An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels DUNIYA MAKARANTA 2 (Hikimomi 251-500) Rubutawar Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto 1 Bugawa da Yadawa: Bugu na farko 1437H/2016 Haqqin Mallaka @ Mawallafi mansursokoto@yahoo.co.uk isbn 9960-49-972-3 2 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Gabatarwa Yabo da godiya da’iman wa abadan su qara tabbata ga Allah. Tsira da sallama da gaisuwa zuwa ga Annabinmu fiyayyen halitta, shugaban Annabawa, jagoran Manzanni; Annabi Muhammad, da iyalansa da Sahabbansa baki xaya. Wannan shi ne littafi na biyu a jerin darussan Duniya Makaranta da muka fara bugawa, wanda tasharmu mai farin jini ta Wisalhausatv take yaxawa a duk marece da safiya. Babu shakka na samu qwarin guiwa matuqa daga karvuwar da littafi na farko ya samu, musamman ganin yadda aka riqa buga shi a garuruwa daban daban ana rarrabawa kyauta ga jama’a a lokutan bukukuwan aure da makamantansu. A dalilin wannan maraba da aka yi da littafin na duqufa ga inganta shi ta hanyar rubuta wani sabon littafi mai suna “Abokin Fira” wanda yake kawo labarun kunne ya girmi kaka masu tabbatar da sahihancin waxannan darussa na Duniya Makaranta. Littafin yana gaf da kammala kuma da yardar Allah kashinsa na farko zai fito ba da daxewa ba. Mai karatu zai lura mun sanya ma waxannan darussa lambobi, ci gaba a kan na farko don sawwaqe komawa gare su. Allah nike roqo ya karvi wannan aiki, ya amfanar da ni da waxanda suka karanta shi. Baban Ramla Jum’ah 8 ga Rajab 1437H (15 ga Afrilu 2016) A Sakkwato Babban Birni 3 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 251. Idan za ka faxi magana ko za ka bayyana wani ra'ayi kada ka xauka maganarka ta fi ta kowa ko ra'ayinka ya fi na kowa. Duk wanda ka gani yana da ra'ayi, yana da fahimta. Fahimta fuska ce, ra'ayi riga ne; kowa da irin tasa. 252. Ba dole ne a kowace magana ya kasance kana da wani ra'ayi ba. Idan kana da shi ba dole ne sai ka faxa ba. Idan ka faxi ba dole ne kowa ya goyi bayanka ba. Wanda bai goyi bayan ra'ayinka ba ba dole ne ya zama maqiyinka ne ba. Mu koyi zaman duniya. 253. Idan kana savani da wani ba dole ne sai ka qaurace masa ba. Idan har ka buqaci qaurace masa ba dole ne kowa ya qaurace masa ba. Sa'ar da kake qin wani sannan wani yake son sa. Kowa da kiwon da ya kama shi. 254. Idan ka ji kana son mutum ka bayyana masa kana son sa, sai danqon zumunci ya yi qarfi a tsakanin ku. Idan ka ji kana qin mutum ka voye masa. Wataqila nan gaba zai amfane ka, ko ya taimake ka, ko ka ga wani alheri tare da shi, sai sabuwar soyayya ta qullu a tsakanin ku. 255. Tsuntsu a kan reshe ba ya damuwa da kariyewar sa. Ba ga reshe ya dogara ba, ga fukafukansa. Saki reshe, kama tushe. Saki kowa, kama Allah. 256. Ka koyi kawaici kamar yadda kake koyon magana. A lokacin da magana ta kasa amfanin ka kawaici zai iya kare ka . 4 257. Idan kana tunanin za ka iya canja duniya, to ka hanzarta ka yi tun ba ka yi aure ba. Idan ka yi aure ko canja tashar talabijin a gidanka sai ya gagare ka. 258. A lokacin da kake saurayi burinka shi ne aure. Idan ka yi aure sai ka riqa addu'a kana son 'ya'ya. Idan sun girma sai ka riqa fatar ka rabu da su, su ma su yi aure. Daga baya za ka gaji da aiki ka buqaci ritaya. Sai ka sake komawa kai kaxai, kewa ta dawo maka. A da, hawa kake yi, a yanzu gangara kake yi. Kana son hardace Alqur’ani amma qwaqwalwarka ba ta xauka. Kana sha'awar koyon larabci amma ba za ka iya ba. Sallar dare da yawan azumi duk suna ba ka shawa amma lokacinsu ya wuce. Wannan shi ne labarinka a duniya. Ka nemi lahira tun da wuri kafin lokaci ya qure maka. 259. Idan ka ji alamar girman kai zai shige ka, ka duba qarqashin qafarka ka kalli qasa wadda ita ce asalinka, ka faxa ma zuciyarka "Daga can muka fito, kuma a can za mu koma". 260. Abu biyu kada ka yi sakaci da su: Abokin qwarai da Aikin qwarai. Abu biyu kuma ka ci moriyar su tun ba su wuce ba: Dama da lokaci. Abu biyu kada ka gajiya da neman su: Lafiya da zaman lafiya. 261. Abu uku suna hanzarta tsufa: Fushi da Hassada da Yawan damuwa. Babban maganin su shi ne Yafiya da sanin Allah da bar ma Allah. 262. Duniya fuska huxu gare ta: Murna da Damuwa da Ciwo da Lafiya. 5 263. Tsadar kaya da araharsu duk ba su hana xan Adam cin arzikin da aka rubuta masa. Nemi halaliya. Saurin nema ba ya kawo samu. 264. Tufafi su ne suturarka ta zahiri. Tsoron Allah shi ne suturarka ta baxini. Yi qoqari ka gyara ciki da wajenka. 265. Idan kana cikin damuwa ka yi shiru. Idan an vata ranka ka yi Haquri. Idan kana da kuxi ka yi kyauta. 266. Ba yarda da kuskurenka ne yake da muhimmanci ba, xaukar matakin gyarawa. 267. Kauce ma maqiyi guda xaya ya fi yin aboki xari. 268. Wasu mutane kamar Sukari suke a cikin rayuwarka. Ko ka daina ganin su amma xanxanonsu yana nan. 269. Idan ka tuna yadda magabata suke duqufa ga karatun Alqur’ani sai ka duba yadda muke duqufa wajen latsa wayar hannu. Kowa da kiwon da ya karve shi. 270. Idan za ka roqi Allah ba sai ka sa kati a waya ba. Ba sai ka yi booking appointment ba. Babu jakada, babu shamaki. Idan ka fara roqon Allah ba buqatar sai ka xaga murya, don ya san abin da ka faxi da wanda ba ka faxi ba. 271. Sassafta muryarka, amma ka gyara zancenka. Da Ruwan Sama ne ake samun shuka ba da tsawa ba. 272. Idan mutane suka riqa gwamatso da kai a sha’anin duniya, bar ma su ita kawai. Amma idan suka gwamatse ka ga sha’anin addini da samun lada yi sauri ka wuce su. Allah yana ba da duniya ne ga kowa da kowa, amma lahira kam sai masoyansa. 6 273. Hudahuda ya yi dalilin musuluntar mutanen qasar Yaman. Tururuwa ta canja ma Annabi Sulaimana hanyar tafiya. Giwa ta qi karbar umurni a lokacin da Abrahata yake nufin rusa Ka'aba. Ko cikin dabbobi akwai masu basira. 274. Wanda yake cikin ginin gilashi ba daidai ne ya yi wasar jefa dutse ba. Lura da ayubbanka da zunubanka, ka manta da na mutane. 275. Banbancin Ilimi da kyan fuska: Allah ya bai wa Annabi Yusuf (Alaihis Salam) ilimi da kyawo. Kyawonsa ya kai shi kurkuku, iliminsa ya fis she shi. 276. Sallah ita ce abu na farko da za a tambaye ka gobe qiyama. Kada ka mayar da ita qarshen abin da ya dame ka. 277. Duniya kowa tafiya yake yi. Hanyarmu xaya ce, amma masauki kowa da nasa. Wasu za su sauke kayansu a aljanna, wasu ko qarshensu makamashin wuta. Ya Allah ka yi mana garkuwa daga shiga wuta. 278. Ababe uku ne suke maganin wahala: Addu'a, da Godiyar Allah, da Taimakon mabuqata. 279. Wasu mutane kamar madubin likita suke. Laifi qarami girmama shi suke yi. 7 280. Hawayenka littafinka ne. Babu mai karanta shi daidai sai masoyanka. 281. Idan za ka yi hukunci kada ka saurari vangare xaya. Sau da yawa mayaudari yake kuka, ga mai gaskiya a gefe yana kallo. 282. Kada ka zama kamar alawa a shanye ka. Kuma kada ka zama kamar maxacci a furzar da kai. Ma fi alherin al'amurra shi ne na tsakiya. 283. Nasiha: Kada ka ci abinci bayan ka qoshi. Kada ka yi magana in da babu buqata. Kada ka zauna da wanda ba ya qimanta ka. 284. Da abinci a hannunka kake bin tsuntsu yana tserewa saboda ya fi son 'yanci da abinci. Wasu' yan Adam a nan tsuntsu ma ya fi su. 285. Annabi Musa Alaihis Salam ya ratsa tekun Maliya a cikin akwati shi kaxai ya fita lafiya qalau. Fir’auna ya ratsa tekun a cikin dubun dubatar jama’arsa amma ya nutse a ciki. Idan kana tare da Allah lamarinka duk mai kyau ne. 286. Idan kana kula da lokacinka, kana jin sauqin ibada, ba ka jin wahalar yin sadaka, kana kwaxayin bin Sunnah, kana kusantar mutanen kirki, to kai ne kake cikin Rayuwa Mai Daxi. 8 287. Ba da kuxi kawai ake sadaka ba. Zikiri da addu'a, da Murmushi da Fara'a duka su ma sadaka ne . 288. Tsakanin Miji da Mata: Idan ya yi kuskure za ta nuna damuwa sai ya ba ta haquri. Idan ta yi kuskure zai nuna damuwa, sai ta yi kuka, sai ya ba ta haquri! Mata ‘yan gata. In ba ku ba gida. 289. A wuri biyu ne ake gane kirkinka: Yin Haquri idan ka rasa, da bayarwa idan ka samu. 290. Sau dubu ashirin da huxu ne xan Adam yake shexawa tsakanin wuni da safiya. Ni'imar Allah dubu ashirin da huxu kenan. Me kake yi ma Allah don godiya? 291. Ka yi abota da duk wanda kake so, amma ka sani abu xaya ne zai abokance ka a cikin qabarinka; shi ne aikinka da ka aikata. 292. An tambayi wani malami mai hikima, ko ka san wanda ake karvar addu'arsa? Sai ya ce, a'a. Na dai san wanda yake karvar addu'a. Wannan shi ya san Allah. Wani kuma mahaifiyarsa ta fashe da kuka yana cikin halin mutuwa, sai ya tambaye ta, idan ke za ki yi min hisabi za ki sanya ni wuta? Ta ce, a’a. Wallahi ba zan iya sanya ka cikin wuta ba. Ya ce, to, Allah yana so na fiye da ke, kuma yana tausayi na fiye da ke. Wannan shi ya kyautata zato ga Allah. 9 293. Da ace bankuna suna cire mana kuxi idan muka ci naman wani su jefa ga akawun xin sa, da mun kama kanmu. Amma da yake ladarmu ce ake cirewa ba mu ji sam, ko a jikinmu. 294. Mai bacci ba ya sanin mafarki yake yi har sai ya farka. Haka duniya take; ba ka sanin kana cikin ruxi sai mutuwa ta riske ka. 295. Idan kana iya yin awa xaya a kan keke don ka rage kitsen jikinka, don me ba za ka iya tsayawa minti goma sha biyar a gaban Allah kana neman rage zunubanka ba? 296. Iya dambe da kokawa ba shi ne qarfi ba. Cikakken qarfi shi ne iya kama kai da haxiye fushi. 297. Ana haifuwar xan Adam a jimqe da hannayensa saboda kwaxayin duniya da Abin da yake sa ran ya samu a cikin ta. A ranar mutuwa yakan buxe su don ya tabbatar bai samu komai ba a cikin ta. 298. Idan mugu ya haxu da na qwarai nan take asirinsa yake tonuwa. In da wahala take shi ne idan mugu da mugu suka haxu, wanne ne ya fi Mugunta! Idan na qwarai guda biyu suka haxu wanne ne ya fi alheri? 299. Mutum komai matsayinsa akan samu givi a cikin tunaninsa, ko kuskure a cikin aikinsa, matuqar shi ba Annabin Allah ne ba. Amma a cikin mutane akwai waxanda bai dace ana faxin kurakuransu ko ayubbansu ba. 10 300. Duk lokacin da Shaixan ya haxu da iyalansa babu abin da suke farin ciki da shi kamar abu uku: Musulmin da ya kashe xan uwansa, da mijin da saki matarsa, da xan Adam mai rowa don tsoron talauci. 301. Babbar musiba ce mai gaskiya ya yi shiru, maqaryaci ya saki bakinsa. Babbar fitina ce malami ya yi kawaici, jahili ya xaga muryarsa. Abin da ya fi wannan hatsari shi ne, mai gaskiya ya yi qarya ko malami ya yi aikin jahilci. 302. Sau da yawa kana buqatar qarfi ne idan za ka aikata mugunta. 303. Ba za ka ji daxin ibada ba sai ka bar abu uku: Ka daina neman yardar mutane ka nemi yardar Allah. Ka daina cin haram ka nemi halaliya. Ka bar abota da Fasiqai ka yi da mutanen kirki. 304. Idan ka bari wani ya gano dalilin kukanka, a gobe shi zai sa ka kuka. Rufa wa kanka asiri don ka tsira da mutuncinka. 305. Dariyarka da kukanka duk ba su tsayar da rayuwa. Komai zai ci gaba idan ka yi murna ko ka yi baqin ciki. Sassafta ma rayuwarka kada ka kashe kanka a banza. 306. Ana son Macce ta mutunta gavovi uku daga jikin mijinta: Hancinsa, da idanunsa, da kunnuwansa. Ma’ana, kada ta bari ya shaqi wari, ko ya ga qazanta, ko ya ji hayaniyar da ba ya so a cikin gidansa. 11 307. Aboki kamar matakalar bene ne. Ko dai ya yi sama da kai, ko kuma ya yo qasa da kai. Zavi abokan da kullum sama suke yi da kai; masu amfanin ka. 308. Soyayya tana dushewa. Mutum yana mutuwa. Idan kana da gata ban da Allah watarana za ka tashi ba ka da gata. Allah abin dogara. 309. A hannunka, yatsan da ya fi kowane nisa da ‘yan uwansa shi ne babban yatsa. Duk da haka sauran ba su iya komai sai tare da shi. Ba kusancin xan uwa ne muhimmi ba, amfaninsa. 310. Mai yawan kuka ba ya rabuwa da baqin ciki. Mai yawan godiyar Allah ba ya shiga damuwa. Idan kuma ya shiga take za ta koma murna. 311. Ba a san coffee zai yi daxi ba sai da aka haxa shi da Sukari da Madara. Haka ne a rayuwa, amfanin wani ba ya tabbata sai da wani. 312. Tuna mutuwa yana sa abu uku: Saurin tuba, da wadatar zuci, da himmar ibada. Manta mutuwa kuwa yana sa abu uku: Jinkirin tuba, da haxama, da kasala wajen bautar Allah. 313. Idan muka rasa kuxi mukan ji ciwo, mu samu damuwa. Amma a kullum muna rasa kwanukanmu na duniya ba mu ji a jikinmu. Kuxi abokan tafiya. 12 314. Sau da yawa nasihar da ba ka son ji ita ce wacce kake buqata. 315. Abin da ya fi komai takaici a alqiyama shi ne, ga ladarka ba ka iya ba iyayenka da 'ya'yanka da masoyanka amma kana kallo za a xauka a ba maqiyinka don ka ci naman sa ko ka zalunce shi. 316. Ba kowa ne zai ga sakamakon aikinsa ba. Amma kuma babu wanda zai samu sakamako sai da aiki. 317. Idan ka yi ma wani alheri ka yi shiru. Amma idan wani ya yi maka alheri ka yayata. 318. Idan ka kalli baya akwai abin da zai sa ka damuwa. Idan ka kalli gaba akwai Abin da zai ba ka tsoro. Kalli sama. Can ne ubangijin da ke tausayin ka yake. 319. Magana mai kyau akan faxe ta da lafazi mummuna. Mummunar magana akan faxe ta da lafazi kyakkyawa. Kafin ka yi tunanin maganar da za ka faxi, yi tunanin yadda za ka faxe ta. 320. Khalid bn Walid ya kasance yakan xauki Alqur’ani ya yi kuka yana cewa, Jihadi ya hana mu karatun ka. Ikon Allah! Mu kuma a yau me yake hana mu karatun sa? 13 321. Duniya kamar maciji ce; ga kyau, ga laushi. Amma fa dafin cikin ta ya fi guba zafi. 322. Idan ka kai qafarka inda bai dace ba, kada ka ga laifin wanda ya zage ka. Idan ka tsoma bakinka a cikin abin da bai shafe ka ba, abin da ya same ka kai ne ka janyo shi. 323. Wanda duk ya xunka tufan kunya ya yi maganin a ga wallensa. 324. A lokacin da wani zai yi tafiyar awa xaya don ya nemo abinci wani kuma zai yi gudun awa xaya ne don ya wargaza abincin da ya runtuma ma cikinsa. Duniya zaman ‘yan Marina. 325. Idan mutum ya mutu abu uku ne suke raka shi. Biyu za su dawo, su bar shi da xaya. Masu raka shi su ne iyalansa da dukiyarsa da aikinsa. Iyalansa da dukiyarsa sukan dawo su bar shi da aikinsa. Tanadin abokin zama ya fi tanadin abokin rakiya. 326. A duniya akwai wanda kake so, akwai wanda yake son ka. Wanda yake son ka a kullum yana shirin ba ka ne. Wanda kake so kuma a kullum shirin karva yake yi daga wurin ka. 14 327. Ba ka samun hutu sai ka daina shiga cikin lamurran mutane waxanda ba su shafe ka ba. Ba ka zama mai ladabi sai ka san maganar da kake furtawa. Ba ka zama gwani sai ka iya kama bakinka. 328. Bishiya ba ta faxi idan ta ji qishiruwa. Ko dai ka ba ta, ko ta mutu salun alun. Haka wani mai rai yake. Ba a sanin darajarsa sai ya mutu. 329. Kada ka wulaqanta wanda ya girme ka, watarana kai ne matsayinsa. 330. Taimaki xan uwanka, tausaya ma qanenka, kyautata ma maqwaucinka. Duniya inwar hantsi ce. 331. Talaka ba shi ne wanda bai da kuxi ba. Talaka shi ne marar ladabi da tarbiyya. Ita kuma Tarbiyya ba a sayen ta, ba a saida ta, koyon ta ake yi. 332. Mutane kamar madubi suke a gare ka. Idan ba ka ganin komai sai sharri a cikin su to kai ne masharrancin. 333. Nasiha: Kafin ka yanke ma mutum hukunci yana da kyau ka saurare shi. Allah yana son adalci. 15 334. Masunci yana kama kifi ne ta bakinsa. Idan kifi ya rufe bakinsa masunci ba zai iya kama shi ba. Rufe bakinka. Akwai masunta da yawa a cikin mutane masu farautar kurakuranka. 335. Idan ka bi ta kan manyan gidaje rayuwarka ta gwada maka cewa Allah ya raba bai ba ka ba, wuce asibiti ka duba. A nan ma Allah ya raba ciwo ba da kai ka. 336. Kishi kyakkyawan ciwo ne da ba shi da magani sai tsoron Allah. 337. Hankali da harshe suna hannun riga ne. Idan hankali ya yi faxi harshe zai taqaita. Idan kuma hankali ya taqaita harshe sai ya qara tsawo. Wanda ka ga maganarsa ta yi yawa ka tuhumci hankalinsa. 338. Masu hikima sun ce: Bango ya ce da qusa me ya sa kike damu na? Sai ta ce ma sa, tambayi mai duka na! Ka riqa yin uzuri ga mutane. Wani lokaci ba za ka iya sanin hanzarinsu ba. 339. Masoya sirri suke yi suna nesa da juna. Mafaxata hargowa suke yi alhalin suna kusa da juna. Kusancin zukata shi ne kusanci ba na gangar jiki ba. 340. Duk mutumin da kake yawan faxa da shi ba za ka iya rabuwa da shi ba. 16 341. Idan Allah ya xaukaka ka masoyanka za su san matsayinka. Idan ka shiga jarrabawa za ka san masoyanka. 342. An tambayi wata mai hikima, wa kika fi so a cikin 'ya'yanki? Sai ta ce, qarami har sai ya girma. Da marar lafiya har sai ya warke. Da wanda ba ya nan har sai ya dawo. 343. Duk mutum bawa ne. Ko ka zama bawan Allah ko ka zama bawan Shaixan ko na son zuciya. Wanda bai yi sharan masallaci ba ya shari kasuwa. 344. Makaho bai tava kallon zunubi ba. Kurma bai tava sauraren qarya ba. Bebe bai tava gulma da bakinsa ba. Marar hannu ba ya sata. Da ni’imar Allah muke savon sa. Mu ji tsoron Allah. 345. Idan kana son sauqin mutuwa yawaita sadaka. Idan kana son hasken qabari yawaita karatun Qurani. Idan kana son sauqin tsallaka Siraxi yawaita Zikiri. Idan kana son maganin qishirwa a gobe qiyama yawaita azumi. 346. Sau da yawa damuwarka za ta sa wasu dariya. Yi qoqari kada dariyarka ta zama damuwa ga kowa. 347. Ka yi kuskure ba shi ne matsala ba. Ka yarda ka yi kuskure shi ke da muhimmanci. Abin da ya fi shi muhimmanci shi ne, ka koyi darasi daga kuskurenka. 17 348. Wanda ya fi mutane hankali shi ne wanda ya fi su kawaici. Wanda ya fi kowa sani shi ne wanda ya fi kasa kunne ya yi saurare. 349. Duk motsin da babu lada a cikin sa zama kurum ya fi shi. 350. Zuciya kamar tukunya ce. Abin da ka dafa a cikin ta shi kake furtawa. Duk wanda ya buxa bakin sa za a san abin da ya dafa a cikin ransa. 351. Wayar Salula da intanet suna kusanto maka wanda yake nesa. Amma idan ba ka yi hankali ba sai su nesanta ka da wanda ya fi kowa kusa da kai, shi ne Allah mahaliccinka. 352. An tambayi wani mai hikima, me ya sa muke ganin sama fara tas? Sai ya ce, don ba mu rayuwa a cikin ta. Ido na raina wanda yake gani kullum. 353. Abu biyu ne suke sa ka ci riba a rayuwarka: Sanin girman kai da barin girmankai. 354. Mutane da yawa da ka san abin da suke faxi a bayan idonka, da ka yanke hulxa da su. Wani rashin sani ma yana da amfani. 18 355. Duk abin da ka yi masoyanka ne kawai kake burgewa. Masu hassada sai dai su yi murmushi don su vatar da hankalinka. Amma fa hasada ga mai rabo taki ce. 356. Ba duk abin da kake so ne kake samu ba. Ba duk abin da ya same ka ne kake fata ba. Qaddara ta Riga Fata. 357. Yin fushi idan ba ka da gaskiya taurin kai ne. Yin fushi idan kana da gaskiya rashin sanin girman-kai ne. Haquri da iyali qauna ce. Haquri da maqwauta dattaku ne. Haquri da jama'a mutunci ne. Haquri da bin dokokin Allah shi ne imani. 358. Daina tunanin baya, ka riqa tunanin gaba. Sanya murmushi ya zama alamarka. Ba ko wane abu ne kyakkyawa yake alheri ba. Amma duk alheri kyakkyawa ne. 359. Masu hikima sun ce: Allah ya raba ‘yan yatsunmu don mu kama hannayen junanmu mu cike su. 360. Idan ka sha ruwan rijiya kada ka jefa dutse a cikin ta. Idan wani ya tava yi maka alheri kada ka yi ma sa butulci. 361. Tsuntsu a tukunyar gidanka ya fi rago a gidan wani. Mugun gatarinka ya fi sari ka ba ni. 19 362. Abu biyu kada ka faxe su: Cutar da mutane suka yi maka, da alherin da kake yi masu. 363. Idan wani ya yi kuri da iya magana ka yi masa kuri da iya kawaici. 364. Babu mugun abu kamar bashi. Yakan tozarta mutum da Rana. Da dare kuma ya hana ma sa bacci. Allah ka tsare mu da sharrin bashi. 365. Abokan zama biyu ne: Wanda za ka qaru da shi, da wanda zai qaru da kai. Na ukunsu banza ne. Ka guje shi. 366. Abu biyu ba su dorewa: Qarfi da Quruciya. Abu biyu ba su vacewa: Alheri da Zumunta . 367. Gara qarewar lokaci da vata lokaci. Idan lokacinka ya qare za ka mutu. Mutuwa tana yanke ka ne daga duniya da abin da ke cikin ta. Vata lokaci kuwa yana yanke ne daga Allah, da jin daxin bautar sa. 368. Duk abu mai daraja yana da mayafi. Alqur’ani yana da makari. Alqalami yana da marufi. Takobi yana da kube. Alawa tana cikin takarda. Lemu da Ayaba, Abarba da Gwadda. Kai, duk abin qwarai ana yi masa sutura. Lulluvi adon matan kirki. 20 369. Idan kana son duniya ka yi karatu. Idan kana son lahira ka yi karatu. Idan kana son duniya da lahira ka yi karatu, sannan ka yi aiki da karatu. 370. Alqur’ani shi ne daminar zukata. Idan ka ga ana karanta Alqur’ani ba ka jin wani tasiri a zuciyarka to ka yi kabbara huxu ga zuciyarka. Ta riga ta mutu. 371. Idan kana son ka ji daxi nan take ka rama abin da aka yi maka. Idan kana son ka daxe kana jin daxi ka yafe abin da aka yi maka. 372. Komai gaskiyar namiji akwai gaskiyar da ba zai iya faxa ma macce ba a lokacin da yake neman ta da aure. Ita ce, niyyarsa ta qarin aure a nan gaba. 373. Shiru ya fi maganar banza. Da zama tare da mugu gara zama kai kaxai. Fitar da ba ta da lada zaman gida ya fi ta. 374. Kada ka yawaita faxin abin da Allah ya ba ka. Bakin mahassada ya fi takobi kaifi. 375. Sadaka maganin matsala ce. Addu'a maganin wahala ce. Azumi maganin cuta ne kuma garkuwa ne daga shiga wuta. 376. Dariya babban magani ce. Amma idan kana yin ta babu dalili to kana buqatar magani. 21 377. A kowace mota gilas xin gaba ya fi na baya girma. Saboda gaba ake son yawan kallo ba baya ba. 378. Abin da ya fi komai daxi shi ne a yabe ka ba ka nan. Abin da ya fi komai haushi shi ne a yabe ka da qarya a gaban idonka. 379. Idan kana neman gata ka nemi Uba. Idan kana neman jigo ka nemi xan uwa. Idan kana neman garkuwa ka nemi aboki. Idan kana son natsuwa ka nemi mata. Idan kana son su duka ka nemi uwa. 380. Haquri iri uku ne: Haqurin abin da kake so idan ba ka same shi ba, da haqurin abin da ba ka so idan ya same ka. Sai kuma haqurin bin dokar Allah. 381. Macce ta gari ita ce wadda ta san Abin da ya dace ta yi idan mijinta yana cikin fushi ko yunwa ko gajiya. Sakarai ita ce wadda ake jin sirrin mijinta daga wurin ta. 382. Namiji sadauki shi ne idan ya samu alheri sai ya nufo gida wurin iyalansa. Sakarai shi ne mai dukan matarsa. 383. Mutum biyu ba a gaskata maganarsu: Mai neman aure da mai neman quri'a. 22 384. A lahira Munafukai su ne a qasan wuta. Amma a duniya sunayensu ne a saman Jarida. 385. Mutum uku kana iya biyan su: Wanda ya fara yi maka sallama, da wanda ya ba ka wurin zama, da wanda ya yo tafiyayya zuwa wurin ka. Na huxu sai dai ka roqi Allah ya biya shi: Shi ne, wanda yake da buqata bai ga inda ya dace ya nemi taimako ba sai a wurinka. 386. Wanda ba shi yawan magana idan ya yi magana ba a manta ta. 387. Soyayya kamar yaqi ce, hura wutar ta yana da sauqi, amma kashe ta sai an jajirce. 388. Kada ka damu da abin da mutane suke faxi a kan ka. Domin ka fi su sanin kanka. Matakin farko na cin nasara ga rayuwa shi ne ka yarda ba za ka iya daxaxa ma kowa da kowa ba. 389. Mai hankali yana da alama. Mahaukaci ma yana da alama. Alamar mai hankali ita ce natsuwa da kyautata ma mutane, da sanin ya kamata. Alamar Mahaukaci girman kai, da raina mutane da qyamar su. Idan ya yi nisa sai ka gan shi yana dariya babu dalili. 23 390. Kada ka damu idan kana yi ba a godewa. Magabata sun ce, aikin jama'a ba a iyawa, ba a gamawa, ba a yabawa. Idan Allah ya yaba aikinka ya ishe ka. 391. Hasara ita ce ka tsaya kallon wani yana savon Allah. Riba ita ce ka ribaci roqi Allah gafara a lokacin da ka ga wani yana savo. 392. A kyauta ake shiga masallaci amma ka gan shi ba kowa. Wuraren shashanci biya ake yi amma ka gan su maqil da jama’a. Mutane suna barin garavasar aljanna, suna sayen wuta da kuxaxensu. 393. Idan kana sallar dare kada ka raina masu bacci. Da yawa ‘yan aljanna waxanda an fi su yawan aiki amma da tsarkin zuciya suka kere mutane. 394. Yaro yana faxuwa. Babba ma yana faxuwa. Idan yaro ya faxi zai tashi ne ya zura da gudu. Idan babba ya faxi yakan waiwaya ne ya ga abin da ya kayar da shi. Idan ba ka nazarin jiya gobenka ba ta kyawo. 395. Idan kana fama da ciwon zuciya, ko baqin ciki ya ci qarfin ka, ka tuna fa a duniya muke ba a aljanna ba. Duk abin da ya ke damun ka a yau zai wuce ya bar ka, ko ka wuce ka bar shi, watarana sai labari. 396. Abu biyu ba su haxuwa ga mutum daya: Rowa da jin daxin duniya. 24 397. Wata tara kake kwance a cikin cikin ta. Shekara uku kake rungume a qirjin ta. A tsawon rayuwarta kana zaune daram a cikin zuciyarta. Uwa da babu irin ta. Mu darajta iyayenmu. 398. Zunubi xaya ne Shaixan ya yi Allah ya kore shi daga aljanna. Zunubi xaya Annabi Adam Alaihis Salam ya yi aka fito da shi daga cikin ta. Mu kuma da tarin zunubanmu ne muke son mu koma a cikin ta. Allah ka cece mu. 399. Abu uku babu daxi idan suna empty: Ciki da Batur da Aljihu. 400. Duk wanda ba shi da manufar da zai iya mutuwa a kan ta, to ba shi da manufar da yake rayuwa a kan ta. 401. Dutsen da ba ya tare maka hanya bai kamata ya dame ka ba. 402. Tsakanin Bidi’a da Savon Allah: Mai savo a kodayaushe yana iya yin tuba domin ya san laifi yake yi. Mai Bid'ah ba zai tava yin tuba ba domin ya xauka a daidai yake. 403. Kada ka faxa ma mutane hizo nawa ka hardace na Alqur’ani. Ka bari su ga Alqur’ani yana tafiya kawai a cikin jikinka. Kada ka damu da ina ka kai a cikin Alqur’ani, ka damu da ina Alqur’ani ya kai a cikin rayuwarka. 25 404. Abu uku wajibin ka ne ka tsare su: Addininka da Mutuncinka da Qasarka. 405. Abu uku ba su da makawa: Iska da Ruwa da Mutuwa. 406. Nasararka ba ita ce wadda mutane suke faxi ba. Babbar nasararka ita ce kyakkyawan aikinka wanda Allah kaxai ne ya san shi. 407. Matsalarka ba ita ce wadda maqiyanka suke faxi ba. Babbar matsala a gare ka ita ce wadda ke tsakanin ka da Allah amma mutane ba su sani ba. 408. Mamaki: Idan muka yi sadaka da Naira 500 sai mu gan su da yawa, amma idan muka je da su kasuwa sai su dawo yan kaxan. Idan muka yi awa biyu muna ibada sai mu gan su da yawa, amma idan muka yi su a kallon movie ko wasar qwallo sai mu ga sun dawo ‘yan kaxan. Idan muna addu'a sai mu kasa daxewa amma idan muna fira sai bakinmu ya buxe sosai. Idan muna karanta Alqur’ani sai mu qosa nan take, amma idan muna chatin sai mu rasa sanin inda lokaci ya tafi. Anya kuwa wannan ba alama ce ta raunin imaninmu ba? Aljanna fa akwai tsada. Mu sabunta imani. 409. Yin abubuwa guda uku yana sa ayi wasu uku: Kallo yana sa ayi Zina, jayayya tana sa ayi faxa, fushi yana sa ayi wauta. 410. Kyauta tana kawo soyayya, kunya tana kawo alheri, tsafta tana ba da lafiya. 26 411. Ni'imomin duniya guda uku ne: Matar qwarai, da maqwaucin kirki da xa mai albarka. 412. Damuwa kamar hadari ce. Idan ta kankama sai ruwa ya sauka. 413. Idan ka mutu aka xauko ka ba za a kira ka da sunanka ba, sai dai ace a xauko janaza. Idan an sauke ka cikin qabari ba za a kira sunanka ba sai dai ace a kawo Mutum. Daga nan sunanka ya vace sai dai a ce “Marigayi”. 414. Duniya kamar ruwan teku ce. Duk ka qara sha za ka qara qishi. 415. Wanda duk ba ka da buqata da shi tsaranka ne. Wanda kake da buqata da shi maigidanka ne. Wanda duk kake kyautata ma sa zai zamo kamar bawanka. 416. Idan za ka aiki xan saqo kada ka aiki wawa. Nemi mai hankali da basira. Idan har ba ka samu ba, to ka je da kanka. 417. Idan mutane suka guje ka a lokacin da ka shiga jarrabawar rayuwa to ka kwantar da hankalinka. Allah bai kore maka su ba sai don yana son ya ishe ka. 418. Kada ka damu idan ka yi kuskure sannan ka gyara. Daga kurakuranka ne kake karanta rayuwar duniya. 27 419. Idan ka samu alheri, yi godiya. Idan sharri ya same ka, yi haquri. Idan ni'ima ta girma ya kamata godiyarta ta girma. 420. Motsin da ya fi kowane sauqi gare ka shi ne motsa harshenka. Amma kuma ya fi kowane hatsari da cutarwa a gare ka idan ba ka kiyaye shi ba. 421. Idan ka saki hawayenka a kan filo ka sake su a banza. Tashi ka kwarara su a tabarmar sallarka. Idan ka yi haka, ka kai qara wurin mai share maka su. 422. Darasin da ya fi kowanne zafi a rayuwa shi ne sanin cewa, ba dukkan mutane ne suke son ka da alheri ba. 423. Kada ka himmatu wajen yawaita abokai. Zavi na kirki ka manta da saura. 424. Abu uku muna da buqatar su a kullum: Jarunta don canja abin da ake iya canjawa. Da Haquri don jure abin da ba a iya canjawa. Da Hikima don samar da canji mai ma'ana. 425. Macce ta fi son ta zama mai kyau fiye da ta zama mai basira. Saboda maza sun fi amfani da idanunsu fiye da amfanin da suke yi da hankulansu. 28 426. Sadaka ita ce maganin bala'i. Yi sadaka a yau. Gobe ba za ka iya ba. Domin likkafani ba ya da aljihu. 427. An tambayi wani gwani a harkar duniya, me ya fi komai nauyi? Sai ya ce rashin akin yi. 428. A lokacin da Allah ya so fitar Annabi Yusuf Alaihis Salam daga kurkuku bai umurci bango ya tsage ba. Mafarki ne ya sanya Sarki yi, sai ya zama dalilin fitar sa da xaukakar sa. Allah mai yi ko babu dalili. Amma yana yi da dalili don mu qara karatu. 429. A addinin musulunci an koya mana cewa, aljanna tana qarqashin qafafun iyaye. Amma a yau wasu na koyar da cewa, aljanna tana bisa gawawwakin musulmi. Suna kashe mutane a tituna da kasuwanni da masallatai. Idan ba ka koya ma xanka addinin qwarai ba zai koyi addini xan jabu. 430. Ruwa ruwa ne ko a cikin me aka sa shi. Kada ka damu da qyaleqyali, nemi gaskiya. 431. Da yawa alherin da ya kubce maka da ka same shi ba zai zame maka alheri ba. Roqi Allah alherinsa, ka bar zavi a hannunsa. 432. Kada ka raina qananan zunubai. Da qaramin dutse ake yin tuntuve ba da babba ba. 29 433. Yahudawa sun zagi Allah. Mushrikai sun zagi Manzon Allah. Idan kana tsammanin ka tsira daga bakin mutane ka yi wauta. Maganar mutane kamar duwatsu ce; ko ka xora su a kanka ka sha wahala ko ka take su a qarqashin qafafunka ka haura sama. 434. Ciwo ba a jiki kawai yake ba. Akwai ciwo a tunani, akwai shi a hali da xabi'a. Idan ka ga mai kaushin hali ka roqa masa sauqi daga Allah. 435. Idan kana da ciwo a jikinka rigarka za ta rufe shi. Idan kana da ciwo a tunaninka bakinka ne yake kware shi. 436. Mutunta Mutum ba ya nuna kana son sa. Amma yana nuna kana da Tarbiyya. Ba sai wanda ake so ake mutuntawa ba. 437. Sau da yawa mutum yake murmushi amma ransa na cikin jin zafi. Domin ya yi amanna cewa, bayan wuya sai daxi. 438. Mai ba da haquri ba lalle ne ya zama mai laifi ba. Wani lokaci iya zama da jama'a ke sa ka ba su haquri alhalin ka fi su gaskiya. 30 439. Wasu Manya a qasashen waje suke yin karatu. Idan ba su da lafiya a qasashen waje suke shan magani. A can ne kuma suke shan iska. Abu xaya ne suke yi a cikin qasarsu, shi ne sata. Kishin qasa shi ma addini ne. 440. A da, malamai ba su damu da abin duniya ba. Masu duniya na bin su da ita don neman iliminsu. A yau malamai ke bin masu duniya don neman ta daga wurin su. Wannan ya sa masu duniya gudu su bar masu iliminsu. 441. Mutum yakan shiga wani yanayi sai ya xauka cewa qarshensa ya zo kenan. Amma daga bisani sai ya gane cewa, wannan shi ne farkon jin daxin sa a duniya. Da yawa qofar da kake zaton ta a kulle idan ka tura ta za ka same ta a buxe tana jiran isowar ka. Kada ka yanke qauna daga alheri. In da rai da rabo . 442. Yi qoqari ka mayar da wuninka kyakkyawa duk halin da ka samu kanka a cikin sa. Idan ka qi ko ka so za ka wuni a cikin sa. 443. Magana mafificiya ita ce ambaton Allah. Kyauta mafificiya ita ce ka yi ma wani addu'a. Rana mafificiya ita ce wadda ba ka sava ma Allah ba a cikin ta. 444. Ababe masu daraja ba su cika maimaituwa a rayuwar xan Adam ba. Shi ya sa kowane mutum uwa xaya kacal gare shi. 31 445. Wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi. Wanda ya sa wani kuka Allah zai sa shi kuka. Duk wanda ya shuka alheri zai ga alheri a rayuwarsa da bayan mutuwar sa. Idan kuwa ka shuka sharri to sharrin ne za ka girba komai daxewa. 446. Kada ka xauka cewa, addu'a makamin raggo ce. Addu'a makamin mumini ce. Da dare yake wasa wuqarta, a wayi gari ya ga aikinta. 447. Ba a son Rowa sai a wuri xaya. Idan ka shiga cikin haqqin mutane za su kwashe ladarka su shige aljanna da ita kana kallo. Yi rowar ladarka. 448. Idan ka shiga gidan mutane ka mayar da kanka makaho. Idan ka fito ka koma kurma. Kamar yadda ba ka son a leqi asirinka kuma a yaxa shi, haka su ma mutane ba su son a leqi nasu ko a yaxa shi. 449. Mai riqe addini ba jin daxi ne bai iya ba. Macce mai hijabi ba ado ne ba ta iya ba. Mai kyauta ba kuxi ne ba ya so ba. Kowannen su ya qware ne wajen sanin abin da ke amfanin sa. Sai ya rinjayi son zuciyarsa. 450. Idan wani ya ce maka wane ya zage ka, ka tambaye shi, ya aka yi ya ji daxin zagi na a gabanka? 32 451. A cikin hadisi Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallam ya hana mutane zagin Zakara saboda yana ta da mutane Sallah. To, me ina kuma ga mai zagin malamai masu wa'azi da karantar da mutane yadda ake Sallah? 452. Yana da daxi ka samu wanda kake so. Yana da daxi ka samu wanda ke son ka. Abin da ya fi wannan daxi shi ne ka samu wanda zai sa ka san Allah, ka so Allah, ka bi Allah. 453. Ka yi hulxa da mutane a matsayinsu na mutane. Kada ka auna mutane da kuxi ko matsayi ko wani abin duniya. Abin duniya mai wucewa ne ya bar xan Adam a kan matsayin sa. 454. Gano Abin da mutane suke so ba shi ke da muhimmanci ba. Abin da yake da muhimmanci shi ne ya za ka zama wanda mutane suke so? Wanda ya fi shi muhimmanci shi ne sanin ya za ka zama wanda Allah yake so? 455. Karanta littafi ba shi yake da muhimmanci ba kamar sanin me ka qaru da shi a cikin sa? 456. Rayuwa tana ba ka wata dama a kullum sunan ta "Gobe". Abin da ya gagare ka a yau sai ka hari gobe da shi. Gobe ma rana ce. 33 457. Kowane mutum yana da wani rubutu a goshinsa wanda ido bai ganin sa amma masu hankali suna karanta shi. Abin da aka rubuta shi ne: "Ka kula da ni. Ka ba ni muhimmanci". 458. Ka je duk inda kake so. Ka vuya duk inda kake so. Amma kada ka manta komai daxewa sai ka tafi wajen Allah. A yau ake aiki, gobe ranar sakamako ce. 459. Wasu mutane ba ka iya tuna farkon haxuwar ka da su, amma sukan zama jigo a rayuwarka. Sanin Maza jari ne. 460. Ka zama kai kaxai ya fi kana tare da wanda bai dace ba. Nemi abokin qwarai. Zama da maxaukin kanwa shi ke sa farin kai. 461. Babu Abin da yake tabbas a duniya sai Canji. Komai ka gani a yau watarana zai canja daga yadda ka san shi. Komai yana canjawa ban da sarautar Allah. 462. Ruwan gulbi da na teku duk ba su iya kashe wutar lahira. Amma hawayenka za su iya. Hawayen tsoron Allah ko na tausayin bayinsa su ke kashe wutar azabar Allah. 463. Maganin ciwo haquri. Maganin wauta kawaici. Maganin gajiya bacci. Maganin matsala addu'a. 34 464. Qwaqwalwar mutum kamar lema ce. Ba ta aiki sai an buxe ta. 465. Ka riqe gaskiya, kada yawan mabiya ya ruxe ka. Shaixan ya fi kowa yawan mabiya, amma ba za su hana shi shiga wuta ba. 466. Duniya rana biyu ce. Ta farko taka ce, ta biyu ta xan uwanka. A ranarka kada ka yi rowa. A ranar xan uwanka kada ka yi raki. 467. Yarda da kai ba girman kai ba ne. Kuskure xaya ba ya nuna mai mugunta. Girma ba a babbar riga yake ba. Mai girma shi ne wanda ake so, kuma ake samun alheri a wurin sa. 468. Kada ka raina kanka don wani ya fi ka iyawa. Koma wani fanni ka nemi taka qwarewa. Kowa da irin hikimar da Allah ya ba shi. 469. Sarki abin girmamawa ne a garin sa. Malami abin girmamawa ne a garin kowa. 470. Babbar bishiya ta fi ba da inwa fiye da yadda take ba da 'ya' ya. 471. Ka aurar da xanka duk sadda kake so. Ka aurar da 'yarka duk sadda ta samu miji. Idan Macce ta samu mijin tsara ba daidai ne ayi masa jinkiri ba. 35 472. Idan Alqur’aninka ya yi qura ka zargi kanka. Duk wanda ya kwana uku bai karanta Alqur’ani ba lallai ne zuciyarsa za ta bushe. 473. Idan ka mutu ma'aikatarka za ta xauki wani ma'aikaci, matarka za ta auri wani namiji, dukiyarka za ta samu wani mamallaki ba kai ba. Ba Abin da za ka je lahira da shi sai aikinka. Gyara lahirarka, kada qyalqyalin duniya ya ruxe ka. 474. Ababe uku suna da wuya amma suna da amfani. Kyauta a cikin talauci, da kamun kai a lokacin kaxaici, da faxin gaskiya a gaban wanda kake tsoro. 475. A lokacin da kake qarami kana ganin laifin manya idan suka yi maka gyara, amma da ka girma sai ka gane su ne daidai. A lokacin kana makaranta kana ganin laifin malamai idan suka matsa ka bi doka, da ka zama Malam sai ka gano ashe su ne daidai. Ka riqa ba da uzuri ga wanda ba matsayin ku xaya da shi ba, wataqila watarana za ka gano shi ne daidai. 476. Gaskiya zuma ce. Akwai harbi amma tana da zaqi. Wanda aka buge shi da bulalar gaskiya bai faxi ba, ka sa masa ido, idan ya qarasa gaba zai faxi. 477. Ana ba da baya wani lokaci ba don tsoro ko jin girman kai ba. Sai don kauce ma karo da wanda bai dace ba. 36 478. Mai hankali idan ya yi magana sai ya kawo hujja. Wawa idan ya yi magana sai ya yi ta rantsuwa. Mai gaskiya ba ya buqatar rantse rantse. Gaskiya ba ta neman ado. 479. Ana samun Rayuwa mai daxi ta hanyar barin wasu abubuwa fiye da yadda ake samun ta ta hanyar samun wasu. 480. Wanda yake ba da turare ba za a rasa qamshi a hannunsa ba. Mai yin alheri ba zai rasa samun alheri ba. 481. Mai mugun hali kamar mataccen shantali ne. Ba a iya amfani da shi, kuma ba a iya mayar da shi ya koma laka. 482. A duniya mutane iri huxu ne: Wani yana bin Allah kuma yana cikin jin daxi. Somin tavi ne aka ba shi. Wani kuma yana bin Allah amma yana cikin wahala. Wannan yana cikin jarabawa. Na uku ba ya bin Allah kuma yana cikin wahala, wa'azi ake yi masa. Na huxu yana cikin savon Allah dumu dumu amma yana walwala da jin daxi. Wannan an yi masa kamun talala, idan mutuwa ta riske shi ba mafita. Allah ya kiyaye mu. 483. 'Ya'ya ba su cika sanin irin son da iyaye ke yi masu ba har sai sun girma sun haifi nasu 'ya'ya su ga yadda suke son su. 37 484. Komai yana da musaya a duniya. Macce za ka auri wata, 'ya'ya za ka haifi wasu, abokai ma za ka samu wasu. Iyaye ne kaxai ba su da musaya. Mu san matsayin iyayenmu. 485. Wayewa ba ita ce sanin duniya ba. Wayewa ita ce sanin manufar da ta kawo ka cikin ta, da neman gamawa lafiya da ita. 486. Mutum xaya, a kwana xaya, zai iya rusa abin da mutum xari suka yi a kwana xari. Gwani shi ne mai gini ba mai rusau ba. 487. Allah ya yi mutane don a so su, ya yi kuxi don a kashe su. A yau muna cikin matsala ne don muna son kuxi, muna kashe mutane. 488. A lokacin da kake cikin damuwa ka tuna wani na can yana fatar kasancewa a cikin yanayinka. Wani yana gudun hijira, wani yana kurkuku, wani yana asibiti, wani ma yana cikin kabari. Gode ma Allah, ka ci gaba da rayuwa. Ba kullum take salla ba. 489. Aljanna da Wuta duk na masu zunubi ne. Wuta ta masu zunubi ce su kangare. Aljanna kuma ta masu zunubi ce suna tuba. 490. Idan ka yi zunubi sannan kuma ka ji cewa Allah ba zai yafe maka ba to Shaixan ya yi maka bugu biyu kenan. 38 491. Wanda ba ya fahimtar shirunka ba lallai ne ya fahimci maganarka ba. 492. Idan zuciyarki ta nuna maki sha'awar ki bayyana sashen jikinki don mutane su gani, ba damuwa. Ki bayyana iya wurin da kike son wutar jahannama ta qone shi. 493. Kafin ka yi alfahari da iyayenka, yi qoqari ka zama abin alfahari ga 'ya'yanka. 494. Mabuxan talauci guda uku ne: Bacci da Rowa da Tsoro. 495. Jin daxin duniya shi ne ka tuna babu abin da zai same ka sai wanda Allah ne ya qaddara maka. 496. A duniya mutane goma ke akwai. Xaya yake aiki, biyu suke yabawa, uku na gunaguni, huxu suna zagin sa. Manta da mutane, ka yi aikin gabanka. Ka tuna: Nasara ba ta da qafafu da za ta cim ma ka, kai ne kake da su. Yi hanzari ka same ta. 497. Ka nisanci mugun zato domin kai yake cutar wa. Ka yi hattara da qeta domin mai yin ta ne take cinyewa. Ka kiyayi hassada domin mai yin ta zuciyarsa ke bushewa. Kada ka zargi iyali domin aure yake kashewa. Tsaftace zuciyarka a wajen hulxa da kowa. Wannan shi zai ba ka ni'imar duniya ta haqiqa. 39 498. Imani shi ne ka nemi yardar Allah ko da mutane za su yi fushi da kai. Kada ka gode ma kowa a kan arzikin da Allah ne ya ba ka shi. Kada ka zargi kowa a kan abin da Allah ne bai ba ka shi ba. Arziki nufin Allah ne, kuma rabo ne da yake bayar wa ba tare da ya yi shawara da kowa ba. 499. Bayarwa ba shi kaxai ne kyauta ba. Hanawa ma wani lokaci kyauta ce. Voye aibin xan uwanka, ko voye masa cutarka, ko kame masa harshenka, duk wannan kyauta ce abar godewa. 500. Idan kana son gane duniya kake so ko lahira? Ka duba, wane ka fi farin ciki da shi wanda zai ba ka, ko wanda za ka ba? Mu haxu a kashi na uku cikin yardar Allah 40 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels