*FARASHIN IZZAH*💅🏽💆🏻‍♀️💍💔 Daga marubuciyar BEYOND THE VEIL(LABULEN SIRRI) a baya ina amfani da jiddatulkhayr writes amma yanzu na dawo Hauwajay writes Hauwa Jibrin Sulaiman (Hauwajay writes) Young talented writers association (YOTA) *Bismillahir Rahmanir Rahim 🤍* Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki, Wanda Ya sake bani ikon dawowa da wani sabon labari. Bayan irin ƙauna da goyon bayan da kuka nuna min a *Beyond The Veil*, kalmomi ba zasu isa su bayyana farin cikina ba. Na ji ku, na karɓi ƙaunarku, kuma hakan ne ya ƙarfafa ni na sake ɗaukar alƙalami domin kawo muku wani sabon tafiya. Ina fatan wannan sabon labarin zai samu karɓuwa a zuciyoyinku kamar yadda na baya ya samu ko ma fiye da haka. Domin na rubuta shi ne da zuciya, da ji, da kuma fata cewa zai taɓa wani ɓangare na rayuwarku. Ku kasance tare da ni a wannan tafiya… Domin wannan ba kawai labari bane rayuwa ce, darasi ne, da kuma wani ɓoyayyen sirri da zai bayyana a hankali. Nagode sosai da kasancewarku tare da ni. 🤍 Jiddatulkhayr writes taku ce✍🏼 _Book 1_ Prologue Da gudu motar ta ƙusa kai dab da gate ɗin makarantar. Da sauri mai gadin ya miƙe daga zaunan da yake ya buɗe gate ɗin sanin motar, ya ɗaga hannu yana gaishe da wanda ke cikin motar, amma motar ba ta saurare shi ba. Wani irin 'brake' motar ta yi bayan ta isa dab da babban hall ɗin da ɗalibai suka taru don rubuta jarabawar WAEC. Buɗe ƙofar baya aka yi. Sai bayan sakanni kafin ta zuro ƙafarta ɗaya daga cikin motar. Duk hankalin ɗalibai ya koma kanta,  duk da cewa idan da sabo sun riga sun saba da hakan Sake sauko da ɗayan ƙafarta ta yi waje, wacce ke sanye da white socks da black expensive Toms shoes. Sannan a hankali ta fito daga motar. Sanye take da white mini hijab, white riga, da black trouser, uniform ɗin ya yi mata bala'in kyau wanda ya sake fitar da anihin kyanta, Zahra kenan 'yar shekaru 18 Fuskarta na sanye da black sunglasses. Ta ɗan zaro glass ɗin daga idonta zuwa kan hancinta, tana bin wajen da kallo. Ta tashi daga jikin motar ta rufe, kamar wacce ba ta son taka ƙasa haka ta ɗan taka zuwa wajen driver. Kamar wacce aka sa dole ta yi magana, ta buɗe baki ta ce ''Zaka iya jira na, dan yau ba daɗewa za mu yi ba'' ''Shikenan, Hajiya'' ya amsa cikin girmamawa ''Hey Fatima!'' Muryar ta katse nutsuwarta. A hankali ta juya, tana kallonsu har suka ƙaraso Murmushi ta yi mai ɗauke da confidence "Point of correction… Asiya" ta ce cikin sanyi "Sunana Zahra, not Fatima" Asiya da Saudat suka kalli juna suka fashe da dariya. "Hey Pretty!" Saudat ta ƙara Zahra ta ɗan karkatar da kai tana murmushi ta ce "Na'am… ai a rubuce yake a fuska ta" Sai fuskar ta ɗan canza, ta koma serious ta ce "Asiya… exams card ɗina da biro?" "Yana cikin jakkata" Asiya ta amsa Ta gyada kai Wayarta ta fara ringing. Ta ciro ta daga aljihun wandonta ta ɗaga kiran. Kawayenta suka kalli juna cikin alamun tambayar yaushe kuma? Amma babu wanda ya san amsar Saida ta gama wayan, ta sauke daga kunnen nata "Zahra, kin canza waya ne?" Saudat ta tambaya Wani murmushi mai ɗauke da izza ya bayyana a fuskar ta "Yaushe ake yayin iPhone 16 Pro… alhali har 17 ya fito?" Ta ɗan ɗaga gira "Jiya Abba ya canza min" Kawayenta suka taya ta murna. An fara kira a shiga hall. Dalibai suka fara tururuwa zuwa tantancewa don kafin shiga Hall ɗin Amma Zahra… ta kama hanyar wani office dake wani ɓangaren "Ke! Baki ganin sauran ɗalibai suna shiga hall ne?" wani sabon malami ya tsawata mata Cak ta tsaya, ta juya,ta naɗe hannunta, ta gyara tsayuwarta Ta kallesa kai tsaye cikin idanu cike da kwarin gwiwa. "Ba zaki bi hanyar hall ɗin bane?" ya sake tambayarta A hankali ta buɗe baki, kamar waccan ake wa dole ta ce "Excuse me… kaga nayi kama da wacce zata yi exam a cikin wancan hall ɗin? With thousands of people? Babu iska… babu fanka?" Malamin ya kasa amsawa sabar shock daya shiga Ta juya, ta fara tafiya cikin izzah kamar ba Malami bane ya tsayar da ita ba Wani malami daga baya ya ce, ''Kyale ta… a office take nata exams, special student ce" Bayan awa biyu… ɗalibai suka fara fitowa daga hall ɗin jarabawar, harda kawayenta a cikin wanda suka fito Ita kuma… ta fito daga office ɗin cikin nutsuwa Ta ci karo da wani malami da tun farko taji bata kaunarsa sbd yadda yake kallonta "Ahh… Pretty girl ce" ya faɗa yana murmushi "Har kin gama?" Ta kallesa sau ɗaya sannan ta ɗauke kai ta ce "Eh" daga haka ta wuce abinta.. "Mu tafi" ta faɗa wa kawayenta bayan ta isa inda suke kiranta "Ina da modelling anjima. Ina son na je gida na huta… it's been a while da nayi posting a Instagram" Suka shiga mota, ta zauna a gaba "Ka ja motar da gudu… bana son slow motion" ta umarci driver Motar ta fice da gudu kamar yadda ta bada umurni Suna cikin tafiya bayan sun shigo wani unguwa wanda kallo ɗaya zaka masa ka fahimci tabbas wannan suna fama da rayuwa, dai dai wani layi ta ce "Tsaya", drivern yayi parking. Ta sauka ta zaga ta buɗe boot. Ta ɗauko wani babban leda. Ta shiga wani lungu, ƙaramin gida mai nuna ana wahalar rayuwa a cikinta nan ta shiga Ta yi sallama, ƙaramin yaro ya fito da gudu yana ganinta ya fara tsalle da dariya yana "Anty!" "Shhh…" ta ce tana murmushi Ta ajiye ledar hannunta, ta ce "Je ka kira mamanka, ka nuna mata laidar idan ta fito" Ba tare da jiran godiya ba… ta juya ta koma mota. Suka ci gaba da tafiya har suka sauke kawayenta kowacce a gidansu Da suka isa gida, ta sauka. Wani mutum mai kimanin shekara 65 ne tsaye a compound yana shirin shiga mota, ga waya kuma ƙare a kunnen sa. Da gudu ta je ta rungume shi. Ya sauke wayarsa ya sumbaci goshinta ya ce ''Baby, ya exams ɗin?'' Ta ce ''Alhamdulillah, Abbah na'' Ya ce "Allah ya ba da sa'a. Bari zan fita, idan na dawo sai mu yi magana" Ta gyaɗa kai tana murmushi haɗi da masa bye bye Ta shiga cikin compound. Wata mata mai kimanin Mid 50s ce tsaye cikin tsadadden kaya, wani saurayi wanda zai kai 30yrs ne tsaye gefenta, da budurwa mai 22yrs wanda take tunkarar su Ta kalli saurayin da gudu taje ta rungume shi. Ya ɗaga ta sama yana dariya "Wai yaushe Zahra zaki yi kiba ne? Ji fa ko nauyi baki da shi!" Ta ce "Toh wa ya ce maka ina son kiba?" Ta kalli matar da fuska a haɗe, "Mummy, ina wuni." Ta amsa a takaice, "Lafiya" Ta kalli budurwar, "Anty Batoul" amma ko alamar ta kalleta bata yi ba sai ma gaba data wuce abinta Ta kalli Yaya Umar ta ce, "Yaya, bari na shiga ciki" Yana murmushi ya ce ''Ki je ki huta" Mummy ta harba mata kallo mai nauyi yayin da ta wuce Ta ce "Dan ubanka idan baka daina taɓa yarinyar nan ba sai na saɓa maka, wawa kawai" Ya ce "Mummy me aibun hakan?" Ta bar shi tsaye ta wuce gaba abinta kamar zata wajen mota Sai kuma ta juya tabi bayan Zahra zuwa babban parlorn nasu Zahra kamar yadda ta saba tafiya haka take yi kamar ba zata yi ba Mummy ta tsaya a wurin, idanunta na bin hanyar da Zahra ta bi har ta ɓace mata Fuskarta a ɗaure, amma ba irin na fushi kaɗai ba ne A hankali ta ja numfashi Sannan ta juya, ta nufi kujerar da take zaune a baya, ta zauna a hankali kamar wacce wani abu ya ɗauke mata ƙarfi Ya Umar daya biyo ta a baya ya kalleta da mamaki ''Mummy… lafiya?'' Ba ta amsa masa ba Sai ta ɗaga hannu a hankali, tana masa alamar ya yi shiru Wani irin shiru ne ya sake mamaye falon Mummy ta kai hannu cikin designer bag ɗinta, ta ciro wayarta Na ɗan lokaci… ta tsaya tana kallon screen ɗin kawai Kamar wacce ke yanke shawara mai nauyi ko kokonton abin da zata yi Sannan ta danna wani number. Wayar ta ɗauki lokaci tana ringing A ƙarshe aka ɗaga. Ba gaisuwa Sai Mummy ta ce cikin murya mai sanyi da ba a taɓa jin irinta a bakinta ba "Ta dawo" Shiru daga ɗayan ɓangaren. Sai muryar da ta fito mai nauyi "Kin tabbata?" Mummy ta rufe idonta na sakanni "Bangane ba, abin da idanu na suke faɗa min ai ba karya bane" Yaya Umar ya ɗan matsa kusa da ita, yana kallonta cikin ruɗani "Mummy… wa kike magana da shi?" Ta ɗaga masa hannu da sauri ba tare da ta kalle shi ba "Ka fita" Ya tsaya cak, ya ce "Mummy......" "Na ce ka fita!" Muryarta ta ɗan daki ɗakin, amma ba kamar fushin yau da kullum ba Wani irin tsoro ne ke ɓoye a cikinta Yaya Umar ya kalleta na wasu sakanni, sannan ya juya ya fita a hankali. Tana ganin ya fita Mummy ta sauke wayar daga kunnenta a hankali. Amma ba ta kashe call ɗin ba. Muryar daga ɗayan ɓangaren ta sake fitowa "An riga an faɗa miki cewa wannan rana za ta zo" Numfashinta ya ɗan rikice. Ta ce a hankali, ''Na yi tunanin… mun gama da wannan'' Ƙaramin dariya mai sanyi ta fito daga wayar ''kina wasa sosai, amma komai yana dab da lalacewa'' Hannun Mummy ya fara rawa kaɗan Ta riƙe gefen kujera da ƙarfi. ''Me kuke so wannan karon?'' Shiru na ɗan lokaci. Sai amsar ta zo a hankali… amma da nauyi "Ba abin da muke so ba... abin da ita ta tuna" Kalmar ta tsaya mata a rai. "Ita ta tuna?" Muryar ta ce "Kuma idan ta tuna... Mun san abin da zai biyo baya" Call ɗin ya katse. Falon ya sake yin shiru. Amma wannan karon… shiru mai nauyi ne, harta zuciyarta yayi mata nawi. Mummy ta zauna ba motsi. Idonta ya tsaya wuri guda. A hankali ta furta ''Ya Allah…'' Sai ta ɗaga kai tana kallon hanyar ɗakin Zahra dake upstairs Idonta cike da wani abu ba ƙiyayya ba, ba soyayya ba… Sai dai tsoro. Tsoron da ta daɗe tana ɓoyewa. Ta ce ƙasa-ƙasa "Da gaske… kin manta komai ne… ko kina wasa ne da mu?" A Bangaren Zahra kuwa, tana hawa sama ta nufi wani ɗaki Zahra na shiga ɗaki ta faɗa kan tsadadden gadonta, ta lumshe idanu. Aka buɗe ƙofar toilet, Mami ta fito tana murmushi, ''Yau kuma a gajiye kika shigo kenan?'' Ta ce, ''Yes Mami… kuma masu aikin nan ba su gama abinci ba, yunwa nake ji wallahi'' Mami ta ce, ''Alright, bari na hado miki oat ki sha kafin a gama'' FARASHIN IZZAH… Ku biyo mu don jin cigaban labarin Fatima Zahra, wacece ita? Wake shigowa rayuwarta... #Jiddatulkhayr writes #08110615256 https://whatsapp.com/channel/0029Vaq17Di3WHTWv5ju0w3Z *FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes Book 1 Chapter 1 Tik... tik... tik... Ƙarar agogon ɗakin ce kaɗai ke ratsa shirun gidan, tana sanar da cikar ƙarfe 12:00 na dare A daidai wannan lokacin ne ta firgita daga zurfin tunanin da ta nutse a ciki, kamar wacce aka taso daga wani mafarki mai nauyi. A hankali ta ɗago kai, idanunta suka sauka kan agogon dake jikin bango. Ganin lokacin ya sanya zuciyarta yin wani irin nauyi, kafin ma ta ankara, hawayen da suka cika idanunta suka gangaro a hankali, suna bin kumatunta kamar an kunna pampo Ta miƙe a nutse, ta nufi window ɗin parlom. Hannunta ta kai ga curtain ɗin, ta ja shi gefe kaɗan. Duk da duhun dare, hasken fitilun compound ɗin ya watsa wani irin haske mai ɗaukar ido, har zaka yi zaton ba dare ba ne. Gidan ya cika da tsari da kyau, amma zuciyarta kuwa cike take da wani irin duhu. Ta janye kanta daga window ɗin, ta juya zuwa stairs. A hankali take taka su kamar mai tsoron kada kowanne motsi ya fallasa wani sirri da take ɓoyewa a ranta. Da ta iso ƙofar ɗakinta, ta kama handle ɗin a hankali, ta murɗa. Kafin ta shiga, ta tsaya cak ta juya zuwa babban ɗakin da ke opposite nata... ta tsaya na ɗan lokaci, kamar mai son tuna wani abu amma sai ta girgiza kai ta shige nata ɗakin. Ta cire kayan jikinta, ta daura towel, ta wuce toilet. Ba ta jima ba ta fito amma ko mai ba ta iya shafawa ba. Idan ka kalleta, zaka fahimci cewa jikinta yana nan tare da ita, amma zuciyarta tana can nesa, a wani duniyar da ba kowa zai iya kaiwa ba. Turare kawai ta fesa, sannan ta saka kayan barcinta. Ta nufi gado, duk da cewa an gyara shi tsaf, sai da ta sake karkade shi kafin ta kwanta kamar mai neman nutsuwa da ba ta samu ba. Addu'ar bacci ta yi, ta shafe jikinta, sannan ta ɗan ɗaga kai ta kalli agogo. 12:55am. Ta lumshe idonta, ta daura hannunta a kirji, cikin murya mai rauni ta furta "Ya Allah… ka sauƙaƙa min wannan halin da nake ciki..." Hawaye suka sake zubo mata. Ta share su da sauri, sannan ta juya ta kwanta, ta rufe idonta. Sai dai… baccin bai zo mata ba. Kamar a mafarki, ta ji karar buɗe gate. Da sauri ta miƙe, ta nufi window ɗin ɗakin, ta ɗan yaye curtain. Motarsa ce. Wani murmushi ya kuɓuce mata, irin murmushin da ba shi da sauƙin fassara. Ba lallai ka fahimci me fuskanta take nufi ba Ta sake rufe curtain ɗin, ta koma ta kwanta kamar ba komai. A waje kuwa, ya fito daga motar tasa da nutsuwa irin ta masu iko. Tafiyarsa cike da kwarjini, yana nufar cikin gidan kamar wanda baya son taka kasa Kai tsaye kitchen ya wuce. Ya ɗauki bottle na ruwa, ya buɗe, ya ɗora a bakinsa ya fara sha. Kittt… Ƙarar buɗe ƙofar bedroom ɗin ta ratsa kunnen ta. Nan da nan ta rufe idonta, ta mayar da kanta pillow kamar mai barci da gaske. Ya ajiye wayarsa a gefe, ya fara cire kayan jikinsa, sannan ya wuce toilet. Yana shiga toilet, ta buɗe idonta a hankali. Ta tashi zaune, idanunta suka sauka kan wayarsa. Ta zuba mata ido kamar wacce take son ganin amsar wata tambaya da ke damunta. Ba ta san tsawon lokacin da ta ɗauka a haka ba… sai jin motsinsa yana fitowa. Da sauri ta koma ta kwanta, ta rufe idonta. Ya tsaya gaban mirror, ya goge ruwan kansa. Daga nan ya wuce wardrobe, ya ɗauki pajamas, ya saka. Sai ya nufi gadon. Ya tsaya kallonta na ɗan lokaci… idanunsa suna nazari kamar yana neman fahimtar wani abu da bai bayyana ba. Daga bisani ya kwanta. Ba da jimawa ba, sautin numfashinsa ya canza alamar bacci ya ɗauke shi. A hankali ta buɗe idonta. Ta miƙe zaune. Idanunta suka sauka kansa… sannan ta taɓe baki A haka bacci ya kwashe ta. Washegari da asuba, karan alarm ɗinta ya tashe ta. Ta mike tana murza idanunta, sannan a hankali ta furta: Bismillahil ladhi ahyana ba'da ma amatana wa ilayka an-nushur. Bayan ta sauke kafafunta kasa, ta wuce toilet ta yi alwala. Bayan ta fito, ta shimfida sallaya sannan ta fara raka'atainin fajr. Tana zaune, ta ji motsin sa ya tashi, ya wuce toilet yana fitowa kuma ya nufi kofa. Jin an tada sallah, ta tayar da sallah. Bayan ta idar, har 6:30 tana kan sallayan tana addu'a, sannan ta mike ta wuce kitchen. Tunanin abincin da zata ɗaura ya fara zuwa mata, ta fara fere potatoes. Can ta ji an buɗe kofar kitchen, sai ta ji ya shigo. A kofar kitchen ɗin ya tsaya; ko ɗaga kai bata yi ba, balle ta gaishe shi. Shi kuma ya yi folding hannayensa yana kallon ikon Allah, kamar mai tsoron magana, ya ce: "Ba a koya miki gaisuwa ba ne a gidan naku?" Itama, kamar ba zata tanka masa ba, ta buɗe baki a hankali ta ce: ''Ai kaima kasan gidanmu akwai tarbiyya." Wani kallo ya watsa mata, yace: "Me kike nufi Zahra?" A takaice ya ce "Ka tsargu ne?" Ya juya ya bar bakin kofar, kamar wanda zai fire sama, ya wuce dakinsa. Ta gama breakfast, ta je ta jera a dining, ta wuce ɗakinta ta yi wanka ta fito. Ya yi daidai da lokacin da shima ya fito, hanyar kofar parlorn. Ta kalli dining kamar ba a taba ba, ta ce: "Haka zaka fita ba tare da kayi breakfast ba?'' Ko kallonta bai yi ba yana gyara briefcase ɗinsa Ya fita ba tare da ya kula ta ba. Zama ta yi ba tare da ta shirya ba. Ta yi tagumi tana kallon wani waje, zuciyarta cike da tunani wannan wace irin rayuwa ce ta fara? A hankali ta lumshe idanunta, tana mamaki ko dama haka ne auren yake nufi? Ta miƙe ta nufi dining. Ganin ko yunwar ma bata ji, yasa kawai ta zuba tea a cup ta fara sha. Bayan ta gama, ta ajiye cup ɗin, sannan ta koma ɗakinta. Ta fara tattare tattare, tayi shara, har da wanke toilet. Bayan ta gama, ta saka turaren wuta, nan da nan gidan ya cika da ƙamshi mai daɗi. Ta ɗauki wayarta ta zauna bakin gado, sannan ta kwanta ta kunna data. Ta shiga Instagram, sai ta ga comments da DMs sun yi yawa. Har yanzu mutane suna taya ta murnar aure. Wani ajiyar zuciya ta sauke. Followers ɗinta sun ƙaru sosai saboda trending ɗin da ta yi a wannan watan. Ta shiga kallon yadda suka kai 1 million ta sauke ajiyar zuciya. Aka yi tagging ɗinta a wani post. Ta shiga account ɗin… Sai ta ga shi ne ya yi posting video ɗinsu na after party tare da wani romantic caption. Na tsawon minti biyar tana kallon caption ɗin Amma ko like ɗin post bata yi ba… balle ta yi reply kamar yadda take yi a satin bikin. A hankali ta kashe data, ta ajiye wayar a gefe. Tunani ya sake lullube ta Shin haka ne auren yake? Ko nata ne daban? Me yasa yake nuna wa duniya kamar ita ce mace mafi sa'a… alhali…? Hawayen da bata shirya ba suka cika idanunta, suka fara zubowa a hankali. A haka bacci ya kwashe ta. Da misalin ƙarfe 11 na safe, vibration ɗin waya ya tashe ta. Ta ɗauka, Suhaima ce. Ta murja idanunta, sannan ta amsa da sallama. ''Amarya, kar dai bacci kike na tashe ki?'' Zahra ta ce, "A'a… bansan sanda baccin ya kwashe ni ba. Shi kuma ya fara fita aiki tun jiya ai" Suhaima ta ce, "Toh ki zo ki buɗe mana gate, muna ƙofar gida" "Really?" Ta ce Da sauri ta miƙe zaune, ta sauka ƙasa. Ta kusa isa gate ta haɗu da Mai gadi ya fito yana cewa zai buɗe gate ɗin ya ɗan shiga ban ɗaki be, amma ta ce "Na riga da na zo ai Baba" Da ta buɗe gate, sai ta gansu tsaye kowannensu da murmushi, ta rungume su tana cewa, "Ku shigo ciki" Kalle kallen gidan Saudat take yi ta kasan ido. Cike da fara'a Zahra ta kai su parlour Suna shiga, Asiya ta ce "Lallai na tabbatar gidan Fatima-Zahra na zo. Ke da kamshi da tsafta, ba a raba ku. Ango dai ya yi sa'a" Dariya suka yi gaba ɗaya. Amma da Saudat tana shiga parlour ɗin… sai nan da nan fuskarta ta canza. Zahra ta ce "Saudat, dama ke ce baki ga gidana ba ko? Banso bikin nan ya zo ba tare da ke ba" Saudat kawai ta ce "It's fine" Zahra ta yi shiru tana kallonta don amshinta ya bata mamaki Suhaima ta ce "Matsalata da ke kenan. Ko ɗan rikicewa ba zaki yi ba? Ko baki kalli gidan da kyau bane? Kalli fah kamar ba'a kasar nan ba fah" Ta ciro wayarta daga jaka ta ce "Na gani. Gidan ya yi kyau… saura kwanciyar hankali....." Maganar ta tsaya a zuciyar Zahra, ta dinga ksllonta da mugun mamaki Suhaima ta matsa kusa da Zahra tana shafa ta ''Zahra, kin yi kyau sosai… amma kin rame. Ko dai ciki ne?'' Nan take Saudat ta ɗago kai tana kallonta Asiya ta ce, ''Nima abin da nake tunani kenan'' Zahra ta ɓata rai ''Ni dai babu wani ciki, yaushe aka yi auren da har ciki zai shiga" sai kuma tayi saurin canza maganar ''Ina kuka bar Firdausi?'' Asiya ta ce, ''Mama ce ba lafiya, shi yasa take tare da ita. Har ma ta sayar da wayarta fah" Zahra ta ce cikin mamaki, "Kamar yaya? Har ta sayar da waya?" Suhaima ta ce "Da alama jikin ya yi tsanani ne" Zahra ta girgiza kai "Ba zata iya gaya mana mu taimaka ba? Me amfanin zaman tare dan Allah?" Suhaima ta ce, "Ai ɗawainiya…" Zahra ta katse ta "No. Babu wani yawa" Nan take ta ɗauki waya, ta yi transfer na 80k zuwa account ɗin Firdausi Ta ɗaga kai ta ce "Please, Suhaima ki biya gidansu ki gaya mata na tura mata kuɗi. Ta sayi waya ko ƙarama ce, sauran ta yi maganin Mama kafin nazo duba ta" Suhaima ta gyada kai Asiya ta ce "Allah sarki… kawa kamarki daban ce" Suhaima ta ce "Wallahix Zahra ta taɓa Saudat "Lafiya kuwa? Na ganki shiru" Ta ce "I'm fine" Zahra ta ƙyale ta Ta ce "Ku je kitchen ku yi girki mana" Suhaima ta buɗe baki "Muna baki zaki bar mu mu yi girki?" Zahra ta harare ta "ku ne baki?" Asiya ta ce "Eh mana! Ke yaka mata ki dafa mana" Zahra ta ce "Bana son jin ƙamshin abinci ne" Dariya suka yi Suhaima ta ce, "Toh ya tabbata ciki kike da shi!" Amma Zahra bata kulasu ba, ta koma ta kwanta. Suka nufi kitchen. Saudat ma ta miƙe "Ni zan tafi… ina da inda zan je" Zahra ta kasa cewa komai dan ganin yadda ta canza Da ta fita, Suhaima ta leƙo "Kin gani ko? Zaki fara yarda da abin da na faɗa miki akanta'' Zahra ta ce "Ya isa. Ku je ku yi girkin, ni zan ɗan yi bacci" Ba ta tashi ba sai bayan Azahar. Su Asiya sun gama girki, suka ci, suka haɗa smoothie ma suka sha, suka mata wanke wanke Bayan sallah ta sauko ta same su suna kallo. Suka fara shirin tafiya. A dai lokacin… aka buɗe ƙofar parlour Sai ga Ibrahim ya shigo Suhaima ta ce, ''Aaa, ashe ango ne!'' Ya zauna, suka gaisa cikin fara'a'' Zahra ta kasa ɗauke idonta akansa, yadda yake dariya yana nuna musu kulawa. Bayan sun gama gaisawa suka ce zasu tafi Ya ce, ''Da zuwana ne zaku tafi?'' Suhaima ta ce "A'a, dama mun shirya zamu tafi ne ka shigo" Ya ciro kuɗi ya miƙa musu "Ku yi TP toh" Suhaima ta karɓa musu, suka yi godiya. Zahra ta ce "Nagode. Ku gaida gida" suna murmushi suka yi sallama.. Bayan sun fita Asiya ta ce a hankali, "Har yanzu bana son Ibrahim Khalil a matsayin mijin Zahra… amma tunda aure ya shiga, babu yadda muka iya" Suhaima ta ce, "Nima haka. Amma tunda na ga yana da kuɗi… na yi mata murna. Kar alherinta ya tafi a banza, Zahra deserve everything and more" Kar a manta ayi following acc ɗina sannan ana danna star dan nasan labarin is giving or not #Jiddatulkhayr writes #08110615256 *FARASHIN IZZAH* YOTA Jiddatulkhayr writes BOOK 1 CHAPTER 2 Bayan fitarsu, zai wuce ɗakinsa, Zahra ta ce, "Ina wuni, ka dawo lafiya?" Bai kulata ba, ya ci gaba da taka stairs. Ta ɗaga kai tana kallonsa da mugun mamaki har ya gama hayewa. Miƙewa tayi ta bi bayansa. Tana isa ƙofar ɗakin, ta ga a kulle. Ta kai hannu a hankali ta buɗe ta shiga. Bin ɗakin tayi da kallo ganin ba ya ciki. Ƙofar toilet ta bi da kallo jin karar ruwa. Ta ƙarasa ciki ta zauna bakin gado tayi tagumi. She can't believe… wai yau 15 days da aurensu, amma gaba ɗaya duk wani soyayya da komai ya riga ya fara fading A haka ta dinga sake-sake har ya fito daga wanka. Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa, ya ci gaba da tafiya zuwa wajen mirror. Ta miƙe ta shiga gabansa ta ce, "Noory, wai wani laifin na maka ne? Idan har ma laifi na maka, ina soyayyar mu da har ba zaka iya yafe min ko ka faɗa min kuskure na na gyara ba?" Wuce ta yayi, ya ƙarasa dressing mirror ya fara shafe jikinsa da mai. Ja da baya tayi ta tsaya tana kallonsa. Har ya gama ya sanya wani kaya na daban. Ba ƙaramin kyau ya mata ba. Tuna yadda yake mata yasa a take mood ɗinta ya canza. Ta ga ya nufi hanyar fita, ta miƙe ta ce "Yau da ka zo da wuri ina murna… ashe fita zaka yi ka dawo yadda ka saba sai cikin dare ko?" Sauka yake akan stairs tana binsa a baya. Suna isa main parlour, ta sha gabansa. "Haba Noory, wai me yasa kake min haka ne? Where is the promise? Haka muka yi da kai?" Idonta ya cika da ƙwalla bayan ta gama maganar. Ya tako zuwa gabanta ya tallabi fuskarta da hannayensa biyu yana kallon cikin idonta dake jike da hawaye. Ya ce, "Zahra… tauraruwa na" yana maganar yana tauna cingam. Still idonsu na cikin na juna, ya ce, "Alkawarin? Faɗa min, menene bana miki a gidan nan?" Ta kwace kanta tayi baya tana masa wani mugun kallo. Ta koma ta zauna kan kujera tana jin yadda zuciyarta ke bugawa. Ya juya zai fita, ringing ɗin wayarta yasa ya dakata. Ta ɗaga kiran, ganin Ya Umar ne. A hankali ta ce, "Hello Yaya…" Yayi shiru kafin ya ce, "Zahra, menene? Ta ce, "Me ka gani Yaya?" Ya ce "Na ji muryarki wani iri ne." Ta ce "Au ai mura nake yi" Yayi shiru, sai kuma ya ce, "Alright, anjima idan baki da wani abu, ki kira Abba ki masa ya jiki, dan kwana biyu bai ji daɗi ba" Ta ce da sauri "What? Abbana ba shi da lafiya, shine ba a faɗa min ba? Noo, ba zan iya kira ba, dole zan zo gida na duba shi" Ya Umar zai yi magana, ta katse kiran. Ta miƙe tsaye, hanyar stairs zata yi.... Ibrahim dake bakin ƙofa ya ce, "Kar ki kuskura ki fita ko'ina" Ta juyo ta ce "Har kana tunanin kana da wani power ne? Kalli yadda kake magana as if kai wani ne." Wani dariya yayi ya ce, "Ni wani ne mana, Zahra. Ko kin manta ke ma saboda kuɗin kika aure ni ne?" Zahra ta sake baki tana kallonsa ta ce "Wai tunani kake yi kai wani ne a hakan? Thank God ka san waye ubana. Kafin ka aure ni, ko motar da nake hawa baka taɓa hawa irin ta ba. Don haka baka isa kayi min gorin arziki ba, dan a cikinta na taso" Ta ɗan dakata sannan ta ce, "Fita kuma, idan har ka isa ka dakile fitan nawa, nagaji… nagaji da wannan halin naka. Idan da na san haka kake, wallahi da ba zan taɓa aureka ba, ko da kuwa a mafarki ne" Daga haka ta juya zuwa sama da gudu tana hawaye. Ibrahim ya juya ya nufi ƙofa. Direct inda motarsa yake ya nufa, ya buɗe, yana shiga ya fice daga gidan. Tana shiga ɗakinta, ta zube a ƙasa tayi kukanta mai isarta. Sannan ta tashi ta wuce toilet. Wanka tayi, ba ta wani daɗe ba ta fito ta sa kaya. Ta fito ta kulle ko'ina sannan ta wuce compound. Gun motarta ta tafi, tana shiga ta kwantar da kanta a jikin steering motar ta fara rera kuka. "Wannan wani irin rayuwa ce…" Sai da ta yi mai isarta sannan ta tada motar, tayi wa mai gadi horn ya buɗe mata. Bayan ta yi tafiya sosai, sai ga shi ta isa unguwarsu. Tana horn, mai gadi ya leko, ganin itace ya buɗe gate ɗin yana mika gaisuwa. Ta amsa masa da fara'a sannan ta shiga ciki tayi parking. Kofar parlour ta buɗe da sallama a bakinta. Mummy ce kaɗai a parlour, tana shan fruits ta ɗora ƙafarta akan stool. Tayi sallama ta shiga. Mummy ta ɗaga kanta tana kallonta da murmushi a fuska ta ce "Waiiii, yau kuma Zahra ce a gidan namu?" Zahra tayi murmushi ta shiga tayi hugging ɗinta ta ce, "Mummy, ya naga ke kaɗai ce anan? Ba kowa ne a gidan?" Mummy na kallonta ta ce, "Duk ba su nan. Kin baro gida lafiya?" Zahra ta ce "Lafiya kalau" Zahra ta ce, "Mummy, ya jikin Abbana?" Mummy ta riƙe haba ta ce, "Wa ya ce miki Abbanku ba lafiya?" Ta ce, "Yaya Umar ne." Mummy tayi tsaki ta ce, "Allah, ban san yaushe Umar zai girma ba. Ace yarinya ko wata bata yi da aure ba, ya wani ce miki Abbanku ba lafiya ki zo gida" Zahra ta yi murmushi ta ce, "A'a fah Mummy, ba cewa yayi na zo ba, kawai cewa yayi na kira shi" Mummy ta kwala ma mai aiki kira, sai ga Zulai ta fito da ladabi. Ta kalli Zahra da har ta kwanta ta lumshe ido ta ce, "Kije ki kawo wa Zahra ruwa, naga kamar ta gaji." Zulai da ladabi ta amsa wa Mummy sannan ta juya ta tafi. Mummy ta jima tana kallon Zahra dake kwance, idonta a lumshe. Bata wani daɗe ba sai ga Zulai ta fito da ruwa a hannunta. Ta duƙa ta ajiye a gaban Zahra. Mummy na kallonta ta ce, "Zahra, tashi ki sha ruwa." Zahra ta buɗe ido tana kallonta, sai kuma a hankali ta miƙe ta zauna. Mummy ta ce xZahra, me ke damunki?" Zahra tayi murmushi ta ce, "Babu komai fah, Mummy." Mummy ta mata wani kallo ta ce, "Boye min damuwarki zaki yi? Gashi duk kin rame, kin yi duhu… anya lafiya kuwa?" Zahra ta ce, "Babu komai fah…" Ta ƙarasa maganar trying hard not to cry Mummy ta ce "ko baki jin daɗin gidan naki ne?" Ta girgiza kai ta ce "Kawai dai kwana biyu bana jin daɗi ne, Mummy." Daga haka ta kyale ta, amma ba wai don ta yarda cewa babu komai ɗin bane... Suna zaune, sai ga su Mami da Abbah, sai Umar dake gefensa yana masa sannu suka shigo parlour. Zahra ta miƙe tsaye ta ƙarasa wajen Abbah da gudu ta rungume shi. Mami sai kallonta take da mamaki ta ce, "Ke kuma, daga yanzu har kin fara fita?" Zahra dai tana rungume da Abbah, wanda babu wani ƙarfi tattare da shi, har ma ya kasa magana. Mami ta ce "Ki sake shi mana, baki ganin ba lafiya gare shi ba?" Ta sake shi tana murmushi mai haɗe da hawaye. Abbah ya ce "Zahra, yaushe kika zo? Ina mai gidan naki?" Zahra ta ce "Abbah, ya jikin naka? Fatan baka jin komai ko?" Ya ce "Da sauƙi" Ta kama hannunsa zata kaisa ɗakinsa, duk suka bisu a baya. Suna zagaye da shi suna ɗan hira sama-sama. Mami sai satan kallon Zahra take yi, haka ma Abbah. Umar kam ya gagara ɗauke kansa akanta.... Gyangyadi ta fara. Mummy ta ce, "Zahra, ki shiga ciki ki kwanta mana, naga kamar bacci kike ji ko?" Ta buɗe ido, sai kuma ta make kafaɗa ta ce, "Ina gefen Abbah na." Abbah ya ce, "Toh kwanta anan ki yi baccin tunda har yana son sace ki." Tana kwanciya kuwa, nan da nan numfashinta ya canza alamar bacci ya ɗauke ta. Abbah yana kallonsu ya ce, "Ko ido na ne, naga Zahra ta canza… kamar tana cikin damuwa sosai.* Mami ma tayi shiru, don abin dake ranta kenan. Mummy ta ce "Ai Alhaji, ina jin kamar albarkar aure ce fah" A ɗan fusace ya ce "Ban gane ba. Haka kawai sai ’yar tawa ta dinga ramewa ace albarkar aure? Ina albarka anan?" Mami tayi murmushi. Mummy ta ce "Toh ai albarkar aure ina nufin ka kusa samun jika ne. Baka gani ba, tun da tazo take ta faman bacci? Wannan ramewan a cikin laulayi ne" Mami ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya. Sai yanzu ta ji hankalinta ya ɗan kwanta ganin kamshin gaskiya a maganar Mummy. Abbah yayi murmushi, amma har yanzu Umar bai daina kallonta ba...... Bayan Magrib, Zahra ta fito daga toilet zata hau kan sallaya, sai ga Mami ta shigo ta ce, "Zahra, ki yi sallah ki ɗan ci abinci, ki samu ki tafi kafin dare ya yi." Sai da gabanta ya faɗi jin maganar. A hankali ta ce "Toh, Shikenan" Daga haka Mami ta fita kawo mata abinci. Bayan Mami ta dawo, ta same ta ta idar amma tana kwance kan darduma. Ta duƙa tana kallonta ta ce, "Baby, me ke damunki ne?" Zahra ta ce, "Menene Mami?" Mami ta ce, "Duk kin canza ne Zahra… ba Baby na dana sani bane a baya. Ko akwai wata matsala ne?" Zahra tayi dariya ta ce, "Babu komai fah, Mami." Mami ta ce "Toh Shikenan… amma bayan bikin ki kin yi period ne?" Zahra tayi shiru tana kallon Mami, dan bata san ma’anar tambayar ba. A hankali ta ce "A'a, ban yi ba" Nan take Mami ta yi murmushi. Sai da gaban Zahra ya faɗi saboda abinda kwakwalwarta ta hasko mata game da tambayar da Mami ta mata... Umar ne yayi sallama a ƙofar ɗakin. Mami ta amsa ya shiga yana kallon Zahra da har ta gama shiri. Ya ɗauki jakkanta tare da riƙo mata hannu ya ce, "Mu je, mijinki ma yana downstairs." Ta kalleshi ta ce "Yaushe ya shigo kuma? Ya ce, "Not long ago" Daga haka ta yi wa Mami sallama suka fita. A corridor, ya tsaya ya ce, "Baby, me ke damunki?" Ta yi shiru. Ya ce "Baby talk… akwai matsala ne a zamantakewar ku?* Ta ce, "Nope." Ya ce, "Ƙarya kike, shine zaki lalace har haka?" Ta yi shiru ta ce, "Yaya, babu komai fah. Ka bari idan na tafi gida zan kira ka na sanar maka abin dake damuna.* Ya ce, "Kin yi alkawari?" Ta ce "Eh, nayi" Daga haka suka fara sauka. Tun a kan stairs Ibrahim ya ɗaga kai yana kallonsu. Satan kallon Abbah yayi, ya ɗauke kansa, ya ci gaba da kallonsu har suka sauka. Ko kaɗan Zahra bata kalleshi ba. Gefen Abbah ta ƙarasa ta zauna ta ɗora kanta a faɗarsa. A hankali ta ce, "Abbah, ya jikin?" Ya ce "Da sauƙi, Baby" Ya ce "Yaushe zaki koma school? Ban ji kina labarin komawarki ba" Ta ce, "This coming Monday nake son na fara zuwa." Ya ce, "Good. Ki fara saboda final year ba shekarar wasa bane." Ta yi shiru. Ibrahim kam ya kasa ɗauke idonsa akanta. Abbah ya ce, "Tashi ku tafi, sai da safe." Umar ya ɗauka mata jakkanta. Abbah ya ce, "A'a, ajiye mata. Ai tare da mijinta zata koma." Zahra ta miƙe tsaye ta ce, "No Abbah, da mota nazo ai" Daga haka tayi hanyar ƙofa. Ibrahim yayi wa Abbah sallama ya bita a baya. Wani kallo Umar ya bishi da shi. Tana isa jikin motarta zata buɗe kenan, ya ce, "Wani irin rashin tarbiyya ne wannan? Baki ganni bane? Ko gaishe ni ba zaki yi ba? Wani zindikin kato zai riƙe hannunki ku fito kamar baki san ina existing a wajen ba…" Ta juyo ta masa wani kallo ta ce, "Dama zama tare da kai akwai wani alkhairi ne? Ko ba matsala muke samu ba?" Ta numfasa ta ce "Abeg ka matsa min a hanya kafin nayi calling attention na mutane." Ta shige motarta ta fita. Shi ma ya bi ta a baya da nasa motar. Tana shiga gida, ta sauka ta wuce ɗakinta direct. Tana cikin toilet, ta ji karar buɗe ƙofa. Tana fitowa, ko kallon inda yake bata yi ba. Ya ce "Gobe after Magrib ina so ki shirya, zamu tafi wani taro. Kuma na san zaki cire ni a kunya. Dan wannan abun zai iya trending sosai, so dan Allah be ready, bana son ki bani kunya." Ta yi banza da shi. Ya ce "Baby, magana fah nake miki." Ta ce "Na ji." Ya ce, "What?" Ya ƙarasa inda take. Ta ja baya ta ce, "Na ji, Allah ya kaimu." Ya ce, "Ameen." Ta kalleshi ta ce, "Khalil, me yasa kake min abubuwan da suke kona min rai? Baka so na shine zaka aure ni? Baka so na shine zamu yi wannan deal ɗin? Ko dai ka manta alkawarin mu ne? Ko wani laifin na maka da zaka ke min haka?" Ya ce, "Calm down… zan canza, baby. Wallahi babu abin da kika min. Sorry kinji." Ta rungume shi tayi lamo a kirjinsa… tana jin yadda zuciyarta ke bugawa. #08110615256 *FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA) Book 1 Chapter 3 ....Sun fi minti biyar a haka, kowa da abin da ke saka wa a ransa. Kawai wayansa yayi ringing. Kallon bed side drawer yayi inda wayan nasa yake. Ga mamakinta, zareta yayi a jikinsa ta tsaya tana kallonsa har ya karasa wajen wayan. Satan kallonta yayi ta gefen ido kafin yayi receiving call ɗin. Shi dai banda amsa da yake bayarwa ma wanda suke waya da “Eh, uhm, okay,” kawai yake cewa, sannan ya kashe kiran ya ajiye wayar. A hankali ta ce, “muje mu ci abinci ko? Ko fita zamuyi?” Tayi hakan ne ba wai don yunwa take ji ba, kawai dan ta samu lokacin sa, ta jasa da magana har ta fahimci meke faruwa. Kallon agogon taga yayi, sannan ya kalle ta yace, “I’m full.” Zata sake magana taga yayi hanyar toilet. Ta karasa jikin gadon ta zauna, ta kurawa wayan nasa ido. Can sai gashi ya fito. Suna haɗa ido ya sakar mata da murmushi. Bata san sanda ta langabar da kai ba tana kallonsa itama da murmushi. Bayan ya gama shiryawa, taga kayan da zai sa. All what she thoughts pajamas zai saka, sai kawai taga ya sanya jamfa da hula. Wani irin bugawa zuciyarta yake yi. Ta bata rai sai daya gama shiryawa saf sannan ya nufa wajen wayansa zai ɗauka. Ta sha gabansa da sauri tana masa wani kallo tace, “ina zaka je kuma a daren nan?” Ya ɗaga mata gira ɗaya yace, “baki ji ana kiran Isha’i bane?” Ta sauke ajiyar zuciya, amma ba wai hankalin ta ya kwanta bane. Taja baya tana kallonsa. Yace, “bari na tafi masallaci.” Ta kasa ce masa komai har ya fita. Ta dade zaune tana sake-sake a rai. Jin har an idar da sallah yasa ta miƙe taje tayi alwala. Tana cikin sallah taji karan fitar motarsa. Har mancewa tayi tana sallah, bata san sanda ta fashe da kuka ba. A haka ta samu ta idar da sallahn. Yanzu kam ta gama jin ta tsane Ibrahim. Tunanin abin daya fado mata rai wanda kullum take kokarin nesanta sa da zuciyarta ne ya faɗo mata. Hakan yasa ta sake fashe wa sosai da kuka, har da shesheka. Ta jingina da gadon tana tunani. Wannan wani irin masifa ce? Mutum babu soyayya, babu kalamai masu dadi, babu zama da miji ayi hira da wasa. Bashi da lokacin ta, baya dawowa gida da wuri sai passed 12 na dare. Idan ya dawo kuma da wuri sai yayi wannan fitan. Babu sannu balle madallah. Toh ita bata ga amfanin wannan auren nata ba. At this point tana jin zata iya hakura da shi dan taga ta fara ɗaurawa kanta damuwa. Tuna wacece ita a social media yasa jikinta yayi mugun sanyi. A hankali tace, “Allah ka taimake Ni, ka sassauta min abin da nake ji a raina. Allah kana gani bana son na kawo wani 3rd party a maganar nan.” Karan ringing ɗin wayarta ne ya katse mata tunanin data ke yi. A hankali ta kai hannu ta ɗauka. Mami taga take kiranta. Sai data daidaita kanta sannan ta daga kiran. A hankali ta ce, “Mami.” Mami tace, “Na’am, kun koma gida lafiya?” Tace, “lafiya lau Mami.” Sai tayi shiru. Mami tace, “Baby meke damunki? Tabbas nasan akwai abun dake damunki dan ba haka kike ba da.” Tayi shiru dan da gaske kuka ne ke son taho mata. Ta daure tace, “Mummy babu komai fah, ki yarda dani. Kawai bana jin dadi ne kwana biyu.” Shiru taji mamin ta mata. Tasan kuma Mami ba zata sake cewa komai ba, dan Mami haka rayuwarta yake da uban miskilanci musamman idan tasan karya kake mata, bata kuma cewa komai. Kittt… kawai taji alamun ta kashe wayan. A hankali ta zare wayan a kunnenta ta ajiye wayan a gefenta. Tace, “Khalil wani irin rayuwa kuma kake son jefa Ni? Ka taimaka min ka dawo Ibrahim Khalil dana sanka.” Wani ringing ɗin tayi. Ta dauka sai taga Firdausi ce. Ta dauka. Bayan sun gaisa, Firdausi tace, “Nagode sosai Zahra, Allah ya saka da Alkhairi ya...” “Its okay Firdausi,” Zahra ta katse ta. “Ai yiwa kai ne. Ni da ke ai mun daɗe da zama daya, so bana son wani godiya.” Tace, “Tohm, ga Mama zaku gaisa.” Zahra tace, “toh bata.” Bayan sun gaisa, ta mata ya jiki. Tace da sauki. Tace, “ya me gidan naki?” Zahra tace, “lafiyansa kalau Mama.” Tace, “Tohm Allah kara hada kanku ya baku zuriya nagari.” A hankali tace, “Amin Mama na gode.” Daga haka suka yi sallama. Bayan Mama ta mikawa Firdausi, Zahra tace, “In Shaa Allah gobe zan shigo na duba Mama.” Daga haka suka yi sallama. Ta miƙe ta naɗe sallayan ta sauka kasa ta haɗa tea tasha. Ta daɗe zaune a parlorn ga wuta amma ta kasa ko kunna TV ne. Ta mike ta wuce daki ta canza kayanta zuwa sleepwear. Ɗaukan wayanta tayi ta wuce gado da shi. Ta shiga media account dinta duk da lots of comments da messages bata jin zata bi takan ko ɗaya. A haka bacci ya ɗauke ta. "Can a cikin baccinta taji ana buɗe gate. Ta buɗe idonta a hankali ta dauki wayan gefenta ta kalli lokaci. Murmushi takaici tayi ganin har 12:20am. Ta miƙe taje ta buɗe curtains taga yayi parking amma still yana cikin motar yana danna danne a waya. Ta kura masa idanu duk da ba wai sosai take ganinsa ba. Ya sauko yana tafiya irin ta kasaita. Ta koma ta kwanta. Can taji yaje ya buɗe kofar dakinsa ya shiga. Taji hawaye mai mugun zafi ya sauko zuwa kuncinta. A haka har taji ya buɗe nata ɗakin ya shigo. Alama dai acan yayi wanka ya canza kaya. Tana ji ya kashe wuta ya kwanta. Ji tayi kamar ta tashi ta bar masa dakin. A ranta tace tasan me zata masa gobe. A haka har bacci ya ɗauke ta. Washegari da safe, bayan ta gama breakfast ko takansa bata bi ba, ta zauna tana nata breakfast ɗin. Sai gashi ya sauko daga sama alamar ya gama shiri. Ya ce, “Baby kin gama breakfast din shine ba zaki min magana ba?” Ta share sa. Yace, “yau kuma da wulakanci kika taso ne? Ko gaisuwa kina jin kinfi karfin ki gaishe Ni?” Har sannan bata ce masa ci kan ka ba. Ya karaso dinning ɗin ya zauna yayi serving kansa a plate ya fara breakfast. Duk idanunsa yana kanta amma ita ko da wata taki yarda ta kalle sa. A hankali ya kamo hannunta cikin nasa yace, “Baby…” Sai sannan ta masa wani banzan kallo. Yace, “haba mana sweetie wai menene?” Ta kwace hannunta tace, “idan baka daina kira na da sweet names ba zaka sha mamaki.” Da mamaki yake kallonta. Ta miƙe tsaye zata bar wajen. Yace, “shikena Tohm, but kar ki manta anjima zamu fita.” Wani irin murmushi tayi mai wuyar fassarawa sannan ta wuce sama. Yana gama breakfast ya dauki briefcase ɗinsa ya fita. Bayan ta fito a wanka tace, “zaka sha mamaki na Khalil.” Shiryawa tayi saf cikin lace. Ta fito a ainihin Zahran ta, the beauty personified. Ta dauki handbag ɗinta ta sauka kasa. Direct wajen motar ta ta wuce ta shiga. Ta kunna sannan ta bar gidan. Bata tsaya ko ina ba sai gidansu Firdausi. A kofar gidan tayi parking sannan ta sauka ta shiga da sallama a bakinta. Brothern Firdausi Abdul ne a compound din yana wanke kayan Mama. Ya daga kai yana kallon Zahra da murmushi yace, “Anty Zahra sannu da zuwa.” Tace, “Sannu Abdul, ya gajjiya?” Yace, “Alhamdulillah.” Tace, “ya jikin Mama kuma?” Yace, “da sauki, ki shiga suna ciki.” Daga haka ta karasa bakin kofar dakin. Mama tace, “Zahra’u shigo mana.” Ta shiga tana murmushi ta zauna ta gaishe ta tare da mata ya jiki. Sai ga Firdausi ta fito tana murmushi tace, “Tauraruwa karaso mana.” Zahra ta miƙe tana dariya tabi bayanta zuwa dakin Firdausi. Bayan sun zauna Zahra tace, “nikam hope jikin Mama da sauki.” Tace, “chap da sauki sosai fah, sai dai yanzu kam muce Alhamdulillah.” Zahra tace, “ai yayi kyau toh.” Zahra ko harda bacci sai can bayan Azahar Firdausi ta tashe ta tayi sallah. Bayan ta idar suka ci abinci. Wasa wasa dai Zahra ta kusa wuni a gidan tun safe. Suna hira can Firdausi tace, “Zahra kiyi hakuri zan miki kasalanda a rayuwar ki nasan ba lallai ki so ba.” Zahra tace, “bana son iskanci yau Ni ɗin har wata bakuwa ba zama a wajenki.” Firdausi tayi murmushi tace, “kin san zuciya fah bata da kashi.” Zahra tace, “Ni dai ina jinki.” Firdausi tace, “kina cikin damuwa ne Zahra? Kinga yadda kika koma?” Zahra tayi shiru. Firdausi tace, “don Allah kar ki boyemin komai Zahra, kin san ba zan taɓa fitar da sirrinki ba. Ki tausaya kar kisa Ni cikin damuwa da tunani.” Zahra ta sauke ajiyar zuciya tace, “Firdausi banda ke ban taɓa fada wa wani ba. Babu wanda yasan halin da nake ciki. Amma tabbas ina cikin damuwa mai tsanani.” Firdausi tace, “SubhanAllah, don’t tell me tsakanin ke da mijinki ne?” Tace, “tabbas Firdausi, nayi dana sanin auren nan. Idan kinga naga Khalil a gida toh cikin dare ne ko kuma da asuba. Amma kwata kwata ya canza. Babu magana mai daɗi, babu lallashi, babu bani lokacina. In takaice miki yadda kika san Ni ba matar sa bace haka ya ɗauke Ni.” “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un,” Firdausi ta dinga maimaita. Tace, “tabbas Zahra wannan abun damuwa ce. Ba zan iya kuma ce miki kala ba yanzu, har sai nayi tunani mafita.” Zahra ta sauke ajiyar zuciya. Khalil banda trying number Zahra da yake yi babu abinda yake yi. Ya kira yafi sau hamsin. Tun karfe biyu ya dawo gida amma yanzu karfe 4 babu Zahra a gida. Damuwarsa ya sanar mata zasu fita amma ta kama tayi tafiyarta dan ta bakanta masa rai. Babu abinda bai saka a ransa ba, sai uban zufa yake haɗa wa. Firdausi tace, “dan Allah Zahra ki tashi ki koma gida. Kinga kar yazo bai ganki ba ku sake samun wani issues ɗin.” Zahra tayi shiru tana kallon wani waje. Can tace, “Firdausi ba zaki gane bane naji na tsane rayuwar gidan ma gaba ɗaya.” Firdausi ta ce, “please ki daure ki tafi. Na miki alkawarin gobe zan shigo.” Sai sannan Zahra ta miƙe ta fara shirin komawa gida. Bayan ta gama ta fito Firdausi ta raka ta taje ta ma Mama sallama sannan suka fita waje har jikin motar Zahra. Zahra tace, “toh Nagode Firdausi, ina jiranki gobe ɗin ko?” Tace, “In Shaa Allah zan shigo. Ni dai damuwa ta bana son kina saka damuwa a rai har kina ramewa kowa ya fara magana.” Ta ce, “Tohm shikenan zan rage.” A haka suka yi sallama. Zahra ta ja motar ta tayi gida. Tana parking ta sauka. Wani farin ciki taji ganin motarsa a parke. Ta tabbata ya neme ta bai sameta ba. Tana shiga parlorn ta gansa tsaye ya haɗe fuska kamar ba shi ba. A ɗan fusace yace, “ke daga ina kike?” Tace, “calm down Malam, ka rage murya kamin magana cikin sanyin murya dan kasan na taso cikin gata ba’a min ihu akai.” Ya sake baki yana kallonta yace, “wai wa kika ɗauki kan ki ne?” Ta ce, “Fatima Zahra tauraruwa wacca ake tururuwa akanta har ta faɗa tarkon maciji.” Wani kallo yake mata yace, “look Zahra baki isa ina faɗa kina faɗa ba. Ya kamata kisan da wa kike magana. Sannan ki faɗa min da wa kika tambaya kafin kika fita.” Ta sake baki tana kallonsa tace, “kamar yadda kake da right na fita at anything kuma ka dawo duk lokacin da kaga dama toh hakan Nima take.” Wani ihu yayi wanda har sai data tsotsa yace, “kar ki gaya min maganar banza mana! Dama naga take takenki ke da wannan banzan Yayan naki mara tarbiyya har yake wani rike miki hannun kuna sauka a stairs yana jin daɗi, nasan akwai wani abu!” Zahra tace, “auzubillahi, lallai yau na tabbatar Khalil kana da ƙarancin ilimi. Yayana ubanmu ɗaya dan ya riƙe Ni har zaka iya kawo wani abu ranka? Lallai abin naka yayi nisa.” Suka dinga exchange words. Can ya buga wani cup yayi zuciya ya fita daga parlorn. Parking space ya tafi ya buɗe motansa ya shiga yayi dialing numbern wata. Tana ɗagawa yace, “ina son mu haɗu nan da 30mins. Babe kiyi wanka na kece raini, zan zo zan ɗauke ki zaki raka Ni wani waje ne.” Tace, “Babe…” Yace, “uhum.” Tace, “meya faru naga ranka a bace?” Yace, “kinji abinda na fada miki?” Tace, “eh naji, waya bata maka rai?” Yace, “ki bari sai mun haɗu.” Daga haka ya kashe kiran. Ya lumshe idonsa, kawai sai ga fuskarta ta bayyana masa. Da sauri ya buɗe ido. Ya manta cewa ba zata iya masa abin da Zahra zata yi ba. Bata da komai...ba kyau ba, ba iya turanci ba, a haka zata fitar da shi a kunya? Kai, gaskiya da sake… wannan sai Zahra don duk Zahra ta haɗa wadannan qualities ɗin. Haka ya sauka a motar. Ya gwammaci yaje ya bawa Zahra hakuri, koma me zai faru su shirya. Ta taimaka su tafi tare. A haka ya nufi hanyar cikin gidan." #Jiddatulkhayr writes #08110615256 *FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes Young talented writers association (YOTA) Book 1 Chapter 4 Da sauri yake hayewa sama saboda yadda lokaci yake tafiya. Ya nufi bakin ƙofar ɗakinta, a hankali ya murɗa sannan ya shiga. Ya same duke a ƙasa tana shesheka. Ya ƙarasa wajenta ya duƙa, ya ɗagota jikinsa. Zata kwace kanta, ya riƙe ta gam. Ya ce, "Haba Zahra, kin san bana son kukan ki fah" Bata san sanda ta masa wani kallo ba. Ya ce "Okay toh… ki daina Please" Tayi shiru, still tana jinkinsa. Ya shiga share mata hawayen fuskanta ya ce, "Na yi fushi ne saboda kin san zamu fita kuma kin sani kika fita… amma na sani bai kamata na ɗaga murya na haka sosai a kanki ba. I'm sorry." Lokaci guda Zahra ta manta da wani ɓacin rai. Yana riƙe da ita, suka zauna a bakin gado. Ya ciro wayansa yana kallonta ya ce "Wata mai makeup ɗin za'a miki booking? Ko kuma kawai tazo nan ta miki?" Kai ta gyaɗa ta ce "Ka shiga IG." Nan take ya shiga ya miƙa mata wayan. Ta yi searching wani account sannan ta miƙa masa Ya ɗauki number ɗin ya kira. Bayan sun gama magana, ya tura mata address ɗinsu. ***** Zahra ta miƙe ta ce, ''Bari nayi wanka." Murmushi ya sakar mata. Sai taji dama wannan murmushi ba zai yi fading a fuskarsa ba… sak Ibrahim ɗinta na da ya fito. Ta sauke idonta sannan ta wuce toilet, jin an fara kiran sallah. **** Bayan ta gama shiryawa, mai makeup ta mata bridal makeup Ba kaɗan ba tayi kyau. Ita kanta artist ɗin sai da tayi content da ita, musamman da ta gani ashe famous Zahra.xx ce Zahra kuwa ta zama tamkar sabuwar amarya a wannan lokacin. Khalil kam ya kasa rufe baki saboda murna. Shi ma ba ƙaramin kyau yayi ba. Sai ya zama kamar yau ne ake bikin nasu. **** Yana riƙe da hannunta suka fita zuwa compound. Ya buɗe mata ƙofar gaban mota ta shiga, sannan ya zagaya ya shiga shima. Ya juya yana kallonta ya ce, "Tauraruwata…" Ta hararesa tana murmushi. Ya ciro wayansa yayi musu hoto, sannan yayi posting da caption 'With my queen tonight My forever peace, my Tauraruwa #PowerCouple #RoyalVibes #MyZahra' **** Suka isa wani babban organization... Northern Elite Business Consortium (NEBC) inda za'a gudanar da taron. Ya yi parking. Ta kai hannu zata buɗe ƙofa, ya ce, "No Gimbiya… ki bari na karasa aikina." Ta sakar masa murmushi. Haka kawai take jin kanta cikin wani yanayi na farin ciki... kamar komai ya dawo daidai. Ji tayi dama su dawwama a haka. Ya sauka, ya zagaya side ɗinta, sannan ya buɗe mata mota. A take idanu suka dawo kansu. Kowa sai kallo. Ya kama hannunta ya saukar da ita a hankali, ta sauka. Ya kai bakinsa gefen kunnanta yayi mata raɗa. Ta yi dariya ta ce, "Ban so… Ya ce, "It's okay, na daina Gimbiya" A haka suka kama hanyar shiga cikin taron Annual Northern Leadership & Investment Gala wani babban taro na manyan ‘yan kasuwa, shugabanni, da masu tasiri a Arewa. *** Suna shiga cikin hall ɗin… ido ya dawo kan Zahra. Kowa sai kallonta yake yi, wasu suna kallon kyawunta. Wasu kuma dama already sun santa a Social Media as Zahra.xx, kuma tun sanda aka aka yi bikin ta, ɗif ta sauke wuta ba'a sake jin motsinta ba a media, wasu suka fara yi wa juna magana a hankali. Ibrahim kuwa... zuciyarsa na cike da wani irin daɗi, Yes ita ce tasa. Ita ce matarsa. Ita ce ke jawo hankalin kowa akansa, kuma yake tafiya viral a wannan watan Amma... Duk lokacin da ya lura kallon ya yi yawa… sai ya ɗan matse hannunta kaɗan, alamar kishi. Suka samu wuri a gaba, inda aka tanadar wa manyan baƙi. An fara gabatar da taron cikin tsari da nutsuwa. MC ya hau stage ya fara da gabatarwa "Ya ku maza da mata, baƙi masu daraja… a madadin Northern Elite Business Consortium, muna maraba da ku zuwa taron shekara-shekara na Northern Leadership & Investment Gala Night" Akq ci gaba da gabatar da manyan baki, shugabanni, da 'yan kasuwa. Ana kira suna… ana tafi ana dawowa… ana yin speeches… Ana cikin tsakiyar taron amma har yanzu ido na kan Zahra. Ibrahim ya jingina da kujera yana kallonta, yana murmushi. Amma a zuciyarsa; yana jin wani abu guda biyu a lokaci ɗaya 'alfahari… da kuma kishi' A tsakiyar taron… ana ta ɗaukar hotuna. Flash na camera na walƙiya lokaci zuwa lokaci. Wasu suna turo musu phones suna cewa, "Please, one picture…" Wasu kuma daga nesa suke capturing ɗin su. Zahra kuwa sai murmushi take yi natural, ba tare da wani Izzah ba MC ya ɗan yi shiru kafin ya fara magana "Yanzu kuma… za mu karrama ɗaya daga cikin manyan ‘yan kasuwa da suka yi fice a harkar sayar da manyan motoci a wannan yanki namu…" Aka fara tafa hannu. "Mutum ne da sunansa ya zama abin alfahari da kuma amana a harkar kasuwanci, musamman a fannin motoci masu tsada…" Zuciyar Ibrahim ta ɗan buga. "Babu shakka, ya bayar da gudunmawa sosai wajen bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi…" MC ya ɗan dakata sannan ya ce da ƙarfi: "Mu marabci… Mr Ibrahim Khalil!" Tafi ya kaure a hall ɗin, kowa ya juya yana kallonsu Zahra ta juya ta kalleshi da murmushi Ya ɗan gyara zama, sannan ya miƙe tsaye, ta miƙe tare da shi. Yana riƙe da hannunta suka nufi stage camera suka karkata kansu. Flash… flash… flash… Kowa na ɗaukar su. Wasu ma suna tashi tsaye don ganin su sosai Suka isa stage, aka miƙa masa award. Ya karɓa da murmushi. Zahra na tsaye a gefensa.. ta zama kamar haske a wajen. Nan take aka fara musu hotuna. Professional photographers na gaba click… click… click… Sannan phones daga audience recording… snapping… Wasu tuni suka fara posting a social media: "Who is she??" "Mr Khalil and his stunning wife" "Power couple spotted tonight" Ana tagging account ɗinta kai tsaye. Notifications suka fara shiga a jere. Zahra dai murmushi kawai take yi cikin nutsuwa Amma a zuciyarta.. tana jin wani irin yanayi. Bayan sun gama, suka sauka daga stage. Har yanzu ana binsu da camera. Ibrahim ya riƙe hannunta sosai.. kamar baya son a raba shi da ita. Suka koma suka zauna. Ya ɗan matsa kusa da ita ya ce a hankali, "Kin ga yadda kike jawo hankali ko?" Ta yi murmushi kaɗan bata ce komai ba Aka ci gaba da taron har aka kai ƙarshe. MC ya yi closing speech. Ak yi addu'a. Sannan aka sanar da ƙarshen taron. Mutane suka fara fita, ana gaisawa, ana musabaha. Ibrahim da Zahra suna tafiya tare, hannunsa riƙe da nata gam. Duk inda suka wuce.. ana tsayawa a gaishe su. "Congratulations, Mr Khalil" "Beautiful couple." "Masha Allah…" Wasu suna kallon Zahra da sha'awa. Wasu kuma suna kallon su da irin kallon da ke nuna hassada. Ibrahim kuwa duk lokacin da wani ya tsaya kusa da ita sosai sai ya ƙara matso da ita jikinsa sosai. A haka suka karasa jikin mota, ya buɗe mata motan, ta shiga. Ya zagaya ya shiga shima, yana kallonta… yana murmushi, itama murmushin take masa, amma a cikin murmushin sa, akwai wani abu, wani abu da ba a fahimta kai tsaye Ya tada motar daga haka suka bar wajen, wani babban restaurant ya tafi da ita, Zahra ba zata iya misilta farin cikin da take ciki ba, daga ranan aurensu sai wannan ranan a kalan farin cikin da take ji. Sosai suke nuna wa juna soyayya da kulawa, ciyar da junan su suka yi, ba tare da sun damu wai akwai mutane ba, suna gama wa yana riƙe da ita haka suka fita daga restaurant ɗin suka wuce mota.. "So exhausted suka isa gida. Yayi parking sannan duk suka sauka, tana riƙe da award ɗinsa. Direct ɗakinsa suka wuce. Ta faɗa kan gado ta ce, "What a stressful day… kasan yadda nake jin gajjiya a jikina kuwa?" Ya ce, "Sorry, bari nayi wanka, nazo na miki massage." Ta hararesa ta ce, "Ko ba massage ba…" Yayi dariya, ya cire kayansa ya wuce toilet. Wayansa ne ta gani ya kawo haske. Ta miƙe a hankali ta ƙarasa wajen. Ta kalli me kiran ‘dovie’, ta kurawa wayar ido har ya yanke. Nan ta ga missed calls ɗin har wajen 8. Tayi shiru tana kallon ƙofar toilet ɗin. Tunanin kamar har da wayansa yake sa suke samun matsala… amma bata jin yau zata bar wani abu ya shiga tsakaninsu, musamman bayan ranar da ta sha wahala. Sai kawai ta kashe wayar baki ɗaya, ta koma ta zauna a bakin gadon. Can sai gashi ya fito. Ta ƙarasa ta ciro masa rigan bacci a sif, ta kai masa kan gado, ita ma ta wuce toilet. Da wuri ta fito, dan duk hankalinta yana kansa kar ya ɗauki wayansa. Ya juya yana kallonta da mamaki, ganin har ta fito. Ya ce, "Yau ke ce da gama wanka da wuri?" Murmushi tayi ta ce, "Ai ba datti nayi ba… shiyasa." Ya gyaɗa kai kawai. Itama ta gama saka kayanta. Washegari… Bayan ta gama breakfast tana kokarin fita da kulolin, sai Khalil ya shigo daga masallaci. Ya tsaya a bakin ƙofar kitchen ɗin. Ta juyo tana masa murmushi ta ce, "Ina kwana?" Ya ce, "Lafiya… amma yau lafiya kika daura breakfast da wuri haka?" Ta ce, "Ohh sorry, ban faɗa maka ba ko? Ai yau zan koma school. Baka ji ba, Abba ma sai da yayi magana. Ya ce, "Really? Toh Allah bada sa'a" Ta ce, "Ameen" Tare suka yi breakfast, suka shirya. ** Suna sauka stairs suna hira da wasa mai ban sha'awa. A haka suka wuce compound kowa ya nufi wajen motarsa. As usual, haka ta shiga department ɗinsu, idanun mutane na kanta. Bayan ta yi parking, sai da ta ɗauki few seconds kafin ta buɗe motar ta sauka. Kaf department ɗin daga lecturers har students babu wanda motarsa ya kai na Zahra tsada da kyau. Shiyasa kusan kowa yake mata fadanci. Ita kuma ta tsani hakan. Duk da tarin makiya da take da su Ta buɗe back seat ta ɗauki jakkanta. Ta fara tafiya kenan, sai ga class rep a bayanta ya ce, "Ahh, anty Amarya ce!" Ta juya ta ce, "Class rep, ya gajjiya?" Ya ce, "Ina kwana, fatan kin dawo lafiya?" Tana murmushi ta ce, "Kalau, sannu da ƙoƙari" ya ce "Haba ai yiwa kai ne, Allah dai kawai ya kara rufa asiri" ta ce "Ameen, naga an bada wani presentation topics na seminar" Yayi murmushi ya ce "Ai tuni na gama miki Hajiya, kawai ban faɗa miki bane, amma ai kema kin san kinfi karfin haka" dariya tayi ta ce "Toh Nagode kwarai" Tana cikin tafiya, sai ga Asiya. "Zahraaa!" ta kira da ƙarfi Zahra ta juya tana murmushi ta ce "Kash Asiya ba zaki taɓa canzawa ba… kalli yadda kike ihu a mainan nasu" Asiya ta ce, "Kyale ni nikam!, ashe zaki zo shine ko magana babu?" Zahra ta ce "Abbah ne ma yayi magana, kuma dama yana raina, Shiyasa nace bari kawai na fara fito wa tunda shima ya koma aiki" Ta karɓi jakar Zahra ta rataya. Suka nufi lecture hall ɗinsu suna ɗan hira Asiya ta ce, "Kee, jiya dai kun daga hankalin mutane a media. Kinga uban kyau da kuka yi, Ma Shaa Allah!" Sai kuma ta ɗan dakata. "Amma kuma ke ban ga kin yi posting ba. Ga Ya Khalil sai uban posting ɗinku yake yi da romantic caption" Zahra ta ce, "Please Asiya, it's early ace mutum har ya fara uban surutu haka" Asiya ta taɓe baki ta ce, "Ashe dai baki canza ba… chap toh Allah yasa Khalil ɗin ma irin ki ne, idan ba haka ba kun dinga samun matsala" Zahra dai bata kuma kulata ba har suka isa cikin hall ɗin, haka colleagues ɗinta suka dinga zuwa suna gaishe ta, saboda uban souvenirs data bayar a kawo musu bayan bikin Ga mamakinsu sai ga Saudat ta shigo, ko da wasa bata yarda tayi inda suke zaune ba, wani raw ma daban ta nufa, Zahra ta kalli Asiya ta ce "Nikam Ko dai laifi nawa Saturday ne?" Asiya ta ce "Kema da ɗaukan damuwa, dan Allah ki share ta, ko ba komai kin ɗaga Saudat har ta zama mutun" #Farashin Izzah #Jiddatulkhayr writes #08110615256 *FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes Young talented writers association (YOTA) Book 1 Chapter 5 Bayan sun gama lectures ɗinsu na farko, Firdausi ce ta zo kansu da sallama a bakinta. Zahra ta mata murmushi ta ce, "Late comer" Dariya tayi ta ce, "Ba zaku fahimta ba ne. Kun san sai na gama aikin gida dukka, tunda yanzu dai Mama ba lafiya ba. A hakan ma Abdul ne yayi wanke-wanke" Asiya ta ce, "Wai har yanzu ne jikin nata?" Ta ce, "Da sauƙi fah, kawai dai saura ta gama warwarewa ne" Zahra ta ce, "Allah ya ƙara mata lafiya" Ta ce "Ameen" Firdausi ta kalli Asiya, ta ɗan kalli wasu colleagues ɗinsu da suke gefenta, sai kuma ta kalli Zahra ta ce "Zahra, HOD yana kiranki. Kamar akwai issues da project topic ɗinki fah" Zahra ta ce, "Ban gane ba. Tunda ba su gane da issues ba sai yanzu da aka yi nisa da practical?" Firdausi ta ce, "Shi ne ai. Nima nawa wai bai gama yarda da practical ba. Yanzu dai ki tashi muje muji menene, dan yace yana neman mu" Asiya ta ce, "Hmm Allah ya kyauta. Amma ai hakan ba daidai bane, tun farko sai ya faɗa muku ai" Zahra ta miƙe a zuciye tana kallon Firdausi kamar itace ta kawo matsalar ta ce "Sai ki wuce muje ai. Shi ma dan muguntarsa ne yasa zai kashe min aiki." Daga haka tayi gaba, Firdausi na binta a baya. Sai da suka je corridor ɗin offices ɗin lecturers ɗinsu, Firdausi ta dakatar da Zahra ta ce, "Mu zauna akan wannan kujerar" Zama suka yi Zahra tana kallonta ta ce, "Toh me kuma amfanin zaman?" Firdausi ta ce, "Magana nake so muyi… amma kin san halin Asiya da baki. Not that tana da baƙin hali, amma zata faɗa wa Suhaima, kuma kin san Suhaima zata iya faɗa wa Saudat. Kuma kin san halin da Saudat ta tsiro, kaf department sai sun ji. Gashi ke makiya da yawa kike da su" Zahra ta sauke ajiyar zuciya tana kallonta ta ce "Menene toh Firdausi?" Firdausi ta ce "Game da ke ne. Ina son sani, ya kuka yi jiya? Kin san wallahi bana jin daɗin yadda kika rame har haka" Zahra na kallon Firdausi ta ce, "At long last dai Firdausi na raka shi. Mun je, and everything went smoothly… kuma kamar dai ba shi ba, har da lallaɓa ta" Firdausi ta ce "Zan so da ace har zuciya ne Zahra, amma kin san menene? Gani nake yi hakan yayi ne saboda ya san kina da rauni. Kuma ya san dole zaki je saboda yadda ya san alakarki da media. Zai ce ko dan ki samu na posting zaki bi sa" Zahra ta tsaya kallonta, ta ce "Amma kin san har da safen nan Khalil kamar ba shi ba? Dan da gaske kamar ya canza" Firdausi tayi dariya ta ce, "Shikenan Zahra. Dama nima fata na hakan ta zama da gaske har ransa. Amma kar ki yi saurin yarda da shi, ki tsaya ki ga gudun ruwansa na kwana biyu" Zahra ta ce, "Alright, thank you Firdausi… amma dai ga dukkan alamu ya canza" Shiru tayi tana kallon Zahra saboda tausayi take bata. Bata fahimtar mai kwanarta saboda Allah, sannan bata fatan abin dake zuciyarta game da Khalil haka ne. Sauke ajiyar zuciya tayi ta ce, "Zahra tashi mu koma lecture hall" Miƙewa Zahra tayi suka fara tafiya a hankali, kowa da tunanin da take yi. Suna komawa cikin hall, zaman su ke da wuya sai ga Saudat a kansu ta ƙaraso tana murmushi. Kamar haɗin baki, har Suhaima data shigo yanzu babu wanda ya kulata. Zahra kam ma hawa IG tayi tana kallon yadda bloggers suke tagging ɗinta. Can Saudat ta miƙe ta bar wajen. Suhaima ta bita da kallon harara ta ce, "Munafuka kawai" Zahra ta ce, "Amma me yasa kuke haka ne?" Asiya ta ce, "Ai tazo ta kwashe kayanta a gidan da muke wai zata dawo hostel. Ita bata son zaman off campus. Amma kin san yadda tayi playing ɗinmu, wani gida aka kama mata ita kaɗai" Asiya ta ci gaba da cewa, "Ni fa problem dina da ita yadda ta canza ne. Musamman ga Zahra. Kullum bata da abin yi sai maganarta. Ko ta manta sanda aka kawo ta level 1 ne? Idan da ba Zahran ta wanke ta ba, akwai wanda zai kalleta ne?" Zahra ta ce, "Enough please. Tun yanzu zaku fara sa ma kanku ciwon kai? Ai maganar tayi yawa" Firdausi tayi dariya ta ce, "Dake ai mu kece da har magana zata sa mana ciwon kai" Duk suka yi dariya. Bayan ta koma gida, duk sammaminta zata ga Khalil, tunda shi 2pm yake tashi ita kuma yau tayi evening lectures ne. Amma shiga compound data yi taga babu mota ne, abin ya bata mamaki. Bayan ta sauka ta juya tana kallon mai gadi ta ce "Sannu Baba" Ya ce, "Yauwa, sannu Hajiya. Ai ɗazu ma kinyi baki nace kina makaranta" Ta ce, "Baki kuma? Ko sun faɗa maka su waye ne?" Ya ce, "A’a gaskiya basu faɗa min ba, amma sun ce zaku yi waya." Ta ce, "Tohm shikenan. Dan Allah Baba, mai gidan ya zo kuwa?" Ya ce, "A’a, tun da ya fita da safe bai dawo ba tukunna" Tayi shiru, sai kuma ta ce, "Na gode" Daga haka ta nufi cikin gidan. Sama ta wuce. Bayan ta cire kayan jikinta ta shiga toilet ta watsa ruwa tare da yin alwala. Ta zo tayi sallar La’asar sannan ta wuce kitchen. Girki ta ɗaura. Bayan ta gama ta sake share gidan duk da babu wani datti. Ta baɗe gidan da turare sannan ta wuce sama. Tana shiga WhatsApp ɗinta sau taga Firdausi na online. Kawai ta danna mata kira. Yana shiga ta ɗaga. Bayan sun gaisa sai kuma tayi shiru. A hankali ta ce, "Firdausi baya gida, kuma nasan maybe sai ya kai yadda ya saba kaiwa. Bana son na fara kai magana gida ne amma abin ya fara yawa, musamman yadda kinsan a gidanmu ba kowa yaso auren ba" Firdausi ta ce "Ki kwantar da hankalinki. Maybe ana Magrib zai zo, tunda kema kinga changes ɗinsa. Kawai ki daina daga hankalinki balle kiyi ta ramewa" Ta ce, "Thank you Firdausi" Daga haka ta kashe kiran. Sai kuma ga wani kiran Firdausi ya kuma shiga. Ta ɗaga. Firdausi ta ce, "Kina jina?" Ta ce, "Eh" Ta ce, "I think gobe ki shirya ki tafi gidan su. Kije ki gaishe da mahaifiyarsa, idan da hali ma ki mata girki" Ta ce, "Toh thank you. School ɗin fah?" Ta ce, "Ai gobe lecture ɗaya gare mu, kuma 2 to 4 ne. Sai ki tafi da wuri idan yaso daga can sai kizo lecture ɗin." Ta ce, "Tohm shikenan, hakan ma zan yi" Tana kashe waya ta fara jin kiran sallah. Ta miƙe ta wuce toilet tayi alwala, ta zo tayi Magrib. Wasa gaske har kusan 11pm babu Khalil balle labarinsa. Kamar ta kirasa amma ta daure zuciyarta. Tayi alƙawarin ba zata kira ba. Ta gama duk wani activities ɗinta na dare ta kwanta. Yau bata jin zama ta jira dawowarsa. Har ta kwanta ta tuna ƙofar a buɗe take. Ta miƙe taje ta saka key sannan ta koma ta kwanta. A haka bacci ya ɗauke ta. Wajen sha ɗaya da rabi sai gashi ya zo gidan. Mai gadi ya buɗe masa gate. Ya shiga yayi parking. Ya kura ac motar ya jingina da seat ɗin sannan ya kirata. Ya ce, "Na ƙarasa gida" Ta ce "Hope kai kaɗai ne?" Ya ce "Ai ni ba yaro bane" Ta ce, "Good. Bayani nake so kamin akan hoton da yake trending jiya a media." Yayi shiru yana saurarenta. Ta ce, "I’m talking to you, kamin shiru" Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Ban san me zan ce ba. Bana son kuma na fara miki karya. Tunda kinga hotuna na da Zahra ne ai shikenan. Bana son wani ciwon kai yanzu" Ta ce, "Hmmm shikenan, na kyale ka" Ya ce, "Better please" Daga haka ya kashe motar tasa ya daura kansa a steering. Sai kuma ya buɗe motar ya sauka. A hankali yake tafiya irin nasa na kasaita. Bayan ya haura sama ya wuce ɗakinsa yayi wanka ya saka kayan bacci sannan ya fito ya nufi ɗakin Zahra. Ya kai hannu ya murɗa ƙofar yaji a kulle. Abin ya bashi mamaki sosai, dan yasan Zahra bata kulle ɗaki. Sake kai hannu yayi ya murɗa da ƙarfi, yaji a kulle. Juya-juya ya fara yana kalle-kalle. Kansa ya kulle. Bata zo gida bane ko kuma ta kulle ɗakin ne kawai? Ai bai san sanda ya sauka ya tafi can ƙasa ba. Ya buɗe ƙofar parlour ya wuce compound. Ganin motarta yasa ya sauke ajiyar zuciya sannan ya koma ɗakinsa. Bayan ya kwanta abin yayi ta bashi mamaki yadda ta kulle ɗakin, a haka bacci ta ɗauke sa. Washe gari… Bayan ta tashi, wani yunwa ce ta addabeta. Tana idar da sallah ta wuce kitchen. A kitchen ɗin ma take Azkar meanwhile tana girkinta. Tana ji ya shigo amma ta daure zuciyarta. Ta juya tana kallonsa bayan ya leƙo kitchen ɗin. Kamar babu komai haka ta ce masa, "Ina kwana, fatan ka tashi lafiya" Ya ce "Lafiya Zahra" Kamar tayi shiru sai kuma taji ba zata iya ba. Ta ce, "Jiya baka zo gida da wuri ba. Wai nikam me kake tsayawa ne yi a wajen Noory? Ni fah yanzu banda wani lokacin ganin ka sai da safe. Mun koma kamar wasu strangers." Ya ce, "Dan Allah kimin shiru. Yau ne na saba kaiwa wannan lokacin? Ko kuma yanzu da asuban fari kike son tono faɗa? Baki da ikon tambayata daga ina nake, amma ni ina da ikon tambayarki. Kaiii… fita ma idan naga dama sai na hana ki, shikenan. Amma ke baki da wannan right na tambayata, Okay?" Wani shiru tayi ganin completely ya sake komawa wannan Ibrahim ɗin nasa. Hawaye ya cika idonta. Ta sauke indomie ɗinta ta zuba ta fara ci. Bayan ta gama ta wuce parlour ta kwanta. Nan da nan bacci ya kwashe ta. Can kuma ta farka. Ta kalli agogo kawai ta miƙe ta wuce sama. Tana zuwa zata wuce, a wall mirror dake manne a corridor akan drawer, wayan Ibrahim ne ke ringing amma volume ɗin an rage sosai. Ta ƙarasa wajen wayar a hankali ta ɗauka. Ta jima tana kallon saving ɗin da aka yi ma wanda yake kira har ya yanke. A take kuma aka sake kira. Ta ɗaga kiran ta kai kunne ba tare data yi magana ba. Wacce ke ɗayan ɓangaren shagwaɓa ta fara yi: "Haba sweetheart, me nayi maka ne kwana biyu ka guje ni? Shekarar jiya fah haka kaki zuwa, jiya ma haka. Baka sanin yadda rashinka yake saka min ciwo ba" Zahra kam mutuwar tsaye tayi a wajen, ta kasa motsi. Ita kuwa a ɗayan ɓangaren, jin shiru yasa ta ce, "Wai nikam ina kake zuwa ne ma kwana biyun nan? Ko dai wata ka fara bi sweetie ban sani ba?" Idon Zahra ya cika da ƙwalla. Bata san ya aka yi ba, bata san yaushe ya fito ba, bata san ya aka yi yazo gabanta ba. Kawai ji tayi mutum ya sa hannu ya karɓe wayar daga kunnenta. Ya kashe kiran sannan ya kai fuskarsa daf da tata yana kallonta. Ita kam dishe-dishe ma take kallonsa. Ya ce, "Wannan shine result ɗin ɗaukan wayan mijin" Daga haka ya juya ya bar wajen. Ta duƙa nan ƙasa. Ai baccin ma data ke ji ta nema ta rasa Ta fashe da kuka. Can kuma ta koma cikin ɗakinta. Bata san how long ta kai ba tana wannan kukan. Kawai ɗaga kai tayi ta kalli agogo har ƙarfe 9 yayi. Ta miƙe ta wuce toilet tayi alwala. Ta zo ta shimfiɗa sallaya tayi raka’a huɗu sannan ta sallame. Ji tayi ba zata iya kai abinci gidan nasu ba ma. A yadda take ji zata iya kona gidan da kanta a ciki. Ambaton Allah kawai take yi. Wayarta ce ta fara ringing. Kamar baza ta kula ba, sai kuma ta miƙe ta tafi ta ɗauka. Ganin Firdausi ce yasa tayi picking call ɗin. Bayan sun gama gaisawa, Firdausi ta ce, "Dama na kira naji ko zaki kai abincin?" "Hmmm…" kawai Zahra ta iya faɗi. Firdausi kuma sai yanzu data ce "hmm" ne ta fahimci kamar Zahra ma kuka take yi. Ta ce, "Zahra ban gane ba… kuka kike yi ne?" Zahra ta ce, "A’a Firdausi… kawai dai na fasa kai abincin ne." Firdausi ta ce, "Noo, ki tashi ki kai. Dan hakan shine mutuncinki, kuma ta nan ne zaki fara sayen zuciyar mahaifiyarsa" Zahra ta ce, "Ba zaki gane bane…" Firdausi ta ce, "Tunda aka yi auren nan Zahra, bayan sanda kuka je tare baki kuma zuwa ba. At least ki fara nuna mata cewa itama uwa ce. Wallahi zata ji daɗi, kuma matsalarki zata zo da sauƙi." Zahra ta ce, *Tohm… bari na daura." Ta bawa Firdausi amsar ne ba wai dan zata yi ɗin bane, sai dai dan Firdausi ta kyale ta. Dan bata buƙatar magana a halin yanzu. #Farashin izzah #jiddatulkhayr writes #08110615256 https://chat.whatsapp.com/IjVCBxrVY1Z4pH5IZhshvA?mode=gi_t *FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes Young talented writers association (YOTA) Book 1 Chapter 6 Ta daɗe tana zaune a wajen. Tabbas maganganun Firdausi gaskiya ne, amma anya za ta iya? Share hawayenta tayi ta miƙe tsaye, kamar mahaukaciya haka ta ɗaura hannu a kanta ta saki ihu, sai kuma ta durƙusa kan gwiwowinta tana kuka. “Khalil me na maka da zafi har haka da za ka saka min ta wannan hanya? Ko dama haka soyayya take? Dama haka zaman aure yake, ko nata ne daban?” Aure ko wata ɗaya bai gama cikawa ba. Ta sake fashewa da kuka tana nanata Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un. Ji take kamar ta cakkawa kirjinta wuƙa kawai ta huta. Ambaton Allah da take yi ne ya fara daidaita mata nutsuwarta. A hankali ta sauka ƙasa ta wuce kitchen. Buɗe fridge tayi ko za ta ga abin da za ta girka, amma sai taji ba za ta iya girki ba a halin yanzu. Kawai ta fita ta wuce ɗakinta. Ta shiga toilet tayi wanka, ta fito ta shirya cikin blue lace. Ba ƙaramin kyau tayi ba. Ta ɗauki handbag ɗinta da keyn mota ta sauka ƙasa. Kitchen ta wuce ta ɗauki wani warmer mai kyau. Bayan ta kulle ko’ina, ta nufi motarta. Ta saka kulolin a back seat, ta koma front seat ta shiga sannan ta tada motar ta fita bayan mai gadi ya buɗe mata gate ɗin. Ba ita ta tsaya ba sai a wani eatery. Ta sauka ta shiga ciki tare da kulolin a hannunta. Bayan ta sayi abincin ta fito ta ci gaba da tafiya. Gaba ɗaya tukin da take yi kamar kwakwalwarta ce kawai tayi recording ɗin inda za ta tafi. Amma idan ba haka ba, ita kanta bata san a wacce duniyar take ba. Ta faɗa duniyar tunani har idanunta suka canza. Bayan tafiyar kusan minti ashirin ta isa wani babban gida. Duk da cewa gidan bai kai gidan mahaifinta ba, amma shima ya gaji da haɗuwa. Horn tayi, mai gadi ya leƙo ganin ita ce ya koma da sauri ya buɗe gate ɗin. Shiga da motar tayi tayi parking sannan ta sauka ta ɗauki basket ɗin kulolin ta shiga da shi. A babban parlorn gidan tayi sallama sannan ta shiga. Wata matashiyar dattijuwa ce zaune a parlorn ana mata pedicure. Ta ƙarasa har cikin parlorn. Matar ta ɗan ɗaga kai ta kalli wacce ke shigowa sannan ta ɗauke kai ta mayar kan TV. Bayan ta ƙarasa wajensu ta ɗan durƙusa kaɗan a jikin sofa tace, “Mama, barka da warhaka.” Matar ta juyo, sai sannan ta sake fuskantarta tace, “Yauwa.” Ta ce, “Ina wuni Mama, fatan na same ku lafiya?” Tace, “Lafiya ƙalau. Ashe kina tafe?” Ta ce, “Eh Mama, dama ina so nazo amma saboda school yasa komai sai a hankali.” Tace, “Ai nasan struggles ɗin final year, balle ma yanzu da kike da aure, not like before da kike off camp da zama. Sai dai kawai Allah yasa a gama lafiya, shine addu’ar.” Tace, “Ameen, nagode Mama.” Matar dake ma Mama pedicure ce ta ɗago kai tace, “Sannu da zuwa Hajiya.” Zahra na murmushi tace, “Nagode, ina wuni?” Tace, “Lafiya ƙalau.” Daga haka suka yi shiru. Mama sai kallon Zahra take yi wanda yasa ta zama uncomfortable. Ta saci kallon Mama suka haɗa ido sai tace, “Mama ga abincin da na kawo miki, nakai dining ne?” Tace, “Har da wahala haka ke da baki da lokaci yanzu? Toh nagode Zahra, Allah yayi albarka. Ɗauki ki kai min dining ɗin.” Ta miƙe a hankali ta ɗauka ta wuce dining ta ajiye. Bayan ta dawo parlorn taga gaba ɗaya hankalin Mama na kan waya. A hankali tace, “Mama bari na tafi, dama ina da school ne shine nace bari na biya ta nan.” Tace, “Ayyah, toh nagode.” Daga haka ta mata sallama ta fita. Sosai taji wani relief. Bayan ta hau kan titi tana tuki, tunanin direction ɗin da za ta yi ta fara. Kawai tayi deciding ta koma gida. Taji ko ta koma school ba lallai bane ta iya gane komai. Bayan ta isa gida tayi parking ta sauka ta wuce ciki. A main parlorn na nan ƙasa kawai ta zauna. Ta ɗauki wayarta tayi dialing numbern sa. Ji tayi kawai ta kira duk da tasan ba wai sun tashi bane, amma zai iya zama sun tashi sallah. Sai kuma ta ajiye wayar nata. A haka bacci mai nauyi ya ɗauke ta. Can a cikin baccinta taji ana knocking na ƙofar parlorn. Da sauri ta miƙe ta kalli ƙarfe biyu da rabi. Wani murmushi tayi ganin yau yazo gida. Da sauri tayi bakin ƙofar ta buɗe. Tana buɗewa taga Ya Umar ne. Kasa magana ma tayi. Ya sakar mata murmushi ya kai hannunsa fusakarta kamar zai taɓa mata ido yace, “Ya haka? Ko baki son gani na ne?” Murmushi tayi ta rungume shi, yayi saurin janye ta. Tace, “Nayi mana Yaya, kawai murna ne yasa kaga na kasa magana.” Ta ja hannunsa suka shiga parlorn. Ya zauna a kan kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, ita kuma ta wuce kitchen ta ɗauko masa ruwa da snacks ta ajiye a gabansa. Ta ce, “Ya Umar me za ka ci?” Yace, “A’a, a ƙoshe nake fa.” Tace, “Ya gida? Ya jikin Abbah na? Ya kuma Mami da Mummy na?” Yayi dariya yace, “Shine sai duk kin jero min wannan tambayar lokaci guda Baby?” Murmushi kawai tayi. Shi dai kallonta kawai yake yi. Wannan shagwaɓan babu. Ya ce, “Duk lafiyarsu ƙalau.” Tayi shiru tana kallon wani waje, shi kuma studying ɗinta yake yi. Can ya ce, “Baby...” Ta juya ta kalleshi da murmushi a fuskarta tace, “Ina Antyn na?” Yace, “She’s fine. Baby meke damunki?” Ta ware ido tace, “Wai wani abu ke damuna?” Ya ce, “Ban sani ba, ina tambayarki kina tambayata.” Sai data ɗan tsorata ganin yadda lokaci guda ya canza tone ɗinsa, dan ba kasafai ransa ke ɓaci ba. Ta sauke idonta ƙasa tace, “Babu komai fa Yaya, kawai stress ɗin school ne.” Yace, “School ɗin da kika fara fita jiya shine ya saka miki duk wani irin canjin da kika zama tun farkon auren nan ko?” Tayi shiru tana kallon wani waje. Ya ɗan sassauta muryarsa yace, “Don’t hide it from me Baby, ki faɗa min gaskiya akwai wani abu dake damunki ne?” Ta girgiza masa kai. Yace, “Toh damuwar ta mecece?” Tace, “Yaya bana cikin damuwa fa.” Wani kallo ya watsa mata yace, “Shikenan Allah yasa. Ba zan saka miki magana a bakinki ba, amma kiyi tunani sosai, kar ki yarda wani abu ya kashe mana ke. Duk abin dake damunki ki tausaya mana ki faɗa min, ko da kuwa a gida ba zasu ji ba.” Ta gyada kai sai kuma tace, “Amma Ya Umar meyasa kace ina damuwa?” Dariya yayi yace, “Zahra tun kina ƙarama nake tare da ke. Babu wani halinki da ban sani ba, babu wani walwalarki da kuma akasin hakan da ban sani ba. Yadda kika zo gida ranan da yadda mijinki ma yazo, and the way you both ignored each other, ya tabbatar min akwai wani abu. Amma zan baki space, nima bana fatan ya zama akwai matsala. Sai dai yanzu babban abin da ya tsaya min a rai shine yadda kika rame, kika yi wani iri har abin tausayi.” Ta kasa cewa komai. Ya miƙe tsaye yace, “Kina buƙatar wani abu ne?” Ta girgiza masa kai tace, “A’a.” Yace, “Sure?” Sai kuma tayi dariya tace, “Sai dai idan za ka ƙara min wani abu a account ɗina, ba zan ƙi ba.” Yayi dariya yace, “Alright toh, idan na nutsu zuwa anjima zaki ji ni.” Tace, “Nagode Yaya.” Ya juya zai fita, tayi saurin cewa, “Yaya baka sa komai a bakinka ba fa?” Yace, “I’m full.” Tace, “Tohm Yaya, ya maganar Firdausi ne?” Sai sannan ya juyo yana kallonta yace, “Ban gane ba?” Ta ce, “Yaya wallahi she’s so nice, kuma tana da kyau. Baka ga yadda Abbah da su Mummy ke yaba mata ba? Please ka so ta, Allah suna wahala.” Yace, “Zahra! So fa ba’a masa dole. Za dai muyi magana anjima.” Buɗe ƙofar aka yi, duk suka juya suna kallonsa. Haka ya shigo parlorn kamar wani boss. Wani kallo shi da Ya Umar suka ma juna sannan ya ɗauke kai ya nufi hanyar stairs, shi kuma Ya Umar ya wuce ya fita. Zahra tayi tagumi. A hankali tace, “Wannan wani kalan mutum ne? At least ko magana ba zai yi wa Ya Umar ba?” Ta miƙe itama zata wuce sama ɗakinta. Bata ji zata yarda su haɗu da shi ba. A corridor suka haɗu. Wani kallo ya mata yace, “Ke ya kike kawo min gardawa cikin gida?” Tace, “Kila baka gani, Ya Umar ɗin ne gardi?” Yace, “Idan ba gardi bane mace ne shi ɗin?” Tace, “Amma kar ka manta cewa Ya Umar shine mutum na farko daya fara accepting ɗinka. Sannan shine ya fara supporting ɗina akan aurenka. Idan za ka canza min halinka bai kamata ka nuna masa ba. Hakan zai saka masa shakku kamar muna samun matsala ne.” Wani dariya yayi yace, “This should be the first and last time da zan sake ganin wannan mutumin a gidan nan.” Sosai ya bata mamaki. Ta ja baya da sauri tace, “What? Yayan nawa?” “Toh ai kuwa idan har kanwarsa tana cikin gidan nan da aure dole yazo.” Yace, “Shikenan, ya ci gaba da zuwa zaku sha mamaki.” Daga haka ya wuce ta ya sauka ƙasa. “Ya Allah...” ta furta da ƙarfi. Ta wuce ɗakinta. Da ba dan baccin da yake ɗaukanta kwanakin nan ba ba tare da shiri ba, ji take da jininta zai hau saboda tunani da damuwa. Can yamma ta fita compound tana kallon flowers dake wajen, amma a baɗini tunaninta baya tare da ita. Wayarta ce ta fara ringing. Ganin Firdausi yasa ta ɗaga ta kai kunne. Firdausi tace, “Gani a cikin gidan ki, ki zo ki buɗe min.” “Toh,” ta amsa mata sannan ta kashe wayar ta koma wajen main entrance. Tana ƙarasa wajen taga Firdausi. Rungume ta tayi tace, “Har an tashi a school?” Ta ce, “Eh fa.” Shiga parlorn suka yi. Firdausi tace, “Ban so ba da baki zo school yau ba.” Tace, “Sorry, bana jin zan iya ne” Tace, “Kin je gidan nasu ne?” Tace, “Eh, kuma Maman taji daɗi.” Tace, “Good. Ita zaki fara siya kafin ki gane kansa.” Wani dogon ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kalli Firdausi tace, “Firdausi ya zama ke kaɗai nake faɗawa magana dan na samu salama. Dan Allah ki riƙe min wannan amanar. Ko da wasa kar ki faɗa ma wani, duk da nasan halinki.” Tace, “Haba Zahra, ai faɗan sirrinki tamkar nawa ne.” Tace, “Nagode.” Sai tayi shiru tana kallonta, can ta ci gaba. “Firdausi, inaga Ibrahim yana neman mata.” Haka taji maganar ya dake ta. Tace, “Ban gane ba? Wannan wani irin magana ne Zahra? A’a no, kar ki fara kawo irin wannan zargin a zamantakewar aurenku saboda hakan zai zama mabuɗin mutuwar aurenku.” Dariya kawai Zahra tayi tace, “Kin san da safe yau an kira shi, na ɗauka kuma mace naji tana magana.” Nan ta faɗawa Firdausi yadda abin ya faru. Ba kaɗan ba Firdausi ta jijjiga da jin maganar. Tace, “Kuma kin masa magana akai?” Tace, “Me zan ce masa bayan na faɗa miki reaction ɗinsa? Nace miki ko ɗan ɗarr yaji saboda na ɗauka amma ko a kulansa, har da cewa hakan shine maganin masu ɗaukan wayar miji. Can you imagine?” Firdausi tace, “Zahra akwai aiki a gabanki sosai. Dole sai kin tashi kin tsaya. Bacci ba naki bane yanzu. Ki dukufa sallahr dare da miƙawa Ubangiji kukanki, dan shine kaɗai zai share miki hawaye. Ni ma zan taya ki da addu’a.” Zahra tace, “In Shaa Allah. Baki san yadda nake ji ba. Firdausi kin fi kowa sanin ina da kishi, amma ace na faɗa irin wannan halin ina tsoron kar na aikata laifin da zanyi dana sani.” Firdausi tace, “Calm down please, kar ki aikata komai. Amma kuma naga Zahra tunda har abin yazo haka, anya ba zaki sake gyara ba? Kiyi haƙuri da abin da zan faɗa, ko dai ba yadda yake buƙata yake samu daga gare ki ba?” Zahra tace, “Ina zan sani Firdausi? Toh idan gyara ne please ki haɗa ni da wanda zasu min gyara. Kinga dazu ai yazo har haɗu da Ya Umar, amma ko minti arba’in bai yi ba ya sake fita. Ni da ganin sa kuma sai asuba.” Tace, “Ya tabbata Zahra gyara zamu sake miki.” Tace, “Ki taimaka min please.” Buɗe ƙofar aka yi wanda yasa dukansu suka juya zuwa ga ƙofar... #Farashin Izzah #Jiddatulkhayr writes #08110615256 *FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes Young talented writers association (YOTA) Book 1 Chapter 7 Shigowa yayi kamar wanda bai san rahama ba a fuskarsa. Ko dan Firdausi bakuwa bai sa ya sassauta fuskar tasa ba. Haka ya shigo kamar wanda ba zai taka kasa ba. Firdausi ta miƙe tsaye tana kallon Zahra tace, “Zahra bari na tafi kawai.” Zahra ta riƙe hannunta haɗi da zaunar da ita tace, “Ke kuma kawai sai ki wani tashi kice zaki tafi bayan muna kan magana?” Wani banzan kallo Khalil ya watsa mata, sai da ya zo dab da ita sannan yace, “Ke wacece wannan?” Wani kallo Zahra ta watsa masa tace, “Firdausi ce, yau zaka ce baka santa ba?” Firdausi kam murmushi take yi tace, “Sannu da zuwa, ina wuni Ya Ibrahim.” Ta kare maganar tana ɗaukan jakkarta. Ko amsa mata bai yi ba, still yana kallon cikin idon Zahra yace, “Bana son kina tara min mutane a cikin gida. Ya kamata ki sani nan ba dandali bane.” Zahra ta miƙe zata yi magana amma Firdausi tayi saurin hana ta, sannan ta juya ta fita. Tuni ya juya ya fara hawa stairs, ita kuma ta fara binsa a baya tace, “Khalil wai wannan wani irin hali ne ka tsiro da shi? Abin naka ya fara yawa. Tun ya tashi akaina ya koma kan Yaya na, yanzu har kawaye na basu tsira ba. Ba zaka yi abin da at least mutane ba zasu zage ka ba? Gaskiya I'm tired of your bad attitude.” Ya juya yana mata wani shegen kallo yace, “Okay, tunda kin gaji it's fine, zaki iya kwasan kayanki ki koma gidan ku.” Mutuwar tsaye Zahra tayi a inda take tana kallon bayansa daya cigaba da hawa stairs har ya gama hayewa. “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...” kawai ta iya furtawa. Kukan ma da take son yi taji ba zata iya ba. Kawai ta juya ta wuce ɗakinta. A hankali ta zauna bakin gado tana sake narrating abin daya faru. Ita har sannan kamar a mafarki take ji. Me ta ma Khalil haka mai zafi? Yanzu abin nasa ya fara yawa. Kifa kanta tayi wasu hawaye masu zafi suka zubo bayan ta tuna da abin da bata kaunar tunawa a rayuwarta. Da daddare tana zaune a parlorn sama taji karar shigowarsa, kuma dama tana tunanin tun ɗazu daya zo bai fita ba sai sallah. Ita dai idonta na kan TV amma bata san me guda ɗaya ake yi ba. Haka ya shigo ta gabanta ya wuce zuwa ɗakinsa. Ta ɗaga ido ta bishi da kallo. Can ya sake fitowa ya shigo ya zauna a hannun kujerar dake opposite ɗin nata. Kai tsaye yace, “Zan yi tafiya gobe In Shaa Allah. Ba zan dawo ba sai bayan sati ɗaya. Wani aiki ne ya taso min shine zan tafi India.” Tace, “Kai kaɗai zaka tafi ba tare da ni ba? Why not na shirya mana tunda sati ɗaya ne kawai zaka yi?” Wani kallo ya watsa mata yace, “Idan da ke zan tafi ni ba zan sani bane ko ba zan faɗa miki bane? Tunda kinga ban ce tare zamu tafi ba, ki sani cewa wannan tafiyar ta wajen aiki ce.” Ta sauke idanunta kasa ta kasa cewa komai. Ya miƙe zai tafi tace, “Ina bukatar kuɗi toh” Wani irin juyowa yayi yana kallonta yace, “Shi Yayan naki ba zai iya baki bane?” Tsabar ɓacin rai Zahra bata san sanda tace, “Saboda Yayan nawa nake aure shiyasa kullum zan tambayesa kuɗi ai?” Yace, “Ke kika sani. Ni yanzu tafiya ce a gabana. Kayan abinci kuma babu wanda babu a cikin gidan nan, dan haka wannan wasan da kika saba da kuɗi zaki dakata da shi.” Ta miƙe tsaye tana kallonsa tace, “Ai ba haka na saba rayuwa a gidanmu ba.” Yace, “Ai ke ma kika ce gidan ku. Kinga nan ai ba gidan ku bane.” Tace, “Wai Ibrahim ka manta sanda ka zo gidanmu kana roƙon a baka ni ne? Ka manta sanda kake roƙona don Allah na baka soyayyata? Ka manta sanda kake min alƙawuran zaka kula da ni ka bani dukkan farin ciki? Ka manta sanda kace ba zan taɓa buƙatar wani abu na rasa a gidan ka ba? Amma yanzu ina guda ɗaya a cikin waɗannan alƙawuran da ka cika? Ka tausaya min, kaji tsoron Allah. Ko hakkin alƙawari zai iya bin ka.” Juyawa yayi ba tare daya ce mata uffan ba. Ita ma ta wuce nata ɗakin tana jin yadda zuciyarta ke ƙuna. Bayan ta gama shirin bacci zata kwanta kenan taga alert na 1 million. Ganin sunan tayi dan duk tunaninta daga Khalil ne, amma sai taga akasin haka, daga Ya Umar ne. Kawai taji hawaye. Ashe naka ne ba zai taɓa gajiyawa da kai ba. Yau take jin dama bata yi wannan auren ba. A hankali tasa hannu tayi dialing numbern Ya Umar. Yana ɗagawa abu na farko daya fara furtawa, “Baby kiyi haƙuri da little abin dana baki. Ina expecting kuɗina cikin week ɗin nan zaki sake jina.” Tace, “Thank you so much Yaya. A'a wannan ba little bane. Allah saka.” Yace, “Ameen. Good night.” Daga haka ya katse. Tana son basa hakuri amma tana tsorom ko yana cikin mutane, tayi deciding zuwa gida da kanya Kiran Firdausi tayi. Tana ɗagawa bata barta tayi magana ba tace, “Please Firdausi kiyi haƙuri. Ni kaina bansan ashe haka Khalil yake ba.” Firdausi tace, “Ba komai, amma tabbas abin ya fara bani tsoro. Sai kace ba mu bane muka zo ranan harda tsokarmu, sai kace ba mu bane yake roka mu taya sa samun ki. Ya Khalil dana sani yana fita da mu outing, har restaurant a school tare da mu, wai shine zai min haka? Tabbas yau na ƙara tsorata da maza. Amma please ki kwantar da hankalinki.” Zahra tace, “Gobe zai yi tafiya. Please ki zo ina so muyi magana.” Firdausi tace, “No, it's better mu haɗu a school tunda zaki shigo.” Tace, “Toh shikenan. Ki ƙara haƙuri please.” Tace, “Ba komai, sai da safe.” Firdausi na kashe kiran ta kalli Mama tace, “Mama da gaske Zahra tausayi take bani.” Ta kare maganar tana share hawayen daya zubo mata. Mama tace, “Itace ta kira yanzu?” Firdausi tace, “Eh. Mama kuma kin san Zahra kwata-kwata bata gane mai sonta na gaskiya. Kin san yanayin rayuwar data taso, bata san wani abu wai shi wahala ba. Shiyasa yanzu take bani tausayi. Ni damuwata kar taje ta saka ma kanta hawan jini ne.” Mama tace, “Idan abin nasa yayi yawa ta samu iyayensa farko kafin ta fara magana a gida. Amma yanzu ki bata shawarar ta same shi lokacin da yake cikin farin ciki ta tambayesa me ta aikata masa. Idan ma ya ƙi cewa komai ta basa haƙuri jikinsa zai yi sanyi.” Firdausi tayi murmushi tace, “Mama baki ga yadda yayi min bane ɗazu? Ashe haka yayi yiwa Yayanta Umar?” Mama tace, “Ikon Allah, aure tun bai tafi ko'ina ba? Toh ko dama ɗan iska ne ba'a sani ba.” Firdausi tace, “Shiyasa tun farko bamu son sa, amma ganin tana son sa kuma ba mu zamu zauna da shi ba shiyasa muka ja bakinmu muka yi shiru.” Duk shiru suka yi. Firdausi ta ɗaura, “Mama baki ga yadda Zahra ta koma ba? Mace mai son kwalliya da ado amma gaba ɗaya yanzu babu wannan vibes ɗin tare da ita.” Mama tace, “In Shaa Allah ko dan kyawawan halayenta Allah ba zai barta cikin wannan damuwar ba. Tunda ita mutum ce mai son cire mutane a damuwa, wannan jarabawarta ce. Allah shiryesa shi kuma.” Ta amsa da, “Ameen.” Wasa gaske har ƙarfe uku bacci ya gagara ɗaukan Zahra. Ta miƙe zaune ta wuce toilet. Alwala tayi ta fito tayi raka'a biyu. Bayan ta sallame, ta daɗe tana addu'a. Daga ƙarshe ta ɗauki Qur'ani ta fara karatu. A haka har aka yi sallar Asuba. Bayan ta idar ne, data kwanta nan da nan bacci ya kwashe ta. Wajen ƙarfe 8:40am ta farka. Data miƙe taji wani irin jiri yana shirin ɗibarta, da sauri ta dafe bango ta zauna. Ta daɗe tana zaune a wajen, can daya yi sauƙi ta miƙe ta wuce toilet. Brush tayi, tayi wanka sannan ta fito tasa kaya ta wuce dining. Cornflakes kawai tasha dan bata jin zata iya girki. Already ma tasan tayi late before ta tafi. Tana gama sha ta kai cup ɗin kitchen ta wanke sannan taje ta ɗauki school bag ɗinta tare da keyn motar. Da ƙyar ta tada motar don yadda take ji a jikinta. Bata son ta zauna a gida tunani ya addabeta, da ba zata school ba. Parking motarta tayi a bakin department sannan ta sauka ta wuce ciki. Tun daga yadda ta kalli wajen babu mutane sosai tasan cewa sun fara lectures. Ta shiga ta back door. Bayan 3 hours lectures suka gama. Suhaima, Asiya da Firdausi suka ƙaraso inda take dan a baya ta zauna. Asiya tace, “SubhanAllah, amma baki da lafiya ne Zahra?” Murmushi ta mata kawai. Suhaima tace, “Ko ɗan Baba ne ya fara baki wahala tun yanzu?” Tace, “Wai ku ɗauka kuka yi ciki gareni? Lallai baku shirya ba ma.” Class rep ne ya ƙaraso wajenta yana mata kirari. Tayi murmushi tace, “Kai dai Class Rep ba'a rasa ka da tsokana.” Yace, “Ba haka bane Hajjaju. Nace ko zamu je ki kalli practical ɗinki ne? An gama cire result yanzu saura miki chapter 5 a project. Ina gama haɗawa zan turo miki sai ki bawa supervisor ɗinki ya duba miki, idan da gyara mu gyara.” Tayi murmushi tace, “Class Rep bana jin daɗi. Duk yadda kayi yayi dai-dai. Nagode sosai. Opay ne ko First Bank?” Yana murmushi yace, “Opay ne Hajiya.” Kai ta gyaɗa masa. Ya juya ya fita yana godiya. Shiga mobile app ɗinta tayi, nan take ta masa transfer ɗin 50k sannan ta jefa wayar cikin jaka ta ɗago tana kallonsu tace, “Ya muke ciki yanzu?” Suhaima tace, “an gama lectures na yau fa, dan kamar Prof ne kawai yace zai yi lectures yau.” Ta miƙe tace, “Firdausi ko zamu wuce off camp kafin mu tafi gida? Ko da akwai abin da zaki yi ne a gidan yanzu?” Tace, “Nope, mu tafi mana.” Haka suka fita dukkansu direct wajen motarta suka nufa. Daga nan ta jasu zuwa University Villa, wannan gidan sai 'ya'yan wane da wane suke kama wa. Nan Zahra take kama musu ita da friends ɗinta tun suna 100 level. Shiga cikin estate ɗin tayi da motar har dab da room ɗinsu sannan tayi parking. Duk suka sauka. Asiya ta buɗe musu ƙofa duk suka shiga cikin ɗakin Zahra tayi murmushi tace, “Wai rabona da nan har na manta.” Dariya suka yi. Ta wuce ta kwanta kan gado. Suhaima tace, “Zahra me zaki ci sai mu dafa?” Tace, “Anything please.” Firdausi sai kallonta take yi, musamman idanunta wanda kallo ɗaya zaka mata kasan ko kuka tayi ko rashin bacci. Tana kwanciya nan da nan bacci ya kwashe ta. Can wajen Azahar ta farka, nan ma sanadiyyar kiran wayarta da ake yi ne. Ta ɗaga taga Abbah ne. Da murmushi a bakinta tace, “Abba na.” Yace, “Na'am Baby na, duk da ma Baby ta manta da Babanta.” Dariya tayi tace, “Abba ba haka bane fa. Ba zaka gane bane Abba amma kullum kana raina.” Yace, “School ɗin ne?” Tace, “Eh Abba, yanzu haka ma ina school.” Yace, “Allah taimaka. Bari sai kin koma gida, just concentrate.” Tace, “Thank you.” Yana kashewa ta miƙe ta wuce toilet. Bayan ta fito da alwala zata yi sallah Asiya tace, “Na saka miki abinci yanzu kafin ki idar?” Tace, “Eh, amma ki haɗa da tea please.” Suhaima tace, “Sai dai kije ki saya sugar a waje dan ƙarshen na sha ɗazu” Asiya tace, “Alright.” Kafin ta idar da sallah har Asiya ta shigo ta saka mata abincin. Bayan nan basu wani daɗe ba suka tafi. A hanya Firdausi tace, “How far, yayi tafiyar ne?” Tace, “Ina zan san masa? Dan wulakanci ko sallama bai min ba.” Firdausi tace, “Call him now. Ki tambaya ya isa lafiya dan wannan hakki ne a kanki.” Tace, “Okay.” Kiran sa tayi while tana tuki. Yana fara ringing ya ɗaga. Tace, “Noory...” Yace, “Uhum.” Ta ce, “Tafiya ba sallama?” Yace, “Naga kamar ranki a bace yake ai jiya.” Tace, “Amma at least koma menene na tafi idan ka faɗa min ai da daɗi.” Yace, “Enough! Bana son wannan unnecessary drama naki.” Tayi shiru kamar ba zata ce komai ba sai kuma tace, “Ka isa lafiya?” Yace, “Lafiya kalau.” Tace, “Toh Ma Shaa Allah, dama na kira naji ne.” Yace, “Alright.” Daga haka ta kashe kiran ta juya ta kalli Firdausi. Firdausi tace, “Zahra no matter what kar ki daina sauke haƙƙinki a kansa. Ki ci gaba da haka. Kinga yanzu shine right time da zaki yi gyara kafin ya zo.” Tace, “Kinsan Allah ko saboda mugun halinsa ji nake kamar na fasa. Yanzu ya fara fita min a rai wallahi.” Firdausi ta gagara cewa komai. Ta wuce taje tayi dropping ɗinta a ƙofar gidansu sannan ta ja motar zuwa nasu gidan. Bayan tayi parking ta sauka sai ga Ya Umar ya fito zai fita Batoul a bayansa. Tayi saurin riƙe masa hannu tace, “Yaya minti ɗaya mana.” Yana kallonta da kamar ba zai ce komai ba sai ya matsa gefe, ita ma ta bishi. Tace, “Ya sorry da abin daya faru. Ba zan iya ce maka sorry a waya bane amma dan Allah kayi haƙuri.” Ya ɗaga mata gira ɗaya yace, “Akwai abin daya faru ne?” Tace, “Haba Yaya, abin daya faru jiya mana, kai da Khalil.” Yayi murmushi yace, “Zahra ban san yaushe kika fara ɓoye min abu ba. Ni nasan kin san cewa nasan kina cikin damuwa amma kika zaɓi shiru. Yes, it's good kin fara haƙuri, amma ki sani ba zan yarda wannan banzan ya cutar da ke ba. Ki je kiyi tunani if you're ready to voice it out. Ni damuwata bana son ganin wannan damuwar a tattare da ke Zahra. I can't take it anymore, naga wani yana cutar mana da ke.” Ta sauke idanunta kasa tace, “Nagode. Sai kun dawo naga fita zaku yi da Ya Batoul.” Daga haka ta fara tafiya tace, “Ya Batoul ina wuni?” Ba tare data ɗaga kanta daga wayar da take daddannawa ba tace, “Lafiya.” #Jiddatulkhayr writes #08110615256 *FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes Young talented writers association (YOTA) Book 1 Chapter 8 Zahra ta wuce ciki. Tana shiga babu kowa a main parlor, hakan yasa ta wuce sama direct zuwa ɗakin Mami. Da sallama ta shiga, ta samu Mami na zaune tana ordern kaya a waya. Da gudu taje ta rungume ta. Mami tayi saurin kashe kiran ta juyo tana kallon Zahra da mamaki, tace, “Zahra me haka kamar wata mai ciwon kanjamo?” Zahra tayi dariyar yake tace, “Mummy kanjamo kuma? Me kika gani?” Hararanta tayi tace, “Kina ganin kanki kuwa? Ko shi mijin naki baya faɗa miki yadda kika koma ne?” Tace, “Mami rashin lafiyan nan ne yasa nake ramewa amma, zan samu sauki ai.” Daga haka ta haye kan gadon ta kwanta ta bawa Mami baya. Hawaye ne suka fara zuba daga idanun nata, a haka bacci ya kwashe ta. Can wajen Magrib Mami na tare da Abbah tace, “Ai Zahra tana nan fa, tana dai bacci ne amma raman ta ya fara damuna.” Yace, “Ko dai wani abu ne yake damunta?” Tace, “Ina zan sani? Amma ba ranar Mummynsu tace ciki ne gare ta ba, kuma dukkan alamu ya nuna hakan ne. Ko zata dawo gida ne tayi laulayin cikin ne har ya girma?” Abbah ya ajiye wayan hannunsa yana kallonta with full attention yace, “Amma kin tabbatar babu abin da yake damunta? Ko da dazu muke waya babu wannan vibes ɗin Baby da na santa da shi. Ke ce uwa, ke ce zaki saka ta a gaba ki matsa mata ta faɗa miki abin dake damunta.” Sauke ajiyar zuciya tayi tace, “Na barta tana bacci ne tun ɗazu, bari zan taso ta tunda Magrib ma yayi. Zaka ga yadda ta sake lalacewa.” Miƙewa tayi tace, “Ka tafi sallah bari na haura sama na tashe ta.” Da “toh” ya amsa mata, ita kuma ta wuce sama. Mami na shiga ɗakin ta samu ta tashi, tace, “Yauwa kin tashi ko? Ki shiga kiyi alwala, Magrib yayi. Idan Abbanku ya dawo daga sallah sai ki sauka ki tafi wajensa.” Kai ta gyada ma Mami, daga haka ta wuce toilet, Mami kuma ta sauka kasa. Can sai ga Mami ta sake buɗe ɗakin ta shigo da tray a hannunta na fruit, ta ajiye mata a gabanta tace, “Ki sha kafin Abbanku ya dawo.” Ta kalli Mami tace, “Nagode.” Apple kawai ta iya sha, ta ajiye bowl ɗin a gefe sannan ta miƙe ta fita a ɗakin. A parlorn ta haɗu da Mummy tana zaune ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tana kaɗawa, kuma ga waya a manne a kunnenta. Zahra tace, “Mummy ina wuni.” Tace, “Yaushe kika zo?” Tace, “Ɗazu ne.” Tace, “Okay, ya mai gidan ki?” Tace, “Lafiya. Bari na tafi wajen Abbah.” Daga haka ta fita zuwa parlorn Abbah. Ta shiga da sallama, yana zaune yana kallon news. Jin sallamarta yasa ya ɗaga kai ya buɗe mata hannayensa alamar ta ƙaraso jikinsa. Karasawa tayi ta shige jikinsa, kawai taji wani kuka ya taho mata tunawa da memories ɗin baya. Yace, “Baby ashe kina gidan nan?” Tace, “Eh Abbah, dazu da muka yi waya shine naji nazo gida na ganka saboda ka yarda ban manta da kai ba.” Murmushi yayi yana shafa kanta yace, “Nasan baki manta ni ba, wasa nake wa Baby na.” Tashi tayi a jikinsa ta zauna gefen ƙafafunsa. Yace, “Ya maganar project ɗinki?” Tace, “Abbah ai yaron yayi nisa da min, har result na practical ya gama cirewa.” Yace, “Ma Shaa Allah. Idan ya gama miki gaba ɗaya ki turomin da numbern sa tare da account details ɗin sa.” Tace, “Alright Abba.” Daga haka suka fara hira sosai, har aka kira Isha’i suna tare. Mami ce tare da Ya Umar suka shigo. Tace, “Wai har yanzu kuna nan?” Dariya tayi tace, “Ina tare da Abbahna muna hirarmu.” Ya Umar ya zauna akan kujera yana kallonta yace, “Sannu ‘yar Abbahnta.” Dariya tayi tace, “Kuma ‘yar Mamin ta, Mummy da kuma Ya Umar ɗinta.” Abbah ya miƙe yace, “Ahtoh.” Sai kuma ya mayar da kallonsa kan Ya Umar yace, “Tashi mu tafi masallaci.” Daga haka suka fita. Mami kuma ta wuce cikin bedroom ɗinsa ta soma gyara wa haɗi da sa turaren wuta, Zahra ta wuce sama. Can wajajen 8:30pm bayan su Abbah sun dawo daga sallar da suka fita tun ɗazu, duk dining suka nufa da niyyar yin dinner. Mami ta leka ɗakinta tace, “Baby tashi, su Abbanku sun dawo zamu yi dinner.” Daga haka Mami ta juya ta fita. Kamar Zahra tace mata a’a ita ta koshi dan bata kaunar a mata zancen ta koma gida, amma ganin Mami ta tafi kawai ta miƙe. Kuma ganin Mami bata mata maganar komawa gida ba yasa ta sake sakin jiki. Fita tayi ta sauka kasa, duk sun cika a dining. A hankali take tafiya. Abbah ya ɗaga kai da mamaki yana kallonta har ta isa. Kujerar dake gefensa ta zauna akai. Yace, “Baby me kike yi har yanzu baki koma gidan ki ba?” Ta sauke kai ta kalli Mami. Mummy ma tace, “Ai kuwa dare yayi ace har yanzu baki koma ba. Ni da banga ki ba ma na ɗauka ai kin koma ne.” Ya Umar shi dai kallonta yake. A hankali ta ce, “Abbah yayi tafiya ne, kuma baya gida. Shiyasa zan kwana anan kawai. Yanzu dare ma ya riga da yayi, gidan zai bani tsoro.” Tun data zauna a wajen ko da wasa Batoul bata ko ɗaga kai ta kalle ta ba. Abbah yace, “Baby ko dai akwai matsala ne?” Kawai ya ciro wayansa a aljihu ya fara dannawa. Mami tace, “Ba dai kiransa zaka yi ba dan confirming?” Bai tanka mata ba, yayi dialing numbern Ibrahim. Yana fara ringing ya ɗaga. Da girmamawa ya fara gaishe da Abbah, Abbah ya amsa masa cike da fara’a. Wayan kuma a handsfree yake. Yace, “Kana ina ne?” Yace, “Ai Abbah nayi tafiya ne yau ɗin nan. Wani aiki ne ya taso min shine na tafi. Akwai wani abu ne?” Yace, “A’a no, dama Fatima ce ba tazo gida ba?” Yace, “Eh tace min zata je ai.” Wani mamaki ne ya kusa kashe Zahra. Yace, “Toh dama shine take son zata kwana. Tace ai kayi tafiya ma, na ɗauka kawai dan tana son kwanan ne yasa ta faɗa haka.” Yace, “Aa no ai zata iya kwana Abba, dan nima ba yanzu zan dawo ba sai nayi 7 days. Nan Dubai na tafi, a barta ta kwana idan har sai na dawo ne ma it’s fine, zata iya zama a gida.” Abbah yace, “Tohm shikenan, Allah dawo da kai lafiya.” Daga haka suka yi sallama. Ita dai Mummy idonta akan Zahra yake. Bayan sun gama dinner Zahra ta tashi ta wuce ɗaki. Har ga Allah Ibrahim ya bata mamaki fiye da yadda take tunani. Tana shiga ɗaki ko kayan jikinta bata cire ba, tana kwanciya bacci ya ɗauke ta. Can Mami ta shiga ɗakinta taga anan Zahra ta kwanta. Nan ta kunna mata AC, ta gyara ɗakin sannan ta kashe wuta ta fita ta ja mata ƙofar. Washegari da safe bayan Zahra ta gama shiri ta sauka tayi wa Mami da Mummy sallama sannan ta wuce ɗakin Abbah. Ganin kamar baya nan yasa ta juya ta fita kawai. Haka kawai take jin kaso 40 na damuwarta ya tafi saboda zaman data yi a gida. Compound ta nufa ta shiga motarta. Direct gidansu Firdausi ta nufa ta ɗauke ta, daga nan suka kama tafiya. Zahra ta ɗan kalle ta tace, “Kinsan a gida na kwana jiya?” Firdausi tace, “Haba dai, kuma Abba ya yarda?” Tace, “Ya yarda mana. Toh tsaya kiji yadda abin ya kasance.” Nan tayi mata narrating ɗin duk abin daya faru. Tace, “Lallai Ibrahim kin san abin da yake yi kamar da gangan ne ko?” Zahra tace, “Shi ya sani, dan ina dab da faɗa wa Ya Umar kuma duk hukuncin daya ɗauka haka zan bi, dan idan na biye ta soyayya tabbas Firdausi mutuwa zanyi.” Firdausi ta ce, “Allah ma ya kiyaye ba abin da zai faru. Komai zai daidaita.” “Hmm,” kawai Zahra tace. Firdausi tace, “Yauwa yau zamu tafi gidan matan nan mai gyara.” Zahra tayi shiru Tace, “Mu je yau. Yanzu yadda za’a yi idan muka tashi a lectures sai mu wuce gaba ɗaya.” Zahra tace, “Ni kam har naji ya fita min a rai gyaran, kamar na haƙura wallahi.” Firdausi tace, “Ai baki ma isa ba Zahra, gyara ya zama dole ki yi In Shaa Allah.” A haka har suka isa school. Basu suka tashi a lectures ba sai can yamma. A gajiye suka fito a lecturer hall ɗin. Asiya ta ce, “Kai wannan Prof ɗin yadda kasan zai cinye mu yau ɗin nan haka yaki sake mu kamar maye.” Suhaima tace, “Maybe ku kun fahimta ma, nikam tun ina fahimtar sa har na daina.” Duk suka kwashe da dariya. Asiya tace, “Zahra yi dropping ɗinmu mana, dan yau bana jin zan iya takawa saboda wahalar zama.” Zahra tace, “Kuzo mu tafi yanzu toh, dan akwai inda zani kar dare yayi mana.” Daga haka duk suka yi wajen motarta. Bayan ta ajiye su Asiya, suka hau kan titi. Ta ɗan juya ta kalli Firdausi tace, “Amma Firdausi zamu wajen can kuwa? Ni fa nagaji.” Tace, “Ai zuwa ya zama dole Zahra. Yaushe zaki koma gidan ki?” Ta ce, “Gobe nake ji, amma yau ma ba iya komawa zanyi ba.” Daga haka Firdausi take nuna mata inda zasu bi, a haka suka kama hanyar shagon matar. Tafiya sosai suka yi dan matar ba cikin gari take ba. Sun zo bin wani roundabout, wani mota ta wuce sai da Zahra ta kusa dukan roundabout ɗin. Firdausi tace, “SubhanAllah Zahra lafiya?” Zahra kam ta gagara bata amsa, kawai ta figi motar da gudu gudun kar motar data gani ya tsere mata. Firdausi ta ce, “Zahra talk to me, me yake faruwa ne?” Amma ina, Zahra sai zufa take yi ga uban shaking da hannunta ke yi. Motar ne taga yasha wani kwana, itama kwanan ta sha ta fara tafiya a hankali ganin kamar motar ta parka a ƙofar wani gida. Da sauri Zahra tayi parking nata motar ta sauka. Duk yadda Firdausi take mata magana amma hankalinta baya jikinta. Da sauri itama ta sauka ta fara ma Zahra magana meanwhile tana bin bayanta. Zahra ta ɓuya bayan wani wall tana kallonsa ya fito a cikin motarsa, ya zaga ya buɗe mata nata side ɗin sannan ya riƙe hannunta ta sauka yana mata murmushi, ita kuma sai shigewa jikinsa take yi. Zahra ta fara ganin dishi-dishi. Gagara tsayuwa tayi, hakan yasa ta fito gaba ɗaya ta nufi inda suke. Firdausi kanta sai data yi mutuwar tsaye ganin Ibrahim da wata a tsaye, looking happy together. Zahra ta fara nufarsa duk da kalan duhun da take gani ga uban juyawar da garin yake yi mata. Bata kai ga karasawa ba tayi wani kalan ƙara ta zube ƙasa sumammiya. Da gudu Firdausi tayi kanta. Ihunta yasa Ibrahim da matar ɗaga kai dan ganin menene. Ai yana ganin fuskar Firdausi bai kai ga ganin fuskar Zahra ba ya fara bari, dan sai yanzu yayi recalling cewa muryarta ne. Da gudu yayi kanta, zai ɗaga ta Firdausi tace, “Bana bukatar taimakon ka.” Ɗaga Zahra da zata yi sai ga jini yana bin ƙafarta. Daga Firdausi har Ibrahim Khalil suka sake ruɗewa. Motar Zahra ya nufa da ita da sauri, itama tana binsa a baya. Riƙe ta Firdausi tayi bayan ya ajiye Zahra, ya zaga driver seat ya shiga, a mugun gudu ya tada motar ya jata. Firdausi sai kuka take tana ta jijjiga Zahra dan ba kaɗan ba ta rude. Sai da suka yi ɗan tafiya kafin suka isa asibiti. Suna zuwa aka karɓi Zahra sai emergency room. Likitoci sun fi biyar akanta. Khalil ya jingina kansa sa wall yana kallon sama, ga shi gari an fara kiran Magrib. Firdausi ta miƙe ta fara tafiya, yayi saurin shan gabanta yace, “Ina zaki Firdausi?” Tace, “Ina ruwanka da ni?” Yace, “Please kar ki bari wani ya san abin daya faru. Ki taimaka min ki rufa min asiri. Zamu iya sorting wannan matsalar, yanzu fatanmu ta samu sauki ne.” Firdausi tace, “Ka matsa min a gaba Malam. Kaji nace zan faɗi wani abu ne?” Yace, “Please Firdausi.” Buɗe ɗakin da take ciki aka yi, hakan yasa duk suka nufi wajen ɗakin nata. Ibrahim na kallon likitan daya fito yace, “Dan Allah ya take? Meya same ta?” Likitan yace, “Kai waye ɗinta ne?” Yace, “Mijinta ne.” Kawai likitan ya juya ya bar sa a tsaye... #08110615256 https://chat.whatsapp.com/IjVCBxrVY1Z4pH5IZhshvA?mode=gi_t *FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes Young talented writers association (YOTA) Book 1 Chapter 9 Wayan hannun Firdausi ne ya fara ringing, ta ɗaga kai ta kalli Ibrahim ta ce “Sai ka kira iyayenta ka faɗa musu inda muke yanzu, dan Mahaifiyarta ce ke kira. Ni kuma ban san me zan faɗa mata ba idan na ɗauka.” Ba tare da ya kalle ta ba ya ce, “Kawai ki kashe wayarki.” Da mamaki ta juyo tana kallonsa. Zama yayi ya dafe kansa, sai kuma ya ciro wayarsa wanda tun ɗazu yake jin vibrating ɗinta a aljihun wandonsa. Unlocking yayi ya ga mai kiran, wani tsaki yaja sannan ya kashe wayar gaba ɗaya. Wani likita ne ya fito daga cikin ɗakin, da sauri Ibrahim ya miƙe yana kallonsa. “Ku ne kuka kawo ta?” likitan ya tambaya. Da sauri Ibrahim ya ce, “Yes, mu ne.” Likitan ya ce, “Follow me.” Duk suka bi bayansa. Suna shiga office ɗin, Ibrahim ya ɗaga kai yana kallon Firdausi ya ce, “Zaki iya bamu waje? Wannan kamar privacy ɗinmu ne.” Wani kallo ta masa sannan ta ce “Sannu ko! ka san kai ne silar shigarta cikin wannan matsalar, ni kuma babu inda zan tafi, dan ina da tabbacin na fi ka kusanci da Zahra.” Likitan ya ɗaga kai yana kallonsu ya ce “Idan baku shirya magana cikin nutsuwa ba ku fita, ina da aikin yi.” Hakan yasa Ibrahim ya ɗauke kai ba tare da ya sake kula Firdausi ba. Likitan ya gyara zamansa sannan ya ce, “Patient ɗin ta shiga cikin shock sosai, hakan ne ya jawo bleeding ɗin da kuka gani. Amma Alhamdulillah, mun samu nasarar tsaida zubar jinin.” Duk suka zuba masa ido suna sauraro. Ya ci gaba da cewa, “Amma akwai wani abu da ya kamata ku sani. Tana da ciki, kuma cikin yana da rauni sosai a yanzu. Ba’a so ta shiga wani stress ko tashin hankali daga yanzu. Haka kuma ku guji duk wani abu da zai dagula mata rai, saboda cikin zai iya zubewa idan ba a kula ba.” Nan Ibrahim ya ɗaga kai da sauri yana kallonsa ya ce, “Dama tana da ciki ne?” Likitan ya ce, “Eh. Cikin yana da kimanin days ashirin da shida a jikinta.” Firdausi ta rufe idanunta tana fatan Ibrahim ɗin nan, abin da ya faru ya sa ya canza. Fita tayi ta barsa a office ɗin. Kiran Mama tayi. “Mama sorry, kin kira ban kula ba ma.” Mama ta ce, “Yau kuma shiru baki ce min zaki koma makaranta da zama ba, kina ina ne?” Ta ce, “Mama ina kan Zahra ne a asibiti. Mun taso ne daga makaranta, shine ta yi ɓari.” Mama ta ce, “Allah sarki, Allah ya bata lafiya toh. Sai da safe.” Daga haka ta kashe kiran. Dialing number ɗin Mami tayi. Mami na ɗagawa ta ce, “Firdausi ina ta kiran ki shiru? Na kira su Asiya sun ce basu tare da Zahra, amma na kira ki. Maman ki ma tace baki dawo gida ba. Lafiya kuwa? Kuma ina kuke?” A hankali Firdausi ta ce, “Mami, Zahra ce ba lafiya, muna asibiti ne.” A rude Mami ta ce, “SubhanAllah! Firdausi meke damun Zahra na? Faɗa min wani asibiti kuke yanzu?” Firdausi ta ce, “Mami please, calm down. Kar ki daga hankalinki. In Shaa Allah Zahra zata samu sauƙi. Bari na turo miki sunan asibitin yanzu.” “In Shaa Allah,” Mami ta ce. Daga haka ta kashe kiran ta tura mata sunan asibitin. Zama tayi ta lumshe idanunta. Da sauri Mami ta sauka ƙasa, kana ganinta zaka san a birkice take. A daidai ƙofar shiga parlour, Mami ta haɗu da Ya Umar. Ya ce, “Mami lafiya?” Ta ce, “Ina Abbanku?” Ya ce, “Yana ciki.” Shiga tayi, kamar zai bar wajen sai kuma ya ji hankalinsa ya kasa kwanciya, hakan yasa ya bi Mami a baya. Mami na kallon Abbah ta ce, “Abban yara, ashe Zahra ba lafiya? Tana asibiti yanzu haka.” Abbah ya miƙe da sauri ya ce, “Wa ya gaya miki?” Ta ce, “Yanzu nayi waya da kawarta Firdausi, ita ta faɗa min. Dama hankalina bai kwanta ba tun da nasan anan take, kuma naga bata dawo ba.” Ya Umar ya ce, “Wani asibiti take? Bari na tafi.” Abbah ya ce, “A’a, mu tafi dukkanmu kawai.” Daga haka Mami ta wuce domin ɗauko hijab ɗinta. A cikin compound ɗin asibitin, Ya Umar yayi parking motarsa. Duk suka sauka, sai ga Firdausi ta fito sakamakon kiran da Ya Umar yayi mata. Ta ƙarasa wajensu ta durƙusa ta ce, “Abbah sannu da zuwa, ina wuni.” Ya ce, “Lafiya lau Firdausi.” Ta gaishe da Mami sannan ta koma kan Ya Umar. Daga haka suka juya zuwa ciki. Duk da ba’a bari a shiga ba, haka aka buɗe ƙofar ɗakin suka shiga. Ibrahim ya sauke kansa ƙasa da ganin su. Wani kallo mai wuyar fassaruwa Ya Umar ya masa, kuma ya ƙi ɗauke idanunsa daga kansa, dan yana ƙoƙarin karantar yanayinsa ne. Ibrahim ya ɗan duƙa ya gaishe da Abbah sannan ya gaishe da Mami, daga haka ya fita daga ɗakin. Wani banzan kallo Ya Umar ya bishi da shi. Ƙarasa kan Zahra dake kwance suka yi. Sun daɗe suna kallonta babu mai cewa uffan, sannan suka koma suka zauna. Mami ta ce, “Firdausi, me ya same ta ne?” Firdausi ta sauke kanta ƙasa, ta rasa ta ina zata fara bayani. A hankali ta soma cewa, “Mun fito daga evening lectures ne. Duk mun gaji, muka fito tare da Zahra saboda zata sauke ni a gida, tunda yanzu tace min tana gida ne. Shine muka biya zamu sayi abu, daga saukarta ke da wuya sai ta yanke jiki ta faɗi. Nan take kuma ta fara bleeding.” Mami ta ce, “Cikin jikinta ya zube ne?” Kai ta girgiza ta ce, “A’a bai zube ba, amma likitocin sun bada ka’idojin da za’a bi. Ba’a son a ɗaga mata hankali, haka kuma ba’a son stress yana samunta.” Mami tayi shiru. Abbah ya miƙe ya ce, “Toh amma me ya kawo yanke jikin nata? Ina likitan da ya duba ta? I need to see him, dan bana son wani abu ya samu baby na.” Duk maganar lokaci guda yayi ta, meanwhile yana fita daga ɗakin. Mami ta miƙe ta bishi. Suma suka fita daga ɗakin. Can sai ga su Mami sun dawo. Ya Umar na kallonsu ya ce, “Mami bari na kai ku gida, idan yaso ni na zauna anan, kuma kinga ga kawarta.” Abbah ya ce, “A’a, ba zan iya barin nan ba.” Mami ta ce, “Kar ka damu, kaje ka huta son.” Ya san halinsu, tun da suka fara faɗin hakan ya san ba lalle bane su yarda su tafi. Yana kallon Firdausi ya ce, “Toh bari na maida ke gida.” Ba dan taso ba, amma tasan suna buƙatar zama kusa da ‘yarsu yasa kawai ta ce, “Tohm.” Sallama tayi wa su Mami. Abbah yayi ta sa mata albarka tare da godiya. Fita tayi yana binta a baya. Bayan sun shiga mota ya tada motar. Ya ɗan kalleta sannan ya maida hankalinsa kan tuƙi ya ce, “Mun gode ko.” Ta ce, “Haba, ai duk abin da zan ma Zahra wallahi yi ma kai ne, dan Zahra tafi yar uwa a wajena.” Bai ce mata komai ba har ya kaita ƙofar gidansu. Parking yayi a ƙofar gidan. Ta kai hannu zata buɗe ƙofar kawai sai yayi locking. Ta ɗaga kai tana kallonsa. Bata rai yayi yana kallon wani waje ya ce, “Faɗa min gaskiyar abin da ya faru da Zahra.” Ta ce, “Ya Umar ai abin da na faɗa ɗazu shine gaskiya.” Wani tsawa ya daka mata har sai da ta firgita ya ce, “Zaki faɗa min ne ko yaya?” Ba shiri balle tayi tunani, nan take ta faɗa masa abin da ya faru har ya jawo Zahra ta fara bleeding. Wani murmushi yayi yana kallon waje. Ta ce, “Zan iya sauka?” Ba tare da ya kalle ta ba ya ce, “Sauka.” Ta ce, “Tohm ai baka buɗe ƙofar ba.” Ya ce, “Zan buɗe, amma sai kin faɗa min me Zahra take ɓoyewa.” Ta ce, “Dan Allah kar ka sa na faɗi abin da Zahra zata ji haushi na, Ya Umar. Is better ka tambaye ta.” Kawai sai taji ya kunna motar suka fara tafiya. Ta juyo a razane tana kallonsa ta ce, “Ina zaka kai ni?” Ya ce, “Baki shirya faɗin gaskiyar bane ko?” Ta ce, “Allah zan faɗa.” Yayi parking gefen wani gida ya ce, “Ina sauraren ki.” A hankali ta ce, “Kawai iya abin da na sani shine, Ya Ibrahim ya canzawa Zahra. Kuma duk wata soyayyarsa yanzu bata samun ta kamar da. Toh abin gaskiya yana damunta. In fact, har ta fara complain cewa soyayyarsa ta ragu a zuciyarta yanzu.” Ta sauke numfashi sannan ta ci gaba da cewa, “Ni kuma gani nake kamar yana using ɗinta ne. Dan idan ka kalli posts ɗinsa, kamar wanda suke zaune lafiya kalau babu matsala. Ranar gala night na promotion ɗinsa ma, babu wanda zai yarda suna samun matsala.” Juya kan motar yayi ya koma ƙofar gidansu. Yayi unlocking motar ya ce, “Sauka. Mun gode.” Ta ce, “Sai da safe, nagode.” Daga haka ta shiga cikin gidansu. Washegari da safe, bayan Abbah ya tafi masallaci, Mami na zaune tana lazumi taji motsin Zahra. Da sauri ta miƙe tana kallonta. Zahra ta buɗe idanunta haɗi da dafe ƙirjinta saboda nawi daya mats. Mami ta ƙarasa kanta da sauri ta ce, “Meke damunki Zahra?” Kai ta girgiza wa Mami. Mami ta ce, “Sannu ko?” Ta ce da raunanniyar murya, “Mami… nan ina ne?” Mami ta ce, “Ki huta Zahra, ki daina wannan surutun kar ciwon kai ya kamaki.” Ta girgiza mata kai ta ce, “A’a Mami, ina ne nan?” Mami tana shafa kanta ta ce, “Asibiti ne Zahra.” Ta ce, “Ina Firdausi toh?” Mami ta ce, “Jiya da dare yayanki ya mayar da ita gida.” Tayi shiru kamar mai nazari. Hakan yasa Mami ta ce, “Kar ki damu, babu abin da ya samu cikin ki. Ki kwantar da hankalinki kinji ko?” Kallon Mami take da rashin fahimta ta ce, “Mami ban gane ba?” Buɗe ƙofar aka yi. Wata nurse ce ta shigo. Bayan ta gaishe da Mami ta ƙarasa kan Zahra. Bayan ta gama mata allurai ta bata wasu magani sannan ta juya ta fita. Mami zata yi magana sai ga su Abbah sun shigo. Ganin ta farka yasa ya ƙarasa wajenta ya rungume ta ya ce, “Sannu Baby.” Ta naɗe hannayenta a wuyansa ta ce da murya mai rauni, “Abbah…” Ya ce, “Don’t cry kinji ko?” Kai ta gyaɗa masa. Ya Umar kuwa kallon tausayi yake mata kawai. Abbah ya sake ta ya ce, “Sannu Baby.” Ta gyaɗa masa kai tana murmushi kaɗan. Ya miƙe ya ce, “Kin san yau zan je ganin likitana a Dubai, ina son na tafi gida dan shiryawa. Ga su Mamin ki anan kinji.” Kai ta gyaɗa masa ta ce, “Allah ya baka lafiya Abbah, ya kuma dawo da kai lafiya.” Ya ce, “Ameen.” Ta sauke idanunta ƙasa. Ya Umar ya ce, “Me kike so kiyi breakfast da shi?” Tayi shiru kamar mai nazari sai kuma ta ce, “Alale.” Bai kai ga rufe baki ba sai ga wayarsa ta fara ringing. Ya ɗaga ya kai kunne ya ce, “Da sauƙi Firdausi, gashi ma ta farka.” Can ɗayan ɓangaren Firdausi ta ce “Me zata ci?” Ya ce, “Ki barshi kar ki bama kanki wahala.” Sai kuma ya ɗan murmusa ya ce, “Toh.” Da alama Firdausi bata yarda ba, dan sai ya sake cewa, “Nasan kina son kiyi mata, amma ki huta.” Ganin suruntun Firdausi har ciwon kai ya fara saka masa yasa ya ce “Alale.” Daga haka ya kashe wayar ya saka a aljihunsa. Sallama aka yi haɗi da turo ƙofar ɗakin. Duk suka juya. Ibrahim ne ya shigo. Nan take Zahra ta ɗauke kanta gefe. Mami ta miƙe tana kallon Ya Umar ta ce, “Ka maida ni gida, ina son na mata breakfast da kaina.” Ibrahim ya duƙa ya gaishe da su Mami. Abbah ya ce, “Haa’an, kamar jiya naganka sai kuma daga baya ban sake ganinka ba.” Yana sosa kai ya ce, “Eh Abbah, ai ganin ku ne yasa na tafi.” Nan suka gaisa. Ya Umar kuwa wani irin kallo yake binsa da shi. Mami da Abbah suka juya suka fita. Ya Umar ma yayi kamar zai bisu. Da Zahra ta ɗaga kai ta ga daga ita sai Ibrahim ne a ɗakin, nan take ta ce, “Ka fita, bana son ganin ka.” Zai yi magana ta ce, “Wallahi zan maka ihu idan ka ce ba zaka fita ba. Bana ƙaunar ganin ka nace.” Ya Umar ne ya dawo cikin ɗakin, dama reaction ɗinta yake son gani. Tana kallonsa ta ce, “Yauwa Ya Umar, dan Allah ka zauna anan kar ka tafi.” Ya ce, “Ba tafiya zan yi ba.” Zama yayi ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kaɗawa haɗi da fara danna wayarsa. #08110615256 #Jiddatulkhayr *FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes Young talented writers association (YOTA) Book 1 Chapter 10 Wani kallo Ibrahim ya bi Ya Umar da shi, sannan ya ɗauke kansa ya mayar da kallonsa kan Zahra. Ita ma wani kallon take masa kafin ta ɗauke kanta. Haka kawai sai taji wani kuka ya ƙwace mata, ta juya kanta gefe ta fara shessheƙa. A hankali Ibrahim ya juya ya fita daga ɗakin. Ya Umar ya ɗaga kai ya kalli ƙofar da ya fita, sannan ya ja ƙaramin tsaki. Ɗan kallonta yayi sannan ya miƙe haɗi da saka wayarsa a aljihu. A hankali ya taka har inda take kwance, ya ɗago ta zaune yace “Baby, kukan me kuma?” Ta girgiza masa kai. Yace, “Please stop it. Bana son ki sake saka wa kanki ciwo, and stop thinking about everything right now. We can talk about it later when you feel better.” Ta gyaɗa masa kai sannan tace, “Firdausi tace zata zo ne?” Ya gyada mata kai yace, “Tana hanya.” Tace, “Wayata fa?” Yace, “Yana wajen Mami” Shiru tayi sannan tace, “Yaya, ka kira min ita.” Miƙa mata wayar yayi, sai kuma tace, “Bari na kira Mami kawai, dama fish pepper soup nake so.” Yace, “Alright, ki faɗa wa Mami masu aiki su girka miki.” Daga nan ta kira Mami. Mami na tsaye a parlour bayan ta miƙa wa Abbah cup of tea. Har ta gaji da mitar Mummy. Mummy tace, “Tabbas da ace kun ɗauke ni wani abu a gidan nan, ba za’a ce wai har Zahra ta kwana a asibiti ban sani ba.” Abbah ya miƙe yace, “Enough, Khadija. Baki san kiyi haƙuri bane? Dare ne fa lokacin da muka sani. Ganin kar a dame ki yasa aka ce a bari sai da safe. Amma yanzu kina ta juya maganar nan tana zama kamar wani babban abu.” Mummy ta girgiza kai tace, “Ai ba zaka taɓa ganin abin da nake gani bane. Mutane a waje su gani suce ni ce mai mugun hali. Yanzu da ace ana ɗauka na a matsayin mahaifiyarta, koman dare ai da za’a faɗa min. Ita ɗin ma ba da dare aka faɗa mata ba. Amma shikenan, ba komai.” Abbah yayi wa Mami magana da ido akan ta koma ciki, hakan yasa ta juya ta fita. Tana shiga ɗakinta sai wayarta ta fara ringing. Dagawa tayi sai taga Ya Umar ne.... Sosai Ya Umar ya ɗauke wa Zahra kai daga duk wani tunani, domin bai bata wani space na yin tunani ba, sai hira yake mata, and she really enjoyed being around him. Buɗe ƙofar ɗakin aka yi, sai ga Firdausi da Mama. Zahra tace, “Laaa, wai Mama! Ke da baki da lafiya, Firdausi ta kama ta ɗago ki?” Mama na dariya tace, “Haba Fatima, ai ni na warke. Sannu da jiki. Ya jikin naki?” Tace, “Da sauƙi.” Firdausi ta ajiye kulan akan drawer kusa da Zahra tace, “Ya jikin naki dai Zahra?” Tace, “Da sauƙi Alhamdulillah.” Firdausi tace, “Ma sha Allah. Na saka miki ne yanzu?” Zahra ta gyada mata kai. Ya Umar ya gaishe da Mama sannan yana kallon Firdausi yace, “Yanzu zaku koma ne?” Tace, “A’a, zuwa ɗan anjima.” Yace, “Bari naje na dawo toh.” Daga haka ya fita. Anty Jiddah ce ta shigo babban parlourn nasu da sallama da zimmar ta wuce wajen Mami. Haɗuwa tayi da Mummy zaune tana danna waya. Tace, “Ah Anty Khadija, ina wuninmu?” Ba tare data ɗaga kai ba tace, “Lafiya.” Abin ya bata mamaki matuƙa. Kawai sai ta fasa maganar da zata yi ta wuce sama zuwa ɗakin Mami. Babu kowa a ciki, hakan yasa ta zauna akan sofa haɗi da cire hijabin jikinta. Sai ga shi an buɗe ƙofar ɗakin, Mami ce ta shigo. Tace, “Ah Jiddah, kin ƙaraso ne?” Tace, “Eh Anty.” Mami ta ƙarasa shiga ta ajiye abin hannunta tace, “Ai ina ɗakin Abban su ne. Dake yau ne tafiyar tasu, shine nake ɗan masa tattare-tattare.” Anty Jiddah tace, “Hmmm… ai naga mutumiyar tawa kamar zata fashe a parlour. Ina gaishe ta ma tana wani ɗaɗɗaga min hanci. Ke ma kinsan ni, daga haka kawai sai nayi tahowa na.” Mami tace, “Ai da kin tura mata a niyarta Jiddah. Kin san tun jiya take masifar ba’a faɗa mata Zahra ba lafiya ba.” Wani kallo Anty Jiddah tayi tace, “Dama expecting gaya mata za’a yi? Eh lallai, sannun ta ma. Komai naki tana son sani, amma abunta ko da wasa ba zaki taɓa sa ni ba.” Mami tace, “Ina zuwa bari naje naga ko ya fito sai mu tafi asibitin tare, tunda shi daga can zai wuce.” Buɗe ƙofar ɗakin asibitin aka yi, duk suka maida kallonsu bakin ƙofar. Mami ce suka shiga tare da Anty Jiddah. Zahra bata san sanda murmushi ya suɓuce mata ba tace, “My Anty Jidddsss, oyoyo!” Anty Jiddah ta ƙaraso tayi hugging ɗinta tace, “Sannu my love. Ashe mun kusa rasa ɗan baba” Zahra ta turo baki tace ƙasa-kasa “Haba Anty, kina ganin Abbah fa yana nan” Tace, “Ya bleeding ɗin? Ya tsaya?” Kai ta gyada mata. Anty Jiddah tace, “Mu dai ki kula mana da jikanmu.” Firdausi ta gaishe su, Abbah ya mata ya gajiyarta na jiya, suka ce babu komai. Abbah ya ƙarasa kan Zahra, murmushi ta masa tace, “Abbah ka shirya ne?” Yace, “Na shirya Baby.” Anty Jiddah ta miƙe ta basu waje. Shafa kanta yayi yace, “Zan wuce Baby. Zan miki transfer na wani abu, ko zaki ji sha’awar wani abin ci then use the money.” Tace, “Nagode Abbah. Allah ya kai ka lafiya.” Da “Ameen” ya amsa, sannan ya miƙe yace, “Ina Ibrahim ne? Ban gansa ba fa.” Tayi shiru tana kallon Anty Jiddah. Daga haka ya juya ya fita. Maman Firdausi ma tayi mata fatan samun sauƙi sannan suka tafi. A ɗakin sai Mami da Anty Jiddah kawai suka rage. Buɗe ɗakin aka yi sai ga Mama da Ibrahim. Nan take Zahra tayi dana-sanin rashin kwanciyar da bata yi ba, ai da tuni tayi pretending ɗin bacci. Shigowa ciki sukayi, aka fara gaggaisawa. Mama tace, “Allah sarki daughter, ashe abin da ya faru kenan.” Zahra taji wani takaici ya tokare mata maƙogaro. Ta sauke idanunta tace, “Ina wuni.” Mama tace, “Lafiya daughter. Sannu, Allah ya baki lafiya.” A hankali tace, “Ameen.” Khalil ya ƙaraso jikin gadon ya ɗan duƙa yace, “Sannu Zahra, ya ƙarfin jikin?” Yadda kasan bango yake wa magana haka Zahra tayi masa. Sai ma ɗan sace kallonsu da tayi, zai kuma sake magana tace, “Dan Allah ka tashi a kaina, zan iya maka ihu babu ruwana da akwai mutane akanmu.” Yace, “Zahra, wannan issue ɗin za mu iya solving ɗinsa a gida. Ki daina stressing kanki da magana kina asibiti.” Tace, “Okay, ka ci gaba da zuwa wajen kowa kuwa zai ji maganar da yake bakina.” Daga haka ta kwanta abinta, ko kaɗan bata damu da ko za’a gane reaction ɗinta ba. Ibrahim ya furzar da iska a bakinsa. Mamakin Zahra sosai ya fara yi. Ya miƙe ya koma can gefe ya tsaya. Anty Jiddah taga kamar a takure yake, ga Mama da Mami sai hira suke sama-sama, ba abin ta ce ko a basu waje ba. Ya Umar ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo. Suna haɗa ido wani kallo ya wurga masa, shima nan ya masa irin kallon. Mama ta miƙe tace, “Bari zan tafi wani waje ne. Ibrahim zaka kai ni, idan yaso sai ka dawo kan matarka, tunda dai yanzu kana hutu a wajen aiki.” Zahra ta ɗago kai jin abin da Mama tace. Da sauri ta rufe ido kar Mama tace zata mata magana. Duk Ya Umar yana lura da ita. Ya gaishe da Mama sannan ita kuma tayi wa su Mami sallama suka fita. Ya Umar ya ƙaraso wajen Zahra ya duƙa. Ta buɗe ido haɗi da miƙewa zaune, yace “Baby, inje in nema miki sallama tunda jikin ya ɗan sauƙa?” Tace, “Yes please.” Dama ita bata buƙatar sake dawowar Ibrahim, kuma dama plan ɗin Ya Umar kenan, yana son idan Ibrahim ya dawo ya tarar babu kowa. Wata nurse ce ta shigo. Ya ɗaga kai yace, “Yauwa Nurse, nace ba za’a sallame mu bane?” Tace, “Za’a sallame ku, amma fa gaskiya idan da so samu ne a barta anan tana bed rest, dan ba’a buƙatar tana wahala ko shiga wani yanayi.” Yace, “Mun sani, dan munyi magana da likitan da ya fara dubata.” Tace, “Toh ku sake zuwa ya muku bayani sannan ya rubuta muku sallama.” Nufar ƙofar yayi, ita kuwa ta tsaya tana tambayar Zahra ko akwai wani abu dake damunta yanzu. Bayan Ya Umar yayi parking a cikin compound ɗinsu, wani murmushin gefen baki yayi. Yanzu yaji wani irin relief ganinsa a gida, dan baya son Ibrahim ya rigasa karɓo mata sallama. Sauka yayi ya zaga ya buɗe wa Mami ƙofa ta sauka, Anty Jiddah ma saukan tayi. Yana riƙe da Zahra suka fara taku a hankali zuwa ciki. A haka har su Mami suka rigasu shiga, dan a hankali yake tafiya da ita. Bayan ya kaita ɗaki ya wuce zuwa ɗakin Mummy. Yana shiga ya same ta tana waya. Ganinsa yasa ta yanke kiran tace, “Lafiya kazo ka saka ni a gaba?” Yace, “Mummy me yasa kike haka ne? Yanzu fisabilillah har aka sallamo yarinyar nan ace baki je kin dubota ba?” Mummy tace, “Toh sannu ubana. Nace sannu ubana. Ai komai nayi a gidan nan sai kace zaka min gyara. Ban taɓa yin abu daidai ba a idanunka, amma uwar da ta tsuguna ta haife ka ai ita kam bata da laifi.” Yace, “Mummy yanzu kuma wannan wani magana ne? Naga duk abin nan bai kai kiyi fushi ba. Ai da sai ki tafi dan 'yar, ba dan uwarta ba.” Ta ce, “Toh ban ga dama ba ubana, nace ban ga dama ba. Tashi ka fita ka bani waje.” Yace, “Dama zan ce miki ne an sallameta.” Tace, “Naji, Zan shiga na duba ta.” Ya miƙe ya nufi ƙofa yace, “A huta lafiya.” Yana fita ya ja mata ƙofar ɗakin. Sosai Zahra ta samu bacci, dan har sai da su Asiya suka zo bata ma sani ba, har suka tafi kuma bata farka ba. Mummy ma ta shiga ta dubata fiye da sau uku amma duk tana bacci. Ya Umar kuwa, kafarsa a ɗakin tafi a irga, amma ganin tana bacci sosai ya saka yaji daɗi matuƙa. Ibrahim ne yayi parking motarsa a compound ɗin asibitin. Ganin babu motar gidansu Zahra yasa yayi murmushi, dan ya fahimci Ya Umar baya nan kenan. Sauka yayi ya ƙarasa ciki. Shi kaɗai yasan abin da yake planning a ransa. Yana zuwa ya buɗe ƙofar ɗakin, wasu fuskoki biyu ya gani zaune, da alama ma hira suke yi. Ya kalli kan gadon sai yaga wani yaro ne aka kwantar akan gadon Zahra. Yace, “Sorry, na ɗauka wannan ɗakin ne, ashe nayi ɓata.” Fita yayi ya nufi ɗakin gaba, amma to his surprise, shi ma ba ɗakin bane. Ya sake dawowa ya buɗe ɗakin farkon yace, “Dan Allah ina waɗanda suke ɗakin nan kafin yanzu?” Suka ce masa basu sani ba, dan ba’a daɗe da kwantar da su ba. Wani irin zufa ne ya fara keto masa. Da sauri ya sauka zuwa office ɗin likita. Shiga yayi ya tambayi patient ɗin ɗakin. Likitan yace, “A’a ai an sallame su.” Ya juya ya fita haɗi da dukan iska yace, “Lalle ne ma.” Sosai abin ya dake sa. Driving yake amma gaba ɗaya hankalinsa baya kan tuƙin. Can bayan Magrib, Anty Jiddah na tare da Zahra a parlourn Mami sai ga Ya Umar ya shigo. Ajiye mata leda yayi, kamshin naman da ke tashi ne ya bugi hancinta. Shikenan, ta miƙe da sauri. Tun kafin ta kai toilet ta fara kwarara amai. Nan take Ya Umar yayi dana-sanin sayowa. Ba kaɗan ba Zahra ta bashi tausayi. Tun daga wannan ranar Zahra ta kulla da laulayi. Ita duk zaton Mami, Zahra tayi magana da mijinta ne shi yasa take gida saboda laulayin, while bata san meke faruwa ba. Ibrahim yasha kiran Zahra amma wayarta kullum a kashe. Idan yazo gidan ma haka zai ƙarasa zamansa a waje, ko yayi aika a kirata bata fito wa. Ko da kuwa zai haɗu da Ya Umar, babu mai cewa ɗan uwansa komai. Ba kaɗan ba Ibrahim ya shiga damuwa, dan wajen sati guda kenan suna neman sulhu amma abin ya ci tura. Ga dukkan alamu kuma Abbah baya nan, hakan yasa yake tsoron zuwansa ace har lokacin Zahra tana gida. #Farashin Izzah #08110615256 *FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes Young talented writers association (YOTA) Book 1 Chapter 11 Ya Umar ne ya shigo parlorn Mami, hannunsa riƙe da bowl ɗin gauta. Zama yayi kusa da Zahra dake kwance a kan tiles ɗin parlorn yace, “Ya jikin?” Ta ɗago kai, sannan ta miƙe ta zauna a hankali tace, “Da sauƙi Yaya.” Miƙa mata bowl ɗin yayi, ta karɓa tace, “Nagode.” A hankali ta soma ci. Kamar ba zai ce komai ba sai yace, “Wani shawara kika yanke?” Ba tare da ta kalle shi ba tana cin abincin tace, “Shawarar me kenan Yaya?” Yace, “Akan mijinki.” Lokaci guda taji gautar ta fita mata a rai. Ta ajiye bowl ɗin tana kallonsa tace, “Yaya ban gane shawarar akan mijina ba?” Yace, “Zahra, ina tare da ke tun ranar da aka haife ki. Kina tunanin wai zaki iya ɓoye min wani abu ne?” Murmushin dole tayi tace, “Ai ban fahimce ka bane.” Yace, “Kenan bakuyi magana da Firdausi ba?” Da sauri ta ɗaga kai tana kallonsa da mamaki, amma a lokaci guda jikinta yayi sanyi. Duk da Firdausi bata gaya mata komai ba, tasan sunyi magana kenan. Tace, “Yaya me ta faɗa maka?” Yace, “Abin da kika sani.” Ta sake yin shiru, can kuma tace, “Yaya nima bansan tunanin me zan yi ba tukunna, shiyasa na kashe waya ta… ban san ma kai ka sani ba. Ka yi haƙuri da ɓoye maka da nayi.” Murmushi yayi yace, “I’m the one who should apologize, saboda na shiga abin da bai shafe ni ba.” Ta girgiza kai tace, “A’a Yaya, ai rayuwata ta shafe ka.” Yace, “Good… dama haka nake so ki sani.” A hankali tace, “Yaya yanzu me zaka ce?” Yace, “Abin da zaki ce shi zan ce.” Duk suka yi shiru. Sai kuma yace, “Kinason komawa ɗakinki ne?” Tayi shiru. Yace, “Talk to me.” A hankali tace, “Yaya ina so kafin na koma… at least ya san value ɗina. Ya yi nadama sannan ya min alkawarin ba zai sake min haka ba. Idan ya tsaɓa zan dawo gida.” Duk da Ya Umar bai so jin hakan daga bakinta ba, sai yayi murmushi ya miƙe yace, “Good. Shikenan, hakan ma it’s okay. Let’s see inda haƙurinsa zai kai shi. Ki cigaba da barin wayarki a kashe.” Tace, “But Abbah jibi zai dawo, me zance akan zaman da nake yi a gida?” Yace, “Saboda kina laulayi mana.” Kai ta gyaɗa masa. Daga haka ya fita, his mind filled with lots of thoughts. Sosai Zahra taji damuwa a ranta. Kullum cikin dare idan ta kunna wayarta sai ta ga countless messages from Ibrahim. Amma ko kaɗan bata ji a ranta cewa da gaske Ibrahim ya shirya canzawa ba. Miƙewa tayi ta wuce bedroom ɗin Mami. Tea yake sha a hankali, amma ko kaɗan bai taɓa abin dake cikin plate ɗin gabansa ba. Kamar ma bai san inda yake ba, gaba ɗaya hankalinsa baya jikinsa. Ta daɗe tana zaune tana kallonsa kafin takaici ya cika ta tace, “Wai kai Khalil, tunanin me kake yi haka ne? Abin cin gabanka ma ka kasa ci.” A ɗan razane ya juya, saboda bai san tana wajen ba. Ya sauke ajiyar zuciya yace, “Mama… babu komai.” Tace, “Yaushe zasu baka matarka ne?” Yace, “Ban sani ba.” Tace, “Ai kafi su ƙarfi akanta. Babu wanda yake da iko yanzu sama da kai. Idan kace kana son a dawo maka da matarka ai basu isa suce a’a ba. Just be a man mana. Kana buƙatar matarka, kuma suka ce a gida zata yi laulayi… ai kai ma zaka iya kula da ita.” A hankali yace, “Okay.” Miƙewa tsaye yayi saboda baya son dogon surutu. Tace, “Ina zaka?” Yace, “Zan koma gida.” Tace, “Abincin fa?” Yace, “Zan tafi da shi.” Daga haka ya ɗauki kulolin abincin yace, “Sai anjima.” Ta ce, “Toh, duk yadda ake ciki ka sanar dani.” Kai kawai ya gyaɗa mata. Bayan ya koma gida, yana trying Zahra’s number, luckily kiran ya shiga. Zahra kuwa, data saka sim ɗinta a ƙaramin waya saboda zata yi transfer ɗin kuɗi, sai taga kiran sa ya shigo. Kallo kawai ta tsaya yi har ya yanke. Wani kiran ya sake shigowa, ta sake bari ya yanke. Ganin da gaske Khalil ba zai barta tayi abin da zata yi ba, ita kuma bata son yin magana da shi, yasa kawai ta kashe wayar gaba ɗaya. Tana kallon mai aikinsu tace, “Dauko min ATM ɗina, zan tura miki wani account number sai a min transfer na 30k zuwa account ɗin.” “Tomm Hajiya.” Daga haka ta juya ta fita. Khalil kuwa ya sake kira, amma cikin mamaki yaji an kashe wayar. “What?!” ya furta a hankali, saboda ba ƙaramin mamaki hakan ya bashi ba. Duk messages da calls ɗin da yake mata bai taɓa samunta ba, amma wannan karon ya nuna masa cewa tana amfani da wayar ne, ganin kiransa ne yasa ta kashe ta. Lumshe idanunsa yayi. Ya rasa ta inda zai fara. Gashi baya son ace ya je wajen iyayenta su gane meke faruwa. Miƙewa yayi daga inda yake ya fita. Washegari Anty Jiddah tazo duba Zahra. Suna zaune a ɗakin Zahra na gidan. Anty Jiddah tace, “Yaushe zaki koma gidan ki ne?” Zahra ta turo baki tace, “Anty Jidss na warke ne toh?” Anty Jiddah tace, “Ai ke da warkewa sai kin haihu. Dan haka ki daina ce sai kin warke.” Zahra tace, “Toh naji… amma gaskiya not now. Dan shima ai baya nan.” A lokacin Mami ta buɗe ƙofar ɗakin ta shigo. Tana kallon Zahra tace, “Zahra ki sauko, kina da baƙo.” “Baƙo kuma Mami?” “Eh mana, anzo gaishe ki da jiki.” Da kyar ta miƙe ta ƙarasa wajen wardrobe ta ɗauki hijab ta saka. Daga haka Mami ta fita ta tsaya bakin ƙofa tana jiranta. Anty Jiddah tace, “Mun shiga uku Zahra. Ciki tun bai girma ba har kin fara riƙe baya da tafiyar masu ciki? Ni tsoro na ma kar kije ki fara posting a social media acc ɗinki” Dariya Zahra tayi tace, “Da gaske Anty Jidss kin manta wacece Zahra? Ai ba komai nake sawa a social media ba.” “Toh ni na sani ne?” ta faɗa tana dariya. Zahra ta nufi ƙofa tace, “Bari na dawo Anty.” Tana sauka ƙasa taji muryar Mami a kitchen. Ta ƙarasa wajen tace, “A ina baƙon yake?” Mami tace, “Je ki second parlor.” Har ta juya zata tafi sai kuma ta dawo tace, “Mami wani kalan baƙo ne?” Mami tace, “Idan kin je ai zaki gani.” Haka kawai taji zuciyarta ta fara bugawa. Ta ƙarasa bakin ƙofar parlorn ta tsaya na wasu seconds, kamar mai nazari. Sai kuma ta buɗe ƙofar a hankali ta shiga, bakinta ɗauke da sallama. Curtains ɗin parlorn a sauke suke saboda sanyin AC, bulb ɗin ɗakin kuma mara haske ne. Gashi bata ɗauko glass ɗinta ba, idanunta ma ba zasu nuna mata mutum sosai ba sai kamshin turare. Kai hannu tayi ta ƙara hasken ɗakin. Sai da idanunta suka sauka kansa sannan ta gane kamshin turarensa ne. Juyawa tayi zata fita ba tare data ce komai ba, amma cikin sauri ya riƙota yadda ba zata wahala ba. Bata san sanda ta daka masa tsawa ba tace, “Ka sake ni!” Yace, “No please Zahra, ki tsaya muyi magana mana.” Tace, “Ka sake ni kafin na maka ihu.” Da sauri ya ja ta ciki sannan ya rufe ƙofar parlorn, ya saka key ya cire. A ruɗe take kallonsa tace, “Wai me hakan ke nufi?” Gaba ɗaya ta tsorata. Yace, “Calm down Zahra, magana nake so muyi.” Tace, “Ka buɗe ƙofar idan kana son na saurare ka.” Yace, “It’s fine then, sai mu cigaba da zama a haka.” Wani kallo take masa, amma a lokaci guda tana kallon Khalil ɗinta da ta daɗe tana missing. Ba kaɗan ba ya zama calm. Yace, “Zahra kin dawo gida ba tare da izinina ba. Nayi ta kiranki baki ɗagawa. Gashi ko nazo baki fitowa… taya kike so mu solve issues ɗinmu a haka?” Wani dariyar takaici tayi tace, “You still have the guts to talk?” Ta cigaba da cewa, “Amma baka da kunya ko kaɗan Ibrahim. Ko ka manta abin da ka aikata ne sai na tuna maka?” Yace, “Please Zahra, mu bar wannan maganar anan. Duk abin da zai faru, idan muka koma gida sai muyi magana akai.” Wani dariya tayi tace, “Ka raina min hankali. Kana tunanin zan koma cikin kurkukun gidanka ne? Ko darajata baka sani ba balle ƙimata. Tausayi ma gaba ɗaya an cire maka a rai. Dan haka ni ba zan taɓa zama da fasiki ba.” “Enough, Zahra!” Yadda ya tsawa mata yasa tayi shiru na ɗan lokaci. Sai tace, “You see your life now? Ka zo kana min ihu a cikin gidanmu.” Yace, “I’m sorry Zahra… but don’t call me a fasiki again.” Tace, “Ƙarya nayi? Ka barni a gida bayan duk rashin kulawar da kayi min, ka kasa sauke hakkin kan ka, ka haɗa da ƙarya… amma ko kaɗan baka ji kunyar abin da kayi ba. Kuma a haka kake so na koma maka?” Ga mamakinta, sai Ibrahim ya durƙusa kan gwiwowinsa ya haɗe hannayensa yace, “Zahra ki tausaya min ki dawo gida. Na miki alkawari ba zan sake saka ki cikin takaici ko nadama ba. I’m very sorry. Nasan nayi kuskure, shiyasa nake nan ina neman gyara.” Zahra tayi shiru tana kallon wani waje. Ita kanta ta fara rasa me zata ce. Ganin yanayinta yasa ya sake riƙo hannayenta yace, “Zahra please… ki tausaya min. Zan canza. Ni kaina nasan ba hankali nake amfani dashi wajen yi miki haka ba. Ki yafe min.” Tace, “Ka buɗe min ƙofa.” Ya girgiza kai yace, “Ki bani amsa Zahra.” Tace, “Gaskiya bansan me zan ce maka ba. Ka yi magana da Ya Umar idan da gaske kana son na dawo.” Wani irin furzar da iska yayi yana hargitsa gashin kansa. A hankali yace, “Idan na samu amincewarsa shikenan ko?” Kai ta gyaɗa masa. Ya miƙe tsaye, ya sumbaci goshinta sannan ya durƙusa ya ɗaga hijab ɗinta da rigarta kadan yayi kissing cikin nata. Ita dai ta kasa cewa komai. Kamar mai raɗa yace, “Ka daina wahalar da mummy baby… be a good son.” A hankali Zahra ta sauke idanunta. Ya miƙe ya buɗe ƙofar yace, “Ki kira Mami ina son muyi sallama… amma ki dawo tare da ita.” Tace, “Gaskiya hawa da sauka yana bani wahala. Let me just call her.” Daga haka ta kira Mami ta sanar da ita cewa Ibrahim zai koma gida ne, yana son yi mata sallama. Ta buɗe curtains ɗin parlorn da ƙofar sannan ta koma ta zauna da kyar. Shi kuwa murmushi kawai yake mata, amma ta hana kanta kallon direction ɗinsa. Can sai ga Mami ta shigo da sallama a bakinta. Ya zame daga kan kujera ya zauna ƙasa yace, “Mami dama zan koma ne.” Tace, “Ayyah Ibrahim, toh ka gaishe da Mamanka ko?” “In shaa Allah.” Sai kuma yace, “Dama tace bai kamata na bar Zahra a gida ba saboda babu daɗi tayi laulayi ba a ɗakinta ba. Shine nace ai ban san al’adunku bane.” Zahra bata san sanda ta sake baki tana kallonsa cikin mamaki ba. Like seriously? Har wannan maganar ma ya iya haɗawa? Mami tace, “Ai nima da ba kuyi magana da ita akan ta zauna saboda laulayi ba, da tuni na maidata ɗakinta. Sai dai yanzu an bamu sharuɗɗa sosai akanta. Ko zata koma sai da mai aiki.” Yace, “Ba damuwa Mami, ai wannan ba wani abu bane.” Mami tace, “A’a anan ma za’a samu mata.” Duk maganar da Mami take babu fara’a a fuskarta. Amma Zahra kam, Ibrahim ya gama cika ta da mamaki. Mami ta miƙe tace, “Bayan aikin da aka ce ba’a so tayi, sannan ba’a son a daga mata hankali saboda komai can happen to the pregnancy.” Yace, “Eh In shaa Allah babu abin da zai faru Mami.” “Tohm yayi kyau.” Daga haka ta fita. Tana fita Zahra ta miƙe zata bi bayanta yace, “Zahra.” Ta juya a fusace kamar dama jira take tace, “Me na kiran sunana? Uwar me zan maka? Ga yadda muka yi magana shine zaka min haka?” Yace, “Nope Zahra, ai dole Mami tasan zaki koma. Shi yasa na mata magana.” Tace, “Toh ka sani, idan har baka samu Ya Umar ba babu inda zani. Ko Mami ta min magana ma zaka sha mamakin abin da zai fito daga bakina.” Ganin yadda ranta ya ɓaci yasa yace, “Kiyi haƙuri… zan yi masa magana Zahra. Anjima zan dawo na same shi kamar yadda kika buƙata.” Tace, “Better.” Daga haka ta fita ta bar masa wajen. #Jiddatulkyar writes #08110615256 *FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes Young talented writers association (YOTA) Book 1 Chapter 12 Sauke ajiyar zuciya Ibrahim yayi, daga haka ya fita shima. A compound suka haɗu da Ya Umar, shima waya ce a kunnensa yana magana. Ga mamakinsa, Ibrahim ya karaso wajensa. Shi kuwa yayi pretending kamar bai gansa ba, ya cigaba da wayarsa har ya haura staircase ɗin bakin main parlorn. Ibrahim kuwa ya juya ya fita. Ya Umar kasa ƙarasa shiga ciki yayi. Ya juya yana kallon Ibrahim ɗin. Duk da ba yau ya saba ganin Ibrahim yana zuwa gidan ba, amma wannan zuwan nasa ko kaɗan bai masa daɗi ba. Musamman yadda yaga ya zama calm sannan yana zuwa towards him cikin nutsuwa, gaba ɗaya abin ya ɗaure masa kai. Juyawa yayi ya shige ciki. Kamar zai hau sama wajen Mami sai kuma ya fasa ya wuce ɗakin Mummy. Anty Jiddah tace, “Toh ke kuma me aka miki ne kika canza tun da kika shigo?” Ta juya tace, “Babu komai fa Anty Jidss.” Tace, “Toh hirar tamu yanzu an fasa kenan?” Tace, “Anty bacci nake son yi.” Tace, “It’s okay, kiyi baccin ki. Amma koma mene ne kar ki sa abu a ranki. Kinji me aka ce miki a asibiti ko?” Kai ta gyaɗa mata, ta gyara kwanciyarta. Nan da nan Allah ya taimaka bacci ya kwashe ta. Can yamma, zuwan su Asiya ne yasa ta sauko ƙasa. Bayan sun gama hirarsu ta raka su har gate sannan ta dawo. Tana shiga parlorn taga Mummy da Batoul, da alama fita zasu yi. Zahra tace, “Mummy ina wuni?” Tace, “Lafiya lau. Ai na ɗauka kin tafi gidanki tunda tun safe ban ganki ba.” Zahra tace, “A’a.” Batoul tace, “Amma dama haka kawai ake zuwa gida ne idan ba matsala aka samu ba Zahra? Lafiya kam yanzu yaci ace kin warke.” Zahra tace, “Ai da saura. Kuma ai yana zuwa yana duba jikina kullum.” Batoul tace, “Uhmm toh Allah ya kyauta. Amma wannan wani irin jibge ne.” Zahra bata sake bi ta kanta ba, ta wuce sama abinta. Tana shiga ɗakin Mami, Mami ta ɗaga kai tana kallonta tace, “Yanzu kuma me ya haɗa ki da su Batoul?” Tace, “A’a wai tambaya take yi, amma tana gaya min magana ne.” Mami tace, “It’s okay, bana son magana. Da zan sauko ai, ina jin ta yasa na fasa.” Zahra tace, “Wallahi saboda Ya Umar ne nake ɗaga mata ƙafa, kar yace bana ji.” Mami tace, “A’a babu ruwanki da su, ki kyale su.” Zahra ta zauna bakin gado tace, “Mami masu aiki me zasu girka mana yau?” Mami tace, “Ai yanzu duk abin da kika ce shi za’a girka.” Tayi shiru kamar mai tunani sannan tace, “Toh Mami ni dai ayi mana saƙwara.” Mami tace, “Tohm shikenan, bari nayi musu magana.” Tace, “Yawwa Mami nagode.” Mami tace, “Toh yanzu sai yaushe zaki koma gidan ki tunda har mijinki ya buɗe baki yayi magana?” Zahra ta sauke kai ƙasa bata ce komai ba. Mami tace, “Ina miki magana kin yi shiru ko baki ji bane? Ai kinji me yasa nake miki magana. Ko baki ji yace har Mamarsa tace ya kamata ki koma gidanki bane?” A hankali tace, “Naji Mami… shi yasa nima bansan sanda zan koma ba tukuna. Bari idan munyi magana.” Mami tace, “Ai na ɗauka yau zaki bar min gida.” Nan take hawaye suka fara zubo mata tace, “Mami dan Allah ki daina min magana akan aure haka. Idan kina haka auren ba zai taɓa samun albarka ba. Ki tausaya min… ki kuma yafe min.” Nan take Mami taji Zahra ta bata tausayi matuƙa, ta tuna maganar likita. Ta rungume ta tace, “Sorry Zahra, ba wai baki nake miki ba. Kawai bana so ki samu matsala da mijinki da dangin mijinki ne. Shi yasa nake son ki dinga obeying abin da yake faɗa miki.” Zahra ta sauke idanunta ƙasa tana wasa da fingers ɗinta. Mami tace, “Zahra.” Ta ɗaga kai tana kallonta. Tace, “Ki sake fuska mana toh.” Tace, “Toh.” Mami tace, “Duk yadda kukayi zaki koma, sai ki fara shiri.” “Tohm Mami.” Mami ta miƙe tace, “Bari naje na sa masu aiki su girka miki saƙwarar.” Kai ta gyaɗa mata. Da Mami ta fita, Zahra ta faɗa kan gado ta sake shiga duniyar tunani. Ya Umar da zai fita sallar Isha’i ya leka ɗakin Mami, saboda yanzu nan-ne wajen zaman Zahra. Yace, “Baby akwai abin da kike so ne?” Tace, “Eh Yaya.” Ya ƙaraso ciki yace, “Me kike so toh?” Tace, “Ragadada… sai kuma Fanta mai sanyi.” Yace, “Sai kuma me?” Tace, “Ai hakanan babu komai.” Yace, “Alright. Idan na tashi daga sallah zan saya.” Daga haka ya mata sallama ya fita. Tana nan kwance tana jin komai boring. Sai ta kunna wayarta, ta shiga Instagram. Nan take memories ɗinta na baya suka fara dawo mata. Can wajen ƙarfe tara na dare Ya Umar ya dawo. Yana parking ya hangi mutum zaune yana danna waya. Da mamaki yake kallonsa har ya fito daga motar ya kulle. Sai da ya kusa isa wajensa sannan yaga Ibrahim ne ya miƙe ya saka wayar a aljihu, ya miƙa masa hannu yace, “Assalamu alaikum.” Ya Umar kamar zai wuce, amma saboda sallamar da yayi sai ya kasa. Ya miƙa masa hannu shima yace, “Wa’alaikumus salam.” Ibrahim yace, “Fatan muna lafiya?” A taƙaice Ya Umar yace, “Lafiya.” Ibrahim yace, “Ina son magana da kai idan babu matsala.” Ya Umar yace, “Magana kuma da ni? Ban gane ba, wani irin magana kenan?” Ibrahim yace, “Toh mu zauna mana. A tsaye muke, ba lallai ka fahimce ni ba.” Ya Umar ya tamke fuska yace, “Me zai hana na fahimta? Ai naga kamar a tsaye ma yafi. Idan har za’a kai fist ma kaga zai fi daɗi a haka.” Murmushi Ibrahim yayi yace, “Toh shikenan. Dama maganar Zahra ce. Ina son zan tafi da matata, shine tace sai nayi magana da kai.” Wani irin dariya Ya Umar yayi. Wannan dariyar ta kona ran Ibrahim amma ya daure. Da kyar Ya Umar ya taƙaita dariyar yace, “Ikon Allah kenan. Ashe zaka iya zuwa neman alfarma. No wonder ma nake yi naga ka zama calm.” Ya gyara tsayuwarsa sannan yace, “Well… amma kai ko kaɗan baka da kunya ne? Har zaka iya sake haɗa ido da ni? Can you just imagine? After everything you did to my sister, har yanzu kana kallona kamar zaka iya danne ni?” Ya ɗan matso kusa da shi yace, “Ai na ɗauka yanzu baza ka iya tsayawa ka nemi taimakona ba ko wani abu makamancin haka. Amma yanzu kai ne a nan.” Ibrahim ya kulu amma ya danne zuciyarsa yace, “Yanzu muna maganar abin da ya wuce ne ko kuma maganar Zahra? Ita ce ma ta aiko ni wajenka. I think maganar baya ta riga ta wuce.” Sosai maganarsa ta ɓatawa Ya Umar rai. Har yaso ya juya ya tafi, amma sai yayi tunanin yin hakan zai bawa Ibrahim damar cigaba da halinsa. Sai ya daure yace, “Matarka zata koma gidanka, amma ka sani sai under certain conditions… ko kuma ka jira har sai Abbah ya dawo.” Ibrahim yace, “Da zan jira zuwan Abbah ai da ban zo ba. Dan haka menene conditions ɗin naka?” Ya Umar yace, “Fine. Mu shiga ciki muyi magana da kyau.” Daga haka ya fara gaba, Ibrahim ya bi bayansa. Bayan sun zauna, Ya Umar yayi murmushi yace, “Ibrahim Khalil, ba wai Zahra ba zata koma gidanka bane. Yes zata koma, amma ka sani wallahi duk wani abu da kake mata sai ka gyara. Ban damu sai kayi min magana ba, saboda nima I have no business with you. Zahra tana under medical observation saboda lafiyarta. Idan ka cigaba da saka kanwata cikin kunci, zaka sha mamaki. Wallahi ko duk abin da na mallaka sai na zuba wajen ganin na rabaka da ita.” Yana gama faɗin haka ya miƙe yace, “Zaka iya zuwa ka ɗauki matarka gobe tunda kun gama magana. Ni kuma na gama magana. Idan naga akasin haka zan ɗauki mataki.” Daga haka ya fita. Ibrahim ma ya miƙe ya bishi da kallo. Da kyar yake calming kansa har ya iya masa magana cikin nutsuwa. Daga ƙarshe shima ya fita gaba ɗaya, amma a zuciye. Bayan Ya Umar ya wuce ɗakinsa, yaji gaba ɗaya hankalinsa ya kasa kwanciya idan baiyi magana da Zahra ba. Can ya sauko a hankali ya wuce parlorn Mami. Ya zauna fiye da minti goma a wajen. Can sai ga Mami ta shigo tace, “Ahh dama Umar kana nan ne?” Yace, “Eh. ɗazu muka yi magana da Zahra akan zan saya mata wannan.” Ya ƙarasa maganar yana nuna mata ledar gabansa. Yace, “Na ɗan tsaya ne a hanya shi yasa nayi dare. Gashi nazo ban san ko tayi bacci bane.” Mami tace, “Anya? Ai naga kamar tana chatting ɗazu. Bari na duba maka.” Ta wuce bedroom ɗinta. Ta buɗe taga Zahra kwance. Tace, “Yayanki yana parlorn nan yana jiranki.” Nan take ta ajiye wayarta ta miƙe tace, “Toh bari na same shi.” Mami tace, “Ki saka hijab mana, ko haka zaki fita?” Tace, “Eh dama zan saka.” Ta ɗauka ta saka hijab ɗin. Mami ta fita, Zahra ma ta fito parlorn ta same shi yana danna waya. Tace, “Yaya ai har na gaji da jiranka. Nace ko lafiya?” Bai ɗago ba yace, “Sorry, na ɗan tsaya ne wani abu shi yasa nazo late.” Zahra ta ƙaraso gabansa tace, “Wannan ne ledar?” Yace, “Uhm shine.” Ta ɗauka tace, “Nagode sosai Ya Umar.” Bai ce komai ba. Ta koma ɗaya seat ɗin ta zauna ta buɗe takeaway ɗin ragadadar ta fara ci a hankali. Sai sannan ya ɗaga kai ya kalleta. Suna haɗa ido ya sauke nasa idon ya cigaba da danna wayarsa. Can bayan ta gama tace, “Ya Umar wai meke damunka ne? Kamar baka jin daɗi.” Murmushi yayi yace, “I’m fine.” Tace, “Okay.” Yace, “Zamu iya magana idan babu damuwa?” Nan take taji gabanta ya faɗi. Ta ɗaga kai ta kalleshi amma ta kasa cewa komai, kai kawai ta gyaɗa masa. Yace, “Baby kunyi magana da Ibrahim ne?” A hankali tace, “Eh, ɗazu ya zo. Ban san ma shi bane Mami tace naje ina da baƙo, da naje sai naga ashe shi ne.” Yace, “Good. Kunyi maganar komawarki?” A hankali tace, “A’a Yaya. Ya durƙusa yana roƙona… sai kuma ya bani tausayi. Na kasa ce masa a’a. Shine nace ya zo ya same ka, duk abin da kace shikenan.” Yace, “A’a? Duk abin dana ce kuma?” Ya ɗan gyara zamansa yace, “Ai tunda kika ce ya zo wajena, kin riga kin gama making up your mind.” “Yaya…” “Yes.” Ya koma ya jingina da kujera sannan yace cikin ɗan fusata, “Har yanzu zaki yarda da abin da zai faɗa miki? Kince ya durƙusa? Kafin ya aure ki ai ya durƙusa yana neman soyayyarki. Saboda haka ne ma na goya miki baya akansa tunda kin yarda da shi. Yanzu kuma zaki sake yarda da salon yaudararsa?” Ya ƙara kallonta yace, “Talk to me, baby.” Gaba ɗaya Zahra ta rikice. Ta tsorata da yanayin Ya Umar ɗin. Tace, “Yaya kayi haƙuri dan Allah.” Yace, “Shut up.” A tsorace tace, “Yaya na fasa komawa.” Ganin yadda tayi maganar yasa ya sassauta muryarsa yace, “Zaki koma Zahra, ba zan hanaki ba. Amma duk abin da yake miki idan bai canza ba ki sanar dani. Dan wallahi akwai alkawarin ba zai sake bata miki rai ba.” Ya ɗan yi shiru sannan yace, “Abin da nake so dake Baby shine, duk abin da zai miki ki sanar dani. Kar kiyi shiru ya cigaba da cutar mana dake, kinji?” Kai ta gyaɗa masa. Yace, “Kina buƙatar wani abu ne?” Ta girgiza kai tace, “A’a babu.” Yace, “Toh zaki iya zuwa ki kwanta.” Ta gyaɗa masa kai. Yace, “You can go.” A hankali ta miƙe. Gaba ɗaya jikinta yayi sanyi. Tace, “Yaya sai da safe.” Yace, “Allah ya tashe mu lafiya.” Har ta fara tafiya yace, “Baby…” Ta juya. Yace, “Please kar ki sa komai a ranki kinji?” Tace, “In shaa Allah. Nagode sosai.” #Jiddatulkyar writes #08110615256 *FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes Young talented writers association (YOTA) Book 1 Chapter 13 Zahra tun data shiga ɗaki ta kwanta, amma sam bacci yaƙi zuwa idanunta. Ko chatting ɗin ma ta ji ba zata iya yi ba. Maganganun Ya Umar ne kawai suke yawo a cikin ranta. Ta sani bata kyauta masa ba, amma ita tausayi ne yasa ta aikata hakan. A hankali ta share hawayen da suka zubo mata. Ƙarar shigowar saƙon waya taji. Wayar ta ɗaga tana kallon sunan da ya bayyana a screen ɗinta, abin mamaki sosai ganin saƙon Khalil. Good night, my Zahratyy Na san kina fushi da ni, kuma kina da duk wani dalili na hakan… amma wallahi tun lokacin da kika fita daga gidan nan babu abin da yake min daɗi. Gidan ya yi shiru babu ke. Ki yi ƙoƙarin ki huta, please. Bana son ki damu da komai yanzu. Abin da nake so kawai shine ki samu lafiya da nutsuwa. Dan kin haifi mana Ɗan mu cikin kushin lafiya Tomorrow zan zo na ɗauke ki in sha Allah. Mu fita lunch ko? Wani wuri mai kyau, just me and you… maybe hakan zai sa ki ɗan murmusa min kamar da. Sleep well, tauraruwa ta Bayan ta gama karantawa, ta kashe wayar saboda bata da abin cewa. Ajiye kanta tayi akan pillow. Ita da take yin bacci da wuri kwana biyun nan amma yau bacci yaƙi ɗaukanta. Har ƙarfe goma sha biyu na dare idanunta biyu buɗe suke. Dakyar dai bacci ya ɗauke ta can wajajen asuba. Washegari da safe, Mami na zaune ita da Zahra suna breakfast a main parlorn ɗinta. Ya Umar ne ya shigo da sallama. Mami ta amsa masa, shi kuma ya ƙaraso ya zauna a kujera yana gaidata. “Ya jiki?” Ya Umar ya tambayi Zahra cikin sanyin murya. “Alhamdulillah,” Zahra ta amsa tana wasa da fingers ɗinta. “Yaya ina kwana?” ta ƙara tambaya a hankali. “Lafiya. Ya ƙarfin jiki?” “Da sauƙi.” Sai ya ɗan kalleta yace, “Akwai abin da kike buƙata ne?” Kai ta girgiza masa. “Idan akwai sai ki yi magana.” “Toh.” ta ce Ya ce “Anjima zaki koma gidan ki ko?” Ta kasa ɗaga kai balle tace eh. Mami ta juya ta kalleta sannan ta maida hankalinta kan Irish ɗin gabanta. “Umar, ka zauna ka karya mana,” Mami tace. “Ai tare da Abbah muka yi.” “Okay.” Zahra ta miƙe ta wuce ciki kamar mai son yin wani abu. Ya Umar ya kalli Mami yace, “Mami me kika yanke akan komawarta?” “Kamar me kuma?” “Ba za’a tura mata mutum ba?” Ya Umar ya ce “Eh, nima nayi tunanin haɗa ta da mai aiki. Yana da kyau ace akwai mutum kusa da ita, shiyasa nake son haɗa ta da mai aiki.” “Good. Nima abin da nayi tunani kenan. Amma akwai wacce kuka yi magana ne?” “Eh, nayi magana da Rabi’a tun jiya. Anjima kanwarta zata zo ta koma can ɗin da zama.” “Okay. Idan tazo Mami ko ina wajen aiki ne, please call me. Ina son na kaita da kaina.” “Toh shikenan, tana zuwa zan kira ka.” Ya ɗan yi murmushi sannan yace, “Amma Mami kina mata addu’a kawai. Kamar har yanzu kina fushi.” Murmushi Mami tayi tace, “Umar wani fushin kuma? Ai komai ya wuce yanzu.” “Yauwa Mami.” “Addu’a kam kullum ina cikin yinta.” Mami ta ce Ya miƙe yace, “Mami bari zan wuce.” “Allah yayi albarka ya bada sa’a.” “Ameen.” Daga haka ya fita. Can sai ga Zahra ta fito cikin shirinta. Mami ta kalleta tace, “Zahra kamar wanda ake kora, ace ƙarfe takwas zaki koma gidan ki?” “A’a Mami, ba gida zan koma ba. Ina son na shiga school.” “Yanzu har kin warke da zaki fara fita school?” “Mami zan bi a hankali. Bana son karatu ya wuce ni. Wannan final semester na ne, kuma tun farkon semester bana zuwa. Kar nazo nayi missing abubuwa da yawa, though su Firdausi suna min attendance.” “Toh, ƙarfe nawa zaki koma gidan?” Mami ta ce “Idan na dawo da yamma.” Mami ta gyada kai. “Toh sai driver ya kai ki school ɗin. Ki faɗa masa lokacin da zaki taso sai yaje ya ɗauko ki. Da yamma kuma Yayanki zai maida ki.” “Toh Mami.” “Allah ya bada sa’a.” “Ameen.” Daga haka ta juya ta fita. A department ɗinsu driver yayi parking. Zahra ta buɗe back seat ta sauko. Kusan duk idanu sun dawo kanta. Idan da sabo ta saba, amma yau sai taji bata son kallon nasu. Tana shiga hall ɗin ta samu waje a edge ɗin gaba. Bata ma damu data nemi su Asiya ba. Firdausi ce ta taso ta ƙaraso wajenta. “Dama Zahra zaki shigo yau?” “Eh, kawai naji ina missing abubuwa ne.” “Hakane kam. Ya jikin naki?” “Alhamdulillah da sauƙi.” Firdausi ta ɗan kalleta sosai. “Amma ya naga kina wani iri ne? Ko dai jikin ne?” Kai ta girgiza mata. Daga haka Firdausi tayi shiru ganin kamar Zahra bata son magana. Duk wanda ya shigo sai ya mata “ya jiki?” A haka har suka yi first lecture ɗinsu na three hours. Gaba ɗaya Zahra ta rasa meke mata daɗi a duniya. Gashi bata isa ta tunkari Mami da wannan maganar ba. Dafe kanta tayi. “Zahra wai nikam tunanin me kike yi haka?” Firdausi tace. “Kar kije ki jawo wa kanki ciwo. Kin manta kina under conditions ne?” “Firdausi ban san yadda zanyi bane… na rasa meke min daɗi.” “Me ya faru?” “Anjima zan koma gidan Ibrahim.” “What!?” Firdausi ta faɗa cikin mamaki. “Yanzu duk abin da Khalil yayi miki sai ki koma gidansa?” Zahra ta dafe kanta. “Ban san yadda zanyi bane Firdausi. Gaba ɗaya nima kai na ya kulle. Har gida yazo yana rokona, shine ma na haɗa shi da Ya Umar.” “Haba Zahra! Yau kika fara sanin Ibrahim ne? Yaushe har zaki yarda da roƙonsa? At least ki basa wahala mana ko da zaki koma masa. Sai kace baki san right ɗinki ba.” Ta ɗan numfasa sannan tace, “Wallahi idan nice a matsayin ki, babu namijin da zai taka ni yana wulaƙanta ni ina kallo na kyale shi. Tuni na koma gidanmu.” “Amma Ya Umar ya masa warning sosai,” Zahra tace a hankali. “Kinga dole zai canza tunda Ya Umar ya shiga maganar.” Firdausi ta kalleta kawai. A ranta ta fahimci Zahra tana son mijinta ne sosai. “Toh shikenan,” tace daga ƙarshe. “Allah yasa hakan shine mafi alkhairi. Allah yasa kuma da gaske ya canza.” “Ameen.” Daga haka bata ƙara cewa komai ba. “Tashi muje masallaci,” Firdausi tace. “Daga can mu wuce cafeteria ki saka wani abu a ciki. Karki zauna da yunwa.” “Toh.” Daga haka suka miƙe suka nufi masallacin. Sosai Ya Umar yayi magana da Farida, kanwar Rabi’a, yana mata bayanin komai da ya dace ta sani game da zaman gidan da kuma kula da Zahra. Farida na zaune tana saurare cikin nutsuwa, lokaci zuwa lokaci tana gyada kai alamar fahimta. A lokacin ne Zahra ta buɗe ƙofar parlorn ta shigo. Ganinsu tare yasa ta ɗan tsaya na wani lokaci kafin tace, “Ya Umar ina wuni?” “Lafiya,” ya amsa yana kallonta. “Ya school ɗin?” “Alhamdulillah.” Farida ma ta gaidata cikin girmamawa, “Ina wuni.” “Lafiya lau,” Zahra ta amsa mata. Daga haka ta wuce ɗakin Mami. Ya Umar ya bita da kallo sannan yace, “Idan kin gama shiryawa sai ki faɗa min na kai ki.” Ta dakata sannan ta ce “Toh.” Ta ƙarasa shiga ɗakin. Kunna wayarta tayi, wacce tun ɗazun Khalil ya addabi rayuwarta da kira. Tana kunnawa kuwa sai wani kiran nasa ya shigo kamar wanda yake jira. Ta ɗaga tare da sallama. “Haba Zahra,” muryarsa ta fito cike da ƙorafi, “ina ta kira baki ɗagawa? Har gida ma nazo aka ce min babu kowa.” A hankali tace, “Na tafi school ne.” “Yanzu inzo na ɗauke ki?” “A’a… Ya Umar ne yace zai kawo ni.” Wani irin shiru Ibrahim yayi. “Hello?” Zahra ta kira a hankali. “Ina ji.” “Ai naga kayi shiru ne.” “A’a… toh sai ya kawo ki ɗin.” “Toh, sai anjima.” Daga haka ta kashe wayar. Kiran Mami tayi. “Mami kina ina ne wai?” “Ina part ɗin Abbanku ne, ina ɗan gyare-gyare kafin ya dawo. Wani abu ne?” “A’a, dama ban ganki bane.” “Kin shirya ne?” “A’a.” “Toh ki shirya. Ni ɗin ma na kusa karasawa.” Daga haka ta kashe wayar. Toilet ta shiga tayi wanka sannan ta fito. Wani dogon gown mai sauƙin kyau ta saka tare da hijab, hand bag kawai riƙe a hannunta kamar mai zuwa unguwa. Da fitowarta parlorn, babu kowa. Zama tayi tana jiran fitowar Mami. Jim kaɗan sai ga Mami ta buɗe ƙofar ta shigo. “Kin gama ne?” “Eh.” “Toh sai kima Yayanki magana, naga yana jiran ki.” Sai kuma tace, “Kin ga kayan da na haɗa miki? Wacce zata riƙa taimaka miki ta fita da su zuwa mota.” “Mami waccece?” “Idan kika je ai zaki ganta.” Ta ɗan tsaya sannan tace cikin kulawa, “Kuma kar kiyi wannan shaye-shayen magunguna idan ba asibiti da likita ya baki ba. Kinsan condition ɗinki.” Kai Zahra ta gyada kawai. “Toh ki sauka ki same su a ƙasa. Allah ya baki lafiya ya raba lafiya.” “Ameen,” ta amsa tana kallon ƙasa. A parlorn ƙasa ta samu Ya Umar yana waya. Daga gani da mace yake magana saboda yadda muryarsa tayi laushi. Yana ganinta sai ya kashe kiran. “Tashi mu tafi.” Miƙewa tayi. A wajen taga Farida tsaye da wasu ledoji a hannunta. “Zo mu tafi,” Ya Umar yace. Bin bayansu tayi zuwa mota. Ya buɗe mata gaba ta shiga, sannan shi ma ya zagaya ya shiga driver seat. Farida kuma ta shiga baya. Ya tada motar suka nufi gidan Zahra. Tun daga lokacin da suka kama hanya zuciyar Zahra ke bugawa da ƙarfi. Wani irin tsoro da fargaba ne suka cika mata ƙirji. Ita kanta batasan me yasa take jin hakan ba. A compound ɗin gidan yayi parking. Ta juya tana kallonsa tace, “Yaya nagode.” “Duk wani abu da zai faru Zahra, just let me know please.” Kai ta gyada masa. “Anjima zan miki transfer.” “Kaiii!” tace tana ɗan murmushi. “Yaya baka gajiya ne?” Ya ɗan murmusa yace, “Ohh… yanzu kin fara girma kenan. Da ke ce ai ina ruwanki da mutum ya miki transfer. Yau gobe sai kice kuɗi sun ƙare.” Dariya ne ya ƙwace mata, kuma hakan ya saka wani daɗi ya ratsa zuciyar Ya Umar. “Toh shikenan,” tace tana buɗe ƙofar motar. “Kafin transfer ɗin ma nagode sosai.” “Alright.” Ta sauka. Shi ma ya sauka tare da Farida. Ya buɗe bayan motar yana kwaso kayan yana miƙawa Farida tana kaiwa baranda. Bayan ya gama ya juya yana kallon Zahra yace, “Mijin naki yana nan ne? Mu gaisa nace na kawo masa matarsa.” “Bari na kira shi. Ka shigo.” Ta buɗe ƙofar parlorn. “Farida, kitchen zaki riƙa kai kayan.” “Toh,” Farida ta amsa tana ɗaukar ledar farko. Ita kuma Zahra ta wuce sama zuwa ɗakin Ibrahim. Tana buɗe ƙofar ɗakin ta same shi yana saka kaya, alamar daga wanka yake. Da suka haɗa ido murmushi ya sakar mata. A take duk fargabar da take ji ta ragu. “Ya Umar yana ƙasa wai ku gaisa.” Ya ɗan matsa kusa da ita yace, “Babu ko gaisuwa ne tauraruwa?” Dariya tayi tana shiga cikin ɗakin. “Har ka tuna min da wannan sunan?” “Ya baby na?” “Kai ni ka bari… kunya nake ji.” “Okay toh, bari naje mu gaisa da Yayanki kafin ya canja shawara.” Dariya tayi. Ya ƙarasa fesa turare sannan ya ajiye kwalbar. Hannunta ya kama suka fito tare. Tun suna saukowa daga stairs Zahra tayi saurin cire hannunta daga nasa saboda ganin Ya Umar a parlorn. Da suka ƙaraso, Ibrahim ya miƙa masa hannu suka gaisa. “Ɗan bani ruwa mana,” Ya Umar yace yana kallon Zahra. Ta juya zuwa kitchen. Da zarar ta bar wajen, Ya Umar ya maida kallonsa kan Ibrahim. “Gashi na kawo maka ita,” yace cikin sanyin murya. “Amma ka sani… idan ka cigaba da musgunawa kanwata, kamar yadda na kawo ta haka zan zo na ɗauke ta. Kuma a lokacin sai ta maka nisa har abada.” Ibrahim yayi folding hannuwansa yace, “Wai ya kake so ne? Ka dinga gaya min magana yadda ranka yaso? Zahra matata ce. Kuma idan son ta ne, ina sonta.” Ya Umar ya ɗan tafa hannayensa a hankali Ya ce “Good. Sai dai idan ba kai ɗin bane.” Ya ɗan matsa kusa da shi yace, “Well… duk yadda kace dai-dai ne. Amma ni kuma, I’m done talking.” A lokacin Zahra ta fito daga kitchen da ruwa da snacks. “Ya Umar har zaka tafi? Ko ka fasa shan ruwan ne?” “Naga an fara kiran sallah ne. Ina son na koma gida.” “Amma ka karɓa mana.” Saka hannu yayi ya ɗauki bottle water ɗin. “Allah ya huta gajiya.” Daga haka ya juya ya fita. Zahra ta bishi da kallo kafin ta juya. A lokacin ne taga Farida zaune can gefe cikin nutsuwa. “Taso bari na nuna miki ɗakin ki,” Zahra tace. “Sai dai akwai ɗan ƙura saboda ba’a buɗe shi ba.” Ta nuna mata ɗakin dake kusa da kitchen. Farida ta gyada kai suka wuce. Bayan ta gama nuna mata komai, Zahra ta dawo parlorn. Ibrahim na zaune ya lumshe idanunsa kamar mai tunani. “Lafiya?” ta tambaya tana tsayawa gabansa. Ya buɗe idanunsa a hankali yana kallonta. “Lafiya Zahra.” Ta juya zata wuce sama sai yace, “Wacece wannan?” “Wacce zata taimaka min aiki ce. Mami ai ta faɗa maka.” “Okay.” Daga haka ta wuce sama direct zuwa ɗakinsu. Toilet ta shiga tayi alwala, sannan ta fito. Darduma ta shimfiɗa tare da tada kabbarar sallah, zuciyarta cike da wani irin nauyi da take fatan Allah kaɗai zai sauƙe mata Ku fara ajiye ishirin, hamsin a asusun ku🤣 akwai chakwakiya ne sosai a book 2 #08110615256 *FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes Young talented writers association (YOTA) Book 1 Chapter 14 Mami na zaune a parlorn tana kallon tv lokacin da taji an buɗe gate. A take ta tuna cewa Mummy bata gidan lokacin da aka maida Zahra, kuma tasan idan taji komai zai iya zama wata magana. Da sauri ta miƙe ta sauka ƙasa domin tararta kafin ta shigo. Sai dai tana isa parlorn, tuni Mummy ta shigo ciki. Bayan sun gaisa ne Mami tace cikin son kaucewa wata magana, “Ai baki san mene ba… yarinyar nan dai ta koma ɗakinta.” Mummy ta ɗan tsaya tana kallonta. “Mijinta yace Mamarsa tayi faɗan wai a barta tayi laulayin a ɗakinta, shine yazo ya tafi da matarsa.” Wani irin dariya Mummy tayi, mai cike da ma’ana. “Lallai ma,” tace. “Ai nasha faɗa da kun nuna mata matsayina tun farko ai da bata yi kan kanta ba. Da zata jira Ni har sai nazo, ko da safe ta faɗa min kafin na fita.” Mami ta ɗan gyara zamanta tace, “Ai Yayanta ne ma ya kai ta, ganin baki nan, ba haka nan ta tafi ba.” “Dama yayan nata baku shanye shi bane?” Mummy tace da ɗan tsaki. Tana gama maganar ta juya ta nufi stairs ɗin sama. Mami ta bita da kallo kawai. Bayan ta ɓace daga ganin ta, sai ta girgiza kai a hankali tana jin wani iri a zuciyarta. Ita kanta tasan akwai abubuwan da suke faruwa da basu kamata ba, amma duk da haka bata son abubuwa su ƙara lalacewa A hankali ta miƙe itama ta wuce ɗakinta na sama, zuciyarta cike da tunani iri-iri. **** Miƙewa tayi daga kan dardumar ta ninke ta a hankali. A daidai lokacin ne Ibrahim ya shigo ɗakin, daga gani ya dawo ne daga masallaci. Kallonta yayi na ɗan lokaci kafin ya ƙaraso kusa da ita ya zare hijabin jikinta cikin sanyin jiki Komawa tayi bakin gado ta zauna, ta ɗauki wayarta tana danna wa ba tare da ta kalleshi ba. Shima ya zauna kusa da ita yace, “Zahra ki shirya, zamu fita yanzu.” Ba tare data ɗago ba tace, “Babu inda zan tafi. Bacci ma nake son yi.” “Zahra ina faɗa miki abinda zakiyi kina ce min no?” Ta ɗago tana kallonsa tace, “Yes, ai ina da right ɗin faɗar hakan, tunda nine zan fita kuma banji zan je ba.” Kallonta kawai yake yi, ita kuma ta kauda kanta ta mayar da hankali kan wayar hannunta. Hannunta ya kamo a hankali yace, “Zahra...” Sai ta ɗago idanunta ta kalleshi ba tare data ce komai ba. “Are you still angry with me?” Wani ɗan murmushi mai ciwo tayi ta kashe wayar hannunta ta ajiye. “Tambayata kake yi? Ibrahim anya kasan wani abu wai shi kunya? Just imagine... idan nice na maka irin wannan ƙaryar, bana tunanin ma zan iya sake haɗa ido da kai.” Ta ɗan yi shiru kafin ta cigaba. “Kasan yadda nake a media, kasan yadda bikinmu yayi trending. Amma har zaka fara cheating tun yanzu? Kana tunanin ba za’a samu wasu su ɗauka su yaɗa a duniya ba?” Hargitsa gashin kansa yayi yana furzar da iska daga bakinsa. “Please Zahra, komai ya wuce mana.” Kai ta girgiza. “Ibrahim baka yi kama da mijin da yake nadama ba. Sau nawa baka zama a gidan nan idan nayi magana ba shi zai sa ka canza ba? Bikinmu ko sati ɗaya bai yi ba amma ka canza. Yaushe rabon da muka kwana tare cikin farin ciki da soyayya? Ashe mata kake bi...” Tsawa ya daka mata. “Kar ki sake cewa ina bin mata Zahra! I hate those words.” Dariya tayi mai ɗaci. “You will never change Ibrahim. Ka dake Ni kawai.” Wani numfashi mai nauyi ya sauke yana kallon gefe. Ta cigaba cikin sanyin murya, “Think well please… kana sauke hakkokina dake kanka?” Shiru yayi. “Na dawo gidan nan ne ba wai dan soyayyar da nake maka ta farko ba. Na dawo ne saboda bana son Abbah ya sani tun yanzu ya ɗauki mataki. Kuma dukkanmu ba zamu ji daɗi ba. Ka riga ka nuna wa Yayana halinka tun kafin ya gama yarda da kai. Firdausi ma ka nuna mata halinka, gashi kuma tare muka kama ka da ita.” Idanunta suka cika da ƙwalla. “Gaskiya bazan iya rayuwa cikin wannan takaicin ba. Tun kafin ka kashe ni da bakin ciki, idan baka canza ba zan bar maka gidanka. Saboda yanzu naga baka sona…” Mikewa yayi da sauri yace, “Enough Zahra! Ban ce bana son ki ba. Idan kuma zaki cigaba da sauraron masu zugaki, ba zaki taɓa ganin son da nake miki ba.” Ta ɗan yi murmushi mai ciwo tace, “Fine.” Har ya juya zai fita sai kuma ya tsaya ya juyo. “Ki shirya. Zamu fita dinner.” Sai ta miƙe daga kan gadon tana gyara ɗankwalinta tace, “Alright.” **** Bayan kusan rabin awa, Zahra ta fito cikin wata doguwar riga mai launin royal blue da ɗan ƙaramin farko blue veil, ƙamshinta na tashi a hankali. Ibrahim dake jingine da motarsa a compound ya ɗago yana kallonta, na ɗan lokaci ya manta komai. Karasowa tayi ba tare data ce komai ba, ya buɗe mata motar cikin gentlemanly manner, ita kuma ta shiga. Shima ya zagaya ya shiga ya kunna motar. A hanya babu wanda yayi magana sosai, sai dai lokaci zuwa lokaci Ibrahim na satar kallonta. Ita kuma tana kallon window kamar bata lura ba. Bayan mintuna kaɗan suka ƙarasa wani babban wajen shakatawa mai cike da haske da flowers masu kyau. Couples ne sosai a wajen, wasu na ɗaukar hoto, wasu kuma na cin abinci cikin nishadi. Da suka shiga, waiter ya kai su wani table na gefe kusa da glass wall ɗin wajen, daga nan ana hangen city lights masu kyau. Zama sukayi. “What would you like to eat?” Ibrahim ya tambaya cikin nutsuwa. Menu ta karɓa tana dubawa, daga ƙarshe tace, “Grilled chicken da fried rice… sai mocktail.” Shi kuma yace, “I’ll go with seafood pasta.” Bayan an kawo musu abincin, shiru ne ya ɗan ratsa tsakaninsu kafin Ibrahim ya ɗauki spoon ya debo rice ya miƙa mata. Da farko kallonsa tayi kawai, sai kuma ta buɗe baki a hankali ta karɓa. Murmushi yayi karon farko cikin dare ɗin. “Good girl.” Ita ma spoon ta ɗauka ta debo pasta ta miƙa masa. “Kar ka ce ni kaɗai ake feeding.” Dariya yayi ya karɓa daga hannunta. A hankali yanayin tsakaninsu ya fara sauyawa. Ibrahim na bata labarai masu dariya har tana dariya tana dan bugun kafaɗarsa lokaci zuwa lokaci. Daga baya suka fita garden area na wajen. Hasken fitilu masu laushi na sauka a jikinsu yayin da iska ke kaɗa veil ɗin Zahra. Ibrahim ya jawo ta kusa dashi yace, “Smile mana ko sau ɗaya ne” Sai ta ɗan turo baki. “Ban so.” “Please…” ya ce A ƙarshe murmushi tayi, nan ya fito da wayarsa suka fara ɗaukar hotuna tare. Wani yana riƙe da hannunta, wani kuma ya rungumota daga baya yayin da ita ke dariya. Har wani couple photographer na wajen ya zo ya ɗaukar musu wasu hotuna masu kyau sosai a ƙarƙashin flowers da lights ɗin wajen. Bayan sun gama, Ibrahim ya riƙe hannunta suna tafiya a hankali. Cikin sanyin murya yace, “Wallahi bana son wannan rashin fahimtar tsakaninmu Zahra.” Ta ɗago tana kallonsa. “Then stop hurting me.” Tsayawa yayi cak, ya kamo hannunta ya sumbaci bayan hannun nata. “I’ll try…” Kallonsa tayi na wasu seconds kafin ta ɗan jingina da kafaɗarsa a hankali, shi kuma murmushi yayi yana ƙara matse hannunta cikin nasa. Dare ya fara nisa sosai kafin suka bar wajen. Tun daga parking lot ɗin har cikin mota, yanayin tsakaninsu ya ɗan sauya, ba kamar yadda suka fita daga gida ba Zahra na zaune tana kallon hotunan da suka ɗauka a wayarta, wani ɗan murmushi na bayyana a fuskarta lokaci zuwa lokaci. Ibrahim kuwa yana driving amma idanunsa na satar kallonta “Wannan hoton yayi kyau sosai,” Ibrahim yace yana nuna wani da ta jingina da kafaɗarsa. Ta ɗan murmusa tace, “Kai dai duk naka ne yafi kyau” “Saboda matar tawa ce a ciki.” Sai ta girgiza kai tana ɓoye murmushinta Da suka isa gida, Ibrahim ya parking motar sannan ya zagayo ya buɗe mata ƙofa. Hannunta ya kama yayin da suke shiga ciki tare. Gidan shiru yake, da alamu na farida ta daɗe da bacci Da suka shiga ɗaki, Zahra ta cire takalmanta ta nufi wardrobe tana ɗauko kayan bacci. Ibrahim kuma ya cire agogonsa da wayarsa ya aje saman side stool. “Zan shiga wanka,” tace ba tare data kalleshi sa ba Kai ya gyaɗa mata kawai. Bayan wasu mintuna ta fito daga toilet ɗin cikin doguwar rigar bacci mai kyau, jikinta na ɗauke da ƙamshin shower gel data yi wanka, gashinta a ɗaure cikin scarf mai kyau. Ibrahim dake zaune bakin gado ya ɗago yana kallonta, idanunsa suka bi ta da wani irin kallo mai cike da so. Ita kuma kamar bata lura ba ta ƙarasa gaban mirror tana shafa handcream a hannunta. Shi ma miƙewa yayi ya shiga toilet ɗin. Lokacin da ya fito, farin towel ne ɗaure a kugu, daya a kafaɗarsa ga ruwa ke ɗiga kaɗan daga gashinsa. Ya sauya zuwa kayan bacci, ya kashe manyan fitilun ɗakin, small bedside lamp kawai ya bari. Zahra ta riga ta kwanta ta juya baya kamar mai bacci. A hankali Ibrahim ya hau gadon ya matsa kusa da ita. Hannunsa ya zagayo ya riƙo ta ta baya. Da farko bata motsa ba, sai kuma ta ɗan sauke numfashi. “Har yanzu kina fushi dani?” ya tambaya cikin ƙasa da murya. Shiru tayi na wasu seconds kafin tace, “Ban sani ba.” Murmushi yayi kaɗan ya matso da bakinsa kusa da kunnenta. “But you’re calmer now.” Ta juya a hankali tana kallonsa. Haske daga lamp ɗin na sauka akan fuskokinsu. “I just want peace Ibrahim.” Kallonta yayi cikin idanunta sannan ya shafa gefen fuskarta a hankali. “And I want you.” Idanunta suka sauka ƙasa na ɗan lokaci. Ibrahim ya janyo ta jikinsa, ita kuma bata ƙi ba. Ta kwantar da kanta a ƙirjinsa yayin da hannunsa ke shafa bayanta cikin lallashi. A haka suka cigaba da hira cikin ƙananan muryoyi, suna tuna abubuwan dariya da suka faru a dinner ɗin, har bacci ya fara ɗaukar Zahra. Ibrahim ya sumbaci goshinta a hankali yace, “Goodnight wife.” Cikin muryar bacci tace, “Goodnight…” Sai ya ƙara rungumota sosai, ɗakin yayi sit cikin shiru da dumin soyayyarsu. **** Ya Umar dake kwance saman king size bed ɗinsa yana scrolling through Instagram kawai idanunsa suka sauka akan sabon post ɗin. Da sauri ya tashi zaune tamkar wanda aka tsikara. Kallon pictures ɗin ya tsaya yi cikin mamaki. Hotunan Zahra ne tare da Ibrahim daga dinner ɗin ɗazu, yadda suke manne da juna cikin farin ciki kamar ba su taɓa samun matsala ba. Zooming yake yi ɗaya bayan ɗaya, yana kallon yadda murmushin Zahra ya fito sosai a hotunan. A hankali ya kashe data ɗinsa ya ajiye wayar gefe ya kwanta saman gadon. Duk da wani irin abu da ya tsaya masa a zuciya, akwai abu guda ɗaya daya saka shi murmushi kaɗan, ganin cewa at least sun daidaita, sun koma kamar yadda ya kamata tsakanin ma’aurata. *** Washegari da sassafe, Ibrahim ne ya fara farkawa. Juya kansa yayi yana kallon Zahra dake kwance kusa dashi cikin bacci, fuskarta na ɗauke da wani irin natsuwa. Murmushi yayi a hankali kafin ya matsa kusa da ita yana shafa gefen fuskarta. “Baby...” ya kira cikin sanyin murya. Ta ɗan motsa tana lumshe ido. “Hmm...” “Sallah fa.” Bata buɗe idanunta ba ta matsa kusa dashi tana ƙara lulluɓe jikinta da blanket. Dariya yayi ƙasa-ƙasa kafin ya sunkuyar da kansa ya sumbaci goshinta. “Zahra...” A wannan karon ta buɗe idanunta a hankali tana kallonsa. “Ka cika damuna da asuban nan.” “Saboda bana son ki makara.” Miƙewa tayi tana murmushi. Ibrahim ya sauka daga gadon ya shiga toilet domin alwala sannan ya shirya zuwa masallaci. Kafin ya fita sai da ya juyo ya kalleta. “Ki tayani addu’a.” Kai ta gyaɗa masa kawai tana sauka daga kan gadon. Bayan ya fita masallaci, Zahra ta idar da sallarta tana nan zaune akan darduma tana addu’o’i. Daga nan ta miƙe ta shiga kitchen. Farida mai aiki na shirin fara breakfast ɗin, amma Zahra tace mata “Barshi yau zan yi. Ke ki fara preparations na lunch kawai.” “To Hajiya. Dama gyara wajen nake son yi naga sunyi kura ne, kafin ki fito shine na share” Kai ta gyada mata, daga haka ta bar kitchen ɗin Egg sauce da tea ta fara haɗawa, sai bread da sausages. Kitchen ɗin ya cika da ƙamshi mai daɗi. Bayan wani lokaci Ibrahim ya dawo daga masallaci. Kai tsaye kitchen ya nufa bayan ya ga babu ita a ɗaki. Yana shiga ya tsaya yana kallonta cikin apron ɗinta tana juyawa a cooker. “Wow...” Ta juyo tana kallonsa. “Meye wow ɗin?” “Matata ce ke min breakfast da kanta.” Idanu ta juya tana murmushi. “Ji sharri sai kace bana yi. Zo ka taimaka min mana.” Nan ya ƙaraso kusa da ita yana tayata haɗa table ɗin breakfast, lokaci zuwa lokaci yana sata dariya da surutunsa. *** Bayan ta shirya tsaf cikin elegant outfit ɗinta, Zahra ta ɗauki keys ɗin motarta ta nufi school. Da ta isa, parking tayi a bakin faculty ɗinsu. Ganin har lokacin lecturer bai zo ba, sannan generator ɗin school ɗin ma ba'a kunna ba yasa ta zauna cikin motar ta saukar da kujera kaɗan ta kunna AC. Wayarta ta ɗauka tana chatting casually kafin ta shiga status ɗin mutane. Tana scrolling kawai status na Ya Umar ya bayyana. Da sauri ta miƙe zaune ba tare data sani ba. “This can’t be...” ta furta a hankali. Da sauri ta buɗe status ɗin. Hotonta ne na jiya ita da Ibrahim yayin dinner ɗinsu. Ibrahim ya rungumota tana dariya. Caption ɗin kuwa: “Lil sis ❤️ Get well soon.” #Jiddatulkhayr writes #08110615256 *FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes Young talented writers association (YOTA) Book 1 Chapter 16 Idanunta suka buɗe sosai cikin mamaki. Zooming hoton tayi tana kallonshi da kyau, kamar zata tabbatar ba mafarki take ba. Sai kuma wani irin dariya ya kwace mata lokaci guda da kunya. Ta rasa dalilin da yasa Ibrahim kullum idan suka ɗauki hoto sai ya saka a media. Yanzu ga shi har Ya Umar ya ɗauka ya saka a status ɗinsa ma. Da sauri ta kashe data ta fita daga WhatsApp ɗin tamkar yana kallonta kai tsaye. A ranta ta tabbatar tunda ya ga wannan ma, definitely ya ga wanda ita da Ibrahim yake kissing forehead ɗinta. “Ya salam...” ta faɗa tana dafe goshinta cikin kunya. AC ɗin motar ma kashewa tayi sannan ta buɗe ƙofar zata fita. Dai-dai lokacin taji muryar Firdausi daga bayanta tana dariya. “Amarya...” Zahra ta tsaya cak. A ranta tace, “Yau nikam na shiga uku...” Karasowa Firdausi tayi tana kallonta da wani irin murmushi mai cike da tsokana. Zahra ta ɗan bata fuska tana gyara handbag ɗinta. “Mu ƙarasa mana,” Firdausi tace tana haɗa hannuwanta. “Dama ganin ki nayi nace bari in zo na tara Anty Amarya.” “Bana son tsokana wallahi,” Zahra ta faɗa tana harararta. “Laaa...” Firdausi tace tana riƙe baki kamar wacce aka zalunta. “Me nayi kuma?” Sai kuma ta matso kusa da ita tana rage murya. “Ni fa ban ɗauka yau zaki zo school ba. Dan jiya media ya ɗauki wuta” “Firdausi...” Zahra ta kira sunanta cikin warning tone. “Ki duba comments section mana....” “Enough Firdausi!” Da sauri Firdausi ta haɗiye dariyarta amma har yanzu murmushi ke son ƙwace mata. “But like seriously...” ta faɗa tana kallon Zahra daga sama har ƙasa, “you fine die. Gaskiya kun tashe kai na.” Kai tsaye Zahra tayi gaba ta barta a baya. “Arrey tsaya mana!” Firdausi tace tana saurin bin bayanta. Suna shiga lecture hall ɗin, Zahra ta lura da yadda idanu da yawa suka biyo ta. Wasu click na kallonta suna murmushi, wasu kuma na raɗa-raɗi tsakaninsu. Har wasu dudes ma sai kallonta suke yi Amma ko kaɗan bata nuna ta kula ba. Kai tsaye ta wuce seat ɗinsu ta zauna tana fiddo notebook ɗinta. Firdausi kuwa tana zaune kusa da ita tana murmushin mugunta. “Wallahi duk sun gane celebrity ta shigo.” Zahra bata ko kalleta ba. “Please keep quiet.” Ana haka Asiya da sauran friends ɗinsu suka shigo. Asiya na ganin Zahra ta zaro ido. “Kaiii Amarya!” “Ke ma don Allah...” Zahra tace tana dafe kanta. Asiya ta zauna kusa da ita tana dariya. “Wallahi jiya kun yi kyau sosai. Har Mom dina sai data tambayeni wai wannan ba kawarki bace?” Firdausi ta fashe da dariya. “Nifa nace muku media ya ɗauki wuta.” Zahra ta rufe fuskarta da notebook. “Allah yasa lecturer ya shigo yanzu.” Kamar maganar ta yake jira, lecturer ɗin ya shigo hall ɗin, nan take kowa yayi shiru aka fara lecture. Bayan first lecture ɗin, sun fito gaba ɗaya cikin gajiya. “Asiya wallahi yunwa nake ji,” Firdausi tace tana gyara hijabinta. “Mu je cafeteria mana bayan sallah,” Asiya ta bata amsa. Duk suka yarda sannan suka nufi masallaci. Bayan sun idar da sallah, suka wuce cafeteria ɗin school. Wajen cike yake da students, hayaniya na tashi ta ko’ina. Suka samu wani table a gefe suka zauna. “Me zaku ci?” Asiya ta tambaya. “Nifa rice zan ci,” Firdausi tace da sauri. “Ke kullum rice,” Zahra ta faɗa tana ɗan murmushi. “To meye matsala idan ina da loyalty ga rice?” Duk suka yi dariya. Zahra ta ɗauki shawarma da yoghurt yayin da Asiya ta siyo noodles. Suna cin abincin, hirarsu ta koma kan school gist da assignments. Amma duk bayan wasu mintuna sai Firdausi ta dawo kan maganar hotunan Zahra da Ibrahim. “Wallahi yadda yake kallonki a pics ɗin nan...” “Firdausi!” “Okay okay na yi shiru.” Asiya ta kwashe da dariya. “Amma gaskiya Ibrahim na sonki, ki jira Suhaima ta zo gobe kin shiga uku ai” A hankali murmushi ya bayyana a fuskar Zahra kafin ta sunkuyar da kanta tana haɗa yoghurt ɗinta. Bayan sun gama, suka ɗan zauna suna hutawa kafin aka fara second lecture. Har zuwa lokacin tashin su, Zahra bata sake shiga social media ba saboda yadda take jin kunya duk sanda ta tuna status ɗin Ya Umar. Da aka tashi, suka fito tare suna tafiya a hankali cikin compound ɗin school. Rana ta fara lafa kaɗan yayin da students ke fita groups-groups. “Ashe yau ma driver ɗinki baizo ba?” Firdausi ta tambaya. “Motata nazo da ita mana.” “Ohooo rich aunty.” Zahra ta girgiza kai tana dariya kaɗan. Kafin su rabu, Asiya tace, “Ki gaida mana Mr Romantic.” Zahra ta cije lips ɗinta tana jin kunya. “Ku bari mana...” Firdausi tace, “Ki gaya masa next time ya rage posting mana, kin kusa zama Layla celebrity.” Duk suka fashe da dariya yayin da Zahra ta shiga motarta tana girgiza kai a kunyace. Zahra na shirin kulle motarta kenan Firdausi tace, “Please bari kiyi dropping ɗina a hanya kawai. Na fasa zaman school yau.” Wani kallo Zahra ta mata kafin tace, “Shiga mana.” Jiran ta tayi har sai da Firdausi ta shiga sannan ta kulle motar suka kama hanya. Tun daga fitarsu gate ɗin school, Zahra tayi shiru tana driving cikin nutsuwa. A fili yake bata buƙatar wata doguwar hira. Firdausi ta ɗan sace kallonta kafin tace, “Amma Zahra... nayi murnar ganin Ibrahim ya canza.” A hankali Zahra ta sauke numfashi. “Toh Allah yasa. Dan haka ya faɗa kuma ni ma na fara ganin alamu.” Firdausi ta gyada kai tana murmushi. “Allah ya ƙara muku fahimta da zaman lafiya.” “Ameen oo,” Zahra ta amsa cikin sanyin murya. A haka suka cigaba da hira kaɗan-kaɗan har ta kai Firdausi inda zata sauka. Bayan ta sauke ta, Zahra ta juya ta kama hanyar gida. To her surprise, tana shiga compound ɗin gidan idanunta suka sauka akan motar Ibrahim a parke. Ta ɗan tsaya tana kallon motar kamar wacce bata yarda da abinda take gani ba. Bata ma tuna yaushe rabon data dawo gida ta same shi a gida da wuri haka. A hankali murmushi ya bayyana a fuskarta kafin tayi parking ta sauka daga motar. Kai tsaye ciki ta wuce. Daga kitchen taji motsin wanke-wanke, hakan yasa ta leƙa. Farida ce ke gyara wajen cikin sauri. Da ganin Zahra, da sauri ta juya tana murmushi. “Sannu da zuwa Hajiya.” “Yauwa Farida, ya aiki?” “Alhamdulillah. Oga ma ya dawo.” Kai ta gyada kawai tana murmushi kaɗan kafin ta juya ta nufi sama. A parlorn saman ta same shi zaune yana kallon ball. A gabansa akwai plate ɗin abinci, sai snacks da drinks a side stool. Bata san sanda murmushi ya subuce mata ba. Yana ɗago kai ya ganta, nan take fuskarsa ta sauya zuwa murmushi. “Welcome back wife.” Sai ya kashe TV volume ɗin kaɗan yana kallonta sosai. “Daga gani dai mutanen nan suna baki wahala.” Karasowa tayi a hankali ta faɗa jikinsa ta kwantar da kanta a kafaɗarsa tare da sauke numfashi kamar wanda yayi trekking mai nisa. “Kai dai ka bari...” Hannunsa ya zagayo bayanta ya rungumota. “Lectures sosai ko?” ya ce “Fafa muke sha saboda final semester.” “Sorry Zahratyy...” Murmushi tayi tana ɗago kai kaɗan. “Thank you Noory.” Daga nan ta miƙe daga jikinsa. “Bari na watsa ruwa.” “Abincin fa?” Kai ta girgiza. “Bana jin cin abinci. Gwara ma nasha tea ko cornflakes.” “Okay.” Ta wuce ɗaki ta shiga toilet. Bayan tayi wanka ta fito cikin wani fitted English wear mai kyau sosai. Kayan sun zauna a jikinta ta yadda suka fito da shape ɗinta cikin tsari mai kyau. Ƙamshinta ya cika ɗakin. Tana fitowa parlorn, Ibrahim dake ɗaga plate ɗin abincinsa ya tsaya kallonta. Wani lallausan murmushi ya saki yana bin ta da ido har ta ƙaraso kusa dashi. Kai tsaye ta ƙarasa ta faɗa jikinsa. Ya rungumeta yana shafa bayanta. “Ya baby na toh?” Ta ɗan bata rai tana ɗaga kai ta kalleshi. “Kaza yake son ci.” Dariya yayi. “Dole kuwa naje na nemo masa.” Sai ya ɗan matsa yana gyara mata zama a jikinsa. Amma kafin ma ya ƙara magana, rufe idanunta keda wuya bacci ya fara ɗaukarta. Numfashinta ya fara sauyawa alamun tayi nisa cikin bacci. Ibrahim ya sauke ido yana kallonta cikin tausayi da so. “A tired baby...” ya furta a hankali. A tausashe ya gyara mata kwanciyarta sosai a jikinsa, ya janyo hijab ya rufe mata ƙafafu sannan ya kashe TV ɗin gaba ɗaya domin kada hayaniya ta tasheta. Daga nan ya jingina da kujera yana ci gaba da kallonta, yatsunsa na yawo a hankali cikin gashinta yayin da ita kuma take bacci lafiya a jikinsa. Can wajajen magrib, Ibrahim ya ɗan sunkuyar da kansa kusa da fuskarta yana hura mata iskan bakinsa a hankali tare da shafa gefen fuskarta cikin tausasawa. A hankali ta buɗe idanunta. Murmushi ya sakar mata yace, “Tashi, mai ciki, magrib yayi.” Har zata sake rufe idanunta cikin kasala, jin yace magrib yayi yasa ta buɗe su sosai cikin mamaki. “Magrib?” Kai ya gyada mata yana dariya yace “Eh mana. Kin sha bacci sosai.” Da sauri ta miƙe ta zauna tana gyara gashinta. “Ban san har haka nayi bacci ba.” Shi kuma ya miƙe daga kujerar. “Bari nayi alwala na tafi masallaci.” Daga haka ya wuce ɗakinsa, ita ma ta miƙe ta nufi nata ɗakin domin alwala da sallah. Washegari da misalin ƙarfe ɗaya na rana, Zahra na kitchen tare da Farida suna girki. Ita ce ke guiding ɗinta lokaci zuwa lokaci saboda tana son komai ya kammala kafin ƙarfe biyu. Ƙamshin girkin ya cika kitchen ɗin gaba ɗaya. Da taga komai ya kusa kammala, sai tace, “Farida idan ya nuna ya gama sai ki kwashe ki zuba a warmer nan. Daga nan ki kai dining, sannan ki fito min da zobon dake fridge ki kai shi ma.” “Toh shikenan Hajiya,” Farida ta amsa cikin girmamawa. Zahra ta gyada kai sannan ta fita daga kitchen ɗin ta wuce sama. Wanka ta shiga tayi. Bayan ta fito ta shafa mai sannan ta saka wani fitted gown mai bala’in kyau. Kayan sun zauna a jikinta tamkar an zana su. Ta yi daurin ture kaga tsiya, sannan ta feshe jikinta da turare masu sanyin ƙamshi. Tana gyara mirror taji an buɗe gate ɗin gidan. Da sauri ta leƙa ta window taga Ibrahim ne ya shigo da motarsa. Wani murmushi mai sanyi ya bayyana a fuskarta kafin ta sake labulen. Can ba’a jima ba sai gashi ya hauro sama. Da jin takunsa, ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito. Yana dai-dai dosar ƙofar suka haɗu. Karasowa tayi ta karɓi jakkarsa tana murmushi. “Sannu da zuwa mijina.” Ya kalleta daga sama har ƙasa kafin murmushi ya suɓuce masa. “Yauwa matata.” Hannunsa ta kama tana jansa ciki. “Ka shiga kayi wanka, na saka maka ruwan wanka. Idan ka fito kuma sai muje muyi lunch.” “Alright Zahratyy na.” Daga haka ya wuce toilet, ita kuma ta fito masa da kayan da zai saka ta aje saman gado sannan ta zauna tana jiransa. Bayan wasu mintuna ya fito daga toilet ɗin cikin fresh look, yana goge gashinsa da towel. Kayan da ta fito masa dasu ya saka, ƙamshin sabulunsa na gaurayawa da nata turaren. Bayan ya gama saka kayan, idanunsa suka sauka akanta. “Kin yi kyau sosai yau.” Murmushi tayi tana ɗan sunkuyar da kanta. “Thank you.” Sai ya ƙaraso kusa da ita ya ɗan taɓa haɓarta. “Very beautiful wife.” Daga haka suka sauka ƙasa tare zuwa dining area. Dining table ɗin ya cika da abinci kala-kala da suka girka. Zobo mai sanyi na gefe sai kamshi ke tashi “Wow...” Ibrahim ya faɗa yana kallon abincin. “Da alama yau akwai special treatment.” “Maybe,” tace tana murmushi. Zama sukayi suka fara lunch ɗin. Lokaci zuwa lokaci Ibrahim na debo mata abinci yana bata a baki, ita ma tana mayar masa. Dariya da hira mai daɗi ne a tsakanin su. “Open your mouth,” ya faɗa yana miƙa mata spoon. Ta buɗe baki tana dariya “Good girl.” ya ce Ita ma ta debo masa chicken tana cewa, “Yau kai ne patient dina.” “Idan ke ce nurse ɗin, zan yarda.” Duk suka yi dariya. Bayan sun gama cin abincin, Zahra ta kwanta a jikinsa akan parlorn chair tana hutawa yayin da yake shafa hannunta. Can kuma sai ta ji wani irin tashin zuciya. Nan take ta tashi kaɗan tana dafe ƙirji. Kallonta yayi cikin damuwa. “Lafiya?” “Amai nake ji...” Nan take ya fara shafa bayanta a hankali. “Sannu... maybe abincin ne.” Kafin su ƙara magana aka buɗe ƙofar parlorn aka shigo ciki. Duk tunaninsu Farida ce, saboda haka babu wanda ya juya. Ibrahim duk hankalinsa yana kan Zahra ne. Sai dai da Zahra ta ɗago kai, idanunta suka haɗu da Mummy. Da sauri ta miƙe ta ja kujera baya sannan ta nufi toilet a guje. “Mummy...” Ibrahim ya faɗa cikin mamaki yana miƙewa. Mummy ta ƙaraso parlorn ɗin da sallama a bakinta. “Wa alaikum salam,” ya amsa cikin girmamawa kafin yayi saurin bin bayan Zahra. A toilet ya same ta tana amai. “Sannu baby...” yake ta faɗa yana riƙe mata baya. Bayan ta gama, ya buɗe ruwa ya wanke mata fuskarta cikin kulawa sannan ya gyara wajen kafin ya fito da ita. A parlorn ta zauna tana maida numfashi. Mummy kuwa sai sannu take mata. “Sannu daughter... meke damunki ne?” Zahra ta ɗan gyara zama. “Ina wuni Mummy.” “Lafiya lau,” Mummy ta amsa. “Sannu. Dama daga aiki na taso nazo na dubaki. Ashe baki gama warkewa ba.” Murmushi kawai Zahra tayi cikin sanyin jiki. A lokacin Ibrahim ya fito daga toilet ya ƙaraso parlorn. #Jiddatulkhayr writes #08110615256 FARASHIN IZZAH Jiddatulkhayr writes Book 1 Chapter 16 Ya gaida Mummy cikin girmamawa, ita kuma ta amsa tana tambayar, “Ya jikin Zahra?” “Da sauƙi,” ya amsa yana kallon Zahra cikin kulawa. Daga haka ya miƙe zai shiga ciki. Mummy ma ta miƙe tana gyara hijabinta. Ta tsaya tana kallon Zahra tace, “Allah baki lafiya daughter.” A hankali Zahra tace, “Ameen.” “Bari na tafi yanzu ko” “Thank you Mummy,” Zahra ta faɗa cikin girmamawa. Murmushi Mummy tayi sannan ta fita. Bayan tafiyarta, Zahra ta gyara kwanciyarta akan kujera tana jin kasala sosai. Ta ce “Kaza nake son ci”. Kafin ma Ibrahim ya dawo daga sama, bacci ya sake ɗaukarta. Saukowa daga stairs yayi yana gyara hannun rigarsa, idanunsa suka sauka akanta tana bacci luf a kujera, sai ya tsaya yana kallonta cikin tausayi da ƙauna. A hankali Ibrahim ya ɗauki keys ɗin motarsa sannan ya sake kallon Zahra dake bacci a parlorn. Blanket ya ƙara gyara mata kafin ya fita daga gidan cikin nutsuwa kada hayaniyar ƙofar ta tasheta. Kai tsaye wani classy eatery ya nufa. Da ya isa, parking yayi sannan ya fito daga motar yana gyara agogonsa. Wajen ya cika da ƙamshin grilled food da hayaniyar mutane kaɗan-kaɗan. Shiga yayi ciki, wani waiter ya ƙaraso da murmushi. “Good evening sir.” “Evening. Ina son grilled chicken, spicy sosai… sannan ku haɗa da fries da chilled juice.” “Okay sir.” Ya tsaya jingine a counter yana jiran order ɗin. Lokaci zuwa lokaci yana duba wayarsa. A zuciyarsa yana tunanin yadda Zahra ta faɗi tana cewa kaza take son ci kafin bacci ya kwasheta. Bayan an gama packing ɗin, ya karɓa ya biya kuɗi sannan ya fita zuwa motarsa. A hanyarsa ta dawowa ne wayarsa ta fara ringing. Ɗaga wayar yayi yana kallon screen ɗin. Unknown number ne. Yatsansa ya ɗan tsaya akan screen ɗin kafin ya ɗaga call ɗin. “Hello?” Wanda ya kiran kuma yayi shiru. Sai ƙaran numfashi kawai ya ɗan ji daga ɗaya ɓangaren. Fuskar Ibrahim ta ɗan canza. “Who’s this?” Har lokacin babu amsa. A hankali ya tsuke fuska sannan ya katse call ɗin ya ajiye wayar a gefe. Bai jima ba aka sake kira. Da sauri ya kalli number ɗin ɗaya ne. Wannan karon bai ɗaga ba, ya share wayar gefe yana cigaba da driving. A haka ya isa gida. Yana shiga compound ɗin, idanunsa suka ɗan ɗaga zuwa balcony ɗin saman gidan kafin ya fito daga motar da ledar grilled chicken ɗin hannunsa. Ciki ya wuce cikin sauri yana son ya ga ko Zahra ta tashi daga baccin nata. Yana shiga parlorn ɗin ya tsaya yana kallonta. Har yanzu bacci take yi cikin nutsuwa, kanta na kwance jikin cushion ɗin kujera yayin da blanket ɗin da ya rufe mata ya ɗan zame gefe. Murmushi yayi a hankali yana girgiza kai. “Baby na…” ya furta ƙasa-ƙasa. Ledar grilled chicken ɗin ya aje saman center table sannan ya sunkuya kusa da ita. Yaso ya ɗagata ya kai ɗaki amma kallon yadda take bacci cikin comfort yasa ya fasa. A hankali ya zauna ƙasa akan carpet ɗin, daga nan kuma ya kwanta ya jingina kansa a jikinta, hannunsa ɗaya na riƙe da nata. A cikin bacci Zahra ta ɗan motsa tana maida hannunta cikin nasa tamkar tasan shi ne. Wani lallausan murmushi ya suɓuce masa. “Sleepy wife…” AC ɗin parlorn na busawa a hankali yayin da hasken evening lamp ke bada wani irin calming atmosphere. Gajiyar yini da sanyin wajen suka fara ɗaukar Ibrahim ma. Idanunsa suka fara rufewa a hankali yana jin ƙamshin turaren Zahra. Kafin wani lokaci ma, bacci ya kwashe sa shima a wajen Zahra na kwance saman kujera cikin natsuwa, Ibrahim kuma na kwance a jikinta akan carpet, hannayensu sarƙafe cikin na juna kamar wasu yara ƙanana da suka gaji da wasa. Farida tana zaune a dakinta, gaba ɗaya ta mayar da hankalinta kan kallon TV. Sai kawai ta ji wayarta na vibration. Ta kalli inda wayar take, sannan ta kau da kai ta mayar da hankalinta kan TV ɗin kamar ba ta ji ba dan bata kaunar abun da zai hana ta kallonta Amma da ta tuna wanda ke kira, sai ta mike da sauri ta je ta dauko wayar. Ta daga, ta kai kunne tare da sallama a hankali. Magana take kasa-kasa take yi, ta fara sauraron abin da ake ce mata. Daga bisani ta ce, “Eh, toh gaskiya ban ga wani abu ba… kuma ai mijinta yana gida.” Ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ƙara da cewa, “Eh… wata mata ma ta zo.” A hankali ta ce, “Kaiii… gaskiya ni dai ina tsoro.” Bayan wanda ke kiran ya ƙara gaya mata wani abu, sai ta mike da sauri ta nufi kofar dakin. Ta bude a hankali tana leƙawa parlorn, sannan ta ja baya ta rufe kofar. Ta ce, “Eh… yanzu dai na gansu, ita da shi duk suna bacci a parlorn su na kasa.” Bayan ɗan lokaci ta sauke ajiyar zuciya. Sannan ta ce, “Toh zan gwada….” A nan aka katse wayar. Ta ajiye wayar, sannan ta koma ta zauna ta cigaba da kallon TV ɗin, amma zuciyarta ta riga ta shiga cikin tunani, rabi da kwata ba ta ma san abin da take kallo ba Can da magriba ta yi, sai ga Ibrahim ya farka. Ya ɗan zauna yana kallon parlorn cikin nutsuwa, idanuwansa na bin ko’ina kamar yana duba yanayi. Daga bisani ya kalli agogo, sannan a hankali ya maida hankalinsa kan Zahra da ke zaune. Ya matso kusa da ita a hankali, sannan ya fara tashinta. Zahra ta motsa idanu tana budewa sannu a hankali, “Meke kamshi?” ta tambaya cikin kasala. Ibrahim ya ɗan yi murmushi, ya nuna mata center table ɗin da ke gabansu. Ta miƙa hannu ta ɗauka, ta fara buɗewa tana duba abin da ke ciki. Shi kuma ya miƙe, ya nufi hanyar sama, sai kuma ya juya yana kallonta da husky voice dinsa ya ce, “Better stand up… kar ayi sallah kina zaune.” Zahra ta gyada kai da ɗan murmushi, idanuwanta har sannan a cike yake da bacci Ganin ya juya kawai ta bude laidar ta fara cin abunta Ibrahim ya tsaya daga sama ya kalleta ya sake cewa cikin taushi, “Please, pray first… sai ki zo ki ci.” Wannan ya sa murmushi ya kubuce mata. Ta miƙe a hankali, ta nufi sama domin yin sallah. Washegari da safe, bayan Ibrahim ya dawo daga masallacin asuba, gidan gaba daya ya cika da kamshin turare, one thing da yake son zahra akwai son tsafta da kamshi Samunta yayi suka hadu tare suka yi breakfast Zahra ta yi serving cikin so da kulawa, ta zuba tea mai ɗumi a cups, ta shirya bread da eggs a plate, sannan ta ƙara fruit a plate, ta dauko burger ta ajiye shima Ibrahim kuwa yana zaune yana kallonta, murmushi a fuska, yana jin dadin yadda take tafiyar da komai ba tare da hayaniya ba. Suka fara breakfast dinsu cikin so, Ibrahim ya ɗaga kai ya kalli Zahra ya ce, “Idan mun dawo yau, zamu je mu gaida Mama.” Zahra ta amsa cikin ladabi, “Allah ya kaimu.” Sannan ta ƙara da murmushi, “Ko lectures ɗin yamma aka sa yau zan dawo, ba zan wani tsaya ba” Ibrahim ya kalle ta kai tsaye, “No, babu ruwa na.” Ta yi dariya Ya sake tambaya cikin wasa, “Ya baki ci?” Ta ce, “Awara nake so. Zan bari idan na shiga school sai na saya.” Ya gyada kai, “Alright.” Bayan sun gama, suka tattara komai suka haura sama domin yin wanka. Daga baya suka sake saukowa ƙasa cikin shiri. Dukansu sun shirya tsaf, kowa cikin shirin fita, keys din ya dauko musu, ya mika mata nata Suna fita compound already an wanke musu motocinsu, ko wanne ya karasa wajen motarsa, a haka suka bar gidan. A gaban department ɗinsu Zahra ta yi parking motarta. Ta zauna a ciki na ɗan lokaci kamar ba zata sauka ba. Idanuwanta a lumshe, zuciyarta cike da nauyin abubuwan da ke mata yawo a kai. Daga ƙarshe ta sauke ajiyar zuciya, ta buɗe motar ta sauka. Class ɗin ta wuce kai tsaye. Bayan sun kammala lectures na ƙarfe 12, bata ji tana da ƙarfin zama a makarantar ba. Duk maganganun da ta yi da ita sun tsaya mata a rai, suna mata nauyi fiye da yadda ta zata. A hanya zuwa gida, ta tsaya a wani lungu ta sauka daga mota. Ta shiga cikin karamin unguwa inda akwai mutane zaune a waje. Da ta shigo, duk da cewa ta saka face mask, hakan bai hana tsohuwa dake zaune a baranda gane ta ba. Nan take fuskarta ta haska da murmushi mai kyau. “Zahra!” tsohuwar ta kira cikin murna. Zahra ta ɗan yi murmushi ta ƙarasa kusa da su, ta gaishe su cikin ladabi. Tsohuwar ta amsa da fara’a tana kallonta da kauna. A gefe kuwa wata budurwar matashiya ce ta fito daga cikin gida, tana ganin Zahra sai ta saki murmushi mai faɗi har da nuna farin ciki sosai. Ta yi saurin ƙaraso ta tsaya kusa da ita tana kallonta kamar wacce ta dade bata ganta ba. “Hajiya Fatima ke ce?” ta ce cikin murna. Zahra ta ɗan yi dariya a hankali, tana gyara face mask dinta da kyau dan bata so ya sauka aga fuskanta “Eh, na dawo,” ta amsa cikin nutsuwa. Wannan tsohuwa ta ɗaga hannu tana murmushi, ta c “Kiyi hakuri nasan ba kinga sakon mu mun kuma dago ki” Zahra ta ɗan sunkuyar da kai cikin kunya. “Kar ki damu Mama” Matashiyar matar tace ki zauna mana kar ki gaji da tsayuwar, murmushi kawai zahra tayi Matashiyar matar ta ƙaraso kusa da Zahra tana murmushi ta shimfida mata sallaya ta ce “Sannu anty Zahra, ki dan zauna kar kafar ki ya gaji” Wani ƙaramin yaro ne daya shigo daga waje ya yi saurin nufar Zahra da gudu kamar zai rungumeta, mahaifiyarsa ta yi saurin riƙe shi. “Kar ka bata mata jiki mana,” tace cikin lallashi. Zahra kuwa dariya kawai tayi tana kallon yaron. “A’a kyale shi mana.” Sai kuma ta kalli matar tace, “Ina sauran? Suna zuwa makaranta kuwa?” “Eh,” matar ta amsa. “Duk suna school yanzu.” Kai Zahra ta gyada a hankali. Daga handbag ɗinta ta ciro envelopes guda biyu ta ajiye musu. Matashiyar matar ta zaro ido. “Anty Zahra wannan kuma….” Amma kafin ta ƙarasa magana, Zahra ta ɗaga mata hannu alamar tayi shiru , ajiye musu tayi Daga haka ta juya zata fita ba tare data jira godiya ko surutu ba. A wajen motarta kuma wasu yara ne suke wasa kusa da titi. Ta kira su. “Kuzo nan.” Da gudu suka taho wajen motar. Ta buɗe booth ɗin motar, wanda ke cike da ledojin kayan abinci da wasu kayayyaki. “Ku kwashe ku kai ciki.” “Toh anty!” suka amsa cikin murna. Nan take suka fara ɗaukar kayan suna kaiwa cikin gidan, kowanne na son ya nuna ƙoƙari. Zahra ta tsaya tana kallonsu na ɗan lokaci. Wani irin nutsuwa ne ya ratsa ta ganin farin cikin da abu kaɗan ya saka musu. Bayan ta tabbatar sun gama shiga da kayan, ta shiga mota ta tada ta nufi gida. A parlorn sama ta tarar da Ibrahim zaune a kujera, laptop ɗinsa a gabansa yana aiki a system ɗinsa. Glasses ɗin idonsa ya ɗan sauko ƙasa kaɗan yayin da hankalinsa ke kan screen. Ko kallonta bai yi da farko ba sai bayan ya ji motsinta. “Kin dawo?” “Hmm,” kawai ta amsa tana cire hijab ɗinta. Ya ɗan kalleta. “Ya lectures?” “Ba dadi ga masu karamin ciki irina” dariya dukkansu suka yi Sai ya lura da gajiyar dake tattare a fuskarta. “Kin ci wani abu kuwa?” Kai ta girgiza masa. “Ban jin yunwa.” Laptop ɗin ya rufe a hankali sannan ya miƙe. “Zahra…” Ta ɗago tana kallonsa. “Come here.” Ta tsaya tana kallonsa na ɗan lokaci kamar mai tunani, kafin daga ƙarshe ta ƙarasa kusa da shi a hankali. Tana isa, sai ya jawota jikinsa ya rungume ta. “Kin gaji sosai ko?” ya tambaya cikin ƙasa da murya. Zahra ta lumshe idanunta na ɗan daƙiƙa kaɗan. Duk da tana ƙoƙarin ɓoye damuwarta, zuciyarta tana son irin wannan kulawar tasa. A hankali tace, “Ka daina bani mixed feelings Ibrahim…” Ya ɗan ja baya yana kallonta. “Me yasa?” “Saboda duk lokacin da nace na tabbatar Kai din nawa ne sai daga baya ka nuna min wani gefenka” Wani ƙaramin murmushi yayi kafin ya shafa kumatunta a hankali. “Zahra mun Riga da mun wuce wancan stage din already, ki daina kawo abun daya riga ya wuce” “Yanzu tashi mu shirya,” Ibrahim yace yana kallonta. “Na faɗawa Mama cewa muna hanya.” Dariya Zahra tayi tana girgiza kai. “Ni fa jiya jin ka kawai nayi. Amma taya zamu je gidan Mama hannu sake? At least bari nayi girki mana.” Ibrahim ya ɗan lumshe ido yana kallonta da wani irin so. “Kin cika raina da soyayyar ki zahra” “Me kuma?” “Saboda duk da abubuwan daya faru… har yanzu kina ƙoƙarin kasancewa matar aure ta gari.” “Is okayyy” ta ce Ko ɗakinta bata shiga ba, kai tsaye ta sauka ƙasa. kitchen ta nufa, tana tunanin abincin da zata haɗa musu. Jim kaɗan sai taji knocking a ƙofar kitchen ɗin. Farida ce ta buɗe ƙofar tana gaidata cikin ladabi. “Ina wuni Hajiya.” “Lafiya lau,” Zahra ta amsa tana murmushi. “Ke kam ko gajiya da zaman ɗaki baki yi ne?” Farida dariya kawai tayi. “Toh fito ki tayani dafa abinci. Zamu kai gidan surkai ne.” “Toh Hajiya.” Zahra ta ce “Bari na ɗan huta kadan, sannan nazo mu haɗa hannu” “Toh… amma me zan dafa?” Farida ta tambaya “Komai ma ki dafa. Duk abin da ya dace da gidan surkai.” Farida ta gyada kai cikin sauri. “Toh shikenan.” Daga haka Zahra ta bar kitchen ɗin ta haura sama. Ko data shiga parlorn bata ga Ibrahim ba. Nan take ta fahimci ya shiga ɗakinsa ne saboda waya ko wani aiki. Ita kuma nata ɗakin ta nufa kai tsaye domin ta ɗan huta. Tana shiga ta kwanta akan gadonta, sai ta lumshe idanunta ta fada duniyar tunani Har ga Allah tana son mijinta fiye da zaton mai zata, Tana tuna yadda yake kallonta jiya da daddare. Yadda ya riƙe hannunta. Yadda yake ƙoƙarin lallashinta ko da bai iya furta nadamarsa yadda ya kamata ba. Wani ƙaramin murmushi ya suɓuce mata. A hankali ta rungume pillow ɗinta tana kallon ceiling. “Allah…” ta furta ƙasa-ƙasa. Saboda ita kanta ta fara jin tsoron yadda take ƙara son mijinta har cikin ranta Afuwan da Jina shiru kwana biyu, na rasa wayata sai jihya na sayi wani, Nagode. FARASHIN IZZAH Jiddatulkhayr writes Young talented writers ass.. (YOTA) Book 1 Chapter 17 Kitchen ɗin gaba ɗaya ya ɗauki ƙamshin girkinta mai daɗi. Farida na tsaye tana miyan kayan lambu yayin da Zahra ke haɗa spicy jollof rice ɗin da ta dafa da chicken mai dadi, Gefe kuma akwai fried meat da salad da suka haɗa cheffing dish “Wallahi Hajiya kin iya girki,” Farida tace tana murmushi. Zahra ta ɗan yi dariya. “Da gaske?” “Eh mana, tun da na fara jin ƙamshin shikenan na fara ji yunwa.” “Ke dai bari kawai,” Zahra tace tana ɗan motsa cokalin hannunta. “Maman Oga tana son abinci mai ɗan haɗi ne shiyasa nace bari muyi abin kirki.” “Toh ai zata ji daɗi sosai.” Bayan sun gama komai, suka fara zubawa a warmers masu kyau. Zahra na gyara yadda komai zai yi neat cikin basket ɗin. “Wannan salad ɗin ki saka a gefe.” Cewar Zarah “Toh Hajiya.” “Kar chicken ɗin ya zube fa.” Dariya Farida tayi. “Toh.” Bayan sun gama jera komai cikin basket mai kyau, Zahra ta sauke numfashi tana kallon abincin. “Alhamdulillah.” Farida tace, “Hajiya ki tafi ki shirya yanzu, ni zan gyara kitchen.” “Kin gaji fah” inji Zahra “A’a wallahi.” Murmushi Zahra tayi sannan ta juya ta fita, haurawa sama tayi Tana shiga ɗakinta ta samu Ibrahim zaune bakin gado yana duba wayarsa. Ya ɗaga kai suka haɗa ido, kallonta kawai ya tsaya yi. “Me?” Zahra tace tana murmushi kaɗan. “Kin ƙara kyau ne ko ido nane” Dariya tayi tana cire hijab ɗinta. “Ka bari Noory.” Ya miƙe ya ƙaraso kusa da ita. “An gama girkin?” “Eh.” “Hmm… Zahra matar aure.” Ta tura shi kaɗan tana dariya. “Please bari nayi wanka.” “Toh madam.” Toilet ta shiga. Ruwa mai ɗumi ta kunna tana jin gajiyar jikinta na sauka a hankali. Bayan ta gama ta fito jikinta na ƙamshin gel tare da kamshin turaren wanka Wani dogon gown mai matuƙar kyau ta saka, colour ɗin wine mai ɗan haske, hannayensa cike da stones masu kyalli. Veil ɗinta kuwa ya yi matching da kayan. Ta tsaya gaban mirror tana ɗan gyara lips ɗinta. A baya Ibrahim ya tsaya yana kallonta ta mirror. “Zahra…” “Hmm?” “Kin sani ko? Duk lokacin da kika shirya haka bana son fita da ke saboda kowa sai ya tsaya kallon matata.” Ta ɗan cije lips ɗinta tana murmushi. “Drama king.” Shi ma ya shirya cikin wata black native mai matuƙar kyau. Agogon hannunsa da turarensa suka ƙara fito da ƙyansa sosai. Bayan sun gama, suka fito tare. A parlorn ƙasa Ibrahim ne ya ɗauki basket ɗin warmers ɗin. Zahra ta kalleshi tace, “Bari na ɗauka mana.” “Karki damu.” Suka fito tare har zuwa wajen motar, suka shiga, Ibrahim ya kunna wata soft love song mai sanyin gaske. A hankali motar ke tafiya yayin da song ɗin ke tashi. Zahra ta jingina kanta jikin seat tana kallon waje, Ibrahim kuma lokaci zuwa lokaci yana kallonta yana murmushi. “Me kuma?” tace bayan ta kamashi yana kallo. “Nothing… ina kallon matata ne kawai.” Ta ɗan kau da kai tana murmushi. Haka suka isa gidan Mama. A compound Ibrahim yayi parking. Ya fito ya zagaya ya buɗe mata ƙofa. Ita kuma ta sauko a hankali yayin da shi ya ɗauki basket ɗin warmers ɗin. Tare suka shiga ciki. Suna shiga kuwa suka haɗu da Mama, shigowarta kenan daga backyard . Tsayawa tayi tana kallonsu, musamman basket ɗin dake hannun Ibrahim. “To oo…” tace tana ɗan ɗaga gira. “Yanzu Ibrahim kai ne da ɗaukar basket? Ko dai dama da gaske ne abinda naji?” Nan take Zahra taji wani iri a ranta, ta ɗan sunkuyar da kai. Ibrahim ma wani iri yaji, amma sai yayi saurin cewa, “Haba Mama ai kinsan Zahra ba lafiya take da shi ba” Sai Mama tayi murmushi irin na manya. “Toh ku shigo mana, kun tsaya a bakin ƙofa.” “Ai Mama ke kika tsayar da mu,” Ibrahim ya amsa. Shiga suka yi. Zahra ta zauna a parlorn tana jin kanta not comfortable kwata-kwata. Ita kanta batasan dalilin da yasa maganar ta tsaya mata a rai haka ba. Ibrahim kuwa dining ya wuce ya ajiye basket ɗin. Yana juyowa zuciyarsa ta ɗan cunkushe. Haka kawai yaji bai so abin da Mama tayi ba. Musamman ganin yadda fuskar Zahra ta canza a take. A parlorn suka zauna tare da Mama suna hira lokaci zuwa lokaci. Mama ta tambayi Zahra ya jikinta, ya makaranta, ita kuma tana amsawa cikin ladabi duk da zuciyarta bata gama sakin jiki ba. Ibrahim kuwa ya lura da canjin Zahra tun bayan maganar basket ɗin, yasan pretending take yi wajen faking murmushi, shiyasa lokaci zuwa lokaci yana kallonta idan Mama bata kula ba. Har aka kira sallar magrib suna gidan. Ibrahim ya tashi ya tafi masallaci, bayan ya dawo sannan suka dawo parlorn suka ci abincin da Zahra ta kawo. Mama ma ta yaba sosai da girkin. “Zahra kin iya girki sosai,” Mama tace tana ɗan ɗiba miyan. Murmushi kawai Zahra tayi. “Nagode Mama.” A haka suka gama dinner. Bayan sun ɗan zauna kuma, suka yi wa Mama sallama. “Allah ya kai ku lafiya,” Mama tace. “Ameen,” suka amsa tare. A cikin mota kuwa daga Zahra har Ibrahim babu wanda yace komai. Song ɗin da aka kunna ma a hankali yake tashi amma dukansu suna cikin nasu tunanin. Ibrahim ya ɗan kalleta sau biyu amma bata ɗago ba. Sai kawai ya juya steering ya tsaya a wani eatery mai kyau. Ta ɗan kalleshi. “Me kuma?” “Mu ci abinci.” “Ai mun ci a gidan Mama.” “Still…” Bata ƙara magana ba suka shiga ciki. Wajen ya yi sanyi da haske mai kyau. Suka zauna a wani corner mai nutsuwa sannan suka yi order. Zahra ta ɗauki noodles da chicken, shi kuma ya ɗauki burger da drink. Duk da suna cin abinci ne, akwai wani irin shiru tsakanin su. A ƙarshe Ibrahim ya sauke spoon ɗinsa yace, “Zahra…” Ta ɗago tana kallonsa. “I’m sorry.” Shiru tayi. “Ban so yadda Mama tayi magana ɗazun ba.” “Ai babu komai,” ta amsa a hankali. “Da gaske?” Kai ta gyada masa. “Please kar ka damu.” Yadda tayi maganar yasa ya ɗan sake. A hankali ya kamo hannunta saman table ɗin. “Thank you.” Ta ɗan murmusa masa. “Ka daina wannan worried face ɗin.” Daga haka ya ɗan saki jiki suka fara hira kaɗan-kaɗan. Har dariya Zahra tayi lokacin da Ibrahim ya fara bata labarin wani abu da ya faru a office. Da suka fito daga eatery ɗin, yanayin dake tsakaninsu ya ɗan lafa. A mota ma Ibrahim ya riƙe hannunta yana driving da hannu ɗaya. Ita kuma duk da zuciyarta bata gama warkewa ba, tayi ƙoƙarin nuna masa komai lafiya ne saboda taga ya damu sosai. Da suka isa gida, Ibrahim ya wuce toilet domin yayi wanka. Ita kuma Zahra kitchen ta tsaya tana duba wasu abubuwa kafin daga baya ta haura sama. Tana shiga ɗakin, idanunta suka sauka kan wayarsa dake gefe tana ringing. Sunan da aka yi saving ɗin number ɗin yasa gabanta ya faɗi. “Lovie Dovie…” Wani irin abu taji ya tsinka mata zuciya. Wayar ta daina ringing. Sai kuma wani call ɗin ya sake shigowa. Kafafuwanta kamar sun manne a wajen. Har ta matsa zata ɗauki wayar… sai kuma ta fasa. Wani irin zafi taji a zuciyarta. Jin motsin Ibrahim zai fito yasa ta bar wajen da sauri. Gaba ɗaya mood ɗinta ya canza. Kai tsaye toilet ta shiga itama dan tayi wanka ba tare data sake kallon inda wayar take ba. Bayan ta fito tana saka kaya, Ibrahim kuma yana gyara sleeve ɗin kayansa a mirror. Sai kuma wayar ta sake ringing. A wannan karon Zahra ta sace kallon wajen. Shi ma Ibrahim ɗin ya ɗaga kai ya kalli wayar. Da ganin number ɗin, nan take ya ƙarasa ya ɗauki wayar ya mayar silent sannan ya saka a aljihu. Sai kuma ya juya da sauri yana kallon Zahra. Ita kuwa tayi kamar hankalinta baya kansa kwata-kwata. Ga mamakinta, sai kawai ya fita daga ɗakin. Zahra ta tsaya tana kallon ƙofar bayan ya fita. A hankali ta ƙarasa bakin gado ta zauna. Ta dauki lokaci ba tare data san tana wajen ba Mintuna suna wucewa… Tara… Goma… Har ƙarfe goma sha ɗaya na dare Ibrahim bai dawo ba. Yanzu kam abin ya fara damun Zahra sosai. Jikinta har rawa yake yi. Ta rungume pillow tana ƙoƙarin hana kanta tunani, amma ta kasa. Batasan sanda hawaye suka fara zubo mata ba. Tasani sarai… idan har ta fita nemansa a wannan lokacin, babu abin da bazata iya aikatawa ba saboda ɓacin rai. A haka bacci ya ɗauke ta cikin kuka da ciwon zuciya. Can cikin dare ta farka a firgice. Da sauri ta kai dubanta gefen gadon. Baya ɗakin. Wani irin mamaki ne ya kamata. Tun daga ranar da suka shirya bayan dawowarta daga gidan su, Ibrahim bai taɓa barinta ta kwana ita kaɗai ba. Sai yau… Sai da wannan “Lovie Dovie” ɗin ta kira shi. Sosai Zahra ta shiga damuwa. Tun daga lokacin da ta farka taga Ibrahim baya ɗakin, zuciyarta ta kasa samun nutsuwa. Wani irin tunani ne ya fara yawo a kanta—tun daga kan “Lovie Dovie” ɗin har zuwa fitarsa daga ɗakin ba tare da ya dawo ba. Ta juya gefe tana ƙoƙarin danne tunanin, amma hakan ya gagara. Daga ƙarshe dai gajiyar kuka da tunani ne suka rinjaye ta, bacci ya sake ɗaukarta. Da asuba ta sake farkawa. Da sauri idanunta suka nufi gefen gadon. Har yanzu babu Ibrahim. Wani irin sanyi taji ya ratsa zuciyarta. Ta daɗe zaune tana kallon wajen kamar tana jiran kawai ya buɗe ƙofa ya shigo. Amma shiru. A hankali ta sauke ƙafafunta daga kan gadon. Gabanta na mata wani irin nauyi. Toilet ta shiga tayi alwala sannan ta fito ta tada sallah. Bayan ta idar, bata tashi daga sallayar ba. Kwanciya tayi a kanta tana kallon ceiling, idanuwanta cike da tunani da ciwon zuciya. Can taji an buɗe ƙofa. Ibrahim ne ya shigo. Da sauri ta miƙe ta zauna akan sallayar. Ko kallonsa bata yi sosai ba tace, “Ina kwana.” “Lafiya,” ya amsa a taƙaice. Muryarsa kaɗai ta sake ɗaure mata zuciya. Ya tsaya na ɗan lokaci kamar zai yi magana, sai kuma ya juya ya fita daga ɗakin. Zahra ta bishi da kallo har ya fita, sannan ta sauke idanunta tana jin zuciyarta na mata nauyi fiye da da. Kai tsaye kitchen ya wuce. Bayan wasu mintuna ita ma ta sauka ƙasa. Tana shiga kitchen ta samu Farida har tayi morning. Irish take ferewa a hankali. “Ina kwana Hajiya,” Farida ta gaidata cikin fara’a. “Lafiya,” Zahra ta amsa da ƙyar. Kitchen ɗin ma gaba ɗaya sai taji bata son ganinsa. Kamar komai a gidan yana tunasar da ita Ibrahim ne. Bata tsaya ba ta juya ta fita. Ta koma sama. Tana shiga ɗakin taga baya nan, hakan ya ɗan bata sauƙi. Kai tsaye toilet ta shiga tayi wanka. Bayan ta fito ta fara shirinta na makaranta cikin sauri. Wani plain gown mai kyau ta saka tare da hijab. Bata tsaya wani gyara sosai ba. Abu ɗaya kawai take ji… Bata son duk wani abin da zai haɗata da Ibrahim yau. Yau gara ta fita ta bashi space ɗinsa, saboda idan ta ci gaba da kallonsa zata iya kasa ɓoye damuwar dake ranta…. To her own surprise, Zahra ta gama shirya wa cikin lokaci ƙanƙani. Ita kanta batasan yadda ta iya haɗa kanta haka ba. Tana gyara hijab ɗinta a mirror kawai sai taji ƙarar buɗe gate. Da sauri ta matsa ta buɗe curtain ɗin ɗakinta. Motar Ibrahim ce ke fita da sauri daga compound. Kamar an dasata a wajen haka ta tsaya cak. Wani irin abu taji ya tsaya mata a zuciya ganin har ya fita bai mata sallama ba. Ko message babu. Ko knocking ɗin ƙofa bai yi ba. Sai yanzu taji ainihin nauyin abin da yake mata. A hankali ta ɗauki school bag ɗinta da key ɗin mota sannan ta sauka ƙasa. Farida na tsaye a dining tana gyara plates. “Hajiya yau ba zaku karya bane?” Kai Zahra ta gyada mata kawai ba tare data tsaya ba. Daga haka ta fita. Har ta isa school bata san yadda tayi driving ɗin ba. Hankalinta gaba ɗaya baya jikinta. A bakin hall ta hango friends ɗinta—Firdausi, Asiya da Suhaima. Suhaima ce ta fara magana tana kallonta sama da ƙasa. “Nikam ni kaɗai naga sai glowing Zahra ke yi?” Wani murmushin yaƙe Zahra tayi kawai sannan ta juya gefe saboda bata da interest a hirar. Firdausi ta lura da yanayinta, shiyasa itama bata ƙara mata magana ba. Daga haka suka shiga lecture hall ɗin tare. Lecturer na shigowa ya fara teaching ɗinsu kai tsaye. Students da yawa na rubutu, wasu na tambaya, wasu kuma hankali tasu na kan board. Amma Zahra… Ko kaɗan bata tare da su a wajen. Pen ɗin dake hannunta ma juyawa kawai take yi. Idanuwanta na kan lecturer amma hankalinta gaba ɗaya yana wani wajen. Tunani take….. Ina Ibrahim ya kwana? Wacece “Lovie Dovie?” Me yasa ya fita haka ba tare da ya dawo ɗakin ba? “Mrs Ibrahim…” Sai taji an kira sunanta. Da sauri ta ɗago. Lecturer ɗin ne yake kallonta. “Can you answer the question?” Wani irin ruɗani ya kamata. Bata ma san wace tambaya yayi ba. Hall ɗin gaba ɗaya suka juya suna kallonta. Firdausi tayi saurin tura mata notebook ɗinta ƙasa-ƙasa tana nuna mata inda lecturer ɗin ya tsaya. Sai Zahra tace da ƙyar, “I’m sorry sir…” Lecturer ɗin ya ɗan girgiza kai. “You need to concentrate.” “Yes sir.” Ta zauna a hankali tana jin kunya na rufeta. Firdausi ta matsa kusa da ita kaɗan. “Zahra lafiya kuwa?” Kai ta girgiza mata. “I’m fine.” Amma ita kanta tasan ba fine ɗin bane ko kaɗan. Zuciyarta gaba ɗaya a cunkushe take kamar zata fashe. #08110615256 FARASHIN IZZAH Book 1 Chapter 18 Bayan sun fito daga lecture ɗin ne aka sanar musu cewa supervisor ɗinsu yana neman duk 'yan group ɗinsu. Zahra na tsaye tare da friends ɗinta amma ko kaɗan bata ma fahimci me aka ce ba. Firdausi ce ta matsa kusa da ita ta maimaita mata a hankali. "Supervisor na neman 'yan group dinku Zahra" Kai Zahra ta gyada kawai ka. Firdausi ta riƙe jakar hannunta sannan suka fara tafiya a hankali suna bin bayan sauran 'yan group ɗin. Bayan sun isa office ɗin, supervisor ɗin ma kallon Zahra kawai yake yi. Daga gani ba cikin normal state take ba kwata-kwata. Ko fara'ar da aka santa da ita babu. Firdausi tayi saurin magana kafin ya tambaya. "Sir bata jin daɗi ne, kuma zata tafi antenatal." "Okay," ya amsa yana kallon Zahra. "You can go. Duk gyaranki zaki gani a hardcopy ɗinki." "Nagode sir," Zahra ta amsa da ƙyar. Daga haka suka fito tare. Tun daga office ɗin har zuwa parking lot babu wanda yace uffan Sai da suka isa wajen motar Zahra suka shiga. Zahra na saka seat belt ta juya tana kallon Firdausi. "Ya akayi kika san I need rest har kika ƙirƙiri ƙarya wa supervisor na?" Murmushi Firdausi tayi. "Zahra idan ban san ki ba, ban cancanci na zama kawa a gareki ba." Ta ɗan tsaya sannan tace, "Zahra yanzu tada motar mu bar makarantar nan." Ba musu Zahra ta tada motar suka fara tafiya. Na ɗan lokaci shiru ne ya mamaye motar. Sai Firdausi ta kalleta. "Zahra meke damunki?" "Nothing." Dariya Firdausi tayi tana girgiza kai. "Zahra bamu saba haka dake ba, kar mu fara." Shiru Zahra tayi tana kallon titi. "Kema kin san nasan ba haka kike ba," Firdausi ta ƙara faɗa cikin tausasawa. "Na zame ki ne a school saboda bana son su Asiya su fahimci wani abu." Sai ta ɗan rage murya "Akan ke da Ibrahim ne ko?" Wani numfashi Zahra ta sauke. A hankali tace, "Firdausi... zuciyata zata buga." Firdausi ta juya da sauri tana kallonta. "Me ya faru?" "Ibrahim zai kashe ni..." muryarta ta ƙarshe tana rawa. Da sauri Firdausi tace, "Haba Zahra! Ki daina irin wannan maganar." Hawaye suka cika idanun Zahra. "Wallahi bana jin dadin raina... tun jiya." Ta ɗan cije lips ɗinta tana ƙoƙarin hana kukanta fita "Na fara jin tsoron abubuwan da nake gani da wanda bana gani..." Nan take Zahra ta fara bata labarin komai. Tun daga yadda suka dawo daga gidan Mama cikin so da kauna, yadda Ibrahim ya nuna mata kulawa har ta tausaya masa ta manta da damuwarta na ɗan lokaci akan reaction din Mama "Mun dawo gida lafiya..." Zahra tace tana kallon gaba. "Har naji maybe ina overthinking ne..." Firdausi bata katseta ba, sai kallonta take yi. "Yana toilet ni kuma na tsaya a kitchen kafin na haura sama." Ta haɗiye wani abu mai nauyi a maƙoshi. "Da na shiga ɗaki... sai naga wayarsa na ringing." "Hmm..." kawai Firdausi ta iya cewa Zahra ta ce "An yi saving number ɗin da... 'Lovie Dovie.'" Firdausi ta ɗan zaro ido. "What?" Kai Zahra ta gyada a hankali. "Da farko ma bansan me naji ba. Kawai zuciyata ta tsinke, har Call ɗin ya yanke sai kuma wani ya sake shigowa." "Kin ɗaga?" Firdausi ta tambaya "A'a... na kasa." Ta amsa Ta share hawayen da suka zubo mata. "Yana fitowa daga toilet ya sake ganin call ɗin. Wallahi Firdausi yadda ya tashi da sauri ya ɗauki wayar... sai ya mayar silent ya saka a aljihu." Firdausi ta haɗe gira. "Then?" "Ya fita daga ɗakin, shine abun daya bani mamaki" "Ya dawo?" Kai Zahra ta girgiza mata. "Har ƙarfe goma sha ɗaya ban ganshi ba. Daga baya ma bacci ya ɗauke ni. Da asuba na tashi... har lokacin baya ɗakin." "Subhanallah..." cewar firdausi "Tun da muka shirya bayan dawowata gida, Ibrahim bai taɓa barina ni kaɗai a dare ba. Sai jiya..." Muryarta ta fara rawa. "Da safe ma babu explanation. Babu inda ya ce ya je. Kawai ya shigo ɗaki kamar babu abin da ya faru." Firdausi tayi shiru tana sauraronta. "Bayan wani lokaci ma ya fita. Ni kuma na shirya zuwa school..." ta sauke numfashi. "Kawai naji ƙarar gate." "Shi ne?" "Eh. Na buɗe curtain naga yana fita da mota." Hawaye suka sake cikowa idanunta. "Wallahi Firdausi kamar an dasa ni a wajen. Ko sallama bai min ba fah, just imagine...." Firdausi ta ɗan dafe kanta. "Ya Salam..." "Shiyasa nace miki zuciyata zata buga." Zahra ta ƙara faɗa cikin kuka. "Bana son yadda nake jin kaina yanzu. Bana son tunanin da nake yi." Firdausi ta kama hannunta. "Shhh... calm down." "Ki gaya min idan ba wani abu bane me yasa zai fita haka? Me yasa zai ɓoye min wayansa? Me yasa zai kwana a waje?" Shiru Firdausi tayi na wasu seconds kafin tace, "Kin tabbatar ba wata business issue bace?" "Da ace haka ne ai zai gaya min." Zahra tace da sauri. "Ibrahim ba irin mutanen da suke waya da mace suna saving number da 'Lovie Dovie' saboda business ba." Wani shiru ya cika motar. Sai Zahra ta runtse idanunta tana kuka a hankali. "Firdausi bana jin zan iya ɗaukar wani ciwon zuciya daga Ibrahim..." Firdausi tayi shiru na ɗan lokaci tana tunani, sannan ta juya tana kallon Zahra sosai. "Pls kiyi kokari ki nemo number ɗin." Zahra ta ɗan haɗe gira. "Number ɗin wa?" "Wancan 'Lovie Dovie' ɗin." Gabanta ya faɗi ta ce "Firdausi kar dai kiranta zaki yi?" Firdausi ta ce da sauri. "No!!! Just find her number ki turomin immediately. Kuma kar ki bari Ibrahim ya sani." Zahra ta gyada kai a hankali. "Amma me zakiyi da number ɗin?" ta tambaya cikin damuwa. "Ke dai ki samo min ita." Firdausi ta bata amsa a takaice Kai ta sake gyadawa. Sai kuma ta sauke numfashi tace, "Firdausi ina zan kaiki yanzu?" "Ki kai ni gida kawai." "Toh." Zahra ta juya steering tana canza hanya. Dukansu suka yi shiru na ɗan lokaci, amma wannan karon shiru ne wanda dukkansu fadawa duniyar tunani suka shi Firdausi na kallon Zahra lokaci zuwa lokaci. Yadda hannunta ke rawa saman steering ya tabbatar mata cewa kawarta tana cikin wani irin hali. Firdausi ta ce "Zahra..." "Hmm?" Cewar Zahra "Kar ki fara conclusions yanzu." Sai Zahra tayi murmushi mai ciwo. "Yaya ba zan yi ba?" Firdausi ta sauke numfashi. "Saboda baki da complete answer tukuna. Kuma idan kika bari tunani ya rinjaye ki yanzu, zaki cutar da kanki ne." Zahra bata amsa ba, kawai ta ci gaba da driving tana jin zuciyarta na mata wani irin nauyi da bata taɓa ji ba. A haka Zahra ta kai Firdausi gida. Kafin ta sauke ta, Firdausi ta sake riƙe hannunta tace, "Please ki kwantar da hankalinki. Kuma ki tuna abinda nace miki." Kai Zahra ta gyada mata kawai. Ta sauka sannan suka yi sallama Daga haka ta juya motarta ta nufi gida. Tana shiga compound ta samu Farida zaune gefen flowers tana gyara su a hankali. Ganin Zahra yasa tayi saurin miƙewa tsaye. "Ina wuni Hajiya." "Lafiya," Zahra ta amsa a taƙaice. Bata tsaya wata magana ba ta wuce ciki kai tsaye. Yau ko baccin rana ma taji bata son yi. Wani irin cunkoso take ji a zuciyarta. Kai tsaye ɗakinta ta wuce. Toilet ta shiga tayi wanka, sannan ta fito tayi sallah. Bayan ta idar ne ta ɗauki magungunanta zata sha, sai kuma ta tuna cewa ko breakfast bata yi ba, a hankali ta sauke magungunan. Sai ta sauka ƙasa ta ɗibo abinci kaɗan. Ko yunwar ma bata ji sosai ba, amma tasan dole ne ta ci saboda maganin. Bayan ta gama ci ta koma sama. Maganin ta sha sannan ta kwanta akan gadonta. Tana lumshe idanunta kuwa, nan take bacci ya ɗauke ta saboda gajiyar tunani da damuwar da ta cika mata zuciya. Wajajen ƙarfe huɗu na yamma Zahra ta farka daga bacci. Da ƙyar ta buɗe idanunta saboda yadda kanta yake mata nauyi. Amma first thing data fara yi shine ta miƙe ta nufi labulen ɗakinta. Da sauri ta buɗe curtain ɗin tana kallon compound. Babu motar Ibrahim to her own surprise, abin ya bugi zuciyarta sosai. Ta tsaya tana kallon wajen kamar zata ga motar ta shigo a lokaci guda, amma shiru. Wani irin faɗuwar gaba taji, da sauri ta fita daga ɗakinta ta nufi nasa ɗakin dan tabbatarwa. Tana shiga kuwa... babu shi, Komai a yadda ya bari yake. A hankali ta juya ta koma ɗakinta, wayarta ta ɗauka hannu na rawa ta kira Firdausi. Tana ɗagawa kawai Zahra ta fashe da kuka. "Firdausi..." ta kira sunan cikin wani irin kuka mai cin rai. "Zahra lafiya!" Firdausi tace a razane. "Bai dawo ba..." Rasa abin cewa Firdausi tayi ta ce "Wa?" "Ibrahim..." ta faɗa tana kuka sosai. "Har yanzu bai dawo gida ba" Firdausi tayi shiru tana sauraron kukanta. "Kw... kwana biyu bayan mun shirya..." Zahra ke magana da ƙyar. "Da wuri yake dawowa... ko biyu bai wuce yake gida..." Ta share hawayenta amma suka ƙi tsayawa. "Amma yau... har yanzu baya nan." "Shhh... calm down." "Firdausi zuciyata zata tsaya wallahi..." ta ƙara faɗa tana kuka. "Ina jin kamar wani abu na faruwa a bayana." Firdausi ta runtse idanunta tana tausaya mata sosai. "Please ki daina kuka haka. Kin gwada kiransa ne?" Kai Zahra ta girgiza duk da bata ganinta. "Bana son ya gane ina tracking ɗinsa." "Okay... toh ki kwantar da hankalinki yanzu. Maybe yana office ne." "Da ace office ne ai zai min magana..." muryarta cike da ciwo. "Tun safe babu call... babu message... babu komai." Da ƙyar Firdausi ta samu ta lallabata. "Listen to me," tace cikin tausasawa. "Kar ki bari tunani ya kashe ki kafin ki gano gaskiya. Ki nutsu farko." Firdausi tayi shiru, tasan kawarta tana cikin wani irin hali. Saboda ita kanta ta fara jin tsoron yadda Ibrahim ke canzawa Zahra a hankali. Ya Duk maganar da Firdausi ke mata, Zahra ko kaɗan bata ɗauka ba. Kuka kawai take yi kamar zuciyarta zata fito. "Zahra ki kwantar da hankalinki mana... Amma ina.... "Firdausi wallahi bana jin daɗi..." ta faɗa cikin kuka. "Ina jin kamar zan haukace." Firdausi ta dafe kanta. Tasan idan ta barta a haka, zata iya cutar da kanta da yawan tunani. "Okay listen," tace cikin ƙoƙarin ɗauke hankalinta. "Ba mun gama plan ɗinmu ba ko? Zaki samo number ɗin toh..." Sai Zahra ta sake fashewa da kuka. Kamar ma maganar ta ƙara tunzura ta ne "Firdausi ya ya kike so nayi?" ta faɗa tana sheshsheƙa. "Ni yanzu bana ma son ganin wayarsa..." A nan Firdausi ta fahimci ba waya ce zata iya kwantar mata da hankali ba. "Okay..." tace a hankali. "Ki kwantar da hankalinki. Zan sake kiranki." Bata jira ƙarin magana ba ta katse kiran. Nan take ta miƙe daga kan gadonta ta fara shiri cikin sauri. Tana gamawa ta fito parlorn. "Mama zan je gidan Zahra," tace tana ɗaukar handbag ɗinta. "Lafiya kuwa?" Mahaifiyarta ta tambaya. "Eh... tana ɗan jin babu daɗi ne." "Toh Allah ya sauƙaƙa." "Ameen." Daga haka ta fita da sauri ta nufi gidan Zahra, zuciyarta cike da tausayi da damuwa kan halin da kawarta take ciki. Bayan mai gadi ya leƙo ya gane Firdausi ce, sai ya buɗe mata gate ɗin. Da sauri ta shiga ciki. A parlorn ƙasa ta haɗu da Farida. Bayan sun gaisa, Firdausi bata tsaya wata magana ba ta wuce sama kai tsaye zuwa ɗakin Zahra. Tana buɗe ƙofar kuwa ta shiga. Zahra dake zaune bakin gado ta ɗaga kai dan ganin wanene. Da ganin Firdausi, nan take ta miƙe da sauri ta ƙarasa wajenta ta rungumeta. Ba kaɗan ba Firdausi tayi mamakin ganin har lokacin Zahra na kuka. Idanuwanta duk sun kumbura sun yi ja. "Ya Salam Zahra..." ta faɗa tana riƙeta. "Har yanzu kina kuka?" Zahra ta ɗago tana share hawaye. "Ba kinga har ƙarfe biyar yayi ba? Bai zo ba.... Muryarta na rawa ta karasa, "Nasan suna tare ne..." Firdausi ta ɗan ja baya tana kallonta. "Wa da wa?" "Ibrahim da ita mana..." ta faɗa tana ƙoƙarin hana sabon kukan da ke tasowa. "Wallahi Firdausi zuciyata na gaya min haka." "Haba mana..." "Tun safe fa!" Zahra ta katseta. "Tun safe babu call babu message. Ni ma bansan inda yake ba." Firdausi ta kamo hannunta suka zauna bakin gado. "Ki nutsu ki saurare ni." Kai Zahra ta girgiza. "Bana iya nutsuwa." "Okay... kin gwada kiransa?" "A'a." Ta ce da sauri "Why?" "Saboda bana son ya ga kamar ina binsa ne." Ta runtse idanunta. "Amma kuma bana iya daina tunani." Firdausi ta dafe kanta a hankali. "Zahra kina cutar da kanki haka." "Me kike so nayi?" ta tambaya cikin kuka. "Tun jiya nake jin kamar bana cikin hankalina." Firdausi ta rungumeta kaɗan tana shafa bayanta. "Shhh... please ki kwantar da hankalinki." Sai Zahra ta ɗago tana kallonta da idanuwan da suka kumbura saboda kuka. "Firdausi idan har Ibrahim ya koma wajen wata mace..." muryarta ta karye. "Wallahi zan mutu." Firdausi ta gama ruɗewa gaba ɗaya. Ta rasa wani tunani zata yi. Ta sani ƙwarai Ibrahim na cutar da Zahra, amma bayan duk abinda ya faru tsakaninsu not long ago na kama shi da wata.... shine zai sake komawa irin halinsa? Wani numfashi ta sauke tana kallon kawarta dake kuka kamar ranta zai fita. "Zahra..." ta kira a hankali. Ta ɗago tana share hawaye. "Yanzu idan ya zo ya ga idanunki sun yi ja zai san saboda shine kika yi kuka. Kinga zai ji daɗi." Kai Zahra ta girgiza. "A'a wallahi ba zai ji daɗi ba..." "Ki bar wannan." Firdausi ta katseta. "Namiji idan ya ga mace na rushewa saboda shi, wani lokacin sai ya ƙara jin yana da power akanki." Zahra tayi shiru tana sauraronta. "Sannan secondly..." Firdausi ta kama hannunta. "Ciki jikinki yana buƙatar ki kwantar da hankalinki. Wannan yawan kuka da tunani bai Kama ce ki ba a halin yanzu" Wani sabon hawaye ya sake zubo wa Zahra. "Ki duba yadda kike rawa..." Firdausi ta ƙara faɗa cikin tausasawa. "Wallahi kina bani tsoro." "Na kasa controlling zuciyata ne..." Zahra tace da ƙyar. "Ina son Ibrahim sosai Firdausi." Firdausi ta runtse idanunta na ɗan lokaci. "Nasan ki na sonsa. Kowa ma ya sani. Amma ki tsaya ki fara son kanki farko ma" Sai Zahra ta sunkuyar da kai. Firdausi ta ɗan matsa kusa da ita. "Yanzu tashi ki wanke fuskarki. Kar ya zo ya same ki haka." "Bana ma son ganinsa..." "Ko baki so ba, dole ki haɗa kanki." Firdausi tace. "Ki nuna masa kina da ƙarfin zuciya." A haka Firdausi ta zauna tare da Zahra har suka yi sallar Maghrib, tana ƙoƙarin lallashinta da rage mata yawan tunani Bayan sun idar, har yanzu Zahra ba ta huce ba. Idanunta sun kumbura, zuciyarta kuma cike take da wani nauyi mai wuyar kwatance Can kuma sai suka ji ƙarar buɗe gate. Firdausi ta yi saurin leƙawa ta window. Sai ta juya a hankali tana kallon Zahra. "Wallahi shi ne..." Zahra ta ɗago kai da sauri. "Firdausi..." "Ni kam wallahi zan tafi." ta faɗa cikin sauri tana ɗaukar jakarta da wayarta. "Please kar ki yi kuka, kar ya gane." Zahra ta miƙe da sauri ta nufi toilet ba tare da ta ce komai ba, tana ƙoƙarin ɓoye kanta daga yanayin da take ciki. #jiddatulkhyar writes #08110615256 Book 1 Chapter 19 Firdausi kuwa ta sauka ƙasa, a compound suka haɗu. Ibrahim yana shigowa, Firdausi ta kalle shi fuska a hade. "Ina wuni," ta faɗa a taƙaice. Shi kuma ya kalleta da wani irin kallon, sannan ya wuce ba tare da ya amsa ba. Ita ma ta bi shi da irin kallon nan na rashin kunya. Wajen unguwar nasu shiru, manyan gidaje ne, babu kowa dan kowa na gidansa. Ta fara tafiya a hankali tana bin titin unguwar har ta kai bakin titi. Da ƙyar ta samu abin hawa ta shiga, zuciyarta cike da tunanin Zahra da kuma halin da ta bar ta a ciki. Ibrahim na shiga parlorn ƙasa, babu kowa. Kai tsaye ya haura sama zuwa ɗakinsa. Ko kallon dakinta bai yi ba, ya cire kayansa sannan ya shiga toilet yayi wanka. Yana fitowa aka kira sallar isha'i, hakan yasa yana gama saka kaya ya sauka ƙasa. Masallaci ya wuce direct. Bayan ya dawo ne ya tsaya a kitchen na ɗan lokaci, kamar mai tunani. Sai ya ɗauki plate ya wuce dining. Buɗe warmers ɗin yayi. Abincin da Zahra ta dafa ne a jere cikin tsari. Wani ɗan numfashi ya sauke a hankali kafin ya ja kujera ya zauna. Ya ɗiba abincin kaɗan sannan ya fara ci a hankali. Dining ɗin gaba ɗaya shiru yayi masa Lokaci zuwa lokaci idanunsa na ɗagawa sama kamar yana sauraron motsi daga upstairs, amma shiru kake ji . Sai kawai ya ci gaba da cin abincin a hankali, zuciyarsa cike da wani irin tunani da shi kansa bai gama fahimta ba. A bangaren Zahra tun kafin Ibrahim ya dawo daga masallaci, Zahra ta riga ta ji motsinsa a cikin gidan. Ko da yake tana cikin ɗakinta, amma ko da wasa bata fita ba, Duk da ta saba idan taji sawunsa tana fita.. Sai dai wannan karon... ta share. Kwanciya tayi akan gadonta tana kallon ceiling ɗin ɗaki, zuciyarta na wani irin bugawa da bata saba ji ba. Duk shawarwarin da Firdausi ta saka mata a kai ne ke yawo a kanta. "Ki nemo number ɗin..." Wannan maganar ta sake dawo mata Sai kuma ta tuna yadda Ibrahim ya kwana a waje, wani rin abu taji ya tokare mata zuciya. Da sauri ta miƙe daga gadon ta nufi toilet. Ruwan ɗumi ta kunna sannan ta fara wanke fuskarta a hankali. Ta daɗe tana wanke idanunta musamman saboda kumburin da kuka ya saka musu. "Ba zai gane ba..." Ta furta a hankali tana sake ɗiba ruwa. Bayan ta fito ne ta goge fuskarta da towel mai laushi sannan ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta. Har yanzu idanunta sun ɗan yi ja kaɗan, amma ba kamar ɗazu ba. Mint sweet ta jefa a bakinta sannan ta fara taunawa a hankali. "Ko muryata ba zai gane ta canza ba..." Wani tsaki ta ja a hankali saboda yadda take ƙoƙarin acting kamar komai lafiya ne alhalin zuciyarta na cin wuta. Wardrobe ta buɗe. Wani English wear mai matuƙar ɗaukar hankali ta zaɓa.. milk colour fitted gown mai taushi wanda ya zauna a jikinta kamar an yi shi saboda ita. Gashinta ta gyara cikin simple style sannan ta saka ɗan turare mai sanyin ƙamshi. Da ta gama shiryawa, ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta. Kamar a ita ba. Kallon agogo tayi, Almost tara na dare, sai kuma gabanta ya faɗi. "Har yanzu bai leƙo ni ba..." Maganganun Firdausi ne suka fara dawo mata. "Namiji idan ya ga mace tana rushewa saboda shi..." Wani numfashi ta sauke. Ta miƙe zata fita, har ta kai bakin ƙofa sai kuma ta tsaya cak. "Anya zan iya?" Wani soro ne ya ratsa ta. Sai kuma last text ɗin da Firdausi ta turo mata ya faɗo mata a rai. "Control yourself first kafin ki gano komai." Wannan ne ya bata wani ƙarfin guiwa. Ta dafe ƙirjinta a hankali sannan ta buɗe ƙofar ta fita, Direct ɗakin Ibrahim ta shiga. Ta same shi zaune bakin gado, waya na hannunsa yana dannawa hankali kwance kamar babu wata damuwa a duniyarsa Da ya ɗaga kai suka haɗa ido, sai ya ɗan tsaya kallonta. Kafin ya ce wani abu, Zahra ta karya muryarta cikin shagwaɓa ta ƙarasa kusa da shi. "I missed you..." Ta faɗa tana zaunawa kusa da shi kamar ƙaramar baby. Ibrahim ya ɗan ɗaga gira yana kallonta. "Tun safe?" Ta ɗan turo baki. "Hmmm." Wani murmushi ya suɓuce masa. "Amma ai kina fushi da ni ko?" Ta ɗan girgiza kai. "Who said?" Sai ta kwanta jikinsa a hankali tana riƙe hannunsa. "Please kar ka sake bace min haka." Maganar ta bugi zuciyarsa kai tsaye. Nan take ya saki jikinsa da ita gaba ɗaya. "Sorry..." Ya furta a hankali yana shafa bayanta. Zahra ta runtse idanunta. Duk da zuciyarta ke mata zafi, ta danne komai. A daren sosai suka sha love kamar ma babu wata matsala tsakaninsu. Ibrahim na mata hira, tana dariya tana responding yadda ya kamata, alhalin zuciyarta na wani irin aiki a ɓoye. Wani lokaci ma sai ta tsaya tana kallonsa tana mamakin yadda yake iya zama normal haka. Bayan wani lokaci ne suka kwanta Zahra tayi pretending kamar bacci ya ɗauketa. Ibrahim ya gyara mata kwanciyarta a hankali, har blanket ya ja ya rufe mata jikinta. Ta ji yadda ya ɗauki wayarsa. A hankali ya sauka daga kan gadon yana rage murya. "Hello..." Sai kuma shiru.... "Yes... I sent the 50k already." Zuciyar Zahra ta buga da ƙarfi. Ta ci gaba da pretending kamar bacci take. Daga can muryar mace ta ɗan fito kaɗan daga wayar amma bata ji sosai ba. Ibrahim yace, "No... don't worry about it." Shiru ya sake yi yana saurare. Sai kuma ya ɗan yi murmushi kaɗan. "You worry too much." Wata magana aka sake masa. Sai yace, "I'll see what I can do tomorrow." Daga haka ya kashe wayar. Zahra ta ji ƙafafunsa sun dawo kusa da gado. Sai ya kashe light ɗin ɗakin sannan ya kwanta kusa da ita. Ita kuwa zuciyarta har lokacin bugawa take yi kamar zata fito. Can wajajen ƙarfe biyu na dare Zahra ta buɗe idanunta a hankali, Ibrahim na bacci. Ta tsaya tana kallonsa na wasu seconds kafin daga ƙarshe ta miƙe a hankali. Wayarsa dake gefensa ta ɗauka. Da hannunta na rawa ta kamo yatsansa sannan ta manna akan thumbprint ɗin. Nan take wayar ta buɗe. Gabanta ya faɗi, da sauri ta shiga recent calls. Last call ɗinsa... "Pretty ❤️" Wani irin mashi ne ya soki zuciyarta. Da sauri ta kwafe number ɗin zuwa wayarta, hannunta har rawa yake yi saboda tashin hankali. Bayan ta gama, ta fita daga contacts ɗin ta kashe wayar gaba ɗaya sannan ta mayar inda ta ɗauka. Sai ta ɗauki wayarta ta turawa Firdausi number ɗin nan take. "This is the number." Daga haka ta kwanta a hankali, abin mamaki kuwa, nan take bacci ya ɗauke ta saboda gajiyar tunani da tashin hankali. Da safe suka tashi tare. Kamar kullum suka yi sallah. Ibrahim ma babu alamar damuwa a tattare da shi. Har lokacin yana treating Zahra normal. Wannan ne ma ke ƙara rikita mata kai. Bayan sun gama shiryawa suka sauka breakfast. Farida ta haɗa musu tea da bread da omelette. Ibrahim na cin breakfast ɗinsa yana ɗan duba wasu files a tablet. Zahra kuma tana ci a hankali tana satar kallonsa lokaci zuwa lokaci. "Yau kina da lectures da yawa?" ya tambaya. "Hmmm." Ta ce masa "Kar ki gaji da yawa." Kai ta gyada masa kawai. Bayan sun gama, suka fito tare. A compound ya tsaya yana kallonta. "Take care." "You too." Sai ya ɗan matso ya sumbaci goshinta a hankali kafin ya shiga motarsa. Zahra ta tsaya tana kallonsa har ya fita... Tana isa makaranta kuwa, bata ma shiga department ɗinsu ba. A wani department ta tsaya ta kira Firdausi. Da sauri Firdausi ta ɗaga. "Kin iso?" "Eh." Zahra ta ce "Ina kike?" Zahra ta gaya mata wajen. "Toh ki tsaya ina zuwa." Bata jima sosai ba sai ga Firdausi ta iso da sauri. Ta buɗe motar Zahra ta shiga. Tana zama, Zahra ta juya tana kallonta. "Meya faru bayan na baki number ɗin?" Firdausi tayi murmushi kaɗan. "Ki bari." "Firdausi..." zahra ta kira sunanta "After school zaki ga abin da nayi." Cewar firdausi Zahra ta haɗe gira. "Don Allah ki gaya min yanzu mana." Firdausi ta girgiza kai. "Nope. Yanzu let's go for lectures first." Sai ta ɗan kalli Zahra. "Kuma please ki haɗa kanki yau, kar aje Ana lectures kina tunani" Wani numfashi Zahra ta sauke kafin ta tada motar. Haka suka wuce lectures tare. A hall ɗin ma Zahra ta fi jiya ɗan nutsuwa saboda yanzu tana jin akwai wani abu da zata gano. Firdausi kuwa lokaci zuwa lokaci tana kallon wayarta tana replying messages a ɓoye. Break time suka haɗu da Asiya da Suhaima. Suhaima tace, "Yau kam Zahra ta dawo normal." Asiya tayi dariya. "Wallahi jiya tsoro ta bani." Zahra tayi murmushi kawai. Daga baya suka wuce masallaci suka yi sallah tare. Bayan sun idar ne suka zauna a harabar masallacin na ɗan lokaci, iska mai sanyi na bugunsu yayin da students ke wucewa suna ta hira. Amma duk da Zahra na zaune tare da friends ɗinta... Zuciyarta na jiran abin da Firdausi zata gaya mata ne kawai. Suka koma suka yi last lecture ɗinsu kafin aka tashi. A hanya suna tafiya tare bayan sun yi sallama da Asiya da Suhaima, Zahra ta juya tana kallon Firdausi. "But kin san wannan wani number ne ba na ranan ba?" Firdausi ta haɗe gira. "How?" Sai Zahra ta fara bata labarin yadda ta sake duba recent calls ɗin Ibrahim da daddare, inda ta ga "Pretty ❤️" maimakon "Lovie Dovie." "Wannan ma wata Pretty ce..." ta ƙarasa maganar cikin sanyin murya. Firdausi ta tsaya cak tana kallonta. "Subhanallah..." Na ɗan lokaci ta rasa abin cewa. Sai kuma ta sauke numfashi tace, "Shiga mota." Zahra ta ce "Inda zamu je?" "Zaki gani." Cewar firdausi Zahra bata ƙara magana ba ta shiga motar. Ita dai gaba ɗaya ta kosa taga me Firdausi take ta ɓoyewa haka. Bayan kusan mintuna talatin na tafiya, Firdausi tace mata inda zata juya. Har suka isa wani babban park mai kyau da manyan restaurants da wajen shakatawa. Parking Zahra tayi suka sauka. Firdausi ta ɗauki wayarta ta kira wata. "Hello... mun iso." Sai tayi shiru tana sauraro. Can ta ce "Okay." Ta kashe wayar sannan ta juya tana kallon Zahra. "Mu shiga." Cike da mamaki Zahra ta bi bayanta. Suka shiga cikin wani cool down restaurant mai nutsuwa da ƙamshin coffee da perfume mai daɗi. A wani corner na wajen wata budurwa ce zaune tana danna waya. Kyakykyawa ce, eh... amma ko kaɗan bata isa ta fito da wani abu na musamman a gaban Zahra ba. Zahra ta fita da komai.. class, kyau, nutsuwa, da wani irin presence da ke sa mutum ya tsaya kallonta. Yarinyar ma tun da suka ƙaraso wajenta idanunta suka tsaya akan Zahra. Suka yi sallama sannan suka zauna. "Ya only you?" Firdausi ta tambaya. "Eh." Bayan sun gaisa ne Firdausi ta gyara throat ɗinta kaɗan. "Kin san Ibrahim?" Yarinyar ta gyada kai. "Eh mana." "Wane Ibrahim?" Ta ɗan yi murmushi. "Ibrahim Khalil." Zahra ta haɗiye wani abu a maƙoshi. Firdausi tace, "How long?" "Almost two months." Firdausi ta ɗan kalli Zahra kafin ta sake maida kallonta kan yarinyar. "Kin san yana da aure?" Nan take yarinyar ta haɗe gira. "A'a." Firdausi ta nuna Zahra dake zaune shiru kamar mutum-mutumi. "Wannan matarsa ce. Kuma yanzu ne ma suka yi wata da aure." Ba ƙaramin mamaki yarinyar tayi ba. "What?!" Sai ta sake kallon Zahra sosai. "Amma taya zan yarda?" Firdausi bata ce komai ba sai ta shiga Instagram page ɗin Ibrahim a wayarta sannan ta miƙa mata. Da sauri yarinyar ta karɓa. Nan take idanunta suka sauka kan hotunan wedding ɗin Ibrahim da Zahra. Pictures masu kyau, videos, posting ɗinsa yana celebrating matarsa. Baki ta taɓe cikin mamaki. "Wallahi ni bansani ba..." tace da gaske. "Bai taɓa gaya min yana aure ba." Zahra dai tana zaune shiru tana kallonta. "Ni ma dama ba aurensa zanyi ba." Yarinyar ta ƙarasa cikin rashin damuwa. "Kawai cin kuɗinsa nake yi." Firdausi ta dafe kanta kaɗan. "Toh dan Allah ki fita daga harkarsa. Kinga matar sa tana nan, kuma ace da dare yana fita wajenta." Yarinyar ta ɗan gyara zamanta. "Wallahi ma zan yi blocking ɗinsa. Amma sai ya turomin kuɗin da zai bani." Zahra ce ta fara magana tun da suka zauna. "Nawa ne?" Yarinyar ta kalleta. "20k." "Account number ɗinki?" Firdausi ta juya da sauri tana kallon Zahra. Ita ma yarinyar mamaki ya kamata. Sai dai ta faɗi account number ɗinta. Nan take Zahra ta ɗauki wayarta tayi mata transfer na 500k. Kusan seconds kaɗan alert ya shiga wayar yarinyar. Da sauri ta zaro ido. "Jesus!" Har ihu tayi tana kallon screen ɗin wayarta. "Half million?!" Ta miƙe tsaye tana dariya harda sallen murna. "Wallahi nagode Anty!" Sai ta juya da sauri tana buɗe WhatsApp. "Yanzu ma zanyi blocking ɗinsa." Nan take ta block number Ibrahim a gabansu. "Anty ko zan iya samun number ɗinki muna gaisawa?" Zahra ta miƙe tsaye a hankali. "Mungode." Sai ta juya tana kallon Firdausi. "Let's go." Firdausi ta miƙe itama tana bin bayanta, zuciyarta cike da mamaki da kuma tausayi ga Zahra wacce duk da ciwon da take ji... har yanzu ta zauna cikin nutsuwa da class. Suka koma suka yi last lecture ɗinsu kafin aka tashi. A hanya suna tafiya tare bayan sun yi sallama da Asiya da Suhaima, Zahra ta juya tana kallon Firdausi. "But kin san wannan wani number ne ba na ranan ba?" Firdausi ta haɗe gira. "How?" Sai Zahra ta fara bata labarin yadda ta sake duba recent calls ɗin Ibrahim da daddare, inda ta ga "Pretty ❤️" maimakon "Lovie Dovie." "Wannan ma wata Pretty ce..." ta ƙarasa maganar cikin sanyin murya. Firdausi ta tsaya cak tana kallonta. "Subhanallah..." Na ɗan lokaci ta rasa abin cewa. Sai kuma ta sauke numfashi tace, "Shiga mota." "Inda zamu je?" "Zaki gani." Zahra bata ƙara magana ba ta shiga motar. Ita dai gaba ɗaya ta kosa taga me Firdausi take ta ɓoyewa haka. Bayan kusan mintuna talatin na tafiya, Firdausi tace mata inda zata juya. Har suka isa wani babban park mai kyau da manyan restaurants da wajen shakatawa. Parking Zahra tayi suka sauka. Firdausi ta ɗauki wayarta ta kira wata. "Hello... mun iso." Sai tayi shiru tana sauraro. "Okay." Ta kashe wayar sannan ta juya tana kallon Zahra. "Mu shiga." Cike da mamaki Zahra ta bi bayanta. Suka shiga cikin wani cool down restaurant mai nutsuwa da ƙamshin coffee da perfume mai daɗi. A wani corner na wajen wata budurwa ce zaune tana danna waya. Kyakykyawa ce, eh... amma ko kaɗan bata isa ta fito da wani abu na musamman a gaban Zahra ba. Zahra ta fita da komai—class, kyau, nutsuwa, da wani irin presence da ke sa mutum ya tsaya kallonta. Yarinyar ma tun da suka ƙaraso wajenta idanunta suka tsaya akan Zahra. Suka yi sallama sannan suka zauna. "Ya only you?" Firdausi ta tambaya. "Eh." Bayan sun gaisa ne Firdausi ta gyara throat ɗinta kaɗan. "Kin san Ibrahim?" Yarinyar ta gyada kai. "Eh mana." "Wane Ibrahim?" Cewar firdausi Ta ɗan yi murmushi. "Ibrahim Khalil." #jiddatulkhayr writes 08110615256 https://chat.whatsapp.com/IjVCBxrVY1Z4pH5IZhshvA?mode=gi_t YOTA Book 1 Chapter 20 Zahra ta haɗiye wani abu a maƙoshi. Firdausi tace, "How long?" "Almost two months." Firdausi ta ɗan kalli Zahra kafin ta sake maida kallonta kan yarinyar. "Kin san yana da  aure?" Nan take yarinyar ta haɗe gira. "A'a." Firdausi ta nuna Zahra dake zaune shiru kamar mutum-mutumi. "Wannan matarsa ce. Kuma yanzu ne ma suka yi wata da aure." Ba ƙaramin mamaki yarinyar tayi ba. "What?!" Sai ta sake kallon Zahra sosai. "Amma taya zan yarda?" Firdausi bata ce komai ba sai ta shiga Instagram page ɗin Ibrahim a wayarta sannan ta miƙa mata. Da sauri yarinyar ta karɓa. Nan take idanunta suka sauka kan hotunan wedding ɗin Ibrahim da Zahra. Pictures masu kyau, videos, posting ɗinsa yana celebrating matarsa. Baki ta taɓe cikin mamaki. "Wallahi ni bansani ba..." tace kana gani kasan tayi mamaki. "Bai taɓa gaya min yana da aure ba." Zahra dai tana zaune shiru tana kallonta. "Ni ma dama ba aurensa zanyi ba." Yarinyar ta ƙarasa cikin rashin damuwa. "Kawai cin kuɗinsa nake yi." Firdausi ta dafe kanta kaɗan. "Toh dan Allah ki fita daga harkarsa. Kinga matar sa tana nan, kuma ace da dare yana fita wajen wata lokacin da yakamata yana gida?" Yarinyar ta ɗan gyara zamanta. "Wallahi ma zan yi blocking ɗinsa. Amma sai ya turomin kuɗin da zai bani." Zahra da tun farko bata ce uffan bane ta ce "Nawa ne?" Yarinyar ta kalleta. "20k." "Account number ɗinki?" Cewar Zahra Firdausi ta juya da sauri tana kallon Zahra. Ita ma yarinyar mamaki ya kamata, sai kawai ta faɗi account number ɗinta. Nan take Zahra ta ɗauki wayarta tayi mata transfer na 500k. Kusan seconds kaɗan alert ya shiga wayar yarinyar. Da sauri ta zaro ido. "Jesus!" Zaro idanu tayi tana kallon screen ɗin wayarta. "Half million?!" Ta miƙe tsaye tana dariya harda sallen murna. "Wallahi nagode Anty!" Sai ta juya da sauri tana buɗe WhatsApp dinta "Yanzu ma zanyi blocking ɗinsa." Nan take ta block number Ibrahim a gabansu. "Anty ko zan iya samun number ɗinki muna gaisawa?" Zahra ta miƙe tsaye a hankali. "Mungode." Sai ta juya tana kallon Firdausi. "Let's go." Firdausi ta miƙe itama tana bin bayanta, zuciyarta cike da mamaki da kuma tausayi ga Zahra wacce duk da ciwon da take ji... har yanzu tana cikin nutsuwa da class. Da suka shiga mota, Firdausi ta daɗe tana kallon Zahra kafin daga ƙarshe ta girgiza kai. "Wallahi kuɗin yayi yawa Zahra" Zahra na driving bata ko juyo ta kalleta ba ta ce "Ba komai." "Haba Zahra, 500k saboda kawai ta rabu da shi?" Sai Zahra ta sauke numfashi a hankali. "Ai kinji ta da kanki... yarinyar nada son kuɗi. Haka ne kawai zai sa ta rabu da shi gaba ɗaya." Firdausi ta ɗan taɓe baki. "Toh amma half million fa..." "Firdausi," Zahra ta katseta a hankali. "Idan wannan ne zai sa ta fita daga rayuwata da ta Ibrahim, wallahi ba yawa bane." Shiru ya ɗan ratsa motar, kowa da tunanin da yake yi Can kuma Zahra ta sake magana cikin wani irin ciwon rai da ta daɗe tana dannewa. "Please..." ta faɗa tana kallon titi. "Mai Ibrahim ya gani a jikin wannan da zai dinga binta?" Firdausi ta kalleta. Zahra ta girgiza kai da murmushi mai ciwo. "Na fita da komai fa..." Wannan maganar tata ta fito ne daga zuciyar kana ji kasan taji zafi "Kinga ni mana... na fita da kyau, ilimi, kudi, komai..." ta haɗiye wani abu a maƙoshi. "Then me yasa?" Firdausi ta sauke numfashi. "Ai maza kenan..." tace a hankali. "Allah kyauta." Sai ta ɗan matsa kusa da Zahra. "Kuma ki daina comparing kanki da wata mace saboda namiji. Wallahi babu inda yarinyar nan ta kai ki." Zahra tayi shiru kawai tana driving. Sai dai zuciyarta bata daina mata zafi ba. A haka ta kai Firdausi gida. Kafin ta sauka, Firdausi ta riƙe hannunta. "Please ki kwantar da hankalinki yanzu. At least kin ga ita ɗin ba wani serious abu bace." Kai Zahra ta gyada mata. "Text me idan kin isa gida." Cewar firdausi "Toh." Ta amsa Firdausi ta sauka ta shiga gida. Zahra kuwa ta juya motarta ta nufi gida, zuciyarta cike da abubuwa mabambanta... ciwo, haushi, da kuma wani irin son Ibrahim da bata iya cirewa daga ranta duk da abun daya ke mata Da Zahra ta isa gida, parking tayi a hankali kafin ta kashe motar. Na ɗan lokaci bata fito ba. Hannunta na kan steering, idanunta kuma a lumshe. Yanzu kam komai ya canza. Ba kamar kwanakin baya ba da take kuka kawai tana jin tsoro. Yanzu tana da tabbaci. Tabbacin da ya zauna mata a zuciya kamar dutse. Ibrahim yana fita wajen wata mace. Wani numfashi ta sauke kafin daga ƙarshe ta buɗe motar ta fito. A hankali ta shiga ciki. Farida ce a kitchen tana gyaran kayan girki. Jin motsinta yasa ta leƙo. "Sannu da zuwa Hajiya." Zahra ta amsa da murmushi kaɗan. "Yawwa Farida." "Tea zan haɗa miki?" "A'a." Daga haka ta wuce sama. Yau bata ji buƙatar kuka ba kamar kullum. Sai dai zuciyarta ta yi wani irin sakayau Direct ɗakin Ibrahim ta shiga. Komai nasa tsaf kamar yadda ya bari da safe. Turarensa har yanzu na tashi a ɗakin. Ta ƙarasa slowly ta zauna bakin gadon. Idanunta suka sauka kan pillow ɗinsa. Sai ta tuna yadda yake kallonta da soyayya... yadda yake rungumeta... yadda yake saka ta jin kamar ita kaɗai ce a duniyarsa. Sai kuma ga gaskiyar nan. Murmushi tayi. Wani irin murmushi mai ciwo. "Amazing..." Ta furta a hankali. Wayarta ta ɗauka ta shiga gallery ɗinsu. Pictures ɗin da suka ɗauka ranar dinner ɗinsu suka bayyana. A ɗaya daga ciki Ibrahim ya rungumeta yana kallonta kamar babu wata mace a duniya sai ita. Zahra ta daɗe tana kallon picture ɗin kafin daga ƙarshe ta kashe screen ɗin. "Ai actor ne..." Ta miƙe a hankali ta nufi wardrobe ɗinsa. Ta buɗe. Shirts ɗinsa neatly arranged. Watches. Perfumes. A hankali ta ɗauki wata shirt tasa ta matso kusa da hancinta. Ƙamshinsa. Zuciyarta ta sake bugawa. Duk da komai... har yanzu tana sonsa. Wannan ne abinda ya fi bata tsoro, sai ta mayar da shirt ɗin ta rufe wardrobe. A dai-dai lokacin ta ji ƙarar gate, ta tsaya cak. "Ibrahim..." Da sauri ta fito daga ɗakin ta wuce nata. Kafin ya shigo sama, ta riga ta zauna kan bed tana duba wani handout kamar mai karatu. Bayan wasu seconds ta ji motsinsa a parlorn sama. Sai muryarsa. "Zahra?" Ta ɗaga kai kamar yanzu ta lura da dawowarsa. "You're back?" Ya shigo ɗakin yana cire agogon hannunsa. "Hmmm." Ya tsaya yana kallonta. Tun daga lokacin da ya shigo yake jin akwai wani abu different a tattare da ita. Too calm. Ba irin Zahra ɗin da zai shigo ta fara tambayarsa ina ya je ba. Ba irin wacce idan ya ɗan ɓata mata rai take showing it instantly ba. Yau... ta yi shiru. "Kina lafiya?" ya tambaya yana matsowa kusa da ita. Murmushi tayi. "I'm fine." Ya ɗan haɗe gira kaɗan. "Sure?" Kai ta gyada masa. "Hmmm." Sai ta ci gaba da kallon handout ɗin hannunta. Ibrahim ya tsaya kallonta na wasu seconds. Wani irin uneasy feeling ne ya ratsa shi. Bai san me yasa ba... amma wannan shirun nata ya fi basa tsoro fiye da surutunta Daren ranar kuwa, bayan sun yi dinner cikin nutsuwa kamar komai lafiya, Zahra ta wuce ɗaki ta kwanta da wuri. Ibrahim kuwa ya daɗe a parlorn sama yana danna waya. Sau biyu yana kiran Pretty... amma busy yake nuna masa, canza dayan number ta yayi yana kira ya shiga, nan ya gane kamar tayi blocking dinsa ne. Ya haɗe gira. "What's wrong with this girl?" Ya sake kira. Still no answer. Wani ɗan haushi ne ya taso masa. Tun da ya san yarinyar, bata taɓa ignoring calls ɗinsa haka ba. Sai ya tura mata message. "What's going on?" Blue tick ta yi amma babu reply. Yanzu kam abin ya fara bata masa rai. Da ƙyar ya jira kusan minti talatin sannan ya miƙe ya ɗauki key ɗin mota. A hankali ya leƙa ɗakin Zahra, ya same ta kwance kamar mai bacci. Sai ya fita. Kusan ƙarfe goma sha ɗaya ya isa unguwar da Pretty ke zama. Parking yayi a waje sannan ya fito. Da farko knocking yake yi amma babu wanda ya buɗe, ya kira ta. Ta ƙi ɗagawa. Har zai juya cikin haushi sai kuma ƙofar ta buɗe. Pretty ta fito. Sai dai yau ba irin yadda take tararsa da fara'a ba. Tsaye tayi a bakin ƙofa hannu a ƙirji tana kallonsa. "What?" Ibrahim ya haɗe gira. "What kind of attitude is this?" Ta yi wata dariya mai raini. "Attitude kuma? Bayan ka ɓoye min kana da mata?" Wani irin mamaki ya kama shi. "What?" "Oh please." ta katse shi. "Ka yi aure har wedding pictures full Instagram amma kana pretending single wajen mutane?" Ibrahim ya tsaya kallonta. A karo na farko ya rasa abin cewa, Dakyar yace "Who told you?" Pretty ta taɓe baki. "Does it matter?" Ya matso kusa da ita. "So wannan ne yasa kika fara ignoring dina ?" Ta yi dariya. "Ibrahim ka raina ni ne?" Ya dafe kansa. "Listen..." "A'a." ta katse shi da sauri. "Ni ba drama zan yi ba. In fact, thanks for the money." Ya ɗago kai da sauri. "What money?" Ta yi murmushi tana ɗaga waya. "Half million fa. Your wife is classy Wallahi" Gabansa ne ya faɗi. "Wait... Zahra ta zo nan?" "Not just her. Har da kawarta." Wani irin shiru ya ratsa shi. Pretty ta cigaba, "Kuma wallahi matar ka ta bani respect. Ba irin yadda nake tunanin zata zo tana zagi da iskanci ba." Ibrahim ya haɗe fuska sosai. "Ta ce miki me?" "Nothing much." Pretty ta taɓe baki. "Kawai ta roƙe ni politely na fita daga harkarka." Sai ta ɗan tsaya kafin ta ƙara da, "Kuma gaskiya... ban san kana da mata mai kyau haka ba." Wannan maganar ta sake ɗaga masa hankali. "Pretty..." "Please." Ta ɗaga masa hannu. "Ni ban son problem. Kuma daga yau kar ka sake zuwa nan." Sai ta ƙara kallonsa sama da ƙasa. "Kuma honestly? Ka ci sa'a." Tana gama faɗar hakan ta juya ta shiga ciki ta rufe ƙofa. Ibrahim ya tsaya a wajen kamar an dasa shi, zuciyarsa cike da mamaki, haushi, da kuma wani irin shock. Zahra ta gano komai knn? Kuma mafi damuwa... bata nuna masa komai ba. Wani numfashi ya sauke yana shafa kansa kafin daga ƙarshe ya juya ya koma mota. Duk hanyar dawowarsa gida jikinsa babu ƙwari, a karo na farko tun bayan aurensu... Ya fara jin tsoron nutsuwar Zahra. Lokacin da Ibrahim ya isa gida dare ya riga yayi sosai. A hankali yayi parking a compound ɗin gidan kafin ya kashe motar, ya ɗan dauki lokaci bai fito ba. Kalaman Pretty ne ke ta dawo masa. "Your wife is classy..." Sai kuma yadda ta ce: "Ka ci sa'a." Wani numfashi ya sauke yana dafe goshinsa, Yanzu kam ya tabbatar Zahra ta san komai. Kuma abinda ya fi dagula masa kai... yadda take acting normal. Ba kuka. Ba faɗa. Ba tambaya. Nothing Nothing Komai nata cikin nutsuwa, wannan ne ya fara tsoratar da shi. A hankali ya fito daga motar ya shiga ciki. Gidan gaba ɗaya shiru, ya haura sama direct. Da ya buɗe ɗakin su, light ɗin bedside lamp kaɗai ke kunne. Zahra na kwance gefe guda na gadon, blanket ya rufe rabin jikinta. Daga gani bacci take cikin nutsuwa Ibrahim ya tsaya bakin ƙofa yana kallonta, na wasu seconds bai motsa ba. Wata irin damuwa ce ta tokare masa zuciya. "Why didn't she say anything..." Ya furta a hankali. A hankali ya ƙarasa ciki ya cire agogon hannunsa sannan ya zauna bakin gadon. Idanunsa na kanta. Ko yanzu ma... tana da kyau sosai. Beautiful. Soft. Calm. But ya maganar contract??? Sai zuciyarsa ta ƙara nauyi. Ya tuna yadda ta zo ɗakinsa jiya da daddare ta rungumesa tana cewa ta missing ɗinsa, ashe duk a lokacin tana sane Wani irin guilt ne ya cika masa ƙirji. A hankali ya miƙa hannu ya gyara mata gashin daya rufe kan fuskarta. Zahra bata motsa ba. Shi kuwa ya daɗe yana kallonta kafin daga ƙarshe ya miƙe ya shiga toilet yayi wanka. Bayan ya fito, ya kashe sauran lights ɗin ɗakin sannan ya kwanta kusa da ita. Sai dai... Bacci ya ƙi zuwa masa. Kowane lokaci sai ya tuna Zahra na zaune a gaban Pretty cikin nutsuwa. Yana tunanin: Ta yi kuka ne? Ta ji zafi ne? Me yasa bata tambaye shi ba? Ya juya yana kallonta a hankali. Har lokacin tana bacci. Sai ya ɗan matsa kusa da ita ya rungumota ta baya. Wani numfashi ya sauke a hankali yana lumshe ido. "Sorry..." Ya furta ƙasa-ƙasa. Bai ma san ko saboda me yake bada haƙurin ba. Saboda ya cutar da ita? Can cikin dare, Zahra ta buɗe idanunta a hankali. Ɗakin gaba ɗaya duhu ne sai hasken bedside lamp mai dan haske. Ibrahim na bacci sosai, hannunsa har yanzu rungume da ita, ta tsaya na ɗan lokaci tana kallonsa. Wani irin ciwo ya sake tokare mata zuciya. "Me yasa..." Ta furta a hankali cikin ranta kafin ta cire hannunsa daga jikinta a hankali kar ya farka, ta miƙe slowly daga kan gadon. Wayarsa na gefen pillow, gabanta na bugawa ta ɗauka Kamar jiya, ta kamo hannunsa a hankali ta manna yatsansa akan thumbprint ɗin. Nan take wayar ta buɗe, da sauri ta shiga messages Gabanta ya sake faɗuwa ganin latest message daga Pretty. "Ko karyan da kayi min ba zan kara yarda da Kai ba. Don't ever text me again." Sai kuma wani. "I'm done. Focus on your wife." Zahra ta daɗe tana kallon screen ɗin, wani rin sanyi ne ya ratsa zuciyarta... wani mixed feeling ne da bata iya fassara wa A hankali ta shiga chat ɗin gaba ɗaya. Ta karanta yadda Ibrahim ke mata magana cikin sweet words. Yadda yake tura mata kuɗi. Yadda yake tambayarta ta ci abinci ko a'a. Wani abu ya tsaya mata a maƙoshi, sai dai bata yi kuka ba, wannan karon ba kuka take ji ba... Daga ƙarshe ta yi blocking number ɗin Pretty daga wayarsa sannan tayi deleting gaba daya Sai kuma ta tuna. "Lovie Dovie..." Da sauri ta shiga search, nan kuwa number ɗin ya fito Hannunta ya fara rawa. Da sauri ta ɗauki number ɗin ta tura zuwa wayarta. Na wasu seconds ta tsaya kallon screen ɗin. Zuciyarta na mata nauyi sosai. "Mutum nawa ne...?" Ta furta a hankali. Sai kuma ta kashe screen ɗin wayar ta ajiye masa ita daidai inda ta ɗauka. A hankali ta dawo ta kwanta. Wannan karon bata sake kallonsa ba, ta juya baya gare shi tana lumshe idanunta. #Jiddatulkhayr writes #08110615256 https://chat.whatsapp.com/IjVCBxrVY1Z4pH5IZhshvA?mode=gi_t Book 1 Chapter 21 Washegari sun makkara wajen tashi da asuba, Zahra ta tashi tun kafin Ibrahim ya farka Na ɗan lokaci ta zauna bakin gado tana kallonsa cikin bacci. Fuskar nan tasa dake cike da nutsuwa kamar babu wata damuwa tare da shi yasa zuciyarta yin wani irin nauyi.... Sai dai yau bata yi kukan data saba ba A hankali ta miƙe ta shiga toilet tayi alwala, daga baya ta tada shi suka yi sallar asuba tare. Ko bayan da suka idar babu wata hira tsakaninsu kamar yadda kwana kin baya suka fara Shi dai Ibrahim yana kallonta lokaci zuwa lokaci kamar yana son ya ce wani abu, amma ya kasa Zahra kuwa ta mayar da hankalinta kan addu'o'inta. Da gari ya gama waye wa Zahra ta shirya cikin wata simple but elegant outfit black fitted skirt da milk colour top mai matuƙar kyau, sai hijab ɗinta daya ƙara fito da kyawun fuskarta. Tun tana shiryawa Ibrahim ke kallonta ta mirror, yau kam akwai wani abu tare da ita . Too calm Ba irin Zahra ɗin da zata tsaya tana masa hira ko shagwaɓa ba ko kuka bane cikin emotion. Shi kuma hakan ne ke sake dagula masa lissafi Bayan sun sauka breakfast, Farida ce ta haɗa musu tea da bread tare da omelette. "Yau kina da lectures sosai?" Ibrahim ya tambaya yana duba tablet ɗinsa. "Eh" ta amsa a takaice "Kar ki wahalar da kanki." Kai ta gyada kawai. Bayan sun gama suka fito tare. A compound ya tsaya yana kallonta. "Take care." "You too." Ta amsa masa calmly sannan ta shiga motarsa Ya tsaya kallonta har ta fita da motar. Wani irin uneasy feeling ne ya sake ratsashi. A makaranta kuwa, Zahra ta yi parking a gaban department ɗinsu as usual, tana saukowa wasu students ne suka fara gaisheta. "Anty Zahra ya jiki?" "Alhamdulillah." Ta amsa da murmushi "Long time fa." Murmushi kawai ta musu tana wuce Tun daga nesa ta hango Firdausi da Asiya zaune a bakin corridor suna hira. Suhaima na ganinta ta miƙe da sauri. "Ga Madam!" Asiya ta yi dariya. "Wallahi yau ma glowing take yi." Firdausi kuwa tun kallon farko ta gane Zahra ba cikin perfect mood take ba. Sai dai yau ta fi controlled Da suka shiga hall, lecture na farko ya fara. Lecturer ɗin Statistics ne yau, yana ta bayani a board amma rabin students ɗin ma sun gaji saboda lecture ɗin na safe ne, gashi Uban calculations ne Firdausi na rubutu tana ɗan kallon Zahra lokaci zuwa lokaci. Zahra kuwa notebook ɗinta a buɗe yake amma gaba ɗaya hankalinta baya wajen lecturer ɗin Sau biyu lecturer ya kira sunanta saboda tambaya. "Zahra?" Sai Firdausi ce ta taɓa hannunta a hankali. Da sauri ta ɗago. "Yes sir?" Class ɗin suka yi dariya kaɗan ganin ta yi lost. Lecturer ɗin ma yayi murmushi. "You seem distracted today." "Sorry sir." kawai ta iya cewa Daga haka lecture ya ci gaba, bayan first lecture suka fita break. Cafeteria suka wuce tare da su Asiya. Suhaima na ta hira akan wani lecturer da ya kama wata student tana cheating a test, Asiya kuwa na ta dariya. Sai dai Zahra yau bata wani shiga hirar sosai ba. Firdausi ce kawai ke lura da ita. "Ki ci abinci mana," ta faɗa tana tura mata juice. "Ok." A hankali Zahra ta fara sha. Can kuma Asiya ta kalleta. "Amarya lafiya dai? Yau kin yi shiru." Murmushi Zahra tayi. "Just tired." Suhaima ta ce "Babyn mune ke wahalar mana da ita" Zahra dariya kawai tayi, daga nan suka wuce masallaci suka yi sallar zuhur tare. Bayan sun idar ne suka zauna a harabar masallacin ƙarƙashin bishiya saboda iska, dan wannan cikin Zahra nan kamar na son wajen ne Students na ta wucewa suna hayaniya amma Zahra gaba ɗaya zuciyarta na wani waje daban. Firdausi ta ɗan matsa kusa da ita. "He texted you?" Kai Zahra ta girgiza. "Kin ga? Relax then." Sai Zahra ta sauke numfashi. "Firdausi... ban san me nake ji ba." Firdausi ta riƙe hannunta a hankali. "Ke dai ki ci gaba da observing ɗinsa. Mun gama da first step kamar kin dawo daidai shine zaki sake komawa gidan jiya" Zahra bata kuma cewa komai ba Da lecture na gaba ya shiga Duk suka miƙe suka koma hall. Har aka gama lectures ɗin ranar, Zahra tana trying sosai ta haɗa kanta, amma duk lokacin da ta tuna messages ɗin wayarsa... sai zuciyarta ta sake yin nauyi. Bayan sun gama last lecture ɗinsu, Zahra da Firdausi suka fito tare daga hall ɗin. Yau rana ta gajiyar da students sosai, kowa na ta neman hanyar gida a gajiye suke sosai A hankali suka isa parking lot ɗin. Zahra ta buɗe motarta suka shiga. Tun tana tada motar tayi shiru na wasu mintuna kafin daga ƙarshe ta kasa haƙuri. "Firdausi..." "How far?" "Kin samu wani abu akan Lovie Dovie?" Firdausi dake danna wayarta ta ɗago ta kalleta. "Not yet." Zuciyar Zahra ya tsinke Sai Firdausi ta ƙara da, "But ina working on it." "Ta yaya?" Zahra ta tambaya Murmushi Firdausi tayi. "Ke dai ki bari idan na gama zamu yi magana." Wannan answer ɗin bai gamsar da Zahra ba, amma ta ga yadda Firdausi ke avoiding magana sosai, hakan yasa ta yi shiru. A haka ta kai Firdausi gida. Kafin ta sauka, Firdausi ta riƙe hannunta a hankali. "Please ki kwantar da hankalinki." Kai Zahra ta gyada mata. "Text me idan kin isa." "Toh." Firdausi ta fita daga motar ta shiga gida. Zahra kuwa ta ja motarta a hankali ta wuce. A hanya zuwa gidan su, gaba ɗaya tunanin ya mamaye ta. Ko red light data tsaya bata ma san tsawon lokacin data yi a wajen ba sai da wata mota ta yi mata horn, sai ta ɗan firgita ta tada motar. Kalaman Pretty suka fara dawo mata kai "Ni ma dama ba aurensa zanyi ba..." Sai kuma yadda Ibrahim ke kallonta da soyayya kamar babu wata mace a rayuwarsa. Ashe wasu can yake tare da su Wani numfashi ta sauke tana jin zuciyarta na mata nauyi. Lokacin data isa gidan su, mai gadi ya buɗe mata gate cikin girmamawa. "Sannu da zuwa Hajiya." Ta amsa masa da murmushi kafin ta shiga ciki da motarta tayi parking Yau gidan yayi mata wani irin comforting, kamar duk lokacin data zo gida tana samun sauƙin numfashi, sauka tayi Tana sauke ajiyar zuciya A parlorn ta tarar da Mami zaune tana gyaran wasu kaya yayin da tv ke kunne yan aiki Da ganin Zahra, Mami ta ɗan yi mamaki "Zahra?" Zahra ta ƙarasa ciki tana gaidata. "Ina wuni Mami." "Lafiya lau." Mami ta ajiye kayan hannunta. "Yau kuma da rana haka Baby?" Ta zauna kusa da ita tana gyara hijab ɗinta. "Na yi missing ɗinku ne, shine nazo gaishe ku" Mami tayi murmushi. "Toh ai muma mun fi missing dinki babu yadda muka iya ne" Da sauri Zahra ta kalleta sosai, sai kuma ta sauke kai kasa Akwai wani abu tattare da Zahra yau da bai mata ba, wani rin sanyin hali. "Lafiya dai ko?" Mami ta tambaya Da sauri Zahra ta gyada kai. "Lafiya kalau Mami" "Kin ci abinci?" "A'a." "Toh tashi ki je kitchen ɗin ki duba abinda zakici." Murmushi tayi sannan ta miƙe .A kitchen ɗin ma ma'aikatan gidan suka fara gaisheta da fara'a. Abincin ta zuba, zama tayi ta ɗan ci abinci kaɗan sannan ta dawo parlorn, ta zauna kusa da Mami tana jingina da cushion Zahra na zaune kusa da Mami tana sauraron hirarta, lokaci zuwa lokaci tana amsawa da murmushi, duk da cewa zuciyarta na wani waje daban Wayarta na hannunta, tana jiran message daga Firdausi. Can sai suka ji karan buɗe ƙofa Mummy ce ta fara shigowa parlorn. Tana riƙe da handbag ɗinta, daga gani yanzu ta dawo daga wani waje. Da ganin Zahra, ta ɗan tsaya sannan ta yi murmushi. "Toh toh, amarya ta zo mana ashe?" Zahra ta miƙe cikin girmamawa. "Sannu da Zuwa, Ina wuni Mummy." "Lafiya lau." Mummy ta amsa tana zaunawa "Yau kuma da yamma haka? Kamata yayi tun safe ne zaki zo mana mu wuni" Murmushi Zahra tayi. "Na yi missing ɗinku ne, amma zan zo na kwana ma idan na gama da project" "Yauwa, haka nake so. Kar dai mijin ya kwace mana ke gaba ɗaya." Mami ta yi dariya. Zahra ma ta yi murmushi. Sai ga Ya Umar ya shigo Wayarsa na hannunsa, amma yana shigowa ya ajiye ta a gefe Da ganin Zahra ya ɗan yi mamaki. "Lallai kuwa... yau muna da babban bakuwa" Murmushi ya sakar mata "Kanwata." Zahra ta miƙe. "Ina wuni Yaya." "Lafiya kalau." Ya ƙaraso ya zauna a kusa da su sannan ya kalleta. "Ya school?" Ya tanbaya "Alhamdulillah." "Ya lectures ɗin?" "Alhamdulillah" ta sake basa amsa Ya Umar ya ɗan haɗe gira."Alhamdulillah kawai?" Mummy ta yi dariya. "Umar kenan, me zata ce idan ba Alhamdulillahn ba?" Shima ya yi murmushi ya ce "Ai na saba da ita yadda take bada amsa ne. Da idan ka tambayeta lectures ɗinta sai ta ba ka labari daga farko har ƙarshe" Murmushi Zahra tayi tace "Lectures muke sha fafa. Mun gama presentation ɗinmu kuma supervisor ya yi mana gyara kaɗan" "Good." Ya Umar ya gyada kai. "Final semester ɗin nan dai ki dage sosai." "In Sha Allah." Ya Umar ya jingina da kujera yana kallonta. "Ya jikinki kuma?" "Da sauƙi." "Magunguna fa?" Ya kuma tambayarta Kai ta gyada. "Ina sha." "Yauwa." Mami ta kalle shi. "Tun da ta shigo kai ma tambayoyi kawai kake yi" Ya Umar ya yi dariya. "Toh Mami ai ina son na san yadda take" kai ta gyada masa Shi dai kallon Zahra kawai yake yi,gaba daya ta canza a Zahran daya santa, ko hawa online ma ta dena Ya ce "Ai Yau tunda kika zo gida Banda aikin yi kin shiga uku da magana kuma" Nan take Mummy ta yi dariya. "Wallahi nima abinda nake tunani kenan, naga bata son magana kaii kuma sai takura mata kake yi, taga ta kwanta yau" Zahra kuwa murmushi kawai tayi tana girgiza kai. "A'a Yaya, stress ne fah" "Da kyau." Ya Umar ya faɗa yana ɗan taɓe baki. "Dan idan 'yan maganarki suka dawo ko kallona kar kiyi dan ba zan kula ki ba" Mami ta ce "Ahtoh tunda shareka ka ma tayi ba!" Dariya suka yi gaba ɗaya Mummy na gama dariyar, ta miƙe tana gyara mayafinta. "Toh ni bari na haura sama, tun ɗazu nake ta zirga -zirga" Mami ta gyada kai "Ki huta Lafiya" Mummy ta juya tana kallon Zahra. "Kar ki gudu fah, yau kina nan har dare" Murmushi Zahra tayi. "Toh Mummy" Daga haka Mummy ta juya ta haura sama Bayan tafiyarta, hirar ta cigaba tsakanin Mami, Ya Umar da Zahra. Ya Umar ne ke bata labarin wasu abubuwan da suka faru an office ɗinsu, lokaci zuwa lokaci Mami na tsokanar sa. Har Zahra ta samu kanta tana dariya da gaske. Lokaci guda taji damuwarta na vanishing a hankali A karon farko tun bayan abubuwan da suka dame ta, ta ji zuciyarta ta ɗan sauƙa. Can bayan la'asar, Mami ta sa aka kawo musu tea da snacks. Suka zauna a parlorn suna sha suna hira. Ya Umar ma daya dawo a masallaci ya cire takalmansa ya miƙa ƙafafunsa yana jin daɗin yadda yasa Zahra ta sake "Wallahi gidan nan ya yi shiru idan baki nan," ya faɗa yana kallon Zahra. Mami ta gyada kai. "Hakane kam, musammam Abbahn ku babu mai damunsa" Zahra tayi murmushi. "Toh ai zan dinga zuwa kullum idan na gama da school" Mami ta ce "Halan baki da hankali ne" Dariya sosai Ya Umar yayi, yace once in a while muke son ganinki Malama" "Yauwa." Mami ta faɗa. "Ko da sau ɗaya ko sau biyu a sati biyu" Ita dai shiru tayi, can data gaji ta kwanta a kafan Mami, a haka lokaci ya tafi kuma abin mamaki, Zahra bata ma lura yadda lokaci ya tafi ba Ta manta da damuwar da take ciki na ibrahim da wata lovie Dovie. Wajen magrib ne aka ji karan buɗe gate, ba jimawa kuwa Abbah ya shigo Da sallama ya shiga parlorn. Mami ta amsa masa Ya Umar ya miƙe ya gaishe shi. Zahra ma ta miƙe da sauri. "Abbah nah" Murmushi ya yi sosai har ana ganin hakoransa "Baby na" Ta sunkuyar da kai tana gaishesa. Ya amsa cikin kulawa kafin ya zauna. "Yanzu kika zo ?" Mami ta amsa masa. "Ta zo mana tun bayan lectures dinsu na 12pm" "Madallah." Abbah ya kalleta. "Hakan yayi kyau. Kar ki manta gidan nan gidan ki ne ko yaushe kina da ikon zuwa idan da izinin mijinki" Wani irin taɓuwa zuciyar Zahra tayi. "Na gode Abbah." Can bayan Insha'i Aka kawo musu fruits, tea da snacks Abbah ya shiga ba su labaran wasu abubuwan da suka faru yayin tafiyarsa. Ya Umar kuma lokaci zuwa lokaci na saka dariya cikin hirar ganin yadda zahra ta fara tafiya duniyar tunani Har Mami ma ta kasa daina dariya. Ita kanta ma tana enjoying companyn su but tunaninta ya fara komawa gida, amma kuma tana jin daɗin kasancewa a wajen Lokaci ya tafi ba tare da ta lura ba. Har karfe 8 Bayan sun gama dinner ne Abbah ya kalli agogo sai kuma ya kalli Zahra. "Amarya, yau dai kin manta da gidan mijin naki ko?" Dariya Mami tayi "Wallahi kuwa." Ya Umar ya ƙara da, "Ni kam tun ɗazu nake tunanin ko kwana ne tazo mana" Dariya ta ƙara tashi a parlorn Zahra ma ta yi dariya Sai dai a zuciyarta... Da gaske ne bata son komawa. A nan tana jin nutsuwa, a nan babu wayoyi da zata duba da dare, babu messages da zasu karya mata zuciya, babu tunanin inda Ibrahim yake ko wa yake magana da ita Abbah ya lura da shiru da tayi, ya ɗan kalleta cikin kulawa. "Lafiya dai ko?" Da sauri ta murmusa. "Lafiya lau Abbah." Ya gyada kai tare da fadin "Madallah." Amma ba kadan ba hankalinsa ya tashi Sai ya jingina da kujera ya ce, "Duk da haka dai, ina ganin lokaci yayi da zaki koma kafin dare yayi sosai." Wani sanyi ya ratsa zuciyar Zahra. Sai dai ta ɓoye komai da murmushi. "Toh Abbah na" Zahra ta koma parlorn ta ɗauki handbag ɗinta Mami tace, "Toh Fatima, Allah ya tsare hanya." "Ameen Mami." Ta rungume Mami sannan ta ma Abbah sallama Abbah yace, "Ki kula da kanki." "In Sha Allah." Tana shirin fita ne Ya Umar ya miƙe yana ɗaukar key ɗin motarsa. "Mu tafi." Da sauri Zahra tace, "A'a Yaya, ai nazo da mota na" Yace "Okay, bari na Kai ki" Nan ma ta girgizaza masa kai Ya Umar ya harare ta. "Me yasa?" "Yaya dare yayi ne." "Dama ni ba dare nake fita ba?" Murmushi Mami tayi. "Ku tafi kawai." Zahra tace, "Amma Yaya idan ka kaini ya zaka dawo?" Ya Umar ya ɗaga kafaɗa. "Zan kira Bolt." "Yaya..." "Zahra." Yadda ya kira sunanta yasa ta yi shiru. "Zo mu tafi." Daga haka ta bi bayansa har suka sauka. A hanya kuwa Ya Umar ne ke hira ita kuma tana amsawa lokaci zuwa lokaci. Sai dai duk da tana ƙoƙarin shiga hirar, zuciyarta na wani irin nauyi. Tun da safe Ibrahim bai kira ta ba. Bai turo message ba. Bai tambayi inda take ba. Wannan ne ya fi ɗaga mata hankali, this shows that baya gidan Ko kuma yanzu ma yana wajen waccan? Ta girgiza kanta tana ƙoƙarin korar tunanin. Bayan kusan mintuna talatin suka isa layinsu. Ya Umar ya rage gudu. Sai dai kafin ya ƙarasa parking a bakin gate ɗin gidan, wata baƙar mota ta shigo layin. Da farko Zahra bata kula ba. Amma da motar ta matso ƙarƙashin fitilar layin... Sai gabanta ya buga da karfi, Numfashinta ya tsaya. Ibrahim ne zaune a gaban motar. Kuma mace ce ke tuƙa motar. Wani irin jiri ya ɗan ɗibeta, ta ƙura musu ido. Matar tana magana, tana dariya har da shafa masa fuska Ibrahim ma biye mata yake dan ko lura da motar Zahra bai yi ba Kafin ya ɗago idanunsa, Idonsa ya sauka kan motar Zahra, tare da Ya Umar Sannan ya ganta Na daƙiƙa guda fuskarsa ta sauya, amma sai ya kau da kansa da sauri, kamar bai ganta ba Wani abu ya tokare zuciyar Zahra "Tsaya." Ta faɗa cikin murya mai sanyi. Ya Umar ya kalleta "Calm down Zahra?" Dan yaga abun data gani "Tsaya Yaya, ko na sauka" Da sauri ya taka birki, bai ma gama tsayawa sosai ba, Zahra ta buɗe ƙofa ta fito "Zahra! Don't gooo" Ya Umar ya fadi da karfi Amma bata tsaya ba, kai tsaye ta nufi motar Ibrahim yana ganin tana zuwa, da sauri ya ce 'ki tada motar' ga matar. Amma kafin hakan ta faru, Zahra ta isa. Ta kai hannu, ta buɗe ƙofar driver ɗin Matar ta dago da sauri Tana kallon Zahra Eid Mubarak! Taqabbal Allahu minna wa minkum, Allah maimaita mana. Kar a manga a cinye goron Sallah a jiye 500 na FARASHIN IZZAHj Chapter 22 Kallon kallo suka shiga yiwa juna, Matar ma kallonta take yi daga sama har ƙasa Na wasu daƙiƙu babu wanda ya ce komai. Sai dai yanayin wajen ya canza gaba ɗaya Ibrahim ya ji gabansa ya faɗi. “Zahra…” Ya kira sunanta cikin kashedi. Amma ko kallonsa bata yi ba Ta ci gaba da kallon matar. “Wacece ke?” Ta faɗa cikin ɓacin rai Matar ta ɗan haɗe gira “Excuse me? Har kin isa kimin wannan tambayar?” “Wacece ke?” Zahra ta kuma tambayarta cikin ɓacin rai Matar ta ɗan taɓe baki ta ce “Da alama kin san wanda nake tare da shi ai.” Wani irin dariya Zahra tayi ta ce “Eh na sani. Shi yasa nake tambayarki” Ibrahim ya fito daga motar da sauri. “Enough Zahra” Ta juya da sauri ta kalle shi, nan take Idanunta suka canza “Enough…? Zaka ce….? Ta maimaita “Ni zaka ce wa enough?” Mutane suka fara fitowa a balconies da bakin gate saboda hayaniyar. Matar ta kalli Ibrahim. “Who’s she?” Gagara magana yayi, Zahra tayi folding hannayenta ta matsa jikin kofar ta ce “Matarsa.” Nan take matar ta juya da sauri ta kalli Ibrahim. “What!!?” Ibrahim ya runtse ido “Listen…” “A’a ka yi shiru, saboda shirun ne ya kamace ka” Zahra ta katse shi, muryarta har tana rawa. Ya Umar ya nade kafarsa ya jingina jikin motar yana kallon ikon Allah Matar ta zaro ido Tana kallonsa “Wait… kana da mata?” Ibrahim ya ji kamar ƙasa ta buɗe ya shige shi. Sai dai maimakon ya natsu… Fushi ne ya fara hawa kansa da borin kunya, Saboda yadda mutane ke kallonsu “Zahra!” ya ɗaga murya Wani banzan take masa “Kar ki tsaya kina yi wa mutane ihu a titi! Ko banzan halin naki ne kike son displaying anan?” Wata dariyar takaici ta kufce mata ta ce “Ihu? Banzan hali?” “Eh ihu na faɗa” Ya nuna wajen “Duba yadda kika tara mutane!” “Ni na tara mutane? Ko kuma rashin adalcin ka ya tara mutane?” “Eh! Ke kika tara mutane!” Ya fara magana cikin zafi. “Kina tsaye kina yi wa mutane rashin kunya a waje!” Ya Umar da tun farko bai ce komai ba yace “Ka bugeta toh tunda Kaga mai zuciya” Matar ta kalli Ibrahim cikin mamaki “Rashin kunya kace take maka?” Ya nuna Zahra “Tun da ta fito daga mota bata bani damar magana ba sai abun data ga dama take fada” Zahra ta ji hawaye sun cika idanunta, ko karin mayarwa ta fara, sosai Ibrahim ya bata mamaki sai kawai ta tsaya tana kallonsa Ibrahim ya cigaba “Kuma ai baki da right ɗin da zaki tsaya kina tuhumata!” Ya faɗa cikin fushi Zahra ta zuba masa ido. “Bani da right?” “Eh!” Ya faɗa da karfi “Kina fita yadda ranki yake so! Kullum kina gidanku! Kullum kina can! Kullum wani ƙato ke kawo ki gida” Matar kuwa… Sai kawai ta fashe da dariya harda tafe hannu ta riƙe cikinta. “Wow!” Ta ce, ta kalli Ibrahim. “Seriously?” Ta nuna Zahra. “Wannan matar taka ce?” Ibrahim ya haɗe gira, matar ta sake dariya. “Wallahi ka bani mamaki.” Ta girgiza kai. “Wai kana da mata irin wannan sannan kana yawo kana neman mata? Me anfanin boyewar cewa kana da mata? Lemme tell you bana son makaryaci hakan na nunawa kayi disqualifying kan ka” Yanzu kam fuskar Ibrahim ta canza. Matar ta cigaba “Ka dube ta mana.” Ta nuna Zahra. “Innocent, Beautiful, classy, respectful.” Sai ta yi masa kallon raini “Yadda ka mata Nima haka zaka min ko da na shigo Ibrahim, dan haka kazo ka karbi kayanka na gidan mu” Wannan maganar ta dake shi sosai Jin furucinta yasa Zahra ta fara ganin bibbiyu, Ya Umar ya karaso wajenta ganin yadda Zahra ta tsaya kamar mutum-mutumi Hawaye kawai ke zuba a fusakanta, Ya Umar ya ji zuciyarsa Tana tafasa Kai tsaye ya kama hannunta “Mu tafi.” Zahra bata motsa ba, har sannan idanunta na kan Ibrahim Ya Umar ya sake matse hannunta “Zahra.” Still bata amsa ba Kamar ma bata jin me yake cewa Ya Umar ya Kama fuskanta “Kanwata.” Sai a lokacin ta ɗan kalle shi.Idanunta sun yi ja. Ya Umar ya girgiza kai “Mu shiga ciki.” Sai hawaye suka fara zubowa kamar an kunna pampo Ba tare da ta ce komai ba Ya Umar ya jata a hankali Kawai binsa take yi Kamar an cire mata lakka Yayin da suka shiga cikin gidan ne, matar ta sake kallon Ibrahim. Ta girgiza kai cikin takaici. “Wallahi ka ci sa’a da ka samu irin wannan matar, idan nice abun da tayi sai na ninkasa sau duba” Sai ta shiga motarta ta rufe ƙofa, taja motar da gudu ta bar layin Ibrahim kuwa ya tsaya kamar Wawa….. Ya Umar na duƙe a ƙasa gabanta, yayin da ita ke zaune kan kujera tana kuka kamar zuciyarta zata fito Da farko yana ƙoƙarin lallashinta ne da magana, amma da ya ga kukan nata na ƙaruwa maimakon ya ragu, sai ya ji zuciyarsa ta kasa ɗauka Hawayen da take yi ba irin na fushi bane, kukan ciwo ne Ya Umar ya sauke numfashi mai nauyi, sai ya miƙe tsaye ya zauna kusa da ita. Kafin ya janyo ta jikinsa Nan take Zahra ta sake fashewa da kuka, ta rike rigarsa tana kuka kamar ƙaramar yarinya Ya Umar ya lumshe idanunsa, da ƙyar yake danne kansa, a ankali ya fara bubbuga bayanta “Shhh… Ya isa haka.” “Wallahi Yaya…” ta ce muryarta na rawa “Sai ya dinga cewa bai da mata? Ni fah?” Ya Umar ya runtse idanunsa, wannan kalmar ce ma ta fi masa ciwo. Ba wai dan Ibrahim ya kula wata mace bane Abin da ya fusata shi shi ne yadda ya tsaya a gaban wata mace yana nuna Zahra kamar rayuwarta ba komai ba ce, valueless, Kamar ba ita ce matarsa ba A hankali ya sake bubbuga bayanta ya ce “Kalle ni” Da ƙyar ta ɗago kanta daga kafaɗarsa, Fuskarta cike da hawaye, Idanunta sun yi ja Ya Umar ya ji tausayinta ya ƙara cika zuciyarsa “Kina ji ni da kyau?” Kai ta gyada masa. “Zahra kina da gatanki, bai isa ya sa wannan gatan naki ya gushe ba” Sabbin hawaye suka zubo mata. “Ko Yau kika dawo gida sai ma sabbin gata da zaki gani, infact kin fisa gata ta ko wani angel ma” Sai ya share mata hawayen fuskarta “Kin yi fiye da abin da ya kamata mace tayi, kinyi hakuri tun ba Yau ba nasani. Kin yi ƙoƙarin gyara abubuwa” Sai ya girgiza kai “Saboda haka kar ki zauna kina zargin kanki, shine kawai ba nagari ba” Zahra ta sauke numfashi tana ƙoƙarin tsayar da kukanta Ya Umar ya ci gaba da magana cikin tausasawa “Kuma dan Allah…” Ya dafa kanta “Saboda cikin jikinki, Saboda lafiyarki, Ki kwantar da hankalinki” “Kar ki bari wannan damuwar ta cutar da ke” Sai ya ɗan yi murmushi mai ciwo “Idan ba saboda kanki ba, toh saboda jaririn da ke cikinki” Zahra ta lumshe idanunta, a hankali kukan nata ya fara raguwa Ya Umar ya ce, “Na yi miki alkawari.” Ta ɗago ta kalle shi. “Zan ɗauki mataki” “Amma ba yanzu ba har sai kin gama gama defense. Yanzu abin da nake so shi ne ki huta, kin ji ni?” Da ƙyar ta gyada kai. Ya sake tambaya. “Kin ji ni?” “Eh Yaya.” “Good.” Sai ya miƙe tsaye Zahra ma ta share fuskarta “Yaya…” “Naam?” “Ina so na kwanta” Ya Umar ya gyada kai. “Hakan ma ya fi” Sai ya tsaya yana kallonta “Amma ki yi min alkawari.” Ta kalleshi “Kar ki kwanta kina kuka, kar ki zauna kina tunanin ki hana kan ki bacci” Zahra ta gyada kai a hankali. “In Sha Allah, Nagode Yaya” Ya Umar ya san ba ta cikin yanayin da zata iya magana sosai, har mamakin dauriyarta take yi Saboda haka bai ƙara mata wata magana ba, ya raka ta har bakin staircase. Yana kallonta har ta haura sama Har ta ɓace daga ganinsa Sai a lokacin ya sauke wani dogon numfashi Tausayinta fal a ransa Bayan ya tabbatar ta shiga ɗaki, Ya Umar ya fito waje A can gefen gate ya hango motar Zahran, ya girgiza kai A hankali ya nufi motar, ya buɗe ƙofar driver’s seat ya shiga Na ɗan lokaci ya jingina da kujera yana tunanin abin da ya faru Sai kuma ya tada motar, a hankali ya juyata ya shiga da ita cikin compound Ya yi parking ɗinta a inda aka saba ajiye motocin gidan, ya kashe motar ɗin, ya zarekey ɗin ya fito Da ya rufe ƙofar motar, ya ɗaga kai ya kalli saman gidan, Inda ya san dakin Zahra, maybe tana kwance tana kuka Wani irin fushi ya sake cika masa zuciya, amma ya haɗiye shi Saboda yanzu… Abin da ya fi muhimmanci a wajensa shi ne lafiyar kanwarsa. Kar na barku sakayau ne shine na sakuro Wanda nayi editing, ban wuni gida bane Yau afuwank https://chat.whatsapp.com/IjVCBxrVY1Z4pH5IZhshvA?mode=gi_t Book 1 Chapter 23 Daren ranar haka Zahra ta gagara bacci. Sai can wajen asuba bacci barawo ya ɗauke ta. Ibrahim kuwa ko zuwa gidan bai yi ba, a waje ya kwana. Wajen ƙarfe shida na safe alarm ɗinta ya fara bugawa, hakan yasa ta farka da ƙyar. Addu'ar tashi daga bacci tayi, sannan ta sauka daga kan gadon ta nufi toilet. Brush tayi tare da alwala, daga nan ta fito ta shimfiɗa sallayarta ta yi sallah. Bayan ta idar, azkar ɗinta ta fara yi a hankali. Da ta gama, ta zauna kan sallayar tana kallon wani waje, hawaye na bin kuncinta. Jin kamar bacci zai sake ɗaukarta yasa ta koma kan gadon, domin bata jin zata iya zuwa makaranta a ranar. Can cikin baccin da take yi ne ta ji ƙarar shigowar message. A hankali ta buɗe idanunta, ta ɗauki wayarta. Firdausi ce. Da sauri ta buɗe message ɗin. "Ki shirya yau. In Sha Allah yau zamu haɗu da Lovie Dovie." Tsaki Zahra ta ja tsaki tana juyawa gefe. "Bana jin zan sake yaƙi da wata saboda Ibrahim." Ta faɗa a hankali. Sai kuma ta sake buɗe idanunta da sauri. Wani tunani ya faɗo mata. Gwamma ta yi hakan, ko ba komai zata cusa masa baƙin ciki ne. Bacci sosai ya fara cin ƙarfinta, hakan yasa ta sa alarm na ƙarfe goma sannan ta kwanta. Nan da nan bacci ya sake kwashe ta. A ɓangaren Ya Umar ma ba a ce ya samu bacci ba. Gaba ɗaya daren jiya ya kwana cikin tunani. Asuba ma sai da Abbah ya tashe shi zuwa sallah. A ransa yake jin kamar ba su kyauta wa Zahra ba da suka aura mata Ibrahim. Lokacin breakfast, dukkansu suna zaune a dining suna karya. Mami ce ta lura hankalin Ya Umar kamar baya tare da su. "Ya Umar, lafiya dai?" ta tambaya. Da sauri ya kalleta, sannan ya kalli Mummy da Abbah. Nan take ya ƙirƙiri murmushi. "Lafiya lau Mami, kawai kai na ne yake ɗan ciwo." Abbah ya ce, "Daga gani ma kamar baka samu bacci jiya ba. Da ƙyar ma ka tashi sallah." Mami ta girgiza kai. "Toh ya kamata ka ga likita kafin ciwon ya shiga jikinka." Ya amsa da, "Toh Mami." Ita dai Mummy tana zaune tana saurarensu, amma ko kalma ɗaya bata ce ba. A haka suka gama breakfast ɗin, amma tunanin Zahra ne ya ƙi barin ran Ya Umar. Har ya gama cin abincin, zuciyarsa na can wajen ƙanwarsa da kuma abin da zai yi wanda zai sa Ibrahim ya gane kuskurensa. Shi ne ya fara miƙewa daga dining ɗin ya wuce ɗakinsa. Yana shiga ya ɗauki wayarsa ya yi dialing number ɗin Zahra wanda ya yi saving da Our Angel ❤️. Kiran na shiga, sai ya ji muryarta cike da bacci. "Hello Yaya." Nan take ya sauke ajiyar zuciya. Wani irin relief ya ji ya mamaye shi. "Kina lafiya?" "Alhamdulillah." "Sorry na tashe ki a bacci ko?" Kallon agogon da ke gefen gadonta Zahra tayi. Ganin saura mintuna goma ƙarfe goma yasa tace, "A'a Yaya, dama ƙarfe goma nake son na tashi." "Alright. Amma zaki shiga school yau ko?" "Eh." "It's good. Ki samu ki tafi, ki zama so lively." Wani ƙaramin murmushi tayi. "Thank you." Ya Umar yace, "If there's anything, just let me know baby." "In Sha Allah." Daga haka suka yi sallama. Zahra ta ajiye wayar sannan ta wuce toilet. Wanka tayi, tana fitowa ta shafa lotion tare da fesa turare mai sanyin ƙamshi. Daga nan ta nufi wardrobe ta ɗauko wata baƙar abaya mai matuƙar kyau ta saka. Ba ƙaramin kyau tayi ba. Ta ɗauki tot-bag ɗinta ta zuba wayoyinta a ciki, sannan ta sanya baƙin flat shoe a fararen ƙafafunta. Sauka tayi ƙasa. Farida na mopping parlorn lokacin. Da ganin Zahra sai ta miƙe tsaye. "Ina kwana Anty." "Lafiya lau Farida, ya aiki?" "Alhamdulillah." Kai ta gyada kawai sannan ta nufi hanyar fita. Da sauri Farida tace, "Amma Anty baki yi karin kumallo ba ne?" Zahra ta juya ta kalleta. "Bana jin yunwa ne." Farida ta haɗe fuska. "Amma fa rabonki da abinci tun jiya. Wallahi yadda na ajiye abincin jiyan nan haka nake zuwa na same shi." Murmushi kawai Zahra tayi. "Idan na dawo zan ci." Daga haka ta juya ta nufi ƙofa. Farida ta bita da kallo har ta fita. Sai kuma ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta juya da sauri ta nufi ɗakinta. Wayarta ta ɗauka. Ganin missed call yasa ta yi saurin kiran number ɗin. Ana ɗagawa tace, "Afuwan, ina aiki ne." Ta yi shiru tana saurare. Sai kuma tace, "Eh, yanzu ta fita." Bayan wani ɗan lokaci ta sake yin shiru. "Amma ana ganinta ansan ba lafiya ba. A yadda ta fita kam" Ta sake sauraron mai maganar sai kuma ta ce "Toh In Sha Allah." Sai kuma ta ɗan yi murmushi. "Amma zata yi dare fa, dan yanzu idan ta fita makaranta tana daɗewa kafin ta dawo gidan." Daga haka ta kashe wayar tana kallon screen ɗin na wasu daƙiƙu kafin ta ajiye ta ta koma bakin aikinta Lokacin da Zahra ta isa makaranta, har an gama first lecture. Duk da ta yi sauri a hanya, hakan bai hana ta tarar da ɗalibai suna ta fita daga hall ɗin ba. Motarta tayi parking a inda ta saba, sannan ta sauka a hankali. Ba tare da ta damu da shiga neman kowa ba, ta nufi wani cool down da ke kusa da department ɗinsu. Zama tayi a ɗaya daga cikin kujerun wajen tana kallon ɗaliban da ke wucewa. Wayarta ce ta fara vibrating. Ciro wayan tayi taga Firdausi ce sai ta ƙyale kiran. Bayan ƴan mintuna kuma sai ga wani. Tsaki Zahra taja sannan ta ɗaga. "Hello." "Madam, ina kike ne?" Firdausi ta tambaya. "Ina makaranta mana." "Na sani. Ina a makarantar?" Zahra ta kalli wajen da take zaune "Ina cool down ɗin kusa da department." "Okay, ki zauna nan. Gani nan zuwa." Kafin Zahra ta ce wani abu, Firdausi ta katse kiran. Bata jima sosai ba sai ga Firdausi ta iso. Tana zuwa ta zauna kusa da ita "Kinga fa, tun safe nake ta kiranki." Murmushi Zahra tayi. "Bacci nake yi." Firdausi ta kalleta sosai. "Kin yi kyau yau wlh" "Thank you." Tace a takaice Sai dai kafin ta ƙara magana, Zahra ta dafe cikinta a hankali Firdausi ta kalleta da sauri, ta ce "Lafiya?" Zahra ta sauke numfashi "Wallahi yunwa nake ji." Firdausi ta zaro ido. "Yunwa? Shine kike zaune bayan kin dan condition dinki?" Kai ta gyada "Har kamar zan yi amai." Da sauri Firdausi ta miƙe tsaye. "Toh tashi mu je cafeteria yanzu." Ba gardama Zahra ta mike Ita kanta ta san jikinta na buƙatar abinci A tare suka nufi cafeteria ɗin makarantar Wajen cike yake da ɗalibai, kamar kullum Da ƙyar suka samu waje suka zauna. Wata ce ta ƙaraso wajensu Firdausi ta kalli Zahra. "Me zaki ci?" Zahra ta ɗan yi tunani kafin tace, "Ina son jollof rice da grilled chicken." "Abin sha fa?" "Fresh orange juice." Ta ce Firdausi ta gyada kai. "Ni kuma fried rice kadai, sannan bottled water." Bayan sun gama order, suka zauna suna jiran a kawo musu. Firdausi na kallon Zahra lokaci zuwa lokaci. Ita kuma Zahra hankalinta yana kan abincin da ake shiryawa Domin yunwar da take ji a lokacin ba kaɗan ba ce. Bayan sun gama cin abincinsu, suka miƙe suka nufi hall ɗin next lecture. A wannan karon Zahra ta yi ƙoƙarin mayar da hankali kan abin da lecturer yake koyarwa, amma duk da haka zuciyarta ba ta gama kwanciya ba sbd Lokaci zuwa lokaci sai ta tsinci kanta cikin tunani Firdausi kuwa tana lura da ita, amma bata ce komai ba. Bayan lecture ɗin ya ƙare, suka fito tare da sauran ɗalibai. A ranar lectures biyu kawai suke da shi, saboda haka kowa ya fara kama gabansa Firdausi na shirin yin sallama da friends dinsu ne, sai Zahra ta riƙe hannunta "Zo muje can." Ba tare da ta jira amsarta ba, ta fara jan ta zuwa wani cool down da ba ya da hayaniya sosai. Da suka isa, suka zauna. Na ɗan lokaci babu wacce ta ce komai. Firdausi ce ta fara magana. "Like seriously, me yasa kika kawo ni nan?" Zahra ta sauke numfashi. "Kamar kar na koma gida." Firdausi ta kalleta. "Why?" Zahra ta yi shiru, sai ta kalli wani waje kamar tana kallon wani abu da babu shi Firdausi ta lura da hakan ta ce "Zahra?" Shiru tayi ba tare data kulata ba "Menene?" A hankali Zahra ta ce, "Ina so na rabu da Ibrahim, shiyasa ɗazu nace ba sai munje can din ba" Firdausi ta ɗan zaro ido tana kallonta sai dai bata katse ta ba. Zahra ta ci gaba. "Wallahi Firdausi ban damu ba ko duniya zata min dariya." Muryarta ya fara rawa "I don't care.... Firdausi" Sai ta haɗiye wani abu da ya tsaya mata a maƙoshi "Kuma zan je na bawa Mami haƙuri." Firdausi ta haɗe gira "Mami kuma?" Kai Zahra ta gyada. "Eh." "Me yasa?" Firdausi ta tambaya "Saboda ina jin kamar harda hakkinta a kaina." Ta sauke numfashi mai nauyi, sai ta lumshe idanunta "Kullum sai na ga kamar har yanzu Mami tana jin haushin abun daya faru" Kafin Firdausi ta ce wani abu, Zahra ta fashe da kuka nan take Firdausi ta matsa kusa da ita da sauri "Hey..." Amma Zahra ta kasa tsagaitawa, kawai kuka take yi Firdausi ta riƙe hannunta. "Ki kwantar da hankalinki." Ta girgiza kai. "Na gaji Firdausi, Na sani komai, Wallahi na gaji" Da ƙyar Firdausi ta lallabata har kukan ya fara raguwa. Sannann ta ce, "Listen to me." Zahra ta share hawayenta. Firdausi ta ci gaba. "Auren Ibrahim yana cikin ƙaddararki. Abin da ya faru ma yana cikin ƙaddararki, kuma babu wanda zai iya canza abin da Allah ya rubuta" Zahra ta yi shiru tana saurarenta Firdausi ta matsa kusa da ita "Yanzu ba lokacin yanke hukunci bane Kin ji ni?" Bata amsa mata ba, ita dai wani wajen take kallo Sai Firdausi ta sake cewa "Ba lokacin da mutum yake cikin fushi da ciwo yake yanke manyan hukunci ba." A hankali Zahra ta ɗaga kai ta kalle ta Firdausi ta ci gaba "Ki bari zuciyarki ta huce. Daga nan sai ki yanke shawarar da zata fi miki alkhairi" Ta ɗan yi murmushi. "Kuma game da Mami, wallahi na san tana sonki, don haka kar ki ɗora komai a ranki, tuni ma idan Mami Dana sani ne ta yafe miki Zara" A hankali Zahra ta share sauran hawayenta, sai ta sauke numfashi Duk zuciyarta bata huce gaba ɗaya ba, amma kalaman Firdausi sun rage mata wani ɓangare na nauyin da take ji A haka suka ci gaba da zama a wajen na wasu mintuna kafin suka miƙe suka kama hanyarsu Da ƙyar Firdausi ta samu Zahra ta sake murmushi kafin suka yi sallama. Daga nan Zahra ta nufi motarta ta kama hanyar gida A hanya ma tunanin abubuwan da suka faru ne ke yawo a ranta, amma ba kamar da safe ba. Kalaman Firdausi sun ɗan kwantar mata da hankali Da ta isa gidan, mai gadi ya buɗe mata gate. Ta shiga compound ɗin a hankali tare da yin parking. Tana sauka daga motar ne kuwa ta hangi wata mota tana shigowa Ta tsaya tana kallo. Ya Umar ne. Yana ganinta ya yi parking shima sannan ya fito daga motar. "Wai Zahra!" Ya faɗa da murmushi. "Yaya." Ta amsa tana murmushi "Kin dawo kenan?" Ya ce "Eh." Ya matso kusa da ita yana kallont "Alhamdulillah. Yau kam kin fi jiya kyau, ko ke fah" Dariya ta yi ta ce "Yaya kenan." "Da gaske nake." Ya karɓi bag ɗinta daga hannunta "Zo mu shiga." A tare suka shiga cikin gidan Sosai ma Mami ta jata a jiki Yau, ganin kamar Tana cikin damuwa. Haka ma Ya Umar ya ƙi yarda ta zauna ita kaɗai. Ko yaushe sai ya samo wani abin hira ko wasa. Bayan ya dawo a masallaci suka zauna a parlorn suna buga game a wayarsa "Daga nan zaki mutu." Ya Umar ya faɗa yana dariya "Yaya cheating kake yi." "A'a ke ce baki iya ba" "Wallahi ka yi cheating" Daga can Mami tana kallonsu. Da ta ji Zahra na dariya sai itama ta yi murmushi Tun jiya take lura da cewa zuciyar Zahra ba a kwance take ba, sai dai bata so ta matsa mata da tambayoyi Hakan yasa ita ma ta shiga jan Zahra a jiki fiye da kullum "Wai ku biyu ba zaku bari a huta ba ne?" Mami ta faɗa tana fitowa daga kitchen. "Shi ne fa Mami" Zahra ta kai ƙara "Yaya ya hana ni cin game ɗin." Ya Umar ya yi dariya ya ce "Ai ke ce baki iya ba." Mami ta girgiza kai tana murmushi. "Ku dai kuna nan har yanzu kamar wasu yara" Ta zauna kusa da Zahra sannan ta dafa kafaɗarta "Kin ci wani abu kuwa?" "Eh Mami." "Da gaske?" Kai Zahra ta gyada. Sai Mami ta kalleta da kyau. "Toh shikenan." Amma duk da haka ta miƙe ta koma kitchen. Ba jimawa ƙamshin gwate ya fara tashi a parlon Ya Umar ne ya fara cewa, "Hmmmmm Mami." Mami ta yi dariya ta ce, "Kar ka fara." Zahra ta kalli kitchen ɗin. "Gwate ne?" "Eh." Mami ta amsa daga ciki "Na dafa miki da kaina" Zahra ta yi mamaki "Danni Mami?" "Eh mana." Mami ta fito da plate ɗin tana ajiye wa a gabanta "Tunda na san kina son shi." Wani abu ya motsa a zuciyar Zahra, ta kalli Mami Sai kawai ta ji idanunta sun cika da hawaye, amma ta yi saurin mayar da su baya Mami kuwa ko kaɗa bata nuna ta lura ba. Kawai tace, "Ki ci kafin ya huce." Murmushi Zahra ta yi "Nagode Mami naa" A wannan yammacin, tsakanin hirar Ya Umar, kulawar Mami da kuma zaman gidan, Zahra ta ji wani sashe na damuwar da ke zuciyarta ya ɗan sauka, Ko da yake ciwon na nan, amma a karo na farko cikin kwanakin nan, ta samu kanta tana dariya ba tare da ta tilasta wa kanta ba #08110615256 #Jiddatulkhayr writes Book 1 Chapter 24 Wajen kwana uku kenan Ibrahim bai tako gidan ba, ba kira, ba message, ba kuma wata alama da zata nuna yana tunanin dawowa Da farko abin ya dinga ci wa Zahra tuwo a ƙwarya, amma sannu a hankali ta fara sabawa Kullum idan ta tashi daga makaranta, gidan su take wucewa kai tsaye. Zama da Mami, Abbah da Ya Umar ya zama wani abu da yake rage mata damuwa. Duk da ciwon da ke zuciyarta, amma akwai lokutan da take mantawa da Ibrahim gaba ɗaya idan tana tare da iyalinta, Duk da ga matsin lanbam Batoul. Yau ma kamar yadda ta saba, ta tashi da safe, ta yi sallolinta da shirye-shiryenta kafin ta nufi makaranta. Da ta isa, ta haɗu da Firdausi a harabar department ɗinsu. Tun daga kallon farko Firdausi ta gane yau Zahra ta ɗan fi kwanakin baya walwala, ta fara dawowa ainahin pretty Zahratyy dinta na baya Bayan sun gama lecture na farko ne suke zaune a wani cool down Firdausi ta matsa kusa da ita ta ce "Na yi magana da Lovie Dovie." Zahra ta ɗaga kai ta kalleta "Me tace?" "Mun yi chatting jiya da dare" Zahra ta haɗe gira. "Toh?" Firdausi ta ɗan yi murmushi "Tace ta dawo gari" "Okay" kawai Zahra ta ce a takaice dan bata kaunar wannan maganar "Kuma ta amince mu haɗu yau bayan lectures" Cewar Firdausi Nan take fuskar Zahra ta canza Ta ce "A'a, babu inda zani" Firdausi ta zaro ido "Meye a'a?" Haɗe rai tayi ta ce "Bana zuwa." "Why?" Firdausi ta tambaye ta "Firdausi na gaji da wannan maganar." Ta ce Tana girgiza Kai "Wallahi bana son ganin kowa da zaina tunamin shi" Firdausi ta matsa kusa da ita "Listen to me, Zahra..." Kai Zahra ta girgiza. "A'a." "Ki saurare ni mana" Firdausi ta ce Shiru Zahra tayi Tana kallon wani wajen daban Firdausi ta ci gaba. "Ba wai saboda yarinyar ba ne, ko shi kansa Ibrahim din" "Toh?" Zahra ta ce "Saboda ke." Zahra ta haɗe gira tana mata wani kallo ta ce "Yaya saboda ni?" Firdausi ta ɗan yi murmushi. "Kin manta yadda kika yi kuka kwanakin baya?" Zahra ta kau da kai "Kin manta yadda Ibrahim ya raina ki a gaban mutane, nuna bayi da mata tamkar con fuska ne Zahra" Shiru tayi ba tare data ce mata kala ba Firdausi ta dafa hannunta "Toh yanzu kina da damar da zaki nuna masa cewa ba zai iya wasa da ke yadda yake so ba, ta Duk inda ya buga kwallon sai dai ya fadi ba dai ya ciki ba" "Bana son ɗaukar fansa" ta ce ba tare data kalli firdausi ba Firdausi ta yi dariya. "Wannan ba fansa ba ne, Zahra" "Toh meye?" "Reality check." Cewar Firdausi Zahra ta kalleta Firdausi ta ci gaba. "Kin san me yasa yake jin zai iya yin duk abin da yake so?" Zahra ta ce "Why?" Firdausi ta ce "Saboda yana tunanin komai zai ƙare da haƙuri." Ta ɗan yi shiru. "Yanzu karon farko zai gane cewa akwai sakamakon abubuwa" Zahra ta fara tunanin maganar firdausi Firdausi ta sake cewa, "Mu tafi kawai Zahra, muje muga yadda abun zai kasance" Zahra ta ce "Firdausi..." "Please." Firdausi ta katseta, ta kama hannunta. "Ko ba komai ki zo ki ji me zata faɗa." Na wasu daƙiƙu Zahra bata ce komai ba, sai daga ƙarshe ta sauke numfashi "Okay." Firdausi ta yi murmushi ta ce "Yauwa, ko ke fah Zahra" "Amma idan na ga bana jin daɗi zan tafi." "No problem." Daga haka suka ci gaba da lectures ɗinsu. Bayan an gama lectures na ranar, suka yi sallama da sauran friends ɗinsu. Firdausi da Zahra suka wuce parking space "Straight." Cewar Firdausi ta faɗa tana ɗaure seat belt Zahra ta tada motar "Kinga dai ban san me kika shirya ba." Firdausi ta yi dariya "Za ki sani nan da ɗan lokaci" A haka suka kama hanya. Bayan kusan mintuna talatin da tafiya, suka isa wani babban garden da ake yawan zuwa shakatawa. Wajen ya yi kyau sosai, ga ciyayi kore, ga manyan bishiyoyi, da kujeru a wurare daban-daban Zahra ta yi parking, ta kashe motar. Sai ta juya tana kallon Firdausi. "Anan?" "Eh." Firdausi ta amsa. Suka sauka tare Yayin da suke shiga cikin garden ɗin, Zahra ta fara jin wani irin bugun zuciya. Ba ta san me zata gani ba, ba ta san me zata ji ba Amma abu ɗaya ta sani... Ayau akwai wani abu da zai fito fili, dole ta sake posting hotonta da Ibrahim ko zai tafi viral A tare suka shiga cikin garden ɗin. Idanun Zahra suka fara kaiwa kan yarinyar tun kafin su ƙarasa. Zaune take a wani gefen wajen, sanye da wasu matsattsun kaya, riga da wando ne a jikinta, sai kanta data daura vintage scarf, tana ta danna waya Firdausi ta ja numfashi "Ga ta can." Ba tare da Zahra ta ce komai ba suka nufi wajen. Da suka isa, Firdausi ce ta fara magana. "Hello." Yarinyar ta ɗaga kai. "Hello." Idanunta suka sauka kan Zahra, ta tsaya kallonta Kallo irin wanda ba a iya gane ko na mamaki ne ko na ƙiyayya ba, sai kallon take yi, tun daga kanta har ƙafafunta. Zahra kuwa ta zauna cikin nutsuwa kamar bata lura da kallon data ke mata ba Firdausi ta gyara zamanta. "Yaya dai?" Yarinyar ta ɗan yi dariyar gefen baki. "Lafiya, Ashe dai kuke son gani na" Amma idanunta suna kan Zahra ta karasa maganar Firdausi ta lura da hakan "Kin san dalilin da yasa muka kira ki ko?" Kai ta girgiza. "A'a, ai sanin gaibu sai Allah" Firdausi ta ce, "Maganar Ibrahim ne, Wanda kike tare da shi, wato khalil" Nan take fuskar yarinyar ta canza. "Toh? Ai nariga da nayi sensing hakan" Firdausi ta nuna Zahra "Wannan ita ce matarsa" Yarinyar ta kalli Zahra, sai ta sake kallonta, daga ƙarshe ta ce, "Na sani, na mata farin sani a media, ai shiyasa Nace miki nayi sensing abun daya kawo ku" Zahra da Firdausi suka kalli juna Firdausi ta haɗe gira. "Kin sani?" "Eh." Tace a takaice Tana tauna cingam "Yaushe kika sani?" Firdausi ta ce "Wannan kuma ruwana ne" Ta ce ba tare data kalle ta ba "Bangane ba?" Firdausi ta ce Ta ɗaga kafaɗa. "Dama ba lalle ki gane ba" Firdausi ta fara jin haushi "Kin san yana da mata amma kika ci gaba da bin sa?" Yarinyar ta kalli Firdausi "Haramun ne dan ina tare da shi?" Firdausi ta yi shiru Tana mata wani kallo, Zahra kam bakinta rufe wa yayi dan mamaki Yarinyar ta ci gaba. "Shi yake bina, ni bana binsa." Zahra dai tana zaune tana kallonta. A hankali ta ce, "Kin san amma auren mu bai dade ba ko?" Yarinyar ta juyo gareta. "Eh." "Toh me yasa baki nesanta kanki ba?" Wani murmushi yarinyar ta yi. "Saboda ba ni ce matsalarki ba." Nan take Firdausi ta fusata. "Excuse me?" Yarinyar ta juya gareta. "Ehhh kar ki tsoma dan ba'a min ihu! Idan mijinta yana bina ai shi ya kamata ki kama, ba ni ba." Firdausi ta matsa gaba "Kin san me kike faɗa kuwa?" "Na sani." Yarinyar ta amsa ba tare da tsoro ba. "Ni ba wata yarinya ce da za a zauna a yi min kashe di ba. Idan Ibrahim ya kira ni, matsalarsa ce" Firdausi ta zaro ido. "Wallahi kina bani mamaki." "Ni kuma ke kike bani." Yarinyar ta mayar. Zahra ta ji kanta yana sarawa. Tun da suka zo ba ta ga wata alamar nadama a tare da yarinyar ba, sai ma wani irin taurin kai. Firdausi ta sake cewa, "Toh idan kin san yana aure me yasa baki block ɗinsa ba?" Yarinyar ta yi dariya. "Saboda bani da tsoro kuma Ina son sa kamar yarda yake mutuwar so na" Nan kam Firdausi ta fusata sosai "Wallahi kina raina mana hankali, wani irin banzar magana ne wannan" "Idan raini ne ma, ai ba ku ne kuka zo nemana ba?" Yarinyar ta mayar da martani Zahra ta ji gaba ɗaya bata son zaman wajen, ta miƙe tsaye. Firdausi ta kalleta." "Zahra...." "Mu tafi" ta faɗa a taƙaice Firdausi ta kalli yarinyar cikin takaici Ita kuwa sai kallonsu take yi, tanaa tauna cingam tare da kaɗa kafa, kamar ma tana jiran su tafi ne dan kamar sun tare mata iska Ba tare da ƙarin magana ba suka juya suka bar wajen. Har suka isa motar Zahra babu wacce ta ce komai, ran kowa a ɓace yake. Da suka shiga mota, Zahra ta dafa steering tana kallon gaba. Sai daga ƙarshe ta juya ta kalli Firdausi. "Kin ga abin da kika jawo mana?" Muryarta cike take da takaici "Wallahi da nan zo ba, gashi munja ma kanmu rai ni" sai kuma ta suke ajiyar zuciya ta ce "Dama daga ganinta bata da tarrbiyya, dagaske nayi nadaman zuwa" Firdausi ta buɗe baki zata yi magana sai kuma ta rasa abin cewa, domin ita kanta ba wannan take tsammani ba Ta yi zaton za su haɗu da wata yarinya mai tsoro ko kunya like pretty, amma sai suka tarar da wacce ko kaɗan bata damu ba lalle taji ɗarr A hankali Firdausi ta jingina da kujera. Shiru ya mamaye motar. Kowacce na nata tunanin. Kuma karon farko tun da suka fara wannan shirin, Firdausi ta kasa samun kalmar da zata kwantar wa Zahra hankali. A haka dai suka rabu da Firdausi. Tun daga hanyar dawowa gida, Zahra bata sake cewa komai ba. Abubuwan da suka faru a garden ɗin ne suke ta yawo a kanta. Ko da Firdausi ta yi ƙoƙarin yin magana, amsawa kawai take yi da "hmm" ko "toh." Da ta isa gida kai tsaye ɗakin Mami ta wuce. Mami tana zaune kan kujera tana duba wasu takardu lokacin da Zahra ta shiga. "Assalamu alaikum Mami." "Wa alaikumus salam." Mami ta amsa tana ɗaga kai. Da kallon farko ta lura Zahra bata cikin yanayi mai kyau. "Zahra lafiya?" Murmushi Zahra ta yi wanda bai kai zuciya ba. "Lafiya lau Mami." "Kinga fa ,kamar ba lafiya ba." "A'a Mami, stress ne kawai." Mami ta ci gaba da kallonta na wasu daƙiƙu. Sai daga ƙarshe ta gyada kai. "Toh Allah ya sauƙaƙa." "Ameen, Mami naa, ta ce Zahra ta kwanta a gefen Mami na ɗan lokaci, amma gaba ɗaya hankalinta baya wajen. Mami ma ganin bata son magana yasa ta ƙyaleta. Can mai aikinsu ta shigo ɗakin da plate din snacks sai kuma smoothie, Zahra ta mike ta karba ta ce "Sannu Fatima" Murmushi tayi ta ce "Bakomai hajiya karama" tama Mami ma sallama daga haka ta juya ta fita Kadan Zahra taci ta sake kwnaciya gefen Mami Daga baya ta miƙe ta wuce ɗakinta na gidan ta kwanta, har aka yi Magrib. Bayan ta idar da sallah ne ta yanke shawarar komawa gidanta. Tayi wa Mami sallama, Mami ta ce "Ki shiga kitchen ki ɗiba abincin kar ki tafi ki shiga kitchen" Murmushi tayi ta ce "Mami kin manta akwai Farida ne, kuma nasan ta ajiye min" daga haka ta sake mata sallama Ya Umar ma ya nace sai ya rakata har gida Da ƙyar ta lallaba shi ta ce zata iya tafiya ita kaɗai. A haka ta shiga motarta ta kama hanya. Tafiyar ma ba daɗi take mata ba. Tunanin Ibrahim ne ya sake dawowa. Kwana uku kenan, babu kira, babu message Babu kuma wata alama daga gare shi. Wani lokaci har tana mamakin ko yana tunaninta ma Da ta iso layinsu, horn tayi mai gadi ya bude mata gate, shiga tayi da motar Sai dai tun kafin ta ƙarasa parking, idanunta suka sauka kan wata mota Nan take ƙafarta ta tsaya, ta sake kallon motar Ta san motar sarai, Motar Khalil ne Wani irin mamaki ya bayyana a fuskarta. "Khalil?" Ta faɗa a hankali Ta kashe motarta amma bata fito nan take ba, zama kawai tayi tana kallon motar Me yake yi a gidan? Yaushe ya zo? Kuma me ya kawo shi bayan duk abubuwan da suka faru? Wani irin bugun zuciya ta fara ji. A hankali ta buɗe ƙofar motar ta fito. Idanunta na kan motar. Har yanzu ma kamar bata yarda da abin da take gani ba. Ta ɗaga kai tana kallon saman gidan. Haske na fitowa daga parlorn ƙasa. Alamar akwai mutane a ciki, ta haɗiye miyau. Sannan ta kama hanyar shiga gidan a hankali. Yayin da take isa bakin ƙofar parlorn, zuciyarta tana bugawa da ƙarfi. Tayi sallama kafin ta tura ƙofar ta shiga. Nan take idanunta suka sauka kan Khalil. Yana zaune a parlorn, shi kaɗai. Kuma kamar wanda ya daɗe yana jiranta. #Farashin izzah #jiddatulhayr writes #08110615256 *FARASHIN IZZAH* Book 1 Chapter 25 Ya miƙe tsaye daga inda yake zaune “Finally.” Ya faɗa yana kallon agogon hannunsa. Zahra ko kallonsa bata yi ba, ta cire key ɗin kofar ta nufi hanyar stairs kai tsaye, kamar ma ba ta gan shi ba haka tayi pretending Da mamaki reacton ɗinta ya bita da kallo, sai data kai kusa da matakalar ne ya ɗaga murya “Malama, dakata anan.” Sauke kafar nata tayi, sannan a hankali ta juya, wani irin kallo ta watsa masa. Kallon da ya nuna bata cikin yanayin da za ta iya ɗaukar rashin hankali, she’s ready to exchange words with him “Me kuma?” Ta tambaya a taƙaice Khalil ya yi wata irin dariya. “Nine zan tambaye ki me kuwa” Ya taka zuwa gabanta “Wane dalili ne zai sa ki dinga bin girlfriends ɗina kina tayar musu da hankali?” Zahra ta ɗaga gira “Au” ta faɗa tana gyara tsayuwarta “Ita Lovie Dovie ɗinka ta faɗa maka kenan?” Fuskarsa ta ɗan canza. “Whatsoever Zahaaaaa…” ya kare maganar da karfi kamar zai dake ta “Abin da ya dame ni shi ne, me yasa kike bin mutanen da ba su san ki ba? Dole sai kin fada musu Ina da mata dan su rabu da ni?“ Zahra ta yi dariyar rainin hankali “Oh wow.” Ta fada tana tafe hannu “So yanzu kai ka zo gidana ne saboda wannan?” “Answer the question.” Ya katse ta. “What is wrong with you Zahra?” Nan take ta zaro ido. “What is wrong with me?” “Yes.” Ya amsa. “Me yasa za ki dinga shiga rayuwar mutane, dole sai nayi rayuwa da ke kadai ne?” Zahra ta yi dariya, dariyar takaici “Khalil, ka tabbata kana son wannan hirar?” “Very much.” Ya amsa “Good” Ta gyada kai “Toh ni kuma ina da tambaya guda ɗaya.” “Ask.” Ya fada yana folding hannaye “Wane dalili ne zai sa married man ya dinga bin mata a waje kamar bunsuru” Khalil ya haɗe gira, sosai maganar ta dake sa “Don’t start Zahra dan zamu samu big issues wlh” “No.”Ta ɗaga hannu “Let’s start, I’m ready for it” Ya furzar da iska. “Kina son drama sosai, amma kar ki yarda nayi maganar da zaki yi kuka” “Drama? Ai ni bana tsoro Ibrahim” Ya ce “Okay.. naga alama Baki da tsoro amma kina dab da nadama kuwa” Zahra ta yi murmushi. Murmushin da bai kai ciki ba “Interesting.” Khalil ya ci gaba. “Ina miki warning ki fita harka ta da Duk wacca ta raɓe ni, kuma idan kina son zaman Lafiya stop touching my phone” “Your business?” Ta katse shi “Really?” “Yes.” Ya amsa “Toh ka daina kawowa har cikin gidana shi harkan naka, taɓa waya kuma ai na daina tunda ba alkhairi kake shukawa ba” Nan take ya yi tsaki “Waye yake causing matsala a tsakanin mu idan ba ke ba, a dole sai kin duba wayata kuma ko sau dari zaki duba ba zamu daina samun matsala ba” “Because you are the problem.” Ta mayar masa ba tare da tunani ba “Excuse me?”Ya matso kusa da ita “Repeat that.” “I said you are the problem.” Ta maimaita tana kallonsa kai tsaye “Khalil, ka daina acting like victim.” “Victim?” Ya yi dariya. “So yanzu ni ne victim?” “A’a” Ta gyara masa “Kai ne culprit.” Wani irin shiru ya biyo baya Kallon juna kawai suke yi Khalil ya girgiza kai. “Unbelievable.” “Ai ni ma abin da nake gani yanzu unbelievable ne” Ta mayar. “Imagine married man yana defending girlfriends ɗinsa, just imagine fah….” “Watch your mouth Zahra” Ya faɗa da gargaɗi “No” Ta amsa nan take. “You watch your actions first” Ya ɗan yi shiru kafin ya ce, “At least they respect me.” Nan take fuskar Zahra ta canza. “What?” “Kin ji ni ai” Ya amsa “At least they know how to talk.” Zahra ta ji wani abu ya tsaya mata a maƙoshi, na wasu daƙiƙu ta kasa magana, sai daga ƙarshe ta yi murmushi, murmushi mai cike da ciwo “Oh” Shi kenan kawai ta faɗa Ta gyada kai a hankali “Oh, I see.” Khalil wani kallo yake mata Ita kuwa ta ɗauki jakarta a zuciye “Congratulations then” Ta faɗa “What?” Ya tambaya “Congratulations” Ta maimaita. “If they make you that happy, good for you.” Sai ta juya. Khalil ya ɗaga murya. “Zahra!” Amma ko juyowa bata yi ba. Kai tsaye ta hau stairs. “Zahra I’m talking to you!” Ya sake maimaitawa Ku waiwayowa bata yi ba balle yasa ran zata kulasa Tana isa sama ta buɗe ƙofar ɗakinta da ƙarfi, ta shiga ciki tare da banke ƙofar a bayanta Khalil kumq ya tsaya a parlorn ƙasan, hannayensa a aljihu, yana huci saboda takaici Ita kuma Zahra bayan ta shiga daki tana tsaye bayan ƙofar ɗakinta, zuciyarta na bugawa da ƙarfi tsabar bakin ciki Ba saboda maganar girlfriends ɗin ba, sai saboda kalmar da ya jefa mata. “At least they respect me.” Kalmar ce kaɗai ta isa ta sake karya wani ɓangare na zuciyarta. Daga ƙarshe shima Khalil ya haura sama zuwa dakinsa. Yana shiga ya banke ƙofar a bayansa da ƙarfi. Wani irin takaici yake ji kamar zuciyarsa zata faso. Har yanzu kalaman Zahra na yawo a kansa Ya cire agogonsa ya jefa kan side drawer. Tsaki ya ja. A rayuwarsa bai taɓa tunanin wata rana za su kai ga irin wannan matsayi da Zahra ba A gefe guda kuma, Zahra na zaune kan gadonta. Hawayen da take hana kanta ne tun a parlorn suka sake kubuce mata, sosai take kuka Kukan da take yi tun daga zuciya ce, a hankali ta dafe cikinta Saboda wani ciwo da yake mata “Wallahi na gaji…” Ta furta a hankali. “Na gama zama da Khalil as miji…” Tafi awa tana kuka, tunawa tayi bata yi sallar isha’i ba yasa ta share fuskarta da sauri, miƙewa tayi ta nufi toilet Alwala tayi cikin nutsuwa sannan ta dawo ɗakin, sallaya ta shimfiɗa, ta tada kabbarar sallah Dogon lokaci tayi tana addu’a bayan ta idar. Addu’o’in da ita kanta bata san lokacin da ta dauka tana yi ba, tana yi ne tana kuka Daga ƙarshe ta jingina da bango tana kan sallayar, tunanin rayuwarta kawai take yi. Can ba tare da ta sani ba bacci ya fara rinjayarta. A haka bacci ya ɗauke ta. Misalin karfe biyu na dare, wani irin yunwa ne ya farkar da ita, ta buɗe idanunta a hankali Da farko bata ma gane inda take ba. Sai can sannan ta tuna, Akan sallayan bacci ya dauke ta A hankali ta miƙe tana jin jikinta babu ƙarfi, ga ciwon da maranta yake yi, ta gyara hijabin kanta sannan ta fito daga ɗakin Ta nufi hanyar stairs domin ta sauka zuwa kitchen Sai dai tana wucewa ta lura da wani abu… Ƙofar ɗakin Khalil a buɗe take. Ta tsaya tana mamaki, toh ko ya shiga dakin ne jiya daya fita sai bai kulle ba? Har ta yi niyyar wucewa, sai kuma wani abu ya sa ta waiwaya A hankali ta ƙarasa bakin ƙofar, ta leƙa ciki Nan take mamaki ya bayyana a fuskarta Khalil yana cikin ɗakin, yana bacci Ba fita yayi ba kamar yadda zuciyarta ta ɗauka ba. Fitilar bedside lamp ce kawai ke kunne Kayan da ya sa tun na daren ma bai canza su ba, ya ana kwance gefe ɗaya, wayarsa a ajiye kusa da shi Alamar dai ya yi bacci ne ba tare da ya shirya ba Zahra ta tsaya tana kallonsa. Wani sashe na zuciyarta ya tuna mata kwanakin da suka yi farin ciki. Kwanakin da ko minti ɗaya baya son ta ɓace daga ganinsa. Sai dai tunanin daren yau ya dawo mata. Nan take ta kawar da idanunta. Ta haɗiye miyau. “Tunani kawai nake yi…” Ta faɗa a ranta. Wani tunani ne yazo mata rai, hakan yasa a hankali Zahra ta ƙarasa cikin ɗakin, har yanzu yana kwance yana bacci, tsayawa tayi tana kallonsa na ɗan lokaci Tunawa da yadda ta yanke hukuncin cewa ba zata iya ci gaba da rayuwa da shi ba yasa zuciyarta sake zama cikin kunci A hankali ta ɗauki wayarsa. Numfashinta ya fara sauri. Allah ya bata sa’a, tana ɗaukar hannunsa ta daura yatsarsa kan fingerprint ɗin wayar. Nan take wayar ta buɗe. Ta saki ajiyar zuciya. Da sauri ta fito daga ɗakin zuwa nata. Zaunawa tayi bakin gado tana riƙe da wayar, abu na farko da ta fara yi shi ne shiga gallery Folder ɗinsu ne ya fara buɗewa, hotuna, videos, selfies, da duk abin da ya taɓa nuna akwai soyayya tsakaninsu Idanunta suka cika da hawaye Sai dai wannan karon bata tsaya tunani ba Ɗaya bayan ɗaya ta fara gogewa, har sai da ta tabbatar babu ko guda da ya rage Daga nan ta shiga wasu folders tana duba ko akwai wani abu da ya rage. Bayan ta gama, sai ta shiga Instagram. Ta yi logging account ɗinsa a wayarta. Ta san idan gari ya waye kuma ta samu sarari, zata shiga ta goge duk wani abu da ya haɗa su. Ta sake komawa gallery domin ta tabbatar da komai ya tafi. Sai kawai idanunta suka sauka kan wani hoto, da farko bata gane ba. Sai da ta buɗe shi, nan take zuciyarta ta buga Saudat ce… Kawarta Saudat da Khalil A cikin ɗakinta ne suka yi wannan hoton shi da ita, jiri ta fara ji ta fara nanata innalillahi wa Inna ilahir rahiun Hannunta ya fara rawa Khalil zallan three-quarter ne a jikinsa. Saudat kuma sanye take da half vest da bombshort. Mirror selfie ne. Kuma daga yadda suke tsaye babu shakka suna cikin sakewa sosai, Dan Saudat a kirjinsa take a kwance Zahra ta sake buɗe wani. Sai wani, sai wani, duk su biyun ne. Wasu tana kwance a jikinsa, wasu suna dariya Numfashinta ya ɗauke na wasu daƙiƙu. Ta ji wani irin zafi ya ratsa ta. Hawaye suka fara zuba ba tare da izini ba Da sauri ta tura wa wayarta duk hotunan. Bata ma san tsawon lokacin da ta ɗauka tana yin hakan ba. Da ta gama, ta yi minimizing gallery ɗin. Ta goge duk wata app da ta shiga. Ta miƙe da niyyar fita. Sai kuma taji muryarsa. “Bani wayata.” A razane ta ɗaga kai. Khalil yana tsaya bakin kofar Idanunsa a buɗe yana kallonta Zahra ta haɗiye miyau. Amma ta daure bata nuna masa komai ba. Ta miƙa masa wayar, ya karɓa Sai ya yi murmushin gefen baki. “Maganin ki da bincika min waya.” Zahra ta haɗe fuska Bata ce komai ba Zai fita ta samu kanta da ce masa “Duk abun da kayi Kai da Allah ne” Ya juyo yana murmushi ya ce “Na ga ko uban naki ma bada mace daya yake tare ba” Nan take Zahra ta ɗago “Enough Khalil” Ta faɗa da ƙarfi “Wasa-wasa kar ka sa ubana cikin maganar nan.” Kallon kallo suka shiga yiwa juna Sai Zahra ta juya ta wuce ta gefensa ba tare da ta sake cewa komai ba Kai tsaye kitchen ta nufa. Tana tafiya tana jin zuciyarta kamar zata faso saboda zafi Shi kuma ya bita da kallo Sai daga ƙarshe ya girgiza kai, ya juya ya koma dakinsa, yana shiga ya kwanta, ba jimawa bacci ya sake ɗaukarsa A kitchen kuwa Zahra ta jingina da kitchen cabinet tana kukan mai tsuma zuciya Kuka irin wanda mutum yake yi idan ya kai ƙarshe, ta rasa me zata yi, ta rasa wanda zata faɗawa, ta rasa yadda zata ci gaba da ɗaukar wannan rayuwar How on earth kawarta wacca suke tare tun day one ta kalli picture dinta tare da mijinta for that matter, kuma a ɗakinta, Innalillahi wa Inna ilahir rajiun, when? How? Itama bata sani ba Daga ƙarshe ta fito ta koma ɗakinta. Wayarta ta ɗauka ta kira Firdausi. Sau ɗaya, sau biyu, sau uku. Ba a ɗaga ba, ta kalli lokaci Kusan ƙarfe uku na dare ne. Nan take ta kashe kiran. “Bari…” Ta faɗa a hankali “Kar na tashe ta.” Ta ajiye wayar Sai dai bacci ko kadan kuma bata ji, Dan ya kaurace mata A haka ta zauna har aka kira sallar asuba tana aikin kuka Da ƙyar ta iya miƙewa saboda wani ciwon mara da ya sake sakota gaba Ta yi alwala, ta yi sallah Bayan ta idar kuma ta daɗe tana addu’a Duk da ciwon da ke zuciyarta, abu ɗaya ya bata ɗan sauƙi Ta tuna cewa ta riga ta goge duk wani abu nata a wayarsa, komai ya tafi Ta daɗe tana zaune kan sallaya Hawayenta na zuba lokaci zuwa lokaci, har gari ya fara waye wa Wayarta ne ta fara ringing, ta ɗauka a hankali, ta kalli screen ɗin sai taga sunan Firdausi Numfashi ta ja sannan ta yi receiving. “Hello?” Firdausi ta fara magana tun kafin Zahra ta ce wani abu. “Lafiya Zahra? Zahra, what happened? You called me around 3 a.m. Please talk to me. I’m really worried Zahra” Zahra ta rufe idanunta, ta ji wani irin ƙulli ya sake tokare mata maƙoshi. Firdausi na can tana jiran amsarta gaba daya hankalinta a tashe “Zahra?” A hankali Zahra ta buɗe baki ta ce “Firdausi…” Sai kuma muryarta ta karye Hawayen da take rikewa suka sake gangaro mata Firdausi ta tashi zaune daga kan gadonta. “Me ya faru? Zahra, talk to me.” Shiru. Sai sautin kukanta kawai. Firdausi ta fara firgicewa. “Wallahi kina bani tsoro. Me ya same ki? Talk to me please Zahra” Da ƙyar Zahra ta samu ta furta. “Firdausi…” “Na’am.” Ta ce “Zan mutu.” Nan take Firdausi ta miƙe tsaye. “What!” “Zuciyata zafi take yi…” Tana gama faɗin haka ta fashe da kuka. Kuka mai ciwo. Kafin Firdausi ta sake cewa wani abu, Zahra ta kashe wayar. “Hello?” “Hello Zahra?” “Hello!” Firdausi ta sauke wayar tana kallo, gabanta ya faɗi dabas ta zauna a kasa A rayuwarta bata taɓa jin Zahra a irin wannan yanayin ba Ba tare da bata lokaci ba ta miƙe tsaye Ta fara neman hijab ɗinta. Da sauri ta saka, ta ɗauki wayarta, ta fito daga ɗakin. A kitchen ta samu Mama tana bakin murhu tana girki. Da alama dama yanzu ta gama zikirin asuba. Mama ta ɗaga kai tana kallonta. “Firdausi lafiya kuwa?” Firdausi ta ƙarasa wajen. “Mama zan tafi gidan Zahra.” Mama ta ajiye cokalin hannunta. “Me ya faru?” Firdausi ta girgiza kai. “Ban sani ba. Yanzu na kira ta, ta ɗauka amma kamar kuka take. Bata iya magana ma.” Nan take fuskar Mama ta nuna damuwa. Duk da ƙarfin halin da take yi, bata ji daɗin maganar ba. “Allah ya sa lafiya.” “Ameen.” Firdausi ta amsa. Mama tace, “Ki gaishe ta. Ki je ki ga yadda take.” “Toh Mama.” Ta juya zata fita. Sai kuma ta sake komawa ɗakinta. Ta ɗauko handbag ɗinta. Hijab ta gyara sosai. Har zata fita sai kuma ta tsaya tana kallon Mama. “Mama zaki iya ko?” Mama ta yi murmushi. “Eh mana. Ki tafi.” Firdausi ta gyada kai. Ta juya. A tsakar gida ta hango Abdul yana wanke-wanke. “Abdul.” Ya ɗaga kai. “Na’am Addah.” “Ka taya Mama idan ka gama da wanke wanken .” “Toh Addah.” Sai ya ƙara cewa, “Sai kin dawo.” Firdausi ta gyada kai. Daga haka ta buɗe gate ta fita, gabanta na ci gaba da faɗuwa A ranta addu’a kawai take yi Allah ka sa Zahra lafiya. Saboda yadda muryarta ta kasance a wayar, ba ƙaramin tsoro ta bata ba #Jiddatulkhayr writes #08110615256 *FARASHIN IZZAH* Book 1 Chapter 26 Firdausi ta fito daga gida ko kallon gabanta bata yi Tun daga lokacin da Zahra ta katse wayar, zuciyarta ta kasa samun nutsuwa A bakin titi ta tsaya tana jiran abin hawa. Motoci na wucewa, napep na wucewa, amma ko ɗaya yaki tsayawa Lokaci zuwa lokaci tana sake danna number Zahra. Wayar tana ringing, amma ba a ɗagawa Hakan ya ƙara dagula mata lissafi. "Ya Allah ka sa lafiya..." Ta faɗa a hankali Da ƙyar dai wani napep ya tsaya, wata tsohuwa ce kawai a ciki, ta shiga haɗi da faɗa masa inda zai kaita Tun daga nan ma wayar Zahra take ta kira, yana shiga amma kuma bata dauka Firdausi ta rasa irin tunanin da zata yi. A rayuwarta bata taɓa jin muryar Zahra kamar yadda ta ji ta yau ba. A ɓangaren Zahra kuwa... Bayan ta kashe wayar, ta zauna bakin gado tana kuka. Kukan da ta yi har ta gaji, har hawayen ma kamar sun fara ƙafewa Wayarta na gefe, amma bata da ƙarfin sake ɗaukarta Hotunan da ta gani ne kawai ke yawo a fuskanta Saudat... Kawarta Saudat... da Khalil. Tana rintse idanunta sai ta kalli hotunan, sai ta bude su da sauri, ta dafe kanta Wani irin ciwon maran kuma yana karuwa mata, a haka ta jingina da bango tana kuka a hankali, ko da wasa bata taɓa ɗauka akwai ranan da zata shiga kunci ko tayi kuka a rayuwarta ba Farida ta fito daga ɗakinta tana tunanin aikin da aka saka ta anya zata iya? Ta fara aikace-aikacenta kamar yadda ta saba, ta share parlorn, ta gyara dining, daga nan ta nufi kitchen. Can aka fara bugun gate din gidan, da farko bugun a hankali ake yi, sai kuma aka fara da karfi Farida ta ɗago kai "Wayyo wa ya zo haka da sassafe?" Ta faɗa tana cire apron ɗinta. Ta fita da niyyar zuwa buɗewa, sai dai kafin ta isa, mai gadi ya fito da sauri daga toilet ya buɗe gate ɗin Firdausi ce ta shigo da saurin ta Kamar ma zata faɗi saboda hanzari Farida ta ƙarasa gareta "Ina kwana Anty Firdausi." "Lafiya lau." Ta amsa ba tare data tsaya ba, kuma ta ce "Ina Anty Zahra?" Farida ta ɗan yi mamaki. "Tana ciki mana." "Ta sauko?" Firdausi ta Kara tambaya "A'a" Farida ta amsa "Tun da safe bata sauko ba." Firdausi ta ji gabanta ya sake faɗuwa. "Okay." Kawai ta iya faɗa. Daga nan ta kara sauri Kai tsaye ta nufi sama, ko knocking bata yi ba, ta tura ƙofar ɗakin ta tsaya kallonta Zahra na zaune kan gado. Idanunta sun kumbura sosai, fuskarta tayi jaa Da alama ma tun daga lokacin da suka yi waya bata daina kuka ba. Zahra na ganin Firdausi... sai ta miƙe da sauri, ta ƙarasa gareta, ta rungume ta gam. Nan take kuma ta sake fashewa da wani kukan. Kuka mai taba zuciya Firdausi ta ruɗe "Zahra!" Ta riƙe ta "Me ya faru?" Zahra ta kasa cewa komai sai kukan da take yi ta cigaba "Wallahi kina bani tsoro, gaba na sai faduwa yake" Firdausi ta ƙara faɗa "Talk to me mana. Me ya faru?" Da ƙyar ta samu ta zaunar da ita bakin gado. Ita ma ta zauna kusa da ita Har yanzu Zahra kuka kawai take yi. Firdausi ta kamo hannunta. "Zahra, ki kalle ni." A hankali Zahra ta ɗago. "Menene?" Sai Zahra ta miƙa hannu, ta ɗauki wayarta, Gallery ta shiga, ba tare da ta ce komai ba ta miƙa mata wayar Firdausi ta karɓa cikin rashin fahimta. Ta fara kallon hoton farko A take ta zaro idanuntan kamar zasu fito fili "Wai me...? Me nake gan..?" Tayi sliding wani, nan take ta miƙe tsaye Wayar ma kusan faɗuwa tayi daga hannunta "What?!!!!" Ta faɗa da ƙarfi Sai ta sake kallon hoton, sannan a jefar da wayar kan gadon saboda tsananin mamaki "Saudat?!" Ta faɗa "Saudat?!" Zahra ta rufe fuskarta da tafin hannunta, sabon kuka ya sake ƙwace mata Firdausi ta dafe kanta. "Wannan yarinyar mahaukaciya ce wallahi." Ta faɗa cikin fushi. "Saudat kuma?" Ta sake ɗaukar wayar Ta sake kallon hotunan. Kowanne ya fi ɗan'uwansa ɗaga hankali. "Wallahi sai tayi nadamar abin da ta aikata, idan har ni kawace ta gari, Duk halarcin da kika mata?" Ta faɗa a fusace "Na rantse sai tayi nadama." Zahra bata ce komai ba. Kanta kawai ta sunkuyar. Firdausi ta sauke numfashi, ta zauna kusa da ita, ta janyo ta jikinta. "Shhh..." Ta fara bubbuga bayanta a hankali "Karki yi kuka Zahra, nasan abun da ciwo musamman yarda kika yarda da ita, Duk da ba sa'arki bace amma haka ko kyamanta bakya yi kika jawo ta jiki, yanzu please kiyi hakuri ki daina kuka musan abun yi" Amma Zahra ƙara fashewa da kuka take yi, Firdausi ta lumshe idanunta Ita kanta ta ji zafin abin, domin ba wata ba ce, ba yarinya daga waje ba ce balle ace bata san zahra ba, ace kawar Zahra. Kawarta? Wacca tasan sirrinta Wacce suke hira tare. Wacce Zahra ta amince da ita. Ta ƙara rungume Zahra. "Ki yi haƙuri." Ta faɗa a hankali. "Wallahi komai zai wuce." "Ki kwantar da hankalinki saboda cikin da ke jikinki Zahra" "Ki bar ni da Saudat." Ta ƙara faɗa cikin fushi. "Sai ta gane kuskuren da tayi." A haka ta ci gaba da lallashin Zahra. Tana bubbuga bayanta. Firdausi ta daɗe tana lallashin Zahra kafin kukan nata ya ɗan lafa Sai dai ko bayan ta yi shiru, idanunta basu daina zubar da hawaye lokaci zuwa lokaci ba Firdausi na kallonta kawai tana jin tausayinta. A hankali ta miƙe tsaye "Ina zuwa" Ta faɗa Zahra bata ce komai ba, kawai ta zauna a bakin gado tana kallon wani waje Firdausi ta sauko ƙasa, ai tsaye kitchen ta nufa. Farida ta samu tana gyara wajen breakfast, da alama ta gama komai Tana ganin Firdausi ta yi murmushi "Kin ga Anty Zahra?" Kai Firdausi ta gyada. "Na ganta." Farida ta lura da yanayin fuskarta "Lafiya dai?" Firdausi ta yi murmushin dole "Eh lafiya." Sai ta kalli abincin da aka shirya "Ta karya ne?" Farida ta girgiza kai "A'a, Kuma wallahi rabonta da cin  shekaran tun jiya." Firdausi ta sauke ajiyar zuciya, ta san halin Zahra Idan damuwa ta yi yawa, bata ma tuna da abinci "Toh" Kawai ta faɗa. Daga nan ta juya ta sake komawa sama. Tana shiga ɗakin ta tarar da Zahra a yadda ta barta. Har yanzu tana zaune, kai a sunkuye Firdausi ta ƙarasa kusa da ita. "Zahra." Ta kira a hankali Zahra ta ɗaga kai tana kallonta "Mu je ki karya" Kai tsaye ta girgiza kai "Ba na jin yunwa." Firdausi ta ɗan haɗe gira "Ba tambayarki ko kina jin yunwa nayi ba, cewa nayi mu je ki karya" Shiru tayi ba tare data ce komai ba "Zahra kina da ciki." Cewar firdausi Har yanzu Zahra ta girgiza kai "Wallahi ba zan iya ci ne" Firdausi ta zauna kusa da ita "Ko kaɗan ne mana Babyn Abbah" "A'a" "Zahra." "A'a Firdausi." Ta katse ta. "Please." Firdausi ta daɗe tana lallashinta, tana bata baki, tana tunasar da ita halin da take ciki Amma Zahra ta firrrr taki Daga ƙarshe Firdausi ta miƙe, ta girgiza kai "Matsalata da ke taurin kai " Ta faɗa Sai ta juya ta fita, a sake komawa kitchen. Farida tana can tana gyara kayan amfani. "Ta sauko?" Farida ta tambaya. Firdausi ta yi tsaki. "Ta ƙi" "Wayyo." Farida ta faɗa cikin damuwa Firdausi ta buɗe warmers ɗin, ta zaɓi abincin da ta ga zai fi sauƙin ci Ta ɗebo kaɗan, ta haɗa da cup na tea, ta kuma ɗauki ruwa. Farida tana kallonta "Ko zata ci kuwa?" Firdausi ta ɗan yi murmushi "Ko da ba zata ci ba sai na sa ta ci" Ta ɗauki tray ɗin, ta nufi sama Da ta shiga ɗakin, Zahra na nan zaune Firdausi ta ajiye tray ɗin a center table, sannan ta ja kujera ta zauna gabanta "Yanzu." Ta faɗa tana ɗaukar spoon "Ko da ni zan baki a baki ne, sai kin ci" Zahra ta kalleta. A karo na farko tun safen nan wani ƙaramin murmushi ya bayyana a fuskarta Firdausi ta nuna spoon ɗin. "Exactly." Ta faɗa. "Ki yi murmushi yanzu, amma idan na fara baki a baki kar ki ce ban gargaɗe ki ba tass zaki cinye" Duk da ciwon da ke zuciyarta, Zahra ta sake ɗan murmushi. Firdausi kuwa ta ji daɗin ganin hakan, kuma aim dinta taci abincin dan zai taimaka mata da kuma jaririn da ke cikinta. Bayan Zahra ta gama cin abincin da ƙyar, Firdausi ta karɓi plate ɗin ta ajiye gefe. Na wasu daƙiƙu babu wacce ta ce komai. Zahra na zaune tana kallon hannayenta. Firdausi kuma tana kallonta cikin tausayawa. Daga ƙarshe Zahra ta miƙa hannunta ta kama na Firdausi. Wata irin nutsuwa ce ta bayyana a fuskarta. "Firdausi..." Ta kira a hankali. "Na'am." "Yau zan koma gida." Firdausi ta kalleta. "Gida?" Kai Zahra ta gyada. "Eh!Gidanmu." Ta gyara. "Na gama zaman gidan nan ne " Shiru ya ratsa ɗakin. Firdausi ta sauke ajiyar zuciya, gaskiya ne, abin ya yi yawa, fiye da yadda zata ci gaba da cewa Zahra ta yi haƙuri, musamman bayan abin da ta gani da idanunta yau "Kin tabbatar you're okay with it?" Ta tambaya "Eh." Zahra ta amsa ba tare da wata shakka ba "Na tabbatar." Sai ta ƙara da cewa, "Kuma na san Ya Umar zai tsaya min wajen komai." Ta haɗiye miyau. "Har wajen ya karɓo min takardar sakina idan ma shi yaki bani" Firdausi ta daɗe tana kallonta, sai daga ƙarshe ta gyada kai. "Toh." Ta faɗa a hankali "Idan wannan ne abin da kika yanke, Allah ya sa alkhairi, ya kuma baki Wanda ya fi shi wanda zai rike ki da gaskiya" Zahra bata ce komai ba, kawai ta gyada kai Firdausi ta miƙe tsaye, kai tsaye wardrobe ɗin Zahra ta nufa, ta buɗe shi Ta fara ciro takardunta masu muhimmanci, credentials, documents, takardun filaye Duk ta tattara ta saka a cikin wani babban backpack. Daga nan ta buɗe drawer, ta fito da gold ɗinta, sarkoki, 'Yan kunne, Zobuna, a saka su a wani pouch sannan ta zuba su a cikin jakar. Bata tsaya nan ba, ta ciro mata inner wears, Sleeping wears, Abayas, da wasu kaya masu muhimmanci da zata iya buƙata na wasu kwanaki Duk ta ci gaba da zubawa a cikin jakar. Zahra dai tana zaune tana kallonta, kamar wacce jikinta ya mutu Bayan Firdausi ta gama shirya komai, ta rufe jakar Sai ta juya tana kallon Zahra. "Is there anything else you will need?" Zahra ta ɗan yi shiru, sai ta girgiza kai "No." "Kin tabbatar?" "Eh." Firdausi ta gyada kai, rufe backpack din tayi. Zahra ta ɗauki wayarta, ta shiga contacts Yatsanta ya tsaya kan sunan Ya Umar ❤️, da alama zata kira shi, sai kuma ta tsaya Ta daɗe tana kallon sunan, daga ƙarshe ta kashe screen ɗin wayar. "A'a." Ta faɗa a hankali. Firdausi ta kalleta. "Me ya faru?" Zahra ta girgiza kai. "Ba zan kira Ya Umar yanzu ba" "Why?" "Zan masa bayanin komai idan na isa" Ta sauke numfashi "Sannan..." Ta ɗan yi shiru "Na fi son na koma gida ya dawo daga aiki" Firdausi ta kama hannunta. "Toh." Ta faɗa cikin tausasawa "Yanzu ki shirya, anjima sai mu tafi gidan" A karo na farko tun safen nan, Zahra ta ji wani abu kamar sauƙi ya ratsa zuciyarta, ba saboda ciwon ya ragu ba Sai saboda ta yanke hukuncin da taji shine mafi alkhairi gareta Zahra ta miƙe a hankali ta nufi toilet, tana rufe kofar toilet din, Firdausi ta ɗauki wayarta tare da ta Zahra Tayi Unlocking wayar Zahra na, yatsunta suka yi wasu abubuwa cikin sauri Can sai ta kashe screen ɗin ta ajiye wayar a gefen gado, wani irin murmushi ne ya bayyana a fuskarta Murmushin da da wuya mutum ya iya fassara ma'anarsa Sai ga Zahra ta fito daga toilet ɗin, Firdausi ta miƙe da sauri Ta ɗauki tray ɗin da suka ci abinci "Barin mayar da wannan kitchen" Ta faɗa Kai kawai Zahra ta gyada, Firdausi ta fito da tray ɗin, anan parlon sama ta ci karo da Khalil Daga gani yanzu ya gama shiryawa ne, yana ganinta kuwa fuskarsa ta sauya "Keeee!" Ya faɗa yana nuna ta. "Me kike yi anan?" Firdausi ta tsaya, amma bata ce komai ba Khalil ya ci gaba "Ina tambayarki ba? Wani munafurcin ne ya kawo ki nan?" Har yanzu shiru ta masa "Da safe shine har za ki zo gidan mutane." Ya yi tsaki. "Idan ba gulma ba me ya kawo ki nan?" Firdausi ta haɗe fuska, amma ko kallonsa bata yi ba. Ta wuce ta ajiye tray ɗin kan center table na parlon Khalil ya bi bayanta yana magana "Baki da aiki sai shiga tsakanin mata da mazajensu." "Ki fita ki bar min gida, ko ki sha mamaki na" Firdausi ta juya ta nufi ɗakin Zahra. Khalil na biye da ita yana ta magana. Da ta shiga ɗakin,suna hada ido da Zahra tayi saurin mata alama, alamar kar ta ce komai, kar ta tanka masa, balle ya gane zata koma gida, Zahra ta fahimta, ta gyada kai kawai, ta koma kan gado ta zauna daddanna wayanta shi kuma yana tsaye bakin kofar yana ta maganganu Firdausi ta ɗauki hijab ɗinta, sannan ta juya tana kallon Khalil A karo na farko ta yi magana. "Well..." Ta gyara jakarta a kafaɗarta "Zan bar maka gidan." Ta ɗan tsaya. Sai ta ƙara da, "Amma ka sani akwai lokacin da za ka neme ni wallahi, lokacin ne nikuma zan baka amsar maganganunka" Khalil ya yi wani irin murmushin raini, ko amsa mata bai yi ba Firdausi ta girgiza kai, ta wuce ta gefensa, ta fita daga ɗakin. Ta sauko ƙasa, daga haka ta tafi Wata matashiyar budurwa ce kwance kan gado bayan ta gama cin abinci. Wayarta kawai take dannawa tana yawo a Instagram ba tare da wani takamaiman abu a ranta ba. Can wani post ya faɗo mata, da farko ta wuce, sai uma ta dawo baya, ta sake kallon hoton Ta matso wayar kusa da fuskarta. "What??!!!..." Ta furta a hankali Ta sake duba sunan account ɗin, ta sake kallon hoton, nan take ta miƙe zaune "Wayyo Allah!" Ta yi ihu da ƙarfi A take ƙannenta biyu suka shigo ɗakin da gudu "Lafiya?" "Me ya faru?" Ba tare da ta iya magana ba ta miƙa musu wayar, suka karɓa. Da farko ba su gane ba, sai ɗaya daga cikinsu ta zaro ido "Haba!" Ta faɗa. "Wai da gaske ne wannan?" Dayar kuma ta karɓi wayar "Subhanallah..." Ta furta "Kinga comments!" Da sauri suka shiga comment section. Tun a lokacin comments ɗin sun fara taruwa "No wonder..." "I feel sorry for the wife." "Wallahi idan wannan gaskiya ne akwai matsala." "Men are wicked." "This is heartbreaking." "Someone said they were happily married." "Kai duniya..." Budurwar ta ci gaba da scrolling, kowane second comments suna ƙaruwa ne haka shares ma suna ƙaruwa Mutane na tagging juna, wasu suna mamaki, wasu suna zagi, wasu kuma suna neman ƙarin bayani nr A hankali post ɗin ya fara bazuwa, daga Instagram zuwa WhatsApp, daga WhatsApp zuwa Facebook Mutane sai screenshot suke suna forwarding, suna magana a kai Kuma cikin ƙanƙanin lokaci... Post ɗin ya fara yawa #08110615256 #Jiddatulkhayr writes *FARASHIN IZZAH* Book 1 Chapter 27 Fitar Firdausi da wuya, aka ji ƙarar mota a compound, Farida ce ta leƙa ta window sannan ta juya da sauri ta haura sama A hankali ta buga ƙofar ɗakin Zahra. "Anty..." Zahra ta ɗago kanta "Na'am?" "Mama ce." Cewar Farida Zahra ta haɗe gira "Wace Mama?" "Maman Alhaji Khalil." Nan take Zahra ta miƙe ta ce "Ina zuwa" Toilet ta shiga ta wanke fuskarta da ruwan ɗumi, ta goge ta da towel sannan ta gyara scarf ɗinta kafin ta fito, hijab ta saka sannan sannan ta fita A parlorn ƙasa ta same ta zaune, da alama daga gida take saboda babu alamar gajiya a jikinta Zahra ta ƙarasa ta zauna "Ina kwana Mama." "Lafiya lau" Ta amsa Sannan ta ɗan yi murmushi. "Na zo ne ina son na wuce office, nace Khalil ya kai min ke. Shine kuma nace bari na zo kawai da Kai na dan Ina da program da yanma" Sai ta ɗan yi shiru. "Amma na ji kun samu matsala har shekaran jiya ya kwana a  can gida?" Zahra ta sunkuyar da kai, fingers ɗinta take wasa da su, A da can zata iya ɓoye mata, amma yanzu? Bata ga dalilin yin hakan ba kawai gwara ta fada ko data koma gida karta ga bakinta Sai ta ɗago kai, a hankali ta fara bata labarin komai, tun daga Pretty, har zuwa Lovie Dovie, har zuwa yadda Khalil yake fita da daddare baya kwana a gida, har zuwa hotunan da ta gani tare da kawarta Maman ta saurare ta ba tare da ta katse ta ba, sai da Zahra ta gama, ta yi shiru na wasu dakiku, sannan tace, "Ai duk maza haka suke Zahra" Zahra ta ɗago kai ta kalleta Jin me tace Mama ta ci gaba "Kuma ke ma kin yi laifi, gaba daya nan laifin ki ne Fatima" "Ni?" Zahra ta tambaya cikin mamaki, bata ma sanda ta furta Ni din ba "Eh." Mama ta gyada kai. "Wani ya ce miki ki dinga taba wayar mijinki?" Zahra tayi shiru tana kallon wani waje sai kuma ta ce "Amma ai Mama sai daya daina kwana a gida shine na fara taba wayar dan ganin menene" "Baki da wannan right ɗin" Mama ta katse ta Zahra ta kasa magana. Mama ta ɗora "Da baki shiga wayarsa ba ma da baki ga komai ba." Wani irin mamaki ne ya rufe Zahra, ta zaci ko da kaɗan ne za ta ji tausayinta, ko ta yi Allah wadai da abin da ɗanta yake yi, sai dai akasin haka ne. Mama ta ci gaba da kare Khalil "Khalil bai taso cikin kunci ba, ki yi ƙoƙari kina faranta masa rai sbd Namiji idan baya samun nutsuwa a gida ai zai fita waje ne" Zahra ta haɗe hannayenta cikin juna tana kallon ikon Allah Mama ta ɗora "Shi kaɗai gare ni Fatima, ba zan yarda wata mace ta saka shi gaba ba, Idan kina son zaman lafiya ki bi mijinki" Daga haka ta miƙe tsaye "Toh ni zan wuce" Ta faɗa, ba tare da ta jira amsa ba ta fice Zahra ta bita da kallo har ta fita, sai kuma ta furta a hankali "Sai dai idan wata matar ce zata bi sa..." Ta girgiza kai "Amma ba Zahra ba" Ta miƙe tsaye, kai tsaye sama ta haura, ta ƙarasa tattara sauran kayanta, da ta gama ta sauko ƙasa. Farida ta fito da sauri "Anty bari na zuba miki abinci." Zahra ta so cewa a'a, sai kuma ta taji kamar yunwa take ji, ta gyada kai Farida ta zubo mata abinci, ta zauna a parlon tana ci a hankali ta ɗauki wayarta, ta kira Ya Umar Yana shiga bai daɗe ba ya ɗaga "Hello Baby." Ya faɗa da fara'a. Zahra ta ɗan yi murmushi. "Yaya." "Uhm Zahrah." "Barka da aiki." "Yauwa. Ya jikin?" "Da sauƙi." Sai ta ɗan yi shiru. "Yaya ƙarfe nawa zaka koma gida?" "Maybe wajen biyu" Ya amsa. "Me ya faru?" "A'a." Ta girgiza kai duk da baya ganinta. "Nima ina zuwa ne, na fitson idan zan tafi kana gidan ne" Ya Umar ya yi shiru na ɗan lokaci. Sai yace "Toh can't wait to see you" Daga haka suka yi sallama, a kashe wayar. Sai ta buɗe Instagram. Tun da ta yanke hukunci rabuwa, tana son goge duk wani abu da ya haɗata da Khalil a page dinsa Ta shiga profile ɗinsa, da niyyar fara goge hotunansu, selecting tayi ta goge su tass, ta fita zata shiga chats dinta da shi Sai dai kafin ta yi wani abu... Wani post ya faɗo mata a timeline, da farko bata kula ba, sai kuma ta sake kallon hoton Nan take gabanta ya faɗi, ta matso da wayar kusa da fuskarta "What...?" Ta furta a hankali. Sai taga notifications suna ta shigowa, ga uban tags Da sauri tayi switching to acc dinta, Tana shiga mutane suna ta tagging ɗinta Da sauri ta shiga post ɗin, zaro Idanu tayi, ta miƙe tsaye ba tare da ta san tayi hakan ba Cokalin da ke hannunta ya faɗi ƙasa, numfashinta ya fara canzawa, zufa ta fara keto mata Comments suna ta shiga babu ƙaƙƙautawa, Likes suna ƙaruwa a seconds, shares suna ta karuwa Ga uban maganar da mutane suke yi, sosai ta hada zufa, mutane suna ta mamaki, wasu suna ta tambaya, abu ne da ya isa hannun dubban mutane cikin ƙanƙanin lokaci. Zahra ta dafe bakinta, ta kasa ko magana. Domin abin da take gani a screen ɗin wayarta... bata taɓa tsammanin zai fito duniya ba "Wai ya akayi...?"Ta furta a hankali. "Ya akayi wannan ya fito?" Yatsunta na rawa ta shiga comment section. Comments kuwa sai shigowa suke yi "Saudat is evil wallahi." "How can you do this to your friend?" "This is betrayal" "Poor Zahra" "Na shiga page ɗin Zahra yanzu ma. Ashe friends ne tun secondary school" "Kai duniya" "Allah ya isa" Wani ya saka screenshots na hotunan Saudat da Zahra da suke tare a Instagram, mutane suna ta ɗauka suna resharing post, suna nuna yadda suke fita tare,yadda Zahra take kiranta sister, yadda suke comment a posts ɗin juna, abin da ya ƙara dagula mutane kenan Wasu na zagin Saudat, wasu na tausayin Zahra, wasu kuma na zagin Khalil "Wife like Zahra kuma ka je ka bi kawarta?" "Khalil should be ashamed of himself." "This man is shameless." "No wonder she looks unhappy these days." "Men can be wicked." Kowane refresh da Zahra take yi sai ta ga sabon zagi, sabon comment, sabon repost. Zahra ta zauna a hankali kan kujera, wayar na hannunta, amma gaba ɗaya jikinta ya mutu Abu ɗaya kawai yake yawo a ranta, waye ya fitar da wannan? Ta yaya ya samu? Saboda hotunan da ta gani a wayar Khalil... ba kowa ne zai iya samunsu ba, sai wanda ya shiga wayarsa, wanda ya samu access ɗinsa Can ta ji ƙarar buɗe gate, amma ko kallon kofar parlon bata yi ba, hankalinta gaba ɗaya yana kan screen ɗin wayarta Har aka buɗe ƙofar parlorn, bata ɗago kai ba, har aka yi taku zuwa ciki Sai kawai taji wata tsawar murya. "KEE!" A firgice ta ɗago kai Khalil ne, fuskarsa a hade kamar kunu Idanunsa sun yi ja, numfashinsa ma a bayyane yake saboda tsananin fushi Tun daga ƙofar parlorn yake nuna ta da yatsa. "ME KIKE SO KI MAYAR DA RAYUWATA NE?!" Zahra ta zuba masa ido kawai, Khalil ya ƙaraso gabanta "Dan uban ki baki ji Ina miki magana bane?" Ya faɗa cikin tsawa. "Saboda baki samu abin da kike so ba sai kika je kika watsa ni a duniya ko?!" Zahra ta ci gaba da kallonsa, kamar ma ba ita yake yi wa magana ba Abin ne ya ƙara ɓata masa rai "Kin yi hauka ne?!" Ya daka mata tsawa "Dama plan dinki kenan ba? Ke da wannan ƙawar taki marar tarbiyyar!" Nan ya fara zaginta itakam tama shiga shock ne Khalil ya tsaya gabanta yana huci, "Ke kika yi wannan ba!"Ya sake faɗa. Zahra ta girgiza kai "Wallahi bani bane, ban san ya akayi waɗannan hotunan suka fita duniya ba" Khalil ya yi wani irin dariyar takaici. "Bayan na kama ki da wayana a hannunki? Har kina da bakin magana?" "Khalil, gaskiya nake yi...." Kafin ta ƙarasa maganar. Paa! Mari ya sauka a fuskarta. Zahra ta karkata gefe saboda zafin marin, wayar hannunta ta faɗi ƙasa Farida dake kitchen ta firgita, da sauri ta leƙo. Sai taga Khalil ya sake kai mata wani marin. Paa! A razane Farida ta juya da gudu ta koma ɗakinta ta kulle ƙofa, gabanta sai bugawa yake Khalil ya gama fita hayyacinsa. "Zaki sa duniya ta zage ni?!" Ya faɗa yana sake kai mata duka "Zaki sa mutane su raina ni?!" Zahra na ƙoƙarin ja baya, Tana kuka ta ce "Khalil ka tsaya! Khalil wallahi ba ni bane! Lemme explain plss" Amma ina, ko sauraren ta baya yi, ya sake fizgota, ya tura ta da karfi Zahra ta juya da niyyar guduwa, sai kawai ta ji wani irin bugun a ƙafa, Khalil ya kwarfeta Da ƙarfi ta faɗi ƙasa, kafin ta miƙe ma ya isa kanta, ita kuma sai faman ihuu take a zo a taimake ta Mari ya fara sauke mata, baji ba gani Zahra ta fara kare kanta da hannayenta "Khalil! Khalil dan Allah! Ka tausaya min, ka yarda da ni bani bane" Amma gaba ɗaya baya jin ta, dukanta yake yi Wani irin azaba ya ratsa mararta, wani sharp pain mai tsanani, nan take ta saki wata ƙara "Wayyo Allah!" Ihun da ta yi ya cika gidan Baki daya Ta riƙe mararta da hannu biyu, Fuskarta har murɗewa yayi saboda azaba A dai-dai lokacin... aka turo ƙofar parlorn da ƙarfi Bang! Ya Umar ya shigo da gudu, Idanunsa sun yi ja saboda fushi. Ko kallon Zahra bai yi ba, kai tsaye ya nufi Khalil Kafin Khalil ya ankara. Poom! Ya Umar ya kai masa naushi a fuska. Khalil ya ja baya sbd azaba, kafin ya gama recovering sai wani naushin, sai wani Ya Umar ya kama rigarsa, ya sake kai masa fist. "Mahaukaci kawai!" Ya daka masa tsawa. "Fuck you, har ni zaka yi fada da?!" Khalil ya yi ƙoƙarin maida martani Ya Umar ya sake kai masa wani naushi, har ya bige da kujera ya ce "Zahra zaka taba???!" Parlorn ya rikice, sai fasa abubuwa suke sun canza ma komai position Zahra kuma ke kwance a ƙasa tana riƙe da mararta, Yayin da Ya Umar ke ci gaba da kai wa Khalil duka cikin fushi irin wanda bai taɓa yi ba Domin abu ɗaya kawai yake gani a gabansa, kanwarsa, kanwarsa mai ciki, da aka daka Farida ta fito daga ɗakinta da gudu, kukan Zahra da ta ji ne ya kasa barinta ta ci gaba da zama a ciki "Anty Zahra!" Ta kira tana duban wajen. Sai kuma ta tsaya cak, gabanta ya faɗi Zahra na kwance a ƙasa, ko motsi bata yi, abin da ya fi firgita Farida kuwa... Jinin da ta gani "Wayyo Allah!" Ta kwalla ihu. A gigice ta ruga zuwa gareta, ta durƙusa "Anty Zahra!" Ta jijjigata. "Anty!"Amma babu amsa Farida ta kalli Ya Umar, hawaye suka cika idanunta "Yaya!" Ta yi ihu. "Yaya dubi Anty Zahra!" Ya Umar yana shirin sake kai wa Khalil naushi ya juya. Farida ta kamo hannunsa, tana jan sa. "Ka dubeta! Ka dubeta mana!" Ya Umar ya bi inda take nunawa da ido. Ganin Zahra kwance cikin jini kawai ya tsaya cak, kamar an dasa shi a wajen. Duk fushin da yake ciki ya gushe lokaci guda. "Ya Allah..." Ya furta a hankali Ya ƙarasa da sauri Ya durƙusa a gefenta. "Zahra." Ya kira. "Baby." Ya sake kira. Amma babu amsa. Farida ta fashe da kuka. "Mu kaita asibiti!" Ta faɗa cikin kuka. "Dan Allah mu kaita asibiti!" Nan take Ya Umar ya dawo cikin hayyacinsa. Ya saka hannu ya ɗaga Zahra Jikinta babu wani ƙarfi, yayi kofar da ita Farida ta ci gaba da kuka tana binsa a baya A lokacin ne Khalil ya miƙe daga ƙasa. Fuskarsa duk ta kumbura saboda dukan da Ya Umar ya masa. Da alama zai sake kai wa Ya Umar hari Tuni su kuma sun fita Farida na binsa tana kuka, suka fita compound. Mai gadi ma ya fito cikin tashin hankali, yana tambayar meke faruwa Amma babu wanda ya tsaya masa. Kai tsaye suka nufi mota. Ya Umar ya buɗe ƙofar baya. A hankali ya kwantar da Zahra. Farida ta shiga kusa da ita.Tana riƙe hannunta tana kuka. "Anty Zahra ki tashi." "Dan Allah ki tashi." "Ki yi magana." Ya Umar ya shiga seat ɗin direba, hannunsa har rawa yake, ya tada motar. Da ƙarfi ya fice daga compound ɗin. A hanya kuwa... Babu wanda yake magana, sai sautin kukan Farida. Da kuma bugun zuciyar Ya Umar wanda yake jin kamar zai faso ƙirjinsa. Karo na farko a rayuwarsa... Ya ji tsoro irin wannan Tsoron rasa mutum Ya ci gaba da sharar gudu, kai tsaye zuwa asibiti Da ƙyar Ya Umar ya iya parking motar saboda yadda hannayensa ke rawa Tun kafin motar ya gama parking,ya buɗe ƙofar baya da sauri, Zahra na kwance babu wani motsi da take yi Farida kuwa kuka kawai take yi. "Dan Allah ku taimaka mana!" Ta fara faɗa tun kafin su shiga cikin asibitin Da gudu Ya Umar ya ɗauki Zahra ya nufi emergency unit, Nurses da ke wajen suna ganinsu suka ƙaraso da trolley "Meyafaru?" Ɗaya daga cikinsu ta tambaya "Babu lokacin bayani, Kawai ku taimaka mata!" Ya Umar ya faɗa cikin tashin hankali Da sauri suka kwantar da ita a trolley suka shiga da ita ciki. Ya Umar da Farida suka bi bayansu, sai dai a bakin ƙofar emergency room aka tare su "Please ku jira a waje." Nurse ɗin ta faɗa. "Amma...." "Please." Nurse din ta katse Ya Umar, daga haka ta shige ciki hadi da rufe kofar Ya Umar ya tsaya yana kallon ƙofar, kamar idan ya ci gaba da kallonta zai ga abin da suke yi a ciki Farida kuwa ta zauna kan kujera tana kuka har sannan, wasa wasa kusan awa kenan, Ya Umar kuma lokaci zuwa lokaci sai ya tashi ya zaga ya kuma dawo ya zauna, hankalinsa ya kasa kwanciya, A ƙarshe wani doctor ya fito. Da sauri Ya Umar ya ƙarasa wajensa. "Doctor?" Likitan ya kalle shi. "Are you a family member?" "Eh." Ya amsa ba tare da wata-wata ba. Likitan ya gyada kai. "Mun fara bata first aid da emergency treatment." Ya Umar ya haɗiye miyau. "Yaya take toh Dr?" Likitan ya ɗan yi shiru. "Sai mun gama wasu checks tukuna, amma tana ƙarƙashin kulawa." "Please ku kwantar da hankalinku." Ya Umar ya gyada kai. Amma hankalinsa ya katsa kwanciya Likitan ya koma ciki. Ya Umar ya tsaya yana kallon ƙofar, sai a dafe kansa Sai yanzu ma ya tuna da Abbah, dole ya sanar da shi A hankali ya zaro wayarsa, ya shiga contacts Yatsansa ya tsaya kan sunan Abbah, sai ya danna call Abbah na daga wa yace "Umar." Muryar Abbah ta fito. "Lafiya dai?" Ya Umar ya lumshe idanunsa Karo na farko muryarsa ta kasa fitowa yadda ya kamata. "Abbah..." Ya kira a hankali. Nan take Abbah ya gane akwai matsala "Me ya faru?" Ya tambaya cikin damuwa. Ya Umar ya haɗiye miyau. "Abbah... Zahra tana asibiti." Shiru Abbah yayi na wasu dakiku, sai kuma a dan rude yace "Asibiti? Me ya same ta?" Ya Umar ya dafe goshinsa Idanunsa suka cika da ƙwalla. "An samu matsala ne..." Ya faɗa cikin sanyin murya. "Yanzu tana emergency." Abbah ya miƙe tsaye daga inda yake zaune "Umar." Ya kira "Ka gaya min me ya faru da Zahra." Ya Umar ya runtse idanunsa "Bleeding take yi, shine aka kawota asibiti" Few pages left, book 1 ya kusa karewa *FARASHIN IZZAH* Book 1 Chapter 28 Chapter 28 Abbah da Mummy suna isa asibitin suka tarar da Ya Umar zaune a wajen emergency unit, kansa sunkuye cikin hannayensa. Farida kuma tana gefe idanunta sun kumbura saboda kuka. Da sauri Mami ta ƙarasa. “Ina take?” Ta tambaya cikin rawar murya Ya Umar ya miƙe tsaye “Tana ciki Mummy.” Abbah ya kalli ƙofar emergency room “Me likita ya ce?” Ya Umar ya girgiza kai “Har yanzu suna tare da ita.” Mummy ta dafe ƙirji, Tana hoping ba abun da zuciyarta take raya mata bane Ta zauna a kujera, tasbihi kawai take yi a hankali Abbah kuwa ya ci gaba da tsaye. Lokaci zuwa lokaci yana kallon ƙofar, lokaci zuwa lokaci kuma yana kallon Ya Umar Yana son tambayar abin da ya faru, amma yanayin da suke ciki bai bashi damar hakan ba Duk hankalinsu yana kan Zahra, saboda haka babu wanda yasan abun da ke yawo a internet. Can bayan wani lokaci suna zaune, suka ji ance “Ya Allah…” Dukkaninsu suka ɗago kai Firdausi ce tare da Asiya, dukkansu numfashinsu a ɗauke, da alama sauri suka yi tun daga parking space Firdausi ta ƙarasa da sauri “Ya Umar?” Ta kira cikin damuwa “Yaya take?” Ya Umar ya girgiza kai. “Har yanzu ba su fito ba.” Asiya ta dafe kai. “In shaa Allah zata samu sauki” Ta furta “Ina ta kiranta bata dagawa shine hankalina ya tashi” Firdausi ta ce “Da ba ta ɗagawa ba ne muka kira Farida.” Farida da ke zaune gefe ta goge idanunta, sabon kuka ya sake taho mata Asiya ta zauna kusa da Mami, ta kamo hannunta “Allah zai bata Lafiya In shaa Allah Mami” Ta faɗa cikin sanyin murya Mummy ta gyada kai kawai, hawaye na cika idanunta Wani irin yanayi ne ya mamaye wajen Kowa ya rasa abin cewa sai addu’a da fatan alheri. Can sai ka wasu likitoco sun fito daga emergency room din, hakan yasa Duk suka mike Dukkansu suka zuba wa likitan ido Likitan ya cire face mask ɗinsa, sannan ya ce, “Patient ɗin tana da internal injuries ne” Gabansu ya faɗi lokaci guda. “Mun samu bleeding a ciki” Ya ci gaba “Alhamdulillah mun shawo kan bleeding ɗin yanzu, amma har yanzu tana ƙarƙashin kulawa.” Mummy ta dafe ƙirji. “Ya Allah” Ta furta Abbah ya matsa gaba “Doctor, za mu iya ganinta?” Likitan ya girgiza kai “Not yet, tana bukatar complete rest, da zarar mun tabbatar komai ya daidaita, za mu sanar da ku” Dole suka amince. Likitan ya koma ciki, suka ci gaba da tsayuwa a wajen A karo na farko tsoro ya bayyana sosai a fuskar Abbah ya ce “Umar wai meya same ta ne? Bangane bleeding a ciki ba? As in how internal injuries” sai kuma ya juya ya bi bayan dayan likitan daya tafi Mami kam bata san sanda ta fara hawaye ba Ya Umar ya juya ya kalli ƙofar emergency room, a ransa kuwa… Abu ɗaya kawai yake maimaitawa… Khalil zai yi bayanin abin da ya aikata Bayan kwana biyu a asibiti… Alhamdulillah, jikin Zahra ya fara ɗan samun sauƙi, ba kamar ranar farko ba da ko idanuwanta da ƙyar suke buɗewa Yanzu tana iya magana kaɗan-kaɗan, tana iya shan ruwa, tana iya gane mutanen da ke kusa da ita Sai dai har yanzu rauni ya yi mata yawa, Internal injuries ɗin da ta samu sun sa likitoci suka ci gaba da sanya ta a ƙarƙashin kulawa sosai Abin da ya fi ɗaga hankalin kowa kuwa shi ne… cikin da take ɗauke da shi bai tsira ba, last last sai daya zube, hakan yasa dole sai da aka yi mata wankin ciki Tun da likita ya gaya musu hakan, Mami ta yi kuka sosai, Munmy ma ta nuna damuwarta ainun , Abbah ma ya yi shiru na tsawon lokaci Amma Ya Umar bai nuna wata damuwa kan zubewar cikin ba, hasali ma a ransa yana jin wani irin sauƙi Daya kalli Zahra dake kwance kan gadon asibiti, sai ya ce a ransa, “Ko cikin bai zube ba shima mai iyasa likita ya zubar ne” Domin duk lokacin da ya tuna cewa ko bayan rabuwarsu wannan cikin ne zai ci gaba da hada Zahra da Khalil… sai ya ji haushinsa yana ƙaruwa. Washe gari da yamma bayan likita ya tabbatar musu cewa Zahra ta fara samun sauƙi sosai. Ya Umar ya fito daga ɗakin da take kwance. A corridor ya tarar da Farida zaune. Tun ranar farko yarinyar take kai-komo tsakanin gida da asibiti Da ganinsa ta miƙe tsaye “Yaya.” Ta gaishe shi. Ya amsa sannan ya tsaya yana kallonta na wasu daƙiƙu. Sai ya ce “Farida.” Ta ɗago kai “Na gode.” Mamaki ta yi, ta ce “Da mene Yaya?” Ya Umar ya yi murmushi karon farko cikin kwanakin nan “Dan kirana da kika yi akan lokaci” Farida ta yi shiru Ya ci gaba “Da ba don ke ba…” Sai ya girgiza kai “Ban san me zai faru ba.” Nan take idanun Farida suka cika da ƙwalla “Ai na tsorata ne sosai Yaya.” Ta faɗa a hankali. Ya Umar ya gyada kai. “Na sani. Sai kuma information da kike bani na komai a gidan, Nagode sosai” Farida ta sunkuyar da kai. Tun ranar da zai kawosu gidan ya saya wa Farida waya da sim, yace Duk abun da yake faruwa a gidan tana Kira tana sanar da shi, ko kuma ya Kira, kasan komai ya Umar ya sani dake faruwa a gidan, ko ta Kira ta ce ga Zahra ba ta cikin yanayi mai kyau. Ko idan ta ƙi cin abinci, ko idan ta yi kuka, ko idan ta kwana babu walwala, ko idan Ibrahim bai kwana a gidan ba Ya Umar ya san komai saboda Farida Shine ranan da irdausi ta zo gidan da sassafe, Farida ta kira shi ta gaya masa Zahra ba ta cikin yanayi mai kyau sam, ta ce har Firdausi ta zo tun safen saboda damuwa. Tun daga lokacin ne kuma gabansa ya faɗi, ya gama abin da yake yi cikin gaggawa ya kamo hanyar ko sanda zahra ta kirasa ma yana areansu, shiyasa ma ya isa gidan da sauri. Ya Umar ya lumshe idanuwansa. Kawai tunanin mintuna kaɗan da ya yi, yaji kamar yaje ya kashe Ibrahim Ya buɗe idanunsa ya kalli Farida. “Nagode sosai Farida, akwai tukuicin ki, Bari mu koma gida” Farida ta yi saurin girgiza kai. “A’a Yaya, Anty Zahra ai kamar yayata ce” Maganar ta ta sa Ya Umar ya yi murmushi Bayan kusan mako guda da suka yi a asibiti, likitoci suka tabbatar cewa Zahra ta samu sauƙi sosai duk da akwai abu da ba’a rasa ba, a ranan kuma aka sallama su Abin da ya fi ɗaga hankalin su Mami shi ne babu ko mutum ɗaya daga gidan Khalil da ya zo balle su Kira suji ya take, ba wani yunƙurin sanin halin da take ciki. Ba su dan abun dake going ba shiyasa dukkansu suka kwallace su arai Bayan sun dawo gida kuwa… Kowa ya dage wajen kula da Zahra. Mami ba ta bari wani ya yi mata komai, abinci, magani, komai da kanta take wa ‘yarta, Wanda Mummy taji haushi gani take ita ya kamata ta kula da Zhara ba Mami ba Ya Umar ma duk lokacin da ya dawo daga aiki sai ya fara tambayar Zahra kafin komai. Yau ma hakan ne Da yamma suna zaune a babban parlorn. Zahra na kan kujera, a gabanta akwai bowl ɗin kaza da Mami ta matsa mata sai ta ci, Ya Umar yana opposite dinta yana bata labarin wani korean movie sanin Zahra na son su Abbah na gefe yana karanta wasu takardu. Mami kuma tana zaune kusa da Zahra. A lokacin suka ji ƙarar mota ta shigo harabar gidan tayi parking, ba da daɗewa ba mai gadi ya shigo da sallama ya gaisu, yana kallon Ya Umar ya ce “Yaya Umar, wasu ne suka zo suna nemanka.” Ya Umar ya ɗago kai. “Su waye suka ce maka?” “Suka cewa lawyers ne.” Ya amsa Ya Umar ya gyada kai “Toh, gani fitowa” Ya miƙe ya fita Abbah ya bi shi da kallo Sai dai bai ce komai ba, haka ma Mami, Zahra kam gabanta ne ya fadi ya fara sake sake a ranta Kusan rabin awa ya ɗauka a waje, can sai gashi ya dawo parlorn. Abbah ya ajiye takardunsa yana kallonsa ya ce “Su waye?” Ya tambaya. Ya Umar ya zauna a hankali. “Barristers ne.” Abbah ya gyada kai “Suna son me toh?” Ya Umar ya yi shiru na wasu dakiku, sai ya saci kallon Zahra suka hada ido yayi saurin dauke kansa Sannan ya ce, “Ai ni na kira su.” Nan take Mummy ta ɗago kai tana kallonsa Abbah ma ya haɗe gira ya ce “Ka kira su? Can’t you explain?” Ya Umar ya gyada kai “Eh” Sai ya ɗaga kansa ya kalli Abbah, sannan ya kalli Mami Daga nan idanunsa suka sauka kan Zahra, wacce take zaune shiru jikinta duk yayi sanyi, bowl ɗin da ke gabanta ma ta daina cin abin cikin A hankali Ya Umar ya ce, “Ina son su karbawa Zahra dakartan saki ne” Parlorn ya yi tsit, kowa ya tsaya da abin da yake yi, Zahra ta sauke kanta kasa Tana wasa da fingers dinta Abbah ya kalli Ya Umar. “Kana nufin me?” Ya Umar ya ja numfashi. A hankali ya fara ba su labarin abin da ya faru, tun daga ranar da ya same su a parlorn, yadda Khalil ya ke kai wa Zahra duka ta ko ina, yadda yake fita ya barta ya kwana a waje, da kuma yadda likitoci suka tabbatar da abin da ya jawo internal injuries tare da zubewar ciki, bai ɓoye komai ba Nan take Abbah ya miƙe tsaye, sai da kujerar da yake kai ta ja da baya “What?!” Ya faɗa da ƙarfi “My baby?!” Fuskarsa ta sauya gaba ɗaya Idanunsa suka yi ja lokaci guda Ya Umar ya gyada kai a hankali “Kabar wannan a hannuna, sai naga uban da zai tsaya masa a kaff kasar nan” Ya fada cikin ɓacin rai Sai kuma ya sauke numfashi ya kalli Zahra, wacce kanta ke sunkuye “Nagode Umar” Abbah ya faɗa cikin rawar murya “Allah Ya albarkace ka, dan ka tabbatar min ko bana raye kai me tsaya wa ne akan gidan nan” Ya Umar ya ce “Ameen Abbah” Mami ta kasa cewa komai, tun lokacin da Ya Umar ya fara magana hawaye suka fara bin kuncinta Ta rufe bakinta, saboda kukan da ke neman ƙwace mata, ta kalli Zahra, her only Baby. Ƴar da ta ɗauka ta shiga gidan aure domin samun farin ciki, ashe tana rayuwa cikin irin wannan azaba. Mami ta kasa jurewa, ta miƙe daga inda take, ta ƙarasa kusa da Zahra, ta zauna gefenta, sannan ta rungume ta Mami na shafa kanta, hawaye na zuba daga idanunta Abbah na kai-komo a tsakaninsu, da tunanin irin matakin da zai dauka Daga ƙarshe Mami ta sauke ajiyar zuciya, har sannan tana rungume da zahra. Muryarta na rawa tace, “Abin da nake gudu kenan, My Dear.” Ta kalli Abbah, idanunta cike da hawaye “Amma kai da Umar…” Ta girgiza kai a hankali. “Duk abin da Zahra take so shi ne abin da ku ma kuke so.” Abbah ya yi shiru. Ya Umar ma bai ce komai ba. Mami ta ci gaba. “Na yi iya ƙoƙarina wajen nuna muku tsoron da nake ji akan wannan yaron, amma Ina…” “Amma saboda kuna son farin cikin Zahra, kuka bi abin da take so.” Ta sake goge hawayen da suka zubo mata. “Yau ga maganata ta fito fili.” Da jin waɗannan kalamai… Zahra ta fashe da kuka Ta miƙe daga jikin Mami, ta durƙusa “Mami…” Ta kira cikin kuka. Mami ta kalleta. Zahra ta kama hannunta. “Ki yafe min Mami” Kuka ya sake ƙwace mata. “Mami ki yafe min, naki sauraren ki, naki karɓi shawararki ba, Mami na sani baki son wannan auren…. Amma na nace. Na zaɓi abin da nake so Hawayenta na bin kuncinta Ta sunkuyar da kanta. “Mami na yi kuskure Ki yi haƙuri. Dan Allah ki yafe min.” Parlorn ya sake yin shiru, Kowa na kallon Zahra cike da tausayi Mami kuwa ta kalleta na wasu daƙiƙu Sai kuma ta miƙa hannu ta kamo haɓarta, ta ɗago fuskarta sama. “A’a.” Ta faɗa cikin sanyin murya. “A’a Zahra. Ba haka bane” Ta share mata hawayen da ke kan kumatunta. “Sau nawa zan gaya miki? Ni uwa ce.” Ta ɗan yi murmushi duk da hawayen idanunta. “Uwa kuma ba ta riƙe ɗanta a rai.” Zahra ta sake fashewa da kuka. Mami ta kamo hannunta. “Ban taɓa riƙe ki a raina ba. Ko da na yi magana a lokacin Ko da ban yarda da zaɓinki ba. Ban taɓa daina son ki ba.” Ban taɓa daina yi miki addu’a ba.” Ta ɗora hannunta kan Zahra. “Wallahi kullum cikin addu’ata kike Kullum ina roƙon Allah Ya ba ki alheri. Ya ba ki farin ciki. Ya kare ki daga duk wani sharri.” Muryarta na rawa “Ko a lokacin da kika zaɓi abin da ba na so, ba yanda zanyi, sbd ke ɗiyata ce.” Nan take Zahra ta mike ta rungume Mami Tana cigaba da kuka sosai Mami ma ta rungume ta back, tana shafa bayanta a hankali Abbah ya juya gefe yana goge idanunsa, shi kansa hawaye sun cika masa ido Ya Umar kuwa ya sauke ajiyar zuciya A karo na farko cikin kwanakin nan… Ya ji kamar wani babban nauyi ya fara sauka daga zuciyar Zahra Ko ba komai ta dawo cikin gidan da ake sonta. Cikin mutanen da ba za su taɓa juya mata baya ba Abbah ya kalli Zahra na wasu daƙiƙu, zuciyarsa cike da tausayin ƴarsa. A hankali ya miƙe daga inda yake zaune ya karasa wajen su “Zo nan” Ya faɗa cikin sanyin murya Ya ɗagota daga jikin Mami sannan ya rungume ta gam a ƙirjinsa. Nan take Zahra ta sake fashewa da kuka Abbah ya rufe idanunsa na ɗan lokaci yana bubbuga bayanta a hankali. “Zahra…” Ya kira sunanta cike da taushi “You’ll be blessed.” Ya ɗan ja baya kaɗan yana kallon fuskarta “Kar ki sa komai a ranki.” “Muna son ki.” “Kuma za mu bi miki haƙƙinki.” Ya ɗaga hannunsa ya share mata hawayen da suka cika kumatunta. “Sannan zan ci gaba da ɗaukar responsibilities ɗinki.” Wani murmushi ya yi mata. “As a pleasure to me.” Sabbin hawaye suka sake cika idanun Zahra, ta kasa cewa komai sai kallon mahaifinta take yi Abbah ya sake rungumeta na ɗan lokaci kafin ya sake ta. buɗe ƙofar parlorn akayi, Mummy ce ta shigo tare da Batoul Sai dai Abbah ko kallonsu bai yi ba, ya san idan sun samu labari yanzu, cikin mintuna kaɗan familyn gaba ɗaya zasu sani Ya juya wajen Ya Umar. “Umar.”Ya kira “Na’am Abbah.” Ya amsa yana ɗago kai. Abbah ya miƙe tsaye “Tashi mu tafi.” Ya Umar ya ce “Yanzu?” “Eh.” Abbah ya amsa kai tsaye. “Make sure ka kira barristers ɗinnan.” Muryarsa ta canza zuwa ta mutum mai yanke hukunci. “Ina son na gansu yanzu.” Ya Umar ya kalli Zahra na ɗan lokaci sannan ya gyada kai. “Okay Abbah.” Ya miƙe tsaye yana ɗaukar wayarsa. Yayin da Mami ke kallonsu Ta san daga yanayin Abbah ba maganar sasanci zai yi ba, ba maganar haƙuri zai yi ba kuma Ya Umar ya fara bin Abbah zuwa waje #Jiddatulkhayr writes #08110615256 *FARASHIN IZZAH* Book 1 Chapter 29 Fitar Abbah da Ya Umar ke da wuya daga parlorn, Mami ta miƙe tsaye. Tun kafin Mummy ta yi wata magana, ta gyara mayafinta. "Zan haura sama." Ta faɗa a taƙaice Mummy ta haɗe gira "Ni kam meke faruwa ne?" Ta tambaya cikin son jin abin da ke gudana Mami ko kallonta bata yi ba. "Babu komai" Kawai ta faɗa, daga haka ta juya ta nufi staircase. Zahra ma ta miƙe a hankali "Bari na sha maganina." Ta faɗa, sannan ta bi bayan Mami Batoul ta kalli Mummy, Mummy ma ta kalleta sai dukansu suka yi dariya "Wallahi akwai wani abu Mummy" Batoul ta faɗa Mummy ta gyada kai "Ni ma haka na gani, amma idan tayi tsami zamu ji" Da suka shiga ɗakin Mami. Mami ta zauna a gefen gado sannan ta kalli Zahra "Zo nan." Zahra ta ƙarasa kusa da ita. Mami ta kama hannunta "Ki kwanta Zahra." Ta faɗa cikin taushi. "Amma dan Allah ki cire duk wani damuwa daga ranki." Zahra ta yi shiru tana kallonta. Mami ta ci gaba. "Kar ki sa wa kanki hawan jini. Abin da ya faru ya riga ya faru, haka taki kaddarar ta zo sai ki karɓa ki ci gaba da rayuwa kamar yadda kika saba" Murmushi Zahra ta yi Ba ta da ƙarfin magana sosai a halin yanzu ɗaya daga cikin masu aikinsu ta shigo da bowl ɗin fruits, ta ajiye a kan side table Mami ta kalleta "Dan Allah ku haɗu ku gyara ɗakin Zahra, tunda yanzu ta dawo gida" "Toh Hajiya." Ta amsa, daga haka ta fita Wani dattijo mai shekaru ne ya zo gidansu Ibrahim, baƙin cikinsa a bayyane yake Mai gadi ya shigar da shi ciki bayan ya bayyana dalilinsa na zuwa Yana tsaye ne a bakin parlorn, bai jima ba Ibrahim ya fito Suka gaisa. Sai dattijon ya gyara tsayuwarsa "Kai ne Ibrahim?" "Eh." Ibrahim ya amsa Dattijon ya gyada kai. "Nine uban Saudat ne." Nan take Ibrahim ya ɗago kai. Dattijon ya ci gaba. "Na zo ne dan na shaida maka." Ibrahim ya yi shiru. "Ina neman magabatan ka dan zan aura maka Saudat" Fuskar Ibrahim ta canza ya koma na mamaki Dattijon ya ɗora "Ka gama cutarta, yanzu babu wanda zai yi sha'awar aurenta don haka yadda kuka fara haka zaku karasa, manyan ka nake son gani dan aura maka ita" Ibrahim ya sauke kansa ƙasa, kafin ya samu damar magana Sai suka ji takun sawu, Mama ce ta fito, tun daga ƙofar parlorn ta ji ƙarshen maganar. "Ai Malam." Ta faɗa tana ƙaraso wa "Yana da mata, sannan bai daɗe da yin aure ba, taya zai auri wata yanzu?" Dattijon ya juya ya kalleta. "Ko mata uku yake da su." Ya faɗa cikin fushi "Ko jiya ya aure su, sai ya aureta." Mama ta haɗe hannu tana masa wani kallo ta ce "A bisa wani dalili?" Dattijon ya kalleta "A dalilin abin da ya bata min ɗiyata." Mama ta yi wata dariya mai cike da raini "Toh dama yarinya naka tana da tarbiya ne?" Nan take fuskar dattijon ta canza "Ke ki iya bakin ki" Ya faɗa da ƙarfi yana nuna ta da yatsa Mama ta matso gaba "An ƙi har talaka da kai zaka zo kana mana ihu a gida?" Dattijon ya kalleta sosai, sai ya gyada kai "Haka kika ce ko?" Mama ta ɗaga kafaɗa. Dattijon yayi wani murmushi yace "Ki jira" Ya faɗa cikin sanyin murya "Za ki gani." Daga haka ya juya ya fice. Ibrahim ya daɗe tsaye a wajen kansa a sunkuye, ba shi da ƙarfin wata magana. Daga ƙarshe kai tsaye BQ ya nufa. Ba ya son jin wata magana daga kowa a wannan lokacin... Abbah da Ya Umar suna fitowa daga wani chamber Barristers uku ne suka rakosu har bakin mota. Suna godiya saboda ba kadan ba abbah ya jikasu da kudi "Mun gode sosai sir" Ɗaya daga cikinsu ya faɗa "Ai irin wannan case din muke so Sir, ya bashi da bakin magana daga shi har Wanda zasu tsaya masa" Abbah ya yi murmushi "Ku tabbatar kun yi aikinku yadda ya kamata." "In sha Allah sir." Suka amsa gaba ɗaya. Abbah ya gyara agogon hannunsa. Sannan ya ce, "Make sure ku kai masa yau." Dukkansu suka gyada kai. "Ai dole ne sir, yau ɗin nan za a kai." Abbah ya gyada kai cikin gamsuwa, daga haka suka yi sallama Ya Umar ya shiga seat ɗin direba. Abbah ya shiga dayan site din, daga haka suka bar wajen Firdausi ce ke sallama a bakin parlorn. Da alama yanzu ta iso. Farida ta leƙo daga kitchen "Laaa Anty Firdausi!" Ta faɗa cikin fara'a. "Shigo mana." Firdausi ta yi dariya, sannan ta shiga Bayan sun gaisa, Firdausi ta tambaya "Ina Zahra?" Farida ta nuna sama "Tana bangaren Mami." Firdausi ta gyada kai. "Toh." Daga haka ta juya ta nufi staircase Kai tsaye zuwa bangaren Mami. Domin tun da ta ji an sallamo Zahra daga asibiti, zuciyarta ta kasa haƙuri har sai ta gan ta da idanunta A parlorn Mami suka fara haɗuwa. Mami na zaune tana duba wasu takardu lokacin da Firdausi ta shigo Da sauri ta durƙusa ta gaishe ta Mami ta amsa cikin fara'a. "Firdausi, sannu da zuwa." "Yauwa Mami." Ta amsa. Mami ta nuna mata ƙofar ɗakin "Ki shiga ciki, tana can." Firdausi ta gyada kai. "Toh Mami." Daga haka ta miƙe ta nufi ɗakin. A hankali ta tura ƙofar. Zahra na kwance kan gado tana duba wayarta. Da ta ji an shigo ta ɗago kai, Idanunsu suna haɗuwa Zahra ta dan bata rai Nan take Firdausi ta lura akwai wani yanayi a fuskar Zahra, ba irin fara'ar da ta saba yi mata ba Duk da haka ta ƙarasa cikin murmushi, ta rungume ta a hankali. "Sorry my friend" Ta faɗa. "Ya jikin naki?" Zahra ta rungumeta back amma babu walwala. "Da sauƙi" Ta faɗa a taƙaice. Sai kuma ta ɗan ja baya ta zauna, Idanunta na kan Firdausi "Firdausi... "Ta kira. "Na'am?" Firdausi ta amsa Zahra ta yi shiru na ɗan lokaci kafin tace "Meya sa za ki yi posting hotunan Ibrahim da Saudat?" Firdausi ta haɗe gira "Ban gane ba." Ta faɗa "Wane hoto kike nufi?" Zahra ta ce, "Wanda yake trending mana" Firdausi ta zuba mata ido. Zahra ta ci gaba. "No matter what, Saudat is still our friend. Why would you want to ruin her life that way?" Firdausi ta zaro ido, sai kuma ta miƙe tsaye, ranta ya fara ɓaci "Enough, Zahra." Ta faɗa. "Nima ban san abin da kike magana a kai ba." Ta nuna kanta. "Akan me yasa za ki dinga zargina haka?" Sai ta girgiza kai cikin takaici. "Can't you see what she did to you? Kin manta wa Saudat take?" Ta matsa kusa da gadon. "Kin manta a department tana ta nuna miki yanzu tafi karfin ki, you're nothing?" "Kin manta lokacin da take cewa, 'gida yayi kyau saura kwanciyar hankali' wasu Asiya da suka zo?" Ta ɗaga hannayenta "How did she know baki cikin kwanciyar hankali?" Zahra ta yi shiru. Firdausi ta ci gaba. "Saudat is a devil. Kuma har yanzu kina iya kareta?" Ta yi wata dariya mai ciwo. "It's okay! Choose Saudat over me, Zahra, ba yau kika fara ba" Zahra kallonta kawai take yi Firdausi kuwa zuciyarta ta cika da bacin rai "A kan Saudat kin taɓa marin ni, Kin tuna? Amma duk da haka ina tare da ke saboda Allah kuma saboda son da nake miki." Sai ta nuna Zahra da yatsa. "Remember, ke kika ɗauki responsibilities ɗinta.m, ke kika taimaka mata, ke kika tsaya mata har ta zama mutum but what?! Yanzu kuma ta zama kishiyarki na waje" Ta girgiza kai. "Abin da ta shuka ne take girba zahra, she's reaping what she sowed" Jikin Zahra ya yi sanyi, ta sunkuyar da kai, sai bayan wani lokaci ta ce a hankali, "No matter what, Firdausi... ita ma mace ce ki tuna.. Na ji babu daɗi ne kawai. Saboda idan ni ce, ba zan so a fito da abin da nake yi a media ba." Sai ta ɗago kai "But please, Firdausi... Ba ke ce kika fitar da su ba?" Firdausi ta zaro ido. "How?" Ta faɗa. "Bayan wayarki tana wajenki?" Sai ta girgiza kai. "Kuma ai da saninsu suka ɗauki hotunan, ba kunya, ba tsoron Allah kuma har murmushi take abun ta, Toh idan sun fito duniya, ni ban ga laifin wanda ya fitar da su ba" Zahra ta yi shiru maganar gaskiya har yanzu bata gama yarda da Firdausi ba. Amma kuma babu wata hujja da take da ita. Suna cikin haka ne Farida ta shigo riƙe da tray mai ruwa da snacks, ta ajiye a gabansu. "Ga ruwa." Ta faɗa cikin murmushi. Daga haka ta fita. Firdausi ta zauna ta ɗauki lemu, sai kuma ta canza zance. "Wallahi lectures sun yi wuta yanzu." Zahra ta ɗago kai. Firdausi ta ci gaba da bata labarin yadda wani lecturer ya shiga ya ba su assignment kamar ba gobe, yadda ɗalibai suka fara gunaguni, tadda Asiya ta yi wata magana da ta sa gaba ɗayan class suka yi dariya. A hankali a hankali zahra ta janyo Zhara da labari Wanda har ta sake. A haka suka ci gaba da hira har Firdausi ta miƙe zata tafi. "Toh bari na wuce kafin Mama ta fara nema na" Ta faɗa tana ɗaukar jakarta. Zahra ta gyada kai. "Okay." Sai kuma ta miƙe tana rakata. Har bakin gate ta rakata. Firdausi ta juya tana kallonta. "Please ki daina tunani da yawa." Zahra ta yi murmushi "In sha Allah." Firdausi ta gyada kai sannan ta fice. Zahra kuwa ta juya ta koma cikin gida. Firdausi na fita daga gate ɗin kuwa ta hango motar Ya Umar tana shigowa layin, murmushi ya suɓuce mata, ta tsaya tana jiransa. Da motar ta ƙaraso ya sauke glass dan ganinta da yayi, ta gaishe shi. Ya amsa cikin fara'a. Sai ya kalleta "Ina zaki?" "Gida." Ta amsa. Ya nuna mata seat ɗin gaba. "Shigo na kai ki." Ba musu ta buɗe motar ta shiga Da farko dukansu suka yi shiru Sai karar AC kaɗai ke tashi a cikin motar Can bayan sun ɗan yi nisa Ya Umar ya kalleta. "Kin ga abin da ke faruwa a media kuwa?" Murmushi ya bayyana a fuskar Firdausi. "Ai hakan ya fi, maganinsu kenan." Ya Umar ya ɗan kalleta. "I wonder ya akayi secret ɗinsu ya fito fili." Ya ɗan yi murmushi "Da yake Zahra ba ta da hakkin su" Firdausi ta ɗan gyara zamanta. Sannan tace, "Ni na tura wa bloggers su yi posting." Ya Umar ya juya ya kalleta da sauri. Ita kuma ta ɗaga kafaɗa. "Saboda yadda zuciyata take kuna a lokacin ne" Ta ci gaba. "Abin da Saudat ta yi wa Zahra ya yi muni, idan aka barta haka ta ci banza kenan, shi yasa na yi Wallahi zuciyata ma ta yi sanyi." Ta ɗan yi shiru kafin ta ƙara da cewa, "At least ba Zahra kaɗai bace zata shiga silent depression." Ya Umar ya kasa hana murmushi bayyana a fuskarsa. "Good job, Firdausi." Nan take ta juya tana kallonsa. "Please kar ka gaya wa Zahra komai." Ya ɗaga gira. "Why?" Firdausi ta yi ajiyar zuciya. "Saboda dazu ma har fada ta fara dani wai ni na fitar da pictures ɗin." Ta girgiza kai. "Na nuna mata I know nothing, kasan Zahra da pure and innocent mind gareta, shiyasa na gwada mata ba ni ba ce, dan idan ta san ni ce, zamu iya samun matsala." Ya Umar ya gyada kai cikin fahimta. "Okay." Firdausi ta sake kallon window. Sannan ta ce a hankali, "Ranar da Zahra ta ga hotunan nan..." Ta haɗiye wani abu da ya tsaya mata a maƙoshi. "Allah na ji tsoro sosai, yadda take kuka, yadda ta koma, yadda gaba ɗaya ta canza." Ta girgiza kai "Shi yasa na yi abin da na yi. Nima cikin baƙin rai ne" Ya Umar ya ɗan yi shiru. Sai daga baya yace, "It's okay. Hakan zai zama lesson a garesu, da kuma masu irin halinsu." Firdausi ta gyada kai. Daga nan babu wanda ya sake magana. Kowannensu na tunanin abubuwan da suka faru cikin kwanakin nan. Har suka isa ƙofar gidansu. Ya Umar ya tsaya. Firdausi ta buɗe ƙofa Ta juya tana murmushi "Thank you for the ride." "Anytime." Ya Umar ya amsa. Ta sauka. Sai da ya tabbatar ta shiga gida lafiya kafin ya ja motar ya tafi. Yammacin ranar... Ibrahim yana zaune a parlorn, wayarsa a hannunsa amma ko abin da yake dubawa baya gani sosai Tun bayan abubuwan da suka faru, rayuwarsa ta rikice fiye da yadda yake son ya yarda. Mama ce ke zaune a gefe tana kallon wani programme a TV. Sai aka ji ƙarar horn daga waje, ba wanda ya kula da farko. Bayan wasu mintuna kaɗan kuwa mai gadi ya shigo parlorn. "Yallabai, wasu mutane ne a waje suna neman ka." Ibrahim ya ɗago kai "Su waye?" "Ban sansu ba amma sunsa kaya kamar masu aikin banki" Nan take Mama ta juya. "Polisawa ne?" "Aa hajiya su ai na San su" Ibrahim ya miƙe tsaye. "Toh bari na gani." Ya fita zuwa harabar gidan Mutane biyu ne tsaye a wajen. Da ya ƙarasa suka gaisa. Daya daga cikinsu ya miƙa masa wasu envelope "Mr. Ibrahim..." Ya kira sunansa cikin hukuma. "An aiko mu, mu kawo maka wannan." Ibrahim ya karɓa. Da ya ga tambarin kotu a saman takardar, zuciyarsa ta yi wani irin bugawa. Ya buɗe. Ya fara karantawa. Kuma yayin da idanunsa ke bin layukan rubutun... Fuskarsa ta fara sauyawa, a hankali, a hankali Har ta koma tamkar wadda aka cire wa lakka Mama da ke tsaye daga nesa ta fara jin gabanta na faɗuwa. Da mutanen suka tafi ne ta ƙaraso da sauri. "Meye ne?" Ta tambaya. Ibrahim bai amsa ba. Kawai ya miƙa mata takardar. Ta karɓa, ta fara karantawa. Da ta gama... "What??!" Ta faɗa da ƙarfi. Idanunta ta zaro "Saki?!" Ta ɗago tana kallon Ibrahim. "Wai Zahra ce ta kai ka kotu?" Ibrahim ya juya gefe, bai ce komai ba. Mama ta sake kallon takardar. A wannan karon ta fahimci lamarin ba wasa ba ne, tunda had suna shirking daukar mataki Ta matso kusa da Ibrahim. "Karka kuskura ka yarda." Ta faɗa cikin tsanani bacin rai Ibrahim ya ɗago kai. Mama ta ci gaba. "Ka ce kana son matarka, karka yarda a raba ka da ita, ko nawa za a kashe, zamu biya, ko me za a yi, zamu yi" Ta nuna takardar "Amma karka yarda." Ibrahim ya yi shiru. Mama ta ci gaba da magana cikin fushi. "Mace idan ta huce zata dawo, yanzu zugan mutane ne, amma idan ka yarda yanzu, komai ya ƙare mana" Ibrahim ya sauke idanunsa kan takardar da ke hannunta. Wani irin nauyin ne ya sauka kirjinsa, da ko Mama na ta magana... Bai san me take fadi ba Book 1 ya kusa karewa, just few pages left Zaku iya fara making payment dinku ta wannan acc no din , 500 ne kacal 7084571222, Hauwa Jibrin, OPay. Evidence of payment ta 08110615256, Nagode *FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes Book 1 Chapter 30 Bayan sun idar da sallar Magrib... Zahra da Ya Umar suna zaune a parlorn sama. A karo na farko cikin kwanaki masu yawa, ana iya ganin ɗan walwala a fuskar Zahra thought ba sosai ba, amma ya fi na baya Ya Umar kuwa yana zaune a kujera kusa da ita, yana bata labarin abin da ya faru da lawyers ɗin da suka haɗu da Abbah "Da farko ma suna mamakin yadda case ɗin ya yi ƙarfi, dan sunci sai ya yarda tukun court zasu raba auren" Ya faɗa "Da suka ga medical reports da sauran evidence ɗin da aka tattara sai suka ce komai zai yi sauƙi." Zahra ta yi shiru tana saurarensa ta ce "Ai yanzu kam Ya Umar ko bai yarda ba idan kotu ta sake ni ai shikenan, sai ya cigaba da halinsa" Kai Ya Umar ya gyada sai kuma ya ci gaba "Abbah ma ya jikasu da kudi sosai, ya ce baya son wani kuskure ko kaɗan." A hankali Zahra ta ce, "Allah ya saka masa da alheri, Kai ma Ya Umar Allah biya ka, thank you" "Amin, Zahratyy" Ya Umar ya amsa Har zai sake magana ne wayarsa ta fara ringing, ya duba screen ɗin, sai ya miƙe tsaye "Bari na ɗauki wannan call ɗin." "Okay." Zahra ta amsa Daga haka ya fita zuwa balcony, Ita kuma ta janyo wayarta. Ta shiga wani game tana bugawa a hankali, gaba daya hankalinka yana kai kawai, kawai taji an bude kofar parlon Batoul ce ta shigo, da ganin Zahra sai ta tsaya, sannan ta saki wata dariya "Toh..." Ta faɗa tana girgiza kai. "Ashe ƙarshen alewa ƙasa ne fah" Zahra ta ɗan ɗago kai Sai kuma ta mayar da hankalinta kan wayarta tamkar ma ba ta ji abin da Batoul ta ce ba. Batoul ta sake dariya. Amma da ta ga Zahra ko kallonta ba ta yi ba, sai ta zauna tana latsa wayarta ita ma A daidai lokacin Ya Umar ya dawo ciki, da ya ga Batoul sai ya haɗe gira, amma bai ce komai ba. Zahra ce ta miƙe "Yaya bari na koma sama" Ta faɗa Ya Umar ya kalleta "Kin fasa hirar kenan?" Zahra ta yi dariya "Ai mun gama magana Yaya" Ta kalli Batoul, "Hira kuma sai anjima ko gobe Yaya" Ya Umar ya gyada kai. "Alright, Baby" Daga haka Zahra ta wuce sama, shima Ya Umar ya sake fita bayan ɗan lokaci. Ba tare da ya ƙara kallon inda Batoul take ba Can bayan isha'i Lokacin dinner ya yi, kowa ya taru a dining area Abbah, Mami, Mummy, Ya Umar, Batoul, da kuma Zahra Da suka iso dining ɗin duk kusan lokaci guda suka iso, Abbah ya lura Zahra tana neman kujerar da zata zauna Kai tsaye ya miƙe, ya janyo mata kujera da kansa "Zauna nan Baby" Ya faɗa cikin kulawa Zahra ta yi murmushi "Thank you Abbah naa" Ta zauna Abbah kuma ya ɗauki serving spoon, da kansa ya fara zuba mata abinci "Kici sosai fah" Ya faɗa "Likita ya ce kina buƙatar ƙarfi." Mummy ta yi wata yar ƙaramar tsaki, ta kau da kai Abbah ya ji amma bai nuna ba Batoul kuwa... Ko kallon inda suke ba ta yi ,tamkar babu wanda ya dame ta a wajen, ta ci gaba da cin abincinta Mami dai tana kallon Zahra lokaci zuwa lokaci, tana son tabbatar da cewa tana ci. Ya Umar kuma lokaci-lokaci sai yana saka mata ruwa ko yana tambayarta ko tana buƙatar wani abu, Mummy sai wani kallo take masa Duk lokacin daya hakan, Zahra na jin wani abu da ta daɗe bata ji ba, jin cewa tana cikin mutanen da suke ƙaunarta... Yau ya Kama ranar zaman kotu na farko... Tun da sassafe gidan Abbah suka fara shiri Zahra gaba daya jikinta ya gama sanyiz, kana ganinta kasan tana cikin tension, Mami ce ta shiga ɗakinta, ta same ta zaune gaban mirror tana kallon kanta Ba kwalliya sosai ta yi ba, wani simple black abaya ne a jikinta da veil dinsa tayi rolling kanta Mami ta ƙaraso ta tsaya bayanta. "Kina lafiya?" Ta tambaya Zahra ta gyada kai. "Alhamdulillah, Mami" Mami ta gyara mata gefen veil din ta ce "Ki kwantar da hankalinki Baby, komai zai zo ya wuce, ko yaki ko yaso dole ya baki takardanki Yau" Zahra ta yi murmushi, amma a zuciyarta wani irin bugun zuciya take ji, ba ta taɓa shiga kotu ba a rayuwarta A parlorn kuwa Abbah, Ya Umar da lawyers suna ta ƙare wasu bayanai na ƙarshe. Ɗaya daga cikin lawyers ɗin ya riƙe file, cike da documents, medical reports, Hospital records, Photographs, da sauran takardun da za a gabatar Da Zahra ta sauko, kowa ya tsaya yana kallonta, ba karamin kyau tayi ba Abbah ya miƙe, ya ƙarasa kusa da ita "Ready?"Ya tambaya Ta gyada kai "In sha Allah." Sai ya dafa kafaɗarta. "Karki ji tsoro, muna tare da ke...." Karfe tara da rabi suka isa harabar Kaduna High Court Tun daga parking area ana ganin mutane na kai-komo Lauyoyi sanye da bakaken suits, wasu sanye da wigs Ga masu kallo, da iyalan waɗanda suke da ƙara Zahra ta fito daga motar a hankali, ta kalli ginin kotun Wani irin yanayi ne ya rufe mata zuciya Ya Umar ne ta kamo hannunta "Hey." Ya faɗa. "Don't panic." Zahra ta yi murmushi kaɗan, sai suka shiga A gefe guda kuma. Ibrahim ya iso tare da Mama. Tun daga parking area Mama take ta magana. "Karka yarda da komai, ka tsaya da ƙafafunka, wannan ai matsalar gida ce, ba ta kai ace na kotu bane, zaku sasanta kan ku" Ibrahim bai ce komai ba, fuskarsa babu walwala Da suka shiga corridor ɗin kotu, Idanunsu suka haɗu da na Zahra Zahra ta kau da kai da sauri Ibrahim kuma ya tsaya yana kallonta da mamaki, ido ya zuba mata na wasu dakiku Sai Mama ta ja hannunsa. "Mu wuce ciki" Da misalin goma na safe.... Aka kira shari'ar Kowa ya shiga. Zahra na zaune a layin gaba tare da lawyers ɗinta. A bayanta Abbah, Mami, Ya Umar da da Anty Jiddah. A ɗaya ɓangaren kuma Ibrahim da Mama. Alkali ya shigo, kowa ya miƙe, sai da ya zauna sannan aka zauna Bayan an gabatar da bayanan shari'ar. Lawyer ɗin Zahra ya miƙe. "My Lord..." Ya fara. Sannan ya gabatar da buƙatar warware auren. Ya bayyana cewa wanda ake ƙara ya aikata abubuwan da suka haddasa mummunan rauni ga matar nasa. Da farko Ibrahim ya zauna cikin kwanciyar hankali, sai dai lokacin da aka fara gabatar da hujjoji, hankalinsa ya fara tashi sosai Likitan da ya kula da Zahra ya bayyana sakamakon binciken da aka yi Shi kuwa ya bayyana irin raunin da aka samu a jikinta, da yadda aka kaita asibiti cikin matsanancin hali Lawyer ya miƙa takardun ga kotu. Alkali ya duba, sannan ya yi wasu tambayoyi Likitan ya amsa. Bayan haka aka gabatar da wani report, aa biyu. A wannan karon, dukan daya mata tana da cikin , gaba ɗayan kotun ta yi shiru Mama ta kalli Ibrahim da sauri. Ibrahim kuma ya ɗago kai, kamar wanda bai gama fahimta ba, Likitan ya ci gaba da bayani "The patient suffered a..." Zahra ta runtse idanuwanta. Mami ta kamo hannunta Lawyer ɗin Zahra ya ci gaba. Ya bayyana yadda aka kai ta asibiti., yadda aka yi mata treating din internal injuries, da yadda rayuwarta ta shiga haɗari, sai ya juya ya nuna Ibrahim. "My Lord." "Muna da hujjoji da shaidu da ke nuna cewa abin da ya jawo wannan kwanciyarta a asibiti shi ne harin da wanda ake ƙara ya kai mata." Nan kotun ta sake yin shiru. Mama ta kasa haƙuri, ta miƙe tsaye "My Lord!" Ta faɗa "Duk ma'aurata suna samun matsala! Ba wai dan sun yi faɗa ba sai ace za'a raba su...." Alkali ya dakatar da ita. "Madam" Ya faɗa cikin tsauri "Zauna." Mama taki zama tana kallonsa, sai da ta ga yadda mutane ke kallonta kafin ta zauna tana gunaguni Bayan kusan sa'o'i biyu ana gabatar da hujjoji da bayanai, Alkali ya yi shiru yana duba takardun da ke gabans Kowa ya zuba masa ido. Zahra kuwa bugun zuciyarta take ji yana karuwa tsoronta kar ace za'a bawa Ibrahim dama Sai ya ɗago kai, ya fara karanta hukuncinsa ya ce "Kotun ta amince da buƙatar warware auren, an rushe auren tsakanin Zahra da Ibrahim!!! Saboda hujjojin da aka gabatar sun nuna cewa zaman auren mai cutarwa ya haramta a tsakaninsu" Nan take hawaye suka cika idanun Mami, Abbah ya sauke numfashi Ya Umar kuma ya lumshe idanuwansa na wasu dakiku "Sai dai ba nan hukuncin ya tsaya ba." Alkalin ya ci gaba. "Saboda raunin da aka tabbatar an haddasa. Kotun ta umarci Ibrahim ya biya diyya da tara kamar yadda doka ta tanada" Mama ta zaro ido. "A'a!" Ta faɗa "Wannan bai kamata ba! Ai kamar zalunci ne, mutum na son matarsa itama haka kuma a raba su?" Amma babu wanda ya kula ta, cos an riga an yanke hukunci Da aka tashi daga case din, Mutane suka fara fita Zahra na tsaye kusa da Ya Umar tana Jin kamar an sauke mata wani nawi ne daga zuciyarta Sai Ibrahim ya ƙaraso wajenta, ya kalleta, aai ya yi wata yar dariya "Ai baki san me ba." Ya faɗa "Ba wai sonki nake yi ba Zahra, abin da nake so shi ne in zama famous, sai kuma ki haifa min kyakkyawan baby like you, that's all, amma me zanyi da mace kamar ki?" Sai ya ɗaga kafaɗa. "Yanzu try as much as possible ki raina min ciki, ki kuma haifa min tare da shayar da shi, daga nan kuma na zo na karbe kaya na" A hankali Zahra ta ɗago kai ta kalle shi a Karo na farko na wasu dakiku ba tare da tace komai ba Sai kawai wani murmushi ya bayyana a gefen bakinta, murmushin da ya sa Ibrahim ya haɗe gira Domin bai san cewa cikin da yake magana a kai... ya riga ya zube ba, hamdala tayi a ranta, cos da farko har taji haushin doctor Akan rashin rasa babynta da tayi amma yanzu tayi farin ciki sabod kalamansa Zahra ta juya, ta kama hannun Ya Umar Suka ci gaba da tafiya, ba tare da ta waiwayo ba Yayin da Ibrahim ya tsaya a wajen. Karo na farko yana jin kamar yayi kuskure dan bai so haka daga gareta ba... Da suka kama hanyar gida daga kotu kowa ya yi shiru a cikin motar. Da suka isa gida kuwa, Mami ta tafi sashenta domin ta yi sallah ta huta. Ya Umar ya fita ya amsa wasu kiran waya daga lawyers, yayin da Zahra ta nufi ɗakinta. Tana cire veil ɗinta ne sai gashi ana sallama, Farida ce ta shigo "Abbah yana kiranki a parlonsa." A hankali ta gyara mayafinta ta fito, ta nufi parlon Abbah. Ta same shi zaune a kujerarsa da Qur'ani a gabansa. Da ta shiga ta durƙusa. "Abbah" ta gaishe shi Ya amsa cikin tausasawa. "Sannu Zahra." Ta ce, "Yauwa Abbah." Sai ya nuna mata kujerar da ke kusa da shi "Zauna." Ta zauna. Na wasu dakiku babu wanda ya yi magana. Abbah ya kalleta, Idanunsa cike da tausayi. "Kin ji sauƙi a ranki?" Ya tambaya. Zahra ta yi shiru na ɗan lokaci. Sai ta ce, "Alhamdulillah, naji Abbah" Ya gyada kai "Madalla." Sai ya ɗan matso gaba "Ki saurare ni da kyau Zahra." Nan take ta mai da hankali. Abbah ya ce, "Rayuwa tana da jarrabawa iri-iri. Wani lokacin Allah yana ba mutum abin da yake so, wani lokacin kuma yana hana shi abin da yake so saboda alheri" Ta sunkuyar da kai. Ya ci gaba. "Abin da ya faru yau ba ƙarshen rayuwarki ba ne Fatima, ba kuma yana nufin kin gaza ba, kada ki bari mutane ko maganganunsu su sa ki ji kamar wani abu ya ragu a gare ki" Hawaye suka cika idanunta. Abbah ya ci gaba. "Ke ɗiyata ce Zahra, kuma wallahi babu ranar da zan yi nadamar kasancewarki ɗiyata, kina da tarbiyya, kina da ilimi, kina da iyaye da suke sonki, saboda haka kada ki bari abin da ya faru ya karya ki Baby" Hawayen da take ƙoƙarin dannewa suka fara zubo mata Abbah ya ɗan yi murmushi. "Ki yi kuka idan kina son yi, amma kada ki zauna cikin baƙin ciki, duk abin da Allah ya ƙaddara yana ɗauke da hikima" Sai ya ɗan yi shiru, sannan ya ce, "Akwai wani abu kuma da nake so ki sani" Ta ɗago kai ta dan kalle sa Ya ce, "Yanzu da kotu ta warware auren, kin shiga iddah" Ta gyada kai a hankali. Ya ci gaba "Ki ɗauki wannan lokaci a matsayin lokacin kusanci da Allah, ki ƙara ibada. Abin da ya rage miki shi ne ki kula da kanki da kuma lafiyarki, Allah baki miji Nagari da kuma dangin miji Nagari" Zahra ta share hawayenta. "Toh Abbah, Ameen Nagode" Ya gyada kai. "Allah ya miki albarka." "Amin, Abbah na" Ta amsa. Nan take Zahra ta sake fashewa da kuka. Ta matsa kusa da Abbah Shi kuma ya rungume ta kamar lokacin da take ƙarama, yana shafa kanta a hankali har sai da kukan nata ya lafa Zaune yake Kansa a kasa yana saurarn matsifar da take yi, inda take shiga ba tanan take fita ba, Kai ya dago ya kalleta sannan ya ce "Nima ban san haka abun zai kasance ba" Ba tare da ta damu da abun da zai fadi ba tace "Dalla kamin shiru, ka bata komai, kwata kwata ba haka na so ba, yanzu ai ka huta" sai kuma ya kalleta ya ce "Akwai wani changes a zuciya ta, na kuma rasa na menene, Allah yasa ba wai na kamu bane" Tsaki ta ja, Tana masa wani kallo sai kuma ta mike ta ce "Daga yanzu kamar yadda ka bata komai, bana bukatar na sake Jin ka ka kira ni dan kana bukatar kudi ko wani abu" daga haka ta wuce zuwa inda drivern ta yayi parking na tare data sake kallonsa ba ita tasan yadda zuciyarta yake kuna Masu bukatar cigaba da book 2, zaku iya fara payment ta 7084571222, hauwa jibrin, evidence of payment ta—08110615256. 500 ne kacal *FARASHIN IZZAH* Book 1 Chapter 31 Watanni suka shuɗe... A hankali rayuwa ta fara dawowa Zahra yadda take a da. Ta gama iddarta lafiya. Ta ci gaba da karatunta ba tare da wata matsala ba, yanzu ma kusan komai ya ƙare External defense kaɗai ya rage mata, idan ta gama shi kuwa sai jiran sakamako. Daga department ta fito, a hankali take tafiya, handbag ɗinta riƙe a hannu, gaba ɗaya a gajiye take Tun safe take zirga-zirga tsakanin offices da supervisors, da ƙyar ta sauko matattakalar department ɗin. A dai-dai lokacin wayarta sabuwa da Abbah ya siya mata ta yi ƙara, alamar shigowar sako, ta ciro ta daga jaka Da farko ta yi tunanin wani ne daga classmates ɗinta, amma da ta duba sai ta ga alert ne na ₦1,500,000. Duba Wanda ya turo kudin tayi taga daga Abbah. Murmushi ya suɓuce mata, ta girgiza kai. "Wato saboda jiya na gama iddah kenan, Kai Abbah" Ta faɗa a hankali. Ta san halin Abbah, duk lokacin da ya ji daɗin tayi wani abu mai kyau , sai ya nemo wata hanya da zai faranta mata rai. Ta saka wayar cikin jaka sannan ta ci gaba da tafiya. Da ta isa parking lot, ta nufi wajen motarta sabuwa. Wadda Abbah ya canza mata bayan komai ya lafa Ta shiga, tare da kunna shi Ba tare da ta jira wasu ƙawayenta ba, dan gajiya ya mata yawa a jiki, gida take son ta koma ta huta. A hanya kuwa wani Kira'a ne ke tashi a hankali. Ita kuma tana driving cikin nutsuwa Karon farko cikin watanni da suka wuce, tana jin salama sosai a zuciyarta. Da ta isa gida. Mai gadi ya buɗe mata gate ta shiga da motar, ta yi parking, sannan ta fito Jakar hannunta a kafaɗa, kai tsaye parlorn ƙasa ta nufa Tana shiga ta hango Mummy zaune Batoul na gefenta. "Assalamu alaikum." Ta faɗa. Mummy ta amsa. "Wa alaikumussalam." Sai ta kalleta "Ashe jiya kika gama iddah?" Zahra ta yi murmushi. "Eh Mummy." Mummy ta gyada kai. "Toh yayi." Sai ta ɗan gyara zamanta. "Yanzu kuma saura wani mijin ya fito." Zahra ta yi shiru tana saurararta. Mummy ta ci gaba. "Amma Fatima ki tsaya ki yi zaɓe, kar ki sake aure ace ko wata biyu ba zaki cika ba a sake sako-ki, kinga yanzu ke yarinya ce, Karamar bazawara za a fara kiranki" Zahra ta yi wani ɗan murmushi. "Na sani mana Mummy." Ta ce. "Amma ai kowa akan ƙaddararsa yake tafiya ba wanda ya isa ya tsallake abin da Allah ya rubuta masa." Mummy ta gyada kai. "Eh! Haka ne." Sai Batoul ta yi wata yar dariya. "Iyeee! Yau ke ce da wa'azi?" Ta faɗa tana kallon Zahra. "Ina anan saboda za ki rigani aure kike yin abin da kika ga dama, Har a family ban tsira ba, ana cewa kanwata ta rigani aure. Yanzu kuma me amfanin auren wata biyu wanda ko cika bai yi ba?" Nan take murmushin Zahra ya ɗan ɓace. Ta kalleta. "Whatever, Batoul" Ta faɗa a nutse "Haka Allah ya ƙaddara min. Sannan ke ma ba ki fi ƙarfin haka ba. Mind you..... Kullum kina gaya min magana. Ina ɗauke kai ne kawai." Nan take Mummy ta zaro ido tana kallonta da mamaki, kamar ba ita ba Batoul ta miƙe tsaye. "What?!" Ta faɗa. "Batoul zaki kirani?" Zahra ta ɗan ɗaga gira. "Dama kin riƙe girman ne? Ai idan ba ki sani ba, yanzu na girme ki a yanayin rayuwa. Ask everyone saboda da kanki kin fada nayi aure kinga ko anan ai na dara miki" Batoul ta matso kusa da ita "Wallahi zan fasa bakin ki yar iska, shegiya!" Zahra kuwa dariya kawai ta yi "Dadin abin kin san ubana balle ki kirani da shegiya, sannan kuma gani a gabanki, ki fasa, wallahi kina taba ni zan Rama" Batoul ta tsaya cak, ta kasa magana na wasu daƙiƙu. Domin ba ta taɓa jin Zahra ta mayar mata da magana haka ba. Zahra kuwa ta juya tana dariya ta nufi staircase. Mami da ke saukowa daga sama ta haɗu da ita. "Zahra." Ta kira. Zahra ta tsaya. "Na'am Mami." "Meyasa zaki biye musu?" Mami ta tambaya. Zahra ta saki murmushi. "Mami ki ƙyale su. Kullum sai sun gasa min bakar magana. Ina kyale su. Kuma Abbah yace Duk Wanda ya gaya min magana Akan aure na yana baya na dari bisa dari na mayar musu da bakar magana, hakan ne kawai zai sa su rabu da ni" Mami ta girgiza kai tana murmushi. Ta lura Zahra ta canza fiye da yadda take tunani, ko kadan mutuwar aurenta bai dameta ba kuma ta cire damuwar komai dan har wani haske da kiba ta kara "Toh je ki cire kayan nan, ki watsa ruwa, sannan ki zo ki ci abinci" Zahra ta gyada kai. "Toh Mami." Daga haka ta juya, ta wuce zuwa ɗakinta Yayin da Mami ke kallonta tana murmushi a hankali. A zuciyarta kuwa tana gode wa Allah. Domin duk da abin da Zahra ta fuskanta... Ta sake tashi tsaye. Mama na zaune a parlorn tayi tagumi, idanunta na kan Ibrahim da ke zaune a gabanta yana danna wayarsa ba tare da wani kuzari ba. Tun bayan rabuwarsa da Zahra abubuwa suka sauya masa. Mutanen da a da suke yabonsa a media kuma suke masoyansa, sun juya suna sukarsa. Followers ɗinsa sun ragu sosai. Deals da yake samu ma sun fara raguwa. Mama ta girgiza kai. "Ai Ibrahim kai ne ka lalata komai." Ya ɗago ya kalleta. "Mama kamar ya kuma?" Ta ɗan matso gaba. "Baka iya buga wasan bane. Ni mace ce amma wallahi har na fi ka iya yadda zaka buga" Ibrahim ya saki ajiyar zuciya. "Haba Mama. Da na yi yadda kike so ma ai da yanzu wani maganar ake yi ba wannan ba." Mama ta miƙe tsaye. "Toh shikenan. Source of income ɗin ya kare ai kenan." Ibrahim ya yi murmushi. "Ba komai. Zan koma, zaki kuma sha mamaki" Mama ta tsaya tana kallonsa sai kuma ta girgiza kai. "Ai bana jin hakan me yuwa ne, kana tunanin ita ɗin da ka sani ce har yanzu?" Shiru ya yi. Mama ta juya ta wuce, ta bar shi da tunaninsa. A ɓangaren Zahra kuwa... Weekend ne yau Ita da Ya Umar suna zaune a parlon sama suna hira Ya Umar na ta ba ta labarin wani abin dariya da ya faru an office. Har dariya take yi tana rike cikinta Can sai ya kalleta. "By the way." Ta ɗago kai "Na'am?" Yace, "Yaushe kika fita solo date na ƙarshe?" Ta yi dariya. "Solo date kuma?" "Eh mana. Kawai ki fita ki yi shopping, ki ci abin da kike so, ki more rayuwarki." Ta ɗan yi tunani "Gaskiya na daɗe." Ya Umar ya ciro wayarsa. "Good." Ya ce, sai kuma ya danyi danne danne Wayarta ta yi ƙara, ta buɗe, ta bude ido sosai tana kallon alert din ₦500,000 Ta ɗaga kai tana kallonsa "Yaya!" Yana dariya yace, "Go and enjoy yourself, ki tabbatar kin kashe dukka wannan umarni ne." Murmushi ya cika fuskarta, ta tashi da sauri ta rungume shi "Thank you Yaya naaa!" Ya Umar ya yi dariya. "Get lost." Washegari da safe Tun da wuri Zahra ta fara shiryawa Bayan ta yi wanka Ta shafa body mist mai sanyin ƙamshi, ta ɗauki wani elegant wine-colored abaya mai sauƙin ƙyalli, veil dinsa tayi rolling Wani ƙaramin gold wristwatch a hannunta, da matching handbag. Babu wani make-up mai yawa Sai light gloss da powder kaɗan. Amma kyau... Kamar an fito da ita daga magazine, ta koma ainahin Famous Zahratyyn ta Da ta sauko ƙasa. Mami har sai da ta tsaya tana kallonta "Masha Allah Zahra" Ta faɗa. Zahra ta yi dariya. "Thank you Mami, zan tafi solo date, Ya umar ne ya bani 500k na fita wai" "Anya Zahra? Solo date ne ko bikin aure?" Zahra ta yi dariya. "Kaiii Mami." Mami ta karaso ta gyara mata gefen veil dinta "Allah ya kiyaye hanya, make sure kinyi addua" "Amin. In shaa Allah" Ta amsa. Tana shiga parlor taga Abbah, Sai ta sunkuya ta gaida shi da ke zaune yana karanta wani file. Abbah ya ɗago ya kalleta. "Enjoy yourself." Ya faɗa. "Kuma don't be home too early." Zahra ta yi dariya. "Kai Abbah!" Ya ɗaga hannu. "I'm serious. Go have fun." Ta gyada kai. "Toh." Tana fita compound ɗin Mai gadi ya yi saurin buɗe mata gate. Ta nufi sabuwar motarta. Black Lexus ɗin da Abbah ya saya mata bayan ta gama iddah. Ta buɗe ƙofa, tana shiga ta zauna sai ta ɗan sauke numfashi. A hankali ta kunna motar. Sai wani murmushi ya bayyana a fuskarta. A hankali ta fice daga gate, ta hau babban titi. Wani cool music mai sanyi na tashi a motar, yayin da take driving, Idanunta na kan hanya, amma zuciyarta cike take da wani irin salama Ta tsaya a wani boutique ta siya wasu kayan Ta shiga wani store ta ɗauki turare Sai kuma ta wuce wani bookshop. Domin duk da komai har yanzu son karatu novels na nan a ranta. BBayan ta gama yawon Sai ta nufi wurin da take son ta zauna Wani upscale garden restaurant, wurin yana da kyau sosai Flowers a ko'ina, korayen bishiyoyi Da ƙananan fountains da ke zubar da ruwa cikin nutsuwa Ta yi parking ta fito daga motar. Iskar wurin ta kaɗa gefen veil ɗinta, wani an murmushi ya sake bayyana a fuskarta. Ta shiga ciki, wata ma'aikaciya ta tarbe ta cikin mutunci da fara'- Ta nuna mata wani wuri mai kyau kusa da garden ɗin. Zahra ta zauna, ta cire wayarta ta ɗora kan table. Ta yi order na abinci da fresh juice. Yayin da take jiran a kawo mata. Sai ta jingina da kujera, tana kallon mutanen da ke kai-komo Ga wani soft music na tashi a hankali tana jin wani irin nutsuwa, lumshe ido tayi Sai taji kamar an kira sunanta, da farko ba ta kula ba Sai kuma muryar ta sake zuwa mata "Zahra..." A razane ta ɗago kai, hadi da bude idanunta dan jin voice din da ba zata taba mantawa da shi ba Wani saurayi ne ke tahowa zuwa gare ta Zaro idanunta tayi waje, ta miƙe tsaye, tana kallonsa Lips ɗinta suka motsa a hankali "Ahmad...?" Saurayin ya yi wani irin murmushi "Zahratyyy..." Yana ƙarasowa gabanta. Wani irin bugun zuciya ya kama ta, ba tare da ta yi tunani ba Ta juya da sauri, ta fara tafiya... "Zahra!" Ya kira "Please tsaya!" Amma ta kasa saurarensa, ta ci gaba da tafiya da sauri Yayin da Ahmad  ke bin bayanta yana ƙoƙarin kiranta... Sai kuma wani abu da ta ji daga bakinsa ya sa ƙafafunta suka fara yin sanyi, ta tsaya cak Numfashinta ya ɗauke na ɗan lokaci, a hankali ta fara juyowa... Sai kuma kamar Wanda aka tsikara ta juya ta fita daga wajen da sauri, kamar wadda ta ga abin da zuciyarta ba ta shirya ba Ahmad ya tsaya a baya yana kiranta, "Zahra! Please just listen to me..." Amma ko da wasa bata tsaya ba, ta yi sauri zuwa inda ta faka motarta Hannunta na rawa ta buɗe ƙofa, ta shiga, ta zauna ba tare da ta duba baya ba Numfashinta na fita da sauri, ta danna start Motar ta yi karan kunnawa, ta fice daga wurin cikin gaggawa A hanya kuwa... Duk abin da ke cikin motar kamar ya koma nisa, Idonta na kan hanya amma zuciyarta ba ta nan, wani nauyi take ji a ƙirjinta, kamar wani abu ya tashi ya tsaya a maƙoshinta A hankali ta rika driving har ta shiga cikin unguwarsu Mai gadi ya buɗe mata, ta shiga ta yi parking kai tsaye, ba tare da ta duba ko ina ba Ta fito daga motar da sauri, ta nufi cikin gida Tana shiga parlorn ƙasa babu kowa, tayi handalah, ta wuce kai tsaye staircase Ta hau sama da sauri, har zuciyarta na bugawa da ƙarfi Tana isa ƙofar ɗakinta ta buɗe, ta shiga ciki da sauri Ta rufe ƙofar da baya, ta jingina da ƙofar A hankali ta lumshe idanunta Numfashinta na hawa da sauka, ta ɗora hannunta a ƙirji. Zuciyarta na bugawa kamar zata fito waje, tayi shiru sai karar agogon bango kaɗai ke ji A wannan shiru ɗin ne ta fara jin tunanin Ahmad yana dawowa mata a hankali Kalaman da bai ce ba, a autin muryarsa da ta yanke mata wata nutsuwarta Ta buɗe idanunta a hankali.... Sai kuma tunanin abubuwan da suka faru a baya ya shiga zuwa mata, hawaye ne suka shiga tsintiri a fuskanta Wasa-wasa abin ya zama kamar al'adarsa Kusan kullum sai Ahmad ya zo gidan, amma Zahra ko sau ɗaya ba ta fito ta gan shi ba Har idan ya haɗu da Ya Umar ma, kasa haɗa ido yake yi da shi shima Yau ma kamar kullum, Zahra na zaune a parlon ƙasa, wayarta a hannunta tana scrolling Instagram. Bayan ta gama iddah ne ta fara posting hotunanta a page ɗinta. Ganin yadda ta ƙara lafiya da kiba, ba ta son mutane su ci gaba da tunanin tana cikin damuwa ko kunci, bayan ta rubuta caption din ne ta sake hoton Sai dai ga mamakinta, tana duba notifications ɗinta ta ga: Ibrahim khalil liked your post. Tsaki ta ja. Nan take ta shiga profile ɗinsa, ta yi unfollow dinsa. Daga nan kuma ta cire shi daga cikin followers ɗinta. Wayar ta ajiye gefe. A dai-dai lokacin Farida ta shigo. "Anty." Ta kira Zahra ta ɗago kai "Na'am?" "Kinyi baƙo." Ta haɗe gira "Baƙo kuma?" Farida ta gyada kai. "Eh." Kai ta gyada "Toh, ina zuwa." Farida data fita, Zahra ta gyara zamanta sai kuma ta dauki wayanta ta shiga pdf tana kallon chapter 5 na project dinta da classrep ya turo mata Har kusan minti 15 Zahra tana zaune, har kusa manta da maganar baƙon tayi Can sai ga Mami ta shigo parlorn, ta tsaya tana kallonta. "Ana jiranki fa." Ta faɗa. Nan take Zahra ta ɗago kai sai ta miƙe ba tare da ta ce komai ba, ta haura sama, ta shiga ɗakinta ta ɗauki hijab. Bayan ta saka shi ne ta fito, a hankali ta nufi parlon baƙi, tana isa bakin ƙofar, ta tura ta ta shiga Kawai idanunta suka sauka a kansa, zuciyarta ta buga. Ta juya da nufin fita. Sai ta ji muryarsa. "Please... ki tsaya." Kawai ta tsaya cak "Let's talk." A hankali ta sauke idanunta ƙasa Hawayen da ba ta san suna taruwa ba suka fara zubo mata, ta ɗaga hannu tana share su Sai ta ji muryarsa a karo na biyu "Zahra..." Shiru ya biyo baya. Kafin ya sake cewa, "Zahra, zaki aure ni? Alhamdu Lillah!! Anan muka kawo karshen book 1 na littafin nan me suna FARASHIN IZZAH Me son book 2 sai ya biya kudi ta wannan account details din; 7084571222, Hauwa Jibrin, OPay. Shaidar biya ta wannan 08110615256. 500 ne kacal ba tsada Ko kuma a karanta a arewapen, Nagode. ALHAMDULILLAH! 🤍✨ A yau mun kawo ƙarshen FARASHIN IZZAH – BOOK 1. 🥹❤️ Na gode da ƙauna, support, votes, comments, shares, da addu’o’inku. Kowanne chapter da kuka karanta ya kasance saboda kasancewarku tare da ni. Ga duk wanda ya raka ni tun daga farko har ƙarshe, ina matuƙar godiya. Allah Ya saka muku da alkhairi. 🤲🏽 Amma ku sani… wannan ba ƙarshen labarin ba ne. Book 2 zai zo da amsoshin tambayoyi da dama, sirrika za su tonu, gaskiya za ta bayyana, kuma farashin izzah bai ƙare ba… Nagode. Ku ci gaba da kasancewa tare da ni. ❤️ Hauwa Jibrin Sulaiman (Hauwajay Writes) Chapter 32 Yarinyar ce ke saukowa daga matakala, sweet na cikin bakinta, fuskarta kuwa cike take da hawaye. Da alama ko ƙafafunta ba za su iya ɗaukarta ba, domin a hankali take saukowa kamar za ta faɗi a ƙasa. Da sauri mutumin ya ƙaraso gabanta, kafin ma ta kai ƙarshen matakalar ya durƙusa ya ɗauke ta cak. Sama ya ɗaga ta yana dariya, sannan ya yi mata kiss a kumatu. Nan take ta kwalla ihu na murna tana cilla ƙafafunta sama. Ya sake yi mata wani kiss, sannan ya fara share mata hawayen da suka ɓata kyakkyawar fuskarta. "Mamana, wa ya taɓa min ke?" Ya tambaya cikin kulawa. Babyn ta juya ta kalli mutanen da ke tsaye a gefe. Nan take ya bi kallonta. Wani matashiyar Mata ya kala, ɗan haɗe gira yayi "Khadijatou, me kika yi wa 'yata?" Ya tambaya Tsohuwar matar da ke zaune a gefe ta yi saurin cewa, "Kul! Kar ma ka soma. Da ba don jika ta fi 'ya ba, da na nuna maka rashin mutunci idan ka ce zaka taɓa Hadiza." Dariya suka yi gaba ɗaya. Khadijah kuma ta masa gwalo Ya haɗe gira yana kallonta, yayin da har sannan yake tsaye tare Babyn Mama ta yi murmushi tace, "Sannu da zuwa. Toh ai sai ka ajiye shalelen naka." Khadijah ta girgiza kai “Ah toh! Ni kam naga ko hutawa bai yi ba, balle a yi maganar cin abinci." Ta nuna yarinyar da ke jikinsa "Idan ka biye wa wannan Baby ɗin taka, ba za ka taɓa hutawa ba." "Ina ruwanku?" Ya faɗa yana rungume da Fatima a jikinsa. Khadijah ta ɗauki jakarsa ta kai masa ɗaki, sannan ta dawo parlon Har zuwa lokacin yana zaune da Fatima a cinyarsa, yana ba Mama labarin tafiyarsa da yadda hanya ta kasance. A dai-dai lokacin wata mata ta fito daga ɗaya daga cikin ɗakunan tare da yara biyu, mace da namiji. Fuskarta a haɗe take tamkar ba ta son ganin kowa. Da ƙaramar yarinyar ta hango shi, da sauri ta yi yunƙurin zuwa wajensa. Sai matar ta watsa mata wani kallo mai kaifi tare da zare mata idanu. Nan take yarinyar ta tsaya cak, ta fasa ƙarasa wa gare shi. Matar ta kama hannunta, sannan ta ja hannun yaron da ke gefenta. Yaron kuwa har hawaye suka fara cika idanunsa, domin yana son zuwa wajen mahaifinsa. Sai dai yana tsoron mahaifiyarsa. Ba tare da ta ce komai ba, ta juya da su suka fita daga parlon. Shiru ya ɗan ratsa wajen. Tsohuwar matar ta sauke ajiyar zuciya. "Wannan wani irin hali ne haka?" Ta faɗa cikin takaici "Karfi da yaji ta rabaka da yaran nan, toh me amfanin zamanta a gidan nan?" Khadijah kuwa kanta a ƙasa yake, ko magana ba tayi ba. Domin ta san ita ce silar matsalar da ke tsakaninsu Mutumin ya ɗan yi murmushi mai ciwo. "Sai ta ci gaba da nisanta su da ni." Ya faɗa a hankali "Akwai ranar da za ta yi nadamar yin hakan." Ya ɗan yi shiru kafin ya ci gaba "Amma ni ba zan taɓa buɗe baki na na mata magana ba." Ya jingina da kujera "Kamar yadda take so, zan bar komai ya tafi a hankali." Khadijah ta miƙe a hankali, kanta a kasa zata wuce Ya ɗan matso gaba yana cewa, "Please ki shiga da ita, bari na watsa ruwa." Ta ƙaraso kusa da babyn zata sauke ta, Babyn ta makyalkale shi da shagwaɓa "Abbah... bana son zuwa wajen Mami." Dariya ya yi a hankali, yana girgiza kai Mami ta yi murmushi ta ce, "Sai ki yi ta zama mana ina ruwa na, karfi da yaji Abbahn ki yasa baki girma” Sai tsohuwar matar ta ce cikin salon umarni mai ɗan zolaya "Ke dai je ki kwanta mana Khadijah, tun safe kike aiki fah, yanzu ki huta, ki bar shi da mai sunansa kawai tunda ita bata son kowa sai shi." Khadijah ta ɗan yi murmushi cike da kunya, ta gyada kai. "Toh." Daga haka ta juya ta nufi ciki a har sannan kuma kanta a kasa yake Shi kuma ya sauke numfashi, ya ce, "Bismillah." Nan take ya miƙe tsaye, ya ɗauke da Fatima har sannan Ya goya ta a bayansa tana manne masa kamar ba za ta bar shi ba, yana lallashinta da muryar da ya saba kwantar mata da hankali A haka ya kaita har wajen Granny, sannan ya sauke ta a hankali Asalin Labarin……. Alhaji Muhammad Nasir attajiri ne na gaske, mutum mai tarin arziki wanda ya yi suna a duniyar kasuwanci. Sunansa ba a Najeriya kaɗai aka sani ba, har ma a faɗin nahiyar Africa ya yi kaurin suna saboda basira da ƙwazon da Allah Ya hore masa. Asalinsa ɗan jihar Bauchi ne, amma shekaru da dama da suka gabata ya dawo da zama garin Kaduna, inda ya gina rayuwarsa da kasuwancinsa. Ya rasa mahaifinsa tun yana ƙarami, kuma mahaifiyarsa ce ta tsaya tsayin daka wajen rainonsa da karatunsa. Da addu'arta da jajircewarta, Allah Ya sanya masa albarka har ya zama ɗaya daga cikin manyan attajiran ƙasar. Alhaji Muhammad yana da mata biyu. Matarsa ta farko ita ce Hafsat. Allah Ya albarkace su da yara biyu, namiji da mace; Umar da Fatima, wacce aka fi sani da Batoul. Sunan mahaifiyarsa ce Sai dai Hafsat tana da wata irin ɗabi'a ta raina mutane. Ko kai waye, ba ta cika ɗaukar kowa da muhimmanci ba. Har mahaifiyar sa ba ta tsira daga halinta ba, ga uban gadara Wannan ne ya sa Alhaji Muhammad ya ƙara aure. Ya auri Khadija, kyakkyawar Bafulatana daga jihar Adamawa. Ita ma Khadija ta taso cikin gata da daula, don haka ba ta da ɗabi’ar raina mutane ko wulakanta mutum, ahasalima mutunce mai son kowa da kuma kyauta Tun bayan shigowarta gidan ne zaman lafiya ya fara yin ƙasa. Da farko Hafsat ta yi fushi matuƙa har ta bar gidan. Sai dai daga baya ta dawo da kanta, amma ta ɗauki wani mataki da ya daɗe yana ci wa Alhaji Muhammad tuwo a ƙwarya, ta hana yaranta kusantar mahaifinsu. Ko Umar, wanda a baya kusan kullum yana tare da mahaifinsa, sai da ta raba su. Hakan ya yi wa Alhaji Muhammad ciwo sosai a zuciya. Sai dai daga baya Allah Ya azurta shi da kyakkyawar diya daga Khadija. Ranar da aka haife ta, tamkar an sauke wani sabon farin ciki ne a rayuwarsa. Saboda tsananin son da yake yi wa mahaifiyarsa, sai ya sake sanya wa yarinyar sunanta, wato Fatima Zahra. Tun daga ranar, Zahra ta zama abar so ta musamman a wajensa. Ita ma Zahra ba ta son kowa kamar mahaifinta. Tun tana ƙarama ya saba da ɗaukar lokacinsa gaba ɗaya yana tare da ita. Shi ke yi mata wanka, shi ke kai ta makaranta, shi ke ɗaukota, shi ke kwantar da ita barci A wurin Zahra, Abbah ba mahaifi kaɗai ba ne, aboki ne, masoyi ne, kuma duniya ce a gare ta Lokacin da Umar ya fara girma, ya fara fahimtar cewa abin da mahaifiyarsu ke ƙoƙarin dasa musu game da mahaifinsu ba daidai ba ne. A hankali ya fara janye jikinsa daga gare ta, ya koma kusantar mahaifinsa. Tun daga lokacin, kusan kullum shi da Zahra za a same su a ɗakin Abbah Wannan ya sa wata irin shakuwa ta musamman ta shiga tsakaninsu,. Shakuwa mai ƙarfi da ta zarce ta 'yan uwa kawai, kamar wasu ‘yan biyu Duk abin da Zahra take so, to Ya Umar ma zai so shi. Abin da ya bata mata rai, shi ma zai bata masa rai. Sannan akwai mutum guda da bai taɓa iya ƙin wani abu da Zahra take so ba... wato Abbah…. A haka rayuwa ta ci gaba a gidan Abbah har Zahra ta girma. A lokacin tana ajin SS2, kuma ta taso cikin tsananin so, kulawa da gata. Tun tana ƙarama, dukiya ba komai bane a wajen ta. Saboda ta taso tana samun duk abin da take buƙata, kuɗi a wajenta tamkar wani abu ne na yau da kullum. Zahra ba ta da ɗabi'ar raina talakawa ko kyamar marasa hali. Akasin haka ma, tana da zuciya mai tausayi da son taimakon mutane, sai dai tana da wani irin Izzah Wanda a koda Yaushe Mami ke mata magana akai Sai dai Mummy ta gwada mata cewa ai mahaifinta attajirine dan haka idan bata izzah za’a rainata kuma ba zata sabo karbuwa ba a wajen mutane Tun tana yarinya take son tsafta, wanka da kwalliya. Wannan ɗabi'ar tata ce ta sa kusan duk kuɗin aljihu da Ya Umar da Abbah suke ba ta suna ƙarewa ne a kan turaruka, kayan kwalliya da sauran abubuwan da take so. Tun tana da shekara goma sha biyar ta fara amfani da social media. Saboda kyawunta, salon rayuwarta da kuma yadda take son fita solo dates lokaci zuwa lokaci, cikin ƙanƙanin lokaci ta fara samun mabiya da yawa har ta zama sananniya a shafukan sada zumunta. hakan ne yasanya zahra bata kaunar rai ni ko kadan A wannan lokacin ne kuma ta haɗu da Asiya, Firdausi da Saudat. Dukkansu sun samu gurbin karatu ne ta hanyar scholarship. A farkon haɗuwarsu, Saudat ta fi shan wahala a cikinsu. Yadda take shiga makaranta da kuma irin tufafin da take sakawa ya sa mutane da dama suna guje mata ko kuma su raina ta. Kasancewar yawancin ɗaliban makarantar 'ya'yan masu kuɗi ne, hakan ya ƙara sa Saudat ta ji ba ta cikin su Suhaima ce kadai a cikinsu iyayenta suke da kudi Wanda tun farko itama a makarantar suke tare da zahra Zahra kuwa a hankali ta ja Saudat a jikinta saboda tana bata tausayi Ba Saudat kaɗai ba, hatta Asiya da Firdausi, Zahra ta kasance tana taimaka musu a duk lokacin da suka buƙaci taimako. Wani lokaci kuɗi take ba su, wani lokacin kuma tana saya musu abubuwan da suke buƙata ba tare da ta jira sun roƙe ta ba. Saboda haka, a hankali dangantakarsu ta ƙara ƙarfi Har ya kai ga ba sa kallon Zahra a matsayin kawa kawai. A wajensu, Zahra Yaya ce, abokiya kuma 'yar uwa wacce a kodayaushe take tsayawa a bayansu….. Kana kallonta ka san a matuƙar gajiye take Tana zaune a kujerar baya a motar, hankalinta gaba ɗaya ya tafi wani wuri. Idanunta na kan titin da suke bi, tana kallon komai ta cikin window ba tare da ta lura da abin da ke kewaye da ita ba Envelope ɗin result ɗinta kuwa tana riƙe da shi tamkar wani abu mai daraja. Ba ta ma lura da lokacin da aka buɗe gate ɗin gidansu aka shiga da motar ba. Sai da motar ta tsaya sannan ta ɗago kai Kallon harabar gidan ta yi na ƴan daƙiƙu, sannan wani faffadan murmushi ya mamaye kyakkyawar fuskarta Tun kafin driver ya gama buɗe mata ƙofa, ta buɗe da kanta ta fito. Da gudu kuwa ta nufi cikin gidan Tana shiga parlon, ko kallon wanda su ke ciki ba ta yi ba. Kai tsaye ta nufi inda Abbah yake zaune. "Abbahhh!" Ta kira cikin farin ciki kafin ta faɗa jikinsa. Dariya ya yi yana rungume ta. "Da alama Baby na yau ma ta sake cin first position." Dariya ta yi tana gyara zamanta a jikinsa. "Sure, my Abbah." Mummy ta ja tsaki. Ba tare da ta ce komai ba ta miƙe ta fita daga parlon Ya Umar da ke zaune kusa da Abbah ya haɗe gira. "Shine ba za ki kula da ni ba kenan?" Ta juya tana kallonsa. "Ka tsaya mana, bari na gama da Abbah na farko” Daga haka ta miƙa masa envelope ɗin. Abbah ya karɓa ya buɗe yana dubawa. Da ganin sakamakon, murmushi ya bayyana a fuskarsa. "Excellent." Ya furta yana kallonta da alfahari. Nan take Zahra ta miƙe tsaye. Ta dafa kugunta tana kallon Ya Umar. "Yaya..." "Na'am." "Me za ka ba ni a matsayin gift?" Dariya ya yi "Faɗi komai." Ta ɗan ɗora yatsa a haɓa tana tunani. Sai kuma ta ce, "System nake so." Ko ƙyaftawa bai yi ba "Consider it done. In sha Allah kafin gobe zan saya miki." Wani irin farin ciki ya bayyana a fuskarta. Mami ta yi dariya. "Eh lalle, Ya Umar. Kai dai ka ci gaba da bata ta” Abbah ya jefa mata wani kallo. Nan take ta yi shiru tana murmushi. Zahra kuwa ta karɓi result ɗinta daga hannun Abbah ta kai wa Ya Umar. Batoul ta miƙe tsaye cikin ɓacin rai, ba tare da ta ce komai ba ta wuce ɗakinsu da sauri, tana shiga ta tarar da Mummy zaune "Mummy! Kina ji Yaya kuwa?” Ta faɗa cikin fushi. Mummy ta ɗago tana kallonta "Me kuma ya faru?" "Yaya wai zai saya wa Zahra system gobe." Wani irin tsaki Mummy ta ja. "Sai mu gani dan ubansa idan ya isa” Ta faɗa tana haɗe fuska "Idan ni na haife shi, sai ya saya mata mu gani” Batoul ta zauna bakin gado "Mummy ko ni fah bai taɓa saya min ba. Sai Zahra da ko secondary ba ta gama ba” Mummy ta kalleta. "Ki yi shiru."Ta faɗa cikin takaici. "Idan Zahra ce, bai isa ya ce zai saya mata ba." Batoul ta haɗe fuska tana jin haushin yadda a duk lokacin da Zahra ta nemi wani abu, kamar umarni ne ga Abbah da Ya Umar Can da yamma. Ya Umar ya shirya fita ne domin ya cika alƙawarin da ya yi wa Zahra na siyo mata system Yana saukowa daga ɗakinsa ne sai ya tuna da wani abu, Mummy ta ce idan zai fita cikin gari akwai abun da zai siya mata, don haka ya juya ya nufi ɓangarenta Yana isa bakin ƙofar ɗakin ya yi knocking kaɗan sannan ya shiga. Mummy na zaune kan gado tana duba wayarta. Tana ganinsa sai ta haɗe fuska. "Mummy” Ya kirata a hankali Ta amsa da wani irin kallo kawai. Ya ƙarasa ciki. "Mummy, kin ce min idan zan fita zan siyo miki wani abu ko?" Bai ma gama maganar ba. Sai ta miƙe tsaye tamkar wadda take jira ya yi magana. "Toh ashe ka tuna da ni kenan?" Ta fara cikin ɓacin rai. Ya Umar ya tsaya yana kallonta. Ta ci gaba da magana "Ba Zahra kaɗai ka sani ba? Kullum Zahra, Zahra, Zahra!" "Idan ta yi atishawa kai ne farkon wanda zai damu. Idan ta nemi abu, kai ne farkon wanda zai miƙe. Ni da na haife ka kuwa kamar ba ka gani na ita kadai kake gani balle a ce Batoul kuma” Ya Umar ya sauke numfashi ya ce "Mummy..." Ta ɗaga masa hannu. "Karka min magana." Ta katse shi. "Yanzu saboda ta ci wani banzan position ne za ka kashe mata kuɗi ka siya mata system. Ni ka taɓa siya min wani abu da irin wannan kuɗin?" Shiru ya yi yana mamakin ko Kai zaiwa Mummy bata gani idan har zai kashewa zahra, sai tace baya mata komai, kamar ba shi bane last week ya tsiya mata wani jewelry gold Ta cigaba da masifar. "Ka ɗauki yarinyar nan ka ɗora ta a kai. Komai nata daban. Komai nata musamman. Ko Batoul da ta fito cikina ba ta taɓa samun rabin abin da Zahra take samu a hannunka ba." Ya Umar ya sauke kansa. A hankali ya ce, "Mummy, ki yi haƙuri idan na ɓata miki rai." Amma kamar ma ya tunzurata nr Ta ci gaba da magana tana kai-komo cikin ɗakin da karfi, da ganin ba za ta saurare shi ba, sai ya sake cewa, "Wallahi Mummy ba haka bane..." Ta juya a fusace. "Ban ce ka fita ba?" Shiru ya yi yana mamakin Yaushe tace ya fita Sai ta nuna masa ƙofa. "Ka fita ka bar min ɗaki." Ya Umar ya kalleta na ɗan lokaci Daga ƙarshe ya girgiza kai kawai. "Toh Mummy, Allah ya huci zuciyarki." Bai jira amsa ba. Ya juya ya nufi ƙofar. Yana fita... Bang! Ta buga ƙofar da ƙarfi a bayansa. Ya Umar ya tsaya na ɗan daƙiƙu a wajen. Sai ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi. Daga nan ya ci gaba da tafiyarsa ba tare da ya sake waiwayowa ba #FARASHIN IZZAH 08110615256 Chapter 33 Da yamma kamar yadda ya yi mata alƙawari, Ya Umar ya dawo gida ɗauke da wani babban carton. Tun da Zahra ta hango shi daga parlon ƙasa, ta miƙe da gudu ta tarbe shi. "Yaya!" Ta kira tana dariya Ya ɗaga carton ɗin yana kallonta. "Me kika ce kina so ma?" Idanunta ta zaro tana masa murmushi ta ce "Kana nufin...?" Ya miƙa mata carton ɗin "Open it." Da sauri ta karɓa. Ko zama ba ta yi ba, a tsaye ta fara buɗe carton ɗin. Da ta hango sabon system ɗin a ciki, sai ta kwalla ihu. "Oh my God!" Ta faɗa tana rufe bakinta da hannu. A gigice ta kalli Ya Umar kamar zata yi kuka ta ce "Yaya... thank you!" Ba tare da ta jira komai ba, ta rungume shi da ƙarfi kamar zata yar dasu Ya yi dariya yana shafa kanta. "Congratulations." Da gudu ta juya tana nuna wa Mama ladi mai aikin gidan. "Mama! Ki zo ki gani!" Mama ladi ta ƙaraso tana murmushi. "Masha Allah Hajiya karama, Allah ya ƙara hazaka da ilimi mai amfani ." Sauran ma'aikatan gidan ma suka taru. Kowa na taya ta murna. "Masha Allah Babyn Abbanta” Daga nan ta nufi Mami dake sauko wa daga stairs, tana karasa sauka ta mika mata "Mami, duba mana! Yanzu Yaya yazo min da shi” Mami ta karɓa tana dubawa, ta yi murmushi "Masha Allah. Allah ya saka masa da alheri." Batoul dake zaune tun dazu ta haɗe fuska, sai kuma ta mike kai tsaye ta juya ta haura sama. Tana shiga ɗakin Mummy ta ganta tana waya, Mummy kuma ganinta yasa ta sauke wayen daga kunnenta ta kashe "Mummy! Ya saya mata." Ta ce tana hade fuska Mummy da rashin fahimta ta ce "Wane abu?" "System mana." Da sauri ta miƙe tsaye, ba tare da ta ce komai ba ta fita daga ɗankinta ta sauka ƙasa Har lokacin Zahra na ta murna tana kallon system ɗin, Mami kuma already ta koma sama Sai kawai ta ji... Paf!!! Mari ya sauka a kumatunta. System ɗin ma ya kusan faɗuwa daga hannunta. Ta dafe kumatunta cikin razana "Mummy..." Ta kira da ƙyar Mummy ta ƙwace system ɗin daga hannunta. "Wai ke me kike ɗaukar kanki ne?” Ta faɗa cikin tsawa "Batoul na university, ba a taɓa saya mata irin wannan ba. Sai ke!" Zahra ta haɗiye hawaye. "Ai... Batoul bata taɓa tambayar Abbah ko Ya Umar su saya mata ba." "Stupid!" Mummy ta katse ta. "Ki yi min shiru!" Ta sake wanke ta da wani mari. Nan take Zahra ta zauna a ƙasa dabas ta fashe da kuka sosai A dai-dai wannan lokacin Ya Umar ya shigo parlon da sauri idanunsa suka sauka kan Zahra dake kuka sai kuma kalli Mummy. "Mummy..." Bai ƙarasa magana ba ta katse shi "Eh, ni ce na mare ta." Ta faɗa tana kallonsa ido cikin ido. "Ka zo ka rama mata mana” Parlon ya yi tsit, Mama ladi ta juya tsum tsum ta koma kitchen Ya Umar ya kalli Zahra da idanunta suka kumbura saboda kuka sai kuma ya sauke idanunsa kasa A hankali ya ce, "Mummy... kiyi hakuri" Ya ƙarasa ya ɗaga system ɗin daga inda ta jefar da shi. Ya miƙa wa Zahra. "Ki je ɗaki." Da ƙyar ta karɓa. Ba tare da ta kalli kowa ba, ta juya ta haura sama tana kuka. Kai tsaye ta shiga ɗakin Mami. Tana shiga Mami ta ganta cikin wannan hali, ta miƙe da sauri. "Lafiya?" Zahra ta faɗa jikinta tana kuka. Nan da nan ta ba ta labarin abin da ya faru. Mami ta yi shiru tana saurarenta har ta gama. Sai ta ɗago fuskarta. "Maganinki ba ke ce kike yarda da duk abin da take faɗa miki ba?" Zahra ta yi shiru. "Ba har kin manta irin abubuwan da take miki a baya ba?" Ɓata fuska tayi tana kallon wani wajen Mami ta ci gaba. "Shi har wani lokacin kike daukar kafarki ki tafi part din can ba, sau nawa nake miki iya ka? Alhali ba ta taɓa son ganin ci gabanki ba” Ta dafa kafaɗar Zahra "Ki saurare ni da kyau." "Daga yau... Idan na sake ganin kin je side ɗinsu ko kina sauraren shawaran da take Baki…wallahi zan ɓata miki rai." Zahra ta share hawayenta. A hankali ta gyada kai "Toh Mami." Mami ta rungume ta tana shafa bayanta. "Ke dai ki ci gaba da zama yadda kike. Allah yana tare da masu zuciya mai kyau." Abbah na shigiwa sai ya nufi ɓangaren Mami Yana tura ƙofar ya shiga, ya tarar da Mami zaune gefen gado, yayin da Zahra ke manne da ita, idanunta duk sun kumbura saboda kuka. Da fara'a ya shigo kamar yadda ya saba. Sai dai da zarar idanunsa suka sauka kan fuskar Zahra... Murmushin da ke kan fuskarsa yayi fading lokaci guda. Ya tsaya cak yana kallon alamun yatsun hannu da suka bayyana a kumatunta. Idanunta kuwa sun yi jajur saboda yawan kuka. A hankali ya ƙaraso gabanta. Ya ɗaga haɓarta da hannunsa. "Baby..." Ya kira cikin sanyin murya. "Wa ya buge ki?" Zahra ta sauke kanta ƙasa. "Mummy ce..." Ta faɗa da ƙyar. Ya haɗe gira, sabar yadda yaji zuciyarsa na tafasa "What!? Saboda me?" Ta haɗiye wani sabon kukan da ya taho mata. "Saboda Ya Umar ya saya min system." Shiru ya ratsa ɗakin. Abbah ya sake kallon fuskar Zahra. Daga nan ya juya ya kalli Mami. Mami ta san daga yanayin fuskarsa cewa ya fusata matuƙa. Bai ce komai ba Ya juya kawai ya fita Kai tsaye ya nufi ɓangaren Mummy, bai ko yi knocking ba, ya tura ƙofar ya shiga Mummy na zaune tare da Batoul. Da ganinsa ta ɗan gyara zamanta. "Alhaji..." Bai bari ta ƙarasa ba. "Hafsat!"Ya kira sunanta cikin tsawa Ta ɗan razana. "Meye haka?" Ya nuna mata yatsa "Wa ya ba ki ikon ɗaga hannu ki mari 'yata?" Ta haɗe gira. "Toh masu ‘ya Wanda ba’a taba musu ita, toh bata da kunya ne shine nake son gyarata? “Ina tambayan ki wa ya ba ki wannan ikon? No matter what Baki da right akanta” Ta ɗan yi dariyar raini. "'Yarka?… Ai Batoul kuma ba 'yarka ba ko? Toh ya kamata ka sani Batoul ce ta cancanci a saya wa abu, ba Zahra ba, tunda Tana gaba da ita” Abbah ya katse ta da ƙarfi "Ya isa!" Muryarsa ta amsa cikin ɗakin. "Ko nawa Umar ya kashe a kan Zahra, ba ruwanki… Kuɗinsa ne…. ‘Yar uwarsa ce. Idan yana so ya saya mata mota ma, ba ki da hurumin hana shi." Ta taso tsaye. "Toh ni kuma Uwarsa Nace bai isa ba…. ace bai taba wa Batoul haka ba sai wata can, ni kuma ba zan lamunta ba tunda Kai da kake Uba ma ko sanin bukatunta Baka yi balle ka sauke” Abbah ya kalleta da wani irin kallo. "Saboda Batoul ba ta taɓa kallona ba a matsayin Uba ba, balle ta tambaye ni abu, kuma ko ta nema... ba ke ce kike hana ta ba” Ta ɗan matsa kusa da shi. "Saboda Zahra ne kake min ihu kamar zaka tashe gidan nan da magana?” Ya sauke numfashi "Hafsat..." Ya faɗa cikin murya mai cike da gargaɗi "Ki ji da kyau. Daga yau..." "Kar ki sake ɗaga hannu ki mari min Zahra. Ba ki da wannan right ɗin, Idan ta yi laifi, ni ne mahaifinta, nine zan mata magana. Ko Khadija da ta haife ta, ba ta taɓa marin yarinyar ba. Ballantana ke. Mummy ta buɗe baki tana kallonsa cike da mugun mamaki Kafin ta samu damar cewa komai, ya ci gaba. "Kuma idan akwai abin da bai yi miki ba, ki zo ki same ni. Ba zan taɓa yarda kina sauke fushinki a kan yarinya ba." Ya juya zai fita Sai ta yi saurin cewa, "Alhaji!" Bai waiwaya ba. "Kada ki kuskura ki sake taba min ‘ya" Shi kaɗai ya faɗa. Daga nan ya buɗe ƙofar ya fita Mummy ta tsaya a wurin bakin a buɗe Har Batoul da ke gefenta, kasa cewa komai ta yi Mummy ta tsaya tana kallon ƙofar da ya fita, fuskarta dai har sannan cike take da mamaki Batoul ta taɓe baki tana girgiza kai. "Tabdijam!" Ta faɗa cikin takaici "Wato saboda an taɓo 'yar goal din nan ne, sai ya shigo yana ta bambami babu kakkautawa." Ta ƙarasa zama bakin gado. "Wallahi Mummy, ni ban taɓa ganin irin son da yake wa Zahra ba. Kamar ba mu ba ne 'ya'yansa, Anya haka aka barsa kuwa?” Mummy ta yi shiru na ɗan lokaci. Sai kuma wani mugun murmushi ya bayyana a gefen bakinta. Ta yi wata 'yar dariya a hankali "Hmm..." Ta furta. "Sannu a hankali." Batoul ta kalleta. "Mummy what...?" Ta ɗaga kanta tana kallon Batoul "Na ce ki kwantar da hankalinki kawai” Ta faɗa cikin kwantar mata da murya. "Zan yi maganin shegu." Batoul ta yi murmushi. "Da gaske?" Mummy ta gyara zamanta. "Eh." "Wai kina ganin zan zuba ido ina kallon yadda kullum ake ɗora Zahra a kan gaba ne, bar ke da kike babba?" Batoul ta girgiza kai. "A'a." Mummy ta ci gaba. "Ki bar komai a hannuna.Lokaci bai yi ba ne kawai." "Amma zan tabbatar na sauke ta daga wannan matsayin da take ganin ta kai." Batoul ta fara murmushi cike da jin daɗi. "Na san Mummy ba za ki taɓa bari ta fi ni ba." Mummy ta shafa kanta. "Ke ce kawai nake gani naji dadi. Ba zan taɓa bari wani ya zo ya karɓe miki matsayinki ba” Batoul ta jingina da ita tana murmushi. A zuciyarta kuwa... ta ji kamar ta samu nutsuwa, domin ta san mahaifiyarta ba za ta taɓa bari Zahra ta rayu cikin kwanciyar hankali ba. Washegari tun da sassafe Zahra ta shirya cikin tsaftatacciyar uniform ɗinta. White shirt ɗinta ta shiga jikinta fes, black skirt ɗinta kuwa ya ƙara fito da tsayinta, yayin da ta ɗaure gashinta cikin ponytail mai kyau Da schoolbag ɗinta a hannu ta sauko ƙasa. A dining ta tarar da Abbah, Mami da Ya Umar, Mummy da Batoul suna jiran ta "Good morning my loves” Ta faɗa tana murmushi. "Morning, Baby” Abbah ya amsa yana nuna mata kujera. Ta zauna suka fara breakfast cikin nishaɗi, sai dai Mummy da Batoul ko kallonta ba su yi ba Bayan sun gama, ta fita tare da Abbah Driver ya buɗe musu motar. Ya Umar ya kalli Abbah. "Abbah, bari ni na sauke ta." Abbah ya girgiza kai. "No." Ya buɗe ƙofar motar. "Today she's going with me." Ya Umar ya yi murmushi kawai. "Alright, Abbah." Cikin ƴan mintuna suka isa makarantar. Da motar ta tsaya a harabar makarantar, Zahra ta juya tana kallon Abbah. "Thank you, Abbah." Ya yi murmushi. "Study well." "In sha Allah." Ta sauko daga motar. Data shiga harabar makarantar, ɗalibai da dama sai kallonta suke yi, wasu kuwa sai mirmushi suke maga Ita ma cikin mutuntawa take mayar musu ɗaya bayan ɗaya. Da ta isa ajinsu, ta tarar da Asiya, Firdausi da Saudat sun riga sun zo. Bayan sun gaisa, morning class suka fara. Da misalin ƙarfe goma sha ɗaya, wani teacher ne ya shigo ajin bayan sun dawo daga break Bayan ya amsa gaisuwar su, ya ce, "I have an important announcement." Nan take ajin ya yi shiru. "An buɗe registration na WAEC." Ya ci gaba. "Duk wanda yake son yayi jumping or yake son making trial toh yazo ya magana cos za’a fara registration ne daga yau." Sannan ya yi musu cikakken bayani kan ranar rufewa, kuɗin registration da kuma abubuwan da ake buƙata. Bayan ya gama, ya fita. Lokacin second break ya yi Su Zahra suka nufi wani wajen zama a harabar makarantar. Firdausi ta fara magana. "Ni kam zanyi a SS2, idan na gama secondary kuma ‘Kasu’ zan tafi” Suhaima, wacce mahaifinta mai hali ne, ta yi murmushi. "Ni ma NILE zan yi." Saudat kuwa ta sauke kanta. "Ni kam... Allah ne kawai ya Sani, amma bana jin zan cigaba” Ta faɗa cikin sanyin murya. "Ko wannan karatun da nake yi yanzu ma iyayena dakyar suke iya sponsoring PTA Dina” Tayi shiru Zahra ta kalleta da tausayi, Firdausi ta ce “ke fah zahra” Ta ɗan yi murmushi "Sai na tambayi Abbah." Asiya ta yi dariya. "Yar Abbah." Duk suka yi dariya. Firdausi ta ce, "Ai Zahra, ke ba ki da matsala. Duk inda kika ce kina so, nan za a kai ki." Zahra ta yi murmushi. "Ina ji ni ma... maybe KASU zan taho tare da ku, bana son bond din nan ya rabu” Firdausi tace "Wallahi fah, ko Duk mu tafi ABU zaria please” Da haka break ya ƙare. Suka koma aji domin ci gaba da karatu Bayan wasu awanni aka tashi. Yau Ya Umar ne ya zo ɗaukar Zahra. Tana shiga mota ta gaishe sa Ya amsa yana tayar da motar. Suna cikin tafiya ne, idanun Zahra suka sauka kan wani babban eatery. Da sauri ta juya tana kallon Ya Umar. "Yaya..." "Na'am?" "Please ka tsaya." Ba tare da ya tambayi dalili ba, ya rage gudun motar. Sannan ya yi parking a gefen eatery ɗin. Ya Umar ya juya yana kallonta. Daidai lokacin Zahra ta marairaice fuska kamar wata ƙarama, tana turo baki gaba. Sai ta ɗaga hannunta tana nuna wani babban eatery da ke gefen titi din "Please, Yaya..." Ta kira cikin shagwaɓa. Ya ɗaga gira. "Na'am?" Ta yi murmushi. "Ka siya min ice cream da shawarma." Ya ɗan kalleta na wasu daƙiƙu sannan ya yi murmushi. "Da kuma me?" Ta girgiza kai da sauri. "That's all." Ya gyada kai yana dariya. "Consider it done." Ya kashe motar, ya buɗe ƙofa sannan ya sauka. Kai tsaye ya shiga eatery ɗin. Bayan ɗan lokaci ya fito ɗauke da leda mai ɗauke da shawarma da ice cream. Ya buɗe ƙofar motar ya miƙa mata. "Thank you, Yaya." Ta faɗa tana wani irin murmushi mai nuna farin ciki. Ya girgiza kai kawai, ya koma mazauninsa, ya tada motar suka ci gaba da tafiya. Bayan sun isa gida, mai gadi ya buɗe musu gate suka shiga. Ta fito daga motar, Zahra na rungume da ledar hannunta tamkar wani zai kwace mata. Ta shiga parlon tana murmushi. Mami na zaune tana duba wasu takardu, Abbah kuma yana zaune kusa da ita. Da ta ganta, Mami ta ce, "Zahra, je ki cire uniform ɗinki, ki yi wanka sannan ki zo ki ci abinci, sabon mu’allim dinki na hanya” Zahra ta yi dariya tana girgiza kai. "Mami, count me out." Ta ɗaga ledar hannunta. "Yaya ya saya min shawarma da ice cream." Mami ta ɗago ta kalli Ya Umar da shigowarsa kenan. Ta girgiza kai tana murmushi. "Ya Umar, ka ci gaba da biyewa Zahra haka. Zata ƙarasar maka da kuɗi." Ya Umar ya zauna yana dariya. "Ai kuɗina nata ne." "Na ta kuma nata ne." Sai ya ɗan dakata yana kallon Mami da wasa. "Shi ya sa ma ko na yi aure..zan ɗauke ta mu tafi tare." Zahra ta kwashe da dariya. Ta juya ta yi wa Mami gwalo. "Kinga ko!" Mami ta nuna ta da yatsa. "Ke! Zo nan." Amma kafin ta ƙarasa maganar, Zahra ta juya da gudu tana dariya, ta nufi matakala. Ya Umar ya bi bayanta da kallo, ya fashe da dariya. Abbah ya girgiza kai yana murmushi. "Ku biyu kam... Allah kaɗai ya san ranar da za ku daina wannan shirmen. Ko ganina ma bata yi ba” Murmushi kawai Ya Umar yayi Abbah ya ce “Allah muku albarka ya raya min ku” Chapter 34 Da daddare, kamar yadda aka saba, kowa ya hallara a dining domin cin abincin dare. Abbah na kan kujerarsa ta gado, Mami na gefensa, Ya Umar kuwa na gefen Zahra. A ɗaya ɓangaren kuma Mummy da Batoul ne suke zaune. Ana cikin cin abinci ne Zahra ta ɗaga kai ta kalli Abbah. "Abbah..." Ya ɗago yana kallonta. "Na'am, Baby." Ta ɗan yi murmushi. "Yau ba? an yi mana announcement a school, an ce an buɗe registration na WAEC, NECO da JAMB ga waɗanda suke son yin jumping." Ta ɗan dakata tana kallon reaction dinsa "Abbah... ni ina so na yi making trial." Lokaci guda Mummy ta ɗago ta watsa mata wani irin kallo. Batoul ma ta taɓe baki tana kallonta. Abbah ya ajiye cokalin hannunsa. "Why do you want to skip SS3, Zahra? You want to write paper in SS2 instead ?” Zahra ta ɗan yi frowning face, tana murza cokalin hannunta. Kafin ta samu damar amsawa, Ya Umar ya yi saurin cewa, "Abbah, ai Zahra tana da ƙoƙari” Ya yi murmushi yana kallon ƙanwarsa. "Ka barta mana ta yi making trial. Ko da ba ta ci ba, experience ne. Though bamu fatan haka” Abbah ya yi shiru na ɗan lokaci, sai ya gyada kai "Okay." Ya kalli Zahra "Since kina so... Gobe Ya Umar zai raka ki makarantar ya yi miki registration na komai” Fuskar Zahra ta cika da annuri "Thank you, Abbah naa” Mami ta ɗan kalleta cikin kulawa. "Zahra... ba ki yi ƙarama ba?" Zahra ta girgiza kai da sauri "A'a Mami Ina so." Abbah ya yi murmushi. "Tunda ita tana so, babu wanda zai hana ta." Nan take Mummy ta yi ƙwafa. "Amma ai kuna gani, a gidan nan babu wanda ya taɓa yin jumping sai ita." Abbah ya juya ya kalleta "Lokacin da 'ya'yanki suke secondary... kin taɓa nuna musu cewa ni ne ubansu?" Mummy ta ɗan cije baki. Abbah ya ci gaba da magana. "Har gwara Umar shi a ɓoye yana zuwa wajena har daga baya ya dawo gaba daya amma ita...” Ya nuna Batoul da kansa "Har yau ba ta ɗauke ni a matsayin uba ba. Duk saboda abin da kika cusa mata tun tana ƙarama." Dining ya yi tsit. Ya ci gaba da cewa, "Shi ya sa na mayar da hankalina kan waɗanda suka ba ni dama na kusance su." Ya sauke numfashi. "Ban san manufarki ba. Maybe akwai wani dalili da ya sa kika raba ta da ni” Mummy ta zaro ido. "Ban gane ba. Zargina kake yi?" Abbah ya kalleta cikin nutsuwa. "Duk yadda kika ɗauka... toh hakan ne." Nan take ta buga tebur da hannu. "Alhaji!" Ta kira cikin fushi "Wannan ai zargi ne kai tsaye." Abbah bai ko motsa ba. Ya ci gaba da kallonta cikin ƙanƙanin lokaci, sai ya ce da murya mai nauyi, "Hafsat..." "Kar ki sa mu yi cacan baki a gaban yara. Saboda idan ba haka ba... wallahi za ki sha mamakina da kuma abun da zai fito daga baki na Wanda ke Baki san na sani ba” Muryarsa ta fito cike da izza da gargaɗi Nan take Mummy ta yi shiru Batoul ta sauke kanta ƙasa. Ya Umar kuwa ya saki numfashi a hankali. Zahra da Mami suka kalli juna na ɗan lokaci, domin sun fahimci wannan shi ne karo na farko da Abbah ya fito fili yana ƙalubalantar Mummy a gaban kowa, dan Abbah mutum ne me son yara Da suka gama cin abincin, Zahra ta goge bakinta da tissue sannan ta miƙe tsaye. Abbah ya ɗago yana kallonta. "Baby." Ta juyo tana murmushi "Na'am, Abbah." Ya miƙa hannu ya shafa kanta cikin kulawa irin ta uba. "Kar ki manta idan kin shiga ɗaki ki yi alwalar barci." Ta gyada kai "In Sha Allah." Ya ci gaba. "Ki yi addu'o'in barci, sannan ki karanta Suratul Mulk kafin ki kwanta." Murmushi ta yi. "In Sha Allah, Abbah." "Good girl." Ta matsa kusa da Ya Umar. Kafin ya ce komai, ya jawo ta kusa da shi ya yi kissing goshintanta "Good luck, little professor." Ta yi dariya Sai ta sunkuya ta rada masa wani abu a kunne. Nan take Ya Umar ya fashe da dariya. "Wallahi kina da matsala." Ita ma ta yi dariya tana girgiza kai. Mummy ta bi su da wani irin kallo. Da ace kallo na kashe mutum, da tuni su biyun sun mutu sbd irin kaifin kallon da take musu Zahra ta ƙarasa wajen Mami. Ta yi kissing kumatunta. "Good night, Mami." Mami ta shafa mata baya. "Allah ya tashe mu Lafiya, ya kuma miki albarka" "Ameen." Daga nan ta sake komawa wajen Abbah. Ta rungume shi ta baya, ta ɗora haɓarta a kafaɗarsa. "Good night, my Abbah." Abbah ya riƙe hannayenta yana murmushi. "Good night, Baby. Allah ya tsare min ke." "Ameen." Ta sake rungume shi na ɗan lokaci kafin ta sake shi. Daga nan ta juya ta nufi matakala tana ɗan tsalle-tsalle har ta ɓace daga ganin su. Mami ma ta miƙe. "Bari na shiga” Ta faɗa tana kallon Abbah. Ta nufin ɗakinsa domin ta gyara masa ko ina tare da kunna turaren wuta kamar yadda ta saba yi masa kowace dare. Ya Umar kuwa da sauri ya miƙe, ya san yanzu idan Abbah ya bar wajen, toh tabbas ya banunsa a wajen Mummy Ya ƙarasa kusa da shi. "Good night, Abbah." Abbah ya gyada kai. "Allah ya tashe mu lafiya." "Ameen." Ya amsa, sai kuma ya juya yana kallon Mummy wacca ta cika take basewa ya sunkuyar da Kansa kasa ya ce a hankali “Mummy, good night” Ta dago ta watsa masa wani banzan kallko Yayi saurin dauke kansa daga nan ya juya ya wuce sama. Da Zahra ta shiga ɗakinta, ta ajiye system ɗinta gefe Ta cire kayan jikinta, ta saka sleeping wear mai launin pink. Kai tsaye ta shiga toilet, ta yi alwalar barci cikin nutsuwa. Da ta fito, ta shimfiɗa sallaya tayi shafa’i da witr kamar yadda Mami ta Saba mata, Tana idarwa Ta yi addu'o'in da ta saba yi kafin kwanciya Bayan ta gama, ta ɗauki Al-Qur'ani. A hankali ta fara karanta Suratul Mulk kamar yadda Abbah ya umarce ta. Da ta kammala, ta ɗaga hannayenta sama. Ta yi addu'a ga iyayenta, Ya Umar, Mami da kuma dukkan muslumai Sai ta tofa addu'ar a tafukan hannunta ta shafa a jikinta. Ta koma kan gado, ta kashe fitilar ɗakin. Ta kwanta tana murmushi. Ta lumshe idanunta. Cikin ƴan daƙiƙu kaɗan... Barci mai daɗi ya ɗauke ta. Washegari tun da sassafe, bayan sun gama breakfast kamar yadda suka saba, Zahra ta fito ɗauke da school bag ɗinta, yayin da Ya Umar ya jingina da motarsa yana jiran fitowarta. Da ta ƙaraso, ya buɗe mata front seat. “Princess.” Ya faɗa yana murmushi. Ta yi dariya. “Thank you, Yaya.” Ta shiga ya rufe mata ƙofar sannan shi ma ya shiga ya tada motar. A hanya Zahra ta riƙa ba shi labarin test ɗin da suka yi makon da ya gabata da kuma yadda take sa ran za ta ci su dukka Ya Umar yana saurarenta lokaci-lokaci yana jinjina kai. “Kin yi karatu kuwa?” Ya tambaya. Ta taɓe baki “Yaya kenan, ai ka san ni.” Ya yi dariya. “Na sani. Amma WAEC, NECO da JAMB ba wasan yara ba ne, ba wai Baki karatu bane just that zaki sake dagewa ne” Ta gyada kai. “Shi ya sa nake son in gwada tun yanzu.” Ya yi murmushi cikin jin daɗin yadda take da himma. Da suka isa makarantar, tare suka fita daga motar, ya bi bayanta suka shiga admin block. A reception suka tarar da wasu iyaye da ɗalibai suma sun zo saboda registration. Bayan sun jira na ɗan lokaci, aka kira su ciki. Class mistress ɗinta ta yi murmushi da ganin Zahra. “Oh, Zahra! So you’ve finally decided?” Zahra ta gyada kai. “Yes, Ma.” Ta juya ta nuna Ya Umar. “My elder brother.” Ya Umar ya gaishe ta cikin girmamawa. Ta amsa tana murmushi. Nan ta yi musu bayanin abubuwan da ake buƙata. Ya Umar ya karɓi form ɗin registration ya zauna yana cikewa cikin nutsuwa, Inda bai gane ba sai ya tambayi Zahra. Da ya gama, ya miƙa mata, ta duba komai. “Everything is correct.” Ta nuna cashier. Ya Umar ya nufi cashier ya biya kuɗin registration ba tare da wata-wata ba. Bayan an ba shi receipt, aka sake ba su wasu takardu da za a adana. Class mistress ta ce, “Ki tabbatar kin ƙara dagewa da karatu Zahra, na san wacece ke, but ki sake d’aura d’ammara’’ Zahra ta gyada kai. “I’ll do my best, Ma.” Ta yi murmushi. “I know you will.” Da suka fito daga office ɗin, Ya Umar ya miƙa mata envelope ɗin. “Ki riƙe shi da kyau, kar naje na bar miki shi a offic Ta karɓa tana murmushi. “Thank you, Yaya.” Ya shafa kanta. “Abin da nake so da ke kawai shi ne ki yi iya ƙoƙarinki, don’t stress yourself too much” Zahra ta yi murmushi mai cike da kwarin gwiwa “In shaa Allah.” Ya raka ta har ƙofar ajinsu.Kafin ya juya zai tafi, ya ce, “Zan karaso In shaa Allah kafin ku tashi” “Okay, Yaya.” Ta yi masa waving da hannu. Shi ma ya daga mata hannu yana murmushi kafin ya juya ya fita daga harabar makarantar. Zahra ta tsaya tana kallonsa har sai da motarsa ta ɓace daga ganinta, sannan ta yi murmushi ta shiga aji, tana jin wata sabuwar ƙwarin gwiwa ta cika zuciyarta, zata bawa Abbah mamaki wannan karon ma… Da aka tashi daga makaranta, Zahra ta fito tana tafiya a hankali. Ko daga kallonta ka san ta gaji matuƙa Registration, classes da test ɗin da suka yi sun ɗauke mata ƙarfi tass haka take ji Da Ya Umar ya zo ɗaukarta ma, ko magana sosai ba ta yi ba, kamar yadda ta saba cikasa da surutu. Ta jingina da seat tana kallon titi ta window, lokaci-lokaci idanunta na lumshewa saboda gajiya. Ya Umar ya kalleta yana murmushi “Exhausted?” Ta ɗan buɗe ido “So much.” Ya girgiza kai. “Kin ce kina son jumping, a haka ne zaki fara university Baki son stress?” Ta taɓe baki “Na sani… amma ban yi tunanin zai gajiyar da ni haka ba.” Ya yi dariya “Wannan fa farkonsa ne.” Da suka isa gida, Zahra ta sauko daga motar tana jan ƙafafunta a hankali. Tana shiga parlour, kai tsaye ta nufi inda Abbah yake zaune yana karanta wasu files. Ko kula da Mummy bata ma yi ba Ba tare da ta ce komai ba ta zauna a gefensa, ta jingina da kafaɗarsa. Abbah ya ajiye files ɗin yana kallonta. “My Baby… Ya school?” Ta sauke ajiyar zuciya. “Alhamdulillah.” Sai ta fara ba shi labarin komai dalla-dalla. Yadda registration ya kasance, yadda aka cika forms, yadda class mistress ta yi musu nasiha, da kuma yadda malamai suka ce rubuta paper ba abu ne mai sauƙi ba. Abbah yana saurarenta yana gyada kai lokaci-lokaci. Da ta gama, ya yi murmushi “I’m proud of you.” Ta yi dariya. “Thank you, Abbah.” Sai ta ɗan matsa kusa da shi. “Abbah…” “Hmm?” Ta ɗan marairaice fuska. “Please… Ka siya min waya mana” Ya Umar da ke zaune kusa da su ya yi saurin cewa, “Wannan dai kin dan responsibility nane ko?” Mummy ta ɗaga kai ta watsa masa wani irin kallo. Karaf Ya Umar idanunsa ya fada cikin nata wanda shima bai yi noticing ba Ya Umar ya haɗiye sauran maganar da zai yi. Sai ya yi saurin ɗaukar remote. “Abbah… wai match ɗin Arsenal yaushe ne?” Abbah ya ɗan kalle shi, ya san sarai dalilin canja maganar, amma bai ce komai ba. Sai ya juya wajen Zahra. “Waya ba za ta gudu ba.Ki fara mayar da hankalinki kan karatu. Ki nuna min cewa kin shirya wannan jumping ɗin. In sha Allah, idan lokaci ya yi, zan saya miki wadda za ki so. Kai ba waya ba ko duniya kike so idan Ina da shi Zahra ni me baki ne” Fuskar Zahra ta sake, ta yi murmushi. “Promise?” Ya ɗan ja hancinta. “Promise.” Ta yi dariya “Thank you, Abbah.” Can da yamma, Duk suna zaune, Mami Tana mamakin yawan ganin Mami a parlon na kwana biyu, amma bata cr komai ba, game take bugawa a wayanta Mummy ta zauna tana latsa wayarta itama amma sauran ba wanda ya kula da ita Sai dai fuskarta ta nuna ba ta cikin nutsuwa, ta buɗe WhatsApp Wani sabon saƙo ya shigo, ta duba sunan wanda ya aiko… Nan take murmushin da bata shirya yin sa bane ya bayyana a fuskanta, ta ɗan waiwaya ta tabbatar babu mai kallonta Sai ta buɗe saƙon. Da ta karanta layi na farko… Murmushinta ya ɓace gaba ɗaya, fuskarta ta sauya. Ta ɗaga kai a hankali ta kalli Zahra da ke dariya tare da Abbah. Sai ta sake kallon wayarta, ta matse ta da ƙarfi a hannunta… A hankali ta furta cikin ƙasa-ƙasa, “Fuck you…” “Wannan ai shirme ne, Abu daban ace kuyi daban?…” Sai ta kashe screen ɗin wayar, ta miƙe ba tare da ta ce wa kowa komai ba, ta nufi ɗakinta Mami ta d’aga kanta ta bita sa kallo sai kuma ta girgiza Kai kawai ta cigaba da game dinta #FARASHIN IZZAH 08110615256 Chapter 35 Rayuwa haka ta cigaba da tafiya Kwanaki suka zama makonni, makonni suka rikide zuwa watanni. Tun bayan registration ɗin da Zahra ta yi na WAEC, NECO da JAMB, gaba ɗaya rayuwarta ta sauya Duk wanda ya san Zahra tun farko zai fahimci canjin da aka samu a tattare da ita Ba wai saboda ta daina dariya ko wasa ba… A’a. Sai dai yanzu tana da manufar da take son cimma Kullum idan aka tashi daga makaranta, kai tsaye gida take dawowa. Da zarar ta ci abinci ta yi sallah, sai ta ɗauki littattafanta ta nufi garden ɗin gidan, wajen ya zama tamkar classroom ɗinta. Ƙarƙashin wata babbar bishiya mai yalwar inuwa aka tanadar mata tebur da kujera. A kan teburin akwai littattafan Mathematics, English, Physics, Chemistry, Biology, Government da sauran subjects ɗinta, kowanne a jere tamkar ƙaramin library. Sau da yawa idan mutum ya zo wuce wa ta wajen, zai same ta ne ta sunkuyar da kanta ne tana karatu, ko kuma tana rubuce-rubuce a wani jotter. Har housemaids sun saba, da zarar lokacin cin abinci ya yi, zasu je su same ta “Baby, Mami tace ki zo ki ci abinci.” Sai ta ɗaga kai da ƙyar. “Ku aje mana please, idan na shigo zan ci” Da farko Mami na matsa mata ta shiga ciki, daga baya ta haƙura Ta fahimci Zahra idan ta sa abu da zuciya, sai ta gama shi ake gane kanta Wata rana da yamma… Abbah ya fito daga office dinsa na gidan a gajiye, yana shiga compound idanunsa suka sauka kan garden, can ƙarƙashin bishiya ya hango Zahra Ba ta ma san ya shigo ba. Headset na kunne, biro na hannunta, calculators biyu a gefe, papers cike da calculations sun warwatse a gabanta Abbah ya tsaya daga nesa yana kallonta Murmushi ya bayyana a fuskarsa. “Ya Allah ka albarkaci iliminta ka ma rayuwarta albarka” Ya furta a hankali. Bai ƙarasa wajenta ba, ya juya ya shiga main entrance din A dining da daddare bayan suna cin abinci Abbah ya kalli Zahra. “Baby.” Ta ɗago. “Na’am?” “Yaushe kika huta?” Ta yi dariya. “Ban huta ba, tukun” Ya ɗaga gira “Meaning?” “Karatu nake yi.” Mami ta girgiza kai “Wallahi Zahra kin fara bani tsoro, ko yaushe kina garden, akwai gajiya fah, ki dinga hutawa mana.” Zahra ta yi murmushi. “Da zarar na gama exams ɗina zan huta sosai.” Ya Umar ya yi dariya. “Abbah.” Ya kira. “Ina ganin idan Baby ta ci gaba haka, a gaba za’a ga amfanin hakan saboda ta Riga da ta Saba da hakan, dole ta yi passing.” Abbah ya yi murmushi. “In Sha Allah.” Murmushi kawai tayi ta cigaba da cin abincinta Lokaci bai tsaya ba WAEC ta zo, Jarabawar farko… English Language. Tun ƙarfe shida na safe Zahra ta riga ta shirya Abbah da kansa ya raka ta makaranta Kafin ta sauka daga mota ya riƙe hannunta. “Nervous?” Ta yi murmushi. “A little.” Ya shafa kanta “Ki shiga, ki rubuta abin da kika sani kada ki ji tsoro, and make sure ki fara da addu’a” Ta gyada kai. “In Sha Allah.” Haka jarabawa ta ci gaba Paper bayan paper. Ko da yaushe idan ta dawo gida, ba za ta fara hutawa ba sai ta fara duba subject na gobe Wata rana Ya Umar ya ce, “Baby…” Ta ɗago. “Hmm?” “Kin san akwai rayuwa bayan exam ko?” Ta yi dariya “Ina so ne in gama da wannan” Ya girgiza kai yana murmushi “Perfectionist.” Da suka gama WAEC… Ba a jima ba NECO ta biyo baya. Shi ma cikin ƙoƙari da addu’o’in iyayenta ta kammala. Ga JAMB data yi Wannan ne ya fi ɗaukar hankalin kowa a gidan Abbah da kansa ya samo mata teachers na musamman da suke zuwa gida suna yi mata revision. Ko Mummy ta yi mamakin yadda yake kashe kuɗi saboda ita. Sai dai ba ta ce komai ba Domin duk lokacin da ta yi magana, Abbah ba ya sauraronta indai Akan Zahra ne Ranar JAMB Tun safe Zahra ta shirya, bayan ta gama Duk addu’o’in da zata yi ta zauna jiran Abbah. Abbah ya raka ta CBT centre. Kafin ta shiga ya ce, “Ki tuna da abin da kika karanta. Kar ki yi rushing. Ki karanta question sau biyu so that ki fahimci me ake cewa” Ta yi murmushi. “Yes, Sir.” Ya yi dariya. “Good.” Ta shiga. Sa’o’i biyu da rabi bayan haka.. ta fito. Tun daga nesa Abbah ya gane ta, ya buɗe mata ƙofar mota tana murmushi harta karaso “How was it?” Ta ɗan daga ido sama kamar mai tunani tace “Alhamdulillah! Ai Abbah In shaa Allah result din zai yi kyau Abbah ya yi murmushi. “In shaa Allah” Bayan kwana biyu ne aka fara bude results din JAMB Ranan kuma suna makaranta suna wani extra lesson, tun safe makarantar gaba ɗaya t cika da hayaniya, kowa na dubawa. Wasu na ihu, wasu kuma fuskokinsu cike da damuwa Zahra na zaune cikin classroom ɗinsu, ba kasafai take shiga cikin mutane ba shiyasa idan ba wai Tana tare da friends bane a compound toh zaka same ta ne a class Firdausi ta shigo da gudu. “Zahra!” Ta kira da sauri “Result ya fito!” Zahra ta miƙe tsaye “Da gaske?” “Wallahi.” Mika mata wayan wata Teacher tayi ta ce “Karba ki duba” Zahra ta karba ba tare data ce komai ba. Hannunta ya fara rawa yayin da ta shiga portal ɗinta, password ta saka Registration number. Ta latsa check. Na ɗan daƙiƙu kaɗan… Screen ɗin ya buɗe Idanunta suka sauka kan total score. 250 Ta zaro ido. Firdausi ta yi ƙara “Allahuu Akbar!” Asiya ta rungume ta. “Congratulations! My love” Ko Saudat ta yi murmushi. “Alhamdulillah, Congrats Teema” Zahra ta kasa magana Har sannan idanunta na kan screen. 250… Ba mafarki take yi ba. Firdausi ta girgiza ta. “Ke! Wai kina jin mu kuwa?” Nan take Zahra ta fashe da kuka Ta rungume su ɗaya bayan ɗaya. “Alhamdulillah…” Shi kaɗai take ta maimaitawa Da aka tashi makaranta taje wajen mistress dinsu ta karba waya Abbah ta fara kira bai ɗauka ba. Sai Ya Umar ya ɗauka. “Baby.” “Yaya!” Ta faɗa cikin murna. “I got 250!” Shiru ya yi na daƙiƙa guda. Sai ya yi wani irin ihu. “What?! 250?!” Ta yi dariya. “Yes!” Ya Umar ya yi murmushi har kunne. “Baby… I’m so proud of you, driver zai zo daukan ki yanzu. Abbah zai yi murna fiye da yadda kike zato.” Zahra ta kashe wayar tana murmushi… A haka har driver yazo ya dauke ta. Tun daga bakin gate take ta murmushi ita kaɗai. Driver ya buɗe mata ƙofa, ta fito da sauri tana rungume da handbag ɗinta. Da shiga parlour… “Abbah!” Ta kira da ƙarfi cikin farin ciki. Abbah da ke zaune yana duba wasu takardu ya ɗago kai. Kafin ya ce komai, Zahra ta ƙarasa ta rungume shi. “Alhamdulillah, Abbah!” Ya rungume ta yana murmushi. “Congratulations, Baby.” Ta ɗago tana kallonsa cikin mamaki. “Kun sani?” Ya yi dariya. “Ya Umar ya riga ya kira ni.” “250…” Ya girgiza kai cike da alfahari. “I’m proud of you.” Ta ce “Kash Ya Umar daya daka bari na fara fada ai” dariya kawai Abbah yayi Mami ma ta miƙe ta rungume ta. “Allah ya ƙara basira. Allah sa matakin nasara ne” “Ameen, Mami.” Ya Umar kuwa yana jingine da bango yana tafa hannu. “Baby ta yi mana abin kirki.” Batoul ta taɓe baki ta kalli gefe. Mummy kuwa… Tun farkon shigowarta take kallon Zahra ba tare da ta daga ido Akan ta ba Abbah ya miƙe tsaye. “Baby.” Ta ɗago. “Ina da wani abu a gare ki.” Ta yi mamaki. “Na me?” Ya yi murmushi. “Ki je ki buɗe drawer ɗin office na Ta ɗan haɗe gira. “Office? Abba?” “Yes. Ki dauko box din cikin” Ta nufi office ɗinsa da sauri. Da ta buɗe drawer ɗin… Wani farin akwati mai ɗauke da tambarin Apple ne ya bayyana Ta tsaya cak. Hannunta ya kai a hankali ya ɗauke shi Bugun zuciyarta ya ƙaru. Ta buɗe… Sabuwar iPhone ce, sabuwar fita. Har yanzu tana cikin wrapping ɗinta. Zahra ta zaro ido. “Abbah…” Ta fito da gudu daga office ɗin. “Abbah!” Ta kira tana dariya. “Mine?” Abbah ya gyada kai yana kallonta cikin ƙauna. “Yours.” “Congratulations!!! Wannan kyautarki ce saboda ƙoƙarin da kika yi.” Zahra ta yi ihu. Ta sake rungume shi da ƙarfi. “Thank you, Abbah! Thank you so much.” Ta yi ta kissing goshinsa kamar yadda ta koya mata Abbah yana dariya. “Easy, Baby. Za ki karya min ƙashi.” Parlour gaba ɗaya dariya ake yi. Sai dai… Mummy da Baroul, Wanda yanzu yabi jinin jikin su duk sanda su Mami suka fito suma sai su zo suga abun dake faruwa GTa kalli wayar Ta sake kallon Zahra Sannan ta kalli Abbah. “Alhaji.” Ta kira cikin sanyi Ya amsa. “Hmm?” “Wato saboda ta ci JAMB ne za ka siya mata wayar da ko manya ba su da ita?” Abbah ya kalleta. “Eh.” Ta yi wata ƙaramar dariya. “Toh! Ni dai ban ga abin burgewa ba 250 ɗin nan ai ba ita kaɗai ta ci ba.” Zahra ta sauke kanta ƙasa. MMurmushin da ke fuskarta ya ɗan ragu. Abbah ya ɗan yi shiru Sai ya kalli Mummy kai tsaye. “Hafsat…” Muryarsa ta sauya. “Shame on you.” Parlour ya yi tsit. Ya ci gaba “Kina kishi da ’yar cikinki?” Ya girgiza kai cikin takaici “Wallahi ban taɓa tunanin haka daga gare ki ba.” Mummy ta buɗe baki. “Kishi?” Abbah ya katse ta “Yes…. Kuma abin kunya ne a gareki Yarinya ta yi abin kirki, maimakon ki ƙarfafa mata gwiwa… amma kina neman yadda za ki kashe mata farin ciki.” Mami ta sauke ajiyar zuciya Ya Umar kuwa ya yi shiru kawai yana kallon wani waje Mummy ta miƙe tsaye “Ku ci gaba.” Ta faɗa cikin fushi Sannan ta fice daga wajen Tana fita… Zahra ta sake murmushi Ta buɗe wayar tana kallonta tamkar mafarki “Abbah…” Ta faɗa a hankali “So Beautiful.” Ya yi dariya. “Kin so kenan?” “So?” Ta rungume wayar a ƙirjinta. “I love it.” Ranan wani Saturday da yamma Ya Umar ya tafi garden Ya tarar da Zahra tana ta solving Mathematics Har ta manta da lokaci ya tafi Ya tsaya yana kallonta na wasu daƙiƙu, sai ya ƙarasa. “Baby.” Ta ɗago kai. “Yaya.” Ya zauna kusa da ita “Kin gama da sabon duniyar naki ne?” Ta yi dariya “Almost.” Ya ciro envelope daga aljihunsa ya miƙa mata. “Take.” Ta karɓa Da ta buɗe… Idanunta suka faɗa kan check din kudin “Two hundred thousand?” Ta zaro ido tana kallonsa “Yaya?” Ya jingina da kujera “Yes.” “Na me?” Ta tambaya Ya yi murmushi. “Tomorrow…” Ki je solo date.” Ta haɗe gira “Solo date?” “Eh! Kina stressing kanki sosai.” “Ki fita, ki ci abin da kike so, ki yi shopping idan kina so, ki huta. Then ki dawo.” Zahra ta yi dariya, ta matsa ta rungume shi “Thank you! Allah ya saka da alkhairi.” Ya shafa kanta. “Ameen.” “Amma fa… Kar ki kashe duka dan na sanki” Ta yi dariya sosai “No promises, dan ka san wacece Zahratyy” Su biyun suka fashe da dariya. Washegari… Tun da sassafe Zahra ta farka cikin farin ciki Bayan ta idar da sallar Asuba, ta zauna kan sallayarta tana karanta morning zikr ɗinta cikin nutsuwa. Ta ɗauki lokaci tana zikiri da addu’o’i, kafin daga bisani ta shafa addu’ar, ta naɗe sallayar ta ajiye a mazauninta. Ta miƙe ta nufi balcony ɗin ɗakin. Ta ɗan buɗe labulen gilashin, hasken safiya ya shigo yana gauraye da hasken dakin, ga AC mai dadi da ƙamshin diffuser da ke ci gaba da fitar da ƙamshi cikin ɗakin Tana tsaye tana kallon lambun gidan ne aka yi knocking sau uku a hankali. “Come in.” Ƙofar ta buɗe ba tare da hayaniya ba. Mai aikin gidan ta shigo cikin uniform mai kyau da safar hannu, tana jan ƙaramin cleaning trolley da ke ɗauke da kayan gyaran ɗakin. “Assalamu alaikum, Hajiya.” “Wa’alaikumus salam.” Zahra ta amsa ba tare da ta juyo ba. “Fatan mun tashi Lafiya hajiya” “Lafiya lau. Kin tashi lafiya?” “Lafiya ƙalau, Alhamdulillah.” “Good.” Cewar Zahra “Hajiya, zan gyara ɗakin?” “Go ahead.” Zahra ta bata amsa “To, Hajiya.” Ba tare da ɓata lokaci ba ta fara aikinta. Ta fara da gyara king size bed ɗin, ta shimfiɗa duvet ɗin daidai ba tare da ko da ɗan lanƙwasawa ba, ta jera decorative pillows cikin tsari, ta gyara labulen da aka buɗe kaɗan, sannan ta share duk wani ƙurar da ka iya sauka a saman furniture da glass surfaces. Daga nan ta buɗe wardrobe kaɗan, ta ɗauko kayan da aka cire jiya ta kai su laundry basket, sannan ta maye gurbin slippers ɗin da sababbi masu tsafta da aka tanadar. Sai ta ɗauko luxury room mist ta feshe sasanninta kaɗan-kaɗan. Nan take ɗakin ya cika da wani ƙamshi mai sanyaya zuciya, ba mai kaifi ba, irin wanda ake jin daɗinsa Bayan nan ta shiga toilet. Marble floor ɗin ta goge har yana walkiya, ta wanke wash hand basin da toilet bowl, ta goge shower glass ɗin har ya yi kamar babu komai a kansa. Ta canja hand towels da sababbi, ta sake jera toiletries ɗin daidai gwargwado, sannan ta tabbatar fresh flowers da ke kan vanity ba su yi yanƙwane ba. Da ta gama, ta fito ta tsaya cikin ladabi. “Hajiya, na gama.” A wannan lokacin Zahra tana zaune kan armchair tana duba saƙonnin wayarta. Ta ɗaga kai ta bi ɗakin da kallo. Komai ya koma kamar an sake shirya shi ne daga farko. “Very neat. Thank you.” “Babu komai, Hajiya.” “Ki gaya wa Aunty Binta ta tabbatar an shirya min green tea kafin na sauko.” “In shaa Allah, Hajiya.” “Thank you.” Ta ɗan sunkuyar da kai cikin girmamawa, sannan ta ja cleaning trolley ɗinta ta fita, tana rufe ƙofar a hankali ba tare da ta yi ƙara ba. Tana fita, Zahra ta sauke wayarta, ta sake shakar ƙamshin da ya mamaye ɗakin, sannan ta wuce toilet tayi wanka sannan ta fito Ta tsaya gaban wardrobe tana zaɓen kaya. Daga ƙarshe ta fito da wata doguwar gown mai launin sky blue, mai sauƙin kyau amma cike da elegance. Ta haɗa ta da farin veil mai laushi Ƙaramar agogon gold ta ɗaura a hannunta. Ta ɗauki handbag ɗinta. Ta kalli kanta a mirror. Murmushi ta yi. “Not bad.” Ta ɗauki waya ɗinta. Ta sauko ƙasa… Perfume ɗinta mai sanyin ƙamshi ya cika wajen. Mami da ke zaune a parlour ta ɗago ta kalleta. “Allah ya tsare.” “Ameen, Mami.” Ta ƙarasa ta sumbaci goshin Mami. Abbah ya ɗago daga newspaper ɗinsa. “My Baby.” Ta juya tana murmushi. “Yes, Abbah?” “Enjoy yourself.” Ta yi dariya “I will.” Ya Umar ya jefa mata key ɗin motarsa. “Drive safely.” Ta kama key ɗin “Roger that.” Batoul ta bi ta da kallo har ta fita, ta taɓe baki “Kullum princess.” Da fitowarta compound, driver ya yi yunƙurin buɗe mata ƙofa. Ta yi murmushi “No, thank you I’ll drive myself.” Ta shiga motarsa cikin nutsuwa, ta daidaita mirror, ta ɗaura seat belt Ta kunna motar. A hankali ta fita daga gidan A stereo kuwa… Wata soft instrumental nasheed ce ke tashi a hankali. Zahra ta jingina da seat tana tuƙi cikin natsuwa, ko da ta tsaya a traffic light, mutane da dama suna kallonta Ba wai saboda motar ba… Sai saboda yadda take da wata irin nutsuwa da kwarjini gashi dama famous ce, kuma ta sauke glass din dukka Bayan kusan mintuna talatin… Ta isa wani luxury restaurant da take yawan zuwa idan tana son ta huta ita kaɗai Parking ta yi cikin tsari, ta fito daga motar. Tana shiga restaurant ɗin, ɗaya daga cikin staff ɗin ya yi saurin ƙarasowa. “Welcome back, Ma’am.” Ta yi murmushi kaɗan. “Thank you.” “Your usual seat?” Ya tambaya “Yes.” Ta amsa Ya jagorance ta zuwa wani gefen restaurant ɗin da ke kallon glass wall, inda ake iya ganin flowers da fountain na waje. Shi ne wurin da ta fi so, ta zauna. Handbag ɗinta ta ajiye a gefenta, ta cire wayarta, ta ɗan duba Instagram. Sai ta ajiye Ba ta zo social media ba yau, ta zo ne ta huta. Waiter ya ƙaraso. “Your order, Ma’am?” Farashin izzah Hauwajay writes Chapter 36 Ta yi ɗan tunani “One grilled chicken with mashed potatoes… fresh orange juice.. and cheesecake later.” “Certainly, Ma’am.” Ya tafi. Zahra ta jingina da kujera. Idanunta na kallon fountain ɗin da ke waje, wani irin nutsuwa ta sauko mata Ta murmusa ita kaɗai, a ranta ta furta, “Thank you, Allah…” Bayan kusan awa biyu da rabi a restaurant ɗin, Zahra ta gama cin abincinta cikin nutsuwa. Ba ta yi saurin tashi ba. Ta ɗan zauna tana kallon flowers da fountain ɗin da ke waje, tana jin yadda zuciyarta ta samu wani irin natsuwa. “Da gaske Ya Umar ya yi tunani” Ta furta a zuciyarta “Na buƙaci wannan hutun.” Waiter ya dawo da bill. Kafin ma ya ajiye, Zahra ta ciro katinta ta miƙa masa. “Thank you, Ma’am.” Ta yi masa murmushi kaɗan. “You’re welcome.” Ya tafi. Ta ɗauki handbag ɗinta, ta gyara veil ɗinta a jikin mirror da ke kusa da ƙofar fita, sannan ta fice daga restaurant ɗin. Da fitowarta waje… Sanyin iska ya bugi fuskarta. Ta tsaya na ɗan lokaci tana kallon sararin sama. Murmushi ya subuce mata Ba ta tuna rabon da ta samu irin wannan nutsuwar ba Kalle kalle ta fara yi, ganin babu kowa fa wuce inda tayi parking motar, wani securities ta gani Ta miƙa wayarta ga wani security guard da ke bakin parking lot din “Excuse me… Please, can you help me take some pictures?” Mutumin ya amsa cikin girmamawa. “Sure, Ma’am.” Ta miƙa masa wayar. Ba ta shiga wani irin posing ba, hotuna masu sauƙi kawai. Wani tana jingine da motarta, wani tana tafiya a hankali Wani kuma tana kallon flowers ɗin da ke gefen parking ba tare da kallon camera ba. Da ya gama, ya miƙa mata wayar. Ta duba, Murmushi ya bayyana a fuskarta. “They’re beautiful! Thank you.” “You’re welcome, Ma’am.” Ta shiga motarta. Ta kunna motar, a hankali ta bar wajen. A hanya… Window ɗinta a ɗan buɗe yake Sanyin iska na shigowa. Wata soft nasheed na tashi a stereo. Zahra tana tuƙi cikin nutsuwa Karo na farko cikin watanni, ta ji kamar ta dawo Zahra ta da. Ba wadda take rayuwa tsakanin school, books da exams kawai ba… Sai Zahra mai son fita ita kaɗai ta sha iska tayi pic ta daura a media handles dinta.. Da ta isa gida… Mai gadi ya buɗe gate. Ta shigo compound, ta yi parking Kanwar Anty Binta ce ta fito da gudu. “Anty Zahra, sannu da zuwa.” Ta yi murmushi. “Yauwa. Ya gida?” “Lafiya.” Yarinyar ta amsa Sai kuma ta karɓi handbag ɗinta. “Na gode.” Suka shiga parlour tare. Abbah da Mami na zaune suna hira. Abbah na hango ta, ya yi murmushi. “My Baby… How was it?” Zahra ta zauna a gefensa. “It was amazing.” Ya yi dariya. “So… Ya Umar’s idea worked?” “It really did.” Ta amsa tana murmushi. Mami ta ce, “Kin gane yanzu? Mutum yana buƙatar ya huta wani lokaci.” Ta gyada kai. “Wallahi Mami! Na ji daɗi sosai” Abbah ya kalleta “I can see! Kin dawo da fara’arki.” Ta yi dariya “Really?” “Very.” Ya shafa kanta cikin ƙauna. “Allah ya ƙara miki farin ciki ya raya mana ke “Ameen.” Daga haka ta mike t wuce zuwa d’akinta Bayan ta yi sallah ta canja kaya… Sabuwar wayarta ta ɗauka Tun lokacin da Abbah ya siya mata wayar, ba ta gama saita komai ba Yanzu ne ta samu lokacin da za ta dawo da duk account ɗinta dake wayan Mami Ta shiga Instagram Ta saka username da password. Cikin daƙiƙu kaɗan… Account ɗinta ya dawo. Ta kalli profile ɗinta tana murmushi Ta daɗe ba ta yi posting ba. Followers ɗinta kuwa sai ƙaruwa suke kullum, ta shiga gallery Ta zaɓi hotuna huɗu daga waɗanda aka ɗauke ta yau Dukansu simple ne, babu wani pose mai yawa, Elegance kawai Ta rubuta caption. “Sometimes… all your heart needs is a little peace. 🤍✨ Alhamdulillah.” Ta danna Post, ta ajiye wayar Ba’a wuce minti ɗaya ba… ❤️ 245 Likes Ta ɗaga gira. “Masha Allah.” Ta ci gaba da kallon comments. “Absolutely gorgeous.” “Queen energy.” “Elegance has a name.” “Our soft life queen is back!” “This smile… we’ve missed it.” “Allah ya ƙara miki farin ciki.” “Simple but classy.” “Fatima Zahra never disappoints.” Ta yi murmushi, ba ta cika shiga reply ba Sai dai idan comment ɗin addu’a ne, nan take ta rubuta “Ameen, thank you. 🤍” Ta sake wucewa, wani ya rubuta, “Marry me.” Ta yi dariya ita kaɗai, ta yi scrolling ba tare da ta ba shi amsa ba, sai kuma wani comment ya ja hankalinta. “Your dignity is what makes you different.” Ta tsaya tana kallon comment ɗin na wasu daƙiƙu, daga ƙarshe ta yi like kawai Domin wannan kalmar… Ita ce ta fi bayyana wacece Zahra. Wata irin izzah da Allah Ya ɗora mata, wadda ba ta neman ta ja hankali da ita, amma duk inda ta bayyana, mutane kan lura da ita. Ta kashe wayarta, ta jingina da headboard ɗin gadonta tana murmushi. Washegari tun da sassafe Zahra ta isa makaranta kamar yadda ta saba Tun daga parking lot ɗin makarantar take tafiya cikin nutsuwarta. Uniform ɗinta fari ne ƙal, an yi masa guga yadda babu ko ɗigon wrinkle. Black shoes ɗinta suna kyalli, hijab ɗinta kuma a nannade sai shatin guga tamkar an zana. School bag ɗinta na rataye a kafaɗarta ɗaya, a ɗaya hannun kuma tana riƙe da file. Ba ta cikin masu hayaniya. Ba ta cikin masu tsayawa suna hira a hanya, kawai tafiya take zuwa school hall din A tara candidates ne a babban hall domin wani bayani daga Principal da wasu external supervisors ne suka yi musu jawabi. Bayan an gama… Ɗalibai suka fara fita a hankali. Hall ɗin ya cika da cunkoso. Zahra tana tafiya a hankali tana ƙoƙarin kauce wa mutane, bayanta kuma Firdausi ce Sai dai… Wani dogon matashi daga science block ya fito da sauri, idanunsa na kan wayarsa. Bam! Ya bugi Zahra da ƙarfi. File ɗinta ya faɗi, takardu suka warwatse Ita kanta ta ɗan ja baya saboda ƙarfin bugun. Sai dai kafin ta gama daidaita kanta… Yaron ya kalle ta na daƙiƙa ɗaya, ya kuma ci gaba da tafiyarsa, tamkar babu abin da ya faru. Firdausi ta zaro ido “Excuse me!” Ta ce, Amma bai tsaya ba A hankali Zahra ta sunkuya ta tattara papers ɗinta, ta gyara hijab ɗinta, ta ɗauki handbag ɗinta. Sannan… Ta ɗaga kanta. “Kai…” Muryarta ta fito sai da bada kara ba, amma akwai wata irin izzah a cikinta da ta sa yaron ya tsaya. Ya waiwayo Ta ɗaga hannu alamar ya dawo Ba tare da ya san dalilin da ya sa yake jin dole ya bi umarninta ba… Sai ya dawo. Ya tsaya a gabanta… Ta ɗan ɗaga idanunta ta kalle shi Ba fushi a fuskarta, amma kallon ya isa ya sa ya ji kamar ya raina kansa Ta ce cikin nutsuwa, “Ka bugeni.” Ya ɗan ɗaga kafaɗa “So?” Firdausi ta yi yunƙurin magana. Zahra ta hana ta da ɗan kallon gefe. Sannan ta maida idanunta kansa. “Saboda na yi shiru… ka ɗauka za ka raina ni ne?” Yaron ya haɗe gira “I didn’t do it intentionally.” Ta yi ɗan murmushi. “Really?” Ta ɗan matsa kusa da shi. “Toh idan ba da gangan ka yi ba…ina kalmar I’m sorry?” Ya yi shiru. Mutane suka fara tsayawa Wasu na kallonsu Ta ci gaba. “Ko a gidanku ba a koya maka cewa idan ka yi wa mutum laifi, ko ba da gangan ba, ka nemi afuwa?” Yaron yayi folding hannayensa “Ba zan taba miki yadda a school din nan suke miki ba, na buge ki ne kuma nace ba intentionally bane” Zahra ta gyara file ɗinta Sannan ta ce, “Listen carefully!! Humility is a choice” “But manners… are compulsory” Ta ɗan dakata. “Okay dan bana magana? Na taba rokon wani akan suyi respecting dina? Mutunci ba ya nufin mutum ba shi da bakin magana bane” Sai ta nuna sa da ɗan yatsarta “Kada ka sake kuskuren raina wani saboda ya zaɓi nutsuwa” Yanzu gaba ɗaya wajen ya yi tsi Ana kallon ikon Allah wani Teacher da yake wucewa ya tsaya, ya kalli yaron. “Young man…Aren’t you going to apologize?” Yaron ya sauke kai. “I’m… sorry.” Zahra ta gyara handbag ɗinta. Ta ce “it’s okay! At least now…” “…you’ve learnt something.” Ta juya cikin nutsuwa, kafin ta yi taku uku… sai ta tsaya ba tare da ta waiwayo ba Ta ce, “Next time …respect people before they demand it.” Ta ci gaba da tafiyarta. Babu wanda ya sake cewa komai. Firdausi ta bi bayanta tana murmushi da suka yi nisa… ta riƙe hannun Zahra. “Wallahi da ni ce… sai na mare shi.” Zahra ta yi dariya kaɗan “Mari?” Firdausi ta gyada kai. “Eh mana.” Zahra ta girgiza kai. “Mari yana warkewa.” Ta ɗan yi shiru Sannan ta ƙarasa da wata irin nutsuwa. “Amma kunyar da mutum zai ji idan aka tuna masa tarbiyyarsa… ita tana daɗewa.” Firdausi ta tsaya cak. Ta kalli Zahra. Sai kawai ta fashe da dariya. “Wallahi Zahra… ke daban ce.” Zahra ta yi murmushi kawai Ta ci gaba da tafiyarta Bayan kammala dukkan jarabawanta… Rayuwar Zahra ta ɗan sauya. Ba wai saboda ta samu wani sabon abu ba… Sai don karo na farko cikin watanni da dama, ta samu lokacin da za ta huta. Da safe za ta taimaka wa Mami da wasu ƙananan abubuwa a gida musamman gyaran part din abbah ko girkin Abbah Wani lokaci kuma ta zauna da Abbah suna hira a library. Idan Ya Umar yana gida kuwa… Sun dunga hira, ko kuma yayi ta tsokanarta kamar ba kanwarsa ba sai ka dauka mate dinta ce yadda suke yi Ko da ta je makaranta ma… Ba don karatu bane take zuwa sai don dama classmate dinta suna ss2 ne dama A haka rayuwa take tafiya.. Kwanaki suka koma makonni, wata rana da rana… Zahra na zaune a parlour tana kallon wani documentary tare da Abbah. Wayarta ta fara vibrating. Firdausi Calling… Da ta ɗauka… Tun kafin ta yi magana… Firdausi ta yi ihu “Zahraaaaa! WAEC result is out!” Zuciyar Zahra ta buga Ta yi saurin miƙewa tsaye. “Really? Yaushe aka sake?” “Wallahi! Na duba nawa yanzu!” Ba ta sake jiran wani abu ba ta katse wayan, Tana kallon Abbah tace Abbah waec result is out” Ko amsar da zai bata ba ta jira ba ta gudu zuwa study room Laptop ɗinta ta buɗe Candidate number PIN Check Result. Numfashinta ya tsaya, ta danna. Shafin ya ɗauki wasu daƙiƙu kafin ya buɗe. Sai… Idanunta suka fara sauka a hankali. English Language A1, Ta yi shiru Mathematics A1. Hannunta ya fara rawa, ta ci gaba. Biology A1, Chemistry A1 Har zuwa ƙarshe… Nine Subjects… Nine Distinctions. “Allahu Akbar…” Shi kaɗai ta iya furtawa, sai ga hawaye sun fara tsintiri a fuskanta Abbah da Ya Umar suka shigo saboda jin shirun da ya yi tsawo “Baby?” Abbah ya kira. Ta juya, Idanunta cike da hawaye, ba ta iya magana ba, sai ta miƙa masa laptop ɗin. Ya karɓa, ya fara dubawa Lokaci guda murmushi ya cika fuskarsa. “My daughter… you did it” Ya rungume ta. Ya Umar ya karɓi laptop ɗin. Da ya gani… Sai ya yi wata irin ihu. “Nine A1! Baby ta kashe su!” Dawowa Parlourn suka yi, Duk fuskokinsu dauke da murmushi Anty Binta har gudu ta yi zuwa kitchen. “Hajiya! Zahra ta samu Nine A1!” Mami ta fito da sauri, ganin fuskokinsu kadai ya isa ya sanar mata, Sai ta rungume Zahra. “Ma shaa Allah Baby” Mummy dake tsaye daga sama tana kallonsu, ta taɓe baki. “Hmm!! Da alama yau ma gidan nan ba za a kwana lafiya ba” Batoul ta yi murmushin gefen baki. “Dama ai… Princess ce fah, ko kin manta ne?” Abbah ya ɗago ya kalle su. Sai dai bai ce musu komai ba Maimakon haka… Ya juya ya kalli Zahra. “My Baby dole na miki kyauta.” Ta yi murmushi “Wace irin kyauta?” Ya girgiza kai “Not now! Amma kafin hakan…” “Ina son ki je ki yi weekend a gidan Uncle Moh” Ta haɗe gira “Weekend?” “Eh Ki je ki huta, kin cancanci hutun.” Ta yi dariya “Toh Abbah.” Juma’a da safe… Tun bayan ta idar da sallarta, Zahra ta fara shiryawa. Ba ta yi wani kwalliya mai yawa ba Doguwar abaya ce mai launin light purple ta saka, haɗe da veil dinsa purple color mai laushi. Sneakers purple ta sanya a ƙafarta, handbag ɗinta kuma ta rataya a kafaɗa Da ta sauko ƙasa… Ta tarar da Abbah, Mami da Ya Umar suna kammala breakfast Mami ta ɗaga kai ta kalleta “Kin shirya kenan?” Ta gyada kai tana murmushi “Na shirya.” Abbah ya ce, “Weekend kawai, that’s kwana biyu kawai fa.” Ta yi dariya “Abbah kamar zan yi wata ɗaya” Ya Umar ya taɓe baki. “Da kin san Uncle Moh, sai ya ƙi sako ki ki dawowa.” Dariya suka yi gaba ɗaya. Mami ta miƙa mata wata ƙaramar basket “Na saka miki wasu fruits da snacks a ciki, ki bawa Anty Maryam na Babban roban Ta karɓa “Na gode, Mami” Ta rungume ta Sannan ta nufi Abbah Ta rungume shi kamar yadda ta saba. “Allah ya kiyaye hanya.” Ya ce “Ameen.” Ya shafa kanta “Ki gaida Uncle Moh da Aunty Maryam.” “In shaa Allah.” Ya Umar ya ɗauki ƙaramar travelling bag ɗinta “Mu tafi, Baby.” Bayan kusan mintuna arba’in da biyar suna tafiya… Motar ta tsaya a gaban wani katafaren gida, ba shi da irin girman gidan Abbah… Sai dai yana da wani irin tsari da nutsuwa. Flowers masu kyau sun zagaye compound ɗin. Da motar ta shiga… Mai gadi ya yi saurin buɗe musu Parking yayi, tun kafin su shiga ciki… Ƙofar parlour aka buɗe Wata mata fara ce mai cike da fara’a ta fito da sauri. “Zahra!” Ta yi ihu. Zahra ma ta fashe da dariya “Aunty Maryam!” Da gudu ta ƙarasa ta rungume ta. Aunty Maryam ta sumbaci goshinta. “Allah! Kin ƙara kyau, Daughter” Ta yi dariya “Aunty… Kullum haka kike faɗa fah “Kuma kullum gaskiya nake yi” Anty Maryam ta bata amsa Karasa cikin parlon suka yi… daga ciki kuma wani mutum mai matsakaicin tsufa ya fito yana dariya. “Toh wai ni fa? Ni ba za a rungume ni ba?” Da jin muryarsa… Zahra ta saki Aunty Maryam “Uncle Moh!” Da gudu ta nufe shi, ta rungume shi Shi ma ya rungume ta yana dariya. “My princess! How are you?” “I’m fine, Uncle.” “Ya Abbah?” Ya tambaya “He’s fine.” Ta basa amsa Ya Umar ya yi sallama, ya shiga yana gaishe su da ladabi Uncle Moh ya rungume shi shima “Umar tuzuru, gaskiya aurar da Kai zamu yi tunda kaki fito da Mata” Murmushi kawai Ya Umar yayi, Uncle Moh ya ce “Sai Yau zaka zo?” Ya yi murmushi “Work, Uncle.” “IKLIMATYYYYYY!” Zahra ta yi wata irin ƙara Wata kyakkyawar budurwa mai kusan shekarunta ta fito da gudu daga staircase Da ganin Zahra… ta yi ihu. “ZAHRAAAAA!” Dukansu suka yi gudu suka rungume juna, suna dariya, suna tsalle Aunty Maryam ta riƙe hab’a “Waɗannan yaran ko Yaushe zasu girma oho “ Iklima ta riƙe hannun Zahra “Wallahi na yi missing ɗinki.” “Nima” ta fad’a Sai kuma wata murya ta fito daga sama “Hmm… Ni kuma fa?” Zahra ta ɗaga kai, jin Muryan Ya Imran ne Ta ga wani dogon saurayi cikin farin T-shirt da black joggers yana saukowa staircase, da zarar ta gan shi… ta yi murmushi “Ya Ims!” Shi ma ya yi murmushi. “Baby Zahra.” Da ya ƙaraso wajensu… Ya buɗe hannuwansa Ta rungume shi, ya ɗan bubbuga bayanta. “Kin manta da mu.” Ta taɓe baki “Exams ne fa.” Ya yi dariya “Excuses kullum haka kike Sai kuma idonsa ya fada kan na Ya Umar dake kallonsa fuskansa cike da murmushi ya ce….. #Farashin izzah 08110615256 Chapter 37 “Omo Dude kace da Kai aka zo mana” daga haka ya sake zahra yayi wajen Ya Umar Parlour ya cika da annashuwa , kowa na tambayar juna Aunty Maryam ta kawo masu fresh juice Uncle Moh kuwa ya kasa daina kallonta. “Muhammad ya raini shalelensa har ta girma haka?, yanzu ta bar Baby kenan” Ya Umar ya yi dariya. “Uncle… Wallahi har yanzu Baby ce!Kuma za ta ci gaba da zama Baby.” Zahra ta yi gwalo. “Exactly.” Suka sake yin dariya. Bayan sun yi hira na kusan awa guda… Ya Umar ya miƙe. “Toh Uncle… Ni zan wuce.” Nan take Zahra ta miƙe “Yaya…” Ya yi murmushi. “Weekend ne fa.” Ta yi frowning face dinta “Ka kula da kanka.” Ya shafa kanta. “Ke ma.” Sannan ya fita, ta bisa a baya, tare da Ya Imran Har ƙofar mota Zahra ta raka shi, shagaɓa take masa shi kuma yana biye ta har ya lallabata ta hakura, Da motar Ya Umar ta fice daga compound… Zahra ta tsaya na ɗan lokaci tana kallonta har ya ɓace daga ganinta. Ya Imran ya koma ciki, jin shiru yasa iklima fito wa Iklima ta ɗan turo ta da kafaɗa tana dariya “Kin gama rakiyar kenan?” Zahra ta murmusa “Ya Ims ma ai idan zai tafi haka nake rakarsa.” “Ke dai.” Hannunta ta riƙa suka koma cikin gidan Bayan sallar Juma’a… Parlour ya sake cika. Uncle Moh ya dawo daga masallaci tare da Ya Ims. Aunty Maryam kuwa ta gama haɗa abinci. Kamshin tuwon shinkafa da miyar taushe ya mamaye gidan. “Zahra!” Aunty Maryam ta kira. “Na’am, Aunty.” “Zo ki taimaka min.” Da sauri ta nufi dining. Ko da wasa ba ta cikin yaran da idan basu gida su nuna cewa basu aiki a gida dan haka ba zasu iya ba a waje Plate-plate ta fara jera wa, spoons, cups Aunty Maryam ta tsaya tana kallonta Ta yi murmushi. “Wallahi Mami ya raini ’yarta da tarbiyya.” Zahra ta yi dariya “Abbah yana cewa idan mutum bai iya yi wa kansa aiki ba, duk dukiyar duniya ba ta isa ta amfane shi ba.” “Allah ya ƙara masa lafiya.” Cewar Anty Maryam “Ameen.” Ta amsa Bayan Duk sun hallara Ita ce ta fara zuba wa Uncle Moh ruwa, Sai Ya Ims, sai Iklima sannan Aunty Maryam. Uncle Moh ya girgiza kai “Wannan yarinya ba ta canzawa har yanxu da kwazonta” Murmushi Zahra tayi basu san takura kanta take yi ba Ya Ims ya yi dariya “Baby Zahra ce fa.” Ta taɓe baki “Ya Ims… Daina kirana Baby.” “Kin girma ne?” Ya tambaya yana dariya Ta haɗe hannu a ƙirji “Very much.” Iklima ta fashe da dariya “Ai idan Abbahnki ya zo nan yanzu zai ce ‘Baby’…” “…za ki amsa.” Duk suka yi dariya. Zahra ta yi kamar za ta mare ta, ta bar dining din da sauri Tana dariya A can gida kuwa… Wata farar Hilux ce ta tsaya a compound. Mai gadi ya buɗe gate mutane huɗu suka fito Dukkansu cikin kayan aiki. Mama Ladi ta fito daga kitchen tana kallonsu. “Malam… Su waye?” Mai gadin ya ɗaga kafaɗa. “Ni ma ban sani ba.” A dai-dai lokacin… Mami ta sauko daga staircase ta back door, ta kalli mutanen. “Sannunku.” “Sannu, Hajiya.” Ɗaya daga cikinsu ya yi gaba. Ya miƙa mata wata takarda. Ta karɓa ta duba. Sai ta ɗaga kai. “Ku biyo ni.” Daga haka suka bi bayanta zuwa sama. Ita ce Mama Ladi ta tsaya tana binsu da kallo. Ta so ta tambaya… Sai kuma ta fasa. Ta juya ta koma kitchen wajen aikinta tana kwalawa Binta kira A gidan Uncle Moh kuwa… Da yamma suka fita garden Ita da Iklima suna zaune a kan swing. Ya Ims yana ta tsokanarsu “Kai Iklima. Ki tambayi kawarki.” Iklima ta kalle shi. “Me?” “Har yanzu tana ƙin samari ne?” Zahra ta harare shi. “Ya Ims.” Ya yi dariya “Me na ce?” Iklima ta haɗa baki. “Wallahi kuwa. Last time wani ya ce yana son ta… Bai gama maganar ba ta bar wajen.” Ya Ims ya riƙe ciki yana dariya “Da gaske?” Zahra ta taɓe baki “Ni ban ga abin dariya ba. Karatu nake yi.” Ya Ims ya ɗaga hannu. “Okay, okay. Doctor Fatima Zahra.” Ta gyara masa. “Professor.” Duk suka fashe da dariya. Yamma sosai yayi A hankali iska mai sanyi ta fara kaɗawa Uncle Moh ya fito daga parlour. Ya tsaya yana kallonsu. “Har yanzu ba ku gaji da hirar ba?” Ya Ims ya ce, “Daddy, yau Zahra ta dawo mana. Ai babu ita babu Hutu” Uncle Moh ya yi murmushi. “Haka nake so.” Ya juya ya kalli Zahra. “Ki ji daɗin weekend ɗinki.” Ta gyada kai. “In shaa Allah, Uncle.” Ta sake jingina da kujerar swing. Fuskarta cike da annashuwa Washegari… (Asabar) Tun bayan sun gama breakfast… Uncle Moh ya shigo parlour yana juya mukullin motarsa a hannunsa. Ya tsaya yana kallon yaran. “Toh… Wa zai fita da ni?” Iklima ta ɗaga hannu da sauri. “Ni!” Ya Ims ya ɗaga hannu shima. “Ni ma.” Uncle Moh ya juya ya kalli Zahra. “Ke fa?” Zahra ta yi ɗan murmushi “Inda za mu je ne ban sani ba.” Ya yi dariya. “Surprise.” Ta taɓe baki. “Uncle… Dama ba na son surprises.” “Dole yau ki tafi to” ya ce Aunty Maryam ta fito daga kitchen tana dariya. “Wallahi tun safe yake cewa idan Baby Zahra ta tashi za su fita.” Uncle Moh ya ce, “She has been studying for months, yau hutunta ne.” Ya Ims ya tafa hannu. “Exactly! Muje mu nuna mata Kaduna.” Zahra ta yi dariya. “Kamar ban san Kadunan ba.” Iklima ta rungume hannunta. “Please mana.” Ta kalli Uncle Moh sai ta yi murmushi. “Okay.” Cikin mintuna talatin… Kowa ya shirya. Uncle Moh ne ke driving. A gaba Ya Ims ya zauna. A baya kuwa… Iklima da Zahra. Tun daga cikin mota hirarsu ba ta tsaya ba. Ya Ims na ta juyowa yana tsokanar Zahra. “Baby… Har yanzu kina da waɗancan snack din da kullum kike ɓoyewa?” Ta zaro ido. “Ya Ims! Ka manta ka sace min dukka ne?” Ya fashe da dariya “Wannan ƙaryar ce.” Iklima ta nuna shi “Ni shaida ce.” Dariya ta cika motar. Har Uncle Moh ya ce, “Ku bar yarinyar nan mana.” Ya Ims ya ce, “Daddy ai ita ce favorite ɗinka na lura .” “Saboda ta cancanta.” Uncle Moh ya faɗa ba tare da tunani ba Ya sa Zahra ta yi murmushin kunya. Wani katafaren recreational park suka fara zuwa. Suna shiga… Iklima ta ja hannun Zahra. “Zo!” Suka fara zagayawa, suna ɗaukar hotuna suna dariya. Ya Ims kuwa yana ta musu photobomb a baya. “Ya Ims!” Zahra ta yi ihu “Ka bari mana.” Ya yi dariya. “Ai wannan hoton ya fi kyau idan ina ciki.” Bayan sun gama… Sai Uncle Moh ya kai su wani restaurant Da suka zauna… Waiter ya kawo menu. Uncle Moh ya miƙa wa Zahra. “Princess, Order whatever you want.” Ta girgiza kai. “Uncle, komai kuka ci ni ma shi zan ci.” Ya kalleta yana murmushi “Har yanzu ba ki canza ba.” Aunty Maryam ta kan faɗa masa kullum… _“Wannan yarinya ba ta da son wahalar da mutane.”_ Ana cikin cin abinci… Sai wata yarinya ƙarama ta zo kusa da teburinsu, ta tsaya tana kallon ice cream ɗin da Iklima ke ci. Zahra ta lura da ita, ba tare da ta ce komai ba… ta kira waiter. “Please… Another one.” Sai gashi ya zo da ice cream, ta karba ta miƙa wa yarinyar. Yarinyar ta zaro ido. “Nawa?” Zahra ta yi murmushi. “Naki ne.” Yarinyar ta yi murmushi sosai. “Thank you.” Ta gudu wajen mahaifiyarta. Uncle Moh ya kalli Zahra. Ya girgiza kai. “Kin gaji wannan halin daga wajen Muhammad.” Ya Ims ya yi dariya. “Baby ba za ta taɓa ganin ƙaramin yaro ba ta wuce.” Zahra ta ɗan sunkuyar da kai. “Abbah na yana cewa…” _“Idan Allah ya ba ka fiye da abin da kake buƙata, akwai haƙƙin wani a ciki.”_ Uncle Moh ya ce “Allah ya ƙara masa lafiya.” “Ameen.” Sai can wajen yamma suka dawo gida. Kowa ya gaji.. amma fuskokinsu cike suke da annashuwa Da suka shiga parlour… Iklima ta faɗa kan kujera. “Wallahi na gaji.” Ya Ims ya yi dariya. “Ke kika fi gudu ai da wasan banza, ba dole ba” Zahra kuwa ta zauna tana kallon hotunan da suka ɗauka. Suka dinga dariya suna tuna yadda Ya Ims yake lalata musu pictures. A haka suka ƙarasa weekend ɗinsu cikin farin ciki….. Meanwhile kuma a wannan ranan a Compound ɗin gidan Alhaji Muhammad Nasir ya cika da zirga-zirga Wata babbar mota ce ta tsaya a bakin gate, daga cikinta wasu ma’aikata suka fito ɗauke da kayan aikinsu. Wasu na riƙe da measuring tape, wasu kuma da manyan cartons, yayin da wasu ke tura trolley ɗauke da kayayyaki. Mama Ladi ta leƙo daga kitchen tana mamaki “Subhanallah… yau kuma me ake yi ne a gidan nan?” Sai dai babu wanda zai bata amsa. Mami ce ta fito daga parlour cikin nutsuwa. Ta gaishe su, sannan ta ja su zuwa sama. Da suka isa gaban ɗakin Zahra… Ɗaya daga cikin mutanen ya buɗe notebook ɗinsa. “Hajiya, nan ne?” Mami ta gyada kai. “Eh. Amma ku kula sosai. Ba na son ko ƙarce ya samu wani abu.” “In shaa Allah.” Nan take aka fara aiki. An fara cire labulen ɗakin, sai carpet. Sannan aka fara kwashe tsoffin kayan furniture ɗin a hankali. Mami ta tsaya bakin ƙofa tana kallonsu. Wani ya tambaye ta, “Hajiya, wannan dressing mirror ɗin fa?” Ta ɗan yi tunani. “A’a… ku cire shi ma.” Bayan wasu mintuna… Ɗakin gaba ɗaya ya koma fanko. Ko Mami da ta saba ganin ɗakin kullum, sai da ta yi mamaki. “Allah Sarki…” Ta faɗa a hankali. “Ashe haka ɗakin yake idan babu komai.” Ana cikin haka… Wata mota ta sake shigowa compound. Ta tsaya, aka fara sauke sabbin kaya Ga wani king size bed, wardrobe mai sheƙi, Reading table, Bookshelves, Dogayen wall mirrors, Sofas, Flowers, Frames, Lighting. Komai ana shigarwa cikin tsari Mami ta shiga ɗakin a hankali bayan an gama jera manyan kayan. Ta tsaya cak, idanunta suka kan ko’ina cikin ɗakin, paint na bangon da aka sauya, sabbin curtains, carpet mai laushi. Komai ya haɗu da juna cikin kyau da tsari irin na young lady Ta lumshe idanunta tana murmushi. “Ma shaa Allah…Wallahi dear yana son yarinyar nan, Alhamdulillah Allah Nagode maka” Mama ladi ma ta shigo a hankali. Da ta ga ɗakin… Sai ta dafe baki. “Hajiya! Wannan ɗaki kuwa…” Mami ta yi murmushi. “Ko ni kaina ban yi tunanin zai yi haka ba.” Mama Ladi ta yi dariya. “Zahra fa?” Mami ta girgiza kai. “Wallahi idan ta dawo, sai ta yi tunanin ba ɗakinta ba ne.” Dukansu suka yi dariya. A can gidan Uncle Moh kuwa… Weekend ɗin Zahra ya kasance cikin annashuwa. Tun safe ita da Iklima suna kitchen suna taimakawa Aunty Maryam. Da rana suka fita ɗan yawon gari da kafa tare da Ya Ims. Suna tsokanar juna, suna dariya. Da yammacin Lahadi… Ya Umar ya zo ɗaukarta. Tun daga ƙofar gida Iklima ta rungume ta. “Wallahi ban so ki tafi ba.” Zahra ta yi dariya. “Ni ma. Amma zan sake zuwa.” Ya Ims ya girgiza kai “Karki manta da mu idan kin shiga university.” Ta taɓe baki. “Ya Ims… Ku ne za ku manta da ni, but not me” Uncle Moh ya shafa kanta. “Allah ya tsare hanya.” “Ameen.” Ta amsa Aunty Maryam ta rungume ta sosai “Ki gaida Abbahnki da Mami.” “In shaa Allah.” Bayan sun yi sallama… Ta shiga motar Ya Umar. Har sai da suka fita daga layin gidan kafin Iklima ta daina daga mata hannu. Tafiyar gaba ɗaya cike take da hira. Ya Umar yana ba ta labarin wasu abubuwan da suka faru a office. Ita kuma tana ba shi labarin yadda suka yi weekend. Har ba su ankara ba… Motar ta shiga compound bayan Mai gadi ya buɗe musu gate. Da sauri Zahra ta fito. “Mami!” Ta kira tana dariya. Babu amsa. Ta yi mamaki. “Ko ina suke ne?” Ya Umar ya yi murmushi kawai. “Ki shiga mana.” Ta wuce parlour.Ba ta ga kowa ba. Sai Farida ta fito daga kitchen. “Anty Zahra… sannu da zuwa.” “Yauwa Anty Binta, ina Mami?” “Tana sama.” Ta gyada kai. “Okay.” Ba tare da ta tsaya ba… Ta nufi staircase. A hankali take hawa tana ɗan gajiya saboda tafiya. Da ta kai corridor ɗin sama… Sai ta tsaya. Ta haɗe gira “Eh?” Idanunta suka sauka kan ƙofar ɗakinta… A buɗe take. Kuma akwai muryoyin mutane daga ciki. Ta ƙarasa a hankali. Da ta tsaya bakin ƙofar… Abin da idanunta suka gani… Ya sa ta kasa ko ƙiftawa Numfashinta ya ɗan tsaya na wasu daƙiƙu. Idanunta suka fara yawo a hankali cikin ɗakin. “…” “Ya Allah!…” Kalmar data iya furtawa a hankali kenan Da farko ta yi tunanin ko tayi kuskure ne ta shiga wani ɗakin ne Sai ta sake kallon calligraphy ɗinto dake bakin ƙofar. Ita ce. Amma…Komai ya sauya. Bed da ta saba gani ba ita bace. Sabuwar carpet mai laushi ce ta mamaye tsakiyar dakin gaba ɗaya. Gadon da ta kwana a kai shekaru ya sauya zuwa wani katafaren bed mai matuƙar kyau, an shimfiɗa farin bedsheet mai haɗe da sky blue duvet, pillows ɗin kuwa an jera su cikin tsari tamkar na hotel. Sabbin curtains masu launin blue da white suna sauka a hankali, iska daga AC tana ɗan motsa su. Reading table ɗinta ma ba ita bace. An maye gurbinta da wata babba, an tsara littattafanta cikin shelves masu kyau. Doguwar mirror tana gefe. Flowers masu kyau suna ƙawata kusan kowane kusurwa. Lighting ɗin ɗakin kuwa… Sai ya sa kamar ba ɗakin da ta saba shiga ba ne. Ta shiga a hankali… Tamkar mai tsoron taka wani abu. Hannunta ta kai kan gadon. Ta shafa bedsheet ɗin. Ta juya tana kallon ko’ina. “Ya Allah…” Har yanzu muryarta ƙasa take. “Nan ne dakina kuwa?” Dariya ta ji daga bayanta. Da sauri ta waiwayo. Mami ce tsaye bakin ƙofa, hannuwanta a haɗe a ƙirji, murmushi ya ƙawata fuskarta. “Kin gama kallo?” Zahra ta zaro ido. “Mami…” Ta sake kallon ɗakin. Ta sake kallon Mami “Mami…” “Me ya faru da ɗakina?” Mami ta yi dariya. “Ki tambayi Abbahnki.” Da jin sunan Abbah… Zahra ta juya da gudu. “Mami! Abbah yana ina?” “Study.” Ba ta jira ta ƙara cewa komai ba. Da gudu ta fita. Veil ɗinta na ɗan zamewa saboda gudun. Ta sauko stairs biyu-biyu. “Abbah!” Ta kira tun kafin ta isa ƙasa. A study ɗinsa… Alhaji Muhammad Nasir yana zaune yana duba wasu files. Da jin muryarta… Ya ɗago kai. Ko bai ga fuskarta ba… Ya san reaction ɗin da take ciki. Ƙofar ta buɗe da sauri. Ta shigo tana haki kaɗan. “Abbah…” Ta tsaya gabansa. Idanunta cike da mamaki. “Na ga…” Ta kasa ƙarasa maganar. Ya ajiye file ɗin hannunsa. Ya ɗaga mata hannu. “Zo nan.” Da sauri ta ƙarasa. Ta durƙusa gabansa kamar yadda ta saba. Ya shafa gefen fuskarta. “Kin so?” Ta ɗaga kai da sauri “So?” “Abbah…? Haba…Na rasa ma abin da zan ce.” Ta yi shiru na ɗan lokaci. Sai kawai ta rungume shi da ƙarfi. “Thank you…My Abbah.” Ya lumshe idanunsa yana murmushi “Wannan ƙaramin sakamako ne.Na farin cikin da kika saka ni.” Ta ɗago tana kallonsa. “Amma…Abbah… Me ya sa duk wannan?” Ya yi murmushi. “Saboda kin cancanta.” Ta girgiza kai. “A’a… yayi yawa.” Ya ɗan ɗaga gira. “Yayi yawa?” Ta gyada kai. “Eh.” Ya yi dariya “Baby…” “Ko da zan ba ki duniya gaba ɗaya…Wallahi zan ga kamar ban yi miki komai ba.” Hawaye suka cika idanunta. Na farin ciki Ta sake rungume shi. “Allah ya bar min kai, Abbah.” “Ameen.”Ya sumbaci goshinta. “Allah ya sa kullum ina ganin murmushinki.” “Ameen.” A dai-dai lokacin… Ya Umar ya shigo parlour ɗin yana jingine da ƙofa. Tun da ya ga Zahra ta rungume Abbah ya riga ya fahimci ta ga ɗakin. Ya yi murmushi. “Baby.” Ta waiwayo. Da gudu ta nufe shi “Yaya!” Ta rungume shi shi ma. “Ka sani ko?” Ya yi kamar yana tunani. “Ban sani ba.” Ta ɗan doke ƙirjinsa. “Ka daina.” Ya yi dariya. “Toh…Na sani.” “Amma ba ni na shirya ba.” “Abbah ne.” Ta ce da sauri. “Na sani.” “Sai dai kai ma ka taimaka.” Ya ɗaga hannu “Little bit. Just the shelves “ Ta yi murmushi. “Nagode.” Ya shafa kanta. “Kawai ki ci gaba da saka mu proud” Ta gyada kai cikin nutsuwa. “In shaa Allah.” A saman staircase kuwa… Mummy da Batoul na tsaye suna kallon abin da ke faruwa a kasa Batoul ta taɓe baki “Princess ta dawo.” Mummy kuwa… Ta ci gaba da kallonsu cikin wani irin shiru, ba tare da ta ce komai ba #Farashin izzah 08110615256 Chapter 38 Washegari tun da sassafe… Mummy ta shirya cikin wata atamfa mai tsada, handbag ɗinta na rataye a kafaɗa yayin da Batoul ke biye da ita har bakin mota “Batoul, idan na kira ki ki ɗaga waya.” “Okay Mummy.” “Make sure kin saka ido, ki makale a parlon, sannan kuma ni Ina Jin zan Kai dare kafin na dawo” “Safe journey” Batoul ta fad’a Da motarta ta fice daga compound Batoul ta juya ta koma ciki Mami kuwa na zaune a parlour tana kallon sunnah tv ana wani program da take so, yayin da Abbah yana office dinsa na gidan kamar yadda ya saba. Ya Umar ma yana gida saboda ranar hutunsa ce. Da misalin ƙarfe goma sha ɗaya… Wata Napep ce ta tsaya a bakin gate. Mai gadi ya leƙa jin an fara knocking “Waye?” “Asiya da Firdausi ce, mun zo wajen Zahra ne” Da Jin sune ya buɗe musu gate suka shiga, gaishe sa suka yi sannan suka wuce ciki Suna shiga parlour, suka tarar da Ya Umar zaune kan kujera, laptop na gabansa, yana duba wasu takardu. Da sallama suka shiga dukkansu “Assalamu alaikum.” Ba tare da ya ɗago kai ba ya amsa “Wa alaikumus salam.” Sai bayan wasu daƙiƙu ya ɗaga idanunsa ya kalle su “Lafiya?” “Lafiya lau, Yaya Umar.” Cewar Asiya Firdausi ta masa wani kallo, irin tambayar rainin hankalin da zai musu kenan Ya gyada kai kawai, ya cigaba da abun da yake yi Asiya tayi murmushi ta ce “Ya Umar mun zo wajen Fatima ne” “Zahra tana sama.” Shi kaɗai ya faɗa, ya maida hankalinsa kan laptop ɗinsa. Firdausi ta yi ƙasa da murya “Wai kullum haka yake ne?” Asiya ta danne dariya “Mu tafi kawai.” Suka haura sama. Da suka shiga ɗakin Zahra Dukansu suka tsaya cak, Idanunsu yana yawo cikin ɗakin gashi babu kowa Firdausi ta buɗe baki “Zahra na jin dad’i gaskiya” Asiya ta taɓa labulen “Ni kam ban taɓa ganin ɗakin da ya haɗu haka ba, sai kace amarya?” Kafin su ƙara magana… Ƙofar toilet aka buɗe Zahra ta fito cikin doguwar rigarta zuwa gwiwa, Tana goge hannunta towel dake ɗigon ruwa Da ganinsu… Ta yi wata irin dariya. “Asiya! Firdausi!” Da sauri suka rungume juna. Firdausi ta sake kallon ɗakin. “Ke, wannan ɗakin naki ne ko an baki wani sabon apartment ne aro?” Zahra ta yi dariya. “Wallahi ni ma da na dawo sai da na yi mamaki, aikin Abbah ne fah Asiya ta gyad’a kai “Abbahnki yana ji da ke.” Dariya Zahra tayi ta ce “Mu je wajen Mami ku gaisa sai mu dawo” Daga haka Duk suka nufi side din Mami, suna shiga parlourn Mami… Ta tarbe su da fara’arta kamar yadda ta saba. “Ah, baƙin Zahra ne ko nawa?” Suka gaishe ta cikin ladabi, ta amsa cikin fara’a. Mama Ladi ce ta shigo kawo wa Mami fruit, Zahra ta juya ta kalleta “Mama Ladi, dan Allah ki dafa mana lunch mana” Mama Ladi ta yi murmushi. “To Anty Zahran mu, farin cikin Abbahnta” Mami ta girgiza kai tana dariya, itama murmushin tayi Zahra ta yi murmushin kunya Zahra ta mike tace “Ku zo muje can” Sosai suka zauna suka sha hira a dakin Zahra, can aka kawo musu abinci, suka zauna suka ci tare Firdausi ta tattara plates ɗin bayan sun gama “Asiya, bari ni na kai kitchen.” Ta riƙe plates ɗin ta nufi stairs, Asiya ma ta mike ta kwashe cups ta bita a baya Sai dai… Da take saukowa, ba ta lura da wani step ba, Ƙafarta ta kauce, ta yi missing step. Kafin ta kai ƙasa… Ta faɗo jikin wani Plate ɗin ya karkata, amma bai zube ba Ta ɗaga kai da sauri. Ya Umar ne Ya riƙe ta kada ta faɗi Tana daidaita tsayuwarta… Sai ya sake ta. Ya gyara rigarsa kaɗan, sannan ya kalle ta da idanunsa masu sanyi Firdausi ta haɗiye yawu “I’m… I’m sorry.” Ya Umar ya ci gaba da kallonta na wasu daƙiƙu, Sannan ya ce cikin murya mai nutsuwa “Ki koyi tafiya a hankali…” Ya ɗan dakata yana kallonta “…as a lady, bai kamata kina acting like namiji ba”Yana gama magana ya wuce ba tare da ya ƙara kallonta ba Firdausi ta tsaya tana binsa da wani irin kallo, ta murguɗa masa baki “Mtsss Malam sai uban zafi, shi ko Baki bai sani ba” A hankali ta faɗa. Asiya ta cije leɓenta kada ta yi dariyar dake cinta Zahra kuwa da saukowarta kenan Tun da ta ga abin da ya faru, ta kasa riƙe dariyarta, ta riƙe cikinta “Wallahi ku biyu…Ban san me ya sa, ba ku taɓa jituwa ba.” Firdausi ta taɓe baki “Ni ma ban sani ba, Kullum kamar ni kaɗai yake ganin mai laifi” Zahra ta sake fashewa da dariya “Wallahi drama ɗinku yana bani joy” Firdausi ta gyara plates ɗin “Ni dai bari na kai kitchen.” Zahra ta wuce parlo Asiya na biye da ita a baya Suka zauna a parlour suna hira na ɗan lokaci, a haka Firdausi tazo ta same su Da rana ta fara ja… Asiya ta ce “Ya kamata mu tafi.” Firdausi ta gyada kai. Suka miƙe tare Zahra ta ɓata fuska ta ce “Allah Sarki, har naji babu ɗaɗi” sai kuma ta gyaɗa kai Lemme talk to Mami sai ku mata sallama, wajen Mami suka nufa, bayan sun shiga parlonta da sallama “Mami, za mu tafi.” Mami ta yi murmushi ta ce “Har zaku tafi? Allah ya kiyaye hanya. Bari Ina zuwa” “Ameen” suka amsa mata suna murmushi Ta miƙe ta wuce ciki bata wani daɗe ba ta dawo rike da nylon a hannunta, ta miƙa musu “Ku riƙe wannan ba yawa” Suka karɓa suna mata godiya Daga nan Zahra ta ce, “Ku zo mu je gaida Abbah na” daga haka suka ma Mami sallama suka fita Har study room na Abbah Zahra ta kai su, da sallama suka shiga Abbah ya ɗago ya yi musu murmushi “Ah… ƙawayen Baby ne ashe” Suka gaishe shi cikin ladabi da kunya ya amsa yana tambayar su ya gida Zahra na kallonsa ta ce “Abbah tafiya zasu yi shine na kawo su su gaishe ka” “Ma shaa Allah” ya ce Ya saka hannunsa a aljihu ya ciro kudin da bai dan nawa bane ya mikawa Fatima ya “Suyi kudin mota” Suka amsa cikin farin ciki, sannan Zahra ta raka su har bakin gate, suka yi sallama Daren ranar… Bayan an idar da sallar Isha’i, gidan ya yi shiru kamar yadda ya saba Abbah bai shigo daga masallaci ba, Mami kuma tana side dinsa tana gyarawa A parlour kuwa… Ya Umar na zaune kan doguwar kujera, laptop ɗinsa a gabansa yana duba wasu files na office. Sai dai… kusan minti goma kenan bai samu ya karanta ko shafi guda ba Saboda….. “Yaya…” Muryar Zahra ta katse masa tunani Ya ɗaga kai. Ta karasa ta zauna kusa da shi, ta jingina da kafadunsu, bayanta kuma na jingine da kujera tana murmushi “Na’am.” Ta ɗan lumshe ido. “Yaya…” “Eh?” “Wai me ya sa kai da Firdausi ba ku taɓa jituwa ne?” Ya Umar ya ɗan haɗe gira. “Waye kuma ita?” Dariya sosai tayi ta ce “Wannan Black beauty friend dina mana da kullum idan ta zo sai kayi mata masifa” Da kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce “Waye ya ce miki ba ma jituwa?” Ta fashe da dariya “Ni mana! Kullum idan ta zo gidan nan sai ka dinga mata irin kallon nan…” Ya ci gaba da duba laptop ɗinsa ba tare daya kulata ba Ta matsa kusa da shi kaɗan “A’a… Ka faɗa min gaskiya ni dai” “Baby…” Ta yi saurin katse shi “Please Yaya…” Ya sauke ajiyar zuciya. “Kin san ranar farko da kika kawo su gidan nan?” Ta gyada kai “Eh.” “Da ta shigo… Ba ta yi sallama yadda ya kamata ba.” Zahra ta zaro ido “Really?” “Eh.” “Na yi mata magana cikin ladabi.” “Ta kuma ba ni amsa cikin salon rainin wayo.” Zahra ta tuna Sai ta fara dariya. “Ai Firdausi haka take idan ta ji kunya.” Ya Umar ya ɗaga gira “Ni ban san kunya ba, abin da na sani shi ne mutum ya san yadda zai yi magana.” Ta riƙe cikinta tana dariya “Shi ya sa kullum idan kun haɗu… “…ku ke kallon juna kamar za ku yi faɗa?” Ya Umar ya ɗan murmusa “Ba faɗa ba ne. Character correction ne” Zahra ta fashe da wata irin dariya “Wallahi Yaya… kai ma akwai taurin kai, halinku ne daya” Ya ware idanu yana kallonta “Me abun dariya anan?” “Ta yi missing step yau saboda kai ne maybe, kasan haka ake a india fah” “It’s Okayy?” “Eh mana” Ta kwaikwayi fuskarsa da maganarsa “‘Ki koyi tafiya a hankali… as a lady…” Ta kwaikwayi yadda ya faɗa har da haɗe gira. Ya Umar ya kasa riƙe dariyarsa “Baby… Allah kin raina ni.” “Ni? Aa rufamin asiri” Ta ci gaba da dariya tana ɗan bugun kafaɗarsa da tafin hannunta A dai-dai lokacin… aka bude Ƙofar parlour, Mummy ce ta shigo Sai yanzu ta dawo daga fitarta na safe Tun daga ƙofar… Idanunta suka sauka kan Zahra da Ya Umar Ta tsaya cak Fuskarta ta canja Ba tare da ta ce komai ba… ta ƙarasa gabansu da sauri. Tas! Sautin marin ya amsa cikin parlour gaba daya Zahra ta rikice ta dafe kumatunta da sauri, ta ɗaga idanunta cikin mamaki “M… Mummy…” Mummy ta nuna ta da yatsa. “Dan ubanki, kar na sake ganin kina manne wa ɗana! Shegiya! Yarinyar sai shegen son maza” Ya Umar ya miƙe tsaye da sauri. “Mummy! Kiyi haƙuri mana amma wannan words din yayi karfi” Mami ta fito daga corridor da sauri, da alama marin ne taji ta fito Da ta ga Zahra riƙe da kumatunta… Idanunta suka sauya nan take, ta ƙarasa cikin sauri Ta tsaya gaban Mummy Murya a sanyaye, amma cike da tsauri ta ce, “Don’t dare you. Kar ki sake daga hannu ki buga min ’ya!!! Abin ya isa haka. Ni ban taɓa dukan miki ɗa ko ɗiya ba” Parlour ya yi shiru Ya Umar ya tsaya kamar an dasa shi, kunyar abin da ya faru ta hana shi magana. Mami ta kama hannun Zahra a hankali, ta ja ta zuwa bayanta Sannan ta kalli Mummy dake mata wani banzan kallo “Zahra fa yarinya ce, kar ki manta shekara goma sha bakwai take yanzu, Idan kina ganin laifi ne ta yi dariya da Yayanta da suka taso tare tun tana ƙarama… to ni ban ga wannan laifin ba dan kallon Uba take masa” Ta ɗan dakata Sannan ta ci gaba da cewa, “Idan kina maganar tarbiyya ne… Ki fara lura da Yayarta da take fita sai can dare ta dawo, ki fara daga nan kamar zai fi miki a matsayin uwa” Mummy ta matso gabanta “Har kin isa kina yi min magana haka?” Mami ta ce a nutse, “Na faɗi abin da na ga ya dace ne” Mummy ta nuna Zahra. “Toh ki ja wa ’yarki kunne. Kar na sake ganinta tana manne wa ɗana.” Mami ta yi murmushi mai sanyi. “Idan kin isa… Ki raba ɗanki da ita mana.” Mummy ta ce “Na dai faɗa miki next time mataki zan dauka kafin ta lallata min d’a” Mami tayi dariya “Tabbas’yar shekara 17 itace ake cewa zata lalata d’an 27 yrs! We’ll Allah ma ya tsare min ‘ya dan nasan tarbiyyar dana bata” Mummy ta cije leɓenta cikin takaici. “Ke… Kin raina ni ma, kar kiyi wasa zaman gidan nan ma ya gagare ki” Mami ta girgiza kai. “A’a! Ba ni da lokacin gardama da ke, amma bari na tuna miki da bokanki na aiki ai da tuni kin cire Ni ke kuma kin zauna a dakin ki” Daga haka ta juya ta kalli Zahra ta kama hannunta, ba tare da ta sake waiwayowa ba… Ta wuce da ita zuwa ciki Ya Umar ya tsaya a wurin yana kallon Mummy Ya sauke ajiyar zuciya “Mummy…” “Wallahi bai kamata…. Ta ɗaga masa hannu. “Karka ce min komai. Ai kai ne ka jawo min Ya rufe baki Ya san duk wata magana a lokacin ba za ta canja komai ba Ya tsaya yana kallon hanyar da Mami da Zahra suka bi… Yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa saboda marin da aka yi wa ƙanwarsa ba tare da wani laifi ba, uwa Uba manyar maganganun da Mummy ta dangan ta wa zahra Mami ba ta tsaya ko’ina ba… Kai tsaye sai ɗakinta. suna shiga… Ta rufe ƙofar a hankali Har yanzu Zahra riƙe take da kumatunta, ba marin ne ya fi mata ciwo ba… Kalaman Mummy ne suka fi tsaya mata a rai. “Tana son maza…” Kalmar ta ci gaba da yawo a kunnenta. Mami ta juyo ta kalleta. Da ganin yadda idanunta suka cika da ƙwalla… Zuciyarta ta taɓu “Zo nan…” Ta buɗe hannuwanta Zahra ta ƙarasa da sauri ta faɗa jikinta. Nan take ta fashe da kuka. kuka irin na wanda aka taɓa zuciyarsa Mami ta rungume ta sosai. Hannunta na shafa bayanta a hankali. “Shhh… Ya isa haka, Karki ƙara kuka haka” Sai dai Zahra ta ƙara manne mata. “Mami…” Muryarta na rawa. “Ni ban yi komai ba ta mare ni “Na sani.” Mami ta amsa ba tare da wata-wata ba “Wallahi na sani.” Ta ɗago fuskarta tana share hawayen Zahra da yatsunta “Kinga ni.” A hankali Zahra ta ɗaga idanunta. “Kin ji tsoron abin da ta faɗa akan ki rabu da Yayanki?” Ta girgiza kai kaɗan Sai kuma ta gyada “Gaskiya… Na ji.” Mami ta yi murmushi mai cike da tausayi “To ki cire wannan tsoron daga zuciyarki! Kin ji?” Ta yi shiru. Mami ta ci gaba “Ya Umar yayanki ne. Jinin Abbahnki ne Kun taso tare tun kina jaririya Ba yau kuka fara hira ba Ba yau kika fara dariya da shi ba” Ta ɗan shafa kanta “Saboda haka…” “Kar ki bari maganar kowa ta sa ki fara jin kamar ba daidai bane dan kina kallonsa a yayanki Kin fahimce ni?” Zahra ta goge idanunta. “A’a Mami… amma Ina tsoron kada ya ji haushi.” Mami ta ɗan yi murmushi. “Ya Umar?” Ta gyada kai. “Wallahi shi ne mutum na ƙarshe da zai ji haushinki! Na san shi Yana sonki fiye da yadda kike zato.” Ta ɗan ɗaga haɓarta. “Don haka… Kada ki canja yadda kike mu’amala da shi saboda abin da aka faɗa yanzu, ki ci gaba da girmama shi, ki ci gaba da ɗaukarsa a matsayin yayanki.” Zahra ta sauke numfashi Sai ta jingina kanta a kafaɗar Mami “Mami…” “Hmm?” “Nagode.” Mami ta sumbaci goshinta “Ba zan taɓa bari wani ya karya miki zuciya ba matuƙar ina numfashi.” Sai ta ɗan ja baya ta kalleta “Wuce ki wanke fuskarki. Ba na son Abbahnki ya shigo ya ga idanunki sun kumbura.” Da jin sunan Abbah… Sai Zahra ta yi murmushi “Idan ya gani fa?” Mami ta yi dariya. “Toh ni zan shiga uku domin zai fara tambayata ko me ya sa na barki kina kuka.” Dukansu suka yi dariya. Mami ta share mata sauran hawaye, ta gyara mata hulanta Ta rungume ta sau ɗaya kafin ta juya zuwa toilet domin ta wanke fuskarta. FARASHIN IZZAH 08110615256 Chapter 39 Mummy na zaune a ɗakinta ita kaɗai Ƙofar balcony ta ɗan buɗe, iska mai sanyi na shigowa tana kaɗa labulen ɗakin Wayarta na manne a kunnenta Muryarta ta yi ƙasa sosai, tamkar ba ta son ko bango ya ji abin da take faɗa balle kuma wani “…na faɗa maka kar ka damu.” Ta ɗan yi shiru tana saurare. “A’a… ba yanzu ba” Ta sake yin shiru Sai kuma ta ce “Zan sake kiranka idan na tabbatar” A dai-dai lokacin… Knock! Knock! Ta ɗago kai. Kafin ta yi magana… Aka buɗe Ƙofar a hankali, Ya Umar ne Da ganinsa… Sai ta yi wata irin razana Da sauri ta sauke wayar daga kunnenta, ta katse kiran ba tare da ta yi sallama ba, ta ajiye wayar gefenta cikin sauri Sannan ta ɗago tana kallonsa Idanunta cike da wani irin ruɗani da ta yi ƙoƙarin ɓoyewa. Ya Umar ya ɗan haɗe gira. “Mummy…?” Ta gyara zamanta “Me ya kawo ka?” Ya ɗan yi shiru na wasu daƙiƙu sannan ya ce cikin ladabi, “Na zo ne…na ba ki haƙuri, game da abin da ya faru ɗazu.” Mummy ta kau da kai, ba tare data kalle shi ba, sai ta ce cikin sanyin murya, “Na ji.” Ya jira ko za ta ƙara magana amma ta yi shiru Ya sake cewa, “Mummy, wallahi ba….” Ta katse shi “Na ce na ji.” Sai ta ɗan ɗago kai “Ka je ka kwanta, mu yi magana gobe.” Ya Umar ya kalleta cikin mamaki. Ba wannan amsar yake zato ba, yawanci idan ya zo wajen Mummy, ko da tana fushi, sai ta yi magana masifa especially idan Akan Zahra ce Amma yau… tamkar tana son ya fita daga ɗakin da wuri, sai Sannan reaction dinta daya shigo ya dawo masa, ya dan kalle gefenta sai kuma ya ce “Toh…Sai da safe.” Ta gyada kai kawai, ba ta ƙara cewa komai ba Ya Umar ya juya ya fita, haɗi da kulle mata kofar, yana kulle kofar Mummy ta sauke numfashi a hankali Ta ɗauki wayarta, ta kalli screen ɗin na wasu daƙiƙu sai ta lumshe idanunta… ba tare da ta sake kiran lambar ba. Washegari… Tun bayan data idar da sallar Azahar, Zahra ta shiga ɗakinta ta shirya cikin wata doguwar abaya mai launin maroon, tayi rolling veil, ta ɗauki handbag ɗinta black tare da sanyawa fararen kafarta black flat shoe, sannan ta sauko ƙasa Mami ce ta fara hangota “Ina kuma za ki?” Zahra ta yi murmushi “Gidansu Saudat zan je, Mami.” Mami ta gyada kai “Allah ya kiyaye hanya, amma kar kiyi yamma” “Ameen, Toh Mami” Tana fita compound driver ya taso “Fita ne Hajiya?” Kai kawai ta gyada masa Malam Bala ya buɗe mata ƙofa ta shiga, daga nan suka fice daga gidan Tafiya sosai suka ɗanyi, sannu a hankali suka bar manyan tituna suka shiga cikin unguwannin cikin gari, titunan sun yi ƙunci dakyar motoci ke iya bi ta wajen Gidaje suna manne da juna, ga gidajen kananu Yara na ta wasa a bakin hanya, wasu mata kuma na zaune a ƙofar gidajensu suna hira. Motar ta tsaya a gaban wani ƙaramin gidan haya mai tsohon gate Driver ya sauka ya buɗe mata ƙofa, Zahra ta sauka, ta ɗan ɗaga kanta tana kallon gidan Ba wani babban gida ba ne… Amma an ana ƙoƙarin tsaftace gidan duk da yanayin rayuwar da suke ciki Ta ƙarasa bakin ƙofar da sallama “Assalamu alaikum.” “Wa alaikumus salam.” Wata dattijuwa mai fara’a ta fito zata hanyar kitchen Tana ganin Zahra… Sai fuskarta ta cika da murmushi nan take “Ah… Zahra! Maraba da zuwa, ’yata.” Zahra ta sunkuyar da kai cikin girmamawa tana murmushi “Ina wuni, Mama?” “Lafiya lau, Alhamdulillah.” “Ya gida?” “Lafiya.” Mama ta matsa gefe “Shigo mana Saudat tana ciki.” “Nagode.” Zahra ta shiga, parlourn gidan ƙarami ne, babu komai a cikinta sai tabarma ce shimfiɗe a ƙasa, tare da wasu ɗa pillows a gefe. Ko da ta shiga… ba ta nuna komai a fuskarta ba Ta yi sallama cikin fara’a “Assalamu alaikum.” Da jin muryarta… Saudat ta fito da gudu daga ɗaya daga cikin ɗakunan “Zahra!” Ta ƙaraso da sauri ta rungume ta “Kai! Ban yi tunanin za ki zo ba.” Zahra ta yi dariya “Me ya sa ba zan zo ba?” Suka zauna a kan tabarmar Sai ga Mama ta shigo da ruwa a cikin wani cup kana gani kasan cup din ya jima sosai Ta ajiye gabanta “Ga ruwa, ’yata.” Zahra ta yi murmushi “Nagode sosai, Mama.” Mama na fita… Saudat ta ɗan matsa kusa da ita “Zahra… karki sha.” Ta yi mamaki “Me ya sa?” Saudat ta sauke numfashi “Ba irin ruwan da kika saba sha ba ne kar wani abu kuma ya same ki” Zahra ta kalli cup ɗin Sai ta ɗago ta kalli Saudat, ta yi murmushi “Waye ya ce miki ban sha?” Ba tare da ta ƙara magana ba… Ta ɗauki cup ɗin Ta ce Bismillah a ranta, sannan ta sha. Ko kaɗan ba ta nuna wata alama ta ƙyama ba, amma ba kadan ba taji kamar tana son tayi amai Saudat ta kasa ɗauke idanunta daga kanta “Zahra…” “Me?” Ta yi murmushi kawai. Bayan sun ɗan yi hira… Zahra ta kalli kawarta “Toh…Kin fara shirye-shiryen university kuwa?” Nan take fuskar Saudat ta sauya, ta sunkuyar da kai Na wasu daƙiƙu ba ta ce komai ba Daga ƙarshe ta ce cikin sanyin murya, “Gaskiya… ba na jin zan ci gaba da karatu” Zahra ta haɗe gira “Me ya sa?” “Kin san halin da muke ciki. Mama ba za ta iya ba, Ni ma ba zan matsa mata ba.” Shiru ya ratsa tsakanin su Sai Zahra ta kama hannunta “Saudat…” Ta ɗago kai tana kallonta “If you’re willing to read… I’m willing to help you.” Saudat ta zaro ido “Kina nufin…” Zahra ta katse ta da murmushi “Eh! Registration, school fees, abin da zan iya… Za mu yi tare.” Saudat ta ci gaba da kallonta Kafin ta ankara… Hawaye suka cika idanunta Ta faɗa jikin Zahra ta rungume ta da ƙarfi ta fashe da kuka. “Na gode… Wallahi ban san ya zan saka miki ba.” Zahra ta shafa bayanta a hankali “What are friends for?” Mama ce ta shigo a lokacin Da ta ga Saudat na kuka a jikin Zahra… Ta firgita “Lafiya kuwa?” Saudat ta share hawayenta “Mama… Zahra ce… ta ce za ta taimaka min na ci gaba da karatu.” Dattijuwar ta tsaya cak Idanunta suka cika da ƙwalla. Ta ɗaga hannayenta sama. “Allah… Ya saka miki da alheri, ’yata. Allah Ya buɗe miki ƙofofin alkhairinsa sannan ya baki abokin rayuwa Nagari” “Ameen” Cewar Saudat Zahra ta yi murmushi cikin kunya “Adduan nan yafi komai ai Mama, Nagode kuma a cigaba da mana addua” Kai kawai ta gyada ta gama zama speeches sai kuma ta kira wani ƙaramin yaro “Aliyu!” Yaron ya shigo da gudu. “Na’am, Mama.” “Ga kuɗi nan Je ka siyo mana alale.” “To Mama.” Daga haka ya fice daga parlon, Mama ta wuce ciki Bayan ɗan lokaci… Yaron ya dawo da alalen a wani kwanon roba Mama ta ajiye a gabansu “Ki ci ’yata, namu abincin ba lalle ki iya ci bane” Zahra ta ɗan yi murmushi “Nagode.” Ta ɗauki kaɗan, a hankali ta fara ci Ba saboda tana jin yunwa ba… Sai don kar su ji kamar ta raina abin da suke da shi, kuma bata so tasa suji wani iri da effort dinsu Duk da haka… da ƙyar ta iya cin rabinsa, amma fuskarta cike take da murmushin dole A zuciyarta kuwa… Ta sake godewa Allah daya azurta Abbahnta sannan karo na biyu data sake jin ta tsane talauci kuma bata fatan ko kaddararsa ya same su Can bayan sun sha hira…. Ta ɗauki handbag ɗinta ta miƙe tsaye “Toh Saudat, zan wuce.” Saudat ma ta miƙe “Da wuri haka?” Zahra ta yi murmushi “Ina son na isa gida kafin yamma.” Ta ɗan buɗe handbag ɗinta Ta ciro wani farin envelope mai kauri ta kama hannun Saudat, ta sanya mata shi a hankali Saudat ta haɗe gira “Wannan kuma?” Zahra ta girgiza kai “Karki buɗe yanzu, ki je ɗaki tukuna idan na tafi” Saudat ta kalleta cikin mamaki “Zahra…” Ta katse ta da murmushi “Make sure kin je kin yi online screening, an fara registration, ba na son ki bari lokaci ya ƙure” Saudat ta ji wani iri Ta matse envelope ɗin da hannunta “Amma…” “A’a” Zahra ta sake katse ta. “Ki ɗauke shi a matsayin taimakon da zaki ma ƙawarki.” Hawaye suka sake taruwa a idanun Saudat, ta gyada kai “In shaa Allah ba zan ba ki kunya ba tunda kina so nayi karatu, Allah ya biya ki Zahra” Mama ta fito daga ɗaki daidai lokacin Da ta ga envelope ɗin a hannun Saudat, ta fahimci abin da ya faru. Ta dafe ƙirjinta. “Kaii ‘yar nan…”Ta ƙaraso gabansu “’Yata…Wallahi ban san irin godiyar da zan yi miki ba.” Zahra ta yi saurin kama hannunta cikin ladabi. “Haba Mama Kada ki ce haka.” “Ku ci gaba da yi min addu’a kawai.” Mama tayi murmushi “Allah Ya saka miki da gidan Aljannah, Allah Ya ƙara wa iyayenki lafiya da arziki.” “Ameen Ameen, Nagode” Zahra ta amsa cikin nutsuwa. Ta rungumi Saudat na ƙarshe “Ki kira ni idan akwai wani abu.” “In shaa Allah.” Ta yi sallama da Mama. Sannan ta juya ta fita. Har bakin gate Saudat da Mamanta suka raka ta. Driver ya yi saurin buɗe mata ƙofar motar. Ta shiga Ya rufe ƙofar cikin girmamawa. Da motar ta fara tafiya… Saudat da Mamanta suka ci gaba da daga mata hannu har sai da motar ta ɓace daga ganinsu. Da suka fita daga ƙunƙuntar unguwar suka hau babban titi… Zahra ta jingina bayanta da seat Ta saki wani dogon numfashi. “Alhamdulillah…” Ta lumshe idanunta na wasu daƙiƙu Sai a lokacin ta ji kamar numfashinta ya dawo yadda ya kamata Tun tana gidan Saudat… Ta yi ƙoƙarin kada ta nuna wani abu da zai sa su ji ba daɗi, amma sosai take jin tashin zuciya Ta buɗe idanunta ta kalli tagar motar, a hankali ta yi murmushi A zuciyarta ta yi addu’a, “Ya Allah… Ka yalwata musu arzikinka, Ka sauƙaƙa wa Mama, Ka kuma ba Saudat ikon cika burinta.” Mai gadi ya buɗe gate cikin girmamawa, bayan yaji horn din motar gidan ne Driver ya yi parking a wajen da ake parking motocin gidan, kafin ya fito ya buɗe mata ƙofa… Sai suka hango Abbah. Yana tsaye a gefen wata motarsa tare da wasu ma’aikata biyu, da alama yanzu ya dawo daga office ne Da ya hango Zahra a bayan motar Sai ya ɗaga hannu. “Tsaya.” Driver ya yi saurin kashe motar Zahra ta buɗe ƙofar ta fits Da murmushi ta nufi wajen Abbah. “Abbah na…” Ta daura kanta kafadarsa tana gaishe shi “Lafiya lau, Baby” Ya amsa cikin fara’a. Ya shafa kanta kamar yadda ya saba “Kin dawo?” “Eh.” “Ya gidansu Saudat?” Ta yi murmushi “Lafiya. Mun yi hira sosai.” Ya gyada kai cikin gamsuwa. “Alhamdulillah.” Ta ɗan ɗaga gira. “Abbah…” “Uhum?” “Za ka shiga ciki ne?” Ya girgiza kai “A’a. Sai dai ina son ki yi min wani aiki.” Ta yi saurin amsawa “Toh.” Ya ciro wallet ɗinsa Ya fito da katinsa, sannan ya miƙa mata. “Ki je Dubai supermarket. Akwai wasu abubuwan da nake buƙata.” Ta karɓi katin tana kallonsa cikin mamaki “Ni?” “Eh.” Ta yi dariya “Toh me ya sa ba za ka aika driver ko Ya Umar ba, ka manta ban Iya selecting ba” Abbah ya ɗan yi murmushi. “Saboda ina so ke ce ki zaɓo min su.” Tayi murmushi “Da alama dai yanzu Abbah ya fara yarda da aike na” Ya yi dariya. “Kin yarda?” Ta gyada kai “In shaa Allah.” Ya juya ya kalli driver. “Ka mayar da ita. Sannan ku wuce supermarket ɗin da na gaya maka, Baby ke kuma ki duba WhatsApp dinki” Driver ya gyada kai “Toh, Alhaji.” Zahra ta sake kallon Abbah “Toh ni zan tafi.” “Allah ya tsare.” “Ameen.” Ta koma ta shiga motar. Driver ya kunna motar Motar ta juya ta sake fita daga compound… Yayin da Zahra ke zaune a bayan mota tana mamakin irin aikin da Abbah ya aike ta yi. Dan bai taba aikanta ba Ta jingina da seat tana murmushi a hankali. “Abbah ma sai ya ce ni ce zan zaɓa masa kaya…” Ta girgiza kai cikin dariya. Bayan motar Zahra ta fice daga compound… Abbah ya juya ya kalli mutanen da tun ɗazu suke jiran umarninsa. “Okay…Ku fara.” Kamar an saki tsuntsaye… Kowa ya kama aikinsa Wasu suka fara sauke manyan cartons daga wata delivery van. Wasu kuma suka shiga ɗauko kayan ado. Cikin mintuna kaɗan… Farin compound ɗin ya fara sauya kamanni An ɗaure manyan balloons fari, gold da sky blue a jikin pillars, bakin parlour da kuma hanyar shiga gidan Flower stands masu kyau aka jera a gefuna Wata ƙungiyar decorators kuwa na ta gyara wajen cikin sauri da ƙwarewa Mami ta fito daga parlour Da ta ga yadda ake ta kai-komo… Sai ta yi murmushi “Allah ya sa Baby ta yi farin ciki.” Abbah ya amsa da murmushi. “In shaa Allah, ai Allah yasa tana zuwa na mayar da su can far supermarket kafin su dawo an gama komai” Ana cikin haka bada jimawa ba… Aka ji ƙarar wata babbar mota tana shigowa Sabuwar mota ce fill… Latest version. Har yanzu nylon na jikin wasu sassan cikinta Da aka sauke ta daga carrier… Aka fara yi mata ado. Manyan ribbons masu launin gold da blue aka ɗaura a kanta Aka zagaye ta da balloons masu tsari Da kallo ɗaya… Za ka fahimci cewa an tanade ta ne domin mutum na musamman. Ya Umar ya fito yana kallonta. Ya yi ɗan busa iska “Abbah… wannan kuma?” Abbah ya yi murmushi kawai “Ka bari za ka gani.” Ya Umar ya girgiza kai yana dariya “Baby za ta haukace da murna.” Mami ta amsa cikin fara’a. “Allah ya sa.” A gefe guda kuma… Wasu ma’aikata suka shigo ɗauke da wani babban banner. Da aka buɗe shi… Sai kyakkyawan hoton Fatima Zahra ya bayyana a tsakiyarsa A sama an rubuta da manyan haruffa masu kyau “Happy Birthday To Our Precious Princess, Fatima Zahra.” A ƙasa kuma aka ƙara da saƙo mai taɓa zuciya “May Allah bless your new age with happiness, barakah, success and endless joy. We love you today and always.” Abbah ya tsaya yana kallon banner ɗin Fuskar sa cike da gamsuwa. “Nan…” Ya nuna gefen garden. “A nan za a kafa shi” Nan take suka ɗauke shi suka kafa a inda ya nuna. A lokaci guda… Wata mota ta sake shigowa Caterers ne. Suka fara sauke manyan food warmers ɗaya bayan ɗaya Ƙamshin abinci ya fara gauraye da iskar compound. A wani gefe kuma… An sauko da wata katafariyar birthday cake mai hawa uku. An yi mata ado cikin launukan fari, gold da sky blue. An rubuta a kanta da golden icing “Happy 17th Birthday, Princess Zahra.” Mami ta dafe baki. “Subhanallah… lallai Yau Dear ka nuna min kafi kaunar Zahra da ni, in ba haka ba yaushe duk ka shirya wannan ban sani ba” Abbah ya yi murmushi “Ba ta cancanci ƙasa da haka ba ne. Ke ma idan kishin zaki fara da ita sai na sani” Dariya tayi ba tare data ce komai ba Da komai ya kusa kammaluwa… Abbah ya kira mai gadi Gatekeeper ya ƙaraso da sauri “Na’am, Alhaji.” Abbah ya kalle shi sosai “Da zarar driver ya dawo da Baby…Kada ka buɗe musu gate nan take.” Mai gadin ya gyada kai cikin kulawa. “Toh, Alhaji.” “Ka fara zuwa ka sanar da ni sai bayan na ba ka umarni… sannan ka buɗe gate.” “Na gane. Ba za a samu kuskure ba, In shaa Allah.” Abbah ya gyada kai cikin gamsuwa. “Madalla.” Mai gadin ya koma bakin gate Shi kuwa Abbah ya ɗan yi wa compound ɗin kallo. #FARASHIN IZZAH #Hauwajay writes #08110615256 Chapter 40 Gidan Alhaji Muhammad Nasir ya fara cika da baƙi. Manyan motoci na shigowa ɗaya bayan ɗaya. ’Yan uwa ne, Abokan arziki, harda ma manyan ’yan kasuwa abokan Abbah na cikin da wajen ƙasa Mata cikin kyawawan atamfofi da leshi masu tsada, haka ma Maza cikin shaddoji masu tsada Kowa na shigowa da murmushi, ana gaisawa, ana tarbar baƙi Garden ɗin gidan ya canza gaba ɗaya kamar Wanda ake biki Videographers da photographers kuwa suna ta zirga-zirga, suna ɗaukar hotuna da bidiyo daga kowane lungu Abbah ya ci gaba da kallon agogon hannunsa. Ya Umar ya matso kusa da shi “Abbah… Ina jin ya kamata yanzu sun kusa dawowa.” Abbah ya yi murmushi “Eh… Kuma ina son a ɗauki reaction ɗinta tun daga bakin gate.” Ya juya ya kalli videographer daya ke tunkararsu “Da zarar motarta ta iso…. Kai ka fita, Ka tabbata ka ɗauki komai Daga lokacin da za ta sauko har zuwa lokacin da za ta shigo ciki” Videographer ɗin ya gyada kai “Okay sir.” A can layi kuwa… Motar Zahra ta ƙaraso, Driver ya danna horn Poo! Poo! Sai dai… ko alamar za’a buɗe Gate babu Driver ya sake danna horn Har yanzu…. Shiru Ya ɗan zaro kai ta window. “Mai gadi! Bude mana gate ɗin mana, mu ne fah” Mai gadin ya leko “Yi haƙuri, bari na je na sanar da Alhaji.” Ya juya da gudu ya nufi cikin gida. Driver ya haɗe gira. “Wannan kuma wani sabon tsari ne?” A bayan mota… Zahra ta gaba cika da fushi “Wannan kuma wani irin iskanci ne?” Ta sake kallon gate. Horn ɗin ya sake dannawa Amma har yanzu… ba a buɗe ba “Wallahi… zai gane ni ya shanya ai wannan ma iskanci ne, shi da Abba Dagaa haka ta buɗe ƙofar motar, ta sauka Da sauri ta nufi bakin gate dan ranta ba kadan ba ya ɓaci A dai-dai lokacin… Ta ji wani irin ƙarar ƙananan fan a sama, ta ɗaga kai “Eh?” Wani drone camera ne ke shawagi a samanta, yana zagaye da ita yana ɗaukar bidiyo daga sama. Ta bi shi da kallo cike da mamaki. “Wannan kuma?” Har ta ɗaga hannunta tana ƙoƙarin buga gate… Sai aka buɗe ƙofar Anty Jiddah ce ta fito tana dariya. “Wayyo… Princess har ta fara fushi kenan?” Zahra ta ɗan sake fuska “Anty Jay… Wai me yake faruwa ne? Mun daɗe muna horn, amma dan iskanci an ƙi buɗewa.” Anty Jiddah ta yi dariya. “Haba… shine har ɗan wannan abun zai ɓata miki rai princess?” Ta kamo hannunta “Zo mana” Zahra ta bi ta da ido Har yanzu dai ba ta fahimci komai ba. Suna shiga cikin compound… Kafafunta suka tsaya cak, Idanunta suka sauka kan wani babban banner Idanunta na bin hotonta dake jikin da kuma wishes message na jikin Numfashinta ya ɗan tsaya na wasu dakiku “Wai…” Ta ƙara ɗaga idanunta tana kallon Balloons, Flowers, Kayan ado, Manyan tebura, Baƙi, Photographers, Videographers Sai ta rasa inda za ta fara zuwa, ta juya a hankali “Abbah…?” Muryarta ta fito can ƙasa saboda she’s speechless A dai-dai lokacin… sai aka fara tafawa Taf! Taf! Taf! Dukkan baƙin suka miƙe tsaye suna murmushi, suna kallonta. A tsakiyarsu… Abbah ya fito, sanye cikin wata farar shadda mai matuƙar ido Fuskarsa cike da murmushi irin na uba mai alfahari da ’yarsa. Ya buɗe hannayensa “Happy Birthday… My Princess.” Zahra ta tsaya tamkar wacce aka dasa, ta kai hannu ta rufe bakinta Idanunta suka cika da ƙwalla nan take “Abbah…” Ta faɗa da ƙyar Ta girgiza kai kamar wacce ba ta yarda da abin da idanunta suke gani ba “All this…” “…for me?” Abbah ya yi murmushi “Everything…” “…is for you, Baby.” Kafin ya ƙara cewa wani abu… Zahra ta yi gudu taje ta faɗa jikinsa da ƙarfi, ta rungume shi gam Hawayen farin ciki suka gangaro a fuskarta “Thank you, Abbah…” “Thank you so much… and I love you more than life itself” Abbah ya rungume ta yana shafa bayanta “Allah Ya ƙara miki albarka…” “Ya sa ki zama abin alfaharinmu kullum.” Mami ta share hawayen farin cikinta Ya Umar kuwa ya yi dariya yana girgiza kai “Na gaya muku…” “Baby za ta yi kuka.” Dukkan wajen ya kaure da dariya da tafi… Har yanzu Zahra na manne a jikin Abbah tana kuka irin na farin ciki Ba ta ma san lokacin da hawayenta suka jike gaban shaddarsa ba. Abbah kuwa bai damu ba Sai shafa bayanta yake cikin kulawa irin ta uba. “Ya isa haka, Baby…” “Yau ai ranar farin ciki ce” Ta ɗan janye jikinta kaɗan, amma har yanzu hannayenta na riƙe da hannun Abbah tamau. Ta share hawayenta tana dariya lokaci guda. “Wallahi ban yi tunanin haka ba. Ko kaɗan.” Abbah ya yi murmushi. “Shi ya sa muka ɓoye miki.” Daga bayan Abbah… Sai aka ji wata murya. “Ai idan mun gaya miki, ina armashin surprise ɗin?” Zahra ta ɗago kai da sauri “Yaya!” Ya Umar ne sanye cikin wata shadda navy blue mai matuƙar kyau ga ɗaukar ido, yana taku a hankali yana murmushi Da ya iso gabanta… Sai ya buɗe hannayensa. “Birthday girl…” Ba ta bari ya ƙarasa ba ta yi saurin faɗawa jikinsa ta rungume shi da ƙarfi “Yaya… Nagode sosai… Wallahi ban san me zan ce muku ba ba.” Ya Umar ya yi dariya yana shafa kanta “Aikin Abbah ne kaɗai” Ta ɗan janye tana kallonsa “Amma na san kai ma kana ciki.” Ya ɗaga kafaɗa cikin wasa “Maybe…” Ta ɗan bugi kafaɗarsa “Ai ba faɗin gaskiya zaka yi ba” Ya yi dariya “Okay… Na amsa laifi na Dukkan mutanen wajen suka yi dariya A dai-dai lokacin… Mami ta fito daga cikin baƙin Sanye take cikin wata doguwar atamfa mai launin champagne gold, veil d’in ya yi matuƙar ƙara mata kwarjini Tun daga nesa… Fuskarta cike take da murmushi. Da Zahra ta hango ta… Sai ta saki hannun Ya Umar “Maamiiii…” Ta nufi inda take da gudu Mami ta buɗe hannuwanta, Zahra ta faɗa jikinta ta rungume ta sosai Mami ta sumbaci goshinta cikin ƙauna “Happy Birthday, Princess Allah Ya ƙara miki shekaru masu albarka. Ya sa ki zama abin alfahari duniya da lahira.” “Ameen…” Zahra ta amsa tana goge hawayenta Mami ta ɗan ja baya ta riƙe fuskarta da tafukan hannunta Ta kalleta daga sama har ƙasa. “’Yar kyakkyawa. Allah Ya tsare miki wannan kyawun.” Ya Umar ya yi saurin cewa cikin dariya, “Mami… Don Allah kada ki fara kuka yanzu, ba ke ce ake yi wa birthday ba.” Mami ta harare shi. “Waya tambayeka? Wai kai ka fi kowa surutu ne?” Dariya ta sake kaurewa a wajen Abbah ya girgiza kai yana kallonsu “Baƙi fa na jiran birthday girl.” Zahra ta juyo ta kalli Abbah. Sai ta yi murmushin da ya haskaka fuskarta gaba ɗaya. Anty Jiddah ta yi dariya tana tafa hannuwanta. “Eh haka ne kuma fah! Baƙi fa duk suna jiran birthday girl.” Ta kama hannun Zahra “Zo da sauri, muje, kafin ki kije ki gishe da Mamas and Babas dinki” Ba tare da Zahra ta samu damar tambayar inda za su ba, Anty Jiddah ta ja ta zuwa ciki suka haura sama, ɗakinta suka shinge Wata garment bag ta ciro daga kan gado, ta buɗe ta a hankali Zahra ta zaro idanu tana kallon kayan “Wooow…” ta furta Doguwar gown ce mai launin baby pink, an yi mata aiki da stones masu kyalli na azurfa a wuya da hannaye, yayin da ƙasan rigar ke shimfiɗewa cikin tsari irin na princess Anty Jiddah ta yi murmushi. “Wannan ce dress ɗinki na yau. Ki sa ki fito.” Zahra ta dafe ƙirjinta “Anty Jay… Kin san ban son abubuwa masu yawa a kaya” Anty Jiddah ta taɓe baki “Toh Yau kuma a haka muke son ganinki, dole ki saka. Ki hanzarta.” Bayan wasu mintuna… Zahra ta fito daga ɗakinta Rigar ta zauna a jikinta tamkar an zana mata ita Pink ɗin ya ƙara fito da hasken fatar jikinta Ɗan makeup mai sauƙi da Anty Jiddah ta mata ya ƙara mata kyau sosai Anty Jiddah ta dafe baki “Ma shaa Allah … Princess kenan.” Ko Zahra kanta sai da ta yi murmushi tana kallon kanta a mirror “Na yi kyau ne?” Anty Jiddah ta yi dariya “Kin yi mana Wallahi idan ba na nace ba kawai a aurar da ke yau.” Dukansu suka yi dariya, da suka sauko ƙasa… Sai aka fara tafi Taf! Taf! Taf! Baƙi suka miƙe tsaye suna murmushi Photographers suka yi ta ɗaukar hotuna. Videographers kuwa suna ta zagayawa suna kama kowane motsinta Ya Umar ya ƙaraso gabanta Ya miƙa mata hannunsa cikin girmamawa. “My Princess.” Ta yi murmushi ta saka hannunta cikin nasa. Ya ja ta a hankali Suka fara zagaya tsakanin baƙin tana gaishe su, wasu ma bata dan su ba, Fatan alkhairi kawai suke mata “Allah Ya ƙara shekaru masu albarka. Allah Ya cika miki burinki.” Ta na amsawa cikin fara’a da ladabi “Nagode sosai! Ameen.” Bayan ta gama gaisawa da manyan baƙin… Ya Umar ya dawo da ita tsakiyar taron A nan ne aka kawo katafariyar birthday cake mai hawa uku. Kowa ya fara rera “Happy Birthday to you… Happy Birthday dear Zahra…” Wajen ya kaure da dariya Zahra ta yi ta dariya tana girgiza kai. Abbah ya tsaya a bayanta Ya ɗora hannunsa a kan nata. “Ready?” Ta gyada kai tana murmushi A tare suka riƙe wuƙar, ta yanke cake ɗin Nan take… Tafi ta sake kaurewa. Flash na cameras suka cika wajen Wasu na ɗaukar pictures. Wasu na recording videos. Ya Umar ya ɗan shafa cream kaɗan a kumatunta. Ta zaro ido. “Yayaa!” Kafin ta rama… Ya riga ya matsa baya yana dariya. “Ba za ki same ni ba.” Dariya ta sake cika wajen. Bayan komai ya ɗan lafa… Abbah ya matso kusa da ita. “Baby.” “Yess Abbah?” “Zo mu je.” Ta bi shi ba tare da tambaya ba Ya tsaya a bayanta. Ya ciro wani silk scarf. “Rufe idanunki.” Ta yi dariya “Abbah… Wani surprise kuma?” “Ki yi biyayya.” Ta lumshe idanunta Ya ɗaure mata scarf ɗin a hankali. Sannan ya kama hannunta “Ku ba mu hanya.” Baƙi suka matsa gefe. Shi kuwa ya riƙe hannunta cikin kulawa. Yana tafiya a hankali Ita kuma tana binsa tana murmushi “Abbah… Ina za mu?” “Ki yi haƙuri. Mun kusa.” Da suka isa… Ya tsaya Ya juya ta, ta fuskanci wani wuri. Sai ya kwance scarf ɗin daga idanunta a hankali. “Open your eyes…” Zahra ta buɗe idanunta. Na farko… Ba ta fahimci abin da take gani ba Sai da ta ƙara lumshewa ta sake buɗewa. Wata sabuwar mota ce Latest model. An yi mata ado da manyan ribbons masu launin pink da gold, Balloons sun zagaye ta. A saman bonnet ɗinta an rubuta da furanni “Happy Birthday, Princess Zahra.” Numfashinta ya tsaya Ta kai hannunta kan bakinta Idanunta suka cika da hawaye. Ta juya a hankali ta kalli Abbah. “Ab… Abbah…” Muryarta ta kasa fitowa sosai. Ta sake kallon motar, ta sake kallon Abbah. “Wai… …tawa ce?” Abbah ya yi murmushi mai cike da ƙaunar uba. “Eh! Ke kaɗai, Kyautarki ce.” Hawaye suka gangaro a kumatun Zahra ba tare da ta iya hana su ba. Ta girgiza kai tana murmushi. “Wallahi…” “Ban taɓa tsammanin haka ba.” Ta yi saurin rungume Abbah da ƙarfi. “Nagode…” “Nagode sosai, Abbah.” “Allah Ya saka maka da Aljannah.” Abbah ya shafa kanta cikin tausayawa “Babu abin da ya fi faranta min rai…” “…sama da ganin murmushinki, Baby.” A bayansu kuwa… Tafi, ihu na murna da walƙiyar cameras suka sake cika sararin gidan, yayin da kowa ke kallon Zahra cikin farin ciki da yi mata fatan alheri. Zahra kuwa ta kasa cire idanunta daga kan motar A hankali ta matsa gabanta. Tamkar mai tsoron kada abin da take gani mafarki ne. Ta kai yatsunta ta shafi bonnet ɗin motar. Sanyi ya ratsa tafin hannunta Sai ta yi murmushi tana girgiza kai. “Abbah…” “Da gaske tawa ce?” Abbah ya saka hannu cikin aljihunsa ya ciro wani ƙaramin velvet box. Ya buɗe shi Key ɗin motar ne a ciki. Ya ɗaga shi yana murmushi “Ki karɓi kyautarki, Princess.” Wajen ya sake kaurewa da tafi “Taf! Taf! Taf!” Zahra ta dafe bakinta Ta karɓi key ɗin da hannaye biyu Ta jingina shi a ƙirjinta. Kafin ta sake rungume Abbah. “Allah Ya bar min kai. Allah Ya saka maka da mafificin alkhairi.” “Ameen.” Abbah ya amsa yana shafa kanta. Mami ma ta matso kusa da su. Idanunta sun yi ja saboda farin ciki. Ta ɗora hannunta kan kafaɗar Zahra. “Ki gode wa Allah, Baby.” “Duk wata ni’ima tana tare da godiya.” Zahra ta gyada kai da sauri. “In shaa Allah, Mami.” “Alhamdulillah… Alhamdulillah…” Ya Umar ya zo ya tsaya a ɗayan gefenta. Ya miƙa mata hannu “Congratulations.” Ta yi dariya ta rungume shi “Thank you, Yaya.” Ya ɗan karkata yana raɗa mata a kunne “Yanzu dai ba za ki dame ni da cewa ‘Yaya ka siya min mota’ ba ko?” Ta tura shi da ɗan ƙarfin wasa “Ni ban taɓa cewa ka siya min mota ba. Amma da ka saya ma zan karɓa.” Ya Umar ya ɗaga hannu. “Kun ji ta ko? Wannan yarinyar ba ta da kunya wajan cinye min kuɗi” Dariya ta sake cika wajen. Anty Jiddah ta yi saurin cewa, “Okay! Lokacin pictures ya yi.” Nan take photographer ya shirya. Abbah da Zahra Ta tsaya gefensa tana riƙe da key ɗin motar. Flash! Sai Mami ta shiga. Flash! Ya Umar ya shiga. Flash! Sai aka kira sauran ’yan uwa, ana ɗaukar group pictures. Bayan hotuna… Abbah ya ɗauki microphone. Hayaniya ta yi ƙasa. Kowa ya juya yanay, Ya gyara tsayuwarsa “Alhamdulillah… Dukkan yabo ya tabbata ga Allah! Yau rana ce ta musamman a gare ni.” “Ba don an yi birthday ba kawai…Sai don Allah Ya ba ni ’ya da kullum take ƙara sa ni alfahari.” Ya juya ya kalli Zahra. “Baby… Duk abin da nake yi miki…” “Ba don ina son in nuna wa duniya wani abu ba ne, Ina yi ne saboda kina da tarbiyya, da kuma sanya min murmushi a fuskata da ko Yaushe kike yi” “Kuma kina ƙoƙarin zama abin da zai amfani addininki da al’ummarki.” Idanun Zahra suka sake cikowa da ƙwalla, ta sunkuyar da kai cikin kunya. Abbah ya ci gaba, “Ina roƙon Allah…” “Ya ci gaba da tsare miki ke. Ya ba ki ilimi mai amfani.” “Ya sa ki zama haske ga iyalanki da duk wanda ya san ki.” “Ameen…” Kowa ya yi tafi Mami ta share hawayenta, tabbas Wanda yayi hakuri zai ga ribarsa Ya Umar ya yi murmushi cike da alfahari Shi kuwa Abbah ya sauko daga inda yake tsaye. Ya kamo hannun Zahra. Ya sumbaci goshinta cikin tausayawa irin na uba. #FARASHIN IZZAH #08110615256 Chapter 41 Ana cikin raha da ɗaukar hotuna… Sai aka ji ƙarar wata mota ta tsaya a bakin gate Gatekeeper ya buɗe gate. Motar ta shigo a hankali Tana tsayawa, wani dogon saurayi ya fito sanye da wata ash-colour shadda mai matuƙar kyau. Fuskarsa cike da murmushi. A bayansa kuma wata kyakkyawar budurwa ce ta fito cikin Abaya mai launin lavender. “Ya Ims!” Zahra ta faɗa da ƙarfi tana dariya, ko jira ba ta yi ba… Ta ɗaga gown ɗinta kaɗan ta yi gudu zuwa wajensu Ya Imran ya buɗe hannuwansa, ta faɗa jikinsa Ya rungume ta kamar ƙanwarsa ta jini “Happy Birthday, Princess. Allah Ya ƙara miki shekaru masu albarka.” “Ameen…” Ta amsa tana murmushi Ya ɗan ja hancinta cikin wasa “Duk da ke kin manta da mu, Weekend ɗaya kika yi a gidanmu kika gudu, baki sake zuwa ba” Ta taɓe baki “Ni? Toh ai ku ko zuwa mana baku yi” Ya yi dariya “Toh shi kenan.” A dai-dai lokacin… Iklima ta ƙaraso “Toh ni fa? Ni ba za ki rungume ni ba?” Zahra ta saki Ya Imran da sauri “Iklimatyyy!” Ta rungume ta da ƙarfi “Na yi missing ɗinki wallahi.” Iklima ta yi dariya “Ni ma. Ai ban gane ki ba, na ɗauka amaryace fah” Zahra ta ɗan bugeta a kafaɗa “Ki bar ni.” Dukansu suka yi dariya. Uncle Moh ma ya fito daga motar tare da anty Maryam Abbah ya ƙarasa wajensa Suka rungumi juna cikin farin ciki. “Lale marhabin.” Su Mami ma suka je suka gaisa da su. Nan take wajen ya sake ɗaukar armashi. Ya Imran ya ciro wani ƙaramin gift bag, ya miƙa wa Zahra. “Wannan kuma daga gare Ni ne.” Ta karɓa tana murmushi “Nagode sosai.” Ta juyo ta kalli Iklima. “Ke ma kina ciki ko?” Iklima ta ɗaga gira “Eh mana. Ni ce ma na zaɓa.” Ya Imran ya yi dariya “Karya take.” Suka fara gardama Zahra ta riƙe cikinta tana dariya. Aka cigaba da shagali Ƙananan yara na ta gudu tsakanin balloons. Manya na hira While Photographer bai daina aikin sa ba Ya Umar da wasu abokansa suna ta karɓar baƙi Mami da Anty Jiddah suna kula baki mata Da magariba ta yi… Baƙi suka fara sallama ɗaya bayan ɗaya Kowa na zuwa ya sake yi wa Zahra fatan alheri. “Allah Ya sa ki gama da duniya lafiya.” “Allah Ya baki Miji nagari.” “Allah Ya ba ki ilimi mai amfani.” Ta riƙa amsawa cikin ladabi “Ameen.” “Nagode sosai.” Uncle Moh ya rungumi Abbah kafin tafiyarsa. “Da dukkan alamu Yau ka faranta mata rai.” Abbah ya yi murmushi “Farin cikinta shi ne farin cikina.” Ya Imran ya ɗan murɗe kunnen Zahra cikin wasa “Ki kula da kanki.” Ta yi dariya “Kash! Wannan fah cin zali ne” Iklima ta sake rungume ta “Ki kira ni idan kin samu lokaci, akwai gist” Kai Zahra ta gyad’a, daga haka ta rakasu har jikin mota Tass Baki suka gama tafiya, hayaniyar gidan ta lafa. Balloons suna ta motsawa da iskar dare, ma’aikata suka fara tattara tebura da kujeru. Caterers na kwashe kayan aikinsu. Photographers suna nuna wa Abbah wasu daga cikin hotunan da suka ɗauka. Abbah ya kalli hoton Zahra tana rungume da shi. Sai ya yi murmushi. “Madalla.” “Ku tabbatar kun haɗa min komai.” “Ba zan so a rasa ko da hoto ɗaya ba.” “Okay sir.” A gefe guda kuma… Zahra ta tsaya ita kaɗai tana kallon motarta. Key ɗin na hannunta. Har yanzu ba ta yarda cewa duk wannan nata ne ba, ta shafa bonnet ɗin motar a hankali, ta yi murmushi. Sai ta ɗaga idanunta zuwa sararin sama “Alhamdulillah… My Perfect Rabb” Ta faɗa a hankali A zuciyarta… Ta yi addu’ar Allah Ya sa ta kasance ’ya mai anfani ga iyayenta, kamar yadda suke ƙoƙarin ganin farin cikinta a kowane lokaci. A parlour… Mami, Ya Umar, Zahra da Anty Jiddah suna zaune suna kallon hotuna da videographer ya fara tura musu a laptop. Lokaci zuwa lokaci… Dariya na tashi Musamman idan aka ga reaction ɗin Zahra lokacin da ta fara ganin motar. Ya Umar ya riƙe cikinsa yana dariya “Wallahi Baby, fuskar nan taki ta cancanci a saka frame.” Zahra ta turo baki. “Yaya… banso! Kuma ai Ni ban san kuna recording ba” Mami ta yi dariya “Shi ya sa reaction ɗin ya yi kyau.” A dai-dai wannan lokacin… Suka ji ƙarar wata mota ta tsaya a compound. Ba wanda ya kula sosai, sai dai… Bayan ƴan daƙiƙu. Bang! Aka buɗe ƙofar parlour da ƙarfi. “Ashe Yau za’a yi bura’uba!” “Wannan wace irin iskanci ce haka?! Da son kai kiri kiri a fili?!” Muryar Mummy ce ta ratsa parlon gaba daya, kana Jin yadda tayi magana kasan ba karamin ɓacin rai take ciki ba Har sai da Zahra ta firgita, ta juyo da sauri Mummy ta shigo tamkar guguwa Fuskarta a haɗe. Idanunta sun yi jawur. Batoul kuma na bayanta. Tun suna kan hanya suka ji labarin abin da yake faruwa a gidan Amma ganin komai da idanunsu… Shi ne ya ƙara hura musu wutar zuciyarta Da Batoul ta hango Zahra cikin doguwar pink gown ɗinta, har yanzu tana riƙe da key ɗin sabuwar motar… Sai hawaye suka cika mata ido. “Mummy…” Ta faɗa da muryar kuka “Wai da gaske…” Mummy ta yi wani irin tsaki. Ta nuna Zahra da yatsa. “Saboda ke ne za a yi wannan almubazzarancin? Saboda ke ne za’a yi uban taro gaki ’yar goal ko?” Zahra ta tsaya cak, ta rasa me zata ce Kawai idanunta suka cika da ƙwalla Ta matse key ɗin da ke hannunta. Anty Jiddah zata tashi Mami tayi saurin rike ta Muryar Mummy ta sake tashi cikin sananin fushi haɗi da zallar kishi “Yau saboda ke aka tara dangi?” “Aka yi party?” “Aka yi cake?” “Aka kawo mota?” “Wai me kika fi sauran yaran gidan nan ne?!” Batoul kuwa ta fashe da kuka. “Wallahi ba adalci ba ne.” “Ni da nake university…” “Ba a taɓa yi min rabin wannan ba.” Zahra ta ɗaga kai a hankali. Ta buɗe baki kamar za ta yi magana… Sai kuma ta fasa. Ta juya da sauri tana kallon Mami da Ya Umar cikin ruɗani Gabanta ya fara bugawa, ba don ta ji tsoron Mummy ba… Sai don ba ta taɓa ganin ta cikin irin wannan matsanancin fushi ba. Thank God… Kafin Mummy ta ƙara cewa wani abu… Sai aka ji takun tafiya daga corridor Abbah ya fito. Fuskarsa ta canza gaba ɗaya Ya tsaya yana kallon Mummy. Sai ya ce cikin sanyin murya, amma mai cike da iko “Ke! Dalla ki rage ma mutane murya.” Mummy ta juyo tana huci “Me?” Abbah ya matso gaba kaɗan. “Na ce ki rage murya.” “Mutanen gidan nan suna hutawa, kar ki zo ki dame mu, ki damu da maƙwabta, kada ki tashe mana gida da ihu.” Parlour ɗin ya yi tsit. Ko Batoul ta daina kukan da take yi Mummy ta tsaya tana kallonsa. Fuskarta cike da mamaki da takaici. Abbah kuwa bai ɗaga murya ba. Amma yadda ya faɗi kalaman… Ya isa ya sa kowa ya yi shiru Ya juya ya kalli Zahra, muryarsa ta lafa “Baby… calm down! Babu Mai taɓa ki ya kwana lafiya “ Sai ya sake mayar da kallonsa kan Mummy dake uban hararansa, Idanunsa cike da gargadi. “Nan gida ne, ba kasuwa ba Kuma ba zan yarda da hayaniya ba.” Shiru ya mamaye parlour na wasu daƙiƙu. Mummy ta tsaya cak tana kallon Abbah kamar zata dake sa Fuskarta ta yi ja saboda tsananin fushi Numfashinta na fita da ƙarfi Sai kuma ta yi wani ɗan dariyar takaici “Toh kenan…” Ta faɗa tana girgiza kai “Shi ke nan! Har za ka raina ni a gaban mutane? Ka faɗa min maganganun banza marasa kan gado a gaban ‘ya’yan cikina” Abbah bai motsa ba, yana kallonta da mamaki Mummy ta ci gaba, “Wallahi ba zan zuba ido ina kallon wannan banbancin da kake yi ba.” “Ba zan taɓa yarda ba.” “Batoul ma sai an yi mata.” “Ko za’a yi tashin duniya ne” Ta ɗan dakata tana cizon leɓenta. “…kuma sai na ɗauki mummunan mataki a kan abin da yake faruwa a gidan nan.” Parlour ɗin ya sake yin tsit. Abbah kuwa… Sai ya yi murmushi Murmushin mutumin da ya gaji da jin irin waɗannan barazanar. Ya ɗan gyara tsayuwarsa . “Bismillah.” Ya faɗa a nutse “Haka muke son ji.” Mummy ta zaro ido tana kallonsa. Abbah ya ci gaba da magana cikin nutsuwa “Kuma ki saurara da kyau, Hafsat.” “Wannan shi ne karo na ƙarshe da zan yi miki magana cikin natsuwa.” Idanun Mummy suka ƙanƙance. Abbah ya ɗora da cewa, “Idan ba ki yi hankali ba…” “Zaman ki ya zo ƙarshe a gidan nan.” Kalmar ta sauka kamar tsawa haka nan a kunnenta Mami ta ɗan runtse idanunta Anty Jiddah ma ta ɗan kalli Abbah cikin mamaki. Batoul kuwa ta tsaya tana kallon mahaifinta, ta kasa ko motsi. Mummy ta yi wani irin dariya mai cike da takaici. “Ni?” “Za ka kore ni?” Ta girgiza kai. “Toh shi ke nan! Ko ba yanzu ba, amma ku jira.” Ta nuna Zahra da yatsa. “Wacce kuke ɗagawa sama.” “Wacce kuke ganin ita ce cikakkiya.” “Ita ɗin nan…” “Sai ta jawo muku abin kunya.” “Ku tuna maganata.” Ta juya da wani irin huci Fuuuu! Ta nufi staircase ba tare da ta sake waiwayowa ba. Takalmanta na bugun matakala da ƙarfi saboda fushi. Batoul ta share hawayenta Ta yi saurin binta a baya ba tare da ta ce komai ba. Har suka ɓace daga ganin mutanen parlour Na ɗan lokaci… Ba wanda ya yi magana. Sai Anty Jiddah da ta girgiza kai a hankali “Allah ya kyauta” Mami ta sauke numfashi Ita dai ba ta ce komai ba. Ya Umar kuwa… Tun lokacin da Mummy ta fara wannan hayaniyar… Kunyar abin da ya faru ta riga ta kama shi Ya shafa goshinsa, ba tare da ya ce komai ba… Ya juya a hankali Ya fita daga parlour. Zahra ta bi bayansa da kallo. Ta san wannan shirun na Ya Umar… Shi ne mafi girman alamar cewa zuciyarsa ta yi nauyi. Abbah ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci, sai ya buɗe su. Ya kalli Zahra da Mami. Ya tilasta murmushi. “Yau ranar farin ciki ce.” “Ba zan bari wani ya ɓata mana ita ba.” Amma duk da kalamansa… Kowa da ke parlour ya fahimci cewa maganar da Hafsat ta yi ko kadan bai dace ba, a haka kowa ta watse Misalin ƙarfe tara na dare… Gidan ya yi shiru gaba ɗaya. A parlourn Abbah… Shi da Ya Umar ne kaɗai suke zaune. Kofunan shayi ne a gabansu, amma babu wanda yake sha. Abbah ya jingina da kujerar da yake kai. Ya kalli Ya Umar yana murmushi. “Umar.” “Na’am, Abbah.” “Na gama magana da L-Cars.” Ya Umar ya ɗaga kai. “Da safe za su zo su ɗauki motarka.” “Su kai showroom.” “Sannan su kawo maka sabuwar Rolls-Royce Phantom Series II.” Ya Umar ya yi shiru na wasu daƙiƙu Sai ya girgiza kai a hankali. “No, Abbah.” Abbah ya ɗan haɗe gira. “Ban gane ba.” Ya Umar ya yi murmushi. “Ni ina son motata.” “Wannan ta ishe ni.” Abbah ya ce, “Amma me ya sa?” Ya Umar ya ɗan gyara zamansa. “Abbah…Idan saboda an saya wa Zahra mota ne za a canza mini tawa…” “Zan ji kamar duk abin da aka yi mata sai an yi mini makamancinsa.” Ya ɗan yi murmushi “Bayan kuma motar da nake amfani da ita ma ta fi sabuwar tata tsada.” “Dama a gidan nan… Ita ce kadai bata da mota. Yanzu kuma ta samu” Abbah ya yi shiru yana kallon ɗansa A hankali murmushi ya bayyana a fuskarsa. “Na yi niyya ne in faranta maka rai.” Ya Umar ya sunkuyar da kansa cikin girmamawa. “Toh shikenan Abbah, Nagode.” “Allah Ya ƙara girma.” Abbah ya yi murmushi “Ameen.” Sai dai kafin ya ƙara magana… Wayar Ya Umar ta fara ringing. Ya zaro ta daga aljihunsa Da ya ga sunan da ke kan screen… Mummy Calling. Ya miƙe tsaye “Abbah, bari in je.” Abbah ya gyada kai “Alright, Good night” Ya Umar ya nufi ɓangaren Mummy. Ya buga ƙofa a hankali. “Shigo.” Muryanta ya ratsa kunnensa Ya shiga. Mummy na zaune bakin gado. Fuskarta babu alamar walwala balle rahama Yana zama bata, ba ta bari ya yi magana ba. “Munafuki!” Ya Umar ya ɗan zaro ido “Mummy…” Ta ɗaga hannu ta dakatar da shi “Kar ka kira ni da Mummy. Ni ka ɗauka ba na ganin abin da kake yi?” “Kullum kana can da su, Baka ɗauke ni Uwa ba…” Ya Umar ya girgiza kai, bai bari ta karasa ba ya ce “Wallahi ba haka ba ne.” “Tohh….” Ta katse shi. “Daga yau… saurara da kyau.” “Idan ka sake bin side ɗin ubanka da Mami… ko ka tsaya kana hira da su ballanta gaisuwa” “Ko ka zauna tare da su…” “To ka ɗauka… zan iya yafe ka” “Kuma Allah Ya isa tsakanina da kai.” Kalmar ta tsoki zuciyarsa kamar mashi, ya zaro ido, nan take ya fara zufa “Mummy… Don Allah!” “Me ya sa za ki ce haka? Su fa iyayena ne! Ta yaya zan daina gaishe su?” Mummy ta harare shi. “Saboda su ne zaka wani rikice min? Kalle ka fah harda wani uban zufa dake sassako maka” Lallai kuwa… Ya Umar bai ma san lokacin da zufa ta fara keto masa a goshinsa ba Zuciyarsa ta cika da ruɗani. A ransa yana ta maimaita “Ta yaya zan rabu da Abbah? Ta yaya zan daina gaishe shi? Ta yaya zan yi kamar Mami ba ta wanzu ba?” Ya haɗiye yawu, saboda wannan abune mai kamar wuya ga uban Baki data masa “Mummy… Don Allah ki saurare ni.” Amma Hafsat ko kallonsa ba ta yi, ta nuna masa ƙofa. “Tashi ka fita” “Na gaji da jin maganarka.” Ya kasa motsi. Ta sake ɗaga murya. “Na ce ka bace min a ɗaki! Kafin na ƙara fushi.” Ba don yana so ba… Ya Umar ya miƙe a hankali. Ya kalli mahaifiyarsa da idanun da suka cika da damuwa. Sai dai ta juya fuskarta gefe. Ko kallonsa ba ta sake yi ba. Cike da nauyin zuciya… Ya buɗe ƙofar Ya fita. Yana tafiya a corridor… Hannunsa dafe a kansa. A karon farko… Ya ji kamar an ɗore shine tsakanin wuta da inuwa, biyayya ga mahaifiyarsa… ko kuma ƙaunar mahaifinsa #FARASHIN IZZAH Chapter 42 Zahra ta shigo ɗakinta cikin gajiya, amma har yanzu murmushin da ke fuskarta bai gushe ba, sai yanzu ta baro ɗakin Mami bayan tafiyar Anty Jay Ta cire heels ɗinta ta jefar a gefe, ta zauna bakin gadonta tana kallon key ɗin motarta. Har yanzu abin kamar mafarki yake mata. Sai wayarta ta fara vibrating. Firdausi Calling… Ta yi saurin ɗagawa. “Hello, Fir!” “Zahra don’t tell me ki ce kike trending” Firdausi ta faɗa da muryar mamaki. “Wallahi duk social media yau ke kaɗai ake ta magana a kanki, kin zama topic of the day” Asiya ta ce “Ke! Shine zaki ɓoye mana wannan birthday party ɗin?” Zahra ta yi dariya. “Wallahi ni kaina surprise ne.” “Ban san komai ba sai yau da na dawo gida daga gidansu Saudat “Karya!” Firdausi ta faɗa. “Da gaske, har yanzu ma ban gama yarda ba.” Asiya ta yi dariya “Princess kenan.” Saudat ma ta shiga conference call ɗin. “Happy birthday once again! Allah ya ƙaro miki shekaru masu albarka.” “Ameen.” “Nagode sosai.” Suka ɗan yi hira na wasu mintuna. Kafin daga ƙarshe Firdausi ta ce, “Ki shiga Instagram, ki ga abin da ke faruwa.” Zahra ta yi dariya “Toh.” Daga nan suka yi sallama Ta buɗe Instagram, tana shiga kuwa Sai notifications suka fara shigowa babu ƙaƙƙautawa. 99+ Notifications. Ta lumshe ido “Wai me haka?” Ta shiga home page, abin da ta gani… sai da ta buɗe baki. Ko’ina a Instagram… Bidiyonta ne, reaction ɗinta lokacin da ta ga motar. Lokacin da ta rungume Abbah, da lokacin da aka yanka cake. Pictures ɗinta cikin pink gown. Manyan pages suna repost, Blogs suna posting. Story mentions kuwa… ba ta ma iya ƙirgawa. @Safiyya___ mentioned you in a story. @Zehra___ tagged you in a post. @Ibtisam___ mentioned you. Notifications suna ta shigowa babu tsayawa, ta shiga comments “Allah ya ƙara miki albarka.” “Princess.” “So elegant.” “Masha Allah.” “The reaction is priceless.” “Father of the year.” “She deserves it.” Ga likes… Suna ƙaruwa a kowane secs Zahra ta girgiza kai tana murmushi Sai ta shiga profile na videographer. Ta ga ya riga ya ɗora edited version na birthday video ɗinta. Editing ɗin ya yi matuƙar kyau. Music mai taɓa zuciya, ga Quality mai kyau, reaction ɗinta kuma ta fito sosai. Ta yi masa direct message. Hi. Please can you send me the edited version? I really love it. Ba a wuce minti biyu ba… Ya yi reply. Sure, Princess. Happy Birthday once again. Ya turo mata full video ɗin. Ta sauke shi cikin wayarta, ta sake kallonsa sau ɗaya. Sai murmushi ya kubce mata, ta ajiye wayar a gefen gado. Ta miƙe tsaye, ta nufi toilet Ta yi alwala cikin nutsuwa. Da ta fito… Ta shimfiɗa sallaya, tayi shafa’i da witr❤️❤️❤️ Sannan ta zauna ta fara karanta Suratul Mulk cikin natsuwa Bayan ta kammala, sosai ta ɗaga hannuwanta sama. “Alhamdulillah…Ya Allah, kamar yadda Ka faranta min rai a yau… da kuma kullum, Allah kada Ka sa ni in manta da Kai.” “Ka sa wannan ni’imar ta zama alkhairi a gare ni, ka kare ni daga hassada da sharrin mutane. Fatan da Mummy ta min Allah kar kasa na aikata abun da zan kunyata iyayena” Ya mike, had’i da naɗe sallayar. Ta kashe babban wutan ɗakin Bed lamp kaɗai ta bari a kunne. Ta haye kan gadonta, ta kashe shi ma, ta ja duvet har ƙirjinta. Ba ta jima da kwanciya ba… saboda gajiyar ranar… Bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita Washegari… Da misalin ƙarfe takwas na safe. Ƙamshin tea da sandwich mai zafi ya cika dining area. Mama Ladi da sauran ma’aikata suka gama shirya breakfast. Abbah ya riga ya zauna sbd saurin da yake yi, Mami ma ta zo ta zauna Bayan ɗan lokaci… Zahra ta sauko cikin wata doguwar riga mai launin purple da farin veil scarf akanta Ta fara gaishe da Abbah da Mami kafin ta zauna. Sai dai su kaɗai kawai ta gani saɓanin sauran ranakun, a hankali ta ce “Mami… Ya Mummy fa? Da Batoul, har da Yaya?” Mami ta kalli Abbah. Abbah ya ɗan yi murmushin manya kawai. “Ki ci abincinki, babu komai Zahra ta ɗan kalli fuskokinsu, ta fahimci akwai abin da ba sa son ta sani. Sai ta yi shiru, ta fara breakfast ɗinta. Suna cikin cin abincin… Abbah ya sauke cup ɗinsa a hankali, ya kalli Zahra. “Baby.” “Na’am Abbah.” “Yanzu an fara online screening, wace makaranta kike so? Na yi waya a miki komai tun da wuri Zahra ta yi shiru. Ta sauke spoon ɗinta, ta dafe haɓa tamkar mai nazari Abbah ya sake cewa, “Nile University? Ko Pen Resource University?” “Kawai faɗa duk Wanda kike so” Mami ta ce, “Ko Baze University.” Zahra ta yi shiru Sai hoton Firdausi, Asiya da Saudat ya faɗo mata a rai. Ta san ba za su iya biyan kuɗin irin waɗannan makarantu ba, dan gwara ma Suhaima, kuma bata son ta rabu da su Sai ta ɗaga kai tana murmushi. “Abbah… Lemme think first.” Abbah ya gyada kai. “No problem, ki yi tunani sosai.” Da suka gama breakfast… Zahra ta koma ɗakinta, tana shiga ta dauki wayanta ta zauna kan gadonta… Ta buɗe group chat ɗinsu. The Queens👑❤️ Ta yi typing. Girls… Wace school kuke planning? Wallahi ni ina son mu tafi school ɗaya, course ɗaya ma idan zai yiwu.🥺❤️ Nan take replies suka fara shigowa. Asiya: Ni KASU nake tunani. Firdausi: Same here. Saudat: Ni ma KASU. Suhaima: Ni Daddy yana so Nile.😂 Firdausi ta yi replying. Ke ɗin daban ce. Mu talakawa muna KASU.😭😂 Asiya: Wallahi idan Zahra ta ce KASU zan fi farin ciki. Firdausi: Please Princess ki zo mana.🥺❤️ Zahra ta yi murmushi. Ta rubuta. Okay… Let me convince Abbah first.❤️ Ta kashe data, ta ajiye wayarta. Kai tsaye… ta nufi ɗakin Mami ta buga ƙofar a hankali “Shigo.” Ta shiga. Mami na zaune tana gyara wasu kaya, ta ɗago tana murmushi. “Fatima ya ne?” Zahra ta zauna kusa da ita, ta ɗan shafa hannunta. “Mami… Ina son magana ne da ke” Mami ta ajiye abin da ke hannunta. “Ina jinki.” “Mami… Ina son na je KASU.” Mami ta ɗan zaro ido. “KASU?” “Eh.” Mami ta yi shiru na wasu daƙiƙu. Ta kalli Zahra sosai. “Ke da kanki… wannan shi ne inda kike so? Ba Nile ba?” “Ba Pen Resource ba? Ba Baze ba?” Zahra ta girgiza kai. “A’a! KASU nake so.” Mami ta ɗan sauke numfashi. “Gaskiy duk da ba na son ki yi makaranta ɗaya da Batoul.” “Amma… gwara ki tafi can da KASU” Zahra ta riƙe hannunta. “Mami… I have made my mind.” “Bana son makaranta mai nisa da gida.” Mami ta san akwai wani dalili da Zahra yasa ta nace, amma ba ta matsa mata ba Sai ta shafa kanta. “Allah Ya sa abin da kika zaɓa shi ne mafi alkhairi.” “Ameen.” Bayan fitarta daga ɗakin Mami… Kai tsaye ta nufi inda Abbah yake, ta buga ƙofar a hankali “Come in.” Ta shiga. Abbah na duba wasu files, da ya ganta… Sai ya cire glasses ɗinsa. “My Princess, kin gama tunani?” Ta yi murmushi. “Eh.” “Wace school?” “KASU.” Abbah ya yi shiru. Ya jingina da kujerarsa. “KASU kuma Baby?” Eh.” Ya haɗe gira kaɗan. “Me ya sa? Ke da za ki iya zuwa kowace university?” Zahra ta ɗan yi murmushi. “Abbah Ina son ta ne, kuma bana son nisa da gida.” Abbah ya ci gaba da kallonta. Ya san Zahra, ba ta da halin nacewa abu sai idan ta yanke shawara Sai ya yi murmushi “Kin tabbata?” Ta gyada kai “One hundred percent.” Abbah ya ɗan yi dariya. “Toh shi ke nan, za a miki process na KASU.” Fuskar Zahra ta cika da annuri “Thank you, Abbah!” Ta yi saurin rungume shi, ya shafa kanta yana dariya. “Allah Ya sa alkhairi.” “Ameen.” Ya juya zata fita, sai kuma ta juyo. “Abbah…” “Yes?” “Ina Yaya?” Abbah ya ɗan kalli agogo. “Gaskiya ban san inda yake ba.” “Ni ma ban gan shi ba tun safe.” Zahra ta gyada kai. “Maybe ya tafi office.” Ta yi murmushi “Sai anjima.” Ta fita daga side ɗin da sauri, tana isa ɗakinta… Abu na farko da ta yi… ta kunna data Ta shiga group chat. Girls!!!!!!🥹❤️❤️ Abbah ya yarda. KASU it is.🥹🎉 Nan take group ɗin ya kaure da murna. Firdausi: Yeeeeeehhhhhh!!!😂❤️ Asiya: Allahuuu Akbar!!!🥹❤️ Saudat: Finally!❤️ Suhaima: Welcome to KASU girls.😂🤍 Zahra ta jingina da pillow tana murmushi. A karo na farko… Ta fara jin daɗin cewa wata sabuwar rayuwa na gab da buɗewa gare su baki ɗaya. Tun safe har la’asar ta yi amma… Babu alamar Ya Umar. Ba wanda zai ce ya gan shi a gidan Ko da yamma ta yi, har aka yi magariba… har lokacin bai dawo ba. Zahra ta riƙa leƙa ta window lokaci zuwa lokaci ko zata gansa, duk ƙarar mota da ta ji… Sai ta ɗaga kai da sauri tana tunanin ko Ya Umar ne, amma duk ba shi ba ne. Sau biyu ta kira wayarsa, bai ɗaga ba A karo na uku… sai aka katse. Da ta sake kira kuma.. wayar a kashe Sai gabanta ya fara bugawa. “Ya Allah… save my brother” Gidan ya yi tsit Mummy da Batoul suna zaune a parlour. Kowacce da wayarta a hannu, ba sa magana. Sai dai lokaci zuwa lokaci suna kallon juna. Aka buɗe kofar parlour Abbah ne ya shigo daga waje. Ya cire hularsa yana miƙa wa ɗaya daga cikin masu aikin compound Kafin ya zauna… Sai Zahra ta fito daga corridor, da alama ita ma fitowarta kenan daga ɗaki. Da ta ga Abbah… Ta ƙarasa da sauri “Abbah…” Ya ɗago yana kallonta. “Yea Baby.” Ta haɗe gira. “Har yanzu ban ga Yaya ba.” Abbah ya ɗan tsaya yana kallon damuwar dake fuskanta “Gaskiya… Ni ma ban gan shi ba.” Zahra ta cije leɓenta. “Na kira wayarsa da farko bai ɗaga ba, yanzu uma a kashe take.” Muryarta ta soma nuna damuwa. “Abbah… ko lafiya?” Abbah ya yi murmushin kwantar da hankali. “Baby… Umar ba ƙaramin yaro ba ne.” “Wataƙila wani meeting ne ya tsayar da shi.” “Ko kuma ya yi tafiya ta gaggawa but zai dawo ai, In shaa Allah.” Ta gyada kai Amma damuwar da ke fuskarta ba ta ragu ba. “Okay…” Ta juya za ta Kama hanyar ɗaki, sai kuma ta tsaya. Tamkar wani abu ya zo mata a rai, ta waiwayo a hankali, Idanunta suka sauka kan Mummy. Ta yi shiru na ɗan lokaci, Kafin ta ƙarasa kusa da inda take. “Mummy…” Mummy ba ta ma ɗago kai daga wayarta ba. “Hmm.” Zahra ta haɗe hannayenta waje ɗaya, cikin ladabi ta ce, “Please…” “Kin ga Ya Umar yau ne?” Mummy ta ɗaga kai a hankali, ta kalleta daga sama har ƙasa Sai ta yi wani murmushi mai cike da ba’a. “Ubanki ne shi?” Zahra ta ɗan zaro ido. Mummy ta ci gaba. “Idan ba ki gan shi ba… ba zaki iya rayuwa bane saboda shi ɗin numfashinki ne ba? Ko yanzu kin koma mai bin Maza ne?” Zahra ba ta ce komai ba, ta sauke idanunta ƙasa. Ta fara murza yatsun hannunta cikin rashin sanin abin cewa. Batoul ta ɗan ɗaga kai ta kalleta, ta wasu daƙiƙu… Babu wanda ya sake magana. Sai Zahra ta girgiza kai a hankali. “Nothing…” Ta faɗa cikin sanyin murya. “Sorry, Mummy” Ba tare da ta sake kallon kowa ba… ta juya a hankali… ta nufi staircase. Takunta ba irin na Zahra mai cike da kuzari ba ne Ko tafiyarta kaɗai ta nuna damuwar da take ciki. Abbah ya bi bayanta da kallo. Ya fahimci sarai cewa duk da kalamansa na kwantar mata da hankali… Yasan hankalinta ba’a kwance yake ba Ko kallon direction din Mummy bai yi ba, balle ya gwada yaji me ta ce, dan yaga da gayya take abubuwanta Ita kuwa Mummy… Sai ta mayar da hankalinta kan wayarta Bayan da Zahra ta shige ɗakinta Har yanzu tambaya ɗaya ce kawai ke yawo a zuciyarta. “Ina Yaya yake…?” Har can dare babu Yaya, Kowa ya koma ɗakinsa. Hasken corridor ne kaɗai ke bayyana, yayin da gidan ya yi shiru masu aiki ma duk sun kwanta Sai dai… Zahra tama kasa kwanciyar, damuwar Ya Umar ta ƙi barin ranta Bacci kuwa haka yaki dukarta, ta juya dama, ta juya hagu, amma bacci ya ƙi zuwa. A ƙarshe… ta sauko daga kan gadonta, ta saka slippers ɗinta a hankali. Ta buɗe ƙofar ɗakin, ta fita Kai tsaye… ta nufi ɓangaren ɗakin Ya Umar. A zuciyarta tana addu’a. “Ya Allah, ka sa ya dawo.” Da ta isa bakin ƙofar sai ta lura ba a rufe ta sosai ba. Ƙofar a ɗan buɗe take, ta tura ta da hankali sannan ta bubbuga Knock… Knock… “Yaya…” Shiru… ta sake tura ƙofar. Data leƙa ciki, nan take idanunta suka sauka kansa. Yana kwance a kan gadonsa, da alama bai daɗe da dawowa ba. Har yanzu bai canza kaya gaba ɗaya ba, riga ce babu a jikinsa, wayarsa kuwa a gefe take Yana kallon ceiling cikin zurfin tunani. Da ya ji ƙarar ƙofar.. sai ya ɗago kai. Idanunsu suka haɗu, ya ɗan zaro ido. “Baby?” Bai ma gama faɗin sunan ba… sai ya ga ta ƙaraso da sauri, ta faɗa jikinsa. Ta rungume shi da ƙarfi. Nan take… Ta fashe masa da kuka “Yaya…” “Meyasa zaka yi min haka?” Ya Umar ya rikice. “Subhanallah…” “Baby…” “Me ya faru?” Ta girgiza kai tana kuka. “Na kira ka.” “Wayarka a kashe.” “Duk throughout ban gan ka ba.” “Na tsorata sosai.” Ya Umar ya lumshe idanunsa. Kalaman Mummy na jiya suka dawo masa. Sai ya ji zuciyarsa ta yi zafi A hankali… Ya janye ta daga jikinsa. Ya share mata hawayen da suka zubo. “Shhh…” “Ki daina kuka.” “Nothing happened.” Sai ya miƙe tsaye.Ya ɗauki wata farar riga ya saka. Sannan ya kamo hannunta “Zo.” Suka fito daga ɗakin. suka isa parlour, ya zaunar da ita kan kujera. Shi kuma ya zauna kusa da ita. Ya riƙe hannunta cikin kulawa. “Baby.” Ta ɗago idanunta masu ja saboda kuka. “Hmm.” Ya ɗan yi murmushi. “Da farko…” “Ina son ki san wani abu.” Ta yi shiru tana saurarensa. “Ba daidai ba ne…” “Ki riƙa shiga ɗakina haka nan.” Ta haɗe gira. “Me ya sa?” Ya Umar ya yi murmushi. “Saboda yanzu kin girma. Eh, ni muharraminki ne, kuma ba wani abu ba ne, amma ba ina son ki saba da shiga ɗakin namiji ba tare da izini ba.” “Ki saba da kiyaye hakan, duk inda kika je, ko da kuwa ɗan uwanki ne.” Zahra ta yi shiru, ta fahimci abin da yake nufi, sai ta gyada kai cikin biyayya. “Okay… ba zan sake ba.” Ya shafa kanta. “Good girl.” Sai ta sake kallonsa. “Amma… Meyasa baka dawo ba?” Ya Umar ya ɗan kau da kai. Ba zai iya gaya mata gaskiya ba Don ba ya son ta san abin da ya faru tsakaninsa da Mummy. Sai ya tilasta murmushi wa fuskansa “Meeting ne. Wani emergency meeting, ya ɗauki lokaci sosai.” Ta haɗe gira “Shi ya sa baka ɗaga kirana ba?” Ya sauke idanunsa. “Na yi busy sosai da na gama kuma… wayata ta mutu, ban samu damar caji ba sai yanzu.” Zahra ta ɗan yi shiru. Sai ta ce da ƙaramar murya, “Da ka kira ka ce min ai, wallahi na damu.” Ya Umar ya ji wani irin tausayinta. Ya ɗan matsa kusa da ita. “Sorry, na yi kuskure.” “Ba zan sake ba.” Ta turo baki irin na yara cikin shugaba ta ce “Promise?” Ya ɗaga hannunsa. “I promise.” Sai ta yi murmushi Ya Umar ya miƙa mata tissue dake aljihun, to goge fuskarki Ta karba ta goge tana kallonsa “Yanzu kin yi murmushi har naji dadi” Ta yi dariya kaɗan. “Ka fi so ina yi murmushin ne?” “Exactly.” “Shi ya sa ba na son ganin kina kuka.” Ya ɗan murɗe mata kunne cikin wasa. Ta ɗan ture hannunsa. “Ouch” Daga nan… Ya raka ta har bakin staircase. “Yanzu…kije ki kwanta, gobe za mu yi magana.” Ta gyada kai. “Good night, Yaya.” “Good night, Baby.” Ta juya ta haura sama. Har sai da ta shige ɗakinta. Ya Umar ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya, ya lumshe idanunsa. A zuciyarsa… Ya san ƙaryar da ya yi mata ta ceci zuciyarta na ɗan lokaci Amma bai san har yaushe zai iya ɓoye mata abin da ke faruwa ba. Da wannan tunanin ya juya a hankali, ya koma cikin ɗakinsa. #FARASHIN IZZAH Chapter 43 Washegari... Da sassafe bayan Abbah ya dawo daga sallar Asuba... Ya zauna na ɗan lokaci yana karanta Al-Qur'ani kamar yadda ya saba. Da ya kammala... Ya ɗaga kai ya kalli ɗaya daga cikin masu aiki daya shigo zai karɓa key ya wanke masa mota "Ka gaya wa Umar ina son ganinsa." "Toh Alhaji." Bai wuce mintuna biyar ba... Ya Umar ya shigo. Ya yi sallama cikin girmamawa. "Assalamu alaikum, Abbah." "Wa alaikumus salam." Ya ƙarasa ya zauna. Sai dai... Tun da ya ɗaga kai ya kalli fuskar Abbah... Ya fahimci akwai magana mai nauyi dan haka ya sauke kansa da sauri saboda guilty questions Abbah ya yi shiru na wasu daƙiƙu, sai ya ce cikin sanyin murya, "Umar..." "Na'am, Abbah." "Kaima yanzu... Uwarka ta raba mu kenan?" Ya Umar ya ɗago kai da sauri "Abbah..." Abbah bai bar shi ya yi magana ba, ya ci gaba. "Kamar yadda ta raba ni da Batoul?" Kalmar ta tsaya wa Ya Umar a maƙoshi, ya sauke kansa ƙasa, ya haɗa yatsunsa wuri ɗaya yana wasa da su, ya rasa abin cewa. Abbah ya jingina da kujerarsa, ya yi wani murmushi mai cike da takaici. "Just go!!! Ba komai." Ya Umar ya yi saurin girgiza kai. "No, Abbah I'm sorry, ba haka bane." Abbah bai ce komai ba yana kallon wani direction Sai Ya Umar ya ci gaba da magana cikin damuwa "Ba wai ta raba Ni da Kai bane, kuma har ace zan ɗauka” "Wallahi ba haka bane." "Kawai..." Ya haɗiye yawu. "Ina tsoron bakin uwa ne Abbah, Mummy ta fusata haikan akai na” Abbah ya ɗaga idanunsa ya kalli ɗansa, a karon farko... Ya ga tsoron da ke zaune a cikin idanun Ya Umar ya bayyana, Kawai yaji tausayinsa Ya Umar ya ci gaba. "Wallahi Abbah, Ina jira ne ta huce sai na sake komawa wajenta na roketa ta janye bakin data min” ya sauke ajiyar zuciya "Amma... ba yadda za a yi In janye jikina daga kai, dan kai Ubana ne ai Abbah” Ran Abbah ya ƙara ɓaci, ba don Ya Umar ya faɗi hakan ba... Sai don ya fahimci irin tasirin da Hafsat ta yi wa zuciyar ɗansa. Ya miƙe tsaye a hankali ya juya baya. "It's okay." Ya faɗa ba tare da ya waiwayo ba. "Just go Umar” Sai ya ƙara da cewa, "Thank God... ba ku kaɗai ba ne 'ya'yana." Kalaman sun soki zuciyar Ya Umar fiye da yadda ake tunani. Ya miƙe da sauri, ya ƙarasa kusa da Abbah a rikice "Abbah, Don Allah ka yi haƙuri. Wallahi ban taɓa nufin hakan ba ko da wasa, kawai tsoron tasirin bakinta nake ji” Abbah ko da wasa bai juyo ba, Ya Umar ya tsaya a wurin yana kallon bayan Abbah da mamaki, domin ya san Abbah…. Mutum ne mai yawan haƙuri, ba kasafai yake nuna ɓacin ransa ba, amma yau... Ya fahimci lamarin ya taɓa zuciyarsa sosai, ya sauke numfashi, sai ya ce cikin sanyin murya, "I'm sorry, Abbah." Abbah ya fice daga ɗakinsa, Ya Umar ya bisa a baya Yana fitowa corridor... sai ya ji wasu hannaye sun zagaye wuyansa daga baya "Abbaaaaa!" Ya ɗan tsorata kafin ya jiyo muryanta, yayi murmushi Sai ya ji Zahra na ƙoƙarin hawa bayansa. "Carry me!" Bai san lokacin da dariya ta ƙwace masa ba "Ke! Baby ashe haka kike da nawi?” Zahra ta yi dariya sosai "Ka ɗauke ni kawai " Abbah ya kama ƙafafunta, ya ɗaga ta a bayansa. Ta rungume wuyansa tana ta dariya, shi ma yana dariyar "Subhanallah! Ashe kina da nauyi haka ban sani ba?” Zahra ta ɗan buga kafaɗarsa "Ni? Ka ce ni ce mai nauyi? Kai Abbah..” Abbah ya yi dariya. "Ahh, na yi zaton har yanzu ƙarama ce ke har yanzu” Ta yi ƙara tana dariya "Kai ma fa... Ashe kana da ƙarfi tunda ka iya ɗaukar Baby mai nawi” Abbah ya sauke ta daga bayansa, ya dawo da ita gabansa, ya gyara scarf ɗinta da ya ɗan zame Sannan ya shafa kanta "Baby." "Na'am?" "Ki shirya” Ta ɗago tana kallonsa. "Driver zai kai ki driving school Ina son ki fara training. Kuma a yi miki driving licence Murmushi tayi ta ce "Really?" Abbah ya gyaɗa kai "Yes, kin fara girma, ya kamata ki san tuƙi” Ta yi murmushi har haƙoranta suka bayyana. "Alright, Abbah na! Thank you." Ta yi saurin rungume shi. Shi kuma ya shafa bayanta yana murmushi. Shi dai Ya Umar na can gefe yana kallonsu da murmushi Abbah kuwa duk da nauyin da ke cikin zuciyarsa saboda abin da ya faru na Ya Umar... Murmushin Zahra ya sake dawo masa da wani ɗan natsuwa da ya rasa tun shigowar Ya Umar Bayan Shekara Ɗaya da rabi... Lokaci... Shi ne babban mai sauya rayuwa inji Malam Bahause Tabbas haka ne, dan a cikin shekara guda... Abubuwa da dama sun faru ko nace harda canji Fatima Zahra ba ita ce yarinyar shekara ɗaya da ta gabata ba. Yanzu ta zama cikakkiyar budurwa mai cike da nutsuwa da izzah. Ba ta shiga harkar kowa, bata son hayaniya, bata son gulma. Ba ta son raini, kuma ba ta ɗaukar raini daga kowa, uwa Uba izzah da take da shi… Idan ta yi magana, toh tabbas sai dai cikin natsuwa. Idan kuma wani ya ƙetare iyakarsa... Kalma ɗaya daga bakinta kan isa ta sanya ya san ya yi kuskure. Mutane da yawa suna kallonta a matsayin mai gadara. Amma waɗanda suka santa sosai sun san ba gadara ba ce Izza ce Da kuma sanin darajar kanta. Karfe 4:30 na asuba Sautin alarm ɗinta ya karade ɗakin, bata yi wata-wata ba, ta miƙe zaune. Hannu ta miƙa ta kashe alarm ɗin, ta sauko daga kan gadonta a hankali tana murya kyawawan manyan idanunta wanda yake cike da bacci Ta gyara night cap ɗinta, kai tsaye ta nufi banɗaki. Ta yi alwala cikin nutsuwa. Bayan ta fito... ta shimfiɗa sallaya Ta tsaya gaban Ubangijinta, tayi raka’a biyu kafin ta ɗaura asuba Bayan ta idar... ta zauna tana karata azkar tana gamawa ta muƙe ta ɗauko Al-Qur'ani ta karanta wash shafuka sannan ta rufe Ta yi addu'o'inta data Saba yi, sai da gari ya fara haske kaɗan... Ta miƙe, ta nufi bathroom, kunna shower tayi ruwan ɗumin yana shiga jikinta yadda ya kamata bayan ta shafa shower gel Bayan ta gama wanka... Ta fito tana goge gashinta da farin towel, ta tsaya gaban dressing mirror Ta buɗe wardrobe ɗinta, bayan ta ɗan yi tunani.. Ta zaro wata atamfa mai tsadar gaske Dark emerald green ce mai ɗan haɗe da gold embroidery a hannaye da wuyan rigar, an ɗinka rigar cikin salo mai sauƙi amma cike da classy Ta saka doguwar skirt ɗinta, haɗi da rigarsa, sannan tayi wani ɗauri Sannan ta ɗaura matching veil mai tsadar gaske Ba ta cika son make-up ba, saboda haka... Light powder kaɗai ta shafa ta ɗan saka nude lip gloss Kafin ta ɗauki turaren oud ɗinta ta fesa kaɗan. Daga drawer, ta ciro agogon zinariya mai siriri ta saka shi a hannunta. Sai bracelet mai kyau Ƙananan diamond studs ne a kunnuwanta, sai zoben azurfa mai ɗan white stone a sakiya Ba ta son cika jikinta da kayan ado, hakan yasa ta bari bata sake saka wani abu ba amma hakan ya ƙara fito da kyan halittarta. Ta ɗauki Schoolbag ɗinta ta saka laptop, notebook da sauran kayan makarantarta Ta ɗauki key ɗin motarta, sai ta dauki wayarta Ta kalla mirror na ƙarshe, ta gyara veil ɗinta, Kafin ta fice daga ɗakin. Da ta sauko parlour... Mami na zaune tana shan tea. “Mami na” ta faɗa da murmushi a fuskanta "Fatima” Mami faa Ta ƙarasa, ta zauna ta gaisheta "Ina kwana Mami." "Lafiya lau, Baby." "Kin tashi lafiya?" "Alhamdulillah." Mami ta yi murmushi tana kallonta. "Allah Ya tsare." "Ameen." Ta zo fita a second parlor ta haɗu da Mummy na zaune tana duba wayarta Da Zahra ta zo za ta fita... Sai Mummy ta ɗago kai “Ahh, Baby har kin fito kenan?” Zahra na murmushi ta gyaɗa kai haɗi da gaisheta Mummy na murmushi tace "A dawo lafiya, Daughter." Zahra ta gyada kai "In shaa Allah, Nagode." Daga haka ta ci gaba da tafiyarta, tana fito compound... Mai wanke motocin gidan yana kan nata motar ne, gogewa yake yi yadda yake ƙara sheƙi Yana ganinta ya yi saurin miƙewa "Ina kwana, Hajiya." "Lafiya." Ta amsa a taƙaice. Ya buɗe mata ƙofar motar, ta shiga Gatekeeper na ganin fitowarta ya buɗe babban gate. "Allah Ya kiyaye hanya." "Ameen." Ta amsa tana kunna motar. A hankali... ta ja motar ta fita daga gidan Safiyar Juma'a ce, hanyar cike take nak da cunkoso saboda kai yara makaranta Zahra na tuƙi cikin natsuwa, duk wani motsinta yana nuna ƙwarewa da nutsuwa. Bluetooth ɗin motarta na kunne Muryar karatun Suratul Kahf ce ke ratsawa cikin motar cikin daɗin sauraro Lokaci zuwa lokaci ta kan maimaita wasu ayoyin a hankali, fuskarta cike da kwanciyar hankali. Bayan kusan mintuna talatin.. ta iso harabar makarantar, ta rage gudun motar tun daga bakin gate Ta nufi parking lot ɗin ɗalibai, ta yi parking, ta kashe motar, ta ɗauki handbag ɗinta. Ta sauka, ta kulle motar Ta gyara veil ɗinta a hankali, ta rataya schoolbag ɗinta a kafaɗa. Sannan ta nufi faculty ɗinsu da takunta masu cike da izzah da kwarjini. A shekara guda da ta shafe a jami'a... Sunanta ya riga ya zama sananne, ba kuma don yadda take a media ba, sai don yadda take rayuwarta a real life A social media kuwa... Shahararta ta ƙara ninkuwa. Solo dates dinta, Classy dressing, Luxury lifestyle. Da kuma yadda take rayuwa cikin mutunci ba tare da nuna surutai ko neman attention ba... Duk sun ƙara ɗaga darajarta a idon mutane. A duk lokacin da ta shiga makaranta... ba sai ta yi magana ba, kasancewarta kawai ya isa mutane su juya su kalle ta. "Isn't that Fatima Zahra? Wancan Famous din?” "Wallahi ita ce." "Kai... she's even prettier in real life." "Yes, tana part 1 ne ai" "What?! Na zata ma 300L ko 400L ce." "Ni ma." "Ban taɓa tunanin 100L take ba." Wasu na rada. Amma Zahra...ko kallonsu ba ta yi Kai tsaye take tafiya Fuskarta cike da nutsuwa, ba murmushin, ba kuma haɗe fuska ba. Irin tafiyar nan da ke nuna mutum ya san darajar kansa. Tana isa gaban faculty.. "Princess!" Ta waigo. Firdausi ce ke tahowa da sauri A bayanta kuma... Asiya, Saudat da Suhaima. Firdausi ta rungume ta "Finally! Ashe yau zaki zo da wuri." Zahra ta yi murmushi "Ke ce kika saba zuwa a makare ai, as usual” Firdausi ta ce “Celebrity." Zahra ta ɗan harare ta. "Fir... Stop it. Ni ba celebrity ba ce." Firdausi ta haɗa hannu. "Okay Hajiya. Influencer." Duk suka fashe da dariya. A dai-dai lokacin... Wasu ɗalibai biyu suka wuce ta gefensu. Ɗaya daga cikinsu ya yi wa ɗan uwansa rada. "Bro..." "Wallahi ita ce." "Fatima Zahra." "Wacce nake nuna maka a TikTok da Instagram." Ɗayan ya ce cikin mamaki, "So anan dama take?" Firdausi ta ji maganar. Sai ta kalli Zahra tana murmushi "Kin ji?" Zahra ta girgiza kai. "Ba abin da ya dame ni." "Mu je class” Ta juya ta fara tafiya. Su huɗun suka bi bayanta. Yayin da ɗalibai da dama ke ci gaba da bin ta da kallo... ba don komai ba sai don kyauwunta Da kuma wata irin izzah da kwarjini da Allah Ya ɗora mata, wadda ke sa duk wanda ya gan ta ya yi tunanin ba sabuwar ɗaliba ba ce, illa ɗalibar da ta daɗe a jami'ar, ko ma wacce take gab da kammala karatu. Ɗalibai suka fara kwararowa zuwa lecture hall. Zahra da ƙawayenta suka ƙarasa cikin nutsuwa. Lecture hall ɗin ya riga ya fara cika, wasu na zaune suna ta hira Wasu kuma sun riga sun buɗe laptops da notebooks ɗinsu. Kai tsaye ta nufi layin gaba, ba ta son zama baya. Firdausi ta kalle ta tana dariya "Ke dai ba za ki taɓa canzawa ba." Zahra ta ɗan kalleta "Meye kuma?" "Kullum front row." Ta ɗan yi murmushi. "Na zo karatu ne Fir, ba yawon kallon mutane ba. As long as zan ji lecture sosai... wurin an ya ishe ni." Asiya ta girgiza kai "Zan zama ke toh" Saudat ta ce, "Ni ma zan dawo gaba daga yau." Suhaima ta yi dariya. "Ni kam daga baya nake ganin komai." Dariya suka yi, suka zauna. Zahra ta buɗe handbag ɗinta, ta ciro laptop ɗinta sai notebook da biro. Ta mayar da wayarta silent mode, ta saka ta cikin jaka. Firdausi ta kalleta "Ke baki ma shiga Instagram ba tun da muka zo." Zahra ba ta ɗago kai ba. "Aji ba wajen social media ba ne, da mun gama lectures...Zan duba." Firdausi ta ɗaga hannu cikin wasa. "I give up. Allah ya ƙara miki son karatu." "Ameen." Kafin su ƙara magana.. Lecturer ya shigo. Nan take... Hayaniyar hall ta lafa. Kowa ya koma mazauninsa. Lecturer ya ajiye files ɗinsa a kan teburi. Ya ɗauki attendance register. Ya ɗaga kai yana kallon ɗaliban. "Good morning, everyone." "Good morning, sir." Suka amsa gaba ɗaya. "Hope you're all doing well?" "Yes, sir." Ya yi murmushi. "Good." "Open your notebooks." "Today, we're starting a new topic." Nan take... Zahra ta buɗe notebook ɗinta. Ta gyara zamanta. Hankalinta ya tattara gaba ɗaya kan lecturer. Abin da ya kawo ta jami'a shi ne neman ilimi. Kuma hakan ne ya sa tun farkon shekararta malamai suka fara lura da ita. Ba don shahararta a social media ba... Sai don yadda take mayar da hankali, yawan yin tambayoyi masu ma'ana, da kuma rubuta duk wani muhimmin bayani ba tare da wasa ko ɗaukar hankali zuwa wani wuri ba. Firdausi ta ɗan matsa kusa da Asiya ta yi mata rada. "Kin ga ta?" Asiya ta yi murmushi. "Idan lecture ya fara... ko sunanta ka kira.. ba za ta ji ba." Su duka suka yi murmushi a ɓoye. Su ma suka maida hankalinsu ga darasin da ake gabatarwa. Da lecturer ya kalli agogo... Sai ya rufe marker ɗin da ke hannunsa. "Alright, that's all for today." "We'll continue next class." "Those going for Jumu'ah can leave now." "See you next week." "Thank you, sir." Dalibai suka amsa gaba ɗaya. Nan take lecture hall ɗin ya fara watsewa. Maza suka fara nufar masallacin jami'ar. Mata kuwa suka fito cikin harabar faculty. Wasu na zaune suna hira, wasu kuma suna jiran friends ɗinsu. Zahra ta saka laptop ɗinta cikin schoolbag, ta miƙe tsaye. Firdausi ta miƙa hannunta tana jan numfashi. "Wallahi lecture ɗin yau ya gama dani." Asiya ta yi dariya. "Ni ma." Suhaima ta ce, "Mu je mu zauna a ƙarƙashin bishiyar can. Kafin a kunna ruwan faculty muyi alwala” A hankali suka fara tafiya tare. Sai dai... Tun daga lokacin da suka fito daga lecture hall... Zahra ba ta cikin hirarsu. Idanunta na kan Saudat. Ba fuskarta take kallo ba... Kayan jikinta take dubawa Doguwar rigar atamfar da Saudat ke sanye da ita ta tsufa sosai. Launinta ya dusashe. A gefen hannun rigar akwai inda aka sake ɗinkewa da hannu. Hijab ɗinta ma ya sha wanki sosai har ya fara rasa sheƙinsa. Takalmanta kuma... Sai da Zahra ta lura an liƙe gefensa bayan ya yage. Ta yi shiru… bata ce komai ba. Ba ta son ta kunyata Saudat a gaban sauran ƙawayensu. Har suka isa wani inuwa kusa da faculty. Firdausi da Asiya suna ta hira. Suhaima ta ce za ta je ta sayi ruwa Sai Zahra ta zauna kusa da Saudat. Ta ɗan kalleta. "Saudat..." "Na'am?" "Kina lafiya?" Saudat ta yi murmushi. "Alhamdulillah. Me ya sa kika tambaya?" Zahra ta ɗan yi shiru, ta sake kallon rigar da ke jikinta. Sai ta mayar da idanunta kan fuskar Saudat. "Babu komai... Na dai ga kin yi shiru ne yau." Saudat ta yi murmushin da ya kasa ɓoye gajiyarta. "Na gaji ne kawai." Zahra ta gyada kai.…. #Farashin izzah Hauwajay writes__08110615256 Chapter 44 Tun bayan dawowarta daga makaranta… Zuciyar Zahra ta kasa mantawa da Saudat. Duk sanda take cikin happy moments sai kuma hoton kayan jikin Saudat da suka tsufa ya dawo mata. Har dare… tunani ɗaya ne kawai ke yawo a ranta. “Ya Allah…” “Ta yaya zan taimaka mata ba tare da ta ji kamar an raina mata ba?” Washegari… Bayan sun gama breakfast… Zahra ta nufi backyard. A can ta tarar da masu aikin gidan guda biyu suna gyara lambu. Da suka ganta… Sai suka yi saurin ajiye abin da ke hannunsu. “Ina kwana Hajiya karama.” “Lafiya.” Ta amsa cikin murmushi. “Ya aikin?” “Alhamdulillah.” Ta ɗan kalli ɗaya daga cikinsu. “Please ina son ku yi min sanitation na ɗakina.” “Duk wardrobe ɗina a sake gyara min kayan ciki, Da shelves ma. Za ku iya?” Nan take suka gyara tsayuwarsu. “Za mu iya Hajiya, kafin azahar ma za mu gama In shaa Allah” Ta yi murmushi “Thank you.” Bayan sun gama lunch, suka raba abincin, suka Kai na dining tare da plate da spoons, sannan suka haura sama zuwa ɗakin Zahra Nan da nan suka fara aiki, ɗaya na sharewa, ɗaya na goge mirrors. Anty Binta ta sauke curtains ta kai laundry. Suka sake tsara tsarin shoes rack, aka share ƙarƙashin king size bed ɗinta Suka sake jera perfumes, lotions, handcream, face mask, da duk wani kayan dake kan mirror ɗin Suka goge glass shelves. A hankali… Ɗakin ya sake canzawa. Ita kuwa Zahra… Ta tsaya gaban wardrobe ɗinta, ta buɗe shi Layuka na dresses masu tsada suka bayyana su atamfa, lace, abayas da Turkish dresses. Ta riƙa ciro ɗaya bayan ɗaya, tana duba su sosai “Na saka wannan sau ɗaya.” “Wannan ma sau biyu.” “Wannan ma ba’a san shi da ni ba both media da school” A haka ta fara ware set by set, ba wai kuma dan sun tsufa bane, hasalima… Da yawa daga cikinsu sababbi ne, sai dai… Ba ta cika komawa ta sake sawa ba, musamman idan tayi hoto da shi, kuma kullum sabbin kaya ake ƙara mata. A ƙarshe… ta ware set goma sha biyar kuma dukkansu masu kyau ne da tsada, ta naɗe kowannensu da kyau. Ta saka su cikin wani babban fancy bag mai kyau, tayi zipping bakin bag din, sai ta ɗora a gefe Anty Binta tana murmushi ta ce “‘Yar Abbanta mun gama?” Dariya tayi ta ce “Zaku iya tafiya, thank you” daga haka suka juya suka fita Can tana kan ware wasu veils da Jibab Mami ta leƙo Ta tsaya tana kallon yadda ɗakin ya canza harda sheki banda kamshim da yake yi Ta yi dariya “Yau kuma… ’yan tsafta ne suka taso?” Zahra ta yi dariya. “Kai Mami…Wallahi jiya ban ji daɗi ba har dare na kasa manta da abun” Mami ta shigo “Me ya faru?” Ta nuna fancy bag ɗin “Kin ga Saudat jiya?” “Kayan jikinta sun yi matuƙar tsufa wallahi abin ya taɓa ni.” “Ba na so mutane su riƙa raina ta shi ya sa na ware waɗannan, zan ba ta” Mami ta buɗe bag ɗin ta ɗauki ɗaya daga cikin kayan sai ta kalli Zahra. “Baby… Ba su yi yawa ba?” Zahra ta girgiza kai. “A’a Mami.” “Besides… ban cika saka su ba, kuma Ita ce ta fi buƙatarsu.” Mami ta yi murmushi cike da alfahari, ta shafa kumatunta “Allah Ya ƙara miki zuciyar taimako Fatima. Kin san sirrin arziki?” Zahra ta girgiza kai. “Mutum ya riƙa taimakon wanda bai da shi. Sai kiga kullum Allah zai na Kara masa ninkinsa saboda ya san hannunsa a buɗe yake.” “Allah Ya ba ki lada.” Zahra ta yi murmushi. “Ameen.” Mami ta juya ta fita. Da yamma… Zahra na saukowa daga sama… Yayi dai-dai da lokacin da Ya Umar ya dawo daga office Da ganinsa… ta yi saurin ƙarasa “Yayaa!” Ya yi murmushi. “My Baby.” Ta karasa ta kama hannunsa. “Zo” Ya kalleta “Ina?” “Zo mana zaka ji koma menene”Ba ta ba shi damar tambaya ba. Ta ja shi har cikin parlour. Yana kallon kofar side ɗinsa ya ce “Ki jira. Bari na yi fresh up.” Mintuna kaɗan bayan haka… Ya fito cikin casual wear. Har sannan ta na zaune tana jiransa, ya zauna a gefenta Sai ta sake kama hannunsa ta miƙe tsaye, ta ja shi zuwa dining area. Ya yi dariya. “Ke… Me ya same ki ne yau?” Serving ɗinsa tayi, ta tura masa abincin gabanta, ita kuma ta ɗora haɓa a hannunta, tana kallonsa sosai. “Yaya…” “Hmm?” “Yaushe za ka yi aure?” Ya kusan shaƙewa da ruwan da yake sha. Ya kalleta. “Not now! Not anytime soon.” Ta haɗe fuska. “Yaya me haka kuma? Idan ba ka da budurwa… Ni zan nema maka.” Ya yi dariya sosai. “Toh ke ina ruwanki?” Ta ɗan turo baki. “Akwai mana, babba ma kuwa” Ya girgiza kai yana dariya. “Toh Madam Matchmaker. Wace kika samo?” Ta yi murmushi “Please… ka auri Saudat.” Ya Umar ya ɗan taɓe fuska “Saudat? Wace ce kuma?” Zahra ta ɓata fuska “Friend ɗina mana wannan farar nan… Wacce take zuwa nan tare da Firdausi.” Ya ɗanyi tunani ya. D “Oh… Ita! Toh me ya sa?” Zahra ta ce cikin fara’a “Saboda tana da kirki, tana da tarbiyya, kuma ina ganin za ku dace.” Ta ɗan yi shiru Sannan ta ƙara da murmushi. “Kuma Kaga babu tuwanta da magana especially idan she’s not comfortable da mutum Ya Umar ya fashe da dariya. “Wallahi ke akwai ki da abin dariya.” Sai kuma yayi shiru sannan ya ɗaura “Baby… Kawarki ba ta min.” “Kuma… She’s not my type, besides… ba yanzu zanyi aure ba maybe after four years.” “By then, zan kai shekara talatin da biyar.” Zahra ta haɗe fuska, ta marairaice “Pleaseeeee…” Ya Umar ya girgiza kai yana dariya. “Sorry!!! No negotiation.” Ta sake ƙoƙarin lallashinsa “Yaya…” Ya ɗaga hannu “Discussion closed.” Ta tsaya tana kallonsa da ɓacin rai irin na shagaɓɓan yara, sai ta yi tsaki a hankali, ta miƙe tsaye. “Ni ba zan sake magana da kai ba.” Ta juya za ta tafi. Ya Umar ya yi dariya har da riƙe ciki. “Baby…” Ta ƙi waiwayowa, ta i gaba da tafiya. Shi kuma ya girgiza kai yana murmushi. “Wannan yarinyar…” “Wai har ita ce zata neman min mata… Tun bayan hirarta da Ya Umar… Zahra ta ƙuduri aniyar nuna masa fushi. Duk da ya san halinta sarai… Ita kam ta ɗauki maganar da muhimmanci. Tun da ta shiga ɗaki ta rufe bata sake fitowa ba. Ko lokacin da Mama Ladi ta kawo mata fruits da juice… Sai ta ce “Ki ajiye a bakin kofar Har yamma ta yi magariba ta gabato har ta shige. Har lokacin dinner ya yi… Zahra ba ta fito ba. A dining room, kowa ya hallara Abbah na zaune a kujerarsa, Mami na gefensa Mummy da Batoul ma suna nan. Ya Umar ya zauna shiru yana cin abincinsa, sai dai lokaci zuwa lokaci idanunsa na bin staircase. Yana jiran fitowar Zahra. Amma shiru… Ba alamar za ta sauko. Abbah ya ɗaga kai ya zagaya dining ɗin da kallo, sai ya haɗe gira “Baby fa?” Ba ta sauko ba?” Mummy ta ɗaga kai daga plate ɗinta “Da yamma dai na ga kamar ta wuce backyard da books a hannunta Maybe karatu take yi.” Mami ta kalleta da mamaki. “Da wannan daren? Sai ta zauna a backyard?” Mummy ta ɗaga kafaɗa “Ni abin da na gani kenan.” Abbah bai ce komai ba, ya ajiye spoon ɗinsa, ya miƙe tsaye Ba tare da ya ƙara wata magana ba… ya juya ya nufi staircase. Ya Umar ya bi bayansa da kallo. A zuciyarsa ya san… Wataƙila har yanzu Zahra na fushi da shi ne Abbah ya hau sama, kai tsaye ya nufi ɗakin Zahra. Da ya isa… Sai ya lura ƙofar ba a rufe take ba. Yayi knocking kafin ya tura ta a hankali, ƙofar ta buɗe. Abin da ya gani… Sai ya sa murmushi ya suɓuce masa. Zahra na zaune a kan gadonta, ta baza littattafai a gabanta, Laptop a buɗe, highlighter a hannu. Hankalinta gaba ɗaya na kan karatu, sai da ta ji ƙarar ƙofar… Ta ɗago kai. Da idanunta suka sauka kan Abbah… Nan take fuskarta ta sauya, ta yi murmushi “Abbah.” Ya jingina da ƙofar yana kallonta. “Har yanzu kina karatu?” Ta yi dariya “Exam is around the corner.” Ya gyaɗa kai cikin tausayawa. “Karatu yana da kyau, amma ba da yunwa ba.” Ya miƙa mata hannu “Help me.” Ta haɗe gira cikin wasa “Da me?” Ya yi murmushi. “Ki zo ki ci abinci kafin cikin ki ya fara kara” Ta rufe littafin da ke hannunta. “Alright, Abbah.” Ta sauko daga kan gadon, ta gyara scarf ɗinta, ta ɗauki wayarta. Sai ta kashe laptop ɗin. Abbah ya jira har ta ƙarasa, sannan suka fito tare. Yana tafiya a hankali Ita kuma na biye da shi. Har suka sauko staircase… Idanun duk waɗanda ke dining suka koma kansu. Musamman Ya Umar. Da ya ga Zahra ta sauko lafiya, sai ya sauke numfashin da bai ma san yana riƙe da shi ba. Shi kuwa Abbah… Ya ja mata kujera kusa da tasa “Zauna Baby.” Ta zauna cikin nutsuwa, Mummy ta miƙe ta fara serving ɗinta. Zahra ta fara cin abincin a hankali. Sai dai… Ko sau ɗaya ba ta kalli Ya Umar ba. Shi kuwa… Lokaci zuwa lokaci idanunsa na komawa kanta. Yana son ya yi magana, amma ya san halin ƙanwarsa. Idan ta ce tana fushi… Sai ta gama fushinta kafin ta dawo yadda take. Kyan zuciyarta ba ta daɗe da riƙe ƙulli ba… Amma idan ta kama, sai wanda ya san yadda zai lallabeta. Ya Umar ya ɗan yi murmushi a a zuciyarsa ya ce ‘Ai Baby… nan da gobe za ta manta’ Karan spoons kawai kake ji saboda babu mai cewa komai… Can… Zahra ta ɗaga kanta ta kalli Abbah “Abbah…” Ya amsa yana kallonta. “Na’am, Baby.” Ta ɗan ajiye spoon ɗinta “Ka ce Ya Umar ya yi aure.” Nan take… Kowa ya ɗaga kai ya kalleta. Batoul ta haɗe gira tana mata wani kallo Mummy ta dai baka gane me fuskanta yake nufi sai dai expressionless Mami kuwa ta kalli Zahra tana murmushi, tana jiran jin abin da zai biyo baya. Shi kansa Ya Umar… Sai da ya kusan haɗiye abincin ba tare da ya tauna ba. Ya ɗaga kansa yana kallon Zahra Abbah ya yi murmushi. “Toh Baby?” Zahra ta gyara zamanta. “I mean it fa Abbah. Kace dole ya yi aure soon.” Ta nuna Ya Umar da spoon ɗinta. “Ko kuma ya bar maka gida. Saboda ai ya girma.” Ya Umar ya dafe goshinsa a hankali “Innalillahi…” Abbah ya kasa riƙe dariyarsa, sosai yake kyasawa, ya girgiza kai “An yi faɗa da Yaya kenan?” Zahra ta girgiza kai da sauri. “A’a. Kawai ya yi aure, Idan ma ba shi da budurwa…” Sai ta ɗan yi murmushi. “Ya zo na zaɓa masa Mata, wallahi… She’s very beautiful, Abbah.” Wannan karon… Abbah ya fashe da dariya Ya riga ya fahimci inda maganar ta dosa Mami ta jingina da kujera tana kallon Zahra cike da nishaɗi Mummy da Batoul kuwa… Sai kallonta suke yi Zahra ta sake kallon Abbah. “Abbah! Ba ka faɗa masa ba fa, ai gashi nan, yana jin ka.” Abbah ya share hawayen dariyar da ta taru a gefen idonsa. Sannan ya juya ya kalli Ya Umar “Umar.” Ya Umar ya ɗago kai “Na’am Abbah.” “Kanwarka tace ka yi aure, kuma idan ba ka da matar… tace ta samo maka.” Ya Umar ya sauke numfashi, sai ya yi murmushi “Gaskiya Abbah… ba ni da ra’ayin yin aure yanzu, Ina da abubuwa da yawa a gabana. Ina so na gama settling ɗinsu. Sai daga baya nayi” Abbah ya gyada kai cikin fahimta. “Okayy” Sai ya juya ga Zahra “Baby.” Ta ɗaga kai. “Aure ba abin gaggawa ba ne, a hankali ake zuwa har Allah Ya kawo lokacin kuma baza a tilasta mutum ya yi aure ba…” “Musamman idan har bai shirya ba, Idan lokaci ya yi… Shi da kansa zai yi.” Zahra ta ɗan turo baki. Fuskarta ta nuna ba ta gamsu ba. Amma… bata yi gardama ba. Mummy ta yi wani ɗan murmushi mai cike da ba’a. “Ai yau na ga abin da bai ishe ni ba. Kowa dai ya tattaru akan kula da Umar.” Ba wanda ya bi maganarta. Abbah bai ko kalleta ba. Mami ma ta ci gaba da cin abincinta cikin nutsuwa. Zahra kuwa… Ta ɗan girgiza kai. “Okay, Abbah.” Ba don ta yarda da abin da ya faɗa ba… Sai don ta fahimci babu wanda zai goyi bayan shirinta a wannan lokacin. Sai ta koma cin abincinta cikin nutsuwa, amma a zuciyarta… Ta riga ta yanke hukunci. “Wannan maganar ba ta ƙare ba sai na nemo wata hanya” Ya Umar ya sace kallonta, ya girgiza kai yana murmushi Bayan an gama dinner… Kowa ya miƙe daga dining Abbah ya nufi parlonsa kamar yadda ya saba. Ya Umar ya tsaya yana magana da ɗaya daga cikin masu aikin gidan. Mummy da Batoul kuma suka haura sama ba tare da sun ce komai ba. Mami kuwa har ta nufa hanyar ɗakinta sai kuma ta waiwaya tana kallon Zahra ta “Baby.” Zahra da ke shirin hawa sama ta juya. “Na’am, Mami?” “Zo ki same ni a ɗakina.” “Toh Mami.” Mintuna kaɗan bayan haka… Zahra ta tura ƙofar ɗakin Mami. Ta yi sallama, ta shiga Mami na zaune kan ƙaramin sofa tana jan tasbaha. Ta ɗaga hannu “Zo ki zauna.” Zahra ta ƙarasa ta zauna a ƙafafun Mami kamar yadda ta saba tun tana ƙarama. Mami ta shafa kanta cikin tausayi. Sai ta yi shiru na ɗan lokaci. “Baby.” “Na’am.” “Na san zuciyarki.” “Kuma na san kina son haɗa alkhairi ne” Zahra ta yi murmushi, amma ba ta ce komai ba. Mami ta ci gaba “Amma akwai wani abu da nake son ki fahimta.” Ta ɗan gyara zamanta “Ba a wuce gaba wajen haɗa aure.” Zahra ta ɗaga kai tana kallonta. Mami ta ce a hankali “Idan aka yi aure kuma aka samu matsala… ba wai namiji da matar kaɗai za su ji zafi ba, duk wanda ya shiga tsakani ma zai shiga damuwa” Ta ɗan yi shiru. Sannan ta ci gaba. “Misali…” “Idan Saudat ta fito da wani hali da ba a sani ba, Ya Umar zai yi kuka da ke Ni, gani zai yi kinsa ni kuma kin boye masa “Idan kuma… Allah Ya kiyaye…” “Ya Umar ne ya fito da wani hali…Saudat ce za ta yi kuka da ke Ne, gani zata yi kin boye mata. Kuma hakan na bata zumunci” Saboda haka… “Ki bar kowa da ƙaddarar da Allah Ya rubuta masa. Idan Allah Ya rubuta matarsa ce… Ko babu wanda ya haɗa su, za su haɗu” Tayi shiru Tana kallon fuskarta, sai kuma ta daura “Idan kuma babu aure tsakaninsu ko duniya ta haɗu… ba za su zaɓa zana mata da miji ba.” Zahra ta yi shiru Tana sauraron Mami cikin nutsuwa, sai kuma ta ɗan haɗe gira. “Mami…” “Taya kika san Saudat ce?” Mami ta yi wani murmushin manya. Ta ɗan ja kumatun Zahra “Da ba ni na haife ki ba… Sai ki yi min wannan tambayar.” Zahra ta fara dariya. “Ashe kin gane?” Mami ta amsa tana murmushi. “Har tun lokacin da kika fara wannan maganar. Na riga na fahimci inda kika dosa.” Zahra ta sauke kanta ƙasa cikin kunya, tana dan murza yatsunta. “Sorry Mami.” Mami ta ɗago haɓarta. “Kada ki ba ni haƙuri. Ki dai koyi darasi.” Zahra ta gyada kai. “Na fahimta Kuma ba zan sake cewa komai ba.” Mami ta yi murmushi cikin gamsuwa. “Better! Allah Ya miki albarka, ya ƙara miki hikima.” “Ameen, Mami.” Zahra ta miƙe tsaye, ta sunkuya ta yi wa Mami kiss a kumatu. “Good night.” “Good night, Baby.” Ta juya, ta fita daga ɗakin. Yayin da Mami ta bita da kallo… Sai ta yi murmushi ita kaɗai. Ta san Zahra tana da zuciyar taimako. Sai dai kuma… Har yanzu tana cikin shekarun da zuciya ke rinjayar tunani. Shi ya sa ta ga dacewar ta koya mata cewa… Ba kowace ƙauna ce ake mayarwa aure ba, kuma ba kowace matsala ce mutum zai shiga tsakani ba #Farashin izzah 500 ne ta wannan acc no 7084571222, Hauwa Jibrin Opay Shaidar biya ta wannan 08110615256 Chapter 45 Ranar Lahadi ce. Tun bayan sallar Asuba, gidan ya kasance cikin nutsuwa. Ba a jin hayaniyar zuwa makaranta ko shirye-shiryen fita aiki kamar sauran ranakun mako. Bayan sun gama breakfast… Zahra ta ɗan yi ta kai-komo a parlour Kallo ɗaya za ka yi mata ka san akwai abin da take son faɗa. Sai dai tana neman lokacin da ya dace. Ya Umar na shirin fita zuwa gymnasium ya ɗan yi training Da ta hango shi… ta ƙarasa gare shi da sauri tana kwala masa kira “Yaya…” Ya waigo. “My Baby.” Ta karasa da sauri ta tsaya gabansa tana murza yatsunta Ya ɗan yi murmushi “Lafiya?” Ta sauke numfashi. “Na zo na ba ka haƙuri.” Ya Umar ya ɗan haɗe gira. “Haƙuri? Na me?” Ta ɗan sunkuyar da kai “Saboda na dame ka da maganar aure.” Ya Umar ya fara dariya a hankali. Ya ɗora hannunsa a kanta. “Baby… ba komai, Ni nama manta.” Ta ɗago tana kallonsa. “Da gaske?” “Da gaske.” Ya amsa mata Sai ta yi murmushi, Nan take fuskarta ta sake. Sai kuma ta ce, “Yaya…” “Ina da wata ƙaramar magana.” “Uhum? Ina ji” “Za ka kai ni gidan Saudat? Ina son kai mata wasu kaya.” Ya Umar ya kalleta na ɗan lokaci. Sannan ya gyada kai “Toh, ba matsala. Idan kin shirya…” “Ki sanar da ni, sai mu tafi” Fuskarta ta cika da annuri. “Thank you, Yaya.” Ta juya da sauri, ta nufi sama, shi kuma ya juya ya fita.. Ranar ta ci gaba da tafiya cikin nutsuwa, har zuwa yamma… Zahra ta gama duk abin da take yi, tanq zaune tana duba wayarta… Sai ta ji knocking, ta ɗaga kai tana kallon kofar sannan ta tashi, ta buɗe Ya Umar ne. Ya jingina da ƙofar. “Ready?” Ta yi saurin gyada kai “Yanzu?” “Eh.” “Idan kin shirya… Mu tafi.” “Okay.” Ta yi murmushi. Da sauri ta koma cikin ɗakin, ta ɗauki wayarta sannan ta fito daga ɗakin. A corridor ta kwala kira “Anty Binta.” Mai aikin gidan ta amsa da sauri. “Na’am Zahra” “Kin ga fancy bag ɗin nan da ke ɗakina?” “Eh.” “Don Allah ki kai shi wajen motar Yaya, ki saka a boot.” Anty Binta ta amsa cikin ladabi. “Toh Hajiya Zahratyy” Nan take ta shiga ɗakin. Ta ɗauko babban fancy bag ɗin da ke cike da kayan da Zahra ta ware wa Saudat, ta sauko da shi a hankali. Ta kai shi inda motar Ya Umar take. Ya Umar ya buɗe boot, ya karɓa daga hannunta sannan ya saka ciki “Nagode.” “Babu komai Alhaji.” A can sama kuwa… Zahra ta sake shiga ɗakinta. Ta canza kaya, ta aka wata doguwar abaya mai launin dusty rose, ta ɗaura matching veil dinsa Ta ɗan shafa turare, ta ɗauki handbag ɗinta, ta kalli kanta a mirror. Ta gyara veil ɗinta kaɗan, sannan ta fito. Kai tsaye ta nufi ɗakin Mami. Ta yi sallama. “Assalamu alaikum.” “Wa alaikumus salam.” Mami ta ɗago kai. “Ina za ki kuma?” “Zan bi Ya Umar. Za mu je gidan Saudat.” Mami ta yi murmushi. “Toh! A dawo lafiya.” “In shaa Allah.” Ta sunkuya, ta rungumi Mami. Sai ta fito. Da ta sauko ƙasa… Ta tarar da Ya Umar ya riga ya kunna motar. Yana zaune yana jiranta. Da ya ganta… Ya buɗe mata front seat. Ta shiga, ta ɗaura seat belt. Ta yi masa murmushi. “Sorry na ɓata maka lokaci.” Ya girgiza kai. “Ba ki ɓata min komai ba.” Mai gadi ya yi saurin buɗe babban gate. Motar ta fita daga gidan A hankali Ya Umar ya ɗauki hanyar unguwar da Saudat suke zaune… Zahra na zaune gefensa, zuciyarta cike da farin cikin cewa yau za ta faranta wa ƙawarta rai ba tare da ta ji an tausaya mata ba Bayan kusan mintuna talatin da barin unguwarsu… Ya Umar ya rage gudun motar Suka shiga ƙunƙuntar layukan cikin gari. Yara birjik na wasa a bakin hanya kamar ko da yaushe A hankali… Ya Umar ya faka motar a gaban gidan Saudat. Ya kashe motar, ya waiwayo ya kalli Zahra “Mun iso ko Madam?” Ta gyada kai. “Thank you, Yaya.” Ta buɗe ƙofar motar ta sauka, ta ɗan kalli gidan.. kamar yadda ta bar shi kwanakin baya… Haka yake. A tsakar gidan ana jin muryoyin yara suna wasa Zahra ta yi murmushi Sai ta ɗaga murya “Aliyu!” Ba jimawa… Ƙaramin yaron ya leƙo daga cikin gidan Da ya hango Zahra… Fuskarsa ta washe “Laa ke ce!” Ya yi gudu ya ƙaraso. “Ina kwana.” “Lafiya lau Aliyu.” “Ya gida?” “Alhamdulillah.” Ta nuna masa motar “Zo mana.” Ya biyo bayanta Da suka isa bayan motar… Ya Umar ya sauko ya buɗe boot. Fancy bag ɗin mai girma ya bayyana. “Ka taimaka ka ɗauka sai ka shiga da shi ciki, ko?” “Toh.” Ya amsa da Ya Umar ya fito daga motar ya karasa wajensu, ya ɗaga bag ɗin ya miƙa masa Aliyu ya karɓa da hannaye biyu Sai da ya ɗan karkata saboda nauyinsa. Ya Umar ya yi dariya. “Zaka iya ɗauka kuwa?” Aliyu ya gyara riƙonsa “In shaa Allah zan iya.” Zahra ta yi dariya “Idan ya yi maka nauyi ka faɗa fah” Ya girgiza kai da sauri. “A’a. Zan iya.” Suka nufi ƙofar gidan tare, suna shiga tsakar gidan… Mahaifiyar Saudat ce ta fito daga ɗaki tana riƙe da ɗan ƙaramin buta. Da idanunta suka sauka kan Zahra… Nan take fuskarta ta cika da fara’a. “Lale Maraba” Zahra tayi murmushi ta gaishe ta cikin mutuntawa “Ya kika baro iyayenki” “Lafiya ƙalau.” Mama ta ɗago idanunta. Sai ta hango Ya Umar tsaye a bakin ƙofar gidan yana jingine da motarsa Nan take ta gyara tsayuwarta cikin girmamawa. “Sannu da zuwa.” Ya Umar ya ɗaga kai Kai kalle tsohuwar Matar, sai kuma ya ɗan sunkuyar da kai cikin ladabi ya karasa bakin kofar ya ce “Yauwa Mama. Barka da warhaka, Fatan an wuni Lafiya” “Lafiya lau.” Mama ta yi murmushi. Ya Umar yana juya ya koma cikin motarsa ganin unguwar babu wata privacy Saudat ta fito daga cikin ɗaki bayan jin muryoyin su Da ta ga Zahra.. ta yi wani irin murmushi “Zahra!” Ta ƙaraso da sauri, ta rungume ta. “Ban yi tsammanin za ki sake zuwa da wuri haka ba.” Zahra ta yi dariya “Na ce bari na zo na ganki.” Aliyu kuwa… Har sannan yana riƙe da babban fancy bag ɗin. Ya ɗan ɗaga shi yana kallon Saudat, sai kuma ya kalli Zahra “Anty Ina zan ajiye wannan” Zahra ta murmushi “Sorry ka shigar da shi ciki, na Saudat ne.” Saudat ta haɗe gira cikin mamaki “Nawa kuma?” Ta kalli Zahra Zahra ta yi murmushi kawai “Mu shiga ciki…” Saudat ta bi bag ɗin da kallo. Zuciyarta ta fara bugawa da sauri. Ta san Zahra ba ta taɓa zuwa hannun empty ba, amma jakkan kuma fah Ya kai abban fancy bag ɗin cikin parlour yana haki saboda nauyinsa Ya ajiye shi a gefen tabarmar da ke parlour. Sai ya waigo yana kallon Zahra. “Anty anan zan ajiye?” Zahra ta gyada kai. “Eh! Nagode sosai Aliyu.” Ya yi murmushi “Babu komai.” Daga haka ya juya ya fita zuwa tsakar gida Idanun Saudat suka koma kan bag ɗin. Sai kuma ta kalli Zahra. Ta haɗe gira cikin mamaki “Zahra… Mene ne wannan?” Zahra ta yi kamar ba ta ji ba. Ta yi murmushi kawai Sannan ta miƙe tsaye. “Ki gyara fuskarki, ki zo ki raka ni waje, kar Yayana ya yi ta jira.” Saudat ta ɗan yi mamaki amma ta miƙe, ta shiga ciki ta ɗauki hijabinta ta saka Da ta fito… Zahra ta kalleta daga sama har ƙasa, ta ɗan taɓe baki cikin wasa. “Joor… Ki sake gyara fuskarki mana, kin fito kamar za ki yi kuka.” Saudat ta saki murmushi “Ke ma dai…” Ta koma cikin dakin ta gyara fuskanta da kyau sannan ta canza hijab, ta sake fitowa “Yanzu fa?” Ta tambaya Zahra ta yi murmushi “Perfect.” Ta juya ta fara tafiya, Saudat ta bita a baya, da suka kai bakin ƙofar parlourn Saudat ta tsaya. “Zahra!” Ta waiwayo “Kin manta kayan nan fa.” Zahra ta girgiza kai. “A’a. Ban manta ba.” Ta yi shiru na ɗan lokaci. Sannan ta ce cikin murmushi “Naki ne.” Saudat ta tsaya cak, kamar ba ta ji daidai ba. “Nawa?” Zahra ta gyada kai “Eh. Naki” Saudat ta zuba mata ido, ta kasa magana balle motsi, Kamar an dasa ta a wajen Zahra ta yi murmushi ta koma baya, ta kamo hannunta. “Mu je mana.” Har sannan Saudat ba ta iya cewa komai ba. Idanunta suka fara cika da ƙwalla, amma ta haɗiye su. Zahra ba ta ba ta damar yin magana ba, ta jawo ta har suka fito tsakar gida. Mama na zaune bakin ƙofa. Da ta ga su… ta yi murmushi “Har za ku tafi?” Zahra ta sunkuya cikin ladabi “Eh! Mama” Mama ta ɗaga hannu. “Toh Allah kiyaye hanya, an gode” “Ameen.” Suka ƙarasa bakin gate. Ya Umar na jingine da motarsa yana duba wayarsa. Da ya ji takunsu… Ya ɗago kai. Zahra ta yi murmushi. “Yaya… ana gaishe ka.” Ya Umar ya ɗan yi mamaki. Mamakin Zahra kawai yake yi, wato wannan ma another plan of her ne, amma bai nuna komai ba Ya gyada “Yauwa. Ya studies” “Lafiya lau.” Saudat ta sauke kanta ƙasa cikin kunya. “Nagode.” Zahra ta buɗe ƙofar motar, sai ta waiwayo. “Toh…” “Bye. Za mu tafi yanzu “ Saudat ta yi saurin sake cewa, “Amma…Kayan nan fa?” Zahra ta yi murmushi “Idan kin shiga ciki… za ki gani, Nace naki ne” Ba ta ƙara ba ta damar magana ba, ta rufe ƙofar motar Ya Umar ya kunna motar. A hankali suka bar unguwar. Saudat kuwa… Ta tsaya nan wajan ta kasa motsi, har sai da motar ta ɓace daga ganinta Ta sauke numfashi, ta juya a hankali ta nufi cikin gida… Yayin da zuciyarta ke bugawa da sauri. Dan ba ta san me Zahra ta bar mata a cikin wannan babban bag ɗin ba. Tun daga bakin ƙofa idanunta suka sauka kan babban fancy bag ɗin da ke ajiye a tsakiyar parlour. Kamar yana jiranta ta ƙarasa kusa da shi, ta durƙusa. Hannunta na ɗan rawa “Me Zahra ta saka a ciki ne?” Ta buɗe zip ɗin a hankali. Tana ɗaga murfin… Sai ta tsaya cak. Ta zaro Idanunta “Innalillahi…” Ta ɗaga rigar farko Sabuwar atamfa ce mai matuƙar kyau, ta ajiye ta gefe Ta sake ɗaukar wata, doguwar abaya ce mai tsada Ta ci gaba da cirowa ɗaya bayan ɗaya tana irgawa Har ta rasa ƙirgawa. ɗan karamjn Parlour ɗin ya fara cika da kaya masu tsada Wasu har label ɗinsu bai cire ba. Saudat ta kasa magana ta rufe baki, sai kuma ta yi wata irin ƙara. “Mamaa!!” “Mama ki zo da sauri!” Muryarta ta sa Mama ta fito da gudu daga kitchen ta shigo parlon “Lafiya? Me ya faru?” Da ta shigo parlour… sai ta tsaya cak. Idanunta suka kai kan kayan da suka bazu ko’ina. Ta kasa motsi, ta kalli Saudat, ta sake kallon kayan. “Subhanallah… Wannan duka fa?” Saudat ta kasa cewa komai. Sai ta nuna bag ɗin da hannu. “Mama… Zahra ce ta ba ni.” Mama ta zaro ido. “Duk wannan?” Saudat ta gyada kai. Hawayenta suka fara zuba. “Wallahi ban sani ba, ta ce na raka ta waje, tana tuna mata da bag ɗin… Sai ta ce Naki ne.’” Muryarta ta katse, ta fashe da kuka, ta zauna ƙasa tana rufe fuskarta. “Mama… Me ya sa take min haka? Me na taɓa yi mata?” Mama ta zauna kusa da ita Ita ma idanunta sun cika da ƙwalla. Ta ɗauki ɗaya daga cikin kayan, ta shafa shi da hannu, ta girgiza kai “Ya Allah Ka saka mata da alkhairi. Ka buɗe mata ƙofofin rahamarka, ka ƙara mata lafiya, ka ƙara mata arziki mai albarka, ka kare ta daga idon hassada. Ka sanya farin ciki ya zama abokin rayuwarta.” “A duk inda ta sa ƙafa… ka sanya alkhairi ya biyo bayanta.” Saudat na kuka. Mama na addu’a. Wannan moments ɗin ya cika da wani irin yanayi na godiya da taɓuwar zuciya. Zahra ba kawai ƙawarta ba ce. Ta kasance wata ni’ima da Allah Ya aiko mata a lokacin da ba ta zata ba. Can sai Saudat ta share hawayenta da bayan hannunta, ta miƙe tsaye da sauri. “Mama… Wayata.” Mama ta nuna mata kan ƙaramin tebur. “Can.” Ta yi saurin ɗauko wayarta. Hannunta har yanzu na rawa, ta shiga contacts. Ta danna sunan Princess Zahra 👑❤️ Nan take wayar ta fara ringing A ɗaya ɓangaren kuwa… Motar Ya Umar na tafiya cikin nutsuwa, sun kusa isa gida Zahra na zaune a front seat tana kallon titi ta window. Wayarta da ke cikin handbag ta fara ringing, ta ciro ta. Da ta ga sunan Saudat… Sai ta yi murmushi. Ta ɗaga wayar. “Hello, Saudaty.” A can ɓangaren… Saudat ta kasa magana, sai kuka kawai take yi. Zahra ta ɗan ɗaga gira “Hello! Saudat Are you okay?” Har yanzu… Shiru sai sautin kukanta Zahra ta ɗan yi dariya a hankali “Ke kuma me ya sa kike kuka?” Daga ƙarshe Saudat ta samu damar magana. “Za… Zahra…” “Meye haka?” “Meye na yi…” “Da har kika yi min wannan alkhairin?” Muryarta na rawa, kuka na katseta Zahra ta jingina da seat, ta yi murmushi mai taushi “What are friends for?” Saudat ta sake fashewa da kuka. “Wallahi…” “Ban taɓa ganin irinki ba.” “Allah Ya saka miki.” “Allah Ya saka miki da gidan Aljannah.” “Allah Ya ƙara miki arziki.” “Allah Ya sa duk wanda ya yi miki hassada…” “Ya kasa ganin daidai” Zahra ta yi murmushi. “Ameen.” Sai ta ce cikin tausasawa, “Saudat! Please ki daina kuka. Kin ji?” “Kayan ba wani abu ba ne. Kuma… kar ki ce ba zaki saka ba” Saudat ta yi saurin girgiza kai. “A’a. Wallahi ba zan taɓa ba ki ba, Nagode sosai.” Zahra ta yi dariya. “Shi kenan.” “Yanzu ki yi murmushi.” “Kuma ki saka ɗaya daga cikinsu idan za ki zo school.” Saudat ta yi murmushi cikin kuka. “In shaa Allah.” “Bye.” “Bye Princess.” Da ta kashe wayar… Ta sake rungume wayar a ƙirjinta Wani irin natsuwa ta mamaye zuciyarta Ya Umar ya ɗan kalli Zahra “Ta yi farin ciki kenan?” Zahra ta yi murmushi tana kallon wayarta “Sosai.” Ya Umar ya girgiza kai cikin gamsuwa “Allah Ya saka miki.” “Ameen.” Ta amsa a hankali. Sai ta mayar da wayarta cikin handbag. FARASHIN IZZAH 500 ne ta wannan acc din 7084571222, Hauwa Jibrin, Opay shaidar biya ta nan 08110615256 Chapter 46 Bayan ɗan lokaci suka isa gida. Mai gadi ya buɗe gate Ya Umar ya shigar da motar compound. Yana parking, Zahra ta buɗe ƙofar motar. Kafin ta fita sai ta waiwayo. “Thank you once again.” Ya Umar ya girgiza kai yana murmushi “Go inside.” Ta gyada kai, ta fita da sauri. Kai tsaye ɗakin Mami ta nufa, ta tura ƙofar tana sallama. Mami na zaune tana karanta Al-Qur’ani. Da ta ga Zahra… Ta yi murmushi “Kin dawo?” “Eh Mami” Ta zauna kusa da ita. Ba tare da ta jira an tambayeta ba… ta fara ba ta labarin komai. “Mami da muka fita… Ban ma bari ta buɗe bag ɗin a gabana ba.” “Muna kan hanya, sai ta kira ni. Kuka take yi wallahi har na tsorata.” Ta yi dariya. “Mami… Kin ji yadda take min addu’a kuwa?” Mami ta yi murmushi. “Allah Ya karɓa.” “Ameen, amm Mami na ji daɗi sosai, na fi jin daɗin farin cikinta fiye da kayan da na ba ta.” Mami ta shafa kanta. “Allah Ya ƙara miki wannan zuciyar.” “Ameen.” Daga haka ta miƙe tsaye tana murmushi ta ce “Mami lemme rest” tana faɗin haka ta wuce zuwa ɗakinta Ana dab da kiran sallar Magrib, sai aka yi sallama daga kofar parlour, kuma babu kowa a parlon sai masu aiki dake girka diner a kitchen Mama Ladi ta yi saurin zuwa, tana buɗe entrance door taga mutane tsaye, murmushi ɗayan tayi ta ce “Mami fah?” “Bari na kirata, ku shigo” ta fad’a daga haka ta nufi sama su kuma suka shigo parlon Ɗakin Mami ta shiga da sallama “Hajiya kinyi baƙi.” Mami ta ɗago kai “Su waye?” “Wata yarinya ce da wata dattijuwa, daga gani kamar mahaifiyarta ce, amma ita yarinyar ina ganinta wani lokacin anan” Mami ta miƙe daga kishingiɗin da take “Toh gani zuwa" Ta miƙe tsaye Ita kuma Mama Ladi ta fita Bayan Mami ta sauko ƙasa, da ta isa parlour… Sai ta ga Saudat ce. A gefenta kuma wata dattijuwa mai kamala, sanye cikin tsaftatacciyar atamfa duk da tsufarta Da suka ga Mami Nan take suka miƙe “Barka Hajiya” “Yauwa, Barkan mu” Mami ta amsa da fara’a “Sannu da zuwa! Bismillah, ku zauna mana” Suka sake zama, Mami ta kalli Mama Ladi “Je ki kira Zahra, ki ce ta sauko” “Toh Hajiya.” Zahra na gyara hijabinta bayan ta yi alwala, Mama Ladi ta turo ƙofa. “Zahra, Mami na kiranki.” “Toh.” Daga haka ta ajiye hijab ɗinta Ta sauko cikin sauri. Da ta shiga parlour… Idanunta suka sauka kan Saudat, sai kuma mahaifiyarta, ta yi mamaki sosai “Mama?” Saudat ta yi murmushi cikin kunya. Mahaifiyarta ta miƙe tsaye, Kafin Zahra ta ƙarasa… Sai ta kama hannunta “’Yata Allah Ya saka miki da alkhairi.” Zahra ta ji kunya ya kamata Ta yi saurin riƙe hannunta. “Mama don Allah kiyi shiru, ba komai na yi ba.” Mama ta girgiza kai “A’a ’yata, a wajenmu ba ƙaramin abu ba ne.” “Kin faranta wa ɗiyata rai Allah Ya faranta miki.” Saudat ma ta yi shiru Sai murmushi take yi, idanunta cike da ƙwalla. Mami ta yi murmushi tana kallonsu “Ai da baku wahalar da kan ku na zuwa ba, duk yiwa Kai ne. Dama kuma Zahra tun tana ƙarama.. tana da son taimakon mutane.” “Idan ta ga wani cikin buƙata… Ba ta samun natsuwa har sai ta taimaka masa” Mama ta kalli Zahra da wata irin ƙauna. “Allah yayi mata fiye da zato” “Ameen.” Mami ta amsa. Mama kam sai addua take Zahra kuma sai jin kunyar irin yabon da ake mata take yi, tana ta ƙoƙarin sauya zancen saboda ba ta son a riƙa ɗaukar abin da ta yi tamkar wani babban alheri ne. Sun ɗan zauna na wasu mintuna suna hira cikin girmamawa. Sai Mama Ladi ta kawo musu lemo da snacks Mahaifiyar Saudat ta ɗan kurɓa kaɗan kawai, ta mayar da cup ɗin a hankali ta ajiye Daga haka ta miƙe tsaye Saudat ma ta miƙe tare da ita. Mami ta ce, “Haba, ai da kun ƙara zama mana.” Mahaifiyar Saudat ta yi murmushi. “A’a Hajiya. Kar dare ya yi mana. In shaa Allah wata rana za mu sake zuwa.” Mami ta gyada kai. “Toh shikenan! Allah Ya kai ku lafiya.” “Ameen.” Zahra ta ƙarasa kusa da Saudat. Ta kamo hannunta “Shine sai kin fito da Mama a wannan Magrib din” Saudat ta yi murmushi cikin kunya. “Wallahi Mama ce ta ce sai mun zo. Ni ma na ce ai ba sai mun wahalar da ku ba, amma ta ƙi.” Mahaifiyarta ta yi dariya. “Toh ai dole ne, ba za a yi mana irin wannan alkhairin mu zauna a gida ba.” Zahra ta yi murmushi. “Nagode da zuwa.” Saudat ta matso kusa da ita, ta rungume ta a hankali. “Allah Ya saka miki.” Zahra ta maida rungumar. “Ameen! Hope yanzu kin daina kuka?” Saudat ta yi dariya. “In shaa Allah.” Daga haka suka nufi kofa Mami da Zahra suka raka su har bakin gate. Suna isa bakin gate… Mai gadi ya riga ya buɗe musu. Mahaifiyar Saudat ta sake juyowa, ta ɗaga hannayenta. “Allah Ya albarkaci wannan gida. Ya haɗa ku da alkhairi, ya kare ku daga dukkan sharri.” “Ameen.” Mami da Zahra suka amsa tare. Saudat ta yi wa Zahra wani kallon godiya. Zahra ta ɗaga mata hannu tana murmushi. “See you tomorrow.” Saudat ta yi murmushi. “In shaa Allah.” Daga haka su Saudat suka fita daga gidan, Mai gadi ya rufe gate A hanyar su ta komawa cikin gidan Zahra ta sauke numfashi a hankali Mami ta kalleta ta yi murmushi. “Kin ga dai wani lokaci ƙaramin alkhairi da mutum yake ganin bai kai komai ba… a wajen wani shi ne mafi girman farin cikin rayuwarsa.” Zahra ta lumshe ido kaɗan, ta gyada kai cikin natsuwa. “Kin yi gaskiya, Mami.” Washegari… Tun kafin ƙarfe shida na safe…Alarm ɗin Zahra ya fara ringing Ta buɗe idanunta a hankali sannan ta kashe alarm ɗin Miƙe wa tayi zaune tana murza idanunta, sai kuma kai tsaye ta nufi banɗaki. Ta yi alwala tare da brush, tana fitowa ta shimfiɗa sallaya sannan ta tayar da Sallah cikin nutsuwa. Bayan ta idar tare da addu’o’in safe da maraice ta fara shiryawa domin makaranta. Ta zaɓo wata doguwar abaya mai launin navy blue, Ƙaramin bracelet a hannunta. Black handbag ɗinta. Da flat shoes baƙaƙe masu kyau Ta kalli kanta a mirror bayan ta gama saka kayan, ta gyara veil ɗinta. Sai ta sauko ƙasa. Ta yi breakfast cikin gaggawa. Ta yi sallama da Mami, ta gaisa da Abbah. Daga haka ta ɗauki mukullin motarta ta fita Mai gadi ya buɗe mata gate. A hankali ta ja motarta ta fice daga gidan…. Saudat bayan tayi sallah ta fita compound kafin karfe 7 ta gama Duk wani abu da zata yi na taimakon gida Mama ta shiga daki tana kallon Saudat ta ce “Saudatu ba zaki shirya ba kar ki makkara?” Saudat ta gyaɗa Kai ta ce “Mama Kaya zan saka ai nayi wanka” Kaii ta gyada mata hadi da barin bakin kofar Saudat ta jawo babban fancy bag ɗin da Zahra ta ba ta, ta buɗe shi, ta ɗan tsaya tana kallon kayan. Har yanzu ba ta saba da ganin su ba, sai ta zaɓi wata doguwar abaya mai launin olive green mai musulmin kyau, ta saka ta a hankali, ta dade tana kallon kanta harta manta da wani boko Ta ɗaura veil, haɗi da shafa lip-balm, ta sake tsayawa a gaban mirror, ta kasa gane kanta Kamar ba ita ba. Mama ta fito daga ɗayan ɗakin Da idanunta suka sauka kan Saudat… sai ta dafe ƙirjinta da sauri tana kallonta “Ehyee! Saude? Kin ganki kuwa? Allah kinyi kyau sosai” Aliyu ma ya shigo daga tsakar gida, da ya ga yayarsa, sai ya zaro ido “Yaya Saudat? Allah kin yi kamar wata Hajiya” Saudat ta yi dariya “Aliyu ka cika surutu.” Mama ta ƙarasa ta shafa stones dake jikin veil din, sannan ta shafa kumatunta “Allah Ya saka wa Zahra.” Saudat ta sauke kai. “Allah Ya saka mata da aljannah.” Mama ta gyada kai “Ameen.” “Yanzu ki je ki yi karatunki, Allah Ya ba ki sa’a.” “Ameen.” Saudat ta ɗauki jakarta, ta i musu sallama daga haka ta fita A makaranta… Students na ta shigowa ɗaya bayan ɗaya, wasu una hira, wasu suna sauri zuwa lecture hall, wasu kuma suna zaune ƙarƙashin bishiyoyi Saudat ta shiga campus tana tafiya cikin nutsuwa. Sai dai… Yau ba kamar kullum ba. Mutane da dama na waigowa suna kallonta, not like before data zama kamar ghost Ita kuwa… Sai ta ƙara gyara veil dinta cikin jin kunya A can parking lot… Zahra ta faka motarta, ta ɗauki handbag ɗinta, ta fito Da zarar ta shiga faculty… Sai idanunta suka sauka kan wata da ke tsaye tare da Firdausi da Asiya. Ta tsaya cak Murmushi ya mamaye fuskarta “Saudaty!” Ta kira da ƙarfi Saudat ta waigo. Da idanunta suka sauka kan Zahra…Ita ma ta yi murmushi Zahra ta ƙarasa da sauri, ta tsaya tana kallonta daga sama har ƙasa Sai ta haɗe hannayenta. “Woooow.Look at you, I like ur Abaya, zan saya irinsa gaskiya dan yayi min kyau” Saudat ta yi ƙasa da kai saboda kunya Zahra ta girgiza kai “Wallahi kayan sun yi miki kyau sosai.” Firdausi ta yi dariya. “Ni ma, daga nesa ban gane Saudat ba.” Aasiya ta gyada kai “Wallahi ta canza.” Saudat ta yi murmushi tana jin kunya. Idanunta suka koma kan Zahra. “Me za ki ce min? Na ce miki ai, ke kyakkyawa ce.” Saudat ta yi murmushi, ba don kayan da ke jikinta ba. Sai don ta ji akwai mutanen da suke ganin darajarta fiye da yadda ita kanta take ganin kanta. Zahra kuwa… Ta ci gaba da kallon ƙawarta cikin farin ciki. Kamar ita ce ta saka kayan. Domin babu abin da ya fi faranta mata rai… Kamar ganin murmushi ya a kan fuskar Saudat…. Lecture ɗinsu na farko ya ƙare kusan lokacin azahar ne, da lecturer ya fita… Students suka fara ficewa daga hall ɗin, wasu library, wasu cafeteria, wasu kuma kai tsaye masallaci Zahra ta rufe notebook ɗinta, ta saka shi cikin handbag, ta kalli ƙawayenta. “Mu je sallah.” “Let’s go.” Duk suka nufi masallacin mata.. Bayan sun yi alwala.. suka shiga mallaci suka yi sallar Azahar cikin nutsuwa Bayan an idar… Zahra ta zauna na ɗan lokaci tana addu’a Saudat na gefenta. Firdausi da Asiya kuma na ɗayan gefen, da suka gama… Suka fito daga masallacin a hankali Iskar rana na kaɗawa Students na ta wucewa suna hira. Firdausi ta sauke ajiyar zuciya “Wallahi ni kam na gaji.” Aasiya ta yi dariya. “Da me kuma?” Firdausi ta ɗan taɓe baki. “Mama ta ce na dawo hostel kawai, ta ce ta gaji da cacan ƙudin mota.” Asiya ta yi dariya. “Ni ma fa jiya Baba ya tambaye ni… ‘Ke ba ku da hostel ne?’” Duk suka yi dariya. Zahra ta kalli su. “Toh…Idan duk za ku dawo hostel Ni ma zan dawo.” Firdausi ta tsaya cak. “Da gaske?” Zahra ta gyada kai. “Eh mana, ba zaku bar ni Ni kaɗai ba.” Sai ta juya ta kalli Saudat “Ke fa? Mama za ta barki?” Saudat ta yi murmushi “Eh Na taɓa yi mata maganar.” “Ta ce idan na samu kuɗi kuma na ga ya dace… ba ta da matsala.” Firdausi ta tafa hannu “Perfect.” Asiya ta yi dariya. “Shi kenan, zamu haɗe abun mu” Zahra ta gyada kai “Da yamma zan yi wa Abbah magana. Na san ba zai hana ni ba.” “Allah Ya sa.” Firdausi ta faɗa cikin farin ciki. Can kuma Zahra ta ce, “Come on! Mu je cafeteria, uunwa nake ji.” Asiya ta yi dariya “Ni ma.” Cafeteria ɗin faculty ɗinsu cike yake da ɗalibai Wajan ya gama gaurewa da aroma Daga shigarsu Idanu suka dawo kansu, wasu suka gaisa da Zahra. Wasu kuma idan suka hada ido sai su mata mutmushi Suka samu wani tebur a gefe, suka zauna Firdausi ta ɗauki menu. “Toh Madam Zahra. Me za ki siya mana yau?” Zahra ta yi dariya “Ke dai kullum ni.” Firdausi ta ɗaga kafaɗa “Ke ce mai mota, ke ce kuma mai kuɗi, ashe ba ke za ki biya ba?” Duk suka yi dariya. Zahra ta girgiza kai “Okay! Order whatever you want.” Firdausi ta yi wata irin dariya “Na san za ki faɗi haka.” Asiya ta ce, “Ni fried rice da chicken.” Firdausi ta ce, “Ni jollof rice da chicken “ Saudat kuwa ta yi shiru. Zahra ta lura, ta kalleta. “Ke fa?” Saudat ta yi murmushi. “Ko ruwa ma ya isa.” Firdausi ta buga hannunta. “Ke fah ki daina wannan halin.” Zahra ta kalli Saudat da ido mai nuna rashin Jin dadi “Saudaty! Order what you want.” Saudat ta ɗan yi shiru. Sai ta ce a hankali, “Toh… Fried rice da chicken.” Zahra ta yi murmushi cikin gamsuwa “That’s my girl.” Bayan ɗan lokaci Waiter ya kawo musu abincin, aka jera plates huɗu. Drinks da bottled water. Firdausi ta ɗauki spoon Ta ce, “Wallahi idan hostel ya haɗa mu…Faculty ɗin nan za ta sha labari.” Asiya ta yi dariya. “Musamman idan Zahra na tare da mu.” Zahra ta ɗaga gira. “Me ya sa?” Firdausi ta ce cikin wasa “Saboda ke ce za ki riƙa feeding ɗinmu.” Nan take… Duk teburin ya kaure da dariya, har Saudat… Wadda a baya ba kasafai take yin dariya da ƙarfi ba… Sai da ta riƙe cikinta tana dariya. Zahra ta kalle ta cikin farin ciki. A zuciyarta ta ce, “Alhamdulillah…” Suka fara cin abinci cikin nutsuwa Firdausi ce ta fi kowa surutu. Asiya na biye mata da dariya. Saudat kuwa yau ta fi kowace rana sakin jiki a cikinsu Bayan da suka gama cin abincin…Waiter ya zo ya kwashe plates ɗin. Zahra ta ciro wayarta daga handbag, ta kunna data Nan take notifications suka fara shigowa. Course rep taga yayi sending message, ta shiga class group ɗin Daidai lokacin wani sabon saƙo ya shigo Course Rep: “Attention everyone, all afternoon lectures have been cancelled due to an emergency meeting involving the lecturers. Students are advised to return to their hostels or homes. Thank you.” Zahra ta sake karantawa don tabbatarwa. Sai wani murmushi ya bayyana a fuskarta. Ta ɗaga kai, ta kalli ƙawayenta “Guess what?” Firdausi ta yi saurin cewa, “Abbah ya ce ki kai mu shopping.” Aasiya ta girgiza kai tana dariya “Wataƙila result ɗin assignment ya fito.” Saudat ta ce “Ko an canja venue lecture.” Firdausi ta ƙara cewa, “Ko kuma yau za ki biya da mu ki saya mana ice cream.” Zahra ta yi dariya, ta girgiza kai “Nope.” Ta ɗauki handbag ɗinta, ta rataya a kafaɗarta, sannan ta miƙe tsaye “Afternoon lectures…” “…have been cancelled.” Ta fada tana murmushi “Whattttt?!” Firdausi ta yi tsalle “Da gaske?” Zahra ta juya wayarta ta nuna musu saƙon. Asiya ta karanta. “Innalillahi, wallahi da gaske ne” Saudat ta yi murmushi “Alhamdulillah, dama I’m tired” Firdausi ta tafa hannu “Best news of the day” Ta yi dariya tana ɗaukar jakarta. “Allah ya albarkaci Course Rep.” Aasiya ta buga mata kafaɗa “Ke ma dai.” Duk suka yi dariya. Zahra ta saka wayarta cikin handbag. “Come on! Mu tafi.” Suka fito daga cafeteria tare Suna tafiya a harabar makarantar cikin hira da dariya. Students ma da dama suna ta duba wayoyinsu. Wasu kuma suna murna bayan sun ga irin wannan saƙon. Harabar makarantar ta fara watsewa a hankali… Saboda kusan kowa ya fara shirin komawa gida ko hostel, yayin da Zahra da ƙawayenta ke tafiya tare, kowacce na ba da shawarar abin da za su yi da wannan lokacin da suka samu ba zato ba tsammani. 500 ne, a biya ta wannann acc din 7084571222, Hauwa Jibrin Opay Shaidar biya ta wannan 08110615256_ Hauwajay writes Chapter 47 Bayan sun yi sallama da juna… Zahra ta juya tana kallon Saudat. “Come with me.” Saudat ta ɗan haɗe gira “Ina?” “Zan kai ki gida mana tunda hanyar mu ɗaya ce” “A’a Zahra, zan hau Napep, hanyar mu ko kaɗan ba hanya ɗaya bace Zahra ta harare “Saudat ki zo. Kar ki sa na sake maimaita magana.” Firdausi ta yi dariya “Ki bi ta kawai, kin san idan ta yanke shawara ba ta saurara” Asiya ma ta gyada kai “Exactly.” Saudat ta yi murmushi cikin kunya “Toh.” Su huɗu suka nufi parking lot. Da suka isa Firdausi da Asiya suka tsaya Firdausi ta yi wa Zahra bye “See you tomorrow.” “In shaa Allah.” Ta amsa Asiya ta rungume Zahra “Drive safely.” “You too.” Saudat ta tsaya tana jiran Zahra ta buɗe motar, da remote ta buɗe. Ta waiwayo “Shiga.” Saudat ta buɗe front seat, ta shiga cikin kunya Zahra ta zagaya ta shiga driver’s seat, ta ɗaura seat belt. Ita ma Saudat ta ɗaura nata Ta kunna motar, a hankali suka fita daga campus Tana driving cikin natsuwa, bayan kusan mintuna arba’in… Ta isa gida bayan ta ajiye Saudat gidansu, Mai gadi ya buɗe mata gate, ta shigar da motar ta faka a inda ta saba. Da ta sauko… Mama Ladi ta karɓi handbag ɗinta. “Sannu da zuwa Maman Babanta” Dariyar da bata yi Nita bace tayi “Oh ni Zahra mai suna iri iri” Mama Ladi data yi gaba ta fara dariya Ta shiga cikin gidan, kai tsaye parlour ta nufa. “Ohh Daddy’s princess is tired” “Must you always complain? Ai dama haka makaranta yake. Dan ma ke kina yi ne cikin gatanki” Mami ce ta amsa daga can Da ta leƙa… Sai ta ga Mami tsaye cikin kitchen. Apron a ɗaure a gabanta. Wasu kayan miya a kan island. Tana haɗa ido da Zahra, ta yi murmushi “Baby.” “Na’am Mami.” “Zo ki zo mu yi girki.” Zahra ta tsaya cak, ta kalli kitchen ta sake kallon Mami. Sai ta haɗe fuska kamar ƙaramar yarinya “Mamiiii…” Mami ta ɗaga gira. “Lafiya?” Zahra ta turo baki gaba “Kai Mami, ba ga masu aiki ba? Shine sai Ni kuma na zo na tayaki girki?” Mami ta naɗe hannayentq tana kallonta “Eh, su na nan amma yau…Ina son ki koya wani recipe, dan ba abun da kika iya sai shopping da order online” Zahra ta lumshe ido, ta yi kamar za ta yi kuka. “Mami wallahi I’m tired, ki tausaya min, yanzu fah na dawo daga school” Mami ta ƙure ta da ido “Toh? Gidan miji idan kika je za ki ce akwai masu aiki ne tun kina amarya?” Zahra ta dafe kanta “Wayyo Allah na, Mami ni dai ba zan yi aure yanzu ba.” Mami ta kasa riƙe dariyarta “Zo nan, ki daina drama ko na saɓa miki” Zahra ta ƙarasa tana taɓe baki “Wallahi Mami kin fi lecturers bada wahala” Mami ta buga bakinta, ta karɓe jakkanta ta miƙawa Anty Binta ta ce “Ki Kai mata ɗakinta" Ya mayar da dubanta ga Zahra “Ke kuma ki fara yanka albasa.” “Ni kuma zan haɗa sauran kayan.” Zahra ta ɗauki wuƙa, ta fara yankan albasa Bayan minti biyu… Idanunta suka fara zubar da hawaye Ta yi ƙara “Mamiiii! Waiii albasa tana cutarwa, kinga har kuka na fara fah” Mami ta yi dariya sosai “Wannan ai ba kuka ba ne Albasa ce kawai, kuma dama haka take. Ci gaba.” Kitchen ɗin ya cika da dariya. Masu aikin gidan ma na ta murmushi a ɓoye suna kallon yadda Zahra ke ta ƙorafi amma tana yin abin da Mami ta ce A hakaa dai dakyar aka samu aka gama wannan girkin, rabi da kwata ita dai bata fahimci komai ba kawai tasan duk abun da aka yanka a tukunya ake zubawa Da daddare bayan sun gama dinner kowa ya watse Abbah na zaune a parlonsa yana duba wasu takardu. Zahra ta shigo a hankali “Abbah.” Ya ɗago kai “My Baby.” Ta ƙarasa ta zauna kusa da shi, ta jingina da kafadarsa. Abbah ya shafa kanta “Lafiya?” Ta ɗan yi shiru, sai ta ce “Abbah…” “Hmm?” “Ina son magana.” “Ina ji Dear” Ta ɗaga kanta “Abbah… Ina so na koma hostel.” Abbah ya cire gilashin karatunsa, ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya kanta. “Hostel?” Ta gyada kai “Eh Abbah. Firdausi za ta koma, Asiya ma haka, Saudat ma, ni kuma ba zanji daɗi ba, kar su zo performance ɗinsu yafi nawa" Abbah ya yi shiru na wasu daƙiƙu yana kallon fuskarta Sai ya ce cikin natsuwa “Kin tabbatar?” Ta gyada kai ba tare da wata-wata ba “Yes, Abbah Ina son na gwada rayuwar hostel, Ina jin zai taimaka min sosai wajen karatu” Abbah ya jingina da kujera, ya ɗan yi murmushi “Toh… Ba zan ba ki amsa yanzu ba, zan fara yi wa Mami magana, sannan mu zauna mu tattauna.” “Idan muka ga ya dace.. shikenan.” Fuskar Zahra ta sake, nan take tayi murmushi, ta rungume hannunsa “Thank you, Abbah.” Ya shafa kanta “Amma ko kin koma hostel karatunki shi ne first priority.” Ta yi murmushi “I promise.” Abbah ya gyada kai cikin gamsuwa “Good girl.” Zahra ta sumbaci hannunsa cikin girmamawa Sannan ta miƙe cikin farin ciki… Tana fatan wannan karon, burinta na zama tare da ƙawayenta a hostel zai cika. Bayan Zahra ta fita zuwa makaranta… Gidan ya yi tsit Abbah ya dawo daga office ɗinsa na cikin gidan bayan ya gama duba wasu takardu. Ya shiga ɗakinsa, ya zauna kan sofa yana huta wa, bayan wasu mintuna… Mami ta shigo ɗakin, a hannunta akwai turaren wuta Da ƙamshinsa ya fara bazuwa a cikin ɗakin tun kafin ta shiga Ta fara zagayawa tana ƙona shi a sasanninta, nan ɗakin yayi wani iron cool kamshi Sannan ta gyara kan gadon haɗi pillow ɗin kan gado Ta daidaita duvet, ta ɗauki wasu rigunan Abbah da aka ajiye kan kujera ta ninke su. Abbah kuwa… Tun shigowarta yake kallonta cikin murmushi, ita ɗin tabbas peace ɗinsa ne Da ta gama komai ta sake masa murmushi, ta nufi ƙofa. “Na gama” Zata fita… Sai ya kira ta “My peace” Ta waigo haɗi da murmushinta dake kashe shi “Na’am?” “Zo mana” Murmushi ta yi ta ƙarasa Ta zauna a kujerar da ke gabansa. “Lafiya dai?” Abbah ya ɗan yi shiru, sannan ya ce “Maganar Zahra ce.” Mami ta gyara zamanta “Na san za ka yi maganarta idan Baby ce” Abbah ya ɗan yi murmushi “Kin san tana son komawa hostel?” “A’a gaskiya bamu yi magana ba, amma tunda ta maka magana tana son komawa ne” Abbah ya gyada kai “Ni ma na lura.” Ya jingina da kujera “My dear, Ke me kike gani?” Mami ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta amsa. “Da farko da ace ta ce Nile University take so kaga ai dole a hostel dama zata zauna, ko ma Pen resource da kake so” Abbah ya gyada kai. “Haka ne.” Mami ta ci gaba “Amma yanzu dan tana KASU zata iya zama, kuma idan aka yi la’akari da zirga-zirga… Lectures, Assignments, Group discussions.” “Wani lokaci ma practical. Hostel zai fi mata sauƙi.” Abbah ya yi shiru yana sauraronta. Mami ta ce “Amma ba za mu tura ta hostel kawai mu ce shi kenan ba” Abbah ya ɗaga kai “Me kike nufi?” “Za mu zauna da ita, mu yi mata nasiha. Rayuwar hostel ba kamar rayuwar gida ba ce, ba kowa ne irin wanda kika saba gani a gida ba.” “Akwai nagari, akwai kuma marasa tarbiyya, akwai masu son karatu, akwai masu son ɓata lokaci. Saboda haka dole ta san abin daya kai ta” Abbah ya yi murmushi “Wannan maganar taki ce” Mami ta yi murmushi ita ma “Ni dai abin da nake so ko ta je hostel, kar ta manta tarbiyyar da aka raineta da ita, kar ta shiga rayuwar kwaikwayo. Kar ta yarda matsi ko ƙawaye su canja mata halinta” Abbah ya gyada kai cikin gamsuwa “Dear wallahi kin faɗi abin da ke raina.” Sannan ya ce cikin natsuwa “Ni ma ban damu da zamanta a hostel ba. Abin da na damu da shi ne ta ci gaba da kasancewa Zahra ɗin da muka sani.” “Mai mutunci, mai kunya, mai son addini, mai sanin darajar kanta.” Mami ta yi murmushi Abbah ya ɗan yi shiru sai ya ce, “Toh idan haka ne, yau da dare idan ta dawo zamu zauna da ita muyi magana sosai, sannan mu yi mata duk abin da ya kamata.” Mami ta gyada kai “In shaa Allah.” Ta miƙe tsaye “Toh bari na je kitchen.” Abbah ya bi ta da kallo har ta kai ƙofa. Sai ya kira ta “My dear” Ta waiwayo “Na’am?” Ya yi murmushi. “Nagode.” Ta ɗan yi dariya. “Na me?” “Saboda yadda kike kula da yaran nan.” Mami ta sauke idonta tana murmushi “Allah Ya sa mu sauke amanar da Ya ɗora mana.” “Ameen.” Daga haka ta fita daga ɗakin… Ƙamshin turaren wutar da ta bari na ci gaba da sanyaya ɗakin, yayin da Abbah ya jingina da kujera, yana jin kwanciyar hankali cewa shi da Mami suna tafiya a hanya ɗaya wajen tarbiyyar Zahra Da yamma… Bayan Zahra ta yi sallar La’asar, ta ɗauki laptop ɗinta da physics notebook, sai assignment sheet ɗin da lecturer ya ba su Kai tsaye ta nufi ɗakin Ya Umar, ta yi knocking sau biyu. “Come in.” Ta tura ƙofar Ya Umar na zaune a kan study table ɗinsa Laptop a gabansa, wasu files da takardu suna warwatse Ya ɗago kai “My Baby.” Ta yi murmushi “Yaya Busy?” Ya ɗan kalli agogon hannunsa “Not really. Lafiya?” Ta ƙarasa ciki, ta ɗaga assignment paper ɗin “Please help me.” Ya ɗan yi dariya “Physics again?” Ta turo baki “Wallahi lecturer ɗin nan baya tausayinmu.” Ya miƙa hannu “Zo gani.” Ta zauna a kujerar da ke gefensa, taba shi paper ɗin, ya fara karantawa Sai ya gyada kai “Hmm ba shi da wahala, amma ina son ki fara solving ɗinIdan kin makale…” “Sai na taimaka miki.” Zahra ta yi wani iri da fuska. “Yaya please ka sani ai.” Ya harare ta da wasa “A’a ba zan miki assignment ba, ni zan koya miki ne sai Ke kuma ki yi da hannunki” Ta sauke ajiyar zuciya “Okay.” Ta buɗe notebook ɗinta, ta fara rubutu, kamar abun arziki ta fara, sai kuma ta tsaya. Ta cije bakin biro “Yaya…” “Hmm?” “Na makale.” Ya ɗan matsa kusa da ita, ya ɗauki biro Ya nuna mata inda ta yi kuskure “Ki duba nan.” “Kin rikita formula, shi ya sa answer ɗin ya ki fitowa.” Ta ɗan karkata kanta tana kallon yadda yake rubutawa. “Oooh… Ashe haka ne” Ya gyada kai “Eh, kada ki yi saurin solving.” “Ki fara fahimtar question ɗin.” Ta sake gwadawa, a wannan karon… ta samu answer ɗin, nan take ta yi murmushi “Yesss! I got it.” Ya Umar ya yi murmushi cikin gamsuwa. “Good, na san za ki iya.” Ta ci gaba da solving sauran questions. Duk lokacin da ta makale… Sai ya bata hint kaɗan ba tare da ya ba ta answer kai tsaye ba. Bayan kusan awa ɗaya… Ta sauke biro Ta miƙa notebook ɗin “Done.” Ya karɓa, ya duba ɗaya bayan ɗaya. Sai ya gyada kai “Excellent Question ɗaya ne kawai kina da ɗa mistake.” Ta yi saurin matsowa kusa “Ina?” Ya nuna mata, ta gyara Sannan ya mayar mata da notebook. “Now It’s perfect.” Zahra ta yi wani irin murmushin nasara, ta haɗa littattafanta. Ta kalli Ya Umar “Nagode sosai.” Ya ɗan taɓe baki. “Da kin ce ba za ki iya ba, Ashe kawai rashin sa kai ne” Ta yi dariya “Saboda kana kusa da ni ne. Shi ya sa” Ya girgiza kai yana murmushi. “Ki je ki sake karantawa kafin ki kwanta, kada ki dogara da abin da muka yi yanzu kawai.” Ta yi salute da hannu cikin wasa “Yes sir.” Ya Umar ya yi dariya “Get out.” Ta yi dariya ita ma Ta rungume notebook ɗinta ta fita daga ɗakin cikin farin ciki… Tana jin wani irin ƙwarin gwiwa cewa physics, wadda ta fi ba ta wahala, yanzu ta fara samun sauƙin fahimta saboda yadda Ya Umar yake koya mata cikin haƙuri ba tare da ya gaji da tambayoyinta ba…. Zahra na zaune a kan gadonta Assignment ɗin physics na gabanta. Tana sake karanta answers ɗin da ita da Ya Umar suka gyara. Lokaci zuwa lokaci sai ta yi murmushi idan ta tuna yadda ya riƙa ce mata, “Think first before solving.” A dai-dai lokacin… Aka yi knocking a ƙofar ɗakinta. “Come in.” Mama Ladi ce ta turo ƙofar. “Zahrau.” Zahra ta ɗago kai “Na’am Mama Ladi.” “Hajiya Mami na kiranki.” Zahra ta haɗe gira “Ni?” “Eh.” Ta ɗora biro a kan notebook “Lafiya dai ko?” Mama Ladi ta ce da wata fuskar da take ƙoƙarin ɓoye dariya, “Ban sani ba, kawai ta ce na kira ki.” Zahra ta miƙe daga kan gado Tana saka slippers ɗinta ta tambaya, “Mama Ladi… Ina take?” Mama Ladi ta amsa ba tare da wata-wata ba, “Kitchen.” Da zarar kalmar kitchen ta fita daga bakinta… Zahra ta tsaya cak, ta lumshe ido sai ta dafe goshinta. “Wayyo Allah…” Ta fara bubbuga ƙafa kamar ƙaramar yarinya. “Kaiii!” “Mama Ladi! Yanzu shikenan zata sake cewa girki wallahi Mami ta dai na tausayi a” Mama Ladi ta kasa riƙe dariyarta. Ta juya tana dariya, “Ni ban ce komai ba fa.” daga haka ta bar wajen Ita kuma Zahra… Ta ɗaga murya tun kafin ta isa kitchen. “Mamiiiiii! Wai kin ƙi yafe min ne idan ma laifi na miki?” Daga cikin kitchen Mami ta amsa tana dariya. “Zo mana my love” Zahra ta ƙaraso bakin ƙofa ta tsaya, ta haɗe hannaye a ƙirji ta turo baki gaba. “Mami… Don Allah wai yau ma?” Mami ta nuna mata chopping board “Eh, yau ma.” Zahra ta dafe ƙirji “Wayyo ni, Mami wallahi na yi assignment na gaji.” Mami ta ɗaga gira “Toh? Ni kuma ban gaji ba ne?” Zahra ta yi shiru Sai ta ƙarasa a hankali. Ta tsaya kusa da Mami, ta kalli kayan girkin da ke kan kitchen island “Kaiii duk wannan?” Mami ta yi murmushi. “Duk wannan, za mu yi.” Zahra ta wani marairaice fuska “Please ki kira Mama Ladi mana.” Mami ta girgiza kai “A’a dole ki koya fah, dan yanzu kin girma.” “Gobe idan kina gidanki…Ba za ki ce Mami ta zo ta dafa miki ba.” FARASHIN IZZAH 08110615256 Chapter 48 Zahra ta yi wata irin ƙara. "Mamiiii ki tausaya min, Ni ba chef ba ce." Mami ta yi dariya "Bance ke chef bace, kawai Ina son mace mai iya kula da gidanta ne” Ta miƙa mata wuƙa "Ga albasa, ki fara." Zahra ta karɓa kamar wacce aka tilasta, ta fara yanka tana ta ƙorafi. "Wallahi Ni dai zan kai ƙara wajen Abbah ya ceci ni." Mami ta yi kamar ba ta ji ba "Ki yanka daidai. Kar ki sare yatsanki." Can bayan mintuna kaɗan... Idanun Zahra suka fara zubar da hawaye saboda albasa kamar yadda jiya ya mata Ta ɗaga kai "Mamiiii Ga shi na fara kuka, haka fa kullum yake min” Mami ta kalle ta Ta kasa riƙe dariyarta. "Albasa ce, ba kuka ba ne, shame on you” Zahra ta share idanunta "Ni dai ban yarda ba. Albasa azzaluma ce." Duk masu aikin kitchen suka yi dariya Mama Ladi har sai da ta riƙe cikinta A ranta taji dadin maganar komawarta hostel ko ba komai zata huta da wannan matsin lamban da Mami ta tsiro sa Mami kuma na ci gaba da koya mata girki a hankali Yayin da Zahra ke ta ƙorafi, duk da a zuciyarta ta san Mami na yi ne domin amfaninta. Daren ranar... Bayan an idar da sallar Isha'i, an gama dinner, kowa ya watse zuwa ɗakinsa Abbah kuwa yana zaune a parlonsa na sama. Mami na gefensa tana karanta masa wani littafin story Sai Abbah ya ɗaga kai "My dear” "Na'am." "Ki kira min Baby." Mami ta gyada kai, ta ɗauki wayarta ta kira Zahra A ɗakinta... Zahra na kwance tana scrolling Instagram Wayarta ta fara ringing, da ta ga Mami ce... ta ɗaga da sauri. "Na'am Mami?" "Zo parlour ɗin Abbahn” “Yanzu, Mami?” "Eh." "Toh Mami." Ta kashe wayar, ta sauko daga kan gado, scarf ta dauka ta ɗaura a kai" Ta fito Da ta isa... Ta yi knocking "Come in." Ta shiga, ta a ƙarasa…. Ta zauna a ƙasa kusa da ƙafafun Abbah kamar yadda ta saba. Ta ɗago tana kallon su biyun "Meye laifi?" Abbah ya yi murmushi "Ba laifi bane Baby, magana ce." Zahra ta gyara zamanta "Ina ji, Allah sa kuɗi zaka bani” “Keep quiet, Baby” Abbah ya kalli Mami sai ya dawo da kallonsa kanta. "Maganar hostel." Da jin haka... Zahra ta ɗan gyara zamanta sosai, ta haɗe yatsunta cikin fargaba Abbah ya ci gaba "Ni da Mami... Mun yi magana sosai, mun kuma yi tunani." Mami ta gyada kai "Eh." Abbah ya yi murmushi "Daga ƙarshe dai mun amince" Na ɗan daƙiƙa... Zahra ta kasa magana, ta zaro ido "Abbah Kuna nufin..." Abbah ya katse ta "Za ki koma hostel." Fuskar Zahra ta cika da wani irin farin ciki, da sauri ta rungume Abbah. "Really? Abbah?" Abbah ya yi dariya "Eh, da gaske." Ta juya da sauri ta rungume Mami "Mamiiii! Thank you." Mami ta shafa bayanta "Amma..." Nan take Zahra ta sake nutsuwa, ta san akwai sharuɗɗa. Mami ta ce "Ba hostel ɗin cikin school ba. Za mu kama miki gida ne a off-campus" "Mai kyau, mai tsaro, kuma inda za ki samu kwanciyar hankali" Abbah ya ɗora da cewa, "Ba za mu yarda ki zauna ko'ina ba, za a nemo wajen da ya dace" Zahra ta gyada kai da sauri "Komai ma ya kasance, na yarda" Abbah ya yi murmushi "Yanzu dai ki saurare ni." Ta zauna da kyau. "Na farko…. Karatunki shi ne abin da ya kai ki can, ba yawon banza ba" "Na biyu... ki kiyaye sallolinki, kada ki bari rayuwar hostel ta canja miki addininki." Mami ta karɓa "Na uku... ki yi hulɗa da mutanen kirki, ba kowa ne aboki ba, ba kowa ne za ki shigar da shi cikin rayuwarki ba." Abbah ya ce "Na huɗu... kada ki yarda wani ya rinjaye ki da abin da bai dace ba, Idan akwai wata matsala... Ni da Mami muna nan” ya sauke ajiyar zuciya “Ki kira, Kada ki ɓoye mana" Mami ta ƙara da cewa "Kuma... Kada ki raina kowa saboda Allah Ya hore miki abin duniya, ki ci gaba da taimakon mutane, ki ci gaba da kasancewa Zahra ɗin da muka sani" Idanun Zahra suka ɗan cika da ƙwalla, ta gyada kai "In shaa Allah, ba zan ba ku kunya ba." Abbah ya shafa kanta "Na san haka. Shi ya sa ma muka yarda." Sai ya ɗan yi murmushi. "Sunday mai zuwa... za ki koma" Zahra ta sake yin murmushi Sai ta juya ta kalli Mami, ta sake kallon Abbah "Sunday?" "Eh." "Kafin lokacin za a gama shirye-shiryen." Sannan Abbah ya ƙara da cewa, "Umar gobe zai fita, daga can zai wuce school dinku, sai ya nemo miki gida mai kyau da tsaro, mai ruwa, mai wutar lantarki. Kuma kusa da school, ba na son ki riƙa wahala" Zahra ta dafe bakinta da hannunta, ta kasa ɓoye farin cikinta. "Ya Allah..." "Nagode Abbah." "Nagode Mami." Mami ta yi murmushi Abbah ya yi dariya "Yanzu je ki kwanta, gobe akwai lectures." Zahra ta miƙe, ta fara sumbatar hannun Mami, sannan na Abbah "Allah Ya saka muku da aljannatul Firdaus." "Ameen ya Rabb” Suka amsa tare Da murmushin da ya ƙi barin fuskarta.. ta fita daga parlon Har ta isa ɗakinta, ba ta daina murmushi ba. Ta faɗa kan gadonta tana rungume pillow, a hankali ta lumshe idanunta A zuciyarta kuwa... Ta fara tunanin yadda rayuwarta za ta kasance Washe gari... Tun da sassafe Zahra ta shirya cikin wata atamfa mai launin navy blue da silver, veil ɗinta a daidaice a kanta, agogon hannunta da ƙaramin bracelet suna ƙara haskata Ta yi sallama da Mami da Abbah, ta wuce compound, ta shiga motarta. Cikin nutsuwa ta kama hanyar makaranta. Da ta isa parking lot... Ta ɗauki handbag ɗinta, ta kulle motar ta nufi faculty Tun daga nesa... Ta hango Firdausi da Asiya suna tsaye ƙarƙashin wata bishiya suna jiranta. Da suka hango ta... Firdausi ta ɗaga hannu "Madam Celebrity!" Zahra ta yi murmushi "Ku daina fa." Ta isa wajensu, suka rungume juna. Asiya ta tambaya "Yaya maganar hostel?" Zahra ta yi murmushi kawai, ba ta ce komai ba. Firdausi ta taɓe baki "Wai kada ki ce har yanzu ba su yarda ba" Sai Zahra ta ce a hankali "They agreed." Na ɗan daƙiƙa... Firdausi ta zaro ido "Wait... da gaske?" Zahra ta gyada kai "Eh, amma off-campus. A can za su kama mana gida" Firdausi ta yi ihu "I knew it!" Ta rungume Zahra da ƙarfi Asiya ma ta yi murmushi sosai "Alhamdulillah, wlh na yi farin ciki" A daidai lokacin... Suhaima ta ƙaraso wajen "Tun daga can nake jin ana ihunku, me ya faru?" Firdausi ta juya da sauri "Suhaima! Guess what? Zahra is joining us!" Suhaima ta kalli Zahra "Da gaske?" Zahra ta gyada kai tana murmushi "In shaa Allah." Suhaima ta yi murmushi sosai "Yeee, ahh Ma shaa Allah, Ashe Duk zamu haɗu” Firdausi ta ce "Ba ma huɗu kawai ba, gida ɗaya, Department ɗaya, Department Course ɗaya, aji ɗaya" Asiya ta yi dariya "Kuma wahala ɗaya" Duk suka kwashe da dariya. Suhaima ta kama hannun Zahra "Allah Ya saka wa Abbah da Mami da alheri." "Ameen” Zahra ta amsa cikin murmushi. Nan suka ci gaba da hira Zahra na ba su labarin yadda ta zauna da Abbah da Mami har suka yi mata nasihohi kafin daga ƙarshe suka amince. Suhaima ta girgiza kai "Wallahi kin yi sa'a da iyaye Zahra, Ni fah is hardly kiga an zaunar da Ni ayi min nasiha duk da rayuwar Jin ɗaɗi da nake yi” Zahra ta sauke kai cikin godiya "Alhamdulillah." Da lecturer ya shigo... Suka wuce lecture hall, kowa ya samu waje ya zauna Lecture ya fara. Kusan rabin sa'a da fara lecture... Wayar Zahra da ke silent ta fara rawar vibration a cikin handbag. Ta ɗan leƙa, Yaya Umar Calling... Ta ɗaga gira cikin mamaki, ta nemi izini wajen lecturer "Excuse me sir." Ya gyada kai. Ta fito daga lecture hall Da ta ɗaga wayar... "Assalamu alaikum Yaya." "Wa alaikumus salam, Kina Ina?" Ya ce cikin nutsuwa “Department dinmu” Ya ce "Ina cikin school ɗinku, gaban Administrative Block. Ki zo na ɗan ganki." "Okay." Ta katse wayar, ta nufi inda ya faɗa Tun daga nesa ta hango motarsa, ya jingina da ita Sanye cikin farar shirt da baƙar trousers, fuskarsa kuma sanye da black sunglasses. Hannayensa cikin aljihunsa. Da ya hango Zahra... ya cire gilashin, ta ƙaraso tana murmushi “My Yaaya” "Baby girl, ya school din?” "Lafiya lau" ta amsa "Ya aiki?" Ta tambaya "Alhamdulillah." Sai ya ɗaga wani file da ke hannunsa "Na gama duba gidaje, akwai guda biyu amma ɗaya ya fi” yayi shiru na ɗan lokaci ya tsaya yana kallonta sai kuma ya ɗaura "Na yi magana da mai gidan da yamma zan kai Abbah ya gani, Idan ya amince... sai mu biya." Fuskar Zahra ta fara murmushi "Da gaske Yaaya?" Ya gyada kai "In shaa Allah zai yi miki, yana kusa da school. Tsaro yana da kyau, kuma akwai ruwa da wuta" Zahra ta yi murmushi "Alhamdulillah" Sai ta ɗan kalle shi "Yaya sannu da gajiya Allah Ya saka da alheri" Ya ɗan yi murmushi "Bakomai Baby, ki koma lecture” Ta yi dariya "Okay” Sai ta yi masa bye da hannu Yayi murmushi shiga motarsa, Ita kuma ta juya ta nufi lecture hall cikin sauri Da ta shiga... Firdausi ta matsa kusa da ita tana raɗa "Me ya faru?" Zahra ta yi murmushi kawai, sai ta raɗa mata "Yaya ne, ya zo duba mana gida." Firdausi ta yi murmushin farin ciki, ta ɗaga babban yatsanta sama "Perfect." Daga nan... Su biyun suka mayar da hankalinsu kan lecturer... har yamma suna makarantar Bayan sun gama lectures na ranar Zahra ta yi sallama da Firdausi, Asiya da Suhaima Ta shiga motarta. A hankali ta ja motar ta kama hanyar gida Cikin tafiyar, zuciyarta cike take da tunanin gidan da Ya Umar ya ce ya gani, sai kuma Saudat da bata gani ba Lokaci zuwa lokaci sai ta yi murmushi ita kaɗai “Allah Ya sa Abbah ya so shi…” Tana isa ta shigar da makarantar Sai ta hangi Abbah zaune a ƙarƙashin gazebo yana shan tea na yamma, wasu takardu kuma a gabansa. Fuskarta ta cike da murmushi ta karasa wajensa “Abbah!” Ya ɗago kai “My Baby.” Ta ƙarasa da sauri, ta zauna kusa da shi, basu ma gama gaisawa ba ta ce “Abba gidan fa?” Ya yi dariya “Kin ma fi ni son sanin labarin” Ta yi dariyar kunya “Please tell me.” Ya ɗan jingina da kujerarsa “Na je” Ta zuba masa ido. “Na gani, na duba komai. Security, Environment, Distance daga school, Ruwa.Wuta, Parking lots, komai” Sai ya yi ɗan shiru. Zahra ta kasa haƙuri. “Abbah… Please…” Ya yi murmushi “It’s okay, I liked it” Nan take fuskar Zahra ta cika da annuri “Really?” Ya gyada kai. “Har ma… an riga an biya” Na ɗan daƙiƙa… Zahra ta zaro ido “An biya?” “Eh, Sunday sai a kai kayanki.” Ba tare da ta shirya ba… ta rungume Abbah “Thank you! Nagode sosai Abbah. Allah Ya saka maka da aljannah.” Abbah ya yi dariya, ya shafa kanta “Ameen! Sai dai…” Ta ɗaga kai. “Kada ki manta da alkawarin da kika yi mana” Ta gyada kai cikin sauri “Ba zan manta ba, I promise” Ya yi murmushi cikin gamsuwa “Good girl” Ta yi masa sallama, ta shiga cikin main parlour Tana taka ƙafarta ciki… Sai idanunta suka sauka kan Mami Tana zaune a sofa, a gabanta akwai wasu magazines da cup ɗin shayi, tana magana wasu Mama Ladi Akan su haɗa mata kayan girki akan Island Zahra ta tsaya cak, ta tuna jiya da shekaran jiya ma haka Mami ta mata Sai ta haɗe bakinta, maganar da zata yi ta komar da shi ciki A zuciyarta ta ce “Innalillahi… shikenan Yau ma haka zan kare a kitchen?” Ta kalli Mami, Mami kuma ba ta lura da ita ba, hankalinta na kan abin da take karantawa Nan take… Zahra ta fara taku a hankali, making sure bata making any sounds , kamar wacce take tafiya a kan ƙwai Data ɗaga kafa, sai ta fara tabbatar da crocs ɗinta ba su yi ƙara ba Ta riƙe handbag ɗinta da ƙarfi don kada zip ɗin ya yi Kara shima Da ta kusa ƙarasa staircase… Sai Mami ta ɗaga kai Zahra ta tsaya nan take, ta lumshe ido “Wayyo…” Amma sai Mami ta sake mayar da hankalinta kan magazine ɗinta Zahra ta saki numfashi a hankali, ta ci gaba da tafiya irin ta ɓarawo A haka har ta haura sama, da ta isa ƙofar ɗakinta… ta yi saurin shiga, ta rufe ƙofar a hankali Ta jingina bayanta da ita, ta lumshe idanunta sannan ta sauke wani dogon ajiyar zuciya. “Alhamdulillah…” Ta yi dariya ita kaɗai “Wallahi Mami za ta mayar da ni chef, ko maid” Ta faɗa tana jefa handbag ɗinta kan gado A can kasa kuwa… Mami ta ɗaga kai ta kalli saman bene, ta yi murmushi ita kaɗai Ta girgiza kai cikin nishaɗi “Wannan yarinyar… ta ɗauka ban gane abin da take yi ba” Ta ci gaba da shan shayinta tana murmushi, yayin da Zahra a ɗakinta ke murna kamar wacce ta tsallake wata babbar jarabawa Sai ga Ya Umar ya shigo parlour ɗin Sanye yake cikin casual wear, makullin motarsa na jujjuyawa a yatsunsa Da ya hango Mami na murmushi ita kaɗai… Sai ya tsaya “Mami?” Ya ƙarasa ya zauna kusa da ita. Ya ɗan karkatar da kai yana kallonta. “Lafiya kuwa? Tun daga ƙofa na shigo na tarar kina murmushi, a fada min bin farin cikin?” Mami ta yi dariya “Hmm Yarinyar nan ce” “Wace?” “Baby mana, Banda ita waye?” Ya Umar ya yi murmushi “Me kuma ta yi?” Nan Mami ta ba shi labarin yadda Zahra ta shigo gida, da yadda ta hango ta zaune a parlour, da yadda ta fara taku a hankali… Kamar wacce ta zo sata Da yadda ta riƙa tabbatar da crocs ɗinta ba su yi ƙara ba Har ta shige sama tana tunanin ba ta lura da ita ba. Da Mami ta gama… Ya Umar ya kwashe da dariya. “Wallahi Baby akwai ta da abin dariya” Mami ta girgiza kai tana dariya “Zan ɗauke mata yanzu, amma tana dawowa gida Hutu ta shiga uku wlh, dan ko space ba zan bata ba” Ya Umar ya ɗan daidaita zamansa, ya ce cikin dariya, “Mami please ki bi ta a hankali, kada ki tsorata ta da kitchen ɗin nan” Mami ta harare shi. “Au? Ni zan bi ta a hankali?” Ya Umar ya yi dariya “Eh mana, Kaɗan-kaɗan” Mami ta ɗaga gira “Toh Idan aka kaita gidan mijinta fa? Inaga zata na kiran ka ne Yaya ka min order breakfast, lunch da kuma dinner, Kaga ai haka ne mijin ma ba zai gaji ba” Ya Umar ya riƙe ciki yana dariya Mami ta ci gaba da cewa, “Dole ne fah ta saka a ranta zata koya, Allah ko na sallame masu aiki ta fara yi, don gobe kada wani ya ce ba a raineta da training ba.” Ya Umar ya girgiza kai yana murmushi “Okay Mami. Na gane” Ya miƙe tsaye Har yanzu dariya yake yi “Allah ya taimake ta ta iya ɗin” Mami ta ce da sauri “Ba ita kaɗai ba Allah ya taimaki wanda zai aure ta ma, don sai yayi hakuri” Ya Umar ya sake fashewa da dariya. “Kai Mami kin gama da ita.” Yana dariya ya juya, ya nufi staircase. Mami kuwa ta girgiza kai tana murmushi, ta ɗauki cup ɗin shayinta Ta ce a hankali, “Wannan yara nawa Kullum sai sun sani dariya, Allah ka albarkace rayuwar su” Ba free book bane, aji tsoron Allah a biya ni hakkina 500 ne ta wannan 7084571222, Hauwa Jibrin Opay Shaidar biya ta nan 08110615256 Hauwajay writes Chapter 49 Kwana biyu bayan haka…Da yamma gidan ya yi tsit as usual Mami na cikin kitchen tare da Mama Ladi, Abbah bai dawo daga office ba Ya Umar kuwa yana wajen aiki Zahra ta sauko daga sama Sanye take cikin doguwar atamfa mai launin peach da farin scarf Wayarta na hannunta, hankalinta gaba ɗaya yana kan chatting da da take yi a WhatsApp Har ta shiga main parlour ba ta ma lura da wanda ke ciki ba Sai dai… “Batoul! Ba zaki yi magana ba?” Wata tsawar Mummy ta sanya ta ɗaga kanta da sauri, ta waigo Mummy na tsaye a tsakiyar parlour. Batoul kuma na zaune a kan sofa, ta turo baki gaba “Meye na ji wai?” Mummy ta ci gaba da magana cikin fushi “Batoul, me ya sa za ki tashi ki zaɓo min talaka?” “Ki rasa wanda za ki tsaya da shi sai mutumin da ba shi da komai?” “Ko kin ga kin yi kama da wacce talaka zai aura ne?” Batoul ta yi ƙasa da kai “Mummy… Please ki saurare ni” “Ni ba…” Mummy ta ɗaga mata hannu. “Rufemin Baki shegiya, kin san me zafin talauci yake?” “Har yanzu yarinya ce ke, ba zan bari ki shiga rayuwar da za ki riƙa wahala ba” “Na taso cikin wahala, kuma ba zan yarda ’yata ta koma cikinta ba.” Zahra dai ta tsaya daga bakin parlour, Idanunta na kai-komo tsakanin Mummy da Batoul, Mamaki ya cika fuskarta A zuciyarta ta ce, ‘Batoul? Talaka? Ban taɓa tsammanin za ki tsaya da mutum irin wannan ba’ A hankali ta sauke idanunta, sai hotunan Saudat.. da unguwarsu da irin rayuwar da ƙawayenta suke ciki… suka ratsa zuciyarta. Ta ɗan girgiza kai a hankali da sauri ‘No impossible, wannan ba zai yiwu ba. Allah Ya yalwata wa kowa Allah Ya fitar da masu wahala daga ƙuncin rayuwa, amma tunanin fadawa wannan rayuwarma zubi ne’ Ta yi wannan addu’ar ne a ranta Sannan ta ci gaba da kallonsu. Mummy kuwa har yanzu ba ta gama masifar nata ba ganin kamar har sannan Batoul bata fahimtarta “Na yi ta wahala kafin Allah Ya ɗaga ni, ba zan bari ki rushe rayuwarki da hannunki ba” Batoul ta ɗan ɗaga kai Idanunta sun cika da ƙwalla “Mummy shi fah mutum ne nagari, yana da ilimi, kuma yana da burin rayuwa” Mummy ta yi wata irin dariyar ganin wautan Batoul “Burin rayuwa?, Buri zai ciyar da ke ne?, Buri zai gina miki gida?, Buri zai siya miki mota?, Buri zai sa ki ci Mai kyau kisha mai kyau?” Batoul ta cije laɓɓanta, ta yi shiru Mummy ta sake cewa “Ki ji ni da kyau, daga yau.. kar na sake jin sunansa, kar kuma na sake ganin kina magana da shi balle ki barsa ya zo gidan nan, Idan kina son zaman lafiya a gidan nan.” Batoul ta sunkuyar da kai, ba ta ce komai ba Sai ɗan gunguni da take yi a hankali, alamar ba ta gamsu da maganar ba Zahra kuwa… Ta tsaya tana kallonsu cikin mamaki, ta rasa me za ta ce, ko me za ta yi Saboda wannan ne karon farko da ta ga Mummy cikin irin wannan matsanancin fushi saboda maganar saurayi kuma ta san tabbas Mummy nada gaskiya Parlour ɗin ya yi shiru na ɗan lokaci, Mummy ta gyara mayafinta ta ja dogon tsaki “Na faɗa miki abin da zan faɗa. Ki yi yadda kika ga dama” Ba ta ƙara kallon Batoul ba, ta juya ta nufi staircase cikin takunta na isa, har ta ɓace sama… Ba tare da ta waiwayo ba. Batoul kuwa… ta zauna na wasu daƙiƙu tana kallon ƙasa, hannunta riƙe da gefen hijabinta Fuskarta ta nuna taɓuwa sosai A hankali ta ɗauki wayarta daga kan center table Ta buɗe ta, contacts ta shiga, ta tsaya na ɗan lokaci tana kallon wani suna Sai ta latsa kira, wayar na ringing… ta miƙe tsaye ta fara tafiya a hankali zuwa staircase Zahra dai har lokacin tana tsaye tana mamakin Batoul, har Batoul ta fara hawa matakalar Batoul ta ci gaba da riƙe wayar a kunnenta, da ta zo wucewa… Zahra ta matsa gefe cikin ladabi ta ba ta hanya, ba a ce komai ba Batoul ma ba ta kalle ta ba, sai kawai ta ci gaba da tafiya Can… a ɗayan ɓangaren wayar aka daga Batoul ta sauke wani ajiyar zuciya, da ƙyar ta ce “Hello…” Muryarta can ƙasa Ba tare da ta tsaya ba… ta ci gaba da tafiya zuwa ɗakinta tana magana cikin siririyar murya har ta ɓace daga ganin Zahra Zahra ta tsaya a matakalar, ta bi Batoul da kallo har ƙofar ɗakinta ta rufe Sai ta ɗan haɗe gira, ta sauke numfashi Ba ta san ko wa Batoul ta kira ba, ba kuma ta damu da bincikensa ba. A hankali ta girgiza kai ta ci gaba da hawa zuwa ɗakinta… A zuciyarta tana addu’ar Allah Ya sauƙaƙa duk abin da yake damun kowa a cikin gidan. Yau ta kasance Asabar…Tun bayan breakfast… Mami na zaune a main parlour tana rubuta wasu abubuwa a cikin ƙaramin notebook Zahra ta sauko daga sama cikin lazzi “Good morning Mami.” “Morning Baby. Ta zauna kusa da ita “Me kike rubutawa?” Mami ta nuna mata notebook ɗin “Abubuwan da za a saya miki.” Zahra ta haɗe gira “Na me kuma?” Mami ta kalle ta “Kin manta ne? Ba tomorrow za ki koma off-campus ba. Ko kina tunanin da kayanki na gida kawai za ki tafi?” Kafin Zahra ta ba da amsa… Sai aka ji muryar Abbah daga corridor “Ready?” Su biyun suka waigo. Abbah ya fito cikin shigar weekend wears dinsa, murmushi kwance a fuskarsa Zahra ta miƙe “Abbah Ina za mu je?” Abbah ya yi kamar bai ji tambayar ba “Driver ya wanke motar?” “Eh sir” Ya Umar ne ya amsa yana saukowa daga sama Abbah ya ce “Mu tafi toh” Mami ta miƙe tana yafa laffayanta dake ajiye a goge a gefe Mami ta ɗauka ta yafa Duk compound suka wuce, suka shiga mota, mota biyu ce ta face daga gidan A gaba… Motar Abbah ne, a baya kuma driver na biye da ita Da suka isa babban shopping mall… Zahra ta tsaya tana kallon girman wajen, ta kalli Abbah. “Abbah… Me za mu saya ne haka?” Abbah ya yi murmushi “Duk abin da za ki buƙata.” Mami ta ce “Ki daina tambaya, koma menene idanunki zasu gani” Suka shiga ciki, Nan ne aka fara zagaya side zuwa side Da farko… Mami ta fara zaɓar mata bed sheets masu kyau, Duvet, Pillows, Pillow cases, Blankets masu laushi, Towels kala-kala, Bathroom mats, Laundry basket, Mirror, Table lamp, Study lamp, Storage boxes, Laundry bag. Zahra ta riƙe goshinta. “Mami!!! Ya yi fa” Mami ba ta ma saurare ta ba. “Wannan ma ƙara” “Ga wannan ma… shi ma ɗauka.” Ya Umar na biye da trolley, yana zuba su Can ya kalli Zahra, ya girgiza kai “Baby Gidan nan ko shop zaki buɗe ne a ciki?” Ta yi dariya. “Wallahi ba ni ba ce, kana gani ai, Mami ce” Mami ta harare su “Ku ci gaba da surutunku. Idan kun kai mata kayan gobe za ku gane dalilin da ya sa nake saya” Daga nan… Suka wuce wani babban boutique Nan Abbah ya ce “Baby Ki zaɓi abin da kike so” Zahra ta fara ƙin yarda “Abbah… Ina da kaya” Ya girgiza kai “Na sani, amma waɗannan na can off-campus ne” Daga ƙarshe… Ta fara zaɓar wasu dogayen gowns, Abayas, hijabai kala daban-daban, Slippers na cikin gida, Flat shoes, Sneakers, Handbags, Perfumes, Skin care products, Jewelleries masu kyau Mami tana biye da ita tana gyara zaɓinta lokaci zuwa lokaci “Wannan ya fi, wannan kuma ya fi dacewa da ke” Ya Umar kuwa… Sai ɗaukar shopping bags yake yi, har ya fara gajiya Ya kalli Abbah “Abbah! Ni kaɗai ne porter a gidan nan?” Abbah ya yi dariya “Kai ne babban yaya, don haka ka ɗauka” Zahra ta riƙe cikinta tana dariya “Sorry Yaya.” Ya nuna mata yatsa “Ke ce silar wahalata yau ba? Zan rama oo” Ta yi dariya sosai. Bayan sun gama… Suka shiga wani restaurant da ke cikin mall, suka yi lunch tare, suna hira suna dariya Abbah lokaci zuwa lokaci yana kallon Zahra, yana jin daɗin yadda farin cikinta ya bayyana ƙarara a fuskarta. Bayan sun gama… suka fito Aka saka duk kayan cikin boot na motoci, sa suka kama hanyar gida… Zahra ta jingina da kujerar motar, ta kalli Mami Ta ce cikin tausayin murya “Mami! Ni ban san me zan ce muku ba, soyayyar da kuke nuna min har ya fara yawa” Mami ta shafa hannunta “Ke ɗaya ce Allah Ya ba ni, kuma ke ce Autar gidan” Abbah ya juyo kaɗan daga gaban motar, ya ce da murmushi, “Ina matukar son yara masu kokari both School da Islamiya and you’re always making me proud, secondly Ina son gani yarana suna nuna mun kauna kuma kullum suna manne da Ni, halinki ne tun kina jaririrr” “So, this is nothing hakkina ne na sauke miki” Zahra ta yi murmushi mai cike da godiya. Ta ɗaga kanta k “Nagode… Allah Ya saka muku da aljannatul Firdaus” “Ameen.” Suka amsa tare… Da suka isa gida, bayan Motocin suka shige cikin compound Suna parking, masu aiki suka fito da sauri, kowa ya fara ɗaukar shopping bags Duk suka kai parlon Mami na sama, suka ajiye kamar Mami kamar yadda ta umarta Zahra tun da ta sauko daga mota… Sai ta fara murza kafa ta ce “Wayyo… Na gaji” Ya Umar ya wani kalleta “Ke kika gaji? Ni da na ɗauki bags ɗin nan fa? kinji nayi complain?” Ta yi dariya “Sorry Yaya, Duk kauna ce” Ya girgiza kai kawai yana murmushi Duk suka wuce ciki Abbah ya wuce ɗakinsa domin ya huta, Ya Umar ma ya nufi nasa Mami da Zahra kuma suna zaune a main parlour, a gabansu akwai fresh juice da Anty Binta ta kawo musu Can… Mama Ladi ta shigo “Hajiya.” Mami ta ɗago kai “Na’am.” “Akwai wani mutum a waje, yace ya zo wajenki” Mami ta gyada kai “Ki ce ya shigo.” “To Hajiya.” Ba a ɗau lokaci ba… Wani mutum mai matsakaicin shekaru ya shigo A hannunsa akwai wata babbar Ghana Must Go mai cike da kaya Da ya shiga… Ya durƙusa cikin ladabi “Barka da warhaka Hajiya” “Yauwa, sannu da zuwa” Mami ta amsa “Ka gama?” Ya yi murmushi “Alhamdulillah Hajiya, na gama duk yadda kika ce” “Kuma na tabbatar komai ya yi kyau, In shaa Allah” A dai-dai lokacin… Zahra ta sauko daga sama, Wanda bata daɗe da hawa ba Da alama ta canja kaya ne, ta ƙaraso parlour, ta zauna kusa da Mami Mami ta waigo gare ta “Baby! Miƙo min wayata” Zahra ta ɗauko wayar Mami daga kan side stool, ta ba ta Mami ta buɗe banking app ɗinta, sai ta ɗaga kai “Faɗa min account number ɗinka.” Mutumin ya fara karantawa a hankali Mami ta shigar, ta sake tabbatarwa, sannan ta danna transfer Wayarta ta yi ƙaramar ƙara “Sent” Ta miƙa masa wayar Nan take fuskarsa ta washe “Haba Hajjiya, ke ce ai, nasan ma ya shigo, inma bai shigo ba toh network ne” “Allah Ya saka da alheri Hajiya!Allah Ya ƙara arziki” “Ameen” Mami ta amsa Yana godiya ya miƙe sannan ya juya ya fita Zahra ta kasa danne son sanin abin, ta matsa kusa da Mami “Mami… Who is he?” Mami ta nuna Ghana Must Go ɗin “Dauka Ki kai sama” Zahra ta turo baki “Na waye? Ina zan kai?” Mami ta yi murmushi kaɗan “Buɗe ki gani mana” Zahra ta zaro ido “Really?” Ta matsa kusa da jakar ta durƙusa, ta buɗe zip ɗin a hankali Tana buɗe wa… ta tsaya cak “Eh?” Ta saka hannu ciki, ta ciro wata sabuwar atamfa, ta buɗe ta Kyakkyawar dinkin ya fito sosai a jikin atamfar Ta ɗaga ta gwada a jikinta, sai ta haɗe gira “Mami… Size ɗina ne.” Ta sake saka hannu, ta ciro wata Ita ma size nata ne, ta sake ciro ta uku Duk… Size ɗinta ne, ta ɗaga kai a hankali Idanuwanta cike da mamaki ta kalli Mami “Mami…” “Duk…” “Nawa ne?” Mami ta jingina da kujera, ta yi murmushi “Eh naki ne” Na ɗan daƙiƙa… Zahra ta kasa cewa komai Ta sake kallon atamfofin, ta sake kallon Mami “Wait.. dama tailor ne? Mami ta gyada kai “Na kai masa su tun kwanaki. Na ce ya gama kafin ki koma off-campus” “Saboda na san daga yau za ki fara tattara kayanki.” Zahra ta buɗe baki cikin mamaki “Ashe wannan ne… Shi ya sa kika riƙa cewa kar na shiga ɗakinki kwanakin baya” Mami ta yi dariya “Kin gane yanzu?” Zahra ta yi murmushi ta rungume atamfar da ke hannunta Sai ta matsa kusa da Mami ta rungume ta da ƙarfi. “Mami… I’m speechless Mami ta shafa kanta cikin taushi Zahra ta sauke kanta a kafaɗar Mami, tana murmushi kamar ƙaramar yarinya… “Wai duk nawa ne?” Mami ta yi mata kallon nan na manya “Ina ga Size dina kika gani” Sai Zahra ta fashe da dariya, man take ta miƙe tsaye Ta riƙe atamfa ɗaya a hannunta “Mami… One minute!” Ba ta jira amsarta ba, ta juya da gudu “Kee! Ki yi a hankali!” Mami ta yi mata tsawa ganin gudu take yi Kai tsaye ta nufi ɗakin Abbah, ta yi knocking sau ɗaya “Come in” ta tura ƙofar Abbah na zaune kan kujerarsa yana shan coffee, ya ɗago… Sai ya ga Zahra na tsaye da wata atamfa a hannunta Ya ɗan yi murmushi “My Baby! Lafiya?” Ta ƙarasa da sauri, ta durƙusa gabansa “Thank you so much Abbah.” Ya haɗe gira “Na me kuma?” Ta ɗaga atamfar “Yanzu tailor ya kawo” “Allah Ya saka maka da alheri” Abbah ya yi murmushi kawai, ya shafa kanta “Sun miki kyau?” Ta gyada kai da sauri.l “Very much! Sun yi kyau sosai” “Nagode.” Abbah ya ce cikin nutsuwa “ki ci gaba da gode wa Allah.” Ta sumbaci hannunsa. “In shaa Allah! Allah Ya ƙara maka lafiya da arziki da tsawon rai” “Ameen, Baby” Ya amsa yana murmushi Ta yi masa sallama, ta fito daga ɗakin cikin farin ciki. Da ta dawo parlour… Mami na zaune a inda ta barta Da ta ga Zahra na ta murmushi… Sai ita ma ta yi murmushi, ta juya ta kira, “Anty Binta.” “Na’am Hajiya.” Ba’a ɗsu lokaci ba sai gashi ta karasa cikin parlon “Dauki Ghana Must Go ɗin nan. Ki kai wa Baby ɗakinta, ki jera mata su cikin wardrobe.” “Toh Hajiya.” Ta ɗaga babban Ghana Must Go ɗin, ta nufi sama Zahra kuwa… Sai bin ta take da ido. Ta juya ta kalli Mami. “Mami! Allah Ya bar min ke.” Mami ta yi murmushi “Ameen. A tsufar Lafiya” Zahra ta gyada kai, sai ta juya ta bi bayan Anty Binta zuwa sama Chapter 50 Ana daf da kiran sallar Magrib… Zahra na zaune a ɗakinta Ta gama shirya sabbin atamfofin da Anty Binta ta jera mata a wardrobe Lokaci zuwa lokaci sai ta buɗe ƙofar wardrobe ɗin ta sake kallonsu tana murmushi A daidai lokacin… Sai ta ji ƙarar motar Ya Umar ta shigo compound Ba ta tsaya tunani ba, ta fito da sauri, tun ɗazu take jiran dawowarsa ta basa labari, ta sauko ƙasa Tana isa harabar gidan… Ta hangi Ya Umar yana saukowa daga motarsa Mai aiki yana sauke wasu manyan akwatuna guda biyu daga boot din motar Ya Umar Manya ne, masu ƙarfi kuma masu kyau wanda ake yayi kuma da tsada Ta karasa wajen Tana murmushi “Yaya sannu da zuwa” Ya Umar ya kalle ta “Baby.” Ta ƙarasa kusa da shi, ta nuna akwatunan “Waɗannan fa? Taru ka fara ne?” Ya ɗan jingina da motar yana murmushi “Naki ne.” Ta zaro ido “Nawa kuma?” Ya gyada kai “Eh” “Abbah ne ya ce in siya miki manyan akwatuna masu kyau” “Saboda duk kayanki za su shiga ciki” Zahra ta dafe baki “Ya Allah… Nagode.” Ya Umar ya riƙe ƙugu yana kallonta. “Duk wannan farin cikin saboda akwati?” Ta yi dariya “Ba ka gane ba, suna da kyau sosai, latest ne fa” Ya girgiza kai yana murmushi “Toh ai shikenan” Da daddare.. Bayan an idar da sallar Isha’i… Mami na ɗakin Zahra, ta kira Mama Ladi da Anty Binta da auran masu aikin gidan Bayan Duk sun haɗu, Ta ce “Ku fara shirya kayan Baby, gobe ba na son ace zaa yi ta gaggawa” “Toh Hajiya” Suka amsa gaba ɗaya Aka fito da manyan akwatunan biyu, aka buɗe su a tsakiyar ɗakin Zahra Mami na tsaye tana ba da umarni “Wannan atamfofin…” “A jera su a wannan akwati” “Abayas kuma a can” “Hijabai a ware” “Takalma a saka a pouch bag ɗinsu” “Perfumes kada su zube.” “Jewelleries kuma a cikin ƙaramin box din can” Mama Ladi da Anty Binta kuwa… sai aiki suke yi cikin tsari kamar yadda Mami take faɗa Zahra kuwa… tana auna gefen gado Hannunta riƙe da pillow sai kallonsu take yi Lokaci zuwa lokaci kuma sai ta tashi “Anty Binta wannan ba a nan za a saka shi ba” Ko kuma ta ce “Mama Ladi Please wannan hijab ɗin kar ya yi squeeze” Mama Ladi ta yi dariya “Hajiya Baby… ba zamu ɓata miki ba, aikinmu ne wannan” Mami ta kalli Zahra, ta girgiza kai “Toh uwar mutane, kina zaune can kina bada directive” Zahra ta yi dariya “Ba haka ba ne, Ina dai son komai ya kasance cikin tsari” Ya Umar kuwa ya shigo ɗakin daidai lokacin, ya jingina da ƙofa Ya ɗan kalli yadda aka cika ɗakin da kaya, sai ya ce da dariya, “Baby… kin tabbata school kuwa zaki koma? Ko boutique za ki buɗe?” Duk suka kwashe da dariya.. Zahra ta ɗauki pillow ta jefa masa Ya kauce, pillow ɗin ya faɗi ƙasa Ya Umar ya ɗauke shi, ya mayar mata “Kiyi ki bar mana gida, dama mun gaji da ke” Zahra ta yi dariya ta ce “Yaya Dan Allah goooo” Ta kalli akwatunan da a hankali suke cika da kayanta, sai zuciyarta ta buga Yanzu kam… Gaskiya ta fara fahimtar cewa saura kwana ɗaya kacal… Sai kuma taji wani iri kamar zata yi kuka Bayan kusan awa guda… Aka kammala komai Duk sun gama jera mata su, ta kalli aikin, ta gyada kai cikin gamsuwa. “Alhamdulillah! Haka nake so” Mama Ladi da Anty Binta suka rufe zip ɗin manyan akwatunan, suka mayar da su gefen wardrobe Mami ta waigo ta kalli Zahra “Yanzu dai kin shirya” Zahra ta yi murmushi “In shaa Allah.” Mami ta shafa kafadarta “Ki kwanta da wuri! Gobe akwai abubuwa da yawa.” “Toh Mami.” Da Mami da masu aikin suka fita… Zahra ta kalli akwatunan nata, ta yi murmushi ita kaɗai. Sai ta zauna bakin gadonta Ta ɗauki wayarta, ta shiga WhatsApp Nan take ta yi conference call da Firdausi, Asiya da Suhaima. Ba a jima ba… Kowa ya shiga Firdausi ce ta fara magana “Madam Off-campus!” Duk suka yi dariya. Zahra ta girgiza kai. “Ku daina fa” “Kin gama packing?”Asiya ta tambaya Zahra ta waiga gefen akwatunan “An gama komai! Mami ta saka an shirya min ɗazu” Suhaima ta yi murmushi “Ni ma na gama, na saka kayana tun da yamma” Firdausi ta ce “Ni ma yanzu na rufe akwati.” Aasiya ta ce “Same here. Na bar saura kayan da zan sa gobe kawai.” Firdausi ta yi dariya “Huh? Wasa wasa dai gobe zamu koma school” Suhaima ta amsa da dariya “Hmm, ki Bari dai, Rayuwar girki, rayuwar wanki, rayuwar biyan bills” Asiya ta ce “Kuma rayuwar assignment babu mai tayaki” Duk suka fashe da dariya. Zahra ta ce “Allah Ya taimake mu.” “Ameen”Suka amsa gaba ɗaya. Firdausi ta ce “Ku kwanta da wuri, gobe akwai aiki” Suhaima ta ce “Kuma kar wani ya makara.” Aasiya ta ƙara da cewa “Da safe zan yi texting ɗinku.” Zahra ta yi murmushi “Shikenan! Good night girls.” “Good night” Suka amsa ɗaya bayan ɗaya Daga nan… Kowa ya fita daga conference call Zahra ta ajiye wayarta a gefen gadonta, ta sake kallon manyan akwatunan nata. Sai ta sauke numfashi cikin murmushi “Gobe…” Ta faɗa a hankali. “Anya zan iya 24/7 ba tare da Mami, Abbah especially Yaya ba?” Toilet ta wuce tayi alwala, tana fitowa ta kwanta kan gado ta kashe bedside lamp Washe gari… Tun kafin fitowar rana gidan ya riga ya cika hayaniya Ƙarar masu aiki na kai-komo, ƙamshin arabian tea da ake dafawa, da kamshin suyan da ke yawo a cikin kitchen din suka haɗu suka ba da wani irin kamshi na natsuwa Zahra ta koma ɗakinta ta karanta Al-Qur’ani na ɗan lokaci kafin ta fara shirin ranar Karfe takwas na safe… Kowa ya hallara dining Abbah na kan kujerarsa ta kullum, Mami na gefensa, Ya Umar ya iso bayan ƴan mintuna Mummy da Batoul ma suka zauna a ɗaya gefen teburin Wanda ma basu gaisa ba nan suka samu aka gaisa Sai dai Zahra ta lura Ya Umar lokaci-lokaci yana kallonta yana murmushi, ta gane saboda yau ce ranar da za ta koma off-campus tasan dole ne ma yayi missing ɗinta Abbah ya ɗaga kai “Baby kin gama shirya komai?” Ta gyada kai “Eh Abbah, komai ya kammalu” “Good” Ya ce yana ɗaukar cup ɗin shayinsa “Kada ki manta, idan kina buƙatar wani abu, ko da ƙarfe nawa ne, ki kira ni za’a miki providing kuma a Kai miki can” Ta yi murmushi “In shaa Allah.” Mami ta ƙara da cewa, “Kuma kar ki cika cin abincin waje, ki riƙa girki idan kina da lokaci, danna sanki da rashin son girki” Zahra ta ɗan turo baki “Mami…, girki againnn” Duk suka yi dariya, Bayan breakfast kowa ya gama watsewa Can Zahra ta nufi ɗakin Mami, ta tarar da ita tana wani aiki ne Ta zauna kusa da ita “Mami…” Mami ta ɗago “Na’am Fatima” “Na yi magana da Firdausi da Asiya da Suhaima.” “Mun yanke shawarar zama tare.” Mami ta ɗan yi shiru Ta kalleta cikin nutsuwa “Kun san juna, kuma idan haka zai fi muku sauƙi, ba komai” Amma sai ta ɗaga yatsa “Abu ɗaya zan ce…” “Kar zaman ƙawance ya sa a manta da karatu” Zahra ta yi murmushi “In shaa Allah Mami hakan ba zai faru ba” Mami ta shafa kumatunta “Toh Allah ya yarda” “Ameen.” Can around 11am, bayan Abbah ya bayar da directive… Nan take aka fara fitar da kayan abinci zuwa boot na motocin gidan Masu aiki biyu suka fito da manyan cartons, Shinkafa, taliya, Semovita, spaghetti, macaroni, Tin tomatoes, Vegetable oil, Buckets, Mop, kayan tea da sauran abubuwan buƙata Driver da masu aikin suka riƙa kai-komo tsakanin store da boot na motar, ana jera komai cikin tsari Abbah ya fito ya tsaya yana kallonsu “Ku tabbatar babu abin da aka manta” “Toh Alhaji” Suka amsa Zahra dake Snapchat tana chatting, ta miƙe zata buɗe window nan taga abun dake faruwa a compound, da sauri ta sake labulen ta shiga bathroom Can bayan ta gama wanka ta fito, ta shafa lotion tare da shafa light perfume Ta saka wata atamfa mai launin blue da pink ɗinki mai sauƙi but elegant, tayi ɗaurin ɗankwali sannan ta yafa blue veil Ƙaramin agogonta na azurfa da bracelet ɗinta suka ƙara mata kwarjini Ta ɗauki wayarta da handbag, ta fito ƙasa Mami ta kalleta daga parlour “Baby.” Ta amsa “Na’am Mami.” “Ki je ki yi wa Mummy sallama kafin ku tafi” Ba tare da gardama ba… ta gyada kai “Toh Mami.” A hankali ta nufi ɓangaren Mummy, ta yi knocking “Shigo.” Ta tura ƙofar ta shiga, ta tarar da Mummy da Batoul zaune kan sofa, da alama hira suke yi Zahra ta yi murmushi cikin ladabi “Barka da gida Mummy” “Yauwa shalelen Babanta” Mummy ta amsa Ta ƙarasa kusa da ita, ta durƙusa “Mummy… zan tafi ne yanzu, shine na zo na yi miki sallama” Mummy ta ɗan yi shiru Sai ta ce, “Allah Ya kiyaye hanya! Ki je lafiya, ki dawo lafiya” Zahra ta yi murmushi “Ameen! Nagode Mummy.” Mummy ta miƙe ta nufi ƙaramin fridge da ke parlon, ta buɗe shi Ta fito da wani takeaway mai kyau Ta buɗe, ƙamshin danbun naman kaza da aka soya kyau ya cika parlon Ta zuba mata yaji mai ƙamshi, hadi da garwayawa Ta sake ɗauko wani takeaway a cike da yaji mai ƙamshi, ta rufe takeaway ɗin. Ta miƙa mata su “Ga wannan, zai tai maka miki musamman yajin, idan kuma kina bukatar wani abu just let me know” Zahra ta karɓa da hannuwa biyu, fuskarta cike da mamaki “Nagode sosai Mummy Allah Ya saka da alheri.” Mummy ta gyada kai kawai “Allah Ya kiyaye.” Zahra ta sake yi musu sallama, ta juya ta fita Ƙofar na rufewa… Batoul ta juya tana kallon Mummy da mamaki “Mummy…Gaskiya ban gane ba, kamar kin yarda da su yanzu” Mummy ta jingina da kujera Wata siririyar dariya mai cike da ma’ana ta kubce mata Ta girgiza kai a hankali “Lallai Batoul… har yanzu yarinya ce ke” Batoul ta haɗe gira “Mummy?” Mummy ta ɗan matsa kusa da ita, ta rage muryarta “Ke dai…” “Ki jira abin da zai faru nan ba da daɗewa ba” “Tsarauniya zata zama….” Ta yi murmushi mai cike da wani sirri Batoul ta zuba mata ido. Gabanta ya ɗan faɗi, ta san wannan murmushin… Ba ya zuwa da alheri….. Sai dai ba ta san me Mummy ta shirya ba amma koma menene she’s happy with it Zahra ta sauko daga benen cikin nutsuwa, murmushi ne kwance a fuskarta. A hannunta kuwa tana riƙe da ƙaramin takeaway ɗin yajin da danbum naman da Mummy ta ba ta Tun kafin ta ƙarasa parlon, ta hango Abbah, Ya Umar da Mami zaune suna jiranta Da ta iso, ta ɗaga takeaway ɗin tana murmushi “Mummy ce ta bani” Abbah ya kalli abin da ke hannunta. Har ya buɗe baki zai ce, ‘Don’t use it… ki kai ɗakin Mami ki barsa acan’ Sai idonsa ya sauka kan Ya Umar da ke tsaye a wajen. Nan take ya haɗiye maganar, bai ƙara cewa komai ba Maimakon haka, ya yi murmushi kawai “Let’s go?” Ya Umar ya miƙa mata hannunsa “Slay Mama” Ba tare da wata-wata ba Zahra ta saka hannunta cikin nasa Mami ma ta miƙe daga kujerar da take zaune “Ni kuma bari na wuce ɗaki.” Ta ɗan matso kusa da Zahra, ta shafa kanta cikin tausayi da kauna irin ta Uwa “Baby, Allah Ya tsare hanya, Ya ba ku sa’a” Ta ɗan dakata kafin ta ƙara da murmushi “Kuma… kar ki canza halin da kuma sanki da shi, kiyi amfani da nasihan da muka miki” Nan take Zahra ta zaro ido tana kallonta “What?” Sai ta ɗan matso kusa “Mami… ba da ke za a je ba ne?” Mami ta yi dariyar da bata son ta saka Zahra Jin wani iri “Eh mana” Da sauri Zahra ta kwace hannunta daga na Ya Umar. “Ai shi kenan!” Ta juya da sauri ta nufi Mami “Mami, mu tafi tare!” Mami ta yi dariya tana buɗe mata hannu, Zahra kuwa ta rungume ta tamkar ƙaramar yarinya. Abbah da Ya Umar suka kalli juna suka yi murmushi. Ya Umar ya girgiza kai yana dariya. “Wallahi Mami, ni dai na rasa matsayina. Da zarar Zahra na nan, ni ba ni da wani amfani.” Zahra ta leƙo daga jikin Mami ta masa gwalo. “Exactly!” Suka cika parlon da dariya, har Abbah da ba kasafai yake yin dariya da ƙarfi ba sai da ya saki dariyar da ta sa yanayin moments dinsu ya ƙara cika da farin ciki Chapter 51 Abbah ya girgiza kai yana kallon Zahra, sannan ya ɗan kalli agogon hannunsa. “It’s okay… muna wasting time.” Da jin haka, nan take fuskar Zahra ta sauya. Ta turo baki gaba, idanunta suka cicciko da ƙwalla, tana kallon Mami cikin shagwaɓa kamar ƙaramar yarinya. “Mami…” Ya Umar ya saki dariya yana girgiza kai. “Haba Mami, let’s just go mana. Kin ga Baby ba za ta yarda mu tafi ba” Abbah ya yi murmushi, sannan ya ce, “Ai yanzu ya zama dole ki je. Tunda Baby ta yi requesting.” Mami ta girgiza kai tana murmushi. “Toh shikenan, ku jira ni.” Ta juya ta haura sama. Bayan ƴan mintuna kaɗan ta fito sanye cikin kyakkyawar doguwar atamfa mai launin ruwan toka da touches of army green ta yafa masa green mayafi, tana riƙe da ƙaramin hand bag ɗinta. “Mu je.” Fuskar Zahra ta haskaka da fara’a Da suka fito compound, motoci biyu suka riga suka yi warming. A mota ta farko, Abbah ne tare da Mami. A ta biyun kuma Ya Umar ne zai tuƙa, Zahra na gefensa. A baya kuwa, akwai motar masu aiki ɗauke da manyan cartons, foodstuffs, kitchen utensils da sauran kayayyakin gidan. Mai gadi ya buɗe babban gate, motocin suka fita ɗaya bayan ɗaya. Bayan tafiya mai ɗan tsawo, suka iso kusa da jami’ar su Zahra Unguwar ta yi tsit, cike da sabbin gidaje masu kyau da ɗalibai ke zama Motar Abbah ta tsaya a gaban wani tsararren gida mai kyau, kallon farko zaka masa kasan Estate ne, kowa da side dinsa Mai gidan ya zo ya buɗe ƙofa cikin girmamawa bayan ya gaisa da Abbah, Students ID ya karba kafin ya barsa suka shiga ciki Suna shiga a block dinsu Zahra suka yi parking , Zahra ta tsaya tana kallon Estate din cikin farin ciki, School Villa ce Falon villa din ba babba ba ne, amma yana da yalwa. Daga falon akwai kitchen mai dan girma, sai corridor da ke kaiwa ɗakuna biyu, kowannensu na da toilet da bathroom a ciki Abbah ya kalli Zahra “How do you like it?” Zahra ta yi murmushi har haƙoranta suka bayyana. “I love it, Abbah.” Masu aiki kuwa suka fara sauke kaya daga mota bayan Abbah ya basu directive An fara shigar da babban refrigerator zuwa kitchen, sai microwave, electric kettle, gas cooker mai burners huɗu tare da cylinder, Rice cooker, blender, electric jug. Kitchen cabinet ɗin dake kitchen din, aka jera plates iri-iri masu kyau, dinner plates, Side plates, bowls, cups, glasses, serving trays da sauran su Pots masu girma dabam-dabam aka jera cikin cupboard A gefe guda kuma aka cika shelves da foodstuffs Buhun shinkafa, semovita, spaghetti, macaroni, Noodles, flour, da duk wani foodstuffs da suka zo mata da shi, har da Kayan miya daban-daban. Kitchen ɗin ya cika tamkar gidan da za’a kawo amarya ne ciki A cikin toilet kuwa, masu aiki suka jera sabbin buckets, basin, mop, broom, toilet brush, body wash, hand wash, shampoo, conditioner, toothpaste, toothbrushes, air freshener da Duk wani abu dai da ake using a toilet, komai aka shirya cikin tsari da tsafta Bedroom ɗin farko kuwa aka shigar mata da akwatinta, aka ajiye shi kusa da wardrobe Aka shimfiɗa bedsheets masu kyau, pillows aka gyara, duvet aka shimfiɗa cikin tsari Mami tana bi tana dubawa, tana gyara inda ta ga ya dace, yayin da Zahra ke binsu tana kallon yadda cikin mintuna kaɗan gidan ya koma tamkar gidan da aka daɗe ana rayuwa a ciki Ta sauke numfashi tana murmushi. “Ayyah Nagode…” Ta juyo ta kalli Abbah da Mami. “Na gode sosai… Allah Ya saka muku da alkhairi.” Bayan an tabbatar an gama komai, masu aiki suka sake zagayawa gidan domin tabbatar da babu abin da ya rage. Kitchen ta cika tsaf da kayayyaki, Falon ya kasance cikin tsari Bedroom ɗinta an gyara shi fes Toilet ma an shirya su yadda ya kamata Mami ta sake dubawa sau ɗaya, sannan ta gyada kai cikin gamsuwa “Alhamdulillah… yanzu gidan ya yi.” Abbah ya kalli agogon hannunsa “Toh, mu tafi. Ko za mu bar ku ku huta ne?” Masu aiki suka fara komawa motocin, su ma suka fito zuwa compound. Da suka iso bakin motar, Zahra ta matso kusa da Mami ta kama hannunta da hannu biyu. “Mami…” Mami ta kalleta da murmushi “Lafiya Fatima?” Zahra ba ta amsa ba, ta ƙara matsowa kusa da ita Ya Umar da ke tsaye jikin motar ya yi dariya. “Haba Baby, kamar ba gobe za mu sake ganin juna ba” Abbah ma ya yi murmushi “Kin san ma gobe idan lectures sun ƙare za ki iya zuwa gida, ba lalle sai weekends ba” Zahra dai shiru, ta ƙara damƙe hannun Mami Sai kawai fuskarta ta canza Nan take hawaye suka fara zubo mata Ya Umar ya ci gaba da dariya. “Wai da gaske kuka kike yi ne?” Amma bai gama maganar ba, sai ya lura hawayen nata na ƙaruwa Murmushinsa ya ɗan kau “Mami… Baby fa da gaske take kuka.” Abbah ya juya da sauri “Baby…” Kafin wani ya sake cewa komai, Zahra ta rungume Mami gam, ta fashe da kuka kamar ƙaramar yarinya “Mami… bana son ku tafi” Muryarta ta karye saboda kuka “Please… ku zauna ko yau ne” Mami ta lumshe ido tana shafa bayanta cikin tausayi “Shhh… Baby na.” Ta ɗago fuskarta a hankali “Me ya sa kike kuka haka?” Zahra ta girgiza kai “Ban sani ba… amma ina jin kamar zan yi missing ɗinku sosai ne” Ya Umar ya sauke ajiyar zuciya ya girgiza kai “Wallahi Baby, kin sa ni ma zan fara kukan zuci” Abbah ya matso kusa da su, ya shafa kan Zahra cikin kulawa. “Baby… wannan ma wani sabon mataki ne na rayuwa. Ba wai kin bar gida ba ne. Gida yana nan, mu ma muna nan. Duk lokacin da kika ji kina son ganinmu, ƙofa a buɗe take gare ki.” Mami ta share mata hawayen da ke zuba “Kuma kin manta? Kin ce kina son independence saboda result dinki yayi kyau?” Zahra ta yi ƙaramin murmushi “Na ce… amma ban san zai yi min wuya haka ba” Dukansu suka yi murmushi cikin tausayi, Mami ta sake rungumota na ɗan lokaci kafin ta saki ta a hankali, ta ci gaba da lallashinta Da ƙyar Mami ta samu ta lallashi Zahra ta ɗan saki jikinta. Ta riƙe fuskarta da hannaye biyu, tana share mata hawayen da suka jika kumatunta. “Baby… kinga fa.” Ta yi nuni da ƙofar compound. “Can compound mates ɗinki za su fara miki dariya. Za su ce ga babbar yarinya nan tana kuka kamar ƙaramar yarinya.” Zahra ta ɗan yi murmushi cikin kuka, ta goge hancinta. Mami ta sake cewa, “Kuma ai su Saudat suna hanya ko?” Zahra ta gyada kai a hankali. “Eh… sun ce suna zuwa.” “Shi kenan. Kafin su iso ma ki gama gyara fuskarki, ko?” Ta sake gyada kai, duk da hawaye na ci gaba da zuba mata. Abbah ya matso kusa da ita yana murmushi. “Baby.” Ta ɗago kai ta kalle shi. “Anjima yayanki zai miki transfer. Idan kina buƙatar wani abu, ki saya. Kar ki tsaya kina wahala.” “Toh Abbah.” Ta amsa cikin sanyin murya. Ya Umar ya ɗan taɓa kanta. “Kuma idan wani abu ya taso, ko ƙarfe nawa ne, ki kira ni. Ko da dare ne, zan zo.” Zahra ta yi murmushi kaɗan “In Sha Allah.” Mami ta sake rungumota na ɗan lokaci, sannan ta sumbaci goshinta. “Allah Ya tsare ki, Ya kiyaye ki daga duk wani sharri. Allah Ya sa albarka a karatunki .” “Ameen.” Abbah ma ya yi mata addu’a, Ya Umar ya yi mata bye , sannan suka juya suka nufi motocinsu Zahra ta tsaya bakin ƙofar compound tana kallonsu. Sai da motocin suka fita daga unguwar, suka ɓace daga ganinta sannan ta juya da gudu ta koma cikin gidan Kai tsaye ta shiga ɗakinta, ta rufe ƙofar a hankali Ba tare da ta cire hijabinta ba, ta faɗa kan katifarta ta rungume pillow da ƙarfi. Nan take ta sake fashewa da kuka. Shiru ya mamaye ɗakin. Sai sautin kukanta kaɗai ke tashi lokaci zuwa lokaci, yayin da take jin gidan da ya cika da hayaniyar su Abbah ɗazu ya koma shiru tamkar ba su taɓa shiga cikinsa ba. Ta lumshe idanunta tana riƙe da pillow ɗin kamar zai rage mata kewar da ta riga ta fara yi wa Abbah, Mami da Ya Umar. Sai sauke ajiyar zuciya da take yi lokaci zuwa lokaci Tring… Tring… Wayarta ta fara ringing Ta ɗan ɗago kai a hankali, ta share hawayen da bayan tafin hannunta kafin ta miƙa hannu ta ɗauki wayar Da ta ga sunan Firdausi a screen, ta yi ƙaramin murmushi sannan ta amsa. “Hello…” “Madam!” Muryar Firdausi ta zo cike da annashuwa. “Kin isa ne?” “Eh, na isa! Ina ma gidan yanzu haka, ke kina ina yanzu?” Firdausi ta yi dariya “Ina hanya na kusa da school Villa. Gani an area ɗinma. Bari na ƙaraso bakin block ɗin, sai ki fito ki ɗauke ni.” “Okay, no problem.” Ta katse wayar. Zahra ta sauke numfashi, sannan ta nufi mirror. Ta ɗan gyara kanta, ta sake wanke fuskarta da ruwan sanyi domin rage alamun kukan da ta yi. Ta shafa powder kaɗan, ta ɗauki mukullin gidan sannan ta fito. Bata jima ba sai ta hango Firdausi na tahowa daga bakin layin A gefenta kuma akwai wata kyakkyawar budurwa mai kama da ita sosai, suna tafe tare da manyan travelling bags guda biyu da ƙananan handbags sai wasu almajirai da suke biye da su a baya da Kaya a hannunsu Da zarar Firdausi ta hango Zahra, ta daga hannu tana murmushi, a haka har suka karaso Suka rungumi juna cikin farin ciki Firdausi ta yi mata kallon tsokana. “Anya kuwa baki yi kuka ba? Idanunki sun yi ja fa.” Zahra ta yi saurin kau da maganar tana dariya. “Ke dai bari.” Firdausi ta nuna budurwar da ke tsaye kusa da ita. “Meet my cousin, Khadija. Ita ma a nan za ta zauna, amma block na gaba.” Khadija ta yi murmushi “Nice meeting you.” “Same here.” Firdausi ta nuna kayanta. “Toh Madam, ga kayan nan. Ko za ki tsaya kina kallonmu ne?” “Ku zo mana.” Zahra ta yi gaba tana jagorantarsu zuwa block ɗinta. Suna tafiya suna hira, har suka isa ƙofar apartment dinsu Ta buɗe ƙofar da mukulli, ta matsa gefe. “Bismillah… ku shigo.” Firdausi ta shiga tana jan babban akwatinta, Khadija kuma ta biyo bayanta ɗauke da sauran kayan, almajiran suka ajiye na hannunsu a baranda, Zahra ta basu kudi suka tafi Da suka shiga falon, Firdausi ta tsaya cak, idanunta na yawo cikin gidan. “Subhanallah… Zahra!” Ta juyo tana kallonta. “Wai wannan gidan Duk saboda karatu ne ko aurar da ke za’a yi a ciki?” Zahra ta yi murmushi kawai, yayin da Khadija ma ta kasa ɓoye mamakinta tana kallon yadda aka shirya gidan cikin tsari da kyau Bayan sun gama shigar da kayan Firdausi cikin falo, dukkansu suka zauna kan carpet ɗin saboda gajiya. Firdausi ta sauke ajiyar zuciya “Wallahi tafiyar nan ta gajiyar da ni.” Zahra ta yi dariya “Ai dole? Ni da na gama Shan kuka na tun ɗazu ma ban gama dawowa hayyacina ba.” Firdausi ta zaro ido “Da gaske kika yi kuka?” Zahra ta ɗan yi murmushi cikin kunya “Ban sani ba” Khadija ta yi dariya. “Ni dai tun da muka zo na lura idanunki sun yi ɗan ja.” “Shikenan fa, kar ku fara tsokana.” Dukkansu suka yi dariya. Suna cikin hira, wayar Zahra ta yi ƙara. Ta duba screen ɗin “Aasiya ce.” Ta amsa. “Hello.” “Zahra, mun iso School Villa.” “Kun iso?” “Eh, amma ban san block ɗinku ba.” “Ki tsaya a entrance, gani nan zuwa.” Ta kashe wayar, ta ɗauki mukulli. “Mu je mu tarbo su.” Su uku suka fito tare. Da suka isa entrance ɗin School Villa, suka hangi Aasiya tsaye tare da wata mata mai kamannin dattaku da kamala. A ƙasa kuwa akwai akwatinta da wasu ledoji. Aasiya tana hango Zahra ta yi murmushi, suna isa suka rungume juna Sai Aasiya ta nuna matar da ke gefenta “Wannan Mamana ce” Nan take dukkansu suka gaishe ta cikin girmamawa. Ta amsa cikin fara’a “Allah Ya muku albarka,” Zahra ta kama ɗaya daga cikin jakunkunan, Firdausi ta ɗauki wani, Khadija ma ta ɗauki ƙarami. A haka suka nufi block ɗinsu suna hira. Da suka shiga gidan, Mamanta Aasiya ta tsaya tana kallon yadda aka shirya komai. Ta yi murmushi “Masha Allah… gidan ya yi kyau sosai.” Bayan sun shigar da kayan, ta juya ta kalli yaran. “Toh ‘ya’yana, ni zan koma yanzu.” Aasiya ta rungume mahaifiyarta “Mama…” Ta shafa kanta cikin tausayi “Ki kula da kanki. Ki kula da ibadarki. Kada karatu ya shagaltar da ke daga sallah.” Ta kalli Zahra, Firdausi da Khadija. “Ku ma Allah Ya tsare ku. Na ga kun zama kamar ‘yan’uwa, ku riƙa zama lafiya. Idan ɗayarku ba ta da lafiya ko tana da wata matsala, ku tsaya mata. Kada ku bari sharrin mutane ko son zuciya ya shiga tsakaninku.” Dukkansu suka amsa da “In Sha Allah.” Ta ci gaba da cewa, “Kuma ku tuna, an kawo ku nan ne neman ilimi. Kada ku bari wani abu ya karkatar da hankalinku. Ku riƙa mutunta junanku, ku kiyaye sunayen iyayenku.” “In shaa Allah Mama” suka amsa Ta yi musu addu’a sosai “Allah Ya ba ku sa’a, Ya tsare ku daga duk wani sharri, Ya sa ku gama karatunku lafiya.” “Ameen.” Suka amsa suna Jin dadi Da murmushi ta yi musu bankwana, sannan ta juya ta fita Da dare ya yi, School Villa ya fara yin shiru. Yawancin ɗalibai sun kammala shiga gidajensu A side dinsu Zahra kuwa, ita, Firdausi da Aasiya ne kawai suka tare yau Su uku suka ɗan gyara falon, suka jera wasu kayan da suka rage a kan teburi, sannan suka kai wasu kitchen. Bayan sun tabbatar komai ya koma cikin tsari, suka zauna a kan carpet ɗin falo suna huta wa. Zahra ta miƙa hannu ta ɗauki wayarta ta shiga group ɗin department ɗinsu. Can sai idanunta suka sauka kan wani sabon announcement. Ta buɗe shi Nan take ta zaro ido. “What?” Firdausi da Aasiya suka juyo gaba ɗaya suka kalleta. “Me ya faru?” Ta sauke wayar tana jan dogon tsaki. “I didn’t expect this.” “Expect me?” Ta miƙa musu wayar “Ai sun saka lectures gobe 8:00 a.m.” “Me?” Firdausi ta karɓi wayar ta karanta. “Wallahi ba su kyauta mana ba. Yau fa muka shigo.” Aasiya ma ta girgiza kai. “Yaushe wai muka saba lectures din safe ne wai?” Zahra ta kwanta da bayanta jikin kujera tana turo baki. “Ni har na yi planning zan huta gobe da safe.” Su uku suka yi dariya, duk da haushin da suke ji. Firdausi ta ce, “Shi kenan, madam. Ki tashi da wuri.” Zahra ta ɗaga hannu “Allah ya kawo mana ƙarfin tashi.” Daga nan ta nemo lambar Saudat ta kira. Bayan ringing kaɗan, ta ɗaga “Assalamu alaikum Zahratyyy” Bayan sun gaisa cikin mutunci da faraa Firdausi ta matsa kusa da wayar. “Madam Saudat, yaushe za ki shigo?” Saudat ta yi dariya “In Sha Allah gobe da safe zan iso.” “Da gaske?” “Eh mana.” Zahra ta ce “Toh ki yi sauri, kin bar mu kaɗai a nan.” Suka ɗan yi hira na wasu mintuna kafin suka yi mata sallama. Bayan sun kashe wayar, Firdausi ta ce, “Ki kira Suhaima ma pls” Nan take suka kira ta. Ita ma tana ɗagawa ta fara dariya. “Kun dai isa lafiya ko?” “Eh. Ke fa?” “In Sha Allah ni ma gobe zan shigo.” “Da safe?” “Eh, kafin lectures.” “Alhamdulillah.” Suka ci gaba da hira suna dariyar yadda har yanzu ba su yarda ba cewa sun fara wata sabuwar rayuwa ba Firdausi ta ce cikin murmushi, “Wallahi har yanzu idan na tuna yau muka dawo off campus, sai na ji kamar mafarki ne.” Aasiya ta gyada kai “Ni ma haka.” Zahra ta yi murmushi. “Ni kuma har yanzu ban gama missing gida ba.” Suka sake yin dariya. Da dare ya ƙara nisa, kowacce ta miƙe zuwa ɗakin domin su huta kafin gobe. Zahra tana shiga ɗakin, ta zauna a bakin gadonta. Ta fara kiran Abbah. Sun yi ɗan hira, ya sake mata nasiha tare da yi mata addu’a. Daga nan ta kira Ya Umar. Ya tambaye ta ko komai lafiya, sannan ya tuna mata da ta sa alarm saboda lecture na ƙarfe takwas. Ta yi dariya. “In Sha Allah.” Kafin ta kashe wayar, ya ce “Good night, Baby.” “Good night, Ya Umar.” Sai ta kira Mami. Muryar Mami kaɗai ta sa fuskarta ta yi laushi. Sun yi hira na ɗan lokaci, Mami ta tambaye ta ko ta ci abinci, ko gidan ya yi mata, sannan ta yi mata addu’a kamar kullum. Da ta kashe wayar, Zahra ta yi murmushi. Ta ajiye wayarta a gefen gadonta, ta kashe fitilar ɗakin, tunda su sun Riga da sun fara bacci Ta lulluɓe jikinta da duvet, tana jin zuciyarta ta yi sanyi bayan jin muryoyin mutanen da ta fi so. A hankali bacci ya fara ɗaukarta…. Chapter 52 Washe gari tun kafin alfijir ya ketare, ƙarar alarm ta cika ɗakin. Tring… Tring… Tring… Zahra ta buɗe ido da ƙyar, ta lumshe su kuma. “Firdausi… kashe mana wannan alarm ɗin.” Firdausi ma ta rufe fuskarta da pillow. “Ni? Ba ni ba ce na saka ai” Aasiya ta yi dariya daga ɗayan gefen gadon. “Ku tashi mana. Lectures fa ƙarfe takwas ne.” Zahra ta ja dogon tsaki. “Wallahi whoever invented morning lectures ba mutumin kirki ba ne.” Su uku suka yi dariya kafin suka miƙe. Suka yi alwala suka yi sallar Asuba, suka zauna suka yi azkar na ɗan lokaci, sannan kowacce ta shiga bathroom ta yi wanka. Cikin kusan awa guda, su ukun sun gama shiryi tsaf. Firdausi da Aasiya sun yi kyau cikin simple dress dinsu, amma Zahra… Dama ko a’ina take sai ta haska Ta fito sanye cikin wata doguwar abaya mai tsada, color ɗinta ya yi matuƙar dacewa da kayan, agogon hannunta da ƙaramin handbag ɗinta sun ƙara mata armashi. Komai nata cikin nutsuwa yake, babu ƙawata mai yawa, amma duk wanda ya kalleta sai ya sake waiwaya. Suna fitowa daga School Villa, ɗalibai da dama ma suna fitowa zuwa lectures na safe. Compound ɗin ya cika da hayaniyar ɗalibai. Wasu na dariya, wasu na gudu saboda sun makara, wasu kuma na jiran ababen hawa. Sai dai kusan duk inda Zahra ta wuce, idanu suna binta ne… “Ba ita ba ce?” “Wallahi ita ce.” Wasu na raɗaɗi, wasu kuma suna waiwaya suna kallonta. Amma Zahra ko kaɗan ba ta nuna alamar jin abin da ake faɗa ba. Ta ci gaba da tafiya cikin nutsuwa, kai a tsaye, tafiyarta cike da kwarjini, fuskarta ɗauke da natsuwa da izza Idan mutum ya gan ta a wannan lokacin, ba zai taɓa tunanin cewa ita ce Zahra mai yawan hira da ƙawayenta ko wacce ke shagwaɓa wa Abbah da Mami kamar ƙarama ba. A wannan lokacin, cikakkiyar budurwa mai cike da kwarin gwiwa ce Da suka fito daga gate na School Villa, sai suka hangi yawancin keken Napep sun riga sun kwashe ɗalibai zuwa makaranta. Babu ko ɗaya a wajen. Zahra ta tsaya cak “Oops.” Ta kalli hanya sannan ta kalli Firdausi “Matsalata kenan.” Firdausi ta ɗaga gira “Wace matsala?” “Ni kam wallahi ba zan iya trekking ba. Ga shi babu Napep.” Aasiya ta yi dariya “Ni ma ban ga ko ɗaya ba.” Firdausi ta kalli agogon hannunta. “Kar mu makara. Let’s try mu fara tafiya, ko za mu samu wani a gaba.” Zahra ta turo baki. “Please… let’s wait zasu iya zuwa yanzu” Ba don ta so ba, ta biyo su ganin sun fita yawa Suka fara tafiya…. Suna tafiya suna kallon ko za su ga Napep Amma babu…. Sun ka ƙara tafiya, har sannan babu Da suka yi nisa sosai, Zahra ta fara rage sauri “Firdausi…” “Hmm?” “Wallahi na gaji.” Firdausi ta yi dariya “Mun rage tafiya ne fa.” “Shi ya sa nake cewa ba zan iya ba.” Ta sake ɗan tafiya “Wayyo ƙafafuna.” Aasiya ta yi dariya “Princess, ki yi haƙuri yanzu kam ai mun iso” “Ban taɓa yin irin wannan tafiyar ba wallahi.” Daga haka suka cigaba da tafiya Amma sai complain take yi duk hanya. “Da ace Napep ya zo.” “Da ace mun fito da wuri.” “Da ace lectures ɗin ba na safe ba ne.” Firdausi da Aasiya dariya kawai suke yi Da ƙyar suka isa harabar makarantar. Zahra kuwa tuni gajiyar tafiyar ta bayyana a fuskarta. Da suka shiga lecture hall, ta sauke jakarta a kan kujera sannan ita ma ta zauna da ƙyar. Ta jingina bayanta tana sauke numfashi “Wallahi… idan zan zauna a School Villa, dole sai na nemo solution. Wannan trekking ɗin ba nawa ba ne.” Firdausi da Aasiya suka kalli juna, suka fashe da dariya, Zahra kam shafa ƙafafunta tana jin kamar sun yi mata nauyi fiye da yadda ta taɓa tsammani Lecturer ne ya shigo hakan yasa class din yayi tsitt Zahra gata zauna a kujerarta na gaba, jingine da baya, fuskarta babu ko alamar murmushi. Duk lokacin da lecturer yake bayani, ita dai lokaci-lokaci tana shafa ƙafafunta a hankali. Lecturer ɗin ya ɗaga kai yana kallon class, sai idanunsa suka sauka kan Zahra. Ya yi murmushi “Zahra, what happened today? You don’t look like yourself.” Class ɗin gaba ɗaya suka waigo suna kallonta. Zahra ta ɗan bata fuska “Sir… I trekked to school because there was no transportation. That’s why I’m exhausted.” Kafin ma lecturer ya sake magana… Sai class ɗin gaba ɗaya aka fashe da dariya Wani har yin wani k’ara “Famous ce fahh” Wata kuma ta ce, “Seriously?” Nan take ran Zahra ya ɓaci Ta juya a hankali ta kalli class ɗin gaba ɗaya da kwarin gwiwa irin nata “What’s so funny?” Nan take wasu suka sake fashewa da dariya. Ta yi ƙaramin tsaki “Mtss.” Ta juya ta zauna ba tare da ta ƙara kallonsu ba. Ko lecturer ɗin sai da murmushi ya kusan suɓuce masa, amma ya daure ya ciye. Ya gyara murya. “Alright, everyone. That’s enough. Let’s continue with the lecture.” Nan ya ci gaba da koyarwa. Da lecture ya ƙare, Zahra ta fito abinta dan gaskiya Yau sun bata mata rai, ta tsaya a ƙarƙashin wata bishiya, ta ciro wayarta Sai ga kawayenta sun biyo ta Kai tsaye ta yi conference call da Abbah, Mami da Ya Umar. Da suka ɗaga, ba ta bari sun yi magana ba. “Wallahi ni dai a kawo min mota ta. Idan ba so ake ƙafafuna su tsage ba. Kun ga yadda nake ji kuwa?” Abbah ya saki dariya “Haba Baby, har haka?” “Abbah, ba zan iya trekking ba wallahi.” Ya Umar ya yi gyaran murya. “Lazy girl” Kamar zata yi kuka ta ce “I mean it fah, yanzu haka kafafun ma dakyar suke amfani” Ya Umar yayi dariya “Za a kawo miki…” Zahra ta yi murmushi “Na sani.” Sai ya ƙarasa da cewa “Pay before delivery.” Ta zaro ido “Haba My Love!” Ya Umar ya yi dariya “Ai kin iya marairaicewa.” Ta kasa haɗiye dariyarta, ta juya ga Mami “Mami, ki sa baki mana.” Mami ta yi dariya. “Ni kam ba ruwa na. Yanzu idan na shiga tsakaninku, daga baya sai ki haɗa kai da shi ku gwale ni.” Dukkansu suka yi dariya. “Kai Mami!” Abbah ya girgiza kai yana murmushi. “Alright. Za a kawo miki motar.” Nan take fuskar Zahra ta washe “I love you Abbah na!!” Ta kashe wayar cike da farin ciki. Firdausi ta ce “Saudat da Suhaima sun iso.” Zahra ta yi murmushi “Really?” “Eh, amma babu key.” Ba tare da ta tsaya ba, Zahra ta buɗe jakarta, ta ciro mukullin gidan ta miƙa musu. “Ku kai musu.” Firdausi ta kalleta “Ke fa?” Zahra ta yi saurin girgiza kai. “Ni? Babu inda zan je. Wallahi idan na sake yin wannan tafiyar, ƙafafuna za su balle.” Su biyun suka fashe da dariya. Aasiya ta karɓi mukullin “Toh Madam Princess, zauna ki huta.” Suna dariya suka juya suka tafi. Zahra kuwa ta nufi wani cool-down spot da ke ƙarƙashin manyan bishiyoyi a harabar makarantar. Ta zauna a hankali tana sauke numfashi, ta buɗe Snapchat, ta ɗauki hotuna masu yawa, ta saka caption tana posting Bayan ta gama, ta koma Instagram. Ta shiga replying messages da chatting, yayin da iska mai sanyi ke kaɗa veil dinta, tana jin daɗin hutun da ta samu bayan gajiyar safiyar da ba za ta manta da ita ba Bayan kusan mintuna talatin tana zaune a cool-down area tana chatting a wayarta, wani matashi ya ƙaraso gabanta. Dogon saurayi ne, sanye cikin riga da Wanda masu kyau, ya tsaya yana murmushi. “Hey…” Zahra ba ta ko ɗaga kai ba. Yatsunta na ci gaba da yawo a kan screen ɗin wayarta. Ya sake matsowa kaɗan “Hello.” Shiru…. Ko kallonsa ba ta yi ba Ya ɗan yi dariya “Baiwar Allah, magana ake miki fa.” Amma kamar ba da ita ake yi ba. Hankalinta gaba ɗaya na kan wayarta. Saurayin ya ɗan dafe kansa cikin mamaki “What’s going on?” A can gefe kuwa, Firdausi, Aasiya, Saudat da Suhaima na tahowa. Tun daga nesa suka hango Zahra zaune, suka kuma ga saurayin tsaye a gabanta yana ta magana, ita kuma ko motsi ba ta yi. Firdausi ta yi murmushi “Guys… akwai drama.” Saudat ta ce a hankali, “Bai dan wacece Zahra ba kenan” Su huɗun suka ci gaba da tahowa. Da suka ƙaraso kusa da ita, Zahra ta ɗaga kanta a hankali. Da ganin Saudat da Suhaima, nan take fuskarta ta canza. Ta miƙe tsaye da fara’a. Ta fara rungumar Saudat “Welcome, darling!” Sannan ta rungumi Suhaima “So good to see you!” Suna dariya cike da murnan ganin juna Saurayin ya zaro ido “Dama kina magana?“ Ya girgiza kai “Na d’auka ai kurma ce ke” Zahra ba ta amsa masa ba, ta ɗauki jakarta a hankali. Sannan ta juya ta kalle shi daga sama har ƙasa, kallon da bai ƙunshi fushi ko murmushi ba, sai cikakkiyar nutsuwa da izza. Ba tare da ta ce masa komai ba, ta mayar da kallonta ga ƙawayenta. “Let’s go.” Ta yi gaba cikin tafiyarta mai cike da kwarjini. Su ma suka bi bayanta A gefen wajen kuwa, wasu ɗalibai da suka ga abin da ya faru suka fashe da dariya. Wani ya taɓa kafaɗar saurayin. “Allah ya ƙara, oga.” Wani kuma ya ce, “Ka ga kamar ita za ka tare? Wrong address, boss.” Dariya ta ƙara tashi a wajen. Saurayin ya sosa kansa cikin kunya ya bar wajen Ita kuwa Zahra, ko waiwayowa ba ta yi ba. Ta ci gaba da tafiya tare da ƙawayenta, kamar ba wani abu ya taɓa faruwa ba. Bayan sun gama ɗan hutun da suka yi, su biyar suka koma lecture hall domin lecture na gaba. Har yanzu lecturer bai shigo ba, ɗalibai kuwa na ta hira cikin ajin. Su ma suka zauna a layinsu. Firdausi ta kasa haƙuri, ta juya tana kallon Zahra. “Madam… Gist us mana. Me ya sa ba ki kula saurayin nan ba ko kaɗan?” Zahra ta ɗaga gira ta kalleta, sannan ta yi mata wani irin kallo. “Firdausi…” “Na’am.” “Kin ga na yi kama da wacce zai tare ne?” Firdausi ta fashe da dariya “A’a ba haka nake nufi ba.” Aasiya ma ta fara dariya “Toh amma gaskiya, ko ɗaga kai ba ki yi kika kalle shi ba. Ta yaya kika san abin da yake so?” Zahra ta ɗan gyara zama, ta ɗora hannunta kan tebur. “Whatsoever… jikina ya ba ni. Kuma da na kalle shi na farko, na ga it’s written all over his face.” Suhaima ta yi dariya. “Wai ke kina ganin mutum sau ɗaya ki gama karanta shi?” Zahra ta ɗan yi murmushi “Ba koyaushe ba… amma wasu mutane, fuskokinsu suna faɗin abin da bakinsu bai faɗa ba.” Saudat ta ce, “Toh idan ba haka ba fa?” Zahra ta ɗaga kafaɗa. “Then that’s not my business.” Firdausi ta girgiza kai tana dariya. “Har naji masa kunya, kin masa rashin M” “Ni?” “Eh mana. Ko amsa sallama ba ki yi ba.” Zahra ta haɗe fuska. “Saboda ban san shi ba. Kuma ban ga dalilin da zai sa na tsaya hira da stranger ba.” Aasiya ta ɗan yi murmushi “Shikenan Madam” Zahra ta ce. “Better” Dukkansu suka fashe da dariya a lokaci guda. A dai-dai lokacin ne lecturer ya shigo ajin. Nan take hayaniyar ta lafa, kowa ya gyara zamansa, aka fara lecture na gaba Da lecture na ƙarshe ya ƙare, ɗalibai suka fara fita daga hall ɗin a hankali. Zahra ta miƙe tana ɗaukar jakarta, ta kalli ƙawayenta. “Girls, mu wuce cafeteria mana, yunwa nake ji” Firdausi ta girgiza kai “A’a, tunda mun gama lectures na yau, gara mu koma gida. Mu dafa abinci kawai, zai fi.” Aasiya ta gyada kai “Ni ma haka nake gani.” Suhaima ta ce “Sure, tunda we’re done for today” Saudat ta yi murmushi “Toh mu koma” Zahra ta turo baki “Toh… abun hawa fa?” Kafin ma ta rufe baki.. Sai wata Napep ta zo ta tsaya kusa da su. Aasiya ta yi dariya “Lucky you!” Firdausi ta ce “Allah ya ji kukanki.” Zahra ta yi murmushin nasara “See? Allah yana sona.” Dukkansu suka yi dariya Suka shiga Napep ɗin suka nufi School Villa. Da suka isa gida, kowacce ta shiga abin da ya dace da ita. Firdausi ta nufi kitchen Ta ɗaura girki, tana haɗa abincin rana yayin da ƙamshi ya fara cika gidan. A gefe guda kuma, Saudat da Suhaima suka shiga ɗayan ɗakin suna gyara kayansu, suna jerawa a wardrobe tare da shirya sauran kayayyakin da suka zo da su. Aasiya na taimaka musu lokaci-lokaci, ita kuma Zahra ta ɗan zauna tana hutawa kafin daga baya ta shiga kitchen tana taimaka wa Firdausi da ƙananan abubuwa Bayan komai ya kammala, suka haɗu gaba ɗaya a falon. Aka jera abinci a kan center table. Kowacce ta zauna ta fara cin abinci cikin nishaɗi Ana cikin ci, Firdausi ta ce, “Guys, kun ji abin da Zahra ta yi yau da safe kuwa?” Nan take Suhaima ta ɗaga kai “Me ta yi?” Firdausi ta fara ba su labarin yadda Zahra ta yi ta complain tun daga School Villa har zuwa makaranta saboda trekking. Ta kwaikwayi yadda Zahra ke cewa “Wallahi ƙafafuna za su balle.” Dukkansu suka fashe da dariya. Saudat har ta dafe cikinta “Ke Zahra!” Aasiya ta ƙara da cewa “Da muka isa lecture hall, kamar za ta yi kuka saboda gajiya.” Firdausi ta ce, “Sai kuma ta kira gida tana cewa a kawo mata mota, wai idan ba haka ba ƙafafunta za su tsage.” Falonsa ya kaure da dariya. Suhaima ta girgiza kai “Princess kenan.” Zahra kuwa, kamar ba da ita ake magana ba. Ta ci gaba da cin abincinta cikin nutsuwa ba tare da ta ko ɗaga kai ba. Daga ƙarshe ta ce cikin sanyin murya, “Ku gama dariyar. Gobe ma idan babu Napep, ni ba zan fita ba.” Wannan maganar tata ce ta sake sa falon ya kaure da wata sabuwar dariya. Chapter 53 Da yamma ta yi liss, kowacce ta kama abin da take yi. Firdausi da Aasiya suna kitchen suna wanke kwanukan abincin da suka ci, Suhaima da Saudat kuma suna gyara ɗakinsu, yayin da Zahra ta fito ta zauna ita kaɗai a ƙaramin balcony ɗin apartment dinsu. Iska mai sanyi na kaɗa veil. Wayarta na hannunta, amma ba chatting take ba. Kallon sararin sama kawai take yi. A can wani ɓangaren gari… A cikin wani katafaren office mai cike da kayan alatu, wata mata ta zauna cikin kujerar fata, tana jujjuya wani glass a hannunta. Fuskarta ba ta nuna komai. Sai wayarta ta ɗauki ƙara. Ta ɗaga. “Na’am.” Muryar wani namiji ta fito daga ɗaya ɓangaren. “Mun tabbatar yarinyar ta koma School Villa.” Ta lumshe ido. “Good.” “Yanzu me kike so mu yi?” Ta ɗan yi shiru kafin ta ce cikin sanyin murya, “Ku ci gaba da sa ido kawai.” “Ba za mu ɗauki wani mataki ba?” Ta yi wani ɗan murmushi mai cike da ma’ana. “Ba yanzu ba…” Ta miƙe tsaye tana kallon waje ta cikin glass window. “Lokacin da ya dace… ita da kanta ba za ta fahimci yadda komai ya fara ba.” Tana kai wa nan ta kashe wayar Washegari da safe. Da ƙarfe bakwai da rabi, Zahra da ƙawayenta suka fito daga School Villa, kowacce ɗauke da jakarta, suna ƙoƙarin samun Napep kafin lecture na ƙarfe takwas. Abin mamaki, yau ma babu ko guda. Firdausi ta yi ajiyar zuciya “Da alama yau ma trekking za mu yi.” Zahra ta haɗe fuska “Wallahi ban shirya ba.” Kafin su fara tafiya, hayaniya suka fara ji tana tashi daga bakin babbar hanyar shiga campus. Mutane suka fara taruwa, wasu ɗalibai suna gudu zuwa wajen. “Me ya faru?” “Wani accident ne wai!” “Napep ce ta bugi wani student!” Nan take Zahra da ƙawayenta suka kalli juna, suka nufi wajen tare da sauran mutane. Da suka isa, taron ya yi yawa, ga wata Napep ta kife a gefe Wani ɗalibi yana kwance a ƙasa cikin ciwo, mutane da yawa kuwa sun tsaya suna kallo kawai, babu wanda ya san abin da zai yi. A dai-dai lokacin ne aka ji ƙarar wata baƙar mota mai tsada tana tsayawa a gefen hanya Door ɗinta aka buɗe Wani dogon saurayi cikin farar shirt mai sauƙi da baƙar wando ya fito da sauri. Ba tare da ya kula da hayaniyar mutane ba, ya kutsa cikin taron. Ya durƙusa kusa da wanda ya ji rauni, ya fara duba yanayinsa cikin nutsuwa. “Someone call the emergency unit. Hurry!” Muryarsa cike take da kwarin gwiwa. Cikin daƙiƙu kaɗan, ya haɗa wasu ɗalibai suka ɗaga wanda ya ji raunin cikin tsari, suka saka shi a motarsa domin a garzaya da shi asibiti. Kafin ya shiga motar, idanunsa suka ɗan zagaya taron kamar akwai abun da yake nema Na ɗan lokaci kaɗan… Idanunsa da na Zahra suka haɗuwa, kallonta yake yi while ita accidentally nema ta kalle sa ta ɗauke kai ba tare data san tama kalle sa ba Amma kafin komai ya faru ko wani yayi noticing, ya shiga motar Sake haɗa ido suka yi, wannan karan tayi noticing saboda yadda aka sauke glass din motar kasa, sai kuma lokaci guda aka ɗaga sama haba ɗaya kuma tinted ne Motar ta ja da sauri ta bar wajen Zahra ta tsaya tana kallon hanyar da motar ta bi. Ba ta san ko waye ba Ba ta ma san sunansa ba Sai dai saboda wani dalili da ita kanta ba ta fahimta ba… Taji tana son sanin wanene shi.. kuma kamar bata yarda da shi ba… Bayan lectures na ranar suka ƙare, Zahra da ƙawayenta suka fito daga lecture hall suna hira. Firdausi ce ta fara magana. “Wallahi har yanzu mutumin nan na safe bai fita a raina ba.” Suhaima ta gyada kai “Ni ma. Yadda ya taimaka ba tare da ya tsaya jiran a yaba masa ba… abin ya burge ni.” Aasiya ta ce, “Da alama ba irin samarin campus ba ne.” Saudat ta yi murmushi. “Toh Zahra fa? Ita dai ko magana ba ta yi a kansa ba.” Dukkansu suka kalli Zahra. Ita kuwa ta ɗaga kafaɗarta “Ya yi abin kirki. Allah ya saka masa.” Firdausi ta yi dariya “Shi kenan? Kawai?” “Eh.” “Ko ba ki son sanin ko waye?” “No.” “Why?” “Saboda bai shafe ni ba.” Suhaima ta girgiza kai tana murmushi “Ke dai kin sha bamban.” Suna cikin hirar ne wayar Zahra ta yi ƙara. Unknown Number. Ta ɗan kalli screen ɗin na wasu daƙiƙu kafin ta ɗaga. “Hello?” Shiru. Ta sake cewa “Hello?” Har yanzu babu amsa. Sai aka katse kiran. Ta ɗan haɗe gira “Waye kuma wannan?” Firdausi ta ce “Maybe wrong number.” “Probably.” Ba ta ƙara tunanin maganar ba. Ta saka wayar cikin jakarta, suka ci gaba da tafiya. A wani ɓangaren garin… Matashin nan yana tsaye a bakin tagar ofishinsa. Wani mutum ya shigo ya miƙa masa file. “Sir, ga takardun da kuka nema.” Ya karɓa ba tare da ya ɗaga kai ba. Mutumin ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce, “By the way… an ce yau kun sake ceton rayuwar wani student.” Ya ɗan yi murmushin gefen baki. “Anyone would have done the same.” Mutumin ya girgiza kai. “No, sir… not everyone.” Ya sake mayar da hankalinsa kan file ɗin. “Anything else?” “A’a, sir.” “Toh za ka iya tafiya.” Da mutumin ya fita, ya buɗe file ɗin. A saman shafin farko an rubuta wasu manyan haruffa F************h Idanunsa suka tsaya a kan rubutun na wasu daƙiƙu. Sai ya rufe file ɗin a hankali. Fuskarsa ba ta nuna komai. Washegari da rana, bayan sun gama lectures na ƙarshe, Zahra da ƙawayenta suka dawo School Villa cikin Napep. Suna shiga compound, Zahra ta tsaya cak. “Wait…” A tsakiyar bakin apartment ɗinsu mota ce mai matuƙar kyau take parke Firdausi ta zaro ido “Wayyo… wa ya kawo min wannan?” Kafin wani ya amsa, aka ji muryar wani saurayi “Baby!” Ta juya da sauri “Ya Umar!” Da murmushi ta ƙarasa wajensa. Ya Umar ya miƙa mata mukullin motar yana jujjuya shi a yatsansa. “Ga abin da aka ce a kawo kafin ƙafafun wani su tsage.” Firdausi, Aasiya, Saudat da Suhaima suka fashe da dariya. Zahra ta karɓi mukullin tana dariya “Thank you!” Ya Umar ya nuna mata motar “Abbah ya ce daga yau ba trekking.” Ta rungumesa cikin shagwaɓa “Allah ya ƙara maka lafiya.” Ya yi murmushi “Ki gode wa Abbah, ni delivery boy ne kawai.” Ta ɗaga wayarta nan take ta kira Abbah. Da ya ɗaga ta ce, “Abbah! Thank you so much!” Daga can ya yi dariya. “Ki kula da ita. Kuma ki mai da hankali kan karatunki.” “In Sha Allah.” Ta sake gode masa, sannan ta kira Mami, ita ma ta yi mata godiya tare da yi mata addu’a. Su Firdausi suka karasa suka gaishe sa, ba tare daya kalle su ba ya amsa Asiya ta ce “Ya Umar, ka ceci rai ai, idan ba haka ba ai wata zata sha wahala” Murmushin gefen baki yayi ba tare daya ma kalleta ba Bayan Ya Umar ya tabbatar da komai lafiya, ya yi musu sallama ya koma. Firdausi ta ce “Princess ta samu abin hawanta.” Suhaima ta yi dariya “Yanzu ba za mu ƙara jin complain ɗin trekking ba.” Zahra ta yi murmushi “Exactly.” Da dare, bayan sun ci abinci suka ɗan huta, kowacce ta ɗauki littattafanta. “Mu fita reading area?” Aasiya ta tambaya “Let’s go.” Zahra ta amsa. Suka nufi wurin karatu da ke cikin School Villa, inda ɗalibai da dama ke zaune cikin nutsuwa suna karatu. Kowacce ta mayar da hankalinta kan littattafanta. Lokaci ya ja sosai kafin suka gama. Da kusan ƙarfe goma na dare suka dawo side dinsu a gajiye. Kowacce ta shiga ɗakinsu, ta yi shirin kwanciya. Zahra na zaune kan gadonsu tana duba wayarta. Can… Wayarta ta yi ringing. Ta kalli screen Unknown Number. Ita ce lambar nan da ta kira ta jiya. Ta haɗe gira “Again?” Ta ɗaga kiran a hankali “Hello?” Shiru. Ta sake magana “Who is this?” Sai ta ji kamar numfashin wani a ɗaya ɓangaren… Amma babu kalma ko ɗaya bai ce ba Kafin ta sake cewa komai… Call Ended. Zahra ta ci gaba da kallon screen ɗin wayarta na wasu daƙiƙu “Waye ne haka?” Ba ta sake kiran lambar ba, ta kashe screen ɗin wayar, ta ajiye ta a gefen gadon Sai dai a wannan karon… Wani irin rashin nutsuwa ya ɗan shiga zuciyarta Ta girgiza kai “Idan da gaske yana da magana ai zai yi.” Ta kashe fitilar bedside lamp ɗin, ta lulluɓe jikinta da duvet. Cikin ƴan mintuna kaɗan bacci ya ɗauke ta. Washegari. Tun da safe, Zahra ta farka cikin farin ciki. Yau babu maganar trekking. Bayan sun yi sallah, suka shirya kamar yadda suka saba. Da suka fito compound, idanun kowa suka koma kan sabuwar motar Zahra “Wow!” “Wallahi motar nan ta haɗu.” “Sabuwar model ce fa.” Wasu ɗalibai suka tsaya suna kallonta. Firdausi ta yi murmushi. “Princess, yau kin zama celebrity na biyu.” Zahra ta yi dariya “Ku shigo mana.” Su biyar suka shiga motar. Zahra ta ɗaura seat belt, ta kunna motar cikin nutsuwa. “Everybody ready?” “Yes!” A hankali ta fice daga School Villa. A hanya, Suhaima ta ce “Wallahi yau na ji daɗin” Saudat ta yi dariya “Ni ma. Allah ya saka wa Abbah.” Firdausi ta ce “Yau ma za ki ce ƙafafunki za su tsage?” Dukkansu suka yi dariya. Zahra ta harare ta “Very funny.” Da suka isa campus, Zahra ta faka motar a parking area. Da suka fito, wasu ɗalibai suka riƙa kallon motar, wasu kuma Zahra. A yayin da suke tafiya zuwa faculty… Sai Zahra ta ji wayarta ta yi vibration. Ta ciro ta. Unknown Number. Ta tsaya na ɗan lokaci. Firdausi ta lura “Ba za ki ɗaga ba?” Zahra ta latsa answer “Hello?” A wannan karon… an yi magana. Muryar namiji ce, mai nutsuwa Ba ta da ƙarfi, ba ta da rauni. “Good morning.” Zahra ta haɗe gira “Who is this?” An yi shiru na daƙiƙa biyu. Sai ya ce, “Ki yi haƙuri da kiran da na yi jiya…” Kafin ya ƙarasa maganar… Sai wata mota ta danna horn kusa da su. “Pooon!” Hayaniyar ta hana Zahra jin abin da ya faɗa “Hello?” Ba a sake cewa komai ba, kiran ya katse. Ta sauke wayar tana kallonta cikin mamaki. Firdausi ta tambaya “Wai waye ne?” Zahra ta girgiza kai. “Ban sani ba… amma wannan karon ya yi magana.” “Me ya ce?” “Ban ji komai sosai ba.” Ta saka wayar cikin jaka “Mu je, lecturer zai shigo.” suka ci gaba da tafiya. Ba wanda ya lura a cikin su.. A ɗayan gefen parking area, wata baƙar mota tana tsaye. Wanda ke cikinta ya kalle su na ɗan lokaci. Da ya ga sun shiga cikin faculty, ya kunna motarsa ya tafi ba tare da kowa ya lura da kasancewarsa ba. A kwana a tashi… Lokaci ya ci gaba da tafiya… Kafin ma su ankara, kusan wata ɗaya kenan da zuwansu Campus A cikin wannan wata ɗaya, rayuwarsu ta sauya gaba ɗaya. Su biyar sun zama kamar ƴan uwa, lecture tare, karatu tare, cin abinci tare, dariya tare Har ma idan ɗaya ba ta gida, sai gidan ya yi musu wani iri, musamman idan Zahra ta tafi weekend . Sai dai akwai abu ɗaya da bai taɓa canzawa ba… Zahra…. Har yanzu ba ta iya aikin gida ba Ko wanke plate ɗinta ba ta iya yi yadda ya kamata ba, ballantana kuma wanki Sau da yawa idan ta cire kayanta ta kai laundry, kafin ta dawo sai ta tarar Saudat ta haɗa da nata ta wanke musu gaba ɗaya Da farko Zahra ta sha faɗa “Saudat, na ce ki daina wanke min kaya mana.” Saudat sai ta yi murmushi. “Ba komai ai, tare da nawa na haɗa ai” “Kullum haka kike fa, ni dai wani iri nake ji Saudat” “Toh me ya sa zan bar naki?” Har ma a weekends, Zahra kan dage ita za ta kai wajen waki Amma idan ta shiga bathroom ta fito ko ta fita.. sai ta tarar a riga an gama. Daga ƙarshe ta gaji da magana, ta bar ta kawai. Yau Lahadi ce Babu lectures. Tun safe gidan ya cika da annashuwa Firdausi na kitchen tana soya ƙwai Aasiya na haɗa tea. Suhaima da Saudat na ta hira a falo Zahra kuwa ta fito daga ɗakinsu tana miƙa Ta kalli kowacce “Girls…” Suka waigo “Na gaji da zama a gida wallahi.” Firdausi ta yi dariya “Toh me kike so?” “Mu fita mana!” “Where?” “Anywhere… just to have fun.” Aasiya ta tafa hannu “Finally! Wannan shawarar ta yi.” Suhaima ta ce, “Cheers” Saudat ta yi murmushi “Ni ma.” Zahra ta miƙe tsaye “Okay then. Everybody… one hour. Mu shirya.” “Deal!” Nan take kowacce ta nufi ɗakinsu, bayan sunyi breakfast Cikin ƙasa da awa ɗaya… Kowacce ta fito cikin shiga mai kyau. Firdausi na sanye da ash-colored abaya Aasiya ta saka navy blue maxi gown da black veil, tana ɗauke da ƙaramin handbag. Suhaima na cikin wine-colored jilbab mai matuƙar kyau. Saudat kuma, duk da kayan nata ba su da tsada, ta fito cikin blue gown mai tsafta da blue veil, kyau da tsarinta suka ƙara fito da ita. Daga ƙarshe… Ƙofar ɗakin da Zahra suke ta buɗe Ta fito cikin wani elegant mocha-colored flowing dress da premium chiffon veil, sanye da farin da black sneakers masu tsada, luxury wristwatch a hannunta da ƙaramin designer handbag. Kamshin turarenta ya mamaye falon tun kafin ta ƙaraso. Firdausi ta zaro ido “Princess…” Aasiya ta yi dariya “Ke kullum sai kin kashe mutane da dressing ne” Suhaima ta ce “One thing about you yadda kike Kara ɗaga mana darajarmu a media” Saudat ta yi murmushi tana kallonta “Masha Allah.” Zahra ta juya a hankali tana kallon kanta a mirror. Ta yi murmushi “So… are we ready?” “Yes!” Ta ɗaga mukullin motarta tana jujjuya shi a yatsa. “Ladies… let’s go have some fun.” Da dariya da hayaniya suka fito daga gidan, Zahra ta buɗe motarta, suka shiga ciki, sannan suka fice daga School Villa cike da farin ciki Chapter 54 Kusan rabin ranar suka shafe suna yawon shakatawa Suka shiga wani babban shopping mall, suka yi window shopping, suka shiga game arcade inda Firdausi da Aasiya suka dage sai an gwada wasu games Suhaima da Saudat kuwa suka dage sai an ɗauki hotunan duk wani move nasu a wajen Zahra ce ta riƙa musu dariya “Wallahi ku huɗun nan ba za ku taɓa girma ba.” Firdausi ta harare ta “Kamar ke ɗinma wata babba ce” Daga nan suka wuce wani restaurant mai kyau, suka ci abinci cikin nishaɗi, suna ta hira da dariya. Kafin su tafi, suka ɗauki group pictures da selfies na short vid masu yawa “Today’s memories are worth keeping,” Zahra ta faɗa tana kallon hotunan. Da yamma ta yi, suka yanke shawarar komawa gida. Da suka isa parking lot, Zahra ta latsa remote, motarta ta yi ƙarar buɗewa. Ta yi wa ƙawayenta murmushi “Ku shiga mana.” Firdausi, Aasiya, Suhaima da Saudat suka shiga motar. Zahra kuma ta zagaya zuwa gefen direba, ta kama handle ɗin motar ta buɗe ƙofar Daidai lokacin… Wani hannu ya riƙe ƙofar kafin ta shiga Ta ɗago kai. Wani matashi ne tsaye gabanta. Dogon saurayi ne, cikin baƙar shirt da jeans, fuskarsa cike da damuwa amma idanunsa na nuna ƙarfin hali. Ya haɗa ido da ita “Hey… excuse me, please.” Zahra ta kalle shi daga sama har ƙasa, sannan ta haɗe fuska. “A taƙaice… are you mad?” Ta nuna inda yake tsaye “Za ka tsaya min a kai haka?” Saurayin ya yi murmushin da bai rasa kunya ba “Eh… gaskiya I’m mad… a kanki Fatima Zahra” Ya ɗan sauke numfashi. “Har mutane suna kallona kamar wani psycho.” Ya yi murmushi kaɗan “Idan kin ce no, zan ji zafi… amma ba zan ji wani iri ba.” Zahra ta ji ranta ya fara ɓaci, ta matso kusa da shi. “Za ka matsa min ne, malam, ko yaya?” Ya ɗan sunkuyar da kansa “Please, Zahra… one minute” “Ki tausaya min.” Ta yi wata ’yar dariyar raini “Fuck you.” Ta nuna shi da yatsa “Who are you?” Ya yi shiru na ɗan lokaci Sannan ya amsa cikin nutsuwa. “I’m nobody…” Ya ɗan yi murmushin gefen baki “But hoping to be somebody… one day.” Zahra ta girgiza kai cikin rashin jin daɗi “Congratulations.” Ta ture hannunsa daga ƙofar motar “Yanzu ka gama? Saboda ni kam ban zo nan don sauraron speeches ba.” Ta shiga motar ba tare da ta sake kallonsa ba, ta ufe ƙofar. Saurayin ya tsaya yana kallon motar cikin rashin abun yi Firdausi, Aasiya, Suhaima da Saudat kuwa suka yi shiru gaba ɗaya, suna kallon Zahra da saurayin, sun kasa cewa komai. Zahra ta kunna motar, ba tare da ta waiwaya ba, ta fice daga parking lot, ta bar saurayin tsaye a wurin yana kallon motar har sai da ta ɓace. Su kuwa har suka fara tafiya, babu wanda ya yi magana na wasu daƙiƙu. Sai ƙarar AC da waƙar da ke tashi a hankali kawai ake ji Firdausi ce ta fara karya shirun, ta juya ta kalli Zahra “Baby…” Zahra na kallon hanya ta ce “Hmm?” “Me ya faru ne tsakanin ki da guy ɗin nan?” “Nothing.” Aasiya ta haɗe gira “Nothing? Kin san shi ne?” “No.” “Toh me ya sa ya kira ki da sunanki?” Zahra ta yi ɗan tsaki “Wallahi ban sani ba.” Suhaima ta ce “Amma kamar ya san ki sosai.” “Ya sani mana,” Zahra ta amsa ba tare da ta juya baya ba. “Mutane da yawa sun san ni.” Saudat ta yi murmushi “Ba wannan nake nufi ba. Kamar… ya san wani abu game da ke.” Zahra ta girgiza kai “I don’t care.” Firdausi ta ce “Amma kin yi masa zafi fa.” Zahra ta ɗan kalleta. “Yanzu idan ke ce wani ya zo ya tare ki haka fa?” Firdausi ta yi dariya “Ni zan tsaya na ji abin da zai ce.” “Ni kuma ba zan tsaya ba” ta mayar mata amsa ba tare data ko kalleta ba Aasiya ta ce, “Wallahi ya yi magana cikin mutunci. Ban ga ya yi rashin kunya ba.” “Mutunci?” Zahra ta ɗan yi dariyar raini. “Riƙe ƙofar motar mutum ba tare da izininsa ba ai ba rashin mutunci ba ne.” Suhaima ta gyada kai “Hakan ma gaskiya ne.” Saudat ta ce cikin sanyin murya “Amma… na ji tausayinsa.” Zahra ta kalleta ta mirro da mamaki “Tausayinsa?” “Eh. Yadda ya ce, ‘I’m nobody… but hoping to be somebody one day.’ Ban san dalili ba, amma maganar ta taɓa ni.” Na ɗan lokaci motar ta yi sit Firdausi ta ce, “Ni dai ina jin ba zai ƙara hakura ba.” Zahra ta ɗan yi murmushi ba tare da ta kalli kowa ba. “Toh ni kuma ina fatan ya yi hakuri. Saboda idan ya sake tare ni… wannan karon ma ba zai ji abin da zai so ba.” Dukkansu suka yi shiru Sai dai kowacce na da abin da take tunani. Saudat na tunanin kalaman saurayin ta rasa dalilin daya sa maganarsa ta bugeta Ita kuwa Zahra… Ta mayar da hankalinta kan tuƙi, kamar abin da ya faru bai da wata muhimmanci a gare ta Suna isa School Villa, Zahra ta faka motar a parking space ɗinsu. Ta kashe motar sannan ta cire seat belt. “Finally… home.” Firdausi ta miƙa hannayenta tana jan numfashi. “Wallahi na ji daɗin outing ɗin nan.” “Same here,” Aasiya ta amsa. Suhaima ta ce “Ya kamata mu riƙa yin haka ko sau ɗaya a wata.” Saudat ta yi murmushi “In Sha Allah.” Suka fito daga motar suna ɗauke da shopping bags ɗinsu. Kafin su shiga block ɗinsu, Firdausi ta ce, “Girls, ice cream fa! Na manta mun saya.” Zahra ta kalli ledar da ke hannunta “Oh… gaskiya.” Aasiya ta yi dariya “Ke dai idan ba mu tuna ba, da kin manta da rabin kayan da kika saya.” Zahra ta ɗan harare ta “Whatever.” Da dariya suka shiga cikin gidan. Da suka shiga falo, kowacce ta ajiye kayan da ta saya. Firdausi ta cire hijabinta ta zauna a kujera “Wallahi ƙafafuna sun gaji.” “Ke kuma?” Zahra ta yi dariya. “Ai ba trekking muka yi ba yau.” “Shopping ma exercise ne fa.” Dukkansu suka yi dariya. Suhaima ta buɗe ledarta “Guys, ku zo ku ga turaren da na saya.” Nan take suka zagaye ta “Wow!” “Smells so nice.” “Try this one.” Kowacce ta fara gwadawa a wuyanta da hannunta. Sai ɗakin ya cika da ƙamshi. Saudat kuwa tana zaune tana kallonsu tana murmushi. Zahra ta lura, ta auki wata ƙaramar leda ta miƙa mata. “Open it.” Saudat ta karɓa cikin mamaki “Mine?” “Of course.” Da ta buɗe… Wani elegant perfume ne da kuma wristwatch mai kyau Ta zaro Idanunta waje “Zahra… wannan fa…” “It’s yours.” “A’a, wannan ya yi yawa gaskiya” “No, it isn’t.” Zahra ta amsa Saudat ta girgiza kai “Wallahi ba zan karɓa ba.” Zahra ta haɗe fuska “Saudat!!!” Ta ɗan yi shiru kafin ta ci gaba “Kin taɓa barina na wanke kaya na?” Saudat ta yi murmushi “Ai wannan ba komai ba ne.” “Toh ni ma wannan ba komai ba ne.” Firdausi ta yi dariya “Please karɓa kawai. Kin san halinta.” Aasiya ta gyada kai “Otherwise ba za ta sake fita shopping da ke ba” Dukkansu suka yi dariya. Saudat ta sauke numfashi “Thank you… Allah ya saka da alkhairi.” “Ameen,” suka amsa gaba ɗaya. A daidai lokacin… Knock! Knock! Kowa ya waiga zuwa ƙofar. Firdausi ta miƙe “Wa zai zo mana wannan lokacin?” Ta nufi ƙofar ta buɗe, wani matashi ne tsaye a waje. Sanye da uniform na dispatch rider. Ya kalli Firdausi “Assalamu alaikum.” “Waalaikumus salam.” “A nan ne Zahra Fatima take?” Firdausi ta juya ta kalli Zahra “Baby… ana nemanki.” Zahra ta ƙaraso “Ga ni” Dispatch rider ɗin ya miƙo mata wani ƙaramin box da aka naɗe da golden ribbon. “An ce a ba ki wannan.” Ta karɓa cikin mamaki “Wa ya aiko?” Ya girgiza kai “Ban sani ba, an biya komai tun da farko.” Ya yi musu sallama ya tafi. Dukkansu suka taru suna kallon box ɗin. Firdausi ta ce da sauri “Open it!” Zahra ta kalli box ɗin na wasu daƙiƙu. Sai wani tunani ya faɗo mata… Unknown Number. Da kuma… Saurayin nan na parking lot Ta haɗe gira “Who exactly is this?” ta ci gaba da kallon ƙaramin gift box ɗin da ke hannunta. Firdausi ta kasa haƙuri “Baby, open it manaa!” Aasiya ta matsa kusa “I’m curious.” Suhaima ta ce “Kar dai ki ce ba za ki buɗe ba.” Saudat ma ta gyada kai “Mu gani mana.” Zahra ta sauke numfashi “Okay.” Ta fara cire golden ribbon ɗin a hankali, ta buɗe murfin box ɗin. Cikin box ɗin… Wata ƙaramar rose mai launin fari ce, tare da wani folded note “Flowers?” Firdausi ta faɗa da mamaki Zahra ta ɗauki note ɗin Kafin ta buɗe shi, Aasiya ta ce, “Read it aloud plsss!” Ta buɗe takardar Rubutun hannu ne mai kyau.. “You don’t know me… and maybe you don’t want to. But I just wanted to say thank you… for unknowingly teaching me that some people are worth respecting from afar. Have a beautiful day, Zahra.” Ba suna, ba number, bakomai da zai yi indicating ɗinsa Shiru ya ratsa falon. Firdausi ce ta fara magana. “Wallahi… wannan ba irin letter ɗin soyayya da muka saba gani ba ne, iyyeee this guy sabi love” Suhaima ta gyada kai “It’s… different.” Saudat ta ce a hankali, “Ya rubuta cikin girmamawa.” Aasiya ta kalli Zahra “Toh… yanzu fa?” Zahra ta sake ninke takardar, ta mayar da ita cikin box Ta ɗauki rose ɗin ta kalla na wasu daƙiƙu sai ta nufi dustbin. Firdausi ta zaro ido “Baby… me kike yi?” Ba tare da ta ce komai ba… Ta jefa gift box ɗin gaba ɗaya cikin dustbin. Firdausi ta riƙe kanta “No way!” Aasiya ta ce, “Haba Zahra” Suhaima ta yi shiru tana kallonta, Saudat ma haka Zahra ta tafa hannunta “Unknown people don’t deserve a place in my life.” Ta juya ta nufi ɗakinsu. Ba wanda ya sake magana A waje, a cikin wata baƙar mota da ke ajiye nesa da gate ɗin School Villa… Mutumin ya hango dispatch rider yana fitowa. Ya ɗan yi murmushi “That’s good!” Ya kunna motar a hankali “The Game is just beginning. Washegari…. Karfe bakwai da rabi na safe. School Villa ta cika da ɗalibai masu shirin fita lectures A kitchen kuma… Firdausi na frying pancakes. Aasiya na haɗa tea Suhaima na shirya lunch warmers Saudat kuma tana goge kitchen Zahra ta fito daga ɗaki cikin wani elegant milk-colored abaya da premium silk veil. A hannunta akwai mug ɗin coffee. Ta tsaya bakin kitchen tana kallonsu “My God… ku huɗun nan ba ku gajiya ne?” Firdausi ta waiwayo tana dariya. “Madam, idan muka jira ki, ai yunwa za ta kashe mu.” Dukkansu suka yi dariya. Zahra ta zauna a dining chair “Seriously, Saudat… na fa ce ki daina yi mana komai ke kaɗai.” Saudat ta yi murmushi “Na kusa gamawa ai.” “Exactly! Shi ya sa nake magana.” Aasiya ta kawo mata plate “Princess, eat first before your daily speech.” Ta karɓa tana murmushi “Thank you.” Bayan sun gama breakfast, suka fito compound. Motar Zahra na sheki, Firdausi ta yi whistle. “Driver madam… your chariot is ready.” Zahra ta jefa mata key. “Since kina surutu, ke za ki tuƙa?” Firdausi ta cafke key ɗin da sauri. “God forbid! Idan na yi scratching ɗin motar nan, Ya Umar zai kashe ni.” Dariya suka yi gaba ɗaya! Suka shiga motar. A hanya, karatu ne ke tashi a motar Suna hira cike da annashuwa a haka suka isa cikin university… Parking area ta cika da motoci. Zahra ta faka motar cikin nutsuwa. Kafin su fito… Sai Firdausi ta dafa hannunta. “Baby…” “What?” Firdausi ta nuna da idanunta zuwa wani gefe “Don’t look immediately.” Zahra ta ɗaga gira “Why?” “Because… he’s here.” Zahra ta juya kai a hankali. Can ƙarƙashin wata bishiya… saurayin nan ne, sanye cikin farar shirt da black trousers. Ba ya kallon wayarsa baya tare da wani balle yayi magana da shi Idanunsa kawai suna kan motar Zahra. Da idanunsu suka haɗu… Bai yi murmushi ba. Sai kawai ya ɗaga hannu kaɗan cikin girmamawa, kamar yana yi mata sallama daga nesa Zahra ta haɗe fuska, ta buɗe ƙofar motar ta sauka “Let’s go.” Duk sauka suka yi suna mamakin nacin mutumin nan, suka fara tafiya. Firdausi ta yi ƙasa da murya. “Wallahi… yau bai zo ya dame ki ba, just to see yhu” Aasiya ta gyada kai “Maybe ya fahimci message ɗin da kika ba shi.” Suhaima ta ce “Ko kuma yana son ya nuna cewa ba zai matsa mata ba ba” Zahra ba ta ce komai ba.. sai dai kafin su shiga faculty… Ta ji wata murya daga bayanta, a sanyaye… cikin girmamawa… “Have a nice day… Zahra.” Ba ta waiwaya ba, ta ci gaba da tafiya kamar ba ta ji komai ba Ranar ta ci gaba da tafiya kamar kowacce rana, sosai yau suka wuni a makarantar saboda lectures Ga lots of Assignments da aka basu, Class discussions da suka yi, Short tests ma, har yamma suna school suka yi ƙarshen lectures na ranar “I’m starving,” Firdausi ta faɗa tana riƙe cikinta Aasiya ta yi dariya “Same here. Cafeteria?” “Definitely!” Kowa ya amince. Su biyar suka nufi cafeteria cike da hayaniyar ɗalibai Bayan sun yi order, suka zauna a wani table da ke gefen window. Firdausi na ta ba da labari Suhaima da Aasiya na dariya. Saudat na cin abinci a hankali. Zahra kuwa tana sipping juice ɗinta kafin ta fara cin fried rice ɗin da ke gabanta. Sai kwatsam… Wata inuwa ta tsaya kusa da table ɗinsu. Firdausi ta ɗago kai “Oh no…” Saurayin nan ne, ya na tsaya cikin natsuwa Ya kalli Zahra kawai “Excuse me…” Zahra ko kallonsa ba ta yi ba, ta ci gaba da cin abincinta. Ya sake magana cikin ladabi “Can I have just one minute?” Still… No response. Ya sauke numfashi “Okay… I’m sorry for disturbing your peace.” Zahra ta miƙe tsaye ta ɗauki jakkanta ta juya zata tafi. Yayi saurin shan gabanta “Dan Allah ki saurare ni zahra… kar ki tafi” Ta fara tafiya a zuciye, jakar da ke rataye a kafaɗarta ta fara zamewa saboda ba ta rufe zip ɗinta sosai ba. Without thinking… Ya miƙa hannu ya riƙe jakar kafin ta faɗi ƙasa. Cikin daƙiƙa guda… PAA! Wani irin mari Zahra ta wanke shi da shi. Sautin marin ya amsa cikin cafeteria. Hayaniya ta tsaya cak. Cokula suka tsaya a sama. Wasu ɗalibai suka miƙe tsaye, kowa ya waigo Zahra ta zuba masa ido cike da ɓacin rai “How dare you?” “Wa ya ba ka izinin taɓa ni?” “How dare you hold my bag?” Saurayin ya dafe kumatunsa Ya kalleta cikin nutsuwa. “It’s not my fault, Zahra.” Ya ɗan nuna jakar “It was falling.” Na ɗan lokaci… Idanunsu suka haɗu Sai ya yi wani ƙaramin murmushi mai cike da takaici “But… have a nice day.” Ya juya ya fara tafiya. Cafeteria gaba ɗaya ta yi tsit. Har sai da ya fita. Firdausi ta kalli Zahra “Baby…” Aasiya ta kasa magana. Suhaima ta haɗe gira Saudat kuwa ta kalli ƙofar da ya fita, sannan ta sake kallon Zahra. Wasu ɗaliban da ke kusa suka fara raɗe-raɗi. “Wallahi bai yi mata komai ba.” “Jakar ta zai faɗi ne ya tare ta.” “Amma marin nan ya yi zafi.” “Poor guy…” Zahra ta ji kalamansu. Ba ta ce uffan ba “Ina waje, if you’re done, sai ku same ni” Ba tare da ta kalli kowa ba, ta gyara jakarta ta fita daga cafeteria Ƙawayenta suka mike suma, suka bi bayanta cikin shiru. Kowa na jin cewa… Wannan karon, abin da ya faru ya fi kowanne rikitarwa Chapter 55 Tun daga fitowarsu daga cafeteria har zuwa School Villa… Motar ta yi shiru fiye da yadda suka saba, ba waƙa, ba hira, ba dariya. Zahra tana tuƙi, idanunta na kan hanya hankali kwance, Firdausi na kallonta lokaci zuwa lokaci Saudat kuwa tunanin abin da ya faru ya hana ta cewa komai. Da suka isa gida, kowacce ta shiga ta sauya kaya, bayan ɗan lokaci suka haɗu a falo. Shirun ya sake mamaye wurin. A ƙarshe Firdausi ta sauke numfashi “Baby… can I say something?” Zahra na scrolling wayarta “Go ahead.” Firdausi ta haɗa yatsunta “I don’t think what happened today was fair” Zahra ta ɗago kai “What do you mean?” “Wallahi… guy ɗin bai cancanci marin nan ba.” Shiru ne ya sake ratsa parlourn Aasiya ta gyada kai “I agree.” “Na ga komai da idona. Jakar ki ce za ta faɗi, shi kuma ya tare ta.” Suhaima ta ce “Ko da ba kya sonsa… at least ya kamata ki saurare shi ko da na minti ɗaya ne.” Zahra ta ɗan yi dariyar raini “So… yanzu ni ce na zama mara gaskiya?” Saudat ta yi saurin girgiza kai “A’a, ba haka muke nufi ba.” “Muna nufin… maybe kin ɗan yi saurin yanke hukunci cikin fushi ne.” Zahra ta jingina bayanta da kujera “Interesting” Firdausi ta ci gaba “Baby, tun ranar farko kina treating him harshly. Amma wallahi har yanzu ban ga ya taɓa yi miki rashin mutunci ba, Ina laifin Wanda yake sonka?” “Rashin mutunci?” Zahra ta maimaita. “Riƙe min jaka ba tare da permission ba ba rashin mutunci ba ne?” Aasiya ta ce cikin nutsuwa “Da niyyar taimako ya yi, Zahra.” “Exactly,” Suhaima ta ƙara da cewa “Babu wani mugun intention a fuskarsa, ba dan zaki tafi bane ya rike ki” Zahra ta miƙe tsaye “Toh idan kun gama kare shi… ku je ku nemo shi mana.” “Maybe one of you should date him” “Since you all like him so much.” Firdausi ta miƙe itama “Baby! This is not funny, muna faɗa miƙe ne saboda muna son ki.” “Muna son ki dinga giving people a chance kafin ki yanke musu hukunci” Zahra ta yi murmushi, amma murmushin mai cike da ma’ana “Oh… really?” “Toh daga yau ku daina shiga tsakanina da duk wanda ya shafe ni” “Because it’s my life.” Saudat ta ce cikin sanyin murya “Zahra… don’t say that, ai an zama ɗaya” Ta waiwaya ta kalli Saudat “Then don’t judge me.” Falon ya sake yin tsit, ba wanda ya ƙara magana. Zahra ta ɗauki wayarta daga kan center table, ta juya ta nufi ɗakinsu Firdausi ta kira sunanta “Baby…” Ko waiwayowa ba ta yi ba ta shiga ɗaki, ta rufe ƙofar da ƙarfi Kaf! Shiru ya sake mamaye falon. Firdausi ta zauna tana dafe goshinta “Mun ɓata mata rai.” Aasiya ta sauke numfashi. “Amma dole ne wani ya gaya mata gaskiya.” Suhaima ta kalli ƙofar ɗakin “Ban taɓa ganin ta haka ba.” Saudat kuwa ta yi shiru.. A zuciyarta tana addu’a kawai, ta san Zahra tana da zuciya mai kyau… Amma kuma ta san idan ta fara yin fushi, tana ɗaukar lokaci kafin ta sauko daga kai…. Tun bayan misunderstanding ɗin da ya faru a falo… Zahra ba ta sake fitowa ba, ta zauna a ɗaki tana scrolling a wayarta, amma ko ita kanta ta san ba ta maida hankali kan abin da take yi ba. Can wajen Maghrib, Firdausi ta buga ƙofar “Baby…” Shiru…. Ta sake bugawa “Abinci ya kusa haɗuwa.” Daga ciki Zahra tayi magana cikin zuciya “I’m not hungry.” Firdausi ta tsaya na ɗan lokaci kafin ta ce “Okay… idan kin canza ra’ayi, ki fito ki ci, dan ko a cafeteria baki ci abinci ba” Daga haka ta bar bakin kofar Can bayan magrib Kitchen ya cika da ƙamshin abincin da Firdausi ta girka. Kowacce ta zauna a parlon a spot ɗinsa, sai spot din Zahra ce kaɗai babu kowa Saudat ta kalli wajen “Ba za ta fito ba?” Firdausi ta girgiza kai “Na mata magana… ta ce ba ta jin yunwa.” Aasiya ta sauke numfashi “Ta yi fushi sosai.” Suhaima ta ce “Mu ba ta lokaci kawai.” Suka ci abincinsu cikin nutsuwa, ba irin dariyar da aka saba ba Bayan sun gama… Zahra ta buɗe ƙofar ɗakin a hankali ta fito bayan ta tabbatar sun gama cin abinci Ta wuce kitchen ba tare da ta ce wa kowa komai ba, ta buɗe cupboard Ta ɗauko corn flakes, ta zuba a wani white ceramic bowl Ta ɗauko chilled milk daga fridge ta zuba a kai. Ta dawo parlorn ta zauna, ta riƙe spoon ɗin tana ci a hankali Ba ta kalli kowa ba, suma cikinsu babu wanda ya yi attempting mata magana Da ta gama… ta wuce kitchen din, ta wanke bowl ɗin da kanta, ta mayar da komai inda ya dace Sannan ta koma ɗaki A falo kuwa… Firdausi, Aasiya, Suhaima da Saudat suna zaune suna hira. Wani lokaci har su yi dariya Amma duk lokacin da suka kalli hanyar ɗakin Zahr ko kuma suka tuna da ita Sai hirar ta yi sanyi. Firdausi ta ce a hankali “Wallahi ban saba ganin ta haka ba, Duk abun ya dame ni” Saudat ta ce “Ni ma.” A ɗaki… Zahra ta kwanta jingine da pillow, ta shiga Instagram. Notifications nata ba su da ƙidaya. Verified pages, Fans, Friends, Messages. Ta riƙa replying kaɗan-kaɗan, Can ta buɗe class group nasu na WhatsApp Nan ta ga wani message pinned 📌 Assignment Due: Tuesday, 8:00 AM. Ta zaro ido “Oh shoot…” Ta tuna Ashe an basu assignment Da sauri ta miƙe ta nufi bakin kofar Sbd kullum idan akwai assignment, Firdausi ce ke tattara su ta kammala musu kafin kowacce ta yi editing nata Ta kai hannunta bakin handle din, sai ta tsaya Ta tuna abin da ya faru da yamma, ta ja hannunta a hankali “No… it’s okay.” Ta koma kan gado ta zauna, ta buɗe contact list, ta nemo sunan Class Rep, ta danna call. Bai daɗe ba ya ɗaga “Hello, Zahra.” “Hi.” “Hope you’re good?” “Yeah… Alhamdulillah.” “Actually, I need today’s assignment.” Zahra ta faɗa “Oh, that’s easy. Ina da soft copy.” “Send it to me, please.” Shiru na daƙiƙa biyu ya biyu baya Sai ya ce cikin wata murya mai nuna alamun ɗan jin daɗi, “Or…” “Since you’re Zahra…” “Just send me your registration number.” Ta haɗe gira “My registration number?” “Yeah.” “I’ll do the assignment for you.” “You don’t have to stress yourself.” Zahra ta ɗan yi shiru sai ta ɗan yi murmushi “Seriously?” “Of course.” “You’re my course mate.” “And… I’d be happy to help.” Ta ɗan yi tunani “Okay… thank you.” Tana kashe wayan ta tura masa registration number ɗinta ta WhatsApp. Nan take blue tick ya bayyana, sai ya aiko mata da reply. “Done. Give me a few minutes.” Zahra ta jingina da headboard ɗin gadonta, ta ajiye wayar a gefe. A karo na farko tun bayan faɗar da suka yi… ta ji ɗan sauƙi a ranta…. Daren ya ƙara yin tsit… Bayan kowa ya gama abin da yake yi, ɗaya bayan ɗaya suka fara komawa ɗakin Aasiya ta ɗauki blanket ɗinta tana miƙewa “I’m sleepy.” Suhaima ta yi hamma “Same here.” Saudat ta ɗauki hijabinta ta naɗe ta a hankali kafin ta ɗora kan sofa. Firdausi ta kalli Zahra, wacce har yanzu take jingine da headboard tana danna wayarta. Ta yi niyyar cewa wani abu sai kuma ta fasa. “Good night, girls.” “Good night,” Aasiya, Suhaima da Saudat suka amsa a tare. Zahra ba ta ɗago kai ba sai dai ta ce cikin sanyin murya, “Good night.” Kowacce ta kwanta a wajenta. Na wasu sakanni… ba wanda ya sake magana Firdausi ta miƙa hannu ta kashe babban hasken ɗakin. Sai hasken bedside lamp kaɗai ya rage, Zahra ta ɗan jima tana kallon ceiling.. sai ta miƙa hannu. Click. Bed lamp ɗin ma ya mutu, duhu ya mamaye ɗakin. Aka fara jin ƙarar AC kawai da numfashin waɗanda bacci ya fara ɗaukarsu. Duk bacci ya ɗauke su a haka… The following day… Ƙarar alarm ta fara tashi da ƙarfe hudu na safe Firdausi ce ta fara buɗe ido, ta miƙe ta kashe alarm ɗin kafin ya tada sauran mutane Sai dai kafin ta juya… ta hangi Zahra tuni ta tashi Tana zaune bakin gadonta, ta riga ta yi alwala, hijabinta a hannunta, tana shirin fita sallar Asuba a masallacin cikin villan Firdausi ta ɗan yi mamaki “Baby… kin riga mu tashi?” Zahra ta ɗan kalleta “Yeah, Ina shirin tashin ku knn” Muryarta a sanyaye take, ba kamar kullum ba, ta saka hijabinta “Na tafi masallaci, a can zanyi sallah Yau” Ba tare da ta jira amsa ba, ta buɗe ƙofar ɗakin ta fita. Firdausi ta bita da kallo, ta sauke numfashi “Maybe… yau za ta sauko daga fushin.” Sai kuma ta juya Tana kallon masu bacci ta yi saurin tashi “Girls… wake up.” Aasiya ta buɗe ido a hankali “Already? It’s Fajr?” Suhaima da Saudat ma suka miƙe, kowacce ta ɗauki hijabinta. Bayan sun yi alwala, suka nufi ƙaramin masallacin da ke cikin School Villa tare suma Garin ta yi tsit, Iskar safiya na kaɗa bishiyoyin da ke cikin estate. Ɗalibai kaɗan ne ke tafiya zuwa masallaci Bayan sun idar da sallah, suka dawo gida. Zahra ta shiga kitchen ta fara haɗa coffee Firdausi ta tsaya bakin ƙofa tana kallonta “Need help?” Zahra ta ɗan juyo “No, I’m fine” Ba ta ƙara cewa komai ba bayan haka Firdausi ta fahimci har yanzu fushin bai gama sauka ba, ta juya ta bar kitchen Cikin mintuna talatin… Kowacce ta yi wanka ta shirya Aasiya da Suhaima suna gaban mirror suna gyara fuskokinsu Saudat na saka wristwatch ɗin da Zahra ta taɓa ba ta kyauta. Firdausi ta fito cikin navy blue abaya “Girls… let’s move.” Zahra ta ɗauki key ɗin motarta daga kan dining table “Come on.” Babu surutu kamar yadda aka saba, suka nufi inda motar take Zahra ta buɗe motar, kowacce ta shiga Motar ya yi ƙara bayan ta kunna, ta fita daga School Villa A hanya… Morning rush ya fara sbd weekdays ne, Motoci, Napep, Students na tafiya zuwa lectures. Firdausi ta kunna rediyon motar ganin yadda motar yayi wani shiru An ɗan yi shiru kafin announcer ya fara gabatar da labaran safe. Sai kwatsam… Wayar Zahra da ke haɗe da Bluetooth ta fara ringing. Screen ɗin motar ya haska Unknown Number. Firdausi ta ɗan kalleta “Again?” Zahra ta haɗe fuska, ta danna Decline. Bai wuce daƙiƙu goma ba… Wayar ta sake ringing Unknown Number. Aasiya ta ce “Maybe it’s important.” “No” Ta sake katse kiran. Karo na uku… Sai ya sake shigowa Wannan karon Saudat ta ce cikin nutsuwa “Baby… try ki ɗaga mana. Wataƙila ba shi ba ne” Zahra ta sauke numfashi, ta danna Accept tare da saka speaker “Hello?” Shiru ne da farkon sai can wata nutsattsiyar murya ta fito “Good morning, Miss Zahra.” Ta haɗe gira “Who’s this?” “Someone who has been trying to apologize.” Nan take ta gane muryarsa, shi ne dai, wannan saurayin nan Ba tare da ta ba shi damar ƙara magana ba… ta katse kiran Ta kashe Bluetooth gaba ɗaya.. Motar ta sake yin shiru Firdausi ta ce a hankali, “Wallahi… wannan guy ɗin bai da sauƙin haƙura” Zahra ta ci gaba da tuƙi Fuskarta ba ta nuna komai ba, dan ma is hardly kace akwai abun dake damunta Amma a cikin zuciyarta… tambaya ɗaya ce kawai ke yawo ‘Ta yaya ya samu number ɗina?’ Ta San numbernta isn’t visible to everyone, a department dinsu ma ba wanda yake da shi Da suka isa university, parking lot ya riga ya cika da motoci Zahra ta faka motarta kamar yadda ta saba Ta ɗauki jakarta, ta fito cikin nutsuwa. Elegant black abaya ce a jikinta, premium silk veil da matching handbag. Tafiyarta kaɗai na ɗaukar hankali Idanunta na gaba, bata waiwaya straight to her front take kallo Suna tafiya zuwa faculty… can nesa kaɗan… Sai ga wani saurayi, shi ne, sanye cikin light blue shirt da black trousers Ya tsaya gefen pathway kamar wanda yake jiran wani. Da ya hango Zahra… Sai ya ɗan gyara tsayuwarsa Idanunsu suka kusa haɗuwa.. amma… Zahra ko kallonsa ba ta yi ba Ta wuce a gabansa kamar iska, ba ta nuna ma ta san yana wurin ba. Shi kuwa… kamar ya biyo ta, amma sai ya kasa biyo bayanta din Sai kawai ya bita da kallo, wani ƙaramin murmushi mai cike da haƙuri ya bayyana a fuskars, ya juya ya nufi wani building daban Da suka shiga lecture hall, lecturer bai iso ba tukuna. Students na ta hira, wasu na duba notes, wasu kuma na ta dariya Su biyar suka zauna a baya Firdausi ta fara buɗe notebook ɗinta, Aasiya na duba assignment. Sai Suhaima ta juya ta kalli Zahra “I’m sorry to say this…” Zahra ta ɗago kai “What?” “Please… ki saurare shi ko sau ɗaya.” Zahra ta haɗe gira “Excuse me?” Suhaima ta ɗan yi murmushi “Besides… guy ɗin kyakkyawa ne.” Firdausi ta yi shiru tana jiran amsar Zahra. Aasiya ta ɗan sosa kai Saudat kuma ta sunkuyar da kai. Zahra ta yi wata ƙaramar dariya ta raini “Ina ruwa na da kyawunsa?” Ta jingina da kujerarta “Kyau ɗin nasa za mu ci idan ya aure ni?” Suhaima ta yi saurin cewa “Ba haka nake nufi ba…” “A’a, bari na gama.” Zahra ta ɗan gyara zamanta. “Ban san me yasa kike magana haka ba, Suhaima.” “Lemme tell you something.” “I’m not his mate… by all means.” “Tsaurin ido ne ma da shi har ya zo ya tare ni yana cewa yana sona.” Ta ɗan yi shiru kafin ta ci gaba. “Baya ganin ko manyan influencers da celebrities da suke flooding my DMs ban ba su kulawa ba?” “Me ya sa yake tunanin shi zai zo kawai ya tsaya gabana, then I’ll suddenly fall for him?” Firdausi ta kalli Zahra “Baby… love isn’t about status.” Zahra ta ɗaga hannu “Please… not again.” “Ni bana son wannan discussion.” A dai-dai lokacin… Lecturer ya shigo, duk hirar ta tsaya Amma Suhaima ta ci gaba da kallon Zahra cikin tausayi, a zuciyarta tana jin cewa… Ba girman kai ba ne ke hana Zahra sauraron saurayin. Akwai wani abu da Zahra ke ɓoyewa, wanda har yanzu babu wanda ya fahimta. Chapter 56 Lecture ɗin ya ɗauki kusan awa biyu.. Ko da lecturer yake bayani, Zahra na rubutu cikin nutsuwa kamar yadda ta saba. Duk da haka, Firdausi ta lura cewa yau ba ta yin tsokaci ko tambayoyi kamar yadda take yi a wasu lokutan. Da aka tashi… Students suka fara fita ɗaya bayan ɗaya “Next class ɗinmu fa?” Aasiya ta tambaya Firdausi ta duba timetable a wayarta “Forty-five minutes break.” “Perfect!” Suhaima ta ce. “Mu je garden mu zauna.” Dukkansu suka amince. Faculty garden ya cika da ɗalibai, kamar kullum dama baya rasa mutane, wasu na karatu, wasu na ɗaukar pictures, wasu kuma na hira Su biyar suka zauna ƙarƙashin wata babbar bishiya Firdausi ta fito da snacks daga jakarta “Who wants chips?” “Me!” Aasiya ta ɗaga hannu. Dariya suka yi. Saudat na shan ruwa cikin nutsuwa Zahra kuwa ta cire sunglasses ɗinta ta ɗora kan gashinta, tana scrolling Instagram. Can… Firdausi ta taɓa hannunta “Baby…” “Hm?” “Don’t look now.” Zahra ta ɗaga gira “What again?” Firdausi ta yi murmushi “Guess who’s coming.” Zahra ta sauke wayarta a hankali, ta ɗaga kai. Can daga nesa… Saurayin nan ne, amma wannan karon ba shi kaɗai ba Yana tare da wasu abokansa biyu, suna ta hira suna dariya Da suka iso kusa da garden ɗin… Ɗaya daga cikin abokansa ya taɓa kafaɗarsa yana nuna inda Zahra take Ya waiwayo.Idanunsa suka sauka kanta. Na ɗan lokaci… ya tsaya. Sai dai abin mamaki wannan karon, bai ƙaraso ba, bai yi ƙoƙarin katse hirarsu ba Sai kawai ya ɗan gyada kai cikin girmamawa, kamar sallama daga nesa Sannan ya ci gaba da tafiya tare da abokansa. Suhaima ta bishi da kallo “See? Yau kuma ko karasowa bai yi ba” Firdausi ta gyada kai “Maybe ya fara respecting your boundaries.” Zahra ta mayar da idanunta kan wayarta “Good! He learned frm his mistakes” Shi kaɗai ta faɗa Amma kafin ya ɓace daga ganinsu… suka kalli ɗaya daga cikin abokansa ya yi masa dariya yana bugun kafaɗarsa Saurayin ya girgiza kai kawai yana murmushi, alamar har yanzu ba su daina zolayarsa ba Saudat ta kalli Zahra “Kin ga? Ko da ya gan ki, bai zo ya dame ki ba.” Zahra ta kashe screen ɗin wayarta ta miƙe tsaye, dan bata bukatar wannan convo ɗin at all “Break is almost over! Let’s go” Ta ɗauki jakarta ta fara tafiya Sauran suka bi bayanta. Shi kuwa a can nesa, ashe tsayawa yayi, ya waiwayo sau ɗaya Ya hango Zahra tana tafiya cikin kwarjini kamar kullum. Sai ya yi murmushi a hankali ya faɗa wa kansa, “One day… ko da ba za ki so ni ba, za ki san ni da gaske nake” Ya juya ya ci gaba da tafiya Kwanaki suka ci gaba da ja.. a hankali… Yanayin da ke tsakanin Zahra da ƙawayenta ya fara komawa kamar da Ba wai ta dawo tsohuwar Zahra mai shagwaɓa ba… Amma ta daina ɗaukar komai a zuciya, suna dariya tare, suna cin abinci tare, suna zuwa lectures tare sai dai abu ɗaya ya canza… Zahra ta daina saka kanta a yawancin hirarrakin banza da suke yi Idan suna ta surutu… Ita sai ta yi murmushi kawai, ta dawo wata nonchalant lady ce Wani lokaci ma ta ɗaga kai daga wayarta ta ce, “You people are unbelievable.” Sai su yi dariya gaba ɗaya. Wata ranar Asabar… Kowacce na gudanar da abin da ya dace da ita. Firdausi na kitchen tana dafa lunch. Saudat na gyara parlour. Aasiya da Suhaima kuma na wanke kayan da aka ɓata Can daga kitchen… Sai aka ji muryar Firdausi. “Saudat!” Saudat ta fito “Yes?” “Ke kika gama vegetable seasoning ɗin nan baki faɗa ba?” Saudat ta haɗe gira “Ni kuma? Ai ke kika yi amfani da shi jiya” “No, ban yi ba.” “Wallahi kin yi.” “Saudat, don’t argue with me.” “Ni ma don’t accuse me of what I didn’t do.” Cikin ƴan daƙiƙu… Murya ta fara tashi sosai, don kamar zasu yi dambe ne “Always kina manta abubuwa!” Cewar Firdausi A mugun zuciye Saudat ta ce “Ni na manta ko ke?” “You always think you’re right!” “And you think everyone is wrong!” A falo… Zahra ta ɗago kai daga laptop ɗinta Ta kallesu kofar kitchen ɗin na wasu daƙiƙu Sannan ta miƙe ta karasa bakin kitchen ɗin ta ce cikin nutsuwar da ba a saba gani a wajenta ba, “Firdausi… enough” Ta juya ta kalli Saudat “You too.” “Ba seasoning ba ne zai sa ku ɗaga wa juna murya.” Firdausi ta yi shiru, Saudat ma ta sauke numfashi Aasiya ta zo ta tsaya tsakaninsu tana murmushi. “See?” “Wannan shi ne abin da nake ta faɗa muku.” “Ba zai yiwu mutane biyar su zauna gida ɗaya ba ba tare da misunderstanding ba.” “Kowa yana da ra’ayinsa.” “Kowa yana da halinsa.” “Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne…” “Idan wani ya ɓata miki rai, ki faɗa masa abin da ya yi cikin lumana” “Kar ki tara shi a zuciya.” “Kar kuma ƙaramin abu ya zama babban faɗa.” Ta kalli Firdausi “Ko da ya kare tunda Duk mu muka amfana da shi bai kamata ki ce haka ba” Firdausi ta gyada kai Ta juya ta kalli Saudat. “I’m sorry… maybe na yi saurin fushi.” Saudat ta yi murmushi “Ni ma I’m sorry.” Firdausi ta miƙa mata hannu, Saudat ta kama. Duk suka yi dariya. Zahra ta girgiza kai tana murmushi “You people can fight for Africa.” Firdausi ta nuna ta da yatsa “Ke dai ki yi shiru amma waya kai ki fushi? Ba ke ce kika taɓa marin mutum a cafeteria ba?” Dariya ta kaure a falon. Har Zahra sai da ta rufe fuskarta tana dariya “Firdausi!” Da yamma. Aasiya na shirin fara girki. Ta buɗe cupboard ta an leƙa. Sannan ta ɗaga murya “Girls!” “Kamar vegetable oil ya ƙare.” Zahra na zaune a sofa tana karanta wani article a iPad ɗinta. Ba tare da ta ɗaga kai ba, ta zaro ATM card daga wallet ɗinta. Ta miƙa wa Aasiya “Take this.” “If you’re going out, just buy it.” Aasiya ta karɓa “Baby, how much should I spend?” Zahra ta ɗan yi murmushi “Whatever we need.” Ta ɗan ɗaga kai ta kalli dukkansu “And please… tun da duk kun san PIN ɗin card ɗin…” “Duk wani household need ba sai kun tambaye ni ba.” “Idan abu ya ƙare, ku saya.” “It’s our home.” “Not mine alone.” Firdausi ta yi murmushi. “Allah ya ƙara arziki.” Saudat ta ce “Ameen.” Suhaima ta riƙe card ɗin tana kallon Zahra “Wallahi… ba ki taɓa sa mu jin kamar baƙi a gidan nan ba.” Zahra ta yi murmushi cikin sauƙi “You’re not guests.” “You’re my family.” Asabar ce. Bayan sun gama lectures na ranar, Zahra ta fito daga lecture hall tana miƙa hannayenta sama kamar wacce aka sauke wa wani babban nauyi. “Oh my God… I’m officially exhausted.” Firdausi ta yi dariya. “Ke ma kin ji gajiyar?” “Today was too much.” Aasiya ta rufe littafinta “So… what’s the plan?” Suhaima ta ɗaga gira tana kallon Zahra. “Baby, don’t tell me we’re going straight home.” Zahra ta tsaya tana kallonsu na ɗan lokaci kafin murmushi ya bayyana a fuskarta. “You know what?” “What?” Duk suka tambaya a tare. “I think we deserve a break.” Firdausi ta yi tsalle “Yeeeees!” “Let’s go somewhere.” Saudat ta ce da sauri “Wallahi ni gida zan koma. Na gaji sosai.” Zahra ta tunkuɗe kafaɗarta tana murmushi. “No excuses.” “Today is on me.” “Shopping?” Aasiya ta tambaya. Ta amsa mata “Shopping.” “Food.” “Ice cream?” “Anything.” Firdausi ta yi ihu “I love this rich friend of ours!” Dariya ta kaure a tsakaninsu, daga haka Duk suka wuce inda zahra tayi parking mota Zahra ta buɗe motarta da remote. Beep! Headlights ɗin motar suka yi flashing. “Everybody in.” Suka shiga. Firdausi ta zauna a front seat Aasiya, Saudat da Suhaima kuma a baya. Da suka ɗaura seat belts… Zahra ta kunna motar. Suna Jin 30% of gajiyarsu ya tafi saboda shopping din da zasu Soft English R&B ya fara fita daga speakers. AC mai sanyi ya mamaye motar. Suka kama hanya A cikin motar babu wanda ya rasa abin faɗi. Firdausi na ba su labarin wani lecturer da ya kasa kunna projector tsawon minti goma. Aasiya da Suhaima suka riƙa dariya har hawaye. Saudat kuwa sai girgiza kai take “You people are impossible.” Zahra ta yi murmushi tana tuƙi. A irin waɗannan lokutan ne take jin nutsuwa, babu hayaniya, babu family drama, babu Mummy, sai ƙawayenta kaɗai. Kusan mintuna ashirin bayan haka… Suka isa babban shopping mall Parking lot ɗin ya cika da motoci. Luxury SUVs, Sedans, Families, Students, Businessmen Da zarar Zahra ta fito daga motar… Kai tsaye idanun mutane suka dawo kanta Wasu suka fara raɗa-raɗi “Isn’t that Zahra?” “Wacce influencer ɗin nan?” “I swear she’s prettier in real life” Dama kullum zancen ɗaya kenan Firdausi ta yi dariya a hankali “Celebrity.” Zahra ta yi rolling eyes “Can we just go?” Suka shiga mall, da farko boutique Firdausi ta gwada handbags kusan guda shida. Suhaima ta dage sai Zahra ta gwada wani designer sunglasses. Aasiya tana ta duba skincare products. Saudat kuwa tana ta kallon prices tana girgiza kai. “Haba… wannan turaren price ɗinsa zai biya semester registration.” Duk suka yi dariya. Zahra ta ɗauki perfume ɗin “Pack it.” Saudat ta zaro ido “Baby!” “What?” “Kada ki saya saboda ni.” Zahra ta miƙa black card ɗinta. “Use this.” Cashier ta yi murmushi “Thank you, ma’am.” Daga nan suka wuce bookstore Zahra ta sayi novels guda huɗu. Firdausi ta ɗauki planner Suhaima kuwa ta sayi colorful sticky notes. Sai suka ƙarasa food court. Burgers, Pizza, Chicken, Milkshakes, Ice cream. Table ɗinsu ya cika da abinci Suhaima ta ɗaga spoon “Moment of silence for this beautiful meal.” Firdausi ta jefe ta da tissue “Drama queen.” Dariya ta sake cika wajen. Har Zahra da ba ta cika dariya sosai ba.. sai data yi Bayan sun gama cin abinci… Suka yi ɗan yawo, suka ɗauki pictures, selfies, videos. Har Firdausi ta tilasta Zahra ta yi TikTok trend da su “No way.” Inji Zahra “Please!” “Never.” A ƙarshe dai suka lallashe ta. Video ɗin ya fito da kyau sosai haka ta dinga posting ɗinsu Karfe shida saura kaɗan Aasiya ta kalli agogo “We should head home oo, traffic will start” “True.” Suka nufi parking lot. Ba tare da sun sani ba… a can ɗaya gefen parking ɗin… Wata black Hilux mai tinted glass tana tsaye tun kafin su fito, mutane biyu ne a ciki, fuskokinsu ba su bayyana ba, Driver ya gyara mirror ɗinsa, Idanunsa suka sauka kan Zahra. Ta buɗe motarta, ƙawayenta suka shiga, ta tada motar, ta fice daga parking lot cikin nutsuwa Mutumin da ke gefen driver ya zaro waya Ya danna wani number. Da aka ɗaga… ya ce cikin sanyin murya “They’re moving.” Daga ɗaya ɓangaren aka amsa “Good! Don’t lose them.” “Follow them…” “But don’t let the girls notice.” Call ɗin ya katse, Driver ya kunna motar, Hilux ɗin ta fara tafiya a hankali… tana bin motar Zahra Motar Zahra ta fita daga parking lot cikin nutsuwa, ba tare data kula da motar dake bayanta ba A cikin motar kuwa… Firdausi ce ta haɗa Bluetooth da wayarta Nan take wata waƙar Khaligraph Jones ft. Nyashinski ta fara tashi. Suhaima ta yi ihu “Oh my God! This is my jam!” Ta fara rawa a zaunen da take Aasiya ta buga dashboard da tafin hannunta tana bin beat ɗin. Har Saudat da ba ta cika shiga irin waɗannan abubuwan ba, sai da ta yi murmushi. Zahra ta girgiza kai tana dariya “You people are crazy.” Firdausi ta juya ta kalleta “Baby, at least smile.” “I’m smiling.” Zahra ta ce Firdausi ta taɓe baki “No, that’s not a smile.” “Kawai kina showing teeth.” Duk suka sake barkewa da dariya. A can baya… Black Hilux ɗin na binsu, ba ta matsowa kusa ba, ba ta kuma yin nisa ba, kawai tana maintaining distance ɗinsu dan kar su fahimta Sai dai duk inda Zahra ta juya… Nan motar ma take yi Mutumin da ke seat na gaba ya ce “Keep your distance.” Driver ya gyada kai “She must not suspect anything.” Mintuna goma suka yi suna tafiya, traffic ya fara yawa, Motoci na shigowa da fita ga uban Napep banda Babur da suka yi yawa Sai wata trailer ta shigo tsakaninsu. Na ɗan lokaci… Hilux ɗin ya ɓace daga ganin Zahra A cikin motarsu Firdausi ta ce “Baby, let’s stop somewhere mu sayi yoghurt, kinga akwai white rice sai mu haɗa” Zahra ta girgiza kai “Tomorrow.” “Please.” Firdausi ta ce “No.” Suhaima ta haɗa baki “Wai ke ba kya taɓa changing your mind ne?” “No.” Zahra ta kuma fada Aasiya ta yi dariya “Stubborn rich kid.” Zahra ta nuna ta. “I heard that.” Da suka wuce wani traffic light… Trailer ɗin ta kauce, Hilux ɗin ya sake bayyana. A wannan karon… Ya fi kusa Saudat ce ta fara lura, ta ɗan kalli side mirror. Sai ta sake kallon gaba. Bayan wasu daƙiƙu… ta sake kallon mirror Hilux ɗin na nan… ta yi shiru. Ta ce wa kanta “Coincidence ne.” Suka sake wucewa wani roundabout Zahra ta juya hagu Hilux ɗin ma ya juya hagu. Saudat ta sake kallon mirror. Gabanta ya fara faɗuwa. Ba ta ce komai ba, ta ci gaba da lura Wani speed breaker ya sa Zahra rage gudu. Hilux ɗin ma ya rage gudu. Da Zahra ta ƙara speed… Shi ma ya ƙara. Saudat ta haɗe gira, a hankali ta taɓa hannun Aasiya. “Aasiya…” “Hmm?” “Please… Ki duba side mirror.” Aasiya ta ɗan waiga “Me zan gani?” “Waccan black Hilux.” Aasiya ta kalla “Na gani.” “Me ya faru?” “Ki ci gaba da kallonta.” Aasiya ba ta fahimta ba. Sai dai bayan kusan minti biyu ta lura. Hilux ɗin ba ya wucewa, ba ya kaucewa, yana binsu ne kawai. Ta haɗe gira, ta sake kallon Zahra. Sai kuma ta yi shiru Ba ta son ta tayar musu da hankali ba tare da tabbaci ba. A gaba… Zahra har yanzu tana tuƙi cikin nutsuwa. Firdausi na ta hira Suhaima na dariya. Ba su san abin da ke faruwa ba. Sai Saudat ta sake kallon mirror. Hilux ɗin har yanzu na nan. Wannan karon… Ta ji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, ta haɗiye yawu Cikin ƙaramar murya da ba kowa ya ji ba… Ta ce “…Baby…” Zahra ba ta juyo ba ta ce “Hmm?” Saudat ta ɗan yi shiru, ta sake kallon mirror. Sannan ta ce a hankali… “I think…” “…akwai wata mota da ke bin mu.” Chapter 57 Kalaman Saudat suka sa motar ta yi shiru na ɗan lokaci Waƙar da ke tashi daga speaker har yanzu tana ci gaba da tashi amma babu wanda yake saurara Zahra ta ɗan ɗaga idanunta zuwa rear-view mirror. Black Hilux, tinted glass! Ba ta iya ganin waɗanda ke ciki. Ta sake mayar da hankalinta kan hanya “Maybe coincidence.” Saudat ta girgiza kai “I don’t think so.” Firdausi ta ɗan juya tana kallon baya ta window. “Where?” “Can…” Ta nuna mata. Firdausi ta leƙa “Oh…” sai kuma ta yi shiru. “Hmm…” Suhaima ta ce “Me kuke gani ne?” Aasiya ta amsa cikin sanyin murya “Wata Hilux.” “Shi me?” Suhaima ta waiwayo ta kalla. “Toh ai mota ce kawai.” Saudat ta ce “Ki ci gaba da kallonta.” Suka isa wani junction, akwai hanyoyi uku. Ba wannan ce hanyar da suka saba bi ba. Zahra ta juya zuwa dama “Baby…” Firdausi ta yi mamaki ta ce “Wannan ba hanyarmu ba ce.” “I know.” Kawai Zahra ta faɗa “Why?” Zahra ba ta amsa ba sai ta ci gaba da tuƙinta kawai A cikin mirror kamar yadda suke kallo… Hilux ɗin ma ta juya zuwa dama, daidai bayansu yanzu kam… Ko Suhaima ta daina magana “Ya biyo mu…” Ta faɗa cikin murya mai rauni. Babu wanda ya yi magana. Zahra ta sake gwadawa… ta shiga wani ƙaramin layi da ma ba hanyarsu bace, ba ta taɓa ma bin layin ba tunda take a kaduna Layin ya yi tsit.. Gidaje kaɗan ne a unguwar. Hilux ɗin… har yanzu na biye da su. Firdausi ta rufe fuska “Ya Allah…” Aasiya ta riƙe handbag ɗinta da ƙarfi. Saudat kuwa ta fara karanta Ayatul Kursiyyu cikin ƙasa-ƙasa. Suhaima ta ce cikin firgici “Baby… they’re following us.” Zahra ta yi ƙoƙarin ta danne tashin hankalin da ke neman bayyana a fuskarta. “No panic.” Ta faɗa a hankali “Nobody panic.” Amma zuciyarta… da sauri take bugawa. A cikin Hilux… Drivern ya yi murmushi “She knows.” Mutumin da ke gefensa ya ce, “Good.” “Let’s keep pushing.” “Don’t get too close.” “Not yet.” Driver ya gyada kai Hilux ɗin ta ci gaba da binsu cikin distance da bai yi yawa ba. A motar Zahra… Firdausi ta zaro wayarta “Baby, should I call Ya Umar?” “Not yet.” Zahra ta ce “Police?” “Not yet.” “Why?” Firdausi ta tambaya “Because I’m still hoping I’m wrong.” Cewar Zahra kenan Sai ta sake kallon mirror Hilux ɗin na nan… ba ta rage gudu ba, ba ta wuce su kuma ba Kawai… ita dai tana binsu ne Numfashin Zahra ya ɗan yi nauyi, ta riƙe steering wheel da ƙarfi. A karon farko… ta fara jin tsoro. Ba don kanta ba… sai don ’yan matan da ke zaune tare da ita. Ta haɗiye yawu. Sannan ta faɗi cikin murya mai cike da ƙwarin guiwa, duk da cewa zuciyarta ba haka take ji ba. “Girls…” “If anything happens…” “Just do exactly what I tell you.” Ba wanda ya yi magana! Kowacce ta fahimci abu ɗaya… Wannan ba coincidence ba ne. Shiru ya mamaye motar, sai ƙarar engine da bugun zuciyoyinsu da ke ƙaruwa. Zahra ta ɗan ƙara saurin motar, ba don gudu take son yi ba… Sai don ta sake gwada tabbacin abin da suke zargi. Da ta ƙara speed… Hilux ɗin ma ya ƙara. Firdausi ta lumshe ido “…Ya biyo mu fahh” Wannan karon babu wanda ya ƙara cewa coincidence ne, kowa ya gani da idanunsa. Suna fita a wannan layin Zahra ta ɗauki wani roundabout. Maimakon ta bi hanyar gida… Sai ta zagaya roundabout ɗin sau biyu Ta sake dawowa daidai inda ta fito. Aasiya ta kalleta da mamaki “Baby… me kike yi?” “Testing.” Ta faɗa ba tare da ta ɗauke idanunta daga hanya ba. Hilux ɗin… Shi ma ya zagaya roundabout ɗin kamar yarda itama tayi sau biyun kuma daidai bayansu. Saudat ta riƙe hannun kujera da ƙarfi “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…” Ta fara maimaitawa a hankali. Suhaima kuwa idanunta suka cika da hawaye “Ya Allah…” Firdausi ta zaro wayarta cikin rawar hannu. “Baby, enough! I’m calling Ya Umar.” “Call him.” Wannan karon Zahra ba ta hana ta ba. Firdausi ta danna sunan Ya Umar❤️ Wayar ta fara ringing. Ring… Ring… Ring… Bai ɗaga ba, ta sake kira Har yanzu… No answer “He’s not picking!” Ta faɗa cikin tashin hankali. Zahra ta haɗiye yawu. “Kira Abbah.” Firdausi ta yi sauri ta koma kan sunan Abbah. Sai dai… Call Failed. “What?” Ta sake gwadawa Network Error “Ya Allah…” Aasiya ta karɓi wayarta “Let me try.” Ita ma ta kira. Amma sakamakon ɗaya ne. Network ya fara ɗauke-ɗaukewa A cikin Hilux… Drivern ya yi murmushi. “They’re trying to call someone.” Mutumin da ke gefensa ya ce “Keep driving.” “Don’t let them out of your sight.” Driver ya ƙara matsowa kusa. A karon farko… Nisan da ke tsakaninsu ya ragu sosai. Zahra ta hango hakan a mirror. Ta murɗa steering wheel cikin nutsuwa, ta hau babban titi mai cike da motoci. “Maybe idan muka shiga traffic za su daina.” Ta faɗa amma babu Wanda ya iya amsa mata Ga mamakinta Hilux ɗin ta ci gaba da binsu Firdausi ta fara kuka. “Baby…” “I don’t like this.” Suhaima ta riƙe hannun Saudat “Ki ci gaba da mana addu’a plsssss” Saudat kuwa ta fara karanta Ayatul Kursiyyu da Suratul Falaq da An-Nas cikin ƙasa-ƙasa. Aasiya ta ci gaba da danna wayarta “Still no network.” Zahra ta matse steering wheel har fararen yatsunta suka bayyana A zuciyarta tana ƙoƙarin ta kasance mai ƙarfi, amma tsoro ya fara shiganta Sai kwatsam… BWAAAAAH! Hilux ɗin ta yi horn mai ƙarfi. Ta ƙara matsowa kusa da bayan motarsu. Suhaima ta yi ihu “Ya Allah!” Firdausi ta waiwayo cikin firgici. “Baby!” Zahra ta ƙara saurin motar. Hilux ɗin ma ta ƙara. “Baby… faster!” Firdausi ta faɗa cikin rawar murya. “Please!” Zahra ba ta amsa ba. Idanunta suna kan hanya. Hannayenta kuwa sun matse steering wheel har jijiyoyin hannunta suka fito. Ta ƙara taka accelerator Engine ɗin motar ya yi wani irin ƙara. Sai dai… Hilux ɗin ba ta rage musu tazara ba. Ita ma ta ƙara gudu. A cikin motar… Babu mai magana. Sai Saudat da ke karanta Ayatul Kursiyyu cikin hawaye. Suhaima ta fara kuka “Ya Allah ka tsare mu…” Aasiya ta ci gaba da ƙoƙarin kiran Ya Umar. Har yanzu… No Service. Ta bugi dashboard da tafin hannunta “Damn it!” Firdausi ta ce, “Try WhatsApp call!” Ta gwada. Bai shiga ba! Network ɗin kamar ya ɓace gaba ɗaya. Gari kuwa ya fara yin duhu, saboda har Magrib ya wuce Hasken motocin da ke kan titi ne kaɗai ke haskaka hanyar. Traffic ya fara raguwa. Motoci sun yi kaɗan. Wannan ne abin da ya fi ba Zahra tsoro, ta fi son titi mai cike da jama’a ba irin wannan ba. Ta hango wani filling station a gaba, nan take ta juya zuwa ciki. Ta yi tunanin idan akwai mutane… Wataƙila Hilux ɗin za ta wuce. Amma… da ta shiga filling station… Hilux ɗin ma ta biyo bayanta, ta tsaya a gefe. Kamar tana jiran Zahra. Firdausi ta kalli motar da idanunta suka cika da tsoro. “They’re still here…” Zahra ta haɗiye yawu. Ba tare da ta kashe engine ba… Ta sake ficewa daga filling station. Hilux ɗin ma ta biyo ta A cikin Hilux… Driver ya yi murmushi. “She’s smart.” Mutumin da ke gefensa ya ce “But she’s getting tired.” Ya ɗauki waya, ya tura wani short message. “We’re close.” Sai ya kashe screen ɗin. A motar Zahra… ta sake kallon mirror. Hilux ɗin ta sake matsowa kusa, kusan babu tazara. Sai kwatsam… BANG! Hilux ɗin ta ɗan bugi bayan motarsu, ba bugu mai ƙarfi ba… Amma ya isa ya sa motar Zahra ta karkace kaɗan. Suhaima ta yi ihu. “Ya Allah!!” Saudat ta riƙe kujerar gabanta. Firdausi ta fashe da kuka “Baby!” Aasiya ta ce da ƙarfi, “Control it!” Zahra ta murɗa steering cikin sauri, da ƙyar ta dawo daidaiton motar. Numfashinta ya fara fita da sauri. A karon farko… tsoro ya bayyana ƙarara a fuskarta. Ta leƙa mirror. Hilux ɗin na sake shirin matsowa. Idan suka sake bugunsu… Wataƙila motar za ta fita daga hanya ko ma ta kwace daga hannun Zahra Sai kuma daga can nesa… Ta hango hasken wata mota mai ƙarfi tana tahowa daga gaba. Fararen fitilunta suka haskaka titin gaba ɗaya Motar tana ƙaratowa da wani irin gudu. Hasken fararen fitilun motar ya ƙara kusantowa. Zahra ta lumshe ido na ɗan daƙiƙa saboda tsananin hasken. “Who’s that?” Firdausi ta tambaya cikin tashin hankali. “Innalillahi wa’inna ilahir rajiun, Baby farautarmu suke yi, gashi kamar network baya son mu” Babu wanda ya iya tanka mata Motar tana ƙaratowa da gudu… Duk sun gama giving up kawai motar kansu zata hau… sai dai abin mamaki… Ba ta wuce su ba, ta yi wani irin juyawa cikin sauri Screeeeech! Ƙarar tayoyi ta cika titin. Motar wata ash-colour Range Rover ta tsaya a tsakiyar hanya. Kai tsaye… Tsakanin motar Zahra da Hilux ɗin. “Baby!” Aasiya ta yi ihu. “Brake!” Zahra ta taka birki da ƙarfi. Motarta ta tsaya da ƙyar, numfashinta na fita da sauri. Hilux ɗin da ke bayansu ma ta taka birki, amma saboda gudun da take yi… Ta kusa karo da Range Rover ɗin. Driver ɗin ya yi saurin kaucewa. Motocin biyu suka tsaya suna fuskantar juna. Shiru wajen ya ɗauka sai ƙarar engines kawai. Door ɗin Range Rover aka buɗe… wani dogon saurayi ya fito. Black jeans ke jikinsa sai wani, white shirt. Bai ko kalli Zahra ba, kai tsaye idanunsa suna kan mutanen Hilux. Firdausi ta ɗan matsa gaba. “…Shi ne.” Suhaima ta zaro ido “Guy ɗin nan?” Saudat ta haɗiye yawu “What?!…” Zahra kuwa… ta kasa cewa komai sbd saurayin nan ne data taɓa mari, Wanda tace bata kaunar sanin komai daga garesa Yana tsaye a gabansu… Kamar wanda ya shirya tsayawa shi kaɗai Mutumin ya ɗaga hannu alamar su tsaya Sai ya yi magana ba tare da ya waiwayo motar Zahra ba ya ce “Lock the doors” Muryarsa ta fito da ƙarfi “Don’t come out.” Zahra ta yi shiru, ba ta san dalilin da ya sa ba… Amma wannan karon… kawai samun kanta tayi da take bin umarninsa Ta danno central lock. Click. A cikin Hilux… Driver ya yi tsaki. “Damn.” Mutumin da ke gefensa ya ce, “I told you someone was watching.” Driver ya buɗe ƙofar motar. “Move him.” Saurayin ya ɗauki matakai biyu gaba, kwata-kwata bai nuna tsoro a tattare da shi ba Ya ce cikin sanyin murya, “Enough!!! Leave them.” Driver ɗin Hilux ya yi dariya “Who are you?” Saurayin ya amsa ba tare da ya ɗaga murya ba. “The wrong person to test tonight.” A cikin motarsu Zahra… Firdausi ta kalli Zahra da sauri “Baby…” “Waye shi?” Zahra idanunta suna kansa. A karo na farko… ba ta da amsar wannan tambayar Sai dai zuciyarta ta fara bugawa da wani irin sauri, ba wai saboda tsoro ba… saboda wani abu da ba ta taɓa ji ba. Mutumin da ta ɗauka matsala ne… Shi ne kaɗai yake tsaye tsakaninsu da matsalar da zasu faɗa Iskar dare ta kaɗa rigar saurayin. Har sannan yana tsaya cak yana jiran su fito daga Hilux ɗin, ba wata alamar tsoro tattare da shi. Sai nutsuwa mai ban mamaki. Driver ɗin Hilux ya fito ya rufe ƙofar da ƙarfi. Bang! Ɗayan mutumin ma ya fito daga bayan motar. Dukkansu sanye da baƙaƙen kaya, gashi suna cikin mask, Fuskokinsu cike da tsaurin ido kuma Firdausi ta saki wata ƙaramar ƙara “They’re three…” Saudat ta fara karanta Ayatul Kursiyyu da ƙarfi fiye da da. Aasiya kuwa ta ce “Ya Allah ka kawo mana ɗauki.” Saurayin ya ɗan juya kansa kaɗan, bai kalli Zahra ba Amma ya yi magana cikin murya mai ƙarfi. “Zahra!!!” Karo na farko da ta ji ya kira sunanta cikin irin wannan yanayin. Ta amsa a hankali “…Yes?” “Ki saurare ni da kyau.” Ta haɗiye yawu. “If I tell you to drive…” “Don’t look back.” “Just go.” Zahra ta yi shiru, gabanta ya faɗi “Amma kai fa?” Bai amsa tambayar ba, sai ya sake maida hankalinsa ga mutanen Driver ɗin Hilux ya yi dariya “Hero kenan? Ka matsa gefe.” Saurayin ya girgiza kai. “No.” “Last warning.” Mask Man ɗin ya ce “No.” Shiru ya biyo baya na wasu seconds Sai ɗaya daga cikin mutanen ya fara takowa zuwa gare shi. A hankali, kuma cikin isa. Saurayin ya tsaya a inda yake, ko motsi bai yi ba Zahra ta riƙe steering wheel, ba ta san dalilin da ya sa zuciyarta ke mata zafi ba Wannan mutumin… ba ta san ko sunansa ba, ba ta san komai game da shi ba. Amma yana tsaye ne yana haɗa rayuwarsa cikin haɗari… kuma for that matter saboda ita. Firdausi ta ce cikin kuka, “Baby… mu tafi.” Zahra ta girgiza kai “I can’t…” Suhaima ta ce, “Idan suka kama shi fa?” Babu wanda ya amsa mata Can nesa… Aka fara jin ƙarar wata mota tana tahowa da gudu Saurayin ya ɗan kalli gefen hanya, sai ya yi murmushi a hankali Mutanen Hilux ba su lura da komai ba, har sannan duk hankalinsu yana kansa Sai kuma… Hasken wata mota ya bayyana daga nesa… yana ƙaratowa da matuƙar gudu Vroooom! Ƙarar engine ɗinta ta mamaye wajen. Mutanen Hilux suka juya gaba ɗaya suna kallonta. Saurayin kuwa…ya ɗan yi murmushi Screeech! Wata baƙar Mercedes G-Class ta tsaya da ƙarfi a gefen hanya. Kafin kowa ya ankara… ƙofofinta suka buɗe, mutane huɗu sanye da baƙaƙen suit suka fito cikin sauri Driver ɗin Hilux ya haɗe gira “Move.” Ɗaya daga cikin sabbin mutanen ya ce cikin sanyin murya, “Kar Wanda yayi motsi” Nan take yanayin ya sauya. Mutanen Hilux suka fara kallon juna, kamar sun fahimci cewa abin zai iya fin ƙarfinsu. Saurayin ya juyo ya kalli Zahra, Idanunsu suka haɗu. Shi kuwa ya nuna mata da hannu. “Go.” Zahra ta girgiza kai. “No…” Ya ɗan ɗaga murya. “Zahra.” “Drive.” “This is not the right place.” Muryarsa ta sa ta yi shiru, ta ji kamar ba za ta iya musu ba. Firdausi ta riƙe hannunta “Baby… please.” Aasiya ta ce “Mu tafi.” Saudat kuwa tana ci gaba da addu’a. Da ƙyar… Zahra ta kunna motar, sai dai kafin ta motsa… Ta sauke glass ɗin window kaɗan. Ta kalli saurayin “…Who are you?” Saurayin ya yi murmushi kaɗan, murmushin farko da ta taɓa gani a fuskarsa. Sai ya ce cikin sanyin murya, “Not today.” “One day…” “You’ll know.” “Now go.” Zahra ta kunna motar, amma kafin ta taka accelerator PAAH! Ɗaya daga cikin mutanen Hilux ya ɗauko wani ƙarfen rod ya buga wa saurayin da ƙarfi. Ya ja da baya mataki biyu. Fuskarsa ta ɗan canza saboda zafin ciwon, amma bai fāɗi ba. “Dee!” ɗaya daga cikin mutanen G-Class ya yi ihu yana nufarsa. Saurayin ya ɗaga hannu ya hana shi. “I’m fine…” Amma bai gama rufe baki ba…Jini ya fara zuba daga gefen goshinsa. Zahra ta zaro ido “Oh my God!” Ba tare da ta sani ba ta buɗe ƙofar motar za ta fito. Firdausi ta riƙe hannunta. “Baby! No!” “He’s bleeding!” Ta faɗa cikin rawar murya. Saurayin ya ɗago ya kalleta. Ko da jini ke bin gefen fuskarsa… sai da ya yi mata murmushi kaɗan. “Go…” Muryarsa ta yi rauni. “Please…” “For your safety.” Idanun Zahra suka cika da ƙwalla, gabanta ya yi wani irin faɗuwa. Mutumin da ta taɓa mara… Mutumin da take masa kallon psycho… Yana zubar da jininsa saboda ita. “Please… don’t do this…” Ta furta a hankali. Sai ya girgiza kai. “Drive, Zahra.” “That’s all I want.” Mutanen G-Class suka kewaye shi suna kare shi. Zahra ta ji zuciyarta ta yi mata nauyi saboda wani mutum da ba ta taɓa ba muhimmanci ba yau shike risking life dinsa sbd ita Da ƙyar ta taka accelerator. Motar ta fara tafiya. Sai dai idanunta suna kan side mirror… Har sai da ta ga saurayin ya durƙusa a hankali, yana riƙe da kafadarsa mai jini… Kafin motar ta ɓace daga gare shi Yanzu wasan zai fara!!! Wanene Ibrahim Khalil? Wannan saurayin daya taimakawa Zahra wanene shi? Ya aka yi yasan Zahra Tana cikin tsananin Neman taimako? Waya saka su wannan aikin? Wanene Ahmad daya shigo rayuwar Zahra a karshen book 1? Toh ku gyara zamanku da kyau dan wasan yanzu zai fara!!!