[7/1, 6:23 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha 🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS ZAW (Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah)🤜🤛 1⃣ Kyakkyawar matashiya ce 'yar kimanin shekara ashirin da bakwai zuwa da takwas ta shigo parlourn, kallo d'aya zaka yi mata kasan cewa a matuk'ar gajiye ta ke. Tana shigowa ta ajje jakarta da mayafi akan kujera, ta nemi wuri ta zauna, tana maida numfashi kamar wadda tayi gudun tsere ta gaji. A hankali ta d'ago tana amsawa Auntynta da ke mata sannu da zuwa, cikin kasalalliyar muryar da ke nuna gajiyawar mai ita. Ta jima zaune kafin ta miqe tsaye, ta dubi Aunty dake zaune hannunta rik'e da remot ta ce ‘’bari na shiga ciki na d'an watda ruwa ko zan ji dad'in jiki na‘’. Idanun ta na kan TV ta amsa mata da cewa "To kiyi sauri dai ki fito ki ci abinci, don nasan tun da kika bar gidan nan baki ci komai ba". Bata ce komai ba sai murmushi da tayi ta wuce zuwa d'aki, tana shiga ta cire kayan jikin ta ta wuce toilet don yin wanka. Ba ta fi minti goma ba ta fito daure da towel a jikin ta, kai tsaye ta wuce gaban madubi ta ja kujera ta zauna, sai da ta goge ruwan jikinta sannan ta shafa mai da powder, sai lip gloss da ta shafa a le6nta ta miqe ta wuce wardrobe don d'auko kayan da za ta saka. Doguwar rigar atampha ta saka, wadda tai mata matuqar kyau, sai turare da ta fesa a jikinta, sannan ta fita parlour don bin umarnin Auntynta. Lokacin da ta fito babu kowa a parlourn, don haka sai ta wuce kitchen ta d'ebo abinci, ta fito ta zauna ta fara ci. Bata dad'e da zama ba Aunty'n ta fito, bayan ta zauna ta ce "amma Hafsat da alama yau kin sha aiki don duk jikinki ya nuna alamun gajiyawa". "Ke dai bari Aunty yau patients ne sukai min yawa ga Dr. Sakeena da zata karb'eni bata sami zuwa ba, ta tafi ta'aziyar wani abokin mijinta da ya rasu". "Allah ya ji k'ansa" "Ameen" Bayan ta kammaka cin abincin ta d'auki plate d'in zuwa kitchen, sai da ta wanke sannan ta dawo parlour ta zauna. A lokacinne Aunty ta tattara hankalinta a kanta bayan ta kashe TV da ke aiki sannan ta kira sunanta cikin nutsuwa. "Hafsat Magana na ke so mu yi da ke, kamar yadda Uncle d'inki ya umarce ni, duk da maganar ba bak'uwa ba ce a gareki. A jiya da daddare Yaya Halliru ya kira shi akan maganar aurenki, domin ya ce gaskiya hankalinsu ba zai ta6a kwanciya ba sai sun ganki a d'akin mijinki. Ki tuna Hafsat duk wani matsayi da zaki taka a rayuwa to martabarki ba za ta ciki ba sai kina da aure, don haka na ke shawartar ki da a cikin masoyanki ki duba ki za6i d'aya ki aura". Cikin sanyin jiki Hafsat ta d'ago idanuwanta tana kallon ta ta ce "Aunty aure again? Me na tsinta a cikin aure da zan sake marmarin yinsa? Don Allah na roqe ki kisa baki a daina min maganar aure, nayi alk'awarin insha Allahu zan kame kaina ba zan yi wani abu na ashsha ba. A yanzu babu maganar da take tayar min da hankali irin maganar aure, wallahi Aunty maza abin tsoro ne, a lokacin da suke son lalla6a mace babu abinda ba za su ce mata ba, amma idan k'addara ta had'a ku zama wuri d'aya a lokacinne zaki gane cewa DUK KANWAR JA CE". "Kar ki ce haka Hafsat duk da a baya kin shiga matsaloli a dalilin aure kar wannan yasa ki yi wa maza kudin goro, domin ba duk suka taru suka zama d'aya ba". Shiru Hafsat ta yi ta kasa bata amsa sakamakon sallamar da ta taji ta yara, alamun yaran gidan sun dawo daga islamiyya. Hafsat ce ta miqe daga inda take zaune ta saka yaran a gaba zuwa d'akinsu, sai da ta tabbatar manyan sun cire unifoam sun saka kayansu, itama ta cirewa k'ananan ta shiryasu sannan ta fito. Lokacin da ta fito daga d'akin yaran sai ta sami Uncle d'inta ya dawo don haka tana yi mai sannu da zuwa ta wuce kitchen don d'ora girkin abincin dare. Tuwon alkama tayi miyar busasshiyar kubewa, ana gaf da kiran sallar magriba ta gama, sai da ta tsaya ta gyara kitchen d'in ta fitar da abincin dining area sannan ta wuce zuwa d'akinta, don yin wanka tun da tasan ba yin sallar za tai ba, saboda tana fashin salla. Bayan sallar isha duk ahalin gidan suka taru a dining table don cin abincin dare, bayan sun gama suka koma parlour kowa yana harkokin gabansa har zuwa 10:00 pm, kowa ya nemi makwancinsa. Sai da ta gama duk wani abu da ta saba kafin kwanciya bacci sannan ta hau gado ta kwanta, amma sai dai sam bacci ya gagari idanunta, sai ma tunanin maganar da sukai da Aunty d'azu da ta shiga dawo mata a k'wak'walwar ta, ta runtse ido cikin takaici, a duniya babu abin da ta tsana irin ayi mata maganar aure, amma ta lura iyayenta ba za su mata uzuri ba duk da sun fi kowa sanin irin bak'in ciki da wahalhalun da ta sha a gidajen aurenta. Babban takaicinta ma shine a shekarunta da basu kai talatin ba a ce tayi aure har sau uku, wannan abin shima yana cin zuciyarta, duk da ta yarda cewa hakan yana ciki k'addarar rayuwarta. Ta dad'e tana tunani har zuwa lokacin da bacci yayi nasar d'aukarta. Da asuba ana kiran assalatu ta tashi duk da ba sallar zata yi ba, kasancewar ta riga ta saba da tashi dai dai wannan lokacin, ta shiga toilet ta sake pad d'in jikinta ta yi alwala, ta fito ta zauna tana tasbihi har zuwa lokacin da masallacin unguwar suka idar da sallah, sannan ta fita kitchen don d'ora break fast. Ummu Aisha [7/1, 6:24 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha 🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS ZAW (Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah)🤜🤛 2⃣ Bata dad'e a kitchen d'in ba Aunty ta shigo suka ci gaba da aikin tare har suka kammala, suka juye komai a warmers, sai ta fita ta fara gyara parlour ta bar Aunty tana gyara wurin da suka 6ata a kitchen, da kuma wanke kwanukan da su kai amfani da su. Zuwa 7:00am sun kammala komai, don har yaran an tashe su daga bacci, masu girman sunyi wanka, sun yiwa qannensu, duk sun shirya cikin unifoam, kowa ya fito aka karya, Uncle ne ya wuce da yaran zai sauke su a makaranta, Aunty ta tsaya tana gyara wurin da akai break-fast, ita kuma Hafsat ta shiga d'aki don k'arasa shiryawa, ta fito ta wuce wurin aiki. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar musu cikin kwanciyar hankali da walwala, sai dai a b'angaren Hafsat babu abin da tak'i jini irin ayi mata maganar aure domin tace naji dad'i shine gari ba na saba ba. Ranar juma'a da misalin 4:30 na yamma Aunty na kitchen tana aiki Hafsat kuma da sauran yaran suna zaune a parlour suna kallon wani indian film, suka ji ana sallama, ai da gudu qananan suka tashi suna murnar Uncle oyoyo, duk suka nufi gurin shi. Fuskarsa d'auke da murmushi ya qaraso cikin parlourn tare da yaran ya sami wuri ya zauna, Hafsat na zaune, sai da ta bari yaran sun gama gaida shi sannan ta gaida shi, amma ko jira ya amsa batai ba ta mik'e ta shige d'aki, kawai ya bita da kallo har ta shige ta rufo qofar. Idan da sabo yaci ace Abubakar ya saba da irin wad'annan abubuwan daga Hafsat, amma ya kasa sabawa, don yanzu ma ji yayi zuciyarsa nayi masa zafi. Ko don zumuncin dake tsakaninsu bai kamata ace tana nuna masa halin ko in kula irin wannan ba, duk da yasan cewa shi mai tarin laifi ne a gare ta amma ai ya bata haquri, kuma ko Ubangiji ma muna masa laifi ya yafe mana bare mu 'yan adam. Fitowar Aunty daga kitchen ne ya katse masa tunanin sa, sun gaisa cikin mutunci yake tambayarta Uncle Tahir, ta ce ya fita. Bai dad'e sosai ba yayiwa Aunty sallama, sai ya cewa Mas'ud ya kira masa Hafsat, shi kuma ya fita harabar gidan yana jiranta. Saqon na isa gareta ta koro d'an aiken, ya fito yana zun6ura baki, Aunty dake qoqarin shiga kitchen ta tambaye shi ya akai? Sai yace "Koro ni tayi tace karna dame ta". Umartarsa tayi da ya koma ya zauna, ita kuma ta shiga d'akin ta sami Hafsat zaune tana daddana wayarta, ta ce "Hafsat bake ake kira ba?" Cikin sanyin jiki ta d'ago kai ta kalle ta, sannan tace "Yanzu tsakani da Allah Aunty me zan masa?Tun tuni na gaya masa ya fita daga cikin rayuwata, ni ko aure zanyi ba aurarsa zanyi ba ya kamata ya shafa min lafiya". Cikin sigar rarrashi Aunty ta ce "To yanzu dai tashi kije, kinsan wulak'anci bashi da dad'i". Dole ba dan zuciyarta ta so ba ta miqe ta d'auki hijab ta saka ta fita don bin umarnin Auntyn ta. Ummu Aisha [7/1, 6:24 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha 🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS ZAW (Gidan zaman lafiya da Amana Allah)🤜🤛 3⃣ Lokacin da ta fito tsaye ta same shi ya jingina da jikin motarsa, tun da tayi sallama bata k'ara ce masa komai ba, sam fuskarta babu alamar walwala. Ya jima yana kallonta kafin daga baya ya yi gyaran murya ya fara magana cikin sigar rarrashi "Hafsat duk da nasan cewa ni mutum ne mai tarin laifi a gare ki, hakan bazai sa na kasa sake rak'on alfarmarki a karo na babu adadi ba, Hafsat ki dubi girman zumuncin da ke tsakanin mu da kuma yaronmu ki amince a mai da aurenmu, ni kaina nasan cewa abin da nayi miki a bayan ban kyauta miki ba, amma wani abu da baki sani ba ni kaina da na aikata abin na fi ki jin baqin cikin faruwar hakan, duk abinda ya faru ya faru ne bisa dole ba da son raina ba, kiyi haquri Hafsat ki manta da abin da ya riga ya wuce, nayi miki alk'awarin irin hakan ba zata sake faruwa a gaba ba. Na tabbatar ko iyayenmu zasu ji dad'in faruwar sake ganinmu a matsayin ma'aurata". Wani murmushi tayi da ke nuna tsantsar takaici, sannan ta ce "Sau nawa zan gaya maka cewa ka daina tunanin ni Hafsat zan koma gidanka? Idan ma mafarki kake ya kamata ka farka, har abada ni Hafsat na gama zaman aure da mutum azzalumi irinka, ka fita daga hanya ta, ka daina takura min domin har abada bazan ta6a komawa gidanka ba, a lokacin da ka tashi tazarta ni ai mantawa kayi da zumuncin namu, sai yanzu da kake son sake cuta ta sannan ka tuna cewar ni 'yar uwarka ce? To don Allah ka fita daga hanyata gidanka dai kam bazan koma ba, ni ka ga tafiya ta sai an jima". Tana gama fad'ar haka ta juya zuwa cikin gida ta barshi a tsaye yana kallonta cikin takaicin maganganunta. Babu yadda zaiyi haka ya shiga mota ya tafi, sai dai ya k'udurce a ransa cewa wannan karon duk tsanani ba zai bari ta kubce masa ba. Lokacin da ta koma cikin gida tayi matuqar qoqari wurin b'oye damuwarta, haka ta ci gaba da harkokin gabanta. An d'ebi kwanaki da yawa ba a k'ara yi mata maganar aure ba, hakan yasa hankalinta ya kwanta, taci gaba da harkokinta cikin kwanciyar hankali. A gurin aikinta ma ta mai da hankali sosai don ganin al'umma sun amfana da baiwar ilimin da Allah (S.W.T) ya yi mata. Sai dai duk da haka tana fama da wasu daga cikin abokan aikinta maza da suke nuna bak'atarsu ta aurenta duk da babu wanda ta bawa fuska a cikinsu. Shima Abubakar tun ranar da ya zo bai k'ara zuwa gidan ba ma, bare ya dame ta, hakan ba qaramin dad'i yayi mata ba, don har ga Allah ita babu batun aure a tsarin rayuwarta. ―― ―― ―― Ranar wata lahadi tun wajen 9:00 na safe Uncle ya fita daga gida sa6anin kowane lokaci, don idan ranar lahadi ce baya fita sai lokacin sallar azahar, idan ya yi sallah ya dawo ba zai sake fita ba sai la'asar, to kuma ba zai dawo gida ba sai bayan sallar isha'i. Tun da ya fita bai dawo gidan ba sai bayan azahar. Da daddare bayan yara sunyi bacci Aunty ta shigo d'akin Hafsat, wadda itama har ta kwanta a lokacin ta ce ta je Uncle d'inta na son yin magana da ita. Haka kawai ta ji gabanta ya fara fad'uwa duk da bata san dalilin kiran ba, amma sam hankalinta ya kasa kwanciya. Dogon hijabi har qk'asa ta sa a kan kayan baccin da ke jikinta ta fito domin amsa kiran da akai mata. Ummu Aisha [7/1, 6:25 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha 🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS ZAW (Gidan zanan lafiya da Amana insha Allah)🤜🤛 4⃣ Zaune ta same shi, da kofin coffee a hannunsa, ta sami gefe ta zauna tana jiran ya gama abin da ya ke. Sai da ya gama shan coffee d'in ya ajje cup d'in a kan centre table sannan ya mai da hankalinsa gare ta. "D'azu Baffanninki Sa'idu da Shehu sun zo, kuma ba akan komai ba sai akan maganar aurenki, Hafsat an baki lokaci iya lokaci don ki fitar da miji amma abin ya gagara. Abin da ya faru abaya ya riga ya wuce, kuma hakan ba zai zama hujjar da za'a zuba miki ido ki zauna haka babu aure ba. Shi mutum duk abin da ki ka ga ya faruda shi to dama yana daga cikin qaddararsa, kuma mutum bai isa ya sauya abin da aka qaddaro masa ba. A yanzu haka mun yanke shawara ranar juma'a idan Allah ya kaimu za'a maida aurenki da Abubakar. A firgice ta d'ago tana kallonsa saboda yadda maganar ta zo mata a bazata, tuni ta ji kanta ya sara mata wani irin ciwo, idonta ya cika da hawaye sai dai tayi qoqarin hana su zubowa. Tun daga nan bata k'ara fahimtar abin da yake cewa ba har zuwa lokacin da ya umarce ta da tafiya. Ai tana shiga d'aki ta fashe da kuka mai cin rai, ba ta dad'e da shigowa d'akin ba Aunty ta shigo itama. Gefen gado ta samu ta zauna sannan ta umarci Hafsat da ta tashi zasuyi magana, babu musu ta tashi sai dai har lokacin hawaye bai bar zuba daga cikin idanunta ba. Cikin sigar rarrashi Aunty ta ce "haba Hafsat a tunanina kuka ba shine mafita ysnzu a gare ki ba, ya kamata ki dage da addu'ar Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gare ki, karki manta wad'anda suka zartar da wannan hukuncin iyayenki ne, kuma kinsan ba za su ta6a aikata wani abu a gareki da nufin cutarwa ba, sannan ko ba komai Abubakar d'an uwanki ne, duk wani miji da zaki aura ba zai fi shi sanin ciwonki ba. Kar ki duba abinda ya faru a baya a tsakanin ku, ke kanki kin san halin mahaifiyarsa, kuma ko babu komai ai gaskiya ta bayyana cewa shima ba a son ransa hakan ta faru ba, sai don babu yadda zai yi ya aikata bisa tursasawar mahaifiyarsa". Babban abinda na ke so da ke shine ki kwantar da hankalinki, kuma ki dage da addu'a Allah ya ku6utar da ke daga sharrin duk wani mai sharri. Tabbas abubuwa marasa dad'i sun faru a rayuwar aurenki amma ki sani Allah yana jarraba Bayinsa muminai ta hanyoyi da yawa, don haka nake shawartar ki da ki daure ki ci wannan jarrabawar. Ta dad'e tana kwantar mata hankali, har sai da taga ta daina kuka sannan ta tafi ta kwanta. Gabad'aya tsawon daren bacci ya qauracewa idanunta, don haka ta tashi tayo alwala tazo ta fara gabatar da nafila don kai kukanta ga Rabbissamawati. Wai shin wacece Hafsat? Mene ne matsayin Abubakar a wurin ta? Mene ne dalilinta na qin aure? Duk wannan amsar tana gareni, kuci gaba da biyoni domin jin yadda za ta kasance. Comments d'inku shi zai qara min qarfin gwiwa wurin cigaba da rubuta labarin. Ummu Aisha [7/1, 6:25 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha 🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS ZAW (Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah)🤜🤛 5⃣ ASALIN LABARIN Garin Rumoh da ke k'aramar hukumar Sumaila gari ne da ya ya had'a al'ummar Fulani da kuma maguzawa, Allah yayiwa mazauna garin albarkar noma, da kiwo. Malam Buba asalin mutumin garin ne tun iyaye da kakanni, yana zaune a cikin garin da matarsa mai suna Goggo Habi da 'ya'yansu. Malam Buba bafulatani ne usul, kuma makiyayi ne domin Allah yayi masa arzik'in shanu da awaki, sannan duk da haka idan lokacin noman damina yayi nanma ba'a barshi a baya ba. Babban d'ansa shine Halliru yana da mata biyu Inna Kulu da Goggo Maryo, sai mai bi masa Shehu shima matansa biyu, sai Sa'idu yana da mace d'aya sannan sai qaraminsu Sani shima tarsa d'aya, sai mata guda biyu, kowacce tana gidan mijinta. Duk mazan kowa a cikin gidan yake zaune da iyalansa, kowa b'angarensa da ban. Duk 'ya'yan malam Buba kowa ya tashi da irin sana'ar Baffansu wato noma da kiwo, sa6anin Sani da tun yana qarami yake da sha'awar kasuwanci, don tun yana da shekaru goma sha biyar ya kafa tireda a qofar gidansu, kuma Allah cikin ikonsa sai ya kawo masa bud'i cikin sana'arsa, don har ta kai ya mallaki babban shago a cikin garin, kuma duk da haka yana had'awa da kiwo, don haka sai ya zama zakaran gwajin dafi a cikin gidansu. Ya fara soyayya da wata 'yar maqoftansu mai suba Sa'a, amma sai dai su ba fulani bane kanawa ne, wannan ne ya tashi gankalin Inna Kulu domin ita burinta ya auri qanwarta mai suna Ma'u. Tayi iyaka qoqarinta wajen ganin maigidanta ya shiga maganar amma fur ya k'i, yace ba shi zai zaunawa Sani da matarsa ba, kuma tun da iyayensu basu hana shi auren wadda ransa yake so ba, to shima bashi da hurumin tursasa shi ya auri macen da ba ya ra'ayi. Dole ba don ta so ba ta hak'ura, saboda babu yadda za ta yi, amma ta k'ullaci wannan auren na Sani sosai a ranta, don ta so ace k'anwarta ce aci arzik'i da su ganin yadda harka ta bud'e masa sosai. Wannan dalilin ne yasa tun daga lokacin da akai auren Sani da Sa'a ta d'ora mata karan tsana, don ma ita Sa'an mace ce mai matuk'ar hak 'uri da kawaici, duk abinda za ta yi mata baza ta d'aga kai ta dube ta ba, bare ta tanka mata. Shekaru biyu da yin bikinsu Sa'a ta haifi yaro namiji aka saka nasa suna Ibrahim, bayan shekaru uku ta haifi mace aka sa nata Hafsat amma suna kiranta Hafsi, daga nan sai Maryam sai Usman. Tun lokacin da aka yaye Hafsi rik'onta ya koma hannun kakarta wato Goggo Habi. Kuma tun Hafsi na da shekaru biyar a duniya Goggo ta sanar da 'ya'yanta ko bayan ranta Hafsi bata da miji sai Abubakar d'an wajen baffa Halliru. Wannan magana ta so tada fitina a gidan don Inna kulu mahaifiyarsa cewa tayi bata amince ba. Amma da yake Baffa Halliru jajirtacce ne dole ta hak'ura don babu yadda za ta yi. Lokaci ya ja sosai abubuwa da yawa sun faru, ciki harda kammala primary school da Su Hafsi suka yi, ita da Rabi 'yar gidan Inna Kulu da kuma Sadiya 'yar Baffa Sa'idu. Jarrabawarsu ta fito sakamako ya nuna Sunci G.G.A.S.S Sumaila, don haka babu 6ata lokaci Baffa Sani ya fara shirye-shiryen kaisu makaranta, don dama shine ya sa su. Ai kuwa Inna Kulu tai tsalle ta dire ta ce babu inda 'yarta za ta je da sunan karatu, sam ba za ta yarda da wannan barbad'arba, da sunan karatu, 'ya mace ba namiji ba ta tafi wani guri ta bar iyayenta. Baffa Halliru kuma yace ba ta isa ba, don bata ida hana d'an uwansa iko da 'yar sa ba. Ita kuma ta dage akan ra'ayinta ta ce babu inda 'yar ta za ta, shima kuma Baffa ya dage akan sai ta je sai da kyar Baffa Sani ya samu maganar ta mutu, bayan Inna ta sa baki. Aka kai iya su Hafsi da Sadiya, ita kuma Rabi aka barta a gida. Ummu Aisha [7/1, 6:25 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha 🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS ZAW (Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah) 🤜🤛 6⃣ Kasancewarsu yara masu k'wazo sai suka mai da kai a kan karatunsu, sam basa wasa, har zuwa lokacin da suka shiga JSS 3. Anyi hutun 1st term suka zo gida, a wannan lokacin ne Goggo Habi ta ce lokaci yayi da ya kamata a aurar da su domin sun isa aure. Amma sai Baffansu Hafsi wato Baffa Sani ta rok'e ta da ta yi hak'uri su k'arasa wannan shekarar su samu su yi ko da J.S.C.E ce, babu gardama ta amince don ta fahimci shi mutum ne mai son ilmin Zamani duk da shi bai yi ba,duba da yadda ya tsaya kai da fata akan karatun yaran gidan maza da mata, don yanzu haka Abubakar ya had'a degree dinsa a BUK a kan accounting, yana zaman jiran ayi post dinsu don tafiya Service,sai Kamalu dan wajen Baffa Shehu shi kuma yana Health technology, sai kuma sauran wad'anda suke Secondary School, kuma duk Baffa Sani ne jigon karatunsu. A wannan hutun ne akai bikin Rabi, abin da yayiwa uwarta dadi kenan y'ar ta tayi aure ta bar sauran sa'anninta a gida, don ita mace ce me son ace komai ita ce a gaba,don bak'arar homa take da karatun Abubakar ba, sai ka ce wanda k'urre biro 🤣 bayan biki da sati daya hutunsu ya k'are suka tattara kayansu suka koma makaranta. Sun maida hankali sosai akan karatunsu don dukkansu sunci burin karatu, don basu da masaniya akan maganar aurensu nan kusa, tun da sunga sun je har secondary, abinda duk gidan babu 'ya mace da ta ta6a yi, don duk sauran yayyensu iyakarsu primary. Bayan sun gama J.S.C.E anyi hutu suka koma gida, kowacce na dokin da an koma makaranta an goge J 😂 an zama seniors. Sai dai abin da basu sani ba tuni an sanya ranar aurensu lokaci kawai ake jira. Lokacin da suka ji maganar aurensu sunji babu dad'i, amma sanin babu yadda zasuyi yasa basu tada hankalinsu ba. Amma Hafsi kam daurewa kawai take don tun da ta taso ta san da maganar aurensu da Yaya Abubakar amma ko sau d 'aya bai ta6a kiranta da sunan zance ba, sannan gashi duk yaran gidan nan tsoronsa suke ji saboda sam baya sakar musu fuska, don ko yaro ne yayi lefi zakiji iyayen na cewa bari Baffa Qarami ya shig a fada masa (saboda sunan Malam Buba yaci shi yasa ake ce masa Baffa Qarami, shi ya hana duk k'annensa kiransa da haka, yace su kira shi da sunansa wato Abubakar) to yanzu yaro zai nutsu don sunsan da ya zo zai qaddamar musu.🤺 An ci gaba da duk wasu shirye-shirye har zuwa llokacin biki, amma ita Hafsi iya auren za'a daura ban da biki saboda kowane lokaci Abubakar zai iya jin kira don tafiya bautar k'asa. Anyi d'aurin aure ranar juma'a kuma a ranar aka raka Sadiya gidan mijinta aka ci gaba da shagulgukan biki har zuwa ranar lahadi, sannan taro ya watse kowa ya kama gabansa. Ita kuwa Hafsi an bar ta a gida har sai Abubakar yaje wurin bautar qasa ya dawo. Ranar talata da yamma ta na zaune sai ga Auwalu k'anin Abubakar dan Goggo Maryo ya zo yace taje Yayansu yana kiranta, sai da gabanta ya fad'i don tunaninta bai ta6a bata haka ba. Kasa amsawa yaron tayi, don bata ssn abin da za ta ce masa ba, sai Goggo ce ta amsa masa da cewa tana zuwa. Ganin da Inna tayi tun tafiyar yaron bata da niyyar tashi yasa ta yi mata magana, ta mik'e jikinta a sanyaye ta dauki Hijabinta ta saka ta fita. Lokacin da ta fito kai tsaye dakinsa ta nufa, da yake hanyar k'ofar gida don tasan dai zai yi wahala ace yana waje, kuma sai Allah ya taimake ta har ta isa babu matar da ta ganta don kowacce tana 6angarenta tana girkin dare. A k'ofar dakin ta tsaya tayi sallama, sai da ta jira ya amsa mata ya bata izinin shiga, sanban ta daga labulen dakin ta shiga. Ummu Aisha [7/1, 6:26 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha 🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS ZAW (Gidan zaman kafiya da Amana insha Allah)🤜🤛 7⃣ Zaune ta same shi a gefen katifa yana daddana wayarsa, d'akin a gyare yake tsab sai k'amshin air freshner yake kamar ba d'akin namiji ba. Kan tabarmar da ta samu a shimfid'e a d'akin ta nufa da niyyar zama, amma sai ya dakatar da ita ta hanyar nuna mata gefen sa. Wani iri ta ji don ba za ta iya zama a kan katifar ba alhalin yana zaune akai, sai ta ja ta tsaya, ta kasa gaba ta kasa baya, don tana tsoron ta yi masa musu ya masge ta. 🤣 Ganin ba ta da niyyar zama yasa Abubakar yi mata magana ‘’Ki dawo nan ki zauna‘’, ya fad'a yana nuna mata wurin da ya nuna mata da farko. Ganin fuskarsa a d'aure yayi maganar dole ta k'arasa ta zauna a d'arare kamar ace mata ket ta yanka da gudu. 🏃🏻‍♀ Bayan ta gaida shi, ta ja bakinta ta yi shiru, shi ma sai yaci gaba da daddanna wayarsa, ba tare fa ya ce komai ba don bai san me zai ce mata ba. Sun d'auki lokaci mai tsayi suna zaman kurame, babu wanda ya yi magana a cikinsu, sannan Abubakar ya fara magana da cewa ‘’Hafsat‘’, ta d'ago kanta tana dubansa tare da amsawa. ‘’Nasan kin san cewa ni yanzu a matsayin mijinki nake, kamar yadda dole a kira da sunan matata, duk da mun rayu a cikin gida d'aya kin san abubuwa da yawa da suka shafi rayuwata, ya zama dole in k'ara sanar da ke, don ki kiyaye, hakan shi zai sa mu fahimci juna domin mu gina rayuwa mai inganci. Hafsat duk da cewa na san kina da tsafta, dole in k'ara jaddada miki, idan na ce tsafta ba iya ta muhalli na ke nufi ba har ta jiki nake nufi, sannan ina son ki zama mai yawan amfani da turare, don kowane lokaci zan so jin matata cikin k'amshi, sanna ki guji gutsuri tsoma, sai kuma bin umarni na, duk abin da nasa ki to ba na son jayayya . Sai abu na k'arshe shine ki girmama iyayena, duk da kema iyayenki ne, kuma ban ta6a jin wani abu na ashsha daga gare ki ba a kan su to ki k'ara kiyayewa.‘’ Da farko bata da niyyar cewa komai amma ganin ya zuba mata ido yasa ta fahimci wani abu abu ka ke so ta ji tace. Cikin sanyin murya ta ce ‘’insha Allahu zan kiyaye.‘’ ‘’Allah ya baki iko‘’ ‘’Ameen‘’ Ganin bashi da wani abu da zai fad'a mata yasa ya sallame ta, ta koma cikin gida. Tun daga wannan ranar sai ya zamto yana yawan kiranta ko ba komai idan taje zai san dabarar da ya yi yayi wasanni da ita, kuma sannan yanzu ita ce mai yi masa gyaran d'aki kullam. Mafarin matsalar ya farane ranar wata Juma'a, lokacin Goggo bata nan, ta tafi Kano wurin y'ar uwarta da ke can, k'anwar ta ce iyayensu d'aya, tun ranar Laraba ta tafi da niyyar za ta yi kwana hud'u ta dawo. Bayan sallar isha har ta kwsnta, sai ga k'anwarta Maryam ta shigo, ita take taya ta kwana kafin Goggo ta dawo, tana k'ok'arin hawa gado tace ‘’ki je inji Yaya Abubakar.‘’ Sai da ta ji gabanta ya fad'i, amma dole ta tashi ta d'auki hijab ta saka, ta fito sai waiwaye ta ke kamar mara Gaskiya, har ta isa d'akin. Lokacin da ta shiga a kwance ta same shi a kan katifarsa daga shi sai boxer, yana ganinta ya wara mata hunnunsa alamun ta zo gareshi, babu musu ta k'arasa ta shige cikin jikinsa. Sun jima suna mak'ale da juna suna wasanninsu, har zuwa lokacin da ta ji yana shirin wuce gona da iri, sai jikinta ya d'auki rawa, ta fara ba shi hak'uri, amma ina, shi bai sanma me take ba, ganin abin ya fara girma yasa My Heenat kami hannuna muka fito sumsum,👭 don dai ganin sirrin ma'aurata ba kyau. Ummu Aisha [7/1, 6:26 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha 🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS ZAW (Gidan zanan lafiya da Amana insha Allah)🤜🤛 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 RAHEENAT ina taya ki murnar kammala littafinki NI DA YAYA AL'AMIN, Allah ya sa darrusan da ke ciki su amfane mu baki d'aya, Allah k'ara basira da kaifin k'wak'walwa. 8⃣ Bayan an d'auki kimanin awanni biyu na koma d'akin, inda na sami Hafsat tana ta kuka, shi kuma sai aikin rarrashinta ya ke, daga gefe kuma ga risho an kunna da alama dai ruwan zafi ya d'ora, nan take mamaki ya kama ni,🤔 dama ashe da shirinsa kenan. Da kyar ya samu tayi shiru, amma zuciyar ta cike take da tsoron kar a gane abinda ya faru a tsakaninsu don babu irin gargad'in da Goggo bata yi ma ta ba, kuma ta yi k'ok'arin ganin ta fahimtar da shi amma sam yak'i fahimtar ta. Sai da ruwan yayi zafi sosai sannan ya surka ya saka ta a ciki, bayan ta dad'e ya zubar ya k'ara sirka wani, sai da ya tabbatar ta ji sauk'in ciwon jikin ta sosai sannan ya rakata har d'kin Goggo ta kwanta ya juya ya tafi zuciyarsa cike da farin ciki. Washe gari da safe haka ta tashi sam bata jin dad'in jikinta sai ta daure don ta na gudun kar a fahimci halin da take ciki, ko lokacin da za ta yi wanka sai da ta cika baho da ruwa mai zafi ta kai ban d'aki sai da ta k'ara gasa jikinta sosai, kuma hakan ya taimaka mata sosai don ba k'aramin dad'in jikinta ta ji ba. Zuwa bayan sallar la'asar Goggo ta dawo, lokacin tuni Hafsi ta warware kamar babu abun da ya faru. Tun daga wannan lokacin Abubakar ya sami dama, kusan kullam yana mak'ale da ita, har aka kira su domin tafiya bautar k'asa. Wani abokinsa ne ya fara sanar da shi cewa Bauchi State akai posting d'in sa, tabbas ya yi farin ciki sosai kasancewar yana Arewa ba a tura shi kudu ba. Sun shiga camp lafiya sun fito lafiya, haka ya dawo gida ya tattara komatsansa ya tafi, zuciyarsa cike da kewar 'yar amaryarsa. Bayan sati hud'u da tafiyarsa Hafsat ta fara zazzab'in dare, sai kuma rashi d'and'anon baki, komai ta ci bata jin dad'insa, amma ko Gaggo bata sani ba, don tana da dauriya sosai, kuma zazza6in idan gari ya waye sai ta ji ta warke sai wani daren. Ranar wata laraba, tun da ta tashi da asuba, ta ji zazza6in ba sauka ba, aikuwa ta na yin salla ta koma ta kwanta ko sharar da take yi wa Goggo bata sami damar yi ba. Ganin hantsi ya daga sosai tana d'aki a kwance ba ta fito ba sai Goggo ta shiga don ta ji ko lafiya tun da bata saba da kwanciya da dai dai wannan lokacin ba, amma sai ta same ta a k'udundune,da sauri ta k'arasa ta ta6a jikinta, aikuwa da sauri ta d'auke hannunta saboda zafin da ta ji jikin Hafsat d'in ya d'ime da shi. Nan da nan ta aika yara aka kira Baffan Hafsat d'in daga shagonsa, yana ganin yadda jikinta yake yace a shirya ta su tafi asibiti. Kai tsaye asibitin Sumaila aka kai ta bayan bincike likita ya sanar da su cewa tana d'auke da shigar ciki na wata biyu da sati d'aya, ya basu magunguna sabida zazza6in da ya ke damunta, bayan sun saya su ka wuce gida. Kafin wani d'an lokaci labarin cikin hafsat ya kai kunnen kowa da ke gidan, sai d'an k'us-k'us ake wai daga d'aura aure ko tarewa ba ai ba ta kai masa kanta, kai lallai yaran zamani basu da kunya. Ita kam Hafsat ba ta san me suke ba, don ta kanta ta ke, don sosai cikin ke sa ta laulayi. Lokacin da labarin cikin ya je kunnen Innar su Abubakar kuwa, ba k'aramin farin ciki ta yi ba, don tana ganin lokaci yayi da zata turawa Sani da matarsa bak'in ciki, kwatankwacin wanda ta ji lokacin da ya k'i auren 'yar uwar ta, da kuma lokacin auren Abubakar da Hafsat . Goggo ce ta ci gaba da baiwa Hafsat duk wata kulawa da ya kamata, amma fa tana shan mita, a gun Goggo na k'in jin gargad'inta da ta yi, ai yanzu gashi nan ya tafi ya bar ta da ciki, shi yana can yana harkokinsa ita kuma tana ji a jijinta. Watansa uku da tafiya ya zo zuciyarsa cike da d'okin ganin matarsa da kuma ahalinsa, kai tsaye d'akin mahaifiyarsa ya nufa, sun gaisa cike da kewar juna, nan ta dama masa fura kasancewar lokacin da ya zo abincin rana ya k'are. Sai da ya sha ya k'oshi, yana shirin tashi ta dakatar da shi da cewa "tsaya akwai maganar da na ke son muyi da kai." Bai kawo komai a zuciyarsa ba ya koma ya zauna. Sai da nisa sannan ta fara magana "ko kana da labarin cewa Hafsi tana da ciki?" Cikin mamaki mai gauraye da tsantsar farin ciki yace "ban sami labari ba Inna." "To ni yanzu na sanar da kai, kuma mahaifinka da 'yan uwansa suna nan suna jiran dawowarka domin ayi tariyarta, ni kuma abinda ba zan yadda da shi bane shine had'a jini da Sani, don haka ina umartarka da cewa duk juyin da za'ayi karka yarda ka ce cijinka ne, sannan umarnina na k'arshe a gare ka ka yi amfani da wannan damar ka sawwak'e ma ta aurenka, kuma saki uku na ke son kayi mata. Ummu Aisha [7/1, 6:27 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha 🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS ZAW (Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah)🤜🤛 SADAUKARWA Wannan shafin naki ne ke kad'ai Aishan Umma, Allah ya k'ara k'auna da zaman tare 9⃣ Nan take ya ji kamar ta watsa masa ruwan zafi a jikinsa, cikin firgici ya ce "A'a Inna kar ki ce haka, idan na aikata abinda kika umarce ni na zalinci Hafsat, kuma nasan Allah ba zai bar ni ba, na rok'e ki don girmab Allah kar k……" Katse shi tayi da cewa "Me kake son nuna min?So kake kace farin cikin Hafsi ya fi nawa muhimmanci a gurinka?" Sai ta fashe da kuka "Lallai Saratu tayi nasara a kaina, sai ta je ta biya malaminta, sun shanye ka kaima kamar yadda suka shanye k'anin ubanka, amma ka sani muddin baka aikata abinda na sakaka ba Nono na da ka sha nan yafe ba." Cike da tashin hankali ya ke kallonta, amma sam babu alamun sassauci akan fuskarta, gabad'aya sai jikinsa yayi sanyi, ya ji nadamar zuwansa gida ta shige shi, tabbas da yasan abinda zai zo ya yarar kenan da gara yai zamansa a can. Da kyar ya yunk'ura ya tashi ya nufi d'akinsa, duk da k'urar da d'akin yai bai damu ba yana zuwa ya kwanta akan katifarsa, zuciyarsa cike da k'unci da bak'in cikin maganganun mahaifiyarsa. Zuciyarsa ta ci gaba da raya masa irin yadda mahaifiyarsa ta k'i jinin Baffa Sani, amma bai ta6a tunanin za ta saka shi aikata irin wannan zalincin ba, duba da tun farko ba wani abu shi Baffa Sanin ya yi mata ba, duk dai maganar akan ta so ya auri k'anwar ta ne, kuma Allah bai nufa ba. Abu d'aya da ya yanke a matsayin masalaha a gare shi shine, da asuba idan yayi sallah zai kama gabansa ya koma inda ya fito. Tun da ya shiga d'akinsa bai fito ba sai da aka kira sallar magariba, sannan ya fito yayi alwala ya wuce masallaci. Bai dawo gidan ba sai da akai sallar isha'i, har lokacin zuciyarsa a k'untace take, yana shirin shiga d'akinsa ya ji Baffa shehu yana masa magana daga bayansa. Juyowa yayi suka gaisa, sai yake ce masa ya same shi a wajensa akwai maganar da yake so suyi. Nan take yaji gabansa ya yanke ya fad'i, don yasan maganar ba zata wuce akan cikin Hafsat ba. Jiki a sanyaye ya amsa masa da cewa yana zuwa. Lokacin da ya je don amsa kiran Baffan nasa a kishingid'e ya same shi a farfajiyar wajen yana sauraron labarai a Radio. Sai da ya gama jin labaran sannan ya kashe Radion, ya juyo yana fuskantar Abubakar ya fara magana "Wato Baffa k'arami ba komai bane ya sa na buk'aci ganinka sai akan magarku da Hafsi, shin ko kana da masaniyar cewa ka tafi ka bar ta d'auke da ciki?" Ya yi shiru ya sauraron amsar da zai bashi. Duk da dukan gudumar da zuciyarsa ta ke yi hakan bai hana shi nuna mamakinsa ba. Baffa bai kula da halin da ya ke ciki ba yaci gaba da magana "Sakamakon haka mun yanke shawarar duk lokacin da ka dawo za ta tare a d'akinta." Duk da halin zullumin da yake ciki hakan bai hana shi furta cewa "A gaskiya Baffa nayi mamakin wannan maganar cikin, kuma ni ban san daga ina ta samo shi ba, don Allah Baffa ku tuhume ta ko za ta fad'a muku inda ta samo shi, kuma ni gaskiya bazan iya zama da ita ba, don haka ta je na sake ta saki uku. Ummu Aisha [7/1, 6:27 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha 🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS ZAW (Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah)🤜🤛 🔟 Baffa Shehu ya girgiza sosai da jin furucin Abubakar musamma irin hukuncin da ya yanke, ya zuba masa ido yana kallonsa ya rasa me zai ce, sannan kuma zuciyarsa bata amince da abinda Abubakar d'in ya ce ba saboda sanin halin Hafsat da ya yi, don ita ko yawo ma bai dame ta ba, idan ba aikenta akai ba zai yi wahala ka ganta a waje, bai ta6a ganin ta da wani saurayi a tsaye ba, bare ace wani ne ya yaudare ta ya yi mata ciki. Duk da ba a da tabbas akan d'an yau, to amma irin tarbiyyar da suka bawa 'ya'yansu zai yi wahala a sami 6ullowar irin wannan al'amarin a cikin gidansu. To amma ba shi da ta cewa, tun da shi dai bai san gaibu ba, kuma dole al'amarin yana buk'atar bincike. Da haka ya sallami Abubakar ya tafi ya barshi zuciya cike da tunani. 。 。 。 Koda ya je d'akinsa zama yayi akan katifa, komai ya dagule masa, ya rasa me ke masa dad'i a rayuwarsa ta duniya, ga kuma tunanin halin da ya jefa Hafsat da tarin soyayyarta dake cikin zuciyarsa, shi kan sa yasan ya tafka babbar asarar da ba zai ta6a mayarwa ba, to amma ya ya iya da Innarsa? Ranar nan kwana Abubakar yayi bai runtsa ba yana karanta wasik'ar jaki😃 (Ni kuwa na ce wa ya ja maka?)🤷🏻‍♀ Yana zaune bai ankara ba yaji masallatai sun fara kiran Salla, nan ya mik'e ya je yai alwala ya tafi masallaci, bayan yayi Raka'atainil fajr, sai ya zauna yayi ta karatun alk'ur ani, har zuwa lokacin assalatu, sai da akai sallar asuba ya fito ya nufi gida da nufin shirin komawa garin da ya fito. Yana shiga shirin wanka yayi, a band'akinsa da ke daf d'akinsa, bayan ya fito ya shirya tsaf, ya nufi cikin gida don yin sallama da mahaifansa. 'Dakin Innarsu ya fara shiga, ko gaisawa bata bari sun yi ba fara tambayarsa akan batun Hafsi, sai ya kwashe komai da ya faru tsakaninsa da Baffa Shehu ya fad'a mata, ai kuwa ranta ya yi fari tas, ko babu komai ya cika burin ta, sun ci gaba da tattaunawa akan abinda ya shafe su sak'on kira daga iyayensu ya iso gare shi, don haka ya fito don amsa kiransu, amma cikin zuciyarsa ji ya ke kamar ya zura da gudu. Da sallama ya shiga, d'akin Gogga Habi, inda duka iyayensu maza suke zaman jiransa, ganin kowa a zaune, ya nemi guri nesa kad'an da iyayen ya zauna, yana satar kallon Hafsat da ke zaune can gefe d'aya ta sunkuyar da kanta. Baffa shehu ne ya fara magana "Kamar yadda kuka sani mun taru anan ne akan maganar Baffa 'Karami da Hafsi gaskiyar magana jiya mun zauna da shi mun yi magana, amma amsar da ya bani ce tayi matuk'ar girgizani, shi yasa nake ganin gara ya fad'i abinda ya ce min a gaban kowa don wak'a a bakin mai ita ta fi dad'i." Abubakar da jikinsa ya k'ara sanyi ya kasa magana, sai da Baffansa ya ce "kai muke sauraro." Abin mamaki babu kunya Abubakar ya ce "Jiya Baffa Shehu ya ce da ni wai Hafsat tana da ciki, to gaskiyar magana ba nawa ba ne don ni tun da nake da ita, babu abin da ya ta6a had'ani da ita, sakamakon haka na ce ni bazan iya zama da ita ba, don haka na sake ta saki uku, sai ta nemi uban cikin ta." Hafsat najin haka ta yanke jiki ta fad'i a gurin da sauri Gogga ta yi kanta, tana dubawa ta ga ai sumewa tayi. Ummu Aisha [7/1, 6:28 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 1⃣1⃣ Ganin yadda Goggo ta gigice ya sa duk iyayen sukayo kanta, amma banda Bffa Sani da ya daskare a zaune,sabofa al'ajabin abinda Abubakar ya ce. A gigice Abubakar ya nufi inda take, sai dai bai kai ga k'arasawa ba Baffa Halliru ya doka masa wata tsawa da ta rud'ar da shi, ya ce "kar ka kuskura ka k'araso inda yarinyar nan take, idan kuma ba haka ba wallahi zaka ga 6acin rai." Jin haka yasa ya dakata jikinsa sai rawa ya ke, ya kasa aikata komai, yana kallo iyayen nasu suka kinkime ta aka fita da ita waje don kai ta asibiti. Asibitin da ke cikin garin aka nufa da ita, ganin halin da take ciki yasa mai'aikacin da ke bakin aiki a lokacin ya bar abinda take ya zo gurinta don bata taimakon gaggawa. Cikin ikon Allah numfashinta ya dawo, nan akai mata allurar Barci dan ana son k'wak'walwarta ta sami hutu. Ganin babu wata matsala duk kowa ya tafi sai iya Goggo aka bari a wurin, don ance idan allurar barcin ta sake ta zasu koma gida. Kimanin awanni biyu ta d'auka tana barci kafin ta farka. Abubuwan da suka faru ne suka dawo cikin k'wak'walwarta, wani irin tashin hankali ya ziyarce ta, a ranar nan Hafsat ta gane cewa kuka ma rahama ne, domin ko d'igon hawaye ta kasa zubarwa, sai wani irin suya da take ji zuciyarta na yi mata, ga wani abu da ya tokare mata k'irji. Goggo da ke zaune kusa da ita ce ta fahimci halin da ta ke ciki, sai ta dinga rarrashinta da kwantar mata da hankali, har zuwa lokacin da hawaye ya dinga zubowa daga idanunta. Har aka sallame su suka tafi guda kuka take, ta rasa dalilin da yasa Abubakar ya yi mata haka, wannan wace irin tazartawa ce? kamar ba jininsa ba, idan har son aurenta bayayi ba sai ya sanar da iyayensu gaskiyaba, amma don zalinci sai ya za6i ta 6ata mata suna. Har dare ta kasa cin komai, in banda kuka babu abinda ta ke, da kyar Goggo ta matsa mata ta sha koko, shima ba mai yawa ba don gaba d'aya ta yi loosen apetite d'inta. Cikin d'an k'ank'anin lokaci labarin cikin da abinda Abubakar ya ce ya bazu a gidsn da ma cikin garin gaba d'aya, kowa da abinda zai ce, wasu ma laifin mahaifinta suke gani, don da bai dage sai tayi karatun boko ba, da bata je ta kwaso musu abin kunya ba. Inna kulu kuwa ta sami abin yi kullum cikin yar da magana ta ke a tsakar gida, don sai da ta hana Saratu mahaifiyar Hafsi walwala a gidan. Iya tashin hankali Hafsat tana ganinsa, don a wannan lokacin mahaifin ta ko gaida shi tayi baya amsawa, kuma k'arin takaicinsa yadda Goggo ta kasa ta tsare ta hana kowa ya yiwa Hafsi magana, domin ta ce ita dai tasan wace ce Hafsin ta, ba zata aikata wannan kaifin ba, shiri ne kawai don a tozarta ta. Gaba d'aya Hafsat ta rame ta fita daga kamanninta, duk gidan babu mai tausayinta sai Goggo. Ganin yadda rayuwarta ta fara lalacewa yasa Goggo ta fara tunanin mafita. 。 。 。 Ranar laraba da hantsi ta shirya zuwa Sumaila, Kai tsaye gidan Binta, y'ar ta ce da ke aure a Sumaila. Bayan sun gaisa tai mata vayanin abinda ke tafe da ita akan maganar Hafsi, da irin taimakon da ta ke so tai mata, Goggo Binta ba jayayya ta amince da abinda mahaifiyarta ta saka ta, don itama zuciyarta ta bata akwai lauje cikin nad'i akan wannan naganar amma lokaci ne zai nuna. Bayan sun gama shirya abinda zasu yi Goggo Habi ta koma gida. Sai da daddare tayiwa Hafsat bayanin komai, kuma ta k'ara kwantar mata hankali, sosai. Ummu Aisha [7/1, 6:28 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 1⃣2⃣ Bayan kwana biyu Goggo Habi ta shirya zuwa Gani duba wani k'aninta da bashi da lafiya, tun asuba suka tafi ita da Baffa Sani da zai kai ta akan Babur. Suna barin gidan itama ta fito d'auke da jakar kayanta da ta had'a tun dare ta fita daga gidan, cikin sa'a kuma babu wanda ya ga fitar ta. Bata yi nisa da gida ba ta sami mota, irin direbobin nan masu sammako, ta hau, a tashar kuka ta sauka, ta nufi gidan Goggonta. Lokacin da ta je itama Goggo Binta ta gama shiryawa, ko zama bata yi ba suka fice, suka koma tasha, suka hau motar da zata kai su Kano. 'Karfe takwas na safe a cikin Kano tayi musu, sun je gidan Goggo A'i, wadda ta kasance yaya ga Goggo Habi, cikinsu d'aya, ita a Kano take aure, yanzu ma ba mijin tuni ya rasu, sai y'ay'a, duk sun zama wasu abu, masu aikin gomnati na yi, masu kasuwannci na yi. An kar6e su sosai cikin mutunci, don dama ita mace ce mai son zumunci, bayan sun karya aka sake gaisawa sannan ta yi mata bayanin duk abinda ya faru da Hafsi d'in tun daga batun aurensu da Abubakar, cikin jikinta har zuwa sakin da ya yi mata, da yanda kowa ya tsangwame ta, da kuma hukuncin da Goggo ta yanke na barinta garin ba tare da sanin kowa ba, har zuwa lokacin da gaskiya za ta yi halinta. Ita kanta Goggo A'i ta yarda da hukuncin da y'ar uwarta ta yanke, don a take ta kira d'anta 'Dahiru da ke aiki a Zari'a,Lacturer ne a A.B.U, bayan sun gaisa tayi masa bayanin abinda ya faru, kuma ta sanar da shi cewa tana so ta sa a rako Hafsat gidansa. Babu jayayya ya yi na'am da umarnin mahaifiyarsa. A ranar kuwa aka sa driver ya kai ta, ita ma Goggo Binta a ranar ta juya gida. Kar6a sosai matarsa tai mata, aka d'auki kayanta aka shigar wani d'aki,ta umarce ta da taje daga ciki ta yi wanka sai ta fito ta ci abinci ta huta. 。 。 。 Cikin kwanaki kad'an sabo ya shiga tsakaninsu, don Aunty Salma akwai kirki da sanin darajar d'an Adam. Satinta biyu a gidan aka samar mata malamin da zai d'inga yi mata lesson, kuma ta mai da hankali sosai. A can Rumo kuwa lokacin da Goggo ta dawo daga Gani ba ta ga Hafsat ba, sai da ta d'agawa kowa na gidan hankali, akai ta nemanta Hankali tashe, amma shiru babu labarinta, ita kuwa Goggo ta yi bulunbuk'wai, kai ka ce bata san ina ta ke ba.🤣 Hafsat ta ci gaba da rainon cikinta gefe d'aya kuma ga karatun ta da ta riga ta fitar da rai da shi. Kafin lokacin haihuwar ta ya yi Uncle Tahir da Aunty Salma sun tanadi komai, sai jiran lokaci. Ranar wata Talata da yamma Hafsat ta haifi yaronta Namiji, bayan yini da tayi tana faman Nak'uda, don tun asuba take fama. Bayan sati d'aya yaro ya ci suna Muhammad Saleem, anyi shagali Sosai, duk da babu wanda ya sani a cikin dangin su, sai dai abokan arzik'in Aunty sunyi musu kara sosai. Ta ci gaba da rainon d'anta k'ark'ashin kulawar Aunty, har yaron yayi wayo. Watan Saleem biyar Hafsat ta shiga makaranta,wata privet ce a nan kusa da su, SS 3 aka sata bayan interview da akai mata, kuma Alhamdulillahi ta ci. A shekarar ta zana S.S.C.E, da JAMB. Har wannan lokacin babu wanda yasan ina take, don ko Kano suka je to a Gadon 'Kaya ake sauke ta gidansu Aunty Salma. Lokacin da result d'insu ya fito ba k'aramin kyau yayi ba, kuma cikin sa'a JAMB d'in tama ta sami point fiye da yadda ake buk'ata, don haka nan da nan aka nema mata admission a A.B.U, kuma cikin hikimar Allah sun bata course d'in da take buri wato medicine. Bayan anyi registration da duk abinda ya da ce ta fara zuwa d'aukar lacture. Duk da bata da saurin sabo hakan bai hana ta yin k'awa ba, wata nai suna Afnan, itama sai da ta lura da nutsuwarta sannan suka k'ulla k'awance da ita. Afnan y'ar Kaduna ce, su biyu iyayensu suka haifa daga ita sai Yayanta Aliyu, wanda shima lecturer ne anan ABU. Ummu Aisha [7/1, 6:29 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 1⃣3⃣ Ranar wata litinin da misalin k'arfe goma sha biyu, suka fito daga lecture, suna tafe Afnan ta dubi Hafsat ta ce tana son ta raka ta wurin Yayanta zata kar6i wasu kud'i a hannunsa. Sai Hafsat d'in ta ce ta je ta dawo tana jiranta, amma fir Afnan ta k'i, sai ma cewa da ta yi "Hafsat ban san me yasa ba kullum na ce ki zo mu je gun Yaya Aliyu sai ki k'i, ko kara ba kya yi min, ko kuma kin ji labarin yana satar mutane ne, ban sani ba." Hafsat ta kalleta ta ce "ba haka ba ne, kawai……" "Kawai me za ki ce? Bayan gashi nan a fili kin nuna min cewa yadda na d'auke ki ke ba haka kika d'auke ni ba." Ganin maganar tana neman yin tsawo yasa Hafsat ta amince ta bita. Da sallama d'auke a bakinsu suka shiga Office d'in, Afnance a gaba Hafsat na biye da ita, wani daddad'an k'amshi ya ziyarci hancinsu. Kai tsaye Afnan ta nufi gaban tebir d'in da ke gabansa, ita kuma Hafsat sai ta sami wuri ta tsaya. Sai da Afnan ta gaida shi sannan Hafsat ma ta gaida shi, ya d'ago idanunsa yana kallon me d'auke da wannan zazzak'ar muryar. Afnan ta kar6i abinda ya kaita, bata tsaya yin wata magana ba saboda a lokacin yana tsaka da yin aiki, suka fito daga office d'in. Bayan kwana uku da zuwansu, ita har ta manta ma da batunsa, sai dai idan Afnan ce tayi maganarsa, kwatsam sai Afnan ta same ta da wani batu da ya zamo mata kamar famin abinda ya wuce. Bayan sun gama lectures d'insu na ranar, suna tafe suna hira, har suka zo inda zasu rabu, don ita Afnan a hostel ta ke, banbanci da Hafsat da ke Staff Quaters. Afnan ce ta sami jikin wata bishiya ta jingina tana kallon Hafsat, sannan tace "Sak'o aka bani wurinki, duk da ban san yadda zaki d'auki al'amarin ba, amma zan so ki fahimci abinda na zo miki da shi. Tun ranar monday da muka je office d'in Yaya Aliyu da ke ya ganki, bayan na koma hostel ya kira ni, ya yi min bayanin cewa yana sonki, kuma da aure, ya ce in sanar da ke. Abinda yasa banyi saurin fad'a miki ba tun ranar ina tsoron yadda zaki d'auki maganar, domin a k'ananan shekaru irin namu, bai kamata ace mun sanya maganar soyayya a gaba ba, musamman idan akai duba da irin course d'in da muke karanta, wanda yake buk'atar nutsuwa, to amma ya shaida min ba wai yana nufin sai anyi auren yanzu ba, zai bari ki k'ara girma nan da kamar shekara biyu haka." Hafsat na sauraronta har ta gama bayaninta, sannan ta yi murmushi t ce "Kafin nace komai tambaya zan fara miki, shin Yaya Aliyu yana da mata ko ba shi da ita?" "A'a bai ta6a aure ba" cewar Afnan. "To idan haka ne ya kamata ke kanki kisan wani abu da baki sani ba akaina, kin ganni nan to na ta6a aure, kuma har ina daro guda d'aya, mun sami matsala ne da maigida na wanda har ta kaimu da rabuwa." Ummu Aisha [7/1, 6:29 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 ASSALAMU ALAIKUM Nasan cewa kun jini shiru, wallahi matsalar waya ta ne sam yanzu ba ta rik'e charge, amma insha Allahu a haka zan lalla6a kafin Allah ya bani ikon sake wata. 1⃣4⃣ Duk da afnan tayi mamakin maganarta, amma sai ta 6oye bata nuna ba, sai ma cewa da "tayi to meye a ciki? Don kin ta6a aure wannan ba zai zama matsala ba, kuma nasan tun da Yaya Aliyu ya furta yana son ki, to da gaske ya ke yi don, don mun dad'e muna jiran wannan ranar, tun lokacin da wadda zai aura ta rasu ana saura sati d'aya bikinsu bai sake kallon wata mace da sunan soyayya ba, duk da damuwa da Hajiyarmu tayi da maganar aurensa, don Allah Hafsat kar ki bazantar da da soyayyar Yaya Aliyu." "Baki fahimce ni ba Afnan, da bakinki kin ce min Yaya Aliyu saurayi ne da ko auren fari bai yi ba, kin ga bai kamata ace ya aure ni ba ina matsayin bazawara har da d'a, gaskiya ina ganin idan na aure shi ban yi masa adalci ba." "Kada ki ce haka Hafsat, shi fa aure nufin Ubangiji ne, kar ki manta Manzon Allah (S.A.W) da bazawara ya fara, idan har hakan ta faru ai koyi kuka yi da sunna." Ta k'arasa maganar tana duban Hafsat. "Ban tari numfashin ki ba, amma karki manta ba ke zaki zauna da ni ba shine, idan kuma har bashi da ra'ayin auren bazawara fa?" "Hhhh, nasan waye Yaya Aliyu Hafsat, tunda ya ce yana sonki, ba yaro d'aya ba ko 'ya'ya goma ne da ke bazai fasa aurenki ba, domin duk abinda yace ya na so, to tabbas da gaske ya ke, sai dai idan ke ce bakya ra'ayinsa to wannan kam dole na hak'ura don ba zan miki dole ba." Cikin murmushi Hafsat tace "zan amince da maganarki amma bisa sharad'i d'aya." Wane irin sharad'i ne wannan?" Ina son ki sanar da Yaya Aliyu da Hajiya abin da na sanar da ke game da rayuwa ta, idan har sun amince to ba ni da matsala nima na amince, amma don Allah idan har kin san akwai matsala kar ki rufe min." "Wannan abu ne mai sauk'i, kuma insha Allahu babu wani dalili da zai hana aurenki da Yaya Aliyu sai ikon Allah, ki bani nan da gobe ko mai ake ciki za ki ji ." Nan suka ya sallama kowacce ta kama gabanta. 。 。 。 Washegari suna zuwa ko lacture basu shiga ba, Afnan ke sanar mata cewa sun yi magana da Hajiyarsu kuma ta amince babu matsala, shima Yaya Aliyun ya amince. Cikin sati biyu wata irin shak'uwa ta shiga tsakanin Hafsat da Aliyu, wata irin soyayya yake nuna mata, wadda ke sata mamaki sosai don ita a ganinta bata kai matsayin da mutum kamar Aliyu zai so haka ba. A haka ya fara maganar ya kamata iyaye su shiga cikin maganar don da wuri ya ke son ayi auren in ya so ta ci gaba da karatun ta a d'akinta. Kai tsaye ta sanar da Auntynta, itama ba ta yi k'asa a gwiwa ba ta sanar da Uncle Taheer, shi kuma ya ce yana son ya d'an yi hak'uri don dole sai iyayenta sun san da maganar. Washegari ya sanar da Hajiyarsa, ita kuma tace lokaci yayi da ya kamata Hafsat ta koma gida don iyayenta su san inda ta ke, in yaso sai ayi maganar auren. Dole Aliyu ya yi hak'uri har zuwa k'arshen semister. Sun gama jarrabawa lafiya, sai shirye-shiryen tafiya ta ke, kuma Unxle yace dole ta je da Saleem domin kowa ya ganshi, don kallo d'aya zakai masa in dai kana da hankali zaka san cewa Abubakar ne mahaifinsa, don babu ta inda yaron ya barshi. Kamar yadda suka tsara ranar Asabar da misalin k'arfe takwas na safe Hafsat ta fito cikin shirin tafiya, shima Saleem an shirya shi sai Safiyya y'ar Aunty Salma, itama da ita za'ayi tafiyar. Driver ne ya tuk'o su, sai da suka tsaya Kano suka bawa Hajiya sak'o, sai da akai Sallar azahar sannan suja nufi Sumaila. Tunda suka shiga Sumaila Hafsat take masa kwatance har suka shiga Rumo, sannu-sannu har suka isa k'ofar gidansu, anan driver ya sami wuri ya yi parking. Cikin nutsuwa dukkansu suka fito, hannunta d'auke da jakarta, Safiyya na rik'e da hannun Saleem suka shiga gidan. Kusan duka matan gidan suna zaune a gidin babbar bishiyar Dirimin da ke gidan saboda zafin da ake yi a lokacin, kowacce tana sabgar gabanta. Sallamar ta ce ta jawo hankulansu gare su, gaba d'aya sai aka kama kallon-kallo, kowacce zuciyarta cike da manakin Ganin Hafsin da har anyi nenanta an gaji. Fuskarta d'auke da murmushi ta k'arasa, tana gaida su, sannan ta wuce zuwa 6angaren Goggo su Saleem na biye da ita. A lokacin in da za'a tona zuciyar Inna Mero abin Kare ba ya ci ba, don wani bak'in ciki taji ya kama ta ganin yanayin cigaban da ta samu. Cikin farin ciki Goggo ta tare su bakinta ya k'i rufuwa, idonta akan Saleem, kallo d'aya ta yiwa yaron wani farin ciki ya kama ta, don tasan yanzu ne kowa zai fahmci cewa Abubakar ya yiwa Hafsi abinda yayi ne don ya ci zarafinta. Cikin d'an k'ank'anin lokaci labarin zuwan Hafsi ya cika gari, yara sai zuwa kallonta suke. Tuni labari ya kai kunnen mahaifinta, ya kuwa nufo gida a fusace, yana shigowa tun kafin ya k'arasa kewayen Goggo ya fara kwala mata kira, yana shiga idonsa ya sauka akan Saleem, da ke zaune shi da Safiyya suna shan furar da Goggo ta dama musu, ita kuma Hafsat tana cikin d'aki tana Sallar la'asar. Ummu Aisha [7/1, 6:30 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 1⃣5⃣ Turus ya ja ya tsaya, ya kasa gaba ya kasa baya, kallon Saleem da ke shan furar sa yake hankali kwance, bai san ma ana kallonsa ba. Goggo da ke zaune cikin d'aki ta yi masa magana, sannan ya sami damar k'arasawa ciki. Kallo d'aya tayi masa ta san cewa har lokacin ransa a 6ace yake. Yana zaune ya kasa cewa komai har zuwa lokacin da Hafsat ta idar da Sallah ta yi addu'a, ta d'ago tana k'ok'arin gaida shi ya katse ta cewa "Sawunki a likkaga ki tashi ki koma inda kika fito, don bama buk'atarki a cikin gidan nan, yadda kika saka k'afa kika tafi a baya to muma a yanzu bamu da buk'atar……" "Ba sai kayi haka ba zan san cewa kai ka haifi Hafsi, har yau ban manta ranar da uwarta ta haife ta ba a cikin gidan nan." Cikin sanyin murya yace "me ya kawo wannan maganar kuma Goggo?" "Babu Sani, ka yanke duk hukuncin da ka ga ya dace da y'arka babu mai hana ka." Ganin ran Goggo ya fara 6aci yasa ya fita cikin takaicin yadda Goggon ta hanashi d'aukar mataki akan Hafsat d'in. Washe gari Goggo ta tara duk y'ay'anta mata da maza, don har Goggo Binta ta zo don tun dare Goggo tasa akai mata waya, cewa ta zo tana son ganinta, bayan duk sun hallara, Goggo ta fara magana da cewa "Dukkaninku nan na tara ku ne anan akan maganar Hafsi, kowa yasan abinda ya faru da ita babu mai buk'atar k'arin bayani, sai dai babban abinda baku sani ba shine, barin Hafsi garin nan ya faru ne bisa umarni na. Ni ce nan na 6oye ta saboda ku gane kuskurenku na yadda kuka tsangwami yarinyar nan , duk da baku da tabbacin abinda kuke zargi, tun da duk cikinku babu wanda ya tsaurara bincike akan gaskiyar al'amarin. Kun riga kun san irin tarbiyyar da ta tashi da ita, zai yi wahala ta aikaya irin abinda ake zarginta da shi, amma sai kuka gogawa idanuwanku toka, duk kuka juya mata baya. Ganin hakan ya tashi hankalinta har ra kai ga matsayin da ko barci bata samu, tsoron kar wani abu ya same ta sai na yanke shawarar raba ta da gidan baki d'aya…… Nan ta kwashe komai da ya faru ta sanar musu, kuma Alhamdulillah, duk sun gamsu da bayananta, sai ta kira Saleem ta nuna musu a matsayin yaron da Hafsi ta ta haifa bayan barin gida. Kowa yayi farin cikin ganin yaron, kuma nan take babu tantama sun amince d'an Abubakar ne, amma sai Goggo tace bata amince kowa yayi masa maganar Hafsi ko Saleem ba, a rabu da shi akwai lokacin da zai kawo kansa da kansa. Bayan sun gama da wannan maganar ne kuma ta sanar musu da zancen Aliyu da jiya da daddare Uncle ya sanar mata, lokacin da Hafsat ta had'asu a waya don yi masa godiya kan irin kulawar da suka bawa Hafsin ta,kuma kowa yayi farin ciki da wannan batu. Bayan gama tattaunawar ne mazan kowa ya kama gabansa, itma Hafsat taci gaba da harkokinta a cikin gidan ba tare da fargabar komai ba. Washegari tun da hantsi ta shirya ta tafi gidan Sadiya, don gaskiya ba k'arya tayi kewar ta sosai. Ba k'aramar murna Sadiya tayi ba, ai kuwa yini sukayi suna hira, kamar ba gobe. A cikin hirar ne ta ke bata labarin Yaya Abubakar, lokacin da ya dawo gida ya ji labarin 6atanta sai da yayi kamar zai ya hauka, kuka sosai ya ke da idanunsa kamar mace, wannan ne ya fara sakawa,mutane zargin anya abinda ya faru babu lauje a cikin nad'i? Har wata rama ya yi, gaba d'aya an rasa kansa, a lokacin ne takardar shaidar d'aukarsa aiki ta fito daga bankin da ya yi service, saboda yabawa da suka yi da k'wazonsa, da rik'on amana. Bayan fara aikinsa Innarsu ta dage sai ya yi aure, amma sai da ya shekara baiyi ba sai daga baya ya auri wata k'anwar abokinsa mai shegen girman kan tsiya, don da ta zo su Inna ana ta d'igimi suruka ta zo, amma ko ruwan gidannan k'in sha ta yi, sai wani yatsina take i kyakkyawa a gidan biki. Ummu Aisha [7/1, 6:30 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 1⃣6⃣ Murmushi kawai Hafsat ta yi don bata da abin cewa, a gidan ta yini har aka yi sallar magriba, sannan ta tafi gida. Tun daga nesa ta hango mota tsaye a k'ofar gidansu, amma bata kawo komai ba, ta ci gaba da tafiyarta, ta shiga zaure ne sukai kici6us da Abubakar da ke k'ok'arin fitowa daga cikin gidan, wanda ya zo tun la'asar, sakamakon kiran da Rabi'u k'aninsa yai masa a waya ya sanar da shi zuwan hafsat d'in, shine fa ya taho gida afujajan. Idanunsa na sauka a kanta ya tsaya cak, ya kasa gaba ya kasa, baya, tana ganin haka ta had'e girar sama da ta k'asa ta zagaye shi ta wuce, har ta shiga cikin gidan ta juya bata ga Saleem da Safiyya da ke biye da ita ba, sai ta juya. Ta same su a zauren yana rik'e da hannun Saleem,ya tsugunna ya zubawa yaron idanu, ko magana ba tayi ba ta sa hannu ta janyo yaron suka wuce ciki, Safiyya na biye da su. Gaba d'aya sai ya ji jikinsa ya yi sanyi, tabbas kallo d'aya da ya yiwa yaron ya ji ya shiga zuciyarsa, kuma tabbas zai kar6i abinsa, don bai ji a zuciyarsa cewa zai iya hak'ura da shi ba. Ita kam Hafsat ya kar6i k'addararsa ta rabuwa da ita, tun da ya san babu yadda za'ayi ta koma hannunsa bayan, saki ukun da ya yi mata, amma ko ba komai Saleem zai d'ebe masa kewar mahaifiyarsa, to amma inda Gizo ya ke sak'a shine ta yaya zai iya tunkarar iyayensu da maganar cewa Saleem d'ansa ne alhali da bakinsa ya tabbatar mu su da cewa babu wani abu na auratayya da ya ta6a shiga tsakaninsa da Hafsat. Tuna hakan da ya yi sai jikinsa yai sanyi, a haka ya fice daga zauren. Da daddare da ya shiga cikin gidan ya so ya shiga 6angaren Goggo ko don ya k'ara ganin Hafsat da d'ansa amma sam Innarsu ta kasa ta tsare ta hanashi, don ba ta son dalilin da zai had'a su da Hafsi, tunda ta fahimci har yanzu zuciyarsa na matuk'ar begen ta. Ita kuwa Hafsat suna shiga gida ta ci gaba da harkokinta, ta ma manta da batun wani Abubakar. Kwananta hud'u a garin Iyayen Aliyu suka zo don neman aure, kuma cikin ikon Allah basu tafi ba sai da aka sanya ranar biki sati uku masu zuwa. Satin ta biyu ta koma Zari'a d'auke da tsaraba sosai. Ai kuwa tana zuwa Aunty ta sa aka fara yi mata gyaran jiki, gefe d'aya kuma ana ta sayayyar abinda ya dace. A tsakanin ne kuma Baffa Halliru ya aiko da kud'i masu yawa a matsayin gudunmawarsu, amma Uncle yace ba zai kar6a ba, ai ko bai rik'e Hafsat ba shi mai yi mata kayan d'aki ne, shi kuma baffa Halliru ya dage, ai gudunmawa ce, da kyar ya kar6a. Ummu Aisha [7/1, 6:31 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 1⃣7⃣ Shirin biki ake sosai daga kowanne 6angare kamar bikin budurwa. Tun ranar laraba su Hafsat suka dira a Rumoh, gabaki d'ayansu, iya Uncle kawsuka bari, a Zari'a, shi sai ranar Juma'a zai zo Kano, ranar Asabar kuma sai yaje d'aurin auren. Komai da suka san zasu buk'ata game da sha'anin bikin Aunty ta taho da shi, hatta kayan abinci sun taho da shi. Ganin irin shirin da ake ba k'aramin k'ona ran Inna Kulu yayi ba, zuciyarta kamar ta fashe don bak'in ciki, da ta san haka Hafsi zata sami d'aukaka da ba ta sa Baffa k'arami ya sake ta ba. Ranar Alhamis akai walima, Juma'a akai yini, kuma Alhamdulillahi yanin ya tara jama'a sosai. Da daddare bayan kowa ya watse sai iya bak'i masu kwana, Inna Kulu ta sami Baffa Halliru har d'akinsa a kan maganar Saleem. Bayan ta sami guri ta zauna ne tace "Malam da magana na zo." Ya d'aga kai yana kallonta sannan yace "ina sauraronki." "Dama akan maganar yaron nan ne d'an wajen Hafsi, sai nake ganin me zai hana mu kar6e shi, tun da kaga aure za ta yi, kuma bai kamata ace ta tafi da shi gidan wani da sunan agolanci ba, tun da mahaifinsa ba gazawa zai yi da kula da shi ba." Ba tare da dube ta ba yace "Au kin san mahainfin nasa kenan." "Wannan wace irin magana ce? Ai ko makaho ya shafa fuskar yaron nan ya san d'an gidan Baffa k'arami ne." Cikin yanayin da ke nuna tsantsar takaici ya ce "Shi Baffa k'aramin ne ya turo ki gurina da wannan maganar?" Tace "A'a nice dai naga dacewar hakan." Girgiza kansa ya yi sannan yace "ki fita daga idona na rufe Kulu, idan haka ba kuma ranki zai 6aci, ji nake a gidan sai da kika hana Saratu fitowa waje? Ke kenan kiran y'arta ta kwaso abin kunya za ta lik'awa d'anki, yaron da kike kira da shege marar asali ne yanzu kuma ya zama jikanki?" "To banda abinka Malam mene ne na tayar da maganar da ta wuce? Yaron nan dai mutum ko ba'a fad'a ba ya ganshi yasan na Baffa k'arami ne." "Tashi ki fita daga d'akin nan Kulu tan raina bai gama 6aci da ke ba, idan ba haka ba kuwa ranki in yayi dubu sai ya 6aci." Ummu Aisha [7/1, 6:31 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 ★Assalamu alaikum Bayan dogon lokaci da aka dauka ba ba tare da kun Jini ba, sakamakon matsalar waya da na samu, Alhamdulillahi a yau Allah ya nufe ni da ci gaba da rubutawa. Jinjina ga ZAMAN AMANA WRITER'S 1⃣8⃣ Jiki a sanyaye ta fice daga dakin zuciyarta cike da bakin cikin rashin nasarar da bata samu ba. Washegari Asabar aka daura auren Hafsat da Aliyu, Wanda d'umbin jama'a Suka shaida. Bayan watsewar 'yan daurin aure masu zuwa rakiyar Amarya suka shirya suka dauki hanya. Sun isa garin Kaduna lafiya, Kai tsaye gidan iyayen Aliyu aka wuce da su, Kuma Alhamdulillahi sun Sami taro na mutunci, sai da kowacce ta ci ta k'oshi, su Kai sallah, Suka huta, sannan aka ce su fito a Kai su gidan amarya su gani. Duk wanda ya ga gidan nan sai ya yaba don ba k'aramin tsaruwa ya yi ba, da gani ba kananan kudi aka kashewa gidan ba, Uncle Tahir da Aunty Salma ba karamin kokari su Kai ba. Masu kaunar Hafsat na ta taya ta murna, masu hassada kuwa zuciyar nan bakikkirin, bayan sun gama gani aka kwashe su zuwa masaukin su. 'Karfe takwas saura aka fara kwasar mutane zuwa wurin dinner da aka shirya a kayataccen hotel, Amarya da Ango sunyi shiga ta alfarma, kowa ya gansu sai sun birge shi. Anci ansha masu guzuri sun yi, zan so kuga mutanen Rumoh a wurin nan sun zuba kauyanci son ransu. Daga wurin dinner kai tsaye aka zarce da amarya gidanta mutanen Rumoh kuma aka mai da su masaukin. Washegari da misalin goma na safe duk 'yan rakiya sun gama shiryawa, bayan kowacce ta karya akace su fito za'a kai su gidan amarya suyi sallama daga Nan a mai da su gida. Kwanakin ta biyar a gidan ya ce ta shirya zai Kai ta ta gaida Hajiyarsa. Ta shirya cikin shiga ta Kamala suka tafi. Ranar Hafsat taga tarairaya kamar Hajiya zata mai da ita cikin don so. Komai ta dauko ta ce na Hafsat ne Afnan sai tsokanar Hafsat ta ke, wai ta kar6e mata fada, it's Kuma Hafsat ta kasa sakewa. Sai dare suka koma gida zuciyar Hafsat cike da farin cikin irin tar6ar da ta samu daga surukarta. Ummu Aisha [7/1, 6:32 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 1⃣9⃣ Zama suke na soyayya da girmama juna, cikin sati biyu sun yi wata irin sha'kuwa, kowanne a cikinsu bai son abinda zai sa ya yi nesa da d'an uwansa. Bayan bikinsu da sati biyu ya koma baking aikinsa, ita kuma ta koma makaranta, Kuma Alhamdulillahi yana ba ta gudunmawa sosai akan karatun ta. Cikin wani weekend suka shirya tafiya Rumoh don ya je ya gaida iyayenta, tare da Afnan aka shirya tafiyar. Da wuri suka d'auki hanya, Aliyu ne ke jan motar Hafsat na zaune a gefensa, sai Afnan da ke zaune ita d'aya a baya. Misalin sha biyu saura kwata su ka shiga garin Rumoh, Hafsat na ta nuna masa hanya har suka isa 'kofar gidan, ya sami wuri ya yi parking. Lokaci d'aya su ka fito daga cikin motar, Hafsat da Afnan suka shiga gidan bakinsu d'auke da sallama. Duk wanda ke gidan ya yi murna da ganin Hafsat, don duk wanda ya kalle ta ya san ta sami kwanciyar hankali da ci gaba a rayuwarta. Goggo don murna kamar ta goya Hafsin ta, ranar Uncle Taheer da Aunty Salma sun sha albarka, don sune tsani ga duk wani ci gaba da Hafsat ta samu a rayuwarta. Inna Kulu kamar ta fashe don ba'kin cikin, don duk 'ya'yan ta mata babu wadda ta kama 'kafar Hafsat. Har cikin gida Goggo ta sa aka shiga da shi, bayan ya ci abinci ya kora da fura nono ya 'koshi, sannan ya bi ya gaida duk matan gidan cikin girmamawa, kuma kowanne waje ya shiga sai ya bi su da alkhairi, kowa sai sam barka yake. 'Karfe uku na yamma suka fito da shirin tafiya, Hafsat kamar kar ta bi su, amma ba yadda za ta yi dole ta bi su ko don karatun. Sai dare suka koma gida duk sun gaji kamar anyi musu duka . Kwanansu biyu da dawo wa daga Rumoh wani abokin Aliyu mai suna Isma'il ya kawo musu ziyara, don lokacin da akai bikin baya 'kasar ya yi tafiya. Sun gaisa da Hafsat cikin mutunci da garmamawa, lokacin da ya so tafiya ya yi mata kyauta ta girma, Hafsat sai mamaki ta ke, amma sai Aliyu ya nuna mata wannan ba komai bane daga halin Isma'il d'in. Ummu Aisha [7/1, 6:33 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 🤦‍♀🙆ILLAR RI'KO* ('yar RI'KO) Na Aisha Isah (Mummy's Friend) Congratulations, ina taya ki murnar kammala novel d'inki Mai ilmantarwa, Allah ya sa mu amfana da darrusan da suke cikin sa, kura-kuran da su ke ciki Kuma Allah ya yafe. Sai mun ji ki a sabon novel. 2⃣0⃣ A kwana a tashi babu wuya, yau gashi har an yi wata hud'u da auren Hafsat, kuma Alhamdulillah, Suna zaune lafiya, babu wata matsala a tsakaninsu. ★ ★ ★ ★ Shi kuwa Abubakar tun bayan da ya saki Hafsat ya koma sai ya rasa kwanciyar hankali, damuwa ta yi masa yawa, kullum Yana cikin tunani da ba'kin cikin rabuwa da abu mafi soyuwa a gare shi. Haka ya ci gaba da rayuwa cikin 'kunci da damuwa har zuwa lokacin da su ka kammala service d'insu. Ba 'karamin tashin hankali ya shiga ba lokacin da ya dawo gida ya sami labarin 6acewar Hafsat. Sai da kowa na gidan ya fahimci akwai abinda ya ke damunsa, ya rame sosai, yayi ba'ki. Da haka ya had'a takardunsa ya fara fafutukar neman aiki, cikin hukuncin ubangiji ya sami aiki a Zenith bank. Cikin watanni uku da samun aikinsa hankalinsa ya fara kwanciya, duk da cewa har lokacin akwai damuwar 6atan Hafsat a 'kasan ransa, musamman idan ya tuna cewa shine sanadi. Cikin wanna lokacin ne kuma, iyayensu suka fara matsa masa da maganar aure. Da farko hankalinsa ya tashi da maganar, amma lokacin da ya sami wani abokinsa mai suna Ahmad da maganar nan take ya share masa hawayensa ta hanyar bashi 'kanwarsa mai suna Zainab. Duk da zuciyarsa bata yi na'am da ita ba haka ya amince, Don ba zai iya watsawa Ahmad 'kasa a ido ba. Ahmad abokinsa ne da sukai karatu tare a BUK, akwai sha'kuwa sosai a tsakaninsu. Tun farkon samun aikin Abubakar ya je har gida don gaida mahaifiyar Ahmad, don tuni dama ta san shi, tun suna makaranta wani lokacin suna zuwa gidan, to fa anan Zainab ta gan shi ta haukace akan son sa, shi kuma Ahmad yace bazai fad'a masa ba, don shi ba yaron aiken ta ba ne. Har lokacin ba ta daina damun sa da maganar ba, sai kuma katsam Abubakar d'in ya same shi da maganar an matsa masa da maganar aure a gida, shi kuma har yanzu bai sami yarinyar da ya ke so ba, to fa shine ya gwada sa'arsa don ganin ko zai iya samawa 'kanwarsa farin cikinta. Cikin sa'a sai Allah ya sa ya amince, cikin lokaci kad'an Suka daidaita kansu har iyaye suka shiga maganar. Cikin watanni shida da akai komai aka gama, ta tare a gidansa da ke Zoo road. Lokacin da ake zancen bikin Inna Kulu sai rawar Kai ake, ita dole d'anta zai auri macen da ta dace da shi, kuma 'yar birni. Biki akai sosai, amma tun kafin 'yan biki su dawo gida aka fara samun matsala, don Zainab irin mutanen nan ce da basa son 'yan 'kauye. Don da suka je yi musu sallama sama-sama ta kar6e su babu wata fara'a a fuskar ta, haka suka gaji da zaman kurame, su kai mata sallama suka tafi. Ummu Aisha [7/1, 6:33 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 SADAUKARWA GA RAHEENAT M. ABUBAKAR (My Heenat) 2⃣1⃣ Lokacin da suka koma gida, kowa sai fad'ar albarkacin bakinsa yake game da amaryar ta Abubakar, da irin kar6ar da ta yi musu Suna zaune babu wata matsala a tsakaninsu in ban da ta 'kin danginsa da suka kasance 'yan 'kauye, sai dai abin da bai sani ba tana family planning a 6oye saboda tana ganin cewa idan ta haihu a wannan lokacin za ta iya samun matsala da karatun ta, wanda ita kuma ba ta fatan hakan. Duk da zaman lafiyar da ke tsakanin sa da matar sa amma hakan bai sa ya dena tunanin Hafsat ba. Kuma a kullum babban burinsa bai wuce ace ga Hafsat ta bayyana ba. Lokacin da Raba'u 'kaninsa ya yi masa waya ya sanar masa da bayyanar Hafsat, ba 'karamin farin ciki ya yi ba, domin ko ba komai a yanzu ya san iyeyenta za su sami kwanciyar hankali, musamman lokacin da ya ganta, kuma ya ji a inda ta ke, sai hankalinsa ya 'kara kwanciyar. ★ ★ ★ ★ Tun bayan zuwan Isma'il na farko gidan ya sami gurin zuwa, ya na yawan kai musu ziyara, sai dai haka kawai Hafsat ta ji bai kwanta mata a zuciya ba, duk da irin amintar da ke tsakaninsa da mijin ta kuwa. Lokacin da aka sami hutun session ne Hafsat ta shirya tafiya Rumoh da nufin yin kwanaki don ta gaggaisa da dangin ta. Driver'n Hajiyansu aliyu ne zai kai ta, sai d'okin tafiyar ta ke. Lokacin da Isma'il ya ji zan cen tafiyar, shima sai da ya bata kud'i masu kauri don ta sayi tsaraba. Hafsat ta so ta 'ki kar6ar kud'in amma sai Aliyu ya ce ta kar6a, haka dai ta kar6a ba don zuciyarta na son kar6ar ba. Ranar asabar aka sa za'ai tafiyar, cikin hukuncin Allah kuma sai tafiyar ba ta yiwu ba sakamakon zazza6in da driver'n ya tashi da shi a ranar dole aka d'aga tafiyar sai washegarin ranar. Da daddare bayan sun gama komai sun kwanta, suka dinga hira, har Aliyu ke tambayar Hafsat yake cewa "ni kuwa Hafsat me yasa idan Isma'il ya yi miki kyauta bakya son kar6a?" Hafsat ta amsa mai da cewa "ni fa ba 'kin kar6a na yi ba, kawai dai ba ba son na d'ora masa d'awainiya ne, alhalin kuma kai baka gaza min da komai ba". "Kar ki ce min haka Hafsat, ba tun yanzu ba na gane cewa duk lokacin da Isma'il ya zo gidan nan kamar yanayin ki yana sauyawa, ko zan san mene ne dalili?" Cakin sassanyar muryar ta tace "a gaskiya idan nace maka ga dalili 'karya nake, amma duk lokacin da na gan shi sai na ji hankali na bai kwanta da shi ba, amma don Allah idan maganata ta 6ata maka rai ka yi ha'kuri". "Ba'ki 6ata min rai ba Hafsat, sai dai ina so na sanar dake cewa Isma'il mutumin kirki ne, tun da na ke tare da shi tun a secondary ban ta6a ganin wani abu na ashsha a tare da shi ba, don haka ki kwantar da hankalinki, ba zai cutar da mu ba". Murmushi Hafsat ta Yi ta ce "insha Allahu zan kiyaye". Ya ce "haka nake so". Sun dad'e suna hira a lokacin kafin suyi addu'ar bacci. Misalin karfe biyu na dare suna tsaka da bacci Aliyu ya farka, ya dinga jiyo motsin mutune daga can harabar gidan , cikin sauri ya tashi Hafsat da ke ta sharar baccinta. Tana farkawa ya ce mata "Hafsat 6arayi sun shigo gidan nan, tashi maza ki 6uya, ba zan so wani abu ya same ki ba, gara duk abinda zai faru ya faru a kai na ni kad'ai". "A'a Aliyu ba zan iya bari su yi maka wani abu ba,don Allah ka barni, duk abinda za su yi su yi mana tare". Ba tare da Aliyu ya saurare ta ba ya nufi wardrobe d'insa ya bud'e ya na cewa "ba mu da lokacin jayayya Hafsat, zo ki shiga cikin nan kuma na ro'ke ki duk abin da zai faru Kar ki you motsin da zai nuna alamar akwai mutum a cikin d'akin nan bayan ni". Ba ta 'kara yi masa jayayya ba ta shige cikin wardrobe d'in, cikin sauri ya tura 'kofar ba tare da ya murd'a key ba, ya koma saman gadonsa ya kwanta ya ja bargo ya rufa, daidai lokacin da aka turo ,'kofar d'akin aka shigo. Ummu Aisha [7/1, 6:34 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 2⃣2⃣ Duk da tashin hankalin da ya ke ciki a lokacin hakan bai sa ya motsa ko ya tashi daga inda ya ke a kwance ba, har suka 'karaso bakin gadon suka zagaye shi. 'Daya daga cikinsu ne ya sa hannu ya d'aka masa duka, cikin sauri ya tashi zaune ya na kallon su. Su biyar ne, dukkansu sanye da ba'ka'ken kaya, fuskar su sanye da mask. Ganin babu yadda za'ayi ya iya gane ko mutum d'aya daga cikinsu, ya sa shi yin 'karfin halin ce musu "su waye ku? Me kuke nema a gidan nan da za ku shigo a irin wannan lokacin?" 'Daya daga cikinsu ya amsa masa da cewa "au tambayarmu ma ka ke? To rayiwar ka muka zo nema, ba wani abu ba." Cikin 'karfin hali ya ce "idan kud'i ku ke so ku fad'i ko nawa ku ke so zan baku amma don Allah kar ku kashe ni. Gaba d'ayan su dariya su ka sanya sannan wanda ya yi magana da farko yace "ba neman kud'i ne ya kawo mu ba kamar yadda ka ji na ce, mu rayuwarka kawai muka zo nema, don haka bama bu'katar kud'in ka abinda muka zo yi kawai shi muka zo aiwatarwa". Kafin ya ce wani abu d'aya daga cikin 'yan ta'addar ya soka masa wu'ka a gefen cikinsa. Wani zazzafan ciwo ya ratsa shi, cikin 'karfin hali ya dinga furta innalillahi wa Inna ilaihir raji'un, hannunsa na da fe da gurin. Bai ankara ba ya sake jin wani sukan, Hafsat da ke 6oye a cikin wardrobe ta sa hannu ta toshe ba'kin ta idan banda rawa babu abinda jikin ta yake. 'Daya ne daga cikin mutanen ya tashi, ya je gaban Aliyu dake dafe da wuraren da aka soka masa wu'ka, ya tsaya, sai da ya 'karewa Aliyu kallo sannan ya cire mask d'in da ya rufe fuskarsa cikin al'ajabi Aliyu ya dinga kallonsa. Bakin sa yana rawa da kyar ya iya furta "Isma'il!" Cikin dakakkiyar murya ya furta "kayi mamaki ko? To ka kwantar da hankalinka, yau zan sanar da kai abinda baka sani ba, shin ko kana da masaniyar ni ne na kashe Hafsat tsohuwar budurwar da za ka aura? Tun lokacin da idanuwa na suka fara ganin ta sai na ji nan duniya babu wata 'ya mace da na ke so sama da ita, a lokacin da na sanar da ita maimakon ta kar6i tayin soyayya ta sai ta watsa min 'kasa a ido. Da farko na yi tunanin na ha'kura, amma daga baya sai naga zuciya ta ba zata iya jure ganin Hafsat da Kai a matsyin ma'aurata ba, wannan ne dalilin da ya sa naga dacewar na d'auki matakin hana faruwar hakan. Tun daga lokacin na shiga tunanin hanyar da ya kamata na bi don ganin na hana yiwuwar wannan auren, har zuwa lokacin da na sami mafita. Lokacin da Hafsat ta shigo hannuma, bayan na raba ta da abinda kowacce mace ke alfahari da shi, na yi tunanin rabuwa da ita, amma sai naga hakan zai iya zama tonon asiri a gare ni, don haka sai na gama da ita. A tunani na shikenan matsala ta 'kare, amma ranar da na zo gidan ka naga matarka Hafsat ta yanzu, daga nan tunani na ya sauya, don ina ji a jiki na bazan iya ha'kura da ita ba, don haka masalaha d'aya ita ce a kawar da kai daga doron duniyar gaba d'aya, hakan zai taimaka min wurin samun cikir buri na. Na yi amfani da wannan lokacin ne saboda na san kai d'aya ne a gidan ita Hafsat ta riga ta yi tafiya. Kaga daga baya sai in zagaya in auri Hafsat bayan ta gama yi maka takaba, don haka yanzu zamu gama da kai". Yana gama fad'ar haka ya bawa yaransa damar su yi abinda ya kawo su, Aliyu yana kallo 'kiri-'kiri suka dinga soka masa wu'ka a jikinsa, sai da suka ga ya daina 'kwa'k'kwaran motsi suka yar da shi a cikin jini suka fice. Ummu Aisha [7/1, 6:34 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 2⃣3⃣ Kimanin minti goma da fitar su Hafsat ta turo 'kofar wardrobe d'in da ta ke 6oye a ciki ta fito, jikin ta in banda rawa babu abinda ya ke, ba 'karamin tashi hankalin ta ya yi ba sakamakon yanayin da ta ga Aliyu a ciki, jikin ta na rawa ta d'auki wayarta ta kira Hajiya mahaifiyar Aliyu. Lokacin da Hajiya taga kiran da Hafsat ta ke mata, sai da gaban ta ya fad'i, don tasan haka kawai babu dalili ba za ta kira ta a irin wannan lokacin ba, cikin 'karfin hali ta d'aga, ko sallama ba ta sami damar yi ba Hafsat ta ce "ya mutu Hajiya, wallahi ya mutu". Cikin 'karfin hali Hajiya ta ce "waye ya mutu?" Hafsat na kuka ta ba ta amsa da cewa "Aliyu". Nan da nan Hajiya ta 'kara gigicewa, a lokacin ta fito ta taso Afnan, suka kira Hashim, d'an wani 'kanin Hajiyar ne da ke zaune a gidan, su ka tafi gidan Aliyun. Lokacin da su ka ga halin da Aliyu yake ciki ba 'karamin firgita su kai ba, don kwata-kwata ba ya cikin hayyacin sa. Cikin sauri su ka nufi asibiti da shi, ganin yanayin da aka kawo shi a ciki likitocin su ka ce sai an kira 'yan sanda kafin su ta6a shi. A lokacin Hashim ya je police station mafi kusa ya samo 'yan sanda, nan da nan likitoci suka rufu a kan sa, don ceto rayuwarsa. Gabad'ayan su suna cikin tashin hankali, duk sun rud'e sai kuka suke. Lokacin da 'yan sanda suka nemi sanin abinda ya same shi, Hajiya ta nuna Hafsat, ta na cewa "gata nan ita ce ta ke yun'kurin kashe shi". Ba Hafsat ba har Afnan sai da ta gigita da jin abinda Hajiya ta ce, ta ci gaba da cewa "ku kama ta ita ce ta ke son ta kashe min d'a na". Nan ta ke 'yan sanda suka kama Hafsat suka wuce police station da ita. ★ ★ ★ ★ Gari na wayewa labari ya fara yawo cewar Hafsat ta yi yun'kurin kashe mijin ta, labari har gidajen TV, nan da man abu ya yad'u kamar wutar daji. Lokacin da labarin yaje kunnen su Uncle ba 'karamin tashin hankali su ka shiga ba, ba su tsaya sauraron komai ba suka wuce Kaduna. Lokacin da aka je da Hafsat police station aka fara bincikar ta akan zargin da ake ma ta. Ta fad'i iya gaskiyar abinda ta sani, don haka 'yan sanda ba su yi 'kasa a gwiwa ba su ka bazama neman Isma'il,duk da cewa itama ba'a sake ta ba saboda case d'in yin'kurin kisan kai ba 'karami ba ne. Lokacin da Isma'il ya sami labarin cewar Aliyu yana gadon asibiti ba 'karamin tashin hankali ya shiga ba, don yasan tabbas Aliyu ya warke to shi kuma tasa ta 'kare. Bai 6ata lokaci ba ya bazama asibiti, don gane wa idonsa gaskiyar al'amari, daga nan ya d'auki duk matakin da ya kamata, don ganin ya kawar da rayuwar Aliyun. Lokacin da ya shiga asibitin bai sami ganin Aliyu ba saboda matakan tsaro da akasa mai, duk nacin sa haka ya ha'kura ya juya gida, zuciyar sa cike da mamakin abinda Hajiyar Aliyu ta gaya masa na cewa Hafsat ce ta yi yun'kurin kashe shi, bayan shi a iya saninsa Hafsat ba ta gari, kuma har suka shiga gidan suka gama abinda ya kai su ko alamar motsin mutum su ji ba bare su gan ta. A hanyarsa ta komawa gida kuma 'yan sanda su ka cafke shi. Ummu Aisha [7/1, 6:35 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 2⃣4⃣ Kwanankin Hafsat hu'du kenan a hannun 'yan sanda, a iya tsayin kwanakin nan babu irin 'ko'karin da Uncle bai yi ba don ganin an bashi belin hafsat, amma abin ya gagara. Sanda su ka je asibiti da nufin duba Aliyu kuwa 'kiri-'kiri Hajiya ta hana su ganin sa. Sai ma wani kallon tsana da ta ke musu, haka suka bar asibitin jiki a sanyaye. Ranar da Aliyu ya dawo hayyacinsa, ba 'karamin dad'i Hajiya ta ji ba, sai tarairayar sa ta ke kamar 'kwai. Cikin 'kan'kanin lokaci aka sanar da 'yan sanda, Kamar yadda su ka ba'kata, sun zo sun gudanar da binciken su ta hanyar yi masa tambayoyi, shi kuma ya na amsa musu. A nan 'yan sandan suka gaskata bayanan da Hafsat ta bayar na cewa Isma'il ne da yaransa suka aikata wannan ta'addancin. Tun lokacin da Aliyu ya farfad'o bai ga Hafsat a d'akin ba ya ke so ya tambaya, amma sai ya yi shiru. Bayan tafiyar 'yan sandan ne ya yi 'karfin halin tambayar hajiya ita. A take hajiya ta sauya fuska, ta ce "me zata yi maka? Yarinyar da ta ke neman rayuwar ka, ka dubi irin halin da ta jefa ka a ciki, ko kuwa neman ta ka ke ta zo ta 'karasa ka?" Cikin mamaki Aliyu ya dubi Hajiyar ya ce "wane irin neman rayuwa ta Kuma? Don Allah Hajiya kar ki 'kara magana makamanciyar wannan, Hafsat fa mata ta ce, ta Yaya za'ai ta cutar da ni irin haka?" "Mene ne nufin ka Aliyu, kana son nuna min cewa, duk wannan abinda Hafsat ta yi maka ba ka damu ba ko kuwa? To wallahi tun wuri ka fita daga zancen yarinyar nan tun kafin rai na ya 6aci." "Kiyi ha'kuri Hajiya, amma wallahi babu ruwan Hafsat a cikin abinda ya same ni, nasan cewa za ki yi mamaki idan ki ka ji cewa Isma'il ne ya yi min wannan aika-aikar." A tunanin sa Hafsat ta yi tafiya ba ta nan, don na gaya masa zancen tafiyar ta ta,har kud'i ya ba ta ya ce ta yi tsaraba, ashe duk yaudara ta ya ke, yana da abinda ya 'kulle a cikin zuciyar sa. Babu abinda ya fi ban mamaki da shi sai da ya sanar da ni cewa shine mutumin da ya kashe marigayiya Hafsat". Nan ya kwashe dukk abinda ya faru a ranar ya sanar da ita, Hajiya ta cika da mamakin abinda ya faru da kuma nadamar abinda ta yi wa Hafsat da iyayen ta. Ita kuwa Hafsat a ranar 'yan sanda su ka sallame ta bayan sun tabbatar da cewa ba ta aikata laifin da ake tuhumar ta da shi ba. Ummu Aisha [7/1, 6:35 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 Sa'kon gaisuwa ta a gare ku 'yan 2006 na G.G.A.S.S SUMAI LA dun inda kuke🙋 2⃣5⃣ Daga police station kai tsaye Hafsat motor park ta nufa, ta hau motar zuwa Zaria, ko kud'in mota bata da shi, sai wata baiwar Allah da suka zauna tare ce ta biya mata. Lokacin da ta isa gida, Aunty ke sanar mata sun yi sa6ani da Uncle, don shima ya tafi Kaduna zai gano ta, a take ta kira shi a waya ta sanar masa cewa ga Hafsat ta zo gida. Washegari ita da Aunty suka je Kaduna suka d'ebo kayan sawar ta, da wasu abubuwa na amfanin ta, suka juya gida. * * * * Satin Aliyu uku a gadon asibiti aka sallame shi, gaba d'aya hankalinsa a tashe ya ke, sakamakon rashin zuwan Hafsat gare shi da duk wani Wanda ya shafe ta, don hakan yana bashi tabbacin cewa ba 'karamin 6ata musu rai abinda ya faru yayi ba. Ranar da ya cika sati d'aya da sallamowa daga asibiti, ya shirya zuwa Zari'a, driver ne ya kai shi, don har lokacin jikinsa bai gama warwarewa ba, tafiyar ma don ya dage ne. Ya sami Uncle yana shirin fita, amma ganin sa sai ya dakatar da fitar. Bayan sun gaisa ya yi masa ya jiki ne kuma yai shiru yana sauraron abinda ke tafe da shi. Kai tsaye Aliyu ya ce wa Uncle "dama maganar Hafsat ne Uncle, na ji wasu abubuwa marasa dad'i da suka faru a lokacin da bani da lafiya, kuma nima tabbas ban ji dad'in hakan ba, amma don Allah Ina son ayi ha'kuri, duk abinda ya faru dama Allah ya 'kaddara sai hakan ya faru". Uncle ya dube shi ya ce " a zahirin gaskiya raina ya 6aci da irin abinda ya faru, yadda mahaifiyar ka ta rufe ido akan maganar nan ko ganin Hafsat ta yi da wu'ka tana sassara ka iyakacin abinda zatai kenan, ta tsaya ta saurare mu ayi magana ta fahimta ma abin ya gagara. Da muka je duba ka kuwa 'kiri-'kiri ta rufe ido ko ganin ka ma hana mu ta yi, sai haka muka ha'kura muka taho. Sannan da ace tayi tunani da Hafsat ce tayi yin'kurin kashe ka da ba zata kira a waya don a zo a kaika asibiti ba, bare har a ceto rayuwarka, a yanzu maganar da nake maka Hafsat ko makaranta zata je sai ta saka ni'kab, kuma kusan kullum idan ta je da damuwa take dawowa, akan abinda ya faru, don haka maganar gaskiya ka same ta ku daidaita idan ta amince zata koma gidan ka bani da matsala, iyakaci in bi ku da addu'ar fatan alkhairi, Amma ni dai kam bazan tilasta mata ba". Shi me ku ke ganin ya kamata? Hafsat ta ci gaba da zama da Aliyu ne ko kuwa? Ina jiran comments d'inku, kafin na ci gaba. Ummu Aisha [7/1, 6:36 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 HAPPY BIRTHDAY TO YOU🎂🎂🎂🎂🎂🎂 Hayat Baba Zubairu Admin of Admins, ina taya ka murnar zagayowar ranar haihuwarka Allah ya 'karo shekaru masu albarka 🎂🎂🎂🎂🎂🎂 🥦DUK KANWAR JA CE🥦 fans naji dad'i da ganin comments d'inku, kuma insha Allahu zan yi 'ko'karin ganin na ci gaba da wannan novel don yanzu ma aka fara😜. 2⃣6⃣ Lokacin da ya sami ganin hafsat, rufe ido tayi ta nuna sam ita bata da bu'katar cigaba da rayuwa da shi,saboda tozarcin da mahaifiyarsa ta yi mata, ankai ruwa rana sosai kafin ta amince ta koma gidansa. Allah cikin ikonsa,bata dad'e da komawa ba sai ta fara rashin lafiya, ana zuwa asibiti bayan bincike, likita ya tabbatar musu da cewa tana da shigar ciki. Wannan lokacin Hajiya kamar ta maida Hafsat ciki saboda tattali, kusan kullum tana hanyar gidan don duba ta. Shi kuwa oga kwat-kwata wato Aliyu ba'a maganarsa, don numfashi ma idan da hali yi mata zai yi. * * * * Hafsat na cigaba da rainon cikinta, wanda zuwa yanzu yayi girmama sosai don kowane lokaci zata iya haihuwa. Duk wani abu da maijego da jariri zasuyi amfanin da shi Aliyu ya tanade shi haihuwa kawai ake jira. Ranar wata alhamis tun safe Hafsat ta fara jin alamomin ciwon naq'kuda amma ta daure bata gayawa Aliyu ba, sai wajen 'karfe uku na yamma ta ji abin ya zama serious, sai ta yiwa Hajiyansu Aliyu waya ta sanar da ita halin da take ciki, to kuma cikin hukuncin Ubangiji kafin Hajiyar ta 'karaso gidan anyi haihuwar, ta haifi yaron ta namiji 'katoto da shi, ganin ban sha'awa. Fad'ar irin murnar da Aliyu da 'yan uwansa suka muna ma 6ata baki ne, Hafsat da jariri ta sun ga kulawa da tattali sosai. Ummu Aisha [7/1, 6:37 AM] Wasila Z . A . W: 💃🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 Shafin yau kyauta ne a gareku, kuyi yadda kuke so da shi Maman Noor Maman Sapi da Amal Naga comments d'inku, kuma nagode Allah ya bar 'kauna. 2⃣7⃣ Ranar suna yaro yaci sunan Muhammad. Ba 'karamin shagali akai na sunan ba, anci an sha, masu guzuri sun yi, DUK KANWAR JA CE Fans ma sun halarci taron sunan, don can na hango su o'o ana tsice naman kan abinci, uhm bari dai nayi shiru 🤭 ba sai na ja suna ba 😜. Mutanen Rumoh ma da yawa sun halarci taron sunan, don mota guda suka ciko. Taron suna ya watse kowa ya koma gidansa lafiya,sai fatan Allah ya raya Muhammad. Sun ci gaba da kula da jaririnsu cikin gata da kulawa, yaron sai 'kara girma yake kamar kazar agric. A wannan tsakanin ne aka yankewa Ismail hukuncin kisa, bayan tsahon lokaci da aka d'auka ana shari'arsa, bayan kotu ta tabbatar da cewa yana da ruwa da tsaki akan kashe marigayiya Hafsat kamar yadda yayi i'kirari, da bakinsa. Bayan kammaluwar shari'ar ne da kwana biyu Aliyu yasa hafsat ta shirya, don su je har gida su gaisa da mahaifiyar Hafsat d'in. Kar6a sosai ta girmamawa akai musu, matar mai kirki kamar ta goya Hafsat, lokacin da ta d'auki Muhammad kuwa sai da ta zubar da hawaye, zuciyar ta na raya mata cewa da yanzu yaron nan d'an Hafsat d'inta ne. Aliyu ya dinga bata ha'kuri, don yasan ta tuna da 'yarta ne wadda da yanzu ita ce zata kasance mahaifiyar yaron. Suna nan zaune suka ji tsaiwar mota a harabar gidan, ba'a d'auki dogon lokaci ba, suka jiyo 'karar takun takalmi 'kwas-'kwas, alamun cewa za'a shigo. Wata kyakkawar budurwa ce ta shigo, jikinta sanye da riga da skirt 'yan kanti, kayan sun bayyana duk wata sura ta jikinta, sai wani 'karamin mayafi da tayi rolling dashi, hannunta ri'ke da jaka kalar takalmim 'kafarta. Kallon mamaki ta ke yiwa Aliyu, sai kuma ta saki wani lallausan marmushi, daidai lokacin da take 'ko'karin zama a kujerar da ke kusa da wadda yake zaune akai. "Dama ana ganinka Yaya Aliyu?" Ta jefo masa tambayar ba tare da ta gaida shi ba. Cikin murmushin 'karfin hali yace "gani kuwa kina gani na Fareeda, yaushe kika dawo 'kasar ne?" 'Yau sati na d'aya kenan da dawowa, mun same ku lafiya?" "Lafiya 'kalau" ya bata amsa, ya karatun? Ya sake tambayarta. "Alhamdulillah" ta bashi amsa a ta'kai ce, tana mi'kewa tsaye. "Allah ya taimaka." "Ameen." Ta amsa tana tafiya, tana cewa "bari na watsa ruwa na fito." Ta shige wani d'an corridor, ko kallon inda Hafsat take batayi ba, bare tasa ran zatayi mata magana, har ta kai su ga gaisawa. Ummu Aisha [7/1, 6:38 AM] Wasila Z . A . W: 💃🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 Shafin yau kyauta ne a gareku, kuyi yadda kuke so da shi Maman Noor Maman Sapi da Amal Naga comments d'inku, kuma nagode Allah ya bar 'kauna. 2⃣7⃣ Ranar suna yaro yaci sunan Muhammad. Ba 'karamin shagali akai na sunan ba, anci an sha, masu guzuri sun yi, DUK KANWAR JA CE Fans ma sun halarci taron sunan, don can na hango su o'o ana tsice naman kan abinci, uhm bari dai nayi shiru 🤭 ba sai na ja suna ba 😜. Mutanen Rumoh ma da yawa sun halarci taron sunan, don mota guda suka ciko. Taron suna ya watse kowa ya koma gidansa lafiya,sai fatan Allah ya raya Muhammad. Sun ci gaba da kula da jaririnsu cikin gata da kulawa, yaron sai 'kara girma yake kamar kazar agric. A wannan tsakanin ne aka yankewa Ismail hukuncin kisa, bayan tsahon lokaci da aka d'auka ana shari'arsa, bayan kotu ta tabbatar da cewa yana da ruwa da tsaki akan kashe marigayiya Hafsat kamar yadda yayi i'kirari, da bakinsa. Bayan kammaluwar shari'ar ne da kwana biyu Aliyu yasa hafsat ta shirya, don su je har gida su gaisa da mahaifiyar Hafsat d'in. Kar6a sosai ta girmamawa akai musu, matar mai kirki kamar ta goya Hafsat, lokacin da ta d'auki Muhammad kuwa sai da ta zubar da hawaye, zuciyar ta na raya mata cewa da yanzu yaron nan d'an Hafsat d'inta ne. Aliyu ya dinga bata ha'kuri, don yasan ta tuna da 'yarta ne wadda da yanzu ita ce zata kasance mahaifiyar yaron. Suna nan zaune suka ji tsaiwar mota a harabar gidan, ba'a d'auki dogon lokaci ba, suka jiyo 'karar takun takalmi 'kwas-'kwas, alamun cewa za'a shigo. Wata kyakkawar budurwa ce ta shigo, jikinta sanye da riga da skirt 'yan kanti, kayan sun bayyana duk wata sura ta jikinta, sai wani 'karamin mayafi da tayi rolling dashi, hannunta ri'ke da jaka kalar takalmim 'kafarta. Kallon mamaki ta ke yiwa Aliyu, sai kuma ta saki wani lallausan marmushi, daidai lokacin da take 'ko'karin zama a kujerar da ke kusa da wadda yake zaune akai. "Dama ana ganinka Yaya Aliyu?" Ta jefo masa tambayar ba tare da ta gaida shi ba. Cikin murmushin 'karfin hali yace "gani kuwa kina gani na Fareeda, yaushe kika dawo 'kasar ne?" 'Yau sati na d'aya kenan da dawowa, mun same ku lafiya?" "Lafiya 'kalau" ya bata amsa, ya karatun? Ya sake tambayarta. "Alhamdulillah" ta bashi amsa a ta'kai ce, tana mi'kewa tsaye. "Allah ya taimaka." "Ameen." Ta amsa tana tafiya, tana cewa "bari na watsa ruwa na fito." Ta shige wani d'an corridor, ko kallon inda Hafsat take batayi ba, bare tasa ran zatayi mata magana, har ta kai su ga gaisawa. Ummu Aisha [7/1, 6:38 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 2⃣8⃣ Bata da dad'e da shigewa ciki ba Aliyu yace su tashi su tafi. Shatara ta arzi'ki Mommy'n ta had'awa hafsat, don taji dad'in ziyarar da suka kawo mata sosai. Tun da suka shiga mota babu wanda yayi magana, har suka bar unguwar, zuciyar Hafsat cike tunanin budurwar da ta gani a gidan, wadda taji Aliyu ya kirata da suna fareeda. Haka kawai taji har zuciyar sam bata kwanta mata ba. Bayan sun koma gida yake mata bayani akan Fareedar, cewa ita d'in 'kanwar Hafsat ce, a Egypt tayo karatun ta, yarinyar nada rawar kai ba kamar 'yar'uwarta ba." Murmushi kawai Hafsat tayi ba tare da tace komai ba. * * * * Yau kwana uku kenen da zuwan su gidan su marigayiya Hafsat da misalin Tara da rabi na dare suna zaune hankalin Hafsat na kan Muhammad da yake shan nono, shi kuma Aliyu yana kallon Network news a NTA, wayarsa ce ta fara ringing, ya d'auka ya duba, ganin ba'kuwar number yasa bai d'aga ba har ta katse. Ganin an sake kiransa ne yasa shi d'agawa duk da bai san waye mai kiran ba, da sallama ya fara, kamar yadda yake al'adarsa idan an kira shi, ko ya kira. Muryar mace yaji tana cewa "ya Aliyu ya kake?" Bai amsa tambayar da akai masa ba sai ya 'kara yin sallama, ganin cewa ba zai saurare ta ba sai ta amsa sallamar, sannan yake tambayar da wa yake magana. Kai tsaye ta sanar masa wace ce, yayi mamakin inda ta sami number sa, kamar tasan tunanin da yake sai take sanar da shi a wayar mummy ta sami number sa ta d'auka. Tun daga ranar kusan kullum sai ta kira shi, duk da ba wani sakewa yake da ita ba, Amma Yana d'agawa ko don darajar mahaifiyarta. Tun Hafsat bata damuwa da yawan wayar da suke har abin ya soma damunta, don Fareeda bata da takamaimai lokacin kira kowane lokaci ma kiransa take. Lokacin da ta sanar da Aliyu burinta na aurensa abin ya bashi mamaki, Amma sai ya bata ha'kuri yace shi bashi da burin 'kara aure iya matarsa ta isheshi rayuwa. Hankalinta ya tashi sosai don tana ganin babu wani d'a namiji da ya dace da ita kamar Aliyun. Ummu Aisha [7/1, 6:40 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 2⃣9⃣ Tsab ta shirya, ta fito, kai tsaye gidan 'kanwar mahaifinta Aunty Maimuna ta nufa, don tasan ita kad'aice zata iya taimaka mata har ta kai ga samun abinda ranta yake so. Don kuwa tana ganin ko za'a hau sama a rikito ba zata iya ha'kura da Aliyu ba, kamar yadda ba zata iya sharing d'insa da kowace mace ba. Bayan sun gaisa batai 'kasa a gwiwa ba ta sanar da ita damuwarta, kan irin son da takewa Aliyu da yadda yadda yadda ke nuna mata halin ko in kula. Murmushi ta saki tana cewa "ki kwantar da hankalinki, tun da kika zo gurina, ni kuma zan yi duk mai yiwuwa don ganin na share hawayenki. Me akai akayi wani Aliyu? Daga shi har matar tasa a tafin hannu na suke, kuma sai sun game kuren su. Yanzu idan da kud'i ki kawo abinda yake hannunki, ni kuma nayi miki al'kawari nan da kwana uku da kanki zaki kira ni ki bani kabari." Jiki na rawa ta zazzage kaf kud'in dake jakarta ta bata, har cikin zuciyarta tayi amanna da abinda tace, don tun da suka taso suke ji da ganin shi'umancin Aunty'n tasu. * * * * Washegari da wuri Aunty Maimuna ta shirya ta fita gidajen malamanta, don nemowa y'ar yayan nata sa'a, sai dai babbar matsalar da ta fuskanta ita ce, sai da ta je wurin mutum uku, amma kowa ce mata yake aure a tsakanin Aliyu da Fareeda ba zai yiwu ba. Ba haka taso ba, amma duk da haka tace tana so ita Fareedar ta mallake shi ta yadda ko uwar da ta haife shi baza ta fita juya shi ba. Kud'i sosai ta bayar don bata so a Sami matsala a aikin. Da ta koma gida Bata sanar da Fareeda gaskiyar batu ba sai ta nuna mata cewa an gama aiki, ta saurari sakamako. * * * * Matsala ta farko da Hafsat ta fara fuskanta da Aliyu itace, wayar dare, saiya d'auki dogon lokaci yana waya, kuma tabbas tasan da mace ne, da tayi magana sai yace ta fiye zafin kishi tana nufin don kar ranta ya 6aci bazai yi waya da kowace mace ba, haka zaiyi ta fad'a, don haka ta daina tankawa, ta zuba masa ido. Ummu Aisha [7/1, 6:41 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 Dominku Badi'a Ahmad Maryam wada Maman Sapi da Amal 3⃣0⃣ Wani sabon salo kuma da ya tsira shine, kullum idan ya dawo daga wurin aiki, yaci abinci, ko hutawa bai zaiyi ba zai d'auki wanka ya fice, ba shi zai dawo gida ba sai kwanciyar bacci. Wanna abu ba 'karamin ciwa Hafsat tuwo a 'kwarya yake ba. Ranar wata laraba tun dare Muhammad yake ta faman koke-koke, sakamakon zazza6in da ya tashi da shi. Bayan ya gama shiryawa zasu fita, don tare suke fita idan sun je Zari'a sai ya sauke ta a asibiti, don tuni sun fito asibiti, sai a bar Muhammad tare da nanny'n shi a gidan. fita Hafsat ta nemi da suyi da shi da nanny sai su tsaya a asibiti likita ya duba yaron, in ya so sai nanny ta dawo da shi gida. Fur ya 'ki amincewa, sai ma yace zata 'ka'kalowa yaro ciwon 'karya don tana son ta walar da shi, to shi babu inda zai tsaya, idan zata tafi ta wuce su tafi idan kuma ba zata ba ta zauna shi yayi tafiyarsa. Ganin ba zata iya wucewa tabar yaron a haka ba yasa ta ha'kura da fitar, tace ya je kawai zata zauna da yaron. Magunguna ta rubuta ta bayar aka je aka sayo mata ta bashi, cikin ikon Allah kafin yamma jikin yaron yayi sau'ki sosai. Bai dawo gidanba sai dare, da ta kawo masa abinci ko kallonsa bai yi ba yace ya 'koshi, ya bar mata kayanta, yayi wanka ya fice, bai sake dawowa ba sai kwanciyar bacci. Washegari jikin Muhammad yayi sau'ki sosai, don haka ta shirya fita, abin mamaki kafin ta 'karasa shiryawa Aliyu yayi ficewarsa, ko karyawa bai tsaya yayi ba, bare ya jira ta. Lokacin da ta 'karasa shiryawa sai motar haya ta je ta shiga. Tun daga wannan ranar bai sake tafiya da ita ba, sai dai ta shiga motar haya. Gaba d'aya damuwa ta yi mata yawa, don ta kaisu matsyin da Aliyu nuna mata yake kamar akan dole yake zaune da ita. Har ta manta rabon Aliyu da cin abinci a gidan, idan tayi magana Kuma ya fita fad'a, don haka sai ta zuba masa ido, sai dai bayan kowace Sallah sai ta ro'ki Ubangiji da ya kawo mata d'auki akan halin da take ciki. Ranar wata lahadi da ta zamo ba'kar rana a ciki tarihin rayuwarta, da misalin biyar da rabi na yamma hafsat na zaune a parlour hannunta ri'ke, da littafin hisnul Muslim tana dubawa ta ji tsaiwar motarsa a harabar gidan, bayan kamar minti hud'u suka shigo, kai tsaye kujera Fareeda ta nufa ta zauna ta d'ora 'kafa d'aya kan d'aya, tana wani yatsina, i kyakkawa a gidan biki. Duk da ran hafsat ya 6aci amma ko d'ago kai ta kallesu bata yi ba, shi kuwa Aliyu dama fridge ya zarce, ya d'auko mata ruwa lemo ya ajje a gaban ta, fuskarsa d'auke da murmushi yace "bismillah." "Haba dear ni da nake jin yunwa me ruwa da lemo zai min, kawai kasa a kawo min abinci." Kallon Hafsat da ke zaune yayi yace "je ki kawo abinci." Cikin takaici take dubansa, da kyar ta iya daurewa ta ce "ban dafa ba." "Ko mene ne dalili?" "Haka kawai" ta bashi amsa cikin halin ko in kula. 'Kwafa kawai yayi, sannan ya kalli Fareeda yace "bari nayi miki takeaway." "No dear ni gaskiyar bana son takeaway ko noodles ne dai ta dafa min." Wani kallon mamaki Hafsat tayi mata, sannan tace amma dai akwai ta6i a 'kwa'kwalwar ki ko? Ina shawartar ki da ki yi saurin dawowa cikin hankalinki, don banyi kama da House maid d'in gidanku ba bare ki sani aiki." Tana gama fad'a ta mi'ke ta d'auki littafinta ta shigewarta d'aki. Ummu Aisha [7/1, 6:41 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 3⃣1⃣ Daga shi har Fareeda da kallo suka bita, har ta shige cikin d'akin ta turo 'kofar. Fareeda ta juyo tana dubansa cikin yanayin kallon kissa ta 6ata fuska tace "yanzu kana ji matarka tace min ina hauka amma ka kasa d'aukar mataki a kai? To gaskiya idan bazaka d'auki mataki ba ni zan d'auka, ko kuma a ha'kura da maganar auren nan, Allah ya had'awa kowa da rabonsa, tunda matarka tafi 'karfinka. "Wa yace miki hafsat tafi 'karfina, ko kuma bazan iya d'aukar mataki akan ta ba? Meyasa daga wannan 'yar maganar sai maganar fasa aure? Ki zaba I kiga abinda zanyi idan ban d'auki mataki ba sai ki fad'i duk abinda kika so." Yana gama fad'ar haka ya shiga d'akin da hafsat ta shiga, a tsaye ya same ta jingine da bango fuskarta sha6e-sha6e da hawaye. Wani mugun kallo yake bin ta da shi, cikin alamun 6acin rai yace "me kike nufi da kalamanki? Mene ne dalilin tahowa da kika yi, alhalin ban gama maganar da nake miki ba? Kina nufin ban isa da ke ba kenan ko me? Ko kuwa tsabar rainin wayo ne yasa muna magana da ke kika wani taho kika bar wurin, to bazan d'auki rainin wayo ba, gara ma ki sake tunani, idan Kuma wasu ke zuga ki to tun dare bai miki ba ki tantance abinda ya dace da wanda bai dace ba." Cikin 'kunar zuciya tace "zan iya jure duk wani abu da zakai min Aliyu, amma banda akan mace, wallahi babu macen da ta isa ta maida ni kamar baiwa, ko abinda kake min a gidan nan da kaga ina kau da kai ina dalili. Shi aure ibada ne, kuma ta ita Kuma ibada dole sai mutum ya had'a da ha'kuri. Duk abinda zakayi ban isa na hana ka ba, kaje kayi, amma girki kam wallahi bazan mata girki ba." "Ni kuma nace sai kinyi idan ba haka ba kuma wallahi sai na d'auki mummunan mataki akanki." "Duk matakin da zaka d'auka na shirya masa, amma girki kam ba zan yi ba." "Tun da ban isa dake ba kije na sakeki, saki d'aya." Maganar tayi matu'kar girgiza ta, wani hawaye ya sake 6alle mata, Cikin rawar murya tace " Aliyu wannan shine son da ka sha cewa kana yi min? Ashe zaka iya rabuwa dani akan wata mace? Sai yau na fahimci dalilin da idan maza suka fara neman aure wasu matan hankalinsu ke tashi, shikenan Aliyu a yau zan bar maka gidanka, amma ina so kasani idan na bar gidannan na bar shi kenan har abada." Cikin rashin damuwa yace "da kin kyautawa kanki." Wanna furuci nasa ba 'karamin ta6a mata zuciya yayi ba, hawaye na 'kara zubowa daga idanunta, zuciyarta na sa'ka mata tambayoyi daban-daban. Wannan wace irin 'kaddara ce? Ita kuma tata kalar 'kaddarar kenan? Yaushe ne zata yizaman aure kamar kowace mace? In Ummu Aisha [7/1, 6:42 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 ZAMAN AMANA WRITER'S Ina mi'ka sa'kon gaisuwa a gare ki gabad'ayan Oganniya (Aisha Umma) Raheenat M. Abubakar Bilkisu Z. Ya'u 🅱K Aisha Isah (Mummy's Friend) Maman Surayya Maryama (Ummi Siddiqui) Princess Rahima 👸Queen BK👸 Sajnah Mommy'n Areef Ummu Junnut Jasmeer 3⃣2⃣ Tana hawaye tana komai ta da'uko akwati, sai da ta cika ta da kayan sawarta da duk abinda tasan zata bu'kata, ta rufe, ta d'auki jakarta da mayafi ta fito zuwa d'akin nanny ta kar6i Muhammad ta goya shi, ta fice. Tun da tabar gidan kuka take har ta isa Zari'a. Ba 'karamin girgiza su Aunty maganar mutuwar auren hafsat tayi ba, nan take Uncle ya d'auki waya ya kira Aliyu don jin gaskiyar abinda ya faru a tsakaninsu, amma sai ya nuna bashi da lokacin sauraronsa. Bayan kwana biyu aka je aka kwaso duk wani abu da yake mallakin Hafsat ne, haka ta ci gaba da idda ga kuma karatunta. Ranar da labarin yaje kunnen Hajiyansu Aliyu, bata ji dad'i ba, aikuwa washegari ta nufi Zari'a don basu ha'kuri. Lokacin da Aliyu ya same ta agida kuwa ba 'karamin fad'a tayi masa ba, kuma ta umarce shi indai yana son zaman lafiya da ita to ya dawo da matarsa, amma ga mamakinta sai ya nuna bashi da ra'ayin hakan. Kuma da ta tambaye shi dalilin rabuwar su ya kasa bata 'kwa'k'kwaran dalili. Tun daga nan tasan dole akwai abinda yake faruwa don banza bata kai zomo kasuwa. Ko Afnan bata ji dad'in abinda yayan nata yayi ba, don tasan ya tafka babbar asarar mace ta gari irin Hafsat. * * * * Hafsat tayi 'ko'kori sosai wajen ganin ta cire damuwar Aliyu daga zuciyarta, musamman ganin yadda Aunty ta damu, kullum burinta shine ta kwantar mata da hankali. Taci gaba da rainon yaronta, gefe d'aya kuma ta maida hankali sosai akan karatun ta. Bayan kammala iddarta zawarawa da yawa sun fito da nufin aurenta, sai dai bata da lokacin sauraronsu. Wani weekend da taje Rumoh, anan suka had'u da Abubakar, har ya sami labarin mutuwar aurenta. Tun daga lokacin ya fara bibiyarta, wai yana so su maida aurensu. Ita kuwa hafsat nuna masa tayi bata da lokacin sauraronsa ma. A wannan tsakanin ya sami mahaifinta da maganar, shi kuma ya sami Goggo, aikuwa ta rufe ido taci mutuncinsa sosai. Tun da Hafsat ta sami labari ta yiwa kanta fad'a, gara ta tsaida mutum d'aya daga cikin masu sonta ta aura, don yasan da gaske babu abinda zaisa ta sake aurensa. Ummu Aisha [7/1, 6:43 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 3️⃣3️⃣ A cikin masu son aurenta akwai wani Alhaji Nasir, shi d'an kano ne d'an asalin Yakasai, amma yana zaune a 'Kofar Nasarawa, yana da mata d'aya da yara hud'u. Sun had'u da Hafsat ne lokacin da suka zo sunan Aunty Maryam 'kanwar Aunty Salma lokacin da ta haihu. Tun lokacin da ya ganta ya fara bibiyarta, tun bata sauraronsa har ta fara sauraronsa sama-sama. Tabbas yanayinsa ya nuna shi d'in mutumin kirki ne. 'Dan kasuwa ne sosai, Kuma Yana Cikin rufin asiri daidai gwargwado. Duk cikin masu son aurenta shine mutumin da hankalinta yafi kwanciya da shi, cikin 'kan'kanin lokaci ta sanar da Aunty cewa ta tsaida mijin aure. Bincike sosai Uncle Tahir yayi akansa, kuma Alhamdulillah ba'a sami wata matsala daga gareshi ba. Cikin lokaci 'kalilan aka gama daidaita magana, aka tsaida ranar da za'a d'aura aure da tariya gabad'aya. Kuma babban abin farin ciki shine ya amince bayan bikin zata dawo Zari'a, saboda karatunta, inyaso duk weekend sai ta dinga zuwa Kano har zuwa lokacin da zata kammala karatun ta. An yi biki cikin kwanciyar hankali, wannan Karion a Kano aka d'aura auren, Amarya ta tare a gidanta cike da fatan wannan Karon mutuwa ce zata rabata da mijinta. Sam Abubakar bashi da labarin auren Hafsat, sai bayan an d'aura auren ne Rabi'u 'kaninsa da aka zo da shi, ya tafi wurin yayan nasa don su gaisa. Iya tashin hankali a ranar Abubakar ya shige shi lokacin da ya sami labarin aure Hafsat, sosai Rabi'u ya dinga bashi ha'kuri yana kwantar masa da hankali. A ranar kwana yayi da zazza6i, zuciyarsa kuwa in banda tafarfasa babu abinda take. "Yanzu shikenan na rasa Hafsat?" Wannan ita ce tambayar da yayi ta nanatawa kansa. Abu d'aya da ya tabbatarwa kansa shine bashi da sa'a, a rayuwa, domin rashin Hafsat ba 'karamar asara ba ce gare shi. Ummu Aisha [7/1, 6:43 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 3️⃣4️⃣ Tun bayan bikin sati d'aya kawai tayi a Kano, ta shirya ta koma Zari'a, ba gidan Uncle take da zama ba, musamman Alhaji Nasir ya samar mata gida take zaune a ciki. Tana yawan zuwa weekend Kano, shima kuma duk san da yake da lokaci yana zuwar mata. Tsakaninta da matarsa ma lafiya, kowacce tana girmama 'yar'uwarta. * * * * Aliyu kuwa tun bayan rabuwarsu da Hafsat, yaci gaba da harkokinsa bashi da damuwa ko kad'an, ko tuna hafsat a rayuwarsa baya yi. Fareeda ta dame shi da maganar ya kamata ya turo a fara maganar aurensu, babu musu ya amince, ya sami Hajiyansu da maganar. Murmushi kawai tayi don zuwa wannan lokacin ta fahimci Aliyu ba a cakin hayyacinsa yake ba, don babu yadda za'ayi mutumin da yake da mace kamar Hafsat ya sake ta saboda Fareeda. Don haka ta 'kudurce a zuciyarta, ko da Allah ya 'kaddara aure tsakanin Aliyu da Fareeda to tana so ayi komai yana cikin hayyacinsa ba wai a cikin irin yanayin da yake yanzu ba. Sosai tasa ake mata addu'a Kuma itama bata zauna ba, kullum cikin yi masa addu'a take, ga sadaka da take yawan yi da tashin dare, duk da nufin Allah ya ku6utar mata da d'anta. Har ankai kud'in aure, an sa'ka rana, dayake Allah maji ro'kom bawansa ne kwatsam sai rigima ta faru akan lefen bikin, abinda ya janyo har Aliyu yace ya fasa aurenta. Yadda abin ya faru kuwa shine, ma'kudan kud'i ya bawa Hajiya da nufin ayi duk abinda ya kamata game da lefe, bayan kwana biyu sai Fareeda take masa maganar ya kamata ya kawo kud'i ta fara sayayyar lefe, shi kuma sai yace Ai tuni ya bawa Hajiya ita zata kula da komai. Ai kuwa nan Fareeda ta nuna 6acin ranta, don me zai bawa Hajiya, bayan ita zata sa'ka kayan, ba Hajiya ba, don haka ita ya dace ta za6i abinda ranta yake so, nan ta faffad'i maganganu marasa dad'i da har fusata shi, har yace ya fasa aure. Ummu Aisha [7/1, 6:43 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 3️⃣5️⃣ Abu na farko da Aliyu ya fara shine zuwa gidan Uncle don bada ha'kuri Akan abinda ya faru tsakaninsu da Hafsat, da kuma neman biko. Bayan Uncle ya sanar da shi labarin auren Hafsat hankalinsa ya tashi sosai, yayiwa Fareeda Allah ya isa yafi cikin kwando, don badan shigowarta cikin rayuwarsa ba, da babu abinda zai rabashi da matarsa. A nan gidan ya sami Muhammad, don bata tafi da shi ba, duk da lokacin auren ta so a maida shi Kaduna, don kar ta d'ora musu d'awainiya da yawa, bayan tarin alkhairinsu a gareta, ga kuma Salim da yake hannunsu, amma sai suka hana ta maida shi. Haka ya tafi zuciyarsa fal 'kunci da takaici. Bayan sati d'aya ya sake komawa shi da Hajiyarsa don kar6ar Muhammad, su Aunty basu so bada yaronba, amma dole suka bada shi, don da sun so sai ya kai kamar shekara bakwai ko zasu maida shi. * * * * Ita kuwa Hafsat tana gidan mijinta hankali kwance, babu abinda ta nema ta rasa. Ga kuma karatunta da ya mi'ka, ta maida hankali sosai tana fahimta. A yanzu, kusan shekararta guda kenan da auren Alhaji Nasir kuma Alhamdulillah basu ta6a samun matsala ba ko kad'an. Ta sami hutu na sati biyu abin tsautsayi, ta shirya tafiya Kano, don tayi hutunta acan, ashe tsautsayi ne yake kiranta. Kwananta hud'u da zuwa Kano ranar da magariba Alhaji ya shigo da wata jaka babba, ri'ke a hannunsa, kuma ranar ita ce da girki, tayi 'ko'karin kar6a ta taimaka masa da ita zuwa d'akinsa, sai yace ta bari ba zata iya d'auka ba, sai ta ha'kura ya shige da abarsa d'akinsa. Duk abinda ya kamata tayi masa tayi har zuwa lokaci kwanciyar bacci, ta nufi d'akinsa bayan ta shirya kamar yadda yadda kowace mace za tayi idan zata tafi turaka. A d'akin ta kwana har asuba, lokacin da ya fita masallaci, ita kuma ta shiga toilet d'insa don yin alwala, bayan ta fito bata je ko ina ba, a d'akin tayi sallar ta. Har lokacin da ya dawo tana zaune akan sallaya, bayan ta had'a addu'o'inta suka gaisa, sannan ta fita, don 'ko'karin had'a break fast. Sai da ta fara gyara parlour sannan ta shiga kitchen ta d'ora girki, zuwa bakwai na safe ta kammala komai. Ta koma d'akinta tayi wanka ta shirya tsaf cikin kyakkyawar shiga ta kamala, tana fitowa d'akinsa ta nufa, sai ta tarar ya ahiga wanka, bata zauna ba sai da ta gyara masa d'akin tsab, ta fito masa da kayan da zai sa. Yana fitowa ta shiga band'akin ta wanke shi tas, kafin ta fito ya gama shiryawa, tana fitowa suka wuce dining area don karyawa. Suna fitowa Hadiza da yaranta suma suka fito, nan suka zauna Hafsat tayi serving d'in su, kowa ya ci abinci, har ya 'koshi. Bayan kowa ya tashi ta tattare komai ta nufi kitchen, sai da ta wanke kwanukan da suka 6ata ta fito, ta sake komawa d'akin Alhaji. A bakin 'kofa suka had'u da shi, yana ganinta ya juya ciki ta bi bayansa, suna shiga ya juyo yana fuskantarta yace "Hafsat ina jakar da na shigo da ita jiya?" Cikin mamakin tambayarsa ta ke kallonsa, sannan tace "ba a cikin wardrobe naga ka ajiye ta ba?" Ga mamakinta sai yace "to d'auko min." Cikin 'kwarin gwiwa ta nufi inda ya ajiye, amma ga mamakin ta sai taga wurin babu komai, ta juyo tana ce masa "ko ka sauya ma'ajiya ne, tun da ni dai jiya anan naga ka aje." "Ni dai ban sauya mata ma'ajiya ba, sai dai ko ke ce kika sauya." "Haba Alhaji ta yaya banyi ajiya ba zan sauyawa ajiyarka wuri? Ka dai tuna ko wani wirin ka mayar da jakar......" Bai bari ta 'karasa fad'a ba ya katse ta da cewa "saurara Hafsat, karki nemi kawo min raini mana, tayaya zan ajiye jaka cike da kud'i in zo d'auka ban gani ba, alhalin daga ni sai ke muka shigo d'akin nan tun da na shigo da jakar har zuwa yanzu." "Me kake nufi Alhaji? Kana nufin zargi na kake da yin sata?" Sai hawaye ya fara shatata d'aga cikin idanunta. "Au zargi ne ma? Kinga abinda nake so dake tun ba wanda yasan halin da muke ciki ki fito min da kud'in nan tun raina 6aci ba. Ummu Aisha [7/1, 6:44 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 Maman Sapi da Amal Maman Noor Ina ganin comments d'inku, kuma ina jin dad'i Allah ya bar 'kauna, nima kuna 💗 d'ina . 3️⃣6️⃣ "Daga ina zan fito maka da su alhalin nima ban san inda suke ba, na ro'ke ka don girman Allah idan ma wasa kake min ka daina, zuciyata ba zata iya d'auka ba." "Wasa?" Wasa fa kika ce hafsat, ni kuwa na rasa akan abinda zanyi miki wasa sai kud'i? Ke ce dai ki ke son kawo min wasan kuma wallahi ba zan lamunta ba, tun wuri ki fito min da kud'ina idan ba haka ba kuma wallahi sai ran kowa ya 6aci." Hankalin Hafsat idan ya kai dubu a wannan lokacin to ya tashi, kuka take kamar numfashinta zai shid'e. Tun suna abinsu su biyu a d'aki, har Hadiza ta san halin da ake ciki. Ganin wankin hula yana neman kai shi dare yasa bai tsaya 6ata lokaci ba ya kira 'yan sanda. Hafsat tana ji tana gani suka tusa 'keyarta zuwa police station, a karo na biyu a rayuwarta bisa laifin da bata aikata ba. Idanunta cikin na Alhaji Nasir ta ce "in Allah ya yarda sai kayi danasanin wannan tozarcin da kayi min Alhaji, kuma ina son ka sani yadda ka 'ki yi min uzuri a yanzu, har abada bazan yi maka uzuri ba." Tana gama fad'ar haka ta juya suka tafi, bayan ta ro'ki 'yan sandan akan tana so su rufe d'akinta har zuwa lokacin da za su gama bincikensu. * * * * Lokacin da Aunty taji abinda ya faru da Hafsat, kuka da dinga yi, ta dinga jerawa kanta tambayoyi ita kad'ai babu mai amsa mata. "wannan wace irin 'kaddara ce? Me yasa duk aurenki sai kin sami matsala? Sai yaushe ne zaki ji dad'in aure kamar kowacce mace?" Duk aiyukan da suke gaban Uncle a lokacin haka ya bar su, ya taho Kano. Ya sami Alhaji Nasir don jin halin da ake ciki, nan ya sanar masa duk abinda ya faru tun daga shigowarsa gidan da jakar har zuwa yadda sukayi da Hafsat d'in. Shi kansa Uncle ya tabbatar cewa Allah ne kad'ai zai iya fitar da ita daga wannan al'amarin, domin duk wanda ya d'auki kud'in nan to dama shi yasan me ya taka. Ya so su sasanta da Alhajin abi abin cikin sau'ki, amma fir ya 'ki. Allah cikin ikonsa washe gari da misalin biyar na yamma, yana zaune a falo ya yi ba'ko, ya tashi ya fita. A 'kofar parlour suka had'u da Naja'atu 'kanwar Hadiza zata shigo, suka gaisa kowa ya wuce. Ba'kon bai dad'e ba ya wuce, shima ya juyo cikin gida, yana zuwa gaf da 'kofar parlour ya ji abinda ya yi matu'kar girgiza shi. . Ummu Aisha [7/1, 6:44 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 3️⃣7️⃣ Muryar Hadiza ya ji ta na cewa "wallahi Naja abu nayi yake neman ya zo ya dame ni." "Kamar yaya kenan?" "Jiya Alhaji ya shigo da wasu kud'i gidan nan, wanda duk ranar da kika ga haka to yayi jinkirin tashi daga kasuwa ne, idan ya je banki ma an rufe, to sai ya taho da kud'insa gida. Ganin ya shigo da wannan kud'in zuciyata ta raya min na sami hanyar da zan shiga tsakanin Alhaji da amaryarsa, ko da basu rabu ba ya zamana babu yarda a tsakaninsu. Yau da asuba bayan na tabbatar da fitar Alhaji masallaci na je d'akin, sai da na tabbatar tana cikin toilet na shiga na d'auko jakar da nufin na shigar da ita d'akinta, kinga idan ya nema ya rasa, zai tuhume ta idan ya ganta a d'akinta daga ranar mutuncinta zai zube a idonsa. Amma abin takaici ina zuwa sai na tarar da d'akin a rufe da makulli, sai na dawo da niyyar mayar da jakar inda na d'auka, na tarar ta fito daga band'akin, na rasa yadda zanyi da jakar kud'in yadda Alhaji ba zai zarge ni ba. Yanzu haka zancen da nake miki Hafsat na police station tun safe, ni kuma ga jakar kud'in a hannuna na rasa yadda zanyi da ita, shi yasa nake son ki bani shawarar yadda zanyi." Sai da Naja'atu ta nisa sannan ta ce "a gaskiya banji dad'in abinda kika aikata ba, ki sani manzon Allah (S.A.W) yace imanin d'ayanku baya cika har sai ya sowa d'an uwansa abinda ya so wa kansa. Na tabbar ba ke akan kanki ba ko ni da nake 'yar uwarki baza ki so ayimin irin wannan sharrin ba, me yasa zaki biyewa rud'in zuciya? Ni tun da aka auro Hafsat d'in nan banga wata matsala daga gareta ba, bare kuma matar da ba tare kuke zaune wuri d'aya ba, sai dai ta zo ta koma. A gaskiya Aunty Hadiza ba ki kyauta ba, ita fa kishiya abokiyar zama ce, musamman idan Allah ya had'a mutum da ta gari, ni yan......." Kasa 'karasa maganar tayi sakamako ganin Alhaji Nasir da ya shigo ya na bin Hadiza da wani irin kallo mai dauke da tuhuma. Nan take jikin Hadiza ya d'auki rawa, cikin rawar murya ta ce "lafiya Alhaji, ko wani abin ne ya ke faruwa?" Ya dube ta cike da takaici ya ce "kin bani mamaki Hadiza, kin ci amanar yardar da nayi miki, amma ina so ki sani wannan abin da ki ka aikata bani ko Hafsat ki ka cuta ba, kanki ki ka cuta, don kin zubar da mutuncin ki a ido na, kuma tashi ki d'auko min kud'i na." Jiki a sanyaye ta tashi ta shiga d'akinta, jim kad'an sai gata ta fito hannunta ri'ke da jakar ta mi'ka masa. Yana kar6a ko kallonta baiyi ba ya shige d'aki da jakar, yana ajjewa ya juya ya fita, kai tsaye police station ya nufa. Bai wani sha wahala ba aka fito da Hafsat, wadda cikin kwana d'aya tayi wata irin rama, ko kallonsa bata yi ba ta nemi hanyar ficewa daga cikin wurin. Da sauri ya taradda ita, yana yi mata magana, ita kuwa ko saurarensa bata yi ba, ta ci gaba da tafiyarta, zuwa ya yi ya shiga motarsa ya zo gabanta ya tsaya yana cewa "Hafsat shigo mu tafi " Sai sannan ta juya ta kalle shi, ta ce "in shigo mu tafi Ina fa?" Ya bata amsa da cewa "gida mana." Wani irin murmushi na takaici tayi, ba tare da ta ce masa komai ba tayi gaba, tana zuwa titi ta tari adaidaita, ta shige. Ummu Aisha [7/1, 6:45 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 Page d'in yau naku ne Aisha Ibrahim (Maman twins) Maman Noor Allah ya ba 'kauma 3️⃣8️⃣ Mai adaidaita bai sauke ta ko Ina ba sai a sharad'a 'kofar gidan Goggo A'i, sai da ta shiga ciki tayiwa Goggo bayani, aka aiko masa da kud'insa. Duk wanda ya danganci Hafsat wannan abinda ya faru bai masa dad'i ba, ganin yadda Alhaji Nasir ya rufe ido, ya nuna ba sani ba sabo. Tun bayan abin yake sintirin ba da ha'kuri amma Hafsat ta 'ke'kasa 'kasa ta ce ta gama zaman aure da shi, kuma babu wanda ya takura mata, tunda shi ya jawa kansa. Ranar da ya kira ta a waya, da farko kamar kar ta d'auka, sai kuma dai ta d'auka, ha'kuri ya fara bata yana cewa "duk da nasan ni mai laifi ne a wajenki amma na ro'ke ki don girman Allah kiyi ha'kuri. Ni kaina daga baya na fahimci cewa abinda nai miki ban yi miki adalci ba, ina so ki sake bani dama, nayi miki al'kawari irin hakan ba zata 'kara faruwa ba, ki yi ha'kuri ki dawo d'akinki." Ciki n takaici Hafsat ta ce "ai in dai nice na bar gidanka kenan har abada, domin a duk lokacin da na bud'e ido na ganka zuciya ta ba zata daina jin zafin abinda ka aikata min ba, kuma dama na gaya maka, akwai ranar da zaka ka yi nadamar abinda ka aikata min, to gashi ta zo. Abu d'aya da nake bu'kata daga gareka a yanzu shine shaidar saki don wallahi na gama zaman aure da kai." Duk nacin Alhaji Nasir dole ba don ya so ba sai da ya saki Hafsat. Tun bayan kammala iddarta ta 'ki sauraron kowa a masu zuwa suna son ta, don tace ita kam ta gama aure har abada. Lokacin da Aliyu ya sami labarin mutuwar aurenta, shima baiyi 'kasa a gwiwa ba, sai da ya dawo, don su mai da aurensu, duk da shima lokacin ya yi wani auren, amma fur ta 'ki. Sai ta nuna masa cewa ita a yanzu babu maganar aure a tsarin rayuwarta. Shima Abubakar bai yi sanya ba, kuma ya yiwa kansa al'kawarin wannan karon duk rintsi duk wuya, ba zai ha'kura da ita ba, ba zai yiwu yana kallo wani ya sake d'auke ta ba. Ummu Aisha [7/1, 6:46 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 DUK KANWAR JA CE Story and Writing by Ummu Aisha *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 3️⃣9️⃣ A haka harta kammala karatunta, tayi house manship ta gama, a yanzu haka service take a Abdullahi wase specialist hospital. Shima Uncle Taheer tuni ya sami transfer, ya dawo BUK da aiki, don haka yanzu a Kano suke da zama. AN DAWO LABARI Bayan gama dogon tunanin abubuwan da suka faru a rayuwar ta, ta dinga share hawaye, wannan ranar duk iya satar bacci ya kasa sace Hafsat, daga 'karshe da taga damuwa ba zata barta ta yi barci ba, sai ta shiga toilet ta d'auro alwala, haka ta kwana tana sallar nafila da kuma karatun Qur'an. Washe gari sukuku ta tashi, ba walwala, zuciyarta a cinkushe, da tasan irin hukuncin da iyayenta za su yanke mata kenan tun farko da ta sami wani a masu sonta ta aura, domin kaf mazan da ta aura babu wanda abinda abinda yayi mata ya fi tsaya mata a rai irinsa. Aunty kuwa tun bayan da ta kammala duk wani abu da tasan zata yi, ta d'auko paper da biro ta fara rubuta abubuwan da suka kamata a saya na auren Hafsat d'in. Tana kallon Aunty tana ta harkokinta cikin farin ciki, wannan ya 'kara 'kuntata zuciyarta, don tasan ko tayi magana babu mai fahimtar ta. Ranar juma'a bayan sallar juma'a jama'a suka shaida d'aurin auren Abubakar Halliru Buba da Hafsat Sani Buba. Ranar Hafsat tayi kuka kamar ba gobe, shi kuwa angon yana can cikin farin ciki da walwala. Aunty ta ro'ki a bari sai bayan sati biyu ta tare, saboda abin ya zo musu a 'kurarren lokaci, basu gama shirye-shiryen da ya kamata ba. * * * * Shi kuwa angon ba 'karamin d'auki ba dad'i sukai da matarsa ba, lokacin da ta sami labarin auren, tamkar sabon kamun hauka haka ta dawo masa, ta tayar da hankalinta sosai, shima kuma ta tayar masa, don sai da ta kai ga ya kira yayanta ya tsawatar mata, sannan ya sami sau'kin abin. Daga gefe kuma ga mahaifiyarsa da ta sa shi a gaba, don itama bata so aka maida aurensa da Hafsat ba don so tayi ya auro 'yar 'kanwarta, shi kuma ya 'ki. Wanna abu ya 6ata mata rai, ganin babu yadda za ta yi yasa ta h'akurin dole, don Baffa Halliru yayi mata takara sosai, akan idan ta sake ya ji abinda bai gamsar da shi ba, to ta sani sai ranta ya 6aci. Wuyar abu sai dai in ba'a saka masa rana ba, sannu a hankali har ranar tarewar Hafsat a gidan Abubakar ta yi. Duk da fushin da take hakan bai hana Aunty shirya 'kayatacciyar walima ba. Wannan karon ma mutanen Rumoh da yawa sun sami halartar bikin. Da misalin 'karfe biyar na yamma aka kawo motoci d'aukar amarya, ba 6ata lokaci, aka fito da ita aka raka ta gidan mijinta da ke Court road. Gida ne ginin zamani mai d'auke da part biyu, sai wani da bai kai sauran girma ba daga can bayan su wanda mutum zai iya shiga d'aga kowane part. Gidan amarya Hafsat yayi kyau sosai, ga shi ya sha gyara, ita kanta Hafsat da ta ga yadda aka 'kawata mata gidan bata san lokacin da hawaye ya dinga zuba daga idanuwa ta ba, don ba karamin 'ko'kari su Aunty su kai ba, ita kam ba ta san da me za ta saka musu tarin alkhairansu a gare ta ba. Haka 'yan rakiyar amarya sukai ta zaga gidan, suna sakawa wurin albarkacin. Kafin wani lokaci duk an watse, sai iya amaryar ita kad'ai aka bari zaune cike da takaicin dawowa gidan Abubakar a matsayin matarsa. Tana zaune a inda aka barta har lokacin da aka Kira sallar magriba, ta tashi ta d'auro alwala, ta gabatar da tata sallar, bayan ta gama addu'o'n da zata yi, tayi azkar, ta tashi tasa makulli ta kulle part d'inta, don bata Abubakar ya ce zai shigo mata, saboda a yanzu babu mutumin da ta tsana sama da shi a rayuwarta. * * * Misalin goma da rabi na dare Hafsat na kwance akan gadonta, duk da ba barci take ba, ga mamakin ta sai ji tayi an turo 'kofar d'akin an shigo, tana duba gurin Abubakar ta gani yana tunkaro wurin da take jikinsa sanye da kayan bacci, milk colour, yana ri'ke da leda mai tambarin Yahuza Suya a hannunsa. Kai tsaye gefen gadon ya nufa, ya so wuri ya zauna, idanuwansa a kanta yana kallonta. Ummu Aisha [7/1, 6:46 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 *DUK KANWAR JA CE* *Story and Writing by* *Ummu Aisha* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛_ 4️⃣0️⃣ Firgigit ta tashi zaune, kamar dama can bacci take, fuskarta a d'aure take tamau, ta 'ki kallon inda ya ke zaune, shi kuma gaba d'aya hankalinsa na kanta, so yake su had'a ido amma sam ta hana shi damar hakan. Sun d'an dad'e a zaune ba tare da kowa yayi magana a tsakaninsu ba, shi fargabar yin maganar ma yake, saboda yadda ta d'aure fuska, ta 'ki ko da kallon wurin da yake zaune. Kamar mai ciwon baki ya fara mata magana "Hafsat har yanzu ba zan gajiya wurin baki ha'kuri ba, domin duk Wanda ka ji ance ya yi ha'kuri to ha'ki'ka an cutar da shi, amma karki manta Ubangiji (S.W.T) yana son bayinsa masu ha'kuri. Sannan shi ha'kuri halayya ce ta fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (S.A.W). Abinda ya faru kuskure ne da ajizanci irin na d'an Adam, amma na yi miki al'kawarin abu makamancin wannan ba zai sake faruwa ba. Ko a baya na tabbatar na fi ki shiga halin 'kunci da damuwa bisa abinda ya faru." Har ya gama duk maganganun da zai yi ko d'ago kai ba tai ta kallashi ba, bare ta tanka masa, ya kai wajen minti talatin a zaune, ganin shirun ta yi yawa yasa ya mi'ke ya fita, bai dad'e ba ya dawo hannunsa d'auke da plate da cups. Ledar da ya shigo da ita d'azu ya d'aukko, ya bud'e, wani lafiyayyen balangu ne a ciki, ya juye a cikin plate sai youghurt mai sanyi da ya juye a cikin kofunan, gaba d'aya ya tura gabanta sai kofin youghurt d'aya da ya d'auka ya fara kur6a. Wani takaicinsa ne ya 'kara kamata, ko kallon plate da cup d'in bata yi ba ta juya tayi kwanciyarta. Ba irin rarrashin da bai yi mata ba akan ta daure ta ci wani abu, kar ta kwanta da yunwa, amma ko kula shi ba ta yi ba bare ya sa ran zata ci. Haka ya koma kitchen ya d'auko wani plate d'in ya rufe naman ya fitar parlour ya ajje a cikin fridge. Sai da ya shiga toilet ya yi brush ya zo ya kwanta a kan gadon daga gefe d'aya. Ai kuwa kamar wadda ya watsawa wuta ta tashi a fusace, tana yi masa wani irin kallo na 'kas-'kanci ta ce "me ka ke nufi da kwanciya a nan? Kai yanzu ko ni nace ka zo inda na ke ka kwanta ai ka ji kunya ka ce a'a, ko kuwa kana tunanin ban san ciwon Kai na ba? Tun dare bai maka ba ka kama gaban ka, in kuma kai ba za ka fita ba to ni zan fice in bar maka d'akin. Ganin yadda ta birkice masa lokaci d'aya, ya sa ya yi mata sai da safe ya fice, ya nufi part d'in sa. * * * * Washegari tun asuba ta tashi, bayan ta yi salla bata koma ta kwanta ba, tana gama addu'o'i da Azkhar, gyara gidan ta fara duk da bai yi datti ba, bayan ta gama ta koma d'akin tayi wanka ta shirya, sannan ta fito parlour ta kunna karatu wayar ta ta na sauraro. Sai wajen 'karfe takwas ta shiga kitchen, ta saka ruwa a kettle, lokaci kad'an ya yi zafi ta juye ya had'a tea ta fito, ta zauna a parlour ta na sha. Ba ta dad'e da zama ba ya shigo, bakin shi d'auke da sallama, kallo d'aya ta yi masa ta d'auke kai, kamar bata san Allah ya yi ruwan tsirar sa ba. _Ummu Aisha_ [7/1, 6:46 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 *DUK KANWAR JA CE* *Story and Writing by* *Ummu Aisha* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S Z.A.W* _(Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah)_🤜🤛 4️⃣1️⃣ Duk da cewa bai ji dad'in halin ko in kula d'in da ta nuna masa ba, hakan bai sa ya nuna 6acin rai ba, domin yasan duk abinda Hafsat za tai masa ya can-canci fiye da haka daga gareta. A kujerar da ke kusa da ita ya zauna, gaba d'aya hankalinsa ya na kanta, cikin taushin murya ya ce "Hafsat an tashi lafiya?" Maimakon ta amsa, kawai sai ta mi'ke ta nufi kitchen da cup d'in da ta gama shan tea. Sai da ta d'auraye kofin ta fito, ta yi wucewar ta d'aki tai kwanciyarta. * * * * Sati uku kenan da komawar Hafsat gidan Abubakar, amma babu wani abu da ya sauya daga zaman nasu, ya yi iya bakin 'ko'karinsa don ganin sun daidaita amma abin ya fi 'karfinsa, dole ya zuba mata ido. Damuwa tayi masa yawa, don duk cikin matan nasa babu mai kwantar mai da hankali, har gara ma Hafsat ita magana ce ba tai masa, amma Zainab rashin mutunci kala-kala babu abinda ta manta. Daga 'karshe dai ganin ya rasa mafita sai ya shirya tafiya Rumoh wurin Goggo , don yasan ita kad'ai ce zata iya taimaka masa a wannan ga6ar. Ranar lahadi tun safe ya shirya ya tafi, kafin 'karfe tara ya je. Bayan ya gaisa da 'yan'uwansa ya nufi d'akin mahaifiyar sa, sun dad'e da ita, tana ta 'korafi wai ya nuna mata ba ta isa da shi ba, tun da ya mai da aurensa da Hafsat, da ta isa da shi ai da bai mai da Hafsat ba. Shi kuma sai ha'kuri ya ke bata, har ya samu zuciyarta ta yi sanyi. Bai sami shiga wurin Goggo ba sai bayan Azahar, sosai tayi murnar ganin jikan nata, bayan sun gaisa ta ke tambayarsa iyalansa da fatan dai suna zaman lafiya? Ganin an zo ga6ar da ya ke so baiyi 'kwauron baki ba, ya fayyace wa Goggo irin halin da suke ciki da Hafsat, daga 'karshe ya nemi taimakon ta akan ta yiwa Hafsat magana ko zata sassauta masa su daidaita. Aikuwa nan Goggo ta hau fad'a, Kamar ta ari baki, sai bata ha'kuri ya ke, ya na nuna mata shifa so ya ke ta yi mata nasiha, har ta sakko. A lokacin Goggo ta shirya tafiya Kano, don ta ce baza ta iya barin Hafsin ta na aikata rashin hankali ba. Ana fitowa daga masallacin sallar la'asar suka d'auki hanya ita da shi a cikin motarsa. _Ummu Aisha_ [7/1, 6:47 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 *DUK KANWAR JA CE* *Story and Writing by* *Ummu Aisha* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS Z.A.W* _(Gidan Zaman lafiya da Amana insha Allah)_🤜🤛 *Sadaukarwa ga* _Maman Abba_ _Maman Noor_ *Nagode da irin 'kwarin gwiwar da kuke bani Allah ya bar 'kauna, in yinku irin sosai d'innan 🤸🏻‍♀️* 4️⃣2️⃣ Ba 'karamin farin ciki Hafsat ta yi da ganin Goggo ba, ta rasa inda za ta sata saboda farin cikin ganin ta. Sai shige da fice ta ke tsakanin parlour da kitchen, bayan kayan motsa bakin da ta ajje mata, girki ta d'ora na musamman duk da Goggon ta sanar mata cewa a 'koshe ta ke. Duk yadda Goggon ta kai da kakkaucewa sai da ta ci ta sha ta 'koshi, sannan ta fuskanci Hafsat da maganar da ke tafe da ita. "Hafsi wace magana na ke ji daga wajen d'an uwanki? Haba Hafsi, idan ki kai haka sai naga kamar baki godewa ni'imar da ubangiji ya yi miki ba. Idan kin nutsu kin fahimci abinda ya faru a baya ba yin kan sa bane, duk abinda ya aikata ya yi ne busa umarnin mahaifiyarsa, wadda ita kuma ba komai ne ya sa tayi hakan ba sai tsaba hassada da 'kyashi. Kar ki manta cewa mai sunan Malam d'an uwanki ne, kuma da gan-gan ba zai yi abinda yasan zai cutar da ke ba, ko a lokacin da abin ya faru, daga yanayin tashin hankalin da ya shiga zai tabbatar miki da irin nadamar da yayi. Nafi kowa farin cikin daidaitawarku da shi, domin nasan duk wanda zaki aura a fad'in duniya ba zai san darajar ki da 'kimarki kamar shi ba, kar ki bari a sami 6araka daga 6angarenki Hafsi don ba zan ji dad'in hakan ba ko kad'an. Kar ki manta abinda ya faru shine ya zama tsani na duk wani matsayi da ki ka taka. Duk wani abu da ki ka ga faru a ruyuwar bawa, dama yana rubuce a cikin littan 'kaddarar sa. Idan ma wanna matakin da ki ka d'auka horo ne, to ki janye shi haka, zuwa yanzu ya Yi horuwar da ko wa'ka za'a saka masa a ma'kogaro ba zai you abu makamancin wanna ba. Lokaci ya yi da zaki yi rayuwar aure kamar kowace mace. Ki yi ha'kuri da duk wani abu da ya faru a baya, ki zauna da mijinki da zuciya d'aya, don ya zame miki tafarkin shiga aljanna." Duk maganganun da Goggo take Hafsat na zaune tana sauraronta, ba ta ce komai ba, har ta kai 'karshe. Ta d'auki lokaci mai tsayi tana bata misalai har zuwa lokacin da Hafsat d'i n ta tabbatar mata da cewa komai ya wuce. Daga nan suka ci gaba da hirar da ta shafi dangi, har lokacin sallar magariba ya yi. Sai bayansa an yi sallar Isha sannan Abubakar ya shigo, ko zama bai yi ba Goggo ta ce ya zo ya kaita gidan 'yar uwarta. Hafsat ta dage sai Goggo ta kwana a gidan, ai kuwa tace ba za'ai wanna abin kunyar da itaba, dole ba don sun so ba ya kai ta. Zuciyarsa fal da zumud'i ya dawo gidan, don da ya sauke Goggo ko cooking gidan bai shiga ba, babban burinsa ya ganshi da Hafsat cikin farin ciki. _Ummu Aisha_ [7/1, 6:48 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 *DUK KANWAR JA CE* *Story and Writing by* *Ummu Aisha* *ZAMAN AMANA WRITER'S Z.A.W* _(Gidan Zaman lafiya da Amana insha Allah)_🤜🤛 4️⃣3️⃣ Bai 'karaso gida ba, sai da ya tsaya wani wajen masu gashin kaji mai rai da lafiya yai yi musu tsaraba. Sai da ya fara zuwa wurin Zainab, duk da har lokacin ko maganar arzi'ki bata had'a su, don ita tana ganin babban cin mutuncin da zai mata a rayuwarta shine ya had'a ta zama da wata. Abin kunya ne a gare ta a gan ta da kishiya, bayan du irin soyayyar da ta ke masa. Lokacin da ya shigo 6angaren Hafsat a parlour ya same ta zaune da computer a gaban ta, daga dukkan alamu wani abu mai muhimmanci ta ke. Sai da ya sami wuri ya zauna ta yi masa sannu da zuwa, ba tare da ta d'aga kai ta kalle shi ba, ta ci gaba da abinda ta ke, ta d'auki kimanin mintuna ashirin da wani abu kafin ta gama, zuwa wannan lokacin shi hankalinsa ya yi nisa a program d'in da yake kallo a tashar Arewa. Ko da ta gama bata tashi a gurin ba, sai dai rufe computer da tai, itama sai ta mai da hankalin ta kan kallon. Bayan sun gama kallon, da kansa ya shiga kitchen ya d'auko plate da cups, ya juye abinda ya shigo da shi, sannan ya umarce ta da ci. Da farko kamar K Kar ta ci, sai dai kuma tana tuno al'kawarin da ta yiwa Goggo, ta tashi, ta shiga kitchen ta wanko hannu ta zo ta zauna suka ci. Har 'karfe goma suna parlour, sannan suka tashi, kai tsaye toilet ta wuce, don yin wanka da alwala, yayin da shi kuma ya tafi part d'insa don shiryawa. Bayan ta fito sai da ta tsaya ta shafa bady lotion a jikinta ta shafe jikinta da turare, sannan ta saka rigar bacci, sai ta d'aura zani a Kai tasa hijab don gabatar da shafa'i da wuturi. Tana tada salla ya shigo, d'akin da sallama a bakinsa, ganin tana salla sai ya sami gefen gado ya zauna, har ta idar, sannan ya tashi ya jagorance su salla raka'a biyu. Bayan sun kammala addu'o'in su, sai kowanne ya nemi makwanci, a wanna rana, wanna dare abubuwa da yawa sun faru, wanda ban san yadda zan fasalta su ba, sai dai zan bar kowa ya 'kissima a ran sa. Abubakar har kukan farin ciki yayi, ya da'de da manta cewa ana samun irin wanna farin cikin a cikin aure, sai yau da Allah ya dube shi da idon rahama ya dawo masa da 'yar uwarsa, kuma masoyiyarsa cikin rayuwarsa. Washe gari da safe duk wani aiki na gida tare suka yi shi, don yana ji a zuciyarsa da akwai hali ko numfashi ba zai bar ta tayi da kan ta ba. Da kyar ya daure ya fita office, gudun kar ya sami matsala a wurin aikinsa. Tun daga wannan lokacin suka sami fahimtar juna, su ke zaman lafiya a tsakanin su. Daga ranar da Zainab ta fahimci sun daidaita ta k'ara tayar da hankalinta, don tana ganin ba ajin ta bane a ce kamarta tana zaune da kishiya. ________________________ Zaman lafiya da kwanciyar hankali ne ya ke gudana a tsakanin Hafsat da Abubakar, a wannan lokacin ne Hafsat ta fahimci ta na da shigar ciki, sai dai ba ta sanar da Abubakar ba. Har sai da cikin ya kai tsawon watanni uku sannan ya sani sakamakon yawan rashin lafiyar da ta ke yi, har suka dangana da asibiti, anan likita ke sanar da shi batun cikin. Fad'ar irin farin cikin da yayi ma 6ata baki ne, don sai yake ganin kamar a lokacin ne za'a fara yi masa haihuwa, kasancewar Uncle Tahir ya hana su Saleem, ya ce su yi addu'ar Allah ya Basu nasu, amma wannan na sa ne. _Ummu Aisha_ [7/1, 6:48 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 *DUK KANWAR JA CE* *Story and Writing by* *Ummu Aisha* *ZAMAN AMANA WRITER'S Z.A.W* _(Gidan Zaman lafiya da Amana insha Allah)_🤜🤛 4️⃣4️⃣ ____________________________________ Hafsat ta ci gaba da rainon cikinta, tare da kulawar mai gidanta, har watan haihuwarta ya kama, zuwa wannan lokacin sun gama duk sayayyar haihuwa, ranar haihuwar kawai suke jira. Ranar lahadi tun da ta tashi da asuba ta ke jin alamun ta fara labour, zuwa 'karfe takwas na safe abin ya kankama sosai, nan da nan suka tafi asibiti, cikin ikon Allah ko awa d'aya da zuwa ba su yi ba ta haifi yarinyarta mace, not take Abubakar ya yi wa Aunty waya, ya kira mutanen Rumoh ya sanar da su. Cikin lokaci 'kalilan sai ga Aunty a asibitin, bakinta kamar gonar audiga don faran ciki. Zuwa Azahar aka sallame su, don an tabbatar da lafiyarsu ita da baby'n, suka koma gida. Lokacin da labarin haihuwar ya je gidansu can Rumoh kuwa, Innar su Abubakar cika ta dinga yi tana batsewa, kowa sai da ya fahimci cewa ba ta farin ciki da haihuwar. _____________________________________ Ba'kin cikin da Zainab ta yi akan haihuwar nan ba d'an kad'an bane, ita a kullum tunaninta yadda za ta raba Hafsat da gidan, ba ta kai ga cimma nasara ba, sai kuma ace Hafsat ta haihu. A ranar da daddare ta sami Abubakar a d'akinsa zata yi masa hauka, ya dakatar da ita da cewa "saurara Zainab, me ki ka d'auke ni ne? Mahaukaci ko me? Duk abinda ki ke don kinga ina rabuwa da ke sai aka ce miki ban san ciwon kai na ba? Ko kin zaci ban san ki na family planning ba? To tun da ke baki shirya Haifa min yara ba Allah ya bani wadda za ta iya meye damuwarki? Ki fita daga nan ki bani wuri tun kafin ranki ya 6aci." Ganin yanayin fuskarsa, yasa ta juyawa jiki a sanyaye ta fice, ta na shiga d'akinta ta fad'a akan gado ta fashe da matsanancin kukan ba'kin ciki. A 6angaren mai jego kuwa suna cikin farin ciki da walwala, ga kulawar ta musamman da suke samu ita da baby'n ta daga 'yan uwa da shi kansa maigidan. Sati ya zagayowa akai suna, yarinya ta ci sunan Goggo, wato Habiba, ana kiran ta da Muhibba, shagali sosai akai na sunan, anan na had'u da su Maryam wada, Badi'a, Maman twince, Maman Abba, Maman Noor, Salamatu, da duk 'yan *DUK KANWAR JA CE* fans, sun zo da abin arzi'kinsu, ana ta kashe salfie da mai jego. Taron suna ya tashi lafiya, kowa yana son barka, sai gab da magariba in 'kokarin tafiya na had'u da Rashma, da Princess sun zo wai zaman jiran 🅱️K suke, ganin dare na neman yi musu suka taho, suka barta. Washegari mutanen Rumoh suka tafi, kowa d'auke da gift d'in da aka raba, na sunan Baby Muhibba. _Ummu Aisha_ [7/1, 6:49 AM] Wasila Z . A . W: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦 *DUK KANWAR JA CE* *Story and Writing by* *Ummu Aisha* *ZAMAN AMANA WRITER'S Z.A.W* _(Gidan Zaman lafiya da Amana insha Allah)_🤜🤛 4️⃣5️⃣ 🔚🔚🔚🔚🔚 Hafsat ta ci gaba da rainon 'yar ta cikin kwanciyar hankali, yarinyarta tana ta 'kara girma. Bayan ta yi arba'in da sati d'aya ta shirya tafiya Rumoh, don gaggaisawa da 'yan uwa, ta had'a tsaraba sosai, Abubakar da kansa ya kaita da nufin bayan kwana uku zai aika a d'auko ta. Sun sami Inna Kulu kwance babu lafiya, take Abubakar ya d'auke ta zuwa asibiti, bayan gwaje-gwaje, an tabbar da ta na da ciwo suger, nan dai aka basu magunguna, aka fad'a musu irin abincin da ya kamata ta dinga ci. A ranar ya juya, ita kuma Hafsat ta zauna, washegari ta dinga ziyartar 'yan'uwa, kowa ta je da abin alkhairin da zata ba shi, kowa yana san barka da ita. Ranar da zata tafi, dagewa tayi sai ta tafi da Inna Kulu don tana bu'katar kulawa ta musamman, da farko Innar ta ce babu inda zata, amma sai Saude babbar 'yar ta a mata dake kula da ita ta ce su je, shine ta amince, amma a ranta ta 'kudurce ba zata zauna a wurin Hafsat d'in ba. Babu yadda Abubakar bai yi ba akan su sauka a 6andaren Hafsat, amma Inna Kulu ta 'ke'kashe 'kasa ta ce ba zata zauna a wurin ta ba. Dole suka sauka a part d'in Zainab, ita kuma sai ba ta so hakan ba, don dai babu yadda ta iya ne. Washegari da wuri suka fita asibiti bisa jagorancin Zainab, bayan ta shirya musu abin karyawa ta kai musu, abin mamaki a lokacin Zainab ko fitowa bata yi daga d'akinta ba bare a sa ran za ta girka wani abu, ko don marar lafiyar. Asibitin Nasarawa aka kai ta, bayan binciken likitoci aka bata gado. Kwanata biyar a asibiti aka sallameta, bayan sallamar ne Abubakar ya ce ba zasu tafi ba, sai jikinta ya 'kara murmurewa. A wannan lokacin ne Zainab ta nuna musu asalin rashin mutuncin ta, dai-dai da abincin da Inna Kulu za ta ci 'kiri-'kiri ta ce ba zata iya girkawa ba, kasancewar an hana ta cin kowane abinci, saboda larurarta. Idan kuwa suka fito parlor ta yi ta mita kenan an 6ata mata wuri, babu girma babu arzi'ki suka tattara suka koma gun Hafsat. A nan suka ga kulawa ta sosai, haka tayi ta tattalin Inna, kamar ta raba ta da ciwon. Bayan an tabbatar da samuwar lafiyar Inna suka koma gida, cike da takaicin abubuwan da Zainab ta yi musu. Shi kuwa Abubakar ashe dama zuba ido ya yi yaga iya gudun ruwanta, aikuwa washegarin ranar da su Inna suka tafi, ya dan'ka mata takardar saki, don yace ba'a haifi matar da zata wula'kanta masa uwa ya zauna da ita ba ko wacece ita. ________________________________________ *Bayan wasu shekaru* Zuwa wannan lokaci abubuwa da yawa sun faru, wasu na dad'i, wasu akasin haka. Tuni Hafsat ta fara aiki a asibitin Abdullahi Wase, tun kammala bautar 'kasarta suka rik'e ta, zuwa wannan lokacin ta haifi yara biyu bayan Muhibba, akwai Fatima sai kuma Musaddiq, da Abubakar ya yiwa kansa takwara. Tuni Inna Kulu ta zubar da makaman ya'kin ta, don duk yadda taso takurawa rayuwar Hafsat Abubakar ya 'ki bata dama, dole ta ha'kura, ga kuma arzi'kin Hafsat d'in da ta ke ci, don kwata-kwata bata da 'kyashi. Kusan duk lokacin da aka sami hutun makaranta ana Kawo Muhammad ya yi hutu, shima Saleem yana zuwa, wani lokacin har weekend ya ke zuwa. Soyayya mai tsabta suke gwadawa junansu, sannan suna kula sosai da tarbiyyar yaransu. Tsakaninsu da iyaye da 'yan uwansu na Rumoh kuwa sai san barka, suna iya 'ko'karisu wurin kyautata musu. *Alhamdulillah* _Anan na kawo 'karshen wannan littafi, kuskuren da ke ciki Allah ya yafe min._ _*Sai kun jini a cikin wani sabon novel d'in da yaddar Allah,*_ _Ummu Aisha_