👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _*page*_ *1-2* Ibrahim Khaleel Matashin saurayi d'an kimanin shekaru Ashirin da takwas,mazaunin unguwar zoo road. Dogo ne me matsakaiciyar k'iba, kalar fatarsa bak'a ce amma ba mai duhu sosai ba,fuskarsa cike take da gargasa tare da gashin baki, wanda y'an zamani ke kira da 'quarter million' yana da cikar gemu amma ba mai tsayi sosai ba, bashi da girman idanu sai dai baza'a kira su da mitsimitsi ba,bashi da dogon hanci amma baza'a ce mishi me fad'in hanci ba,yana da sanyin murya tare da sanyin hali. Tsohon telan mata ne, wanda ya fara d'inki tun yanada shekaru goma sha biyar,har izuwa yanzu bashi da wata sana'a bayan d'inkin mata. Ya yi karatunsa na N.C.E a kwalejin tarayya da ke kano wato F.C.E. Yana da sani a b'angaran islama dai dai gwargwado. Duk wanda ke zaune da Ibrahim zai bada shaidar shi mutum ne ba mai zafi ba,komai nasa cikin sanyi ya ke yinsa.me yawon kyauta da tsananin zumunci. Mahaifiyar sa ta rasu kimanin shekaru goma da suka wuce, suna zaune ne a gidansu dake unguwar zoo road kan titin hausawa sabon titi. Su hud'u mahaifansu suka haifa,babban yayan su namiji Yaya Muktar sai shi Khaleel,sai k'anwarsu Mace Zakiyya dake gidan mijinta,sannan autan su Jabir me shekaru goma sha takwas. Mahaifinsu Malam Sule na raye sai dai girma daya kamashi ga lalurar yau da kullum wadda ba'a raba tsofaffi da ita. Gidansu gida ne da yake da girma Wanda ya tara tarin d'akuna.hakan yasa Yaya Muktar yake zaune da iyalinsa cikin gidan,daga farko kana shiga d'akin Mahaifunsu ne jere dana Ibrahim da Jabir tare da k'aramin band'aki a gefe,sannan in ka shiga cikin gidan kuma d'akuna shida ne,wasu rufe wasu a bud'e, duk wanda suke bud'e Sakina ke amfani dasu ita da y'ay'anta hud'u,akwai wadatar tsakar gida me d'auke da babban bayan gida da d'akin girki. Kwanan abuncin Ibrahim da Jabir da mahaifnsu duk yana tukunyar Sakina.wadda suke zaune lafiya da ita matsayin ta na matar yayansu kuma tamkar uwa ce gare su duk da ba wani yawon shekaru gare ta ba amma suna girmamata sosai. ******** Tsaye yake bakin tebur d'in da yake yanka d'inki cikin zagayen farko dake Shagon d'inkin nasa,wanda yake bakin titin shiga gidan zoo. Su'ada tai sallama ta shigo shagon cikin fara'arta ta fara gaisawa da Jabir da ke tsugunne yana fifita gawayi cikin dutsen gugu. D'ago kai Ibrahim yai tare da mata mirmishi ya maida kansa ga yankan da yake. Ita kam ciki ta shige ta gaggaisa da sauran telolin da ke cikin shagon sannan ta dawo in da yake tsaye taja kujera ta zauna tana fad'in "Yallab'ai barka da yamma, ya aiki?" Bai bar yankan da yake ba ya amsa mata cikin fara'a "Barkanki dai Yallab'iya,ya school d'in?" "Hhhhmmm school gata tana garamu saura k'iris dai insha Allah mu huta.Allah yasa dai an gama min d'inkina." Cikin tsokana yace "D'inkinki ko yanka shi ba'ai ba sai zuwa gobe ko jibi." D'an zaro ido tai tare da marairecewa tace " Wai da gaske Khaleelee? gobe ne fa dinner d'in, kuma bazan samu fitowa ba goben don zanje k'unshi da gyaran kai." Jim yayi kamar yana tunani can yace "Gaskiya akwai matsala,don kinga duk su Musa akwai d'inkuna a wajansu dana yanka musu sun had'e miki zuwa dare ko da safe." K'ara marairaicewa tai tana fad'in "Haba Khaleelee kasan fa ni ban jin dad'in d'inkin kowa in ba naka ba,ni dai don Allah kasan yanda zakayi ka d'inka min zuwa gobe da yamma kaji." Gyad'a kai yai yana kallon cikin shagon yace "Umar mik'omin waccan ledar in gani." Fito da kayan ciki ya farayi yana y'ar dariya yace"kamar ma Wannan ne kayan ko?" D'an turo baki tai mirmishi kan fuskarta tace" Allah Khaleelee ka maidani ma abar tsokana,wallahi har kasa jikina ya mutu. " "A'a kar ya mutu don Allah ga kayanki nan maza d'auki ki je gida." Cikin fara'a ta amshi ledar tana mik'o mai cikon kud'in d'inkinsa naira dubu uku. Sannan tai musu sallama ta fita a shagon fuskarta d'auke da fara'a. Ita kam bata san me yasa Khaleel ke birgeta ba,komai nasa sha'awa ya ke bata,musamman tsananin tsaftar sa, Allah yayi shi da tsafta kullum tsaf zaka same shi, haka ma shagonsa ko yaushe a gyare ga k'amshi in ka shiga kamar karka fita. ________________ Sa'adatu Mustapha Sarki Darki matashiyar budurwa me shekaru goma sha tara a duniya, Kowa na kiranta da Su'ada, fara ce ba sosai ba,bata da tsayi kuma bata cikin gajeru,amma dai za'a iya kiranta me k'aramin jiki, kallo d'aya zaka mata ka gane kamanninta da fulanin asali. Su'ada tana da matuk'ar hak'uri da yawon fara'a.haifaffiyar garin kano ce a unguwar sharad'a,a can tai primary d'in ta da secondary da islamiyya. Daga nan Suka dawo unguwar Medile k'aramar hukumar kumbotso.yanzu tana karatun ta a Aminuddeen college of education. Cikin gidansu su bakwai ne,yayar ta d'aya tana da aure sai ita,sannan k'annanta mata guda hud'u sai autansu Ibrahim Wanda suke kira Khaleelee.(don haka take kiran Ibrahim tela da Khaleelee) wanda ya kasance shi kad'ai namiji a cikinsu.don haka suka d'au son duniya suka d'orawa Khaleelee. Mahaifinsu bafulatanin garin darki ne dake kano,kasuwanci ya fito dashi daga k'auyansu. d'an kasuwa ne me safarar takalma da les daga legos zuwa kano. Mahaifiyar su kuma cikakkiyar bahaushiya ce y'ar unguwar gwale gudundi. ma'aikaciyar lafiya ce a asibitin yara da ke kano wato ASIYA BAYERO. Akwai wadatacciyar tarbiyya a cikin gidansu,don mahaifiyarsu jarumar mace ce me tsaye a kan lamarin iyalinta,kasancewar Allah ya wadatata da yaya mata yasa duk motsinsu ke idonta. Wayayyiyar mace ce ba ruwanta da wani kauda ido akan d'a,tana jansu a jikinta sosai don haka basa iya b'oye mata sirrinsu. Wani sa'in in kaje gidan kaga yanda take mu'amala da y'ay'anta zakai tunanin k'annanta ne ba y'ay'a ba.bata da abokan hira ko shawarar da suka wuce y'ay'anta, don haka suma dukkan shawarar su tare da ita suke yi. _*da yuyuwar nan gaba ya koma na kud'i*_🥰 *Ku biyoni yanzu na fara* 👌 *Taku ce* *y'ar mutan Ja'oji*🙋 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _*page*_ *3-4* Misalin sha d'aya da rabi na dare tana kwance kan gadonta d'auke da wayarta kallo d'aya zakai mata kasan chart take don yanda take sakin mirmishi lokaci zuwa lokaci. Pic's d'in dinner d'in da suka dawo ne yau ta d'ora kan status d'in ta,comments da ake tayi kan pic's ne yake sata yin mirmishi don duk wanda ya bud'e zai ce kamar kece amaryar kinsha kyau. A nan Sak'on Telanta ya shigo a "Assalamu Alaiki,biki yi bacci ba kenan?" Cikin zak'uwa da d'oki ta bashi amsa da "Um ban yi ba tukun,ina dai niyar yi." Bayan y'an sekonni amsar shi ta dawo " Ansha dinner ko? Ina fatan dai d'inki yayi kyau? " Mirmishi ta saki tana rubuta mai amsa "Hhhmmmm bari Khaleelee d'inki ya d'au magana fa wallahi, har na samo mana wata costumer wai zata min pic tana son a mata irin gown d'in,nace a'a bana bari a d'aumin d'inki sai dai in had'a ta da tela na zai Mata irinta sak. To yanzu dai na bata number d'inka zaka jita." Cikin jin dad'i ya maida mata amsa" 👍👍👍 ina godiya fa Regular costumer da k'ok'arin kullum shago ke k'ara tsaiwa ." Sosai taji dad'in yabon da ya Mata "Hhhhhmmm kullum ina cema ka daina min wannan godiyar ya kamata ace ka daina tun tuni, naji dad'i ai shine gari,kai dai kawai ka ci gaba da tsatsubo min d'inki ina d'aukan magana 😄." "😂😂😂 karki damu Su'ada ai ke ko da d'inki ko babu kina d'aukan magana fa." "A'a fad'a kawai kake yi Khaleelee🙄 ." "Da gaske na ke Su'ada kinga fa yanda kika dakushe duk emmatan gun dinner d'in nan,ina ta kallon status kyau yasa ma na kasa magana😂 ." "Hmnmm Khaleelee baka rabo da tsokana wlh,amma ni dai na San duk kyan kwalliya in ba'a d'ora Mata had'ad'd'an d'inki ba dakushewa take." Juyi yai kan katifarsa yana y'ar dariya sannan ya bata amsa, " Hhhmmmm to insha Allah zan ta k'ara dagewa da k'aro fikra don in ta fito da Su'ada😂😂😂😂 ." "Yawwa haka na ke son ji daga gareka, zan kwanta sai da safe ko." "OK Allah ya tashemu lafiya." "Amin na gode." Juyi kawai ya ke kan katifar ya na tunani cikin ransa, mintina arba'in yaga bai samo mafita ba kamar kullum don haka ya kashe wayar tare da yin addu'a ya lumshe ido yana fatan bacci ya d'auke shi da wuri. ********** Yau tsahon sati guda kenan da Su'ada ta fara sak'a da warwara kan neman mafita.tabbas da gaske duk abunda take ji game da Telanta ta fara gasgata so ne.to amma ta yaya don mutum na birgeka kuma kuna zumunci sai kawai so ya kunno kai tsakaninku, a zahiri ta tabbata in so ya mata haka bai mata adalci ba,don bata cikin matan da zasu iya tunkarar namiji da tayin so ko da kuwa son ne silar ajalinta,ta dad'e da gano halin maza na wulakanci ga duk macan da suka fahimci tana mutuwar sonsu koda kuwa suma su na son nata, to balle ita da kullum zumunci da shak'uwa take gani cikin idanuwan Khaleelee tare da ita, bata tab'a ganin wata alama ta so ga Khaleelee ba, hasali ma shi in dai ya ga mace ta fiye rawar kai da shishshigi tsakanin sa da ita had'e gira ne,don ya ce duk mu'amalar sa da mace bazai bari son gaske ko na wasa ya had'a su ba matuk'ar harkar d'inki ce ta had'a su,domin kuwa duk telan matan da ya sa soyayyar costumer cikin sabgarsa bazai wani tsinana abun arzik'i ba,daga ya fara soyayya da wannan costumer in wadda tafi ta ta zo zai koma kanta.tasha jin yanawa yaran shagonsa wannan maganar kan su tsaya iya bakin sana'ar su akan ko wace costumer kawai,in yaso in sun bar shago suje su yi soyayyar su. To mutumin da ke jawa yaransa kunne kan haka ta ina shi zai fara hakan. A zahiri maza da yawa ke sonta cikin danginta da jama'ar gari,so na aure kuwa,amma bata tab'a ganin abun birgewa tare da su,ga namiji har namiji dai abun birgewa amma ita in ya zo mata da batun so sai taji duk bai birgeta. Tun tuni tsarin halittar Khaleelee ke birgeta,halayensa da tsaftarsa ke k'ara fizgarta gareshi,da tai tunanin kawai iya birgeta ya ke yi,amma yanzu ta tabbatar mugun sonsa ya hudata ya kama zuciyarta,yanzu dole ta nemawa kanta mafita, d'ayan biyu dole a yi d'aya ko dai ta nisanci Khaleelee ta jawa kanta mutunci da girma,in kuma ba haka ba taci gaba da zuwa shagon Khaleelee tabbas asirin zuciyarta zai bayyana.daga nan kuma girmanta da k'imarta da yake gani kuma su shek'e. Wanne kenan za tayi? Ta tambayi kanta cikin tsananin damuwa, wannan take ta sak'awa da kuncewa har bacci yai gaba da ita. Amma farka warta da wannan batun ta farka,bayan tai sallar asuba ta shiga kaiwa Allah kukanta kan yai Mata maganin wannan ciwo daya kamata, nan wajan bacci ya k'ara gaba da ita. Jidda k'anwarta da suke kwana d'aki d'aya ce ta ga har wajan k'arfe bakwai bata tashi ba kuma tace musu tana da exam k'arfe takwas don haka ta fara tashin ta "Aunty Su'ada ki tashi kin makara fa." Da sauri ta mik'e tana salati tare da kallon ogogo,a hanzarce ta tashi ta wuce band'aki. Duka a gurguje tai shirin nata data fito ko break bata tsaya tayi ba ta amsa kud'i wajan mamansu ta fice. Tana tafiya cikin adai daita ji take kamar tai iska ta kai kanta school don duka mintina kad'an suka rage takwas ta cika. Allah ya taimaketa lokacin data isa ga d'akin jarrabawar a sannan malaman da zasu jiresu suka k'araso don haka kusan a tare suka shiga, babu wata ishshshiyar nutsuwa tare da ita sai data ga ta zauna tsaf an bata question pepper a sannan ta saki ajiyar zuciya tasan ta tsira. *********** Zaune yake kan dakalin k'ofar gidansu bayan ya gama sharar wajan,cikin ransa yake fad'in 'kwana biyu Su'ada shiru ko wucewarta ban gani ba yau tsahon sati biyu kenan, duk zasu fara exam amma ai in zata wuce ta bakin shaginsu tana d'aga musu hannu, ya dubata online ma bata hawa,duk daman in zata fara exam kashe wayanta take babbar sai dai tabar k'aramar a hannunta' Ciro wayarsa yai cikin aljihu ya fara nemo number d'inta,ringing d'aya biyu ta d'auka yai mata sallama cikin cool voice d'insa,itama cikin fara'arta ta amsa duk da k'ok'arin ta na danne zakuwar ta na karya gane nishad'in da take ciki, "Malama Su'ada kin b'uya gaba d'aya." "Hhhmmm bari kawai Khaleelee exam ta binne ni,ban gane komai in ba farar takarda in cikata da bulun Biro ba." Dariya sosai maganar ta bashi bayan ya gama darawa yace "To Allah ya bada sa'a ya sa a fito da kyakykyawar sakamako." "Ameen na gode Khaleelee, insha Allah yau zan kawo d'inkunan ankon graduation d'inmu,yanzu da mun fito exam zamu wuce kasuwa mu siyo zan kawo ma guda takwas har dana su K /Mata." "OK sai kin kawo Regular costumer." Dariya tai kawai ta kashe wayar. Wani farin ciki taji ya lullub'eta na jin muryar tasa. ********* Bayan awa guda su ka fito da ga exam d'in mutum uku suka wakilta zuwa kasuwa cikin su takwas da za suyi ankon kala d'aya, daman tuni sun fiddata a waya kowa ya san kalar da kud'in. Mudatex suka shiga kai tsaye don a nan suka San zasu same ta bada wahala ba. Bayan sun siyo sun fito a bakin titi sukai sallama kowa yai hanyar unguwarsu ita kuma ta taho da duk atamfofin kamar yanda su ka shirya Ibrahim zai musu d'inki duka iri d'aya. _*da yuyuwar nan gaba kad'an ya koma na kud'i*_🥰 *Taku ce* *Y'ar mutan Ja'oji*🙋 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ *18/10/2019* _*page*_ *5-6* Tunda ta sauka cikin adai daita sahu ya ke binta da kallo,ji yai kamar yayi watanni bai ganta ba, a sannu ta k'araso shagon da ledar kayan,Jabir ya fito ya k'arb'i kayan hannunta. A gajiye ta k'arasa ta zauna da fad'in "Ya Allah." Cikin kulawa su ka gaisa da jama'ar shagon sannan a hankali ta juya gareshi yana amsa waya mirmishi ya sakar mata ita ma ta maida mai martanin mirmishin tana kauda kai gefe. Bayan ya gama wayar ya juyo gareta da fadin"hajjaju kin karaso kenan ya exam d'in?" "Hhhhhmmm gani na karaso Khaleelee amma kamar zan fad'i don gajiya." "Ayya sannu,ai an kusa dai a huta gaba d'aya ko." "Eh insha Allah nan da two weeks zamu k'are gaba d'aya." "To Allah ya nuna mana." "Ameen ya Allah, ga d'inku nan zuwa gobe zanzo ma awan wanda baka dashi da kudin ma gaba d'aya." "Ok ba damuwa,ina godiya." Mik'ewa tai tare da fad'in"na wuce sai goben." "To Allah ya kaimu,ki gaida Mama da takwara." "Ok zasu ji insha Allah." Ta fad'a tana fita a shagon. *********** Da dare suna zaune a falo tare da mamansu kallo suke yayin da rabin hankalin Su'ada yana ga bitar karatun ta wani sashin na zuviyarta kuma na tsinkulin ta da maganar Khaleelee, a hankali ta zame ta kwanta kan kujerar da take zaune,lumshe idanuwa tai tana hasko fuskar Khaleelee d'auke da wannan k'ayataccan mirmishin nashi,ita ma ji tai mirmishin ya sib'ice mata. Mama da ta juyo za tai mata magana ta ga ta rufe ido tana ta mirmishi ita kad'ai,zuba mata ido tai tana karantar yanayin da take ciki a hankali tace "Su'ada karatun kike ko bacci ko ko tunani." Da sauri ta bud'e idonta tana d'an yak'e tace "Mama karatu fa tuni na gama dashi,kinga duk in da na duba cikin handout d'in ma sai naga na gama da wajan." "Ok haka ake so, na ga kin kwanta ne kinata mirmishi ke kad'ai kamar an miki albishir da wani abu,ko akwai wata a k'asa ne bamu sani ba." Ta k'arasa da d'an dariyar tsokana. Langab'e kai Su'ada tai da fad'in "Mama meye a k'asa wanda zaku kasa sani,kawai dai tunanin duniya nake." "Hhhhmmm ko tunanin surukina ake?" Da sauri ta zaro ido tana fad'in "lah Mama wane suruki kuma,Allah ni dai a'a fa." Dariya Mama tai da su jiddah ganin yanda ta wani rikice kamar bak'on abu ne a gurinta. Husna tace "Aunty Su'ada kin san me? Jiya yaya Nazeef ke tambayata wai don Allah ko dai kina yin zance da wani ko dashi ne baki son tsayawa kullum yace zai zo sai ki ce karatu karatu." Hararar ta Su'ada tai tana tab'e baki tace "ku kuka sani ke da shi,daman na san ke ce abokiyar gumata dashi." "Aa fa ni tambaya ta kawai yayi na bashi amsa da cewa exam kike maybe in kin gama zaki bashi dama ya rink'a zuwa." kafin Su'ada tai magana Jidda ta d'auka da fad'in "ke dilla k'yale shi,shi shegen tambaya gareshi kamar ya aje mutane." Dak'uwa Mama tai Mata da fad'in "Dan gidanku yayan ki ne fa kike mai haka,to wai ma ke yace ya na so ne ko me da kike tada jijiyar wuya haka." Su'ada ta ce " Mama fa ni wallahi ban sonsa ko kad'an shi kamar bai karatu ba,wallahi da a darkin ma ya ke da zama ban san irin gidahumancin da zai yi ba." Fulon da ke kusa da Mama ta cillowa Su'ada tare da dak'uwa "Wallahi ku kiyayeni da wannan iya shegen,wai to ma in bi ki bawa masu sonki dama yanzu ba sai yaushe? Eh Su'ada nace sai yaushe? da karatu ya rik'eki mun goya miki baya yanzu kuma meye ya rik'e ki tunda dai karatun nan duka kwanaki ya rage a gama shi." Sassauta murya ta k'ara yi taci gaba da fad'in " Su'ada ki tsaya ki nutsu cikin tarin samarinki ki fidda wanda ya fi kwanta miki a rai,kinga yanzu saura watanni ki cika shekaru ashirin, gashi saura sati biyu ki gama N.C.E d'inki,kinga aure shi yafi dacewa da ke yanzu,don haka na baki lokaci daga nan har zuwa wata guda ki nutsu ki fidda guda wanda hankalinki ya fi kwanciya dashi kinji." D'aga kai nai a hankali nace "To mama insha Allah zan fidda." Tun daga wannan lokacin ban k'ara cewa uffan ba har tsawon lokaci na mik'e zuwa d'aki ina cewa "Mama zan kwanta sai da safe." "Allah ya tashemu lafiya." Mama ta amsa Mata. Tunda ta shiga d'aki ta fad'a gado k'irjinta na wani irin bugawa, rintse ido tai tana fad'i cikin ranta ' Allah ka dafa min Allah karka barni da zab'in raina kai min zab'inka,Allah dukkan abunda zai zama alkairi gareni da rayuwata Allah ka zab'a min shi,kai kasan halin da nake ciki kuma kai zaka min maganinsa." Juyi take tayi tana rok'on Allah mafita, ba ita tai bacci ba sai k'arfe d'ayan dare. Da safe haka ta tashi jiki ba k'arfi ta shirya ta tafi school. Tun daga wannan ranar Abubuwa suka cakud'ewa Su'ada ga karatun exam ga tunanin wa zata zab'a cikin tarin samarinta, ga ciwon son Ibrahim dake k'ara azalzalar zuciyarta, nan da nan ta rame tai fiyau da ita. ********** Ya rage kwanaki Biyar su zana final Pepper ranar basu da exam da yamma tace Jidda ta shirya ta rakata Wajan Khaleelee ta anso d'inkunan su,don da safe take son tafiya musu dashi school. Tana sanye da doguwar riga marron colour me adon yello me duhu mayafin da tai Rollin kanta yellow sai plat shoe d'in ta shima yello wayarta kawai ta d'auka ban da jaka, tana tsaye cikin gate tana jiran Jidda ta fito su tafi taji tsayuwar mota a k'ofar gate d'in nasu,bata maida hankali ga gate d'inba don bata tunanin gidan nasu za'a shigo, a sannan Jiddah ta fito tana fad'in " Sorry sis na tsaya d'auko wannan material d'in nawa ne in bawa Khaleelee ya d'inka min na gaji da ajiyarsa a akwati. Ita dai Su'ada bata amsa mata da komai ba illa sa kai da tai don fita a cikin gidan. Kicib'us su kai da Jameel yana k'ok'arin shigowa,D'an jenyewa tai gefe tana fad'in "Oh soja kana gari Ashe? Zaka bigeni da k'arfin allurarka." Dariya yai a taka'ice yace "ina zuwa haka na kawo muku ziyarar bazata.hajiya Jidda har dake za'ai tafiya ma?" Cikin dariya Jiddah tace "Yaya Jameel ai bamu San kana tafe ba wallahi,zamu je zoo road ne mu amso d'inki." "Ok to bari in shiga mu gaisa da Mama sai in fito in kaiku ko." Da sauri Su'ada tace " A'a ba zamu wahalar da kai ba ka barshi kawai wlh zamu hau Napep ma." D'ora hannunsa yai a baki alamar tai shiru daga haka ya wuce cikin gidan. Cikin k'unk'uni Su'ada ta je ta tsaya jikin motar tasa tana fad'in "Wai ayi ta takurawa mutum haka kawai,ni nace ban son hawa motar amma ya wani zaro min ido kamar ubana,mutttsss." Y'ar dariya Jidda tai tace "Kai Aunty Su'ada meye laifin yaya Jameel wai don Allah yanzu shima duk k'ok'arin sa kanki baki gani,duk sanda yazo garin nan yata nacin zuwa wajanki kina yarfa shi,ni kam wlh ban ga aibunsa ba Sam." "Dallah malama rufemin baki ke me yasa bazaki soshi ba?" "A'a ai ke yace yana so ba niba amma dai gaskiya Aunty Su'ada a shawarce karki wuce yaya Jameel a cikin zab'enki wlh don mutumin yayi fa." Ta bud'e baki zata bata amsa ya fito don haka ta gintse kawai amma ta watsa mata harara." Cikin fara'arsa ya k'araso yana fad'in " kuyi hak'uri na tsaida Ku ko? Ku shiga mu tafi." Ya bud'ewa Su'ada gaba sannan ya zagaya ya zauna mazauninsa. *Taku ce* *y'ar mutan Ja'oji*🙋 [2/23, 11:51 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _*page*_ *7-8* *19/10/2019* Tunda su ka d'au hanya Jameel da Jidda ke hirarsu amma Su'ada tai tsit ta tafi duniyar tunani bama ta jin me su ke fad'i. Lokacin da su ka tsaya k'ofar Shagon su Khaleelee Su'ada ta kalli Jameel da fad'in "Soja muna godiya fa." D'an hararar ta yai cikin wasa da fad'in " zan bige wannan bakin in ya k'ara min godiya,sannan zan juya da ku ai,ba sai kun shiga ba d'aga musu hannu su mik'o muku kayan." Cikin k'osawa Su'ada tace" A'a wane kalan su mik'o mana kuma? Wannan shagon fa da amana tsakaninmu da su,zamu shiga Jidda ma zata bada d'inki." "Ok to Jiddah in kin bada d'inki naki sai ki amso mata natan." Kallon sa Su'ada ta tsaya yi zuciyarta na mata zafi da Wannan k'arfa k'arfa haka,tace" Wai ne yasa zan zauna ni d'in a nan?na fad'a ma ga abunda daman ya fito damu kuma sai in coge cikin mota? In ka ga da takura Allah ba damuwa kaje zamu hau Napep mu koma." D'an mirmishi yai da fad'in "Su'ada dai so kike in tafi ni kam k'afata k'afar ki, kishi nake ji ki shiga tsakiyar mazan nan wallahi." Kafin ya k'ara d'ora wata maganar Su'ada ta bud'e mirfin motar ta fito ranta bace. Jidda ma ta rufa mata baya. Ganin haka shima sai ya fito ya bi bayansu. Da sallama suka shiga shagon amma fuskar nan ta Su'ada ba walwala sam, bayan sun gama gaisawa da yaran shagon ta juya ga Ibrahim tana d'an k'ok'arin sassauta fuskata "Khaleelee ina fatan komai ya zama Ready?" Da fara'arsa yace "Insha Allah kuwa." A dai dai nan Jameel ya shigo hannayensa hard'e cikin wando, d'aga musu hannu yai tare da Sallama suka amsa banda Ibrahim da yai kamar ma baiga shigiwarsa ba. Babbar leda me d'auke da kayan su ciki aka d'auko musu,Jidda ta amsa,tana fad'in "Khaleelee wannan d'in kin Jabir mutumina ne zai min don naga tuni yake k'ok'arin finka zafi yanzu." Dariya suka sa,Su'ada ta d'an harareta "karyar mutum yafi Khaleelee iya d'inka,ke dai kawai kina son kiyiwa Jabir dad'in baki ya tsatsuboki." Nan ma dariya suka sa, yayin kuma da tsakin Jameel ya sa suka maida hankalin su gareshi amma sai suka ga ya juya ya fita yana cewa "Jiddah tunda kun gama mu wuce mana." D'aukan ledar tai ta bi bayan sa, ita kam Su'ada wani tsaki taja na takaicin wannan milkin na Jameel. "Hajiya ki wuce oga na jira." Wani da suke wasa da Su'ada ya fad'a. Shima harara Ta watsa mai tace "kai kaga Oga ni ban ganshi ba wallahi." Had'e rai sosai Ibrahim yai kawai sai ya fara duba wayar sa. Ita kam cikin jin haushi ta juya ta fita tana musu sai anjima. Tunda ta shiga motar ta cona baki gaba tana kallon gefe,shima bai tanka mata ba balle Jidda dake baya. Suna zuwa k'ofar gate d'in su yaja ya tsaya Jidda dai ta fita tana fad'in "Yaya Jameel sai anjima." Itama tana k'ok'arin bud'e motar ya dakatar da ita da fad'in "Su'ada ban son kina zuwa wannan shagon,kin zauna kina ta wani hira da dariya." Cikin mamaki da takaici take kallon sa,ta ma rasa me zatace don haushi kawai sai ta juyar da kanta gefe. Ya d'ora da fad'in "Su'ada kin san dai yanda nake sonki da kishinki, ban San naga wani namiji na kulaki wallahi, Su'ada yaushe ne zaki ban dama na fito? Ko yaushe na miki magana sai kice karna turo in jiraki, in dai don karatu ne ne ya k'are kuma saura me?" Yamutsa fuska tai cikin k'osawa tace " Ka bari zamuyi magana don Allah yanzu akwai uzirin da zanyi a ciki." Zuba mata ido yai cikin nazartarta can zuwa y'an dak'ik'u yace "Alright, ki je zamuyi waya." Tana sa k'afarta waje tace "Tnx." ********** Da dare tana kwance bayan ta gama k'ara dudduba takardunta,tunani take a kan maganarsu da Jameel ta d'azu, wato shi yanzu tana cewa ya fito sai aure a shirye ya ke, gashi Mama ma abunda take jira kenan,in har fa ta bawa Jameel dama ya fito shikenan Ta rabu da Khaleelee,ita fa wallahi bata da wani buri bayan nashi. Wata zuciyar ta tunasar da ita wai ke ma Ibrahim ca yai yana sonki harda kike lissafinsa cikin masoya, ki kama kanki fa ki san me kike yi. Wannan tunanin yasa taji gabanta ya fad'i, tai ta juyi tana jin kanta na wani sara mata don rashin madafa. ______________ Kwanaki biyar da suka biyo baya su Su'ada suka kammala final exam kuma a ranar sukai waleeman su wanda ta k'ayatar su kai abubuwa cikikn tsari,har yamma lis sannan aka tashi kowa da tarin y'an uwansa da abokan arziki da suka zo taya su murna. Suna cikin motar komawa gida wayar Su'ada tai ringing tana dubawa taga sunan Khaleelee ya bayyana kan wayar" mirmishi ne ya bayyana kan fuskarta ta d'aga tare da sallama" Ranki ya dad'e barka da yamma ya hidima?" "Me zakace min Khaleelee ina ta zuba ido in ga ta inda zaka b'ullo amma tsit har aka tashi ba komai." "Kiyi hak'uri d'inkuna ne suka rik'e ni sosai amma naso zuwa,duk da haka zanzo har gida in yi tawa murnar." "Tom shi kenan ka wanke kanka,kuma ina nan ina zuba ido daga yau har gobe har jibi ." Dariya yai yace "To shi kenan,Allah ya kaimu zaki ganni kuwa." Bayan sun kashe wayar kawai sai take ta jinta cikin nishad'i da walwala fiye da wadda take ciki yau d'in. ******* Tana Sallar Magriba ta d'auko wayarta tana duba pic's d'in da sukai yau har ba adadi,kunna Data tai ta shiga WathApp abunda ta dad'e batai ba,jimawa da yawa network ya wadata nan fa ta shiga d'ora Status ba kama hannun yaro. Sak'onnin taya murna tai ta samu daga contacts d'in ta,replay ta shiga maida da godiya har lokacin sallar isha'i yai ta tashi tayi,cikin d'oki ta k'ara d'ukan wayarta tana bin duk sakkonin. can sak'on Ibrahim ya shigo,da azama ta bud'e " _Hhmmm gimbiya sarkin kyau da kwalliya ki babu, ko ina kika shiga sai kin haska mata,gashi dai komai naki da nasu iri d'aya Amma duk da haka kin k'eresu nesa ba kusa ba_." Y'ar dariyar jin dad'i tai sannan ta maida masa amsa " _Hhmmm Khaleelee baka gajiya dai da tsokanta fa_" " _kullum gani kike kamar wai tsokanar ki nake,ni kuma gaskiya na fad'i, Tabbas wannan bawan Allah ya dace kuma yayi zab'e me kyau,duk da naga shi D'an zafin kai ne_." " _Hhhhhmmm Khaleelee kenan,ai ni ba wanda zai ce ya sameni ya dace da matar aure,don banma fidda mijin ba balle shi yace ya samu_ ." " _b'oye min dai kike yi,amma da ganin yanda ya ke had'e fuska yana wani d'aukan zafi ai yasan ya kama waje a zucuyarki_." " _hhhhhmmm Khaleelee kenan,kasan me? Wlh Jameel bai cikin kalar mazan da na ke so,kawai dai shi ke hidimar sa amma ni bai da waje a zuciyata_." " 😳 _wannan hadaddan gayen ne bai cikin mazan da kike so? Ai kuwa naga matan yanzu irinsa su ke so_." " _hhhmmmm matan yanzu ai kace,ni dai bai cikin tsarina Sam_" " _To me yasa bai cikin tsarin naki?kuma wannan kala ne ya ke cikin tsarinki_." Y'ar dariya tai tana gyara kwanciyar ta don hirara tasu ta fara mata dad'i. duk da tasan in batai taka tsantsan ba zai rafkota. *Taku ce* *Y'ar mutan Ja'oji* 🙋 [2/23, 11:51 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ *Na sadaukar ga wannan page d'in gareku dukkan k'awayena na media, bazan manta da Ku ba har abada*🤝🤝🤝 _*page*_*9-10* Typing ta fara yi tana bashi amsa. " _Da farko dai kaga Jameel soja ne,ni kuma banda ra'ayin auran soja,sannan kaga kalarsa fari ne sosai,ni kuma namiji fari baya min kwarjini ko kad'an wlh,sannan dai cikin halayensa da yawa basu min ba,don yana da zafin rai da nuna gadara duka banson namiji irin haka,wannan dalilin ne yasa sam bazan iya auran saba_." Kallon rubutun Ibrahim yai tayi yana k'ara maimaitawa mamaki yake ganin yanda tace farin namiji bai mata kwarjini,sannan shi dai kallo d'aya yaiwa Jameel yasan ya ajiye yayan bankin, yanzu ko dan kud'in sa Su'ada bazata soshi ba kenan.ya dad'e kafin ya bata amsa yana nazarin maganganunta. " _To wane Namiji ne kalar zabinki_?" " _Da farko kaga ni ina son Namiji dogo, sannan ina son namijin da yasan darajar mutum,ba mai d'aga kai da gadara ba,sannan_. . . _ko dake sauran sirrina ne kawai_" " _hhhmmmm Su'ada manya,to shawara ta kiyi ta addu'a kina neman zabin Allah, karki nemi zabin ranki kinji_." " _Na gode Khaleelee, ko yaushe cikin addu'a nake wlh musamman yanzu da mama tasa min lokaci in fidda miji cikin samari na_." Ji yai gabansa ya fad'i da cin furucinta, shin me ke damunsa ne kan Su'ada, me yasa yake shayin fad'a mata sirrin ransa.tabbas yasan babban abunda ya tokareshi daga gareta to rik'e mutuncinsa ne,bai son cusa kansa in da za'a ga k'ask'ancin sa,ko yaushe yana tsayawa ne iya huruminsa da inda za'a ga mutuncin sa,amma tabbas ya san zuciyarsa na kwad'aita mai soyayya da Su'ada sabida kyawun halayenta da nagartarta. Jin shiru bai maida mata amsa ba yasa tai zaton ko ya shiga wani uzirin ne,amma bayan mintina sai taga amsa ta dawo. " _To Allah yai miki zabin mafi alkairi cikin rayuwar ki_." Daga haka ya sauka ya kashe datar ya shiga tunani da nemon mafita. *********Kwana biyu tsakani Su'ada ta matsawa Ibrahim da maganar zuwan da yace zai yi,don haka a ranar yace mata zai zo. ta sanar da mamansu cewa kana Ibrahim tela yace zai zo har gida yai mata murnar kammala karatu,cikin kawa maman tace a shirya mai abun motsa baki kafin yazo. Danbun naman kaza da cake Su'ada ta shirya tare da lemon kwakwa me d'an karan dad'i. Zuwa k'arfe hud'u ta gama komai tai wanka,bata wani yi kwalliya ba sai powder kawai tasa tare da lipstick, ta zira doguwar rigar material tare da yafa k'aramin bakin mayafi. Lokacin da Ibrahim ya tsaya k'ofar gate d'in su Su'ada kawai sai yaji gabansa na fad'uwa, k'ok'ari yai ya tattaro mazantaka,kiranta yai a waya ya sanar da ita ta k'araso. Cikin y'an mintina ta fito fuskarta d'auke da mirmishi sosai tace "Khaleelee a gidan mu,lalle yau mun ja babbar sa'a." Y'ar dariya yai yana shafa kai yace "Ai komai kamawa ta ke Su'ada gashi yau nazo kuma ina fata daga yau nai ta zuwa har sai an gaji dani." D'an zaro ido tai da fad'in "Waye zai gaji da kai d'in Khaleelee? Ai kai baka cikin mutanan da za'a gaji da su, zo mu k'arasa ciki na tsaida ka da magana." Bin bayan ta yai zuwa cikin gidan,a sitting room tai mai masauki bayan sun gaisa ta mik'e tana fad'a mai " Ina zuwa Khaleelee minti biyu." Kallonta yai ido cikin ido sannan fuskarsa na bayyana wani k'ayataccen mirmishi yace "Na baki minti biyar ma Su'ada." Farrr tai da wadatattun idanuwanta tace " Tom na gode." Cikin gidan ta shiga cikin farin ciki take sanar da Mama Khaleelee ya na sitting room. Mama tai mirmishi tace "To ina masa barka da zuwa,ki karramashi yanda ya kamata kinji ko?" Gyad'a kai tai alamun amsawa sannan ta fita zuwa kitchen tana k'walawa Jidda kira,cikin k'osawa Jidda ta k'araso kitchen d'in "Oh Aunty Su'ada kamar zaki tsaga min kai da wannan kiran naki. Ya k'araso ne?" "Eh ya k'araso don Allah sa mayafinki ki kai mishi ruwa da lemo ina zuwa yanzu." "Ok ba damuwa Jidda tace tare da juya zuwa d'aki ta d'auko mayafi. ruwan roba da lemo tasa kan farantin tangaran da glass cup ta tafi kai mai,ita kam Su'ada tsara plate tai sosai yanda zasu ja hankalinsa ya ji yana son cin abunda ke ciki. Sannan ta samu glass juck ta zuba Lemon kwakwa d'in,a babban faranti ta jera ta d'auka zuwa sitting room d'in,da sallama a bakinta ta shiga,su na ta hira da Jidda ya amsa mata kallon agogon hannunsa.ta San me ya ke nufi don haka bayan ta ajiye kayan ta d'ago tana kallon sa da dariya tace" Amin Afuwa Khaleelee na wuce lokacin da aka bani ko?" Gyad'a kai yai ya ce "Don ma ga Jidda ta zauna tayani hira da an bar bak'o shi kad'ai." "Sorry don Allah, yanzu dai ga abu ka ci sai mu yi hira." "A'a ni ba abunda zan ci na koshi sosai gashi nasha lemo ma." Had'e rai tai tare da kauda kai fuska alamar fishi. Jiddah dariya tai tana mik'ewa tace "Bari na koma ciki maybe don ni ne baza kaci ba." "Kinji ki cikin Ku waye bak'ona,kawai dai a koshe nake ne,ni da cin wani abu kuma sai dare." "Tab' d'in ni dai ba ruwana kai da mutuniyar don naga ta ci murrr." Dariya yasa shima yayin da Jiddah ta fice tana tayashi. Ganin tai shiru bata k'ara Magana ba yasa ya shima yai shiru na wasu y'an dak'ik'u,yanayin zaman nasu sai ya ke hararo mai abubuwa da yawa cikin ransa bai aune ba ya ji mirmishi ta kufce mai wanda har yasa hak'oransa bayyana.gyaran murya yai cikin kwantar da harshe yace "Su'ada irin karb'ar da a kaiwa bak'unci na kuma kenan?" Turo baki tai cikin kalar shagwab'a ta ce" To ba kai ne ba na b'ata lokaci na wajan had'a ma abu kace wai ka k'oshi." "To in dai don wannan ne ki yi hak'uri zan ci kinji." D'an mirmishi tai da fad'in "Yawwa ko kai fa Khaleelee." Yanda tai maganar sai abun ya bashi dariya ya girgiza kai ya na d'aukan cake guda d'aya ta kai bakinsa. Mik'ewa tai da ta na cewa "Bari na baka waje ka gama ko." "A'a ki yi zamanki ba damuwa." Duk ji tai kunya ta kamata bazata iya sashi gaba yana cin abinci ba. Dabara ta fad'o mata tace "OK to bari na d'auko wayata." ya gane take son mai kawai don ta fita d'in ne don haka yace "To na baki minti biyu in kika wuce kuma kisha bulala." Dariya tai tare da fita. Shi kam Ibrahim duk yau sai ya ke jin sa wani iri,kamar ba shiba,ga wani nishad'i da yake ji ma ratsashi. Cake d'aya kawai ya ci da danbun nama kad'an ya d'an sha lemon kwakwar rabin kofi. Har minti biyar yaga bata dawo ba don haka ya d'auki wayarsa ya mata flashing. Can sai gata idonta kan kayan tace "Hhhmmmm Khaleelee k'afarka k'afar kayan nan fa,don bazaka barni dasu ba,in ka je gida da dare kaci." "Su'ada Allah don ke ce ma fa kawai na d'an tab'a, ni ban son cin komai in ba irin lokacin cin abinci ba,cikina bashi da zurfi sam,ko abinci ba wani me yawa na ke ci ba." "Tab d'in matarka zata sha fama kenan." "Haba? Faman me zata sha?" "Sabida ba ka son abinci,ko yaushe sai tai rarrashi zaka ci." Y'ar dariya yai tare da shafa gemu yace "Ba ko wace mace bace ke damuwa da cikin mijinta,wata in dai ta dafa ta yi me wuyar ko kaci ko ka barshi bata da matsala." Cikin mamaki ta ke kallon sa" Lalle wannan wace irin mata ce haka,ni wlh in nai abinci naga ba'a ci da yawa ba duk sai in shiga damuwa,in yi ta tunanin ko dad'i ne bai yi ba aka k'i ci." "Hhhhhmmm ke kenan Su'ada amma matan da yawa muna tare da su muna kallon d'abi'unsu sai hamdala kawai." "To Allah ya shirya su." Cikin dariya yace "Amin dai ." Khaleelee ne ya yi sallama k'ofar d'akin, A tare suka amsa mai,sannan ya shigo fuskarsa cike da fara'a yace "Aunty sannu da gida." "Yawwa my Khaleelee, ga takwaranka ya zo." K'arasawa yai wajan Ibrahim ya gaida shi, shi kam rik'o hannunsa yai yana tsokanar sa "Kwana biyu Khaleelee an daina zuwa da kai wajanmu,gashi ka zama k'ato ko hanya na ganka ban iya shaidaka." Cikin yarinta Khaleelee yai dariya da fad'in "Haba dai Kana ganin pic's d'ina fa a wayan Aunty Rannan ma tace kace wai kana gaida ni." Dariya Su'ada da Ibrahim su ka sa,Ibrahim na ta jan sa da hira da tambayarsa school.To Khaleelee Radio nan ya kunce da surutu,Ita kam Su'ada jefi jefi ta ke s musu baki cikin hirar sai dai mirmishi kawai ta ke. biyar da rabi ya dubi agogonsa ya na jawo ledar da yazo da ita,mik'o mata gaban ta yayi yana cewa "Ayi hak'uri ga kyauta ba yawa,ina tayaki murnar kammala karatu lafiya,Allah ubangiji ya sa ki amfani karatun ki." Cikin jin dad'in addu'ar sa tace "Ameen Ameen Khaleelee na gode sosai,ga shi har da wahala haka,wlh zuwan naka yafi min komai dad'i fa." "Nima na gode sosai da irin taryar da akamin, yanzu in ba damuwa zan gaishe da Mama." "Lah ba damuwa bari nai mata magana." Bayan ta shiga ta sanar da Mama tace yazo su shiga. A falo take zaune ya shiga su ka gaisa cikin girmamawa tana tambayar sa Sana'a don daman shine telanta itama. Amsa mata yai da Alhamdulillah.sannan tai mai fatan alkairi ya taso suka fito tare da Su'ada da Khaleelee d'an rakiya. A bakin gate su ka tsaya hannayenta d'auke da ledar da ta juyo mai cake da danbun naman da bai ci ba. "Su'ada kin rantse dai sai na tafi da kayan nan ko?" "Eh ka ci ka bawa Jabir.ka san gauraye da kwad'ayin cikin dare." "Inye lalle kin ci bashi zan rama kuwa da." "A'a yi hakuri Khaleelee wasa na ke ma ." Kafin yai magana wani me napep da ya ajiye wasu ya fito cikin layin.tsaidashi yai ya fad'a mai in da zaije, bayan ya shiga ta mik'a mai ledar ta na ta mai godiya . *25/10/2019* *Taku ce* *mutan Ja'oji*🙋 [2/23, 11:51 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _*page*_ *11-12* Bayan Su'ada ta shiga gida ta d'auki ledar da Ibrahim ya kawo mata ta kaiwa Mama.kayan kwalliya ne da turaruka na mata masu kyau da k'amshi. Mama tace "To an gode mai Allah ya bar zumunci." D'aukan ledar tai ta wuce da ita d'akin su tana k'ara duba kayan fuskarta d'auke da mirmishi. Bayan Sallar magrib ta d'auki wayarta ta kunna data,Sakon ban gajiya ta turawa mai da karin godiya,duk da bai online,itama kashe datan tai ta fito falo don cin abincin dare da dukkan y'an gidan kamar yanda al'adar gidan take. Wajan k'arfe tara bayan sun gama hira ta dawo d'aki ta cire wayarta jikin charge, bayan ta hau WhatsApp sak'on Ibrahim ne ya fad'o cikin zak'uwa ta bud'e,shima dai godiyar ya mata da karamcin da su kai mai,mirmishi tai ta na bashi amsa. " _Ka canci fiye da haka a gareni Khaleelee, ina jinka tamkar d'an uwana na jini, fatana zumuncin mu ya dore fiye da haka_" Ibrahim da ke zaune k'ofar gida kan dakali yana shan iska kasancewar ba wuta yai mirmishi bayan karanta sakon nata,sannan shima ya maida mata amsa. " _Insha Allah zumuncin mu me d'orewa ne,ni ma matsayin k'anwa na d'auke ki Su'ada, kuma insha Allah nan gaba ma matsayin ki zai zarce hakan_" Maimaita rubutun tai ta yi,tana tunanin in matsayin ta ya zarce na k'anwa a gun Ibrahim to me zai koma? Bata da amsar tambayar don haka ta maida mai amsar " _Haka na ke fata insha Allah_" " _ki cewa takwara ina mai bangajiyar surutu fa_" 😂" _zan fad'a mai da safe yanzu ya yi bacci_" Wata hirar suka shiga daga nan kuma. Su'ada na ta juyi kan gado cike da farin ciki,don yau Ibrahim ya bata lokaci sosai sun sha hira duk da rabi duk kan matsaltsalun karatu ne da rayuwar makaranta amma sun d'au lokaci suna tattaunawa sannan su kai sallama. ***************** Tun daga wannan ranar sai wata shak'uwa sosai ta k'ara shiga tsakanin Ibrahim da Su'ada, kasancewar yanzu ba school tana samun lokacin chart sosai,shi kuma in bai da aiki kawai sai yaji yana zamu d'in bud'e data ko zai ganta online su yi hira. A haka wata guda cif da Mama ta d'ibawa Su'ada ta fidda miji cikin samarinta ya cika,kuma a lokacin ne Jameel ya bud'e mata wuta kan ta bashi dama ya aiko, kullum sai dai tace ya bata lokaci, ba ma shi kad'ai ba ke damunta kan suna son fitowa.duk ta rasa sukuni, Allah ya taimake ta Mama batai mata maganar ba,har Abbansu ya dawo gari,hankalin Mama ya koma ga kula da mijinta. Yau da dare suna chart da Ibrahim take bashi labarin halin da take ciki. Ji yai wani gumi ya yanko mai ya ji gabansa na fad'uwa, cikin ransa ya ke tunanin anya bai son yin sake kuwa,anya wankin hula bai shirin kaishi dare kuwa? Lalle in ya ci gaba da wannan zurfin cikin zai kwana ciki. Tattaro nutsuwa ya yi ya sawa kansa,sannan ya fara typing " _Su'ada ashe y'an takarar taki da yawa haka? An yi masu k'ananun jam'iyu zasu iya tsayawa takarar neman wannan kujera kuwa_?" Bata gane zancan nashi ba,sai taga ma kamar wata yake son bawa amsa ba ita ba,don haka tace mai " _Ban gane ba Khaleelee ko baka fahimci maganata ba_" Mirmishin yak'e yai daga kwancan da yake don cikin damuwa ya ke jinsa sosai. " _Na gane mana Su'ada, na san me kike nufi nine dai biki fahimci maganata ba_" Amsa ta maida mai da " _Eh gaskiya hakan ne ban fahimci zancan naka ba_" " _Su'ada yanda tarin maneman auran ki su ke,kuma su ka shirya aure a yanzu, shin yanzu in me k'aramin k'arfi kuma wanda zai iya yin aure amma nan da shekara guda ya zo neman soyayyarki a yanzu zaki bashi dama kuma ki soshi_?" Ji tai kanta ya wani yi gim ta fara gane me Ibrahim ke son cewa,in har kuwa hakan ya kasance za tayi farin cikin cikar burinta. " _Abunda ba ka sani ba Khaleelee duk cikin masu neman auran nawa ba wanda hankalina ya kwanta da shi,wlh duk wanda na zab'a cikin su na cuci kaina,don duk basu cika sharud'an da nake so mijin da zan aura ya cika ba,basu da wasu quality's da nake buk'ata ga mijina_." " _Su'ada shin namiji irina me irin halayena zai iya zama cikin zuciyarki_?" Hannayenta har rawa su ke wajan maida mai amsa " _Mai zai hana Khaleelee? Ban Neman komai tare da mijin aure na irin kyawawan halaye, sam abun duniya bai birgeni ga namiji matuk'ar halayensa muyagu ne,abu na gama cikar halitta wannan itama ina fatan samu,ba kuma wai kyawun fuska ba,Aa kawai dai in namiji ya kasance kalar sadauki shima yana birgeni_"🙈 "Alhamdulillah." Ya furta a fili tare da d'ora wayar kan k'irjinsa, lalle ya san ba zai sha wahala ba wajan Su'ada ya fuskanci samun soyayyar ta cikin ruwan sanyi. " _Su'ada_! " " _Na'am Khaleelee_" " _Shin Ibrahim zai iya bayyana miki ya na cikin y'an takarar neman soyayyar ki_" "Wayyo Allah na,Allah Allah wai gaske ne wannan rubutun da Khaleelee ke yi ko tsokana ya ke?" Su'ada ta fad'i bayan ta mik'e tsaye tana k'ara kallon screen d'in wayarta. Rasa me zata maida mai amsa tai sai yarfe hannu take kamar me jin fitsari, minti goma cif yaga bata maida mishi amsa ba don haka yace " _Su'ada biki ce komai ba,ko dai ban kai in shiga cikin y'an takarar ba_?" Saita kanta tai wajan bashi amsa " _Khaleelee_🙈" " _Hhhmmmm bud'e idon kiyi magana mana_" "🙈 _kunya na ke ji,ban San me zance ma ba_" Wadataccan mirmishi yai yana jin wani sukuni na ratsashi. " _Karki damu fad'a min duk abunda ke ranki_" " _Ba komai a ran Su'ada sai Khaleelee_🙈🙈🙈 Tana tura mai tai saurin kashe datar da wayar ma gaba d'aya. Shi kam rubutun yai ta maimaita karantawa yana sakin wani mirmishi me cike da zallar shaukin so. ********* Su'ada kwana tai mafarkin Khaleelee. Da safe kowa ya ga tsananin fara'a tare da ita,duk da ita d'in me fara'ar ce amma ta yau ta banbata, Jiddah ta gaji dai bayan sun zauna break take cewa "Aunty Su'ada wai meye labari naga kinata fara'a tun asuba?" "Kai Jidda gulma ko,daman can ni me fara'a ce." Abbansu ne ya d'ago yana kallonsu cikin mirmishi yace "Su'ada daman me fara'a ce Amma nima naga yau tai yawa." Duk dariya suka sa,ita kam abincinta taci gaba da ci tana k'ok'arin rage farin cikin da ke kan fuskarta,duk da yak'i b'oyuwa. Bata bud'e wayarta ba sai bayan sha d'aya a k'ok'arin ta na danne zumudinta ga Khaleelee. Tana bud'ewa sak'on sa na fad'owa ta message. _Amincin Allah da rahamarsa su tabbata gare ki,Ina fatan gimbiyar mata ta tashi cikin k'oshin lfy, kin d'arsa min Zuma a baki kin gudu,tun daran jiya har zuwa yanzu nake ta kiranki wayar a kashe,ki barni ko Kalma d'aya in fad'a miki kin k'i,kin sa na kwana cikin maraici da zumudin kasancewa da ke,don Allah da kin bud'e wayar ki sanar dani_" "Wash Allah Khaleelee na." Ta fad'a tana dafe k'irji, yanzu ta ya zata iya sanar mai ta kunna waya,message zata mai ko kiran sa zatai? Kai duka ba zata iya ba,kunna Data tai tana son duba sak'onninta na WhatsApp, nan ma da sak'onsa,ta karanta ta k'ara karantawa,tana jin wani sukuni na ratsata. K'arar wayarta ce ta dawo da ita duniyar tunanin da ta shiga, sunan Khaleelee ta ga na yawo kan wayar ji tai gabanta ya fad'i, Karo na farko da zata fara waya dashi matsayin saurayi ba telanta ba. Har ta katse tana taraddadin d'auka,wani kiran ya kuma shigowa cikin sanyin jiki ta d'aga da kara wayar a kunnanta, shiru ne ya biyo baya na y'an sakanni. " *Su'ada*" Can k'asan ta amsa kamar tana tsoron ajita, " "Na'am,ka tashi lafiya" "Um um,kin sa ciwo ya kamani tun jiya." Kamar yana kallonta ta zaro ido da fad'in "ciwon me kuma?" "Hhhmmmm ciwon sonki mana." Shiru tai tana jin kunyar zancan nasa, shi kuma jin tai shiru yasa ya d'ora, "Me yasa kika kashe wayar ki jiya,kuma yau kika k'i kunnawa da wuri,kin san abunda hakan ya haifar min kuwa?" Cikin shagwab'ar da bata san ta yi ba tace"Um to ni ban San me zance ma ba shi yasa na kashe." "In ke biki San me zaki fad'a min ba ai ni Ina da abun fad'a, kinsa jiya na kwana ina juyi da kiran sunanki,sai da Jabir yai tamin addu'a yai zaton ko gamo na yi." Bata San lokacin da dariya ta sub'uce mata ba tace"Khaleelee, wai gamo." "Eh mana gamo nai ammifa a so da kyakykyawar yarinya me d'abiun mutanan kirki, duk ta mamaye zuciyata." "Hhhhm" kawai tace,shi kam kalamai kawai ya rink'a sakar mata wani tayi mirmishi wani tai dariya wani ko shiru ta ke kamar ruwa ya cita, minti ashirin sukai sallama,ya barta da waya a hannu tana tunanin daman haka Khaleelee yake,tana mai kallon shiru shiru ashe fallallene shima. ******* cikin d'an lokaci soyayya me k'arfi ta shige tsakaninsu, ko yaushe kaga Su'ada mak'ale da waya a kunne,in har ka samu basa waya to aiki ya sha kansa a shago, da rana waya da dare charting ko yaushe cikin sakarwa junan su kalamai suke,kuma yace duk lokacin da Mama ta k'ara mata zancan fidda miji a shirye yake ya turo manyan sa. Wannan ya k'ara sawa Su'ada nutsuwa da shi ta kuma sakankancewa da soyayyar sa. *Taku ce* *Y'ar mutanan Ja'oji*🙋 [2/23, 11:52 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _*page*_*13-14* Mama na lura da duk sabgar da Su'ada ke yi,kuma ta fahimci da Ibrahim ta ke yawon yin wannan wayar,don haka ta k'ara bata lokaci su fahimci juna tunda ta lura soyayyar tasu sabuwa ce. wani sa'in ta na ji in suna waya zata Kira Khaleelee tace yazo ya gaisa da takwaransa,ko kuma su jidda su amsa su yi ta hira har su Sajida ma. yanda Mama ta lura Ibrahim na jan y'an uwan Su'ada a jiki ya sa ta k'ara nutsuwa da lamarin sa,duk da dai Su'ada bata fad'a mata abunda ke tsakanin su ba amma ita uwa me kula ai bata buk'atar bayani da ga halin da y'ay'anta ke ciki. ********* K'arfe tara na dare Ibrahim na zaune cikin gidan su,abinci ya ke ci a tsakar gida suna hira da matar yayansa Sakeena. rabin hankalinsa na ga wayarsa,ihsan k'aramar y'arta tazo ta dafashi tana mai surutun su na yara,dariya yai yana nuna mata hoton da ke kan wayarsa,yace "Ihsan kin ga Auntyn ki ko?" Da sauri Sakeena ta mik'a wuya da ga inda take tana son hango hoton, ganin me ta ke yasa Ibrahim shiga cikin gallery ya fiddo hoton Su'ada guda d'aya ya mik'awa Sakeena wayar yana fad'in " Maman Abbah ga k'anwar ki insha Allah very soon tana tan tafe." Da hanzari ta amshi wayar tana k'arewa hoton kallo "Kai Ibrahim ina ka samo wannan bafulatanar haka?" Y'ar dariya yayi yace "Costumer ta ce a da,amma a yanzu matar da nake son aura ce insha Allah." "Gaskiya masha Allah da ita. amma da gani ba ta jin hausa ko?" Wata dariyar yai sosai yace hausa iya hausa kuwa,Mamanta bahaushiya ce, Babanta ne bafulatani kuma ko jin filatancin ma basa yi. bari na kirata Ku gaisa." Amsar wayar yayi daga hannunta ya fara danna kiran number d'in Su'ada, bugu biyu ta d'auka cikin shagwab'ar da ta saba mai tace "Yau an manta dani tun k'arfe d'aya na rana." "Ayya, Yi hakuri aiki ne ya rik'e ni sosai sai yanzu ma na shigo gida,ya kike ya kowa?" "Kowa lafiya amma ni dai ba lafiya ba." "Subhanallah me ya sameki?" Ya fad'a cikin fad'uwar gaba. "Rashin ka tare dani mana,yau haka na yini ba sukuni." Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace, "Kiyi hak'uri kinji,kinsan yanayin sana'ar ta mu wani lokacin sai godiyar Allah.ga Matar Yaya muktar zaku gaisa." Dai daita muryar ta tai ta dawo normal, Sakeena ta amshi wayar da sallama,itama ta amsa mata su ka gaisa cikin girmama juna ta tambaye ta yara,ta amsa mata da duk suna lafiya,daga nan su kai sallama.amsa yayi ya mik'awa Ihsan da ke ta mik'a hannu tana son ya bata, Cikin maganar ta ta yara suka gaisa tana ta mata shirme,ita kam ta biye mata ta na ta dariya. k'arb'a yai duk ya bawa yaran suka gaishe ta sannan ya tashi ya shige d'akin sa. Nan ya narke mata cikin soyayya duk yanda Su'ada take mishi shagwab'a In ya fara mata tashi dariya kawai take mai. don Ibrahim irin mazan nan ne masu bala'i bala'in iya soyayya, cikin d'an lokaci ya ke haukata Su'ada da kalamai, wani lokaci in tai fishi har kuka zata ji yana mata cikin waya wai duk na rarrashi ne,nan da nan zata rikice ta dawo rarrashin sa ita ma. To yanzu ma haka ya kashe ta da kalamai ya kawai da k'orafin da ta ke. juyi kawai take kan gado tana lumshe ido don yanda kalaman sa ke ratsa dukkan zuciya da gangar jikin ta. ********* Wannan karon Abbansu Su'ada wata biyu yayi a gida sannan ya koma sari. kwanansa biyu da tafiya Mama ta kira Su'ada d'aki,bayan ta zauna tace "Mama ga ni." Kallonta mama tai na d'an lokaci sannan ta gyara zama ta fara magana,"Su'ada ya maganar da mukai da ke tun watanni biyu ko uku da su ka wuce?" D'agowa tai ta kalli Maman kamar ba ta gane inda ta dosa ba. "Eh maganar Fitar da mijin aure da nace kiyi cikin masu son ki." K'ara k'asa tai da idonta tana wasa da gefen rigarta, jin tai shiru ya sa maman fad'in "Ina sauraran ki Su'ada maza fad'a min wa ki ka fitar cikin su?" Karon farko da taji tana kunyar mahaifiyar ta wajan sanar da ita wata magana,amma ba yanda ta iya haka ta daure ta fara magana,"Mama daman Ibrahim ne yanzu dai . ." sai kuma tai shiru. "Um hmm ina jinki,wane Ibrahim d'in?" Daurewa tai tace "Khaleelee tela." "Ok shima son naki ya ke?" Gyad'a kai tai idonta a k'asa. Numfashi Mama ta sauke tare da fad'in "Su'ada ban son ki yi gaggawa cikin zab'in ki shi yasa na k'ara miki dogon lokaci don ki k'ara nazartar wanda ya fi kwanta miki a rai kuma ki ka yarda da ingancin sa,shin Kin tabbatar Ibrahim d'in ya miki kuma shima d'in da gaske ya ke?" Muryar ta a sanyaye tace "Eh Mama da gaske ya ke,ya ce duk sanda aka min magana zai turo manyan sa." "To masha Allah, Allah ya sanya alkairi. Tabbas nima na aminta da d'abiun Ibrahim da tarbiyar sa,Allah ya sa abokin rufin asirin ki ne." D'an mirmishi tai amma kanta a k'asa ta kasa amsawa da Ameen. cikin zolaya Maman tace "Wai yau kunya ta ki ke ji ne Su'ada? Sai sunne Kai ki ke kamar kina gaban surukar ki." Dariya tai tana d'ora hannayen ta a fuska.Maman ma darawa tai sosai cikin farin ciki, don ita farin cikin y'ay'anta shine nata. musamman yanda ta lura Su'ada na son Ibrahim matuk'a. "Shi kenan za muyi magana da Abbanku insha Allah, in yaso sai manya su shiga cikin maganar,tashi ki je Allah ya yi muku albarka." Mik'ewa tai tana fad'in "Ameen,muna godiya,Allah ya ja da rai." Wannan addu'ar su ga Mahaifiyar su ce ko yaushe. Allah Allah take Ibrahim ya kira waya tai mishi albishir, ai kuwa da ya kira ta sanar dashi kamar an ce mai an tsaida ranar auran su haka ya ji. ya sanar da ita zai fad'awa mahaifin sa kome ake ciki. ********* Ibrahim ya yi magana da yaya Muktar sannan su ka sanar da mahaifin su,yaji dad'i kuma ya yi farin ciki don kullum mita ya ke Kan rashin auran na sa.nan dai ya tura y'an uwansa guda biyu su kai mai binciken gidan su Su'ada, komai an same shi yanda ake fata, sannan ya ce ya sanar da Su'ada ta fad'a a gida za'a zo kawo kud'in aure. Su'ada kam Lokacin daya sanar da ita za'a kawo kud'in aure tamkar ranar ce ma tazo haka ta ji, duk yanda ta danne murnarta sai da ya gane don haka dariya kawai yai ta mata ya na tsokanar ta. Bayan ta sanar da Mama itama ta sanar da mahaifin Su,ya kira danginsa can Darki da kuma amininsa da ke nan cikin gari, ya ce su yi bincike kan Ibrahim duk da an sanar dashi halin kwarai gareshi,amma su k'ara bincikawa in an samu komai yanda ya dace to su tsayar musu da ranar da zasu kawo kud'in auran. Bayan dogon bincike kan Ibrahim Manyan Su'ada basu sami komai ba sai shedar arzik'i daga kowa.hakan yasa ba Jan lokaci aka basu damar su kawo kud'in auran. Sun kawo kud'in su dubu talatin na aure kasancewar sa me k'aramin k'arfi. Akai fatan Allah ya sanya alkairi da albarka. To fa Su'ada da Ibrahim an yi baiko nan magana ta yad'u kowa ya ji, ciki harda samarinta da yanzu su ka fahimci daman ba sonsu take ba.Jameel ya yi takaici kamar kamar me amma ya hak'ura ya san ba matar sa bace daman can. Ita kam Su'ada ko a kwalar rigar ta farin cikin ta kawai ta ke sha,ta fara shanshano auranta da burin ranta. ********* Lokacin azumi ke tunkarowa da gaske wanda ya rage kwanaki goma a d'auka,zuwa lokacin Sam Ibrahim ba shi da wadataccen lokacin kansa bare na soyayya, don kullum cikin aiki su ke,kaya kamar zasu tsaga shagon su,tunda ya San hidimar da ke tunkaro shi yanzu ta aure yasa ya k'ara himma wajan tara kud'i,ahi ya sa ya ke d'inkin sa ba kasala.Su'ada ta San yanda ya ke shiga busy lokacin azumi tun asali don haka bata damu da rashin nemanta da ba ya yi sosai ba,a haka watan ya kama komai ya kara cab'ewa,ko yaushe dai in ansha ruwa zata kirashi ta mai barka da shan ruwa,to a wannan d'an tsakanin ne kawai su ke samun yin waya kafin a kira isha'i a hakam ma hankalin sa duk a rabe ya ke yi,ya na fama da jama'a, ya na waya.To in sun yi Sallama daga nan kuma sai washe gari. Wannan karon Mama ta hana kowa kaiwa su Ibrahim d'inkin Salla,ta ce yanzu ya zama suruki ba zai yuyu a tara mai d'inki sama da goma ba kuma ya ga ya k'i amsar kud'in,Wannan ba girma bane. Badan sun so ba su ka kai wani shagon don duk basu saba da kai d'inki wani wajan ba. Da kansa ya ke tambayar ta ba zasu kawo dinkunan su ba,ta sanar da shi Mama ta hana, da ya tambayi dalilin ta fad'a mai, ya nuna rashin jin dad'in sa a zahiri,amma ba yanda zai yi tunda an riga ma an kai su wani wajan ba damar amsowa. *********** Ranar da azumi ya yi sha biyar a ranar Ibrahim ya yiwa Su'ada zuwan bazata,don su na idar da sallar Asham ta ji kiran wayar sa,da zumud'i ta d'auka don daman yau ko barka da shan ruwa ba ta mai ba,wayar sa a kashe take, d'agawa tai tare da sallama. Bayan ya amsa kafin tace komai yace "Ina k'ofar gida yanzu ." Mirmishi tai tace, "Hhhmmmm tsokana ta ko?don kaga na matsu da son ganin ka." "Da gaske fa ina bakin gate." Da sauri ta mik'e ta na fad'in "Bari a shigo da Kai to." Kashe wayar tai da murna ta ke kiran Sajida, "Sajida maza je waje Khaleelee na nan ki shigo dashi sitting room,ki kai mishi ruwa da lemo in ya shigo." Juyawa tai cikin d'aki da sauri ta cire kayan jikinta zuwa Riga da siket na atamfa sannan ta duba fuskarta ba komai jiki kasancewar bayan shan ruwa tai wanka,powder ta goga kawai ta gyara gashin idonta da maskara,sannan ta gyara girarta,bakinta ta d'an gogawa jan baki me saukin k'ala,ba ta sa d'an kwali ba sai mayafin kayan da ta rufa tare da fesa turare me saukin k'amshi, plat d'in takalmi ta saka ta fito zuwa d'akin Mama don ta sanar da ita zuwan Ibrahim d'in, Mama tace to sannun shi da zuwa,a kai mai ko fruits ne da lemo. Amsawa tai ta fito cikin zumud'i. Da siririyar sallama ta shiga,kansa na ga TV d'in da ke ta aiki, a hankali ya d'ago ya zuba mata ido cikin mayataccen kallon sa me narkar da ita. Ji tai wata kunya ta lullub'eta ta da su ka had'a ido,ta sa hannayen ta biyu akan fuskarta bayan ta lallab'a ta zauna kan kujerar da ke farko. Cikin shauki ya ke kallonta, gaba d'aya sai ya ga ta canja mai,yanda ta rufe fuska ma sai ta bashi sha'awa, k'asa sosai ya yi da murya yana fad'in " To tunda ni ba'a min barka da zuwa ba ni bari in miki barka da gida, Allah ya taimaki Gimbiyar mata zak'in zuciyar Ibrahimal Khaleel, ina fatan na same ki cikin koshin lafiya." A hankali ta zame hannayen ta amma idonta a k'asa tace "Sannu da zuwa ya Ibada ya aiki?" Y'ar dariya yai yace "Ni ba'a amsa gaisuwar da nai ba an min wata,to Sannunki, Ibada Alhamdulillah, aiki kuma gashi muna fama kullum ba sauk'i. Ya Mama da sauran y'an gidan?" "Duk su na lafiya qlau,Ya jikin Baba?" "Baba jiki da sauk'i Alhamdulillah." Shiru ne ya d'an biyo baya,shi ya k'ara kauda shurun da fad'in "Kin rame Su'ada ko azumin ne?" d'agowa tai karo na biyu su ka had'a ido,ya k'ara narkar da idanuwansa cikin nata, kauda kai ta d'an yi cikin kaucewa kallon tace"Kowa haka ya ke fad'a, amma ni banga ramar da nai ba." "Hhhmmmm ko kowa ma bai gani ba ni zan gani ai,kinga alamun ci gareki yanzu ba'a samun yanda ake so shine aka rame haka." Da sauri ta kalleshi da fad'in "A'a fa, Allah ni banda ci,kawai ulcer ta tayar min ne jiya da yau,amma ba azumi bane." Mirmishi yai yana kallonta sosai,don ta mishi kyau k'warai da gaske.ganin kallon ya yi yawa yasa cikin Shagwab'a tace "Oh Khaleelee kallo haka." Kwaikwayon muryar ta shima yai yace "Oh Su'ada kyau iya kyau haka." A tare suka saki dariya, daga nan kuma suka shiga hira me gardi irin ta Masoya. Awa guda cif ya yi ya ga goma ta yi,kallonta yai tare da kallon agogo yace "Hajjaju dare ya yi ko?" D'an turo baki tai kalar na shagwab'a tana girgiza kai tare da marairaicewa. "Wasssh Allah wannan salon fa zai iya hanani tafiya don Allah a barni in tafi kinji." Juyar da kai gefe tai tana buga k'afa alamar tak'i yarda d'in. Gaba d'aya abunda take k'ara narka Ibrahim take,yama rasa me zaice don ta wullashi duniyar shauk'i sosai,daurewa ya yi ya sauko da ga kujerar sa ya tsugunna gaban ta yana had'a hannaye alamar ban hak'uri, "Zan tafi ne badan na so ko na gaji ba,sai don lokaci ya nuna kamatar in tafi,sannan kin ga akwai tarin ayyuka agaba na, zan je in d'ora inda na tsaya,in harhad'a musu d'unkunan su su harhad'a min kud'ad'e na in samu in yi aure, kullum in ta zama tare da shagwab'ab'b'iyar mata ta." Bata San sanda ta sa dariya ba har duka hak'oran ta su ka bayyana. Ya na ganin haka ya mik'e shi ma ya na dariyar, ita ma mik'ewar tai tare da hard'e hannayen ta a k'irji ta tsare shi da lumsassun idanuwan ta,sosai shima ta narkar da nasa su ka sark'e idanuwan junan su cikin mayen so. Ita ta fara janye nata a kasalance tace "Sai kuma yaushe Khaleelee?" Sauke ajiyar zuciya yai Sannan yace " Sai zuwan Salla kuma,in na samu kaina zanzo in miki awa uku cikakku kinji." D'aga mai kai tai cikin gamsuwa. Shi kuma ya saki mirmishi ya na nuna mata ledojin da su ke gefe, "Su'ada ga wannan ba yawa kin san mijin naki me k'aramin k'arfi ne." " Don Allah me yasa ka wahalar min da kanka wajan siyayya,Allah da ka barshi amma har wannan uban kayan." Zare ido ya yi ya na d'ora hannunshi kan lips d'in sa kamar ya na tsoratar da yaro. "Kin san me ye a ciki kike cewa da yawa? Kuma ban wahalar miki da kaina ba wajan siyayya ba wani abu ne me yawa ba fatana kawai su yi miki." Annuri ne ya k'ara k'aruwa a kan fuskarta tace "To na gode Khaleelee, Allah ya k'ara bud'i da arzik'i me amfani,Allah ya tsare min kai." Sosai ya ji dad'in addu'ar ta cikin fara'a matuk'a yace"Ameen Ameen Sweet Su'ada. in kin shiga ki gaida min Mama ki yi mata barka da shan ruwa, ki gaida Takwara me baccin wuri." "Ok duk za su ji insha Allah." Rakiya tai mai gate ya fidda mashin d'in sa da ya zo da shi, cikin kewar juna su kai sallama ya tafi. Da ta dawo ta d'auki ledojin manya guda biyu ta shiga dasu gida,a falo ta samu kowa duk su na kallo,ajiye ledojin tai gaban Mama tana fad'a mata sak'on gaisuwar sa,Mama ta amsa cikin jin dad'i. Ita dai wucewa tai d'aki don cire kayan jikin ta.Jidda ce ta bud'e ledojin, ta farko Atamfa ce me kyan gaske, d'inkin riga da siket abunka da masu abu,an tsantsara d'inki, sai material royal blue me laushi an mai d'inkin doguwar riga, yaji stone work, sannan takalmi kamfanin Vinci, da mayafi kalar takalmin. D'aya ledar kuma kayan ciye ciye ne fal su cake da su ice cream da lemuka. K'alawa Su'ada kira Mama tai, ta fito da ga d'aki, kallon tuhuma ta kafe ta dashi,a sanyaye ta k'araso ta zauna kusa da ita. "Su'ada wannan kayan fa?" "Mama shi ne ya kawo min." Ta amsa mata. "Na San shi ya kawo miki ai,ina miki maganar sun yi yawa ne,ban son kina takurawa bawan Allah fa,Su'ada a rayuwa kin san kowa da yanayin k'arfin sa, Ibrahim akwai hidima a gaban sa, bai kamata ya sawa kansa damuwa a ire iren wannan hidimar da samari ke yiwa y'an mata ba, aure ne a gaban sa,fata na ki samu kwanciyar hankali a gidan auran ki ba wani k'yale k'yale ba. Su'ada karki rink'a nuna mai ki na son ya miki wata hidima kinji ko,duk da na san ba halinku bane son abun wani,amma ki k'ara kiyayewa kinji." Jiki a mace ta gyad'a kai da fad'in "To Mama insha Allah zan k'ara kiyayewa." Bayan Jidda ta shigo mata da kayan sawar dak'i ta bubbud'e su tana dubawa,mirmishi kawai ta ke, a ranta ta ke cewa 'Allah sarki Khaleelee na,Allah ka k'ara bud'a mishi ka dafa mishi cikin sana'ar sa." *28/10/2019* *Taku ce* *Y'ar mutan Ja'oji*🙋 [2/23, 11:53 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ *Dedicated 2* *Aunty Maimuna OG* *malamata ta adabi . . .* *Maryam Obama*🤭🤣🤣🤣 *Hassan and Hussain 80k* *Alherin Allah ya kai muku har gadon barcinku*💃 *page 15-16* An kasafta gidan su Ibrahim an fidda mai b'angaran sa, d'akuna takwas da ke cikin gidan ya zama guda hud'u nashi guda hud'u na Muktar amma kasancewar Baba na zaune a d'aya, Jabir d'aya, kuma cikin rabon Muktar na sun ya ke ya sa ya zama biyu ya ragewa Muktar duk su ka kwashe kayansu su ka had'e a d'akuna biyu,Wannan dalilin ya sa Sakeena ta fara magantuwa da k'unci ta ke k'orafin tunda dai Amarya za'a kawo ai ita d'aki biyu ma ko uki sun ishe ta,ita dai gaskiya an shiga hakkinta,duk surutun da ta ke yaya Muktar bai kulata ba. Kud'in da ke hannun Ibrahim da kud'in filinsa da ya siyar ya bashi damar sauke duk d'akunan na sa da yankin tsakar gidan da aka fitar masa ya shaci gini lafiyayye, a kai mai tsarin gini na zamani,falo babba da d'akuna biyu sai kitchen da band'aki duk cikin falon sannan d'an k'aramin tsakar gida a ka fitar da k'ofa zuwa tsakar gidansu yaya Muktar. Wata biyu a ka d'auka wajan ginin don a sannu ake yin komai,kafin me lafiyayyan waje ya fito ya yi fes da shi, har tsakar gidan su Sakeena a ka gyara zuwa k'ofar gida. A b'angare guda kuwa Hajiya Uwa wata uwar d'akin Ibrahim ce kuma y'ar uwar mahaifiyarsa ce,harkar saida kayan sawa ta ke,su na shiri sosai da shi don shi ke d'inka ma ta kayan saidawar ta,Ita ya d'ora kan had'a lefe,komai ita ya ke bawa ta na siyo mai,kasancewar ta wayayyiyar mace kuma tsohuwar y'ar kasuwa ya sa ta ke siyo mai kaya na d'aukan magana. ************** Wata k'awar Maman su Su'ada principal a makarantar emmata ta karb'i takardun Su'ada ta samo mata teaching,kai tsaye Ibrahim ya amince mata a lokacin da ta sanar dashi,kuma ya bita da addu'ar alkairi, cikin d'an lokaci ta fara koyarwa a secondary d'in. A bangare guda kuwa lokacin bikin su sai k'ara k'aratowa ya ke an cinye watanni yanzu har ya rage sati biyar. Dukkan abunda a ke buk'ata a lefe an gama had'awa, Hajiya Uwa tai wa Ibrahim namijin k'ok'ari don ta had'a mishi komai ba raini.Yaya Muktar shi ya siya mai akwatina set guda 6 peaces kamar yanda yai alk'awari. Ranar a ka kawo kayan gidan su Ibrahim don y'an uwa su gani kafin a kai. Ranar Hassada ta biyu ta fara kama Sakeena a kan Su'ada, ta gama hassadar ginin da a kai mata sannan ta zo hassadar ganin irin kayan da a ka had'a mata. Cikin mutane ta na ta murna kamar me,amma da ta shiga d'aki ji tai kamar ta zubda hawaye don takaici. Da dare bayan Ibrahim ya dawo ta ke tsokanar sa cikin barkwanci da ga nan ta soko mai a bunda ke ranta "Ibrahim wannan kaya haka na ce anya kuwa ba a yi k'arya ba wajan had'a su,ina ganin kamar ka k'are k'arfin ka a lefan nan,Allah ya sa ma dai Hajiya Uwa ba ta had'a ma harda bashi ba duk da na ji Zakiyya ta na cewa komai kud'i ka ke badawa a siyo ma." Cikin mamaki ya ke kallon ta,can ya ce" Maman Abba me ye abun k'arya cikin wannan kayan? Akwati shida shi ne k'aryar?lalle don bi ki san wace Su'ada ba shi yasa har ki ke zaton an yi k'arya wajan had'a mata wannan kayan. To kin san me?cikin kayan nan babu a bunda ya ke bak'on ta,duk ta saba amfani da irin su har ma na sama da su.wannan kayan ba komai bane wlh don da ina da kud'i Su'ada ta fi k'arfin wannan kayan zan ninninka mata su." Cikin takaici da mutuwar jiki Sakeena ta ce" A'a wai daman ba haka na ke nufi ba,ina ganin wai kamar rayuwar ka San canji canji ce, da ka tattala kud'in hannun ka kwa siyi kayan abinci,ka ga kar da ga zuwan amarya a fara k'a k'a k'ara k'ak'a." Zuwa yanzu kuma Sakeena ta k'ular da Ibrahim don haka a d'an fusace ya ce "Allah ba zai hanani a bunda zan yi wa Su'ada hidima da shi ba, da ga zuwan ta ba zan rasa a bunda zan bata ta ci ba." Mik'ewa yai ya na shigewa d'akin su. Ita kam Sakeena tagumi tai ta na nazarin wai wace ce wannan Su'ada haka da aka cikawa mutane kunne da ita,y'ar uban waye da za'a ce ta fi k'arfin ma Wannan uban kayan in dai ba rainin wayo ba. Ranar a ka kawo kayan gidan su Ibrahim don y'an uwa su gani kafin a kai. Ranar Hassada ta biyu ta fara kama Sakeena a kan Su'ada, ta gama hassadar ginin da a kai mata sannan ta zo hassadar ganin irin kayan da a ka had'a mata. Cikin mutane ta na ta murna kamar me,amma da ta shiga d'aki ji tai kamar ta zubda hawaye don takaici. Da dare bayan Ibrahim ya dawo ta ke tsokanar sa cikin barkwanci da ga nan ta soko mai a bunda ke ranta "Ibrahim wannan kaya haka na ce anya kuwa ba a yi k'arya ba wajan had'a su,ina ganin kamar ka k'are k'arfin ka a lefan nan,Allah ya sa ma dai Hajiya Uwa ba ta had'a ma harda bashi ba duk da na ji Zakiyya ta na cewa komai kud'i ka ke badawa a siyo ma." Cikin mamaki ya ke kallon ta,can ya ce" Maman Abba me ye abun k'arya cikin wannan kayan? Akwati shida shi ne k'aryar?lalle don bi ki san wace Su'ada ba shi yasa har ki ke zaton an yi k'arya wajan had'a mata wannan kayan. To kin san me?cikin kayan nan babu a bunda ya ke bak'on ta,duk ta saba amfani da irin su har ma na sama da su.wannan kayan ba komai bane wlh don da ina da kud'i Su'ada ta fi k'arfin wannan kayan zan ninninka mata su." Cikin takaici da mutuwar jiki Sakeena ta ce" A'a wai daman ba haka na ke nufi ba,ina ganin wai kamar rayuwar ka San canji canji ce, da ka tattala kud'in hannun ka kwa siyi kayan abinci,ka ga kar da ga zuwan amarya a fara k'a k'a k'ara k'ak'a." Zuwa yanzu kuma Sakeena ta k'ular da Ibrahim don haka a d'an fusace ya ce "Allah ba zai hanani a bunda zan yi wa Su'ada hidima da shi ba, da ga zuwan ta ba zan rasa a bunda zan bata ta ci ba." Mik'ewa yai ya na shigewa d'akin su. Ita kam Sakeena tagumi tai ta na nazarin wai wace ce wannan Su'ada haka da aka cikawa mutane kunne da ita,y'ar uban waye da za'a ce ta fi k'arfin ma Wannan uban kayan in dai ba rainin wayo ba. Washe gari a ka kai lefe gidansu Su'ada, koya ya yaba da kaya kuma ya yi ala san barka. Su'ada kanta ba tai zaton wannan kayan haka ba,dalili ta san Ibrahim ba shi k'arfi ga hidimar ginin wajan zama da ya yi don ya mata hoton wajan ta gani an kashe kud'i sosai. Ai kuwa da dare ta kirashi ta na mai Addu'a Allah ya k'ara bud'i da arzik'i,shima cikin jin dad'in addu'ar ta ya shiga jera mata sa albarka da fatan ta zama uwar gidansa har aljanna. ********** Saura kwana uku a fara Biki a ka je jere, Mata da ba'a raba su da abun fad'a tun da ga k'ofar gida wasu su ka fara gunagunin wajan zaman Su'ada, wai an kawota gidan gargajiya gidan dangin miji,yarinya ta taso cikin gata amma ammata aure da telan mata,daman ai sai dai zaman hak'uri ba wai na nishad'i ba. Wasu da suka ga yanda aka tsara gini a part d'in na ta sai su kai shiru,don ko tayil bango da bango ne,ko ina na wajan layil ne,falonta k'ato da d'akunan ta biyu manya ba inda ba'a cika mata da kaya ba, kayan d'aki set biyu a kai mata ga Rolay chair's d'in ta manya manya, sun cika falon, kayan wuta babu abun buk'atar da babu,kama da ga kayan kallo na zamani firji zuwa kayan amfanin wuta na kitchen, ko ina na kitchen d'in ta an cika shi da kaya,sauran ma d'aki aka sa mata cikin sif don sun yi yawa. Sakeena fa tun da ta ga an fara shigo da wannan uban kaya zuciyar ta ta fara bugawa,ciwon da bai da magani ya taso mata wato ciwon hassada.kyashi da bak'in ciki su ka turnik'e ta,yak'e wanda ya fi kuka ciwo ta fara yi,tun bayan da su ka gaisa da y'an kafin ta shige d'aki ta na ta k'unci,tana tunanin yanzu haka zata zauna da FACALA wadda ta fita komai?. _____________ An kama biki ganga ganga, Ranar Alhamis a kai kamu da traditional day,Ranar Juma'a a kai party cikin gidan zoo don nan k'arfin sa ya ke,Ranar Asabar Maman su tai yinin ta,Sai Ranar lahadi a ka d'aura aure da misalin k'arfe sha d'aya na safe. Tun da a ka d'aura auren nan Su'ada ta fara kuka don yanzu kam ta tabbatar barin gida ya zo,duk yanda k'awayen ta ke tsokanarta ta zama ta Khaleelee ba ta saurare su ba.ganin kukan ya yi yawa ya sa wata k'anwar mahaifinta ta jata d'aki tai ta rarrashin ta da mata nasiha,Sai a sannan ta samu kukan ya tsagaita, ta ce ta k'ara gyara fuskarta don angwaye za su shigo a yi hotuna. K'awarta Khairi ce ta k'ara gyara mata kwalliyar ta sannan ta sake mata d'aurin da d'an kwalin Shaddar da ke jikin ta. Dummmm ta ji gabanta ya fad'i lokacin da a ka ce ga su Ibrahim sun shigo gaida iyaye,ba ta san dalili ba duk yanda ta kai ga d'okin son ganin wannan ranar amma sai ta ke ta jin fad'uwar gaba tun safe. Cikin kunnanta ta ji muryar Jiddah ba fad'in angwaye sun ce me hoto ba jira su fito a yi.jikin ta ba k'wari ta mik'e rik'e da hannun Khairi da sauran k'awayen su su ka fita cikin gate inda tarin cincirundon abokan Angon su ke. A hankali ta ji hannunsa cikin nata lokacin da a ka fara sakar musu camera a ka.duk ilahirin jikinta rawa ya ke,mamaki ya kama Ibrahim yanda ya ga ko ido ta kasa d'agawa ta kalleshi. Rage tsayinsa yai ya na mata magana cikin kunne "Su'ada me ke faruwa ne?wannan fa ranar farin cikin mu ce, nai tunanin ganin ki cikin farin ciki da nishad'i amma sai na ga duk jikin ki ya yi sanyi, ko a kwai matsala ne?" Ya k'arasa maganar da tambaya, a hankali ta girgiza kai alamar ba wata matsala. "To me ne ne ki kai sanyi da yawa,ko ba ki son a kawo ki gareni yau?" D'aga kai tai alamar Eh,ai kuwa bai san lokacin da dariyar sa ta bayyana ba,ya k'ara matse hannayen ta cikin na sa, kallon da ya ga kowa na musu ya sa ya basar kawai. Haka a ka gama hotunan har su ka tafi Su'ada ba ta bari sun had'a ido da Ibrahim ba duk kuwa da k'ok'arin sa na yin hakan. Bayan tafiyar su da kamar a wa guda ya yo mata message Wanda ya k'ara kashe mata jiki. _Matata farin cikina,wannan ranar mu ka dad'e mu na fatan Allah ya nuna mana,yau ga ta ta zo an d'aura mana aure Su'ada ta zama matar Ibrahim amma kuma na kasa ganin farin ciki a idon Su'ada sai Tsoro da fargaba kawai na gani,me ya sa? me ya sa Su'ada fargaba haka?In har a bunda na ke hasashe ne to ki kwantar da hankalin ki,za ki samu mijinki me hak'uri da kauda kai ki shigo gidan auranki cikin farin ciki kinji Matata._ Lumshe ido tai bayan gama karantawar ta na wani tunani cikin ranta. A hankali kuma ta saki k'aramin murmishi. A gidan su Ibrahim ma yinin biki su ke sha abunsu,don har da y'an DJ su ka d'auko,y'an uwa da abokan arziki su ka rak'ashe.wajan k'arfe biyar su ka taho d'aukan Amarya,in da aka ware mata uku masu karb'ar Amaryar, Hajiya Uwa sai wata Goggo k'anwar Mahaifinsu,da wata yayar mahaifiyar su, Sakeena ta dage itama da ita fa za'a yaya Muktar ya ce mata ta zauna,fit tak'i don ita burinta ta je ta gano gidan su Su'ada.cikin b'acin rai yaya Muktar ya ce "ke wai me ke damunki ne yanzu,nema ki ke ki canja hali,kawai a bunda ki ke so shi za ki yi? In kin zauna har d'akin ki za'a shigo miki da Amaryar." Ganin abun na neman zama rigima tsakanin ta mijinta ya sa Goggo ta ce "Sakeena ai ke me karb'ar bak'i ce kuma Amaryar ma in ta zo ke zaki tare ta bai kamata ki fita ko ina ba." Da haka dai ta koma ciki ranta bai so ba,don ta so ganin k'wak'waf. ****** Zuwan dangin Ango ba b'ata lokaci a ka basu amarya,Su'ada kuka y'an uwanta kuka duk sun bawa jama'ar wajan tausayi. Su kuwa abokan Ango da shak'iyanci sai vedio su ke wai za su Nunawa Ango. *Taku ce* *Y'ar mutan Ja'oji* [2/23, 11:53 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _*page*_ *17-18* *Sadaukarwa ga y'an uwa abokan aiki jama'ar k'ungiyarmu ta zamani writers Association* *Isah kin boy* *Kamal Minna* *Hussain 80k* *Zaid Ibrahim barmo* *Oga Bamai A.Dabuwa* *Mubarak Locorst* *Abu Sale Alkurami* *Y'an mata kuma ta Ku tafe* 🥰 Kai tsaye d'akin mahaifin Ibrahim a ka shiga da Su'ada ta gaisheshi nasiha sosai ya yiwa Su'ada kan hak'uri a zaman aure sannan da ga bisani ya bita da sa albarka.daga nan kuma a ka kaita d'akin Sakeena nan manya su ka had'a su su kai musu fad'a kan zaman lafiya a ka damk'a amanar ta ga Sakeena tunda sama ta ke da ita sosai, kuma ita ta tarar. Kamar yanda ya ke a al'ada barin k'awayen amarya su zauna tare da ita bayan tafiyar y'an kawo amarya. Yanzu ma ya rage Su'ada kawai da k'awayen ta biyu da y'ar uwarta Jiddah. Takura mata su kai kan ta tashi tai sallar magriba da Isha,haka ta shanye kukan ta ta je tai sallar,zama tai kan Sallayar bayan idarwar ta ta rafka wani uban tagumi,y'an uwan Angon da ke ta kararaini wajan shiga da fita su su ka k'ara takura ta ta kasa ko d'an yaye mayafin ta fito da fuskarta. Khairi ce ta hana kowa shigowa cikin d'akin ta ce duk wanda ya shigo ya tsaya falo don ta na son Su'ada ta gyara fuskarta. Tai tai Su'ada ta tsaya ta d'an k'ara mata kwalliya amma ta k'i yarda, turare ma humra da ta ce ta k'ara gogawa tace ba ta buk'ata,haushi ya kama Khairi ai kuwa ta hau fesa mata turare ta ko ina, duk ta feshe mata jiki. Su'ada ta d'ago hawaye na d'iga a idonta tace "Ki bari don Allah, wallahi kaina kamar zai fad'o ya fashe don ciwo, k'arfin hali kawai na ke." Dariya Khairi tai tace "Duk Wannan fa nok'e nok'en da kike a banza wlh,kin dai san yau babbar rana ce don haka dole ta zama ta musamman. " Hararar ta kawai tai tai k'asa da kanta,don yanda ta ke jin k'irjin ta na bugawa da wani fargaba abun ba magana. K'arfe tara na dare abokan ango su ka yo mai rakiya.bayan gabatar da addu'o'i da fatan alkairi ga Ango da Amarya a ka tab'a barkwanci tsakanin abokan Ango da k'awayen Amarya.da ga nan dai su ka d'auke su a mota don maida su gida. Tun fitar su falon ya yi tsit,Ita Su'ada fargaba da bak'unta sun lullub'e ta,shi kuma farin ciki da wani yanayi sun dabaibaye shi,hannu biyu ta sa ya tallafe fuskarsa yana kallon ta,ganin yanda ta duk'unk'une waje guda tana sheshshek'a a hankali ya san kukan bai k'are ba,daman abokansa sun nuna mai vedio d'in da su kai mata tana kuka a gida. A hankali ya mik'e tare da cire babbar rigar da ke jikin sa ya ajiye kan kujera, taku biyu uku ya k'araso ga kujerar da take zaune ya tsugunna,hannayen ta rik'o ya na bin k'unshin hannun da kallon sha'awa don shi kam filawa da jan lalle na matuk'a burfeshi ga mace,jin ta na k'ok'arin janye hannun ya sa ya k'ara rik'ewa da kyau,kusan mintina uku su na a haka can ya saki hannun ya mik'e da fad'in "Ina zuwa ki tashi ki yi alwala kafin in dawo kinji." Ko eehhmm ba ta ce ba balle ta amsa,fita yai zuwa d'akin Babansu, zaune ya sameshi ya na ta faman murd'a Radio a hankali ya tsugunna gaban sa da fad'in "Baba ba kai bacci ba ?" Cikin fara'a ya ce "Yanzu dai zan yi Ibrahima,kai me kake ba ka je ga iyalinka ba har yanzu?" Kansa k'asa cikin jin nauyin wai yau shi a ke kira me iyali yace "Eh daman fitowa nai in ma sai da safe Baba." "To madalla, Allah ya tashemu lafiya ya yi muku albarka." "Ameen Amaee Baba." Da ga haka ya mike ya fito. Bai same ta a falo ba don haka yai tunanin ko alwala ta ke,d'aki ya shiga don ajiye hular sa da babbar rigar sa. A kan gado ya isketa ta duk'unk'une cikin lifayar da ke jikin ta,d'an mirmishi ya saki tare da K'arasawa bakin gadon ya rank'wafa kanta sosai,da sauri ta runtse ido ta na k'ara duk'unk'unewa, sanyaya murya ya yi sosai ya sa bakinsa a kan kunnan ta,"Su'ada! meke damunki,nace ki yi alwala mu yi salla. " Cikin muryar ta da ba ta fita sosai tace"Ba ni da lafiya fa." "Subhanallah, ne ya same ki?" Ya fad'a fuskarsa d'auke da mirmishi don ya san neman mafaka kawai ta ke a halin yanzu. Kanta ta nuna mai da hannu alamar shi ke mata ciwo. "Sannu kinji,kukan da ki kai ne,yanzu ki k'ok'arta ki tashi ki yi alwala mu yi salla don nuna godiyar mu ga Allah da ya nuna mana wannan ranar wanda dubban matasa da y'an mata ke burin riska,yi hak'uri ki tashi kinji." Da k'yar ta mik'e ta je tai alwalar shima ya yo.bai tsawaita ba a sallar Raka'a biyu ya yi tare da addu'oin neman alkairai cikin aurensu da neman tsari da ga shed'an. Bayan sun shafa ya waiwayo da duban sa gareta cikin kulawa da k'ara sanyaya murya ya fara magana "Su'ada ba ni da tantama a kanki,dukkan tambayar da zan miki kan addini na san zan samu amsarta,b'angaren halaye duk ina da kyakyawan sani a kanki,kuma ina kyautata miki zaton d'orewa a haka,fatana Allah ya tabbatar mana da rayuwa me inganci." Shiru na d'an lokaci ya ratsa tsakanin su,can ya mik'e ya d'auko ledojin da su ka shigo da shi ya fiddo kayan ciye ciyen da ke ciki,takura mata yai kan taci wani abu ciki amma fir tace ta k'oshi ba ta son cin komai, k'arshe da yace ko taci ko ya yi mata d'ura kawai sai ta sa mai kuka,shi kam mamaki ta ke bashi,wani abu ta ke kamar ba ta saba da shi ba,ko ganin farko ta fara mai,rarrashin ta ya yi yace taje ta kwanta. Ba don zafin da ake ba da bata cire lafayar jikinta ba,don a tsorace sosai take dashi,amma ko kusa ko da wasa ba ta cire atamfar jikin taba,d'an kwalin ma ta kunce ta lullub'e jikin ta da shi. Shi kam ya na falo ya na cin kazar don sosai ya tara yunwa yau yini guda. Bayan ya ji ya koshi yai hamdala tare da had'e kayan ya kaisu kitchen. Kayan jikin sa ya sauya zuwa na bacci,a lokacin har bacci ya fara d'aukan Su'ada ta ji motsinsa a d'akin k'ara matsewa gefe guda tai tana addu'a cikin ranta Allah ya sa karya kwanta a gadon na. Ya na kula da motsin da take ta yi,amma bai ce mata k'ala ba ya lallab'a can k'arshen gadon ya kwanta tare da addu'o'i ya tofe jikinsa,tun da ga nan ko k'ok'k'waran motsi ya k'i yi don tai tunanin ma bacci ya ke. Ita kam Su'ada tun ta na zaton jin hannun sa a jikintea, har ta fidda tsammani,don haka ta samu nutsuwa a hankali bacci yai gaba da ita. Saukar numfashin ta da ya ji ya tabbatar tai bacci, a hankali ya tashi ya kunna haske ya na k'are mata kallo,ta rame tabbas sai dai kuma ta k'ara wani sirrintaccen kyau,musamman da ke ta sha gyaran jiki, gashin kanta ya bi da kallo Wanda d'an kwalin ya zame gefe,k'yalli da bak'in gashin su ka k'awata zuciyarsa,a hankali ya dawo da ganin sa ga hannayenta ya na k'arewa kunshin kallo,kai komai ma na Su'ada abun birgewa ne ga kowane d'a namiji.cikin ransa ya ji ya na sha'awar sa ta a jikinsa Ya kai hannu da niyar tab'ata tai motsi,da sauri ya janye hannunsa ya koma ya kwanta,don ya san dalilin wannan canjawar ta ta to duk tsoron abunda zai iyq zuwa ya dawo ne,don haka insha Allah shi kuwa ba zai je gareta ba har sai ta samu nutsuwa a gidan. Kiran Sallar asuba ne ya farkar da shi,da addu'a ya farka,a hankali ya mik'e zuwa falo don d'auro alwala,sai da zai fita masallaci sannan ya tashe ta ya wuce. Bayan ya dawo a masallaci ya taddata kan sallaya,tana lazimi,bai tanka ta ba ya wuce gado bayan ya cire jallabiyar da ke jikin sa. Ya kai mintina goma a kwance yaji muryar ta tana cewa "Barka da asuba." Ta shi yai ya zauna bakin gadon yana y'ar fara'a yace "Amarya kin tashi lafiya?. Kanta a k'asa tace " lafiya k'alau Alhamdulillah. " "Masha Allah, ya kan naki ya daina cuwan." Bata amsa ba sai gyad'a kai da tai. Shiru na d'an lokaci ya biyo baya,sannan yace "Ki zo ki kwanta mana ko baccin ya k'are." Tashi tai ta nad'e sallayar ta wuce can gefe ta kwanta. Dukkan su kowa da abunda ya ke rayawa cikin ransa,shi kam Ibrahim mamakin Kansu ya ke bai zaton zasu riski Kansu cikin d'ari d'ari da juna haka ba,la'akari da soyayyar da su ke gwadawa juna,ya na wannan tunanin bacci me k'arfi ta yi gaba da shi. Su'ada kam baccin bai k'ara d'aukar ta ba ta gaji da sak'awa da kwancewa ta mik'e a hankali don karta tashe shi tai falo. Kitchen ta shiga kai tsaye tana k'arewa ko ina kallo,ledojin da ta samu ta bubbud'e, kayan Tea ne a cikin ta farko, ta biyun kuma kaji ne gasassau sai manyan lemukan jarka da fresh milk, k'aramar ledar kuma kayan amfanin gida ne, su man wanke baki, sabulun wanka,omo da dai sauran su,d'aukan lemukan tai ta zo falo ta sasu a firji sannan, sannan sauran kayan kowanne ta sashi inda ya dace,kajin kuwa warming d'insu tai,sannan ta tafasa ruwan zafi ta sa cikin flask d'in tea, Komai tsaf ta shirya a tsakiyar falon ta gyara ko Ina, lokacin ta duba ogogo k'arfe bakawai,ba ta shiga d'aki ba kawai ta shige toilet tai wanka,har tazo ta shirya cikin atamfa d'inkin riga da siket sun amsheta sosai,ta d'auko mayafi mahad'in kayan ta ajiye gefen gado.ta na tsaye gaban madubi ta na fesa turare ya farka,bayanta ya bi da kallo tsawon lokacin da take bakin mudubin,ta juyo da niyar fita a d'akin su ka had'a ido,da sauri ta kauda kanta gefe ta na k'ok'arin d'aukan mayafinta ta yafa,k'afa ya sa ya danne mayafin, ganin haka ya sa ta d'auke hannun ta da sauri ta fice falo,d'an mirmishi yai ya mik'e yana salati, bin bayan ta yai zuwa falon amma sai ya ga ta shige toilet, zama yai kan kujera ya na jiran ta fito,can ta fito kanta a k'asa tace mai "Ga ruwan wanka na had'a." "To sannu Allah ya saka da alkairi." Bata ce komai shima bai k'ara magana ba ya wuce toilet d'in. Da sauri ta shiga d'aki ta gyara gadon ta share shi,sannan ta sa turare ko ina, ta na shirin fita a d'akin shi kuma ya sako kai su kai kicib'us,da sauri tai baya ta na fad'in "Sannu don Allah, ban lura ba ." Mirmishi mai sauti ya saki ya na matsowa gareta,ja da baya ta fara ta na d'ora hannayenta a saman fuskarta don d'an towel ni kawai a jikin sa, sai da ta Kai ga bango ta tsaya shi kam yai mata k'awanya ya sa duk hannayensa ya tokare ta yanda ba za ta iya samun wajan fita ba. Duk jikinta rawa ya ke zuciyarta na bugawa,a hankali ya fara magana " Su'ada wai tsoron na mene ne duk kin takura kamar ba tare ki ke da Khaleeleenki ba? don Allah ki saki jikin ki kinji,ba abunda zan miki fa." Yanda ya ke maganar cikin cool voice ga shi ya matseta sosai kuma cikin kunnanta ya ke aje numfashi duk sai tsigan jikinta ta fara tashi. Cikin tsoro da shagwab'a ta fara magana "To ni dai don Allah ka matsa kuma ka sa kayanka." "Hhhhhmmm wai tun kafin me afkuwar ta afku ki ke jin kunya haka?" Yarfe hannu ta farayi idanuwanta a runtse ta ce"Wayyo ka bari don Allah, ban hanya in wuce falo na jira ka." A hankali ya saki dariya ya na matsawa ya ce "To wuce na matsa." Da sauri ta fice zuwa falo,wata ajiyar zuciya ta sauke bayan ta zauna kan kujera. Ta na zaune wajan mintina ashirin ya fito sanye da wani lafiyayyan yadi me laushi, fari k'al ne me layi layi sannan shara shara ne ana hango farar singlet d'in da ke ciki,ba hula a kansa sai gashin sa da ya gyara, daman ga gyaran fuskar da ya sha na angonci hakan ya k'ara fito da kyan sumar ta sa. Kallo d'aya tai mai tai k'asa da idonta,k'arasowa ya yi gabanta ya tsugunna tare da rik'o hannayenta biyuYace " Amarya na gama shiryawa,d'ago ki gani nai kyau?" A sace ta kalleshi sannan ta gyad'a mai kai alamar ya yi kyau. "Ok me ki ka girka na ga flask?" "Ruwan Tea ne kawai sai wancan naman da na d'umama." "Sannu da aiki kin yi k'ok'ari, raso mu ci to." A kunyace dai ta daure su ka karya, sannan ya taya ta su ka wanke cups da plate d'in da su ka b'ata. Lokacin k'arfe tara ta yi, yace mata zai fita ya gaida Baba da sauran mutan gidan,mak'alewa tai za ta je,ba ja yace ta sa mayafi su je. A tsakar gida ya sami su Zakiyya da sauran y'an biki da basu tafi ba su na ta aikin had'a abun karyawa.kowa ca ya yo kan Amarya da gaisheta,ita kam kunya ta lullub'eta sai tadabarbarce,ganin haka ya sa yace su k'arasa wajan Babah.a d'akin sa ya na zaune ya na jin Radio su kai sallama shi a gaba ita a baya ,cikin dattako ya amsa gaisuwar da Su'ada ke mai, sannan ya amsawa Ibrahim,nan ya k'ara musu nasiha sosai kan hak'uri da juna,sun jima a d'akin duk jikin su ya mutu. bayan sun fito d'akin Sakeena su ka shiga,Su'ada ta gaisa da jama'ar d'akin da bata san su waye ba,nan ma ta dad'e zaune don shi fita yai ya barta. Zakiyya ce ta kawo mata k'osai da kunun tsamiyar da su kai na karyawa, ita dai ba ta ce ta k'oshi ba kuma ba ta ci ba,har Khaleelee ya k'ara shigowa ya samu duk an fita an barta wai ta karya, dariya yai ya na kallonta ya ce"To ke ki sha kunun mana ki ka sashi a gaba." A hankali tace mai "Allah na k'oshi kuma kunya na ke ji nace ba zanci ba." "To taso mu koma wajanmu sai nace musu a can zamu ci ko." D'aukan abincin yai ta biyo bayan shi, a tsakar gida yace wa su Zakiyya wai kunya ta ke ji zata ci a can. ****** Janta yai ta yi da hira don ta saki jikinta, a hankali ya jawota jikinsa ta na k'ok'arin matsawa ya k'i bata dama,a hankali ya kai hannunsa wuyan rigarta yace "Ban San ya a kai d'inkin nan ya miki yawa ba,zan ragesu in kin cire don ban san ki na yawo cikin d'inki." Nok'e kafad'a tai da fad'in "um um karka rage,ramar da nai ce ta sa haka." "Oh da jikin ba haka ya ke ba ashe,ni ramar fuskar kawai na gani ai,ashe jikin ma ya rame,to wai me ya sa ki ramar ne ." K'ok'ari ta ke dole sai ta tashi a jikin sa shi kuma ya k'i yarda,kamar za tai kuka tace "Don Allah ka barni,ni bacci na ke ji fa." Y'ar dariya yai ya na k'ara gyara mata kwanciya a k'irjinsa yace" ki yi baccin ki a nan,nan shine makwancin ki." Shiru tai ba ta k'ara ko k'wak'k'waran motsi ba,ta lumshe ido a ranta ta ke tunanin, yau ita ce kwance jikin Khaleelee matsayin matarsa, Allah abun godiya ne,don haka ba zata gaji da gode mai ba,da ya mallaka mata muradinta abun alfaharita ba. Ga Khaleelee shi ma wannan tunanin ya ke, yana ta hamdala cikin ransa. ********** K'arfe d'aya na rana y'an uwan Su'ada su ka zo da gara nik'i nik'i. Kayan abunci masha Allah, shinkafa manyan buhu biyu,ta tuwo babba d'aya,taliya kwali uku macaroni uku indomi uku ga buhun semo biyu,manyan jarkar man k'uli da manja,ga magi kwali biyu, sauran kayan yaji su duk cikin robobi,dangi su citta,kanumfari,yaji,kub'ewa kuka,kanwa da dai sauran su, b'angare guda kuwa kayan alkali da dubulan da su nakiya su cin cin ne ciki manyan Mazubi. Sai da aka fitarwa dangin miji kayan ciye ciyen na su tsaf,sannan a ka warewa Baba na shi daban. Wannan gara ta k'arawa Su'ada k'ima a idon y'an uwan mijinta balle shi ma uban gayyara don aka mishi gata matuk'a, a Wannan zamanin duk namijin da a ka had'awa wannan gara ai an mai gata. Sai yamma y'an uwan Su'ada su ka tafi, zuwa lokacin duk sauran y'an su Ibrahim na da ke gidan su ka tafi,ya rage sai ya su ya su. Ibrahim na shigowa gidan ya ji tsit, k'ofar d'akin Sakeena ya tsaya ya na magana "Maman Abba bak'i sun tafi sun barmu mu kad'ai ko?". A wani ya mutse ta amsa mai " Wlh kam kowa ya koma inda ya fito." Bai damu da yanayin da ta amsa bai ba ya d'ora "To Allah ya saka da alkairi, ai ansha hidima sannunku da fama da jama'a." Gidan ya bi da kallo ko ina ba kintsi,ya gyad'a kai kawai ya wuce b'angaransa. Su'ada ba ta k'ok'arin had'a girkin dare,kitchen d'in ya lek'a ya na mata sannu da aiki,ta amsa itama ta na mai sannu da shigowa. D'aki ya wuce ya cire kayan jikinsa ya sa wando 3 quarter da riga k'arama. Fitowa yai tsakar gidan Sakeena ya kira Abba ya na tara mai ruwa a famfo ya zage ya wanke gidan tsaf har band'aki sannan ya wuce k'ofar gida ya share tas. Ya na shigowa ciki ya wuce toilet yai wanka tare da d'auro alwalar sallar magriba. Ita kam Khadeejah bayan ta gama girkin ta tsaka wanka cikin wata doguwar riga y'ar saudiya me duwatsu ta yafa mayafin rigar, Sai bayan magriba ya shigo gidan,a nan su ka ci abunci dare,bayan sun gama ya had'a musu kayan kallo, a nan ma janta yai ta yi da hira ba laifi ta sake sosai yanzu har tai ta bashi labarin biki. *TAKU CE* *Y'AR MUTAN JA'OJI*🙋 [2/23, 11:54 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ __*Sadaukarwa ce gareku Y'an Zamani Writers Association, y'an uwa abokan aiki.* *Nasmat Muhd Ark'illa* *Amah Alh.Kabir* *Zainab Shazee* *Zeesa* *Fatima Zara Eyman* *Meenauwal* *Hafsah Usman waziri* *Hafsah I Umar* *Aysha xeryeesher* *Princess Deejah* *Bilkisu M33RAH* *Umaima Muneer* *Baby Fara* *Haseena Baby* *Deebersh* *Bilkisu Abdallah* *Na gaisheku kyauta wlh*👌😂 *page 19-20* Kwanan Su'ada uku a gidan amma Ibrahim ya sa mata ido,so ya ke duk fargabar da ke tare da ita ta kau, a cikin y'an kwanakin ta sake da shi,za su ci abinci tare ba tare da tai nok'e nok'e ba,har zai sa ta a jikinsa ma ba ta ture shi ba,da wannan damar yau yai amfani,su na kwance a gado bayan sun yi shirin bacci ya kunna game a wayarsa yace mata su yi tare,ai kuwa kasancewar wayar na hannunsa ya sa ta shiga jikinsa sosai su na game d'in, lokacin da hankakinta ya koma duk ga game d'in shi kuma a lokacin idanuwansa su ka koma ga k'irjinta da rigarta ta yo k'asa ta ba su damar bayyana. duk jikinsa ya mutu,tunaninsa ya fara nisa,ya ji ya d'okantu da kasancewa da ita,a hankali ya janyo ta jikinsa ya na karb'e wayar da ga hannunta ya kashe,tirjewa ta fara yi cikin y'ar shagwab'a ta ke cewa "Ni dai Allah ban yarda ba,ni dai ka bani in ci gaba,don ka ga zan cinyeka shi ne ka k'wace ko." Rik'e hannayenta duka biyu ya yi da ta ke k'ok'arin k'wace wayar a hannunsa,ta fara birburwa a jikinsa ta na goga kanta a k'irjinsa,cikin dashashshiyar murya yace "Su'ada ki na yin barna fa wannan abun da ki ke yi." Hannayenta da ta samu ya cika ta shiga cusawa a bayansa za ta d'auko wayar,a hankali ya sa duka hannayensa ya rungumota jikinsa tare da shanshanar kanta zuwa wuyanta. da fari tai luf ba tai zaton abunda zai ba, sai da taji hannunsa ya fara kewaye sassan jikinta ya na son isar da sak'onsa ko ina,anan ta birkice ta fara son ceton kanta amma ya k'i bata wannan damar.Ibrahim ya na cikin maza y'an soyayya da su ka san yanda a ke shigar da so cikin jiki da zuciyar wanda a ke so,don haka yai amfani da hikimarsa sosai wajan kashe jikinta da sa mata wani feelings, da ga nan ya ida nufinsa. Kuka magiya ba kalar da Su'ada ba tai ba amma yai nisa bai jin kira.sai bayan ya cimma manufarsa sannan ya shiga rarrashin ta,ita kam Su'ada a lokacin ko hannunta ba ta jin zata iya d'agawa,ji take tamkar an sauyata ko ba ita bace,hawaye kuwa ya k'i daina zarya a fuskarta. A hankali ya sa hannunsa a kanta ya na magana "Su'ada Allah ya yi miki albarka, Allah ya sa haske da walwala cikin rayuwarki sama da Wanda ki ka sani a halin yau,kin gama shayar dani duk wani dad'i da namiji ke samu a wajan mace,kin biyani komai Su'ada, yanzu ke ki ke bina bashi,ke ki ke bina bashin kyautatawa,ke kam ko iya nan ki ka tsaya kin biya.Allah ya sa kiji dad'in rayuwarki ta yanzu da ta nan gaba. Haka yai ta mata kalamai masu dad'i ya na shafa kanta da bubbuga bayanta a haka har bacci yai gaba da ita. Shi kam tashi yai ya je ya tsarkake kansa tare da d'auro alwala,sallolin nafila yai ta jerowa don nuna godiyar sa ga Allah, sannan yai taiwa Su'ada addu'a ya na rok'a mata gafarar ubangiji.sai da bacci ya kama idonsa sosai sannan ya shafa ya tashi, ya na son tashin Su'ada ta je tai tsarki don ba kyau kwanciya da najasa a jiki,kuma ya na tausayin ta,don da gani baccin wahala ta ke yi,lalura ta sa ya rabu da ita,ya kwanta,bai dad'e ba bacci ya yi gaba da shi. Wajan k'arfe uku da rabi Su'ada ta farka, juyin farko ta tuno da halin da ta ke ciki,a hankali ta bud'e idonta,rashin wadatar haske a d'akin ya sa ta jima bata mik'e ba,can bayan y'an mintuna ta mik'e ta na laluben hanyar falo,hasken glof d'in tsakar gidan da ya ke shigowa falon ya bata damar kai kanta toilet,bokiti ta d'auko ta dawo kitchen ta juye ruwan zafin da ke cikin tea flask,a daddafe ta ka koma toilet d'in ta gasa jikinta sosai da sosai,duk da azabar da ta ke ji ta zage ta gyara kanta don ta san ba ta da wata hanyar da ta fi wannan. Bata koma d'akin ba sai ta shiga other room d'in ta kwanta, ba jimawa wani baccin yai gaba da ita. Sun so makara yau,don sai wajan shida Ibrahim ya farka,da sauri ya mik'e ya yo falo,kai tsaye ya wuce toilet ya d'auro alwala, sai da ya fito ya ke tunanin ina Su'ada ta shiga Kuma, labulen d'aya d'akin ya d'aga ya hangota kwance kan gado,bai shiga ba ya wuce da sassarfa ya tada salla,bayan ya idar ya shiga d'akin don tashin ta. Cikin bacci ta ji ana shafa mata gashi,ga iska ana busa mata saman ido,a hankali ta bud'e idanuwanta karaf sai cikin na shi,da azama ta maida ta rufe,d'an mirmishi ya yi ya na d'agota da ga kwancen yace "tashi ki yi salla shida har ta wuce." Kamar ba ta jiba,ko motsi ma tak'i yi,bai k'ara magana ba ya d'agata zuwa toilet d'in, bayan ya direta yace " bari na kawo miki ruwan zafi,da sauri ya koma kitchen d'in ya d'auko ruwan zafi ya kawo mata. Yana zaune kan kujera ya na jiran fitowarta ta fito d'aure da towel,ganin sa zaune ya sa ta juya da sauri harda y'ar k'ararta,da sauri ya tashi ya isa gareta,ita kam runtse idanuwa tai ta na yarfe hannu tace " Don Allah ka ban hanya in je d'aki, ka daina kallona don Allah. " Matsawa baya yai yace "Je ki maza ki sa kaya ki yi salla to." A tsantsame ta wuce shi, bai bita ba ya zauna falon don ya bata damar shiryawa,kusan mintina goma sha biyar ya tashi ya shiga d'akin, samun ta yai jingine jikin gado idonta a lumshe alamar tunani take,a sannu ya je gabanta ya zauna tare da rik'e hannunta d'aya, da sauri ta runtse idanuwanta,don ba ta fatan abunda zai sa idanuwansu su sark'e da na juna. Cikin zolaya yace "Amarya kin sha k'amshi, kin tashi lafiya?" Shiru ba amsa,ganin haka ya sa ya shiga tsokanar ta,ai kuwa ta rasa ya za tai kawai ta saki kuka. Tun ya na d'auka wasa ya ga kukan ya k'i tsaiwa, sai ma k'ara shashshek'a ta ke,a hankali ya janyota jikinsa ya shiga biting bayanta,tare da mata kalamai "Haba Su'ada sirka tsananin farin cikin da nake ciki da b'acin rai,kukanki ba abunda ya ke sawa zuciyata face k'unci,in biki daina ba nima zan yi kukan fa." K'asa k'asa ta fara rage k'arfin kukan,ci gaba yai da mata kalmomi masu sanyi,da ga nan kukan ya d'auke duka, yana share mata hawaye ya ke tambayarta "Me yasa min Matata kuka,ko cinnaka ne ya cije ta take kukan nan haka?" Turo baki tai har lokacin dai idonta a rufe,tace "Ba kai ne ba,kai ta min abu Ina baka hak'uri amma ko kulani ma ba kai ba." Cikin salon da tai maganar shima ya yi, "To ni ai banji ma lokacin da ki ke ta ban hak'urin ba,hankali na fa duk bai tare da ni." Shiru tai tak'i tanka mai, ya d'ora "yanzu dai ki yi hak'uri kinji,ba zan k'ara ba,dad'in da na sha jiya ya ishe ni da ga nan har ji bi sai in k'ara." "Wayyo Mamana,Allah ka bari ban so,ni ba abunda za ka k'ara,ka daina min wannan maganar ma ni." Cikin dariya yace "Wannan maganar ta zama dole fa,waye yace miki ana manta dad'i, ai duk wanda ya sha dad'i to kullum cikin zancensa yake." Ture shi ta fara yi ta na bubbugun sa cikin kukan shagwab'a. Shi kam dariya ta ci k'arfinsa ya kyaleta ta gama borinta ta kwanta k'irjinsa luf,ganin haka ya sa ya gyara mata kwanciyar yana shafa bayanta kamar y'ar baby,a haka wani baccin ya yi gaba da ita. Sai da tai nisa a baccin ya jawo filo ya d'ora kanta,sannan ya tashi ya shiga gyara gidan. To fa! Ibrahim ba'a iya girki ba,ga ranar d'ora tukunya ta zo,ya na son ya dafa mata abu me nauyi kafin ta tashi kuma bai iya ba,takaici ya kamashi cikin ransa ya ke raya ya zama dole ya koyi girki ko don Su'ada, ai dole wata rana buk'atar hakan ta taso,gashi ma tun kan ai nisa an fara. Ganin zaman ba zai mai ba ya sa ya shiga kitchen d'in, kallon komai ya ke,can dai yai dabarar tafasa ruwa tunda ya ga yanda ta ke kunna gas d'in, flask biyu d'in ya cika su da ruwa don ya san za tai amfani da shi in ta tashi. Sai bayan takwas ta farka,lokacin ya na wajan Babah,da dingishi ta k'arasa kitchen don d'ora ruwa,tana tab'a flask d'in ta ji a kwai, k'ara gasa jikinta tai sosai,eh kam ta ji dad'in jikin sai dai tafiyar ta ta ce kana gani ka san hhhmmmm. Zama tai tai kwalliya me sauk'i cikin material riga da siket marasa nauyi, kasancewar zafi ake a gari. Har ta kammala shiryawa ta shiga kitchen bai shigo ba,ba ta jin k'arfi sam a tare da ita,amma haka ta daure ta ke gudanar da aikin ta a nutse, chiefs tai, ta soya bred da kwai,ta na jejjera kayan a falo ya shigo,ta na jin bud'e k'ofar sa ta saurin komawa kitchen d'in, kai tsaye can ya nufa,ta juya baya tana jera cup's a cikin plate, a hankali ya k'araso daf da ita ya sa hannu ya k'arfi cups d'in, ya na mata magana cikin kunne,"Aiki ki kai Su'ada, ba ki jin dad'i fa,da kin hak'ura na samo mana wani abu munci." Muryar ta can k'asa tace "Ba komai,ai ba wani me wahla nai ba." Rik'o hannunta yai su na fitowa a kitchen d'in,bayan sun zauna kan kujera yace"Sannu kinji,yau kam nai dana sanin da ban iya girki ba,amma da ga yau in za kiyi girki k'afata kafarki." D'an mirmishi tai kanta a k'asa, don har yanzun ta k'i yarda su had'a ido. Shi ya had'a mata tea d'in yace zai bata a baki,tace ita dai a'a zata sha da kanta. A haka a kayi break d'in, ita idonta na k'asa,shi idonsa na kanta. Duk taji ta takura,don ko ba ta d'ago ba tasan kallon ta yake,ta na mik'ewa yai saurin rik'o ta da fad'in "Ina zaki je?" "Zan je kitchen na yi wanke wanke ne." Mik'ewa yai zuwa kan kujera da ita a jikinsa, k'ok'ari yake dole sai sun had'a ido,yace "Wai yau rowar idon nan ake min ne? Tun safe an hanani arba da k'wayar idon,kallonta na saukar min da walwala, don Allah Su'ada ki kalleni kinji." Ji tai wata kunya ta k'ara dabaibayeta,ta rasa inda za ta cusa kanta,sai kauda kai take. Hannu ya sa ya d'ago fuskar ta ta ya na kallon yanda ta lumshe ido eyelashes d'in ta suka kwanta gwanin sha'awa, a hankali ya kai bakinsa kan lips d'in ta ya na gogawa cikin wani salo,yarrrrr taji tsikan jikinta ta tashi,shi kam daban so ya ke ya karya lagonta,don haka yai ta bin wasu hanyoyi yana aika mata zafafan kisses, tun tana janyewa har ta fara bashi hadin kai,don yanda ya ke sarrafa bakinta cikin nashi dole bazata iya jurewa ba. Tsawon lokaci ya d'auka wajan ladaftar da jikinta, ai kuwa tai tik'is jikin ya mutu,sai idanuwan da suka k'ara lumshewa,a hankali ya zare bakinsa cikin nata,yai k'ok'arin had'a wasu kalmomi don ya kunna kanshi shi ma d'in, "Su'ada! wato aure ni'ima ne,dukkan abunda ke cikinsa ni'ima ce ta ubangijinmu gare mu,bayan aure ba abunda zai halasta min wannan yanayin me dad'i,duka kwanakin nan ina jina wani sabon mutum,na rasa gane wace duniya na ke,musamman musamman jiya,hhhmmmm jiya ko . . ." Da sauri ta sa hannunta ta rufe mai baki ,wani kiss ya sakarwa tafin hannun,tai saurin janyewa don shock d'in da taji ya harbeta. D'an mirmishi yai yace "Su'ada bud'e ido ki kalleni din Allah." Cikin cool voice tace"Bazan iya ba fa." " Me yasa ba zaki iya ba" "Kunya na ke ji wlh." "Kunyar me?komai fa ya riga ya faru,ai batun kunya tsakaninmu ya k'are, tun ranar d'aurin aure ki ka tsiri wata jin kunyata, duk wannan tsumamman kallon an daina aiko min shi,kuma na san dalilin to tunda an kauda dalilin ba sai a barni haka ba in kalli sarauniyar kyau da ga cikin ido har k'asa." Kanta na kwance a k'irjin sa tace" To duk kallon da kai bai isheka ba,ka kalli duk abunda ka so ai jiya." Dariya sosai maganar ta bashi,yace "A'a ni jiya ban kalli komai ba,aikin gabana kawai nai,amma yanzu zan kalla in more da ga sama har k'asa." K'ok'arin fara zuge mata zif ya ke,tai saurin rik'o hannayensa, shi kam dariyar da ke cinsa ya ke k'ok'arin dannewa,ya na k'ara janye mata rigar, Ba ta san lokacin da ta bud'e idon ba da sauri ta na mai magiyar ya bari ya bari,a lokacin k'wayar idon nasu ta sark'e, wani shagalallan kallo su ka shiga aikawa juna,dukkan su idanuwan su tamkar masu jin bacci haka ya koma,sai da su ka kalli juna su ka more sannan ta maida idon ta k'ara wani lumshe su,cikin jin wani mayen feelings ya bi saman idon nata da lafiyayyen kiss,a hankali tai ajiyar zuciya, mik'ar da ita tsaye yace su je kitchen su yi wanke wanken. Komai tare su kai har girki ya na tsaye ya kafa ya tsare a dole sai ya koyi girkin,duk nauyin da take ji sai da ya bi hanyar da ta saki jiki su ta daina kakkauda kai. A ranar wanka ma dagewa ya yi sai da su kai tare,karon farko da yace su yi a taran,don ca yai komai ya riga ya kau a tsakanin su,batun kunya babu ita tunda an k'etare boda🙈 *Ta kuce* *Y'ar mutan Ja'oji*🙋 [2/23, 11:55 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _*page*_*21-22* Yau satin Su'ada guda gidan Ibrahim,zuwa lokacin wata shak'uwa da tsantsar k'auna ce ta lullub'e rayuwar su,ko yaushe su na manne da juna,kulawar da su ke bawa juna dole ta birgeka, don ko motsi d'aya ya yi to a kan idon d'ayan ne. Kullum da safe Su'ada in ta gama aikin ta za fito su gaisa da maman Abba,sannan ta je d'akin Baba ta gaida shi,to wani sa'in ta kan tsaya su d'an yi hira sama sama,ta koma wajanta,musamma da ke ko yaushe da rana cikin yin bak'i ta ke da dare kuma ta na tare da Oga. B'angaran abinci kullum in ta dafa na rana za ta kaiwa Baba, sannan da dare ma za ta kai mishi,haka na Jabir ta sa mai kwano a wajanta duk da ya na sa kwano a a tukunyar Sakeena.haka ma yaran Sakeena duk wanda ya shigo cikin au hud'un za ta zuba mai ya ci ya k'oshi. Yau da rana Su'ada tai girki tare da had'a lemon kwakwa, ta d'auko sabon food flask d'in ta da ta warewa Baba shi,ta zuba mai jalof d'in shinkafa da waken da tai,sannan ta d'auko wani juck ta zuba mishi lemon, a tire ta jera ta d'auka don kai mai. Ya na bacci ma sallamar ta ta tashe shi,bayan ta ajiye abincin ta ke mai barka da rana ,ha amsa cikin fara'a sosai, "Sannu Sa'adatu, sannu da k'ok'ari, ya bak'unta? Ko dake yanzu kin zama y'ar gida ko." Kanta a k'asa ta na d'an mirmishi,ya fara bud'e abincin, k'amshin kad'ai ne ya cika hancin Baba amma ya ji wani nishad'i ya saukar mai,duk da shekarun da su kaiwa Baba yawa amma harshen sa na son d'and'ano,da ke da an yi arzik'i komai ci ake kamar a banza,to sa karayar arzik'in ta zo sai tazo dai dai da rashin me d'aki, wannan yasa komai ta cakud'e,abinci sai Wanda suruka ta dafa ta bashi, ba shi da ikon fad'in kalar abincin da ya ke so,ba wai don BA za'a mishi ba,a'a kawai yakana kawaici irin na iyayen da,ba su son takura suruki ko kad'an. Ganin zai fara cin abincin ya sa Su'ada tashi ta fita. A tsakar gida ta sami Sakeena ta na ta fama da gwawayi yak'i kamawa gaba d'aya, ga shi lokacin tafiyar yaran makarantar Islamiyya ya kusa,sai k'orafi su ke yi.zama tai kan kujera y'ar tsugunne ta na fad'in, " Maman Abba wannan gawayin anya ba ruwa ne ya tab'a shi ba?. Cikin b'acin rai da gajiya tace "Su'ada wane ruwa,yaushe ma damunar ta zauna kawai dai mara cin ne,tun ranar da aka kawo buhun gawayin nan nace wa Abbansu ba mai kyau bane,nace ya maida amma taurin kai ya sa ya kafe da fad'in me kyau ne,yanzu kinga tun sha d'aya na ke fama na kunna ya mutu na kunna ya mutu gashi har d'aya ta yi." Cikin mamakin kalmar da Sakeena ta fad'awa mijinta wai tsabar taurin kai,ta jinjina kai da fad'in " Ba mamaki ruwan ne ya tab'a, tunda kinga da ga kudu a ke kawowa kuma su tuni ruwa yai nisa mu ne dai ruwan bai zauna ba, to ki kunna risho ki hak'ura da gawayin." "Wane risho Su'ada, ai tun tuni yaran nan su ka mirjemin shi ya lalace." Karaf Abba yace" To Umma ki d'ebo wancan sauran icen da a kai amfani da shi da biki ki kunna mana." Zaro ido tai tace "Wa? so kake yau a silleni kenan,ka na ganin da bikin ana girki Ibrahim na k'orafin hayak'i na b'ata gida,tun tuni ka san ya tsani yaga an hura ice a gidan nan,balle yanzu da ya sa kud'in sa yai wa gidan fenti." Haushi da mamaki su ka k'ara cika Su'ada, wato ita dai Sakeena ba ta iya tauna magana, kawai duk abunda ya zo bakinta fad'in shi take yi,cikin basarwa tace " To ai lalura ne,za'a zauna ba'ai girki bane,tunda gawayin ya k'i kamawa kuma akwai icen ki kunna mana." Tashi Sakeena tai da ga durk'ushen hura gawayin ta na fad'in "To k'ila tunda kinsa baki ba zai k'orafi ba,bari na hura icen." Su'ada kam binta tai da ido kawai,tun zuwanta gidan ta fahimci Sakeena a kwai raunin tsafta a tare da ita,don da ga zanin da take yawo dashi a tsakar gida ma kawai za ka gane k'azantarta,sannan ga ga yaranta ma,wani lokaci sai su Kai yamma ba wanka,su yi ta yawo cikin datti. Maganar Islam ce ta dawo da ita nazarin da ta tafi, "Aunty ki bani abinci unwa ike ci." dariya ta baiwa Su'ada yanda take maganar,cikin tsokanar ta tace "Ni ba zan baki abincina ba,y'an makaranta zan zubawa su ci kar su makara." Kuka ta tsanyare da shi,ai kuwa yaran su ka sa dariya Su'ada ma tai d'an mirmishi tana mik'ewa tsaye ta rik'e hannunta "zo muje in baki to karki tara mana jama'a." Kulan da ta cikawa Jabir ta juye musu a wani babban plate ta k'walawa Abba kira, ya zo ya d'aukar musu. Taliya ta dorawa Jabir don ta san yanzu zai shigo gidan shima,abinka da aikin gas nan da nan ta dahu,ta na tacewa ta jiyo muryar Ibrahim a tsakar gida. D'an lumshe ido tai ta na fad'in "My Khaleelee." Ya na shigowa ta na fitowa a kitchen d'in,tsayawa yai harde da hannayensa a bakin k'ofa,ita ma ta hard'e hannu ta tsaya k'ofar kitchen, sun Kai y'an mintuna su na kallon juna a haka,da ga bisani ya tako a hankali gareta,bud'e hannayenta tai ta fad'a jikinsa,bayan ya yi hugging d'in ta na d'an lokaci ya cikata yana fad'in " Na gaji da yawa yau fa." Cikin sanyin murya da kissa tace " Me ya faru ?" "Na sha wahala a gurin gyaran keken nan fa." D'an marairaice murya tai tana shafo sajensa zuwa gemunsa tace "Eyya sannu my Choice, zo muje in had'a ma ruwan wanka ." Rik'o Hannayenta yai ya na kashe ido yace "Ba wanka kad'ai na ke buk'ata ba fa." "To da me kake buk'ata ?" Rank'afowa ya yi yana mata magana cikin kunne,y'ar k'ara ta saki ta na janyewa baya tace "A'a ni dai bari a gama da wannan d'in." Kai tsaye ta wuce kitchen ta d'auko mai ruwa me sanyi da cup's, Bayan ya sha ya koma ya kwanta kan kujera,ita kuma ta shiga toilet ta had'a mai ruwan wanka, sannan ta fito da towel, mik'a mai hannu tai ya tashi zaune,ta tsugunna ta na balle mai botir d'in gaban rigar,shi kam idonsa na kanta,duk motsinta ta cikin idonsa. Bayan ta taimaka mai ya cire kayan duka ya d'aura towel d'in, rigima irin tasa ya dage sai dai tazo ta taya shi wankan.k'wayar idonsa ta ke kalla cikin wani salon so tace "Rigima ko?" D'an b'ata fuska yai da marairaicewa yace "Ni ba rigima ba,ai kin san na gaji da yawa,ba zan iya wanke bayana ba,ba inda ma zan k'ara fita sai gobe." Y'ar dariya tai tace "Da wa yake wanke ma bayan in ka gaji." Haka na ke barinsa,amma yanzu ai da a kwai me wankewa ,kuma ma ai nata ne,tafi kowa amfana dashi yanzun." Da sauri ta juya ta na fad'in "To bance amin tonon silili ba ni,zo muje na tayaka amma fa ni ba zan yi ba." Gyad'a mata kai ya ke cikin mirmishi su ka shige toilet d'in. Rashin wayo irin na Su'ada ya hillaceta itama sai da yai mata wankan. Bayan sun gama k'ailulansu su ka shirya,ita kam k'aramar riga ta sa mara hannu,tsayinta iya gwiwa,shara shara ce,sabida zafin da ake,shi kam ko riga bai sa ba wando kawai three quarter ya sa. Su na zaune su na cin abincin ta jiyo muryar Jabir ya na wa Islam wasa, mik'ewa tai zuwa kitchen ta d'auko flask din abincin da ta zuba mai,ajiyewa tai gaban Khaleelee tace "Don Allah ko zaka mik'awa Jabir, ka ga Maman Abba ba ta dad'e da d'ora girki ba,abincin sa ma na bawa su Abba au kaci zasu tafi islame,shi taliya na k'ara dafa mai." Hankakinsa ba ga abincin sa yace " Sa Hijab d'inki ki je ki kai mai." D'aki ta koma ta d'aura zani sannan ta saka katon hijab ta fito,binta yai da kallo harta fita a falon. A tsakar gida ta same shi ya na cin sauran abincin da ta kaiwa Baba,cikin fara'a ya d'ago ya na fad'in "Aunty na barka da gida ." "Sannu da dawowa, ga abincin ka harka fara cin wani,amma wannan taliya ne fa." "Wallahi kinga yunwa na ke ji ,kuma Maman Abba bata k'arasa ba kawai na d'auko sauran na Babah,amma kawo taliyar ma duk zata shiga ai,kin san cikina na maza ne ba kalar na angonki ba." Ya k'arasa da tsokana, Dariya tai ta ajiye mai kulan ta na fad'in "Ba ruwana ai ya na jiyo ka." Sakeena ta saki wani tsaki tana fifita wuta. Juyowa tai ta kalleta har za tai magana taga ta wani d'aure fuska,don haka bata tanka ba ta juya ta koma wajanta. Bayan sallar Magriba Su'ada na kwance jikin Ibrahim ya kamo kunnanta yana magana k'asa k'asa " Ke ce kika bada damar a kunna ice a gidan nan ko?" Rik'e hannun da ya kama mata kunnan tai cikin kukan shagwab'a tace "Wayyo Allah, Abbana mamana,kun kawo ni za'a cire muku kunne na." Sosai maganar ta bashi dariya yace "Yanzu wannan kunnan ai nawa ne,ko na cire ni zan yi kuka, amma kin San me?" "Um um sai ka fad'a." "Ban san inga ana kunna ice a gidan nan tun asali,sabida matar gidan tana da rauni wajan gyarawa,in ta kunna ice sai ki ga duk gidan ya fita hayyacinsa, don haka ma shi kansa Yaya Muktar ya hana,sai gawayi ta ke amfani da shi,to d'azu da nazo naga ta kunna ice nace ga gawayi me yasa ta kunna ice ,shine tace wai ya k'i kamawa sai kika ce ta kunna icen kawai." Gyara kwanciya tai a jikinsa tans wasa da gashin da ke kwance a Hannayensa, Cikin sanyin murya tace " Ka kan wani abu ne? Gawayin da take amfani da shi bai ci,ya sha ruwa kuma lokaci na ta k'urewa ba ta d'ora girki ba,shi ne Abba ya ke ce mata ga sauran icen biki ta d'iba,to sai na ga ta nuna ko za kai fad'a ne ni kuma na ce mata me ne ai lalura ce don ta kunnna ice kamawa tai." Shafa kanta ya ke cikin wani salo ya fara magana " Su'ada wlh Maman Abba ba ta kulawa da gidan nan,sai ta Kai yamma ba tai wanke wanke ba,shara kuwa ba batunta,sai kwana biyu ake yi,sai dai in an b'ata waje a tattare iya gun,ga yara dole gida ya rink'a buk'atar gyara kullum,Wannan dalilin yasa na d'auke sharar gidan nan ta dawo kaina,kin ga band'akinmu ba d'aya ba amma haka nake wanke namu na wanke na su, wanke wanke ma don Baby ta kawo girma ne ake yinsa a kan kari,to kinga shekarar ta takwas yarinyar amma ita ke wanke wanke safe da yamma,wani lokaci da safe ina jinta ta ba kuka tana wanke wanke sabida ga makaranta ga aiki,wankan yara wahla ya ke mata,na sha kama yaran nan nai musu wanka,in naga su na yawo da datti,Maman Abba ta na da son kiji da k'iywa,ni kuma na tsani kazanta,duk rashin son maganata ba na shiru in naga k'azanta ,to in kin jini da ita k'azanta na gani,ban so ban so wlh." Juyi Su'ada tai a jikinsa Wanda ta san dole zai tsirga mai,da sauri ya Tsantsameta ya na fad'in "Kan kujera fa mu ke sai kin fad'o ko?" Mik'a ta k'ara yi sannan tace "To in na fad'o ai laifinka ne. Kasan me? Maman Abba mace ce,kuma duk mace ta na buk'atar uziri cikin rayuwar ta,maybe abubuwa ne su kai mata yawa,ga yara ga aikin gida,amma Yanzu tunda yaranta sun fara girma za ka ga komai ya dai daita,k'azanta ba ta dad'i ko kad'an amma wani ta zame mai jiki." Kiran Sallar isha'i ya sa su ka mik'e don yin salla. Bayan sun dawo daga masallaci ya shiga yiwa Babs sai da safe,zai mik'e yace ya zauna.bayan gyaran murya ya fara magana "Ibrahima daman batu ne kan abinci,ka ga tun zuwan matarka gidan nan ta samin kwano itama,ga ba wajan Sakeena, to abincin ya na min yawa,kuma duk wadda ban ci nata ba zata ji ba dad'i, kaga d'azu ban ci na Sakeena ba sabida na k'oshi a lokacin da ta kawo,nace yaran su cinye,to hakan bai mata dad'i ba har ta kaiwa mijinta k'orafi, d'azu da magriba ta ke min zancan, don haka shima na fad'a mai ko wacce ta rink'a kawo min abinci sau d'aya, wata da rana wata da dare,kaga hakan zai fi ko?" Jinjina kai ya yi da cewa "Hakan yayi Baba, amma ita Su'ada sai ta rink'a kawo ma na dare,sabida kaga tana koyarwa kuma da safe ne,yanzu ma hutu su ka bata,kafin ta dawo ta d'ora girki lokaci zai rink'a k'urewa,amma na daren ta na gida." Gyad'a kai Baba yai da fad'in "Hakan ya yi,Allah ta yai muku albarka ya hore muku abinda za ku kula da iyalenku." "Ameen Ameen Baba,Allah ya tashemu lafiya." Sai da dafe ya yi mai ya fito. Sai da su ka zo kwanciya ya kewa Su'ada maganar da su kai da Baba,ita kam mamaki ne ya cika ta,amma sai ta basar kawai tace "To ai ba damuwa,duk d'aya ne." ******** Da safe Baba ya na jiran abun karyawa har wajan goma Sakeena ba ta kawo mishi ba,ya saba tun wajan takwas take kawo mishi,tunda mijinta da wuri ya ke fita tare da yara ya saukesu a makaranta,to yau har yaran su ka fita shiru,har ya koma baccin safe ya tashi ba labari, bai ce komai ba ya shirya ya fita k'ofar gida, a nan ya samu yara masu wucewa da abun siyarwa ya sai kunun gyad'a ya sha. Su'ada kam daman ita na rana da dare ta ke bashi,to kuma yanzu ance sau d'aya, ba ta san Baba bai karya ba balle ta aiko mai. Ibrahim ya gama shirin sa zai tafi shago, ta rako shi kamar yanda ta saba,d'akin Baba su ka shiga don gaisheshi, sai su ka samu bai ciki,bakin soro ta rakoshi su kai sallama ya tafi. ganin Sakeena ba ta tsakar gida ya sa Su'ada tsayawa k'ofar d'aki tana gaisheta, a dak'ile ta amsa mata,Islam ta d'aga labule ta na mata surutu,ta tsaya ta na tsokanar yarinyar,ta rik'e hannunta su ka wuce wajanta, ba ta bi ta kan uwar ba. Tsawon kwana uku Su'ada ta ga Sakeena ta canja mata sosai,abun na bata mamaki,ita dai ta san ba abunda tai mata amma sai cin magani take. Ganin haka ya sa ta tsantsame jikinta,don duk kirkin Su'ada ba ta d'aukan wulakanci sam. B'angaran Baba kuwa kwana uku ya na fama da yunwar safe,ba wanda ya kula cikin yaransa,dalili Jabir daman da safe ya ke fita school,Yaya Muktar ma tun bayan sallar asuba in ya shiga su ka gaisa to sai yara sun yi shirin boko ya ke fitowa su tafi tare,to anan ma in ya shiga mai sallama ba dad'ewa ya ke ba,shima Ibrahim in su ka gaisa bayan dawowa daga sallar asuba to sai goma in zai fita ya ke k'ara shiga wajansa. Hak'uri kawaici irin na mutanan da ya sa cikin kwana ukun Baba bai magantu ba,sai dai kullum in hantsi ya d'aga ya fita k'ofar gida ya zauna,in masu kunu sun zo wucewa ya siya ya sha. Ganin da yai yunwa na neman mai illa ya sa yau yai magana,lokacin da Ibrahim ya zo mai Sallama zai fita ya tsaida shi. "Ibrahima in babu takura ka cewa me d'akinka ta sa kwanan safe da ni,ita Sakeena sai ta rink'a kawo min na rana kawai." "To Baba ba damuwa,na ranar ma don ka k'i ne wallahi." "A'a a yi hakan kawai,na safe da na daran ma Allah ya yi albarka ya bud'a muku." "Ameen Baba, Allah ya k'ara lafiya ya k'ara nisan kwana." Nan yai mai sallama ya tafi. ******* Da dare ya sanar da Su'ada ta rink'a girkin safe da Baba,ta amsa da to, ba ta k'ara cewa komai ba,cikin ranta ta ke nazarin al'umuran da ke faruwa,tabbas in haka zaman gidan zai rink'a tafiya ba zai dad'i ba. *Taku ce* *y'ar mutan Ja'oji*🙋 [2/24, 12:05 AM] LAYUZA KABIR: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _Allah ya k'ara maka lafiya my Grandfather, Allah ya tashi kafad'arka ya sauk'ak'a maka_🙏🙏🙏 _*page*_ *23-24* Washe gari kam Su'ada da wuri ta had'a abincin karyawa, kunun tsamiya ta dama kasancewar ta san Baba ya na sonshi,sannan ta d'an nik'a wakenta a blander tai mai lafiyayyiyar alala wadda ta ji kifi da k'wai, da yawa ta zuba mishi kunun a flask,sannan alalan ma ta zuba mishi da yawa. Bayan sun yi wanka kafin su zauna karyawa Ibrahim ya kai mishi. Sakeena na tsakar gida ta ga ya wuce da abinci ya kaiwa Babah,tsaki ta ja tana fad'i cikin ranta '' Aikin banza sabon sanabe,za a gaji a bari tunda mu ma muka saki'' Bai kula da yanayin fuskarta ba,gaidata kawai yai ya wuce. Ita kam zuciyarta fal k'unci taita k'ananun maganganunta. Tun daga ranar sai ya zamana ko yaushe da wuri Su'ada ke tashi tai abin karyawa sabida Babah,ko da su ba lokacin zasu karya ba. Sosai Babah ke sa mata albarka dare da rana,wanda hakan ke sa taji dad'i kuma yake k'ara mata karsashi wajan yi mai hidima. ************ Lokacin hutun da Su'ada ta d'auka na aure ya cika, don haka wannan satin tai shirin komawa bakin aikinta. Sassafe ranar Monday tai shirinta,bayan ta gama abincin karyawa Khaleelee ya kaiwa Baba nashi,ita kam a tsatstsaye ma ta sha ruwan tea. Kamar yanda ya tsara kullum shi zai rink'a kaita, don haka tare su ka fito,Ta tsaya k'ofar d'akin Sakeena ta gaisheta,sannan tai mata sallama. Bata san ina zata ba,ta dai amsa mata da "To sai kin dawo". D'akin Babah ta shiga su ka gaisa ta fad'a mai ta koma aiki,yai mata addu'a sosai,cikin jin dad'i take amsawa, fito su ka wuce. Har cikin makarantar ya sauketa,su kai sallama. Yini gudu yau a tsaye ta yi shi,duk ta jigata. Bata dawo gida ba sai k'arfe d'aya da rabi,a gajiya take,don d'an hutun da ta samu yau duk sai take jin kamar yau ta fara teaching d'in. Lokacin da ta shigo gidan Sakeena na sallar azahar,yaran duk basu dawo ba,Islam kad'ai na ta wasanta a tsakar gida,ta d'an tsokaneta ta wuce wajanta. Kai tsaye alwala ta d'aura tai salla, bayan ta idar ta shiga kitchen don samarwa Khaleeleenta abincin rana,Jalof d'in taliya ta mai Wanda yaji kifi bushashshe. Wajan k'arfe biyu da rabi ta shiga wanka, ta na fitowa ta kirashi a waya,ta sanar dashi ta gama girki fa kuma taji shiru bai dawo ba. Cikin jin dad'i ya sanar da ita yana nan shigowa gida. Sai uku ya shigo, lokacin har bacci ya fara d'aukanta, da mirmishinsa kamar ko yaushe ya zauna gefenta yana matsa mata k'afa yace " Madam sannu kinji,yau an taro gajiya ko?" Cikin fara'a take amsa mai bayan ta mik'e zaune "Wlh yau ko,hhhmmmm duk jikina ciwo yake kamar kamar me". Hannu ya sa ya fara mammatsa mata k'afafu,a hankali yake magana " Eyya sannu kinji Babyna,ni nai tunanin ma baza kiyi girkin ba shi ya sa ban dawo ba,sannu kinji bari a miki tausa sosai." Sosai ya mammatsa mata jikin,ai kuwa taji dad'in jikin,da k'arfinta ta mik'e tana had'a musu abincin. Bayan sun gama ci ya ke mata maganar in ta dawo ta daina wahalar girkin rana kawai ta rink'a yin girki d'aya in ta dawo su ci da rana su ci da dare. Ita kam tace A'a aiki ba zai shafi kula da ayyukanta na gida ba,kowanne zata bashi hakkinsa. Bayan sallar la'asar ya koma shagon d'inkin sa, nan ta sami damar fara had'a girkin dare. Tana cikin gyaran gyad'ar miya Sakeena ta shigo mata,faran faran su ke d'an hira,can Sakeena tace "Lafiya wai Su'ada naga yau kin fita da sassafe haka?" "Lafiya k'alau wallahi Maman Abba na koma aiki ne Yau." Da azama ta kalleta harshenta har yana had'uwa waje guda take fad'in "Wane irin aiki kuma?daman kina aiki ne?" Bata damu da yanayin ta ba take bata amsa" Eh ai ina koyarwa a makarantar secondary ta maza, to daman hutun aure na d'auka, yanzu kuma hutun ya k'are. " Wani dummmmm Sakeena taji gabanta ya fad'i, amma sai ta dake ta ci gaba da jero tambayoyinta wanda daman su su ka shigo da ita, "Ah kice malamar makaranta ce,amma baki tab'a fad'an ba kusan watanninki biyu a gidan nan,kinga kuwa Allah in nice ba zan k'i fad'a miki ba." D'an mirmishi Su'ada tai tace "Nima dai Allah ne bai kawo hirar ba amma da na sanar da ke,meye a ciki." Jinjina kai kawai Sakeena ke yi,can tace "Kice a wata kina fin me gidanma samun kud'i, tunda kin San shi fa d'inki sai sanda ya samu,wani sa'in sai kiga an yi wata guda ba'a sami d'inkin dubu goma ba,shi yasa da yawan mata ba su fiye son auran tela ba in dai da Sana'a d'aya kawai ya dogara,don wata rana za'a tashi abinda ma za'a ci ya gagara." Wani k'ululun bak'in ciki ne ya zo wuyan Su'ada ya tokare, bata son cin fuska a rayuwa,amma ta lura Sana'ar Sakeena kenan cin fuskar mutum a gabanshi,in ba ma wulakanci ba meye za ta rink'a kushe sana'ar mijinta a gabanta. Basarwa tai kamar maganar bata b'ata mata rai ba tace " La ai duk Sana'a ta gaji haka Maman Abba, maybe dai ke ce biki San da hakan ba,amma ko wace Sana'a a kwai lokacin da ta fi ci sosai,kuma shi d'inki da ki ke gani ai sirri ne,ba kowane tela ne yake zama ba d'inki a hannu ba,balle tela irin Khaleelee, shi da ya kama manyan mutane,kuma ya rik'e gaskiya da amana, ni fa ko da can ban tab'a zuwa shagon su Khaleelee na ga ba d'inki ba,sai dai wani sa'in za'a samu sauk'in yawan sa, kuma daman haka rayuwa take,yau bud'i gobe rashi,don haka nake mamakin matan da su ke sawa ransu su kullum sai sun ji su cikin wadata,ai kawai in an samu a rak'ashe in babu ayi hak'uri. Kuma kin san Allah Maman Abba? ni a duniya ba saurayin da ke birgeni kamar tela, ashe rabon tela zan aura,ni kam ina son tela na a haka a dad'i ba dad'i, shi nake so ba wani abu ba. " Gyad'a kai Sakeena tai tana fad'in "Ah lalle Su'ada ke yarinya ce,ko dake yanzu ai ki ka fara rayuwar auran,bari zama yai nisa y'a'ya su fara samuwa,a lokacin za ki gane maganar da nake fad'a miki, kina ganin Abbansu Abba, Sana'a nawa ya ke yi? Amma wani lokacin in abun ya had'e sai ki ga kamar mun zagi sama." Sosai maganar ta bawa Su'ada dariya, amma sai ta gintse tace "Mu dai addu'a za muyi taiwa Mazajanmu Allah ya hore musu ya bud'a musu k'ofofin samun su,Allah ya tsare su daga haram ya had'a su da halalinsu." Murgud'e baki gefe Sakeena tai da fad'in "Wa???ni zan rink'aiwa Miji addu'ar bud'i? Allah ya sitiri bukwi,to wlh duk randa kika damu wajan yiwa miji adduar ya sami kud'i,bud'i yazo, to randa duk bud'in yazo ke zaki fara hawaye, don da kishiya zai fara nuna miki bud'i yazo. Ke ni fa kullum addu'ata Allah ya rufawa mijina asiri yanda zai d'auke duk buk'atunmu da na yaranmu, amna wani sarari ko waye waye a dai yi sha'ani kawai." Tsantsar mamaki fal zuciyar Su'ada, ita kam bata tab'a ganin mace kalar Sakeena ba,komai nata kalar na jahilai take yi,in ba jahila ba wa zai ke fad'in wannan magana haka,tabbas bayan ta fad'a mata tayi makaranta kuma boarding school har tai candy Allah da tace ko hanyar aji Sakena bata tab'a bi ba,amma dai duk da haka wallahi ilimi yai gaddama. Kawai sai taji hirar ta gundureta gaba d'aya, don haka ta fara amsa mata da eh ko a'a,ta maida hankalinta ga girkinta, ganin haka yasa Sakeena tashi tace bari ta koma d'akinta. Bayan fitar ta,Su'ada tai ta bitar hirar tasu,ba abun d'auka duk cikin zancen Sakeena, tsantsar wauta da jahilci ne kawai.ganin bai da wani amfani tunanin zancan ya sa ta kauda zancan cikin ranta ta shiga hidimarta kawai. Bayan sallar magriba duk yaran Sakeena su na Falon Su'ada don an kawo wuta,kallo su ke,su na ta hayaniyarsu,ita kam tana cikin d'aki ta na kwalliya,k'ananan kaya ne jikinta wanda su kai masifar kamata,dogon bak'in wandon jeans da farar riga me adon bak'i da gwaldin a gaba,kayan sun masifar yi mata kyau,ta tufke gashinta cikin bak'in k'aton ribom wanda ya dace da shigar da tai,ta gama rikita jikinta da turaruka masu d'aukar hankali. Bak'ar doguwar riga after dress ta d'auko ta ajiye a gefen gado zata sa,don ba zata fita falo cikin yara haka ba da wannan shiga, tana tsaye gaban mirror ta na mak'ala barimar d'an kunne a kunnanta taji Islam ta tsanyara wani gigitaccen kuka wanda ya sa ta fita da sauri don ganin me ke faruwa ta manta ma da batun d'ora wani abu a kan kayan jikinta. Samun y'an uwan tai duk sun yo kan yarinyar,itama da sauri ta k'arasa ta d'agata daga fad'uwar da tai,rarrashinta ta shiga yi,don sosai take kuka sabida bakinta ya d'an fashe,toilet ta shiga da ita ta wanke mata bakin. Khaleelee ya shigo falon da Sallama,ganin yaran duk a tsaye duru duru ya sa yabi su da kallo,kafin ya tambaya Faruk yace "Uncle Islam ce ta fad'i ta fasa baki ta na band'aki Aunty na wanke mata jinin." Da sauri ya k'arasa shigowa yana fad'in "Subhanallah garin ya ta fad'i, kuna was an banza ko?" Bai saurari amsarsu ba ya sa kai toilet d'in, ta d'ago zata fito ya shigo, su ka had'e, da sauri tai baya ta na fad'in "Sannu da zuwa." Binta yai da kallo kafin ya kai idonsa ga Islam yace "Yawwa sannu, garin yaya Islam tasha k'asa harda fashe baki?" "Wlh ban sani ba,ina d'aki ina shiryawa naji kukanta." Bin jikinta yai da kallo ya kafe idonsa a k'irjinta don yanda rigar ta kamata sosai abun ba magana,ganin kallon da ya ke mata ya sa tai d'an mirmishi rana fad'in " A bamu hanya mu fita a toilet mana yallab'ai." Shima mirmishin ya yi tare da rik'o hannun Islam ya juya. A falo ya zaunar da ita kan cinyarsa ya na rarrashinta yace "Abba garin yaya ta fad'i ne kuna falon a zaune." Cikin in ina Abba yace "Wallahi Uncle ban sani ba,ni kallo ma nake kawai naji kukanta." Cikin salon rarrashi Khaleelee yace " Duk kuna zaune kun zubawa T.V ido kun barmin yarinya ta fad'i, duk wanda ya k'ara bari Islam ta fad'i sai na Zane shi." Duk amsawa su kai da to, Su'ada ta fito daga d'aki da Vaseline ta tsugunna ta na shafa mata a bakin. Ba wata gamsashshiyar Sallama Sakeena ta fad'o d'akin tana fad'in "Islam meya faru wannan kuka haka,ina salla tamkar na yanke nazo naga kukan me kike." A tare Su'ada da Khaleelee su ka d'ago ido,kafin ma su bata amsa yaran su ka ce "Umma fad'uwa tai ta fasa baki." Cikin rashin kalami tace "To garin yaya ta fad'i kamar ba manya a wajan." D'an mirmishi Su'ada tai tace "Ina d'aki,su kuma su na kallo,maybe zamewa tai ba su lura ba." Bata wani gamsu da amsar da ta bata ba ta mik'owa yarinyar hannu fuskar nan a tamke tace "Taso muje ." Ba musu Khaleelee ya sauketa a kan cinyarsa yana kallon sauran yaran ma yace "kuma Ku je Ku yi sallar isha." Bayan duk sun fice ya kamo Su'ada jikinsa yana magana k'asa k'asa "Wannan wankan fa yabi jiki Baby na,komai ya bayyana yanda zan more kallonsa." Tura kanta tai cikin k'irjinsa tana wani miskilin mirmishi, cikin muryar shagwab'a tace" Ni ba ruwana, ba wani abu daya bayyana fa." Shafa kanta ya yi cikin y'ar dariya yace " Ni naga abunda ya bayyana d'in ai,amma kin san me? ban son ki na fitowa gaban yaran nan da English wear's, sabida kayan sun kamaki sosai." "Wallahi harna d'auko after dress fa da zansa na fito falon naji kukan Islam shine na manta ma na fito a haka." Shafo gefen fuskarta ya yi yana cewa "Ok ba damuwa.amma fa kayan sun miki kyau sosai." Mirmishin jin dad'i tai,don a kullum burin Su'ada tai abu Khaleelee ya yaba to ta gama jin dad'i. " Bata k'ara cewa komai ba ta mik'e daga jikinsa tana fad'in "Taso ka watsa ruwa muci abinci." Hannunta ya kama ya mik'e tare da bin bayanta. ************ Sakeena tun da ta fita a gun nasu take ta mita, wai ana kallon yara baza'a kula dasu ba,don rashin sanin darajar haihuwa,ba komai ai a sannu mutum zai haihu ne zai san meye d'a da dad'in sa. Bayan ta gama wannan mitar kuma ta d'ora wai Su'ada ta na sa kayan da basu dace ba gaban yara zata b'ata mata tarbiyar y'ay'anta. Yaya Muktar na jinta yai mata banza, don sabbin d'abiun da Sakeena ta samo abun na b'ata ransa matuk'a. ************* Wajan k'arfe goma na dare su na kwance kan gado tai matashi da k'irjinsa, shi kuma yana wasa gashinta,a hankali tace "My choice!" "Um Zuciyata." K'ara shigewa jikinsa tai sosai tace "D'azu fa naga kamar Maman Abba tai fishi kam fad'uwar da Islam tai,kuma ka k'ara laifi bayan wanda nima nai,ka kori sauran yaran." D'an tsaki ya yi yana tab'e baki yace "Au ke abun ya dameki kenan,har kin kasa cireshi a ranki tun d'azu." Gyara kwanciya tai a jikin nasa tana magana cikin nutsuwa tace "Ba haka bane, ka gane My Choice, duk uwa bata k'aunar jin kukan d'anta,kuma kaga ita za tai tunanin ko ina falon yarinyar ta fad'i, sannan da tace Islam tazo su tafi bai kamata kace sauran ma su tashi ba,za tai tunanin wani abu a ranta." Cikin rashin damuwa yace "Rabu da ita,ina sane nace su je,kina ganin yanda tazo ta tsaya kan mutane ba wata gamsashshiyar sallama fa ta fad'o mana falo,kuma tazo tana ta wani ciccin magani,da gangan za'a bar yarinya ya fad'i ne,kuma ita fad'uwa in tazowa yaro ko a cinya yake ai zai fad'i har tana wani fad'in wai kamar ba babba a wajan,wallahi wannan abun da Sakeena na yi sam ta fara fice min a rai." Jin da tai muryarsa ta fara canjawa alamar fishi yasa ta shiga shafa k'irjinsa a hankali take fad'in "Kayi hak'uri kaji,wata rana sai labari, amma don Allah karka k'ara cewa yaran su fita daga wajan nan kaji." Gyad'a kai kawai yai yana juyar da ita,cikin tsokana yace "Kin daddaneni kin d'ora min nauyi,nima bari in rama gaskiya." Bubbuga k'afa ta farayi a gadon tana fad'in "A'a ban yarda ba,kullum cikin danneni ka ke,don na d'an d'ana shine zaka min wayo." Bai bari ta k'ara cewa komai ba yasa bakinsa cikin nata. 🤐 *Taku ce* *y'ar mutan Ja'oji*🙋 [2/24, 12:05 AM] LAYUZA KABIR: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _*Congrat Xeryisher, ina tayaki murnar kammala littafinki na KUCAKAR KISHIYA,Abunda ki kai dai dai Allah ya baki ladan,abunda ki ka kuskure Allah ya yafe miki*_🙏 _*page*_*25-26* Rayuwa taci gaba da garawa Su'ada a gidan Khaleelee, bayan matsalar matar wan miji (FACALA) Su'ada bata da wata damuwa,mijinta yana bata kulawa d'ari bisa d'ari, uban mijinta yana mu'amulantarta tamkar y'ar cikinsa,haka y'an uwan mijinta su ke zaune da ita lafiya lafiya,kowa Son barka,don haka mafi yawan lokaci in tasa damuwar halin Sakeena aranta kuma ta tuna alkairan sauran mazauna gidan sai ta gode Allah taji komai ya fice a ranta. Yanzu kuma wani sabon balli da Sakeena ta sako a gidan shine, wai dole Jabir ya koma d'akin Baba da kwana don tun bayan bikin su Su'ada tare su ke kwana da Abba a d'akin sa, to Jabeer baya shigowa gida da wuri sai sha d'aya, shi kuma Abba ga baccin wuri, ko yaushe sai dai ya kwanta a falo don Jabir baya barin key tun randa ya lalata mishi wayarsa da ya barta jikin charge yaje bacci yai danne danne ya lalata mishi,shi kuwa yace ya daina barin key d'insa,sai dai in ya shigo a tashe shi yaje ya kwanta, yanzu kam ta mirje idanuwanta tace sam bazai yuyu ba,d'aki dai cikin kason mijinta yake, don haka ita me 'Ya'ya hud'u an had'ata da d'aki biyu,sauran dakunanta biyu kuma uban miji da k'anin miji sun gaje, ga amarya ma da bata da kowa an shatar mata waje ita guda ko don ita an san y'ar masu dashi ce. Tun safe yau take mita,kasancewar week end ne,Su'ada na gida, tana ta y'an gyare gyaran ta, haka ma Jabir Yau ya tashi da wanki kuma yana ta kwalemar d'akinsa. Duk yarda maganar da take Jabeer yana jinta sarai amma sai ya kauda kai,uzirin da su kewa Sakeena ko yaushe shine, da can ba haka take musu ba,in ka d'auke k'azanta da rashin son gyara gida bata da wata matsala,amma tun auro Su'ada gaba d'aya ta firgice ta zama wata fitinanniya,ko hira ka fiye yi da Su'ada sai ta fara had'ema rai. Bayan ya gama wankinsa ya fito da kayan gadon ya ke ta gogesu,da sauran tarkacen d'akin, can ya jiyo muryarta tana magana. "Wallahi Allah cutar da ake min a gidannan ta isheni, gashi yanzu ina ji a radio wani malami yana fad'i cewa da yaro namiji ya tasa a raba shi da 'Ya'ya mata,to sabida ni bani da gata cikin gidan nan,yaro d'an shekara goma sha an barshi yana raba dare cikin mata,yo kullum yaro sai yayi barcin farko cikin mata sannan a tashe shi,kuma yanzu ga faruk ma ya fara girma shekara shida ai shima ya dace ace na cireshi a d'akin nan,ya dace ace Baby kad'ai ke kwana a falo ita da Islam amma da nai magana sai ace na fiye k'orafi da rashin son zaman lafiya,wallahi dole asan abun yi,tunda dai duk d'akunan nan sun zama mallakin ubansu,ya dace a barsu su wayata kuma,yo in banda ma lalura ace mutum ya zauna gida tun da k'uruciyarsa cikin garadan maza kuma har yanzu ba canji, tunda dai shima mutum an bashi matsugunni sai ya koma can da zama in an taki gaskiya fa." Iya k'uluwa Jabir ya gama k'uluwa, duk sanyi irin na y'an gidan shi kam babu shi ciki,don sam baida hak'uri don haka bai son shiga sabgar mutane. Yanzu d'in ma wani k'ululun bak'in ciki ne ya turnik'eshi,sam Sakeena bata gane dalilin da yasa yake mata kara,ta d'auka isarta ne ko wani abu,amma bari yau ya nuna mata shima d'an zamani ne. Fitowa tsakar gidan yai ya tsaya cikin b'acin rai ya ke fad'in "Ke malama wai me ki ke son cewa? Fad'i abunda ke bakinki kai tsaye ki daina kwana kwana hakan zai sa nafi saurin d'aukan haske." To daman me neman abokin tayi,nan da nan Sakeena ta shiga ruwan bala'i. "Kar kai min rashin kunya kaji ko,kuma duk maganar da nake ai kaji kuma kasan Inda ta dosa,don haka d'aki nake son a bani guda zan had'a 'ya'ya na maza a can,kuma ba zan yarda da wani cewa ku rink'a had'uwa tare ba,yaro yayi barci tun sallar isha'i sannan sai bayan shad'aya a tashe shi, don haka naje karshe,hak'urina ya k'are wallahi dole a san abun yi." Cikin fishi ya fara maida mata martani yace "Fad'a min cikin gidannan bulo nawa kika kawo da za'a gina?har kike ikirarin dole sai an baki d'aki kinsa 'yay'anki maza,to baza'a bayar ba k'arfinki ya k'watar miki, don tsabagen rashin mutunci har kina fad'ar wai sauran d'akunanku guda biyu uban miji da k'anin miji sun gaje, wallahi Allah Maman Abba ki gyara halinki sam wannan halin da kika samo ba d'abiar arzik'i bace,kuma ki shiga taitayinki kan yin duk furucin da ya fito a bakinki don wata rana zakiyi furucin da zai zame miki danasani." Bambami fa Sakeena tai tayi kamar ta ari baki,ganin abun yak'i k'arewa ya sa Su'ada fitowa daga b'angarenta,hak'uri take ta bata,sannan taiwa Jabeer magana kan yayi shiru haka nan.amma me sai abun yake neman komawa kanta,ganin haka yasa ta koma b'angarenta taci gaba da ayyukanta. Cikin ikon Allah sai ga Ibrahim, yana shigowa yaji yanda Jabeer ya ya ke caccakawa Sakeena magana,cikin tsawa yace "Kai Jabeer meye haka? baka da hankali ne? rufewa mutane baki dalla." Cikin bala'i da masifa Sakeena tace "A'a ka barshi dai ai d'aurin gindi ya samu,in ba rashin mutunci ba yaron da na raina a hannuna cikin gidan nan amma shine yake k'ok'arin zagina." Hak'uri Ibrahim ya fara bata yana fad'in "Meya faru ne haka? Me yai miki don Allah?" "Ka tambayeshi mana,ka tambayeshi wace rashin kunya yake min." Ibrahim ya juya ga Jabeer yana Tambayar sa meya had'a su. Bai rage komai ba,ya fad'a mai duk maganganun da tai mai da Wanda shima ya maida mata. Fad'a Ibrahim ya shiga mai yana fad'in "Kai zafin kanka har a cikin gida,Sa'arka ce,duk abunda tai maka bazaka iya kai k'ararta ba sai ka zauna kana cacar baki da ita.karka bari na k'ara jiyo muryarka wallahi." Daga haka ya juya ya shige b'angaransa.ita kuwa Sakeena an samu yanda ake so nan ta k'ara bud'e wuta da yara maganganu. Shi kam Jabeer kamar zuciyarsa zata fito haka yake ji,yanzu duk abunda Sakeena ta fad'a bai zama laifi ba sai nashi ne laifi,cikin fishi ya fice cikin gidan. Ibrahim kam yana shiga ya zauna falo dafe da kansa,Sam shi bai son hayaniya a rayuwarsa, matsalolin gidan nam sun fara mai yawa. Hannun Su'ada yaji a cikin nashi ta zauna jikinsa tana magana "My Choice sannu da zuwa,daina tagumi kaji don Allah." Ta janye mai hannayensa daya dafe Kai. Zuba mata ido yai ransa a b'ace yace " kina ji Suna rigima amma kika kasa kirana a waya ki sanar min." D'an lumshe ido tai tana k'ara matsa hannunsa e cikin nata tace "Me yasa zan kiraka kana wajan sana'arka na tashi hankalinka, na fita na bata hak'uri bata jiba don haka na barta, tun d'azu nake fatan Allah ya dawo da Baba ko Yaya Muktar d'in, sai kuma ga ka Allah ya kawoka,matsalar nan abun dubawa ce my Choice, wani sashin Maman Abba tana da gaskiya,kawai yanda zata kai kokenta ne bata iya ba,a k'aidar musulunci daman Abba da Faruk bai dace su na kwana cikin su Baby ba,in ba da wata babbar lalura ba,kawai rashin iya magana ne yasa ba za'a fahimceta ba." Lumshe idanuwansa yai yana d'an cizon lips d'in sa yace " Su'ada ba wannan dalilin ne yasa Sakeena take wannan borin ba,kishi ke damunta, tun lokacin da Baba yace ya bar mana gidan nan ni da yaya Muktar kuma ya kasafta ya bawa kowa rabonsa take bori,borin kuma taga duk d'akunan da take wadak'arta dasu sun shigo rabona,taga na ware sashi na na keb'ence shi,tun sannan taga gidan ya tsuke mata ta shiga masifar d'akuna biyu sun mata kad'an da y'ay'anta, wannan dalilin yasa nace Abba ya rink'a kwana tare da Jabeer tunda ni na bar d'akin, to bayan wannan me Sakeena ke nema kuma Su'ada? " Tsam tai da ranta tana nazari can tace "D'aki d'aya take so a k'ara mata." "To wane d'akin za'a bata? Na Baba ko na Jabeer?" Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace " Na Jabeer take hari,da akwai shago a k'ofar gida da ya koma ya bar Mata." Zamewa kawai yai ya kwanta bai k'ara magana ba. Ganin haka yasa Su'ada ta tashi ta ci gaba da ayyukanta. Jabeer kam yana k'ofar gida zaune shi kad'ai sai huci yake,a lokacin su Baba su ka dawo daga d'aurin Auran da su ka je, ganin Jabeer d'in dafe da kai fuska d'aure tamau yasa Baba saurin tambayar sa me ya faru. Cikin k'unar rai ya juyewa Baban komai har fad'an da Ibrahim yai ta mai kuma akan gaskiyarsa. Shiru Baba yayi na d'an lokaci sannan yace " Tashi muje ciki." D'akin Baban su ka shiga,bayan ya rage kayan jikinsa ya dubeshi da kyau yace "Jabeer! abunda kai Sam baka kyauta ba,shin ka manta Sakeena matsayin uwa take gareka,shekaru goma sha fa tana rainonka,sauyin halin da tai bashi zai sa kuma Ku sauya ba,duk rashin mutuncin mutum karka manta alkairin da ya tab'a yi maka, kishin matar k'anin miji (FACALA) ke cin Sakeena, kuma ba akanta aka fara ba,sai dai kuma shi kishin jahilci ne,ba wani dalili da zaisa kai kishin matar da baku had'a miji da ita ba,a da can mata sun maida kishin FACALA abun yi,har sai kaga wata macen bata kishin kishiyarta kamar yanda take na FACALA, amma a yanzu da ilimi ya wadata wayewa tai yawa duk an zubar da wannan abun,sai dai dai daikun mata ne irin Sakeena basu gane hakan ba,abunda nake jan hankalinka Kai tai mata uziri karka bari wannan halin yasa ta zama abokiyar fadanka,sannan kamar yanda kowa ya sani wannan gida a da can ne yake nawa,yanzu kuwa ya zama mallakin Ibrahima da Muktar don haka matansu nada iko dashi, ni da kai duk cin arzik'i muke na d'an lokaci, kwanaki kad'an su ka rage min a duniyar,yayin da kai kuma lokaci na zuwa kaima za kai auranka ka zauna a naka gidan, don haka yanzu kana ji ko,ka had'a kayanka tsaf ka dawo d'akin nan muyi zamanmu mu biyu,daman d'akin yamin girma ai,kaga ko cikin dare ka rink'a taimakona in ciwo ya tayar min." Tofa Baba ya gama kulle Jabeer, banda tsananin biyayyarsu da mahaifnsu ba abunda zai sa bai musawa Baba ba,amma ba yanda ya iya,haka ya amsa ya tashi ya fice. Ibrahim ya fito sallar azahar Baba yake sanar dashi shawarar daya yanke ta dawowar Jabeer d'akin sa,bai so amma bai nuna ba yacewa Baba Allah yasa hakan yafi alkairi, nan ya zage ya taimakawa Jabeer d'in su ka kwashe duk kayan su ka dawo dashi d'akin Baba, gefe duk ya jera kayansa,sai dai gado bazai samu waje ba duk da k'arami ne,Baba yace ba komai nashi ya ishesu su biyun ai,yace ya bar gadon a d'akin su Abban sai su rink'a kwana,habawa bak'in ciki kamar ya kashe Jabeer ya kasa dannewa har Baban ya gane ya sassauta murya da fad'in " Ashe ba zaka iya yiwa y'ay'an d'an uwanka hidima ba? Shin me Sunana da faruku da zasu rink'a kwana a d'akin akan gadonka shi kakewa bak'in ciki,ko ba ran Muktar Kai me rik'e mai y'ay'a ne don haka karka sa b'acin ran uwarsu a ranka har ya shafesu,kayi mu'amala dasu kamar y'ay'an cikinka kaji ko?" Gyad'a kai kawai yayi yaci gaba da jera kayansa,da yawan wasu abubuwan dole ya barsu a d'akin don ba wajan ajiyar su. 05/12/2019 *TAKU CE* *Y'AR MUTAN JA'OJI*🙋 [2/24, 12:05 AM] LAYUZA KABIR: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ *Sadaukarwar gareku D'alibai masu albarka* *'Daliban makarantar Intisharul Qur'anil Kareem* *Da 'Daliban Nusratul Aulad Islamiyya* *Allah yai muku albarka ya sawa iliminku albarka,ya sa musulunci yai alfahari da ku,Al'umma su amfana da ku*🙏🙏 *Kuna cikin raina ina sonku sosai duk da irin charger min k'wak'walwa da Ku ke*😕 _*page*_*27-28* Bayan sallar la'asar Baba ya tako har tsakar gidan ya samu Sakeena bakin murhu,cikin fara'a ya fara yiwa yaran wasa yana tsokanar su, daga nan ya kalleta ba wata damuwa tare dashi yace "Sakeena ki had'owa me sunana duk kayansa da Faruku ki dawo musu dashi wancan d'aki na Jabeer, shi ya koma dakina da zama har sanda Allah zai raba zaman, ga gado nan da yar durowar kaya nace ya bar musu asa musu kayansu ciki." Ya juya yana duban Abba yace "Sulaimanu daga yau wancan d'akin ne naku kaji ko?" Gyad'a kai Abba yayi kawai don yaji abun banbarakwai a kansa. Daga haka Baba ya koma d'akinsa. Tofa maimakon murna sai jikin Sakeena yai sanyi k'alau,sai ta fara tunanin Allah yasa dai ba wani abun aka fad'awa Baban ba,don ko bata d'akin za'ai bata hanyar Baba taso abun ya biyo ba,taso Muktar ne da kansa ya shiga maganar ya 'kwatar mata y'ancinta,ita yanzu ma bata san ya za tai dashi ba. Jikinta a mace har dare, lokacin dawowar yaya Muktar yai nan cikinta ya k'ara d'urar ruwa. Bayan ya gama cin abinci yai wanka ya fita sallar isha'i, anan Baba yace mai "muje dakina ina son magana da kai." Bai bud'e mai abunda ke faruwa ba kawai ca yai mai "Muktar sabida lalura da yanayin rayuwa nace Jabeer ya dawo d'akin nan mu rink'a kwana tare,kaga da yawa ciwo cikin dare Ke kamani,kuma na samu abokin d'ebe kewa ma. d'akin sa kuma nace ya barwa me sunana da Faruk su rink'a kwana a ciki." Tsam Yaya Muktar yai da ransa,ko ba'a fad'a mishi komai ba to yaji a jikinsa kamar a kwai wata a k'asa, don haka ya kalli Baba ya na tausasa murya yace "Baba Allah ya sa dai ba wani abu ne ya faru ba?" Cikin kauda zancen Baba yace "A'a ba abunda ya faru,je ka abunka." Kawai shi Yaya Muktar sai ya ji zuciyarsa ta kasa nutsuwa, don haka ya na barin d'akin Baba sai ya fito k'ofar gida,wayar Ibrahim ya kira yace don Allah ya fito waje ya sameshi za suyi magana. Shi kam Khaleelee har ya cire kayansa ma ya maida ya fito,a kan dakali ya samu yaya zaune,bayan ya zauna gefensa,Yaya Muktar ya zuba mishi ido na d'an lokaci, can yace "Ibrahim kaji hukuncin da Baba ya yanke kan Jabeer ya barwa su Abba d'akinsa ?" Gyad'a kai yai yana fad'in "Eh haka yace, wai ko don ciwonsa wani sa'in in ya tayar mai cikin dare ga mutum kusa dashi." Yanayin amsar da Ibrahim ya bawa shi Sam bata gamsar dashi ba,mik'ewa yai yana fad'in "Allah ya kyauta." Daga haka ya bashi hannu su kai musabaha yace "mu koma ciki Allah ya tashemu lafiya." Shi kam Ibrahim ba dan Baba ya kwab'eshi da kar ya sanar da Muktar fad'an da Sakeena tai da Jabeer akan d'akin ba tabbas da ya sanar dashi komai,amma ya san bai da wannan damar,haka ya koma wajan sa yana cire zancen a ransa. Yaya Muktar baiwa Sakeena maganar ba har sai da su ka zo bacci,har ta kwanta ya bubbuga k'afarta ta tashi zaune,zuba mata ido yai yana nazartarta don ya ga kamar a tsorace ta tashi.mutstsika ido ta fara yi ganin ya kafeta da ido, can dai da taga yak'i magana sai tai fuaka tace "Me ya faru wai?" Cikin d'aure fuska yace mata "Ke zan tambaya me ya faru? maza ke nake jira fad'a min me ya faru kan batun d'akin Jabeer da ki ka 'kwallafa rai a kansa,shin wane rashin albarka ki kai har d'akin ya zama mallakar y'ay'anki?" Cikin tsoro da kuma rashin kunya a sashi d'aya tace "Me kuwa ya faru,ni ba ruwana, Me d'akin ne ya min rashin kunya ni kuma na taka masa burki,na nuna masa ni ba Sa'arsa bace, to ni daga haka ban san me kuma ya faru ba." Eh lalle zarginsa ya zama gaskiya, nan fa Ya Muktar ya sata gaba da masifa in da yake shiga ba nan yake fita ba,yaci mutuncinta tas kuma ya ja mata kunne kan sanin me take yi don wata rana za tai abunda za tai danasani. To Sakeena dai baki ya mutu, sai muzuran k'arya take tana turo baki,shi kam ya juya mata baya ya kwanta. Tsawon kwanaki uku duk Sakeena ta rasa me ke mata dad'i, ga d'aki dai an bar mata yara suna kwana a ciki,to amma miji yak'i sakar mata fuska sam,ga Jabeer da kullum ya shigo gidan zai tai mata muzurai,don k'ala bata had'a shi da ita yanzu,abincinta ma ya bar ci,duk wani kayan ta da ya ke amfani dasu ya daina,a gabanta zai wuce wajan Su'ada yace "Auntyna don Allah ban aran abu kaza." To ita Sakeena hakan ne bata so,tab'a ana fifita Su'ada ko ana huld'a da ita. Ita kam Su'ada ba ruwanta,yanda ta saba mu'amala da ita haka take,sai tab'a ma kwana biyun ta canja duk wannan d'aukan kan ta ajiye komai a sanyaye take yinsa. ******** A lokacin kuma watan azumi ya fara tunkarowa,duk musulmi nata shirye shiryen tararsa. Ana jibi za'a d'au azimi Zakiyya k'anwarsu Khaleelee tazo gida gaida Baba,duk suna zaune a tsakar gida har Su'ada ana ta hira,a yanayin hirar rayuwa da su ke Su'ada ta fahimci Zakiyya mijinta bashi da k'arfi kuma su na buk'atar taimako a halin yanzu,don magini ne kuma harkar ta tsaya musu ba kasuwa.duk sai Su'ada taji jikinta ya mutu ta bata tausayi. bayan ta gama abincin rana ta kawo mata falon Sakeena tace "Zakiyya bari in d'an kwanta,ai sai yamma zaki tafi ko?" Amsa mata tai da "Eh sai bayan la'asar insha Allah." "OK yo bari na d'an huta ." Cikin dariya Zakiyya tace "To a huta da kyau Amaryarmu,ko har Babyn namu ya fara wahalar dake ne?" D'an zaro ido Su'ada tai da fad'in "Wa? rufa min asiri ni ba ruwana,bari kiga na gudu ma." Daga haka ta juya tana dariya. Sakeena da ke zaune ta tab'e baki fa fad'in " Tab' d'in,ke kinga alamar wani Baby anan? Ai y'ar boko ce ita,kinsan y'an boko basa haihuwa da wuri." Ita kam Zakiyya bayan ta kai lomar abincinta baki ta had'iye tace "Yo boko tana hana haihuwa ne sai dai in Allah bai kawo ba,kuma ni tsokanar ta ma nake,don naji tace zata huta ne,ai tana ma k'ok'ari koyarwa akwai wahla,don yau Friday ne ma ta samu ta dawo da wuri.gashi daga dawowarta har ta d'ora abinci ta gama dole ta bu'kaci hutawa." Cikin jin takaici Sakeena tace "To k'ok'arin me take? in kud'in yazo aljihun wa yake shiga? kuma da kike gani da safe abin karin kumullo kawai take musu ta shirya ta fice ko in ce ma ya kaita.sai bayan ya kaita ga dawo sannan yazo yai wanke wanke ya gyara gidan ya wanke sannan shima ya fita shago." Gane inda zancen ya dosa yasa Zakiyya k'ara 'k'ular da ita ta hanyar cewa "Ma'auratan gaskiya kenan,su rink'a taimakawa juna,wallahi Yaya Ibrahim ya birgeni. Kinga da baya tayata da wasu ayyukan ai da yanzu sai ta dawo kuma tayi ga girki duk ita kad'ai." Cikin 'kulewa da yanda Zakiyya ke so dole dai sai ta kare Su'ada, tace "Ba wani fa hutawa da za tai,wallahi shiryawa zata je tai ta tari miji ai yanzu zaki ganshi lokacin zuwa cin abincinsa yayi,ba ta so ne wani ya shigar mata yasa tace bacci za tai." Kafin Zakiyya ta kai ga bata amsa su ka jiyo ihun yaran Zakiyya na fad'in "Kawu Ibrahim Oyo yoo." Cikin fara'a ya fara d'aga k'ananan yana fad'in "Su Mamana da Babana da Humaira da Zainab da Salama duk ina musu oyo yooo." Dariya duk yaran su ka sa, Zainab tace "Kawu Ibrahim ba kaiwa Ummanmu ba fa." Labulen falon da ya jiyo muryar Zakiyya tana mishi sannu da zuwa ya d'aga,cikin fara'a sosai yace "To inaiwa Y'ar Uwata Ummansu Zainab Oyo yoo." Sosai yaran ke dariya da murnar ganin shi, don shi akwai wasa da yara da jansu a jiki, shi yasa su ka saba dashi sosai. Zakiyya ta gaidashi cikin fara'a itama,yana tambayarsa ya aiki ya iyali,duk ya amsa mata da Alhamdulillah. ya d'an dad'e wajansu sannan ya rik'e hannun Zainab da ta cikwikwiyeshi yace "Zee zee muje in baki abun dad'i." Da sauri sauran 'k'ananun biyu suma su ka rirrik'eshi,manyan kuwa Ummy da Ummu Salama su na gefe su na dariya. Shima dariyar ya ke ya sa hannu ya d'aga Islam yana fad'in "Ni duk kun hana ma Isy tazo wajena,kun kakkare mata Babanta ko." Islam ta d'aga kai cikin dariya da murna. Duk jansu yai wajansu. Zama yai kan Kujera suna baibaye dashi yace "Su'ada kawo min alawar nan na basu." Bayan ta kawo mai duk ya basu yana musu yana ta musu wasa.can yace "To kuje Ku barni na huta,anjima in na fito sai aje kantin Mahrazu a siyo wani abu." Da murnarsu su ka fice su na tsalle." Su'ada da ke tsaye hard'e da hannayenta tana kallonsa cikin sha'awar yanda yake wa yaran,tai mirmishi da fad'in "Sannu da zuwa Kawun yara." K'arasowa yai gareta yana kawota jikinsa yace "Um Sannu da gida Aunty Amarya in ji yara." Y'ar dariya tai tana shafo gefan fuskarsa tai k'asa da murya sosai tare da kashe ido tace "Ka yi kyau sosai fa,ban tab'a ganin namijin da manyan kaya kewa kyau irinka ba." Cikin farin ciki yace "Don kina ganin kyana ne kike ganin komai namin kyau,kince k'anan kaya namin kyau kince manya namin,kince Babbar riga tafi min kyau sama da komai, kinga alamun son kai yasa kike ganin hakan,wata ma haka take ganin mijinta,umm nama manta rannan ma haka kika ce, inna d'aura towel zan yi wanka kyau nake miki kamar ki had'iyeni." Y'ar k'ara tasa cikin wani salon k'issa ta kai hannu tana rufe mai baki tace "Ni dai yaushe nace haka? Ni fa ban fad'a ba,ba ruwana." Cikin dariya sosai ya rik'o hannayenta yana k'ara sata cikin jikinsa yace " To naji biki fad'i haka ba,wasa ne,amma rannan kin fad'i abunda yafi haka fa." Cikin wani jan hankali ta d'an ware idonta akan nasa tace "Yaushe m kuma me na fad'a?" K'asa sosai yai da muryarsa yana sa bakinsa a kunnanta yai mata rad'a. Ai kuwa ta cikwikwiyeshi tana d'an bugunsa a k'irji tace "Ni dai ban fad'i ba,gaskiya in ma na fad'a to ban cikin nutsuwata." Ta k'arasa maganar da dariya. Shima dariyar ya ke sosai yace "Eh daman a wannan lokaci ai ba batun wata nutsuwa tare da ke,ke don fa ina rufa miki asiri ne,amma wasu maganganun ma da kike ai bazasu fad'a ba." Ture shi tai a jikinta tana d'an mai hararan soyayya tace "A'a Allah kaine me surutai kai ta sambatu,wani sa'in ma sai na toshe ma baki,amma shine zaka mak'ala abun a kaina." Baya shima yai yana d'an d'age kafad'a alamar bai damu ba yace " To ni ko zaki kwana kina fad'in nai surutai nai sambatu sabida ke ai bazan damu don kuwa nasan ina yi,kuma kin kai kinma zarta ai kukan dad'i sabida ke." Juyawa tai zuwa d'aki tana dariya tace "Ni kam nai shiru yau naga duk da tsokana ka tashi, an jima ma had'e kawai." Bin bayanta yai zuwa d'akin yana k'ara tsokanarta da cewa " A'a yanzu zamu had'e yasin ba wani anjima." Ita kam bata k'ara biye mai ba ta taimaka mishi ya rage kayan jikinsa,sannan ta had'a musu abinci,bayan sun gama ci ta tattaro duk hankalinta gareshi ta fara magana "My Khaleelee, daman zanma magana ne kan Zakiyya, na fuskanci kamar suna cikin matsin rayuwa,a yanayin hirar da mukai d'azu,shine nace don Allah me zai hana mu had'a Mata kayan abinci,kaga dai kayan abincin mu kullum kamar bama tab'awa kar ma su zo su lalace, gashi kuma y'ar uwarmu na buk'ata." Wani dad'i ne ya lullub'e Ibrahim, a ransa yake k'ara tabbatarwa lalle ya sami matar rufin asiri, ta sami mace ta gari abokiyar shiga aljanna,don duk macen da ke son y'an uwanka ai dole ka d'aga mata kafarka ta shige aljanna zuruf. Rik'o hannunta yai cikin mirmishi yace "Na gode angle, na gode yanda kike kula da lamuran y'an uwana, Allah ta saka miki da alkairi, kiyi duk yanda kika ga ya dace kinji,Allah yai miki albarka mace ta gari." Fara'a sosai a fuskarta ta amsa da "Ameen nima na gode da bani dama mijin wuce sa'a." A tare duk su kai dariya. Lokacin da zai koma shago ya bata dubu biyu yace ta bawa Zakiyya su yi kud'in mota. Da ya fito ya tsaya su kai sallama da Zakiyya,sannan ya bawa yaran d'ari biyu yace su je kanti su siyo biscuit. Su'ada kam ta sami buhu ta zubawa Zakiyya shinkafa kwano uku,tasa mata ta tuwo kwano biyu,Sannan taliya guda biyar macaroni guda biyar,cous cous ,ta auna mata man gyad'a da manja,su magi da dai duk abun buk'ata, sannan ta d'auko dubu uku ta d'ora kan dubu biyun da Khaleelee ya bayar a bata ta had'a su ka zama 5k. Bayan sallar la'asar Zakiyya ta lek'a zatai mata sallama,tace "Au daga bakin k'ofa ma? to bazan amsa sallamar ba gaskiya." K'arasawa ciki tai tana fad'in "To ai yamma tayi ne Amarya,kuma zamu je mu d'ora tuwon dare,ga masu d'orawar kafin na dawo to duk sun biyoni. Bayan ta zauna Su'ada ta jawo buhun da ta had'a duk kayan a ciki tare da kud'in ta bata tace inji Khaleelee. Murna ta cika ran Zakiyya tai ta godiya bakinta yak'i rufuwa. Su ummi ta k'walawa kira su ka zo su ka ja buhun,kud'in ko ta ninkesu a jaka. D'akin Baba taje ta nuna mai kayan da kud'in yai mirmishi cikin jin dad'i yace " Masha Allah, an godewa Ibrahima da matarsa,don tabbas na san wannan aikinta ne,Allah yai musu albarka gaba d'aya." Ta amsa da amin tana mai sallama. Sakeena har soro ta rakasu tana k'ara kallon buhun,don bata san meye a ciki ba,kuma Zakiyya bata ce mata komai ba,amma koma meye tasan kyauta aka bawa Zakiyya don yanda ta fito daga gun fuskarta fess cike da fara'a tasan samuwa tai. Don haka da tai mata rakiya soron tace "Zakiyya me aka samu ne haka?" Zakiyya tace "Wallahi kayan abinci ne da dubuta biyar,ai yau nayi farin zuwa gidan nan,ki tayani godiya wajan Amarya don Allah." Tab'e baki tai tana juyawa ciki tace "Ku gaida gida." A ranta tana fad'in 'kinibibi da neman gindin zama. Zakiyya kuwa tana zuwa gida ta kira Ibrahim a waya tana mai godiyar kayan abinci da dubu biyar d'in daya bata.cikin mamaki yace "Dubu biyar ko biyu?". Tace mai biyar Su'ada ta bata. Yace To Su'ada ce dai ta k'ara mata amma shi biyu ya bada. Godiya sosai tai mishi,sannan ta kira number Su'ada tai ta mata godiya itama. Bayan Ibrahim ya dawo gida da dare yake ma Su'ada maganar kud'in da ta bawa Zakiyya ta had'e rai tana d'an turo baki tace "To sai dai in so kake ka nunamin y'ar uwakka ce kai kad'ai banda." Godiya sosai yaita mata,yana k'ara sa mata albarka. *Taku ce* *'Yar Mutan Ja'oji*🙋 [2/23, 11:56 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _*Innalillahi wa'inna ilaihi ra'jiun.Ha'ki'ka dukkan me rai mamaci ne,Wannan aya ta tabbata a kan mahaifin malamina, ina rok'on Allah ya jik'ansa ya gafarta zunubansa ya kyautata makwancinsa,Allah yasa mutuwa hutu ce gareshi*🙏🙏🙏😢 _*page*_*29-30* A Sannu cikin aminci a ka fad'a cikin watan Ramadana, a lokacin kuma ayyuka sun gama shan kan Khaleelee, duk da yana k'ok'ari wajan ganin ya bawa Su'ada lokacinta don kar ya shiga hak'k'inta,hakan yasa ya tsara lokutansa na dawowa gida. K'arfe goma na safe zai fita,ba zai dawo ba sai gab da shan ruwa,to in yasha ruwa ya d'an huta, da an kira asham in yaje yai salla ya dawo gida zai yo,to duk lokacin nan nata ne,sai wajan sha d'aya na dare zai koma shago,ba zai dawo ba sai yayi sallar asuba. Sosai su ka tsara abubuwansu don kaucewa shiga shingen Allah, sabida Khaleelee ya saba mata matuk'ar ya na gida to ko yaushe tana jikinsa, shi kanshi ya saba bai so ya ganta nesa dashi,to da Allah ya taimakesu da rana duka yana shago,lokacin da zai dawo kuma kad'an ya rage asha ruwa,kafin yai wanka ya shirya an kira salla,sauran lokutan kuma duk nasu ne,anan suke more soyayyarsu su maida tsinkakken yawu.😝 Da asuba kuwa in ya dawo ya taro gajiya da bacci yana shigowa sai bacci, yana kwance ma take shiryawa ta tafi aiki. Wai wani aiki sai FACALA wai wannan dawowar ma da yake gida na dare sai da ya zama abun k'orafi a gun Sakeena, sabida rannan ya dawo su Baby sun shigo kallon (dad'in kowa) yace su je bacci zai yi ya kashe kayan kallon,to da su ka je su ka fad'a mata da safe tai ta yada magana. Su'ada na jinta tana fad'in "Mace me jarabar namiji dai bata wani lasting, ko yaushe miji manne da kai kamar fata, da azuminma ba za'a hak'ura ba Allah dai ya kyauta." Sosai Abun ya bawa Su'ada dariya tana ayyukanta tana dariya,don ita yanzu abun Sakeena ba kowanne ke damunta ba,duk da ma yanzu an d'an sami sauk'i tun da a Kai case d'in d'aki bata k'ara tado wata ba,sai dai habaici kam Su'ada na shanshi. Sati guda da d'aukar azumi Abban su Su'ada ya dawo,nan ya aiko mata da k'wai cikin wani dogon farin boket,Su'ada ta kira Abbanta tai ta mai godiya, da Khaleelee ma ya dawo ya gani ya kira waya yai godiya,bayan an sha ruwa Su'ada tai maganar "Khaleelee kaga nace kaga muna da k'wan da ka siyo daman,kuma yanzu ana zafi sosai tunda k'wan da yawa zai iya lalacewa kafin wani lokaci,nace me zai hana mu raba uku a bawa Maman Abba kaso d'aya a aikawa Zakiyya kaso d'aya?' Idanuwansa da ke lumshe ya bud'e a kanta yana mata kallon shiga rai,sannan a hankali yace " Duk yanda ki kai ya yi my world, komai kika tsara banda ja a kai don duk shawarar da ki ka kawo me kyauce,ki basun Allah yayi miki albarka ya baki babban rabo a duniya da lahira matar rufin asiri." Cikin farin ciki ta fara godiya "Nima na gode mijin wuce sa'a, ko yaushe 'karfafa min gwiwa ka ke akan duk abunda nazo da shi,ina jin dad'in hakan kuma ina alfahari da kai a kowane lokaci." Washe gari da safe Su'ada ta raba k'wan ta kawowa Sakeena, kadaran kadahan ta amsa tai godiya, sannan Su'ada tace "Don Allah Maman Abba zan aiki Abba gidan Zakiyya ya kai mata sa'ko in ba inda za ki aikeshi." "Ba inda zan aikeshi,sai dai kin San dake ya na azumi kuma da gani yana bashi wahla." Da sauri yaron yace "A'a Mama ni dai zance don Allah, ba wani wuya da azumin ke bani,kuma ai a napep zan je ko Aunty?" Gyad'a mai kai Su'ada tai da fad'in "Eh zan baka kud'in mota wanda za'a kaika har k'ofar gidan in ma jiranka zai ka kai ka fito Ku dawo duk zan bada." Bai k'ara bi ta kan uwar ba ya shiga cire kayan jikinsa don sauya wasu. Ita kam Su'ada komawa tai d'akin ta sami bokiti me murfi zuba k'wan a ciki,da kansa ya biyo ta d'aki ya amsa sak'on. *Manege plss*🥰 *Taku ce* *Yar mutan Jaoji*🙋 [2/23, 11:58 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _ALLAH KAI MANA MAGANIN DAMUWARMU_🙏🙏🙏 _*page*_*31-32* Haka aka ci gaba da gudanar da ibadar azumin Ramadan cikin falala ta ubangiji, lokacin da azumi ya raba Su'ada ta shirya zuwa gida yi musu barka da shan ruwa,tun safe ta tafi,sai bayan sallar Isha'i Khaleelee yaje ya d'auko ta,da abinci ta taho don ba girki Zata yi ba,ai kuwa suna zuwa gida yace "Su'ada zuba min abincin nan in ci,na kasa yin bud'e baki gamsashshe duk abunda nasa a bakin sai naji ba d'and'ano,kin gama saba min da girkinki Su'ada, ban jin dad'in wani abinci bayan naki." Cikin jin dad'in yabon da yake mata tai y'ar dariya tare da fad'in "To shi wannan d'in da za ka ci kasan wa ya dafa ne?" Shima mirmishi yai da fad'in "Koma ya dafa in dai daga gidanku yake to d'and'anon iri d'aya ne,in Mama ce tai to zaifi ma naki dad'i,tunda gunta ki ka koya,in kuma su Jidda ne su kai to d'and'anon zai zamo d'aya tunda duk gu guda kuka koya." Tana dariya ta zuba mai,Sannu ta dawo kusa dashi take bashi a baki,a hankali cikin kwantar da murya take mai hira "Khaleelee na,kasan me kuwa? Allah ko yau nima ban wani maida hankali wajan shan ruwa ba,sabida duk sai naji ni wani sakayau, na saba komai tare da kai,daurewa kawai nai fa,amma da kamar na kiraka nace kazo na kasa cin komai." Kanne ido d'aya yai yana d'age mata gira sannan ya ce "Eh da kin kirani,don a dai dai lokacin nima hakanne tare dani,duk da na san ke fa harda kewan wani abu ya hanaki sakewan." da sauri ta d'an zaro ido da fad'in "Kai, kewan me kake so kace?" Kauda kai yai cikin basarwa yace "Kewan wannan jikin mana,kin saba kina cin abinci ina miki abubuwa,kina mak'alemin a jiki kamar mage." Turo baki tai tace "A'a ni dai, abunda na san zan dawo na sameshi,kuma yanzuma ka jangwalo kaci gaba da ci da kanka ni kuma in kwanta anan." Ta fad'a tana zamewa a jikinsa. Ci gaba yai da cin abincinsa yana k'ara tsokanarta da wai daman haka take so,ita dai bata tanka shi ba tai lamo a jikinsa. Da k'yar Su'ada ta rok'i Khaleelee ya barta zuwa kasuwa a lokacin da salla ta rage sati guda,K'annanta taiwa siyayya duk da da taje gida ta tadda an gama sai musu komai to amma hakan ba zai hana ta kyautata musu ba,under wear's ta sai musu da kayan kwalliya,sannan ta siyawa k'aninta Khaleelee wasu takalmi masu kyau. 'Ya'yan Zakiyya kuwa da Baby ta sai musu y'an kunne da sark'a sa su Abun hannu,ta siya musu kayan kwalliya,sannan ta had'awa Baby harda jaka,sabida tana jin kullum yanda yarinyar ke nacin Sakeena ta siya Mata jaka duk 'kawayenta an sai musu,amma uwar tai mirsisi da rantsuwar ba zata siya ba,kuma fa badan bata da kud'in ba kawai siyan ne ba niyya kuma alhalin Ubansu ya bada kud'in ai musu siyayya.mutuniyarta Islam kuwa wata riga da wando masu kyau y'an kanti ta siya mata da kayan kitso dasu ribbons masu kyau kalar kayan. Itama taiwa kanta siyayyar duk abunda take da buk'ata, sannan ta tsaya wajan y'an girki ta had'a duk wani abu da tasan za ta buk'ata da sallar nan. Lokacin da ta dawo gida bata baiwa kowa abunsa ba,sai da dare data Nunawa mijinta sannan ta fito da na su Baby ta k'wala mata kira,da gudu yarinyar tazo da fad'in "Aunty gani." Mik'a mata kayan tai tace "Sark'a dasu dan kunne da jaka naki ne,sauran kuma duk na Islam ne." Ihun murna yarinyar tasa ta fita a guje ko damar godiya bata samu yi mata ba don murna. Lokacin yaya Muktar na nan ta shiga falo da kayan tana ihun murna,ajiyewa tai a gabansa tana d'aukar jakar tace "Abba kaga Aunty Amarya ce ta siyo min jaka,Wallahi Abba kaga daman kullum sai nacewa Mamanmu ta siya min sai tak'i,gashi Aunty ta siya min,kai wallahi naji dad'i na godewa Allah na godewa Aunty Amarya,Abba sauran kayan na Islam ne." Ganin yanda duk ta rud'e da murna yasa Abban nasu dariya yace "Kai gaskiya yau Aunty Amarya tasa Maman mamanta cikin farin ciki,To maza koma kice mata an gode don da ganin yanda kike a rude biki ma yi godiya ba." Juyawa tai da sauri sak'ale da jakarta ta koma taiwa Su'ada godiya. Islam ma tana murna da aka gwada mata kayan,yace kema je kicewa Aunty an gode. Bayan fitarta ya kalli Sakeena da take d'an yak'e kadaran kadahan yace "Sakeena je kicewa Su'ada nace na gode ." D'an tab'e baki tai tace "To godiyar me kaikuma za ka mata,ba ga yaran sun je sun yi ba,kuma nima in ta fito da safe zan mata." Tsayawa kawai yai yana kallonta da takaici yace "Yanzu mutum yai wa 'ya'anki wannan hidimar amma ki zauna sai da safe zaki gode mata,alhalin kuna gida guda,Tashi don Allah ni ki je ki mata godiya." Ba dan taso ba ta tashi ta fice. A turb'une tai sallama hakan ya sa ba suji Sosai ba,ita kuma bata k'ara ba ta sako kai falon a dai dai lokacin da Su'ada ta haye kan ruwan cikin Khaleelee tana k'ok'arin k'wace wayarta da ya d'auka wai zai shiga wani group d'in ta na WathApp da yaga an sa SIRRINMU MATA, sosai su ke kokawa da juna,dariya taci k'arfin Khaleelee wanda yasa take k'ok'arin cin galaba ta k'wace wayar. Sakeena da ke tsaye tana kallonsu wani k'ululun bak'in ciki ya turnik'eta,wato ma suna jinta su ka k'i amsawa,sabida su na wasan jakai😃🤭,juyawa tai ta bar falon,data koma tacewa Yaya Muktar ai tai mata godiyar. Da safe da Su'ada ta fito gaida Baba,ta tsaya su na gaisawa anan take mata godiya.Su'ada tace ai ba komai duk yiwa kai ne. Kiran number d'in Zakiyya tai tace ya turo Umma Salama ta amsa musu y'an kunnaye,Zakiyya tai ta godiya. A haka aka cinye watan Ramadan a kai salla cikin k'oshin lafiya,Su'ada ta taka rawar gani sosai,don tai abincin Salla wadatacce duk gidajan danginta dana dangin miji ta aiaika musu.mijinta ma ta fiddashi kunya wajan aboka,domin kuwa taron cin abincin salla a kai a shagon d'inkinsa,wanda Su'ada ta shirya musu abinci iri iri da lemuka. Daga gajiyar hidimar salla sai ciwo ya rafke Su'ada, ciwon kai yak'i sauka tsawon kwana uku,tun tana shan magani a gida har Khaleelee ya takura mata zuwa asibiti. Da kansa ya kaita asibitin,gwajin farko su ka tabbatar musu yaron ciki gareta na wata guda,tofa murna farin ciki nishad'i su su ka had'u su ka lullub'e rayuwar Khaleelee a lokaci guda,ya rasa ina zai sanya ransa,godiya yai tayi ga mahaliccinsa,ita kam Su'ada ciwon kai mara misali ya sakota gaba ko ido bata iya bud'ewa, ji take kamar kanta zai tsage,tana dafe da kannata ya kamata ta tashi, su ka fito zuwa bakin titi don daman a a dai daita su ka zo. Da farin cikinsa ya shiga gidan, tun da ga k'ofar d'akin Baba yake tambayarsu ya jikin nata, cikin fara'a sosai Khaleelee ya amsawa Baba da fad'in "Da sauk'i sosai Baba." Yanayin da Baba ya ga Khaleelee na farin ciki ko bai tambaya ba ya bashi amsar dalilin ciwon nata. Tun fa daga wannan ranar sai ciwo ya 'kara sako Su'ada gaba kamar an k'ara hankad'oshi, laulayi sosai ta keyi,amai,ciwon kai,zazzab'i, kwad'ayi ,tsirfa ci wannan k'in wannan, sai ya zamana ko 'kanshi ba ko wanne Su'ada ke so ba,dukka turarukanta taji ta tsanesu,sai na Khaleelee kawai ta ke so,babu abunda ya dami Khaleelee game da tsirfarta,duk abunda tace tana so shi zai mata,duk aikin gidan ya dawo kansa, kama daga girki, wanke wanke,shara da gyaran gado, dukka shi ya ke yi,ko wanka bai barinta tai da kanta, kulawa ta musamman ya ke bata,don tausayi ma take bashi sosai,yanda kullum jikinta bai rabo da zafin zazzab'i,in an samu ya sauka to rana ta take,a nan kuma ciwon kai zai tsananta tai ta tsiyayar hawaye. Ranar da Mamanta ta zo dubata taga wahalar da take sha ga aiki Khaleelee nata fama dashi,tace Jidda ta zauna ta rink'a musu aikin gida shima Ibrahim ya rink'a fita neman kud'insa, don baya samun zama a shago ko yaushe hankalinsa na gida in ya fitanma. To zuwan Jidda ya sa Khaleelee samun rangwamin aiki,don yanzu bai aikin komai sai na kula da ita in yana gida, yawon aman da take yi yasa likita ya rubuta musu drip yace a rink'a sa mata,to dake Jidda daman fanninta ne sai take d'aura mata drip d'in kullum d'aya ake k'ara mata,har zuwa lokacin da jikinta zai yi k'wari. Sakeena kam kullum zata shigo sau d'aya tai mata sannu sai kuma washe gari,don da tai bak'i take basu labarin irin laulayin da Su'ada ke yi take fad'a musu wai tsabagen iskanci da tsirfa ne,da nuna ita wata ce,d'aya cikin k'awayen nata tace "Haba Sakeena kamar biki tab'a haihuwa ba,ai ke mace ce kin san ciki kowa da kalar nasa,sannan ita na fari ne dole zai bata wahla." Tab'e baki Sakeena tai da fad'in "Ba wani fa,da iskanci ko da laulayin,kullum sai tace ga abunda zata ci kuma sai an dafa tak'i ko kallonsa sai ta canja wani abun,shi yasa take ban haushi, wai ita dole gata me ciki." Haka taita surutanta na son dole sai ta kushe Su'ada a gun duk wani da ya santa. To ga wata sabuwa,rana tsaka Su'ada ta tashi da fad'in wai bata son warin gass da an kunna sai tai ta 'ko'karin amai nan da nan kuwa za tai ta kwara shi,abunda duk aka samu taci sai ta fito dashi, Jidda ta d'ora girki haka ta sauke,sai ruwan zafi ta jona musu a kettle su ka sha Tea,da rana kam su ka rasa abunda zasu ci, dole Khaleelee yaje siyo musu abinci,sam Su'ada tak'i ci, tana kallon abincin ta kauda Kai,don ji tai har kanta ya fara juyawa.can tana ta kwance taji yo kamar 'kamshin girkin Sakeena, nan da nan taji shi take son ci,ta kalli Jidda cikin yanayin wahla da ciwo tace "Plss Jiddah ce Maman Abba don Allah ta zuba min girkin ta in ci." Ba musu Jidda ta sanar da Sakeena sa'kon Su'ada, ba dan taso ba ta amsa da to. Bayan ta gama girkin ta zubo mata a wani d'an kwano Wanda bai taka kara ya karya ba,ai kuwa Su'ada kamar ta kwana bata ci ba haka ta hau abincin nan da ci, kafin ta gama dashi,Jidda kallonta kawai cikin mamaki tace "Wai Aunty Su'ada dad'in wannan girkin kika ji haka? To in jalop d'in ki ke so a yi miki mana." Girgiza kai Su'ada tai tana fad'in "Wannan d'in tamin dad'i, da zan sami 'kari ma zan 'kara, girkin yai dad'i sosai." Shiru Jidda tai tana mamakin lamarin ciki irin haka,a ranta tace "Allah karka had'ani da wannan lalura ni kam ko da lokaci na ya zo." To da dare ma haka Su'ada tace Sakeena ta sa mata abincinta, Kai tsaye Sakeena tace ita tuwo tai, da Jidda ta fad'a mata tuwo ne tace koma meye ta bata. Nan ma ba wani me yawa ta zuba mata ba,hannu baka hannu 'kwarya Su'ada ta cinye ta na sud'e hannu.Khaleelee da mamaki shima ya ke kallonta,Jidda tace mai da rana ma haka tasa na amso mata ta cinye kamar ta samu nama. Y'ar dariya yai yace "Ai Alhamdulillah ma tunda an samu in taci bata aman, bari zansa m Maman Abban magana ta rink'a sa sanwa da ita tunda abuncinta kad'ai take so,mune dai ban san ya zamuyi ba Jidda,Kinga bata son warin gass kuma ba zamu zauna da yunwa ba,meye Shawara?" Shiru Jidda tai na d'an lokaci kafin tace "Yaya kawai ka siyo mana murhun gawayi,sai ka siyo mana gawayin mu rink'a amfani da shi." "A'a ko dai risho Jiddah,kin iya amfani da gawayi ne?" Cikin dariya tace "To ai ni risho d'in ne ban iya amfani dashi ba,sabida ban tab'a kunnawa ba,amma kaga a gida wani sa'in in aiki ya mana yawa ba waje a gass muna kunna kol d'in." Mik'ewa yai yana fad'in "OK bari na duba naga me gawayin bakin titin nan bai tashi ba." Daga haka ya fita. ********** Tsawon sati kullum Su'ada ba ta iya Kai komai bakinta sai girkin Sakeena, ya zama shi kad'ai take jin dad'in sa,safe dare rana.ita dai Jidda zata dafa musu su hud'u ita da Khaleelee da Baba. Tun Sakeena na yin Kara harta fara turb'unewa,wai a dole ita ta zama wata abar ana nema a wajanta. Wata ranar litinin Sakeena tak'i d'ora girki har k'arfe d'aya saura ,yara su ka dawo makaranta ba abinci ga Su'ada can ms nata jin yunwa,kawai sai tacewa yaran bata jin dad'i itama,ba zata iya wani shiga rana ta d'ora girki ba,kowa yasha gari da suga da gyad'a. " Haka yaran su ka jik'a garin su ka sha suna ta murna,don a marmarce suke shan abunsu,Baba kam tuni Jidda ta kai mishi abincin da ta girka,lallashin Su'ada tai tayi akan taci wanda ta girka,ganin yanda Jiddan ta damu ya sa tace ta d'ebo mata,ai kuwa lomarta uku ta fara amai,ita kam ba ta San dalilin da yass yanzu bata iya cin komai ba sai girkin Sakeena. Ganin yanda ta ke ta amai ga ba komai a cikin yasa Jidda kiran Khaleelee a waya ta shaida mai halin da ake ciki, ba jimawa ya shigo gidan, lokacin ta gama aman tana kwance kan cafet tana ta juyi,Ya d'agota jikinsa ya na tambayarta me take so ya siyo mata. Cikin muryar rashin lafiya tace "Shinkafa na ke so,amma ta maman Abba ga Jidda tace wai ba tai girki ba yau." cikin tausayawa ya ke shafa kanta,a hankali yace "Kiyi hak'uri ki canja wani abun na siyo miki yanzu yanzu." Girgiza kai tai idonta na cika da kwalla tace "Ban son komai wallahi, shinkafar kawai na ke so,kuma tunda babu zan jira in tai na dare sai naci." "A'a Su'ada ya zaki zauna ba abinci ko kad'an a cikinki,tun safe fa sauran gyad'ar nan kawai ki ka ci,kuma ki zauna har dare." Baccin da ya fara daukanta ya sa bata k'ara tankashi ba ta gyara kwanciya sosai a jikinsa. Shi kam gashinta kawai ya shiga shafawa yana matsa jikinta da hannu guda sabida taji dad'in yin baccin. Ai kuwa ta saki jiki tana sakin minshari alamar baccin yayi nisa. *TAKU CE* *'YAR MUTAN JA'OJI*🙋 [2/23, 11:58 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _*page*_ *33 34* Sai la'asar Khaleelee ya koma shago,ita kam Su'ada har lokacin bacci take,to sanin yawan baccin da take yanzu yasa basu damu ba. Wajan magriba ta farka,ai kuwa ta farka da mahaukaciyar yunwa,cikinta yai yamutsawa,har jikinta rawa ya ke,tace"Jidda yunwa nake ji sosai wallahi, ji nake kamar hanjina zai tsinke. " Dafa kai Jidda tai da fad'in "Yanzu ya zamuyi? Kuma naga Maman Abba yanzuma ko girkin bata d'ora ba." Su'ada ji tai wasu hawaye na zubo mata,dob ta gama sa rai a cin abincin gashi babu,daddafawa tai taje ta d'aura alwala tai salla daga zaune,ta idar tana addu'a Khaleelee ya shigo, Jidda ta mai sannu da zuwa, ya amsa cikin fara'a sannan yace "Yanzu ta tashi ko ta dad'e?" "A'a bata dad'e ba,yanzu ma ta gama batun yunwa take ji ." To je ki amso mata wajan Maman Abban mana, Jidda tace "To ai batai fa girkin ba." Da sauri yace "Yanzun ma? Innalillahi, to me yasa ba tai ba?" Gyad'a kai Jidda tai da fad'in "Wai tace bata jin dad'i." Cikin damuwa ya dafe kai,can ya fita zuwa gun Sakeena a bak'in k'ofar d'akin ya tsaya yana sallama. Yaya Muktar ya amsa mai yana d'age labulan yace "Ibrahim ya dai?" Cikin damuwa Khaleelee yace "Daman Maman Abba zan tambaya ko da abinci agunta ta bawa Su'ada, wlh tun safe bata ci komai ba,da rana batai girkinba shine tace in tai na dare taci,to yanzu ta farka daga bacci yunwa take ji sosai wallahi." Shafa kai yaya Muktar yai yace "jeka ina zuwa,amma dai ka samar mata wani abu kafin abincin ya sauka, kaga ba'a son barin me juna biyu da yunwa irin haka." D'aga kai Khaleelee yai alamar to,ya koma wajansu da sauri. Yaya Muktar kuwa bayan ya zauna bakin gado ya zubawa Sakeena ido,wadda take ta cika tana batsewa,ita a lallai karya samu fuskar mata fad'a, shima had'e rai ya yi da kallon tsakar idonta yace"Sakeena wai me kika d'au rayuwa ne? Me yasa kika canja dukkan d'abiun ki, da dai ba haka kike ba,amma yanzu duk abunda akace min kinyi Wallahi ba zanyi musu ba, yanzu Sakeena meye dalilinki na 'kin yin girki da rana gashi da daran ma bikiyi ba." Turo baki tai cikin had'e gira tace "Nifa na gaji da ciyar da 'katuwa,Wallahi ba zai yuyu sabida samun waje tace kullum sai girkina zata ci,ko kai da kake mijina baka cin abincina sau uku a rana,kullum sau biyu kake ci,to balle kuma FACALA, kullum ba fashi safe,dare,rana ai ko uwata ce sai haka,in banda kinibibi ai Jidda tana d'ora musu girkin amma tace wai bata cin nata sai nawa,to ban iyawa,bab d'auka wlh,na satin ma da nai Allah ya ban lada,don in har na sake har ta haihu nawa zata rink'. . . ." Bai bata damar K'arasawa ba ya d'aga mata hannu,"dakata Sakeena me kike son cewa? Matar d'an uwana kike cewa ba zaki rink'a bawa abincin dana siyo da kud'ina ba? kuma ma Sakeena ke ba mace bace,biki san lalurar ciki ba,a cikin Baby biki tsinci kanki a wannan halin ba,kin manta yanda kullum sai an k'arb'o miki abincin makota,kuma kullum basu gajiyawa da ke ba har tsawon wata tara, sai ke zaki gajiya da bawa matar d'an uwana? To Wallahi Wallahi matuk'ar kina nemawa kanki zaman lafiya dani to ki canja wannan halin naki,kuma ki tashi ki d'ora mana girki yanzu,don ba zaki bar min yara su kwana yunwa ba." Kallansa tai cikin mamaki tace "yanzun zan d'ora girki an kusa sallar isha'in?" Had'e gira yai sosai yana kauda kai gefe yace "Eh haka nace,in kuma ba zakiyi ba in ji yanzu." Mik'ewa tai tana zunb'uro baki ta fice, Allah ya taimaketa tana da miya don haka kawai farar shinkafa ta dafa tana yi tana 'kunci,sai wajan 'karfe tara ta gama ta zubawa yaran ta zubawa yaya Muktar amma bata zubawa Su'adan ba. Yana kwance a d'aki ta shigo ta ajiye mai flasks d'in,ko kallanta bai ba ta fice ta koma falo. Can ya mik'e ya bud'e abincin, jim yai yana d'an nazari,kira ya 'kwalawa Baby,da ta shigo yace "Mamanku ta zubawa Su'ada abinci?" Gargiza kai tai da fad'in "A'a bata zuba mata ba,na tambayeta ina na Aunty tace bata sani ba." Turo mata kulan yayi da cewa "Maza d'auki wannan ki kai mata." D'aukan flask d'in shinkafar dana miyar tai ta wuce wajan Su'ada. Su'ada na kwance cinyar Khaleelee yana ta shafa kanta don bacci ya fara d'aukanta,sai Jidda kuma na d'akin da take kwana,Baby tai sallama cikin falon tana fad'in "Uncle ga abincin Aunty." Da sauri ya fara tashin Su'ada yana fad'in "Tashi kici ga abincin nan Pretty." Ajiyewa Baby tai ta fice, Jiddah ta fito don taji maganar abincin, kitchen taje ta d'auko plat da cokali tazo ta d'ibar mata wanda take ganin zai isheta. Khaleelee da kansa yake bata don jikinta duk ba k'arfi, tas ta cinye tace a k'ara mata,shima wanda aka k'ara ta cinye tas tasha ruwa,ai kuwa tuni wani daddad'an bacci ya k'ara gaba da ita. Ajiyar zuciya Khaleelee ya sauke cikin ransa yake fad'in "Ashe haka iyaye mata ke shan wahala, lalle ba zai gushe ba yana mai yiwa mahaifiyarsa har ranar da zai bar duniya." Jidda kam tana kwance a d'aki tana kwasar takaici,haka nan taji Sakeena ta bala'in fice mata a rai,jin wata muguwar tsanarta take. Sakeena kam na falo kwance bacci ya fara d'aukanta ,don haka bata ji sanda Yaya Muktar ya kira Baby ya bata abinci ta kaiwa Su'ada ba,sosai tai nisa a baccin taji maganar Yaya Muktar d'in yanawa su Abba magana kan su tafi d'akinsu su kwanta dare yayi.cikin mayen bacci ta d'ago ta kalleshi,ganin ledaji a hannunsa ya tabbatar mata daga waje yake.shi kam ko ta kanta bai ba ya juya ya shige d'aki,ledar abincin da ya siyo ya bud'e ya fara ci. Ba sallama ta daga labulen ta shige,ta gefen ido ta bi ledar da kallo,duk ji tai d'akin ya gauraye da kamshin abincin da ta san na nata ba,gabansa ta 'karaso tana duba ledar wani mak'uk'un bak'in ciki na taso mata,ta zuba mishi ido cikin rashin fahimta,dube dube ta fara yi bata ga flasks d'in data kawo mishi abincin ba,da sauri ta fita kitchen nan ma bata gansu ba,ta dawo falo basa nan,Baby ta kalla tana zare mata ido tace "Ke ina abincin Abbanku?" A tsorace yarinyar tace "Ai ya ban na kaiwa Aunty." Da sauri ta juya d'akin tana 'kare mai kallo tace "Ni zan dafa maka abinci ka d'auka ka kaiwa matar 'kaninka? Wai me kake nufi dani?Wallahi yau sai dai ayita ta 'kare a gidan nan,ai Su'ada ba uwata bace da zan yi girki a daran nan don ita,daman kasan ba ci zakai ba kasa dole na dafa." Kan yaya Muktar na k'asa yana ta cin abincin sa bai ko d'ago ba,balle ya tanka mata. Duk bala'in da take a kunnan Khaleelee da Jidda, ita ko Su'ada ma baccinta take. Ganin yak'i tanka mata yasa ta k'ara k'arfin muryarta 'karshe ta fashe da kuka,wai ana cutarta a gidan ita barin gidan za tai. Baba ne ya fito zuwa tsakar gidan yana fad'in "Muktar kana ina?" Da sauri ya fito a d'akin yana cewa "Baba gani." Juyawa Baba yai yana fad'in "Kuzo Ku biyun." Bayan sun shiga d'akin sun zauna Sakeena nata goge 'kwalla ita a dole an cuceta,Baba ya gyara zama kafin ya fara magana"Muktar wato abunda ba halinku ba zaku fara yanzu,tsakaninka da matarka da can baku samin matsala amma yanzu nema ku ke Ku zama kamar kaji,cikin daran nan Sakeena zaki rink'a d'aga murya ma'kota najinki,kowa sai ya san kin sami sab'ani da mijinki kenan. Fad'a min meya had'aku kai Muktar? " Yawun takaici yaya Muktar ga had'iya sannan ya fara zayyanewa Baba komai kan batun abincin.bayan ya kai aya Baba ya kalleta yana son jin ta bakinta"Shin Sakeena abunda Muktar ya fad'a duk haka ne?" "Baba tunda Su'ada tace girkina take son ci kullum safe rana da dare ni ke bata abinci,tsawon kwana takwas yau,to nima yau na tashi ban jin dad'i ban yi girki ba ta aiko na bata nace ban yi ba,da dare ta aiko ban yi ba,shine ya sani gaba a masifa wai dole in tashi in d'ora, haka na tashi da daran nan na girka abincin,to sabida bacci ya d'auke ni sai ya kwashe nasa da na kai masa ya duka ya bata,shi kuma yaje ya siyo wani a waje,Baba yamin adalci kenan?" Girgiza kai Baba yai cikin halin dattako yace "Muktar laifinka ne a nan, tunda kullum tana bata yau d'aya da uziri yasa bata bata ba bai kamata kai mata fad'a ba,kuma ma tunda tace bata jin dad'i sai ai mata uziri ai,ka tilastata ta girka kuma sannan ka'ki ci, in ma bata bawa Su'adan ba sai ka raba biyu ka bata rabi kai kaci rabi,baka san mace bata son mijinta ya'ki cin abincin ta ba? Karka 'kara irin haka, Su'ada 'kanwa ce gun Sakeena ai,ba'a shiga tsakanin yaya da 'kanwarta,wata rana zasu had'e kai su barka kaida d'an uwanka a gefe." Juyowa yai cikin muryar rarrashi ya kalli Sakeena, "Sakeena kina jina ko? Ki 'kara hak'uri kici gaba da girkawa da ita,in ma kud'in cefanan bai isa sai ya 'kara miki,kinga lalurace ta kawo hakan,nan da d'an lokaci sai kiga ta koma cin nata girkin,ki daure ke babbace, Su'ada 'kanwa ce gareki,a wannan halin tallafinki take nema bata da wata me taumakonta yanzu bayan ke,ki nuna mata duk abunda bata sani ba game da lalurarta har Allah ya sauketa lafiya kinji.tashi kije Allah yayi muku albarka." Mi'kewa Sakeena tai jiki a sanyaye ta fice,gaba d'aya Baba ya gama kashe mata jiki,dattijon nada kwarjini da haibar da bazaka iya mishi musu ba,balle yayi amfani da kalamai masu sanyi wajan yin sulhun,haka zata ha'kura taci gaba da ciyar da 'katuwa ya ta iya. Bayan fitar ta Baba ya dubi Yaya Muktar yace "Muktar duk nasan halin Sakeena, na san gajiya tai da bawa Su'ada girkinta,amma bata haka ya dace ka fito mata ba,kullum ina fad'a muku mata y'an rarrashi ne,duk tsaurin mace in ana rarrashin ta akan a'kidarta ana samun ta sassauta,amma in mace ta kafe kaima ka kafe to ba'a samun biyan buk'ata, ko ta sauko don dole to Wallahi ba zatai abunda ake soba,amma in ka lallab'ata ka rarrasheta sai taji a ranta eh an bata girmanta da matsayin ta,sai kaga ta sauko tayi yanda ake so ko fiye ma da yanda ake tunanin za tai.ka 'kara ha'kuri da ita kaji,kuma ka daina nuna mata ka fifita d'an uwanka ko matarsa a kanta hakan zai sa mata wani 'kullinsu a ranta taji duk ta tsanesu,kai ta ha'kuri kaji ko?" Gyad'a kai yai yana fad'in "To Baba insha Allah za aita hak'urin." "Yawwa tashi kaje Allah yai muku albarka Ku da zuri'arku." *TAKU CE* *'YAR MUTAN JA'OJI*🙋 [2/24, 12:02 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _Allah kai ne masani kan dukkan damuwarmu,Allah kai zaka bamu maganin ta, Allah ga hannayen mu sama muna rok'onka🙏🙏🙏 Allah ka dafa mana kai maganin matsalar mu_😢 _*page*_ *35-36* Jidda kam tunda taji maganganun da Sakeena ke tayi duk akan abincinta ranta yai matu'kar baci,kallon Khaleelee tai da ke zaune dafe da kai,jin tsantsar tsanar Sakeena yake a cikin ransa,bai tunanin samun matsala ga Sakeena ba a rayuwa,yai tunanin matsayin da su ka d'auketa na uwa ko babbar yaya zai sa taci gaba da rungumarsu da kauda dukkan damuwarsu,amma sai gashi Sakeena ta zame mai matsala a rayuwar auransa. Juyawa Jidda tau da sauri cikin d'akin ta jawo wayarta ta danna kiran mamansu, bugu d'aya Maman ta d'auka tana tambayarta ya jikin Su'ada, a gaggauce ta amsa sannan ta shiga fad'awa mama halin da ake ciki,sannan ta d'ora da fad'in "Mama me zai hana kiyiwa Yaya Khaleelee magana Kawai ya bari mu taho gida da Aunty Su'ada, halin da take ciki ba zata tab'a hak'ura da abincin Sakeena ba,ita kuma ba zata gaji da yi mata wulak'anci ba,tunda gashi akan abincin yanzu tana ta fad'a da mijinta,amma in muka dawo gida kinga zata hak'ura tunda tasan ba samu za tai ba,in Allah yasa hankalinta ya koma ga son wani abu sai ta dawo d'akin ta ko?" Cikin gamsuwa da batun na Jidda mama ta kashe wayar,sannan ta kira number d'in Khaleelee, bayan sun gaisa cikin girmamawa tace "Ibrahim daman alfarma zan rok'a a gunka." Cikin tsananin jin kunya da mamaki Khaleelee yace "Mama alfarma kuma? ai ke uwa ce kinfi 'karfin neman alfarma sai dai ki bada umarni,fad'i ko mene mama insha Allah za'a miki." Cikin jin dad'in furucinsa mama tace "To Ibrahim daman don Allah so nake in ba takura ka dawo da Su'ada gida zuwa lokacin da Allah zai kawo mata sauk'i duk da irin Wannan lalura sai an rabu lafiya ke samuwa,amma yanda Jidda ke fad'a min halin da take ciki nake ganin in ta dawo kusa dani zan san irin taimakon da zan rink'a bata." Shiru Khaleelee yai don bai zaton jin wannan daga mamanba,amma ba yanda zai yi,ba zai bijirewa umarnin mama ba sannan a halin ma da suke ciki yanzu k'ara tai nesa da gidan,don haka ya k'ara k'asa da murya yace "Ba komai Mama kin fi k'arfin komai ai, balle wannan. insha Allah da safe ko zan kawo ta." Da fara'a sosai mama tace "To na gode,Allah yai maka albarka ya baku masu yi muku biyayya kuma." Cike da kunya yake amsa mata har su kai sallama. Kiran Jidda yai bayan ta fito yace "Jidda mun yi waya da mama,insha Allah da safe zaku koma gida har zuwa lokacin da Allah zai bawa Su'ada lafiya,yanzu ki had'a mata duk kayan da kike ganin zata buk'ata kema ki had'a naki,da safe zaku tafi." Gyad'a kai tare da fad'in "Tom Yaya Allah, ya kaimu, bari na had'a kayan." Ta shige bedroom d'in cikin ranta tana murna shawarar ta ta karb'u. Tun sallar asuba Jidda bata koma ba,ta shiga kitchen ta shirya musu abun Karin kumallo,sannan ta d'ora girkin rana, ba dan wai su zasu cu ba,a'a sabida Baba da Jabeer,wajan k'arfe takwas ta kammala girkin,wanke wanke tai tare da gyara ko ina,bayan duk ta kammala sa gyaran gidan sai ta shiga wanka.tana fitowa a lokacin Su'ada ta tashi,itama ruwan wankan ta had'a mata tai,tana fitowa tace "Jidda d'umamamin guntun shinkafar nan ta jiya.kallon ta Jidda tai tana y'ar dariya tace " Na san zaki nema don haka tuni na d'umama,shirya ki fito kici." Girgiza kai tai tana zama kan kujerar dake k'ofar toilet d'in tace "a'a kawo min yanzu na ci,da k'yar ma nai wankan nan don yunwa nake ji sosai. Ita kam Jidda bayan ta kawo mata shinkafar wucewa d'aki tai don ta k'arasa shiryawa. Nauyin bacci yau Khaleelee yai,don haka har Su'ada ta gama cin abincin ta koma d'aki sannan ta tadashi. cikin mayen bacci ya ke kallon idanuwanta,itama shi d'in take kallo cikin d'an mirmishi tace " Ka tashi ka shirya karka makara a shago tara ta wuce tuni fa ." Mik'a yai yana salati yace "Um nama manta,Wallahi yau dogon baccin na samu sosai." Tashi yai ya zauna yana duba agogo yace "Pretty jiya fa mun yi waya da mama,zaki koma gida sabida jikin ki,in kin d'an k'ara warwarewa sai ki dawo." Da murna ya kalleshi tace "Wayyo amma naji dad'i Wallahi, k'arfe nawa zamu tafi?" Mik'ewa yai yana fad'in "Bari dai nai wanka tukun ." Bayan Jidda da Khaleelee sun gama karyawa ya fita wajan Baba ya sanar dashi Su'ada zata koma gida.bai ce komai ba sai fatan samun lafiya da yayi mata. Wajan sha d'aya su ka tsaya da keke napep a k'ofar gidansu Su'ada, shi da Jidda ne su ka d'auki jakan kayan nasu zuwa ciki. Bai samu mama a gida ba tana wajan aiki don haka bai jima ba yai musu sallama ya tafi. *********** K'arfe biyu ma rana mama ta dawo,cikin fara'a take amsa gaisuwar Su'ada tana fad'in " Maman biyu sannunki ya jikin ?" Rufe ido Su'ada tai cikin jin kunya tace "Kai Mama ni dai fa." Sai kuma tai shiru,maman ma dariya tau ta wuce d'akin ta. Sai da tai wanka tai salla sannan ta fito falo,kowa nata cin abinci amma Su'ada ba kwance kan kujera,mama ta zauna tana cewa "Su'ada ke baki cin abincin ne kike kwance?" D'an turo baki tai da fad'in " Ni mama ban son k'anshin abincin ma Wallahi. " Cikin kwantar da murya mama tace "Eh daman yanzu kam ai sai kin yi hak'uri komai ba zaki ji dad'in sa ba,balle kin samu ciki me laulayi sosai,yanzu bari in dafa miki wani abu me dad'i nasan zakiji dad'insa sosai." Kud'i mama ta bawa Khaleelee tace "Maza auta jeka k'ofar gida gun me kayan miya ka siyo min yakuwa." Da kanta ta shiga kitchen d'in ta fara harhad'a kayan da zatai wa Su'ada fatan tsakin masara. Zuwa k'arfe uku ta kammala, lokacin har bacci ya d'auketa ma,bata tasheta ba sai data farka da kanta sannan ta zubo mata faten yana ta turirin zafi. Da fari kam Su'ada ca tai bata ci, sai da mama taita rarrashinta sannan ta d'ibi kad'an a cokali ta kai baki,Jim tai jin tsami tsamin ramar ya ratsa kanta,ta k'ara loma d'aya taji yai maya coy, ai sai ga Su'ada ta mik'e k'afa tana zuba loma,sai da ta cinye tas tasha ruwa,mama tai mirmishi tana cewa "Ko a karo wani?" Girgiza Kai tai da fad'in "A'a mama yanzu na k'oshi, amma a ajiyemin anjima zan k'ara." ********** Bayan sallar isha'i duk su na zaune su na ta hira, wayar Su'ada tai k'ara, mik'o mata mommy k'anwarta tai,bayan ta d'aga daga d'aya b'angaran Khaleelee ya amsa mata"Pretty ina hanyar zuwa gidan,me zan zo miki dashi?" Jim tai tana tunani can tace "Kifi karfasa amma me zafi sosai,kuma a zuba yaji da yawa." "Ok shi kenan ko da wani abun?" "A'a ba komai shi kad'ai yayi." Ba'a jima ba sai gashi ya zo,bayan sun gaisa da mama ya koma sitting room. d'an kwalin kayanta ta yafa tabi bayan sa.tana shiga yaje kan cinyarsa ya zauna tana Rik'o hancinsa cikin tsokana tace "har na fara missing wannan dogon hancin fa." Had'e fuskarsa da tata yai yana goga mata hancin kan nata,a hankali yake magana " shima zai yi ya fara kewan ki, ni fa da za'a ban wajan kwana nima had'o kayana zan yi mu dawo nan d'in gaba d'aya. " Lumshe ido tai tana janye fuskarta ta kwanta a jikinsa sosai,sabida yanzu sam bata jin kwarin jikinta,yawon kasala da zafin jiki duk sun zame mata jiki. Shafa fuskarta yake a hankali yace "Tashi ga kifin karya huce." K'asa su ka sauka ya bud'e mata, a hankali take ci cikin jin dad'in sa,gashi sai nad'ar yaji take." Kad'an ta rage ta nannad'e wai anjima kafin tai bacci zata ci,shi kam binta kawai yake da kallo yana mirmishi, gida ta shiga ta wanke hannayenta da bakinta,sannan ta ajiye d'aura kifin ta dawo wajan sa. ************ Kullum da dare sai Khaleelee yazo,kuma sai bayan goma yake tafiya. Zakiyya ma tazo gida ta dubata,Baba ma ya kirata a waya,haka ma yaya Muktar ya kikkirata ya mata Sannu, balle kuma d'an gidanta Jabeer, shi kam duk kwana biyu ma sai yazo sun sha hirar Sakeena kam sai da kunyar kanta ta isheta ganin yaya Muktar bai ce mata uffanba kan ta kira ko karta kira.gashi in dai Jabeer na gida zai kirata ya had'a ta da Islam, to da kanta ta gaji ta kirata tai mata sannu,daga ranar kuwa bata k'ara ba . B'angaran Su'ada kuwa a gidansu ta sami lafiya masha Allah, tayi wani sharrr da ita ta k'ara fari da,har k'iba tai,sai dai fa zazzab'i kullum dashi take kwana,b'angaran abinci kuwa ta bud'ewa faten tsaki da alala wuta,in taci alala da safe to da rana zuwa dare fatan zatai ta sha,sai Zob'o wanda ta maidashi shine ruwan shanta. ********** Yau sati uku da zuwanta gida,don haka ranar Mama tace ta shirya kayanta da dare in Khaleelee yazo ta bishi ta koma d'akin ta tunda lafiya ta samu.da ta fara rigimar ita ba zata koma ba,amma ganin mama ta had'e rai tasan ba wasa,don haka ta nutsu.ai kuwa nan da nan k'annanta su ka had'a mata kayanta waje guda,ita dai tana ta zumb'ure zumb'ure,mama tai kamar bata ganta ba. ******** Da dare kamar kullum Khaleelee yazo,yana zaune sitting room, Khaleelee yazo yana ta damunsa da surutu, sai biye mai yake suna shiririta,can Khaleelee yace "Yaya Khaleelee kasan me kuwa?" Kai ya girgiza yana d'an mirmishi yace " ban San me ba sai ka fad'a my takwara." Cikin y'ar dariya yai tsalle tare da gyara zama yace " Mama tacewa Aunty Su'ada yau d'in nan zata koma gida,yanzu ma tace kana zuwa zaku tafi tare." Ware ido Khaleelee yai yace "Da gaske kake mutumina?" Kafin yaron yai magana aka turo k'ofa aka shigo. Ido ya d'ago yana kallonta,d'an mirmishi yai ganin yanda ta wani had'e rai ta kauda kai gefe.a hankali ya kalli Khaleelee yace "Takwara je kace ina gaida mama da Aunty Jidda." Da gudu yaron ya fice. A hankali ya dawo kusa da ita ya zauna tare da sakar mata wani numfashi a wuyanta,cikin k'asa da murya yace "Pretty yau ba'ai murna da ganina bane?" D'an turo baki tai tana kauda kai gefe tace "um um ni ba Mama ce tace wai sai na koma yau ba,ni kuma ban son tafiya Allah." Zuba mata ido yai na d'an lokaci, kafin ya fara magana "pretty na,me yasa baki son komawa? Ko bi kiyi kewana bane?" K'ara turo baki tai cikin shagwab'a tace"To ai ni ban gama warkewa ba fa,kulleda zazzab'in nake kwana. " Shafo gefan fuskarta yai yana k'ara shigewa jikinta sosai,hannunsa cikin nata yana k'ara matsa mata su,a sannu ya d'ora fuskarsa saman tata yana magana murya a mak'ogaro "kiyi hak'uri kinji sweetheart, ba zan iya ja da maganar mama ba amma da naje nace ta k'ara miki ko sati guda ne,amma ki yi hak'uri mu tafi,insha Allah zazzab'in zai daina ma gaba d'aya." Yanda yake mata ne ya sa jikinta mutuwa tsikan jikinta ya fara tashi,rik'o hannayensa tai tana fad'in "A'a ka bari,ka cikani to." Maimakon ya cikata kamar yanda tace Aa sai ya k'ara mak'ale mata yana mata cakulkuli,hakan yasa ta fara kyalkyala dariya tana tuttureshi. K'wank'wasa k'ofa a kai,da sauri ya cikata ya koma wata kujerar ya zauna,sannan ya bada izinin shigowa,Mommy ce ta shigo tana gaidashi,bayan ya amsa ya d'an tsokaneta sannan tace"Yaya daman mama ce tace wai kazo." Mik'ewa yai da sauri yana fad'in "To muje maza." Itama Su'ada bin bayansa tai har zuwa cikin gidan,a falo ya samu Mama a mutunce kamar ko yaushe su ka gaisa,Mama tace"Ibrahim Allah yasa dai tama bayanin yau zaku tafi tare?don haka ba sai an zauna hira ba yanzu yanzu Ku wuce gidanku kwayi hiran a can." K'asa yai da kai cikin jin kunya yace "To Mama mun gode,Allah ya k'ara girma ya k'ara lafiya, Allah ya ja da rai." Amsawa Mama take tana k'ara sa mai albarka,sannan ta dubi Su'ada da ke gefe a tsaye ta harde tana ta turo baki. 'dan mirmishi Maman tai sannan tace "To hajjaju je ki sako hijab Ku wuce ko? Mommy Ku rakata da jakar kayanta waje." Har kwalla Su'ada tai don takaici, tabbas ba k'aramin jin dad'in zaman gidan tai ba,yanda kullum take rayuwa cikin y'an uwanta ga mamanta na ta shagwab'a ta,ita da za'a barta ma ta har ta haihu tai arba,in da taso hakan. *Taku ce* *'Yar mutan Ja'oji*🙋 [2/24, 12:02 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ *Ina buk'atar addu'a daga bakunanku masu albarka* _*page*_*37-38* A hanya Khaleelee ya tsaya yaiwa Su'ada na kayan ciye ciye sosai,suna tafe yana mata hira amma tak'i tanka mai, don haka yaja bakinsa yai shiru, aransa ko fad'i yake ai 'Mama tai min gata, daman kwana biyun nan a d'ari nake jina,don haka yau hhhhmmmm'. A k'ofar gida ta sauka a mashing d'in don bashi damar shigo dashi soro, k'ofar d'akin Baba ta tsaya da sallamarta,Jabeer ne ya amsa yana fad'in "Aunty kin dawo? Sannu da zuwa." K'arasowa yai ya d'age labulan yana fad'a Mata Baba ya jima da yin bacci sabida bai jin dad'i. cikin damuwa tace "Ayya,Allah ya bashi lafiya, bari da safe ma gaisa,Ashe dole in ganka da wuri haka a gida." Y'ar dariya yai yana shafa kai yace"Aunty ya jikin naki dai?" "Alhamdulillah d'an uwa,jiki ya warware,bari in k'arasa kar mu tashi Baba." A lokacin Khaleelee ya k'araso janye da akwatinta. Tana sallama a tsakar gidan Baby da batai bacci ba da Abba su ka fito da gudu suna ihun murnar Aunty Amarya Oyo yoo,itama cikin fara'a ta tare su,tana fad'in"A'a banga mutuniyar ba ko tai bacci?" Sakeena ce ta d'aga labulen d'akin ta ta fito,yau kam fuskarta da fara'a takewa Su'ada sannu da zuwa,itama cikin fara'ar ta amsa su ka gaisa,Yaya Muktar ma ya fito su ka gaisa tana k'ara tambayar ta jiki,ta amsa mai da sauk'i. K'arasawa tai wajanta da Khaleelee ya bud'e k'ofar,tana shiga ta cire hijab d'in ta ta wullar kan kujera,toilet ta shige tai brush ta wanke fuska,sannan tazo tai shirin bacci. Yana kallon yanda take ta zumb'ure zumb'uren baki,amma sai ya kauda kai,shima shirin baccin yai ya kashe haske, a hankali ya fad'o kan gadon,ya na jawota jikinsa,k'ok'arin tureshi ta fara yi,amma yak'i bata damar hakan,a sannan yake sarrafata da hannu guda,tun tana ciccijewa da kauda kai har yai nasarar saka harshensa cikin nata, cikin salonsa na iya soyayya ya shiga juya harshensa cikin bakinta,Su'ada dai tun ba'a so har jikinta ya fara sauyawa,dole ta mik'a wuya.sun tabbatar sunyi kewar juna fa,don basu tab'a d'aukan wannan lolacin basu gamu ba tun auransu,amma gashi tunda ta fara laulayin nan kusan wata biyu basu had'u ba,duk suna buk'atar juna, dole su ka zage su ka more junan su. Da safe Su'ada ta had'awa Khaleelee kayan break fast,sannan ta shiryawa Baba nashi,ita kam k'ullin k'osan data nik'a a blander shi ta d'iba ta d'aura alala guda biyu ta zabga attaruhu,sai kunun gyad'ar data damu musu ita ta zuba nono da yawa a cikin nata,don yanzu kullum wannan shine abun karyawarta,da rana kuma zuwa dare ayi ta shan faten tsaki. Bayan tai wanka ta shirya Khaleelee daya taimaka mata wajan aikin shima ya shiga wanka bayan ya gyara d'an tsakar gidan nasu da ya b'aci da toka, dake har lokacin bata son warin gass a gawayi duk tai aikin. Basu zauna karyawa ba Su'ada tace "Bari na duba Baba sai na karya." Mik'ewa shima yai ya d'auki kayan break d'in Baban yabi bayanta. Idon sa biyu yana zaune yana lazimi da carbi hannunsa. Da sallama Su'ada ta shiga d'akin,cikin fara'a Baba ya d'ago ta kalleta,sannan ya Shafa addu'ar da ya ke,cikin sakin fuska sosai ta amsa sallamarta,bayan ta zauna ta gaidashi cikin girmamawa,kallo d'aya za kaiwa Baba kasan yaji dad'in dawowarta,don haka da Y'ar dariya yace"Ah masha Allah lafiya ta samu, sannu kinji,da asuba Jabeer ke fad'a min kin dawo jiya ina bacci,ya kika baro mutan gidan? " Kanta a k'asa ta amsa da duk suna lafiya suna gaidashi,nan tai mai ya jiki ya amsa itama yana k'ara tambayarta ga nata jikin,bata iya amsawa ba don nauyi taje ji,Khaleelee ne ya matso kusa dashi sosai yana gaidashi da mai sannu sannan ya bud'e mai abincin yana fad'in "Baba ga girkin Y'arka ya dawo." Dariya Baba yai yace "Su'ada daga dawowa sai d'ora tukunya? To sannu Allah ya k'ara afuwa da k'arfin jiki." A zuciya ta amsa da amin,sai Khaleelee ne ya amsa a zahiri.sun d'an zauna su ka fito,nan Su'ada ta tsaya su ka gaisa da Sakeena shima Khaleelee ya gaidata sama sama,don yanzu Sam bata birgeshi a komai. Bayan sun koma sashinsu su karya,su nayi suna hira,Khaleelee yau cir bai fita ba yana nanik'e da Su'ada,ita kanta Su'ada bata tabbatar tai kewar mijinta haka ba sai yanzu,don haka itama take ta mak'ale mai tana zuba shagwab'arta. ************** Kwanaki na tafiya watanni sun yi nisa zuwa yanzu ga cikin Su'ada ya kai wata tara, haihuwa ake jira yau ko gobe da ikon Allah, batun kayan haihuwa fa ba abunda basu siya ba,Khaleelee yayi bajinta sosai,don ya had'a duk abunda ake buk'ata, koda Su'ada tace zata sai wani abu da kud'in ta sai yace A'a ta ajiye kud'in ta shi hakkinsa ne ya saiwa y'arsa komai,daman sun ui scanning an tabbatar musu da mace ce,don haka duk siyayyar su ta mace su kai. Yayar Abbansu ce tazo daga can darki zata zauna da ita,amma bata zo gidan ba tana can gidan su Su'ada sai an yi haihuwar zata zo. *********** Tun farkon wata suke sa rai da haihuwa,don abunda edd d'inta ya nuna farkon wata zata haihu amma gashi wata har ya kai kwana ashirin shiru,da farko Khaleelee ya tada hankalinsa amma a sanar da Mama sai tace ba komai daman yana haka ba lalle yanda edd ya nuna ake haihuwar ba hakan iko ne na Allah, amma dai su k'ara zuwa ga likita,to sun koma asibiti akai gwaje gwaje komai lafiya kawai lokacin fitar Babyn ne bai ba,sai a lokacin hankalinsu ya kwanta. ******* Yau ashirin da bakwai ga wata, Su'ada na zaune Khaleelee nata matsa mata k'afa, don duk sun kumbura,duk da cikin bai wani k'ato ba amma ya kumburata,kallon Khaleelee tai idonta na cikowa da hawaye tace "Khalbee Wallahi cikin nan ya dameni,nauyinsa nake ji kamar kamar me." Matsowa yai jikinta yana shafa kanta a hankali yake magana cikin kwantar da hankali yace"Ki daina cewa kin gaji dashi kinji pretty, ibada kike yi,kuma Allah yana baki ladan wannan wahalar da kike sha,sannan ki k'ara hak'uri kan wanda kikeyi,lokaci ne a sannu Allah zai kawo mana Babyn mu lafiya,fatanmu Allah ya rabaku lafiya,ki kwantar da hankakinki kinji." Gyad'a kai tai tana maida hawayen daya cika idon. Ci gaba yai da rarrashinta cikin kwantar da hankali yana shafa kanta,daga baya yaci gaba da mammatsa mata k'afar har ta fara gyangyad'i,kwantar da ita yai yana k'ara matsa mata jikin kafin shima baccin gaba dashi. Can tsakiyar dare Khaleelee ya fara jin nishin Su'ada tana kiransa,kamar a mafarki yake jin ta,can yaji ta k'ara kiransa cikin muryar kuka,da sauri ya bud'e ido,amma dake d'akin sa duhu bai ganin komai don haka ya lalubo makunnar glop ya kunna,da sauri da diro a gadon hangota da yai a k'asa tana ta murk'ususu.rik'o ta yai yana salati da fad'in "Su'ada mene ne,me ya sameki ?" Idonta a runtse tace "Marata ke ciwo, ka taimaka min don Allah." Gaba d'aya ya rikice ya rasa me zai yi ma." Rik'o hannunsa tai cikin dauriya tace"Ka bani wannan ruwan addu'ar da umma ta kawo,tace da naji ciwo in sha." A rikice ya tashi ya d'auko mata gorar ruwan tare da d'ago kanta tai bisimilla tasha ruwan. Tofa ciwo yace gashi zuwa,tun suna abu su biyu a d'aki har ya fita ya sanar da Yaya Muktar yace zaije ya taso wani abokinsa me adaidaita su wuce asibiti. Yaya Muktar ya taso Sakeena yace taje wajanta,sannan yabi Khaleelee su ja fita zuwa k'asan layinsu,Usman abokin Khaleelee su ka taso a shagonsa,ba b'ata lokaci ya fitto adaidaitarsa daga garejin da yake ajiyarta,a ciki ya d'auko su suka k'araso k'ofar gidan. Zuwa Lokacin Su'ada tai lak'was, da sauri Khaleelee ya ciccib'eta ya sata a daidaitan,sannan ya dawo ya d'auki akwatin da suka had'a kayan haihuwar, Ita da Sakeena a baya shi ya mak'ale a gefe su ja tafi yaya na mata addu'ar sauka lafiya,basu tashi Baba ba sabida jikin nasa ba dad'i, shi kuwa Jabeer uban y'an nauyin bacci duk bai ji abunda ake ba. ********* Dake a asibitin gidan zoo take awo BA nisa tsakani su ja k'arasa, da gaggawa aka amsheta zuwa labour room,Sakeena da Khaleelee na zazzaune suna dako,Wanda zuwa lokacin ilahirin jikin Khaleelee ya gama yin sanyi,don sai yake jin kamar wani abune zai sami Su'ada, haihuwa na bashi tsoro, yanda yake ganin mata na matuk'ar shan wahaka. Har aka kira salla shiru, yaje masallaci yai salla ya dawo,Sakeena ma cikin masallacin mata ta shiga tai sallar, har gari ya waye ba labari, yaya Muktar nata kiran waya amma sai suce shiru,wajan k'arfe bakwai Allah ta sauketa. Khaleelee na can gefe a zaune ya dafe kai,cikin addu'a ya rasa wacce ma zai yi,yaji wata ma'aikaciyar asibitin ta fito tana fad'awa Sakeena ta sauka an sami y'a mace,ai a d'ari ya k'araso gareta yana fad'in "Da gaske ta haihu?na godewa Allah, amma ta take yanzu ya jikin nata ?" Cikin kwantar da hankali tace mai "Eh ta haihu an sami mace,zamu gyarasu yanzu,anjima zaka gansu,duk suna cikin k'oshin lafiya. Cikin murna yai taiwa Allah godiya,sai a sannan ya samu damar sanar da Mama, cikin farin ciki tace gata nan zuwa asibitin ita dame kula da Su'adan,bayan ya kashe ya kira Yaya Muktar ya sanar dashi,nan kuma ya shiga kiran y'an uwa da abokan arzik'i yana sanar dasu haihuwar,kowa murna yai ta tayashi da addu'ar Allah ya raya. Kafin k'arfe takwas mama da Innaro su ka 'karaso asibitin. *Taku ce* *Y'ar mutan Ja'oji* [2/24, 12:02 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ *Ina barar addu'a daga bakunanku masu albarka* _*page*_*39-40* Innaro ce ta Fara d'aukan Babyn tana fad'in "Madalla da hikimar ubangiji,wannan kama ta b'aci." Mik'awa Mama Babyn tai fad'in "Duba min wannan kama ki gani don Allah." Sosai mama ke kallon yarinyar, cikin memory d'in ra take tuno ranar data haifi Su'ada, babu wani abu daya banbanta fuskarsu, lalle yarinyar na tsananin kama da mahaifiyarta. Rungumeta tai cikin jikinta tana mata addu'a da jin tsantsar k'aunar y'ar ba ratsata. Cikin tsokana ta Mama tace "Wannan y'a da kalen kama kike,ki rasa kamar wa zakiyo sai ta mijina to ahir d'inki, mijina ba tsaranki bane(dake Su'ada kamarta d'aya sak da mahaifinta) Dariya innaro tasa tana fad'in" To me ma zatai da mijinki fata duk tai laushi,ita kam Wannan d'iya mijinta ma na Saudi yana karatu." Dariya suka sa gaba d'aya, sai a sannan Mama ta k'arasa ga Su'ada dake kwance, gaba d'aya kunya ta rufeta,yau kam ji take har Maman kunyarta take,tunda ya haihu ta kasa had'a ido da kowa. Mama tace "Sannu Su'ada, yanzu me kike ji a jikin naki?" Girgiza kai tai idonta b kallon gefe tace"Ba komai Mama." "To Alhamdulillah, an gode Allah, haihuwa tai kyau ai,tunda an haihu lafiya ." A lokacin Khaleelee ya shigo daga gun doctor, da sauri ya tsugunna yana gaidasu,su ka amsa suna mai barka, kansa a k'asa yake amsawa, sannan yace "Mama zan d'an je gida na dawo,don sun ce sai k'arfe goma zasu sallamemu,to Sakeena ma yanzu nace taje gida sabida yara,nima zanje na dawo." Innaro ce ta amsa da fad'in "Jeka ai ba damuwa,muna nan,kamar yanzu goman za tai." Mik'ewa yai yana musu sallama ya fice. ******* Wajan k'arfe goma da rabi likita ya bawa Khaleelee takardar sallama,Wanda ya dawo tun tuni daman wanka yaje yai. A motar Mama su ka wuce gidan,shi kuma Khaleelee ya biyosu a mashing d'in sa. To fa yau dai ga jika taja Baba har d'akin Su'ada, duk da baida lafiya,amma haka ya sa sandansa ya dogara zuwa d'akin, Khaleelee yana fad'in "Baba ka bari a kawo ma ita d'aki." Yace "A'a miji ai shi ke tarar matarsa,barni naje na ganta." Cikin mutunci su ka gaisa dasu Mama,suna mai sannu da jiki,bayan ya d'auki y'ar yai mata addu'a sosai,sannan ya dubi Su'ada da ke zaune kan filo kanta a k'asa yace"Sannu Su'ada kinji, Allah ya k'ara lafiya,abunda nake son sanar dake shine, yanzu Allah ya d'ora miki wani nauyi ne me girma,rayuwarki data baya ba d'aya ba,kin zama uwa,don haka duk abinda zaki aikata yanzu to karatu ne ga yarki,duk abunda za kiyi na kirki ko akasin haka to nad'ewa za ta rink'a yi,kece makarantarta,don haka kiyi k'ok'ari ki zama malama me koyar da ita karatun sanin Allah da manzansa, kiyi mata tarbiyar da duniya zatai alfahari da ita,kar kiyi wani abu na Allah wadarai gaban y'ar ki,kina jina ko Su'ada? " Gyad'a kai Su'ada tai da fad'in "Eh Baba ina ji." Yace "To masha Allah, Allah yai muku albarka ya baki lafiyar shayarwa,kai kuma ya baka arzik'in kare duk buk'atun iyalinka." Su Innaro ne su ke amsawa da Amin amin. Sosai Mama taji Dattijon ya k'ara birgeta,ta k'ara tabbatarwa y'arta tayi aure gidan tarbiyar. *********** Ba jimawa Mama ta koma gida aka bar Innaro me zaman dab'aro. Sakeena kam yau ba kyashi ta zage taiwa Su'ada hidima,kama daga ruwan wankanta zuwa na Baby, gyaran gida duk ita tayi. Sai da Zakiyya tazo ne ma ta amsheta,da yamma kuma su Jidda su ka zo,su sukai girkin dare su ka k'ara gyara gidan.Khaleelee ya takura sai da aka bar Husna,me bin Jiddda, yace ta zauna sabida girki kar aikin yayiwa Innaro yawa ga girma. ********* Kowa yazo barka sai ya jinjina kamar da Baby ke yi da mamanta,in ka d'auke tsayi da yarinyar ta debo na Khaleelee don doguwa ce sosai masha Allah, to babu abunda ya rabata da uwarta. Ranar kwana biyu da haihuwa Su'ada ta shiga bedroom kaiwa Khaleelee wayarsa data gama kira da ita,tana mik'a mishi ya jawota jikinsa yana fad'in "Sai wani baya baya ake dani me nayi wai?" Janyewa take son yi daga jikinsa yak'i,ta d'an turo baki tana fad'in"Ba wani baya baya da ake da kai fa,kawai jego ne." Kamo fuskarta yai yana k'ok'ari kissing d'in ta tai baya da sauri tana zare ido, Y'ar dariya yai yana gyara tsaiwarta a jikinsa yace "Kin min wayo pretty, kowa sai ya gano kamar da Babyna ke yi dake,kin cini wasa a wancan karon amma a gaba zan bud'e wuta,nan da wata goma zaki bani me kama dani." Zaro ido ta k'ara yi,tana dafe k'irji tace "Don Allah ka rufamin asiri,wane wata goma kamar tattabara,sai na huta fa,shekara uku ko hud'u." Hararanta yai cikin wasa yace "Shekara uku lokacin kin haifi uku." Da k'arfinta ta tureshi ta fice da sauri. Dariya yasa ya koma gado ya kwanta. ************ Aunty Bilkisu wato babbar Yayar su Su'ada dake aure a katsina tun kwana d'aya da haihuwa tazo, daman kullum jiran sak'on haihuwa take.tun zuwanta kullum gidan take yini sai yamma ta koma gidansu ta kwana. Shirye shiryen suna ake sosai,daga b'angaran gidansu Su'ada da kuma b'angaran Khaleelee. Ranar kwana biyar da haihuwa aka kawo kayan barka daga gidansu Su'ada, kaya ne na alfarma Abbansu sa Mama sukai rawar gani wajan had'awa,don tunda Jidda ta turawa Abban su pic d'in Baby ya gani yace wannan ta dabance don dashi take kama bama da Su'ada ba,don haka ya sakarwa Mommy kud'i sosai tai siyayya.kansa kayan Babyn abun kallo ne,riguna zafafa masu d'aukar hankali da tsada, haka ma akwatin Su'ada damkam da kaya,sannu Khaleelee shaddarsa shima yadi biyar kusa biyu da hula,sai dank'areriyar atamfa da Mama ta aikowa Sakeena sabida hidimar da tai a asibiti. Ranar kam Sakeena ta k'ara tabbatar da Iyayen Su'ada masu zuciya ne,don komai a wadace su ke mata shi. Washe gari ma kayan da Khaleelee ya had'a aka fito dashi,shima yayi k'ok'ari matsayinsa na me k'aramin k'arfi,yaiwa Baby riguna guda goma,mamanta kayan fitar suna ma guda bakwai,kuma kaya masu tsada. Ana gobe suna fa gidan yai damk'an da alumma,dangin su Su'ada na darki duk sunzo wai haka ma da yawa suna gidan mama,way'anda zasu yi aiki kad'ai suka zo kwana anan. ********Ranar suna yarinya taci sunan kakarta mahaifiyar Khaleelee wato Aminatu, anma za'a mata lak'abi da (Nusrat) Sosai fa taron suna yayi taro,gida tamkar ana biki ba suna ba,kasancewar Su'ada y'ar dangi kuma me mutane da yawa yasa gidan ba masakar tsinke,k'arshe dai Khaleelee Canopy yayi ranting da kujeru aka sa k'ofar gida duk jama'a su ka zauna,a sannan aka samu sukuni cikin gidan. Su'ada a b'angaranta bata da abun siya da kud'inta komai n mata mijinta ya tsare mata komai haka iyayenta,don da tacewa ma Khaleelee tana son badawa ai mata jaka da calanda na Baby yace ya bayar ayi jaka,sannan Jabeer yayi kalanda stickers.daga haka bata kara magana tana ta tunanin me zatai itama da kud'in dake cikin account d'inta, don albashinta ba wani abun take dashi ba sai abunda ba'a rasa ba.bayan tai dogon nazari ta yanke hukuncin siyawa yarinyar d'an kunnan gold,don haka tasa a ranta da an gama hidimar suna zata siya mata. Taro yayi kyau kowa sai fad'i yake masha Allah, ko a b'angaran abincin suna da lemuka kowa ya shaida Khaleelee gwarzon namiji ne,ga ragunansa manya guda biyu daya yanka na hakika. ******da daddare taro ya watse ya rage mutum uku a gun Su'ada, Innaro da Aunty Bilkisu sai k'anwar mamansu Aunty iyami. Ruwa me zafi aka had'awa Su'ada tai wanka sannan a kaiwa Baby Nusrat,ta fito a wankan tana zaune bakin gado tana shafa turare a jikinta kasancewar tsananin zafin da ake yasa ko mai bata shafa ba,ko wankan ma badan jikin jego ba ba zata iya sa ruwan zafi a jikinta ba.su Aunty Bilkisu nata gyarana gida da wanke tsakar gidan da akai kaca kaca dashi,ita d'aya ce a d'akin ya shigo da sallama,kallonsa tai tana mirmishi don sosai taga kyansa cikin idonta.yana sanye da Sabuwar shaddarsa gak light blue an mata aiki da dark blue d'in zare,haka hular kansa da takalmi duk kalar aikin rigar.ganin kallon da take masa me nuna tsantsar birgentan da yai yasa yaja ya tsaya jikin k'ofar shima yana kallonta fuskarsa wadace da mirmishin. Kauda kai gefe tai tana d'an dariya tace "Wannan kallon kamar za'a siyeni ." Lumshe ido yai ya bud'e yana y'ar dariyar shima ya bata amsa da "Hhhmmmm siya kuma na nawa? An siya an biya har an jujjuya an sami ribar farko gata a kwance." Mik'ewa tai tana saka doguwar rigar data d'auko mara nauyi kuma bata da Babban hannu,yana tsaye yana kallo ta gama sawa sannan ya k'araso cikin d'akin sosai yana k'arasawa ga bakin gadon yanawa Nusrat wasa da wak'a. "Mamana tafi ta kowa, Mamana sarkin kuka,amma kukan ma da dalili,Mamana y'ar albarka,Mamana Ummyn Abba." Juyowa tai da mamaki tana kallonasa kafin tace "yaushe ka fara wak'a?" Dariya yai bayan ya zauna sosai ya d'auki Nusrat Sannan yace "Tun ranar da na zama Abba." Jijjiga kai tai da d'an mirmishi tace "Ba ruwana, Allah yasa wani ya jika kanaiwa y'ar fari wak'a." Sosai maganar ta bashi dariya,sai da yai mai isarsa sannan yace"Ke in bakiyi ni bani waje,ko a gaban Baba zan mata wak'a da rawa." Zaro ido tai da fad'in "La' ni kam ba ruwana Wallahi, ni ka fita ma kar aga kazo ka dad'e a d'akin ayi wani tunanin." Bai kara tanka mata ba ya ci gaba da yiwa yarinyarsa wasa harda kwanciya kan gadon, ita kam Su'ada data gaji da magiyar ya fita yak'i sai ra fito ta bar mai d'akin. A falo a tadda Aunty Bulkisu na ta sharewa su kam su Innaro na tsakar gida.tace Aunty sannunku da aiki,da kun huta ma da safe ai kwayi." "A'a k'ara mu rage yanzu, kuma shara ma ai ba'a barta ta kwana ba,kina ganin fa yanda duk wajan ya jagale,ki koma d'aki don moping zan yi." "To sannunku da aiki" ta fad'a tana komawa d'akin. Jan stool tai ta zauna bakin gadon tana kallonsa na d'an lokaci sannan ta lumshe ido. Shima kallontan yai ya kauda kai da fad'in "da ganin Wannan kallon na kewa ta ne." Turo baki tai kamar zatai kuka tace "Ni bance ba,gaskiya ka bari,kawai don na kalleka sai ya zama abun fassara." Ajiye Nusrat yai ya taso zuwa Inda take,d'an rank'wafowa yai saitin fuskarta yana magana can k'asa "Ko baki fad'a ba yarinya na gani cikin idonki, kuma duk abunda ido ya nuna gaskiya ne." Yana fad'i ya mik'ar da ita tsaye tare da rungumeta,maimakon ta tureshi yanda take mai tunda akai haihuwar sai yaga sab'anin haka,don lif tai a k'irjinsa tana sauke tagwagen ajiyar zuciya. Shafa bayanta ya ke a hankali yana jin wani bala'in bukatarta na taso mai,idonsa a lumshe yake ta sansana gashin kanta dayasha gyara yana bada k'amshi. Sun dad'e a haka,maganganun su Innaro da sukaji a falon yasa su sakin juna a d'an hanzarce,Innaro da bata San Khaleelee yana wannan d'akin ba don tasan bai shigowa yana can dayan d'akin, ta turo k'ofa da sallama,ganin Khaleelee tsaye Su'ada zaune kan stool a gabansa yasa da sauri ta juya. Shima da saurin ya d'auki Nusrat ya biyo bayanta,a d'an kunyace yace "Inna sannunku,ya gajiyar taro data aiki?. Cikin kulawa ta amsa mai da " Alhamdulillah. " Dayan d'akin da ya zama makwancinsa yanzu ya shige,bayan ya ajiye Babyn a gado ya cire kayan jikinsa tare da kwanciya ya d'ora ta a cikinsa yana d'an shafa bayanta don bacci take. A d'aki kam cikin hikima Innaro ke k'ara jawa Su'ada kunne kan kame jikinta daga Miji,a dabara take ta bata labarin rayuwar su ta da,yanda mace ke gujewa miji a duk sanda take jego har sai tai arba'in ko dama da haka ma.duk da bata bayyana zancen akan Su'adan ba amma ita tasan da ita take,sabida yanayin data riskesu d'azu duk wanda ya gansu yasan da magana. ********Washe garin suna y'an uwan Su'ada suka gyara nama suka soyeshi,bayan sun gama suka rarraba shi kamar yanda akeyi,kowa dake da hakki aka fidda mishi rabonsa. A ranar su Aunty Bilkisu duk suka tafi,gida ya koma daga Su'ada sai Innaro. ********Jego me tsafta Su'ada keyi da Babyn ta,ba zaka taba shigowa wajanta ka sami wani abu na k'i ba,kullum cikin ado take da k'amshi, haka ma Nusrat, Baby kam ta zama y'ar raino,data dawo makaranta take yada zango taita fama da goyo. Bayan Su'ada tai shawara da Khaleelee ta had'a kud'ad'an data samu na barka dubu 700 tacewa mai tana son siyawa Nusrat d'an kunne,bai k'i ta tata ba amma yace tasa dubu hamsin a account d'inta, dubu ashirin kuma tasai mata k'arami,a gaba in ta k'ara girma sai tasai mata babba. ba gaddama ta yarda da shawararsa,ta aikawa mama kud'in aka siyowa Nusrat d'an k'aramin d'an kunne. *******A yanzu kam Sakeena sai dai ace Masha Allah, don tunda akai haihuwar nan bata nuna wani halinta ba,ta nutsu tai komai kamar yanda ya kamata,duk da dai abubuwa da yawa a lokacin sun sosa ranta,yanda akai komai kamar sunan wata y'ar attajirai. Su'ada a ranta take fad'in Ashe duk mugun halin FACALA tana da rana,ita kam taga ranar FACALA a lokacin da haihuwa tazo mata,don Sakeena ta taimaka mata sosai,har addu'a Su'ada keyi Allah yasa Sakeena ta gyara halinta kenan, zasu zauna kamar yanda sauran facaloli je zama da junansu. *Taku ce* *Y'ar mutan Ja'oji*🙋 [2/24, 12:03 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _*page*_*41-42* A sannu kwanaki suke ja,yau ya rage kwana uku Su'ada tai arba'in,suna ta shirye shiryen zuwa gida suyi kwana biyu sannan su zagaya dangi,zuwa Yanzu kam Nusrat kamarta da mamanta k'ara fitowa take sosai,har rashin k'iba na Su'ada ne,sai tsayi fa Masha Allah ta d'auko Khaleelee don kana d'aukanta zaka tabbatar da doguwar yarinya ce ita,sab'anin Su'ada da bata da tsayi bata da k'iba. A iya tsakankanin Khaleelee ya bud'ewa Su'ada wuta ko yaushe fad'a mata yake hak'urinsa ya k'are amma ita kam ta kafe mai sai Innaro ta bar gidan zata iya kula dashi,don tasan yanda kullum Innaro ke fad'a Mata tayi taka tsantsan da shigewa namiji a Lokacin da take jego dukda ta sami tsarki amma taki yarda dashi. Ranar da sukai arba'in ta zaga dangin Khaleelee duk da suke kusa tai musu yawon arba'in, washe gari kuwa suka wuce gidansu Wanda a ranar Innaro tai sallama dasu gaba d'aya. Sun sami kwana biyu a gida suna zaga dangi, ranar da suka kwana biyun da dare yazo ya dauketa. Ta shirya mai tsaf don itama tai kewarsa,don haka batai sanya ba wajan sa hannu bibbiyu ta amshi mijinta. ************ Lokacin da Nusrat ta shiga wata biyu dai dai Su'ada ta koma bakin aikinta,a Lokacin kuma hidima tai mata yawa,amma haka take tsara komai cikin lokutanta.bata shiga hakkin mijinta dana yarta sabida aiki.wannan yasa kullum Khaleelee ke k'ara bata kwarin gwiwa kuma yake taimaka mata da dukka ayyukan gida. To tsakanin Sakeena da Su'ada ba yabo ba fallasa, zaman ya dawo irin na farko,don lokuta da dama Su'ada tana ganin Abu sai dai ta kauda kai,musamman kan yanda Baby Ke kulafacin d'aukan Nusrat, wani lokaci tana ji za taita mata fad'a kan yawon goyon da takewa Nusrat d'in wai k'irjinta zai bud'e, sosai ran Su'ada ke soyuwa amma sai ta danne,wani lokaci har sai tayi kamar zata hana yarinyar d'aukan ta amma sai ta fasa,don yanda baby ke nacin Nusrat d'in ba magana. Wata ranar Asabar da safe Sakeena na tsakar gida tana aiki, tacewa Baby ta kawo mata robar magi a falo,Baby ta amsa amma bata kawo ba har wajan mintina biyu,Sakeena ta k'ara magana,sannan ta fito tana gyara goyon Nusrat da ke bayanta, cikin fishi Sakeena ta kawo mata duka da fad'in "Kina goyon k'anwar uwarki dole nayi magana ki share ai, ta bud'e baki zatai magana ta k'ara kai mata bugu,tai baya da sauri hakan yasa kan Nusrat buguwa a bango,karar data tsanyara yasa Su'ada dake tsakar gidanta tana aiki sannan tana jin duk abunda su keyi ta fito da sauri,da azama ta k'arasa ga Baby wadda duk ta gigice tana ta jijjiga yarinya tace " Aunty Wallahi ban sani ba,mama ce za ta dakeni nai baya shine na bugeta." D'an mirmishi Su'ada tai bayan ta kwance ta a bayanta tace "Karki damu,ai nasan da ganganci ba zaki bigeta ba Baby." Wajanta ta shige zuciyarta na mata k'una,bayan ta rarrashi yarinyar tai shiru sannan ta sauke ajiyar zuciya tana shafa mata kai,a ranta take mamakin wai meye dalilin da yasa Sakeena tsangwamar Baby don tana d'awainiya da Nusrat,tabbas tasan sarai da Sakeena nada iko da tuni ta hana Baby jigilar d'aukan yarinyar. Amma ya zama dole ta d'au mataki,duk nacin Baby zata daina bata Nusrat tunda uwarta bata son hakan. " ****** Da Rana Khaleelee ya dawo cin abinci ya kula sam Su'ada bata da walwala, don haka ya ajiye cokalin da ya d'ebo abincin ya zuba mata ido,kanta da ke k'asa ta d'ago don taji alamun kallona ta yake,d'an mirmishi tai tana kauda kai gefe,bai d'auke idonsa a kanta ba haka bai ce mata uffan ba,gajiya tai don kanta tace "Wai wannan kallonfa?" Janye plat d'in abincin yai daga tsakiyarsu tare da rik'o hannunta ya d'an matsa cikin nashi. Sanyaya murya yai sosai ya fara magana"meye matsalarki? Na hango damuwa tare dake." Sosai tai k'ok'arin wadata fuskarta da fara'a kafin tace"Ba abunda kW damuna, kawai ban jin dad'in yanayin ne Yau. " Cikin kallon ban yarda dake ba ya k'ara fad'in "Damuwar dake kan fuskar ki tafi k'arfin ace rashin jin dad'in jiki ne ya saki haka,ki fad'a matsalar ki Su'ada, ko akwai wanda yafi cancanta da jin matsalar ki sama da mijinki?* Girgiza kai tai cikin sanyi tace " Kasan me? Wallahi Nusrat ce ta buge d'azu,kukan da tai da yawa shi yasa duk zuciyata tamin rashin dad'i. " Zaro ido yai da fad'in "Wane irin bigewa?garin yaya hakan ta faru?" D'an motsa hannunta dake cikin nasa tayi kafin tace "tsautsayi,a bayana take nazo shiga kitchen na bugeta,ta bugu sosai ,tai kuka da yawa,shi Yasa duk jikina ya mutu ." Tashi yai a hankali zuwa kujerar da yarinyar ke kwance tana bacci ya d'aukota tare da zama yana dudduba fuskarta zuwa jikinta.d'agowa yai yana kallon Su'ada da d'an mirmishi yace "Da sauk'i ai,ki kwantar da hankalinki kinji." Gyad'a kai nai nima ina d'an mirmishin. Daga haka bai k'ara bi takan abincin ba ya kwanta tare dasa yarinyar a k'irjinsa yana d'an shafa bayanta. ___________ To tun daga ranar sai Su'ada ta rage bawa Baby Nusrat, in ta shiga wajanta dai zata bata ita tai ta mata wasa amma bata bari ta fito da ita tsakar gidansu. Ganin haka yasa duk jikin Sakeena sanyi.duk da Su'ada bata wani canja mata a fuskaba amma tasan sarai abun na ranta,yo in maye yaci ya manta uwar d'a ai bazata manta ba. ********** Rayuwa na ja,abu da yawa na faruwa, a haka har Nusrat ta sami watanni bakwai, kuma alokacin ne wani cikin ya b'ullo a jikin Su'ada, na watanni biyu,Su'ada bata da zab'i sai zab'in mijinta,don taso tun da wuri ta fara tsarin iyali amma Sam Khaleelee ya zubawa idonsa toka yace bai san batun ba, bata ja cancan ba ta bari,to haka yanzuma da cikin ya bayyana taji fargaba sabida duka Nusrat watanninta bakwai,akwai d'awainiya sosai a kanta.ga aiki ga hidimar gida,amma tasan tunda Allah ya tsara mata hakan to bazai kasa basa hanyar da zata sami sauk'i ba. A b'angaran Sakeena ma tana nan tana ja,haihuwa yau ko gobe don tsohon ciki gareta. Su'ada bata da mugunta kk rowa,ita komai nata bai rufe mata ido ba a rayuwa, hakan yasa ake samun sauk'i cikin zamanta da Sakeena, tabbas da yanda d'abiun Sakeena suke haka nata suke to lalle da abun bazai kyau ba. Amma dake ita komai nata cikin nutsuwa da ilimi take sai wani d'abiun shirme na facaloli bata yi,don ita har ko yaushe d'aukan FACALA take matsayin Y'ar uwa. Wannan karon cikin bai bata wahla sosai,don haka bayan ita da mijinta bama Wanda ya san tana da shi. ************ Cikin ikon Allah Sakeena ta haihu lafiya,y'arta mace.ba kyashi ko hassada Su'ada ta harhada kayan Nusrat na jinjirantaka kaf, ta baiwa Sakeena, duk da tasan anan gaba kad'an duk abunda ta bayar d'in sai ta k'ara siya,amma hakan ba damuwarta bace,tunda tasan Allah ya hore Mata abunda zatai hidima dashi. Sosai Sakeena taji dad'in wannan tulin kaya da Su'ada ta bata don daman abubuwa da yawa bata dasu sabida ta kwana biyu bata haihunba,duk da taci burin yin hidima sosai a Wannan haihuwar sabida yanda taga Su'ada tai abubuwa tamkar biki abun ya birgeta,kuma ta K'ara jin kishi a ranta na itama sai tayi kwatankwacin haka.Lokacin da tajewa yaya Muktar da abubuwan da take so yai mata,ya kalleta cikin mamaki da fad'in"Sakeena shin kin manta yanda rayuwar nan ta canja ne,kina kallon wannan term d'in duka sati d'aya da komawa na kashewa yara kud'in makaranta da sabon uniform da littattafai,a gabanki na buga lissafi uban kud'in dana kashe,account d'ina gaskiya yanzu ba wani kud'in kirki a ciki,kud'in dana ware zan sai rago ne kawai dana abincin suna,don haka kiyi hakuri yanzu kam gaskiya bazan iya miki way'annan uban abubuwan ba sabida bani da Wallahi. " Tumzuro baki gaba tai cikin b'acin rai tace"Amma ai haihuwa ba mutuwa bace,tun ciki ba wata guda ake mai tanadi,mutuwa ce ke zuwa bagatatan,don haka gaskiya ba zai yuyu ace duk haihuwa sai dai inyi malejin komai ba,yanzu shekara biyar rabona da haihuwa, ya kamata ace an min komai na bajinta,fisabilillahi fa." Shi duk mamaki ma ya gama cikashi, bai tab'a zaton rashin lissafin na sakeena ya Kai har haka ba. "Wai Sakeena yanzu haihuwa ta nawa kikai don Allah?" Wani kallon rainin wayo tai mai kafin tace " kai za'a tambaya wannan ai,dalili kuwa kai kake yin cikin don haka zakafi gane lissafin yawon haihuwar. " "To Yanzu Sakeena in kina da lissafi ko a haihuwar fari ne kika ce nai miki Abu nace miki bani dashi kya yimi uziri,balle haihuwa ta biyar, meye ban yi miki ba lokacin da babu hidima sosai a kaina? Kafin kice nake miki, amma yanzu in kika ce nai miki abu nace bani dashi sai abun ya zama tashin hankali? Ki ci gaba in kina kallon wannan hanyar ce me b'ullewa a rayuwar ki.Amma bazan gaji da fad'a miki ba cewa na kusa gajiya da halinki.kuma kin sani randa duk hak'urina ya k'ure a kanki abun ba zai mana kyau ba." Jin ya hau sama ya sa tai tsit da bakinta sai kumbure kumbure take kamar fanken da ya sha yis. *********To iya dai abunda Allah ya horewa Yaya Muktar yayi iya yinsa na abincin suna,haka nan kayan barka yayi abunda zai iya. Khaleelee ma ya bashi gudunmawar dubu biyar sannan ya siyawa Babyn riguna masu kyau guda uku. Su'ada kam tai mata kunun aya da yawa sabida taji tana fad'awa wata k'anwarta tana son yin kunun aya da alale na suna kuma bata sa kud'i, to daman tana ta tunanin me zata mata na sunan don haka tai mata kunun ayan da alale da yawa. Y'an gidansu Su'ada sun zo suna harda maman su,da atamfa turmi d'aya da riguna biyu masu tsada maman ta bawa Sakeena. Sakeena a zahiri taji dad'in abunda Su'ada tai mata da wanda mamanta tai mata,amma kasan ranta take kishin inama itama tana da dama kalar ta Su'ada, ace komai zaka fidda kud'in ka kayi shi yanda kowa zai gane kayi bajinta, Amma ba wannan damar,k'arshe ma wadda kake kishin akanta wai ita zata taimaka maka,kaicon wannan rashin kud'i. *********** Lokacin da cikin Su'ada ya kai wata bakwai lokacin Nusrat ta cika shekara guda,don haka ta yayeta ta kaita gidansu kamar yanda mama ta buk'ata. ******* Tashin hankali Wanda ba'a sa masa rana,ranar wata Alhamis ne cikin dare Khaleelee yaji Jabeer na bugun k'ofar su cikin tashin hankali ,jiki na rawa Khaleelee yazo ya bud'e mai daga shi sai gajeran wando. kafin ya tambayeshi meye Jabeer ya fara fad'a mishi"Yaya Khaleelee wuta ta kama a shago,yanzu su hamza ke kirana a waya wai wuta nata ci cikin shagonmu. Kan Khaleelee rik'ewa yayi,hankalinsa yai bala'in tashi, da gudu ya koma d'aki yana neman riga yasa,Su'ada data biyo bayansa jikinta na rawa take fad'in "me ya faru ne Abban Nusrat? Don Allah fad'a min abunda ya faru." Tana saka jallabiyarsa yake fad'in "Su'ada wuta ce ta kama a shagonmu." Daga haka ya fito da sauri, a waje yaya Muktar har ya rigashi fita shi da Jabeer. Lokacin da suka je shagon waje ta turnuk'e fa wuta ce ke ci bilhakki,don kusan shaguna hud'u ne su ke ci a wajan. Jama'a duk sun fito duba shagunansu. Lokacin da y'an fire services suka zo wutar taci abunda taci don tai b'arna matuk'a,sabida shagon dake kusa da su na saida katifu ne,na hannun hagun kuma na saida yadika ne. Sai wajan sallar asuba akayi nasarar kashe wutar,a lokacin ne kowa ya fara duba shagon sa, babu wani abun mora komai ya k'one murus sai k'arafuna, 'Innalillahi wa'inna ilaihi ra'jiun' Shine kalmar da Khaleelee keta maimaitawa lokacin da yaci karo da sif d'in da yake zuba kayan da bai d'inka ba,ta k'one k'urmus ita da abunda ke cikinta. *Taku ce* *Y'ar mutan Ja'oji*🙋 [2/24, 12:04 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _*page*_*43-44* To kamar yanda kowa ya sani wuta na da cin rai,amma kuma k'addara ce da jarrabawa,in ka mik'a lamuranka ga Allah sai ja sami nutsuwa kuma ya maida maka mafi alkairi. Khaleelee yayi ta maimaita kiran 'Innalillahi wa'inna ilaihi ra'jiun' hakan yasa yake samun nutsuwa. Yau kwana biyu da yin gabarar,duka kostomomin sa da yasan da kayansu gurinshi ya sanar dasu halin da ake ciki.kuma fad'a musu duk wanda yake ganin a biya shi kayansa to yayi mishi magana,wanda ya yafe kuma ya gode. To dake lokacin kusan azimi ne akwai bala'in kaya a shagon nasu jama'a nata kawo d'inki,kuma mafi yawon kayan shagon masu tsada ne kasancewar yana hurd'a ne da masu hannu da shuni. To ba'a raba su da sabbin customers ko yaushe, don haka duk wa'yanda basu wani saba ba suka nuna kin amincewarsu,wasu suce a raba asara ya biyasu rabi wasu suce a biyasu duka. List yayi na wa'yanda suka nemi hakkinsu,da kud'in kayan nasu. Tofa! Abun da yawa,lissafin da yayi kusan kayan dubu d'ari uku ake nema ya biya,dukda masu Neman basu fi mutum goma ba amma adadin kayan nasu yakai wannan kud'in. Da farko Jabeer ca yai babu wanda zasu biya komai,don suma asarar da sukai bata misaltuwa,kekunansu babu Wanda zai moru,daga na d'inki har zuwa na surfani.k'arshe ma sa suka had'a karafunan y'an gwangwan ne suka siya. Damuwar da Khaleelee ke ciki ta bayyana jikinsa, dukda k'ok'arin sa na boyeta. Sosai Su'ada take kwantar mai da hankali,tana nuna mishi jarrabawa ce, yayi hak'uri, Allah zai maida mishi mafi alkairi. Da kalamanta yake samun nutsuwa,haka Baba duk da yana cikin rashin lafiya amma zai kirashi d'aki yayi tamai nasiha da kalamai masu dad'i. ******* Khaleelee ya had'a kud'in da suke cikin account d'insa duka budu d'ari da hamsin ne,kuma dubu saba'in ta mutanan da sukai mai transfer kud'in d'inkinsu ne,to tunda d'inki bai samu ba sun yafe mai kaya ai dole ya maida musu kud'in su. Bayan ya maidawa kowa ya rage dubu tamanin,tanan ya fara ragewa sabbin kostoman nasa. Ranar litinin da Su'ada taje aiki, ta tsaya banki ta fito da kud'in cikin account d'inta duka,daman ita ba amfani take da kud'in albashinta ba,ko ya shigo barshi take ciki,in kaga ta cire kud'i to biki ko suna ne zatai gudunmawa ko anko,sai kuma alheri da takewa mutane. A ranar ta bashi kud'in yaje ya bibbiya sauran kud'in su, duk da sunsha fama kafin ya k'arb'a, ca yai ba zai amsar mata kudinta ba,sai dai in rance ta bashi,sai da yaga da gaske tana mai kuka sannan ya amsa. Bayan ya biya su duk kud'insu,sauran ya dawo Mata dasu,ta ajiye.sabida so take ta bashi ya sai keke ko guda biyu ne. ********** Yau wata guda da yin gobarar su Khaleelee gashi har an shiga azumi. Sun yi tsammanin hukumar dake kula da shagunan kasancewar shagunan gwamnati ne zata gyara musu shagunan da wuri amma har azumin ya kama ba'a gyara ba. Kud'in da Su'ada ta bashi ya sai keke,guda daya siya ya ajiye a gida, wa'yanda suka sami labarin yana d'inki a gida ne suka d'an kawo mai ba wani me yawa ba. To Alhamdulillah Abban Su'ada yayi rawar gani wajan basu gudunmawa a azumin nan tunda yasan halin da Khaleelee ke ciki,don haka kayan abincin da zasu buk'ata har na tsawon watanni ma ya had'a musu,dai dai da gishi sai da aka had'awa Su'ada cikin kayan abincin,tamkar da gara haka aka had'a musu. Ba magana fa wajan nuna jin dad'in da Khaleelee yayi,yaje gida yayiwa Abba godiya sosai. Abba yace ba komai ai dole ne ya kula dasu. Har kayan salla ma sai sa Abba tayiwa Su'ada kala uku, duk da yasan Su'ada ba rasa kaya tai ba,amma shi kayan salla in ka saba duk sanda rashi yasa ba kayi ba sai kaji ba dad'i, don haka ta had'a da y'an uwanta yayi mata. Ita kuwa Nusrat daman tana can gidan tun yaye basu dawo da ita ba.don shi Abba ma so yake wai su bar musu ita,don yanda take kama da yaran gidan ya b'aci, hakan yasa Abban ke bala'in ji da yarinyar. Alherin da Su'ada ta saba bata canja ba,satin salla taje kasuwa taiwa su Baby da y'ay'an Zakiyya siyayyar d'an kunne da sarka da dai y'an tarkacen yara mata. ******* Ba wani d'inkin kirki Khaleelee ya samu ba amma dai yafi babu,da kud'in su kai girkin salla da y'an sauran hidima,babu yanda za'ai dai mutum yace yaga wani rashi a tare dasu,duk kuwa da babu wani kud'i a hannun Khaleeleen. ******* Sannu sannu cikin Su'ada ya shiga wata tara, kamar yanda edd d'inta ya nuna tsakiyar wayan zata haihu,wannan karon Khaleelee bai mata wata siyayya ba,sabida har zuwa lokacin bai zauna daram a shago ba,duk da an gama musu gyara komai da komai,harma sun koma,to duka keke biyu ne a shagon Wanda Su'ada ta bashi kud'i ya siya sai kuma d'aya da Abbanta ya aiko masa dal a cikin kwalinsa.to ana dai samun abunda ake samu,dashi suke d'an cefane. Don haka kudinta na watanni biyu na albashi da ta amsa bayan gobar nan shi ta had'a ta bada dubu sittin aka siyo mata rago da tunkiya a k'auyensu dake,Wanda tace a barshi sai ta haihu a kawo. Sauran kud'in hannunta taje kasuwa tai siyayyar Haihuwa,sabida bata da komai duk ta baiwa Sakeena. Don haka yanzu haihuwa kawai take jira da fatan sauka lafiya. ********* Da ikon Allah kuwa tsakiyar wata ta haihu,d'anta namiji, cikin koshin lafiya. Bayan sun dawo gida daga asibiti mama ta buk'aci Khaleelee daya taimaka ya bar Su'ada ta dawo tai wanka ko na sati uku ne a gida, sabida wannan karon babu me zama da ita Innaro bata da lafiya, sannan k'annanta duk suna makaranta ba cikin hutu ake ba Babu yanda Khaleelee zai iya don haka ya amince,mama tazo da motarta ta d'auke su. Sakeena dai tunda akai gobarar nan taji a jikinta, don ta tausayaa Khaleelee matuk'a, to amma a wani sashi na ranta take fad'in 'yanzu dai ba wani rawar kai tunda ba'a da komai,amma bayan d'an lokaci tana ta sa ido taga ta inda Su'ada zata gaza amma babu,komai yanda take a wadace haka take abunta. Washe garin da akai haihuwar Khaleelee yaje gidan su Su'ada, bayan sun gaisa da Mama ya shiga d'akin da Su'ada take,tana zaune tana cin abinci ya shigo,da mirmishi ta tareshi,amma sai ta hango damuwa kan fuskarta, tsam tai da ranta har ya k'araso kusa da ita ya zauna yana d'aukar jinjirin. Ji tai abincin ya fita a kanta,don haka ta tureshi gefe tare da maido duka hankakinta ga Khaleeleen. A sanyaye ta gaisheshi ya amsa yana kirkiro mirmishin da bai kai zuci ba. Kafeshi tai da ido cikin kallon tuhuma,abunda yasashi sakkowa kusa da ita ya zauna tare da damk'e hannunta cikin nasa,kallon juna suke na d'an lokaci kafin ta d'ora kanta a kafad'arsa.cikin k'aramar murya take mai magana. . . . [2/24, 12:04 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _*page*_*45-46* Bayan tafiyar Khaleelee Su'ada taje d'akin mama ta sameta tanaiwa Nusrat shirin bacci. Zama tai gefen gadon tana duban mama. Bayan ta k'arasa sa mata riga ta kwantar da ita gefe sannan ta dawo da hankalinta ga Su'adan "ya akayi ne Su'ada?" Gyara zama tai tana kallon maman cikin serious voice ta fara magana"Mama daman wata magana mukai da Abban Nusrat yanzu da yazo,kan batun taron suna ne,hidima ta mai yawa,kuma kinsan har yanzu ba wai gama had'a shagon su kai ba,to shine nace mai kawai ba sai anyi taron suna ba." Cikin girma da nutsuwa mama tace "Na sani Su'ada, na san halin da mijinki yake ciki don haka nace ki dawo gida,ai bazan rasa me zauna miki ba,kawai dai ban son a k'ara mishi nauyi kan wanda yake kansa yanzu,don haka ki kwantar da hankalinki kinji,komai na taron suna za'a yi,kuma zan fad'a mishi karya kashe naira biyar d'insa,yaji ma da gyaran wajan Neman kud'insa, ni da mahaifinki muna dashi Su'ada to in bamu taimaka muku ba meye amfanin samun namu,kuma kema kullum ina k'ara Jan hankalinki,duk abunda zaki samu ki d'auka keda abun karkashin igiyar aure kuke,don haka karki zauna tara kud'i cikin account mijinki yana cikin matsalar kud'i, ki fiddasu ki bashi ya rink'a hidima dasu,basu da wani amfani bayan wannan." Gyad'a kai Su'ada tai da fad'in "Mama ba kud'i cikin account d'ina duk na fitar dasu na bashi,dasu ne kuma aka bada kud'in ragunan a darki, sannan mukai siyayyar haihuwa,sauran abunda ke hannuna yanzu dubu goma ne,sune daman zan baki ki Siyo ma yaron rigunan fitar suna." Cikin jin dad'i mama tace "Masha Allah, haka nake sonki dashi Su'ada, ki zama me tausayin mijinki ako wane lokaci, shima zai zama me tausayinki komai runtsi. ****Bayan fitar Su'ada a d'akin, mama ta tashi zuwa d'akin Abba,anan ta zayyane mai duk yanda sukai da Su'ada, jinjina kai yayi,yana fad'in "To yanzu yanda za'ayi kiyi list na duk abunda kike ganin zaku buk'ata sai ki lissafa kud'in ki fad'a min in baku,kuma insha Allah in na koma zan k'ara turo da kud'i ki bawa Ibrahim d'in ya k'arasa gyaran shagon. Godiya sosai Mama tai mai,shi yasa a duniya take jin tsananin son mijinta,don Abban su Su'ada yana iya juyewa iyalansa duk abunda ke aljihunsa ya tashi ba ko sisi a jikinsa,shi yasa kuwa Allah yake k'ara bud'a mishi harkar samunsa.ko Wannan dawowar da yayi sai da ya k'ara gyara musu gidan,har sabon fenti akai. Sai da safe Mama take fad'awa Su'ada yanda sukai da Abba,inda sabo Su'ada ta saba da hidima da kyautatawar mahaifinsu garesu,amma wannan karon tana jin nauyi da wata irin ninki k'aunar mahaifan nata a zuciyarta. Zuwa tai d'aki ta sami Abban yana zaune Nusrat na kan cinyarsa,tanata gwalangwalan d'inta,bayan ta zauna ta gaida Abban,ya amsa cikin kulawa yana tambayarta ya Jinjirin,cikin yanayin da ta saba yiwa Abban nasu magana cikin shagwab'a tace" Abba wannan yaron kuka gareshi, sam bai barinmu barcin dare, Nusrat ta fishi hakuri, ni duk ji ma nake kamar na dakeshi." "To ai da kin dake shin zai yi shiru da wuri,kinga muma kunnuwanmu sai su huta sa kukan nashi." Mama dake shigowa d'akin d'auke da jinjirin ta fad'a. Dariya Su'ada da Abba su kai a tare,sannan Su'ada ta tsaida hankakinta waje guda tana yiwa Abban godiya. Shi dariya ma abun ya bashi,yace "Su'ada don na muku hidima shikenan kike ta wannan godiyar? Shin kina da wani me yi miki bayan mu iyayenki da kuma mijinki? hakkinki duka yana kanmu da mijinki,kuma Ibrahim yaron kirki ne,kullum k'ara yaba hankalinsa nake,bayan wannan jarabtar data sameshi na san zuwa yanzu da tuni ya gama komai daya rataya a wuyansa,kamar yanda Mamanku ta sanar dani irin namijin k'ok'arin da yayi a wancan karon,to a wannan karon ma tunda munsan babu ne mu iyaye sai mu tallafa ai." Tsawon lokaci Abba ya d'auka da Su'ada yana mata nasiha da k'ara sanar da ita girman mijinta gareta, har kwalla sai da tai.tana k'ara yiwa iyayenta addu'ar fatan dacewa duniya da lahira. ********* Yau ma da dare Khaleelee yazo gidan,a waje suka had'u da Abba, bayan sun gaisa cikin girmamawa,Khaleelee ya k'ara k'asa da kansa sannan yace "Abba daman ina son maka maganar sa suna,nai mai hud'uba da sunanka." Sosai fara'ar Abba ta k'aru,yace "To madalla Allah ya raya mana shi cikin aminci yayi musu albarka." Cikin jin kunya Yake amsawa sannan ta tashi ya k'asara ciki. Abba yaji dad'in takwarancin da Khaleelee yai mai,don haka yana shiga d'aki yake sanar da Mama zancen,itama taji dad'i sosai. ****Lokacin da ya shiga d'akin duk su Jidda na ciki,bayan sun gaisa su ka fita su ka basu waje,a kujerar gefen gadon ya zauna yana fad'in "Washhh yau d'inkin ki ya gajiyar dani fa matar tela." Y'ar dariya tai tana gaidashi tare da tambayarsa gida dasu Baba,yace "To Baba yana can yana fama da jiki sai godiyar Allah." Cikin tausayawa tace "Allah sarki Baba,don Allah kai mishi sannu in ka koma." Jinjina Kai yai yana fad'in "mik'o min Abban.ko yau rowarsa ake min." Kallonsa tai cikin rashin fahimta tace "Abba kuma? Ya za'ai ma rowar abunka." Bayan ta mik'a mai shi tace "Naji kace Abba." Gyad'a kai yai yana mirmishi yace "Sunan Abba nasa mai,da fatan yayi miki." Da fara'a sosai tace "Wayyo, amma naji dad'i fa,Allah ya raya mana shi cikin aminci." "Amin ya Allah, kin san Yanzu naga Nusrat hannun Khaleelee wai nace tazo ta mak'ale kafad'a,ina ganin fa ta manta ni." "Ah haba ya za'ai ta mantaka, kawai yanzu ta saba dasu ne,ko nifa bata yarda dani." Cikin tsokana yace "To ko mu barmusu ita ne?" Itama cikin tsokanar tace "In zaka iya ba." "Kiji wai in zan iya,meye don na barwa Mama ita." D'age gira tai tana y'ar dariya tace "Kasan Abba ma jiya sai da yace wai wannan y'ar ai tasu ce,mu ga namu mun Haifa." Dariya yai sosai yace " Damu da su duk muna karkashin Su Abba muke." D'an gyara zama tai kafin ta fara bashi Labarin Abunda Abba yace kan suna da duk abunda suke buk'ata ." Sadda kai yai kafin ya d'ago yace "Su'ada ni kam a wannan rayuwar akwai namijin da ya kaini Sa'ar surukai? Ina tabbatar miki ni d'in na daban ne a Wannan rayuwar,ana dad'ewa ba'a sami surukai irin nawa ba.bazan gajiya dayi musu addu'a ba,Allah ya bani ikon k'ara rik'e musu ke da amana." "Ameen Ameen" Su'ada ke amsawa a lokacin da yake ta yiwa su Abba da mama addu'a. Tashi yai zuwa gun Abba yayi godiya sosai. *****Sakeena dai tun Randa Khaleelee yaje sukai magana da Su'ada kan cewa ba taron suna daya dawo gida yake fad'a mata ba suna,to tana kan hakan cewa ba suna,amma kwana hud'u da haihuwa da haihuwa Su'ada ta kitara a waya tace don Allah ta fad'awa mak'otansu zancen suna, bata ce mata Khaleelee yace ba suna ba ta bita da to.bayan ta kashe wayar ta jijjiga kai da fad'in "Wato mijinki yace ba suna,shine ke don son iyawa zaki ce in fad'awa mak'ota ko,to wannan karon zaki sha kunya, don zan miki gayyar da zaki rasa abun basu,tunda ke kin iya k'i fad'i." Tun a lokacin ta tashi yara ta rink'a aikasu gida gida wai suce Su'ada tace a fad'a musu zancen suna a can gidan iyayenta medile,har bayan layinsu da kewaye ta ai aika. Ai kuwa mutane da son abun duniya sunga wancan karon yanda akai wadak'a da abinci da nama,ga take away in mutum zai tafi, wannan yasa kowa d'ora aniyar zuwa suna medile,ca suke don dai kud'in mota naita d'ari ta kaika ta dawo da Kai. Hhhhhhhhh kaji son banza fa. *********Mama ta shiga kasuwa ta siyowa Su'ada tsadaddan less da dank'ararriyar shadda, ga takalma da mayafai,sannan yaro ma aka siyo mai kayansa rankacakaf. Abunka da matar tela, tuni ya kawo mata wancan kala biyar din data bashi sannan ya k'arb'i less da shaddar suma yace zuwa fan suna da safe zai gama. ******** Ranar suna yaro ya amsa sunan Muhammad Mustapha,za'a rink'a kiransa da Fudail. Hidimar suna sosai ake a gidan,dangin Khaleelee da suka zo Waje daban aka saukesu tare da kayan abunci ci iya cinka, ga lemukan jarka kala kala. Da azahar kam sai ga gayyar y'an unguwar su Su'ada inda kasan an kunna famfo haka suka rink'a shigowa.sosai Su'ada tai mamakin yawonsu,amma taji dad'i sosai,suma tarya akai musu ta girma. Aka wadatasu da abinci kala kala da lemuka,ai kuwa nan suka shiga zance da watsa shinkafa,wata cikinsu da bakinta bai iya shiru tace "Kai masha Allah, Ashe dai da gaske da ake fad'a yarinyar man y'ar masu dashi ce, ji gida don Allah, dasss ko ina fees. gashi dad'i na da hidimarau abunci ba k'auro,kinga wannan haihuwar ma da take ta biyu komai rabajau." Wani kululu ne ya tasowa Sakeena, a duniya in kana son ganin bak'in cikinta to ka rink'a fad'ar arzikin su Su'ada a gaban ta.tabbas da tasan wannan hidimar aka shirya da bata gayyaci kowa ba,ita da tai gayya don aji kunya amma sai akasin hakan. Dangin Khaleelee sun San wannan hidimar bashi yayi ba,tunda sun san yanzu halin da yake ciki,don haka su kaita sawa iyayen Su'ada albarka. Khaleelee ma lokacin da yake shago yaga almajirun au Su'ada da kayan abinci nik'i nik'i, yayi mirmishi yayi cikin ransa yana fad'in "Allah ka sakawa iyayen matata da gidan aljanna, itama kai mata sakayya da alkairi ya bani ikon kula da ita. Bayan sun yi walimarsu a shago, da la'asar ya d'and'asa wankansa cikin sabuwar shadda ya nufi gidan suna don Su'ada nata kiransa da wai yazo me hoto yazo,shi da Jabeer suka je,suma aka k'arasa hidimar Sunan dasu. ***Tunda Sakeena ta dawo gida take bak'in cikin hidimar da akai a gidansu Su'ada da yanda taga an k'ara gyara musu gidan,wani kishin data kwana biyu ba tai akan Su'ada yau taje ji,haka ta kwana rai ba dad'i. (Ya Allah! Wai don Allah me had'a facala kishi da facalarta,ke baku had'a miji ba baku,had'a tukunya ba,Baku had'a komai ba Sai y'an uwar takar mazaje amma Ku zauna kishin juna." *Taku ce* *Y'ar mutan Ja'oji*🙋 [2/24, 9:17 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _*page*_ *47-48* Kula sosai Mama take bawa Su'ada a zaman jegonta,sati guda da suna Abbansu ya tafi legos, kwana uku da tafiyarsa ya turowa Khaleelee dubu d'ari wai ya k'arasa shirya shagonsa.lokacin da wannan sak'on yazo ga Khaleelee ji yai ya rasa ma da wane baki zai yi godiya, sabida alkairan Su'ada da iyayenta gareshi sun yi yawa,shi ya kamata yayi dawainiya da iyayen matarsa,amma gashi sune suka bashi ya kuma suke dawainiya dashi, lalle samun surukai irin wannan sai an tona. Kiran Abban yayi a waya yana mai godiya, Abba kam ya kamashi da fad'a kan cewa shi uba ne a gareshi, duk abunda yai masa bai buk'atar godiyarsa,don haka ya daina godiya a tsakaninsu. Da Khaleelee ya fad'awa Baba shima godiyar yai tayi,yanawa iyayen Su'ada addu'ar alkairi. Da sallar isha ma da suka had'u da yaya Muktar a masallaci yakw fad'a mishi bayan keke ga dubu D'ari Abban Su'ada ya k'ara mai,godiya shima yayi,har suka shigo gida suna maganar, Sakeena dake tsakar gida tana d'aura alwala tana jin me suke tattaunawa,jin abunda Abban Su'ada ya yiwa Khaleelee ya sa jikinta mutuwa murus,,ta san ita kam in mijinta ne ya samu wannan jarabtar Babanta bashi da ko dubu goman da zai iya tallafa mai,tunda gobarar nan ta afku ko yaushe cikin hidima yake da su, ga keken daya siya mishi industrer iyayen dubunnai ya fidda ya siya,ga hidimar suna da yai musu, sannan ga wannan kud'i ya bashi,eh Lalle Khaleelee auran jari kawai yayi. Abunda tai ta maimaitawa a zuciyarta kenan jin wani d'acin Bak'in ciki na tasowa daga mak'ogaranta zuwa harshenta. ________Cikin ikon Allah Khaleelee ya shirya shagon sa kamar da,sai dai har zuwa yanzu kekuna basu k'aru ba,daga Wanda Su'ada ta bashi ya siya,sai Wanda Abbanta ya siya mai,sai kuma wata uwar d'akin sa ta bashi bashin keken surfani guda d'aya duk wata zai rink'a biya. Ai kuwa sai ga shago yayi ras. ************ Lokacin da Su'ada tai ar'bain ta rok'i Khaleelee ya barta taje garin Abban su wato Darki,da farko yaso yak'i yarda Amma tai tai mishi magiya, ba dan yaso ba ya barta. Tare suka tafi da dukkan k'annanta,kwana biyu su kai suka dawo. Washe garin dawowarta Ta koma gidan mijinta. ___________ Haka rayuwa taci gaba da garawa yau da dad'i gobe babu,fannin miji kam sai godiyar Allah,don Su'ada kullum cikin godewa Allah take,bata da wata damuwa tsakaninta da mijinta,ko yaushe cikin kyautatawa juna suke. Fannin FACALA kuwa me hali bai fasa halinsa sai dai a samu sassauci wata rana,to haka Su'ada ke k'ara hak'uri kullum ga Sakeena,don bata fasa halinta na kishi da hassada. *BAYAN Y'AN WATANNI* ********* Wata ranar jumma'a Khairiyya tazo gidan Su'ada ta taho da Nusrat don har yanzu ba'a dawo da ita ba. Kwalliyar kawai da akaiwa yarinyar abun kallo ce,ga tsananin kyawu da kullum take k'arawa, harma wasu na cewa duk kamarta da mamanta tafi maman nata kyau. Masha Allah, dake kuma ta d'auko tsayin mahaifinta sai ake ganin saurin girmanta,duka lokacin shekarunta biyu,amma zaka ce tayi uku ko ma tafi haka,sanyin halinta sak na mahaifinta,duk da Su'ada ma akwai hak'uri to gado biyu tayi, zaka dad'e baka ji hayaniyar yarinyar ba,balle kaji kukanta,sam bata da rikici irin na yara da rigima,sosai zaka tabbatar da hak'urinta. An mata kwalliya cikin riga da wando y'an kanti,wandon Jean's bak'i,sai wata riga me jikin santsi kalar ruwan madara me haske sosai,duka gaban rigar an sa stones me d'aukan ido,k'afar ta sanye da wani bak'in d'an ubansu takalmi sau ciki,kallo d'aya za kaiwa takalmin kasan da iyayen kud'i aka siye shi,kanta kuwa wani k'ananun kitso ne da aka sawa bit tako ina, ga wasu k'ananun ribbons an jera, dake Allah ya mata baiwar gashi me cika da tsayi tamkar mamanta,kai da kaga yarinyar kaga jinin fulanin asali.kuma dake akwai kula sosai da gata tare da ita sai kaganta tamkar d'iyar turawa. A tsakar gida Kairiyya ta iske Sakeena na girki, bayan ta dire Nusrat da ga hannun ta zuwa k'asa ta gaida Sakeena cikin girmamawa, itama cikin fara'a ta amsa amma duk hankalinta na ga Nusrat,kallon yarinyar take tamkar bata santa ba,cikin d'an yak'e tace "A'a Nusrat y'an mata,yau an kawo mana ziyara kenan, zo in ga kwalliyar taki." Tsayawa yarinyar tai tana mata kallon rashin sani,amma dake bata da k'iwa sai ta k'arasa gareta,Sakeena ba tai la'akari da bak'in gawayi da maikon dake hannunta ba ta Kai mata cacima tana d'orata a cinya,d'an wasa tai mata sannan ta sauketa ganin kairiyya ta ja ta tsaya tana jiran ta direta su k'arasa. Su'ada da ta jiyo muryar khairiyya tun shigowarta amma taji shiru bata shigo ba,a ranta take fad'in'To Khairiyya da bata shiri da Maman Abba me ya tsaida ta a gunta' Bata gama zancen zucin ba taji sallamarta ta shigo,da fara'a ta tare ta amma sai ta ga khairiyan ta turo baki gaba,alamar ranta a b'ace yake,dubanta tai tana fad'in "A'a ke kuma ke da wa naga kina kunkuni." Wulla jakarta tai kan kujera gami da zama tana yatsina fuska tace "Kai Aunty Su'ada Wallahi matar nan ba ta da nutsuwa,fisabililla kallin abunda tai min." Ta k'arasa maganar tana nunawa mata gefe gefen rigar Nusrat.cikin rashin fahimta Su'ada tace "Meya faru ne ban gane ba,ke da waye?" K'ara yatsina fuska tai cikin b'acin rai tace "Wannan Maman Abban mana,dubi yanda ta d'aukar min yarinya hannunta duk bak'i da maik'o, sabida k'azanta,in tasan hannunta bai da kyau ai sai ta hak'ura da d'aukan ta ba dole a Kai mata ba." Dariya Su'ada tai tana rik'e baki tace"Kai!lalle ma,to don ta miki kara ta d'auke ta sai ya zama abun haushi. " "To ni nace ta d'auke ta ne,jifa yanda ta b'ata mata riga,mutttttssss." Ta k'arasa maganar d'auke da tsakin takaici. Ita dai Su'ada dariya abun ya bata sosai,ko dake daman tasan Khairiyya sam ba hak'uri gareta ba,amma anan kam bata ga abun mita ba,kuma tasan sarai da Sakeena bata d'auki yarinyar ba hakan ma sai tai k'orafi tace ko kula Y'ar ba tai ba. Kukan muklees da Su'ada ta jiyo a d'aki yasa ta shige da sauri,tana fad'in "Yauwa Babana sarkin kuka an farka da kukan kenan." Khairiyya dai cirewa Nusrat kayan tai gaba d'aya, ta barta daga ita sai base da d'an pant,dake daman zafi ake sosai a lokacin. Bayan Su'ada ta d'auko muklees ta zauna kusa da Khairiyyan tana fad'in "Uwar masifa ko gaisawa ba muyi ba fa." Y'ar dariya Khairiyyan tai kafin ta gaida ta,tana tsokanar Muklees "Su Abbanmu sarkin kuka sarkin tsotso." Harararta Su'ada tai da fad'in"Abban ake cewa sarkin kuka ko?" Cikin dariya Khairiyya tace "To ai ba k'arya nai ba,jifa daga farkawa daga bacci ya cika gari da kuka,yasin yaron nan badan sunan Abbanmu gareshi ba bazan had'a jam'iyya dashi ba." "To karki had'a mana,ni ina had'e da Abuna,kin fi son ki ganshi salo salo kamar y'arku,ah Allah ya kiyaye, Abbana namijin duniya ne me k'arfin sojoji." Khairiyya na dariya ta d'ora Nusrat akan cinyarta tana fad'in "Ai Wallahi yarinyata bata da makusa, d'abiun ta kalar na mata,jan aji da nutsuwa ne yasa bata hayaniya tun tana jinjira, komai nata cikin class take,amma wannan Abban ai kalar garada ne." Ta kai k'arshen zancen da dariya sosai. Yatsina Fuska Su'ada tai tana kallon kayan da aka cirewa Nusrat d'in tace "Wai don wulak'ancinku kawai don ta d'an goga mata maik'o shine kuka cire kayan? Yasin baki da kara fa." D'age gira Khairiyya tai da watsa hannu alamar ko a jikinta tace "To akan me zan barta da kaya me datti a jiki? Ah haba wai baki da labarin y'ata me tsada ce ne?" Mik'ewa Su'ada tai tana dire muklees a kan cafet,ta wuce kitchen, don bata dad'e da dawowa daga makaranta ba,don ma yara exam's suke da wuri suke tashi Girkin data d'ora taje ta duba,sannan ta dawo suka d'ora hira. Sallamar Baby ce tasa su tsayawa da hirar suna amsa mata,da fara'arta ta k'araso tana fad'in "Yanzun nan ina shigowa Islam tace min Nusrat tazo." Tsugunnawa tai tana kamo hannun yarinyar,tana gaida Khairiyya, sannan ta dauketa zasu fita Muklees yasa kuka yana mik'awa Babyn hannu. Tafa hannu Su'ada tai da fad'in "Eh lalle Baby,sabida kinga Nusrat shine zaki wulak'anta min uba,to ai zata tafi ta barmu da ke ne." Dariya Babyn tai tana jutowa ta d'auki muklees d'in a d'aya hannunta. bayan Sun fita Khairiyya tace "Allah sarki Baby,Wallahi sam ba tai halin Uwarta ba,yarinyar na birgeni." Gyad'a kai Su'ada tai tace "Ita kam halin Babanta tai,ba ruwanta,rayuwar ta komai da sauk'i take yinsa." Daga wannan hirar suka koma hirar bikin Jiddah, Wanda ya rage wata biyu. ****** Baby dai na can d'akinsu tana ta fama da su Muklees, musamman Nusrat da take ta hannun damanta,sai ina naka sa ina naka aje take da yarinyar. *********K'arfe daya da rabi Khaleelee ya dawo gida don yin shirin sallar jummaa,dake su masallacin murtala suke bi,kuma sai k'arfe biyu ake salla a masallacin. A tsakar gida ya tarda Baby ta na goye da Muklees, tana bawa Nusrat abinci a baki,cikin mirmishi yake amsa sannu da zuwan da yaran ke masa. Rik'o hannun Nusrat d'in ya yi yana fad'in "Mamana yau an waiwayomu kenan, ke da wa kuka zo?" Cikin gwarancinta tace "Aunty Khairiyya ne." Gyad'a kai ya yi yana mik'awa Islam hannu su ka tafa,yace "Maman mama me aka ci ne baki ke maik'o " Girgiza kai tai cikin dariya tace "Abinci muka ci fa me dad'i." Yana y'ar dariya ya wuce ciki. A falo ya same su suna cin abunci,Khairiyya ta gaisheshi ya amsa yana tsokanarta don Bayan Khaleelee cikin y'an gidan yafi wasa da Khairiyya. Kad'an ya d'an zauna yana tambayarta gida dasu mama, sannan ya wuce d'aki. Bin bayansa Su'ada tai zuwa d'akin, yana k'ok'arin rage kayan jikinsa yace "Madam a had'a min ruwa,ji nake kamar ban tab'a wanka ba,gaskiya yau ana zafi sosai." Taimaka mishi tai ya cire kayan jikinsa zuwa jallabiya.sannu ta fito ta had'a mishi ruwan wanka. Sai wajan k'arfe uku Khaleelee ya dawo gidan daga masallaci. Khairiyya na d'aya d'aki tana bacci, yayin da Su'ada ke falo tana marking exam's d'in d'alibai, Muklees ma baccin yake sai Nusrat a gefenta tana mata hirarsu ta yara. Zama ya yi kan kujera yana amsa sannu da zuwan Su'ada, idonsa naga Nusrat,sosai yake kallon yarinyar yana ganin kullum k'ara girma take,dukda yana wata guda ko giye bai ganta ba,amma duk sanda zai ganta sai yaga tai tsayi. Yana wannan tunanin har Su'ada ta kawo mishi abinci.bayan ya sauko k'asa inda zai ci abincin yace "Mamana zo mu ci abincin ." Girgiza Kai tai alamun ta k'oshi, mirmishi kan fuskarsa yace " Su'ada yarinyar nan ta kusa kamoki a tsayi fa." Dariya Su'ada tai kafin tace "Tunda tai gadon tsayi ai in ma ta fini tsayin ba damuwa bace." D'agata yai cas ya d'ora ta kan cinyarsa,wani k'aunar yarinyar yake ji na ratsa b'argo da jijiyarsa,tabbas kara da kawaici ne kawai ba za su barshi yace a dawo mai da y'arsa gida ba.ya San yanda ake kula da ita a can ko gidan ma sai haka,to amma fa shima ya na buk'atarta kusa da shi. Wasa take tayi da gaban rigarsa ,yayin da idanuwansa ke tsaye a kanta,mirmishi yak'i barin fuskarsa,ko yaushe in yana tare da yarinyar sai ya riski kansa cikin farin ciki. Su'ada idanuwanta a kansa ta san sarai tunanin da yake,ko yaushe bakinsa kan maganar Nusrat yake,tasan kara yake mata kawai,don kafin ta haihu yasha fad'a mata shi fa a rayuwa bai tab'a iya yin kyautar d'a, yanda yake da son y'ay'a ba zai rink'a barin d'ansa yayi nisa da shi ba ko na sati guda.to amma ga shi yau tsawon shekara guda tun daga yaye iyayen ta sun rik'e Nusrat,kuma ko ita akan kanta tana jin k'aunar kasancewa da yarinyar tare da ita,amma ba zata iya cewa zata karb'eta ba in ba su suka dawo da ita ba. *******Ana kiran Sallar la'asar Khaleelee ya mik'e da Nusrat a jikinsa yana fad'in "Mamana bari naje salla." Mak'ale kafad'a ta yi tana k'ara shegewa jikinsa. Da yai zaton wasa ne abun,amma da ya fara k'ok'arin sauketa k'asa sai ta k'ara rik'eshi cikin b'ata fuska tace"Zanje fa." Komawa ya yi ya zauna a kujera yana y'ar dariya yace"Zauna, in naje masallaci na dawo zan d'aukeki muje yawo." Kuka ta fara yi sosai,abunda ya sa Khairiyya fitowa daga d'aki da sauri don cikin bacci ta jiyo kukanta. "Me ya faru take wannan kukan?" Su'ada dariya tace "wai masallaci zata bishi, kullum kuyi ta cewa y'ar Ku bata rigima to gashi tayi mun gani." B'ata fuska Khairiyya tai kafin tace "wallahi ba ta rigima,in kinji Ku kanta da dalili,shi yasa da naji kukan na tashi da sauri." Jin an fara tada sallar ya sa da sauri Khaleelee ya mik'e da ajiye ta kan kujera ya shige ban d'aki don d'aura alwala. Sosai fa Nusrat take kuka,ita dole zata bi Abbanta. Khairiyya ta d'auketa tana rarrashinta,ita kuwa Su'ada tashi tai don yin salla ta barsu wajan. Har khaleelee ya dawo a salla tana kuka,hakan ya sa yace Khairiyya tasa mata kaya yaje da ita shagonsa,in ta fito sai ta tsaya ta karb'eta. Jakarta ta bud'e ta d'auko mata wata y'ar doguwar riga Mara hannu. Nan da nan tai mata y'ar kwalliya ta shafeta da farar powder sabida zafin da ake,sannan ta canja mata Pampers. Yana d'aukan ta ta fara dariyar murna,shima dariyar ya yi,yana fad'in "Yau dai Mamana ta zama Muklees sarkin rigima." Su'ada tace"Ah daman da kukanta,kawai tana dad'ewa ne batai ba,ba Muklees ne kad'ai akoke ba." Fita yayi sab'e da ita yana dariya yace "Khairiyya sai kin fito." Ta amsa mishi da to. A tsakar gida Sakeena taga Khaleelee d'auke da Nusrat ta kalleta da sabuwar kwalliyar sa akai mata,ta had'iye wani yawu kafin tace "Nusrat kukan me take ne? Naji ihunta ina salla." Khaleelee yana sa kai zai fita yace"Rigima take wai in fita da ita." Daga haka ya fice. Ita kuma ta tab'e baki cikin ranta take cewa 'To in banda ma abu yarinya da gidan ubanta amma an barta gidan kakanni,sabida son abun duniya da kwad'ayi kawai.' Ba Wanda ya jita balle ya bata amsa,ita kad'ai take ta nunk'ufurcinta kamar y'arta. *** Shi kuwa Khaleelee tunda yaje da Nusrat shago yaran shagon keta fad'in "kai masha Allah, wai haka ta girma." Sosai ta ware dashi a shagon tana ta mai gwaranci. Wani kanti Dan gefen shagonsu ya shiga yayi mata siyaugar biscuit da alawowi.ta sha kad'an bacci ya d'auketa. Ya kwantar da ita a cinyarsa yana d'an pitting bayanta. Sai wajan k'arfe shida da mintina Khairiyya ra tsaya a adaidaita tanaiwa Khaleelee magana. Tasowa yayi ya kawo mata Nusrat d'in yana fad'in "Khairi Wannan yarinyar taki yau ta had'a ni da aiki,kinga da zuwanmu fa tai bacci." Dariya Khairiyya tai bayan ta gyara mata zama a jikinta tace"Um a bani abata,duk kunsa tai kuka da yawa daga zuwanmu gidanku." Dariya yai lokacin da yake bata ledar da yayiwa Nusrat d'in siyayya,sannan ya d'aga mata hannu yana cewa ta gaida mama. ***** Bayan sallar magriba a gudansu Su'ada, duk suna zaune falo don cin abincin dare,Mama ta dubi Khairiyya tana cewa "Wai ya akai Nuarat tai miki bacci a hanya ne yau?" Gyad'a kai Khairiyya tai tana cewa"Kuka ta sha,shine kuma sai tai bacci." "Wane irin kuka kuma?abunda ba cinikinta ba." Cewar mama. Nan Khairiyya ta basu labarin sanadin kukan. Mama tace "Ai da kin barta ta kwana biyu,ko zuwa jibi sai a d'auko ta." Zare ido Khairiyya tai da fad'in "Tab' d'in, haka kawai da ga nan suce sun rik'e ta." Da mamaki maman ke kallonta tace "Ah to in sun raketa ma ba y'ar su bace, ko daman kunyi da su sun ce miki kyauta su ka bamu?" Turo baki Khairiyya tai,don zancen bai mata ba,Jiddah dai kam sai dariya take,mamy me bin Khairiyya tace "A'a wallahi mama,ba mai d'auke mana ita,sai da ta shak'u da mu,muma muka shak'u da ita,sannan sai su d'auke ta,tab' d'in, ai Wallahi nasan Abba ma ba zai yarda ba." Sosai mama ke mamakin yaran nata, cikin dariya tace "To shi Abban y'ar sa ce da zaki ce ba zai yarda ba,shi ba ga nashi nan ba birjik,wa ya tab'a baiwa ko aro bare kyauta,ko ni lokacin da Ku ke k'anan haka kowa ke son in bashi ko d'aya cikinku amma Abban naku ya yi k'irmishishi ya hana,duk da yawanku kuwa. To Wallahi in ma zaku cire rai ga y'ar aro to ku cire,don na tabba ko yanzu ko nan gaba za su k'arb'i abarsu.kuma tunda ta nuna tana son zama gun mahaifinta daga yanzu duk jumma'a za'a rink'a kaita,lahadi sai a karb'ota,a haka ma za tafi sabawa." *Taku ce* *Y'ar mutan Ja'oji*🙋 [2/24, 10:54 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ _*page*_*49* Duk Kansu ba wanda ya k'ara magana,don jikinsu ya mutu,su sun gama sakankancewa fa Nusrat ta zama tasu,amma ga mama na zuwa da wani batu. ******* Satin da akai hutun makaranta Mama tasa Jidda ta had'awa Nusrat kayanta da y'an yawa tace ta kaita gida tai musu hutu tunda Su'ada na gida yanzu. Dukkansu ba wanda baiji kewar tafiyar Nusrat ba,amma ba yarda su ka iya. Har cikin ran Su'ada taji dad'in hakan,Khaleelee ma da ya dawo ya ganta har da kaya fara'a tak'i barin kan fuskarsa. ****** Sosai Nusrat ta sake a gidansu,musamman da Baby kullum suna tare,da an mata wanka Baby zata d'auketa,in islamiyya zasu je tare da ita take tafiya,wata rana a korosu wata rana a barsu. ******* A y'an kwanakin ne jikin Baba ya matsa,dole aka basu gado a asibiti,ciwo kullum gaba ya ke,har ya zama bai gane kowa. Ranar jumma'a da asuba Allah ya k'arb'i ran Baba,tashin hankali wanda ba'a sa masa rana,tabbas Khaleelee da y'an uwansa sun shiga rud'ani,haka su Su'ada ji take tamkar Abbanta ne ya rasu,kuka ta yi shi ta gode Allah. K'arfe bakwai na safe aka kai Baba makwancinsa. Da daddare bayan y'an zuwa gaisuwa sun tsagaita sai y'an uwa na jiki kawai, Khaleelee ya daddafa ya shigo wajansa,ko gani ba yayi sosai sabida yanda kansa ke bala'in ciwo. Kallo d'aya Su'ada tai mishi tai k'asa da kanta don wani bala'in tausayinsa take ji. Ruwan wanka ta had'a mishi ta shigo d'aki ta sameshi kwance kan gado ya dafe kansa da hannu biyu idanuwansa a lumshe sai d'an hawaye ke bin gefen fuskarsa,zama tai gefensa tana rik'o hannunsa cikin sanyin murya tace "Abban Nusrat,kayi hak'uri don Allah, a wannan lokaci baba addu'ar mu ya fi buk'ata sama da hawayenmu,ka daure ka bar kukan haka." Tashi yai ya zauna dafe da kansa cikin dashashshiyar murya ya fara magana "Su'ada Baba ya tafi,shike nan ya bi umma,yanzu bani da wata majingina ta iyaye.Su'ada Baba ya sha wahala kafin rasuwarsa,tun daren jiyan nan numfashinsa ke zuwa da dawowa,sai asuba Allah ya k'arb'i ransa." Ya k'arashe maganar yana tsiyayar da hawaye masu zafi. Dafo shi tai jikinta tana d'an pitting bayansa, tare da share mai hawaye,kalamai ta rink'a masa masu kwantar da hankali,har taji yana ta sauke ajiyar zuciya,sannan ta d'ebo ruwan sanyi ta bashi yasha. shayi ta had'a mai mai kauri,don tasan rabonshi da abinci tun jiya da dare. Da k'yar ta lallab'ashi ya sha. Sannan ta raka shi band'aki ta taya shi ya yi wanka. Daren gaba d'aya bai wani samu bacci ba,haka ya ke ga sauran y'an uwansa,ko baccin ya d'auke su bai yin nisa,don duk Wanda a kaiwa irin Wannan mutuwar bacci na wahalar zama a idonsa. Haka aka ci gaba da karb'ar gaisuwa,tsawon kwana bakwai, kullum da ga gidansu Su'ada sai an kawo abincin sadaka manyan kula. Abban Su'ada tun ranar da akai rasuwar ya taho daga legos, da shi ake zaman kullum yana gidan.haka ma mama da y'an uwanta,sun yi kara sosai sa sosai, har aka share zaman makoki. ***** Kwana goma da rasuwar Baba aka koma makaranta, ranar kuma Khairiyya tazo ta d'auki Nusrat. Amma tun ranar duk Friday sai an kawota lahadi Khaleelee ya maidata. *Bayan wata guda* ****** Shirin bikin Jidda ake ta yi,tunda aka fara shirin biki sosai Su'ada bata zama ko yaushe su na tafe siyayyar kayan biki. Su'ada ta kawowa Sakeena atamfar yini kyauta,sannan taiwa Baby ankon duka kala uku,don tace da ita za ta tafi sabida kula mata da Muklees, wanda lokacin ya ke shekara guda,yana yawonsa ko ina, da ke shi yana da kuzari da kazar kazar sosai. To fa! Sakeena dai ta fara saduda,don zuwa yanzu tasan Su'ada tafi k'arfin ta, ta k'ere mata matuk'a,tun randa aka fara bikin ta gano harkar arzik'in da ya d'aure mata kai,don yanzu take k'ara tabbatarwa su Su'ada manyan mutane ne,kawai dai don su ba masu nuna abun bane. Hidima akai sosai ta auran Jiddah, Su'ada fa ta gyagyaje ta sha sha'aninta,daman ba ta da wata damuwa da Muklees don ko yaushe yana tare da Baby,to ita ma Nusrat ganin Baby ya sa ta daina yarda da kowa a gidan balle taga ana biki,duk jama'a sun cika ko ina. Ranar yini Su Zakiyya duk sun wa Su'ada kara,don duk Wanda ta gayyata y'an uwan Khaleelee da mak'ota ba wanda bai zo mata ba. Haka akai hidimar biki aka k'are lafiya. Ranar da su Su'ada za su dawo gida fir Nusrat ta k'i zama,wai sai ta bisu,musamman yanzu da ta shak'u da Baby,don ko zuwan kwana biyun tai ko yaushe tana gun Babyn. Su'ada tace ba zata tafi da ita ba,sabida ba week end bane,ita kullum bata gida ina zata rink'a barinta. Tana fad'a Baby tai caraf tace"Aunty sai ki rink'a barinta a guna,tunda yanzu yamma nake,in kin dawo sai na tafi. Abba na jin haka yace ta tafi da ita,kar a barta kanta ya yi ciwo.duk yanda yake nacin son zaman yarinyar tare da su. Khaleelee na gida su ka dawo, yana ganinsu da Nusrat yace "A'a y'ar week end yau fa litinin me ya had'oku da ita?" Su'ada bayan ta dire kayan hannunta ta sauke goyon Muklees tana fad'in "Kuka take ta yi wai sai ta biyo mu,Abba yace mu d'aukota bayan ya san ina fita ko yaushe." Kallonta yai qur, zuwa can yace "Ni nai murna da zuwan ta." Kallonsa tai kamar ba ta gane me yake cewa ba tace "Ban gane ba." Gyad'a kai yai bayan ya d'aga yarinyar yace "Eh na ga ke kamar bi kiyi murnar biyoki da tai ba ." D'an mirmishi kawai tai ta wuce cikin d'aki. A can ya isketa ta na rage kayan jikinta,ya tsaya bakin k'ofa hard'e da hannayensa,jiyowa tai ta na d'an kallonsa tai mirmishi kafin tace " Ya gida? Ya zaman shiru?" Gyad'a kai yai ya na fad'in "ga zaman kad'aici ya dameni,amma ai yanzu ya k'are tunda kin dawo." Dariya tai kawai ba ya k'ara tankawa ba sai da ta canja kayan sannan ta k'araso gareshi tana sakar mishi wani lafiyayyan kiss,shi ma ya maida mata martani cikin zak'uwa da kewa. Taimaka mata yai su ka shiga kitchen kafin a kira salla ta d'an dafa musu abinci me sauk'i. Nusrat na can wajan Baby har ma tai bacci.sai da za su kwanta ne Khaleelee ya je ya amsota. _________________ Washe gari Su'ada ta shirya tafiya zuwa makaranta, Nusrat ba ta tashi ba,don haka Khaleelee yace ta barta in ta tashi shi zai mata. *********" Tun daga ranar ko yaushe in Su'ada ta tafi wajan koyarwarta shi ke shirya Nusrat ya bata abinci sannan in zai fita shago wajan sha d'aya sai ya kaita gun Baby. Shi kuwa Muklees daman akwai me renonsa A cikin makarantar da ta ke,don haka da ta je take kai mata shi. ************ Rayuwa ta mik'a,yayin da zaman Nusrat ya dawo gida da gaske, don haka Khaleelee ya sanyata makaranta.duk da k'arancin shekarunta amma tana da surutu.tun daga lolacin in Khaleelee Su'ada ke fita da ita ta ajeta a school d'insu da ke gaban layin kad'an. """""''''''Wata ranar lahadi Sakeena ta tashi da ciwon nono,abu kamar wasa sau gashi zuwa washe gari ciwo ya tsananta,sunje asibiti aka had'o mata magunguna,amma kullum ba sauk'i sai gun Allah. Kacokan Su'ada ta daukewa Sakeena duk ayyukanta, ita ce mata girki shirya yara,sannan ta kula da ita.haka Su'ada za ta yini a tsaye wajan hidima,ga tata ga ta Sakeena,dole ta d'auki hutu a makaranta. Ciwon Sakeena ya tsananta hakan ya sa aka basu gado a asibiti,duka d'auniyar Yara ta k'ara ninkarwa Su'ada, sannan ga girki fa take dare da rana ta aika musu asibiti.kullum da dare kuma Khaleelee ya d'auketa su je dubata. Satinta biyu a asibiti Allah ya bata lafiya su ka dawo gida, a nan ma Su'ada ba ta bar hidima ga Sakeena da y'ay'anta ba.don doctor yace ta nisanci zuwa kusa da wuta,hakan ya sa Su'ada bata bar mata girkinta ba. Bayan wata guda,Sakeena ta warke ras,har ta fara cike ramar da tai. Wata ranar jumma'a da dare,duk yaren na tsakar gida a zaune,Nusrat na kwance gefe ta fara bacci,Sakeena ta fito daga d'akin ta,kallon Nusrat da tai bacci tai,sannan ta kalli Baby tana mata fad'a "Baby ya ki ka bar Nusrat kwance cikin sauro, kin ga har ya fara hawa jikinta,maimakon da tai baccin ki shigo da ita d'aki." Kafin Baby ta taso Sakeena ta tsugunna ta ciccib'i yarinyar ta na shiga da ita cikin d'akin ta, kan gado ta d'orata tare da sakar mata net,sannan ta fito tsakar gidan itama ta zauna,kasancewar ba wutar NEPA kum injinsu babu mai a ciki. Su'ada da ke tsakar gidanta tana jiyo sanda Sakeena kewa Baby fad'a akan Nusrat,mirmishi tai k'asan ranta kuma da mamakin yanda yanzu gaba d'aya Sakeenan ta canja,duk halayenta na kyashi da hassada ta ajiye,wata irin kula ta ke bawa Nusrat da Muklees, sai tai musu abu ma ba taiwa y'ay'anta ba.tun farfad'owarta da ga ciwo duk tai sanyi. Fitowa Su'ada tai tsakar gidan Sakeena sab'e da Muklees,da fara'a Sakeena tace "Wai har yanzu bai bacci ba wannan sojan?" Y'ar dariya Su'ada tai ta ajiye shi kan tabarmar tana fad'in "Rigima ta hanashi kwanciya,ga Abbansa bai dawo ba da na jonasu nai aikin da ke gabana,na tara singing sosai na students." Rik'o hannunsa Sakeena tai sannan tace "Ai da kin kawo shi nan kin yi aikinki,ga Nusrat har tai bacci shi ido biyu,barshi ki je ki aikin ." Juyawa Su'ada tai tana fad'in "Yauwa ai kuwa kin kyauta,bari nai sauri sauri na gama." Sakeena kuwa d'aukan Muklees d'in tai ta sashi a jikinta tana ta lallab'ashi har yai bacci sannan shima ta kaishi d'aki kusa da Nusrat ta kwantar da shi. Wajan k'arfe tara Yaya Muktar ya dawo,yana shiga d'aki ya iske su Nusrat a shimfide kan gadon Sakeena, abunda ko y'ay'anta ba ta bari su kwanta mata a gado,abun ya mishi dad'i, shi kanshi yanzu canjin da yake gani tare da ita abun na birgeshi sosai. D'an mirmishi yai yace "Bak'i ki kai a d'akin?" Cikin yar dariya tace "Su Nusrat ne fa." Kamar bai gane ba yace "Au,mamansu bata nan ne?" "A'a aiki dai za tai ne,ta kawoshi nan,Nusrat kuwa daman ka san sai tai bacci take shiga d'akin su." Zama yai gefen ta yana rik'o hannunta ya fara magana cikin k'asa da murya, "Sakeena! sosai nake jin dad'in yanda ki ka d'auki Su'ada yanzu tamkar k'anwarki,hakan na faranta raina,musamman da kike k'ara Jan yaran nan a jikin ki, hakan zai sa su k'ara shakuwa da y'an uwansu,na tabbata ko bayan ranmu y'ay'an mu zasu zarce da karfaffan zumunci.na gode sosai Sakeena, ki k'ara had'a mana kan zuri'armu matsayin ki na babba kin ji." Gyad'a kai tai jikinta a sanyaye tace "Daman can shed'an ne ke sani kin Su'ada, don Su'ada ba ta tab'a yin abunda zai bata raina da gangan ba,tana ban girmana yanda ya kamata,sannan a wannan rashin lafiyar tawa na gasgata cewa FACALA y'ar uwa ce,kuma abokiyar hadin kai ce,yanda Su'ada ta tallafeni da yarana da duk hidimarmu ni na kasa mata hakan a lokacin da take laulayin ciki,na ji kunya matuk'a da yanda tai ta d'awainiya da ni,bata kyankyamina haka za ta zauna ta wanke min wajan ciwon nan tas ta samin magani,sannan ta shirya min yarana, tai musu girki.lalle FACALA ba abokiyar fad'a da gaba bace.kullum ina son bawa Su'ada hak'uri kan abubuwan da nai mata na rashin kyautawa a baya amma ina jin kunya wlh." Fara'a sosai kan fuskarsa yace "Karki damu,kawai ki bata hak'uri ki cire jin nauyi ko wani abu a ranki,hakan zai sa ku k'ara kusanci da juna." Gyad'a kai tai kafin tace "Insha Allah da safe zan mata maganar." *Taku ce* *Y'ar mutan Jaoji*🙋‍♀ 👭 *FACALA* 👭 *NA* *LAYUZA KABIR* *ADAM* 👩🏻‍💻👨🏻‍💻 *ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📝 _We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_ 💔💔💔💔💔💔💔 *Na sadaukar da wannan page d'in kacokan ga k'awa kuma Aminyata. Amrah Auwal mashi,Allah ya tsareki a duk inda ki ke,ya sa kece amrya kuma uwar gida a gidan uncle Aliyu sadauki*😍🙏 *page 50* 🔚🔚🔚🔚🔚🔚 **************** Tun da ga wannan lokacin wata shak'uwa da k'arin zumunci ya karfafa tsakanin Sakeena da Su'ada, har ta kai Sakeena ta hana Su'ada bawa me raino rikon Muklees, ko yaushe wajan ta take barinshi,ita zata shiryashi ta bashi abinci, don daman shi ba mai kulafacin nono bane don haka ta yaye shi. *Bayan wasu shekaru* Abubuwa da yawa sun faru,na dad'i da akasin hakan,ciki kuwa harda k'arin haihuwa da Su'ada tai,wanda zuwa lokacin take da Yaya bakwai,autanta me sunan Yaya Muktar ma a lokacin shekarsa takwas, sai sakeena da ta k'ara haifar y'an biyu duk mata. Zuwa lokacin Abba yana da shekaru talatin a duniya,kuma yana can k'asar Niger inda yake safarar waken suya, yayi karatun degree dinsa a fannin kasuwanci,lalurar ciwon suga da ta zaunar da Mahaifinsa waje guda ya sa shi ke d'auke da wani sashi na nauyin gidansu,yayin da Khaleelee ke d'auke da kaso mafi yawa na dawainiyar tasu. Su'ada da Khaleelee a yanzu ba sa kano, suna zaune a Kaduna, kasancewar tuni Khaleelee ya bar d'inki, ya sami aiki a karkashin hukumar costume.yanayin karatu ya sa basu tafi da Nusrat da Muklees can ba,suna zaune gun Sakeena,sai sauran ne tare da su. Fannin gida kuwa suna dai wannan gidan,sai dai Khaleelee ya rusheshi duka kowanne ya mai sabon gini sama da k'asa, babu wanda zai ce Wannan gidan na su ne,in sun zo hutu nan su ke yada zango.duk karatun y'ay'an yaya Muktar da na shi shine d'aukan nauyi. ___________________ Hajiya Su'ada zaune tana wayarta don nemo number Hajiya Sakeena,Jim kad'an da shigar kiran ta d'aga, daga b'angaran Hajiya Sakeena tace "Hajjaju yanzu na ke shirin kiranki fa,da gaske yaronki ya matsa number ba ba za'a d'aga mishi biki ba,wai dole ayi kamar ya da aka sa." Dariyar kamilallun manyan mata Hajiya Su'ada tai kafin tace "To daman ai Kune da son kai,in ba haka ba ansa biki lokaci ya k'arato kawai yarinya ta bullo da wani batu Ku kuma Ku biye mata,tabbas da Nusrat kusa da ni take zata sha bugu,to kin sata a gaba tana yin yanda taso,don haka fatana Allah ya dawo da Abba gida lfy,sati guda da dawoqarsa za'a fara biki." Cikin mirmishi Hajiya Sakeena tace "To an fi karfinmu dai ni da y'ata, shi kenan Allah ya kaimu lokacin." "Ameen Ameen." Hajiya Su'ada ta amsa. Bayan sun yi sallama ta kashe wayar tana bin labulayen da su kaiwa falon k'awanya,wani tunanin take a ranta na shekaru ashirin da su ka wuce. Tana tuno rayuwarsu da Sakeena tun farkon aurenta har zuwa yau,wato har kullum tana k'ara tabbatar da cewa FACALA ba abokiyar ga da fad'a bace,FACALA y'ar uwace,zuwa yanzu gashi zumuncin da ke tsakanin ta da Sakeena har za su had'a yayansu na fari aure,wato Abba da Nusrat. Wani mirmishi ta k'ara saki tana fad'in *ALHAMDULILLAH* _*Anan na kawo k'arshen Wannan littafi nawa na FACALA, ina godiya ga sarkin da ya bani ikon rubuta shi, abunda nai dai dai Allah ya ban ladan,abunda na kuskure Allah ya gafarta min*_ _Masoya da su kai jimirin bina cikin labarin ina godiya matuk'a da gaske, Allah ya bar zumunci_ *Sharhi ko shawara*👇 *07067270055* _Layuza kabir Adam_🥰😍🙋‍♀🙋‍♀🙋‍♀