*FAƊIME...💋🌸💕* _(Dangin Jinnu)_ ©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star *Dedicated to Salma Ahmad Isah (Candy)* *بسم الله الرحمن الرحيم* *A love & Laugh story that will capture your heart and soul.* 01 *ƘAUYEN KINKIBA, KADUNA STATE.* *GIDAN MALAM YAHAYA* Lami ta saki shewa a karo na barkatai zuciyarta cike fal da zallar farin ciki na ganin halin da Abokiyar zamanta Ummah ke ciki na tsananin azabar naƙuda, amma hakan bai sa Lami ta tausaya ma ta ba, sai ma ƙari sa shiga cikin Ɗakin da ya haɗu daidai gwargwado kuma kana gani kaga Ɗakin Amaryar da bata shekara ba, wani irin kallo take jefa wa Ummah dake tsakiyar Ɗakin tana faman nuƙurƙusu cikin halin naƙuda, kafin ta ƙari sa wurin da take tare da durƙusa wa a gabanta ta ce. “kin yi kaɗan kuma kin tafka Babban kuskure da har kika yarda kika kasance matsayin kishiya a gareni wannan azabtar ma kaɗan kika gani sauran a kan abin da zaki haifa zai koma domin nayi miki alƙawarin ɗaiɗaitawa da tarwatsa Rayuwar koma wane ne jaririn da zaki haifa tun da duk irin abin da nayi domin cikin ya zube tun yana ƙaraminsa amma abu ya gagara, to ya fito ya haɗu da uƙubata domin sai ya zama abin tausayi sanadiyyar uƙubar dana tanadar masa.” Tana gama maganar ta miƙe tsaye tare da kwance ɗaurin zanin jikinta ta ciro wani garin magani ba imani ba bare tausayi da ganin halin da Ummah ke ciki haka Lami ta daddage ta juye wannan garin maganin a gaban Ummah cike da rashin tausayi sannan ta koma gefe tana jiran sakamako tana kuma tuna maganar Malam Kasan komai da ya tabbatar ma ta da muddun ta zuba garin maganin a gaban Ummah lokacin da take tsaka da naƙuda to fa abin da zata haifa ba lallai ne ya zo a raye ba in ma ya rayu to fa zai kasance mara amfani domin zai kasance banbancinsa da matacce shi ne numfashi, baya da haka Ummah ba zata ƙara haihuwa ba tsawon Rayuwarta, duk wannan za su biyo baya ne muddun Lami ta aikata komai yadda ya umarce ta, a ka sin haka kuma to fa abin da zai biyo baya ba zai haifar musu ɗa mai ido ba daga shi har ita shi ya sa kafin ya bata maganin sai da ya zuba ma ta kakkausar gargaɗi na yadda zata yi amfani da maganin ta aiwatar da komai yadda ya buƙata.... Zuwa yanzu kuma da ta kammala sai ta ja gefe tare da naɗe hannu tana jiran tsammani. Ai kuwa a take a wurin naƙuda ta ƙara tsanani ga Ummah gadan-gadan haihuwa ta taho a daidai lokacin kuma mai gidansu wato malam Yahayah da ya fita kiran Ungozoma ya dawo afujajan yayin da Matar mahaifinsa kuma ungozoma ta garin take biye da shi ganin haka ya sa da sauri Lami ta ƙari sa wurin Ummah tanayi ma ta sannu tare da ƙoƙarin taimaka ma ta daidai lokacin da ungozoma Iya Suwai ta shigo Ɗakin ne kuma jaririya ta faɗo ai da azama ta ƙari sa ciki domin taimakawa da abin da ba'a rasa ba. Bayan wasu mintina jaririyar tana hannun Lami ta zuba ma ta ido tana ƙare ma ta kallo cike da takaici na ganin jaririyar tubarkallah ma sha Allah ƴar dumurmur da ita. Kamar almara haka Lami taga kamar Jaririyar ta gifta ma ta ido. Zaro ido Lami ta yi cikin son tabbatar da abin da idonta ya gani ita ma ta zaro ma Jaririyar nata idanunta, sai kawai taga jaririya ta fashe da dariya sai ga haƙora sun bayyana a bakin Jaririyar tashin hankali ya sa Lami ta kwaɗa ihu tare da miƙe wa tana ƙoƙarin jefar da jaririyar ta ranta a guje sai ji ta yi tamkar an saka gam an manne Jaririyar a hannunta haka kuma ta kasa tashi tsaye jikinta ne ya shiga rawa na tsananin tashin hankali da dabara ta waigo da dubanta saitin Jaririyar wai don taga ina Jaririyar take duba ai sai taga Jaririyar ta kafeta da manyan idanunta tana turo ma ta harshe waje. Muƙut! Lami ta haɗiye yawu na tsoro cike kuma da tashin hankali bata kai ga motsi ba taji Jaririyar ta ce. “Baabaah Lami ba zakiyimin wankan ba ne so kike sanyi ya kamani?.” Lami da sai lokacin ta tuna dalilin ɗaukar Jaririyar da ta yi shi ne don ta yi ma ta wanka, sai taji gaba ɗaya jikinta ya saki bata da sauran kuzari saboda tsananin tsoro take ta fara tunanin ya a ka yi a ka haihu a ragaya ne, bayan kuma Malam kasan komai ya sanar da ita a Macce jaririn zai zo in ma bai zo a matacce ba to zai kasance da shi da mataccen basu da bambanci ne. Lokaci guda ta fara tuna yadda ta aiwatar da komai lokacin da zata zuba maganin ta fara nazarin ta ina ne a ka sama matsala. Dam-du-dum dam! Kirjinta ya buga da sauri lokacin da ta tuna kwaɓar da ta yi domin ta yi Magana kafin ta saka maganin in bata manta ba har shewa ta yi da hakan ke nufin aiki ya ɓaci kuma kamar yadda Malam Kasan komai ya faɗa abin da zai biyo baya ba zai yi musu kyau ba muddun aikin ya ɓaci. Lokacin da Lami ta zo nan a tunanin tashin hankalinta ya ƙaru sai kawai ta fashe da kuka domin ji take shi ne abin da ya kamace ta a wannan taƙin. Kukan nata ne ya jawo hankalin Iya Suwai da ta shigo Ɗakin ɗauke da bahon da za'ayi ma Jaririyar wanka. “Ke Lami lafiyarki kuwa wannan kukan fa?” Cewar Iya Suwai tanayi ma Lami kallon mamaki. Lami ta fyace majiya tana faɗin. “ba komai Iya Suwai ai wannan kukan duk a cikin farin ciki ne wai yau dai Allah ya nufa ƴar uwa Ummah ta haihu, ta haifowa Malam wannan Jaririya kyakkyawa da ita ma sha Allah. Lami ta ƙare maganar tare da ƙara sautin kukan tana ɗan gantsarewa sakamakon wani azaba da ya ziyarci gadon bayanta ji ta yi kamar an mintsineta aikuwa tana dubawa taga Jaririyar ce ta mintsineta a baya. Tsananin mamaki ya sa bakinta ya fara rawa tana so ta yi magana amma ta kasa sai dai tana mamakin ya a ka yi hannun Jaririyar ya kai har gadon bayan ta ga ɗan banzan zafi da ta ji a bayan tamkar an saka allura mai tsini, da sauri ta kalla Iya Suwai dan son tabbatar da ita kaɗai take ganin wannan tashin hankalin ko kuwa dai ita ma Iya Suwai ta gani, don son ta tabbatarwa sai ta ce ma Iya Suwai. “wai Dan Allah Iya Suwai kina lura da abin da wannan Jaririyar take yi kuwa?.” Murya a raunace ta yi maganar domin ta gama sadaƙarwa da lamarin wannan Jaririyar tasan wannan Jaririya dai ba Dangin Mutane ba ne sai DANGIN JINNU domin ba yadda zatayi Jaririya daga haihuwa ta yi magana kuma take yin irin wannan abun haka dole dai akwai wata ƙasa ai ya zamar ma ta dole anjima ba sai gobe ba ta koma wurin kasan komai domin lamarin yafi ƙarfinta ita ɗaya. “mene ne kikaga Jaririyar ta yi?” Iya Suwai ta tambaya da mamaki. Muƙut Lami ta haɗiye yawu don ta tabbatar ita kaɗai ke ganin wannan tashin hankali. Cikin sanyin jiki dana murya ta furta. “ah ba komai ai batayi komai ba kawai dai na tambaya ne?” Ta faɗa tana ƙoƙarin miƙa ma iya Suwai Jaririyar. Takaici ya sa Iya Suwai ta girgiza kai tana faɗin. “kema dai Lami halin ki saike wasu lokutan sai kike abu kamar mai shafan jinnu ina ce ɗazun kika gama roƙona a kan ke zakiyi ma Jaririyar wanka shi ne yanzu kuma kike miƙomin ita...” “zakiga shafan aljanu ganin idonki lokacin da kika karɓe wannan dangin Jinnun daga hannuna ai.” Lami ta faɗa ƙasa ƙasa lokacin da ta samu Iya Suwai ta karɓi Jaririyar bayan ta gama sababi. Cikin ƙanƙanin lokaci a ka gama shirya mai jego da jaririyarta yayin da Lami da Iya Suwai suka gyara Ɗakin tsaf a lokacin kuma dangi da maƙota suka fara cika gidan cike da murnar samun ƙaruwa da Malam Yahayah ya yi kuma cikin amincewar Ubangiji a ka sama ɗiya Mace a abin da ya daɗe yana nema ke nan domin duka ya'yan Lami maza ne su uku, sai wannan karon da Ummah ta haifo masa Mace ga jaririyar jajur da ita tayo mahaifiyarta a haske yayin da kamanni tas ta kwaso na Mahaifinta malam Yahayah ai kuwa zo kuga rawar ƙafa wurin Malam Yahaya abin dai ba kama ƙafar yaro, yayin da gefe guda tsaban baƙin ciki da takaici ya taru ya yi ma Lami cunkus a zuciya, ga wannan ɗan banzan kyau da Jaririyar take da kamar wata ƴar larabawa ga kuma baƙin ciki na rawar ƙafar da Malam Yahaya yake yi sai kace ba'a taɓa yi masa haihuwa ba, gefe guda ga alhinin yadda zata sama Malam Kasan komai da wannan mummunar labari na kwaɓewar aiki da kuma abin da ya fara biyo baya a Ranar dai bata samu ta bar gidan zuwa wurin Malam kasan komai ba saboda mutane masu ganin mai haihuwa da jaririya da suka dingi shigowa haka ma washe gari ayyuka suka taru suka yi ma ta yawa a taƙaice dai har Ranar suna Lami bata samu ta fita zuwa wurin Malam kasan komai ba duk kuwa da yadda taso sai dai inda ta gode Allah shi ne tun daga wancan Ranar Jaririyar bata ƙarayi ma ta wani abu da zai firgita ta ba hakan ne ya ɗan kwantar ma ta da hankali amma kaɗan. Jaririya taci sunan mahaifiyar Malam Yahaya wato Fatima hakan kuma ba ƙaramin ƙauna yaja ma ta ba a cikin dangin da ma wurin ita kanta Mahaifiyar Malam Yahaya wato Iya Fatuh yayin da hakan ya ƙara wutar ƙiyayyar wannan Jaririya a zuciyar Lami domin taci burin Malam ya sakama Yarinyar da zata haifa wannan suna sai dai hakan bai faru ba sakamakon bata taɓa haihuwar mace ba. A taƙaice dai a Ranar sunan Lami ta samu ta faki ido ta bar gidan zuwa wurin Malam kasan komai domin neman mafita na wannan al'amari domin so take daga Jaririyar har uwan nata duka su baƙunci halira. Sai dai sosai jikinta ya yi sanyi lagwas lokacin da ta ƙari sa wurin Malam kasan komai tun kafin ta sanar da shi abin da ya faru ya rufe ta da masifa kamar zai cinye ta ɗanye sakamakon kuskuren da ta tafka ya kuma tabbatar ma ta ba shi ba koda wurin wani Malamin tsubbu ko boka zataje to fa ba mai iya kashe ma ta wannan Jaririya Muddun ba Allah ne ya so hakan ta kasance ba. Sai dai duk da haka bata karaya ba ta buƙaci a yi aikin da zai sa Malam ya dena bawa uwan da Jaririyar kulawar da yake basu a saka yaji duk Duniyar nan babu waɗan da ya tsana kuma bai san gani fa ce Ummah da ƴarta. Anan ne kuma Kasan komai ya tabbatar ma ta da aiki zai yiwuwa muddun zatayi biya mai kyau kuma ta cike da wasu matakai, ba musu ya yarje masa a taƙaice dai kafin ta bar wurinsa sai da suka yi abin da suka saba muddun ta kai masa ziyara to fa sai sun kusanci juna.... _______ ________ _______ TO FA! ANA DARA GA DARE YA YI. GA DAI DA YADDA LABARIN NAMU MAI TAKEN FAƊIME (DANGIN JINNU) YA FARA. YA KUKE GANIN ZATA KASANCE? TO MU DAI HAƊU A FEJI NA GABA, KAR A MANTA DA YIN LIKE, SHARE FISABILILLAH ZAHRAH ROYAL STAR CE TARE DA NAINARH KD SUKA TSARA KUMA SUKA RUBUTA ✍️🤍 *FAƊIME...💋🌸💕* _(Dangin Jinnu)_ ©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star *Dedicated to Salma Ahmad Isah (Candy)* *بسم الله الرحمن الرحيم* *A love & Laugh story that will capture your heart and soul.* 02 *ƘAUYEN KINKIBA, KADUNA STATE.* *GIDAN MALAM YAHAYA* *Five Years later* "Haba Auta miye Fad'ime tayi maka ne da zaka kai mata wannan dukan haka, ai K'anwarka ce". Cewar Umma ta k'are maganar tana jawo Fad'ime dake zaune a k'asa tana wasan k'asa irin na yara duk da dukan da Auta ya kai mata batai kuka ba bare tari sai ma wasan data ci gaba tana kallonsu da idanuwanta masu haske cikinsu kamar na mage. "Baki ga miye tamin bane?, nifa na tsaneta bana sonta haka kawai duk ta zo tafi y'an gidanmu kyau k'ila ma ba y'ar gidanmu ba ce can akaje a ka samo mana ita a ka k'ak'ubama Abbanmu ita" "Kaii Auta ubanwa ya gaya maka wannan maganar" Umma ta idasa maganar tana neman kai masa mari a fuska. Wuffff Lami ta fito daga d'aki har zanin dake d'aure a k'ugunta na neman kwancewa tsabar masifa har bakinta na kunfa wajan cewa. "Lahhh karki kuskura ki ce zaki tab'a min Yaro, bamu kwashi y'an kallo dake ba yanzun nan ehee" "Amma Iya Lami kina jin abunda yake fad'a min, kuma kin san hakan bai dace ba ina a matsayin matar ubans...... Lami ta katseta da hanzari tana cewa "Kee kinga bana son jin soki burutsinki. Kuma ai Yaro gaskiya ya fad'a duk cikin dangin Malam babu mai kyan wannan d'iyar taki mai kama da Iskokai ai Yaro ya fad'i gaskiya yo wa ya sani ma ko cikinta akaje aka yo daga waje aka zo aka k'ak'uba Malam shi" Umma tayi shuru tana jin zuciyarta na zafi sosai bata san sadda hawaye suka cika mata ido ba. Batai aune ba taga Fad'ime ta gangaro har inda take tana tab'a mata k'afa, jiki a sanyaye tasa hannu ta d'auki d'iyarta, ga mamakinta sai taga Yarinyar tasa hannunta tana d'an share mata hawayen dake mata zuba. Wani dogon tsaki Lami ta saki tana juya ga Auta ta dafasa tana cewa. "Kai da'aAllah rabu da ita je abunka ka ci gaba da wasanka, naga ubanda ya isa ya hanaka watayawa a cikin gidan ubanka". Umma bata sake cewa komai ba kusan a tare zasu juya domin barin wajan Auta dake wasa kawai suja ji ya fasa wata gigitacciyar k'ara ya fad'i a k'asa yana shure-shure. Habawa ai a haukace Lami tayo kansa Umma ma ta aje Fad'ime a k'asa tana yo wajan. Lami ta kamasa tana faman jijjigasa tana tabbayar miye ya sameshi miye yake masa ciwo duk ta rud'e ta fita hayaccinta. Ganin Umma na neman b'atasa yasa Lami a haukace muryarta har tana shak'ewa ta dubi inda Umma take ta d'aga mata hannu tana cewa. "Karki sake ki tab'a min d'ana karki sake ki k'araso inda muke. Kuma wallahi komi ya sami Yaro na to wallahi wannan y'ar iskar yarinyar taki ce sila domin naga ana tab'a ta aljanunta ke d'aukar mataki to ni dai nafi k'arfinsu nan gani nan bari, yo waye ma yasan k'ila aljana kika haifa ba mutum ba ce". Wata dariya Lami taji an b'ab'b'ake da ita a zabure ta kai dubanta wajan Fad'ime inda take jiyo dariyar, wani zaro ido tayi waje tana kallon yadda yarinyar ke kallonta tana mata dariya harda tab'a hannu. Sakin Auta tayi tana murza idonta da k'arfi ta bud'e again dai dariyar take mata had'e da gwalo ma take gani. "Innallihi wa'inna alaihir raju'on na shiga uku na, Wallahi Malam an haifar maka masifa a cikin gida, wallahi wannan d'iyar taki masifa ce a cikin jama'a" Umma ta waiga inda Lami ke kallon ita dai D'iyarta ta gani zaune hasalima wasanta take irin na Yara. Tsaye tayi kawai tana kallon ikon Allah. Zuwa can Malam ya fad'u gidan kamar wadda akai ma kiranye. Shima a rud'e kamar wadda akace ma Auta ya mutu ya nufi inda yake. Ai Lami na ganin Malam ya shigo ta fashe da kukan munafurci tana cewa. "Ni dai wallahi Malam na gaji, na gaji wallahi gara na bar maka gidanka dana zauna bak'in cikin matarka ya kashe ni, ita da aljanar yarinyar can tata, Fisbilillahi yanzu nan suna wasa da Auta yarinyar nan kawai mukaji Auta ya fad'i yana shure-shure, kuma na rantse da Allah ita ce tayi masa wani uban, dan haka wallahi idan Yaro na bai dawo yadda yake ba, na rantse da tsarkin mulkin Allah yau koto ce zata rabani dake wallahi". Lami ta k'are maganar tana kallon Umma data daskare waje d'aya. Gani tayi Malam ya mik'e ya nufi inda Fad'ime take kawai sai dai taji saukar k'arar Mari, ba shiri ta zabura ta nufi inda Malam yake ganin yadda ya Mari y'ar yarinyar da bata san miye duniyar take ciki bama. Ido a waje Umma ta warce yarinyarta tana shafa fuskarta yarinyar ko tari batai ba bare tayi kukan Marin da Malam d'in yayi mata, hasali ma dariyarta take masa tana wangale masa bakinta wadda ba hak'ora cikinsa. Shi kansa Malam d'in mamakin yarinyar ya fara kashe zuwa yanzu, kwata-kwata ji yake ba wadda ya tsana irin uwar d'iyar nan da ita kanta yarinyar. Umma cike da tsananin mamakin Malam d'in a kullum da yake k'ara kashe mata jiki ta ce "Malam yanzu dana barka saika ci gaba da dukan wannan y'ar yarinyar?, da bata san miye ma take yi ba, yanzu komai aka fad'a maka sai kawai ka hau sama ka zauna ka yarda, miye wannan yarinyar zatai ma Auta Fisbilillahi kawai saboda anga ina hakuri kuma bana magana, kai kuma baka son gaskiya yanzu sa....... Tasssss Rauntse idonta tayi da k'arfi had'e da dafe k'uncinta, bata san hawa ba bata san sauka ba kawai taji an d'auke ta da Mari, Abun bai sake bata mamaki sai da taga ashe Malam ne da wannan aiki yana tsaye kanta sai huce yake kamar wani Zaki kamar ace masa takk ya rufeta da duka gaba d'aya. Lami tana daga gafe sai sakin dariya take had'e da jin dad'in yadda yanzu ta gama malke Malam gaba d'aya sai abunda ta ce shine yake yi, idan aka tab'a ta da ita da yaranta kuwa yi yake kamar ya yanka mutum tsabar yadda yake mugun tsoronta a yanzu. Wasu zafafan hawaye ne suka shiga zarya akan fuskar Umma ba abunda take sai kallon Malam. Tunda take dashi bai tab'a daga hannunsa da sunan ya dake ta, sai a yanzu duk da tsawon shekarun nan taga abubuwa na wulakanci daga garesa da Matarsa Lami wacce abun ya samo asali ne tun washe garin da aka haifi Fatima, Lami ta fita ita ce bata dawo ba sai wajan dare kuma tunda ta dawo Umma taji gabanta na fad'uwa sosai saboda ganin yadda Lami ke sakar mata wani irin murmushi mai kamar gugar zana. Tun wannan lokacin shikenan zaman lafiya da jin dad'i ya k'are ma Umma da ita da abunda ta haifa yau bak'i gobe fari. Gashi gaba d'aya Yaran Iya Lami sun raina Umma rashin kunya babu wacce bata gani bare Auta yafi kowa iya rashin kunya sai ya gaya mata maganar da ko a mafarki bazaka ce shine yayita ba, garama sauran su sun zama manya ba wani zama gidan suke ba sosai. "Malam...... "Kimin shuru, ki sauk'e d'iyar nan taki ta warware abunda tayima Auta idan ba haka ba ranki daga ke har ita sai yayi mummunan b'aci wallahi" Nuna kanta take Umma tana kiran. "Malam yanzu miye wannan yarinyar zata yi ma Auta, duk fa wannan abun canfi ne fa ni yarinyata mutum ce kamar kowa bata da wani abu wallahi". Ganin Auta ya mik'e sai raba ido yake yasa Lami rungumesa tana kallon Umma ta mik'e dashi rik'e a jikinta tana cewa. "Barta Malam sa'arta d'aya D'ana ya mik'e, bance kuma ka sake ta ba har sai lokacin dana ga damar ta bar min cikin gidana daga ni sai Yara na, ai tunda kika ce zakiyi kishi da Lami shige ka fasa wallahi". Ko a jikin Malam kamar wadda ake ba umarni haka ya fara gyad'a ma Lami kai sai ka ce wani Yaronta wadda ta haifa da cikinta. Ta sake kallonsa tana cewa. "Muje ciki Malam" Sumi-sumi ya bi bayanta suka shige d'akin Lamin Umma na tsaye tana kallon ikon Allah. A hankali taji ana share mata hawaye, k'aro ma d'iyar tata ido tayi tana mamakin yarinyar indai zata ga tana kuka to tabbas ita ce zaka sameta tana share mata hawayen dake zubo mata, wayonta bai kai tasan hakan ba, kallonta take tana so ta gano miye yasa Mutane ke mata kallon wacce ba mutum ba, bare su Iya Lami dake hurara abun a wajan mutane suna muzanta mata yarinya. Wani irin taji a jikinta tana jin tausayin yarinyar tata a yau d'in, haka nan taji a jikinta ba lallai suyi rayuwa mai tsawo da yarinyarta, wani irin tsananin tausayin d'iyarta ne ya rufeta, ya rayuwarta zata kasance idan bata nan?, miye zai faru da ita idan bata gidan Mahaifinta?, tana gidan ma ya aka k'are inaga kuma ace bata nan babu idonta a cikin gidan........... *FAƊIME...💋🌸💕* _(Dangin Jinnu)_ ©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star *Dedicated to Salma Ahmad Isah (Candy)* *بسم الله الرحمن الرحيم* *A love & Laugh story that will capture your heart and soul.* 03 *One week later.* “Innallihi wa'inna alaihir raju'on, jama'a ku kawo ɗauki gini ya danne Umman Faɗime da ita kanta Faɗimen ku kawo agaji jama'a!” Iya Lami ce ke wannan kururuwar ta ɗaura hannu a ka cikin tashin hankali yayin da take tsaye gaban gidan Malam Yahaya dake ta faman rushewa yadda ka san an kasa motar rushe gini ana rusawa haka ginin gidan ta ko'ina yake ci gaba da rushewa yayin da Iya Lami take ci gaba da kururuwar neman taimako, ai kuwa lokaci ƙanƙani jama'a suka cika ƙofar gidan kowa yana tambayar abin da yake faruwa, ita kam Iya Lami ta ruɗe ba abin da take iya faɗa fa ce a kawo ɗauki gini ya rufe FAƊIME da mahaifiyarta, ai kuwa hankali tashe jama'a suka fara neman yadda za'a ɓullo ma lamarin kar a rasa rai biyu ana cikin haka sai ga Malam Yahaya ya dawo hankali tashe domin labari ya kai masa ai kuwa da ƙari sowarsa bai kula Iya Lami dake ƙoƙarin yi masa bayanin yadda al'amarin ya kasance ba, gadan-gadan ya nufa cikin gidan da ya gama rushewa faɗi yake. “Mata ta! 'yata! Jama'a ku taimaka ‘yata da Matata suna ciki gini ya rushe da su.” Ganin da gaske dai ƙoƙarin shiga ciki yake ne ya sa maƙocinsa Malam Idi ya yi saurin riƙo shi yana bashi haƙuri. Ita kam Iya Lami tsabar baƙin ciki da ganin halin ruɗani da Malam Yahaya ya shiga ya sa ta dakata cak daga kukan munafurcin da take yi duk da ta wani bangaren zuciyarta fal domin tasan koba komai FAƊIME da Mahaifiyarta sun mutu sanadin wannan rushewar ginin da ita ce sila. Curko curko kowa ya yi cike da alhini na wannan abu da ya faru sai da ƙyar ma wata ta sama zarafin faɗin. “amma garin ya ya wannan lamari ya kasance?” Ta kai maganar tana kallon Iya Lami da ta yi nisa Duniyar tunani a kan yadda zata ɓullo wa lamarin malam dan ta lura aikin baya ya fara sakin jikinsa dole yana buƙatar sabon aiki. “ah eh uhm! E dama fa, dama...” “dama me?” Malam Idi Mijin Matar da ta yi tambayar ya katse Iya Lami da faɗin hakan sai kuma kallo gaba ɗaya ya koma kanta, Iya Lami ganin asirinta yana shirin tonuwa ta yi saurin faɗin. “dama daga maƙota nima na fito kwatsam naga gidan yana rushewa kuma FAD'IME da umman ta duk suna ciki....” Ƙoƙarin zubewa ƙasa da Malam Yahaya ke yi ya sa ta kasa ƙari sa maganar ta yi saurin kamo shi tana kiran sunanshi. Sosai jikin mutanen wurin ya yi sanyi ganin irin halin da malam yahaya ya shiga domin sambatu ya shiga yi faɗi yake. “Allah Sarki Rayuwa shikenan kuma na rasaki Umman Fatima matar kirki duk irin cin kashin da nakeyi miki da wulaƙanci keda ‘yarki baki taɓa buɗe baki kin yi ƙorafi ba kullum cikin haƙuri kike dani gashi yau na rasa ku gaba ɗaya wayyo rayuwa kaico...” “haba mana Malam me ya sa kake faɗin hakan ne ai wani sai ya ɗauka Mugun wuya kake bawa Umman FAƊIME ka gyara kalamanka dai” Cewar Iya Lami tana zazzaro ido kamar wacce ta yi ma sarki ƙarya. Malam Yahaya bai kulata ba sai ma miƙe wa daga zaunen da yake da ya yi tare da nufar hanyar gidan nasa da ya gama rushewa zuwa yanzu. Yayin da wata cikin matar unguwa dake wurin ta katse Iya Lami da faɗin. “ke dai Lami kiyi shiru kawai in ba so kike ayi 'yar tone-tone ba domin kam wuya dai Umman FAƊIME tana sha a hannunki dan ma Allah yayi ta mai haƙuri ne da kuma kauda kai shi ya sa kawai...” Shiru kakeji Iya Lami bata tanka ta ba domin ji take tana ƙara magana asirinta ne zai tonu, a ka ce mara gaskiya ko'a ruwa gumi yake..... Buguzun buguzun haka take tafiya irin nasu na tsofi har ta ƙari so Anguwan da 'yan kullin kayanta a hannu sai dai tun daga shigowarta layin take hango mutane tsai-tsaye bata gama mamaki ba ta hango har da ɗanta Yahaya tsaye a wurin ta buɗe baki da mamaki sai kawai ta hango saitin gidansa da ya zama fili sai bulon ginin da ya rushe ai ba shiri a tamanin ta ƙara sauri tana faɗin a bata hanya ta ga abin da yake faruwa da kyau ko dai makuwa ta yi ba gidan ɗan ta Yahaya ba ne. “Iya kece anan kuma?” Malam Yahaya ta tambaya murya sanyin ƙalau yana ƙoƙarin ƙari sawa wurin da Mahaifiyar nasa take. “ni ce ɗan nan ka ganni da safen nan gajiya nayi ina so naga Takwarata mai sunan manya kwana biyu ana yi min rowarta shi ne nazo da kaina na ganta ka ganni harda tsaraba nayo ma ta ita da mahaifiyarta mai kyawun hali dana fuska ba irinsu oh oh ba, sai dai gashi na ƙari so gidan naga lissafin ya canza kamar na rikice a toh Fisabilillah ban da na rikice me zai sa na dinga ganin fili a wuri maimakon naga ginin gidan ka...” Wani kuka ne ya taho ma Malam Yahaya jin kalaman da mahaifiyarsa ke yi sai ya daure amma ya rasa ta inda zai yi ma ta bayani domin bai san ta inda zai fara ba, ita kuma taƙi shiru sai tambayar abin da yake faruwa take. Da ƙyar dai ya samu ya buɗe baki ya ce. “Fatima da mahaifiyarta...” Kasa ƙari sa maganar ya yi sakamakon hango FAƊIME da ya yi ta shigo layin a guje fuskarta ta yi futu futu da ƙasa da alama daga wasar ƙasa take sam bata lura da mutanen dake tsai-tsaye curko curko a wurin ba kai tsaye ta wuce wurin gidansu. Sai dai cak ta ja ta tsaya tana ƙare ma yadda gidan ya koma da kallo tashi ɗaya sai kawai ta fasa ihu tare da juyawa gadan-gadan ta nufa wurin da Iya Lami take tana gwarancinta tun kafin ta ƙari sa Malam Yahaya ya yi saurin riƙo ta ya haɗa da jikinsa yana sauke ajiyar zuciya da hamdala ga Allah na ganin ashe FAƊIME bata cikin gidan. Sai lokacin ya sama zarafin yi ma Iya Fatuh bayanin abin da yake faruwa, ai kuwa ta yi matuƙar girgiza da jin wannan al'amari ta kuma fusata jin kalaman da matan unguwan ke yi na irin zaman haƙuri da Ummah takeyi a gidan kuma bata ƙara tabbatarwa ba sai ganin ƙiri-ƙiri FAƊIME taƙi zuwa wurin Malam Yahaya duk kuwa da yadda ya so, ai kuwa kunyar Duniyar nan da kuma dana sani ya cika shi. Daga ƙarshe dai an samu an sama wasu sun fito da gawar mahaifiyar FAƊIME daga cikin gidan yayin da Iya Fatuh ta wuce da FAƊIME can gidan gado da take zaune da sauran iyalanta dama Malam Yahaya ne kawai yake gidansa daban dan bashi da ra'ayin zama a gidan gado sai dai sanadin wannan iftila'in da ya faɗa masa na rushewar gida da ba'a san mene ne sila ba ya sa ba shiri ya koma gidan gado shida Lami da sauran yaransa, a ranar a ka yi ma mahaifiyar FAƊIME sallah da komai a ka wuce da ita gidanta na gaskiya, yayin da kacokan raino da riƙon FAƊIME ya koma hannun Iya Fatuh dama taso tun ya ye a bata ita to Malam Yahaya ne yaƙi yarda yanzu kuma bashi da bakin musu haka Rayuwar ta ci gaba da gangarawa yayin da Malam Yahaya suke zaune a gidan gado da sauran dangi gefe guda kuma riƙon FAƊIME ya koma hannun Iya Fatuh gaba ɗaya dan ta rantse koda Aure malam yahaya ya ƙara to fa ba zata bashi FAƊIME ba bare kuma ace bai ƙara aure ba kuma ya yi zaton zata bawa Matarsa Lami Matar da batasan mutunci ba dan sam Lami da Iya Fatuh basa ga maciji tsakaninsu kuma hakan ya samo asali ne tun lokacin da Malam Yahaya zai Aure Lami ita Iya Fatuh bata so amma haka Malam Yahaya ya kafe dole a ka yi auren. WANNAN KE NAN. *Eleven years later* *FAƊIME...💋🌸💕* _(Dangin Jinnu)_ ©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star *Dedicated to Salma Ahmad Isah (Candy)* *بسم الله الرحمن الرحيم* *A love & Laugh story that will capture your heart and soul.* 04 *FAD'IME POV* "Inna Fatuh kiyi sauri ki ban kud'in nik'an mana, K'awaye na na jira a waje fa" Fad'ime ta k'are maganar tana kallon k'ofar d'akin Inna Fatuh. Da sauri Inna Fatuh ta fito tana k'irga kud'i, ta kalli Fad'ime dake dubanta ta ce. "Y'ar albarka Fad'ime ta, dan Allah karki tsaya wasa da jan matune fad'a kinji, kar a kawo min k'ararki yau kinji, karki tsaya ko ina ki amso nik'an kawai ki dawo gida kinga yamma tayi" Turo baki kawai Fad'ime tayi tasa hannunta ta amshi kud'in tayi waje da gudu. Tana gaf ficewa daga zauran gidan kawai taji ta bangaje mutum, bata tsaya bada hakuri ba zata k'ara gaba, taji an jawota ta baya an d'auke ta da wani irin Mari tasssss. "Kan uba".... Fad'ime ta fad'a tana ware idonta akan Auta dake tsaye yana kallonta cike da jin haushinta sosai, duk da yasan tab'a Fad'ime a wajansa ba abu bane mai dad'i da zai biyo baya. "Banza shashasha kawai mai kama da aljanun farko, komai mutum zaiyi bayayi irin na mutane, dubi ke dan Allah kamar wacce aka tonu daga kabari". "Auta ni ka mara?". "Na mare ki ko zaki rama ne?" "Hmmm bazan rama ba amma ka guje abunda zai biyo ba, sanadin wannan marin da kayi min wallahi". "Idan kin fasa yi min wani abu kin raina Allahn daya halacci ki kinji?, aikin banza kawai". Ya k'are maganar yana k'arawa gaba ya shige cikin gidan. "Uhmmm" Kawai Fad'ime ke yi tana rik'e da kuncinta har yanzu, wani mugun haushin kanta ma take ji mi yasa ma bata d'aga hannu a nan take ta sauke masa marin ba, komai ta fanjama fanjam. Juyawa tayi ta idasa ficewa daga gidan. Tana fita ta iske su Laure da Sa'ade na jiran fitowarta. K'awayenta ne tun sadda suka dawo gidan Gadonsu, a unguwar suke, tasu ta zo d'aya tsabar suma ba jin magana suke ba. Tafiya suke buguzun-buguzun, basu aune ba suka ji wani Yaro dake d'an nesa dasu yana cewa. "Wayyo Jama'a ga dangin Jinnu can ta biyo hanya dangin Aljanu kenan" Ya idasa fad'ar haka yana nunama wasu Yara dake kusa dashi. Wani mugun b'acin rai ne ya kama Fad'ime duk duniya idan akwai abunda ta tsana to ace mata dangin Jinnu. Da gudunta ta k'arasa inda suke, kwai sai dai suka ga tsayuwarta a gabansu kamar wata walk'iya. Zaro ido sukai a waje suna rarraba ido, wadda ya fad'i maganar ne yayi saurin juyawa zai baza da gudu, kamar walk'iya Fad'ime ta rik'o hannunsa tana kallonsa, jijjga jikinta take tana jefa masa wani mugun kallo. Laure ce ta rik'e sauran yaran ita da Sa'ade suna cewa. "Ubanwaye kuke kira da dangin Jinnu iyee?" "Wallahi Allah bada ku muke ba" Cewar wani daga cikinsu yana fad'ar maganar jikinsa na d'aukar rawa. Wadda Fad'ime ta rik'e kuwa yana ji da rashin kunya bai san abunda zai biyo baya ba, yana ji da rashin kunyarsa, saboda wani abu bai tab'a had'asa da Fad'imen ba sai yau. Ya ce "kaii Isah an fad'a d'in, ance K'anwar Jinnu, ai haka mukaji mutane na fad'a, muma kuma munje mun fad'a, laifi ne mukayi dan mun fad'i sunan da mutane ke fad'i akanki?". Wata muguwar shak'a da Fad'ime tayi masa, yasa shi fasa wata gigitacciyar k'ara, bai gama dawowa dai-dai ba, tasa d'ayan hannunta ta d'aukesa da wani gigitaccan mari. Wasu taurari ne yaron yaji sun gifta masa, kunnansa ne yaji yayi wani dummmmm, gaba d'aya jinsa ne ya d'auke kwata-kwata baya jin abunda ke wakana. Fad'ime ta kallesa tana cewa. "Daga yau idan kunga na taho ku tsaya dan Allah ku jani kunji, idan banci kutumar uban Yaro ba". Duk abunda take fad'a fa kwata-kwata yaron nan baya ji, jinsa da gaske ya d'auke. Ai ko yana fahimtar haka ya saki wani mugun kuka mai k'ara yana fad'uwa k'asa yana birgima yana magana da k'arfi yana cewa. "Wayyo Allah na shiga uku na, jama'a ta dod'e min kunne bana ji kwata-kwata, jama'a ku taimaka min na shiga uku". Abunda yake fad'a kenan yana uban kuka. Sauran yaran kuwa wani fitsari ne ya kwace masu, sakinsu su Laure sukai suna dariyar mugunta suka kalle suna cewa. "Abunda yasa zamu barku kuma dan baku fad'i sunan nan bane, kuma zaku iya zuwa ku gaya ma iyayensa, sai a fara nemar masa magani, dan da alama ya kunnansa ya daina aiki". Suna fad'ar haka Fad'ime tayi gaba suka take mata baya. Sunzo wani wajan mai tsire kawai Fad'ime ta tsaya tana had'iyar miyau, matsawa tayi kusa sosai da mai tsiren tana cewa. "D'an juma mai tsire a yanka min na d'ari uku" Washe baki D'an juma mai tsire yayi yana kallon kyakykyawar fuskar Fad'ime yana lashe baki ya ce. "Ahh masoyiya Fad'ime ke ce a tahe keda K'awayenki?". Murtuke fuska Fad'ime tayi tana jin haushin D'an juma mai tsire, wai masoyayirshi, Ubangiji ya kiyaye mata ta so wannan bawan Allahn. Wani tsaki taja tana k'ank'ance ido ta ce. "Kaga D'an juma idan zaka bani tsire na d'ari ukun dana ce ka yanke min, ka bani kawai bana son yawan surutu kaji Malam, ko wace ma masoyayir tashi?". Ta k'are maganar tana harararsa. Washe baki ya sake yi, shi dai tunda za'a masa ciniki ai ta wuce, domin son kud'i ne da shi baya jin ko yana sonta zai iya bata tsiren nan a kyauta. Sa'ade ta matso ta kalli Fad'ime a sadda D'an juma ya mik'o mata tsire yana cewa a bashi kud'insa. Hararsa tayi ta ce "kaga na cinye na tafi ban baka kud'inka ba?". "Ahh to ai kin san bana da mutumci akan kud'i na" Banza dashi tayi tana jin Sa'ade na cewa. "Amma Fad'ime karki ci masa tsire kuma al'halin baki da ko sisi fa". Wata harara itama Fad'ime ta maka mata, ba shiri Sa'ade ta tsuke bakinta tayi shuru. Guda d'ai-d'aiya ta basu suka amsa suka cinye suna tand'e hannu. Sai da ta gama ci sana ta kalli D'an juma ta fiddo kud'in nik'an da Inna Fatuh ta bata naira d'ari ce ta mik'a masa. Amsa yayi tana washe baki, can ya murtuke fuska tamau ganin naira d'ari ce, kallon Fad'ime yake, bala'i cike da cikinsa. "Kan uba Fad'ime kinga nawa kika bani kuwa?". "Na sani mana" "To miye kike nufi dani". "Yo mifa nake nufi da kai, iya kud'in da nake da su kenan, kama gode Allah ka samu d'ari d'in". "Ai ko yau akwai bura uba a garin nan, keeeee Fad'ime ni zaki ci ma tsire ki tsaya ido cikin ido ki ce bazaki biya ni sauran kud'i na ba?, to ai ko uwar data haife ce ta dawo duniya na rantse d........ Maganar ce ta katse jin an wasa masa k'asa har kan idonsa. Murza idonsa yake a haukace, yana murja ido da kyar ya bud'e idon nasa muten sun zagaye shi. Ihu ya saki ganin yadda tsirensa ya b'aci da uwar k'asa a cikinsa gaba d'ayansa ya lalace, babu wadda zai iya cinsa a haka. Hango su Fad'ime yayi sun baza da gudu. Wani ihu ya saki yana cewa. "Na rantse da tsarkin mulkin Allah yau sai na ci kutumar uban wancan yarinyar Mai kama da aljanu, wallahi Mutane sunyi gaskiya da ake ce mata dangin Jinnu, ai wallahi yau ko za'ayi yak'in duniya na biyu sai an biyani duka kud'in tsire na na rantse kuwa". Hakuri mutane suka rink'a basa amma ina sai tsine ma su Fad'ime yake daga ita har K'awayen nata, yana Allah wallahi sai an biyasa kud'in tsirensa ko za'ayi mi. ______________ Dai-dai sun iso wajan amsar nik'a, suka ja birki suna sauk'e lumfarfashi. Dariya kawai Fad'ime keyi su Laure na tayata. "Kee amma Fad'ime kin shammace sa fa, kawai sai dai yaji saukar k'asa akan kayan sana'arsa". Cewar Laure tana rik'e cikinta domin ji take ya d'aure sosai, saboda gudun da suka sha da kuma uwar dariyar da suke. Sauk'e lumfashi Kad'an Fad'ime tayi tana yin gaba taje inda ake saka layi domin amsar nik'a, ita bata sa layi ba ta shige gaba kawai. Tana cema su Laure. "Ai kad'an ma ya gani ya ci gaba da tab'a min iyaye sai na yi sanadiyar rugujewar sana'ar tasa walla... Maganar Fad'ime ce ta mak'ale jin yadda aka wani bangajeta ta fita daga gaban data shiga. Wata yarinya ce mai jiki sosai k'ibarta har tayi yawa tana kallon Fad'ime data ture tana cewa. "Keee baki ga layi ake sawa bane?, sai ke isassa kin wani zo kin shige gaba, dama na dad'e ina jin rashin kunyarki to yau da alama zan sauk'e miki ita ne". Tashi tsaye Fad'ime tayi tana kakkab'e jikinta saboda har sai da ta fad'i lokacin data bangajeta, domin ba k'arama bace wacce ta ture tan, bata jin wannan ko d'an bigeka tayi ba zakai taga-taga zaka zube k'asa ba, yo wannan abu kamar buhu. Duk irin girman yarinyar hakan bai sa Fad'ime jin wani abu ba, bare azo ga tsoro. Rik'e k'ugu tayi tana matsowa sosai inda take ido cikin ido ta kalleta ta ce "Ni kika bangaje?". "An bangaje ki d'in, ko akwai abunda zaki yi ne?". Ta fad'a a tsawace tana sake matsowa sosai kusa da Fad'ime kamar zata had'iyeta da ranta. D'an shafa kanta Fad'ime tayi tana kallon su Laure kyafta masu ido tayi, ai ko suna ganin haka suka shige wajan nik'an da gudu suka warto nik'an dake ajiye, an nik'a shi, suka fito da gudu sukai gaba, mai nik'a na faman kiransu su bashi kud'i, amma Ina sunyi gaba. Fad'ime kuma ganin hankalin mutane ya koma wajan su Laure har wacce ta tureta ma tana binsu da kallo. Batai aune ba kawai taji anyi sama da ita an fyad'a da k'asa ji kake timmmmmmmmm. Yadda kasan an kada gini. Kamin ta gama dawowa dai-dai taga Fad'ime ta haye ruwan cikinta ta kama fuskarta sai yakushi take tana kai mata naushi a ciki, sai k'ok'arin k'are kanta take amma ina, taji uwar bari sai kuka take tana kiran azo a ceceta zata kasheta. Duk irin taruwar da jama'a sukai wajan suna k'ok'arin b'anb'are Fad'ime a jikin yarinyar nan amma Ina abun ya gagara. Shi kansa Mai Nik'an dole tasa ya fito daga Shagon nik'an aka taru dashi ana sun kwace Fad'ime daga jikin baiwar Allahn. Da kyar da sub'in goshi aka samu Fad'ime ta saki Y'ar mutane, tana uban nishi, tana tashi kuma bata tsaya ba ta k'ara gaba da uban gudu kamar wata zakanya. Tashi tayi da kyar yarinyar tayi tana kuka. Wata ce ta rik'eta tana cewa. "Binta mi yasa kika ja Fad'ime, wadda kowa yasan Fad'ime duk garin nan shaid'aniya ce, duk bala'inka waccar yarinyar ta fika". Kuka Binta ta k'are fashewa dashi tana cewa. "Na rantse da Allah bazan yarda ba, idan na yarda Allah ya tsine min, wallahi saina gaya ma Innata, wallahi yau sai an d'akko masu Y'an Sadda ko waye ya tsaya mata a garin nan wallahi". Buguzun-buguzun ta wuce gidansu tana k'ara b'are baki. __________________ Dandazon jama'a ne a k'ofar gidan su Fad'ime sun taro kowa na tofa albarkacin bakinsa, hayaniya ta kaure sosai a k'ofar gidan mutane na cewa. "Ai wallahi a fiddo mana ita nan muci uwar shegiya tunda ta addabi kowa a cikin gari". Inna Fatuh dake tafe har sauran kad'an ta kife a k'asa, ta fito k'ofar gidan tare da su Inna Lami da Malam dake biye dasu, da duk mutanan gidan. "Wai miye ne da naji anata kiran sunan Jikata ne?" D'an juma mai tsire ne yayi saurin cewa. "Ai na rantse da Allah yau sai an biyani kud'in tsire na, Jikarki Fad'ime taje ita da K'awayenta suka watsa min k'asa a cikin tsire na, dan haka tsire na, na kusan dubu talatin ne, kuma wallahi ko za'a sake yak'in duniya na biyu sai an biya ni kud'i na, ko mu had'u a Ofishin Y'an Sadda". "Ai ba kai kad'an bama Malama D'an juma, ni Yaro na ta kama ta kantsama ma Mari har jinsa ya d'auke, dan haka wallahi ko za'ayi mi yau sai tazo ta maido masa da jinsa yadda yake wallahi, ina nan ina jiran Jikar taki". Cewar wata mata dake rik'e da Yaron har yanzu baya jin abunda ake cewa sai kuka yake. Inna Fatuh ta wani k'ank'ance ido tana kallonsu d'aya bayan d'aya ta ce. "da'aAllah Malamai ku tsaya min na ce, nasan dai Jikata bata jan fad'a sai an tab'a ta, su yaran naku baku tabbaye su miye sukai mata bane?, Kai kuma D'an juma akwai abunda kayi mata kaima wallahi. Kuma bamai tab'a min Jika wallahi ehee". Inna Fatuh ta k'are maganar tana turo kallabi gaban goshinta, dan ko hijab bata sa ba, wani gyale na yafo saman kafad'arta. Zasu sake magana wata mata ta shayo kwana ita da d'iyarta rik'e a hannunta had'e da Y'an Sadda guda biyu biye da ita fuska murtuke. "Mun shiga uku, ku kuma fa, daga Ina?". Cewar Inna Lami tana rik'e k'ugunta. "Zuwa mukai a kama Fad'ime ta kama Y'ata Binta ta haye ruwan cikinta ta kama bugunta kamar ta sami Jaka, yo ko ni dana haifeta ban tab'a mata irin wannan uban dukan ba, dan haka banga ubanda ya isa ya bigeta haka na kyale shi ba wallahi". "Wayyo Allah na shige su ni Inna Fatuh, ace duk garin nan duk an tsani Jikata, kamar ita ce kad'ai yarinya a cikin garin nan. Shine ke baiwar Allah harda zuwa ki kwasu Y'an Sadda domin kawai su kama Jikata?, ai ko wallahi banga wadda ya isa ya kama Jikata ba ehee kiji da kyau". "Haba haba haba Inna Fatuh, Fisbilillahi sai tare ma Fad'ime fad'a kike al'halin kinsan ita ce wacce keda laifi. Ki bari kawai ma ta dawo daga yawon ta zubar d'inta su kamata su wuce da ita can Ofishin Y'an Saddan, su lallasa mana ita ma ko ta d'anyi halkali ma" Cewar Auta yana duban Inna Fatuh. Wata dak'uwa Inna Fatuh ta makama Auta tana cewa. "Ungo nan Auta, kaci gidanku na ce kaji, idan kaga an tafi da Fad'ime to sai dai a had'a da ni da Ubanka duka a tafi damu wallahi". "A'afa wannan d'aya, sai dai keda Fad'imen za'a tafi da ku amma dai banda Malam wallahi" Malam ne ya kalli Auta ya ce . "Karka sake magana a nan wajan, wuce ka shige gida na ce". Malam ya fad'a yana nuna Auta dake kallon Inna Fatuh fuska ba Rahma. "Yo ka barsa mana tunda ai uwarsa ce take d'aure masa gindi yayi ma mutane rashin kunya ai". Inna Lami ta katse Inna Fatuh tana d'aga mata hannu ta ce. "Kinga Inna Fatuh tunda aka fara wannan kicimulin baki ji baki na ba, dan haka kar a sake saka ni a ciki a'ato". "Ai kawai ki fito fili ki ce zaki zage ni Lami, dama ai kema ba k'aunar Fad'ime kikeyi ba wallahi, bakik'i ma Fad'ime zuwa yanzu ta mutu ba ai, to Fad'ime dai nan gani nan bari ajiyar Allah ce wallahi". Lami zata sake magana ranta a b'ace Malam ya d'aga masu hannu zuciyarsa babu dad'i ya kalli dandazon jama'ar dake wajan ya ce. "Kowa ya fad'i kud'in da tayi masa asara da wadda zasu je asibiti sukai Y'ay'ansu. Dan Allah kuyi hakuri kuma, Yaro ne ka haifesa baka haifi halinsa ba". Jama'ar wajan tausayin Malam ne ya kamasu dan haka da kyar wasu suka hakura nan take yasa aka kamo Akuya har biyu aka saida, aka biya kowa kud'in da ya kamata, sai mutum d'aya ce bata karb'a ba, wacce Yaronta jinsa ya d'auke ita ce tsaya a wajan yanzu tana cewa. "Babufa kud'in da zan amsa naku, iyakaci a fito min da Fad'ime ta bud'e ma Yaro na kunnansa, idan ba haka ba kuma nima wallahi wajan Y'an Saddan zan kai k'ara, domin ni kud'inku babu uwar da zasu min". Inna Fatuh zatai magana ta hango Fad'ime dake tafe ita da zugar K'awayenta. Ganin Ibrahim zai nufi wajanta Babban Yayansu ta d'aga masa tsawa tana cewa. "Na rantse da Allah karka sake ta tab'a min Jika, karka sake na ce". Duk maganar da take yi hakan baisa Ibrahim tsayawa ba, sai da ya kamo hannun Fad'ime dake zare ido waje y'an cikinta na k'ara, domin tasan an kawo k'ararta tun kan ta iso gida, tana jin tsoron Ibrahim shine kad'ai duk cikin familynsu take d'an shakka shima kad'an. Sai da ya d'auketa da Mari har sau biyu, yana zare mata ido yana cewa. "Dan Ubanki abunda aka ce kije kiyo kenan?, kin san iyayen mutanan da suka zo kawo k'ararki? Ke wai wacce irin y'ar banzar yarinya ce ne?, shegiya kamar shaid'aniya, ke kullum kece y'ar kawo k'ararki wajan mutane, dalla wuce min a nan karna karya miki k'afafu yanzu nan wallahi". "Karyata mana, ai kawai ka idasa min ita na ce kaji Ibrahim?" Cewar Inna Fatuh data warce Fad'ime daga hannunsa yanzu tana b'alla masa uwar harara. Banza yayi da ita ya kalli sauran K'awayen yana zare masu ido ya ce. "da'aAllah can kuma kubar wajan nan". Aje nik'an sukai da sauri suka juya da gudu suka bar wajan. Sake fisgo Fad'ime yayi a hannun Inna Fatuh ya matso da ita inda Matar nan take da Yaronta yana cewa. "Kiyi Maza-maza ki bud'e ma Yaron nan kunne idan ba haka ba kuma na rantse miki na lahira sai fiki jin dad'i". Matsowa Inna Fatuh tayi wajan tana cewa. "Wai kai Ibrahim wane irin abu ne wannan kake haka, kana ma yarinya tsawa sai ka ce ba ubanku d'aya ba, ai ku duka ba k'aunarta kuke ba, shikenan kullum ace cikin hantarar kuke, to wallahi ranka zaiyi mummunan b'aci ne". Nan d'in ma ba tanka mata yayi ba. Sai k'ok'arin bugu da yake son kaima Fad'ime domin yaga yadda ta wani tsaya bata niyar yin abunda ya ce. Yasa Inna Fatuh kallon Malam dake tsaye cike da jin haushinsa shima ta ce. "Idan har ni ce na haifeka to kaba Yaronka umarnin cewa karya sake ya sake tab'a min Jika, idan ban isa dashi ba, ai kai na isa da Kai". Ba dan Malam yaso ba ya dakatar da Ibrahim daga dukan da yake son kaima Fad'ime. Malam ya matso a hankali cikin kwantar da murya ya ce. "Fad'ime y'ar albarka ki bud'e ma yaron nan kunnansa kinji". D'an sakin fuskarta tayi domin da tun farko da lallami aka bi da ita da tuni tayi abunda suke so. Dan a duniya Fad'ime ta tsani a d'aga mata murya. A hankali ta juya wajan Inna Fatuh tana cewa. "Suje gida Kunnan nasa zai bud'e". Tana fad'ar haka ta shige cikin gidan. "Kutumar uban can, ni Lami naga takaina, ace yarinya tayi laifi amma ko a jikinta, ko da yake d'aurin gindi ta samu ai, dole tayi abunda take so ai, ta taka wadda take so ". Inna Lami ta fad'a cike da bak'in cikin Fad'ime, yau so tayi a tafi Police teshin d'in da ita ace ubanta sosai. "Ohhh dai ba kuma yadda za'ayi da ita kuma ba". Cewar Inna Fatuh. Lami ta shige gida tana jin bak'in cikin dawowarsu wannan gidan, da ace suna can gidansu ai da sai yadda tayi da wannan aljanar yarinyar. Kamin su wuce ga mamakin Matar nan uwar yaron nan sai ji tayi Yaronta na cewa yanzu yana jin komai cike da murna yake fad'ar haka. Inna Fatuh ta kallesu tana cewa. "To daga yau sai kiyi ma D'anki gargad'in cewa karya sake Jan Jikata, dan k'ila a gaba zai iya rasa idanuwansa ma". Itama ta k'are maganar tana d'aukar nik'anta dasu Laure suka aje, ta shige cikin gidan. Malam ne ya tsaya ya sake ba Matar hakuri sosai........... *FAƊIME...💋🌸💕* _(Dangin Jinnu)_ ©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star *Dedicated to Salma Ahmad Isah (Candy)* *بسم الله الرحمن الرحيم* *A love & Laugh story that will capture your heart and soul.* 05 *BAYAN SATI ƊAYA* Abin Duniya da halin FAD'IME ya gama isar Malam Yahaya hakan ya sa ya yanke shawarar aurar da ita domin ta kai minzalin Auren har ma ta wuce domin shekarunta goma sha shida tana gab da shiga na sha bakwai sa'anninta ma zalla duk an aurar da su sai waɗan da ba'a rasa ba irinsu Sa'ade ƙawayenta da suka addabi ƙauye. Da wani mutumi mai suna Ɗan Abba Malam ya yanke shawarar aurar ma FAD'IME kuma hakan ya biyo bayan maganganu ƙarya da gaskiya a kan FAD'IME ne da Lami ta faɗa masa kuma ita ta nema da ya aura wa Ɗan Abba FAD'IME kuma ba musu Malam ya amince domin ta riga ta gama da shi sai abin da take so shi yake yi ba tare da musu ba koda kuwa hakan shi bai kwanta mishi ba sai dai ganin Ɗan Abba mutumin kirki ne a idon kowa na ƙauyen, kuma ma har Mata yake da ita da yara biyu shi ya sa ba tare da wani dogon bincike ba Malam ya yarda zai aura masa FAD'IME dama kuma sara ne a kan gaɓa domin Ɗan Abba ya daɗe da mutuwa a kan son FAD'IME sai dai bata ma san yanayi ba kuma ko yanzu da Mahaifinta ya bashi ita sai wani farin ciki ya cika shi shikenan zai sama muradin ransa FAD'IME ba tare da ɓata lokaci ba a ka tsayar da lokaci da Ranar Aure nan da sati ɗaya kuma a ka fara shirya shirye sai dai a ɓoye ba tare da FAD'IME da Inna Fatuh sun sani ba, gudun abin da zai je ya dawo ya sa Malam ya ɓoye musu batun don ya san muddun FAD'IME ta ce bata so to fa ko sama da ƙasa zata haɗe ne Inna Fatuh ba zata taɓa yarda a ɗaura Auren ba. Sai dai abin da Malam bai sani ba shi ne tuni Ɗan Abba da Inna Lami sun baza labari a ƙauye cewar FAD'IME zata aura Ɗan Abba kuma tuni gari ya ɗauka daga masu fatan Alkhairi sai masu kushe abin, kuma tuni labari ya koma kunnen Zulay Matar Ɗan Abba ai kuwa tsabar kishi na hauka yi ta yi kamar ta zare ta rasa inda zata saka kanta dan baƙin ciki.. *Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja Nigeria.* A jere dakakku kuma tsadaddun motocin guda biyar suka faka a harabar airport ɗin securities ne suka fiffito suka tsai tsaya suna jiran ƙari sowar wanda suka zo tarba ba'a ɗauki lokaci ba jirgin ya yi landing fasinjoji suka fara sakkowa ciki kuwa da har da shi dogo ne kuma kyakkyawa ajin farko ɗin nan yanayin fatarsa fari ne mai kyau kana ganinsa kaga wanda hutu ya sama wuri ya zauna tare da shi, sannan jikinsa a murɗe yake kai da gani ka san yana samun kulawa mai kyau ta hanyar yawan motsa jiki, a dake yake tafiya sanye cikin expensive luxury suits Dolce & Gabbana ga wani glasses na gayu da ya maƙala saman fuskarsa, yayin da gefe guda wasu Kyawawan yara ne da ba zasu haure shekaru Biyar ba a duniya mace da namiji cikin shiga ta alfarma suke tare da shi ga kuma tsananin kamanni da suke, cikin taku irin na nutsuwa da salo suka ƙari sa wurin motocin da sauri security ya buɗe masa motar dake tsakiyar ya shiga bayan ya saka yaran ciki, sannan gaba ɗaya suka koma cikin motocin suka tayar a nutse suka bar airport ɗin. *SAL Estate, Shehu Shagari Way Abuja Nigeria.* Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo da a ka fi sani da SAL cikakken ɗan kasuwa ne kuma ɗaya daga cikin manyan mutane da a ka san da zamansu a faɗin Afirka yana da mata biyu da yara shida maza uku mata uku, Matarsa ta fari ita ce Hajiya Salima yaranta huɗu maza uku sai mace ɗaya auta, sai kuma Hajiya Haleema da ke da yara biyu mace da Namiji yaran Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo sun taso ne cikin tarbiyya da mutunta juna shi ya sa ko bayan da kowannensu ya gama karatu duk sai suka taimakawa mahaifinsu ta hanyar ci gaba da tafiyar da harkokin kasuwa cikin ilimi da hikima ai kuwa lokaci ƙanƙani cikin amincewar Ubangiji arzikin Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo ya ƙara haɓaka sosai, ko zuwa lokacin da kowanne daga cikin yaran nasa ya yi Aure sai ya gina musu tanƙameman Estate da suke zaune ciki har wa yau da aka saka ma suna SAL ESTATE dake Shagari Way cikin garin Abuja. Zuwa lokacin da yaran Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo SAL suka fara tara iyali ne kuma matsaloli ya fara kunno kai hargitsi da rashin fahimta ya fara shiga tsakaninsu duka a kan dukiya sai dai basu taɓa bari mahaifinsu ya fahimci hakan ba, amma ta ciki na ciki kowa shi ya san shirin da yake yi a kan ɗan uwansa hatta yaran Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo mata a nan Estate ɗin suke zaune da mazajensu kuma hakan ya samo asali ne daga wurin Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo da ya buƙaci hakan domin burinsa bai wuce ganin iyalansa kansu a haɗe ba kuma suna zaune wuri guda a kaf cikin iyalan Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo Mutum ɗaya ne baya zaune a wannan Estate ɗin hasali ma baya ƙasar gaba ɗaya shi ne yaron Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo na uku yana zaune ƙasar Faransa da Matarsa da iyalansa har zuwa wannan lokaci. Safiuddin Ahmad Sa'id Lamiɗo wanda a ka fi sani da Young SAL sakamakon nickname ɗin sa da ya kasance dai dai dana kakansa wato Mahaifi a wurin mahaifinsa, Safiuddin ya kasance jika na huɗu a familyn SAL sai dai ya kasance daban da sauran Jikokin familyn shi ya sa kakansu Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo yake kiransa da gagabadau yayin da sauran Jama'a ke kiransa da SAL, Safiuddin Ahmad SAL ya kasance mutum ne na daban da tsarinsa da yanayin Rayuwarsa yasha banbanta da na sauran jikokin SAL family domin ya kasance bai damu da shiga harkar kowa ba kuma Mutum ne mara san hayaniya da kuma surukutu shi ya sa wasu ke kiransa da Miskili sai dai hakan bai dameshi ba rayuwarsa yake yadda yake so sam mata basa gabansa abin da ya saka a gaba shi ne aikinsa na Soja ta gefe guda kuma shi ne mai kula da Babban Companyn SAL dake ƙasar America idan yana can idan kuma ya dawo Nigeria to shi ne mai kula da Companyn SAL na ɗaya dake ƙasar, shi ya sa ya zokale idon da yawa daga cikin Familyn SAL musamman masu jin haushinsa da ganin gatan da Kakansu da ya ɗaura shi a kan muƙamin ya yi masa a ganinsu su ne suka cancanta tun da sun girme shi baya da haka suna da Aure shi kuwa Bama auren a gabansa hakan ma ya sa shi da kansa Tsoho Alhaji SAL ya haɗa Safiuddin Young SAL da ɗaya daga cikin jikokinsa mata da yake ji da ita wato Fidaus ya haɗa su da Safiuddin a kan su fahimci juna sai dai Safiuddin duk da ya kwashe shekaru baya ƙasar hasali ma bai san wacece Fidaus ɗin ba kasancewar a ƙasar Faransa ta taso ta yi karatu a can wurin Yayan Mahaifiyarta dake can, amma Safiuddin ya ce ya yarda da zai aureta koda basu san juna ba tun da har Tsoho Alhaji SAL ya yaba da ita shikenan ai kuwa ba ƙaramin farin ciki Tsoho SAL ya yi ba kuma ba tare da ɓata lokaci ba a ka tsayar da Ranar Auren Safiuddin da Fidaus wata guda ke nan kuma a halin yanzu Safiuddin AkA SAL ya dawo Nigeria ne hutu daga nan idan an yi bikinsa da Fidaus nan da watanni uku ke nan masu gabatowa zai koma da Matarsa can inda yake zaune. Sai dai gefe guda ya dawo da abin mamaki su ne waɗan nan twins mace da namiji da ya dawo da su bayan kuma ya kasance bai taɓa Aure ba, baya da haka akwai wani babban dalilin na dawowar Safiuddin a halin yanzu... WANNAN KE NAN. *ƘAUYEN KINKIBA, SOBA LOCAL GOVERNMENT, KADUNA STATE NIGERIA* *FAD'IME POV* Tafiya suke ita da su Sa'ade buguzun buguzun gasu biji-biji sai ɓallar raken da suka samo a can fadama gonar ɗan mai gari suke ba abin da ya damesu sai ma fira da suke kwasa cike da garɗin rake har wani waƙa ma suke biyawa wai ita ALJANNATA na mawaƙi Auta Waziri. Gefe guda Laure da Sa'ade ne ke faman ƙusin-ƙusin sun rasa ta inda za su sanar da FAD'IME maganar da ke bakinsu a kan labarin Aurenta da suka samu duk da sun fahimci duk abin da a ke bata ma sani ba, sai da ƙyar Laure da ta shanye raken hannunta ta duba FAD'IME dake biye sautin waƙar cike da kwarewa yadda ka san ita ta raira ta ce. “Wai FAD'IME duk abin da yake faruwa a ƙauyen nan baki sani ba?” Ba tare da FAD'IME ta gama shanye raken da ga gabza ba ta ce. “ke Laure banason gulma fa ki bar wani nuƙu-nuƙu ki fito ki sanar dani mene ne yake faruwa...” “au da gasken baki sani ba ke nan to dai gobe aurenki da Ɗan Abba Mijin Zulay kacao-kacao gaba ɗaya ƙauye labari ya ɗauka a kan za'ayi miki Auren dole da Ɗan Abba Mijin Zulay kacao-kacao....” “Kutm*r ub*a! kayyasan can...” Zagin da FAD'IME ta mulmulo ya sa Sa'ade da ta katse ta tana bayanin ta yi tsitt tana zaro ido don kuwa a yadda FAD'IME ta yi wannan ashariya zata ɗauka mutanen nata ne suka motso.... “wata FAD'IMEn kike magana a kai! Sa'ade kada ki ce mini ni FAD'IME kike nufi?” FAD'IME ta yi maganar idanunta a wani wawware tana duban su Laure da Sa'ade gaba ɗaya sai dai wannan karon ba a zafafe ta yi maganar ba, ba kuma cikin nutsuwa ba sannan ta yi maganar ne tana nuna kanta tare da sakin wani shu'umin murmushi. Sai dai kafin ga ɗayansu ya kai ga bata amsa suka ga an yi sama da FAD'IME sannan a ka saketa ta faɗi ƙasa bata gama dawowa hayyacinta ba a ka shiga kifa mata wasu zafafan maruka hagu da dama sai lokacin suka lura da Zulay kacao-kacao da wasu ɗirka-ɗirkan maza biyu dake tare da ita kuma ɗaya daga cikinsu shi ne ya yi ma FAD'IME wannan aika-aika yayin da ɗayan shida da Zulay suke tsaye sai wani numfashin tafarfasan zuciya Zulay ke fitarwa ta riƙe ƙugu tana bin FAD'IME da kallon banza. FAD'IME da mamaki da kuma ɓacin rai ke nuƙurƙususarta ta miƙe tsaye tana karkaɗe jikinta sannan ta dube mutumin ta ce. “Waye kai ɗan uwa kuma waye ya saka ka yi gangancin ɓata lafiyar Dangin Jinnu to ina tabbatar maka da ka taɓo tsuliyar dodo domin ba zamu taɓa lamunta ba dole a yi maka hukunci daidai da abin da kayi.” A tare Laure da Sa'ade suka kalli juna jin kalaman da ke fitowa daga bakin FAD'IME da ta juya musu baya tana fuskantar mutumin sai dai kafin ɗayarsu ta kai ga furta komai Zulay ta wani saki dariyar bosawa tana kallon FAD'IME ɗaiɗai ta ce. “sannu Dangin Jinnu! Nace sannu Dangin Jinnu to ina tabbatar miki da ba Dangin Jinnu ba ko Dangin ifritu ce ke yau ban ga mai hana na lallasaki ba...” Kalaman Zulay suka tsaya cak sakamakon juyowa da FAD'IME ta yi tana fuskantarta idanunta sun sauya kala daga na Brown kamar na mage zuwa baƙi mai ratsin ja. Murmushi FAD'IME ta saki tana faɗin “mene ne na hanzari Aunty kacao-kacao ai sai ki bari nazo kanki ko” Ta faɗa tana ƙari sawa wurin da Zulay take tsaye jikinta na rawa amma duk da hakan ta yi ƙarfin halin faɗin. “ai kuwa dole nayi hanzari tun da har kika shiga gonata a tunaninki zan bari inaji ina gani ne ki auremin miji hahaha ai bazan taɓa bari hakan ta faru ba shi ya sa ma na hayo waɗan nan ɗirka-ɗirkan mazan majiya ƙarfi su lallasa min ke ta yadda ba zaki ƙara moruwa ba har abada. John a fara aiki.” Zulay ta ƙare maganar tana sakin dariyar mugunta tare da kallon Wanda ke kusa da ita, ta yi tana yi masa nuni da FAD'IME dake tsaye ta harɗe hannu ko'a jikinta da jin kalaman Zulay.. *FAƊIME...💋🌸💕* _(Dangin Jinnu)_ ©By Zahrah Royal Star & Nainarh KD 06 Aikuwa mutumin da Zulay ta kira da John gadan-gadan ya nufi FAD'IME yana sakin dariyar ƙeta cike da annashuwa na ganin banza ta faɗi Yarinya kyakkyawa haka a ɓagas. Sai dai me? Taku ɗaya biyu ya yi a na ukun ƙafarsa ta maƙale ya kasa gaba bare baya duk kuwa da yadda yaso sai dai duk da hakan bai haƙura ba ganin wanda suke tare shi ma ya nufa Faɗimen gadan-gadan yana suɗe baki ya sa ya kai hannu zai fizgota ai kuwa saukar hannunsa saman kafaɗar Faɗime ya yi daidai da wani irin azababen duka da a kai masa a gadon baya Yayin da hannun nasa yaji shi tamkar ya sauka a kan wuta saboda wani raɗaɗin azaba da ya ziyarce shi ai kuwa ba shiri ya durƙushe a wurin tare da fasa ihu jin an ci gaba da zuba masa duka a gadon baya. Cike da takaici ɗayan yaja wata doguwar tsuka yana kallonsa ya ce. “amma fa gaskiya John ban taɓa sanin haka kake ba ai ka bada maza Bara kaga yadda cikakken Namiji yake ji da Mace irin wannan kucakar ƴar ƙauyen domin ba Dangin Jinnu ba ko ƴar sarkin Jinnun ce da kanta tun da har an biyani ban ga abin da zai sa na kyaleta ba.” Ya ƙare maganar tare da ƙari sawa wurin Faɗime har da gudunsa yana wani ihu tamkar ɗan kwallon da ya sama nasara. Baya Faɗime ta yi daidai ya miƙo hannunsa da niyyar fizgota ta yi saurin sa hannunta ta riƙe hannun nasa da kyau tare da murɗewa ji kake Hannun ya bada ƙara alamar an karya shi ai kuwa sai ya zube shima a ƙasa yana zambaɗa ihu tare da magiyar ta saki Hannun. Sakin hannun nasa Faɗime ta yi tare da nufar Zulay da ta fara ja da baya cike da tsoro baki na rawa ta ce. “ku...kuyi haƙuri na tuba Wallahi nabi Allah na kuma biku haƙiƙa na yarda Faɗime Dangin ku ne kuma ba wanda ya isa yaja da ita ya zauna lafiya...” Zulay ta kai maganar wani fitsarin tsoro yana ƙoƙarin kwace ma ta hawaye da macijina sun gama wanke baƙar fuskarta. Dariya Faɗime take tana dunƙule hannu ta ce. “me ma kika ce yau zaki saka a mayar dani ta yadda ba zan ƙara moruwa ba ko? To kafin ki mayar dani haka ni bara na fara canza miki halitta tukunna.” Faɗime ta kai maganar tare da saka yatsunta mai cike da ƙumba ta karce gefe da gefe na fuskar Zulay ai kuwa take wurin ya fara fidda jini kaɗan kaɗan Zulay kuwa ta saki ihun azaba tana riƙe fuskarta tare da birgima a wurin faɗi take. “jama'a ku kawo ɗauki Faɗime ta kasheni zane ta yi min a fuska da zaƙwa-zaƙwan ƙunbarta” “mun shiga uku Faɗime ki kyalesu haka kizo mu gudu tun kafin kiyi kisan kai.” Cewar Laure cikin tashin hankali tana janyo Faɗime ai kuwa da gudun bala'i suka bar wurin gudu suke basu dakata ba sai da suka shiga kwanar da zai sadasu da anguwansu Laure sannan ne suka tsaya kowaccensu tana faman sakin numfarfashi na gudun da suka sha. Laure ta ce. “faɗime kin faɗar min da gaba wallahi nayi zaton da gaske ba ke ba ce.” Ita kuwa Sa'ade cewa ta yi. “wai Allah su Zulay kacao-kacao kuma shikenan an yi ma ta zanen barebari.” Gaba ɗaya suka kwashe da dariya. Sa'ade ta ƙara da faɗin. “wai amma Faɗime ba zakiyi wani abu ba haka kina ji kina gani zaki bari gobe a ɗaura miki Aure da wancan Ɗan Abban bayan kin fi kowa sanin halinsa na neman Mata?” Dariya Faɗime ta ɗan yi sannan ta kallesu gaba ɗaya ta ce. “a tunaninku zan bari hakan ta faru ne? Ai ba zata taɓa saɓuwa ba Bindiga a ruwa...” “to yanzu mene ne abin yi?” Laure ta faɗa cike da damuwa. “ai tuni na samo mana mafita, ku matso kuji.” Cewar Faɗime tana sakin dariya ba musu suka ƙari sa ƙasa-ƙasa ta sanar da su shirin da ta ratsa ai kuwa a tare suka saki murmushi cike da farin ciki Faɗime ta ce. “kun ga dama yazo mana a daidai ke nan ko?” Gaba ɗaya suka ce E, Laure ta ƙara da faɗin. “lallai Faɗime ƙwaƙwalwarki na ja.” “hhhh to an faɗa miki ni ɗin jahila ce, ku ƙara matsowa ma kuji wani abu...” Faɗime ta faɗa cike da fariya sannan ta ci gaba da sanar da su yadda shirin nasu zai wakana basu suka rabu ba sai da suka gama tsara komai da zasuyi sannan suka rabu bayan Faɗime ta gama jaddada musu a kan gobe su shirya da wuri sannan ne kowacce ta wuce gida. ______ Ba sallama ta faɗa gidan abin ta tana ƴar waƙarta cike da nishaɗi tana lura da irin kallon da matan gidan ke yi ma ta suna gulma ƙasa-ƙasa amma ta yi kamar bata gani ba sai ma dariya da take yi ta shige Ɗakin Inna Fatuh sai dai bata tarar da ita ba da alama bata dawo ba daga Anguwan da ta tafi hakan ya sa Faɗime ta yi kwanciyarta ba abin da ya dameta ba'a jima ba kuwa bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita duk da lokacin yammaci ne kuma ko can anjima da Inna Fatuh ta dawo ta tarar da ita bata yi yunƙurin tashin ta ba domin a Ganinta hakan babu amfani sai ma tashin hankali da zai biyo baya dan kuwa fitan da ta yi ta sama labarin da ya girgizata a kan batun Auren Faɗime da Ɗan Abba ta kuma fusata da yadda labarin ya zagaye ƙauyen amma ita bata da labari yanzun ma ta dawo ne tana jiran Malam Yahaya ya dawo daga kasuwa ta turkeshi sai ya sanar da ita dalilinsa na ɓoye ma ta batun auren Faɗime da ya yi. Ai kuwa an yi sallar isha'i ba jimawa Malam ya shigo gidan kuma har lokacin Faɗime bata tashi ba dan so take ta yi bacci ta darje dan akwai abin da ta shirya zata yi a daren yau shi ya sa ta nutsu tana bacci cikin kwanciyar hankali domin ta rantse yau babu mai rintsawa a gidan tun da har a ka munafurceta yau ba zata kyale kowa ba kowa sai yaji a jikinsa tun da har ita za'a ɓoye ma ta magana a kan aurenta ke nan da sai dai taji labarin an ɗaura aure... Kai tsaye Ɗakin mahaifiyarsa Inna Fatuh Malam Yahaya ya wuce a nutse ya Gaishe ta tare da fara kama kame a kan ta yadda zai sanar da ita maganar dake tafe da shi dan ya yanke shawarar sanar da ita maganar auren in yaso ya lallaɓata ta yarda ita kuma Faɗime zuwa da asuba zai zaunar da ita ya yi ma ta nasiha mai ratsa jiki sannan ya sanar da ita maganar auren. Da ƙyar ya samu ya iya zayyanewa Inna Fatuh kalaman dake bakinsa. Tun da ya fara maganar har ya kai aya Inna Fatuh ta zuba uban ta gumi hannu bibbiyu tana saurarensa ba tare da ta katse shi ba har sai da taji ya kai aya sannan a fusace ta ce. “ka gama? Nace ka gama surutun banza da wofin e mana banza da wofi mana domin ba zan lamunce ba, amma yahayah ka bani mamaki har lalacewar taka ta kai haka ban sani ba?” Sai kawai Inna Fatuh ta saka kuka tana ci gaba da faɗin. “shikenan zama bai sameni ba, Lami ta gama dani Lami ta mallakemun ɗa wayyo ni Fattuh.” Shi dai Malam Yahaya yana zaune gefe abin duniya ya haɗe masa goma da ashirin domin ji yake muddun bai aurar da Faɗime ba a gobe to fa Akwai matsala, da ƙyar ya iya furta. “dan Allah Inna kiyi shiru ba fa abin da kike tunani ba ne kawai dai ni ne naga hakan ya dace shi ya sa na yanke aurawa Faɗime wannan yaro amma idan na ɓata miki rai bisa ɓoye lamarin da nayi a gareki kiyi haƙuri....” “Yahaya ka tashi ta fitarmin daga ɗaki tun muna mumu biyu.” Inna Fatuh ta faɗa a fusace tana nuna masa hanya ba musu Malam ya tashi cikin sanyin jiki ya fice. Sai Inna Fatuh ta mayar da dubanta wurin da Faɗime ke kwance kamar mai bacci sai dai tun shigowar Mahaifin nata ɗakin ta farka sai dai bata yi motsi ba. “Allah sarki Baiwar Allah marainiyar Allah ta'ala muddun ina raye ban ga meyi miki Auren dole ba.” Inna Fatuh ta kai maganar tana ƙara fyace majiya wai duk cikin tausayin Faɗime sannan ta miƙe tsaye tunawa da ta yi bata yi sallahr isha'i ba ta fita domin ɗauro al'wala. Hakan kuma ya bawa Faɗime damar sakkowa daga gadon na Inna Fatuh da ake kira da mambari ta tsaya tsakiyar Ɗakin tana tunanin ta inda zata fara, murmushi ta saki dan bataso duk abin da zai faru a daren yau Inna Fatuh ta sani tun da ita tana goyon bayanta. Aljihun doguwar rigar jikinta ta saka hannu ta ciro abin da ta siyo ɗazu kafin ta shigo gidan ta yi saurin barbaɗawa cikin miyar tuwon dare a ka kawo ma Inna Fatuh bataci ba, sai da ta juye duka sannan ta yi ma za ta fito daga Ɗakin ai kuwa suka buga karo da Inna Fatuh da gata ɗauro al'wala tana shirin shiga Ɗakin. Washe baki Inna Fatuh ta yi tana faɗin. “ƴar albarka Faɗime na kin tashi ke nan? To ma za kiyo al'wala kiyi sallah sannan kizo mu ci abinci kinji?” Inna Fatuh ta faɗa tana kamo Hannun Faɗime domin tayar da ta yi komai amma ban da abubuwa guda biyu su ne; ƙin yin sallah da kuma zama da yunwa. Turo baki Faɗime ta yi cike da shagwaɓa ta ce. “Ni Inna Fatuh bana jin yunwa kuma zan yi sallahr amma sai anjima yanzu zan je wurin ƙawata Sa'ade ne akwai abuna dana manta ban karɓa ba a wurinta.” “amma kuma ba zaki bari sai zuwa da safe fa Faɗime gani nayi dare ya ɗan yi...” “karki damu Inna ai zan iya kare kaina kuma ba zan daɗe ba yanzu zan je na dawo.” Faɗime ta faɗa tana yin gaba Inna Fatuh ta jijjiga kai sannan ta shige Ɗakin ta gabatar da sallahr taso ta jira Faɗime ta dawo su ci tuwon tare amma ƙamshin miyar kukan dake dakar hancinta ya sa ta gaza haƙura ta buɗe kwanon tuwon ta loda abin ta har da tanɗe hannu a fili ta ce. “yau kuma su Salaha an yi abin kai kome ta sakama miyar nan ta yi wannan maganaɗisun daɗi ohoo.” Inna Fatuh bata yi minti biyar da gama cin tuwon ba bacci mai nauyi ya ɗibeta ai kuwa ta jingine a Wurin tana kwasar bacci. Ita kuwa Faɗime kai tsaye sashen Inna Lami ta nufa ta kuwa yi Sa'a ƙofar a buɗe da sauri ta ƙari sa ciki ta jiyo motsin Lami a bayi, hakan ya sa ta yi wuff ta shige Ɗakin Auta domin muguntar ta kansa za'a fara kwanon tuwonsa ta gani a gefe da alama bai ci ba, murmushin ƙeta ta yi dan kuwa ta san yadda Auta ke muguwar son tuwo ba abin da zai hana shi cin tuwon nan ɗayan maganin dake aljihun ta ta ciro tare da barbaɗewa gaba ɗaya a cikin miyar tuwon Auta ta saka hannu ta juya cike da mugunta tana shirin miƙe wa taji alamun za'a shigo Ɗakin ai da mugun sauri ta ƙari sa bayan ƙofa tare da ɓuya, Auta ne ya shigo yana danna waya da alama chatting yake sai faman sakin murmushi yake yi, da sauri ganin ya juya baya Faɗime ta yi wuff ta fice daga Ɗakin, shi kuwa Auta zama ya yi tare da buɗe kwanon tuwonsa ya naga abin sa yana ci gaba da chatting ɗin sa hankali kwance. Faɗime fitowa ta yi daga ɓangaren Inna Lami duk da bata gama da su ba amma zata fara komawa shashen sauran mutan gidan Matan yayyi da ƙannin mahaifinta duk ta yi musu abin da ta shirya dan ta rantse yau dai babu mai yin Bacci a gidan.... *FAƊIME...💋🌸💕* _(Dangin Jinnu)_ ©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star 07 Inna Khande ce ta fito daga band'aki, Matar K'anin Malam ce, kamar ance ta waiga taga iniwara mutum tsaye a kanta. Zaro ido waje tayi y'an cikinta suka hautsina, bata san lokacin data saki butar dake rik'e a hannunta ba. Wata shegiyar dariya mai amsa kuwwwa Fad'ime ta kece da ita, wadda tasa Inna Khande idasa rud'ewa had'e da sakin wani marayan kuka. Domin ta gefen idonta take ganin wata mace sanye da farar kaya sai ta zama fatalwace tsaye a gefen nata. "Na shiga uku na lalace ni Khande, yau kuma miye nayi gamu dashi a tsakiyar daren nan?". "hhhhhhh Inna Khande kike kowa?". "It....ita...ita ce wallahi Khande nake". Ta idasa maganar jikinta na d'aukar rawa kamar mazari. "Dan girman Allah kumin rai wallahi tallahi ban san miye nayi maka ba kuyi hakuri ku kyale ni na tafi". "Hhhhh yau gaba d'aya gidan nan sai kun gane shayima ruwa ne, ubanwa yasa a had'a munafurci daku ace za'ayi ma Fad'ime auran dole shine ku kuma munafikai, kukayi shuru to yau jikin kowa sai gaya masa mun rantse" "Innallihi wa'inna alaihir raju'o.. Wani uban bugu da aka kaima bakinta ne yasa Khande datse salatin data d'akko. Dafe bakinta tayi da take jin lokaci d'aya ya haye yayi suntum, ga wani azababben zafi da yayi ma Kwakwalwar kanta dirar mikiya, wasu sabbin hawayen ne ya sake b'arke mata akan fuskarta. Bata san lokacin data fasa k'ara had'e da rugawa da gudu ta shige d'akinta har tana bangaje k'ofar d'akin ta bada wani sauti karauuuuu. "Innallihi wai Inna miye haka Kinga yadda kika fad'o d'akin nan kuwa?". "Ke da'aAllah can rufe min baki ki..... Dariya ce ta sarke ta tana nuna Inna Khande da hannu harda rik'e ciki. "Bura'uban can, ni kike ma dariya Halima?, dan kund'in ubanki". "Hhhh Inna baki ga yadda bakinki ya haye yayi suntum bane shi yasa, wallahi abun gwanin ban dariya fa, dan Allah Inna miya Koro ki haka ne daga zuwa bayi". Sauk'e lumfashi kawai Inna Khande keyi tana kallon K'anwarta wacce yau suka zo bikin Fad'ime da ake shirin yinsa gobe. "Na rantse da Allah Halima gamo nayi a hanyar band'aki". "Gamo kuma Inna Khande?, ko dai kawai tsoro ne kika sama kanki, yanzu baka babu abunda kika gani". Inna Khande zatai magana su duka suka fara jin wasu maganganu sama-sama had'e da ihu yana fitowa daga sansa na gidan. Wata zufa ce ta yanke koma Inna Khande ba shiri ta ruga a guje tana matsawa sosai inda Halima take, itama tayi mutuwar tsaye. K'ank'ame juna sukai suka cure waje d'aya. Zaro ido Halima tayi tana duban Inna Khande a hankali kamar mai tsoron magana ta ce. "Inna Khande mun shiga uku, dama gidanku nada aljanu ban sani ba?". "Na rantse da Allah nima yau na fara ganinsu" "Amma gaskiya kin cuceni Inna Khande miye yasa kika bari na taho bikinga baki gaya min, akwai Tanbotse a wanga gida naku ba na shiga uku nahh ni Halima". Ta k'are maganar jikinta na d'aukar rawa domin wata iska suka ji tana busosu had'e da wani irin kuka irin na aljanu irin kamar kana cikin mak'abartar nan haka suke juyowa. Wani mugun duka suka ji an kaima bayansu ba shiri suka saki juna suna sakin ihu. Kamin su gama dawowa dai-dai suka ji an gwara kansu waje d'aya ji kake gummmmmm. "Wayyo wayyo Allah na shiga uku kaina zai fashe". Kusan a tare suka fad'i hakan. A d'akin Inna Lami ma a kwance take sai nishari take kawai bata san hawa ba bata san sauka ba taji an zuba mata wani gigitaccan mari akan kumatunta. Wani uban ihu ta saki had'e da tashi a haukace tana cewa. "Na shige su ni jikar mutum hud'u, mafarki nake ne ko gaske wannan ne irin Mari ne haka aka d'auke ni dashi a cikin bacci?" Duk maganar da take a rud'e take yinta, tana faman dube-dube, da kuma dafe a k'uncinta. Saukar bulala taji a gadun bayanta wadda tasa ta d'auke numafashi had'e da wata irin gantsarewa, na azabar zafin da ya kewaye kwanyar kanta. Ihun data saki ma ciki-ciki tsabar yadda bulalar nan taji ta. Bata ga wadda ya zuba mata bulalar ba sai wata murya dake mata amsa kuwwwa a cikin kunnanta. "Hhhhhh Lami wato ke muguwa ko?, kin zuga Malam yayima Fad'ime auran dole ko?, ai ko yau sai kin gwamce dama baki je kika had'u wannan tungun naki ba, daga yau bazaki sake marmarin shiga gonar god'iyarmu ba hhhhhhhh". Dariyar da aka idasa maganar ce tasa Lami zubewa k'asa tana fashewa da wani kukan tausayi tana had'e hannunwanta waje d'aya murya na rawa take cewa. "Dan girman Allah kumin rai na rantse da Allah ni banyi abun nan dan na musguna mata ba, ai gani na gata nayi mata kawai bawai bana sonta bane ai". Wata bulalar aka sake zubama Inna Lami wacce tasa Lami sakin fisarin dole tana sake fashewa da kuka. Abunda ya k'arasa Inna Lami rud'ewa kuwa shine d'agowar da zatai taga wata mace sanye da wasu kaya farare tass dogowa tsawonta har ya wuce misali ga bakinta dake zubar da wani irin jini bak'ik'k'rin dashi, kwarin idonta kuwa fari ne tass babu d'igon bak'in nan idonta cikinsu fari tass. Wani uba-uban ihu Inna Lami ta saki tana furta. "Wa'innahu sulemanu wa'innahu biss..... Bata idasa maganar da take son fad'a ba taga matar na nufo inda take haba wa, tuni Inna Lami ta zube a sume a wajan. Wata dariyar aka kece da ita matar ta b'ace bat kamar ba'a tab'a wanzuwarta a wajan ba. _______ Auta dake chatting d'insa sai murmushi yake hankali kwance. Wata zabura yayi yana sakin wayar dake hannunsa ya mik'e tsaye ba shiri jikinsa na d'aukar rawa. A cikin wayar yana cikin chatting d'insa kawai a fuskar wayarsa yaga hoton Fad'ime tana masa wani mugun kallo na gargad'i. "Kai ko dai ba gani nayi ba sosai, ya za'ai naga aljanar yarinyar can a wayata, kai gizo kawai take min ai hakan bamai yiyuwa bane ma". Hannunsa ya kai zai d'auki wayar yaga an zanye wayar daga inda take, an matsar da ita daga inda take. Zaro ido waje Auta yayi nan take ya sake shiga wani yanayi tsananin rud'ani, had'e da wani masifaffen tsoro da ya mamaye masa zuciya da ruhi. Curewa Auta yayi waje d'aya yana kallon wayar, koda gigi bai k'ara kai hannunsa domin tab'a wayar ba. Gani yayi wayar na matso shi tana nufo inda yake, yanzu wayar a sama take, ita ba sama ba ita ba k'asa ba. Matsawa ya rink'ayi tana matso shi haka suka rink'a yi yana zagaye d'akin. Tun yana yi a hankali ya rink'a gudu a cikin d'akin, tun yana yi ta dad'in rai har ya fara gajiya, sai zufa ke yanko masa. Wani gigitaccan mari aka d'auke Auta dashi ne yasa shi damtse bakinsa da k'arfi yana hana ihunsa fitowa fili. K'ara d'aukesa akai da wani marin a d'ayan kuncinsa nanma da k'arfi ya rufe bakinsa da tafin hannunsa. Ba abunda yake sai hawaye dake zubo masa. Wata irin murya ce ta cika masa kunne wacce zai iya rantsuwa da Allah muryar nan zata iyasa ma mutum sumewa nan take tsabar rashin dad'inta da ban tsoro. "Hhhhhhh Auta kayi kuskuren marin Fad'ime god'iyarmu, saida tayi maka gargad'in hakan, amma kai mai kunnan k'ashi baka ji ba ko? Sana harda kai ake bada shawarar aurar da Fad'ime ko?" "Na rantse da girman Allah ni babu ruwa na a cikin auran da za'ama Fad'ime, wallahi Inna Lami ce ta fara kawo shawarar" "Shine kai koma ka biye mata kuka zuga Malam ko?" "Wallahi a'a hi.... Ni... Ni babu ruwa a cikin wannan abun, kuyima girman Allah ku kyale ni karku cutar dani". Ya k'are maganar had'e da fashewa da kuka. Domin wata inuwa ya fara hangowa ta gefensa tana nufo inda yake tsaye jikinsa na sake d'aukar rawa.. _______________________ *SAL Estate, Shehu Shagari Way Abuja Nigeria* Haj Saratu ce zaune tana kallon Firdausi dake zumin d'in had'a kayan abinci da za'a tarbi Young SAL. Rawar kanta wajan SAL tayi yawa hakan yasa Haj Saratu ta kamo hannun Firdaus dake ba y'an aikin gidansu umarnin su gyara wajan sosai. "Amma Miya faru?" Cewar Firdaus. "Ya kamata Firdaus ki rage yawan rawar kan nan da kike akan SAL d'in nan haka nan" "Amma, bazaki gane bane ina bala'in son Young SAL" Tab'e baki kawai Haj Saratu tayi tana sake kallon Firdaus zata sake magana suka ji shigowar Sudas K'ani ga Firdaus d'in, wadda su biyu ne a wajan Haj Saratun. Kallonsa Haj Saratu tayi tana cewa. "Kai kuma lafiya da shigowa ba sallama?". "No Amma am sorry, naga motocin Young SAL ne sun shigo, kawai sai na tsaya har ya kama fitowa, abun mamaki kawai na gansa da wasu yara guda biyu, kamarsu d'aya da juna kamar y'an biyu, kuma wallahi Amma kamarsu d'aya da SAL, duk wadda ya gansu gaya jinin Young SAL na asali, tabbas kamar shine ya haife su". Wata irin zabura had'e da mik'ewa tsaye Haj Saratu tayi, ba shiri. Firdaus kuwa da gudu ta fice harabar gidan domin gane ma idonta abunda Sudas ke fad'i. "Sudas kana da hankali kuwa? Ya za'ai ya tafi shi d'aya k'asar waje kuma ace yau rana tsaka an ganshi tare da Yara har biyu, kuma masu kama dashi? Inahh koda Sudas baka gani sosai bane?". "Na rantse da Allah Amma da gaske nake, zo ta bakin window ki gani". Kamo hannunta yayi ya matsar da ita bakin window tana iya hango harabar estate d'in motoci ne jere sai kace wani d'and'an shugaban k'asar ne ya dawo. Gaban Haj Saratu ne ya bada wani sauti dummmm dummm dummmm. Sakamakon tozali da tayi da wasu y'an biyu mace da namiji sunsha kaya iri d'aya da SAL d'in, kamarsu dashi harta b'aci, kowa waye yaga wa'innan Yara tabbas nan take zai iya rantsuwa da Allah nashi ne na cikinsa. Sauke wani irin huce Haj Saratu tayi tana dafe kanta dake take ji lokaci d'aya na sara mata. Rik'eta sosai Sudas yayi yana d'an tab'e baki yana kallon window yadda SAL ke tafiya cike da izzarshi wacce ta riga da ta zame masa jiki. Da kyar suka kai kujera Sudas yana kallon Amma a hankali ya ce. "Nifa dama na tsani wancan Safiuddin d'in can, saboda Jiji da kansa yayi yawa, yana d'aukar kansa wani shege ni shi, ni kuma nake ganin duk matsayi d'aya muke". Tashi tsaye Haj Saratu tayi tana cewa. "Dole ne naji a ina ya samo wa'innan yaran, Allah yasa ba zargin da nake yi bane ya zama gaskiya, idan ko haka ne magauta na gidan nan namu zasu samu yi mana dariya, saboda akwai y'an matan family d'in nan dake tsananin sonshi, amma aka hanasu aka y'ata, itama kuma Saida na dage na mik'e tsaye har Alhaji Sa'id Ahmad Lamid'o ya yarda Young SAL ya auri Y'ata, dole ne na riga jin miye ya kawo wa'innan yaran a tare dashi". Shuru Sudas yayi domin ya lura Amma tayi nisa tama manta da wadda take magana. ______________ "Kee koma miye kika sakko kina murmushi haka" Kallon Mahaifiyarta tayi tana idasa sakkowa k'asa ta zauna a kusa da ita ta nuna mata wani photo dake cikin wayarta. Zaro ido waje tayi ta mik'e tana cewa. "Kee Asma ina kika samu wannan pic d'in, na SAL da wa'innan Yaran?". "Hhhh Momy kenan ai tunda Alhaji ya ce ya zab'i Firdaus a matsayin matar SAL nake addu'ar Allah ya kawo abunda zai sama tarwatsa wannan had'in, sai gashi rana tsaka anga SAL ya dawo da Y'ay'anshi shegu daya je yayo cikinsu a k'asar waje, ya dawo da abun kunya a cikin Family" Zama Momy tayi tana d'an jin wani abu a zuciyarta kamin ta ce. "Ai tunda Haj Saratu ta tari gabana to tabbas itama tasan bazamu wanye lafiya ba, duk da tana matsayin Ƙanwar mijina, tasan abunda na dad'e ina burin Y'ata ta auri SAL shine tayi min d'aurin goro taje ta had'a mugun abu har Alhaji Sa'id ya amince yaba ɗan ɗansa Magajin dukiyarsa ita, hmmm lallai naji dad'in wannan labarin saura kuma mu tsaya jin miye zai biyo baya"....... *FAƊIME..💋🌸💕* _(Dangin Jinnu)_ ©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star 08 Dawowarsa ke nan daga masallaci sallahr asuba har ya yi gaba sam bai lura da ita ba ganin haka ya sa ta ce. “Baba!” Da sauri ya juya sai kuwa ya yi ido huɗu da Faɗime tana tsaye har ta so ma ta ba shi tsoro, domin sam bai lura da ita ba. “Fatima me kike yi anan?” Malam ya tambaya da mamaki. Faɗime tana shirin magana ta hango fitowar Auta daga banɗaki yana dafe bango cike da gajiya domin kwana ya yi yana zarya zuwa bayi. Gimtse dariya Faɗime ta yi gudun kar Malam ya ɓaro jikinta shi kuwa Malam ganin inda take kallo ya sa shi mayar da dubansa zuwa wurin. “Zubair! Lafiya kuwa kake riƙe bango kamar mai naƙuda?” “Ba..ba bakomai Baba dama gudawa nakeyi tsawon dare shi ya sa duk nabi na galaɓaita” Auta ya faɗa tamkar ya fashe da kuka. Juyawa gefe Faɗime ta yi tana sakin dariyar ƙeta tana ji Malam yana yi ma Auta faɗa a kan yawan ciya-ciye daga ƙarshe ya yi masa sannu ya kuma taimaka masa ya koma Ɗakin. “ƙari so ciki dama ina so nayi magana dake.” Malam ya faɗa lokacin da ya dawo da kallonsa kan Faɗime. Ba musu tabi bayansa har zuwa sashensa ta zauna saman tabarma tana jira taji ta yadda sai fara. “wato Fatima wani babban laifi nayi miki ban kuma san ta yadda zaki karɓa al'amarin ba.” Faɗime ta ɗa go tana yi ma mahaifin nata kallon ƙasan ido, wato ya ɗauka batasan komai ba ke nan. “Wani abu ne ya faru Baba?” Ta faɗa cikin ladabi kamar ba ita ba dan ta ƙosa ya yi ya gama ta fice ta aiwatar da ƙudirinta. “dama...” “ai Bama abin da ya faru kawai dai ni ce na yanke shawarar kaiki Birni aikatau ai kina so ko?” Lami da ta yi wuff ta shigo Ɗakin ta katse Malam da yake shirin magana da faɗin hakan. Da kallon mamaki Malam ya bita, yayin da Faɗime ta saki murmushi a zuciyarta ta ce. ‘lallai su Inna Lami anji Uwar bari an canza taku.’ A fili kuwa sai cewa ta yi. “Birni kuma ni ba zan je ba” Ta faɗa tana miƙe wa tsaye ta fice daga Ɗakin tana sakin dariya domin kuwa ita a nata tunanin faɗuwa ce tazo daidai da zama. Gidan ta fice gaba ɗaya kai tsaye ta wuce zuwa gidansu Sa'ade, a hanya suka ji karo da Sa'ade dake ta faman sauri tana waige-waige ga tumin kaya a hannunta. “laa Faɗime ashe kece ni wallahi har kin ban tsoro amma ina naki kayan ne kodai ba zaki tafi da komai ba?” Sa'ade dake ta faman zuba ta yi shiru ganin Faɗime tana dariya. “ke ni barni da wannan zancen dan ya zama tsoron labari yanzu dai batun aure babu...” Sa'ade ta zazzaro ido waje sai kuma cike da zumuɗi ta ce. “amma naji daɗi sosai hahaha cike su Inna Lami an ji uwar bari ke nan bani labari yadda ta kaya.” “hmmm ke dai bari kawai domin labarin da tsayi a taƙaice dai yanzu ta ce Aikatau zata kaini Birni....” “Aikatau kuma?” Sa'ade ta katse Faɗime tana zazzaro ido. “matsalata dake Sa'ade bakyajin ribar zan ce ki bari mana na kai aya.” Cewar Faɗime, sannan ta ci gaba. “eh kuma da fari zan nuna banaso sai da ƙyar zan amince idan kuma naje ba aikin zan yi ba zai dai kasance na sama hanyar zuwa birni domin cika burina na zama Mawaƙi” Faɗime ta kai maganar tana lumshe ido cike da zumuɗi bata jira Sa'ade da mamaki ya sa ta kasa magana ba ta ci gaba da faɗin. “saboda haka yanzu kije tun kafin Laure ta fito ki faɗa ma ta labari ya sauya ba batun guduwa.” Faɗime tana gama maganar ta juya abin ta zuwa gida domin zumuɗin zuwa birni take. _____ DA RANA Inna Lami ce durƙushe gaban Inna Fatuh tana faman yi ma ta magiya a kan ta bari a tafi da Faɗime Birni aikatau a gobe. Yayin da Faɗime take zaune gefe tana faman kai loma kamar batasan abin da ke wakana ba. “ke Lami nafa san ba mutunci ne dake ba ki faɗa min abin da kike shiryawa da kike wannan magiyar a kan na bar Faɗime taje Birni aikatau salon ki cutar min da ita ko to kuwa ba zata saɓu ba ehe wato saboda kin ga auren bai yiwu ba shi ne kika ɓullo ta nan.” Inna Fatuh ta ƙare maganar tana bin Inna Lami da kallon banza. Wani takaici ya cike Lami amma ta daure domin ita kaɗai ta san abin da take shiryawa a kan zuwan Faɗime Birnin, hakan ya sa ta ce. “wallahi Inna Fatuh ba abin da nake shiryawa kawai dai nayi nadama ne da irin abubuwan da nake yi ma Faɗime a da.... ouch” Ta kai maganar tare da sakin ƙara na azaba sakamakon wani tsunƙuli da a ka yi ma ta a baya. Faɗime ta saki dariyar mugunta a fili da hakan ya sa duk suka dubeta sai ta ma ze da faɗin. “Inna Fatuh kawai ki yarda kika sani ma ko na samo zuƙeƙen miji a can Birnin” Washe bari Inna Fatuh ta yi jin kalaman Faɗime sai kawai ta duba Lami dake sakar ma ta harara a fakaice. “to ai sai ki tashi ki bani wuri tun da ta amince kuma kada ki kuskura na gano kina shirya wani abin ne dan ba zan kyaleki ba.” “ai Inna Fatuh ba ma abin da nake shiryawa.” Cewar Lami sannan ta bar wurin cike da farin ciki ta lalubo ƙaramar nokiya ɗin wayarta ta kira Dillaliya ta sanar da ita halin da a ke ciki. _____ “wai Faɗime shikenan yanzu tafiya Birnin zakiyi?” Laure ta tambaya lokacin da su ukun suka haɗu a wurin da suka saba haɗu wa. Sai da Faɗime ta gwagwiyi goribar hannunta sannan ta ce. “da gudu ma, ke Laure ko dai baƙin ciki kike min ban sani ba?” Da sauri Laure ta ce. “Ni a wa Allah baki haƙuri kawai ina jajatawa ne zamuyi kewarki” Sai Faɗime ta yi dariya tana faɗin. “mu je nayi ɓarna na ƙarshe kafin na tafi birni domin ban san ranar dawowata ba.” Ɗunguma suka yi suka nufa hanyar fadamar mai gari da suka ɗibo rake jiya. ____________ Hajiya Saleema uwar gidan Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo tana da yara huɗu sun haɗa da Alhaji Ahmad da shi ne Babba sai kuma mai bi masa Eng. Khamis sannan sai Alhaji Tasi'u da kuma Prof. Ridwan sai kuma Auta wato Hajiya Saratu... Sannan sai Hajiya Haleema yaranta biyu, Alhaji Dauda sai kuma Hajiya Laraba. Duka suna zaune ne a SAL Estate tare da iyalansu baki ɗaya. Hajiya Saratu wato mahaifiyar Fidaus ta kasance mace ce da bata yarda wani yafita da komai ba zata iya aikata komai muddun wani muradi nata da ta saka a gaba na son duniya zai cika sam bata yarda da faɗuwa ba al'amarin ta shi ya sa sam basa shiri da Mommy Matar Alhaji Dauda kasancewar Mommy ita ma halinta kusan ɗaya ne dana Hajiya Saratu na son abin duniya sai dai ta wani ɓangaren sun sha bamban. Kowacce tana Burin ganin tafi ɗaya a komai shi ya sa har yaransu sun taso a haka sam basa wani ga maciji tsakaninsu kuma hakan ya samo asali ne daga iyayen nasu mata, domin su iyayen maza kullum burinsu bai wuce ganin kan yaran nasu ya haɗu ba. Alhaji Ahmad SAL yana da mata biyu Hajiya Zakiya da ake kira da Mamy sai kuma Hajiya Lubabatu da a ke kira da Nur. Mamy yaranta huɗu curr, Salim, Maryam, sai kuma Muhammad da Saddika, yayin da Hajiya Lubabatu take da yara Biyar duk da kasancewarta mace ta biyu a gidan Alhaji Ahmad SAL sai dai ita ce macen da ya fara so tun ƙuruciya yayin da Hajiya Zakiya ta kasance auren haɗi a ka yi musu sai daga baya ne ya Aura Hajiya Lubabatu wato Nur, kuma ita ce mahaifiyar Safiuddin, Safiya ita ce ƴarta ta fari sai kuma Safiuddin mai bi ma ta sannan sai Jalil da Jalila twins sai kuma Auta Shaheeda. Shekarun baya Mahaifan Safiuddin suka yi hatsarin mota lokacin suna tare da Jalilah a motar gaba ɗayansu babu wanda ya yi rai. Zo kuga tashin hankali wurin waɗan nan Ahali sosai suka girgiza da wannan mutuwar musamman ma Safiuddin da ƴan uwansa. Prof Ridwan Matarsa ɗaya yaransu biyu rak, mace da namiji kuma suna zaune a ƙasar Faransa har wa yau kasancewarsa Ambassador. Haka ma Eng. Khamis da Alhaji Tasi'u duk matansu ɗaiɗai kuma kowannensu Allah ya azurtashi da yara. Sai kuma Alhaji Dauda Mijin Mommy matansa biyu Mommy ce ta biyu yayin da Hajiya Saima da ake kira da Ammiey ta kasance ta farko, Mommy yaranta biyu Asma da Fahat sai kuma Junaidiya da Sudais da kuma Firdaus yaran Ammiey. Tsayawa ƙiyasa adadin familyn SAL ba abu ne mai sauƙi ba mu dai afka gadan-gadan cikin labarin a hankali za'a san kowa kuma halin kowa ya bayyana mu dai ci gaba da gashi kawai....🔥 *FAƊIME...💋🌸💕* _(Dangin Jinnu)_ ©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star *Dedicated to Salma Ahmad Isah (Candy)* *بسم الله الرحمن الرحيم* *A love & Laugh story that will capture your heart and soul.* 09 *FAD'IME POV* Inna Lami dake kallon Fad'ime shirye take domin yau aminiyarta Inna Zubaida ita ke dillancin kai Yara aikatau tunda sanyin asubahi tayi mata a gidan su Fad'ime. Jikin Inna Lami har yana rawa wajan zuwa k'ofar d'akin Inna Fatuh domin taso k'eyar Fad'ime su wuce. "Wai nikam Lami wannan sammako haka tunda uwar safiyar nan, miye kike buk'ata ne?". Fad'in Inna Fatuh tana kallon Lami data fad'o masu d'aki tunda uwar safiya. Sosa k'ayarta Inna Lami tayi tana inina wajan fad'in. "Uhum uhum....da...dama...dama ga wacce zata tafi da Fad'ime can ta zo domin tafiyar wuri take". Wani kallon rashin gaskiya Inna Fatuh ke bin Lami dashi d'an tashi tayi tana kallon Fad'ime dake bacci hankalinta kwance ta b'ararraje akan gadon Inna Fatuh sai baccinta take. "Wace irin tafiya ce haka tunda sanyin asubahi?, to gaskiya bada ni ba wallahi domin sanin kanki ne kin san ba'a tayar da Fad'ime idan tana wannan baccin nata, idan ko tsautsayi yasa ka tayar da ita wallahi kaine masha wuya". Wani duba Inna Lami tayi ma Inna Fatuh a zuciyarta zai dannk'ara ma Inna Fatun zagi take, a fali kuma ta saki murmushin yak'e tana cewa. "Haba Inna Fatuh ai ke babu abunda take miki idan kika tayar da ita d'in, kawai ki tada ta ko sun wuce kar waje ya k'ure, karma ta ce ta fasa kaita wajan aikatau d'in". Inna Fatuh zatai magana Fad'ime ta saki hamma mai sauti had'e da wata mik'a ta bud'e idonta, domin tun d'azo take jin y'ar hayaniya a cikin d'akin, maganganun su ne suka tayar da ita. D'an tashi tayi tana duban Inna Fatuh da Inna Lami dake tsaye a tsakiyar d'akin d'an sak'o k'afarta tayi k'asa tana duban Inna Lami ta kalli Inna Fatuh tana turo baki gaba ta ce. "Inna Fatuh sai hayaniya kuke min har kun tayar dani, Fisbilillahi basai ku fita waje kuyi firar tak'u ba". D'an murmushi Inna Lami ta saki tana maganar zuci. "Kaji y'ar iskar yarinya, ai insha Allahu idan na samu kika tafi keda gidan nan har abada wallahi, domin ba wani aikatau d'in da zaki je inda za'a wargaza rayuwarki can zakije, ai dama nayi rantsuwa bazan tab'a bari ki zama wani abu ba Fad'ime, ba aljanu ba, ko kuka ce a kanki inda za'aje dake yau sai kin Gwammace kid'a da karatu, ke saima kinyi danasanin zuwanki duniya Dan........ Maganar da Inna Fatuh ke mata ce ta katse maganar zucin da take fad'a tana yi ma ta kallon Fad'ime tana jefanta da murmushi, mai cike da gugar zana. "Wai ke Lami tunanin miye kike haka?, sai magana nake na jiki Shuru, sai kallon Fad'ime kike kina murmushi, shin wai ko dai akwai muguntar da kike k'ullawa ne?, nifa tun farko ban yarda dake ba dama". Fad'in Inna Fatuh tana k'arema Inna Lami wani kallon tuhuma sosai. Cike da d'an firgice ta maze tana cewa da sauri "Haba Inna Fatuh ki daina min irin haka mana, miye zan k'ullama Fad'ime ne, da duk da banyi mata mugunta ba sai yanzu kuma". Tab'e baki Inna Fatuh tayi tana cewa "Yo waye ya sani abu a duhu, kuma ai waye bai sanki ba da can baya, idan banda ido na, da bana raye Allah kad'ai yasan abunda zaki yima wannan marainiyar Allahn ai wallahi ke kima yi istigfari Lami waye bai san baki k'aunar Fad'ime ba" A fakaice Inna Lami ke hararar Inna Fatuh dake maganar. Fad'ime ta saki wani murmushin gefen baki tana duban Inna Lami ta ce. "Nifa Inna Fatuh nama fasa tafiyar nan wallahi, domin wani mafarki nayi akanta, dan haka bazanje ba". Baki a bud'e hankali a tashe kuma Inna Lami ke saurin fad'in, sai dai tun kamin ta fad'i abunda ke cin ranta, Inna Fatuh ta tari hanzarinta. Da fad'in "shikenan falin lahil amdu, ai ni dama can ban wani ji tafiyar nan a raina ba, saboda nasan bak'in hali irin na Lami, tana iya kai ki inda za'a datse lumfashinki". Baki na rawa Inna Lami ke fad'in. "Haba Fad'ime wai kuwa kin san irin gidan da za'a kaiki kike fad'in baki zuwa, gida ne irin na y'an gayu mai bene sama da k'asa, gashi har makaranta za'a sakaki, kiyi kallon abubuwan duniya, amma kina zaune a k'auyen nan miye zaki sani a duniyar nan, da abunda ke cikinta, koni nan da dai basa son Manya ai ni ce zanje bake ba wallahi, ki dai yi shawara Fad'ime kar ayi tafiyar nan babu ke". D'an shuru Fad'ime tayi, tana tunani, hak'ik'a tana son birni ita mayiyar son zuwa cikin birni ce, da son ganin abunda ke cikin birnin, to amma kafin tashinta tayi wani mafarki wata mata tazo mata tana jaddada mata cewa karta sake ta yarda da tafiyar da Inna Lami take ta matsawa tayi, tana gama fad'a mata haka ta b'ace shine ita kuma ta farka kawai ta iske Inna Lami a cikin d'akin, suna magana akan tafiyar da aka gama gargad'inta da kar taje a cikin baccinta. Inna Lami dake kallon Fad'ime tana d'an murmushi ganin maganar tada fad'a mata kamar tayi tasiri a cikin ranta, domin ganin yadda ta fad'a duniyar tunanin. "Uhuhmm kuma fa hakane Inna Lami tabbas ina son ganin yaya birni yake, domin idan na dawo naba K'awaye na labari, domin garin nan mutane d'ai-d'ai ne ke zuwa birni". Fad'in Fad'ime tana duban Inna Lami dake murmushi sosai a yanzu. "Yawwa ashe kin gane, kuma idan kece kika fara zuwa birnin nan kamin su, ai kin wuce da ajinsu nesa bama kusa ba, zaki dawo y'ar gayu a k'auyen nan namu, ki dawo kinfi kowa iya d'aukar wanka". Dariya Fad'ime ta saki tana sakkowa ta kalli Inna Fatuh data saki baki da hanci tana duban Inna Lami dake murmushi kamar ta Allah. "Inna Fatuh ki had'a min kayana zanje birnin aikatau d'in yanzu". Rik'e baki Inna Fatuh tayi ta dafa kafad'ar Fad'ime tana ji gabanta na d'an fad'uwa da tafiyar Fad'imen, domin Allah ya sani har cikin ranta bata aminta da tafiyar ba, bata kwanta mata a rai ba. "Fad'ime miye ya canza miki tunanin a d'an k'ank'anin lokaci haka?, ke nan yanzu har Lami zata gaya miki magana ki yarda lokaci d'aya, har tayi sanadiyar canza tunaninki a d'an lokaci haka?". Turo baki Fad'ime tayi tana ji itafa Allah wallahi saita je birnin nan, domin Inna Lami ta gama saka mata rai da abubuwan k'aryar data shinfid'a mata. Ganin rigimar da take son farawa yasa Inna Fatuh cewa da sauri. "Allah ya baki hakuri bari na had'a miki, indai birni ne gaki can kinje ai, ni bana son ganin b'acin ranki ai. Duk dai inda kike ai k'aryar mutum ya iya cutar dake a'ato, idan ma mutum ya manta gara ya tuna". Ta k'are maganar had'e da gogar zana da take ma Inna Lami. Inna Lami kuwa tana jinta sai ma jawo kayan Fad'ime tayi ta cewa bari ta had'a mata da kaina ma, ba sai Inna Fatun ta had'a ba. Abunda Inna Lami take da zumud'in tafiyar nan ta Fad'ime fa, k'ara ba Inna Fatuh mamaki yake had'e da tsoron wani abu take shiryawa wallahi. Auta ne yayi sallama a k'ofar d'akin Inna Fatuh yana cewa. "Inna ki fito ga Haj Bintoto can fa ta fara gajiya da jiranki. Ita kuma Fad'imen da ake jira dan ubanta bata fitowa ne ita zatai jira ne?". Fad'ime data dawo d'akin yanzu bayan ta wanki idonta tayi tsakar tsaka tsami tana saka kaya da sauri sai zumud'in tafiyar take sosai. Turo baki tayi tana murgud'a ma k'ofar d'akin Inna Fatuh baki had'e da harara kamar Auta ne take gani wajan. Inna Lami da sauri ta jawo hannun Fad'ime da k'ullin kayanta ta ce. "Kai Auta ina ruwanka da ita, bana son irin haka fa tom". Auta dake murmushin gefen baki shima yabi Fad'ime da harara yana cewa. "Kai yau dai zamu huta da kawo k'arar shaid'aniyar yarinyar nan, haba mutum yana mutum amma kamar Aljani tsabar jaraba da rashinji, anya Fad'ime ba rabi aljan rabi mutum aka haifeki ba kuwa?". Dak'uwa Inna Fatuh tayi masa tana binsa da wata uwar harara tana cewa. "Kai Auta ka fita ido na, na rufe na rantse da Allah ka kiyaye ni fa". Gaba Auta yayi bai tankama Inna Fatuh dake masa masifa har lokacin ba. Inna Lami dake cikin d'akinta bayan ta fito da Fad'ime ta barta waje ita dasu Inna Fatuh da Auta. Ta kalli Bintoto a hankali tana cewa. "Bintoto kin tabbatar gidan yankan kai zaki kaita?". Bintoto dake murmushin cin nasara da samun kud'in da zatai idan ta kai Fad'ime wajan Alhaji Bukhar, ba k'ananun kud'i zata samu ba, harma da ita Inna Lami za'a bata wani abu daga ciki, shi yasa ma ta amince. Kallabin dake kanta ta k'ara turo shi gaba, domin daka kalli yanayin Bintoto zaka shaida y'ar duniya ce ta gidan gaba, sai wani taunar chingum take idonta kansa an baura masa kyalli, ta ce. "Haba Lami sai kace baki sanni ba, ai nake gaya miki idan Fad'ime ta tafi ta tafi kenan bazata tab'a dawowa ba, kuma nake sanar dake ba gidan yankan kai zan kaita ba, kamar suna anfani da mata ne suna tsafi dasu, kamar k'ungiyar asiri dai haka, ai kina jin labarinsu ko?". "Eh tabbas muna jin labarinsu, dama duk masu kud'in nan dake cikin birni ai da yawansu ba kud'in Allah da Annabi bane, na tsafi ne". "Yawwa, tun da kin gane mubar maganar a nan saina dawo zan taho miki da naki kason, domin Alhaji Bukhar ya dad'e yana neman yarinya budurwa mai shekaru irin na Fad'ime ba'a samu ba, sai ni ya ba cigiyar ya ce idan har na samo masa zai bani kud'i masu yawan gaske, dan haka kema dole ki samu kud'i masu yawa daga ciki". Wani kalar murmushi Lami ta saki tana kallon Bintoto kamin zatai magana suka ji muryar Inna Fatuh na cewa. "Wai Ina Lamin ne, da ita Bintoton miye kuke k'ullawa ne cikin d'akin, idan ba rashin gaskiya ba ai sai ku fito waje kuyi maganar da zakuyi mana". Da sauri Lami ta kamo hannun Bintoto suka fito tana fad'in. "Haba Inna Fatuh miye zamu shirya kuma?, kawai fa ina sake gaya mata ne ta kula da Fad'ime sosai". Wani kallo kawai Inna Fatuh tabi su dashi tana tab'e bakinta ta ce. "Hmmmm Ohho maku dai, idan ma akwai abunda kuke k'ullawa gara tum wuri kuma daina, kuje tun wuri ku warware abunda kuke shirin aikatawa domin dai Fad'ime ba mutum ce kamar kowa ba da...... Da hanzari Inna Lami ta tari hanzarin Inna Fatuh tana cewa. "Inna Fatuh mi ya kawo duk wannan canzan Kuma?". "Uhuhmm ai kin san miye nake nufi dashi Hajiya". Inna Fatuh ta k'are maganar tana b'alla masu harara su duka. Bintoto data gaji da maganar ta su ta kalli Fad'ime dake tsaye sai murna take ita ta ce. "Fad'ime muje ko gari na haske bamu bar cikinsa ba kuma, na so iyanzu mun kusa cikin garin Kano wallahi". Rik'o hannunta Bintoto tayi. Inna Fatuh kamar zata fashe da kuka tayi saurin cewa. "Baza'a bari Babanta ya dawo suyi ban kwana bane?, kofa K'awayenta basuyi sallama dasu ba". Inna Lami da sauri ta ce "a'a Inna Fatuh indai Malam ne zan sanar dashi da kaina, dama kuma ai yasan da tafiyar tasu a yau d'in, K'awayenta kuma ai Inna Fatuh nake ganin kin san tun jiya ta sanar dasu, ai sunyi bankwana tun jiyan ko Fad'ime?". Ta k'are maganar had'e da duban inda Fad'ime take rik'e da hannun Bintoto. "Eh munyi sallama dasu idan sunzo sun tambaye ni Inna Fatuh ki ce na tafi birni saina dawo, zanyo masu tsaraba idan zan dawo". Wasu y'an hawaye Inna Fatuh ta share tana fad'in. "Ai shikenan Fad'ime Allah Ubangiji ya tsare ki da tsarewarsa, za'a gaya masu hakan". Inna Lami ta tab'e baki a fakaice tana dannama Inna Fatuh harara. Har k'ofar gidan Inna Lami da Auta suka raka su Bintoto Inna Fatuh kuwa k'in fita tayi. ___________________ Tafiya suke sun mik'e hanya domin zuwa inda zasu hau mashin domin fitar dasu daga K'auyen, babu yawan mutane a hanyar sai y'an tsiraro suma sai a d'auki lokaci basu had'u da wani ba. Fad'ime kamar ance ta waiga ta hango matar nan da tayi mafarkinta d'azo cikin bacci, yanzu ma tana nesa da ita take ce mata. "Fad'ime karki sake kibi Matar nan zuwa birni, bana fad'a miki ba karki sake kije?". D'an sake waro ido waje Fad'ime tayi, kawai saita sami kanta da d'aga k'afad'arta tana cewa. "Ni sai naje wallahi, haka kawai nayita zama a K'auye nida nake so na zama y'ar gayu na auri mai kyau d'an gidan y'an gayu, wallahi saina naje". "Karki sake ki bita zakiyi nadama Fad'ime". Turo baki gaba tayi ta sake d'aga kafad'arta alamar bazata ji maganar abunda take gaya mata ba. Bintoto dake rik'e da hannun Fad'ime jin tana magana ita d'aya yasa Bintoto juyowa a zabure tana kallon inda Fad'ime ke kallo tana magana, sai dai bata ga komai ba, hasali ma maganar Fad'imen ce kawai take ji. D'an girgizata Bintoto tayi tana cewa. "Ke Fad'ime kanki d'aya kuwa kike magana ke d'aya". Da sauri Fad'ime ta juyo inda Bintoto take tana murmushi ta ce. "Babu komai wata mata ce fa na gani take ce min wai kar na biki zuwa birni". A haukan Bintoto bata kawo komai a ranta ba saima cewa tayi. "Hhhh so take tayi Miki bak'in cikin zuwa birni ne, manta da ita kawai muje waje na k'ure mana".........✍️ *FAƊIME...💋🌸💕* _(Dangin Jinnu)_ ©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star 10 Last Free Page. *ABUJA CITY* Tun da suka shigo garin Abuja bakin Fad'ime yake a washe tun kafin su fito daga motar ta baza idanu tana ƙare ma ko'ina kallo irin na ƙauyanci. Ta juya bakiwashe domin ta yi ma Hajiya Bintoto magana sai dai kafin ta kai ga furta komai Hajiya Bintoto ta yi wuff tare da fesa ma ta wani abu kamar turare a fuska, galala Fad'ime ta yi tana dubanta da mamaki sai dai kafin ta yi wani yunƙuri tuni idanunta sun fara lumshewa wani nannauyar bacci ya yi awon gaba da ita, sai ta faɗa jikin Hajiya Bintoto. Shu'umin murmushi Hajiya Bintoto ta saki suna haɗa ido da drivern Motar suka sake sakin murmushi a tare dama iya su kaɗai ne a motar tuni sauran mutanen sun fi ce, tada Motar drivern ya yi da dama shi ne abokin cin mushen Hajiya Bintoto duk wata bak'ar harƙalla da take yi tun daga kan safaran ƴan mata da yara ƙanana da take yi duka da taimakonsa ne. Hanya ɗoɗar ya ɗauka yana tsala gudu tun suna kan titi har suka fara shiga daji-daji sai da suka yi tafiya mai tsawon gaske tukunna suka iso bakin wani kogo da bazakayi tunanin akwai wani abu ciki ba. Fitowa suka yi daga Motar Hajiya Bintoto tana riƙe da Fad'ime ita da drivern suka ƙari sa bakin kogon sai dai basu shiga ba suka tsaya sannan Hajiya Bintoto ta ciro waya tare da dannawa Alhaji Bukhar kira bugu ɗaya ya ɗauka yana zuba ma ta kirari da. “sai ke uwar mata kuma uwar duk wasu masu harƙalla kinci dubu sai ceto mai faɗa da cikawa Hajiya Bintoto ikon Allah kin faɗa kuma kin aikata.” Yanayi mata kirarin ne yayin da kan Hajiya Bintoto yake ƙara girma ɗan kwaran gwan tanajin ita ɗin ta kai, yayin da ta gefan Alhaji Bukhar tsananin farin ciki ne ya sa yake yi ma ta wannan kirari dan ya san in yaji kira daga gare ta to fa tabbas ta samu ne bare kuma yanzu da suka yi za su haɗu ta bashi Yarinyar da a ka samu shi kuma ya bata cikon kuɗin dan kuwa ya bata adibas. “ni dai yanzu ba wannan ba Alhaji Bukhar gamu fa a bakin kogo nasan kuma a daidai wannan lokaci kana ciki shi ya sa nace da Rabilu Driver mu taho nan kai tsaye.” Hajiya Bintoto ta kai maganar tana taunar cingum har da bada sautin. Tiss! Tass! Toss!! Dariya Alhaji Bukhar ya yi ya ce. “kwarai kuwa ina ciki ko zaki ƙari so ciki ne?” Ya tambaya da sigar wasa. Hajiya Bintoto ta zaro tana faɗin. “wa? Ni wai? Allah sitira ai in ka ganni a lahira kaini a ka yi kai dai ka ƙari so kawai ga Yarinya lafiyayya an samu sweet 16 to 17 years da ita.” Wata uwar dariya Alhaji Bukhar ya yi tare da amsa ma ta da faɗin. “gani nan tafe” Ta katse kiran ba'a jima ba sai gashi ya fito daga kogon da in za'a kashe Hajiya Bintoto da Rabilu Driver basa ce ga taƙamaimai ta inda ya fito ba. Koda ya ƙari so Hajiya Bintoto ta nuna masa Fad'ime da ke sharar bacci, ya yi dariya yana suɗe baki ganin kyakkyawar yarinya haka. Ta ke a wurin ya tura ma ta cikon kuɗin ta asusunta miliyan uku dama miliyan biyu ya bata, cike da farin ciki Hajiya Bintoto ta miƙa masa Fad'ime sannan suka yi sallama ta shiga mota Rabilu yaja suka bar wurin yayin da shima Alhaji Bukhar ko minti guda bai sake bayan ya karanto wasu latsumai daga shi kar Fad'ime suka ɓace daga wurin. *FAD'IME POV.* A hankali take motsa manyan idanunta da take jin sun yi ma ta wani irin nauyi, tarr! Ta ware su tana kallon saman ceiling na saitin da take kwance. Lokaci ɗaya abin da ya faru ya fara dawo ma ta ƙwaƙwalwa. Ta zazzaro ido tana ƙoƙarin tashi miƙe a razane sai dai ji da ta yi ta kasa ya sa ta yi saurin kallon jikinta zaro ido ta sake yi ganin ba kayan da ta baro ƙauye da su ne a jikinta ba, wannan wata doguwar riga ce ta yadi kamar irinta ta asibiti sai dai wannan launin baƙi mai ratsi-ratsin ja ne, ga ƙafafunta ɗaure da wata kakkaurar igiya hannunta ma haka, tashin hankalinta ya ƙaru fahimtar abin da ke shirin faru da ita duk a tunaninta ma sace ta a ka yi hakan ya sa ta daddage iya kar ƙarfinta ta kwala ihu wanda ba iya Ɗakin ba gaba ɗaya duka gidan ma sai da ya amsa, ihu take zubawa wai don ko wani zai kawo ma ta a gaji sai dai har ta gaji bata ga kowa ba, maganar da taji ta gefanta ne ya sa ta ɗan juya a razane, ai kuwa idanunta suka yi kyakkyawan gani da santalelan kan Budurwar dake a aske irin rigar jikin Fad'ime shi ne a jikinta ta saka hannu ta toshe kunnenta sakamakon ihun Fad'ime. Shiru Fad'ime ta yi tana ƙare ma Budurwar kallo duk da ga halin da take ciki amma sai da dariya ta kwace ma ta lokacin da wannan Budurwar ta ɗa go fuskarta ashe ba iya gashin kanta ba hatta da gashin girarta ma ba'a kyale ba, sai da Fad'ime ta yi dariya san ranta sannan ta tsagaita tana duban Budurwar da ta zuba ma ta idanu ba tare da ta ce ma ta ƙala ba duk da tasan da ita take wa dariyar. “Wai Dan Allah Baiwar Allah na tambayeki ya a ka yi kika koma haka ne kin ganni ki kuwa caɓɗi-jan sai kace Sule almajiri wai ma ina ne nan wurin?” Fad'ime ta ƙare maganar tana ƙare ma Ɗakin kallo. Tare da ƙoƙarin kwance ɗaurin da a ka yi ma ta. ‘lallai yarinya baki da hankali wato ma baki san ina ne nan ba sai dai nayi miki uzuri dan da gani daga ƙauye kike' Budurwar ta raya hakan a ranta, kafin a fili ta furta. “Gidan ƴan yankan kai ne” Ta faɗa a taƙaice tare da yin tsitt. Lokaci ɗaya wutar Fad'ime ta ɗauke na ƴan daƙiƙu kafin ta duba Budurwar cikin tsananin tsoro da zaro ido ta furta. “Gidan ƴan yankan kai dai? Kamar fa haka kika faɗa wai kuma da gaske kike?” “ni abokiyar wasar ki ce da zan yi miki wasa?” Budurwar ta faɗa cikin gatse a zuciyarta kuma tana dariyar ganin yadda Fad'ime ta koma lokaci guda daga jin an ambaci gidan yankan kai. “wayyo Allahna wayyo Inna Fatuh wayyo ni Fad'ime tawa ta sameni” Fad'ime ta dage ta fashe da kuka tana faɗin hakan kuma bata dena ƙare ma Ɗakin kallo ba da babu uwar komai ciki domin hatta su a saman tayar tiles suke. Banko ƙofar a ka yi a fusace wani jibgegen mutumi ya shigo yana zazzare ido ya duba Fad'ime da bata dena kuka ba ya ce. “idan baki rufemin wannan wawwaran bakin ba sai na ƙari so wurin na yankaki na kaima dodo” Yadda kasan an yi ruwa an ɗauke haka Fad'ime ta yi tsitt da jin kalamansa. Ya kyaɗa kai ganin barazanarsa ta yi aiki ya juya domin komawa ya ci gaba aikinsa na tsaro, sai dai ji ya yi Fad'ime ta ƙara fashewa da wani kukan da ya fi na baya tana kiran sunan Inna Fatuh. A mugun fusace ya juyo domin ya ƙari sa ko kifa ma ta mari ne ya yi kota dawo hayyacinta sai dai juyowar da zai yi ya ganta tsaye a gabansa kamar wata aljana, gabansa ne ya yi wani irin mummunar bugawa ganin yadda idanunta suka sauya kala jin ƙarar abu na ɗiga ya sa ya yi saurin kallon ƙasar wai ashe fitsari ne ya suɓuce ya fito masa dan tsabar tsoro ɗagowar da zai yi ya sake dubanta Fad'ime ta shammace shi ta hanyar kai masa wani rikitaccen naushi a tsakiyar kansa domin sai da ta wani daka tsalle kamar yar wasan ƙwallon kwando dake shirin jefa kwallo. Take a wurin ya zube ƙasa sumamme. Juyawa Fad'ime ta yi tana dariya ta duba Budurwar data miƙe tsaye tana bin ta da kallon tsoro cikin rawar murya Budurwar ta furta. “wa..wace ce ke? Kuma me kike shirin aika tawa?” Fad'ime ta yi dariya sannan ta ce. “Fad'ime suna na kuma ni Mutum ce sai dai a ƙauyenmu anai mini laƙabi da DANGIN JINNU, kefa mene ne sunanki?” “Jiddarh” Cewar Budurwar cikin sanyin murya. Fad'ime tana shirin magana taji muryar wancan Matar ta mafarkinta a gefenta da sauri ta juya ai kuwa taga matar tsaye a gefanta tana faɗin. “ki gudu muddun kinaso ki tsira da ranki ni zan taimaka miki ki kuɓuta daga sharrin wannan gidan” Da mamaki Fad'ime ta ce. “wacece ke kuma me ya sa kikeson taimaka min?” “zan faɗa miki amma ba yanzu ba kedai ki yi sauri tun kafin su cim miki ki bar gidan nan.” Shiru Fad'ime ta yi tana nazari duk da gefe guda na zuciyarta tsoro ne fall musamman dataji ance gidan nan na ƴan yankan kai ne, amma kuma tana tsoron ta yarda da wannan matar ita kuma ta cutar da ita. Ido kawai Jiddarh ta zuba ma Fad'ime tana bin ta da kallon tsoro ganin yadda take magana ita ɗaya sai dai batajin abin da take faɗa. “na amince zan biki domin ki fitar dani daga gidan nan sai dai da sharaɗin zaki sanar dani wacece ke” Cewar Fad'ime ba musu Matar ta ce ta amince. Kallon Jiddarh da tsoro ya cika ta Fad'ime ta yi sannan ta ce. “in kinga zaki biyo ni mu gudu a tare tohm, in kuma kinga zaki tsaya har zuwa lokacin da za'a raba kanki da gangar jikinki ne sai dai nace miki bissalam” Shiru Jiddarh ta yi tana nazari ba so ɗaya ba kuma ba biyu ba ta sha ƙoƙarin guduwa daga gidan amma ana kamota wani lokacin ma sai ta sha tafiya sosai sai ta fahimci wuri ɗaya kawai take zagayewa wato bakin kogon, gashi gobe ne kwananta zai ƙare a gidan shi ya sa a ka aske ma ta gashin ta domin gobe ne za'a sadaukar wa da dodo jininta. Ganin Fad'ime tana shirin fita daga Ɗakin ya sa ta yi saurin bin bayanta cikin ƙasa da murya take faɗin. “ki fa yi a hankali domin Akwai hatsari abin da kike shirin aikatawa.” “muke shirin aikatawa dai tun da gaki kin biyoni” Cewar Fad'ime tana dariya shiru Jiddarh ta yi da yake tasan hanya ita take nuna ma Fad'ime inda za su bi kuma sai ya zama na duk inda ta faɗa ya yi daidai da inda wannan matar take nuna wa Fad'ime sun yi tafiya mai nisa sosai cikin gida kuma Allah ya taimaka ba wanda ya gansu, Fad'ime ta yi mamakin irin shegen girman da gidan keda ga wani irin malkwataɗaɗɗen gini da ta rasa gane kansa ita har ta fara gajiya da tafiyar ma suka ƙari sa wani ƙaton fili na gidan da suna iya hango makeken gate ɗin sai kace na wata Masarautar mai shegen girma. Sai dai me zai faru? Wata iriyar Mahaukaciyar dariya suka ji an kece da ita kuma ba Muryar Mutum guda ba ne da alama na mutane da yawa ne. Cak! Suka dakata zuciyoyinsu na bugun lugude Fad'ime da Jiddarh suka cure wuri guda jin dariyar bata ƙarau ba ce. Ai kuwa take mutane da maza da mata suka fara bayyana a wurin suna zagaye su Fad'ime da hakan ya da ɗa, ɗaga hankalin su Fad'ime. Mutanen sanye suke cikin wasu jajaye da bakaken dogayen riguna wurin su goma sha ne mafi yawa daga cikinsu jajayen doyayen riguna zumbula zumbula ne a jikinsu ga wata uwar hula dake jikin rigar da suka rufe fuskokinsu da shi. Cikin Wata kalar murya mai cike da amo su Fad'ime suka ji an fara faɗin. “wato kune tauraƙaƙu ko muna tsaka da shagalin bikin shekararmu goma sha biyar da kafuwa shi ne kuke ƙoƙarin guduwa ai kuwa kun tafka Babban kuskure domin a yau ba sai gobe ba zaku sama hukunci na daidai da abin da kuka aikata a yau jininku zamu sadaukar da shi ga dodon tsafi.” Bayan muryar mai amon ta gama wannan bayani duka mutanen suka sake fashewa da dariya kafin su fara karanto wasu latsumai. Cikin tashin hankali Fad'ime ta duba Matar da ta bayyana gefanta ta furta. “kin cuceni kin ce na gudu gashi kinja za'a kasheni.” Da mamaki da kuma tsoro Jiddarh ta kalla Fad'ime jin tana magana tana duban wurin da ita bataga kowa ba. Ɗaya daga cikin mutanen ne mai sanye da bak'ar riga ya fara tunkaro su Fad'ime suna ja da baya cike da tsoro. “ki daure karki ji tsoro yana matsowa dab dake ki yi ƙoƙarin tuge hular da ya rufe fuskarsa kinji?” Matar ta faɗa wa Fad'ime. Kasa magana Fad'ime ta yi ganin ya ƙari so wurin nasu tare da ƙoƙarin saka hannu ya riƙo su Fad'ime ta dage iya ƙarfinta ta daka tsalle tare da tuge hular kansa ai kuwa take fuskarsa ta bayyana, cike da tsoro Fad'ime ta zaro ido yayin da Mutumin yaja baya yana kare fuskarsa domin a ka'idar ƙungiya ba'a ganin fuskokin juna. Cikin tashin hankali da kuma mamaki ɗaya daga cikin matan wurin da ita sanye take da jan kaya ta rufe fuskarta kamar kowa take duban wannan mutumin da Fad'ime ta buɗe wa fuska. Alamar jinjina Matar nan ta yi ma Fad'ime sannan ta furta. “ki rufe idonki zan taimaka na tserarta dake kamar yadda nayi alƙawari yanzu ma na bari sun ganki ne saboda kiga wannan fuskar saboda ina da Dalili. Fad'ime bata sama zarafin furta komai ba ta ƙara riƙe hannun Jiddarh da kyau tare da furta, “matuƙar kinaso ki kuɓuta ki rufe idonki zamu tsira tare.” Ba musu Jiddarh da jikinta babu inda baya rawa ta yi saurin rufe idonta ita ma Fad'ime haka ai kuwa take a wurin suka ɓace, hankalin waɗan nan matsafa ya ƙara tashi ganin abin da ya faru.....✍️ _______ Laifin daɗi....🤷🥱 Wannan shi ne ana wata ga wata. To dai kunji yadda ta kaya, wai shin kuwa kuna ganin su Fad'ime za su tsira, mene ne zai biyo bayan tsirarsu, akwai ƙura fa, shin wanene wancan Mutumin da Fad'ime ta buɗe wa fuska, kuma wacece Matar da ta ganshi sannan me ya sa ta yi mamaki, wacece wannan Matar da take taimakawa Fad'ime, shin yaya rayuwar Fad'ime zata kasance a cikin birni bayan batasan kowa ba??? To dai duka amsoshin nan suna nan cikin wannan labari na mu mai farin jini wato FAD'IME (Dangin Jinnu) 😂 kuma anan Free Page's suka ƙare. Kada ku manta dama already mun sanar daku Wagga littafi na kuɗi ne a kan farashin Naira Ɗari hudu kacal, (400₦ only) Ku tura kuɗaɗen ta wannan asusun: 8081129487. Sabi'u Khadija, MoniePoint Mfb. Sai ku tura shaidar biya ta nan. Chat via WhatsApp. 0813 047 9973 Or 07067953066. Sai mun jiku.... Zahrah Royal Star ce 💋 da Nainarh KD.❤️