FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar marubuta Wannan kagaggen labari ne dani Autar marubuta na zauna na kirkire shi .Ban kuwa yi dan kowa da komai ba, idan ya yi kama da tsarin rayuwar wasu ma auratannn, tom ni dai kawai arashi ne mai kashe auren wawa.🎍 Editing d'in ma a wannan karan bai samu ba🙏 ________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Page 1 _5 SAUDIYA Dawowarsu ke nan daga asubiti , Najib da Ahmad tare da mahaifiyar su da bata da lafiya, eh tabbas wannan iyalin kana iya ganin tsantsar soyyayar mahaifiyar su , bama dai wannan ba tafkeken gidan da suka shiga ga wasu motoci a zube a harabar gidan . Gida Nigeriya ✔ "A duniya bani da burin da ya wuce na mallaki Zarah,tabbas rayuwata dan ke aka yi ta , wayyo Zarah , Zarah ina kaunar ki sama da dukkan ma'anar kalma ina miki san da babu misali , Allah ya bani ke matsayin matata habibty." Wani saurayi ne had'ad'ad'd'e mai kimanin shekaru 29 yake zayyano wannan kalamai yana daga kwance a kan gadonshi . Ba tare da ya sani ba mahaifiyarshi tana ta saurararshi , da abin ya ishe ta , ta fara kiran sunanshi "Kamal , Kamal." Sam bai ji kiran mahaifiyar tashi ba ya zurfafa cikin matukar kewar Zarah , sai da mahaifiyarshi ta sa hannu ta dungure 'kafar shi da ya jinginar jikin bango sannan ya dawo hayyacinsa . Murmushi ya yi kafin ya tashi zaune yana sosa 'keya "Mommy ina kwana ." Kamal ya fad'a yana sunkuyar da kai kasa "Bazan amsa ba mara kunya , tun yaushe na shigo d'akin , kana can kana zantukan hauka a kan wannnan yariyar ." Mommy ta yi maganar kamar mai shirin kaiwa d'an nata duka a Kamal mi'kewa tsaye yana ri'ke hannunta yana cewa, "Yi hakuri dan Allah mommy, wallahi bansan kin shigo ba haba masoyiyata uwata ta kaina." Mommy ta yarfe hannunshi daga hannunta cikin muryar saukakawa ta ce, "Ba shakka tun da ka mai dani kakarka , sai ka fito break fast." Tana gama maganar ta fita tana murmushi tare da godewa Allah da wannan yaro da ya bata . Shima bayanta yabi kafin ta 'bace masa suna isa teburin cin abinci Hajjiya ta zauna a kujerarta ta kusa da Alaji Mansur Kamal ma ya ja kujera dake tsakanin 'kannenshi biyu Nasir da Laila sannan ya zauna . Alaji mansur ne ya fara tashi daga karin kumallon bisa godiya ga Allah ya shiga ciki a wannan lokacin ne Nasir ya yi maza ya koma kujerar Alaji. Wani kallo mommy ta jefa masa tare da cewa ,"Me ya sa baka da kunya ne Nasir , ka raina kowa mene haka ne ." Sum-sum ya tashi ya koma inda ya bari yana cewa, "A yi hakuri mommy." Kamal dariya ya yi sannan ya dubi fuskar Nasir da duk babu annuri yana cewa, "Karka damu na gidana idan na yi aure d'akinka guda wallahi a gidana." Mommy ce ta yi dariya tana cewa, "Eh tabbas kuwa ya kashe auren ." Dariya laila ta kwashe da ita harda tuntsurawa, fuskar Nasir kuwa sam yaki sakinta Bayan Laila ta shanye dariyarta da 'kerrr ta dubi kamal tana cewa, "Yawwa Yaya Kamal ni fa ban ta'ba ganin Aunty Zarah ba." Kamal da jin maganar Laila ya wani yi mutuwar farin ciki a zaune yana murmusawa Ba tare da ya cewa Laila komai ba ya fara dunmiyawa tunanin Zarah. Iyalan gidan Alaji Mansur ke nan tsohon soja ,babban mutum mai magana guda . Yana zaune da matarshi Hajjiya Amina wato mahaifiyar Kamal , tare da d'ansu guda daya tilo shi ne Kamal, sai kuma Laila wacce ta taso a gidan tun tana karama sakamakon rasuwar mahaifiyarta 'kanwar Alaji Mansur. Sai Nasir wanda Hajjiya ce ta d'anko shi daga kauye tun yana sheakara 18 a wajen yayanta da suke uba daya.Ya dawo nan suna zama tare. Anan cikin wani katafaren gida kuwa yasha ban-ban da wancen suma dai suna zaune kan teburin cin abinci irin nasu na gayu suna karin kumallo . Da gani babu tambaya zaka gane wane mai gayya mai aiki mai wannan gida a cikinsu , sanye yake da jallabiya fara babu far'a a fuskarshi yana shan shayi Duk da kuwa tarin kayan abincin dake kan teburin bai d'auki komai ba , Daga karshe yaja dogon tsaki ya tashi ya bar wajen Wasu manyan mata ne fara da ruwan tarwad'a da suma suke zaune suka kalli juna , Yayin da kowacce taci gaba da cin abincinta. Gidan Alaji Mustapha ke nan , shima tsohon soja ne ,sannan babban aboki ga Alaji Mansur, sai dai shi Alaji Mustapha iyalinshi ba kamar na Alaji Mansur ba ne , kusan kullum 'bacin rai yake 'kunsa a wajen matansa . 'Ya'yanshi guda 6 ne wanda duk suna raye sun girma, guda uku suna nan Nigeria a kusa dashi , Khalid da Habib wanda su ne mazan , sannan sai Fatima wacce ita ce kad'ai mace da Allah ya ba shi . Hajjiya Binta da Hajjiya Rukayya, a halin yanzu su ne matan Alaji Mustapha, wanda kowacce tana da yaro guda daya Sai kuma uwar gidanshi matarshi ta farko kafin su rabu , Hajjiya Samira wacce ita ce mahaifiyar Fatima, sannan kafin Fatima tana da wasu yaran maxa su uku wanda kusan su ne manyan 'ya'yan Alaji Mustapha Amma a halin yanzu basa Nigeria, suna can Saudiya wajen mahaifiyar su ita kuma fatima tana gaban mahaifinta Duk da cewa Hajjiya Samira mahaifiyar Fatima bata gidan Alaji bata kuma kasar , hakan bai hana su Hajjiya binta cigaba da kishi da ita ba , Sakamakon yadda ta fisu 'ya'ya da kuma yadda Alaji yake yawan yabon ta har yau musamman idan yaga d'iyarta Fatima. Zan so kiran dukkan 'ya'yan Alaji Mustapha yanzu domin gabatar mana da kansu , sai dai duba ga tafiyarmu da nisa da kuma tsawon jiran da zami na saudiya su zo yasa na fara cewa daku Faruk shi ne d'an Alaji Mustapha na farko wanda yanzu haka soja ne a saudiya , sai kuma Ahmad wanda yake kasuwanci shima a can kusa da mahaifiyar su, sai Najib d'an jarida Sannan autar Hajjiya Samira Fatima wacce take nan Nigeria tana aikin lauya 🎓 Sannan Habib dan Hajjiya binta , soja ne , tare da Khalid dan Hajjiya Rukayya duk sojoji ne . Wannan su ne iyalan Alaji Mustapha. Gida ne na alfarma wanda ya gaji da had'uwa tabasss an zuba daula a wannan gida , domin gida ne da ake yawan misali da shi wannan gidan bana kowa bane face gidan Alaji Sale mashahurin mai kudi da yake da hanyoyin samu bila a dadin masha Allah Daga cikin falon gidan wata kyakykyawar halitta ce zubin karshen hutu take kwance kan d'aya daga kujerun alfarmar falon na farko Ga dukkan alamu dai chatin take , sai dai idanunta na kaiwa kan agogo tai sauri ta tashi ta shige wanka Babu jimawa ta fito tana zun'buro baki gaba , musamman ma ganin mahaifiyarta Hajjiya Sa'adatu ta shigo kamar kuwa yadda tai tsammanin jin mahaifiyartata zata mata magana haka taji . "To ke kuma lafiya Zarah kike fushi."? Hajjiya Sa'adatu ta tambaya " Mommy na gaji bana son suna asubiti da rana wallahi. " Zarah tai maganar kamar za tai kuka Kawai dariya Hajjiya ta yi mata kafin ta ce , "Wallahi wannan mitar ce bana so , shi ya sa kawai nake jiran ranar da zaki tafi gidan Kamal na huta ." Da jin haka Zarah taji wani shauki mai hade da kunya ya ziyarce ta , hakan ya sa ta nemi kofar dakinta da gudu ta shige Dariya Hajjiya Sa'a ta yi ta samu guri ta zauna , zaman ta ke nan sai ga Alaji Sale ya shigo , yayin da wasu samari kyawawa masu kama da Zarah suka biyo bayanshi Alaji Sale salisu duk wata hanyar samun kudi ba ya bari , haka ya d'ora yaranshi a kai , hakan ya sa arziki kullum gudana yake Babban d'anshi Mahmud, wanda ya yi nisa a kasuwanci , sai Zarah da tai karatu a kasar misira , wanda yanzu haka likitan zuciya ce , sannan d'aya daga cikin marubuta masu matukar hazaka da masoya Sai ’karaminsu Umar shima dai .... Anan cikin gidan Alaji Mustapha, farin ciki ya ishe shi sakamakon ziyarar Alaji Mansur da ya kawo masa Bayan sun ci abinci sun sha sannan suka fara hira suna ta'bo 'bangarori da dama Ana cikin hirar ne Alaji Mansur ya ce ,"Ni kam ya maganar matarka Samira ne ." Dariya mai cike da ya'ke Alaji Mustapha ya yi kafin ya ce ,"Ka ji ka Alaji da wani zance , ka ce dai tsohuwar matata mutuniyar kirki, ai wallahi na yi rashin mace ta gari kawai sai dai Allah ya maida alheri ,ka ga shekaru nawa da rabuwar mu amma tana zuciya ta." Cikin tausayi Alaji Mansur ya kalleshi ya ce ,"To Alaji Mustapha ni bama wannan ba , ya Fatima take akwai maganar da nake son yi a kanta ." Numfashi Alaji Mustapha ya aje kana ya ce ,"Fatima ai wallahi tana shan wahala , yarinyar nan ta girma ,tarbiya da mutunci ba a magana , amma duk da haka su Hajjiya Binta basu da abin wulakantawa kamar ita." Alaji Mansur ya ce ,"Shi ya sa na zo maka da wani zance Alaji domin kasan Fatima 'yata ce." Murmushi Alaji Mustapha ya yi yana cewa ,"Fad'a mini kai tsaye Alaji Mansur. " Haka Alaji Mansur ya sanar da Alaji Mustapha abin dake ranshi , nan take farin ciki da sabuwar kaunar juna ta rufe su , musamman Alaji Mustapha abin dai ba a cewa komai Lokacin da Alaji Mansur ya tashi tafiya , har bakin get wajen mota Alaji Mustapha ya rakoshi sa'ilin da yake cewa ,"A gaskiya na jima ban ji farin ciki irin wannan ba , ka gama mini komai Alaji, wannan shi ne abota , Allah ya bar zumunci." Cikin farin ciki shima Alaji Mansur ya fara cewa ,"Karka damu ai kawai mu fara shiryawa domin babu abin da zai lalata mana wannan zumuncin ,kawai Allah ya kaimu ranar ." Alaji Mansur ya karasa maganar yayin da driver ya bude masa mota ya shiga . Sannan sukai sallama da juna , driver ya tu'ka motar suka tafi . Fatima ce kwance kan gado tana kokarin yin bacci gefe guda ta kalli wasu curin takardu tana tsaki "Allah ka bani hutu , yanzu na dawo daga office, kaina ciwo yake wallahi ya kamata na yi bacci , ni koma ya jikin umma." Ta karasa maganar tana daukar wayarta domin kiran Ahmad Amma tana d'auko wayar sai ga kiran Najib ya shigo , babu jira ta d'auki kiran tana cewa ,"Yanzu nake shirin kiran Ahmad. " Daga can cikin larabci ya fara mata magana yana cewa, "'Yar Nigeria ya aiki ya Nigeria, daman mommy ce ta ce zaku gaisa." Murmushi Fatima ta yi , kana cikin yaren Hausa ta fara cewa ,"Aiki kalau kuma haka kasarku Nigeria tana lafiya , wallahi ina kewar ku." Najib ya yi dariya sannan ya canza harshe ya koma Hausa yana cewa, "To ya shari'ar ko ba a yi." Fatima ta yi ajiyar zuciya tana cewa, "Dan Allah ka ba mommy na wayar , ina matukar mutuwar son jinta yanzu." Najib ya yi dariya sannan ya bawa Hajjiya Samira wayar . "Assalamu alaikum ." Fatima ta amsa sallamar mahaifiyar tata cikin matukar kewar ta "Mommy fatan kinji sauki sosai wallahi ina kewar ki mamana." Murmushi ta yi sannan ta ce ,"Naji sauki Fatima, ai banso suka sanar dake bani da lafiya ba , sun d'aga miki hankali. " Fatima ta ce ,"Haba mama ke fa uwa ce a gare ni , bani da fatan da ya wuce ki samu lafiya , in sha Allah ciwon zuciyarki sai ya zama tarihi ." Hajjiya Samira ta ce ,"Fatima ke nan , to ya mutanen gidan , nasan zaman hakuri kike Fatima, aita hakuri wata rana sai labari ." A jiyar zuciya Fatima ta yi kafin ta ce ,"Babu wani zaman hakuri mommy, ni kawai kewar ku nake , kuma ina nan zuwa ." Hajjiya ta yi murmushi tare da cewa ,"Fatima ke nan nifa nasan ba rayuwar farin ciki kike ba kawai dai bakya son fada mini ne." Fatima cikin wayantar da zancen ta ce ,"Ni fa mommy gaskiya zaku gànni wajen shekara biyu fa banganki ba , sai dai video call, dasu yaya Faruk da Ahmad, ina aunty Murja ." Hajjiya Samira ta sanar da ita kowa lafiya kuma komai daidai Bayan sun gama wayar ne sai ga Murjanatu ta shigo wato 'kanwa ga Hajjiya Samira.... Yadda Fatima taji kewar mahaifiyar ta da yadda idan ta tuna yadda take rayuwa a gidan mahaifinta ya sa ta fad'a gadon nata ta fashe da kuka , kuka take mai gwanin ban tausayi abin ta Yayin da taji ana mata bugun kofa ne ya sa ta tashi da sauri tana share hawayenta , sannan ta bud'e kofar Hajjiya Binta ta gani tsaye tana kallonta wata harara ta jefawa Fatima sannan ta ce ,"Kin dawo daga office, shi kuma wanke-wanke da girkin daren wane zai mana ko so kike aiki ya kashe mu ne ." Ajiyar zuciya Fatima ta yi tana cewa, "Dama mommy yanzu nske shirin fitowa ." Hajjiya Binta ta juya tana cewa, "Ya dai fi." Sannan ta koma falo inda Alaji Mustapha yake zaune tare da Hajjiya Rukayya Fatima kanta yana matukar ciwo ta fito , tana nufo falo ta ga Alaji shima yana zaune ta nufi bangaren madafa wato d'akin girki , kafin ta sa 'kafa ta shiga taji muryar mahaifin nata yana kiran ta Hakan ya sa ta juyo ta nufi wajen shi , tana isa ta zauna a kasa cikin matukar tsoro da fargaba , domin tasan tunda ta ga wannan makiran matan nasa biyu to tabbas sun had'a ta da mahaifinta 'Tashi ki zauna a kujera ."Alaji Mustapha ya fad'a cikin takama Fatima ta aiwatar da umarninsa kamar yadda taji "Mene zaki a dakin girki ."? Ya tambaya cikin jiran amsa " Daddy zan yi abu ne ." Jin amsar Fatima ya sa Alaji Mustapha wani murmushin takaici yana dariya mai ciwo Yayin da kuma ya fara cewa ,"Fatima ke ce kawai Allah ya bani 'ya mace , hakan yasa koda muka rabu da mahaifiyar ki Samira ban bari ta tafi dake ba . Amma sai dai Allah ya jarabe ki da zama cikin azzaluman kishiyoyin uwa da basa kaunar ki ." Cikin mamaki Hajjiya Binta da Hajjiya Rukayya suka kalli juna Hajjiya Rukayya ta tari numfashin Alaji tana cewa, "Haba Alaji, duk kokarin da muke wa yarinyar nan baka gani , ai ko 'yar muce ....." "Yimin shiru." Alaji Mustapha ya katse ta cikin matukar fushi , sannan ya d'ora da magana "Duk kallon ku nake tarrrrr wallahi, Fatima tana shan wahala a hannunku matuka, amma na zuba muku idanu domin ganin gudun ruwanku , tsawon lokaci yarinyar nan ko sau daya ba ta ta'ba kawo karar ku ba . Amma dake baku da imani ko a jikin ku." Cikin huci Alaji Mustapha ya dubi kowacce a cikinsu yana cewa, "To daga yauuuu kar wacce ta sake saka Fatima aiki a cikin gidan nan , komai mene ne na haramta . Mene ne amfanunku , duk wacce baza ta iya ba ga hanya Allah ya tsare." A karo na biyu suka sake kallon juna Alaji Mustapha kam ya ci gaba da fad'an shi yana cewa, "Tsinke idan Fatima ta sake d'auka a cikin gidan nan zaku ga yadda zami daku , ai wallahi kawai shiru nake muku babu irin kissar ku da munafunci da ban sani ba tun lokacin Samira , Samira ta fiku komai kawai kaddara ce ta raba mu . To wallahi kun yi na farko kunyi na karshe , kun yi na marmari ya gundire ku , an yi walkiya na gama ganin ku , kuma ni da ku shege ya fasa ku tashi ku bani waje mutanen kawai." Zumbur suka tashi Hajjiya Binta na gajeren tsaki wanda Alaji bai ji ba Bayan sun fita Alaji ya yi ajiyar zuciya, yayin da Fatima ta kalli mahaifinta tana cewa ,"Dan Allah Daddy ka yi hakuri." Alaji Mustapha ya ce ,"Karki damu Fatima ba zaman lafiya suke so ba , Ke yarinya ce mai tausayi da hakuri kamar mahaifiyar ki .Allah ya yi miki albarka." Fatima ta amsa da ,"Amin Daddy. " Alaji Mustapha zama ya gyara yana kallon Fatima da niyyar fara sabuwar magana "Sannan kuma Fatima akwai al'amarin da nake son sanar dake , domin ina da tabbacin baza ki bani kunya ba." Ta ce ,"In sha Allah Baba. " Jin haka ya sa ya cigaba da cewa ,"Na yi magna da mahaifiyar ki , sannan na sanar da ita na tsayar da ranar auren ki." Cikin mamaki da tashin hankali Fatima ta kalli Alaji "Aure kuma Daddy." Cikin mamaki Ya kalleta cikin sake jaddadawa ya ce ,"Eh Fatima aure , baki da mahaifin da ya fini , kuma zan yi domin farin cikin ki , duk inda zan shiga in fita domin sama miki farin ciki shi ne burina Fatima, kuma zan shiga dukkan hatsari domin baki kariya, wannan shi ne za'bin da na miki a matsayina na mahaifin ki Fatima. " Ya yi shiru yana jiran Fatima ta ce wani abu Jin bata ce komai ba ya sa shi cewa ,"Baki ce komai ba Fatima. " Murmushi ta yi sannan ta d'ago kai tana cewa ,"Daddy ni fa 'ya ce a gare ka , na yi imani kana son farin ciki na , ka yi mini komai Daddy, wallahi na amince da wannan auren har cikin zuciya ta." Wani abu Alaji Mustapha yaji ya takure masa ran sa na farin ciki da matukar tausayin Fatima Cikin ajiyar zuciya ya fara sabuwar magana ,"Ban yi zaton abin dana shirya zaki kar'ba ba , ban yi zaton farin cikin da nake hangowa zan samu ba ." Kawai Alaji kuka ya fashe dashi cikin wani yanayi mara dadi Hakan yasa Fatima tashi tsaye cikin tashin hankali tana cewa, "Dan Allah ka dena kuka , Baba ka haifa ne mene amfanina idan ban share maka hawaye ba kawai ka dena kuka dan Allah na roke ka." Ajiyar zuciya ya yi mai zafi sannan ya share hawaye ya dubi Fatima "Dole na yi kuka Fatima, domin a wannan zamanin akwai wahalar samun 'ya kamar ke, Allah ya yi miki albarka ya sa ki ciki da Kalmar shahada." "Amin ya Allah Daddy." Abin da fatima ta fad'a ke nan Kallon shi tai cikin kunya da son jin amsa ta ce ,"Da waye za ai Daddy. " Sai da ya yi mata murmushi ya gyara zama kana ya ce ,"Zumunci mai kyau Fatima zamu kasance har a aljanna tare , Yaron Alaji Mansur wato Kamal. " Dauuuuuu Abin da zuciyyarta ta fad'a ke nan , tasan dai da cewa Alaji Mansur guda daya ne kuma haka Kamal shi ne d'anshi wanda ta sani Murmushi ta yi kawai ba tare da cewa komai ba domin karta 'batawa mahaifinta yanayin da yake ciki "Allah ya faran ta maka Baba ya cika muradan ka." "Amin Fatima ki fara shiryawa a sanarwa ga duk wanda ya dace , sannan kamal din yana nan zuwa." Wata zabiya ce ta rad'o sallama cikin falon , hakan ya sa maganar tasu ta dakata Sa'arr Fatima ce ta shigo gidan cikin shiga da zamu iya cewa matar aure ce Nan ta durkusa suka gaisa da Alaji cikin ladabi da biyayya . Sannan su kai cikin daki da Fatima Bayan sun gaisa Fatima ta kwanta kan gado kamar mai shirin bacci hakan yasa kawar tata mai suna Fiddausi ta ce ,"Fatima ke nan hala dai kina da damuwa." Sai da Fatima tai wani irin kashe idanu tana kallon Fiddausi sannan ta tashi zaune tana cewa, "Rasss nake kawata , kawai dai ina sanar dake mun kusa shigowa sayun ku." Ta karasa maganar cikin kasalalliyar murya Dariya Fiddausi ta yi tare da cewa ,"Kina nufin fa aure ke nan ." Nannauyar ajiyar zuciya fatima ta aje tana cewa,"Kwarai kuwa nan da wata guda ma." "Abin mamaki wannan aure bakatatan haka Fatima, amma dan Allah waye angon." Murmushi ta yi kafin bata amsa cikin nutsuwa Fatima ta fara cewa ,"Na shirya tunkarar kaddarata ko wacce iri ce , bani da damuwa ko fargaba Fiddausi, duk yadda rayuwata ta juya mini zan yi abin da ya dace ." Ta aje maganar tana kallon Fiddausi, sannan ta d'ora da cewa ,"Kin san dai abokin baba Alaji Mansur to d'ansa ." Cikin mamaki matuka Fiddausi ta kalli Fatima "Wai kamal kike nufi ."? Ta jefa mata tambaya da mamaki Dariya Fatima ta yi , daga bisani ta ce ," Ke ma dai kinsan ba shi da wani d'ah banda Kamal. " "Tabbbbb! Jan aiki kika d'auko ki ce ." Fiddausi ta fad'a tana ri'ke ha'bar ta Bata jira cewar Fatima ba ta cigaba da magana ,"Wannan gayen da kowa yasan yarinyar da yake so Zarah Sale .Wannan yarinyar da suke da uwar kudi da kadarori , sannan gata marubuciya mai masoya , kuma likita ce fa.Me ya kai ki ke kuwa Fatima ga Kamal. "? Tsaki Fatima taja najin haushin kalaman kawar tata hakan ya sa ta fara cewa ," Ke kika san wata Zarah Sale da kike karanta novels, amma koma wace ita , ni Fatima na tabbatar baza ta fini komai ba , kudin banza Fiddausi, muna da kudi muna da komai , dan haka shima Kamal d'in ko ya yake santa shi ya sani ga zabin iyayensa ." "Babbar magana." Cewar Fiddausi "Ai ko dai da kina karanta novels zaki san Zarah sale Salisu.To wannan aure ni dai Allah ya nuna mana ." "Haka za ki ce kawai." Fatima ta fad'a tana hararar kawar tata. 07040805269 WhatsApp only Alkalamin Autar marubuta ne . FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta ________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing❌ Page 6 & 7 Washe gari Karin kumallo suke cikin hira da farin ciki Hajjiya Sa'adatu kawai abincinta take ci ba tare da tana shiga hirar 'ya'yan nata ba . "Alhamdulillah yau ba aiki sai zaman gida ." Zarah ta yi magna da farin ciki tana gyara zaman Bluetooth d'in dake kunnenta Umar ne ya ce ,"Hmmm aunty Zarah ke nan , kwana biyu kin dena rubutu." Wani kallo ta jefa masa tana cewa ,"Yanzu na fi bawa gidan television d'in mu muhimmanci , dah ni za su tura Dubai wallahi na 'ki zuwa." Mahmud kawai murmushi ya yi , sannan ya kalli Mommy yana cewa ,"Yau babu dadi breakfast Daddy ba ya nan ." Sai a lokacin Hajjiya ta d'ago kai tana cewa, "Yau ai sammako ya yi yana gidan gona." Sannan ta kalli Zarah tana cewa, "Ya yi mini magana a kan ki da Kamal ya ce ki masa magana a yi a wuce wajen babu amfanin 'bata lokacin." Murmushin ya'ke Zarah ta yi tana kallon 'ya uwan nata Yayin da sukai mata murmushi suma tabbas wannan rana Zarah ke jira ita da Kamal. Haka suma gidan Alaji Mansur suna zaune suna jiran fitowar Alaji domin su fara cin abinci "Laila ki temake ni ki mini guga dan Allah, kin ga na kusa komawa makaranta." Cewar Nasir Wata harara Laila ta buga wa Nasir tana cewa ,"Hmmm mommy kin ji shi yanzu fa ya gama cewa bani da amfani , to wallahi bazan maka ba." Hajjiya ta kwashe da dariya kafin ta ce ,"Ai gaskiya kawai aure zan had'a ku na huta , kuje can ku 'karata.Shikenan tuwo na mai na ." Nasir Cikin jin haushin maganar da Laila ta fad'a masa ya ce ,"Tabb mommy, ni me zan da wannan yarinyar gata mummuna Allah na fita kyau tabb , waye ma zai aure ki." Sai a lokacin Kamal ya yi dariya yana sake baza kunne yana sauraran hirar tasu , lokacin guda kuma yana tunanin idan zai fita company zai biya ya ga Zarah. A ajiyar zuciya Laila ta yi sannan taja tsaki tana kallon Nasir, "Ni wallahi gara ma ka koma makarantar na huta ." A lokacin Alaji Mansur ya fito cikin farin ciki ya samu guri ya zauna Haka zalika suma duk sun kula da irin wannan gagarumin farin ciki da ya ke ciki Bata abinci yake ba ma shi magana ya fara kamar haka ,"Gaskiya na ji dad'in ganin du duk anan domin akwai magana mai daraja da muhimmanci da zami ko na ce da zan sanar daku ." Kamal ya kalli mahaifiyarshi cikin murmushi, haka Nasir ya kalli Laila Mommy ce ta ce ,"Ai ni Alaji tun jiya da kaje gidan Alaji Mustapha na kula da wani farin ciki da kake , na ce mene ka ce kawai ni ma na gode Allah na yi murna bayan baka fad'a mini komai ba ." Wata dariya Alaji Mansur ya ke ce da ita Hakan yasa duk su Nasir suma dariya "Daddy dan Allah ka fad'a mana mene wannan farin cikin ." Cewar Laila Alaji Mansur ya kalli Hajjiya yana cewa ,"Wato Hajjiya ina d'aki yanzu, sai Alaji Mustapha ya kirani , to naji dadi sosai yadda Fatima ta nuna masa ya isa da ita , wato Fatima ta amince da auren Kamal kun ji dai abin farin ciki. " Dauuu dauuu kowa yaji a cikin zuciyarshi, duk suka canja yanayi zuwa rashin fahimtar maganar Alaji Babu wanda ya ce dashi komai , ya cigaba da cewa Hajjiya, "Wato kin san mun yanke shawarar auren Kamal da Fatima." A karo na biyu zukatansu suka sake shiga rudani ,"Wai wanne Kamal kake magana ne Alaji. "? Hajjiya ta yi tambaya da mamaki " Ahhhh kin jiki fa , akwai wani Kamal bayan wannan. "Ya nuna kamal da ranshi yake a rikice da matukar tashin hankali " Ai mun shirya tsaf ni da Alaji Mustapha domin samun cikakken zumunci."Alaji ya kara musu bayani Kallon juna suke da matukar mamaki , Kamal dauriya ya yi yayin da kanshi yake matukar sara masa ya ce ,"Daddy wai Zarah kake nufi ko Fatima. "? Murmushi Alaji ya yi yana cewa," Fatima dai 'yar Alaji, amma ai zaka iya kiranta da zaran idan haka kake so , daman an ce fatimatuzzahara'u." A take Kamal ya sake jin kanshi ya matukar sara masa idanunsa sun ciko da ruwa "Haba Alaji, wacce irin Fatima kuma , yaron nan fa Kamal Zarah yake so 'yar Alaji Sale , amma ka zo kana wata magana kuka." Mommy ke nan Lokaci guda Alaji Mansur ya fusata yana cewa, "Ni bansan wata maganar Zarah ba , Fatima na sani kuma ita na za'ba." Ya juya ya kalli kamal dake cikin matukar rudani yana cewa, "Karka yadda ka nuna mini ban isa da kai ba , mene ai bun Fatima da zaka na kira mini wata Zarah, to wallahi Kamal ni ne ubanka , kuma ba a canjawa tuwo suna , mun tsaida ranar auren ku , ban yi maka dole ba , idan kana da hankali zaka yi abin da ya dace ." Yana gama maganar ya tashi ya fita cikin fusata Wasu hawaye suka zubowa kamal masu zafi ,kafin wasu su dire wasu na biyo bayansu Laila da Nasir suka kalli juna da tashin hankali, Hajjiya ma haka taji wani ba'kon yanayi . Tun da Fatima ta amince da auren Kamal, Alaji Mustapha duk ya canza mata farin cikin matukar gaske , domin har sabuwar mota Alaji ya canza mata Lokacin da 'yan uwanta suka kirata video call, nan suke bayyana mata irin shirye-shiryen da zasi a wannan biki , zasi shagali sosai Ita dai Fatima tana fatan auren Kamal alheri ne a gareta , ba samuwar wata sabuwar kaddarar ba . Lokacin da dare ya yi Alaji Sale da Mahmud Umar duk suna zaune a falo hadda Hajjiya suna hira suna kallo A lokacin Zarah ta shigo da gudu kanta babu d'ankwali ta fad'o jikin Hajjiya tana wani rurucewa da kuka . Kafff hankulansu ya tashi tsaye da jin irin wannan kuka na Zarah Hajjiya ta d'agota a jikinta , amma Zarah ta'ki tashi ta fuskanci kowa kawai kukanta take shekawa "Mene ne ya faru ne haka."? Alaji Sale ya tambaya da tashin hankali Haka suma Mahmud da umar duk sun 'kagu su ji dalilin wannan kuka na yayarsu da basu ta'ba ganin ta a irin wannan yanayi ba " Mene ya ke faruwa ne Zarah." Mommy ta sake tambaya yayin da ta yi nasarar d'ago Zarah Idanunta sun yi jajir yayin da wasu hawayen suke turereniya Zarah taso fara magana amma wannan kukan ya sake shan kanta . Cikin kokari ta d'ago tana kallon furkar mahaifiyar ta tana cewa ," Mommy amana ta yi 'karanci , mutane babu mommy Kamal aure zai ." Wani tashin mamaki suka ji ya bugo musu zukata Wasu sabbin hawaye suka sake zubo wa Zarah Ta ci gaba da magana cikin takaici da bacin rai tare da hawayenta ,"Mommy nan da wata daya , wata zai aura ba ni ba , baban shi ne ya sama masa mata." Ta karasa magna tana sake shiga wani hali tana kwanciya a jikin Hajjiya "Innalillahi, kamal din ne ya ce miki zai aure? Kamal din ."? Mommy ta yi magana cikin mamaki tana kallon Alaji sale Alaji sale a wannan karan ma dai bai iya cewa komai ba Har Zarah ta sake fashewa da kuka tana cewa," Mene ya sa haka mommy, me ya sa Kamal zai barni , shi ne fa ya kirani yake fadan zai yi aure, shi ke nan na rasa shi mommy. " Ta aje maganar cikin wani gwanin ban tausayi na kuka A lokacin Alaji sale ya kalleta yana cewa ,"Ba za ki rasa shi ba ."... Alkalamin Autar marubuta ne Zasu same ni a WhatsApp a wannan number 07040805269 FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar marubuta ________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing❌ Page 8 & 9 Diff Zarah ta yi ta d'ago tana kallon Alaji sale, Duk hankalinsu ya koma kan Alaji da jin wannan magana "Mene ka ce daddy." Zarah ta tambaya cikin jajayen idanunta na kuka Alaji cikin kwanciyar hankali da nuna kauna ga Zarah ya fara cewa ,"Allah ya halicceki da kyau, sannan ya mahaifinki da mahaifiyar ki suna tare dake , sannan ga 'yan uwan ki masu baki farin ciki ." Jikin kowa ya yi san yi yayin duk suke sake kasa kunne domin sauran mahaifin nasu . Haka Alaji ya cigaba da cewa ," Baki ta'ba neman abu kin rasa ba , amma ga shi a yau kina kuka cikin bakin ciki sakamakon Allah ya jarabce ki da rashin Kamal. " Zarah ta sauke kanta kasa cikin wani yanayi Alaji sale ya ce ,"Idan Allah ya rubuta Kamal mijinki ne , to dole zaki aure shi , matukar Kamal yana son ki , komai daren dadewa baza ki bar zuciyarshi ba ." Zarah ta dago ta kalli mahaifinta cikin sabon hawaye Ba tare da jiran komai ba , ya cigaba da cewa ,"To sai mene idan Kamal zai auri wata !Abin da nake son ki sani , karki yadda duniya ta rudeki , karki yadda kibi rudin zuciyarki , wannan lamarin kar ya shigar dake wani hali kiji kin tsani Kamal ko matar da zai aura , sannan matukar kina son shi ko mata 3 ya yi ya ce zai aure ki cikon 4 karki yadda ki dubi wannan matan a gabanki domin zaki halaka , ni a matsayina na mahaifinki duk san da Kamal ya zo min da zancen auren ki , matukar kina son shi to babu makawa zami farin ciki , kuma mu yi shagali sosai na bajin ta da nuna babban gida ne mu." Ajiyar zuciya Zarah ta yi tana jin farin cikin kalaman mahaifinta Hakan ya sa ta fara magana ,"A gaskiya na gode Allah da wannan a hali daddy, matukar tsanar Kamal naji ta rufe ni kafin wannan maganar taka Na gode daddy, ina fatan na zamo tamkar haka , yayin da damuwa ta samu 'ya'yanmu mu juya musu kaddararsu zuwa nasarori ." Mahmud ya yi ajiyar zuciya yana cewa, " Gaskiya ne Zarah, babu iyaye kamar namu mu godewa Allah, sannan ina baki shawara ki d'auki maganar Daddy, domin amfaninta yana tare dake duniya da lahira ." Murmushi Zarah ta yi tana kallon yayan nata tana cewa, " Daddy, mommy na rungumi kaddara , amma ina san ku sani ina san Kamal, ina bukatar addu'oinku idan kamal alheri ne gare ni Allah ya bani , idan aka sin haka ne Allah ya nisanta mu dashi." Ta karasa magana tare da radadin rashin Kamal hadda wasu hawaye a idanunta A lokacin hajjiya ta ce ,"To alhamdulillah Allah ya muku albarka." Umar ya ce ,"Amin mommy. " Zarah ta koma ta kwanta kafar Hajjiya tana ajiyar zuciya, lokaci guda kuma tana yiwa Umar murmushi yayin da suka had'a idanu . Fatima kuwa tun da gari ya waye babu wani sukuni a tare da ita domin yau Kamal zai zo , haka kawai take jin kamar Kamal zai zo mata wulakanci ne , haka dai ta runga zullumi a karshe ta shirya tunkararshi da dukkan irin fuskar da zai zo mata . Hajjiya Amina ce zaune a dakin Kamal, yayin da Kamal yana tsaye yana sanya agogo bayan wata hula da ya sanya wacce ta hau kan fatar shi sosai , sannan ya matsa bakin mudubi yana fesa turare. Yana gamawa ya juyo ya kalli mommy yayin da take masa murmushi Murmushin ya'ke ya mata yana cewa, "Mommy zan tafi Allah ya sa ina zuwa wannan yarinyar ta ce ban mata ba da naji dad'i wallahi mommy." Hajjiya Amina dariya ta yi tana kallon yaron nata wanda duk ya rame ya yi wani dogon wuya tana cewa ,"Banda abinka Kamal, ai ba yarinyar da zata ganka ta ce baka mata ba , ni dai kawai abin dana ke so da kai , kar ka yadda wani abu ya faru wanda ran mahaifinka zai 'baci, ka yi hakuri komai mai wucewa ne ." Kamal ajiyar zuciya ya yi kamar mai shirin kuka yana cewa. "In sha Allah Mom bazan baku kunya ba , ko dan girman darajarku , zan rike wannan kaddarar na tunkareta a duk yadda ta zo min , zan nunawa daddy ya isa dani mommy." Hajjiya wani dadin gaske taji dajin zancen Kamal Hakan ya sa ta bud'i baki tana cewa. "Allah ya yi maka albarka, wannan umarnin na mahaifinka shi ne farin cikin mu." Cikin wani yanayi Kamal da matukar tausayin kanshi ya ce. "Yanzu mommy shi ke nan na rasa Zarah." Ita ma Hajjiya wani matukar tausayin d'an nata taji ya kamata lokaci guda, amma cikin kwarin gwiwa ta ce dashi .In ji waye Kamal, Allah ne yasan mene ya tsara maka , rabon kwad'o baya hawa sama Kamal, ko ya hau sai ya sakko .Dan haka karka damu ." Kamal ko kad'an zancen Hajjiya bai kwantar masa da hankali ba , haka suka fita daga d'akin suka nufi babban falon yayin da mommy take kara ja masa hankali a kan abin da ya dace . Suna karasawa sai ga Nasir da Laila sun fito daga 'bangaren Alaji Mansur Nasir sanye da wata babbar jaka a bayansa ta 'yan makaranta. Mommy ce ta ce ,"To har ka fito Nasir ."? Nasir ya ce ." Yes mommy na fito , dan Allah a cigaba da mana addu'a domin satin biyu zami mu fara jarabawa .Kuma kin san mu manyan yarah idan muka fad'i akwai damuwa mommy. " Hajjiya ta'be baki ta yi tana cewa. ."Ka ga Nasir , kawai ka dage da abin da ya kai ka , kuma wallahi ina jan hankalinka kan yaran nan marasa tarbiya 'yan shaye-shaye , matukar kana so gobenka ta yi kyau dole ka barsu ." Kamal ya girgiza kai alamun haka ne , sannan mommy ta cigaba da cewa ."Yanzu dai kamar wannan yaron na gidan Alaji Sani ai ba aboki ba ne ." Hajjiya Amina mamaki ne ya rufe ta gani dajin yaron da take magana ya shigo kai tsaye cikin falon "Ina kwana maman Nasir ." Abokin nashi ya fada cikin harshen turanci da muryar shaye-shaye idanunshi jajir dasu "Haba Abba Alaji ya zaka shigo babu sanarwa." Nasir ya fada cikin takaici da haushi Tsaki Kamal ya ja yana cewa, "Kai me ya sa baka da hankali ne , to wallahi duk ranar da ka sake zuwa gidan nan iya ka cinka can waje , zan matukar 'bata maka rai wallahi." Abba Alaji ya sunkuyar da kai yana 'kun'kunai "Ka fita waje ka jira ." Kamal ya sake fada cikin haushi Abba Alaji ya bud'e kofa yana kallon Nasir da cewa . "Ka yi sauri fa ka fito ." Sannan ya fita Tsaki Hajjiya ta yi tana fad'in ."Kun gani ba , Allah ya kyauta." Nasir ya yi ajiyar zuciya yana cewa. "Ku yi hakuri mommy." Kamal ya ce ."Ba dai wata matsala ko ." Ya yi maganar yana kallon Nasir Nasir ya ce. "Babu komai Yaya Kamal na yi sallama da Daddy, zamu tafi ." Nan su kai sallama baki dayansu , sannan Nasir ya fita ya samu Abba Alaji sannan suka d'auki hanyar Ibadan Laila ita ma ta shige ciki, yayin da Kamal yake cewa da mommy. "Bari na tafi mommy." Mommy ta ce ."To Allah ya tsare hanya , a dawo lafiya." "Amin mommy." Kamal ya fada yana fita waje Yana fita yaje bakin motarshi ya tsaya cakkk , sannan ya yi ajiyar zuciya yana cewa. "Kai rayuwa karki mini haka mana , amma ba komai ta bakin mommy din wataran sai labari komai zai wuce , duk abin da hakuri bai baka ba tashin hankali ba zai kawo shi ba. " Ya shige motar tashi yana ajiyar zuciya, yayin da mai gadi ya bud'e masa get . Bayan Kamal ya isa kofar gidansu Fatima mai gadi ya bud'e masa get , yayin da ya shigo ya yi burki ya fito Mai gadi da gudu ya taho yana cewa. "Barka da zuwa Alaji, sannu da zuwa bakon barrister fatima." Cikin mamaki da duhun maganar da mai gadin ya yi Kamal ya nanata cikin ranshi ."Barrister kuma ." Sannan ya kalli mai gadin yana cewa. "Wato kasan da zuwana ke nan ."? Mai gadin da shegen surutunshi ya kuma cewa ." Ai yalla6ai bani da aiki sai bacci , sai a zo ai ta hon bana ji .Hakan ya sa barrister fatima ta sanar min da zuwanka domin kar nai bacci , domin tasan hali na ."Ya karasa magana yana yankare baki yana dariya. Shima Kamal dariyar ce ta kamashi , sai dai ya kasa gane mene ya sa ake kiranta Barrister Daga can gefe Kamal yaji murya tana cewa. "To sarkin surutu Haruna mai gadi ." Kamal ya juya da murmushi dan ganin waye Alkalamin Autar marubuta ne. FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar marubuta ________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing❌ Page 10 & 11 Habib ne ya karaso cikin far'a suna gaisawa da Kamal Yayin da mai gadin yake masa kirari ."Ka ga daya daga cikin sojojin mu , ka ga jarumi Habibu dan Alaji. " Habib ya ce ."Dan Allah Haruna ka tafi ." Kamal yana dariya Sannan mai gadin ya koma bakin aiki yana sake musu kirari "To ya na same ku bro ."? Kamal ya fad'a yana kallon Habib cikin farin ciki A lokacin Khalid ya shigo yana tura kofa , yayin da me gadin shima yake masa kirari Kai tsaye Khalid ya nufo wajensu Kamal yana cewa." Ahhh Habib bako ka yi ne ." Yayin da yake mikawa Kamal hannu suna gaisawa "Kaji ka Khalid, tom sirikin mu ne ." Habib ya bawa Khalid amsa Cikin mamaki Khalid ya ce ."Au haba dai , ai wallahi ban gane shi ba." Ya sake mika hannu suna gaisawa Wani farin ciki Kamal yaji ya rufe shi da ganin 'yan uwan fatima Haka sukai masa jagora har cikin babban falo suka zauna Nan Habib ya kawo musu kayan motsa baki , kafin kace komai kuma hira ta 'barke tsakaninsu Wajen minti biyar ke nan su kamo can su kamo can cikin farin ciki , kamal duk sai yaji ba abin da yake damun shi Lokacin da Habib yake basu wani labari suka ke ce da dariya , sai ga Alaji Mustapha ya shigo falon Girgiza kai ya yi alamun mamaki yayin da ya fara takowa wajen su ya fara cewa ."Sannunku jarumai , yanzu dama Kamal d'in ne ya zo amma kun sa shi a gaba kuna ta wani dariya , maimakon ku sanar da fatima amma kuna ta masa surutu." Kamal ya zube kasa yana gaida Alaji Mustapha cikin girmamawa Bayan sun gaisa Alaji ya ce ."Yi hakuri fa Kamal, wai nan duk sojoji ne , amma babu kai ." Dariya ce duk ta kusan kwace musu dajin zancen Alaji Habib ya mi'ke yana cewa. "A yi hakuri Daddy bari a kira masa Fatiman." "Wacce Fatima kuma zaka kira , yanzu lokacin kun cinye shi , dan haka ku tafi masallaci ku dawo tukun ." Habib ya ce ."To Daddy bari muje kafin mu rasa sallar ." Alaji ya dubi Khalid da Habib yana cewa. "Saura idan kuka dawo ku sake sashi gaba kuna zance, kuna dawowa ku sanar da Fatima." Khalid ya ce ."In sha Allah Baba. " Sannan suka wuce suka d'auro alwala suka tafi masallaci . A 'bangaren Zarah babu abin da ya canza , domin yanzu tana tafe cikin motarta ta nufi asubiti, tana zuwa babu jira ta fara duba marasa lafiya . Bayan su Habib sun dawo daga masallaci, suka shiga ciki suka kira masa Fatima, yayin da suka shige ciki. Minti biyar ke nan Kamal yana zaune, kafin daga nan yaji sautin tafiya daga saman bene , wanda hakan ya tabbatar masa da cewa wannan Fatima ce take zuwa Idanu ya zuba mata kafin ta karaso , tsayinta daidai dana Zarah, wannan tafi Zarah hanci da manyan idanu , ta sanya bakar riga tare da ash din mayafi , cikin fatar hutu da kyau Numfashi yaja yana kauda kanshi kafin ta fahimci yana kallon ta , ya yi ajiyar zuciya Lokacin da Fatima ta karaso gaban Kamal duk yabi ya rude ya kid'ume sakamakon wani kwarjini da take masa "Assalamu alaikum." Fatima ta yi sallama tare da zama cikin nutsuwa 'Dago kai ya yi ya kalleta , maimakon ya amsa sallamar da tai ,cikin kidumewa ya ce ."Baku da yarah ne a gidan ." Murmushi Fatima ta yi domin tabbas ta fahimci halin da ya shiga da ganin ta Kamar za tai dariya ta ce ."Bamu da yarah , fatan ka zo lafiya ." Sa da ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce ."Lafiya kalau wallahi tun d'azu nazo muna ta hira dasu Khalid har mun je sallar mun dawo ." Murmushi ta sake yi a karo na biyu yayin data kasa cewa komai ta durkusar da kai kasa Shima haka Kamal ya gaza magana domin duk ya rasa kalmomin da zai magana dasu Wajen minti guda kowa yana sa'ke-sa'ke a cikin ranshi Sannan Kamal ya yi kokari ya ce ."Malama Fatima, nasan kin san iyayen mu sun saka ranar auren mu . Nan bada jimawa ba zasi mana aure. " Fatima ta d'ago kai tace dashi ."Haka ne." Sannan Kamal ya yi ajiyar zuciya yana sake cewa ."Rayuwa kaddara ce , a matsayinmu na musulmai dole mu amshi kaddarar , a ko yaushe ta zo ." Ya karasa magana yana kallon Fatima Murmushi Fatima tasa kana ta fara magana."Gaskiya ne , ina son karka mini karya a kowanne yanayi ka sanar dani gaskiya komai muninta da zafinta ." Kamal ajiyar zuciya ya yi daga bisani ya kalli Fatima ya fara cewa ."Najin dadin jin hakan , kamar yadda kika sani suna na Kamal, aikina a company ne , sannan ina da Zarah wacce kullum ita ce mafarkina da nake son aura , amma Allah ke ce ya zaba mini ." Ya kalli Fatima tare da sake cewa ."Sai dai banajin koda na aure ki bazan auri Zarah ba , ina son Zarah kuma in sha Allah idan Allah ya so ita ma zan aure ta ." Fatima wani zafin kishi taji ya dakar mata zuciya, amma lokaci guda ta share shi ta fuskanci kamal tana fad'in ."Eh to yin Allah shi ne daidai ." Murmushi ya sake mata a karo na ba adadi yana cewa ."Amma ni ban san komai game dake ba ." Ita ma murmushi ta yi sannan ta d'aga idanunta tana kallon Kamal Sannan ta fara magana. "Uhm . Na yi karatun lauya a yobe , ni 'yar kasuwa ce , sannan kuma a halin yanzu ni lauya ce , ina kuma fuskantar kowacce irin shari'a." Murmushi ya yi har sai da hakoranshi suka bayyana Sannan cikin ranshi yake cewa ."Okay yanzu kin fiddani duhu barrister. " Sannan ya fito fili yana cewa. "Barrister Fatima. Tabbas kuwa zan aikata abin dana ke so ko."? Dariya Fatima ta yi sannan...... Hajjiya Amina ce zaune a falo ita da Laila Laila ce take cewa ." Mommy kin ga har yanzu Yaya Kamal bai dawo ba ." Hajjiya ta ce ."Ai duk inda yake yanzu yana hanyar gida ." Laila ta sosa 'keya ta kalli Hajjiya, sannan ta fara cewa ."Mom Ahmad ya ce fa zai turo ." Kallon Laila ta yi tana cewa. "Wai me yake ci na baka na zuba , yanzu ta auren Kamal ake , ya bari a gama tukun ." "To mommy a had'a mana dana yaya da namu ." Hajjiya ta kalli Laila cikin mamaki tana cewa ."Eh gaskiya ne zamani ya lalace , to sannu Laila da wannan 'karfin halin , to kije ki sanarwa da Alaji mana ai shi ne zai miki auren ." Dariya Laila ta kwashe da ita tana kwanciya a kafar Hajjiya Ita ko Hajjiya tana sake jin mamakin zancen Laila ta ce ."To ai kuwa ana yin na kamal zan sa Alaji ya kawar dake tunda kin fara tuna ....." Bata karasa magana ba , sallamar Kamal ta katseta Kamal ya karasao ya zauna tare da cire hular kanshi ."Sannu da zuwa Yaya Kamal. " Laila ta fad'a Yayin da ya amsa mata ."Mommy na dawo kuma Fatima tana gaidaku ." Kamal ya fad'a yana cire agogon hannunshi Murmushi najin dadi Hajjiya ta yi, ganin yadda d'an nata yake ta farr 'a Kafin ta ce komai ya tashi yana cewa. "Bari na watsa ruwa Mom." Ya nufi sama Bayan wasu kwanaki IBADAN Samari ne su uku suna zaune suna karatu a cikin dakinsu cikinsu kuwa har da Nasir , duk babu wanda yake cewa da kowa komai , duk booklet ce a hannunsu Sautin kawai Bashir ake ji , da yake yin karatun a zahiri Tun d'azu Khalifa yake gallawa Bashir harara , sannan yaja tsaki "Wai Khalifa idan baza kai karatun nan ba ka ajiye mana , sai tsaki kake mana ." Nasir ya yi magana yana aje handout nashi Cikin haushi Khalifa ya ce ."Wannan banzan ne mana Bashir ya yi karatu a zuciya ya'ki sai damuna yake. " Dariyar 'keta Nasir ya kwashe da ita . Yayin da Khalifa ko sauraransu bai yi ba , ya cigaba karatun shi Haushin hakan ya sa Bashir fisgar handout din yana jefarwa gefe Nasir ya sake fashewa da dariya , kawai Khalifa yaja tsaki yana fad'in ."Ka kiya ye ni fa , ni wallahi ma inajin nan da sati zanje gida ." Nasir ya ce ."Ka bari sai bikin Yaya Kamal wallahi sauran kwana kad'an , muje ana d'aura aure mu dawo ." Bashir ya ta'be baki yana cewa. "Allah ya sauwake muna exam a lokacin zamu je kano mu dawo, wallahi baza ni ." A lokacin Abba Alaji ya ban kad'o kofa ya shigo , alamun ya sha ya bugu , yana shigowa ya fad'a gado ya fara bacci . Ran Khalifa ya matukar baci ya kalli Nasir yana cewa. "Wallahi wataran sai na yiwa Abba shegen duka ." .Su ka kwashe da dariya . Alkalamin Autar marubuta ne . FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta _______________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing❌ Page 12 & 13 Duk ana ta shirye-shiryen biki , 'kanwar Hajjiya Samira, Murja sun zo ita da sauran yaran Alaji Mustapha Domin gobe ne d'aurin aure Alaji Mansur ne a zaune a falo, yana waya A lokacin Kamal ya shigo ya zauna a kasa ."To Alaji Musa bari. , sai kun shigo goben, dan Allah a sanar dasu ambassador da Malam Mu'azu ." Alaji Mustapha shiru ya yi sakamakon abokin nashi daga can barin yana magana , bayan ya gama Alaji ya ce ."To shi ke nan , na gode sosai sai mun had'u." Sannan ya aje wayar cikin farin ciki ."To ya maganar gidan naka ya yi maka ."? Alaji ya tambayi Kamal Kamal cikin girmamawa ya ce ."Daddy ya yi babu wata damuwa ." Alaji ya ce ."To alhamdulillah, Abin dana ke son ka sani Kamal, wannan sabuwar rayuwa ce zaka fara , ka sauke hakkin Fatima, kar ka cutar da Fatima, matukar ka cutar da ita ka cutar dani duniya da lahira ." Da sauri Kamal ya kalli mahaifinsa cikin mamaki ."Haba Daddy, wallahi bazan cutar da Fatima, ka za'ba mini Fatima, kuma naji na gani na amince kuma Daddy samm bazan baka kunya ." Murmushi Alaji Mustapha ya yi kana ya ce ."To gaskiya naji dadi kamal, Allah ya yi maka albarka ya sa ka gama da duniya lafiya. " Kamal ya ce ."Amin daddy. " Sannan Alaji ya sallami Kamal ya tafi , yana fita ya nufi arabar motoci sannan ya hau mota ya nufi gidansu Fatima Isar shi ke nan suka gaisa da mai gadi sannan ya shiga ciki Bayan ya gaisa da Hajjiya Rukayya, suka gaisa da Murjanatu nan ake sanar masa kanwar mahaifiyar Fatima ce Cikin girmamawa ya gaisa dasu faruk da Ahmad nan ake ta farin ciki Bayan ya tashi tafiya ne Fatima ta rakoshi har wajen motarshi yayin da ya zuba mata idanu Ta yi wani kyau matuka irin na amare sai sheki take ."Uhm lafiya kuwa Kamal. " Fatima ta fad'a yayin da ta ga kallon ya mata yawah Ajiyar zuciya Kamal ya yi sannan ya fara cewa ."Lafiya mana Fatima , ko lefi ne dan na kalli amaryata ." Wani yammm Fatima taji sakamakon karan farko da ya fara nuna mata irin wannan yanayi Ta masa murmushi Sannan Kamal ya ce ."Fatima ina son sanar dake na shirya rayuwa dake komai tsanani , zan kula dake ga dukkan iyakar kulawata , duk yadda Allah ya tsara maka rayuwa shi ne daidai , a domin haka ina son ki sani ina son ki , ina kaunar ki , domin kin zamanto mini wani babban sashi lokaci guda a rayuwata, son ki ya kamani a yanayin da ban yi tsamani ba, wallahi Fatima daga zuciya ta ne wannan sakon yake zuwa gare ki ." Murmushi Fatima ta yi na matukar jin nauyin Kamal Sannan ta kau da kai tana cewa ." Masha Allah Kamal, hakika naji dadin jin wannan. " Shima Kamal murmushi na farin ciki ya yi yana cewa ."To yanzu mene ne kike da bukata.".. BAYAN AURE Kamal da Fatima tuni ansha biki , komai ya yi matukar kyau , an sha shagali sosai da sosai , har mutanen saudiya sun koma , auren Kamal da Fatima babu wata matsala. Hajjiya Amina ce da Alaji Mansur a zaune suna hira Sallamar Kamal ce tasa su duk shiga wani farin ciki Nan ya durkusa ya gashshe da iyayen nasa ."To ya 'yar tawa ."? Alaji Mansur ya tambayi Kamal Murmushi Kamal ya yi yana cewa. "Tana lafiya Daddy." Hajjiya Amina ta ce ."To masha Allah, Allah ya kara zaman lafiya ." Alaji ya kalli kamal yana cewa. "Mene yake tafe da kai ne , domin tun jiya kake zuwa kuma akwai magana a bakin ka ." Kamal ya durkusar da kai yana sosa 'keya. Alaji ya yi dariya yana cewa. "Ai ni na sani ,wannan yaron naki akwai maganar da take kawo shi ya kasa yi ." Ya karasa magana yana kallon Hajjiya Hajjiya ta ce ."Ai Alaji a kan maganar auren yarinyar nan ne Zarah yake son kasa baki a kai ." Alaji Mansur ya 'bata rai lokaci guda yana cewa. "Wanne irin Zarah kuma , wata kuma zaka kuma aura ? Yaushe ka auri Fatima." Jin hakan ya sa hankalin Kamal tashi tsaye , take ya shiga wani hali Ya d'ago cikin maraicewa ya ce ."Daddy dan Allah, ka duba .".... Alaji ya dakatar dashi yana cewa. "Ka yi min shiru Kamal, karka sa yanzu na bata maka rai." A take yaji kanshi yana sara masa ya kalli mahaifiyar tashi Hajjiya Amina cikin matukar damuwa da shiga wani hali . Cikin takaici Hajjiya Amina ta kalli Alaji tana cewa. "Haba Alaji , Kamal kuwa bai cancanci haka ba wallahi, ka dubi yaron nan yadda ya maka biyayya a auren Fatima, bayan ba shi da ra'a yinta , amma saboda ganin girmanka da tasiri ya amince , amma yanzu ya zo da zance a ce masa ba haka ba , ai kuwa wallahi Kamal bai cancanci wannan ba daga gare mu ." Babu annuri ta karasa magana tana ajiyar zuciya ta takaici Shima Alaji Mansur ajiyar zuciya ya yi yana cewa.. "Alhamdulillah Hajjiya Amina, kin yi gaskiya, shi ya sa nake sake kaunar ki , da zarar na bar hanya kike dawo dani daidai .Allah ya miki albarka." Ya kalli Kamal yana cewa. "Kamal Allah ya maka albarka kai ma , kuma wannan yarinyar Zarah take ko wa , in sha Allah zaka aure ta ." Wani farin ciki ne ya rufe zuciyar Kamal da Hajjiya Amina Bari ma Kamal ya kasa rufe baki "Daddy na gode Allah ya saka da alheri ." Kamal ya fad'a yana washewa mommy baki Alaji ya ce ."A'a dena godiya, ka wuce haka , babanta naji kamar ana cewa Alaji sale ne ko ."? Kamal ya ce ."A Dad shi ne ." Alaji Mansur ya ce ."To masha Allah. " Bayan wasu kwanaki Kamal ne zaune a cikin falo , ya d'auki wayarshi ya kira Zarah, bugu daya ya yi ta d'auka bayan sun gaisa ne Fatima ta shigo falon ita ma ta zauna, nan kamal ya cigaba da wayarshi da Zarah suna ta soyayyarsu Fatima kuwa tana ta danna wayarta Bayan ya gama ya dubi Fatima yana cewa. "My love ya ya aka yi ne , wai ko kishina ba kye yi koh." Dariya Fatima ta yi tana cewa ."Kishi kuma , ai ni wallahi dear na matsu Zarah ta shigo gidan nan ." Kamal yaja ajiyar zuciya yana cewa. "Tabbb gaskiya kina bani mamaki , amma ai shi ke nan . Na ji kina zaki je office to ki shirya nima zani company sai na aje ki , sannan na biya gidan Hajjiya." Fatima ta ce ."Dah ka bari na tafi a mota na ." Kamal ya galla mata harara yana cewa. "An ki , ni fa ko kad'an bana so kina nesa dani , kishirya idan ma zaki dawo ni ne zan d'auko ki." Bai jira ta ce komai ba ya tashi ya koma kujerar da take zaune Sannan ya karbi wayar dake hannunta ya aje gefe yana cewa. "A karon farko dana kalli shari'arki kin sani jin sabon alfaharin da nake yi dake matata .Kin iya aikin ki my life, na yi matukar farin ciki sosai Fatima ina kaunar ki ." Murmushi ta yi tana sake damke hannayenshi tana cewa. "Ina alfarin zamowa matarka Kamal nima ina kaunarka ga dukkan yaki nina." Junansu suka rungume cikin matukar shaukin juna Sannan Kamal ya ce ."Kuma ki shirya ina nan zan aikata 'barna domin nasan zaki wanke ni a kotu ." Fatima tsare shi tai daga jikinta tana kallon shi da cewa ."Kana aikatawa zan aje aiki ." Dariya ya kwashe da ita yana cewa. "Oho dai gara ma ki shirya , domin shari'ar dazan jayo miki me wahala ce , kuma dole ki karbo ni Barrister Fatima ta ." Dariya ta yi tana cewa ."To mu shirya kafin lokaci ya 'kure ." Ta yi maganar cikin harshen turanci Minti 30 suka bata da suka fito Kamal ya aje Fatima a wajen aikinsu Yayin dashi kuma ya karasa gidansu Kamal yana shiga tunkan ya karasa falo ya fara jin muryar mahaifiyar tashi , sama-sama sai fad'a take Yana shiga ya yi sallama , Laila ta amsa ya shigo ya sa mu guri ya zauna Yadda ya kalli Nasir ya tabbatar mommy shi ne takewa fad'a Lokaci guda Kamal ya canja ya karbi bakin mommy ."Wai kai wanne irin yaro ne Nasir, kullum sai ka 'batawa mommy, yaushe ma ka baro makarantar. " Mommy ta amshe da cewa ."Rabu dashi kanshi ya yi wa asara gashi nan an kore su a makarantar ai. Ba shi ke nan ba ." Cikin mamaki kamal ya ce ."Mommy kamar ya an kore su a makaranta." Autar marubuta. FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta ____________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing❌ Page 14 & 15 Mommy kawai ta kauda kai cikin takaici Kamal ya kalli Nasir cikin fushi ya kuma fad'in. " An kore ku kamar ya ?Wanne rashin mutuncin kuka aikata ."? Nasir yaja doguwar ajiyar zuciya na takaicin wannan yanayi , sannan ya kalli Kamal cikin nuna damuwarshi yana cewa ."Wallahi yaya Kamal, ba abin da muka yi , Abba Alaji ne ya yi laifi duk ya shafe mu , daman suna neman hanyar rage d'aluban , amma bami komai. ".. Kamal ya dakatar dashi yana cewa." Yi min shiru dan Allah, zan cen banza , Abba Alaji ubanka ne ko ran ka ne da baza ka barshi ba . To wallahi na yi abin da zan iya maka , saboda karatun ka ne har yau bamu bud'e sabon company ba , zan nemi wani kawai , kaje kai ta rashin mutuncinka ." Cikin sauri Nasir ya kalli Kamal idanunshi sun ciko da hawaye yana cewa. " Dan Allah yaya karka mini haka , wallahi ba a san raina komai ya faru ba , na yi iya yina don gudun hakan ." Ya share hawayen da suka zubo masa sannan ya cigaba da cewa ."Ka yi hakuri dan Allah ka sake bani wata damar ka nema mini wata makarantar ko anan kano ne , in sha Allah bazan baka kunya ba Yaya. " Kamal ya sunkuyar da kai kasa bai ce komai ba Ganin haka ya sa Nasir kallon Hajjiya Amina yana cewa ."Mommy dan Allah, wallahi ina yin komai dan in gyara gobe na ki roka mini Yaya Kamal dan Allah. " Laila cikin jin tausayin yayan nata ta kalli Kamal tana cewa. "Yaya ka yi hakuri." Hajjiya Amina ta kalli Kamal tana cewa. "Shi ke nan Kamal, ka masa kokari , amma idan ka nema masa makarantar ya koma gidan ka da zama nima na huta ." Kamal ya d'ago yana aje ajiyar zuciya sannan ya ce da Nasir. "Shi ke nan amma dole ne ka rabu da wannan mahaukacin abokin naka ." Nasir ya ce ."In sha Allah zan yi iya yina Yaya Kamal na gode. " Barrister Fatima ce zaune cikin office, tana duba wasu takardu da zatai shari'a a kai A lokacin wata barrister Khadija ta shigo tana shigowa ta dubi Fatima tana mata dariya ,sannan ta nemi guri ta zauna . Fatima kallon ta ta yi ba tare da tace komai ba , sannan barrister Khadija ta ce . "To Fatima ya kika ga shari'ar zaki karba ne ." Ajiyar zuciya Fatima ta yi tare da rufe kundin tana cewa. "A'a gaskiya Khadija, domin wallahi bana son shari'a me wahala yanzu. Kawai zan karbi shari'ar Alaji Muhd zan tsaya masa " Tabbb sannu ." Cewar Barrister Khadija Sannan ta cigaba da cewa ."Kawai dai kice aure ya sangartaki , wannan shari'ar wallahi baza ta miki wuya ba , shari'a nawa kika yi wacce tafi wannan wahala, sai yanzu zaki ce wani-wani .Kawai dai Kamal ya sangartaki kuma zan masa magana ." Ta karasa magana tana wani jujjuya fuska Dariya Fatima ta yi sannan ta juya suka gaisa da wani Barrister Aminu Barrister Khadija cikin kasa-kasa da murya ta kalli Fatima tana cewa ."Yawwa barrister Fatima, zancen da nake ji gaskiya ne wai. "? Fatima ta zubo mata idanu tana cewa ." Wanne zance ke nan ." Barrister Khadija ta ce ."Wai Kamal zai kuma aure, har invitation fa na gani ." Barrister Fatima ta yi murmushi ."Au haka ne mana Barrister Khadija, aure Kamal zai kinji daidai ." Yadda Fatima ta aje maganar babu wata damuwa a fuskarta , sai jawo wasu takardu da take yi gabanta tana shirin fara aiki a kan su . Ajiyar zuciya Barrister Khadija ta yi tana kallon Fatima a wannan yanayi kana ta ce ."Wai ke da kanki Fatima kike fad'in haka , yaushe kuka yi aure da Kamal da har zai kuma wani . To wallahi karki yadda, wannan ai cin mutunci ne da rainin wayo ." Barrister Khadija cikin takaici ta aje maganar Dariya Fatima ta yi tana kallon Barrister Khadija. "Au dariya ma zaki mini Fatima, ai wallahi akwai sake ." Khadija ta kuma fad'a Barrister Fatima ta marairaice tana cewa. "To yanzu mene mafita ke nan ." Ta kasa kunne tana jiran abin cewa daga Barrister Khadija Barrister Khadija ta kalli Fatima cikin kissa da kasa da murya tana cewa. "Tashi zaki ki hana auren wallahi, abin sauki ki hanashi sukuni a kan me zai miki kishiya ,hauka ake ." Dariya Fatima ta kwashe da ita cikin yanayi na nishadi Sai da taci dariya sosai , sannan ta kalli Barrister Khadija Sa'ilin da ta fara cewa ."Sannu fa Khadija, wallahi dama so nake na bigi cikin ki ." Ta sake kwashewa da dariya , sannan cikin harshen turanci ta cigaba da cewa . "To ni wallahi Khadija ban'ki kamal ya aura mata 4 ba nan gaba , ko a jikina to sai me Barrister Khadija. Ni dai nafi 'karfin kallon banza wallahi, bani da lokacin wata, kuma sannan bugu da 'kari Zarah Sale zai aura fa ." Barrister Fatima ta canza harshe zuwa Hausa kana ta cigaba da cewa ."Kuma tun kafin ni suke kaunar juna , a kan me zan shiga tsakaninsu , ni fa ba shi ne ya kawo ni duniya ba ." Barrister Khadija ta tashi tsaye tana tabe baki , sannan ita ma da yaren turanci ta ce . "Abin kunya dai , kin bani haushi wallahi, bari na koma ki dage dai ki yi aiki a kan wannan shari'ar ." Barrister Khadija ta juya ta nufi hanyar fita , Barrister Fatima na yi mata dariya Bari mu bar wannan page din iya nan kawai .Dama ba wani comments d'in arziki nake gani ba 😏😏 Sai aukin a yi mana update, sis yau ba update ne 😒 Yo ai shi ke nan dai ana tare 😅😝 Autar Marubuta . 07040805269 WhatsApp only FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta ________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing❌ Page 16 & 17 Gidan Alaji Mustapha Hajjiya Rukayya ce zaune da Hajjiya Binta suna hira Hajjiya Rukayya take cewa ." Wai har yau Abba Alaji basu gama makaranta ba ne Hajjiya? Ai ya ci ace sun kammala ." Hajjiya Binta ta yi ajiyar zuciya ta damuwa tana cewa .'Uhm lamarin Abba kuma ai sai addu'a , mahaifinshi ya kirani yake fad'an an kore shi a makaranta, yaron nan babu abin da yake nema wa mutane banda rashin mutunci, sai dai Allah ya shirya kawai ." Cewar Hajjiya Binta kanwar mahaifin Abba Alaji. Ana ta shirye,-shiryen biki masha Allah, komai yana tafiya daidai babu wata damuwa. BAYAN WATA UKU DA KWANAKI Da misalin karfe 8 na safiya Zarah ta gama had'a break, hakan ya sa ta nufi kofar dakinsu Fatima ta kwankwasa musu kofa , Bayan sun fito ne suka zauna suka fara cin abin da Zarah tai musu Zarah ta kalli Fatima, sa'ilin data juya idanunta ta kalli Kamal tana cewa. "Dear dan Allah ka samo mana mai aiki mana , zamu ji saukin wasu abubuwan , saboda duk fita muke yi ." Fatima ta tabe baki kana ta fara magana ."Gaskiya ba wani aiki , to mene aikin cikin gidan , abin ma daba yarah ne damu ba ." Ta aje maganar tana kallon kowannen su A lokacin Kamal ya d'ago yana cewa. "Nima haka na gani , babu wani aiki ai ." Zarah ta had'a ranta lokaci guda Ganin haka Kamal ya ce. "To amma ke idan kina so sai a samo miki ai ." Cikin fushin Zarah ta ce ."Bana so ." Fatima ta kalli Zarah suka had'a ido, dariya ta yi mata tana kauda kanta . Zarah abin ya sake sata , fusata A lokacin Fatima ta kalli Kamal tana cewa ."Yawwa daman wallahi baby a kan maganar get din gidan nan ne ." Sai da Kamal ya kai lomarsa sannan ya ce ."Me ya same shi ." Fatima ta ce ."Wallahi bud'e shi akwai wuya , kullum fa haka muke, dan Allah ka nemo me gadi ." Kamal ya yi ajiyar zuciya yana cewa. "Me gadi kuma , me gadi ko neman magana , a'a ni babu wani me gadi da zan d'auka wallahi." Zarah ce ta ce ."Gaskiya kam dai bama so , mene abin wahala a bud'e get ." Kamal yace ."Ai shi ne ." Fatima ta kufula da jin wannan zance, ta had'a ido da Zarah, Zarah ta kwashe da dariya Fatima ta dauke kanta cikin takaici , a lokacin Zarah ta ji sanyi , saboda Allah ya kawo abin da zata rama dariyar da Fatima ta yi mata Cikin wannan jin dadin Zarah ta kalli Fatima tana cewa. "Yau baki da aiki ne ." Da murmushi Fatima ta ce ."Nima abin da zan tambayeki ke nan , yau kina da aiki ki tashi ki tafi kawai ." Zarah tace. "Ni kam bani da aiki ." Dariya Fatima ta yi kana ta ce ."Yau fa asabar , kawai dai dan kinga yalla6ai ba shi da aiki nima bani dashi kike son zama a gida ." Zarah ta yi murmushi ta ce ."Ashe kin gane Barrister Fatima." Fatima ta yi murmushi kana ta ce." kema kinji Barrister kika ce , to barristers ba wasa ba ne ." Zarah ta ji wani abu ya tokare mata zuciya ta kalli Fatima tana shirin magana sai ga Nasir ya fito yana hamma lokaci guda kuma yana karasowa wajensu yana saurararn Zarah. "Haba Fatima, ai Dactoci ba sa an nin lauyas ba ne , aikin su yafi na Low." A lokacin, Kamal ya hade rai yana cewa ."Wallahi shi ya sa ma bana so ranar da babu aiki ta zo . To yanzu mene ne amfanin wannan abin da kuke yi haba dan Allah. " Ya karasa musu maganar suna ganin 'bacin ransa Nasir ne ya yi murmushi da yake tsaye yana cewa. "Hhh ai yaya da sauki tun da ba dambe suke yi ba, ai daman mata biyu dole se da haka ." Cikin wani sabon 'bacin rai da mamaki da fad'a Kamal ya kalli Nasir yana cewa. "To ai gaka ka sunan kasa su , su yi damben ." Jin haka Nasir ya ce ."Allah ya huci zuciyarka yaya , shi ya sa na dena fitowa breakfast sai kun gama . " Ya kalli Fatima da Zarah yana cewa. "Bari na koma , idan yayana ya huce sai na fito mu gaisa ." Ya juya ya koma dakin shi , Kamal na bin shi da kallon takaici. A nan cikin gidan Alaji Mansur kuwa , an sanya ranar auren Laila, eh tabbas za'a sha shagali. Zarah ce , zaune a falo tana danna laptop, ga dukkan alamu aiki mai matukar muhimmanci take yadda ta maida hankali. Fatima ce ta turo kofa ta shigo sanye da kayan lauyoyi a jikinta , tana yin sallama ba tare da jiran amsawar Zarah ba , ta shigo ranta a 'bace tana jefar da jakarta gefe ta samu guri ta zauna. Dariya Zarah ta yi sannan ta ce ."Ikon Allah, yau kuma haka aka dawo hala dai shari'ar ba nasara ." Ta fad'a tana kallon Fatima Fatima shiru ta yi mata kawai ko kallon inda take bata yi ba , Hakan ya sa Zarah sake dariya tana sake fad'in ." Na fa gama abinci naki yana dining idan kin huce ." Tana gama maganar ta cigaba da danna laptop dinta tana murmushi Sabon takaici ne ya turnike zuciyar Fatima, Ta kalli Zarah da wannan takaici tana cewa ."Tun da nake ban taba shiga shari'a na fadi ba , kuma kisa ido ki ga yadda zan yi nasara." Fatima ta canza harshe zuwa turanci ta cigaba da cewa ."Za ki ga yadda aljihuna zai cika , sai yafi karfin salary din ki ." Zarah ta d'ago kai ta kalli Fatima tana cewa ."A'a ni bani da lokacin ki , domin kin ga ina kan rubuta sabon littafi da zai hau matakin duniya daloli zan shigo dasu . Kuma ki dena hade mana rai kina fushi ,me ya sa lokacin da zaki karanta low d'in baki dauki Company low , family low , commercial dispute resolution low ba , kika dauki wanda zaki na shan wahala , ai bani na aike ki nan ba , yanzu gashi kin rasa kwanciyar hankali. Fatima ta gyara zama tana yakice rigar jikinta tana cewa. "Ohhh to ke meyasa da kika tashi karanta likatan zuciya ,baki karanta electro physiologist, ba , ko Invasive ba , da sauransu . Ina ce ra'ayinki kika d'auka ? To nima nawa nabi , to ki barni kawai domin lauyoyi ba sa'annin yin dactoci ba ne ." Zarah ta saki baki tana mamakin jin hakan , Ta rufe laptop d'in dake gabanta Sannan cikin yaren turancin nan dai ta fara cewa ."Madam ! A cardiologist is a dactor who's an expert in heart and blood vessels diseases ." Cikin huci ta karasa magana kana ta sake d'auka da cewa ."Mene ne kuma a bangaren Barrister da har suke da alfahari ." Fatima wani shaukin kaunar aikinta taji na lauya , cikin wannan yanayi ta fara cewa ."The best salary for Barrister range from $ 134,493 to 172,431 with the average base salary $154,334." Barrister Fatima na saukewa ta sake d'auka da cewa ."A junior Barrister earns an average of £42,00 per year, while a senior Barrister earns up word of £132,000 annually. To barristers ba abin wasan ki bane dactor Zarah. " Barrister Fatima ta rufe maganar da yaren Hausa Murmushi Zarah ta yi na matukar alfahari da jih da kai sannan ta ce ."Yanzu wannan'kananun kudaden shi ne kika tadah jijiyoyin wuyah Fatima, wallahi sam ki ce wahala dai kuke yi .To kinsan mene ne salary na cardiologist dactor kuwa . To interventional cardiologist salary is $ 356,000---$ 400,000per year, and electro physiologist salary is $678,495." Zarah ta yi ajiyar zuciya kana ta cigaba da cewa ."Ki sa a ranki mu ba sa anninki ba ne Barrister Fatima Mustapha. " Alkamin Autar Marubuta 07040805269 WhatsApp only FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta _________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing❌ Page 18 & 19 Zarah ta dora da cewa ."Mu cardiologist ba sa an nin ku bane Fatima, kuma kisa a ranki ko babu Lauyoyi to al'uma zasu rayu ." Fatima ta yi murmushi kafin ta ce ."Ko babu likitocin zuciya, baza ai asarar al'uma ba , amma matukar bamu taimakawa mutane ba , mu lauyas a lokacin kuke samin hanyar cin abin cin ku da salary din da kuke takama dashi , Da zamu cire hannu mu daina shiga kotu , to tabbas ina tabbatar miki marasa lafiyan zuciya zasu karu sosai , amma idan muka hada kai muna yin aiki , to lallai a karshe zaku rufe asubitocinku , domin babu me zuwa gare ku Rashin samun kulawar lauyoyi a al'uma ina tabbatar miki babbar annoba ce , amma a wannan yanayin marasa lafiyan zuciya zasu yawaita sanadin rashin samun kulawarmu da kwato musu hakki a cikin kotu ." Zarah ta nutsu ke nan don shirin fara magana wata zabiya mai zazzakar murya ta doko sallama Ji da ganin ran Fatima zai sake baci ya sa ta tattara kayanta ta nufi cikin dakinta . Tashi Zarah ta yi tsaye tana murmushi tare da taro bakuwar tata kuma kawarta , nan ta zauna a falo suka gaisa "Atika kin buya wallahi." Cewar Zarah tana magana da kawar tata da hankalinta ba ya kanta . Atika ta yi kasa da murya tana cewa ."Wai fad'a kuke yi ne , na ga ta tashi ta shiga daki ranta a bace ." Murmushi Zarah ta yi tana kallon kofar dakin Fatima, kana ta juyo ta na cewa ."Fad'an lafiya kuma Atika , ta dawo daga kotu ne , kinsan shari'a akwai wahala to gajiya ta yi shi ya sa ." Atika taja tsaki tare da tabe baki tana cewa. "Aikin kawai ai wallahi kin bani mamaki Zarah kin kuma bani haushi da kunya ." Zarah ta kalli Atika cikin matukar bukatar karin bayani ."Kunya fa kika ce , mene na aikata to ." Atika ta gyara zama da samun guri ta ce ." Kina marubuciya , mai rubuta labarai kala-kala , amma kina zaune da kishiya , masoyanki ma duk abin haushi yake basu , karki ka yadda ake kus-kus a social media. " Atika ta sake fad'in "Gaskiya zamanki da kishiya bai yi ba , dan haka a sake lissafi kawai ta yi waje ." Murmushin takaici Zarah ta yi , kana ta tashi ta koma kujerar da Atika take Ta dafa ta tana fad'in ."Ni fa kawai 'yar Adam ce kamar kowa , matan Kamal su biyu ne Fatima da Zarah, Abin da nake so ki sani Atika , Fatima bata damuna Ina da kudi , tana da kudi Ita lauya ce , ni kuma doctor ce Tana da kyau , ina da kyau ." Zarah taja ajiyar zuciya tare da cire hannunta a kan Atika Sannan ta cigaba da cewa ." Bani da wata damuwar da zance sai tabar gidan nan , kuma maganar social media ni ban taba ji ba sai yau. Idan ma ana yi , to a zo shafina a yi dani , amma ni bani da damuwa da Fatima. " Atika da ranta ya matukar baci dajin zancen Zarah ta tashi tsaye ."Au haka ma zaki ce ."? Zarah ta ce ."Eh mana ai gaskiya ce ." "To shi ke nan Zarah, ki cigaba da zama da ita , Allah ya kawo ranar da zata nuna miki bakin halinta ." Ta juya ta nufi kofar fita , kafin ta kai zuwa kofar Ta juyo tana fad'in "Kar ki manta darajarki ce da mutuncinki a ce Kamal ke kadai yake aura , na barki lafiya ." Ta ja kofa ta fice Zarah ta juyo ta kalli laptop din ta Kana ta ce ."I kon Allah, ko ruwa bata sha ba ma , sai kace Fatiman a kanta take ." Ta tabe baki tana fad'in. Allah ya kyauta ya shirya mu ." Ta zauna a kasa ta bud'e laptop ta cigaba da typing. Wajen minti goma taji ana buga kofa , jin maza ne kuma ta shaidi murya , ya sa ta amsa sallamar tana tashi da daukar mayafi . "Ku shigo ." Cikin far 'a su Habib suka shigo gidan Ita ma tana farin cikin ganinsu ta basu guri suka zauna ."Lallai kam yau an tuna damu ke nan , su Habib da Khalid, kamar mun yi laifi ." Zarah ta fad'a cikin far 'a ."Hhhh wallahi ba haka bane kawai dai ayyukan ne sai a hankali. " Khalid ya fad'a yana kallon Habib dake murmushi "To shi ke nan , ya gidan yasu baba ." ? Zarah ta tambaya Habib ne ya ce . "Lafiya suke wallahi suna gaida ku sosai ." Fatima ta shiga madafarsu ta d'auko abinci ta zube musu , ta kawo musu kayan marmari Khalid ya ce ."Haba dan Allah, sai ka ce baki ne mu ." Zarah ta yi dariya, kana ta ce . "To ai saboda ku ba ba'ki bane shi ya sa zaku cin ye min shi tasss , sannan na kira muku Fatima." Dariya suka sake yi a karo na biyu Habib ya ce . "Wallahi ba yunwa muke ji ba ." Zarah ta ce ."Okay saboda ba Fatima ba ce ke nan koh ." Habib ya ce ."A'a wallahi ai duk kun zama daya ." Ta kallesu da cewa . "To idan gaske ne sai ku ci ai ." Khalid ya yi dariya yana cewa "Wallahi halunku daya da Fatima kun iya kafa tarko ." Dariya sukai baki dayansu Yayin da su Habib suka kai hannu suka fara shan wannan kayan marmari Sannan Zarah ta nufi sahin Fatima ta kira ta Sai gasu sun fito a tare Da matukar farin ciki Fatima ta karaso wajen yayannin nata "Manyan baki kam , gaskiya yaya Habib naji dadin zuwanku , kwana biyu duk kun manta dani ." Ta karasa magana tana zama kusa da kujerar da Zarah take tsaye Khalid ne ya yi dariya kana ya kalli Habib yana cewa ."Wai kaji mun manta da ita ." Kafin wani ya sake cewa komai Zarah ta sunkuya ta dauki laptop din ta tana cewa ."Bari na shiga na shirya yau night ne dani Fatima. " Ta karasa magana tana kallon Fatima lokaci guda kuma tana cewa dasu Khalid "Ku fa cinye abincin nan dan Allah." Tana murmushi ta nufi sashinta Ya yin da Habib yake cewa ."To mun gode sosai ." Fatima da murmushi ta ce dasu "Yasu Daddy ya ayyukan naku ." Khalid ne ya ce "Aiki kalau wallahi, suma gida lafiya Amma naji ance kina shari'a ta dau lokaci, to ya akai haka." Murmushi Fatima ta yi kana ta gyara zaman ta a kujera tana fadin "Wallahi lamarin ne , amma in sha Allah ranar 20 ga wata za ai zaman karshe ." Khalid ya ce . "To masha Allah, fatan nasara ." Fatima ta ce . "In sha Allah yaya na gode ." Ta kalli abincin da Zarah ta kawo musu tana cewa. "Ku ci abincin mana yaya." Habib ya ce . "Keee mu fa ba yunwa muke ji ba kuma gashi min sha fruit." Khalid ya kalli Fatima yana cewa. "Ina Kamal d'in fa ."? " Kamal bai dawo ba wallahi yana company. " Fatima ta ba shi amsa Kad'an sukai hira suka tashi kamar wanda aka muntsu suka tashi a tare . "Haba Yaya muna hira kuma zaku tafi , to ku bari Kamal d'in ya dawo mana ai yanzu yana hanya ." Fatima ta yi musu maganar yayin da suke a tsatstsaye Khalid ya ce . "A'a fa sai wani lokacin, ki gashe shi kawai ." Suka isa wajen kofar Tana taka musu zuwa wajen kofa tana cewa a gaida mutanen gidan. Habib yana sa hannu zai bud'e kofar Nasir ya turo kofar ma'kale da jakar makaranta, ga dukkan alamu daga makaranta ya dawo . Yana hada ido dasu ya sakar musu murmushi. 07040805269 WhatsApp only. FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta ________________________________________ Editing❌ Page 20 & 21 "Ka ga sojoji barkan ku wai har zaku tafi ." Nasir ya yi magna a sanda yake shigowa ciiki Suma duk murmushi sukai fara masa kafin Habib ya ce . "Ai kuwa har zamu tafi ya makaranta, ya mancewa damu ." Nasir ya yi dariya kana ya ce . "To wallahi makaranta ce take boye ni , domin so nake kawai na kammala karatun nan na koma gidan mommy, yaya Kamal ya buden company na ." Habib ya ce . "To Allah ya taimaka Nasir." Sannan ya basu guri suka wuce tare da sallama Suna fita Fatima ta rufe kofar "Aunty Fatima na dawo ." Nasir ya yi magana da Fatima Halinta na murmushi ta masa sannan ta ce . "To sannu da zuwa ." Ya shige dakinshi yana murmushi Yana shiga ya aje jakar shi , sai yaji wayarshi ta fara ruri Kafin ya cire takalmin kafarshi ya duba wayar don ganin me kira Dogon tsaki yaja yana cewa. "Abba Alaji ko mayen mutum wallahi." Ya sake jan tsaki yana katse kiran Kamal da Fatima ne zaune a falo suna kallo Misalin karfe 8saura na dare A wannan lokaci Zarah ta fito daga dakinta, sanye da rigar likitoci da jakah a hannunta Fatima tana ganin haka ta kauda kai tana dariya Zarah tana kula da hakan ta yi murmushi, kana ta ce da Kamal. "Zan tafi saida safe." Kamal ya d'ago yana cewa. "Ohhh kina da night ko , to Allah ya tsare hanya." "Mene kike mini dariya."? Zarah ta tambayi Fatima Fatima ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce . " Shi kin ga aikina babu fitar dare , ga shi zaki barni da Kamal a gidan ." Fatima ta yi maganar cikin son cusawa Zarah kishi Zarah ta kauda kai , kawai ta fice cikin haushi Kamal ya kalli Fatima yana cewa. "Data kula ki baza ta tafi yanzu ba , ga shi ta samawa kanta samala ." Dariya Fatima ta yi sannan ta ce . "Wallahi ba 'kin kulani tai ba , nasan zata rama ne ." Kamal ya ce . "Wato Fatima ina alfahari daku ina san ku fiye da komai . Amma wannan kace-nace d'in tsakaninku Allah ya nunan ranar dena shi ." Fatima ta yi dariya. Wasu kwanaki Nasir da Kamal suna zaune suna kallo , Zarah kam tana duba wasu takardu Babu sautin da ake ji saina gidan TV da suke kallo Fatima ce ta turo kofa sanye da kayan lauyoyi da bakar jakarta ta gun aiki . Cikin matukar far'a a tare da ita ta ce . "Assalamu alaikum wanda nafi kauna a duniya ta ." Jin hakan ya sa duk suka d'ago suna kallonta Kamal ne ya fara murmushi yana cewa. "Ga dukkan alamu an gama shari'a cikin nasara ." Fatima ta saki wani murmushi ta samu guri ta zauna Fatima ta kalli Kamal tana cewa . "Wannan gaskiya ne dear ." Sannan ta kalli Zarah cikin wannan farin cikin dai tana cewa . "Wato Zarah yau na kammala shari'a cikin nasara ,kar ki ga yadda komai ya yi daidai a kotu , farin ciki matuka, zan so a ce kin shiga kotun an yi a gaban ki ." Zarah ta tabe baki sannan ta ce cikin yaren turanci. "Na ta ya ki murna ." Sannan ta juya harshe zuwa Hausa ta cigaba da cewa . "Allah kar ya nunan ranar da zan shiga kotu a rayuwata, domin bani da lokacin ta ." Fatima ta yi dariya Nasir ya ce . "Aunty Fatima ni kam zan so watarana ki gayya ce ni kotu , nasan in dai ke ce zaki karbi shari'a to tabbas dole a sara miki ." Fatima ta yi murmushi sannan ta ce da Nasir. "Kar ka damu akwai wata shari'ar ma ." Kamal ya ce . "Naji dadin nasarar ki sosai ." Ta yi masa murmushi. Fatima ta ce . "Ya Allah na gode maka da wannan nasarori da kake jaraftata dasu ." Zarah ta kalleta yayin da suka hada ido , ta kauda kanta . Wayar Nasir ce ta fara ringin , ya yi sauri ya katse ta , aka sake kira ya yi sauri ya kuma kashewa . Kamal ya jefa masa wani kallon zargi , Nasir ya yi masa murmushin ya'ke Bayan minti guda ya ji shigowar sako wayarshi . "Ka fi to ina waje ." Abin da aka turo ke nan Ya yi ajiyar zuciya ta bacin rai ya tashi ya fita waje . Yayin da Kamal yake binshi da kallo Fatima tana ta duba wani abu cikin fayil tana murmushi, Ita ma Zarah ta na aikinta . Nasir yana fita Ya ci karo da Abba Alaji. Cikin mummunan bacin rai Nasir ya fara masa magans . "Wai kai uban mene kake bukata ne Abba , wallahi ka rabu dani abotar an dena ka rabu dani mana ." Abba Alaji ya ce . "Haba Nasir ni ne fa , zuwa na yi mu gaisa , wai waye ya shiga tsakanin mu ne ." Nasir ya ce . "Wallahi ka kiyaye ni , babu ni ba kai , kai matsala ne mai haddasa annoba , duk sanda na fara samun nasara kana nufoni komai ya ke lalacewa . Wallahi ka kuma kirana ,ai yaya Kamal yana falo ka cigaba ." Yana gama magana ya koma ciki bai jira cewar komai daga Abba ba . Cikin wata fuska ta rashin gaskiya ya koma ciki , a wannan lokacin dai Kamal yana masa wani kallo , har ya zauna , amma Allah bai nufe shi da ya furta komai ba . Fatima ta rufe fayil din da take dubawa , lokaci guda kuma tana kai idonta kan TV Nasir cikin son Kamal ya dena masa kallon zargi ya ce . "Bikin laila fa ya zo .Ga shi ban fara aiki ba ." A lokacin kamal ya yi murmushi sannan ya ce . "Ai kai ne ka yi wa kanka , da tuni kana aikinka , yanzu ma idan ka yi wasa da damar ka babu abin da zan iya maka . To mene idan ka fara aikin mene zaka mata kake wani zance." Nasir ya sosa kanshi , sannan ya ce . "Wallahi yaya Kamal mota nake son siya ." Zarah ta d'ago kai ta ce . "In sha Allah nima kafin bikin zan canja mota ." Fatima ta ce . "Canza mota ai dole ne nima ." Kamal ya ce ."Ai akwai motoci masu kyau wajen Alaji Mamman sai ku samu a can kawai ." Zarah ta ce ."Eh tabbas akwai motoci masu kyau a gun shi , can zamu je ." Fatima ta bata rai jin yadda Zarah ta yabi motors din Sannan ta ce . "A'a ni gaskiya bazan se mota a can ba , babbar motarshi bata wuce million 5 ba , dan haka bazan siya a can ba ." Ita ma Zarah ranta ya baci yadda taji Fatima na magana "Me kike nufi Fatima."? Fatima ta ce . " Ina da kudin da zan se motar sama da million 5 don haka bazan siya anan ba , ba karama nake so ba ." Zarah ta rufe takardun dake hannunta ta aje su gefe sannan ta fara magana . "Ke kin san ina da kudin da zan se motar da baki isa ki hau ta ba , kin sanni kin san mahaifina, kinsan yadda na yi suna a harkar rubutu , to ki tabbatar dole kina baya na ." Nasir ya zuba kunne cikin mamaki yana kallonsu Yayin da ran Kamal ya matukar baci dajin abin da suke Fatima ta yi murmushi na kasaita kafin ta ce . "Kwarai kuwa nasan mahaifinki yayi suna , amma ina tabbatar miki ba zai nuna maka kudi ba , sanin kan ki ne su waye iyayena , mahaifiyata tana saudiya , tare da yayannina , kuma ina mai tabbatar miki komai kudin ku , baza ku fimu ba , kuma ina da darajar da zan shiga wani guri , wallahi baki isa ki shige shi ba ." Zarah ta ce. "To shi ke nan , mu zuba ni dake muga wanda zai se motar da tafi karfin wani ." Kamal ne ya tashi tsaye tare da daka musu wata tsawa yana cewa. "Wannan wanne irin hauka ne ." Duk suka sha jinin jikinsu Autar Marubuta 07040805269 Ku ne meni a WhatsApp FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta ________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<>< ><><><>🌹<>< Editing❌ Page 22 & 23 Kamal cikin fushi da bacin rai ya cigaba da cewa . "Kuna son nuna wa duniya ilmin ku , duk na banza ne ke nan , na yi muku shiru tsawon lokaci, amma abin naku gaba yake yi , Mene amfanin hakan , almubazzaranci daidai ne ? To wallahi duk wacce baza ta hau motar kasa da million 7 ba , duk na haramta muku siye , aikin banza , wallahi zan yi maganinku ." Ya wuce ya futa waje ya bar musu gidan . Nasir ma ya yi ajiyar zuciya , ya tashi ya nufi dakinshi . Fatima ce kawai a cikin gidan , sakamakon Kamal yana company tare da Nasir. Zarah kuma tana wajen taron karawa wani marubucin abikinta girma . Yau babu wanda yake da aiki a cikin gidan . Gama girkinta ke nan , Fatima ta d'auka wayarta don ganin meke faruwa a duniya . Sallama taji ana yo wa amma an kasa shigowa jin muryar mace ce ya sa ta fadin . "Shi go ." Hajjiya Sa'adatu ce ta fara shigowa sannan Mahmud da Umar suka biyo bayanta . Murmushi na farin ciki Fatima ta saki , tai saurin tashi tana taro su . "Oyoyo mommy sannu ku da zuwa ." Su ma su mommy murmushi sukai mata , ta musu iso suka zauna Bayan sun gaisa Fatima take cewa . "Mommy bari na kawo muku abinci domin yanzu na gama shi ." Bata jira sun ce komai ba ta nufi dakin kirki . Mahmud ne ya kalli mahaifiyar su hajjiya Sa'adatu yana cewa. "Masha Allah mommy, suna zaune lafiya ." Murmushi hajjiya ta yi sannan ta ce . "Ai dama haka ake so ." A lokacin fatima da murmushi ta kawo abinci, ta koma ta kawo lemo da ruwa . "Tom mommy ga abinci, nasan wata kila kafin ku gama Zarah zata iya dawowa ." Hajjiya Sa'adatu ta kalli Fatima sannan ta ce. "Au bata nan ." Fatima ta ce . "Eh taje wani taro , amma bari ma na kirata ." Ta dauki wayarta tana kokarin kiran lambar Zarah Kafin ta kira ne hajjiya Sa'adatu ta ce . "Ba sai kin kirata ba Fatima, ai dama lafiyarku muka zo gani , idan ta dawo kafin mu tafi sai mu gaisa ai ." Fatima ta yi murmushi tana cewa. "Wallahi mommy da an kirata ." "Ba sai kin kirata ba wallahi Fatima." Cewar Hajjiya Fatima badan taso ba , ta fasa kiran Zarah. Bayan su Hajjiya sun gama cin abinci ne , suka fara shirin sallah da zummar idan Zarah bata dawo ba , zasu koma A wannan lokacin ne ta ji ana kwankwaso kofar falon Ta tashi ta nufi kofar tare da bud'e ta Wani ihu ta kwalla ta rungume wanda ya fara shigowa wato mai sanye da kayan turawa wato Ahmad Sannan cikin farin ciki ta sake rungume dayan wanda shi ne Najib "Haba matsala dake ke nan 'yar Nigerian nan idan kin yi kewar mutane baki iya hakuri ba ." Ahmad ya fada cikin farin ciki yana sake shigowa cikin gidan , lokaci guda kuma yana hango su Hajjiya Sa'adatu a zaune "Wayyo Allah gaskiya kun yi mini zuwan ba zata Yaya ." Ta yi magna cikin shagwaba da matukar shaukin kaunar su . Suka nufo inda su Hajjiya suke zaune domin samun masauki Hajjiya ta kalli Umar tana cewa. "Su waye kuma su ." Umar ya ce . "Wallahi ban sani ba mommy." Bayan sun zauna lokacin da Hajjiya ta kare musu kallo tabbas tana iya ganin kamanninsu da Fatima. Hakan ya sa ta saki fuska da jiki suka gaisa cikin girmamawa Bayan sun gaisa ne Fatima cikin wannan fatin cikin ta kalli hajjiya tana cewa. "Mommy wannan 'yan uwana ne daga saudiya ." Ta nuna Ahmad tana cewa. "Wannan shi ne Ahmad, ga kuma Najib ." Shi ma ta nuna Shi Lokacin hankalin Hajjiya ya sake kwanciya, suka sake sabuwar gaisawa tare da tambayar mahaifiyar su . Fatima ta kalli su Ahmad tana cewa. "Wannan mahaifiyar Zarah ce , ga kuma 'yan uwanta ." Wani farin ciki ya sake rufe su , suka fara hira Umar ne ya ce . "Kun sha hanya sannuku ." Najib ne ya mayar masa da cewa . "Ai dake ma muna can gidan mahaifin mu , kuma yanzu zamu koma domin nan da minti kad'an jirginmu zai tashi ." Fatima ta murtuke ranta matuka tana cewa. "Wanne irin yanzu kuma yaya gaskiya ni wai mene haka ."? Bacin rai ya bayyana a fuskarta . Najib ya ce. " yanzu kuwa , zamu koma ." Hajjiya ce ta ce ."Fatima baki kawo musu komai ba , kina ta murna ." Fatima ta dafa kanta alamun sha'afa tana cewa. "Wallahi mommy na manta ." Najib ya ce . "Kar ki kawo mana komai domin daga gidan Alaji mu ke , kuma ba za mu bari mu rasa jirgi ba ." Fatima ta sake hada ranta jin cewa da gaske tafiyar za si . Ahmad ya kalleta kana ya ce. "Wai ina Kamal din ne da Zarah."? Tana cuno musu baki ta ce . " Sun fita amma zaku jira su dawo ai . Me ya sa Aunty Murja bata zo ba ."? Najib ya yi murmushi kafin ya ce . "Zata zo ne , mommy na nan zuwa a sabon wata mai kamawa in sha Allah." Wani dadin gaske Fatima taji tana sake bazo idanunta tana cewa. "Allah ya kawota wallahi na yi kewar mommy na ." Hajjiya Sa'adatu ce ta yi murmushi tana cewa. "Ai dole , amma dan Allah idan ta zo karta tafi baki hada mu ba Fatima, domin bazan ji dadi ba ." Fatima ta ce ."In sha Allah mommy zan hada ku , idan ta zo ." "Ta shi mu koma Ahmad." Najib ya fada cikin yaren larabci Duk suka tashi tsaye "Haba dan Allah yaya wai tafiya zaku yi ."? Fatima ta fada da matukar haushi . Ahmad ya CE ." In sha Allah, kina so mu kwana anan ne , karki damu nan da wata biyu zamu zo mu yi sati a Nigeria. " Ya karasa magana yayin da sukai sallama dasu Hajjiya da Mahmud Kafin su isa bakin kofa Kamal da Nasir suka shigo suna dariya suna hirarsu . A wannan lokacin ne suka lura da irin manya manyan bakin da sukai Kamal ya ma kasa cewa komai , domin ya rasa dasu waye ma zai fara magana Da sauri ya karaso cikin falon yana cewa. "Ka ce yau manyan baki mu kai , ai dana san zaku zo babu inda zan fita ." Suka mika hannu suka gaisa da su Ahmad da Najib dake tsaye Sannan ya karasa ya gaida Hajjiya suka kuma gaisawa da su Mahmud Kamal ya kalli Fatima yana cewa. "Yana gansu a tsaye ." Fatima ta ce .. "Wai tafiya zasi fa ko minti 30 basi ba ." Kamal ya karasa gabansu yana cewa. "A haba dai yaushe rabon ku zo , kuma ku ce zaku tafi Ahmad." Ahmad ya yi dariya sannan ya ce . "Wallahi zamu rasa jirgi dole mu tafi , tunda Allah ya yi zamu gaisa da kai ." Najib ya ce . "Gaskiya ne , sai wani lokacin kuma ." Suka nufi hanyar fita yayin da Kamal da Zarah su kai musu rakiya Bayan sun dawo ne Hajjiya take cewa . "Ku tashi ku yi sallah muma mu tafi ." Kamal ya dubi Fatima yana cewa. "Wai ina Zarah ne , ko dai bata dawo ba ." Fatima ta ce . "Eh." "Bari na kirata mana ." Ya dauki wayarsa Hajjiya ta ce . "A" a barta wallahi, Fatima ma tace zata kirata ni na hanata , ai baza mu jira ba gaskiya, in tana son ganin mu ta zo gidan kawai ." Kamal ya yi ajiyar zuciya ya aje wayar yana cewa. "Ai ya ci a ce ta dawo ." Hajjiya ta tashi ta dauro alwala , bayan suma su Mahmud sun yi sallah suka koma gida . Next page in sha Allah🙏 FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta ________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing❌ Page 24 & 25 Lokacin da Zarah ta dawo ta yi matukar takaici na rashin samun bakin da akai . Anan cikin gidan Alaji Mustapha kuwa Hajjiya Binta ce , zaune a falo ita da Abba Alaji, sakamakon yau ya zo gidan Kallon shi ta yi sannan ta ce . "Yau kuma an tuna dani ke nan har an kawon ziyara , To ka gama makarantar ne ."? Murmushi Abba Alaji ya yi sannan ya d'ago yana cewa. " Tun yaushe ma kuwa ai sakamakon ya yi kyau ." Dogon tsaki hajjiya Binta ta ja kana ta ce . "Ka ji makaryacin banza , daman jin bakin ka zan , tun yaushe Alaji yake sanar mini , ka yi abin da ka yi an kore ka ." Abba Alaji ya d'ago yana kallon ta da idanunsa na rashin kunya yana cewa. "Au to tunda kin sani mene na tambaya kuma ." Hajjiya Binta ta yi ajiyar zuciya tana sake kallon takaici ga Abba tana cewa. "Wallahi ka kiyayi duniya Abba, yayana yana iya yinsa don ganin ka zama mutumin kirki , amma kai kullum kana yawo kana jawo masa magana ana zaginsa , to ka cigaba Allah ya gani ai idan ka kashe shi sai hankalin ka ya kwanta ." Abba Alaji ya d'ago da jajayen idanunshi yana cewa. "Ke kinji ki Aunty ta ya Daddy zai mutu, ai kuma Daddy yana sona ." Hajjiya ta ce . "Dah ne yake son ka wallahi Abba da zaka zama mutumin kirki, ba karamin dadi za ka samu wajen Alaji ba , amma kai ne can neman fitina iri-iri . To wallahi daman ya ce komai ya ishe shi zai jire hannunshi a kan ka . To tun kafin haka ta faru ka gyara halinka , ka zama mutumin kirki, ka dena shaye-shaye, yanzu dubi irin askin dake kanka kamar ba d'an musulmi ba ." Abba Alaji cikin bacin rai ya tashi tsaye yana cewa. "Ke kinji ki , shi ya sa bana son zuwa gidanki wallahi , gara ma na tafi sai anjuma .".. Ya nufi kofar fita tana kiran shi , ko juyowa bai ba ya fice abinsa . Ta yi ajiyar zuciya tana cewa. " Allah ka shirya mana wannan yaro ." Yau su Fatima suka kai ziyara gidansu kamal, har suka gano kayan lefen Laila wanda biki sauran sati biyu . Misalin 9 na dare . Duk su kamal suna zaune a falo suna kallo . A lokacin Laila ta turo kofa ta shigo tare da sallama da wasu ledoji a hannunta. Kamal ya yi ajiyar zuciya kafin ya ce . "Yanzu a wannan daren Alaji ya barki kika fito , ba an ce ki bari gobe ki kawo kayanka ba ."? Laila ta tabe baki tare da fara yo taku zuwa cikin falon tana cewa. " Wallahi yaya bana son fita da rana ." Kamal ya ja tsaki Nasir ya ce . "Ka ga wai ita amarya tabb , za a ga wani abu ." Fatima da Zarah sukai dariya Laila ta kalli Nasir tana cewa. "Kai dai kaji kunya wallahi, kullum tsokana mtww." Nasir ya yi dariya yana cewa. "Naji dadi ma sanda zan dawo gidan ba kyanan ai gara ...." Bai karasa magana ba kamal ya katse shi da cewa . "Zaka bari ta yi abin da ya kawota ko kuwa sai dare ya kuma yi ." Nasir ya yi shiru , Laila ta masa kwalo , sannan ta zo ta zauna "Aunty Fatima da Aunty zarah ga kayan zuwa dinner din ku , yau muka am so su har da nawa ." Suka amsa suka bud'e nan suka yaba katafaren kyan da dinkin ya musu . "To tashi Laila tashi maxa dare na yi ." Cewar Kamal Laila ta tashi tana cewa. "Haba yaya kamal daga zuwana ." Zarah ta ce . "Ai shi ne ." Kamal ya ce . "Ni wallahi bansan me ya sa su mommy suka bari kika fito ba ma ." Ya kalli Nasir yana cewa. "Tashi ka rakata har gida ." Haka Nasir ya sa Laila gaba har suka isa gida Zarah ce ta ce . "Za'a sha dinner kam zamu sha liki ." Fatima ta yi murmushi Kamal ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce . "To duk nasan halinku wallahi kar wacce taje ta lika sama da Naira , na dai fada muku ." Ya tashi ya shiga ciki . To Allah ya kai mu wannan biki , domin Alaji Mustapha ya yi matukar yin sa don samun farin cikin Laila, yadda ya riketa bata taba kukan rashin iyaye ba , to haka ma a wannan biki ya aje mata abin da zatai alfari dashi matukar gaske . Kowa ya shiryawa wannan biki , musamman wajen dinner irin babban mawakin da aka gayyato , ga baki duk sun hallara , 'yan uwan amarya dana ango gurin taro ya cika fall masha Allah. Ga Alaji Mustapha da Alaji Mansur duk sun sha ado , su Hajjiya Amina iyayen amarya Kamal ma an sha kyau matuka, ga Nasir da abokanshi , Fatima da Zarah sun sha kaya irin daya sun yi matukar kyau Kawayen amarya da manyan baki sai murna ake A can daga saman stage ga Laila amarya👰 Tare da angonta Dactor Sadiq sun hadu sosai sai jan hankali suke . Mawakin da aka gayyato yana fara wakarsa , su Alaji Mustapha suka ja zugar su , domin yin wani pati din da ya shirya don haka babu wasu manyan iyaye maza a gun Gurin sai tashin kamshi yashe da walwali A lokacin ne aka saki wakar da aka yiwa amarya ta fito ita da angonta suna takawa . Kafin ka ce komai 'yan uwa suka fara zuba liki Hajjiya Amina ce ta zo da wasu kudi dummm tuli guda zugar dubu-dubu tana likasu Shima kamal ya kwaso nashi ya zuba musu ya koma Fatima da Zarah suka taso Zarah ta fara likin dari biyar biyar masu yawa , Fatima na ganin haka , ta maida kudin hannunta ta d'ebo dubu-dubu tana lika musu Lokacin da Zarah ta fahimci hakan , sai ta zaro daloli a cikin jakarta tana rawa tana likawa Ita ma Fatima wannan dalolin ta kwaso a jaka kawai tana watsawa . Tuni guri ya rude , kowa hankalinshi ya koma gun su , maxa da mata kuwa ana fadin "matan Kamal ne Da Fatima da Zarah, daya lauya ce dayar kuma likita ce ." Haka wanda basu san masoyiyarsu Zarah Sale ba suka ringa farin cikin ganinta . Guri ya rude da dalolin dasu Zarah suke watsawa Shi kam Kamal ranshi idan ya yi dubu , to duk sun 'bata masa shi Ya matukar jin bakin ciki yadda suke gasar zubar da kudi a gurin nan ko a jikinsu .Bayan jan kunnen da ya yi musu amma sun yi watsi da maganar sa. Haka ran kamal ya sake matukar baci , kawai ya fita , ya hau mota ya nufi gida . Yana tuka mota abin yanata damunsa a ranshi "Yanzu me suke nufi ban isa dasu ba ke nan kome , kudi hauka ne , suna da ilmi amma vasa amfani dashi ." Cikin bacin ran nan ya koma gida , ya zauna a falo abinsa . Anata cakarewa ana murna bayan an tashi suka nufo hanyar gida . Nasir ne ya fara shigowa bai ma kula da Kamal ba , hakan ya sa ya nufi dakinsa. Fatima da Zarah suka shigo suna magana , inda Zarah take cewa . "Bari kuma gobe , ai wannan kudin ba komai ba ne , dan ma dear ya hana canza mota mai tsada ." Fatima ta ce . "Zancen kike so an ce da gwauro ya iyali ." Suka karasa falon a daidai wannan lokacin suna zama Wani bakin ciki Kamal yaji ya sake turnike masa zuciya, wato ma ko nadama basa yi Yadda Kamal yake jinshi zai iyay musu komai idan bai kai zuciyarshi nesa ba , don ji yake kamar ya rufesu da duka . Haka Allah ya hani kowacce a cikin su da ta lura da halin da Kamal yake ciki , bare si masa magana . "Aikin kawai dadin abin ni na canza mota , ke ce ta gagare ki." Cewar Fatima Zarah ta ce . "Dan kin canza mota ai ba .. " Kafin Zarah ta karasa magana taji saukar mari a kuncinta , kafin Fatima ta kula da abin da yake faruwa ta ji ita ma an sauke mata wannan mari . Kamal ne a tsaye a kansu idanunsa sun yi jajir , jijiyoyin kanshi duk sun tashi , sai wani huci yake , ka ce wani zaki. Ya kalli kowacce dake rike da kuncinta cikin mamaki da suke kallon shi "Ku wanne kalar marasa tunanine da rashin hankali. Ni ban isa daku ba , duk irin maganar dana fada muku , bayan kun aikata abin da kuka gadama a wajen dinner kun zo gida kuma zaku tayar mini da hankali." Yaja dogon ajiyar zuciya mai zafi sannan ya cigaba da magana . Next page 07040805269 WhatsApp only. FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta ________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing❌ Page 26 & 27 "Ina hankulanku suke , ko daman babu ne ."? A wannan lokacin Fatima ta sunkuyar da kai wasu hawaye suna zuraro mata "Kun bani kunya , kun bakantan zuciya da rayuwa, tun a gida na sanar daku bana son almubazzaranci amma dake ni ba komai bane a wajen ku , kuka ture magana , kun nuna ban isa daku ba koh."? Ya jefa musu tambayar yana zare jajayen idanunshi. " To daga yau zan dau mataki a kan ku , tunda aikin lauya d Likita kuke takama dashi duk zaku janye shi , zan yi maganinku ." Ya nufi kofar dakinshi cikin huci . Zarah ta cire hannu a wajen marin tana ajiyar zuciya. Anan gidan Alaji Mustapha kuwa Suna falo tare da Hajjiya Binta da mahaifin Abba Alaji wato Alaji Sani Bayan Alaji Sani ya gaisa da Alaji Mustapha, nan suka gaisa da kanwarshi Hajjiya Binta "To Alaji yanzu babu wata makaranta da aka samawa Abba Alaji ne ."? Hajjiya Binta ta tambayi yayanta . Alaji Sani murmushi na ciwo ya yi sannan ya ce . " Dan Allah ki dena mini zancen Abba, Allah ya gani na yi abin da zan yi akanshi , na gaji wallahi, Allah ma ya sani , idan ba so yake ya kashe ni ba, Yaron nan zan aje kudi na , kudin mutane duk ya kwashe , a'a wallahi na gaji , in ya shigo hannuna ai wallahi sai dai a kwace shi ." Cikin bacin rai ya aje magana. Alaji Mustapha ne ya ce . "Ai hakuri za kai Alaji Sani , hannunka ba zai ribe ka yanke ka yar ba , kawai addu'a zaka runguma komai zai wuce in sha Allah." Alaji Sani ya sake murmushi na takaici yana cewa. "Addu'a ta nawa kuma Alaji Mustapha, kuma idan hannuka ya rube dole kuwa ka yanke ka yar ." Alaji Mustapha ya ce . "A dai cigaba da addu'a zai shiryu in sha Allah, Allah ya shirya mu ya shirya kowa da kowa ." Hajjiya Binta ta ce . "Amin ya Allah." Alaji Sani ya tashi tsaye , yana cewa. "To bari na koma ga shi kuwa dare ya yi ."...... Washe Gari da safiya ta yi Kamal babu wacce ya ce da ita komai, ko abinci bai saurara ba ya fara shirin tafiya company. Ganin haka yasa Fatima da Zarah suka tare shi suna ba shi hakuri . Samm Kamal ba shi da niyyar hakura , Amma da suka fahimci duk laifunsu ne da suka kai shi bango har kuka suka yi suna ba shi hakuri. A lokacin zuciyarshi ta karaya , ya tabbatar musu ya yafe musu , domin ma saida ya karya sannan ya fita . Sannan aka samu saukin rayuwa a cikin gidan . Misalin karfe 1 na dare kowa ya kwanta, Gama karatun Nasir ke nan zai fara bacci yaji wayarshi na ringin yaja dogon tsaki ya katse kiran " Abba Alaji ko mara zuciya, uban me zan masa ma a wannan daren , ni bansan ma me yasa ban goge number shi ba ." Nasir ya aje maganar yana tsaki Yayin da kiran Abba Alaji ya sake shigowa . Nasir ya dauki wayar cikin masifa yana cewa. "Mene kuma a wannan lokacin." Nasir daga can kasa ya jiyo muryar Abba Alaji cikin jigata yana cewa. "Dan Allah Nasir ka fito ka taimaka mini , ina kofar gida ." Nasir yaja tsaki ya kashe wayar Mamaki yaji ya kamashi yadda yaji muryar Abba cikin wani hali Hakan yasa ya tashi ya bude kofar shi ya leka falo , yaga babu kowa , sannan ya fito cikin sanda ya bude kofar fita a hankali ya fita ba tare da ya rufe ba Ya fita waje Yana fita yaga Abba Alaji da farar singlet jikinshi duk jini, fuska duk ta kunbura da gani babu tambaya wannan duka ne da wani abin aka masa "Me ya sa me ka haka ."? Ya tambaye shi da mamaki Abba Alaji cikin haki da wahala ya ce . " Daddy ne ya dake ni wallahi, badaban na gudu ba kashe ni ma zai ." Nasir ya kwashe da dariya Sannan ya kalli Abba yana fadin . "Allah sarki daddy wato ka kai shi bango , toni yanzu da ka zo mene zan maka ."? Abba Alaji cikin yanayin tausayi ya ce . " Wallahi jiki na duk ba dadi Nasir, ka temakan na kwana a dakinka zuwa safiya na tafi ." Nasir ya zaro ido cikin rainin wayo yana cewa. "Tabbb amma ka rainan wayo , dakin nawa da yake a cikin gida, kawai wani kato da kai zaka shigar musu gida , to gaskiya a'a 'kara gaba kawai ." Abba Alaji cikin wata fuska ta matukar tausayi ya sake kallon Nasir yana cewa. "Yanzu ina zani Nasir, ina zani dan Allah kai ne kawai zaka taimake ni , safiya na yi ko asuba zan fito babu wanda zai sani ." Nasir ya dan yi jimmm yana tunani Abba ya yi shiru Nasir ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce "To shi ke nan , amma wallahi ba wannan shegen baccin naka zaka yi ba , asuba na yi zan tashe ka , Yaya Kamal yana tafiya masallaci zaka fito ." Abba ya ce . "Naji na kuma yadda ." Ya juya yabi bayanshi , a hankali suka shiga gidan suka rufe kofar suka koma daki . Ya ba shi kaya ya canza , ya gasa jikinshi da ruwa , har magani Nasir ya ba shi , sannan Abba aka kwanta aka fara bacci . Kamar kuwa yadda su kai yarjejeniya asuba na yi Nasir ya duba ya ga ba kowa a falo , sannan ya tusa 'keyar Abba ya fita. Allah ya taimaka babu wanda ya ganshi. Bayan kwanaki SAUDIYA Duk suna zaune cikin harabar gidan, Kanwar Hajjiya samira ce ta ce . "Wallahi aunty bada ban gidan abincin nan sabo ba ne da tare zamu tafi ." Faruk ya ce . "Gaskiya ne aunty kuma wallahi bana son mommy ta tafi Nigeria ita kadai , da Najib zai bita su tafi ko a fasa tafiyar sai sabon wata mu tafi tare ." Ya karasa magana yana kallon mahaifiyar shi . "Lallai ma yaron nan tun kafin a haifeka nake zuwa Nigeria na dawo , shi ne yanzu zaka zo min da wata magana ? Shi Najib ba shi da aiki ne da zai bini, yaushe rabon na ga 'yata, kuma kwana daya zan yi kawai ." Faruk ya ce . "To mommy a gaida mana da mahaifin mu da kuma Fatima." Hajjiya Samira ta ce . "Za su ji in sha Allah." Da yaren larabci ta yi magana A lokacin Ahmad ya shigo yana cewa. "Jirginku fa mommy sauran minti 30 ya tashi." zumbur Hajjiya Samira ta yi ta tashi tana fadin . "Bari na dauko jakata ." Ta shige dakinta Faruk ya yi murmushi yana bin mahaifiyar tasa da kallo cikin matukar kauna Tana shiga daki ta ji kanta ya matukar sara mata ga wani jiri yana dibar ta . Da sauri ta samu bakin gado ta zauna tana haki , Ta dafa kirjinta tana cewa. "Innalillahi wa inna..... ." Tai dauriya ta tashi ta zuge jakar tafiyar ta, ta zaro magani ta sha Ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce . "Ya Allah na shekara da yawa banga 'yata ba , ina rokonka da karka kashe wannan baiwa taka ba tare da ka hada uwa da 'ya sun gana ba ya Allah, ka bani dama na kuma ganin Fatima a rayuwa." Ta jayo akwatinta ta fito cikin karfin hali , gudun kar su Murja su fahimci halin da take ciki su hana ta zuwa . Har suka kaita filin jirgi basu iya fahimci komai ba . Allah ya kai ki ga Fatima lafiya Hajjiya Samira . NIGERIA Yau Fatima irin tsumudin da take se Allah, domin tunda satin zuwan mahaifiyar ta ya kama kullum sai irga ake Bari kuma yau da take da tabbacin tana hanya . Ga shi Nasir ya tafi daukota a filin jirgi . Fatima da Zarah suna zaune a falo duk sun kagu da shigowarsu Nasir A wannan lokacin suka ji ana kwankwaso kofa Da gudu Fatima ta mike har da bigewa da kujera da sauri ta bud'e kofar cikin shauki . Tana budewa ba wai haushi taji ba , yake ta yi tana cewa. "Sannu da zuwa Mama."? Wacce ta kira da mama ta amsa tare da shigowa falon .wato Hajjiya Rukayya A lokacin zarah ta kwashewa da Fatima dariya . Alkalamin Autar Marubuta 07040805269 WhatsApp only FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta ____________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing❌ Page 28 & 29 Iso ta yi wa Hajjiya Rukayya ta zauna a falo Yayin da take cewa" basu karaso ba ne Hajjiya."? Murmushi Zarah ta yi tana cewa. "Wallahi basu karaso ba amma suna hanya ai shi yasa nake wa Fatima dariya ta yi zaton su ne ." Ita ma Hajjiya Rukayya dariyar ta yi sannan ta ce . "Hmmm". Fatima ta gashsheta tare da tambayar mutanen gidan, nan ta tabbatar mata kowa lafiya ita ma ta samu labarin zuwan Hajjiya Samira ne yasa ta taho domin mata Oyo yo. Suna cikin hirar ne Nasir ya turo kofa rike da akwati a hannunshi yana yiwa Fatima murmushi. Cikin tashin hankali na farin ciki fatima ta tashi tsaye tana jiran shigowar ta . Cikin wannan'kaguwar ne kawai hawaye suka fara zubo mata, lokacin da Hajjiya ta sanyo kafa zata shigo. Da gudu Fatima ta nufi wajen ta fada jikin Hajjiya Samira, Hajjiya Samira ma cikin kewar gaske ta rike 'yar tata a jikinta Gamm suka rike juna cikin matukar farin ciki , Zarah duk abin ya burgeta ta tashi tsaye ita da Hajjiya Rukayya. " Allah na gode maka ." Hajjiya Samira ta fada da larabci Fatima ta kalli mahaifiyar ta idanunta cike da hawaye tana cewa. "Na yi kewar ki sosai ." Hajjiya ta yi mata murmushi, Nasir ya kalli Fatima yana cewa. "To ga akwatin ta ." Fatima ta juya suka karasa falon tare sannan ta samu ta zauna, Fatima ta jingine akwatin a gefe ta zauna kusa Hajjiya Lullubun dake jikin ta ta cire yayin da take duban yanayin tsarin gidan nasu Sannan tai ajiyar zuciya tana cewa. "Alhamdulillah." Tana hada ido da Hajjiya Rukayya Murmushi hajjiya Rukayya ta yi mana kafin ta ce . "Sannunki da zuwa Hajjiya, fatan kin zo lafiya ." Hajjiya Samira da murmushi ta fara magana tana bata amsa . "Na zo lafiya kalau Hajjiya Rukayya, fatan haka na same ku." "Mommy sannu da zuwa ." Zarah ta fada tana murmushi Hajjiya Samira ta yi ajiyar zuciya tana kallon Fatima da cewa . "Wannan ita ce Zarah, abokiyar zamanki."? Fatima ta ce . " Eh mama ita ce Zarah. " Sannan Hajjiya ta kalli Zarah cikin murmushi tana cewa. "Sannu 'yata Zarah fatan kuna lafiya ."? Zarah ta ce . " Lafiya kalau mommy barka da zuwa ." Hajjiya ta kalli Nasir tana cewa. "Sannu kai ma Nasir, wallahi ka girma, tun muna Nigeria ina matar Alaji lokacin kana dan karami , kana zuwa kana komawa har Hajjiya Amina ta dawo da kai gidan ." Nasir ya yi dariya yana cewa. "Kuma ai ban manta ki ba Hajjiya." Hajjiya ta yi dariya tana cewa. "Kamal kam tunda na ganshi a video na biki duk ya girma ." Hajjiya Rukayya ta yi dariya tana cewa. "Girman dan mutum ba wuya ai ." "Ina Hajjiya Binta da kuma sauran yaran ."? Mahaifiyar fatima ta tambayi Hajjiya Rukayya Bayan ta bata amsa Ne ta dora da cewa . " Amma dai wata guda zaki mana ko hajjiya domin an juma ba a haduba ." Hajjiya Samira ta yi dariya tana cewa. "Wata kuma ana zaune kalau , ai jirgin gobe zan koma Saudiya in sha Allah." Fatima cikin matukar rashin jin dadi ta ce . "Goben lafiya kuma Mama, yaushe rabon ki zo gaskiya a'a." Hajjiya Samira ta kalli Fatima tana fadin . "Gobe kuwa in sha Allah, daman ke na zo gank kuma ga shi na ganki to ai shi ke nan , to shi Faruk ma cewa ya yi kar na zo ." "Gaskiya mommy baza mu bari ki tafi gobe ba ." Cewar Zarah Fatima ta ce . "Gaskiya kam domin akwai guraren da zaki je har gidansu Zarah." Hajjiya ta ce . "To ai a goben ma zan iya zuwa , amma bazan wuce kwana biyu ba ." Hajjiya ta ce . "To ai kuwa idan na koma zan sanar da Hajjiya Binta ta zo ku gaisa karki tafi baku hadu ba." Fatima ta tashi tana jayo akwatin cikin bacin rai ta nufi dakinta tana cewa. "Gaskiya ba za ki tafi gobe ba ." A lokacin kamal ya turo kofa ya shigo , yana nufo falon ya hada ido da sirikar tashi Ya saki wani murmushi mai matukar kayatarwa . Nan suka gaisa ana ta hira a kamo can a kamo can Abin dai ya yi Bayan d'an lokaci kuma Hajjiya Rukayya ta koma gida . Bayan an yi sallar isha'i nan ma dai suka ringa hira kala-kala Lokacin da Hajjiya Rukayya ta koma gida take sanar da Hajjiya Binta cewa gobe Hajjiya Samira zata koma ai ko hakan yasa ta ce gobe da safe zata gidan su gaisa. Misalin 12 na dare sunata hirarsu cikin farin ciki, a yi dariya a yi dariya a kamo can a kama can . Abin da ya matukar ruda musu hankali suna cikin hira Hajjiya Samira ta yi dif idanunta suka kakkafe Nan hankali kowa ya tashi sukai kanta Zarah ta bara dubata "Amma tana da ciwon zuciya ne ."? Cewar Zarah ta yi tambayar ga fatima cikin tashin hankali Fatima ma cikin wannan tashin hankali ta kalli Zarah tana cewa. " Tana dashi Zarah. " Zarah ta kalli Kamal tana cewa. "Karku damu mu tafi asubiti yanzu, domin babu wani kayan aiki anan ." Kafin ka ce komai Nasir har ya dauko mota suka nufi asubiti. Suna isa aka bawa Doctor Zarah Sale daki tare da kayan aiki . Hankali na Fatima ya matukar tashi hakan ya sa ta fara kuka "Haba mana Fatima ki yi hakuri zata samu lafiya karki damu dan Allah." Kamal ya yi magana yana rike hannayenta Fatima kawai ta kauda kai ta cigaba da kuka Kamal ya yi ajiyar zuciya yana kallon kofar dakin da aka shigar da Hajjiya Samira. Nasir ma ya matukar damuwa sosai da halin da ake ciki . Duk jiran tsammani suke . Masu abu da abun su doctor Zarah ce ta fito daga dakin tare da wani doctor Ahmad Murmushi ta sakar musu tana nufa wajensu Suma duk kanta suka yo , duk da sun ga tana murmushi amma hankalin su bai kwanta . "Ya jikin Mama Zarah."? Fatima ta tambaya cikin matukar son jin amsa Murmushi Zarah ta yi tana cewa . " To mene na kukan kuma , ta fa samu lafiya ." Doctor Ahmad ne ya kalli Zarah yana fadin . "Bari na kira nurse a canza mata daki zuwa dakin hutu." Ya fara tafiya Zarah ta dakatar dashi da cewa . "A'a dactor Ahmad, ba wani tsanani bane dan haka baza mu kwana a asubiti ba , zamu tafi gida ." Dactor ya ce . "To shi ke nan dactor." Ya wuce ya tafi Nasir ya duba agogon hannunshi yana cewa. "Yanzu karfe 1:35 fa , dare ya yi ." Fatima ta kalli Kamal tana cewa. "Tom ya kamata mu tafi ." "Amma Zarah babu damuwa idan muka koma gida ." Zarah da jin tambayar ta Fatima ta yi wani murmushi na kasaita kafin ta ce. "Kin manta wace ni , dactor Zarah babu abin damuwa in sha Allah." Fatima ta kauda kai da takaicin yadda ta samu amsar a gun Zarah. Bayan sun dawo gida misalin karfe 2 daidai ne Hajjiya Samira ta ce . Su barta a falo domin bata jin bacci Haka suka so ta kwanta ta yi bacci amma ta ki Har asuba ta yi tayi sallah, ta zauna a falon tare da carbi A lokacin Fatima ta shigo, yayin dasu Kamal suka dawo daga masallaci. Hajjiya ta kalli Fatima tana cewa. "Fatima tafiyata fa na nan yau zan koma saudiya." Kafin Fatima ta ce komai ma . Kamal ya fara cewa . "Haba mommy ta ya zamu barki ki tafi saudiya ko baki da gata ai sai haka , gaskiya babu inda zaki je." Murmushi hajjiya ta yi tana cewa. "Duk na tada muku da hankula amma ina baku hakuri ." Lokacin zarah ta shigo tana ajiyar zuciya da cewa . "Haba mommy duk muna kaunar ki , babu wani abu a ciki , Allah muke fatan ya baki lafiya kawai ." Cikin jin dadin yadda Fatima ta ji maganar Zarah ta kalleta tana fadin . "Na gode Zarah, kin yi mini komai bazan manta da hakan ba ." Wata harara Zarah ta dokawa Fatima tana cewa. https://chat.whatsapp.com/BxsOc6eKfrTAE5lgAlJQHQ FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta _______________________________________ Editing❌ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< https://www.facebook.com/profile.php?id=61550626300848 Page 30 & 31 "An ce miki ke ce kawai kike son mommy ne ." Hajjiya ta yi murmushi hira sukai ta yi har gari ya waye . Zarah ta kawo abinci aka karya sannan ta danko magunguna ta bata . Fatima ta ce . "Gaskiya kishi nake duk kinbi kin rike mini mommy komai ke kike mata ." Zarah ta yi dariya tana cewa. "Wallahi Fatima ina kaunar mommy a cikin jini na ." Kamal ya yi murmushi Nasir ne ya tashi tsaye yana cewa. "Bari na shirya na tafi makaranta, mommy Allah ya kara miki lafiya ." Ta yi murmushi ta ce. "Amin ." Ya wuce daki domin shiryawa . Kamal shima ya tashi tsaye yana cewa. "Mommy bari naje gidan Alajin mu na dawo ." Hajjiya Samira ta ce. "To Allah ya tsare dan Allah ka gash she mini da Hajjiya Amina sosai d sosai ." Kamal ya ce. "In sha Allah zata ji , domin ma ba dadewa zan ba yanzu zan dawo in sha Allah." Sannan ya kalli Fatima yana cewa. "Ai da kin shirya na aje ki , tunda Zarah karfe 9 zata fita har ma kin dawo ki zauna da mommy." Fatima ta ce. "A'a kaje kawai Allah ya tsare , sukai sallama ya tafi." Zarah ta kalli Fatima tana cewa. "Yau kina da aiki ne daban ."? Fatima ta ce . " A'a zanje bada basu takardu ne kawai asa mini hannu ." "Okay to kije ki shirya , zan shirya na jira ki , idan kin dawo na tafi asubitin ." Cewar Zarah Fatima ta ce . "To." Tana tashi tsaye Hajjiya Binta ta shigo da sallama. Duk ran Fatima kawai ya baci Zarah ce ta amsa sallamar, yayin da Hajjiya Binta tana hango Hajjiya Samira ta taho da gudu tafa fadin . "Oyoyo oyoyo Hajjiya ta ." Ta rungume Hajjiya Samira dake zaune cikin karfin hali. Murmushi ta sakar mata suka fara gaisawa , Fatima ta tabe baki ta nufi dakinta . Zarah ta gaida Hajjiya Binta yayin data fara kwashe kayan abincin da suka ci tana kaiwa wajen da ya dace . A lokacin Fatima ta fito suka gaisa da Hajjiya Binta, har wani soyyaya take nuna mata wai dan ta ga a gaban mahaifiyar ta ne . Fatima kuwa abin duk kona mata rai yayi ta kalli Hajjiya Samira tana cewa. "Mommy bari naje yanzu zan dawo in sha Allah." Ta ce ."To Fatima Allah ya tsare ." Fatima ta fita . Nasir yana shirin tafiya makaranta ne wayar shi ta fara ringin yana dubawa ya yi murmushi ya daga tare da karawa a kunne . "Hello dan Alaji ka fito ke nan , nima ina hanya ." Daga can bangaren Nasir yaji abokin nashi yana cewa. "Kai gaye sha zamanka wallahi professor ba zai zo ba nima ka ganni ina gida ." Nasir ya kwashe da dariya yana cewa. "Alhamdulillah naji dadi wallahi ka ce kawai mu huta ." Daga can ya ba shi amsa da cewa . "Eh wallahi sai mun hadu kawai ." Nasir ya kashe wayar yana murmushi yana cewa. "Ahhhhh yau ba lecture ai kawai bacci zan ." Ya hau gado tare da wayarshi . Anan falo kuwa Hajjiya Binta tana ta yiwa Hajjiya Samira hira ba tare da tasan ma bata da lafiya ba . Lokacin Zarah ta shigo tana cewa. "Mommy bari na shiga ciki na shirya kafin fatima ta dawo ko kina bukatar wani abin ne ."? Hajjiya Samira ta kalli Zarah tana cewa. " Bana bukatar komai 'yata Allah yayi miki albarka. " Zarah ta yi murmushi ta nufi sashinta Shigowar kira na biyar ke nan wayar Nasir, Abba Alaji ya dame shi da kira Nasir ya girgiza kai yana cewa. "Zan koya maka hankali Abba." Kira na 6 yana shigowa Nasir ya daga ya kara a kunne . "Hello Nasir wallahi yanzu zan shigo gidanku yunwa nake ji Allah." Wani 'bacin rai ne ya daki zuciyar Nasir yayi ajiyar zuciya yana cewa. "Abba kai wanne irin bakin maye ne mara ilmi mara zuciya, jahili kawai , to wallahi na rantse maka idan ka taka kafa kazo , zan maka rashin mutuncin da tunda ubanka ya haife ka ba a taba maka ba ." Yana gama maganar ya kashe wayar ya kwanta cikin bacin rai Suna cikin hira Nasir ya turo kofa Ciki da mamaki hajjiya Binta ta kalleshi tana cewa. "Kai kuma lafiya Abba wajen wa ka zo a wannan gidan." Abba Alaji ya sosa keya yana cewa. "Wajen Nasir mana ai a bokina ne ." Hajjiya Samira da hankalinta bai kwanta dashi ba ta kalleshi tana cewa. "To ai Nasir yana makaranta." Abba Alaji ya dubi lungun-lungun gidan sannan ya lura da inda dakin Nasir yake sakamakon lokacin da ya shigo dashi da dare "Bari in shiga na duba ." Ya sha ta gabansu Ya nufi dakin Nasir Hajjiya Binta ta yi murmushi tana cewa. "To idan ya shiga yaga baya nan ya fito ai ." Hajjiya Samira ta hade rai tana cewa. "Wane kuma wannan." "Yanzu baki gane shi ba , yaron Alaji Sani ne fa yayana ." Hajjiya Samira ta yi ajiyar zuciya Cikin wayantar da zancen Hajjiya Binta ta ce . "To Hajjiya d'an ko mini turare na kinsan kamshi ba a wasa dashi ." Hajjiya Samira ta yi murmushi na yake tana cewa. "Tom bari na shiga ." Ta nufi dakin Fatima inda kayanta suke Doctor zarah ta shirya , rigarta ta likitoci kawai zata sa ta fito . "Uwarka ta yi asarar haihuwa Abba, ta haifo maye kuma annoba mara jin magani , wallahi ina tabbatar maka da iyayenka sun san kai zasu haifa dasun kasheka tun kana ciki . Na ce ka rabu dani ka bar rayuwata haka , amma kaki shege matsiyaci kawai." Nasir yayi maganar cikin matukar hassala Maganar ta batawa Abba Alaji zuciya hakan yasa ya kalleshi yana cewa. "Ni kake fadawa wannan Nasir."? Nasir cikin wata sabuwar fusata ya ce . " Eh din ai takaita ma na yi domin kafi haka , idan kuma ka yi zuciya ka barni har abada. " Cikin bacin rai da bakin ciki da takaici Abba ya juya ya fita cikin mahaukacin yanayi . .............. Zarah ce da Hajjiya Binta kan Hajjiya Samira dake kwance a kasa Cikin tashin hankali zarah ta fara kiran . "Mommy tashi mommy mene ya same ki." Yadda suka ga yanayin nata yasa su matukar tashin hankali Hajjiya Binta ta kwallah kara tana kallon Zarah da cewa . "Shi ke nan kin kasheta , kin kasheta hankalin ki ya kwanta ." Ta rushe da kuka Zarah ta kalli kwalbar turaren da Hajjiya Samira ta dauko daga gefe tana sake fashewa da kuka . Lokacin Kamal ya shigo tare da Hajjiya Amina wato mahaifiyarshi Zarah wani Tashin hankali taji ya ziyartar mata zuciya dajin abin da Hajjiya Binta take fada Da gudu su Kamal suka yo kanta yana tambayar . "Mene ya sameta mommy mene yake faruwa Zarah." "Ta kasheta ta kasheta ." Hajjiya Binta ta cigaba da fada tana kuka Lokacin Fatima ta turo kofa daidai da sanda take maganar Zarah mutuwar tsaye ta yi ta kasa cewa komai kawai hawaye ne suke zubo mata . Da gudu Fatima ta karaso tana jefar da takardun hannunta "Innalillahi mene ya faru da mommy mene yake faruwa." Ta zube a kasa gaban mahaifiyar tata tana kiran sunanta tana jijjigata Zarah ta sake fashewa da kuka Fatima cikin kuka ta kalli Zarah tana cewa . "Mene ya sameta dan Allah Zarah." Kafin Zarah ta bude baki ta yi magna Hajjiya Binta ta sake fadin . "Ta kasheta hankalin ta ya kwanta innalillahi wa inna'ilaihir raji'un ." Fatima ta kalli Zarah cikin wani mummunan yanayi da matukar mamaki , Zarah ta kalli Kamal ta sake fashewa da kuka Sannan ta ce . "Dan Allah kamal mu kaita asubiti bai kamata mu zauna ba ." Ta fadi kasa tana cigaba da kuka Hakan kuwa akai duk suka rankaya asubitin cikin mummunan tashin hankali. Nasir kuwa yana daga daki yake jin komai, saidai tashin hankali ya hanashi fitowa , saida suka tafi asubitin ya hau mota yabi bayansu . Koda suka isa cikin asubiti Zarah bata shiga inda aka aje Hajjiya Samira ba Dactor Ahmad ne cikin kwarewa ya shiga aikin shi Suna cikin tsananin jiran fitowarshi ne , dactor ya fito "Allan da ya baku shi ne ya amsa ina baku hakuri dactor Zarah." Ya karasa maganar sanda Nasir ya shigo , tare kuma da kallon zarah. Autar Marubuta 07040805269 WhatsApp only. wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing❌ Page 32 & 33 Zarah kawai bangon dake gefenta ta fara bi tana zamewa cikin mugun yanayi , Nasir da ya kasa gane lissafin kamar kanshi ya buga yake ji Hajjiya Binta kuwa sai kuka Ita kuwa Hajjiya Amina innalillahi wa innailaihir rajiun take ta ambata . Kamal shiru ya yi yana jinjina lamarin ubangiji Fatima kuwa babu hawaye a idanunta amma tamkar zuciyarta ta fito take ji Karfin hali ta yi ta kalli Kamal tana cewa. "A yanzu komai ya kare Kamal a sanarwa da kowa mu koma gida ." Zarah wani kuka ta ruruce dashi tare da zaucewa cikin wata murya da baza a gane me take cewa ba ta kalli Fatima tana kauda kai tana fadin . "Bani da idanun kallon ki Fatima. Fatima da idanun kallon ki Fatima." Fatima ta fashe da kuka Yanzu Alaji Mustapha da Alaji Mansur suke samin labari Kafin ka ce komai kuwa zance ya isa saudiya. Kowa aka kai masa labarin to zancen Zarah yana shigowa ciki Dactor Ahmad ya tabbatar musu ba ciwon zuciyarta bane ya tashi har yayi sanadin mutuwarta , domin tun binciken farko da suka yi matakin ciwon shi ne dai harta rasu , kuma bai motsa koina ba , bare ya yi sanadinta Nan Hajjiya Binta take tabbatar musu Zarah ce ta bangajeta ta fadi bata motsa ba rai ya yi halinsa Alaji sale hankalinsu ya matukar tashi da samun wannan mummunan labari . Karfe biyu Faruk da Murja,Ahmad da Najib suka iso Nigeria cikin matukar bakin ciki Lokacin da suka zo , suka shigo cikin gidan . Gida kuka wiwi na mutane ,har da su Barrister Khadija. Haka waje karku ji yadda Alaji Mustapha yake kuka abin tausayi. Zarah tana zaune idanunta sun yi jajir , tare da mahaifiyar ta Faruk yana shigowa Fatima ta fada jikinshi tana kuka Lokacin da Ahmad ya shigo ta koma jikinshi tana sake rurucewa da kuka . "Daga kanta ta yi sama tana kallon yadda wata 'yar sanda ta shigo rike da ankwa " Ina Zarah Sale ." Cewar police din Tashin hankali Fatima taji ya sake ziyartarta Ta kalli Zarah tana ajiyar zuciya mai zafi Zarah cikin kuka ta bar jikin mahaifiyar ta Hajjiya Sa'adatu tana tashi tsaye da cewa . "Ni ce ." Tana kuka 'Yarsandar ta karaso gaban ta tare da ware ankwar tana shirin sa mata tana cewa . "Muna zarginki da kisan kai , don haka zamu tafi dake domin bincike ." Zarah kawai mika hannu ta yi , tana kallon mahaifiyar ta cikin mummunan yanayi Hajjiya Sa'adatu ta fashe da kuka tana kiran sunan Allah Fatima ta kasa cewa komai kawai kallon Zarah take Zarah ma tana kallon ta yayin da suka je gaff da fita Zarah ta yiwa Fatima murmushi mai matukar ciwo. Fatima wani abu taji ya daki zuciyarta na bacin rai Kawai ta sake fashewa da kuka A lokacin aka fito da gawar Hajjiya Samira. Gurin ya sake rurucewa da kuka . Ahmad da Najib ma kukan ne ya ke ce musu suka yi waje , suna fita waje nan ma wani tashin hankali ne , domin Alaji Mustapha suma ya yi Faruk sam bai yi kuka ba , saida lokacin da ake sallatar gawarta lokacin ya ringa zuba nashi kukan kamar mai shirin ham'budewa Allah sarki Alaji Mustapha . Kowa haka ne kawai lokaci muke jira , domin mutuwa guda daya ce , sanadi kawai ta tara, Allah ka sa idan karshenmu ya zo mu cika da hasken imani . Haka aka kai gawarta zuwa .... Har dare ya yi wannan gida na Kamal kuka bai ragu ba . Zarah kam tana nan a kulle cikin mummunan yanayi, domin su ma su Alaji sale da su Umar duk hankulansu a tashe suke . Bayan kwana biyu Duk suna dai zaune a falon Fatima suna ta juyayi Ahmad ya ce . "Ba a tara sani ga Allah, mommy ashe ajalinki yana Nigeria da bamu barki kin zo ba ." Cikin matukar tausayi da karayar zuciya ya karasa magana Faruk ya yi ajiyar zuciya ya kalli Ahmad yana cewa . "Gobe zaku shirya mu koma Saudiya, domin zaman mu ba shi da amfani , idan aka yi addu'ar 3 gobe tafiya kawai zami , ita kuma data kashe mana mahaifiya doka zatai aiki a kanta ." Murjanatu ta ce . "To Allah ya kaimu , ai baza ta ci banza ba, sai an kasheta , Allah ya jikanki yayata ." Hawaye suka zubo mata Kamal duk wani yanayi mara dadi yaji ya mamaye shi Fatima ta kalleshi tana cewa . "Kamal a kan wanne dalili ne zarah zata kashe mommy." Kamal da hawaye a idanunshi ya tashi ya nufi daki Ajiyar zuciya Fatima ta yi sannan ta tashi ta bishi Washe Gari Bayan an gabatar da addu'a, su Faruk suka fara shirin tafiya, domin har sun yi wa mahaifin su sallama, nan yaci kuka ya ce su kula da kansu Allah kuma ya basu hakurin rashi. Umar da Faruk da Hajjiya Sa'adatu suna zaune a falo Alaji sale ya fito cikin hanzari daga daki zuwa inda suke . Duk tashi tsaye sukai ganin haka , kafin wani ya ce komai ya fara magana cikin masifa da takama "Wannan wulakancin ya ishe ni, an ce musu bana son Zarah ne , haukan banza dan anga na yi shiru , kuma na yi shiru ne domin naga gudun ruwansu , ni na san Zarah baza tai kisa ba , dan haka yanzu gidan kamal din zani a yita ta kare ." Ya fita harabar motoci , Mahmud da Umar suka bi shi . Bayan su Faruk duk sun shirya , sun d'ebo kayansu daga gidan Alaji Komai ya yi musu daidai domin kawai sallama zasi su tafi Ana wannan lokacin ne suka ji ana kwankwaso kofa Nan suka bada izinin shigowa Kamal yana ganin wanda suka shigo ya tashi ya nufi wajensu . Alaji Sale ya dakatar dashi da hannunshi da kuma karin magana yana cewa . "Ba gurin ka na zo ba ." Kamal yaja da baya ya tsaya cikin matukar mamaki Alaji Sale ya kalli Faruk yana cewa. "Wajen ka na zo wato ma tafiya zaku yi tunda kun fa an rufe 'yar iska mara gata koh." Faruk yaja baya ya jingine akwatin shi yana cewa da Fatima. "Waye wannan."? Fatima cikin hawaye ta ce . " mahaifin Zarah ne ." "Ohoooo ! Wato kaine wanda yarka ta kashe mana uwa ke nan ." Faruk ya fada Alaji Sale ya doka masa tsawa da cewa . "Shiru ! Karka kuma kiran 'yata da ta yi kisa, daman na yi shiru in ga iyakarku , to yanzu komai ya kare ko ni ko koh." Fatima ta fashe da kukan bacin rai da takaici. Haka shima Kamal ya rasa inda zaisa kanshi Faruk yayi murmushi yana cewa. "Komai ya kare kuwa , dole a kashe Zarah yadda ta kashe mana uwa , domin rai bai fi raiba ." Alaji Sale ya ce . "Ni nasan a haife na haife ka , dan haka kawai mu hadu a kotu , zan ga dokar data isa ta kashe mini yarinya." Najib dai basu ce komai ba . "Kana ganin zaka kayo lauyan da zai wanke 'yarka , to ai shi ke nan mu hadu a kotun ." Ya kalli Fatima yana cigaba da cewa . "Fatima zata tsaya mana a kan wannan shari'ar ka je ka shigar da kara duk inda kake so muna jiran sammaci ." Fatima ta sake fashewa da wani kuka mai matukar gwanin ban tausayi tana cewa . "A'a, A'a Yaya faruk bana jin Zarah ta kashe mini mommy, zuciyata ta kasa amsar wannan yanayi, bansan mene ya kashe mommy ba ." Cikin sabon kuka ta cigaba da cewa . "Ni na zauna da Zarah nasanta nasan abin da zata iya . Don haka ku yi hakuri, ni bazan tsaya muku a kotu ba , zan tsaya kare Zarah ne Yaya, zan kare Zarah a kotu shi ne abin da nake nufi ." Dauuu kowa yaji zuciyarshi ta yi bugun mamaki da rashin gane inda maganar Fatima ta dosa. Fatima ta cigaba da kuka A wannan lokacin Ahmad ya dubi Fatima yana cewa. "Ban gane mene kike nufi ba Fatima zaki kare wa ne ."? Fatima cikin wannan kukan ta sake fadin . " Idan har sai an shiga kotu , to ina nufin ku je ku nemi lauyan da zai tsaya muku, amma ni Zarah ..." Kuka ya kuma cin karfinta Babu I zuciyar Faruk da yake jin matukar mamaki na abin da Fatima take fada Shi kuwa Alaji Sale dasu Umar duk jikinsu ya yi sanyi . Murja cikin kishin Hajjiya Samira ta jefawa Fatima kallo tare da tunanin "An ya kuwa Fatima jininsu ce ." 07040805269 Autar Marubuta FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta ________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing ❌ Page 34 & 35 Najib ma wani matukar mamaki ne ya rufe shi dajin zancen yayartashi , Murja cikin mamaki d takaici ta so fara magana amma bata samu damaba sakamakon Alaji Sale da ya fara cewa . "Na gode Fatima, amma karki damu. Ni zan nemo lauyan da zai tsaya mini a wannan shari'a karki damu." Fatima taji ajiyar zuciya tana fadin . "Ka yi hakuri Daddy, amma bazan bari ka kira wani lauyan ba domin ..." Fesssss fessss Fatima ta ji an dauke fuskarta da mari har guda biyu lokaci guda Kamal duk ya rasa me yake masa dadi a wannan rayuwa. Kowa kallon Faruk ya yi da yake huci , dalilin marin da ya ajewa Fatima "Tunda haka kika ce , mu zuba mu gani duk inda zaki je ki dawo mu ne jininki , mun gode da butulci ." Murja a lokacin ta samu damar magana ta fara cewa . "Rabu da ita Faruk , asararriya mara kishin mahaifiyar ta , rashin zaman da kika yi da ita yasa kike jin tamkar ba mahaifiyar ki ba ." Lokacin Fatima ta fashe da wani kuka mai radadin gaske , dajin irin zancen da 'yan uwanta suke a kan ta . A wannan yanayi ta fara magana cikin kuka tana cewa. "Shi ke nan aunty, ku yi duk abin da kuke so ,amma ina so ku sani zan koyi da bayan Zarah , idan kun so ku dauko lauyan da zai sanya a kashe Zarah a zaman farko , ni kuma zan yi iya yina domin bayyana muku gaskiya, cewa Zarah ba tai kisa ba duk da bani da hujja , amma Allah ya sani kuma zai bayyana gaskiya." Faruk ya ce . "To shi ke nan sai mun hadu a kotun , amma ina tabbatar miki karki sake kukan rashin mahaifiya, kuma karki sake tunanin kina da wasu 'yan uwa a wannan duniya." Ya karasa magana cikin matukar zafi da fusata Sannan ya kalli su Ahmad yana cewa . "Ku tashi mu tafi zamu samu gida mu zauna, har zuwa kammala wannan shari'ar ." Wani zafi Fatima taji ya daki zuciyarta dajin cewa zasu bar gidanta Kamal ya fara basu hakuri amma Faruk ya tasa su a gaba tare da kayansu suka bar gidan. Wani kuka Fatima ta sake rude wa dashi tana cewa. "Ya Allah , yanzu mene laifi na dan kawai ina son bayyana gaskiya." Ta kai kasa tana kuka mai matukar ban tausayi Duk su Mahmud suka ji tausayinta ya rufe su , bari ma Nasir da hawaye suke zubo masa . "Allah sarki aunty Fatima, dalilin Zarah dubi halin da take ciki ta rasa mahaifiyar ta kuma 'yan uwanta duk sun tafi sun barta , Allah Ka kawo mana dauki ." Nasir ya karasa maganar a cikin zuciyarshi yana gangaro da hawaye . ..... Kotu ta sanya ranar fara sauraran shari'ar Zarah da ake tuhuma da kisan kai , wannan zance yana matukar yawo a tsakanin masoyan rubutun Zarah Sale Salisu A halin yanzu Fatima tana hanyar zuwa gidansu sakamakon kiran da Alaji Mustapha ya yi mata . Cikin gidan Alaji Mustaphan kuwa Abba Alaji ne zaune a falo shi da Hajjiya Binta. Abba Alaji ansha wasu manyan kaya , har da hula , saidai kayan ba wani kyau sukai masa ba , saboda bai saba sawaba kuma wannan halayyer tashi da 'yan shaye -shaye bai dena ta ba . Hajjiya Binta ta kalleshi d murmushi tana cewa. "Haba kai kuwa Abba wallahi har ka fito ka yi kyau , ai idan ka dore a haka Alaji zai ji dadi ." Abba Alaji akai dariya kafin a ce . "Ai in sha Allah na tuba aunty." Ta ce ."To Allah ya tabbatar. " A lokacin Hajjiya Rukayya ta shigo tana murmushi nan ita ma taji dadin ganin Abba Alaji a wannan yanayin . Daga nan kuma su kai sallama ya tashi ya tafi Nan su Hajjiya suka cigaba da hira yayin da Fatima ta shigo tare da sallama Babu wacce ta amsa mata sallamar a cikinsu Sai Hajjiya Rukayya dake cewa . "To mene kuma aka zo yi mana gida , ai muma yanzu dole mu nisanta dake a kashe mahaifiyarki amma ko a jikinki banza mara ilmi ." Fatima ta sunkuyar da kai cikin rashin jin dadin jin maganar ta hajjiya Rukayya. Hajjiya Binta ma dorawa tai da cewa . "An dai yi asara ma'asaranciya ." A lokacin Alaji Mustapha ya fara sakkowa daga saman bene , yayin da ya hangi Fatima a kasa ne ya dakata da sakkowar yana cewa. "Au Fatima ashe kin karaso to bismillah hawo sama ." Ya juya ya koma , Fatima ta wuce ta barsu suna harararta suna tsaki Tana karasawa saman ta samu guri ta zauna a falo , sakamakon nan ta ga mahaifin nata yana zaune . "Ina yini Daddy."? Ba tare da ya amsa ba ya ce da ita . " Tashi ki hau kujera Fatima. " Babu musu ta mike ta zauna Bayan sun gaisa sai Alaji Mustapha yake cewa . "Da gaske ne kun yi fada dasu Faruk kuma kin zabi kare zarah a kotu ."??? Ya jefa mata tambayar lokaci guda Wani faduwar gaba Fatima ta ji ya ratsa mata zuciya Cikin daburcewa da kame kame ta fara cewa ." Daman Daddy daman .".. Alaji Mustapha ya dakatar da ita cikin gaggawa yana fadin . "Dakata kawai amsata eh ko a'a ce ." Cikin kwarin gwiwa Fatima ta ce . "Eh haka ne ." Ajiyar zuciya ya yi sannan ya fara cewa . "Allah ya bayyana gaskiya ki je kotu ki yi abin da ya dace Fatima, domin ni yanzu na yarda da ke , kuma komai zai wuce Allah ya kare ki ya bada sa'a Allah ya jikan mahaifiyar ki ." Fatima wani farin ciki taji ya rufe ta dajin yadda mahaifin ta ya goya mata baya , Cikin kauna ta kalleshi tana cewa. "Daddy na gode da goyan bayanka , hakan yake nuna tabbatar zan samu nasara , babu wanda ya fahimce duk a cikin su , hakika Daddy ina kaunar 'yan uwana amma yanzu duk sun juya mini baya ." Murmushi Alaji Mustapha ya yi yana kallon Fatima da cewa . "Karki damu Fatima, ai komai lokaci ne , kuma gaskiya zata bayyana karki sa komai a ranki, idan Zarah ce ta kashe mahaifiyar ku , to tabbatar dole za a hukuntata amma Allah ne mafi sanin daidai." Ajiyar zuciya ta yi tana fadin. "Gaskiya ne Daddy , bani da shaidar cewa ZARAH bata kashe mommy ba , amma babban amincin yana daga zuciyata domin Zarah baza ta aikata ba ." Alaji Mustapha ya ce . "Allah ya sa mu dace Fatima.".. Fatima tana komawa gida ta samu kamal a zaune a falo , duk ya wani rame dashi yayi baki kamar ba shi ne ba Murmushi kawai ya yi mata sanda ta yo sallama, saida ta karaso ta zauna sannan ya amsa sallamar. " Daddy yana goyon bayana Kamal, har naji komai zai tafi daidai tabbatar Yanzu na samu kwarin gwiwa." Murmushi ya kuma yi na jin dadin batun nata yana fadin . "Ai Daddy mutum ne mai fahimta Fatima hakika ina alfahari dashi matuka." A lokacin Barrister Khadija ta turo kofar falon tare da sallama Ta karaso Nan suka gaisa da Kamal ta sake masa ta'aziyya sannan ya tashi ya shiga ciki . Nan suka gaisa da Fatima tare da sake mata gaisuwa Barrister Khadija ta kalli Fatima tana cewa. "Duk kin rame wallahi Allah ya jikan Mom." Fatima ta yi murmushi tana gyara zaman rigar jikinta tana cewa. "Amin Khadija, to ya shari'a kin kammala ne ."? Barrister Khadija ta yi ajiyar zuciya tana cewa. " A wallahi. Dama wani zance nake ji da ban gane kanshi ba , zaku shiga kotu sannan kuma kin tsaya domin kare Zarah Sale kin bar 'yan uwanki ." Ta aje maganar tana wurgawa Fatima kallon takaici Fatima ta yi murmushi tare da gyara zama tana kallon barrister Khadija. Alkalamin Autar Marubuta ne FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta ________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing❌ Page 36 & 37 Fatima haka kawai taji ta kasa cewa da Barrister Khadija komai Hakan yasa ta kuma ajiyar zuciya Gani da jin haka ya sa Barrister Khadija cewa . "Okay ashe gaskiya ne ai dole ki rasa abin cewa , amma wallahi kin bawa ahalinki kunya , sannan kuma ina sanar miki Barrister Nuhu suka d'auka , sai ki shirya kare me laifinki da gaske ." Barrister Khadija ta tashi tsaye tana cewa. "Na tafi Allah ya kyauta sai mun hadu a kotun ." Ta fita ba tare da Fatima ta iya cewa komai ba A take a gun Fatima taji wani ciwon kai ya risketa mai matukar radadi Kawai kujerar da take zaune ta kasheta ta fara bacci Anan kuwa Alaji sani ne zaune a falo shi da matarshi Matarshi Hajjiya Nana ta kalleshi da fadin "Wai Alaji yau na ga duk farin ciki ya same ka , ko kuma ma batun yau na kula da hakan ba ." Alaji Sani dariya ya yi yana cewa. "Haba Hajjiya Nana kema dai kinsan farin cikina ba zai wuce Abba ba , kamar yadda bakin cikina ba ya wuce shi ne sula." Dariya Hajjiya Nana ta yi tana fadin . "Wannan haka ne muna godiya ga Allah da ya fara shirya mana shi ." Alaji ya ce . "Ina son yaron nan wallahi Hajjiya, halinshi ne bana kauna amma yanzu alhamdulillah." Hajjiya Nana ta yi dariya tana kallon agogon dake dakin yayin da take kuma sauraran kiran sallar la'asar . Fatima har yanzu tana falo tana bacci a lokacin Kamal ya fito daga daki yana kallon inda take kwance cikin mamaki Da sauri ya karaso ya fara tashinta Lokacin da ya ga ta bud'e ido tana mammatsa idanu tare da dafa goshi ya fara cewa . "Haba Fatima kin san zamu je gurin Zarah, ga shi kwanaki kad'an ya rage shiga kotu amma kin kwanta bacci haba dan Allah idan na rasa Zarah ya zanyi ." Wani abu Fatima taji ya sake tokare mata zuciya cikin bacin rai ta sakko ta tashi tsaye yayin da kanta ya ke sara mata ta fara cewa. "Mene haka dan Allah, kowa ba ya iya fahimta , sanin kanka ne ina cikin tashin hankali kamal na rasa abubuwa da yawah saboda Zarah." Wasu hawaye ne suka zubo mata cikin kuka da karyayyar zuciya ta cigaba da cewa . "Ya zan yi ne dan Allah ni kam ." Shima kamal cikin karyewar zuciya ya rungume Fatima a jikinsa yana ajiyar zuciya tare da cewa . "Yi hakuri Fatima, wallahi ina cikin tashin hankali bana ga ne yanzu waye zan yi wa fada komai na babu dadi Fatima, dan Allah ki yi hakuri." Fatima ta janye jikinta tana cewa . "Bari na shiga na shirya sai mu tafi ." Ta wuce ciki Kamal ya zauna , a lokacin Nasir ya fito daga dakinshi yana isowa falo Yayin da Kamal ya kula dashi ya fara cewa . "Kai dama kana ciki ."? Nasir yayi murmushi yana cewa. " wallahi Yaya Kamal ina ciki , na rasa mene yake mini dadi , shi ya sa na fito domin na tafi gidan Alaji. " Kamal ya ce . "To shi ke nan muma muna nan zuwa ." Nasir ya nufi hanyar fita yana fadin . "To sai kun zo ." Bayan Fatima ta shirya suka nufi police station suna isa barrister Fatima ta tabbatar musu ita ce lauyan da zata kare Zarah kuma tana da bukatar ganinta . Nan DPO ya bada umarnin a fito da ita . Lokacin da aka taho da Zarah, Kamal da Fatima hankalinsu ya matukar tashi ganin wani mugun yanayi da take ciki Da gudu ta karaso gaban Fatima ta zube a kasa tana kuka Fatima cikin matukar dauriya ta sunkuya ta d'agota tsaye Kamal kawai kauda kanshi gefe ya yi yana zubar da hawaye daga bisani ya sharesu ya dawo da hankalin shi gare su "Ki dena kuka Zarah." Cewar Fatima Zarah cikin kukan ta fara cewa . "Fatima Daddy ya zo ya kuma fadan ke ce zaki kareni a kotu , ina cikin mugun yanayi Fatima mara dadi , mommy fa ake zargin na kashe Fatima, dan Allah karki tsaya mini mahaifiya ba wasa ba ce." Ta sake fashewa da sabon kuka Kamal ya share hawayen da baisan ma sun zu bo masa ba A lokacin Fatima ta yi murmushi tana rike hannayen Zarah tana fadin . "Haba doctor zarah, ko kin manta mommy kike kiran mahaifiyar mu , sannan kika bata kulawa yayin da ciwonta ya tashi . Ni kuma kawai sai na zama kamar kowa ? Kawai abin da nake so dake ki samu kwarin gwiwa ina tare dake , ki amsan dukkan tambayoyina Zarah ." Zarah ta sake damke hannayen Fatima tana fara magana . "Wallahi bansan komai ba Fatima, ina zaman jiran ki dawo na tafi asubiti, ina cikin daki na gama shiryawa, sai na fito falo , ina fitowa na ga Hajjiya Binta a kan mommy dake kwance a kasa tana kiran ta tashi tana jijjigata , da sauri naje wajen domin ina tunanin ko ciwonta ne ya motsa ." Zarah ta yi ajiyar zuciya ta cigaba da cewa . "Ina sa hannuna a jikinta , shi ke nan Hajjiya Binta ta fashe da kuka tana fadin na kasheta , har hakan ya yi sanadin zuwana nan Fatima ki dubi halin da nake ciki ." Ta sunkuyar da kai tana kuka Fatima ta kalli Kamal , Kamal ya sunkuyar da kai Fatima ta maida hankali ga Zarah tana cewa . "Zarah mawuyacin abu ne ki kwantar da hankalin ki , ni na sani , amma ina tabbatar miki wannan shari'ar baza tai tsawo ba komai zai bayyana , domin yadda aka shirya komai cikin sauki ne , kuma Hajjiya Binta dole abar zargice ." Fatima taja ajiyar zuciya tana kallon idanun Zarah da cewa. "Bazan ce ki kwantar da hankalin ki ba , idan har wannan kalaman nawa basu sa kin samu sukuni ba ." Zarah ta yi murmushi tana cewa. "Har yanzu kina nan da halinki koh ."? Fatima ta yi dariya ta ce . " Kwarai kuwa dactor Zarah. " Murmushi Zarah ta kuma yi tana kallon fuskar Kamal shi ma ya mata murmushi Bayan Fatima ta gama komai suka dauko hanya suka dawo yayin da suka tsaya gidan Alaji Mansur. Duk suna zaune a falo ,Alaji ne kawai bayanan, domin ita ma Laila ta zo Kamal da Fatima suna shiga aga gaggaisa Fatima ta ce wa mommy. "Mommy ina Daddy na fa ." Hajjiya Amina ta yi murmushi tana cewa. "Baban naki da baya son zama waje guda , ai yanzu haka zaki iya ganinshi ya dawo ." Nasir ya yi dariya yana cewa . "Daddy manya ke nan Allah yaja kwana ." Hajjiya Amina ta ce "Fatima yaushe ne za a shiga kotun ne ? Allah dai ya bayyana gaskiya." Fatima ta yi murmushi na ya’ke tana kallon Kamal sannan ta ce . "Ai mommy komai zai zo da sauki ku ta ya mu da addu'a domin bani da wata hujja a hannu ." Laila ta ce . "Kaiii aunty kuma haka za a shiga kotun ."? Murmushi na ya'ke Fatima ta sake yi sannan ta ce . " In sha Allah Laila ai zamu samu hujjojine daga lokacin da shi lauyan da zai tsaya musu zai gabatar da nashi hujjojin tom zamu samu makama ." Nasir ya ce . "Tabb Allah dai ya temaka .Lamarin naku sai ku aunty, a ce zaku shiga kotu amma vabu hujja ." Kamal dai ya yi ajiyar zuciya tunda dai suka gaisa bai sake cewa komai ba . Laila ta kalli mommy tana cewa. "Wallahi mommy karki ga yadda masoyan Zarah suke matukar damuwa a social media , har wani program nake saurara a gidan redio da suke yi a kanta ." Hajjiya ta ce . "To ya za ai , haka Allah ya so .kowa da irin tashi jaraftar ." Ta kalli Kamal tana sake fadin . "Ka kwantar da hankalinka Kamal karka sa damuwa a rai ta maka illa duk wannan abin masu wucewa ne ." Kamal ya kalli mahaifiyar tashi yana cewa. "In sha Allah mommy." Yayin da suka hada ido da Laila sukai wa juna murmushi. Sannan ya kalli Fatima yana fadin . "Mu koma Fatima." Kafin Fatima ta ce wani abu ne Hajjiya ta ce "A'a dama ba wuni za ku yi ba ."? Kamal ya tashi tsaye yana cewa. " Eh mommy gida muka yi ga shi har zamu tafi Daddy bai dawo ba , a gaidashi ." Hakan ya sa Fatima ta mike , nan sukai sallama sannan suka koma gida . 07040805269 WhatsApp only FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta ________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing❌ Page 38 & 39 A nan suma su Faruk sun shirya tsaf domin tunkarar kotun da za a shiga A yanzu haka suna zaune da Barrister Nuhu suna tattaunawa Murja ce ta kalli barrister da cewa . "Wannan shari'ar zata dau lokaci kuwa barrister."? Barrister Nuhu ya kalli Murja a domin bata amsa . " Banajin hakan matukar ba wani babban lamari ne ya bayyana ba daga su wanda muke kara ." Faruk ya ce . "Gara mu yi mu gama mu bar kasarnan domin Wallahi zamanta ya ishe ni ." Barrister Nuhu ya yi murmushi Su dai su Ahmad babu abun da suke cewa rashin mahaifiyar su ma kawai ya ishe su . ........ A yau aka gabatar da zaman kotu na farko , kotu ta cika ma'kil da al'umma sai dai ba wani fafatawa akai ba alkali ya ce za a sake zama a ranar 17 ga watan da ake ciki . Anan cikin gidan Alaji Mustapha duk iyalan nasa suna zaune ana ta hira domin har su Faruk yau sun kai wa mahaifin nasu ziyara , duk ya yi ya yi dasu kan su dawo gidan su zauna akwai isassun d'akuna amma suka 'ki saida suka je suka kama waje , haka ya hakura da su . Su Habib da Khalid sun yi farin ciki sosai da ganin 'yan uwansu an sha hira an more , sannan suka koma gida . Ranar kotu Daga nan falo Kamal yana zaune yana jiran fitowar Fatima a domin su tafi Cikin cikakkiyar shigarta ta fito ta yi matukar kyau sosai . Kamal ya mike tsaye yana murmushi yana fadin. "Ohhh my life , idan kika sa kayan nan matukar kwarjini ki ke mini wallahi, ina fatan nasara a gare mu ." Fatima ta yi murmushi ta ce . "In sha Allah, mu tafi kar mu makara." Suka shige suka tafi Mutane har sun fara shiga ciki , wasu kuma suna waje , ga 'yan jarida duk sun hallara ,a lokacin ne aka zo da Zarah , babu jimawa alkali ya karaso babu bata lokaci kotu ta fara gudana. Nan Barrister Nuhu ya tashi ya mika gaisuwa ga alkali tare da gabatar da kanshi da mataimakansa . Ita ma Barrister fatima ta mika gaisuwa da gabatarwa tare da abokin aikinta Barrister Muhd Nan alkali ya yi rubutu cikin takardar dake gabanshi sannan ya d'ago yana fadin. "Kotu ta shirya sauraran 'bangarori ." Barrister Fatima da Barrister Nuhu suka hada idanu , sannan barrister Nuhu ya tashi tsaye da wasu takardu a hannunsa ya fara magana lokaci guda ya na mika takardun ga alkali . "Ya mai girma mai shari'a.Dukkan alamu sun nuna Zarah Sale wacce ake tuhuma ita ce ta kashe Hajjiya Samira, sannan daga bangaren lauyan dake kareta babu wata shaida da suka bayyana mana da zata kore haka ." Barrister Nuhu ya gyara tsaiwarsa ya cigaba da cewa . "Ya mai shari'a Hajjiya Samira marigayiya tana dauke da ciwon zuciya, sai dai likitoci sun tabbatar mana wannan ciwon nata bai tashi ba har ta rasu , sannan shaidarmu wacce komai ya faru a gabanta Hajjiya Binta ta tabbatar min yadda komai ya faru kamar yadda za tai wa kotu bayani. Duba da wannan bayanai ya mai shari'a, muna rokon kotu mai albarka da ta biwa Hajjiya Samira hakkinta a domin hukunta Zarah sale." Barrister Nuhu ya matsa kusa da Zarah da take tsaye cikin akwatin tuhuma yana fadin. "Zarah Sale mene ya sa kika kashe Hajjiya Samira."? " Ina da ja ya mai shari'a. " Barrister fatima ta yunkuro ta fada da babbar murya Alkali ya ce . "Kotu ta amsa Barrister Fatima." Fatima ta ce . "Barrister Nuhu yana kokarin razana wacce nake karewa tare da shirin sanya mata magana a baki ." Alkali ya kalli Barrister Nuhu yana fadin. "Ka gyara barrister Nuhu ." Barrister Nuhu ya ce . "To na gode ya mai shari'a." Barrister Fatima ta koma ta zauna Barrister Nuhu ya baro gaban Zarah ya fuskanci alkali yana cewa. "Ina son wannan kotun mai albarka ta bani damar gabatar da shaida ta gaba ." Alkali ya sunkuya ya gabatar da rubutu sannan ya d'ago ya kalli Barrister Nuhu da cewa . "Kotu ta baka dama Barrister." Barrister Nuhu ya bukaci da Hajjiya Binta ta fito zuwa akwatin tuhuma Bayan ta fito ne ya kalleta yana fadin. "Hajjiya Binta shin mene alakarki da marigayiya Hajjiya Samira." Hajjiya Binta ta yi ajiyar zuciya kana ta fara magana . "Ni da ita miji guda muka aura tsawon wani lokaci kafin Allah ya rabamu , ma" ana kafin Alaji Mustapha ya sake ta ." Barrister Nuhu ya ce . "Alhamdulillah kina nufin dai abokan zama ne a dah ."? Hajjiya Binta ta ce ." Eh ." Barrister Nuhu ya ce . "Hajjiya Binta ki sanar da kotu yadda wannan lamarin ya faru har ya kai ga hajjiya Samira ta rasu , wato ma'ana yadda komai ya faru a gaban idonki ." Hajjiya ta gyara mayafin dake jikinta kana ta fara cewa . "A wannan ranar na kaiwa Hajjiya Samira ziyara sakamakon ta zo daga saudiya kuma zata koma da wuri , ana cikin haka sai Fatima ta tafi wajen aiki wanda ita 'yace ga marigayiya Hajjiya Samira, dama shi mijinsu Kamal ban same shi a gidan ba , Sai ya zama babu kowa cikin gidan sai mu 3 , ni da Hajjiya muna hira a falo, har na ce mata ta dauko mini tsarabar turare na , sai ta tashi a domin ta kawomin , Ita kuma a wannan lokacin Zarah ta fito daga dakinta ta tsaya mini a ka tana hararata, sai ga Hajjiya ta fito tare da turaren da taje kawo mini ." Hajjiya Binta ta aje ajiyar zuciya sannan ta cigaba da cewa. "Kawai Hajjiya Samira tana yiwa Zarah magana , sai ta fara mata rashin kunya ta hankad'eta ta fadi . Shi ke nan rai ya yi halinsa Amma na tabbatar cewa ita Zarah batai tsammanin abin zai kai ga mutuwa ba ." Barrister fatima ta yi wani murmushi na takama da mamaki Zarah ta sunkuyar da kai dajin yadda Hajjiya Binta ta tona mata asiri Barrister Nuhu ya kalli alkali yana fadin. "Ya mai girma mai shari'a, wannan shi ne abin da muke son sanarwa kotu , ina rokon wannan kotu mai adalci data gaggauta yankewa Zarah sale hukunci .Na gode ya mai shari'a." Cikin takun isa ya koma ya zauna Alaji Sale ajiyar zuciya ya sauke yana kiran sunan Allah Shi kam Kamal ba a cewa komai. "Barrister Fatima shin kina da abin cewa ."? Alkali ya jefawa Fatima tambaya Cikin girmamawa Barrister ta tashi tsaye tana cewa. " Ina da abin cewa ga Hajjiya Binta ya mai shari'a. " "Kotu ta baki dama." Alkali ya mayar mata Barrister Fatima ta karaso gaban Hajjiya Binta Sannan ta fara cewa . "Ya mai girma mai shari'a, wacce ake zargin Zarah ta kashe da mommy take kiranta , sannan a daren da marigayiya ta zo Nigeria , to ciwon zuciyarta ya tashi kuma Zarah da ake tuhuma ita ce likitan data duba lafiyarta a cikin dare ." Barrister fatima ta gyara rigarta ta cigaba da cewa . "To me yasa idan Zarah tana son kashe Hajjiya Samira bata kasheta tun a asubiti ba? Sai da aka dawo gida , kuma ta rasa yadda zata kasheta sai ta hanyar da Hajjiya Binta ta bada bayani ."? Alaji Mustapha ya girgiza kai tare da cigaba da saurara " Ya mai girma mai shari'a, ina rokon wannan kotu mai adalci data sake komawa baya domin bibiyar wasu zantuka na kuskure da Hajjiya Binta ta yi yayin had'a labarin ta ." "Ina da jah ya mai shari'a." Barrister Nuhu ya yi saurin kai farmaki "Mene Barrister." Alkali ya tambaya Cikin sauri ya fara cewa . "Barrister Fatima tana shirin karya mana hujja tare da danganata da kagaggen labari ." Alkali ya kalli Barrister Fatima yana fadin. "Ki gyara barrister Fatima." Barrister ta yi godiya ga alkali ta cigaba da cewa . "Ya mai shari'a, ina rokon kotu data dubi kyakykyawar alakar dake tsakanin marigayiya da Zarah , domin ko kallan banza Zarah bata ta'ba yiwa Hajjiya Samira ba . Amma ina rokon kotu data bani damar tambayar Hajjiya Binta domin sanin mene ne ya kawo Zarah ta yi wa Hajjiya rashin kunya, wato muna son ta sanar da kotu da wanne irin kalamai Zarah ta yi amfani dasu yayin rashin kunyar da kuma irin martani da ita marigayiya ta yi wa zarah har ya sa Zarah fusata ta bangajeta ." "Ina da jah ya mai shari'a." "Tun da aka ce rashin kunya kowa yasan rashin kunya barrister Fatima na shirin ja mana shari'a ta yi nisa bayan komai ya bayyana." Inji barrister Nuhu Alkali ya ce . "Barrister Nuhu korafinka bai ansu ba ." Alaji Mansur ya yi murmushi na farin ciki yana sake kasa kunne a domin sauraran wannan shari'a Alkali ya kalli Fatima yana fadin. "Kotu ta baki dama ." Barrister Fatima ta yi murmushi tana kallon Hajjiya Binta da cewa . "Kotu na sauraranki Hajjiya kuma malama Binta." 07040805269 WhatsApp only FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta _______________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing❌ Page 40 & 41 Hajjiya Binta kawai ta fara kuka tana kuma shirin fara magana "Ni-ni ni Allah ya sani na shiga tashin hankali." Ta kuma fashewa da kuka harda majina "Na shiga rudani babu abin da zan iya tunawa." Wani takaici Barrister Fatima taji ya sokar mata zuciya ta kalli Hajjiya Binta tana cewa "Kotu na sauraran ki ." Hajjiya Binta ta cigaba da kukan ta Lokacin Fatima ta baro gabanta ta fuskanci alkali tana cewa. "Ya mai shari'a Hajjiya Binta akwai wani abu da take boyewa kotu , sannan wannan kotu ta tuna cewa babu babu kowa cikin gidan sai su biyu . Amma ya mai shari'a me yasa ZARAH ce kawai zata zama abar zargi , shin ita Hajjiya Binta kotu ta yadda da ita ne ? Hajjiya binta muna da bukatar ta bude baki ta yi wa wannan kotu bayani. Amma hakan ya gagara , da haka nake rokon wannan kotu mai adalci data sake bamu lokaci a wani zaman domin samun hujjoji ga wacce ake kara .Na gode ya mai shari'a." Ta yi godiya ta koma ta zauna "Lauyan wanda yake kara kana da ta cewa ."? In ji alkali Barrister Nuhu ya ce . " Eh ya mai shari'a. " Ya nufi gaban Zarah yana cewa. "Shin Zarah kuna da 'yar aiki a gida ."? Zarah ta kalli Fatima, sannan ta ce ." A'a babu." "Me gadi fa ."? Ya sake jefa mata tambayar Zarah tai ajiyar zuciya ta kuma cewa . " A'a babu ." "To me ya sa babu ? Bayan da cewa duk mazauna gidan fita kuke yi , sannan akwai motoci akallah guda shida a cikin gidan amma babu mai bude get ." Zarah ta kalli barrister Nuhu tana cewa. "Bamu da ra'ayinsu hakan ya sa bamu d'auka ba .Kuma mene alakar wannan da shari'ar."? Barrister Nuhu ya kalli alkali yana cewa. " Na gama ya mai shari'a. " Ya koma ya zauna Bayan alkali ya yi rubutunsa ya d'ago yana cewa. "Wannan kotu ta d'age shari'a zuwa kwana uku, a tare da hakan wacce ake tuhuma Zarah Sale za a maida ita zuwa gidan gyaran hali kafin sauraran shari'a ta gaba." Alkali ya fad'a tare da mikewa Kuka Zarah ta fashe dashi tana kaiwa kasa , yayin da Mahmud yaji matukar tausayinta ya sake rufe sa , sai da yaji wasu hawaye sun gangaro masa Haka Fatima dauriya kawai tai duba da dandazon mutane , ga 'yan jarida , ga shi bata da wata hujja da zata tunkari kotu a zama na gaba . Bayan Kamal ta bi da ya fice waje , domin ya ga an yi waje da Zarah za a sata a motar gidan yari wacce aka kawota a ciki . Kawai kuka ya fara yana rungume mahaifin shi Alaji Mansur, Alaji Mansur wani yanayi na matukar tausayin d'an shi yaji ya fara keta masa zuciya. Lokacin Fatima ta karaso inda suke , babu annuri a fuskarta ko kad'an "Fatima yaushe shari'ar nan zata kawo karshe ."? Alaji Mustapha mahaifin ta ya yi mata tambayar Sai da taja dogon numfashi sannan ta kalli Kamal , kana ta kauda kai cikin tsananin tausayinshi ta kalli Barrister Nuhu da yake tsaye can nesa dasu Faruk suna zantawa ta ce . " Barrister Nuhu na yi shari'a dashi sosai Daddy , koda yaushe ni nake nasara , amma bai taba karaya ba , a wannan karan yana tafe sosai domin ya karbi bangare me saukin hukunci ." Wani tashin hankali Kamal ya sake rufe masa zuciya da jin kalaman Fatima harda kuma hawayehawaye "Ban ce Nasara baza ta samu ba Baba amma koma mene zai faru zama na gaba kotu zatai hukunci, domin ba shari'a ce me sarkakiya ba ." Alaji Sale ta kalla cikin rurucewa da kuka tana sake fadin . "Idan kotu ta yankewa Zarah hukuncin kisa , sai dai mu daukaka kara." Fatima ta tsuguna kasa tana kuka , wani firgici ne ya ziyarci kowanne su , babu kamar Alaji sale da Kamal Kamal ya saki hannun mahaifin shi ya durkusa gaban Fatima yana kuka "Kina nufin kin karaya kuma Zarah kasheta za ai."? Idanunshi sun yi jajir Fatima ta kalleshi cikin matukar damuwa ba tare da tana da niyyar cewa komai ba Alaji Mustapha ne ya durkusa ya jawo hannunshi suka taso Sannan ya kalleshi yana cewa . " Ka yi hakuri dan Allah Kamal , duk muma fa muna cikin wannan tashin hankalin, ita shari'a ai mace ce me ciki , ba a san mene zata haifar ba , Allah ya kaimu zama na gaba kawai mu cigaba da addu'a Allah zai bayyana gaskiya. " Alaji Mansur ya ce . "Wannan gaskiya ne ." Kamal ya zare hannunshi ya nufi mota Haka kowa ya kama hanya aka koma gida . Yana sauran kwana 1 za a koma kotu Kamal duk yabi ya sake lalacewa dashi Fatima tana zauna a falo Ta zurfafa matuka cikin tunani domin har Nasir ya shigo ya zauna bata sani ba A lokacin ya yi ajiyar zuciya yana cewa. "Aunty Fatima lafiya kuwa." Fatima ta kalleshi ba tare da ta ce komai , sannan Nasir ya sake fadin "Na shigo baki sani ba kina ta tunani haka." Ajiyar zuciya ta yi sannan ta gyara zama tana cewa . "Gobe za a koma kotu Nasir, bani da wata hujja, bani da kwarin gwiwa, dole rayuwata baza tai mini dadi ba ." Nasir shima ya yi ajiyar zuciya yana cewa. "Aunty, akwai abin da zan fada miki , wata kila ya zama wani abin daban ." Da sauri Fatima ta kalleshi tana cewa. "Ina jinka Nasir." Ajiyar zuciya ya kuma ajewa me zafi sannan ya ce . "A ranar da abin nan ya faru aunty Fatima ina gida babu inda naje , ina tsoron zama abin zargi shiyasa ban yi bayani ba , amma wallahi bansan komai game da mutuwar mommy ba duk da ina cikin gidan." Da sauri Fatima ta gyara zama tana fadin . "Karka damu Nasir ka sanar dani duk wani abu da ya faru wanda ka sani , kuma wanne dalili ne ya hanaka zuwa makaranta a wannan ranar bayan ka tafi ." Nasir ya fara mata bayani filla- filla kamar yadda take da bukata . "Haba Alaji dan Allah yanzu haka gobe za a koma kotu , kana gani wannan yarinyar tana wani tsare Hajjiya Binta da tambayoyi harda rashin mutunci a kotu ." Hajjiya Rukayya ta fada tana kallon Alaji Mustapha Ita kam Hajjiya Binta kawai ta sunkuyar da kai "Ya kamata a yi wani abu akai Alaji amma wannan bai kamata ba , kuma duk fatima tana zargin Hajjiya Binta ne da zata kashe hajjiya Samira .Amma ka yi shiru akai ." Ta karasa maganar ta Alaji Mustapha ya kalli Hajjiya Rukayya Sannan ya fara cewa . "Idan zaki ja da shari'a ne ga hanya , banda rashin hakuri irin naki ki bari gaskiya ta bayyana mana, kuma fatima babu wani abu da ta yi ko kece abin da zaki ke nan ." A lokacin ne Habib da Khalid suka shigo Hajjiya Rukayya ta ce . "Ai shi ke nan ." "Kotu ta shirya cigaba da sauraran bangarori ." Cewar alkali Barrister Nuhu ya kalli Barrister Fatima Barrister Fatima ta jefa masa murmushi😇 Autar Marubuta ce 😤 FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta ________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing❌ Page 42 & 43 Barrister Fatima ta tashi ta nufi wajen Hajjiya Binta dake cikin akwatin tuhuma Sannan Barrister ta kalli alkali tana fara cewa . "Ya mai girma mai shari'a, kowa ya sani sanda aka kashe hajjiya Samira mutum biyu ne cikin gidan, amma ya mai shari'a wannan a zahiri ke nan ." Alkali ya sake gyara zama yana sauraran Barrister Fatima, tare da kowa hankalinshi yana wajenta . "Ya mai girma Hajjiya Binta ta boye mana cewa Nasir yana cikin wannan gidan , a baya da haka ma d'an gidan yayan ita Hajjiya Binta ya shigo cikin gidan yayin da wannan kisan yake gafff da faruwa." Wani firgici ne ya mamaye zuciyar Hajjiya Binta, taji duk ta rude ta razana Babban tashin hankalin ta ma saida Barrister Fatima ta matso kusa da ita tsoronta ya bayyana a zahiri "Malama Binta me yasa kika boyewa kotu wannan.Bayan kin sani sarai wannan ya sake tabbatar wa akwai abin da kike boyewa kotu." "Ina da jahh ya mai shari'a." Barrister Nuhu ya yi hanzari ya fada Alkali ya kalleshi da cewa . "Kotu ta baka dama." "Barrister Fatima tana son dawo mana da shari'a baya ya mai shari'a, tare da shirin sanyawa Hajjiya Binta maganar da bata da tushe cikin bakin ta ." Barrister Nuhu ya 'kar'kare Alkali ya mayar masa da cewa . "Barrister Nuhu kotu guri ne na sauraran bangarori , ka bar barrister Fatima ta fito mana da abin da take son kotu ta sani ." Barrister ya koma ya zaunazauna Fatima ta kalli alkali tana cewa . "Ina rokon wannan kotu mai adalci data bani dama domin fito da babbar shaidar nuna cewa dan Hajjiya Binta yaje wannan gida domin kare inkaren barrister Nuhu ." "Kotu ta baki dama ." Alkali da babban murya ya fada Nan Nasir ya fito ya tsaya, tun a gida kamar yadda Fatima ta bukaci kar yaji tsoro komai ya tsaya cikin kwarin gwiwa , haka Nasir ya tsaya babu wani tsoro a tare dashi Sannan ta matsa kusa dashi tana cewa . "Malam Nasir shin mene ne tsakanin da Kamal ."? Nasir ya ce . " Shi yayana ne kuma gidansa nake zaune ." Fatima ta ce . "Alhamdulillah, kana nufin wannan kisan ya faru kana gidan ke nan ."? Wani tsoro ne ya ziyarci Nasir dajin wannan magana ta Fatima Yayi saurin fara cewa . " A'a ba haka nake nufi ba. " "Zaka iya sanar da kotu abin daka sani a wannan ranar , bayan kuma kana da lecture a makaranta, amma ka kasance a gida ." Ajiyar zuciya Nasir ya yi sannan ya fara magana . "A wannan ranar kowa na gidan ya sani har ita marigayiya Hajjiya Samira cewa zanje makaranta, domin a gaban idanunsu na tashi na tafi dakina a domin shiryawa , bayan na fara shiri sai ga kiran aboki na yake tabbatar mini professor bazai zo makarantar ba . Hakan yasa na fasa zuwa makaranta kuma nayi farin ciki da hakan Ina kwance a daki sai ga kiran wayar abokina wanda shi kamar d'an yake gurin Hajjiya Binta yake sanar dani cewa zai zo wai yana jin yunwa . Ni kuma nace kar ya zo amma yace sai yazo ." Ajiyar zuciya ya yi sannan ya dora. "Na fada masa zan masa rashin mutunci idan ya zo , amma saida ya zo hakan yasa ban fasa yi masa rashin mutunci ba ya fita cikin fusata , wanda babu jimawa na jiyo kuka a falo, amma ni sam bansani ba cewar ma Hajjiya Binta ta zo wannan gidan ." Barrister Fatima ta kalli Nasir tana cewa . "Nasir kotu zata so taji wanne dalili ne yasa baka son zuwan wannan abokin naka ."? Nasir ya ce " Saboda ya sha sa na rasa damammaki na cigaba a rayuwata, karatu na wanda sanadinshi aka kore mu a makaranta, sannan yayana Kamal ya bani dama ta karshe , shi yasa nake gudun wannan abokin nawa domin gina rayuwata. " Fatima ta yi murmushi tana cewa . "Kana son sanar da kotu ba abokin kwarai bane ke nan ."? Nasir ya ce . " Haka ne domin har shaye-shaye yana yi." "Mene sunan abokin naka ."? Ta tambaya A takaice Nasir ya ce . " Abba Alaji. " Barrister ta yi murmushi ta kalli alkali ta fara magana "Ya mai girma mai shari'a, ina fatan wannan kotu mai albarka ta fahimci wannan sako na Nasir, Hajjiya Binta tana falo Abba Alaji ya shigo , sannan tana falo ya fita , babu jimawa kuma kisan ya faru ." Ta kalli Hajjiya Binta tana cewa. "Shin ko ke da Abba Alaji kuka kashe Hajjiya domin wata manufar."? Cikin matukar hassala da babban murya Barrister Nuhu ya ce . "Ina da jah ya mai shari'a. Barrister Fatima tana yunkurin juya wannan lefi ga Hajjiya Binta har ma ga dan yayanta ." Ya kalli Nasir yana cewa . "Malam Nasir kana shaye-shaye."? Nasir ya ce . A'a ko cigare ban taba sha ba." "To me yasa kake son cinnawa abokin ka wuta har kake kiran yana fita wannan kisan ya faru , shin kaima ba abin zargi bane ."? Nasir kamar yadda yaji jan kunne na Fatima kan karya ji tsoro ya fara magana cikin kare kai " Ita Hajjiya Binta shaida ce , tunda ta zo bata ganni ba , har Abba Alaji ya shigo ya fita bata ganni ba ko da wasa , ta ya kuma zanzama abin zargi bayan wacce aka kashe tana tare da ita ." Wani murmushi fatima ta saki najin dadin yadda Nasir ya bada amsa lokaci guda kuma tana kallon ZARAH Sannan ya koma gaban Zarah yana cewa . "Shin kina ina sanda wannan yaron ya shigo ."? Zarah tai ajiyar zuciya mai zafi kana ta ce . " Ina cikin daki, sannan ban ma taba ganin shi ba , kawai sunanshi..." Barrister Nuhu ya dakatar da ita da cewa" kin bani amsa ta ". Sannan ya yi godiya Barrister ya koma ya zauna Fatima ta kalli Hajjiya Binta tana cewa. "Zaki iya fada mana dangane da shigowar Abba Alaji cikin gidan, shin ya hadu da Hajjiya Samira ko ya akai."? Wani yanayi ne mai matukar wuya ya rufe Hajjiya Binta, kowa yana hangar wannan yanayi na tashin hankali a tare da ita " Kotu na sauraran ki ." Fatima ta sake tunatar da ita Wani takaici ne ya rufe Barrister Fatima hakan yasa ta kalli alkali ta fara maganar da ta sake tadawa Hajjiya Binta hankali. "Ya mai girma mai shari'a Hajjiya Binta tana tsoron bayyanawa kotu cewa ita ta kashe Hajjiya Samira, wanda nasan da cewa da tasan Hajjiya Samira ciwonta ya tashi ,lokacin da ta zo Nigeria to da wannan zata fake , amma rashin sanin hakan yasa ta dorawa Zarah Sale kazafi na kisa. Me yasa kika kasheta."? " Ina da jah ya mai shari'a. " Barrister Nuhu ya fada Kotu taki amincewa da jansa Hakan ya sa Hajjiya Binta ta fara kuka tana cewa. "Wallahi ba haka bane akan mene zan kashe Hajjiya Samira, babu abin da ta yi mini duk da cewa mum yi zaman kishiyoyi, ni wallahi bazan iya kasheta ba ." Barrister Fatima ta ce. "To me yasa kike tsoron sanar da kotu cewa Abba Alaji shi ne ya kasheta. Tun da bake bace , shin kina tsoron a kashe shi ne ."? Sabon kuka ta sake fashewa dashi Tana cewa. " A'a A'a ya mai shari'a, Abba Alaji ya shiryu. Bani da burin da ya wuce naga wannan yaron ya samu rayuwa mai kyau , shima haka mahaifin sa . Kwarai da gaske Abba ya shigo a wannan ranar ." Cikin sabon kuka ta sake cewa . "Ya shigo a wannan ranar , muna zaune da Hajjiya a falo Kai tsaye ya shige dakin Nasir, Ni kuma a wannan lokacin nake cewa hajjiya ta bani turare na , Ta shiga ciki domin ta dauko mini . Da wowarta ya yi daidai da fitowar Abba daga dakin Nasir cikin fusata ya bangaje Hajjiya Samira ta fadi." Nan kowa zuciyarshi ta fara bugun .... "Da sauri na nufi gunta , amma bata iya ko bude idoba , hakan ya bawa tunani cewa ta mutu . A ranar naga tashin hankali a idanun Abba wanda ban taba gani ba Ya ringayi mani magiya kan na rufa masa asiri daga yau ya dena komai ya tuba , Hakan yasa na amince ya tafi , saboda ko ba komai d'ana na daukeshi ." Wani kuka take kamar mai shirin shidewa "Hakan ya sa na nemi mafita , nasan da cewar Nasir baisan abin daya faruba , A wannan yanayi sai Zarah ta fito , shi ke nan na dora mana wannan laifi domin samin salama ta da Abba Alajiiiiiii." Ta kai kasa tana kuka Dactor Zarah wani yanayi ne ya rufeta kawai ta fara kuka Kotu aka barke da hayaniya , caaaaaa shaaaa wannan ya ce wannan ya mayar masa . Alkali ya bukaci a yi shiruuuushiruuuu 07040805269 WhatsApp only Autar Marubuta FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta ________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing❌ Page 44 & 45 Bayan kotu ta yi shiru , kawai kukan Hajjiya binta kawai ake ji Zarah kuwa hawaye take Nan alkali ya bada sammacin kawo Abba Alaji a duk inda yake Aiko yana gida mahaifin shi yana shirin su tafi filin jirgi domin Abba zai koma makaranta, basu kai ga tafiya ba Aka kamo Abba Alaji aka taho kotu , nan Hajjiya Nana da Alaji Sani hankali su ya tashi suka biyo bayansa. Ana shigo da Abba Alaji ya kalli Hajjiya Binta yana cewa. Cikin kuka "Wato saida kika bayyana komai , bayan kin yi mini alkawarin rufa mini asiri , wannan ita ce soyyaya da kike mini ,bayan na shiryu na dena kin yaudare ni ." Kotu ta sake barkewa da ka ce, na ce , alkali ya bada umarnin shiru Nan kotu ta karantawa Abba Alaji irin tuhumar da ake masa, nan ya amsa laifinsa bisa kuskure Hankulan jama'a suka sake tashi sosai Barrister Fatima ji take kamar ta fesawa Hajjiya binta mari domin wani abu take jin ya tsaya mata a zuciya Su kam su Faruk yau gasu ga makashin mahaifiyar su kawai hukunci suke jiran kotu ta yanke . Zarah kukan farin ciki take yi da bakin ciki a hade, Kamal kuwa zuciyarshi cike da zumudi Nan Alkali ya fara gabatar da irin tuhumar da aka yiwa Zarah Sale Nan ya tabbatar wa al'uma kotu ta wanke Zarah Sale bisa wannan zargi da ake mata , sannan kotu ta sallameta . Abba Alaji bisa wani shashi na kundin tsarin mulki aka yanke masa hukuncin zama a gidan yari har karshen rayuwarsa . Sannan Hajjiya Binta bisa kazafi na kisa data dorawa Zarah Sale Duba da wasu shashin kundin tsarin mulkin kasa Alkali ya tabbatar mata da dangwama a gidan yari har karshen rayuwarta . Sannan alkali ya sallami wannan shari'a tare da wanda bai yadda da wannan shari'a ba yana da damar daukaka kara cikin watanni uku . Khalid kuka ya fashe dashi na matukar tashin hankali dajin irin wannan hukunci da aka yankewa mahaifiyar shi . Da gudu Zarah ta nufi mahaifiyar ta da mahaifin ta tana rungumesu cikin wani kuka mai karya zuciya A wannan lokacin wasu zafafan hawaye suka zubowa Fatima sanda ta tuna da mahaifiyar ta Kamal kuwa duk ya rasa inda zaisa kanshi farin cikin da yake ciki Alaji Mustapha da Alaji Mansur ba a cewa komai Suna gani aka sanya Hajjiya Binta a motar gidan yari tana kuka, Alaji Mustapha ya kauda kanshi, yayin da ya hangi Khalid cikin mugun yanayi Kawai ya tsinci kanshi shima cikin wannan yanayi Alaji Sani abin ya yi masa yawah ga danshi ga kanwarshi , duk yabi ya susuce , to sai dai Allah baya dorawa mutum jarabawar da zata fi karfin shi . 'Yan jarida kuwa sai neman labarai suke , sai dai samm basu samu damar magana da Zarah ba . Haka Fatima bata saurare su ba Lokacin da Fatima take kuka ne Kamal ya rike hannunta A lokacin su Faruk suka fito daga cikin kotun suka wuce ta gabansu "'Yan uwana .'! Fatima ta fada cikin muryar kuka Su faruk suka dakata ba tare da sunce komai ba Cikin wannan yanayin ta ce . " Ina kaunar ku , bani da sama daku , duk shari'a ta gaskiya nake bi hakan yasa nake yin nasara." Faruk ya sa kai ya wuce , suka bi bayanshi suka tafi Fatima ta sake fashewa da kuka tana cewa Kamal. "Ina kaunar su sosai ." Kamal ya mata murmushi yana cewa. "Suma suna alfahari dake , kuma zaki gani ." Ta masa murmushi cikin kuka Sannan ta ce . "Mu tafi gida kawai domin nasan Alaji sale tare da Zarah zasu tafi sun yi kewarta ." Kamal ya kuma yi mata murmushi sannan suka wuce suka tafi Alaji Mustapha ya matukar shiga wani yanayi, haka kowa na cikin gidan, Hajjiya Rukayya ma abin yana matukar dukanta Khalid ya matukar zautuwa haka Habib ba a cewa komai Haka su Alaji Sale suka wuce gida cikin matukar jin dadi , Mahmud da Umar farin ciki ya ishe su . Washe Gari da wajen karfe 12 Sai ga Alaji sale da Hajjiya Sa'adatu da Umar, Mahmud da Zarah sun nufo gidan Kamal Ai kuwa Nasir da kamal duk suna gida Bayan su Alaji sun shigo sun zauna aka gaggaisa cikin farin ciki da wasa da dariya Sannan Fatima ta kalli Zarah tana cewa. Cikin harshen turanci "Barka da dawowa likitan zuciya." Kowa murmushi ya yi , Zarah tai dariya sannan ta ce . "Hmm abin dai kamar mafarki a karshe gaskiya ta bayyana ." Fatima tai murmushi tana fadin . "Ai karki damu ki aikata duk abin da kike so." Dariya kowa ya yi sannan Zarah ta ce . "Kar dai ki cika mini baki naje nayo kisa ki barni a ciki ." Dariya Fatima ta kwashe da ita sannan ta ce. "Allah dai ya kyauta Allah ya jikan mommy na ." Wasu hawaye suka gangaro mata Zarah ta tashi ta koma kusa da ita , kana ta rike hannayen ta tana cewa. "Ina matukar baki hakuri Fatima, ina jajanta rashin mommy, dan Allah ki yi hakuri amma ai muna da wata uwar." Zarah ta karasa maganar tana nuna mahaifiyar ta tana murmushi Murmushi Fatima ta yi sannan ta had'a ido da Hajjiya Sa'adatu cikin wannan hawaye . Hajjiya Sa'adatu ta fara mata murmushi tana fadin . "Haka ne Fatima, ki dauke ni uwa , domin kin yi mana abin da bamu da abin da zamu biyaki .." "Haba ,haba mommy dan Allah." Fatima ta fada tana share hawaye "Zarah ce ta fara komai , ta kula mini da mommy matuka , hakan yasa zan iya sadaukar da komai a domin ce to ta dan Allah kar ku yi mini godiya." Ta aje maganar tana kallon Alaji Sale Nasir ya yi murmushi yana kallon Kamal, kamal ma ya maida masa da murmushi na farin ciki. Alaji Sale ajiyar zuciya ya yi sannan ya dubi Fatima ya fara mata magana . "Bani da komai da zan biyaki Fatima, hatta kalaman da zan nuna miki matsayinki a guri na bani dasu , ki gafarce ni." Murmushi Fatima ta sake yi tana kallon Zarah, Zarah ma ta maida mata da murmushi tana cewa. "Wallahi Fatima ina kaunar ki matukar gaske dan Allah ki yafe mini duk abin dana yi miki wanda baki ji dadi ba." Dariya Fatima ta yi tana cewa. "Jibeta dan Allah." Nasir da yanayin ya masa dadi ya yi dariya A lokacin aka fara kwankwaso kofar falon . Kafin kowa ya yi motsi aka fara kallon -kallon domin basa tsammanin zuwan kowa a halin yanzu Nasir ya tashi ya nufi kofar a domin budeta Yana bud'e wa ya ga Faruk ya fara shigowa , yana shigowa ya kalli falon ya gansu duk a zaune suna kallon shi Lokaci guda kuma suna had'a ido da Alaji Sale. Fatima ta mike tsaye Sannan su Ahmad dasu Murja ,Najib suka shigo Kamal ya tashi ya nufi wajensu yana musu nuni dasu karaso Suka kalli juna , sannan suka nufo falon , Duk suka zazzauna , yayin da kujerun suka cika ne babu gurin zama shi kuma Faruk yana tsaye . Alaji Sale ya kalleshi tare da matsawa gefe yana ce masa "Faruk karaso ka zauna ga guri ." Ya kalleshi tare da tuna irin sa'insar da sukai kafin shiga kotu , sannan yayi ajiyar zuciya tare da duba agogon hannunshi ya nufi wajen shi ya zauna. Autar Marubuta FATIMA DA ZARAH🎀 Na Autar Marubuta _______________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Editing❌ Page 46 & 47 ________the end Sannan ita ma Fatima ta zauna tana kallon kowanne su , shiru aka yi kowa yanata sake-sake cikin ransa Jin wannan shirun yasa Faruk ya kalli Fatima ya fara magana cikin sanyin rai . "Ba ke ba ce lauyan mu , amma tamkar ke ce kika bamu kariya . Bawai nufin mu shi ne tozarta Zarah ba , muna cikin radadin da yunwar rashin mommy hakan yasa idanun mu suka rufe ." Alaji Sale ya yi murmushi yana sake kasa kunne "Komai ya faru cikin fushi ,hakan yasa na zo neman a fuwarki Fatima ki yafe mini da abin da ya faru ." Murmushi Ahmad ya yi na farin ciki yana kallon Najib Fatima ta kalli murja kana ta maida ido ga yayan nata tana cewa. "Babu abin da kayi mini Yaya faruk, ni ce na yi muku laifi dan Allah ku yafe mini ." Murja ta ce . "A yanzu muna matukar alfahari dake Fatima wancen rudanin muna cikin yanayi ne . " Fatima ta ce . "Karki damu aunty na , komai lokaci ne , kawai na shiga damuwar rashin ku da rashin mommy a lokaci guda amma tunda kun dawo gare ni komai ya wuce ." Ahmad ya ce . "To alhamdulillah Fatita." Ta masa murmushi Sannan Faruk ya kalli Alaji Sale dake gefenshi yana fadin "Ina mai baka hakuri bisa rashin jituwar da ..." Alaji ya dakatar dashi yana cewa . "Baka yi min komai ba, domin duk wani d'an na gari shi ne abin da zai yi a kan iyayensa , kuna da kanwa jaruma babu abin da kuke bukata ." Murmushi Faruk ya yi a karon farko kana ya ce "Na gode Allah Allah ya sake had'a kan mu ." Suka had'a baki suka ce . "Ameen ." Lokacin Murja ta ce . "Tom mufa daga nan zamu wuce saudiya domin har gidan Alaji mun biya mun yi sallama." Kamal ya ce . "A haba dai aunty a yau kuma ."? Ahmad ne ya fara ba shi amsa da cewa . " In sha Allah kuwa nan da mintina jirginmu zai tashi ." Zarah tai murmushi tana cewa. "Dan Allah Yaya faruk ku yafe mini idan nayi muku laifi ." Murmushi ya kuma yi a karo na biyu yana cewa da Zarah. "Ba ki mana komai ba Zarah, mune zaki gafarta ." Murja ta ce . "Haka ne ." Zarah ta kuma fadin . "Hakika kuna da 'yar uwa ta musamman. Fatima mutuniyar kirki ce ." Fatima tai saurin cewa . "Ai ban kai ki ba ." Zarah ta galla mata harara Faruk ya tashi tsaye hakan yasa zugar shi duk suma suka mike , sannan kowa da kowa ya tashi Lokacin Alaji Sale yake cewa. "Ya kamata ku zauna mu yi addu'a." Kowanne su ya zauna sannan suka gabatar da addu'a har aka sanya mahaifiyar su, suka yiwa annabi salati suka shafa . Sannan suka tashi Fatima ce tace . "A gaida mini da kowa dan Allah, su Abu Junaid da Habibullah da Hafiz da kowa da kowa gaisuwa ta ta isa gare su kafin na zo ." Murja ta ce . "Zasu ji insha Allah." Alaji Sale ya ce . "Ai zamu zo saudiyan in sha Allah zamu kawo muku ziyara ." Faruk ya ce . "To Allah ya kawo ku muna ta zuba ido." Sannan duk suka rankaya suka fita , Nasir ya hau mota guda a domin kaisu filin jirgi, nan aka sake sallama suka wuce . Shima Alaji nan suka hau motarsu suka koma gida Bayan... Yau Burin Nasir ya cika , karatun da ya jima yanayi domin a bud'e masa company yau Allah ya tabbatar, domin yau aka gabatar da taron bude wannan company Bayan sun dawo gida suka zazzauna a falo , Nasir ya shige ciki Sai gashi ya fito da katuwar jakarshi yana cewa "Tunda mafarkina ya zama gaskiya yau zan koma gidan Alaji." Duk suka zuba masa idanu a tare "Lallai ma yaron nan tun yau zaka koma ."? Cewar Kamal Nasir ya yi dariya mai cike da farin ciki yana cewa. " Tabbas kuwa Yaya zan koma kusa da mommy, daman karatu ne ya kawoni tom yau nima na zama babba zan koma gida ina maka godiya Yayana." "Ka bari sai gobe mana ka karasa shiryawa ." Fatima ta fada Nasir ya kuma dariya yana cewa. "Ai na gama shiri aunty tun jiya wallahi, kawai gida zan yi yau ." Kamal ya yi dariya yana cewa. "Har ka bani tausayi ka bari mu zo mu kai ka mana ." Dariya Nasir ya kumayi yana fadin "A'a Yaya kusha hutunku , domin nima mata biyu zanyi wannan rayuwar taku tana burgeni , mata biyu zan auro nima ." Kamal ya tabe baki yana cewa. "Kunji shi , to wallahi kar ma ka fara domin matan ba haka suke ba , ni ne dai kawai Allah ya za'ba ya bani su , ka bari idan Zarah ta rubuta labari a kan mu , idan matan sun yi sanyi sai ka auro gudu 4 ma ." Dariya duk suka kwashe da ita dajin zancen na Kamal Nan Nasir ya wuce ya tafi suna masa fatan alheri . Zarah ta kalli Fatima tana cewa. "Yanzu mun zama jini daya aunty Fatima, babu sa'insa ." Fatima ta yi murmushi tana cewa. "In sha Allah Zarah ta ." Kamal ya rungumosu a tare yana cewa "Ina alfahari daku matana fiye da rayuwata." Suka had'a ido sukai murmushi Bayan wasu shekaru Zarah ce ta fara haifowa Kamal mace , wacce ta ci sunan Hajjiya Samira marigayiya. Sannan ita ma Fatima ta sunlubo tata 'yar wacce aka sawa Suhaila Shima Nasir tun tuni ya yi aure har matarshi ta haifo 'yan biyu Mace dana miji Na mijin yaci sunan mahaifin shi , yayin da macen ta samu sunan mahaifiyar Kamal , wato Hajjiya Amina . Haka gidan Kamal ya cigaba da kasancewa cikin farin ciki da kwanciyar hankali, wadata da girmama juna a tsakanin su . ALHAMDULILLAH... Komai ya yi farko zai karshe da ikon Allah Anan ni Autar Marubuta na kawo karshen wannan kagaggen labari nawa mai suna FATIMA DA ZARAH. Godiya ga dinbin masoya a duk inda suke masu yin sharhi , Allah ya bar kauna. Ina fatan sake kasancewa daku cikin wani sabon labarin nan bada jimawa ba in sha Allah. A bin da ya faru na daga kuskure Allah ya ganar dani , wanda ya faru sanadin karancin ilmi Allah ya haska mini a nan gaba, Allah ya bada ikon daukar darasin dake cikin wannan labari. To anan zan barku ni Autar Marubuta na ke cewa Allah ya sada mu da alheri.🙏 07040805269 WhatsApp ____________________________💔