🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *DIKKO AHMAD* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail majidadi* *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Bismillahir rahmanur rahim Dedicated to DIKKO AHMAD (DK Excellency) Gajeran labari Page 1 Tsayawa Ummi tayi jikin k'ofar d'akin D'an nata tana murmushi,matace da bazata gazawa shekara 45 ba tasha wanka cikin tsadadden leshinta juyanta da hannayenta duk gwalagwalai kallo d'aya zaka mata kasan cewa dukiya ta ratsata da Kuma hutu,k'arasa shigowa tayi cikin d'akin ,ko kad'an beji shigowarta ba,sai da ta k'araso ta janye head phone din da yakebin wak'ar daya rairai,bud'e lumsassun idanuwansa yayi masu Kama dame jin barci ya saukesu akan Ummi din tashi,fara'ar fuskarsa ta yawai yace"Ummi yaushe kika shigo?",zama tayi gefen bed din tace"DIKKO ya za'ayi kasan na shigo kana nan kana sana'ar taka"gyara zamansa yayi tare da sosa kai yana dariya yace"Ummi kinsa wak'a fa burina ce,kuma farin cikina",gyad'a kai tayi tace"nasan wannan,Kuma kasan ni da Abbanka da y'an uwanka duka muna goyon bayanka ,tunda haryin wak'a besa ka watsar da karatunka ba,yanzu ka tashi muje kaci abinci saika dawo ka daura daga inda ka tsaya"hannunsa ta ja zuwa main parlo na gidan.Dikko kyakyawan namiji ne,ba fari bane ba kuma zaka kirass bak'i ba,dogone sai dai ba zaka kirasa mai jiki ba,a ko wanne gefen fuskarsa yana da alamar lotsawa wato dimful,fuskarsa dauke da saje Wanda ya k'ara k'awata kyawun fuskarshi,dai dai gwargwado DIKKO namiji ne Wanda ko wacce mace zatayi burin mallaka a matsayin mijinta.su ukku ne a wurin Mahaifinsa Alhaji Ahmad Canji,babban yayansa Aliyu sai shi sai kuka k'anwarsu Zainab.suna cikin farin ciki da k'aunar junansu,a parlo suka samu duka y'an gidan nan fa suka fara fira ba k'akkautawa cike da zallar soyayya suke gabatar da komai. "Fatyma wai yanzu ba makaranta zakije ba?,shine kika tsaya kallon wak'a a TV"Umma ta fad'a rike hab'a. Wacce aka Kira da Fatyma ta juyo da sauri ta kallon Umma,ganin Umma tayo kanta yasa tayi waje da gudu tana dariya.Dariya Abdul ya saka yace"kai Umma har yanzu baku daina wasan kwaikwayon nan ba kenan?",dawowa Umma tayi ta zama a d'aya daga cikin chairs din parlon tace"wallahi Abdul abun yarinyar nan harya fara damuna,ada ina dauka yarinta ce,ashe ba haka bane bata da abunyi saijin wak'ar wannan yaron ,inko taga pic dinsa ko video dinsa yadda kasan zatayi hauka haka take komawa,ina tsoron ranar da Daddynku zai iya gane wannan nasan daga ni har ita bazamu tsira ba".sosai Abdul ya tattaro hankalinsa ga Umma yace"kedai kiyi mata addu'a kawai,sannan Kuma yadda Daddy yake son Faty nasan zai iya sadaukar da komai akanta ,insha Allah komai zaizo da sauki"Gidan Alhaji Kabir babban gida ne kallo d'aya zaka masa kasan an zuba nera tayi kuka a gidan,matansa biyu da yara hud'u,Umma itace Babba tana da yara Abdul da Fatyma,sai Aunty tana da yara Aysha da Salma,Abdul shine Babba a gidan sai Aysha sannan Fatyma sai Salma Auta,suna zaune cikin fahimtar juna da kwanciyar hankali Wanda bazaka tab'a iya cewa gidan Wai kishiyoyi ke rayuwa ba kansu a had'e yake,sai dai matsaloli na yau da gobe Wanda baza'a rasa ba. Kallon Faty Aysha tayi tace"Allah yayi kin fito kenan?,saura kad'an nace Driver ya tafi ya barki can kwa had'e da Umma,tunda bakya da aekin yi".dariya Faty tayi tace "haba Yaya Shooly ae nasan kece me hana a tafi a barni,tunda dai kinsan a dole na kalli muradina kafin na iya aekata komai a safiyar nan".binta da kallo Aysha tayi harta shiga mota girgiza kai tayi zuciyarta cike da tausayin k'anwar tata. Koda sukaje scul nasha mamaki da ganin sunan da kowa ke Kiran Faty da shi FD(FATYMA DIKKO),wani ma besan ainahin sunanta ba. Tana zama ta kalli Zainab tace"k'awata Allah yasa yau baki manto da Album din ba?" "Inafa zan manto kihauni da neman rigima,kaini na k'agara ayi hutu ko zan samu na koma gida kuwa" Wani kallo Faty tabi zainab dashi tace "kajimun yarinya sai kace ba jiya kika dawo daga Abujan ba,amma har kin Kuma son gida?" Dariya Zainab tayi tace"wa yak'i gida,aeni kam zaman kano dole kawai ya zame mani" "Yanzu dai ba wannan ba,ki bani abunda kika kawo mun". Girgiza kai Zainab tayi ta ciro albums guda biyu na wak'ok'in Yayan nata ,Wanda bata so ko da wasa Fatyma tasan gidansu d'aya ,ta mik'a mata tace"ke ae baki da wata tsaraba data wuce wannan". K'ara fara'a Faty tayi ta karb'a tana jerowa Zainab addu'o'i kala kala. Faty kyakyawar yarinya ce,ba zata gazawa shekara 18 ba,y'ar gatace a wurin iyayenta musamman Daddynta yana matuk'ar sonta,tana da matsakaicin jiki haka ma tsawonta,farace ita,gata kyakyawa ajin farko,tun ranar data fara jin wak'ar DIKKO ta makance akan tsananin soyayyarsa bata da burin daya wuce ta gansa a rayuwarta ko da sau d'aya ne.wannan kenan. Tunda suka dawo daga scul ta kure volume da sautin kid'an a d'akinta sai juyi takeyi tana jin wani matsanancin farin ciki a ranta. "Wai waye kejin wa'an nan wak'ok'in ne?kinsan bana son wanann abubuwan,meye ma a tare da wannan mabaratan"Daddy ya fad'a. "Mabarata Kuma Alhaji "Umma ta maimaita. "Kwarai kuwa ,ae duk mawak'a mabarata ne,meye wanann inba rok'oba da rashin abunyi,shashanci da b'ata lokaci"ya Kuma bata ansa. Jinjina kai Umma tayi hakika tasan tabbas Alhaji Kabir ya tsani talakka ya Kuma tsani mawak'a a cewarsa mabarata ne da Kuma rashin aekinyi yasa sukeyin haka,cikin sanyin murya tace"Fatyma ce ,kasan ita kad'ai kejin waka haka". Tofa koya zata Kaya ga wannan sark'ak'iya,kudai ku biyoni danjin ya zata kasance. Taku har kullun majidadi Show me some luv by sharing dis. Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *DIKKO AHMAD* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail majidadi* *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* *Dedicated to DIKKO AHMAD (Dk Excellency)* Page 2 Masu neman wak'ok'in Dk Excellency zaku iya tuntub'ar wannan number din 07033636337 Ummu batace komai ba ta wuce d'akin Faty ta kashe wak'ar da kanta,d'agowa tayi da sauri da niyyar zabga masifa sai kawai taga Ummu saurin sunkuyar da kanta tayi ta kasa cewa komai sai faman shagwab'e fuska takeyi. Ummu kam ficewa tayi tana hasaso abunda ke shirin faruwa a gidan nasu. Tashi Faty tayi ta wuce part din Auntynsu dan tasan Daddy yaukam ba wurinta yake ba,da sallama ta shiga anan ta samu duka y'an gidan nasu suna fira,kallonta Yaya Abdul yayi yace"tofa y'ar gidan Daddy yau Kuma meke faruwa ne?" Dariya Salma ta saka tace"yo ta wuce Ummu ta hanata sana'ar nata kasan shi kad'ai ke b'ata mata rai" Wani uban harara ta zabgawa Salma tace"wallahi zanci k'aniyarki a gidan nan,toma yaushe na zama k'awarki". Shiru Salma tayi tasan nan fagen ba wasa indai akan DIKKO ne. Murmushi kawai Aunty tayi tace"kinga y'ata yi hakuri kije d'akina babu kowa sai kiji abunki a tsanake"rungume Aunty tayi ta baya tace"I love u Auntyna"sanann ta ruga da gudu kamar wacce ake tillawa rashin k'ibarta yasa ko kad'an Faty batajin nauyin jikinta. "Ni banga abunson zuwa a taron nan ba Dikko,baka gajiya da tafiye tafiye,wallahi wannan kad'ai yasa nake shakkun wak'ar nan taka"Ummi ta fad'a tana gyara zamanta. Matsowa kusa da ita Dikko yayi ya Kama hannuwanta duka biyu yayi k'asa da murya yace"Ummina ta kaina,kinsan iyakata Kano fa,Kuma wannan taron yana da mahimmanci a gareni a matsayina na mawak'i,wannan taron zai tara manyan mutane da manyan mawak'a Kuma kinsan na riga na gabatar da wak'awa ta Fyad'e illa ga mata,ina jerin wa'anda zasuyi wak'a a wurin,ki sakamun albarka kawai Ummina". Kallonsu Aliyu yayi yace"Allah Ummi ba wata damuwa yaron nan wannne gari ne baya zuwa sai nan da kano kice a'a ,nima zanje ammafa ni bazan kwana ba" "Shikenan na yarda yaje amma saidai ka zauna gidan Aunty balaraba inda Zainab take zaune,Kuma ka kula da kanka sosai,bana son shirmen yaran zamani ka rik'e tarbiyar da muka baka,amma in kaje yaushe zaka dawo?"Ummi ta fad'a tana kallonshi. Shiru yayi alamar tunani sannan yace"Ummina ina kewar Kano zanyi kamar 2weeks acan"Dikko ya fad'a. Zaro ido Ummi tayi tace"haba Son zaka tafi ka bani kewa har haka?" "Gaskiya Son 2weeks yayi yawa,zaka barmu mu kad'ai"Abba ya fad'a Wanda shigowarsa kenan,zama yayi kusa da Dikko cikin tsananin soyayya yace"anya zan iya hak'ura har 2weeks kuwa,kasan fa a gidan nan kaine kawai kayi karatu a garin nan,ko Aliyu zuwa jibi zai wuce gidan zaiyi babu dad'i". Dariya Dikko yayi cikin tsananin kaunar iyayensa yace "to Abbana bazan kaiba insha Allah,nima zanyi kewarku sosai". Murmushi Aliyu yayi yace"yaro kamar wani jariri ko mace kullun yana gida tare da ku bakwa barinsa yaga duniya". "Ae Son baya da maraba da jaririn"Ummi ta fad'a tana dariya tare da shafa kanshi. Shagwab'e fuska yayi yace"ni dai Ummi na girma yanzu ae".dariya duka sukayi. Next day Tun da wuri suka fito da shirin tafiya,a mota aka saka masa kayansa sai yaransa da suke aeki tare suka shiga motarsa ,shi kuma suka shiga shi da Aliyu driver yaja suka dauki hanyar kano,wurin k'arfe 3 suka isa Kai tsaye gidan Aunty Balaraba suka wuce,dan k'arfe 4 ake fara program din.da gudu Zainab ta fito tana masu oyoyo,"ke har yanzu baki girma Mai goshin jirgi"tsuke fuska Zainab tayi tace"Allah Yaya D ka daina,nasan na fika kyau ae".waro dara daran idanuwansa yayi tare da bud'e baki yace"tab dana daina fita yarinya"ya Kama hanyar wucewa ciki.dariya Aliyu yayi yace"Allah ta fika haskawa yar Beautyn Ummi". "Lallai yau muna da babban bak'i a gidan nan,ni wallahi Dikko har nayi fushi ae".sosai Kai yayi yace"Aunty B kin dai San Ummin ce bata so inayin nisa". "Aeni Ummi abun nata gaba yakeyi,aeko aure zamuyi maka kabar mata gidan muga ya zatayi to".haka sukaita fita kwanin birgewa sai da suka dawo sallah sannan suka soma shirin taiya wurin taron. Kwance take tayi rubda ciki tana jin wak'ar na ratsata tako ina,shigowa Salma tayi d'akin tana kiran"Ya Faty,Ya Faty"amma shiru zare ear piece din kunnenta tayi tace"aeta magana bakiji Yaya Faty". Wani uwar harara Faty ta zabga mata tace"bansan Iskanci Salma,wai ke bazaki daina mun irin haka ba ko?". "Kiyi hakuri dama Yaya Aysha tace na duba ko kin shirya zakije wurin taron". Tsaki Faty taja a hassale tace"bazanje ba,kuyi tafiyar ku".juyawa Salma tayi ta tafi ba jimawa saiga Yaya Aysha ta shigo kallonta tayi tace"dallah tashi ki shirya,kinsan taron yana da mahimmanci Kuma zaki iya ganin masoyin naki a wurin,kinsan taron manyan mawak'a nefa". Zunbur Faty tayi ta diro da sauri tace"wallahi Yaya na manta banyi tunanin haka ba "da gudu ta fad'a toilet. Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe. Stylish star Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *DIKKO AHMAD* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail majidadi* *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Page 3 Dedicated to DIKKO AHMAD (DK Excellency) *Happy birthday Hayat Baba zubair,Allah yaiwa rayuwa albarka* Cikin mintina kad'an Faty ta shirya tsab cikin tsadaddiyar leshinta kamar ruwan madara bubu ce rigan tayi masifan yi mata kyau sai pattern din pink ,hakan yasa shoe da mayafinta da bag suka kasance pink ,lite make-up tayi amma ta haska sosai sai zuba k'amshi takeyi,kamar wacce zataje gasar kwalliya,kallonta Aysha tayi tace"Masha Allah kai,Faty wannan kyau haka?,Anya mun kera dake kuwa?",dariya Faty ta saka tace Yaya muje kada lokaci ya k'ure mana.sun isa akan lokaci dan haka suka shiga tare da samun wuri suka zauna Faty kam sai raba ido takeyi.babu b'ata lokaci aka fara program din,anyi jawabi sosai akan illar Fyad'e ga mata da matakan daya Kamata a dauka sannan mawak'a suka fara baje basirarsu a wurin,lokacin da kunnuwanta sukaji an ambaci sunan Dikko Ahmad a matsayin mawak'i na gaba wani irin bugawa gabanta yayi da k'arfi duka tsigar jikinta ya tashi da k'yar ta hadiye numfashi ta mik'e tsaye zunbur tana fara kallonshi tun daga k'asa,sanye yake cikin gizna blue colour sai shoe covers bak'ak'e ,hulace dara ya murza a kansa ita kalar bak'a ga tsadaddiyar agogon hannunsa ,lokacin da idonta yakai akan fuskarshi batasan ta saki hawayen farin ciki ba,yaune rana ta farko a rayuwarta data tab'a ganin mamallakin zuciyarta,ji takeyi duk duniya babu Wanda ya kaita sa'a ko farin ciki a yau,duk abunda takeyi Yaya Abdul da Yaya Faty na kallonta ganin abun zaiyi yawa yasa Yaya Aysha girgizata tace"Wai meye haka?ki zauna dan Allah kada ki bada kanki a wurin nan".ina ko jinta Faty batayi idanuwanta da hankalinta suna ga Dikko ga wak'arsa dake ratsa duk wani sassa na jikinta(ga masu buk'atar wannan wak'a ko wak'ok'in sa zasu it's tuntub'ar wanann number kamar haka 07033636337).samu tayi ta zaunar da ita amma gaba d'aya Faty ta gama zauncewa da susucewa a wurin,neman hanyar kaiwa ga Dikko kawai takeyi shine zai iya sakawa ta samu sauki a zuciyarta.harya gama ya koma ya zauna amma bata daina binsa da Kallo ba. Da misalin k'arfe 6 na yamma taron ya tashi,juyowar da Salma zatayi taga babu Faty wayam a inda suke,zaro ido tayi tace"Yaya ina Yaya Faty,badai ta tafi wurinsa ba?"."Salma nima ina zan sani kin dai san halinta ae". Takawa takeyi a hankali harta k'arasa inda yake tsaye da yaransa,kasa furta komai tayi sai kawai taji wani kuka ya sub'uce mata tayi saurin toshe bakinta da hannunta,Dikko kam tunda ya kalli inda take sau d'aya be Kuma kallonta ba yaci gaba da aekin danna wayarsa.Zainab dake bayansa sarai ta gane Faty Kuma tasan halin Yayan nata dan haka ta fito da sauri taja hannun Faty gefe tace"meye kike k'ok'arin yi?,Wai abun har yakai haka?"Zainab ta fada.kukan Faty ta ida saki tace"Zainab zan mutu idan be kulani ba,tabbas mutuwa zanyi,ki tab'a zuciyata kiji yadda take harbawa,dan Allah ki taimakeni kada ya tafi banyi magana dashi ba".zaro ido Zainab tayi tayi matuk'ar tausayawa Faty duk ajinta da kyanta da irin mazan dake binta amma yau itace take kuka akan wani D'a namiji.hannu tasa ta goge mata fuskarta tace"ki nutsu zamuje ku gaisa yanzu,nayi maki alk'awari komai xaiyi daidai"godiya Faty ta soma zubawa Zainab kamar wacce tayi mata wani aeki,hannunta taja har zuwa gaban Dikko tace"uhm ga bak'uwa zaku gaisa,k'awatace".ya dauki tsawan minti ukku kafin ya d'ago ya sauke fuskarsa kan Faty yad'an saki fuska yace"bak'uwa sannu".ji Faty tayi numfashinta zai dauke lokacin dataji muryarsa ,murya na rawa tace"ya...yauwa,ina wuni".da lafiya kawai ya ansa,daurewa tayi tace"wak'a yayi Allah ya k'ara basira,sunana Faty".murmushi ya Kuma sakar mata yace"nice name,n gode,sai anjima"ya juya yayi gaba abunsa.wani ihun dadi Faty ta saki ta fad'a jikin Zainab tana saka mata albarka.da k'yar su Yaya Abdul suka jata zuwa gida sai da yayi mata alk'awarin zai samo mata number din Dikko sannan ta yarda suka wuce gida,sai zuba masu surutu takeyi a kanshi tana washe baki. Suna shiga gida da Daddy suka ci karo a parlo,gaishesa sukayi har zasu wuce ya Kira Faty tare da ajiye jaridar dake hannunsa yace"ki shirya anjima zakiyi ba'ko yaron aminina ne Alhaji Abbas wato Munnir zaizo ya ganki zamu saka ranar aurenku in Allah yaso next week"be kula da yanayin da take ciki ba ya mike ya fice abunsa.wani uban ihu Faty ta saki ta fad'i k'asa tana rike saitin zuciyarta ta fara rolling a k'asa tana k'walawa Umma Kira. Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe Stylish star Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *DIKKO AHMAD* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail majidadi* *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* A gigice Umma da Aunty Amarya suka fito suna tambayar ko lafiya,cikin sauri Aunty Amarya ta k'arasa gareta tace"Shima dai Alhaji sai da na fad'a masa kada yayi wannan kuskuren"dafe zuciya Faty takeyi tana fad'an"Aunty wallahi bana sanshi mutuwa zanyi,dan Allah ku cewa Daddy a'a,ni dai ya barni".Umma kam mutuwar tsaye tayi dan bata tab'a tunanin abun zai kai haka ba,da k'yar Yaya Abdul ya lallashe suka samu bacci ya dauketa kowa yana hango gagarumar matsalar dake doso gidan. Zama Zainab tayi tsakiyar Dikko da Aliyu tace"Yaya kaiwa Ya Dikko magana dan Allah ko sau d'aya ya saurareni mana",kallonta Aliyu yayi yace"akwai wata matsalar ne?",shikam Dikko wayarsa yake latsawa kamar bema san Allah ya halicci mutane a kusa da wurin ba,a zahiri wayar yake latsawa amma sam a cikin zuciyarsa surarta yake gani ,gizo kawai takeyi masa,tunda ya sauke idanuwansa akanta ya tsinci kansa da matsanancin sonta a yanzu baya gane yareyen da sukeyi nema Faty kawai yake maimaitawa a ransa."Yaya k'awatace ke San Yaya Dikko,wallahi ina tausayinta ban tab'a ganin wacce take yin so irin haka ba, yarinyar nan tana da tarbiyyah bata rasa komai ba,amma da tazo gaisheshi baka ga yarda ya ansa mata ba "ta k'are maganar cikin shagwab'e fuska kamar zatayi kuka.murmushi Aliyu yayi yace" to ke meye naki a ciki?,ki lallab'ashi ki gane ko yana santa shine kadai mafita". girgiza hannun Dikko tayi tace"Yaya pls"cikin basarwa yace"me Kuma ya faru sarkin rigima?"kuka Zainab ta saka tace"Yanzu Yaya baka ma san me nake cewa ba"ta daura hannu saman kai zata fasa masu ihu.ko kad'an Dikko baya son hayani gashi yana matuk'ar son Zainab da sauri ya toshe mata baki yace"lil dan Allah ki rufamun asiri ban shirya ciwan kai ba yanzu,ki gayamun meye kike so?".turo baki tayi tace"Yaya kace kana santa,wannan wacce mukazo kuka gaisa"."to Zainab in banda abunki ni ya za'ae na gane Mata nawa sukazo gaisheni?,bazan iya tunata ba,amma indai tayi maki ,to bana da matsala da wannan".tsalle Zainab ta daka ta rungume Dikko tace"that's why I luv u sweetheart".wayarta ta dakko ta soma nuna masu hotunan Faty,Aliyu yace"masha Allah".kawar da kai Dikko yayi yana yatsina fuska yace"nifa basai na wani ganta ba"ya mike zai bar wurin.cikin sauri Zainab tace"Yaya dan Allah kayi mata wak'a ina so sakon soyayyarka ya isa gareta ta wata hanya daban".kai kawai ya gyad'a mata ya wuce d'akinshi,yana shiga ya jingina kansa da k'ofar d'akin wani k'ayataccen murmushi ya saki tare da dafe saitin zuciyarsa yace"Faty,Fatyma,tabbas ina zuwa gareki,Kallo d'aya nayi maki na gane kinyi daban da saura,kedin bugun zuciyata ce".ba k'aramin farin ciki ya kasance a ciki ba,kawai ya soma raira mata wak'a. Da yamma Aunty ta lallashi Faty ta shirya cikin atamfa riga da siket tayi matuk'ar kyau duk da idanuwanta a kumbure suke saboda kukan da tasha.mayafi Aunty ta yafa mata tace"kije kiga bak'on bana son ran Daddynki ya b'aci in yaso daga baya ni zanyi masa bayani da kaina cewa baki sanshi,amma sai kinyi mun alk'awarin bazaki kuka ba ko Kuma wani abunda bai dace ba". gyad'a kai kawai Faty tayi tana k'ok'arin mayar da hawayen dake son zubowa ga xuciyarta dake bugawa da k'arfi.kamar marar lakka haka ta nufi d'akin da Munnir yake,can ciki tayi sallama tun kafin ta shiga k'amshin turarensa ya cika hancinta k'arasa tayi ta zauna can nesa dashi d'ago kanta tayi ta kalleshi babu laifi babu wacce zata kalli Munnir tace beyi ,katse Mata tunani yayi da cewa"Malama Fatyma barka da yamma,fatan na sameki lafiya?".can ciki tace"Alhmdllh ,Ina wuni".da lafiya ya ansa sannan yaja dogon numfashi yace"ina tsammanin kinsan dalilin zuwa nan wurinki?"gyad'a masa kai akwai tayi .yace"baki zaki bud'e kiyi magana,nikam dai Alhmdllh kinyi mani Kuma ina fatan zaki karbeni hannu bibbiyu".hawayen da take b'oyewa ne suka zubo cikin rawar murya tace"Munnir kayi hakuri,babu maccen da zata ganka tace bata sanka ko Kuma bakayi mata ba,sai dai ina mai baka hakuri na riga na kyautar da zuciyata bana tunanin zan iya k'arbota daga inda na badata ,da hakan zai yiwu dana hak'ura na faranta ran mahaifina,sai dai Kuma na gagara yin haka,kayi hakuri"saurin toshe bakinta tayi jin kuka na niyar kwace mata tayi waje da gudu,kai tsaye d'akinta ta shiga ta saka key ta fad'a saman bed ta rushe da kuka mai cin rai. Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe Stylish star Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *DIKKO AHMAD* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail majidadi* *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Shiru Munnir yayi yana tuna kalaman Fatyma,harga Allah yaji yana matuk'ar sonta sai dai ya hango tsantsar gaskiyarta a kwayar idonta,to waye wannan Wanda take so?,yayiwa kansa tambayar da bata da ansa,jiki ba kwari ya mike yabar gidan. Babu yarda y'an gidan basuyi ba akan Faty ta bud'e k'ofa amma sam ta k'iya hasalima shiru tayi ta gyalesu,cikin kankanin lokaci wani irin zazzabi da ciwan kai suka rufeta da k'yar take iya d'aga ido kwananta biyu a d'aki rufe,in taji jinwa sai dai ta sha chocolate da biscuits da take ajiyewa duk ta rame ta fice a hayyacinta . Kayane riki riki aketa shigowa dasu Kama daga biscuits,sweet da dai sauransu kaya jibge aka ajiye a parlon sama,kallon Daddy Ummu tayi tace"wannan kayan Kuma fa na menene?".sai da ya zauna sannan yace"kayan saka ranar auren Fatyma ne da Munnir nan da 2weeks za'ayi bikin".ba Ummu kadai ba sai da kowa ya raxana a wurin,Faty da tun shigowar Daddy take lekensu ta window ta saki ihu ta soma b'ari da duk wani kayan daya tari gabanta,kwalaben turare taketa jifa dasu duk abunda ya tari gabanta sai ta zubar dashi,kwalba duk ta fashe mata hannu jini yanata d'iga,muryarta ta dishe tsananin tashin hankali ko hawaye d'aya ya kasa d'igowa daga idonta,kawar da kai Daddy yayi lokacin da kowa yayi wurin d'akin yana bubbuga k'ofar tare da Kiran sunanta,tashi yayi yabar gidan gaba d'aya. Shigowar Zainab kenan gidansu Faty dan tanata gwada number dinta amma a kashe,ita da gudu ta k'arasa saman tace"Ummu lafiya?,meyake faruwa ne?".hawaye kawai kebin kuncin Ummu ta kasa furta komai cikin Kuka Salma tace"Yaya Faty ce yau kwana ukku tana rufe a d'aki,Wai dan Daddy ya saka ranar aurenta da Wani,gashi sai jiwa kanta ciwo takeyi".ba k'aramin firgici Zainab taji ba,buga k'ofar tayi da karfi tace"Fatu ki saurareni kada ki illata kanki,indai Yaya Dikko ne kin samu kin gama yanzu ma shine ya aekoni wurinki,ki saurareni dan Allah,Shima yana matuk'ar sonki kinji"tunda Zainab ta ambaci sunan Dikko Faty ta tsaya cak sai dai ta kasa motsawa daga inda take.zainab taci gaba da cewa"baki yarda dani bane yanzu zakiji shaida",da gudu ta koma cikin parlon hannunta na k'yarma ta kunna CD din da tazo dashi ta saka volume yarda zai kai har wurin Faty. Na tantance bugun zuciyata Fatyma ce take rud'ani,dan Allah ki yarda na turo gidan ku dan ayo mana baiko,duk cikin sahun y'an mata Fatyma ke nasa a gabana ,Babu ke a tare Dani ki sani tamkar bulo sunana. Haka taji muryar Dikko yana ratso ko wanne sak'o na jikinta yana sakar mata kalamai dake fallasa sirrin zuciyarsa zuwa gareta.ae da gudu ta k'araso kofa ta fito bata kula kowa a wurin ba tayi parlo,tsayawa tayi tana kallon TV din kamar zata gano Dikko a ciki,duka tsigar jikinta ya gama tashi sak'onninsa suna ratsa duk wata kafa ta jikinta.cikin rawar murya wadda tasha kuka bata fita sosai tace"I...n...a kika....gan...shi".Kama hannuwanta Zaibab tayi tace"ki tuna nace maki Babu abunda bazan iyayi saboda ke ba,Dikko Yayana ne uwa d'aya uba d'aya,na tsaya ne inga wanne irin so kike masa shin ya cancanci na baki shi,Kuma naga Babu wata y'a mace data dace da Yayana bayan ke,Ina maki albishir da cewa Yayana yana matuk'ar kaunarki". "Never,abunda bazai tab'a yiwuwa ba kenan in har ina da rai,bazan tab'a aurawa maroki kaskantacceba y'ata mafi soyuwa a gareni,har abada hakan bazata faruba,meya mallaka ?meke gareshi?,ko matsayin mai aekin gidan nan be kaiba balle kuma ya nemi auren Faty,wannan wani shirmene kukeyi,hakan bazai faru ba".wani irin gigitacciyar k'ara Faty ta saki ta fad'i a wurin sumammiya. Da gudu sukayo kanta,Aunty Amarya ta fashe da kuka tace"mun gaji da wannan ra'ayin cutar da yaran naka,shin kaima ae Allah ya baka kud'in,kuma Shima baka San tanadin da Allah yayi masa gaba ba,zaka kashe y'arka da kanka saboda wani ra'ayi na daban".ganin Faty bata numfashi yasa suka kwasheta sai asibiti kai tsaye akayi Emergency da ita.ko da ta fara farfadowa Babu abunda take fad'a sai sunan Dikko kawai. Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe Stylish star Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *DIKKO AHMAD* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail majidadi* *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* End Kawar da kai Daddy yayi ya kalli Ummu yace"kisan yarda zakiyi y'arki ta daina kiramun sunan mabaracin can"kai tsaye yabar wurin."kai Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,Wai me yake damun Alhaji ne?,baya duba halin da y'arsa take ciki sai kawai ya biyewa wani ra'ayinsa na daban"Aunty ta fad'a.dama bekai ga tafiya ba dan haka ya dawo ya nuna Aunty da yatsa yace"ki shiga hankalinki ,dama Ashe da saka hannunku duk iyan shegen da yarinyar nan takeyi?,to bari in gaya maku ko gawar Faty ce sai an kai gidan Munnir sannan a wuce da ita mak'abarta,ita tayi kad'an ta zubarmun da daraja ta,wannan Sam bazai yiwu ba"ya wuce fuuuu,shiru sukayi yayin da Faty taci gaba da Kuka San ranta,ganin Daddy yabar wurin yasa Aunty tace"yanzu Ummu kina ganin zamu zuba ido yarinyar nan ta mutu?,bazai yiwu ba yaskiya zanyi komai dominta in yaso yamun duk hukuncin da yaga dama".kallon Abdul tayi tace"ka karb'i number Dikko wurin Zainab ka kirasa dan Allah yazo ya ceci ran yarinyarmu"ba wani canza shawara kam ya Kira wayar Dikko,ganin be d'aga ba yasa Zainab kiransa da kanta yana dauka ta fashe da kuka tana fad'in"Yaya Allah gatanan a asibiti,Yaya karta mutu kazo sunanka kawai take Kira Yaya ka taimake mu"."Wai meye kike fad'a Zainab?,yanya kina cikin hankalinki kuwa?".wani kukan ta k'ara fashe mass dashi ta gaya masa in da zai sameta,be wani b'ata lokaci ba ya k'araso wurin.Zainab na hangoshi tayi kanshi ta rungume tare da kara sakin wani kuka."ya isa haka,bana San kukan nan,ae gani nazo komai zaiyi daidai da yardar Allah,ina Fatyman take?"nuna masa d'akin tayi tun a waje ya hango su Umma k'arasawa sukayi cikin ladabi ya duka ya gaishe su.cike da fara'a da mutunta mutane suka ansa kafin Aunty tace"Dikko ka taimakemu yarda Allah ya taimake ka,ka ceci rayuwar y'armu mafi soyuwa a garemu".k'asa yayi da kansa yace"Aunty ae umarni zaki bani ba roko ba,ae kin girmeni".take dukan Wanda ke wurin yaji son Dikko danya k'ara tabbatar masu cewa mawak'a ma suna da tarbiya da Kuma ganin mutuncin manya.har cikin d'akin Abdul yaja hannunsa ya shiga da shi,daidai saitin fuskar Faty ya duk'a a hankali yace"Fatyma,Fatyma".kamar a mafarki taji ana Kiran sunanta da muryar da take muradin ji a ko wanne second na rayuwarta zumbur ta mik'e zaune tana jujuya ido,a hankali ta soma bud'e kyawawan idanuwanta farare tas Wanda ko b'acin rai baya canza masu launi sai dai su dan kumbura kad'an Wanda hakan kyau yake k'ara mata,tun d'aga k'afarsa take kallonsa tanajin zuciyarta kamar zata fito fili harta sauke idonta akan fuskarshi wacce take dauke da murmushi da haske na annuri,hannu tasa ta k'ara murza idonta bakinta na rawa tace"D..i..k..ko"tana nunashi da hannu,hannun nata ya Kama ya had'e da nasa yana murmushi kamar ko yaushe,ido d'aya ya kashe Mata yace"Faty Dikko,y'an Matan Dikko ba mafarki kikeyi bafa,nine dai naki a gabanki yau cikar burinki yana tare da ke".rasa abun fad'a tayi ta kuma kasa dauke idonta a kanshi gani take kamar data dauke ido daka kanshi zai b'ace yayi Mata yarda ya sabayi a mafarki,hannunsa ya had'a tare da bugawa a gaban fuskarta yace"bafa mafarki kikeyi ba farin cikina".wasu zafafan hawaye ne suka soma zarya akan fuskarta a hankali ta furta "Alhmdllh ya Allah".b'ata fuska Dikko yayi tare da shagwab'e fuska yace"ni gaskiya bana son kukan nan"yasa hannu yana share Mata hawaye,fad'awa tayi cikinshi ta kuma sakin kuka da k'arfi.bashi da zab'in daya wuce ya karb'e a wannan lokacin dan haka ya saka hannuwansa tare da soma bubbuga bayanta a hankali a kunne ya rad'a mata"Farin cikina zanyi kuka nima inhar baki daina ba,inajin kukanki tamkar ana soyamun zuciyata,kedin kaddaratace,kedin tawace bana da wani burin daya wuce na sameki a matsayin matana tun daga lokacin Dana daura idanuwana akanki,kedin ta dabance Kuma kinyi daban,to dan Allah a sassautawa zuciyata wannan wahalar da ake bata bana bukatar kukan nan".kamar an ingizoshi haka ya shigo d'akin yace"karya kakeyi mabaraci,mai shirya zance nanma din studio ne ?,ni Alhaji kabir zaka yaudarar wa y'a harka wuce ko ina ka k'araso inda take kana makaskanci Wanda sai ka sayar da muryarka kake samun abunda zakaci kai da iyayenka sannan Kuma kazo wurin y'ata?.wayarsa ya dauka yayi magana kad'an babu Wanda yaji abunda yace kawai sai ganin y'an sanda sukayi sun shigo da yawa,kai tsaye kan Dikko sukayi suka hau kansa da duka kamar Allah ya aeko su.wani irin razannaniyar k'ara Faty ta saki ta fad'a akan Dikko tana kare masa duk dukan da aka kawo,rungumesa tayi kwarai taki ta sakeshi,kuka su Ummu suka saka Aunty tace"Alhaji ka duba girman Allah ka hana dukan nan,yaran nan be aekata maka komai ba"."ke kiyimun shiru,kema ina zuwa kanki dan dole ki karb'i hukuncin karya dokata".da kyar aka banbare Faty daga jikin Dikko tana ganin y'an sanda sun kwashesa jina jina ta sulale wurin a sume.shikam a mota kamar zasu zare masa rai dan tsananin dukan da sukeyi har suka isa office dukanshi sukeyi kafin suka jefashi cell.Ummu kasa cewa Daddy komai juyawa kawai tayi tabar masa d'akin.waya Zainab ta dauka ta Kira Aunty Balaraba dan Yaya Aliyu ya tafi gida tun d'azu a can police station suka had'u ,idanuwan Zainab sun kumbura sunyi jajir saboda tsabar kuka.ko da suka shiga da ky'ar aka basu damar ganinshi,Aunty B na ganin yarda duk jikinsa ya fashe dama ga jikin Dikko ba San wahala yakeyi ba hutu ya gama ratsa shi,ta saki kuka tana tab'a fuskarshi data kumbure lokaci d'aya tace"me suka yi maka ?,wannan Sam ba adalci bane ba"cikin dauriya da rashin son nuna ba damuwa ba yace"Aunty B kada ku damu ni tawa jarabawar a soyayyah kenan,komai zai wuce".girgizashi Aunty B tayi tace"kayi hauka ne?,ka gaya masu baka son Faty,ae ba ita kadaice autar Mata ba,kana da kudin da kyau da ikon da duk macen daka taya zata soka,ko cikin wad'anda suke kawo maka kansu Dikko zaka iya zab'a,me Alhaji Kabir ya tara bare harya wulak'antaka haka,yako san ko kai d'an waye?,sannan kai kanka meka mallaka?"."ya isa Aunty maganar so akeyi ba alfahari ba,Aunty bazan it's rabuwa da Faty ba,Kallo d'aya na Mata na kamu da matsanancin sonta,dama ae komai ya gaji jarrabawa to zan jure ko wacce iri ce,rayuta fansace akan soyayyarta".basu k'ara wata magana ba aka janyeshi aka mayar dashi Cell,da kuka suka fito wurin,cikin kyarma Aunty B ta Kira Abba a waya ta shaida masa abunda ke faruwa.a razane ya mike yace"bazai yiwuba ,bazan tab'a d'agawa Wanda ya wulak'anta D'ana haka ba ko waye shi"."me yake faruwa Alhaji?"Ummi ta tambaya,kallonta kawai yayi yace "ki dauko gyalenki zamu Kama hanya yanzu"kawai ya fice.Ummi Kam sai faduwa gabanta yakeyi gashi ya ki gaya Mata komai.tunda taga sun nufi hanyar kano zuciyarta ta cinke tunanin mafi soyuwar yaranta takeyi kawai Dikko.cikin y'an awanni suka isa Kano,dan ba k'aramin gudu Driver din yayi ba nisa umarnin Abba,kai tsaye gidan Aunty B suka wuce ,ba wani b'ata lokaci ta gaya masu abunda ke faruwa,Kuka Ummi ta saka tace"sai da nace karyazo,meye wata Faty yarona da ko magana bayayi shine aka wulak'anta haka saboda mace?"."ki kwantar da hankalinki zasuga Dikko yana da gata,zasuga Uba irin Wanda ake ado dashi,tabbas yau sai sunyi Dana sanin tab'amun D'ana".daga shi sai Zainab da masu tsaranshi suka je police station din.tun daga waje manyan mutane da manyan y'an sanda suke tarbarshi da gaishe shi suna bashi girma, office inspector Anas aka kaishi danshi yakeyin case din,bak'in k'ofa ya tsaya,da sauri Alhji Kabir ya mike yace"a'a ranka ya d'ad'e,yau kai da kanka a garin namu,naga munyi waya d'azu baka cemun zaka shigi ba Kuma".murmushi ya sakar masu ya k'araso ciki tare da zama musabaha sukayi yace"wallahi zuwanne babu tsari a gaggauce ya kamani,D'an wajena aka Kama a nan"."subhanallah aeda kayi waya zanzo na karbeshi da basai kazo ba".shigowar Zainab yasa kowa d'agowa turus tayi ganin yarda Abba da Daddy suke gaisawa tace"Abba kabar gaisawa dashi,shine ya Kama Yaya Dikko yasa aka masa duka ,yana ce masa mabaraci dan yanayin waka".kallonsa Abba yayi amma bece komai ba, inspector Anas ya kalla yace"a kawo mun Dikko Ahmad"wani irin xaro ido Daddy yayi sai yanzu ya tuna da sunan Dikko Wanda yawanci komai na Alhaji yake da sunan yaron,sai yanzu tunaninsa ga kawo masa cewa Dikko shine yaron Alhaji Ahmad Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un in haka ne tabbas ya tabka babban shirme,ganin yarda aka janyo Dikko ya bugu da ky'ar yake iya d'aga kai yasa Alhaji Ahmad mik'ewa da sauri yayi kanshi yana Kiran"Dikko shine aikayi maka haka?",Dikko Kam jikin Abba ya fad'a tare da sumewa.farar rigar jikin Abba dukta b'aci da jini,d'aukar D'an nasa yayi be kula takan kowa ba yaui mota da gudu da shi kai tsaye asibiti suka nufa akayi Emergency dashi,Babu abunda Dikko yake Kira sai sunan Faty.."hajiya nayi kuskure, Alhaji Ahmad shine karfin arzikina shine Wanda da taimakonsa na kai wannan mataki har gobe shi take bani kaya,shi yake bani kudaden da nake juyawa ina d'aukar ribar". murmushi kawai Ummu tayi tace"ae ba'a yanke hukunci da zafi haka,kaga yarda ake musaltawa ko kusa baka tara abunda Dikko ke gareshi bama balle Kuma mahaifinsa". After 1 week An sallami Dikko daga asibiti,bayan zaryar da Alhaji Kabir da iyalansa sukai tayi wurin dubasa,ba arziki yabar Faty ko yaushe tana wurin Dikko har aka sallameshi,tare su duka suka koma gidan Aunty Ba.hakuri Alhaji Kabir yaita bawa Abba,kallonsa Abba yayi yace"ya wuce ae,sai dai a tari gaba kawai a Kuma kiyaye irin wannan,wlh nayi niyar daukarwa yarona fansa to sai Kuma naga Kaine shiyasa na hak'ura,amma maganar Aure a barta Allah ya had'a kowa da rabonsa".da sauri Dikko ya kallesa yace"No Abban DK i still luv her,dan Allah kayi hakuri kada ka rabamu"jinjina kai Abba yayi yace"Amma kasan anyi baikonta da Munnir ko".kafin kowa ya bada ansa sukaji muryar Munnir dake shigowa yanzu yace"nikam na hak'ura,Babu amfanin rabasu,insha Allah ni zan auri Aysha inhar ta amince".albarka su kaita saka mashi da jinjina kokari irin nashi.kallon Daddy Ummu tayi tace"to Alhaji ina so kasan yin waka ko film ko rubutu ko makamancin haka muradine ,da cikar buri,zai iya zama kuma mafarkin mutun,Kuma Koda baka da ko sisi hakan baya nufin dan kayi irin sana'o"in nan ya zama kai mabaraci ne,yin hakan wata baiwace daga Allah Wanda ba kuma kowa keda irinta ba sai Wanda Allah yaso ya bawa,ga misali ka gani a kanka wak'a ta zama cikar burin Dikko badan ya rasa komai ba,kasan har jikokinsa ba zasuyi talauci ba Koda kuwa bayayin aekin komai,yabi ra'ayinsa ne Allah yasa mu dace". *Dole iyaye su canza kallon da sukewa sana'o'in da suke bawa maza auren yayansu,su daina kaskantar da sana'a koya take,Allah shiya halicci mai kudi da talakka komai akan ikonsa ne,Allah yasa mu dace*. Take a nan aka saka auren Dikko da Faty,Aysha da Munnir,komai ya daidaita,Kuma kowa cikinsu ya d'auki darasi . Alhmdllh na godewa Allah daya bani ikon gama wannan gajeran labarin nawa,Allah ya yake mani kurakuren dake ciki,Allah yasa Kuma mutane su amfana da abunda suka karanta. Ayi azumi lafiya jama'ar musulmi baki d'aya. Jorderh majidadi Stylish star