An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels %%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 1 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . . SHIMFIDA Ilham bata san yau ne ranar da mijinta Ma'aruf zai bar duniya ba." . Sun tashi barci lfy kamar kullum. Ya je masallaci ya yi sallar asubahi yana dawowa sai ta ga ya dauko jakarshi ya fara xuba takardunshi na aiki yana sauri. Tun kafin ta tambayeshi inda yake shirin tafiya, ya fada mata cewar yana so ne zai koma Katsina inda yake aiki. . "Ba jiya ka dawo ba, ko ka mance ne yau fa asabar, sai jibi litinin zaka koma da safe." . Ma'aruf ya dakatar da matarsa Ilham ba tare da ya juyo ya kalleta ba." . "Manaja ne ya kira ni a waya ynxn nan wai wani aikin gaggawa ya taso. ya ce in yi sauri in koma Katsina yana son gani na." . Ilham ta 6ata ranta, sbd lkc-lkc irin wannan aikin gaggawar ya kan taso wanda yake sa mijinta Ma'aruf ya tsallake ya barsu a gida ya koma Katsina inda yake aiki a hukumar wutar lantarki ta qasa. Yana sashin gudanarwa ne a hukumar matsayin muqaddashin manajan shiyyar cikin birni. A duk sati ya kan yi kwana hudu a Katsina, sannan sai ya dawo Malumfashi inda gidan sa yake....inda iyalinsa suke. Matarsa Ilham da 'ya'yansu biyu Khairat da Aiman yayi kwana uku tare dasu. . Wadannan kwanaki uku da Ma'aruf yake dawowa gida ya yi tare da iyalinsa' sune ranakun so a wajen Ilham . Juma'a....Asabar.....lahadi..... Sau da yawa ta kan yi fatan xuwan qarshen mako. . "Don Allah juma'a ki yi sauri ki zo." . Sbd a ranar ne mijinta Ma'aruf yake dawowa gida ya same su, suyi ta murna da tsalle ita da 'ya'yansu. Duk sanda zai koma a ranar litinin da safe sai kuma duk farin cikin su ya koma su shiga damuwa. . "Dan Allah litinin kada ki zo." . Idan zai tafi sai ta kamo hannun Khairat babbar 'yarsu, wacce ke da shekaru hudu, sannan ta dauki Aiman a kafadarta su hadu su duka su rako Abba kamar yadda 'ya'yanta suke kiran mahaifinsu. Har xuwa inda yake ajiye motarsa a harabar gidan . "Ku cewa Abbanku sai ya dawo." . A lkcn ne Ma'aruf zai kamasu daya bayan daya ya daukesu, yana yi masu wasan rarrashi da maganganu don kada suyi kuka idan sun ga ya shiga mota ya tafi. . Ilham ba zata iya jurewa ba yau da wannan tafiyar gaggawa da ta tasowa Ma'aruf mijinta. sbd tayi zaton a wannan makon zai zauna tare dasu ya yi kwana ukun da ya saba yi. Ya koma ranar litinin da safe. Bata yi zaton zai koma yau da sauri haka ba daga kawai yayi kwana daya. . Ma'aruf ya gama shirya takardunsa da yake buqata a cikin jakarsa. Ilham tana tsaye tana kallonsa. Ya gama daukar komai har da mabudin motarsa ya juya ya dubeta a lkcn da ya dauki jakar zai fita. . Bai sa rai yau zata iya yi masa murmushi ko kuma ta dauki jakarsa ta kama hannunsa suyi bankwana ba." bai sa ran yau zata iya rakashi har inda motarsa take ba a can waje...kusa da qofar shigowa gidan...bai sa rai yau zasu rabu yana dariya tana dariya ba." sbd ya san in har bata son su rabu to bata da qwarin guiwar da zata iya jurewa ta saki jikinta ta bar abin a xuciyarta. . Ya san idan ya tafi a nan zai barta a dakinsa....ko kuma ta fita falo ta zauna ta yi tagumi. Ko ta fita can bayan harabar gidan inda suke da shuke-shuke tayi zamanta akan kujera. Yau Ilham wunin zata yi a cikin damuwa, don kuwa bata yi zaton wannan tafiya ta gaggawatunda sassafe zata bijirowa Ma'aruf ba." . Bayan ya fuskanceta sai ya ce da ita. . "ki yi haquri Maman Aiman, duk da ban san me yasa manaja ya ce in je in same shi ba, ina sa ran ba wani aiki bane mai wahala da zai daukemu wani dogon lkc. Anjima da yamma zzan dawo inshaa Allah. Bai fi in yi awa biyar a can ba." . Ma'aruf yayi dariya ganin yadda Ilham ta 6ata ranta bata so ya tafi....bata so su rabu. Sbd qaqqarfar soyayya da shaquwar dake a tsakaninsu. Ilham bata ce masa komaI ba." idan ta ce masa bata damu ba tayi qarya. . Ma'aruf ya juya ya tafi, ya fita ya barta cikin sauri har ya je inda motarsa take Ilham tana nan a daki bata motsa ba." tana tunanin sai yaushe Ma'aruf zai mayar dasu Katsina tare da 'ya'yanta su zauna a can ya daina xuwa yana dawowa? . Sai da ya shiga motar ya tayar da ita. Sannan ta fita waje ta tsaya a bakin qofar tana kallonshi. A lkcn ne Khairat ta fito daga dakin barci tana kiran mahaifiyarta Ilham . Ta kunno kanta waje ta kama jikin mahaifiyarta, suka qurawa Ma'aruf ido, a lkcn ne shima ya juyo ya kallesu yana a cikin motar. Ya daga masu hannu. Ilham ta dan saki ranta kadan, 'yarta Khairat ta dagawa mahaifinta hannu tana sanye da rigar barci fara, kanta zane da kitson (Calabar) . Su duka biyun suka taru suna kallon mutumin da ba zasu sake zama tare dashi ba daga wannan ranar...kamar yadda shima ba zzai sake ganinsu ba...ba zai sake zama tare dasu ba har bada..... . . . Lp=2%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 2 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn Ishak (madun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Kamar yadda shima ba zai sake zama tare dasu ba har abada. . Ilham ba ta ce da mijinta Ma'aruf ya sauka lfy ba kuma bata tambayeshi abin da ta san suna buqata ba a gidan kafin ya dawo, ba don bata yi masa ladabi ba." sai don kawai tana so ta riqa nuna masa damuwarta qarara a Kodayaushe na barin su da yayi a garin baya zama Kullum. Me zai hana shi ya mayar dasu Katsina, tunda dama can ne garin su? . Bayan zaman aure, ta san zata zauna a kusa da 'yan uwanta....qawayenta da kuma 'yan uwan mahaifinta. Sbd a can aka haifeta. . Ma'aruf bai damu ba ya tuqa motarsa ya fita daga gidan ya hau titi. Yana sa ran zai dawo, bai san cewar har abada ba zai sake dawowa gidan sa ba." Ilham ta kama hannun 'yarta khairat ta janyeta suka koma cikin gida. Da shigarsu ta saki ranta kamar babu abin da yake damunta. Ba da 'ya'yanta take fushi ba, da mahaifinsu take fushi. Ma'aruf ne yayi mata laifi gashi kuma ya tafi. Ba ta san abin da zai faru ba shi yasa bata tsare shi sun yi magana ba...ba su yiwa juna bankwana ko da kallon qarshe ta yi masa ba." Ilham ba ta san cewar yau ne ranar da mijinta Ma'aruf zai bar duniya ba." . . . *** *** . A haka ya kama hanya yana tuqi yana tunanin rayuwa shi kadai a cikin motarsa. Lkc ya yi da ya kamata ya dauke iyalinsa su koma Katsina don hankalinsa ya kwanta. Bai ta6a ganin laifin matarsa Ilham ba akan damuwar da take nunawa idan zai tafi ya barsu ba." ya san irin zuzzurfar soyayyar soyayyar da ke tsakanin su." musamman idan suna zaune tare da 'ya'yansu biyu suna kira a falo ko kuma idan suna cin abinci. . Khairat tana xubo surutu cikin gwarancinta suna yi mata dariya. Ko kuma idan Aiman yana qoqarin jawo wani abu suna kai hannu suna hana shi. . Ma'aruf ya yi nisa a tafiyarsa, ya wuce Mai gora. Ba a jima ba ya zo ya wuce Dayi. Ya wuce marabar Musawa kafin ya kai Jiqamshi ne yazo daidai wani qaramin qauye wanda yake da qarancin mutane a gefen titi ya iske wata doguwar motar jigilar man fetur ta lalace a tsakiyar titin, ta kashe rabin titin baki daya dole sai wata motar ta tsaya sannan idan wasu sun zo su ke wucewa. . Ma'aruf bai lura da babbar motar ba sai da ya qurace ta, ya dago kai ya kalleta kamar an jefo masa ita. Ya yi saurin taka burki a lkc guda. Har sai da tayoyin motar suka yi kuwwa a titi. Kafin ya samu nasarar tsayar da motar ne, ta cimma bayan doguwar motar tankin. Ma'aruf ya yi salati a tsorace sanda motarsa ta cusa kanta a bayan babbar motar, ta tarwatse hade da wata qara mai furgitarwa. Abin da Ma'aruf kawai zai iya tunawa kenan, amma sauran abin da ya biyo baya bai sani ba." . Ya dai farfado ya samu kanshi kwance a wani fili kusa da ciyayin dake a bakin titin, mutane sun zagaye shi sai surutai suke yi kowa yana fadar albarkacin bakin sa cikin jimami da tausayawa da kuma tsoro. Wani Dattijo ya ce....' . "Da qyar muka samu muka 6an6aro shi daga jikin sitiyarin motar, duk haqarqarinsa sun karairaye. Muna gama ciroshi motar ta kama da wuta tare da tankin." . Wani mutum ya ce....' . "kamata ya yi a hanzarta kai shi asibiti." . Wani ya ce....' . "An gano ko'ina yake kuwa?" . Wanda ya yi magana da farko ya ce....' . "Mun duba duk aljifansa bamu samu wani abu da zai taimaka mana ba wajen gano inda yake. Da wayarsa da takardunsa duk suna a cikin motar sun qone." . Wani a cikin mutanen ya sake cewa. . "Don Allah a taimaka a samu mota a tsayar da wani ya kai shi asibiti. Ku duba halin da yake ciki, yana buqatar taimakon gaggawa." . Ma'aruf bai sake jin komai ba tun daga wannan lkc. Baya iya motsa ko'ina a jikinsa. Kuma bai san inda ya samu rauni ko karaya ba." bai san ko a wane hali yake ciki ba." . Ba a dade ba mutanen da suka zo wajen da hadarin ya faru, suka dauki Ma'aruf a mota suka tafi dashi asibitin Musawa, amma kuma duk wanda yaga halin da yake ciki sai dai ya kawar da kai ya yi masa addu'a kawai. Sbd Ma'aruf ya samu karaya a kusan ko'ina na jikin sa. . Motar da ta tafi da Ma'aruf ta bar daidai wajen da hadarin ya faru a daidai lkcn da motocin biyu suke ci da wuta rigi-rigi. Mutanen da suka tsaya taimako suka yi dandazo daga baya suna kallo. Titin ya cunkushe babu damar xuwa ko dawowa sai dai wadanda suke yi ribas suna komawa inda suka fito. . Motocin da suka fito daga Katsina xuwa malumfashi ko kuma motocin da suka fito daga Malumfashi xuwa Katsina. . . *** *** . . A can gida Ilham ta ji ta kasa samun sukuni a xuciyarta tun bayan tafiyar mijinta Ma'aruf. Ta ji haka kawai Ma'aruf yana bata tausayi. Me yasa sanda zai fita bata saki ranta sun dan yi wasa da dariya ba, me yasa tayi fushi suka rabu cikin damuwa? . Har bayan awa daya da tafiyar Ma'aruf Ilham tana zaune a falo ta kasa tashi ta yi wani aiki. Ta ji duk jikinta ya mutu. Tana jin Aiman yana ta kuka a daki amma ta kasa tashi ta je ta daukoshi. Tana ta kallon Khairat na ta kaiwa da komowa ta zo ta hau jikinta ta kira sunanta. . "Mama." . Ilham ta dafa kan 'yarta ta kira sunanta. . Ilham ta dafa kan 'yarta ta kira sunanta itama. . "Ya aka yi ne Khairat?" . Ta dauketa ta dora akan kujerar dake a falonsu. Khairat ta rabu da mahaifiyarta ta mayar da hankalinta akan hotunan mahaifinta adanda suke cikin (Frames) masu ban sha'awa an kafe su a kowanne bango na falon. . Ilham ta kai hannu kan (Tv stand) dinta ta dauko wayarta ta nemo lambar wayar Ma'aruf don ta kira shi ta ji muryarsa....don ta bashi haquri ta nuna masa ta saki ranta, sbd shima ya saki nasa ran tunda dai yana can xuciyarsa tana cike damuwar halin da ya barta. . Ta kira wayarsa ta ji a kashe. Abin ya bata mamaki sbd ta san Ma'aruf baya kashe wayarsa don yana cikin mota, ko akan hanya yake idan ta kira shi zai dauka ya fada mata yana mota ne, ya fada mata garin da yake, ya fada mata zai kirata idan ya sauka. . Ilham ta yi murmushi da ta yi zaton ynx haka Ma'aruf ya kashe wayarsa ne don shima ya bata haushi tunda ya san dai dolene ta kira shi kafin ya kai Katsina. Bata sake kiransa ba." ta rabu da shi, tana ran idan ya bude wayar shi da kanshi zai kirata ya fada mata ya isa Katsina lfy. . Koda a ce ma ya dauki wayar dama maganar da ta saba fada masa idan yana kan hanya, zata fada masa a halin ynxn. . "Don Allah Abban Aiman ka tafi a hankali kada ka yi gudu. Allah Ya sa ka sauka lfy." . . . *** . An kai Ma'aruf asibitin Musawa, har xuwa lkcn bai san inda kanshi yake ba." lkcn da aka dorashi akan gadon marasa lfy ka gungurashi xuwa dakin 'yan hadari ne ya farfado a karo na biyu. . A lkcn ne ya yi qarfin hali ya bude baki da qyar ya fara qoqarin yin magana jini yana xubo masa ta hanci ta baki. Ma'aruf ya kama rigar daya daga cikin mutanen da suka kawo shi asibitin. . Ganin haka sai suka dan saurara don su ji ko zai iya yin magana ya fai ko shi mutumin ina ne?" Ma'aruf ya ce da wanda ya riqe wa rigar. . "...ku je Malumfashi.....ku sami matata....ku fada mata na yafe mata....kuma ina sonta." . Mutanen da yake bar wa wasiyyar suka tambayeshi. . "zaka iya tuno lambar wayar matar taka?" . "A wacce unguwa kake a Malumfashi?" . Ma'aruf bai samu damar iya amsa masu ko daya cikin tambaoyin da mutanen suka yi masa ba. Ya yi tari jini ya xubo. Ya yi kalmar shahada ya sake maimaitawa. Tun daga nan bai sake cewa komai ba." jikinshi ya yi laushi ko'ina ya daina motsawa. . Mutanen da suka taimaka suka kawo shi asibitin basu yi gaggawar nemo wani likita a cikin ma'aikatan asibitin ba, sbd sun san wannan mutumin da basu san ko wanene ba ya rasu tun kafin likitoci su amshe shi. . . . Lp=3%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 3 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafIn ba." . Sbd sun san wannan mutumin da ba su san ko wane ne ba ya rasu tun kafin likitoci su amshe shi. . Mutanen suka yi cirko-cirko suna tunanin abin da ya kamata su yi. Ina zasu fara xuwa? Kuma wa zasu damqawa wannan gawar tunda dai su hanya kawai ta biyo dasu inda aka yi hadarin suka taimaka suka kawoshi asibiti? . Kowa ya yi ta xubar da hawaye a cikin su." mutane suka zagaye gawar Ma'aruf suna tambayar ko wane ne?" amsa daya ce kowa zai iya bayarwa akan shi. . Kafin ya rasu ya ce shi mutumin Malumfashi ne a nan jihar Katsina. Ya ce a je a samu matarsa. A fada mata ya yafe mata kuma yana sonta. . Ma'aruf ya rasu yana begen matarsa Ilham . . *** . . Ynx Ilham ta gama yi wa yaranta wanka, ta share dakin barci da falo ta gyara ko'ina. Ta hada shayi ta xubawa 'yarta Khairat ta dauka. Ilham ta hada nata har zata kur6a sai kuma ta ji tunanin Ma'aruf ya sake fado mata a rai. Ta fi so ace yana gida su zauna a falo su karya kumallo tare da 'ya'yansu. . Da ace wannan tafiyar bata bijiro masa ba, da ynx yana nan a gida tare dasu a halin ynx. Jiya da daddare yake fada mata cewar tunda yau yana gida, zasu je sabon layi su gaishe da wani mahaifin abokinsa wanda yake fama da jiki. . Da wannan xiyara da zasu kai Ilham ta kwana a xuciyarta. Ta kwana biyu bata shiga cikin garin ba." shi yasa tun sanda Ma'aruf ya tashi ya ce zai tafi Katsina Ilham ta rasa me yake yi mata dadi. . Ta yi fushi ne, shi yasa ta qi tsayar dashi ya karya. Ta rabu dashi ya tafin...xuciyarta cike da damuwa. . Ilham ta ji ta kasa shan shayin. Ta ji ba zata iya cin komai ba a yau. To amma ba anjima da yamma Ma'aruf ya ce zai dawo ba?" indai ba wani abu zai tsayar dashi ba ta san ba zai wuce qarfe hudu da rabi xuwa biyar na yamma ba." . Ilham ta tabbatarwa kanta yau ba zata ci komai ba, sai Baban Aiman ya dawo..." . Ta yi wanka ta kunnawa su Khairat kallo, suka zauna a falo tana yi wa Aiman wasa. Ilham ta shiga daki ta kwanta ta dauki waya ta ci gaba da qoqarin sake kirawo Ma'aruf mijinta amma ko sau daya ba ta same shi a wayarsa ba." a kashe take. . Ta san ynx ya kai Katsina. To me yasa ya qi bbude wayarsa, ko cajinsa ne ya qare? Ilham ta rubuta masa saqo (tsxt) cikin sauri. . "Ina fatan ka isa lfy. Don Allah ka kira ni idan ka kunna wayar...ina son ka Baban Aiman." . Ilham ta karanta saqon ta tura masa tana murmushi. Tana kwance akan gadonsu na aure. . "Allah Sarki Baban Aiman. . Abin da Ilham bata sani ba shi ne, a lkcn mijinta Ma'aruf ya kai awa guda da rasuwa. . , Ma'aikatan asibitin musawa suka hadu da mutanen da suka zo da Ma'aruf wanda ya rasu tun kafin a yi masa aiki. Amma dole sai an je an fadiwa 'yansanda sun turo mutanensu don su ganewa idanun su, sannan a yi qoqarin daukar mota a kai shi Malumfashi tunda kafin rasuwarsa ya ce a can yake. . A ka je aka sanarwa Jami'an tsaron dake a garin Musawa suka dauki bayanin a rubuce, sannan suka tura 'yansanda biyu don su je asibitin, su kuma je inda hadarin ya afku don su tabbatar da gskyr bayanin. . Kafin a kammala duk wadannan shige da ficen rana ta yi. Gawar Ma'aruf na gefe daya a wani dakin jinya an lulli6e shi da wani mayafi wanda wani mutum ya bayar da sadakarsa a asibitin. Abokan aikinsa da yan uwansa da iyalinsa suna can suna ta harkokinsu, basu san abin da yake faruwa ba." . Lkcn dora abincin rana ya yi. Ilham ta fito daga dakin barcinSu ta shiga kicin ta fara tunanin abin da zata girmka yau a gidan. Ma'aruf yan son (couscous) da miya. Don haka shi ne abincin da zata dafa, ba zata ci nata ba sai ya dawo anjima da yamma, zata fada masa cewar yau tunda saf da ya tafi bata ci komai ba a gidan, tana jiransa sai ya dawo, tunda dai shi ya daukar mata alqawarin zai dawo a yau, ba zai kwana a Katsina ba." , Da qarfe daya saura 'yan mintoci Ilham ta gama abincin. Ta xubawa su Khairat da Aiman ta ce su zauna a falo su ci kada su jirata. Ta dauko (flask) din abinci ta cika shi fal, ta rufe ta koma daki ta kwanta don ta huta. . Ta yi mamaki da har ynx Ma'aruf bai kirata ba." ta fara razana da ta ji har ynx idan ta kira wayarsa a kashe take, don kuwa ba halinsa ba ne kashe waya, kuma baya yarda cajinsa ya qare sai dai ko idan wani abu ne ya faru. Har qarfe daya da rabi Ilham bata samu mijinta Ma'aruf a waya ba." ta tashi ta yi sallar Azahar ta dawo ta sake kwanciya. . Ta rufe idanunta ta fara gyangyadi xuciyarta ciki da wasi-wasi da xullumi. . Da qarfe biyu da rabi barci ya kwasheta. . Bata dade da fara barcin ba ta farka a gigice tana kuka. Sbd wani mummunan mafarki da ta yi. . Ilham ta daina kukan ta fara salati, tana karanta addu'oin neman tsari daga bala'i. . A lkcn ne ta ji a jikinta babu shakka wani abu mara dadi ya faru da mijinta Ma'aruf...amma bata san ko mene ba." . . . *** *** . . Sai da qarfe uku da rabi tayi sannan Jami'an tsaro suka zo da gawar Ma'aruf Malumfashi, suka damqa gawar a hannun abokan aikinsu, suka yi masu bayanin dan abin da suka sani a game da mutumin, wanda ba a samu duba komai ba a motarsa wacce ta qone. . Ba a jima ba aka sanar da mai gari da masu unguwanni. Wani mutum da ba a san ko dan wacce unguwa ba ne ya yi hadari ya rasu akan hanyarsa ta xuwa Katsina. . Mutum na farko da ya fara samun labarin mutuwar Ma'aruf a cikin mutanen da suka san shi wani maqwabcinsa ne da suke a layi daya mai suba Malam Haruna. Ya je har ofishin 'yansanda ya ga gawar Ma'aruf ya ce maqwabcinsa ne sunansa Ma'aruf. a Katsina yake aiki, yana xuwa ne yana dawowa a qarshen sati. . 'Yansanda suka ce ya je ya sanarwa iyalin mamacin da sauran maqwabtansa da mai unguwar layin su, su zo su amshi gawar tunda an gane ko wane ne. . Malam Haruna ya dawo unguwarsu cikin sauri ya nufi gidan Ma'aruf don ya fara fadawa matarsa Ilham. Ya je gidan ya samu qofar a kulle daga ciki. Kamar yadda kodayaushe yake kasancewa a rufe idan Ma'aruf bashi nan. Malam Haruna ya fara qwanqwasawa matar mamacin qofa. . Baya son xuwa fadar mutuwa, sbd wani abu ne mai razanarwa wanda ke tayar da hankalin duk wanda aka fadawa. . A halin ynx matar Ma'aruf tana cikin gida ita da 'ya'yanta basu san me yake faruwa ba." ynxn nan wani baqin labari zai zo ya iske su. . Wanda zai tarwatsa masu jin dadin rayuwarsu. . . *** . . Ilham ta dade a zaune akan katafaren gadonta tana mayar da numfashinta. Bata iya tuno duk abubuwan da ta gani a cikin mummunan mafarkin da ta yi ba daxu. Wanda ya sa ta farka a dimauce tana kuka. . . . Lp=4,%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 4 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Ynxn nan wani baqin labari zai zo ya riskesu. . Wanda zai tarwatsa masu jin dadin rayuwarsu. . . *** . Ilham tana zaune a kan katafaren gadonta tana mayar da numfashi. Bata iya tuno duk abubuwan da ta gani ba a cikin mugun mafarkin da ta yi ba dadewa, wanda ya sa ta farka a tsorace tana kuka. . Za ta dai iya tuno kamar suna tafiya su biyu ita da Ma'aruf... kamar sun ga wani rami a gabansu wanda basu san da shi ba." qafar Ma'aruf ta fada cikin ramin ya yi iya qoqarin sa ya ciro qafar amma ta qi ciruwa. xuwa can kuma sai wuta ta tashi daga cikin ramin, ta fara kamawa Ma'aruf qafar sa. . Ilham ta fara 6urari a cikin mafarkin tana kiran mutane don wani ya zo ya taimakesu. Ta bar Ma'aruf a inda wutar take cin qafar sa a cikin rami, ta fara taran-taran tana neman wanda zai zo ya ciro mata mijinta daga cikin ramin da ya fada. . Sai daga baya ta ga wani tsoho a zaune a bakin hanya yana barci ya tasa qaramin qoqon sa wanda babu komai a ciki. Ilham ta durqusa a gaban Tsohon ta fara yi masa magiya ya taimaketa ya zo ya ciro mata mijinta daga rami wuta ta kama masa qafar sa. Tsohon ya kalleta cikin tausayawa. Ta ji ya kira sunanta kamar dama ya san ta sannan ya ce da ita, . "Ki yi haquri Ilham. Rayuwar mijinki ta zo qarshe, ki tafi gida ki barshi a cikin ramin nan da ya fada. Sbd babu wani abu da zaki iya yi masa a halin ynxn sai dai ki yi masa addu'a." . Ilham ta ji maganar Tsohon ta saki xuciyarta. Ta ce dashi a fusace . "Qarya ka ke yi babu abin da zai samu mijina sai alheri. Kana so ne ka tsorata ni, baka isa ka rabani da mijina ba." ba zan tafi gida in barshi a nan ba." ba zan yarda da abin da kake fada mani ba." . Ilham ta tashi ta bar wajen Tsohon ta garzaya ta koma wajen Ma'aruf mijinta tana kuka. Kafin ta yi nisa ne ta ji Tsohon ya yi magana muryarsa cike da tausayawa ya ce....' . "Ban ce dole sai kin yarda da magana ta ba yarinya. Amma ki sani cewar mutuwa tana kan kowa..." . A lkcn ne Ilham ta farka daga barcin tana kuka. . Khairat ta fara jin ana qwanqwasa qofar gida. Ta tashi ta bar falon ta garzaya dakin mahaifiyarta Ilham don ta shaida mata cewar wani yana qwanqwasa qofa a waje. . Khairat ta samu mahaifiyarta a zaune akan gadonta tayi tagumi. Da yake shekarunta basu kai na yadda zata fahimci halin xullumi da rudanin da mahaifiyarta take ciki ba, sai Khairat ta ce da ita kai tsaye. . "Mama ana sallama a waje." . Ta yi sauri ta juya don ta koma falo ta ci gaba da kallon wasannin tseren da ake nunawa a wata tashar wasanni ta tauraron dan adam. Ilham ta yi ajiyar xuciya ta fito daga cikin dakin nata, ta zo falo ta sami 'ya'yanta biyu, Aiman yana wasa kwance akan darduma. Khairat ta qurawa tangamemen tibin su idanu ko qiftawa bata yi fuskarta cike da fara'a. . Kafin Ilham ta fito ne ta dauko (remote) ta rage sautin tibin ya dawo kadan-kadan ake iya jin maganar. Ta fice ta bar 'ya'yanta suna cike da farin ciki a falo. Ta tafi xuwa inda zata ci karo da wani labari wanda har abada ba zata iya mancewa dashi ba....tare da mutumin da yazo ya fada mata. . Ilham ta je qofar gida ta zare sakatar qofar ta bude ta, tana tsammanin ganin wata mace a cikin qawayenta da suke yin adashi a layin. Ko kuma wadanda suke xuwa makarantar islamiyya ta matan aure. Ta yi sauri ta ja baya da ta ga wani mutum ne dake a layin su mai suna malam Haruna wanda gidan sa yake a can kan kwana . Ta mance bata sako lulli6i ba ko hijabi da zata fito. Sbd xuciyarta a rude take, to amma bata koma ba, tunda dai tana sanye da doguwar rigarta baqa wacce ta kai har qasa, ta hade da kallabinta. . "Sannu, ina yini?" . Ilham ta gaishe da malam Haruna tana dafe da qofar gidan. Tun kafin ya amsa mata ta yi saurin cewa. . "Ai kuwa gashi mai gidan baya nan, ya tafi Katsina tun safe, sai anjima zzai dawo da yamma." . Ilham tana qoqarin mayar da qofar ta rufe kenan don ta koma ta ci gaba da begen mijinta wanda bashi nan.....mijinta wanda take sa ran dawowarsa nan ba da jimawa ba." malam Haruna ya dakatar da ita ya ce....' . "Nazo ne in fada maki cewar mijinki ya yi hadari akan hanyarsa ta xuwa Katsina." . Maganar ta daki xuciyar Ilham. Wanda ya sa ta bude baki ta kasa cewa komai. Idanunta suka furfito bakinta ya bushe tana dafe da qofar gidan. Tun kafin malam Haruna yazo ya yanke shawarar zai fada mata komai kai tsaye sbd yayi sauri ya tafi. Don baya son ya tsaya yaga halin da zata shiga a dalilin abin da yazo fada mata. . Malam Haruna ya sake cewa da ita. . "Ki yi haquri matar Ma'aruf, ki yi wa mijinki addu'a, Allah Ya yi masa rasuwa a sakamakon hadarin. Ynx haka gawarsa tana nan a wajen 'yansanda zamu je da mai unguwa mu amsota. Na biyo ne in sanar dake don ki sanarwa 'yan uwanki da 'yn uwan mijinki, su zo ayi jana'iza tare dasu. Allah Ya jiqan Ma'aruf ." . Malam Haruna ya juya ya fita cikin sauri, ya barta a nan tsaye a bakin qofar gida ta kasa motsawa ta kasa cewa komai. Tsoro da razanar abin da mutumin nan ya fada mata ya sa ko'ina a jikinta ya bushe. Kunnuwanta basa tuno komai, sai 6ur6ushin maganar maqwabcin nasu lkcn da yake cewa. . L....ki yi haquri....mijinki addu'a.....a a sakamakon wannan hadarin mota....gawarsa.....'yansanda muje mai unguwa......" . Maganar ta zo ma a daburce. Maganar ta rikita dodon kunnenta ta kasa fahimtar sahihiyar ma'anar abin da mutumin ya fada mata. Ilham ta saki qofar gidan ta batra a bude. Ta kasa rufe ta, sbd yn jikinta ba qarfi. Ta koma cikin gida idanunta basa iya ganin komai, ta shiga falo ta wuce 'ya'yanta suna kallo bata dago kai ta kalle su ba. Xuciyarta tayi nisa a cikin firgici da rudani, ya yin da xuciyar yaran ta yi nisa akan abin da suke kallo. . Ilham ta shiga dakinta a rude ta fada kan gadonta. Ta sake qoqarin tuno abin da malam Haruna ya fada mata. Babu shakka mijinta ne ya rasu. Dama tun daxun ita ta ji a jikinta. Dama tun safe ta ji ta rasa me yake yi mata dadi kamar bata da lfy. A lkcn ne Ilham ta fashe da kuka jikinta yana kyarma sbd tsananin kaduwar da ta yi. Yn shi kenan Ma'aruf ya tafi....shi kenan ba zzata sake ganinsa ba a duniya?....shi kenan ba zata sake jin muryarsa ba idan yana sanar da ita wani abu yana murmushi?....shi kenan ba zasu sake yin wasannin su ba na soyayya....? Ba zasu sake zaunawa tare da 'ya'yansu ba su yi barci.... Su tashi.... Su ci abinci tare....su tafi unguwa....su yi bankwana in zai yi tafiya....? . Ilham ta ji juwa ta dauketa, duniyar ta fara juya mata. Bata san lkcn da ta sulmiyo daga kan gadon ba ta fado qasa. A nan...a yashe a tsakar dakin ta xube ita kadai tana kuka da alhinin begen mijinta. . . . Lp=5%?%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 5 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Ba ta san lkcn da ta silmiyo daga kan gadon ba ta fado qasa. A nan a yashe a tsakar dakin ta xube ita kadai tana kuka da alhini tana begen mijinta. A lkcn ne ta fara tuno baya. Ta fara tuno abubuwan da suka faru a rayuwar ta...tun farkon haduwarta da Ma'aruf masoyi ne na gsky kuma jarumi a cikin maza sbd ya yi mata halacci mai yawa a rayuwar ta... Ilham ta fara tunani. . . . BABI NA DAYA * * An haifi Ilham a cikin birnin Katsina a unguwar Filin samji. Mahaifinta Alh. Ayuba Tsohon ma'aikacin gwamnati ne wanda ya dade da yin ritaya ya dawo ana hada-hadar siyasa tare da shi. . Ilham ba ta girma tare da mahaifiyarta ba tun tana qarama 'yar shekara uku mahaifinta ya rabu da mahaifiyarta, kuma ya hanata tafiya da ita. Ilham ta taso kamar marainiya a gidan su tare da yayyenta su takwas uku maza biyar mata, wadanda duk mahaifiyarsu daya wato Haj. Kubra. . Faraira ita ce mahaifiyar Ilham. wata bafillatanar jihar nassarawa ce a cikin garin Lafiya. Wacce Alh. Ayuba mahaifin Ilham ya hadu da ita a wajen yawace-yawacen canjin aikin da aka sha yi masa, bashi a wannan gari bashi a wancan. . Ilham ta dauko kamannin mahaifiyarta sak, bata bar komai ba." wankan tarwada ce wacce take da kafar gashi a jikin ta...gashin idanunta da girarta da kuma yalwataccen gashin kanta, da wasu baqaqe sirara wadanda suka fito mata a hannuwanta, sun isa su sa kowa ya fahimci akwai wani jinsi dake tattare da ita na wasu mutane ko wata qabila, wacce ta sha banban da na mahaifin ta Alh. Ayuba. . Ilham tana da kyakkyawan jiki, ba ramammiya ba ce, duk da yake ba zai yiwu a sakata a layin masu qiba ba." lkcn da tana makarantar firamare a unguwarsu mutane da yawa sun ce idanunta sun fi komai basu sha'awa. Duk sanda aka tashe su tara idan Ilham tana wasa da yara ko in zasu dawo gida, wani mai tireda dake a layin su wanda yake da budurwar xuciya ya kan kirata ita kadai ya bata kyautar cingam ko alawar tsotso don kawai ta kalleshi ya ga idanunta. . Amma da Ilham ta je makarantar kwana gashin kanta da qananun gashin da suke fito mata a haanu yafi burge qawayenta wadanda suke daki daya. Idan Ilham ta fito wanka kafin ta bushe ta kan sa hannunta ta riqa kwantar da gashin kanta ya kwanta ya yi ta sheqi a bayan. Qawayenta suna kallo daga kan dagajensu suna ji ina ma sune suke da gashin Ilham . Da Ilham ta gama karatun sakandire ta dawo gida ta zama cikakkiyar budurwa komai dake tattare da ita yana burge mutane. Shigarta, maganarta' fara'arta, dabi'unta da kuma uwa uba kamun kanta da jan ajinta, sbd a duk fadin unguwarsu ba za a samu maza uku wadanda take yiwa magana ba." idan ma har za a samu to sai dai wadanda take mutunci dasu. Ko dai inda take sayen katin waya ta bayar da caji. Ko kuma wani matashi dake sayar da kankana da lemu a bakin qofar gidan su." Ilham bata kula mutane barkatai. Ba maza ba, hatta 'yan mata yawanci sai wadanda ta san sun yi karatu tare. Duk fadin unguwarsu bata da qawa ko daya. . Mahaifin Ilham yana sonta sosai, kuma hakan shi ya jawo mata baqin jini da tsana a wajen sauran 'yan uwanta. Duk lkcn da Alh. Ayuba zai yi wa Ilham wani abu, to qura ta taso kenan a cikin gidansa. Mahaifiyar manyan 'ya'yansa wato Haj. Kubra, ata taso ita da 'ya'yanta su nuna atafau!! Basu yarda ba." idan kuma wani abu ne wanda za a yiwa kowa da kowa, to sai 'yan uwanta sun san yadda suka yi mata kutunguila da bi-ta-qulli suka karkatar da ra'ayin mahaifinta ya fasa yi mata nata abin da take so. : Tun a wajen makarantun da Ilham ta yi ta ke samun matsala da 'yan uwanta. Lkcn da zata je sakandire aji daya, makarantar 'yanmata ta Gwamnatin tarayya (Federal Government Girls College) da ke Funtuwa Ilham ta ce da mahaifinta tana so ta je. Kafin ya nemar mata makarantar ne, sai ya kira yayyenta su uku maza wadanda suka gama karatu suke zaune a gida ba aikin yi ya fada masu abin da da Ilham ta ce tana so. . Babban yayansu Auwal ya ce da mahaifinsu. . "Baba ai Ilham ta yi qanqanta da xuwa (Boarding school) a dai samu wata (Day) nan kusa dake a gida a kaita." . Yayansu na biyu wanda ke bin Auwal mai suna Mustafa ya ce da mahaifinsu. . "kuma ga nisa baba. Ko hutu aka yi sai an sha wahala kafin a je a dawo da ita." . Qaramin yayanta a maza wato Jamilu ya ce....' . "Bayan nan kuma kaga ba wani qoqari gareta ba Baba. Yawancin yaran da ake dauka a irin wadann makarantun masu qoqari ne....! Amma gsky Ilham ba zata iya ba." . Suka rushe maganar xuwan Ilham makarantar da ta ce tana so. Mahaifinta don a zauna lfy a gidan don kada Haj. Kubra ta ce an fi son Ilham akan 'ya'yanta sai ya bi shawarar da su Auwal suka bashi. Aka sa Ilham a wata qarammar makarantar sikandire jeka-ka-dawo dake a layinsu. A haka ta yi karatun tsawon shekaru uku cikin fushin rashin cimma buri. . Da ta kammala aji ukun farko zata je babbar sakandire a nan ma sai da aka kai ruwa rana. Ilham ta yi sha'awar xuwa makarantar kudi ta 'yanmata. Amma Auwal ya yi ruwa ya yi tsaki akan dole sai sai dai idan makarantar kwana take so ta za6i wata amma ba dai wacce take so ba." a qarshe Ilham ta je makarantar kwana dake a Kabomo, qaramar hukumar Bakori. Anan ta gama karatunta na sakandire. Ta dawo gida cike da burin zana jarrabawar share fagen shiga jami''a. . Duk sauran 'yanmatan da suka taso yayyen Ilham da suka yi aure. Babu wacce ta wuce sikandire. maza ne kawai su Auwal da Mustafa da Jamilu suka yi difloma, suma babu wanda ya je jami'a a cikin su." Da labari ya riskesu cewa Ilham tana so a biya mata jarrabawar share fagen shiga jami'a (jamb) sai duk suka yo mata caaa!! . Auwal ya ce da mahaifinsu. . "Me Ilham zata iya yi a jami'a Baba? Muma da muke maza kuma yayyenta mun haqura mun yi diploma ita sai ta ce dole sai ta yi digiri....?" . Mustafa ya qara da cewa. . "kamata yayi kawai ta fito da miji a yi mata aure Baba, ba wani karatu da zata iya yi a jami'a." . Jamilu ya ce a qarshe. . "To yaushe ma zata gama karatun, abin da Kodayaushe ba a rabuwa da yajin aiki a jami'o'in qasar nan? Gsky Baba ka qyale maganar jami'ar nan a dai nemo mata wani abin..." . Mahaifinsu ya dauki shawarar 'yan uwan Ilham duk da yake cewar ya san ya hana Ilham abin da take so fiye da komai a rayuwarta. Daga baya ya kirata ya ce da ita ta yi haquri ta shiga (FCE) TUNDA 'YAN UWANTA Basu goyu bayan xuwanta jami'a ba." Ilham ta ce da mahaifinta ta haqura da karatun baki daya, Ta tashi ta koma dakinta tana kukan baqin cikin wannan qiyayya da tsana da 'yan uwanta suke nuna mata. . Gashi kuma mahaifiyarta wata irin mace ce wacce Ilham ta kasa gane ta. Sai ta shekara uku cur bata zo taga ilham ba a Katsina. Tunda suka rabu da Alh. Ayuba ta koma jihar Nassarawa, ta mance da Ilham kamar ba ita ta haifeta ba." bata ta6a niqo gari takanas-ta-kano ta zo don ta ga Ilham ba, sai dai idan wani abu ya kawota Katsina ta biyo ta ganta a gurguje ta tafi ta ce sauri take yi. . Ilham tana so duk sanda mahaifiyarta ta zo su zauna ta fada mata inda danginta suke. Tana so ta sansu ta riqa xuwa inda suke komai nisan garuruwansu, sbd da su kadai ne zata yi alfahari, tunda dai 'yan uwanta da suke uba daya basu damu da ita ba, kuma sun tsane ta...tun . Furaira ba ta ta6a fadawa Ilham inda wasu 'yan uwanta suke ba." da Ilham ta tambayeta to wa take aure ynx bayan rabuwarta da mahaifinsu? Sai ta ce da Ilham har ynx bata sake yin wani auren ba. Ilham ta fahimci mahaifiyarta zaman kanta kawai take yi. Sb ko a wani xuwa da ta yi Katsina wani qaton baqin mutum mai kudi ya kawota a mota, wai sun zo wajen wani taron siyasa da ake yi na jam'iyyarsu. . Tun daga lkcn Ilham ta tsinke da lamarin mahaifiyarta ta daina xumudin ganinta. Don kuwa ta fahimci bata kama kanta ba. Ta riqa jin kunyar yadda mahaifiyarta take gudanar da irin wannan rayuwar ba aure. . . . Lp=6%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 6 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun Taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Tun daga lkcn Ilham ta katsa da lamarin mahaifiyarta. ta daina xumudin ganinta domin kuwa ta san bata kama kanta ba." ta riqa jin kunyar yadda mahaifiyarta take gudanar da irin wannan rayuwar ba aure. Kuma bata damu da kowa ba sai kanta kawai, da abubuwan da take so a rayuwar ta...tun . Ilham ta rasa da wa zata zzauna ta ji dadi a duniya? Ba tare da mahaifiyarta. mahaifinta kuma yana tsoron ya nuna mata so. Sbd kada matarsa uwar manyan 'ya'yansu ta ji haushi. Su kuma yayyenta sun tsaneta, gashi kuma ita kadai mahaifiyarta ta haifa a gidan, ta tafi ta barta. . Ilham ta fasa karatun ta zauna a gida tare da sakamakonta na sakandire kadai...tare da kyakkyawar surar jikinta wanda a Kodayaushe yake jawo mutane ta ko'ina xuwa gareta suna kawo mata farmakin soyayya ita kuma Ilham tana gocewa makamin soyayyar namiji. Bai ta6a fadawa kanta ba. Ba ta ta6a yin soyayya da kowa ba." . A zamanta haka nan a gida ma bata tsira ba." mahaifin ta ya ce da yayyenta ya kamata a samarwa Ilham da sana'ar da zata riqa yi kafin tayi aure, tunda dai babu karatun. Sanda Alh. Ayuba ya kira 'yan uwanta zasu yi wannan shawarar, ba a kira Ilham ba, ta dai zo wucewa ta falon mahaifin su ta ji suna magannar. Alh Ayuba ya c masu. Zai saya mata babban injin saqar kaya ta koyi saqa don idan tayi aure ta dogara da kanta. . Auwal ya ce da mahaifinsu cikin damuwa. . "Gskyr magana Baba Ilham ba zata iya yin saqa ba." wannan san'a ce ta masu kazar-kazar, ba san'aa ce ta masu son jiki irin Ilham ba, 6arnar kudi kawai za'ayi ko an sayo mata injin don kuwa ba zata iya ba." . Mustafa ya ce....' . "in haka ake so ai yafi ma a saya mata keken dinki, amma yaushe Ilham zata iya yin wani saqa?" . Jamilu ya ce....' . "irin wadannan kayan ma Baba ko an saye su ba dadewa suke yi ba, nan da nan suke lalacewa. Kawai ka barta tunda dai ba ita ta ce tana so ba." . Ilham ta girgiza kai ta yi tafiyarta. Ta bar 'yan uwanta a falon tare da mahaifinsu suna ta kushe abin alherin da mahaifinsu ke son yi mata. Shi kuma ya riga ya saba' bai ta6a yi mata wani abu ba sai ya kira su yayi shawara dasu' matsayin manyan 'ya'yansa. . A haka rayuwar ta ci gaba da xuwar wa Ilhamm ta yi haquri ta ci gaba da zama tare da 'yan uwanta wadanda suka dora mata karan tsana, akwai abubuwa da yawa da ta rasa a rayuwarta. Akwai abubuwa da yawa da take so, amma da yake ta san ko ta tambaya ba zata samu ba, sai ta riqa yin haquri tana barin abin a xuciyarta. Kuma da yake Ilham tana da haquri da zurfin ciki, bata ta6a fitowa waje ta fada ba." kadan ne daga cikin mutanen da suke makwabtaka dasu suka san abin da yake faruwa da irin zaman da Ilham take yi a gidansu tare da 'yan uwanta wadanda ba mahaifiyarsu daya ba." . A ranar wata alhamis...tabbas ranar alhamis ce da yamma, Ilham ba zata ta6a mancewa da wannan rannar ba mai dumbin tarihi a rayuwarta. A ranar ne Ma'aruf ya fado cikin rayuwarta ba zato ba tsamman. . Ilham ta fito kenan daga gida tazo shagon sayar da katin wayar dake kusa da gidan su a kan layin nasu. Ta iske samari kusan biyar a zazzaune a kan benci tare da mai shagon suna labarin qwallon qafa. Ilham ta yi sallama ta ce da Khalid mai sayar da katin ya bata (MIN) na dari biyu. Ta miqa kudin. A sanda tazo wajen kowa yayi shiru a cikin matasan da suke zaune a bakin shagon. Ilham bata daga kai ta kallesu ba, ta san ita suke kallo. Ta hadefuskarta har lkcn da Khalid ya ciro latin ya bata. Da ta juya ta tafi ne ta nufi gidansu ta ji wani a cikin samarin ya ce da Khalid mai shagon. . "wannan kuma wace ce a nan layin Khalid? Kune 'yan gari mu baqi ne....! Don Allah wace ce?" . Ilham ta ji Khalid ya yi dariya amma bai cewa wanda ya yi masa tambaya komai ba akanta. . A sannan ne Ilham ta tabbatarwa kannta duk da bata waigo ba, babu shakka wani a cikin samarin ya kamu da sonta....a nan take daga kawai ta zo sayen kati. . Kamar yadda mutane da yawa suka sha kamuwa da sonta amma har ynx bata hadu da wanda ya ji ya yi mata ba ranta. . . . *** . . Da qarfe takwas na dare bayan ann idar da sallar Isha'i ya zo har ggidansu ya aiki yaro ya kai mata wasiqa har gida. Ilham tana kwance a katifarta yaron yayi sallama ya miqa mata takardar. . "Gashi in ji wani ya ce wai a baki." . Ilham ta kalli takardar cikin rashin kulawa. . "wane ne ya baka ya ce ka kawo min?" . Yaron ya ce....' . "nima ban sanshi ba, yana nann a tsaye a waje." . Ilham ta amshi takardar, a yayin da yaron ya fita ya bata wuri. Ta warware taga rubutu ne bai wuce layi hudu ba bashi da yawa, ta fara karanta. . . Assalamu alaikum. Ilham suna na Ma'aruf. Daxu na ganki da yamma a sanda kika zo sayen kati a shagon Khalid ina so ne in fadi maki wata magana, ina so ki fito ina qofar gidanku ina jiranki ynxn nan. na gode. . . Ilham ta dubi takardar bayan ta gama karanta ta. Ta sha cin karo da irin wadannan saqonniin ba sau daya ko sau biyu ba. Ta sa hannu biyu ta keta takardar, ta watsa ta a kwandon shara dake bayan qofar dakinta. . A lkcn ne ta sa qafa ta tura qofar ta rufe, ta jawo mayafinta ta rufa sbd ana sanyi. Ta rufe idanunta. Bata yi minti ashirin a baka ba ta fara barci. . A daren sai da Ma'aruf ya kai awa uku a zaune yana jiran fitowarta. Da ya tabbatar ba zata fito bane ya tafi ya rabu da ita. . A rana ta biyu tun da safe ya zo gidansu don ya ganta su sake yin ido da ido. Ya nemi lambar wayarta kamar gwal a ruwa amma duk fadin layin bai samu wanda yake da lambar Ilham ba. Shi kanshi Khalid mai sayar da kati duk da yana mutunci da Ilham bata ta6a bashi lambarta ba." shi yasa tun farko bai ba Ma'aruf qwarin guiwar xuwa ya sameta ba." don ya san da wahala ta amince masa. Ilham ba kamar sauran mata ba ce. . Da fitowarta zata shiga gidan dake hade da nasu kenan sai Ma'aruf ya taso sameta yana fara'a. Ilham ta samu kanta tana fuskantar wani farin saurayi dan kimanin shekaru talatin da haihuwa. Sanye da baqin wando da rigar masu bautar qasa. Ilham ta tambayeshi da taga ya tsaya mata a hanyar wucewa. . "Lfy malam..?" . Ma'aruf ya ce da ita. . "ni ne Ma'aruf din da na aiko miki da takarda jiya da daddare ki qi fitowa. Shi ne na sake dawowa ynx da safe, sbd na qosa mu hadu in fada miki abin da yake raina." . Ilham ta ce dashi cikin fushi. . "Dakata malam, kaga bana son irin wannan, kada ka sake biyoni gidan mu. Kaga kai ba qaramin yaro ba ne, bana so in yi maka wani abu ka ce nayi maka rashin kunya. Don Allah ka rabu da ni bana so, kawai ka rabu da ni, na gode. . Ma'aruf ya rage fara'ar dake a fuskarshi ya ce da Ilham . "na gode sosai da kika fada min gsky tun ynx. Ban san cewar na takurawa rayuwarki ba a dalilin biyoki da nayi har gida ba. Li yi haquri Ilham." . Ta kauce ta bashi wuri ta shiga cikin gidan da zata shiga ta barshi a tsaye a waje cikin damuwa. . . . Lp=7%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 7 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun Taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Ta kauce ta bashi wuri, ta shiga cikin gidan da zata shiga ta barshi a tsaye cikin damuwa. Da yake Ilham ta san Khalid ne ya fadawa mutumin ko ita wace ce? Ba a dade da yin haka ba da rana ta taka ta je har shagon wayarsa ta same shi babu kowa yana zaune yana gyara wata waya akan teburi. Ilham ta ce da Khalid a fusace. . "wajen ka nazo Khalid." . Ya dago kai ya kalle ta...tun . "ya aka yi ne Ilham?" . Ta ce dashi . "Kaga ina jin kunyarka Khalid, na daukeka kamar yayana a layin nan, amma shi ne zaka je ka na fadawa mutane suna na da gidanmu suna biyoni suna takura mani tunda sassafe? Gsky ban ji dadi ba, don in banda kai ne har ga Allah sai an jimu. Idan mutum ya yi min haka. Gsky bana so Khalid kada ka qara yi min haka." . Khalid ya tsaya da gyaran wayar ya tattara hankalinsa waje guda ya ce da Ilham . "da farko zan fara da baki haquri Ilham, ki gafarceni don ban san haka abin zai kasance ba da ban fada masa ba. Kin san kin zo nan jiya kin sayi kati. To a sannan ne ya ganki. Baqo ne yazo (service) dakinsa na can gaban 'Yaryara. Shima dan nan jihar ne, a Matazu yake. Ya ci sa'a ne an turo shi nan Katsina, duka-duka yau kwanansa shida da xuwa. To kin san halin Baqo musamman in aka ce mutum yayi karatu, zaki ga yana qoqarin shiga mutane a san shi, ni kaina ban so na fadiwa Ma'aruf sunanki ba' to ya matsa mani ne, yana sonki sosai Ilham, tunda ya ganki jiya ya rude, amma ki bari idan yazo anjima zan fada masa ya bari, kin ce bakya so." . Ilham ta dan sauko daga fushin kadan. Ta ce da Khalid . "shi kenan ya wuce." . Ta koma gida tana tunanin...sai yaushe irin wadannan samarin masu nacin tsiya zasu barta ta huta da fushi? A ranar da yamma wani yaro ya shigo ya kawo mata wani faffadan katin saka muhimman saqonnin soyayya da gaisuwa wanda aka yiwa rubutu a samansa kamar haka:-) . Please forgive me. . Ma'aruf ne ya aiko mata da saqo yana roqonta tayi haquri. ta bude cikin katin ta ga qaramar takarda a nannade ta cirota ta warware. Ta ga ya rubuta mata qaramar wasiqa kamar haka. . Ilham Ki yi haquri da abin da ya faru a tsakanina da ke. A wani lkc da dadewa na ta6a jin wani ya ce, duk wanda ciwon so ya kama baya iya ganin komai. Na dauka ba gsky bane, amma ynx na yarda da maganar a dalilin haduwata da ke. Ki yi haquri.... Na gode, daga masoyinki Ma'aruf. . Ilham ta kekketa wasiqar ta xubar da ita a waje. Ta kira wata yarinya wacce tazo gidansu 'yar wata yayarsu ta miqa mata katin ta ce da ita. . "gashi idan kina so basira ki yi wasa da shi." . Yarinya ta amsa tana murna ta fita waje dashi. Awa daya bayan haka har Basira ta fara wasan qasa da katin ita da yara a qofar gida. . Bayan kwana biyu Ma'aruf ya sake aiko mata da wani katin wanda yafi na farko kyau da ban sha'awa jikinsa an rubuta. . I hope I'm forgiven. . Wato yana fatan ta yi haquri ta yi masa afuwa bisa fushin da take yi dashi sbd kawai ya ce yana sonta. Sai dai a wannan karon bai sako wani saqo a rubuce ba." ya dai hado mata da wani zobe ne na azurfa wanda zai burge Ilham da ace tana son Ma'aruf . Ilham ta rasa me yake yi mata dadi. Ta cire zoben ta sake ba yara katin ta ce su yi wasa idan suna so. A ranar ta ba wani almajiri zoben kyauta. Wanda yake debo masu ruwa a gidan. Ta ce a xuciyarta. . "idan har bana son mutum to kayansa ma bana so." . Tun daga ranar, kusan Kodayaushe sai Ma'aruf ya aiko mata da kyaututtuka irin su kayan kwalliya, sarqoqi da turaruka masu tsada. Ilham bata ta6a yin amfani da ko daya ba a cikin su." a ranar da suka zo itama a ranar take kyautar dasu. Ta san idan ya gaji wata rana zai bari don kanshi, zai rabu da ita... Indai ba shi ne sarkin marasa xuciya ba." . Wata rana Ilham ta je sayen katin waya wajen Khalid maqwabcinsu, sai ya ce da ita. . "Ilham duk da dai baki son ayi maki zancen mutumin nan, yau dai ya cika mani fuska ya bar min saqo wai in kin zo in baki. . KHALID YA miqo mata wani abu a cikin leda. Ilham ta amsa ta duba ta ga wani hadadden takalmi ne a cikin kwalinsa dake kama da gilashi. Takalmin ya burgeta, sai dai kuma wanda ya aiko mata da takalmin ne bai ta6a burgeta ba, kuma tana zaton ba zai ta6a burgeta ba." ta ce a xuciyarta. . "lkc ya yi da ya kamata in dakatar da wannan shashashan." . "ka ce dashi na gode, kuma idan ya zo ka ce ina son ganin sa anjima da daddare a gidanmu. Ya zo da qarfe takwas." . Khalid YA amsa mata cikin murna. . "zan fada masa Ilham. zan je ynxn nan in fada masa. Na san tukuicina mai tsoka ne." . Ya yi dariya. Ilham ta tafi gida da takalmin a cikin baqar leda. Da xuwanta dakin ta ta jefar dashi ya hadu da bango. . Bata sake waiwayen inda yake ba." . Da qarfe takwas daidai na daren ranar ko minti daya Ma'aruf bai qara ba." ya zo gidan su Ilham. ya aiki yaro ya ce, ya shiga ya fada mata Ma'aruf yana kiranta. . Yaron ya fito ya ce dashi. . "ta ce tana xuwa." . Ma'aruf ya tsaya cike da farin ciki, ya qosa Ilham ta fito. Sbd tana sa ran haqarsa ta cimma ruwa. Ilham ta amshi soyayyarsa da hannu biyu. Yarinyar da yake so fiye da komai. Wacce yake kwana yake tashi da radadin begenta, tun ranar da ya fara ganinta. . Ilham ta fito dauke da takalmin da ya aiko mata dashi a hannu ba ma a cikin ledar da ya sako takalmin ba." Ma'aruf ya fara yi mata fara'a, kafin yayi mata magana ne ta watso masa takalmin suka fada a jikinsa suka xube a qasa....... . . . Lp=8%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 8 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . TAre da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun Taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Kafin ya yi mata magana ne ta watso masa takalmin suka fada a jikinsa suka xube a qasa..akan qafafuwansa. Ma'aruf ya bude baki cikin razana yana kallon abin da tayi masa. Ilham ta nuna masa yatsa ta ce dashi cikin kakkausar murya. . "ina so wannan ya zama gargadi na qarshe a tsakanina da kai.... Kada ka sake aiko min da komai, bana buqata, kamar yadda bana son ka sake xuwa inda nake. Ina fatan zaka kiyaye, idan har kana so ka karewa kanka mutunci." . Ilham ta juya zata shiga gida kenan sai Ma'aruf ya kira sunanta. . Ilham dakata." . Kamar ba zata tsaya ba, sai kuma ta juya ta ce dashi. . "na tsaya' mene ne kuma?" . Ma'aruf ya dan sake matsawa inda take, da yake akwai haske a qofar gidan, Ilham ta ga yadda fuskarsa ta koma, akwai alamun qunci da nadama a ko'ina a fuskarsa. Duk da haka sai ya yi mata murmushi ya ce....' . "laifina ne duk abin da ya faru Ilham. Baki da laifi sbd na san ba a soyayya dole. To amma ba yadda zan iya yi, ni kaina na san abin da nayi bai cancanta ba, ba zan iya hana kaina sonki ba." ban san yadda zan yi in hana kaina sonki ba. Ba zan iya dakatar da xuciya ta ga barinn begenki ba." . Ya dan saurara sannan ya ce da ita. . "Amma tunda baki sona, nayi maki alqawarin daga yau ba zan sake xuwa inda kike ba, kuma ba zan sake aiko miki da komai ba." ina fatan zaki gafarceni a bisa 6ata miki ran da nayi na saki fushi, a yayin da kike zaune cikin kwanciyar hankali tare da iyayenki da 'yan uwanki. Ki yi haquri Ilham na shiga rayuwarki." . Ma'aruf ya sake mayar da numfashi kafin ya sake cewa. . "kafin muyi bankwanan qarshe, zan so ki ara min minti daya domin in fada miki dalilin da yasa har kika ga na nace akan sonki naqi yin fushi akan abin da kike yi min. . "Ilham a rayuwata ni maraya ne....! Na taso cikin rashin kula. Babu wanda yake sona. Iyayena sun rabu tun ina jariri dan wata uku, mahaiffiyata ta barni a wajen mahaifina a sakamakon zazzafar rabuwar da suka yi. Mahaifiyata ta tsaneni sbd irin wulaqancin da mahaifina ya yi mata. Haka shima mahaifina ya tsaneni a cikin 'ya'yansa, sbd tsanar da yayi wa mahaifiyata. Bai barni a gidansa ba, da na rayu ban mutu ba tun ina jariri, mahaifiyata ta barni a tsumma ta yi tafiyarta, sai ya kaini Matazu wajen mahaifiyarsa wato kakata. A hannunta na girma, cikin rashin kula da quncin rayuwa. . Ilham ta bi Ma'aruf da kallo tana saurarenshi, jikinta a sanyaye. Tarihin rayuwarsa da yake fada mata, kamar yana tuno mata da kwatankwacin nata Tarihin rayuwar ne. Itama da irin wannan azabar rashin kulawar ta taso a rayuwarta. . Ma'aruf ya ce da ita. . "mahaifiyata ta dade da rasuwa, ni kaina sai daga baya na samu labari. A lkcn ina a makarantar firamare, bana iya xuwa garin da take, ita kuma bata iya xuwa wajen kakata don ta ganni." . Ilham ta tuno yadda take damuwa idan mahaifiyarta ta dade bata zo ba." ta tuno irin maganganu da take fada mata. . "Mama me yasa baki son xuwa Katsina in ganki? Gashi kin qi nuna min 'yan uwanki, ban san kowa ba a danginki mama." . Ma'aruf ya ci gaba da cewa Ilham . "mahaifina yana da 'ya'ya da yawa. Amma ganin bai damu da ni ba." suma basu damu da ni ba. Basu kulawa da ni, suna daukata kamar wani bare ba dan gidansu ba." . "Baba Ilham ta yi qanqanta da xuwa makarantar kwana. A rabu da ita kawai a samu wata (Day) a nan kusa..." . Ma'aruf ya ci gaba da fada mata cewa. . "ina da qoqari a makaranta Ilham. Dana gama sakandire a MATAZU naso in je jami'a, amma aka hana mahaifina ya biya mini. Dole sai dai nayi ta fadi-tashi na samu kudin da na shiga (Federal polytechnic) dake a KADUNA. A can nayi (HND) na gama. Duk da haka sauran 'yan uwana dake tare da mahaifina a halin ynxn basu ta6a yi mani fatan alheri ba. Ban ta6a yin wani abu da na burgesu a duniya ba." . "me Ilham zata iya yi a jami'a baba..?" . Ma'aruf ya sake cewa. . Xuwa da nayi garin nan nazo bautar qasa ne....! Na hadu da mutanen arziqi wadanda suka nuna mani qauna. Kuma na gode. Ina son a nuna min qauna sbd ita ce abin da na dade ina nema ban samu ba." na taso cikin wata irin rayuwa mai wahala Ilham. Mutanen duniya kadai suke ganin mutuncina da darajata. Amma mahaifina da 'yan uwana basu yarda zan iya zama wani abu ba a duniya." . "gaskiyar magana Ilham ba zata iya yin saqa ba, ba sana'a ba ce ta masu son jiki irin ta..." . Ma'aruf ya sake cewa Ilham . "ganinki sa na n a karo na farko, sai naji haka kawai Allah Ya sa min sonki a xuciyata Ilham. Da ace na samu kulawa a rayuwata, na san ba zan yi ta binki ina roqonki ki soni ba." to amma kiyi haquri daga yau nayi miki alqawarin ba zan qara takurawa rayuwarki ba. Dama wannan shi ne dalilin da yasa kika ga na qwallafa raina a kanki, na san ynx ba zaki ga laifina ba, kuma zaki daina daukata a matsayin mahaukaci, na gode Ilham, ina yi maki fatan alheri a rayuwarki." . Ma'aruf ya juya zai tafi, ya duqa zai kwashe takalman da ta watso masa a jiki. . Ilham ta ji xuciyarta ta sosu sosai. Bata ta6a haduwa da namijin da ya yarda da ita ba, ya dauketa da muhimmanci har ya fada mata gskyr rayuwarsa babu yaudara irin Ma'' . Ta ji ma' ya zama kamar dan uwanta a nan take. Sbd duk wani abu da ya fada mata a cikin Tarihin rayuwarsa irin qalubalen nata rayuwar ne....! . . Lp=9%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 9. . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun Taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Ta ji Ma'aruf ya zama kamar dan uwanta a nan take. Sbd duk wani abu da ya fada mata kwatankwacin abin da itama take fusksnta ne a rayuwar ta. Ba wani dalili dama da yasa Ilham take qin amsar soyayyar samarin da suke sintirin sonta ba, sai kawai don kawai don taga rayuwar ta cike take da damuwar rashin kulawar da ake nuna mata, tana jira ne har sai ta samu saurayin da zai fahimci rayuwarta ya riqe ta amana domin idan har ba ta samu miji na-gari ba wanda zai riqe ta amana ba, to tabbas rayuwarta da ta 'ya'yanta da zata haifa tana cikin garari. . Ilham ta ji Ma'aruf ya zama kamar dan uwanta, kamar wani babban amininta. Ta ji xuciyarta ta gamsu dashi sbd shi ma yana cikin irin rayuwar ta. Shi kadai ne namijin da ta fara haduwa dashi wanda ya dandani abin da ta dandana a rayuwarta. Shi kadai ne zai tausaya mata yayi mata adalci akan duk wata mu'amulla da zasu yi, sbd ya san irin matsalar da ta sani a rayuwarta. . Bayan Ma'aruf ya duqa ya dauke takalmin da ta watso masa ne kafin ya tafi sai ta ce dashi. . "Ina zaka tafi min da takalmina da naga ka duqa ka dauka Ma'aruf, ko ka fasa yi min kyautar ne?" . Ma'aruf ya dubeta cikin kaduwa da mamaki ya ce....' . "ke ce fa kika watso min su kika ce baki son kyautar da nayi miki. Nima kuma baki sona." . Ilham ta ce dashi cikin nadama. . "ka yi haquri Ma'aruf, na san nayi maka abubuwan da basu dace ba." amma ka gafarceni ynx komai ya wuce." . "kada ki damu Ilham, baki yi min laifin komai ba." . Ilham ta matso Inda yake ta miqa hannuwanta ta ce dashi. . "ynx dai fara bani takalmana tukuna kada in mance dasu." . Suka yi dariya tare ita da Ma'aruf. ya miqa mata takalman ta amsa cikin ladabi. . "na gode da kyautar da kayi min, da kuma duk sauran kyaututtukan da kayi min a baya Ma'aruf. Allah Ya saka da alkhairi." . Ma'aruf ya kasa magana sbd farin ciki, abin yazo masa a ba-zata. Bai san yadda akayi Ilham ta canza ra'ayin ta ba a cikin lkc qanqani. Duk qiyayyar da ta nuna masa kwana da kwanaki, ynx ta rikide ta zama gagarumar soyayya. Ma'aruf ya tambayi Ilham cikin wasi-wasi. . "ynx kina nufin kenan kin dawo kin amshi soyayyata Ilham? kin amince da ni in zama masoyinki?" . Ilham ta kalleshi har cikin idanunsa ta ce . "wacce soyayya kuma zamu fara yi, ai har mun yi ta mun gama a cikin dan abin da ka fada mini na minti biyun da suka wuce. Ynx ina so gobe kazo mu je wajen Babana ya ganka. Tun yau zan fada masa na samu mijin da zan aura." . Ma'aruf ya rufe idanunsa ya sake budesu. Bai ta6a yarda ba mafarki yake yi ba, sai da ya bude idanunsa yaga Ilham a gabansa tana yi masa murmushin soyayya riqe da takalmin da ya bata a hannunta. . . . *** *** ** . . . Babi na biyu. . Duk wanda zai ce ya ta6a ganin soyayya ta gaske....soyayya ta ban mamaki a duniya indai ya ta6a ganin soyayyar Ilham da Ma'aruf to labarin ta zai fara bayarwa. . Ba a dade ba duk wani mutum dake a layinsu Ilham ya san tayi wani saurayi wanda ake sa ran shine zai aureta. A wajen Ma'aruf Ilham bata tsaya kawai a masoyiyarsa ba." ya dauketa tamkar 'yar uwarsa ce ta jini, duk wani mutum da Ilham zata nunawa Ma'aruf ta ce dan uwanta ne, a wajen Ma'aruf shima dan uwansa ne. Bai ta6a mance sunayen mutanen da Ilham ta ta6a fada masa sunayen su ba a gidansu da 'yan uwanta na nesa da na kusa. Sbd ya daukesu da muhimmanci . Ma'aruf ya kan je gidansu Ilham ko tana nan ko bata nan. Idan tana nan yayi hira da ita, idan kuma bata nan sai ya zauna tare da yayyenta a qofar gida suyi hira, a nan zai wuni ya kai har dare, sbd ko'ina ya je in har baya kusa da Ilham baya jin dadi. . Ita kuwa Ilham sanin kowa ne cewar ko a cikin qawayenta idan har ana zancen samari da wahal ta tsoma bakinta tayi magana, amma tun haduwarta da Ma'aruf, tun sanda ta fara sonshi ta fara bada labarin shi a duk inda ta zauna. Qawayenta da ba unguwa daya suke da ita ba. Suka qosa su ga kowanene wannan Ma'aruf din, wanda Ilham ta dame su da zancensa, har sun fara gajiya da jin sa. . A wani bikin auren da wata qawarsu zata yi a 6atagarawa Ilham ta gayyaci Ma'aruf ta ce tana so yazo don ya gaisa da qawayenta. Ma'aruf ya yi mata alqawarin zai je. Yawancin qawayenta sun yi zaton Ma'aruf wani miloniya ne wanda yake hawa manyan motoci, sbd a yadda suka san Ilham bata kula kowa, ba qaramin mutum zai iya shiga xuciyarta haka duk ta rikice da soyayyarsa ba tayi ta zancensa a ko'ina . Sai da yamma da Ma'aruf ya je wajen bikin a qasa, yana sanye da kodadden shudin wando da takalmi (sandal) sai rigarsa mai dogon hannu. Da Ilham ta gabatar dashi a wajen qawayenta sai duk kunya ta kamasu. . Kowacce ta riqa mamakin me Ilham ta gani a wajen wannan saurayin. Me zai bata a rayuwa? Ta yaya ma zai iya riqeta? Don kuwa sun san mutane da yawa masu kudi sun dade suna son Ilham, bata amince masu ba." ta yaya kuma zata amshi soyayyar Ma'aruf wanda bashi da komai? . Ilham tana cike da farin cikin ganin Ma'aruf yazo wajen bikin. Bata damu da ganin samarin qawayenta da suka xo a manyan motoci ba." kuma bata ji kunyar gabatar masu da Ma'aruf ba tana murmushi. . "ga masoyina Ma'aruf da nake baku labarin sa, wanda nake so ki tayamu addu'a, Allah Ya cika mana burinmu mu zama mata da miji." . Qawayenta sukan kalli juna su rasa abin da zasu ce, sbd abin yana basu kunya. . . . Lp=10%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 10 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun Taska). . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Qawayenta sukan kalli juna. Su rasa abin da zasu ce sbd kunya. Bayan Ma'aruf ya tayasu farin ciki da zai tafi sai Ilham ta rakashi har bakin titti inda zai hau mota ya koma gida kafin Ilham ta dawo gida idan sun gama bikin da daddare . Bayan Ilham ta dawo wajen qawayenta ne cike da farin cikin xuwansu masoyinta Ma'aruf' ta same su sunyi tsam' a tsaitsaye suna mamaki ta ce dasu . "bari ku ji wani abin dariya da ya faru tsakanina da Ma'aruf ynx nan da muka tafi na rakashi. na tambayeshi ne ya ya yaga bikin nan da muke yi? Me zai ce, shi ne sai ya ce da xuwansa ya ji ina ma da ace bikinmu ake yi ni dashi? Wai idan an tashi (engagement) dinmu, kwana uku kawai za a sa a daura aure." . Ilham tayi dariya . Babu wacce tayi dariya a cikin qawayenta . . Duk abin da Ilham take so a rayuwarta shi Ma'aruf yake so. Haka itama tana son duk abin da yake so. Idan Ma'aruf yazo gidan su wajenta, Ilham ta kan bude falon mahaifinta su zauna suyi hira idan baya nan. Sau da yawa idan Ma'aruf yazo sun fi yin kallo. Ilham tana son fina-finan indiya fiye da kowanne irin fim. Shi yasa ba ta da wata tashar da take kamowa fiye da (Zee Aflam) indai ita kadai zata yi kallo. . A ranar da ta fara shiga da Ma'aruf falon gidan su suka yi hira da ta kunna kallo sai ta tambayeshi . "kana kallon fina-finan indiya kuwa?" . Ma'aruf ya dubeta . "me yasa kika yi min wannan tambayar?" . Ilham ta ce dashi. . "sbd ina sha'awarsu fiye da duk wani abu da zan kalla na debe kewa. Ban sani ba ko kai baka sha'awarsu." . A qa'ida Ma'aruf bai ta6a zama ya kalli fim din indiya ba sbd basu yi masa ba." in har kallo zai yi yafi son ya kalli (Wrestling) ko wasannin qwallon qafa. . Bai fadawa Ilham baya so ba." ya ce da ita. . "nima ina sha'awarsu...suna burgeni." . Ilham ta kunna musu kallo, aka fara nuno 'yan wasa. Ta fara sanar da Ma'aruf ra'ayinta akan jaruman da take so. Maza da mata, ta ji yayi shiru ya kasa magana sbd bai sansu ba." Ilham ta yi dariya ta bar abin a xuciyarta, ta fahimci Ma'aruf baya kallon fina-finan indiya, yaqi fada mata gsky ne, don dai ya goyu bayanta kada ya kushe mata abin da take so. . Washe gari da Ma'aruf yazo gidansu suka zauna a falo suna hira, sai Ilham ta kunna masu kallo har ta kamo tashar qwallon sai ya ce da ita ta canza tasha ta kamo masu fim din indiya suyi kallo. Ilham ta dubeshi ta yi murmushi . L"Ma'aruf na fahimci baka kallon fim din indiya, me yasa zaka 6oye min abin da baka so, don kawai Kaga ni ina so?" . Ma'aruf ya ce da ita. . "wa ya fada maki bana kallon fina-finan indiya? ina kallon su sosai." . Ilham ta yi dariya ta ce dashi. . "zan qure ka fa, kada mu fara kallo in tambayeka sunan wani ka kasa fada min." . Ma'aruf ya ce da ita. . "duk wanda kika tambayeni zan fada maki sunansa." . Ilham ta kamo tashar tana dariya, ta san cewar Ma'aruf bai san kowa ba a cikin jaruman indiya. tana kamo tashar suka iske ana tallar sabbin fina-finai masu fitowa. Jarumar da aka fara nunowa tana rera sassanyar waqa a cikin sahara, iska na kada dogon gashin kanta da kuma gyalenta mai shara-shara, tun kafin Ilham ta tambayeshi ya ce da ita. . "wannan ita ce Kareenah Kapoor, wacce 'yar uwarta itama tsohuwar fitacciyar jaruma ce wato Karishma Kapoor. Kareena tana daga cikin manyan jarumai mata a fagen fina-finan indiya. tayi fim din Bewafaa tare da Akshay kumar. Tayi Asoka, tare da Sharukhan. Tayi Khabi Khushi Khabi Gham tare da Hirthic da su Amita Bacchan." . Ilham ta yi mamakin yadda akayi Ma'aruf ya san wannan jarumar haka sosai, bayan ta san bai ta6a kallon fim dinta ba." xuwa can bayan ta gama waqar sai aka sake nuno wata jarumar tana wasa da shuke-shuke a wani qayataccen lambu. Ma'aruf ya ce da Ilham . "ita kuma wannan ita ce Aishwariya, wacce ta kasance tauraruwa sha kallon duk wani fim da zata fito sbd daukakarta. Ta yi fina-finai tare da duk wani jarumi dake tashe. Tayi fim da Devdas tare da Sharukhan. Wanda fitaccen daraktan nan ya bayar da umarni wato Sanjay Leela Bansalay. Sannan tayi fim din jordan Akbar tare da Hirthic. Fitaccen fim dinta wanda ake ganin babu kamarsa shine Aor Pyar Hogaya, wanda ta fito tare da Boby Deol." . Ilham ta bi Ma'aruf da kallo cikin kaduwa da mamaki. Ita kanta bata san duk wadann fina-finan da yake fada mata ba." aka sake nuno wani jarumin akan babur Ma'aruf ya ce da ita. . "wannan shi ne Abishek Bacchan shine ya auri ita Aishwariya, kuma shine dan tsohon jarumi Amitab Bacchan. Abishek yayi fim din Run ya yi fim din Drona, da kuma Doom 1 da Doom 2 ya fito a fim din Dus tare dasu...." . Ilham ta dakatar da Ma'aruf ta tambayeshi . "Ya akayi ka san wadann fina-finan da jaruman Ma'aruf? na tabbatar jiya da kazo nan baka san kowa ba a cikin jaruman fim din indiya. ba ka ta6a kallon fim dinsu ko daya ba." ya akayi ka sansu daga jiya xuwa yau?" . Ma'aruf ya dubi Ilham ya ce da ita. . "gsky ne Ilham, ban ta6a kallon fim din indiya ba ko daya, kuma ban san sunan ko daya ba a cikin jarumansu. Jiya ne da nazo wajenki na fahimci kina so, shi yasa nima naji ina so. Duk abubuwan da kika ji na fada maki, da kuma wadanda ma ban fada maki ba, nayi bincikensu ne a wajen mutane daban-daban na sansu daga jiya xuwa yau. A ynx ina sha'awar indiyan fim sbd naji kina sha'awarsu. Duk abin da kike so a rayuwarki Ilham nima shi nake so a rayuwata." . Ilham ta kasa magana. Ta qurawa Ma'aruf masoyinta ido. A lkcn ne ta tabbatarwa kanta cewar ba zata sake samun masoyi kwatankwacin Ma'aruf ba a duniya. . . Lp=11%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 11 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun Taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Ilham ta kasa magana ta qura wa masoyinta Ma'aruf ido. A lkcn ne ta tabbatar wa kanta har abada ba zata sake samun wani masoyi a duniya kwatankwacin Ma'aruf ba." . . A zamantakewarsu Ma'aruf ya saba ko me ya samu tunanin shi na farko shi ne me zai yiwa Ilham wanda zai faranta mata rai da shi? Ma'aruf ya saba ya yi ta kashewa Ilham kudi da saye-sayen kayayyakin kyaututtukan soyayya. To amma Ilham ba ta san yaya yake qoqarin yi mata irin wadannan hidindimun ba a matsayin sa na wanda yake aikin bautar qasa. . Ilham tana so ta tambayi Ma'aruf amma tana jin kunyarsa. Sai da abokinsa Khalid ya ta6a bata wani saqo da Ma'aruf ya aiko shi sannan Ilham ta tambayeshi, ko ya san yadda Ma'aruf yake samun kudaden da yake kashe mata haka? . Khalid ya ce da ita. . "gsky Ma'aruf bashi da wata hanyar samun kudin da ta wuce dan alawus din da ake basu a inda yake aikin sa na (Service) sai kuma wata makaranta da yake xuwa yana taimaka masu a ranakun litinin da talata amma su bana jin yana amsar kudi. Kyauta yake yi musu." . Tun daga ranar Ilham ta fahimci duk abin da Ma'aruf yake samu a rayuwar sa akanta kawai yake qarar dasu baki daya. A lkcn ne tayi alqawarin ba zata qara amsar duk wata kyauta da Ma'aruf ya yi mata ba." . Tun daga ranar kome ya kawo ya bata, bata amsa, kuma duk sanda irin haka ta faru a tsakanin su sai ta fada masa ya daina yi mata dawainiyar komai. Ta gode! Ta gode!! Ta gode!!!..amma ba zata amsa ba." . Don kada ta riqa damuwa sai Ma'aruf ya daina bata kyautar komai. Ba a dade ba watan babbar sallah ya tsaya. Mahaifin Ilham ya tambayi 'ya'yansa irin kayan da za a siyasa a dinka da sallah. Kowa ya fadi irin kayan da yake so a saya masa. Ilham ta ce da mahaifinta ita tafi son atamfar England. Mahaifinta ya ce kada ta damu zai saya mata. . Sun yi wannan maganar da kwana daya, da wani a cikin yayyenta ya samu labarin irin atamfar da Ilham ta ce tana so a saya mata sa sallah, sai ya yi mata kutunguila ya soke alqawarin da mahaifinta ya yi mata. . Alh. Ayuba ya kira Ilham ya ce da ita. . "gsky atamfar nan da kika ce kina so ba zaki sameta ba Ilham. sbd nayi bincike an fadi mani bata da nagarta ga kuma tsada. Ynx ki bari a samu ko leshi ne na dubu uku a saya maki, ko kuma shadda, sai ki za6i wanda kike so a cikin biyun." . Ilham ta ji baqin ciki ya soki xuciyarta. Ta san wani ne ya je yayi mata wannan munafurcin a wajen mahaifinta. Don ya hana a saya mata atamfar da zata sa da sallah. Ilham ta ce dashi. . "Baba ka barshi kawai sai wani lkcn in ina da rabo na san wata rana zaka saya mani, tunda kayi niyya ba komai." . Ta tashi ta tafi tana share hawaye. Ta gwammace ta wanke tsofaffin kayanta ta ci sallar dasu. Ko ya akayi har Ma'aruf ya samu wannan labarin?... Kowa ya fada masa tayi wannan badaqalar da 'yan uwanta a gida? Ita dai bata sani ba, kuma bata fadawa kowa ba." . Saura kwana biyu sallah Ma'aruf ya xo gidansu ya sa aka kirata. A lkcn qarfe goma na safe Ilham ta fito cike da mamakin dalilin xuwan Ma'aruf wajenta da safe haka ko lfy har yake cewa tayi sauri ta zo? Da xuwanta Ma'aruf ya ce da ita. . "nazo ne ina so ki raka ni wani waje, amma zamu dade ba ynxn nan zamu je mu dawo." . Akwai yarda...akwai amincewa tsakanin Ilham da Ma'aruf. Bata yi ko kwalliya ba, haka nan ta fito da kodaddun kayanta, ta yafa qaramin gyalenta qafarta sanye da silifas. Ilham ta ce da shi. . "bari in shiga gida in canza kaya in sa takalmi, kaga silifas ne a qafata." . Ma'aruf ya ce da ita. . "ba komai, mu je a haka sauri nakw yi Ilham." . Ta ce dashi. . "shi kenan mu tafi.l" . Sai da suka fara tafiya taga ya tunkari wata qaramar mota (Civic) wacce ke a bakin hanya sannan ta fahimci shi ne ya zo da motar. Ma'aruf ya bude motar ya shiga kafin Ilham ta bude tata qofar ne ta tambayeshi. . "yaushe ka yi ciniki ban sani ba Ma'aruf?" . Ya yi dariya. . "ba tawa ba ce. Ilham ta wani abokina ne da muke zaune gida daya, shima corper ne." . Ma'aruf ya tashi motar, ya tuqa suka tafi.l Ilham tana zaune a gefe daya ya dauki hanya suka kama hanyar fita Katsina. Da taga gudun da yake yi yayi yawa, sai ta tambayeshi cikin wasi-wasi. . "wai ina zamu je ne Ma'aruf? naji ka xxe ba nisa kuma kana ta gudu, don Allah ina zamu je?" . Ma'aruf ya yi murmushi ba tare da ya dubeta ba ya ce....' . "kada ki damu kano zamu je, ai ba nisa ynxn nan zamu je mu dawo." . Ilham ta dafe qirji cikin mamaki. . "kano...? Ma'aruf ya baka fada mani ba, baka ganin yadda nake? Dubi fa silifas ne a qafata, dubi kodadden gyalen da na yafa. Gsky mu koma gida in canza kaya." . Ma'aruf ya juye ya dubeta ya ce. . "indai don takalmi da gyale ne ba sai mun koma gida kin canza wasu ba." naji kamar an ce ana sayar dasu a Kano." . Ilham ta roqeshi cikin natsuwa. . "ynx duk wannan wasan mu ajiyeshi a gefe daya. Ka fada mani gsky. Me zamuyi a Kano Ma'aruf?" . Ba tare da ya juyo ya kalleta ba ya ce da ita. . " zamu je mu sayi kayan sallah ne. Naji ance atamfar england kike so ki sa a wannan sallar. Shi ne zamu je ki za6i irin wacce kike so ki sa a wannan sallar a Kantin Kwari. Tun sanda labarin yadda kuka yi a gida ya sameni, na dauki alqawarin ko kaina zan sayar in samu kudi, sai kin ci sallah da irin kayan da kike so." . A sannan ne xuciyar Ilham ta shiga yi mata kirari: . Kin dace da masoyi Ilham....kin dace da mijin aure. Samun masoyi kwatankwacin Ma'aruf abu ne mai wahala a duniya. . . . Lp=12%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% PAge 12 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Ilham tana hangenshi ya fito da qwallo, wasu yara manya 'yan aji shida suna biye dashi cike da murna, Ma'aruf ya jasu xuwa filin qwallon makarantar. Ya rabasu gida biyu, ya fara yi masu nasiha, sannan ya sa masu qwallon suka fara wasa, shi kuma ya zama alqalin wasa, ya riqa hura usir yana binsu a guje duk inda qwallon ta nufa, . Wasu yara biyu suka yi karo da suna suka fadi suna kuka. Ma'aruf ya tsayar da wasan, ya kama qwallon ya riqe ya dawo da hankalinsa kan yaran da suka ji ciwo. Ya lallabe su suka tashi, sauran yaran suka zo suka zagaye shi. . Ma'aruf ya duba raunin da kowanne ya ji ya riqa lallashinsu da kalamai masu dadi, sannan ya kira wani dalibin ya ce dashi ya je dasu ofishin hedimasta a sa masu magani a raunin . Ma'aruf yana son daliban kamar yadda suke son shi. Ilham ta sirare ta tafi, ta koma gida ba tare da ya ganta ba." a xuciyarta tana tunanin shin idan ta auri Ma'aruf, haka zai riqa kulawa da 'ya'yanta...'ya'yansu da zasu haifa? Haka zai zama uba na-gari mai adalci da tausayin 'ya'yansa? Haka zai riqa kyautata masu? . Sai da yamma da yazo gidansu ta ce dashi tana dariya . "Daxu na je makarantar da kake koyarwa, na dade ina kallon ka, baka ganni ba." . Ma'aruf ya ce....' . "kamar da gaske." . Ilham ta ce dashi. . "ka tuna lkcn da yaran nan da suke qwallo suka yi karo. Ka tsayar da wasan ka zo wajen su tare da sauran yaran da ke qwallon?" . Ma'aruf ya ce da ita. . "amma baki yi min magana ba in zo Ilham?" . Ta ce dashi. . "6oyewa nayi, dama bana so ka ganni. Na ga ka sha gudu kai da yara, ya tsamin jiki?" . Suka yi dariya . "Ai na saba, bana jin wuya a haka muke wuni muna wannan guje-gujen ni dasu." . Ilham ta tambayeshi . "kuma da gaske kyauta kake yin aiki a makarantar Ma'aruf' basu biyanka komai?" . Ya ce da ita. . "Ai ni na san kaina Ilham, ba don kudi nake yi ba, ina yi ne don in taimaki al'ummata da kuma qasata." Ilham ta bi shi da kallo, bata ce dashi komai ba." Ma'aruf ya qara da cewa. "lkc ya yi da ya kamata mutane su fahimci muhimmancin aikin taimakon kai-da-kai.... Duk a yadda ka samu kanka, to ya dace ka binciko irin baiwar da Allah Yayi maka, ka taimaki al'umma da ita ka bayar da taka gudunmawar." . Idan mutum ya kalli duniya zai ga cike take da kayayyakin more rayuwa, wadanda wasu mutane suka samar dasu da tunaninsu da basirarsu. Kodayaushe yana da kyau mutum ya jajirce shima ya ga ya samar da wani abu da zai amfani mutane koda qanqani ne....! Koda yaushe na kan dora rayuwata akan wata magana da na yarda sa ita wacce ke cewa." . "Hanya daya da zaka rayu har abada shi ne ka bar wani aiki na alheri a bayanka." . Ilham wacce ta qurawa Ma'aruf ido ta ce a xuciyarta . "Na kamu da so...na kamu da so..." . . . *** *** ** . . Babi na uku. . . Da kowa yaga abin dai da gaske suke yi. Ilham da Ma'aruf sun riqe soyayyarsu da hannu bibbiyu, suna son junansu kamar su hadiye kansu sai Alh. Ayuba ya kira Ilham ta same shi a falonssa ya ce da ita. . "Ilham duk abin da ki ke ciki ke da yaron nan da yazo bautar qasa, ban ta6a cewa da ke komai ba." ina ganin lkc ya yi da ya kamata in yi magana da ke akan wannan al'amarin." . Ilham ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba. Alh. Ayuba dake zaune akan kujera ya ci gaba da cewa. . "na fahimci yadda kuka shaqu ke da shi, kuma a yadda naga alama da gaske yake yi. To amma kin kuwa tsaya kin yi tunani sosai akanshi Ilham? Kina jin idan ya aureki zai iya riqe ki da mutunci? Ki a lamarin ku na yara baku tsayawa ku ba komai lkc, kuna matuqar yanke hukunci matuqar xuqatanku suna son wani abu. Me kika fahimta a game dashi, wanda ya baki qwarin guiwar jin shi mutum ne na-gari kuma zai iya riqe ki tsakani da Allah?" . Ilham ta yi ajiyar xuciya. Ba tare da ta dago kai ta dubi mahaifinta ba." ta ce da shi a sanyaye. . "Baba kowa yana shaidar Ma'aruf a unguwar nan, ko mutane ka tambaya zaka ji ance yana da mutunci da...." . Alh. Ayuba ya dakatar da 'yarsa Ilham . "zancen shirme kenan! Don mutane sun ce yana da mutunci sai ki dogara da haka? . . Lp=13%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 13 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun Taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Ilham tana hangenshi ya fito da qwallo ya riqeta da hannunsa biyu, wasu yara 'yan aji shida manya suna biye da shi cike da murna. Ma'aruf ya ja su xuwa filin qwallon makarantar. Ya raba su gida biyu, ya fara yi masu nasiha, sannan ya sa masu qwallon suka fara wasa, shi kuma ya zama alqalin wasa, ya riqa hura usur yana bin su a guje duk inda qwallon ta nufa. . Wasu yara biyu suka yi karo da juna suka fadi suna kuka. Ma'aruf ya tsayar da wasan, ya kama qwallon ya riqeta ya dawo da hankalinsa kan yaran da suka ji ciwo. Ya lallashesu, suka tashi, sauran yaran suka zo suka zagaye shi. . Ma'aruf ya duba raunin da kowanne ya ji ya riqa lallashinsu da kalamai masu dadi, sannan ya kira wani dalibin ya ce da shi ya je dasu ofishin hedimasta a sa masu magani a raunin . Ma'aruf yana son dalibansa kamar yadda suma suke son shi. Ilham ta sirare ta tafi, ta koma gida ba tare da ya ganta ba." a xuciyarta tana tunanin shin idan ta auri Ma'aruf, haka zai riqa kulawa da 'ya'yanta..'ya'yansu da zasu haifa? Haka zai zama uba na-gari mai adalci da tausayin 'ya'yansa? Haka zai riqa kyautata masu? . Sai da yamma da yazo gidan su ta ce dashi tana dariya . "Daxu na zo makarantar da kake koyarwa, na dade ina kallonka, baka ganni ba." . Ma'aruf ya ce....' . "kamar gaske." Ilham ta ce dashi. "ka tuna lkcn da yaran nan da suke qwallo. Suka yi karo ka tsayar da qwallon ka je wajen su tare da sauran dalibai?" . Ma'aruf ya ce da ita. "amma ba ki yi min magana ba in zo Ilham?" ta ce da shi. "6oyewa na yi, dama bana so ka ganni. Na ga ka sha gudu kai da yara. Ya tsamin jiki?" suka yi dariya tare. . "Ai na saba, bana jin wuya a haka muke wuni muna wannan guje-gujen ni da su." . Ilham ta tambayeshi "kuma da gaske kyauta ka ke yin wannan aikin a makarantar basu biyanka komai?" . Ya ce da ita. "Ai ni na san kaina Ilham. ba don kudi nake yi ba, ina yi ne don in taimaki al'ummata da kuma qasata." Ilham ta bi shi da kallo bata ce komai ba, Ma'aruf ya qara da cewa. "lkc ya yi da ya kamata mutane su fahimci muhimmancin aikin taimakon kai-da-kai.... Duk yadda ka samu kanka, to ya dace ka binciko irin baiwar da Allah Ya yi maka, ka taimaki al'umma da italian ka bayar da taka gudunmawar." idan mutum ya kalli duniya, zai ga a cike take da kayayyakin more rayuwa wadanda wasu mutane suka samar dasu da tunaninsu sa basirarsu. Kodayaushe yana da kyau mutum ya jajirce shima ya ga ya samar da wani abu da zai amfani mutane koda qanqani ne....! Kodayaushe ina dora rayuwata akan wata magana da ke cewa. "Hanya daya da zaka rayu har abada ita ce ka bar wani aiki na alheri a biyanka. . . . *** *** . . Babi na uku . . Da kowa yaga abin dai da gaske suke yi. Ilham da Ma'aruf sun riqe soyayyarsu da hannu biyu, suna son junansu kamar su hadiye kansu, sai Alh. Ayuba ya kira Ilham ta sameshi a falonsa. Ya ce da ita. . "Ilham duk abin da kike ciki ke da yaron nan da yazo bautar qasa, ban ta6a cewa da ke komai ba." ina ganin lkc ya yi da ya kamata in yi magana dake akan wannan al'amarin." Ilham ta sunkuyar da kanta ba ta ce komai ba. Alh. Ayuba dake zaune akan kujera ya ci gaba da cewa. . "na fahimci yadda kuka shaqu ke da shi, kuma a yadda naga alama da gaske yake yi. To amma kin kuwa tsaya kin yi tunani sosai akanshi Ilham? kina jin idan ya aureki zai iya riqeki da mutunci? Ku al'amarin ku na yara baku tsayawa ku ba komai lkc, kuna gaggawar yanke hukunci matuqar dai xuciyarku tana son wani abu. Me kika fahimta a game da shi, wanda ya baki qwarin guiwar shi mutum ne na-gari, kuma zai riqe ki tsakanisa da Allah?" Ilham ta yi ajiyar xuciya. Ba tare da ta dago kai ta dubi mahaifinta ba." ta ce da shi a sanyaye. "Baba kowa yana shaidar Ma'aruf a unguwar nan, ko mutane ka tambaya zaka ji sun ce yana da mutunci da..." Alh. Ayuba ya dakatar da 'yarsa Ilham ya ce....' "zancen shirme kenan! Don mutane sun ce yana da mutunci sai ki dogarA da haka? Ke ce ai ya kamata ki lura da halayensa da dabi'unsa, ba jira zaki yi sai wani ya fada maki ba. Ke me kika fahimta a game dashi?" Ilham ta numfasa ta ce da mahaifinta. "to gsky baba nima a yadda na fahimci Ma'aruf mutumin kirki ne. Ni kaina da ban gamsu da halayensa ba, ba zan bashi damar ya riqa xuwa nan gidan ba." . Alh. Ayuba ya gyara zama akan kujera ya ce....' "shi kenan idan kin ga yayi maki a rai kina sonshi ni a wajena babu matsala. Wanda kika ce kina so to shi zan baki. Amma abin da bana so shi ne, kada wani abu ya je ya dawo bayan an yi auren nan, ki dawo mani da wani qorafi ko wata maganar daban, ba zan lamunci wannan ba. Shi yasa nace ki tsaya tukuna kada ki yi gaggawa, ki bari sai an dauki lkc mai tsawo, bayan kin fahimceshi sai ki yanke hukuncin da zaki yanke." . Ilham ta yi shiru xuwa can ta ce da mahaifinta. . "to baba, duk abin da ka ce ba zan iya qetare maganarka ba. amma dai ni tuni na gama yin duk wani tunani da xan yi a game da shi. Sai dai kai idan zaka yi naka binciken akan shi. Don kaima ka tabbatar da hakanl" Alh. Ayuba ya ce. "A'a, bani da wani lkc da zan yi bincike akan wanda kika kawo gidan nan kika ce kina so. Haqqina ne in za6 maki miji na-gari, sbd haka idan ya yi maki. Kin tabbatar mutumin kirki ne, shi kenan sai ki fadi masa ya turo magabatansa su zo a yi magana. . . . Lp=14%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 14 . . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun Taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Sai ki fada masa ya turo magabatansa su zo a yi magana. ni kaina nafi son ki yi auren in dai kin samu miji na-gari." Ilham ta yi shiru a zaune ba ta sake cewa komai ba, Alh. Ayuba ya ce da ita. "iyakar maganar kenan dama, ki tashi ki tafi dakin ki, idan ya zo ki ce da shi nace ina son ya turo magabatansa su zo." dadi da farin ciki suka lulli6e Ilham, ta tashi cikin kunya ta tafi dakinta da sauri. Tana xuwa ta turo qofa ta rufe ta fara tsalle tana muna...me ya fi wannan ranar a rayuwata? Mahaifinta ya amince ya bata wanda take so a xuciyarta.? Ilham ta yi rawa da murna ita kadai a cikin dakinta, sbd sabuwar rayuwa ta zo." . Ta rasa duk wani abu da take so a duniya. sai ynx a karo na farko zata fara samun abin da take so a Tarihin rayuwar ta. . A ranar Alh. Ayuba ya kira manyan 'ya'yansa uku, Auwal da Mustafa da Jamilu ya ce dasu cikin farin ciki. "Qanwarku ta samu miji zata yi aure." ya saurara sannan ya sake fada masu cewa. "Yaron nan ne dake xuwa nan gidan, wanda yake (service) din nan. Na bata shi tunda ta ce shi take so, na ce ya turo iyayensa su zo muyi maganar aure. Na kira ku ne don in sanar da ku a matsayin ku na 'yan uwanta." . Su dukansu ukun sun san maganar soyayyar Ilham da Ma'aruf. Abin da yasa basu ta6a nuna baqin cikin su ba shi ne, sun san Ma'aruf bashi da komai. Baqo ne a garin, yazo bautar qasa ne kuma bai fara aiki ba." ko suturar arziqi Ma'aruf bashi da ita, sau da yawa mutanen da ya saba dasu a layin suke taimaka masa. Sun tabbatar idan ya auri Ilham a cikin wannan halin da yake, ba qaramar wahala zata sha ba." abin da zata ci ma sai ya gagareta. Wannan labarin da mahaifinsu ya kira su ya sanar dasu ba qaramin abin farin ciki bane a gare su." Auwal ya dubi Mustafa suka gintse dariya. Jamilu ya dubesu yana murmushin qeta. Ya fara yin magana ya ce....' . ""gsky mutumin nan yana da kirki Baba. Ni dai na yaba da halayensa. Ba wanda ya cancanta a ba Ilham sai shi. Allah Ya sa alheri. Mun yi murna." . Auwal ya nuna farin cikinsa a fili ya ce....' . "Baba Ma'aruf ai ya kai mutum, kowa yana yabonsa a unguwar nan, tunda ya zo ba a ta6a rabashi da kowa ba yana da haquri' ya san mutuncin mutane. Indai shi Ilham ta za6a to ta sami miji na-gari." . Mustafa ya qara da cewa. . "Baba da iyayensa sun zo kawai a amshi maganar nan, kada ma a tsaya wani 6ata lkcn yin bincike. Ma'aruf mutumin kirki ne, zai riqe mana qanwarmu da mutunci, indai shi ta za6a da kanta, to muma shi muke so, ya yi mana." . Bayan Alh. Ayuba ya gama sauraren ra'ayin 'ya'yansa akan Ma'aruf sai ya ce dasu. . "to Alhamdulillah naji dadi sosai bisa haka, sbd kunga wannan yarinyar bata da uwa a gidan nan, kada wani abu ya sameta mutane su ce na zalunceta. To amma tunda kuna ce kuna gamsu da halayen yaron ai babu damuwa, idan magabatansa suka zo sai mu amshi maganar, Allah Ya sa alheri." . Su duka ukun suka ce....' . "amince Baba." . Suka tashi suka fita suka bar mahaifinsu a babban falonsa. Da fitarsu suka qyalqyata dariyar mugunta, suka tafi dakin mahaifiyarsu suka sameta tana cin abinci a zaune. Had. Kubra ta tsaya da cin abincin tana kallo su, kamar masu ta6in hankali. . "me ye haka kuka shigo kuna dariya bako sallama?" . Mustafa ya sassauta dariyar ya ce da mahaifiyarsu. . "wannan sokuwar yarinyar ce wai za a a wa aure. Shi ne Baba ya kira mu ynx yake fada mana." . Had. Kubra ta 6ata rai ta ce....' . "to shi ne abin ya baku sha'awa, don zata yi aure har kuke murna kuna dariya? Kuna san ko nawa Alhaji zai kashe idan wannan hidimar ta taso? To ina nan zan gani, idan har ya ce zai yi mata wasu kayan daki masu tsada fiye da na 'ya'yana da akayi masu a baya, Wallahi sai na qarqare zaman lfy a nan gidan, zan xuba ido kuma in gani." . Mustafa ya ce da mahaifiyarsu . "tsaya ki ji mama. Ai ba ta kayan daki ake yi ba." saurayin da Ilham take so bashi da komai. Kawai daga ya zo bautar qasa ta liqe masa, wa ya san ko sai yaushe zai samu aiki? Ynx don mutum yana taqamar yana da digiri a nan qasar, sai ya shekara goma bai samu aiki ba." . Haj. Kubra ta saki ranta ce....' . "YAUWA 'YAR BANZA! Ai na ji dadi, ta aureshi ya qerata ba ci ba sha, kuma bata isa ta ce zata riqa xuwa nan gidan tana kawo mana matsala ba, ba zan dauka ba." . Jamilu ya qara da cewa. . "mama ke da kin ganshi zaki san fatara da talauci sun yi mashi kanta a jiki. Idan yana cikin abokanshi ko (Pure water) sai sun sai masa, a haka ne zai iya riqe mata? Shi Baba yana murna ne 'yar lelenshi ta samu miji har yana wani kiranmu. Ki barshi kawai muna nan sai wannan yarinyar ta zama abar tausayi." . Haj. Kubra ta yi murmushi ta ce....' . "yauwa ai haka ya yi. Ba dai mu ake so a riqa takawa ba ba gidan nan? To ko uwar Ilham tana nan a gidan bata isheni ba ballantana ita wacce nake kallonta a tafin hannun..... . . Lp=15%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 15 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Ballantana ita wacce nake kallonta a tafin hannuna. Da ga ni har ku 'ya'yana mun fi qarfin a takamu a gidan nan, mune gida babu wanda ya isa ya zo ya keta mu." . Haj. Kubra da 'ya'yanta suna cike da jin dadin ganin Ilham ta auri mijin sa bashi da komai da .zai bata. Ita kuma Ilham tana cike da jin dadin zata auri mijin da zai bata abin da ta dade tana nema bata samu ba." . Soyayya...kyautatawa..qauna...kulawa. . . *** *** * . Kamar wasa! Ilham ta fito gida cike da farin ciki tana murmushi ta samu Ma'aruf a waje yana jiranta. Da xuwanta ta fara fada masa abin da yake yi mata qaiqayi a xuciyarta . "Daxu Baba ya kira ni, ya ce in fada maka wai ka turo magabatanka su yi magana." . Ma'aruf ya kalleta cikin xumudi. . "da gaske kike yi Ilham?" . Ta yi dariya cikin kunya. . "kaima ai ka san ba zan fadi maka wannan maganar da wasa ba." da gaske nake yi mana. In kuma dama ba sona kake yi da gaske ba a ynx ne zan fahimta." . Ma'aruf ya kalleta har cikin idanunta. kallon soyayyar da ya saba yi mata idan suna tare. Ya ce da ita. . "bai kamata in yi karambanin fadi maki irin soyayyarki dake a xuciya ta ba, sbd harshe ma ba zai iya jure tsawon lkcn da zan dauka ba wajen fada maki ko ke wace ce a wajena ba." abin da kawai zan iya fada maki shi ne....! Ilham ke ce abin gdy da yabawar da na samu a rayuwata, wacce har in bar duniya, babu sauran wani abu da zan sake samu kwatankwacin ki. Rayuwata gi6i ce ba zata cika ba sai tare da ke Ilham. Idan har na yarda na rasa ki kamar na rasa raina ne....! Ta yaya kuwa zan amince ds gangan in rasa rayuwata Ilham?" . Maganar ta bata dariya...maganar ta faranta mata rai sosai. A daren maganar ta riqa tunowa. Ta dauki lkc mai tsawo har qarfe daya na dare bata yi barci ba, tana ta juye-juye ita kadai a kwance akan katifarta. Tana tunanin sai yaushe wannan babban masoyin nata zai zama mijinta su zauna tare? . . Washe gari tunda sassafe Ma'aruf ya shirya ya tafi Matazzu garin iyayensa da kakanninsa. Ya samu mahaifinsa da sauran 'yan uwansa, wadanda duk sanda ya zo gidan ya kawo masu ziyara basu yi masa kyakkyawar tar6a. . Da ya fadawa mahaifinsa cewar ya samu aure ne yana so a je a tambayo masa iyayen yarinyar a Katsina, tun kafin ya gama sanar dashi ya ce....' . "to ni zaka zo ka fada mata ka samu aure don baka da kunya? Ga 'yan uwana nan kafi qarfin ka je ka same su sai ni' zaka dubi qwayar idona ka yi min rashin kunya. Rashin mutuncin da uwarka ta yi mana a nan gidan, wato ynx kaima ka girma shi ne zaka yi mana ko?" . Ma'aruf ya ba mahaifinsa haquri ba don ya yi masa laifin komaI ba." ya san san dama dolene sai ya sha fada da zagi indai zai zo wajen mahaifinsa. Qiyayya da gabar dake a tsakanin mahaifinsa da mahaifiyarsa ita ce ta jawo masa wannan tsanar a gidan su." mahaifiyarsa ta rasu tun yana yaro amma har xuwa ynx da Ma'aruf ya girma, mahaifinsa bai yafe mata ba, sbd tsabar riqo da zafin rai, Ma'aruf ya sake baiwa mahaifinsa haquri. Ya je wajen qannen baban nasa. Ya fada musu abin da yake faruwa. Basu yi masa jayayya ba suka amince zasu je a yi maganar auren. Ma'aruf ya yi masu jagora xuwa Katsina, ya kai su wajen mahaifin Ilham. Ba a tsaya wani 6ata lkc ba." Alh. Ayuba ya ce ya ba Ma'aruf 'yarsa, sannan kuma ya sara masa sadaki naira dubu ashirin. . A satin Ma'aruf ya kai kudin auren. A ka tsayar da lkcn biki. Wata biyu masu xuwa. Allah Shi ne Mai rufawa bawan sa asiri akodayaushe. Ma'aruf bai ajiye komai ba, kuma bashi da komai. amma sbd mutuncinsa da kyautatawarsa, da kuma iya zama da mutane, ya yi ta samun gudunmawa a wajen ma'aikatan da yake aikin bautar qasa a ma'aikatarsu. Da sauran mutanen da yake zaune tare dasu a unguwar su Ilham . Wadansu suka riqa bashi kudi, wasu turamen zannuwa wasu shaddoji da takalma, wata mata wacce ko sunanta Ma'aruf bai sani ba, a layin ta aiko masa sa sarqoqi masu tsada kala biyar, ta ce a sa a kayan lefe. . Ma'aruf ya ce da wanda matar ta aiko, bai san yadda akayi ta sanshi ba, har ta yi masa wannan kyautar. Mutumin da ya kawo masa sarqoqin ya ce....' . "Sunanta Haj. Zainab, ta ce tun sanda kazo layin nan duk sanda zata ganka sai ka gaisheta. Shi ne aka bata labarin zaka yi aure." . Ma'aruf ya ce ya gode...ya gode. Wani direba dake a kusa da gidan da yake zaune ya aiko masa da babban leshi guda daya. Tun sanda Ma'aruf ya ciro dansa da ya fada a cikin rami ya kawo masa shi har gida, mutumin ya yi alqawarin duk sanda ya samu hali zai yiwa Ma'aruf wani abin alkairi..... . . Lp=16%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 16 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun Taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Mutumin ya yi alqawarin duk sanda ya samu hali zai yiwa Ma'aruf abin alheri indai suna tare a unguwar. . Ma'aruf ya ce a fada masa shima ya gode, Allah Ya bar qauna a tsakanin sa da duk wadanda suka taimaka masa, manyan abokansa su Khalid mai sayar da kati, suka hada guiwa su hudu, suka ce sun dauki nauyin duk abincin da za a ci a wajen bikin Ma'aruf. suka buga katin gayyata suka rarrabawa mutane. . Saura sati daya a daura auren Ma'aruf da Ilham ne ya samu gidan da zasu zauna. Wani attajiri dake a unguwar ne ya bashi gidan haya akan dubu arba'in duk shekara daya. Amma sbd kyakkyawar shaidar da Ma'aruf ya samu a wajen mutane, mai gidan ya ce ya yafe masa na rabin shekara ya zauna kawai, bayan wata shida idan ya samu aiki sai ya fara biyansa. . Auren ya yi albarka... Ya yi kwarjini sosai. Abin da Ma'aruf bai ta6a zato ba, bai ta6a tsammani ba." saura kwana uku a daura auren. Manajansu wanda Ma'aruf ya yi aikin bautar qasa a qarqashinsa a babban ofishin hukumar wutar lantarki ya kira shi har ofishin sa. A ranar da abin ya faru an kai sati uku da kammala bautar qasar da Ma'aruf ya yi a wajen su, har ya yi bankwana da su ya tafi.l . Manajan ya miqawa Ma'aruf takarda yana dariyar taya murna. Ya ce ya amsa ya karanta ya ga abin da ta qunsa. Ma'aruf ya amsa ya duba, ya dago kai cikin kaduwa da xumudi, ya ce da Manajan . "Ranka ya dade wannan ai (Offer) ce....' na samu aiki ne?" . Manajan ya gyara zama ya dubi Ma'aruf yana murmushi . "qwarai kuwa Ma'aruf, takardar shaidar daukarka aiki ce, daga yau kaima ka zama ma'aikacinmu, ina tayaka farin ciki. Na san ka yi mamaki, don da baka sa ran samun aiki a nan ba." to amma ina so in tabbatar maka da cewa tun xuwanka aikin bautar qasar da ka yi wajen mu, nake ta qoqarin ganin na samar maka aiki sbd kyawawan halayenka da gskyrka. Bamu ta6a zama da mutumin da muke so irin ka ba a wannan ma'aikata tamu, tun wata biyu da suka wuce wannan takardar ta fito, ta maqale ne a wani ofishi, don haka za a baka albashin wata biyu da suka wuce, ko yau kake so za a baka kudin ka." . Ma'aruf ya rasa abin da zai cewa Manajan, ya duqar da kai ya fara rusa kuka. Ya samu madogara a daidai lkcn da zata amfaneshi, sauran kwana uku a daura auren Manajan ya ce da Ma'aruf . "ba kuka zaka yi ba, ka godewa Allah ne Ma'aruf. An ce halin mutum jarinsa. Kasancewar ka mutum na-gari da kyawawan dabi'unka, su suka jagoranceka ga samun wannan aikin da ka yi, amma kamar yadda zaka gani a jikin wannan takardar ba a nan aka ajiyeka ba, a Malumfashi zaka yi aiki a ofishin mu dake a can, kaga da amarya ta zo sai ku dunguma kawai ku tare a can, ku sha amarcinku tare da sabon aiki." . Ma'aruf ya yi murmushi ya share hawayen dake a idonsa. . . A ranar ya amshi kudinsa da manaja ya fada masa na albashinsa na wata biyu da suka wuce. Ma'aruf ya qara akwatina uku na aure akan guda dayar da ya saya a baya, ya sayi duk abubuwan da bai saya ba a baya, ya hada kayan lefe cikakku, wanda ko ita kanta Ilham bata yi tsammanin samun su daga wajen Ma'aruf ba." . Labari ya watsu a unguwar. Cewar Ma'aruf ya samu aiki ana gab da yin aurensa. Mutane suka yi ta taya shi murna goma da goma. Ga aiki ga amarya. A ranar Ma'aruf ya aika da kayan lefe gidan su Ilham ' an kai kayan kenan an tarasu a dakin haj. Kubra, da Ilham ta shigo ta gansu bata tsaya jiran komai ba sai ta kira Ma'aruf a waya. . "ina son ganinka ynxn nan a gida, ka yi sauri ka zo." . Ma'ya zo fuskarsa cike da farin ciki, ya samu Ilham a zauren gidan su tana jiran xuwansa. . "ya akayi ne amarya? Saurin me kike yi ne da kike ta faman kira na?" . Ilham ta ce dashi cikin damuwa. . "na fada maka kada ka qure kanka wajen kayan lefe, ma' na san halinka ynx haka sai da ka yiwa kanka qarqaf akan sayen wadann kayan. Ka tuna fa zaman aure zamu yi ba zaman qarya ba. Idan baka bar komai a hannunka ba bayan aure me zamu ci? Gsky zan sa a dawo maka da kayan, ka sayar da guda uku, akwati daya ya isheni na gode, na san kana sona, amma bana so ka sha wahala a kaina." . Ma'aruf ya ci gaba da saurarenta yana murmushi. sai da ya ji ta qai qarshe. Sannan ya ce da ita. . "nima na gode da tausayina da kike ji Ilham, hakan yana qara mani sonki a xuciyata. Amma a wajen kayan aure bai kamata ki tsaya kina wahalar da kanki kina tausayin muqaddashin Manajan hukumar wutar lantarki a shiyyar qaramar hukuma ba." duk kayayyakin da na saya ban qure kaina ba Ilham kada ki damu. Har ynx ina da sauran kudi a hannuna, kuma sun ishemu kashewa koda bayan biki ne....! . Ilham ta kalleshi cikin rashin fahimta. . "wane ne muqaddashin Manajan da ka fada mani ynx?" . Ma'aruf ya ciro takardar shaidar daukarsa aiki da yazo da ita Ilham ta gani, ya nuna mata sannan ya ce da ita. . "na samu aiki a inda nayi (Service) Ilham, sun tura ni ofishinsu dake Malumfashi. Ki fadawa su Baba idan kin shiga gida. Su tayamu murna." . Ilham ta tafa hannuwanta ta yi tsalle a gaban Ma'aruf ya na kallonta yana yi mata dariya. Ta daga hannu ta yiwa Allah gdy. Ta garzaya cikin gidansu da gudu don ta fadawa 'yan uwanta da Haj. Kubra su yiwa masoyinta murna ya samu aiki. Mijin da zata aura wanda ake ta cece-kucen bashi da aikin yi, ynx ya samu madogara. . Da labarin ya je kunnen Haj. Kubra dama kuma tana cike da baqin cikin baqin cikin akwatuna hudu lefe da Ma'aruf ya turo, sai ta sanar 'ya'yanta halin da ake ciki. Cewar gida babu lfy. A zo a zauna a nemo mafita, don kuwa in aka xubawa Ilham idanu ga alama zata yi nasara akan su." mijin da zata aura wanda ake ta murnar bashi da komai bai wuce ya yi mata akwati daya ba. To ya samu aiki, kuma tun ynx kafin ayi auren har ya fara yi mata sha-tara ta arziqi. A haka za a sa mata ido tana tsalle tana murna ba a yi komai akanta ba?" . . . Lp=17%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 17 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun Taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . A haka za a sa mata ido tana tsalle tana murna a cikin gidan ba za a yi komai ba akan ta?" . Mustafa ya ce da mahaifiyarsu a fusace. . "ba zai ta6a yiwuwa ba." ba zamu ta6a yarda ayi wannan auren ba." bari mu je mu samu Baba idan ya dawo." . Da daddare sanda mahaifinsu Alh. Ayuba ya shigo gidan ne suka same shi a dakinsa su duka ukun, fuskokinsu cike da damuwa qarara. Suka fada masa abin da yake tafe da su." Auwal shi ya fara yin magana a matsayin sa na babban yayansu a gi.... "Baba mun yi kuskuren amincewa da Ma'aruf, wanda qanwarmu Ilham zata aura. Mun yi bincike mun gano tantirin mai neman mata ne, ba zamu yarda a bashi qanwarmu ya je ya kwaso cuta ya sa mata ba, don haka a fasa wannan auren a mayar masa da kayansa kawai." . Mustafa ya fadi tashi matsalar kamar zai yi kuka. . "bayan wannan ashe yana sata, sai daxu ake liissafo mana mutanen da ya satarwa kaya a unguwar nan. Kuma Baba ka san sata tana bin xuriya, ba zamu yarda qanwarmu ta auri 6arawo, 'ya'yanta su taso suna sace-sace ba, ana cewa 'yar uwarmu ta haifesu. Wannan 6ata suna ne....!" . Jamilu ya qara da cewa. . "sannan kuma majiya mai qarfi ta tabbatar mana da cewa an ganshi yana shan giya. Idan aka bashi Ilham bamu san abin da zai yi mata ba, kada ya je ya shawo, ya kamata da bugu, ya hallaka mana 'yar uwarmu. Don haka abu mafi alheri shi ne a yi haquri da auren nan, a barta ta samu wani mijin, wanda ya fito daga gidan mutunci ba irin Ma'aruf ba." . A karo na farko tun zamanin da aka yi suna kawowa mahaifin su duk wata shawara yana dauka, a wannan karon sai ya taso su da fada kamar zai buge su." . Tuntuni kun san da wannan matsalar amma kuka 6oye min baku fada ba, sai ynx da lkcn ya qure saura kwana uku a daura aur? Kuna so ne mutane su zage ni a gari? Kome yake yi dolene a daura wannan auren, kuma kome ya samu Ilham laifinku ne ku da ita, sai da na taraku itama na tuntu6eta in kun san yaron nan ba yaron kirki ba ne kada ku amince da zancen nan. Ku ka ce kun yi bincike mutumin kirki ne, ita ma tace min ta ji ta gani shi take so. Sai ynx zaku zo min da wannan tadin banzan? Ku tafi ku bani wuri sakarkarun banza marasa hankali." . Alh. Ayuba ya kore su, suna rige-rigen fita daga dakinsa, suna ji suna gani har ranar daurin aure tazo. Aka daura auren Ilham da Ma'aruf. Baqin ciki kamar ya kashe yayyenta. Ba ma kamar yadda suka ga mutane sun zo sun cika qofar gidansu daga ko'ina. abokan Ma'aruf ne na kusa da na nesa, da wadanda suka yi bautar qasa tare, da malaman makarantar da yake xuwa yana taimakawa a unguwar yana koyar da yaran su." . Mutane sun nuna masa kara, sun yi masa halacci, bayan an daura auren ya yi ta gaisawa dasu yana yi masu gdy. Da fatan kowa zai koma gidan sa lfy. Qawayen Ilham suma sun yi mata halacci da kara, sun mutunta bikinta wajen yin anko mai tsada, tare da walimar da suka dauki nauyi a aljihun su." bikin masoya ne wanda ya ba kowa sha'awa. . Aka dauki amarya da yamma aka kaita gidan da Ma'aruf ya kama tun sati biyu da suka wuce, kafin ya tsayar da ranar da zai tashi su koma Malumfashi inda zai fara aiki. Ilham ta yiwa yayyenta da mahaifinta bankwana, tana kuka tana roqonsu su yafe mata. Ta durqusa cikin ladabi ta nemi gafarar HaJ. Kubra. ta san ta zalunceta don ba ita ta haifeta ba." ta nuna mata banbanci da qiyayya don ba ita ta haifeta ba, amma ta yafe mata. . Ta yafewa duk wanda ya cuceta, kuma har abada babu wanda zata riqe da gaba a xuciyarta. 'Yan uwanta 'yan uwanta ne har abada, haka yayyenta ne....! Kafin a tafi da ita xuwa dakinta Alh. Ayuba da ke yi mata nasiha ta zauna da mijinta lfy ya ce....' . "muma mun yafe miki Ilham." . Sun zauna da ita tun tana jaririya...tun sanda aka haifeta gashi yau radar da zasu Rabe ta zo." Ilham zata tafi dakin aure. Kwanansu goma kawai a Katsina bayan biki. Ma'aruf ya dauki matarsa suka koma Malumfashi inda zai fara aiki. Burin masoya ya cika! Ilham da Ma'aruf sun zama miji da mata. . . . *** *** *** . . Babi na hudu . . . Soyayyarsu bata ragu ba." qaunar da suke yiwa juna tare da matsanancin begen junansu idan basu tare duk suna nan daram a zamantakewar aurensu. Su biyu kawai suke zaune a gidan, idan Ma'aruf zai je aiki da safe sai Ilham ta biyoshi har kusa da waje kamar ta bi shi su tafi tare. Yana so Daga tana qorafin zama a gidan ita kadai, shi kuma yana yi mata dariya. Ya sha fada mata cewar: . "idan kika yi haquri wata rana duk wannan kadaicin zai zama tarihi Ilham. Ynx dai gamu mu biyu qwal muke zaune, inda rayuwa wata rana zamu kai mu goma ko ashirin." . Idan a zaure ya fada mata haka, idan ta rakoshi zai fita sai ta tsaya a jikin qofar tana hangenshi har ya yield nisa ya bar unguwar, sannan sai ta koma cikin gida. . Basu dade da xuwa Malumfashi ba Ilham ta saba da maqwabtansu, ta fara sada xumunci da qawance tare da matan da tazo ta samu a unguwar. Duk inda Ilham ta je da ta zauna zata fara duba agogo. . "bari in je gida mijina ya kusa dawowa." . Ko gidanta aka zo ba a wani sakewa a zauna a yi hira, sai ta fara maganar mijinta ko kuma ta dauko waya ta kira shi suyi ta hira tana dariya, ta bar baquwarta gingirin a zaune. . Wannan ne dalilin da yasa mata suka fara tseguminta suna cewa 'Dadi miji' . Da maganar ta dawo kunnen Ilham bata yi fushi ba." abin ma dariya ya riqa bata wai mutane suna jin haushinta ta cika son mijinta. To amma abin ba haka yake ba, Ma'aruf ya zame mata tamkar rumfa a rayuwarta, shi ne yake lulli6eta ta ji bata da sauran wata damuwa. A dalilin samun Ma'aruf ne da tayi a duniya ta ji cewar 'yanchi ya zo mata kamar kowacce mace. Kafin xuwansu Ma'aruf ita baiwa ce, shi ne wanda ya fara 'yanta ta daga cikin qangin bauta, damuwa da takaici. Shi ne wanda ya fara share mata hawayen da ya dade yana sartu a kumatun ta tun shekara da shekaru....tun tana qarama. Ta yaya kuwa zata 6oye jin dadin da Ma'aruf ya zo mata dashi cikin rayuwarta? Me yasa mutane zasu ga laifinta? . Farin cikin Ma'aruf bai wuce yaga matarsa tana cikin farin ciki ba." da zarar ta shiga damuwa kowa sai ya sani. Don kuwa Ma'aruf ya gama annashuwa daga lkcn. . . . . Lp=18%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 18 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak Madugun taska . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Farin cikin Ma'aruf bai wuce yaga matarsa Ilham cikin farin ciki ba." da zarar ta shiga damuwa kowa sai ya sani, don kuwai Ma'aruf ya gama annashuwa daga lkcn . A safiyar wata laraba, wata hudu da yin aurensu, Ma'aruf ya shirya zai tafi wajen aiki da safe, Ilham ta dauko farantai da kofuna da suka sha shayi zata wanke su, sai tsautsayi ya ratsa kofi daya ya su6uce mata, ya fada akan qafarta ya fashe ya yanketa a babban dan yatsan qafarta. . Ilham ta riqe qafar ta runtse ido, Ma'aruf ya xubar da takardun dake a hannunsa ya rugo ya kamata, ya taimaketa ya zaunar da ita a jikin bango. Inda gilashin ya yanketa ba wani rauni bane mai girma, amma da yake ana zafi jini ya dan xuba sosai a qasa. . Ma'aruf ya rude yana yi mata sannu. Jikinsa ba inda ba ya tsima. Tunda suke tare bai ta6a ganin Ilham ta ji rauni ba a Tarihin soyayyarsu sai a wannan karon. Ya shigo daki ya dauki bandeji, Ilham tana zaune tana kallo, tana cije baki don zafi. . Sannu Ilham, ki yi haquri .... Sannu Ilham." . Ya nannade mata dan yatsan yana bata haquri kamar qaramar yarinya. Yana nan tare da ita yana rarrashinta ne Manajan sa ya kira shi a waya. Taro zasu yi akan matsalar rashin wuta da mutane suke ta qorafi a garin, shi ake ta jira tuni kowa ya zo." duk ma'aikatan dake ofishin su sun hallara, an gayyaci masu gari da 'yan kasuwa da qungiyoyin matasa, wadanda suka kawo kuka a ofishin wutar lantarki. Manajan ya ce da Ma'aruf a waya. . "kai fa muke jira tun daxu Ma'aruf. Zaman me kake yi yi a gida tun daxu har ynx baka zo ba?" . Ma'aruf ya ce da shi murya na rawa. . "ba lfy manaja. Matata ce ta ji ciwo ynxn nan, bana jin zan iya xuwa wajen aiki yau, a gafarceni:" . Manajan ya ce....' . "Tana wane asibitin ne?" . Ma'aruf ya ce da shi. . "Ynxn dai muna gida tukunna' ina nan tare da ita." . Manajan ya kashe wayar ya dubi mutanen da suka halarci taron a can ofishin sa ya ce da su." . "jama'a da sauran ma'aikatan mu ina so a yi mana afuwa zamu daga wannan taron da zamu yi sai xuwa gobe ' sbd matar muqaddashina tana can bata da lfy, ynx nima zan je in ga ko a wane hali take ciki, don a yadda naji muryarsa da muka yi waya ynx lallai abin ba qarami ba ne' yana buqatar a tallafa masa." . Sauran mutane suka nuna damuwarsu, suka yi addu'ar Allah Ya bata lfy. Manajan ya tashi ne sai kowa ya ce zai bi shi su je a jajantawa mal. Ma'aruf, tunda dai ana tare, kuma da ace lfy da ynx haka yana nan tare da su a ofishin . Tawagar masu xuwa duba wacce bata da lfy suka dungumo ayari kusan mutum talatin. Duk mahalarta taron, da sauran ma'aikatan dake a ofishin su ba wanda aka bari a baya, tunda ance matarsa tana cikin wani hali da ba a sani ba." . Da xuwansu gidan, manaja ya shiga kai tsaye tunda larura ce, sauran mutanen suka tsaya a waje. Da ya shiga gidan ne ya samu Ma'aruf a zaune a falo tare da matarsa Ilham sun kallo fuskarsu cike da annashuwa ya dauki qafarta ya dora a jikinsa, don ji sauqin zogin raunin da ta ji. . Manaja ya yi masu sallama ya tsaya daga bakin qofar falon, Ma'aruf ya yi saurin amsawa, ya dauke qafar Ilham ya ajiye ta akan kujerar ya tarbi manajansa, wanda ya yi tsaye yana kallon abin mamakin da ya zo ya tarar. Ya yi zaton zai zo ya ga Ilham a kwance bata ko iya motsawa don a yadda Ma'aruf yake magana a waya, muryarsa cike da damuwa. Wani in ya ji sai ya rantse mutuwa aka yi masa. . Ilham ta yiwa manaja sannu da xuwa ya amsa. . "ya jikin naki?" . Ta ce . "da sauqi na gode." . Manaja ya girgiza kai cikin mamakin abin da yake damun wadann ma'aurata. Suka fita waje shi da Ma'aruf, suka tsaya a cikin falon, Ma'aruf ya bashi hannu suka gaisa. Manaja ya tambayeshi . "ka ce matarka bata da lfy, amma naga gata nan a zaune tana kallo' har ta warke ne?" . Ma'aruf ya ce da manajansa. . "gilashi ne ya yanketa a qafa, na tausaya mata don ba ka ga yadda jini ya riqa xuba a qafarta ba." na tausaya mata matuqa, ina so ne ta huta anjima mu je asibiti a duba qafar a gani." . Manaja ya kalli Ma'aruf sosai, ya tabbatar abin da yake fada masa har cikin xuciyarsa. Sbd takaici bai ce dashi komai ba, bai ce da shi yazo da tawagar mutane suna waje ba sun zo dubiyar matarsa. Ya sa kai ya juya ya fita ya bar gidan, ya ba mutanen da yazo dasu haquri, tare da sauran abokan aikinsu, ya ce ba kowa a gidan, Ma'aruf ya fita kaita asibiti idan an samu lkc zai je ya dubata. Ya janye mutanen suka koma da sauri don kada wani ya san gskyr abin da ya faru su ji kunya. . Sai da manaja ya koma gida ne ya fara bambami yana fadawa matarsa abin da ya faru. . "in banda shashanci don kawai matarsa ta yanke da gilashi zai qi xuwa aiki, a yatsanta fa ta ji raunin, ko qaramin yaro awannan ciwon ba zai hana shi yin komai ba, amma shi ga mai mata ya sa ta a gaba sun zauna a falo yana jinyar qafarta. Kai wannan sakarci na Ma'aruf Allah Ya raba mu dashi. " . Matar manaja ta yi dariya sosa, ta ce da mijinta. . "kada ka ga laifinsa don ya nuna mata irin wannan soyayyar. A irin son da Ilham take yi masa ko rabi bai nuna mata ba, ka bari wata rana tazo gidan nan idan kana ka ji da kunnenka, da wahala ta yi minti goma bata kira mijinta ta ji halin da yake ciki ba, koda a gida ta baro shi kuwa. Haka suke shi da ita, itama haka muke yi mata wannan tsiyar." . Manaja ya girgiza kai cikin mamaki' tun sanda Ma'aruf ya fara aiki tare da su, bai ta6a sanin wannan sirrin ba sai a ranar da wannan al'amarin ya faru. Tunanin da manaja ya fara yi a xuciyar shi shi ne....! . Ya wadann ma'auratan zasu kasance idan mutuwa ta dauke daya ta bar dayansu? Babu shakka faruwar hakan zai zama babban abin tausayin da ba a saba gani ba." . . . *** . . Zo mu zauna' zo mu sa6a, kamar yadda masu iya magana suke cewa.kamar a mafarki duk da gagarumar soyayyar dake tsakaninsu sai da wata shu'umar bazawara ta so ta shiga tsakaninsu. Hakan ya faru ne bayan kusan kimanin shekara daya da yin aurensu, a lkcn Ilham tana da cikin 'yarsu Khairat, wanda ya kai wata shida. Haka kawai wata bazawara ta qwallafa ranta akan Ma'aruf, daga kawai suna sayen naman kaji a wajenta, a can inda take kai talla a wajen aikinsu. . Ta riqa kiran Ma'aruf a waya babu dare babu rana, tun Ilham bata sani ba har ta san abin da yake faruwa. Ma'aruf bai san Ilham tana da zazzafan kishinsa ba sai a ranar da bazawarar ta turo masa da wani saqo ta wayarsa. Tana fada masa cewar kada ya ji komai zata iya zama da matarsa lfy, kuma ba sai ya yi mata wasu kaya ba, kome Allah Ya hore masa ya kawo a daura aurensu, ita shi kawai take so ba kudinsa take so ba." . Ilham bata san lkcn da ta daga wayar mijin nata Ma'aruf ta makata da qasa ba ta tarwatse bayan ta gama karanta saqon, ta fara yi masa kuka wiwi tana cewa ya kasheta ta huta. . "Ba sai ka yi wahalar tsayawa jiran baqin ciki ya kashe maka ni ba, ka sa hannunka ka sa hannunka kaqareni in yi sauri in mutu tunda haka kake so. Duk alqawarin da ka yi mini a baya cewar zaka riqe ni amana ashe yaudarata ka ke yi Ma'aruf? . . . Lp=19%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%% Page 19 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun Taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . "ba sai ka yi wahalar tsayawa baqin ciki ya kashe maka ni ba' ka sa hannunka ka maqareni in yi sauri in mutu tunda haka kake so. Duk alqawarin da ka yi min a baya cewar zaka riqeni amana ashe yaudarata ka ke yi Ma'aruf? Duk murnar da nake yi a dalilin samunka da nayi ashe akwai ranar da zata zo ka gujeni ka koma wajen wata 'yar iska a can waje?" . Ilham ta rude... Ta riqa 6urari tana fadawa Ma'aruf duk irin kalmomin da suka zo bakinta. Ya yi iya qoqarin sa ya bata haquri amma ta qi fahimtar sa...ta qi yin shiru. Tana kuka tana fada masa magana . Ta fara hada kayanta a cikin akwati ta ce zata bar masa gidan sa, zata koma Katsina ya auri wacce yake so tunda ita ya gaji da ita. Ma'aruf ya yi wa Aliya matar manajansa waya, dama ita ce babbar qawar Ilham, ya fada mata abin da yake faruwa ya ce ta zo ta ba Ilham haquri ta ce zata tafi Katsina, daga kawai sun dan samu sa6ani. . Kafin Ilham ta gama shiri ne Aliya ta zo gidan ta sameta a falo tana kuka. Ma'aruf ya fita waje ya basu wuri. Bai san yadda aka yi ba har ya yi kuskuren baiwa wannan bazawara dama tana kiransa a waya, tana turo masa da saqo ba, gashi tazo suna zaune lfy ta girgiza masu aurensu na soyayya. Ma'aruf ya yi alqawarin ba zai sake yadda koda wasa ya saba da wata mace ba a waje, an yi na farko an yi na qarshe. . Da Ilham ta ga Aliya ta shigo gidan nasu ne, ta share hawayenta ta daina kukan' suka zauna a falo suka fara magana ta fahimta. Ilham ta ce da qawarta. . "ki bani shawara Aliya, ni kawai ina ganin rabuwa zan yi da Ma'aruf, ba zan iya jure abin da yake shirin yi mani ba." gara in bashi dama ya auri wacce yake so idan bani a gidan." . Aliya ta ce da ita . "shawara daya kawai yafi dacewa in baki Ilham." . "ina saurarenki Aliya, me ya kamata in yi?" . Aliya ta yi ajiyar xuciya ta ce da ita. . "ki yi sauri yau din nan ki je asibitin mahaukata a duba maki lafiyarki." . Abin ya basu dariya su duka biyun. Suka yi dariya. Ilham ta kaiwa Aliya duka a baya. Ta riqe hannunta. . Tun daga nan rigimar ta zo qarshe. Ilham ta dawo cikin hankalinta. Ta haqura ta yafewa Ma'aruf' don kuwa abin da Aliya ta fada mata gsky ne....! In ba hauka ba ta yaya zata yi tunanin rabuwa da Ma'aruf mijinta? Har ynx Ma'aruf yana nan da matsayinsa na jarumi a gare ta, wanda yake yaqi da matsalolin rayuwarta, wanda yake kafa harsashin gina duk wani abu da zai kawo mata ci gaba a rayuwarta. . Suka dawo suka shirya, suka ba juna haquri . Kowa ya ce shi yake da laifi. . "baki yi laifi ba Ilham kome ya faru ni na jawo." . Ilham ta ce ba haka bane. . "ni ce ban fahimceka ba Ma'aruf, ka yi haquri da maganganun da na fada maka, na yi kuskure ka gafarceni." . A tarihin zaman aurensu wannan shi ne sa6anin da suka ta6a samu sau daya kawai. Tun daga ranar da abin ya faru Ma'aruf ya fahimci a yadda suka ba juna amanar rayuwarsu shi da Ilham, ba zata iya jurewa ya karkata koda kashi daya a cikin kashi dari na soyayyar da yake yi mata ba xuwa ga wata macen, kamar yadda shima ba zai iya jurewa ba idan ta ce zata tafi ta barshi. . Da cikin Ilham ya isa haihuwa ne ta haifi 'yarsu ta farko Khairat. A daidai lkcn ne lkcn ne kuma suka tashi daga gidan da suke zaune wanda dama ba nasu ba ne, suka koma gidan da Ma'aruf ya gina. Ba a kammala gyare-gyaren ba a cikin gidan, haka nan suka koma sbd qosawar da Ma'aruf ya yi su shiga nasu gidan . Sa'ar da Khairat ta kai wata biyar ne da haihuwa aka yiwa Ma'aruf canjin wajen aiki, aka mayar dashi Katsina. Ma'aruf bai so wannan canjin da aka yi masa ba." . Ya saba da mutanen da yakee zaune tare da su a Malumfashi, ga sabon gidan sa da ya gina, inda suke zaune. A ranar da yazo da takardar gida ya nunawa matarsa Ilham, sai ta fara murna, domin kuwa ta san lkcn da zasu koma Katsina ne ya zo." Ma'aruf ya juyo ya kalleta tana dariya, ya ce da ita. . "dama kin daina wannan murnar, ba zamu tashi daga nan garin ba, na gwammace in riqa xuwa ina dawowa a qarshen kowanne mako." . Ilham ta tsaya da murnar da take yim ta hade fuskarta ta matso wajen Ma'aruf, don ta ji dalilin sa na qin amincewa su tashi su koma Katsina tunda an mayar dashi can da aiki. Wannan ne lkc na farko da damuwa ta fara kawo ziyara a zzamantakewar auren su." . Lkc ya riqa xuwa yana wucewa da gudu, wasa-wasa har suka yi shekara biyu...shekara uku. Bayan Ilham ta yaye Khairat ta samu wani cikin ta haifi Aiman dansu na biyu...shekara idan Ma'aruf ya koma Katsina 'ya'yanta sune abokan zamanta. Khairat tana da saurin girma da kuma wayo, da ta shiga cikin shekararta ta uku ne aka sa ta a makaranta. Ba nisa daga makarantarsu xuwa gida, tun Ilham tana kaita har Khairat ta fara xuwa ita kadai. Idan an taso daga makaranta ta dawo gida, sai Ilham ta zaunar da ita ta koya mata karatun addini. . Ma'aruf yana son 'ya'yanshi, idan ya dawo gida duk inda ya sa qafa a cikin garin Khairat tana nan biye dashi, wani lkcn ya kan dauki Aiman duk da qanqantarsa ya kai su shagon daukar hoto shi da Khairat a yi masu hotuna. Wani lkcn tare da shi ake yi msu. . A shekara daya kawai Ma'aruf ya cika falonsu da dakin Ilham da hotunan 'ya'yansa, wani lkcn ma sai an cire masa wasu hotunan a jikin bango ake sake kafe wasu sababbi. Idan daya daga cikin 'ya'yansu bashi da lfy, Ilham bata so tana fada masa. Sbd ko a ina yake idan ta fada masa zai yi sauri ya dawo gida a rude. Ma'aruf baya sake samun ssukuni sai yaga sun samu sauqi sun fara walwala. . Aiman ya ta6a yin zazza6i lkcn da ya kai wata biyar, Ma'aruf ya dawo a qarshen sati ya ga yadda aim ya rame. A ranar ko abinci bai iya ci ba, ya zauna ya yi tagumi ya dauko magungunan da Ilham ta zo dasu daga asibitin da ta kaishi, ya bude su ya riqa ba Aiman a baki yana rarrashinsa, don kada ya yi kuka. . Da dare ya yi sun kwanta su duka akan faffadar gadonsu. Da misalin qarfe biyu na dare da Ilham ta farka ta ga mijinta a zaune yana kallon dansa Aiman ya kasa yin barci ta ce da shi. . "kai dai ka cika son 'ya'ya. Don Allah ka yi haquri hakan ka kwanta ka yi barci." . Kafin Ilham ta gama abinci da rana, musamman idan a ranakun qarshen sati ne Ma'aruf wuni yake yi a gida suna wasa shi da 'yarsa wacce itama ba ta gajiya da guje-guje, in har abokin wasanta ya dawo gida. Akwai wani qaramin daki da babu komai a ciki sai kayan wasannin da yake sayo masu' Khairat ta kan debo su tazo dasu falo, idan sun karye Ma'aruf ya kan zauna da kanshi ta gyara mata. . Aiman zama kawai ya iya yi' sai dai a bashi qaramar mota mai danjoji, ya yi ta qoquwa da ita. Idan ya fara kuka sai Ilham ta shigo falon inda Ma'aruf yake tare da Khairat tana hawa bayansa shi kuma yana hanata suna kokuwa...suna dariya . Ilham ta kan dauki Aiman ta tafi dashi dakinta. . "Allah Sarki Bawan Allah, kana ta kuka ba ta kai suke yi ba." . Idan sallah ta zo Ma'aruf ya kan bata isassun kudin da zata sayi kayanta da kuma na 'ya'yansu. Ana dawowa daga masallacin Idi, baya tsayawa ko'ina zai zaqulo motarsa ya dawo wajen iyalinsa. . Kowa zai ci kwalliya da sababbin kayansa....abokansa suna kawo masa ziyara suna yiwa 'ya'yansa wasa. Ana yiwa juna barka da sallah! Bayan an gama gaisawa da abokan arziqi sai su shirya ya daukesu a mota su tafi Katsina da MAtazu su gaishe da iyaye da 'yan uwa. Komai dare basu kwana a can Malumfashi suke dawowa su kwana a gida, su zauna a cikin far ciki. Tun suna su biyu, gashi yau wani zamani yazo sun zama su hudu. Idan suna zaune a falo tare da 'ya'yansu hayaniya takan cika gidan. Aiman yana kuka ana bashi haquri. Khairat tana ta faman surutu, Ma'aruf yana bata amsar duk tsokanar da ta yi. Ilham ta kan yi dariya, idan ta tuno maganar da Ma'aruf yake fada mata a lkcn tana amarya, idan zai tafi wajen aiki. Zai barta a gida ita kadai. . "idan kika yi haquri Ilham, watarana zaki wayi gari ki ga xuri'armu cike fal a gida nan sun kewayeki." . Har Ilham ta kai shekaru hudu da yin aure sau biyu kawai mahaifiyar Ilham tazo gidan. . . . Lp=20 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels