DUK DAYA 3 Na HAFSAT SODANGI (Mrs. Yusnusa Abdullahi Dabai) 1 Hakkin Mallaka (M) HAFSAT C. SODANGI COPY RIGHT HAFSAT C. SODANGI 2 GODIYA Godiya ta tabbata ga Allah majibincin dukkan al'amura mai kowa mai komai mahaliccin sammai bakwai da kassai bakwai tare da abin da ke cikin su. Tsira da amincin Allah su tabbata ga cikamakin annabawa shugaban manzanni annabin karshe annabi Muhammad SAW tare da alayen sa da sahabban sa da wadan da suka bima tafarkin sa na gaskiya har zuwa ranar alkiyama. SADAUKARWA Sadaukarwar littafin ta kuce makaranta littafi na cikin kasa da waje ubangiji ya saka da alheri ya kuma kara karíata zumuncin da ke tsakanin mu. 4 FADAKARWA Don Allah a lura da littafin don na bayar da addu'a wacce ayace ta Al-kur'ani mai Girma, alura ina yin bayar da addu'o'i saboda sanin ba kowanne yake iya kulawa da littafi ba in ya shiga hannun shi, to amma saboda yawan tanbayar da mata keyi- shi yasa na bayar da addu'ar cikin littafi na biyu da kuma wannan na ukun (3) akiyaye fatan alheri gare nmu duka na gode da kulawar ku. JINJINA Jinjinar takune Hajiya Lubabatu Shehu Illelah Gidan Rediyon Beijing, China. Da Jamila Usman Lamir Gidan Rediyon tarayya Kaduna, na gode kwarai da kulawarku. FATAN ALHERI Fatan alherin nakune Hairat Muhammad Muhammad G. Biu da Mrs. Lawan lai-lai Kankiya. Zaliha Abu Datti. Na gode. 5 GORO Shafa'atu Yahaya Sani mai nagge Maimuna Sani daga Katsina, Amina Adamu Garba a Maiduguri, Maimuna S. Musa, Nusaiba M. Abubakar, Zainab Dodo a Katsina, Binta hashim a Shanera, Amina Abdullahi 'Mee- Mee na gode da kulawar ku. KUNA RAINA Hafsat Lamara Azare, Zainab Dauda Benue' da Salamatu Dauda Rashida Dauda dukan ku iyalan gidan Alhaji Dauda dan Malikun Ikara, Hauwa isa FGC Nusaiba M. Abubakar, Zakiyya Abdullahi Katsina, Hadiza lalundi Hadejia, Amina 'Mee-Mee. YABO Yabon nakune Hajiya Salima Sulaiman mrs. Usman Maraya na huche Zamfara state, Allah ya raya mana takwarata 'Hafsat'. 6 INA SANE DA KU Murja maman Sultan, Army Barrack Warri da Zainab Zubairu bello, Amina Jafar Gumel, Zuwaira Muhammad Ibrahim, Zulaikha Musa yabubihd Zainab Rufa'I a Katsina, Zainab Abubakar liman, Zainab Sabo Sale Rijiyar-Lemo. Na gode da sakomin ku Allah ya bar zumunci. Amin. Na gode Hadiza Muhammad Sokkoto da Shawarar ki. TA'AZIYA Ina mika ia'aziya tag a Saudat Usman a Taraba, bias rasuwar yar-uwarta, ubangiji ya ji kanta da rahamar sa, mu kuma in tamu tazo da Allah ya azurtamu da cikawa da imani amin. 7 BAN MANCE DA KU BA Maimuna Muhammad kwanar Aforestation Yamadawa a Kano, Yasira Ahmad Lagos Yakubu Yahaya Azare Walida Aliyu Sokkoto, Uwani Bashir Abubakar Ummul- Khairi Umar mezun di Ummi Waziri Gidado, Fatima alheri ssgareku tare da iyalan ku. GAISUWAR SADA ZUMUNCI Gare ki da iayalan gidan ki duka. Hajiya Zainab Barau Patiskum, Ubangiji ya saka miki da alheri ya kuma kara kaunar dake tsakanin mu na gcde. HAKKIN MALLAKA Hakkin mallakar littafin na marubuciyar shi ne HAJIYA HAFSAT CHINDO SODANGI 08025078968 8 DAGA LITTA1TAFAN SODANGI 1. Uwar miji 2. Naga ta kaina 3. dabon wando 4. cikar alkawari 5. tabbataten al'amari 6. waiyo ya 7. yiwa 8. abu na 9. kifi na ganin ka 10. mata masu duniya 11. nufin Allah 12. me zamuce da maza? 13. da kamar wuya 14. shamaki 15. hattara 16. Biyan bukatar rai 17. Gani gareka 18. Mata da Kicin Din Su 19, Duk daya 9 Littatafan dukan su anyi sune kawai don fadakar wa da nishadantarwa ana neman uwa ga duk wanda yaga wani abin da yayi kama da al'amarin shi bada shi ba dole ne kawai, na gode. 10 Tsananin hakurin da maizube ke baiwa Ardo kan shirmen da na tabka ya sanya shi juyawa ya tafi ba tare da yace komai ba, shi kanshi Mahmud wai wayawa kawai nayi naga ya bar wurin tsugunon shi, amma bansan sadda yayi hakan ba. Bansan yanda Ardo yayi da su Mahmud da iyayenshi ba, na dai ganshi kawai yana yi musu rakiya zuwa inda suka ajiye motar su. Hakannan naci gaba da zama na a gida ina gudanar da al-amura na cikin nutsuwa da kwanciyar hankali a dalilin babu wanda ya sake taso mun da maganar data shafesu, nima kuma dama nafi son hakan don kuwa duk yanda nakai da son auren mutanen in har na tuna auren su yana tayar mun da hankali, yana nufin na bar Arco, wannan shi kadai ko da a yanzu yana da wasu 'ya'ya-mazan amma kuma ai basu 1sa komai ba, gashi zan bar zuwa Cin kasuwa zan bar zuwa farauta zan bar hasswa doki na, in dena zuwa wasan kirgel sai in tsinci kaina da tanbayar kaina anya sudin zasu iya debe min kewar abubuwan da zan raba dasu? Na riga na 11 saba dasu sun zama bangaren rayuwa ta gashi a birni nasan babu wurin yin sharo ba'a cin kasuwa balle su farauta. Bodejo kuwa gaba daya ya fito fili ta nuna mun bata son barina gida don haka zuciya ta ta zamo cikin kai kawo mai tsannani. Yan kwanaki kadan da tafiyar su Mahmud sai kuma ga sa'id ya sake dawowa da nashi iyayen, gaban na ya rinka faduwa gannin irin tashin hankalin da ya same shi wancan karon a lokacin da Mahmud da iyayen shi suka zo. Ina kwance kan gadon bodigo na rufe ido na ina barci don bana son tayi mun wata Magana akan zuwan nasu sai naji shigowar maizube ta samu wuri a bakin gadon bodijo ta zauna tace bodijo wurin ki na zo, ta kalle ta cikin natsuwa tace mata lafiya dai ko? Tace lafiya man, akan zuwan mutanen nanne Ardo yace inzo in sameki muyi shawara ga sa'idu da iyayen shi sun sake dawowa shi kuma yana so ya basu auren don ya hutar dasu dukan su zirga-zirgar da suke yi,.kuma koda tace ita dukan su tana son su a fahimtar da yayiwa mu'amalar ta dasu dukan su yana ganin sai' idu ne ya dace da 12 auren ta, domin kuwa akwai kunya da girmamawa mai yawa a tsakaninta da shi ko kuwa ke me kika gani? Bodejo tayi kamar ba ta ji abin da takc fadi ba, balle ta bata amsa, maizube ta gaji da jiran amsar ta, da ta gaji ta tashi tayi tafiyar sta, saboda ta gane ba zata amsa ba. Washegari, kuwa da safe ina jin Ardo yana gayawa maizube ya shedawa iyayen sa'idu cewar daurin auren zai zamo biyu ga watan Sha'aban don inyi azumi a daki na, maizube tace mishi yayi dai-dai. Jin labarin sanya buki na da Ardo da wani can wanda shi din ba cikin Kabilar mu ta bodii yake ba, ya jawo cece-kuce mai yawa a cikin kabilar tamu, su kuwa hausawa da yake mu mu'amala dasu cizon yatsa suke yi suna fadin inda sun san hakanne ai da suma sun shiga cikin maneman seungel. Kwanakin bukina suna matsowa cikin sauri tunda dama ba wani dibansu da yawa aka yi ba, rannan da sassate Ardo ya ware garke hudu na manya-manyan bijimaye yace aje a sayar da su a kawo kudin ayi musu suyaiyar kayan daki da dasu, maizube da sarkin fawane 13 suka hana Ardo yin hakan sukace ai bijimaye goma ma sun isa in yaso in anje anga ana bukatar kaii sai a kara da biyar aka samu ya yarda. Tun daga ranar 27 ga watan Rajab aka soma hidimar bukina a gidan mu wato tun kwanaki biyar kafin ranar daurin auren cikar da akayi a gidan mu ya wuce a tsaya ana bada labari, 'yari-uwa da abokan arziki na nesa da na kusa duk sun iso, ko ina ka duba a gidan mnu jama'a ne daga can kuma hidimar yanka da girki a keyi. shi kanshi sarkin fawa da iyalin shin sun dawo gidan mu da zama har sai an gama biki kafin su koma gidan su. Ranar Laraba 30 ga watan Rajab ranar ne akayi bukin saukar Al-Kur ani na, ranar ne kuma Ardo yayi alkawarin z2'a yi mun zaen asali na wato zanen da zai baiyanar da asalina ga kowa abin nufi shi ne dasu ko ina ka ganni ka gane ni din yar kabilar :caii ce. A wannar ranar ne kuma sa'id da tawagar abokan shi suka iso cikin su kowa har da Mahmud sune kuwa suka hana shi zanen da za' ayi mun ta hanyar biyan kudi masu yawan gas ke. Washegari da safe aka sanyani a lalle ko ban fada ba kuwa ansan madara aka fesa mun ran jumma'a da sassafe mahaifin sa' id 14 ya iso cikin tawagar mutanen tanfar ba daga nesa suka taho ba. Bayan san kowa daga sallar jummaa ne aka daura aurena da sa id ana gama daurin auren kuwa aka goce da wasanni iri-iri cikin su kuwa har da na sharo da daddare ganin duk jama'a sun nufi wurin kallon wasa saura dagani sai maizube, sai nayi nufin fita in tafi dakin bodigo don kuwa nasan in dai ba wannan damarce zanyi amfani da ita ba to kuwa ba ko shakka za'a tafi dani ba tare da munga juna ba, ni da ita ina fitowa na biyo ta bayan bukkar maizube ina tafiya a hankali cikin nutsuwa sai kawai naji wata mury1 mai sanyi ta kira suna na a hankali cikin rada-rada 'seungel' tun kafin in wariwaya in ganshi nasan wannen ne mai wannanmuryar naga na tsaya cikin mamaki da kadiwa ganni da matsanan cin tsoro da ya haddasa mun haduwa cikin rawar murya mai tsananin nace mishi Mahmud me kakeyi anan dukkansu suna wurin kallon wasa? WASAA..'ya fadi hakan da kakkaurar murya data fahintar dani kuskurena kana bin da na gaya mishi. Kina nufin kallon wasan anren ku da sa iduune ya kawoni? Zuwa nayi don in sheda miki cewar kinyi kuskure da kika zabi 15 sa idu akai na, kinyi kuskure da kika watsamun kasa a ido a kan sa'idu, kinyi kuskure da kika auri sa'idu kika barni bayan kin san ni din na riga shi ganin ki, na rigashi cewa ina son ki, na fishi son ki, na fishi bukatar ki, amma dole da hakan baki ji kunya taba kiak mun irin wannan cin zarafin, to nima kuma ba zanji kunyar gaya ba cewar zaman lafiya da zaki samu a gidan takaitacce ne, kwarai don kuwa zanyi ruwa inyi tsaki wajen ganin baki sami zaman lafiya da kwanciyar hankalin da kike bukata ba, na kai matukan wajen tsorota da kalaman na shi *ban* in sam in in dan mai * yazre* har in ganza mishi cewar *bunice na zabi sa'idu na barshi ba tuni haryayi nisa don kuwa cikin sauri yake tafiya ina hangen shi harya bata cikin jama'ar dake kallon Sharon da akeyi, neman wuri nayi na tsuguna in wani iridn matsanancin kuka me zaisa Mahmud yayi nun haka? Me zaisa ya zargeni da cewarna zabi Sa... sunan ya kasa karasawa a bakina. Maizuabe ta iso wurin cikin sauri tana mai haskani datachil,me ya fito dake nani ta tambayeni tana mai zuba mun ido, ban iya cewa komai ba,in bandakukan danakeyi, tasa hanu sta kamoni ta dawo dani dakin ta tana 16 tambaya ta nace mata Mahmud ne na bata labarin irin magan-ganun da ya gaya mun, hannu biyu ta saka ta rufe baki cikin salati, tace shi din ? ai kuwa da dai bai kamata ace ya fadihaka ba, shi aure ai ikon Allah ne, amma bari inje in gayawa ardo don a kira shi a bashi hakuri tun da ba asan me yake nufi da fadin hakan ba, da sauri ta juya ta fita ba'a wani dade ba saiz gata ta dawo, ardo yana biye da ita suka shigo, ardo ya zuba mun ido yana kallo na cikin natsuwa, yace a ina kika ga Mamuda sengel? Cikin muryar kuka na gaya mi shxi sai da ya gama jin ba ani na sai ya kalli mai zusbe yace mata ni ina da tabbacin ba Mamuda ta gani ba, domin shi akan idox na ya shiga mota tare damahaifin sa'idu suka kama hanyar tatiya gida bayan daurin aure, sauka yayi a hanya ya dawo ko kuwa ? kuma a irin mutuncin mahmudu ace ya fadi irin wannan maganganu, amma dai bari na tura samari ta ko ina su dubo mun shi, in shi din ne nan da wasu yan mintoci za'a zo da shi tun da bazai yiyu ya tsere musu ba, tun da tafiyar ta kafa ce. 17 Har gari ya waye babu Mahmudu babu wani wanda yace ya gan shi, duk wanda aka tanbaya sai yace ai ana gama daurin auren shi ya tafi tare da mutanen da suka tafi a wannan lokacin, wannan dalili yasa maizube ta kafe kan cewar wai wata kila wani cikin aljannun dake dajin na gani, shi ne ya fito mun cikin siffa dakamannin Mahmud,nikam kara firgita nayi da bayain na maizube, menene gani na da aljanin dajin da zai zomun cikin kamannin Mahmud yana mun irin wannan maganar ? Washe gari, ranar Asabar ne aka shirya za'a tafi daasuba na sake fitowa inje in sadu da mahaifiya ta ko akwai wata maganar da zata gaya mun nayi sa'a na sameta ita kadai tana zaune bakin gado tana shayar da Yusuf, durkusawa nayi a kafa, nan da nan kuma hawaye suka kama zubowa daga idanu na, cikin kuka nace mata inna ki yafe mun ta dan kalle ni kadan ta kawar da kan ta gefe takce nikam me kika mun ? ki danje ki roki ardo gafara, nace mata to, mun danyi shiru na lokaci kadan, sai naji ta soma yimun magana in kinje can din sai kiyi hakuri, saboda zama cikin bare 18 ba karami bane, rayuwar yau din nan dakike gani shi aure kayi shi cikin dangin ka ma yaya ka kare dasu ? balle kayi shi cikin mutanen da basu san asalin ka ba, basu san dangin ka ba, daga ganin mutane kawai kin kama kan ki, 'yan uwanki a dalilin su jikina ya sake yin sanyi jin maganganun ta nan take na katse kukan da nakeyi nacemata inna bakice mun kar inyi ba, tace to, akan me zan fadi hakan tun da ardo bei hana ba 2 tsawon lokaci tana mun nasiha game da zaman aure da kuma zama da mutum, shi kan shi data gama sai tace min in harkika bi magangannun dana gaya riki ka daici zại miki sauki don ba zaki rasa abokan mu'amala ba,jin dadin ganin yandata saki jiki tayi magana da ni zai yasa na gaya mata abin da ya tsaya mun a rai, game dadan uwana nace mata inna don Allah ki taimaki yaya jauro ki sa ido kan al'amarin zaman shi da matarshi kar kuce ku manya ne, babu ruwan ku da su, jume wahala take ba shi dana ga bata kwabeni kan maganar tawa ba,sai na bata labari tun farkon zuwan jume gidan har kawo abin daya faru tsakani na daita na bina rafi da tayi da kalaman da ta gaya mun da nayi shiru sai ta kalle ni tace mun jeki 19 kargari ya gama waye wa,mutane su fito su gan ki anan, nace to, na tashi na fita, na kasa wucewa in nufi dakin mai zube, a dalilin shima yaya jauro ina son ganin shi, ina dosowa kusa da bukkar su na hango shi a rakabe jikin dakin ganni ba, sai dana iso wurin shi nace mishi yauma ta kore ka ne ? yayi zunbur alamar bai yi zaton gani na ba, 'seungel' yana kiran sunan nawa sai kuwa hawaye suka zubo sharrrrrr daga idanu shi, nayi maza na sa hannaye na biyu na share mi shi ina fadin karkayi kuka yaya jauro, maza basa kuka, barni ni inyi ni dazan tafi in bar yan-uwa na in barku dan sukan ku inje in gamu dawasu mutane can da ban da bansan komai nasu ba, jume ta leko ta gan mu tayi wani lalataccen murmushi tace za kuma ki tafi ki barni da shi yaya kenan ? na tayata murmushi nace zaki ci karen ki babu babbaka, amma na dan takaitaccen lokaci ne na kamahannun yaya jauro na ja shi-muka koma bayan bukkar mai zube muka tsuguna don kar a hango mu, mu kayi ta magana, tausayin shi yayi matukar kama ni, na kalle shi nace mi shi ka yafe min abin da nayi maka, yaya jauro kudin ka da ka binne a yashi ni na dauka. 20 Da sauri yace kai! Aradu jume akwai wayo dama tashe kene kika sace nache mata kul dangin mu bama sata, tome yasa kiaka min haka, sengul gashi yanzu danban bata kudin buki da yawa bata hanani bar shi tun da akafara bukin nan ban yi barshi sosai ba, to yanzu ina sauran suke ? ko kin kashe duka ? nace mi shi ban kashe ko kwabo ba, na dai cusa sune cikin ciyawar dakin goggo, ta barin kudu, in ka cusa hannuka zaka ciro su, ya zuba min ido cikin takaici yace to yaya za ayi in dauka a nan me yasa baki cusa a dakin goggo na ba ? wato bodejo' race to, kayi hakuri, yaya jayro ka yafe mun, yace babu komai, sengel aike yar uwata ce yanzu dai damuwar itace sai yaushe zan sake ganin ki? Na daga ido na kalle shi, hawaye suka zubo mun a ido na nace ban sani ba, yaya jauro na dai san kawai na kwaremu dana yarda na bar auren korijo da kullum sai mu rin ka hadawa arafi muna hirar mu mai zube ce ta sake fitowa tanan wurin ta dakamun tsawa me ya sake fito dake? fitinanniyar yarinya kawai, nayi maza na tashi na koma dakin ta, shi ma yaya jauro ya nufi nashi wurin. 21 An shirya tafiyar da karfe goma na safe ne, abin da naji mai zube tana gayawa mutane kenan tun tara bata yiba aka kaini wurin ardo yana zaune akan gadon shi ya bani umurnin yin hakan yaya jauro na, ya shigo ya zauna kusa da ni,ardo ya kalle shi yace mishi jauro yau zaka rabu da'yar uwar ka, yaya jauro yayi maza ya sunkuyar da kai kasa, alamar boye hawaye yakeyi, ardo yayi amurmushi yace aure kenan karfin shi yana da matukar yawa yanzu dai ga shi zai dauke seungel daga wannan dajin namu ya akai ta can wani wurin da mu bamu sani ba, ya kuma hadata da mutanen da tata sani ba, hakane ko ba haka bane ? yaya jauro yayi maza sssyace hakane ardo, to shi aure sunane amma daga zarar anyi shi sai kuma wajibai su shigo cikin shi tsawon lokaci ardo yana smun bayani akan girma da daagrajara aure, daya gama sai yace min kuyi matsaikaiciyar rayuwa ke da mijin ki, kar ku tsananta kwadayin duniya saboda wani hadisi na Manzon Rahama SAW da yake cewa "Wani lokaci zai zowa al' ummah ta da zasu so abubuwa guda biyar (5) zasu so rayuwa su manta da makomar su, zasu so dukiya sai su manta da hisabi, zasu so abin 22 halitta su manta da wanda yayi halittar), zasu sO sabi, wato aikata zunubi su mance da yawan tuba, ma'ana neman gafara, zasu so mallakar manya manyan gidaje su mance da kabarin su. Ardo ya kalle ni cikin tausayawa yace nayi miki sha'awar rayuwar da kika guda rayuwa mai sauki, rayuwar da babu tsanani mai yawa a cikin ta, tun da mukan ai jeji muke zaune, to amma kowa da kaddarar rayuwar sa. Mata biyar ne kawai ardo ya yarda suyi min rakiya, abin yayi matukar batawa maizube rai, kanwar ardo da suke yaya maza turai sai yayar bodejo da suke daki daya daso kakata mahaifiyar bodejo, ita kuma sai ta wakilta kanwar ta mogurun,matarz aminin ardo altine sai ko kanwar maizube takko shikenan sai ko maizuben kanta suka zama shida. Motar da ta dauke mu hudu ne, ni da maizube a baya, sai ko Hajiya daso da tasi'u kamin sa'idu a gaba, ta biyu wanda shi ne mai yin tukin wai sunan shi jamilu, sai sauran motocin suka biyo baya, wandana angone da abokan shi, da suka tsuya-ganin wasannin da akayi. 23 Tafiyar ba mai tsanani akayi ba, a dalilin motar su sa'id dake biye da tamu suna ganin tasi'u zai daga kafa zasuyi maza su tsawatar mishi suna tanbayar shi saurin me kake yi haka? Don haka tafiya akayi cikin nishadi, muna tafe suna sanya mana kasunan wa'azi, mafi yawan ci kuma suna magana ne kan aure da kuma ma'auratan ga kuma kayan ciye-ciye iri iri sai dai nikam ban iya cin komai ba saboda kukan da nakeyi. Mun shigo birnin Kano ne cikin dare fitilu masu tsananin haske ko'ina akan tituna, nikam hanken har haskemun ido ya rin kayi a zuciya ta nace iko sai Allah, wato abirni ashe ba'a duhun dare, babu zirgar motoci akan shinfidaddiyar kwaltar, a haka tasi'u ya rinka bi daga wannan kwaltar ya koma wancan har muka iso inda ya shiga wani layi daya tsaya, a kofar wani gida, abin mamaki ban san yanda akayi ba ina bude ido sa'id na faragani a tsaye tare damutane masu yawasuna jiran isowar mu ko yaya akayi suka shige mu oho ? Sannnun ku da zuwa, sannun ku da zuwa, irin abin da mutanen ke ta fadi kenan, sa 24 hannu akayi aka bude kofar danake aka fito dani sai dai banga wanda yayi hakan ba saboda a lullube nake, sai da aka kaini wani wuri mai tsananin kanshi sannan naji ance mun zauna anan, na zauna na dan bude ido a hankali sai naga ashe daki ne mai matukar kyau, ganin maizube a kusa da ni ya sani naji dadi na gyara na tankwashe ajikin ta na kwanta sai shigowa mutane sukeyi suna yi mana barka da zuwa, ruwan sanyi suka fara kawo mana sannan suka fura aka kawo mana suka shigo mana da nau'o'in abinci iri iri, wadan da ma nikam ban taba ganjn su nayi ba, an dai yi sa'a sun yi dabara sun hada mana da fura da nono mai kyau, abin da yawancin mu muka ci kenan, sai ko naman kajin. Ranar lahadi itace ranar da iyayen sa'id suka yi wunin bukin su, abin da ya tabbatar mun da cewar lalle sa'id dan dangi ne daga yawan matan dake zuwa suna tsokana ta alamar abokan wasane su na gane yawan su ba na kadan bane. Washegari litinin, baki na kusa kusa sun tafi, duk wani wanda ya saura a lokacin to daga nesa yake, mahaifiyar sa'id wacce naii suna 25 kira umma ta shigo ta kira iyaye na cewar baban su sa'id yana son ganin su, suka tashi suka fita suka barni kadai, sai naga wata yarinya mai fara'a da murmushi ta shigo dakin da saurin ta tazo ta tsuguna a gabana, ni kuwa nayi maza na gyara lullubina na juya mata keya, sai naji tace mun kinga ai nice sahurar da yaya sa'id ya baki labari na wanke-wanke, mukayi na bari nazoi don ki gan ni in gan ki, ina jin ta fadi haka na juyo nima na kalleta mukayiwa juna murmushi, kama da sa'id takeyi sai dai ta fishi haske tace mun nayi murna da kik a yarda kika auri yayan mu, kin nuna mana kauna da son mu dama kuwa ya bamu labarin irin taimakon da kikayi mishi mu kuma..... bata gama ba su maizube suka shigo da gudu ta tashi ta fita ta koma wurin aikin ta. Maizube ce ta ban labarin abin da akayi cewar baban su sa'id ya roke su su tsaya suga an gama shiryamun dakina kafin su tafi, tunda shi ardo ya dankawa kudin a hannu yace mishi yaje ya saya mun irin abinda yake saiwa yayan shi mata idan zai yi auren su, shine tace mishi a'a ba sai sun tsaya sun ga wannan ba, su 26 kwana biyu ardo ya basu don lhaka gobe in Allah Ya kaimu zasu tafi. Umma ta shigo ta nemi wuri ta zauna tace gaskiya maizube bai kamata kiyi haka ba, ai in kun tsaya an gama komai shima zakuje ku bashi labari, maizube tayi murmushi tace seungel ai ta fita hannun ardo ta zama taku, ba zai damu da sai yaji abin da aka yi mata ba, ku dai kuyi hakuri da ita, saboda dalilai guda biyu, na farko ita din yarinyace da ta fito daga jeji, bayan haka kuma bata da kowa anan tana fadin haka hawaye suka zubo mata, nima ina ganin awayen maizube na kama wani sabon kukan. Umma ta shiga baiwa maizube hakuri tana fadin ai kuwa in Allah Ya yarda maryam gida tazo, babu abin da zai faru sai alheri, ita amana ai dayace, sannan in nasan bazamu iya yiwa yarinyar nan adalci ba bazan bari sa'idu yaje ya rabota daku ba, don haka don Allah ku kwantar da hankalin ku, kuma ina ganin zaku daga tafiyar gobe zuwa jibi,don ku din huta tukunna. Maizube tace a'a ai shima maigidan yayi wannan maganar na gaya mishi bazai yiyu ba, 27 don umurnin da ardo ya bayar kenan tace hakane. Bayan salar isha'I, ina kallo umma ta shigo da manyan jakankuna guda biyu, tace wa maizube baban su sa'id ne yace akawo musu, ta kuma kawo manyan kwallaye guda biyu na kayan tsarabar buki da sukayi, tunda sun san mu bayi zamuyi ba, don bamu sanda shi ba tace ayi tsaraba na kalli maizube nace mata goggo tafiyan zakuyi? tun kan taban amsa na fara y1 mata kuka ita da umma sukayi ta rarrashina sai dai kuma na kasa yin shiru, tasi'u ya sake shigowa dakwando nar. goro guda uku da dabino cikin kwarya da kuma kwalayen minti ya ajiye yace wai gashi na ardone maizube sai faman godiya takeyi tana fadin irin dawainiyar da akeyi dasu, shikam tasi'u murmushi kawai yayi yace shi kuwa yaya sa'id cewa bai taba ganin inda ake dawainiya da mutumin da ba'a sani ba, ba asan inda ya fito ba irin rugar su, maryam in kuwa hakane, goggo to mu me muka yi kunyi hidima da dan uwan mu kun kuma bashi aure ai mu bamu da abinda zamuce muku da alheri kuma gobe in Allah Ya kaimu 28 daga yin sallar asuba ne zamu tafi, maizube da sauran sukace mishi to Allah ya nuna mana. Tun kafin ayi sallar asuba har sun gama wanka sun shafa mai sun kintsa, umma ta kawo musu abin karyawa ga kuma wasu manya- manyan kuloli guda biyu wai maganin yunwar hanya,nikam tunda naga haka na kama kuka, umma ta shigo dakin tace mun ga ruwa can na kai miki maryam, shiga kiyi wanka,nace mata to, ta juya ta fita maizube tace mun to sengel kin dai san mutanen da kika zabi zama dasu, mutanene dabaki hada komai da su ba, na zumun ci, halin ki mai kyau ne kadai zai taimake ki a zaman da zakiyi da su, na umarce ki da ki rike al'anura guda biyu, hakuri da kunya, ban iya amsawa ba, saboda kukan da nakeyi, ta dan sakaici idon mutane tasa hannu cikin aljihun silet din ta ciro wani dan kwalban turare ta mika mun nasa hannu biyu na karba, tace a kirji zaki dan rinka mustsukawa, duk lokacin da kika san zakije kusa da mijin ki nace to, umma ta sake shigowa maryam ruwan nan sai yayi sanyi ? nace mata to, na tashi na shiga wanka, abin takaicin shine sai fitowa nayi 29 na samu babu su maizube, babu dalilin su, ai kuwa ban shafa mai ba dikunkunewa nayi cikin zani, nayi ta saman kuka, kuka kuwa mai tsananin gaske, umma tayi ta rarrashi na har ta gaji ban dena kuka ba, sahura ma ta shigo ta zauna kusa da ni haba anti maryam ba aure kika Z0 yiba? dama zaki sake bin sune ku tafi tare? Kiyi hakuri mana, kar ki jawa kanki wani ciwo, yauwa ni gam,a yay sa'idu ya shigo ina jin ta fudi unan shi ban san yanda akayi ba sai kawai naji kukan ya tsaya cak, rashin banji wani motsiba ya sa na dan dago kaina wai in gani ko zolayata take yi sai kawai muka hada ido da shi yana tsaye a bakin kofar cikin dakin, sanye da doguwar riga, jallabiya mai ruwan madara me ya saneta take kuka sahura? yayi tanbayar cikin wata irin murya mai cike da nutsuwa. Sahura tsace don iyayen ta da 'yan uwanta sun tafi sun barta yana matsowa cikin wata irin tafiya mai cike da takama yana magana a hankali gaya mata mana sahura nan gidan ma akwai umma da su tasi' u sannan kema gaki ko kuwa ? tayi murmushi tace hakane yaya. ummata shigo yayi maza ya ja 30 baya nuna alamar girmamawa yace mata ni zan fita tayi maza ta waiwaya ta kalle shi tace da sauri hakan? Yace eh umma zan jene in kaiwa masu zanin nan zanin su, tun shekaran jiyan can ya kamata akai musu, tace hakane amma sai ka tsaya ka karya tukuna don haka kake yi kace zaka fita yanzu ka dawo inka fita sai an ganka ya danyi murmushi yace bazan dade ba umma ai ma kinga rigar dake jiki na kiyi hakuri ki barni inje in dawo sai in karya a natse tace to maza jeka ka dawo yace to yayi maza ya fita ya tafi. Umma ta kalli sahura tace ke.haka zaKi bar yayar taki ba komai? Bazaki dauko dan abin kallo kikawo mata ba? Nan da nan sahura ta mike ta fita taje sai gata ta dawo rungume daT.V. Karami flat screening ta ajiye ta koma ta dauko D.V.D. ta jona ta sanya mana kallo abin yayi matukar burgeni, saboda ban taba ganin shi ba gaba daya na zuba idanuwa na kan T.V., ina kallo baki da hanci duk abude, sahura ta tashi taje ta kawo mana abin karyawa, masa ce da miya ga kuma kunun gyada dana tsamiya ta kuma sake fita taje ta kawo flask cike da 31 rowan zafi da kuma kayan tea nan ma ta ajiye sannan ta nemi wuri ta zauna tace da wanne zaki fara? Ni dai masa zanci da kunun gyada don zafi nake ji, bazan iya shan tea ba, na kalleta kawai nace kema kenan da garin kune kike jin zafin to balle ni kuma dana fito manbila' yankin da kowa yasan irin niimar dake cikin shi, me zaki karya shi? Ta bukaci sani nace ni na koshi ta zuba mun ido tana kallo na to ai mu ko bako baya cewa bazai ci abinci a gidan mu ba, umma ta karbi bakuntarshi ba kale ke umman ta shigo dakin da alamar wani abu tazo dauka tace me kika zukawa yayar taki sahura? Naji dadi da sahurar bata ce mata nace mata bazan ci koma1 ba, tace waina zan fara zuba mata da kunun gyada ta zuba tace muci a tare in kin ki mu in cinye ince tare mukanci kinga ba mai gane cewar ke kadan ki ka ci. Muna ci muna kallo sahura na mun bayanin firm din tana kuma gaya mun sunayen mutanen na asali da wanda suka fito suna amsawa wanda nikam gani nake tankar mutum daya ne kawai yake ta faman caccanza kaya irin sakin jikin da sahura tayi dani da kaunar da ta 32 nuna mun na farat daya, gashi kuma dama ban girme taba, bata girmen ba, sa'o'in juna muke sai nayi matukar jin dadin mu'amala da ita. Sa'idu ya dawo dakin alamar shigowan shi kenan daga inda ya tafi kannen shi sukayi mishi sannu da zuwa, banji abinda ya gaya musu ba na dai ga kawai sun yi maza sun tashi sun fita ya karasa shigowa cikin dakin yace sahura yaya bakuwar taki dai? Tayi murmushi tace lafiyar ta kalau ya dan kalle ni da gefen ido ya kawarda fuskar shi yace sai dai banga alamar kin iya saukar bako ba. Tayi maza tace da nayi me yaya? Yace to bikuwa a takure? Ta makure wuri daga ido duk hawaye da gani kasan ta tasa abubuwa masu yawa atare da ita? Tace to ai ita taki shafa mai yadan tabe baki yace to zuba mun kunun tsamiya a kofin can ki bani ki kumate ki samo mun abin nan tayı maza tace to ta zuba ta bashi ta fita ta tafi dauko abinnan din da yace mata wanda nayi ta zuba ido inga dawowan ta inga menene abin nan din? Yana ganin ta fita ya ajiye kofin kunun ya matso gabana ya tsuguna ya sakan mun wani irin murmushi daban taba sanin ya iya ba a 33 hankali cikin Magana mai sanyi da natsuwa yace Allah sarki, yau maryam din yaya jauro ta zama maryam din wannan mutumin ko ba sunan da kike kirana da shiba kenan? Na kara sunkuyar da kaina kasa ba tare da nace mishi komai ba, ya dan rage fara'arshi yace hidimar bukin nan ta sanyaki matsananciyar rama maryam gashi kuma banga alamar kina shirin yin abinda zaki daidaita da umma cikin sauri ba, ita umma da kike gani zaka ji dadin zama da ita in har zaki kiyaye al'amuran ta, nayi maza na dago kai na kalleshi don inji al'amuran ta yace ita din Fata son musu da taurin kai duk abin da tace miki kiyi ki rinka yin kokari kina yinshi nace mishi to ya sake kallona yace zaki ci abinci kuwa ko kuwa kin fiso inje nemo miki gittere? Na kawar da kaina kawai ya mike tsaye ya kwallawa sahura kira nan da nan ta dawo yace mata kizo kuyi kallon ku bari in karo muku yasu kasunan tace mishi to. Muna nan a daki da sahuira kallon mu mukeyi ko abinci aka gama turowa akeyi akawo mun inma Sallah zamuyi tare muke alwala muzo muyi sallar tare amma kuwa duk 34 lokacin da zata shigo dakin zata miko wani abu tare ko nono ko nama ko dai yayan itace. Washegari da yanma su tasi'usuka dawo daga kai iyaye na gida da sukayi sun kuwa dawo cikin farin ciki tare da fadin alherin da ardo yayi masu na baiwa kowa kyautar saniya, tasi'u ya shigo har inda nake ya durkusa ya gaisheni sannan ya miko mun wani dan kurlin abu cikin tsunma yace wai gashi inji yayan ki, nayi maza na sa hannu biyu na karba, na kwance shi zoben yaya jauro ne na azurfa daa yake matukar so ya aikomun da shi nan naji kewar yaya jauro ta sake kamani nayi ta kuka sahura tana ta bani hakuri har ta gaji ta mike tace bari inje in kira umma ko yaya sa'idu don kar suzo suce ban iya kula da bakuwa taba sannan ne na share hawaye na. Kwana biyu muna nan a haka aikin mu kenan ni da sahura kallo sai ko ciye-ciye wanda bai da lokaci kowanne lokaci ci mukeyi, saboda abubuwa ne ba masu nauyi ba, su inabi tuffa kankana cob-cob ganyaki kowanne lokaci zakaji umma tana cewa sahura dauko abu kaza. 35 Kwana na hudu a dakin umma, rannan ma nayi wanka na jawo kaya na na manbila na sanya sahura ta kalle ni tace Allah Ya sauwaka, kullum kina cikin wadannan matsastsun kayan masu kama da ajikin ki aka dunka su sai kace bamu miki kayan aure ba? In baki sani ba in gaya miki akwatuna hudu yaya sa'id ya shake da kaya, gudumowan da akayi mishi ko tsinke biai samu shuga ba bagasu can a wancan dakin umma ta tarasu, ban san sa'id yana falon a zaune ba sai da naji yace sahura bakuwar taki kikewa wannan carin? Tace ai yau ba bakuwa bace yaya tunda ta wuce kwana uki na kuma yimata alkunya na wadancan kwanakin yayi dariya yace kina da gaskiya, to in karbo muku dinkunan ku dai kenan? Tayi maza tace mishi eh ya kuwa tashi ya fita zuwa can sai gashi ya dawo da kaya har da kayan shafe-shafe da na gyaran gashi da turaren ka dukan su na kayan kwąlliyar jojo ba, kai rinka gani sai kayi zaton bai yi kayan aure ba. Sahura tazo ta zauna tana dubawa cikin murna da farin ciki kai kace itace matan. 36 Da daddare umma ta shigo tazo ta zauna, abinda bata taba yi ba don haka nima na kara natsuwa na kuma rasa yawan hankalin da yake wurin kallon da nake ganin tanfar har abada bazan gaji da shiba tace mun maryamina wuni ? nayi maza na gyara zama cikin natsuwa kasa amsa gaisuwar da tayi mun don haka ni na shiga gaishe ta tana amsawa da aka sake natsuwa sai tace mun inaso ki dauka ke da sahura duk daya kuke awuri na babu wani banbamci in Allah Ya yarda kuma ni bazan banbanta ku ba sai in kece kika ki yarda da hakan. Duk wani wanda yayi mili wani abu a gidan nan da bai yi miki dai dai ba ki gaya mun in kinga abinda kike so inyi miki shima ki gaya mun ina kuma so in gaya miki bakuntar ki ta isa haka nan gidan mijin ki ne, kiyi walwalarki ba ayi ta ganin ki a takure ba, nace mata to. Ranar juma'a da safe bayan mun idar da sallah, umma ta shigo dakin na gaishe ta sai tace ke sahura taimaki maryam ta tsefe wannan kitson nata, tace to muka zauna da kibiya gudu biyu ni ina tsefe gefen dama ita tana tsefe gefen hagu, kitson amare mai matukar kyau ne akan 37 nawa wanda sai da aka zabo gwanar makitsiya tayi mun shi inda cikin dangin mu nayi aure wannan kitso da yasha manshanu kafin a tsefe shi. Sahura ta kidime ganin gashina, tace waw!!!, dama ashe boye gashin kitson yayi? Don Allah anti maryamwai manshanun da kuke shafawa kankune yasa gashin ku yake tsawo da kyau haka? Nace mata eh kema sai kiyi ta shafawa umma tana daga falo tace ai kuwa kin bata amsa mai kyau. Maryamn Sahura ce ta taimake ni na wanke kaina da ruwan shampoo yayi fes, sannan a sanya dirayar hannu ta lousar mun da gashin bayan an tajeshi tsaf, ya bushe ta shafe mun shi da mayuka kala-kala sannan aka shafa nayi wanka na fito na dawo daki na zauna na shafa mai na shafa hoda la'akari da 'yanmayin kwalliyar mutane da nake gani ya sanya dana shafa sai kawai na saka kwalli na bari haka, sahura ta sake warware gashin nawa tana tajewa tana fadin kai, umma zo ki ga gashin indiya kawai, yaya sa'id yaje ya auro mu gani dama kike kama? Ta sake dawowa gabana ta tsura mun ido cikin 38 nazari, jimawa kadan tace 'manisha patel' tace cikin dinkunan da yaya sa'idu ya karbo miki zaki sanya ko cikin' kayan auren ki? Bari in kawo miki kayan auren ki gani nayi maza tace mata a'a sahura, a'ina kika ga mutum yana kallon kayan auren shi? Ta kelkele da dariya tace to wa zai sa miki in aki kalla ba? Hi'um ai nikam dani za'aje yin soyaiyar kayan aure na, nace tafdi, siket da pant din dana sanyan sune na farko dana taba sanya irin su don haka ba karamin dadi suka mun ba, sahurace ta tilastani sanya brazier tunda ban taba sanyawa ba, sannan na zaka /ata doguwar riga mai rowan madara tasha ado ko da ban san darajar kaya ba nasan rigace mai daraja na dinko gyaran tana yafe a kaina bayar, sahurata nade mun gashin ya zama tanfar gammo abaya ta dauko turare tana fesa min tana fadin kai ashe dai yaya sa'idu yasan abin da ya gani, bari Allah Ya kawo yaya babba yau ta ganshi itace mai cewa bata ga abinda ya gani ba ajikin ki da yaje yayi wannan wahalallen aure na cin mutuncu nace mata waye yaya babba? Tace itace babbar yayar mu nan take sai na tuno da maganar su da Mahmud dana taba ji ina cikin wannan tunanin 39 Sahura ta katseni ta hanyar gaya mun kinga wadannan dogayen rigunan duk da tsadar su Buda goma sha biyu yaya sa'idu ya zuba miki a Cikin kayan ki, ai zaki sha ado tayi maza ta juya ta dauko madubi ta miko mun kalli kanki don Allah kiga irin kyan da kika yina karbi madubi na kalli kaina ni kaina da kyar ya rage ince mata ko dai bani bace na dai daure nayi shiru. Sa id yayi sallama ya shigo dakin wata yar rigance kawai kawai a jikin shi sai wani wando tirikwata, yayi matukar yin kyau ga kanshi shin a koyaushe a tare da shi ya danyi Waige-waige tanfar yana neman wani abu, sahura tana kallon shi tana murmushi ya dan gaji yace sahura ina amar yata fa nake nema tace ai gatanan ya bata fuska yace ina wasa dake ne? Amarya ta ta manbila maryam nake gaya miki ta kelkele da dariya tace ai itace ta zama 'manisha yaya ya dan rage fara'a yace mata ina umma? Tace mishi vanzu baba ya kira ta tana can yace to, jeki ki gyara mun dakina, tace to, ta karbi makullin a wurin nashi taná barin dakin yasa hannu ya saki labulan windunan hasken da ke dakin ya ragu ya matso 40 kusa da ni ya kamani nan take naji tanfar nunfashi na zai dauke, saboda tsorata da nayi na bude baki zan mishi ihu ya zare min ido yace shhhhh!!! Nayi maza na koma cikin natsuwa ta yace ne kike nufi da man da zakayi? Umma ta san an daura mana aure mene ne? a tsorace nace mishi me zaka mun saboda ganin irin rukon da yayi mun, yace ba komai zan dan mutsustsuka kine kawai don in fahintar dake cewa yanzu da dah ba daya bane. Yana fadin haka ya shiga aiwatar da wasu al'amura a kidime na kwala kira umma!!! Yace ki kira ta mana in ta zoma yi zatayi kamar bataga abindda nake yi ba, da sauri umma ta shigo alamar taji kiran da nayi mata tana shigowa taga sa id yana kokarin maida labulayen yanda suke, tace mishi kai sa' id kar in sake ganin ka a dakin nan, yace to, umma tayi waje, ita kuma ta karaso cikin dakin tace mun muje ki gaida baban ku ko? Nace mata to, na biyo bayan ta zuwa falon shi yana zaune kan kujera mai zaman mutum uku, ita kuma umma ta koma kan wata kujerar ta zauna, ni kuma na durkusa a kasa na gaishe shi, yayita sa mun albar ka daya gama sai umma tace mun kije ki gyara mana dakunan suyi kyau 41 ki debo gaushi a kicin ki sanya mana turaren wata nace mata to, naje na kama aikin da tasani sa'id ya sake shigowa zai sake yimun irin abinda yayi mun dazu, nace mi shi zanyi ihu, yace kiyi mana, sai ta gane na matsa dake tayi gaggawan mayar mun da ke wurina ba shikenan ba? Ranarda na cika sati guda a gidan ranar ne su yaya babba da yaya balaraba suka zo suka hadu suka kayi aikin gyaran wuri na suka jera mun kayan da babana ya bayar da kudi yace a saya mun, wuni sukayi suna aikin sai bayan sallar magariba suka tafi gida. Kamar kullum, sa'id ya shigo yayi hirar shi a falon umma da ya tashi zai tafi sai ya dan rage murya yace mata umma tace na am, ya danyi shiru jimawa kadan sai ya sake ce mata umma tace mene ne? yace uma inace dama rashin gyaran wurin tane yasa take zaune anan? Tace a'a ba shine dalili ba, yace ai to sai da safe, tace Allah Ya tashe mu lafiya. Ina zaune a wurin umma cikin kwanciyar hankali tayi mun hikimar dana saki jiki da ita yan kananan aikace aikacen ta ni take sanyawa bani ruwa in 42 sha maryam, dauko mun wancan kawo mun wannan in anyi baki tace inzo in gaishe su, wani lokaci ma in sahura bata kusa tace inje kicin in kawo musu abinci, shima sa'id din yanzu in ya shigo ni take sawa inyi mishi abinda yake bukata, tana bani umurnin inyi mishin kuwa zata kauda jiki ta barmu mu biyu shi kuwa yana ganin ta fita zai fara Magana yanzu nan ke umma gata tayi miki data rike ki a wannan tsohon dakin? Kinga yanda aka gyara miki wurin ki kuwa? Kice mata zaki shiga ki gani na makale kafada nace uh uh yace to muje yawo a mota zaga gari ki ga birnin Kano daga nan sai muje insaya miki abin nan na shekaranjiya tunda naji kina gayawa sahura yayi miki dadi. tace uh'uh banaso ya bata rai yace to kiyi ta zama a cikin dakin nace mishi to ya tashi ta fita da daddare ranar ma sai da ya sake tanbayar umma, umma ni sai yaushene ita maryam din zata koma wurin ta? Tace mishi sai Allah ya kaimu anyi sallah lafiya kannan ta gama wastsakewa ta zama 'yar-gida, yace to Allah Ya kaimu, ya tashi ya fita ko sai da safe baice ba, alamar ya fusata. 43 Washegari kuwa wajen karfe takwas da rabi na dare muna cikin kallon wani fim mai matukar kayu ni da sahura, umma ta lekoi tace mata jeki ki hadawa maryuam rowan wanka, taje tayi ina zaue a wurin ina jin kanshin abubuwan da ta zuba a ciki ta fito tace mun in shiga nace to, a tsaida kallon sai na fito, tace gaskiya sai dai in kin fito a mayer baya nace to, naje nayi wanka na mai kyau ga dadi saboda irin kanshin nayi matukar fita, gashi kuma dama tuni na kara kayau na kara 'yar-kiba a dalilin hutun dana samu na fito na shata mai, sahura tn tayani gyara gashi na wanda nake ganin tanfar kullum karuwa yake yi, saboda irin kulawar da yake samu, wani boil mai matukar kyau umma ta baiwa sahura ta pani na sanya dinkin shi ma yayi kyau har bai yiwu in tsaya kwatan tawa siket ne da doguwar rigan sai dankwali dan karami, a dalilin rigar taci yadi maiyawa, gashi tasha adon zare abin gwanin sha'awa, ta cire mun 'yankunne abin wuya da wara-warai duka na zinariya na sanya tunda nazo gidan ban taba kyau irin nayau ba, dana gama na feshe jiki na da turare don na riga na saba kuma na koma na zauna sahura ta na cewa 44 kan uban can, ke aima ni yau sai naga kamar kin fiye mun manisha patel din kyau, bari in sake kallon ki in gain dawa kuma kike mun kama? Umma tace mata ke matsani ki bani wuri mara kunya kawai, umma ta nemi wuri ta zauna tace mun ga gyale mahadin kayan nann a gefen ki yafa zan kai ki wurin baban ku yasa miki albarka daga nan kuma sahura zata raka ki dakin ki sai muyi fatan ubangiji ya baku zaman lafiya dafahintar juna ke da mijin ki, inajin umma ta soma wannan bayanin na soma kuka ita kuwa sai rarrashi na takeyi bafa wani wuri . ne mai isa na,ga gidan can ga kofar shigannan a tsakar gida, duk lokacin da kike so zaki shigo don haka bamu rabu ba, muna nan tare ina kuka nace mata kiyi hakuri ki barni anan, kawai tace bazai yiwu bane nima bay au naso komawan naki ba, naso ne sai anyi sallah tukunnah, to sa'idu yaje ya kaini kara wurin baban ku sai kuma yace yau din nan in baiwa sa'idu matarshi ai kuwa kin ga babu hali in kin bi wannan umurni tashi muje yayi muna gardama dake yayi zaton taurin kai ke gare ki akan dole na mike na biyo bayan umma zuwa dakin 45 babana, durkusa a kasa ko gaishe shi ban samnu yiba saboda kukan da nakeyi. Baba yayi gyaran murya ahankali yace mu karanta Salatin Manzon Rahama 'S.A.W da aka shafa fatiha sai yace maryam sai kiyi hakuri wurin sa'idu, danan duk dayane na bada umurnin ki koma can ne yau saboda shi din yafi kowa hakki da son ki, kuma taya shi mukayi a zaman da zakuyi in har tana so mijin ta yasota kinj ko? Nace mishi to in kinje dakin ki duk abin da kika gani nakine, mahaifin kin e ya bani kudi bisa amana yace inyi miki irin yanda nake yiwa yayana to nasa yayan ka sun zo sun je miki siyaiyar san kuma zo sun gyara miki komai har yanzu kuma kudin ki basu kare ba, su da sunje a kara suya miki zinari tunda ajiyar kudine bayan haka kuma abin adone nace to sai shawara mijin ki takuna tunda shike da hakki kan fadin abinda ya dace ayi miki da dukiyar, to shi da na gaya mishi sai yace kar asuya miki Zinari tunda shi ya sanya miki kala biyu a cikin kayan auren ki, kudin ki yace a ajiyesu ya kai miki ajiyar su a banki kin gane ko? Yace tashi ku tafi, sahura Ubangiji Allah Yayi muku 46 albarka, umma tace amin. Suka fito tsakar gida na dan tsaya kadan tanfarb azan tafi ba, sai naji umma tace kuje mana,sahura sai ki tayata kwana tace to, na danji dama-dama na bita muka shiga kofar. Faffadan tsakar gida mai cike da furanni masu ban sha'awa muka fara tararwa can nesa kadanne gidan yake, harabar gidan cike yake da fitilu masu kama da bishiyoyi ta ko'ina haskene, nan take maganar da sa' id yayi mun a manbila ta fado mun 'ni talaka ne maryam bani da komai amma ina son ki ina kuma da sanar dake azan iya rike ki. Muk nufi inda ginin gidan yake, a bakin kofar shiga sahura tayi sallama daga can ciki na jiwo muryar shi yana amsawa, shigo mana, sahura tace ai ni da anti maryam ne nan da nan ya fito kice kin kawomuun amarya ne to ga wurin kin an ku shiga muka shiga muka tarar falone da dakunan kwana biyu sai kicin da toilet guda biyu daya a babban bed room din daya kuwa a cikin falon anyi matukar kawata wurin da kayan alatu da furanni mai kyau gashi duka dakunan guda biyu Suma ansanya musu gadaje sun kuma sha 47 shinfida sai kamshi wurin yake yi, nayi mamaki cikin zuciyata da baba yace komai na gani ardo ne ya bada kudin shi harma wasu kudin sun ragu ko nawa ya bayar oho? Kai wurin yayi kyau inji sahura, su tasi'u da jamilu suka shigo alamar dama suna tare da shine a falon shi sa'id ya biyo su yace ke sahura ga kicin ki kawo muku dan abinda zaku citare to, ta tashi ta shiga taje ta kawo suka hadu suka ci, suna kira nikam nace na koshi su tasi'u sukayi mnun sallama tafi. Sa'icl ya sake shigowa ya gan yace au ke baki tafi bane sahura? Tace ai ni tayata kwana zanyi yace au to yana da kyau to zo in aike ki suna fita na dauko turare na cikin faduwar gaba na mustsuka a jiki na kamar yadda maizube ta gaya cewar inyii da zarar an kaini daki na, sa'id ya dawo babu sahura nace mishi ina take? Yace taje gida ban taba ganin inda akayiwa ango irin abinda umma take mun ba, ta rike mun ke kwana goma sha daya, sannan yanžu ta kawo mun ke tare da yar taya kwana, tashi kiyi alwala muyi sallah, banyi musu ba, koni ardo yasha gaya mun muhinmancin wannan sallar, mun idar ya zauna yana mun yan hire-hire, 48 yawanci akan manbila ne, ina bashi amsa can sai yace mun kina tunawa da dokin ki kuwa? Nace mishi eh yace to zo muje kiga zanen shi da nayi-nayi hamzarin yarda da bin sa'id don inga zanen dokina da yace mun yayi sai muka wuce falon shi, wanda yake babbane kwarai don ya kusa biyun nawa nan din ma dai fa fatin shi kusan irin na wuri na ne can cikin dakin shi, muka shiga wanda yayi matukar kayatawa ga hoton dokin naki yaya ki ka gani? Ya dauko shi ya bani nace kai amma Allah Ya san kaiya zane ai komai na jikin yidi akwai shi a zanen nan. yayi murmushi yace to na gode Allah tunda kika gaya mun haka da bakin ki ya karbi hoton ya ajiye na juya zan tafi yayi maza ya tsare kofar yace kira na kira ki muyi bawai don kiga dokin bane kawai... ya tsareni ya shiga aiwatar da wasu al'amura a tare da ni dana gane abin da yake nufi sai na bijire mishi gaba daya saboda kashedin dana sabaji maizube tana mun cewar yin hakan ba karamin laifi bane maimakon yayi kokarin fahintar dani a natse sai kawai yayi anfani da karfi abinda ya hardasa tsoro mai tsanani a tsakani na dashi, na zama babu abinda nake tsoro kamar shi, duk lokacin 49 dana ganshi sai jikina ya dauki rawa a rinka kuka ina rokon a mai dani manbila wurin iyaye na, abinda yayi matukar daga mishi hankali shi dakanshi ya lura sahura yace mun in bita mu koma wurin umma, da sauri nayi hakan na koma kan gadona da dama muke kwana ni da sahura sai dai ya shigo nan ya ganni a yanzu kan ma ko gaisheni yayi ban amsawa. Umma kuwa ta tasani agaba kowanne lokaci rarrashi na take yi tana gaya mun maganganu masu dadin gaske da zasu kwantar mun da hanakali ince mata to in tace to yau zaki koma dakin ki ko? Sai yace mata a'a nibazan sake komawa wannan gidan ba, ta zuba mun ido cikin damuwa tace to yaya za'ayi ayi auren a haka? Maryam bafa mu muka auro ki ba, shi wannan da kike tsoro shine mijin ki, ban san tunanin da tayi ba sai ta soma aikena ni da sahura in mun shirya zamu tafi sai tace bari sa'id ya kaimu a motar shi, shi kuwa in muka fita sai ya biya damu ta shagunan sai da kayaiyakin ciye ciye iri-iri, wani lokaci har wuraren yawon shakatawa yake kai mu sai mun gama sai ya kaimu wurin aikan umma,kafin mu 50 dawo gida, a haka har sai umma ta fara aikena ni kadai tace ya kaini in muka fita sai yayi ta yawo dani gidajen abokan shi masu aure, in muna dawowa a hanya ya rinka mun Magana, kenan ke maryam yanzu ke a ina kika ga mata tana tsorosn mijin ta in ba ke ba? Yanzu gidansu wane da wane da muka je baki ga irin mu'amalar da suke yi ba? Amma ke kullum kina tsoro na, kiyi hakuri ki dawo dakin ki kin ji? Ince mishi uh uh. Rannan dai ana gobe za'a fara azumin watan Ramadan umma ta sake zaunar da ni a gaban tat a shedamun cewar zan koma daki na don bai kamata ace har acikin wannan wata mai albarka bazan iya zama da miji na in samu ladan shi ba, kuma bata so taga hawaye a ido na in har na yarda cewarita din uwace a wurina. Don haka banyi kuka ba, tashi kawai nayi nayi sallah na kuma ce mata sai da safe, sahura tayi mun rakiya ta dawo ina zuwa na nufi wuri na sa'id ya leko yana murmushi kin dawo ne maryam? Nace mishi uh bai sake kulani akan wani alamari sai dai da asuba kawai zai tashe ni inyi sahur. 51 Rannan ranar shabiyu ga watan azumi na tashi cikin wani hali da ban saba da shi ba, shine na ganin wani abu a tare dani, hankali na yakai matuka wajen tashi, nayi ta kuka yazo ya same ni yana tanbaya ta mene ne? na gaya mishi ya dan tabe baki yace to ai duk lefin ki ne, maryam ana zaune tare kince sai kowa ya rinka kwana a dakin shi, kinga da muna tare ai da haka bai faru ba, nayi maza nace mishi Ciwone ya kama ni? Yace a'a ba ciwo bane sai dai inajin rashin kula da aure ne ya kara kawo hakan daga yanzu ni zan rinka zuwa nan ina taya ki kwana don br zai yiwu muyi ta zama a haka ba, yanzu tunda abin da kike ciki kenan sai kici abinci kawai inya so bayan sallah sai ki rama azumin, na kalle"shi nace nifa rabon da insha azumi har na manta yace to wannan dai kici abincin ki kawai tun da ai bazan saki kiyi wasa da addinin ki ba, gashi kuma naji iyayen mu duk suna cewa kiyi mun biyaiya da irin wadannan kalaman sa'id ya sani na karbi tea din da ya hada mun nasha. Tun daga rannan sa' id ya dawo da kwana daki na, kullum mukan fara kwanciyar ne ina 52 karshen gado shi yana farko, sai dai in na farkane sai ingi lamarin ya canza, a haka - a haka har na saki jiki da miji na. Ranar sallah bayan sakkowa daga Sallar Idi sa'id dawani abokan shi da suke yawan harka tare Umar da Tasi'u suka nufi manbila bayan sun jibgawa motar tasu tsaraba mai matukar yawa tasi'u ne yake tuka su, ni kuwa suna tafiya na dawo wurin umma da zama, mukayi hidimar sallar mu tare, amma kuma nayi matukar jin dadin sallah ta, saboda irin kayan kwalliyar da aka tara mun ga kuma abubuwan-ciye ciy gashi jamilu yayi ta kaimu yawo da gidajen yan-uwa duk abinda aka zo dashi kuwa sai umma tace wai ni in dauki kashi biyu sahura da jamilu kashi daya, sai nice nace a'a umma,muyi raba dai dai kawai, sahura tace a to, mun gode miki kinji, antin mu ita umma bata san mun fiki son kudi' ba, tunda ke aikin riga kin kama yaya sa'idu a hannun ki me kuma kike nema? Nace ai haka kika ce? To na fasa raba dai dai din, sahura tayi maza fa shiga bani hakuri ita kam umma dariya tayi ta tafi ta bamu wuri. 53 Kwana biyu da tafiyar su sa'id suka dawo lokacin kuwa da yanma ne muna dakin umma muna hira, sai kawai naji wata yar siririyar murya tayi sallama cikin sauri na dago kaina don tabbatarwar da nayi mai muryar tawa ce gani nayi tasi'u yana tashe daita da karfi na bugi kirjina nace hiii malle.............. . sai kawai na soma kuka gaba daya dakin suka kwashe da dariya ita kuwa umma kamo malle tayi tanata faman yi mata sannu da zuwa har sa'id ya shigo ban dena kuka ba har ya gama abinda zai yi ya fita yace zaije yayi sallah. Bayan sallar isha'I, Tasi'u ne ya fara shigowa yayin da sa'id yake wurin baba, Tasi' u suka gaisa da umma tace kai kun sha tafiya ina umar dim yake? Yace ai sai da muka iso tace to yaya baku sauke mishi nashi tsarabar ba? Tasi'u yace komai da kika gain raba shi biyu muka yi, muka ajiye mishi rabi muka dauki rabi, umma tace madalla Allah Ya saka musuu da alheri. Tasi'u ya kalle ta cikin natsuwa yace mata umma ban taba ganin karanci irin wanda akayi mana agidan su maryam ba, ardo ya 54 tanbayi yaya sa'id abin da yake so ya bashi? Yaya sa'id yace malle yake so a bashi yayi shiru alamar baiyi zaton abin da za'a tanbaye shi ba kenan, jimawa kadan sai yace to sa'idu ka wuce ka tanbaye ni wani abu, komai tsananin shi in hanaka in banda haka babu babu abinda zai sa in baka malle don kuwa itace madadin 'yar-uwarta a wuri na, duk da nace bazan hanaka ita ba, hakanan kuma ba kai zan baiwa ita ba, kai tsaye sai dai in baka ita ka kaiwa mahaifin ka, shin abáiwä rikon ta da mahaifiyar ka, amma ba kai da suengel ba, Lurma tayi murmushin girmamawan de ardo yayi musu tace Ubagiji ya raya mana ita, yaci gaba, mu kuwa nan da kike gaNn mu fulani ne don ni da yaya umar shanu hudu ardo ya bamu ya kuma kaiwa yaya sa'idu shanu goma ya kuma tsaya akan sai mun dauko su mun taho da su, da kyar ya yarda da rokon da yaya Sa'idu yayi mishi na cewar ya bari muzo mu debe su a lokacin da ya dace muyi hakan. Umma ta shiga godiya tana fadin Ubangiji Allah Yayi mishi sakamako da gidan Aljannah, da aka dan natsu sai umma tace mun 55 Jeki wurin mijin ki, ina jin bazai dawo nan ba, kuma don ya riga ya gaji banyi musu ban a tashi na tafi banga sa'id a falo ba, ban kuwa ganshi a dakin shi ba, ashe bayan kofa ya buya, ina cikin dube-dube sai kawai naji caraf ya rike ni, nayi matukar tsorata har na kwala ihu ya kelkele da dariya, na bata rain ace bukatar ka ta biya ka tsorata ni, yayi murmushi yace mifuitala' ma'ana wai bazai sake ban a taya shi murmushi nace kace mun in ka juri zuwa manbila wata ran zaka zama bafulatani, yayi murmushin gamsuwa da jin maganar da nayi yace ga dukkan alamu na riga na zama, kin dai ji bayanin irin alherin da baffa yayi mana maryam har ga Hafsat nan nazo da ita amma bamu ya baiwa ba nayi murmushi nace kai dai Allah Ya saka maka da alheri da kayi dabara ka tanbayO mana ita. Ana natsuwa da su hidimar shagalin sallah da akayi sa' idu ya sanya ni a makarantar koyon girke girke da yaki da jahilci, kullum zai saukeni da safe hakan nan zai dai-daici tashin mu yazo ya daukeni in muna dawowa kuma zamu biya kasuwa muyi cefene na abincin da 56 aka koya mana, in mun dawo gida shi zan girka mana a matsayin abincin dare, dama kuma na daren kawai nakeyi, ita kuwa malle wacce yanzu aka hana ni kira malle sai dai Hafsat tuni ta soma zuwa nmakarantar boko da Islamiyya, ko'ina tare da sahura suke zuwa komai nata a dakin umma take yi, tuni ta mai zama ta zama yargida, kullum umma cikin saya mata kayan kwalliya take in zata unguwa kuma itace 'yar rakiyar ta, takan shigo wurin na da safene kawai ta gaishe mu ni da sa'id ta tashi tayi tafiyar ta, malle tayi matukar shiga ran umma a dalilin ladabin ta da biyaiyar ta, gata mai aiki in dai tana wuri to babu yanda za ayi kaga wurin da datti. Zan iya cewa ban taba ganin ko inji labarin uwar miji mai hali irin na umma ba, sai ta hana sahura abut a bani, sai dą nayi wayo, shi ne in ta bani abinda nasan sahura tana so sai ince naci girma a bata ko kuma in karba ita in saya mata wani. Ni da sa'id kuwa babu abinda zance sai godiya zan iya cewa ya same ni ayanda yake so, shi sa'id mutun ne mai tsananin tsabta 57 wanda bai raina kazanta komai kankantar ta, ni Kuwa daman na riga na horu da aiki don haka komai.zanyi bana ganin wahalar shi. A wannan lokacin nayi nufin in burge miji na ta hanyar tsara girke girtke masu ban sha' awa a lokacin hidimar babban sallah. Tun ana jibi sallah ni da sa'id muka shiga kasuwa don yin sayaiyar kayaiyakin da nake bukata don yin abincin sallah, mun dawo gida na zauna ina kallon tulin kayan sallar da aka tara mun, lesuna biyu masu tsada dama dai wadannan nasan na sa'id ne tare da gyale da takalmi da jaka ga turaruka tare da under wears babama ankon leshi yayi mana ni da sahura, umma ma tayi mana ankon atanfa classic yaya babbama tayi mun atanfa yaya balaraba ma haka nace kai dadi kasheni ni yasu. Ana gobe sallah kuwa tun safe muka soma aikin abinci ni da sahura muka fara da kwabe-kwaben fulawa na cin cin da na cake, muka gama sannan muka shiga shirye shiryen nau'o'in da zamuyi wuni mukayi rannan a kicin har wajen karfe goma na dare, a lokacin nan kuwa gidan gaba daya ya gauraye da kamshi 58 har wajen su umma aiken jamilu biyu yana karbar tabi wai yaji wani sabon kanshin yana tashi. Sa'id ya leko kicin din cikin nuna dama kosawa yace aikin nan faya isa haka, ke sahura jeki ki kwanta ki huta na kalle shi nace ai anan zata kwana don mu tashi da asuba mu karasa baiyi magana ba, ya juya ya tafi nima ban tsaya a nayi maza nabi bayan shi yana shiga dakin shi ya juyo ya rufeni da fada, haka ake yi, sai kawai ki zartar da hukunci ba tare da kin shawarce ni ba, ban son kwanan nata anan, Ta? Ko kuwa neman sanadin kice tunda tana nan... .. nayi maza nace mishi ko kadan ba haka bane, tana wurina ni kuwa ina nan yace to jeki ki kawo mun cake din dana gain nace wane a ciki? Yace oho ina nasan sunan su? Ke dai kawo kawai in gani nace to nayi maza naje kawo mishi, yana kallon na cikin murmushi to gaya mun sunanyen su tukun na kafin in ci na tayashi murmushi nace mishi wannan sunan shi spiced honey cake, wannan family fruit cake, wannan surprise cake, ga kuma speedy orange cake, ga sponge cake, wane zaka ci a ciki? 59 Yace duka nayi dariya nace ba dai yanzu ba yayan sahura tunda nasan yanda cikin naka yake, kai dai bari in dan yankan maka a wannan kaci dandan in mai da saura. Duk da tsawon daren ba wani rantsuwa mukayi ba ni da sa'aid hakan kuma bai hana ni jaruntakar tashin sahura ba karfe biyar na asuba, muka cigaba da aikin mu kan gari yagama wayewa tuni mun kamala aiyukan mu har mun gyara kicin da gidan gaba daya, ko ina sai kamshi yake yi tanfar ba'ayi aikin komai ba, na shiga dakin sa' id na samu y agama kwalliyar shi hularshi yake gyarawa zai sa.iya na kalle shi nayi murmushi ya harareni, yace yau sallah ma bazaki iya bude bakin ki kice ma mijin ki yayi kyau ba, a hankali nace mishi kayi kyau, Allah Yasa yawan rai akayiwa yace t0 amin, ko kefa? Allah dai yasa abincin ya kammala kafin sakkowa daga masallaci. Nace aim un riga mun gama har na zuzuba dama zuwa nayi in gaya maka ko zaka zo ka gani ya biyo ni zuwa kofar kicin din na miko mizhi naman miyar a cokali yasa hannu ya karba tare da fadin kokarin ki dai bai wuce 60 ki koya mun cin tsame ba, in yaso 'yanmata suyi ta tsamenina kale shi kawai nayi murmushi ya dan lumshe ido nuina alamar jin dadin abin da yake ci sai ya sosa kunnen shi da dan yatsa sannan yace uh, lalle ne maryam na yarda kin iya girki, kin zama gwana ko maggi menu conpetition na kai ki nasan bazan ji tsoro ba, to bubbude in gani na shiga bude mishi manya-manyan kulolin dake rufe ina mishi bayanin su, sai da n agama sai yace to na cikin gida fa? Nace ai na riga nasa sahura ta shigar tuni don ina so baba yafara cin namann kafin yaci na saura yayi murmushin jin dadi yace kin keuta maryam Allah dai yayi miki albarka, nace amin, nan da nan ya kira jamilu da tasi'u yace musu maza kuje sukai su dawo kafin lokacin tafiya masallaci yayi, su kace to, suka tafi ya sake kallona aiki yayi yawane ya hana ki yiwa baba danbun namar da nace ko? Nace ai anyi duka na hada an kaiwa umma, yace to sannun ki ke dai Ni kam daga kan sa'id ne na dena yarda da cewar fari yana fin baki kyau, saboda farar fatar shi sa'id dogone baki mai kwarjini bakar 61 fatar shi sheki takeyi ma'abucin iya sanya sutura ne, zai yi wuya kwarai in ya sanya kaya kaga wani wanda ya fishi dacewa da irin wannan kayan. Nayi wanka na zauna nayi matukar gyara jiki na da gashi na don kuwa a yanzu nayi matukar kwarewa da iya gyara a dalilin kullum idan ya kaini saloon akayi mun gyaran kai kona faratu in muna dawowa gaya mun yake yi ki dai rinka kula da abinda suke yi nan ba da dadewa ba kayan zan suyo miki ki rinka yiwa kanki a gida ince mishi to. Kayan sailar da baba yayi mana anko ni da sahura na sanya sunyi matukar karbata na feshe jiki na daturare na kara gyara wurin gaba daya na fesa air freshner mai kamshin dadi sannan na fito na shiga wurin umma a kicin na sameta tana tuyan masa, na tsuguna kusa da ita na gaishe ta nayi mata barka da sallah ta masa cikin murmushi, tace mun ga abincin sallah maryam Allah Yayi muki albarka, na matsa can gefe ina zuba miya a kwanukan da sahura ta ajiye, umma ta kalleni tace kin yi kwalliyar ki zaki zauna cikin kicin din nan, banyi Magana 62 ba, naci gaba da zubawa ina tanbayar ta wannan yayi koa kara? In ta duba wani tace yayi wani kuwa tace kara nama da ruwan miyar, matar gidan mai iyali ce, ince to. Malle ta shigo rungume da kwano alama ta kai masune gidajen makwabta tasha kwalliya cikin wani leshi mai ruwan malmo, dinkin yan gayu umma ta sa akayi mata ga 'yankunnen tan a zinari a kunnen ta ga warawarai sun kama hannunta kanta yasha kitso da adon ribbon abun gwanin sha'awa dadi ya kamani cikin raina nace ina madai ardo yaga malle yau a irin kwalliyar nai da aka mata malle tace umma bakin ce zanbi su yaya tasi'u sallar idi ba? Umma ta bar abin da take yi tace kwarai kuwa tace to na ganshi a waje nace zan bishi yace wai a'a ba zaije dani ba tace yigudu ki kira mun shi, malle ta juya da sauri taje ta kirashi suka shigo tare shima tasi'u yasha kwalliya cikin manyan kaya ya kalle ni yayi dariya, anti a bamu barka da sallah na Harare shi nace Allah ya kiyaye kana irin wannan sabon rigar kace in baka barka da sallah in bayar. 63 Umma tace kai tasi'u ka tafi mun da hafsat masallaci mana, yace nifa masallacin gidan mai martaba sarki zani ba kuma zan dawo ba sai naga hawan sallah tace eh nima ai don nasan can din kake zuiwa shi yasa nace kaje mun da ita yace to tazo mu tafi. Sahura ta fito daga dakin umma itama tasha kwalliya irin kayan jikina ta sanya nayi murmushi nace kingan ki kuwa/ sahura kin zama tanfar.....,.... .. zan fasda tayi maza ta katseni tace uh uh ban san zuga wai don kar ince kin cionye kwalliyar ta shigo ta debi saurian abincin da aka zuba taci gaba da rabawa. Muna tare da umma a kicin har aka sauko daga sallar idi baba yana shigowa ta fita ta bar aikin ta nufi wurin shit a dan jima kadan kafin ta fito tace mana kije ki gaishe shi da ni da sahura muka shiga muka mishi barka da sallah shi kuwa yasa mana albarka da zamu fito sai yace sahura ga barka da sallar ku ta tsaya karba ni kuwa na fita. A cikin umma tana shirya abincin da zata kaiwa baba sahura tazo ta miko mun mikakkun 64 kudi na karba na kirga nace duba daya ne, sauran fa? Ta dan yi wani murmushi na sakarci alamar wai dabara take son yimun tace kin ga aika baba ko bah aka ba da yake mudin mun riga mun shiga hannun ki ko bakya shafa komnai mun riga munji mun gani ko kuwa anti? Umma ta kwalkyale nda dariya ni kuwa nace ban kudina ban yarda da wannan wayon ba, tace to ke dai Allah dudu hudu ne kin gani? Umma tace dubu hudun ne aka baku kika bata dubu daya bata kudin ja'ira mai waton banza in banda itama ai shi Allah dari biyar zai baki goron sallah, sahura ta yamutsa fuska tace a'a unmmau ni da anti mun fi kusa har kince ta mata da miji ba'a shiga tsakanin mu. Umma ta dauki tiren data gama jera abincin ta fita tana fadin karbi kudin ki maryam dari biyar zaki bata, shima sai kin miko dama tana fita sahura ta miko mun kudin nace mata rikesu sahura tace Allah? Tayi Tsalle cikin murna tace na gode Allah Ya kara girma. Wajen bayan salalr azahar ne sa'id ya samu shigowa cikin gida a dalilin tsayawar da yayi a a wajke aka yanka dabbobin da aka yi 65 laiyan da su a gidan, nima sa'id yayi mun laiya da tikekken rago lokacin nan kuwa mun hadu a falon umma muna ta hra dasu jamilu da yayan yan uwansu da suka zo barka da Sallah sai da ya shiga wurin baba sannan yazo falon umma har zai zauna sai umma tace ma shi ai da wurin ka kaje ka dan huta, Allah dai Yasa baka manta da wani cikin mutanen cikin gari ba a rabon naman yace aiban tsaya an gama ban a shigo su tasi u suyi rabon in sun dawo tace to ya wuce zai tafi nayi maza na wuce shi a dalilin da nayin na kulle wurin nayi maza nasa key na bude mishi waui ya shige i kuwa in dawo wurin hirar mu tunda tana mun dadi sai kawai naga ya turani cikin gidan ya jawo kofar ya rufe na daga ido na kale shi yayi matukar daure fuska kekam Allah Ya ta:make ni kiyi dabara da wuri a ina kika ga ana zama wurin hira a kyale miji shi kadai? Baki bani abinci ba, banga kwalliyar ki ba, amna kina sauri ke zaki koma nace to kayi hakuri na biyoshi muka shiga na kawo mashi abincin na shirya mushi wanda baici ba sai da yayi wanka ya canza kayan jikin shi sai ma nayi zama na nan mukayi wasannin mu da sukafi hirar da na baro dadi da daddare da nayi wanka 66 kayan da sa'id yayi munna sanya kayan da kwalliyar tawa tayi mishine ya sanya yace mun dauki gyalen ki muje ki kira sahura da Hafsat suyi mana rakiya zuwa ungwa ne dani sai dai ina matukar boyewa tunda na nuna zumudi na a sarari kan zuwa wata ungwa yace ya fasa. A falon umma ne naji yana ce mata zamu je gidan yaya babba da yaya balaraba da Alhaji sunusi wanda duk wadan nan gidajen an kai musu abincin sallah tace to sai kun dawo. Gidan yaya balaraba muka fara zuwa don shi ne a kusa, hannu bibbiyu ta karbe mu cikin murna da farin ciki ita da mijin ta da kishiyar ta abin gwanin sha'awa aka danyi hira da bar kwanci har kishiyar ta tan ace mishi ashe dai da hikimar ka da kaje can ka samo matar ka gyara abinka, sukayi rahar su da zamu tafi mijin su alhaji baba yayi mana alheri itama kishiyar ta haka hakannan yaya balaraba kayan shafa ta bamu cikin leda mai giwa shi kuwa sa'id sai mita yake yi waibasu gajiya da hidima, ga kayan sallah sunyi ga kuma irin wannan dawainiyar. A gidan alhaji sunusi kuwa wanda na fahinci abokin harkokin sa'id ne, sai dai ya 67 girme sa'id din, matarshi hajiya salma hannu bibbiyu ta karbemu cikin mutunci da karramawa tayi ta juna da hira dama kuma mun riga mun dan saba da ita, saboda duk lokacin da alhaji sunusi zai zo wurin sa'id tare suke zuwa, ai ke kam maryam abin naki gwanin sha'awa gashi har sa'iusu yaje ya dauko miki yar kanwar ki tana debe miki kewar gidan ku, gashi ya rike miki ita gwanin sha'awa nace aima ba'a wurin mu take ba, a wurin umma take ta rike baki tace ke don Allah nafa dade inajion labarin kirkin mahaifin su a wurin mutane ko da yake wasu suna cewa wai mallake mijin nata tayi ta hanashi yin ayre, murmushi kawai nayi ban bata amsan komai ba, da zamu tafi itama kayan shafa ta bamu, mijin ta kuma kudi, mukayi godiya mun fito tana mana rakiya take tanbayar sa'id irin wannan iya tsakina da amarya, tayi da zaka yarda ai da sai ta rinkayi ana kawowa super market dina ana saidawa yayi maza yace Allah Ya sauwaka tun bat agama amarciba ta soma wata sana'ar kwabe-kwabe gaba daya akayi dariya, mijin ta yace rabu da ita tanace kowama irin tane tun bata shekaraba a giudan nan ta hana kanta sakat wai to ga mai sana'a 68 tace a'a ya daifi ai in zauna ina jiran sai an bani. A gidan yaya babba kuwa muna shiga gidan zumudi na ya ragu a dalilin irin kallon da tayi mun na sheke sheke na samu wuri na zauna cikin natsuwa na gaisheta sai wani kallona take yisama da kasa jimamwa can ta gaji tacewa sa'id iko sai Allah, yau ga inda baki suka zo suka fi 'yangida kyan gain ji yarinyar da aka kawo kamar za' a hure ta ta fadi tazo ta zama wata dindimemiya in ba wanda ya sani bama ba zaice itace ba to ga kanwarta ma. Sa'id yayi maza ya rage fara'ar dake fuskar sshi, yacemata ina maigidan da amarya? Tace suna saman su, ai ni gaskiya kaci mutunci na sa' idu ace a baka yarinya a gidan nan amma kayi mun irin abinda kayi to ni dai in gaya har yanzu ban gaya nusu tasawa lenyi ba cewa nayi wannan din sadaka aka baka don haka in ka dan huta kadan za'ayi wannan din. Bai ce mata komai ba, ya mike yace in sun sauko kya gaishe su kuma munga kayan sallah Allah Ya kara girma. 69 Mun iso gida wajen sha daya ne ammna duk da haka sai da muka kara wata hirar a falon urima kafin muka iso wurin mu Anyi sallah kwana uku rannan na caba kwalliya cikin wata shadda ta kayan aurena ina falon umma muna hira bayan sallar azahar sai sa'id yayi mun waya wai inzo in kawo musu abinci yayi bakin cikin sauri na mike na taho nayi maza na shiga kicin dina na shirya abinci tire daya kaya ciye ciye na motsa baki tire daya ga ku.na abin sha nayi Magana da shi yazo ya debi tirarrukan guda biyu yace mun biyoni da guda biyu yace n.un biyoni da guda daya ana dauka nabi bayan shi zuwa falon na shi, ina shigo mukayi ido biyu da Mahmud, nan take naji lanfar zuciyata tana neman tsayuwa saboda firgita da tayi jikina ya dauki rawa har bansan lokacin da na saki tiren dake hannu na ya kife ba, da gudu na fita na nufi dakina nayi maza nah au gadona na ruhu sai karanto addu'o'i na keyi saboda tsorata da nayi mutufmin da na gani a matsayin Mahmud da kuma maganganun da ya gaya mun suka dawo mun shin Mahmud na gani ko kuwa dai ta 70 maizuben ne da tace wai cikin aljanun dajin mune wani yazo mun cikin kamannin Mahmud din, ina cikin wannan hali-sai ga sa'id ya shigo dakin a fusace wai mene ne wannan abin da ki keyi? Fusatar da yayi ya kara tayar mun da hankali nayi matukar kankame jiki na cikin wani Karin tsoron saboda ban taba ganin shi cikin wannan halin ba, nan take naji zazzabi mai tsananin zafi ya kama ni kwana biyu ajere ina kwance amma sa'id ko lekawa yace mun ya jiki? Baiyi ba bal;le ya wani muna mun kulawar shi sai umma da sahura ne suka yi taji dani ita umman ce ma tasa tasi' u ca jamilu suka kai mu asibiti aka saman mun magunguna har naji sauki bai sauko ba, nima kuwa na shareshi muka koma zaman kowa harkar gaban shi kawai yake yi, ni kam na gaji da gabar, a dalilin ban saba ba, ban taba samun kai na cikin halin da wani baya Magana da ni ba, na girma ne a giodan mu bani da abokin fada balle a/ce ga wata rana da wani zai ki Magana dani, sai da na bari ya gama shirin say a fita ba tare da yayi mun saliama ba, kamar yarda ya tsiri yi, sannan na tashi na shiga wurin umma ta daga ido cikin natsuwa ta kalleni tace zazzabin nan ya ramar 71 dake da yawa maryam ko kuwa kina da wata damuwar ne baki gaya mun ba? Na kale tan ace a a umma sai dlai duk da a'an da nace sai da hawaye suka zubo mun sharrr daga idanuwa na. Umma tayi maza tace yi hakuri, kiyi hakuri maryam, aure kenan kowa kika ga yana zaman shi hakuri yake yi, hakurin data rinka bani sai yasani tsanan ta, kukan da nakeyi sai naji baba abinda nake os irin in ganni a manbilka gaban iyaye na da yan uwa na da basu iya fushi dani, tashi ki je ki kwanta banyi mata musu ba, abin da naji kenan don kuwa nasan shin ya dace dani har dare yayi ina dakin umma, ta shigo tace mun yaya maryam, zaki yi hakuri ki koma dakin kine ko kuwa? Nace mata a'a, tace to yi kwanciyar ki, zaki sha tea ne? nace a'a na riga na koshi ta juya ta fita na koma falo ta zauna tana hirarta da Hafsat. Sa'id yayi sallama ya shigo ya nemi wuri ya zauna ya sake gaishe ta sannan yace mata maryam tana nan ne? tace mishi eh, ya cigaba da zama jimawa can yace mata akwai abinci ne? tace banyi da kai ba don haka duka na bawa 72 almajirai, ya dan yi shiru jimamwa kadan sai ya sake cewa to maryam zo ki san 2binda zaki girkamun da sauri don yunwa nake ji, tace a'a ba zata ko'ina ba, yanzu ta riga tayi wanka ta kwanta bai sake cewa komai ba sai jimawa can yace anan zata kwanane? Tace mishi eh. Malle ta tashi ta fita, jimawa kadan ta shigo rungume da food flask ta ajiye ta sake komawa ta kawo miya da plate da ruwan wanke hannu ta ajiye fhishi ya kalli, malle yace mata ina kika samo mun abincin? tace na dumamen baba ne na safe na kwao maka zanje in sa ruwva yanzu sa: a sake tuka wani tuwon, ta juya ta fita sa' id ya kama cin abincin sai da ya koshi sai yace unmma dama akwai abincin kika hanani ? tace to bazan hanaka ba akan me? ai ni kwanakin nan ma da kake zuwa kana cin abinci anan ina baka ne don ban san yajin cin abincin matar ka kake yi ba, sai dazu da Isahura yake gaya mun yace ai laifi tayi mun tace eh ai dama hakan da kayin shine dai dai ya gama hirar shi ya tashi yace sai da safe tace Allah Ya tashe mu lafiya. 73 Tun sa'id yana zuwa yayi hira ya tashi yace sai da safe yayi tafiyar shi a dalilin wai shi laifi nayi mishi har ya gaji ya yiwea umma magan kan bai san dalilin dawowa na nan wurin ba tace tro ai ka makara tun da baka nemibayani ba, tun farkon dawowanta sai yau kaje kayi ta zaman ka kai kadai ba sai kuna tare zata rinka bata maka rai ba, sa'id juyin duniya da umma akan in koma dakina, shi abin ya wuce a wurin shi, tace ai ita wanda tayi baiwuce ba a wurin ta, ganin haka yasa ya dawo ta wurina yanaso mu sasanta in yaso ni ince zan koma nima nayi matu'ar share shi takaici ya kara kama shi in ya shigo ya gai da umma sai ya nemi malle ta kawo mishi abinda yake bukata ko gaishe shi nayi baya ansawa. Rannan ranar wata lahadi ne da hantsi sai da ya kammala, sannan ya shigo wajen karfe goma da rabi muma mun kammala har nayi wanka nasha kwalliya ta cikin wata doguwar riga yana gama gaida umma ya kira sahura tazo ta tsuguna tace mishi gani ya mika mata sako yace ita da hafsat suje su kai inda ya gaya musu sukace to, suka tashi suka tafi suna fita sai ya 74 Kalli umma yace umma ban san abin da nayi ba kika rike maryam anan kwanaki da yawa har kuma banga alamar zaki ce ta koma ba don Allah in wani laifi nayi miki a gaya mun tace a'a nikamme zaka mun tsaka ninka dai kai da matar ka yace to umma indai ni da itane da ta kawo kara na ai sai akirani a gaya mun ba'a rike taba ni a hakan sai naga kamar an mara mata baya kan wulakancin da ta mun. Wulakancin me tayi ma ka umma ta bukaci sani bai boye mata abin da ya faru ba har lokacin kuma da alamar bai rabu da sakaicin abin ba, saboda yanda yake jadda da fadin ina samin ta dashi, mene ne dalilin da jikin ta zai dauki rawa saboda ta ganshi ? in har tasan tana mishi irin wannan Son me yasa.... umma ta katse shi ta hanyar yi mishi tsawa kai karfa ka kawo mun shirme, kai meysa ka shigo mata da shi cikin gidanta? Yaya kake nema ka takurawa yarinya? Dama akan wannan ne ka tsira gaba da ita? Umma ta rufeshi da fada ta inda take shiga ba tanan take fita ba, yayi ta saman bata hakuri da kyar ya samu tayi shiru 75 yayi maza ya tashi ya fita don kar yaci gaba da zama ta sake taso wata maganar. Washegari da safe bayan nayi wanka na gyara jiki na nazo na samu umma don in gaishe ta sai ta kalleni tace mun yau kam zaki koma dakin ki don kar mijin ki ya maidani wata iri ko kuwa? Ban amsa mata ba, sunkuyar da kaina kasa kawai nayi ki rinkayin hakuri ki kuma rinka girmama mijin ki kina mishi biyaiya nace mata to umma sa' id yayi sallama ya shigo ya nemi wuri ya zauna ya gaida umm anima na gaishe shi ya amsa farai farai na tashi naje kawo mishi abin karyawa na same shi yana cewa umma to ai yau sai ta koma ko tunda maganar ta kare, tace zata koma amma zan gaya maka ban yarda da irin wannan fushin naka ba, in ta maka laifi kawai ka rinka gaya mata ai na san zata baka hakuri yace to umm azan kiyaye ya dan kallen ai zaki dawo wuri kiyi girki ko ba sai dare ba? Kan in bashi amsa sai umma tace mishi a'a ba kin cin abincin kake yi ba inta girka? Na dan sunkuyar da kaina kasa cikin ladabi nace mata kiyi hakuri umma ki barni kawai inyi mishi, ya dan kale ta cikin 76 murmushi don Son ganin yanayin ta bata canza ba, sai kawai naji tace to tashi ku koma can din yanzu, nayi maza nace kiyi hakuri umma tace a'a ai. kinga yanzuma ba wani karyawa yayi ba kuje .can ki shirya mishi abin karyawa Allah Ya kiyaye na gaba yace amin, umma Allah Ya kara girma ta tashi ta fita yace to tashi muje mana maryam nace a'a sai da yanma yace haba maryam bayan umma tace mu tafi yanzu nace gaskiya ina jin kunyar umma yace to bari in leka miki tsakar gida in gani in bata nan sai kawai ki wuce abinki a hankali ba mai jin takun kin ace mishi to yayi maza ya tashi ya leka yą gani sannan ya dan yafutoni da hannu nazo kin gani ba kowa yi ki wuce nace to nayi maza na lwuce na shiga wurin mu. Sa'id yana shigowa yasa makulli zai kulle kofar da dan key nace a'a yaya zaka kulle kuma? Yace sai kinyi adadin kwanakin da kika yi can baki shiga gidan ba, nima ramawa zanyi badai ke komai aka miki sai kije ki kai kara gurin umma ba? Ita kuwa tace miki kiyi zamanki ba tare da tayi binciken abinda kikayi ba, saboda ke tana son kin a zuba mishi ido ina 77 kallonshi cikin tsoro yai yi muirmushi yace kar ki rinka jin tsoro na maryam girmamawa ne tsakani na da ke, kin gane? Nace uh ba tare da na saki jiki ba muje kiyi mun abin karyawa, kinji ko? Baki lura kwanakin nan na dan ragu ba? Ban tanka mishi ba na shiga kicin ina shirya mishi shima ya shigo yana tayani, wunin ranan bai fita ko'ina ba, muna tare a gida duk kokarin shi bai wuce nason ganin dashi mun koma kamar da ba wanda ba'a wani dauki lokaci mai tsawo ba, hakan ya yiwu. Kammala karatuna na yaki da jahilci da kuma koyon girki sai na zama babu abinda nakeyi in banda zaman gida naso kwarai ace sa'id ya bar ni na shiga makaranta, don ina matukar sha'awar karatu amma sam yaki bisa hujjar da bai wuce kishi ba. Wai wannan ma abinda yasa naga ya sanyani don matane ke tafiyar da dukkan al'amuran inna tashi da safe kan kace meye wannan? Na kanmala dukkan aiyuka na bani da wani abinyi sai ko in dan dauko littafi ina karantawa wajen buda baki, wannan dalili ya sanya shawarar da hajiya salma take yawan bani na in nemi sana' ar da 78 zan rinka yi yayi matukar karbuwa a zuciyata sai dai sa'id ne bai yarda ba, babu yanda banyi da shi ba, babu irin rartashin da ban yi mishi ba yaki, rannan dai na yanke shawarar zuwa in samu umma kan maganar nayi mata bayani tace to bari sai ya dawo zata hadamu muyi maganar nace mata to. Da daddare kuwa yana falon ta malle tazo ta kirani nasan maganar ne don haka da zan tafi sai na tafi mishi da abincin shi ina shiga na ajiye mishi tare da yi mishi sannu da zuwa sannan na nemi wuri na zauria nace wa umma gani, umma tace maganar da kikazo kika mun ne nayi mishi maganar shine yace yana son sanin abin da yasa kika matsu sai kinyi sana' ar akwai wani abinda ya rage miki ne? Na sunkuyar da kaina kasa cikin ladabi nace mata a'a, umma ba abinda nake nufi kenan in ranshi y abaci yayi hakuri ni dai kawai na gane wuni nake yi a zaune bana aikin komai, ni kuma ban saba haka din ba, bana jin dadin zaman ina bukatar wani abinda zan rinkayi don in rinka motsa jikina, ni shine kawai bukata ta. 79 Umma tace to kai kaji bata raina abinda kake mata ba, saboda haka in kaga baka son yin sana'ar iat a to ka barta mana ta rinka zuwa makaranta tare da su sahura tunda gashi hart a dan fara iya karatu da rubutu, ai ina ganin ba zai mata wahala ba, yace zanyi tunani tukuna akai, tace to Allah Yayi mana zabi na alheri yace amin. Rannan da yanma ina tare da shi a dakin shi, shagwaba nake mishi ya zuba mun ido yana kallo na cikin natsuwa, jimawa can sai yace ke maryam muyi zaman mu haka kina taraita ta baifi miki dadi. ba? Ki fiso sai kin kinkimo wani aiki da zai dauke hankalin ki daga gare ni? Kofa amarci baki gama ci ba, kwata kwata yau watan ki tara ne a gidan nan, na sake langwabe a jikin shin ace mishi sana'ar da nake son yin ba zata shafi komai game da abinda na saba yi maka ba shi ya sa ma nake so in gaya maka aduk lokacin da ka amince da yin sana'ar to zanyi tane bisa sharuddan da zaka kafa mata, kuma maganar amarci yayan sahura ai kace mun amarcin nawa ba zai taba karewa ba, yayi murmushi yace haka ne maryam, amarcin kin a 80 har abada ne, nace to ai nima bazan yarda ya shafi amarcin mu ba, kana ganin za'ayi hakan sai ka dauki matakin hanawa yace to shike nan. To da haka na fara sana'ar yin cake, meat pie, cin-cin da dai sauran abubuwa da suka shafi bekin, ana kaiwa shagon hajiya salma ana ajewa duk da akwai kudi na wurin sa'id bai yarda nayi anfani dasu a matsayin jari ba, kudin shi ya zuba ya saya mun dukkan kayaiyakin da nake bukata, wai in sana'ar taci gaba shike nan, inma ta tsaya a hanya sai kayan su zama kayan anfanin gida, hakanan su flour, sugar, butter da dai sauran su duka da kudin shi ya saya. Mun fara ne da kadan sai gashi tana aiken a kara yawan abin da akeyi, kowanne sati kuma zata aiko mun da kudi na, ni kuma duk kwana uku zuwa hudu nake aikawa da sabo a hankali sai ya zamo ana bukatar in bayar kowanne kwana biyu, na hada kudin ajikin da akayi na watanni biyu na kawa sa'id nayi mishi bayanin komai yayi matukar jin dadin ganin yanda abin yake tafiya ya kalleni cikin murmushi yace dadi na dake ke din jarumace, na taya shi murmushin nace mishi sai dai 81 gaskiya bukatar taimako, don aikin ya soma mun yawa, inka yard azan nemi mai aiki zan kuma sanya sahura da jamilu a cikin abin ya kalleni kamar yaya? Nace tunda akwai samun alheri a ciki zan jawo sahura mu rinka yi tare muna raba ribar da ake samu shi kuwa jamilu ya zama shine mai zuwa kasuwa ya rinka sayo mun abubuwat da nake bukata, in an gama kuma ya dauka ya kai mana, shi sai a rinka bashi nashi kason. Sa'id ya kalleni cikin jin dadi da alama yaji dadin yanda zan jawo yan uwanshi cikin lamarir yace bari kiji yanda zakiyi, zaki rinka tara riba ne a wata kiga nawa aka samu, sai ki cire kudin ma'aikata tunda kince kina bukata har da masu aiki in kin biya su abin da ya saura sai ki kasa shi kashi hudu daya ki ajiye, saboda kayan aiki kin san dole wata rana kya bukaci sabbi ko kuma kari nace eh yace to kashi daya ki rabawa sahura da jamilu sauran kashi biyun kuwa sai ki rike tunda kece mai sana'ar nace to amma in ka yarda a rinka rabawa kashi uku kawai kayan aikin daya, ni daya, sahura da jamilu daya, yace to shike nan. 82 Shigarda sahura da jamilu da nayi cikin harkar ba karamun dadi yayi mun ba,na farko dai ni da sahura sai muka kara dunkulewa muka zama abu daya ko umma bata sanin abin da ke tsakanin mu, shi kuwa jamilu sai ya zama kullum a cikin nemo mana sabbin kostomomni yake, kan kace meye wannan sai abu ya zama gagarumihar bai yiwu wa kazoo kai tsaye kace kazo saye yau ka samu sai dai kayi bukin, nan da nan sai gani da yan aiki har guda biyar, aikin yayi matukar bunkąsa, kasan kowanne sati sai na baiwa sa'id kudi nace akai mun banki. In wata yak are kuwa dauko takardąr da mke rubuta ciniki abinda muka saya da wanda muka sayar nakeyi inji lissafi in san biyan ma'aikata, ta nawa ya kamata in baiwa su jamilu na maida umma ta zama tanfar mahaiti yata, kusan kowanne lokaci a cikin yi mata hidima nake, in mata dinki in bata kudi in sai mata abin da na gani ya bani sha'awa. Rannan sa'idu ya dawo gida da yamma kamar kullum nayi maza na wanke hannu na cire rigar sApron dake sagale a wuya na, na rataya na barwa sahura aikin da nakeyi nazo na 83 same shi yana tsaye da alamar dai wani abu yadan sosa mishi zuciya, nayi mishi sannu da zuwa tare da tanbayar shi lafiya? Naga kamar yadan canza? Yace mun lafiya kalau, banyi baki yi baki ba bayan fita na? nace mishi a'a a sanina dai babu wanda yazo, zaka ci abinci yanzune ko sai ka huta? Yace sai na huta nace to, na zauna tare da shi ina yi mishi abubuwan da suka dace inyi mishi don wastsakar mishi da damuwar dana hanga tare da shi sai dai banga alamar gamsuwa ba a tare da shi, na gaji nace mishi me ya faru ne naga kayi wani iri? Ya daga ido a hankali ya kallen cikin natsuwa a hankali ya bude baki cikin wani yanayi mai kama da na maijin tausayin kanshi yace mun jna Sonki maryam wata irin matsananciyar soyaiyar da nake bukatar gaskiya da amana a tsakanin mu na danja jiki daga gare shina koma gefe na zauna ina kanllon shi cikin natsuwa nace abin da kake bukatar shine a tsakanin mu yayan sahura in banyi maka gaskiya ba ban rike maka amana ba to wa zanyi wa? Yayi maza yace yauwa, abin da nake so ki gane kenan don haka gaya mun gaskiya daga shekaran jiya zuwa yau su waye suka zogidan nan? Na lissafa 84 mishi kamar yanda damana gaya mishi tun zuwan su, shikenan din su? Na sake cewa eh, a sanina dai shike nan yace to naji jeki wurin aikin kin a tashi na fito cikin rain a ina tunanin irin wannan hali na sa'id kullum cikin bincike da kidaddiga kuma amsa daya bai gamsar da shi, un kuma kace mene ne yace bä komai. Nikam hidimata nakeyi mai dadi babu abinda ke faranta mun rai irin mu'amala ta da umma da kuma 'yar wan sa'id ko da yake a fili yake ina da mas'ala a tsakanina da yaya babba, kiyaiyar da take nuna mun tana da yawa don wani lokaci ma na taba jin umma tana gaya mata cewar da kin bar wannan abinda kike yi don kuwa ba gane ki zata raina ki, kinga kuma ba laifin ta bane, in hakan ya faru gashi kuma ina matukar samun kudi nayi sa'a sana'ata tayi matukar karbuwa, in har ina da wani abinda yake muntsinin zuciyata bai wuce dabi'ar sa'id ba ta yawan tuhuma gashi kuma wani lokaci a sarari yake nuna rashin yarda kan amsar da aka bashi hakannan duk da gaya mishi da umma tayi in nayi mishi laifi ya gaya mun in bashi hakuri maimakon yayi ta fushi da ni, hakan bai 85 yiwu ba, sa'id yana shafe kwanaki goma koma fiye da haka baya magana da ni baya kuma cin abinci na sai dai kuma duk da zafin da hakan yake yi mun na dena zuwa in kai karar shi a wurin umma saboda komai kankantar abin da yayi mun ta rinka yi mishi fada kenan wannan dalili yasa nayiwa kaina fada don banga anfanin kullum in rinka sanyawa mahaifiyar shi tana yi mishi fada ba don haka sai na dauki matakin zuba mishi ido, bance mishi komai ba, sai randa naga alamar fushin nashi zai zo karshe ni kuma sai in tsiri nawa daga ranar wanda shi kuma ba jura maimakca ya fahinci nima so naake in rama abinda yake yimun sai kuma yace wai zai sa karfi wajen kawo karshen abin, to a haka zaman namu ya kasance yau fari gobe tsumma, babu kuma mai iya cewa ga wani takamanman abinda ke hada mu, na dai sani kawai yana yawan fadin wai ina cutar da shi, ni kuma nace ya gaya mun cutar da nakeyi mishin, ba zai fada ba don haka sai kawai na dauka yana fadin hakan ne don bakar magana. Rashin cikakken zaman lafiyan dake tsakanin mu shin e yayi dalilin da sa'id yaki 86 yarda da rokon da nakeyi mishi na ya barni inje in gano iyaye na, kuma na riga na kudurawa raina bazan sake kai kararshi wurin umma ba, kan wani abin da yake yi mun kokuma yaki yimun don haka sai mukayi ta zama a haka. Rannan muna zaune a falo na muna hira ranar kuwa bana mantawa dasawa mukayi sosai mun kai azumi ne muka yi buda baki tare, azumin kuma na watan Rajab ne, na kalli sa'id Cikin natsuwa nace mishi yayan sahura in Allah Ya kaimu daya ga watan Sha'aban zan cika shekaru biyu rabona da inga iyaye na, amma har. yanzu taka ce mun ga ranar da zaka barni inje ba, yace ko baki jeba aini ina zuwa daga bikin mnu zuwa yanzu naje manbila sau uku, kwanannan ma kuma zanje to mene ne na dole ke sai kinje tunda ni ina zuwa? na daga ido na kalle shi nace bance dole ne sai naje ba tunda ba kaso kuma ban san dalilin ka nayin hakan ba, amma na dauka koni baka tausaya mun ka barni naje saboda ni kaina ba zaka tausayawa baffa ka barni inje saboda ya ganni tunda ka sani ya dauki duk abinda yake so ya baka, hawaye suka zubo sharrr a idanu na, 87 tausayin ardo ya kara kamani da nayi tunanin yayi kewata har ya hakura. Sa'id ya matso kusa dani ya shiga rarrashi na kiyi hakuri ki bar kukan hakan wannan karon in Allah Ya yarda dake zani manbila. Tunda daaga ranar na soma shirye shiryen zuwa manbila nayi shiri, nayi tsaraba na adana kudi saura sati guda muyi tafiyar sa'id ya kawo kudi masu yawa ya bani yace inyi wa mutanen da nake ganin sun dace tsaraba, bance mishi na riga nayi ba don kar yace nayi gaban kai na sai kawai na karba nayi mishi godiya an shirya tafiyar ne akan zamu jene mu kwana biyu mu dawo, ummace tace a'a tunda na dade banje gida ba, haka ba sai abarni inyi sati biyu ko uku kafin in dawo don in samu damar ziyartar dangi so sai, don haka sai sa'id yace to in shi zai jene a lokacin zai dawo dai dauko ni don haka tasi'u ne zai je ya kai ni, ni kuwa sai na roke shi nace to ya bani izini in tafi da sahura da jamilu tun da dukan su suna cikin hutu bai hana ba, itama umma murna tayi da taji na fada haka dan banda kudin daya bani 88 babu kuma wanda bai yiwa dinki ba a rigar mu, ya kuma kawo kudi yace in basu kowa da nashi ga kuma tsarabar su doya su kayaiyakin masarufi iri-iri haka nan umma da baba sumna dukan sunyi mun tsaraba. Daga yin sallar asuba muka bar gida duk da nauyin motar da irin karfin tafiyar da aka yi mun isa rugarmu ne bayan sallar magariba rannan kusan babu wanda ya gane n1 a gidan mu, abinda kawai suke fadi shi ne 'yan-uwa mijin sengel ne suka zo kuma ;da yake basugaa malle ba sa id yace wai za'a bar umma ba kowa sai zai zo zai taho da ita, ardon yazo wurin yana y1 musu sannu da zuwa ya ganni yace ikon Allah "din seungel hande to wuro gun? " Ma ana seungel ce yau a gidan, nace eh baffa sai kuwa gaba daya yara suka fara ihu suna oyoyoyoyo, kai tsaye dakin ardo na shiga yayin da su tasi'u suka nufi masaukin da akayi musu ardo yana kallo na yana murmushi yace seungel ta zama matar hausawa, na taya shi murmushin Cikin yanayin jin kunya nace mishi a'a baffa, ai ni kullum bodice ina kuma alfahari da hakan ya sake wani murnmushin yace hakane seungel 89 amma fa kar ki rinka dauka ko bodi yafi wanda ba bodi ba kin gane ? nace eh baffa muna nan wurin muna hira ni da ardo har yaya jauro ya dawo daga cin kasuwar kara daya tafi ya shigo ya durkusa yana gai da ardo, daya gama sai yace mishi naga mutanen su seungel ne sukazo don na hangi mota, ardo yace mishi eh ba gata ba yaya jauro ya gyara tsuguno ya shiga gaishe ni ina amsawa cikin zuciyata kuwa kamar in kyalkyale da dariya don na tabbatar bai gane ni ba sai daya gama gaisuwar sai yace kai to ita seungel din fa? na kyalkyale da dariya nace haba yaya jauro in owa bazai gane niba kuwa ai ya kamata kai kam ka gane ni ardo yace kwarai kuwa seungel tunda yana iya sheda saniyarshi duk inda ya shiga ai ko ya kamata yafi sheda ki nace yauwa baffa ni da ardo mukayi dariya shi kuwa jauro sai kallona yake yi yana fadin Aradu kamar ba seungel ba. Rannan kwana mukayi ni da ardo da yaya jauro muna hira, sai da akayi sallar asuba sannan nikam na nufi dakin maizube na kwanta, ita kam sahura tana dakin bodejo su tasi'u da jamilu kuma suna bukkar da aka sauki 90 sa'id suma aka sauke su, hidima sosai akayi tayi masu. Bayan sha biyu ne na tashi nayi wanka nayi sallar azahar sannan na karya naga su tasi'u sannan na dawo dakin maizube muna hira bayan naje na gaida innan su yusuf da yakubu suka shigo dakin na jawosu jikina na zauna dasu ina cewa ikon Allah, baffa yayi yan tagwaye maizube tayi murmushi tace aj kuwa dai shima abinda yake fadi kenan muna cikin hirar maizube tace mun ai kuwa kunzo dai dai yau saura kwana goma ayi bukin sumaye, na rike baki.cikin nuna alamar mamaki nace wato goggo inda bamu zo ba da shike nan sai ayi bamu sani ba, tace eh to dama dai ardo yana cewa watakila mijin ki ya samu daurin auren don kusan lokacin zuwan shi kenan mukayi hira da maizube sai famar tarairaya ta take yi tana taji dani ina fitowa daga dakin ta na nufi dakin jume tana ciki ta mulmula kiba tayi gwanin kyau da ita shi kuwa yaya jauro yana gefe sai dogon wuya na samu wuri na zauna muka gaisa muka kuma shiga hira ina tanbayar ta mutanen gidan su da kasuwa tana bani labari 91 tanfar dai babu wata rashin jituwa a tsakanin mu. Kwanan mu uku da zuwa na soma kai ziyarar dangi babu inda banje ba cikin dangin ardo da na bodejo har da na maizube duk wani tanadi na tsaraba da nayi kuwa dama tun daga nasu bodejon danan 'yan-uwan su duka ban bantaba har kasuwar manbila da gidajen su sarkin fawa duk naji inda duk muka je kuma yaya jauro ne mai yiwa wadan da basu gane niba bayani, seungel ne fa, wannan da tayi sharo da majo din nan sai kuma a kama fadin kai jau.o shi kuwa yayi ta fadin Aradu, to zan muku karya ne ? suce a'a a'a jauro ai ba sana'ar ka bace, abin mamaki ne dai yake da yawa har shagon idi tela naje. Na kai mishi shima tashi tsarabar tare da iyalin shi. Muna zaune a gida ni da yaya jauro a bayan bukkar maizube muna hira na kalli yaya jauro cikin kulawa nace mishi yaya jauro me ya same kane? Naga duk ka fita haiyacin ka kamar ba kai ba, dubi yanda ka rame ka kare ka zama sai dogon hanci. 92 Ya dan kalleni yace kar ki gayawa kowa, nace haba yaya jauro ai yanzu nib a yarinya karama bace, yanzu yace hakane seungel, jume ne take damuna da fitina, gashi yanzu tace wai ni din bani da lafiya bana haihuwa har ma ta matsamun sai da muka je wurin wani mai magani ya bamu magani yace in dinga sha ni kadai wai abin a wuri na yake, ya sake dan waiwaya don ya rada mun magana kuma mai maganin yace wai shanu biyar za'a bashi nace bazan iya ba, don ardo ba zai yarda ba, ita jume tace wai za'a iya diban shanun shi ardo bai sani ba, to kuma naga kamrr kafar shanu tayi cikin duwatsu shin e nace ko har sun diba ne? ban sani ba shi yasa rannan naje kasuwar kara don in gani ko zanga shanun a can ban gani ba. Na zubawa yaya jauro ido cikin tausayawa nace kai yaya jauro kai kam baka dace dasamun mata ta kirki ba, ina ganin maganin abin kawai shi ne akara aurar maka wata matar su zama su biyu watakila kadan Samu sassauci, yaya jauro ya kama ihu yace kai seungel wannan shawaran naki na banzane, ni inacema zaki ce ne a mayar mun da kitso na 93 kawai dama jume ta koma gidan su amayer? Maka da kitsonka yaya jauro? Ka koma saurayifa kenan? A ina kaga ana yin haka bayan ka riga ka tsufa kuma kace kana son ka dawo saurayi, ai bazai yiyu ba, kai dai bari zanyi tunanin abin da zamuyi akai yayi maza yace amma kar kice zaki zage ta don tace inna hadata dakewa wai zaki tafi ki barmu nace to yaya jauro. Ina hira tare da bodejo dadi ya kamata sai faman murmushi take yi tace mu muna nan muna jiye miki zama cikin bare ashe ke kina can abinki Allah Ya hadaki da miji mai kirki, na kalli bodejo kawai na taya ta murmushin cikin zuciyata ji nake tanfar in dan fada mata wani abu game da irin zaman da muke yi da sa' id, amma na kasa fada mata, ji nake tanfar zan huda ciki nane in yiwa kaina, su dai su bodejo a yanzu babu wani wanda suke so fiye da sa' id in an tanbaye su mutumin da yafi kowa kirki a duniya yanzu zasu iya cewa sa'id ne, to in gaya mata laifinshi wuri na to akan me? Nayi maza na sake tsuke baki na nayi shiru muka ci gaba da hirar mu mai dadi har na samu na sako 94 maganar dake damu na ta yaya jauro da matar shi, inna tayi maza ta yamutsa ido tace kul!! Kar ki sake kawomun maganar shin ace Allah sarki inna in baki taimaki yaya jauro ba wa zai taimake shi? Tace uh uh zai sa raini ya shiga tsakanina dasu kan fitowar da yakeyi yana kwana a waje dana mishi fada sai yaje ya kwashe ya gaya mata haka da nayi mishi maganar yaje yaga wata yarinya yar gidan su takko innace zan rinka sa ido akan su raina ni kawai zai sa ta rinka baci na sake lankwashewa ina baiwa inna hakuri nace in kin yi niyyar taimakon shi inna kinsan abin da zakiyi. Satin mu guda a manbila sai ga sa'id da malle sun iso maimakon sai munyi sati biyu da yace, gaba daya hankalin mutanen gidan mu ya koma kan malle saboda yanda ta canza musu tayi matukar yin kyau ta girma ta zama 'yar gaye kwalliyar English wears take yi, don shi sa'id irin kayan da yake sai mata kenan, ga kanta akowane lokaci bai rabo da kanannan kitso ga ribbon masu kyan gaske. Na samu sa'id a sabon dakin da ardo ya gina don saukar shi nace yaya akayi kuma yau 95 na gan ku? Ni da na dauka sai sati mai zuwa zaka zo ya kalleni cijkin natsuwa yace ai gidan ba dadi in bakya cikin shi, basa hakuri, nayi nace bari dai inzo muyi zaman bakuntar tare na kalle shi kawai nayi murmushi cikin zuciyata kuwa cewa nayi kamar da gaske, in ina nan kaki yarda a zauna lafiya yanzu da na barma gidan kabiyoni kana fadin gidan babu dadi. Duk da sa'id baizo da shirin bukin sumaye ba amma hidima sosai yayi ya kuma kyaleni dai da aka gama bikin sarai na raka sumaye gidan mijin ta har muka maida ita daga yada sawun da tayi wanda tun daren farko tayi shi sannan yayi mun maganar yaushe nake ganin zamu tafi? Nace aiko gobe kace mu tafi sai kawai mu daga, tun da an gama komai yace to zanje in samu baffa zan gaya mishi ina so zuwa jibi in Allah Ya Kaimu sai mu tafi, nace mishi to ina shiga gida na gayawa maizube don nasan itace zata shirya mun tsaraba. Ina zauna tare da inna ta a cikin dakin ta dambun naman da nazo musu da shi na samu tanaci na bude jaka ta na debi kudi masu yawa na bata ta karbesu tana kallonsu tace a wannan 96 jejin namu me zanyi da wadannan kudin in dai ba shanu kike so in kara ba, nayi maza nace mata a'a inna ina baki kudi ba shanu nake so ki kara da suba, kashe su nake so kiyi ki rinka cin dadi ta kalle ni tayi murmushi tace in rinka cin irin wannan abin kenan da kika kawo mana? Nasan inna gatse tayi mun don kuwa babu abubuwan dana kawo musu ariga takaici ya kama ni ina ma dai kusa dasu nake da kuwa na jiyar da su dadi da irin girke-girken da na iya. Rannan a dakin ardo na tare don hira, kusan raba dare muka yi mu biyu, muna zaune ardo ya kalle ni yace mun yaya dai seungel ke da jauro shiru babu wani motsi? Allah dai Ya sa mas' alar ba daga wurin ku take ba, bance mishi komai ba sai da naji yayi shiru sai nace mishi baffa baza ku taimaki yaya jauro ba? Ardo yayi murmushi yace ai jauro bani a cikin al' amarin shi kuma tun da bodejo ta zuba mishi ido kowa ma zai gaji ya zuba mishi ido. Sannan ina so ki gaya wa mijin ki yayi kokari ya dibi shanun shi a wannan lokacin nace mishi to. Sa'id da kanshi ya samu ardo yayi mishi bayani kan shirin da yake yina zuwa diban 97 shanun nashi, sai dai yana bukatar ardo ya dan kara hakuri kadan yace to Ubangiji ya nuna mana lokacin yin hakan yace amin. Tsarabar ruga sosai aka shirya mana nayi sallama da yaya jauro cikin tausayawa na kawo kudi masu yawa na bashi nace mishi ya kai cikin yashi ya boye ya rinka diba kadan kadan yana bata kar ya yarda ya bata lokaci daya yace ai ba zaiyi haka ba. Mun dawo gida da kwana uku nayi barin ciki wata uku hankalin sa'id yayi matukar tashi baran ma da likita ya bayar da dalilin barin akan tafiya mai nisa da nayi da 'dan karamin ciki ina kwance kan gadon asibiti amma bai fasa fadanda yake yi ba, wannan ma ai ganganci ne da rainin wayo, ai kin san kina da shi kika kama hanya kika luluka wannan tafiyar kikaje kina ta kaiwa da kawowa a jeji. Umma tace to maryam kuwa inda tasan da haka ai bana zaton zata yi wannan tafiya tunda ita ma ai zata so ta ga kwanmta yaya babba tace a'a umma infa yarinyar nan tayi laifi ki rinka bari ana nuna mata kuskuren ta, hauka kenan take yi in har zata dauki ciki wata har 98 uku a jikinta bata san da shi ba, haka fa kwanakin baya akace mun wai tayi barin sati shida sanadin barekatan da ta sha, shima kuskure ne? bata fi kowa sanin irin wannan abin a tunda ita ai "yar magori ce. Umma ta mike tsaye tace mata bar asibitin nan tunda ke baki iya kwantar da fitina sai dai tayar da ita, wuce ki tafi ki bani wuri, yaya babba ta wuce ta tafi tana fadin soyaiyar da kike yiwa wannan yarinyar tana sawa kina rufe idonki kan cutar sa idu da takeyi inma hidimar da take yi kike dubawa ai tana wanke kaifi.ne da ruwan jikin shi, tana fita umma ta koma kan sa'id ta rufe shi da fada kai kam abinda kake yi har kunya yake bani ni ban san abinda yake bani in ban san abinda yarinyar nan take maka ba da kowane lokaci kake fusace da ita me take maka ne? Me take maka da yake hanaka tausayin ta? A irin wahalar da maryamn tayi yau ace wai bar kana iya yi mata tashin hankali ai kuwa abin da ban mamaki yace umma cuta ta takeyi tuni kuma na dade da sanin tana nadamar aure na wannan bari-barin da takeyi duk da gangan take zubar da cikin don 99 bata son haihuwa da ni, umma ta kama salati cikin kaduwa da jin mamakin kalaman shin ai kuwa cikin rai na naso ta tanbaye shi cutar da nake yi mishi sai dai batayi hakan ba. Nima kuma banyi ba don kuwa ba dani yake maganar ba bayan hakan kuma tun farko ban nuna musu ido na biya ba ni kaina al'amarin sa'id yana matukar bani mamaki, ban taba zaton inna aure shi irin zaman da zamu yi da shi ba kenan, kulluma cikin kokacin kyautata mishi nake amma kuma duk a banza bana burge shi ko anyi kamar zai dan lafa sai kuwa abin ya dawo wani lokacima kiri kiri ya rinka nuna manr tsana da kin jinni a sarari ni dai ina kallon shi ina kuma yin addu'a kwana biyu nayi a asibitin sannan na dawo gida har lokacin bai fasa fushin da yake yiba, nima kuma ban kula shi ba ina cika kwana bakwai na koma kan sana' ata sai dai ban bari hakan ya hanani shirya mishi abin shan ruwa akan lokaci ba har akayi sallah ba, ba wani shiri muke yi da shi ba sai dai kuma hakan bai hanashi yimun dukkan abubuwan da suka dace ba, tun daga wannan lokaci sai na samnu kaina cikin halin yawan yin balri akai akai abinda yayi matukar sanyani cikin wani hali ga dai 100 wahalar da nake ciki gashi kuma duk lokacin da hakan ya faru sai mun shiga wani hali na fitina tsakani na da sa'id, saboda zargina da ya keyi da cewar ni nake zubar wa don bana son haihuwa da shi. Rannan ya same ni a dakina ina kwance akan gadona ya nemi Wuri ya zauna a gefen gadon yace mun maryam wurin kin a zo inaso muyi Magana ta gaskiya dake, kin san dai Allah ne ya hada mu ko ba haka ba? Nace mishi haka ne, yayi bayanai masu gamsarwa sannan yace mun ina so ne kiji tsoron Mahaliccin mu ki gaya mun gaskiya mene ne laifi na a wurin ki da kike nuna mu kiyaiya da tsana? Nace da nayi maka me? Yace kin fini sanin abin da kike yi da dalilan ki na yin hakan. Ko ba komai dai kina gwadamun kiyaiya ta hanyar boye mun kina da ciki sai in kin kasa zubar da shi cikin sirri sannan in sani na kalle shi cikin natsuwa nace mishi yanzu yayan sahura da gaske kake yin maganar nan cewa ni ke zubar da cikin da nake da shi? Yace to in bake bace wane ne? Tunda nayi-nayi dake in kinga kina dashi ko wata daya ne ki gaya mun ni zan san matakin da zan dauka akai amma kin ki. 101 Nace to ina sanin ina da shi ne? ni ina al'ada kowanne wata uku uku ne ta yaya zanyi in san da shi? Ya danyi shiru jimawa can yace to shikenan kiyi hakuri, daga wannan lokacin zaki rinka zuwa yin test kowanne wata don in kina dashi a gane da wuri nace mishi to. Tun daga wannan lokaci na fara zuwa gwaji duk karshen wata, rannan likita ya tabbatar ma sa'id ina da shigar ciki sati uku ya fadi abubuwan da zan kiyaye cikin su kuwa har da yawan aiki ya kuma shawarci sa' id daya dan saurara mun a wannan dan tsakanin yace to, muka dawo.gida sa'id yace in barwa sahura gudanar da al'amuran, aikin mu gaba daya in yaso sai arage yawan abinda akeyi nace mishi to, ya kira sahura yayi mata bayani tace mishi aima ba sai an rage ba tunda akwai masu aiki sosai ni da shi muka koma cin abincin umma safe, rana da dare don kuwa bana aikin komai daga kwanciya sai ko sallah ko ruwan wanka ma shike hada mun wata ran ma ya tsaya ya cudani muna cikin haka har cikina ya wuce wata biyar ya shiga na shida ya riga yayi kwari sai na gayawa sa'id ina so in rinka taya su sahura aikin da suke yi don aikin yana yi mata 102 yawa sai takai goman dare bata kwanta don ma tana da kokari yace to kar dai taimakon ya zama mai yawa, nace mishi to. Abinka da kaddara kwana na hudu da komawa kan aiki na sai na wayi gari ina Ciwon mara nayi maza na gayawa umma ta hanzarta kaini asibiti shi kuma sa'id jamilu yayi mishi waya ya sheda mishi cewar ina asibiti ya iso asibitin ne dai dai lokacin da aka fito da ni daga dakin haihuwa aka kawo ni kan wani gado aka kwantar da ni yava dai umma? Cikin kotsawa ya tanbaye ta, kan ta bashi amsa sai nos din nan ta sake shigowa tana tambayar ame zaku karbe shi? Sa d yayi maza ya mika mata babbar rigar gi anan nos ta juya ta tafi ba tare da ta karbi rigar ba taje ta kawo shi cikin tasan da suka sanya shi tun farko umma ta zubawa tasar dake hannun sa id ido tana kallon shin an take hawaye suka soma zuba daga idanun ta tana fadin iko sai Allah, na miji ne an gama mishi halittar shi har ya fara girma ji hannuwan shi komai nashi irin naka ne. a hankali yace ba komai umma, kiyi hakuri bari in kaiwa baba shi sai abinne shi, yasa hannu ya dauke ya nade shi cikin rigar shi ya juya ya tafi ya barni tare da umma wacce ba 103 sai an gaya mun ba ita kanta hankalin ta yayi matukar tashi da abinda ya faru wannan karon sa'id kam tunda ya sa kai ya fita da yaron da aka bashi bai sake dawo wa ba, har bacci ya sake dauke ni sai farkawa nayi naji yaya babba tana fadin a'a umma, tunda dai hakane ni na tafi zan iya cewa a wannan lokacin sahura da tasi'u ne kawai basu juya mun baya ba, na shiga wani hali na kuncin rayuwa, kalaman mahaifiyata na game da auran bare ayi nesa da gida sukayi ta dawo mun inda ba kusa da dangina da iyaye na nake anya irin wannan zata sam ni? Na kasa hana hawaye na zuba nayi ta kuka nan take naji babu abinda nake so irin in ganni gaban iyaye na, ganin ina kuka ya sanya umna ta sassauto daga bacin ranta ta shiga bani hakuri kwana daya da wuni nayi aka sallame ni. Muka dawo gida ban yarda na zauna a dakin umma ba, kamar yadda tace dakina kawai na wuce a wannan lokacin naji ina bukatar zaman kadaici, tunda abinda na zabanwa kaina kenan tunda naki zama cikin dangina. Ina zaune a dakina sa'id dai kullum yakan gaishe ni ne da safe, sai kuma wata safiyar ita kuma umma dama ba shiga wurin 104 mu take yi ba tunda ta shiga ta duba ni sau biyu bata sake ba sai ko ita da baba su turo malle ko sahura suzo suce suna gaisheni, yaya jiki? Ince da sauki. Rannan ina kwance a dakina bayan azahar inajin shigowar sa'id da yaya babba ga dukkan alamu da ga gidan ta suke sai naji tana cewa ina matar gidan take? Yace ai inajin bacci take yi tunda babu motsin tat ace to ai gara kasan abinda kake ciki don wannan yarinyar ba sonmu take yi ba, aure shekara hudu amma har yanzu bata yi sha'awar ta bar mana konmu mu gari ba shekaran jiya dana je gidan mansura naga yan ta gwayen ta sai da naji kamar kwalla zata zubo mun nace da yanzu wadannan kyawawan yaran mu aka haifawa su yace yantagwaye fat a Haifa ko? Tayi maza tace eh baka gamsuba kyawawa ga lafiya mace da na miji amma ita wannan sai aukin neman kud tunda yake ita dama fatauci tazo yi ta samnu kudi ta hura gida ayita kara mata shanu sa'id yar dariya yace kina yawan fadin maryam tama sayen hanu a garin su ina ganin don baki taba zuwa gidan su bane da kin san ita mai shanu ce, shaņu basa cikin abinda zata saya. 105 Tace shanu suna ransune ba dukiyar gado bane? Ai daga gan wannan ne su koma gun wancan ba iya cinsu suke yi ba sai dai suyi ta wahala dasu kuma ni koma dai mene ne ina so in gaya maka yana da kyau ka kara aure ko don kaji dadin zama da ita tunda ka nace kana son ta in taga wata tazo bayan ta tana goya danta ai watakila tayi sha'awar ita ma ta haifa, ita mace in ka gane ba so take ka karu da ita ba ai sai ka kama kanka, yace mata hakane. Mas'alar da ta ke tsakani na da sa'id sai ya baiwa yaya babba alamar shigowa cikin lamarin aure na tayi ruwa teyi tsaki kullum tana tare da shi tana cikin gaggaya mishi maganganu yana kara fushi akan fushin shi na da nima inna fara sana'ata tun safe sai na kanmala komai nake tashi bani da wani lokacin barin aiki na saboda inyi na gida sai wajen umma yake aikawa a kawo mishi abinci ko kuma yaje can yaci. Rannan ranar lahadi ne ya wayi gari yana gida ban tsaya na shirya mishi abin karyawa ba ina cikin aiki na sai naji yana kwala mun kira na dauraye hannuna naje na same shi nace mishi gani ya tsura mun ido wai ke me ya same 106 kin e kike wani cika kina batsewa ana kallon ki? Nace shi ne dalilin kiran nawa? Yace eh ko yayi kadanne? Nace shi ne dalilin kiran nawa? Yace eh ko nayi kadan ne ? nace a'a ba ka yi amma kasan ina da abin yi in shike nan ina so zan tafi yace to ba laifi jeki, na juya na fita na koma wurin aiki na sai kawai na ganshi ya fito da saurin shi yan matan da suke tayani aiki ya kira yana rabawa kudin wata bayan banfi kwana hudu da biyan su ba, da ya gama basu sai yace kuje gida sai an neme ku ko, sukace to suka kama hanyar fita ya leko dakin da nake yace fito daga nan na hana wannan sana'ar daga yau, sahura ta ruga da gudu ta shiga cikin gida wurin su umma sai gasu sun shigo tare meke faruwa ne sa'idu? Yaya zaka koran mata ma'aikata ka hana ta sana'ar ta? Ya fito daga ciki ta samu ta shiga ta ganni a tsaye ina kuka kuzo nan ku biyoni muje can ni da shi muka bita sahura kuwa ta tsaya tana kokarin ganin munyi cake din da aka riga aka kwaba don kar muyi asarar shi. Muna gaban umma sa'id yana bayanin sana'ar ta ishe shi, baya anfanin taba don taja mishi asara iri iri da bacin rai don haka daga yau bai yarda ba, bai yarda a sake 107 yin wani abu don sayarwa ba, tunda ya lura ma sana ar tawa tana kara bani damar raina shi, umma ta juyo gare ni ban iya ce mata komai ba, kuka kawai nake yi ta gaji tayi mana nasiha tasallame mu muka tashi muka tafi bayan sa'id ya dage kan cewar zan koma kan sana'atane kawai bayan mun zauna mun ajiye sabbin sharuda ni da shi. Shikenan daga wannan lokacin na koma irin zama na na farko bana komai daga wanka sai yan aiyukan da basu taka kara sun karya ba, sai ko kwanciya, a haka dai sa'id ya lallabani muka shiry a a dalilin bani da wata hujja ta kin daidaitawa da shi, abubuwan da suka faru maganar sana ata kuwa yace shikam a yanzu ya zama mishi wajibi ya kiyaye duk wani abinda zai iya kawo mun mas'ala inna sake samun wani cikin tunda shikam ya matsu yaga ya samu kwanshi, to ni kaina haihuwar nake so duk da nikam ina boyewa amma da za'a tona cikin Zuciyata babu mamaki a tarar na fishi matsuwa da ita, don kuwa gani nake tanfar haihuwar itace kadai zata rage mun mas'alar da nake ciki, gani kuma anan daga ni sai malle kullum kuwa inna ta kan gaya mun cewar in 108 Allah Ya baki haihuwa kiyi tayi ki tara yaya da yawa sai kiga kin fita cikin kewa. A wannan lokacin sai muka yi matukar zaman lafiya ni da sa'id lokaci mai tsawo babu wani abun da ya sake faruwa a tsakanin mu abinda bai taba faruwa ba nikamna saki jiki na sosai ganin irin yanda yake tarairaya ta da ji dani sai na zama akowane lokaci in banda kara son shi babu abin da nake yi. Rannan ya dawo daga wurin harkokin shi da yamma naje na same shi a dakin shi nayi mishi sannu da zuwa ya amsa na tanbaye shi za'a kawo abinci yanzu ne? yace a'a ai, kin san na karya kenan na fita nace eh yace yanzu dai zo tukuna in miki bayanin fili na, nayi maza na matsa kusa da shi na zauna yace to wannan dana gaya miki na hanyar dan batta kudin shi sunyi yawa don kin san na gaya miki babba ne kwarai dari da dari wajen goma sha biyu ne aciki ni kuma zan sone in sayi flin da zan iya katangewa in gyara komai don in tura manbila a debo mun shanuna in zuba in kuma bude wurin kaji don haka zan bar wannan inje in duba na can hanyar wudil in naga zan iya sai in saye shi. 109 Nace to amma shi wannan din zaifi dacewa da kiwo sosai, tunda shi yayi nesa da garin nan, hanyar wudil aiya zama cikin gar sannan nan din a yalwace kwarai yake ina ganin da zaka yarda sai ka dauki kudin da suke account di na ka hada kayi amfani da su tunda inka hada ai zasu gama maka aikin yayi maza yace a'a a'a, bar kudin ki kawai, na kalle shi cikin natsuwa nace mishi akan me ? akan ni ba abokiyar rufin asirin ka bane ? yace a'a ba haka bane, nace to na sha ganin ka kana rancen kudi wurin su yaya babba da yaya balaraba, wato nice da ban? Yace ba haka bane, yayi mun bayani mai tsawo sai dai ban gamsu ba ganin na matsa da hakan sa' id ya amince da karbar kudi na, amma a matsayin rance in ya samu zai maido mun su, nace mishi to kwana uku bayan nan ya dawo gida da rana ya kirani dakin shi ina shiga na tarar ya juye tulin kudi akan gadon shi dukan su takardun naira dubu dubu ne,nace kai kai ina ka samo mana kudi haka? Ya zubamun ido yana kallona yace wadannan duk kudin kine seungel da kika yi ta wahala kina neman su, kusan shekaru hudu baki taba daukan ko kwandala ba, gashi kin bani su a 110 matsayin rance babu wanda ya sani, watakila kuma kin taba jin labarin cin manar maza da kuke cewa ko ince rashin alkwarin su na matan su su tallaba musu lokacin da suke wani abu na neman ci gaba in kuma bukatar su ta biya sai suyiwa matan nasu tukuici da kishiya, bakya tunanin nima zan iya yi miki haka? nace ban sani ba, ni dai abinda na sani shine kawai alheri nake nufi yace haka ne, to misali innayi miki irin wannan din fa tunda nima miji ne ban kuma banbanta da sauran maza masu yin hakan ba yaya zakiyi? Nace Allah ba zai hanani yanda zanyi ba, ya sake cewa hakane, 'n kara tunani in gani ko zan karbi kudi na kawai a sayamun wata kadara ko shiga na a matsayin rance, nace mishi yayi amfani da su kawai. Nan da nan aka sayi fili aka Katangeshi aka gayara komai aka gama ni da umma da tasi'u muka je ganin wurin umma, ta tara ce mishi ai kuwa dah har kace zaka hakura da wannan din, saboda kudin ka baza su kai ba yace eh umma maryam ce ta bani kudin ta tace in hada umma tace to Allah ya kara rufa asiri yace amin. Wata guda bayan nan tasi'u suka dawo 111 daga manbila, shanun da ardo ya baiwa sa'id sukaje daukowa suka hado da nasu, ni ma ardo ya aikomun da yanmatan shanu wadan da basu taba haihuwa ba guda ashirin da bijimaye uku da akuyoyi irin na manbila masu manyan kunnuwa, suma guda goma da bunsurayen su uku, yace a kawo mun inyi iri, shikenan sai aka soma kiwo an riga an sanya kaji a wurin su, an zuba leyas an zuba buroilas. Tasi'u sa'id ya sanya a matsayin mai kula da gonar ya kuma dibi ma'aikata su hudu tare da masu gadin gonar suma su hudu, a haka aka soma. Ranran ya dawo daga gonar da. yanma hankalinshi a tashe yake yana gaya mun wani yanayi da ya gani a jikin shanun ya kuma kira likitan dabbobin da yake duba su ammaa bayanin da yayi mishi shi bai gamsu da shi ba, nace to ko zanje ne in duba in gani gobe in Allah Ya kaimu? Yace yau wa maryam in kinyi hakan ai kin taimaka. Washegari da safe nayi shiri kwalliya mai kyau nayi cikin wata doguwar riga har kasa dinkin senegal na daura dankwali a kaina na kuma yafa gyale na madaidaici na sanya takalmi na lowshoe mai kyan gaske ga 112 waraiwarai da zobuna sun kama hannu na sai daukan ido sukeyi nayiwa umma sallama muka fita ni sa' id zuwa gonar nayi matukar jin dadin ganin dabbobin gidan mu cikin murmushi da jin dadi na shiga cikin su sa'id yana mun kashedin harbi fa suke yin ace mishi ai sun sanni ba zasu manta niba, na matsa jikin su ina duba su nace mishi bafa wata mas'ala ban, canjin wuri ne kawai da kuma ciwon da wasu sukayi a kofato da za'a bani sabuwar reza da almakashi zan gyara musu kofato da sauri, ya sa aka kawo mun ina karba sai yace mun to bari inje nan wurin da ake Fada mana abincin su ba bazan fi minti taiatin ba, zan dawo sai in kaiki gida nace ko awa daya ba laifi yace to sai na dawo nace to Allah Ya bada sa'a. Said yana barin wurin na shiga yin aiki na har n agama ina kara dudduba su sai naji ina shakkar kamshin wani turare da baimun kama da na miji na ba, na juya maza na waiwaya don inga waye mai wannan kamshin? Mahmud na gani tsaye a bayana gabana yayi matukar fadiwa don kuwa nayi ma rabon da in ganshi tun zuwan da suka yi da sa'id nayi musu bari sai ko yau, ya sakn mun wani lallausan 113 murmushi yace sengel kenan kin kara kyau kin kara gwarjini kin waye kin zama matar birni banyi kokari ba dana hango ki daga nesa na gane ki? Rabon da in ganki fa tun kina amarya saboda na gane mai gidan bai son zuwa na gidan shi, a zuciyata nace babu damuwa tunda dai nasan kina so na, nayi maza nace mishi waya gaya maka haka? Ya sake wani murmushin yace aiyukan ki suke nuna mun rashin jaruntakar ki a kusa da ni shike kara baiyanar mun da asirin zuciyar ki in daga ido don in baiwa Mahmud amsa sai kawai ga sa id a bayan shi yana tsaye fargaba da tscro suka a kamani jikina ya sake daukan wani rawan ganin yanda yanayi naya sauya gaba daya yasa Mahmud yayi saurin juyawa don ganin abin da ke faruwa yana murmushi kuwa bai motsa ba daga yanda yake, hannayen shi duka biyu suna cikin aljihun shi yace mishi barka dai. Bansan yanda aka yi ba sai na tsinci kaina dace mishi har ka dawo? Ya zubamun ido Cikin natsuwa yace nayi sauri ko? nayi maza nace mishi a'a don na gane kuskuren tanbayar da nayi mishin, yaya in kin gama mu tafi ko? nace to na wuce na barsu shi da Mahmud ban 114 san me suka tattauna ba. Tun daga hanya na lura shan iska yake yi nima sai na tsira muna isa gida kuwa naje na gaya wa uinma dawowan mu na wuce dakina na turo kofa ta na rufe har na hau gado na na kwanta sai gashi yazo ya tsaya mun a bakin kofar dakina dama kun shirya zaku hadu acan ne? bakin ciki da takaicin tanbayar yasa na amsa cewar eh, ya zubo mun ido cikin natsuwa yace yayi kyau, haka din ba kuma laifin ki bane, sakarci nane ya jawomun hakan in bah aka ba ai na dade da zargin akwai wani abinda ke gudana tsakanin ku amma na krsa daukan mataki mai tsanani, saboda ina tsoron abinda zai kawo batanci a tsakanina da ke nayi maza nace me kake nufi yayan sahura da irin wadan nan kalaman naka? Yace abinda kika gayamun kin san kowanne dan adam yana da jarrabawar shi a rayuwa, ai an jarrabe ni da son wacce bata sona duk abubuwan da kike yi tayi mun na nuna mun kiyaiya a zahiri na kasa hakura da ken a kasa daukan mataki mai tsanani akan ki, saboda zuciyata ta kasa jaruntakar yin hakan to gashi yanzu gashiii... .. yana cikin maganar ya soma haki da sauri da sauri saboda tsananin 115 bacin rai nayi maza na isa gare shi don in kai mishi dauki tare da fadin bah aka bane yayan sahura ina dora hannuna a jikin shi yayi maza ya hankade ni kar ki sake kar ki sake yin wànnan gangancin ki barni kawai ki kyale ni ki fita hanya ta kar ki sake taba ni. Tsoro ya kara kamani ganin yanda sa'id ya fita cikin haiyacin shi cikin dan takaitaccen lokaci na taso nazo kusa da shin a durkusa yayan sahura bafa komai tsakani na da Mahmud da sauri yace mun karki karamun wani bakin cikin kar ki nemi ki mai da ni wani mahaukaci sabo da rawai kinga duk abinda kike yina kasayin komai bayan na fara zargin wannan al'amarin bana kama wasikan Mahmud da yawa a gidan nan sunanan kuma ina ajiye dasu nama dauki sabon complimentry card din shi a cikin falon nan na kuma san bani nazo da shi ba, na zaro ido cikin matsananncin tsoro ban taba sanin akwai irin wannan zargin a tsakani na da shi ba, zargi a tsakanina da mijina, wannan al'amari ya muna na Inna Lillahi Wa Inna llaihir Raju'un' abinda kawai nake ta fadi kenan cikin zuciyata. Zama na da sa'id ya shiga wani hali na 116 wani irin matsanancin tsananin da ban taba tsanmanin zama tsakanin mace da mijin ta yakan kai wannan matsayin ba, na rasa inda zansa raina inji dadi nayi kamar inje in kai maganar wurin umma sai kuma nayi wani tunani nace to ai watakila su dukan su sun dade suna mun irin wannan zargin dana zauna nayi tunani mai zurfi sai naga ni karshen wulakanci da tozartawan da sa'id zai mun kenan, shi ne nay a zauna dani yana zargi na akan ina auren shi ina mu'amala da wani can daban to akan me? Akan bukata ta ta zarce tashi ko kuma akan zai bani wani abin duniya? Ina zaune da sa'id a haka rannan sai aka wayi gari da safe ban ji motsin shi ba har yamman tayi bangan shi ba babu shi babu dalilin shi, hankali na yayi matukar tashi saboda ko bama kula juna ni da shi amma kuma muna jin motsin shiga da fitar juna, na tashi na fito cikin dare na bude kofar dake tsakanin na da umma don inje in tanbaye ta ko ta san wani abu game da shi ina shiga cikin gidan sai na fasa yin hakan, saboda yanda na same su dukkan su suna barci, na tabbatar idan yana cikin wani hali babu yanda za'ayi gidan yayi shiru haka, na juya na dawo wuri na 117 nayi alwala nayi sallah sannan na hau gadona na kwanta. Washegari da safe wurin malle na samu labarin sa'id ya na Senegal sai da ya cika sati biyu ya dawo ina jin kwarainiyar oyoyon da akc mishi ban je ba, har ya gama zaman shi wurin umma ban shiga ba, ya shigo wurin mu ya nufi wurin shi ban kula shi ba, ina kwance a dakina sai naji yana kwala nin kira na taso nazo batare da na amsa ba. Sau nawa mahmud yazo gidan nan da bana nan ? ban tanka mishi ba na juya zan koma dakina sai kawai naji ya figoni ya wurgar dani Ian kujera nayi mummnunan faduwa, ai in riga kinyi kuskure da kika zabe ni kika barshi tun farko da dai kinyi hikima kin dauke shi kika bar ni a wancan lokacin to da na nuna nuna miki halacci na don bazan taba daga ido in kalle ki da wani kallo ba face na matar aboki na to amma tunda shi yaga zai keta haddin aure na ke kuma kin yardan mishi yayi hakan to zan nuna muku iyakar ku ke da shi, ina da hakuri da tawakkali akan al amura na amma akan wannan cin zarafin da kuka mun zan tsaya inga iyakar abin da kuke nufi ya juya zai bar wurin sai ga wata takarda a yashe a kasa ya sunkuya ya 118 dauke ta ya zuba mata ido zuwa can ya juyo yace ga wasikar ki na karba ina duba wa, ga abin da aka rubuta: "Na gode kwarai da alkwarin da kika samu cika mun jiya, nima kuwa nayi kokarin cika nawa da nayi miki in har zaki samu sarari tsakanin gode da jibi zan so mu sake haduwa sai dai zan shawar ce ki, da ki kula kwarai don kin san mutumnin in har yana gari to zaisa ido kwarai a kanki, don haka in har kinhango fitan naki zai zamo da mas ala to kar ki damu sai mu jira sai ya sake yin wata tafiyar Sai mun sake saduwa Na Gode Da Kaunar Da Kike Nuna Mun. Na saki takardar ta fadi a kasa na daga ido na kalli sa id nace mishi yayan sahura na gaji da wadannan al amuran da suke faruwa, kafi kowa sanin inda kaje ka dauko ni, in akwai tarbiya a gidan mu ma ka sani, in ma babu kasani, baka da hujjar zargina da abubuwan da kake zargina inyi mu'amala da wani na miji bayan kai, akan wane dalili? Ban taba yin sha'awar data zarce taka ba, kaima yaya na kare da kai balle inje ina neman wani? Ya zubo ido 119 yana saurarona cikin natsuwa lokacin da wani sako ya shigo cikin wayar shi ya duba sakon sannan ya miko mun wayar na karba ina dubawa daga bankin da yake mun ajiya ne aka turo mishi ana baiyana mishi an sake sabunta account din da wasu zunzurutun kudi da ban tsaya kallon sub a itama wayar na sake ta a kasa yace wannan ba alkawarin da akace an cika miki bane? Nace shine bazan sake musu da kai b akan wannan al amarin abu daya dai kawai da zan sheda maka a yanzu shine ban bukatar zama da kai tunda har zuciyar ka ta yarda ta amince da cewar zan 1y aikata wadannan abubuwan da kake zargina akan su in ka manta bari in tuna maka kaje ka daukoni ne a gidan da ake ganin dan halal baya zina kaje ka daukoni ne a gidan da ake gudun abin kunya saboda kawai an baka ni ka kawo ni inda bani da kowa kazo kana wulakan ta ni to ka maidani cikin dangina sub a zasu taba zargina da abinda kake yiba, hankali yakai matuka wajen tashi in banda kuka babu abin da nake yi, sa'id ya juya zai koma dakin shi sai kawai na mika hannu na rike rigar dake jikinshi, a sanyaye yace mun sake ni maryam tun ranki bai baci ba, sannan daga yau 120 zan miki kashedin inma shi ya bakı shawarar in muna maganar dake ki rike ni to kar ki sake sakemun rigata nace bazan saki ba sai ka salla.....ban karasa ba ya juyo cikin sauri ya dauke ni da wani gigitaccen mari sai da ya kifar da ni a kasa ya wuce yayi tafiyar shi ya shige dakin shi ya turo kofa ya rufe, na gama kwanciyata anan har na gaji na tashi na koma daki na kama shirye-shiryen tafiya manbila zan koma gaban 1yaye na zan koma rayuwata ta farko ta fimun wannan rayuwar da nake yi a yanzu, na kara gane gaskiyar ardo da yace mun babu komai cikin rayvwar birni in banda kwarauniya da kwamacala na kammala shiri na tsaf sai dai kuma abin takaicin shine ban mallaki komai ba in banda naira dubu daya da dari bakwai a dakina na tsaya ina tunanin ina zan samu kudin mota'? Nayi ta tunani na rasa sai nace to bari tunda tafiya zanyi bari inje in tunawa sa'id rabon da ya bani kudin aiwatar da hidimar gida kusan kwana arba' in ne in yaso in ya bani sai inyi amfani da su kawai, ina išowa dakin nashi sai kawai naji shi yana cewa aikin sun da itan kika bugomun wayar a yanZu tunda kuwa tsoron da kike magana akai bai hanaki 121 bugomun wayar dare ba nima kuwa ai bazai hanani amsawa ba da sauri na bar wurin saboda wani abin da naji zuciyata tana yi ban taba jin maganar sa'id da wata mata ba tsawon zaman da nayi da shi sai ko yau har gari ya waye ina tsaye a dakina ban samu zama ba balle inyi tunanin kwanciya malle ta shigo ta sameni a tsaye gaishe ni kawai tayi ta juya zata tafi nayi maza nace mata zo mana malle ta dawo ta tsuguna tace ganı nace mata zani manbila yanzu kizo mu tafi amma karki gaya wa kowa tace a'a, bazan biki ba, nayi maza nace mata akan nme malle? Na zauna ina rarrashin ta ta yarda ta bini mu tafi, tace mun a ajiya da daddare tayi wa yaya sa' id alkawarin zata zauna da shi na sake kallon ta nace alkawari malle kina haukane? Tace mun kiyi hakurI amma na gaji da irin sabinda kike mishi ace shi da gidan shi amma wai jiya ya kwana a waje sabaoda gudun fitinar da zakiyi mishi bayan daga tafiya ya dawo kuma ai baffa yace mana abinda duk muka san bama so ayi mana to muma kar muyiwa wasu da matar yaya jauro take koro shi waye yake kwana ai tashin hankali kuka rinkayi da ita to yaya ke kuma zaki so kina Koran yaya 122 sa'id? Da sauri nace mata ke malle wane irin maganar banzane wannan nice zan iya Koran yayan sahura daga cikin gidahnan? In baki sani ba jiya har duka na yayi na kuma ji shi yana waya a dakin shi suna hira da wata mata nan take ta kama kuka dadi ya kamani don ina ganin kukan tausayi na take yi sai kawai naji tace mun Allah sarki da-da in zaki mance da komai ai bai kamata ki mance da nasihar baffa ba ko don soyaiyar da yake miki shi kuwa nasha jin shị yana cewa mafi munin abinda dan adam zai yi shine fadar maganar da ba gaskiya bace kinre mun ya þuge ki kuma kin jişhi yana hira da wata a waya bayan kumá ni yaya sa id a dakin mu ya kwana yana gaya nmun ya bar nan dinne sabodd gudun fitinar ki, a kidime nace mata a wurin ku yayan sahura ya kwana malle? Tace kwarai kuwa nace to waye ya bugenswaye naji yana hira da mata a dakin shi? Tace uhun ta juya tayi tafiyar ta ta barni nan a zaune tsoro ya sake kamani ha tabbatar al'amarin dake faruwa dani don haka babu abinda ya kamace ni illa in koma gaban iyaye na, a yau dinnan ko bani da kudin mata da sauri na tashi na dauki akwatina na saci idon mutanen gidan na nufi 123 tasha na dauki shatar mota zuwa manbila har cikin iugarmu na cewa direba to ai zaka shiga ne ka dan huta sai gobe ka tafi ko? Yace a'a ni yanzu zan juya nace to bari in shiga in miko ma kudin ka yace a'a aini an riga an biyani nace wa ya biya ka? Yace a'a w2ce irin tambaya ce wannan nace to bari ina zuwa nayi maza na tafi na kira yaya jauro don yazo ya tanbaye direban motar mutumin dayake cewa va biya shi muna dawowa muka ga babu shi habu dalilin shi, na kalli yaya jauro cikin matsanancin tsoro da fargaba nace mishi yaya jauro anan fa direban motar ya tsaya yace ashe har ya ar nan wurin ya bace daga tsaunukan nan da suke kewaye da mu? Yaya jauro vace ke suengel nifa dama ban wani ji motsin wata mota ba ganin ki kawai nayi kin shigo da jakar ki. Ina jin yaya jauro ya fadi haka na yanke jiki na fadi a kasa na suma. Masu karatu sai ayi mun hakuri abiyo ni littafi na hudu don jin karslhen labarin ayi hakuri kwarai don kuwa ban so jan labarin haka ba, bai zai kammalau bane cikin littafi na uku ba. 124 Na Gode. Taku Hafsat Chindo Sodangi. SADAKA GA MATA DAKE DA MAS ALA DA MAZAJEN SU Su yawaita karanta wannan ayar dake cikin Suratul Yusuf (Alaihis - Salam): "Rabbi Kad Ataita Ni Minal Mulki Wa Allamtani Min Ta'awilil Ahadis Fadirus Samawati Wal Ardi Anta Waliyyi Fidduniya Wal Akhira Tawaffani Musliman Wa Alhikni Bissalihin" Ubangijin Mu Allahu Yasa Mu doge Amin Sunma Amin. In Kika Dimance karanta ta Allah Zai Baki Zaman Iafiya Da Mijin Ki. 125 SAKO Ga wadan da suka samu mas'alar rashin fahintar wani abu cikin littafin matn da kicin dinsu suna iya aiko da tanbaya ta cikin wannan layin dana bayar cikin wancan littafin. 07035586299, Allah Ya taimake mu amin. 126