Sunana Aisha farida umar, 'yar asalin jihar katsina amma zama ya kai kakannina garin shagamu. Anan aka haifi mahaifi har yayi aure aurensa ya hayayyafa don haka babu garin da muka fi sani wanda ya wuce shagamu. Mahaifiyata ma 'yar garin shagamu ce. Yanzu shekaruna ashirin da uku a duniya, na fito daga dangi wadanda suke talakawa liki. Ilahirin dangina kakaf na wajen uwa dana wajen uba basu da hali. Koda yake akwai daidaiku masu rufin asiri amma ba za a kira su masu arziki ba amma dai sunfi wasu. Wannan dalili yasa bamu cika karatu mai zurfi ba wasu daga primary suke tsayawa, wasu sun shiga scondary amma talauci sai yasa a cire su basa karasawa. Masu dan gara gara ne ma suke kammala secondary amma fa jami'a ta gagaresu sai dai kallo. Danginmu suna da dimbin yawa mata da maza, yara da manya gamu da tsofaffi tukuf tukuf Allah Ya ara musu tsawon rai. Mahaifina yana daya daga cikin dattijan domin ya tsufa jagof, tun tashi na daman a tsohonsa na ganshi har ya makance saboda tsufa. Shine babba a cikin 'yan gidansu don haka yafi kannensa tsufa kuma yafi sauran 'yan uwansa talauci kasancewar yafi su tara mata har guda hudu da tulin 'ya'ya har guda arba'in da uku. Nice 'ya ta arba'in da biyu a wajensa, kanwata guda daya kacal mai suna munauwara. Mu biyu ne kadai muke uwa daya uba daya a gidan domin mahifiyarmu ce amaryarsa, ya aure ta tana kankanuwa yayin da yake tsohonsa. Sauran matansa ma duka sun tsufa wasu daga cikin manyan 'ya'yansa sun girme ta suma har sun aurar da 'ya'yansu suna da jikoki wadanda suka fini ma. Don haka ban mori dadin uba ba, sanda na fara wayo baya ganina kasancewar ya makance. Aikina shine kullum inzo dakinsa in riko hannunsa in fito dashi kofar gida sai in zaunar dashi akan kujerar katakonsa sannan ni kuma in zauna a gefensa ina sauraron hirar da sukeyi shida abokansa, makwabtansa da 'yanuwansa tsofaffi. Ina jin dadin sauraron tsofaffi labarai masu al'ajabi na mutanen da. Ina fahimta sosai kuma ina rikewa a kwakwalwata tas, babu abinda nake mantawa harma idan suka fadi wata kalma da ban sani ba sai in tambayesu su bani amsa. Idan babana ya aike ni dauko ruwa, fura ,koko ko kuma kurtun tofin yawunsa a dakinsa sai inji duk raina ya baci saboda za'a tsallake wani shashi daga cikin hirar. Sai in zura da gudu don inyi sauri in dawo kada a wuceni, idan na dawo kuwa na sa su dole su dawo da labarin baya. Anan na koyi iya magana mai ma'ana da jan hankalin mai saurarona da kuma fitar da lafazai masu girma da hikima tamkar wata babba. Daga nan na samo suna "Farida tsiri" inji kawayena haka suke kira na domin duk wanda na zauna dashi zaiyi tunanin wayona yayi yawa zan cuce sho ko zanyi masa dubara ko in yaudare shi. Duk sanda zanji labarin anyi gulmata bai wuce ace na cika iyayi ba da dadin zance rai-rai-rai kamar aku. Ko kuma ace na cika kissa da kisisina bana fushi ko ma za'ayi min, ga tsiri ina magana kamar wata tsohuwa wacce taga jiya taga yau. Ina jin dadin halayena kuma dashi nake cin ribar zaman duniya. Zan iya zama da kowanne irin mutum ne komai bakin halinsa da muguwar zuciyarsa, duk sharrinsa ko alkhairinsa haka kuma duk in da ya kai ga masifa da zafin rai zamu zauna lafiya. Da kowacce irin kabira zan iya zama lafiya. Da bakar fata da inyamuri, hausa, babarbare, bafillatani, bayarabe, ibira ne, tangale ne, mumuye ne, margi ne, basayi ne, ba'are ne, dan niger ne ko kuwa adon dawo ne dan bur sudan duk na san yadda zan tafiyar dasu. Mahaifina yana da yawan magana ba zai iya zama shi kadai ba, ba tare da bakinsa yana motsi ba, sai na gado sho don haka tamu tazo daya sai mu hadu muyi tayi. Har baya so in matsa daga gabansa don haka ban cika zuwa makaranta ba, ko yayyena zasu korani sai in ruga da gudu dakinsa in labe a bayansa. Sai yace musu "inga mara kunyar da zai shigo ya banbare aisha daga bayan, baza taje makarantar ba nan dakin ma makaranta ce". Aji ne mai zaman kansa don darasi take duka na iya rayuwar zaman duniya. Ku fada min ko a jami'a wanne darasi ne za'a zaunar da dalibi a karanto masa rayuwa karara balle dan primary aji daya? To ku kyale ta ba in da zata je sai ta ga dama sannan zata je makarantar. Dalilin zuwanta makaranta don ta koyi rubutu ne kawai. Idan sukaji yana fada basa karasowa cikin dakin, su gama labe-labensu ina hango inuwarsu ta jikin asabari sai inki fita, sai sun gaji da jirana sannan su tafi. Idan hantsi yayi sai inje zaure in kinkimo kujerar katako in kai masa kofar gida, sannan in share wajen in shimfida tabarmi a kasa wasu tabarmin in shimfida akan wasu dakali biyu da suke kofar gida. Sannan in dawo dakinsa in mika masa sandarsa na riko hannunsa in fito dashi kofar gida wajen kujerarsa, sai ya laluba ya zauna sannan in koma gefensa in zauna sai ya fara bani labari ko tatsuniyoyi. Sannu a hankali sai 'yan majalisarsa su fara bulbulowa daga gabas wasu daga yamma wasu daga barin kudu, wasu daga arewa. Yawancinsu kannensa ne uwa daya uba daya, ko uba daya. Wasu kuma kakanni suka hada, wasu makwabtaka ce ta hada ko auratayya, wasu kuwa manyan abokansa ne da akayi kuruciya tare. Babu wanda yake da kasa da shekaru sittin a wajen. Anan na samu tarbiyar girmama babba duk kankantarsa, domin idan na gaishe su daga tsaye ko daga zaune ba zaus amsa ba ko kuma inji duka dal a bayana wai nayi rashin da'a. Sai kaji sun daka mintsawa suce inzo in durkusa har kasa sannan in gaishe su. Tun ina jin haushin inyi kuka har na daina, tun ina mantawa har na saba. Sannan na koyi durkusawa har kasa idan zan mikawa babba abu koda kuwa da kadan ya girme ni kuma da hannu biyu. Sun hana ni mikawa sa'ana ko yaron dana girma abu a wulakance ko da hannun hagu. Sun gargadeni ni da na guji wulakanta dan adam ko da kuwa almajiri ne domin babu kyau wulakanci da girman kai. Anan nakoyi daubarun cin jarabawa a makarantar boko ko kuma saurin haddace kur'ani a makarantar allao. Sunce in zamana mai yawan kallon bakin malamina ina sauraro, ina ganin yadda yake fitar da lafazinsa daga hanka, ganda, tantanin makwallato da kuma dumbarun bakinsa. Yin haka zai sa in dinga fitar da kalma yadda ake bukata a fada. Kada in dinga zama a bayan aji, ko da yaushe kujerata ta zamana a gaban malam saboda gudun yin wasa da yara. In zama mai yawan tambayar duk abin da ban gane ba anan take ba sai an wuce wajen ba. Sannan in dinga kwafar rubutu daidai in da ban gane ba ko ban gani ba in tambayi malam ko wani na kusa dani wanda nasan yasan abin da yake yi. Kada in sake in koma gida in yarda jakata ko allona ba tare da nayi bita ba. Sunce da zarar naci abinci na huta in samu lungu in shiga inyi ta tilawa zanji na fahimci abin da ban gane ba a a aji watakila saboda yunwa ko gajiya ta hana in gane a lokacin. Suka shawarce in yawaita yin aikin gidan (homework) tare da yayyena wadanda suke ajin gaba dani, kada in sake in dinga yi ni kadai ba tare da wani ya duba min ba. Duk abinn nan dana fada min na haddace sai dai anan nake zubarwa saboda bana kaunar zuwa makaranta, har gara ma makarantar allo dan itama a kofar gidanmu take dole inje. Idan rana ta bude sai majalisa ta yoye, ni kuma sai kama hannun tsohona in shiga dashi daki sannan inje in karbo masa abincin rana daga wajen matar da take da girki. Tuwo ne dai na masara ko na dawa, miyar kuka ce ko danyen karkashi. Shinkafa sai jifa jifa ake siyowa a dafa ko kuma idan an samu wani dan albarka cikin yayyena ko sirkiai su kawo mana a dafe ko danye. Da yamma sai in sake zuwa inyi shimfida in fito dashi, 'yan majalisarmu basa tashi basa manta lokacin sai kagansu daya bayan daya suna bulbulowa. Duk wannan zance da nake yi muku ina da shekara hudu ne zuwa tara, ban cika shekara goma ba a duniya Allah Ya karbi ran mahaifina. Mahaifina ya rasu a ranar wata juma'a da safe. Bazan taba manta wannan ranar ba saboda itace ranar dana taba makara ban tashi da karfe bakwai na safe banje wajensa ba, domin kullum karfe bakwai a dakinsa take min. Wannan kuwa ya faru ne a sanadiyar wata kasala da wani yanayi da jikina yake min ba dadi. Ni ba mai barci ba, haka ni ba ido biyu ba. Tamkar wani abu mai nauyi aka saka aka dirirritseni na kasa juyi. Sai dai kuma idona a rufe ba kamar mai tunani kamar mai mafarki domin abinda nake nanatwa hirar da mukayi da mahaifina ce a daren jiya kafin inzo in kwanta. Daga ni sai shi bayan 'yan majalissa sun watse muna labari kamar yadda muka saba. Ya laluba ya dafa kaina yace aisha ki zama mai rikon amana a rayuwarki yin haka zai ja miki farin jini a wajen al'umma. Ki kiyayi munafunci, ma'ana gulma shine yi da mutum yin haka zai zubar miki da kima. Ki guji sata duk rintsi kada ki taba abin wani yin haka zai zubar miki da mutunci ke da zuri'arki gaba daya za'a dinga yi muku gori. Ki guji yin zina, laifi ne a wajen Allah kuma rashin mutunci zai dasu a idon jama'a zaki zama abar zagi, kowa ya fada miki magana, sai ki zama ballagaza ko yaro karami ba zai girmamaki ba. Ki kiyayi kwadayin abin wani, ki nema naki na kanki duk kankantarsa ki hakura kiyi amfani dashi shine zaman lafiyarki da farin cikin rayuwarki. Kada ki raina baiwar da Allah ya baki, kada ki dinga ganini wadanda suka fiki. Kada zuciyarki ta mutu kice ba zaki shiga ku fafata ba, ki zama mai karfin zuciya da kudiri na alkhairi kada zuciyarki ta dinga karaya. Sannan ki zama mai godiya ga Allah a duk halin da kika tsinci kanki na dadi ko wuya. Ki zama mai yawan kyauta ko abinda kika mallaka kalilan ne kada ki makale hannu kice baki dashi, sai ranar da kika samu da yawa zaki dinga bayarwa. Ki nemi ilimi mai yawa, na muhammadiyya dana zamani komai wuya domin kada a barki a baya a rayuwar duniya da lahira. Allah Yace mu nemi ilimi a duk inda yake domin sai munsan shi zamu bauta masa. Allah baya karbar ibadar jahili, har baccin mai ilimai yafi jahilin da zai kwana yana sallah. Sai naji mahaifiyata tana girgiza ni tana ta ambaton sunana, idan na bude ido na dube ta sai in koma in kwanta har sai da ta daga ni zaune. Tace dani wanne irin bacci ne haka har tara da rabi tayi baki je kin kaiwa babnki koko ba, bayan kinsan baya jin dadin jikinsa? Cikin magagin bacci nace mata yau baba ya fita kofar gida da kansa, yayi shara yayi shimfida da kansa. Sai ta harareni tace karyar banza, a mafarki ko a ido biyu? Yaushe kika ganshi ke da na tashe ki dakyar? Sai na tuna ashe mafarki ne don haka na mike a firgice ko sallah banyi ba na fita kofar gida na hau shara, na fitar da kujerarsa da tabarmi kamar kullum. Sannan nazo na dauki koko a kwanon sha da kudaya na duma na nufi dakin tsohona. Wata irin al'ada ce matan gidanmu sukeyi wai mata mai girki bata shiga dakin miji saboda kada ayi gulmarta ace ta cika jaraba, tsohon Allah sai anje an nanike maka, makahon da yake ta kansa yau da lafiya gobe babu. Kina shiga dakinsa za'a fara lekowa ta lungu lungu ana kus kus, kina fitowa kuwa zaki hadu da harara , zumde, yafice da habaice habaice. Tsakanin shi dasu gaisuwa daga bakin kofa ya fadi abinda zai fada ki juya idan kin zuba masa abincin ki aiki 'ya'yanki ko jikokinki su mika masa. Daga baya ma da aka ga nice karama mai shiga wajensa kullum sai aka dora min alhakin kai masa abinci kullum, duk wacce ta gama sai ta kwalla min kira inzo in kai masa abinci. Na shiga dakinsa sai na iske shi a lullube kamar mai bacci, sai na zata lambo yayi ko fushi yake yi dani dan banzo da wuri ba. Nayi ta sallama shiru, sai nazo dai dai kunnensa na durkusa na gaishe shi bai amsa ba, sai na shiga yi masa bayanin abinda ya tsayar dani, shimfida nayi har su malam shehu sun fara zuwa. Sai naji yayi shiru bai motsa ba, sai kawai na bude lullubin sai ga idanuwansa a kakkafe yana kallon sama kamar mai murmushi. Nace lallai baba kana jina ashe kayi kasake kana kallon sama kana murmushi. Sai bai bani amsa ba! Ni kuma sai naji raina ya baci, sai nayi fushi na tashi na fita bakin kofar dakin na zauna ina kumbure kumbure. Matan gidan suka fara yimin tsiya suna cewa ke kuma me akayi miki? Ke da baban naki ne kuma yau ake jin kanku "yar lelensa wacce baya bari a taba ki. Sai nace dasu yana ji ina tayi masa magana yaki kulani, idonsa biyu yaki yi min magana idanuwansa suna kalllon sama kamar yana murmushi. Sai jikinsu ya fara basu tabbas akwai wata matsala domin suma sun leka suna gaishe shi bai amsa ba duk da dai anji motsin alwalarsa da asuba amma baya baccin safe. Sai matansa suka kutsa cikin dakin da sauri kuma a gigice. Kururuwa da lafazansu ne ya gigita ni, har yau ban kara jin mummunar kalma a kunnena irin ta ranar ba. Suka ce wayyo malam babu, malam ya mutu, munga ta kanmu, ihu mun shiga uku, rumfa ta gaji da shirgin kaya ta rushe. Ire iren kalaman da suke fada kenan suna rusa kuka kururuwa. Sai naji zuciyata ta hau dukan uku, na dafe kirjina na fada a bayyane nace Innalillahi wainnailaihi rajiun. Allah Ya jikanka baba, Allah ya sa aljannah ce makomar ka. Allah da Ya karbi abunSa dan yafi mu sonsa, daga gareka muka zo kuma gare Shi zamu koma. Da ka tafi ba kayi gaggawa ba haka mu da muka rage ba muyi nawa ba. Sai manyan maza da mata suka jeru a kaina suna kallona babu wanda ya kara magana balle ihu. Mamaki marar iyaka zaka dinga hangowa daga cikin idanuwansu. Ina salati ina hawaye cikin natsuwa ba tare da kwarmato ba. Sai yaya hussaini ya fashe da kuka yace farida lallai baba ya shigar dake makaranta, ya saka ki a aji ya koyar dake darussan dako a jami'a ba za koya miki ba. Baba yayi gaskiya da yake hana ki tafiya daga wajensa har sai da kika koya ilimi wanda zai isheki zaman duniya da lahira. Ya juya ya duba iyayensa da 'yan uwansa yace wannan abinda farida ta fada ya zama darasi a wajenku, wa'azi ne, nasiha ce zuwa gare mu. Ihu da kwarmato da dora hannu aka kuna fadin mun shiga uku, ina zamu saka kanmu? Gatanmu ya fadi. Dawa zamu zauna a duniya? Rumfa ta gaji da shigi ta rushe. Dukka sabo ne, bata ne, jahilci ne, azaba kuke karawa mamaci. Tabbas idan ka saba da abu ranar da zaka rabu dashi akwai ciwo, kuka wajibi idan akayi mutuwa amma ba'a son ihu da kururuwa. Kamata yayi ayai ta karanta innalillahi wainna ilaihi rajiun sannan ayiwa mamaci fatan samun aljannan. Ku dubi karamar yarinya nan farida itace kusan wacce tafi kowa kankanta a cikin gidan nan amma ita kadai ce tayi abinda ya dace , itace wacce tafi mu shakuwa dashi, tafi mu sonsa, kuma itace tafi mu nuna masa kaunar da take yi masa shine data yi masa addua. Muyi koyi da ita don tafi mu ilimi, tafi mu sanin ya kamata. Sai suka daina ihu suka koma suna ambaton sunan Allah. Yaya hussaini ya tashe ni tsaye yasa gefen rigarsa ya goge min hawaye. Yace ki daina kuka 'yar karamar kanwata, kowa yasan ke aka yiwa mutuwar nan sai kuma kika fi kowa yin tawakkali haka Allah yake so. Ina mai yi miki albishir Allah ba zai bari ki wahala ba, da izininsa ba zakiyi kaskantaccen maraici a rayuwarki ba, duk da kin rasa mahaifinki a lokacin da kike da karancin shekaru saboda baki mance da Ubangijinki ba wanda shine gatan ki. Allah Yana tare da duk wanda yasan da Shi kuma wanda yake neman taimakonsa. Farida nayi miki alkawari zan dauki nauyinki, zan rike ki amana har izuwa ranar da zan aurar dake saboda wannan tawakkalin da kika nuna, zan rike ki tamkar 'yar dana haifa ta cikin. Wacce hakkin cinta, shanta, suturarta, tarbiyyarta, iliminta da suka wajaba a kaina har zuwa ranar da zan aurar da ita sannan nauyinta ta koma hannun mijinta. Ki shiga ciki wajen baba kiyi masa sallama, kiyi masa irin adduar da kika yi masa yanzu ta neman gafara da rahamar Ubangiji. Mutuwa ce kadai ta raba kaunar dake tsakaninku. Na juya da sauri na shiga wajen tsohona, durkusa a gabansa setin kunnensa na tofa masa kulhuwallahu ahad uku, sannan nayi masa adduar samun aljanna da neman hasken kabari. Nayi masa fatan Allah ya sa ya tashi a cikin gafartattun bayi a cikin alummar manzon Allah (SAW). Sannan mahifiyata ta jawo hannuna muka fito waje, cikin kuka mai tsanani tace dani farida na yafe miki duk abin da kika yi min. Allah yayi miki albarka a rayuwarki ta duniya da lahira. Alhamdulillahi nayi dace da 'ya ta gari, mai jin kan iyayenta. Ina fatan nima zakiyi min irin wannan adduar idan na riga ki tafiya. Muna zazzaune a tsakar gida maza suka shiga sukayi masa wanka, suka hada shi suka fita da shi akayi masa sallah. Aka dauke shi aka tafi dashi gidansa na karshe, gidan da ba'a fitowa unguwa, gidan da ba'a leke, gidan da ba'a jiyo motsinka balle a gaishe ka ka amsa wato kabarinsa. Bakina bai gushe da karanta masa kulhuwallahu ba da inna a'adaina kalkausar har karshe. Shi ya bani adduar yace ita ake so a dinga karantawa mamaci. Da akayi sadakar bakwai sannan aka watse, lokacin mutuwa ta dawo min sabuwa fil, idan aka tashe mu daga bacci za'a tura mu tafi makarnatar boko sai in nufi dakinsa zan buya sai in ga a rufe sannan in tuna ashe ya rasu, dole a tura keyata zuwa makaranta raina baya so, da yamma ma sai a tura ni makarantar allo. Ina tuna nasihohin da tsohona da abokansa sukayi min na dabarun samun nasarar karatu, sai nake bin duk yadda suka umurce ni sai naga ina ganewa kuma ina cin jarabawa don haka saina fara jin dadin makarantun da nake zuwa, na dawo ina zuwa makaranta da kaina ba sai an tura ni dole ba. Ranar asabar da lahadi muna zuwa makarantar allo da safe da yamma amma ranar alhamis da juma"a da yamma ba ma zuwa koina don babu makarantar allo, sai na fitar da kujeran babana in shimfida tabarmi kamar yadda na saba. Sai inga tsofaffin nan suna zuwa daya bayan daya suna zuwa suka taru kamar yadda suka saba da, don har sun daina taruwa tun bayan da ya mutu. Baba ahmadu ne ya maye kujerar babana shine babba ina gefensa koda yaushe, duk sanda suka kalle ni sai inga suna hawaye suna tausayina da alama suna tunawa da yayansu, abokinsu, amininsu, makwabcinsu, abin kaunarsu. Zaman majalisar yakoma ranar alhamis da juma'a ne kawai da yamma. Kuma munci gaba da hirarrakin mu kamar yadda muka saba. Bayan rasuwar mahaifinmu da shekara guda yaya hussaini yayi aure, ya auri 'yar kanin babanmu mai suna abida dai dai lokacin daya sami dan karamin aiki a union bank, da certificate dinsa na secondary a matsayin masinja a branch na kano dan haka kano ya kauro damu. Da zamu tafi mahifiyata ta hada min kayana kakaf tana kuka ina kuka, kanwata munauwara ma tana kuka, 'yan gidan kacokan suka fito suna mana fatan Allah Ya kiyaye hanya da fatan Allah Ya bamu zaman lafiya, Ya hada mu da abokan arziki a can. Muka tare masu babura biyu muka hau da jakunkunan kayanmu muka nufi tasha, muka hau doguwar mota mai zuwa kano. Kano ta dabo tumbin giwa, mai mata da motoci ko da me kazo an fika. Rabona da shagamu kenan har yau ban sake komawa da sunan zama ba sai dai inje da sunan ziyara. A wata unguwa a cikin kano mai suna sharifai zauran tudu, yaya hussaini daman ya kama mana haya tun kafin muzo, a gida mai dakuna bakwai muka kama dakuna biyu. Don haka mutane ne da yawa a cikin gidan, bandakin daya ne kacal, kicin daya da tsakar gida daya ake amfani dasu mata da maza, yara da manya. Abunka da gidan yawa, kazanta ba'a magana. Gashi daman gidan ya tsufa ya farfashe ba gyara sai warin bola da kwata kowa kyashi ya hana shi gyarawa. Idan ka share cikin dakinka da kofar dakinka ka gama shara babu wanda zai share tsakar gidan da zaure balle kofar gidan. Ga gida a lungu ko mota bata shiga lokon, ga wata tafkekikyar kwalbati da ta cinye fadin lungun, kowa a tattakure babu sakewa, yara basa iya wasan guje guje su more sboda matsi. Haka kowacce mace ta baza kayan san'arta a cikin gida, cikin zaure ko kofar gida saboda sai an taimakawa mazan rayuwar zata tafi dai dai. Daman mazan da yawansu buga buga sukeyi, wani sai ya dawo gida babu abinda ya samo, da dan kudin sana'ar natar za'a yi cefane kuma ta bawa yaranta kudin makaranta. A gidan ma har gara yaya hussaini tunda yana daukar albashi duk tsiya dai karshen wata zai samu duk da dai dan albashin bashi da yawa kuma rabin kudin a acaba yake tafiya, kafin wata ya kare sai anci bashi dole kafin a biya an jigata. Duk da haka dai munfi sauran, muna dan cancanawa dai muna rayuwa. Ni da abida muka fara sana'a, muna soya wainar fulawa a kofar dakinmu, kuma ana saya ba laifi duk da cinikin naira biyar biyar ne, duk da haka muna samun na sayan maggi, gishiri, a ciki ake bani kudin makaranta da kudin dinkin tsummokaran mu idan sun yayyage. A makarantar bokon cikin unguwa aka saka ni, kamar sauran yaran unguwar haka aka saka ni a makarantar allo da yamma ta islamiya da daddare. Bana fashin zuwa makarantar kullum saboda ina tsoron yaya hussaini sosai, baya yi min wasa koda yake matarsa ma baya sakar mata fuska , mutum ne mai zafin zuciya. Lallaba shi muke kamar kwai. A daki daya nake zaune babu komai a ciki daga 'yar karamar katifa sai 'yar jakar kayana ta buhu a gefe ko ledar daki ba'a shimfida ba sai tsurar ragargajejjen siminti da wani yagulallan labule. Dakin su abida da mijinta ne mai labule mai kauri, an shimfida leda a kasan da katuwar katifa sai akwatin kayansu a gefe. Kayan kitchen da danyan abinci suna dakina wasu a dakinsu. Haka muke rayuwa amma muna farin ciki saboda mun sami ci gaba fiye da a garinmu tunda daman can a cikin talauci aka haife mu. Bayan kaurowar mu da shekara daya mahaifiyata ta tara kudin motarta da guzurinta tazo ganina sabida tun kaurowarmu bamu je shagamu ba, saboda matsalar tattalin arziki sai ita tazo dan taga yadda muke rayuwa don koda yaushe magana ta takeyi don tana sona sosai har fiye da 'yar autarta. Nayi murna matuka da ganinta har ita ta fini murna, yaya hussaini da matarsa ma sunyi murna da ganinta kuma sunji dadin tsarabar da ta kawo mana. Ni da abida atamfa dai dai ta kawo mana, yaya hussaini ta kawo masa yadi, sannan ta kawo mana doya, dankali, ayaba da lemo jifgi guda. Allah cikin ikonsa cikin daren data zo muna kwance da ita a dakina ciwon ciki ya turnuke ta kafin in bugawa yaya kofa ya fito don a kai ta asibiti rai yayi halinsa. Ummata ta mutu a gabana ina kallonta ban isa in hana ta tafiya ba, Ubangiji ya nemi kayanSa. Sai na tuna wasiyyat da ta bar min cewar idan ta riga ni mutuwa inyi mata addua kamar yadda na yiwa mahaifina. Nayi mata addua sosai kuma ban manta ambaton innalillahi wa'innalialhir rajiun ba har gari ya waye. Sai dai nayi kuka mai yawa saboda na kara wayo na san zafin mutuwar sosai ba kamar da ba, na tausayawa kaina sai nafi tausayin kanwata munauwara. Gata karama ita kadai ta rage babu uwa, babu uba, babu ni 'yar uwarta. Nasan a gidanmu 'yan ubanci akeyi kowa yana tattalin 'yan dakinsu, nasan sai dai dangin mahaifiyta ne zasu dauke ta suma kuma duka kanwar ja ce, talauci ne tsagoronsa. Rashin kudin motar da za'a kai gawarta shagamu shi ya hana yaya ya kai ta can a binne sai kawai ya buga waya ya sanar dasu wannan mummunan labari. Sun kuwa gigice da jin haka sai suka yanke shawara gara wasu su taho kanon ayi jana'iza a binne ta anan. Allah Ya rubuto anan kasarta take. Da suka iso sai akayi mata sallah aka binne ta. Kafin kwana bakwai wasu daga cikin danginmu sai da suka zo kano sukayi gaisuwa sannan suka koma, wasu da yawa basu sami damar zuwa ba, da yake a can ma ana zaman makokin don ba kowa yake da kudin zuwa ba. Da akayi albashi ni da yaya hussaini da matarsa mukaje shagamu don yin gaisuwa da kuma zancen abinda ta bari. Baiwar Allah bata da komai daman mijinta bai bar mata komai ba, dan matan basu samu gida ba! Basu samu gona ba. Ko mu 'ya'yan kudi kadan aka bamu da akayiwa gidan da gona kudi wani yayanmu ne ya saya dan ba zai rabu ba. Daga ragargajejjen gadonta sai tsumokaren kayanta aka ajiye mana shine gadonmu. Na kasance marainiya babu uwa ba uba, sai ni sai halina sai kuma yayana hussaini da matarsa sai Allah. Kuma ina godiya ga Allah a kowanne lokaci don ban mantawa da nasihohin da mahaifina yayi min ta karshe. Allah yana ganina, kuma Yana taimakona, Bai bari na tagayyara ba. Babbar baiwar da Allah ya min itace daya bani jama'a, masu sona suna da yawa a duniya, mata da maza. Yara da manya kowa yana yabon halayyata koda kuwa an kushe ni sai kaji ana yabona. Na godewa Allah Shine gatana shine majibancin al'amurana. Aisha farida ta rushe da kuka hade da hawaye mai radadin fita. Hawaye ne yake ta kwaranya tamkar an bude ruwa a famfo. Barrister Mu'azzam ya juya ya dubi abokinsa barrister nuruddeen shima ya kalle shi sannan suka juya su dukka suka sake duban aisha farida, suka cigaba da mamakin wannan yarinya mai surutu da zazzakar murya, ga iya magana tana fitar da kalamai dalla dalla a jejjere tamkar wacce wani ya labe yake rada mata. Wannan itace fadi ba'a tambaye ki ba, amma fa sunji dadin sauraron labarinta, yayi ma'ana kuma sun karu da abubuwa da yawa na game da zamantakewar rayuwa. Sannan sun tausaya mata, ta cancanci a tausaya mata domin rayuwarta tana cike da abubuwan ban tausayi. Daga ganin ta a kidme take a dimauce ta fado musu ta gaishe su, kafin su amsa ta sami kujera ta zauna ta hau basu labari. Yau ne rana ta farko da suka fara ganinta a rayuwarsu itama haka, farida batasan wacce irin damuwa bace ta hana su zama a gidajensu suka fito a cikin daren nan suka zauna a wajen shakatawa mai suna "fish park" dake nassarawa GRA. Barrister muazzam ya zaro dan karamin handkerchief fari kal daga gaban aljihun rigarsa (suit) ya mika mata ba tare da yayi magana ba, ta dago da jajayen idanuwanta tana gogewa wani sabon hawaye fil yana bulbulowa daga idanuwanta. Barrister muazzam ya mika hannu a sanyaye kan teburin dake gabansu ya dauko wani kwalin lemo ya tsiyaya a cikin kofuna biyun da suke gabansu ya mika mata, sai ta karba sannan tayi godiya ta fara kurba a cikin nutsuwa yayin da shima ya dauki daya kofin ya kwankwadi lemon a cikin kofin ya mikawa abokinsa shima ya karba ya fara sha ba tare da wani daga cikinsu yace uffan ba. Sai aisha farida ta fara tunanin ko kurame ne bata sani ba tazo ta hau su da surutu, saboda tun sanda ta zo ta zauna ana fiye da mintuna talatin babu wanda yayi ko tari a cikinsu har yanzu sai kallonta kawai sukeyi da ido. Ta kurbi lemo ta ajiye kofin akan teburi ta sharce hawaye da hankicin dake hannunta tayi murmushi. Tace bayin Allah shin baku magana ne, ko kurame ne? Kallonta kawai suke yi har yanzu babu wanda ya tanka mata, su kalleta su juya su kalli junansu. Sai taji hankalinta ya tashi, tayi ajiyar zuciya tace yaya sunanku? Barista nuruddeen ya dubi barr muazzam ya kifta masa ido alamar kada yayi magana. Suka ci gaba da sauraronta tana ta magana ita kadai, sai taji ta zama tamkar wata mahaukaciya wacce bata san ma abinda take yi ba, taji duk ta tsani rayuwarta, sai ta tashi a sanyaye ta juya zata tafi. Barr muazzam yaji tausayinta sai yace aisha farida meyasa zaki tafi? Ta juyo da sauri ta dube shi sai ta girgiza kai tace kuyi hakuri ban san na takura muku ba, na shiga masifa, na shiga kunci har na dimauce ban san dalilin da yasa nazo wajenku na dinga zazzago muku labari baku tambaye ni ba. Na ganku kammalallu dan haka na zata zaku karbe ni hannu bibibuy , kuba bani shawara dan ban san abinda zanyi ba anan gaba. Barr muazzam yace dawo ki zauna, shirun da mukayi miki don bamu sanki ba kuma bamu san manufarki ba kinsan duniya abar tsoro ce bai kamata nan da nan ka yarda da mutumin da baka taba gani ba. Kuncin rayuwar kuwa mun fiki shiga shine ya fito damu nan ko Allah zaisa muji dan sanyi. Ta dawo ta zauna a sanyaye ya yin da take tuhumar kanta da laifin rashin hankali,tana jin haushin kuskuren data tafka daga ganin mutane bata san su ba kawai ta zo ta zauna ta hau basu labari,ta fadi sirrinta bayan ba'a tambaye ta ba,lallai dole suyi mata kallon wata sakarya. Ta tambayi zuciyarta shin ko cutar tabin hankali ce ta kama brain din ta domin sanda ma ta fara magana bata sani ba. Mu'azzam ne ya ktse tunanin da take yi ya ce "ni sunana Barr Mu'azzam,abokina kuma Barr. Nuruddin. Mecece takamaimiyar matsalarki? Menene dalilin da ya fito da ke daga gidanku zuwa nan a cikin daren nan? Naga ba tare da mijinki ku ka zo sayan kifi ba kamar yadda nake ganin wasu ma'auratan hausawanmu na yi? Me kika fito nema? Wanne irin taimako kike nema daga garemu? Kina so mu saya miki kifi ne ko kuwa kudin mota ki ke nema? Ta yi murmushi ta ce "gaskiya ne,na cancanci a tambaye ni domin ban yi kama da mai kamun kai ba. A rude na shigo nan dan yau ne rana ta farko dana taba zuwa nan,ban san inda zan nufa ba sai na hango ku kawai na ji a raina tamkar naga yayyena,wadanda zasu iya taimakona shine na taho wajen ku ko Allah zai sa ku kwace ni daga mugun dan sandan da yake shirin cutar da rayuwata. Barr nuruddin ya dubi abokinsa ya tsuke fuska ya ce "kai kada fa ka yayumo mana ruwan dafa kanmu,ka bar yarinyar nan ta kama gabanta. Me yasa ka dawo da ita har ta yi niyyar tafiya? Ka cika kwashe- kwashe kamar baka san irin yan matan nan ba ne yan club? Idan ba yar club ba wacce budurwar kirki ce zata baro gidan iyayenta ta shigo wajen nan da dare? Ka duba ka ga nisan unguwarsu tun daga cikin gari zuwa nan? Zuwa ta yi ta tsara mu ko daya daga cikinmu zai dauke ta. Ke yarinya ki kama gabanki mu ba irinki bane,je ki can ki sami yan uwanki irin ki. Shawarar da zan baki kuma ita ce ki koma skul ki taimaki lyf din ki don yawan duniya ba riba sai asara,akamr yadda kika ce mahaifinki ya yi maki wasiyya kafin ya rasu" aisha farida tayi dariya maimakon ta ji haishi sai ta gyada kai tace "gaskiya ne yayana na ji dadin shwararka kuma zan dauka insha Allah zanyi amfani da ita. Sai nauyi da kunya ya kama barrista mu'azzam ya ji kamar ya nutse a cikn kasa saboda baranbaramar da abokinsa yake yi,baya kara,ba kunya balle jin nauyi yake maganarsa,ya harare shi yace haba nuraddin kai fa mtsalata da kai kwaba mahgana babu taunawa. Ka bari ka ji uzurinta idan ka gama jin inda ta nufa sai ka yanke mata hukunci. Kamar ba lauya ba ai sai ka gama sauraron labarinta tun daga farko har karshe sannan ka gama jero mata tambayoyi ta gama amsawa ka kula da inda ta nufa sannan ka yi mata nasiha ba fada ba. Yanzu da a kotu muke sai ka fadi a sharia dan kawai kana jin haushin ka sai ka huce akan yar mutane,to ba ita ta kar zomon ba ko rataya ba'a bata ba. Posted by Bashir Sani Mahmud on 22 Aug 2017 Aisha farida tayi karfin hali tace ba damuwa, ai laifina ne dan banyi kama da mai kamun kai ba, tunda ba'a tambaye ni ba nazo na fara yi muku surutu, nasan ba'a son mace marar kamun kai. Barr muazzam ya girgiza kai yace zuwanki nan ba laifi bane dan kin zo kin zauna a kusa damu, kujeru ne a jejjere kowa zai iya zuwa ya zauna. Da kika zo kika same mu kinyi mana sallama duk da tun kafin mu amsa har kin zauna. Daman kamata yayi ki gabatar mana da kanki kuma kinyi hakan sai dai kika zarce da bamu labari shine abinda ya daure mana kai kenan. Kallon junan da kikaga muna yi ina tunanin ya sanki ne, shima yana tunanin ko na sanki ne. Aisha bani labarin takamaiman abinda ke damunki, muma nan da kika ganmu matsala ce take addabarmu, ki saki jiki ki fada mana mu dake sai mu taimaki juna da shawarwari. Barr nuruddeen ya fusata ya mike tsaye ya dubi abokinsa yace malam in ka gama kazo ka same ni a cikin mota mu tafi, dan ba zan iya zama ina sauraron wannan shirmen naku ba. Bansan sanda ka zama marar aji ba, daga haduwa da 'yar tasha sai ka hau hira da ita kai ma kana baza sirrinka, idan taji matsalar ka me wannan zatayi maka? Itama bata san yadda zatayi da kanta ba balle ta bawa wani shawara. Kada ka sake ka ambaci sunana a cikin labarinku kai dai ka fadi taka matsalar. Ya juya a fusace ya tafi bai daina fada ba yana tafe yana magana yana wurwurga hannu har ya fice daga cikin gate din. Aisha farida da barr muazzam suka bishi da kallo har sai da suka daina hango shi. Ta sunkuyar da kanta kasa sai hawaye ya fara zubowa daga idanuwanta. Kada ki yi kuka aisha, ki mayar da komai ba komai ba. Kece fa kika gama bani labarin cewa zaki iya zama da kowanne irin mutum a duniya. Inji brr muazzam. sai tayi murmushi ta shiga goge hawayenta tace ko kusa ban damu ba, banji haushi ba. Kawai dai abokinka yayi min kallon ballagar mace, 'yar tasha, 'yar club, karuwa kenan. Shine mutum na farko a rayuwata daya taba jifata da wadannan munanan sunaye, saboda bai sanni ba, sai dai ina fatan ya sanni nan gaba. Barr muazzam yace yi hakuri kanwata, ki cigaba da bani labarin rayuwarki, ina jin dadin sauraronki. Haqiqa Aisha farida,labarinki yakai maqura gurintausayi,nayi kuka sosai,rabena da irinkukannan yaukimani wata takwas kenan.tunrasuwar yayata,ayau nafisa mamawa kinsani cikintausayin ki,maganardanakeyi yanzuhaka nakasa tsayarda hawayendake zuba'a idona. kitaimaka kibani lbrin cigabanki da daukakardakikasamu kozansamisukuni yau...wallah nafisa natausayamiki sosai. BABI NA BIYU Da na karasa makarantar primary sai yaya hussaini ya kaini wata makaranta a wajen sabongari na zana jarabawar common entrance ta shiga makarantar federal. Allah cikin ikonsa sai naci jarabawa aka turani makarantar da na zaba wato FGC kano. Yayi min sayayya iya karfinsa ya kaini, ya bibbiya dukka kudaden makarantar da aka bukata, ya dawo gida ya barni a can. Nayi kuka saboda rashin sabo, gashi bansan kowa ba a makarantar amma daga baya na saba da dalibai 'yan uwana sai na fara jin dadin rayuwar makarantar. Jama'a na sona saboda yadda nake da fara'a, ladabi da son aiki bana kiwa don haka kowa yana son ya jani a jiki saboda ina da matukar tsafta. Na yi suna a makarantar nan da nan malamai ma suka sanni saboda kwazona da wayo, ga iya magana. Na gama aji uku hutun da zamu shiga aji hudu aka cireni, abu ya ci tura hidimomu sun karu, yayana ba zai iya cigaba da yi min siyayya ba da biyan kudin makaranta ba kasancewar shima ya hayyayyafa. A jejjere ba kakkautawa abida take haihuwa, 'ya'yanta na farko ma 'yan biyu ne maza abubakar da umar, sai ta haifi mace mas'uda ga wani cikin a jikinta ko yaye ta goyen bata yi ba. Ga kudin haya ya karu, cefane ya karu, farashin abinci ya karu, gashi an kara kudin makaranta ya kusa ninka na da ma. Daman duk sanda zan koma makaranta sai ya ciyo bashi kafin ya harhada ni in tafi. Ya kira ni daki ya zaunar da ni yayi min bayanin halinda ake ciki, sai ya bani hakuri cewar zai mayar dani makarantar gwamnati ta ;yan mata dake shekara. Dole na koma makarantar shekara naci gaba da karatu, daga aji 4 na fara, sai na zama zakaran gwajin dafi nafi kowa kokari saboda dana sami horo a FGC a wajen yaran kabilun da basa jin hausa da yaran hausawan da suka sami horon turanci tun daga primary. Ajin kimiya na shiga (science class) har Allah ya kaini aji shida aka bani shugabar dalibai, duk wata gasa ko muhawara ta turanci tsakaninmu da wasu makarantun ni nake tsayawa makarantarmu, idan bana nan babau abinda yake tafi dai dai. Shugabar makarantar mu tana alfahari dani, kullum tana kwatance dani saboda kokarina. Da muka gama makarantar ita da malamai sai da sukayi takaicin rashina saboda ba'a sami madadina ba. Bayan gama makarantata da wata uku yayana ya harhada 'yan kudadensa ya bani kudin mota da guzuri na zuwa shagamu, saboda duksanda yake zuwa shi da matarsa da 'ya'yansa ina makaranta ba'a zuwa dani. Tsofaffin abokan hirata har sun gaji da tambayata wasu ma sun mutu, haka wasu daga cikin yayyena sun murmutu duk banje ba. Ina samun wasikun kanwata munauwara akai akai duk sanda ta sanda ta sami mai zuwa sai ta bayar an kawao min, ta shaida min cewar an cire ta daga makaranta tana secondary aji 3 anyi mata aure saboda rashin kudi. Ni kadai yaya hussaini ya saka a mota zuwa shagamu, dana isa garin shagamu a tasha na hau acaba zuwa gidanmu, ban manta hanya ba. Da yawan 'yan gidanmu basu shaida ni ba sai daga baya suka gane ni, sunga na girma nayi kyau. Duk da rashin wadatar da muke ciki a kano sai naga na fisu kyawun gani, cikakkiyar lafiya da gogewa. Na zagaya dangi na kusa dana nesa har sai da naji kafafuwana zasu gutsire saboda yawansu. Na ziyarci gidan kanwata dake agege a lagos anan take aure, rayuwarta abin tausayi, gida ne irin na haya mai dauke da dakuna fiye da ashirin, yare kala kala kamar hausawa, yarbawa, igbo, da wasu yaruka daban daban. Bandaki daya ne kacal, tunda asubahi ake fara layin shiga bandaki. Mijinta iliyasu shima dan shagamu ne amma a lagos yake facin taya, ita kadai ce sana'arsa. 'Ya'yansu biyu a lokacin. Saboda tausayin halinda na same ta kusan dukka kayana na sakawa na bata kyauta, sannan na hada mata mayafai, sarkokina, takalmana, guda dai dai na rarrage. Duk kudaden dana samu na bata dukka kudin mota na komawa ta kano kadai na ware. Muka sha kuka tare da nazo tafiya, kukan da muke na tunawa da iyayenmu ne da kuma kukan rabuwa, don munsan zamu dade kafin mu sake haduwa. Na dawo kano jakata kwalam babu komai duk na rabar da kyana kuma da masu kyan na tafi dasu. Tsummokaran, tsofaffin, yagaggun kadai na bari a gida. Haka nazo na dinga karancin kaya duk sun ragargaje dan haka na daina zuwa taron biki ko gidan kawayena. Abida tayi ta min fada tace nayi garaje ai ba'ayin haka tun da nasan ban ajiye wasu ba a lufge kuma bani da mai dinka min wasu ai bai kamata in rabar ba. Idan fita ta kama ni dole sai dai in ari kayan abida in saka inje, ina dawowa in cire mata. Abinka da cakudi, zaman saka ido, kowa yana kula da shige da ficenka. Gulmammaki iri iri bayan zumde da yafice zaka ga anayi mana, abin ya kai har su dinga kiran 'ya 'yan abida suna bugun cikinsu suna tambayarsu wai ina kayana suka ga ina arar na abida? Irin wannan gutsiri da tsomar sai da ta wuce kan matan gida ta koma wajen mazansu, su kuma suka tseguntawa yayana hussaini, suka ce masa bai dace in dinga arar kayan abida ina fita kofar gida ina tsayawa da samari ba, ina yawo da kawayena a gari. Idan ba an lura ba in a duhune sai a zaci abida ta fara bin maza. Sukayi ta zuba masa bayanan da dole hankalinsa yayi matukar tashi, ransa yayi mummunan baci. Ya shigo dakina ransa a bace ya iske ni a kwance yace min in kira abida itama ta shigo nan dakin yana da magana da ita. Mukazo muka durkusa a gabansa muna karkarwa saboda yadda muka ga ransa a bace gashi mutum ne mai zafin zuciya. Ya umarci abida ta fada masa gaskiya kada ta kuskura tayi masa karya akan abinda zai tambayeta, haka nima ya gargadeni kafin ya yi mana tambayoyin. Muka yi masa alkawarin zamu fada gaskiya, ba zamuti karya ba. Cike da fargaba mai tsanani muke sauraron abinda zai fada mana. Ya cewa abida da gaske ne aisha farida tana aron kayanki ta saka ta fita yawo a gari? Sai abida ta dafe kirji tace Innalillahi wainna ilaihir rajiun! Ya daka mata tsawa mai firgitarwa yace baki bani amsa ba. Nan da nan ta fara hawaye, jikinta na karkarwa tace eh haka ne. Sai ya kai mata mari har sai da ta fadi kasa, ya fada cikin fushi yace to ta hada kayanta ta tafi gidansu. Na rushe da kuka na dinga rokarsa ya yafe mata ba laifinta bane nice na tambaye ta. Nima din ya yafe min na daina daga yau. Sai ya rufe ni da duka yana duma, yana tattaka ni da kafa tamkar zai kashe ni. Munafukan matan gidan ne suka zo suka kwace ni dakyar, ransa yayi matukar baci sai fada yake yana zaginmu wai sai mun harhada kayanmu mun bar masa gidansa. Ana bashi hakuri tamkar zuga shi akeyi dakyar ya haukra ya kyale mu amma tun daga lokacin baya raga mana, komai mukayi sai ya hantare mu, sai harara koda yaushe. Sai na daina fita koina , koda yaushe ina fama da dinkin yaga da zare da allura. Abida ta iske mijinta a dakinsu ta ajiye masa abinci sannan ta durkusa ta gaishe shi. Ya amsa dakyar cikim fushi, bata damu ba ta zauna a kusa dashi ta dauko muhuci ta fara yi masa firfita. Sai yayi mata tsawa yace ta bari baya so, ta tashi ta fita ta bashi waje. Cikin lallausar murya tana zubar da hawaye tace ka yafe mana laifukan da muka maka, munyi kuskure, fushin da kake yi damu ya hanamu sukuni, bama jin dadin rayuwarmu, rayuwa tayi mana kunci. Dan ban fada maka bane halin da ake ciki kada ranka ya baci, ashe dana fada maka ma zaifi sauki. Aisha farida ce ta rabar da kayan sakwarta kakaf a shagamu saboda tausaya musu da tayi, ta gansu cikin tsumma, shine ta dawo bata da kaya sai yagaggu. Dan haka bata iya fita wajen kawayenta shine nake bata aron kayana ta saka tana dawowa take cirewa, bansan abinda 'yan gulma suka fada maka ba har ya jawo ranka ya baci ka dauki mataki cikin fushi. Sai yayi shiru yana sauraronta can yace ai duk laifinki ne, meyasa ba zaki fada min halin da ake ciki a cikin gidana ba har sai da wasu suka fada min a waje? Kinsan irin zaman da mukeyi da 'yan gidannan, zaman saka ido ne, duk shige da ficen mu akan idonsu. Ashe gaba daya lungunnan gulmar ku ake yi shiyasa raina ya baci. A take ya bata naira dubu biyu yace ta bani inje in sayo atamfofi guda biyu 'yan naira dari takwas takwas inyi dinkin dari bibbiyu. Abida mace mai hakuri da tsananin wayo, ta iya zama da mijinta duk zafin zuciyarsa, tabbas macen da bata da hakuri da wayo ba zata iya zama dashi ba, sai gashi da kansa yayi nadamar aninda yayi mana, sai yaji kunya yazo yana lallaba mu. DUK KYAN TAKALMI 5 Saurayina guda daya nake kulawa mai suna musbahu, lungun mu daya dashi kowa yasan mu tare, yana sona sosai nima haka saboda yana kula dani. Tun sanda na gama sakandire yake so ya aiko gidanmu ayi zancen aure sai aka sami matsala daga gidansu, mahaifiyarsa bata sona 'yar kanwarta take so ayi musu auren gida, shi kuma ni yake so ya aura.mahaifiyarsa ta tsane ni haka kawai, ko a hanya na gaishe ta bata amsawa shiyasa na daina zuwa gidansu don da ina zuwa wajen kanwarsa jamila kawata ce ajinmu daya a shekara. Musbahi ma yaji labarin duka dana sha saboda aron kaya, sai naga ya siyo min leshi guda daya da atamfa ya hada min da naira dari biyar kudin dinki, sannan yayi min fada in daina boye masa sirrina saboda yadda yake sona a ransa, matsalata ai matsalarsa ce. Yace duk sanda na shiga matsala in fada masa ko bashi da kudi zai ciyo bashi yayi min komai in dai baifi karfinsa ba. Yaci gaba da bani hakuri akan halinda yake ciki shi da mahaifiyarsa, ita ta hana shi ya turo gidanmu zancen aurenmu. Ya umarce ni da mu dage da addu'a Allah Ya karkato da zuciyar mahaifiyarsa kaina taji tana sona ayi auren dani. Sakamakon jarabawar mu na sakandire ya fito naci credit takwas, geography ne kadai naci pass shima dan a ranar da muka yi jarabawar bani da lafiya. Sai misbahu yace idan ya sami kudi zai saya min form din jamb in wuce jami'a. Sai nace ba zan iya karatu a jami'a ba saboda 'ya'yan masu kudi ne sukeyi, bani da mai bani kudin mota da kudin sayan handout, gashi dole sai an saka sutura masu kyau. Sai shima ya gasgata zancena yaga shima bashi da halin da zai dauki nauyin duk wadannan sabida dan abinda yake samu ba mai yawa bane. Duk da wasu lokutan sukan sami ayyuka da yawa suna samun kudi a business center yake aiki, suna typing a computer, suyi kalandu ko meme. Sai yace to zai samo min management in fara, nan ma nace bana so nafi son inyi schl of nursing saboda ba ruwana da neman kayan sakawa, suna da uniform, sai yace shikenan zai binciko yaji duk yadda akeyi a shiga amma in fara jin ra'ayin yayana. Yayana ya amince da shawararmu kuma yaji dadi musamman da musbahu yazo har kofar gidanmu ya sa akayi masa sallama da yayana hussaini ya kara yi masa bayani. Yace zai taimaka min da wata dawainiyar kudin makarnatar sai ya amince yayi masa godiya. Musbahu da yayana ne suka hada gwiwa suka bani duk kudaden da ake bukata na shiga makarantar koyar aikin jinya ta malam aminu kano dake unguwar court road. Karatun shekara uku ne a shekara ta uku ne muke zuwa asibiti koyar aiki don haka karatu na yi tayi haikan, ban taba samun matsala ba cinye jarabawata nake yi koda yaushe. A asibitin malam aminu kano ake horar damu koyar aiki (attachment). Ina zuwa kkullum daga unguwarmu sharifai zuwa court rd akan acaba saboda idan nace zan hau bus zan bata lokacina zanyi in makara. Kudin acabana kit da kit babu canji wata rana ko purewater zan sha sai dai kawayena su saya min. Duk da idan za'a je sayan abinci ko shan lemo sai in gudu bana binsu saboda kullum sai dai su saya min, ni kuma na fara jin kunya sun gane bani dashi. Kawata khadija sani ismail kadai wacce bata gajiya da taimakona kuma duk sanda tace muje cin abinci naki zuwa ko na sulale na gudu sai ranta ya baci, har tayi fushi dani. Sai inyi tayi mata bayanan karya in kirkiro uzurin dana je nayi ba guduwa nayi ba sai ta ki yadda tasan karya nakeyi. Ba ita nake ji ba, sauran kawayenmu nakeji don suna nuna min bakin hali daga baya kuma in dinga jin kananan maganganu cewar na cika san banza kullum bana fitar da kudina ina sayawa kaina abu balle in sayawa wani, sai dai ni kullum a saya min. Rashin sani yafi dare duhu, kallon kitse sukeyi wa rogo. Hakika ni mai yawan tsafta ce in kula da fararen kayan makaranta ta, kullum tsaf dani, ina kalkale jikina tas a wanke ga karin guga. Gani nafi duk 'yan ajin mu kokari yawanci ni nake basu amsa. Khadija bazata iya rabuwa dani ba dan bata da kokari sai dai gata, tunda iyayenta suna da hali. Duk wasu manyan littattafai na karatu (text book) babanta yana saya mata duk tsadarsu, sai nafi morarsu don ni ce mai hazakar karatun ba ita ba. Da taimakon Allah da taimakon khadija sani nake cin jarabawa dan ba zan iya sayan littattafan nan masu tsada ba. Badan Allah Ya sa na iya kitos ba ina yiwa makwabta, da wata rana ma ba zanje makaranta ba saboda duk ranar da yaya hussaini ya tashi bashi da kudi sai yace in hakura kada inje makaranatar randa ya samu naje. Ni kuma bana so inyi fashi, da kudin kitson nake harhadawa in tafi duk da kitso a unguwar bashi da tsada, kan manya naira talatin ko arba'in, na yara kuwa naira ashirin ko goma ne. Ban taba fadawawa kawayena sirrina ba, duk da yawan kawayen da nake dasu a ajinmu mata da maza, sai dai ayi hayaniya wasa da dariya a watse, ina taka tsantsan da harshena a koda yaushe. Babu wanda a cikinus ya san yadda gidanmu yake, basu taba zaton haka nake rayuwa ba, sai dai sun fahimci wani abu akwai wasu matsaloli wanda ba zasu boyu ba. Suyi ta zargi da sake sakensu a ransu su kadai, ni dai bazasu ji daga bakina ba kuma ba zasu iya tara ta su tambaye ni ba. Ni daman bana zuwa gidan kowa balle azo gidanmu, mu hadu a abkin gate ne mu rabu idan an tashi. Bana jin dadin rayuwata a wannan bangaren saboda bani da wata takamaimiyar kawa ko masoyin da zan amayar musu da radadin da zugin matsalolin da suke addabata. Kawata guda daya, itace aminiyata, yayata, masoyiyata wato matar yayana abida. Muna zama ni da ita mu raba dare ko mu yini muna tattauna matsalolinmu, koda yaushe ina samun nutsuwa da kwarin gwiwa idan abida ta bani hakuri akan talaucin da na tsinci kaina da shawarwari, sai inji sanyi a raina, tawakkali ya kama zuciyata sai inji ta tuno min da nasihohin da mahaifina yayi min a baya. Idan nayi haka sai in dawo da walwalata, ni burina guda daya ne shine in gama karatuna in fara aiki in taimaki kaina, in taimaki 'yan gidanmu. Babbar matsalar ma da tafi damuna shine zaman cakudi a gidanmu, cikin tsagoron kazata da cinkosa, babban burina ba wuce inga mun bar gidan nan da umguwar mu canja gida ko haya ce dai mu kama gidan da muke mu kadai. Dakina daya da yara, ga dakin dan karami mun cunkushe gashi su dukka yaran abida fitsarin kwance sukeyi dan haka sun ruba katifar sai zarni take dan haka na hakura da katifar na bar musu. Na koma kwana akan tabarma, idan na tashi da safe sai inyi salla akai in nada in jingine a lungu sai zan sake yin wani sallar sannan in shimfida. Har yanzu kayana a jakar bagco yake a gefen shimfidata, rayuwata ba irin na 'yan matan 'yan boko bace, tamkar a kauye nake ba'a birni ba. Ko inyi tunanin shiga hanyar banza, ban taba sha'awar makalewa gidan kawaye ba ko arar kayan kawa, na rike talaucina na kama kaina bana sha''awar kayan wani. Daga makaranta sai gida, a gidan ma nafi zama a daki kullum ina karatu. Idan kaga na fito aiki nazo taya abida, wankan 'ya'yanta , tsarkinsu ko aikin girki. Sai 'yan gidanmu da sauran 'yan unguwa suka shiga yimin shaidar girman kai ne dani dan ni 'yar boko ce, basa ganin fara'ar da nake yi musu. Kullum ina gaishe su ko basu ganni ba, tabbas mutum ba'a iya iya masa, saboda dan Adam ya kasance mai butulci ne. BABI NA UKU Wata rana ranar litinin da misalin karfe daya na rana muna cikin a sibiti, a bangaren marasa lafiya muke wadanda aka kwantar dasu sakamakon wasu kurajen da suka feso a jikinsu. Muna biye da ma'aikaciyar jinya matron maryam tana nunnana mana yadda ake aiki, domin neman karin bayani sai tace bari ta hada mu da kwararren likita wanda ya kware a bangaren fata. Ta tura wani daki ta shiga muma muka bita a baya da alama dakin daukan darussa ne sabida naga kujeru ne zalla da allo makale a jikin bangon. Kamar yadda naji ta ambaci sunansa, dr shureim imran. Mun iske shi tsaye a tsakiyar ajin tare da wasu daliban likitoci guda 3 maza biyu, mace daya da alama sunzo sunyi masa tambayoyi ne akan wasu abubuwan da basu gane ba. Bayanai yake yi musu cikin harshen turanci kai kace baturen america ne, kalmomin kimiyyar (botanical names) da yake ta ambato yana jerowa layi layi da ka ba tare da yana duba littafi ba, kai kace shine ya lakaba musu sunan don ya haddace. Muna sake kutsawa cikin ofishin yayin da zazzakar muryarsa, daddada take sake shiga kunnuwanmu sai duk muka kagu mu isa gabansa don mu kalli fuskar mai muryan nan daddada. Kasancewar kofar ta cushe muna shiga don muna da yawa, ga dalibai likitoci nan suna kokarin fitowa sun gama daukar darasin. Kowa ya kagu yayi ido hudu da mai daddadar muryar nan, keyarsa kawai na fara hangowa daga nesa sai na tabbatar bakar fata ne dan uwana saboda ban hango jan kunne ba da farin gashi irin na turawa ba. Bakin gashi ne tattaura irin namu na hausawa, sai dai gashin a gyare yake yana shekin mai kuma ya kwanto lambar zuwa karshen keyarsa. Kansu babu hula, yana sanye da bakaken kaya riga da wando (suit), farar riga mai dogon hannu daga ciki, ya daure wuyansa da jan kyalle wato necktie. Dana matso ciki sai na fara hango gefen fusakarsa, wata lafiyayyiyar fata na fara hangowa mai dauke da launi mai tsananin kyau. Irin kalar da take tsada a duniya wato hasken duhu (chocolate color). Ko dana sake samun daman na matso kuda dashi sai ga gefen fuskarsa tar ina gani wato idonsa daya da gefen hancinsa, sai kawai naji wata mummunar fadywar gaba ta far min ni ma bansan dalili ba har wadanda ke kusa dani zasu iya jiyo karar ajiyar zuciya danayi. Tunda nake a rayuwata ban ta ba ganin irin wadannan dara daran idanuwan ba masu tsananin haske daga ciki, da bakar kwayar ido mai tsananin baki, aka zagaye idon da wasu gashin ido da gashin gira masu yawa da tsananin baki, ya gyara su sunyi kira mai kyau suna sheki. A nutse ya waiwayo da kyakkyawar fuskarsa gaba daya ya dube mu, bani kadai ba duk wata 'ya mace da take wajen sai dataji a ranta dama ace wannan kadarar mallakarta ce. 'Yan uwansa maza ma sai da suka raya a ransu dama ace sune shi, ga kyau ga ilimi. Ashe a da dana ke hango gefen fuskarshi ban hango komai ba, kyau mai sunan kyau sai ka kalle shi gaba dayansa daga kafarsa zuwa kansa. Dogon mutum ne sosai ma kyawun sura, bashi da kiba da yawa, haka bashi da rama. Yayi kama da irin bakaken turawan nan da ake kira african American, hukuncin da na yanke masa kenan dan ko kusa baiyi kama da 'yan nigeria ba! Tabbas ruwa biyu ne suka hadu suka same shi bakar fata da farar fata. Saurayina guda daya nake kulawa mai suna musbahu, lungun mu daya dashi kowa yasan mu tare, yana sona sosai nima haka saboda yana kula dani. Tun sanda na gama sakandire yake so ya aiko gidanmu ayi zancen aure sai aka sami matsala daga gidansu, mahaifiyarsa bata sona 'yar kanwarta take so ayi musu auren gida, shi kuma ni yake so ya aura.mahaifiyarsa ta tsane ni haka kawai, ko a hanya na gaishe ta bata amsawa shiyasa na daina zuwa gidansu don da ina zuwa wajen kanwarsa jamila kawata ce ajinmu daya a shekara. Musbahu ma yaji labarin duka dana sha saboda aron kaya, sai naga ya siyo min leshi guda daya da atamfa ya hada min da naira dari biyar kudin dinki, sannan yayi min fada in daina boye masa sirrina saboda yadda yake sona a ransa, matsalata ai matsalarsa ce. Yace duk sanda na shiga matsala in fada masa ko bashi da kudi zai ciyo bashi yayi min komai in dai baifi karfinsa ba. Yaci gaba da bani hakuri akan halinda yake ciki shi da mahaifiyarsa, ita ta hana shi ya turo gidanmu zancen aurenmu. Ya umarce ni da mu dage da addu'a Allah Ya karkato da zuciyar mahaifiyarsa kaina taji tana sona ayi auren dani. Sakamakon jarabawar mu na sakandire ya fito naci credit takwas, geography ne kadai naci pass shima dan a ranar da muka yi jarabawar bani da lafiya. Sai misbahu yace idan ya sami kudi zai saya min form din jamb in wuce jami'a. Sai nace ba zan iya karatu a jami'a ba saboda 'ya'yan masu kudi ne sukeyi, bani da mai bani kudin mota da kudin sayan handout, gashi dole sai an saka sutura masu kyau. Sai shima ya gasgata zancena yaga shima bashi da halin da zai dauki nauyin duk wadannan sabida dan abinda yake samu ba mai yawa bane. Duk da wasu lokutan sukan sami ayyuka da yawa suna samun kudi a business center yake aiki, suna typing a computer, suyi kalandu ko meme. Sai yace to zai samo min management in fara, nan ma nace bana so nafi son inyi schl of nursing saboda ba ruwana da neman kayan sakawa, suna da uniform, sai yace shikenan zai binciko yaji duk yadda akeyi a shiga amma in fara jin ra'ayin yayana. Yayana ya amince da shawararmu kuma yaji dadi musamman da musbahu yazo har kofar gidanmu ya sa akayi masa sallama da yayana hussaini ya kara yi masa bayani. Yace zai taimaka min da wata dawainiyar kudin makarnatar sai ya amince yayi masa godiya. Musbahu da yayana ne suka hada gwiwa suka bani duk kudaden da ake bukata na shiga makarantar koyar aikin jinya ta malam aminu kano dake unguwar court road. Karatun shekara uku ne a shekara ta uku ne muke zuwa asibiti koyar aiki don haka karatu na yi tayi haikan, ban taba samun matsala ba cinye jarabawata nake yi koda yaushe. A asibitin malam aminu kano ake horar damu koyar aiki (attachment). Ina zuwa kkullum daga unguwarmu sharifai zuwa court rd akan acaba saboda idan nace zan hau bus zan bata lokacina zanyi in makara. Kudin acabana kit da kit babu canji wata rana ko purewater zan sha sai dai kawayena su saya min. Duk da idan za'a je sayan abinci ko shan lemo sai in gudu bana binsu saboda kullum sai dai su saya min, ni kuma na fara jin kunya sun gane bani dashi. Kawata khadija sani ismail kadai wacce bata gajiya da taimakona kuma duk sanda tace muje cin abinci naki zuwa ko na sulale na gudu sai ranta ya baci, har tayi fushi dani. Sai inyi tayi mata bayanan karya in kirkiro uzurin dana je nayi ba guduwa nayi ba sai ta ki yadda tasan karya nakeyi. Ba ita nake ji ba, sauran kawayenmu nakeji don suna nuna min bakin hali daga baya kuma in dinga jin kananan maganganu cewar na cika san banza kullum bana fitar da kudina ina sayawa kaina abu balle in sayawa wani, sai dai ni kullum a saya min. Rashin sani yafi dare duhu, KALLON KITSE sukeyi wa ROGO. Hakika ni mai yawan tsafta ce in kula da fararen kayan makaranta ta, kullum tsaf dani, ina kalkale jikina tas a wanke ga karin guga. Gani nafi duk 'yan ajin mu kokari yawanci ni nake basu amsa. Khadija bazata iya rabuwa dani ba dan bata da kokari sai dai gata, tunda iyayenta suna da hali. Duk wasu manyan littattafai na karatu (text book) babanta yana saya mata duk tsadarsu, sai nafi morarsu don ni ce mai hazakar karatun ba ita ba. Da taimakon Allah da taimakon khadija sani nake cin jarabawa dan ba zan iya sayan littattafan nan masu tsada ba. Badan Allah Ya sa na iya kitos ba ina yiwa makwabta, da wata rana ma ba zanje makaranta ba saboda duk ranar da yaya hussaini ya tashi bashi da kudi sai yace in hakura kada inje makaranatar randa ya samu naje. Ni kuma bana so inyi fashi, da kudin kitson nake harhadawa in tafi duk da kitso a unguwar bashi da tsada, kan manya naira talatin ko arba'in, na yara kuwa naira ashirin ko goma ne. Ban taba fadawawa kawayena sirrina ba, duk da yawan kawayen da nake dasu a ajinmu mata da maza, sai dai ayi hayaniya wasa da dariya a watse, ina taka tsantsan da harshena a koda yaushe. Babu wanda a cikinus ya san yadda gidanmu yake, basu taba zaton haka nake rayuwa ba, sai dai sun fahimci wani abu akwai wasu matsaloli wanda ba zasu boyu ba. Suyi ta zargi da sake sakensu a ransu su kadai, ni dai bazasu ji daga bakina ba kuma ba zasu iya tara ta su tambaye ni ba. Ni daman bana zuwa gidan kowa balle azo gidanmu, mu hadu a abakin gate ne mu rabu idan an tashi. Bana jin dadin rayuwata a wannan bangaren saboda bani da wata takamaimiyar kawa ko masoyin da zan amayar musu da radadin da zugin matsalolin da suke addabata. Kawata guda daya, itace aminiyata, yayata, masoyiyata wato matar yayana abida. Muna zama ni da ita mu raba dare ko mu yini muna tattauna matsalolinmu, koda yaushe ina samun nutsuwa da kwarin gwiwa idan abida ta bani hakuri akan talaucin da na tsinci kaina da shawarwari, sai inji sanyi a raina, tawakkali ya kama zuciyata sai inji ta tuno min da nasihohin da mahaifina yayi min a baya. Idan nayi haka sai in dawo da walwalata, ni burina guda daya ne shine in gama karatuna in fara aiki in taimaki kaina, in taimaki 'yan gidanmu. Babbar matsalar ma da tafi damuna shine zaman cakudi a gidanmu, cikin tsagoron kazanta da cinkoso, babban burina ba wuce inga mun bar gidan nan da umguwar mu canja gida ko haya ce dai mu kama gidan da muke mu kadai. Dakina daya da yara, ga dakin dan karami mun cunkushe gashi su dukka yaran abida fitsarin kwance sukeyi dan haka sun ruba katifar sai zarni take dan haka na hakura da katifar na bar musu. Na koma kwana akan tabarma, idan na tashi da safe sai inyi salla akai in nada in jingine a lungu sai zan sake yin wani sallar sannan in shimfida. Har yanzu kayana a jakar bagco yake a gefen shimfidata, rayuwata ba irin na 'yan matan 'yan boko bace, tamkar a kauye nake ba'a birni ba. Ko inyi tunanin shiga hanyar banza, ban taba sha'awar makalewa gidan kawaye ba ko arar kayan kawa, na rike talaucina na kama kaina bana sha''awar kayan wani. Daga makaranta sai gida, a gidan ma nafi zama a daki kullum ina karatu. Idan kaga na fito aiki nazo taya abida, wankan 'ya'yanta , tsarkinsu ko aikin girki. Sai 'yan gidanmu da sauran 'yan unguwa suka shiga yimin shaidar girman kai ne dani dan ni 'yar boko ce, basa ganin fara'ar da nake yi musu. Kullum ina gaishe su ko basu ganni ba, tabbas mutum ba'a iya iya masa, saboda dan Adam ya kasance mai butulci ne. BABI NA UKU Wata rana ranar litinin da misalin karfe daya na rana muna cikin a sibiti, a bangaren marasa lafiya muke wadanda aka kwantar dasu sakamakon wasu kurajen da suka feso a jikinsu. Muna biye da ma'aikaciyar jinya matron maryam tana nunnana mana yadda ake aiki, domin neman karin bayani sai tace bari ta hada mu da kwararren likita wanda ya kware a bangaren fata. Ta tura wani daki ta shiga muma muka bita a baya da alama dakin daukan darussa ne sabida naga kujeru ne zalla da allo makale a jikin bangon. Kamar yadda naji ta ambaci sunansa, dr shureim imran. Mun iske shi tsaye a tsakiyar ajin tare da wasu daliban likitoci guda 3 maza biyu, mace daya da alama sunzo sunyi masa tambayoyi ne akan wasu abubuwan da basu gane ba. Bayanai yake yi musu cikin harshen turanci kai kace baturen america ne, kalmomin kimiyyar (botanical names) da yake ta ambato yana jerowa layi layi da ka ba tare da yana duba littafi ba, kai kace shine ya lakaba musu sunan don ya haddace. Muna sake kutsawa cikin ofishin yayin da zazzakar muryarsa, daddada take sake shiga kunnuwanmu sai duk muka kagu mu isa gabansa don mu kalli fuskar mai muryan nan daddada. Kasancewar kofar ta cushe muna shiga don muna da yawa, ga dalibai likitoci nan suna kokarin fitowa sun gama daukar darasin. Kowa ya kagu yayi ido hudu da mai daddadar muryar nan, keyarsa kawai na fara hangowa daga nesa sai na tabbatar bakar fata ne dan uwana saboda ban hango jan kunne ba da farin gashi irin na turawa ba. Bakin gashi ne tattaura irin namu na hausawa, sai dai gashin a gyare yake yana shekin mai kuma ya kwanto lambar zuwa karshen keyarsa. Kansu babu hula, yana sanye da bakaken kaya riga da wando (suit), farar riga mai dogon hannu daga ciki, ya daure wuyansa da jan kyalle wato necktie. Dana matso ciki sai na fara hango gefen fuskarsa, wata lafiyayyiyar fata na fara hangowa mai dauke da launi mai tsananin kyau. Irin kalar da take tsada a duniya wato hasken duhu (chocolate color). Ko dana sake samun daman na matso kusa dashi sai ga gefen fuskarsa tar ina gani wato idonsa daya da gefen hancinsa, sai kawai naji wata mummunar fadywar gaba ta far min ni ma bansan dalili ba har wadanda ke kusa dani zasu iya jiyo karar ajiyar zuciya danayi. Tunda nake a rayuwata ban ta ba ganin irin wadannan dara daran idanuwan ba masu tsananin haske daga ciki, da bakar kwayar ido mai tsananin baki, aka zagaye idon da wasu gashin ido da gashin gira masu yawa da tsananin baki, ya gyara su sunyi kira mai kyau suna sheki. A nutse ya waiwayo da kyakkyawar fuskarsa gaba daya ya dube mu, bani kadai ba duk wata 'ya mace da take wajen sai dataji a ranta dama ace wannan kadarar mallakarta ce. 'Yan uwansa maza ma sai da suka raya a ransu dama ace sune shi, ga kyau ga ilimi. Ashe a da dana ke hango gefen fuskarshi ban hango komai ba, kyau mai sunan kyau sai ka kalle shi gaba dayansa daga kafarsa zuwa kansa. Dogon mutum ne sosai ma kyawun sura, bashi da kiba da yawa, haka bashi da rama. Yayi kama da irin bakaken turawan nan da ake kira african American, hukuncin da na yanke masa kenan dan ko kusa baiyi kama da 'yan nigeria ba! Tabbas ruwa biyu ne suka hadu suka same shi bakar fata da farar fata. Duk da tashin hankalin da na shiga da naji bayananta sai nayi murmushin karfin hali nace subhanallah! Bai kamata kice zaki bi kowacce hanya ba gara ma kice zaki bishi da addua in da alkhairi Allah ya yi. Khadija tace bawai ina nufin zan fita daga musulunci ba akansa ba, amma fa dole saina saka malamaina sunyi min addua. Na fahimci maryam ahmed da mansura mahmud suna sonsa kin san su da bin malamai, in ban dage ba sai sun janye hankalinsa. Gaskiya tunda nake a duniya ban taba ganin Kyakkyawan bakar fata irinsa ba, ko kin taba gani? Na girgiza kai nace ban taba gani ba, amma shima yana ji da kansa dan yasan ya hadu kuma mata suna nuna masa haka. Ba kya ganin 'yan matan nan medical student suna ta kawo hare harens garshi? Khadija tace tabbas na gani, shiyasa nace sai nayi da gaske fa. Ai mu uku ne kadai muka amayar da maitarmu a waje, nasan mata da yawa sun dasa a ajin fada ne kawai basu yi ba. Kin burge ni aisha umar, sai naga kwata kwata ba ya gabanki, ko a bayan idonki muna yabonki don kina kama kanki bakya shiga rigimar da tafi karfinki. Sai kawai nayi murmushi nace a raina kallon kitse kike yiwa rogo, aini zuciyata tuni ta kunsa min abinda zuciyoyinku basu kunsa muku ba. Tabbas nasan burina da fatana akan dr shurain yafi nasu. Aisha umar kalli motar can, inji khadija yayin da ta matse 'yan yatsunna don gigicewa. Na juya da sauri, sai naga wata dankareriyar mota baka mai farin gilashi. A cikin motar kuma zankadeden mutum ne, sanye da farar riga da bakin gilashi a fuskarsa. Ya kalle mu, muma kallonsa mukayi sai ya kawar da kai ya fisgi motarsa da gudu ya nufi gate din fita. Na dubi motar har da waiwaye sannan na juyo na dubi khadija nace motar nan ta hadu, haka mutumin da yake cikin motar ma ya hadu. Wanene shi? Tace au baki gane shi bane? Dr shuraim ne likitan da muke zancensa yanzu. Dan halak yaki ambato. Sai nace kai bashi bane, ai shi bakar suit ya saka. Tace bakar ta saman ya cire, ya bar farar ta ciki. Baki shaida jan neck tie din bane? Sai nayi shiru saboda haduwarsa tafi karfin tunanina, sama ta yiwa yaro nusa ba zai iya tabawa ba sai dai ya daga ido ya hango. Sai na tuna ai Allah ne ya halicce shi wanda ya halicce ni, babu wanda yafi wani a wajensa sai wanda yafi bauta masa don haka na daina raina kaina. Na kudira a raina zan sake rikar addinina yadda zan sami babban rabo a lahira, koda kuwa ban sami wanda nake so a duniya ba. Zuciya ta fara warwarewa daga kuncin daya damke ta na son maso wani. Tun ina sauraron surutun da khadija takeyi har na daina ganewa, burina kawai in ganni a gida na shige lungun dakina. Ina hau yamutsattsiyar tabarmata in kudindina inyi ta aiyano ni tare da abin kauna ta shuraim. Ina daukar jakata sai nayi musu sallama na nufi gate din fita a sanyaye ina tafe ina tunani. Na fita waje na tsayar da acaba kamar kullum na haye ya kai ni kofar gidanmu. Tun daga zauren gidanmu nake cin karo da matan gidan suna ta hidindimunsu na saye da sayarwa da surutin da suke yini suna yi, ayi gulmar wannan, a zagi waccan, yau sai suka ganni ba kamar kullum ba. Da bayan na gaishe su sai in dan zauna ayi barkwanci sannan in wuce cikin gida, yau babu kanta da kyar nake magana, sauri kawai nake yi in shige ciki. Sunyi zaton yunwa nakeji, har suke zolayata da cewa abida ba ta nan, ba'ayi abinci ba. Na wuce abu na, na iske abida tana dafa a binci a risho. Tana ganina tayi kasake tana kallona, ta san akwai damuwa tunda bata jiyo muryata ba, bata gano murmushina ba saboda ina da yawan dariya. Ta dube ni tace aisha farida kalau kuwa, ko allura zakiyi wata mara lafiya ta kwace ta tsira miki? Nayi dariya nace haba dai ayi haka kuwa? Bana jin dadi dai. Tace Allah ya sawake, shiga daki kihuta kafin abinci ya dahu ki ci zaki murmure. Ina shiga daki na cire uniform dina sai na daura tawul na dauki kwandon wanka zan je in watsa ruwa dan inji dan sanyi a jikina saboda na kwaso rana.sai na ga abida ta shigo tana dariya tace da ni "af ashe wanka zaki yi da labari zan baki mai dadi kuma marar dadi." Na ajiye kwandon wanka na jawo hannunta muka zauna.Na ce bani in sha ai na fasa wanakan,me ya faru? Ta yi dariya tace labarin musbahu tsohon saurayinki da matarsa lubabatu zan baki daman,aure dai yaki dadi har ya yi mata saki daya dazun nan aka yi rigimar. Lungun nan ya cika da mutane mahaifiyarsa dai sai a taya ta da addua don ta cika naci,ce masa tayi idan ya sake furta kalmar saki sai ta tsine masa dole sai ya zauna da lubabatu tasan akan aisha farida yake yi mata wulaqanci kala- kala. Tayi rantsuwa tace ko bayan ranta idan ya saki lubabtu ya aure ki Allah ya isa. Kin ji wata kiyayya sabuwa ko? Na yi murmushin karfin hali nace,Allah ya kyauta,ta ma daina kokarin tsinewa danta a kaina tuntuni na yi masa sallama nace ya bi mahaifiyarsa don ya sami rahama. Ya na aiko min da kudi tun ina karba sai na daina karba daga baya idan ya aiko sai in mayar da dan aiken in ce bana so don zaman lafiya. Abida tace haka ya fi,ai gara da kika yi. Masa haka kin taimake shi. Ni na dauka ma zancen kika ji tun daga zaure da na ga kin shigo ranki a bace. Amma fa ki godewa Allah AF saboda kin samu kyakkyawon yabo a ung nan. Ba kiji. Yadda kowa yake yabonki ba,ake ta tsine mata ita kuma. Kowa ya dinga cewa me ye laifin AF har da bata so danta ya aura? Yarinya mai nutsuwa da hankali mai ilimi da fara'a tana gaishe da mutane. Ta zo ta tauyewa yaro rayuwarsa ta cusa masa dakalkalalliyar macen da ba ta da tsari. Nace au daman an sanni da yawa a ung nan haka? Abida tace "ji ki da Allah da neman magana waye bai sanki ba,musamman da kika shiga skul of nursing kina karbar haihuwa kina allura a cikin ung sai ki ji kowacce mata tana cewa wajen aisha likita zan je ta rubuta min magani. A nan dai muka tashi muka rufe hirar nan zuciyata cike da tausayin musbahu ba don mahaifiyarsa ba ta sona ba da na aure shi mun zauna mun rufawa juna asiri,in huta fadawa cikin hatsarin da nake shirin jefa kaina. Bayan na yi wanka na ci abinci sai na wartsake na shiga cikin matan gidan muna ta hira har ma na ji na fara mantawa da abunda yake damuna a zuciyata. Sai da kowa ya shiga barci dare ya fara nisawa sai tunanin Dr shureim imran yace da wa Allah ya hada ni in ba da ke ba,sai na ji gaba daya daya zuciyata ta kasa sukuni. Da zarar na rufe ido sai in ganshi tamkar a zahiri. Sai na yi ta yaki da zuciyata ina ture shi daga tunanina.kai in takaice maka a cikin satin nan ban gane kaina da kaina saboda tsananin tunaninsa. Idan na je asibiti bana walwala haka idan na dawo gida ba na jin dadin zuciyata kada ma dare ya ji labari sai ka ga idona ya wartsake garau na burma tunanin DR shureim imran. Da gaske sonsa nake,so ba da wasa ba.tun ranar kuma ban sake ganinsa ba sai dai kullum sai khadija ta yi min labarinsa.Albishir din da ta yi min shi ne ta sami lambar wayarsa amma tana tsoron kira don tana ganin zai yi mata wulaqanci. Ta shaida min ta rabawa malamai kudi ana ta ragargaza mata addu'a ta koina,a kalla ta raba musu zunzurutun kudi ya kai N25,000 so take sai an gama addua tas sannan ta kira shi dolensa ya amince. Sai na sake jin jikina ya yi sanyi na sake yi wa zuciyata fada da ta yi ta- ka tsan- tsan ta daina cusa abunda zai iya kasheta.idan da khadija. Zata lura duk sanda ta fara yi min zancen Dr shureim sai jikin yayi sanyi kuma na kan rasa amsar da zan bata ko shwara. Kallonta kawai nake tsayawa ina yi yayin da zata iya ganin hawaye yana cika min ido sai inyi sauri in mayar da shi ina tauisayinta na fi tausayin kaina domin na san zuciyata ta fi tata shiha hatsari kuma ta fini sanin yadda zata yi da kanta. Ni ko wayar ma bani da ita babu kudin saka kati balle in saka rai ko zan karbi lambar in kira inji dadi. Na zama na rasa walwala ta ko abincin kirki bana iya ci na dukufa da adduar Allah ya yaye min don sonsa ya zame min ciwo.naji duk na tsani kaina karfi da yaji nake fisge tunaninsa daga cikin zuciyata.amma abu ya ci tura sai ma karuwa yake yi. Idan naki tunaninsa karfi da yaji a ido biyu da zarar na kwanta sai nayi mafarkinsa, sai gani cikin dare ina kuka wiwi ina sallah da adduar Allah Ya yaye min, Allah Ya kawo abin da zai sa inji na tsane shi ma. Duk satittikan nan da nayi ina jinyar sonsa ko a hanya ban hadu dashi ba balle ma in ji dan sanyi a raina, ina so ina kara ganin suffarsa don in kawata tunanina domin kamanninsa suna kokarin disashe min. Ranar talata da sassafe ina dirowa daga kan acaba a kofar shiga gate din asibitin aminu kano sai na yi kicibus dashi a cikin wannan tsaleliyar motar tasa. Na waiwaya da sauri na dube shi yayin da shi ma yake dubana har da rage tafiya amma fa duban da yake yi min bana kauna bane, hararata yake yi game da nuna tsana mai yawa a bayyane. Sai yayi tsaki ya girgiza kai ya kada sitiyarin motarsa yayi wucewarsa. Sai na dankare a tsaye ni ban ciro kudin mai acaba na biya shi ba, ni banyi gaba ba balle ace mantuwa nayi. Bani kudin mana, inji zalamamman dan acba. Na ciro kudin na mika masa ya karba yana shirin ya miko min canjina naira ashirin sai na girgiza kai nace kayi min sadaka, ku taya ni addua don bani da lafiya. Sai ya tsaya yana kallona cike da tausayi yace to ko gida za a mayar dake idan ba zaki iya aikin ba? Ai komai sai da lafiya akeyi. Nayi murmushin karfin hali nace ciwona addua yake bukata ba hutu ba, ko shan magani. Sannan maganin ciwon yana cikin asibitin nan, idan na koma gida ai babu maganin a can. Yace gaskiya ne duk wani magani yana asibiti. Allah Ya yaye miki kowanne irin ciwo ne wannan. Na amsa da amin nagode. Na juya a sanyaye ina tafiya kamar kwai ya fashe min a ciki. Ina mai matukar mamaki da takaicin kallon wulakancin da yayi min. Na kasa tantance ni kuwa laifin me nayi masa a rayuwata da ya tsane ni, yaushe ma ya taba ganina banda sau daya shima a rubibi, yaushe zai ganeni? Aisha farida umar, karaf naji an kira sunana daga gefena. Nayi firgigit na juyo da sauri. Khadija sani ismail na gani ta tsaya da motarta hience 2008 ta sauke gilashin wundonta kasa, na tsallako inda take na bude gaban motar na shiga. Ina kokarin gaishe ta sai ta katse ni cikin murna take magana tace albishirinki? Na kira Dr shuraim imran jiya ya dauka, sai dai mun fara magana yace in bashi bane wanda nake newa wrong number ce, ya katse wayar. Sai na tura masa sako nace ni dalibarsa ce , na kira in gaishe shi. Kinga amsar daya bani. Sai ta miko min wayarta, sai hannuna ya hau kakkarwa, har sai da ta tsaya tana kallona saboda gaba daya jikina bari yake yi. Na duba na karanta sai naga ya runuta "thanks". Sai na lumshe ido don dadin ganin rubutunsa da lambarsa, naji dama nice nake yi masa waya da tura sako da ko amsar da ya bawa khadija na samu ya bani kadai na gama jin dadin rayuwata, ta isheni abin farin ciki. Na bude baki nayi magana da kyar, nace lallai kinji dadi. Tace dadi ka-n jiya ai jar da barci da munshari don samun kwanciyar hankalin dana ji. Dole in karawa malamaina kudi su sake dagewa da addua sosai. Nayi ajiyar zuciya nace ya san sunanki? Tace bai tambaye niba, ki kyale shi sai a hankali, dan wulakanci ne fa wannan da kike gani. Muka isa bangaren da muke,mun bar bangaren masu kuraje mun koma bangaren yara. Muna shiga ciki muka iske 'yan ajinmu a tsaitsaye kowannensu da dan littafinsa a hannu da biro, da alama matron ta fara bayani akan wannan yaro mai ciwon amai da gudawa. A tsaye nake ina kallon bakin yaron a hannun mahaifiyarsa yana tsala kuka, amma ban fahimci bayanan matron ba, ko kadan ban san me take cewa ba. Tunanina kawai daman ace dana ne wannan jaririn muka haifa tare da Dr shureim imran. Sai da ta gama bayani ta juya, naga an bi ta duuu a baya zuwa gadon wani yaron marar lafiya, shi kuma mai ciwon pneumonia ne, sai na ja birki na tsaya cak na ki bin su saboda kafafuwana da kwakwalwata sun gaji ba zasu iya daukar abubuwa guda biyu ba, tunanin dr shuraim imran shi yafi matsa min, gara in yi shi shi kadai, shi yafi muhimmanci a gareni don haka na juya na nufi ofishinmu inda muke zama mu huta da ajiye jakunkunan mu. Ina shiga sai naga maryam ahmad tayi kasake a zaune akan kujera tana matsa wayarta, fuskarta babu walwala. Nayi mata magana sai naji da kyar take amsa min. Na tambaya cikin damuwa maryam lafiya? Me ke damunki? Baki da lafiya ne. Ta girgiza kai tace lafiya kalau. Ni dai na dame ta da tambaya lallai sai ta fada min abin dake damunta. Ko a mafarki ban zata amsar da zata bani ba kenan. Budar bakin ta ke da wuya tace waye inba dr shureim ba? Sai naji gabana ya fadi daf! Na fada a gigice me yayi miki? Sai ta dube ni kwalla ta cika mata ido tace aisha farida na yarda dake shi yasa zan fada miki sirrina, na san kina da rike sirrin jama'a ba ataba fada miki magana kin yada ba, na san zaki bani shawarar da ta dace. Ina matukar son dr shureim imran, har zuciyata sai naga da in tsaya labe labe shi ma mutum ne kamar ni, me zai hana in tunkare shi in fada maas tunda ni bazawara ce, kunyar me zanji? Duk inda mace ta kai na kai, ina da kyauna da ilimina da arzikina, gani 'yar asali karewa ma 'yar sarauta. Dazun nan na tare shi a bakin ofis dinsa yana ganina ya bata rai na gaishe shi ya amsa da kyar, ya bude kofar ofis dinsa ya shiga sai na bi bayansa. Muna shiga sai ya daka min tsawa yace lafiya? Nace nazo in gaishe shi ne. Ya fada a fusace yace to naji sai anjima. Nace kuma ina da magana da nake tafe da ita. Sai yace fadi maganarki ki fita. Nace so nake mu saba in karbi lambarka, ka karbi tawa. Ko rufe bakina banyi ba yace bana bukatar in saba da ke, haka bana son lambarki, sai anjima. Sai ta fashe da kuka ta rungumeni. Bansan sanda na dora hannu aka ba nace mun shiga uku, Allah Ya jikaina. Maryam ta dago cike da mamaki tace aisha farida menene? Nayi sauri na gyara zancen nace ai da kika fada min abin da yayi miki sai naji kama zan hadiyi zuciya in mutu, shine nace Allah yaji kaina. Tace meye shawararki? Shawarar da na ba wa kaina ita nake kokarin in bata, itace tayi hakuri ta rabu dashi, taci gaba da addua. Allah ya yaye mata sonsa ya hadata da mai sonta wanda yafi shi. Sai tace a'a ai ba isa ba, sai ya san ita yayi ma wulakanci. Ai ko zata salwantar da dukiyarta kakaf sai ta rama abinda yayi mata. Sai tayi masa asirin da sai ya kwanta a kasa ta murje shi da takalmin kafarta. Ban sake magana ba na tsaya kawai ina kallonta, yayin da naji tausayinsa ya kama ni, bana so a wahalar min da abin kaunata. Daga nan na kara cire ran mafarkin samun dr shuraim imran a rayuwata. Naci gaba da jinya ina jiran ranar ajalina domin mutuwata ce kadai zatayi min maganin ciwon nan. DUK KYAN TAKALMI 7 Sai ta fashe da kuka ta rungumeni. Bansan sanda na dora hannu aka ba nace mun shiga uku, Allah Ya jikaina. Maryam ta dago cike da mamaki tace aisha farida menene? Nayi sauri na gyara zancen nace ai da kika fada min abin da yayi miki sai naji kama zan hadiyi zuciya in mutu, shine nace Allah yaji kaina. Tace meye shawararki? Shawarar da na ba wa kaina ita nake kokarin in bata, itace tayi hakuri ta rabu dashi, taci gaba da addua. Allah ya yaye mata sonsa ya hadata da mai sonta wanda yafi shi. Sai tace a'a ai ba isa ba, sai ya san ita yayi ma wulakanci. Ai ko zata salwantar da dukiyarta kakaf sai ta rama abinda yayi mata. Sai tayi masa asirin da sai ya kwanta a kasa ta murje shi da takalmin kafarta. Ban sake magana ba na tsaya kawai ina kallonta, yayin da naji tausayinsa ya kama ni, bana so a wahalar min da abin kaunata. Daga nan na kara cire ran mafarkin samun dr shuraim imran a rayuwata. Naci gaba da jinya ina jiran ranar ajalina domin mutuwata ce kadai zatayi min maganin ciwon nan. Abida ta lura bana cikin walwata kullum ina cikin damuwa, ta tambayeni har ta gaji na kasa fada mata wannan badakalar cutar da zuciyata ke fama da ita, babu abinda nake boyewa abida amma wannan dai ba zai fadu ba. Na gwammace a dauki gawata a dinga tunanin fuju'an na mutu babu ciwo ni da Ubangijina munsan abinda ya kashe ni. Sai na shiga tunanin ko shi yasa ya dinga hararata saboda masu irin uniform dina ne suke damunsa ya zata nice? Haka ne ma babu tantama ya dauka khadija da maryam ce ni. Bansan takamaiman ofis dinsa ba, don haka kaina tsaye na tunkari ofishin dr lukman likitan kwakwalwa dauke da file din matron maryam ta umurce ni da in kai masa. Ofis na uku tace min daga hannun dama, don haka kaina tsaye nan na kwankwasa na shiga tun kafin a bani izini, saboda saurin da nake yi don inyi in koma wajen daukan darasi. Abin da nagani a cikin ofishin shi ya firgita ni har sai da kowa ya gane na tsorata, dr shureim imran na gani a zaune a kan kujera da laptop dinsa akan table yana danne danne, maimakon mai ofis din dr lukman. Wace wannan? Ya kika koma da sauri? Wa kike nema? Tambayoyin da na jiyo ana yi min kenan daga cikin ofishin ni kuwa tuni nayi waje. Na rufo kofar a hankali na fara sanda zan juya, jikina yana rawa ina gudun wulakancinsa. Wata murya naji an kira ni, har na kai kan barandar waje. Ina juyawa naga mai gadi ce (security). Tace inje inji doctor. Hankalina ya tashi kan kace kwabo na fara gumi tamkar ana gasa ni a garwashi. Ofishin dr lukman kuwa ta nuna amma ban ga kowa a bakin kofar ba, kuma har yanzu kofar a rufe. Ni kaina ban san ayoyin da nake karantawa ba har na isa bakin kofar, na tura kofar na shiga ina mai jan dan gajeren hijabina ina rufe rabin fuskata. Ina sauraron yadda Allahi Zaiyi dani kuma. Nayi sallama na shiga amma na kasa daga ido in dube shi. Yaya kika leko kika koma? Wannan karon kuma wata sabuwar murya naji daban ba irin ta dazu ba, sai na dago ido da sauro na dube shi. Dr lukman na gani zaune yana danna laptop dinsa ba dr shureim imran bane. Sai mamaki ya rufe ni a zahiti har ya fahimci haka, na tabbatar son dr shureim yayi min yawa da har ya fara yi min gizau. Nayi murmushi na dauka ba ofishin na shigo ba shiyasa na juya. Na matso na mika masa file din yana dubawa ya girgiza kai yace me yasa matron zatayi min haka, ni ba wannan nace ta aiko min ba. To iyakacin kalmar da na fahinta kenan daga nan na daina sauraronsa saboda dr shureim imran na gani ya fito daga bandaki da alama alwala yayi don jikinsa daruwa. Kallo daya nayi masa na zazzare ido sai na sunkuyar da kai kasa yayin da jikina ya hau rawa, zuciyata ta hau tsalle tana oyoyo ga abincin da na dade ina yunwarsa. Shine ma dai yayi min kallo sau biyu ya watsar ya shige lungu ya shimfida abin sallah. Kafin ya tayar da sallah dr lukman ya tsokano shi da ci gaba da hirar da suke yi. Yace wato dr shureim ka tsani ka ga 'yan acaba kenan? Yayi dariya yace yadda naki mutuwata haka naki inga mutum ya hau acaba musamman mace ina takaicin wannan abu, sai inga ba gara mutum yaje ya kwanta a sibiti ba yace a zuke jininsa gaba daya a rabawa marasa lafiya saboda ya mutu, gara yace a yayyanki duk sassan jikinsa a raba sadakatul jariya. Dr lukman ya kwashe da dariya har da buga kafa a kasa. Yace haba dai doctor har abin ya kai haka? Yace haka ne mana, saboda yadda zaka ga suna kutsawa a jikin tirela. Na fada maka fa acaba ne ya kashe san uwa na uwa daya uba daya, kuma ina tsaye ina kallo ya kutsa dashi karkashin tirela. Daha cewa dan acaba kai ni can in siyo batir motarmu ta mutu a hanya, shikenan ya warce shi sai karkashin tirela sai gawarsu aka kwakulo. Tun daga lokacin idan naga mutum akan acaba sai kaga na bar abun da nakeyi na rike kai, ina taya shi da addua har sai na daina hangensu. Musamman mace sai inji kamar in fasa ihu ince ga motarta nan zo ki hau na tafi da kafa. Wadanne irin maza ne zasu bar matarsu taje ta hau acaba, ko bashi da mota ai sai ya bata kudin drop har inda zata je a mota. Sai a lokacin na tabbatr da dalilin da yasa yake hararata rannan ashe, don na sauko daga kan acaba ne. Ya tayar da sallah, dr lukman ya miko min file biyu da wanda nazo dashi da wanda yayi cike cike yace in mayar mata ince bashi ba, koren file din zata bayar. Na durkusa na karba na fito da sauri, yayin da zuciyata ta cika da murna saboda yau taga abinda take muradi. Sai ya sake burge ni dana ga yana sallah, naji dadi danaji dalilin hararar da yayi min rannan ba tsana ta yayi ba. Sai na fara tunanin hanyar da zanbi in shiga harkarsa ba tare da yayi min wulkanci ba. Naci sa'a kuwa ina zuwa nayi mata bayani sai ta miko min koren file din da yace ta bani in kai masa. Na taho hanya ina farin ciki hade da fargabar abun da zanje in tarar. Na isa ofishin sai faduwar gaban da nake ji ta karu, na fara karanta ADDUAR WANDA YAJI TSORON MUTANE "Allahummakfinihim bimaa shi'ita" (Ya Allah Ka isar mini dasu da abin da kaso). Ina tura kai sai nayi sallama. Dr lukaman ne ya amsa, har yanzu gogan nawa yana kan abin sallah ya idar amma yana jan carbi. Na dago ido na dube shi a hankali, sai muka hada ido ni dashi, bansan wanda ya fara kawar da kai gefe ba. Na matsa lungu ina jiran dr lukman ya gama dubawa sai da na tabbatar lungun da na shige ko ya daga ido ba zai ganni ba. Na nutsu kai kace a gaban sarki nake, yadda nake sanda kai kace da kayan sata aka kamani, za'a yanke min hukunci. Wayar dr shuraim imran ce take ruri, kidan ringing tone din yana tashi a hankali, wakar soyayya ce ta celen dion mai taken come bake to me, sai ya danna amsa. Kalmar da ya fara ambato a cikin harshen turanci ita ta gigitani, tasa na dimauce sai na tsinci kaina har da kwalla mai radadin fita saboda kishi. Daga ji ba sai an fada min ba da matarsa yake magana, wacce yake tsananin so da kauna fiye da kowacce 'ya mace a duniya. Tunda nake a rayuwata ban taba jin namijin bahaushe da ya fadawa matarsa wannan kalma, ko da yake ni 'yar gargajiyace na tashi cikin 'yan gargajiya tsakanina da matansu sai ke zo nan, dauko, dafa, wanke, goge. Kullum sai hantara dube ki ballagaza, kazama, kwadayayyiya. Haka na saba ji tun tashina tsakanin miji da matarsa. Amma dr shuraim imran yace da abar kaunarsa, salam my dear, my heart, my life how are you and how is your trip? Hope cool. Duk da ban jiyo abinda zata fada ba itama da daddadar kalma ta mayar masa. Ya juye harshe sai turanci yake zazzagowa ya tambaya kuna ina yanzu? Sai ta bashi amsa, banji amsar ba sai yace ok kun bar london yanzu kuna amsterdam? Awa nawa zaku yi transit din? Ta fada masa, sai yace karfe goma dai dai zaku iso kano, ni kuma karfe tara a airport zata yi min da izinin Ubangiji. Ina kewarki, ina babyna? Can sai naji ya fara magana cikin muryar yara yana yiwa yaro wasa, sai na tabbatar 'yarsa ce itama da turancin yake mata magana. Kalmar da ya fada ta karshe daga ita ya kashe waya itace "I love u baby, I miss u too, I am eager to see ur beautiful face. Take care bye". Na dinga dauki ba dadi da zuciyata don so take ta tsinko fado kasa ta ragargaje don tashin hankalin da ta shiga. Dr lukman ya dube shi yayi dariya yace madam ce? Ya lumshe ido tace madam ce ita da baby sun taho yanzu suna amsterdam sun baro london. Kaji matar da take makaranta shine ta bar karatunta ta biyo ni. Dr lukman yace ah da gaskiyarta, yaushe zata zauna a can mijinta yana nan? Dr shureim imran yace toh ai matsalar ba zata iya zaman bane a nan, tana yin sati biyu a daddafe zata fara magiya inzo mu koma london, ita ba ta zauna tayi karatunta ba a can, ita bata bar yarinya tayi karatunta ba. Dr lukman yace ai da ta dinga barin yarinyar a gidan iyayenta ba suma a london din ba gidansu yake? Sai iyayenta su rike muku 'yar kai da ita ku karaci walagiginku tsakanin london da Nigeria. Dr shureim imran yayi dariya yace toh ai yarinyar harta fi uwar damuwa ai ita tace take so uwar tace sai an kawo ta ta ganni, sai tasa uwar tayi min waya fiye da sau goma a rana ace min ga baby tana kuka, wai tana son magana dani. Ina daukar wayar kasan abinda zata ce min? Daddy I miss you, sai ta kashe waya shikenan. Su dukka suka kwashe da dariya, dr lukman yace gaskiya ku canza tsari, ko kai ka hakura da zaman nigeria ka koma can ku zauna, daman a can kuka hadu. Dr shureim imran ya rike baki yace cafdi! Ai ba zai yiwu ba, ka manta halin babana ai ba zai bari inyi aiki a can ba, kasan shi da kishin kasar nan, babu dansa da bai dawo nigeria ba yanzu. Karatu kadai ya amince muje muyi, aiki kuwa dole mu dawo mu bautawa kasarmu, mu taimaki alummar hausa, fulani, musulmai 'yan uwanmu, bai damu da yawan albashin can ba. Dr lukman yace haka ka fada min, gaskiya ya burge ni. Ina ma za'a sami dattijan arewa irinsa masu kishin YARENSU DA ADDININSU da kasar nan, da kasar nan ta gyaru. Dr shureinm yace ai kuwa sanda zanyi aure hana ni yaso yi, dana dage ina so ni da ita ya shimfida mana sharudda masu tsauri. Tace taji ta gani zata bi duk abinda yace. Sharadi na farko da ya shimfida mana shine dole ta biyo ni nigeria mu zauna dindindin idan munje london hutu muka yi da zarar hutu ya kare mu dawo. Sannan dole ta bar shigar dan siket da wando ta saka atamfa ko leshi da mayafi don shi ya tsani english wears. Tace ta yarda yanzu ma zaman da ya bari tana yi na dan shekaru ne saboda karatu, ta kusa kare makarantar da zarar ta kare yace ta hado kayanta kakaf ta kaura kasar nan, dole anan kasar zatayi aiki ba a can ba. Tags : Itama kuma bata iya zaman kasar na, tsoron sauro takeyi, ko kuda ta gani sai ta hau kuka ta tashi da gudu. Baby kuwa tana burge ni babu abinda ba taci, kuma babu in da bata shiga ta zauna lafiya a kasar nan, bata damuwa da duk wani canji kuma itama a can aka haifeta kamar yadda aka haifi uwar a can. Dr lukman yayi dariya yace ah wannan ita ta biyo kakanta alhaji, komansu na gargajiya , babu zancen cewa ma kai ta biyo, don kai ma bature ne. Dr shureim imran yace ai kuwa baka san bature ba, ai ni ko a gidanmu sun san nina biyo alhaji sak, saboda ko wajen abinci bana cin su shinkafa, taliya , cake, macaroni da sauransu. Idan aka ga naci irin wadannan toh a london nake, ko abj don babu yadda zanyi. Nifa har kwano nake bawa direbana ya dauka ya tafi cikin gari unguwar su wani abokina neman danwake, dambu, ko gurasa mai kulikuli. Dr lukman ya kwace da dariya yace har da yawon neman dambu kake sawa ayi? Lallai dagaske kake. Ni kuma abinda ba'aci kenan a gidana ko tuwo zasu yi sai dai suyi min abincina daban, haba ai an wuce wannan lokacin ina yaro in nadi dambu da tuwo, yanzu da wayona da 'yan canjina a aljihi inci dambu? Ko ba haka ba 'yar boko, har yanzu kina cin dambu? Ya tambayeni, sai nayi sauri na dubi dodona dr shuriem, domin shi nake tsoro. Gogan nawa sai yayi dif bai sake magana ba, yaji an dako dani a zancensu. Jikina ya sake yin sanyi, nayi murmushi nace bana cin dambu nima. Dr lukman yace yawwa ashe bani kadai ne na gaji da cin tuwo ba, muna da yawa. Daga lokacin hirar ya koma ni da dr lukman kadai, dr shureim yaki tsoma baki. Dr lukman yace dani ke 'yar gidan matron maryam ce, naga kuna kama? Wannan karon ne ma naga dr shureim ya dubeni kasa kasa, sai yayi wuf ya mike tsaye yana nade abin sallah, ya linke ya ajiye sannan ya shiga daura neck tie a wuya, ya saka bakar suit dinsa. Cikin sanyi jiki nace a'a ni ba 'yarta bace, malamata ce kawai, muna shiri sosai. Dr lukman yaci gaba da rubutu yana magana yace ke ba 'yar gezawa bace kenan. Tunda matron maryam 'yar gezawa ce. Nayi dariya nace a'a ni ba 'yar kano nace ba ma, ni 'yar shagamu ce. Sai ya tsaya da rubutun ya dube ni ta cikin gilashinsa yace da gaske kike, ko kanwar yahaya umar ce? Babban abokina ne, ajinmu daya a sakandiren da muka yi a yobe. Sai nayi caraf nace yayana ne, babanmu daya. Sai ya fasa rubutun ya ajiye biro yace yanzu dan Allah yahaya umar yayanki ne? Na gyada kai nace yayana ne. Yace llallai kuwa naga kama, kina cewa ke 'yar shagamu ce sai naga fuskarku iri daya daman tun sanda na fara ganinki na rasa wanda kika min kama. Yana ina yanzu? Yana nan lagos yana aiki a tasha dan union ne. Yace subhanallah! Yanzu duk kokarin nan na yahaya umar bai cigaba da karatu ba a aikin tasha ya kare? Kinsan fa ni dashi muka kudiri niyyar sai munyi karatun likita. Tunda muka gama makaranta a. Yobe na dai ganinsa, naje gidansu a nan yobe nemansa ban same shi ba aka ce ya koma garin babansu shagamu, ashe dangin mahaifiyarsa ne a yobe ko? Shikenan rabuwarmu dashi, sai dai duk sanda aka ambaci shagamu sai na tuno shi, saboda dan shagamu muke ce masa. Mun shaku sosai dakinmu daya, ajinmu daya. Nayi murmushi nace eh dangin mahaifiyarsa ne suka rike shi a yobe, tun yana yaro, daya gama sakandire sai ya koma gida shagamu, bai cigaba da karatu ba kuma. Ina rufe bakin dr shureim ya shirya tsafa, ya dauki jakar laptop dinsa ya dubi abokinsa dr lukman. Yace ni na tafi sai kuma gobe. Dr lukman yace aini ma na tashi, ka jira ni yarinyar nan zan sallama kawai, ka ga ashe ma ni kanwata ce, haba tun sanda nake ganinta nake ganin kamar na san fuskar, ashe kanwar abokina ne childhood frnd yahaya umar. Ya tabe baki yace a'a ni dai nayi gaba, sai ka taho kawai. Ya fice ya bar mu. Bai ma bada amsar labarin da ya bashi ba saboda a kaina ne ba zai tsoma baki ba, sai na fara dankarawa zuciyata zagi akan ko taki ko taso sai ta rabu da son wannan marar mutuncin. Me yayi zafi? Dan kawai Allah yayi masa baiwa kala kala, yayi masa farin jini, ana sonsa sai ya dinga wulakanci, shi waye? Namiji ne fa kamar kowanne namiji, gasu nan birjik a titi suna bin mace tana musu yanga kafin ma ta kula su. Suna 'yar murya suna yi mata wahala, don ta saurare su. Haka na dinga kushe shi a zuciyata don in samu sukuni, duk yadda zanbi in raba zuciyata da sonsa bi nake yi don shine samun saukina. Dr lukman ya rufe file ya bani, tambayi lambar wayar abokinsa yayana yahaya. Nace bani da waya, amma zan karbo masa lambar a wajen yayana hussaini gobe zan kawo masa. Sai yayi mamaki don nace bani da waya, sai ya tambaye ni, yace faduwa wayar taki tayi ne? Kuma baki hadda ce lambarsa ba? Na amsa da eh faduwa tayi. Saboda sauri nake in fice daga ofishin saboda abin kaunata baya nan, daman saboda shi naji tsayuwar da nake yi bata isheni ba tun dazu, yana barin ofishin sai naji duk ofis din ya gindure ni. So nake in fito inga in daya nufa, kuma da wacce irin mota yazo yau. Nayi wa dr lukman sallama na fito bakin barandar da sauri, na waiga kowacce kusurwa sai ban ganshi ba, ko alamunsa babu, sai naji haushin dr lukman ya rufe ni, da bai bari na fito da wuri ba, gashi nan har ya tafi. Sai zuciyata tace ke da kike yi min fada in rabu dashi, ina ke ina takaicin don baki gan shi ba? Nayi ajiyar zuciya mai karfi naci gaba da tafiya maimakon inbi doguwar baranda sai na sauko na dinga kutsawa ta kasa cikin motoci. Ban sa ran ganinsa ba ko kadan amma dai nasan dole ta nan ya bi, idan zai dauki motarsa ko sawun takalmansa na taka ai naji sa'ida a raina. Kamar daga sama naji wata murya mai shige da tasa daga gefena, abin da yake fada kuwa shine "wait, wait dr hidaya, na fada miki na sake fada miki don Allah ki daina damuna da waya cikin dare, yau matata zata zo kasar na, bana so ki jawo mana matsala. Aiki ne ya hada mu anan idan an tashi daga aiki to ban sanki ba kowa ya kama gabansa. Wanne irin abu ne haka, ina zan saka raina? A asibiti a dame ni har gida ma kun fara bina? Yaya akayi kika nemo gidanmu har kika ba mai gadinmu sako ya bani? A wanne dalile zakiyi min sayayya ki kai min gida? Zaki jefa rayuwata cikin damuwa tsakanina da matata, da kuma iyayena. Na dinga tafiya a hankali ina kallonsu, a tsaye suke a jikin motarsa har ya bude mota zai shiga sai ta tsayar dashi. Ransa a bace yake magana cikin matsanancin fushi, sai ita ma ta fusata ta magana cikin kuka da fada. Dr shureim in har ni 'yar halak ce a cikin uwata da ubana na kyale ka, har abada ba zan sake nemanka ba. Ya fada cike da gadara yace shi yafi sauki, naji dadi sosai kuwa. Ta juya a fusace tana sharce hawaye, yayin da farin gilashin idonta ya fado kasa, ido daya ya fita. Na karaso da sauri na dauko mata na mika mata, sai ta dube ni jajayen idanuwanta ta karba gami da ce min thank u very much. Ta wuce da sauri. Dr shureim ya dube ni, ya sake bude ido ya kalle ni sosai, na tsaya cak kamar yadda yake tsaye kyam yana dubana. Na harare shi sama da kasa naja dogon tsaki na kada kai na wuce na bar shi nan a tsaye bai daina kallona ba, ni dai ban waiwaya ba. Na san ya cika da mamakina, ni dai burina ya cika tunda na fara ramawa kaina wulakacin da yayi min da sauran wahallalun mata da 'yan uwana masu sonsa. Na kudiri aniyar kallon arziki ya daina hada mu sabida na san ba zan same shi ba kamar sauran da suka fini haduwa, ga kyau basu same shi ba. Kamar daga sama naji wata murya mai shige da tasa daga gefena, abin da yake fada kuwa shine "wait, wait dr hidaya, na fada miki na sake fada miki don Allah ki daina damuna da waya cikin dare, yau matata zata zo kasar na, bana so ki jawo mana matsala. Aiki ne ya hada mu anan idan an tashi daga aiki to ban sanki ba kowa ya kama gabansa. Wanne irin abu ne haka, ina zan saka raina? A asibiti a dame ni har gida ma kun fara bina? Yaya akayi kika nemo gidanmu har kika ba mai gadinmu sako ya bani? A wanne dalile zakiyi min sayayya ki kai min gida? Zaki jefa rayuwata cikin damuwa tsakanina da matata, da kuma iyayena. Na dinga tafiya a hankali ina kallonsu, a tsaye suke a jikin motarsa har ya bude mota zai shiga sai ta tsayar dashi. Ransa a bace yake magana cikin matsanancin fushi, sai ita ma ta fusata ta magana cikin kuka da fada. Dr shureim in har ni 'yar halak ce a cikin uwata da ubana na kyale ka, har abada ba zan sake nemanka ba. Ya fada cike da gadara yace shi yafi sauki, naji dadi sosai kuwa. Ta juya a fusace tana sharce hawaye, yayin da farin gilashin idonta ya fado kasa, ido daya ya fita. Na karaso da sauri na dauko mata na mika mata, sai ta dube ni jajayen idanuwanta ta karba gami da ce min thank u very much. Ta wuce da sauri. Dr shureim ya dube ni, ya sake bude ido ya kalle ni sosai, na tsaya cak kamar yadda yake tsaye kyam yana dubana. Na harare shi sama da kasa naja dogon tsaki na kada kai na wuce na bar shi nan a tsaye bai daina kallona ba, ni dai ban waiwaya ba. Na san ya cika da mamakina, ni dai burina ya cika tunda na fara ramawa kaina wulakacin da yayi min da sauran wahallalun mata da 'yan uwana masu sonsa. Na kudiri aniyar kallon arziki ya daina hada mu sabida na san ba zan same shi ba kamar sauran da suka fini haduwa, ga kyau basu same shi ba. Da na koma gida, dare yayi sai bacci ya gagare ni, na shifa zulumi da fargabar kallon da nyi masa. Naji kwata kwata ban kyauta ba, tausayinsa ya rufe ni, yayin da sabon sonsa ya tsatsafo daga cikin zuciyata. Na dora hannu aka ina fadinn na kashe kaina da kaina, me ya kaini yi masa wulakanci ni da nake addua, ina saka ran zan same shi watarana? Na shiga adduar Allah Ya sa baiji haushina ba. Gari na wayewa na shiga shiryawa, na tsaya na tsarawa fusakata kwalliya yadda zanyi kyau sosai. Nayi sauri na tare yaya hussaini zai fita aiki, nace ya bani lambar yaya yahaya wani abokinsa likita ne ta ke nema. Naci sa'a ya rubuta min akan wata 'yar takarda anan take ya miko min, ko karya kumallo ban tsaya na yi ba, na fice. Allah cikin ikonSa ina sauke kafata daya daga kan acaba ko dayar ban sauke ba a bakin gate din asibiti, sai ga dr shurim ya karyo zai shiga gate. Ya galla min harara sannan ya figi motarsa ya wuce, sai naji dariya ta subuce min, nasan dalilin hararar da yake min bai wuce don na hau acaba ba, ni kuwa ko a jikina. Acaba kuwa yanzu na fara hawa tunda ya tsani yaga mace akan acaba. Idan baya so mu hau sai ya saya mana motar hawa ni da 'yanuwana mata masu hawa acaba. Sai na tsinci kaina ina tafe ina farin ciki, ko babu komai dai yanzu ya fara sanina, hararar dana samu ma naji dadi, nafi wadanda bai san suna raye ba. Kai tsaye ofishinsu na bishi, kafin in isa har ya kai cikin ofis. Ina murda kofa sai ta wangale sai gani kicibus gabansa, bai amsa sallamata ba sosai a ciki ciki ya amsa kamar baya so, kallo daya yayi min ya dauke kai yaci gaba da dube duben littafin da yake kan teburinsa , yana tsaye. Na gaishe shi yayi kamar baiji ba, na fada cike da gatsali dr lukman nake nema. Ya fada cike da takaici, kuma aka ce miki nan ne ofishinsa ko? Na fada cikin tsiwa eh a nan na ganshi jiya shi yasa yau nazo nan nemansa. Sai ya dago da sauri ya dubeni cike da mamaki. Can ya dukar da idonsa kasa, yaci gaba da dube dubensa, bai bani amsa ba. Na rike kugu nace ga sakonsa dan Allah ko zaka ajiye masa? Ya sake dagowa a fusace ya fada cikin fushi, ke an fada miki nan ba ofishinsa bane, kije ki tambayi inda ofis dinsa yake. Ko nayi miki kama da wanda zaki bawa sako? Na murguda baki nace saboda nan matron maryam tace min inzo in same shi jiya shiyasa yau ma nazo. Na juya a fusace na fice na ki rufo masa kofar sosai. Sai naga ya biyo bayana, ya dade a tsaye yana kallona ina tafiya har na fice daga harabar, na barshi zuciyarsa cike da takaici. Na fara samun sa'ida a zuciyata tunda na fara samun damar yin magana dashi, duk da ba maganar arziki bace. Dana dawo ofishin da rana, sai na sami dr lukman a ofishin dr shureim baya nan. Mun dade muna hira da abokin yayana, naki tafiya da wuri ina saka ran ko zai dawo sai bai dawo ba, takaici ya isheni. Na koma gida cike da tunaninsa da sonsa zokar a cikin zuciyata, ko rufe idona nayi suffarsa ce ke fado min. Ina matukar son abinda ba zan samu ba, sai inyi kuka inyi dariya ni kadai bana mantawa da addua, ina neman agaji daga wurin Ubangijina. Nafi adduar Allah Ya yaye min sonsa akan adduar Allah Ya karkato da tunaninsa kaina, saboda a ganina shi zaifi yi min sauki duk da babu abinda ya gagari Allah. Sai inyi ta shawagina cikin asibiti a satin nan ko Allah zai sake hada ni da dr shureim, ban ganshi ba ko a hanya, ni kuma bana so inje ofishinsu saboda zai gane akwai wani abu a zuciyata. DUK KYAN TAKALMI 9 Sai dai kash! Na rabu da karatuna har 'yan ajinmu sun gane hankalina baya kan abinda ake koya mana, ban ma cika tsayawa a wajensu ba, bini bini a neme ni a rasa. Nima na rasa kaina, duk likitan da naga ya wuce da bakar suit sai na bishi da kallo in zata abin kaunata ne, sai inga ashe bashi bane, raina yayi ta baci. Matron maryam ta lura da haka sai tayi ta tambayata, amsar dai ita ce babu komai, idan aka dame ni ince bana jin dadin jikina. Haka ma dai a gida amsar iri daya ce, data makaranta ga duk wanda ya dame ni da tambaya. Na zama tababbiya a cikin satin nan da ban ganshi ba. Addua nake Allah Ya yaye min amma tamkar sonsa karuwa yake a zauciya, ban taba sanin haka dacin soyayya yake ba a rayuwata ko a film da littafi ban taba ganin irin abin da ya faru dani ba. Haka kawai na fara son mutumin da bai san inayi ba. Shiyasa a rayuwa ba a so ka cika baki akan abu, muddin ka cika baki akan wani abu tabbas abun nan sai kaga ya same ka. Bazan manta ba shekaru hudu da suka wuce akwai wata kawata ummi, ajinmu daya a shekara. Allah Ya jarrabe ta da son wani malamin mu mai suna abdul yasar, shima danji da kaine kamar dr shureim. Duk sanda taje wajensa sai yayi mata wulakanci ita kuma tazo tana kuka tana fada min, takaici ya kama ni maimakon in bata hakuri sai inyi ta zaginta, ina Allah wadari da halinta. Kullum sai ince mata me akayi aka yi da namiji? Har zata je yana wulakanta ta, duk a cikin samarinta ma babu kassararre, talaka, bakauye ma irinsa, duk sunfi shi haduwa ta rabu dashi mana. Sai tace min ita dai shi take so bata son sauran. Kuma taci gaba da nace masa tanayi masa wahala bayan mun gama makaranta daga karshe ya aureta. Ranan wata asabar da hantsi na shirya naci ado da wata atamfata shudiya, tunda ranar babu makaranta saina zankadawa yayana da matarsa karya nace a asibiti ake nemanmu zamu yiwa yara allurar rigakafi, yayana ya zaro kudin acaba naira dari biyu kamar yadda ya saba bani kullum. Na nufi gidan ummi domin inji hanyar da ta bi ta samu mai gidanta abar kaunarta abdul yasar. A kofar nasarawa gidanta yake duk da na dade banje gidan ba, amma naci sa'a na gane, rabona da gidan tun ranar da muka kai ta, haka da ta haihu ma a gidansu muka same ta muka yi mata barka, 'yar unguwar zango ce. Cike da fargaba na shiga gidan don kada ace min bata nan inyia asarar kudin babur din da na kashe nazo, ga na komawa gida. Sai naci karo da maigidanta a zauren gidan. Nayi sauri na duka na gaishe da malamina, ya amsa a gaggauce ko kallon kirki baiyi min ba, da alama dama ya tsane ni. Nasan dadin soyayya yasa ummi ta zazzage masa shawarwarin da na sha bata cewar ta rabu dashi bakauye ne, bai hadu ba. Babu wanda ya fada min haka, na lura tun a lokacin bikin yana kula sauran kawayenmu nice kada baya son yiwa magana. Na wuce cikin gidan sadan sadan don banga fuskar da zan tambaye shi tana nan ko bata nan ba. A tsakar gida na ganta ta buga tagumi da alama akwai damuwa a tattare da ita. Tana ganina sai ta mike da sauri ta rungume ni, na dauka dariya takeyi, sai naga hawaye. Na cika taf! Na tumbatsa da mamaki na rike ta ina tambayarta ko lafiya? Taja ni zuwa cikin dakinta muka zauna a gfen gado tana magana cikin kuka. Tace aisha farida wulakancin da yassar yake min ya isheni, don kawai yaga bazan iya rabuwa dashi bane. Nayo shiru na kasa magana, yayin da na shiga hankalina na fasa tambayar abin da nazo tambaya. Ashe har yanzu da sauran rina a kaba, ko a yanzu na auri dr shureim ashe idan naje gidan ma wulakanci yana nan zokar. Zuciyata ta fara yimin fada tana cewa farida ki yi ta kanki, ki cire son dr shureim imran idan ba kin zabi ciwon zuciya ya zama ajalinki ba. Na tambaya cikin sanyin jiki wai ke ummi yaya aka yi ma tun farko ya amince ya aureki bayan baya sonki? Tace ashe ba dake muka je ba, da maijidda lawan mukaje wajen wani malami a kurna. Sai na dafe kirji na fada a gigice, na shiga uku ummi! Malami kuma? Ta gyada kai tace shine yayi min aiki yace dole sai yasar ya zo ya aure ni ko ba a hayyacinsa ba. Kuma yazo din ya aure ni, har nake juya shi yadda nake so, sai bayan da na haihu ban koma ba. Kinsan ance idan mace ta haihu duk wani sihiri da tsarin da yake jikinta karyewa yake yi, sai tayi sabon shiri. Kuma kin san halin malaman zamanin nan sunfi so ka dauwama kana zuwa wajensu kana kai musu abin da ka kwakwala daga wajen mazan, idan ka dauke kafa bayan bukata ta biya sai su karya maka aikin, komai sai ya cakude dole sai ka dawo. Sannan yanzu bani da waya, bama magana dashi ta waya, daya fada min irin sadakar da zanyi dan duk ranar laraba yanayi min waya yace nayi sadakar sukari ko nono na aljanar da take kula da soyayyar da yasar yake min, kinga na dade banyi sadakar ba. Hankalina ya tashi, abin da nake gani a film yazo har gida. Nace ummi tsafi kenan fa? Tace haba dai tsafi, babban malami ne fa ya iya jan aya, baki ga matan manya da masu kudin garin da suke layi a gidansa ba, talakawa irina kadan ne. Ya iya aiki fa. Zuciyata ta fara rabuwa gida biyu, inje ko kar inje? Amma fa jikina bari yake yi, naji tana ambaton aljana a cikin al'amuran. Daga karshe zuciyata ta yanke min, kawai inje ni ma ayi min asirin da dole zaizo ya so ni ko da daga baya asirin ya karye ai dai naci riba tunda bani da buri a rayuwata irin in ga na same shi yayi min magana ma kawai, balle ace yazi gidanmu har anyi maganar aure dashi, ya aure ni na tare gidansa, ai ba karamar riba bace a rayuwata. Kuma idan haka ne in anyi auren ai sai in ringa komawa wajen malamin ina kara masa kudi yana cigaba da sona, yana fada min abinda zan bayar sadaka ina yin sadakar yadda son ba zai tafi daga zuciyarsa ba. Tunda kafin lokacin bikin na gama makaranta na fara aiki, ko da albashina na dinga biyan malam ko bai bani kudinsa ba. Sai na gyara zama nace ummi nima fa matsalar da take tafe dani kenan, nima irin naki ne ta same ni. Allah ya jarrabe ni da son wani likita a asibitin da nake attachment, amma fa likitan yafi ni haduwa nesa ba kusa ba, gashi daji da kai da wulakanci, har yafi malam yasar dinki. Na rasa yadda za'ayi ya saurareni ma balle ayi zancen soyayya. Baki ga yadda hadaddun likitoci mata suke binsa ba yaki sauraronsu. Kawayena biyu suke yi masa asiri dan ya sosu amma bai kama shi ba, ina jin ya shirya kansa asiri baya cinsa. Wani babban tashin hankali ma yana da mata ina jin ma baturiya ce a london suka hadu sukayi aure, ita ma yanaji da ita, nasan ta fini kyau nesa ba kusa ba. Ya zanyi? Ummi ta daki kafada ta tace ke dalla wawuya daman ke irin wannan mutumin kika samu amma zaki bari ya subuce miki? Lallai kin cika wawuya baki da wayo. Ai kawai kije a zuba miki aiki tuntuni zaiji ya tsani baturiya ya biyo ki, balle mai kudi ne, kina shiga zaki fanshe kudafen da kika kashe a kansa. Na girgiza kai nace babu ruwana da taba matarsa, suyi zamansu ni dai yaso ni kawai, tunda ina sonsa. Idan kuma akwai abin da malamin zai yi min na daina sonsa ni nafi son haka, saboda nayi iyakacin adduar da zanyi don na daina jin sonsa na kasa dainawa kullum karuwa yake ma. Ummi tace yaya za'ayi kice a cire miki sonsa ai shirme kenan. Ace yaji abin da kike ji koma ince fiye da yadda kike ji don an fi son namiji yafi na mace sai afi zama lafiya. Ke ban da abinki wata budurwar ba irin wannan take nema ba ma ta kai shi wajen malami a rike mata sai ko ta wanne hali, ko ba komai ai ka tsira da kudi ko babu soyayyar. Na girgiza kai nace ai ni ba kudinsa nake so ba, shi nake so. Ni na yadda ya so ni kada ma yabani kudinsa, na yarda idan na fara aiki in ciyar da kaina ba sai ya ciyar dani ba. Ummi ta rike baki tace Aisha farida haka kike sonsa kamar ki cinye shi? To ko asiri yayi miki irin wannan son dai bana lafiya bane. Na girgiza kai nace ko kadan, Allah ne yayi masa baiwar kyau, ilimi, arziki, da jan aji dole mata suke sonsa. Shi kansa baya son haka. Bai ma san inayi ba balle ace shi ma yana sona har yaje yayi min asiri. Jarraba ce kawai ta afka min, nima ba don ina so ba, haka Allah ya tsaro min. Sai na fashe da kuka. Ta rungume ni tace taso muje in kai wajensa yanzu, nima daman ina shawarar zuwa yau ko gobe, al'amarina ya cabe ni da yassar. Na mike tsaye ina goge hawayena yayin da ita kuma ta canja kayan jikinta ta saka wata jar atamfa riga da zani ta goya 'yarta da take barci akan gado, muka fito ta kullo dakin. Ta leka tayi wa matar kanin mijinta sallama wacce katanga ce kadai ta rabu tace da ita zamuje bakin asibiti zata raka ni inyi sare sare. Muka fito muka kama hanya tun a hanya na sanar mata ko kudin mota bani dashi, tace babu komai zata biya min, gakudin cefanenta nan yau ko cefanen ma bazatayi ba. Ce masa zatayi dan aiken ya zubar da markade. Ta juyo ta dube ni tace to ke yanzu da baki da kudi yaya za'ayi miki aiki? Dole fa sai kin kashe kudi idan kina son aiki yace. Tafiya mai nisan gaske mukayi a motar bus mai zuwa kurna, sai da muka hau acaba muka niki tafiyar kafa saboda babur ma ba zai iya shiga lokon ba, wahala iri iri muka sha kafin muka isa gidan. Nace muje dai muji, na san yadda zanyi. Sai na fashe da kuka. Ta rungume ni tace taso muje in kai wajensa yanzu, nima daman ina shawarar zuwa yau ko gobe, al'amarina ya cabe ni da yassar. Na mike tsaye ina goge hawayena yayin da ita kuma ta canja kayan jikinta ta saka wata jar atamfa riga da zani ta goya 'yarta da take barci akan gado, muka fito ta kullo dakin. Ta leka tayi wa matar kanin mijinta sallama wacce katanga ce kadai ta rabu tace da ita zamuje bakin asibiti zata raka ni inyi sare sare. Muka fito muka kama hanya tun a hanya na sanar mata ko kudin mota bani dashi, tace babu komai zata biya min, gakudin cefanenta nan yau ko cefanen ma bazatayi ba. Ce masa zatayi dan aiken ya zubar da markade. Ta juyo ta dube ni tace to ke yanzu da baki da kudi yaya za'ayi miki aiki? Dole fa sai kin kashe kudi idan kina son aiki yace. Tafiya mai nisan gaske mukayi a motar bus mai zuwa kurna, sai da muka hau acaba muka niki tafiyar kafa saboda babur ma ba zai iya shiga lokon ba, wahala iri iri muka sha kafin muka isa gidan. Nace muje dai muji, na san yadda zanyi. Munci sa'a babu layi sosai, mun tarar da maza uku a kofar gida, mata biyu a cikin gida. Muka gaishe su muka bi layi. Gabana sai faduwa yake tamkar zuciyata zata fito sarari, sai in zunguri ummi ince na fasa ta tashi mu tafi. Sai ta mintsine ni tace ba inda zamu je sai mun shiga. Na daure har layi yazo kanmu, muka shiga ciki. Daga sanda naga kasar duba da dogon carbi sai na tabbatar na kauce hanya, domin nasan makomar masu bin 'yan tsubbu masu duba, in har kaje wajen mai duba ya fada maka gaibu ka yarda dashi, to baka da sallah har tsawon kwanaki arbain. Allah ba zai karba ba. Ya san ummi sosai, ya san matsalolinta don haka sai ya hau mata bayani. Tace malam a bincika min dai. Sai ya jawo farantin kasa yayi zane zanensa ya hau yi mata bayanai kamar wanda ke karantawa. Na dubi kasar naga babu rubutu babu alamarsa na rasa inda yake karanto wadannan labarai, sannan na dubi sama da kasa banji motsin wanda yake fada masa ba. Yace ummi wannan tsohuwar budurwar nan tasa da yake so itace take raba ku, ta tashi tsaye tana asiri sai ta fitar dake ta shiga gidan, sannan faccalatki matan kanin mijinki da kuke gida daya, itama tana saka miki hannu saboda mijinki ya fi nata zuciyar nema, kin fi ta hutawa, don haka take so ta raba ku. Tags : Ummi ta fusata ta hau bayani. Lallai biri yayi kama da mutum, domin tun sanda mijina ya siyo mana generator sai ta yini a daki baata fito tsakar gida ba, haka ma zance tsohuwar budurwarsa ba su rabu ba suna tare har yanzu, naga sakonta a wayarsa. Yanzu malam yaya za'ayi? Sai naga ya karkace ya zayyano mata abubuwa kamar su turarruka na wuridi, kaji, dan akuya ja, farin kyalle da kudin yaran dazasu zauna aiki, dubu ashirin da biyar. Ko ta nuna damuwa ma batayi ba sai kawai ta ce gobe zan kawo dubu goma sha biyar a fara, don Allah malam ka ragargaza min su kamar yadda suke son su raba ni da mijina suma a rabasu da mazansu, ni kuma mu zauna daram ina so a kama min shi don wulakanci yake yi min kwanan nan har da cewa bai san inda yake kallo ba ya aure ni, don ni ba irin tsarin rayuwarsa bace. Sakacinki ne inji malam. Ya juyo ya dube ni sai na takure a lungu kirjina yana dukan ukuk uku. Yace ke fa meye matsalarki, ko baki fada ba zan iya ganin asiran da akayi miki a jikinki, ki tashi tsaye wajen neman tsari. Ummi ta kwanto da 'yarta daga bayanta ta gyara zama tace malam, aisha farida kawata ce, a taimaka mata. Matsalarmu kusan iri daya ce, ayi mata bincike tukunnan. Ta bukaci ina saka abin sadaka kafin ya fara, sai ummi ta zaro dari biyu zata mika masa na rike hannunta nace ba sai an bincika min ba malam zan fada da bakina. Na koro masa bayani tas, sai yayi dariya ya kyakyata yace wannan karamin aiki ne a wajena, idan har zaki sayi kayan aiki na baki kwana biyu inda dr shureim imran ne kim gama samunsa. Ina jin haka sai naji farin ciki ya lullube ni nayi dariya, na tambaye shi me dame za a siya? Sai yayi min zancen abubuwa daban daban, wasu na sansu wasu ban sansu ba. Aka hada kudin ya kama naira dubu ashirin da daya. Sai na dafe kirji nace malam bani da kudi ko zaka yi min bashi idan komai ya kankama sai in biya? Ya dubi ummi cike da bacin rai yace ina kika samo min wannan yarinyar? Baki fada mata dokar aikina bane? Sabon shiga ce ko? Toh ni bana fadar farashi a nemi ragi balle ace inyi a bashi, a cikin kudin nan babu sisi nawa, duk na rauhanai ne. Ummi tace ayi hakuri malam, laifina ne ban fada mata dokokinka ba zamu dawo gobe tare zamu nemo kudin mu kawo. Mun goda. Banyi godiya ba na kada kai na fito, hankalina ya gama tashi. Muna fita kofar gida ummi ta hau yi min fada tana cewa me yasa ban bari anyi min bincike ba inji bayani dalla dalla ba, sannan me yasa nace ayi min aiki bashi alhali tun a kan hanya na baki labarinsa? Nace to bani da kudi ko naira hamsin ta kaina bani da ita. Me zance? Tace ki sayar da kadararki mana. Nace ai bani da ko barimar gwal balle dan kunne. Ta tabe baki tace ni dai shawarar da zan baki itace kije kisan abinyi don nima nan da kika ganni bashi zanje in ciyo in kai masa idan aiki yaci da kansa zai baki kudi kije ki biya. Malamin nan fa aikinsa kamar yankan wuka, sha yanzu magani yanzu. Kije kiyi tunani zuwa gobe ki samo kudi, kizo mu kai don ni ma daga nan gari zan shiga neman bashi. Ta bani kudin mota mukayi sallama na shiga motar unguwarmu, ita kuma ta shiga motar dawanau ban san inda ta nufa ba. Ina zaune a mota tamkar gunki ina tunani, sai da kondasta yyayi ta magana sannan na gane dani yake, na mika masa kudin mota. Haka da aka zo inda zan sauka ma na manta har aka wuce dani, sannan na ankara nace a sauke ni. Saida na dawo baya. Na shiga gida a cakude, narasa inda zan saka raina, tunanina gaba daya ya koma wajen inda zan samo rancen kudi in kaiwa malam gobe. Cikin unguwar nan da batsewarta babu matar da zata iya fitar da dubu biyar ma kai tsaye saboda talauci. Da yamma na shirya na fita neman kudi gida gida, da kyar na hado rancen dubu biyu. Na zarce kai tsaye shagon da musbahu yake sana'a. Sai yayi matukar mamakin ganina ya tambayeni lafiya ya ganni a hargitse haka? Na fada masa cewar matsalar kudi ce ta taso min, bani da lafiya. 'Yar karamar tiyata za ayi min gobe a asibitin ana neman naira dubu ashirin. Sai ya dafe kirji yace aisha farida babu inda zan sami dubu ashirin a yau. Ai ko bashi babu in da zan samu. Ko idan anyi wa likitan bayani zai yarda yayi miki aiki a bashi karshen wata sai in biya shi. Na girgiza kai nace babu zance bashi kuma dole in hada kudin daga yau zuwa dare. Yace to inje gida zai aiko yaro ya kawo min abin da ya sauwaka. Zaije ya fita ya nemo abinda ya samo. Nayi godiya na tafi. Ko awa guda banyi ba da shiga gida sai ga dan aike da dubu uku har da doguwar wasika yana mai bani hakuri abin da ya samo kenan. Amaa zaici gaba da nemowa zuwa gobe. Ya jero min kalaman soyayya ko gama karantawa banyi ba na yayyaga na zubar, burina in hada kudin nan in kai. Ina zaune a mota tamkar gunki ina tunani, sai da kondasta yyayi ta magana sannan na gane dani yake, na mika masa kudin mota. Haka da aka zo inda zan sauka ma na manta har aka wuce dani, sannan na ankara nace a sauke ni. Saida na dawo baya. Na shiga gida a cakude, narasa inda zan saka raina, tunanina gaba daya ya koma wajen inda zan samo rancen kudi in kaiwa malam gobe. Cikin unguwar nan da batsewarta babu matar da zata iya fitar da dubu biyar ma kai tsaye saboda talauci. Da yamma na shirya na fita neman kudi gida gida, da kyar na hado rancen dubu biyu. Na zarce kai tsaye shagon da musbahu yake sana'a. Sai yayi matukar mamakin ganina ya tambayeni lafiya ya ganni a hargitse haka? Na fada masa cewar matsalar kudi ce ta taso min, bani da lafiya. 'Yar karamar tiyata za ayi min gobe a asibitin ana neman naira dubu ashirin. Sai ya dafe kirji yace aisha farida babu inda zan sami dubu ashirin a yau. Ai ko bashi babu in da zan samu. Ko idan anyi wa likitan bayani zai yarda yayi miki aiki a bashi karshen wata sai in biya shi. Na girgiza kai nace babu zance bashi kuma dole in hada kudin daga yau zuwa dare. Yace to inje gida zai aiko yaro ya kawo min abin da ya sauwaka. Zaije ya fita ya nemo abinda ya samo. Nayi godiya na tafi. Ko awa guda banyi ba da shiga gida sai ga dan aike da dubu uku har da doguwar wasika yana mai bani hakuri abin da ya samo kenan. Amaa zaici gaba da nemowa zuwa gobe. Ya jero min kalaman soyayya ko gama karantawa banyi ba na yayyaga na zubar, burina in hada kudin nan in kai. Uwani uwar adashe ita kadai na tabbatr zan iya samun rancen kudi a wajenta ko nawa ne saboda itace naga koda yaushe mata suna aiko mata da zubin kudin adashe, ina hango shigarsu da fitarsu daga windon dakina domin dakinta na kusa da dakina. Ina idar da sallar magriba na tabbatar abida tana daki tana wuridi ba zata fito tsakar gida ba, sai tayi sallar ishai kamar yadda ta saba. Sai nayi sanda na fito dakina na fada dakin uwani, sai tayi mamakin ganina a wannan lokaci, naci sa'a maigidanta bai dawo ba. Ta saka fitilar kwai a gaba tana kirga kudi kashi kashi. Farin ciki ya rufe ni da naga kudin nan sai na shiga marairaice mata inayi mata dadin baki cewar ta ranta min dubu goma sha bakwai zan biya ta gobe da yamma. Ta tsorata matuka har da dafe kirji ta tambaye ni, me zakiyi da kudi haka? Na shaida mata kawata ce zata haihu a asibitinmu ance ba zata iya haihuwa da kanta ba sai an yi mata tiyata. Ga mijinta ba ya gari yana lagos. Amma ya sako kudin ta banki, to kasancewar asabar ce babu banki, lahadi ma babu aiki ba za a iya fitar da kudin ba, sai ranar litinin. Shine tace in ranto mata zuwa litinin zata biya. Uwani tace a'a aisha farida kinsan halin mutane kayi musu rana suyi ma mutum dare. Ki zo ki taimake su suki biya, ko kuma ni in taimake ki, kiki taimakona. Kinsan dai kudin nan da kika gani kudin cizo ne, bana kashewa bane da masu shi. Gobe haj rabi ce zata dauki adashen nan dubu talatin. Mace dayace bilki bata saka mata ba, na aika tace gobe zata aiko yana aikowa sai in hada in aikawa haj rabi daukarta. Yanzu idan na baki aka zo aka sami matsala yaya zanyi? Kinsan bani dashi, lada suke bani duk wata dubu daya dan tarawar da nakeyi. Niko ikon sgiga adashen ma bani dashi dan bani dashi. Nace na sani uwani, idan Allah Ya yarda babu matsala, ranar litinin da sassafe zanje bankin da kaina in karbo miki. Tace to shikenan gashi nan. Ta kirgo dubu goma sha bakwai tabani, na karba na kirga sun cika cas, nayi godiya. Sannan na roki arzikin ta rufa min asiri kada ta fadawa kowa ko abida kada taji, salin alin zan dawo mata da kudinta. Tayi min alkawari babu wanda zaiji. Na shiga daki na hada kan kudina na adana a jaka. Naira dubu ashirin. Farin ciki fal a zuciyata, har sai da abida ta fuskanci haka a daren, a da bana iya cin abinci sosai, amma a daren taga har da kari nayi. Da bana son magana sai taji na isheta da labari a ranar. Ta san na daina fara'a amma a ranar na ishe ta da kyakyata daria har da wake wake. Saboda na riga na sami kudin da bana tantama na gama samun dr shureim imran. Gari na wayewa na shiga tunanin karyar da zan shiryawa yaya hussaini wacce zai bari in fice, domin ranar lahadi ce babu aiki, kuma kulle yake min. Na shirya tsaf na kira abida gefe na shirga mata karyar cewa zanje asibiti yau ma, ana yiwa wata nurse bikin gama aiki, tayi retire ance kowa sai yaje kuma da kayan gida. Na santa da wayo ta san yadda zata fadawa maigidanta ya aminta da ita. Ta shiga daki ta tsaro shi sai ga ta da dari biyu kudin babur. Naji tausayinsu ya kama ni saboda nafi su kudi yanzu, da sun san kudin da yake jikina da basu rabu da dari biyunsu ba. Nayi godiya na karbe na tafi, abida ta rakani har zaure tana yi min fatan alkairi. Tana jaddada min in ragowa 'ya'yanta kayan walima. Na amsa mata da zan rago musu da yawa ma kuwa. Ina fita na hau acaba sai gidan ummi kawata. Da yake sassafe ne mijinta ma bai fita ba yana daki, tajani zuwa falonta muka zauna muna magana cikin sirri. Ta tambaya yaya ake ciki, na samo kudin kuwa? Na ciro mata himilin kudin daga jakata sai ta rike baki tace lallai kinyi kokari, nima na hada dubu goma sha biyar bari inje inyi masa karya inzo mu tafi. Yau lahadi ba zai fita da wuri ba, gara muyi tafiyarmu. Ta shiga daki ba dadewa ta fito a shirye da goyonta muka nufi kofar fita, har mun kai zaure faccalarta ta biyo mu da sauri. Tana cewa ummi unguwa zakije baki fada min ba mu fita tare? Yau ne sunan mariya 'yar jummai, ki tsaya in shirya mu fita gaba daya mana. Ummi ta doka mata harara tace dani aisha faida da Allah muje, dole ne sai mun fita tare. Myka kada kai muka fice muka bar ta a tsaye tana kallonmu har abin tausayi. Muna fita nace da ita haba ummi ya za ayi kiyi mata wulakanci? Ai sai ki bata amsa mai dadi ko ba kya so tabimu. Ummi ta tabe tace ai na daina raga mata tunda bincike ya nuna bata kaunata. Ni da mutunci da ita har abada. Nace to amma ai maganar malamai ce, babu tabbas zaiyiwu kirkira yayi. Ta harare ni tace lallai kina wasa da aikin malamin nan. Idan yayi miki duba tabbas zaki ga komai a hankali daya bayan daya. In bai gani ba zai fada ne ko da ya taba ambato sunanta in ba yanzu ba, kuma nima na lura tun sanda muka sayi generator ta canja min, taga mun cigaba a rayuwa. DUK KYAN TAKALMI 11 Bansake magana ba dai har muka isa gidan malam. Yana ganin mu ya fara washe baki, fara'ar yau tafi ta jiya. Muka zazzage masa kudaden jakarmu kakaf domin bayan dubu ashirin da dayan da ya karba sai da ya sake kwakwalo min wasu kudaden daban daban har dubu biyar da dari biyar. Kuma na harhada na bashi, a takaice dai har cikon dubu daya da dari biyar nan gaba zan ciko masa. Ita ma ummi ya kara mata wasu kudin, idan ta tashi cikowa ba dubu goma zata ciko masa ba, goma sha uku zata ciko. Yace ya bamu kwanaki uku mu dawo, ranar laraba kenan kafin komai zai daidai ta. Muka fito muna murna, ummi tana tabbatar min komai zai daidaita in kwantar da hankalina. Na tafi gida ita ma ta koma gidanta, na sake shirgawa abida wata karyar tunda ban taho da kayan walima ba, naso in siyo musu lemo da biskit amma na juyewa malam kudin dukka, da kyar ma na karaso gida, sai da kudi ya kare. Ko kusa ban damu da himilin bashin dake kaina ba, burina aiki yaci in mallaki dr shureim shine a gabana. Na yina ina hidindimuna da 'yan gidanmu cikin walwala da farin ciki. Da dare yayi na shiga barci sai na tsinci kaina na canza tunanina ba irin na da bane. Yanzu tunani nake gani a gidansa har mun zama ma'aurata, gani dare- dare a cikin hadaddiyar motar nan tasa muna tafe muna hirar soyayya. Na dade ina tunaninsa sannan nayi bacci, na dora da mafarkinsa mai dadin gaske. Na sa wa zuciyata na sami dr shureim na gama kamar yadda malam ya bani tabbaci. Naso in makara saboda dadin mafarki, na tashi a gaggauce na shirya na karbi kudin babur a wajen abida. Yayana ya bata ta bani donshi yana riga ni fita ma. Sai uwani ta biyo ni zaure da sauri ta tsayar dani tace yanzu zaki karbo kudin daga banki? Ko sai kin taso zaki taho dashi? Bilki ta kawo zubinta jiya na wajenki kawai nake jira in aikawa haj rabi na fada mata yau da rana zan aiko mata. Sai zuciyata ta hau dukan uku uku na fara zullumin inda zan nemo wadannan makudan kudi. Na hau rawar murya ina kame kame, nace sai an taso zan taho da kudin. Ina kan babur ina tunanin yadda za'ayi idan na dawo gida babu kudin? Ina shiga cikin asibiti naji farin ciki ya lullunbe min zuciyata saboda ko ba komai an fara aiki, zuciyarsa ta fara bugowa gare ni. Sai kuwa naci sa'ar a ranar an tura mu bangarensu dole zan ga ofishinsa ko ba ma wajensa aka mu tura mu ba. Muna shiga kuwa dakin darasin muka ci karo dashi da dr lukman suna fitowa medical students suna biye dasu zasu je zagayen marasa lafiya (ward). Na tare su da sauri na gaishe su, sai naji caraf ya amsa hadda kallon fuskata, ba murmushi yake ba haka bai bata rai ba. Dr lukman ne yake dariya, har yake yi min wasa yace ke 'yar shagamu ina kika shiga kwana biyu, rannan har yahaya umar yace in baki waya ku gaisa, nace ba kya kusa. Nayi dariya nace to yaushe zanzo ka kirawo min shi a wayar muyi magana? Da yake yana tafiya ne sanda yake magana, har yakai barandar waje banji abin da yace ba. Sai wani dalibi ne yake bayansu ya juyo yace min cewa yayi kizo gobe. Na yini ina farin ciki saboda naga canji wajen amsa gaisuwata da kuma kallon mutuncin da dr shureim ya min. Ban fara fargaba ba sai da aka tashi daga makaranta na tunkaro hanyar gida. Na shiga zullumin karyar da zan gina wacce ba za'a rutsoni ba, dakin uwani na nufa kai tsaye sai ta fara murna tana gyara hannu zata karbi kudi ta kidaya. Sai na zube a gabanta ina marairaice murya ina bayani. Nace wallahi tun safe ban huta ba muna ta kai kawo a cikin asibitin saboda matar bata da jini, don haka ba za'a yankata ba dole sai an kara mata jini. 'Yan uwanta ne suka zo maza da mata muna ta auna jinin har a sami wanda ya dace da nata shi yasa ban samu fita daga asibitin ba naje banki, amma gobe da sassafe zanje in karbo. Uwani ta bata rai, yadda ta amsa min a ciki ciki na san bata so haka ba, ta bini da kallo har na fice daga dakin. Ina cin abincin rana na fice wajen musbahu ban same shi ba, na bar masa doguwar wasika. Nazo giftawa ya makoftanmu nayi ido hudu dahare ta leko kenan ta ganni, ita ma dari takwas ta ranta min kudin dinkinta zata kai domin ta kusa haihuwa, ita ma ranar litimin din nace zan kawo mata. Dole na shiga gidan na tsara mata karya iri iri na ce gobe zan kawo mata. Itama ta nuna min bataji dadi ba, har mijinta yayi fada da yaga kayan dinkin a ajiye bata kai ba. Naji hankalina ya sake tashi na fito a gigice na shiga gidan mu har sai da abida ta shiga damuwa ganin yanayin da na shigo. Tayi ta tambayata ko lafiya? Nace lafiya kalau. Idan naji damuwa ta gallabeni sai in tuno menayi da kudin, kuma nan gana me zan samu. Sai inji sanyi a raina. Washe gari talata na fita zuwa makaranta, kai tsaye ofishin dr lukman na wuce. Ina shiga na iske shi zai fita. Yace dani ke kuwa baiwar Allah ai ba da sassafen nan zaki zo ba, sai da rana in aiki ya lafa ko? Nayi turus banji dadin amsar daya bani ba, ya wuce abinsa ya barni a tsaye. Sai ga gogan nawa yau kuma shigar hausa yayi, shadda ruwan bula tazarce ya dora hular da ta dace da kalar kayansa. Ya ratayo laptop dinsa a kafadarsa sai naga ya kara yin kyau matuka babu wacce zata kalle shi bata sake kallonsa ba. Ya tari dr lukman sukayi magana, sannan kowa ya wuce. Sai naji zuciyata na tafarfasa saboda shaukin so, kai kace zakanya ce mai tsananin jin yunwa ta ga nama haka zuciyata ta dinga zillo tamkar ta ballo ta fito da taga abincinta. Sai dai wannan abincin bana lasa bane, yafi karfinta. Tamkar soyayyen nama ne aka soya yana kamshi amma aka zazzaga masa guba kaga duk kwadayin mutum doke ya kalla ya wuce ko da kuwa marmarin naman zai kashe shine. Na fara takawa a hankali na matsa daga bakin kofar kafin ya karaso. Tun daga nesa na amshi wata galleliyar harara daga gareshi. Daya karaso bakin kofa kafin ya lalubo mukulli ya bude kofar sai da ya waiwayo bayansa inda nake a tsaye ya wurgo min wata hararar wacce tafi ta dazu wulkilewa. Sai nayi sauri na juya na fara tafiya ba tare da nasan inda zanje ba, sai gani a bakin gadon marasa lafiya nayi wuki wuki suna kallona ina kallonsu. Sannu likita, zoki duba cikinsa ki gani ya kumbura. Inji wata tsohuwa mai zaman jinyar danta. Na girgiza kai nace ki kira likita ni ba likita bace. Nayi saurin barin wajen na dawo bakin kofar ofis din na tsaya, nayi kamar in tura kofar in shiga sai na fasa. Na hakura na tafi ba don zuciyata tana so ba. Ina zuwa ofishinmu na iske kawayena suka hau min surutu. Wai aisha farida ina kike shiga ne aka nemeki aka rasa kullum har anyi test jiya ba kya nan? Nayi shiru na koma gefe na zauna na rasa abun da yake min dadi. Naci sa'a khadija sani tace inzo in rakata ta siyo ruwa zata sha magani. Ashe itama ta kunso labarai kala kala take so mu kebe ta fatsar. Ta dube ni ta tabe baki tace baki tambayeni dr shureim ba. Sai naji gabana ya fadi, sai na zargi kaina ina ganin kamar kowa yasan halin da nake ciki. Na zabura nace kamar yaya ban tambaye ki dr shureim ba? Tace kin manta inda muka kwana na nuna miki sakonsa a wayata? To in fada miki an gasa minshi da addua, ba adadi har sai da yaji ba dadi. Ina kiransa ya amsa, yace dani wacece? Sai na fada masa sunana khadija sani ismail. Ni daliba ce a schl of nursing tanan aminu kano, kuma ina attachment a nan cikin asibiti, sai yace yayi kyau lafiya? Nace lafiya so nake yayi saving lambata zan dinga kira muna gaisawa. Na dafe kirji nace yayi saving lambar? Tace kwarai kuwa, don da na sake kira sai da ya ambaci sunana. Sai naji kwalla ta cika min ido, kishi ya kamani, jikina yayi sanyi kalau. Taci gaba da cewa da na sake kira sai yayi tsiyar. Na tambaya a sanyaye meye tsiyar? Tace wulkanci yayi min kamar zai zageni, wai kada in sake kiransa. Kuka wiwi nayi da hawaye na hakura dashi ma ni yanzu. Allah Ya sa bai san fuskata ba, na goge lambarsa na daina kiransa yanzu. Dadi ya rufeni, amma fa na kara tausayawa kaina. Na bata shawarar tayi hakuri taci gaba da addua, Allah Ya musanya mata da abin da yafi alkhairi. Ta amsa min da ameen. Da aka tashi daga makaranta sai na kasa komawa gida, sai nacewa khadiji sani ismali zanbi ta gidansu somin 'yan gidanmu ba sa nan sun tafi unguwa sai dare zasu dawo. Khadija tayi farinciki da jin haka, sai muka dunguma muka tafi har yanzu labarin dr takeyi min. Ban cika bata amsa ba, tamkar tana min famin gyambon da yake damuna da zugi ne. Kwakwalwata ta cunkushe na rasa abin da yake min dadi, na kasa tantance abin da zanyi. Abinci kala kala aka jera min a gabana, amma na kasa ci da yawa saboda damuwa. Khadija sani ta dube ni tace wai don Allah aisha farida me yake damunki ne kwana biyu kin susuce tamkar bake ba. Ba kya son magana, ba kya son karatu gashi ba kya son cin abinci tundazu dan abincin da kika zuba kin kasa cinyewa, bakiga yadda kika rame ba, kika kwanjale ba. Kin cika zurfin ciki, ba a jin sirrinki daman. Wai me yake faruwa ne? Nayi murmushi nace haka kowa yake ambata, malaria ce ke cin jikina. Tace toh kisha magani mana, yaya zaki zauna da ciwo kina malamar asibiti, ko in saya miki babu kudi hannunki? Ta soso min inda yake min kaikayi, na gyara zama nace kamar kinsan satin nan cikin matsalar kudi muke, kinga yanzu haka yayana ne aka bashi ajiyar kudi, ya kawo gida aka shiga har daki aka sace, ya rasa yadda zaiyi. Mai kudin yana ta damunsa har da zai kai shi police station yake ambato. Khadija tace a garin yaya aka shiga har daki aka yi muku sata, babu mukulli ne? Nace maso abinka ya fika dabara, kinsan rayuwar cikin gari, gidan yawa aka shiga aka dauke. Khadija tace babu dadi, Allah Ya kiyaye gaba. Shi kuwa mai kudin bai san kaddara bane? Yayi hakuri mana sai ya samu ya biya shi. WaLlahi nima a cikin matsala nake, domin na karbi kudi a wajen abba yayi dubu hamsin kwanan nan haka ma a wajen mama. Har sun gane ba'a makaranta nake kashewa ko na tambaya basa bani. Sai tambayata suke me nayi da kudi a cikin satin nan, naki fada, ai ban isa ince malamai na kaiwa ba sai a kusa kashe ni. Tags : Bansake magana ba dai har muka isa gidan malam. Yana ganin mu ya fara washe baki, fara'ar yau tafi ta jiya. Muka zazzage masa kudaden jakarmu kakaf domin bayan dubu ashirin da dayan da ya karba sai da ya sake kwakwalo min wasu kudaden daban daban har dubu biyar da dari biyar. Kuma na harhada na bashi, a takaice dai har cikon dubu daya da dari biyar nan gaba zan ciko masa. Ita ma ummi ya kara mata wasu kudin, idan ta tashi cikowa ba dubu goma zata ciko masa ba, goma sha uku zata ciko. Yace ya bamu kwanaki uku mu dawo, ranar laraba kenan kafin komai zai daidai ta. Muka fito muna murna, ummi tana tabbatar min komai zai daidaita in kwantar da hankalina. Na tafi gida ita ma ta koma gidanta, na sake shirgawa abida wata karyar tunda ban taho da kayan walima ba, naso in siyo musu lemo da biskit amma na juyewa malam kudin dukka, da kyar ma na karaso gida, sai da kudi ya kare. Ko kusa ban damu da himilin bashin dake kaina ba, burina aiki yaci in mallaki dr shureim shine a gabana. Na yina ina hidindimuna da 'yan gidanmu cikin walwala da farin ciki. Da dare yayi na shiga barci sai na tsinci kaina na canza tunanina ba irin na da bane. Yanzu tunani nake gani a gidansa har mun zama ma'aurata, gani dare- dare a cikin hadaddiyar motar nan tasa muna tafe muna hirar soyayya. Na dade ina tunaninsa sannan nayi bacci, na dora da mafarkinsa mai dadin gaske. Na sa wa zuciyata na sami dr shureim na gama kamar yadda malam ya bani tabbaci. Naso in makara saboda dadin mafarki, na tashi a gaggauce na shirya na karbi kudin babur a wajen abida. Yayana ya bata ta bani donshi yana riga ni fita ma. Sai uwani ta biyo ni zaure da sauri ta tsayar dani tace yanzu zaki karbo kudin daga banki? Ko sai kin taso zaki taho dashi? Bilki ta kawo zubinta jiya na wajenki kawai nake jira in aikawa haj rabi na fada mata yau da rana zan aiko mata. Sai zuciyata ta hau dukan uku uku na fara zullumin inda zan nemo wadannan makudan kudi. Na hau rawar murya ina kame kame, nace sai an taso zan taho da kudin. Ina kan babur ina tunanin yadda za'ayi idan na dawo gida babu kudin? Ina shiga cikin asibiti naji farin ciki ya lullunbe min zuciyata saboda ko ba komai an fara aiki, zuciyarsa ta fara bugowa gare ni. Sai kuwa naci sa'ar a ranar an tura mu bangarensu dole zan ga ofishinsa ko ba ma wajensa aka mu tura mu ba. Muna shiga kuwa dakin darasin muka ci karo dashi da dr lukman suna fitowa medical students suna biye dasu zasu je zagayen marasa lafiya (ward). Na tare su da sauri na gaishe su, sai naji caraf ya amsa hadda kallon fuskata, ba murmushi yake ba haka bai bata rai ba. Dr lukman ne yake dariya, har yake yi min wasa yace ke 'yar shagamu ina kika shiga kwana biyu, rannan har yahaya umar yace in baki waya ku gaisa, nace ba kya kusa. Nayi dariya nace to yaushe zanzo ka kirawo min shi a wayar muyi magana? Da yake yana tafiya ne sanda yake magana, har yakai barandar waje banji abin da yace ba. Sai wani dalibi ne yake bayansu ya juyo yace min cewa yayi kizo gobe. Na yini ina farin ciki saboda naga canji wajen amsa gaisuwata da kuma kallon mutuncin da dr shureim ya min. Ban fara fargaba ba sai da aka tashi daga makaranta na tunkaro hanyar gida. Na shiga zullumin karyar da zan gina wacce ba za'a rutsoni ba, dakin uwani na nufa kai tsaye sai ta fara murna tana gyara hannu zata karbi kudi ta kidaya. Sai na zube a gabanta ina marairaice murya ina bayani. Nace wallahi tun safe ban huta ba muna ta kai kawo a cikin asibitin saboda matar bata da jini, don haka ba za'a yankata ba dole sai an kara mata jini. 'Yan uwanta ne suka zo maza da mata muna ta auna jinin har a sami wanda ya dace da nata shi yasa ban samu fita daga asibitin ba naje banki, amma gobe da sassafe zanje in karbo. Uwani ta bata rai, yadda ta amsa min a ciki ciki na san bata so haka ba, ta bini da kallo har na fice daga dakin. Ina cin abincin rana na fice wajen musbahu ban same shi ba, na bar masa doguwar wasika. Nazo giftawa ya makoftanmu nayi ido hudu dahare ta leko kenan ta ganni, ita ma dari takwas ta ranta min kudin dinkinta zata kai domin ta kusa haihuwa, ita ma ranar litimin din nace zan kawo mata. Dole na shiga gidan na tsara mata karya iri iri na ce gobe zan kawo mata. Itama ta nuna min bataji dadi ba, har mijinta yayi fada da yaga kayan dinkin a ajiye bata kai ba. Naji hankalina ya sake tashi na fito a gigice na shiga gidan mu har sai da abida ta shiga damuwa ganin yanayin da na shigo. Tayi ta tambayata ko lafiya? Nace lafiya kalau. Idan naji damuwa ta gallabeni sai in tuno menayi da kudin, kuma nan gana me zan samu. Sai inji sanyi a raina. Washe gari talata na fita zuwa makaranta, kai tsaye ofishin dr lukman na wuce. Ina shiga na iske shi zai fita. Yace dani ke kuwa baiwar Allah ai ba da sassafen nan zaki zo ba, sai da rana in aiki ya lafa ko? Nayi turus banji dadin amsar daya bani ba, ya wuce abinsa ya barni a tsaye. Sai ga gogan nawa yau kuma shigar hausa yayi, shadda ruwan bula tazarce ya dora hular da ta dace da kalar kayansa. Ya ratayo laptop dinsa a kafadarsa sai naga ya kara yin kyau matuka babu wacce zata kalle shi bata sake kallonsa ba. Ya tari dr lukman sukayi magana, sannan kowa ya wuce. Sai naji zuciyata na tafarfasa saboda shaukin so, kai kace zakanya ce mai tsananin jin yunwa ta ga nama haka zuciyata ta dinga zillo tamkar ta ballo ta fito da taga abincinta. Sai dai wannan abincin bana lasa bane, yafi karfinta. Tamkar soyayyen nama ne aka soya yana kamshi amma aka zazzaga masa guba kaga duk kwadayin mutum doke ya kalla ya wuce ko da kuwa marmarin naman zai kashe shine. Na fara takawa a hankali na matsa daga bakin kofar kafin ya karaso. Tun daga nesa na amshi wata galleliyar harara daga gareshi. Daya karaso bakin kofa kafin ya lalubo mukulli ya bude kofar sai da ya waiwayo bayansa inda nake a tsaye ya wurgo min wata hararar wacce tafi ta dazu wulkilewa. Sai nayi sauri na juya na fara tafiya ba tare da nasan inda zanje ba, sai gani a bakin gadon marasa lafiya nayi wuki wuki suna kallona ina kallonsu. Sannu likita, zoki duba cikinsa ki gani ya kumbura. Inji wata tsohuwa mai zaman jinyar danta. Na girgiza kai nace ki kira likita ni ba likita bace. Nayi saurin barin wajen na dawo bakin kofar ofis din na tsaya, nayi kamar in tura kofar in shiga sai na fasa. Na hakura na tafi ba don zuciyata tana so ba. Ina zuwa ofishinmu na iske kawayena suka hau min surutu. Wai aisha farida ina kike shiga ne aka nemeki aka rasa kullum har anyi test jiya ba kya nan? Nayi shiru na koma gefe na zauna na rasa abun da yake min dadi. Naci sa'a khadija sani tace inzo in rakata ta siyo ruwa zata sha magani. Ashe itama ta kunso labarai kala kala take so mu kebe ta fatsar. Ta dube ni ta tabe baki tace baki tambayeni dr shureim ba. Sai naji gabana ya fadi, sai na zargi kaina ina ganin kamar kowa yasan halin da nake ciki. Na zabura nace kamar yaya ban tambaye ki dr shureim ba? Tace kin manta inda muka kwana na nuna miki sakonsa a wayata? To in fada miki an gasa minshi da addua, ba adadi har sai da yaji ba dadi. Ina kiransa ya amsa, yace dani wacece? Sai na fada masa sunana khadija sani ismail. Ni daliba ce a schl of nursing tanan aminu kano, kuma ina attachment a nan cikin asibiti, sai yace yayi kyau lafiya? Nace lafiya so nake yayi saving lambata zan dinga kira muna gaisawa. Na dafe kirji nace yayi saving lambar? Tace kwarai kuwa, don da na sake kira sai da ya ambaci sunana. Sai naji kwalla ta cika min ido, kishi ya kamani, jikina yayi sanyi kalau. Taci gaba da cewa da na sake kira sai yayi tsiyar. Na tambaya a sanyaye meye tsiyar? Tace wulkanci yayi min kamar zai zageni, wai kada in sake kiransa. Kuka wiwi nayi da hawaye na hakura dashi ma ni yanzu. Allah Ya sa bai san fuskata ba, na goge lambarsa na daina kiransa yanzu. Dadi ya rufeni, amma fa na kara tausayawa kaina. Na bata shawarar tayi hakuri taci gaba da addua, Allah Ya musanya mata da abin da yafi alkhairi. Ta amsa min da ameen. Da aka tashi daga makaranta sai na kasa komawa gida, sai nacewa khadiji sani ismali zanbi ta gidansu somin 'yan gidanmu ba sa nan sun tafi unguwa sai dare zasu dawo. Khadija tayi farinciki da jin haka, sai muka dunguma muka tafi har yanzu labarin dr takeyi min. Ban cika bata amsa ba, tamkar tana min famin gyambon da yake damuna da zugi ne. Kwakwalwata ta cunkushe na rasa abin da yake min dadi, na kasa tantance abin da zanyi. Abinci kala kala aka jera min a gabana, amma na kasa ci da yawa saboda damuwa. Khadija sani ta dube ni tace wai don Allah aisha farida me yake damunki ne kwana biyu kin susuce tamkar bake ba. Ba kya son magana, ba kya son karatu gashi ba kya son cin abinci tundazu dan abincin da kika zuba kin kasa cinyewa, bakiga yadda kika rame ba, kika kwanjale ba. Kin cika zurfin ciki, ba a jin sirrinki daman. Wai me yake faruwa ne? Nayi murmushi nace haka kowa yake ambata, malaria ce ke cin jikina. Tace toh kisha magani mana, yaya zaki zauna da ciwo kina malamar asibiti, ko in saya miki babu kudi hannunki? Ta soso min inda yake min kaikayi, na gyara zama nace kamar kinsan satin nan cikin matsalar kudi muke, kinga yanzu haka yayana ne aka bashi ajiyar kudi, ya kawo gida aka shiga har daki aka sace, ya rasa yadda zaiyi. Mai kudin yana ta damunsa har da zai kai shi police station yake ambato. Khadija tace a garin yaya aka shiga har daki aka yi muku sata, babu mukulli ne? Nace maso abinka ya fika dabara, kinsan rayuwar cikin gari, gidan yawa aka shiga aka dauke. Khadija tace babu dadi, Allah Ya kiyaye gaba. Shi kuwa mai kudin bai san kaddara bane? Yayi hakuri mana sai ya samu ya biya shi. WaLlahi nima a cikin matsala nake, domin na karbi kudi a wajen abba yayi dubu hamsin kwanan nan haka ma a wajen mama. Har sun gane ba'a makaranta nake kashewa ko na tambaya basa bani. Sai tambayata suke me nayi da kudi a cikin satin nan, naki fada, ai ban isa ince malamai na kaiwa ba sai a kusa kashe ni. DUK KYAN TAKALMI 12 Sai naji hankalina ya tashi, har na fara nadamar katobarar da na tafka. Ta bude jakarta ta zaro dukka kudin da yake jakarta, dubu daya da dari biyu ne kacal sai 'yan canji. Ta miko min naira dubu daya, na karba nayi ta godiya. Tayi ajiyar zuciya tace wallahi dr ya cuce ni, na kashe kudina a banza ko gezau baiyi ba. Na fada cikin marainiyar murya nace karki damu kaddara ce Allah Ya aiko mana. Sai nayi sauri na gyara zancen son naga tayi sauri ta dubeni, sai nace ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, tunda ya shafe ki nima ya shafe ni. Bakiji yadda zuciyata take tafasa ba don takaici. To shi dr dame yafi sauran likitoci su basa wulakanci sai shi? Khadija tace yafi sauran mana ke kuwa, shifaa a london yayi karatunsa, ke har pri sa secondary duk a can yayi rabin rayuwarsa, sai da yazo nigeria fisha ya tafi. Ance dai yayi aiki a asibitin nan shekara 2 a lokacin yana karamin likita. Sai ya koma ya sake shekaru hudu ya zama consultant sannan ya dawo kwanan nan. A bangaren ilimi addini kuwa a saudia yayi karatun kurani, larabawa suka koyar dashi, ance yafi kowanne likita sanin kurani. Don tun yana yaro yaje saudia sai da ya sauke ya dawo london, ya karasa primary kinga kuwa Allah Ya yi masa baiwar da ba kowa yake da ita ba. Gashi dan attajiri shima attajiri, ga ilimi dukkan bangarorin biyu, ga wani kyau tamkar sai da zaba aka bashi. Kowacce mace dole taso shi, sai dai idan ta ga ba ta samu bata hakura irina. Maryam ahmad ma na gano sonsa takeyi, har wani kishi takeyi dani, nace kije na bar miki in dai shureim ne zaki gaji ki kyale shi. Amma ke aisha farida naga bai dadaki da kasa ba, ko zancensa ma ba kya so. Kowa yana yabon kyawunsa, ke ko ki kula. Baiyi miki bane? Sai naji tamkar an saki bom a kahon zuciyata, saboda faduwar gaba. Nayi firgigit nace yanzu khadija ina ta kaina ina ni ina cusa kaina wajen irin wannan halitta? Ai sai ku kyawawa, masu mota 'ya'yan attajirai. Khadija tace kin hutawa kanki wallahi kina burge ni yadda kike tafiyar da rayuwa, ba kya jajubo wa kanki abun da zai wahalar dake. Nima nayi nadama ba zan sake shiga irin wannan hatsarin ba. Yanzu mun bata da malaman nan makaryata, wai yaga aurenmu har da haihuwar 'yan biyu. Shine ai na saki jiki nayi ta tura musu kudi suna cemin zai zo da kafarsa nemana ga mutum kamar zai yayyaga ni cikin waya don masifa. Bani ba wani malami ai yanzu na rufawa kaina asiri nace mohd ya aiko da iyayensa muyi aure. Ina laifinsa yaro matashi, yana da mota da gidan kansa da aikin bankinsa, nima da aikina ya ishe mu rayuwar duniya. Sai naji hankalina ya tashi, dana sani ta afko min. Na gyara zama nayi tagumi ina duban khadija na rasa in da zan saka raina, sai yanzu na fara gane kuskuren da na tafka a rayuwa. Ummi ta cuce ni. Na fada a cikin zuciyata yayin da hawaye ya cika min ido. Nace da khadija kina so kice min gaba daya asirin da malamanki suka sha zabgawa ko daya bai taba shi ba, asiri baya cinsa kenan? Tace baya cinsa tunda bai ci shi ba, babu abin daya yi masa. Malamina daya ne ya fada min gaskiya tun da farko naji haushinsa, daga karshe na gane gaskiya ya fada min. Yace dani yaron nan da kike so gaskiya ya rike adduar neman tsari dare da rana, da wuya a jefe shi ya taba shi, sai dai kawai kije kiyi addua in da alkhairi Allah Ya hada ku ta wata hanyar, a dadin rai yazo, kuma ina so ki sani ba'ayiwa Allah dole. Khadija tace aiki ma daina damuwa, Allah Ya ganar dani har na dade ina istigfari. Su maryam anmad ne suka rage suma Allah Ya ganar dasu. Shiyasa aka ce wani kyau bala'I ne, sai a dilmiyar da kai in bakayi taka tsan tsan ba. Yanzu dr shureim in ba don Allah Ya sa nutsatte bane da mata sai sun halakar dashi. Haka ma mace mai kyau idan baatayi a hankali ba maza su halakar da ita, su rude ta da kudi tabi su koda kuwa tana da aure. Ke dai Allah Ya sa mu gane gaskiya. Sai naji khadija ta burge ni, tafi ni gaskiya. Ina ma a llokacin da naje neman shawara wajen ummi khadija na samu ta fada min abinda ta fada yanzu, da ba wa zuciyata hakuri, da ban je na jefe kaina a rigima ba. Yanzu gashi komawa gida ya gagareni. Da me zan biya wannan dimbin bashin na kaina gashi babu alamar nasara a aikin malamin. Khadija ta katse min tunanina tace duk inda ya kai da takama da kwalliya, da yanga karshen alewa dai kasa. Dole mace zai aura, ba auri kansa da kansa ba. Kuma dole yayi 'yar murya kafin a bashi ita, dole ya kashe kudi ya bauta mata saboda Allah Ya wajabta masa ciyarwarta, sutura, kula da lafiyarta, muhallinta da duk wata dawainiyarta. Daman dai ance DUK KYAN TAKALMI dole kafa ce zata saka sannan a taka kasa. Lallai zanso inga irin macen da zai aura, karshenta fa ya kare a mummuna, baka, 'yar talakawa, kinsan karshen irinsu kenan. Nace yana da mata fa har da 'ya, kema kinsan dr shuriem ba zai auri kucaka ba. Khadija tace ke aisha farida wa ya fada miki wannan? Nayi murmushi nace matarsa ma baturiya ce a london suka hadu, a london take zaune. Da bakinsa naji yana fada. Kuma a gabana sukayi waya da ita cikin harshen turanci ko hausa bata ji. Khadija ta gyara zama tace don Allah da gaske kike? Ni da kin fada min haka tuntuni ai da ban wahalar da kaina ba wallahi. To wai ina kika ganshi ne har kika ji yana waya, nifa tun ganin nan nasa da mukayi yana motarsa ban sake ganinsa ba. Ko dai ba shi kika gani ba? Nace shine wallahi, abokin dr lukman ne, likitan kwakwalwa wanda matron maryam take aikena wajensa. Kinsan tana da kanwa mai matsalar kwakwalwa, to yana duba to ko ba ranar clinic ba. Khadija tace lallai ba zai saurari kujari-kujari irinmu ba, mai mata baturiya mai zaiyi damu? Naji zuciyata tana kokarin bugawa, sai na mike na tayar da sallar la'asar daman da alwalar azahar dina bamu dade dayi ba. Nayi sallama nayi addua, Allah Ya biya min bashin da yake kaina. Na yunkura zan mike in tashi, sai khadija tace dani aisha farida gaskiya akwai abinda yake damunki, saboda duk jikinki yayi sanyi, yanzu ko yanayin sallarki ya canza ba irin na da ba, ba kya samun nutsuwa wajen yin sallh, kin daina doguwar addua bayan kin idar da sallah. Nayi shiru ina tunani nace a raina yanzu son dr shureim har addinina zai taba, bayan karatuna da ya tava ga zaman lafiya dana rasa. Sai na zuba wani zazzafan hawaye nayi sauri na boye fuskata don kada ta gane. Na dauki jakata na rataya nace mata zan tafi gida. Ta rako ni har bakin titi na hau acaba na tafi, ita kuma ta koma gida. Sai a hanya na fara tunanin halin da zan fada idan naje gida, don haka nace dan acaba ya kai ni zango gidan ummi kenan. Ina isa cikin gidan na tarar da kofarta a kulle alamar bata nan, sai naji banji dadi ba don haka na leka bangaren faccalarta na tambayeta. Tace min bata nan tun jiya ta tafi. Sai naji zuciyata ta buga na dafe kirji na tambaya kafiya? Ta tafi unguwa tun jiya bata dawo ba? Amsar da ta bani itace babu komai. Na sami kujera na zauna nace da ita ki fada min gaskiya, ummi kawata ce bata boye min komai. Sai tace to kiyi mata waya mana sai ta fada miki da bakinta tunda aminiyarki ce. Na jikina a sanyaye nace to sai anjima na tafi. Sai naga ta bini da kallo alamar tausayawa tace dani gaskiya ummi tana gidansu mijinta ya sake ta. Kuna fita shekaran jiya ya kai mata takardar sakinta gidansu, ashe bai bata izinin fita ba ta biki kuka fita har ina cewa ku jirani in shirya kuka ki. Na dawo na tsuguna a gabanta nace innalillahi wainna ilaihir rajiun. Yanzu yassar saboda dan wannan dalilin ya saki ummi? Tace a'a ba wannan kadai ba, daman akwai wata kasa. Ummi bata da kunya, ga ta da bin bokaye da 'yan tsubbu kowa yasani, mijinta ya sani saboda yana tono binne binnen da takeyi, da kuma barbade barbade da takeyi masa a abinci. Da zarar sun fada mata karya sai ta zai tana habaici ta bata da kowa, har uwarsa da ta haife shi bokanta yace uwar mijinta bata sonta. Yanzu ya dace ace ummi tazo ta zazzageni? Jiya ita da kannenta da kyar aka fitar dasu daga gidan nan wai sai sun dake ni. Har da cewa yadda na raba zamanta da mijinta nima zamana da mijina sai ya kare, sai in babu malamai a kano. Kinga kenan malaminta ne ya fada mata ina yi mata asiri. Ta tabe baki ta harareni tace to ai fitar da kukayi gidan boka kuka je, saboda yassar yabiku a baya har yaga inda kuka nufa, shi yasa ya kai takardar sakinta gidansu. Ko kin dauka ban gane ki bane munafuka kin san inda take. Aiko ki tayi kizo ki barbada min wani abu ko? Na zabura na mike tsaye na dafe kirjina nace ni?? Wallahi bansan ummi ba ta nan ba da bazan zo ba. Ba na irin wadannan halayya kuma ba da wata manufa nazo ba. Tace dani fita daga gidan nan kafin in tara miki jama'a. Kuma duk ranar da kika kuskuara kika hadu da yassar yace sai ya balla miki kafa, tun a sakandire kike yi mata hudubar tsiya, yasan kin tsane shi, shine kika biyo ta har gidan aurensu kika kai ta gidan boka, wato a kashe shi kuci gado ko? Tunda nake a duniya ba a taba yimin cin mutunci, kazafi da wulakanci irin na wannan ranar ba. Duk irin gulmace gulmacen nan da ake yi a lungunmu tun ina yarinya ba ataba cewa ga abin da aisha farida tace ba. Lalli na jefa rayuwata cikin wani mawuyacin hali saboda son dr shureim imran. Na gaggauta ficewa daga gidanta kafin ta tara min jama'a kamar yadda ta fada, kuka nake wiwi na hau acaba ba tare da nasan inda na nufa ba. Sai da dan acaba ya tambaye ni sau uku hajiya ina zan kaiki? Sannan nace ka kaini gadon kaya. Gidansu maryam ahmad kenan. Ita ma inje inji halin da take ciki da dr shureim dinta. Duk da haka ban daina sonsa ba. Maryam ahmad tayi mamakin ganina, amma ganin ina fara'a ta san lafiya kalau kenan. Tace dani shegiya aisha farida umar daga ina kike, ba ki koma gida ba ne har yanzu na ganki da uniform a jikinki? Nace ke dai bari, yau bana jin komawa gida da wuri, zumunci nake ji, zuwa nayi in gaishe da su mamarki. Sai taji dadi taja hannuna har dakin mahaifiyarta muka gaisa, na gaisa da kannenta da 'ya'yanta biyu wanda Allah Ya yiwa mijinta rasuwa ya barta dasu amma fa da dimbin dukiya. Muka koma dakinta muka zauna akan wani makeken gado, ta kunna mana AC yayin da ta dinga kwallawa 'yan aikin gidansu kira suna kawo min abubuwa kala kala kamar su juice, kayan marmari, cincin da cake. Sai taga duk na kasa ci sosai, ina yawan yin shiru idan tana magana kamar hankalina baya tare da ita. Sai ta zungureni nake dawowa hankalina, na rasa yadda zan dauko mata maganar dr shureim domin kada ta zargi wani abu ta gano saboda zancensa na zo gidansu. Domin ban taba zuwa ba gidansu haka kawai ba, sau daya na taba zuwa kuma daga makaranta muka zo muka yi mata gaisuwar mijinta, da yake gidanta na kallon gidansu ne. Muka shigo nan ma muka yi mahaifiyarta, to anan na san gidansu. Da kanta ta dauko min hirarsa tace baki tambayeni likitana ba dr shureim. Sai na zauna dai dai nace yaya akayi? Ki bani labari, akwai cigaba ko? Tace wanne ci gaba ni da tun kafin aikin da na rabawa malami bai je ko ina ba abu ya dagule gaba daya, nace to su daina adduar yafi karfina. Dr shureim yafi karfin ya kwanta in taka shi da takalmin kafata, kinji. Anya mutumin nan haifarsa akayi ba tikowa yayi daga sama ba? Ace mutum ya hadu ta ko ina babu aibu a tattare dashi? Sai naji na kara tsanar kaina, na fada cikin shamulalliyar murya, me ya faru? Tace mutuminki na same shi a ofis dinsa wancan sati, malamina ya bani laya na kunshe a karkashin harshena wai in dai da layar nan duk abin da nace masa ya zauna babu musu. Bayan turarukan da na dume jikina da goshina dasu, wasu masu wari kamar na 'yan bori, ni kaina sun isheni da wari balle shi dan gayu. Ina shiga kaina tsaye ko fargaba banayi saboda an bani tabbaci, ni kuma na yarda da cewar na same shi na gama kamar yadda suka bani tabbaci. Shi da wata likita mace ina jin dai daliba ce, bata gama ba. Ta cika tayi taf kamar zata fashe saboda fushi. Ta wani galla min harara nima na harare ta saboda abin da ya kawo ta shi ya kawo ni. Da na gaishe su babu wanda ya amsa sai na sami kujera na zauna a kusa da ita, shima yana zaune a kujerarsa. Ya juyo ya dubeni sarai sannan ya dukar da kansa yaci gaba da rubuce rubucensa. Ya gama ya mika mata takarda, gami da cewa Allah Ya sawake jeki. Ta tabe baki ta dubi takardar da alama magani ya rubuta mata sai tace inje in sha wannan kenan? Ya ce eh In sha Allah kurajen zasu warke. Sai tace doctor muje ka kaini chemist din mana, nina fi so ka tabbatar masu kyau ne. Sai ya bata rai yace ba aikina bane in rubuta miki magani, kuma in raka ki zabar miki wanda zaki saya ba, komai a rubuce yake zasu karanta su baki. Tace kaki zuwa ka duba ni a gida, kwanana biyu ban fito ba har waya nayi na fada maka. Na turo maka sakon adireshina kaki zuwa. Sai ya harare ta yace bani da lokacin zuwa duba dalibaina don basu da lafiya. Ta sake turo baki tace amma ai daliban daban daban ne, ba daya nake da sauran ba. Ya daka tsawa ya zazzare mata ido yace dalibaina dukka daya suke, daidai kike da wannan. Ya nuna ni, ita kuma ta wurgo min harara, nayi murmushin jin dadi nima na harare ta sama da kasa. Yace idan baki da abin da zaki fada min mai ma'ana game da karatunki ki tashi ki tafi, kada ki kara shigo min ofis. Ta fice sai ya juyo wajena ya tambaye ni cikin fushi, ke kuma fa? Menene? Ina fitowa na kira malamin da ya bani laya da turaren nan mai daga hankali don wari kamar na 'yan bori. Yana daukar wayar sai yace malama an sami nasara kuwa? Nace nasarar me mutum kamar zai mare ni? Sai yace to an sami kuskure ne daga wajenki ina ganin baki yi yadda nace ba. Nace komai daidai nayi banyi kuskuren komai ba. Yace yaushe zaki zagayo sai in sake bincikawa muga ta hanyar da zamu sake bullowa kuma? Nace Allah Ya sawake in sake kashe wani kudin bayan wanda na tula maka na baya har da yankan rago amma a banza..... Kafin in rufe bakina ya kashe wayarsa, nayi ta kira har yau a kashe. Ko yau ma na gwada a kashe, yaga na gane shi dan damfara ne babu abin da ya iya. Haka nabi duk sauran malaman naci musu mutuncu sukayi ta kame kame, sai yanzu na gasgata cewar malaman zamanin nan sun raina wa mata wayo, sun mayar dasu jahilan karshen zamani. Idan kura tana maganin zawayi tayi wa kanta, ke kina ganin malaman kinga wahalallu masu matsala sun kasa maganin matsalarsu, wai suce zasuyi wa wani maganin matsalar su, sai suyi ta canke canke don basu ma san ya ake duban ba. Ai ni na dawo daga rakiyarsu na goge lambar kowannensu, ko sun kira ni tsuye su nakeyi, sai su waya da sauro. Ko wata na gani zata bata lokacinta wajen bin malamai zan hanata sai dai idan taki yadda in kyale ta, idan taje taga uwar bari zata dawo da kanta tayi min bayani. Duk wadannan bayanai da maryam keyi tuni sun ragargaza min zuciya, kwakwalwata ta riga ta dau gobara, na rike kai kawai tamkar mai ciwon kai yayin da na sulale na kwanta akan gadonta tamkar sumammiya. Na yarda da cewar komai ya sami bawa rubutacce ne, in ba haka da ya za'ayi tun farko inji wadannan labarai akan malamai kuma in dauki zunzurutun kudi in kai wa wani? Nace a raina me yasa na fara zuwa gidan ummi neman shawara banzo wajen khadija da maryam sun fada min halin malaman zamani ba? Tun daga lokacin na tabbatar kudin sun mula kuma ba zan sami dr shureim ba. Maryam labari take bani kala kala, amma bana fahimta ina can ina tunanin abin da zanje in tarar a gida, haduwata da uwani mai adashe da sauran makoftan da na ciyo bashi, sannan bayanan da zanyi wa yaya hussaini in da naje na kai dare bayan tun karfe biyu na rana muka tashi. A gidan su maryam nayi sallar magriba, na yi ishai muka ci abincin dare. Taga bani da niyyar tafiya sai ta fara mamaki, tana jero min tambayoyi iri iri kasancewar ta sanni ba mai bin gidan kawaye bane kwata kwata balle tace na saba daman. Sai da na fuskanci har ta fara gyangayi , tara da kwata na dare sannan na fara haramar tafiya gida ba don naso ba, saboda niyyata sai karfe goma sha daya na dare zan koma gida kafin nan kowa yayi bacci. dole na fito ta raka ni kofar gidansu na hau babur na tafi. Ina tafe ina adduoi har na isa unguwarmu, daga nesa da gidanmu nace mai acaba ya sauke ni, don bana so 'yan gidanmu suji karar babu na san idonsu yana kan hanya suna zuba idon dawowata. Na biya dan acaban kudinsa yayin da nake tafiya tamkar hawainiya ina yi ina waige waige tamkar barauniya. Da sanda na shiga zauren gidanmu naci sa'a babu 'yan matan gidan masu zance a zaure da samarinsu. Sai na leka tsakar gidan, nan ma ban ga kowa ba. Sai na cire takalmana na rike a hannuna ina sanda dana zo giftawa ta windown dakin uwani sai na tsugunna nayi duku duku na wuce don kada taga giftawata, najiyo motsin mutum a daki ina kyautata zaton ba ta yi bacci ba. Da yake babu wuta sai hasken fitilar kwai da kyandira zaka dinga hangowa a dakunan don haka na hango kyallin kyandir a dakin abida ina hango inuwarta a tsaye jikin labule, sai dai ba zan tantance abin da takeyi a tsaye ba. Na duba kofar dakin sai naga takalman yaya hussaini da alama ya dawo, nan da nan tsoron da nake ciki ya karu. Nayi maza na tura kofar dakina na shiga na iske ta shimfidar da 'ya'yanta ta rage hasken fitilar kwai a gefe. Shiga ta dakin ke da wuya ko jakata ban ajiye ba naji motsi a kofar dakinmu, nan da nan na tsuguna na takure a lungu. Sai na sankare saboda firgici. Abida ce ta shigo hankalinta a tashe, tana ambaton subhanallahi, yaya zanyi yau. Tana rufe bakinta sai muka hada ido yayin da zaka dinga hango mamaki a cike da fuskarta gami da firgici. Ni kuma ina tsugunne ina kokarin daidaita numfashina domin na shide, don tsoron yaya hussaini da uwani a tunanina daya daga cikinsu ne. Aisha farida lafiya? Yaushe kika dawo? Ina kika shiga yau tun safe? Abida ce ta jero min wadannan tambayoyi masu wuyar amsawa. Na mike tsaye a sanyaye ba tare da na san abinda zance mata ba. Ta sakke kallona tace da ban ganki ba yanzu da kin jawo min masifa yau, saboda yanzun nan yayanki ya shigo ko minti biyar baiyi da shigowa ba, ya shigo da ciwo a kafarsa sun fadi akan babur shine yace in taso ki, ki rubuta masa allura ko maganin da zai sha ko ki dauko akwatin taimakon gaggawa (first aid box) ki zo kiyi masa dressing. Na kasa ce masa bakya nan, shine na shigo nan ina tunanin abin da zance masa. Ina kika shiga kika sa hankalina ya tashi ko abincin dare banci ba? Me yake faruwa tsakaninki da uwani tayi ta zuwa nemanki ranta a bace tunda rana? Na zazzare ido nace me tace miki? Abida ta girgiza tace nayi nayi ta fada min dalilin nemanki din da takeyi, sai tace inkin dawo in tambayeki ita ba zata fa. Ranta fa a bace har zage zage nake jiyowa tanayi daga dakinki. Ke kuwa aisha farida me ya hadaki dasu uwani ke da ba a zama a yi gulmar wani dake, me ya kai ki tsoma baki a maganarsu? Nasan wata gulma suka hado aka ce dake a ciki, to ni shawarar da zan baki gobe da sassafe kafin ki fita kije ki samu uwani ku sulhunta, idan kinsan kin fada ki basu hakuri, idan baki fada ba ki wanke kanki tun kafin yayanki yaji abinda yake faruwa yaci miki mutunci, kinsan halinsa. Duk kin susuce a kwanakin nan kin canja halinki sai kiya ta nuku nuku kamar mara gaskiya. Nayi shiru ina sauraronta yayin da na cire kayan makaranta na saka doguwar rigar baccina na saka katon hijabi na dauko 'yar akwati na wuce gaba, tana tsaye tana kallona cike da mamaki da takaici. Nayi sallama a kofar dakinsu, yayi min izini na shiga, na durkusa na gaishe shi yayin da ya miko min kafarsa naga ciwon nayi masa sannu da adduar Allah Ya kiyaye gaba. Sannan na bude akwatin na shiga aikin saka iodine da auduga. Ita kuwa abida tana can tana kinkimar 'ya'yanta daya bayan tana kai su fitsari. Naga gama masa yayi min godiya na fito. Har yanzu abida na dakina tana jirana bata gama jero min tambayoyin da suka cika zuciyarta dam! Ta dube ni ta yatsune fuska tace baki fada min ba fa in da kika je ko daman kinsan da maganar su uwani shiyasa baki dawo gida da wuri ba? Na bata rai na turbune fuska nace ni ba wannan bane ya tsayar dani, bayan mun tashi daga asibiti aka ce mu dawo za'ayi mana darasi daga karfe hudu zuwa shida, wani sabin likta ne zai gabatar da wata sabuwar cuta shine naga ba zan iya dawowa gida ba in sake komawa da yamma ba, sai nabi khadija sani gidansu da yamma muka koma, bamu baro asibiti ba sai da karfe bakwai ana sallar magriba, tace inzo gidansu idan nayi sallah sai in wuce. Shine kuma muka zauna muna hira bansan dare yayi haka ba. Abida ta tabe baki da alama ba ta yadda da bayanai na ba. Ta sake dubana tace aisha farida me ya hadaki da musbahu kuma shima ya dinga aiko wani yaro da wasika, zuwansa biyu. Nayi nayi ya bayar a ajiye mike yace a'a, ance hannu da hannu zai baki. Sai na sake gigivewa na hau kame kame nace musbahu kuma? Meye hadina dashi? To ina jin bani aisha faridar ba. Abida tayi murmushin takaici tace kila na fara zama kurma har a ambaci aisha farida inji ba daidai ba. Babu abinda zance miki tunda boye boye kike yi min tun yanzu. Sai dai kiyi hankali da mutane, ki kuskuri bin shawarar batattun kawaye, ki rike mairaici da talaucinki. Ta juya ta fice ta rufo mana kofa. Na sulale na kwanta na dora hannu aka ina juye juye, sai dai ban fasa karanto innalillahi wainna ilaihir rajiun ba. Yadda naga rana haka naga dare, barci ya gagareni. Fargaba da tunanin haduwata dasu uwani ta gallebe ni. Haka na kwana ban rintsa ba saboda tashin hankali, don haka da asuba kiran sallar farko na mike na shiga bandaki nayi wanka, duk da sanyin ruwan ban damu da saina dumama ba, na fito nayi sallar asuba na kakaba kayan makaranta. Na dauki jakata na dauko biro da takarda na rubutawa abida wasika na ajiye takardar a bude akan tabarmata yadda zata gani daga shigowarta. Na fita daga dakin ina sanda tamkar barauniya nayi sauri na fice, da yake kofar gidan a bude take maza masu zuwa masallaci sun bude. Na rufe fuskata saboda kada inci karo da mazan gidanmu, duk da banji motsin fitowar yayana ba, daga dukkan alamu kafar ta matsa masa da ciwo tunda bai fito sallar asuba ba, dan baya fashi in dai lafiyarsa kalau. Sai nayi ta tafiya da kafata sabida rashin babura kasancewar gari bai waye ba duku duku ne. Na dade ina takawa da kafata sannan Allah Ya jeho min mai babur na hau, mun dade da fara tafiya ba tare da nasan inda zance ya kaini ba. Ya sake tambayata malama ina zan kai ki? Da farko nace masa asibitin aminu kano, har munyi nisa na canza shawara nace ya kaini jakara, umguwarsu ummi wato gidan iyayenta. Muka isa kofar gidan na sauka daga kan acaba sannan na biya shi kudinsa. Abinka da cikin gari 'yan gargajiya basu san baccin safe ba kowa ya tashi ya shiga safgoginsa. Mai kosai ta ta fara suya, masu waina suna danawa. Haka masu koko da masu shayi da biredi sun fara tafasawa. Duk inda ka waiga yara ne dauke da 'yan kwanuka a kansu an aiko su sayan abin karin kumalllo. Na shiga cikin gidansu ummi cike da fargabar abinda zanje in tarar, ummin na iske a tsakar gida ita kadai ta saka buta a gaba da alama alwalla za tayi, tunani da damuwa sun hana ta sukuni. Ta buga tagumi kamar mai tunani yayin da idanuwanta sukayi luhu luhu. Tayi matukar firgita data daga ido ta dubeni , ta cika da mamakin ganina a daidai wannan lokacin. Ta fada cikin firgici aisha umar lafiya? Sai na fara zubar da hawaye shar shar shar daga idanuwana. Ta mike tsaye da sauri taja hannuna zuwa dakin da take kwana, a cike yake da yara daga dukkan alamu kannenta ne, yara 'yan kuci kuci da masu dan wayo. Kowannensu barci yake da munshari yayi da zarnin fitsarinsu da warin daudar jikinsu suka daki hancina. Kamar inyi amai, na dai daure na zauna akan wata dakwalkwalalliy ar katifa da ummin take kwana don naga 'yarta a shimfide a gefe. Anan tace in zauna bari taje tayi alwala tayi salla sai tazo mu zauna. Kallonta kawai nakeyi tamkar gunki na kasa magana, na dubi yaran da suke linkaya a cikin fitsari babu abinda ya dame su. Naji dama nice su nake linkaya a cikin fitsarin nan da irin wannan rayuwa da na jefe kaina. Ba jimawa ummi ta shigo sanye da hijabi da alama ta idar da sallah ko addua batayi ba sabida rashin mutuswar dake tattare da ita. A firgice ta shigo tana sauri kamar zata ci da kai, ta goya 'yarta duk da himilin fitsarin da ta ci a napkin, zarni kwar. Tace in taso mu tafi gidan malam. Na mike da sauri muka fice ba tare da ta leka dakin mahaifiyarta tayi mata sallama ba. Tafiya muke fankam fankam tamkar fatake, muna tafe muna tayar da kura kamar shanu, mu dukanmu hankalinmu a tashe. Na juya na dube ta nace ummi malamin nan kuwa yana da gaskiya? Nifa har yanzu banga komai ba. Ummi ta tabe baki tace uhmm ke dai bari. Ai shiyasa nake so muje mu ritsa shi kafin ya gudu, macucin banza. Kinsan mijina ya sake ni kuwa? Korar kare yayi min fa. Na zabura na dafe kirji nace au daman kinsan macuci ne kika kaini wurinsa. Tace ke dai muje muji abinda zai ce mana. Na fada a bayyane innalillahi wainna ilaihir rajiun. Allah ba Ya dorawa bawanSa abinda ba zai iya ba sai dai bawa ya dorawa kansa. Ina zan sami himilin kudin da na ranta in biya masu shi, ummi yaya zanyi? Ummi ta dubeni a fusace tace to ni kinsan irin zaryar da ake yi min a gidanmu saboda bashi? Ke dai kawai Allah ya rufa mana asiri. Na fusata nace babu wanda ya taba saka ni a tozarci da tashin hankali a rayuwata irinki. Ta harare ni tace dan Allah aisha ki rufe min baki, gara kema baki aure shi ba balle ya sake ki, nifa har da goyo, na zama bazawarar karfi da yaji. Haka dai muka tafi muna ta fada a hanya kamar zamu cinye kanmu a cikin bus. Tana jin haushina ni har nafi jin haushinta fiye da malamin ma. Muka iske shi a zaure yana ganawa da wasu guda biyu da alama hamshakan masu kudi ne, daga ganin motar da suka zo da ita da kuma kayan da yake jikinsu. Malam yana ganinmu sai ya bata rai, bai amsa gaisuwarmu bai sai bakinsa ne suka amsa. Muka wuce jikinmu a sanyaye zuwa cikin gidan, da kyar daya daga cikin matansa ta bamu tabarma muka zauna sai wani irin kallon banza suke yi mana dan suna suyar dakwalen kajin da aka karba daga wajen mutane na sadaka amma suke juyewa a cikinsu babu wata sadaka. Shi da iyalansa sun zama tika tika saboda da cin kaji da raguna da suke karba da sunan za'a rabawa almajirai. Na zunguri ummi na nuna mata kajin da ido, ta gyada kai ta fada a hankali tace eh kudinmu ne, ai yau sai na masa rashin mutunci. Can malam ya shigo ko kallonmu baiyi ba ya wuce dakinsa, yayin da matarsa daya ta dinga wucewa da abinci kala kala tana kai masa, kamar shayi, kaji soyayyu, wainar kwai da biredi. Mu dai muna zaune muna kallon ikon Allah. Su kayi kasonsu a faranti yara da manya suka dauka kowa yana ci babu ko sala daya da suka bamu. Malam yaci ya gyatse, yazo ya wuce ya shige wanka. Ya fito ya shiga daki ya fesa kwalliya da farar shadda mai kyau sannan yazo ya wuce ciki daki in da yake ganawa da baki. Sannan ya aiko matarsa yace ta kiramu. Muka shiga muka iske shi a tsaye a tsakiyar dakin, muka sake gaishe shi ya amsa a gaggauce. Yace daman yau mu kayi daku zaku dawo? Haushi ya kama mu, sai ummi ta kalle ni, nima na kalle ta sai ta murguda baki tace yau ne laraba ko? Kuma yau kace mu dawo. Ya kalli agogo yace kuma ce muku nayi kuyi sammako? Ummi ta fada a fusace, kamawa tayi ka ganmu yanzu kasan ba lafiya ba. Ni dai ina zaune a lungu nayi kuri ina kallon irin wannan damfara kiri kiri, a lokacin da zai karbi kudinmy yana fara'a yanzun da muka zo karbar aiki rai ya baci. Ummi tana durkushe tana kokarin sakko da goyonta. Sai yace ba sai kin sauke goyonki ba yanzu zan sallame ku akwai inda zanje don sauri nake yi. Ummi tace ko yanzu zaka sallame mu ai na sakko da 'yata tasha nono ko? Tunda ta farka tana kuka. Yace meye ma yake tafe daku? Ummi ta waigo ta sake dubana tace kinji ya manta ma. Saina sankare a zaune na tabbatar mun fada hannun mayaudati kamar yadda kawayena khadija da maryam suka fada. Ummi ta sake cewa malam gaskiya komai ya kwabe tsakanina da mijina, har ya sake ni. Ga kawata ma taji shiru bai zo ba. Yace kuje zan bincika naga abinda yake faruwa, amma aiki dai na gama. Ummi tace wanne bncike kuma, kai da ka mance abinda muka fada maka. Ya zazzare mata ido yace ke ba'ayi mana tsiwa ana kibi a hankali. Ummi ma ta zare masa ido tace tsiwwa ko zance gaskiya? Ni dai ba zan gidan nan ba sai an san abin da za'ayi, kudin da muka biya a banza kenan, bashi muka ciyo muka kawo maka. Aisha farida kiyi magana kyayi shiru. Na fada a sanyaye mai zance ummi? Ya jawo wata jakar leda a fusace sai ga daurin rubutu kashi kashi, ya miko min daya ya mikawa ummi daya, ya sake kwance wata ledar ya miko min laya daya, ya mika mata daya. Duk iri daya ce. Yace kuje kusha rubutun nan a tsaye, sannan ku kasance layan nan a jikinku sai kuyi kokari ku hadu da mazan da kuke so, ku tambayesu duk abinda kuke so daga gare su zasu yi muku. Ummi ta karba ta tabe baki tace mu fa ba wani abu muke nema a wajen mazan ba illa soyayyarsu. Yace to ai haka nake nufi ko soyayya ko kudi duk zasu baku. Na zuba abubuwan daya bani a cikin jakata na mike tsaye nace da ummi taso mu tafi. Ta mike a fusace tace zamu tafi malam, sai dai gaskiya idan bamu ga canji ba zamu dawo, asan abinyi dan bangane irin wannan aikin ba. Muka fice yayin da ya bimu da harara, muka fito tsakar gida dukkanin mu rai a bace. Matansa sunyi carko carko suna kallonmu domin suna jiyo duk abubuwan da ummi take fada. Ta harare su tace Allah Ya isa kudinmu da ake damfarar mu ana cin kaji, ko wacce shegiya tayi bul- bul da abincin haram. Ni dai nayi wuf na fice kada a biyo mu da duka, har zaure suka rako ummi suna zaginta tana zaginsu. Naja hannunta muka tafi, a hanya ta fashe da kuka don takaici, ni kukan ma na kasa yi sabida tsananin tashin hankali. Tace dani aisha kinga macutan malamai ko? Wallahi ni ban taba kula da cutar da wannan dattijon yake min ba sai yau. Duba kiga yadda komai ya dagule mana. Nayi ajiyar zuciya nace yanzu ummi meye abinyi? Tace kije wajensa ki gwada ki gani bayan kin sha rubutun kin daura layar. Nima yanzu gidan yassar zanje in gani ko zai kula ni, idan abinda ya bani bai yi aiki ba wallahi sai na dawo na tarawa malamin nan mutane. Nace kina ganin wannan rubutun da layar daya bamu ta gaskiya ce? Ta wa da naki fa iri daya ne, babu wani suna daya tambaya balle ace kowa daban, rubutun ma daga gani ba namu bane saboda baiyi niyyar bamu komai ba sai da yaji kince babu inda zakije idan baiyi wani abu ba sannan ya bamu. Tace ke dai muje mu gwada mu gani. Mukayi sallama na hau acaba zuwa asibitin malam ummi kuwa ta hau bus zuwa unguwar zango gidan yassar. Ina sauka na bude jakata na zaro kullin runutu na tashi tsaye kamar yadda ya umurce ni na shanye, yayin da na ciro layar nan na damke a hannuna na nufi ofishin sahibina. Ina mai karanto adduoi don neman dacewa. Zuciyata cike da fargaba. Na tura kofar ofishin a sanyaye gami da yin sallama, zazzakar muryarsa ce ta amsa sannan na tura kai na shiga. Kallo daya yayi min ya dukar da kansa kasa bai sake dagowa ba yaci gaba da rubuce rubucensa. Na gaishe shi ya amsa a shelake yayin da fuskarsa babu annuri. Na dade a tsaye bai ce dani komai ba kuma yaki dagowa ma ya kalle ni. Nayi ajiyar zuciya na tambaye shi a tsorace dr lukman ya zo kuwa? Da yazo da baki ganshi ba. Amsar da ya bani kenan. Nace likita ina da tambaya game da kurajen fuska. Sai yace dani ke fita ki bani wuri, nan ba ofishin dr lukman bane, ya koma ofishinsa a room 8 an gama masa gyaran, kada ki sake shigowa nan nemansa. Nayi sadan sadan na fice, na dade a tsaye a bakin kofar daga waje ina takaici tamkar in rusa ihu. Sai wata zuciyar ta raya min ko in saka layar a bki in tauna zata fi aiki. Sai na zura ta a baki ina taunawa na sake tura kofar na zura kaina ciki. A tsaye a tsakiyar ofishin na iske shi yana duba wani littafi a jikin durowar littattafan dake kusa da bakin kofar. Nace dan Allah likita zan iya bar ma sako ka bawa dr lukman? Naje ofishinsa baya nan..... Ban rufe bakina ba naji ya banko kofar ya rufe booom saura kada ya bame da fuskata, ba dan na daka tsalle nayi baya ba, daya illata ni. Tunda na kalli kofar waje bansake waiwayr ofishinsa ba, na saka a raina ni dashi har abada koda kuwa zan mutu banyi aure ba a duniya dan wannan wulakancin ya isa. Naji na tsane shi na tsani kaina. Na tsani ummi da ta saka ni a hanyar halaka kuma na tsani malamin daya cuce ni ya tagayyara ni. Na toho da layar daga bakina na farke ta saiga takadda a ciki babu abinda yake ciki sai zanen wani hatimi mai gida gida an rubuta alifun, ba'un, ta'un kawai aciki. Na fusata na yayyaga kuci kuci na watsar yayin da kuka ya turnuke ni. DUK KYAN TAKALMI 14 Kawata ummi wacce na taba baki labari tana son wani malamin mu a sakandirw abdulyasar shi kuma baya son ta amma daga baya ya fara sonta har ya aure ta, ita na tuntuba don ta bani shawara. Sai tace dani malamai ne suka yi mata aiki, dole akayi masa yazo ya aure ba a hayyacinsa ba. Don haka sai ta jani wajen malaminta ya ce in kawo masa naira dubu ashirn da biyar zaiyi min asirin da dr shureim zai zo har inda nake da kansa, ya aure ni. Dogon salati abida ta dauka ta dafe kirji tace farida boka? Me ya kaiki bin bokaye akan wannan 'yar karamar matsalar? Sai na daga ido da sauri na dube ta, ina mamakin yadda ta ambaci matsalata 'yar karamar matsala. Nace a raina lallai abida bata san yadda dr shureim take ba da yadda halayensa suke ba shiyasa take ambaton haka. Abida ta dora hannu aka tace innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Aisha farida kinyi kuskure. Wai shin ina wayon nan naki? Ina dubarunki? Ina iya zama da jama'ar da kika koya daga wajen magabatanki? Ai wannan matsalar taki karama ce. Ke kika zamar da ita babba gashi kin cuci rayuwarki duniya da lahira. A duniya kin jawowa kanki bashin da zai kaiki zuwa ga kotu a daure ki, kin dauko hanyar rugurguza karatunki. Sannan kin taba lahirarki domin ibadae ki ta ragu saboda damuwa da kika jefa kanki, kinje wajen boka mai duba wanda Allah Ya haramta, duk wanda yaje wajen mai duba, mai zuba wuri ko mai bugun kasa kuma ya gasgata abin da ya duba ya fada masa tabbas bashi da sallah har kwana arbain , Allah ba zai karba ba. Idan kika mutu a tsakanin wadannan ranakun me zaki cewa Ubangijinki? Kin zama makaryaciya domin karairayi iri iri kike shirgawa wanda ada ba halinki bane kuma kinsa makomar makaryaci wuta ce. Baki kyauta min ba farida da baki fada min matsalarki ba har sai da komai ya cabe. Na girgiza kai nace na hakura da dr shureim yadda iyayena suka bar duniya na san na rabu dasu har abada haka na rabu da shi daman bai san abinda nake yi ba. Wallahi anty abida ba da ganfan na dorawa kaina sonsa ba haka na tsinci kaina, nima ba da son raina ba. Abida tace haba haba kamar yaya zaki hakura dashi bayan wadannan bala'I da kika fada a dalilin sonsa ai ba zai tafi a banza ba. Nayi miki alkwarai da izinin Allah (SWT) sai kin sami soyayyar dr shureim cikin ruwan sanyi. Na kasa kunne ina sauraron maganar abida tamkar tatsuniya. Na dauke ta a matsayin mai iya zance don hankalina ya kwanta kawai. Duk da nasan babu abin da ya gagari Allah, amma abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa. Abida ta luta da tunanin da nake yi a zuciyata ta ga alamar ban yarda da abubuwan da ta fada min ba. Tace aisha farida kin manta da yadda akayi na auri yayanki hussaini? Kin manta ra'ayinsa na son girma ba zai auri kanwarsa ba a lokacin da iyayenmu suka yi sha'awar hadamu aure yake kokarin bijirewa? Kin manta yadda muka fara zama dashi a gidan nan, ni dake muna tsoronsa ko muryarsa muakji jikinmu sai ya dau rawa muna guje guje? Yaya kika ga zamana dashi a yanzu? Bari in fada miki abinda baki sani ba farida, yayanki hussaini a tafin hannuna yake yanzu idan naso in daga shi sama, idan naki sai in kifa shi kasa ya fado. Yaya hussaini a halin yanzu baya iya bacci idan ina fushi dashi sai ya bani hakuri na hakura sannan hankalinsa yake kwanciya. Hussaini baya boye min komau na game da samunsa, baya boye min duk halin da yake ciki na game da abokan sa zuwa danginsa balle 'yan matan waje domub mazan zamaninan ba'a rasa su da 'yan matan zamani, ko basu ce suna sonsu ba su 'yan matan zasu kawo kansu. Ki tambaye ni ya akayi haka ta faru? Ta ina na samo kansa? Farida wallahi ban taba zuwa wajen wani boka ko malami ba nace ina neman a mallake min hussaini. Mutane suna mamakina yadda nake tankwasa hussaini yake yin abinda nake so, har wasu kawayena da 'yanuwana suke tsokana ta wai ina hada su da malamina wanda ya tankwara min hussaini. Idan na fada musu ban taba zuwa wajen wani malami ba a rayuwata sai suki yadda. Aisha farida bana addua har karshen rayuwata in taka kafata wajen wani malami ko boka don yayi min adduar mallaka. Ina daga hannayena sama in roki Allah Ya mallaka min mijina, mu zauna lafiya, yasoni kamar yadda nake sonsa. Na girgiza kai nace na fada cikin kuka anty abida na hakura da dr shureim saboda bai san halin da nake ciki ba, mutumin da baya kallon fuskata baya amsa min gaisuwata, ta yaya zai soni? Kawayena guda biyu har mota gare su kyawawa ne, ko khadija bata fini kyau ba. Maryam ta fini kyau suma dole suka gaji da wulakancinsa suka hakura dashi. Na rasa yadda zanyi in daina sonsa duk da adduoin da nake kwana ina yi don Allah Ya yaye min sonsa amma sai karuwa yake yi na fada tsaka mai wuya, hatta da karatuna ya tabarbare saboda sau biyu supervisor dina yana zuwa yana duba ni daga makarantar mu bana nan. Don haka na san in banyi da gaske ba dole sai na maimata attachment dinnan wata shekarar. Ko a littafi ban taba karanta labarin wacce ta fada irin wannan matsananciyar soyayyar da na fada ba, makauniya kuma gurbatacciyar soyayya don bai san dani ba balle ya san abinda nake yi ba. Sai na rushe da kuka. Abida tayi murmushi ta dafa kafada ta sai ta girgiza ni tace haba farida, ke macece fa, dama akwai wani da namiji da zai baki tsoro duk haduwarsa? Ina so ki yadda da kanki, ki dauka duk in da wata mace ta je zaki iya zuwa, ki dauka duk abinda tayi zaki iya yi. Ki manta da farar fatar baturiyar da yake aure, ke bakar fata sai ki fita a wajensa. Sai naji abida ta fara bani haushi da wadannan maganganun nata masu kama da almara. Na rasa yadda zanyi in fahintar da ita waye dr shureim. Na tambaye ta cike da damuwa ta yaya zan samu soyayyarsa, har nafi baturiya farar fata da yake matukar so? Na fada miki fa bai sanni ba, yana dai ganina daga dukkan alamu ma ya tsane ni da zara ya ganni yake hada rai. Abida ta sake yin dariya tace kin manta kissar matan nan da akayi mana a makarantar islamiya? Kin manta matar nan da take wajen malami ta nemi da ya bata abinda zata mallake mijinta. Kissar ta rabu gida biyu, an samu sabanin malamai, sabanin malamai kuwa rahama ce duk dai abu daya suke nunawa. Na farko aka ce ta da ta fadawa malamin cewar maganin mallaka take so ya bata, sai ya umurce ta data je cikin daji ta nemo masa gashin idon zakanya mai rai da shi zai hada mata asirin mallaka. Matar nan ta firgita da jin wannan babban aiki sai tace dashi malam ina zanje in samo gashin idon zakanya mai rai ai bazata bari a tsinka ba saboda fadanta. Cinye mutane take yi. Malam yace shi dai gaskiya saida wannan gashin zai iya hada mata wannan magani. Matar nan ta tashi ta koma gida zuciyarta cike da zullumin tadda za'a yi ta iya cirar gashin idon dabbar da tafi kowacce irin dabba a duniyar nan hatsari. Da farko sai taje kasuwa ta sayi rago aka fede mata ta dauki himilin nama ta shiga dawa, tana hango zakanya da 'ya'yanta daga nesa suka fita neman abinci sai taje bakin ramin ta ajiye mata naman nan ta gudu ta labe. Da zakanya ta dawo sai ta iske abinci lafiyayye a kofar dakinta ita da 'ya'yanta suka taru suka ci. Washe gari ma haka matar nan ta kawo gyararren rago ta ajiye mata bayan ta tafi kiwo ta sake labewa bayan ta ajiye. Zakanya taje neman abinci ta dawo ta iske abinci har gida suka ci ita da 'ya'yanta. Haka matar nan ta dinga yiwa zakanya sai dai su dan matsa daga bakin ramin don su dawo su tarar da abinci. Da zarar sun matsa kuwa matar sai tazo ta ajiye musu sai su dawo su tarar da abinci kamar kullum. Zakanya ta tabbatar lallai kawai wata mai kirki da take kyauatta mata dan haka ko sanda taga matar ta ajiye mata abinci bata biyo ta nemi ta lahanta ta ba. Ba sai dai tazo taci kawai. Har suka fara sabawa tana ajiye mata abinci a gabanta bata guduwa. Har ta kai ta kawo matar ta fara shafa jikin zakanyar nan bata motsawa. Tayi ta shafata don sabo har ranan matar ta samu ta tsigi gashin idon zakanya ba tare da zakanyar taji zafi ba. Mata ta kaiwa malam gashin nan ya karba ya duba ya tabbatar gashin idon zakanya ne mai rai don yaga jini jini a jikin gashin. Sai ya cika da mamaki ya tambayeta ta yaya akayi ta samo gashin? shine ta bashi labarin yadda tayi. Malam yace to haka zakije ki yiwa mijinki kamar yadda kika yiwa wannan zakanya babu wata mallaka da tafi hanyar nan da kika bi kika saba da zakanyar nan. Na tambaye ta cike da damuwa ta yaya zan samu soyayyarsa, har nafi baturiya farar fata da yake matukar so? Na fada miki fa bai sanni ba, yana dai ganina daga dukkan alamu ma ya tsane ni da zara ya ganni yake hada rai. Abida ta sake yin dariya tace kin manta kissar matan nan da akayi mana a makarantar islamiya? Kin manta matar nan da take wajen malami ta nemi da ya bata abinda zata mallake mijinta. Kissar ta rabu gida biyu, an samu sabanin malamai, sabanin malamai kuwa rahama ce duk dai abu daya suke nunawa. Na farko aka ce ta da ta fadawa malamin cewar maganin mallaka take so ya bata, sai ya umurce ta data je cikin daji ta nemo masa gashin idon zakanya mai rai da shi zai hada mata asirin mallaka. Matar nan ta firgita da jin wannan babban aiki sai tace dashi malam ina zanje in samo gashin idon zakanya mai rai ai bazata bari a tsinka ba saboda fadanta. Cinye mutane take yi. Malam yace shi dai gaskiya saida wannan gashin zai iya hada mata wannan magani. Matar nan ta tashi ta koma gida zuciyarta cike da zullumin tadda za'a yi ta iya cirar gashin idon dabbar da tafi kowacce irin dabba a duniyar nan hatsari. Da farko sai taje kasuwa ta sayi rago aka fede mata ta dauki himilin nama ta shiga dawa, tana hango zakanya da 'ya'yanta daga nesa suka fita neman abinci sai taje bakin ramin ta ajiye mata naman nan ta gudu ta labe. Da zakanya ta dawo sai ta iske abinci lafiyayye a kofar dakinta ita da 'ya'yanta suka taru suka ci. Washe gari ma haka matar nan ta kawo gyararren rago ta ajiye mata bayan ta tafi kiwo ta sake labewa bayan ta ajiye. Zakanya taje neman abinci ta dawo ta iske abinci har gida suka ci ita da 'ya'yanta. Haka matar nan ta dinga yiwa zakanya sai dai su dan matsa daga bakin ramin don su dawo su tarar da abinci. Da zarar sun matsa kuwa matar sai tazo ta ajiye musu sai su dawo su tarar da abinci kamar kullum. Zakanya ta tabbatar lallai kawai wata mai kirki da take kyauatta mata dan haka ko sanda taga matar ta ajiye mata abinci bata biyo ta nemi ta lahanta ta ba. Ba sai dai tazo taci kawai. Har suka fara sabawa tana ajiye mata abinci a gabanta bata guduwa. Har ta kai ta kawo matar ta fara shafa jikin zakanyar nan bata motsawa. Tayi ta shafata don sabo har ranan matar ta samu ta tsigi gashin idon zakanya ba tare da zakanyar taji zafi ba. Mata ta kaiwa malam gashin nan ya karba ya duba ya tabbatar gashin idon zakanya ne mai rai don yaga jini jini a jikin gashin. Sai ya cika da mamaki ya tambayeta ta yaya akayi ta samo gashin? shine ta bashi labarin yadda tayi. Malam yace to haka zakije ki yiwa mijinki kamar yadda kika yiwa wannan zakanya babu wata mallaka da tafi hanyar nan da kika bi kika saba da zakanyar nan. Don haka babu wani asiri da ci idan babu biyayya, na kaskan da kai, ba tsabta, ba kalamai mai taushi tsakanin mata da miji. Nima nan da kika ganni da wannan kissar nayi amfani har na sami hussaini tamkar jaririn da sai an dauka, sai an juya, haka zaki bi ki samu soyayyar dr shureim. Na dube ta a shelake nace ta yaya? Ta nisa tace zan fada miki abubuwa guda biyar idan kika kiyaye zaki sami shureim a garabasa ba tare da kin wahala ba, kamar kibtawar ido da bismillah. Fardida duk inda namiji ya kai da ji da kai, da daga kai karshensa dai mace zai aura kuma dole ta bautar dashi ko yaki dan kada ya bare sai yayi dan Allah Ya wajabta akansu dole suyi. Dole ne miji ya ciyar da matarsa, dole ne tufatar da ita, dole ya nemo mata muhalli, dole ya kai ta asibiti idan bata da lafiya. Idan aka sami marar tsoron Allah wanda ba zaiyi dan Allah ba to zaiyi ko dan kada duniya ta zageshi. Dan idan ya bar ta cikin tsumma, ba abinci za'a nuna ta agari ace matar wane ce baya kula da ita. Dan haka DUK KYAN TAKALMI, duk tsadar takalmi, ba za'a daura shi a wuya ba ko a goshi ba, dole kafa za'a saka kuma a taka a kwata, shiga daji, a shiga bandaki, a tako kazanta, a taka bola ko a tako kaya dashi. To haka dr shureim zai zama a wajenki da izinin Ubangiji, babu boka babu malam. Naji tamkar tana busa mi sarewa a kunnuwana saboda dadadan bayananta, na gyara zama nace meye abu biyar din da zan kiyaye....? Ban rufe bakina ba sai muka ji ana buga mana kofa kamar za a karya, hayaniyar matan da muke jiyowa daga nesa ya matso bakin kofar dakin mu. Fadi ake ke aisha farida, ki fito ko a balle kofar nan. Yaya zakici kudin mutane ki shiga daki ki buya, ga 'yan sanda nan an kira su, suna kofar gida za'a tafi dake. Ko ki bude ko a kirawo su, su shigo ciki su tafi dake. Na dora hannu aka na fashe da kuka nace anty abida yaya zanyi? Na shiga uku , yanzu ankwa 'yan sandan nan zasu saka min su wuce dani ta gaban mutanen unguwar nan ko kamar wacce nayi sata kowa yana ganina ko? Hawaye ya zubo daga idanuwanta itama, sai ta mike tsaye ta tashe ni tsaye nima, ta dafa kafaduna da hannayenta biyu. Tace kiyi ta karanta innalillahi wainna ilaihir rajiun. Ki fita kice da yan sanda su rufa miki asiri kamar yadda Allah ya rufa musu asiri, su taimake ki kada su saka ki a gaba, zaki hau babur kije can sai su same ki acan ba sai sun saka ki a gaba ba. Nace ai bazasu yadda ba, sai sun saka ni a gaba kamar wacce tayi sata. Tace ke dai kici gaba da addua, ki fada musu hakan zasu yadda. Idan kinje can ki basu hakuri kice a baki kwanaki biyu zaki nemo kudin ki biya su, ni kuma anan zan tilastawa yayanki dole ko rance ne ya fita ya nemo a biya su kudinsu kaddara ce ta hau kanki kada ki damu. Kuma koda wasa kada ki sake ki fadawa wani ko wata abinda kikayi da kudin nan, dan kada ma labari ya dawo kunnen yayanki kenje wajen boka, ki barshi a kawarki kika taimakawa aka yi mata tiyata mijinta bashi da hali, yafi sauki dan idan muka kusukura mu ka bari yaji wannan labari sai ya bata mana rai. Dazu na siyar da samiruna hudu na biya su maijidda, dahare da dija dillaliya da kikaje suma kika ranto kudadensu. Wata tace dari takwas kika karba mata, wata dari bakwai, wata dubu daya, suma na suka zo suke daga min hankali suna nemanki danaji kudin ba yawa sai na aika kasuwa aka karyar min da su nazo na bibbiya su. Na uwani ne naji kudin da yawa ba zan iya biya ba. Kiyi hakuri aisha farida, kiyi ta istigfari game da wajen bokan da kika je, kinyi wa Allah laifi kuma kiyi ma Sa alkawari har ki koma gare shi ba zaki sake zuwa ba. Kiyi ta karanta wannan adduar ta neman biyan bashi "Allahumma bi jalika an haramika wa agnani fadhlika amman siwaka". Sannan ta bude kofa da sauri muka fito saboda bugun da ake yi ya tsananta. Dandazon matan gidanmu da matan unguwa da yaransu sun taru suna kallona. Abida na rike da hannuna muna kuka muka nufi hanyar waje. Muryar yaya hussaini mukaji ya daka tsawa mai firgitarwa har sai da kowa ya firgita. Yace da matarsa ta sake ni in tafi ni kadai ta dawo daki inje can in karata ni kadai. Ni da ita muka fashe da kuka. Ta rungumeni sannan ta lalubo hannuna ta damka min kudi naira dari biyu. Ta juya ta bar mi, sai na cigaba da tafiya a sanyaye na fice yayin da dandazon mata suke biye dani suna ta cece kuce. Masu bada hakuri nayi, masu neman ba'asi nayi, haka masu zuga nayi. Uwani kuwa sai mayar da zancen take yi. In da Allah Ya taimake ni duk sanda nazo wucewa ta ofishin 'yan sandar unguwarmu sai na duka na gaishe su kullum, suna ganina suka gane ni nima na gane su. Kalmar da suka fara ambato itace ah kece daman? Ke kuwa yarinyar nan mai hankali meya jawo kika shiga rigima irin wannan? Na fashe da kuka nace ku taimake ni dan Allah ina neman wata alfarma guda daya. Sai mai kivar cike yace yarinya ai babu wata alfarma da zamu iya yi miki anan, duk wata alfarma sai dai ayi ta a ofishinmu. Tunda an riga an kira mu dole mu tafi dake. Nace daman zanbi ku, bana so ku saka ni a gaba da ankwa ku wuce dani ta gaban mutanen unguwa yara suna bina suna kallo kamar wacce tayi sata. Zan hau babur ya kain ni sai mu hadu a can. Wallahi ba zan gudu ba. Sai suka yi dariya suka ce idan kin gudu ma ai zaki dawo, ba gamu a kofar gidanku ba. Ko zaki shiga duniya ki bar iyayenki saboda bashin da bai kai dubu ashirin ba? Suka yi min izini na tari acaba na hau, duk da babu nisa daga gidanmu. Na dan dade ina jiransu sannan suka karaso, aka shiga da mu uku ofishin mataimakin DPO, 'yan kallo aka barsu a farfajiyar suka ci gaba da gulmace gulmacensu. Saii a lokacin na gane makiyana wadanda ada na dauka masu kaunata ne, wadanda ada bana kulawa ashe sune masu kaunata, sune masu jimamin abinda ya same ni, sune masu nemar min afuwa a wajen wadanda na yiwa laifi, sune masu fada har da tayar da jijiyoyin wuya idan aka zage ni. Uwani ta mayar da zance, haj rabi ma haka sai aka tambayeni shin abinda suka fada gaskiya ne kuwa? Na amsa nace haka ne, sannan na basu hakuri gami da yin alkawari zan biya nan da kwana biyu. Uwani ta zabura tace karya nakeyi bani da ko kobo, don haka yace a kulle ni babu ruwansa. Mataimakin DPO ya sake tambayata haka aka yi? Na amsa masa da haka ne. Don haka yace aje a kulle ni har sai yayana yazo yayi belina kuma yayi alkawarin zai biya sannan a fito dani, idan kuwa yaki zuwa sai a kaini kotu alkali ya yanke min hukuncin dauri daidai laifina. DUK KYAN TAKALMI 2* 1 BABI NA BIYAR Washegari misalin karfe bakwai saura kwata na safe aisha farida ta shirya tsaf tana sauraron 'yan gidan su tashi. Ta hada kudaden nan ta kidaya naira dubu goma sha biyu ne cif cif tasan dai uwani zata daga mata kafa tunda sauran naira dubu biyar ne kacal har zuwa wani lokaci. Abida ce ta fito kofar daki tayi hamma tayi mika yayin data murtsike luhu luhun idanuwanta wadanda suka kumbura a sanadiyyar kukan da ta sha yi a cikin dare, ga rashin bacci. Ta tura kofar dakin aisha farida don ta duba yaranta, tayi matukar firgita a lokacin da ta ga fararen kayan jikin aisha farida a tsaye a tsakiyar daki har sai data daka tsalle tayi kara. Nan da nan aisha farida tayi magana tace anty abida lafiya kika firgita? Nice fa. Abida ta dafe kirji tayi ajiyar zuciya tace aisha yaushe kika dawo? Tayi murmushi tace ai anan na kwana. Abida ta tambaya cike da mamaki yaya akayi kika fito daga wajen 'yan sanda? Aisha farida ta sake yin murmushi tayi ajiyar zuciya sannan ta fito da himilin kudin nan daga aljihun wandonta. Tace kinga na hado naira dubu goma sha biyu saura naira dubu biyar. Ai zasuyi min hakuri har in samu ko? Abida tayi shiru kamar mai tunani yayin da hankalinta yayi mummunan tashi ta dubi aisha farida cike da fargaba. Ina kika sami wadannan makudan kudin a dare daya? Anya kuwa aisha kin kwana a gidan nan? Kada ki boye min komai, ni mai baki shawara ce a gaba daya matsalolinki. Matsalarki matsalata ce, damuwarki damuwata ce, haka duk abinda kika yi aka zage ki a gari bake kadai aka zaga ba, ni sai na fiki jin zafin zagin. Yadda hankalin abida ya tashi na aisha fariida sai ya fi nata tashi, nan da nan ta dago ta kafawa abida ido tana kallonta yayin da kalma daya rak ta gagare ta furtawa don tashin hankali. Kan kace kwabo hawaye ya fara zazzagowa daga idanuwan ta. Abida ta lura da tashin hankalin da farida ta shiga sai itama ta fara hawaye ta fara magana cikin sanyayyiyar murya. Aisha farida ba wai ina zarginki bane sai dai ina gudar miki fadawa mummunan rayuwa a sandiyar dan karamin bashin nan. Kije ki cuci rayuwarki a banza. Dole in tuhume ki don nima nasan dole yayanki zai tuhume ni haka kuma ya kamata a shariance. Aisha farida ta matse hawaye ta langabar da kai tace tabbas na kwana da shirin zaki tambayeni haka amma ban taba zaton zance a gida na kwana ba ki karyata ni ba shine abinda ya bata min rai amma inda zan yiwa Allah godiya shine na hadu da yaya dazu da tsakar dare ina fitowa daga bandaki shi kuma zai shiga har ya ambaci sunana na amsa da alama shima yayi mamakin gani na. Abida ta gyara tsayuwar ta da alama taji dan sanyi a ranta ta dubi aisha farida ta tambaya cike da zumudi. Yaya akayi kika fito daga ofishin 'yan sanda? Kuma a ina kika samo wadannan makudin kudi? Aisha farida tayi murmushi ta jawo hannun abida suka zauna akan tabarmarta tayi ajiyar zucia sannan ta gyara zama ta zayyanowa abida labarin duka abinda ya faru da ita jiya tun daga sanda ta fita qofar gida wajen 'yan sanda da yadda sukayi acan ofishinsu da zamanta dakin da aka kulleta zuwa lokacin da akayi belinta da kuma zuwanta fish park harta hadu dasu barrister mu'azzam da hirar da sukayi Har zuwa yadda ya bata kudi da kuma sanda ya kawota gida abida ta gamsu da labarin Aisha humaira kuma taji dadi har saida ta daga hannun sama tayi wa Allah godia ya taimakesu ya basu yadda zasuyi su biya bashin da basu dashi.kibani kudin nan sannan ki tashi ki tafi makaranta salin. Alin basai yan gidan sun tashi sun ganki ba kuma babu ke babu bawa wasu labarin abinda ya faru ko labarin inda kika samo kudi gudun kada yayanki wata rana yaji yazo ya titsiyeni da tambaya sannan kibarshi akan kin yi mata tiyata kada ma ki sake kiyi zancen malam kika kaiwa kudi koda wasa kibarni dasu ni nasan Ni nasan yadda zanyi inyi musu bayani kada kice komai jikin A.farida na karkarwa da dauki jakarta ta rataya tana gaggawa ta nufi qofa zata fice abida ta kira sunanta a sanyaye ta juyo ta kalli abida da cike da tausayiabida tace kina da kudin acaba ne? A.farida ta gyada kai tace inada naira 150 ragowar wanda canjin 200 dinda kika banina hau acaba jiya zuwa ofishin yan sanda.abida tayi ajiyar zucia tace kiyi haquriki gyara duk abubuwanda aka wuce ki ki mayar da hankalinkisosai harsai kin kamo 'yan ajinku domin anbarki baya.A.farida ta gyada kai tace insha'allah zan mayar da hankali akan karatuna na tafi saina. Dawo ta juya a gigice cikin sauri ta kuwa ci sa'a bata ci karo da kowa ba a tsakar gida haka qofar gidansu harta fito unguwarsu sannan ta samu acaba ya fisgeta sai asibitin malam aminu kano tana shiga cikin asibiti sai ta nufi bangaren da pfishin gogan nata yake ba har sauri ta qara gami da kawar da kai gefe don kada ma ta kalli bangaren.bata marmarin taci karo dashi ma balle ta tuna dinbin bacin ran da ya kimtsa mata a baya ta qudiri niyya a ranta ita dashi har abada koda kuwa shine kadai da namiji da yayi saura a fadin doron qasa.tana shiga aji sai yan aji suka mata caaa!suna tambayarta ina ta shiga ne ta bace kwata-kwata ba'a ganinta koba da lafia ne? kasancewar ramar datayi kuma duk tayi baqi don wahala.ai kuwa kun san amsar da zata basu balle ma sun saka ta akan hanya cewar ko bata da lafia ne? tuni ta amsa musu da eh bani da lafia ta qara da cewa harda kwancia a asibiti'',haka tayi ta bin metron da nurses tayi musu irin wadannan gunduma-gunduban karairayi su kuwa suka bita da sannu Allah ya sauwaqe dole su yarda mana saboda tsananin ramar da tayi gata daman ba jiki ba.bata yi qarya ba tabbas data sha jinyar zuci jinya a zucia kuwa wani lokacin har tafi jinyar jiki ta rame qurqet saboda tashin hankali. Daga nan ta duqufa tambayar abubuwan da kayi bata nan ta dinga kwafar jotin dinda frnds sukayi akan cuttutuka da yawa ta tabbatar an wuce ta sosai a cikin satitikan da take qin zuwa.tambaya take tun qarfi abun daba ta gane ba daga dalibai ,metrons da doctrs abun da ya shafa sannan ta bazama ta koma makarantarsu wajen malamin da yake alhakin duba ta wato (supervisor )dinta yazo har sau 2 baya samunta don haka tana cikin matsananciyar matsala idan batayi da gaske ba.saita maimaita attachment din nan next year hankalin A.farida yayi matuqar tashi a lokacin da yan ajinsu suka zagayeta ta suna neman mata mafita kowa yana bata shawarar abun daya kamata tayi ta shiga matsancin kokonto ana tantama anya kuwa har akwai wani bayanin da zata yiwa malam basiru ya saurare ta yadda ransa ya baci yana ta fada akan yazo 2X duba ta bai same ta.hawaye mai radadi ne ya surnano daga idanunwanta yayin data tuno wanda yayi mata silar abun daya same ta taji haushin 5r shuraim ya rafe ta .ta cije lebe ta girgiza kai tace a ranta shuraim na biyewa sharrin zucia a karo na farko na wahalar da kaina insha'allah ba za'a sake ba a. Karo 2 zucia nafi qarfinki yanzu duk inda kika kai ga hango haduwar dr shuraim bazan saurare kiba kece kika yi qayatamin shi a rai kika dinga zuga ni gashi a kusa-kusa zan same shi kikayi ta zurmuqani a rami har sai dana yi zurfin da na kasa fita saida aka agaza min na fito to ba za'a sake ba zanyi yaki dake har inda qarfina ya qare babu ke babu hasko min dr shuraim shi daban ni daban kowa ya tsaya a matsayinsa.ta sharce hawaye ta miqe ta suri jakarta ba tare da tayi wa kowa sallama ba ta fice daga asibitin kai tsaye ta nufi makarantarsu ofishin malam basiru ta nufa sai dai kash ta daki gurbi ya fitaa ita kuma tazo abokan aikinsa suna ce mata yanzu zai dawo-yanzu zai dawo taki qarewa abun qarfe 12 na rana sai ga Aisha farida a zaune ofishinsa har qarfe 5pm dole ta tafi gida tinda bai dawo ba. Ranta bace hankalinta a tashe ga qishin ruwa da yunwa yini guda bataci abinci ba dadinta ma dai tana zuwa tayi salla sannan ta dawo tavi gaba da jira domin A.farida bata wasa da sallarta.ta iso gidansu da misalin 5:45saida ta hadu da jama'ar unguwarsu da dama qofar gidansu zauren gidansu da tsakar gidansu sai suke jin kunyarta wasu ma basu iya hada da ita.tana gaishe su suna qasqantar da ido a qasa tamkar sunga surukarsu sai mamaki ya rufe ta tana shiga dakin aunty abida ta tura kai ta shiga kasancwar yay husaini bai dawo ba kafin abida tace mata wani abu Aisha.farida ta jero mata tambayoyi zokat suka mata zucia tace anyi abida lafia yan gidan nan kuwa?me yake faruwa ne?me kika fada musu suke kasa hada ido da ni?ko suna zargina da aikata wani abun kunya ne? abida tayi murmushi ta girgiza kanta tace ko daya kada kiyi zargin duk wannan jeki ki cire kayan makarntarki ki dauki abincinki kici yana gefen kayan ki kici naga alamar kina jin yunwa ki saurareni ina zuwa dakin naki yayanki ne yasani aiki yanzu zan gama kada ya dawo ya iske ban gama ba ransa ya baci.A.farida ta fice a sanyaye a zuciayarta cike da fargabar abun da abida zata fada mata ta cire kayan makarantarta ta saka wata yar yaloluwar t-shirt fara da baqin skirt kan ba kwali ta shinfida yar tabarnarta ta jawo kwanon abincinta ta bude wake da shinkafa ne da mai da yaji ga tashin hankali ga abincin ya sanqare sannan ga matsananciyar yunwa turawa take da kyar take hadiyewa maqogwaronta ya tsuke yayin da hanjin cikinta duk sun kanannade. Ta miqe da sauri ta bude wani farin bokiti mai murfi da moda akai shine ruwan da suka tadana na musamman don shansu ta debo a kofi ta dao ta zauna tana tura garau- garau tana korawa da ruwa ta kusa gama ci sai ga abida ta shigo fuskarta cike da murmushi tazo gefen Aisha ta zauna yayin da Aisha tayi qasaqe tana sauraronta abida tace Aisha. Yay makaranta?yaya kuma gogan naki likita?nan da nan Aisha ta hade fuska murtuk daga gani zuciayrta ce ta dugunzuma da jin kalmar sunan likita abida bata sami wannan amsar ba don haka saita sauya hira nan da nan.tace Aisha tayi ajiayr zucia tace na shigo unguwar nan sai na ga jama'a musamman mata suna ta kawar da kai basa iya kallona idan na gaishe su sai naga sun sunkuye-sunkuye haka dana shigo gidan nan ma duk basa iya hada ido dani me yake faruwa ne?abida ta tuntsire da daria tace ai daman haka rayuwa take maganinsu nayi''maganinsu kamar yaya? Aisha farida ta tambaya yayin data ajiye cokalin da yake hannunta gaba daya ta tattara hankalinta gaba daya wajen abida abida ta langwabar da kai gefe tayi shiru zuwa wani dan lokaci tace bayan fitarki dazu da safe nayi fiye da mintina 30 ina zaune ina tunanin qaryar da zan shiryawa su uwani da husaini yadda zan wanke ki daga zargi na tshi na shiga daki na iske husaini sai na fito da kudaden nan ina qidayawa yayi min tsawa yace ina na samu kudi da sassafe? Nace masa ai kudin nan a hannuna ya kwana tun bayan magrib aka kawo min sai yace waye ya kawo min?na gyara zama nace mace mai jegon da Aisha ta taimaka mata itace ta taso da ita da mijinta suka kawo kudin da yake Aisha tayi musu waya ta fada musu halin data shiga a sanidiyyar bashin data ci don ceto rayuwarta.dole suma hankalinsu ya tashi a lokacin suka bazamo suka hado kudin nan 12k suka kawomin sannan suka je office din yan sanda suka fito da Aisha ai a gidan nan ma ta kwana a daki ta labe taqi fitowa sai da safen nan ta shirya ta fice makaranta husaini yayi shiru can yace dani ashe da gaske ne kudin asibiti ta biyawa qawarta,ba qarya take ba?nace da gaske ne mana me Aisha zata yi da zunzurutun kudi kudin nan yarinyar da abin dunia bai dame taba,bata da buri ko kadan duk abun da ta samo komai kanqantarsa sai ta godewa Allah.yace yanzu saura nawa ne cikon kudin nace saura saura cikon 5k shima sunce zasu je su nemo su cika a cikin satin nan ma zasu kawo sai ya miqe ya je ya bude aljihun rigarsa ya zaro wasu kudade yan dubu_duba sai ya qirgo 5k ya bani yace gashi idan wadancan sun kawo sai a bani nima ba kudina bane kudin qungiya muke hadawa a office don tallafawa duk wanda ya shiga damuwa a cikinmu rashin lafia ko aka yimasa haihuwa ko kuma idan zaiyi aure a bashi tallafi''na karba cike da murna gami da durqusawa nayi masa godia bayan na shirya shi na shirya yara sun tafi nima nayi wanka na kammala dan aikin gida.hantsi yayi kowacce ta fito da tabarmarta tsakar gida ta zauna majalisar gulma ta hadu ta cika tayi damqam da munafukan mata har maqota kowacce ta zaro gyale ta shigo taji inda aka kwana da maganar kudin wajen Aisha.a wanne hali kike a can ofishin yan sanda? shaci fadi iri-irihaka mugaye kalamai ne ke fitowa daga bakunan masu dadin zance sai sun ga nazo giftawa ma sannan ake sake daga murya ana ambato sunanki,harda mai cewa lallai Aisha ta dauko ruwan dafa kanta a shekara 1 ma bazasu iya wadannan kudade ba sai dai tayi zaman gidan yari kawai. Na dauko kujerata na nufo inuwar da dandali yake fuskata cike ta da murmushi na gaishe su wasu ne suka amsa a sheleqe wasu kuwa sai suka kawar da kai gefe suka yatsune fuska suka ci gaba da ambaton Aisha tayi ganganci gobe ma ta qara na dade a zaune na buga tagumi ina dubansu ba kunya ba tsoron Allah a gabana basu daina mugayen furucinsu ba akanki.talaka ya shiga 3 a duniayar nan maganin abun kada ka taba kayan wani saika zauna lafia amma muddin ka shiga gonar wani tofa ka hadu da wulaqanci Allah yabamu yadda zamu yi don alfarmar Annabi Muhammad (S.A.W)''Aisha farida ta karbi salatin suka qarasa a tare suka shafa ta dafe qirji saboda tsabagen fargaba ta qagu taji abun da ya far tace me kika ce musu ke kuma? abida ta gyara zama tace biyi kisha labari daman sai irin haka ta same ka zaka su waye jama'ar da kake zaune dasu su yan gidan nan ashe haushin abin da kika yi ba ma suke ji ba suna yi mana baqin cikin ashe daman can akan irin rufin asirin Allah yayi mana ne suke adawa.ummulkhairi ta tabe baki tace ato qarshen alewa qasa qarshen tika-tiki tik! qarshen qarya dai yazo da anayi mana yatsuna ana wanka ana qalqale qafa ana siyowa yara gwanjo suna tsukewa ana yi mana gani-gani mu ba mu iya kula da miji ba sai iya bini-bini ana kusa da miji ana yimasa fari da ido.uwani tace kin manta a dafa abinci haka kawai sai an zuba kori yayi qamshi an yayyanka salat da tomatoes da albasa''Mairo maqoriyarmu tace au irin wannan iyayin ake yi muku ashe a gidan lallai kuna shan kallo. Ummulkhairi tace idan kince kallo ma ai daya ke nan sai idan miji zai shiga bandaki zoki ga yadda za'ayi ta kuza ruwa ana sharewa ana yayyafa abin qamshi kamar fin mazanmu yayi su da suke shiga da zarnin''uwani tace kun manta yar gayun gidan nan wai ita 'yar boko Aisha magana daya sai an sako turanci goma kullun ana qalqale kayan makaranta ana goge kaushi anayi wa manu yan matan gani-gani saboda suna soya awara a qofar gida su basu zuwa boko''Aisha ta zubo da hawayen daya cika mata ido ta girgiza kai anti abida me ya kawo duk wannan? daman haushinmu suke ji? abida ta zubo da hawaye tasa gefen zaninta ta matse tace ke kya fada farida daman sun dade suna so suci min mutunci to basu ga fuska ba don bana shiga harkarsu zunde da yafice kala-kala kullun suna yimin basu isheni. Kallo ba sai in nuna ban san suna yiba saboda iya zama da jama'a.zan gaishe su ko baza su ansa ba. Zan bawa ya'yansu duk abun dana dafa ko su basu amsa ba zan bawa 'ya'yansu duk abunda dana dafa ko su ban basu ba.bana bari suga hudar da zasu shigo jikina balle ayi gulmar wata dani haka ban damu da sai naji gulmata da akeyi ba.bani da lokacinsa sai lokacin mijina da ya'yana kema bakida lokacin kanki ma balle na wasu mu ba yan gari bane amma munfi sy yan garin sanin jama'ar arziki da samun Alkhairi shine haushinsu sai yanzu suka sami damar amayarwa da abun da yake zuciyarsu.yadda kika ga na zuciyarsu.yadda kika ga na zubo da hawayen nan sau 1 na sharce da gefen zanina haka nayi bance komai ba sai na saka hannuna a gefen zanina na zaro wadannan kudi na miqawa uwani ta zazzare ido sai hannunta ya dauki karkarwa ta karba a sanyaye.tana qirgawa a yayin da idanuwan masu leqe suka fi nata firfitowa masu kama baki sunayi haka masu susar tsohuwar kwarkwata suka fara yi ba tare da sun san ma abun da suke yi sunyi matuqar mamakisun razana haka sun ji kunya uwani da yan tayinta suka kidaya kudi naira 17k ta cika cif-cif. Uwani bata iya dago da ido ta dube ni ta iya ce min komai ba sai nice tambaye ta nace sun cika ko da saura kudin da farida ta ranta?ta gyada kai tace sun cika haka suke nace to ki kaiwa haj rabi kice tayi haquri ba za'a sake ba yanzu ma qaddara ce Allah ya aikowa Aisha tayi jihadi ne don ta ceto ran qawarta data qoqarin mutuwa akan gadon asibiti zata haihu saboda bata da jini kuma ba zata iya haihuwa da kanta ba sai tiyata shine tazo ranci kudin ta kai kafin mijin ya aiko daga lagos anan aka sami matsala da bai aiko da wuri har ta kai aka kai ta wajen yan sanda aka daure.Allah yana bayan mai gaskia. Allah yana taimakon wanda ya nemi. Taimakonsa Allah yana duban zuciyar na gari da mugu kuma yayi hukunci a kansu tun daga nan dunia da qawar Aisha mai jego taji labarin halin da Aisha ta shiga a dalilinta tuni ta taso daga kan gadon asibiti taje ta fito da farida ta kawo ta gida ta hado kudin nan da aka ranta Allah ya dubi zuciyar Aisha yaga kyakyawar niyyarta ya taimaketa ya fitar da ita daga tozarci da abin kunya. A gida aisha farida ta kwana, ta tashi da safen nan ta tafi makaranta taci gaba da karatunta. Yanzun abinda ya rage shine idan ta dawo da yamma kuje wajen 'yan sanda ku tabbatar musu da ta biya kun janye kara, sai a soke shikenan a zauna lafiya. Uwani mun gode da taimakon da kikayi mana, akasi aka samu har ya zama rigima. Kiyi hakuri, itama ba haka taso ba. Su dukka suka yi shiru kamar wadanda ruwa ya cinye su. Nayi murmushi na dube su daya bayan daya nace ku gafarce ni, daman ina da matsala daku bansani ba, kuma babu wacce ta tare ni ta sanar dani? Ai da tuntuni kun sanar dani halin da ake ciki don ban san inayi muku laifi ba ma a tsawon zamana daku, kusan shekaru goma. A bangarena bani da matsala daku ko kadan, ina taka tsantsan kada in batawa wani, ina iyakacin kokari inga na fitar da hakkin makotaka da Allah Ya wajabta a kaina shine inyi muku sallama, in gaishe ku duk sanda muka hadu a tsakar gida, in duba ki idan baku da lafiya, inyi muku jaje ko gaisuwa idan kun rasa wani dan uwa ko wani abu. In taya ku murna idan aure ko haihuwa sun same ku. Menene yayi saura kuma baya ga duk wadannan? Ku gafarce, laifi daya ne da nake muku, kuma ba zan daina ba shine ina kula da mijina yadda ya kamata, ku kuma ba kwa so. Nayi alkwari bazan daina tsafta ba, haka ba zan daina ciwa 'ya'yana ado ba da gwanjo, haka ba zan daina wankewa mijina bandaki ba duk sanda zai shiga, haka ba zan daina sanya curry ba ina dafa masa dadadan abinci, koda kuwa ace mijinmu daya ne daku, balle babu hadina daku. DUK KYAN TAKALMI 2* 2 A gida aisha farida ta kwana, ta tashi da safen nan ta tafi makaranta taci gaba da karatunta. Yanzun abinda ya rage shine idan ta dawo da yamma kuje wajen 'yan sanda ku tabbatar musu da ta biya kun janye kara, sai a soke shikenan a zauna lafiya. Uwani mun gode da taimakon da kikayi mana, akasi aka samu har ya zama rigima. Kiyi hakuri, itama ba haka taso ba. Su dukka suka yi shiru kamar wadanda ruwa ya cinye su. Nayi murmushi na dube su daya bayan daya nace ku gafarce ni, daman ina da matsala daku bansani ba, kuma babu wacce ta tare ni ta sanar dani? Ai da tuntuni kun sanar dani halin da ake ciki don ban san inayi muku laifi ba ma a tsawon zamana daku, kusan shekaru goma. A bangarena bani da matsala daku ko kadan, ina taka tsantsan kada in batawa wani, ina iyakacin kokari inga na fitar da hakkin makotaka da Allah Ya wajabta a kaina shine inyi muku sallama, in gaishe ku duk sanda muka hadu a tsakar gida, in duba ki idan baku da lafiya, inyi muku jaje ko gaisuwa idan kun rasa wani dan uwa ko wani abu. In taya ku murna idan aure ko haihuwa sun same ku. Menene yayi saura kuma baya ga duk wadannan? Ku gafarce, laifi daya ne da nake muku, kuma ba zan daina ba shine ina kula da mijina yadda ya kamata, ku kuma ba kwa so. Nayi alkwari bazan daina tsafta ba, haka ba zan daina ciwa 'ya'yana ado ba da gwanjo, haka ba zan daina wankewa mijina bandaki ba duk sanda zai shiga, haka ba zan daina sanya curry ba ina dafa masa dadadan abinci, koda kuwa ace mijinmu daya ne daku, balle babu hadina daku. Menene laifin aisha farida kuma a cikin gidan na, ko kuma ince a cikin unguwar nan? Hana idanuwanta baccin da take yi ne take zuwa karbar haihuwarku komai dare? Ko kuwa allurar da takeyi muku idan likita ya rubuto muka ta hutar daku zuwa chemist? Kitson da take yi muku kyauta ko kuwa ko yawa 'ya'yanki karatun da takeyi, duk sati ba tare da ko sisinku ba? Taya ku girki da takeyi, ko kuma rainon 'ya'yanku da take yi muku koda yaushe shi ya zama laifi? Gaishe ku da takeyi koda yaushe, ko hirar da take zama kunayi da ita shine laifinta? Allah sarki rayuwa, ai kuwa Aisha farida mutum ce babu wacce bata morarta a cikin gidan na, koma nace a layin nan gaba daya. Ummulkhairi na dade da sanin cewar ke kike wanke kafa kike zuwa ki sami mahaifiyar musbahi ki caccaka mata karya da gaskiya don ta tsani aisha farida a matsayin surukarta, burinki ya cika har sai da kika haddasa wannan gaba a zuciyar uwar musbahu, ta tsinewa aurensa da aisha farida, tace idan dai tana raye ba zai aure ta ba. Na sani aisha farida ta sani, musbahu ne ya fada mata shima ya sani. Sai ummulkhairi ta mike tsaye ta hau bambamin fada mai tafe da borin kunya tsagwaronsa. Tana jan Allah Ya isa ba zata yafe sharrin da nayi mata ba. Na mike tsaye nima na nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane, haka shiru shiru ba tsoro bane gudun magana ne. Kalmar da na fada mata ta karshe daga ita na gaggauta barin wajen itace kinji dadi, kin raba auren musbahu da farida, amma baki isa ki hana Allah Ya bata wani mijin ba, daga wani bangaren, bangaren da baki sani ba. Kuma wanda baki da matsayin da zaki taka kiyi gulma. Ummulkhairi ke da sauran makiya, ku bude idonku sosai zaku sha mamaki, zaku sha kallo, zaku ga irin mijin da aisha farida zata aura idan har muna raye. Insha'allah sai Aisha farida tayi auren da babu wacce ta taba yin irinsa a gaba daya unguwar nan bana a layin nan ba ko gidan nan Allah yana tare da mu kuma da shi muka dogara yan gulma suka hau gasgata maganata suka hau nadama suna fadar alkhairin Aisha farida data taba yimusu a rayuwa nan da nan na bar wajen na kyale su suna ta kame- kame kanka ce kwabo dandali ya rore ya qare daya bayan daya suna ta sulalewa suna guduwa saboda kunya Aisha farida ta riqe baki don mamaki gami da farin ciki abunda abida tayi.tayi mata dai-dai ta burgeta tayi murmushi tace anty abida dama ke iya fada?amma bantaba ganin kinyi ba?abida tace habah meye abun burgewa a iya fada kuma?ni zubar da mutunci ne fada dole ce tasani sun kaini qarshe ina ruwansu da tsakanina da mijina idan zancen kudi ne zasu suyi duk zagin da zasuyi suyi akan haqqinsu ne mu muka taba su haqqinsu ne muka jawo wa kanmu amma ace tsaftar dana keyi da girki dana keyi da tsaftace 'yayana duk laifi ne ina ruwansu?aida haushi mu ba mijinmu daya ba balle suce nazo zan kwace musu miji banzaye,qazamai maimakon suyi koyi dani saina na zama abar zagi,abar kyama daqa-daqa dasu sai suyi kwana 3 ba wanka suna yawo da dauri qirji a tsakar gida ba kitso bare yankan qumba,bare ayi zancen su qunshi da turaren wuta ko turaren jiki basu gyara jikinsu ba ina zasu gyara yara bare wani miji? Insha'allah sai Aisha farida tayi auren da babu wacce ta taba yin irinsa a gaba daya unguwar nan bana a layin nan ba ko gidan nan Allah yana tare da mu kuma da shi muka dogara yan gulma suka hau gasgata maganata suka hau nadama suna fadar alkhairin Aisha farida data taba yimusu a rayuwa nan da nan na bar wajen na kyale su suna ta kame- kame kanka ce kwabo dandali ya rore ya qare daya bayan daya suna ta sulalewa suna guduwa saboda kunya Aisha farida ta riqe baki don mamaki gami da farin ciki abunda abida tayi.tayi mata dai-dai ta burgeta tayi murmushi tace anty abida dama ke iya fada?amma bantaba ganin kinyi ba?abida tace habah meye abun burgewa a iya fada kuma?ni zubar da mutunci ne fada dole ce tasani sun kaini qarshe ina ruwansu da tsakanina da mijina idan zancen kudi ne zasu suyi duk zagin da zasuyi suyi akan haqqinsu ne mu muka taba su haqqinsu ne muka jawo wa kanmu amma ace tsaftar dana keyi da girki dana keyi da tsaftace 'yayana duk laifi ne ina ruwansu?aida haushi mu ba mijinmu daya ba balle suce nazo zan kwace musu miji banzaye,qazamai maimakon suyi koyi dani saina na zama abar zagi,abar kyama daqa-daqa dasu sai suyi kwana 3 ba wanka suna yawo da dauri qirji a tsakar gida ba kitso bare yankan qumba,bare ayi zancen su qunshi da turaren wuta ko turaren jiki basu gyara jikinsu ba ina zasu gyara yara bare wani miji? Aisha farida kwarai kuwa hakane ai ana zuba qazanta a gidan nan dukansu qazamai ne duk dakin daka nufa warin datti ne abida tace kece ma mai iya shiga dakunansu har ki zauna ki cakumi gashinsu ki kitse ni ina zan iya jure wari?ai shi yasa. Nakeso kici gaba da dagewa har sai kin sami dr shuraim shi kadai yafi dacewa da rayuwarki wani juyi Aisha farida tayi tashin farko ta kifa ta kwanta ta juya baya bata sake cewa komai ba saboda bata da abun fada taki jinin a ambaci sunan dr shuraim a halin yanzu balle ayi hirarsa.Abida tayi dariya tace au kiran sunan shuraim ma ba kya so shi ne kika juya mun baya? masoyin naki ne ya zama haka yanzu a wajenki?haba farida kada kiyi fushi kada ki sare da wuri mutane suna rasa ransu wajen neman abinda zuciyarsu keso ke yanzu wacce wuya kika ji har da zaki zame?keda shuraim kuna nan daram ba gudu ba ja baya ina nan akan bakana duk kyan takalmi qafa ce zata tattaka shi''Aisha farida ta jawo filo ta dora kanta ta toshe kunnenta sabida bata buqatar ci gaba da sauraron abun da abida ke cewa tamkar tana zuraro mata tsohon gyambon data dade da warkewa bata fatan gyambon nan ya dawo mata danye tafi son idan ya warke ya warke kenan har abada bata buqatar dayen ciwo ko maqiyinta bata masa fatan ya shiga halin data shiga. Abida ta fice tana daria ciki-ciki fitar abida ke wuya sai ta tashi zaune ta jawo jakar makaranta ta zubo littafanta da manyan text books dinda ta aro daga wajen khadija isma'I'll don ta karanta abubuwan da akayi bata nan.tabbas an wuceta. Da yawa sai tayi da gaske zata kamo su tana karatu zuciyarta na zogi idan ta tuno dalilin daya ja mata wannan matsalar sai taji haushin kanta da kanta ta qudiri niyyar ba zata sake bawa zuciyarta wannan dama ba balle takai ta ta baro ta.bata fito ba sai data ji ana kiran sallar magrib fitowarta keda wuya tayi kicibis da yayanta ya dawo daga aiki ya kuwa wurgo mata harara sai ta zube a qasa ta kwashi gaisuwa ko amsa mata baiyi ba ya shige dakinsa Aisha farida ta sake gasgatawa har yanzu da sauran rina a kaba maganar bata wuce ba kenan da saura?ta miqe a sanyaye taje tayi alwala ta dawo daki tayi sallah kafin ta idar taji motsin shigowar abida daga dukkan alamu wajenta tazo don har yanzu tana tsaye a kanta sai da ta idar da wuri taji abinda ke tafe da ita tana idarwa ta juyo ta dubi abida tace aunty lafia? Abida tace ki zo inji yayanki amma kada ma ki damu ba wani abu bane kinsan dai duk abubuwan dana shirya to duk abunda ya tambayeki ki haka zaki tsara masa yanzu ya du da mijin uwani a qofar gida suka tattauna suka wa juna haquri shine zasu je wajen yan sandan su sunar musu cewar an sulhunta an janye qara ba sai kun je ba.Aisha farida ta miqe da sauri dafe da qirji tace anti abida me zance masa game da cikon 5k dinsa da kike ce zasu ciko min?Abida tace a hakan zaki barshi zasu ciko din,idan basu ciko ba ai laifinki bane kuma ba zai kai ki qara ba dai shima sai ya dauki asara daba ki samo 12k bama ai dole ya nemo yayi belinki ba tunda ba zai bari a daure ki ba wata da watanni.nasan dai zaki sha fada ne da zagi kawai zagi kuwa baya qari idan da sabo ai kin saba'' Abida ta wuce gaba Aisha na biye da ita a baya ta sunne kai a cikin hijabi hannayenta kuwa dukka 2 na dafe da qirjinta sai karanto addu'io take iri-iri ba adadi tana mai neman agaji daga wajen rabbil samawati duk abun da zai zo yazo mata da sauqi.Allah mai amsar addu'ar bawansa sai ya sanyaya zucia yaya husaini maimakon yayi mata fada data bayyana a gabansa sai ya shiga yi mata nasiha yaji tamkar shima ya fashe da kuka lokacin daya ga hawaye a idon qanwarsa sai yaji tausayinta ya shiga nasiha mai hade da rarrashi yace farida haha farida kefa mai hankali ce mai sanin ya kamata ga natsuwa nayi mamakin yadda kike jefa rayuwarki cikinmatsla don kawai ki fitar da wasu daga matsala ba'a hana taimako ba amma kina so kina so kice min bata da dangi ne ko dangin mijin sai ke kika fiso sonta dasu?suna raye zasu bari ta mutu ne basu samo kudin da za'ayi mata tiyata ba sai ke?farida kinsan halin da muke ciki,ta kanmu muke yi,bamu da wani mataimaki sai Allah kullun hade-hade da kame- kame mukeyi sannan muci abinci sai naji tamkar na bar garin nan saina tuna talauci dana baro a shagamu har gara nan ma.ki riqe maraicinki ki riqe talaucinki ki riqe matuncinki ki riqe karatunki ki lallaba ki gama ki fara aiki ko zamu sami sa'ida babu ke babu sake cin bashin wani babu ke babu katsalandan akan matsalar wani ki tashi ki tafi Allah ya kiyaye gaba Aisha farida ta rushe da kuka tace nagode insha'allah zan kiyaye ta fice ta nufi dakinta ta shige ta takure tayi ta rusa kuka tana nai tuno iyayenta da suka rigamu gidan gaskia tabbas husaini ya fada mata gaskia dole ta nutsu tasan me ye a gabanta kuma ita wace ce a rayuwa?hawaye ya surnano daga idanuwan husaini yasa hannu ya goge abida ta matso kusa dashi ta fada cikin sassanyiyar murya tace yaya kaima kukan kake yi?kada ka damu fa kada ka saka damuwa a ranka ciwo ya same ta tsautsayi ne qaddara ce komai yazo qarshe ba za'a sake ba insha'allah. DUK KYAN TAKALMI 2* 3 Husaini ya girgiza kai yace ina son Aisha saboda babanmu yana sonta tayi kama dashi don haka idan na dube ta ina yawan tunawa dashi hawayenta ne yake tayar min da hankali.farida abar tausayi ce marainiya babu uwa ba uba nida nake riqe ta talaka ne ina matuqar tausayinta idan na ganta a cikin qawayenta yan gata masu mota baiwar Allah bata damuwa a haka take daurewa tayi karatu sai naji tamkar dama ina da yadda zanyi farida mata sami duk abubuwan da yan mata suke buqata kamar kayan kwalliya da dinkuna to babu misbahun ma da yake sonta yake taimakonta shima an raba su fatana Allah ya fito mata da miji na gari inda zata huta ko bayan raina ta taimaki kanta kota riqe min 'ya'yana ba''Abida tayi shiru tana tunani a ranta tace babu mijin daya dacewa da ita irin dr shuraim insh'allah farida saita sami shuraim ko don na hucewa mijina takaici a ransa ko don in cika masa burinsa na ganin farida ta sami gidan hutu nayi alqawalin zan yaqi zuciyar shuraim da addu'a da kuma kyautatawa har sai yaso farida yaya husaini ya katse tunanin da abida keyi yayi cimak ya miqe tsaye yace zanje waje malam yusha'u na jirana mijin uwani zamu je wajen yan sanda nan don a janye casa dinsu Aisha.Abida tayi masa fatan ya dawo dashi lafia ya fice da sauri.da Aisha ta idar da sallar isha'I ko abinci bata ci ba wajen datayi sallak kan tambarmarta a wajen ta kudindine ta kwanta babu abin da take yi sai sheshekar kuka da ajiyar zucia har barci ya dauke ta. Babu irin tashin da abida bata yimata don taci abinci taqi tashi tace ta qoshi a haka ta kwana saboda gajia da barcin data keji basu bari taji yunwaa ba bata farka ba sai da asuba kiran assalayu a kunneta ta miqe a nutse tana mai addu'io taje tayi alwala tayi sallah sannan ta shiga cuku-cukun yin wanka da saka kayan makaranta so take gari ya waye ta fice saboda gidan ya zama mata tamkar kurkuku haka tunaninta da hankalinta kakaf ya koma kan karatunta bata da wani buri illa taga ta gyara inda ta kuskuren kuma ta kamo yan ajinsu inda suka wuceta ta zamana mai nadama akan kuskuren data tafka a rayuwarta a kwanakin baya a dalilin shuraim sai kuma ta qudiri niyyar natsuwa da cire duk wani abu da zai gundiri rayuwarta giftawar husaini ta gani ta tagar dakinta ya dawo daga masallaci zai shiga dakinsa sai tayi wuf ta fito ta durqusa ta gaishe shi ya juyo ya dube ta duba mai cike da tausayi kasancewar yaga ta rame idanu wanta duk sun kode mata musamman data kwana 2 baka kwalli ba ya fada cikin yar siririyar murya farida lafiayar qalau kuwa ko baki lafia?tayi sauri ta sunkuyar da kai qasa gami da yin murmushin qarfin hali ta girgiza kai tace babu abinda yake damuna yay yace za a tafi makaratar ne har kinci dumame?ta gyada kai tace eh yasa hannu a aljihu ya dauko wata tsohuwar 200 ya miqa mata kamar kullun kamar yadda ya saba bata kudin acaba zuwa da dawowa da kuma na shan pure water.ta durqusa ta karba tayi godia ta shiga daki shima ya shige daki tana shiga ta mistsika yan powder a fuskarta ta gyara dan guntun hajabin da yake jikinta sai ta rataya jakarta a kafada gami da saqula 200 a zip din dake jikin jakar ta fito a bakin qofa suka hadu da abida lokaci daya suka yiwa juna murmushi Aisha ta gaishe ta abida ta amsa gami da cewa har kin fito ki tsaya kisha koko mana.Aisha tace sauri nake kada na makara supervisor nake son gani abida tace yunwa kuwa baza ta dame kiba ba kici komai da daddare ba na jiya da ranar ma da yawa kika ci ba Aisha ta langwabar da kai tace ba damuwa idan na dawo zanci abida ta kuncegefen zaninta ta dauko 100 ta miqawa farida tace kici abinci a can don nasan dole kiji yunwa farinciki yaa lullube Aisha ta karba gami da murmushi ta duqa tayi godia sannan ta juya ta nufi hanyar fita harta kai zaure sai taji muryar abida ni kiran sunanta sai ta juyo ta tsaya cak!tana dubanta kanar marar gaskia ta qarso inda take taja. Hannunta zuwa bayan kyauren zauren. Ta fada cikin rada daman inaso na tambaye ki dazu, to nasan halin kunnen hussaini, sai ya jiyo mu. Hankalin farida ya tashi ta dafe kirji tace me ya faru? Abida tace dr shuraim mana, zaku hadu yau kuwa? Kafin kace kwabo farida ta bata fuska ta kara da kai gefe, ta zumburo baki. Tace ba zamu hadu ba. Ta juya a fusace zata fice. Abida ta sake jawo hannunta tace fushi kike don naayi mmiki zancen shuraim? Kin daina sonsa ne? Aisha farida tayi caraf ta fada cike da gadara da takaici tace eh. Sai abida ta kwashe da dariya, yayin da aisha farida ta fice a fusace ko waiwayowa ba ta sake yi ba. A hanya ta hadu da musbahi ya fito daga gidan akan babur dinsa zai tafi wajen nema, sai ya tsaya a kusa da abar kaunarsa yana mata murmushin kauna. Sai dai kash! Zuciyar masoyiyar tasa a bace take, sai ta kawar da kai taki yin dariya ta gasihe shi ranta a bace. Wai kwana biyu nan wa yake taba minke? Musbahu ya fada yayin da yake duban fuskarta, yake murmushi. Ta kawar da kai gefe ta fara tafiya ba tare da ta bashi amsa ba. Yayi sauri ya sake biyo ta, ya tari gabanta har yanzu yana zaune akan babur dinsa. Abun mamaki sai yaga hawaye yana zubowa daga idanuwanta, nan da nan sai hankalinsa ya tashi ya shiga lallashinta yana bata hakuri, gami da rokonta ta hau bayan babur dinsa ya kai ta asibitin. Da farko taki sai da kyar ta hau suka fara tafiya. Ba tare da wani ya sake magana ba a cikinsu, sheshekar kuka kawai farida keyi a ciki ciki. Cikin marainiyar murya ta ambaci sunansa tace makarantarmu za ka kaini ba asibiti ba. Nan da nan ya amsa mata da to...to farida. Har bakin ofishin malam basiru ya kaita, ta sauko tayi masa godiya ba tare da ta dube shi ba. Ya kira sunanta cikin lallausar murya, ta juyo a tsanake tana sauraronsa, sai taga hawaye ya surnano daga idanuwansa, ta sake dubansa sosai, sai tayi mamaki tace lafiya? Yace farida kiyi hakuri ki yafe min nima ba da son raina haka ta faru ba. Ta tambaya cike da damuwa meya faru? Yace kwanan na ga kin shiga matsananciyar damuwa, har aka ce an kai wajen 'yan sanda an kulle ki duk da ba fada min takamaiman laifin da kikayi ba. Farida da ace tun sanda kika gama sakandire muka yi aure, da na killace ki duk da haka ba ta faru ba. Amma nasan komai mukaddari ne daga Allah, bawa bai isa ya tsarawa kansa rayuwar da yake so ba, sai yadda Allah Ya so dashi. Sanin kanki ne duk duniya ke nakeso, kuma har abada ba zan daina sonki ba, matsalar daga wajen goggo ne ba don ita ta haife ni ba ina tsoron bakin uwa ba da tuni nayi faci da maganarta munyi auren mu. Na kasa son matar da ta aura min, na kasa cire raina a kanki. Ba yadda zanyi nace kada kiyi aure ki jirani, idan nayi haka na zalunce ki, tunda bansan ranar da goggo zata hakura ba amma kada kiyi gaggawar yin aure ki barni, kullum ina ta fadawa Allah, nasan kema kinayi. Toh muci gaba. Farida ta rushe da kuka, tabbas musbahu yayi gaskiya, abin da yake ranta kenan, cewar ba don yaki aurenta ba da ya za'ayi ta afka cikin wannan hatsarin? Sai ta juya da sauri ta nufi ofishin da tazo, yayin da musbahu yake kwalla mata kira taki ta waiwayo ma balle ta amsa. Tana shiga ofishin taci s'a ta iske malam basiru yana nan shi da abokinsa malam sulaiman. Bayan ta gaishe su sai ta barke da kuka marar kakkautawa, sai suka shiga damuwa suka shiga yi mata tambayoyi, lafiya take kuka? Suka bata kujera ta zauna cikin sheshekar kuka ta fara bayani. Sannan suka fahimci inda ta nufa da kuma dalilin kukan nata. ba 31 da 32 zan ci gaba da 33 Supervisor ya turo hula gaban goshi yace rashin lafiyar da kikeyi ce ta hana ki aiko 'yan uwanki suzo su fada min ko kuma ki aiko a rubuce a kawo min? Gashi yanzu sau biyu ina zuwa duba ku ba kya nan, yaya kike so nayi miki yanzu? Kije kawai wata shekarar ki dawo ki maimata attachment din. Ta sake fasa kuka taci gaba da ba da hakuri. Mal sulaiman ya dubi abokinsa yace a'a ba za'a yi haka ba, ka dai duba ka taimaka mata. Itace fa monitor kasan aisha umar bata da wasa, lalura ce ta jawo haka da dai Khadija sani ce, kawarta ba zan ma shiga zance ba, don nasan bata da kokari. Malam basiru ya gyada kai yace shikenan kije nan da kwana biyu zan shigo asibitin in duba kiki zama cikin shiri dan a koda yaushe zan iya fadowa. Ta durkusa tayi godiya. Aisha umar ta fito tana matse hawaya, amma zuciyarta cike da farin ciki, hankalinta ya fara kwanciya. Tayi mamaki da ta iske musbahu har yanzu yana nan yana jira bai tafi ba. Jikinsa na rawa ya kunna babur ya karaso inda ta ke yana tambayarta ta gama su tafi, ko akwai inda zai kaita kuma? Ta girgiza kai tace cikin asibiti kawai zanje. Ta hau babur suka tafi har yanzu ma dai babu wanda yake magana a cikinsu, tana nuna masa hanya har ya kaita inda take so, sannan ya tsaya. Tana saukowa sai taga ya dauko kudi ya mika mata, dubu daya 'yan dari biyar guda biyu. Yace karbi wannan bashi da yawa, a cikin kudin da na ranto miki ne ma zanje na biya su, amma ba zai gagara ba. Daga nan zuwa yamma zan cika in biya su. Aisha farida ta girgiza kai tace ka barshi na gode. Yace a'a ki karba farida babu komai, a shirye nake nayi miki duk abin da kike so idan baifi karfina ba, ko bani dashi zan nemo bashi na baki. Ta mika hannu ta karba a kunyace, ta duka tayi godiya. Ta dube shi sai taji sanyi a ranta ganin annuri a fuskarsa murmushi kawai yake yi mata naso da kauna. Ta rike kan babur dinsa tana murmurdawa ta dube shi tayi fari da ido. Tace musbahu na gode da dawiniyar da ka dade kana yi dani, nagode da kulawarka da damuwar da kayi dani a tsawon zamana da kai baka taba gajiya dani ba. Ko kadan ban taba zarginka ba akan rashin aurenmu, nasan daga inda matsalar take, ina adduar Allah Ya zaba mana abin da yafi alkhairi amma ba zan boye maka ba musbahu bana jin a jikina zamu iya aure, don banson nayi auren da zan kasance bani da kwanciyar hankali. Saboda mahifiyarka ta fito baro baro bata son abun. Koda naji sonka zai mamaye min zuciyata nakan yi addua Allah ya yaye min, sai nayi sauri na juya akalar zuciyata wani bangaren. Musbahu ya girgiza kai alamar takaici yace yanzu aisha farida har addua kike Allah Ya cire miki sona a ranki, koda yake bakiyi laifi ba idan kinyi hakan, amma ni ban taba fatan na daina sonki ba, ko da kuwa bama tare. Wa kike so yanzu bayan ni? Nasan dai ba zaki rasa ba, tunda a maganarki yanzu kin furta wata kalma da take nuna hakan....ke 'yar shagamu, lah lah lah zance ma kikeyi da sassafen nan? Muryar da ta jiyo daga bayanta kenan ita da musbahu suka waiwaya da sauri, maza biyu ne suke tafe akan doguwar barandar, su dukka suna sanye da wando da riga na bakar suit wuyansu sakale da abin gwaji. Ko ba a fada maka ba manyan likitoci ne. Dr lukman ne mai maganar, na kusa dashi kuwa dr shureim ne, daga dukkan alamu daga duba marasa lafiya suke, domin da daliba na biye dasu a baya. Ta dubi dr lukman tayi murmushi ta rufe ido da hannayenta biyu ta fada a kunyace a'a ba zance nake yi ba, yayana ne. Musbahu yace yayanmu ai kanwata ce na kawo makaranta. Gogan naka dr shureim baice komai ba, amma yana tafe yana dubanta kasa kasa har suka wuce. Kallo daya tayi masa ta watsar ba ta sake waiwayarsa ba, taci gaba da duban abin kaunarta musbahu, ta shiga yi masa bayanin inda tasan dr lukman. Abin mamaki abinda ya sake tsorata ta sai taji musbahu yana yabon kyawun dr shureim. Yace shi kuma daya likitan yay sunansa? gaskia yana da kyau irin wannan ne fa yake sawa wasu mazan suke hana matansu zuwa aiki idan suna ganin mazaje kyawawa irin wannan sai su tsani mazan su sai taji zuciayarta ta harba bumm! don fargaba ta tambayeshi me kace?ya maimaita abun da fada tace a ranta haqiqa na daukowa kaina ruwan dafa kaina amma Allah ya hayar dani dana gane gaskia gaskia ce wato 'yar uwansa maza ma kyawunsa suke gani balle yan mata lallai shuraim ba sa'an soyayyarta bane zuciata tayi garajen cusa kanta wajen ajalinta.tayi zuciayarta ta yamutse fuska tace bansan sunansa ba nima dai ina ganinsa dai kawai misbahu yace kina burgeni farida duk irin kyalkyalin dunia bai cika damunki ba har dana fara kishi musamman dana ga yana kallonki qasa- qasa na dauka shima ya sanki Aisha tayi murmushi tace ni banma kalleshi ba balle insan yana kallona kai ka lura da hakan misbahu yace aini tun daga nesa na hango su suna tahowa kece baki gansu saboda kin juya baya tunda ya tunkari mu yake kallo har na tsorata na dauka shima yana ciki Asiha tace aa ni ban ma sanshi bama zai wuce babur dinka yake harara bana ji ance ya tsani yaga mace ta hau babur.misbahu ya kwashe da daria yace kai dalibai akwai sharri waya fadawa haka?a zamanin kuwa ai sai an hada da hawan babur abu zai tafi dai- dai ba kowa yake da kudin daukar taxi drop na musamman mu talakawan da muke zaune a lunguna koda yake su manya ne matansu ba zasu hau babur ba sai mota ko? farida ta tabe baki tace shi ya sani wannan matsalarsa ce ni har bana son zancensa ma ya cika dagun kai. Dadi ya kama misbahu kansa ya fara huruwa wato saboda sonsa da farida keyi har bata ganin fuskar wani da namiji sai shi sai ya shiga washe baki tamkar sakaran daya ga sabon dinki yace in dawo na dauke ki idan kin tashi? ta riqe baki ce rufa min aisir misbahu qasada ce ma yanzu dana hau mashin dinka a unguwarmusaboda safiya ce babu jama'a da bazan hau ba sai a yi mana sharrin da ba zamu fita ba.anga mun fita tare sannan da yamma aga mun dawo me kake tunanin za'a ce mana?kaje kawai nagode sai wani lokaci idan Allah ya sake hada mu a hanya don goggo ta hana ka zuwa qofar gidanmu kuma bana so ka saba mata ta juya ta tafi tabarshi zaune akan babur yana dubanta zuciyarsa cike da da tsananin sonta gami da takaicin abun da mahaifiyarsa tayi masa ina ma za'a hada farida da matarsa?aiko kusa basu hadu ba farida mutun ce kuma abar so ce yarinya kyakyawa mai fara'a ga son mutane iya magana tafiya a nuste da dadadan kalamai mai dadin murya da iya kallo da sai kaji kwakwal war kanka za zillo.ga kyakyawan halaye bata da hassada ba kyashi ko mugunta bai motsa ba har sai da ta bace masa ya daina hango ta yayi ajiyar zuciya ya girgiza kai ya kunna babur dinsa ya tafi a sanyaye gabobinsa sunyi sanyi. DUK KYAN TAKALMI 2* 4 Cikin satin nan kakaf babu abinda farida keyi sai karatu agida da makaranta. Bata shiga kawaye, har a gida ba ta fitowa tsakar gida. Tana lungu ko da yaushe littafiinta ne a hannunta. Burinta ta kamo 'yan ajinsu inda suka wuce ta, ga uwa uba a cikin satin supervisor dinta zai zo ya duba ta. Ta cire damuwa a ranta, haka bata da sauran tunani yanzu, sai karatunta. Abinci ma ba ta fiye son ci ba, sallah ce kawai ta zame mata dole ta tashi tayi, sai bacci barawo idan ya sace ta, tayi kadan ta farka taci gaba. Kafin kace kwabo farida ta rame, kowa ya kalle ta sai yayi maganar ba ta damu ba, haka bata tsahirta ba. Burinta taci nasara akan abin da ta sa a gaba. Duk da wannan jajircewar da tayi, da dagewa ta haddace kusan duk inda take tunani za'a tambaye ta daga kowane bangare na karatunsu zata amsa. Amma sai ta hada da addua tana mai neman taimakon Allah akan karatunta. Alhamdulillah da supervisor yazo dubata a karo na farko ta amsa tambayayin dukka har sai da yayi mamakinta. Sati mai zuwa karo ba biyu ya sake zuwa ya duba ta, a wannan lokacin ta sake shiri sai yaji rugurguza tambayoyin da ya jero mata har ma tana kara masa bayanai akn abin da bai tambaye ta. Ya jinjina mata, kuma ta burge shi matuka. Taci maki da yawa don tafi dukkanin 'yan ajinsu ci. Daga karshe ya shawarce ta yadda take da kokari ta daina wasa da karatunta, taci gaba da dagewa ta fita da sakamako mai kyau, shi kuwa yayi mata alkawari zai taimaka mata wajen neman aiki, kuma ko cigaba da karatunta take so zai taimake ta. Farida dai sai farin cik take tana yi masa godia ji take tamkar an sauke mata nauyin da yake kanta sai yanzu hankalinta ya kwanta walwalarta ta dawo ta shiga cikin qawayenta kamar da suka ci gaba da karatunsu da kuma koyon aikinsu.idan ta dawo gida taci gaba da wasa da dariyarta ita da abida da 'ya'yanta duk da Asiha bata nunawa 'ya gidansu da maqotansu bacin ranta akan abubuwanda da suka yimata suna gaisawa sosai tayi musu fara'a amma ta daina zama cikinsu tayi hira dasu kuma sai suka dinga jin kunyarta ba kasafai bama suke iya hada ido da ita ba saboda kunyar abun da suka yimaya domin Aisha tana da kirki kuma tana taimaka musu ta kowace hanya.tun yaya husaini na tambayar kudin da ka ranta 5k har ya gaji da dadin bakin abida yayi shiru ya daina tambayarta.ranar lahadi misalin qarfe goma sha biu na rana bayan abida da aisha sun gama aikin tsaf sunyi wanka sunyi wa yaransu wanka sun tura su islamiyya yayin da yaya husaini ke cikin daki yana shigar baccin gajia kamar yadda ya saba ranar labadi ce kawai baya zuwa aiki itace kadai ranar hutunsa a sati.don haka abida da yaranta basa garajen yin shige da fice a dakin abida kada a tashe shi tunda sassafe take hado musu yan komatsansu ta kawo dakin Aisha a karo masa qofa daga ya karya kumallo yake kwacia saida azahar kuma zai farka.Aisha ta gama rangawa abida kitso ras a kanta kai ka ce fula ce akasa dan kyau sannan itama abida taya ta tsifar nata kan Aisha na kwance akan tabarta yayin data dora kanta akan cinyar abida wacce ke zaune ta mimmiqe qafa hira kala-kala Aisha ke zaune ke rerowa abida hirar da data yanzu ta shagamu data kano hade da qawayenta na makaranta.abida ta dubi Aisha sai tayi murmushi misbahu kuwa yana nan? farida ta gyada kai gami da yin murmushi .misbahu yana nan kin manta kwanaki na fada miki yabani 1k harna saywa sa'id takalmi kito? abinda tace haka ne na tuna Allah sarki misbahu yana sonki har yanzu amma wannan uwar tasa bata kyautawa danta ba taci amanar haihuwa koda yake mijin wata baya auren matar wani mijinki na nan tafe.Aisha ta dago ta dubi abida saita mayar da kai ta kwanta jikinta a sanyaye ta fada cikin marainiyar murya insha'allahu.Abida tace ina dr shuraim? Takaici ya hana ta magana har zuwa wani lokaci mai tsawo babu wanda ya sake magana a cikinsu abida tayi ajiyar zucia tace farida kin cika sarewa baki da juriya akan abunda kike nema ki zama jaruma ki jajirce har sai kin sami duk abunda kike so kada ki tsorata domin qaramin aiki ne samun shuraim amma kin biyea maganar qawaye duk sun tsorata farida ta girgiza kai tace ba zai yiwu ba nan da nan farida ta juyo ta dube ta cike da mamaki marar misaltuwa ta fada a bayyane ikon Allah yai naga abunda yafi qarfina sai suka kwashe da dariya su duka abida ta gyara zama taci gaba dayi mata tsifa yayin da har yanzu farida na kwance ta dora kanta akan cinyarta abida tace idan dai har yanzu kina son shuraim bana so ki fitar da ran sumunsa domin Allah yana bawa bayinsa duk abin da suka roqe shi;farida ta girgiza kai tace aunty na haqura da dr shuraim ko maganarsa bana so ayimun abida tace kin haqura akan dole ko kin daina sonsa ne kwata-kwata?Aisha tayi shiru yayin da hawaye ya cika mata ido idan ta matse sai wani ya sake tsattsafowa abida ta shafa kanta tace kiyi haquri kukan naki zai koma dariya da izinin ubangiji idan baki manta ba na umarce ki daki riqe abu 5 wannan abu 5 din zai kaiki da samun nasara ki sami shuraim cikin ruwan sanyi uhmmm farida ke ambato tana kwance ta kasa magana sai bugun zuciyarta ke tsananin yi.Abida tace bazaki tambayeni abu 5 din bane? cikin sanssayar murya tace meye abun 5 da zan riqe? abida tayi murmushi gami da jiyar zucia tace Alhamdulillah a cikin 5 din nan zan fara fada miki 3 daga baya inga miki saura 2 a hankali.Aisha ta daga kanta a hankali ta dubi Abida zuciyarta cike da fargaba abun da abidar zata fada tana tantama ko zata jure su don ta qudiri aniyyar ba zata sake yin wahala ko zubar da ajinta ba wurin shishigewa dr shuraim abida tayi daria tace kada ki tsorata zaki iya ba wani abun wahala bane.farida tayi ajiyar zucia ta dafe qirji ta lumshe ido gami da qirqiro wani basashen murmushin da bai kai zuci ba ita dai a ranta tafi son abar maganar dr shuraim kawai shi yafi sauqi.abida tace abu na farko dana keso ki riqe a rayuwarki itace addu'a idan kika yawaita addu'a akan dukkan lamuranki zaki ci nasara Aisha ta gyada kai tace ina addu'a sosai ma kuwa abida tace wannan ta musamman ce a tsakaninki da shuraim ki roqi Allah ya zabar muku abinda da yafi alkhairi amma ke alkhairin wajenki shine ki sami soyayyarsa tunda kina sonsa,babu hijabi tsakanin ubangiji da bawansa ki roqi duk abunda kike nema a dunia da lahira idan dai halak ne ki zayyano masa duk yadda kike so babu kunya Allah mai karbar addu'a ne idan kika riqe addu'a ki yarda Allah zai amsa miki kin cika abu daya.Aisha ta gyada kai naji menene na 2? Abida tayi ajiyar zucia tace abu na 2 da zaki riqe bayan addu'a shine kizama mai tsananin haquri sai mai haquri ne yake cin ribar rayuwa ki daure ki jure duk abunda zaki gani haka duk nisan lokacin da za'a dauka ki daure kada ki qagu ko ki girgiza ko ki razana ba'a yiwa Allah dole kuma gaggawa daga shaidan take ma'ana duk tsawon lakacin da za'a dauka kafin shuraim ya karkato gareki kada ki gaji kiyi fushi kice kin haqura.sai na 3 shine ki riqe mutumcinki. Kada ki fito da maitarki fili ya gane halin da kike ciki na sonsa ma'ana kaja ajinki.Aisha ya yamutse fuska alamar nuna rashin fahimtarta a fili abida tayi murmushi tace zaki fahimce sai a hankali.farida ta tashi zaune ta dubi abida zuciyatra cike da quna tace aunty abinda kina nufin inyi ta bin shuraim ina zubar da ajina yana wulaqantani shine haquri? idan ba haka ba yaushe shuraim yasan dani balle yasan ina haquri dashi wata rana yaso ni?kin kasa gane waye shuraim idan ba office muka je ba bama ganinsa abun da ya fiye min sauqi shine na rabu dashi ni yanzu ko a hanya ma bana so mu hadu bawai na tsane shi bane ko yayimun wani laifi aa ko kadan bana zarginsa don bai ma san abun da anke yi ba sai dai don na samarwa zuciya ta salama.abida ta girgiza kai ai wannan itace juriyar da haqurin da nake kiyi ki taka inda yake ki ganshi ya ganki sannan kija masa aji Aisha taji tamkar abida ta dora mata dunia akanta don nauyin da kanta yayi taji hawayen takaici ya tsatsafo mata ta girgiza kai tace aunty abida zancen jan aji kuma a nan in har naje inda yake? ai na sayi wulaqanci da kudina abida tayi murmushi tasa gefen hannunta ta gogewa farida hawaye tace ki biyo ni a sannu a hankali zaki fahimce ni kuma zaki ga canji a wajen dr shuraim insha'allah ke dai kija mu je ki riqe matakan 3 addu'a.haquri da riqe mutunci.farida ta koma ta kwanta akan cinyar abida a sanyaye yayin da hawaye yayi ta zuba ta tuna mata abinda taci gaba dayi mata tsifa tana zayyano mata dadadan kalamai game da yadda zata sami shuraim idan har zata riqe addu'a zata riqi haquri.Aisha farida tana yin duk abun da abida ta shawarceta ta duqufa da yin addu'a safe da rana harda tsakar dare dama can ita gwanar yin addu'a ce tana da juriyar yin addu'a sai dai lokacin taji a ranta kamar abun ba zai yiwu ba bata lokacinta kawai takeyi sai ta tuno abubuwan da abida ta fada mata cewar ta roqi Allah duka abinda take so kada ta boye babu hijabi tsakanin bawa da ubangijinsa sai taci gaba dayi bata gajiyawa.tafi ambaton Allah kasan ina son shuraim idan da alkhairi shima ya soni. A CIKIN ASIBITI Aisha farida ce ke zaune akan wata doguwar kujera tana jiran matron maryam ta fito daga duba mara lafiya a babban dakin mata, zata bata sakon data aike ta ta karbo. Duk da ita ma daliba ce zata iya shiga, amma security ta hanata wucewa tace sai dai ta jira anan kasancewar shugaban asibitin aminu kano ne yake zagaye. Don haka manyan likitoci sai tururuwar wucewa ciki suke yi. Tana zaune tana jira har ranta ya fara baci, don ba don sakon nan ba da babu abinda zai rabota da karatunta, ita yanzu bata so a wuce ta koda dakika daya ne. Taji tamkar ta barwa security sakon inta fito ta bata, sai ta tuna zai iya bata kuma sakon yana da muhimmanci, don ba dan faridar ba ma da matron ta yadda da ita babu wacce zata aika ta karbo mata. Kudi ne da wasika ta karbo mata daga wajen matron aisha, a dakin 'yan awo. Aisha farida taja dogon tsaki sannan ta harari security din da ta jawo mata wannan dogon bata lokacin, sannan ta duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta. Karfe goma da rabi na safe daidai, ta daga ido zata kalli kofar dakin da matron ke ciki. Kicibus idanuwanta sukayi da abin da ya gigitata har sai ta zuciyarta ta daki allon kirjinta don firgici. Bata manta da ambaton innalillahi wainna ilaihi rajiun ba, yayin da ta daure bata nuna razanar da tayi a fili ba. Dr shuraim ne ya tunkaro inda take a zaune, yana tafe tamkar dawisu, cikin kyakkyawar shigarsa wato bakar suit, hannunsa rungume da file. Kallo daya tayi masa tayi saurin dauke idanuwanta, haka nan da nan ta kawar da fuskarta gefe daban, ko da ya karaso saitinta sai tayi sauri ta sunkuyar da kanta kasa har ya wuce bata dago ba. Wucewarsa ba dadewa sai taji wata sassanyar murya wata mata tayi mata sallama, da ta daga kai ta dubi matar sai taga wata zankadediyar ce fara sol, doguwa 'yar gayun gaske, mai kamshi na alfarma. Gefenta kuwa wata 'yar budrwa ce ke goye da yaro a baya, da alama dai mai aikinta ce ke goye da danta. Aisha farida tayi murmushi gami da amsa mata sallamar. Ta zauna kusa da aisha farida, sannan ta umarci mai aikinta ma tazo ta zauna, yayin da ta dubi aisha farida ta gaishe ta hade da tambayarta. Sai dai fargabar da farida ke ciki ta sake karuwa, don wannan zankadediyar matar dr shureiim take tambayarta. Aisha farida tayi sauri ta girgiza kai tace a'a bansan shi ba, sai dai ki tambayi security, nasan dai duk manyan likitoci suna ciki. Sai matar tace ai naga kamar security din nan bata da mutunci, bari kawai in kira shi a waya, da zan fito daga gida munyi waya yace min yana nan female medical ward, naga kuma ba a bari a shiga. Ta jawo wayarta sabuwa dal kirar blackberry ta matso sunan dr shureim idanuwan aisha farida na kai yayin da taci gaba da zazzare ido tana tunane tunane kala kala daban a ranta. Shin wannan wacece take neman abin kaunata? Toko matarsa ce? Cikin harshen turanci tayi masa magana tace faridarka ce ina nan female medical ward, an hana ni shiga. Aisha farida ta maimaita a zuciyarta. Faridah! Faridah!! Daman yana da wata farida bayan ni? Lallai abida tana so ta kaini ta baro ni, domin wahala kawai zansha babu alamar nasara a nan. Sai ta tuna da abubuwan da abida tace cewar tayi addua kuma tayi hakuri. Farida ce ta katse tunanin da aisha farida keyi, ta dube ta tace gashi nan zuwa ashe, baya ciki ya dan fita. Aisha farida ta gyada kai tace okay! Matar ta sake duban aisha farida tace yaya na ganki a nan zaune, ke ba ma'aikaciya bace, ko wani kike jira? Aisha farida tayi murmushi tace wata matron nake jira, ta shiga ciki aini daliba ce. Security ta hana ni shiga. Kuma dai yau ne ake hana mu shiga shima saboda shugaban asibitin yana zagaye. Haj farida tace toh shiyasa naga duk an koro 'yan zaman jinya a waje? Alla dai Ya ba wa kowa lafiya. Nima wallahi yarona na kawo bashi da lafiya, kwana yayi zazzabi kuma ga amai. Aisha farida tace subhanallah, ko hakori ne? Haj farida tace anya kuwa hakori ne? Bana jin hakori ne, don ya gama hakoransa, shekarunsa fa biyu da rabi, don kin ganshi a baya ne kamar jariri. Ina ga canjin yanayi ne, kinsan sauron kasar nan. Aisha farida ta gyara zama tace daga wacce kasa kukazo? Haj farida tace daga london, ai can nake aure. Nan da nan jijiyoyin jikin aisha farida suka rike, ta kasa cewa komai, babu makawa itace matar dr. To amma sai dai in 'ya'yan nasa guda biyu ne babbar mace ce, kuma tayi wayo don tana amsa waya radau. Cikin sanyin murya aisha farida ta tambaya shi kadai ne danki, ko akwai wasu? Haj farida tayi murmushi tace akwai yayarsu na baro ta a gida. Tabbas matar dr ce wannan, amma Allah yayi kyau da gayu a nan. Ai ruwa ma ba sa'an kwando bane, ina ni ina jera kishi da wadannan mata masu shigen kama da matan hurul ain? Aisha farida ta fada a ranta. Taji gaba daya bata da sauran wani tunani, kuma tasan shuraim yayi mata nisa. Rashin sanin shuraim na hakika ne abida take wannan daddagwar tana cewa sai anyi. Haj farida ta dubi aisha tayi murmushi tace yaya sunanki? Aisha farida tayi jim kadan, can tace sunana farida. Wow! What a coincidence is that? Sunanmu daya ai nima farida sunanan. Matar ta fada yayin da takeyin dariya, fararan hakoranta suka dau walkiya. Aisha farida ma tayi dariya tace oh haka ne kuma naji sanda kina waya kin fadi sunanki. Yaya sunan yaronki? Tace rislan. Aisha farida ta gyada kai tace rislan suna mai dadi, yaya sunan yayarsa ta gida? Tace sunan mamanmu ne aka saka. Aisha amma muna kiranta da momi. Aisha farida tace Allah Ya raya su. Haj farida tace amin. Yawwa ga dr shuraim nan zuwa. Aisha farida tahi wuyanta ya sage, har ba zata iya juyawa ta dubi bangaren da ya taho ba, don haka can gefe ta juyar da kanta har ya karaso gabansu ya tsaya. Kamshin turaren jikinsa mai sanyi shine ya daki hancin aisha farida, yayin da tattausar muryrasa da hadadden turancinsa yake ta dukan dodon kunnuwanta a inda aka hau dambe tsakanin zuciyarta da idanuwanta, idanu suka su juya su kalle shi, yayin da zuciyar ke son kallon abin da take kauna. Idanu suka rinjayi zuciyar aisha farida taki dagowa ta kalle shi Me yake damun dana ne? Oh my God rislan ciwo ne ya taba min kai? Inji dr shuraim a lokacin da yake shafa kan rislan. Haj farida tace jiyya bamuyi bacci ba wallahi, sai naji kamar yau in yanki ticket in juya london. Dr shuraim yayi murmushi yace no kar ki damu, mu nan asibitin muna da kwararrun likitocin yara, bari in kira kawata dr rukayya. Ya dauko hadaddiyar wayarsa kirar blackberry ya matso sunan dr rukayya ya fara da sallama, sannan ya gabatar da kansa. Yace dr shuraim imran ne yake magana, nasan baki san wannan layin nawa ba ko don sabo ne? Dr rukayya tayi murmushi tace ai kowa ya sanka da canje canjen layi kullum. Ya aiki? Dr shuraim yace alhmdlh, dama ina so in turo miki patient dinku, sister tace farida imran yaronta bashi da lafiya nake so ki duba shi, duk wani taimako da ya kama kiyi musu. Dafatan dai kina cikin asibitin? Dr rukayya tace haba meya abin yi min magiya, kanwar ka ai kanwata ce, to ka turo ta razo ina nan speciality yanzu. Dr shuraim yace nagode, gata nan zuwa. Sannan ya kashe wayar ya mayar aljihunsa DUK KYAN TAKALMI 2* 5 Aisha farida taji wani irin sanyi a ranta da Allah Ya sa kanwarsa ce ba matarsa ba, sai a lokacin kamanninsu suka bayyana. Tabbas kamarsu daya tamkar an tsaga kara. Har yanzu bata kallonsa ta juyar da kanta can gefe, amma fa kunnuwanta radau a bude tana sauraronsu. Dr shuraim ya dubi 'yar uwarsa yayi murmushi yace kinga ni yanzu ina tsakiyar aiki, bari in samo wacce zata raka ku speciality don nasan baki san kan asibitin nan ba, da sai in kwatanta miki, kuma ma da nisa. Ya dade yana kallon aisha farida, sai taji a jikinta kamar ana kallonta, tana dago ido sai suka hada ido dashi, nan da nan ta bata fuska, har da murguda baki, ta kawar da kanta gefe, don kada ma yaga fuskar aikenta. Shima yayi saurin dauke idanuwansa daga kanta ya bata fuska, ya juya ya nufi wani office ba jimawa ya fito tare da wata daliba likita na biye dashi a baya. Suka iso inda aisha farida ke zaune. Haj farida kuwa sai takalo aisha farida takeyi da hira, yayin da ita kuwa bata cikin hayyacinta. Dr shuraim ya kade mata hankali gaba daya ta rasa me yake damunta, sai da ta sake ganinsa ta tabbatar har yanzu sonsa na nan dankare a zuciyarta sai taji haushin zuciyarta da take jawo mata masifa iri iri. Dr shuraim yace ga dr zainab dalibata ce zata raka ku, kuma zata tsaya ki gama komai, sannan ta dawo. Dr zainab farin ciki fal a zuciyarta fara'a cike a fuskarta saboda yau dr shuraim ya kula ta har ya zabe ta ta raka kanwarsa, don haka ji take tafi kowa samun shiga. Tayi sauri ta duka ta gaishe da haj farida yayin da ta hau shafa kan rislan tana ta faman iyayi. Tanayi tana satar kallon dr shuraim, shi kuwa gogan abin da yafi tsana kenan, irin wannan shishigin sai ya fara bata fuska. Aisha farida tayi murmushi a zuci tace a ranta wayyo zainab ina tausaya miki indai dr shuraim ne zaki hadu da tsagewar zuciya bama bugun zuciya ba. Muma nan munyi mun warke. Haj farida da mai aikinta suka mike suka dunguma suka fara tafiya har haj farida ta wuce sai ta tuna ba tayiwa aisha farida sallama ba, sai ta waiwayo da sauri. Tace af kawata, takawarata na tafi ko, sai Allah Ya kara sada mu da alkhairi. Aisha farida ta dube ta, tayi dan murmushi ta gyada kai. Tace yawwa sai anjima Allah ya sadamu da alkhairi, Allah Ya bashi lafiya. Yayin da dr shuraim ya dubi kanwarsa ya juya ya dubi aisha farida da alama yana mamaki kuma daga dukkan alamu akwai alamomin tambaya a tattatre da bakinsa. Abin da kunnen aisha farida ya jiyo mata bayan sun juya suna tafiya shine ya dubi kanwarsa yace a ina kika san wannan yarinyar har ta zama kawarki, kuma takwararki? Haj farida tayi murmushi tace a nan na santa, yanzu ma na taba ganinta a duniya. Dr shuraim yayi dariya ya girgiza kai yace hmm mata, akwai kwashe kwashe, daga dan zaman da kukayi tare shikenan har kunsan juna, har da dogayen lanarai da sanin sunan juna. Suna ta maganar har sukayi nisa ta daina jiyo abin da suke cewa Aisha farida tayi ajiyar zuciya yayin da farin ciki ya rufeta, tasan dr shuraim yanzu ya santa duk inda suka hadu zai shaida fuskarta sannan zai tuna da sunanta tunda dai ba zai mance sunan kanwarsa ba uwa daya uba daya ba. Ko ba komai aisha farida taci riba tunda har ya damu yake yi wa kanwarsa tammbayoyi akanta. Ta fara Allah Allah a tashi daga asibiti taje gida ta bawa abida labrin cigaban da aka fara samu......bata gama tunanin da takeyi ba taji karan takalmi ana tahowa a baranda, ko da ta daga ido dr shuraim imran ta hango yana tahowa. Kallo daya tayi masa sai tayi sauri ta kawar da kai gefe, sai da ya wuce ta sai ta sake juyar da kai wani bangaren ta rantse shi dinne dai ba zata kalla ba. Abin mamaki sai taga ya wuce yana kallonta har da waiwaye. Don son ya gasgata abun da yake gani, sai ya dawo ya sake wucewa ta gabanta, wannan karon ma can gefe ta muskuta bayan kan ma har da jikinta ta juya ta nuno masa keya. Ya fice ya sake dawowa, sai yaga ta juya daya bangaren gaba dayanta. Tabbas ya shaida dashi take ba zata kalle shi ba. Baifi minti uku da shiga ba dakin marasa lafiya ba, sai gashi ya fito a karo na uku yana ta waya, amma fa yanayi yana duban aisha farida donya ga abun da zata yi. Sai tayi saurin dangwafar da kanta kasa ba ta dago ba har ya wuce waje, iyakacinsa kan baranda yaje ya dawo har yanzu wayar yake yi, da alama da kanwarsa farida suke magana tana wajen likita. Bata dago ba, sai da ta tabbatar ya shige babban dakin kwanciya na mata. Sai mamaki ya rufe aisha farida matukar mamaki kuwa. Wato ashe rububin nan da mata sukeyi a kansa da kallonsa, da shishige masa dadi yake ji kenan? Da gangan yake basarwa yasan ana sonsa kenan, ai ga shi yanzu bai ji dadi da ta share shi ba, tabbas ya bata satar amsa ya hadu da shariya sai ta rama duk abubuwan da yayi mata, inyaso ta rabu dashi daman ta fitar da ran samunsa. Bata gama tunanin da takeyi bi sai ta tsinkayo shi ya fito shi da matron maryam suna tafe suna magana har da kyakyata dariya. Dariyarsa tana tayarwa da aisha farida hankali, saboda sai yayi dariya kyawunsa yake kara bayyana. Aisha farida ta mike tsaye a nutse tana duban Matron maryam ita kadai, yayin da suka tunkaro inda take tsaye. Bai kalle ta ba, haka itama. Matron maryam ta dafa kafadarta tace Allah sarki 'ya ta yi hakuri na zaunar dake ko? Ina so in fito aka tsayar dani ai munyi waya da ita tace ba ta baki sakon ma yana nan waje shima yazo tun dazu, gezawa zai kai. Wannan shiriirta tawa dai Allah Ya shirya na barku ku biyu kuna jira, ke baki sanshi ba shi bai sanki ba balle ince ki bashi. Gashi baki da waya da na baki lambarsa, dole dai sai nazo. aisha farida tayi murmushi tace babu komai matron. Ta duka cikin ladabi ta mika mata 'yar karamar ambulan din. Matron maryam ta karba tayi godiya fuskarta cike da fara'a. Dr shuraim na tsaue a gefe hannayensa dukka biyi na cikin aljihun wandonsa kansa a sunkye a kasa bai cika kallonsu ba, yayin da aisha farida take gaggawar barin wajen, matron kuwa sai tsayar da ita take tana damunta da surutai barkatai. Dr shuraim ya dubi agogon dake hannunsa ya huya ya dubi matron yace sister maryam zan koma ciki, zamu hadu anjima, kinsan ina duba patient. Tsaya tsaya kanina, gara mu gama magana don idan ka zille min bansan sanda zan sake nemo ka ba, da gaske nake ni da mijina muna neman visa london ya za'ayi kenan? Aisha faroda ta samu ta sulale ta barsu nan a tsaye suna magana. Tana tafe tana mamakin wannan kyauta da Allah yayi mata a yau, Ya jeho mata sahibinta ta ganshi har ta gaji sabanin da, da sai ta yini tana zagaye bata ganshi ba. Tabbas abida tayi gaskiya, babu abinda yafi irin ka daga hannu ka roki Allah abinda kake so, zai biya maka bukatunka cikin gaggawa. Ta kudiri niyyar zagewa ta lullunka yin addua fiye da yadda take yi a baya. Ta isa wajen 'yan ajinsu sunyi aiki yadda ya kamata, har zuwa lokacin tashinsu, kowa ya lura yau aisha farida tana cikin walwala har ma wasu na tambayarta meyasa take murna yau. Da ta isa gida tun daga tsakar gida abida ta lura da yawan fara'arta don haka sai tabi ta cikin daki tana tambayarta. Lafiya meya faru yau naga kina ta fara'a? Ko aisha farida bata fada ba, abida ta canki daidai cewa tayi nasan dr shuraim ne ya saka ki walwala yau. Aisha farida ta kwashe da dariya ta gyara zama ta zayyane mata duk abubuwan da suka faru a yau. Tambayar da farida ta furta itace anty meye abunyi a nan gaba? Abida har kamar tafi farida farin ciki, sai tayi dariya tace ki zuba min ido gobe ni nasan abin da zanyi masa. Mamaki mara iyaka zaka iya gani daga idanuwan farida, zatayi tambaya abida ta katse ta, tace kada ki tambayeni, ki saka min ido kawai. Allah Ya kaimu gobe. Asuba ta gari AISHA SHURAIM!!! Washe gari da asuba kiran farko aisha farida ta bude ido, abin mamaki sai ta dinga jin motsi a kofar dakinta. Ta kame a kwance sannnan dai ta tabbatar ba aljanu bane, haka ba bakin dare bane wato barayi. Motsin abida ne don ta jiyo tarinta. Aisha farida ta cika da mamaki me ya fito da abida ne daidai wannan lokaci? Shine me takeyi a waje ta dade haka? Aisha farida ta mike a hankali tana sanda taje ta tura window ta leka duhu kirin tsakar gida, amma da hasken fitilar kwai a gaba abida, tana gaban murhu tana dahuwa. Sai mamaki ya sake lullube zuciyar aisha farida. Ta ambaci sunan abida atsorace a hankali cikin rada. Nan da nan abida ta dago ido ta dubi window tayi murmushi tace farida tsoro kika ji? Kada ki firgita nice dahuwa nakeyi. Aisha farida ta maimata dahuwa? Me kike dafawa da tsakar daren nan? Abida tayi dariya tace asuba ce ai yanzu, idan ya dahu zaki gani. Tayi wuf ta bude kofa ta fito tana kokarin bude tukunyar don taga abin da ake dafawa. Abida ta rike mata hannun. Tace idan ya dahu da safe zaki gani, abincin mijina ne. Aisha farida tace bulaguro zaiyi? Abida tace eh. Aisha farida tace ina zaije? Abida tace lagos. Aisha farida tace zai bi ta shagamu? Abida tace ba lallai bane don daga ofis zasu tafi. Aisha farida tace zai dade ne? Abida tace zai kwana biyu, kina da sako ne a fada masa? Aisha farida tace a'a zan so muyi sallamai dai kafin ya tafi saboda halin tafiya. Abida tace kada ki damu zan masa magana kafin ya fita sai kuyi sallama. Aisha farida tayi murmushi tace anti bari nayi alwala inyi nafilfili kafin a kira assalatu, sai inzo inci dadi, ina jin dai kaje ne ake rababbaka mana. Abida tayi dariya ba tare da ta bata amsa ba. Doguwar sujjada aisha darida keyi tana ta addua tana kai kukanta wajen Ubangijinta Ya bata abin da take so wato dr shureim idan har shine mafi alkhairi a gare ta. Idan kuwa babu alkhairi tana rokon Allah Ya yaye maata sonsa Ya bata wanda ya fishi alkhairi. Sai taji hawaye yana surnanowa daga idanuwanta, don tana tausayawa kanta da kanta, halin da ta tsunduma na soyayya. Ba ta bar kan tabarmar sallarta ba sai bayan datayi raka'atanil fijr da kuma sallar asuba, ta tofa adduoi a tafin hannunta ta shafa a fuska sannan ta mike zuciyarta cike da farin ciki tana da tabbacin Allah Ya amshi adduointa. Don shi kadai ne mai bayarwa wahidul kahharu. Daga nan sai ta shiga cuku cukun yin wanka da shiryawa saboda tafiya asibiti. Kafin ta kammala gari ya waye wasai, sai ga abida dauke da dan faranta da cokali a ciki ta mikawa farida. Aisha farida ta karba da sauri cike da mamaki, sai ta duba taga ai dambun shinkafa ne ya sha zogale da gyada, ya tiraru kuwa sai kamshi yake yana hayaki, da zafinsa kau. Ta koma ta zauna ta dandana, sai taji zakwai ya sha maggi da gishiri, ga dan yaji yaji sabida attaruhu da albasar da aka yayyanka yiri yiri a ciki, aka turara dasu sai kamshi yake tashi, hade da kamshin man gyada ziryan. Aisha farida ta girgiza kai ta sosa kunne tace tunda Allah Ya halicce ni ban taba cin dambu mai dadi irim wannan dambun ba. Lallai yaya yana cabawa irin wannan haduwa haka? Abida dai na tsaye a kanta murmushi kawai take yi bata ce komai ba har yanzu yayin da aisha farida ke faman turawa a cikinta tana ta santi. Aisha farida ta dagi ido ta dubi abida tace abin mamaki kuma dambu da aka sanshi da shakewa mutum makogoro sai gashi wannan dambun baya shake mutum silif silif yake wucewa. Wai, yaushe rabon in karya kumallo a gida, lallai yau zanfi jin dadin aiki don cikina yayi nauyi. Allah dai ya saka da alkhairi, Yaya hussani yayi sa'ar mata. Da dambun zai tafi a cikin food flask su dinga ci a hanya? Abida ta fita bakin kofa, sai ga tata shigo riki riki dauke da dan kwandon roba mai marika, irin wanda ake saka flask din abinci. Aisha farida tace lallai haduwa irin wannan sabon food flask haka? Yau aka bude shi daga leda duk saboda yayana tabbas babu mu babu kara aure. Abida tayi dariya tace bude ma kiga yadda aka shirya ciki. Aisha farida ta jawo kwandon ta daga wani babban hankici sakin ulu, wanda dashi aka lullube saman. Ta zaro wani dallelan flask mai madaidaicin girma, tsaka tsaki karkashinsa kuwa farantai biyu ne na tangaran da babban cokalin diba wato serving spoon da cokula biyu dukkansu sababbi ne filfil a wanke tas tas. Aisha farida ta gyada kai tace lallai wannan kwandon abin sha'awa ne tun kafin na bude ma abinda yake ciki. Abida tace bude mana ki gani. Aisha farida tayi bismillah ta bude, tana budewa sai wani kamshi ya daki hancinansu. Aisha farida tace humm lallai abin ma son kaine ko anty, ashe har da hanta da koda aka yayyanka a ciki shine ba a sako min bako daya sai maigida aka tulawa gasu nan burjik a ciki. DUK KYAN TAKALMI 2* 7 Abida tace me kika yi masa haka a rayuwa da zai tsane ki? Ba zai tsane ki ba, saboda kin riga kin kai kararsa wajen mahaliccinsa, zan sake baki wasu adduoi masu zafi wadanda suke kara soyayya da tausasa zuciyar wanda kake so. Idan kina karanta su hakika dole yaji yana sonki sosai. Adduar itace "Allahumma ya mukallibul kulubi wamusarrafuha kaifa ya sha'u usaibarul muhabbati fi kalbi (ambaton suna) bi hakki ismikal wadudu Ya wadudu. Ya wadudu sai dubu daya da dari daya da goma sha daya. Kiyi tayi kullum har zuwa lokacin da zai sanke kece mai dambu sai ya hadu da kaunar dambun da aikin wanna adduar su fara aiki. Ni kuma a lokacin zan fada miki abu na hudu da zaki rike nan gaba, kinsan yanzu uku na fada miki shine ADDUA, HAKURI da RIKE MUTUNCI. Bazan fadi na hudun ba, sai a lokacin da kika tabbatar min ya gama saninki. Idan ya ganki a ko ina zai shaidaki, zai kira sunanki, zaiyi miki murmushi, zaki gaishe shi ya amsa cikin farin ciki, to sai na jeho miki makami na hudu wato taryo soyayyarsa. Aisha farida ta lumshe ido don dadi tace kamar a mafarki nake jina. Sai nake jin bayaninki kamar na samu shuraim na gama. Abida tace shi yasa ake so mutum ya rike Allah, Shi zai biya masa bukatunsa banda bin boka ba ko 'yan bori. Shiyasa mata muka fi yawa a wuta, saboda karamin tunaninsu da gaggawa. Gaggawa kuma daga shaidan take, yanzu da kika riki Allah zaki ga yadda Allah zai taimake ki, ko baki samu shuraim ba zai musanya miki da wanda ya fishi, kuma zai tanadar miki babban rabo a lahira. Aisha farida ta gyada kai tace haka ne. Allah Ya sa mu dace, wadanda suka bata irin su Ummi Allah Ya ganar dasu gaskiya. Abida tace amin. Ci abinci ki fita kije ki cefano min kayan dambu. Asuba ta gari AISHA SHURAIM!! Washe gari aisha farida tayi sammakon zuwa ofishin dr lukman tayi sa'a kuwa tana isowa kamar tare suka zo, shima yazo yana bude ofis dinsa, don haka sai suka dunguma suka shiga tare. Ta gaishe shi ta ajiye katon kwandon mai dauke da katon food flask din abinci, babban na jiya ne da farantai hudu da cokula hudu. Dr lukman yayi murna da ganin dambu kuma yayi godiya. Yau ma yayi kokarin bata kudin taki karba, tayi gaggawar fita daga ofishin ta rufo masa kofa. Misalin karfe uku da rabi ta koma ofishin ta iske ofishin a kulle baya nan, amma ta jiyo muryarsa a ofishin dr shuraim, don haka sai ta sadada ta bar wajen. Ta dade a labe tana hango kofar ofishin ko zai fito bai fito ba, sai ta hakura ta tafi gida. Yau dai bata walwala sosai, don bata jiyo sakamakon jarabwar dahuwar dambu ba. Shin gogan nata yaci koma bai ci ba? Ya yaba ko ma bai yaba ba? Data fadawa abida sai tayi dariya tace ai ya ci ma kawai tunda kika jiyo muryar dr lukman a ofishinsa suna tare, babu yadda za'ayi yaga dambun yaki ci. Aisha farida tace ya za'ayi kuma gobe? Abida tace dan wake zanyi musu ki kai musu tunda shuraim yana son dan wake. Aisha farida tace a'a kada ayi, ki bari dai a kwana biyu kada lukman din ya zargi wani abu, ko yaji tsoro. Abida tayi darriya tace tsoron me? Idan kika kai musu dan waken kika dauko duka food flask dinn sai muyi shiru muji abinda zasu ce, kuma muji wanne suka fiso, suka fi jin dadinsa. Sai mu dinga yi musu shi. Aisha farida tace ni sai nake ganin kamar duk ba zai damu da sai yasan waye yake dahowa ba, balle ya sanni. Abida tayi murmushi tace kin manta abinda nake fada miki, ki zama mai hakuri duk mahakurci shi yake cin riba. Aisha farida ta jinjina kai tace haka ne, shikenan zanci gaba da hakuri. Abida tace yawwa tashi muje mu daka yaji mai dadin gaske yadda zasuji dadin danwaken sosai. Sai ki siyo tumatur, albasa, kokunba duk a yayyanka musu a ciki. Aisha farida tayi dariya tace har naji yawuna ya tsinke, gaskiya danwaken nan zaiyi dadi, zaiso shi. Rana ta uku ranar alhamis kenan kamar kullum da sassafe aisha farida ke fitowa daga gida tana fin kowa sammako. Tayi jira fiye da awa biyu sannan dr lukman ya iso. Sai da ya jima da shiga sannan tabi bayansa. Yayi farin ciki da ganinta, sai dai yayi matukar mamaki da jin dadi da ya ga ta sake dire masa wani kwandon abinci a gabansa. Yace lafiya, meye wannan kuma? Dama kin dauki kwandon jiya? Ta girgiza kai tace nazo baka nan sai na wuce gida kawai. Wannan wani ne na kawo muku, wannan karon ba dambu bane, wani launin abincin gargajiyar ne. Dr lukman yace a'a 'yar shagamu kinaso muyi fada ko? Yaya zaki tayi mana wahala, kartai muna taruwa muna cinyewa babu ko sinsinmu? To gaskiya bazan karbi wannan ba, ki koma dashi gida, ko ajiyar ma bazan yi ba. Aisha farida tayi dariya tace yi hakuri yayana, daga yau shikenan. Yace kwanukan jiya suna ofishin dr shuraim, kuma bana jin yazo yanzu, don bai cika zuwa da wuri ba. Ina da mukullin ofishinsa bari in bude in dauko miki kwandon da farantai da cokulan, amma ainahin food flask din ta tafi dashi gida, dambun jiya yayi dadi sosai, har yafi na shekaran jiya. Sai yace dole ya kai wa babansa yaci yaji irinsa, donshi ya koya masa cin dambu. To wallahi kinji yadda akayi, sai anjima zai zo zan ma sake yi masa waya kada ya mance dashi a gida, lallai lallai ya taho dashi. Tuni farin ciki ya cika zuciyar aisha farida, taji tamkar ta daka tsalle don murna. Tayi dariya tace ba koma dr ai ko food flask dinnan ba yanzu zan dauka ba, sai da yamma. Yanzu aji zan tafi. Sukayi sallama aisha farida ta tafi, kowannensu na farin ciki. La'asar sakaliya Aisha ta tunkaro ofishin dr lukman saita hango gogan nata yana shige da fice tsakanin wannan ofishin zuwa wancan dauke da wasu fayil don haka saita diro daga kan barandar ta shige lungu ta samu waje ta zauna har saida ta ga fitarsa ya shiga motarsa ya tafi gida bata bari ya ganta ba.ta tashi cimak ta nufi ofishin dr lukman hankalinta a kwance baby wata fargaba dr lukman ta iske shi kadai da alama shima ya miqe yana shirin tafia gida yana ganinta yayi dariya yace yar shagamu gaskia kin iya girki kice daman tun farko a shagamu na nemi mace ba'a yobe ba kinsan yadda mukayi santin dan waken nan dr shuraim har cewa yayi week end zaizo in kaishi ya gaida kakata mai dambu da dan wake da yake nace musu itace take daho min Aisha ta tuntsire da daria tace lallai kuwa daka zo shagamu an baka mata daka sha girki mai dadi ya miqo mata kwandunanta guda 2 yana godia tana godia suka yi sallama ta tafi tana fitowa bakin get ta dane acaba sai gida tana mai farin cikin zuwa sanrwa da abida labari.Abida na ganinta sai tabi ta daki suka rungume juna suna murna tun ma kafin abidar taji labarin abunda ya faru. Aisha tace zauna in baki ki sha suka zauna Aisha ta zayyana mata suk abubuwan da suka faru yau tsakaninta da dr lukman da abunda dr shuraim ya fada.Abida tayi murna sai ta shiga bubbude food flask din ta bude na farko saiga kudi yan 500 sabbi har guda 4 tayi sauri ta bude daya food falsk saiga yan 1k har guda 3 suma sabbi sai su duka suka bude baki suna mamakin wannan kudi da suka gani Aisha tasa hannu a hankali ta debo yan dari biyar din ta shinshina saita a jiye a gefe ta sake yan 1k ta shinshina saita lumshe ido tayi murmushi ta dubi abida tace wadannan kudin daga dr shuraim suka fito shinshina kiji qamshin turarensa Abida ta karba da sauri ta shinshina tace ehmm qamshi farida har a jikin kudi kike gane qamshin turaren masoyinki?lallai kin laqanci qamshin turarensa to shine ya zuba wadannan kudi kenan dr lukman ya zuba yar dari 500 dinnan daya ga kinki karba?Aisha tayi fari da ido tace Allah sarki mai karbar addu'a kalli daki-daki yana koro mana hanyar haduwa da shuraim a cikin ruwan sanyi yanzu ga kudinsa ya shigo hannu cikin hikimar ubangiji sai ta fara kuka Abida tace kada kiyi kuka kici gaba da dagewa da addu'a to yanzu kin ga kudin dr shuraimkinyi kuka ina ga ranar da kika ganshi kacokan a qofar gidanku yazo zaance balle ranar da zaki ganshi a dakinki a matsayin mijinki?sumewa zakiyi kenan don dadi?Aisha tayi daria tace gobe jumu'a yaya za'ayi a sake musu ko a bari?abida tace aa tsahirta gobe jumu'a sai kije ofishin dr lukman kice doctor ranar litinin me kuke so a dafo mukudambu ko dan wake kiji abunda zai zaba saiki zo tun ranar asabar mu fara aikin hada musu mai dadi da kunun gyada ko kunun tsamiya zakiyi musu mu zuba kofuna qanana zasu so shi kinga suma duk abincin gargajiya ne Aisha tace gaskia koba a fada ba dr shuraim zai so kunu sosai shike nan haka za'a yi.Anan dai suka bar hirar Aisha ta hadawa abida dukka kudin 5k ta ce ta riqe a wajenta ba sai ta dau ko sisi ba tunda ita ce take cefanen nan a aljihunta asuba ta gari farida shuraim. Khadija sani isma'I'll ce ta duni Aisha tace wai me yasa kullun idan nace kizo ki rakani babban daki na maza saiki turje ki tsaya daga nan kice inje in dawo ba kya son shiga?Aisha tace babu komai wlh ni dai kibar ni nan kije ki dawo zan jiraki ko hour nawa zakiyi khadija tace idan dai bazaki raka ni ba nima ba zan je ba daman ba wani abu zanyi ba illa in leqa ta wajen ofis din kyakyawan likitana dr shuraim musu mukeyi da mrym kinsan yanzu ta saki ranta ta daina kishin dani data ga ta rasa nima na rasa kuma bazamu samu ba mu duka sai dai in mun hadu muyita labarinsa cewa tayi yafi kama da larabawa ni kuma nace kyan indiyawa gare shi shine nake so mubi ta ofishinsa mu tantan ce nida ke kinjin Aisha ya ne ya buga bummm!don fargaba nan da nan taji hankalinta ya tashi tace a ranta daman har yanzu khadija da maryam basu daina son abuda nake matuqar so ba? Lallai ashe akwai hargitsi a nan gaba gara ma dai kawai in haqura da son mutunmin nan in hutawa raina abida ce taqi haqura dana cije na daure na watsar da son koda kuwa zuciata zata lahanta koda ciwon zucia zai zama shine ajalina in mutu in huta.sai taji kwalla ta cika mata ido sai khadija ta mungure ta sannan ta fara fahimtar maganar khadija keyi khadija ta kalli farida tayi murmushi tace kiyi min wannan taimako yau dai ki raka ni har ofishinsa ba komai zanyi ba illa in kare masa kallo in tantance nidai nasan akwai wanda yayi min kama dashi a film din india Aisha ta fusata tace shirme kenan haba khadija kamar wasu yan primary?ki tuna fa jami'a muke shirin gamawa kuma manyan ma'aikata muke shirin zama ma'aikatan ma na jinya masu kula da lafia jama'a wadan ake girmamawa a al'umma ya kike abu kamar marar ilimi?kinsan mutumin nan kinsan halinsa ke za ki fadawa wani irin salo da launin wulaqancinsa.ke kika cemin min kin haqura dashi baki yadda kika burge ni ba har kika umarci muhammad saurayinki ya kawo kudin aure ya kawo aka saka muku rana tamkar matar aure kike saboda anyi miki baiko ma'ana anyi wa wani alqawalin bambancinki da matar aure kadan ne mijinki kyakyawa dan gayu mai ilimi babban ma'aikacin banki da kadan shuraim yafi shi kyau habah khadija kada kibani kunya mana ashe har yanzu akwai namijin da zai burge ki bayan mijinki?kada fa ki zama irin matan nan da zasu yi aute kuma suna son wasu mazan a waje babban bala'I ne yin haka dunia da lahira halaka ce.idan kin san zuciayarki bata kwanta da auren muhammad ba gara kada ayi kice kin fasa kizo mu tayaki yaqin neman soyayyar wannan dan wulaqancin!kahadija ta tuntsire daria tace dadina dake Aisha umar akwai fadar gaskia komai dacinta wlh ko dan bazan zama daga cikin irin matan nan da kika zano ba insha'allahu ba zan sake zuwa ganinsa ba daman sai na manta dashi sai maryam ta tsokano min zancen itace har yau bata gama haqura ba Aisha umar ta kalli barandar can ki gani. Aisha ta wurga ido da sauri dr shuraim imran ta hango yana tahowa tafia yake a tsanake fuskarsa cike da fara'a jama'a suna ta gaishe shi yana amsawa idonsa ne ya wurga ya wurgo kansu Aisha farida wadanda ke tsaye a jikin bishiyar dake kusa da barandar da yake tafe kai kace ita da khadija saurayi da budurwa ne suke zantawa sun fuskanci juna suna tsaye cirko- cirko babu wanda ya sake magana a cikinsu yayin da khadija ke kallonsa tana yi masa murmushi. Aisha kuwa sauri tayi ta juyar da kanta gefe bata duban bangaren da yake ma Aisha taji tamkar ta kurma ihu don takaici tada ji khadija ta maqe murya ta gaishe shi saii ya amsa cikin farin ciki ya wuce abinsa sai da yayi nisa khadija ta zungure ta tace amma bakida kirki kina ganin malaminki amma kika qi gaishes shi ? naga alama fa baiji dadin ba da baki gaishe shi ba Aisha ta tabe baki tace yaya akayi kika san baiji dadi ba? Khadija tace saboda naga irin kallon da yake yi miki ne leqen fuskarki yane tafe yana waiwaye so yake ki juyo ya ganki Aisha tace ai ba dole ne in gaishe shi ba tunda in an gaishe shi sai yaga dama yake amsawa ke rabi ni da wahala kinji ta kaina nake bani da lokacin kowa.khadija tace kin huta ai shiyasa kike burgeni ina son halinki ko bayan idonki ina fada daman tun farko ma dai naga alamar kin tsani dr shuraim ko zancensa ba kya ayi miki Aisha tayi wani lalausan murmushi ta gyada kai tace me yasa zan tsani musulmi dan uwana ?aa wlh ban tsane shiba ko kadan ina sonsa so tamkar raina zai fice kamar yadda nake son dan uwana na jini saboda shi ma musilmi ne musulmin ma mumini mai riqe addini irinsa khadija tayi doguwar ajiyar zucia ta dauka Aisha ma zata ce itama ta mato a sonsa yadda itama take sonsa sai taji farida tayi kwana.suna tafe suna firarsa har zuwa bangaren da suke wato wajen masu ciwon hawan jini da ciwon suga Akan barandar da suke tafe a nan shuraim ya taho suna daga ido sai suka hango shi daf dasu shi yana tahowa su suna tafia sai suka yi gum da bakinsu don birarsa suke a lokacin dan halak yaqi ambato inji khadija Aisha ta duqar da kanta qasa bata sakw dagowa bahar sai daya gifta ya wuce kamshin jikins ya daki hancinta sai ta lumshe ido ta fada a zuciayar ya Allah ina son wannan bawa naka sannu likita sanna da qoqari kalaman da suka rikito kunnen Aisha ke nan daga bakin khadija take fadawa dr shuraim dai-dai sanda yazo giftawa ya fada cikin qasaita thank u ya wuce abinsa Aisha farida tafia take kawai amma tamkar ta hadiyi zucia don jin haushin barar da ajin da khadija keyia wajen bawan Allah nan. Khadija ta zunguri Aisha tace saki dago da kanki dodon naki ya wuce don naga ko kallonsa ba kya son yi ikon Allah shi kuwa sai ya tsura miki iso yayi ta kallonki don Allah ki dinga gaishe shi bin na gaba fa bin Allah ne Aisha tayi ajiyar zucia tace Allah yabamu ikon bin shugabanninmu amma wadanda suke bin Allah khadija tayi daria tace shegiya Aisha umar akwai iya magana nasan baki yarda da abun dana fada miki ba zaki dinga gaishe shi ba kenan?kin jini ne dai kawai Aisha tace uhmm kawai take fadin sai kuma gyada kai take tayi tamkar kadangaruwar ta kasa cewa komai saboda ganin dr shuraim dinnan da tayi yau yayi mummunan fama mata son data keyi masa Aisha shuraim haquri shine maganin zaman duniya! Aisha ta cika mamaki a lokacin da yaro ya leqo dakinta yace tazo wani yana sallama da ita a qofar gida a motarsa a zaune ta duba agogo karfe 7:30 na dare ko isha'I ba'a kira ba yadda take zaune akan abun sallarta sanye da hijabi da carbi a hannuta haka tayi zunbur ta miqe tace da yaron tsaya ni mu tafi tare ka kai ni wajen mai yin sallamar dani faruk ta gani dan abida a tsakar gida tace idan mamarka ta idara salla a kace mata anyi kirana a qofar gida ina zuwa ya amsa da to aunty Aisha zaki siyo mun alewa da biscuit?aisha ta girgiza kai banyi maka wannan alqawalin ba nima nan daka ganni na dade ban sha alawaba ta wuce da sauri ita da dan aike ta kama hannunsa tace yaro a ina mai motar yake?wayace ka kira?yaron yace a wajen ya tsaya kafon a hayo sai ya kirani yace inzo nan gidan nan mai bishiyar dirimi in kira masa Aisha umar qanwar husaida mijin abida shine nake ta leqawa ina tambaya har aka nuna min dakinki mamaki ya sake lullube farida ta dafe qirji tace inalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah yasa baqon nan baqon Alkhairi ne toni waye wannan?ba dai dr lukman bane balle in saka ran dr shuraim sune kadai nasani a dunia masu mota su kuwa basu san gidanmu ba haka yaro yaya suffar mutumin take?yaro yace dogo ne haka fari mai dan gemu a habarsa kyakyawa mai kudi motar hadaddiya Aisha ta juya kawai tana kallon yaron tana mamakin yadda yake suffanta mutumin.tabba s suffofin dr shuraim ya zano mata amma tana tabbacin ba dr shuraim bane a wanne dalilin ma zata saka ran dr shuraim zaizo gidansu mutumin da har yanzu bai game gane taba a hanya balle wata hulda ta hada su harma ya tako a qafarsa ya zo inda take don haka ta cire dr shuraim a tunanin ko shine sai ta koma sake saqen wasu daban suna tafe fakam- fakam sai sauri suke zubawa ta sake juyowa ta dubi yaron tace yaro shi kadai ne koda macea motar?yace shi kadai ne! Aisha ta fada a bayyane toni Aisha waye wannan da akwai mace a motar sai ince khadija ce ta kawo min mijinta mu gaisa yaro kawo bakin wata dalleliyar motar qirar BMW baqa wuliq sabuwa dal!har sheqi take ya ce ga motar mutumin yana ciki, Gabanta ya yanke ya fadi daf-daf taja ta cije ta tsya a gefe tace kwankwasa masa gilashi kace masa gata ka kira ta don inga ko waye yaro ya qarasa da sauri ya daddage ya daki glass kai kace qofar qarfe yake bugawa lallausan hannu hade da kyakyawar fuskar dan adamu ne ta fito fili sai gashi ya bayyana a lokacin da ya sauke gilashin wundonsa qasa Aisha ta kaikace tana leqensa daga nesa har yanzu bata gane shi ba kasancewar akwai duhu wajen duk da akwai hasken redio motarsa na haska shi kadan yaron ya dawo wajen farida yace ki qarasa kinga har yabani N100 Aisha tace lallai ka caba kaje na gode tafia take a nutse amma a tsorace kamar ace kulle tace cas!nauyi kunya fargaba da tsanaanin tsoro sun gallabe ta ta isa jikin window da yake zaune ya zuba mata ido yana kallonta fuskarsa cike da annuri yana nuna farin cikin da ganinta ta kasa kallonsa saita duqa ta gaishe shi ya amsa cike da fara'a hadi da cewa hajia Aisha farida yar shagamu nasan zakiyi mamakin ganina ko?wannan karon da sauri ta dago kai ta dubi kyakyawar fuskarsa domin tana jin muryarsa ta gane ko wanene tabbasa muryarsa ta tabbatar mata dashi dinne wanda take zato a lokacin data dubi fuskarsa.dadi marar misaltuwa suka tabbata a zucia yar Aisha ta dafe qirji ta fada cike da mamaki marar adadi barista mu'azzam yau kaine a gidanmu nayi matuqar mamaki hade da dinbin farin ciki dana ganka a gidanmu ka kyauta gaskia Allah ya bar zumunci yayi daria yace miki wannan shine zuwana na farko aina sha zuwa nansai in aika yaro ya dawo yace min. Ance ba kya nan kai rannan ma ce min kayi gidan naga wasu maza 3 a zazzaune akan tabarma suke cemin kina ciki amma shwararda zasu bani kada in sake dawowa ba kula zaki yiba haka yayanki ma idan ya ganni korar kare zaiyi min.na fahimci dai hassada ce kawai na tafi na barsu yau dai Allah yasa na sami yaro mai wayo nace ya shiga ciki ya nemo har. Dakinki ya kirawo ki amma wanne irin zama kuke da mutanengidanku haka shin bakwa shiri ne? sai hawaye ya fara surnanowa a idontaAisha tana sharbewa da hijabinta barista mu'azzam ya warwaro toilet paper ya miqa mata yace aa qanwata kin fara koke -koken naki ko?bana son kukan nan yanzu zaki kore ni fa Aisha farida ta goge idanuwanta tace na daina kuka yayana abun ne yabani mamaki muna zaune dasu zucia daya muna qoqarin kyautata musu su basa qaunarmu ba'a son ci gabanmu ko zaka rufe motar kazo muje kan dakalin qofar gidan mu zauna kada in shiga motarka ayi ta yamudidi dani a unguwa da sharri kala-kala Alhamdulillah daka san yadda mutanenmu suke. Barista mu'azzam yace kwarai kuwa yi gaba zan biyo bayanki kada a ganmu mun jera muna tafia Aisha tayi sauri ta shiga gida don dauko sallaya da pure water. Abida tabi ta daki a gigice tana tambayarta wai waye yazo a dalleliyar mota ne, naji matan gidan nan suna ta yamadidi, har suna aika 'ya'yansu suje su gano musu ke. Aisha farida ta rike baki tace mun shiga uku da zaman haya, au faruk ba fada miki sakon dana bashi ba, nace ana kirana a waje na tafi. Abida tace bai fada min ba a tsakar gida nake jiyo gulmar. Kada fa kice min dr shuraim ne? Aisha farida tace in dr shuraim ne ba sai mu gudu ba? Bashi bane, barister muazzam ne. Ta kwashe labarin daya bata ta fadawa abida, na 'yan hassada. Mamaki ya rufe abida ita ma sai da tayi kuka. Aisha farida ta hanzarta daukar sallaya da pure water guda biyu ta fice da sauri ta iske har barrister muazzam ya karaso kofar gidan, kasancewar bayan magriba ne don haka yawancin mazan gidan duk suna masallatai, sai anyi sallar ishai zasu dawo. Ta shimfida akan dogon dakalin mai fadi, sannan ta umurce shi da ya zauna. Yana zama sai ta duka ta mika masa pure water ko sanyi babu, ya karba yayi murmushi yace nagode ki zauna mana ya zaki tsaya a tsaye, ai ina ganin akwai tazara a tsakanin mu idan kin zauna a karshen dakalin, ni ma ina karshe ba za a ce kinyi rashin kunya ba dai ko? Don naga alamar unguwar nan taku abar tsoro ce, suna da saka ido da gulma, koda yake duk cikin gari haka suke, 'yan gargajiya ne kawai. Babu maganar wayewa a tattare dasu. Aisha farida tayi murmushi ta zauna a tsorace ta sake gaishe shi, sannan tace yaya muazzam sai hakuri, bamu da fridge kuma inda ake sayar da ruwan sanyi babu saboda munfi sata ba a kawo mana wuta ba, zaka ji ruwan babu sanyi. Muazzam yayi dariya yace kada ki damu, yanzun nan na sha ruwa har roba biyu a mota, na karba ne dai don kar kiji babu dadi, nagode. Aisha farida tayi dariya tace a'a nice da godiya, naji dadi da na ganka, Allah Ya bar zumunci. Ina abokinka barr nurruddin? Ina baraka matarsa? Ina kuma matarka dr janan? Barr muazzam ya kwashe da dariya yace har kin daura mana aure ne ta zama matata? Duk suna nan lafiya kamar yadda kika barsu, babu wanda ya sauya a cikinsu. Nuraddin yana nan yana taurin kansa, da gallazawa baraka. Haka itama baraka tana nan tana hakuri. Ko da yake kwanan nan ta fara ce min hakurinta ya fara karewa, zata fadawa magabata a raba auren. Ita kuwa janan tana nan a daure ana ta tafka sharia babu wani canji a tsakanina da ita. Iyayenta ne dai kawai suke ganin kokarina da nake a kanta, ita har yanzu bana gabanta. Ni har haushin kaina nake ji wata rana ince to wai me yasa na nace sai janan bayan a gari ga 'yan mata nan reras wadanda ma suka fi ta kyau da kwalliya, saboda a yanzu idan kika ga yadda janan ta koma idan kinsan ta a da ba zaki ce ita bace, kamar wacce aka sauya ta gaba daya duk tayi muni, tayi baki, an aske wannan gashin nata mai tsawo sai kwas kwas. A ficika wani ba zai dauke ta ba, amma har yanzu zuciyata bata daina sonta ba, kuma ita kadai nake so bana son wata. Wannan al'amaro yana bani tsoro da mamaki. Aisha farida ta girgiza kai tace Allah sarki rayuwa, har naji tausayinka. Wannan shine ake kira soyayyar gaskiya, so saboda Allah kenan ba don wani abu ba. K KYAN TAKALMI 2* 9 Dr lukman yace kin tabbata baki gane abin da yake nufi ba? Kada ki boye min komai. Aisha farida ta girgiza kai ta zubo da hawaye da ya cika mata ido tace bansani ba wallahi. Yace to jeki zanyi miki waya anjima kada kiyi kuka. Aisha farida ta tashi da sauri ta fice yayin da dr shuraim ya bi ta da harara. Tana fita sai ta rufe kofar kuma ta labe ta dora kunne a jikin kofa tana sauraronsu. Dr lukman ya juya ya dubi shuraim yace wai me yake faruwa ne? Yarinya ce fa kimtsatsiya. Tana bin maza ne ma'aikata? Dr shuraim yace kaji matsalar ku kenan, baku da kyakkyawan zato, nan da na sai ku ballo bala'I. Meya kawo wannan zargin kuma? Dr lukman ya juya ya dubi dr mohd yace don Allah dr a kasar hausa idan aka dubi mace akace ki kama mutunci da darajarki ta 'ya mace meke nan? Ba 'yar iska ba kenan? Dr mohd yace kwarai kusa, kasan bature ne su a london ustazan mata ake fadawa haka. Suka kwashe da dariya su dukka, dr shuraim yace uhumm kai kake ganin hankalin yarinyar na, ai ni tuni nasan maciji sari ka noke ce. Nafi ku karantar halayanta. Wato tunda Allah Ya halicce ni a duniya tsakanin jinsin mace ko namiji ban taba ganin wacce ta iya hawa acaba irin wannan yarinyar ba. Sai su dr lukman suka kwashe da dariya, yayin da dariya ta kubcewa aisha farida sai tayi sauri ta toshe bakinta. Dr shuraim ya bata fuska yace ai ku abin ma dariya ya baku? Wallahi ba abin dariya bane, ya kamata kayi mata fada. Hawan jini ne kawai rannan banyi ba, shekaran jiya ne ma ba adade ba. Caraf zaka ga ta haye acaba da yake ba nauyi ne da ita ba, kuma ta kware. Dan acabar nan ya wulwula da ita suna kallon kudu sai sai gasu sun juyo arewa ba tare da ya duba ko ya saka sigina ba, suka rufta kan wasu 'yan acabar suka tafi tangal tangal kamar zasu fada kwalbati. Allah Ya kiyaye basu fada ba, ya tashi hayaki da kara mai tsanani, sannan ya zuga da gudu kamar zai tashi sama. Kunsan yarinyar nan ko a jikinta, mutane babu wanda bai dora hannu a ka ba ya dau salati don ni sankarewa nayi a zaune wallahi na dade a daren banyi bacci ba. Dr lukman yace to don wannan ne ma shine kaki fada a gabata, kaga ka tayar mata da hankali har tana kuka. Dr lukman yace to don wannan ne ma shine kaki fada a gabanta,kaga ka tayar mata da hankali har tana kuka. Dr shuraim yace kukan munafunci ne, tasan abinda nake nufi ai tana shigowa ta kalli idona ta dauke kai, tasan na ganta kuma da zata lura dani tasan na tsani hawan acaba to yadda kasan tsokanata take yi, ina yawan hango ta ta dane. Da ace tasan ni ta san ra'ayina akan tsanar mace ta hau babur da sai ince da gangan take yi, don inji haushi. To bata sanni ba, amma tana bani haushi wallahi. Dr lukman yace ni kuwa yarinyar burge ni take yi, tana da natsuwa. Dr shuraim yace tana da hankali amma da ace zata rabu da hawan acaba da tafi hankali. Aisha farida ta shafa kirji tayi ajiyar zuciyar jin dadi, ta daga idonta sama tayi wa Allah godiya, sannan taci gaba da kasa kunne tana sauraronsu. Bata damu da mutanen da suke wucewa suna ta kallonta ba, ko tantama babu sun san gulma take saurare. Dr lukman yayi dariya yace zaka sake ganin hankalinta ma idan yau na sanar maka cewa ita ce mai yi maka daddadan dambun nan da danwake wanda kake ci kana santi kullum. Yanzu ma kiran da nayi mata kenan zan fada mata ta daho mana gobe. Shine daga shigowarta kuka hau yi mata shakiyanci, har kuka sakata kuka, shikenan duk kun huta gobe ba cin dambu. Dr shuraim ya sankare, ya dade baiyi magana ba. Sai dr mohd ne yace ba ruwana wallahi, data gaishe mu ma ni kadai na amsa, dr shuraim ne ya share ta. Dr lukman yayi dariya yace kai ka fara iskantarta kake cewa wai ko kanwar zamani ce, alhali lallabata nakeyi, don kada ta zata mun mayar da ita baiwar mu. Ko kudin na bata ba ta karba, duk kyauta muke ci in dai ba dubara ba zata karba ba. Gashi daga dukkan alamu ba su da hali sosai, dole ce ma yake sawa ta hau acabar ba zata iya biyan shatar adaidaita sahu ba, inajin kuma gidansu ba hanyar bus bane. *nxt page din is damaged, bana ganin rubutun sosai* Dr lukman yayi dariya yace zaka sake ganin hankalinta ma idan yau na sanar maka cewa ita ce mai yi maka daddadan dambun nan da danwake wanda kake ci kana santi kullum. Yanzu ma kiran da nayi mata kenan zan fada mata ta daho mana gobe. Shine daga shigowarta kuka hau yi mata shakiyanci, har kuka sakata kuka, shikenan duk kun huta gobe ba cin dambu. Dr shuraim ya sankare, ya dade baiyi magana ba. Sai dr mohd ne yace ba ruwana wallahi, data gaishe mu ma ni kadai na amsa, dr shuraim ne ya share ta. Dr lukman yayi dariya yace kai ka fara iskantarta kake cewa wai ko kanwar zamani ce, alhali lallabata nakeyi, don kada ta zata mun mayar da ita baiwar mu. Ko kudin na bata ba ta karba, duk kyauta muke ci in dai ba dubara ba zata karba ba. Gashi daga dukkan alamu ba su da hali sosai, dole ce ma yake sawa ta hau acabar ba zata iya biyan shatar adaidaita sahu ba, inajin kuma gidansu ba hanyar bus bane. *nxt page din is damaged, bana ganin rubutun sosai* Dr shuraim ya ja doguwar ajiyar zuciya yace Lukman don Allah da gaske kake ita ce ke dafa ma dambun nan da kanta?dan iska kace kakarka ce ko kakarku daya ne? Dr L yayi dariya yace ka taba ganin dangina a kano balle in yi kaka? wallahi itace ta ke kawo min da farko ma ajiya ta kawo ta dahowa kawarta an kwantar da ita anan asibitin to bata san an sallameta ba nace mata za mu dandana tace mu cinye dukka" dr Sh yace to me yasa ka boye mana kace kakarka ce take dahowa? Lukma yace kawai don inji dadin bakina ni ma kun koya min shakiyanci ne ai? Dr sh yayi shiru can yace kuma yarinyar ta tabbatar maka da hannunta take dafawa ko dai mamanta? Lukman yace eai kai me ye abun mamaki ta tabbatar min ita take dafawa zata min karya ne?Shuraim yace ashe alkawarinmu ya tashi ke nan da muka saka ran zuwa gaishe da tsohuwa mai dambu,ashe karyarka ce? Lukman yace ga yarinya mai dambu ta gaishe ka ka ki ka amsa ka yiwa kanka"shuraim yayi murmushi yace Daman ai don kai take yi ba don ni ba idan ka yi mana bakin ciki don kada mu ci to ai shi ke nan don ta ni mai sauki ne don kada mu ci to ai shi ke nan don ta ni mai sauki ne .kada yake Abbana fa ya kamu da son dambun nan jiya ma ya tambaye ni yaushe zan kawo masa dambun nan mai dadi inda ya sake son dambbun ma da nace ba na gidan sayarwa bane a gida ake yinsa na musamman ga tsafta" Lukman yace ka ci albarkacin abba bari in kirata ta zo in ce ta yi mana"dr shuraim yace kada ka bari ta san mune muke ci kasan abun da zaka fada mata"Dr L yace ban iya karya ba ko karyar kuma zaka koya mani? Ya dauko wayarsa ya lalubo sunan Aisha farida ba ta ankara ba ta ji wayarta tana kokarin daukar kara alhali ga ta a jingine a jikin kofarsu sai ta falla da gudu ta fita daga farfajiyar ofisoshin sannan ta matsa dr Lukmn ya ce kanwata kina kusa ne ki zo mana ina da magana dake"Aisha ta amsa masa na da yi nisa yayana sai nan da minti 30 zan karaso"yace babu komai sai kin zo tana ganin Dr Shuraim da Dr Mohd suka fita daga ofishin Dr Lukmn don kada ta zo ta same su ita ma saboda su din ne ta ki zuwa da farko da suka fice sai ta yi wuf ta fada ofishin.Dr L yayi murmushi da ganinta yace a'a ai ko minti 5 baki yi ba kika zo?ta ce Ashe zamu gama da wuri na dauka zamu dade kasan tafiya shi ne muka dan harhada kayayyakinmu"yayi dariya yace mata dai duk inda kuka je sai an barbaza shirgi wato dan zaman da kukayi asibitinmu har kun baza mana shirgi kenan? Aisha Farida ta yi dariya tace Wallahi kuwa don wasu jaka guda cika a nan suke cire kayan makarantasu wata ma jakar kayan siyarwarta a nan take bari duk a ofishin metron Maryam. Doctor ina so inyi muk dambu da danwake gobe, ina fatan kana gari ko? Yayi dariyar farinciki yace kai haba! Kina wahala da kanki, ki bari kawai. Aisha farida tace a'a ai nayi niyya ba a mayar da hannun kyauta baya. Dr lukman yayi dariya yace koda yake na bankwana ne ko? Gashi zaki tafi ba ganinki zamu dinga yi ba. Aisha farida tace haba yayana ko kasar ka bari inda hali ai zan ziyarce ka balle nan da nan. Ai duk sanda kake da bukatar dambu ko ba kai bane, ko abokanka ne kada kaji komai, kayi min waya kawai. Dr lukman yayi godiya yace to amma abin da yasa zaki sage min gwiwa idan na baki kudi ba kya karba, ni kuwa banga dalilin da tika tika damu mun daukar albashi mai tskoka zamu zauna muna tsotse dan alawus din dalibarmu. In kina so mu shirya to duk abin da na baki ki karba, idan da ciko na yadda ki cika mana idan babu yawa, idan kudin sunyi yawa ki rike canjin. Haka ake rayuwa, sai muma mu sami kwarin gwiwar cewa a kawo mana gobe. Aisha farida tace to yayana amma banji dadin kudin da zan dinga karba ba, adduarku manyanmu muke nema. Dr lukman yace kaji uwar iya magana, kin cika wayo kanwata. Baki tambaye ni laifin da abokina yake zarginki dashi ba. Kin fita kina kuka, na dauka kina shigowa abin da zaki fara tambaya ta kenan. Aisha farida tayi murmushi ta langabar da kai kasa tace bana son in cika tambayar manya, amma tambayar tana raina. Dr lukman yace uhmm aisha tsiri kenan, ko ba haka bane sunanki, don naji haka yahaya yake kiranki. Kina da hankali sabanin 'yan matan zamanin nan. Dr shuraim yace kina da hankali amma da zaki daina dane bayan acaba da sai kinfi hankali. Suka tuntsire da dariya su dukka. Dr lukman yace ai baya son yaga mutum akan acaba, musamman ma mace. Aisha farida tace a zuciyatya ni da acaba kuwa har abada, tunda yin haka zai jawo min samun kaunar wanda nake kauna. Kudin da dr lukman ya miko mata ne jimus dashi ya firgita ta, ta dafe kirji tace na meye wannan kudin? Karbi mana. Ya fada cikin tsawa a lokacin da yake zunguro mata kudin gabanta. Ta girgiza kai tace dr kudin yayi yawa fa. Yace nawa ne kike tunani? Naira dubu uke ne fa kawai, ba yawa don dai 'yan dari bibbiyu ne shiyasa kika gansu da yawa. Nifa bana son mu dinga irin wannan abun, ke fa ni yayanki ne. Bana son ina baki abu kina kin karba. Aisha farida tasa hannu biyu ta durkusa ta karba sannan tayi masa godiya tayi masa sallamaa ta tafi. Yau farin cikin da yake lullube a cikin zuciyarta Allah ne kadai Ya sani, saboda ta sami canji da yawa daga wajen masoyinta. Ba ta da wani buri wanda ya wuce ta ganta a wajen abida ta bata labarin abubuwan da suka faru tsakaninta da dr shuraim a yau. Ai kuwa tana isa gida ta iske abida a zaune ita da matan gida dankar suna hira, suna ta soya awarar siyarwa. Aisha farida ta kasa daurewa ta bari har sanda abida zata gama ta shiga daki sannan suyi hira don haka sai ta damko hannunta. Tace maman farouk zo muje ciki in baki sakonki daga shagamu. Abida na biye da aisha farida har cikin daki. Suna shiga aisha farida ta jefar da jaka. Tace Allah Shine Allah, Allah Shi ne mamallakin duniya da lahira, Shine mai yawan kyuta ba Ya gajiyawa. Tsarki da yabo sun tabbata ga Ubangijina, sarkin sarakuna. Bai haifa ba, ba a haife shi ba. Abida ta runguma aisha farida yayin da ita ma farin ciki ya lullube zuciyarta tun kafin taji abin alherin da ya sami aisha farida, ko ba a fada ba tasan akan dr shuraim ne. Tace alhmdl farida me ya faru? Dr shuraim ko? Aisha farida ta jawo hannun abida suka zauna ta jawo jakarta ta zaro kudin da dr lukman ya bata ta mika mata. Tace inji dr lukman suna son dambu da danwake gobe. Abida ta karba cike da murna, ta kirga ta daga ido ta dubi aisha farida ta harare ta. Tace na dauka dr shuraim ne ya baki kudin da kansa yace a yi masa? See Translation DUK KYAN TAKALMI 2* 10 Aisha farida tace antina kin cika gaggawa, karkade kunnenki kiji labari. Aisha farida ta zazzagewa abida labarin abin da ya faru yau a asibiti tsakaninta da dr shuraim babu dadi babu kari. Daga karshe ta zurawa abida ido. Tace kinji abin da ya faru, meye shawararki kuma meye abinyi nan gaba? Abida tayi dariya tace Ikon Allah kenan, farida kinga faidar addua ko? Kinga banbancin madanfaran bokaye ko? To duk abin da kike so ki nema a wajen Allah Shi kadai, kuma ki yarda Zai baki. Aisha farida ta gyada kai tace na yadda da haka na dade da yin imani da wannan. Abida tace a yanzu da Allah Ya sa shuraim ya sanki, yasan kina raye, yasan sunanki, yasan kina da amfani a wajensa, ya fara damuwa da rayuwarki, ya fara gane halayyarki, ya yabe ki da bakinsa. To anzo gangara, lokaci yayi da zan fada miki mataki na hudu da zaki taka. Aisha farida ta gyara zama ta dafe kirji da hannayenta biyu taja doguwar ajiyar zuciya tace Allah Ya sa zan iya. Abida tayi dariya ta dafa kafadar aisha farida tace kada ki damu, ba abu ne mai wuya ba, guda ukun na farko sun fishi wahala. Ai abin bi da bi ne, na daya yafi na biyu wahala, na biyu zai fi na uku wahala, na uku zai fi na hudu wahala, na biyar duk yafi su sauki. Har yanzu dai ajiyar zuciya aisha farida take yi, zuciyarta sai dukan uku uku takeyi don fargabar abin da abida zata fada, so take taji mai yiwuwa ne ko ba mai yiwuwa bane? Abida tayi shiru kamar mai tunani, can dagao ta kalli aisha farida tace idan na fada miki wannan mataki na hudu, ba wai ina nufin ki zubar da matakai uku na baya ba, a'a duk zaki hada kici gaba. Kici gaba da addua sosai ki ma kara wata akan ta da. Haka hakuri sai kin sake ci gaba sannan ki hada da na ukun ki rike mutuncinki sai na hudun da zan fada....saboda kaguwa aisha farida ta katse ta tace fadi na hudun wannene? Abida tayi murmushi ta gyada kai tace ki zamo mai yawan biyayya da ladabi a gare shi. Jikin aisha farida sai ya dauki rawa ta rike abida cike da rudani tace antina ban fahimce ki ba, ta yaya zanyi masa biyayya ni da ba ganina zai dinga yi ba, musamman ma mu da zamu bar asibiti? Abida ta mike ta dube aisha farida tayi murmushi tace haba farida bafa na son rikicewa, kina tsoron shuraim kamar wani malaikan da zai dauki ranki alhali TAKALMIN da zaki sura ne ki saka a kafarki. Ki dauki wannan ruguntsumin da ake ciki tamkar wasan 'yar tsana ne da yara suke yi, ki dauka tamkar wasan kwaikwayo ne don nishadi, ki dauka tamkar cartoon din tom and jerry ne da yara suke kallo a talabijin, sai ki daina fargaba. Ko kin manta DUK KYAN TAKALMI KAFA CE MAI TAKA SHI? Nace ki saka a ranki daurin dan kwalin da kike yi a kanki yafi wahala akan samun dr shuraim. Abu ne sassauka dalilina kuwa shine kince yana da ilimi, yana da wayewa, yana da tausayi uwa uba yana da riko addini, ma'ana tsoron Allah ne. To sai kibi duk hanyoyin nan da kika san yana so kiyi kane kane. Abin nufi ki zama mai amfani da iliminki duk abinda zakiyia agabansa, ki zama mai wayyayyen kai, idan yana wajen. Ki zama abar tausayi don ya tausaya miki, sannan ki nuna masa kinfi shi rikon addini, sai kiga hankalinsa ya karkato gare ki. Aisha farida ta dora hannu biyu aka tace anti kin sake rudani, don Allah yi min misalin yadda zanyi. Abida ta girgiza kai tace bazan fada miki yadda zakiyi ba, saboda ke mace ce, kuma nayi imani kowacce mace an haife ta da irin tata kissar a jikinta. Musamman ke aisha tun kina yarinya kin kware da iya zama da mutane da lafazai dadada. Haba kin manta zamanki a cikin tsofaffi ne? Kin manta halinki na kissa wanda ko zaginki akayi sai kiyi dariya ki ba wa mai zaginki hakuri? To shine wannan. Kije Allah Ya baki sa'a, sai mun hadu a mataki na biyar in kinci nasarar cinye wannan jarabawar. Abida ta juya zata fita, aisha farida ta lngwabe kai tace anti mataki na hudu yafi na daya dana biyu dana uku wahala. Abida tace hakuri yafi komai wahala, tunda kikayi hakuri zaki iya wannan. Idan baki gane biyayya ba, to bansan yadda kike so nace miki ba. To bari dai in baki misalain abin da nake nufi, ki durkusa har kasa ki gaishe dashi a duk inda kika ganshi, zaki fita daban daga cikin 'yan mata a idanuwansa, don 'yan matan yanzu basu da wannan tarbiyar. Ki rabu da hawan acaba tunda baya so, sauran kuma kinfini sani. Aisha farida tayi ajiyar zuciya tace sai yanzu na fahimce ki, godiya nake. Abida ta fice yayin da aisha farida ta daka tsalle ta rungume pillow gami da cewa waYyo shuraim dina. Da tazo kwanciya ta jima tana juyi, don tunanin shuraim yayi mata katutu a rai, ta rasa dalilin da yasa ta tsinci kanta tana cikin farin ciki yau. Ta kagu gari ya waye ta dauki dambu ta kai masa da alama hadin da sukayi wa dambun nan zaiyi dadi. Daga barci ya soma wartarta sai tayi firgigit ta bude ido ta jawo wayarta ta duba agogo tana gudun kada asuba ta shude su makara ba ta tashi ta dora dambu ba. Karfe uku saura ta mike taje tayi alwala tazo ta fara sallah. Rakaoi ba adadi, doguwar sujjada take yi tana zayyanowa Allah yadda take so ta kasance a cikin zuciyar shuraim. Karfe hudu da rabi ta fita ta fara kokarin dora dambu don ya turara sosai, bayan ta dora da jimawa sannan taji motsin fitowar abida daga daki. Abida ta shigo dakin ta dube ta tayi dariya. Tace kaji mai himma, wato kin daura dambun tun kafin assalatu tayi, koda yake aikin shuraim ne babu bata lokaci. Aisha farida tayi murmushi ba tare da ta bata amsa ba, saboda tana wuridi. Karfe 8 saura kwata a babur din a daidaita sahu ta yi wa aisha Farida ita da kwandunan abincinta har guda 2.ba ya ga kayataccen food flask guda 2 manya,daya a shake da hadadden dambu daya a shake da danwake sai farantunan tangaran 3 sai cokulla sai wasu robobi 3 yan kanana masu murfi daya yaji ne mai dadi gaske ya sha maggi daya man gyada zaryan aka soya da albasa sai kamshi yake dayar kuwa salad ne aka yanka shi kanana da tumatir da albasa da kokunba.ta isa ofishi kanta tsaye babu shajja ba tsoro,don ba ta ga motar gogan nata ba tasan bai iso ba don bai saba zuwa da wuri ba. Karfe 8 saura kwata a babur din a daidaita sahu ta yi wa aisha Farida ita da kwandunan abincinta har guda 2.ba ya ga kayataccen food flask guda 2 manya,daya a shake da hadadden dambu daya a shake da danwake sai farantunan tangaran 3 sai cokulla sai wasu robobi 3 yan kanana masu murfi daya yaji ne mai dadi gaske ya sha maggi daya man gyada zaryan aka soya da albasa sai kamshi yake dayar kuwa salad ne aka yanka shi kanana da tumatir da albasa da kokunba.ta isa ofishi kanta tsaye babu shajja ba tsoro,don ba ta ga motar gogan nata ba tasan bai iso ba don bai saba zuwa da wuri ba. Ta kwankwasa kofa sai ta murda ta tura kai dauke da kwandunan abinci riki-riki a hannunta ta yi sallama ta shiga sai ta ga wayam babu kowa a ofishin.babu tantama ko ya shiga bandaki ne don haka sai ta daiki gwandunan ta tura lungun da take ganin yana ajiyewa dan ta kawo masa.tana tsaye a gaban teburin tana jiran ya fiti amman shiru kuma abun da ya bata tsoro ba ta jin motsin komai a bandakin. Motsi ta ji an turo kofa da karfi yayin da ta waiwaya da sauri fuskarta cike da fara'a tana murna da ganin yayanta.tace a ranta ashe ba'a bandaki yake ba yana waje"sai dai kash da ta hada ido da mai shigowar ba fuskar Dr Lkman ta gani ba tayi matukar firgita gami da razana a bayyane wanda shi kansa wanda aka yi razanar dominsa ya gane. Kallonta yake yi a nutse har sai da ya shigo cikin ofishin ya mayar da kofar ya rufe ya fara tafiya a hankali zuwa gaban teburin kusa da inda take a tsaye. Numfashinta ne yake kokarin daukewa, idanuwanta kuwa sai suka kasa tsayawa a waje guda suka dauki farfari yayin da ta nemi yawun bakinta ta rasa, balle ta samu damar fitar da lafaxi guda daya. Ya dauke kansa daga kanta ya zagaya ya jawo kujera ya zauna yaci gaba da bincike wani file. Da taimakon addoui aisha farida taji numfashinta ya daidaita, ta sami nutsuwa a cikin zuciyarta. Ta dube shi cikin kunya hade da ladabi ta sunkuyar da kai kasa, sannan ta kaskantar da muryarta kasa ta zakaka makoshinta, ta duka har kasa ta gaishe shi. Dr shuraim ya daga ido ya dube kasa kasa da alama yaji dadin yadda ta gaishe shi, sai ya amsa cikin sakin fuska. Ya kara da cewa kina neman lukman ne ko? Ta gyada kai ba tare da ta iya hada ido dashi ba, tace eh. Ya dube ta da gefen ido yace ai bai karaso ba, sai anjima nine na bude ofishin. Aisha farida ta duka tace nagode. Sannan ta juya zata fita. Kamar a mafarki taji yayi mata magana. Babu abinda za'a ce masa? Ta juyo a nutse ta dube shi sannan tayi masa wani dandasheshen murmushi, wanda ta tabbatar an sha tabbatar mata idan tayi shi yana kara mata kyau. Siririyar wushiryarta ta bayyana yayin da kumatunta gefen dama ya lotsa, fararen hakoranta sai su sake haske. Tace dama sakonsa ne na kawo masa, gashi can na ajiye masa. Sai ta nuna lungun data ajiye kwandunan. Ya wurga dara dara idanuwansa ya kalli wajen sannan yaci gaba da dube duben file dinsa. Har yanzu aisha farida tana tsaye a jikin kofa ta rike kofa ita bata fita ba, ita bata dawo ciki ba. Ya dago da kai a hankali ya dube ta, yayin da ita kuma ta sunkuyar da kanta kasa a hankali. Yace okay zan fada masa. Tace kace masa kanwarsa ce aisha farida umar. Ya dago da kai ya dube ta da alama yaso yayi mata wata tambaya ya fasa, sai ya gyda kai yace idan nace masa kanwarsa mai hawan acaba ai ya sani. Sai ta ya danyi murmushi lokacin da yake karshen maganar. Ta langwabe kai ta marairaice ido kamar mai shirin fasa kuka. Tace yaya lukman ya fada min laifina jiya, nayi kuskure bazan sake ba, nima nayi tunanin naga ban kyauta ba. Sai ya kalle ta kawai ya ci gaba da rubutu, can yayi magana ba tare da ya sake dubanta ba. Yace hakan dai zaifi, ki yiwa kanki fada, don ke mace ce, a addinance ma bai dace ba. Dan wasu 'yan acaba ba su da hankali. Ta duka tayi masa godiya ta murda kofa ta fita. Ta jawo kofar a hankali ta tafi. Taji kamar ta fasa ihu, ko ta daka tsalle ta dire don murna. Ta shaki iska ta lumshe ido ta daga ido sama tayi wa Allah godiya gami da yiwa alkawarin zata yi ma Sa azumi gobe don godiya, da Ya fara karkato da hankalin dr shuraim kanta. ALLAH ABIN GODIYA!! BABI NA GOMA Nan da nan aisha farida ta ajiye aikin ta take yi ta jawo gyalenta da sauri ta biyo dan aike ta fito don taga mai sallama da ita da yammacin nan. Tana fitowa sai taga muazzam ne. Sai ta ji farin ciki ya rufe ta, tayi sauri ta durkusa har kasa ta gaishe shi, yayin da ta nemi izini a wajensa zata shiga ta dauko sallaya ta shimfida masa akan dakali. Sai ya dakatar da ita, yace ta bari kawai daman daga wajen aiki yake hanya ta bullo dashi tanan, shine yace bari ya karaso su gaisa. Aisha farida tayi murmushi ta lngawabar da kai tace sai in rasa harshen da zanyi amfani dashi wajen gode maka yayana. Allah Ya saka maka da alkhairi da wannan zumuncin da kake gudanwarwa a tsakanin mu, nagode. Ai na sayi waya da wannan kudin da ka bani, ashe ban karbi lambarka ba, na rasa inda zan nemo ka, dole na hakura. Na kagu inji halin da kake ciki, kai da janan. Muazzam ya lumshe ido yace alhamduliilahi kanwata, naga falalar addua da hakuri, kuma na rike mutuncina yadda kika ce. Naje mata da siyayya iri iri na kaimata, ko kallona takiyi. Sai na sami waje na zauna nace mata janan ina so ki saurari bayanina kiji dalilin zuwana wajenki yanzu. Ada na soki ba kya sona, a yanzu naso ki bakya sona, don haka na hakura ba a dole a soyayya. Allah Ya sauya min da wacce take sona har ma an saka mana ranar aure. Kiyi hakuri da takura miki dana yi a da. Ina so a yanzu ki saki jikinki dani, ki dauke ni a matsayin yayanki, kuma lauyanki bayan nan babu wata alaka tsakanina dake. Ina gama fada naga alamaun jikinta yayi sanyi. Kullum naje sai inga tana yawan kallona tana kuma bude baki tayi min magana, duk tambayar da nayi mata. har na hada baki da wata matar yayan, sai tayi ta kirana a waya a dai dai lokacin da nake tare da jana, sai na dinga amsawa kamar da budurwata nake magana. Sai inga fuskarta kamar bata jin dadi. Aisha farida ta cika da mamaki tace duk a kurkukun ake wannan? Barr muazzam yace eh ai ana bari na in shiga sai a kirawota a hado ta da maikaciyar kurkukuk daya,ta kawo ta inyi mata tambayoyi saboda neman hujjojin da zan bayar da kuma nemo shaidu a kotu. Aisha farida tace lallai ni abin da na lura janan tanan sonka, tsabar jan aji take yi maka don ta tabbatar kana sonta, kuma baka fushi duk wulakancin da zatayi maka. Muazzam yace haka ne wallahi, sai yanzu na yadda da haka. Ai nuna mata nake bata gabana kwata kwata yanzu. Baraka ma ta samu sauyi na fada mata duk yadda zatayi, kuma ta aiwatar tana addua kuma tana hakuri, sannan kuma tana jan ajinta tana yi masa girki, ta tsaftace gida, ammma ta fita harkarsa bata bari ma su hadu a gidan, kwana biyu ko uku tana gidan bata bari ya ganta. Sai gashi yana fada min wai baraka ta sauya halinta yanzu ta daina damuwa dashi, in bashi ya leka dakinta ba, ita ba ta fitowa. Sai na kalle shi na watsar nace au har dakinta kake takawa ita da kake korarta da idan ta shiga dakinka? Sai yace ai dole in leka inga halin datake ciki, kar inje ta shiga daki ta kashe kanta ko ta hadiyi zuciya ta mutu. Nace masa ashe kasan kana kuntata mata har zata iya hadiyar zuciya ta mutu ko? To kaji tsorn Allah. Sai yayi shiru bai ce komai ba. Itama barakar take cemin wallahi ya fara sauyawa, yanzu da kansa yake dawowa gida yaci abinci, dga lokacin cin abinci yayi, da kuwa har kifarwa yake yi a gabanta idan ta matsa masa yaci. Aisha farida tayi dariya tace alhamdulillahi, Allah Ya kara yi mana jagoranci. Barr muazzam ya dube ta yace ni naga duk kin rame, lafiya kuwa? Ko dai shuraim din ne ya taba min ke? Aisha farida ta girgiza kai tace babu ruwansa bawan Allah, wlhi antina ce abida bata da lafiya sosai, gabobinta gaba daya tun daga kafa har wuyanta duk inda mahadar kashi take ta kumbura suntum, tana yi mata ciwo, da kyar take tafiya. Shien muke ta sunturi asibitin kashi na dala (autopeadic). Anyi xray da gwaje gwaje sunce basu ga komai ba, ciwo kima sai karuwa yake. Yanzu da kyar take iya takawa komai sai anyi mata. Shiyasa kaga duk na susuce. Subhanallah, Allah Ya bata lafiya. Inji barr muazzam. Aisha farida tace amin ai munyi sati biyu da barin asibiti, rabona da dr shuraim kenan amma akwai cigaba sosai. Ta zayyanowa barr muazzam labarin abubuwan da suka faru tsakaninta da dr shuraim da kuma mataki na hudu da abida ta karanto mata. Barr muazzam ya dubi aisha farida cike da rashin fahimta yace to ni kamar ni ta yaya zan yi mata biyayya? Kuma kamar baraka wacce tayi biyayyar a baya bata ci riba ba, sai da ta share shi ta fara samun saukin wulakancin? Aisha farida tace ai a ganina duk daya ne mu ukun. Yanzu kamar baraka taci gaba dayi masa haka har lokacin da zai karkato sosai, yana son zaman nata sai ta dawo tayi masa biyayya sosai, tayi duk abin da yake so, ta bar abinda baya so, ta nan zai fara mantawa da nafisa. Ko kuma zai fara kokonto ko ya rike matarsa ne, ya rabu da waccan don na tabbata ba zatayi masa biyayyar da baraka take yi masa ba. Saboda wadannan dalilan nawa na farko kace babba ce har ta dade da gama jam'ia. Na biyu tasan yana sonta don haka zatayi ta jansa a kasa kasan halin mata. Barr muazzam ya gyada kai yace lallai kanwata na yadda da tunaninki, kamar kina zaune a wajen duk yadda kika fada haka ne. Aisha farida tayi dariya tace kai kuma a bangarenka kaci gaba da nuna mata ka sami wata bata gabanka yanzu. Kada ka bari alakarku ta rabe, ku cigaba da yawan haduwa ko bayan ta dawo gidan a matsayin abokinta zaka ga ta dawo. Kada ka fada mata da wasa kake da wuri, kayi ta kyautata mata, kanayi mata duk lallashi da tarairaya. Kayi ta yin duk abin da kasan tana so, ka kiyaye wanda ba taso tabbas zataji kai kafi dacewa da rayuwarta, ko bata zo tace tana sonka ba, zata nuna alamu. Barr ya gyada kai yayi murmushi yace gaskiya ne wannan kinyi hikima, Allah Ya sa mu dace. Bani lambarki don muci gaba da tattaunawa a waya. Ya zaro wayarsa daga aljihun, aisha farida tana karanto masa lambar yana rubutawa har suka cika. Sannan ya kira lambar ta shiga, amma wayar tana gida. Aisha farida tace idan na shiga ciki zanyi saving. Barr muazzam ya zaro kudi daga aljihu, naira dubu biyu ne 'yan dubu dubu guda biyu, ya mika mata nan fa ake tataburzar, don aisha farida ta tubure ba zata karba ba, shi kumwa yace sai ta karba. Ko zubarwa zatayi sai dai ta zubar. Sai da ta ga ya dage sosai har ransa zai baci sannan ta durkusa ta karba, tayi masa godiya suka yi sallama ya tafi, tashiga gida cike da farin ciki kamar kuwa yasan suna cikin tashin hankalin rashin kudi, asibiti duk ya cinye musu kudin. Cefane ma sai harhade harhade ake yi, a dafa a ci ba dadi don kar a mutu. Ciwon abida kamar da wasa, abu ya fara tsananta hankalin kowa ya fara tashi, don har hussaini yayi waya ya sanarwa da iyayenta da 'yanuwansu na shagamu. Babban likitoci yanzu take gani a asibitin kashi, don ciwon ya wuce kananan likitoci. Magani take dirka amma fa a banza, ko alamun canji bata ji a jikinta. Daga nan sai suka rabu da zuwa asibitin kashin ma, suka dawo gida aka fara na hausa, wannan yace sanyin kashi ne, waccan tace mayu ne. Kowanne magani hussaini yaji sai ya karbo ya kawo, burinsa matarsa ta sami lafiya. Abinka da mai ilimi aisha farida bata son wannan gwafje gwafejen magungunan gargajiyar ko hussaini ya kawo ya bata, sai ta boye bata bari tasha. Gara ma na shafawa a gabobi tana shafa mata kamar na sanyin kashi da aka karbo musu a wajen sarkin ruwa na wudil. Maganin sanyi kashi ne da man shanu ake kwabawa a shafa a gababin. Sai man tafarnuwa dashi ma akace ta dinga shafa mata a gabobi shima tana shafa mata kullum da daddare kafin su kwanta. DUK KYAN TAKALMI 2* 11 Babu abinda abida ke iya yi, sai anyi mata tana kwance kawai. Amma tana magana radau kuma idan an bata abinci tana ci sosai. Sai tsananin sanyin da take ji, sai tayi ta makerketa duk da bargunan da aka lufga mata, kuma a lokacin zafi ne. Ba asiha farida da hussaini da 'ya'yan abida ba kadai, duk wani mahalukin da yake da dison imani a cuciyarsa hankalinsa sai ya tashi idan yaga ciwon nan kuma ya tausaya mata. 'Yan dubiya basa karewa layi layi mata suna shiga, wasu na fitowa. Sai yanzu 'yan gida da 'yan unguwa suke zayyano kyawawan halayen abida. Idan akace yau asabar da lahadi ce lokacin yaya hussaini yana gida baije aiki ba, to mazan unguwa da abokan aikinsa sai suyi ta tururuwar zuwa dubiya. Kuma yawanci basa zuwa hannunsu haka , suna riko kayan dubiya kamar ayaba da lemo, ko kayan shayi, wasu kuma sai su ba da dan kudi suce a sayi magani. Aisha farida ta labe tayi kuka har ta gaji, addua take Allah Ya tashi kafadun abida uwarta, ubanta, yayarta kuma kawarta, sannan aminiyarta mai bata shawara. Aisha farida ta tari yaya hussaini a bakin kofar dakinsa ya shirya ya fito zaije aiki. Bayan ta gaishe shi ta shawarce shi tana son ta kai abida asibitin malam aminu kano a duba to ko Allah zai sa a dace. Hussaini yayi shiru can yace kina ganin aje asibitin nan alhali na tabbatar ba ciwon asibiti bane, tunda ga kasusuwan sun kumvura suna ciwo, amma likitocin kashi sunce basu ga komai ba. Aisha farida tace ina ga ai ba bangarensy bane, wata kila ciwon ba a jikin kashi yake ba, gara in kai ta tunda can akwai likitoci manya manya zasu gano ciown. Hussaini yace kinga abin da yasa nace bana asibiti bane, idan tana bacci sai tayi ta zabura har sai na rirrike ta cikin dare. Aisha farida tace haka ne yaya, ai asibitin ma suna da maganin razana da zabura. Ya lalubo kudi ya bata yace suje, Allah Ya sa adace. Aisha farida ta harhada 'yan kudaaden da take adanwa na masu dubiya, misbahi ma dubu daya ya bata, haka wani yayansu da yazo daga shagamu shima dubu daya ya bata, taje ta hado cefanen dambu ta shirya wa rabin ranta dr shuraim. Bayan ta yi wanka ta fesa kwalliya da wata doguwar rigarta bakai mai dankwali (abaya). Sai ta shirya abida aka kirawo musu mai adaidaita sahu yazo har kofar gida. Sai da matan gidan suka taimaka mata aka rirriko abida aka saka ta ciki domin duk gabar da aka rike mata ciwo takeyi mata. Sai ta dau kuka kamar wacce ake balla mata kashinta don azaba. Aisha farida rike da kwandon abincinta ta shiga adaidaita sahi suka tafi. Ta dubi abida ta zubo da hawaye don tausayi tace wannan dambun ne nayi wa su dr shuraim in kai musu ko in kyale su? Abida tayi murmushin karfin hali ta cije baki saboda tsananin ciwo ta gyada kai tace ki kai masa. Mai adaidaita sahu ya kai su har bakin GOPD kafin su sauka, sai aisha farida ta shiga ciki da sauri tayi magana da maikatan suka bata kujerar tura marar lafiya. Lebura daya ta dauko kujerar ta biyo ta da ita. Nan ma sai da aka agazawa aisha farida sannan aka dora abida akan kujerar saboda tsabar ragargazar da kashinta ke yi har kara zaka ji yana yi bas! Bas! Idan ta motsa. Aka turata aka shiga dasu wajen bude file kasancewar duk ta sanu ba ta bi dandazon layi ba aka bude musu, nan da nan aka mika musu file din dakin likita. Nan ne fa za asha jira sabida likitoci basu karaso ba, don haka dole a sha jira akan bencina. Aisha farida ta dubi abida wacce har yanzu take kan wheel chair tace inje ofishin dr lukman in dawo, zaki iya zama ke kadai? Abida tayi murmushi tace kije a tsanake ki gama abinda kike yi, kada ki damu don kin barni, ni kadai zan zauna a cikin kabarina. Ni kadai zan zauna babu mai tayani zama, saini sai halina. Sai aisha farida ta runtse ido yayin da kuka ya kcece mata, ta kasa magana saboda jama'ar dake kallonsu. Cikin sanyin jiki ta dauki kwandon abincin ta tagi. Hawaye yake ya tsaya har ta kusa isa ofishin dr lukman don haka ta sami lungu ta labe tayi kuka har ya isheta, ta goge hawayen ta fito. Amma kuwa kallo daya zakayi mata kasan kuka ta sha, don idanuwan sunyi luhu luhu. A sanyaye take tafiya cikin nutsuwa ta kwankwasa kofar ofishin dr lukman ta shiga. Bata iske shi ba, sai wasu daliban likitocu guda biyu ta samu suna zazzaune suna jiransa. Bayan sun gaisa sai ta tura kwandon abincin a lungun da saba ajiyewa, sannan ta tambaye su inda ya tafi. Suka tabbatar mata yace su jira shi yanzu zai dawo, ba zai dade ba. Sai ta sami kujera ta zauna tana zama sai taji an bude kofa, yayin da gaba daya hankalinsu ya tafi wajen kofa. Dr lukman ne a gaba, dr shuraim ba biye dashi. Kowannensu da laptop dinsa a rataye a kafadarsa. Idanuwan dr shuraim akan aisha farida ya fara dira, yayin da ya jima yana kallonta sannan ya dauke idonsa. Ita kuma murmushi kawai takeyi tana mai sunkuyar da kai tana jin kunya. Dr lukman ya dube ta yayi dariya yace 'yar shagamu daga ina kika diro? Na dauka ai da aka gama karatu sai kika hada 'yan komatsanki kika koma shagamu. Tayi dariya tace ina nan yyayana, kai ka share ni ai ba ka nemana gashi kuwa na taso takanas na zo in gaishe ku. Dr lukman yayi dariya yace kin kyauta 'yar shagamu, ni daman nasan kinfi ni kirki, to bari inje in sallami daliban dana zaunar tun dazu suna jirana. Ya juya ya dube su yace to ku taso muje lab din in nuna muku. Suka bi shi a baya suka fice, sai ita sai gogan nata dr shuraim kadai aka bari a ofishin. Yana zaune akan kujera ya bude laptop dinsa yana dube dube. Ta dubi zankadediyar fuskarsa sai taji zuciyarta ta hau dukan uku uku saboda tsananin kyawun dataga ya kara yi. Ta fara tambayar kanta da kanta “anya kuwa mutumin nan bai fi karfina ba? Anya kuwa zan kai labari a tafiyar nan? Anya kuwa hakata zata cimma ruwa”? Sai bayanan abida ya fado mata cewar babu abinda ya gagari Ubangiji, samun dr shuraim ba wani abin wahala bane idan har ta rike matakan nan guda biyar. Ta silmiyo daga kan kujera ta gaishe shi cikin wata kintsatsiyar murya bata mike daga durkuson ba har sai da ya amsa mata, sannan ta koma ta zauna. Tayi shiru kanta a sunkuye a kasa, sai dai su biyu suna hada ido in dai ta dago zata kalle shi, sai taga shima ya dago ido ya dube ta. Sunyi mintuna biyar cur babu wanda ya sake magana a cikinsu. Sai taji muryarsa kamar a mafarki ya ambaci sunanta. Yace aisha farida, 'yar shagamu, 'yar acaba. Wanne ne sunanki a cikin su. Sai ta dago ta dube shi tayi masa lallausan murmushi ta sunkuyar da kai ta sosa goshi alamar kunya. Tace sunana aisha farida umar shagamu. Yayi wani dan siririn murmushi yace kin amsa sunayen uku daya kika cire, mai yasa? Ta girgiza kai tace ai na daina hawan acaba yanzu. Yayi murmushi yaci gaba da daddanna laptop dinsa. Yace kinsan sunan wa kike dashi? Sunan mamana ne aisha, haka farida sunan kanwata ce wacce take bina. Ya akayi kike amfani da sunaye biyu? Aisha farida tayi murmushi tace mai suna aisha ai farida ce duk daya ne. Yace okay kenan ummata da farida sunansu daya ni ban ma taba ji ba. Aisha farida tayi murmushi tace haka ne, ai ba kowa ne ya sani ba. Ya dube ta da wutisyar ido yace baki da lafiya ne? Ta dago ido da sauri ta dube shi cike da mamaki ta girgiza kai tace lafiyata kalau. Ya girgiza kai yace shikenan, naga kinyi kama da marar lafiya ne, ko kuka kikayi ne? Wannan tambayar tasa ta sake bata matukar mamaki, sai taji kamar a mafarki. Tayi shiru har zuwa dan lokaci sannan tace eh. Ya dago ido da sauri ya dube ta sai ya cika da mamaki yayin da ya maimaita amsar da ta bashi eh??! Yaci gaba da duban laptop dinsa ya ma rasa tambayar da zaiyi mata. Ta sharbe hawaye tace yayata ce bata da lafiya sosai, har bata iya tafiya ita na kawo asibiti. Yayi shiru na wani dan lokaci sannan ya nisa ya ce me yake damunta? Aisha farida ta zubo da hawaye mai dumbin yawa tace an kasa gano ciwon. Dr shuraim ya girgiza kai yace a'a bakuje inda za'a gano muku ciwon ba dai, har akwai ciwon da ba a ganewa, ko wanda bashi da magani? Aisha farida ta matse hawaye da hannunta ta dagi da jajayen idanuwanta ta dube shi, ta girgiza kai. Tace asibitin kashi na dala muka yi ta zuwa suna bata magani, amma bata jin sauki. Sai ma gaba yake. Shine yau na kawo tana, tana GOPD a layi, likitocin ne basu karaso ba. Ya tambaya cike da kulawa yaya take jin ciwon? Aisha farida ta kwatanta masa duk yadda ciwon ya fara har izuwa yanzu. Sai yayi shiru can yace ciwon yayarki rheumathoi athritis ne ko systemic lypus erythramatosis. Aisha farida ta kalle shi cike da rashin fahimta tace na'am? Ya girgiza kai yace kada ki damu likitocin da zasu duba ta yanzu zasu hada da likitan da ya dace. Allah Ya bata lafiya. Aisha farida tace amin nagode. Sai ta mike a nutse ta duka tace zan tafi saboda kada likitocin suzo a kira mu bata iya tafiya, nice zan shiga da ita. Ya gyada kai yace okay, Allah Ya ba da sauki. Ta fice cike da farin ciki, tana fita ta dafe kirji tana ambaton Allah na gode ma Ka, Allah Ka sake cika min burina akan shuraim. Tana tafe tana fara'a tamkar an biya mata kujerar makka. Sauri take ta karsa wajen abida ta bata labari, amma da ta tuna abida babu lafiya sai jikinta yayi sanyi musamman data je ta iske abida ta galabaita a inda take zaune, ta gaji da zaman duk jikinta ciwo yaje. Hawaye kawai ke fitowa daga idanuwanta. Ita kadai tasan me takeji, sai dai duk wanda ya dube ta yasan tana jin jiki saboda gaba daya gabobinta a kumbure suke. Aisha farida ta rike ta, ta gyara mata zamanta tana mai lallashinta tayi hakuri likita yazo. Suna zaune shiru aisha farida na ta sake maimaito hirar da suka yi da rabin ranta, sai tayi murmushin jin dadi ta waiwayo da sauri ta dubi abida tana shirin ta bata labarin dr shuraim sai taga mawuyacin halin data ke ciki, sai taji hawaye ya cika mata ido. BABI NA GOMA SHA DAYA Aisha farida tayi kuka, har ta godewa Allah a wannan rana ta asabar saboda jikin abida ya matsa, babban yayanta yaya lurwanu yazo da mota har kofar gida, yace a bashi ita ya tafi da ita shagamu ayi maganin hausa. Yaya hussaini ya zama bashi da zabi kasancewar shima yana ganin ciown bai yi masa kama da na asibiti ba, don sunyi ta yin na asibitin babu alamar jin sauuki, kullum ciow kamar kara shi ake yi. Aisha farida ta dage wajen yi musu bayani, sunki su fahimce ta, suna ganin don ita 'yar boko ce kuma malamar asibiti shiyasa take son a dauwama da na asibiti don likitoci ba sa kaunar a hada maganinsu dana gida. Sunfi karfinta, tana ji tana gani yaya hussaini da yaya lurwanu suka ciccibi abida tamkar 'yar jaririya da kayanta aka saka ta a mota. Yaya lurwanu ke tukawa, yaya hussaini yana zaune a gefensa, yayin da ita kuma aka kwantar da ita a bayan mota. Aisha farida ta mika hannu ta tagar motar ta rike kumburarrun yatsun abida a hankali yayin da hawaye ya surnano daga idanuwansu su duka. Aisha farida tace Allah Ya baki lafiya. Abida ta girgiza kai tace ba zan dawo ba farida, ki kula da 'ya'ya na, kada ki manta abu uku dana fada miki. Ki zama mai yawan addua, mai tsananin hakuri mai yawan kama mutuncinki. Biyun kuwa ba yanzu zan fada miki ba sai nan gaba idan ban mutu ba. Yaya hussaini ya juyo da sauri yana kallonsu ba tare da ya fahimci abin da suke ba, shi da lurwan suka cika da mamakin jin kalaman da marar lafiya ta ke furtawa. Hussaini ya tambayi aisha farida meye hakan kuma yake nufi? Zance me kuke yi? Aisha farida ta goge hawaye tace a'a sako take bani. Yace sakon me kuma naji ana maganar soyayya? Ki koma gida ki kula da yara, gasu can suna ta kuka, nima gobe zandawo na bar miki dari biyar a daki akan katifa. Idan anyi wa yara hutun makaranta sai mu dunguma mu tafi shagamu, ni ina jin ma gara ku kaura can kacokan, ni zan dinga zuwa ina dawowa, gara mu hakura da zaman kanon ma. Kirjin aisha farida ya buga bamm! Don fargabar tana tunanin yaDda zata rabu da rabin ranta dr shuraim. Ta zame hannunta a hankali daga hannun abida, sai abida ta dago ido ta dube ta, tayi mata murmushi. Tace Allah Ya baki nasara akan abin da kike nema. Kuka yaci karfin aisha farida, ta rushe da kuka. Tace Allah ya tashi kafadunki anti abida. Nan da nan yaya lurwanu yaja mota ya tafi, saboda suma sun fara jin hawaye yana zubo musu don tausayi. Idanuwan yaya hussaini ya cika fal da kwallah. Aisha farida ta kame a inda take tsaye tana kallon motar har sai da suka kure sannan ta juyo gida. A hanya jama'ar unguwa sai sannu suke yi mata, da kuma fatan Allah Ya ba wa abida lafiya. Kowa ya tausaya wa aisha farida ganin kukan da take sharba, idanuwanta sunyi jajawur. Ita kanta tana so kukan ya tsaya, amma yaki saboda tsananin kunar da take ji a ranta. Ta kama hannun 'ya'yan abida su hudun dukka maza, faruk, sa'ad, muhd, da ishak idan taja hannun wannan sai wannan ya arce da kuka. Da kyar matan gida suka taya ta da kamo su ana lallashi da alewa da biskit. Da kyar suka zazzauna a daki suka daina kukan. Aisha farida ma tazo ta zauna a gabansu tana kallonsu, ba tare da ta iya musu magana ba. Abin duniya ya ishe ta, ta rasa abin da yake yi mata dadi. Ji take tamkar zuciyarta zata fashe. Tana ambaton Allah kar ka kashe abida, ina son abida a rayuwata. Wayarta ce tayi kara, ta mika hannu a sanyaye ta dauka, ta duba wata lamba ce bakuwa babu suna, sai dai lambar ta musamman ce, saboda kusan lambobin duk iri daya ne. Tayi ta kallon lambar amma batayi mamakin wanda ke kira ba, domin 'yan ajinsu da dama suna karbar lambarta su kira ta maza da mata. Saboda bata cikin hayyacinta , don haka bata son yin magana har wayar ta katse ba ta amsa ba. Can ta mike ta fito tsakar gida ta jawo risho ta dora ruwan zafi a karamar tukunya, ba tare da ta san abin da zata dafa ba. Ta dubi babban dan abida faruk tayi murmushin karfin hali tace yaya me zamu dafa yau? Maganar ma shi ma dakyar yake yi, sai ya langwabar da kai yace wake da shinkafa. Ta dubi sa'ad mai binsa tace kai fa dan lelena mai zan dafa muku? Shima yace wake da shinkafa. Sai ishak yace shinkafa da miya. Mohd yace a'a tuwon shinkafa da miyar taushe. Aisha farida tayi dariya tace a'a su yaya sun fiku gaskiya, ku rage min aiki tunda muna da yaji mai dadi da daddare sai inyi mana tuwo. Tana zaune a dokin kofa tana tsice wake sai wayarta ta dau ruri. Nan da nan yara suka hau tseren dauko waya, ana dambe dai kamar za a yar da wayarta samu ta karba. Taba dubawa taga lambar dazu ce, sai ta tabbatar ko waye wannan mai kiran wayar tana da muhimmanci tunda ya sake kira, don haka nan da nan ta danna. Cikin nutsuwa tayi sallama, taci gaba da sauraron mai wayar, mace ko namiji? Muryar namiji taji ya amsa da wa alaikumul salam. Tayi kasake tana sauraon abinda zai fada mata, har yanzu bata gane muryar ba. Amma daga dukkan alamu ta taba jin kamilalliyar muryar. Ya tambaya don Allah ina magana da aisha umar ne? Ta amsa da eh aisha ce. Yayi gyaran murya kadan yayi murmushi yace farida kina magana da dr shuraim imarn ne, daga nan asibitin aminu kano. Tsarki ya tabbata ga Ubangijin talikai. Kalmar da aisha farida ta fada kenan a cikin zuciyarta, yayin da ta sulale ta durkusa gwiwoyi guda biyu a kasa don mamaki da kidimewa. Ta rasa kalma daya da zata furta, sai gumi take jikinta yana bari, ta rasa inda take. Shin mafarki ne, ko kuma idonta biyu? Ya ambaci sunata har sau biyu. Farida! Farida!! Tayi doguwar ajiyar zuciya, ta lumshe ido ta amsa cike da ladabi, cikin sassanyar murya na'am. Yace kina mamaki ne? Kada kiyi mamaki. Na sami lambarki ne daga wajen dr lukman jiya aiki ya hana in kira ki, sai yau da yake weekend ne, ina gida. Ta mike ta shige dakin abida ta turo kofa ta datse saboda hayaniyar yara, ta sami lungu ta shige ta takure kai kace sanyi take ji. Ta gaishe shi cikin nutsuwa. Ya amsa cike da fara'a ya tambayeta ya mai jiki? Cikin sanyi jika tace da sauki. Yace yaya maganin da take sha, tana samun sauki? Tayi jim kadan tace tana sha dai, amma ciwon kamar gaba yake tayi. Yace subhanallah, to yanzu abinda za a yi, ranar litinin ki kawo ta wajen zan hada ta da likitan da ya kamata ta gani, wato rheumatologists. Ba damuwa idan nayi masa magana zai duba ta ko babu appointment. Hawaye ya surnano daga idanuwan farida, ta marairaice murya tace ai bata nan, anzo daga gida an dauke ta, wai na hausa zaayi. Babu yadda banyi ba su kyale ta muci gaba dana asibiti suka ki....... Bata rufe bakinta ba sai ta rushe da kuka cikin wata irin sautin murya mai ban tausayi. Dr shuraim ya zabura yace subhanallahi, wannan suna so su jawo mata ciwon koda, daman ciwon yana da alaka da ciwon koda. Kada su sake su bata sassake sassake ta sha, don akwai mummunan hatsari wajen shan jike jike. Kuka kawai farida ta keyi, ba tare da ta iya magana ba. Yayi ajiyar zuciya ya ambaci sunata cikin wata lallausar murya. Yace farida kuka kike yi? Daman ke haka kike sarkin kuka ce? Na hadu dake fiye da sau hudu kullum kina kuka, meya damuwarki? Ta girgiza kai ta goge hawaye tace babu abinda ban fada musu ba, babu irin maganar da banyi ba akan su kyale ta, suka ki. Mijinta ma tun ba ya yadda yanzu har ya yadda. Yanzu ko nay waya shagamu nayi bayani kada su bata maganin hausa ba zasu saurare ni ba. Shine nake jin tsoro kada su jawo mata ciwon koda.... Ta sake barke wa da wani kukan DUK KYAN TAKALMI 2* 12 Ya sake jan doguwar ajiyar zuciya yace kada ki damu, mu dukka muslmaii ne, mun yadda da Allah Shi ne mai warkarwa, ba magani ba. Muyi addua Allah Ya bata lafiya, Allah Ya tsare duk wani tsautsayi. Ya ya kike da ita marar lafiyar ne, mamarki ce? Aisha farida ta marairaice murya tace anti abida yayata ce, kakanninmu daya, kuma tana auren yayana da muke uba daya, itace marikiyata tun ina karama, itace tamkar uwata, ubana, yayata, kuma aminiyata mai bani shawara akan duk lamurana. Sai yayi murmushi ya lumshe ido yace amma kin iya kwatance yadda mutum zai gamsu. Ko kon taba bata labarin wani dr lukman da abokinsa dr shuraim da suke cinye miki dambu da danwake? Aisha farida ta kwashe da dariya tace a'a baka bani izinin na sanar mata ba. Yayi dariya yace nasan kin fada mata. Ta sake tuntsirewa da dariya tace sai dai yanzu na fada mata. Yayi dariya yace to Allah Ya sauwake Ya bata lafiya sai anjima. Aisha farida tace nagde Allah ya saka maka da alkhairin, sai anjima. Ya kashe wayar yana lumshe ido saboda jin dadin muryarta. Har yanzu aisha farida sankare take a lungu ta kasa sauke wayar daga jikin kunnenta. Ji take tamkar mafarki take yi, yayinda farinciki marar misaltuwa suka cika zuciyarta, ta cika da mamaki marar adadi, sai ta tuna da bayanan ABida da tace babu abin da ya gagari Ubangiji. Idan bawa ya roke Shi, yana amsa ma sa duk sanda Ya so. Ta ajiye hannunta a hankali daga jikin kunnenta ta dafe kirji taji sassanyayiyar bugun da zuciyarta take yi. Ta daga hannu sama tayi wa Allah godiya sai ta malale ta kwanta akan katofa tamkar ruwa. Ta jawo wayar da sauri ta duba lambar, ta kayatu ita kanta lambar abar kallo ce, sai ta sumbaci wayar. Ta dannan lambar ta kira, bugu daya ta shiga ta fara ruri, sai taga an kashe. Hankalinta yayi mummunan tashi, nan danan ta zabura ta tashi zaune ta dafe kirji, yayin da farin ciki datake yi ya koma ciki. Ta fada a bayyane innalillahi wainna ilaihir rajiun! Me ya kaini sake kiransa, gashi ya katse? Shikenan zai tsane ni. Ta na zaune ta hada kai da gwiwa tana tunani sai taji wayarta tayi ruri. Nan da nan ta zabura ta dauka ta duba, sai taga lambar dr shiraim ce, tay sauri ta dannan gami da yin sallama cikin nutsuwa. Ya amsa mata gami da cewa naga kin kira ko? Ta lumshe ido tace eh daman zan tambaye ka ne, ranar litinnin dambun zan kowa muku ko danwake? Ya girgiza kai tamkar yana gabanta yayi murmushi yace a'a babu, ba sai kin kawo mana komai ba, mungode. Ta marairaice tace haba doctor meyasa, ni ina so na kawo muku. Yace a'a ki bari sai wani lokaci, idan muna bukata zamu fada muki. Yanzu na kira ne naji halin da marar lafiya ke ciki, don na damu nasan ciwon nan yana da tsananin zafi, sannan na damu da yadda naga kinta ta koke koke na kora najji halin da kuke ciki. Tayi murmushi tace nagoda ka kyauta, nayi farin ciki da jin kiranka. Ko zan iya saving din lambarka don mu dinga gaiswa. Yace ba damuwa, zaki iya. Tayi godiya, shima yayi mata godiya, suka kashe waayar. Tayi tsalle akan katifa ta dire don murna. Ta dubi gabas da yamma, kasa da sama tana tunanin wanda zata ba wa wannan kyakyawan labari. Ta tuno abida, taji yau dama abida na nan ta fada mata yadda sukayi da dr shuraim. Taji hawaye ya cika mata ido, ta fada a bayyane. Allah sarki anti abida, Allah ya baki lafiya. Tana rufe bakinta faruk ya shigo dakin da gudu ya ce anty aisha ruwan da kika dora a wuta yana ta tafasa tun dazu, har ya kusa ya kone. Ta zabura da gudu ta fito don ita har ta manta da shi, tabbas yaro yayi gaskiya , ruwa dai ya gaji da tafasa har ya kusa konewa. Sai da ta kara wani yayi zafi sannan ta zuba wake da shinkafa suka dahu. Ta ba wa yara suka ci, yayin da farin ciki ya kosar da ita, ta kasa ci, yunwar ma bata ji. Bayan tayi sallahr azahar sai ta dinga jero nafilfili ba adadi, duk ta godiya ce ga Allah da ya kawo mata dr shuraim. A cikin satin nan haka take yini cike da farin ciki, saboda ta sami dr shuraim, sai dai matsala daya ce take addabarta a rayuwa, idan ta tuno rashin lafiyar abida sai taji jikinta yayi sanyi lakwas. Koda yaushe sai ta saka lambar dr shuraim a gaba tayi ta kallo, sai taji kamar ta kira shi ko ta tura masa sako, sai kuma ta fasa. Amma ranar juma'a ta tura masa sakon adduoin juma'a amma bai bata amsa ba. Ta fara shiga damuwa, amma sai tayi masa uzuri , watakila bai cika karanta sakonni ba kasancewar aiki yayi masa yawa. Ranar litinin da misalin karfe goma da rabi na safe aisha farida na kwance akan tabarmarta tayi shiru tana tunani, rashin lafiyra abida tana damunta matuka, musamman yanzu da tayi waya shagamu tayi tayi su ba wa abida waya suyi magana, aka ce bacci take yi. Sai take ganin kamar jikin ne yayi tsanani suke boye mata. Tana so ta tashi ta dora abincin rana, domin yara sun kusa dawowa daga makaranta, amma ta kasa tashi saboda damuwar da tayi mata yawa a zuciya. Wayarta tayi ruru tayi sauri ta dauka ta duba, sunan yaya hussaini ta gani, sai tayi matukar mmaamki da ganin kiransa, don bai dade da fita aiki ba ya bata kudin cefane. To me yasa ya kira? Ko mantuwa yayi ne a gidan? Take tambayar kanta da kanta. Tayi sauri ta dannan gami dayi masa sallama cike da tsananin fargaba, tayi shiru tana sauraron abin da zai fada mata. Yayi gyaran murya yace yaya kuke? Gidan duk lafiya? Yara basu dawo daga makaranta ba ko? Sai tace eh basu dawo ba. Ina gida kowa lafiya kalau. Yace to madallah, daman na kira ne naji halin da kuke ciki. Kada ki damu, ki cigaba da hakuri, kici gaba da kula da yara. Muyi wa abida addua, naga kin damu duk kin rame, kina yawan koke koke. Nima na damu har bana iya aiki yadda ya kamata, har 'yan ofis dinmu sun gane ina cikin damuwa. Yanzu na yanke shawara a raina idan yara suka yi hutu sai nima na dauki hutu mu tattara mu kaura shagamu. Idan hutuna ya kare sai na dawo, idan kuma na samu aikin yi a shagamu ko wata sana'a sai muyi zamanmu ba sai mun dawo kano ba. Rashin abida a kano ya zama tamkar tuwo gaya babu miya. Ni, ke da yara duk bamu jin dadin rayuwarmu. Ko abinci kika dafa babu wanda yake iya ci yadda kika kawo min haka kike zuwa ki dauke, haka na lura yara ma ba sa iya ci, kema haka. Tulin abinci ake juyewa almajirai kullum. Aisha farida ta rushe da kuka, yayin da shima kukan ya turnuke shi, sai yayi sauri ya katse waya. Ta kifa kai akan filo tayi ta rusa kuka tamkar idonta zai fashe. Tana ta addua Allah Ya yayewa abida wannan ciwon. Wayarta ce ta sake yin kara. Nan da nan ta katse kukan ta dauka ta duba sunan barr muazzam ne. Ta goge hawaye da sauri ta tashi zaune, sannan ta matsa waya da yin sallama. Barr muazzam yayi murmushi yace kanwata kwana biyu, kina nan kuwa? Tayi murmushi tace ina nan yayana, na sha kiranka baka amsawa, ko aiki ne yayi maka yawa? Yace kwarai kuwa, satittikan nan uku duk bana zama, daga bakwai na safe zuwa na dare. Alhmdlh abin da ake nema ya samu. Daman case din dr janan ne an tafka sharia na shawo kanta, ta bude baki tayi bayani, ta tonawa su izzuddin asiri, ta kuma fadi inda za a iya samunsa shi da abokansa. Aka yiwa 'yan sandan can garin waya don su kamo shi. Sun kawo mana shi kano, har ya bayyana a kotu, kuma ya amsa laifinsa. Yanzu haka kotu ta wanke janan, an tabbatar ba ta da laifi, an sake ta tana gidansu shi kuma yana daure. Farin ciki ya lullube aisha farida, tayi dariya tace alhmdlh, Allah Mai iko, amma yaya muazzam na taya ka murna, Allah ya kiyaye gaba. Yanzu a wanne hali kuke ciki kai da ita? Yayi murmushi ya lumshe ido yace komai ya daidaita amma dai ba dukka ba, kinsan komai sai a hankali. Kanwata na riki abubuwan nan guda uku, nayi addua, nayi hakuri matukar hakuri kuma naci riba. Naja mata aji, na nuna mata yanzu babu zancen soyayya a tsakanin mu, ina da wacce zan aura. Na nuna mata bani da wata alaka da ita face ta aiki. Ta bani hadin kai kawai in gudanar da aikina yadda ya kamata. Data tabbatar da haka, sai ta saduda ta ajiye wannan zaren da take ja na aji ta bude baki ta amsa duk abubuwan da na tambaye ta, sannan ta gudanar da duk abin da na umurce ta tayi a kotu. Na lura ashe daman tana sona, boyewa kawai takeyi, ko kuma nace yanzu ta fara sona da taga halaka. Ni daman bani da matsala da iyayenta, tun da can suna sona balle da suka ga irin taimakon da nayi musu. Ji suke tamkar su dauko ta su kawo min ita gidana. Ba soyayyar iyayenta nake nema ba, ina so janan ta soni da kanta ba sai wani ya tilasta mata ba, ko don wani dalili ba. Ta soni don Allah, muyi zaman so da yadda a tsakanin mu, ko babu ran mahaifanta. Aisha farida tace gaskiya ne wannan. Allah Ubangiji Ya tabbatar da alkhairi. Yace amin malamata, menene mataki na hudu da zan taka, kin san fa duk abin da kika ce dashi nake amfani, don kin fini wayo ke kuma anti abida ta fiki wayo. Ku dora min karatun. Aisha farida ta kyalkyale da dariya, tace uhmm yayana kenan, har ka bani dariya wallahi. To mataki na hudu da abida ta fada min shine tunda yanzu ta san da kai, ta kuma san abinda ake ciki, sai ka zama mai yawan kyautata mata, da haka zata so ka fiye da kowa. Barr muazzam yayi murmushi yace idan haka ne to ai na riga na haye mataki na hudu don ni mai yawan kyautata mata ne, har ita da kanta ta rubuto min sakon godiya a waya, ta yaba da hakan. Dazun nan ta rubuto min wannan sakon. Mene mataki na biyar kuma, ko baka taka shi ba? Aisha farida tace eh to inaga nima a mataki na hudun nake amma abida ta fada min mataki na biyar din tace ka nuna kama sonta tamkar kafi kowa sonta a duniya. Kamar kulawa da duk halin da take ciki, da kuma tattalinta, tamkar kwai, ka nuna ko kuda ba kaso ya taba ta. Idan ka yi mata haka ita ma zata so ka, zatayi kokarin ta mallake ka a rayuwarta, kaga sai ka aure ta. Barr muazzam yayi ajiyar zuciya yace kice min gangaro na kusa samun janan kenan? Zanje na dorawa baraka wannan karatun. Aisha farida tace af! Na manta ban tambaye ka baraka ba, ina take? Wanne hali take ciki? Yayi dariya yace mutuminki nurudden dai ya saduda daya ga ta share shi, sai yake shishige mata, ita kuma tana watsar dashi. Yanzu haka ya fara neman shawarata wai yana ga zai rabu da nafisa. Yace min baraka tace ta amince ta auro nafisa ya hada su, su biyu. Ita kuma nafisa tace sai ya saki baraka kafin ta aure shi. Shine yake cemin da ya saki baraka gara ya fasa auren, domin baraka ce mace ta gari da take yi masa biyayya. Aisha farida tace yawwa ka cewa baraka ta taka mataki na hudu shine taci gaba da kyautata masa fiye da na da. Sannan mataki na biyar ta nuna masa tsantsar soyayya kamar tafi kowa sonsa a duniya fiye da yadda nafisa ke sonsa. Brr muazzam yace lallai ke malama ce, ke kuma yaya naki gogan, me kuke ciki? Tayi murmushi ta lumshe ido tace alhmdl. Dr shuraim yasan dani yanzu, ya san sunana, har ya damu da halin da nake ciki. Ta kai ta kawo dr shuraim ya nemo lambar wayata ya kira ni a waya ya gaishe ni ya tambayi jikin antina abida. Ina ga yanzu zan taka mataki na hudu, zan cigaba da kyautata masa sosai har sai ya kaunace ni yaji sona tamkar ransa zai fita, sai ya saki jiki dani, don bana tantama ya fara sona. Sai in taka mataki na biyar shine ina nuna masa tsantsar kauna nima. Barr muazzam yace amma abu yayi kyau, Allah ya tabbatar da alkhairi, Ya zaba mana abin da yafi alkhairi a rayuwarmu. Har yanzu jikin anti abidar ne bataji sauki ba? Aisha farida ta marairaice tace ba za'a ce babu sauki ba, amma har yanzu ana nan ana fama. Babbar matsalar ma da 'yan uwanta suka zo suka dauke ta shine dr shuraim din yake fada min kada su jifga mata sassake sassake ya jawo mata ciown koda, domin ciwon yana da alaka da ciwon koda. Barr ya girgiza kay tace subhanallah! Allah Ya kiyaye, Allah Ya bata lafiya. Kiyi kokari ki kira su a waya ki fada musu abinda likita ya fada, kada su bata sassake. Yanzu zan turo miki katin waya don kiyi magana dasu yadda ya kamata. Aisha faida ta matse hawaye tace nagode da wannan hidima da kake yi min ko wani dan uwan nawa na jini ba yayi min abin da kake yi min.....sai ta rushe da kuka. Ya girgiza kai yace dadina dake saurin kuka kamar wata tsohuwa. Ki daina kuka kinji ko? Duk abin da ya samu bawa Ubangiji Yana sane, kuma Zai yaye masa. Sai kinga sakona sai anjima. Aisha farida tace sai anjima, Allah Ya saka da alkhairi. Ya kashe waya ba dadewa taji kara a wayarta, da alama sako ne ya shigo. Tayi sauri ta duba sai taga brr ne ya turo mata da kati. Data loda sai taga na 1500 ne. Ta kira shi har ta katse bai dauka ba, sai ya kirata daga baya. Tace dama godiya zanyi maka, naga kati na gode. Yace ba damuwa ba sai kin yi min godiya ba, don nabaki wannan dan kati. Ya kashe wayar ta koma ta kwanta ta dubo lambar dr shuraim tayi ta kallo tana shawara a ranta ta kira shi ko kada ta kira shi? Sai ta yanke shwarar ta kyale don ta lura baya son damu, idan ya kira da kansa zaifi kamar yadda rannan yaga dama ya kira da kansa. Sai ta jiye wayar a gefe zuwa jimawa sai ta sake jawo wayar ta fara rubuta masa sakon gaisuwa da fatan alkhairi. Har zata tura sai ta fasa ta goge da ta tuna ta tura masa na juma'a bai bata amsa ba, kuma bai kira ba. Ta duba agogo karfe goma sha daya da rabi 'yan makaranta karfe goma sha biyu zasu fara dawowa daga makaranta, gashi bata dora abinci ba, don haka sai ta mike tsaye zata je ta dora abincin sai taji wayarta ta dauki ruri. Ta dawo ta zauna da sauri ta jawo wayar ta duba, sunan dr lukman ne ya bayyana, sai farin ciki ya rufe ta, tayi murmushi tayi sauri ta danna, cike da fara'a tayi masa sallama gamu da cewa yayana ina ka shige ne kwana biyu naji ka shiru? Yayi dariya yace kaji marar kunya. Ni zan neme ki ko ke zaki kira ki gaishe ni ki samu lada? Ko baki kirani ba naga flashing ko pls call me ai zan kira ki. Amma baki neme ni ba. Ko da yake jan aji ne irin na 'yan mata ko? Yanzu muke maganarki da abokina dr shuraim. Aisha farida ta dafe kirji ta lumshe ido ta tambaya cike da zumudi, me yace? Dr lukman yace yanzun nan ya fice da yaga zan kiraki. Daman nace sai na fada miki ko baya so. Wai ya akayi kike burge abokina ne, ni tunda nake dashi a asibitin nan shekara da shekaru ban taba ganin macen da ya taba maganarta ba balle ya yabe ta, sai ke? Yace kina burge shi saboda kina da hankali. Ga ki da kunya, kara, kawaici, ga hakuri da shiga ta mutunci, uwa uba kin da aji ba ki cika shishigi da rawar kai irin na 'yan matan yanzu ba. Sannan haka kawai yake tausayinki musamman da ake ce ke marainiya ce. Sannan yace kina da matukar kirki da yaji ashe kace kike daho mana dambu da danwake. Kinsan da hannunsa ya dauki lambarki a wayata, yace zai kiraki ya ji jikin yayarki. Aisha farida tayi ajiyar zuciya tayi dariya. Tace Allah sarki, haka Allah Ya ke shirya al'amuran Sa duk yadda yake so. Dr lukman yace munafukai ne ke dashi, kunsan abin da yake tsakaninku. Ai idan tayi tsami zamuji. Shima sai kwana kwana yake yi min, idan na tambaye shi. Amma gaskiya na sha mamaki da naga yana yawan USA Novels BOOK DUK KYAN TAKALMI 2* 13 Damuwa dake, don ni nasan shi nasan ra'yainsa, nga yadda yake kushe mata. Ban taba jin ya yabi wata budurwa a duniya ba ma balle a cikin asibitin nan, shine na kiraki naji meye sirrrin? Aisha farida ta kyalkyale da dariya tace ba wani sirrri wallahi, Allah ne Ya hada jininmu, nima yana burge ni sosai. Dr lukman ya gyada kai yace gaskiya kanwata idan har wannan abu zai tabbata tsakaninki da shuraim zanfi kowa taya ki murna, don kinyi dace da mutum na gari, mai tsananin kirki da tausayi, mai kulawa. Aisha farida ta dafe kirji ta lumshe ido tace Allah yayana haka ne? Yace inayi miki fatan alkhairi, sannan ina taya yayarki da addua ta samin sauki. Zanje wajen marasa lafiya, sun taru suna jirana. Ya katse hiran. Aisha farida ta sulale ta kwanta, tayi shiru tana sake maimaita kalaman dr lukmann, mamaki ya rufe ta, tamkar a mafarki ba a ido biyu abubuwan suke faruwa ba. Anya kuwa itace, ko dai mafarki ne? Take tambayar kanta da kanta. Ta sake gasgatawa babu abin da yafi addua da hakuri a duniya. Ta dinga yi wa Allah godiya da Ya nuna mata wannan rana. T dinga kwararo addua tana rokon Allah ya karawa dr shuraim sonta, kuma Ya sa ya aure ta. Ta tuno abida taji daman abida tana nan taji irin wannan dadadan labari. Sai tayi wa abida addua Allah Ya bata lafiya. Tana zaune ta kasa tashi ta dora abinci bata ankara ba, sai taji muryar 'yan makarnata sun fara dawowa. Ta ji wani kara kwarakwacam anyi wurgi da jaka da robar abinci a bakin kofar dakinta, ta san gajiya ce da yunwa take addabarsu. Tayi wuf! Ta fito. Ta shiga llallabasu tana yi musu dubaru tana koda musu dadin garin kwaki da mai da yaji, ta aika su suka siyo ta kwada musu suka ci suna murna. Tace musu haka 'yan makarantar kwana suke yi, gara ku fara koyon ci kafin ku tafi sakandire ta kwana. AISHA SHURAIM HIMMA BA TA GA RAGO!!! BABI NA GOMA SHA BIYU Fiye da sati biyu dr shuraim bai kira aisha farida ba, itama bata kira shi ba. Don haka sai ta fara shiga kokonto anya kuwa dr shuraim yana sonta? Da yana sonta ai ba zai share ta haka ba, wata kila tausayinta kawai yake yi ba soyayya ba. Jikinta yayi sanyi, ta fara shiga damuwa, bata da walwala abubuwa suka taru suka yi mata yawa. Kowa ya kalle ta sai ya tambaye ta me yasa ta rame. Taci gaba da daurewa tana ta addua tana neman agaji daga Ubangiki Mai kowa, Mai komai. Son dr shuraim ya zame mata tamkar ruwan shanta, ya zame mata abincin cinta, kuma mayafin lullubarta. Duk da daurewa da tayi, sai da ta kai ta kasa cigaba da daurewa saboda ji take tamkar zuciyarta zata yi bindiga ta fashe don kunci. Tsananin son dr shuraim da kuma rashin abida abokiyar shawararta, itace mai bata shawara da kwantar mata da hankali. Tasan da tana nan da tuni ta fada mata abin da ya kamata tayi nan gaba. Ranar talata bayan yaya hussaini ya fita aiki, yara sun tafi makaranta, sai ita kadai a gida. A kwance take a daki ba tare da tana jin dadin kwanciyar ba. Ta yanke shawarar tunda ga dan kudi a hannunta bari ta harhada tayi musu danwake, ta kai musu asibiti ko Allah Zai sa ta dace ya ganta ya tuno da ita don tana tunanin ya manta da ita ne. Tayi zumbur ta miike ta shiga shirye shiryen yin dan wake. Kafin karfe goma na safe ta gama tsab, ta zubawa yara na su a flask. Ta shiga tayi wanka ta fito ta dauki fiye da mintina talatin tana kwalliya. Wata sabuwar atamfarta ta saka diamond mai kore da ja, aka dinka mata riga da skirt matsattsu, ta sami bakin gyale da bakin takalmi ta saka. Sai dai kash! Ta juya ta sake juyawa ta dubi jikinta sosai, sai taji ba zata iya fita a haka ba. Ta san shi kansa dr shuraim din ma ba burge shi zatayi ba. Don haka ta ajiye gyalenta ta dauko bakin hijabinta sabo dal ta siya kwanan nan naira dubu daya irin wanda ake siyarwa a dinke mai hannaye kamar riga. Ya shiga da takalminta mai dan tsini. Ta kullo kofar dakunan bayan ta debowa yara kayan makarantar islamita da flaski din abincinsu ta mika dakin uwani taroke ta arziki idan yaran sun dawo ta basu abincin su ci su sauya kaya idan lokacin islamiya yayi su tafi. Tace itama ba dadewa zatayi ba, zata kai wa marar lafiya abinci a sibiti. Uwani ta amsa mata cike da fara'a gami da alkwarin zata aiwatar da abin da ta umurce ta, ta hada ta yiwa marar lafiyar adduar samun sauki. Aisha ta dauki kwandon da ta saka flask din abinci da plates da cokula, bayan yaji dakakke a 'yar roba, da 'yar robar mangyada. Tana tafe cikin nutsuwa har ta fito daga lokonsu ta sami adaidaita sahu nan da nan ta haye. Ita kanta tasan tayi kyau, ko ba a fada mata. Jama' da dama sun dasa don samari suna ta binta sun kai su uku sunayi mata magana. Suna sonta bata kula su ba. Kuyi hakuri an riga an bada ni. Amsar da take ba su kenan. Tana isa cikin asibitin malam ta doshi ofishin dr lukman, sai taji kirjin ta ya fara dukan uku uku, don fargabar abinda zata tarar daga dr shuraim. Tana hawa kan barandar ofishin sai ta hango dr shuraim da wasu dattijai maza su uku sun tunkaro ta, ma'an suna fitowa ita kuma tana shiga. Sai taji wani mummunan faduwar gaba. Ya tsura mata ido sosai yana kallonta, har sai ta taji kunya ta sunkuyar da idanuwanta kasa. Suka wuce ita ma ta wuce, ta juyo a hankali zata dube shi, shima ya juyo sai gaba dayansu suka gaggauta juyawa da sauri. Ta shiga fargaba saboda ta dimauce, bata gaishe shi ba, kuma ya kamata ta gaishe shi din. Don haka ne ma yake ta kallonta har da waiwaye. Abin da zuciyarta ke zayyano mata kenan. Jikinta a sanyaye ta shiga ofishin dr lukman, taci sa'a yana nan shi da abokinsa dr mohd. Bayan ta gaishe su, sai ta ajiye kwandon abinci a gaban dr lukman. Tace ga danwake nayi muku. Yayi farin ciki, yayi godiya sosai. Dr mohd ta dubi dr lukman yace lukman zaka bani 'yar kanwar nan taka kuwa? Ina sonta tun ranar da na fara ganinta. Kirjin aisha farida ne ya burededen dukan uku uku har ta fara dana sanin zuwanta nan a yau. Ana wata sai ga wata, yanzu idan dr shuraim yaji ko da wasa dr mohd ya furta yana sonta, ai bar masa zaiyi ba zai kara nuna alamar so ba. Ta tsunduma cikin wannan dogon tunani, sai da dr lukman ya ambaci sunanta ta dawo da hankalinta gare su. Yace kanwata kinji wai in bashi ke? Tayi murmushin karfin hali tayi shiru. Dr mohd yaci gaba da kallonta, kallo mai cike da so da kauna. Ta sunkuyar da kanta kasa, tana mai tsananin jin kunya hade da bacin rai. Dr lukman yayi dariya ya daki kafadarsa yace kai da kake min tsiya wai ba kanwata bace, bamuyi kama ba, sai inga wanda zai baka 'yar. Dr mohd yayi dariya yace yi hakuri don Allah, yaya na daina. Yana rufe bakinsa sai dr shuraim ya shigo. Nan da na hankalin aisha farida ya sake tashi. Ta fara addua kada Allah Ya sa acigaba da zancen soyayyar nan. Tayi sauri ta sulalo daga kan kujera ta gaishe shi. Ya amsa cike da far'a, sannan yaci gaba da kallonta. Can yace lukman dama kanwarka ce na hadu da ita a baranda nake mata kallon sani, amma ban gane ta ba. Naga ta sauya. Aisha farida ta dube shi a kunyace ta sunkuyar da kai. Dr lukman yace me ka ga tayi? Ta sake yin kyau ko? Ai an gama makaranta ana hutawa a gida. Dr mohd yace kai fa lukman yaya ne ka bari in fadi da bakina mana, sai kace tayi kyau, kai yayan kwabo ne ko? Su biyu suka tuntsire da dariya yayin da dr shuraim ya tsaya cak! Ya dubi dr mohd ya juya ya dubi dr lukman ya juyo ya dubi aisha farida nan da nan taji zuciyarta na dukan uku uku. Daga dukkan alamu dr lukman ma baiji dadi da dr mohd ya fadi haka a gaban dr shuraim ba, domin yana kyautata zaton dr shuraim yana son aisha farida, furatwa ne kawai baiyi ba. Dr shuraim ya gaggauta daukar ajiyarsa a loka ya fice da sauri. Aisha farida ta kame a zaune, yayin da numfashinta yake kokarin daukewa gaba daya, babu wanda yake magana a tsakanin su biyun, dr mohd ne kadai yake surutunsa. Haushi da tsanarsa suka bayyana a fuskar aisha farida. Ta dauke shi a matsayin tamkar mutumin da ya dauko wuka mai kaifi ya dubi cikinta ya burma mata, ma'ana ya kashe ta. Domin ya rugurguza mata walwalar rayuwarta duniya da lahira. Dr mohd yayi ajiyar zuciya, ya dubi aisha farida yace bani lambar wayarki aisha umar. Ta dago da sauri ta dube shi, duba na takaici ba tare da ta iya furta kalma gida daya ba. Dr lukman yayi sauri yace ita zaka tambaya ko ni yayanta zaka tambaya na ba izini ka karba? Ita ma na umurce ta ta baka? Tayi murmushin karfin hali ta mike tsaye a sanyaye ta yi musu sallama zata tafi. Dr mohd ya nemi ta kara zama suyi hira, tace gidan babu kowa sai ita kadai, don haka take so ta koma da wuri. Dr lukman ya ciro naira dubu daya ya mika mata, yace tayi kudin mota. Tace ya bari ba zata karba ba, tana kudin motarta. Dr mohd ya zabura yace ka bari kawai zan bata ko kuma ma marasa lafiyan da suke jirana suyi hakuri sai na kai matata gida sannan zandawo. Dr lukman yace wannan kyautata ce ta daban a matsayin na yayanta, kai da ita kuma daban. Kuma wallahi sai kin karba kinji ma na rantse. Aisha farida ta saka hannu biyu ta karba gami da yin godiya, cikin sassanyiyar murya. Dr mohd yace Allah sarki, kaji yarinya mai ladabi, gaskiya nifa da gaske nake. Lukman zanje in kai ta gida in dawo muyi maganar gaskiya ba wasa nake ba. Tayi wuf! Ta fice da sauri don bata so ya biyo ta, shima ya fita da sauri ya biyo bayanta ta, ya umurce ta ta jira shi su tafi tare. Wani babban tashin hankalin kuma sai ya tura kofar ofishin dr shuraim ya leka sai ga dr shuraim a zaune a kan kujerarsa yana danna laptop. Ya dagi da kyawawan idanuwansa ya dubi dr moh sannan ya sake daga ido ya hango aisha farida a gefensa. Sai ya sunkuyar da kai, yaci gaba da danne dannensa. Amma daga kallon fuskarsa kasan zuciyarsa a bace take. Dr mohd yace abokina zo muyi rakiya, wancan dan iskan lukman yaki yace shi a dole babban yaya ne. Ya girgiza kai yace nima yaya ne, ba zanje ba. Kaje sai ka dawo. Aisha farida tayi wuf! Ta bar wajen, tafiya take ba tare da tasan inda take jefa kafarta ba. Kawai wani lungu ta samu ta dinga kutswa cikin asibitin maimakon ta nufi bakin gate sai tayi ciki. Kafin dr mohd ya waiwayo sai yaga wayam! Bata nan. Ya fito da sauri ya dudduba hanyar gate ba ta nan. Ya duba kudu da arewa, babu ita babu dalilinta. Sai ya cika da mamaki, ya shiga kokonto da wasi wasi don haka ya koma ciki da sauri don ya shaidawa yaya lukman. Dr lukman yayi dariya yace kunyarka takeji, kuma tana da tarbiya bata so a ganta da namiji , ni nasan halin kanwata. Dr mohd ya takura sai an kitay a waya yaji inda take. Aisha farida ta isa ofishin matron maryam ta iske bata nan, sai sababbin dalibai da aka turo daga makarantarsu. Yawancinsu ma duk sun santa. Bayan sun gaisa ta tambaye su matron sai suka ce ta fita. Aisha ta jawo kujera ta zauna tana huci, nan da na suka hau tambayarta bata da lafiya ne? Tace gajiya ce kawai, tana so ta huta sannan ta tafi. Bata rufe bakinta ba sai wayarta ta dau kara. Ta bude 'yar karamar jakar da ta saka kudin motarta da wayar ta zaro wayar, sunan dr lukman ne ya bayyana. Sai taki amsawa har ta katse. Tana katsewa ya sake kira, don haka ta tabbatar kiran yana da amfani, sai ta amsa. Tambayar da ya fara mata itace kina ina? Tayi inda inda sannan tace ina cikin adaidaita sahu hanyar komawa gida. Yace toh shikenan. Allah Ya kaiki gida lafiya. Ya kashe wayar tana jiyo muryar dr mohd amma bata gane abin da yake cewa ba. Anan zan dakata mu hadu a DUK KYAN TAKALMI 3 kuji yadda zata kasance. Daga 'yar uwarku JUT. See Translation January 10, 2015 at 7:26pm · Public 35 DUK KYAN TAKALMI 3* 1 Tayi ajiyar zuciya mai karfi.sannan ta kwantar da kanta akan teburin da yake gabanta don ta rasa abun da yake yimata dadi innalillahi wa inna ilahi raji`un,ta ke ta ambato,sai da ta dauki tsawon mintina 20 bata iya dago waba,ta mike tsaye da kyar yayin da idanuwanta suka yi ja,alhalin kuma ita ba kuka takeyi ba daliban dai har yanxu tambayarta sukeyi,anya kuwa lafia? tace lafia kalau kawai dai gajiya ce. Tayi musu sallama tabar musu sako su gaishe da metron maryam sannan ta tafi,ta cikin lunguna ta kurkurda ta fito gate,tana fitowa taci sa`a ta sami A dai- daita sahu babu kowa a ciki,don haka tayi wuf ta shigo batare da ta fada masa inda zai kai ta ba balle suyi cinikin kudin da zai karba,tana shiga ta zauna tana daga kanta, sukayi ido hudu da dr shuraim cikin tsaleliyar motarsa discussion continues,shi ma kallonta yake yi alokacin da yake kokarin tsallakawa titi,ta sunkuyar da kanta da sauri,yayin da shikuma ya tsaya cak yana kallonta,daga dukkan alamu yana mamaki da ya ganta yanxu,mai adaidaita sahu yaja ya tafi yayin da aisha farida ta rike kai,saboda nauyin da taji kan yanayi mata sai da mai adaidaita sahu yayi da gaske sannan ta bashi amsa, ta fada masa inda zai kaita tana shiga gida sallan azahar kawai tayi ta shiga lungun ta kwanta ba tare da ta san a duniyar da take ba,taji dadi da ganin yara a zaune a dakin uwani,sunci abinci suna hutawa,don haka tace suyi zamansu a nan zatayi aiki idan lokacin makarantar islamiyya yayi su tafi,saboda kawai bata son damu da magana cikin wanan hali da ta riski kanta Allah sarki soyayya ruwan zuma tayini tana duban numbr dr shuraim,sai taga kamar shi take gani,koda yaushe kunnenta da idanuwanta ta suna yi mata gizau,taga kaman shine yake kiranta da zaran an kirata,idan taga bashi bane sai ranta ya baci tana so takirashi amma tana tsoro kada ya wulakantata kuma bata ma san abun da zata ce masa ba idan takira din. washegari ta tashi acikin bacin rai kaman yanda ta yini a jiya ta yankewa kanta shawarar gara ta hada ta kaura shagamu kawai tayi rayuwarta acan ,idan sakamakonsu na exm ya fito ta karbi takardunta taje can ta nemi aiki a asibitin garinsu shi yafi mata sauki,saboda son dr ya zamar mata annoba musamman idan tana ganinsa. wayarta tayi kara alokacin da take wanke-wanke ta arto da gudu ta dauka tana addu`a Allah ya sa dr ne,sai taga wata bakuwar no ce,ta yi sauri ta danna,muryar wani kamillan mutum taji ya ambaci sunanta,aisha umar ce ko? ta amsa eh,nice" yace dr mohd ke magana! Ta sulale ta zauna,yayin da takaici ya lullube xuciyarta,ta gaishehsi taja bakinta tayi shiru tana sauraronsa,yace sai kika gudu kuma ko tsorona kike ji? ta kame a zaune,domin tana jiyo muryar dr lukman da dr shuraim a gefensa,hankalinta ya tashi har abada sai hawaye ya surnano daga idanuwanta bata iya bashi amsa ba,yace ki kwatanta min gidanku zan zo,tayi shiru can tace ai zan shigo asibitin gobe zan karbi kwanukan da na kawo muku,yace kash gobe ai bana gari sai dai ki zo jibi tana jiyo muryar dr lukman yana cewa to ka fasa tafiyar mana idan da gaske kake yin son? dr shuraim kuwa bai sake furta komai ba yana gefe guda yana kallonsu,tayi sauri ta katse wayar ta rushe da kuka,tayi sauri takira wayar shagamu gidansu abida,lambar mamarta,bugu daya ta dauka ta gaisheta,ta shaida mata aisha farida ce daga kano,kasancewarta tsohuwa ba iya karanta suna tayi ba. Goggo tace ai na gane muryarki yar baba,kamar yadda wasu suke kiranta da haka,ina anti abida,ya jikin nata? goggo ta amsa,mungode Allah,amma dai jikin abida to sai yadda Allah yayi,gata nan yanzun nan tace a tashe ta zaune ta gaji da kwanciya,aisha farida ta fashe da kuka,goggo ma ta fashe da kuka,aisha tace a bawa abida wayar,goggo tace sai dai in kara mata wayan a kunne,bata iya daga hannunta, bazata iya rike wayar ba. Muryar abida ce ke karkawa tace farida maiyasa kike kuka? zan samu lafiya da izinin Ubangiji. Aisha ta matse hawaye tace, anti abida so nake ayi wa yara hutu na taho shagamu na dinga ganinki bana jin dadin gidan nan Bana jin dadin kanon, duniyar ma gaba daya ta isheni,Allah ya baki lafia. Hawaye ya surnano da idon abida, tace bana so ki kaura shagamu,har sai kin cika burinki akan dr, Farida ta fashe da kuka tace anti bana jin zan cika wannan burin nawa,domin yanxu wani abokinsa ne yake sona,mai suna dr mohd kuma har dr shuraim din ya sani,nasan zai hakura ya bar wa dr mohd ni kuma bana son dr mohd din,shuraim nake so. Yanxu haka suna tare,kuma agaban dr din yayi min waya,abida ta cije baki saboda tsananin ciwon da yake addabarta,tace kada ki damu duk irin abunda zai faru ki zubawa sarauta Allah ido,ki gode masa kici gaba da addu`a,kanwata duk irin wannan wata hikimar Allah ce wacce ba ki sani ba,ki ci gaba da nemawa zuciyarki abun da take so har sai kin cika burinki,ina yimiki fatan alheri. Farida ta katse wayar ta rusa kuka ita kadai a daki ta fada a bayyane,wayyoh abidata wayyoh shuraim,inna lillahi wa inna ilaihi raji`un, Allah ka taimake ni ka cikamin burina,ka karbi adduoina guda biyu,kaba wa abida lafia ka bani dr. Tayi kuka tayi addua har muryarta ta ddisashe,yau ma dai yara sun sha wahala har karfe 2 basu ci abincin rana ba,don bata iya dorawa da wuri ba. kuyi hakuri ku yafemun yara ni kadai nasan halin da nake ciki inji farida lokacin d take cuu-cukun xuba musu abinci bayan da ta tabbatar sun galabaita. Faruk ya dubeta yace anti aisha meyasa kullun kike kuka? ko mamarmu ta mutu ne? Hawaye ya surnano da idonta tayi saurin ta dukar da kanta kkasa don kada ya gane kukan zata sakeyi ta girgiza kai tace mamanku bata mutuba ta samu sauki,na muku alkawari ranan asabar zansaka kati a wayata inkiramuku ita daya bayan daya kuyi magana da ita zakuji muryarta radau taji sauki sosai. sai taga sun hada ido sunhadu sunyi daria suka hau murna bayan tabasu abinci sunaci a tsakar gida tashiga daki tarufe tashige lungu tadinga kuka tana addua ya Allah kana sane da halin danake ciki kasa abida ta warke nasani baka barin wani dan wani yaji dadi Allah ka duba kananan yaranta har hudu ka tashi kafadunta,suna tanbayata mamarsu yaya zance musu idan tarasu Allah kada kabarsu sutashi a marayu kaman ni,Allah kabani mijin danake so dr, insan dadin aure dan idan na auri wani bashiba farin cikina ragaggenai. Ya Allah kafini sanin abunda yafi Alkhairi a rayuwata Allah nagode maka kaciga da taimakona da kai kade na dogara, adduoin da Aisha farida keta zubawa kenan a wannan yinin,bata iya fitowo tayi hira da yan gidan ba,har sai da ta tabbatar magruba ta karato yaya husaini ya kusa dawowa sannan ta fito,ta fara cukuncukun dora abincin dare. Washegari jummaa ta shirya da wuri ta fita,karfe tara a cikin asibiti tayi mata,kasancewar juma`a ce don kada a rufe hanya,ta isa ofishin dr.lukman sai taji a kulle wata kila bai iso ba,tunda bai isoba tasan dr shuraim bai karaso ba. Amma dai taja jikinta ofishin ta tsaya,ta karanta sunansa ta sake karantawa sai taji sanyi a ranta,ko sunansa ta gani a rubuce dadi takeji ,ta lumshe ido,tasa hannu a hankali ta rike hannun kofar,sai taji tamkar ta shafi hannunsa ta san tabbas ya taba da hannunsa,ta murda da wasa don tana da tabbacin a kulle take,bai karasoba kwatsam sai taga kofa a bude har ma ta wangale sai ga dr radau a zaune akan kujera suna hada ido taji tamkar ta zura da gudu don fargaba, tayi wuki-wuki da ido tana kallonsa cike da mamaki yayin da shima haka har tsawon lokaci suna kallon juna. Shigo mana inji shi, ta fara tafiya a hankali kanta a sunkuye a kasa cike da kunya,sai yanxu ta dubi kayan da ta sako a jikinta,birkideden hijabi ne har kasa yana jan kasa,shi ma mai hannu ne kaman riga ake sakashi,maroon color sai ta saka takalmi shima kalar hijabin mai dan tsini,yayin da fuskarta bayan hoda bata kara komai ba,babu kwalli balle jagira,don bata saka ran zata hadu da shi ba.niyyarta tazo ta kwashi kwanunkanta tayi wa asibitin sallama daman tasan dr mohd baya nan yau shi yasa ta garzayo dan bata son su hadu. Sai kallonta yake tundaga sama har kasa,har saida ta karaso gabansa ta durkusa har kasa ta gaishe shi yace tashi tashi ki hau kujera ki zauna, ta tashi a hankali ta zauna kan kujerar har yanxu kanta a sunkuye yake a kasa,har zuwa lokaci mai tsawo batayi maganaba shima haka danne dannensa kawai yakeyi a laptop. Can ta dago ta dube shi sai taga ya dago da sauri ya dube ta,tayi murmushi tace yaya lukman be karaso bane?? naje ofc dinshi a kulle,ya gyada kai kawai bai yi magana ba sai taji hankalinta ya tashi,ta tabbatar yana jin haushinta ta yunkura ta mike tace,bari in jirashi a waje ya girgiza kai ba tare da ya kalleta ba,yace ba damuwa ki zauna a nan har yazo,ta koma ta zauna yayin da taji dan sanyi a ranta,taci gaba da sunkayar da kai, idan ya dago ya dubeta sau daya, sai yaci gaba da kallon laptop dinsa. Kamar daga sama taji ya ambaci sunan ta,ta dago da luhu-luhun idonta ta dubeshi ta amsa cikin nutsuwa. Ya tsaya cak da abunda yakeyi yace lafiyarki kalau,ko akwai abunda yake damunki ne? tayi murmushin karfin hali mai kayatarwa,tace lafiata kalau dr. Yace bawan da yataba gayamiki kin rame kwanan nan? ta sake murmushi ba tare da tasan amsan da zata bashi ba, yace don wa kike dafa abincin nan da kike kawowa? Shi kansa yasan ta firgita da jin wannan tambaya,domin ta dago da sauri ta dubeshi ta tabbatar yau wulakancinsa yau ya motso kanta ,taji hankalinta ya tashi,sai kwalla tacika mata ido,ya sake maimaita tambayarsa, hakika amsa yake bukata kuma ya xuba mata ido,ta runtse ido tayi shiru. Can ta dago ta dubeshi tace saboda kai da dr lukman nake kawowa. Yayi daria yace harda ni ba saboda lukman kawai ba? to mun gode kuma munji dadin abincki sai dai ina rokonki ki daina wahala da mu,kada ki kara kawowa. Kallo na rashin fahimta take yimasa,har sai da ya gane haka. Yayi ajiyar xucia yace bana so naga mace na wahala,macen ma mai suna mai daraja irin naki AISHA FARIDA. Sai taji dadi ya rufeta tasa hannu ta sosa goshinta saboda kunya,tayi murmushi tace dr ba damuwa ni ba ya damuna,in har zaku ci,ya girgiza kai yace kiji maganata,ki daina kawowa in muna so zamuyi miki waya ki kwatanta mana gidan mu zo mu dauka,ba sai kinxo ba kinji ko? nan da nan ta amsa da to,in sha Allah zanyi amfani da abunda kafada. Yace yawwa na gode yaya mai jiki,ta langwaba da kai,tace tana can shagamu tana fama har yanxu bana jin tana samun sauki, sai ta fara kwalla. Ya tsaya cak ya daina abinda yake,yana dubanta yace ban taba ganin randa zan ganki ba kya kuka ba,farida waya gaya miki ke kadai kike da matsala a duniya,mu me yasa bama kuka kullum? Waye ya shagwabaki kike yawan kuka? tasa hannu ta matse hawaye,tayi dan murmushi tace ba kowa....yace kidena kuka ni kukan yaro ma bana so balle babba kuma mace,baki san duk sanda naga hawaye a idonki ba ,idan kika tafi damuna yake a xucia ba? to ni haka nake a rayuwata,matsalar wani matsala tace,ki fadamun ko akwai abinda yake damunki a rai,sai in baki shawara nima abokin lukman ne. Tayi dariya ta girgiza kai tace babu komai idan ma akwai ina fadawa Allah ya kawo mun sauki. Yace wannan yayi kyau ko meye damuwarki ki fadawa Allah. Kuka da saka damuwa a rai matsala zaki jawowa lfyrki,mu likitoci bama son haka. Musamman bangaren yayanki lukman kwakwalwa suna hana mu2m yawan 2nani da damuwa. Ki kiyaye kina karamarki zaki cuci rayuwarki a banza. Ta gyada kai tace naji likita ngd. Yace shigarki tayi min kyau ta burgeni. Sai taji tmkr ba shi yake magana ba. Ta kalle shi ya kalleta, shima ya gane ta shiga mamaki. Sai yai murmushiyace,kina burge ni fa, i lyk ur style. Dgwar ajiyar zuciya yaji taja, har yanzu kallonsa takeyi kawai. Yace zaki jira ni in tashi daga aiki na mayar dake gida? Wannan karon ma sake zaro ido tayi ta dube shi cike da mamaki. Yayi dry yace, ba kya bani amsa fa, me yasa kike mamamki ne? Tayi mrmshin krfn hali tace, to. Yace ki jirani a nan ofishin bayan sallar juma'a sai na dauke ki a motata mu fita,idan na kaiki gidana kika gani muka dan huta bayan magruba sai muje in mayar dake gidanku nima naga gdnku. Ko ban zo ba ke saiki zo gidana 2nda ni kadai ne a gdn kema kuma antinki bata nan, babu wanda zaisa miki ido. Yau dr. Lk ba zai xo ba,tare suka yi tafiya da dr. Mohd saini kadai kinga sai kiyi zamanki a ofishina ki jira har bayan sallar juma'a ko? Kuma dk abunda zai faru a tsakaninmu bana si ki bari wani ya sani har lk sirri ne. Ta zazzare ido tana dubansa,taga shi ko a jikinsa maganarsa yakeyi kansa a tsaye. Sai taji a ranta ta tsani kanta, kuma t tsani rayuwarta. Ashe dan iska ne bata sani ba,har take yabonsa? Sai taji gaba daya ya sure mata taji daman bata sanshi ba,bata taba ganinsa a raywrta ba. Ya dubeta duba na kurilla yayi mrmushi ya daga mata gira yace,baby kin amince dani? Zan kawo miki canji a rayuwa. Soyayya da jindadi ga dukiya mai yawa. Dn Allah ya dora min sonki a lkc guda kece baki sani ba,kina da kyau,gaki da diri,kinfi sauran mata. Taji tmkr ya caka mata wuka a kahin zuciya ta fada a zuciyarta, innalillahi wa'inna ilaihir rahi'un! Dr shuraim me yasa halinka ya zama haka? Wayyo Allah na dama ace yadda kake da kyau kanada kyawun halyya a boye kmr yadda a zahiri kake kamilalle mai rukon addini Ya katse 2naninta yace, bari inje clinic ona da patient zan bar miki ofishin ki bude firij akwai fruits da juices kisha wanda kike so. Ya dauki laptop dinsa ya fice yayin da ta bishi da kallo harya fita. Ta dafe kirji ta zabura ta mike tsaye sai taji jiri ya kwasheta ta koma ta zauna ta rushe da kuka. Ta fada a bayyane, Allah ka fini sanin dalilin daya sa na tsinci kaina a cikin irin wannan rayuwa. Ina abida? Abida ko zo kiji halin da nake ciki. Tayi kuka ta gaji,ta dubi ko ina a cikin ofishin babu abnda take hangowa a cikin lokokinsa daga manyan littafan likitoci dai kur'anai izifi sittin-sittin. Ta daga ido ta dubi bango taga gaba daya firem ne a rubuce da sunan Allah da manzonsa. Ta dubi kasa sallayar sallarsa a lungu da carbi dan yayi sallah yake ja. Sai taji ranta ya sake baci,ta fada a ranta. Dr shuraim ya zama babban munafuki a addini a fili yana nunawa shina Allah ne,fasikancu ne kuma a boye. To ashe duk 'yan matan nan da yake wulakantawa dk sai daya gama lalata su tukunnan sannan ya koresu? Ka cuci kanka, ka cuci kyakkyawar hallitarka. Allah ka yaye min son fasikin mu2m a rayuwata. Ta sake rushewa da kuka,tayi zumbur ta mike ta bude kofar ta leko taga bayanan, sai ta fito ta jawo kfr ta rufo. Tana tafe tana waiwaye waiwaye. Abin mamaki sai taga ofishin dr lk a bude har wani dalibi ya kwankwasa ya tura kfr ya shiga. Ta sake tabbatarwa dr S makaryaci ne,makiri,azzalumi,yayi niyyar cutarta. Tayi kmr ta shiga ofishin ta dibi kwanukanta, in yaso tayi sallama dasu har abada. Sbd abokin fasiki shima in ba a yi sa'a ba fasikin ne. Sai taji ranta kawai har kwanukan bata so,suje su rike. Tayi wuf! Ta fice da sauri tfy take ko waiwaye bata yi burinta kawai ta ganta a cikin adaidaita sahu. UK KYAN TAKALMI 3* 2 Tazo fita ta get kenan sai taji wayarta ta dau ruri tayi sauri ta dauko 'yar jakarta,ta duba sai taga sunan dr. Lk ta danna a sanyaye sai yace, Aisha Farida kina inane? Ta dafe kirji tayi shiru can tace ina gida. Yace ashe bake bace wata na gani a cikin asibiti kmr ke sak! Ta gifta. Sai ya katse wayar, ta tsaya cak! Ta dubi hanyr ofishinsa ta dubi hnyr waje. Yayin data dinga shawarwarin inda zataje. Taji kmr ta koma ofishinsa ta shaida masa abun da abokinsa yayi mata,sai taga meye amfanin shaida masa din? Watakila ma bakinsu 1. Dn haka tayi tfyrta. Tana cikin a dai daita sahu tana sharbar hawaye ta sauka a unguwarsu ta gangara gida, dk wanda ya hadu da ita a hnya saiya tmbyeta farida lfy? Tace bani da lfy. Sbd sunga kuka takeyi haikan, kuma tfy take kmr zata fadi. Ta kunshe fuska a cikin hijab, ta shiga gida dn bata son mutanen gida su gane tana kuka. Ta bude daki ta shiga sai ta yaye hijabin ta urgar ta dora kannu aka ta rusa kuka mai sauti. Tayi sauri tasa hannu ta kunshe bakinta, dn kada 'yan gidan su jiyota. Ta drkushe kasa tana fadin, Allah ngd maka daka bayyana min waye dr.S 2nda wuri. Allah ka yaye min sonsa, ka masanya min da wanda yafi shi alkhairi. Ashe abida tayi gsky data ce in rike addu'a, Allah shi yasan dai-dai idan bawa yana son abu yaga Allah bai bashi ba. Bai sani ba ko abun ba alkhairi bane a gareshi. Na rasa Dr S,na rasa ka har abda, na hakura da kai. Bana sonka, bana marmarin in sake haduwa dakai a rayuwata. Ta jawo wayarta ta nemo sunan goggon mahaifiyar abida,dk da tasan halin da abida ke ciki,amma babu yadda zatayi ne, dole ita din zata fadawa don in bata fada ba zuciyarta zata iya fashewa a yau. Ina anti abida? AF ta tmbyi goggo ko gaisuwa babu. Lfy? Ta tmbya cike da damuwa. Jikinta zan tmbya,kuma ina so a bata waya mu gaisa. Inji AF. Goggo tace bana so kuna maganr nan, dn kuka naga tanayi, ban san me kike fada mata ba. Marar lfy baya son damuwa fa farida. Ta jiyo muryar abida tana cewa, googgo ki kawo min wayar, bakiu san abn da zata fada min ba. Farida bata da kowa a duniya saini. Idan da sauran nmfashi na a duniya ban mu2 ba,ai zan saurari matsalolinta. Goggo taje ta karawa abida waya a kunne. Abida ta ambaci sunanta sai AF ta rushe da kuka. Tace anti ashe Dr.S dan iska ne? Wai zai kaini gdnsa mu huta. Abida tayi dariya tace,kada ki yanke hukunci,kibi a hnkl. Ba gsky bane, kici gaba da addu'a kanwata. Takaici ya sake bullowa daga cikinzuciyar AF da taji amsar abida, saita katse wayar. Karar shigowar sako ne ya shigo wayarta. Ta duba da sauri sunan Dr.Lk ne nan da nan ta cika da mamaki. Tana kokarin budewa ta karanta sai wani sakon ya shigo. Ta duba taga sunan Dr.S ne,ta gyara zama ta mike kafa yayinda hawaye ya hadu da gumi suka damalmale mata fuska, ta dora hannu aka ta fasa kuka. Taji hnklnta ya tshi dn bai kamata ta zama haka ba a wajensu dr.lk ba, abn arzikin data keyi musu bai dace su saka mata da tsiya ba. Me tayi musu a rayuwa da zasu hada aki su cuce ta. Ashe son da Dr. Mohd yace yana yi mata dk tsokana ce,yaudarata sukeyi kenan? Zuciyarta tana duka 3 3 a lkcn da zata bude sakonnin dn fargabar abnda zata karanta. Sai idanuwanta sikayi dusu dusu har bata gani sosai sbd tsananin kuka. Ta bude na frko ta karanta,sai ta dafe krji yayin da ta bude na 2 ta karanta,sai ta damko wuyanta dan mamaki,kuma sakonnin iri daya ne babu ko digo daya daya bambanta. Ta zabura ta mike tsaye ta sake karanta dukka 2n hakika abn data gani dazu shine ba gizo idanuwanta keyi ba,gsky ne. Kin ci jarabawa Aisha Umar,fito muna kofar gidanku". Abinda Allah ya nuna mata kenan a cikin wayarta(kunji ta fa sai kace wani wahayi wai Allah ya nuna mata lols) sako daga Dr.S da Dr.Lk,dukka abu daya suka rubuta mata. Ta cika da mamaki sai tayi sauri ta jawo wani tsohon zaninta ta fafface ta goggoge fuskrta tayi wasai,sannan ta goggoga 'yar hoda ta sake saka hijabnta. Hannunta sai karkarwa yake ta sala takalminta ta fito a nutse tana sanda. Bata tabbatar da abunda suka rubuto mata ba ko gske ne,amma dao gara taje ta duba. Da fitarta Dr. S I ta fara hangowa tayi sauri ta sake duban na kusa dashi, Dr. Lk ne,sai taga sun dubi junansu sun kyalkyale da dariya. Ta snkyr da kanta kasa ta karaso gabansu ta durkusa ta gaishe su. Dr. Lk yace,srkn kuka, kin daina kukan ne? Dr.S yace,farida kin bar min ofishina a bude har an yashe ni. Tay ajiyar zuciya,ta grgza kai ba tareda tasan abnda zata fada ba. "Kin ci jarabawa Aisha Umar,fito muna kofar gidanku". Abinda Allah ya nuna mata kenan a cikin wayarta(kunji ta fa sai kace wani wahayi wai Allah ya nuna mata lols) sako daga Dr.S da Dr.Lk,dukka abu daya suka rubuta mata. Ta cika da mamaki sai tayi sauri ta jawo wani tsohon zaninta ta fafface ta goggoge fuskrta tayi wasai,sannan ta goggoga 'yar hoda ta sake saka hijabnta. Hannunta sai karkarwa yake ta sala takalminta ta fito a nutse tana sanda. Bata tabbatar da abunda suka rubuto mata ba ko gske ne,amma dao gara taje ta duba. Da fitarta Dr. S I ta fara hangowa tayi sauri ta sake duban na kusa dashi, Dr. Lk ne,sai taga sun dubi junansu sun kyalkyale da dariya. Ta snkyr da kanta kasa ta karaso gabansu ta durkusa ta gaishe su. Dr. Lk yace,srkn kuka, kin daina kukan ne? Dr.S yace,farida kin bar min ofishina a bude har an yashe ni. Tay ajiyar zuciya,ta grgza kai ba tareda tasan abnda zata fada ba. "kinsi jarabawa farida". Inji dr.S. Dr.Lk kuma yace wlhy abokina gwadaki yayi muna zazzaune a cikin motata a lkcn da kika fito kika nufi get shiyasa nayi miki wannan wayar. Niyyarmu mu dauko ki mu dawo dake gida,sai yace gara mu biyo ki a baya muga gidanku. Ta sake yin dgwr ajiyar zuciya ta dago da sauri ta dubi Dr.S sai yayi mata mrmshi ma kayatarwa. Taji sanyi a cikin zuciyarta,farin ciki marar misaltuwa ya tabbata a zuciyarta. Ji take tmkr anyi mata albishir zata shiga aljanna. Dr.S yace yanzu ke in aka ce miki haka nake zaki yarda? Ina da kyakkyawan zato a kanki saina ke so in tabbatar da hakan, dn haka ni da abokina muka shirya jarabawa muka baki. Allah cikin ikonsa sai kika cinye dukka. Mrmshi takeyi har yanzu,bata ce komai ba, mun baro aiki da yawa muka taho a yi hkr a gafarce mu idan munyi laifi da muka shiryo wannan gwaji,sbd mun saka ki kuka da yawa. Ta rufe ido tayi dariya tace, bakuyi laifi ba yayana. Dr.Lk yace,idan akwai yaro yazo ya biyo mu mota ya karbar miki kwandon ki mun taho miki dashi. Tace, to bari in shiga gida in turo yaro ngd sai anjimanku. Kallonta kawai Dr. S yakeyi harta shige ciki. Ya grgza kai yace, lk nan ne gidansu da gaske? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Yanzu daman a irin wannan gidan take rayuwa? Dr Lk yace, da alama kuwa gidan haya ne basu kadai bane dn ina nan a tsaye ina ganin mata iri iri suna leko mu. A cike gidan nan yake, irin hayar nan ta dakuna birjik,bandaki daya. Yanzu a cikin bakin gidan nan daman ake dafa mana dambu da danwake muke ci? Dr.Lk yace, to bakin gida, bakar tukunya ce? Ai kanwata tana da tsafta,a tsaftace abincinta. Kai fa a ni'ima kake shiyasa baka san ana wahala ba a kasar nan. Dr.S yace, gsky ana wahala aini ban taba shigowa lungun nan ba 2nda Allah ya halicce ni. Ai bansan irin wannan gidan farida take ba, daban zargeta ba don tana hawa acaba. Alla srki ashe rashi ne yake sakata hawa acaba. Bai rufe baki ba saiga wani dakwalkwalallen yaro hancinsa fal da majina yace, wai gani inji Aisha Farida kuna kirana. Dr S ya dubi yaron ya juya ya dubi Dr.Lk sai suka tun tsire da dariya. Dr.S ya ce Allah mai halitta,yaro Allah yasa kayi ilimi ka fita fili ka rabuda irin wannan rayuwa. Ya kama hannunsa yace, zo muje abokina,yaya sunanka? Yaro yace,sunana Dahiru. Dr. S yana tafe yana sake waiwayawa yana duban gidan su Aisha Farida,yana sake kallom unguwar da kwatoci, baya ga sauro da kudaje suna ta shawagi. Dr. S ya dorawa Dahiru kwando aka ya bashi naira #500 suka shiga mota suka tafi. Har suka isa asibiti Dr. S bai fasa jajantawa wadannan bayin Allah ba, musamman abar kaunarsa AF. Yaji ya sake tausaya mata, ya kara sonta,kuma ya kudiri niyyar taimakonta. AF ta shiga gida zuciyarta cike da frn ck,harma ta kasa fasalta irin frn ckn data tsinci kanta a yau. Tana shiga daki ta cire hijabi ta dauki waya ta kirasu abida aka ci sa'a knwrta maimuna ce ta dauka. Byn sun gaisa sai tace tabwa anti A zasuyi mgna. Maimuna ta karawa Abida a kunne. Abida tace AF ya ake ciki? Tayi dry tace, Anti A ngd wa Allah ngd miki. Yanzu Dr.s yabar kfr gdn nan shida Dr.lk ashe mgnr nan daya fada min so yake ya gwasa ni yagani 'yar iska ce ni? Yace naci jarabawa. Abida tayi mrmshi tace, naji a jikina Dr.s m2mn kirki ne, ko byn raina ki zama mai kyakkyawan zato a kansa. AF taji jiknta yayi sanyi tace,zaki ji sauki anti,ki daina fdr haka. Ngd. Abida tayi mrmshi tace, yanzu zaki wuce mataki na 4 zaki taka mataki na 5 shine ki nuna masa tsantsar soda kulawa. Idan ya gasgata kina sonsa sbd Allah sima zai soki a zuciyarsa,yasoki harma ya fara 2nanin yadda zaki kasance a matsayin matarsa, ku zauna din-din-din. AF taja dgwr ajiyr zuciya tace, to antina ngd,Allah ya baki lfy. Abida tace Amin. BABI NA GOMA SHA UKU Dr. S ya shigo falon mahaifinsa a wannan safiya dn ya gaishe shi,ya iske shi a zaune akan dgwr kujerarsa. Byn sun gaisa shrm ya zauna a kasa kan kafet a gabnsa yayi murmushi ya dubi mahifinsa. Yace, Abba naga alama kana jin dadin jikinka,maganin nan da aka sauya maka yafi wancan karbarka. Ya jawo kafarsa ya dora akan cinyarsa yana mammatsa masa yatsun kfrsa. Abba ya dubi S shima yayi mrmshi yace, Alhmdllh,ciwon kafar yana yin sauki. Dr.S yace,Allah ya kara lfy abba. Ka dinga rage zirga'zirga ina ganin kana dan takurawa kfr da yawn tfy,dk da ana so a dnga dan tattakawa amma ba dgn yawo ba yadda kake yi,baka son yawo amota sosai. Abba yayi dry yace, shuraim zumunci a kafa yake,idan da kfr nan zata to tabbas bazan zauna ba sai na taka naje na gaisa da 'yanuwa da abokan arziki. Kada ka damu,dk anda kaga m2m yayi sai yanada halin yi zaiyi, musamman lfy. Idan a kwance nake ina ciwo ai zama ma sai an zaunar dano. Haka idan ina kabari,ai zancen ziyara ya kare 2nda ina raye to dama ce dani. Ka sani kada ka yanka zumunci,dmn zumunci abune mai girma,shi zikai ka aljanna. DUK KYAN TAKALMI 3* 3 2ni dr.s ya sulale ya kishingide akan dgwr kujerar da yake zaune,sbd tsananin jin dadin kalaman abar kaunarsa dadada. Yayi mrmshi ya lumshe ido yace, kin ceto rayuwata wacce take cikin garari da hatsari ada, dn 2nu na fara sallam frn ck akan rashin samun bayananki. A zatona na fada trkn mace, allah zai sakawa wadanda suka dade suna son maso wani, kuma suna zargina nine sila. AF tayi mrmshi tace, na fhmce ka, ni zan baka labarin wannan, dmn mune a bayn fage, mun fika ganin abubuwan da suke faruwa. Kai takalmi ne mai tsananin kyau da tsada dmn tmkr anyi ka daruwan zinare da lu'u'lu'u. A ganina,ko kuma nace a wajena, ban taba ganin kyakkyawan takalmi kayatacce irinka ba,sai masu kudi ne suke iya takawa dk da haka ba a sallama musu ba. Mu talakawa kuwa daman sai dai mu daga ido mu kalla, ko kusa dashi ba zamu iya karasawa ba, balle mu gani sosai harmu taya. Sai mai takalmin wanda ya halicci takalmin da kansa, Wato Allah (s.w.t) ya ce farida ga takalmin nan na baki kyauta babu ko sisisna. Ka kwatanto wanne itin frn ck ne bazanyi ba? Dole na fashe da kuka dn murna. A halin yanzu sbd tsananin kyawun takalmin bana so yayi kura,bana soya wahala. Takalmin da aka sanshi a kafa sai gani ina daura shi a goshina,mutane suna kallona sbd basu taba ganin tsadaddade kuma kyakkyawan takalmi kmr irin nawa ba. Abnda suke tmby ta shine yaya akayi kafata babu takalmi ina yawo a titi a haka,maimakon in saka takalmon sai kuma na daura a goshi? Amsar itace, wannan takalmin daban ne bana takawa bane a kafa,dmn yafi karfin kafata. Dan naso na rasa raina,na rugurguza rywata akan neman takalmin nan, ubangiji ya dube ni, ya bani tabbas zanfi kowa tattalinsa shiyasa ma nake daura shi a goshi dn bana so yayi kura. Dr.s yayi shiru yana sauraronta, 2nda Allah ya halicce shi bai taba haduwa da yarinya mai kima da iya magana ba, hausa ckn jausa,sai AF. Ya fhmci wasu abubuwa data ke nufi, wasu kuwa sai ita da ubangijinta suka sani. Yayi mrmshi yace, "Lallai kin kawata takalmin nan,har kin kara masa kyawun da bashi dashi. Kin kara masa drjr da bai kai can ba. Dole mutane su kalleki idan suka ga ki daura takalmi a goshi,maimakon ki saka a kafa. Nima baz zanso ki zama abar kallo da nunawa ba a duniya,sbd kyakkyawan takalminki,kyawun takalminki baifi na kowacce mace ba. Dk iri 1 ne a idanuwanki ne ke kadai kike ganisa da kyau,da daraja irin yadda kika suffanta shi. Idanma yana da kyau, to baifi krfn a saka shi a kafa ba a taka, ina umartarki daki sauko da kyakkyawan takalmin nan naki daga gshnki ki saka shi a kfrki ki tattaka shi, domin 'DUK KYAN TAKALMI' a kafa ake takawa. Yayi dariya ya kashe wayar ba tareda ya jira abinda zata fada ba. Tana zaune ta daskare ta zama tmkr an sassakata sbd al'ajabin abubuwan dta ga suna gudana. Ta fada a ranta, banda ubangiji wa zaiyi min wannan kyautar haka? Haka dr.s ya fara sona yanzu? Tsarki ya tabbata ga ubangijin talikai. Allah ngd maka,Allah ka bawa abida lfy,ta zo ta ganni tare da dr.d a wannan kyakkyawar inuwar da muke ciki. Sai yanzu sakon katin brsta mu'azzam ya shigo,ta kalla tayi mrmshi tace, yayana aika makara 2n yaushe takalmin goshina ya dawo kafata? Sai dai ban fara taka kasa dashi ba har yanzu ina zaune akan katifa dashi. BABI NA GOMA SHA HUDU Rayuwa mai sauya salo dr.s baya jin dadin rayuwarsa idan bai kira AF sau 3 ko 4 a rana ba. Kiran sassafe, da hantsi ko da rana, wataran ya kira da yamma sannan kiran dare sole ne idan yazo kwanciya. Tana mamaki dajin dadadan kalamansa,sai ta fara neman bakin ciki da damuwa ta ra,dk sun baje. Abu daya ne ya kasa gushewa a ckn zuciyarta,kuma ta kasa daina buya tana kuka a kanshi,shine rashin lfyr abida. Tana ma2kar addu'a Allah ya bawa abida lfy,tazo ta ganta da dr.s. Allah mai yadda yaso da bayinsa,abida na can a kwance jiya-i-yau, sai an tayar sai an kwantar. Allahu akbar. Sati uku ya rage yara suyi hutu yaya hussani ya tattara su,su kaura shagamu kacokan, musamman wannan satin da yaje dubata yaga yadda ta sake kumburewa, sai hnklinsa ya tashi yana kuka suna kuka haka suka rabu. Harya fara shirye shuryen barin aiki yana 2nanin sana'ar da zai fara a shagamu,son idan babu abida a kano babu zancen sauran jin dadi a kano a rayuwarsa. Ya sanarwa da AF dn ta fara kammala kayansu gaba 1 a waje daya, hnklnta ya tashi ma2ka sbd rabuwa da dr.s shine kadai abnda zatayi takaicin rabuwa dashi a kano,bayan shi dk sauran wasa ne. Ta kasa 2nkarar yayanta ta fada masa tsakaninta da dr.s haka ta kasa fadawa dr.s zasu kaura shagamu,dn kada ta tayr masa sa hnkli. Yace,sweet heart yaya akayi ne? Nazo fa daf da zauren gidanku,ina bakin kofa. Taji zuciyarta ta sake harbawa,muryarta na karkarwa tace,gani nan zuwa. Ta danna lmbr y.husaini dn ta nemi izini, bai dauka ba,dn haka saita tashi da sauri ta sauya kayan jikinta. Wata sabuwar atmfrta ta daura mai suna binta,dinkin raga da siket ne, matsattsu,hoda da kwalli kawai ta saka ta dauko hijabinta ta saka. Sai taji wayarta tana ringin ta duba taga yayanta ne yake kiranta dn yayi mamaki da gani kiranta a daidai wannan ljcn sai hnlklnsa ya tashi ma2ka,zuciya mai sake sake saita dinga sassaka masa abubuwa daban2. Babu abnda bai tuna ba,ya aiyana a ransa ko bala'i ne yasamu dya daga ckn 'yayansa ko ita AF, ko kuma mai kacokan abar kaunarsa ce ta mutu aboda. Cikin sauri ta amsa, muryrsa na karkarwa ya tmbyta farida,lfy? Kmr yadda ya shiga tshn hnkl haka ya jiyo alamun itama tana ckn hnkli irn nasa dan haka sai ya sake sukurkucewa. Mryarta na rawa tace, yaya,dr.s ne yazo yana kfr gida inje wajensa? Ya fusata ya daka mata tsawa yace, waye dr.s? Tace mu2min daya zo rannan.makwabta suka fada maka kace karka sake ganinsa a gidan nan. Ya sake hasala yace, kince nace kada ya sake zuwa, me ya kawoshi yanzu? Kice masa yabar min kfr gidana idan nazo sai naci mu2ncin ku keda shi. Ya katse waya. Ta dora hannu akai ta rushe da kuka tana fadin, innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Yau ya zanyi? Wayyo sr.s dina,ina sonka bana so na rasaka. Yaya me nayi maka zaka rabani da frn ckn rayuwata? Wayar tace tayi kara saita duba taga s ne,nan da nan ta damma ba tareda tasan abnda zata ce masa ba yana magana ckn marainiyar murya. Yace,sry farida,na takura miki ko,nazo ba tareda na sanar dake ba? Ba damuwa bari na tafi zamu hadu wani lkcn. Sai taji hnklnta ya sake tashi kuka mai tsanani ya rifto mata. Yace,kukan meue kike farida? Cikin sheshekar kuka tace, dr.s kayi hkr ka yafe min. Sai ya sulale ya zauna akan dakalin kfr gidan dan da a tsaye yake sbd gigicewa. Lfy? Ya tmbyeta. Kuka kawai take ba tareda ta iya yi masa bayani ba sai ajiyar zuciya. Yace,farida fito ina kfr gdnku muyi magana sosai. Ya kashe waya yacigaba da huci sbd tafrfasar da zuciyarsa takeyi masa. Da aka jima bata fitoba dr.s ya sake kiranta sai ta amsa kuka kawai take ba tareda ta iya yi masa bayanin komai ba. Yayi ajiyar zuciya yacemfarida,fito ina kfr gidanku muyi magana sosai. Saiya kashe wayr bai bari ta bashi amsa ba. Ta yanke shawarar ta fita wajensa koda kuwa yaynta zai kasheta. Tana fitowa sai taga abin kaunarta yayi shiru kmr mai 2nani,hnklnsa dk a tashe. Ta durkusa ta gaishe shi,bai amsa ba sai hararar daya dinga harba mata,musamman yadda yaga idanuwanta sun kumbura sunyi jajur sbd tsananin kukan da tasha yi. Ya grgza kai dn takaici yace, faridah,haduwata dake wani sirri ne kuma hikima ce daga Allah, ba zato babu tsammani Allah ya jeho ki sikin rayuwata,kuma cikin hikimarsa ya smr miki wajen zama mai fadi a ckn zuciyata. Na tsinci kaina ina mai frn ck da saninki,dn naji a jikina ke alkhairi ce a gareni. Naji ina sonki,halayyarki a zahiri tayi min. Sai dai kash kina da wata damuwa,ko manufa a ckn zuciyarki wacce tayi bam bam da tawa. Ina zafgn bakya sona na takura miki ko kuma ince akwai wanda kike so,amma kun rabu wala Allah ya rabu dake kina tsananin sonsa,koya rasu kina cikn kaunarsa,idan nazo ko kikaji maryata sai inyi miki fami ki 2no dashi. Haka ne koba haka bane? tayi sauri ta girgixa kanta hawaye ya sake kwaranyowa tace ba haka bane yaya abinda kake xargina dashi.kuma ina patan xaka yarda da abubuwan da xan pada maka yanxu don bana 2nanin ko a maparki in pada maka karya a rayuwata saboda kana daya daga cikin mutanen da sukeda muhimmanci arayuwata Tayi sauri ta girgiza kanta,hawaye ya sake kwaranyowa,tace,ba haka bane yaya,abun da kake 2nani gaba 1 baiyi shige da abun da kake zargina dashi ba. Kuma ina fatan zaka yarda da abubuwan da zan fada maka yanzu dn bana 2nanin ko a mafarki in fada maka karya a rayuwata,sbd kana 1 daga cikin mutanen da suke da mahimmanci a rayuwa. Dr s, zaka iya mamaki idan nace kaina kadai frn ckn rayuwata, ina yi maka son dakai baka yimin. Haka ina maka son da ban taba yiwa wani d'a namiji ba a duniya. Son da zan iya shiga halaka idan na rasa ka. Kuka da nakeyi na frn ck ne sbd Allah ya amsa addu'ar dana dade ina yi akan Allah ya hadani da bawansa mai kyawawan halaye,kuma mai kaunata sbd Allah yasoni a yadda nake talaka,kuma marainiya. Ya kawo min kai wanda ko makahon dabai taba ganin duniya ba ya tsaya a tsakiyarmu yasan ka wuceni a komai. Dr.s bazan boye maka komai ba,yau kukan da nake na tshn hnkli ne,domin yayana yana kokarin ya rabani dakai,frn ckn rayuwata a sanadiyyar 'yan gulma da suka soke ka. Yaki ya tsaya nayi masa bayaninka, da kuma inda muka hadu,yace, na cika shige2,na dauko wanda yafi mu zan jawo masa masifa da tshn hnkli kada in jawo azo a kama shi. Y.husaini zai tafka babban kuskure idan yayi gangancin rabani da frn ck na, dn zai iya rabani da rayuwata gaba daya. Ta fashe da kuka yayinda dr.s yana zaune ya zuba mata ido yana dubanta kawai tmkr a hoto. Babu abnda yake sai mamakin yadda Allah ya sauya masa rayuwarsa nan da nan akan mace. Bai taba tsintar kansa ckn irin wannan hargitsin ba, abn da yakeji a gari yazo kansa. Bai iya cewa komai ba har yanzu kallonta yake,ta sharbe hawaye face2 a hannayenta. Tana waigawa gefenta saita hango yaya husaini ya sauka daga kan acaba. Nan take dr.s yaga tana makyarkyata ta fara ja da baya. Da sauri ya soma tmbyrta, mene ne kuma? Ta nuna yayanta da hannu tave, yaya hussaini ne, idan ya sameni anan dukana zaiyi. Dr s ya umarce ta data shiga gida,tayi wuf ta fada cikin gida jikinta na bari. Cincirindon matan gida da 'yayansu ta gani a lallabe suna leko su. Ta kalle su sama da kasa ta watsar ta shige daki taci gaba da kuka, ta kasa zaune ta kasa tsaye,addu'a kawai take kwaranyowa tana fatan Allah ya huci zuciuyar y.husaini kada ya yiwa dr s wulakanci. Idan ta zauna saita zabura ta mike tsaye tana ta kai kawo daga frkn daki zuwa karshen bango tmkr zararriya. Gashi babu tagar da zata leka ta hangosu. Bata san halin da suke ciki ba. Dr s ya dubi y.h yayinda shima y.h yake kallonsa 2n daga nesa kallo ne mau tafe da harara galleliya,kokari y.h yake ya shige cikin gida ba tareda ya tsaya sun gaisa da dr s ba. Shi kuwa dr s saiya 2nkaro shida sauri yayi mrmshi yayi masa sallama gamida mika masa hannu. Babu yadda y.h zaiyi a dole ya amsa masa sallamar ya mika masa hannu ba dn zuciyarsa naso ba. Suka janye hannunsa a lkc 1. Har yanzu y.h kokari yake ya shiga gida yabar dr s a tsaye. Ya sake matsowa yasha gabansa. Yace, sunana dr s i. Ina aiki a asibitin malam aminu kano. Nine wanda nake zuwa wajen af kanwarka. Y.h ya yamutse fuska a dole ya tsaya cak ya saurari dr s yace,na sami labarinka ai. Dr s yayi lallausan mrmshi alhali zuciyar na cike da tsananin takaicin wulakancin leburan nan keyi masa. Yace, nazo in nemi alfarma 1 shi ne,kada ka zargi kanwarka,kada ka zageta,koka doke ta bata da laifi ni nake sonta,kuma na biyo ta gidansu ko a yanzu fitowar data yi tazo ta fada min ka hanata fitowa inyi hkr in tafi sai gaka nan ka dawo. Na 2 kuma nazo neman izini,kabani dama in dinga zuwa wajen kanwarka,sbd ina sonta,idan kuma Allah ya lamunce min inaso in aureta. Y.h ya sake daga ido ya dubi dr s cike da mamaki,yayi masa kallon mayaudari. Yace, ta yaya zaka aureta? Dr s yayi mrmshi yace, malam husaini yi hkr da tmbyr da zanyi maka. Da Allah kana ganin nayi maka kama da lalatattun samari zauna gari banza,masu yausarar 'yan mata? Am i nt responsible..... Dakata ba wannan na tmbyeka ba malam,farida kanwata ce ina da alhakin in zaba mata mijin da yayi dai- dai da rayuwarta,inda ba zata wulakanta ba. Y.h ya fada a fusace gamida dago hannunsa ya tsayar da dr s. Ai anan dr s ya daskare a tsaye yana kallonsa kawai ba tareda yasan kalma 1 dazai furta ba. Hakika ya kasa gane ida y.h ya dosa. Yabi shi da kallo har ya shige ckn gida. Ya sulale ya zauna akan dakalin kfr gidan yayi shiru kansa a sunkuye a kasa yana 2nani. Babu abnda zuciyarsa bata aiyana masa ba. Ya aiyana ya tashi yayi tfyrsa kawai ya rabu da Aisha farida har abda, sai ya tuna nasihar da mahaifinsa yayi masa cewar, ya zamana mai yawan hkr a wajen neman auren,domin aure ya gaji irin wadannan sabani da matsaloli daga kowanne bangare. Yaji yana son farida a ransa ba karamar wahala zaiyi ba idan yayi garajen rabuwa da ita. Yaji a jknsa jihadi zaiyi babba idan ya aure ta ya fitar da ita daga wannan kangin talaucin. Saiya saka a zuciyarsa zaiyi damarar yaki tsakaninsa da y.husaini har saiya wayar masa da kai ya gane kyautar da Allah ya 2uro masa har gida. KYAN TAKALMI 3* 4 Yaga maza suna ta daura alwala suna tunkarar wani karamin masallaci kusa da gidan,don haka sai shima ya bisu a baya. A bakin masallacin ya samu buta ya tsugunna yana alwala sai ga y.hssn ya wuce shi zai shiga masallaci. Da alama y.hssn yayi matukar razana zuciyarshi ta cika da mamaki da yaga dr shrm bai tafi ba, kallon kallo suka dinga yi har ya shige domin har an tayar da ikamar sallah. Da aka idar da sallar magaruba da yawa basu tafi ba, sai aka hau kara karatu a takaice dai islamiya ce ta maza. Dukda babu wutar lantarki babu genereto sai fitilon kwai da hasken wayoyi ake haskawa ake karatun. Ya hssn yana daga cikin dalibai sai dr shrm ya matso gefen sa ya zauna yayain da shima ya samu qurani ya bude yana karanta duk surar da ake dora masu. Kallon dr shurm kawai suke ba tare da sun san daga inda ya fito ba, musulmi danuwan musulmi ne saboda haka basu razana ba, basu tsorata ba kuma basu damu su tambayeshi daga inda ya fito ba. Da aka idar da karatu sai aka kiRa sallar ishai kan kace kwabo masallaci ya cika sai aka tayar da ikamar sallar ishai. Ya hssn ya fito da shi da yangidan su suka nufi kofar gidan bayan an idar. Tsilun ya sake ganin Dr shrm a cikin tawagarsu suka iso har kofar gida akan tabarmin su suka zauna, inda aka fara fito da kwanukan abinci daga kowanne daki ma'ana ciyayya suke idan anci na wannan sai aci na wannan. Malam yushau ya dubi Dr shrm cike da mamaki yace samari daga ina? Tundazu nake ganin ka a masallaci yi hakuri da tambayata bamu sanka ba. Ya hssn yayi caraf yace tare muke dashi. Sai su duka suka cire tsoro da damuwar da suka tsunduma tuntuni, amma tambayoyi ne cike a zuciyoyin su, ina hssn ya samo wannan fallelen yaron, gashi masinja wannan kuma sai dai ace manaja ne a bankin, ina suka hadu suke abota? Dr shrm yaji dadin amsr da ya hssn ya basu ya samu kwarin guiwar fuskantar ya hssn yace yaya zan tafi ina ganin ba sai na tsaya cin abinci ba a koshe nake. Sai mutanen wajen suka yi masa caa akan ya tsaya yaci abinci harda yaya hssn. A dole dr shrm ya saka hannu ya gutsuri wani tattauran tuwon masara gabza wacce ba'a tankade garin da tsaki ba aka tuka shi, haka ya dangwalo wata bakar miyar kuka wadda ba'a sa nama ba sai warin daddawa kawai take. Ya kai baki babu abinda yake ji sai dandanon kafi zabo kawai a bain sa cauuu! Kan kace kwabo zuciyarsa ta hautsine yana shirin ya kwalaye amai amma ya daure da kyar ya runtse ido ya hadiye. Tun daga wannan lomar bai sake garajen kara kai wata lomar bakin saba, haka dai ya rinka tsoma hannu kamar ci yake ya debo tuwo ya dangwalo miya ya sake danna hannunsa cikin kwanon tuwon. Su kuma gogayen basu lura ba lomar tuwo kawai suke kaiwa cikin bakin su, kasancewar duhu ne babu mai ganin wani dadin abincin su suke ji yankan tuwon nan kawai suke suna kwaso miya suna afka shi a birnin cikin su. Kai kace naman kaji ne ko na talo talo. Mamakin su kawai dr shrm keyi yadda yaga suna iya cin wannan gabzar, sai yaji imani ya sake shigar shi, yaji ya sake godema Allah akan baiwa da ni'imar da yayi masa. Idan suka cinye wannan kwanon sai su janyo wani, a na janyo kwanon Aisha farida dr shrm yaji a jikinsa wannan na Aisha fard ne,saboda wasu dalilai da yaji a jikin sa, na farko ga irin food flask din da take kai musu abinci, na biyu ana budewa yaji irin kamshin abincinta na ukku kuma ga irin dambun da take kai musu. Ya dauki buta ya wanke miyar kukar da ta bata mai hannu, sannan yazo ya luma hannu cikin dambun da shi aka ida cinyewa cin gaske yai ma dambun. Kuma yana farin ciki don yasan daga masoyiyarsa ne. Ko tantama ba yayi yasan saboda shi tayi dambun nan saboda da zafin sa kauu! Ba a dade da sauke shi ba, yasan tana da labarin yana nan bai tafi ba. Tunda ga kan abincin nan yasan farida ta fita daban da sauran matan unguwannan, girkinta yafi na kowacce mace dadi da tsabta, haka yaji sauran mazan suna santi da yabawa. Saboda tsananin ansan cewa shine mai dadi sai aka barshi shine karshe. Da suka gama ci sai suka wanke hannu, dr shrm yaga alamar ya hssn bai da niyyar sake mike kafa yai ana sabuwar hira, sai ya mike ya babba su hannu yayi musu sallama, da alama ya hssn bai da shirin biyoshi su kebe, don haka sai ya dube shi yace yayana zan tafi kuma ban gama baka sakon da nazo ma da shi ba. A dole ya taso ya biyo dr shrm suka tafi can gefe guda suka tsaya. Dr shrm ya dubi ya hssn har yanzu sai cin magani yakeyi, zuciyar shi zuciyar shi tana yi masa kuna amma ya daure ya duka yace yayana zan koma amma fa bazan bar kofar gidan nan ba sai naji amsa daga bakinka. Amsar me ya fada cike da gadara. Dr shrm yai ajiyar zuciya yace ka bani dama in zauna da ku ahankali zaka san ko yaya nakeson farida. ... Wurin is not clear.. Tana da bukatar nazari sosai, ka bani lokaci har sai na nemeka. Dr shrm yayi shiru na wani lokaci yana kallon ikon Allah, ya rasa me yai ma ya hssn haka ya tsane shi, ko da wasa bai taba tsammanin zai tsinci kansa a cikin hali na wulakanci irin haka ba, lallai ashe da bai san rayuwa ba sai yanzu ya fara sani? Da kyar ya bude baki yayi magana yace to yaya na gode ISA zaka sameni mai kiyayewa kuma da yin biyayya akan duk abinda kace, kuma yadda kace haka za'a yi. Ka bani lambar wayarka sai na kiraka naji duk abinda ka yanke. Ya zaro dalleliyar wayarshi sai yaga msd calls din AF har guda ukku, yay hssn ya karanto mashi nmbr ya rubuta ya kira nmber ya hssn ya ciro kwarabbyar wayarsa ya kalli nmber yace to na gani zan adana nmbr. Dr shrm yayi godia suka yi sallama ya nufi motarsa yayn da ya hssn ya dawo kofar gida inda ya barsu ya iske su suna hira da suka ganshi ma basu daina yi ba domin yaji abinda suke fadi. Mllm sadisu ne ya dubi mllm yushau yace ni wannan ba shine mutumin da suka zo wajen AF ba wadanda suka zo da wata babbar mota ba, mllm yushau yace shine mana ai daga ganin wannan yaron mayaudari ne, ba maganar aure bace ta kawo shi. Malm lawal yace to ni ba wannan ba ma, mutumen da ba'a san asalin sa ba ba'a san asalin kudin suba. Ya hssn dai yana gefe yana kallon su yayin da zuciyarsa ta ci gaba da gasgata zancen su, mllm sadisu ya kalli ya hssn yace kai yaro ne kuma kai bako ne mu muka san kano muka san mutanen ta, don haka ka gaggauta raba shi da kanwarka, gara dan unguwa da aka san asalinsa da sana'arsa. Sauran ma suka tsoma baki suna goyon bayan abinda mallm sadisu ya fada. Ya hssn yaji kanshi yai nauyi kamar zai fashe saboda toshewar tunani, ya yanke a ransa raba AF da Dr shrm shine abu mafi sauki a rayuwarsa. Dr shrm ya kira AF yana fitowa daga unguwarsu, basu daina magana ba har sai da ya iso gate din gidansa, mai gadin sa ya bude masa gate. Ya shaida mata ya iso gida zai shiga yayi wanka ya ci abinci zai kirata kafin ya kwanta. I love you baby ita ce kalmar karshen da yake gayama duk lokacin da suka gama waya. Ta sulale ta kwanta akan tabarmarta don dadin da zuciyarta keyi, Dr shureim yayi mata hira mai dadi wanda bai taba yi mata irinta ba tun sanda suka hadu, ya fayyace mata abinda ke cikin ransa watau irin dimbin kaunar da yake mata, yace ta kwantar da hankalin ta, duk rintsi yana tare da ita babu gudu ba ja da baya. Yana da kykkyawan zaton matsalolinsu sun kusa karewa saboda ya fara shawo kan ya hssn sannan ya shaida mata ra'ayin sa akan ta idan Allah ya ruboto mas uzasu zamanto miji da mata yana da ra'ayin ya aureta. Dama ta dace da irin matar da ya keson zama da haka ma mahaifinshi. Dukkan godia sun tabbata da Allah SWT abinda Aysha f take ta maimaitawa kenan take kuma fadi a zuciyarta. Kamar bango zai tsake ras haka ta ji ana ambaton sunanta muryar yaya hussain ne daga dukkan alamu a fusace yake. Sai tayi firgigit ta tashi zaune ta dafe kirjinta tana fadin innalillahy wa inna ilaihir rajiun! har yanzu bai daina kwala mata kira ba sai ta mike da saukri, tana amsawa muryarta na kakkarwa ta fito da ga dakin ta sauri ta iske shi a bakin kofar dakin, tayi sauri ta durkusa a gabansa cike da ladabi. Ki biyoni dakina ya fada a fusace sai ya juya.... Maganar boye boye ta kare dan kowa yau zai fadi ra'ayinshi yau ita da shi, don daga dukkan alamu baiyi amanna da zuwan Dr shrm ba itama kuma ba zatayi amanna ya raba ta dashi ba. Ayau tayi damarar tunkarar duk wata muzgunawa, zagi, duka da duk bakaken maganganun da zai yi mata, don ba zata iya dadada masa ba ita ta kuntata rayuwarta. Bata taba yi masa mus ba amma yau zata fara saboda kyakyawan takalminta Dr shurm. Ya hussn ya shiga daki ya zauna a gefen katifa yayin da AF ta tsugunna a bakin kofa. Ya daka mata tsawa shigo ciki ki zauna munafuka. Ta shige lungu yayin da jikinta yake ta rawa don fargaba. Ya dade yana harbo mata harara, takaici yasa ya kasa magana, can yayi tsaki yayi ajiyar zuciya yace. Farida yaushe kika zama jin magana, marar daukar magana? Waye yake zugaki kike yin abinda kika ga dama? Wai ke kin waye ko kina ganin yanda wayayyun kawayenki sukeyi kina kwaikayonsu, to bari kiji in gaya maki bazan dauki nauyin wannan a gidan nan ba. Ta sunkuyar da kanta kasa ta kasa magana sai hawaye ne ke ta kwarara daya bayan daya. Yay hssn ya ci gaba da magana cikin fusata tun rannan na fada maki kada ya sake zuwa baki ji ba, a waya nace kada kije wajen sa kika fita din, in yaso in kashe ki. Sannan yazo ya nace man yaki tafia sai na saurtare shi, to ki fada masa karshen magana kar in sake ganin kafarshi a gidan nan don kowa yasan yaudarece yakeyi ba auren ki zaiyi ba. Yaje can ya auro dai dai shi yar masu kudi, kima ki samu talaka dai dai ke ki aura yafi kwanciyar hankali. DUK KYAN TAKALMI 3* 5 Ta sa hannu ta goge hawaye ta gyara durkuson da takeyi, ta dube shi duban keke da keke tace yaya hussaini naji abinda kace amma naso ka bani dama nayi maka bayani kaji ta bakina nima tunda kaji ta bakin masu kawo maka gulman. Ya fusata yaji tamkar zai kai mata bugu sai ya fasa. Ta fada cike da tabbaci tace mutanen gidan nan mata da mazansu, wadanda ba sa kaunarmu da alkhairi. Burinsu kullum suga mun tozarta. Baka sani bane dan baka zama dasu a gidan. Ya sake fusata yace da na turaki karatu makaranta aka tura ki asibiti sai akace kije jajibo soyayya? Ashe daman ba karatun kike yi ba? Ke gwanar iya magana zakice min magulmata ne suke hadawa? Bangani da idona bane ko bai fada min shi likita bane daga asibitin? Ni bani da hankali sai wani ya fada min? Toh barikiji farida bake babu mutumin nan, idan kina so ki cigaba da jin dadin zama dani a rayuwarki. Farida ta dago da sauri ta dube shi tace naji abinda kace yaya, na yadda da abin da ka fada, amma ka sani raba ni da shuraim dinnan da kake kokarin yi tamkar rabani da raina ne. Sai ya dago ido da sauri ya dube ta yayi mamakin ganin idanuwanta a tsaitsaye tana magana cike da tabbaci ko alamar kuka ma babu. Ta sake cewa shuraim bashi da aibu, kuma shi mai sona ne tsakani da Allah. Ina son shuraim fiye da yadda yake sona kuma sai da naci uwar wahala kafin na same shi. Anti abida tafi kowa sanin yadda abubuwa suka faru. Babu irin masifun da ban shiga ba a sanadiyyar sonsa. Sai yanzu da Allah Ya amshi adduata ya kawo min shi har gida sannan zasu zuga suce a raba mu? Ya sake cika da mamaki da jin kalamenta, yaci gaba da yi mata duba na rashin fahimta. Can yace farida me kike so kice min? Kina nufin kun dade tare dashi? Tun abida na da lafiya? Aisha farida ta muskuta ta zauna sosai ta fayyace masa gaba daya labarin abin da ya faru tsakaninta da dr shuraim tun daga ranar da ta fara ganinsa a duniya har zuwa rana irin ta yau. Yaya hussaini yayi shiru yana jujjuya maganan nan yadda abida tayi kicin kicin a cikin maganar. Sai yanzu da ta fada masa wannan labarun yake ta tunano wasu abubuwa da ya gani suna faruwa. Shiru kawai yayi musu. Misali a ofishin 'yan sanda ance wani namiji ne yazo ya fito da aisha farida babu mace yayin da abida tace masa mata da mijinta ne suka fito da ita. Haka yana sane da girke girken da sukeyi da asuba a jujjuye a sababbin foodflask , idan ya tambaya abida tace mara lafiya ake kaiwa kawar aisha farida Yaya hussaini yana matukar son abinda abida take so, shima zai so ace ya cika mata burinta koda bata raye. Yayi mata nuni da hannu alamar ta tashi tafi ya sallame ta don ya kasa sake cewa komai. Aisha farida tayi wuf ta fice daga dakin yayin da ta danji sanyi a cikin zuciyarta don taga alamar zai saduda. A cikin daren sunyi waya da dr shuraim kuma ta shaida masa yadda sukayi da yayanta. Duk da dai bata fada masa duka ba amma ta fada masa abubuwan da ta fada masa cewar raba ta dashi tamkar yana shirin raba ta da ranta ne. Sai dadi ya rufe dr shuraim, ya cika da mamaki. ASUBA TA GARI 'YAR SHAGAMUN LIKITA!!! BABI NA GOMA SHA BIYAR "Zuwa nayi ki maimaita min kalmar da kika fada min a waya a daren jiya. Inji dr s yake fadawa af a lkcn da suke tsaye a kfr gdnsu suna zance da yammacin ranar asabar. Af tayi mrmshi tasa hannu ta rufe ido dn kunya. Yace, daman na sani ba zaki iya fada ba,idan kika ganni amma a waya harda fada da maimaitawa. Toni bari na fada miki 2nda ba zaki iya fada min a fili ba. Ina sonki kmr yadda kaza take son kwanta,bazan iya rabuwa dake ba kmr yadda ba za a iya raba hanta da jini ba. Koba haka kika ce min jiya ba? 2nda nake ban taba jin irn wadannan kalamai ba sai jiya a bakinki. Kin iya hausa,sannan da wuya ki fadi marar amfani,shiyasa kike kara shiga raina. Na yaba da yadda kike sona sbd allah haka iana jindadin yadda kike kula dani a kowanne hali nake ciki,kina kula ki turo min sakon tausayawa da tausasa zuciya. Duk da har yanzu y.husaini baice min komai ba akn hukuncin daya yanke a kaina. Idan na kirashi ina jinsa faram2 nasan babu matsala.idan ma akwai matsala ina addu'a allah ya kawar da ita ya tankado mana da alkhairai. Af ta marairaice ido tayi mrmsh tace, amin ya allah. Tana rufe bakinta sai taji an daka mata duka a baya ance,shegiya aisha umar zance kikeyi da yamman nan? Tayi sauri ta waiwaya cike da takaici sai taga ummi kawarta ce. Al'amarin ummi sai addu'a sbd ta zama abar a tausaya mata, kai kace sabuwar mahaukaciya ce sbd rashin kwanciyar hnkl da talauci ko zanin daurawar kirki babu a jikinta,ita da goyon bakikirin a cikin tsummokarai. Yadda dr s ya kaikaice yana kallon ummi sama da kasa shiyasa af jin kunya. Da kunya ta nuna ummi tace kawarta ce,dk da ba zaman karya suke yi ba ita dashi. Sai suru2 ummi takeyi barkatai babu nutsuwa idan tayi magana daya saita dakawa farida duka ta dauko ashar ta kwararo mata,ta dauka burge shuraim takeyi. Kokari take ta tonawa farida asiri dn harta fara cewa badai wannan mu2min an bane,yazo da kafarsa? Suna shiga dakin af sai ummi tace,aisha umar wanne malamin ne ya tsaya miki kika sami wannan tsalelen,nima ki raka ni? Kada dai kice min likitan nan ne da kikeso baya sonki,wanda malam yayi miki aiki a kansa. Kinsan aikin malamn nan fa yanaci,yanzu gashi naki yaci yazo har kfr gidanku,gsky mu2mn nan ya hadu nifa na zaci baya jin hausa,na dauka farar fata ne,mu2min nan kadara ne,ga kyau ga kudi harya fiki kyau fa. Daman banda aikin malami yaya za a yi mu2min nan ya kalle ki,kinga yadda yake sonki kuwa naga sai wani kallonki yakeyi. Nima dai ba laifi ina dan ganin cigaba a ckn ayyukan dana rarrabwa malamai kashi-kashi matsalar da ake samu ni inayi,budurwarsa ma tanayi,uwarsu ma tanayi dn su raba mu. Shiyasa bana ganin abubuwana suna tafiya dai-dai. Dadin dadawa bani da kudi,kin san aiki sai da siyen kayan sadaka,duk kayan dakina sun kare,yanzu ko kmen zanyi ma banida ko katifa dk na siyar. Kinga yanzu ma daga wajen wani nake a lungun sharifai makociyarmu ta hadani dashi,shima dubu 3 yace nakai za a yi aiki,sannan a yanka kaza,shiyasa naji dadin dubu biyun nan daya bani. Af tayi shiru dn takaici ko iya kallon fskrta batayi na,tacigaba da kirga himilin kudinta data iske a cikin ambulan din daya bata. Sababbin 'yan dubu dubu ne har guda ashirin,dubu ashirin ya bata hade da wani dan karamin kati (greeting card) mai dauke da kalaman soyayya dadada 2nda Allah ya halicce taba a taba yi mata kyautar kudi mai dimbin yawa ba irin wannan,dadin dadawa kyautar daga wajen masoyinta ne. Ta gama karanata katin, saita rungume shi a kirjinta, tace Allah srk likitana. Kai Allah kaine abun godiya ngd maka. Ummi tazo ta nanikewa af,tace,cafdi dk wannan himilin kudin,ke ya bawa? Daman ance ana yin asirin bada kudi sai kaga mu2m yanayi maka kyauta ba a hayyacinsa ba,irinsa nake so a yiwa yasar. Dn Allah farida ki raka ni wajen malaminki,kinga tsakaninmu dake babu boye-boye. Takaicin abn data ke fada da warin dattin bakinta,dana 'yarta ne suka addabi af,taji kmr zata yi amai,tmkr xuciyarta zata hautsuno ya fito waje. Ta daga ido tana kallon ummi dn takaici ta kasa ce mata komai. Ta mike tsaye ta daga labulen kofa dn iska ta shigo,ta kade kauri da karnin da dakin ya kidime. Ta wuce taje kwandon kayan wanke wanke ta dauko kwano da kofi ta zubo mata abnci da ruwan sha ta kawo mata. Taga alamar yunwa sukeji daga ita har 'yarta. Tana kawo musu suka hau ci hannu baka hannu kwarya tmkr wadanda suka kai azumi a lkcn rani. Af ta koma gefe taci gaba ga rangadawa masoyinta sakon gdy a cikin wayarta,ta tuttura masa. Ummi zata sake yi mata maganr bokaye af ta dakatr da ita da hannu. Tace ummi dn Allah kici abincinki kiyi shiru,kada ki kware idan kin gama kya yi mun tatsuniyar. Ummi ta maimaita, tatsuniya kuma? DUK KYAN TAKALMI 3* 6 Af tace,ai gara ma tatsuniya,yara suna karuwa sbd dk tatsuniya gargadi ce,amma wannan lbrn naki gara in saurari kidan garaya da in cigaba da sauraronki.allah ya shrye ki ummi. Ummi ta koma ta zauna tayi kulas tana ci tana gyada kai tana fadi a ranta,lallai dan adam, wulakanci aisha umar zatayi min dk irin halaccin danayi mata na rakata inda aka jawo mata hnklnsa yazo yana sonta,har yake cusa mata kudi,shine na zama abar kyara a wajenta? Da ummi da 'yarta suka gama con abinci aisha farida ta kwashe kwanunkan ta dawo ta zauna, ta dubi ummi wacce 2ni alamomin bacin rai sun bayyana fskrta. Af tace, ummi yaya su hjyrki? Ta tabe baki tace, suna na kalau. Keda naki sake nemana ba 2n ranar da muka rabu dake daga gidan malam. Ai kya zo kice min wannan bukata ta samu kiyi min godiya. Amma shiru babu ke babu labari. Koda yake ba zaki zoba dn kin fara samun daula,gashi harda waya a hannu kina daddannawa ai dole ki guje ni.af tayi mrmshn krfn hali tace, naje nemanki mana na tarar ba kya gidanki,facalarki tace an sake ki. Har kinyi rshn m2mci kala2 kince asiri sukayi miki ke ma saikin ga bayansu. Haba ummi me yake damunki ne,kina abu kmr baki taba shiga aji ba? Ummi ta fusata tace, dole mana kice haka,ai ke aiki yaci ni da baici ba sai in zauna in zura ido? Kina ganin har yassar yayi aurensa yaki ya mayar dani ko ganina baya son yi. Af tace, yayi min dai-dai gsky ba dn kin tako kinzo gidanmu ba har aba bana son ganinki,kuma koda kuskure bazan kara taka gidanku ba. Sbd kin kusa halaka ni,kin tozarta ni duniya da lahira. Ke ba kawar kirki bace ummi,dk mai yawo dake ma sai ya halaka. Ummi ta fusata tace, to naji kuma dk wulakancin da kika yimin nina tako nazo gidanku, dk ranar da kika ganni a gidanku kiiyi min dk wulakancin da kika ga dama. Ta zabura zata mike af ta riketa ta mayar da ita ta zaunar. Tace, yo hkr gsky nakeso na fada miki,ita kuwa gsky daci gareta. Ummi,fada miki ne ban yi ba amma jana gidan boka da kikaui kika zuga ni na ranto kudi,kin jawo min bakar masifa a rayuwata. Aikinsa bai min amfanin komai ba,har kulle ni akayi a ofoshin 'yansanda sbd wannan kudi,shi kuwa wanda akayi min asirin dn yasoni saima ya sake tsanata. Ummi bazan boye miki ba saida nayi kuka da hawayena,nayi allah wadai da halayenki. Ni mai yafiya ce, na yafe miki,amma fa kin cuceni. Ummi ta harari af tace me kike so kice min bayan nan kin samu,gashi nan yazo wajenki? Af ta soko mata tata harara tace har yanzu baki saduda bako, ba zaki daina gasgata karairayin 'yan danfara bako? To bari na fada miki wannan mu2min da kika kaini wajensa macuci ne,kema kinsan da haka,tawada ce ya zuba a ruwa ya bamu sai laya aka rubuta alifun,ba'un da sauransu tsabar ya mayar damu jahilai. Ke bari ma na baki labarin dk abnda ya faru bayan rabuwata dake. Kinci sa'a anti abida bata nan, da yau saita wanke ki,sbd taki jinin taga mace mai bin bokaye. Habba ummi yanzu mai bin boka ya kara miki,kin kadar da dk abnda kika mallaka a duniya kina yawo a cikin tsumma keda 'yarki ko wanka babu. Mai yassar zaiyi dake a haka kmr tababbiya? Ai har abada ba zaki ga dai'dai ba idan dai baki daina bin bokaye ba. Ummi da nayi istigifari na mayr da gaba daya lamurana wajen Allah a saukake. Ya kawo min dr s cikin kwanciyar hnkl. Ina ma zaki bi hanyar dana bi dakin samu yassar cikin sauki ba tareda kin kashe ko sisi ba. Da rayuwarki ta gyaru duniya da lahira,hnkli ya kwanta,kin fita daga talauci dacin bashi. Ummi tayi sororo da alama jikinta yayi sanyi,ta fada cike da sanyin jiki. Aisha umar fada min yadda kika yi. Af ta gyara zama ta bawa ummi labarin dk abnda ya faru da ita,2n daga ranar da suka rabu da ita,har izuwa rana irin tayau. Ummi ta buga tagumi tana sauraron af daga dukkan alamu tana gasgata nasihohinta. Da af takai aya,sai ummi tayi ajyr zuciya. Tace,aisha umar kinyi gsky,to yanzu meye shawararki? Ta ina zan fara? Af tayi dry tace, ta inda na fara zaki fara,kum kema ki riki wadannan matakai biyar da abida tabani, ki riki kissar malamai nan da yasa matar na ta debo masa nonon bauna. Ki rabu da bin 'yan tsibbu ba sai wani ya fada miki ba,kema kin san babu riba. Ummi ta sharce hawaye tace, gsky ne, nima ina tsoron haduwata da ubangiji,sannan ga sunanan ya baci a garin nan dk wanda ya danni,yasan ina bin bokaye,har da 'yan ina da kare nake bi. Yanzu yaya zanyi aisha umar? Saita rushe da kuka. Af tace, laifin da kikayi tsakaninki da ubangiji zai yafe miki,idan kika tuba. Laifin da kikayi wa wani ne Allah bazai yafe miki ba saikin je kin nemi gafarar wadanda kika yiwa laifin. Wannan shine mataki na farko da zaki fara takawa. Kiyi ta istgifari da lahaula kiyi ta addu'a akan Allah ya juyo miki da hnklin yassar ya dawo gareki. Abu na biyu ki zamo mai tsananin hkr, karki ga idan kinga an sami jinkiri,bai kuyo gareki bada wuri. Na 3 ki kama mu2ncinki,kija ajinki kada ki sake binsa ko waninsa kina rokonsa ya mayr dake. Idan kika rike guda ukun nan zaki ga yadda Allah zai yi dake. Ummi ta zauna shiru tana 2nani,ta kasa cewa komai,canta dago ta dubi af. Tace, yassar fa ya tsaneni, ya tsani ya ganni ko a hanya. Sai naje nayi masa hayaniya nema yake aiko min da dubu 1 ko 2 a wata na abincin 'yarsa. Af tace,to saime? Bake kika jawa kanki ba? Ai halin mu2m ke sawa a tsane shi,ki gyara halinki ki gani idan baiso kiba. Ki dinga wanka kina tsaftace jikinki dana 'yarki,ki rage magana barkatai da yawo a gari,ki zauna a gidanku ki riki sallah da zumi da lazimi,kina ta addu'a kiga yadda Allah zai sauya ki. Ummi tace, insha Allahu zanyi duk yadda kik ce min, yanzu ma daga nan gidan sirikata zanje na nemi gafararta da facalata dashi kansa yasar din,nace kuskure nayi dana biyewa zancen malamai. Sai in koma gida in zauna in daina yawo in dinga sana'a ina biya dimbin bashin dake kaina. Aisha umar ngd,madalla sai kin ganni kuma. Ta tashi ta dauko 'yarta ta goya a baya,jikinta sanyi kalau. Af ta bude jakar kayanta ta tsinto mata atamfofi kala biyu tsofaffi ta bata,ta sake zaro nairi dubu 1 daga cikin kudin da dr s yabata ta hada mata. Sai gdy ummi keyi tana murna. Ta rakata har bakin titi ta hau acaba ta tafi. Af ta dawo gida cike da tausayin kawarta mayi mata addu'ar Allah ya shirye ta, Allah ya sa abunda take fada a bakinta ya shiga har cikin zuciyarta ASUBA TAGARI UMMIN YASIR BABI NA GOMA SHA SHIDA Yaya husainai ne yaketa shige da fice tsakanin dakinsa zuwa kfr dakin 2n kafin gari ya karasa wayewa. Da duku-duku af ta tashi dn tayi sallah ta kuma kai yara fitsari kasancewar lahadi ce babu mkrnta,in yaso bayan sunyi sallah saisu koma suci gaba da bacci. Tayi mamaki da ganin y.h a tsakar gida yana tsaye cak kmr mai 2nani. Mamakinta ya sake karuwa alkcn data fito daga bandaki har tayi alwalla bai koma daki ba,dai kai kawo yake tayi tsakanin dakinsa zuwa zaure. Ya shiga ya fita. Bayan tayi sallah yaran dk sunyi sallah,saita sake kwantar dasu sannan tayi wuf! Ta fito dn taga y.h yana nan? Ta iske shi a tsaye daf da kfr dakinta ya sakale hannayensa a bayansa ya sunkuyar dakai kasa kmr mai 2nani. Saita dafe kirji dn bugawar da zuciyarta keyi. Yaya lfy? Ta tmbyeshi. Ya dago jajayen idanuwansa ya dubeta da kyar ya iya bude bakinsa yace,lfy? Ta tsaya a jkin kofa tana kallonsa babu abnda zuciyarta bata aiyana mata akan abida ba. Tasan tabbas wannan damuwar tasa tana da alaka da abida. Yace, aisha yaushe ne zaa yiwa yara hu2n mkrnta? Muryarta na rawa tace, gobe litinin zasu fara jarabawa, ranar juma'ar kuma za a yi musu hutu. Lafiya? Sai yayi shiru, can ya dago sai taga idanuwansa sharkab da hawaye, yace, ina ganin su hkra da jarabawar ki hada muku kayanku mu tafi shagamu yanzu. Ta sulale ta durkusa ta dora hannu aka ta fasa kuka mai tsananin sauti da gigitar da mai sauraro. Tace, Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Wayyo Allah anti abida,wayyo antina, Allah ya jikanki,Allah yayi miki gafara. Sai y.h ya fisgota ya toshe mata baki ya grgza ta fadi yace, rufe min baki,waye yace miki abida ta mu2? Kan kace kwabo yaran abida suma sun fito daga daki da gudu,suna kuka. Mutanen gidan yaransu da manya,maza da mata sun firfito a gigice suna tmbyrsu ko lfy? Af dai bata ji bata gani,ba kuma ta gane dk abubuwan da jama'ar da suka taru akanta suke fada ba. Kuka take,faduwa take ana riketa bata kakkautawa. Abida bata mutu ba. Kalmar da y.husaini keta ambato,amma fa shima din kuka yake yi haikan. Mutanen gida maza da mata sai suma suka dinga hawaye dn tausayawa su AF. Af ki hada kayanku a babbar jaka da dk wani abu mai amfani ki shiga dakina ki harhada kayana dana abida kakaf gara mu kaura shagamu meyi jinyarta 2nda har yanzu bata warke ba,ni bance miki ta mutu na. Bari naje na nemo mana tasi wacce zata kaimu tasha. Ba dn ma tfyr ba ta shiri bace, aida motar ofis zan aro in zuba mai mu da kayan mu kakaf mu tafi, to ba shiri. Af ta tsh tsaye daga kasan datake burgima jikinta yayi bududud yayin da fskrta ta hadu ta damule,bayan hawaye da yayi face- face,idanuwan da fskr dk sun kumbura luhu-luhu. Ta kade jikinta ta dubi yayanta tace,yaya ina da magana dakai. Saita suce daki, ya biyo ta a baya. Ta jawo jkrta ta binciki,sai ta damko himilin kudi ta mika masa har naira dubu goma sha takwas. Ya karba cike da mamaki ya tmby,af waye ya baki wadannan makudan kudi? Ta matse hawaye tace, dr s ne ya bani dubu ashirin wancan satin da yazo. Ya kalmashe ya zura a aljihu yace,ki nutsu ki hada muku kayanku a tsanake ni bance miki abida ta mu2 ba. Ta fashe da kuka tace,haba yaya nima fa musulma ce,kuma mai hnkli nasan tawakkali. A gabana babana ya mutu ba a dade ba uwata ta mutu,me yasa zaka boye min mu2war abida? Yace,ni dai bance miki ta mu2 ba. Ya ficce yabarta a drksh ta jawo wayarta da sauri ta kira lmbr goggo mahaifiyar abida taji a kashe. Ta kira lambobin mutanen gdnsu har su 3 babu mutum 1 data samu,dk sun kashe waya. Wannan ya tabbatar mat abida ta rasu. Saita kira kanwarta munawwara a lagos taji muryar knwrta rangadau cikin fara'a take magana. Af cikin kuka tace,baku da labarn mu2war abida ne? Sai taji munauwara ta kwalla ihu ta wurgar da wayar tana salati. Aisha farisa ta tabbata lbrn mu2war bai isa garesu ba. Ta kira yaya yahya sai tci sa'a bugu daya ta shiga,nan da nan ya amsa. Ta rushe da kuka,tace, yaya ka fada min gsky,abida ta rasu ko. Hello,hello kawai yake cewa,kasancewar yana cikin hayaniya baya jinta. Yace aisha zan kiraki bana jinki. Saiya katse wayar. Ta mimmike kafa ta ske bude wani sabon shafin kuka. Kukan dako a mu2wa iyayenta batayi irinsa ba. Bata manta da ambaton innalillahi wainna ilaihi rajiun ba. Babu anda tafi 2nawa sai irin gudunmuwar da abida ta bata wajen yakin neman soyayyar dr s. Allahu akbar,allah mai yadda yaso,ga dr shuraim ya samu ita kuma ta tafi. Tace a ranta, tabbas rabuwa da dr s shine kwanciyar hankalina 2nsa babu abida, muddin na kasance da shuraim babban fami zai dinga yimin ina tunowa da ita. matan gida suka biyo ta daki suka zagayeta suna bata naki, su ma sun shiga rudani kasancewar husaini yace bata mutu, to idan bata mutu ba mai yasa xai tashi tfy a yau, gashi kuma yana rusa kuka shima uwani ta matse hawaye, tace AF tashi ki hada muku kayan kafin yayanki ya dawo don ya tafi ya samo mota" AF ta girgixa kai , tace"baxan iya ba ku kyaleni kawai" taci gaba da rusa kuka baji ba gani. nan matan gida suka shiga hada musu kayayyakinsu suna durawa a jakunkuna da buhuhunan kama daga kayan sawarsu takalmansu da kwanukansu. faruk ne yake ta jawo akwatinan mamansu da babansu daga cikin dakinsu yana fitowa dashi tsakar gida,matan suna ta harhadawa. himilin kaya dauri dauri aka kawo zaure aka himila, katifu ne kawai basu dauka ba amma babu abinda ba'a harhada ba. ha yanzu AF na zaune a daki ta hada kai da gwuiwa, kukan da takeyi yaki ya kafe sai ita tasan abinda takeji a cikin zuciyarta, kuna ,suya da tafarfasa duk sun tabbata a kirjinta. ta fada a baiyane" Abida.....abida mutunce. muyane nagari basu cika dadewa a duniya ba. sai yanzu na cika marainiya nayi rashin yar uwata garkuwar jikina. dama in mutu a yau in huta da takaici rayuwa. bani da sauran farin ciki a rayuwata kuma.... U.khairi ta rushe da kuka ta durkusa a gaban af tace,ki yafe min, abida ta yafe mana abubuwan da muka dinga yi muku a zamanmu daku a gidan nan,hakika mun zalunce ku,kullum muna cikin gulmarku,yi muku kazafi,makirci kala2 ku baku sani ba. Allah ya jikan abida mace mai hkr,sai a zageta a gabnta ta juyo t kallemu tayi mrmshi ta wuce ba zata rama ba,kuma bazata tabayin gaba damu ba. Ban san abida idan ta tafi ba zata dawo ba, dana nemi gfrarta a ranar da za tafi da ita. Farida, ki yafe min koke ma idan kin tafi kin tafi ba zaki sake dawowa kano ba. Tabbas nice nayita hada makirci a wajen mahaifiyar musbahu dn kada ya aureki. Laure,uwani yaya ku kayi shiru bayan daku mukeyi musu komai. Suma sai suka gyara zama sukace haka ne farida ki yafe mana, mun zalunce ku, mun zalunci kanmu. Zazzafan hawaye ne ya dinga tsattsafowa daga idanuwanta. Ta tsura musu ido tana kallonsu kawaita kasa furta kalma 1 sbd tsananin data ke ciki. Kalamansu tmkr ruwan wuta suke fesa mata,saita daga hannu ta dakatar dasu. Tace,ya isa, dn Allah kubar fada min, dk nasan abunda yake frauwa,kuma abida ta fada min komai. Naji abnda kukace,kuma na yafe muku,na tabbatar abida ma ta yafe muku,dn bata taba kwana da wani a ranta ba. Su dukka suka cigaba da koke. Muryar yaya hussaini suka jiyo a zaure dashi da maza suna ta jidar kaya a zaure ana kaiwa mota ana lufgawa. Har sai da aka kwashe kayan tatas ya leko dakin yace aisha farida da yara su fito su tafi. Sai da su uwani suka daga ta tsaye wannan tana taro mata zaninta zai fadi, wannan tana gyara mata hijabi. Takalmi silifas sai da aka tura kafarta a ciki don ta manta yadda yake sawa saboda tsabar kidimewa. Wayarta ce kawai a hannunta don ko kofofin dakunan sai da yaya hussaini ya datso, kanta tsaye ta fice ba tare da ta iya waiwayowa baya ba. Bata iya amsa adduoin ta'aziya da fatan Allah Ya kiyaye hanyar da jama'ar gida da makota suke yi mata ba. Tafiya take tamkar kwai ya fashe mata a ciki. Bata ma san inda take jefa kafarta ba, 'ya'yan abida na nanike da ita, idan ta kalle su sai taji wani gagarumin tashin hankali ya sake taso mata. "Faridah!!" Tattausar murya taji a gefenta don haka ta waiga da sauri. Musbahu ta gani idanuwansa sharkab da hawaye, itama sai hawaye ya fara kwaranyo mata. Tayi sauri ta sunkuyar da kanta kasa ta dinga tafiya wurin mota. Yace Allah Ya jikan abida, naji ance kun kwashe kayan ku kakaf kun kaura shagamu. Yanzu shikenan ba zan sake ganinki ba? Ki sani har abada ba zan daina sonki ba, babu yadda zanyi ne. Sai ta sake rushewa da kuka, shima haka yana biye da ita har ta shige mota ita da 'ya'yanta. Yaya hussaini ya shiga gaba shi da direba, su kuma a gidan baya. Kaya kuwa suna can baya irin motar nan ce mai kama da na 'yan sanda bayanata kamar a kori kura. Cincirindon mutanen unguwa ne suka firfito yara da manya, maza da mata suna ta daga musu hannu har suka ja motar suka tafi. Sabon kuka ne ya sake sarkewa aisha farida. Sun fita daga kano kenan sai dr shuraim ya kirata, da farko tayi kamar ba zata dauka ba, sai dai ta daure ta amsa. Magana yake cikin shaukin soyayya. My love kin tashi kalau? Jiya kuma muna magana sai kikayi bacci ki ka barni ko? Ta runtse ido dan tsananin tashin hankali yayin da hawaye ya dinga tsartuwa daga idanunta. Bata iya bashi wannan amsar ba. Yayi murmushi yace banji kinyi magana ba tun dazu, ko baki jina ne? Tayi magana cikin sansanyiyar murya tace dr muna hanyar shagamu. Abida ce ta mutu. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun dr shuraim ya sake maimaitawa har sau uku. Yayin da kuka ya barke mata. Dai dai lokacin kuma yaya hussaini ya hasala ya juyo a fusace ya fizge wayar, ya murtsike ya kashe ya rufe ta bambamin fada. Waye yace miki mutuwa tayi har kike yadawa a waya? Wai ke wace irin yarinya ce mara jin magana? Cikin kuka tace haba yaya me yasa kake boye min mutuwar anti abida? Ya ja dogon tsaki ya girgiza kai ya juya ya cigaba da kallon haya, ya saka wayar ta ta a aljihunsa. Dr shuraim yayi ta gwada kiran aisha farida ji wayar a kashe , sai hankalinsa ya kara tashi matuka. Yasan duk inda take yanzu bata cikin hayyacinta, kuka kuwa yau ko kogin maliya sai haka. A gigice ya tashi zaune ya fizge bargon da ya lulluba ya diro daga kan gadonsa yafito falonsa ya zauna ya cigaba da kiran wayarta a kashe. Ya kira dr lukman shima har sau uk bai amsa ba ,sai na hudun ne ya dauka yana magana cikin magagin bacci. Dr shuraim ya fada a dimauce, lukman ka wartsake daga baccin nan ka saurareni. Farida ce take cikin wani hali gashi kuma na rasa ta waya. Ka kira yayanta yahaya umar ka tambaye shi dan inji halin da take ciki. Dr lukman yayi firgigit ya tashi zaune yace ban fahimce ka ba, meya samu farida? Yace yanzu na kira ta tana kuka ta shaida min suna hanyar shagamu Allah Ya yiwa antinta abida rasuwa, mara lafiyar nan. Dr lukman ya zabura ya dauki doguwar salati yace kashe wayar ina zuwa barin kira yahaya umar. Bayan mintuna 15 dr lukman ya kira dr shuraim yace ka kara hakuri dai zuwa anjima don yanzu nayi ta kira ba dauka ba. Daya dauka ma sai naji shi a cikin hayaniya yake, yace na kashe zai kira ni anjima. Kaga kenan suna makabarta ko wajen zaman makoki. Dr shuraim ya dafe kai ya cije lebe yace halinda farida zata shiga shine babbar matsalata. Idan ka duba yadda kullum take kuka saboda rashin lafiyar nan inaga idan ta mutu? Lukman yaya za'ayi kenan? Dr lukman yayi ajiyar zuciya yace babu abinda sai dai muji ra zuwa anjima muji ta bakin yayan nata tukunna. Nayi maka alkwari yana kirana zan kiraka kaji halin da ake ciki. Dr lukman yayi godiya suka kashe wayan. Har yanzu kiran wayar aisha farida yake yi taki shiga. Sai ya tuno yana da lambar yaya hussaini don haka ya cire kunya ya kirashi. Yaci sa'a kuwa yana kira ta shiga, nan da nan yaya hussaini ya amsa. Ya ambaci sunan shi tangararau dr shuraim ne? Caraf aisha farida ta dago ta dubi yayanta. Dr shuraim yace sannu yaya, ya akaji da hakuri? Sai yaya hussaini ya gallawa aisha farida harara yace af! Kai ma ta fada maka anyi mutuwa ne? To wannan fadarta ne kawai, ni dai nace ta shirya mu tafi shagamu sai ta dau kuka da ihu. Dr shuraim ya cika da mamaki kafin yace wani abu yaya hussaini ya mikawa aisha farida wayar. Tayi ajiyar zuciya tayi sallama cike da sansanyar murya. Dr shuraim ya fara magana cikin tattausar murya. Yace farida meyasa kike da rudewa ne haka? Ga yayanki yyace bai fada miki ta mutu ba. Ta fashe da kuka tace haba dr nifa ba karamar yarinya bace nagane komai, meyasa za'a boye min? Ni nasan anty abida ta rasu, ko an fada min me zanyi, dole in dangana. Yaya hussaini ne ya sake yi mata tsawa yace kada ya sake ji tayi maganar rasuwan nan. Ta rushe da kuka mai tsanani, hankalin dr shuraim ya sake tashi ya shiga damuwa, yace yi shiru baby, kiyi hakuri duk mai rai mamaci ne , dukkanmu nan zaman jiranta mukeyi. Kiyi mata addua Allah Ya yi mata rahama. Ki kunna wayarki mu dinga magana. Tace wayar bata wajena yaya ya karba ya kashe tundazu da muke magana. Dr shuraim yayi yace to anjima zan kiraki a wannan layin. Idan anyi bakwai zaku dawo ko? Ta girgiza kai kamar tana gabanshi, ta zubo da hawaye masu yawa. Tace dr shuraim ina ganin wannan wayar da muke da kai itace rana ta karshe da zaka a duniya ballantana ka ganni. Kuka ya barke mata. See Translation KYAN TAKALMI 3* 7 Yayi zumbur ya mike tsaye ya dafe kirji yace farida me kike so ki fada min? Kina so kice min zaki kashe kanki ne saboda anti abida ta mutu? Ta girgiza kai tace bazan kashe kaina ba, saboda nima musulma ce. Rashin anti abida babban ciwo ne a zuciyata wanda bazan taba warkewa ba har abada, kuma duk sanda na ganka ko naji muryarka zaka zama min fami a wannan ciwon nawa. Ba lallai bane ka gane abin da nake nufi yanzu ba, kuma ba zan iya fada maka yadda zaka gane din ba. Ni kadai nasan abin da nake nufi da hakan. A sanadiyyar anti abida nasan ka, da ba zaka sanni ba ma balle ka fara sona, nima haka ba donn yakin da tayi ba da tuni na manta da shuraim a rayuwata. Abida itace silar hada soyayyarmu, naso ace abida na raye ta ganmu tare. Ta mutu ba tare da burinta ya cika ba, komai ya fita a raina tunda babu abida. Ya daka mata tsawa domin ya gigice gaba daya da jin kalamanta. Yace farida kin kuwa san abinda kike fada min? Anya kuwa kina cikkin hayyacinki? Ta fashe da kuka tace nasan abinda nake fada likita. Nayi sallama da kano ko hanya bana so ta biyo dani ta kano , tunda babu abida. Kayi hakuri ka yafe min, nasan irin ciwon da zaka ji a zuciyarka saboda nina fara shiga ciwon so kafin ka shiga. Sai ta mutsike wayar gaba daya ta rike a hannunta ba tare da ta mikawa yaya hussaini ba. Ya juyo ya dube ta cike da mamaki ba tare da yasan abinda zai fada mata ba. Dr shuraim yayi ta gwadar wayar, ya kira yaji an kashe mudik , sai ya sulale ya zauna akan doguwar kujerar falonsa yana sosa kai. Yace innalillahi waiinnna ilaihirajiun. Meyake shirin faruwa dani ne? Dama wannan shine cutar son da ake fada a gari? Ashe ban taba sanin so ba sai yanzu? Inama zan iya hakura da son farida in huta. Ya jawo wayarsa a sanyaye ya kira dr lukman. Cikin sanyin murya yace abokina kazo muyi magana ka bani shawara , don ina cikin masifa wacce zata iya kaini da kamuwa da son zuciya. Farida tace in kyale ta bazata iya cigaba da son ba saboda babu ran abida. Dr lukman yayi tsaki yace wannan ai shirme ne, zafin mutuwa ne ya shige ta, zata dawo hayyacinta ta neme ka. Dr shuraim ya girgiza kai yace a cikin hayyacinta take magana ba zafin mutuwa bane. Na kasa gane abin da suke nufi. Yayanta yace min bata mutu ba, ita kuma tace min abida ta mutu. Abin da na fuskanta boye mata yake yi don yaga ta damu. Ga shagamu da nisa kar ta sume masa a hanya. Dr lukman yace nima na fi yadda ta mutu don yanzu yahaya ya turo min sako a waya ta yace inyi hakuri yana cikin mutane zai kira ni anjima. Dr shuraim yace idan ba zaka zo ba gani nan zuwa gidan naka muyi shawarar, don bansan yadda zan iya yini a cikin wannan halin ba. Dr lukman yace naga ka damu da yawa abokina, bari nayi wanka inzo tunda gidanka babu kowa zaifi dadin magana. Dr shuraim yace don Allah kazo da wuri ina jiranka. Suka kashe waya. Dr shuraim ya kame a zaune ko yatsarsa baya iya dagawa balle ya tashi yayi wani abu. Shi kansa yana tausayin kansa da kansa, halin da zai shiga idan ya rasa aisha farida. Ya rasa yadda akayi ya zurmuka cikin ramin kaunar ta wanda yayi zurfin da ya kasa fitowa. Ya fada a bayyane lallai karshen namiji a karkashin mace yake. DUK KYAN TAKALMI a kafa ake taka shi. Sai ya zubo da wani zazzafan hawaye daga idanuwansa. TABBAS DUNIYA RAWAR 'YAN MATA CE, NA GABA SAI YA DAWO BAYA IDAN AKAYI WANI JUYIN. ASUBA TA GARI LIKITAN AISHA FARIDA!!! BABI NA GOMA SHA BAKWAI Mako guda kenan dai-dai da tfyr su aisha misalin karfe 5 na yamma. Dandazon maza tsofaffi ne suka cika a majalisar hirarsu ta 2ntuni,wato kfr gdnsu aisha farida. Mahaifin abida shine ya gaji kujerar tsohon af shine kadai yake zaune akan kujera sauran dukka a zazzaune suke akan tabarmi a gefensa. Af ita kadai ce mace a cikinsu,tana zaune akan kujera, sauran dukka a zazzaune suke akan tabarmi a gefensa. Af ita kadaice mace a cikinsu,tana zaune akan dakali ta lanqwashe kafa,sanye take da bakr riga abaya ta yafa dankwalin a kanta. Ta jima tana kallon tsofaffin nan daya bayan daya,sai ta 2na da a lkcn da mahifinta yake raye,mahaifin abida ya juye shi sak! Kmrsu 1 a yanzu shine babba a cikinsu. Tabbas abida da mahifinta tayi kama sak! Sai taji hawaye ya cika mata ido ta grgza kai dn tausayi. Tace a ranta, Allah sarki, wata rana sai a shafe kowa kmr ba a taba yin mu2m a doron k'asa ba. Haka ake tfy daya byn daya. Baba iliyasu ne ya dubi aisha farida yayi mrmshi yace, kai girman dan mu2m babu wuya, kmr ba 'yar yarinyar nan bace, 'yar karama aisha, yanzu ga yadda ta girma. Af tayi dry tace,kaima aika tsufa inda zaka san an dade kenan. Sai suka hau hirar 2na baya,abun tausayi a jajanta,abn dry a kyalkyace Tsayuwar wata tsaleliyar mota baka mai duhun gilashi ce ta katse hirar,sai hnklnsu gaba daya ya koma kallon motar. Mazaje 4 ne suka bude kofofin moyar guda 4 suka fito. Af ta cika da tsananin mamakin data kasa boyewa,sai cimak ta mike tsaye, yayin da aka hau kallom-kallo a tsakaninsu. Dr s, Dr Lk, Dr Dayyab da yahya umar ne suka nufo inda su af suke. Suna isowa sai su duka suka zube a gaban tsofaffi suka kwashi gaisuwa. Nan da nan suka matsa musu waje suka umarce su dasu hawo kan tabarma su zauna sosai. Bayan kowannensu ya zauna sai af ta durkusa ta gaishe su ckn sanyayyar murya. A lkc guda suka amsa, yayinda Dr S ya kafa mata ido yana kallonta, ko ba a fada ba ansan yayi kewarta,sati guda kenan bai ganta ba. Cikkin kunya kanta a sunkuye a kasa ta yunkura zata tsh ta shige gida. Yahya umar yace ta daawo ta zauna zaiyi magana. Sai taji zuciyarta ta harba, a ckn ranta ta hau addu'a ALlah yasa alkhairi zai fada. Numfashinta ya fara cikewa,yayin da da babu abnda tafi bukat irin ta shige gida kada ayi maganar nan a gabanta,tasan koma dai me za a ce ya shafe ta. Ta fada cikin ladabi,ruwan sha zan kawo muku. Yahya yace munan ea kika ganmu a koshe muke,su kuma basa shan ruwan randa irin naki, sunada ruwansu na rba a mota. Sai dukkansu sukayindariya. Af ta dawo jikin dakali ta rabe kmr marar gsky. Ahya yagyara zama ya dubi tsofaffin yace, baba, wadannan gudaukun da kuke gani baki netun daga kano,kuma gaba dayansu likitoci ne a asibitin aminu kano. Sai tsofaffin sukasuka hautsine da maganasuna cea, likita bokayen turesai,ai da ga gani babu tmby gasu nan a nutse kowanne cikin kyakkyawan shiga. Wasu shaddoji ne suka saka masu kyau,kowacce tsasaddiya ce sai daukan ido takeyi. Farare sol sol anyi musu dinkin surfani dinkin boda,rigar iya gwiwa. Su shuraim dai dry kawai sukeyi. Yahya ya cigaba da byani,ya nuna DR LK yace wannan sunansa dr lk, babban abokina ne tun. Una yara a yobe tare mukayi sakandire. Ya nunaDR S yace ga shuraim babban liktan fatar da akeji dashi a kano shima aminin lukman ne, kuma shine yake so r AIsha FArida. Sai gaba daya suka juyo suna suka dubeta,tayi sauri. Ta sunkuyar kkasa yayi akwakalra tsg aito m da y yanaa,tmakr lma. Tana tmbyr zuciyarta ''ANya kuwaa mafarki nakeyi ba,yau shuraim ne ya fara mgnr aure na. Allah mai ikobabu abndaya gagari ubangiji. Dr shuraiam har yanxxu kallon aishaa f yakeyi kasa kasa yana soyaga yanayinta da taji mgnr aurensu. Ya fusknci ta cika da mamkikuma yaga annuri a fskrta yya karu, dn haka ya sake csamun kwari. Gwiwar tana sonsa. Tsofafi sai suka shiga jan dogayen addu'oi. B.Sule ya dubi farida yace,ja'ira ashe kin ruso miji kyakkyawa daa kano haka kikeboyewa. Yanzun nan ika gama cewa bakidasaurayi. Sai su dukka suka tintsire da dry,harda ita. Yahya umar ya nuna dayyan yazxe,wannan sunansa DR Dayyabu shima a sibitin m. Aminu kano yake aiki sunaji dashi ko kuma ma ince a arewa anaji dashi. Reumatologist ne,likitan daya shafi ciwon cikin kashi da jijyoyi. Shine likitan daya shafi ciwon abida,dn haka nema suka tzho dashi. Sai gaba daya suka zabura suna kalonsa,musamman ma aisha f. Mahaifin abida ya grgza kai, yace, ciwon abidaaiba naasibiti bane kada ma ku wahalar da kanku. Dr lk yayi gyarsan murya yace, baba ni babu waniciwo da za'a ce babu maganinsa a asibiti. Kada ku hana shi gwadawa,abunda ya karanata kenan,aikinsa ne shiyasa muka tahho dashia. Baban abidaya grgza kai yaxe, me likta zaiyi mata, yarinyar da htta gashin knta ya kde dukka,kan nan kmr anyi mata kwal-kwal,I wannan aikin kowa yasan iska ne. KYAN TAKALMI 3* 8 Dr dayyabu yayi murmushi yace ciwon ya gaji haka, yana zubar da gashi, yana saka ciwon ido, yana sa mutum yayi ta zabura, kuma da kumburin gabobi, wani lokacin da yawan jin sanyi. Idan ciwon ya tsananta zai iya taba dukkan kayan cikinta kamar koda, zuciya, mahaifa da kuma kurajen baki. Allah dai Ya kiyaye. Nan da nan tsofaffi suka fara gamsuwa da bayanan dr dayyabu, domin ya zano duk abubuwan da abida take ciki. Ya kara da cewa kurajen suna iya feso mata a kirjinta, baya, wuya, da kuma fuskarta. Na fuskar zai zagaye kumtunta da kuma kan hancinta. Zai yi siffar malam buda mana littafi a turance muna kiransa butterfly rashes. Aisha farida ta dafe kirji tace likita wannan wane irin ciwo ne? Yaya sunan ciwon? Kuma me yake kawo shi? Dr dayyabu yayi dariya har sai da kyakkyawar wushiryarsa ta bayyana. Ya girgiza kai yace bazan iya tantancewa ko me yake damunta ba har sai anyi gwaji. Gwajin ciwon kuma ba a yinsa a kasar nan, sai a south africa ko a beiruit. Aisha farida ta dafe kirji yayin da kake iya ganin gigicewa a fuskarta. Tace likita yanzu dai sai an kaita can sannan a gano ciwon? Sai ta fara hawaye saboda tunawa da tayi basu da wannan gatan. Dr shuraim yayi sauri yace kada ki fara koke koken nan. In Sha Allah komai yazo karshe tunda kika ganmu da likita. Sai ki shekara a AKTH baki samu damar ganinsa ba, amma gashi mun kawo muku shi har gida. Kuma zaiyi mata duk abin da ya kamata har sai ta ji sauki in sha Allah. Dr dayyabu ya girgiza kai yace ba sai an dauke ta an kai ta south africa ba, za dai mu tura jininta wani lab a abj su zasu aika jinin can idan anyi gwajin sai su turo mana da sakamakon online. Idan na duba sai in tantance takamaimain matsalarta, sai in bata magani. Amma bayan wancan gwajin mu ma anan akwai gwaje gwajen da zamuyi mata kala kala muga ko akwai matsala a cikin jikinta kamar su koda, zuciya, hanta da dai sauransu. Kowa yayi tagumi yana kallon bakin dr dayyabu zuciyarsu cike da fargaba da tausayin abida. Yayi murmushi yace kada ku damu, ba wani abu bane na daban. Anayi kuma ana warkewa sai dai don masu irin ciwon basu da yawa ne a duniya. Yaya hussaini ne ya fito daga cikin gida, baba ahmadu yace yawwa hussaini zo ka zauna kaji da kunnenka, likitoci ne suka zo daga kano suna bayani akan ciwon matarka. Yaya hussaini cike da mamaki yake kallonsu, bai san sauran biyun ba amma ya gane dr shuraim. Yazo ya mimmika musu hannu suka gaisa, ya samu waje ya zauna ya cigaba da sauraron bayanin dr dayyabu. Dr dayyabu yace daga yadda yahaya umar ya min bayani yadda ciwon nata yake yayi min kama da Systemic lupus erythramatosis (SLE). Sai kowa ya gyara zama suka mika tunaninsu gaba daya kan likita dayyabu. Yaya hussaini yace me kenan? Me yake kawo ciwon? Dr dayyabu ya lankwashe kafa yace SLE ciwo ne wanda yake samuwa jikin wanda Allah Ya dorawa. Lupus is an auto immune disease characterised by acute and chronic inflammation of various tissues of the body. Auto immune disease are illness that occur when the body tissues are attacked by its own immune system. Bansan yadda zan fassara muku ba, amma dai ba a gado, kuma ba'a daukar ciwon. Ciwon yafi ga 'yan america bakaken fata (africam americans) da kuma 'yan chinese da japanese. Anfi samun SLE a jikin mata fiye da jikin maza. Kuma yafi kama masu shekaru ashirin zuwa arbain da biyar. Malam ahmadu yayi dariya yace likita bokan turai, ai ni wannan bayanin naka kamar tatsuniya nake ji, mu nan 'yan chinese ne da zai zo ya kama 'yarmu? Ai ciwon abida sammu ne, daman ance tana da makiya a kanon nan, musamman da awararta tafi kowacce dadi suka jefe ta. Aisha farida ta girgiza kai tace a'a baba ahmadu, ka bari ku bari ya bata magani. Yau wata nawa kuke yin na sammun amma babu alamar sauki sai ma ciwon gaba yake ci. Yahaya yace gaskiya fa tunda yazo a dakatar da duk wani hayaki a zuba masa ido. Da yawa daga cikin tsofaffin suka kushe maganin asibitin har da mahaifin abida. Kadan ne suka goya bayan likita. Daga karshe yaya hussaini yayi magana yace ya yadda likita yazo ya duba abida ko Allah zai sa a dace. Gidan su abida da gidan su aisha farida babu nisa, don haka aisha farida, hussaini, yahaya, da likitocin guda 3 suka dunguma gidan su abida. A zauren gidan aka iskesu an daukota tamkar tsumma , wata mata mai maganin gargijiya ta shafe jikinta sharkab da man shanu ta tilo mata itatuwa a leda tace ayi ta jika mata a sabuwar kwarya. Hankalin likitocin ya tashi da ganin irin wannan kwabe kwaben. Yaya hussaini yayi wa surukarsa bayanin likitocin, tashin farko taki amincewa ita da mata mai magani, tace ba'a hada aikinta da na asibiti. Yaya hussaini dai ya takura sai likitoci sun duba matarsa. Mahaifiyar abida da mata mai magani suka yi fushi suka bar wurin a fusace daya ta shiga gida, mai magani ta fice dauke da buhunta a kai. Hakika abida tana jin jiki matuka, kamar ba ita ba, gaba daya halittarta ta sauya, yanzu ko magana bata iya yi saboda azaba. Sai gyada kai, sai hawaye kawai zaka ga yana zuba saboda tsananin wahalar da take sha. Aka kawo musu tabarmi suka zazzauna yayin da dogon turanci ya hautsine tsakanin likitocin uku, likitan fata, likitan kwakwalwa da likitan kashi da jijiyoyi. Dr dayyabu ya bude jakarsa (brief case) ya jawo allurar intramuscular injection wacce ake kira dexamethasone 8mg start. Ya umurci aisha farida tazo ta juya masa ita. Yayi mata allurar sannan ya debo wasu magungunan kala kala har kala biyar ya mika ma maigidanta yace lallai a dinga bata magungunan nan, kuma akan lokaci har tsawon sati biyu za aga canji In sha Allah kafin a gama gwaje gwajen jininta, idan an gama tantance takamaiman ciwon. Dr dayyabu ya dubi aisha farida yace matso kusa nayi miki bayanin yadda za a dinga bata maganin. Ga prednisole nan ta sha kullum guda uku HOQ daya da safe, daya da dare, calcium kuma kullum tasha daya. Sai kuma methothroxate ranar asabar zata sha 10ml. Ranar lahadi kuma ki bata folic acid guda 2. Yanzu zan dauki jininta kashi kashi in tafi dashi, wasu a kano zamuyi gwajin wasu kuma a abj zamu aika lab suna harhada jinin mutane da yawa, su tashi mutum a kai south africa a gwada. Yaya hussaini ya langabar da kai yace nawa ne kudin maganin? Kuma nawa ne zamu bada na wannan gwaje gwajen naji har da wanda za aika kasar waje. Dr dayyabu yayi murmushi ya girgiza kai yace kada ka damu da wannan, abokina shuraim ya gama shirya komai. Dan yanzu ma lagos zanje in hau jirgi cikin dare in isa abj in bada wannan jinin, kwana goma zaiyi sannan ya fito, to sauran gwaje gwajen ma sai inyi a national hospital abuja don yawo da jini babu dadi, duk dr shuraim zai biya. Gwajin jinin wanda za'a aika south africa ma dubu sittin za a biya, yace shi zai biya. Sai aisha farida ta fara hawaye haka itama abida hawaye ya fara kwaranyo daga idanuwanta dan tana jin duk abin da ake cewa. Yaya hussaini ya hau godiya yana shi albarka. Dr dayyabu ya zaro sirinji da kwalabe ya zuzzuki jinin abida ya ciccika. Ya dauko wata 'yar akwati ya jera su ya mayar ya rufe. Suka mike suna yiwa abida sannu da fatan Allah Ya bata lafiya. Aisha farida da yaya hussaini ne suka kinkimi abida suka shiga da ita cikin gida. A take yaya hussaini yace aisha farida ta dibo ruwa ya bata magani, bayan ya bata ta sha sai yace aisha farida ta boye maganin a wurinta. Sanda zata sha tazo ta bata kada ta barsu a fili goggo ta zubar dan bata yadda da maganin asibiti ba. Yaya hussaini ne kadai ya dawo wurin su dr shuraim suka dunguma zuwa kofar gidan su aisha farida wajen tsofaFfi. Babu abinda yaya hussaini da yahaya umar sukeyi sai godiya da shi albarka. Yaya hussaini ya yiwa tsofaffin bayanin duk abubuwann da ya faru da irin zunzurutun kudin da dr shuraim ya kashe da wanda zai kashe nan gaba. Sai suka kacame da yi masa godiya da shi albarka, shi da abokansa sauran likitoci. Hussaini ya gyara zama ya dubi tsofaffin nan ya nuna shuraim yace shine mai son farida, da farko naki amincewa saboda ko ba a fada ba shi ba sa'an aurenta bane, mu talakawa ne kuma baki. Toh a haka muka rabu. Yahaya umar yace kayi kuskure hussaini tunda kayi wannan tunanin, ai al'amarin soyayya ba a ayin ta don kudi, shi ya ganta yana so, itama tana sonsa kayi garaje da ka tarki raba su. Ba 'asan inda rana zata fadi ba, haka baka san wanda zai yi maka amfani a rayuwa ba. Ga shi dai yanzu ya taimake mu a lokacin da bamu zata ba, kuma bamu da matsayin samun wannan. Dr lukman ya fada min komai daga haduwarsu har zuwa tahowar aisha farida. Naji ra'ayin shuraim akanta alkhairi ne kuma aurenta yake so yayi. Yanzu wannan tahowar da sukayi sunzo dan su duba abida su bata magani kuma su nemi auren farida ayi magana daya. Hussaini ance ka kauro gida kacokan zaka bar aiki, to zamanka a shagamu ba zai yiwu ba, ko ba dan aisha da shuraim ba, kuma ba dan karatun 'ya'yanka ba , don lafiyar matarka da rufin asirinka aikinka sai ka koma kano don abida yanzu dole ta kasance kusa da likitanta dr dayyabu yawan yawan bincikar lafiyarta. Yaya hussaini yayi shiru yana gyada kai don ya gasgata maganar yayansa. Can ya dago ya dubi yahaya yace tabbas ka fadi gaskiya, dama ni ban gama tsayar da shawarrar barin aikin ba, na dauko hutu ne na shekara. A cikin hutun ne dama nake so naga yadda halin zaman namu a shagamu zai kasance idan na samu abinyi sai in zauna. Idan ban samu ba in koma kano iyalina in barsu a nan. Yahaya yace to iyalinka ne ma zaman a kano ya kamasu saboda lafiyar matarka, wannan likitan da kake gani babu inda zakaje a kasar nan ka samu iirinshi , su biyu ne kadai rheumatologists , daya na kudu shi yana arewa. Saboda masu irin ciwon basuyi yawa ba. Saboda haka hutunka na karewa ko bai kare ba ka hada su ku koma dan naji yace sati biyu zai gama hada sakamakon gwaje gwajen sannan ya gano kan ciwon. Yaya hussaini fadi yake gaskiya in sha Allahu zamu koma nagode. Tsofaffi ma suna bayan yahaya, shawara suka ci gaba da bawa hussaini su hada su koma kano. Dr lukman ya gyara zama yace toh mu dai yanzu munzo a shirye tafi da gidanka mukayi, ma'ana muna neman auren aisha farida. Yahaya ya dubi tsofaffi yace toh me za a jira tunda gaku kacokan kun hallara? Mutumin nan sananne ne tunda ga lukman nasan gidansu yasan gidanmu. Farida na son shuraim shima yana so, ayi magana kawai. Dr shuraim ya sunkuyar da kai kasa yace saboda rashin lafiyar nan ne ta abida bamu san yadda zamu tarar da jikin bane yasa bamu taho da iyayena ba. Amma tunda komai yazo da sauki idan an amince mana sai mu bada kudin aure, sai kuyi magana da mahaifina a waya ya lamunce in nemi auren. Su dukka suka ce babu damuwa ai. Dr shuraim ya dakko wayarsa ya kira tsohonsa , bayan sun gaisa ya shaida masa gashi a gaban iyaye da kakannin aisha farida kakaf sun hallara , kuma sun amince zasu karbi kudin aurensa. Abban shuraim yace masa ya basu wayar, daya bayan daya abban shuraim ya dinga gaisawa dasu suna yi masa fatan alkhairi, shima yana yi musu har suka kashe wayan. Dr lukman ya tashi yaje mota sai gashi ya dawo da bakar jakar leda yazo ya zauna, sai ya mikawa yahaya umar. Yahaya ya bude yaga damin kudi dauri biyu 'yan naira dubu daya-daya. Kowanne dami dubu dari ne, dami biyu dubu dari biyu kenan. Dakata yahaya. Inji baban abida. Kowa yayi carko carko yaji abin da zai fada. Yace ba himilin kudi ba, haka ba wayar da mukayi da tsohonsa bane aure. Shin an tambayi yarinya tana sonsa? Don idan yayana umar yana da rai zai iya yiwa kowacce 'yarsa auren dole banda aisha farida. Don yana matukar sonta, baya son abinda zai bata mata rai. Hankalin dr shuraim ya tashi, sai yayi ta zungurar dr lukman wai yayi magana. Hussaini yayi murmushi yace wallahi tana son shi, matukar so kuwa. Don nine shaida saboda ni ta tara tace min ina kokarin raba ta da shuraim, to in sani kamar ina kokarin raba tane da rayuwarta, don tanayi masa tsananin son da zata iya rasa rayuwarta. Babu wanda bai kyalkyace da dariya ba a cikinsu, yayin da dr shuraim yayi ajiyar zuciyar jin dadi. Salati goma ga annabi (SAW) suka fara kawowa, sannan dr lukman ya fara warware kudade yana bayani. Naira dubu 100 shine kudin na gani inaso, naira dubu 50 gaisuwar uwa da uba, sai naira dubu 50 kudi ne kyauta a rarrabawa dangi , wani a siya alawa da goro shaidar an bada ita. Sai tsofaffi suka rike haba don mamaki da jin wadannan makudan kudi tunda suke aurar da 'ya'yansu da jikokinsu babu wacce ta taba yin tsadar da farida tayi. Sai wasu suka barke da kukan dadi don ko naira ashirin babu a aljihunsu. Wasu kukan tunawa da mahaifin farida sukayi. A lokacin malam sule ya shiga yiwa farida kirari irin wanda baban yake yi mata tun tana karama. "Aisha sarauniyar mata, fara mai farar aniya, kinfi mata dubu". Kowa yana ta adduar fatan alheri da fatan ayi auren cikin sa'a da zaman lafiya. Dr dayyabu ne zai tafi a yau, dr shuraim da lukman zasu kwana sai washe gari zasu koma, da mota suka taho don haka yahaya zai raka su masauki. Wani tsadadden hotel zai kaisu, sai suka yi musu sallama suka shiga mota suka tafi. HAUSA Novels BOOK DUK KYAN TAKALMI 3* 9 Aisha farida tana zaune a gefen katifar abida tayi shiru tana sauraron bambamin fadan da goggo keyi, saboda an kawo likitoci sunzo sun korar mata mai magani da suka kashe kudi sannan ta yadda tazo. Tana shiga tana fita, ta na fada ita kadai, babu wanda ya tanka mata a cikin gidan saboda ranta yayi matukar baci. Ko hakuri aka bata sai taji tamkar an zage ta. Abida ta dubi aisha farida tayi dan murmushi yayin da itama ta dube ta tayi murmushin. Abida ta yi magana a hankali sai da aisha farida ta dora kunnenta a kusa da bakin abida sannan taji abinda take cewa. Cewa tayi allurar nan da akayi min naji dadinta, yadda kika san yawo takeyi kusurwa kusurwa duk inda ciwon yake tana wanko shi. Gashi ina iya daga hannaye sama. Dadi ya rufe aisha farida tayi dariya tace mungode Allah, Allah Ya karo sauki. Abida tace amin, naga shuraim, Allah Ya sa ayi auren nan. Aisha farida tayi dariya tace samun lafiyar ki shine fatan mu , kafin ayi wata magana antina......bata rufe bakinta ba saiga maimuna ta fado cikin dakin budik! Ko sallama babu kai kace jeho ta akayi. Sai haki take daga gani tasha gudu. Cikin sheshekar gudu ta rirrike aisha farida tace albishirinki? An bada ke, yanzu aka kawo kudin aurenki dubu dari biyu. Kallon rashin fahimta aisha farida da abida sukeyi wa maimuna. Aisha farida ta rike baki da daya hannun ta dafe kirji ta dinga fadin Allah mai iko, Allah abin godiya. Wai nice yau ake maganar aurena da dr shuraim? Maimuna ta fice ta barsu suna mamaki. Wayarta ce ta hau karan sai tayi sauri ta duba ta zaci rabin ranta ne, sai taga sunan barr muazzam ta danna da sauri sai taji muryarsa cike da farin ciki. Yace gani a kofar gidanku, na kira wayarki taki shiga sai da na aika yara suka fito suka ce min wai kun tashi, kun kaura shagamu. Ance anyi muku mutuwa ko? Yanzu yara suke fada min. Aisha farida tayi murmushi tace kai dai bari yayana, tafiyar ce babu shiri, a kidime muka taho jikin anti abida ne ya matsa har ta suma an zaci ta mutu ne shine muka dungumo, muna nan dai a shagamu har zuwa wani lokaci. Kafin muga yadda Allah zaiyi damu. Amma yanzu an samu rabin warakar ciown, tunda an samu likita da ya gano matsalar. Barr muazzam yayi ajiyar zuciya yace har naji sanyi a raina, ai tuni hankalina ya tashi da naji ance anyi mutuwa. Sai na kawo anti abida ce, Allah dai Ya bata lafiya. Albishir nazo miki dashi sai gashi ba kya nan banji dadi ba. Aisha farida ta rike baki da daya hannun ta dafe kirji ta dinga fadin Allah mai iko, Allah abin godiya. Wai nice yau ake maganar aurena da dr shuraim? Maimuna ta fice ta barsu suna mamaki. Wayarta ce ta hau karan sai tayi sauri ta duba ta zaci rabin ranta ne, sai taga sunan barr muazzam ta danna da sauri sai taji muryarsa cike da farin ciki. Yace gani a kofar gidanku, na kira wayarki taki shiga sai da na aika yara suka fito suka ce min wai kun tashi, kun kaura shagamu. Ance anyi muku mutuwa ko? Yanzu yara suke fada min. Aisha farida tayi murmushi tace kai dai bari yayana, tafiyar ce babu shiri, a kidime muka taho jikin anti abida ne ya matsa har ta suma an zaci ta mutu ne shine muka dungumo, muna nan dai a shagamu har zuwa wani lokaci. Kafin muga yadda Allah zaiyi damu. Amma yanzu an samu rabin warakar ciown, tunda an samu likita da ya gano matsalar. Barr muazzam yayi ajiyar zuciya yace har naji sanyi a raina, ai tuni hankalina ya tashi da naji ance anyi mutuwa. Sai na kawo anti abida ce, Allah dai Ya bata lafiya. Albishir nazo miki dashi sai gashi ba kya nan banji dadi ba. Aisha farida ta dafe haba tayi dariya tace albishir din meye? Yace alewar saka aurena da janan na kawo miki. An bani ita har an kai kudi da kayan sa rana , nan da wata uku za a sha biki. Alewarki ta musamman ce, bounty na kawo miki har jaka biyu saboda matsayin ki a auren nan, sai gashi ba kya nan. Ko 'ya'yan yayanki suna ciki a kirawo mun su na basu? Aisha farida tayi dariya tace Allahi abin godiya, amma na taya ka murna yayana. Kuma na gode da karramawar da kayi min. Babu kowa a 'yan gidanmu, dukka muka taho. Nima kuma yanzu zan zankado maka nawa albishir din. Dr shuraim yana shagamu yazo da likita an duba anti abida, ya siya mata magunguna , ya biya makudan kudi za a kai jininta kasar waje a gwado. Sannan daga karshe ya kunso kudin aurensa ya kawo yanzu yanzun nan nima labari yazo min, suna can a kofar gida shi da yayyena da tsofaffin maza. Barr muazzam ya cika da farin ciki da mamaki, ya kyalkyale dariya yace ikon Allah, Allah mai yadda yaso. Wato auren namu ma tare za'ayi kamar yadda muka fara nema tare. Na taya ki murna kanwata. Baraka ma komai ya daidaita, ita da mijinta suna cikin farin ciki, ya rabu da nafisa , hankalinsa kacokan akan baraka. Ciki ne ma da ita, sai ririta cikin yake yi. Tace in gaishe ki da kyau, kuma tana matukar yi miki godiya, tana so ta ganki a rayuwarta. Tace in gayyato ki suna idan ta haihu. Aisha farida tayi dariya tace Allah Ya kaimu , idan dai ina kano zanje. Sukayi sallama ya kashe waya. 3 missed calls din dr shuraim ta gani a wayarta a lokacin da take waya yake kira, sai ta fara kokarin kiransa, shima ya kirata. Ta amsa sallamarsa cikin nutsuwa kafin ta gaishe shi ya jero mata tambayoyi guda uku, ta rasa wacce zata fara amsawa a cikinsu. Farida da wa kike waya nayi ta kira har sau 3 naji call waiting? Meyasa da kika shiga gida dazu baki fito ba mun gaisa har na tafi? Meyasa kwana biyun nan naga alamar kin daina damuwa dani? Sai ta lumshe ido tayi ajiyar zuciya sannan tayi murmushi. Tace bari na fara amsa maka tambayarka ta uku, sannan a gangaro ta biyu, sai in gangaro ta daya. Zancen na daina damuwa da kai wallahi ba haka bane, tunda ina tuna ka a rana sama da dubu. Sannan tambayarka ta biyu ina shiga gida na bawa anti abida magani sai na zauna ina saurarom fadan da goggo keyi mana ni da yaya hussaini, wai mun kawo likitoci sun duba ta sun bata musu aiki. Yaya hussaini ya wuce ba dadi, nima na fita. Sanda nagama zan fita aka ce min kunja mota kun tafi. Tambayarka ta farko kuma wanda nake waya dashi wani ne sunansa barr muazzam , bansan kai kira ba da na bashi hakuri na katse wayarsa na amsa taka. Amma kayi hakuri. Sai ya tashi zaune daga kwanciyar da yakeyi yace waye barr muazzam? Na fahimci dalilin da yasa yanzu bana gabanki, kinyi min kishiya, laifin me nayi bansani ba? A ina na kuskure in gyara? Taji tausayinsa ya kamata sannan tambayar ta daga mata hankali. Tayi ajiyar zuciya tace Allah sarki my love , sai naji kamar zanyi maka kuka da ka jera min wadannan tambayoyin. Nagode ma Allah da Ya sa duk abubuwan da ka tambaya bai zamo gaskiya ba. Yaya shuraim kai kadai ne a raina, ko a gaban idonka, ko a bayan idonka kai nake so. Baka taba yi min laifi ba balle naji haushi na canza ka. Haka baka kuskure ba, balle nayi tunanin wani. Barr muazzam wani bawan Allah ne da Allah Ya hada ni dashi a kano, ya taimake ni a lokacin da na shiga ukuba, sai muke gaisawa. Ya kawo min alewar bikinsa da dr janan bai same ni ba, shine yake shaida min a waya. Dr janan sunusi? Shuraim ya tambaya cike da mamaki. Aisha farida tace kwarai kuwa itace, dan ya taba bani tarihin rayuwarsa da ita. Wacce kwanakin baya ta shiga matsala har aka tsare ta ko? Dr shuraim yace tabbas ta dade ana shariar nan wacce aka ce ta nemo izzudden taki nunawa. Nasan janan, kawata ce ai. Kwarai Kwanaki tayi min waya ta fada min zatayi aure, ashe kin sansu? Aisha farida tace ban taba ganinta ba, sai dai mijin da zata aura. Dr shuraim yace shikenan ba matsala. Ki bani labari mai dadi mana wanda zai sani inyi bacci mai dadi tunda lukman yayi mun bakin ciki yau bazan ganki ba. Yace ya gaji anjima ba zai rakoni in ganki ba. Aisha farida tayi dariya tace zanso nima ka kwanta ka huta don kun sha hanya. Sai na biyu ina so in mika doguwar godiyata a gare ka bisa dawainiyar da kake yi mana da jinin jikinka da kuma dukiyarka, Allah Ya saka da alkhairi. Sai labarin da yafi kowanne dadi, yau farida ta zama ta shuraim, shima ya zama nata. Sai ya kyalkyale da dariya yace bani labarin me ya faru? Haka dai suka cigaba da hirarraki masu dadi cike da so da kauna har tsawon awa guda. Abida na kwance ta kafawa farida ido sai murmushi takeyi, tana murna a zuciyarta tamkar ta mike tayi rawa don babu hali ne. Tana adduar Allah Ya tabbatar da alheri a yi auren nan ko bayan ranta. ASUBA TA GARI AISHA FARIDA!!! BABI NA GOMA SHA TARA! Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba. Auren farida da shuraim sai kankama yake sake yi. 'Yan lungu yanzu sun gasgata, don da jita jita akeyi ko kuma ana ganin abin ba mai yiuwawa bane, wahalar da kanta kawai zatayi, yaudararta zaiyi ya tafi don ba ajinta bane. Sai gashi idan da a sati sau daya ake ganinsa , yanzu a sati a kalla yazo sau biyar. Ba sai an fada ba, rayuwa da tukunyar su aisha farida ta canja gaba daya, sun fara bankwana da talauci, dr shuraim ya tsaya musu. Tun ba a yi auren ba ma har ta kidime ta canza salo da yanayi, kai kace ba wannan faridar bace ta da. A yanzu farida ta zama gangariyar 'yar gayu. Komai nata mai tsada ne (high class) , kama daga suturunta, takalmanta, da jakunkuna, mayukan shafawarta da kayan kwalliyarta. Sai ta canja tafiya, ta canja magana ta kuma canja tsarin rayuwarta. Bata wulakanta 'yan lungu amma bata cika shiga cikinsu a yita wasannin banza ba da surutai barkatai. Zama da dr shuraim ta koya nutsuwa ga jan aji , magana ma sai an daidaita baki. Haka ba a cika dogayen jimla da hausa ba sai an tottoshe da turanci. 'Yan lungu sunyi gulmar, sunyi zumden, sunyi yaficen, abin ya wuce tunaninsu. Sai cigaba suke gani kala kala musamman da suka ga ta fara aiki ya daukar mata mai adaidaita sahu ya kaita ya dawo da ita. DUK KYAN TAKALMI 3* 10 Abida na tsakar gida tana kallon bakinsu bata ce musu komai ba suka gaji, har takai ta kawo ma sun zo sun same ta don suji wani labari game da wannan aure na farida, sai ta nuna musu ba lallai sai dr shuraim ba, duk wanda yafi alkhairi a farida shi zata aura. Basu ankara ba sai suka ji tashinsu, sai ana gobe zasu koma sabon gidansu suka fada musu. Mamaki ya rufe jama'a, 'yan rakiya mata lodi lodi suka bisu don su ganewa idanuwansu. Gida mai kyan gaske babu abinda ba'a zuba ba, tun daga gadaje a dakuna uku da kujeru a falo duk shuraim ya siya, gida gini bulo da bulo sama da kasa duk tiles. Rayuwa sabuwa ta tabbata a gidan hussaini, farida bata rasa kudi. Dr shuraim yana bata, ta dauki albashinta kuma. Babur ta fara siyawa yayanta, kuma ta canja wa 'ya'yanta makaranta ta kudi anan court rd, mai adaidaita ya kaisu ya dauko su. Sun koma sabon gida ba dadewa aka saka ranar kawo kayan sa rana da na lefe gaba daya. Kudin mota baiyiwa su aisha farida wuya ba, suka turawa magabatansu a shagamu, mata bakwai maza uku suka shigo mata suka zo kano don karbar kaya. Abida bata mance da kawayenta na tsohon gidansu ba, fiye da bus uku suka ciko suka zo don su ganewa idanuwansu. Tunda kan 'yan uwan shuraim kallo ya fara kafin a bude kayan lefe. Masha Allah! Tabarakallah! Kaya sun yi kyau. Akwatuna shida da kit biyu. Da saitin sarkokin gwal da awarwaraye hudu manya. Wata uku kacal aka saka ranar bikin, kowa yana sam barka tsakanin dangin amarya da dangin ango, har aka watse. An sha dauki ba dadi a bangaren dr shuraim kan maganar aurensa, 'yan uwansa mata da yawa basu son auren, kasancewar sun iske dangin amarya basu da hali. Cece kuce kala kala sukayi tayi amma shuraim bai damu ba , tunda mahaifansa sun yadda, sunyi masa fatan alkhairi , don haka suje suce duk abin da zasu ce. Da farko dai mahaifiyarsa taki yadda, amma da yake tana jin maganar mijinta, kuma kaifi daya ne, duk abin da ya fada ya zauna a gidansa dole a bi. Amma a sanda guguwar rigimar ta buso daga bangaren matar shuraim wato faiza sai ta kore ta danginsa saboda tafi karfi. A sanda shuraim ya shaida mata a waya cewar zai kara aure aure cikin lallabawa da tattausan kalamai, sai ta hasala tayi ta zage zage har da koke koke wai bata yadda ba. Ya shaida mata aikin gama ya gama, saura wata uku, kuma ba zai fasa ba. Haka aka tashi dai baram baram a wayar, shi ba dadi, ita ma ba dadi. Bayan sati guda da wayarsu sai gata a Nigeria ita da mahaifiyarta. Ba sulhu ne ya kawo su ba, rigima ce tsantsarta. Mahaifiyarta tace sai dai ya saki 'yarta , dama can ita ba son auren take yi ba. Tunda yace zaman nigeria zaiyi tasan zai cuce su. Ta gangaro kan mahaifansa tace dama sun tsani 'yarta faiza, sune suke hadasu fada. Da kyar rigiman nan ta lafa, su dai mahaifan shuraim ba su rama ba, amma 'ya'yansu sun rama musu, akayi ta cece kuce. Shuraim ne yayi ta bada hakuri har aka samu hayaniyar ta sauka, zuciyar kowa ta dan lafa aka zauna taro a babban falon mahaifinsa aka fara bayanai da yadda za'a gano bakin zaren. Kiri kiri matar shuraim ta fada wa mahaifiyarta tana son mijinta, ba zata iya rabuwa dashi ba. Mahaifin shuraim yace to ki kwaso kayanki kizo ki zauna da mijinki da 'yarku a gabanku. Karatun fa? Inji mahaifiyarta ta fada a fusace tana harararta. Tace saura 'yan watanni na gama, zanje na gama na dawo na zauna. Ta sha adduoin albarka a wajen mahaifin shuraim da shuraim din kansa, gami da danginsa. Yayin da ta sacewa mahaifiyarta gwiwa don ba haka taso ba. Ta fusata tace to ko sau daya kada kizo kice an miki wulakanci, kije can ki karata. A daddafe ta bari sukayi kwana uku sannan suka koma london. Kafin su tafi kullum kuka faiza take yi wa shuraim tana cewa baya sonta yanzu tunda zai auri wata. Ya iya dadadan kalamai masu kwantar da hankali, gami da bayanai masu ma'ana ya hada da yi mata alkawari zaiyi musu adalci a tsakanin su. Sai taji sanyi a ranta, ta kuma yadda da duk abinda yake fada mata. Rabuwar lafiya yayi da matarsa, uwar ce dai ko sallamarsa bata amsa ba a airport. Hankalinsa ya kwanta a wannan bangaren kuma bashi da sauran rigima. Duk dauki ba dadin da suka yi aisha farida bata sani ba, bai bari ta sani ba. A bangaren ta matsala kadan ta samu daga musbahu, a inda ya tayar da hankalinsa, ba ci ba sha da yaji abar kaunarsa zatayi aure ta barshi. Ya hada kayansa zai bar garin, zai shiga yawon duniya a rasa shi har abada. Tunda ya rasa farida, to shima mahaifiyarsa da matarsa sai sun rasa shi. Hankalin 'yan gidansu da mahaifiyar sa ya tashi, mahaifiyarsa da kanta tayiwa aisha farida waya ta shaida mata halin da musbahu yake ciki kuma suka roke ta tazo ta bashi baki ko zaiji. Sai kawai ta fashe da kuka ta kashe wayar. Abida tazo ta iske ta tana kuka ta tambaye ta suka zauna suka yi shawara. Ta bata shawara ko bata je wajensa ba, ta saka kati a waya ta kira ta bashi hakuri akan yayi tawakkali , ya daure ya karbi kaddararsa , zai yiwu shi ba alkhairi bane a gareta, itama haka. Ya zauna kada yace zai gudu, baisan inda zai fada ba. Kuma Allah Zai barshi da gudun tunda bai yadda da hukuncin da Ya yanke masa ba. Haka aisha farida tayi, sai bayan kwana biyu ta kira shi a nutse tayi masa nasihu masu ratsa zuciya. Har sai da yaji ba zai tafi ba, ya fasa. Yana kuka, tana kuka, tanayi masa fatan alkhairi da godiya. Shima irin wadannan adduoin ya dinga zuraro mata har ta kashe wayar. Banbancin bikinta da na barr muazzam sati uku ne, don haka sanda taje dinner party'n bikinsu a tahir guest palace da daddare ta tafi musu da katin bikinta ita ma. Barr muazzam yayi farin ciki da ganin farida da shuraim a wajen bikinsu. Da farko ma bai ganeta ba, saboda kyan da tayi ta goge, ta waye ta tsatso da wani kyau na daban. Duk da dandazon taron nan kowa yana kokarin ya gaisa da ango da amarya, sai da muazzam ya taso ya tare su ya kamo hannun amaryarsa ya gabatar mata da aisha farida da ya dade yana bata labarinta. Daman ta san shuraim har ta gayyece shi bikinta, shuraim ma ya gabatar mata da farida a matsayin amaryarsa. Daga karshe muazzam ya kaisu wajen barr nuruddin suka gaisa, suka zauna a kurkusa. Tabbas daga gani babu tambaya, nuruddin yayi mamaki da ganin farida, shi bai taba tunaninta ba tun wacccan ranar, sai ya dinga tuno wulakancin da yayi mata a baya, yana jin nauyinta. Ya sake yin mamaki da yaga matarsa ma ta santa, sun kebe sai hira suke yi kuskus suna ta tuntsira dariya kamar sun saba. Ya kalli shuraim ya sake kallonsa, ya tabbatar ya hadu, Allah Ya tsara halittarsa a nan ko ba'a fada masa ba yasan akwai kudi da ilimi, kuma ita zai aura. Ya tara tambayoyo jifgi guda a zuciyarsa yana so ya samu muazzam ya jero masa su akan farida. Baraka ta dubi aisha farida tayi murmushi tace ina ta jin labarin aisha farida kullum, sai yau Allah Ya nuna min ke. Babu abinda zance miki ni da muazzam a duniya sai dai godiya, kin ceci rayuka. Ni da na zata ma soyayya kukeyi da barr muazzam, sai daga baya na gane jininku ne ya hadu, ya bani labarin ki da likita, kuma naji dadin ganinku a tare. In Sha Allah kuma zanzo bikinku duk da watan haihuwana ne wannan. Farida tayi dariya tace nafi kowa farin ciki da dukkanin mu Allah Ya amsa adduar mu , Ya bamu wadanda muke so. Ina nafisar ta sa take? Yaya suke a yanzu? Baraka tayi dariya tace ai ko zancenta ba yayi, ko kiransa tayi sai ya katse. Baya son abinda zai bata min rai, yanzu duk abinda nake so shi yake min. DUK KYAN TAKALMI 3* 11 Tunda bikin farida da shuraim ya rage saura sati guda basu zauna ba, daga ango da amarya har danginsu. Sai shirye shirye akeyi kala kala. Bayan yinin biki da kowanne bangarorin biyu zasuyi, akwai shagulgula har guda biyu da dangin ango da amarya zasu hadu a waje daya ayi. Daya da yamma za'ayi a tahir guest palace sai dinner a Chinese dragon da daddare za'ayi, kowanne kuwa sai da aka fitar da anko. Kayan fitar bikin ango da amarya daban aka dinka musu yadda zasuyi shigar kala iri daya tsadaddun gaske. Asabar ce yau misalin karfe biyar na yamma n shuraim ya sauke aisha farida a kofar gidan kawarta khadija sani dake sokoto td don ta mika mata katin gayyatar bikinta ta fito su tafi. Saboda akwai wurare da yawa da zata kai kafin magriba ya mayar da ita gida,saboda dokar da yaya hussaini ya saka mata cewar duk inda taje ta dawo gida kafin magriba ko da kuwa tana tare da shuraim ne tunda ba a daura aure ba. 'Ya'yan abida dukka hudun ne 'yan rakiya suna zazzaune a bayan mota sunyi dai dai da kayan ciye ciye da shuraim ya dau nauyin tulo musu. Suci biskit su kora da alewa, sai su dora da ice cream da shawarma. Ehm! Dadi kan dadi wai kunama ta harbi gyambo, abinda basu taba ci ba a yau gashi sun samu. Kada ki shiga ki zauna kiyi ta labari fa a ciki. Shuraim ya fada a lokacin da ya kashe mota dai dai wani bakin gate. Ta dube shi tayi murmushi ta gyara farin gilashin fuskarta tace bazan zauna ba yayana, yaya za'ayi in iya zama inyi hira alhali nasan kana jirana? Ina mika mata zan fito. Ta juya ta dubi yara tace ku zauna yanzu zan fito ba sai kun bini ciki ba. Ta bude mota ta fito, takawa take a nutse kafarta sanye da wani cogen takalmi mai tsinin gaske, launin baki da bakar jakarsa. Sai ya kara mata tsawo. Doguwar rigar jikinta (gown) da aka dinka mata a jikin super holland purple da baki ta sake fitowa da kyauwn dinkin. Dr shuraim ya bita da kallo saboda kyauwnta da yake gani, ji yake tamkar zai hadiyeta don kauna. Tana shiga gidan khadija ta iske ta a falo ita kadai tana kallon MBC action, bayan ta amsa sallamarta ta nuna mata kujera ta zauna, sannan ta sake kallonta sosai, sai a lokacin ta gane aisha umar ce. Khadija ta zabura ta mike tsaye, ta jawo dogon salati ta dire, ta rike haba tare da dafe kirji. Tace aisha umar dama kece na kasa gane ki? Ikon Allah kece kika zama haka? Daman maryam ahmad tace idan na ganki yanzu ba zan gane ki ba. Saboda kin sauya gaba daya kin zama 'yar gayu. Dariya kawai farida ke kyakyatawa, khadija ta matso kusa da ita ta zauna ta shafa jikinta, ta sake nanikarta don ta tantance kamshin turaren da take ji a jikinta , tabbas designer ne. Kudinsa ba zai gaza dubu ashirin ba. Ta janye dankwalinta don taga gashinta. Sai taga waccan cunkusheshen gashin na farida mai tauri da ba a shamfo sai kitson zane kullum yanzu ya sha mai (relaxer) yayi yalo yalo kamar na larabawa, baki sidik da shi, ya warware ya mike daman can mai yawan gashi ce da tsawo, don haka ya wuce kafadarta. Babu abinda khadija ke kira sai ikon Allah! Aisha umar yaushe kika zama haka? Aisha farida tayi sauri ta gyara daurin dankwalinta ta mike tsaye tana dariya tace Khadija bana son wulkanci, wane irin tonon silili kike yi min haka? Ke dai wani labarin zamuyi shi idan muka hadu, yanzu sauri nakeyi na bar shi a kofar gida. Katin bikina na kawo miki, rana ita yau yini da party. Ta zaro wasu hadaddun katina guda biyu ta mika mata daga cikin hadaddiyar jakar dake rataye a kafadarta. Ta juya da sauri ta fara tafiya. Khadija sani ta watsar da katunan akan kujera ta biyo bayanta da sauri. Tace ke aisha umar ko ruwa ba zaki tsaya ki sha ba? Dan mai adaidaita sahu ba sai ki sallame shi ba sai in mayar dake anjima da daddare ba? Ko angon ne ya fara hana ki kaiwa dare a waje? Lallai kina ji da wannan angon naki, ance mai kudi ne shi ya tsaya miki, ance yana sonki tamkar ransa. Auwal dan ajinmu yace min a likita zaki aura , rannan na hadu dashi auwal din a ministry of health yace min tare kuke aiki. Wai meye gaskiyar maganar? Aisha farida dai har yanzu dariya take yi, tace khadija don Allah ki ajiye tambayoyin nan naki sai mun nutsu zan amsa miki su. Daidai lokacin khadija ta tura kofar gate din suna kokarin fitowa, ta daga kai ta dubi dankareriyar motar da aka kawo aisha farida a ciki, sai tayi ajiyar zuciya kafin tayi magana. Sai ta daga kai ta hango santalelen saurayin da yake tsaye a jikin motar. Ya kalle ta, ta kalle shi, ta daka tsalle ta koma cikin gida da gudu, ta labe a jikin gate din tana salati. Aisha farida ta firgita itama tabi bayanta da sauri ta rike ta tana tambayarta lafiya? Khadija ta rike kirji tace aisha umar kamar dr shuraim nake gani a kofar gidana? Lafiya ya biyoni? Ba dai asirin da nayi masa bane yanzu ya fara cinsa ya biyo ni har gidan mijina? Yaya zanyi yau? Aisha farida tayi dariya tace ta yaya dr shuraim zai san gidanki har ya biyo ki? Wa ya fada miki asiri yana ci? Tabbas sihiri gaskiya ne amma bai cika kama wanda yayi imani da Allah ba. Dr shuraim ni ya kawo, don ni yazo gidannnan, shine angona. Khadija ta bude ido da baki gaba daya tana duban aisha farida, mamaki marar misaltuwa zaka gani a idanuwanta. Tace aisha umar yanzu dr shuraim zaki aura shine baki fadawa kowa ba? Ashe daman kema kina sonsa a lokacin da muke sonsa kika boyewa kowa? Ta ya kika same shi? Ke kuwa wane irin asiri kikayi masa haka? Aisha farida ta girgiza kai tace babu asiri acikin lamurana, sai dai addua. Addua na rike, ita ta kaini ga matsayin da ban taba zato ba. Khadija nayi alkwawri idan na samu nutsuwa zan fada miki dalla dalla yadda muka hadu da dr shuraim har ya zama mallakina. Sai anjima, sai kinzo bikina, adireshin wuraren duk suna jikin katin. Aisha farida ta juya ta tafi, yayin da ta bar khadija a sankare a tsaye, baki a bude don gigicewa da mamaki. Daga gidan khadija, gidan maryam ahmad suka wuce dake unguwar sallari. Irin wannnan mamaki da figici da ya samu khadija sani shi ya fadawa maryam ahmad. A lokacin da ta fito har mota don su gaisa da angon kawarta, ta iske dr shuraim ne. Sai da aisha farida ta tare ta don ta kusa faduwa don tsorata. Ta shiga yiwa farida rada tana cewa ke dr shuraim ne wannan ko kaninsa? Aisha umar ina kika same shi har zakuyi aure? Labarin yana da tsawo! Amsar da ta bata kenan ta shige mota suka ja suka tafi ta bar maryam a sankare a kofar gida. Aisha farida ta sake kyalkyalewa da dariya tace tunda kace Allah ai ka gama daure min jijiyoyin jikina. A lokacin tabbas nima mutum ce kamar kowa, kuma mace yadda suke mata. Naji abinda suka ji a raina, amma sai na fisu hakuri da tawakkali. Na sama raina har abada ba zan same ka ba gara ma kada in jefa kaina cikin wahala. Don haka ban cusa kaina ba, ina gefe ina addua, Allah masanin komai, sai Ya bani kai a lokacin da ban taba zata ba. Dr shuraim yayi murmushi ya lumshe ido yace na fahimce ki, kuma na gamsu da bayananki. Amma maiyasa kika tsorata baki zo kin gwada sa'arki ba? Kika sani ko kici nasara ki same ni? Ta girgiza kai tace karfina ko wayona da kwarkwasata ba zasu amfana min komai ba. Saboda naga 'yan mata da suka fini komai basu same ka ba. Yayi dariya yace kin taba sanin kina da kyau kuwa? Kyawun da tunda nake ban taba ganin wacce ta yi min kyau kamar ke ba. Tun ranar da na fara ganinki a duniya na tabbatar kina da kyau , da zan iya samunki da naji dadi. Sai aisha farida ta dafe haba ta bude baki tayi ajiyar zuciya ta langwabar da kai gefe. Tace shikenan my dear tunda har abin ya zama ba'a. Dr shuraim ya juyo a hankali ya dubi kwayar idon abin kaunarsa yace na taba yi miki karya ne? Toh ki yadda da magana ta, kina da kyaun da ba a ko ina ake samunsa ba, babu kantin da za'a iya samunsa a saya. DUK KYAN TAKALMI 3* 12 Yace,na taba miki karya? toh ki yarda da maganata,kina da kyan da ba a koina ake samunsa ba,babu kantin da za a iya samun irinsa a saya saboda dalilaina masu zuwa.na daya kina da kyakkyawar fata irin ta 'yan kasar itiofiya,mai hasken duhu(chocolate color).na biyu,kina da gashi mai kyau,irin na asalin Africa mai gazar-gazar da baki,irin wannan gashin shine a girarki da fatan idonki.na uku,kina da kyawun kwayar ido dara dara,farare sol!idan kina kallon mutum sai yaji wani yarr a jikinsa saboda kina da idanuwan nan da ake kira sexy eyes.na hudu,hancinki bashi da tsayi sosai,haka bashi da fadi ya dace da fuskarki.na biyar,bakinki dan karami,kina da hakora farare sol,ga 'yar siririyar wushirya a tsakiya.ga ki da fara'a idan kika yi dariya sai gefen kuncinki su loba dukka biyun,na shida,Allah yayi miki wata irin murya mai dadin gaske,wacce ko yar uwarki mace taji muryarki sai ta waiwayo balle da na miji.dadadan lafuzzanki su suke karawa muryarki dadi.na bakwai,Allah ya miki kirar jiki mai kyau,a dire kike,baki da kiba,ba ki da rama.sannan bakiyi gajarta ba,ba kiyi tsawo zalolo ba.amma duk wannan bai jaa hankali na na fara sonki ba,sai da na gama karantar halayenki na tabbatar kina da hankali,kirki,t awakkali,sannan kina da aji. Abubuwa biyu ne suke tafiya da tunanina a wajen mace,shine,idan mace tana da aji da kuma kamun kai wacce ba yar iska ba.kin yi sa'a kina da duk wadannan.aisha farida tayi hamdala a zuciyarta,tayi murmushi a sarari,ta dube shi tayi fari da ido.ta ce,nayi sa'a da nayi dace na sameka.Dr shuraim hakika kana da kyau babu inda Allah ya rage ka tun daga halittarka,ilimi da dukiya.duk wadannan basu dameni ba,sai na dinga lura da halayyarka.na shiga halin damuwa alokacin da ka gwada ni cewar zaka tafi da ni gidanka ko ba kayi bayani ba na fahimci abun da kake nufi,sai na kudiri niyyar rabuwa da kai har abada,kyawunka, dukiyar baza su taba burgeni ba,tunda kake sabawa Allah.sai daga baya na tabbatar ba haka kake ba,kai mutum ne mai tsoron Allah da tausayi shine na saki jikina na tabbatar nayi dace da miji nagari.su dukka sukayi dariya a lokaci guda. Dr shuraim yace kin cika mai hankali mai zurfin yunani,kuma ba zakiyi da na sani ba tunda kika farga kika san kyau da kudi ba komai bane in dai mutum bashi da hali na gari.matsalar da ke damun yanmatan zamanin nan ke nan,shi yasa ake samun matsala a zaman aure,sakin aure ya yawaita a kasar hausa.hirar so da kauna da fahimtar juna suka yi tayi,har suka isa kofar gidansu.yayin da yaran suke baya suna ta hidima da kayan dadi,sai ci suke tayi,ya ki ya kare saboda ledoji da yawa ya ciko musu.aisha farida tayi godiya suka fito daga motar suka shiga gida,dr shuraim yana daga muau hannu,su ma suna daga masa har ya tafi.su dukka suka ji kamar kada su rabu da juna,sai kuma gobe idan Allah yaa kaimu zai dawo don yanzu ba ya fashin zuwa wajen farida.ASUBA TA GARI LIKITAN AISHA!!! BABI NA ASHIRIN BIKI!BUDIRI! BIREDEDE! Rana bata karya sai da uwar diya taji kunya.tun ranar laraba aka fara gudanar da shagalin bikin farida da angonta dr shuraim.akayi kamu laraba,alhamis akayi kunshi,jumaa akayi sisters eve da yamma.ranar asabar aka daura aure da misalain karfe goma sha daya na safe abisa sadaki mafi kankanta don neman albarkar aure,kuima a ranar akayi yinin biki.dangin farida sunzo da yawa maza da mata daga shagamu,tun sanda biki ya rage sati guda suka fara zuwa don su taya ta murnar biki.a ranar asabar da daddare akayi hadadden party a hotel din tahir guest palace,wanda mutane da dama suka halacci wajen. Manyan likitoci abokan ango da kawayen amarya,da yanuwaansu da abokan arziki kowa yazo.makada kala kala sunzo kamar mai dawayya,dan asharalle,yaron saadu bori,fati niger,rabi mustapha,kowannensu an bashi fili ya cashe.wannan yayi sai ya matsa ya baiwa wani fili.babu abun da ake kira sai likita shuraim angon sista farida.barista muazzam da amaryarsa janan,barista nuradin da uwargidansa baraka su ma sun hallara.yan unguwansu ta da duk sun zo babu wanda yasan adadin wadanda suka zo,saboda yawansu.taro yayi taro har amarya da ango basu iya gane wadanda suka zo da wadanda basu zo ba.kallo daya zaka yi wa ango da amarya ka tabbatar suna tsananin murna.idan ka kalle su zaka san maauratan nan suna tsananin son junansu.sun ba wa kowa shaawa sosai saboda sunyi kyau matuka,shigarsu ta burge kowa,kowacce rana akwai kalar kayan da zasu saka kala daya. Kawayen amarya su ma sunyi nasu ankon,dangin ango da irin nasu ankon daban.'yan shagamu ma da irin nasu ankon daban.masu daukar hotuna da bidiyo suna ta aikin dauka,sai yau mutane da yawa suka gasgata shuraim yayi saar mace mai kyau,don kyawunta ya fito kamar ba ita ba.ana daf da za a tashi sai ga uwar gidan shuraim faiza ta shigo fili,ta yi wa kowa ba zata ita da kawayenta guda biyu hafsat da halima su ma mazauna london ne,tare suka zo daga can.don da shuraim yayi yayi tazo bikin tace baza ta zo ba,toh ashe ta taho bai sani ba.ta danne kishinta tayi ta musu kari da daloli sai a lokacin aisha farida ta fara ganinta,ita ma haka,don ko a hoto ma bai taba nunawa ko wacce ba.kyawunta bai tsorata aisha farida ba ko kadan,don bata fita kyau ba.fari kawai zata nuna mata,tsayinsu daya,har farida ta fita tsawo da yawan gashi.faiza ce ma ta tsorata da ganina aisha farida saboda tayi mata ba zata,ba ta zaci ta hadu haka ba,don 'yan gulma sun tsegunta mata yar talakawa ce,baka mummuna,ashe abun ba haka yake ba. Faiza ta kudiri aniyar zama na kishi,ba kishin dokedoke da zage zage ba sai dai zata nuna mata ruwa ba saan kwando bane.wayewa da gogewa a cikin wayayyun duniya tabbas abun da ta sani farida bata sani ba,kuma ba zata taba sani ba.zata san tayi garajen aure mata mili,don mai karbar shuraim ahannunta sai yayi shirin yaki sosai DUK KYAN TAKALMI 3* 13 Sai dr shuraim yaji dadi da ganin faiza ta saki ranta,suka gaisa da farida sosai,har da baby yarsa mai kama da uban kamar an tsaga kara.babu wacce ta fi jin mamaki da ganin aisha farida ita ce amarya sai kanwarsa da suka hadu da ita a asibiti.suna ganin juna suka shaida kansu,suka gaisa cike da farin ciki. Washegari ranar lahadi da yamma akayi walima da yamma a farfajiyar gidansu farida,aka zuba kujeru da yawa da manyan dardumai.mata ne zalla da kananan yara sai amarya da ta sha alkyabba,kawaye nta suka zagayeta tana kan darduma a zaune daga gabagaba. mata guda uku ne suka yi waazi a wannan waje,dukkaninsu akan falalar bin miji suke magana.saboda yadda aazin ya ratsa zuciyoyin mata,sai kowacce jikinta yayi sanyi har da masu zubar da hawayen imani.daga karshe abida ce ta karbi lasifikata hau kujerar malamai ta dubi dandazon matan da suka taru a wajen,yawansu ya kai yadda baza su kirgu ba,yara,manya,yanmata da tsofaffi.sai tayi murmushi tayi musu sallama,sannan tayi bismillah,ta dubi aisha farida. Like · 2 · 9 April 2013 Hajara Haruna Mahmud Ta ce,nasiha zanyi miki ya ke kanwata farida game da zaman aure.na farko iani miki nasiha da ki bi mijinki domin aljannar mace tana karkashin tafin kafar mijinta.yake kanwata,ki fi shi farin ciki idan yana farin ciki,sannan idan yana bakin ciki ki fishi bakin ciki.ki kwantar masa da hankali.ya ke kanwata aisha,ki lura da lokacin cin abincinsa,domin mayunwaci mafadaci ne.duk lokacin da kika lura lokacin cin abincinsa yayi toh ki tanadar masa kafin ma ya iso.idan ya shigo gida bayan kinyi masa tara irin ta darajawa,toh ki gabatar masa da abinci ba sai yace ina abincina ba?don idan bari ma ya tambayi abinci to ransa ya baci ma kafina a kawo masa abincin.wani ma sai yaji baya shaawar abincin,sai yaji gara ya tafi hotel ya ci mai dadi,duk ranar girkinki sai yaki dawowa yaje yaci awaje. Ya ke kanwata ki lura da lokacin da mijinki yake jin bacci,ki bar shi ya kwanta ya huta saboda wadansu matan sai sanda mijinsu yake jin barci zasu tayar da shi su ce suna da magana,yayi-yayi ta bar maganar sai da safe tace wlh sai ka saurareni.daga lokacin da kike hana mijinki yayi bacci a lokacin da yake jin barcin to kina haddasa kakkaurar gaba ce wacce ba zata gushe a tsakaninki da shi ba. ya ke kanwata ki zauna a shirye ki nunawa mijinki koda yaushe kina bukatarsa.duk wani yanayi na kwarkwasa ki dinga nuna masa.duk lokacin. Da kike zaune da shi. Ki dinga shafar dukkanin sassan jikinsa yadda zai yi farin ciki. Ya ke kanwata ina horarki da yin ado ki lura da ina yake fara kallo a jikinki da zarar ya shigo cikin gida. Wani mijin fuskar matarsa yake fara kallo,wani mijin da ya shigo kirjin matarsa yake fara kallo,wani bayanta yake fara kallo. To ki nutsu ki gane inda naki yaje fara kallo. Idan fuska ce ki kula da lokacin dawowarsa kafin ya shigo sai ki gyara fuskar ki wanke ki saka hoda ki saka jagira,jan baki,eye shadow da dai sauransu yadda fuskar zata yi kyau sosai. Da ya zo sai ki yi kokarin nuna masa fuskar kina murmushi. Idan kirjin yake fara kallo to ki tanadi bra mai kyau,irin mai karfen nan mai gyara kirji. Tunda kin san kirjin yake fara kallo to ba zai so kirjin ya ragwargwabe ba. Ko bayan kin haihu sai ki bi duk hanyar da za ki bi kada ki bari ya tamule,don wasu matan su suke kwararraba kansu da zarar kin haihu sau daya yaga kin tsufa sai ya fara sha'awar ya auro wata budurwar mai kirji a cike. To amma idan kika iya kula da kanki,ba ki lalace ba ba zai tunanin neman wata ba In a gargajiyance ne akwai abunda larabawa suke yi kirjinsu ba ya tamulewa,alkamadin nan da kuka sani tana da amfani. Da zarar kin sa rananr da zaki yaye danki kamar sati uku kafin ranar da zaki yaye shi sai ki dinga yin kunun alkama da nono ko madara,madarar fulani ba yar kanti ba. Ki sha kofi daya da safe kofi daya da yamma. Bayan kin yaye yaron ma sai ki sake yin sati uku kina sha,sati 6 kenan. Sannan randa kika yaye yaron kuma sai ki saka bra wacce ta matse ki sosai to wannan zai hana shi ya zube duk da gyara ba zai yi kamar kari ba. Ya ke kanwata ki lura da wuraren da mijinki yake sa ido a jikinki in bayanki yake fara kallo to akwai bukatar ki koyi tafiya idan yace miko min buta sai ki juya kina jujjuyawa ki wuce gaba yana biye da ke kice za ki kai masa har bandaki. Ya ke kanwata kada ki yarda mijinki yaga abun ki a jikinki, ki kiyaye hancin mijinki kada ki yarda hancin sa yaji wani karni,doyi ko bashi a jikinki to duk lokacin da ya shigo dakin ki ko baby warin sai yaji kamar da warin ba zaki taba yin farashi a wajensa ba,kin zubar da ajinki a wurinsa.saboda dauda ta dade tana kashe aure sai a dauka wata aljana ce take zuwa ta raba aure nan kuwa alnakiya ce kawai. Ya ke kanwata ki kyaye kunnen mnki kada ki yarda ya ji mummunar magana daga bakinki. Ya zamanto duk abinda zai fito daga bakinki zuwa kunnen mijinki to magana ce ta girmamawa,jan hankali ko ta tayar da sha'awa. Misali da na ganka sai naji jikina ya yi wani zim don dadi (haha) yake kanwata a lokacin da mijinki yake kwance dake ki nuna tunda kike a duniya ba a taba dadada miki ba irin a wannan lokacin domin wannan zai sa kullum ya yi sha'awar kasancewa tare dake. Ya ke kanwata magana ta karshe da zan fada miki ki guji bakin kishi,kishin da zai sa ki kasa zaman lafiya da mutanen gida. To wannan kishin zai saka tsana a zuciyar mijinki,kishin da mace za ta yi shine wanda na fada a baya,ya zamanto ba ya ganin wata mace a duniya sai ke.duk abunda zaki yi ya zamanto idan yana rumfar kasuwarsa ko office ke yake tunawa.amma kishin da zaki sa mijinki,abokiyar zamanki ko makotanki cikin fitina to wannan kishi ne na lalatar zamantakewa na aure. Allah ya nuna mana ladubba na aure babu laifi mace taci abinci tare da mijinta.ta bangaren maza kuma addini ya nuna kada ango yaje dakin amaryarsa haka hannu ba komai ya nemi dan wani abu da zasu lasa kamar dan nama,lemo ko dan cincin ya tafi da shi dakin amarya. Da farko yayi mata sallama ita kuma wajibi ne ta amsa ba wai ta dinga noke-noke ba wai sai an sayi baki. To bakin dukka ya biya tunda ya biya sadaki. Bayan nan sai ya shiga dakin da farko ya kama gashin madigarta ya rike sai yayi addua yana tsaye a kanta. "Allahumma inni as'aluka min khaira ha wa khaira ma fiha wa khaira ma jabaltaha alaihi wa'auzubikha min sharriha wa sharri ma fiha wa sharri ma jabaltaha alaihi. Ma'ana "ya Allah ina rokonka alkhairin wannan amaryar tawa da alkhairin da ka halicce ta akai kuma Ya Allah ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin da yake tare da ita da sharrin da ka halicee ta akai" saboda wata ballagazar daga ya kai hannunsa kanta sai ta buge hannun ta ce zai murde mata kai. To iyayenta basu taba fada mata ba ko malamanta. Ko da ya manta to ki cire dankwalinki ki mika masa kai,ki tuna masa idan ma bai sani ba ki fada masa yadda zai yi idan ke kin sani. Kuma ba amrya kawai ba ko da wani abu kika siya kamar gida,mota ko dabba kafin ka fara amfani da abin ka yi wannan addua. Idan dabba ce an ce ka dafa bindin kamar kaza sai ka kama bindinta ka yi wannan addua to ba za ki ga wani abun bakin ciki game da wannan dabbar ba. Haka idan sabon gida ne ya dafa saman gidan yayi wannan addu'ar in mota ya siya ya daga saman motar yayi wannan adduar. Bayan ya yi wannan adduar to sai ya zauna a kusa da ita su rungumi juna su yi godiya ga Allah da yasa suka zama halal ga junansu sannan ya gabatar da wannan dan kayan makulashen da ya shigo da shi su ci,ana ci ana hira ta sha'awa da bege. Amma an fi so kafin ciye- ciyen su fara gabatar da sallah raka'a biyu nafila,kai ne daman liman sai ka daga hannu ka yi muku addua,Allah ya raba ku da sharrace-sharac cen makiya,ya baku zuria ta gari,amarya tana cewa amin.in duk sun kammala wannan suka shiga kwanciya miji ya kusanto matarsa sai yayi wannan addu'ar yace bismillahi Allahumma jamnibnashaidan a wa jannabul shaidana ma razaktana. Ma'ana,da sunan Allah,ya Allah ka nisantar da shaidan daga garemu,kuma ka nisantar da shaidan daga abunda ka azurtamu da shi. Manzon Allah (S.A.W) ya ce idan Allah Ya azurta su da da a wannan saduwar da suka yi to babu rabon shaidan a jikin wannan dan. Ba zai iya cutar da shi a jikinsa ba ko a zuciyarsa ba. Ba ranar angonci kadai ba duk randa zaku sadu miji yayi wannan addua idan ya manta ki tuna masa. Ba amarya kawai ba,babu wacce bata karu da nasihohin abida ba. Kuka yayi mata face-face a ido kafin ta gama kamar yadda ya yiwa aisha farida. Ta tabbatar yau abida ta cika amanar da ta dauka ta rike ta tun tana karama har zuwa wannan ranar data aurar da ita,ranar da za ta damkata a hannun mijinta. Aisha farida ta taso da sauri tana kuka ta rungume abida suna ta kuka.kanwar amarya manauwara ita ma ta taso ta zo ta rungume su suna kuka.yayin da yan'uwa da sauran jama'ar dake zaune a wajen suka dinga fashewa da kuka don tausayinsu. Aisha farida ta dago ta dubi jama'ar dake wajen ta sharce hawaye. Tace" aunty abida ta yi min komai wanda uwa da uba suke yi wa yarsu. Tun ina karamata har izuwa ranar da zata raka ni gidan mijina. Alllah shi ne gatana abida ita ce jigo kuma jagorar data kaini ga samun nasarar komai da na samu a rayuwata.karatuna,zama da jama'a,farin cikina da mijin da na aura. Abida ta hana dan cikinta abu ta bani dan uwana yana hana ni abu ita ta ba ni.anti abida bata son taga damuwata,balle ta ga kukana. Ina yi mata fatn Allah ubangiji Ya saka mata da gidan aljanna,Ya raya mata 'ya'yanta Ya yi masu albarka ko bayan ranta.Allah ka bani ikon cigaba da yi mata biyayya da amfani a rayuwa duk da nasan ba zan iya biyanta ko da rabin2 abun da tayi min ba. Aisha farida ta rushe da kuka sai jama'a suka dauka gaba daya suna shi albarka suna gasgata bayanan Aisha farida,musamman yan uwansu yan shagamu.sannna aka watse daga wurin walima domin ana ta kiran sallar magriba. Bayan sallar isha'I aka sake cancada kwalliya kawayen amarya ne kawai da abokan ango babu yara babu tsofaffi. Hadaddiyar dinner ce za'a yi a royal tropicana daga can za'a wuce da amrya gidanta da yake ahmadu bello way,sai su hadu da sauran mata da tsofaffi yan rakiyar amarya a can, duk da daman wasu tunda yamma suke can suna ta jere. Dr shuraim ya kawata sabon gini a sabon gida wanda ya tsantsara shi tamkar a turai mai dauke da bangarori biyu iri daya sak. Kowanne ya kunshi dakuna uku,faluka biyu,dinning area,katafaren kicin da bandaki guda biyu. Dakuna biyu!falo daya kicin da dinning area dr shuraim ya zuba kaya gaba daya yan waje ne,carpet da labulaye da fenti duk sun yi iri daya,kalolin purple da pink. Ita kuma amarya suka zuba nasu kayan a daki daya da parlour daya ta roke shi da kyar ya yarda ya bar musu don da ya ce komai ma su bar shi. Tana gudun surutun danginsa saboda an daukaki alada,haka gara ma sai da danginta suka mata. Adashi yaya husaini yayi abida da ita kanta faridar. Yan shagamu ma sun taka rawar gani wajen hado kudade aka hada da kudin aure da sadaki aka siyo mata komai dai-dai karfinsu. Sai a yau su uwani su ummulkhair suka sake gasgata maganar abida da tace su zuba ido su ga mijin da aisha farida zata aura. Yau sun gani kuwa da idanuwansu. Tun daga gate din shiga gida zuwa farfajiyar gidan ma abar kallo ce don an kayata da shuke-shuke da tsuntsaye,liluka,swimming pool kamar ba a kano ba. Cikin gida kuwa ba ya kwatantuwa aisha ta haye a rayuwar duniya dai,yadda bangarenta yake haka bangaren kishiyarta faiza yake,bambancin kala ce kawai ita komai nata shudi ne da baki. Gidan iyayen ango aka fara wucewa da amrya,abban shureim yayi mata nasihohi akan ta zauna ta bi mijinta lafiya,nasihohin da yayi mata masu ratsa jiki ne.daga can aka zarto da ita gidanta,bangaren kishiyarta fa'iza aka wuce da ita suka iske falon nan nata a cike dankar da hadaddun mata kai kace su suka zabi kyawu da kudi sannan Allah Ya basu. Kawayenta ne da kawayen mahaifiyarta,danginta da wasu daga cikin dangin dr shureim masu bin bayanta.wasu sunyi musu faram-faram.wasu kuwa ban da hararta da kallon banza babu abinda suke yi musu,kai ka ce su aka yi ma kishiyar. Faiza kuwa na zaune ko uffan ba ta iya cewa har aka gama bayanai saboda tsananin kunar da zuciyarta ke yi mata. Dangin farida ne masu bayani har suna kiran ga 'yar su amana,farida bata da matsala tana da ladabi akwai bin na gaba ga hakuri da kawaici. Suka yi kidansu suka yi rawarsu suka fito. Hankalin aisha dai ya fara tashi taga alaamr ko faiza na da niyyar su zauna lafiya wadannan matan da suka baibayeta zasu iya zuge ta ta burkuce. Koma dai me ye ba ta damu ba ba abun da ya kawo ta ba kenan. Kuma zata yi iya kokarinta don ta cika burinta. Ita ma kanta ta ga kyawu da tsarin gidanta sai ta ji kukan dadi ya rufe ta,ta yi ta godewa Allah a zuciyarta. Babu abin da jama'a suke cewa sai addua da shi albarka da fatan nemar musu zaman lafiya.Allah ya sa gidanta ne sai dai mutuwa ta raba. Sai kuka ya sake kece mata a lokacin da ta ga duk sun watse an barta ita kadai,fiye da awa biyu sannan abokan ango suka rako shi. Bayan su dr lukman sun gama yi masu tsiya da barkwanci suka tafi suka barsu. Aisha ta iske angonta mai ilimin addini ya aiwatarda duk addu'o'I da nafilfilin daya kamata ango ya yi shi da amaryarsa a daren farko. Ya cika da tsananin farin ciki mai dimbin yawa,so da yarda ya karu akan amaryarsa a lokacin da ya same ta cikakiyar budurwa wacce ta kare kanta daga wasu mazan kafin ta yi aure. KYAN TAKALMI 3* 14 Kuskuren da wasu yan matan zamanin nan ke tafkawa kenan a rayuwa,daga inda suke fara jawo tsana,zargi,ras hin yarda har karshen auren,kuma babu inda auren yake zuwa ake rabuwa idan suka bari wani da namiji ya fara saninsu a waje. Don haka dole 'yan mata su yi yaki da zuciyoyinsu su yi taka tsan-tsan da mayaudaran samarin zamani ko da kuwa zasu aure su ne to a guji zina har sai bayan an daura aure. Allah yasa mu dace. Satin ango guda a dakin amaryarsa kamar yadda shari'a ta tanada.sati guda nan da yayi ya fiye masa shekaru hudun da yayi da aurensa a baya,don ya sami nishadi. Lallausan lafazai,ladabi da girmamawa bayan abinci masu dadi daga wajen amaryarsa. Ya yi wa Allah godiya da ya sami farida a matsayin matarsa. Ya kudiri niyyar cure ta ba zai bari ta subuce masa ba a rayuwarsa. Sai yaji bambarakwai da ya koma bangaren fa'iza saboda rayuwar hutu ta iya.sai sha biyun rana take tashi daga bacci. Kafin ma ayi maganar abun karin kumallo kuma ba ita zata yi ba.kofa zata budewa masu aiki su shigo gidan daga can bangarensu.kuku ya shiga kicin,mai shara da wanke- wanke da goge-goge ta fara.wanka kawai zata yi ta ci ado da riga da wando ta zauna a falo tana game ko kallo. Anci sa'a dai tana sallah da zarar lokaci ya yi sai ta tashi,bayan wannan bata san a yi wa miji wahala ba. Da zarar ya bata mata rai zaka ji tana ce masa 'you are very stupid' su a can karamar kalma ce wannan dan mace ta furtawa miji. Sabanin abin da ya ga farida na yi. Tunda asuba take tashi ta shiga hidimar miji da kalkale gida,ta ce ba ta bukatar masu aiki.ko cokali zata ba shi sai ta durkusa har kasa,haka idan ya kira ta. Sai yake jin kansa yana fasuwa tamkar ya zama sarki,sarki da ake girmama shi a fadarsa. Hutu ya dauka daga wajen aikinsa yayin da ya sa farida ta rubuta takardar barin aiki saboda ba ya bukatar ta yi ta wahala saboda dan albashi. Ya yi mata alkawarin zai bata babban aiki da zarar sun kammala ginin katafaren asibitin da suke ginawa shi da mahaifinsa a zoo road. Shi dai ba zai bar aminu kano ba zai dinga shiga lokaci2 amma zai fi ba wa asibitinsu muhimmanci. Kafin nan faiza ta kammala karatunta ta dawo gaba daya ita ma sai ya sakata a asibitin a bangaren data karanta wato acct section. Watanni biyu faiza tayi tare da farida kafin lokacin jarabawarta yayi don sun kusa fara jarabawar karshe. Shureim yayi kokarin samarwa aisha visar london,kamr ta sa har ta tsawon shekaru biyar duk sanda suke son shiga sai si shiga kawai. Don haka shuraim,farida da faiza tare zasu tafi su yi zaman wata biyu har sai ta kare su kauro gaba daya. Takaici ya cikawa faiza zuciya don bata so ba shuraim yace zai taho da farida,da ta so su tafi su biyu abar ta saboda a fara zame mata barazana wajen dauke zuciyar mijinta. A cikin watannin nan biyu data yi Aisha ta gama da mijinta,ta gama da iyayensa,ta gama da danginsa kowa yana sonta saboda da'arta,kyauta, ladabi,iya karbar baki dss. Har wasu na tunanin ko da wani baki. Asiri ta shigo ta asirce gida gaba daya, yayin da masu hankali suka lura tsabar kirkinta ne da iya zama da mutane ya jawo mata duk wannan. Abida tayi mata nasihohi masu ratsa jiki a lokacin da ta je ta yi mata sallama zasu tafi london su zauna har tsahon wata biyu. Aisha farida tayi mata alkawarin yin amfani da duk abunda take fada mata,kudi mai dimbin yawa ta tulewa abida da mijinta a gabansu har sai da suka tsorata da ganinsa suka tambaye ta in da ta samu. Ta shaida musu shureim ne yake bata kyauta wani ragowar na cefane ne don kudi mai yawa yake ba su kullum har ya fi karfin na cefanen. Sannan mahaifin shureim ya ba su kudi(dollars) mai yawa da zasu yi wannan tafiyar kadan ta dauka ta canza musu sauran. Ta umarce su da su cika su sayi fili a unguwa mai kyau a hankali zata gina masu. Kafin ta tafi sai da ta turawa kanwarta munawwara kudi dubu hamsin ta fara yin jari kafin ta dawo. Wannan shine karo na farko da aisha ta fara hawa jirgi,suka hay daga bab zuwa lagos daga can suka hau zuwa london. A katafaren gidan mahaifin shureim suka sauka sai dai su kaiwa mahaifiyar faiza ziyara.babu irin kallon banza da wulakancin da yan'uwan faiza basa yi mata idan taje gidan,har shuraim ya fara jin haushi ya fara kin son ya kaita,ita kuwa sai tayi ta rokonsa sai sun je tare saboda tasan kishi ne kawai ke damunsu. Da suka zauna da ita sai suka fara gane halin aisha tana da kirki suka fara sakar mata fuska,haka baby yar gidan faiza ta shaku da ita sosai koda yaushe suna tare duk inda zasu je. Aisha tayi kallon duniya da abunda ke cikinta kyau da tsari a garin london ba'acewa komai. Sun zagaya koina a birnin har sun shiga kasashen da suke makwabtaka dasu don bude ido sunyi siyayya sun shakata su dukka ukun. Watanninsu biyu a london faiza ta gama zana jarabawarta ta karshe ta kammala degree,sannan suka dinguma suka wuce saudiyya,ya zo daidai da lokacin aikin hajji suka sauke faralli,duk da su shureim ba hajjinsu ta farko ba ce.farida ce ta farko. Ta nutsu ta yi hajjinta yadda Allah yace,sannan ta yi addu'oin nemam zaman lafiya da kwanciyar hankali a aurenta,da rayuwarta ta duniya da lahira gaba daya. Tayi wa Allah godiya da ya bata wanda take so a duniya shi ma yana sonta kuma yana kula da ita.suka dawo gida kano aka bude sabuwar rayuwa zama ne na din3. Aka samarwa baby makaranta mai kyau a akno ta shiga. Bayan an kammala ginin asibitin aka saka masa suna imran memorial hospital,ya samarwa kowacce a cikinsu ofishinta a cikin asibitin da albashi mai tsoka. DUK KYAN TAKALMI 3* 15 Af mai kula da dukkan nurses da leburorin asibitin, yayin da fa'iza ce mai kula da duk kudin da yake shigowa asibitin, abban shuraim shine mai kula da duk likitocin da suke asibitin, shima yana zama ya kula da masu matsalar fata kudine sosai ake biy kafin a ganshi. Dr lukman yana zama a asibiti duk ranar litinin da laraba, dr dayyabu yana zuwa duk ranar alhamis da yamma. dr janan mu'azzam likitar mata (gynae) duk ranar juma'a sda asabar da yamma. Dr muhd lktr tiyata yana zuwa duk ranar talata da laraba.dr ruqayya lktr yara tana zuwa ranar lahadi da juma'a da yamma bayan likita daban daban da suke asibitin na dindindin. barr. mu'azzam shine babban lauyan asibitin shima da ofishinsa a ciki don haka duk wani mai isa da kudi da mulki a kano koma ince a kasan nan ya bude file a asibitin nan saboda iya aiki tsafta da tsari. makudan kudi suke samu a kowacce rana wanda yake isarsu su biya duk wani ma'aikaci hakkinsa dakuma karo kayan aiki daga kasar waje. bayan shekara 1 dr.s ya dauki nauyin karatun AF don ta karo ilimi abangaren nurse, tayi amfani da takardunta suka bata shekara 1 n half zata sami shaidar degree akan nursin.Hutu kawai take zuwa nigeria kuma da albashinta take zuwa bayan kudin abinci da shuraim yake aika mata.kan ka ce kwabo AF ta rikide gaba daya ta zama yar gayun gaske, haka kyakkyawa har kamar sai an wanke hannukafin a taba ta. haka naira da pounds sun zauna mata, tuni ta kaftarawa su yaya hussaini gida mai tsananin kyau a unguwar jan bulo, ta siya musu motar hawa. ta canza masa aiki ta samar mas a asibitinsu a matsayinsa na mai kula da masu gadin asibitin suma da ofishinsu. kan ka ce kwabo rayuwar hussaini ta canza dashi da iyalansa tayi kyau, ya saka 'ya'yansa a makaranta mai tsada, shima kansa da abida har suna iya taimakon danginsu na shagamu ba sai sun jira AF ta aiko musu ba. Allah bai bawa AF haihuwa da wuriba har sai da ta kammala karatunta ta dawo gida, sannan ta samu ciki don a lokaci faiza ta sake haihuwar mace mai suna fadila har ta yayeta. santalelen jariri AF ta haifa mai kama da shuraim aka saka masa suna imran, sunan mahaifin shuraim. yadda abba yake ji da imran kai kace bai taba yin jika ba a duniya sai a kansa. wannan kauna ta samo asaline da kaunar da yakeyima uwar dan wato AF a sanadiyyar kula da girmamawan da take masa. idan kaji abba yayi kukan yunwa tabbata AF bata kasan don da tananan gida ko office xata aiko masa da abinci kala kala kamar kunun gyada, tsamiya, kanwa, dalayi da sauransu. idan a bangaren abincine dambu, danwake, kwadon zogale, rama, masa, sinasir, wainar 'yar tsala, farfesun kaza ko naman rago amma dahuwardadawa na gargajiya shi yafiso. haka take yiwa mahaifiyarsa hidimomi na dafe dafe da ladabi da biyayya. komai takeso kan tace tayi har tayi mata, don haka suke son AF ba don faiza taji haushi ba sai don bazasu iya boyewa ba. ita kanta faiza baza ta iya cewa AF tayi mata laifi ba sai dai kawai tayi kishi da ita don ta aure mat miji,amma babu wata kyautatawa da girmamawa da bata yi mata ita da 'ya'yanta. a dole Faiza ta fara canzawa tana kwaikwayon wasu abubuwanda AF keyi duK da bazata iya yin duka don bata saba da wahala ba. yau falon AFa cike yake da kawayenta kai kace hada baki sukayi a rana daya suka kawo mata ziyara har su hudu kowacce kuma da ban tazo. hidima kawai AF take tayi masu da kayan abinci, lemo da kayan marmari kalakala. maimuna kanwar abidace ke zama a gidan tana taimakonta da hidimomin gida kuma take rike mata yaro. suka jera musu kayan dadi kalakala babu wacce bata cika tumbinta ba a cikinsu har suka bari. bayan ciki ya dauka sai murya ta washe sannan falo ya hautsine da hira. hoton shuraim da AF khadijah sani isma'il ta kafawa idanu tayi ta kallo,can tayi ajiar hrt tace "ikon allah ashe dr.s mijinkine, mukayi ta wahalar da kanmu a kansa? maryam ahmad tayi ajiyar hrt ta sake rungume danta tana jijjigawa tace " matar mutum kabarinsa kana taka allah na tasaa.gashi nima na auri miji mai sona ina jin dadin zama dashi. rakiya musa tace, "nifa da gani nayi kamarAF ta tsani dr.s basa shiri kwata kwata." ummi yasar tace" ai ni yau takanas zuwa nayi in dauki darrussa akan zamantakewar aure. yanzu yasar ya dan fara yabawa da hankalina shiyasa ya mayar dani gidansa sai dai kash! har yanzu kishiyata surayya ta fini fada a wajensa duk da haka dai muna zaune lfy da ita da surukata da facalata. yanxu so nake in samu in sake shiga hrt dinsa ba da neman gudunmawa daga bokaye ba kamar yadda nayi imanin bakya bin bokaye amma kika sami shuraim. kin zama abar kwatance a cikin mata. kece babbar malamata wacce tayi min silar canza rayuwata daga gurbatacciyar hanya zuwa hanya madaidaiciya. ada na sha wuya a sanadiya bacewar basira na sabawa mahaliccina" A.f tayi tagumi tana kallonsu 1by1 har suka gama maganarsu. murmushi kawai takeyi yayin da dadi ya kamata tana farinciki da suka gane komai. ta gyara zama tace "nagodewa Allah daya ganar daku, nadode da kyautar da Allah yayi min a duniya wacce zata zamemin hanyar shiga aljannah a lahira. dan daga lokacin da mace tayi dace da samun miji ngari addininta ma ya gyaru. mace dakinta guda2 ne gidan mijinta sai kuma na2 kabarinta, na shiga gidan mijina ba fita inshaAllah sai kuma kabarina ne ya rage nabi ta hanyar data dace na auri masoyina da nake yimasa soyayya saboda Allah, narike kissar matar nan data debo nonon 'bauna ina lallashinsa muna zaune lafiya sannan na rike nasihohin nan guda goma wanda Abida tayimin a ranar walimar aurena wacce uwa ya kamata tayiwa 'yarta a ranar da za'a kaita gidan miji. na haddace su a kwakwalwata kuma ina yin amfani dasu ina ganin falalarsu. a yau shureim baya kallon wata mace a duniya sai ni AF, baya son ya jiyo muryar kowacce mace sai tawa, bashi da wani tunani sai nawa kuma babu boka ba mallamai sai tsabar kyautatawa shima kuma bashi da buri a duniya irin ya kyautata min. wannan kishin da mata sukeyi da kishiyoyinsu baya gabana bantaba saka mata ido ba inga abunda takeyi balle inji haushinta haka bani da burin in koreta, burina kadai in zauna da mijina lafiya.shureim yana da adalci a tsakaninmu baya bambamtamu. a halin yanzu na mallaki komai a duniya daidai gwargwado, motocinmu na hawa na zamani guda bibbyu babu ta kasa da million4 suturuna masu tsadar gaske, mayukan shafawa da kayan kwalliya masu tsada (designers), abinci sai wanda na zaba zanci.shureim baya dannewa iyalansa hakkinsu tsakanina dashi sai addu'ar Alkhairi da fatan yazi gaba da samun budi a rayuwarsa ta duniya da lahira.yayimin komai sannan yayiwa 'yanuwana dan yanzu dangina 'yan shagamu sunyi sallama da wannan dankararren talauci da muka sha fama. na dauki nauyin 'yan sakandire da yawa harsu gama,na dauki nauyin masu shiga jami,oi DUK KYAN TAKALMI 3* 16 na dauki nauyin taimakawa iyaye da suka tashi aurar da 'yan mata da kayan daki ko samarin da suke hada lefe.kanwata Munauwara ta rabu da turmutsitsi da wahalar zaman haya na siya mata gida a shagamu mai kyau na siminti, na bawa mijinta motar haya bus yana tuki yana samun na cefane, na biya mata makka taje ta sauke farari ta dawo na hada mata jari tana 'yar sana'a a cikin gida tana samun na batarwa,ita da 'ya'yanta suna saka sutura masu kyau suna makaranta mai kyau. Musbahu tsohon saurayina kuma tamkar dan uwana yanzu shima nayi masa rana don na bashi dubu saba'in ya kama shago na siya masa computers 3 da injin photocopy ya bude business center tasa ta kansa ya daina aiki a karkashin wasu. sai ga mamarsa data tsaneni da matarsa an rakosu gidan nan tana ta kuka tana neman gafara a bisa tsana da cin mutuncin data yi min a baya.harda cewa dama ace baya zata dawo mana data bar Musbahu ya aureni ashe ina da mutunci haka.tayita kallon gidana tasan nayi musu zarra, kyauta ta ban girma nayi musu na suturu da kudi mai yawada zasu tafi kadan kenan daga irin rahamomin da Allah yayi min duk a sanadiyyar shureim bai rageni da komaiba dan nima ban rageshi da komai ba.khadija tayi ajiyar zuciya tace"ai ko baki fada ba Aisha umar kallo 1 za'ayi miki mu2m yasan kina cikin daula,jikinki ya nuna kuma muma shaidu ne don babu abinda bakya yi mana,kici gaba da godewa Allah sai ya kara miki"Ummi tayi ajiyar zuciya tace"shiyasa nazo daukar darasi kibani dama indinga zuwa kullum har tsawon wata guda inji ina ganin abubuwan da kikeyi ni ban iya komai ba.AF tayi dariya tace"zaki iya zuwa kullum amma banda ranar weeEnd don mijina yana gida"Ummi tace to, a wata zan zo sau KWANA ASHIRIN DA HUDU. Saboda naga alamar har yanzu GANGAR JIKINSA NA AURA, zuciyarsa na wurin amaryarsa surayya. gara inkoma kacokan indinga koyi da abinda YARENA ADDININA, yazo mana dasu.duk wanda na tara na fada masa abunda Yasar yakemin sai yace INA RUWAN WANI, dan abaya anyi min shaidar tsiya as sanni da bin bokaye. nakan cewa Yasar KAI KAFI CANCANTA' ka lura da cewar na canza yanzu bana bin bokaye irinna da bai cika kallonaba ma balle yasan nayi kwalliya tsabar yariga dayayi min shaidar kazanta abaya.sai Ummi ta fashe da kuka.Khadija ta tabe baki tace wannan shi ake kirada ADON DAWA'kenan kinyi kwalliya abanza don baya lura"AF tayi murmushi ta dafa kafadar Ummin Yasar ta girgizata tace"kwantar da hankalinki kawata,sannu ahankali zaki gane kan mijinki.Yasar zai zama takalmin takawa tana rufe bakinta sai ga Dr.shureim ya shigo, ya dubesu 1by1 yayi murmushi. yace Farida, hakika ni takalmin kafarki ne, nayi miki lamuni ki takani kije duk inda kikeso dani 'DUK KYAN TAKALMI' a kafa ake takawa......................** *************** *************** *************** *********ALHAMD LILLAHI karshe DUK KYAN TAKALMI 4 Aisha farida tayi karfin hali tace ba damuwa, ai laifina ne dan banyi kama da mai kamun kai ba, tunda ba'a tambaye ni ba nazo na fara yi muku surutu, nasan ba'a son mace marar kamun kai. Barr muazzam ya girgiza kai yace zuwanki nan ba laifi bane dan kin zo kin zauna a kusa damu, kujeru ne a jejjere kowa zai iya zuwa ya zauna. Da kika zo kika same mu kinyi mana sallama duk da tun kafin mu amsa har kin zauna. Daman kamata yayi ki gabatar mana da kanki kuma kinyi hakan sai dai kika zarce da bamu labari shine abinda ya daure mana kai kenan. Kallon junan da kikaga muna yi ina tunanin ya sanki ne, shima yana tunanin ko na sanki ne. Aisha bani labarin takamaiman abinda ke damunki, muma nan da kika ganmu matsala ce take addabarmu, ki saki jiki ki fada mana mu dake sai mu taimaki juna da shawarwari. Barr nuruddeen ya fusata ya mike tsaye ya dubi abokinsa yace malam in ka gama kazo ka same ni a cikin mota mu tafi, dan ba zan iya zama ina sauraron wannan shirmen naku ba. Bansan sanda ka zama marar aji ba, daga haduwa da 'yar tasha sai ka hau hira da ita kai ma kana baza sirrinka, idan taji matsalar ka me wannan zatayi maka? Itama bata san yadda zatayi da kanta ba balle ta bawa wani shawara. Kada ka sake ka ambaci sunana a cikin labarinku kai dai ka fadi taka matsalar. Ya juya a fusace ya tafi bai daina fada ba yana tafe yana magana yana wurwurga hannu har ya fice daga cikin gate din. Aisha farida da barr muazzam suka bishi da kallo har sai da suka daina hango shi. Ta sunkuyar da kanta kasa sai hawaye ya fara zubowa daga idanuwanta. Kada ki yi kuka aisha, ki mayar da komai ba komai ba. Kece fa kika gama bani labarin cewa zaki iya zama da kowanne irin mutum a duniya. Inji brr muazzam. sai tayi murmushi ta shiga goge hawayenta tace ko kusa ban damu ba, banji haushi ba. Kawai dai abokinka yayi min kallon ballagar mace, 'yar tasha, 'yar club, karuwa kenan. Shine mutum na farko a rayuwata daya taba jifata da wadannan munanan sunaye, saboda bai sanni ba, sai dai ina fatan ya sanni nan gaba. Barr muazzam yace yi hakuri kanwata, ki cigaba da bani labarin rayuwarki, ina jin dadin sauraronki. Haqiqa Aisha farida,labarinki yakai maqura gurintausayi,nayi kuka sosai,rabena da irinkukannan yaukimani wata takwas kenan.tunrasuwar yayata,ayau nafisa mamawa kinsani cikintausayin ki,maganardanakeyi yanzuhaka nakasa tsayarda hawayendake zuba'a idona. kitaimaka kibani lbrin cigabanki da daukakardakikasamu kozansamisukuni yau...wallah nafisa natausayamiki sosai. BABI NA BIYU Da na karasa makarantar primary sai yaya hussaini ya kaini wata makaranta a wajen sabongari na zana jarabawar common entrance ta shiga makarantar federal. Allah cikin ikonsa sai naci jarabawa aka turani makarantar da na zaba wato FGC kano. Yayi min sayayya iya karfinsa ya kaini, ya bibbiya dukka kudaden makarantar da aka bukata, ya dawo gida ya barni a can. Nayi kuka saboda rashin sabo, gashi bansan kowa ba a makarantar amma daga baya na saba da dalibai 'yan uwana sai na fara jin dadin rayuwar makarantar. Jama'a na sona saboda yadda nake da fara'a, ladabi da son aiki bana kiwa don haka kowa yana son ya jani a jiki saboda ina da matukar tsafta. Na yi suna a makarantar nan da nan malamai ma suka sanni saboda kwazona da wayo, ga iya magana. Na gama aji uku hutun da zamu shiga aji hudu aka cireni, abu ya ci tura hidimomu sun karu, yayana ba zai iya cigaba da yi min siyayya ba da biyan kudin makaranta ba kasancewar shima ya hayyayyafa. A jejjere ba kakkautawa abida take haihuwa, 'ya'yanta na farko ma 'yan biyu ne maza abubakar da umar, sai ta haifi mace mas'uda ga wani cikin a jikinta ko yaye ta goyen bata yi ba. Ga kudin haya ya karu, cefane ya karu, farashin abinci ya karu, gashi an kara kudin makaranta ya kusa ninka na da ma. Daman duk sanda zan koma makaranta sai ya ciyo bashi kafin ya harhada ni in tafi. Ya kira ni daki ya zaunar da ni yayi min bayanin halinda ake ciki, sai ya bani hakuri cewar zai mayar dani makarantar gwamnati ta ;yan mata dake shekara. Dole na koma makarantar shekara naci gaba da karatu, daga aji 4 na fara, sai na zama zakaran gwajin dafi nafi kowa kokari saboda dana sami horo a FGC a wajen yaran kabilun da basa jin hausa da yaran hausawan da suka sami horon turanci tun daga primary. Ajin kimiya na shiga (science class) har Allah ya kaini aji shida aka bani shugabar dalibai, duk wata gasa ko muhawara ta turanci tsakaninmu da wasu makarantun ni nake tsayawa makarantarmu, idan bana nan babau abinda yake tafi dai dai. Shugabar makarantar mu tana alfahari dani, kullum tana kwatance dani saboda kokarina. Da muka gama makarantar ita da malamai sai da sukayi takaicin rashina saboda ba'a sami madadina ba. Bayan gama makarantata da wata uku yayana ya harhada 'yan kudadensa ya bani kudin mota da guzuri na zuwa shagamu, saboda duksanda yake zuwa shi da matarsa da 'ya'yansa ina makaranta ba'a zuwa dani. Tsofaffin abokan hirata har sun gaji da tambayata wasu ma sun mutu, haka wasu daga cikin yayyena sun murmutu duk banje ba. Ina samun wasikun kanwata munauwara akai akai duk sanda ta sanda ta sami mai zuwa sai ta bayar an kawao min, ta shaida min cewar an cire ta daga makaranta tana secondary aji 3 anyi mata aure saboda rashin kudi. Ni kadai yaya hussaini ya saka a mota zuwa shagamu, dana isa garin shagamu a tasha na hau acaba zuwa gidanmu, ban manta hanya ba. Da yawan 'yan gidanmu basu shaida ni ba sai daga baya suka gane ni, sunga na girma nayi kyau. Duk da rashin wadatar da muke ciki a kano sai naga na fisu kyawun gani, cikakkiyar lafiya da gogewa. Na zagaya dangi na kusa dana nesa har sai da naji kafafuwana zasu gutsire saboda yawansu. Na ziyarci gidan kanwata dake agege a lagos anan take aure, rayuwarta abin tausayi, gida ne irin na haya mai dauke da dakuna fiye da ashirin, yare kala kala kamar hausawa, yarbawa, igbo, da wasu yaruka daban daban. Bandaki daya ne kacal, tunda asubahi ake fara layin shiga bandaki. Mijinta iliyasu shima dan shagamu ne amma a lagos yake facin taya, ita kadai ce sana'arsa. 'Ya'yansu biyu a lokacin. Saboda tausayin halinda na same ta kusan dukka kayana na sakawa na bata kyauta, sannan na hada mata mayafai, sarkokina, takalmana, guda dai dai na rarrage. Duk kudaden dana samu na bata dukka kudin mota na komawa ta kano kadai na ware. Muka sha kuka tare da nazo tafiya, kukan da muke na tunawa da iyayenmu ne da kuma kukan rabuwa, don munsan zamu dade kafin mu sake haduwa. Na dawo kano jakata kwalam babu komai duk na rabar da kyana kuma da masu kyan na tafi dasu. Tsummokaran, tsofaffin, yagaggun kadai na bari a gida. Haka nazo na dinga karancin kaya duk sun ragargaje dan haka na daina zuwa taron biki ko gidan kawayena. Abida tayi ta min fada tace nayi garaje ai ba'ayin haka tun da nasan ban ajiye wasu ba a lufge kuma bani da mai dinka min wasu ai bai kamata in rabar ba. Idan fita ta kama ni dole sai dai in ari kayan abida in saka inje, ina dawowa in cire mata. Abinka da cakudi, zaman saka ido, kowa yana kula da shige da ficenka. Gulmammaki iri iri bayan zumde da yafice zaka ga anayi mana, abin ya kai har su dinga kiran 'ya 'yan abida suna bugun cikinsu suna tambayarsu wai ina kayana suka ga ina arar na abida? Irin wannan gutsiri da tsomar sai da ta wuce kan matan gida ta koma wajen mazansu, su kuma suka tseguntawa yayana hussaini, suka ce masa bai dace in dinga arar kayan abida ina fita kofar gida ina tsayawa da samari ba, ina yawo da kawayena a gari. Idan ba an lura ba in a duhune sai a zaci abida ta fara bin maza. Sukayi ta zuba masa bayanan da dole hankalinsa yayi matukar tashi, ransa yayi mummunan baci. Ya shigo dakina ransa a bace ya iske ni a kwance yace min in kira abida itama ta shigo nan dakin yana da magana da ita. Mukazo muka durkusa a gabansa muna karkarwa saboda yadda muka ga ransa a bace gashi mutum ne mai zafin zuciya. Ya umarci abida ta fada masa gaskiya kada ta kuskura tayi masa karya akan abinda zai tambayeta, haka nima ya gargadeni kafin ya yi mana tambayoyin. Muka yi masa alkawarin zamu fada gaskiya, ba zamuti karya ba. Cike da fargaba mai tsanani muke sauraron abinda zai fada mana. Ya cewa abida da gaske ne aisha farida tana aron kayanki ta saka ta fita yawo a gari? Sai abida ta dafe kirji tace Innalillahi wainna ilaihir rajiun! Ya daka mata tsawa mai firgitarwa yace baki bani amsa ba. Nan da nan ta fara hawaye, jikinta na karkarwa tace eh haka ne. Sai ya kai mata mari har sai da ta fadi kasa, ya fada cikin fushi yace to ta hada kayanta ta tafi gidansu. Na rushe da kuka na dinga rokarsa ya yafe mata ba laifinta bane nice na tambaye ta. Nima din ya yafe min na daina daga yau. Sai ya rufe ni da duka yana duma, yana tattaka ni da kafa tamkar zai kashe ni. Munafukan matan gidan ne suka zo suka kwace ni dakyar, ransa yayi matukar baci sai fada yake yana zaginmu wai sai mun harhada kayanmu mun bar masa gidansa. Ana bashi hakuri tamkar zuga shi akeyi dakyar ya haukra ya kyale mu amma tun daga lokacin baya raga mana, komai mukayi sai ya hantare mu, sai harara koda yaushe. Sai na daina fita koina , koda yaushe ina fama da dinkin yaga da zare da allura. Abida ta iske mijinta a dakinsu ta ajiye masa abinci sannan ta durkusa ta gaishe shi. Ya amsa dakyar cikim fushi, bata damu ba ta zauna a kusa dashi ta dauko muhuci ta fara yi masa firfita. Sai yayi mata tsawa yace ta bari baya so, ta tashi ta fita ta bashi waje. Cikin lallausar murya tana zubar da hawaye tace ka yafe mana laifukan da muka maka, munyi kuskure, fushin da kake yi damu ya hanamu sukuni, bama jin dadin rayuwarmu, rayuwa tayi mana kunci. Dan ban fada maka bane halin da ake ciki kada ranka ya baci, ashe dana fada maka ma zaifi sauki. Aisha farida ce ta rabar da kayan sakwarta kakaf a shagamu saboda tausaya musu da tayi, ta gansu cikin tsumma, shine ta dawo bata da kaya sai yagaggu. Dan haka bata iya fita wajen kawayenta shine nake bata aron kayana ta saka tana dawowa take cirewa, bansan abinda 'yan gulma suka fada maka ba har ya jawo ranka ya baci ka dauki mataki cikin fushi. Sai yayi shiru yana sauraronta can yace ai duk laifinki ne, meyasa ba zaki fada min halin da ake ciki a cikin gidana ba har sai da wasu suka fada min a waje? Kinsan irin zaman da mukeyi da 'yan gidannan, zaman saka ido ne, duk shige da ficen mu akan idonsu. Ashe gaba daya lungunnan gulmar ku ake yi shiyasa raina ya baci. A take ya bata naira dubu biyu yace ta bani inje in sayo atamfofi guda biyu 'yan naira dari takwas takwas inyi dinkin dari bibbiyu. Abida mace mai hakuri da tsananin wayo, ta iya zama da mijinta duk zafin zuciyarsa, tabbas macen da bata da hakuri da wayo ba zata iya zama dashi ba, sai gashi da kansa yayi nadamar aninda yayi mana, sai yaji kunya yazo yana lallaba mu. DUK KYAN TAKALMI 5 Saurayina guda daya nake kulawa mai suna musbahu, lungun mu daya dashi kowa yasan mu tare, yana sona sosai nima haka saboda yana kula dani. Tun sanda na gama sakandire yake so ya aiko gidanmu ayi zancen aure sai aka sami matsala daga gidansu, mahaifiyarsa bata sona 'yar kanwarta take so ayi musu auren gida, shi kuma ni yake so ya aura.mahaifiyarsa ta tsane ni haka kawai, ko a hanya na gaishe ta bata amsawa shiyasa na daina zuwa gidansu don da ina zuwa wajen kanwarsa jamila kawata ce ajinmu daya a shekara. Musbahi ma yaji labarin duka dana sha saboda aron kaya, sai naga ya siyo min leshi guda daya da atamfa ya hada min da naira dari biyar kudin dinki, sannan yayi min fada in daina boye masa sirrina saboda yadda yake sona a ransa, matsalata ai matsalarsa ce. Yace duk sanda na shiga matsala in fada masa ko bashi da kudi zai ciyo bashi yayi min komai in dai baifi karfinsa ba. Yaci gaba da bani hakuri akan halinda yake ciki shi da mahaifiyarsa, ita ta hana shi ya turo gidanmu zancen aurenmu. Ya umarce ni da mu dage da addu'a Allah Ya karkato da zuciyar mahaifiyarsa kaina taji tana sona ayi auren dani. Sakamakon jarabawar mu na sakandire ya fito naci credit takwas, geography ne kadai naci pass shima dan a ranar da muka yi jarabawar bani da lafiya. Sai misbahu yace idan ya sami kudi zai saya min form din jamb in wuce jami'a. Sai nace ba zan iya karatu a jami'a ba saboda 'ya'yan masu kudi ne sukeyi, bani da mai bani kudin mota da kudin sayan handout, gashi dole sai an saka sutura masu kyau. Sai shima ya gasgata zancena yaga shima bashi da halin da zai dauki nauyin duk wadannan sabida dan abinda yake samu ba mai yawa bane. Duk da wasu lokutan sukan sami ayyuka da yawa suna samun kudi a business center yake aiki, suna typing a computer, suyi kalandu ko meme. Sai yace to zai samo min management in fara, nan ma nace bana so nafi son inyi schl of nursing saboda ba ruwana da neman kayan sakawa, suna da uniform, sai yace shikenan zai binciko yaji duk yadda akeyi a shiga amma in fara jin ra'ayin yayana. Yayana ya amince da shawararmu kuma yaji dadi musamman da musbahu yazo har kofar gidanmu ya sa akayi masa sallama da yayana hussaini ya kara yi masa bayani. Yace zai taimaka min da wata dawainiyar kudin makarnatar sai ya amince yayi masa godiya. Musbahu da yayana ne suka hada gwiwa suka bani duk kudaden da ake bukata na shiga makarantar koyar aikin jinya ta malam aminu kano dake unguwar court road. Karatun shekara uku ne a shekara ta uku ne muke zuwa asibiti koyar aiki don haka karatu na yi tayi haikan, ban taba samun matsala ba cinye jarabawata nake yi koda yaushe. A asibitin malam aminu kano ake horar damu koyar aiki (attachment). Ina zuwa kkullum daga unguwarmu sharifai zuwa court rd akan acaba saboda idan nace zan hau bus zan bata lokacina zanyi in makara. Kudin acabana kit da kit babu canji wata rana ko purewater zan sha sai dai kawayena su saya min. Duk da idan za'a je sayan abinci ko shan lemo sai in gudu bana binsu saboda kullum sai dai su saya min, ni kuma na fara jin kunya sun gane bani dashi. Kawata khadija sani ismail kadai wacce bata gajiya da taimakona kuma duk sanda tace muje cin abinci naki zuwa ko na sulale na gudu sai ranta ya baci, har tayi fushi dani. Sai inyi tayi mata bayanan karya in kirkiro uzurin dana je nayi ba guduwa nayi ba sai ta ki yadda tasan karya nakeyi. Ba ita nake ji ba, sauran kawayenmu nakeji don suna nuna min bakin hali daga baya kuma in dinga jin kananan maganganu cewar na cika san banza kullum bana fitar da kudina ina sayawa kaina abu balle in sayawa wani, sai dai ni kullum a saya min. Rashin sani yafi dare duhu, kallon kitse sukeyi wa rogo. Hakika ni mai yawan tsafta ce in kula da fararen kayan makaranta ta, kullum tsaf dani, ina kalkale jikina tas a wanke ga karin guga. Gani nafi duk 'yan ajin mu kokari yawanci ni nake basu amsa. Khadija bazata iya rabuwa dani ba dan bata da kokari sai dai gata, tunda iyayenta suna da hali. Duk wasu manyan littattafai na karatu (text book) babanta yana saya mata duk tsadarsu, sai nafi morarsu don ni ce mai hazakar karatun ba ita ba. Da taimakon Allah da taimakon khadija sani nake cin jarabawa dan ba zan iya sayan littattafan nan masu tsada ba. Badan Allah Ya sa na iya kitos ba ina yiwa makwabta, da wata rana ma ba zanje makaranta ba saboda duk ranar da yaya hussaini ya tashi bashi da kudi sai yace in hakura kada inje makaranatar randa ya samu naje. Ni kuma bana so inyi fashi, da kudin kitson nake harhadawa in tafi duk da kitso a unguwar bashi da tsada, kan manya naira talatin ko arba'in, na yara kuwa naira ashirin ko goma ne. Ban taba fadawawa kawayena sirrina ba, duk da yawan kawayen da nake dasu a ajinmu mata da maza, sai dai ayi hayaniya wasa da dariya a watse, ina taka tsantsan da harshena a koda yaushe. Babu wanda a cikinus ya san yadda gidanmu yake, basu taba zaton haka nake rayuwa ba, sai dai sun fahimci wani abu akwai wasu matsaloli wanda ba zasu boyu ba. Suyi ta zargi da sake sakensu a ransu su kadai, ni dai bazasu ji daga bakina ba kuma ba zasu iya tara ta su tambaye ni ba. Ni daman bana zuwa gidan kowa balle azo gidanmu, mu hadu a abkin gate ne mu rabu idan an tashi. Bana jin dadin rayuwata a wannan bangaren saboda bani da wata takamaimiyar kawa ko masoyin da zan amayar musu da radadin da zugin matsalolin da suke addabata. Kawata guda daya, itace aminiyata, yayata, masoyiyata wato matar yayana abida. Muna zama ni da ita mu raba dare ko mu yini muna tattauna matsalolinmu, koda yaushe ina samun nutsuwa da kwarin gwiwa idan abida ta bani hakuri akan talaucin da na tsinci kaina da shawarwari, sai inji sanyi a raina, tawakkali ya kama zuciyata sai inji ta tuno min da nasihohin da mahaifina yayi min a baya. Idan nayi haka sai in dawo da walwalata, ni burina guda daya ne shine in gama karatuna in fara aiki in taimaki kaina, in taimaki 'yan gidanmu. Babbar matsalar ma da tafi damuna shine zaman cakudi a gidanmu, cikin tsagoron kazata da cinkosa, babban burina ba wuce inga mun bar gidan nan da umguwar mu canja gida ko haya ce dai mu kama gidan da muke mu kadai. Dakina daya da yara, ga dakin dan karami mun cunkushe gashi su dukka yaran abida fitsarin kwance sukeyi dan haka sun ruba katifar sai zarni take dan haka na hakura da katifar na bar musu. Na koma kwana akan tabarma, idan na tashi da safe sai inyi salla akai in nada in jingine a lungu sai zan sake yin wani sallar sannan in shimfida. Har yanzu kayana a jakar bagco yake a gefen shimfidata, rayuwata ba irin na 'yan matan 'yan boko bace, tamkar a kauye nake ba'a birni ba. Ko inyi tunanin shiga hanyar banza, ban taba sha'awar makalewa gidan kawaye ba ko arar kayan kawa, na rike talaucina na kama kaina bana sha''awar kayan wani. Daga makaranta sai gida, a gidan ma nafi zama a daki kullum ina karatu. Idan kaga na fito aiki nazo taya abida, wankan 'ya'yanta , tsarkinsu ko aikin girki. Sai 'yan gidanmu da sauran 'yan unguwa suka shiga yimin shaidar girman kai ne dani dan ni 'yar boko ce, basa ganin fara'ar da nake yi musu. Kullum ina gaishe su ko basu ganni ba, tabbas mutum ba'a iya iya masa, saboda dan Adam ya kasance mai butulci ne. BABI NA UKU Wata rana ranar litinin da misalin karfe daya na rana muna cikin a sibiti, a bangaren marasa lafiya muke wadanda aka kwantar dasu sakamakon wasu kurajen da suka feso a jikinsu. Muna biye da ma'aikaciyar jinya matron maryam tana nunnana mana yadda ake aiki, domin neman karin bayani sai tace bari ta hada mu da kwararren likita wanda ya kware a bangaren fata. Ta tura wani daki ta shiga muma muka bita a baya da alama dakin daukan darussa ne sabida naga kujeru ne zalla da allo makale a jikin bangon. Kamar yadda naji ta ambaci sunansa, dr shureim imran. Mun iske shi tsaye a tsakiyar ajin tare da wasu daliban likitoci guda 3 maza biyu, mace daya da alama sunzo sunyi masa tambayoyi ne akan wasu abubuwan da basu gane ba. Bayanai yake yi musu cikin harshen turanci kai kace baturen america ne, kalmomin kimiyyar (botanical names) da yake ta ambato yana jerowa layi layi da ka ba tare da yana duba littafi ba, kai kace shine ya lakaba musu sunan don ya haddace. Muna sake kutsawa cikin ofishin yayin da zazzakar muryarsa, daddada take sake shiga kunnuwanmu sai duk muka kagu mu isa gabansa don mu kalli fuskar mai muryan nan daddada. Kasancewar kofar ta cushe muna shiga don muna da yawa, ga dalibai likitoci nan suna kokarin fitowa sun gama daukar darasin. Kowa ya kagu yayi ido hudu da mai daddadar muryar nan, keyarsa kawai na fara hangowa daga nesa sai na tabbatar bakar fata ne dan uwana saboda ban hango jan kunne ba da farin gashi irin na turawa ba. Bakin gashi ne tattaura irin namu na hausawa, sai dai gashin a gyare yake yana shekin mai kuma ya kwanto lambar zuwa karshen keyarsa. Kansu babu hula, yana sanye da bakaken kaya riga da wando (suit), farar riga mai dogon hannu daga ciki, ya daure wuyansa da jan kyalle wato necktie. Dana matso ciki sai na fara hango gefen fusakarsa, wata lafiyayyiyar fata na fara hangowa mai dauke da launi mai tsananin kyau. Irin kalar da take tsada a duniya wato hasken duhu (chocolate color). Ko dana sake samun daman na matso kuda dashi sai ga gefen fuskarsa tar ina gani wato idonsa daya da gefen hancinsa, sai kawai naji wata mummunar fadywar gaba ta far min ni ma bansan dalili ba har wadanda ke kusa dani zasu iya jiyo karar ajiyar zuciya danayi. Tunda nake a rayuwata ban ta ba ganin irin wadannan dara daran idanuwan ba masu tsananin haske daga ciki, da bakar kwayar ido mai tsananin baki, aka zagaye idon da wasu gashin ido da gashin gira masu yawa da tsananin baki, ya gyara su sunyi kira mai kyau suna sheki. A nutse ya waiwayo da kyakkyawar fuskarsa gaba daya ya dube mu, bani kadai ba duk wata 'ya mace da take wajen sai dataji a ranta dama ace wannan kadarar mallakarta ce. 'Yan uwansa maza ma sai da suka raya a ransu dama ace sune shi, ga kyau ga ilimi. Ashe a da dana ke hango gefen fuskarshi ban hango komai ba, kyau mai sunan kyau sai ka kalle shi gaba dayansa daga kafarsa zuwa kansa. Dogon mutum ne sosai ma kyawun sura, bashi da kiba da yawa, haka bashi da rama. Yayi kama da irin bakaken turawan nan da ake kira african American, hukuncin da na yanke masa kenan dan ko kusa baiyi kama da 'yan nigeria ba! Tabbas ruwa biyu ne suka hadu suka same shi bakar fata da farar fata. See Translation