɓe shi ya saka shi a mota suka bar wajen zuwa gida Yana zuwa gida kai tsaye part ɗin sa ya shiga yana rungume da Mubarak da ya yi shiru yana kalle-kalle,tausayin yaron ya kama shi sosai, gaba ɗaya bai san menene jin daɗin rayuwa ba,bai san menene farin ciki ba, rayuwarsa cike take da ƙalubale a sanadin kuskuren da iyayensa suka aikata Ranshi ya sake ɓaci lokacin da ya ga Nimra a sashensa ta yi ɗaiɗai tana kallon TV tana cin porpcorn,wata sexy dress ce a jikinta,tana ganinsa ta tashi da gudu ta faɗa jikinsa tana yi masa oyoyo,a fusace ya ture ta gefe yana faɗin "ba kya kula ne? Ba ki ga yaro a hannuna bane?ko sai kin buge shi?" Ja baya ta yi, cikin rashin damuwa ta ce"oh sorry! A ina ka samo shi?so cute little boy Kai what's your name?"shi dai Mubarak da alamun babu cikakkiyar lafiya a tare da shi kanshi yana kwance akan kafadar Haisam yana kallonta, Haisam ya ja tsaki ciki-ciki ya wuce da shi ya kwantar akan kujera,ya gyara masa kwanciya sannan ya wuce banɗakinsa don ya yi freshen up Kafin ya kammala shiryawa Nimra ta gabato masa da nau'ikan abincin da ta shirya masa wanda ta san yana matuƙar so,sai dai ko kallo biyu bai yi musu ba ya shiga kitchen don ya dafa musu noodles shi da Mubarak Nimra ta biyo shi tana shagwaɓe fuska, cikin sanyin muryarta ta ce"ba ka son abin da na dafa maka ne kake ƙoƙarin boiling noodles?" Bai kalle ta ba ya ce"a'a kawai dai I'm craving noodles ne, shiyasa ma ban yi takeway ba" "To ka kawo na yi maka mana"ta faɗa tana ƙoƙarin karɓar girkin Murmushi ya yi ya ce"No kin wahala akan wancan girkin, thanks ba sai na sake wahalar da ke ba,ki je ki taya yaron can zama da muka zo tare ki yi masa hira, I'm sure you will like him, idan kika yi haka I'm okay with it" Kallonsa ta yi kamar mai nazari,sai kuma ta juya ta fice daga kitchen ɗin ba tare da ta yi magana ba A parlourn ya same su a zaune,ta taƙarƙare tana ta yi wa Mubarak hira,shi dai kasancewar ba shi da saurin sabo kallonta kawai yake yi daga inda yake kwance Haisam bai kula ta ba ya ɗaga shi zaune,ya fara ba shi abincin yana nazartar yadda yake a nutse, Nimra da ta gaji da pretending ta ce"yaya Haisam wannan yaron fa? Ina ka samo shi?" Kai tsaye ya amsa mata ba tare da ya kalle ta ba"ƙanin Amna ne" Take fuksarta ta sauya,ranta ya fara sosuwa, Amnan da take so ta san yadda zata yi ta sa ya tura ta ga mahaifiyarta shine za'a ɗauko wani ƙaninta,dama tana da wani ƙani? Ranta a ɗan ɓace ta ce"to amma meyasa ba ka bar shi a hannun mahaifiyarsa ba? Kalle shi fa,har Amnan fa ya dace a ce suna gaban mahaifiyarsu, meyasa ka ɗauko su?". Kai tsaye ya ce"ra'ayi, dukkansu za su zauna tare da ni,shi dai wannan da yiwuwa ya koma hannun mahaifiyarsa amma Amna tana hannuna" Nimra ta ce "to me yasa ba za ka mayar da amnan ba sai shi kaɗai?" Haisam da ya fara gajiya da tambayoyin ya ce "saboda shi ba ba ni na haife shi ba,amma shima idan mahaifiyarsa ta so zan rike shi a hannuna" "To menene alaƙarka da shi da za ka rike shi? Babu wani mai rike shi ne sai kai?" Banza ya yi mata,sai da ya tabbatar Mubarak ya ƙoshi sannan ya rungume shi da kyau ya dube ta ya ce"ni zan riƙe ɗana,ban ce wani ba, ballantana ke"yana kai wa nan ya miƙe ya fice daga sashen don ya kai wa Nanny ɗin Amna shi, Nimra ta bi shi da kallo zuciyarta tana raɗaɗi,tana jin dole sai ta raba shi da yaron nan *MALIYA ESTATE, KANO STATE, NIGERIA* Ƙaton katafaren parlourn gidan ya ɗauki shiru tamkar babu wani mahaluki a ciki, ba'a jin komai sai ƙarar AC da shashsheƙar kukan Arfa da ya karaɗe parlourn, Alhaji Yusuf da yake zaune a inda ya saba zama ya yi shiru yana kallon Arfa da take ta kuka,tun da aka kawo masa maganar sakin da Muyassar ya yi mata yake cike da tsananin mamaki Gashi an kira wayar Muyassar ɗin ba'a samun sa,da alamu ma ba ya ƙasar tunda ya aikata abin da yake so Gyaran murya ya yi, ilahirin matansa da Hajiya Sa'adatu da Hajiya Salma da da sauran ƙannensa maza suke zaune suka mayar da hankali kanshi don jin abin da zai faɗa,gaba ɗaya jikinsu a mace #Nusy_bee Page 28 Rai a tsananin ɓace,irin ɓacin ran da ba za su iya tuna yaushe rabon shi da shiga ba ya fara magana "Abin nan ya ba ni mamaki kuma ya ɗimauta ni, Muyassar dai, yaron da muka sani da biyayya da girmama na gaba, wanda ba ya taɓa yin wani abu ba tare da ya yi shawara da manyansa ba,ya saki matarsa da muka aura masa ya kama gabansa ya tafi, wannan wanne irin abu ne? Sa'adatu!me yake faruwa ne?" Kan Hajiya Sa'adatu a ƙasa ta ce "ban sani ba yaya, wallahi ba da yawuna ya yi hakan ba, ban ma san ya yi ba" Alhaji Yusuf ya dubi Arfa da take ta kuka ya ce"ke Arfa menene ya faru?ko kun samu wani saɓani ne?" Gyara zama ta yi tana goge hawayenta ta ce"wallahi Abba lafiya ƙalau muke zaune, tunda aka kama Shaheeda sai ya canja,ya yi ta yi min faɗa,ya yi min tsawa,ya gaya min ni ba mace ba ce Shaheeda ce mace,ya ce ya tsane ni dole ce ta sa ya aure ni, Shaheeda yake so A saboda haka kullum da irin rashin mutuncin da yake yi min, wallahi Abba na gaji da wannan tozarcin"ta ƙarashe tana fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi Gaba ɗaya parlourn ya ruɗe da salati da sallallami, Ummeey ji ta yi ta sake muzanta,kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki saboda tashin hankali Hajiya Sa'adatu ce ta fara magana cikin kuka"ni dai Allah ya jarabce ni, wannan masifar kusan a kanmu ta ƙare kenan,ta tarwatsa gidan ɗana, Allah ka yi min maganinta " Hajiya Atika cikin sigar rashin mutunci ta ce"Allah ya kyauta dai kam,amma tabbas Muyassar ya faɗa mugun hannu,dama ina zargin yawancin abubuwan da aka ce yana yi ba yin kanshi bane, Allah ya sa dai haka aka bar ku" Hajiya Sa'adatu ta ce"to Allah ya sa,don yanzu mutum mai shiru -shiru ya fi matsala " Cikin rashin mutunci Hajiya Ruƙayya ta ce"ba dai wani dabam ba,ke ma ya kamata ki nunawa ɗanki cewa ƙanwata tana da daraja,dama ai tun farko a wulaƙance ya ɗauke ta,kuma babu abin da kika yi akai,idan ma akwai asiri to akwai hali" Gaba daya parlourn ya yi shiru,ran Hajiya Sa'adatu ta ɓaci sosai,amma kafin ta kai ga yin magana Alhaji Yusuf ya riga ta "Duk wannan cecekucen ba zai yi ba,mafita za mu nemo kawai,ina buƙatar ganin Muyassar a yau zuwa gobe"ya dubi Hajiya Zainab da ta yi shiru ya ce"Zainab menene shawararki akan hakan? Kin ga dai abin da yaron nan ya aikata mana,ya saki yarinya ba tare da wani dalili mai girma ba,kuma ya haura ya yi tafiyarsa bai sanar da kowa ba, ya kike gani?" Kai tsaye Hajiya Zainab ta ce"Alhaji Allah ya kyauta kawai za'a ce,yaran zamani ne ka haife su ba ka haifi halinsu ba,amma duk da haka ya kamata mu ji ɓangarensa tukunna, kafin mu yanke hukunci......" "Ni ƙanwata ta samu ingantacciyar tarbiyya,a dai bincika a inda aka samu matsala "a cewar Hajiya Ruƙayya tana katse Hajiya Zainab Hajiya Zainab ta ja baki ta tsuke ba tare da ta sake magana ba, Alhaji Yusuf ya cigaba da bayani ba tare da ya saurari maganar Hajiya Ruƙayya ba "Arfa zata zauna a nan,za mu jira Muyassar har sai ya dawo, sannan na yanke hukunci " Hajiya Ruƙayya ta dube shi fuska a ɗaure ta ce"a'a da dai ta koma gidan ubanta, kamar zata fi ƙima a can"ba tare da Alhaji Yusuf ya kalle ta ba ya ce"na gama magana! Ta koma sashen Muyassar na nan gidan kafin ya dawo,in sha Allah za'a san abin da za'a yi"ba tare da kowa ya sake tankawa ba suka jinjina kai,kai tsaye ya ce"ku je na sallame ku "Hajiya Zainab ce ta fara miƙewa,ragowar matan ma duka suka fito,suka bar shi da ƙannensa maza waɗanda suka yanke shawarar da ta yi musu Da sauri Ummeey ta yi gaba don shiga sashenta,amma ina,sai da Hajiya Sa'adatu ta cim mata tana huci Duk da yadda gabanta yake faɗuwa amma hakan bai hana ta ƙaƙaro murmushi ba "Sannu Hajiya! Akwai....."duk inda kika kai min ɗana ki dawo min da shi,na ɗaga ƙafa na tsawon lokaci,na yi kara da kawaici amma na ga abin naki ya zama wulaƙanci,to wallahi idan har ba ki dawo min da ɗana ba abin ba zai yi mana kyau ba Ƴarki ta shiga duniya ta yi tambaɗewarta, shiyasa nima za ki raba ni da nawa? Shi tasa ga ki nan kullum shiru -shiru,ai mun daɗe da sanin lumbu-lumbu kike yi, abin da ya samu ƴarki mugun aikinki ne yake koma miki,asirinki ne Allah ya tona,don haka tun wuri ya kamata ki nemo min ɗana" Kallonta kawai Ummeey take yi ba tare da ta yi magana ba,zuwa yanzu ta fara kai wa ƙarshe,duk da irin abubuwan da suka same ta a dalilin tilon ƴarta,da abubuwan da suka sami ƴar tata,babu wanda ya tausaya musu,shine za'a zo ana yi mata maganar wai ta fito da Muyassar,wai me mutanen nan suke nufi da ita ne? Hajiya Sa'adatu ta katse mata tunani da faɗin"na yi miki magana kin zuba min idanu, wallahi Allah ɗaya idan har ba ki fito min......" "Hajiya Sa'adatu! A maimakon wannan complain da kika zo kina yi me zai hana ki kai ƙara sama? Na gaji da maimaita magana ɗaya,da masu zargi da masu zagi kar wanda ya fasa,ya rage naki ki je ki nemi ɗanki ko ki zo nan ki yi ta hayaniya,ba ni waje"ta zagaye ta a fusace ta wuce zuwa sashenta Hajiya Sa'adatu ta bi ta da kallo zuciyarta tana ƙuna,amma kafin ta iya ɗaga ƙafarta sai ga Hajiya Ruƙayya ta ƙaraso wajen tana huci Hajiya Sa'adatu ta kalle ta fuska a ɗaure ta ce"ai ni Ruƙayya kin ba ni mamaki,ban yi tsammanin ko kowa zai zagi ɗana ya juya masa baya ke za ki......." "A'a Hajiya dakata!don kina matsayin babba kar ki yi tunanin za ki taka mu ki zauna lafiya! Ya yaronki zai yiwa ƙanwata sakin wulaƙanci kuma ya yi tafiyarsa kamar ya saki mara galihu amma ki kasa ɗaukar mataki?kar ki manta kwanaki fa dukanta ya yi,ko don kin ga na yi shiru,to wallahi ba zai yiwu ba,ba zan zuba idanu ba,idan ba haka ba wallahi zan fasa ruɓaɓɓen ƙwai warin ya damu kowa wallahi " Kallonta Hajiya Sa'adatu take yi cikin wani irin yanayi na tsananin baƙin ciki da mamaki, kafin ta iya ɗaga harshenta da ƙyar ta fara magana "Amma ban tsammaci haka daga gare ki ba Ruƙayya,kin ba ni mamaki,ban taɓa tsammanin wai ke,ke dai,ke da na yiwa abin da ban yiwa yaran cikina ba,wai ke ce kike kallon tsabar idanuna kina yi min barazana ba Kin manta a yadda na same ki?na aurar da ke ga yayana wanda yake da wadata?ya sakar miki?duk wani taimako da kulawa ba babu wanda ban ba ki ba,amma shine za ki zo kina yi min barazanar za ki tona min asiri? To ki tona!na yi miki alƙawarin duk lokacin da kika yunƙura tona min asiri wallahi sai na yi miki abin da ba ki taɓa zato ba,babu wanda ya isa ya yi min butulci. ........." "A'a fa Hajiya! Kar ki yi min wannan maganar,kar mu fara haka da ke! Kin san kin amfana min,amma ba ki san na amfana miki ba?ko don an ce ɗan adam butulu shiyasa za ki nuna min halin? To kar ki sake yi min gori,idan kika sake wallahi gwara kowa ya ɗauki hanyarsa, zan fasa ƙwai kowa ya ji wari Sai magana ta gaba,ya rage naki ki yiwa ɗanki magana ya mayar da ƙanwata kafin maƙiya su ji su yi mana dariya,akasin haka kuma ran kowa ya ɓaci"tana kai wa nan ta wuce fuuu zuwa sashenta ranta a ɓace Itama Hajiya Sa'adatu rai a ɓace ta shiga motarta ta fice daga gidan zuwa nasu cikin tashin hankali, abubuwa suna neman ruguje mata a lokacin da ya kamata a ce ta fi kowa farin ciki,wai Ruƙayya, Ruƙayya dai, wadda ta zamarwa gata,ta fito da ita daga rana ta kai ta inuwa ita ce ta tsaya tana kallon idanunta tana gaya mata zata tona mata asiri,a fili cikin wata iriyar murya mai cike da mamaki da ruɗani take faɗin "eh fa! Ba shakka! Allah ya sawwaƙe!!" Haka ta yi ta sambatu cikin tsananin mamaki da firgici har ta isa bakin gate ɗin gidansu,a ranta tunani take yi ta hanyar da zata yi maganin wannan masifar da ta danno mata kai,ga ɗanta ya saki matarsa, ba tare da sanin cewa ya ɓallo musu ruwa ba,ga wannan tutsun da Ruƙayya take yi, wanda hakan yana nufin abubuwa da yawa a gare su Jikinta babu ƙwari har ta shiga sashenta na gidan ba tare da ta nemi kowa ba,tana jin lokacin da Salma ta shigo don yi wa innayyo sallama zata tafi gidanta,amma ta yi musu shiru,don abin da yake damunta ma ya ishe ta *ROCKY ESTATE* Da sallama ya shiga sashen Nanny ɗin Amna,ta ɗago da fara'a tana amsa sallamar tashi, kafin ta rissina tana faɗin"sannu da zuwa yallaɓai" Murmushi ya yi yana faɗin"sannu Nanny,ya yaran? Sai kika ga na ƙara miki nauyi"Nanny ta yi saurin girgiza kai ta ce"a haba! Allah ya raya mana gaba ɗaya " Haisam ya zauna yana kallon Amna da ta kwanta tana bacci a parlourn,ya kalli Mubarak da yake kwance a kan one sitter ya takure yana bacci,ya ce"ya baƙon naki? Ina fatan za'a samu daidaito tsakaninku?" Ƴar dariya Nanny ta yi ta ce "to Allah ya sa ko nan gaba,don yau dai ba'a wanye lafiya ba, ƴar'uwar tana ta rawar ƙafar ta samu ɗan'uwa amma shi sai kuka yake yi yana kiran mamansa, juyin duniya ya ƙi ya yi shiru,sai da bacci ya ɗauke shi a kan kujerar da yake kwance sannan na samu nutsuwa,da na motsa shi zan gyara kwanciyar na ga zai tashi ya cigaba da kuka na ce sha zamanka ka yi baccinka " Dariya sosai Haisam ya yi yana kallon Mubarak da ya kasance photocopy na mahaifiyarsa, soyayyar yaron yake ji har cikin jinin jikinsa,ya matsa inda yake kwance ya shafa fuskarsa yana faɗin"bai ci abinci ba ya zama dole ya tashi, gudun kar ya tashi ce cikin dare Tunda bai saba ba bari na tafi da shi,idan ya saba sai na rinƙa barinsa a nan ɗin,kar a haɗa miki aiki"Nanny tana murmushi ta ce "to ranka ya daɗe,ina matuƙar godiya, Allah ya sa ka fi haka" Haisam ya ce "Ameen! Zan yi miki ƙari, saboda yaron yanzu zamansa ya dawo hannuna, sannan kuma bashi da ishashshiyar lafiya,sai kin ba shi kulawa sosai"Nanny ta sake rissinawa tana godiya, Haisam ya saɓa Mubarak a kafaɗa a hankali, ya yi mata sallama ya fice zuwa sashensa Yana zuwa daf da ƙofar sashen nashi ya hango Nimra a tsaye a wajen, murmushi ya yi,ɗazu ya sa aka zo aka canja makullin sashen,don haka yanzu dole ta jira idan ba ya nan,ya gaji da yadda take shigar masa sashe kamar wasu dabbobi ko marasa addini Ita kuwa yaron hannunsa ta bi da kallo da wani irin yanayi a fuskarta,bai kalli sashen da take ba ya zo zai shige sashensa, ranta a ɓace ta ce"excuse me! Ina Amna ɗin?"tambayar tata sai ta ba shi dariya,amma bai yi ba,kuma bai kalle ta ba ya shige part ɗin sa,ya biyo shi a baya tana faɗin "bacci yake yi kuma za ka ɗago shi? Ba zai tashi ba?"banza ya yi mata,yana shigewa sashensa ya mayar da ƙofa ya rufe Yana kwantar da Haisam akan gadonsa ya fara jin bugun ƙofa na hauka kamar za'a karya ƙofar,har sai da Mubarak ya firgita,ya tashi yana ƙoƙarin fara kuka, Haisam ya lallaɓa shi ya samu ya koma sannan ya tashi ya nufi bakin ƙofar inda ake ta bugun Bai yi mamakin ganin Nimra ba a tsaye tana ta huci, abin ma sai ya ba shi dariya,ta dube shi ta ce "yau kuma?abin da wulaƙanci ya zo?ka san ina biye da kai shine za ka mayar da ƙofa ka rufe? Meyasa kake yi min irin wannan wulaƙancin ne?don kawai ina sonka?"hawaye Masu zafi suka zubo mata,take kuma ta fashe da kuka sosai Ɗan ƙaramin tsaki ya ja,ya ce"Nimra,kin san yadda aikina yake,kin san ina buƙatar hutu da kwanciyar hankali da dogon nazari akan aikina, menene dalilin da ya sa kike so ki ƙara ba ni ciwon kai ne? A tunanina ke ma mai taimaka min ce na samu nasara akan aikina, menene dalilin da ya sa ke ce kike saka ni wasa da aiki? Look Nimra,akwai gobe,akwai jibi,akwai sauran kwanaki,za mu iya zama mu yi maganar da kike so,amma yanzu bacci ya kamata na yi please " Nimra da take jefa masa wani kallo ta ce"to kai da kake buƙatar ka kwanta ka huta me ya haɗa ka da yaro karami? meyasa ba ka bar shi a wajen mai rainonsu ba?tun farko na menene alaƙarka da yaron da kake ƙoƙarin fifita shi akan kowa?" #Nusy_bee Page 29 Kallonta kawai Haisam yake yi a wulaƙance har ta gama jero masa waɗannan tambayoyin, kafin ya sake kallonta ya ce"yanzu dare ya yi, kamar yadda na gaya miki ina buƙatar Hutu,duk lokacin da na samu dama sai na ba ki amsoshin tambayarki,amma kafin nan kar ki sake buga min ƙofa Please, respect yourself,good night"yana kai wa nan a maganarsa ya mayar da ƙofar ya rufe ba tare da ya sake sauraren abin da zata ce ba Cikin dare Mubarak ya farka yana ta kuka yana kiran Mama,da ƙyar Haisam ya iya tashi yana lallaɓa shi,amma ya ƙi komawa baccin,sai kuka yake yi sosai,jikinsa ya ɗauki zafi zau,hankalinsa ya tashi sosai Lokaci ɗaya kuma numfashinsa ya fara neman harɗewa,ƙirjinsa ya rinƙa ɗagawa sosai,dole ya shirya ya canja kaya,saɓa shi a daren ya fita da shi zuwa asibiti A can asibitin yana zuwa likitoci suka yi gaggawar karɓarshi,kai tsaye aka ba shi gado aka tura shi emergency saboda lokacin da Haisam ya isa asibitin Mubarak ya fara kakkafewa,hakan ya tayar da hankalin Haisam sosai Ya kai aƙalla awa guda kafin likitan da ya karɓe shi ya fito, yana duban Haisam ya ce"officer biyo ni office za mu yi magana"babu musu Haisam ya miƙe jikinsa a sanyaye,ya bi bayan likitan suka nufi office ɗin likitan Sai da suka zauna likitan ya dube shi,a sanyaye ya ce "officer patient ɗin naka bai ci abinci ba,kuma gashi akwai alamun ba'a ba shi kulawa sosai game da ciwonsa,me yake faruwa ne?" Kallonsa Haisam ya yi a sanyaye,da farko kasa magana ya yi,sai daga baya da ƙyar ya iya faɗin "wanne irin ciwo ne haka? I'm sorry yaron baƙo ne" Likitan ya girgiza kai ya ce "yana da matsalar asthma,kuma ta taɓa masa huhu sosai,ta kai wani mataki wanda dole sai an saka masa idanu sosai A yanzu dai ba ya cikin matsala in sha Allah,amma ya kamata a ba shi kulawa sosai, saboda gudun matsala" Haisam ya yi shiru,gaba ɗaya kanshi a kulle,dama yaron nan yana da asthma ne ko kuma daga baya ya same ta? Cikin jimami da tausayawa ya girgiza kai ya ce"Allah ya ba shi lafiya, shikenan,in sha Allah za'a ba shi kulawa sosai,na gode sosai doctor"doctor ya ba shi hannu suka yi musabaha sannan ya mike ya fice daga office ɗin cikin yanayin damuwa Washe gari wajen ƙarfe tara na safe aka ba wa Mubarak discharge letter, Haisam ya ɗauke shi yadda ya saba suna hira suka nufi gida Yana shiga sashen Nanny ya samu Amna a zaune,tana ganinsu ta taso da gudu ta rungume shi tana faɗin "Daddy ban ganka ba,na duba kuma ban ga ƙanina ba,ina kuka je?" Janye ta ya yi gefe,ya ce"ba shi da lafiya Amna, idan kina yin magana da ƙarfi za ki saka masa ciwon kai,yau me kike yi har yanzu ba ki tafi makaranta ba?" Yar dariya ta yi ta ce"Daddy ai yau da gobe Friday muna hutun mid-term holiday,babu school"Haisam ya jinjina kai, sannan ya ƙarasa kan kujera ya kwantar da Mubarak da yake ta bin su da kallo Nanny ce ta fito, cikin girmamawa take faɗin "barka da dawowa yallaɓai" "Barka dai Hajiya,ya aikin,ya fama da yaran kuma?" Nanny ta ce"alhamdulillah,ashe mutumina ba shi da lafiya haka?"Haisam ya ce"wallahi fa,ashe wai ciwonsa na asthma ne ya tashi,amma yanzu alhamdulillah da sauƙi"cikin tausayawa Nanny ta ce"ya Salam! Allah ya ba shi lafiya ya tashi kafadunsa"Haisam ya ce"Ameen,bari na je,zan wuce wajen aiki ne "Nanny ta ce"to Allah ya bada Sa'a yallaɓai "ya ce "Ameen "ya fice daga sashen A gaggauce ya kammala komai ya fito cikin shigar suit baƙaƙe,sai addu'a yake yi Allah ya sa kar ya haɗu da Nimra, don ya makara,amma ina! Yana fitowa suka yi kiciɓus,ya ja baya a firgice,daga baya ya ƙaƙaro murmushi yana faɗin "good morning Nimra " Kallonsa kawai take yi tana nazartarsa, fuskarta a ɗaure ta ce"good morning,Ina zuwa haka?" Kai tsaye ya ce"aiki mana!ko kin manta yau ina da zuwa wajen aiki?" Gyara tsayuwa ta yi tana yi masa wani irin kallo ta ce"ka san da haka ai ka ƙi kwana a gida,gashi ka yi min alƙawarin za mu yi magana da kai, meyasa yanzu ka zama mai alƙawari da saɓawa ne?" Sauke ajiyar zuciya ya yi ya ce"yaron da muka zo da shi ne babu lafiya, shiyasa na kai shi asibiti" "Allah ya ba shi lafiya,ina fatan ka mayar da shi ga iyayensa,tunda ka ga ɗaukar alhaki ne barinsa a hannun wani a wannan halin,bayan ga iyayensa" Kallonta ya yi fuska a ɗan ɗaure ya ce"yana nan,da wani abu ne?" Taɓe baki ta yi ta ce"a'a,babu komai,kawai dai na yi mamaki ne, saboda Mamie ta ce har yanzu baka ce mata komai game da zaman yaron a gidan nan ba" Haisam ya tsare ta da idanu ya ce"okay zuwa kika yi kika tambaye ta Kenan?"shiru ta yi kanta a gefe tana taɓe baki,ya yi ƙokarin sauke temper ɗin sa ya ce"bana son ki rinƙa yi min irin haka,tunda ni da kaina na ce zan gaya miki ki jira na gaya miki, meyasa kike yin abu tamkar wadda bata yi karatu bane?ko yaron nan akanki yake da zama ne?" "I'm sorry "ta faɗa a daƙile,ya ce"sai na dawo, yanzu zan tafi aiki"yana kai wa nan ya kewaye ta ya wuce ya bar ta a wajen Bin shi ta yi da kallo fuska a ɗaure, kafin ta koma cikin gida tana taɓe baki,ranta a ɓace, don haka kawai take jin ta tsani yaron,kuma bata yarda da zamansa ba,tana jin akwai ayar tambaya Kai tsaye ta wuce sashen Hajiya Mamie, wadda itama take nata shirye shiryen don tafiya aiki,tana shiga sashen bata yi wata-wata ba ta faɗa ɗakin yayar tata tana huci Kallonta Hajiya Mariya ta yi, fuska a ɗaure ta ce"ya dai? Ya za ki faɗo min daki haka kamar wata karamar yarinya?" Nimra tana huci ta ce"Aunty ki tambaye shi inda ya samo yaron nan, bashi da niyyar gaya min, kuma wallahi zuciya ta fara raya min wata ya yiwa ciki ta haifar masa,don dai gashi kin ce ƴa ɗaya suka haifa shi da tsohuwar matarsa,gata nan Amna " Shiru Hajiya Mariya ta yi ba tare da ta yi magana ba,sai cigaba da gyara daurin ɗankwalinta da ta yi,sai da ta gama ta juyo tana kallon Nimra da saura ƙiris ta fashe saboda takaici,hankali a kwance ta ce "ina fatan dai ba shirmen naki kika je kika yi masa ba ko? Menene abin da zai dame ki akan ƙaramin yaron da har yanzu ba ki da tabbacin Wanene shi?" Nimra cikin ɓacin rai ta ce "shine abin da yake damuna aunty,ya gaya min mana idan yana da gaskiya,ita kanta Amna bana jin zan iya riƙe ta ballantana wani yaro da aka samo a kwararo,tsintacciyar mage" Hajiya Mariya ta ce"ai kuwa idan da irin wannan zuciyar za ki zauna da namiji ina mai tabbatar miki ba za ki taɓa cin riba ba, ita mace ma da aka santa da kissa? da ace hakan kika yi masa da tuni ba'a wuce wajen ba?kina tunanin wannan rigimar da kika ɓallo da ita zai biye miki ne ko zai ji tsoronki? To ba'a yiwa namiji haka,ki gyara yadda za kiyi mu'amala da shi,kar ki manta matsayin sa na mijinki ma gobe,kuma har yanzu neman soyayyarshi kike yi bai kai ga amincewa ɗari bisa ɗari ba,har yanzu abubuwan da za su faranta masa za ki koyi yi,ba wanda zai baƙanta masa ba Idan kina da hankali kamata ya yi ki kwantar da kai akan batun yaron nan,ki ja shi a jiki,da kanshi zai sanar miki da ko wanene shi,ai nima ba son zama na yi da shi a gidan nan ba,amma da na kwantar da kai gashi nan ke shaida ce, yadda na mallake ubansa " Nimra ta jinjina kai ta ce"I will try Aunty,da farko raina ne ya kai ƙololuwar ɓaci,amma yanzu na sauko,zan yi amfani da dabarunki in sha Allah" "Better!"a cewar Hajiya Mariya, sannan ta ɗauki handbag ɗinta da labcoat ɗinta,ya dubi Nimra ta ce"sai na dawo"ta fice daga ɗakin *HAISAM* Zama ya yi a office ɗin sa yana nazarin abubuwa da yawa,na farko labarin Roxy,bata kai ƙarshen labarin ba,amma daga yadda ya ga yanayinta har ya fara fargabar abin da zata ce masa a gaba, musamman game da iyayenta da danginta Ga lamarin auren da ta yiwa kanta,ya yarda laifinta ya fi yawa,amma tun daga farko ya ga laifin iyayenta,sam sam bai kamata su nuna mata ƙarfi a wajen hana ta auren masoyinta da liƙa mata auren cousin brother ɗin nata ba Sai maganar rayuwarta tare da Arnold,ta ba shi tausayi sosai, musamman yadda ta yarda da Arnold amma ya yaudare ta,kuma hakan ya karya mata zuciya sosai,a ƙarshe duk da yadda ya zama a gare ta ya kasance abin dogaronta,ya mutu ya bar ta Ko daga nan ta tsaya ya samu amsar dalilin da ya sa ta zama ƴar ta'adda, tunanin mace ba shi da tsawo sosai,kai ko da ace namijin ne mummunan halin da ta shiga daga wannan zuwa wannan zai iya sauya halayensa zuwa wani mutum dabam Yana nan zaune Musa ya shigo bayan ya yi masa izini,ya ɗaga kai yana kallon Musa,,Musa ya gaishe shi cikin girmamawa yana sara masa,cikin sanyin murya ya ce "ka haɗa min zama da team ɗin mu da muka yi operation na kama yarinyar nan" "Sir wacce yarinya kenan?" Haisam ya sauke numfashi ya ce "Shaheeda" "Ko dai Roxy yallaɓai?"rai a ɗan ɓace ya ce" ba dai ka gane ba? To sai ka yi min abin da na saka ka ko?"babu musu Musa ya sara masa, sannan ya fice daga office ɗin Bayan mintuna goma suka hallara gaba ɗaya su shidan, Haisam ya yi shiru yana nazarin ta inda zai fara Dakewa ya yi ya fara magana ganin gaba ɗaya sun ba shi attention,ya fara da faɗin "a ƙarshe dai ga Roxy ta shiga hannunmu,ina godiya da dukkan waɗanda suka taimaka min ma kama ta Sannan abu na gaba,a cikin mu shidan nan akwai wanda Roxy ta siya don ya faɗa mata sirrinmu, kuma ta yi nasara,ta siye shi ya fitar mana da sirri,a ƙarshe ta yi nasara akaina a karo na farko,sai dai a karo na biyu ban yi wautar sanar da kowa shirina ba,kuma cikin hukuncin Allah sai gashi na kama ta ba tare da wata matsala ba Ban damu da sanin wanene baren a cikinmu ba, abu daya zan faɗa muku kawai, shine ko ma wanene ya kiyayi gobe, saboda muddin zai cigaba da fitar min da sirri to tabbas zan gano shi watarana,kuma abin da zai faru zai ba ku mamaki Na sallame ku"yana kai wa nan ya mike ba tare da ya sake kallonsu ba ya fice daga office ɗin Sai da ya kammala abubuwan da zai yi,da lussafe-lissafensa sannan ya miƙe ya fice daga office ɗin, kai tsaye ya faɗa mota ya nufi jail ɗin da aka rufe Roxy Yau ma dai kamar kullum sai da ya nuna ID card ɗinsa sannan aka shigar da shi,aka fito da Roxy wadda gaba ɗaya ta yi wani irin sanyi Kallonta ya yi sosai, cikin kwantar da murya ya ce"kuka kika yi?" A hankali ta ɗago ta kalle shi, cikin sanyin murya ta ce"bani da dalilin kuka ne?" Haisam ya ce"of course kina da dalilin yin kuka,amma sai nake ganin kamar kukan ba mafita bane ko? Murmushi ya yi a sanyaye tana girgiza kai, sannan ta ce"Shi kadai ne makami na a yanzu,akwai lokacin da nake ƙyamatarshi, saboda na ɗauke shi a matsayin raunin da zai karya ni,amma a yanzu kuma shine maganina, shine babban makamin da nake da shi" Haisam ya girgiza kai ya ce"Roxy bai cancanci ta karaya irin haka ba" Kai tsaye ta ce"Roxy dama can a karye take,dakiya da gujewa rauni ne ya sa ake yi mata kallon jaruma " Haisam ya ce"yanzu kuma bai kamata ta rungumi raunin nan ba kuwa, saboda....." "Saboda me? Rayuwarta ta tsaya ko?ai na sani,babu babbar asararriya a duniya number ɗaya kamar Roxy, saboda......" "Zan iya samun cigaban labarin Roxy?"ya yi azamar katse ta da faɗin hakan yana kallonta,a ranshi yana danne yanayin da ta fara jefa shi Murmushi ta yi,ta ce "menene abin jan hankali a labarin Roxy ne har haka da ya kasa gundurarka?" Gyara zama ya yi, shima yana murmushi ya ce"Tun da na buƙace shi ke ma kin san dole zai yi min amfani,ke dai ki cigaba kawai"babu musu ta jinjina kai ta ce" haka ne kuma,to ga cigaban labarin Roxy........" #Nusy_bee Page 30 💫 A Murtala Muhammad airport da ke Lagos jirginsu Shaheeda ya sauka, tunda jirgin ya sauka gaban Shaheeda yake dukan uku-uku, tsananin firgici da tashin hankali ya bayyana akan fuskarta Ta san su wanene iyayenta, musamman mahaifinta,ta san yadda yake da zafi,kuma ba ya ɗaukar wargi,tana tsananin fargabar abin da zata je ta tarar Hotel ɗin da suka kama lokacin da za su tafi Spain ita ta sake komawa,ta kama ɗaki don ta huta, gobe ta bi jirgi zuwa Kano A wannan daren ko sau ɗaya bacci bai kawo mata farmaki ba,banda tashin hankali da fargaba, sai tunane-tunane da suka cunkushe mata ƙwaƙwalwa,a ranta tana addu'ar Allah ya ɗora ta akan Abba, Allah ya sa hukuncin da zai yi mata ya zamo da sauki A ranar dare ya yiwa Shaheeda tsawo,duniyar ta yi mata ƙunci, fargaba ta mamaye mata zuciya, tunani da taraddadi suka cunkushe mata ƙwaƙwalwa,ji take yi a duniya ta fi kowa shiga mawuyacin hali,kuma ta fi kowa shiga tashin hankali Washe gari ma ko ruwa ta kasa kai wa bakinta,jiki babu ƙwari ta yi booking jirgin da zai nufi Kano,kuma ba tare da ɓata lokaci ba suka hau zuwa kano Ta kai a ƙalla awa ɗaya tana nazarin yadda zata tafi gida, kafin daga baya ta yi shahada kawai ta tafi, bayan ta sauka ma taxi ta hau zuwa Maliya estate,tana tafiya a taxi ɗin banda matsanancin tunani babu abin da take yi,sai share hawaye A bakin maliya estate ta sauka daga taxi ɗin,ta sallame shi sannan ta ja akwatinta,amma ta kasa motsawa ko nan da can Kamar daga sama ta ji Muyassar yana faɗin "Shaheeda! Shaheeda daga ina haka?" A firgice ta ɗaga kai tana kallon Muyassar da yake ƙare mata kallo,jikinta babu inda ba ya rawa,amma duk da halin da take ciki babu abin da ta ji kunya da muzanta irin ganin ta da ya yi da tsohon ciki, musamman da ta kula idanunsa suna kan cikin nata yana kallonta da wani irin yanayi Da ƙyar ta lalubo nutsuwa,muryarta na rawa,kanta a ƙasa ta ce"ina kwana yaya Muyassar" Maimakon ya amsa sai ya ce"tsayuwar me kike yi anan? Wuce ki shiga ciki mana"shiru ta yi bata tanka ba,ya sake faɗin "wuce mu je na kai ki,kin zo kina tsayuwa a nan"ya wuce gaba,ta bi bayanshi jikinta a sanyaye,suka nufi cikin gidan Shaheeda ta sake muzanta ganin duk ta inda suka wuce sai an kalle su kafin su isa sashen Ummeey,suna zuwa ta ja ta tsaya tana lafewa a jikin bango, Muyassar ya kalle ta yana faɗin "ya dai? Ki wuce mu shiga ciki mana" Hawaye suka zubo mata,ta ce "ka bar ni a nan kawai,ina tsoron Ummeey" Yar dariyar takaici ya yi,ya ce"Shaheeda kenan! Wasu abubuwan kafin mu aikata su za muyi tunanin yadda makomarmu zata zama ba sai mun aikata ba, yanzu misali, menene amfanin wannan abu da kike yi yanzu? Ummeey mahaifiyarki ce,ke kaɗai ta mallaka wadda zata kalla ta ji sanyi na cewa eh tana da zuri'a a duniya,amma ba ki tuna hakan ba kika yi abin da zata yi kuka, why Shaheeda?" Ita dai Shaheeda bata tanka ba, sai kukanta da ya fara tsananta, Muyassar ya kwantar da murya ya ce"alright,komai ya wuce, na san ba za ki sake irin wannan aikin ba, Allah ya kyauta ya kiyaye gaba,tashi mu wuce ciki"babu musu ta miƙe, jikinta duk babu ƙwari suka nufi cikin sashen Ummeey Ummeey tana zaune a parlour tana shan tea a hankali sai ta ji sallama,a gigice ta ɗago tana kallon Shaheeda wadda gaba ɗaya ta fita hayyacinta, Shaheeda ta kasa jurewa ta taho da gudu ta faɗo jikinta tana kuka mai gunji, Ummeey bata yi wani yunƙuri ba sai kukan da ta fashe da shi ita ma, tana bin tilon ƴar tata da kallo, wadda gaba ɗaya ta fice a hayyacinta tamkar ba dirarriyar ƴarta Shaheeda ba,mai kazar kazar da yawan surutu Yanzu duk ta yi sanyi ta canja,ta rame sosai,mafi girman tashin hankalin da ta gani a tare da ita shine tsohon cikin da yake jikinta "Ummeey don Allah ki yafe min!na yi kuskure!na bijirewa maganarki,a ƙarshe ban samu sakamako mai kyau ba,don Allah Ummeey ki yafe min,don Allah Ummeeyna"kunnuwanta suka ɗauko mata sautin Shaheeda cikin gunjin kuka Da ƙyar Ummeey ta iya ɗaga harshenta ba tare da ta kalli Shaheeda ba,ta fara magana cikin karayar zuciya "Shaheeda! Allah ne shaida,a tsawon lokaci tun da na haife ki ƙoƙarina shine na ba ki tarbiyya,bani da kowa a kusa da ni daga ke sai mahaifinki,ke ce kaɗai ƙwan da Allah ya ba ni, wanda nake saka ran samun walwala daga gare ta,amma a ƙarshe a dalilinki na yi nadamar haihuwa,wasu mutanen suna kuka saboda ba su haihu ba,wasu mutanen suna alfahari da ɗaya ko da yawa da Allah ya ba su,amma ga ni ina kuka saboda na haihu,ina nadama saboda ɗaya da Allah ya ba ni, meyasa Shaheeda?me nayi miki da zafi haka?" Kukan Shaheeda ya tsananta, cikin kuka ta sake rungume Ummeey tana faɗin"don girman Allah Ummeey ki yi min rai, Ummeey ki yafe min, wallahi na yi nadama, ba zan sake ba,don Allah Ummeey kar ki juya min baya, wallahi ina sonki Ummeey,ke ce....."a fusace Ummeey ta hamɓare ta daga jikinta tana aika mata da wani mugun kallo,hawaye bai tsaya a idanunta ba ta ce"kina so na Shaheeda?a hakan? ƙarya kike yi!!! Da kina so na da ba ki so raina ya ɓaci ba ko yaya ne Shaheeda da kina so na da ba ki guje ni ba,da ba ki jefa ni a cikin baƙin ciki da tashin hankali ba! Shaheeda kin san a halin da na samu kaina da na rasa ki a kusa da ni kuwa Meyasa? meyasa za ki yi min haka?me na yi miki?"ita dai Shaheeda wannan karon babu baki,sai kukan da ita ma take yi cikin tsananin tashin hankali, fargaba da damuwa Sun kwashi mintuna a haka, kafin Ummeey ta dubi Shaheeda fuska babu rahama ta ce"sai abu na gaba! wanene ya yi miki cikin jikinki?" Muryarta a shaƙe saboda kuka ta ce"Arnold ne" Shiru Ummeey ta yi gabanta yana faɗuwa,ta ce"wanene Arnold?"daidai nan Muyassar ya dawo parlourn da sallama, fuskarsa babu walwala Kanta a ƙasa,tana jin wata muzanta da nadama, muryarta tana rawa ta ce"wanda na aura " "Kika aura?"a cewar Muyassar yana kallonta da wani irin yanayi,"yaushe kuka yi auren?kuma wanene ya ɗaura miki auren?" Kanta a ƙasa ta goge hawayenta ta ce "kafin na tafi, wajen malami muka je aka ɗaura mana auren" Shiru Muyassar ya yi yana bin ta da kallo cikin tsananin mamaki da takaici,ya ce"wanne malami ne haka da kuka je ya ɗaura muku aure ba tare da ya yi tunanin abin da zai je ya zo ba" Tana shashsheƙar kuka ta ce"ku yafe ni don Allah, Ummeey don Allah ki yafe min" A fusace Ummeey ta kalle ta ta ce "tambayarki ake yi amma kin zauna kina shirme!kin san tsaf zan lakaɗa miki duka a gidan nan?ba ki san a ƙule nake da ke ba ko?" Jikinta yana rawa ta fara ba su labarin abin da ya faru tana kuka,suka zuba mata idanu suka kallonta cikin tsananin mamaki,har ta kammala labarin,tun daga lokacin da suka yi aure da Arnold har zuwa lokacin da Diego ya saka ta a jirgi ta dawo Nigeria,da ƙyar ta kai ƙarshe kafin ta sake rushewa da kuka mai tsanani tana faɗin"don Allah Ummeey ki yafe min, zuciyata ciwo take yi min,don Allah Ummeey,zan mutu ki taimaka ki yafe min, Ummeey ki yi min addu'a don Allah,don Allah Ummeeyna"ta faɗa da ƙarfi cikin muryarta da bata fita sosai tana rungume Ummeey da ƙarfin tsiya, wadda itama zuwa yanzu kukan take yi sosai Muyassar ne ya kama hannunta ya janye ta daga jikin Ummeey, wadda har yanzu bata yi wani yunƙuri ba, banda kukan da take yi kamar ranta zai fita,ya zaunar da ita yana faɗin "kukan ya isa haka Please,ki daina wannan kukan, abin da ya faru ya riga ya faru, Allah ya kyauta ya ba ki ikon cinye wannan jarrabawar,amma ke ma ya kamata ki daina taurin kai da gardama, Allah ya raba ku da abin da ke cikinki lafiya ya albarkaci rayuwarsa,ki kwantar da hankalinki kin ji? In sha Allah komai zai daidaita,ki daina kuka"ya ƙarashe maganar yana goge mata hawaye Cikin kuka ta ce"yaya ina tsoron abbana, Ummeey har yanzu tana cikin fushi da ni, tsoro nake ji yaya" Muyassar ya ce"kin san dai ke favourite ɗin abba ce ko? To ki kwantar da hankalinki, in sha Allah ba zai ɓata miki rai ba, Ummeey kuma ki ba ta lokaci zata huce Ya kamata zuwa yanzu a ce kin kwantar da hankalinki,kin fawwalawa Allah komai kin ji yar ƙanwata?idan ba haka ba kuma ba zan sake shigowa wannan sashen ba,idan ma na shigo to wajen Ummeey kawai na zo,ba wajenki ba"Shaheeda ta yi saurin goge hawayenta tana faɗin"na daina kukan yaya,na daina,amma don Allah ka cewa ummeey ta yafe min"Muyassar ya ce"ki kwantar da hankalinki,in sha Allah ta yafe miki ma,me za ki ci yanzu?" Shaheeda ta girgiza kai ta ce"na ƙoshi yaya" Muyassar ta ɗaure fuska ya ce "okay ba ki huce ba kenan?" Da sauri ta girgiza kai ta ce "a'a yaya,ka kawo min avocado,ina so zan ci"Muyassar ya yi murmushi yana lakace mata hanci yana faɗin "that's my little ƙanwa! Sai na dawo,ki kula kin ji"ya miƙe ya fice daga sashen yana ɗaga mata hannu Bayan fitar Muyassar aka fara zaman kurame tsakanin Ummeey da Shaheeda,sun kai aƙalla mintina goma kafin Shaheeda ta dubi Ummeey ta yi ta maza, cikin raunin murya ta ce"don Allah Ummeeyna ki yafe min Kin ji Ummeey?ko zagina ne ki yi, Ummeey ki dake ni ko za ki huce,amma don Allah ki yafe min,ki yafe min don Allah,kin ga halin da ma shiga a sanadin fushin da kika yi da ni,don Allah ki yafe min na samu sassauci kin ji Ummeeyna?" Duk da yadda zuciyar Ummeey take zafi,amma abinka da ɗa da uwa,sai ta ji zuciyarta ta karye, tausayin Shaheeda ya rufe ta,ta dube ta, cikin sanyin murya ta ce"Allah ya ƙara ganar da ke, Allah ya raba ku lafiya , Allah ya ba ki lafiya, tashi ki je ki yi wanka ki sauya kaya,me za ki ci?" Murmushi ya ƙwacewa Shaheeda,ta rungume Ummeey tana faɗin "na gode Ummeeyna, Ummeey ko menene kika dafa zan ci, Allah ya saka miki da alkhairi Ummeeyna"daga haka ta miƙe ta shige zuwa ɗakinta tana farin ciki Jikinta ya yi sanyi sosai lokacin da ta ga wasiƙar da ta rubutawa Ummeey a inda ta bar ta, Allah sarki Ummeey! yanzu haka don kar damuwa ta dame ta ne ta kasa shigowa ɗakin, Allah sarki Ummeey!ta goge hawayenta ta shiga wanka A parlour kuwa Ummeey tana zaune sai ga Hajiya Atika kamar an hankaɗo ta, kallonta Ummeey ta yi gabanta yana faɗuwa,amma ta dake ta ƙaƙaro murmushi ta ce"a'a! Maman Malika!ya yaran?" "Yara alhamdulilla!sune suke gaya min wai Shaheeda ta dawo, menene gaskiyar maganar?" Jikin Ummeey a sanyaye ta jinjina kai,ta ce"eh Shaheeda ta dawo,tana ciki ma, yanzu ta shiga" Hajiya Atika ta jinjina kai ta ce "to kenan gaskiya yaran suka faɗa da suka ce ta dawo da tsohon ciki kenan?" Ummeey ta kalle ta jiki a saɓule kafin ta yi ƙasa da kai, Hajiya Atika ta ce "tambaya nake yi Hajiya,da gaske ne?" Ummeey ta ce"da gaske ne,ta dawo da ciki"Hajiya Atika ta rafka salati tana rike haɓa ta ce"oh Allah ka dube mu! Wai cikin shege a gidan Alhaji Yusuf Maliya duk da tarin tsaro da tarbiyyar gidan? To Allah ya sawwaƙe,da kika ce mata ta dawo yau ai alhajin nan da abin da bai wuce sati guda ba ma zai dawo,shi da kanshi ai zai yi abin da ya dace,don dai mu ma muna da ƴaƴa mata, gaskiyar magana kenan"ta juya fuuu ta fice daga parlourn Ummeey ta bi ta da kallo kawai ba tare da ta iya ce mata komai ba,ta sani hakan zata faru, fiye da haka ma zata iya faruwa, gashi Hajiya bata nan ballantana ta tura ta gidanta,amma zata yi magana da Hajiya Jamila,zata je gidanta ta zauna,don ba zata iya wannan tashin hankalin ba,ba za'a yi haka da ita ba Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci maganar dawowar Shaheeda ta bazu a maliya estate,da yawa sai zuwa ake yi a ganta, musamman idan an faɗi da tsohon ciki ta dawo,babu wanda yake da tunanin ya tambaye ta daga ina ta samo cikin, banda wanda Muyassar ya yi mata,shi kuwa Muyassar ya ce mata kar ta damu da kowa, Allah ma ya sani ba zina ta yi ba,ba ɗan shege bane a jikinta don haka kar ta wani damu,idan ta haihu ma shine zai zama baban yaron Hakan ya sa ta yi kuka sosai,ta yi nadama,amma ta san auren Muyassar ya fi ƙarfinta,don ta ji an ce watanni uku ne suka rage a yi aurensu da Arfa, wadda tun da Shaheeda ta zo bata ganta ba,alamun tana gidan iyayenta Kwanan Shaheeda biyu da dawowa,da daddare suna zaune a parlour, Shaheeda tana cin avocado da yanzu ita ce abincinta,yau ma through out ta kasa cin komai saboda jikinta da ya motsa sai da Ummeey ta kai ta asibiti,ba su juma da dawowa ba ma Wayar Ummeey ce ta yi ƙara,sai da gabanta ya faɗi ganin wanda yake kira, Abba ne #Nusy_bee Page 31 Kallon Shaheeda Ummeey ta yi, wadda take ta kallonta tunda wayar ta fata ringing,don ta gane abbanta ne ya kira daga yanayin ringing ɗin, Ummeey ta ɗauke idanunta saboda hango damuwa da fargaba da ta yi a idanun ƴar tata,ta ɗaga wayar da sallama a bakinta A gaggauce Abba ya amsa,ya kira sunanta "Zainab!"gyara zama tayi tana amsawa "na'am Alhaji" "Menene gaskiyar maganar da na ji na cewa Fatima ta dawo gida?" Sai da Ummeey ta kalli sashen da Shaheeda take zaune ta yi tsumu, sannan ta ce "eh haka ne,ga ta a gida" Abba ya ce "to da kyau"kafin ta yi wani yunƙuri ya kashe wayarshi Shiru Shaheeda ta yi tana kallon Ummeey,tashin hankali yana bayyana a kan fuskarta, cikin rawar murya ta ce"Ummeey me ya ce?" Ummeey ta kalle ta da kulawa ta ce"bai ce komai ba,ki kwantar da hankalinki,babu abin da zai faru sai alkhairi in sha Allah,ke dai ki yi ta addu'a kawai,kin ji?"Shaheeda ta jinjina kai cikin sarewa, sannan ta miƙe don mayar da abincin zuwa kitchen,don gaba ɗaya ya fita a ranta,Ummeey ta kalle ta ta ce"ina za ki je?" Shaheeda ta ce "na ƙoshi,zan mayar da abincin kitchen"Ummeey ta ce "to dawo ki zauna,idan kin manta bari na tuna miki,a dokokin da aka kafa miki ɗazu har da ta hana zama da yunwa,maza zo ki zauna ki ci"babu musu ta dawo ta samu waje ta zauna,ta cigaba da cusa abincin Ummeey tana kula da yadda ta tsangwami kanta tun wayar da suka yi da Abba,don haka ta fara ba ta labarai masu ɗebe kewa,tun Shaheeda bata sakewa har ta fara Washe gari da fargaba Shaheeda ta tashi, duk daily activities ɗinta da ta yi a sanyaye,ita kanta a yanzu bata da burin da ya wuce Abba ya dawo ta san makomarta a gidan,ko dukan tsiya zai yi mata bata damu ba muddin zai yafe mata,ya bar komai ya wuce kamar Ummeey Haka ta yini zullumi da fargaba har zuwa bayan la'asar,bata juma da idar da sallar la'asar ba ta ji alamun dawowar mahaifin nasu Gabanta ya faɗi,ta yi tagumi tana jin yadda zuciyarta take lugude,bata taɓa tsammanin akwai wata rana a duniya da zata zo ta yi fargabar ganawa da mahaifinta ba, saboda irin yadda suka shaƙu, kuma suke tsananin son juna Ummeey tana kule da ita, ganin tunanin ba zai ƙare ba sai ta dube ta ta ce"Shaheeda wai lafiyarki kuwa?tun ɗazu kina abu ɗaya? tunanin me kike yi ne haka?" Hawaye suka cika mata idanu, cikin sanyin murya ta ce "Ummeey ina tsoron gamuwa da Abba ne,ina tsoron hukuncin da zai yanke akaina,don Allah Ummeey ki ba shi haƙuri,na yi nadamar abin da na yi a baya" Tausayin ƴar tata ya kamata,amma sai ta ɗaure fuska ta ce"ai damuwa kuma kin yi ta gamuwa da ita kina fargaba kenan, tunda kika yiwa kanki tabon da ba zai gogu ba, yanzu bari na je na yi masa barka da zuwa,idan ya buƙaci ganinki sai na kira ki, idan ya ce baya buƙatar ganinki kuma sai zuwa gobe wataƙila"Shaheeda ta jinjina kai ba tare da ta yi magana ba, Ummeey ta saka hijabi ta fice daga sashen Kamar yadda aka saba a babban parlourn Alhaji Yusuf iyalan nashi suke haɗuwa da ɗaiɗai da ɗaiɗai don yi masa barka da dawowa daga ƙasar Ghana da ya je wani taron kasuwanci nashi,kamar yadda ya saba yana ta tambayar kowa yadda yake, musamman ƴan makaranta Shigowar Ummeey ta rage masa walwala, sannan kuma ta haifar da wani kallo daga sauran matan,amma sai ta yi kamar bata gani ba,ta gaida Alhaji Yusuf,bai amsa ba ya ce"ina Fatima?" Gaban Ummeey yana dukan uku-uku ta ce"tana sashena "Abba ya ce"to babu laifi,kira min ita"Ummeey ta miƙe ta fice daga parlourn ba tare da ta yi magana ba, kishiyoyinta suka raka ta da kallon banza Yadda ta bar Shaheeda haka ta dawo ta same ta,ta ce "Shaheeda taso mu tafi, Alhaji yana nemanki" Sai da Ummeey ta taimakawa Shaheeda ta tashi,don gaba ɗaya jikinta karkarwa yake yi,har ƙafafun nata suke neman gaza daukarta Suna zuwa bakin ƙofar sashen Abba Shaheeda ta coge gabanta yana bugawa, fuskarta ta bayyanar da tsoro, Ummeey ta kalle ta, fuska a daure ta ce"wuce mu je mana, bana son sakarci fa" "Ummeey tsoro nake ji,ban san me Abbana zai yi min ba, don Allah Ummeey ki ba shi haƙuri kin ji" Ummeey ta ɗaure fuska ta ce "bana son shirme Shaheeda, wuce mu tafi,idan ba haka ba kuma zan koma na ƙyale ki da shi"tana faɗin haka ta yi gaba ta shiga parlourn,itama Shaheeda bata da wani zaɓi wanda ya wuce ta bi bayan Ummeeyn duk da yadda ƙafarta take rawa Da sallama suka shiga,kan Shaheeda a ƙasa,da ƙyar take iya controlling kanta saboda yadda jikinta yake rawa Suna shiga gaba ɗaya idanun mutane ya yo kansu,gaban Ummeey ya faɗi ganin sauran yaran da ba sa wajen ma yanzu duk sun hallara,har da Hassan da Hussaini da Na'ima,ga ƙannen mahaifinta maza, uncle Habib ne kawai babu,ga wasu daga cikin yaransu su ma duk a zazzaune Sai da ta kusa faɗuwa, Allah ya sa Ummeey tana kule da yanayinta ta riƙe ta,ta taimaka mata ta zauna,ba ita Shaheeda ba,ita kanta Ummeey jinta take yi a muzance,suka samu waje suka zauna, Shaheeda ta rissina bakinta yana rawa tana faɗin"Barka da dawowa Abbana!" Shiru falon ya ɗauka kowa yana kallonta, ƙasa-ƙasa take jiyo tsaki da maganganu daga wajen mutanen parlourn Abba ya gyara zama sosai yana dubanta, kafin ya kira sunanta"Fatima!"a firgice ta ɗago ba tare da ta iya amsawa ba, ƙirjinta sai tsananta bugu yake yi saboda tashin hankali da fargaba da taraddadi, Abba ya sake faɗin "Fatima! Ki amsa mana!"jikinta yana rawa, bakinta ma yana rawa ta amsa da faɗin "na'am Abbana!" Abba ya yi wata dariyar takaici ya ce"a baya nake amsa wannan sunan Fatima,amma daga lokacin da kika shaidawa duniya akwai wani mutum da ya fi ni ƙima da daraja a idanunki na san cewa na rasa wannan ƙima da darajar Yanzu dai ki faɗa kowa ya ji,ina kika samu ciki?kuma me ya dawo da ke gida bayan tsawon lokacin da kika ɗauka ba tare da kin tuna cewa kina da mu ba?" Kuka sosai Shaheeda ta fashe da shi mai gunji, kafin ta fara faɗin"don Allah Abba ka yafe min,Abba ka yafe min don girman Allah, wayyo Abbana don Allah......." "Dakata min!"ya daka mata tsawar da ba ma ita ba,da yawan mutane a ɗakin sai da suka firgita,ita kuma ta dafe cikinta da ta ji ɗan cikin ya yi zillo kamar zai fito duniya, Abba bai kula ba ya cigaba da magana cikin kaushin murya"ki ba ni amsar abin da na tambaye ki, shine abin da ya tara mu anan kawai,me ya faru har kika tuna da mu kika dawo?"cikin kuka da rawar murya Shaheeda ta fara bada labarinta kamar yadda ta ba wa Ummeey, kafin ta gama gaba ɗaya ta fice hayyacinta saboda matsanancin kukan da take yi,ga fargaba da tashin hankali da take ciki Tana gamawa kuma Hajiya Atika ta fara da faɗin"ikon Allah! Dama an ce duk wanda bai ji bari ba ya ji hoho,yawan bariki ai ba shi da daɗi,don wannan maganar an dai samu manya sun yi mata kwaskwarima ne dai kar sunan ƴaƴan ya ɓaci,amma wata maganar mutum yana ji ya san faɗarta kawai aka yi" Hajiya Sa'adatu ta cafke maganar da faɗin "Ni na rasa ma abin da zan ce,to Allah ya kiyashe mu da damalmalewar zamani,sai a san yadda za'a yi,ko na ce matakin da za'a ɗauka saboda namu ƴaƴan " Abba ya kalli Shaheeda da ta takure tana kuka sosai,ya kalli Ummeey da kanta yake a ƙasa,babu mai gane yanayin da take ciki,ya fara magana cikin ɗaci da kaushin murya "A Tsawon shekarun da kika yi a duniya daidai gwargwadon iyawa babu irin gatan da ban yi miki ba,abu ne sananne a cikin Maliya family gaba ɗaya ke na zaɓa a matsayin wadda na fi ji a raina, kasancewarki ƴata ta fari, sannan kuma ƴa ɗaya a wajen mahaifiyarta,a wancan karon ba zan yi musu ba ba kya son ɓacin raina ko da wasa,don haka nima nake jinki a raina Amma kwatsam!kika zaɓi ki zubar da wannan martabar daga gare ni,kika nuna wani kika zaɓe shi a matsayin wanda kike son ki cigaba da rayuwa da shi, wanda na ba ki kika bijire masa,kika zaɓi ki bi wani ki bar ni,ki bar mahaifiyarki ba tare da kin yi tunanin cewa wata rana irin haka zata zo ba,to gashi ta zo,kuma kina kan girbar abin da kika shuka,to madalla,hakan ya yi daidai,dama duk abin da mutum ya shuka a rayuwa shi zai girba,don haka ke ma ki cigaba da girbar naki Yanzu abin da na kira ki na sanar da ke shine,a baya ke kika nuna ba kya buƙatarmu,kika tafi kika bar mu, yanzu kuma da duniya ta yi miki juyin kwaɗo sai kika dawo gare mu,to mu ma a yanzu ba ma bukatar ki!!!"a gigice Shaheeda ta ɗaga kai tana kallon Abba idanu a waje,bai damu ba ya cigaba da faɗin"don haka yanzu za ki tattara ya naki ya naki ki koma inda kika fito, sannan da buƙatar ki manta a duniya kina da uba mai suna Yusuf kamar yadda na cire ki a sahun ƴaƴana na bar wa duniyar da kika shiga ke Na ba ki awanni uku ki tattara ki bar min gida,akasin haka kuma ranki sai ya ɓaci fiye da tunani,sai na sa kin ji a duniya ban taɓa saninki ba" Kuka mai tayar da hankali Shaheeda take yi yana faɗin"Abba na yi nadama,ka yafe min abbana, don girman Allah, Abba na shiga uku,don Allah Abba ka taimaka min " Hajiya Sa'adatu da ke gefe tana ɗan murmushi ta ce"a'a Alhaji,tunda dai ta yi nadama,kuma gashi mun gani komai ya ƙare mata,ga tabo ya kamata a duba don Allah " Hajiya Ruƙayya ta kalle ta da sauri ta ce"ya kamata ki rinƙa duba makomar yaranmu kafin a aiwatar da wani abin Idan aka yafe mata nan gaba ma wani daga cikin yara zai yi sha'awar Hakan saboda ya san za'a yafe masa, don haka yana da kyau a hukunta ta"Ummeey dai kasa jurewa ta yi,ta miƙe jikinta a sanyaye ba tare da ta kalli kowa ba ta fice, Shaheeda ta kasa tashi tana gunjin kuka mai tsanani Da ɗaiɗai da ɗaiɗai aka fara miƙewa ana ficewa,itama Shaheeda ta miƙe ta fice,sai dai bata koma cikin gidan ba,ta raɓe a jikin bango tana kuka mai sauti Uncle Aliyu ne ya dubi Abba fuska a ɗaure ya ce"yaya idan ka yi min izini ina son zan riƙe Shaheeda,ko da ace kana ganin bata horu ba ni zan yi mata wani horon da ba zata sake marmarin yin abin da ta yi ba, ballantana ma duk wanda ya ganta ya san tana cikin nadama mai yawa sosai,ina tsoron kar ta jefa kanta a cikin wata trauma wadda zata yiwa rayuwarta illa " Alhaji Yusuf cikin ɗaurewar fuska ya ce"ban ba ka izini ba,ko a yau ko a gobe, trauma kuma ta daɗe bata shiga ba,amma ni bana buƙatarta a gidana ko a area da ta shafi gidana,kai ma idan kana buƙata sai na sallama ka kamar yadda na sallama ta,na sallame ku" Duk maganganun Abba a kunnen Shaheeda,ta yi shiru tana jinginar da kanta a jikin bango, lokaci guda kuma ta ji zuciyarta ta ƙeƙashe,kukan da take yi ma ta daina,a hankali ta ja ƙafafunta ta fice daga gidan,ta cigaba da tafiya a ƙafa har ta fice daga cikin maliya estate,ta hau titi Babu ko sisi a jikinta,ga gari ya fara duhu,alamun magriba ta kusa,ga yunwa da take ji saboda ta kasa mayar da hankali ga abinci,a hankali ta ɗago zoben gold ɗin hannunta, wanda ba zata manta ba Abban ne ya bata da hannunsa a wata tafiya Dubai da ya yi,ita kaɗai ya yi wa tsarabar irin zoben,ta shafa kunnenta,ɗan kunnen da Ummeey ta kawo mata ne a wata tafiya Umrah da ta yi,su ne abubuwa na ƙarshe da take da su,a lokacin da tana rayuwa a Spain tare da Arnold su take kalla take tunawa da iyayenta Amma a yanzu tana jin cewa lokaci ya yi da zata rabu da su ko da a ce bata son hakan,tana buƙatar ingantacciyar rayuwa ita da abin da yake cikinta,bata da komai,kuma bata da kowa sai wannan zoben da ƴan kunnayen,da su zata gina rayuwarta da na yaron da ya shiga masifar rayuwa da tangarɗa tun kafin ya shaƙi iskar duniya Ta shafa cikinta a hankali,ta yi ɗan murmushi jin yana motsi,ta ce"kai kaɗai gare ni a duniya yanzu,ina addu'ar Allah ya da ka zame min sanyin idaniya,ka zama duk abin da na rasa, ka share min hawaye, mamanka tana sonka ka ji masoyina, Allah ya kawo min kai lafiya"ta ƙarasa magana yana goge hawaye, zuciyarta tana sake karyewa #Nusy_bee Page 32 Tafiya ya cigaba da yi a hankali, lokaci lokaci tana share hawayenta,kafin ta koma gefe ta zauna ta yi shiru tana kallon masu wucewa da komawa Tana nan a tsugunne har dare ya soma yi sosai,ga bacci,ga gajiya,ga yunwa, abubuwa sun yi mata yawa sosai, lokaci lokaci take share hawaye Bata san inda zata dosa ba, ballantana ta san me zata yi, tana nan a zaune ta ji magana kamar daga sama "Baiwar Allah lafiya?me kike yi a nan wajen?" A firgice ta ɗaga kai tana kallon mutumin da zai iya kai wa shekaru arba'in ko ma fiye,amma sai ta kasa ba shi amsa,ya sake tambayarta "baiwar Allah na ce lafiya? Me kike yi a nan da wannan tsohon daren?" Goge hawayenta ta yi ta ce "ni baƙuwa ce,ban san inda zan je bane,garinmu ana tashin hankali ne,an kashe mijina gashi bani da kowa"ta samu kanta da yin wannan ƙaryar Duk da cewa ba shi da tabbas na maganarta amma ya tausaya mata sosai,ya ce "to Allah ya kawo mana ɗauki,tashi ki shiga a daidaita sahuna gata nan,sai na kai ki gidana, zamanki a wajen nan a matsayinki na mace hatsari ne"Shaheeda ta rissina tana godiya,ta shiga a daidaita sahun tashi,ya tayar suka bar wajen Wata ƴar ƙaramar unguwa ta masu ƙaramin ƙarfi ya nufa da ita,a ƙofar wani tsohon gida suka yi parking, Shaheeda ta fara bin gidan da kallo,a ranta tana tsarkake Ubangiji,dama akwai irin waɗannan mutanen masu rayuwa a irin wannan gidan a duniya? Bata sake tsinkewa da lamarin Ubangiji ba sai da ta shiga gidan,ɗakuna ne a jere,kusan guda shida,amma da alamu wannan mutumin ba shi kaɗai bane a gidan,don ta ga wasu maza guda biyu, ɗaya ma suna tare da matarsa,da alamu su ma mazauna gidan ne Wasu ɗakuna ya nufa a cikin ɗakunan gidan,ya shiga wani da sallama Matar da take zaune tana gyarawa wasu yara shimfiɗa ta ɗago tana kallonsu tana faɗin"sannu da zuwa! Ka daw....."maganar ta maƙale a bakinta ganin Shaheeda a bayanta, wadda ta yi tsuru-tsuru kamar a ce mata 'kyat'ta zura da gudu Mutumin bai tankawa matar ba,ya dubi Shaheeda da kulawa ya ce"mata ƴan mata shigo,ga waje ki zauna "babu musu Shaheeda ta shigo cikin ɗakin, sannan ta zube a gaban matar tana gaishe ta A yatsine matar take kallonta da cikin jikinta, kafin ta amsa da" lafiya "Sannan ta miƙe ba tare da ta sake kallon sashen da suke ita da mijin ba ta fice daga ɗakin,shima kuma babu ɓata lokaci ya bi ta, Shaheeda da take zaune ta bi su da kallo duk jikinta a sanyaye Su kuwa suna shiga ɗaya ɗakin da ya zama na kwanansu ta dubi mijinta da ya shigo ta ce"baban faruku wacece wannan yarinyar da kuka zo tare?a ina take?" Baban faruku ya samu waje ya zauna,ya dube ta ya ce"haba Rabi, menene abin ɗaga hankali ne? zauna sai na gaya miki ko?"babu musu rabi ta zauna,baban faruku ya gaya mata komai da Shaheeda ta gaya masa Shiru ta yi na ɗan lokaci tana kallonsa, kafin ta ce"to yanzu da ka kawo ta ya kake ganin za'a yi da ita? Ka san dai ɗakunan da ka kama mana guda biyu ne,kuma ɗaya nawa ɗaya na yarana,don haka a bayyane yake bata da wajen kwanciya a gidan nan,sai kuma maganar matsayi,a matsayin wa ka kawo ta gidan nan?" Shiru baban faruku ya yi na wasu mintuna kafin ya ce"ai ba zama zata yi mai tsawo ba,na ga tana buƙatar neman taimako ne,ga dare, na san za ki taimaka kasancewarta mace shiyasa na kawo ta,kuma ba a matsayin kowa ba sai na baiwar Allah musulma mai buƙatar neman taimako, shine za mu taimaka mata kawai" Rabi ta haɗe rai ta ce "to ta zauna,amma ba daɗewa zata yi ba, sannan kuma ban yarda da mu'amala tsakaninku ba,kuma na ɗan lokaci ne zata tafi,ni ba don cikin jikinta ba ma da sati guda zan ɗebar mata ko ta tafi ko na kore ta wallahi " Murmushi ya yi ya ce"to babu matsala in sha Allah,amma yanzu ki ba ta abinci idan akwai"Rabi bata kalle shi ba ta ce"babu,sai dai ko naka"kai tsaye ya ce"a ba ta nawa babu matsala,kin ga ta fi ni buƙata saboda abin da take ɗauke da shi"rabi ta kalle shi tana taɓe baki sannan ta miƙe tsaye ta ɗauki kwanon dambun da ta yi ta fice don kai wa Shaheeda Shaheeda tana zaune ta takure kamar mai jin sanyi, zuciyarta cike da fargaba,sam bata ga laifin matar nan ba idan ma korarta ta yi ko ta hantare ta,ita da mahaifinta ma ya kore ta,ya nuna baya buƙatarta? Ta goge hawayenta tana gyara ƙafarta da ta yi tsami, kafin ta yi wani yunƙuri sai ga Rabi ta shigo tana sallama ciki-ciki Shaheeda ta amsa murya a sanyaye, rabi ta kalle ta a fizge,sai da gabanta ya faɗi,don kyan yarinyar ya ba ta tsoro, a ranta ta ji dole ma ta saita mata hanya nan ba da jumawa ba,kar mijinta ya sauya tunani akanta A sanyaye Shaheeda ta sake gaisheta,ta amsa da "lafiya,ga abinci nan ki ci,idan kin gama ci ga buta can sai ki yi alwala ki yi sallah,ya sunanki ne ma?" Shaheeda ta yi shiru na ƴan seconds, kafin ta ce "sunana Fatima" "To ya yi kyau Fatima"ta jefa mata wani tsohon labule duk ya yi ƙura,ta ce"kyau shimfiɗa a can wajen,daga bakin ƙofa, saboda kin ga babu waje"Shaheeda ta ɗauka tana faɗin "to na gode aunty"rabi ta kalle ta ta taɓe baki sannan ta fice daga ɗakin Alwala Shaheeda ta ɗauro,ta zo ta tayar da sallah,ta rama magriba da isha'i da bata yi ba, sannan ta zauna ta fara cusa abincin,su da daɗin da dambun ya yi mata,abinka da mai ciki,amma ta kasa cin shi sosai, ragowar sai rufe shi ta yi ta koma ta kwanta a takure,bayan ta shimfiɗa labulen da aka ba ta, saboda tsananin gajiya da nauyin jiki irin na mai ciki cikin ɗan ƙanƙanin lokaci bacci ya yi awon gaba da ita A ɓangaren Ummeey kuwa,da ƙyar ta danne kukan da take yi ya shiga sashenta,kanta har wani jiri yake yi ta lalubo wayarta,babu ɓata lokaci ta dokawa Hajiya Jamila kira Bugu biyu ta ɗaga da sallama, Hajiya Zainab ta amsa tana faɗin"Hajiya Jamila kina nan?" Hajiya Jamila ta yi shiru na ɗan lokaci tana nazartar muryar Hajiya Zainab, kafin ta ce"me yake faruwa ne Hajiya Zainab? Ko dai wannan matsalar ce?" Kuka ya ƙwacewa Hajiya Zainab, cikin karayar zuciya ta ce"ta faru ta ƙare ma Jamila, Alhaji ya kori Shaheeda,ya ce ya cire ta daga cikin ƴaƴansa" Hajiya Jamila ta ji dukan maganar,ta san dole abin zai yi wa Hajiya Zainab ciwo, ƴarta ɗaya, Allah ya jarabce su akanta,amma mahaifinta maimakon ya zaɓi ya gyara ya gwammace ya nunawa duniya cewa shi yana da wasu yaran ko da ace bata tare da shi,ya manta komai daren daɗewa matsayinta na ƴa a wajensa ba zai taɓa canjawa ba Amma sai ta dake ta ce "to Hajiya Zainab ki kwantar da hankalinki,ki turo ta nan,ko da babu driver,baban nata yana cikin ɓacin rai ne,amma yana hucewa shikenan in sha Allah,komai zai daidaita ki kwantar da hankalinki " Hajiya Zainab ta girgiza kai ta ce"ba za ki gane bane Hajiya, tunda ya nuna ba zai amshe ta ba to ta zauna, Alhaji yana da kafiya musamman akan ra'ayinsa Kuma Allah ya gani tun sanda aka ce za'a kai ta makaranta ban so ba, saboda Shaheeda yarinya ce ƙarama,amma mahaifinta ya dage,ya ce ya ji ya gani,a ƙarshe gashi nan ni nake girbar shukar, ƴata ce ta lalace shi babu abinda ya yi masa zafi tunda yana da wasu yaran,Ni gani an bar ni a cikin tashin hankali da baƙin ciki,ko da wannan cikin ai ni nake ganin damuwa" Hajiya Jamila ta girgiza kai ta ce"Hajiya bawa bai isa ya kauce ƙaddarar da Allah ya rubuta masa ba,ko ta wanne hali,da ni da ke da kowa ma mun san wacece Shaheeda mun san abin da zata iya da wanda ba zata iya ba,mun yi mata kyakykyawan zato, abin da ya faru ƙaddara ne da jarrabawa,mu san Shaheeda ba maza ta bi ba, aure ta yi, duk da cewa bata yi auren akan yadda ya dace ba,amma dai ba zina ta yi ba,ɗanta ɗan Sunnah ne,yaudarar da aka yi mata bata isa ta saka ɗanta ya zama shege ba, ki kwantar da hankalinki hajiya Yanzu dai ki turo ta,ko da ma a ce Alhajin naku bai yarda ta koma gidansa ba ni zan riƙe ta ni da nawa Alhajin,kar ki damu Hajiya "Hajiya Zainab ta yi murmushi tana faɗin"na gode, sai,in sha Allah yanzu zan turo ta, sai kin ji ni Hajiya "suka yi sallama ran kowa a cikinsu babu daɗi Tana sauke wayar Muyassar ya yi sallama, Ummeey ta ɗaga kai tana kallonshi ta amsa da murmushi a fuskarta,ya ƙaraso cikin falon yana kalle-kallen ta inda zai gano Shaheeda Cikin girmamawa yadda ya saba ya gaida Ummeey, Ummeey ta amsa cikin fara'a tana faɗin"ango ya shirye-shirye?"Muyassar ya ce"alhamdulillah Ummeey Ina Shaheedan?na ji abin da ya faru da ita,ban ji daɗin abin da ya faru ba,amma babu komai, za'a san yadda za'a yi kafin a samu Abban ya huce in sha Allah Ki yi haƙuri Ummeey " Ummeey ta sauke numfashi ta ce"babu komai Allah ya kyauta kawai Shaheeda ai na bari ta a falon Alhaji,ban sani ba ko ta taho " "Wai falon Abba?"ya faɗa yana kallonta da yanayin mamaki akan fuskarsa Bata damu ba ta ce"eh can na baro ta, wataƙila ta shigo yanzu Na yi magana da ƙawata ma,zan tura ta can gidanta kafin abubuwa su lafa a san yadda za'a yi" Muyassar yana kallonta da yanayin mamaki da damuwa ya ce"amma kuma yanzu na baro wajen Abba,amma kamar bata can" "Ba ta can?"ta faɗa a ɗan tsorace,bata jira amsarshi ba ta miƙe da sauri ta fice daga sashen ta nufi sashen Abba Sai da ta je ta samu tabbacin cewa tun da ta fita Shaheeda ta fita, a lokacin kasa nuna kararta ta yi,a gigice ta dubi driver tana faɗin"don Allah kai ni na duba ƴata,kar ta faɗa wani halin,don Allah mu bi hanya yanzu......." "Zainab!"ta ji muryar Abba a fusace Juyawa ta yi a gigice tana kallonsa,sam bata kula da jama'ar gidan da suka taru suna kallonta ba, Abba ya dube ta fuska a ɗaure ya ce"ban hana ki nemo ƴarki ba ki riƙe abarki,amma ki zaɓa ko aurenki ko ƴarki,daga sanda kika fita daga gidan nan da niyyar kin tafi neman ƴarki daga lokacin ki saka a ranki kin datse igiyar aurenki da kanki,zaɓi ya rage naki "yana kai wa nan ya kewaye ta ya bar wajen Hajiya Ruƙayya da abin yake yi mata daɗi ta dubi Ummeey da take daskare a wajen ta ce"Allah ya kyauta dai! Dama bahaushe yana cewa rana dubu ta ɓarawo ɗaya ta mai kaya,banda haka da ta yaya za mu san masu zuga yara suna lalacewa a gidan nan? Allah ya kyauta"Hajiya Atika ta taɓe baki tana faɗin "Ameen dai"suka fara watsewa daga wajen suna kama gabansu Da ƙyar Ummeey ta ja ƙafarta ta koma ɗakinta,tana zuwa ta zube a tsakar dakin tana mayar da numfashi, ƙasa-ƙasa ta samu zarafin ambaton"Inna lillahi wa inna ilayhi rajiun!!!" Shikenan ta sani a yanzu,ta rasa ƴarta,komai ya ƙare mata, Allah ya kawo mata dauki Tana jin wayarta tana ringing amma ta kasa ɗagawa, saboda tashin hankalib da take ciki,duk da cewa ta san Hajiya Jamila ce ya kira akan batun Shaheeda 💫 Shaheeda kuwa saboda tsabar gajiya tunda ta kwanta bacci bata iya tashi ba sai da washegari Rabi ta shiga ɗakin tana tayar da yaranta don su yi Sallah,ta tashi da ƙyar,ta ɗauki buta don ta je ta yi fitsarin da ya matse ta a mara Bayan ta yi Sallah tana zaune ta yi zuru,yaran da ɗaiɗai da ɗaiɗai suke zuwa suna gaishe ta,ta amsa tana murmushin yaƙe Ɗaya daga cikin yaran, wanda ta ji ana kira da faruku,da alamu shine babban shine ya kawo mata abincin karyawa,kunun gero ne da yar tsala,shima wannan abincin ya shiga ranta sosai,don haka ta ci da yawa,dama gashi da yunwa ta tashi, kamar ba ta ci abinci ba Wajen ƙarfe bakwai da rabi yaran suka fice zuwa makaranta, Shaheeda ta kwanta ta lumshe idanu kawai tana tunanin yadda rayuwa take wujijjiga ta Baban faruku ne ya yi sallama ya shigo ɗakin,ta tashi zaune tana amsawa,ya shigo sosai ya samu waje ya zauna, Shaheeda ta rissina ta gaishe shi Ya amsa da sakin fuska, sannan ya dube ta da kulawa ya ce "Ni zan fita aiki,ga wannan"ya miƙa mata ɗari biyar,ya ce"na san ba za ki rasa abin da kike sha'awa ba,sai ki siya ki ci ko?"Shaheeda ta karɓa tana rissinawa, cikin sanyin murya ta ce"na gode Allah ya saka da alkhairi"baban faruku ya amsa da Ameen sannan ya fice daga ɗakin Wajen ƙarfe sha ɗaya na rana,a lokacin bacci ya fizge ta, cikin baccin ta rinƙa jiyo hirar matan gidan "Umman faruku wai wacece wannan matar da na ga sun zo tare da baban faruku juya?baƙuwa kika yi ne?"umman faruku ta taɓe baki ta ce "wacece ni? Mai gidan dai,nima tare na gansu ai" "Mai gida kuma umman faruku? Ƙanwarshi ko yar ɗan'uwanshi?" "Mhm!ke ma dai kuma faɗa maman jidda, wallahi babu ɗaya,a hanya ya ce ya tsinto ta" "Kan uban can!sannu umman faruku! Wallahi kaf duniya babu wanda ya isa ya yi min haka, tabɗijam!"a cewar ɗaya matar Maman jidda ta ce "maman Ahmad ni ba wannan nake tunani ba, wallahi na fi zargin ƙarya take yi,karuwa ce kawai,ko wadda idanun ba su gama buɗe idanu a yawon dandi ba,mu je mu tuhume ta ya rantse abin da ta faɗa gaskiya ne,idan bata rantse ba wallahi mu fatattake ta, saboda tsaf sai ta lalata mana mazaje wallahi,ba zai yiwu muna zaman lafiya da mazanmu ba daga taimako a ɗauko mana masifa Ni bari ma ku gani, wallahi ba zan yi sanya ba"ta miƙe ta nufi ɗakin da Shaheeda take ciki da Adams, don har wani zafi take ji a ƙirjinta,ji take yi ma kamar ta ga mijinta tare da wata macen,ko ma ya ce zai aure ta, dama ta fi sauran matan gidan zafin kishi #Nusy_bee Page 33 Maman Ahmad da umman faruku ma ba su yi sanya ba suka rufawa maman jidda baya zuwa ɗakin da Shaheeda take, Shaheeda kuwa wadda take jin duk abin da suke cewa tuni ta tashi zaune tana jiran shigowarsu,ko ma me za su yi mata su yi mata,ita yanzu ta daina tayar da hankalinta akan ko menene ma zai same ta rayuwa,gwara ta koyawa zuciyarta dakewa da juriya Ko sallama maman jidda bata yi ba ta bankaɗa labule ta shigo tana aikawa Shaheeda wani mugun kallo, Shaheeda ta dai ko motsawa daga inda take zaune bata yi ba,sai idanu da take ta bin ta da shi,babu jumawa Kuma sai ga umman faruku d maman Ahmad su ma sun shigo ɗakin Da wani mugun kallo maman jidda take kallonta, kafin ta ce"wacece ke? Daga ina kike? Ina kika samu cikin jikinki?ina buƙatar ki gaya min gaskiya, sannan kuma ki rantse min da Allah cewa gaskiya kika faɗa idan har kina son ki cigaba da zaman gidan nan" Ita dai Shaheeda ko motsi bata yi ba, asalima bata da niyyar motsin,maman jidda da ta fi su fusata ta ƙaraso inda Shaheeda take ta ɗauke ta da wani mari,sai da ta tintsira Gigicewa ta yi,don marin ya shige ta,amma saboda taurin kai bata yi magana ba sai hawayen da ta fara zubarwa Maman Ahmad ta kalle su tana faɗin "maman jidda rabu da ita,amma mu fincike ta mu jefar a bakin titi idan bata tashi ta bar mana gida ba Matsiyaciyar yarinya tun kina ƴar mitsitsiyarki amma kin san makirci?kuma kin san ki kwanta da namiji?" Har yanzu kuka Shaheeda take yi, kuma babu niyyar tashi,a fusace maman faruku ta fincike ta,ta ƙanƙame jikinta tana runtse idanu,amma hakan bai hana su fincikarta ba,a fusace maman faruku take faɗin "yau ko gidan ubanki ne nan ɗin sai kin bar shi wallahi,shegiya munafuka"ganin za su illata ta ya sa ta miƙe tana kuka ta gyara zaman hijabinta,ta kalle su ta ce"Allah ya ba ku haƙuri"sannan ta goge hawayenta ta nufi hanyar waje Maman Ahmad ta watsa mata mugun kallo ta ce "Ameen!sai a bi wani sarkin kuma, shegiyar yarinya kalle ta kamar ta Allah"maman jidda tana huci ta ce"haka suke ai,su yi maka lumbu-lumbu su shiga jikinka su cuce ka su bar ka da wayyo Allah, irin wannan kyasa-kyasan da ake samu akan irin waɗannan mutanen ai suna da yawa,shine ba za muyi hankali ba?kuma sai abin ashsha ya faru mu ɗorawa ƙaddara?" Maman Ahmad ta gyara tsayuwa ta ce"an taɓa samun makamancin haka fa da ƴar babbar yayarmu,wai mijin ya taimakawa wata yarinya ya kai ta gidanta, shegiya ashe tana biye-biye, ƙarshe ta aure mijin ta kori waccan matar,daga baya ma ta yi mata asiri ta kusa haukacewa, Allah ya taimaka aka shawo kan abin" Maman jidda ta riƙe haɓa ta ce"oh Allah! Ki ce mutanen nan matsiyata ne,ki taimaka musu ki janyo su daga rana zuwa inuwa,daga sun ji sanyi sai su tura ki wuta, a'a wallahi,su yi zamansu a rana, Allah ya raba mu da mugun ji da mugun gani"ta fice daga ɗakin tana jinjina abin,su ma sauran matan suka fito suna kakabin lamarin Shaheeda, musamman yadda ta kafe ta ƙi magana,hakan ya tabbatar musu bata da gaskiya Shaheeda kuwa tana fita ta goge hawayenta,kai tsaye ta nufi titi ta samu abin hawa,ta ce a kai ta kasuwar gwal,babu musu ya ɗauke ta suka tafi A hanya sai sauke ajiyar zuciya take yi, saboda ta ji daɗin abin da ya faru ma zata ce kai tsaye,jiya da ta rasa yadda zata yi,ga yunwa ga rashin matsuguni,kuma babu ko sisi a hannunta,sai Allah ya kawo mata baban faruku,a gidansa ta kwana kuma ta ci abinci,kuma a ƙarshe ya ba ta kuɗin da zata kashe, wanda ya zamar mata kuɗin mota Yana sauke ta ta nemi inda zata siyar, kasancewar babu receipt ya sa ba'a siya da daraja sosai ba,don zoben ƙimarsa zata kai 600k saboda diamond stone da yake jikinsa,amma a 400k ya tashi,hakan bai dame ta ba,ta karɓi kuɗinta ta wuce kasuwa ta siya kayan jarirai, sannan ta samu laptop wadda bata gama shan jiki ba,da waya ƴar madaidaiciya ta siya, sannan ta wuce inda zata kama hotel Mai sauƙin kuɗi ta kama na kwana uku,don ta san zai iya janta waɗannan kwanakin kafin ta sami gidan da zata zauna Ai kuwa da ƙyar ta samu,don bata san kowa ba,sai da ta je gidan mai unguwar yankin,ta shirya ƙarya kamar yadda ta shiryawa baban faruku,mai unguwa ya tausaya mata,har ya ba ta dubu biyar,ta yi ta godiya Gida ne madaidaici aka samar mata,sai dai ba ita kaɗai ba ce,gaba ɗaya gidan ɗakuna uku ne,wasu sun kama biyu ita kuma ta kama ɗaya,a ranar ta siya madaidaiciyar katifa da yan abubuwan buƙatu bayan ta siyar da ɗan kunnenta,duk da nauyin cikin jikinta ta miƙe zata fara gyaran ɗakin Sallama aka yi mata,ta juyo tana kallon matar wadda ba zata wuce ta ba a shekaru,amma saboda talauci da babu gaba ɗaya ta lalace, ƙuruciyarta ma tana neman ta ɓuya, Shaheeda ta yi wa matar murmushi itama tana kallonta,matar ta ce"bari na taya ki ko?" Shaheeda ta ce"na gode"daga nan suka mayar da hankali sosai ga gyaran ɗakin,amma matar ita ce ƙarfin aikin Bayan sun gama Shaheeda ta yi ta yi wa matar godiya,matar tana murmushi ta ce"kar ki damu,ba komai,bari na zubo mana abinci"bata jira amsar Shaheeda ba ta yi waje " Faten tsaki da yakuwa ne,ya burge Shaheeda,duk yadda ta so ta yi kara kasawa ta yi, saboda yadda faten ya rinƙa tsinka mata yawu,ai kuwa ta ci shi sosai,ta yi ta yiwa matar godiya, matar tana murmushi ta ce"ai ke ƴar'uwata ce,ya sunanki? Ni sunana AZEEMA,ni da mijina daga wani ƙauye muke a can Ghana,bamu da kowa a nan"Shaheeda ta jinjina kai ta ce"Ni kuma sunana Fatima,mijina ya rasu babu jumawa,gashi bani da kowa"Azeema cikin jimami ta girgiza kai ta ce"Allah sarki! Allah ya ji ƙanshi ya yi masa rahama "Shaheeda ta lumshe idanu kawai bata ce komai ba Wat guda da tariyar Shaheeda,gaba ɗaya damuwarta a yanzu ta kau, saboda Azeema da mijinta RABI'U sun ɗauke ta tamkar ƴar'uwarsu, musamman da ya kasance mijinta ya rasu,kuma bata da kowa,su ma kuma ba su da kowa sai kansu,sai kuma ita da Allah ya kawo ta rayuwarsu Shaheeda ta kula da yadda talauci ya ci jikinsu sosai,wani lokacin ma abin da za su ci sai sun yi da gaske suke samu,amma duk da haka in dai sun yi girki ko yaya ne sai sun ɗibar mata Karamcin mutanen yana matuƙar burge ta,har ta ji a ranta ya kamata ta zama wata itama don ta taimake su watarana Tun daren jiya take ta fama da matsanancin ciwon mara,amma kasancewar bata taɓa haihuwa ba sam bata kawo naƙuda take yi ba,sai da abin ya tsananta,tana durƙushe tana fama da kanta Azeema ta shiga da sallama Ɗagowa ta yi idanunta suna chanja kamanni tana kallon ta, Azeema ta ƙaraso da sauri tana faɗin "me ya faru? Ba ki da lafiya ne?" Murya ƙasa-ƙasa ta fara faɗin "bayana!marata!!ji nake yi kamar zan mutu"gaban Azeema ya faɗi,a tsorace ta ce "ko dai haihuwa ce?"gaban Shaheeda ya faɗi,a tsorace ta ce"ina ga ita ce"Azeema ta miƙe a tsorace tana safa da marwa,bata san yadda zata yi mata ba,itama Shaheedan bata san yadda za'a yi mata ba,gashi ba su da kuɗin motar da za su tafi asibiti,gashi Rabi'u baya nan,yana wajen aikinsa na gini da yake yi idan ya samu Haka Shaheeda ta wuni ta malelekuwar azaba,tun tana kuka Azeema tana taya ta,har bakin ya mutu Sai daf da magriba Allah ya yankewa Shaheeda ta haifi ɗanta,sai dai kallo ɗaya Shaheeda ta yi masa,duk bata san yanayin jariri sabuwar haihuwa sosai ba, kasancewar Ummeey bata haihuwa,kuma matan gidansu ko sun haihu sai ta ga dama take shiga,kuma ba sa ba ta ɗan,amma a haka ta gane nata jaririn ba shi da ƙoshin lafiya, musamman yadda numfashinsa yake fita da yadda yake kuka a wahale Azeema ce ta yi ƙoƙarin ɗaukarsa ta goge masa jiki, ta yi masa wanka,don dama ita ta iya kula da jariri kasancewar ta taɓa haihuwa ɗan ya rasu bayan ta gama shirya shi sannan ta fita maƙobtansu,akwai wata tsohuwa,ita ce ta taimakawa Shaheeda ta yi wanka ta gyara jikinta Sai da suka nutsu, Shaheeda tana cin abinci sai ga Rabi'u,ya yi murnar ganin Shaheeda ta haihu lafiya,amma ya yi ta yiwa Azeema fadan meyasa ko maƙobta bata shiga ta aro waya ta kira shi ba, Azeema ta ce ta sha'afa ne, saboda yadda suka gigice a lokacin Ya ce"ki dai rinƙa kulawa, yanzu dai alhamdulillah,amma duk da haka sai mun je asibiti an sake duba ta,ga wannan kuɗin ki adana"ya miƙa mata dubu biyu,ya ce"wannan kuma"ya nuna mata kuɗin da za su iya kai wa biyar zuwa sama ya ce "sai a duba ta da yaron ko?" Azeema ta ce"tabbas ka kawo dabara,don wallahi yaron magana ne kawai ban yi ba,amma kamar bashi da lafiya,ni kaina a tsorace nake wallahi, daɗinta ma uwar bata san yadda jariri yake ba da alamu,amma yaron nan ba shi da lafiya" Da haka suka yiwa Shaheeda magana,bata yi musu ba ta bi su suka nufi asibiti A can aka duba ta,ita dai babu wata matsala sosai, amma jaririn nata likitoci sun bayar da tabbacin cewa yana ɗauke da larurar asthma, wadda alamu ya tabbatar da gadonta ya yi Hankalin Rabi'u ya tashi sosai,ya koma ya same ta yana tambayarta da yi mata bayani, bata damu ba sosai,kuma bata yi mamaki ba,ta dube shi ta ce"tabbas haka ne, mahaifinsa ya tabbatar min da cewa nashi mahaifin an ce ciwon asthma ne ya kashe shi,babu mamaki don ya samu shima"Rabi'u ya jinjina kai cike da jimami ya ce"Allah ya ji ƙansu baki ɗaya Kin tanadar wa yaron suna?" Girgiza kai Shaheeda ta yi, Rabi'u ya ce"ya sunan babansa?" Shiru Shaheeda ta yi, kafin ta yi shahada ta ce"Mubarak!" Rabi'u ya ce"to ai kuwa za'a mayar masa da sunan babansa, Allah ya raya shi ya albarkaci rayuwarsa, Allah ya raya mana MUBARAK" Kallonsa ta yi tana ɗan murmushin yaƙe, don bata so hakan ba,amma gudun kar asirin da ta binne ya tonu ya sa bata yi magana ba, Rabi'u bai kula ba ya ce"me za'a rinƙa kiransa?" Shaheeda kanta a ƙasa ta ce"a kira shi da Mubarak ɗin sa,ya fi daɗi ma" Ba su juma ba aka sallame su,bayan an ɗora Mubarak akan magani da ganin likita, sannan ga dokokin da aka kafawa Shaheedan akanshi Ranar suna Rabi'u ya yi ƙoƙari, don hakika ya yankawa Mubarak banda kayan jarirai da suka yi ƙoƙarin shigowa masu sauƙin kuɗi duk da cewa itama Shaheedan ta siya,ya yiwa Shaheeda ɗinki mai kyau,aka yi taron suna daidai misali, wanda ya saka Shaheeda tsananin farin cikin da ta juma bata yi shi ba Dukkansu daga Rabi'u har Azeema ba su ɗauke ta komai ba sai ƴar'uwa,sun riƙe ta da zuciya ɗaya,sun cike mata gurbin da ya yi mata saura, to ita kuwa me zata yiwa bayin Allan nan ta biya su?ko ta faranta musu? Hakan ya sa bayan ta yi arba'in ta fara tunanin ta bi kamfanoni don neman aiki,amma kafin ta fara wannan yunƙurin sai da ta gayawa su Rabi'u Dukansu sun goya mata baya tare da fatan Alkhairi, Azeema tana murmushi ta ce"ki ce mun kusa zama cele a garin nan,don masu aikin kwamfutan nan Allah kuɗi suke samu sosai,su ne fa za ki ga suna hawa jirgi suna barin ƙasar nan" Ƴar dariya Shaheeda ta yi, Azeema ta ce"Allah da gaske,ko don ke ma watarana ko ba mu hau jirgi ba ai za mu gani, Allah ya kai damo ga harawa kawai"Shaheeda ta yi murmushi tana girgiza kai,da Azeema ta santa ai ba ma zata fara faɗar hakan ba Cikin lokaci ƙanƙani ta fara neman aiki,da wani kamfanin software ta fara,bayan ta gama ganawa da Manager ɗin kamfanin ta sanar masa da abin da ta karanta, kai tsaye ya buƙaci ganin takardu Idanunta suka yi ƙwal-ƙwal,a sanyaye ta ce"ban ƙarasa karatun ba ai, saboda matsalolin rayuwa da suka sha min kai,amma....."mutumin ya katse ta faɗin"ba ki da takardu kuma kike tunani za mu ɗauke ki aiki?" Shiru ta yi jikinta a sanyaye, kafin ta ce"na iya aikin fa,ku gwada ni ku gani,ban damu ba ko da ace rabin kuɗi za ku bani ba,ni dai ina roƙonku don Allah ku ba ni aiki, ko yaya za ku biya ni zan yi"mutumin ya ƙare mata kallo, ganinta matashiyar yarinya mai jini a jika,kuma kyakykyawa sai ya gyara zama ya ce"to zan ba ki aiki a companyn nan,babban matsayi ma, amma da sharaɗi" Cikin ɗoki tana murmushi ta ce"menene sharadi?"kai tsaye ya ce"za mu kwana tare,kuma duk sanda na neme ki za ki biya min buƙata,idan kika yi haka I'm ready" #Nusy_bee Page 34 Shaheeda dai ko zata ganta a bakin wuta ba zata taɓa canjawa daga Shaheeda ba,don haka ta dube shi a zafafe ta ce"idan karuwanci zan yi ba zan wahalar da kaina na zo nan ina roƙonka aiki ba,na san hanyoyi da yawa da zan yi karuwanci ba sai na wahala wajen wani aikin dabam ba,idan karuwa kake so ba sai ka bada aiki ba,ka san inda za ka same su"ta ja tsaki ta miƙe ta fice daga gidan a fusace A ranar yini ta yi cikin ɓacin rai saboda abin da aka yi mata,amma hakan bai saka ta karaya ba, washe gari ma ta sake fita neman aikin Haka ta yi ta yawon neman aiki a kamfanoni,amma rashin takardu ne yake yi mata cikas,na ƙarshe ma ce mata ya yi"ki nuna min wata shaida na cewa kin taɓa yin karatu a matsayin software engineer,na yi miki alƙawarin zan ɗauke ki aiki a kamfanin nan"jikinta a sanyaye ta tashi ta fice daga office ɗin,don dai a yanzu bata da wata shaida,bata sake nadamar banzatar da karatunta akan soyayya ba sai yanzu Lokacin da take ba wa su Azeema labarin abin da yake faruwa idan ta je neman aiki daga ita har Azeema kuka suke yi, Rabi'u ne ya ja numfashi ya dubi Shaheeda ya ce"Fatima,akwai alamun cewa ba komai kika gaya mana game da kanki ba, lokaci ya yi da ya kamata ki faɗa mana komai,kin ga an zama ɗaya,kuma ba mu san ta inda zai yiwu mu taimaka miki ba Na gane kamar ke ba irinmu ba ce, ƴar ƙauye ko yar talakawa, saboda yanayin mu'amalarki da mutane da kuma wayewarki,don Allah ki gaya mana gaskiyar abin da ya same ki idan har kin ɗauke mu kamar yadda muka ɗauke ki" Babu musu ta goge hawayenta,a hankali ta fara ba su labarinta tun daga tafiyarta karatu zuwa ƙasar Belgium har zuwa lokacin da ta kama haya a gidan nasu,ta ƙarasa cikin matsanancin kuka, saboda ita kaɗai ta san irin ciwon da take ji a duk lokacin da ta tuna mahaifinta ya yi disowning ɗinta,ya bar wa duniya ita, duk da yadda yake tsananin sonta,kuma itama take tsananin sonshi Kafin ta kammala labarin Azeema ma ta yi kuka har da shiɗewa,shi kanshi Rabi'u sai da ya dake sosai ya hana kanshi zubar da hawaye, labarinta ya dake shi sosai, ya taɓa masa zuciya sosai,a haka ma ta yi juriya,da wata ce tsaf trauma zata jefa ta a cikin wani mawuyacin halin Cikin dakewa ya dube ta, cikin sanyin jiki ya ce"babu komai, Allah ya ji mana mai kyau, rayuwa ce sai da jarrabawa, Allah ya ba ki ikon hayewa,mu ma haka muke rayuwa ba mu da kowa,dama ita Azeema marainiya ce,ni kuma ni kaɗai uwata ta haife ni, waɗanda muke uba ɗaya suna da wadata sosai,amma sai mu wuni ba mu saka ko ruwa a bakinmu ba saboda talauci,a gabanmu za su ci abinci mai rai da lafiya amma amma babu wanda zai yi tunanin yi mana tayi,ganin wahala da wariya zata iya yi mana illa ya sa kan dole muka bar garin muka dawo birni,gashi nan kuma muna gurgura rayuwar, sai fatan Allah ya kawo mana ɗauki" Daga lokacin sabo da kulawa ya sake shiga tsakanin Shaheeda da ma'auratan,ta ɗauke su a matsayin ƴan'uwan da ta rasa a rayuwarta, Rabi'u shine cin su,shan su,suturarsu da duk wani jigo nasu,hakan ya sake kwantarwa da Shaheeda hankali sosai Tsawon watanni uku suna tafiya a haka,ba su da wata bayyananniyar matsala,sai dai wadda ba'a rasawa,a lokacin kuma Allah ya kawo musu wata Sabuwar jarrabawa Tun Rabi'u yana jinya a tsaitsaye har ya kwanta sosai,gashi fama ake yi da kuɗin maganin Mubarak, wanda Shaheeda take kai shi ganin likita lokaci zuwa lokaci, kuma dama Rabi'u ne yake biyan kuɗin maganin Tun ciwo yana ƙarami har ya girma, dole aka kwashi Rabi'u zuwa asibiti Tashin hankali ba'a saka maka rana! tashin farko aka buƙaci kuɗi masu yawa don a yiwa Rabi'u gwaji, kuɗin da ko kwatankwacinsu ba su da shi, hankalinsu ya tashi, dole Shaheeda ta koma ta kwashi ƴan kunnanyenta na Gold ta shiga da su kasuwa ta siyar, duk da cewa ba'a siya da daraja sosai ba amma bata damu ba,biyan buƙata ta fi dogon buri Bayan ta biya kuɗin gwaje-gwajen aka zo aka ɗauki sample ɗin da ake buƙata ita kuma ta dawo kusa da Azeema ta zauna, suka cigaba da jimami da fargabar amsar da za'a ba su Sai ga sakamakon ciwon hanta,kuma ana buƙatar kuɗi mai yawa don a yi masa treatment,sannan kuma a ɗora shi akan magani, hankalinsu Shaheeda ya tashi,don ba su da kuɗin da aka buƙata ba su da dalilinsu,tuni Azeema ta fashe da kuka cikin tsananin tashin hankali,don ta san idan ya mutu sai ta fi kowa shiga wani hali Shaheeda ce ta kwantar mata da hankali, sannan ta ce "ki daina dansa, in sha Allah zuwa anjuma na ga wasu gidaje masu manyan gate,ba za'a rasa na Allah a cikinsu ba,sai mu nema masa taimako,zan tafi da katin maganin,ke kuma sai ki zauna a wajensa"Azeema tana murmushi ta ce "na gode Shaheeda,ki bar Mubarak a nan saboda rana, kuma kin ha yana ta fama da zazzaɓi"babu musu Shaheeda ta kwanto shi daga bayanta,ta miƙawa Azeema shi,dama bata son yawo da shi sai dole saboda larurarsa Gidajen masu hali ta fara bi don neman taimako,tana nuna takardun asibiti na Rabi'u,sai dai babu abin da ta samo,sai ma a gidan ƙarshe da aka sakar mata karnuka ta fito a guje,ta yi kuka sosai, zuciyarta cike da ƙuna da baƙin ciki,daga nan ta fara bin masallatai,shima dai ba wani abu ta samo ba, kasancewar yau ɗin ba juma'a ba ce Daka ƙarshe dai titi ta dawo tana bara tana roƙon a taimaka musu da kuɗin magani,ta yi matukar gajiya,ga yunwa,don tun safe ta fito, yanzu ana maganar ƙarfe biyar na yamma,bata karya ba,ko ruwa ma bata sakawa cikinta ba Gaba ɗaya abin da ta samu Naira dubu shida da ɗari huɗu ne,ga shi abinci mai ba su da shi,kuma gobe take saka ran mayar da Mubarak asibiti, saboda jikinsa da ya fara dawowa,don tun wancan satin ya kamata a ce ta koma asibiti an sake duba shi Wujiga-wujiga ta shiga asibitin, Azeema da take zaune rungume da Mubarak da yake ta bacci ta taso da sauri tana faɗin "Fatima na ji ki shiru, Allah ya sa lafiya,ga jikin Mubarak yana ta tsananta,tun ɗazu yana ta kuka jikinsa yana zafi,ga numfashinsa dai ƙoƙarin ɗaukewa yake yi, likitoci kuma sai magana suke yin bar yaya ba'a biya kuɗin magani ba"hawaye suka zubo mata tana kallon Azeema ta ce "kuɗin ba su da yawa Azeema,ga abubuwa suna ta ƙara yi mana yawa,ina tsoron jikin Mubarak Azeema, zazzaɓi yake sosai,gobe kawai zan je kasuwa na siyar da laptop ɗina da wayata na biya Bill ɗin yaya na kai shi asibiti shima" Azeema ta kwantar da murya ta ce"babu komai,mu zuba idanu kawai mu ga abin da Allah zai yi,amma kar ki siyar da kayan da kika ce da su za ki fara aiki, ba'a san abin da gobe zata haifar ba" Shaheeda ta goge hawaye ta ce"biyan buƙata ya fi dogon buri Azeema,yaya fa yana kwance babu lafiya,shine mai kula da komai namu,ga Mubarak shima, yanzu idan muka rasa ko ɗaya a cikinsu ne ya kike tunani? Gwara na siyar kawai,zuwa nan gaba Allah zai kawo wani"Azeema ta rungume ta suka cigaba da kuka tare, cikin damuwa da jin rashin gata Ilai kuwa a ranar da zazzaɓi Mubarak ya kwana, numfashinsa yana sarƙafewa,ga Rabi'u wanda kuɗin da aka bayar ba su isa ba,amma an fara duba shi,ga damuwa,da ƙyar Shaheeda ta iya cin abinci kaɗan,duk da tarin yunwar da take ji Washe gari kuwa da wuri ta koma gida,ta ɗauko laptop ɗinta da wayarta don ta je ta siyar Wani darasi da Arnold ya taɓa koya mata ne ya faɗo kanta, don haka ta zauna ta gwada don ta gani Cikin Sa'a kuwa ya yi, lokaci guda Naira dubu ɗari biyar ta faɗo account ɗin ta Ai kuwa wani ihun farin ciki ta yi har tana taka rawa,shikenan yanzu zata biya kuɗin maganin Rabi'u,ta mayar da Mubarak asibiti,su ci abinci mai kyau,ta kamawa Rabi'u ɗaki mai kyau ma,dama kullum sai tsangwama da hantararsu ake yi a ward ɗin su Rabi'u, saboda ɓangaren maza ne,ga su kuma mata,sam ba sa wani sakewa a wajen Ai kuwa nan da nan ta wuce banki,a can ta yi ATM card da bata da shi, sannan ta ciro dubu ɗari biyu ta wuce asibitin,tana zuwa ta biya kuɗin maganin Rabi'u,ta biya aka canja masa ɗaki zuwa VIP,sannan ta siyawa Azeema lafiyayyen abinci ta kai mata Azeema ta saki baki tana kallon abincin,ga nama iya nama,sai haɗiyar yawu take yi,ta ce "Fati idan muka kashe kuɗin kuma fa? Gashi ko Mubarak ɗin ba ki kai asibiti ba"tana murmushi ta ce"ke dai ci,babu abin da zai gagara in sha Allah,komai zai warware da ikon Allah"Azeema ta girgiza kai ta ce "ba zan iya ci ni kaɗai ba alhali na tabbatar ba ki ci ba,ki zauna mu ci tare to" Shaheeda ta girgiza kai ta ce "ba zan iya cin abinci a wannan halin ba, dole sai na kai Mubarak asibiti tukunna,ke dai ci abinci kawai"daga haka ta yi waje ba tare da ta sake sauraren Azeema ba Yau bata juma ba a asibitin ta dawo asibitin da aka kwantar da Rabi'u,ta yi mamakin ganin Azeema bata ci abincin ba,ta dube ta tana faɗin "meyasa kika ƙi cin abincin Azeema?ke ma fa akwai ki da taurin kai" Azeema ta girgiza kai ta ce"ke ma kin san ba zan iya cin abinci ba alhali na san ba ki ci ba,ki zauna kawai mu ci"babu musu Shaheeda ta zauna suka fara cin abincin tare Kwana uku suka ƙara a asibitin aka sallami Rabi'u,a lokacin Azeema ta fara tsorata da hidimar kuɗi da Shaheeda take yi musu, saboda komai na su ya canja,cima yanzu lafiyayyiya suke ci, ba'a maganar na Rabi'u ma,da Shaheeda ta tanadar masa duk abubuwan da likitoci suka ce su zai iya ci Sai da suka nutsu a gida,bayan sun gama cin abinci, Rabi'u yake tambayar Shaheeda ina ta samu wannan kuɗin da ko hanyar rabinsu ba su da shi? Azeema ta dube shi da mamaki ta ce"yaya kwamfutarta fa ta siyar da wayarta,ka gansu ai masu kyau da tsada ne"Rabi'u ya kalle ta, Shaheeda ta girgiza kai ta ce"ba su bane,wata hanyar samu ce ta buɗe min" Azeema da ɗoki ya kama ta ta ce"wacce hanyar samu ce haka?" Kai tsaye Shaheeda ta ce"ka san na je neman taimako wajen ƴan siyasa da masu madafun iko na gwamnati,neman taimako da ba ka da lafiya,amma duka sun hana mu,ni kuma na ga ai kuɗinmu ne,don haka na yi amfani da ƙarfin ilmin computer da Allah ya ba ni na fasa account na bankin na ɗibi kuɗi, dama ai namu ne, don haka rabona na ɗiba" Wani kallo suke yi mata a tsorace, Rabi'u ya ce"kina so ki janyo mana masifa dai ko Fati? Shiga harkar gwamnati fa!kina gaya min za ki rinƙa ɗibar kuɗin gwamnati,ba kya tsoron kamu da hukunci?" Kai tsaye Shaheeda ta ce"babu mai iya kama ni,idan kuka ba ni haɗin kai komai zai yiwu,ba saka ku zan yi a cikin wannan aikin ba,asalima dole zan ɗauke ku zuwa nesa,shima Mubarak zan yi nesa da shi,ko don jinyarsa,ba zan iya riƙe shi ba,gwara na kai wa wata ƙanwar mahaifiyata shi " Yanzu kam sun fara yi mata kallon taɓaɓɓiya, Azeema ta ce"to tunda ba kya son Mubarak ɗin ki ba ni na riƙe shi" Wani kallo Shaheeda ta yi mata ta ce"wa ya ce miki bana son shi? Kawai hakan ya fi ne,za mu bar nan,za mu samu ingantacciyar rayuwar da muke muradi,na yi karatu mai kyau a jami'ar Ghent University ta ƙasar Belgium, mahaifina ya narkar da kuɗi mai yawa,kuma nima na takure kaina na koyi karatu sosai, mijina ya koya min abubuwa da yawa,sai kuma a ce bayan duk wannan saboda wasu common takardu a ce ba zan wasa basirata ba? Ba zai yiwu ba kuwa! yadda na wahala na yi karatu ya kamata na ci moriyar karatun,na samu ka rufawa kaina asiri haka nan Yanzu dai ku shirya,nan da kwana uku za mu bar garin nan,don bayan kuɗin magani na sake hacking na samu kuɗi million biyu,sai mu san yadda za muyi ko?" #Nusy_bee Page 35 A zabure suka kalle ta,ko a jikinta ta miƙe da system ɗinta a hannu ta koma ɗakinta,suka bi ta da kallo cikin mamaki da firgici Rabi'u ya dake zama da Shaheeda akan ta duba ƙudurinta,ta dube shi cikin idanu ta ce "yaya na yanke maganata,a yi hakan kawai Lokacin da na je ina neman a taimaka min akan wata gagarumar matsala wulaƙanta ni aka yi, yanzu kuma ba lokacin neman taimako ne, lokacin taimakawa kai ne,don haka ka yi shiru kawai yaya"ta miƙe tana yar dariya ta ce"kar ka damu yaya,iya manyan gwamnati kawai zan yiwa,babu ruwana da sauran mutane"ta yi tafiyarta ɗakinta hankalinta a kwance ,shi kuwa ya bi ta da kallo,a tsorace yake, don yana tsoron a kama ta,ko wani abu ya same ta A ranar ta shirya Mubarak,da daddare ta ce zata kai shi gidan wata ƙanwar mahaifiyarta, Azeema cikin jimami ta ce"shikenan yanzu za mu rabu da Mubarak, sai mun kawo maka ziyara ko?" Shaheeda tana murmushi ta ce"ai ba mazauniyar ƙasar nan ba ce,a Chad take da aure,tana zuwa duk bayan shekaru biyar, kin ga kuwa ganin Mubarak ba yanzu ba"yanayin Azeema ya canja, Shaheeda ta goya Mubarak tana murmushi ta saka hijabinta ta fice daga gidan Tana tafiya tana sharar ƙwallar rabuwa da ɗanta,amma har a lokacin zuciya tana sake ingiza ta akan ta kai shi inda zai fi samun kulawa da tsaro, sannan kuma ta daina ganinsa a kusa da ita yana sake tayar mata da mikin baya,a yanzu Mubarak ne kaɗai abin da ya rage da zata rinƙa kalla tana tuna baya tana kuka,gwara ta ɗan yi nisa da shi, ko zata fi samun ƙwarin gwiwar aikata abin da yake ranta Wajen ƙarfe ɗaya na dare Shaheeda ta shigo wata unguwa ta masu ƙaramin ƙarfi, saboda yanayin unguwar ga kuma katangun gidajen da suka fara zaizayewa,a wannan duhuwar Shaheeda ta lallaɓa ta ajiye Mubarak wanda yake ta shan baccinsa hankali kwance, sannan ta rakuɓe a jikin wani gini tana kallon ɗanta Ta kai kusan awanni uku a tsaye a wajen kafin ta ga wani dattijo ya fito yana ta sauri,da alamu ladani ne zai tafi kiran Sallah masallaci,ya ci karo da Mubarak da har zuwa lokacin bai farka ba,kuma shima dattijon albarkacin fitilar hannunsa ne ya sa ya ganshi Ya ɗan razana da farko,ya fara ambaton sunan Allah da sauri, sai da ya samu nutsuwa sannan ya sake dubawa, tabbas jariri ne ɗan kimanin watanni huɗu,ya ɗauki yaron ya shiga gidansa Bai juma ba ya sake fitowa ya tafi masallacin da zai je Tana ji bayan ya idar da kiran sallar ya sanar da cewa ya tsinci jariri a wajen gidansa Bata tafi ba sai da aka isar da sallar asuba,ta yi kuka sosai, musamman da mutane suka taru a bakin gidan dattijon,ya tabbatar da cewa zai riƙe yaron,har ma wasu suka ba shi shawara ya sanar da gidan marayu, sannan ya nemi izinin ɗaukar yaron Shaheeda bata koma gida ba sai wajen tara na safe,tana zuwa ta fara haɗa nata kayan, sannan ta ce wa Azeema itama ta haɗa nata Ita dai Azeema sai kallon yadda ta yi sanyi take yi,bata yi mamaki ba, don rabuwa da ɗa akwai ciwo Sai da ta ci abinci sannan Azeema ta ce"ya kika baro su?ashe ma a can za ki kwana" Shaheeda ta ce "eh kin san yau zata tafi,sai da na raka su har tasha sannan na dawo gida" Azeema ta ce "Allah sarki! Allah ya tsare hanya, Allah ya kiyaye"Shaheeda ta ce"Ameen Kun gama shiryawa ne? gobe ne tamu tafiyar fa" Azeema ta ce"mun gama,ranar tafiya kawai muke jira" Washe gari suka nufi tasha su uku, Shaheeda ta kama shatar mota ƙarama,suka ɗauki hanya suka nufi Abuja A can Abuja bayan sun sauka ɗaki mai kyau ta kama musu haya a hotel,ita nata dabam su ma nasu dabam, kowa ya wuce ɗakinsa don hutawa Kwanansu uku ta samar musu gidan haya a cikin Abuja,ta biya kuɗin haya 4m,sannan suka koma can Already ta siya abubuwan da ake buƙata,babu ɓata lokaci suka fara gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali Sai dai damuwa maimakon ta ragu a wajen Shaheeda sai ta ƙaru sosai,don haka ta komawa shan ƙwayoyin da take sha sosai, musamman ma don ta ragewa zuciyarta yawan tunanin iyayenta da ɗanta Mubarak Mutumin da take siyan ƙwayoyi a wajenta shine ya fara nuna mata sha'awar siyar da su,da farko ta yi tunanin hakan zai iya zamar mata cikas ga rayuwarta,amma da ya kwaɗaita mata kuɗaɗe masu yawa sai gashi tuni ta amince,kuma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta zama dealer a harkar Tun tana siyar da abinta iya cikin gida har ta fara fitar da su,tun Rabi'u yana tsoro da tunanin kar asirinta ya tonu har shima ya shiga ya taya ta,shi baya shan komai amma kuma yana taimakawa sosai wajen siyarwa Saboda neman costumers Shaheeda ta fara yawon zuwa clubs,wani lokacin ma idan aka yi order na ƙwayoyin ana ba ta location na zuwa club ɗin A can ta koyi shan shisha,sai ya zamana ma ta mayar da rayuwarta ta zama idan babu shisha babu abin da take iyawa,sau tari idan tana aikinta na hacking ta kan ajiye shisha a kusa da ita,tana aiki tana zuƙa, Zuwa yanzu Rabi'u, wanda ya samu laƙabin Oga boss a wajen tashi sana'ar ta ƙwayoyi ya fara taka ƙasa,tuni Azeema ta koma makaranta ta fara karatu, kuma har zuwa yanzu suna tare a gida ɗaya a Abuja Tsawon shekara guda suka ɗauka a haka kafin Shaheeda ta yi tunanin zuwa ta duba ɗanta, kamar yadda ta saba haka ma yanzu ta yi ɓat da kama ta tafi Kano, kuma kai tsaye ta nufi unguwar Ta samu gidan,amma kuma mai gidan Allah ya yi masa rasuwa sati biyu da suka wuce,hakan ya ƙara mata karsashi,ta nuna cewa ta'aziyya ta zo yi,ta bayar da kuɗi 200k Matar tana ta yi mata godiya amma ita a fakaice ɗanta take kallo, wanda ya lafe a jikin matar yana sauke numfashi Kallonsa ta yi ta kasa jurewa,ta ce"Mama ba shi da lafiya ne?" Cikin jimami Mama ta dubi yaron ta ce"Abubakar ai ya kwana biyu yana jinya,shi dama daga damina ta zo ko sanyi to sai dai a yi ta lallaɓawa,kuma ga yadda ake fama da rayuwar" Shaheeda ta bayar da wani kuɗin 100k ta ce"gashi Mama a kai shi asibiti, ba'a wasa da jinya"Mama tana murmushi ta ce"to baiwar Allah kin bayar da wasu kya sake bayar da waɗannan kuma?kin ga....." "A'a Mama kar ki damu, Allah dai ya raya miki su ya yi musu albarka,ni zan tafi, Abubakar Allah ya ƙara sauƙi"ta miƙe don fita Mama ta yi ta yi mata godiya, sannan ta raka ta har bakin ƙofa, Shaheeda ta fice daga gidan zuciyarta a raunane,don sau ta ji kamar ta karɓo ɗanta Bata koma Abuja ba sai da ta sake komawa unguwar su Abubakar bayan sati biyu,tana tsaye tana tunanin yadda zata ganshi sai ga su sun dawo daga yawo,yana riƙe a hannun ɗaya daga cikin yaran Mama, sauran ƙannensa suna biye da shi Da dabara da hikima ta yi zuzzurfan bincike game da Mama da ahalinta,anan ta gane kafin rasuwar mai gidan ma babbar yarsu Fauziyya ta rasu tana aji ɗaya a jami'a, sannan suna fama sosai da rayuwa Da haka ta samu take tallafa musu lokaci lokaci,amma bata taɓa bari sun gane ita ba ce Bayan watanni shida Shaheeda tana zaune a ɗakinta wayarta ta yi ƙara, ba tare da ɓata lokaci ba ta ɗaga Mutumin ya sanar mata da cewa ƙwayoyi yake buƙata,suka yi ciniki,ya gaya mata location ɗin da za ta kawo masa Bata ɓata lokaci ba ta je don kai masa,sai dai tana zuwa a maimakon sabon customer ɗinta sai ta ga ƴan sanda,kuma ba tare da ɓata lokaci ba suka yi ram da ita Kwananta biyu a kulle babu wanda aka bari ya ganta,dama bata da kowa da ya damu da ita sai Oga boss da Azeema,su ma an hana su ganinta,amma a rana ta ukun sai gashi qan bayar da belinta an fito da ita ba tare da wata matsala ba,bayan kuma an tabbatar mata da cewa ba za'a bayar da belinta ba,sai an gurfanar da ita a kotu Tana daf da fita daga harabar police station ɗin wani ɗan sanda ya taho da gudu yana kiran "Madam!ji mana!"babu musu ta tsaya ya waiga tana kallonsa,ya ƙaraso ya miƙa mata wani kati ya ce "wanda ya yi belinki akwai number ɗinsa a jikin katin,ya buƙaci mu ɓatar da file ɗinki, kuma mun ɓatar,ya kamata ki yi masa godiya" Shaheeda ta amshi katin tana ƙare masa kallo, kafin ta juya ta fice daga police station ɗin ba tare da ta yi masa magana ba Tana shiga gida Oga boss da Azeema suka ɗago suna kallonta a firgice,kuma a cikin mamaki, Azeema ta miƙe da gudu ta rungume ta tana murmushi, kafin ta ja hannunta ta kai ta don ta yi wanka ta shirya Bayan awa guda Shaheeda ta kammala shiryawa,ta ci abinci sannan suka zauna suna jajanta abin da ya faru Oga boss ya dube ta ya ce"sau uku ina zuwa amma ana ce min wai ba zan ganki ba,sai an tura ki kotu, hankalina ya tashi sosai,yau kuma abin mamaki sai gashi kin dawo gida,ya aka yi kika fito haka?" Shaheeda ta sauke numfashi sannan ta ba su labarin duk abin da ya faru,sun yi mamaki sosai,kuma sun yi farin ciki, Oga boss ya ce"ai kuwa tunda an ba shi number ɗinki ya kamata ki kira shi ki yi masa godiya, idan ya kama ma ki je ki yi masa,sai mu raka ki,amma ya kika gani?" Shaheeda ta girgiza kai ta ce"ba wannan ne abin dubawar ba,abin dubawar shine dole ba haka nan ya fito da ni ba,akwai dalili,idan don Allah ne akwai waɗanda suka fi ni buƙatar hakan, waɗanda suka yi ƙaramin laifi meyasa su ba'a fitar da su ba?' Shiru Oga boss ya yi, kafin ya ce"haka ne kuma,gaskiyarki,amma dai ya kamata ki yi masa godiya"babu musu ta karɓi wayar hannunta,ta saka numbern da ke jikin katin ta danna kira A mutunce suka gaisa da mutumin, cikin girmamawa ta ce"Alhaji na ga karamci na gode,na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi " Shiru ya ɗan yi na ɗan lokaci kafin ya ce"amma ban gane mai magana ba"tana ɗan murmushi ta ce"Fati ce, yarinyar da ka yi beli ɗazu " Alhaji ya yi murmushi ya ce"oh na gane! ƴar kasuwa kenan"murmushi kawai Shaheeda ta yi, Alhaji ya cigaba da faɗin"idan ba za ki damu ba zan iya ganin ki zuwa gobe?"sai da ta ɗan yi shiru tana nazari, kafin ta ce"eh babu damuwa,turo min location ɗin"daga nan suka yi sallama Tana kashe wayar ta bawa su Oga boss labarin yadda suka yi, Oga boss ya ce "to ki je,amma fa ki yi taka tsantsan,ko ma na raka ki kawai"Shaheeda ta ce"ba sai ka je ba,nima ya kamata a ce na kai lokacin da zan iya ƙwatar kaina,zuwa anjuma in sha Allah zan je"Oga boss ya ce"to shikenan babu damuwa, Allah ya tsare,sai ki kula "Shaheeda ta ce"babu matsala " Ai kuwa bayan magriba ta shirya ta tafi location ɗin da aka tura mata, ba'a bar ta ta shiga ba sai aka yi mata iso, Alhajin ya ce a bar ta ta shigo Ta yi mamaki mai tsanani ganin mutumin, Alhaji Sa'idu wada, ministan ilmi na lokacin,bata nuna masa a fuska ta yi mamaki ba ta gaishe shi,ya amsa yana murmushi, sannan ya sa aka gabatar mata da kayan sha,har da tukunyar shisha da ƙwayoyi A yatsine ta kalli komai ta ɗauke kai,ta ce"Alhaji ai ni bana cikin yanayin yanzu,kai dai ka gaya min abin da kake buƙata,ma gani,idan ina iyawa na yi, idan bana iyawa kuma na kama gabana "Alhaji yana murmushi yana shafa gemunsawya ce"haba zazzafa za ki iya mana Yanzu dai bari na fara ta kan abu na farko,an ce ke ɗin mai siyar da ƙwayoyi ce,kina da kwastamomi a hannu,don haka nake son mu yi magana,ina son a rinƙa shigo min da ƙwayoyi daga waje,har ma da cocain da sauran kayayyaki,amma ke nake so ki zama agent,idan kika yi haka zan yi miki biya mai kyau,sai adadin miliyoyin da kike so zan ba ki,kuma zan tsaya miki kar wani jami'in tsaro ya yi nasara akanki Sai kuma abu na biyu, yarinya tun sanda na fara ganinki na ji kwaɗayinki, shine nake so idan zai yiwu a bani dama,na yi miki alƙawarin miliyoyin kuɗi idan hakan ya samu,zan mallaka miki irin gidan da kike so,mota kuwa sai wadda kika zaɓa,amma menene ra'ayinki?" #Nusy_bee Page 36 Wani banzan kallo Shaheeda take aika masa daga inda take zaune, fuska a ɗaure, cikin fusata ta fara magana "A harkar business ka gan ni,ka yi business da ni,idan da ace zan yi karuwanci ba sai ka gaya min ko yaudare ni da wasu ƴan kuɗin ka ba,idan kuɗi ne ko ban siyar da ƙwaya ba ina da hanyar samunsu,don haka hattara! Ka yi abin da ya kawo ka kawai,kaya ne kake so,idan ka shirya a shigo maka ko a fitar maka da kaya,ka kashe waccan mummunar aƙidar taka to Shaheeda tana maraba da kai"ta miƙe a fusace zata fita "A haba kyakykyawa!haba kyakykyawa!ya da haka ne? Don Allah ki yi haƙuri,na rusa waccan maganar, na ɗauka ke ma ƴar hannu ce,amma yanzu na gane,zauna mu yi magana"tana daga tsaye ta ce"yi maganarka ina jin ka"ya marairaice ya ce"don Allah ki yi haƙuri ki zauna"babu musu ta zauna tana aika masa da wani mugun kallo Yana murmushi ya ce"haba kyakykyawa!don Allah ki saki fuskarki, wallahi ba kya yin kyau a haka,haba kyakykyawa "ɗan sakin fuskar ta yi,amma bata yi murmushi ba,ta sake faɗin"yi bayani,ina jin ka"babu musu ya fara bayani "Akwai kayana a Columbia,ina so su shigo Nigeria,kuma ke nake so ki shigo min da su, don Allah bana son a samu matsala " Babu bata lokaci ta ce"consider it done in sha Allah, menene ƙimar kayan? Kuma menene kasona na abin da zan samu?" Alhaji ya ce"kayan sun kai ƙimar dala million hamsin,kuma kina da 5%"yatsina fuska ta yi tana yi masa kallon hadarin kaji,ta ce"albarka!" "To kashi goma idan kin amince "miƙewa ta yi tsaye ta ce"idan ka shirya biyan kaso ashirin da biyar sai ka yi min magana "ta kama hanya don ficewa daga parlourn "A haba yarinya ki duba mana! Kashi ashirin da biyar ai da yawa fa,ribar me zan samu kenan?"juyowa ta yi tana kallonsa ta ce"Ni baka duba tsananin kasadar da zan ɗauka ba? Sai kai akan kuɗinka?to yadda kake son kuɗi haka na fito neman kuɗi,ya rage naka ka saki kuɗi ka samu kuɗi,ko ka riƙe kuɗi ka huta"ta juya hankali kwance zata fice daga parlourn "Na yarda,na yarda,haba ranki ya daɗe"babu ɓata lokaci ta juyo ta samu waje ta zauna tana fuskantar shi Da kanshi ya tsara mata yadda abubuwa za su tafi,kuma bata tafi ba sai da ya tura mata Miliyan ashirin na cin chewing gum Bayan ta koma gida ta sanar da su Oga boss yadda suka yi,sun yi farin ciki sosai, Oga boss ya sake jaddada mata cewa ta kula, saboda irin su ba su da tabbas Alhaji Sa'idu wada da kanshi ya haɗa ta da mutanen da za su taimake ta,wasu daga cikinsu yan sanda ne,har ma da ma'aikatan hukumar DSS,daga kan state directors zuwa kan masu muƙamai, ba'a maganar ma'aikatan customs da immigration wadanda suka zama sune manyan yaranta wajen shigar da kayan Cikin nasara kuma ba tare da ɓata lokaci na ta fara aiwatar da aikinta,sai dai kamar yadda Oga boss ya bata shawara ta sauya sunanta daga Fatima zuwa ROXY Banda waɗanda suka santa a baya,da waɗanda suke jikinta babu wanda ya san asalin sunanta,a tsawon shekara ɗaya da fara wannan sana'ar tata ta hadu da mutane da yawa,ciki har da babban yaronta David, wanda yake taimaka mata a kasuwancin nata Ta koyi dabaru kala-kala na rayuwa da gujewa jami'an tsaro,bayan ta tabbatar ta tsaya da ƙafafunta har gida ta je ta sanar da Alhaji Sa'idu wada cewa ta gama yi masa aiki,itama yanzu ta kama gashin kanta Duk yadda ya so ta koma ta cigaba da yi masa aiki ta ƙi,hakan ya fusata Alhaji Sa'idu, babu ɓata lokaci ya bayar da hotonta a kama masa ita,don a lokacin ya kasa tantance wanne suna ne asalin sunanta Ɗaya daga cikin jami'ai, wanda ya kasance ita yake yiwa aiki ne ya kira ta ya sanar da ita,hakan ya sa ta yi murmushi,kuma ta ƙudurce a ranta dole ne ta sake shiri Shirin farko da ta fara yi shine gayawa duniya da take yi a sirrance cewa babu mai iya kama ta, saboda ta yi dukkan wasu dabaru don gujewa hakan,ta fara amfani da harufan NOCCM, waɗanda babu wani abu da suke nufi sai NO ONE CAN CATCH ME,kuma ta yi farin ciki ganin jami'an tsaro sun mayar da hankali don gane abin da haruffan suke nufi,ita kuma ta mayar da hankali don abin da yake gabanta Daga nan barin ƙasar ta yi,ta koma Spain, inda ta cigaba da sana'arta cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba Sai da ta shirya cif sannan ta dawo Nigeria,ta saka idanu sosai akan dukkan wani jami'in tsaro da zai fara bincikarta,daga an fara bincikarta zata saka a bincika mata wanene jami'in,zata shiga rayuwarsa ta yi masa barazana,da haka zai yar da case ɗin saboda tsoron abin da zai faru gare shi ko ga iyalinsa A ɗaya ɓangaren kuwa bata fasa saka idanu ga ɗanta ɗaya tilo ba,kuma bata fasa zuwa wajen kantamemen gate ɗin MALIYA ESTATE ba,wani lokacin idan ta ga fitowar Abba ko Ummeenta tana yin kuka sosai, tana tsananin son su,amma yanzu sun yi mata nisa Amma har zuwa yanzu zuciyarta baya karaya ba,kuma duk yadda take jin damuwa bata taɓa barin wani ya sani ko ya gane,ta cinye abarta ita kaɗai,sai idan abu ya dame ta ta sha kwayoyinta ta yi bacci Da haka CSO HAISAM ABDULMALIK MADAKA jami'in tsaro na hukumar DSS ya shiga rayuwarta ya fara farautarta,da farko bata ɗauki case ɗin sa da zafi ba,ta ɗauka shi ɗin gama garin jami'i ne kamar sauran jami'an tsaron da suke farautarta,sai da ta yi kyakkyawan bincike akansa ta gane yadda take hatsabibiya haka yake da hatsabibanci,har ma ya fi ta, hankalinta ya tashi,ta yi dukkan mai yiwuwa don ta guje masa,ta yi masa barazana da iyalinsa,ta yi masa da ranshi amma duka a banza,a ƙarshe sai da ya san yadda zai yi ya ga bayan aikinta da ta gina tsawon shekaru uku Wannan shine labarin FATIMA SHAHEEDA, wadda a yanzu take amsa sunan ROXY saboda yanayin aikinta ko sana'arta, abubuwan da suka faru da ita har ta tsinci kanta a cikin wannan halin 💫 Shiru ya biyo baya na yan sakwanni,kan Haisam a ƙasa,gaba ɗaya jikinsa a mace, kafin a hankali ya ɗaga kai ya kalle ta,sassanyan murmushi ta sakar masa,ya ɗaga gira alamar ya dai?ta girgiza kai ba tare da ta yi magana ba,sun ƙara jan wasu seconds ɗin kafin ya ce"na san lokacin da na je kama ki a Spain akwai wanda ya sanar da ke batun tafiyar a tawagata, wanda shine yake ba ki bayanai akaina da yunƙurina,shin za ki iya gaya min wanene shi?" Sauke numfashi ta yi tana kawar da kai gefe, kafin ta ce"I'm sorry to say,ba zan iya gaya maka sunansa ba, saboda bana son ya rasa aikinsa,idan haka ta faru kuma ban san wanne irin criminal gobe zata haifar ba,ka bar shi a yadda yake,duk bala'i bai isa ya fito ya yiwa ƙasa zagon ƙasa Kamar yadda na yi ba" Haisam ya ce"babu abin da zai samu aikinsa,asalima manya ba za su ji ba, maganar tsakanin ni da shi ne kawai" Shiru ta yi tana kallonshi,ya yi murmushi ya ce"nima ba ki yarda da ni ba ko?"girgiza kai ta yi ta ce"A'a, kawai ina so na tabbatar da gaskiyarka ne, kamar yadda na faɗa maka bana fatan wani ya rasa aikinsa ta dalilina Amma zan gaya maka,ba kowa bane sai abokin aikinka Awwal! Ya daɗe yana yi min aiki,in fact,yana daga cikin yaran da state director na Kano State ya saka don su rinƙa taimakona " A razane Haisam yake kallonta, kafin da ƙyar ya furta"You mean? State director da haɗin bakinsa a wannan badaƙalar?" Jinjina kai ta yi, sannan ta ce"akwai bakinsa, amma shima Alhaji Sa'idu wada yake yiwa aiki,kuma bijirewar da na yiwa Alhaji Sa'idu ita ce ta janyo ya kware min baya ya fara farautata" Haisam ya jinjina kai ya ce "Wanene ya ba ki dabarun gujewa jami'an tsaro?" Gyara zama ta yi tana ɗauke kanta,ta sauke numfashi ta ce"a duk lokacin da mutum yake ji ba zai iya aikata wani abu ba to bai same shi ba, ballantana ni da duk lokacin da na saka a raina zan yi abu to sai na yi shi Kar ka manta nice na rainawa iyayena hankali,na auri wani ba tare da saninsu ba,na bi shi muka bar ƙasar baki ɗaya ba su sani ba,har yanzu a makaranta mataki na biyu nake,amma na yi abin da dubban masu Masters ba su yi ba da nasu,a taƙaice dai,duk wani abu da mutum ya saka kanshi to tabbas sai ya iya Ni yanzu na san na gama tunda kuka kawo ni nan,mafi ƙarancin abin da zan iya fuskanta a kotu shine hukuncin ɗaurin rai da rai, saboda na san laifina babban laifi ne,abu ɗaya ne damuwata a rayuwa,shine ɗana mubarak"ta ɗago duk da babu alamun damuwa a fuskarta,amma ya gani a cikin idanunta,ta ce"a karo na biyu ina sake roƙonka,a wanne hali Mubarak yake ciki? Kar ka manta na haife shi a maraya, wanda yake cikin ganiyar rashin gata,nima na yi masa laifi, saboda zaɓar duniya na watsar da shi na kama rayuwata,bai san daɗin iyayensa ba,bai san wani daɗi na rayuwa ba, musamman duba ga inda ya taso Zan so a ce nan gaba ya samu farin ciki kamar kowa,ya samu ingantacciyar rayuwa, sannan kuma ya yi min addu'a " Haisam ya yi murmushi ya ce"a matsayinki na wa zai yi miki addu'a?" Ta kalle shi sosai tana ɗan murmushi ta ce"a ƙalla in samu darajar ɗaukar ciki da haihuwa mana officer " Yana kallonta ya ce"ke mahaifiyarsa ce tabbas,ban isa na ce ba kya son shi ba, saboda na san ƙarya nake yi,amma meyasa za ki watsar da rayuwar tilon ɗanki ki kama rayuwar da kike so? Na san dai babu jin haushin mahaifinsa a tare da ke, musamman da kika fuskanci laifinki ne " Girgiza kai ta yi,ta ce"na kasa jurar hakan ne,matsayin Mubarak na ɗan Arnold, kamar yadda na gaya maka a baya idan na kalle shi ina tuna cewa Arnold ya yaudare ni,na aure shi na rabu da iyayena,amma shi ya watsa min ƙasa a idanu,ya tozarta ni,a ƙarshe a dalilin sa na shiga wannan rayuwar da nake ciki Larurar Mubarak da ya gado daga wajen dangin babansa ta sake dasa min wani ciwo,hakan ya sa na zaɓi na nisance shi, gudun kar na illata shi akan laifin da ba nashi ba,kar na zalunce shi " Haisam ya ce"ai kin gama zaluntar shi Shaheeda! Tunda kika kasa zaɓa masa uba na gari, gashi a ƙarshe rayuwarsa ta koma wani sashen dabam na wahalhalu, meyasa kika yi hakan?" "Wannan ƙaddarata ce da ban isa na tsallake ta ba a rayuwa,da a ce kowanne bawa shine yake tsarawa kanshi rayuwa da na tsarawa kaina yan'uwa daga mahaifiyata, waɗanda za su damu da ni ko da a ce ita mahaifiyar tawa bata kula ni ba,da ban tsarawa kaina soyayya irin wadda zata makantar da ni daga hangen abin da zai je ya dawo ba,da ban tsarawa kaina lalacewar rayuwata saboda abin duniya ba A tsawon shekaru uku da na kasance a wannan halin sam bana cikin farin ciki,ko babu komai tsinuwar al'umma aba ce mai tasiri ga rayuwar mutum"ta ɗaga kai tana kallonsa, kafin ta ce"Ni yanzu abu ɗaya nake fata idan zai samu,a yanke min hukuncin kisa kawai,ina fatan hakan ya zama kaffarata "kukan da take riƙe da shi ya kubce mata Miƙewa ya yi cikin jarumta jin zata karya masa zuciya,ya fara magana cikin kwantar da murya"ranar Monday za'a shiga da ke court,gobe idan Allah ya kai mu za mu zo da lawyer ɗin ki,in sha Allah komai zai zo da sauƙi,ina fatan don Allah kar ki yi mata taurin kai "a hankali ta jinjina kai, kafin ta ce"na yi maka wata tambaya amma har yanzu ba ka ba ni amsar da ta gamsar da ni ba A karo na biyu ina roƙon ka ba ni amsa don Allah " Kallonta yake yi ya ce"wacce tambaya ce?" Sauke numfashi ta yi,ta ce"ɗana Mubarak,yana ina? Sannan kuma a wanne hali yake ciki don Allah?" #Nusy_bee Page 37 Haisam ya yi ɗan murmushi ya ce"Mubarak yana hannuna a yanzu haka,idan za ki bar min shi ma ina so, because I love the boy so much,kuma ina fatan watarana mahaifiyarsa ta dawo gare shi ta cigaba da riƙe abinta" Murmushi ta yi sosai,duk da hawayen fuskarta ta ce"na bar maka shi,kuma ina fatan watarana idan ya girma ka ba shi horo ya yaƙi mutane masu irin sana'ar da nake yi, maganar rainonsa kuwa kai ma ka san ba abu bane mai yiwuwa a gare ni a yanzu dai" "Babu abin da ba ya yiwuwa da izinin Allah,ke dai in sha Allah za mu dawo mu tattauna akan batun shiga kotun In Sha Allah za ki fita daga nan,kuma za ki sake ganawa da ɗanki,amma ina so na yi miki wata tambaya ɗaya"jinjina kai ta yi ba tare da ta yi magana ba Kai tsaye ya ce "a Labarin da kika ba ni,ba ki sanar da ni cewa kin yi karatun addini ba, menene gaskiyar lamarin?"kai tsaye Shaheeda ta ce"na fara ba ka labarina ne tun sanda na kammala secondary,amma na haddace Alqur'ani tun ina SS2,na karanci littafai da yawa, dalilin haka ya sa na daina zuwa ma" "To duk lokacin da kika ji damuwa da ƙunci,kin taɓa ɗauko Alkur'ani kin karanta?ko kin taɓa tashi cikin dare kin roƙi Allah ya duba ki ya ba ki maslaha akan matsalolinki?"shiru ta yi tana kallonsa, don tabbas bata taɓa yi ba,ya ce"to kin gani ko? A duk lokacin da kika ce Allah zai yi miki to tabbas zai yi miki ɗin,amma idan kika gwada dabara da iyawarki to tabbas Allah zai bar ki da iyawarki " A hankali ta jinjina kai cike da gamsuwa,ta yi ɗan murmushi ta ce"na gode sosai da karamci,na gode,ka yi abin da iyayena ma suka kasa yi min"Haisam ya ce"babu ta inda iyayenki suka rage ki,sun yi dukkan ƙoƙarin da za su yi miki,ke ce a yanzu suke bi bashi" "Ni kuma?ta yaya zan iya biyansu bayan ka san a yanzu tawa ta ƙare?" "Weather taki ta ƙare ko kina da sauran dama lokaci ne zai bayyana haka,shekarunki nawa a yanzu, ashirin da nawa?" Shaheeda ta ɗaga yatsunta guda uku ba tare da ta yi magana ba, Haisam ya zaro idanu yana murmushi ya ce"har yanzu ke ƙwaila ce Shaheeda,yarinya ce ke sosai,kin yi ƙoƙari sosai,na jinjina miki yadda kika rinƙa gwara kanmu da ƙananun shekarunki,I salute you Ma'am "ya faɗa yana sara mata yana murmushi Sunkuyar da kanta ta yi ƙasa tana kallon handcuff ɗin hannunta tana murmushi ita ma, Haisam ya ce"alright then,ni zan tafi,sai na dawo zuwa gobe "ta sake yi masa godiya,suka yi sallama *MALIYA ESTATE* Izuwa yanzu al'amura sun sake rincaɓewa a gidan Alhaji Yusuf Maliya,don a wannan karon Ummeey ta kasa jure halin da ƴarta take ciki, da gaske ciwon da take ciki ya taɓa ta,kuma kallo ɗaya za'a yi mata a gane hakan Hakan ne ya sa Alhaji Yusuf ya fita daga sha'aninta,don a ganinsa saboda ƴarta tana son ta fara karya masa doka Hakan ya sa ta fusata ta fara shiryawa don komawa gida,don ita ta gaji da wannan auren da tunda ta yi babu abin da take samu banda baƙin ciki da ɓacin rai Tana shirin fitowa daga sashenta sai ga Hajiya Atika,tana yi mata wani kallo ta ce"Hajiya sai kuma ina?" Bata amsa ba, Hajiya Atika ta sake faɗin"dama Alhaji ne ya ce na yi masa kiranki "tana kai wa nan ta juya ta bar wajen Bata yi niyyar zuwa ba,amma sai ta canja ra'ayi ta tafi, tana zuwa ta samu Alhaji Yusuf a tsaye, fuskarsa a ɗaure Bata nuna ta gane halin da yake ciki ba ta ce"Barka da warhaka Alhaji" "Samu waje ki zauna Zainab"ta manta rabon da ya kira ta da wannan sunan,amma ko a fuska bata nuna damuwa ba,ta samu waje ta zauna Daga nan ɗaga waya ya yi ya yi kira,ana ɗagawa ya ce"Ruƙayya ku taho tare da Arfa,ki cewa Sa'adatu itama ta zo,ina buƙatar ganinta"sannan ya kashe wayarsa Babu jumawa suka iso,sau ɗaya Hajiya Zainab ta kalle su ta ɗauke kai,daga amsa sallamar da suka yi ba ta sake magana ba, musamman da ta ga ko sashen da take ba su kalla ba Alhaji Yusuf ya ɗaga kai ya kalle ta,a ɗan fusace ya fara magana "Zainab an kawo min ƙararki a gidan nan,ban san menene matsalar da take son ta canja ki ba,ko don kina ƙoƙarin ki nuna min ban isa da Shaheeda bane ya sa kike yin haka ban sani ba" Hajiya Zainab ta ɗaga kai ta kalle shi ta ce"Alhaji me kuma aka ce na yi?" Alhaji Yusuf ya ce"ina Muyassar ya je?" Hajiya Zainab ta dube shi sosai ta ce "Muyassar? Alhaji ta ina zan san inda ya je?" Alhaji Yusuf ya kalli Hajiya Sa'adatu,kamar jira take yi ta fara magana a fusace "ɗana tunda nake da shi ban taɓa ba shi umarni ya kauce ba sai akan ke da ƴarki,me kuka taka ne haka? Da me kika fi sauran mutane ke da ƴarki? Har ga Allah zuwa yanzu na fara gajiya,na gaji da yadda nake tarbiyya kuna rusawa,don haka ki saka ɗana ya dawo gida kawai ya mayar da matarshi Kamar yadda kika saka ya sake ta,don na san ke ce kika saka shi ya sake ta sannan ya yi nisa da ita, saboda an kama gallafiriyar ƴarki " Kallonta kawai Hajiya Zainab take yi har ta kai aya, sannan ta yi murmushi ta ce"hattara dai Hajiya Sa'adatu! Me ɗa ba ya yiwa wani gorin lalacewar ɗa idan da tunani, babu uwar da zata so ɗanta ya lalace ko da ace ita lalatacciyar ce kuwa, kin ga......." "Saurara Hajiya Zainab! Ai lalacewa kuma sai dai ki ganta akan ƴarki wadda take zuba rashin tarbiyya da rashin mutunci tun tana ƴar ƙanƙanuwarta amma kin kasa tsawatar mata,idan ma wani asirin kika yi don lalacewar yayanmu to Allah ya mayar miki da masifar kanki,amma yayanmu sun fi ƙarfin lalacewa da ikon Allah " "To madalla! Da kika san da haka,na cewa ƴaƴanki suna jin maganarki ai da ɗan naki ya yi nisa shi za ki tunkara ki ce ya dawo,ba ni za ki zo kina zaƙalƙalewa ba,ƙaddarar Shaheeda kuwa idan Allah ya so zai iya mayar da ita ba komai ba,ni fatana koda yaushe Allah ya shiga rayuwarta ya zama gatanta " Wani kallo Alhaji Yusuf ya yi mata, cikin ɓacin rai ya ce "wato kina nufin da na ce a manta da ita a gidan nan ba ki manta ba kenan ko me?"miƙewa ta yi tana kallonsa cikin idanu ta ce "Ko zan manta komai,ai ba zan manta cewa Shaheeda ce ta mayar da ni uwa,nake tuna cewa na haihu ba tare da na ji zafin wani gori ba,a lokacin da kowacce uwa take ƙyamatar na nuna ɗanta na ce nawa ne a lokacin ne nake alfahari saboda na tuna cewa ina da Shaheeda,kuma ban taɓa nadamar haifarta ba,don haka ka ma cire a ranka cewa akwai ranar da zata zo har ta wuce ban yiwa Shaheeda addu'a ba,ko kuma ban ji ta a raina ba" Arfa da Hajiya Ruƙayya da mamaki suke kallon Hajiya Zainab wadda iya tsawon zamanta a gidan ba'a taɓa jin ta mayarwa da wani amsa ba saboda tsananin haƙurinta,amma sai gashi yau ga tana mayar da magana Hajiya Sa'adatu ta kama haɓa da mamaki tana kallonta ta ce"ke yanzu idan banda rashin kunya da rashin ɗa'a irin na wasu mutanen yanzu har Shaheeda ta kai a yi tutiya da ita? Wallahi ni dai a nawa ganin da haihuwar irin su Shaheeda gwara zama babu haihuwar ma gaba ɗaya,me ake da ɗa irin Shaheeda,haka kawai a haifarwa duniya Annoba?" Hajiya Zainab ta yi murmushi ta ce"idan kin tashi haihuwa ki haifo limamin harami bisa wayonki da dabararki,Ni wannan ba matsalata ba ce Allah shine ya san hikimar ba ni Shaheeda ba tare da yan'uwa ba, sannan ya jarrabe ni da halayenta,amma a hakan na godewa Allah,kuma har yanzu ban cire rai zata zamar min abar alfahari ba watarana,ban cire rai zai sake haɗa mu ba"daga haka ta juya da sauri ta fice daga parlourn tana mayar da zazzafan hawayen da ya fara cika mata idanu,da wanne zata ji ita kuwa? Da halayen Shaheeda?ko da baƙin cikin korar da mahaifinta ya yi mata wanda shine tushen komai,ko da abubuwan da aka ce ta aikata?ko da kamun da aka yi mata?ko da wadannan surutan da ake yi mata,da baƙaƙen maganganun da ake gaya mata dare da rana Daga sashen Alhaji kai tsaye parking space ta nufa ta shiga motarta ta tayar ta fice daga gidan,tana tafiya a mota tana share ƙwalla, aranta tana ambaton dukkan sunan Allah da ya zo mata rai Kai tsaye gidan Hajiya Saudat ta nufa,a bakin gate ta tsaya ta kashe wayar ta sannan ta shiga cikin gidan,a ranta tana ganin gwara ta ba wa kowa hutu kawai, ita ma ta samu nata hutun *ROCKY ESTATE* Sai da ya yi sallar isha'i sannan ya shiga sashen Nanny ɗin su Amna,yana shiga da sallama Amna ta taso da gudu ta ɗane shi tana murna,ya rungume ta yana murmushi,ya mayar da kallonsa ga Mubarak wanda yake raɓe a gefe guda Sauke Amna ya yi, Nanny tana faɗin "Barka da zuwa ranka ya daɗe"ya yi murmushi ya ce"Barka dai Nanny,ya na ga yallaɓai a zaune ya takure?" Nanny ta yi murmushi tana kallonsa ta ce"wai nan fushi yake yi saboda na ba shi magani,ka san baya son magani ko da wasa"Haisam ya yi ƴar dariya ya ƙarasa inda Mubarak yake zaune yana kallonsu, fuskarshi duk hawayen da bai gama gogewa ba,ya sa hannu ya ɗago shi yana faɗin "abokina ya dai? Wa ya taɓa min abokina ne?me yake faruwa? Nanny ce ta ba ka magani?ba ka so ko?"ya gyaɗa kai fuskar nan a ɗaure, Haisam ya ce"ai tafiya ma zamu yi mu bar mata sashenta ko?"ya sake gyaɗa kai yana shagwaɓe fuska, Haisam ya yi murmushi ya ce"Weldon my friend,zo mu tafi ko?"Nanny tana murmushi ta ce"tafiya za kayi ka bar ni?"ya juyo ya kalle ta ya ɗauke kai, Amna ta ce"Daddy nima zan bi ku" Daddy ya ce"ba yanzu ba tukunna, sai da safe sai ki zo, yanzu ki zauna a wajen Nanny "ya ja hannun Mubarak suka bar sashen Ya ɗan ɗauki lokaci yana yi masa wasa,har shima Mubarak ya fara sakin jiki yana ba shi amsa,shi dai kallonsa kawai yake yi,ganin exactly fuskar Shaheeda, babu inda ya bar ta,sai hasken fata da ya fi ta Wajen ƙarfe tara Haisam ya samu Mubarak ya yi bacci,ya kwantar da shi sannan ya miƙe ya nufi sashen iyayenshi,don Abba ya yi masa magana yana son su gana A parlour ya same su a zaune,ya yi mamakin ganin Nimra da ya fara gajiya da ɗan banzan nacinta,amma ko a fuska bai nuna ba, bayan ya gaida su abbansa ya nuna masa kujera yana faɗin"zauna Haisam " Babu musu ya zauna, Abba ya ce"har yanzu baka cewa kowa komai ba game da yaron da ka kawo gidan nan,gashi mu kuma ba mu san shi ba" Haisam kai tsaye ya ce"Abba ba ku sanshi ba,amma yanzu ya zama ɗaya daga cikinmu, ɗan criminal ɗin da na kama ne, kasancewar ba shi da kowa sai na kawo shi ya zauna a cikinmu" A kusan tare Nimra da Hajiya Mariya suka razana, Abba ya ce"menene hikimar hakan Haisam?na san dai baka yin abu sai da dalili" Haisam ya gyara zama ya ce"haka ne Abba! Akwai ƙwaƙwƙwaran dalili kuwa, saboda shi yaron ba shi da kowa,asalima"ya ba su labarin Shaheeda a taƙaice yadda za su fahimta Abba ya tausaya mata sosai,su kuwa Hajiya Mariya da Nimra kallonsa kawai suke yi sun kasa magana, Abba ya ce"Allah sarki! Dama a rayuwa ba kowa bane za ka ganshi da wani hali ya zama laifinsa ne,wasu trauma ce,wasu kuma dole ne,to ina yi mata fatan Allah ya fito da ita lafiya ta riƙe ɗanta,don bai kamata abu irin wannan ya shafi rayuwarsa ba Allah ya kawo mafita,shi kuma yaron Allah ya raya shi ya yi masa albarka " Haisam dama ya sani zai samu goyon bayan Abba, dattijo mai nutsuwa da hangen nesa,mai tsananin tausayi da mayar da duniyar ba komai ba, kafin Haisam ya sake magana Alhaji Abdulmalik ya cigaba da Magana "Akwai kuskure sosai a tozarta rayuwar ƴa mace a lokacin da ta aikata kuskure,da ba'a tozarta ta ba an sallama ta da yanzu wataƙila ta zama wata mai amfani,amma hakan da aka yi mata gashi nan baiwarta ta zama barazana ga al'umma Muna buƙatar yara irinsu a society ɗin mu,bai kamata mu yi musu haka ba" Haisam ya yi murmushi yana gyara zama, kafin ya yi magana Hajiya Mariya ta kasa haƙuri ta ce"Haisam ni kuwa sai na ga kamar baka yi dabara ba Me zai hana ka kai shi gidan marayu?amma menene amfanin kawo shi nan?mu da ba mu da alaƙa da uwar tashi?" #Nusy_bee Page 38 Kallonta Haisam ya yi fuska babu walwala, kafin ya yi magana Abba ya ce fuska a ɗaure "shine ya so hakan,ya kawo shi da radin kanshi don ya inganta masa rayuwa,idan zai yiwu ki bi shi da addu'a kawai,idan ba zai yiwu ba kuma ki yi shiru,amma ko da a ce kina so ko ba kya so yaron nan yanzu zai fara zama a gidan nan da izinin Allah" Shiru Hajiya Mariya ta yi ba tare da ta yi magana ba,ita kuwa Nimra ji ta yi kamar ta kurma ihu Haisam ya dubi Abba ya ce"na gode Abba, Allah ya saka da alkhairi In Sha Allah zuwa next term idan an fara enrolling yara a makaranta zan saka shi a makarantar su Amna" Abba ya jinjina kai ya ce"hakan yana da kyau, Allah ya taya riƙo, riƙon maraya akwai lada da alfanu mai tarin yawa ,fatan shi ne Allah ya raya shi ya albarkaci rayuwarsa "Haisam ya amsa da"Ameen " Daga nan hira suka fara,suna tattaunawa akan abubuwan da suka shafi kasuwancinsu shi da abban, Nimra ganin ba'a yi batunta ba ya sa ta fara zungurin Hajiya Mariya, fuska a ɗaure Hajiya Mariya ta dubi Alhaji Abdulmalik ta ce "Ni ko Alhaji ba mu ƙarasa Maganar da muka fara kwanaki ba" Alhaji ya dube ta ya ce"wacce maganar ce?" Hajiya Mariya ta ce"maganar ya kamata a haɗa Haisam da Nimra aure mana,tunda dai yanzu ga ka ga ni,gashi kuma ga Nimra ɗin kawai gwara a yi a gama ko?amma kai ya kake gani?" Alhaji Abdulmalik ya kalli Nimra ya ce"da izininta kika yi wannan maganar?"Hajiya Mariya ta ce"da izininta ne,ka sake tambayarta ka ji"Alhaji Abdulmalik ya jinjina kai ya ce"to kai Haisam ya kamata ka ware lokaci ka san abin yi, tsawon lokacin da ka ɗauka baka yi aure ba ya kamata ko me aka yi maka zuwa yanzu a ce ka huce, riƙo a wajen ɗan musulmi ba shi da amfani sam, ballantana ma wadda ta yi maka laifin dabam da wadanda kake hukuntawa,ya isa hakanan Haisam "jinjina kai ya yi,a sanyaye ya ce"to shikenan Abba,komai ya wuce, Allah ya shige mana gaba ya yi mana jagora " Alhaji Abdulmalik ya ce"Ameen Ameen! Yanzu ga Nimra, menene ra'ayinka akanta? Ka ga dai ita ka santa,kuma ina da yaƙinin ba zata ba ka matsala ba in sha Allah,kuma zata riƙe maka yaran da kyau,amma kai me ka gani?" Haisam ya ɓoye mamakin rashin kunyar nan,ya ce"Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi,amma ya kamata ta ƙarasa karatunta, idan ya so sai a yi maganar auren" Cikin zumuɗi Nimra ta ce"za'a iya yi min transfer ma na dawo Kano,ba dole sai a Abujan zan yi karatun ba" Haisam ya watsa mata wani mugun kallo,tuni ta nutsu, fuska a ɗaure ya ce"za'a yi auren bayan ta kammala makaranta in sha Allah, Allah ya bada sa'a " Abba bai damu ba ya ce"Ameen Ameen, Allah ya sa albarka "Haisam ya miƙe ya ce"sai da safenku"ya fice daga sashen zuwa nashi Washe gari ko cikin gidan bai shiga ba ya shirya ya ɗauki Mubarak da yake bacci ya kai shi sashen Nanny shi kuma ya fice daga gidan zuwa office ɗin sa,akwai wani aikin bincike da zai bayar akan wani mutum da ake zargin yana safarar ƙwayoyi,har da samfurin cocain,da kuma muggan makamai,amma duniya tana yi masa kallon mutumin kirki,don yanzu ma shirye-shiryen fitowa takara yake yi Ɗaga kai ya yi yana kallon Awwal da yake shigowa, kafin ya ce"Awwal ƙaraso,ina son yin magana da kai"babu musu ya ƙaraso ya sara masa yana faɗin"morning Sir!" "Have a sit Awwal "ya faɗa ba tare da ya kalle shi ba Waje ya samu ya zauna yana kallonsa, Haisam ya ɗaga kai ya kalle shi ya ce"ya ake ciki game da case ɗin Alhaji Yunusa Datti ne?me kuka gano akanshi?" Awwal ya ce"Sir da farko dai mun gano yana bincike da wasu manyan mutane a guest house ɗin sa, waɗanda ya kamata mu san me suke tattaunawa da suke yawan zama cikin dare,da yiwuwar ba hannunsa bane kaɗai a cikin wannan badaƙalar,akwai waɗanda suke yi masa aiki,ko kuma suke aiki tare"Haisam ya jinjina kai cike da gamsuwa ya ce"ya kamata a duba kuwa,amma ba yanzu ba, saboda na fuskanci kamar ana sanar da shi sirrin aikinmu,zai iya mamayarmu ya yi nasara akanmu"ya ƙarasa magana yana kallon Awwal Ɗan murmushi ya yi ganin alamun razani a fuskar Awwal duk yadda ya so ya ɓoye hakan, Haisam ya cigaba da magana "don mun yi magana da Roxy,ta tabbatar min da cewa akwai waɗanda suke taimaka mata,duk da dai bata faɗi sunansa ba,amma tabbas akwai na yarda,kuma ka ga zai iya ɓata mana aiki ko?" Dakewa Awwal ya yi ya ce "haka ne sir!" Haisam ya ce "very good! Yanzu sai a je a fara shiri, very soon zan iya nemanka akan maganar"Awwal ya ce "okay Sir!" "You can leave"Awwal ya sara masa ya juya ya fice daga office ɗin Murmushi kawai Haisam ya yi,ya san yadda zai yi ya kama shi da laifinsa ba tare da wata matsala ba,sai ya cire masa sha'awar cin amana da izinin Allah Lawyer ɗin da suka yi magana ce ta kira shi a waya,kai tsaye ya ce mata ta jira shi gashi nan zuwa,kuma ba tare da ɓata lokaci ba miƙe ya fice daga office ɗin Kai tsaye chamber ɗin BARRISTER HIBBA IBRAHEEM AYYO ya nufa,(barrister Hibba Novel 😍kada ku sake a ba ku labari💯)bayan an yi masa iso ya shiga,ya gaishe ta ta amsa, sannan ta nuna masa waje ya zauna Barrister Hibba ta ɗago tana kallonsa, cikin jimami ta ce"akwai matsala sosai a ƙasa officer "Haisam ya gyara zama ya ce"menene matsalar barrister?" Barrister Hibba ta mayar da kanta jikin kujerar da yake zaune, cikin jimami ta fara faɗin "yarinyar nan tana cikin matsala fa,seems like akwai manyan da suke da hannu akan kamun nan da aka yi mata, Haisam me kake ɓoye min ne? Ka yi min bayani bana son nuƙu-nuƙu,ka san wacece ni" Ɗan murmushi ya yi kanshi a ƙasa,a hankali ya fara yi mata bayanin gaskiyar batu game da laifukan da ake tuhumar Shaheeda da shi,wani kallo ta yi masa cikin ɓacin rai ta ce "Ban taɓa tsammanin jami'in tsaro mai gaskiya da riƙon amana irinka zai so na kare mai tarin laifuka irin wannan ba,why ba za ka bari a hukunta ta ba, wannan yarinyar barazana ce fa ga ƙasarmu,ta yaya kake so na yi defending ɗinta bayan ka san abin da ta yi?kana son ta fito ta ɗora daga inda ta tsaya ne? Why not ka bari doka ta hukunta ta?" Haisam ya gyara zama ya ce"I'm sorry Ma'am!ba zan iya bari a hukunta ta ba, musamman ga laifinta, saboda....."ƴar dariya barrister ta yi ta ce"saboda ka faɗa soyayyarta ko? Wow! very interesting!zan so na ga yadda wannan soyayyar zata tafi"girgiza kai ya kama yi yana murmushi,ya ce"ba soyayya bane barrister,tausayinta nake ji,bari na ba ki labarin yadda rayuwarta ta tafi,har ta samu kanta a wannan halin "a hankali ya warware mata komai Murmushi ta yi hawaye suna cika idanunta,a sanyaye ta ce"Allah sarki rayuwa!kowa da irin tashi jarrabawar,ita mahaifinta shine mafarin jarrabawarta,ni kuma rashin mahaifina shine mafarin tawa jarrabawar Shikenan babu komai, yaushe kake so na tattauna da ita?" Haisam yana murmushi ya ce"ko yau ne,kin ga ranar Monday za'a shiga Court" Jinjina kai barrister Hibba ta yi ta ce"a ƙa'idar doka hukuncin life imprisonment ne hukuncinta, saboda safarar miyagun ƙwayoyi da take yi, wadanda suka haɗa har da cocain,kuma tana importing,shine babbar matsalar,ga hukuncin da za'a yi mata na hacking da take yi,abin da yawa Zan yi magana da ita, za'a san yadda za'a ɓullowa lamarin,amma fa dole zata yi zaman prison ko da na shekara ɗaya ne ko biyu"cikin rashin jin daɗi ya ce"okay Ma'am! Thanks for your effort"barrister Hibba ta sauke numfashi mai nauyi ta ce"to yanzu ina ɗan nata yake?" Haisam ya ce "yana wajena,na mayar da shi gidana yanzu"barrister Hibba ta yi murmushi ta ce"Haisam wato ya fara yin gaba kafin uwar tashi ta biyo baya kenan, Weldon!"Haisam ya yi murmushi ya ce"Ma wai ba ki yarda bane? believe me kawai ina son na zame mata wani bango ne na taimake ta,amma ba wai soyayya ba ce tsakaninmu, I promise you"barrister Hibba ta ɗaga kafaɗa ta ce"alright then! To Allah ya dafa ya yi mana jagora,anjuma kaɗan ka zo mu tafi can inda aka rufe ta,da buƙatar mu tattauna da ita,don na san ta inda zan fara "Haisam ya rissina ya ce"I'm grateful Ma'am "daga nan suka yi sallama,ya fice daga office ɗin Bayan wasu awanni Haisam da barrister Hibba suka isa zuwa jail ɗin da aka rufe Shaheeda,tare suka shiga bayan kowannensu ya nuna ID card ɗinsa,kai tsaye suka buƙaci ganin Shaheeda Babu jumawa aka fito da ita,kanta a ƙasa, Hibba ta zuba mata idanu a ranta tana jinjina tsantsar yarintarta A sanyaye ta rissina tana gaishe su,suka amsa,ya dube ta da kulawa ya ce"to Shaheeda,ga barrister Hibba,na san kin taɓa jin labarinta ko?babbar lawyer ce,kuma shugabar ƙungiyar lawyers kuma shugabar ƙungiyar tallafawa marasa galihu "Shaheeda ta ce"na sani duka Ina matuƙar godiya da karamcinki Mommy!"Hibba ta yi murmushi ta ce "never mind dear! Na ji duk abin da ya faru, I'm so sorry,but still za ki iya amending mistakes ɗinki,you still have a time" Kallonta Shaheeda ta yi a sanyaye ta ce "it's too late for me Ma!na san ke ma kin san da haka, saboda Ni kaina na san laifina ba irin wanda ake yafewa bane,ko da a ce a kan ɗaya aka tsaya ballantana....." "Amma kamar jiya mun yi magana da ke ko? Na gaya miki ki mayar da lamuranki ga Allah,hala kina ganin ba mai yiwuwa bane?ko idan na yi alƙawari ba zan cika bane?"girgiza kai ta yi a sanyaye,a hankali ta ce"I'm sorry " Hibba ta yi murmushi tana kallonsu, kafin ta ce"yanzu kwanaki uku suka rage a shiga Court in sha Allah,duk abubuwan da na tsara miki shi za ki je ki faɗa,kar ki kuskura ki yi min ba daidai ba, saboda ni ina hukunci "sunkuyar da kanta ta yi a hankali, Hibba ta fara tsara mata duk yadda take buƙatar ta yi a Court ɗin A hankali Shaheeda ta ɗago da confused face tana kallonta, kafin ta yi magana Hibba ta ce"bana son taurin kai,just do as I say, okay?"Shaheeda ta jinjina kai Kwantar mata da hankali Hibba ta cigaba da yi cikin sigar lallashi,har Shaheeda ta saki ranta,da za su tafi Haisam ya bata izfi sittin ɗin da ya fansar mata a hanyarsu ta zuwa jail ɗin Shaheeda ta yi farin ciki sosai,ya jadadda mata ta dage da addu'a,in sha Allah za'a yi nasara,ta tabbatar masa da in sha Allah zata yi addu'a *RANAR ZAMAN COURT* Kotu ta cika maƙil da mutane,kuma yawancin mutanen sun zo ne don ganin wacece wannan Roxy ɗin da ta firgita ƙasa ta tsayar da tunanin jami'an tsaro waje ɗaya,da ake tunanin wata babba ce ta a zo a gani?ko ƙarfin ƙwaƙwalwa kawai gare ta? tunda da yawan mutane har yanzu ba su santa a hoto ba Wasu kuma al'ummar Alhaji Sa'idu wada ne,da ya turo su su ga yadda shari'ar zata kaya,ya shaida faɗuwa ƙasa wanwar da zata yi, wanda ya alamta hakan a matsayin sakamakon butulcin da ta yi masa Yana sane da shiga maganar da BARRISTER HIBBA AIYO ta yi cikin case ɗin, wanda hakan na nufin zai iya zama ƙila wa ƙala,nasara ko saɓanin hakan a gare shi,don ya daɗe da sanin wacece BARRISTER HIBBA AIYO,wasu shekaru can baya sai da ta yi silar shigar abokinsa Alhaji Adam doguwa jail,kusan shekaru sha biyar yanzu kenan amma har yanzu bai fito ba A ɓangaren barrister Hibba itama ta je tare da tawagarta ta lauyoyi,duk inda ta wuce sai an dare an ba ta hanya cike da girmamawa,ko ba don kanta ba,ko don mijinta wanda ya kasance ministern lafiya a halin yanzu Babu jumawa aka kawo Shaheeda da take cikin matsanancin tsaro,dama tun can a tsarin doka bayan jami'an tsaro da lauyoyinta babu wanda ya isa a bari ya ganta #Nusy_bee Page 39 Ƙirjinta ya buga da ƙarfi lokacin da ta ga tarin jama'ar da suka halarci kotun da sunan sun je kallon shari'arta,take kanta ya sake kawo mata cewa za'a yi Shari'a da ita ne akan ana tuhumarta da safarar miyagun ƙwayoyi da kuma satar kuɗaɗen mutane ta yana(Yahoo),take ta ji ta muzanta sosai,bata taɓa jin tsoro da shakkar aikata wani abu ba sai yanzu,sosai ta ji ta shiga razani da ɗimauta, jikinta ya hau rawa sosai Ɗaga kai ta yi a sanyaye,hawaye suna kwantawa akan ƙwayar idanunta,caraf idanunta suka faɗa cikin na yayanta Muyassar,take ta ji wata kunya da bata taɓa ji ba,wai a gaban Muyassar wanda ya zame mata gata da duk farin ciki za'a tuhume ta da wannan gagarumin laifin! Magatakardar kotu ta gabatar da ƙara ta gaba, wadda ake tuhumar ROXY ko kuma Fatima Shaheeda da laifin safarar miyagun ƙwayoyi,danginsu cocain da ƙwayoyi,sai satar kuɗin al'umma ta yana da take yi Har cikin kanta ta ji wannan tuhumar da ake yi mata,tashin farko Ummeey ce ta faɗo mata a rai,ta fara tunanin ya zata ji idan ta ganta a wannan halin?tabbas bata yi mata adalci ba, kafin ta gama tunanin aka bayar da umarnin a kawo ta zuwa kusurwar tuhuma,babu musu ƴan sanda suka rako ta,ta sunkuyar da kai,har yanzu jikinta yana rawa,duk da jarumtar da ta aro Lawyern gwamnati ne ya fara miƙewa ya gabatar da kanshi,bayan ya gaida alƙali "sunana barrister Sulaiman Yusuf,ni ne prosecutor da yake ƙalubalantar wadda ake ƙara"ya koma ya zauna Barrister Hibba ta ɗaga kanta, cikin izza da take shigarta a duk lokacin da ta samu kanta a bakin aiki,ta miƙe a dake ta ce"sunana BARRISTER HIBBA IBRAHEEM AIYO,nice lawyern wadda ake ƙara" Alƙali ya ba wa lauyoyi damar magana, barrister Sulaiman ne ya fara miƙewa ya ƙarasa kusa da Shaheeda da kanta yake ƙasa,ya ce "kotu tana buƙatar jin ainihin cikakken sunanki" Bata amsa ba, kamar yadda bata motsa ko da kanta da yake sunkuye ba,har sai da barrister Sulaiman ya sake maimaita mata tambayar Kanta a ƙasa ta amsa"sunana FATIMA SHAHEEDA YUSUF MALIYA!" Take kotun ta ɗauki hayaniya sosai,sunan Yusuf Maliya da Shaheeda ta ambata a matsayin mahaifinta ya ba wa mutane da yawa mamaki,ko da yake akwai masu zargin Alhaji Yusuf Maliya shine mahaifinta,amma ya fito ya yi hira da ƴan jarida ya barranta kanshi da ita,har wasu suke ganin kamar tana amfani da sunansa ne don tabbatarwa,amma sai barrister Sulaiman ya ce"kina nufin ke yar Alhaji Yusuf Maliya ce?mamallakin MALIYA GROUPS OF COMPANIES?" Kanta tsaye ta amsa masa da faɗin "eh,kai tsaye ma na ce nice babbar ƴarshi" Barrister Sulaiman ya jinjina kai ya ce"dama haka na iya faruwa. To Malama Shaheeda!kotu tana tuhumarki da laifin safarar miyagun ƙwayoyi tsawon shekaru uku,da satar kuɗaɗe ta yana wato Yahoo, menene gaskiyar maganar?" Shiru ta yi da farko, jikinta a sanyaye, kafin ta ɗago a hankali suka haɗa idanu da barrister Hibba, Hibba ta jinjina mata kai alamun ƙwarin gwiwa,don haka ta fara zayyano bayani kamar haka"eh haka ne! Amma ba shekara uku bane, shekara ɗaya ne!" Shiru kowa ya yi yana kallonta da tsananin mamakin jin abin da ta faɗa, barrister Sulaiman ya ce"amma menene hujjarki ta cewa shekara ɗaya ne?bayan kowa ya san shekaru uku kika ɗauka kina aikata wannan laifin?" Shaheeda ta gyara tsayuwarta ta ce"shekara guda na ɗauka ina aikata wannan laifin saboda wata larura da ta same ni, wadda ya zamto bani da mafita sai hakan, tsawon shekaru biyun kuma nemana ake yi kawai ina guduwa,amma ba aikata laifi ba" Barrister Sulaiman ya jinjina hakan cikin tsantsar mamaki, kafin ya ce"amma kuma duniya ta shaida cewa kin cigaba da aikata miyagun laifukan,har ma ana kyautata zaton jami'an tsaro sun kama ki ne bayan tarko da suka yi miki, menene gaskiyar wannan maganar?" Ita kanta Shaheeda ta yi mamakin wannan ƙaryar da ta ji an yi mata,kuma zuwa yanzu ta sake tabbatar da maganar barrister Hibba da take ce mata ba don a ƙarfafa doka aka kama ta ba,sai don wani ƙudiri na dabam,don haka kai tsaye ta buɗe baki da niyyar magana,amma sai barrister Hibba ta riga ta "Objection ya mai shari'a! Barrister Sulaiman yana so ya ɗora ƙarfin zargi akan wadda ake tuhuma bayan ta musanta hakan,mai Shari'a ya kula da hakan"babu ja mai Shari'a ya yi masa gargaɗi,ya bayar da haƙuri sannan ya cigaba da tambayoyinsa Ya sake duban Shaheeda ya ce"kina da hujjar abin da kika faɗa? na cewa kin dakatar da duk wani aiki da kike yi a tsawon waɗannan shekaru?" Shaheeda ta jinjina kai ta ce"eh! Ina da hujja " Barrister Sulaiman ya ce"menene hujjarki?" Shaheeda ta ce"tun a lokacin da aka kama ni a Abuja na dakatar da komai,sai dai Alhaji Sa'idu Wada, tsohon minister a wancan lokacin ya buƙaci na cigaba da yi masa aiki,na fara na ɗan lokaci,daga baya da na ga na tara abin da nake nema,dama ba gaya maka akwai dalilin da ya sa nake yi,sai na daina komai To saboda na yi masa bore na ce ba zan cigaba da yi masa aiki bane sai ya sa aka fara bibiyata don a kama ni " Barrister Sulaiman da yake aika mata wani kallo ya ce"wanne Alhaji Sa'idu Wada kike nufi?" "Alhaji Sa'idu Wada dai wanda ka sani,kowa da yake nan wajen ya sani,wato tsohon ministan ilmi" Take waje ya kaure da hayaniya,don dama wasu mutanen suna zarginsa da aikata ɓarna,wasu kuma sun yi mamakin bayyanar sunansa a cikin maganar,sai da alƙali ya buga guduma sannan aka yi shiru, barrister Sulaiman ya ce"ko kina da shaidar hakan?"kai tsaye ta ce "Eh,na turawa lawyerna, barrister Hibba Aiyo evidence,zata nunawa kotu"ita kanta bakinta rawa yake yi ta ƙarasa, saboda bata san me barrister Hibba ta taka ba ta ba ta umarnin ta faɗi haka Alƙali ya buƙaci barrister Hibba ta fito,ta miƙe ta fito daga wajen zamanta,gaba ɗaya kallo ya koma sama,don an tabbatar da cewa barrister Hibba bata bari a yi nasara akanta tun tana matashiya,har zuwa yanzu da girma ya fara cim mata,ta taso ta dawo gaban alƙali ta fara magana "Ya mai shari'a,kafin na gabatar da hujjojin Shaheeda a gaban kotu zan so kotu ta ba ni dama na yi mata wasu ƴan tambayoyi"alƙali ya bata izini,ta rissina ta ce"na gode ya mai Shari'a "ta dubi Shaheeda ta ce"a bayananki na ɗazu kin shaidawa kotu cewa akwai dalilin da ya sa kika faɗa harkar safarar ƙwayoyi da Yahoo, shin za ki iya sanar da kotu wannan dalilin?" A hankali ta jinjina kanta, sannan ta fara ba da labarinta a hankali,bata dakata ba har sai da ta kai ƙarshen labarin, kafin ta kai ƙarshe kusan rabi da quarter da suke kotun sai da suka zubar da hawaye Bayan Shaheeda ta kai ƙarshen bayanin barrister Hibba, wadda ita zuwa yanzu ta daina kuka akan irin wannan case ɗin ta ɗauko laptop ɗinta ta danno wasu hotuna da Roxy da Alhaji Sa'idu Wada suke tattaunawa,har ma da CCTV footage da ta samu oga boss ya samar Mata na lokacin da Alhaji Sa'idu Wada yake tattaunawa da Roxy,ga bayanai nan raɗau sun fito,ga muryarshi ga hotonsa Tuni kotu ta sake kaurewa da hayaniya,mafi yawa suna tsinewa Alhaji Sa'idu Wada da suke ganin a matsayinsa na ministan ilmi abin da ya dace shine ya tallafi Roxy ta yi karatu ya daƙile wannan sana'ar tata,to amma bayan munin abin da ya nema a wajenta har ma ya nemi ya yi haramtacciyar tarayya da ita,hakan ya sa mutane suka fara tsine masa,da yawa kuma suka fara yabawa Roxy saboda yadda ta nuna kai tsaye cewa ba zata siyar da mutuncinta akan wani kuɗi ba Sai da alƙali ya buga guduma sannan aka yi shiru,ya ba wa barrister Hibba izinin cigaba da bayani "Ya mai Shari'a,abu ne sananne a nan cewa Fatima Shaheeda ta aikata laifukan da ake tuhumarta tabbas,kuma daidai ne ta fuskanci doka,amma kuma ya kamata a ce wanda ya yi silar faɗawarta ciki shima ya fuskanci doka Sannan ya mai Shari'a,duba da halin da Fatima Shaheeda ta shiga a rayuwa,muna roƙon wannan kotu mai adalci da ta yi mata rangwame,ko babu komai a ba ta wata dama a rayuwa" Kotu shiru ta yi,kowa yana jiran abin da alƙali zai ce game da shari'ar da ake kan gabatarwa, wadda take a cukurkuɗe, alƙali ya juma yana rubuce-rubuce kafin ya ɗago yana gyara zaman glasses ɗin idanunsa,ya dube su ya ce"kotu ta saurari hujjoji daga dukkan ɓangarori,kuma ta yi dubanta don yanke hukunci,amma an ɗaga shari'ar zuwa takwas ga watan gobe,wato nan da sati biyu kenan Kotu ta bayar da umarnin a cigaba da tsare Fatima Shaheeda ba tare da beli ba zuwa ranar, sannan ta bayar da umarnin a kamo tsohon ministan ilmi,wato Alhaji Sa'idu Wada,don tuhumarsa bisa ga laifukan da ake zargi ya aikata"daga haka ya buga guduma,mutane suka miƙe suna faɗin "koooootuuuuuu!!!" Daga nan jami'an tsaro suka fito da Shaheeda barrister Hibba ta tare su, Shaheeda ta ɗago kai a sanyaye ta kalle ta, Hibba ta yi mata murmushin ba da ƙarfin gwiwa,amma zuciyar Shaheeda ta karye, hawaye suka cika mata idanu, Hibba ta goge mata hawayen, cikin kwantar da murya ta ce"khairan in sha Allah daughter! Very soon za ki fita kin ji? Allah yana tare da mu gaba ɗaya,ki daina zubar da hawayenki a inda bai cancanta ki yi asararsu ba"Shaheeda ta jinjina kai a hankali, Hibba ta dafa kanta, sannan ta wuce ta bar wajen, jami'an tsaro suka wuce da Shaheeda zuwa motar da za su kai ta gidan kaso,duk da ƴan jarida suna ta jefo mata tambayoyi *NILE UNIVERSITY NIGERIA,ABUJA* Ɗan murmushi ta yi bayan sun kammala kallon yadda shari'ar su Shaheeda ta gudana, ƙawarta Hanan da take zaune kusa da ita suke kallon tare ta kalle ta ba tare da ta yi magana ba, tana murmushi ta ce"seriously Hanan I'm very proud of this lady, wallahi Abba ya yi asarar brainy girl irinta,ya kasa gane su Mommy da sauran matansa hassada suke yi masa na samun one in town irin aunty Shaheeda,i like her so much wallahi,ba ƙaramin daɗi na ji ba da aka ce ita ce wadda ta rinƙa jijjiga ƴan sanda,ko zuwa nan gaba na san sun gane cewa ba iyawarsu ba ce ta sa suka kama ta ba,ikon Allah ne kawai" Hanan tana dariya ta ce"gaskiya Na'ima ba ki da mutunci, Mommyn kike cewa tana yiwa Abba hassada?" "Let's keep joke aside Hanan,kin san wacece Mommy na, saboda yayan mamanki ta aura, which is our father,dukkanmu muna iya tuna yadda ta wahalar da dangin nan namu,da a ce mum ɗinku ce ta wahalar da mu kamar yadda mum ɗina ta wahalar da ku da ba mu isa mu zauna a waje ɗaya ba I'm very sure su Mommy na sune suka janyo Abba ya kori Aunty Shaheeda Kin san babban yayanmu Muyassar ya so ya aure ta,tun muna yara, Allah bai yi ba,su Mommy suka hana, suka aura masa wata matsiyaciya,for God sake Hanan na tsani yarinyar nan,bata da tarbiyya ko kaɗan,amma Mommy bata gani saboda tana sonta, shiyasa na zaɓi na koma wajen Mom ɗinki kawai na zauna,ko wajen Uncle Ismail (ƙanin babanta)" Hanan ta riƙe hannunta, cikin lallashi ta ce"Na'ima,duk lalacewar iyaye fa iyaye ne, ba'a taɓa fushi da su,sai dai a yi ta haƙuri ana nuna musu hanya, ba'a fito na fito da su,yin hakan kuskure ne,kuma ba'a gyara kuskure da kuskure,ki yi duba ga maganata please " Na'ima ta taɓe baki, Allah ya sani tana jin ciwon halayen mahaifiyarsu,mace mai tsananin son kanta da ƙyashi,tana jin haushin yadda take dakile Abba tana shigarwa Ummeey hanci da ƙudundune,mace ta gari, wadda a kowanne lokaci take sha'awar zama mai irin halayenta Daga nan Na'ima chanja topic ta yi,amma har yanzu a ranta tana jin Shaheeda ta yi daidai,kuma zata iya zama irinta,banda haka ma sai ta san yadda aka yi yayanta ya aure ta *ROCKY ESTATE,KANO STATE* "Ikon Allah!anan nake jin son zuciya, wadda hausawa suka ce ɓacinta"Hajiya Mariya ta dubi Nimra mai wannan maganar tana riƙe haɓa,ta ce"me kika gani?" Nimra cikin ɓacin rai ta ce"wannan shari'ar da aka canjawa ma'ana mana, wallahi ko kaffara ba zan yi ba duk abubuwan da aka gabatar ba haka suke ba,haka kawai an wani rage mata laifi,an shirya ƙarya da sharri an saka babban mutum kamar Alhaji Sa'idu a matsala? Gaskiya wannan yarinyar masifa ce,kuma in sha Allahu ba zata gama da duniya da lafiya ba"ta ƙarasa magana cikin ƙunan rai Hajiya Mariya da take kallonta ta ce"ke menene matsalarki da ita ne?" Nimra ta ce"ya Haisam ya damu da ita da yawa,bana son na zarge shi akan wani abu dabam, Allah Allah nake yi ta zo ta amshi ɗanta,ni da ban ga kamannin halfcast a tare da shi ba ma da na ce ɗan na Haisam ne,ta shiga rayuwarsa da yawa,babu wata criminal da ya yi chasing da nake ganin yana kallon hotunanta yana murmushi sai ita,why?duk saboda ta yi laifi ne ko me?" #Nusy_bee Page 40 Hajiya Mariya ta yi murmushi ta ce"oh Allah! Nimra meyasa abin da ya zama damuwa da wanda bai zama ba duka saka shi kike yi a ranki? Ba kya tsoron wani ciwon na zamani? Ki kwantar da hankalinki ki cirewa kanki damuwa,tunda ya zaɓe ki a matsayin macen da zai aura ai komai mai sauƙi ne Allah na tuba ko da a ce ya ce zai aure ta ne ke ba mace ba ce?ba ki san yadda za kiyi kissa irin tamu ta mata ki mayar da abin tarihi ba? Ni ba ki ga yadda nake zaune a gidan ubansa ni kaɗai ba?ko an gaya miki haka kawai a banza nake zaune?" Nimra ta jinjina kai, Hajiya Mariya ta ce"ko ke fa! Mace da ta isa bata taɓa yin hayaniya akan namiji,idan kika ga mace tana hayaniya akan namiji to kucaka ce" Nimra ta yi shiru tana jin huɗubar yayar Tata,kuma tana shiga kanta,a ranta ta ƙudurce tabbas sai ta koyawa Shaheeda hankali muddin bata fita sabgarsu ita da Haisam ba *HAISAM* Sun sake tattaunawa sosai shi da barrister Hibba,duk da ya ji relief na alamun cewa za su yi nasara a zaman kotun to amma ya ji babu daɗi da barrister Hibba ta tabbatar masa ko yaya ne zata yi zaman kaso,amma ganin babu wata mafita sai wannan ya sa ya haƙura Bai koma gida ba sai wajen ƙarfe takwas na dare,kuma kamar yadda ya saba yau ma sashen Nanny ya nufa Ya sha mamaki da ya shiga sashen ya ga Nimra a zaune tana kallon cartoon tare da su Amna,amma fa Amna ce a kusa da ita, Mubarak kuwa yana kusa da Nanny wadda take goge musu kaya zata jera musu a wardrobe Da fara'a ta fara gaishe shi da yi masa sannu da zuwa,ya amsa fuska babu yabo babu fallasa, Amna ta miƙe ta tafi da gudu ta ɗane shi,ya ɗaga ta ya sauke, sannan ya kira Mubarak,ya taso fuska babu yabo babu fallasa,ya ɗaga shi ya dire yana murmushi, kafin ya ce"abokina ya ne? Ka ci abinci kuwa?"Mubarak ya ɗaga kai, Amna ta ce"Daddy ɗazu ma ya yi kuka yana kiran mamana!mamana!!"ta faɗa tana kwaikwayon yadda Mubarak ɗin yake faɗa Murmushi Haisam ya yi,ya ɗauki Mubarak da yake kallonta,yana faɗin "abokina yanzu fa kai babba ne,ya kamata fa a ce ka daina rigima" Nanny ta yi ƴar dariya ta ce "tsokanarsa ƴar'uwar ta yi,shine dalilin kiran maman" Haisam ya harari Amna,ta sunkuyar da kanta da sauri,ya ce"wato kuka kike saka friend ɗin naki ko? Sai na ɗauke shi na mayar da shi tunda ba kya so" Da sauri ta ce"I'm sorry Daddy ina so"ya ce"Weldon! Sai ki daina tsokanarsa"ya kalli Mubarak ya ce"kana jin bacci?" Mubarak ya gyaɗa kai a hankali, Haisam ya ce"yawwa mu boy!mu je mu kwanta ko?"nan ma ya gyaɗa kai yana kwantar da kanshi a kafaɗar Haisam Abin ya yiwa Nimra ciwo sosai,ganin ko kallo bata ishe shi ba,sai ta wannan matsiyacin yaron yake,a ranta ta ƙudurci sai ta raba shi da shi su huta, tunda gashi yanzu ma ko ta yar cikinsa baya yi Har ya juya baya ta ce"Good evening yaya Haisam!"ya juyo ya ce"evening Nimra!"sannan ya kalli Nanny ya ce"Nanny na manta, Mubarak ya sha maganinsa kuwa?" Nanny ta ce"ai bana yi masa wasa ko kaɗan Alhaji,na ba shi tun ɗazu "Haisam ya yi murmushi yana sake rungume Mubarak ya ce"Weldon Nanny muna godiya sosai,sai da safe ko?"Nanny ta ce"Allah ya tashe mu lafiya Alhaji" Amna ta ɗaga masa hannu tana murmushi tana faɗin "Daddy Good night"ya ce"Good night angel"ta ce"Mubarak Good night" Kamar yadda Nimra ta yi zato sai kuwa ta ga Haisam ya ja ya tsaya yana murmushi yana kallon Haisam,ya ce"ka ce"mata good night "da farko kamar ba zai faɗa ba,amma sai ya ce"good night!"da yanayin gwaranci a maganarsa Dariya suka yi su duka banda Mubarak da Nimra, sannan Haisam ya fice daga sashen Yana fita Nimra ta kalli Nanny ta ce"Nanny yaron ba shi da lafiya ne?" Nanny cikin jimami ta ce"wallahi kuwa Hajiya! Yaro abin tausayi,wai ciwon asma,jiya da numfashin ya riƙe ai sai da na kusa faɗuwa,don na ɗauka barin duniyar zai yi" Nimra cikin fuskar tausayi ta ce"Allah sarki! Allah ya ba shi lafiya"Nanny cikin jimami ta ce"Ameen Hajiya! yaron abin tausayi wallahi,gashi sam ba shi da saurin sabo da mutane" Nimra bata sake magana ba,ta cigaba da kallonta, ƙarshe ma da ta ga Amna ta fara jin bacci ta raka ta ta kwanta sannan ta miƙe ta fice zuwa sashen Hajiya Mamie *MUYASSAR* Yana tsaye a jikin windown ɗakin da ya kama a katafaren hotel ɗin yana leƙen titin da yake bayan hotel ɗin,gaba ɗaya duniyar ta yi masa zafi,damuwa ta ishe shi sosai,a yanzu yana jin ba shi da wani farin ciki ko walwala sama da mallakar abincin ruhinsa wato Shaheeda,amma jiya a gabansa aka gudanar da wata zazzafar shari'ar da yake kyautata zaton cewa Shaheeda ba za ta fita ba, sai ta yi zaman kaso Sau uku yana zuwa don ganinta, amma abu ɗaya ake sanar masa shine babu wanda zai ga Shaheeda,daga jami'an tsaro sai lawyer ɗin ta, hakan ya sake tabbatar masa da case ɗin babba ne tun a wancan lokacin, wanda hakan ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba Duk wannan dambarwar ba ita ba ce ta dame shi kamar rashin damar auren Shaheeda, mafi girman tashin hankalin kuma shine rashin soyayyar da Shaheeda take yi masa, kenan hakan ya nuna cewa dakon wahala yake yi? Nooooo! Impossible ya san Shaheeda ko bata so shi ba yanzu zata so shi wataran Arfa ce ya faɗo masa a rai,wani baƙin ciki ya tokare masa maƙoshi tuna yadda Arfa take ƙare masa zagi shi da iyayensa don kawai tana taƙama ba zai sake ta ba, saboda umarnin mahaifiyarsa, yanzu gashi nan ya sake ta ɗin,ta je can ta shirya duk makircin da zata shirya,shi yanzu ma nan da shekara guda ba za'a sake ganinsa ba, don yan kwanakin da ya ɗauka babu Arfa a tare da shi har ya fara samun nutsuwa ya dawo hayyacinsa Kira ne ya shigo wayarsa,bai damu da ganin mai kiran ba ya ɗaga wayar,kamar yadda ya zata kuwa haka ɗin ne, Na'ima ce "Yaya!kana tare da Ni?" A hankali ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ce"ina tare da ke Na'ima,ya school?" "Yaya!ka kalli shari'ar su aunty Shaheeda kuwa?" Muyassar ya ja numfashi ya fesar ya ce"na kalla Na'ima,in fact a gabana aka yi komai,sai mun dage da addu'a sosai, don Shaheeda tana cikin gagarumar matsala" Na'ima ta yi murmushi ta ce"yaya kenan! Kana kallon Shaheeda a matsayin wadda ta faɗi,ni kuma ina kallonta a matsayin jarumar da ta jijjiga ƙasa baki ɗaya da kaifin ƙwaƙwalwa da fikirarta, wallahi ko a yau aunty Shaheeda ta bar duniya tarihi ba zai manta da ita ba" "Ke bana son shirme! Ba fa abin a zo a gani ta yi ba, ƙwayoyi ta siyar, sannan kuma Yahoo girl ce, menene abin alfahari a nan?" "Yaya yahoo ai na masu basira ne,Ni na yi mana,ko kai! Sannan abu ka gaba kar ka manta yaya, manyan ƙasa waɗanda ya kamata su tallafi rayuwarta da sana'ar yi da ƙwaƙwƙwaran ilmi su ne suka ba ta hanya,ko na ce suka yi amfani da ita don aiwatar da wannan muguwar sana'ar,a wannan lokacin ahalinta sun watsar da ita,sun nuna ba sa buƙatarta, not even her,ko ni idan na gamu da wannan trauma ɗin ban ce zan iya riƙe kaina ba, musamman da ya kasance kana jin tarihin da ta bayar ai,ta ce ta nemi aiki a kamfanoni,amma ko'ina daga mai neman takardu sai me nemanta,kuma ƙarin alfaharin da nake yi da aunty Shaheeda shine rashin siyar da mutuncinta,ta yarda ta amsa sunan criminal amma bata yarda a yaga mata rigar mutunci ba,yaya aunty Shaheeda ta dabam ce "Muyassar da ya yi shiru yana sauraren maganganun Na'ima da ya ɗauka shirme ya ce"na ji Na'ima,Ni dai sai anjuma kar ki saka ni ciwon kai da wannan surutan naki "ya kashe wayar yana jin ta tana ƴar dariya Sai kuma ya zauna yana nazarin maganganun ƙanwarshi Na'ima, ya tuna lokacin da Shaheeda ta dawo gida bayan rasuwar Arnold,da alamun nadama masu yawa a tare da ita,ga ciki,ga babu,amma hakan bai hana Abba ya kore ta ba, ba tare da tunanin a wanne hannu zata faɗa?ko wanne hali zata shiga ba? A ina ta cigaba da rayuwa?ta haihu?me ta haifa? tabbas ya tuna ƴan sanda sun fitar da rahoton cewa da ɗanta aka yi mata tarko, kenan wannan ɗan na Arnold ne kenan? Ya aka yi yan sanda suka san da zamansa da za su yi mata tarko da shi? A ina ta ajiye shi take kasuwancin nata?ko da shi take tafiya?ya dafe kai cikin ruɗewa, gaba ɗaya sabgar nan tana kulle masa kai, gashi an hana shi ganinta ballantana ya je ya ji dukkan bayanai daga gare ta,har da tambayar ina yaron ya shiga? Kwantar da kanshi ya yi a jikin kujerar da yake zaune ya lumshe idanu, tabbas Shaheedansa tana cikin matsala,amma matsalar da yake hangowa a gaba ta fi wadda ake ciki yawa *RANAR KOTU TA BIYU* A yau kam kotu ta cika ta tumbatsa fiye da zaman baya,kuma yawancin mutane dalilai biyu ne ya kawo su,na farko ganin hukuncin da kotu zata ɗauka akan Shaheeda,na biyu kuma ganin Alhaji Sa'idu Wada, kamar wancan karon, yau ma Muyassar ya samu zaman kotun, Hakazalika Haisam da tawagarsa Bayan an shigar da Shaheeda don fara zama,a can ta hango Oga boss da Azeema a cikin mutane,suna haɗa idanu da Azeema ta ga hawaye sun fara wanke mata fuska,ta yi murmushi tana girgiza mata kai An fara zama kamar dai wancan karon,an sake karanto gaɓar da aka tsaya a zaman baya, Shaheeda ta sake tabbatar da cewa eh lallai ta aikata, sannan alƙali ya buƙaci ganin Alhaji Sa'idu Wada,a nan yan sanda suka tabbatar da cewa ya bar ƙasar tun kafin a gama zaman baya, da alamu ma a shirye yake da hakan Hakan ya sa alƙali ya bayar da umarnin gani da kamu a duk inda yake, sannan ya duƙa ya cigaba da rubuce-rubucensa,kotu ta yi tsit tana jiran hukuncin da za'a yankewa Shaheeda, wadda a wannan lokacin da za'a tsaga jikinta bai zama lallai a ga jini ba saboda yadda ta daskare tana jiran ikon Allah, duk da cewa a yanzu ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali sosai sakamakon karatun alƙur'ani da take yi a yawancin lokuta Alƙali ya ɗago ya fara magana "kotu tana tuhumar Shaheeda da safarar miyagun ƙwayoyi,wanda ta amsa ta yi hakan da kanta, sannan tana tuhumarta da sata ta yana,wato yahoo,bayan ta yi hacking asusun mutane Don haka kotu ta yanke mata hukuncin shekaru bakwai a gidan gyaran hali bisa samunta da laifin safarar miyagun ƙwayoyi, rangwamen hukuncin ya samo asali ne saboda halin rayuwa da ta samu kanta,da kuma wanda ya zama shine mai alhakin hakan Na biyu kuma kotu ta yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan kaso bisa samunta da laifin satar kuɗaɗen mutane ta yana wato Yahoo, sannan kotu ta ƙwace dukkan abin da ta mallaka na dukiyarta da kadarorinta,idan bata yarda da hukuncin ba,tana da damar ɗaukaka ƙara zuwa kotun gaba nan da kwanaki talatin"daga nan ya buga guduma,mutane suka miƙe suna faɗin "koooootuuuuuu!!!!" Tirƙashi!!! (Yanzu wani wasan zai soma!!!" *Wannan shine ƙarshen book one,akwai ragowar chakwakiya masu ɗimbin yawa a gaba,ni kaɗai ce nake tunanin akwai wani abu tsakanin prisoner ɗin da wanda ya yi arresting ɗinta?😁baya ga haka shin ya rayuwar Shaheeda zata kwashe a prison tsawon shekaru goma? Ga Ummeey da ta kasance abar tausayi kuma wadda take cikin ƙunci da damuwa,shin damuwar tata zata tafi a banza ne ko zata samu sakamakon haƙurinta? Nice dai Nusaiba Ibrahim Rimi (Nusy bee)ku kasance da ni a littafi na biyu don jin yadda zata kaya Book one shine Free, Book 2 Paid ne both Whatsapp and Arewa pen,ga mai buƙata ya tura #500 kacal ta wannan account number 8125952284 Nusaiba Ibrahim Rimi moniepoint,sai a tura shaidar biya ta wannan number 08125952284,kada ku sake a yi babu ku,ina iyalan Roxy da na yallaɓai CSO Haisam ne? Sai na ji ku. #Nusy_bee