*♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 01 بسم الله الرحمن الرحيم. __ Sassanyar iska ke tashi, wadda ke haɗuwa da ƙamshin jar jiƙaƙƙiyar ƙasar da ke malale a tsakar gidan. Hakan ne ya sa iskar da ke shiga hancin duk mahalukin da ya shaƙe ta, ta kasance daddaɗa. Ruwa ne kwance a wani gefe na tsakar gidan, ya yin da wani wajen ƙasar ce kawai a jiƙe. Wanda hakan ze alamta maka cewa ba a daɗe da ida ruwan sama ba. Tana zaune a kan kujera 'yar tsuguno, gaban murhu da tukunya ke ɗore a kai tana fifita wutar da ke ƙoƙarin mutuwa. Sautin sauke numfashin da ta soma jiyowa daga cikin ɗaya daga cikin ɗakunan da ke gidan ne ya sanya ta dakatawa daga fifita wutar da take. Ta sake ƙanƙance idanunta da suka ɗan sauya kala saboda yajin da ke shiga cikin idanunta, na icen da ke ci cikin wuta. "Wayyo Allah! Wayyo.." Ta sake jiyo sautin a wahalce. Ba ta san lokacin da ta jefar da mificin hannunta ba, ta miƙe da sauri har tana ƙoƙarin tuntuɓe, ba ta tsaya ba ta yi gaba kai tsaye zuwa cikin ɗakin. Hannu ta saka ta yaye yalolon labulen da ya hana ta ganin abin da ke faruwa cikin ɗakin, har sai da ta shiga. Ta sauke idanunta a kan motsatstsiyar katifar da ke cikin ɗakin. Matashiyar budurwa ce zaune a kan katifar tana sauke numfashi a wahale, hannunta ɗaya dafe da turtsetsen cikin da ke gabanta, ya yin da ta yi amfani da ɗayan hannunta wajen damƙe gefen katifar da wani irin ƙarfi da ba ta san tana da shi ba. Idanunta a rufe suke gam tana jujjuya kanta cikin tsananin azabar naƙuda. Jin alamar an shigo cikin ɗakin ne ya sanya ta buɗe jajayen idanunta ta yi ƙarfin halin kallon matar da ta shigo. Cikin raunanniyar murya ta ce "Dada marata, Dada zan mutu.." Ta ƙare maganar tana yarfe hannunta da ta ɗauke daga kan cikinta. Duk da ba ta da tabbacin ko Dadar za ta taimaka mata, ko za ta bar ta ne ba tare da ta yi yunƙurin taimaka mata ba. Murmushi wadda aka kira da Dadar ta yi tana faɗin "Alhamdulillah!" Ta ƙare maganar tana maida idanunta kan Inna-wuro. A ranta tana ji kamar ta taka rawa don tsananin murna. Cikin ƙarfin hali tare da danne duk wani abu da take ji tace "Sannu Inna-wuro." Ta faɗa tana ƙarasawa kan katifar. Duk da tsananin azabar da Inna-wuro ke ji hakan be hana ta kallan Dadar ba, ta lumshe idanunta tana jin wata ƙwalla na tarar mata a cikin idanunta. Duk wani ƙoƙari da za ta iya dan ganin Inna-wuron ta haihu lafiya Dadar ta din ga yi. Kasancewarta Ungozoma ya sa ba ta nemi wani taimako ba, ko yunƙurin kiran wani dan a kai ta asibiti ba. Ita dai burin ta kawai Inna-wuro ta haihu lafiya, ko da abin da ke cikinta be fito lafiya ba wannan ba damuwarta ba ce. An kwashe wajen minti 30 kafin wani dattijon bafulatanin mutum ya shigo cikin gidan da sallama ɗauke a bakinsa. Dada ba ta iya amsawa ba saboda cigaba da taimakawa Inna-wuro da take. "Kina ina ne Uwar gida." Ya faɗa yana zame hular kansa. Shirun da ya ji ya sanya shi ƙarasowa cikin gidan, yana dab da ƙarasawa Dada ta fito. Ya kalle ta sosai yana nazarin yanayinta. Tun kafin yace komai ta ce "Naƙuda ce ta tasowa Inna-wuro." Zaro idanunsa ya yi, da sauri ya kai hannunsa yana lalubar aljihunsa. "Bari na kira..." "Ka kira wa?" Ta katse shi da faɗin hakan bayan ta tattaro girar sama da ƙasa ta haɗe waje ɗaya. Dakatawa ya yi daga ƙoƙarin lalubo wayarsa da yake, cikin 'yar rikicewa ya ce "A'ah.. wai da a kira shi a sanar da shi ta soma naƙuda." Numfashi Dada ta sauke har lokacin ba ta saki fuskarta ba, ta ce "Toh ga ka ga wayar nan ai sai ka kira." Daga haka ta juya ta koma cikin ɗakin. Fahimtar gatse take masa ya sanya shi bin ta da kallo kawai ba tare da ya sake yunƙurin taɓa aljihunsa ba. Daidai lokacin da ta saka ƙafarta cikin ɗakin, ya yi daidai da lokacin da kukan jariri ya cika cikin ɗakin. Da sauri ta ƙarasa, cikin mamakin yadda haihuwar ta zo wa Inna-wuron a sauƙaƙe duk da kasancewa ta fari ce. Kukan jaririn da take ji be sanya ta kula inda yake ba. Sai ƙarasawa da ta yi cikin tashin hankalin da ya rufto mata lokaci guda. Ta sanya hannu ta riƙo Inna-wuro da tun da babyn ya fito ta zube a wajen ba ta sake motsawa ba. Idanunta da ke motsawa a wahalce ne ya sanya Dada sakin ajiyar zuciya. Sai a lokacin sannan ta miƙe ta saka hannu ta ɗauki babyn da ke ta rusa kuka. Ta sanya shi cikin zani ta ajje gefe. Farawa ta yi da gyara Inna-wuro, cike da kulawa kamar wani ƙwai haka take kula da ita. Abin da ya saka Inna-wuro sakin baki tana kallanta cike da maɗaukakin mamaki. Sai dai ba ta ce komai ba, ta cigaba da bin komai da ido. .. "Zan iya sanar da shi abin da aka samu?" Baffa da ke zaune a kan kujera ya faɗa yana kallan Dada da ta fito daga cikin ɗakin. "Hohoho.. Wai ni kam Malam me ye damuwarka da wannan haihuwar ne? Yoh har wani ma abin alfahari ne a wajenmu da yarinyar nan ta haifi mace? Ka dai san a kan yarjejeniyar da aka rabu, saboda haka don Allah ka dena mini maganar nan. Ka bar ni in ji da abin da nake ji." Lumshe idanunta ta yi lokacin da kunnuwanta suka gama jiyo mata maganganun Dada. A hankali ta kai kyawawan fararen idanunta kan babyn da ke kwance cikin zani tana bacci. Hannunta ta kai ta ɗauke ta, ta ɗan gyara zamanta tana runtse idanunta. Murmushi ne ya suɓuce mata a kan fuska lokacin da idanunta suka sauka a kan kyakkyawar farar fuskar jinjirar da ke bacci cikin kwanciyar hankali, tana sauke numfashi a hankali. Kafe ta ta yi da idanunta tana jin wata irin ƙaunar ta na ratsa duk wata gaɓa ta jikinta. Sai dai cikin ƙanƙanin lokaci idanunta suka fara juyewa zuwa ja. Ƙalubalen da ke cikin rayuwarsu shi ya soma faɗo mata. Shin ko ita ɗin mahaifinta ze yi farin ciki da zuwanta duniya? Shin mahaifinta ze karɓe ta kamar yadda kowanne uba ke karɓar ɗan da ya haifa? Shin akwai mutanen da ke farin ciki da zuwan wannan halitta duniya ko kuwa ita kaɗai da ta haife ta ita ke farin ciki da zuwan ta? Sabuwar ƙwallar da ta tarar mata a idanu ita ce ta sanya ta lumshe idanunta, tana jan kyakykyawar babyn ta rungume a ƙirjinta. Wani irin sanyi na ratsa ta. Soyayyar ɗiyarta na shigar ta. Kwana 5 da haihuwar jikinta ya soma komawa daidai. Ta ji daɗin jikinta ainun. Babynta ma da yake tana samun isasshen abinci ya sanya ta yi kyau abin ta. Duk a tsawon kwanakin nan ta ɗauka za ta ji Dada ko Baffa wani ya ce mata Alhaji Baita ya kira ta a waya dan jin lafiyarta. Sai dai har aka shafe kwanaki ba ta ji daga gare shi ba, duk da dai ta san da ma hakan kan iya faruwa. ... "Ya ce a ɗauki kuɗin rago cikin kuɗaɗen da yake turowa, sannan ya kuma ba ki wuƙa da nama a kan zaɓar wa 'yarki suna. Ba shi da matsala da hakan, saboda haka wane suna za a raɗa mata?" Baffa ya faɗa yana kallan Inna-wuro. Wani irin yawu me ɗaci ta haɗiye, karyayyiyar zuciyarta na sake karyewa. Tausayin rayuwar ɗiyarta na sake kama ta. Kenan har rashin muhimmancinta, da kuma son nuna be damu da abin da ta haifa ba ya kai ya kasa sakawa 'yarsa suna? 'yar da ya haifa da cikinsa? Ta ja wani numfashi da ƙyar kafin ta ce "Baffa ka saka mata duk sunan da ya maka." Ta faɗa cikin ƙarfin hali, tana jira ta ji amsar da za ta fito daga bakin Baffan. Kamar yadda ta tsammata kuwa sai cewa ya yi "A'ah, kin ga ni fa cewa na yi ki faɗi sunan da za a sanya wa yarinya. Me ye garin gamina da ita kuma? Ubanta ma be saka mata suna ba sai ni karan kaɗa miya?" Ya ƙare yana nuna kansa. Daidai lokacin da Dada ta fito daga cikin ɗakinta tana kallan su. Ta taɓe baki kafin ta wuce banɗaki. Dalili kenan da ya sa ba ta son cika magana da Baffan nata, don abubuwa da dama kan zo cikin ƙwaƙwalwarta, tana sake ji duniyar na mata zafi, komai yana sake juye mata saboda halin da Baffan ke nuna mata. Baffan nata da be daɗe da sauyawa ba. "DANEEN, Allah Ya raya ta da imani." Ta faɗi abin da daga shi har Dadan suka kasa faɗa tun da ta haihu. Tana gama faɗa ta miƙe. "Ameen." Baffa ya faɗa. Ita kuma Inna-wuro ta wuce cikin ɗaki. Daidai lokacin da babyn ta soma kuka, ta ƙarasa da sauri tana sakin murmushi ta ɗauke ta. Ta yi amfani da hannunta ɗaya wajen ɗauke ƙwallar da ta sakko mata a kan fuska. "Ya isa haka Shalele." Ta faɗa tana ƙarasawa ta zauna, ta shiga shayar da yarinyar tana kallan kyakykyawar fuskarta da kullum kyawunta sake fitowa yake yi. A duk lokacin da za ta kalli fuskarta sai ta tuna abubuwa da dama, abubuwan da suka faru a baya, da ma waɗanda take hasaso tabbas za su faru nan gaba, idan dai ba Allah ne Ya taƙaita ba. A ranar aka yanka rago aka kuma sanya wa yarinya suna DANEEN. Haka Inna-wuro ta cigaba da kula da ɗiyarta cikin kulawa, so da kuma ƙauna. Ta gefe guda kuma Dada na sanya ido a kan duk wani motsinta, sai dai ga mamakinta ba ta taɓa damuwa da ya Daneen ta tashi ba, ya ta kwana, kullum burinta ta san lafiyar Inna-wuron. Dalili kenan da ya sa ta maida hankali sosai wajen kula da 'yarta, tun da dai ita kaɗai ce ke son rayuwa da kuma lafiyarta. .. Cike da damuwa ta ɗauki Daneen ta taɓa jikinta da ya yi zafi zau kamar wuta. Ta runtse idanunta tana jin duk jikinta babu daɗi, ƙirjinta har wani bugawa yake saboda tsoro. Kuka yarinyar ke yi sosai, Inna-wuro na rarrashinta. Tun tsakiyar dare har sai wajen asuba kafin zazzaɓin ya sauka. Sai a lokacin sannan wani wahalallen bacci ya kwashe ta. A hankali ta sauke ajiyar zuciya tana kafe Daneen da idanunta. Tausayinta na kama ta. Addu'a ta karanto ta tofe ta da ita, ta ɗan ja zani ta sake lulluɓe ta da shi tana addu'ar Allah Ya sa kar zazzaɓin ya sake dawowa. .. Dada na tsakar gida tana dama kunu lokacin da ta fito daga cikin ɗakin, Baffa kuma na kan kujera suna hira da Dadar. Ƙarasawa ta yi a hankali ta tsuguna, ta gyara kwanciyar Daneen da ke hannunta ta ce "Baffa don Allah alfarma nake nema a wajen ku." Ta faɗa tana jin ƙirjinta na bugawa, duk wani fatanta a ce su amince da abin da za ta faɗa. Ba tare da ya ce komai ba ya ɗaga kai ya kalli Dada da ta juyo tana kallan Inna-wuro. "Me ya faru?" Dada ta faɗa cikin tsare gida. Sauke numfashi ta yi tana tunanin ta inda za ta fara. Sai dai ta yi ƙarfin halin soma faɗin "Don Allah Dada ku taimaka ku kira mini shi a samu a kai yarinyar nan asibiti. Wallahi kullum da zazzaɓi take kwana cikin dare. Kun ga har ta fara ramewa wallahi." Ta ƙare tana sauko da Daneen daga kan kafaɗarta. Ba tare da kowannen su ya ce komai ba, Dada ta kai hannu goshin yarinyar ta taɓa. Ta ja tsaki kafin ta soma faɗin "Maƙaryaciyar banza, ina zazzaɓin yake a nan? Kina jin jikin yarinya sanyi ƙalau ki ce zazzaɓi? A'ah asibiti ne a kanta." Girgiza kai Inna-wuro ta yi ba tare da ta kalli Dada ba ta ce "Wallahi da gaske nake Dada. A kwanakin nan kullum cikin dare da shi take kwana, ko bacci ba ta iya wa sai ya sauka. Toh ina tsoron kar wani abu ya faru kuma." "Ki ji nemawa kai bala'i kuma.." Dada ta faɗa tana riƙe haɓa. "Kin ga ke.. Inna-wuro, maza koma ɗaki ki zauna tun da dai babu zazzaɓin. Yoh ki je ma ki cewa likitocin me tun da babu zafi jikinta? Ki zauna duk sanda zazzaɓin ya dawo sai a san abin da za a yi." Baffa da tun ɗazun be ce komai ba ya faɗi hakan. Ba ta sake cewa komai ba, sai miƙewa da ta yi a sukwane, jikinta a matuƙar sanyaye ta saɓa Daneen a kafaɗarta ta wuce ɗakinta. "Ko dai a kira shi a ji ta bakin nasa ne?" Baffa ya faɗa bayan ya ga shigar Inna-wuro ɗaki. Da sauri Dada ta juya ta kalle shi "Wai ni kam manta yadda aka yi da shi ka yi? Dududu kwana nawa ya rage ta bar gidan nan? Idan mun yi haƙuri da kansa fa ze zo ba sai mun kira shi ba. Kamar yadda aka yi da shi wata biyu ciff bayan haihuwar, ina da tabbacin ba ze ƙara ba. Toh ni dai kar na sake jin kana wani zancen kiransa. Mu kira shi mu masa me? A'ah don Allah." "Toh shi kenan Uwar gida, ai komai kika ce ya zauna." Ya ƙare yana murmushi. Ita ma murmushin ta yi tana maida hankalinta kan kunun da ke hannunta a cikin kofi. .. Cikin ikon Allah kwanakin da suka biyo baya Daneen ba ta sake kwana da zazzaɓin ba. Farin ciki kamar me haka Inna-wuro ta ji, ta din ga gode wa Allah tana cigaba da kula da 'yarta. Bayan wasu kwanaki ga maɗaukakin mamakinta sai ta ga Dada da kanta ta soma gyara ta. Magunguna kala-kala, da na sanyi da na gyara jiki haka ta din ga ba ta. Ita dai jiki a sanyaye haka take bin Dadar, don ba kirki ne da ita ba. Ba ta ƙi ta ci mata cin mutunci ba a kan ko mene ne. ... Tana zaune a cikin ɗakin, hannunta ɗauke da Daneen da ta yi wayo sosai. Ta ƙara kyau, jikinta ya murje matuƙa. Ita kanta Inna-wuron ta ƙara wani irin kyau, don sosai jegon ya karɓe ta, ta murje ta yi kyau abinta. Tun ɗazu take jiyo hayaniya daga tsakar gida, sai dai ba ta yi ko da yunƙurin fita ba ne, tana cikin ɗakin tana hira da ɗiyarta. "Inna-wuro! Inna-wuro." Ta jiyo muryar Baffa daga tsakar gida. Da sauri ta miƙe, sai dai cike da takatsantsan, saboda Daneen da ta fara bacci. Ta kwantar da ita a hankali tana sake jin kiran da Baffa ya yi mata har cikin kanta. Cikin ruɗewa ta amsa tana miƙewa ta fice, hannunta ɗauke da ɗankwalin atamfar jikinta. "Na'am Baffah." Ta sake faɗa daidai lokacin da gama fitowa daga ɗakin. Mummunan ganin da ta yi, shi ne ya sanya ta dakatawa. Take zuciyarta ta soma harbawa lokacin da idanunta suka sauka a kan Alhaji Baita, da ke zaune kan wata kujera, ya yi shirim. A ƙalla a shekaru ya ba wa 40 baya. Don a haife ya haifi Inna-wuro, wadda take da shekaru 18. Sai dai ba kowa ba ne shi, face mijinta, mahaifin abin da ta haifa. Mutumin da kwata-kwata ba ta so ƙara ganin fuskarsa a rayuwarta ba, ko don saboda nunawa da ya yi ƙiri-ƙiri ba ya son abin da ta haifa. Sauke idanunta ta yi ƙasa, tana ji duk jikinta na yin sanyi, ko'ina na jikinta ya ɗauki rawa. Ba ta san lokacin da ta zube a wajen ba, tana jin wata irin ƙwalla na taruwa a cikin idanunta. Shi kuwa Alhaji Baita, tun da Baffa ya soma kiran sunan Inna-wuro ya kafe ƙofar ɗakin da idanunsa, har zuwa lokacin da ta fito. Ya kafe ta da jajayen idanunsa, gaba ɗaya hankalinsa na tafiya kan jikinta. So yake ya ga ko akwai wani canji da ze gani a jikinta. So yake ya ga ko ta sauya daga ainahin Fatima, me kyau, me diri, wadda ta haɗa duk wani abu da yake buƙata a wajen mace. Don kuwa ko daidai da canji ɗaya ya gani a jikinta, ko raguwar kyawunta, ko kuma yamutsewar wani sashe na jikinta, toh tabbas a wajen zai sakar musu 'ya ba tare da an je ko'ina ba. Wannan rawar jikin da duk wani abu da suke ba ze yi tasiri a wajensa ba... Toh Alhamdulillah, bayan wani lokaci yau Allah Ya sake haɗa mu cikin wannan tafiyar, fatan za ku karɓi wannan labarin da hannu bibbiyu kamar yadda kuka saba. Ina faɗa muku zazzafar tafiya ce, me tsaya wa a rai. 😍❤️ *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 02 __ Sai dai ga maɗaukakin mamakinsa, sai idanunsa suka ganar masa tamkar ma sauya masa Fatiman aka yi. Ta ƙara kyau, ta wani irin murje. Duk da da ma Fatiman ba baya ba ce wajen kyawun jiki, amma yanzun ta ƙara cika ta ko'ina. Ya saki murmushi har lokacin ya kasa ɗauke idanunsa daga kanta. Hannunsa ya kai ya shafa kumatunsa kafin ya lumshe idanunsa yana sauke wani gajiyayyen numfashi. "Ina kwana?" Inna-wuro ta yi ƙarfin halin faɗin hakan, saboda wata uwar harara da Dada ke jefa mata kamar idanunta za su faɗo ƙasa. "Ahh lafiya ƙalau Fatima." Ya faɗa yana murmushi, kafin ya ɗora da faɗin "Ya kamata mu tashi mu tafi koh?" Ya ƙarasa maganar har lokacin yana kallan Inna-wuro. A hankali ta ɗaga idanunta da suka yi laushi ta kalli Baffah, sai dai maimakon idanunta su faɗa cikin na Baffah sai suka faɗa cikin na Dada. Tana shirin kautar da kanta ta jiyo muryar Dada na faɗin "Ai kam dai ya kamata.. Ka ganta nan ta yi kyau abinta, ai tun jiya na gama gyare maka ita tass, kawai tafiya za ku yi babu wani ɓata lokaci. Malam ɗakko kayan Inna-wuro da na shirya mata cikin jaka." Kallon Baffahn da ya tashi zungwui-zungwui Inna-wuro ta yi, tana mamakin jin wai har an haɗa mata kaya amma duk ba ta sani ba. Toh yaushe? Kuma tana ina hakan ta faru? "A'ah, dawo ka yi zaman ka. Ba sai an ɗauko komai ba, ni da ma Fatima na zo ɗauka ba wani abu ba." Alhaji Baita ya katse Baffa daga yunƙurin shiga ɗaki da yake. Sai ya juyo yana faɗin "Kai dai kullum ba ka gajiya da ɗawainiya. Toh madallah." Ya ƙarasa maganar yana murmushi, lokaci guda kuma yana neman waje ya zauna. Miƙewa Alhaji Baita ya yi yana gyara zaman babbar rigar jikinsa, ya saka hannu ya zaro kuɗi a aljihunsa ya dire a gaban Dada yana faɗin "Ta same ni a mota." Daga haka ya juya don ficewa daga gidan. Cikin farin ciki Dada take faɗin "Mun gode sosai, Allah Ya saka da alkhairi, Ya ƙara arziƙi." Be ce komai ba ya fice daga gidan. Sai a lokacin Baffa ya kalli Inna-wuro ya ce "Maza tashi ki wuce ku tafi, kar ki bar shi yana jira." Idanunta ta ɗaga ta kalli Baffa, kallo irin wanda take fata ya ji tausayinta, ya kalle ta da idon mahaifi, ya kalle ta da soyayyar mahaifi, ya kalle ta da wannan tausayin da yake kallan ta da shi tun haihuwarta, soyayyar nan tata da ta ƙaru a wajensa tun da ta rasa mahaifiyarta. Sai dai kashh, wannan kallan ya daɗe da zama tarihi. Wannan tausayin ya daɗe da zama shuɗaɗɗe. Baffan da take gani yanzu zaune a gabanta ba halinsa ɗaya da Baffanta na da ba. "Ki tashi ana miki magana, kin zauna kin kafe mutane da idanu kamar za ki cinye mu. Kin tashi ne ko sai na tashi na kai ki da kaina." Dada ta faɗa a zafafe. Miƙewa ta yi a hankali tana jin yadda jiri ke ɗibar ta. Ba ta damu da hakan ba sai shiga ɗaki da ta yi, ta saɓa Daneen da har lokacin take bacci a baya. Ta ɗauki dogon hijabi ta saka. Abubuwan da ta san dole tana da buƙatar su ta tsaya ta ɗauka a gurguje sannan ta fito. Gaba ɗaya jikinta ya yi wani mugun sanyi haka ta fito, kamar ba za ta ce komai ba sai kuma ta lumshe idanunta ta ce "Na tafi." Daga haka ba ta jira sun ce komai ba ta fice daga gidan. A cikin motar ta hango shi ya yi ƙwam a driver seat. Ƙarasawa ta yi ta ƙarasa buɗe murfin gaban motar da ya soma buɗe mata, ta shiga ta zauna. Kamar yadda be ce komai ba haka ita ma ba ta ce komai ba, ya tashi motar suka bar wajen. Sun yi nisa da fara tafiya ya kalle ta, ya saki murmushi kafin ya maida kansa kan titi kana ya ce "Kin ƙara kyau abin ki 'yar fara tass tawa." A hankali ta ɗaga idanunta ta kalle shi, ta lumshe su tana jinjina kai, ta buɗe baki a sanyaye ta ce "Na gode." Bai sake cewa komai ba har zuwa lokacin da suka ƙarasa ficewa daga rugar gaba ɗaya, suka miƙi hanya cikin gari. Ga mamakinta maimakon ta ga sun yi gida, sai ta ga ya yi parking motarsa cikin wani private hospital, ta juya ta kalle shi cikin son jin ƙarin bayani. Be kula ta ba sai fita daga motar da ya yi ya ce yana kallan ta. "Fito." Ya yi maganar cikin bayar da umarni. Sake kallan cikin asibitin ta yi, ita dai ba za ta ce ga takamaimai abin da ya kawo su ba, tun da ya zo gidan kuma bai tambayi lafiyar ɗiyarsa ba, ballantana ta ce ko ya kawo su ne domin a duba lafiyarta. "Ki fito mana, a'ah.." Ya sake faɗa. Hannu ta saka ta buɗe motar ta fito, tana cigaba da kallan cikin asibitin. Be ce da ita komai ba sai gaba da ya yi, babu ɓata lokaci ta bi bayansa. Kai tsaye ɗakin likitan suka shiga, bayan doguwar gaisawar da suka yi da Alhaji Baita, wanda hakan ke nuna sabon da ke tsakaninsu. "Matata ce wannan, kamar yadda aka saba nake so a yi mata. Idan da akwai maganin da za a ba ta kwata-kwata ta dena haihuwa a ba ta don Allah." Cikin wata irin ruɗewa Inna-wuro ta kalli Alhaji Baita, zuciyarta na wani irin bugu da ya wuce na ƙa'ida. Girgiza kanta ta soma yi tana jin yadda tarin ƙwalla ta cika idanunta. Ilahirin jikinta na rawa kamar mazari, cikin karyayyiyar muryarta da ke rawa saboda tsabagen ruɗewa ta ce "A'ah don Allah kar ka mini haka, kar ka cuci rayuwata, kar ka zama sanadin katsewar farin cikina, ina son na haihu, ina son ganin 'ya'yana ko da guda nawa Allah zai ba ni ina son su. Don girman Allah kar ka yi mini haka." Ta ƙare lokacin da wasu kyawawan hawaye suka sauka a kan fuskarta. "Ni kuma ba na so, ba na so kwata-kwata. Ke kan ki kuma kin san ba don ki haihu na aure ki ba. Kar kuma ki yi tunanin don kin ce in ƙyale ki hakan na nufin zan ƙyale ki ko na datse alaƙar da ke tsakaninmu. A'ah zama da ni yanzu kika fara, domin iyayenki sun riga sun ba ni ke halak malak, don haka dole ki zaɓi mafita ɗaya. Ko dai ki zaɓi a cire mahaifar gaba ɗaya, ko kuma ki yi planning na shekaru, wanda za ki din ga sake wa daga zarar lokacin lalacewarsa ya yi." Alhaji Baita ya faɗa yana kallon cikin idanun Inna-wuro. Shiru doctor ya yi yana saurarar duk abin da ke gudana. Lallai Alhaji Baita shege ne, kuɗi kuma kan su shegu ne, tun da ga shi mata kala-kala na yarda su zauna ƙarƙashin Alhaji Baitan duk da yadda yake yadda ya ga dama da su. Kanta ta ji yana wani irin juya mata, tana tsoro kar ta je ta amince da abin da ya faɗa a yi mata abin da ya buƙata tun da farko. Idanunta da ke a rufe ta buɗe a kan fuskar Alhaji Baitan. Ta riga ta san ba ta da wani 'yanci na neman saki a wajen Alhaji Baitan, tun da iyayenta suka riga suka mallaka masa ita, duk da ba ta son sa, kuɗin da ya din ga musu ɓarinsa ne ya sa suka ba shi ita. Ta buɗe bakinta da ya yi mata nauyi da ƙyar ta furta "Na amince." "Likita na shekara biyar nake so, kar a yi na ƙasa da haka. Shekarun na cika kuma za mu dawo" Alhaji Baita ya faɗa yana kallan Likitan. Hannunsa da ya haɗe waje ɗaya ya raba su kafin ya ce "Kar ka damu Yallaɓai. Ka bar komai a hannuna, ba za ka yi dana sani ba." "Godiya nake Doctor." Alhaji Baita ya faɗa yana murmushi. .. Har dare ya yi bai nemi ya ga ɗiyar da aka haifa masa ba. Tana zaune cikin ɗakin ta fito daga wanka ya shigo ɗakin, ƙarasowa ya yi yana kallanta lokacin da take ɗaure da towel. Ya lumshe idanunsa kafin ya ce "Ki ɗauki yarinyar ki miƙa ta sashen 'yan aiki su kula da ita zuwa safiya. Sai ki taho sashena ina jiran ki." Da matuƙar mamaki ta ɗaga kai ta kalle shi, bakinta har rawa yake lokacin da ta furta "Watanta biyu ne fa..?" "Ko yau kika haife ta.." Ya ba ta amsar cikin rashin kulawa. Kafin ta kai ga cewa komai ya ce "Ina buƙatar ki, ki same ni a ɗakina. Ba na son ɓata lokaci." Daga haka ya juya yana shirin ficewa, jin ba ta ce komai ba ya sanya shi dakatawa, ya juya ya kalle ta kafin ya ce "Kin ji koh?" Jinjina kai ta yi kafin ta lumshe Idanunta daidai lokacin da ya fice daga ɗakin. Ta kai wajen minti 10 a cikin ɗakin tana tunanin abin da ya kamata, kafin ta share hawayen fuskarta ta ja Daneen a jikinta ta rungume, kusan mintuna 2 kafin ta sauke ta, ta shayar da ita na tsawon mintuna masu yawa kana ta miƙe ta fice daga ɗakin. Kai tsaye sashen 'yan aikin ta nufa, zuciyarta cunkushe da tunane-tunane kala-kala. Shin idan ta yi hakan ta yi wa yarinyarta adalci kuwa? Da wannan tunanin haka ta ƙarasa, ta samu Atika da ta yarda da ita sosai ta miƙa mata yarinyar. "Ki kula mini da ita don Allah. Idan ta farka ki ba ta ruwa ta sha In Sha Allah za ta koma bacci. Zuwa safiya zan zo na karɓe ta." Yadda take maganar a hankali kamar wadda ke shirin yin kuka ya sanya Atika faɗin "Rankiyadaɗe lafiya kuwa?" Ta tambaya tana karɓar fidar da Inna-wuron ta miƙa mata. Murmushin yaƙe ta yi kafin tace "Lafiya ƙalau. Ki kula mini da yarinya." "In Sha Allah Hajjaju kar ki damu." Ba ta iya sake cewa komai ba ta fice daga sashen gaba ɗaya. Kai tsaye sashen Alhaji Baita ta nufa, gaba ɗaya zuciyarta a cunkushe, jikinta kuma a matuƙar sanyaye. Tana shigowa ya miƙe ya rungumo ta fuskarsa ɗauke da murmushin da rabon da ta ta gan shi a kan fuskarsa tun bayan da ya fahimci tana da cikin Daneen. Ƙarasawa ya yi da ita a jikinsa zuwa kan gadon. Kamar koyaushe cikin ƙanƙanin lokaci ya shiga fiddo da zilamarsa a kanta a fili. Duk wata kewar jikinta da ya yi na tsayin kwanaki sai da ya fanshe a daren. "Shi ya sa kullum nake ƙara jin son ki a cikin zuciyata Fatima." Ya ƙare maganar yana shafa doguwar baƙar sumar kanta da ke kwance kamar wadda ke saka wa relaxer. Wasu hawaye masu ɗumi ne suka samu damar sakkowa zuwa kan fuskarta, waɗannan kalaman da ya faɗa babu abin da suka haifar mata sai raunin zuciya da sake kashe mata jiki. Shin kowacce mace haka take fuskanta a gidan aurenta? Shin da ma aure ana yin shi don wannan abun ne ko kuwa dai ita nata kalar auren ne daban da na mutane? Ba ta taɓa samun farin ciki, ba ta ganin murmushinsa idan ba a kan wani abu da ya shafi jikinta ba. ... Sam ta kasa zaune, ta kasa tsaye. Daga ta je can sai ta dawo nan. Ban da bugawa babu abin da zuciyarta ke yi. Kanta gaba ɗaya ya kulle, tsoro da fargaba take ji matuƙa. Idan dai har ba kuskure ta yi ba, tun da ta dawo daga gida haihuwar Daneen ba ta sake ganin baƙon watanta ba. Duk kuma wasu alamomi da ta ji farkon cikin Daneen shi take ji a yanzu. 'Kar dai abin da take tunani shi ne?' Ta tambayi kanta tana jin sabuwar faɗuwar gaba na ziyartar ta. A hankali ta kai idanunta kan Daneen da ke kwance kan gado tana ta wasa, don yanzu ta sake wayo sosai, ta yi ɓul-ɓul abin ta. Tausayinta ya kama ta, kawai sai ta ji ƙwalla ta taru a idanunta. Daidai lokacin da Alhaji Baita ya shigo ɗakin. Ta yi saurin ɗauke ƙwallar tana juyawa da sauri ta kalle shi. "Me kike yi ne har yanzu ina jiran ki ba ki ƙaraso ba? Ko kin manta yau kwanan ki ne?" Ya tambaya ba tare da ya damu da yanayin da ya gan ta ba. Girgiza kai ta yi kafin ta ce "A'ah, Daneen ke kuka na tsaya rarrashin ta." Ta yi maganar idanunta a kan Daneen. "Toh ki yi da jiki." Ya ƙare maganar yana fice wa daga cikin ɗakin. Ta bi shi da kallo kamar me son gano wani abun. Sai da ya ida ficewa kafin ta dawo da duban ta kan Daneen. Tun dawowar ta gidan har zuwa yau ɗin nan bai taɓa kula ko tambayar lafiyar Daneen ba, bai taɓa jin yaya ta kwana ko yaya ta tashi ba. Bai taɓa damuwa da ya ɗauke ta ba, ko da hakan zai janyo ƙauna ta shiga tsakanin su ba. Shi dai kawai abin da ya sani, tun da ba ya son cikin, ko da ta haihu ma ba ya ƙaunar abin da ta haifa ɗin. Tun da da ma kamar yadda yake faɗa, be aure ta ba ne don ta haihu. Sai da ta tabbatar ta ƙoshi sosai kafin ta ɗauke ta kamar yadda aka saba ta kai ta wajen Atika kafin ta wuce ɗakin Alhaji Baita. .. Su uku ne zaune a kan dinning suna break, Alhaji Baita, Hajiya Amina sai Inna-wuro da ke zaune, ita ba cin abincin take ba, sai dai ta riƙe cokali ne kawai tana caccakawa cikin abincin. Hira Alhaji Baita da Hajiya Amina (Abokiyar zaman ta) suke, sam hankalinta ba ya wajen. Ƙoƙari kawai take ta iya tare kanta, ta riƙe kanta kar wannan ƙamshin abincin da ke tashi ya sanya ta yin amai. Wani yamutsawa da 'ya'yan cikinta suka yi, shi ne ya sanya ta jefar da cokalin hannunta. Ta guntse bakinta tana jan wata ajiyar zuciya, duk don kar ta yi abin da take ta gudu, ko don gudun tonuwar abin da ta riga da ta tabbatar da lallai tabbas shi ne. Sai dai ina kwata-kwata ta kasa, cikin sauri ta miƙe ta nufi toilet ɗin da ke cikin palourn ta shiga kwara amai kamar za ta amayar da kayan cikinta. Cikin sauri Hajiya Amina ta ajje cokalin hannunta, ya yin da Alhaji Baita har bai san lokacin da cokalin hannunsa ya suɓuce ba. Cikin tashin hankali suka bi ta da kallo, sai dai babu wanda ya iya furta komai. Har bayan wajen minti 5 sannan Inna-wuro ta fito daga banɗakin cikin mutuwar jiki, ba tare da ta kalli inda suke ba, ta fara ƙoƙarin komawa ɗakinta cike da fatan kar ya yi mata magana. Sai dai tun kafin ta yi taku 5 ta jiyo muryarsa cikin kaushi yana faɗin "Ke!" Dakatawa ta yi jikinta na ɗaukar rawa, ta runtse idanunta daidai lokacin da ta sake jiyo muryarsa yana faɗin "Kar ki sake ki je ko'ina, ƙaraso wajen nan tun kafin raina ya ɓaci na yi miki abin da ba za ki taɓa mantawa ba." Cike da sassarfa ta juya akalarta zuwa inda suke. Tun kafin ta ƙaraso ta jiyo muryarsa da ke ɗauke da zallar tuhuma ya ce "Me ye ma'anar wannan aman da kika yi? Me kike nufi? Ciki ne da ke?" Ya yi tambayar duka a jere. Kasa ɗaga ido ta yi ta kalle shi, ballantana ta ce wani abu. Ta rasa me za ta ce, ta rasa ya za ta yi, gaba ɗaya kanta a kulle yake. "Tambayarki nake ciki ne da ke?" Ya yi maganar yanzu a tsawace. Runtse idanunta ta yi tana jin yadda ta ji muryar tasa har cikin kanta. Ta buɗe baki da niyyar yin magana, ya katse ta da faɗin "Kar ki sake ki faɗa mini ba daidai ba, sanar da ni abin da ke faruwa da gaske. Ciki ne da ke?" Jijjjiga kai ta shiga yi tamkar wata ƙadangaruwa, har lokacin kuma ba ta kalle shi ba. "La ha ila ha illal lahu.." Hajiya ta soma faɗa tana tafa hannu. Shi kuwa Alhaji Baita shiru ya yi don gaba ɗaya kansa ya kulle, ya ma rasa me ya kamata ya yi. Ciki? Ciki ne da Fatiman? Abin da yake ta masa yawo a ƙwaƙwalwarsa kenan. Ya sauke wani zazzafan numfashi yana tunanin ta ina zai fara? Tabbas yana ƙaunar Fatima, uwa uba kuma jikinta. Kaff matansa, da duk irin aure-auren da yake har yanzu bai samu irin Fatima ba. Duk kuwa da ta haihu, amma kullum jin ta yake kamar sabuwa. Sai dai duk da haka ba ya tunanin ze iya zama da ita. Don yana da tabbacin idan dai har ya cigaba da zama da ita, toh kowacce shekara sai ta haihu. Be san yawan adadin shekarun da za su ɗauka tare ba tare da ya gaji da ita ba, kenan 'ya'ya nawa za ta haifa? Ya kuma san ko me ze yi ba za ta yarda a yanke mahaifarta ba, don kuwa ya kwana da sanin ko kaɗan dukiyarsa ba ta gaban ta. "Ciki kika sake yi?" Tambayar da ke ta masa yawo a ƙwaƙwalwa, ta samu damar fitowa kan laɓɓansa yana kallan Inna-wuro. Da mamaki ta ɗaga jajayen idanunta tana kallansa, kafin ta kai ga cewa komai Hajiya Amina ta ce "Toh ai Alhaji ina ganin kamar laifinka ne, garin yaya ka bar ta ta shigo cikin gidan nan da mahaifa? Ka san fa 'yan ƙauye da ma akwai zilama." Be bi ta kan abin da Hajiya Amina ta faɗa ba, duk da ta wani ɓangaren maganar tata ta shige shi, amma kuma tun da mai afkuwa ta afku zancen yaushe kuma? "Wai ba kafin mu shigo gidan nan sai da na kai ki asibiti aka tabbatar mini an tsayar da haihuwar ba? wace irin zulamammiya ce ke? Duk da planning ɗin da kika yi amma sai da kika ɗauki ciki?" Alhaji Baita ya ƙarasa maganar yana jin yadda zuciyarsa ke tururi, tarin baƙin ciki da ɓacin rai na sake tunzura fusatacciyar zuciyarsa. "Ka yi haƙuri Alhaji." Hajiya Amina ta faɗa cikin salo na kwantar da murya. "Kin ga maza je ki tattara kayanki ki bar mini gida, ki ɗauki abin da kika haifa, da wannan cikin da ke jikinki ki fice a gidan nan. Wallahi ba zan iya cigaba da zama da ke ba. Idan na ce duk macen da na aura za ta haihu, 'ya'ya nawa zan tara kenan? Ni ba don ki haihu na auro ki ba. Na auro ki ne don ina son zama da ke ke kaɗai, amma saboda ƙauyanci da gidadanci cikin watannin da za a ƙirga su a hannu har kin yi ciki biyu? Ba zan iya ba. Ki je na sake ki saki uku, na kuma yafe abin da kika haifa da kuma wanda za ki haifa nan gaba. Ki je ki riƙe kayanki ba na so, ke kar ma ki taɓa tunanin suna da uba. Kar kuma ki taɓa nuna musu suna da uba. Ki manta cewar ba ke kaɗai kika haife su ba, na yafe har gaban abada. Ke ke kaɗai kika haife su. Saboda haka ke da kika haifa ke kaɗai suke da. Na bar miki su halak malak." *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 03 __ Idanunta a runtse suke tun daga lokacin da ya fara magana har ya kai ƙarshe. Duk yadda ilahirin jikinta ke rawa hakan be sanya ta yi yunƙurin nema wa kanta waje ta zauna ba. Kalaman Alhaji Baita ne kawai ke cigaba da yi mata amsa-kuwwa cikin kunnenta. A hankali wasu hawaye masu ɗumi suka gangaro daga cikin Idanunta da har lokacin suke a rufe. Cikin ƙanƙanin lokaci bugun zuciyarta ya ƙaru fiye da farkon lokacin da ya fara magana. "Ki bar wajen nan." Ya faɗa a zafafe yana nuna mata hanya, ba tare da ya kalle ta ba. Don ba ya so ya kalle ta ɗin ka da wani abu ya ɗarsu a ransa, har ya saka ya yi nadamar abin da ya aikata. Ya riga ya tabbatar wa kansa daga yau Fatiman ba tasa ba ce, komai nata ya zama ba nasa ba. Saboda haka kamar yadda ya yanke alaƙarsa da ita har abada ba ya so ya sake kallon fuskarta, jikinta ko kuma ma duk wani abu da ya dangance ta. Maganar da ya yi ita ce ta sake tuna mata da zafafan kalaman da suka yi nasarar jefa zuciyarta cikin wani irin yanayi mara misaltuwa. A hankali ta ɗaga ƙafafunta da suka mata nauyi ta soma takawa don barin wajen, daidai lokacin da ta buɗe idanunta da suka rine suka yi jajir, hawaye sun cika sun tumbatsa cikin idanun, wanda hakan ya sanya take ganin dishi-dishi. Bugu da ƙari kuma maganganun nasa da suka sanya jinta da ganinta ya ɗauke na wucin gadi. Babu abin da ke cigaba da zama daram a ƙwaƙwalwarta, suka fi kuma kowaɗanne kalmomi maimaita kan su sai "Ke da kika haife su ke kaɗai suke da. Na bar miki su halak malak." Da ƙyar ta iya kai kanta ɗaki, sai a lokacin zuciyarta da ke cunkushe, ta ba ta damar fashewa da wani irin kuka me cin rai. Kukan da ke fito wa tun daga ƙasan zuciyarta, me zafi wanda ke taimakawa wajen rage raɗaɗin da zuciyarta ke ciki. Ta kwashe fiye da rabin awa tana kukan, ta kasa hana kanta dena wa. Ba sakin da Alhaji Baita ya yi mata ne ya fi damunta ba, face yadda ya nuna ba ya son abin da ta haifa, da wanda za ta haifa nan gaba, wanda ke cikinta a yanzun. Shin ya rayuwar 'ya'yanta za ta kasance idan suka taso suka gane waye mahaifinsu? Wane hali za su tsinci kansu duk lokacin da suka ji labarin mahaifinsu ba ya son su tun samun cikinsu har haihuwarsu? Har ma an saki mahaifiyarsu ne saboda haihuwarsu? Haihuwar da wasu suke ƙarar da dukiyarsu da duk abin da suka mallaka don su samu. Haihuwar da a kanta wasu suke fitowa daga gidajensu. Lallai Allah mai mabambantan halittu, masu kuma mabambantan halayyya. Wani numfashi ta ja tana runtse idanunta, kafin ta miƙe ta ƙarasa inda Daneen take, ta ɗauke ta ta saɓa a baya. Hijab kawai ta ɗauka, ta ɗauki kuɗin da ta san ze kai ta gida, bayan nan ba ta taɓa komai da ke cikin gidan ba. Don kuwa ba ta buƙatar komai da ya dangance shi kuma. Kai tsaye ficewa ta yi daga ɗakin. Dab da za ta gifta inda suke zaune, Alhaji Baita ya saka hannu cikin aljihunsa ya fito da kuɗi, ya jefa mata ƙasan ƙafarta daidai lokacin da ya ce "Ki yi kuɗin mota." Ba ta yi niyyar tankawa ba, sai dai yadda zuciyarta ke bugawa, tana ƙara zafafa da wannan cin mutuncin da ya mata ya sa ta ji ba za ta iya ba. Shirun da za ta yi tamkar nuni ne da ta ji haushin fitar ta daga gidan, wanda ta san tabbas hakan ze yi masa daɗi, ba ma shi kaɗai ba har Hajiya Amina. Sai dai tana dakatawa da niyyar juyawa ta yi masa magana, zuciyarta ta ƙeƙashe, tarin takaici ya cika zuciyarta. Ba ta jin tun da take a rayuwarta akwai fuskar da ba ta ƙaunar sake gani kamar ta Alhaji Baita. Kamar yadda ya ce babu shi babu ita, babu kuma shi babu 'ya'yansa, toh har abada sun rabu ɗin kenan. Daga haka ta gewaye kuɗin ta fice daga ɗakin ba tare da ta sake ko da waiwayowa ba ne. ... A ƙofar gidansu ta tsaya tana kallan ƙofar gidan kamar wadda ta fara ganinsa yau. Ta yi shiru tana cigaba da kalla zuciyarta na harbawa. Tunanin abin da ke cikin gidan take, tunanin da wane ido za ta kalle su ta sanar da su Alhaji Baita ya sake ta take. Sai dai ko ma mene ne zai biyo baya ta shirya karɓarsa. Tun da ba ta da inda ya wuce mata nan ɗin. Tuna hakan ya sanya ta ɗaga ƙafafunta ta jefa cikin gidan nasu, da sallama ɗauke a bakinta ta shiga gidan. "A'uzubillahi minash shaiɗanir rajim." Shi ne abin da Dada ta ambata ƙirjinta na bugawa tana kallan Inna-wuro. Dakatawa Inna-wuro ta yi, jin da ta yi tun a lokacin gaba ɗaya ƙwarin gwuiwar da ta ji kafin ta shigo gidan yana rugujewa yana yin nasa wajen. Tun kafin ta ƙara taku ɗaya Dada ta matso tana faɗin "Me ya dawo da ke gida kuma? Me kika zo yi mana a gida?" Buɗe baki ta yi jiki a matuƙar sanyaye ta ce "Dada.." "Kar ki sake ki ƙara kiran sunana. Daga ganin idanunki akwai abin da kika shuka, faɗa mini me ya faru. Me ya dawo da ke gida?" Girgiza kanta ta soma yi, daidai lokacin da wasu sabbin hawayen suka sake cika idanunta taff, ta buɗe baki kamar me koyon magana ta ce "Ya.. sake.. ni." Salati da sallallamin da Dada ta soma yi shi ne ya fito da Baffa daga ɗaki, ya ƙaraso yana faɗin "Lafiya kuwa Uwar gida?" Ya ƙarasa maganar daidai lokacin da idanunsa suka sauka a kan Inna-wuro, da zuwa lokacin hawaye har sun jiƙa fuskarta. "Inna-wuro?" Ya ambata yana kafe ta da idanunsa. Ɗaga jajayen idanunta ta yi ta kalli Baffan, daidai lokacin da Dada ta fashe da kuka. "Subhanallahi me ya faru?" Baffa ya tambaya yana kallan Dada. "Tambayi 'yarka, tambayi 'yarka kai kam. So take ta kashe ni wallahi" Shi ne abin da take maimaitawa cikin tsananin ƙunar zuciya. Juyawa ya yi ya kalli Inna-wuro, ya buɗe baki da niyyar tambayar ta, Dada ta ji ba za ta iya tsayawa har sai ta faɗa da bakinta ba. Don haka ta buɗe bakinta ta ce "Alhaji Baita ya sake ta, ya sake ta. Mu kuma shi kenan mun shiga uku." "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Baffa ya ambata yana kallan Inna-wuro da ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ne. Idanunta na kallan ƙasa cikin rashin sanin abin yi. Kamar wadda aka tsikara Dada ta miƙe ta dawo gaban Inna-wuro, ta goge hawayen fuskarta sannan ta ce "Saki nawa ya miki?" Ta tambaya cikin tsananin tashin hankalin da ba ta ji makamancinsa lokacin da Inna-wuron ta ce an sake ta ba. "Ɗaya ya miki koh?" Dadan ta sake ambata kafin Inna-wuron ta kai ga cewa komai. Cike da tsoron jin abin da zai fito daga bakinta. Shiru Inna-wuro ta yi tana tunanin ta inda za ta fara, sai dai kuma tana tsoro kar Dadan ta kawo mata duka, saboda wani irin kallo da take bin ta da shi. "Saki uku." Ta faɗa jikinta na ƙarasa mutuwa gaba ɗaya. Ta riga ta saddaƙar yau ɗin Allah ne kaɗai ze raba ta da Dadan. Sai dai Dada kasa cewa komai ta yi, ban da komawa da ta yi baya ta yi zaman ɗabaro ta yi shiru, ban da bugawa babu abin da zuciyarta take, ta kuma kasa furta komai. "Inna-wuro ashe ba ki da hankali? Me kika yi wa mijinki ya sake ki?" "Baffa babu abin da na masa.. Wallahi ban masa komai ba Baffa." Ta ƙare maganar tana kuka jajayen idanunta a kan Baffa. Cike da fatan yau ɗaya ya ji tausayin ta, ko da kafaɗarsa ne ya ba ta ta ɗora ta yi kuka ko da za ta ji sassaucin abin da take ji a cikin zuciyarta. "Ƙarya kike munafuka, ƙarya kike yi. Yo ko yankar namanki yake ai kya zauna. Uban me bakinki yake lokacin da kika ji yana ƙoƙarin ambatar sakin, mai ya hana ki saurin katse shi ba tare da ya ƙarasa ba. Ashe mahaukaciya ce ke Inna-wuro ban sani ba? Ashe bayan kanki da kike yi wa baƙin ciki har mu kike yi wa? Wallahi ko ki faɗa mini dalilin da ya sa ya sako ki ko in miki shegen duka yanzun nan. Ki buɗe baki ki mini magana kafin na ci ubanki." Duk da zagin ta da ta yi hakan be sanya Baffa ko da kallan ta ne ba, ballantana ya nuna ya ji zafin hakan. Shi kansa kallan Inna-wuron kawai yake don jin amsar da za ta fito daga bakinta. "Baffa ciki ne da ni, shi kuma ba ya so. Wallahi shi ne kawai dalilin, ya ce ya yanke duk wata alaƙa ta da shi, har 'ya'yana ma." Ɗauke wuta gaba ɗaya kansu ya yi, musamman Baffa. Ya rasa me ze ce? Ya ma rasa ta ina ze fara. Sai kawai ya kama bakinsa ya yi shiru yana jira ya ji abin da Dada za ta faɗa. Wane hukunci za ta yanke a kan Inna-wuron wanda duk hukuncin da ta yanke ya riga ya zauna daram. "Kin cuce mu wallahi, kin cuce mu." Dada ta yi maganar cikin ƙunar zuciya, tana fashewa da wani sabon kukan baƙin ciki. Ji take kamar ta rufe Inna-wuron da duka ko ta ji daɗi, sai dai yadda take jin zuciyarta idan ta fara dukan ta san za ta iya mata lahani. Tsabar takaici ma ta kasa ko da yunƙurin dukan Inna-wuron ne. "Toh yanzu da kika ɗauko ƙafa kika dawo gida, ba ma ke kaɗai ba har waccan yarinyar da ke bayanki, da kuma abin da ke cikinki kina nufin mu za mu din ga ciyar da ku? Toh wallahi kin yaudari kanki. Shigo idan zaman gidan kike so ga ki ga shi, amma fa tabbas ki sani za ki yaba wa aya zaƙinta." "Ki yi haƙuri Uwar gida." Baffa ya faɗa ƙasa-ƙasa ko hakan ze sa Dadan ta sakko daga fushin da take. Sai dai cikin ɗaga murya ta ce "Da Allah ni ƙyale ni, ka rabu da ni in ji da abin da ke damu na. Idan ba haka ba daga kai har 'yar taka zan haɗa in ci wa mutunci wallahil azeem. Don na ga kai ma ka fara canja hali, za kuma mu haɗu da kai." Bin ta Baffa ya yi da sauri yana ba ta haƙuri, sai ka ce yaron da ya yi wa uwarsa laifi yake so ta haƙura. Ita kuma ko kallan inda yake ba ta yi ba ta wuce ɗaki, ya bi bayanta ba tare da ya sake bin inda Inna-wuro take da kallo ba. Runtse idanunta Inna-wuro ta yi, tana jin yadda tausayin kanta, da na mahaifinta na kama ta. Ta ɗaga ƙafafunta da suka sage, tana jin yadda Daneen ke mutsu-mutsu a gadon bayanta, wanda hakan ke alamta mata farkawar da ta yi. Ƙarasawa ta yi cikin ɗakinta da ya canja. Ta ɗan gyara a gurguje ta sauko da Daneen, kafin ta nemi waje ta zauna. Gaba ɗaya yinin ranar babu wanda ya sake kula ta, daga Dadar har Baffan. Sai ita ma ta kama kanta ta yi shiru cikin ɗakin tana tunanin yadda rayuwarta da ta 'ya'yanta za su kasance cikin gidan. ... Karɓe kwanon da ke hannun Baffa, Dada ta yi da sauri tana faɗin "Wallahi ba za ta ci ba, ba ka isa ba. Ƙatuwa da ita da 'ya har da cikin wani a ce mu za mu din ga ciyar da ita? Toh wallahi ba a gidan nan ba. Waye ya hana ta zaman aure? Idan da ita wata ƙatuwar mai hankali ce komai yake mata ai zauna wa za ta yi. Amma da yake shashasha ce duk irin arziƙin da ke gidan Alhaji Baita sai da ta yi abin da ya sa ya sako ta. Toh wallahi ko dai ta fidda miji ta yi aure ko kuma takura da gallazawa yanzu ta fara ganin su cikin gidan nan." Shiru Baffa ya yi jikinsa a sanyaye don be yi tunanin Dadar za ta gan shi lokacin da ya kawo wa Inna-wuro abincinsa ba. Ya haɗiye shakkarta da yake ji ya ce a hankali "Don Allah ko don shayarwar da take ki bar ta ta ci abincin nan don Allah." "Na ce ba za ta ci ba." Ta faɗa tana shirin barin wajen, bayan ta makawa Inna-wuro wata uwar harara. "Toh ko yaya ne a din ga ba ta. Tun da dai kin ga yanzu ba ta damar yin aure har sai ta haihu, daga nan duk abin da kike so sai a yi." Baffa ya faɗa yana kallanta cike da fatan ta amsa roƙonsa. Wani kallo ta ƙarasa juyowa ta watsa masa, mamakinsa na kama ta. Lallai dole ne ta tashi tsaye a kan mutumin nan. "Malam..?" Ta ƙarasa ambatar sunan nasa da alamar tambaya. "Ki yi haƙuri." Ya yi saurin faɗin hakan yana shirin juyawa jiki a sanyaye da irin kallan da ta masa. Kafin ya kai ga wuce wa Dada ta ce "Shi kenan. Na yarda da abin da ka faɗa, amma fa tabbas sau ɗaya zan din ga ba ta abinci, zuwa lokacin da za ta haihu. Daga nan ko dai ta fidda miji, ko kuma ta koma ciyar da kanta, ko kuma gaba ɗaya ma ta bar gidan." Ba ta jira wani daga cikin su ya ce komai ba ta bar wajen, ta bar su da bin ta da idanu. "Na gode sosai Baffa." Inna-wuro ta faɗa da sanyayyiyar muryarta, a ranta tana addu'ar Allah Ya sake dawo mata da Baffanta daidai ko ta ji sauƙin rayuwarta cikin gidan. Haka rayuwar Inna-wuro ta cigaba da tafiya ita da ɗiyarta. Baƙin cikin yau daban na gobe daban. Ko da wani lokacin Baffa ya yi niyyar taimaka mata ko kallanta da idon rahama sai Dada ta san yadda ta yi ta hana hakan faruwa. Shi kuma da ta yi magana shi kenan yake shiga taitayinsa. Sai dai zuwa lokacin Dada tana yarda ta ba ta abinci sau ɗaya a rana, daga nan kuma ko kallan inda take ba za ta sake yi ba. Wani lokacin sai dai a ɓoye Baffa ya kawo mata nasa. I zuwa lokacin kuwa ta soma ramewa, musamman da ya kasance ga shayarwa da take, ga kuma cikin jikinta. Sosai abubuwan suka haɗe mata, cikin lokaci ƙanƙani ta soma sauyawa daga ainahin Inna-wuronta, ga babu isasshen abinci, ga babu laifi cikin na matuƙar ba ta wahala, lokaci guda kuma ga Daneen da ke fama da rashin lafiya, duk ta bi ta rame saboda haƙori da ya saka ta gaba. Wannan ya taka muhimmiyar rawa wajen sake taɓarɓarewar lamarin Inna-wuron, ta zama abar tausayi. Idan ka yi mata kallo ɗaya ita da Daneen sai sun ba ka tausayi, musamman ma dai ita da duk ta bi ta lalace tamkar ba a gidan mahaifinta take ba. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 04 __ Babu wani sauyi da ya samu har zuwa lokacin da ta haife abin da ke cikinta, a cikin gida kamar yadda ta haifi Daneen cikin sauƙi da rangwamin Ubangiji. Sai dai wannan karon namiji Allah Ya ba ta, kyakykyawa mai kama da 'yar'uwarsa. Lokacin da ta haihu shekarar Daneen ɗaya, don haka ta yaye ta a wannan lokacin. Ko arba'in ba ta kai ga yi ba, ta ga zama cikin gidan nan haka kawai ba zai yi mata ba. Idan ba haka ba, ba jaririnta ba, ba Daneen ba, ita kanta yunwa za ta mata lahani. Dalili kenan da ya sa ta tattara duk wani abu da ta mallaka ta siyar, ta siyar da saniyar da Allah Ya taimake ta Dada ba ta ƙwace ta yi rara-gefe da ita ba. Kasancewar ba a gidan take kiwon ta ba. Da wannan kuɗaɗen ta haɗa ta soma siyar da abinci da fura da nono a cikin kasuwar ƙauyen nasu. Yaro ta samu shi ne wanda yake taya ta ayyuka saboda kula da 'ya'yanta. Wannan sana'ar, ba ƙaramin taimaka mata ta yi ba, domin kuwa za ta samu ta ci abinci, Daneen ma ta ci, sannan kuma jaririnta da ya ci suna Ameer ma ya samu ya ci. .. "Ni fa na faɗa maka ba zai yiwu ba. Ta yaya za a yi a ce ƙatuwar mata har da 'ya'ya biyu a ce a gida za ta din ga zama. Daga wannan layin sai wancan layin. Fisabillahi a haka za a rayu? Haka za mu cigaba da zuba mata idanu ta yi ta zama babu aure?" Ta jiyo muryar Dada daga tsakar gida, daidai lokacin da take shayar da Ameer, ya yin da Daneen ke kwance a kan cinyarta. Runtse idanunta ta yi, ita kam ta rasa me Dada take nufi da ita. Duk salon rashin ƙaunarta ne yake cigaba da fito wa kusufa-kusufa haka? Ta nuna ba za ta ciyar da ita ba, ta yi haƙuri ta zauna. Yanzu kuma tana ciyar da kanta ma ba ta tsira ba? Wannan wace irin rayuwa ce. Sai dai cikin sakannin da ba su wuce biyar ba, ta buɗe idanunta lokacin da ta jiyo muryar Baffa na faɗin "Ba kuma zai yiwu ba gaskiya sai dai ki yi haƙuri. Tun da dai sana'a take don ta ciyar da kanta da 'ya'yanta ba za mu hana ta ba gaskiya." Ya faɗa ba tare da ya kalli Dadan ba, duk da yadda yake jin wata irin shakkar ta. Amma ya danne, ya cije ya faɗi abin da ke masa yawo a zuciya. Lumshe idanunta Inna-wuro ta yi tana jin wani irin sanyi na ratsa ta. Wasu hawaye masu ɗumi suka zubo a kan kuncinta. "Ya Allah Ka ƙara dawo da hankalin Baffana kaina. Ka kare shi daga sharrin wannan matar." Ta faɗa a hankali, har lokacin idanunta na a rufe. Buɗe idanunta ta yi lokacin da ya sauka a kan Daneen da ke ta kallon ta, zuwa lokacin uwar ramar da ta yi duk ta yi nata wajen. Sai ta sakar mata murmushi tana kamo kumatunta ta ja. Zaro idanu Dada ta yi zuciyarta na bugawa, cikin matuƙar tsoro ta ce bakinta har rawa yake "Umar.." Ta ambata tana kallansa, kafin ya ce komai ta sake faɗin "Ni kake faɗa wa haka?" Ta faɗa har lokacin bugun zuciyarta bai koma daidai ba. "Toh ai gaskiya ce." Ya faɗa yana juya wa ya bar ta a wajen tsaye kamar wadda aka dasa. Ta kai wajen minti 5 tsaye a wajen ba tare da ta motsa ba. Gaba ɗaya ƙwaƙwalwarta ta toshe, kanta ya kulle. Mai take ganin yana shirin faruwa? Lallai ta yi mugun sake. A daren Dada ta fice daga gidan zuwa gidan wata 'yar'uwarta. Kuka kawai ta fashe da shi tana faɗin "Ni kam na shiga uku Hanne, ki taimaka mini kafin rayuwa ta juya mini baya. Umar ya fara juya mini baya." A ranar suka saɓi jiki zuwa wajen Malamin da ya saba musu aiki faka-faka. _BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYAR_ A cikin shekarun nan abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa har da sauyawar Dada kaɗan, saboda wani dalili da ita kaɗai ta bar wa kanta sani. Duk da shekarun da suka tafi, hakan be sa ta watsar da makamanta ba, ko don yadda girma ke ƙara kama su. Domin kuwa daga zarar ta ga Baffa ya soma ɗan sassautawa, yana ja da abin da ta faɗa za ta yi saurin koma wa wajen malaminta ya yi mata aiki a kansa. Kai daga ƙarshe ma sai ta nemi a yi mata aikin da har abada ba za ta sake dawo ba. Nan da nan Malamin ya nemi da ta kawo kuɗaɗe masu yawa, ta kuwa siyar da saniyarta ta biya kuɗin aikin, domin kuwa abin da take ƙoƙarin aikatawa ta san zai kawo mata ninkin ba ninkin kuɗin Saniyar da ta kashe. Daga nan kuwa al'amarin Baffa ya sake rikicewa fiye da da, ya zama shi ma ya koma muzgunawa Inna-wuro a cikin gidan nan. Kwata-kwata babu sauƙi ita kam a kowanne ɓangare sai a wajen Allah. Sai kuma idan ta kalli 'ya'yanta da take fata nan gaba su zame mata sanyin idaniya, kamar yadda tun yanzun su kaɗai take kalla ta ji daɗi. Daneen da Ameer sun taso ne tamkar 'yan biyu. Don kuwa tun da Ameer ya fara girma sai da ya kamo Daneen, sai ya zamana idan ma ba ka sani ba kana kallan su za ka kira su da 'yan biyu, saboda tsananin kamar da suke, uwa uba kuma kansu ɗaya. A tare suka taso da wata irin muguwar shaƙuwa, da tsananin soyayyar junansu. Ɗaya ba ya son abu ya samu ɗaya. Idan ɗaya ba shi da lafiya ba za ka taɓa gane waye bai da lafiya ba, saboda gaba ɗaya haɗuwa suke su yi jinyar tare. Wanda hakan ba ƙaramin tada wa da Inna-wuro hankali yake ba. Ta rasa inda za ta jefa kanta, har sai mara lafiyar ya warke kafin take samun nutsuwar zuciya, ita da mai taya jinyar. Har zuwa lokacin tana siyar da abinci kala-kala, har ma da wasu abubuwan buƙata. Da wannan sana'ar ta yi amfani wajen saka 'ya'yanta a makarantar da ke nan bakin kasuwar da take siyar da abinci. Nan suke zuwa su same ta idan an tashi kafin idan ta gama abin da take su tafi gida. Da daddare kuma su je makarantar dare, wadda take babu nisa daga gidansu. Duk wannan abubuwan har zuwa lokacin Dada ba ta canja ba. Sai dai wasu abubuwan sun ɗan yi sauƙi saboda gajiya. Uwa uba kuma da ya kasance watarana ma idan ta ga Inna-wuron da safe sai dare sannan za ta kuma sanya ta a ido. Dalili kenan da ya sa ta ɗan yi sanyi tana jira lokacin da Malam ya ce mata ta jira ya yi. Sai dai kuma maimakon haka sai ta ɗauki rabin tsanar da ta yi wa Inna-wuro ta maida ta kan Daneen da kuma Ameer, ba su da damar su fito tsakar gidan yin wasa, ko wani abun sai ta hantare su. Har gwara ma Baffa, duk da shi ma ba ya wani kula su, amma dai ba ya hantarar su kamar yadda Dada take. Da ma kuma tun da suka taso suka fara wayo suka fahimci ko ma wace ce Dada ba ta ƙaunar su, don su ɗin yara ne masu matuƙar wayo. Don akwai ranar da suna kasuwa siyar da abinci, Ameer ya kalli Inna-wuro ya ce "Inna.." "Na'am Ameer." Inna-wuro ta faɗa bayan ta juyo ta kalle shi da murmushi ɗauke a kan fuskarta. "Wai me ya sa Dada ba ta sonmu?" Ya yi tambayar da ta sanya Inna-wuro janye murmushin fuskarta. "Ameer?" Ta yi ƙarfin halin faɗar hakan fuskarta a haɗe. Ba ta taɓa zata ba, ba ta taɓa kawo wa tun a yanzu za su fahimci cewa Dadar ba ta ƙaunar su ne ba. Sai dai ga shi sun shammace ta. Kafin ya ce komai ta ɗora da faɗin "Waye ya ce maka ba ta son ku?" Ta tambaya a sanyaye. Ɗan ƙaramin bakinsa ya buɗe ze yi magana, sai kuma ya juya ya kalli Daneen da ke zaune suna kallan juna. Dara-daran idanunta farare ƙall ta ɗaga ta zuba wa Ameer ɗin su tana jira ta ji me ze ce. Ganin yana shirin buɗe baki ya yi magana ya sanya ta soma girgiza masa kanta, ƙasa-ƙasa da siririyar muryarta mai daɗin saurara take faɗin "Inna ba ni ce ba." "Adda Neen." Ya faɗa yana nuna ta, lokacin da ya turo bakinsa. Don babu yadda ze yi, ba ya so Innar ta kama shi da laifi kwata-kwata musamman da ya ga ranta ya ɓaci. Sai dai in da a waje ne, ko ma wane irin laifi Adda Neen ɗin tasa za ta yi ya gwammace ya ɗauki laifin. Shi ya sa sau da dama ko a makaranta sai dai a yi faɗa da shi ba dai da Daneen ba. Don kuwa zama yake tamkar shi ne yayan ita kuma ƙanwar. Maida duban ta Inna-wuro ta yi kan Daneen da ta yi rau-rau da idanunta kamar me shirin saka kuka, ta buɗe baki za ta yi magana Daneen ta ɗaga yatsanta guda ɗaya ta kai saitin bakinta tana faɗin "Inna na rantse ba haka ba ne." Dariya ta ba ta, don haka ta sanya hannu ta janye hannun tana faɗin "Ya isa haka, kar na sake jin wani a cikin ku ya ce haka. Dada tana son ku sosai Uhmm?" Jinjina kai kawai suka yi suna murmushi. "Ya yi kyau. Abin da nake so da ku kawai ku dage ku yi karatu, ina so ku zama wasu, ku zama waɗanda kullum zan din ga alfahari da su." "Inna da ma muna ƙoƙari ai ko?" Ameer ya faɗa yana murmushi. "Kuma dai na fi Ameer ƙoƙari." Daneen ta faɗa tana rausayar da kai, sassanyan murmushi na fita daga kyakykyawar fuskarta. Haka suke yini cikin farin ciki idan suna tare, sai dai daga zarar sun koma gida sai farin cikin ya gushe, musamman idan halin Dadan ya motsa. Haka za su yi gum a ɗaki ta yi ta jarabarta ita kaɗai. Idan Inna-wuro ta tanka ta ce za ta mata rashin kunya. Idan kuma ta yi shiru ta ce ta maida ta mahaukaciya tana magana ta mata shiru. Wannan dalilin ne yake sanya Inna-wuro kasa sanin takamaimai abin da za ta yi. Sai kawai ta haɗa kan 'ya'yanta ta rungume cikin rashin sanin abin yi. Wannan kenan. *** *** *** __ Ƙaton palour ne da ya amsa sunansa palour. Haɗaɗɗe, me ɗauke da zafafan kujeru masu ɗaukar hankali, kyau da nutsuwa. Ƙatuwar T.V ɗin da ke gefe, inda take zaune a tsare babu hayaniya ce ke ta aiki. Sai dai ga dukkan alamu babu wanda ya damu da abin da ake haska wa a ciki. Wata dattijuwar mata ce zaune a kan ɗaya daga cikin lausasan kujerun da ke zagaye da ɗakin, ƙafarta ajje a kan wani tattausan pillow, wata matashiyar budurwa na matsa mata ƙafar. Can gefe kuma wata kyakykyawar mata ce zaune, sanye cikin atamfa doguwar riga ɗinkin kaftan, ta yi ɗauri wanda ya dace da shekarunta. Har bayan wajen mintuna biyar babu wanda ya ce ko uffan. Zuwa can wata matashiyar budurwa ta shigo cikin ɗakin da sallama ɗauke a bakinta. Hannunta ɗauke da tsadaddiyar wayarta, tana sanye cikin wata doguwar riga da ta matuƙar karɓar jikinta. Neman waje ta yi ta zauna gefen wannan dattijuwar fuska a narke tana kallanta. Girgiza kai dattijuwar ta yi kafin ta ce "Toh.. za a yaudare ni ne?" Ta ƙare tana taɓe baki. Turo baki matashiyar ta yi kafin ta ce "Babu wata yaudara fa Dadaji. Allah kuwa magana na zo mu yi da ke mai muhimmanci." Jin hakan ya sanya wadda ke yi wa dattijuwar tausa miƙewa, don ba hurumin su ba ne jin wata maganar da ta shafi 'yan gidan. Don haka ta ce cikin girmamawa. "Rankiyadaɗe bari na je." Amsa mata Dadaji ta yi tana maida dubanta kan Hidaya ta ce "Me kuma ya faru?" "Dadaji har zuwa yanzu fa Yah Tareeq bai fito ba. Na yi wa Maama magana ta ce na bar shi zuwa an jima, na kikkira wayarsa ya ƙi daga wa kuma Aminu ya tabbatar mini da ya ga shigowarsa cikin gidan nan, ni kuma na kasa haƙuri." "Oh ni 'yar nan. Toh ni kuma meye nawa a ciki Hidaya? Ke ɗin da kuke ɗasawa ma da shi bai ɗaga kiranki ba me zan yi masa? Da ma ya aka cika ballantana kuma wani abu ya faru? Ni kam ban san me zan masa ba kuma." Dadaji ta faɗa. "Kai don Allah.. Wallahi dai ya kamata a tausaya wa Yaya.. Ni fa ina tsoro wallahi, kin dai san shi da saka abu a rai. Maama don Allah ki saka baki kin ji?" Ta ƙare maganar tana juyawa ta kalli ɗayar matar da ke cikin ɗakin. "Hidaya na faɗa miki ki bar shi yana buƙatar kaɗaici koh?" Maama ta faɗa tana kallan Hidayar. "Ah toh." Dadaji ta faɗa tana jinjina kai. Jiki a sanyaye Hidaya ta ce "Tohm." Daga haka ta miƙe ta wuce ɗakinta, har lokacin tana sake kiran number Yayan nata amma be ɗaga ba. ... Bayan tsawon mintuna masu yawa da ya kwashe a toilet ɗin, inda ya sakar wa kansa ruwa me sanyi. Ɗaure da towel a ƙugunsa ya fito daga toilet ɗin. Nannaɗaɗɗen gashin kansa jiƙe sharkaf da ruwan da ya daɗe a cikinsa. Farar fatarsa ita ce ta tona asirin baƙar gargasar da ke jikin gaɓɓai da yawa na jikinsa. Musamman ma dai ƙirjinsa zuwa kan hannunsa, wadda duk da yadda take a jiƙe hakan be hana ta miƙewa ba. Be yi tunanin duk daɗewar da ya yi cikin ruwan nan zai cigaba da jin ɓacin rai ba. Sai dai yadda zuciyarsa ke tafasa, tana sake yin zafi ya sa hatta numfashinsa yake fita da sauri. Tsigar jikinsa har lokacin ta ƙi dena tashi, wadda ita ta taimaka wa gargasar jikinsa wajen ƙin lafe wa a kan faffaɗan ƙirjinsa. Cikin takun nutsuwa ya ƙarasa bakin mirror ya tsaya, daidai lokacin da kyakykyawar fuskarsa ma'abociyar wani sassanyan kyau ta bayyana. Kyakykyawa ne na gani na faɗa, irin kyan nan me ruɗar da duk wanda ya yi tozali da shi. Fari irin farin nan me mugun kyau, wanda ƙasumbar da ke zaune ras a kan fuskarsa ta ƙara ƙawata kyawunsa da kuma farin nasa. Wasu idanu ne da shi na musamman, farare masu ɗauke da baƙa wuluk ɗin ƙwayar ido. Ɗan ƙaramin baki ne da shi tamkar wata mace, ja kamar wanda ke shafa wani abun. Yadda kwantacciyar ƙasumbar fuskarsa ta zagaye fuskarsa har tana ƙoƙarin rufe mitsitsin kyakykyawan laɓɓansa. Hannunsa ya kai ya ɗan shafa saman girarsa idanunsa a lumshe yana ɗan fidda numfashi a hankali ko zai samu ɓacin ran da yake ji ya tafi, ya manta da abin da ya faru, ya ɗauka ya jefa shi cikin kwandon sharan abubuwa mara sa amfani, amma ya kasa, ya kasa kwata-kwata. Daidai lokacin wayarsa da ke yashe a kan gado ta ɗauki ƙara. Be ko motsa ba, ballanta ya yi yunƙurin ɗaukar wayar. Wani kiran ne ya sake shigo wa bayan wancan ya tsinke. Duk da ba a ɗaga ba, hakan be sa an dena kira ba, ya lumshe idanunsa yana jan ƙaramin tsaki, sabon ɓacin rai na taso masa. A nutse ya juya ya ƙarasa kan gadon ya ɗauki wayar, yana shirin kashe ta gaba ɗaya sabon kira ya sake shigo wa. Ya dafe kansa da yatsu biyu kafin ya kalli me kiran nasa. Sauke ajiyar zuciya ya yi har lokacin kyawawan idanunsa ɗore a kan wayar. Dab da za ta tsinke ya ɗauka. Daga can ɓangaren aka ce "Tareeq.. Me ya sa za ka yi haka ne?" Ya faɗa a gajiye. Maida wayar ya yi ya riƙe da ɗayan hannunsa kafin ya gyara tsayuwarsa, kafin ya kai ga cewa komai aka sake faɗin "Don Allah ka fito. Wallahi ka ɗaga mini hankali." Ya faɗa dan ya san halin abokin nasa da saka abu a zuciya, ƙaramin abu ma idan ya saka a zuciyarsa an banu, ballantana wannan lamari da dukkanin su babu wanda ya taɓa tunanin hakan za ta iya faruwa. "Abdoul don Allah ka ƙyale ni, zuciyata na buƙatar hutu, idan har ba so kuke ta tarwatse ba." Ya ƙarasa maganar a gajiye, yana fesar da wani huci da ya fito tun daga ƙasan zuciyarsa. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 05 __ "Tareeq!" Abdoul ya faɗa bayan ya sauke ajiyar zuciya. Bai ce komai ba sai ajiye wayar da ya yi, ya koma ya zauna a gefen gadon hannunsa ɗaya cikin sumar kansa, idanunsa a lumshe, zuciyarsa na sake cunkushe wa waje ɗaya. A ɗaya ɓangaren kuwa kallan Abdoul Maama ta yi ta ce "Ya katse ne?" Ta tambaya tana kallan sa. Gyara zaman wayar ya yi a hannunsa kafin ya jinjina kai, a nutse ya buɗe baki ya ce "Ehh, amma dai sauƙin ta ɗaya yana cikin gidan nan." Ajiyar zuciya Maama ta sauke kana ta ce "Ku bar shi, kar wanda ya sake kiran sa don Allah, ni da kaina zan je na same shi zuwa gobe, na san kafin nan In Sha Allah zuciyarsa ta yi sanyi." "Toh shi kenan." Abdoul ya amsa da hakan. Daga haka ya yi sallama da su ya fice daga ɗakin. ... Tura ƙofar ɗakin ta yi, cikin sa'a kuwa sai gashi ta buɗe. Ta sauke ajiyar zuciya tana saka kanta cikin ɗakin da sallama ɗauke a bakinta. Yana zaune a kan haɗaɗɗiyar kujerar da ke cikin palourn, sanye cikin ƙananan kaya da suka matuƙar yi wa jikinsa kyau. Laptop ce gabansa yana dannawa cikin ƙwarewa, gaba ɗaya fararen idanunsa na kai, da alama wani aikin yake mai matuƙar muhimmanci. Duk da kusan duk hankalinsa na kan laptop ɗin, hakan be hana shi jin lokacin da aka turo ƙofar ba. Ya ɗaga manyan fararen idanunsa ya kalli ƙofar a nutse. Daidai lokacin da Hidaya ta ƙarasa shigowa cikin ɗakin, kamar koyaushe babu abin da ke tashi sai sassanyan ƙamshin jikinsa da kuma na cikin ɗakin. Wanda suka cakuɗu suke bayar da ƙamshi me daɗin gaske. Rufe laptop ɗin ya yi kafin sassanyan murmushin da ya ƙawata fuskarsa ya bayyana a kan laɓɓansa. Sai dai yadda tsagoron kyawunsa ya sake bayyana, ga duk wanda ya kalle shi zai so a ce ya zauna a hakan ne ko da yaushe. Ita ma murmushin Hidaya ta yi tana ƙarasawa ta nemi gefensa ta zauna ta ce a narke "Kai Yah Tareeq, da ma ka gama fushin amma shi ne ba ka nemi kowa ba?" Kallan ta ya yi, kafin cikin er basarwa ya ce "Ni na faɗa miki ina fushi?" Ya ƙare kamar da gasken ba shi ne ya yi mugun fushi jiya ba. Sanin halinsa ya sanya ta yin murmushi kafin ta ce "Yah Tareeq.." "Uhmmm." Ya amsa yana ɗaukar wayarsa da ke ajje a gefen sa. Daidai lokacin da Hidaya ke faɗin "Yaya tun jiya duka gida sun damu da ganin ka, ni ma kasa jurewa na yi shi ya sa na sake zuwa in duba ka. Please ka je ko za su ji daɗi." Jinjina kai ya yi, har lokacin idanunsa na kan waya. Miƙewa Hidaya ta yi ta ce a nutse "Bari na je Yaya, na ga kamar aiki kake yi." Sai a lokacin ya ɗaga idanunsa a nutse ya kalle ta. Ya ɗan lumshe idanunsa kafin ya buɗe, ya buɗe bakinsa kamar wanda ba ya son yin maganar ya ce "Olright, take care of ur self soulsis. Zan shigo zuwa an jima In Sha Allah." Ya ƙare da ɗan gajeren murmushin nan nasa da ya kasance na dabi'a. Yana matuƙar ƙaunar er uwar tasa, kasancewar ta mace ta farko da ta fi kowa damuwa da damuwarsa, ta fi kowa fahimtar sa idan yana cikin damuwa. Ta fi kowa shiga damuwa idan ta gan shi cikin rashin walwala. Shi ya sa duk lokacin da take kusa da shi, ya kan yi ƙoƙari wajen wanzar da murmushi ko da kuwa yana da damuwa don kar ma ta fi shi shiga damuwa. "In Sha Allah Yaya. Amma don Allah ka cire Diyana a ranka, ka manta da rayuwarta.." Hannu ya ɗaga mata alamar ta dakata kar ta ƙarasa maganar da ta fara. Tuni annurin fuskarsa ya ɗauke. Shi haka rayuwarsa take, idan dai har ya bar abu toh ya bar shi har abada. Shi ya sa ma ba ya saurin yanke hukunci har sai ya tabbatar da abu. Ganin tana shirin ɓata masa rai ne ya sanya ta faɗin "Don Allah Yaya ka yi haƙuri.." Ta faɗa tana kama kunnenta. Ɗan sauke gajeriyar ajiyar zuciya ya yi kamin ya ce bayan ya ƙaƙalo murmushi a kan fuskarsa "Kar ki ƙara." Girgiza kai ta yi tana faɗin "Ba ma zan ƙara ba har abada." Ta ƙare tana murmushi. Daga haka ta yi sallama da shi ta fice daga ɗakin. Ya ja laptop ɗin gabansa ya cigaba da abin da yake yi a ciki. .. Sanye take cikin doguwar rigar atamfa mai matsakaicin kyau, tana sanye da hijabi dogo wanda ya wuce gwuiwarta. Tafiya suke yi tare ita da wani ɗan saurayi wanda kusan tsayin su ɗaya, sai dai kasancewar namiji ya sa ya fita tsayi. Jefi-jefi su kan ɗan yi magana, har zuwa lokacin da Ameer da ya kalli Daneen ya ce "Adda wai kin ma san wani abu kuwa?" Girgiza kai ta yi tana ɗaga manyan fararen idanunta ta kalle shi sannan ta ce "A'ah." Ta yi maganar tana cigaba da tafiya. A haka idan ka kalle su za ka iya cewa Ameer ne babba, sai dai nutsuwa da yanayin yadda Daneen ke abubuwanta da suka wuce na shekarunta, ya sa ake gane ita ce babba. Kyawun nan da ta taso da shi tun yarinta, har yanzu babu abin da ya ragu. Sai ma ƙaruwa da ya yi, ta ƙara zama wata irin kyakykyawa, don kaff rigarsu tana sawun farko cikin kyawawan 'yan matan ƙauyen. Idanunta manya ne, kamar yadda tun yarinta suke, sai dai yanzu asalin kyawunsu, da kuma yadda suke a halitta sun ƙara bayyana. Tamkar idanun mage haka suke, masu kyau da kuma ɗaukar hankali. Wani irin shape na da su na musamman, wanda ko iya kyawun idanunta aka tsaya an gama tashi. Siririn hanci gare ta, wanda ta gado shi daga wajen Inna-wuro. Don ko kaɗan, daga ita har Ameer ba su ɗauko ko abu ɗaya daga wajen Alhaji Baita ba. Bakinta kuwa ƙanƙantarsa kaɗan ne ya ƙaru tun yarinta. Haka yake ɗass a bakinta, ja ne matuƙa, irin jan nan mai ɗaukar hankali. Don sau da dama idan ta je makaranta a kan ce sai ta goge jan bakin da ta shafa a bakinta kafin ta shiga aji. Idan ta ce ba ta shafa ba, wasu ba sa yarda, har sai ta saka gefen hijab ɗinta ta goge bakin nata, sai dai maimakon janbakin da suke iƙrarin ta shafa ya fita, sai bakin ya sake ɗaukar ja saboda gurje shin da ta yi. Duk wani abu da ake buƙata a jikin kyakykyawar mace Allah Ya ba wa Daneen. Ƙarancin shekarunta ba su nuna wa a jikinta saboda tarin nutsuwa da take da ita. Sai dai idan fuskarta ka kalla shi ne za ka gano zallar yarintar da ke tattare da ita. Sanyi ne da ita tamkar me, ba ta da hayaniya ko kaɗan. Ko da kuwa a cikin jama'a ne, za ka same ta shiru babu hayaniya, idan dai har ba tare da rabin jikinta Ameer take ba, toh shi ne za ka ji bakinta sosai. Shi ma Ameer kyakykyawa ne, don kamar su ɗaya ma da Daneen ɗin, sai dai duk kyawunsa ta fishi, musamman kuma don kasancewarta mace. "Mutumin nan fa yau ma sai da ya." Tun kafin ya ƙarasa ta katse shi da faɗin "Kaa ga Ameer na faɗa maka ka fita harkar wanda ba ka sani ba koh? Wallahi ba ka jin magana." Ta ƙare maganar tana hararar sa. Dariya ya yi, yana so ya ga Daneen ɗin na masa faɗa, sam ba ma ta iya haɗe ran ba. Kuma ma wani idan ya gan su tana masa faɗan zata zai yi rashin kunya take yi wa yayanta. Tun da dai a tsaye ya fita girma, dan ma dai ba shi da ƙiba ne, haka yake siriri sai tsayi. "Toh Adda na dena." Ya faɗa daidai lokacin da suka iso ƙofar gida. Da sallama suka shiga cikin gidan, Dada na zaune kan kujera tana cin gyaɗa marau, ya yin da Baffa ke zaune kan tabarma yana saurarar Radio. Dukansu girma ya bayyana sosai a jikinsu, sun sake zama dattijai matuƙa. Tun da suka shigo gidan sai suka kama kan su, don sanin halin masu gidan. "Baffa barka da wannan lokacin, Dada barka da wannan lokacin." Suka haɗa baki wajen faɗar hakan. Ba tare da sun jira jin cewar wani daga cikin su ba suka wuce ɗakinsu, ɗakin da yanzu Inna-wuro ta yi masa dabara ta samu ta fitar wa da Ameer inda yake kwana. Don sun san in dai Dada ce ba amsa wa za ta yi ba, shi kuma Baffa ko ya yi niyya idanun Dada ba za su bar shi ya amsa ba. "Sai da na ce miki mu tafi wajen Inna ba ta dawo ba, ni na ji hakan a jikina." Ameer ya faɗa lokacin da suka gama shiga ɗakin nasu babu Inna-wuro a ciki. Ita ma Daneen ɗin tura mitsitsin bakinta gaba ta yi kafin ta ce "Allah na ɗauka ta dawo fa." "Toh mu koma mana." In ji Ameer. Girgiza kai ta yi ta ce "Dada na tsakar gida shi ne za mu fita, chaɓɓ.. Ba inda za mu je." Ta ƙarasa maganar tana neman waje ta zauna. "Kai Adda." "Na gama magana." Ta faɗa tana jefa masa harara. "An gama The Babbar Yaya." Ya ƙarashe maganar yana dariya. Shi ma neman waje ya yi ya zauna, sai suka shiga bitar littafan makaranta. Don ko a makarantar ma ajinsu ɗaya har islamiyya. Sai dai ko minti 10 ba su yi ba muryar Dada da ta ke magana cikin ɗaga murya ta katse su. "Ina waje ina aiki kuna cikin ɗaki koh? Toh ku fito kai ka je mini gonar Habule ka tsinko mini zogale. Ke kuma ki zo ki je ki ɗebo mini ruwa.. Za ku fito ne ko sai na ci uwarku." Ambatar sunan uwar da ta yi ya sanya duk jikinsu ya yi sanyi, ɓacin rai ya taso wa Ameer da yake ya fi Daneen zuciya. Shi idan ta shi ne in da ubansu ta ce toh da sauƙi. Tun da dai be san waye uban nasu ba, abu ɗaya ya sani kawai duk lokacin da suka yi wa Inna-wuro zancen wani abu da ya shafi mahaifinsu ranta kan ɓaci. Wannan dalili ne ya sa suka jefar da maganar tasa gefe suka dena yi. Girman mahaifiyarsu na ƙaruwa a zuciyarsu, domin su a wajen su ita ce uwa, kuma ubansu. Miƙewa Daneen ta yi, ganin Ameer be ko da motsawa ba ne ya sanya ta faɗin "Ameer tashi mu je." "Ni ba inda zan je." Ya faɗa yana ɗauke kai. Hannunta ta kai ta dafa kafaɗarsa a sanyaye ta ce "Don Allah ka yi haƙuri Ameer ka tashi mu tafi, idan Inna ta ji Dada ta saka mu aiki ba mu yi ba ba za ta ji daɗi ba. Ka yi haƙuri ka ji?" Shiru ya yi na tsawon sakanni kafin ya miƙe ba don ya so ba. Ya haɗe fuska don ba kaɗan ba ransa ya ɓaci. Kuma sanin kanta ne ita Dadar Habule ya hana mutane shigar masa gona tsinkar wani abun, don ba shi da mutunci ko kaɗan, a kan ko da ganye ɗaya ne be ƙi ya ya ci maka mutunci ba, ya zage kaff danginku hankalinsa kwance. Ɗebo ruwa kuma da ta aiki Daneen ta yi ta san sarai an hana mata zuwa rafin, saboda gurɓatattun samari da ke zama a wajen. Ko kuma su laɓe, ba sa tashi fitowa sai 'yan mata sun zo ɗibar ruwa. A can aka kama wasu samari su huɗu sun yi wa wata yarinya fyaɗe, kafin a kai ta asibiti ta rasu. Wannan dalilin ne ya sa aka hana mata zuwa ɗibar ruwan, aka kuma samar da rijiyoyi don abin ya zo da sauƙi. "Kar ka sake ka siyo mini na siyarwa ba na so, idan ma shi ka siyo zan gane. Ni ba sa'ar ka ba ce, don haka inda na aike ka can nake nufi ka je. Ke kuma sauri nake na ba ki mintuna biyar ki kawo mini ruwa in ɗora tuwo kar ya min dare. Idan kika sake kika wuce billahillazi sai na ci ubanki a cikin gidan nan." Dada ta faɗa lokacin da suka fito daga ɗakin. Ba su ce komai ba, sai ficewa da Ameer ya yi, ya yin da Daneen ta ƙarasa ta ɗauki wani tulu ta yi waje da shi. Baffa da tun da ta fara magana be ce komai ba, sai a lokacin ya bi su da kallo, har lokacin kuma be ce komai ba. Dogon tsaki Dada ta ja tana ƙarasa jefa gyaɗa guda ɗaya da ta yi ragowa a hannunta, sannan ta miƙe don iza wutar girki. "Wai ana sallama da Baffan Inna-wuro." Wani yaro da ya shigo gidan bayan fitar su Daneen ya faɗa yana kallan Dada. Juyawa ta yi ta kalle shi kafin ta maida duban ta kan Baffa, ba ta ce komai ba, sai sake mayar da idanunta da ta yi kan yaron ta ce "Je ka ce yana zuwa." Fice wa yaron ya yi daga gidan, ya yin da Dada ta ɗaga murya tana faɗin "Ai dai kana ji ana sallama da kai." Miƙewa Baffa ya yi yana faɗin "Naa ji kam." Daga haka ya fice daga gidan. A bakin mota ya hango wani mutum tsaye, sanye cikin babbar rigar shadda, da hula zannabukar a kansa. Tsayawa ya yi da mamaki shimfiɗe a kan fuskarsa yana kallansa, don kwata-kwata bai shaida fuskar ba. Ganin fitowar Baffa ya saka mutumin ƙarasawa cike da girmamawa ya miƙa wa Baffa hannu yana faɗin "Salamu Alaika.." Karɓar hannun nasa Baffa ya yi yana amsa wa a hankali kamar wanda ke jin tsoro. Cikin girmamawa mutumin ya sanar da shi shi ne wanda yake sallama da shi. Gyara tsayuwa Baffa ya yi kafin ya ce "Sai dai ban shaida fuskar ba." Sauke numfashi mutumin ya yi kafin ya soma faɗin "Da farko dai sunana Abubakar Bashir, ni ɗan kasuwa ne, wanda ke harkar siye da siyarwa a cikin garin Kano har ma da wajen ta. Matata Allah Ya Yi mata rasuwa, ina da 'ya'ya waɗanda ke tare da ni. A taƙaice dai na ga 'yarka ne, wadda aka tabbatar mini da nan ɗin nan ne gidan mahaifinta shi ya sa na zo don neman izini." Cike da mamaki Baffa ya ce "Wace 'yar tawa kenan?" "Fatima!" Ya faɗa kai tsaye. "Ikon Allah." Baffa ya faɗa cike da mamaki, don kuwa zai iya cewa a tsayin shekaru sha biyar da suka gabata, babu wani da ya taɓa zuwa ya ce yana son Inna-wuron. A hankali Baffa ya ɗaga kansa ya dubi kamilallen mutumin, bai san me ze ce masa ba a yanzu dai kam. Domin kuwa tamkar ba shi ne uban ba, ba shi da ikon yanke hukunci sai abin da Dada ta faɗa. Don ko ya ce zai yanke ma, idan Dada ta faɗi saɓanin abin da ya yanke dole ne ya bi. Shi ya sa ma ba zai yi gaggawar yanke hukuncin ba, saboda kar mutunci ya zo ya zube daga baya. Dada da ke leƙe daga soro, ta sake leƙo da kanta don sake tabbatar da da gasken mota take gani zaune a ƙofar gidansu, kuma mallakin mutumin da ya zo neman auren Inna-wuro?? #MAFARI.. Na gode sosai da addu'oinku. Waɗanda suka kira ni, waɗanda suka mini gaisuwa ta DM, har ma da waɗanda suka mini cikin group. Thank yhu all for your kind words and condolences. I do appreciate, Allah Ya bar zumunci. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 06 __"Shi kenan, In Sha Allah zan neme ka zuwa gobe. Zan ɗan yi tunani sannan na yi shawara da matata, duk yadda muka yanke gobe sai ka dawo ka ji." Maganar da ta ji Baffa ya faɗa ita ce ta ta sanya ta ji tamkar ta daka tsalle don farin ciki. Da alama lokacin da ta daɗe tana jira ya zo. Ba ta sake jiran komai ba ta koma cikin gidan tana jiran dawowar sa. Kwata-kwata ta kasa tsaye ta kasa zaune, ji take kamar ta fita kawai ta sanar da mutumin cewa an ba shi auren Inna-wuro. Sai ta shiga zagaye tsakar gidan, tana ta saƙe-saƙe a cikin ranta. Babu dadewa sallamar Baffa ta ratso cikin gidan. Ta juya da sauri cikin farin ciki, abin da ya manta ma da mata tana faɗa wa mijinta, yau ɗin sai ga shi ta furta "Sannu da zuwa." Ya kalle ta, sai ya ji daɗin hakan. Saboda haka ya saki murmushi yana ƙarasowa cikin gidan. A ɓangaren Daneen da Amir kuwa, ko da suka fito kallan Amir Daneen ta yi ta ce "Toh yanzu ya za mu yi?" Shiru ya ɗan yi na wasu sakanni kafin ya ce "Kawai ki je rijiyar majalisa, nan ne mata suke zuwa." "Ba ni ba Amir.. Kai kuma ya za ka yi?" "Adda in dai ke kin yi sauri kin dawo ai ni babu matsala." Ya faɗa a nutse. Girgiza kai Daneen ta yi ta ce "Ba ka tsoron faɗan Dada koh? Idan ma ta kama ta haɗa da duka ko?" Ta ƙare a sanyaye. Shi ma girgiza kan ya yi kafin ya ce "Amma dai Adda kowanne duka za ta mini ba za ta kashe ni ba ai dai koh?" Harara Daneen ta jefa masa, don har ta haddace wannan maganar tasa. Daga zarar ta masa maganar Dada, kullum amsar sa kenan, ai dai ba za ta kashe shi ba. "Adda kar fa ki wuce mintunan da ta ba ki. Ki tafi ki je ki ɗebo. Ko kuma ki kawo in ɗebo kafin na je na siyo mata zogalen." Ya faɗa yana ƙoƙarin karɓar tulun hannunta. Janye wa ta yi ta ce "A'ah, ka yi sauri ka je ka siyo. Ni kuma bari na je na ɗebo ruwan." "Toh shi kenan." Ameer ya faɗa yana yin gaba. Ita ma hanyar da za ta sada ta da rijiyar ta yi da sauri saboda gudun kar ta ƙara lokacin da Dada ta ba ta. Duk da mawuyaci ne ma hakan ba za ta faru ba. Saboda ko daga fitowar su daga gida sun ci wajen minti nawa. Tun daga nesa ta soma hango bokitai, robobi ajiye a gefen rijiyar. Wasu a hannun mamallakansu wasu kuma sun ajiye. Mutane da dama zagaye da rijiyar kowa na ɗiba da gugan da ya zo da shi. "Wayyo Allahna!" Ta ambata cikin sanyayyiyar muryarta tana lumshe idanunta. Sauke wani nannauyan numfashi ta yi, tana rasa yadda za ta yi. Ta yi shiru tana tunanin ta ina za ta fara jiran wannan layin har ya zo kanta? Anya kuwa ba ƙundunbala za ta yi ta nufi rafin nan ba? Kawai sai ta buɗe idanunta, ta sake kallan inda mutanen ke tsaye suna cigaba da ɗibar ruwansu, babu alamar za su ragu. Soma takawa ta yi tana barin wajen, kai tsaye ta nufi rafi, cikin zuciyarta tana karanto duk addu'ar da ta zo mata. Duk da yadda take jin tsoro, amma ba ta sare ba, ta dogara da addu'ar nan da take yi, ta san in Allah Ya yarda babu wani abu da zai faru. "Daneen.." Ta ji an ambata lokacin da take dab da ƙarasawa rafin. Da sauri ta juyo cike da mamakin jin muryar Innarsu. Da mamaki Inna-wuro ke kallan ta. Fasa tafiya Daneen ta yi ta dawo da baya zuwa wajen Inna ta ce a mamakance "Inna.." "Na'am, ina za ki je?" Ta ƙare tambayar tana kallan tulun hannunta. Ita ma Daneen ɗin kallan tulun ta yi kamar wadda ta manta da wanzuwarsa a hannunta. A narke ta soma faɗin "Inna, Dada ce ta ce na je na ɗebo mata ruwa.. Kuma ta ba ni ƙididdigaggun mintuna. Na je rijiyar majalisa mutane sun fi nawa, shi ne zan je na ɗebo a rafi. Amma ina tafiya ina addu'a." Ta ƙare maganar tana kallan fuskar Innar don ganin yanayinta. "Ya ilahy." Inna ta faɗa tana dafe goshinta. Sai kuma can ta ɗago ta kalli Daneen ta ce "Kar na sake ji Daneen.. Kar na sake ji kin ji koh? Ba ni tulun." Ta faɗa tana miƙa hannu, babu musu ta saki tulun Inna ta riƙe. Ta juya ta kalli almajirinta da ke kwasar mata kaya idan za ta tafi kasuwa ko kuma idan za ta koma gida. "Ɗan yi maza ka je ka ɗebo mini ruwa." Babu musu ya amsa yana karɓar tulun. Bayan mintuna kaɗan sai ga shi ya dawo. Cigaba da tafiya suka yi har zuwa ƙofar gidan. Sai a lokacin Daneen ta karɓi tulun, Inna ta karɓi kayanta ta shiga da su cikin gida. Inda Daneen ta ci sa'a, zumuɗin da Dada ke ciki ya sanya ta mantawa ma kwata-kwata da aiken da ta yi. Burinta kawai Inna-wuro ta dawo ta sanar da ita sun yi mata miji. ... Su uku ne zaune cikin palourn, manyan mata guda biyu, ya yin da matashiyar budurwa ke zaune ita ma a kan kujera. Sanye cikin wata doguwar rigar atamfa da ta matuƙar yi mata kyau. Kyakykyawa ce ba can ba, hasken fatar da Allah Ya ba ta shi ya haska kyawun nata. Hannunta ɗauke da waya tana dannawa, lokaci lokaci ta kan ɗaga ido ta kalli iyayen nata da ke magana. Zuwa can ma sai danna wayar ya gagara, musamman da ta ji maganar da suka fara ɗin ta shafe ta. Don haka gaba ɗaya ma sai ta ajje wayar ta maida gaba ɗaya hankalinta kan su. Daidai lokacin da Momynta ke faɗin. "Amma Maama ba kya ganin tun da bare ta watsa mana ƙasa a ido, me zai hana mu haɗa shi da Jawahir, er uwarsa wadda dukka kowa ya san halinta" Murmushi matashiyar ta saki tana sake kama kanta a kan kujerar da take. Ita a lallai dole kunya ta ji, saboda tana gaban sirikarta. Buɗe ido Maama ta yi, kafin ta shiga jinjina kai "Babbar magana.. Tareeq ɗin?" Ta ambata ba tare da wata damuwa ba. Jinjina kai ita ma Momy ta yi tana faɗin "Ehh shi fa Maama.. Ai hakan shi ne daidai. Don na san daga ke dai har Yaya ba za ku sake bari ya nemo wata a waje ba, ballantana har a zo a samu matsala." "Ba wannan ba ne Hajiya A'isha.. Na san halin Tareeq, ke kan ki kin san halinsa. So bayan duk abin da ya faru ba na tunanin a nan kusa ze iya amincewa da wata kuma. Kin san dai yadda abin da ya faru ya illata zuciyarsa. So gaskiya yana buƙatar lokaci kafin a je masa da irin wannan maganar." "Ba don kar ki ce na katse ki ba, da na sake tuna miki Jawahir fa er uwar Tareeq ce ta jini. Wadda ya san halayenta, uwa uba kuma tana ƙaunar sa." Momy ta ƙarasa maganar tana dafa kafaɗar Jawahir. Sake yin ƙasa da kai Jawahir ta yi tana wasa da yatsun hannunta da murmushi kwance a kan fuskarta. Fatan ta ɗaya Maaman ta amince da wannan haɗi. Don ta san idan dai har ta amince toh fa shi ma Tareeq ɗin abu mai sauƙi ne zai amince. Jin Maama ta yi shiru ya sanya ta sake faɗin "Ki yi tunani a kan wannan al'amari, sannan ki duba abin da idon basira. Za ki gane da gaske Jawahir ce kawai ta dace da auren Tareeq.." Abin da ya tsinta kenan lokacin da ya kawo kansa cikin ɗakin. Sai dai yadda fuskarsa take, kai ba za ka taɓa cewa ya ji ko da makamanciyar maganar da suke yi ba. Yana sanye cikin wasu sheggun ƙananan kaya da suka karɓi jikinsa. Ya yi wani shahararren kyau tamkar da ma don shi aka yi kayan. Ya sakaya baƙar sumar kansa da wata haɗaɗɗiyar facing cap, hakan ne ya sa ba a iya ganin sumar tasa. Sai dai ka hangi sumar da ke kwance luff a ƙeyarsa. Da sallama ya shiga cikin ɗakin, ba tare da ya kalli kowa da ke cikin ɗakin ba. Duk kuwa da tun kafin ya shigo ɗakin ya gama ganin su waye a ciki. Don haka gefen Maama ya je ya zauna. Cikin girmamawa ya gaishe da Momy da ta katse zancen ta saboda ganin shigowar sa. "Lafiya ƙalau Tareeq.. Ya kuma wannan abu da ya faru? Toh Ubangiji Ya sa haka ne mafi alkhairi." "Ameen." Kawai ya amsa da hakan yana maida duban sa kan Maama, don kwata-kwata ba ya so zancen ya yi tsayi. Ya kuma san halin Momyn sarai na son gutststsira zance. Don haka dan kada ma ta sake ce masa komai ya ce yana kallan Maama "Barka da wannan lokacin Maama." "Barka dai Tareeq, kana lafiya?" Shi ne kawai abin da ta faɗa. Duk da tana so su yi magana sosai da ɗan nata, amma wanzuwar Momy a wajen ya sa ta kama bakinta kawai. "Alhamdulillah.. Hidaya ba ta nan ne?" Ya tambaya saboda rashin ganin gilmawar ta, bayan hakan ba ɗabi'arta ba ce, kusan kodayaushe ta fi zama gefen mahaifiyar tasu. Sai dai idan sister ɗinta na nan, kuma ya san ba sa cikin gidan ma yanzu haka. "Ohh, ta bi driver zuwa ɗakko su Sultanah." Maama ta faɗa. Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba, yana shirin miƙewa Jawahir da ke ta sake gyara zama, tana tsara yadda za ta masa magana ta ce "Barka da wannan lokacin Yah Tareeq." Sai a lokacin sannan ya ɗaga idanunsa ya mata kallo ɗaya, kafin ya ɗauke idanunsa. Ya ɗan ƙaƙalo murmushin da ya tsaya a kan laɓɓansa ya ce "Barka Jawahir.." Daga haka ya maida duban sa kan Maama ya ce "Bari na ɗan fita.." "Toh Allah Ya tsare." Maama ta faɗa cikin kulawa. Amsawa ya yi da "Ameen" yana ficewa daga ɗakin. Jawahir ta bi shi da kallo tana jin wani irin farin ciki na ziyartar ta. Wato duk lokacin da aka ce wannan kyakykyawan, haɗaɗɗen guy ɗin ya zama mallakinta nata ita kaɗai, ba ta san kuma a wane yanayi za ta tsinci kanta ciki ba. "Allah sarki! Kin ga har yanayinsa ya ɗan chanja wallahi. Taimako ɗaya za mu masa mu nuna masa ƙauna ta hanyar aura masa Jawahir a kurkusan nan ko don ya manta da raɗaɗin da mace ta sanya shi a ciki." Momy ta sake faɗar hakan bayan fitar Tareeq babu daɗewa. Sauke numfashi Maama ta yi, ita kam i zuwa yanzu ai ya ci a ce ta bar maganar gaba ɗaya ko don fahimtar da ta yi ba ta da ra'ayi a kai. Don ita dai haka kawai ta ji haɗin bai kwanta mata ba. Musamman kuma da ta san halin Tareeq ɗin. Ga kuma abin da ya faru. "Amma me ya sa ba ki samu Yayanki ko Dadaji kin mata maganar ba?" Murmushi Momy ta yi kafin ta ce "Ke fa ke ce mahaifiyar Tareeq. Ke kika fi dacewa na fara tuntuɓa da wannan maganar. Idan har ke kika fara masa maganar zai fi ɗaukar ta da muhimmanci. Kin fi kowa sanin halin ɗanki shi ne dalili." "Toh shi kenan, Ubangiji Ya zaɓa abin da ya fi zama alkhairi." "Ameeeeen.." Momy ta faɗa tana jan Ameen ɗin cikin farin ciki. ... A nutse ta ƙarasa fitowa daga cikin ɗakin jikinta a matuƙar sanyaye. Don haka kawai ta ƙi jinin kiran Dada, domin da wuya idan na alkhairi ne. Ƙarasawa ta yi ta nemi waje ta zauna cikin ladabi ta ce "Dada ga ni." Ƙarasa abin da take Dada ta yi, kafin ta dawo ta nemi waje ta zauna gefen Baffa ta ce "Toh ke sai ki fara shiri, domin kuwa mun yi miki miji. Miji ya zo, Baffanki ya gan shi ya masa, ni ma kuma na gan shi ya yi mini. Don haka gobe zai zo ki je ku gaisa. Ba wani da yawa za a saka ba, cikin ƙanƙanin lokaci za a yi komai a gama." Dada ta faɗa maganar tamkar da ita mutumin da ya zo suka yi magana. Tun lokacin da Dada ta ambaci miji ta ji zuciyarta ta buga. Ba ta tsaya ba, sai cigaba da bugawa da ta yi. Ta runtse idanunta tana tuna lokacin da suka gabatar mata da Alhaji Baita a matsayin mijin da za ta aura. Daga zuwa siyar nono. Ba tare da sanin waye shi ba. Mene ne asalinsa, su waye iyayensa duk ba su sani ba. Haka kawai suka ɗauke ta suka ba shi don kawai ya yi musu ɓarin kuɗi. Toh idan kuma shi ma wannan ɗin halinsa ɗaya da Alhaji Baitan fa? Abin da ya fara zuwa kwanyarta kenan, tana jin wani sabon tashin hankalin na ziyartar ta. Duk wani tunaninta, burinta, da duk wani fatanta ba ya wuce a kan inganta rayuwar 'ya'yanta. Toh idan dai har suka ce ta yi aure yaya rayuwar 'ya'yanta za ta kasance? Ko kuwa wanda suka sake zaɓar mata a karo na biyu zai yarda ya riƙe 'ya'yanta? Tunanin nata ya katse ne, lokacin da hayaniyar da ake a waje take sake kusanto gidansu. "Ɓarawo, Ɓarawo.." Shi ne abin da kafatanin mutanen ke faɗa cikin ɗaga murya. Haka nan kawai ta ji ƙirjinta ya sake bugawa a karo na barkatai. Daidai lokacin da aka soma buga ƙofar gidan da ƙarfi, wanda ke bugawa ɗin yana faɗin "Ina mutanen gidan suke ne? Ku fito tun kafin in ba wa mutane umarnin shigowa su muku rashin mutunci wallahi. Ku fito na ce.." Ya ƙare maganar yana sake dukan ƙofar kamar wanda ze jijjige ta. Kusan a tare dukansu suka miƙe. Daneen ma da ke cikin ɗaki ta yo tsakar gidan babu shiri. Gaba ɗaya suka nufi ƙofar gidan don ganin abin da ke faruwa, ko kuma ma ya farun.. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 07 __ Dandazon mutanen da ta gani a ƙofar gidan nasu, shi ne abin da ya sake tsinkar mata da gaba. Ta runtse idanunta tana ambaton sunan Allah, lokaci ɗaya tana buɗe idanun, a daidai lokacin da ta sauke idanunta a kan Habule da ke riƙe da kwalar rigar Ameer. Ya cukwuikuye ta kamar wanda ke shirin zame ta daga jikinsa. "Ɓarawo." Kunnenta ya sake tsinto mata wannan kalmar. "Ya isa haka.." Mutumin da ke riƙe da kwalar rigar Ameer ya faɗa bayan ya yi amfani da hannunsa wajen alamta musu abin da ya faɗa. Kamar dama shi ya saka su, sai kuwa suka yi shiru. "Ameer." Daneen ta faɗa idanunta da take suka sauya a kan Ameer, ban da lugude babu abin da zuciyarta take. "Na shiga 3 ni Hanne.. Me kuma ya faru?" Dada ta faɗa har da dafe ƙirji kamar gaske. "Na san zuwa yanzu kun fahimci abin da ya faru. Yaron nan ya yi mini satar zogale. Ni kuma wallahi ba zan haƙura ba, don haka zuwa na yi a biya ni kuɗin abin da ya tsinkar mini." Habule ya faɗa yana gyara tsayuwarsa. Tun da suka zo wajen kwata-kwata Ameer ya kasa ko da ɗaga idanunsa ne ballantana ya kalli mutanen da ke tsaye a wajen. Shi kaɗai ya san yadda kalaman da ake faɗa suke sukar zuciyarsa. Ya rasa abin da ze yi, ya rasa ya ze yi. Be san cewa mutane da dama ƙiris suke jira a kansu ba sai yanzu, sai da abin nan ya faru. "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Ameer! Yanzu nan sai da ka nuna halinka a waje? Sata da farar ranar nan? Oh jama'a.. Jinin Hadeeza sun shiga 3." Dada ta yi maganar tana tafa hannu. Babu shiri Ameer ya ɗaga idanunsa ya kalli Dada, cike da mamakin maganganun da suke fito wa a bakinta. Cikin sauri kuma sai ya mayar da idanunsa kan Inna-wuro da ta runtse idanunta cikin rashin sanin abin yi. Girgiza kai ya shiga yi tamkar tana kallansa "A'ah Inna, kar ki yarda da abin da suke faɗa, wallahi ban yi masa sata ba. Ɗansa ne ya ce mini in je in tsinka tun da ban samu na siyarwa ba. Inna kar ki yarda, wallahi ban yi masa sata ba Inna." Ya ƙare maganar gwanin ban tausayi. Shi gaba ɗaya abin da mutanen ke masa be dugunzuma masa hankali ba kamar tsoron ka da Innarsa ta yarda da abin da suke faɗa. "Dallah rufe mana baki ɓarawon banza ɓarawon wofi." Wani da ke gefen Habule ya faɗa yana tunkuɗa masa ƙeya. Ya tafi kamar ze kifa kafin ya dawo a kan ƙafafunsa. I zuwa lokacin zuciyarsa ta yi taurin da yake ganin ba ze iya jure wannan cin mutuncin ba. Wani irin zafi zuciyarsa take masa, ji yake kamar ya fasa ihu ko ze ji sauƙin abin da yake ji. Don haka a fusace ya juya ya cakumi wuyan wanda ya tura shi yanzun. Cikin ƙanƙanin lokaci maganar mutane ta soma tashi a wajen, kowa da abin da yake faɗa. Tuni ya ƙwace jikinsa daga hannun Habule. Kamar yadda ya cakumi wuyansa, haka shi ma wancan ɗin ya cakuma, suna shirin soma faɗan ya ji an riƙo hannunsa. Cakk ya dakata, ya ɗaga idanunsa ya sauke a kan fuskar Inna da ta riƙe hannunsa. Ta girgiza masa kai a sanyaye, muryarta ma a sanyaye ta furta "Rabu da shi.. Allah zai saka maka." Ta ƙare maganar tana jan hannunsa. Babu musu ya sake shi, har lokacin yana jin yadda zuciyarsa ke cigaba da wani irin zafi, gefe guda kuma wani rauni ne a cikinta. Ganin da Habule ya yi Inna-wuro ta ja hannun ɗanta ya sanya shi saurin faɗin "Ina za ku je ba tare da kun.." "Daneen ɗakko kuɗi ki ba shi." Maganar Inna-wuron ta katse masa maganar da ya soma. Ya ja ƙwafa yana faɗin "Ah toh." Kusan a tare suka shige gidan su ukun, har lokacin Inna-wuro na riƙe da hannun Ameer. "Don Allah ka yi haƙuri, ka san halin 'ya'yan yanzu.. Ka yi haƙuri amma tabbas zan tsawatar masa, ta yadda ba zai sake marmarin ɗaukar abin wani ba." Maganar Dada kenan, wadda ta sauka a kunnen Daneen lokacin da ta fito daga cikin gida, hannunta ɗauke da kuɗi ta miƙa wa Habule, ba ta jira ya ce komai ba ta koma cikin gidan tana cigaba da tariyar kalaman Dadan. "Babu komai." Habule ya faɗa lokacin da yake ƙirga kuɗin hannunsa. "Ka yi haƙuri." Baffa da tun ɗazun be ce komai ba ya faɗa yana kallan Habulen. Jinjina kai Habule ya yi yana kallan mutanen da suka biyo shi ya ce "Ku wuce mu je." Duk sai suka ɗunguna suka bi bayansa. Dada da Baffa suka bi bayansu da kallo har sai da suka ɓace musu da gani. Ƙwafa Dada ta ja ba tare da ta ce komai ba ta shige cikin gida, babu daɗe wa Baffa ma ya bi bayanta zuwa ciki. A ɗaya ɓangaren kuwa, a sukwane Daneen ta nemi gefen Ameer ta zauna, yana zaune kansa ɗore a kan gwuiwarsa. A hankali ta kai hannunta ta dafa kafaɗarsa, cikin sanyi ta ce "Ɗan'uwa." Runtse idanunsa ya yi kafin ya buɗe, ya ɗago a hankali ya kalli Daneen. Girgiza mata kai ya shiga yi yana jin yadda zuciyarsa ke karyewa. "Adda wallahi ba sata na yi masa ba." Ya ƙare yana riƙo hannunta. Idanunta da suka cika taff da hawaye ta lumshe tana buɗe wa a lokaci guda. Sai ta shiga jinjina kai tana riƙe hannunsa sosai. "Na sani Ameer.. Inna ma ta sani, ka dena damun kanka." "Amma kin ji abin da Dada ta faɗa koh? Tun da nake na taɓa sata a rayuwata ne? Me ya sa ne muke rayuwa a cikin gidan nan Adda? Babu wanda ke sonmu fa sai mu kanmu. Ni ba ɓarawo ba ne Adda. Wallahi ba ɓarawo ba ne ni." Ya ƙare yana fashe wa da kuka. Sai a lokacin kukan da ita kanta Daneen ɗin ke riƙe wa ya fito fili, ta ja Ameer jikinta ta rungume ita ma tana fashe wa da kukan. "Ya isa haka Ameer.. Ya isa haka.." Ta yi ƙarfin halin faɗa. Cigaba da girgiza kai ya yi, don tabbas abin da ya faru ya masa zafi, kukan da yake shi ne kaɗai zai sanyaya masa zuciya. Ita ma Daneen ɗin ba ta hana shi ba, ta bar shi ya yi kukan, dan ta san hakan zai taimaka wajen rage raɗaɗin da yake ji a zuciyarsa. "Ku dena kuka In Sha Allah, Allah zai kawo mana mafita nan ba da daɗewa ba." Inna ta faɗa tana haɗa su su duka ta rungume. Ba ta so ta bar wata alama da zai sa su fahimci ita ma tana cikin damuwar. Sai dai za ta iya cewa abin da take ji cikin zuciyarta ya fi wanda suke ji. Ita kaɗai ta san abin da take ji a duk lokacin da kalmar 'ɓarawo' ta faɗo mata cikin rai. Mummunar kalmar da aka jefi ɗanta da shi. Mummunar kalmar da mutane da dama suka kira ɗanta da shi. Kawai sai ta runtse idanunta tana jin yadda Ameer yake sauke ajiyar zuciya cikin ƙunar rai. Lallai yau ɗin tabbas abin ya taɓa zuciyar Ameer, tun da har yake kuka, duk kuwa da ƙarfin zuciya irin nasa duk da ƙananun shekarunsa. Ranar dai haka suka wuni babu walwala. Cikin sa'a kuma ita ma Dada sai ba ta kula su ba. Ta cigaba da harkokinta daga tsakar gida zuwa cikin ɗaki. Washegari da ta kasance babu makaranta bin Innar suka yi kasuwa. Ba su suka dawo gidan ba sai da yamma. Har kuma zuwa lokacin Ameer be koma daidai ba. Daneen da Inna-wuro ke ta ƙoƙari wajen ganin sun kwashe damuwar da ya ɗora wa kansa. ... "Kin sanar da shi kin amince?" Tambayar da Dada ta jefa mata kenan tun kafin ta ida shigo wa soron gidan. Gaba ɗaya sai ta ji jikinta ya yi sanyi, ta girgiza kai kafin ta ce "Na sanar da shi zan yi shawara, sannan kuma na nemi zaɓin Ubangiji." Inna-wuro ta faɗa a sanyaye, cike da fatan Dadan ta amince da hakan, ko dan kasancewar yanzu ba kamar da ba ne. Tun da yanzu da hankalinta ba kamar da ba. "Toh ki koma ki sanar da shi kin amince.. don wallahi ba shawararki muke nema ba, umarni ne muke ba ki. Ki koma ki sanar da shi kin amince, ko kuma yau ɗin nan wallahi ki ga abin da zan muku cikin gidan nan, babu ruwa na da wasu 'ya'ya da kika tara wallahi ci miki mutunci zan yi." Dada da ke dab da soro ta faɗa tana maka mata harara. Girgiza kai Inna-wuro ta yi ta ce a sanyaye "Dada.." "Ka saka baki Malam.. Wallahi ba kirki ne da ni ba, ka da ki ɓarar mana da wannan damar." Dada ta faɗa tana kallan Baffa da ke zaune a tsakar gidan. Ɗaga idanunsa ya yi ya kalli Inna-wuro ya ce "Kin ga maza koma ki sanar da shi kin amince. Mun riga mun zaɓa miki shi, babu buƙatar wani tunani kuma." Duk da yadda zuciyarta ke bugawa hakan be hana ta juya wa ba, ƙafarta har wani rawa take lokacin da ta bi umarnin mahaifinta wajen koma wa wajen mutumin. Har ya shiga cikin motar ya tayar da ita, ya hangi Inna-wuro da ta fito. Sai ya kashe motar cike da mamakin abin da ya fito da ita bayan sun yi sallama. Kai tsaye inda take tsaye ya nufa yana kallan ta. "Ina so mu yi wata magana." Inna-wuro ta faɗa jikinta a matuƙar sanyaye. Ita kam ta rasa wannan wace kalar rayuwa ce. Ta rasa mafita a rayuwarta. Tana so ta inganta rayuwar 'ya'yanta, sai dai da alama Dada tana so ta yi mata cikas. Maimakon a ce yanzu haka maganar auren 'yarta ake, amma wai nata ake. Ba ta san dalilin Dada na saka mata ido ba. Ba ta san me ye ƙudurin Dada a kanta na son sai ta yi aure ba. "Ikon Allah! Ina sauraron ki." Alhaji Abubakar ya faɗa yana gyara tsayuwarsa. Sauke numfashi Inna-wuro ta yi tana tunanin ta inda za ta fara. Sai dai kawai ta yi ƙundunbala wajen soma faɗin "Ina da 'ya'ya guda biyu.. Ina neman alfarmar idan dai har za ka aure ni ka bar ni na taho da su. Ni ba zan ɗora maka komai ba. Ni zan din ga musu komai da ake buƙata, ni dai buri na kawai ka amince na zo da su gidanka." Cikin matuƙar farin ciki ya ce "Kina nufin idan dai har na amince da hakan kin amince za ki aure ni?" Runtse idanunta Inna-wuro ta yi, kafin ta shiga jinjina kanta a sanyaye. Murmushi ya yi, har cikin ransa yana jin daɗi. Ya buɗe baki a nutse ya soma faɗin "Ni da ba ki guje ni ba duk da ina da 'ya'ya, kika kuma amince za ki kula da su, mai zai hana ni ma na kula da naki? Idan dai har kin amince da aure na, ni mai iya haɗa 'ya'yana da naki ne na kula da su In Sha Allah." Wani irin sanyi ta ji yana ratsa zuciyarta. Farin cikin da ta daɗe ba ta tsinci kanta a ciki ba yau ta ji shi. Har ba ta san lokacin da wani irin sassanyan murmushi ya suɓuce a kan fuskarta ba. A kan laɓɓanta ta furta "Alhamdulillah." Ta buɗe idanunta a nutse ta kalli Alhaji Abubakar ta ce muryarta na bayyanar da farin cikin da take ciki "Na amince. Allah Ya tabbatar da abin da yake alkhairi a gare mu." Ta ƙare maganar tana lumshe idanunta, a ranta tana fata hakan ya zame mata alkhairi, kamar yadda take fata. Ko ma wane irin hali ne da Alhaji Abubakar ɗin, idan dai har tana tare da 'ya'yanta za ta ji sauƙi. Ta kuma san In Sha Allah Allah zai taimake ta, ya taimaka mata wajen kula da rayuwar 'ya'yanta. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 08 Kusan a tare suka sauko daga cikin motar. Dukkansu fuskarsu ɗauke da annurin da ke bayyana farin cikin da suke ciki. Hidaya ce, sanye cikin doguwar rigar da ta matuƙar amsar jikinta, ta kuma haska kyakkyawar farar fuskarta mai kama da Tareeq. Gefen ta wata budurwar ce, wadda a kallan farko za ka iya kiran su da sa'anni. Ko ma kai tsaye ka kira Hidaya da babba saboda yadda ta fi Sultanah cika ido. Sai dai a zahiri Sultanah ta ba wa Hidaya kusan shekaru biyu ne, wanda a ido ba za ka taɓa faɗa ba idan dai har ba faɗa maka aka yi ba. Uwa uwa kuma yadda suke abubuwan su tare, suke komai tare, kai tsaye idan ba ka kira su da tagwaye ba, za ka kira su da sa'annin da suka fito daga gida ɗaya. "Na yi matuƙar kewar gida." Sultanah ta faɗa tana murmushi. Ita ma Hidaya murmushin ta yi kafin ta ce "Ki bari kawai Sisi, shi kansa gidan ya yi kewar ki." Ta ƙare dimple ɗin da ke gefen kumatunta na lotsawa. Daidai lokacin da wata babbar mace sanye cikin wata hamshaƙiyar atamfa ɗinkin bubu ta fito daga cikin motar da su Hidaya suka fito daga cikin ta. Kunnen ta kare da waya tana amsa wa. Idanunta saye cikin glass, hannunta kuma ɗauke da jakar da ke ɗore a tsintsiyar hannunta. Ba tare da ta dubi inda 'yan matan ke tsaye ba, kai tsaye ta wuce sashenta tana cigaba da amsa wayar. "Sultanah bari na je, ki fara zuwa ki huta yanzun dai." Hidaya ta faɗa tana kallan Sultanah. Girgiza kai ta yi kafin ta ce "A'ah ni kam.. Sai na fara zuwa na gaishe da Dadaji, tun da dai yanzu haka Abeey ba ya cikin gidan nan." Dariya Hidaya ta yi kana ta ce "Toh shi kenan mu je." Daga haka suka maida akalarsu zuwa sashen kakar tasu. Daidai lokacin da Tareeq da Abokinsa Abdoul suke dab da ƙaraso wa wajen. Ƙirjin Sultanah ya buga, ta runtse idanunta tana ambaton sunan Allah. Daidai lokacin da suka ƙaraso. "Yah Tareeq." Hidaya ta faɗa kyakkyawan murmushin nan da ke ƙara wa fuskarta kyau kamar koyaushe yana kan fuskarta. "Da alama shi kaɗai kika gani?" Abdoul ya faɗa yana kallan Hidaya, lokaci ɗaya yana ɗage girarsa. Dariya kawai ta yi tana gaishe da Abdoul ɗin. "Yah Tareeq barka da wannan lokacin." Sultanah ta faɗa tana jin kewar yayan nata. "Barka sweetsis.. Kin dawo lafiya?" Jinjina kai ta yi kafin ta ce "Eh, na yi kewar ka sosai." Ta faɗa kawai, dan ta so ba a gaban abokinsa ba ne, da hugging nasa za ta yi. Sassanyan murmushi ne ya tashi a kan fuskarsa kana ya amsa da "Missed you more Sulty." Sai a lokacin sannan ta maida duban ta kan Abdoul ta gaida shi. Tun da ta masa kallo ɗaya ba ta sake bari ta kalle shi ba. Don kwata-kwata ba ta iya jure kallan nasa. Daga haka ba su ƙara mintuna masu yawa ba, Sultanah da Hidaya suka yi sashen Dadaji, ya yin da Tareeq da Abdoul suka wuce. Tun kafin su ƙarasa shiga ta tafi a guje tana faɗin "Dadaji tawa." Ta faɗa tana rungume tsohuwar da ke zaune a kan lallausan carpet ɗin da ke malale a tsakiyar ɗakin. "Oh ni ɗiyar babana, yau ga Sultanah na neman karya ni." Ta ƙare tana yamutsa fuska. "Kai Dada tsananin kewar ki da na yi ne fa." Sultanah ta ƙare tana turo baki. "Eh dole ai ki yi kewa ta mana.. Ke ni ba wannan ba, tun da dai yanzu Allah Ya dawo mini da ke lafiya, maza tashi ki shiga kitchen." "Kai Dadaji daga dawowa ta?" Ta ƙare tana waro ido. Taɓe baki Dadaji ta yi ba tare da ta ce komai ba. Sultanah ta sake faɗin "Ga Hidaya nan da babu gajiyar komai a tare da ita." "Ni! Raba ni da wannan malalaciyar." Dadaji ta ƙare tana auna wa Hidaya harara. Dariya Hidaya ta yi tana faɗin "Toh shi kenan ki bari Sulty ta shiga tsakaninmu. Ni dai babu ruwa na." Ta ƙare tana gyara zamanta. Dariya Sultanah har ma da Dadajin suka yi jin abin da Hidaya ta faɗa. ... A ɗaya ɓangaren kuwa cikin ƙanƙanin lokaci aka tsaida ranar auren Inna-wuro da Alhaji Abubakar. Babu daɗewa Inna-wuro ta sanar da su Daneen canjin da suke ƙoƙarin samu, na barin ƙauyen gaba ɗaya zuwa can wani waje su rayu. Farin ciki kamar su taka rawa haka suka ji. Ko babu komai za su rabu da Dada. Matar da zuwa yanzun suka sake fahimtar kwata-kwata ba ta ƙaunar su, ba ta son duk wani abu da ya shafe su. Musamman ma dai Ameer da tun da abin nan ya faru ya ɗauki gaba da Dadan. Sai da Inna-wuro ta fahimci abin da ke faruwa sannan ta tsawatar masa. Shi ne ya sassauta saboda gudun ɓacin ran Innar tasu. A ƙofar gidan ya yi parking na matarsa, kamar kodayaushe sanye cikin shadda ɗinkin babbar riga. Bai kai minti 3 da tsayuwa ba, Baffa ya fito daga cikin gidan. "Ƙaraso ciki mana, ai yanzu ka tashi daga ɓako ka zama ɗan gida. Kwana nawa ne ya rage?" Baffa ya ƙare maganar yana murmushi. Shi ma murmushin Alhaji Abubakar ya yi kafin ya gaishe da Baffan cikin girmamawa. Ya amsa yana yin gaba don ba wa Alhaji Abubakar damar shiga gidan. Babu musu ya bi bayansa, cikin ransa yana saƙa lallai ko ma mene ne dalilin kiran nan nasa yana da matuƙar muhimmanci, tun da har aka umarce shi da shiga cikin gidan. A soro suka dakata, Baffa ya nuna masa wata tabarma ya ce "Bismillah." Babu musu Alhaji Abubakar ya tuɓe takalmansa, ya nemi waje ya zauna bayan ya tattare babbar rigarsa. Baffa da takaimaimai bai san dalilin kiransa ba ya shiga gidan don kiran Dada. Tun kafin ya ƙaraso ta ce "Mu je, ai na shirya ma." Ta faɗa tana gyara zaman gyalen da ta yafa a kanta, sai dai gaba ɗaya ta kwashe shi zuwa kan kafaɗarta, har rigar jikinta ana gani. Babu musu ya juya, ya bi bayanta, don har ta riga shi fita. Da mamaki shimfiɗe a kan fuskar Alhaji Abubakar yake kallan Dada, ƙwarai da gaske ya yi mamakin ganin ita ke son magana da shi. Duk da tun bayan da ya ya soma zuwa wajen Inna-wuro ya soma fahimtar halayenta. Amma duk da haka bai yi ƙasa a gwuiwa ba wajen gaishe ta cikin girmamawa. "A'ah lafiya ƙalau Alhamdulillahi. Wallahi mun gode Allah." Ta faɗa tana gyara zama. Kafin ya ce komai ta cigaba da faɗin "Dama abin da ya sa na kira ka.. Ba wata doguwar magana ba ce. Magana ce a kan 'ya'yan Inna-wuro da na ji ka ce za ka riƙe. Toh ka san yanzu yadda rayuwar nan ta sauya, 'yan gulma sun yi yawa. Sai a dinga gulmar ko ma dai mata biyu ka aura ne ba ɗaya ba. Toh saboda gudun hakan ya sa na ce bari na faɗa maka.. Idan har niyyar kula da su ka yi, ni ɗin nan kakarsu ce, zan iya kula da su fiye da yadda kake tunani. Idan ya so duk wata sai ka dinga yo aiken abin da za a kula da su. Ai hakan ba wani abu ba ne." Ta ƙare tana dariya gami da gyara zama. Shiru Alhaji Abubakar ya yi na tsawon wasu sakanni yana nazarin maganganun Dadar. Kafin can ya ce, bayan ya sauke ajiyar zuciya "Babu komai Baba. Ni ma ina da 'yan matan har guda biyu, shi ya sa ma nake so na haɗa su waje ɗaya. Hakan ba abin damuwa ba ne. Zan kula da su idan babu damuwa." "Toh! Ikon Allah!" Dada ta faɗa a wani sheƙe tana kallan Alhaji Abubakar. Ji take kamar ta tashi ta rufe shi ta tsinannan duka ko ta ji daɗi. Sai dai kafin ta ida tsara abin da ke cikin ranta ta jiyo muryarsa yana faɗin "Ga wannan.. Na gode sosai Allah Ya saka da alkhairi." Ya yi maganar bayan ya ajje kuɗi a gaban Dadan. Don ba tun yanzu ba ya fuskance ta, ya kuma fahimci me ye damuwarta. Sai kuwa ta fashe da murmushi tana riƙo kuɗin lokaci ɗaya tana furta "Duka dai? Kai dai ba ka gajiya." Ta ƙare tana murmushi. Shi dai be sake cewa komai ba ya miƙe ya saka takalmansa. Ya yi sallama da Baffa ya fice daga gidan, a ransa yana cigaba da bitar kalaman Dada. Babu jimawa lokacin da aka saka na biki ya zo. Ranar wata juma'a aka ɗaura auren Inna-wuro da Alhaji Abubakar. Tuni dama Inna-wuro ta ajiye sana'ar nan tata. Musamman da ya kasance a lokacin tana da kuɗin da za su yi amfani da shi wajen harkokin yau da kullum. Ga kuma Alhaji Abubakar da shi ma ba ya barin ta haka, duk da yadda take nuna ba ta so. Amma sai ya nuna mata tamkar yadda ya yi alƙawarin kula da 'ya'yanta to zai fara ne tun yanzu. Ita dai Inna-wuro sai dai ta runtse idanunta tana gode wa Sarki Allah buwaya gagara misali, wanda ya ba ta Alhaji Abubakar. Mutumin da tun kafin a yi nisa duk wasu kyawawan halayensa suka bayyana, mutumin da ya nuna ƙaunar 'ya'yanta, ya nuna zai kula da su duk da kasancewar ba shi ya haife su ba. Ita kuwa me za ta yi idan ba ta cigaba da gode wa Allah ba?. Tana sanye cikin atamfa riga da zani, da mayafi sabbi gall. Ta yi kyau matuƙa, idan dai har ba sani ka yi ba, ba za ka ce ita ce ta ajje Daneen da Ameer ba. Sabuwar wayarta da Alhaji Abubakar ya ba ta ita ce ta shiga ƙara. Ameer da ya fi kusa da wayar ya ɗauka ya miƙa mata yana faɗin "Inna ana kiran ki." Miƙa hannu ta yi tana faɗin "Miƙo mini." Babu musu Ameer ya miƙa mata, ta karɓa idanunta a kan fuskar wayar don ganin mai kiran. "Inna in haɗa har da wannan?" Daneen da ke haɗa kayanta da na Ameer ta faɗa tana kallan Innar. Ɗaga kai Innar ta yi ta kalli kayan kafin ta ce "Eh ki haɗa da shi, haɗa da wancan ma." Ta ƙarasa maganar tana mai nuni da wasu kaya cikin kayan da Daneen ɗin ke duba wa. Sai ta ɗauka kuwa ta haɗa cikin waɗanda take haɗa wa. Ya yin da ita kuma Inna-wuro ta ɗaga kiran da ake mata. "Amarya ba kya laifi." Daga can ɓangaren Alhaji Abubakar ya faɗa yana murmushi. Duk sai ta ji kunya ta kama ta. Ta yi murmushi tana gaida shi. Amsa wa ya yi, kafin ya ɗora da "Na san dai kina cikin gida yanzu haka. Toh idan babu damuwa ki leƙo akwai wata muhimmiyar magana da za mu yi." Haka nan kawai ta ji faɗuwar gaba ta ziyarce ta, sai dai ta basar kafin ta ce "Toh ga ni nan." Daga haka ta katse wayar. Ta ɗan yi shiru na wasu sakanni kana ta maida duban ta kan Ameer ta ce "Ameer ka tashi ka taya Addarka shirya kayan nan, ka bar ta tun ɗazun tana yi ita ɗaya." Miƙe wa ya yi yana faɗin "Toh Inna." "Kafin na dawo kun gama uhmm?" "Toh Inna sai kin dawo." Daneen ta faɗa har lokacin idanunta na kan kayan da take shirya wa. Kamar yadda ya faɗa ɗin kuwa, yana ƙofar gidan, ganin ta da ya yi ya sanya shi faɗaɗa murmushin kan fuskarsa. Ya ƙaraso yana sake zolayarta. Ita dai sai babbasarwa take yi dan har ga Allah kunya yake ba ta. "Amm.." ya faɗa bayan ya yi gyaran murya. Nan ma sai da ta ji gabanta ya tsinke ya faɗi. Ta yi saurin runtse idanunta tana ambatar sunan Allah. "Wato Fatima tafiya ce ta taso mini bagatatan, yau yau ɗin nan zuwa Abuja ya taso mini. Yanzu ma haka ni ake jira mu wuce. Ban san da wane ido zan kalle ki in sanar da ke yau ɗin za mu wuce Abuja ne tare da ke kawai ba. Idan ya so da mun tashi dawo wa, kai tsaye nan za mu dawo mu ɗauki 'ya'yanmu mu wuce da su gida." Cikin lokaci ƙanƙani zuciyarta ta cigaba da bugawa fiye da zato. Jin da ya yi ba ta ce komai ba ne ya sanya shi faɗin "Kar ki damu, kwata-kwata ba za mu wuce sati ɗaya a can ɗin ba. Na kuma yi miki alƙawarin daga can ɗin nan za mu wuto babu wani tsaye-tsaye." Ya ƙare a tausashe duk dan ta fahimce shi. Duk da yadda ya yi maganar tabbas ta ji ta yadda da abin da yake faɗa, sai dai ba ta san dalilin da ya sa zuciyarta ta ƙi na'am da hakan ba. Sam hankalinta ya ƙi kwanciya, ji take kamar ba za ta iya barin 'ya'yanta na tsawon sati guda cikin gidan nan bayan ba ta cikinsa ba. Sam ta kasa gane dalilin hakan. Ga kuma faɗuwar gaban da ta ƙi barin ta har zuwa yanzun. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 09 Jin da ya yi ta yi shiru na fiye da tsawon minti ɗaya, ya sanya shi gyara tsayuwarsa ya ce a tausashe "Ki yi haƙuri, kar ki ce ban yi miki adalci ba. Ban san wannan tafiyar za ta taso ba, ina mai sake ba ki haƙuri." Kalmar haƙurin da yake ta maimaitawa tabbas ta yi matuƙar tasiri a zuciyarta, sai dai duk da haka, ba ta dena jin bugun zuciyar ba. Ta yi ƙarfin halin buɗe baki da ƙyar ta ce "Babu komai, Allah Ya sa haka ne mafi alkhairi." Sai a lokacin ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce "Ameen, na gode." Shiru ne ya wanzu a wajen na tsawon mintuna, zuwa can Alhaji Abubakar ya ce "Bari na jira ki sai ki shirya koh? Kafin nan mun yi magana da Baffa." Da kai ta amsa masa maganar, ba ta sake cewa komai ba ta faɗa cikin gidan tana tunanin ta inda za ta fara sanar wa da 'ya'yanta tafiyar sati da za ta yi ta bar su cikin gidan. Kamar yadda ta umarci Ameer kuwa, yanzu haka tare da Daneen ta same su suna shirya kayansu cikin jaka. Ya yin da ragowar da ba za su ɗauka ba suna ninkewa suna mayar da su wajen kayansu. Ƙarasawa cikin ɗakin ta yi jikinta a matuƙar sanyaye ta nemi waje ta zauna tana cigaba da kallan su. "Inna mun gana haɗawa fa." Ameer ya faɗa yana murmushi. Ji yake tamkar ya yi ta tsalle saboda farin ciki, don zai iya cewa kaff cikin su ya fi su farin ciki da barin ƙauyen nan da za su yi. Murmushin yaƙe Inna-wuro ta yi kafin ta ce "Ku zo ku zauna ku ji." Kusan a tare Ameer da Daneen suka ɗaga ido suka kalli Innar tasu jin yadda maganarta ta sauya cikin ƙanƙanin lokaci. Wannan ɗin ba sabon abu ba ne a wajen su, fahimtar halin da ɗaya daga cikin su ke ciki ko da ta magana ne kuwa, ba tare da ya sanar da su ba. Ajiye Hijab ɗin da ke hannunta Daneen ta yi, ta ƙarasa gaban Innar tasu da sauri ta zauna, ya yin da Ameer ma ya zauna a gefen ta, gaba ɗayan su jiki a sanyaye. "Ku buɗe kunne da kyau ku saurare ni, ba don na so ba sai don haka Allah Ya tsara, zan bar ku cikin gidan nan na tsawon sati guda. Kai tsaye nan za mu dawo mu ɗauke ku mu wuce da ku inda za mu zauna. Kar ku damu, kar ku ɗaga hankalinku." Ta ƙare maganar a nutse, duk da ita ma ba ta da nutsuwar zuciya, sai don kawai ta ba wa 'ya'yan nata ƙwarin gwuiwa. "Inna.." Shi ne abin da Ameer ya yi ƙarfin halin faɗi yana cigaba da kallan Innar. Wata ƙwalla da ta ji ta taho mata ita ce ta sanya ta saurin saukar da kanta ƙasa, wajen sakanni 30 kafin ta ɗago tana kallan su su duka. Ta kamo hannayensu ta sanya cikin nata. "Ba mu taɓa rabuwa ba tun da muke, sai ga shi yau ɗin za mu rabu na tsahon kwana bakwai. Ina so na yi amfani da wannan damar wajen neman alfarmar yin haƙuri da zama da Dada cikin gidan nan bayan ba na cikinsa. Akwai kuɗi a cikin jakata, duk abin da kuke buƙata ku yi amfani da shi. Daneen ga Ameer nan, ki kula mini da shi har na dawo. Ameer ga Daneen nan ka kula mini da ita har na dawo. Allah Ya yi muku albarka, Ya albarkaci rayuwarku, Ya raya mini ku." I zuwa lokacin gaba ɗaya jikinsu ya yi sanyin da suka kasa amsa addu'ar Innar. Kowanne da abin da yake saƙa wa a cikin ransa. "Kar ku mini kuka." Inna ta faɗa tana girgiza kai lokaci ɗaya tana kallan su duk da ita ma nata idanun cike suke da ƙwalla. "Toh maza ki fito Hajjaju ta ɗaka, mijinki na jiran ki. Ko kuwa ƙaramar yarinya ce ke da sai an zo an rarrashe ki kafin ki fito." Ta jiyo muryar Dada na faɗin hakan. Hannu ta kai ta goge fuskarta da zuwa lokacin hawaye sun fara sauka, ta yi saurin ɗauke su don kar ta sake karyar wa da 'ya'yanta zuciya. "Toh gani nan." Ta ɗaga murya wajen faɗar hakan, don Dadar ta ji. A hankali ta miƙe har lokacin hannunta na cikin na 'ya'yanta da suka kasa furta komai. "Ku yi haƙuri kar da ku karya mini zuciya. Ba na tafi kenan ba, nan da sati ɗaya zan dawo in ɗauke ku da yardar Allah." "Inna don Allah kar ki tafi." Daneen ta faɗa da muryarta da ke rawa, lokaci ɗaya tana rungume Innar. Kukan da Inna ta ji ta fashe da shi shi ne ya sanya ta runtse idanunta, ta saka hannu ta ja Ameer jikinta, ta haɗa su ta rungume waje ɗaya. Sun kai wajen minti biyu a haka kafin suka saki juna. Inna-wuro ta saka hannu ta ɗauki jakar kayanta. Bin bayanta suka yi har zuwa tsakar gidan. Kafin su kai ga fita daga cikin gidan wata da take kusa da Dada ta ce "Wai dama ba a nan za ta zauna ba." "A'ah nan cikin Kano ne fa za ta zauna." In ji Dada tana gyara zama lokacin da Inna-wuro ta nemi waje ta zauna. Ba wata addu'a daga Dadar har Baffan suka yi mata ba, haka dai ta ja ƙafafunta suka fice daga gidan. A sanyaye su Daneen suka gaishe da Alhaji Abubakar, ya amsa cikin sakin fuska kafin ya karɓi jakar hannun Inna-wuro ya saka cikin mota. "A kula, Allah Ya tsare mini ku, sai na dawo." Inna ta faɗa tana kallan su. "Allah Ya tsare Inna." Suka haɗa baki wajen faɗar hakan. Ta lumshe idanunta tana juya wa a hankali ta soma tafiya zuwa wajen motar. Dab da za ta ƙarasa, ta sake juya wa ta kalli 'ya'yan nata. Sai ta juya da sauri ta shige cikin motar, saboda yadda ta ji a yanzun ba za ta iya jurewa ba, zuciyarta ta gama karyewa. Ƙarasawa Alhaji Abubakar ya yi ya shiga motar, bayan wasu sakanni ya tashi motar. Ƙasa da kanta Inna-wuro ta yi don tabbas idan ta cigaba da kallan 'ya'yanta za ta iya bijire wa umarnin mijinta ta ƙi binsa ta cigaba da zama da su. Don haka har ya soma tafiya ba ta ɗaga kanta ba. Daneen da Ameer, suka cigaba da bin motar da kallo, har zuwa lokacin da ta ɓace wa ganin su. Hannun Ameer Daneen ta kama ta riƙe sosai tana runtse idanunta. Wani irin bugu zuciyarta take yi. A hankali kuma sai ta soma takawa zuwa cikin gidan, ya yin da Ameer ya rufa mata baya. Bin su da kallo Dada ta yi lokacin da ta ga shigowar su cikin gidan. Ta taɓe baki tana jinjina kanta. Ita dama burinta bai wuce a bar mata 'ya'yan Inna-wuro a wajenta ba, ko babu komai ta san za su dinga zuwa a kai a kai ana ajiye mata kuɗi da sauran su. Amma idan suka tafi da 'ya'yan suka manta da ita da wa ta ɓare kenan? Bar mata su da aka yi yana nufin samun wata mafitar kafin su dawo, wadda za ta hana su tafiya da su duk da sun yi niyya. Kai tsaye ɗakinsu suka nufa suka yi shiru kowa da abin da yake saƙa wa. Ranar haka suka wuni kamar masu zaman makoki, babu wanda ke cewa da ɗan'uwansa ko uffan ne. Washegari jiki a sanyaye duk suka farka, sai suke jin su wasu daban, ba su taɓa farkawa ba su ga Innarsu ba sai a yau ɗin. Ba su taɓa rabuwa da Innarsu ba sai a wannan karon. Suna ta farin ciki abin farin ciki ya same su, ashe ba su sani ba kafin samuwar farin cikin sai sun soma rayuwar kaɗaici. Da yake ranar babu makaranta ya sanya suna gida, tun safe bayan sun fito daga ɗaki ba su koma ba. Shi Ameer yana can aiken da Dada ke ta masa, da kuma wasu ayyukan. Ya yin da Daneen ke yi wa Dada girki da sauran ayyukan cikin gida. .. "Me kake yi haka ne Ameer?" Daneen ta faɗa tana kallan Ameer da ke cusa kayan sakawarsa cikin jakar islamiyya. Sai da ya ƙarasa cusa wadda ya ɗakko sannan ya ɗaga ido ya kalle ta ya ce "Inna zan bi." Da mamaki matuƙa Daneen ke kallansa idanunta a waje. Cike da mamakin dai ta ce "Inna kuma Ameer? Ka san inda ta je ne?" Jinjina kai ya yi kana ya ce "Ehh, jiya na ji Dada tana faɗa wa ƙawarta wai sunan garin Kano. Ko ban san gidan ba, na san muna zuwa muka tambayi Mai gari gidan Alhaji Abubakar ya sani. Tunda kin ga mu ma a garin nan gidan waye Mai gari bai sani ba?" "Ni yi mini shiru dallah.. Tashi ka tafi toh." Daneen ta faɗa tana shirin miƙe wa. Maida ta ya yi ta zauna ta hanyar riƙo hannunta. Ya shiga girgiza kai yana faɗin "Kar ki mini haka Addata. Idan har ke ba ki amince mini ba waye zai amince mini? Don Allah ki duba abin da na faɗa ki bari mu tafi. Ni ba zan iya cigaba da zama da Dada ba wallahi. Ko ba ki amince na bar garin nan ba, toh zan bar cikin gidan nan in tafi ko ma ina ne." "Wai Ameer ba ka da hankali?" Daneen ta faɗa tana kallan sa a tsorace. "Toh ki yarda da abin da na faɗa." "Ba zan yarda ba." Ta faɗa tana jefa masa harara. "Don Allah Addaneen tawa ni kaɗai. Don Allah.." Ya ƙare a marairaice. Sai a lokacin sannan ta sake juyawa ta kalle shi sosai ta ce a hankali kamar me raɗa. "Ameer wai da gaske kake?" Jinjina kai ya shiga yi lokaci ɗaya yana furta "Wallahi da gaske Adda. Ji nake kamar ana azalzalata da in bar gidan nan, ki taimaka ki amince mu bi Inna garin da ta je." Shiru Daneen ta yi na tsawon wasu mintuna. Rashin yawan tazarar shekarun da ke tsakaninta da Ameer ya sanya wayonsu kusan ɗaya ne. Wani lokacin ma har ya fita wayo. Don idan ya yi wani abun sai ka ɗauka shi ne babba, sai kuma wani lokacin ko ba a faɗa maka ba za ka fahimci Daneen ce babba. "Amma idan Inna ta yi faɗa fa? Tun da ka ga ta ce nan da sati ɗaya za ta zo ta ɗauke mu." "Ba za ta yi ba Adda, ba za ta yi ba. Shi ma kuma sabon Abban ai yana da mutunci. Sai mu ce zuwa muka yi mu gaishe su." Shiru Daneen ta yi na tsawon wasu mintuna kafin ta shiga jinjina kai ta ce "Toh." Ta ƙare tana ajje numfashi. "Yawwah Addata." Ameer ya faɗa yana murmushi. Cikin zuciyarsa yana jin wani shahararren farin ciki na kama shi. Da gaske har cikin ransa ji yake tamkar ana azalzalarsa da barin gidan. Kuma da gaske yadda ya faɗa ɗin tabbas da Addar tasa ba ta amince da bin Innarsu ba, yau ba zai kwana cikin gida ɗaya da Dada ba. Shi da kansa ya tashi ya ɗauki jakar islamiyyar Daneen ya shiga saka mata kayan sakawarta ciki. Ya samu dama da yawa kuwa sun shiga saboda yadda yake cusa su don ma kar a gane meye a ciki. Sai da suka gama tsaff, kafin ya miƙe ya ce "Adda riƙe jakarki mu tafi." Babu musu ta karɓa ta rataya ta cikin hijabin makarantar islamiyya da ta saka. Shi ma ya rataya tasa jakar saman uniform ɗin islamiyyar. Ba tare da tunanin komai ba suka fito daga cikin ɗakin. Dada na zaune tana jin Radio a kan tabarma, ya yin da Baffa ke mata fifita yana daga gefen ta. "Dada, Baffa mun tafi." Daneen ta faɗa, don tana da tabbacin idan ba ta faɗa ba Ameer ba zai faɗa ba. Ɗaga idanunta Dada ta yi ta kalle su, Radion da take ji ya sa ba ta iya tantance iya Daneen ce kaɗai ta mata magana ba. Tsaki ta ja kafin ta soma faɗin "Ni fa makarantar ma na gaji da ganin ku kuna zuwan ta wallahi. Haba." Ta ƙare yanzu kuma tana sakin ƙwafa. "Kin ga ƙyale su su tafi, kar shirin nan ya wuce ki. Idan kin gama ji in ya so duk hukuncin da za ki yanke sai ki yanke kafin su dawo." Baffa da ke cigaba da firfitarsa ya faɗa yana kallan ta. Shiru ta yi na tsawon wasu sakanni kafin cikin na'am da zancen nasa ta ce "Haka ne kuma.. Ku tashi ku tafi." Tun kafin ta ida faɗa har Ameer ya miƙe, kafin ka ce mene wannan ya fice daga cikin gidan. Ta ja ƙwafa tana cije gefen leɓenta, a ranta tana saƙa yadda za ta yi maganin yaron cikin ƙanƙanin lokaci. "Kin gani ko Adda? Kin ga abin da nake faɗa miki koh? Kin ji fa wai makarantar ma hana mu zuwa za ta yi, toh me ya sa?" Ya ƙare tambayar yana kallan Daneen da ta sauke ajiyar zuciya saboda ganin da ta yi Dada ba ta gane kaya ne a cikin jakunkunansu ba. Jinjina kai ta yi ba tare da ta ce komai ba. Cigaba da tafiya suka yi, sai da suka yi tafiya mai nisa kafin suka isa wani titi. A nan suka samu motar da za ta fitar da su inda za su samu motar da za ta kai su Kano. Da kuɗin da Inna ta ba su suka yi amfani wajen biyan mai motar kuɗinsa lokacin da ya sauke su. Sai suka sake tarar wata motar wadda ita ma dai ba Kanon direct za ta wuce ba. Don haka bayan ta sauke su a nan suka yi tambaya suka samu motar da za ta wuce Kano. Cikin matuƙar farin ciki suka hau motar. Motar da ba ta kai ga cika ba, don haka aka tsaya ana jiran wasu passengers ɗin kafin motar ta tashi. "Adda yunwa nake ji." Ameer ya faɗa yana ɓata rai. Hannu ta saka ta karɓi jakar hannunsa, ta ce tana kallan waje "Ka ga wata mai siyar da awara can, je ka siya ka ci." Ta faɗa tana zaro kuɗi a jakar Inna ta miƙa masa. Hannu ya saka ya karɓa yana sauka daga motar, kai tsaye wajen mai awarar ya wuce. Ta bi shi da kallo tana lumshe idanunta, daidai lokacin da bugun da numfashinta ke yi ya cigaba da fita a gurguje kamar wadda ta yi tsere. Bayan wasu mintuna sai ga shi ya dawo. Yana dawowa kuma, motar na gama cika. Don haka bai daɗe da zama ba, motar ta tashi aka soma tafiya. .. "Maza maza mun zo tasha. Ina na Kano su sauko." Abin da kwandastan motar ke ta faɗa kenan lokacin da yake a waje, hannunsa ɗore a kan motar yana ɗan bubbugawa. Kallan juna Daneen da Ameer suka yi, kafin a sukwane suka sakko daga cikin motar. Dama tuni sun ba wa kwandastan kuɗinsa, don haka sai suka soma taka wa suna rarraba idanunsu a inda suke. Daneen ta haɗiye wani busshashshen yawu da ya haɗu cikin bakinta da ƙyar zuwa maƙogwaronta. Ta kalli dogon titin da suke kai, wanda kwata-kwata bai yi mata kama da titin ƙauyen su ba. Ita kwata-kwata ma ba ta ganin ƙarshensa, kai ba ma ƙarshensa ba, wajaje take gani duk inda ta juya, maimakon ta gan su a haɗe kamar yadda nasu gidajen suke. Sai dai kwata-kwata ma ita ba ta hangi wani gida ba, kenan ina ne gidan mai gari? Shi dai Ameer ban da sake rungume jakarsa babu abin da yake yi, lokaci ɗaya kuma yana bin garin da duhu ke sake mamaye shi da kallo. A karo na barkatai suka sake kallan juna, idanun kowannensu ya yi tsilli-tsilli, ya raina fata, gaba ɗayansu kuma da abin da suke saƙa wa a cikin ransu. Sai dai abin da ya fi yawo a zuciyar kowannen su shi ne 'Shin ina ne nan ɗin suka kawo kansu?' *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 10 Idanunta da suka yi rau-rau ta ɗaga ta kalli Ameer ta ce jikinta a matuƙar sanyaye "Na shiga uku Ameer, ina ne nan?" Cikin rashin sanin abin yi Ameer ya girgiza kai kafin ya ce "Ni ma ban sani ba Adda." Ya faɗa yana sake maida kansa inda suke. Duk da yadda take jin tsoro na sake shigar ta, hakan bai hana ta kallan wani mutum da ke gefen su ba. Cikin sanyin murya ta gaida shi, ya amsa yana kallan yanayin shigarta. "Don Allah gidan Mai gari muke nema." Ta yi ƙundunbalar faɗin hakan, cike da fatan su samu abin da suke so. "Toh ikon Allah! Mai gari ko Mai Unguwa?" Ya tambaya yana kallan ta. Shiru Daneen ta yi tana tunanin abin da ya kamata ta ce, sai dai kafin ta ida tunanin ta tsinto muryar Ameer ya ce "Eh shi." Ya yi maganar yana jinjina kai kamar ƙadangare, lokaci ɗaya kuma yana sake rungume jakarsa a hammata. "Toh da yake dai babu nisa daga nan, ku biyo ni na nuna muku, idan ya so sai na wuce inda zan je." Cikin matuƙar farin ciki suka shiga yi masa godiya, a ransu duka ji suke tamkar su taka rawa. Bin bayan nasa kuwa suka yi kamar yadda ya faɗa, suka soma tafiya. Duk inda suka gifta sai sun bi wajen da kallo. "Ai dama na faɗa miki Adda, yanzu ba ga shi ba har mun samu gidan." Ameer ya faɗa farin cikin da yake ji na bayyana a kan fuskarsa da kuma muryarsa. Ita ma murmushin ta yi kana ta ce "Ai kuwa dai. Allah har na ƙagu na yi ido biyu da Innarmu." Ta yi maganar daidai lokacin da mutumin ya juyo ya kalle su, sai da ya soma nuna musu wani gida da ke ɗan nesa kaɗan da inda suke kafin ya ce "Kun ga wancan gidan, shi ne gidan Mai Unguwar nan Unguwar." Ba tare da damuwa da bayanin da ya musu ba suka sake masa godiya cikin matuƙar farin ciki. Daga haka ya yi musu sallama ya ƙara gaba, ya yin da suka nufi inda ya nuna musu. Lokacin da suka isa, sun samu wani yaro tsaye a ƙofar gidan. Suka sanar da shi abin da ke tafe da su na son ganin Mai gari. "Ai kuwa dai Mai Unguwa ba ya nan, ya yi tafiya an yi masa mutuwa. Amma idan wani abun ne ku faɗa sai na taimaka muku." Kallan juna Daneen da Ameer suka yi, kafin suka maida duban su kan yaron. "Dama zuwa muka yi mu tambayi gidan wani Alhaji Abubakar, wanda ya yi aure kwanan nan, ya auri wata Fatima." Tsayawa yaron ya yi yana kallan su irin kallan rainin hankalin nan. Sai dai abin da ma ba su sani ba, cikin ransa tunani yake anya kansu ɗaya? Ya duk girman unguwar nan amma su zo suna tambayar gidan Alhaji Abubakar wai wanda ya auri Fatima. Anya kuwa? "Ba a nan garin kuke ba ne?" Girgiza kai suka yi. A wannan karon ma dai Ameer ne ya ce "Daga ƙauyenmu muke. Muna neman su ne shi ya sa muka taho kai tsaye gidan Mai gari. Tun da yadda muka sani duk wani gida da ke a ƙarƙashin ƙauyen Mai gari ya san masu gidan,lll shi ya sa muka zo." Sai a lokacin yaron ya kaɗa kai, shi dama ya san a rina, ashe daga ƙauye suke. "Kun ga, nan fa ba ƙauye ba ne. Ba a ƙauyenku kuke ba. Kun ga ku rufa wa kanku asiri ku koma inda kuka fito, tun da ba ku san inda waɗanda kuka fito nema suke ba. Wannan garin yana da faɗi, ba kamar yadda ƙauyenku yake ba. Mu nan ba iya garin nan ba, duk wata unguwa da ke cikin garin nan tana da Mai Unguwa, kuma Mai Unguwa ba shi da hurumin sanin mutanen da ke cikin unguwarsa. Ka ga kenan ba za ku taɓa samun abin da kuke nema ba." Tun da ya soma maganar suke kallan sa, har ya ƙare. Jiki a matuƙar sanyaye suka yi masa godiya. Bayan ya yi musu sallama ya wuce cikin gida. Ba su taɓa tunanin haka abin yake ba. Sun ɗauka tamkar yadda ƙauyensu yake nan ɗin ma haka yake. Shi ne dalilin da ya sa suka taho ba tare da wani tunani ba. *** "Sister ban san ta ina zan fara ba." Sultanah ta faɗa jikinta a matuƙar sanyaye. Gyara zama Hidaya ta yi kafin ta ce "Kin ga ki fara ko ta ina ne. Na ƙagu na ji me ke damun ki, tun da kuka dawo gida dama na fahimci tabbas akwai abin da ke damun ki." Shiru Sultanah ta yi tana kallan Hidaya ba tare da ta tanka ba. Hidaya ta kamo hannunta ta jinjina mata kai don ba ta ƙwarin gwuiwa. "Ki sanar da ni." Ta faɗa har lokacin tana kallan ta. Ajiyar zuciya ta sauke, ta lumshe idanunta kana ta buɗe bakinta ta ce a hankali "Er'uwa ban san yadda za ki ɗauki zancen ba ke kanki, ballantana kuma har in yi wa Yah Tareeq maganar. Amma tabbas na tsinci kaina dumu-dumu cikin ƙaunar Yah Abdoul." Ta ƙare maganar tana jin yadda mikin da ke cikin zuciyarta ke famuwa. Hannunta Hidaya ta zare daga cikin na Sultanah tana kallan ta sosai cike da matuƙar mamaki. "Yah Abdoul kuma Sultanah?" Jinjina kai Sultanah ta yi a sanyaye, tana jin duk wani ƙwarin gwuiwarta na zagwanyewa, ganin tilon er'uwarta da take saka rai a kanta tana neman watsa mata ƙasa a ido. "Kar ki zama mutum ta farko da za ki fara ganin laifi na Hidaya don Allah." Sultanah ta faɗa tana kamo hannun Hidaya. Murmushi Hidaya ta yi don saboda kar ta zubar wa da er'uwar tata ɗan ƙwarin gwuiwar da take da shi ta ce "Ba watsa miki ƙasa a ido zan yi ba Sultanah. Kawai dai abin ne na ji shi tamkar a mafarki, na kuma yi matuƙar mamaki. Amma In Sha Allah zan taya ki da addu'a idan rabon ki ne shi ɗin Ubangiji Ya juyo miki da hankalinsa tun kafin ki sanar da shi. Don ban san ta yadda za mu sanar wa da Yah Tareeq kina ƙaunar Abokinsa ba." Ajiyar zuciya Sultanah ta sauke kafin ta ce "Ni ma abin da nake tunani kenan Hidaya. Ina tsoron Yah Tareeq ya ji zancen nan, amma ban san yadda zan yi ba. Abin yana damu na matuƙa a cikin zuciyata." "Ki yi haƙuri Sisi, In Sha Allah komai zai zo da sauƙi." "Ke! Maganar wa na ji kuna yi?" Maami da ta fito daga cikin ɗaki yanzun ta faɗa tana kallan su, tana sanye cikin doguwar rigar atamfa. Tsananin kamar da suke da Sultanah shi ne zai bayyana maka mahaifiyarta ce. Gaba ɗaya ɗaga kai suka yi suka kalle ta a tsarge. Da sauri Sultanah ta shiga girgiza kai "Babu komai Maami." "Anya kuwa?" Ta sake faɗa tana kafe Sultanah da ido, kamar mai son gano gaskiyar abin da take faɗa a kan fuskarta. "Ehh Maami." Hidaya ta faɗa. Jinjina kai kawai Maamin ta yi, tana wuce wa kitchen ɗin da dama abin da ya fito da ita kenan. Wata gauruwar ajiyar zuciya Sultanah ta sauke kafin ta ce "Na gode wa Allah." Ta faɗa tana dafe ƙirjinta. Bin ta da kallo Hidaya ta yi, tana mamakin yadda ruɗewar Sultanahn ta yi yawa. Sai dai sanin halin Maamin ya sanya ta girgiza kai kawai. *** Ɗaga kansa ya yi ya kalli wanda ya shigo office ɗin, ya amsa sallamar yana maida dubansa kan takardun, ba tare da ya kalli abin da ke rubuce a cikin su ba ya haɗa su waje guda. Ƙarasawa Abdoul ya yi ya nemi waje ya zauna shi ma hannunsa ɗauke da wasu takardun. "Ga waɗannan takardun, duk dai cikin na Diyana ne." Abdoul ya faɗa yana miƙa masa takardun. Ba tare da ya ce komai ba, ya karɓa ya haɗa su waje ɗaya. Ba dan ba dan ba, yanzun nan zai saka wani ya ƙoma masa takardun, sai dai ko ma mene ne, ba ya so komai da ya shafe shi ya fita waje. Don haka bayan ya gama haɗa su waje ɗaya, sai ya nemi waje ya killace su. Sai a lokacin ya mayar da duban sa kan Abdoul ya ce "Ya ake ciki?" "Na tura maka komai ta E-mail naka, ka bincika bayanin komai na ciki." Jinjina kai Tareeq ya yi kafin ya ja laptop ɗin da ke gabansa ya shiga dannawa cike da ƙware wa. Kyawawan idanunsa na bin duk wani rubutu da ke bayyana a kan fuskar laptop ɗin, kai ka ce haddace kowacce kalma yake yi, saboda yadda yake bin su cike da takatsantsan da son tabbatar da duk abin da ya gani gaskiya ne. *** Sosai dare ya sake tsalawa har lokacin suna tafiya, wani lokacin idan sun gaji su nemi waje su zauna. Wani lokacin kuma su cigaba tafiya. Sai dai har zuwa lokacin ba su san takamaimai inda za su je ba. Kuɗin da ya rage a hannunsu dududu bai fi na abincin da za su ci ba, ballantana su yi tunanin komawa ƙauyensu, tun da dai wannan gari Allah Ya masa faɗin da sanin inda Innarsu take kamar ba mai yiwuwa ba ne. I zuwa lokacin ban da kukan tsuntsaye, da motsin ƙalilan ɗin ababen hawa babu abin da kake iya ji. Tsoro da fargaba tuni sun cika zuciyoyin Daneen da Ameer. Musamman ma dai Daneen da ke cigaba da raba ido kamar munafuka. "Adda wai tafiya za mu yi ta yi, ba za mu nemi inda za mu kwana ba." Ameer ya faɗa yana dakatawa. "Toh Ameer a ina za mu kwana? Ni na rasa ma mai zance wallahi." "Kawai mu nemi wani wajen wallahi, kin ga fa titin babu kowa yanzu. Idan ya so gobe sai mu nemi mafita." Cikin na'am da zancen Ameer ɗin Daneen ta gyara zaman jakarta, suka cigaba da tafiya suna kalle-kalle, ko za su samu inda za su yar da haƙarƙarinsu. Lumshe idanu kawai Daneen ke yi, saboda baccin da ke ta kawo mata hari, dalili kenan da ya sanya manyan idanunta suka ɗan taasa kamar waɗanda suke ciwo. "Bacci kike ji ko Adda?" Ameer ya faɗa cike da kulawa. Jinjina kai ta yi tana kai hannunta saitin bakinta lokacin da ta yi hamma. Ta ɗan runtse idanunta tana sake buɗe su, daidai lokacin da ta jiyo muryar Ameer na faɗin "Laa Adda kin ga wani waje can wallahi ki zo mu je. Za mu iya kwana abin mu." Ya faɗa yana jin yadda farin ciki ke mamaye ilahirin jikinsa. Inda yake nuna wa ta bi da kallo. Trader ce irin ta mai shayi. Wadda da alama mai ita ba ya zama, ko kuma wani dalili ya hana shi zama yau ɗin. Saboda yadda masu shayi kan kai wa dare, bai ci a ce har ya tashi i yanzu ba. Juya wa Daneen ta yi ta kalli titin da motoci ke cigaba da wuce wa. Kafin ta dawo da dubanta kan trader. Kawai sai ta ji jikinta ya sake yin sanyi. Tabbas da ta san ba za su haɗu da Innarsu ba, ba za ta taɓa yarda su fito daga gida ba ko me Dada za ta musu. Ba ta taɓa tunanin akwai gari mai girman da za a ce kowacce unguwa akwai nasu mai unguwar ba sai yanzu. Ba ta taɓa tunanin ƙaddarar rayuwa kan iya jefo su har suna shirin kwana a kan titi ba. Shin me ya sa ta biye wa Ameer suka fito daga ƙauyensu zuwa wannan garin mai girman da da alama ya ninka ƙauyensu sau babu adadi. Shin me ya sa suka yi wannan gangancin na biyo Innarsu ba tare da sun san takamaimai inda take ba. "Ki zo mu ƙarasa." Ameer ya faɗa yana jan hannun Daneen, ganin da ya yi da alama ta yi nisa a tunanin da ta tafi. Babu musu ta bi bayansa. Shi ya fara yin gaba, ya yin da ta bi bayansa. Har ciki suka shiga kasancewar babu ƙofa. Sai dai wajen irin keɓantaccen nan ne. Don haka ko da suna ciki babu wanda zai iya ganin su. Karɓar jakar hannunta Ameer ya yi, ya ajje ta gefe, ya sanya hannunsa ya ɗakko rigunansa guda biyu ya shimfiɗa, kana ya kalli Daneen ya ce "Adda taho ki kwanta." Ya yi maganar lokacin da yake gyara zaman jakarta don ta ji daɗin yin pillow da ita. Kallan Ameer ɗin Daneen ta yi, ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba. Ƙaunar Ameer a gare ta yawa gare ta, haka zalika ƙaunar ta gare shi tana da yawa. Don ji take tamkar ta fi ƙaunarsa ma a kan yadda take ƙaunar kanta. "Kai fa?" Ta tambaya tana kallan sa. "Ki fara kwanciya, ni ma zan kwanta." Ƙarasawa ta yi ta kwanta, zuciyarta cike fall da tunane-tunane. Sai dai abin da ya fi tsaya mata a rai, shi ne yadda za su samu kuɗin motar da za ta maida su ƙauyensu. Sai a lokacin sannan Ameer ya nemi waje shi ma ya yi shimfiɗa ya kwanta. Sosai dare ya cigaba da tafiya, gari na sake yin shiru, ƙarar kukan tsuntsaye na daɗuwa. Sautin ababen hawa na raguwa. Har zuwa lokacin da motsin su ya ɗauke kwata-kwata. "Baba yau fa so nake na afa aji garau ɗin nan da yawa, don wallahi so nake na haura hazo na yi ta shawagi ni ɗaya." Sautin da ke fita a daddaƙire, cikin irin muryar en shaye-shaye ta doki dodon kunnen Daneen da baccin nata kwata-kwata bai yi nisa ba. "Kar ka damu. Ni kaina yau ɗin nan so nake na yi mugun cajin da na daɗe ban yi ba." Wanda suke tare ya faɗa. Lokacin da suke ƙara kusantar trader. Kai tsaye can suka nufa, suka nemi waje suka zauna. Cikin ƙanƙanin lokaci suka baje kayan harkarsu. A hankali Daneen ta tashi zaune, tana jin yadda zuciyarta ke buga wa tamkar za ta faso ƙirjinta. Ta lalubi fuskar Ameer ta taɓa, ta ji bacci yake. Sai ta ɗauke hannun nata tana koma wa ta zauna a kan shimfiɗarta, bugun zuciyarta har wani sauti yake bayar wa 'dif, dif, dif' saboda tsananin tsoron da take ji. "Kai.. Ni fa kamar motsi nake ji a cikin abar nan." Ɗaya daga cikin su ya faɗa yana ɗan waigawa. Buɗe idanunta Daneen ta yi jin abin da ya faɗa, daidai lokacin da wasu hawaye suka samu damar zubo wa a kan kuncinta lokaci guda. "Kai ni ma fa kamar na ji. Waye a nan?" Ya faɗa a ɗan tsawace yana kallan cikin trader. Runtse idanunta Daneen ta yi tana karanto duk wata addu'a da ta zo ranta, lokaci ɗaya tana haɗe jikinta waje ɗaya, kanta ɗore a kan cinyarta, zuciyarta na wani irin harbawa, tsoron da tun da uwarta ta haife ta ba ta taɓa jin sa ba na cigaba shigar ta. "Ya kamata mu duba fa." Ɗayan ya faɗa yana miƙe wa. Shi ma miƙe wa ɗayan ya yi suka shiga takawa zuwa inda su Daneen suke. I zuwa lokacin zuciyar Daneen bugawa ne kaɗai ya rage ba ta yi ba. Kawai sai ta cigaba da addu'a tana miƙa wa Allah lamarinta kawai. Don ba ta san kuma abin da ya kamata ta yi ba bayan wannan. "Kai! Wallahi kamar mace nake hange a ciki fa. Kar dai a ce yau rabon farka wata yarinya ne ya fito da mu." Wanda da alama ya fi ɗayan tantiranci ya faɗa yana dariya, lokaci ɗaya yana kallan Daneen, hannunsa a kan haɓarsa yana shafawa. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 11 "Ke don tantiranci ma kawo kanki kika yi? Lallai abin zai bayar da citta." Ya ƙare lokacin da ya ida ƙarasa tura kansa cikin wajen da su Daneen suke. Har kuma lokacin shu'uman idanunsa na kanta, yana bin ta da wani kallo kamar tsohon maye. Cikin saurin da ba ta san tana da shi ba, ta miƙe daidai lokacin da ta ida buɗe kumburarrun idanunta a kansa. "Me ye haka kuma? Ina kike ƙoƙarin zuwa? Maada ƙaraso da gulafarka ciki mana." Shi dai wanda ya soma magana tun farko ya sake faɗa. Kamar cikin mafarki Ameer ya soma jiyo maganganu ƙasa-ƙasa. Babu shiri ya buɗe idanunsa da ke ɗauke da bacci. A kan Daneen ya sauke su lokacin da take zube a kan ƙafafunta, kyawawan idanunta sharkaf hawaye. Tun da Inna-wuro ta haife ta, ba ta taɓa tsintar kanta cikin tashin hankali irin wannan ba. "Don girman Allah kar ku yi mana komai, ku bar mu mu tafi don Allah. Wallahi ba za mu sake zuwa wajen nan ba, don Allah." Ta ƙare hannayenta biyu a haɗe waje guda. Dariya Maada ya sheƙe da ita, yana kallan Dawa kafin ya ce "Kaa ji me take cewa fa." Ya faɗa yana nuna Daneen da yatsan hannunsa. A tare suka sheƙe da wata sabuwar dariyar suna kallon Daneen da har lokacin take zaune a kan gwuiwoyinta. "Bari ka gani." Dawa ya faɗa yana soma sassauta ɗaurin tazugen wandon da ke jikinsa. "Adda." Ameer ya faɗa yana miƙe wa lokacin da ya gama fahimtar maza har biyu sun shigo cikin trader yana bacci. Ga kuma abubuwan da ya ji suna faɗa. Abin da ya tayar masa da hankali kenan, ya kamo hannun Daneen ya riƙe gam cikin nasa, kafin ya maida dubansa kan su ya ce "Don Allah ku yi haƙuri." Da mamaki Dawa ya ɗaga ido ya kalli Ameer, don kwata-kwata bai lura da wanzuwarsa cikin wajen ba sai da ya yi magana. "Maada yi mini waje da wannan wawan, kai ma ka ɗan ba mu waje, idan na gama sai ka shigo ka ɗora." Tun kafin ya ida maganar, Maada ya ƙarasa ya cafki hannun Ameer da niyyar fidda shi daga cikin trader. Ganin da Ameer ya yi da gaske so suke su fitar shi, ya bar su kenan tare da Addarsa? Hakan ne ya sanya shi sake riƙe hannun Daneen gam-gam cikin nasa, ita ma hakan ce ta faru. Duk da yadda ilahirin jikinta ke ɓari, sai ka ce wadda zazzaɓi ke shirin rufe wa, ko kuma ya rufe ɗin ma. Gaba ɗaya ta rikirkice, ta ruɗe, ta rasa abin da ya kamata ta yi. Sai dai har lokacin ba ta dena ambatar sunan Allah cikin ranta ba. Ganin da Maada ya yi Ameer zai ɓata masa lokaci ne ya sanya shi saka hannunsa gaba ɗaya ya soma ƙoƙarin saɓa shi a kafaɗa. "Ka sake ni, ka sake ni malam. Ka sake ni." Shi ne abin da Ameer ke ta faɗa yana ciccije wa, yana kuma sake riƙe hannun Daneen da ke cigaba da riƙe na shi. Duk inda Maada ya ja shi sai Daneen ta bi shi, don haka kawai ya saɓe shi gaba ɗaya. Daidai lokacin da hannun Ameer da na Daneen ya rabu, ta buɗe duk wata murya da take da ita ta yi wata ƙara, da tunani tare da fatan wani ya ji ya zo ya taimaka musu. "Ka sake ni, kar ku cutar mini da Addatah. Kar cutar mini da Addatah, kar ku taɓa mini ita. Ka sake ni." Ameer ya cigaba da faɗa lokacin da yake kafaɗar mutumin, yana dukansa da duk wani ƙarfi da ya san yana da shi. Amma ko bi ta kansa bai yi ba, sai cigaba da tafiya da ya yi da shi. "Toh ke sai ki haƙura ai mu sarara." Dawa ya faɗa yana kallan Daneen da ke kuka kamar ranta zai fita. Tana kuma ƙoƙarin bin inda su Maada suka yi don fice wa daga wajen, amma Dawa ya ƙi ba ta dama. Ganin da ya yi idan ya cigaba da biye mata za ta ɓata masa lokaci ya sanya shi yin kanta gadan-gadan yana ƙarasa zame tazugen wandonsa gaba ɗaya. Wata ƙarar Daneen ta saki cikin dashashshiyar muryarta. I zuwa lokacin ji take zuciyarta na dab da fito wa daga ƙirjinta. "Wallahi kika sake yi mini wannan ihun za ki ga yadda zan wulaƙantaki cikin daren nan." Dawa ya faɗa a fusace, don tsoro yake ji kar garin ihun nan nata ta tona musu asiri tun kafin su shana. Kwalar rigarsa da ya ji an kama babu zato babu tsammani, ita ce ta sanya shi dakatawa cike da mamaki. Ya san babu yadda za a yi Maada ya yi masa haka, shi ya sa ya yi mamaki, sai ya ɗaga kai ya kalli wanda ke riƙe da kwalar rigar tasa har lokacin. A cikin idanunsa ya sauke nasa idanun. Cike da mamaki ya gyara tsayuwarsa "Waye kai?" Ya faɗa cikin ƙarfin hali. Murmushin takaici Tareeq ya yi kafin bai ce komai ba ya ja Dawa ta hanyar jan kwalar rigarsa zuwa waje. "Malam me ye haka ne?" Ya faɗa cikin muryar nan tasa da ta jiƙu da shaye-shaye. Karo na farko da ya buɗe baki, bayan ya kalli Abdoul da ke tsaye a wajen ya ce "Ba shi ɗaya ba ne, ina iya jin sautin murya daga baya. Taimaka ka taso ƙeyar kowaye mu miƙa su." Iya abin da ya faɗa kenan, har lokacin bai saki Dawa da ke cigaba da kallan sa ba. Amsa wa Abdoul ya yi yana yin gaba. Daidai lokacin da Dawa ya soma faɗin "Ka san wani abu Boss? Ka yi haƙuri ka rufa mana asiri kar ka miƙa mu wajen kwalawa. Wallahi tallahi babu abin da na yi wa yarinyar mutane. Dama razanarwa ce kawai ehh ka gane ai. Ban da haka babu wani abu. Ba na son haɗuwa ta da kwalawa ko kaɗan, muna da case da su dama. Ka yi haƙuri ka mini afuwa ka bar ni na je, ba ma za ka sake gani na a arear nan ba." Ya ƙarasa maganar daidai lokacin da Abdoul suka ƙaraso da su Maada da Ameer. A guje Ameer ya ƙarasa ya rungume Daneen, a ruɗe yana faɗin "Babu abin da ya same ki ko Adda? Babu abin da ya same ki?" Ya faɗa shi kansa jikinsa ko'ina rawa yake. Rungume shi ta yi, ko ta ji sauƙin abin da take ji cikin zuciyarta. Ta shiga jinjina kai har lokacin hawaye ba su dena sintiri a kan fuskarta ba. "Taso mu tafi Adda, ba za mu sake kwana a wajen nan ba. Taso mu tafi." Ameer ya faɗa bayan ya miƙe, yana riƙo hannunta. Ita ma miƙewar ta yi, tana saka hannunta ta goge gefen fuskarta. "Ki dena kukan toh kin ji?" Ameer ya faɗa cike da kulawa. Jinjina kai ta yi tana jin zuciyarta na sake karye wa. Sai dai ba ta bari hawayen sun zubo ba. Ta saka hannu ta ɗauki jakarta, shi ma tasa ya ɗauka bayan ya tura kayansa ciki kafin suka fito. Suna tsaye su biyu, Tareeq na daga baya, ya yin da Abdoul ke gaba. Da alama dama inda suke ya nufo. Ɗaga ido suka yi suka kalle su kafin suka ɗauke. "Ina za ku je?" Abdoul ya tambaya yana kallan su sosai don fahimtar su. Shiru suka yi kamar masu tunani. Kafin Daneen ta gama tsara abin da za ta faɗa Ameer ya ce "Gida." "Kuna da gida mai ya kawo ku nan?" A wannan karon Tareeq ne ya yi maganar yana kallan su sosai, duk da ba ya iya ganin takamaimai ya fuskarsu take, saboda ƙarancin hasken da aka samu a wajen yanzu ba kamar ɗazu ba. "Wuce wa muka zo yi. Mun je unguwa shi ne muka yi dare." Ameer ya sake faɗa. Cigaba da kallan sa Tareeq kawai ya yi, sai dai bai ce komai ba. "Ko ma ina ne kuka je ku dena kai wa dare haka, kuna ganin gari ya yi shiru haka, babu kowa. Ga ɓata gari sun yi yawa. Yanzu ga shi kuna gani ba don Allah Ya taƙaita ba, da sai dai Allah Ya tsare. Ku din ga kula, kai wa dare a waje ba na 'ya mace ba ne." Abdoul ya faɗa. Jinjina kai kawai suke yi kamar wasu ƙadangaru, ita dai Daneen ko ɗaga ido ta kasa yi ballantana ta kalle su. Sai a lokacin Tareeq ya gyara tsayuwarsa, ya kalli Abdoul ya ce "Ka ɗauke su ka kai su gida please, na kira Nuhu yana jira na." Ya ƙare yana kallan Abdoul, kafin a karo na barkatai ya sake kallan Ameer. Sai dai har lokacin bai sake ce masa komai ba, suka yi sallama da Abdoul ya wuce. "Ku wuce in kai ku gida." Abdoul ya faɗa yana kallan su. Babu musu suka yi gaba, kamar da gasken suna da gida. Har inda motarsa take suka ƙarasa, ya buɗe musu suka shiga, kafin ya tayar da motar. Shiru kawai Daneen da Ameer suka yi jin yadda motar ke tafiya tamkar ba a kan titi ba. Ameer ya kalli gefen su, don sake tabbatar da da gaske a kan titi suke tafiya ba wani wajen ba. "Mai ya sa ba ka bari mun ce masa ba mu da gida ba, ka sani ko ya samar mana aikin da za mu yi mu samu kuɗin da za mu koma ƙauyenmu." Daneen ta faɗa ƙasa-ƙasa tana kallan Ameer. "A'ah.." "Wacce unguwar ce?" Abdoul ya katse wa Ameer maganar da ya fara. Sai kuma idanunsu ya yi tsilli-tsilli, suka kalli juna cikin rashin sanin abin yi. "A kan titin nan ne ai." Daneen ta yi ƙundunbalar faɗin hakan jikinta a matuƙar sanyaye. Cigaba da driving ɗin ya yi har zuwa lokacin da Daneen ta sake yin ƙarfin halin faɗin "Ya isa haka, nan ne." Ta faɗa ƙirjinta na wani irin bugawa. Sauka ya yi daga kan titin, kafin ya ce "Bari na ƙarasar da ku." Ya faɗa yana shiga cikin layin da ta nuna masa. Daga ita har Ameer sai da cikinsu ya ɗuri ruwa. Amma haka suka yi shiru, suka cigaba da rarraba ido kamar shege a rabon gado. "Ya isa haka, mun gode." Daneen ta faɗa cikin sanyin muryar nan tata da ta sake yin sanyi matuƙa. Jinjina kai ya yi yana tsaida motar, suka sauka bayan sun yi masa godiya sosai. "Babu komai." Ya faɗa yana murmushi. "Allah Ya saka da alkhairi." Daneen ta sake faɗa a karo na barkatai. A wannan karon murmushi kawai ya yi, ba tare da ya ce komai ba. Ya bi su da kallo lokacin da suka shige wani waje da ke nuni da gidan da suka nufa nan suke ƙoƙarin shiga. Sai a lokacin ya tayar da motarsa ya bar wajen. Ajiyar zuciya Ameer ya sauke kafin ya ce "Addaneen." "Na'am." Ta faɗa tana kallan sa. "Allah Ya taimake mu, amma yanzu ya za mu yi?" Ya tambaya a dame. Kallan inda suke ta yi na tsawon sakanni, kafin ta ce "Kawai mu zauna a nan zuwa gobe mu nemi aikin da za mu samu kuɗin koma wa gida. Ni ba na son garin nan, kwata-kwata bai yi mini ba. Ba na son shi." Daneen ta ƙarasa maganar tana lumshe kyawawan idanunta. Kallan jar fuskarta da ko'ina na jikinta ya yi jajir Ameer ya yi kana ya ce "Ni ma haka, ba na so. Ina so mu koma ƙauyenmu kafin Inna ta dawo. Na yi kewar ta, ina so in gan ta." Ba ta san lokacin da murmushi ya ƙwace mata ba. Ta nemi waje ta tsuguna, tana tunanin ta inda za su fara. Cikin ikon Allah tun da suka zauna a wajen, babu wanda ya fito daga cikin gidan da suke zaune a ƙofarsa, ko kuma wani ya zo wuce wa. Musamman da yake gidan ba a waje yake sosai ba, an yi wasu en dabaru wajen kare shi. Hakan ne ya sa suka zauna a nutse, sai dai fa bacci babu shi babu alamar sa. Suna nan zaune har aka kira sallahr Asuba. Ameer ne ya samo musu famfo suka je suka yi alwala, suka dawo suka yi sallah a wajen, kafin suka cigaba da zama. Lokacin da gari ya ida buɗe wa, sosai Daneen ta shiga buɗe idanunta tana kallan irin gidajen da ke zagaye da su. Gidaje ne waɗanda ba ta taɓa tunanin akwai su a gaske ba. Gidaje ne maka-maka, haɗaɗɗu na gani na faɗa, waɗanda ba ta taɓa ganin irin su ba. "Kin ga wancan Adda." Ameer ya faɗa yana nuna mata wani gidan da shi ma ya gaji da haɗu wa. "Kuma gidan ne fa da gaske koh?" Ta tambayi Ameer a sakarce. Sai da juya ya kalli bayansu kafin ya ce "Toh mu gwada buga wannan mana sai mu tabbatar." Riƙo hannunsa ta yi da sauri tana girgiza kai "A'ah babu ruwa na wallahi." "Ba sai mu ce aiki muke nema ba, idan za su ba mu kin ga ai sai mu yi mu samu kuɗi." Ya ƙare maganar yana murmushi. Shiru Daneen ta yi kamar me tunanin wani abu, kafin ta sake ɗaga kai ta kalli gidan. A sanyaye ta kalli Ameer ta jinjina kanta ta ce "Toh mu gwada koh?" Ta sake tambayarsa. Sai ya jinjina kai yana murmushi. "Kin ga idan ba su ɗauke mu ba ma ai dai mun ga gidan nasu mun yi musu wayo." Ya ƙare yana dariya. Ita ma er ƙaramar dariyar ta yi tana sake kallan gidan a karo na biyu. Sai da gari ya sake yin nisa sannan Daneen ta amince Ameer ya je ya ƙwanƙwasa gidan nan. Shi ko tsoro ma ba ya ji, ita ya bar ta da faɗuwar gaba. Shiru babu alamar za a buɗe. Ya juya ya kalli Daneen, kafin ya ce komai ta ce a hankali "Ko dai ba gida ba ne?" "A'ah fa gida ne ke kam." Ya ba ta amsa cike da tabbatarwa kamar da gasken ya sani. Be jira ta sake cewa komai ba ya juya ya cigaba da ƙwanƙwasawa. Babu daɗe wa suka ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar. Kallan juna suka yi shi da ita, Ameer ya yi murmushi kawai, ba tare da sun ce komai ba suka maida duban su kan wadda ta zo ta buɗe ƙofar. Tun daga sama har ƙasa take kallan su, kamar wadda ta ga baƙin halittu. Tana sanye cikin wata doguwar rigar da ba ta kai ƙasa ba. Hannunta ɗore a kan gate ɗin tana cigaba da kallan su. "Lafiya?" Ta faɗa kai tsaye tana jefa musu wani kallo. Kallan juna Daneen da Ameer suka sake yi kafin Daneen ta buɗe baki a nutse ta ce "Aiki muka zo nema, ko kuna da buƙata." Har za ta buɗe baki ta ce ba sa buƙata, sai kuma ta yi shiru. Ta sake kallan Daneen a karo na barkatai kafin ta ce "Ku shigo." Ta yi maganar tana ba su hanya. Babu musu suka sanya ƙafafunsu zuwa cikin , gaba ɗaya idanunsu a kan cikin gidan, suna kallan irin zubin da aka yi masa, tamkar ba a duniya mutum yake ba. Gaba matar ta yi, ya yin da suka cigaba da bin bayanta. "Ka sanar wa da Auntyyy ta yi baƙi." Ta faɗa lokacin da suke dab da wuce wani da ke zaune a kan kujera yana danna waya. "Auntyyy, kin yi baƙi." Wani gabjejen mutum da muryarsa ta fi kama da ta er budurwa ya faɗa yana kallan matar da ke zaune a kan kujera. Sanye cikin doguwar rigar wani material, a ƙalla a shekaru ta ba wa 50 baya. Fuskar nan ta yi ɗau ta yi jajir da farin bature. Sai dai wani sashe na fuskarta duk ya yi baƙi-baƙi, musamman ma daga gefen idanunta. Kanta ɗaure da ture kaga tsiya, ta baza uban ƙananun kitson da suka zuba har gadon bayanta. Kujerun da ke gefen ta kuwa wasu manyan alhazai ne su biyu, da ke sanye cikin shadda ɗinkin babbar riga. Kowanne da ka gan shi ka san kuɗi ya zauna masa babu wai. "A shigar mini da su ɗaki, ka dai san ina tattauna wa ne mai muhimmanci. Zan ƙaraso daga zarar na gama." Ta ƙare maganar tana wani karairaya kamar wata yarinya er shekara 20. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 12 Kallan juna Daneen da Ameer suka yi, lokacin da suke ƙoƙarin zama a ƙasan kujerar ɗakin da aka shigar da su. Babu wanda ya ce da su ko uffan, haka aka fice aka bar su ciki su kaɗai. A karo na barkatai suka sake kallan junansu kafin Ameer ya ce "Adda kar fa mu je en yankan kai ne." Ya faɗa yana sakin jakar hannunsa idanunsa sun yi tsilli-tsilli. Wani yawu da ya tsaya wa Daneen a maƙogwaro ta haɗiye tana sake bin ɗakin da kallo ta ce a sanyaye "Toh mu jira dai mu gani." Ta faɗa tana gyara zaman ta. Cikin ranta tana fatan Allah Ya sa ba gidan en yankan kai suka kawo kansu ba. Bayan wajen minti 30 suna zaune cikin ɗakin amma shiru babu wanda ya leƙo. Zuwa lokacin sun fara ruɗewa. "Ni dai wallahi ki tashi mu tafi, hmm uhmm." Ameer ya faɗa yana girgiza kai. Ita ma a ɓangaren ta hakan take saƙa wa a ranta, su tashi su fice daga gidan, don da alama ma waɗanda suka kawo su sun manta da rayuwarsu. Tun da ga shi tun da suka tafi ba su sake bi ta kansu ba. Kafin wani a cikin su ya sake cewa komai, sai ga motsi an shigo cikin ɗakin. A tare suka ɗaga ido suka kalli matar da ta shigo. Wannan matar ce ta ɗazun da ke zaune da wasu maza. Cikin shigar ɗazun dai take, da alama ta gama da waɗancan ɗin shi ne tayo nan. Tun da ta shigo idanunta ke kansu, har ta ƙarasa ta nemi waje ta zauna tana cigaba da bin su da kallo. "Ina wuni?" Suka haɗa baki wajen faɗar hakan. Sai da ta ɗan yi jimm kafin ta ce "Lafiya, ku ne baƙin nawa?" Ta faɗa tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta sake ganin gaba ɗaya yanayin Daneen, zubin halittarta da komai na jikinta. Jinjina kai suka yi kafin Daneen ta ce cikin siririyar muryarta "Eh." "Kuka ce aiki kuke nema?" Ta ƙare tana jin wani murmushi na taho mata. "Eh." Daneen ta sake amsa wa a wannan karon ma. Jinjina kai Auntyy ta shiga yi kana ta ce "Toh, kun samu." Cikin wani irin farin ciki suka ɗaga kai suka kalle ta. Ta sake jinjina kai sannan ta ce "Ƙwarai kuwa. Abin da nake buƙata kawai sirri, da kuma haɗin kai. Ba na son taurin kai ko kaɗan. Yin sa kan sa na kori mutum na har abada. Idan dai har kun amince shi kenan, maganar kuɗi kuma za ku iya samun sa duk ranar da kuka yi aiki. Ke aikin ki ya fi yawa, saboda haka da ke zan fara." Ba tare da kawo komai a kan zancen ta ba Daneen ta ce "In Sha Allah ba za ki yi kuka da mu ba." "Haka nake so." Aunty ta faɗa, kafin ta ɗan ɗaga murya ta ce "Shanawa zo ka shigar mini da yarinyar nan ciki." Shiru ne ya wanzu a wajen, zuwa can wannan mutumin na ɗazu ya shigo cikin ɗakin. Cikin muryarsa ta mata ya ce "Aunty ga ni. Ina yarinyar?" Ya faɗa yana jefa idanunsa da yake ta wani fari da su cikin ɗakin. "Tashi ki bi shi, zai kai ki inda za ki yi wanka ki shirya." Kallan Ameer da shi ma ita yake kalla Daneen ta yi, kafin ta maida duban ta kan Aunty a sukwane ta ce "Wannan ƙanina ne." Ta faɗa tana nuna shi. "Kar ki damu, zai zauna a ɓangaren maza ne. Ki je ki yi wanka ki shirya ke dai, shi ma zai je ya gyara jikinsa." Jin abin da ta faɗa ya sanya ta ji daɗi. Ta miƙe tana ɗaukar jakarta. Da sauri Aunty ta ce "A'ah ajiye ta, akwai komai na buƙata a ciki." Babu musu ta ajiye ta, ta kalli Ameer ta ce "Bari na je, ka je ka shirya kai ma ka ji? Sai mu fara aikin da wuri ka ga gidan na da girma." Ta faɗa ƙasa-ƙasa. Jinjina kai Ameer ya yi. Daneen ta bi bayan mutumin nan. Tafiya suka soma yi, suna tafiya yana karairaye karairayensa, shi a lallai dole mace. Ita dai sai taɓe ɗan mitsitsin bakinta take saboda haushi da ya ba ta. A haka har suka ƙarasa wani ɗaki. Tsaya wa ya yi a wajen, ya dakata ya yi knocking na ƙofar, zuwa can aka zo aka buɗe. Wata dattijuwar mata ce da a ƙalla za ta yi shekaru 40 ko da wani abun. Tana sanye cikin riga da zani da ɗan'kwali irin na da ɗin nan. "Toh ke ga baƙuwa nan kin samu. Na san Aunty ta gama miki bayani." Jinjina kai matar ta yi kafin ta kalli Daneen ta ce "Shigo." Haka nan kawai ta ji ƙirjinta ya buga, har sai da ta kira sunan Allah, kafin ta soma taka wa. Ta saka ƙafarta cikin ɗakin. Daga haka shanawa ya juya, ya yin da matar ta rufe ƙofar bayan Daneen ta shige cikin ɗakin. Kallan ta matar ta shiga yi kamar wadda ta ga sabuwar halitta, sosai ya yaba da kyawun Daneen matuƙa. Don kuwa idan ban da kayan da suke jikinta, a kallan farko idan ka yi wa fuskarta za ka iya kiran ta da er'india, saboda tsananin kyan da Allah Ya ba ta irin mai ɗaukar hankalin nan. Babu abin da ma ya fi tashin kai a kan fuskarta irin cat eyes ɗinta, masu wani irin shape na musamman. "Mu je ciki banɗakin na ciki." Ta faɗa tana nuna wa Daneen ciki. Kallan inda ta nuna ɗin ta yi, kafin ta ce "Toh." Ta yi maganar a sanyaye. Sai da matar ta ƙarasa ta haɗa wa Daneen komai da ta san za ta buƙata na wanka kafin ta fito. Daneen ta ƙarasa ciki tana kallan irin tsarin da aka yi wa banɗakin kamar ba banɗaki ba. Don sau dubu ya fi ɗakin da suke kwana a ƙauyen su. Jinjina kai ta yi tana ƙarasawa ciki. Ta fi minti nawa tana tunanin ta inda za ta fara, kafin zuwa can ta yi ƙarfin halin soma wankan a sanyaye. Ta ɗauki wajen minti 30 kafin ta soma ƙoƙarin fito wa, ta mugun jin daɗin jikinta. Har wani sassanyan murmushi ke tashi daga kyakkyawar fuskarta ta fito. "Mu je in wanke miki kai." Matar nan ta faɗa tana kallan ta. Ita ma kallan ta Daneen ta yi kafin ta juya a hankali ta koma cikin banɗakin. Haka tana ji tana gani, ta buɗe kanta a gaban matar, ta shiga wanke mata sassalkan gashin kanta da ya fi kama da wanda ya jiƙu da tsadaddun maya-mayai. Yadda yake a kwance, a miƙe sai ka ɗauka wani shahararren gyara take masa na fitar hankali. Hakan ne ya sa ba su daɗe ba ta wanke mata kan da ruwa kafin suka fito. Ita ta taimaka mata ta gyara mata kan tsaff ta tufke mata shi da wani ribbon, ya kuwa zuba har gadon bayanta. Tana gama wa kuwa Daneen ta ɗauki ɗankwalin da ta cire ta lulluɓe kanta, don ta riga ta saba idan dai har ba a gaban Innarsu ba ko Ameer ba ta taɓa iya buɗe kanta. Sai ga shi yau wata ce ma ta wanke mata. "Kar ki mayar da kayan nan, ki bari yanzu zan kawo miki wasu." Matar ta faɗa tana ƙoƙarin juya wa. Bin ta da kallo Daneen ta yi, ba don ba don ba da sai ta ce matar nan ta fiya iyayi. Dan dai kawai babba ce. Ta gyara zama tana cuno bakinta fuskar nan a haɗe. *** Ta kai wajen mintina goma tana juya wayar a hannunta, ta rasa ta ina za ta fara. Number Abdoul ta daɗe cikin wayarta, ji take kamar ta kira su gaisa ko ta ɗan samu sassaucin abin da take ji a cikin zuciyarta. Sai dai da ta kai hannu za ta kira, sai ta fasa. Ba ta so ta yi wani abu ba tare da sanin Yah Tareeq ba. "Sultanah." Ta jiyo muryar Maami ta ambata daga gefen ta. Da sauri ta ɗaga kai ta kalli Maamin, don kwata-kwata ba ta ji zuwan ta wajen ba. Tsaya wa ta yi tana kallan ta na tsawon sakanni, kafin ta gyara tsayuwarta. "Ba ni wayarki na gani." Maami ta faɗa cikin tsare gida tana kallan Sultanah. Jikin Sultanah a matuƙar sanyaye ta miƙa wa Maamin wayar idanunta a kan fuskarta. Daidai lokacin da wayar Maamin ta shiga ruri, ta kalli mai kiran ta, kafin ta maida duban ta kan Sultanah ta ce "Kar na ji kar na gani Sultanah." Ta faɗa tana miƙa mata wayar. Jinjina kai ta yi da sauri, tana saka hannu ta karɓi wayar. Maami ta yi cikin ɗaki tana amsa wayarta, ya yin da Sultanah ta bi ta da kallo. Ita gaba ɗaya ta kasa fahimtar Maamin a kwana biyun nan. Gaba ɗaya ta kasa gane dalilin da ya sa ta saka mata idanu a kwanakin nan, bayan hakan ba ɗabi'arta ba ce. Yah Tareeq ya fi kowa saka wa rayuwarsu ido ita da er'uwarta, sai dai ga shi cikin kwanaki kaɗan gaba ɗaya Maamin ta bi ta sauya, ta tsiro da wani nau'i na takura, wanda kwata-kwata ba ta saba da shi ba. Ta sake rungume wayar cikin tafin hannunta tana rasa ta inda za ta fara. Gaba ɗaya zuciyarta a dame take, ta rasa yadda za ta yi. Ko ishashshen bacci ba ta samu a kwana biyun nan. *** "Yah Tareeq don Allah ina son mu yi wata magana." Shi ne saƙon da ya gani a saman wayarsa bayan ya kunna ta. Cikin mamaki ya ɗan ƙanƙantar da kyawawan ƙwayar idanunsa yana kallan number da ta turo saƙon. Maimaita saƙon ya sake yi kafin kai tsaye ya danna kiran number Sultanah yana miƙe wa tsaye. Ya riga ya san idan har irin haka ta faru, toh tabbas wani babban abu ne. Kwata-kwata ba shi da wasa a kan duk wani abu da ya shafi ƙannensa. Sanin hakan ne ma ya sa ko da wani abu ne ya faru, shi suke fara samu da maganar, ko da wata matsala ce shi suke sanarwa. Shi kuma ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya magance musu ita da taimakon Ubangiji. Tun da kuma ya ga Sultanahn ba ta kira shi kai tsaye ko ta masa magana da baki ba, ya san tabbas wani abun ne. "Sultanah." Ya ambata lokacin da ya fara taka wa kamar mai shirin fita daga office ɗin. "Na'am Yah Tareeq." Ta faɗa a sanyaye. "Ba ki da lafiya ne?" Ya tambaya a nutse, kamar wanda ba ya so a ji abin da ya faɗa. Girgiza kai ta yi kamar yana kusa da ita kafin ta ce "A'ah lafiya ta ƙalau." "Ohk, kina gida?" "Eh, ina nan." Ta ba shi amsa tana tashi zaune daga kwancen da take. "Toh mu haɗu palourn Dadaji." Ya faɗa, sanin da ya yi ta ji shi ne ya sa kafin ta kai ga amsa wa ya tura wayar cikin aljihunsa ba tare da ya kashe ba ya fice daga office ɗin. *** A ɗaya ɓangaren kuwa tana nan zaune bayan wajen minti 10 sai ga matar ta dawo hannunta ɗauke da wasu kaya cikin leda. Ta ƙarasa inda ta bar Daneen da kalle-kallen tsarin da aka yi wa ɗakin ta ajje kayan kafin ta ce "Ga shi nan ki saka, zan jira ki a palour. Kar ki daɗe." "Tohm." Ta faɗa a ranta tana tunanin irin wannan iyayin. Don kawai za su yi musu aikin wanke-wanke da shara har sai sun yi wanka, har da wani wanke kai da wasu kaya. Ita ba ta san haka en birnin suke da fi'ili ba. Matar ba ta sake cewa komai ba ta fice daga ɗakin. Daneen ta bi ledar da kallo, kamar ba za ta taɓa ba. Sai kuma ta janyo ta, ta shiga fidda kayan da ke ciki. Rigar da ta soma gani ta ɗaga tana kalla. Rigar ta fi kama da irin ta arnan nan, domin kuwa idan mutum ya saka, wuyansa duk a waje yake. Don kuwa har rabin ƙirjinsa kan iya fito wa. Ta jinjina kai tana cigaba da kallan rigar. "Chaɓɓ! Wace er iska? Wallahi ba zan saka ba." Ta faɗa tana hararar kayan. Abin da ta ji ya faɗo daga cikin rigar shi ne ya sanya ta kai idanunta ƙasa. Ta ajiye rigar hannunta, tana kai hannu ta ɗauki abin da ya faɗi ɗin. Da mamaki take bin abin da ta gani a hannunta. Idan dai har idanunta ba su yi ƙarya ba, sharbale ce take gani. Ta kai hannu ta toshe bakinta cike da mamaki. Ita duk sai ta ji kunya ma ta kama ta. Duk da tun a ƙauyensu Inna ta siya mata half vest amma ai ba ta kai ta saka sharbale ba, dududu ma nawa take? Ina ƙudan yake ballantana romonsa? Jefa ta kan gadon gefen ta ta yi tana faɗi a fili "Babba da ita amma ga wani iskanci." Ta ƙare maganar tana harara tamkar idanunta za su faɗo. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 13 Ta kai wajen mintina goma zaune a gefen gadon tana ta saƙe-saƙe. Tana kuma cigaba da kallan cikin ɗakin. Sai ji ta yi an taɓa ƙofar ɗakin. Da sauri ta ɗaga idanunta ta kalli mai shigowar. Matar ɗazun nan ce dai, tun da ta shigo take kallan ta, har ta ƙaraso. Da mamaki shimfiɗe a kan fuskarta ta ce "Me kike jira har yanzu ba ki shirya ba?" Ta tambaya tana sauke idanunta a kan kayan da ta ba ta. Ita ma Daneen kayan ta kalla kafin ta maida duban ta kan matar ta ce bayan ta girgiza kai. "Ba zan iya sakawa ba." Sake kallan kayan matar ta yi, kana ta sake maida duban ta kan Daneen ta ce "Ba su yi miki bayanin abin da za ki yi cikin gidan nan ba?" Ta tambaya a mamakance. Ba don ta fahimci abin da matar ke nufi ba ta girgiza kai. Matar ta shiga jinjina kai na tsawon sakanni, kafin ta juya ta fice daga ɗakin. Daneen ta bi ta da kallo tana mamakin wane irin gida ne wannan suka kawo kansu? Ko kuwa dama haka en birnin suke? Haka suke saka kaya waɗanda marabar su da babu duk ɗaya ne? Ita dai ba zuwa ta taɓa yi ba, ballantana ta san haka ɗin ne ko ba haka ba. Tana nan zaune bayan shuɗewar wasu mintuna, haka nan ita dai ta kasa samun sukuni da zaman. Ban da bugun zuciyar da ya ɗan yi sanyi yanzu da take ji. Sai kuma yadda kusan rabin hankalinta na kan ɗan'uwanta. Ɗaga dogwayen lashes ɗinta ta yi ta kalli ƙofar ɗakin jin da ta yi an turo. Maimakon ɗazu, yanzu su biyu suka shigo da Aunty. Kallan ta Aunty take yi tun daga ƙasa har sama. Wato duk yadda ake so yarinyar nan ta kai. Ta riga ta san tabbas yau kuɗin da za ta samu suna da yawa. Kyau Allah Ya ba wa yarinyar. Gashi tamkar er india. Duk da yadda take babu wayewa, hakan bai hana kana mata kallo ɗaya ka gano tsantsar tsagoron kyawun komai da Allah Ya ba ta ba. Duk kuwa da ƙananan shekarunta hakan bai hana fitowar dirinta ba. Ita har tunani take idan da ta fi haka girma da ya za ta gan ta? Murmushi ne ya suɓuce mata a kan fuska, lokacin da ta ƙarasa dab da Daneen. Gabanta ya yanke ya faɗi, ta ɗan lumshe kyawawan fararen idanunta da babu kwalli cikinsu. "Ga waɗannan kayan maza ki saka ana jiran mu." Aunty ta faɗa tana watsa mata wani sassanyan murmushi. Ba ta san lokacin da ajiyar zuciya ta ƙwace mata ba, ta saka hannu ta karɓi kayan, ba tare da ta ce komai ba ta shiga duba su. Kaya ne irin na mutane masu mutunci, riga da skirt. Sai a lokacin ta ji hankalinta ya kwanta. 'Wato kenan wannan ta fi waccan matar hankali' Ta raya hakan a cikin zuciyarta. A fili kuma sai ta ce "Toh." Daga haka ta juya banɗaki don sakawa. Har matar nan na ƙoƙarin dakatar da ita, Aunty ta yi azamar dakatar da ita ta ce "Rabu da ita, bi ta a hankali, yarinya ce." Jinjina kai matar ta yi ba tare da ta ce komai ba. "Ki kawo mini ita palourn ƙasa ina jiran ku yanzun." In ji Aunty. "In Sha Allah Rankiyadaɗe." Ta amsa da hakan cike da girmamawa. Daga haka Aunty ta fice daga ɗakin. Babu daɗewa Daneen ta fito daga banɗakin sanye cikin kayan da suka matuƙar karɓi halittar jikinta. Sai jan rigar jikinta take tamkar wadda ta ɗage mata. Duk sai take jin ta a takure, duk da kayan ba kama ta suka yi ba. Sai dai duk da haka sai ta tsinci kanta gefe guda tana jin daɗi. A rayuwarta tana son sabon kaya, shi ya sa duk lokacin da Inna-wuro ta siya musu sabon kaya farin cikinsu na ranar daban yake. A hankali ta ɗaga idanunta ta kalli matar da ita ma ita take kalla, daidai lokacin da ta ce "Yawwah, mu je koh?" Ta faɗa tana murmushin da ya sa Daneen sake kallan ta. Don za ta iya cewa wannan shi ne karon farko da ta ga murmushinta tun shigowar ta ɗakin. Ɗaukar mayafin da ke ajje Daneen ta yi, ta lulluɓa kamar yadda suka saba a ƙauyensu, idan sun tashi saka mayafi musamman da sallah. Ba tare da ta ce komai ba ta bi bayan matar suka soma tafiya. Tafiya mai ɗan tsayi suka yi, kafin suka isa wani ƙaton palour. Kai tsaye matar ta afka ciki, har lokacin Daneen na bayanta suka shige cikin ɗakin. Ƙaton palour ne irin sosai ɗin nan. Aunty na zaune daga gefe can kan wata kujera. Ya yin da wasu maza su huɗu ke zaune kowa a kan kujera mabambanta. "Hajiya ga ta." Matar nan ta faɗa kanta a ƙasa. Ba kuma ta jira amsar Aunty ba ta fice daga ɗakin. Neman waje Daneen ta yi ta zauna tana jin yadda ƙirjinta ke bugawa. Kafin ta kai ga cewa komai Aunty ta dubi waɗannan gabza-gabzan manyan mutanen da ke zaune gaban ta. Waɗanda a shekaru a ƙalla gaba ɗayan su za su ba wa 40 baya. "Ga haja nan fa, kai tsaye ku faɗi farashi ba sai an ɓata lokaci ba. Kun san sabgogi sun yi mini yawa." Ta faɗa tana murmushi. Ita dai Daneen ta yi ƙwam, don kwata-kwata ba ta fahimci inda zancen Auntyn ya dosa ba. Amma haka nan kawai kamar ɗazun ta kasa sukuni. Ta ma rasa wanne irin aiki aka ɗauke su ne ita kam. Gaba ɗaya zuba wa Daneen ido suka yi na tsawon mintuna. Kowanne na kallan duk wata halitta ta jikinta da za su iya hasashe, tun da tana lulluɓe ne cikin mayafi. Wani daga cikinsu ya gyara zama, yana murmushi ya ce "Na karɓa a 500k." Duk tunaninsa za su bar masa ita ne, su ce ta yi ƙanƙanta. Don shi ƙanƙantarta ya soma gani, ya kuma san dukkansu ma za su gan ta. Kuma idan aka yi sa'a ya same ta tabbas zai huta da kyau, don shi kaɗai ya san abin da ya hango. Sai dai tun kafin ya ajiye zancen nasa, wanda ya fi kusa da shi ya ce "Na ƙara 200k a kai." Cike da mamaki ya kalle shi yana ji tamkar ya miƙe ya masa duka, sai dai maganar da ya ji daga ɗaya gefen nasa ita ce ta sanya shi juya wa jiki a sanyaye. "Na karɓa a 900k." "Na cike ya zama 1million." Ya yi ƙarfin halin faɗa don so yake ba sai an ja da nisa ba kawai su bar masa yarinyar ya tafi da ita ƙasar da zai tafi su shana a can. Haka suka dinga yi, kamar waɗanda ke siyan kaya. Idan wannan ya ji wani ya kere su, sai wannan ya ƙara kuɗi masu yawa. Har zuwa lokacin da duk suka yi shiru bayan da ɗaya daga cikinsu ya faɗi kuɗin da ya kere su matuƙa. Abin ya ba wa Aunty nishaɗi, don haka ba ta so aka tsaya a iya nan ba. Ta so sun cigaba da tayawa kuɗin da za ta samu su yi ta hauhuwa. Amma duk da haka, yau ɗin ta samu kuɗi masu yawa ta dalilin Daneen. "Kar ku damu za a kawo wasu kayan ko zuwa gobe ne." Aunty ta faɗa tana kallan waɗanda suka miƙe. Ɗaya ne kawai ya iya amsa mata, ya yin da ragowar ficewa kawai suka yi. Wanda ya yi nasarar biyan kuɗin da suka shallake na kowa ya ce "Sai haƙuri fa, kara wa da ni sai an shirya." Ya ƙare yana murmushi. Ita dai Daneen gaba ɗaya duk wani ruwan kanta ya tsotse, jikinta ya yi sanyi, ya yin da duk wasu abubuwa da ke faruwa cikin ɗakin ke sake ruɗa ta, suke kuma tunkuɗa kwanyarta cikin tunanuka barkatai. 'Anya kuwa?' Ta tambayi kanta tana jin yadda zuciyarta ke bugawa kamar za ta faso ƙirjinta. Ita dai ta ji suna maganar kaya, haja, amma kuma ba ta ga wasu kaya a wajen ba. Hasalima idan maganar kaya za su yi, ba ta ga amfanin wanzuwarta a wajen ba. "Za ki ji Alert yanzu, abin da ya rage kawai ki ba ni yarinya." Murmushi Aunty ta yi kana ta ce "Ba ni da matsala da kai, ai kai nawa ne. Yarinya kuma ga ta nan. Maza tashi ki bi shi shi ne zai samar miki aikin." Aunty ta faɗa tana taɓo Daneen. Wani tsinke wa da gaban Daneen ya sake yi ya faɗi shi ne ya sanya ta saurin runtse idanunta tana faɗin "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Mutumin ya sake bin Daneen da kallo lokacin da ta ɗago idanunta ta kalli Aunty. "Shi zan bi?" Ta tambaya kamar wadda ba ta ji abin da Auntyn ta faɗa ba. Don kar shakku ya shiga zuciyar Daneen ɗin ya sanya Aunty faɗin "Eh, shi zai kai ki gidan da za ki dinga yi wa aiki, kar ki damu." Shiru ta yi na en wasu sakanni kafin ta sake ɗaga ido ta kalli Aunty. Abin da yake ta mata yawo a ƙwaƙwalwa shi ne ya sa ta buɗe baki ta ce a sanyaye "Ƙanina Ameer." Ta faɗa cikin sanyayyiyar muryarta. Mutumin da ya yi nasarar biyan kuɗin da suka take na kowannensu ya wani lumshe ido yana jin yadda sanyayyiyar muryar Daneen ke neman kashe shi a zaune. "Don Allah tashi ki kira mini ƙanin nata mu tafi." Ya faɗa yana miƙewa. Kallan sa Aunty ta yi ta ce da mamaki "Da ƙanin nata za ku tafi?" "Rabu da ita, kira mini shi, shi ma za a samar masa aikin yi. Ki yi da jiki please." Ba ta sake cewa komai ba, ta ɗauki wayarta ta bayar da umarnin fito da Ameer da ke can ɓangaren mazan gidan. Babu daɗewa kuwa sai ga shi wani ya rako shi, lokacin har sun fito waje, mutumin na ƙoƙarin shiga motarsa ya yin da Daneen da tunane-tunane ke ta shigar ta tana tsaye daga gefe. Sai a lokacin ta saki murmushi tana kallan Ameer, shi ma murmushin ya maida mata yana ƙarasawa ya kama hannunta ya ce "Adda." "Uhmm Ameer." "Har na yi kewar ki Addatah, na ɗan wannan lokacin." Ya faɗa yana murmushi. Hannunta ta kai ta ja kumatunsa tana faɗin "Ni ma haka ɗan'uwa." Daga haka babu daɗewa, suka shiga motar mutumin. Daneen na gaba, ya yin da Ameer ke baya. Ya shiga motar ya tayar, babu ɓata lokaci suka fice daga gidan. .. A parking space na gidan ya yi parking na motarsa, kai tsaye palourn Dadaji ya wuce, yana cikin shigar ƙananan kayan da suka matuƙar yi masa kyau. Kansa babu komai sai tulin sumar da Allah Ya ba shi mai matuƙar kyau da ɗaukar idanu. Cikin nutsuwa da tafiyarsa mai cike da mazantaka ya ƙarasa ɗakin Dadaji, bakinsa ɗauke da sallama. Ya yi mamakin hayaniyar da ya ji tana tashi tun kafin ya ƙarasa cikin ɗakin. Sai dai duk da haka bai fasa shiga ba, ya shige cikin ɗakin. "Wa alaika salam. Barka da zuwan Tareeq." Dadaji ta faɗa tana kallan sa. Sassanyan murmushin da ya kan daɗe wa bai yi shi ba ya wanzu a kan fuskarsa. Wanda idan ba sanin ainahin yadda fuskarsa take ka yi ba, ba za ka ɗauka murmushin ya yi ba. "Dada ji." Ya faɗa lokacin da ya nemi waje ya zauna a kan kujerar ɗakin. "Hala dai koro ka aka yi da farar yammar nan." Murmushi ya yi mai sauti yana gyara zamansa ya ce "Dada jiii." Ya faɗa yana jan ƙarshen sunan nata. Kafin ta kai ga amsawa ya ce "Hayaniyar me nake ji ne?" Kallan inda zai sada ka da cikin gidan Dada ji ta yi kana ta ce "Kar ka nuna kamar ba ka san abin da ke faruwa ba mana." Girgiza kai ya yi da mamaki shimfiɗe a kan kyakkyawar fuskarsa. Gane abin da yake nufi ne ya sanya Dada ji faɗin "Ba gobe ne Alhassan zai dawo ba?" Cike da mamakin dai ya cigaba da kallan Dada ji. Bayan shuɗewar wasu sakanni ya ce "Abeey zai dawo, amma Maama ba ta sanar da ni ba? A taƙaice ma dai babu wanda ya sanar da ni. Rashin muhimmancin nawa ya kai haka?" Ya tambaya a nutse yana kallan Dada ji. "A'ah, kar ranka ya ɓaci Tareeq. Duk na gida ne suka zo fa. Ƙannen mahaifinka ne kaɗai cikin gidan nan ba na waje ba." "Sultanah ba ta shigo ba?" Ya kawar da waccan maganar ya kawo wannan. "A'ah ta shigo babu daɗewa, uwarta ta aiko kiran ta za ta taya ta aiki. Ka san ita ma tana can tana shirye-shiryen dawowar Abeeyn naku." (Don en gidan gaba ɗayansu ba dai takatsantsan ba, musamman a kan abin da ya shafi cimarsu. Shi ya sa duk girman gidan nan babu mai dafa abinci, sai dai en aiki masu yin wasu ayyukan. Amma duk wani abu da ya shafi cikinsu su suke yi da kansu. Ko dai su iyayen su yi, ko kuma 'ya'yan su yi. Ko a ɓangaren Dadaji ma da take uwar masu gidan, ba ta da mai dafa mata abinci. Daga ɓangaren matan ɗan nata ake kawo mata. Ko kuma Sultanah ko Hidaya wata ta je ta girka mata idan tana free.) Jinjina kai Tareeq ya yi kafin ya miƙe daidai lokacin da yake faɗin "Bari na je, zan kira Abeeyn zuwa dare In Sha Allah." "Toh Allah Ya yarda. Ɗazun nan ma Jawahir ke tambayarka." Har ya soma tafiya sannan ya ce "Ki gaida ta, ina sauri ne." Daga haka ya fice daga ɗakin. Kai tsaye inda ya ajje motarsa ya nufa, yana tafe yana waya da Sultanah da ya sanar da ita za su yi maganar tun da yanzu da baƙi a gidan kuma tana aiki. Sosai ta yi wa yayan nata godiya kafin suka yi sallama. Har ya buɗe ƙofar motarsa yana ƙoƙarin shiga, sai kuma ya dakata idanunsa a kan wayarsa. Kusan mintuna wajen nawa yana kalla, kafin ya rufe motar kai tsaye ya koma cikin gidan. Part ɗinsa ya wuce a ɗan hanzarce zuciyarsa cike fall da saƙe-saƙe. ... A bakin wani tafkeken restaurant ya yi parking na motarsa, Daneen da Ameer suka bi shi da kallo lokacin da ya juya ya kalle ta ya ce "Ku yi haƙuri ina ɗan zuwa, ba daɗewa zan yi ba." Jinjina kai kawai Daneen ta yi, don a lokacin ji take bakinta ya yi mata nauyi. Buɗe motar ya yi ya fice kai tsaye ya shige cikin restaurant ɗin. Bayan wasu sakanni Daneen ta juya ta kalli Ameer ta ce "Guduwa za mu yi Ameer." "Me ya sa Adda?" Ameer ya faɗa da mamaki. "Kawai tafiya za mu yi Ameer, hankalina ya kasa kwanciya da mutanen nan, duk yadda aka yi akwai wani abun da suke ɓoye mini." Ta ƙare maganar muryarta a raunane. "Amma na ji ya ce gidan aikin ze kai mu." "Ameer zuciyata ta kasa samun sukuni, tun fitowar mu daga gida har zuwa yanzun. Yanzu kuma da zuwan mu gidan nan faɗuwar gaba ta ƙi bari na, duk kuwa da addu'ar da nake ta yi. Ina ganin babu alkhairi zuwan mu gidan nan. Da ƙyar idan haɗuwar mu da mutanen nan alkhairi ce. Kawai mu gudu mu bar su." Shiru Ameer ya yi yana cigaba da nazarin yayar tasa. Duk wasu alamomin ruɗewa sun bayyana a kan fuskarta, yadda take magana kuma kana gani ka san daga zuciyarta ne take faɗa. Don haka cikin son ba ta ƙwarin gwuiwa ya ce "Toh mu tafi ɗin. Amma ta ya ya?" Ba tare da ta amsa wa Ameer tambayar da ya yi mata ba ta sanya hannunta a kan murfin ƙofar da ke gefen ta. Cikin karambani ta ga wajen da tabbas ya fi kama da inda za ta taɓa ƙofar ta buɗu, kamar yadda ta ga ya yi da zai fita. Sai dai kwata-kwata ta ƙi buɗuwa. Ta taɓa ta taɓa ta ƙi buɗuwa. Ameer da ya lura da yadda take yi, shi ma ya taɓa gefensa amma shiru ta ƙi buɗuwa. "Ko dai ba haka ake ba?" Girgiza kai Daneen ta yi kafin ta ce "Tabbas nan ya taɓa da zai fita. Sai dai kuma idan ana iya kulle wa kamar ƙofa." "Eh kuma haka ne." Ameer ya faɗa yana jinjina kai. "Toh yanzu ya za mu yi?" Kafin Daneen ta kai ga tunanin komai ko ta ce wani abun, aka buɗe ƙofar aka shigo. Mutumin ya ajje ledar hannunsa kafin ya tashi motar suka cigaba da tafiya. Shiru ne ya wanzu cikin motar, kowa da abin da yake saƙa wa cikin ransa. Har zuwa lokacin da ya sake tsaida motar, kamar ɗazun ya sake juyawa ya kalli Daneen ya ce "Minti 1 gimbiya." Wannan gimbiyar da ya ambata ba ƙaramin kaɗa 'ya'yan cikin Daneen ya yi ba, cikin ƙanƙanin lokaci bugun zuciyarta ya ƙaru. Ta yi ƙarfin halin jinjina kai kawai. Hakan ne ya sa ya fice daga motar. "Adda ya yi nisa fa." Ameer ya faɗa yana kallan Daneen da ke zaune tamkar wadda aka dasa. Duk da yadda tsoro ke shigar ta, wanda ya yi silar saka wa jikinta ya soma rawa. Hakan bai hana ta runtse idanunta ba, ta kai hannunta kan ƙofar ta sake tura wa cike da takatsantsan, cikin zuciyarta tana fatan kamar yadda suka tsammata su yi tozali da hakan, wato su ga ya bar motar a buɗe, a maimakon ɗazu da ya kulle su. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 14 Cikin sa'a kuwa sai jin ƙofar ta yi ta tafi, ta juya cikin wani irin farin ciki ta kalli Ameer. Farin cikin da ya gaza ɓoyuwa har a kan fuskarta. Ba tare da ta ce masa komai ba, ya saka hannu ya buɗe ƙofar gefen sa. Cikin sakannin da basu wuce biyar ba suka fice daga cikin motar. Ko tsayawa su rufe ma ba su yi ba, gaba ɗaya hankalinsu ya yi gaba. Don haka da gudu suka soma barin wajen hannayensu cikin na juna. Kasancewar duhun magribh ya mamaye garin ya sanya waɗanda ke lura da su ɗin ba su da yawa. Musamman da ya kasance hankalin da dama ya tafi kan masallacin da suke ƙoƙarin zuwa. Sai da suka yi mugun nisan da suka san sun yi wa mutumin nan nisa kafin suka suka soma rage gudun. Wani irin numfashi a gurguje a gurguje Daneen ke saukewa saboda yadda numfashinta ke sarƙewa. Hannun Ameer ta sake riƙowa tana dawo da shi baya lokacin da ta zube a wani waje tana ji tamkar numfashinta na ƙoƙarin barin gangar jikinta. "Ameer.. na.. gaji." Ta harhaɗa kalmomin ta faɗa hannunta dafe da ƙirjinta. Dawowa ya yi ya zauna cikin matuƙar tashin hankali yana kallan fuskarta ya ce "Sannu Adda. Ƙishirwa kike ji?" Ya tambaya yana kallan yadda take cigaba da ajje taggwan numfashi tana wani lumshe idanunta. Jinjina kai ta yi, har lokacin idanunta na lumshewa suna kuma buɗewa. "Ki zauna a nan kin ji? Bari na je na samo miki ruwa." Ya faɗa yana miƙewa. Hannunsa ta sake riƙowa tana girgiza kai ta ce "A'ah kar ka je ko'ina, zauna kawai." Girgiza kai Ameer ya yi tausayin er'uwar tasa na kama shi ya ce "A'ah Adda, ƙishirwa kike ji. Ki zauna a nan don Allah kar ki je ko'ina ruwa kawai zan samo miki yanzun nan kin ji?" Be jira ta amsa ba, ya zame hannunsa ya bar wajen. Cigaba da zama ta yi kanta na kallan ƙasa tana ji tamkar ba za ta ƙara ƙwaƙwƙwaran minti 1 a wajen ba ran da ke gangar jikinta zai bar ta. Babu daɗewa kuwa sai ga Ameer nan ya dawo a guje hannunsa ɗauke da robar ruwa, ya ƙarasa da sauri yana kiran sunan Addar tasa. "Tashi ki sha kin ji?" Ya faɗa yana ɗago ta, babu musu ta tashi zaune sosai. Ta karɓi ruwan duk da yadda hannunta ke rawa, ta kai baki. Tun da ta kafa ba ta sauke ba sai da ta shanye tass, kafin ta ajje tana sauke ajiyar zuciya. "Sannu." Shi ne abin da Ameer ke ta maimaitawa yana kallan Daneen ɗin jikinsa a matuƙar sanyaye. Yana daga cikin halayensa shiga damuwa duk lokacin da Addar tasa ba ta da lafiya, shi ya sa ma ya fi so shi ya yi cutar a kan ita ta yi, don ta fi shi shan wahala. Musamman kuma a yanzu da suke su kaɗai babu Inna-wuronsu. Lallai sun yi matuƙar kuskuren baro ƙauyensu. Be ƙarasa tunanin ba ya jiyo muryar Daneen na faɗin "Mu je mu yi Sallah, bacci nake ji Ameer." Kallan inda suke ya yi, idan har be yi kuskuren fahimta ba, kamar cikin kasuwa ne nan ɗin suke. Kuma lokacin da ya je nemo mata ruwa, ya ga mutane mata da maza ƙanana, almajirai da sauransu kowa ya kama waje kamar dai masu shirin kwana a wajen. Kenan idan haka ne su ma za su iya kwana a cikin kasuwar? Ya tambayi kansa yana cigaba da kallan cikin kasuwar. "Sai dai mu kwana a cikin kasuwar nan Adda, na ga ba mu kaɗai ne mara sa gida ba. Idan ya so zuwa gobe sai mu nemi inda za mu samu kuɗin koma wa ƙauyenmu." Da sauri Daneen ta ɗaga idanunta ta kalli Ameer. Wato duk abin da ya faru tunani yake za su kuma shiga wani gidan su nemi aiki? Ta girgiza kai kafin ta ce a sanyaye "Kowanne aiki za mu yi ba za mu kuma shiga gidan mutane ba. Gwara mu yi ko da aikin ƙarfi ne a cikin mutane mu karɓi kuɗinmu mu tafi." Ta ƙare tana ɗan sauke numfashi a hankali. Jinjina kai Ameer ya yi cike da amincewa da zancen Addar tasa. .. A ɗaya ɓangaren kuwa, hannunsa ɗauke da wata leda ya fito. Tun kafin ya ƙarasa inda motar take ya ji gabansa ya faɗi, saboda yadda idanunsa ke masa wani mummunan gizo. Haka dai ya ƙarasa, sai dai tun kafin ya kai ga buɗe motar ya hangi yadda gaba ɗaya ƙofofi biyun motar suke a buɗe. Cike da fargaba ya ƙarasa, ya duba cikin motar, babu kowa. Ya sake dubawa duk da ya riga da ya tabbatar ba sa cikin motar. Juyawa ya shiga yi ko Allah zai sa ya hango inda suka nufa, sai dai ko ƙurarsu bai gani ba. Hannunsa har rawa yake lokacin da ya fiddo da wayarsa ya shiga neman layin Aunty, har wani huci yake fitar wa daga bakinsa. "Yarinyar nan ta dawo ne?" Ya tambaya duk da a karan kansa sai da ya ji tambayar da ya yi kamar rainin hankali ce. "Ban gane ba? Wace yarinya kenan?" "Yarinyar da na siya yanzu a wajen ki mana." Ya ba ta amsa a fusace. Cikin tashin hankali da rashin sanin abin yi Aunty ta miƙe tsaye, tana jin faɗuwar gaba na ziyartarta. Da ƙyar ta iya ƙarfin halin faɗin "Ba tare kuka fita ba?" Be ce komai ba sai katse wayar da ya yi. Ta sauke wayar daga kunnenta tana bin ta da kallo. Kenan yarinyar guduwa ta yi ko kuwa? Amma shi wane irin sake ya yi da har ta gudar masa, bayan uban kuɗin da ya biya ya siye ta? Soma zagaye ɗakin ta yi tana cigaba da tunane-tunane, ita ba komai ke ci mata tuwo a ƙwarya ba, illa yadda za ta maida masa da kuɗinsa idan har da gaske yarinyar guduwa ta yi. .. A wajen su Daneen suka cigaba da zama har lokacin da dare ya yi. Suna ganin yadda mutane ke cigaba da kai komo, har zuwa lokacin da garin ya yi shiru. Sai er hayaniyar da ba a rasa ba. Zuwa lokacin Daneen ta lulluɓe jikinta cikin mayafi saboda wani irin sanyi me shiga jiki da ke ta ratsa ƙasusuwanta. Ameer dai na gefen ta, yana kallan abubuwan da ke wakana a gari, zuwa can dai sai ya juya ya kalli er'uwar tasa kafin ya juya ya cigaba da kalle-kalle. "Addaneen." Ya faɗa yana kallan ta. Ɗaga lumsassun idanunta da suka buɗe da ƙyar saboda wani irin ciwon kai da ya zo ya mata dirar mikiya lokaci guda ta yi ta kalle shi, ba ta iya amsawa ba sai kallan sa kawai da ta yi. "Ko ba ki da lafiya ne?" Ya tambaya yana kallan ta sosai. Jinjina kai ta yi, tana sake haɗe jikinta waje ɗaya ta ce a hankali "Zazzaɓi nake ji Ameer." Cikin lokaci ƙanƙani fuskarsa ta sauya, ya shiga kallan ta cike da tausayawa "Sannu Adda kin ji?" Ya faɗa bayan ya gyara zamansa. Jinjina kai ta yi tana ƙaƙalo murmushi ta wanzar a kan fuskarta. Haka suka cigaba da zama a wajen har cikin dare daga ita har shi babu wanda ya runtsa. Ita zazzaɓin ya hana ta baccin, ya yin da shi kuma tausayin er'uwarsa ne ya hana shi yi. Kafin safiya sosai zazzaɓin ya sake rufe Daneen, Ameer ya rasa yadda ze yi. Wajen ƙarfe 8 na safe ne, zuwa lokacin en kasuwa duk sun soma fitowa. Ya kalli Daneen ya ce "Adda mu bar wajen nan tun da masu wajen sun fara zuwa." Kallan cikin kasuwar ta yi da idanunta da suka ɗan ƙanƙance kafin ta ce "Toh." Daga haka ta soma ƙoƙarin miƙewa. Sai kuma Ameer ya katse ta da faɗin "Zauna a nan bari na je na samo miki abinci." Girgiza kai ta yi da sauri tana faɗin "A'ah mu je kawai." Duk da yadda take jin jikinta hakan be hana ta ƙoƙartawa ba, Ameer ya taimaka mata suka bar wajen. Sun yi tafiya me ɗan tsayi babu laifi, suna tafiya suna tsayawa saboda ta huta. Har zuwa lokacin da ta shiga sauke numfashi lokacin da take zaune a wani waje. "Ameer na gaji." Ta faɗa a wahalce. "Kina jin yunwa?" Ya tambaya don ya san dole za ta ji, dan ko shi ma yana jin ta. Yanzu kam babu musu ta jinjina kai. Ya kalli inda suke, ya sake kallan inda suke kafin ya maida duban sa kanta ya ce "Ki jira ni a nan komai daɗewar da zan yi zan nemo mana abin da za mu ci kin ji? Kar ki je ko'ina a nan zan zo na same ki." Kallan sa ta yi na tsawon sakanni kafin ta ce "Ameer ina za ka je?" "Zan je ko ma ina ne Adda, yunwa kike ji. Zan yi aiki kowanne iri ne don na ga kin samu abin da za ki ci. Ki jira ni kin ji?" Ya sake faɗa yana kallan ta. "Na fi so ko'ina za ka je ina kusa da kai Ameer, ba na son ka tafi wani wajen ni kuma ina nan." "Adda ba ki da lafiya ai shi ya sa. Ki jira ni kin ji?" Sai ta jinjina kai kafin ta ce "Allah Ya tsare." "Ameen." Ya amsa da hakan da murmushi ɗauke a kan fuskarsa. .. A ɗaya ɓangaren kuwa, ya shafe fiye da rabin awa a toilet ɗin, bayan ya sakar wa kansa ruwa mai ɗumi. Duk kuma daɗewar da ya yi tunani ne jibge a cikin ƙwaƙwalwarsa. Zuwa can dai ya ɗauro tattausan towel ya fito ɗakinsa. Be bi ta kan wayarsa da ke ajje kan gado ba, kai tsaye ya ƙarasa gaban mirror ya shiga sake kwantar da sumar kansa da ko da ze kwana nawa ba tare da ya taɓa ta ba ba za ta nuna ba. Sai dai da yake ya riga ya saba, duk lokacin da ya fito daga wanka ya kan gyara ta yadda take sake zama haɗaɗɗiya, mai matuƙar birgewa. Be jima ba ya ida shiryawa cikin wata tattausar jallabiya da ta matuƙar ɗaukar kalar fatarsa. Kasancewar ba zai sake fita daga gidan ba ya sanya shi jan laptop zuwa kan gadonsa, saƙon nan dai ya sake nemowa ya shiga yana sake karanta abin da ke rubuce da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai kamar wanda ke koyar yadda ake karatun. Ya yi nisa ba tare da ya ankara ba sai ji ya yi an turo ƙofar ɗakin. Da sauri ya ɗaga idanunsa ya kalli mai shigowar. Wata ƙatuwar ajiyar zuciya Maama ta sauke lokacin da ta ga ɗan nata zaune da alama cikin ƙoshin lafiya. Saurin rufe laptop ɗin gabansa ya yi, yana ajje ta gefe ya soma ƙoƙarin sakko wa daga kan gadon. Ƙarasawa Maama ta yi. "Tareeq ina ka shiga ne tun ɗazu ina kiran wayarka ba ka ɗagawa? Ka san fa ba na son hakan, kana tayar mini da hankali wallahi." Maama ta faɗa tana kallan sa bayan ta nemi waje ta zauna. Sai da ya duba inda ya ajje wayarsa, ya janyo ta ya kunna ta. Tarin missed calls ɗin da ya gani danƙare a kan wayar tasa ya sanya shi ɗaga kai ya kalli Maama. "Ki yi haƙuri Maama, na ajje wayar ne ban san kin kira ba." "Wani abin kake yi ne?" Sai da ya ɗan kalli laptop ɗin kafin ya shafi gefen kansa ya girgiza kai "A'ah, na ɗan duba wani aiki ne. Ki yi haƙuri Maama." Ya sake faɗa a karo na biyu. Murmushi ta yi kafin ta gyara zama ta ce "Shi ke nan, za mu iya yin wata magana?" Jinjina kai ya yi kana ya buɗe bakinsa ya ce a nutse "Eh." Sai da ta ɗan ja wasu sakanni kafin ta ce "Ina takardun nan na Diyana?" Shiru ya yi kamar mai tunanin wani abin, kamar ba ze ce komai ba, sai kuma ya ɗan fesar da iska daga bakinsa kana ya ce "Na ƙona su gaba ɗaya." Kallan sa Maama ta cigaba da yi, ya yin da ya basar duk da ya san shi take kalla. "Toh Allah Ya ƙara kiyayewa. Amm kaa ga gobe idan Allah Ya kai mu Abeeynku zai dawo, Umman Jawahir kuma tana ta cigaba da yi mini maganar haɗa ka da Jawahir. Tun hankalina bai kwanta da hakan ba, har kuma ya zo ya kwanta. Tun da ko babu komai dai Jawahir er'uwarka ce. Don haka nake so na ji daga bakinka, idan dai har ka amince zan sanar wa da Abeeynku wannan maganar sai a san abin yi. Idan kuma ba ka amince ba shi ma ka sanar da ni, amma abin da nake so ka tuna shi ne ni mahaifiyarka na amince da haɗin ɗari bisa ɗari, musabbabin hakan kuma saboda kasancewar Jawahir er'uwarka." Tun da Maama ta soma magana yake kallan ta har ta ƙarasa. Ya yi mamaki matuƙa da ya kasance Maaman da kanta take yi masa zancen wata mace bayan abin da ya faru kwata-kwata ba a daɗe ba. Kamar ta san me yake tunani, sai cewa ta yi "Kar ka damu Tareeq, na yi hakan ne sanin cewar a kurkusan nan ba lallai ka iya samun nutsuwar fitar da matar aure ba. Shi ya sa na amince da wannan al'amari. Ka yi tunani sosai zuwa gobe sai mu yi magana." Maama ta ƙare maganar tana kamo hannunsa ta riƙe har lokacin tana kallan sa. Ɗan dafe ƙirjinsa da ya yi masa nauyi ya yi, kafin ya janye hannunsa cikin sakannin da ba su wuce uku ba, ya ɗan lumshe idanunsa kafin ya buɗe a kan Maaman, yana tunanin abin da ya kamata ya ce mata. Shin ya amsa da cewar ya amince bayan abin da ya faru tsakaninsa da Diyana? Ko kuwa ya ce be amince ba saboda fidda rai da ya yi a kan mace. Idan ya buɗe baki ya ce ya amince ya kuma kasance ita kanta Jawahir ɗin halin su ɗaya da Diyana fa? Tun da ita ma Diyanan duk daɗewar da suka yi bai taɓa sanin halinta na zahiri ba sai ana dab da ɗaura musu aure. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 15 Cigaba da kallan sa Maama ta yi tana jira ta ji ko ze ce wani abu. A hankali ya zuro ƙafarsa daga kan gadon zuwa ƙasa. Ya miƙe a kan ƙafafun nasa kafin ya ce "Shi kenan Maama, duk abin da kika yanke wa rayuwata daidai ne. Amma tun da kina son ji daga bakina In Sha Allah zan yi istihara duk yadda ake ciki zan sanar da ke. Babu damuwa za ki iya sanar da Abeey kafin lokacin." Ya ƙare maganar fuskarsa babu yabo babu fallasa. Cikin ransa fata yake ka da Maaman ta sake jan maganar da nisa, don kuwa har ta ginshe shi. Ba don ma Maaman da kanta ke masa maganar nan ba, da ko haɗin kai ba ze bayar ba. Murmushi ne ya wanzu a kan fuskar Maaman, ta miƙe ita ma kafin ta ce "In Sha Allah. Allah Ya tabbatar mana da abin da ya fi zama alkhairi." "Ameen." Ya amsa a saman laɓɓansa yana kai hannunsa guda cikin sumar kansa ya shafa. Maama ba ta ƙara mintuna masu yawa cikin ɗakin ba, ta fice ta bar shi tsaye cike da saƙe-saƙe. .. "Yah Tareeq ka yi haƙuri, ban san wane irin kallo za ka mini ba, ban kuma san wane irin hukunci za ka yi mini ba, idan na sanar da kai cewa na kamu da soyayyar abokinka Abdoul. Ka yi haƙuri Yaya." Hidaya da ta karanta saƙon da Sultanah ta gama rubutawa ta tura. "Wallahi Hidaya ina tsoron fushin Yah Tareeq." Sultanah ta faɗa kamar za ta yi kuka. "Ke ki dena jin tsoro, ina tare da ke fa." Hidaya ta faɗa tana riƙo hannun Sultanah, duk da ita kanta tana jin tsoron, amma don ta ba wa 'yar'uwarta ƙwarin gwuiwa ya sa ba ta nuna ba. Ganin alamar blue tick da suka yi ne ya sanya kusan a tare suka gyara zama. Sultanah ta haɗiye wani yawu da ƙyar tana jin yadda bugun zuciyarta ke ƙaruwa. Ba ta san yadda za ta yi da zuciyarta ba, ba ta san lokacin da ta faɗa ƙaunar Abdoul ba. Farga kawai ta yi dumu-dumu cikin wata matsananiyar ƙaunarsa irin mara adadi ɗin nan. Tun tana ganin za ta iya jurewa har ta kasa, don kuwa yanzu haka ita kaɗai ta san irin zafin da zuciyarta take yi, na rashin isar da saƙon zuciyarta gare shi, har zuwa wannan lokacin. Ta san halin yayansu, shi ɗin mai damuwa da damuwarsu ne, sai dai ba ta sani ba, ko a wannan karon ma ze bi bayanta ne bayan ta sanar da shi tana ƙaunar abokinsa. Ba ta sani ba ko ma hukunci ne ze biyo baya. "Har yanzu fa be yi reply ba Hidaya." Sultanah ta faɗa ganin da ta yi bayan wajen minti 5 da ganin saƙon da Tareeq ya yi amma har yanzun be yi reply ba. "Ze yi ne Sulty, mu ƙara lokaci." Hidaya ta faɗa a sanyaye, saboda yadda ta ji gaba ɗaya ɗan ƙwarin gwuiwar da ta yi nasarar haɗa shi yana ƙoƙarin zagwanyewa. A ɓangaren Tareeq kuwa ya karanta saƙon nan ya fi sau uku. Daga ƙarshe dai sai ya sake dubawa don tabbatarwa da gasken Sultanah ɗin ce ta turo masa saƙon. 'Tabbas ita ce' Ya tabbatar wa da kansa hakan yana sake kallan saƙon. Shiru ya yi na tsawon lokaci, tabbas abin ya matuƙar ba shi mamaki, ya kuma ɗaure masa kai. Be taɓa tunanin ƙanwar tasa za ta iya yin hakan ba, har kuma ta sanar da shi. Sai dai kuma da ya nutsa tunaninsa sai ya ga abin da Sultanah ta yi kamar shi ne daidai. A matsayinsa na yayanta mai ƙoƙarin samar mata mafita a kowanne yanayi ne, shi ya kamata ta sanar wa da abin da ke faruwa. Abu na biyu kuma shi ɗin aminin Abdoul ne, wanda ze iya amfani da kasancewar hakan wajen samar wa 'yar'uwarsa mafita. Sauka ya yi daga Whatsapp ɗin kai tsaye ya nemo number Abdoul ya kira. Ringing 1_2 ya ɗauka, kafin Tareeq ɗin ya ce komai Abdoul ya ce "Barka Aboki." "Yawwah, kana lafiya?" Tareeq ya faɗa hannunsa na kan goshinsa yana ɗan murzawa. "Alhamdulillahi. Ya ake ciki?" In ji Abdoul. "Kana gida ne?" "A'ah, yanzu na ɗan fita ne karɓo saƙo." Sai da Tareeq ya ɗan gyara zaman sa sannan ya ce "Ohk, gobe za ku shigo ai?" Murmushi Abdoul ya yi kana ya ce "Eh mana, da wuri ma kuwa In Sha Allah." "Allah Ya nuna mana, akwai wata muhimmiyar magana da nake so mu yi da kai." "Ikon Allah! Wacce magana ce wannan?" Abdoul ya faɗa cike da mamaki. Ɗan murmushi ne ya wanzu a kan laɓɓan Tareeq kafin ya ce "Kai dai za mu haɗu." "Malam ka sanar da ni kawai please." "Sai kuma ka yi ai." Tareeq ya faɗa cikin basarwa. "Kai fa dama ɗan rainin hankali ne wallahi.." Abdoul ya dakata daga haka, kafin ya yi ƙwafa kana ya ɗora da faɗin "Amma ya na iya.. Allah Ya kai mu." Murmushi mai sauti Tareeq ya yi kana ya amsa da "Ameen." a nutse. Daga haka suka yi sallama. ** Washe gari sosai gidan ya tashi da karɓar 'yan'uwa na kusa. Waɗanda ke ta shirye-shiryen dawowar Alhaji Alhassan Dikko. Jawahir da ba su kwana a gidan ba, da sassafe suka diro gidan don tarbar Abeeyn. Tun safe duk suna sashen Dada ji, Maama, Hidaya, Sultanah, Jawahir da Mamanta. Maamin Sultanah ce kaɗai tun wayewar garin kwata-kwata ba ta shigo ba. Duk kuwa da cewa ayyukan da ake gabatarwa sun fi yawa a sashen Dada ji ɗin kamar yadda aka saba. Duk kuma da cewa ta san duk en gidan suna sashen nata, hakan be sanya ta zuwa ba. Tana can sashenta tana shirya wa mijinta abubuwa na musamman. Babu kuma daɗewa ƙawarta, aminiyarta Hajiya Zulaiha ta iso gidan. Mata ga Aminin Abeey, kuma mahaifiya ga Abdoul Aminin Tareeq. Su biyu suka iso gidan, Abdoul ya wuce sashen Tareeq, ya yin da Umma ta wuce kai tsaye sashen Maami. Da sallama ya shiga palourn, idanunsa a kan Tareeq da ya kwantar da kansa a kan kujera idanunsa a lumshe. Ya ɗora hannunsa ɗaya a kan fuskarsa, wanda hakan ya yi nasarar kare idonsa guda ɗaya. Sai da Abdoul ya ƙarasa ya zauna a gefen sa ya ce cike da mamaki "Tareeq." Da sauri Tareeq ya buɗe idanunsa, don kwata-kwata be ji shigowar Abdoul ba. Idanunsa da suka ɗan janye saboda daɗewar da suka yi a lumshe ya sauke a kan Abdoul. Ya ja wani nannauyan numfashi da ya fito daga ƙirjinsa a takure kafin ya ce "Yaushe ka shigo?" "Bayan ka yi nisa a tunanin." Tareeq ya faɗa yana karantar yanayinsa. Iska kaɗan Tareeq ya fesar daga bakinsa kafin ya gyara zamansa, ba tare da ya ce komai ba, har lokacin da Tareeq ya ce "Anya kuwa lafiya Aboki?" Ya faɗa yana sake karantar yanayinsa. Cikin basarwa Tareeq ya ce "Lafiya mana, wani abu?" Ya ƙare har lokacin dai cikin basarwa. "Ko dai har yanzu maganar Diyana ne?" Be san lokacin da tsaki ya suɓuce masa ba. "Me kake so na ce maka ka yadda na daɗe da cire Diyana a babin rayuwata? Allah ɗaya ne koh? Toh ina rantse maka da shi, ko kaɗan babu damuwar Diyana a tattare da ni. Ina ga zuwa yanzu ya kamata ka amince da ni." Numfashi Abdoul ya sauke kana ya ce "Shi kenan, amma tabbas idan babu wannan akwai wani abu da kake ɓoye mini." Da sauri Tareeq ya girgiza kai. Ba tare da ya kalli Abdoul ba ya ce "Kar ka damu kanka, babu wani abu." "Amm.." Abdoul ya buɗe baki ya fara magana Tareeq ya yi saurin katse shi da faɗin "Maganarmu.." Girgiza kai Abdoul ya yi, jin yadda ya basar da zancen. A ransa yana saƙa tabbas ko ma mene ne, idan ta yi tsami ze ji. Idan dai har abin da ya kamata ya sani ne, toh ya san Tareeq ɗin ze sanar da shi ko ba yanzu ba. Hakan ne ya sanya shi faɗin "Ina jin ka." Gyara zama Tareeq ya yi, sai dai kafin ya ce komai wayarsa ta soma ƙara. Ya janyo ta yana kallan mai kiran nasa. "Yaya wai ka fito muna palourn Dada ji." Hidaya ta faɗa, bayan Tareeq ya amsa wayar. "Ohk." Ya amsa da hakan, yana mayar da kallan sa kan Abdoul ya ce "Tashi mu je, Abeey na dab da iso wa." Ya faɗa yana miƙewa. Be jira Abdoul ya ce komai ba ya shige bedroom ɗinsa. Bayan shuɗewar wasu mintuna ya fito, suka fice daga sashen gaba ɗaya. ... A ɓangaren Daneen kuwa, da mayafin da ke jikinta ta yi amfani wajen nannaɗe fiye da rabin jikinta. Ta kifa kanta a kan gwuiwarta tana lumshe idanunta. Kewar mahaifiyarta take matuƙa gaya, kewarta ce ke ratsa duk wata gaɓa ta jikinta. Yanzu ko tana ina?Tana can tana tunanin suna zaune a ƙauyensu suna jiran ta? Tana can ita ma duk inda take hankalinta yana kansu, kamar yadda nasu hankalin ke kanta? A nutse ta sake lumshe idanunta tana jin yadda wani bacci ke ƙoƙarin fizgarta. Haka ta yakice shi, don duk wani hankalinta yana kan Ameer. Ta kwashe fiye da awa ɗaya tana ta saka ran jin muryar Ameer ya yi mata magana, amma shiru. Tun tana cigaba da kwanciya har ta gaji ta tashi zaune, ta shiga rarraba manyan idanunta da suka ɗan faɗa, cikin rashin sanin abin yi. Wasa wasa, har bayan wajen awa uku, babu Ameer babu alamarsa. Har ba ta san lokacin da ta miƙe a kan ƙafafunta ba, duk da jikinta da babu ƙwari hakan be dame ta ba, burin ta kawai ta san yadda za ta yi ta je ta nemo inda Ameer ya yi, ya bar ta a nan tana ta jiransa. Har ta soma takawa don barin wajen, kamar wadda aka tsikara kuma sai ta dakata. Ta sake kallan inda take tsaye, sai ta mayar da ƙafarta baya. Gaba ɗaya tunaninta ya tafi kan Ameer, idan kuma har ta bar wajen nan, kai tsaye ba ta san inda za ta nufa ba. Bayan kuma ya faɗa ya sake jaddada mata da kar ta je ko'ina komai daɗewar da ze yi ta jira shi. Idan ta bar wajen kuma shi ya dawo be gan ta ba fa? Daga nan me zai faru? Cikin sauri ta shiga girgiza kanta kamar wadda ke magana da wani. Cikin matuƙar sanyin jiki ta koma da baya ta zauna inda ta tashi. Tana nan zaune har ta ji an soma kiraye-kirayen Sallahr Azahar, amma babu Ameer babu dalilinsa. Gaba ɗaya wani tunaninta ya tafi kan inda ya tsaya. Haka zalika tambayar da ke ta mata yawo a cikin kwanya ita ce 'Ina ya tsaya? Me ya sa har yanzu bai dawo ba?' Cikin sakannin da ba su wuce biyu ba, ta ji bugun zuciyarta ya ƙaru, nan take jikinta ya ɗauki rawa, fararen idanunta tuni suka soma sauya kala, cikin sakanni ƙalilan, hawaye suka taru. Kawai sai ta shiga juye-juye, cikin rashin sanin abin yi, sai ka ce wadda aka cewa idan ta juya ɗin za ta hango shi. Duk kuma lokacin da ta kalli mutanen da ke kaikawo a wajen, sai ta ga kamar za ta hango Ameer ɗin a cikinsu, babu kuma abin da take ji, sai ƙarin faɗuwar gaba, da bugun zuciya. A yi manage da wannan, In Sha Allah gobe ma za ku samu Update. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 16 Kamar idanunta za su faɗo, haka take ci gaba da kallon hanyar da ta ga Ameer ya bi. Zuwa can dai ta miƙe a kan ƙafafunta, ba ta kuma san yadda za ta iya ci gaba da zama a wajen ba, bayan takamaimai ba ta san inda ɗan'uwanta yake ba. Ga shi kuma har an idar da Sallahr Azahar. Sai dai miƙewar da ta yi ya yi daidai da lokacin da muryar Ameer ta daki dodon kunnenta. "Adda." Ai ba ta san lokacin da ta juya da sauri ba. Take idanunta suka sauka a kan Ameer. Wani murmushi mai haɗe da ƙwalla suka wanzu lokaci guda a kan fuskarta. Idan ta ce tana farin ciki ma ɓata baki ne, don kuwa fuskarta kawai za ka kalla ka fahimci tsananin farin cikin da ta tsinci kanta a ciki bayan ganin Ameer. "Ameer ina ka je?" Ta yi tambayar da ke ta ci gaba da yi mata lugude a ka. Murmushi ne ya suɓuce masa kafin ya ce "Aiki na samo Adda, kina zaune zan din ga yin aiki muna samun kuɗi. Mu samu na cin abinci da komai ma, har kuma mu tara na koma wa ƙauyenmu." Ya ƙare yana murmushin dai. Wani sabon murmushin ne ya sake ƙwace mata, ta ce "Da gaske?" Jinjina kai ya yi kafin ya ce "Ehh, amma dai ki zauna ki fara cin abinci yanzu. Ya jikin naki?" Sai da ta harare shi kafin ta ce "Bayan duk ka gama tsoratar da ni." "Wallahi Adda ina can ina tunanin kar ganin na daɗe ki ce za ki je ki nemo ni, in zo kuma ban gan ki ba in shiga 3." Ya ƙare fuska a marairaice. Har ba ta san lokacin da dariya ta suɓuce mata ba. "Mu je mu samu ruwa mu yi sallah tukunna." Ta faɗa. Be musa mata ba, ya amsa da "Toh." ... Tun daga farkon layin idan ka kalla za ka fahimci lallai wani gagarumin al'amari ke faruwa. Saboda yadda motoci ke ta kai-kawo cikin layin, 'yan sanda na ta zagaye, haka zalika mutane na ta kai da kawowa. Kowa ka kalli fuskarsa cikin annushuwa yake, wanda hakan ze alamta maka cewa ko ma mene ne abin da ke faruwa abin farin ciki ne. Tahowar wata ƙatuwar hamshaƙiyar mota da kallo ɗaya za ka mata ka san kuɗinta ba na wasa ba ne, shi ne abin da ya sa masu gadin gidan wangale ƙatuwar ƙofar gidan tun kafin motar ta ƙaraso. Tuni kyakykyawan dattijon mutumin da ke sanye cikin farar shaddar da ta matuƙar yi masa kyau, ta kuma sake bayyana kwarjininsa da kamalarsa ya gyara zamansa. Tun kafin ya ce komai, drivern ya yi hanzarin wangale glasses ɗin motar. Wanda hakan ya ba wa mutanen da ke tsaye suna jiran zuwan Alhajin nasu damar soma ganinsa. Cikin lokaci ƙanƙani fuskarsa ta cika da annuri, ya yi amfani da hannunsa wajen ɗaga musu hannu fuskarsa na cigaba da nuni da yadda ya yi farin cikin ganin su. Alhaji Alhassan Dikko kenan, mutum mai matuƙar kima da mutunci a idon jama'a, mutum mai matuƙar taimako da jiki da dukiyar da Allah Ya ba shi. Mai kirki, mai matuƙar kula da buƙatun mabuƙata, maƙotansa da kuma mutanen gari. Wanda hakan ya saya masa soyayyar mutane da dama, ya kuma ƙara masa kimar da tun tale-tale yake da ita. Har sai da suka dangana da cikin gidan sannan mutane suka haƙura. Daga haka aka rufe gate ɗin bayan motocin da ke bin bayan ta Alhaji Alhassan su ma sun shige cikin gidan. Shi har ya riga ya saba, duk lokacin da ya yi tafiya irin wannan haka mutane ke masa duk ranar da ze sauka a ƙasar. Don kuwa ƙarya ne mutum ya ce be yi kewarsa a en kwanakin da ya yi ba ya ƙasar ba. Saboda yadda ya kasance mutum mai matuƙar kula da duk wanda ke kusa da shi. Duk da kafin ya tafi yana ɗora wani a kan abubuwan da yake yi, amma duk abin da ze yi, ba ze kai wanda yake yi ba. Shi ya sa idan yana nan abubuwa da dama suka kasance na daban, suke kuma tafiya a tsari. Ko a cikin gida ma hakan ce ta kasance, mutanen da ke zaune cikin gidan tuni suka fara zuwa suna kwasar gaisuwa, kamar kodayaushe fuskarsa cike da annuri yake amsa musu. Kai tsaye sashensa ya wuce kamar yadda ya saba, sashen nasa na nan a gyare tsaff-tsaff kamar yadda ya tsammata. A gaggauce ya watsa ruwa a jikinsa kana ya sake shiryawa cikin babbar rigar shadda ita ma fara. Kai tsaye ya wuce sashen Dada ji da gaba ɗaya iyalan nasa ke jiran sa a can ɗin. Ai kuwa cikin matuƙar farin ciki dukka suka tarbe shi lokacin da ya iso. Kowa ka kalli fuskarsa ka san tabbas yana cikin farin ciki. Sai da ya shafe wajen mintina goma, sannan Maami ta iso, ita da Mom Abdoul, ba ta yi tsammanin kai tsaye nan ɗin ze wuto ba. Shi ya sa ta din ga tsumayin ganin inda ze nufa, sai dai shirun da ta ji ne ya tabbatar mata da tabbas nan ɗin ya nufo. Wannan ne dalilin da ya sa ta ɗebo 'yan matan ƙafafunta ta taho, duk da ta so tare suka shigo. Dan da ta san ma ba zai shiga sashenta ba, tun a harabar gidan za ta je ta tarbe shi don su shiga sashen Dadan a tare. Ko minti 5 ba su yi da zama ba, bayan sun yi wa Abeey barka da zuwa, Amininsa Alhaji Bashir ya iso gidan, mahaifi ga Abdoul. Sosai farin cikin Abeey ya daɗu. Bayan kwanaki masu yawa, yau ga shi tare da iyalansa, ga kuma abokinsa ƙwalli ɗaya takk da yake da shi tun yarinta shi ma. Wannan dalilin ne ya ƙara ƙawata zaman nasu. Nan aka shiga hirar yaushe gamo. Kafin zuwa can aka nufi ɗakin da ya kasance na cin abinci, nan cikin sashen Dada ji. Sultanah, Hidaya da Jawahir su ne suka kwaso komai daga kitchen ɗin Dada ji suka jere shi kan dinning ɗin. Abubuwa ne kala-kala masu aji, waɗanda aka yi abubuwan da Abeeyn ya fi so a rayuwarsa. Baƙin-ciki kamar ya kashe Maami, da ta tuna abincinta na can jibge yana jiran Abeeyn. Kenan idan ya zauna ya ci abincin a nan, ita kuma nata ya za ta yi da shi? Ita fa dama wannan tsohuwar tana matuƙar shige mata hanci da ƙudundune, tana yawan kawo mata cikas a cikin al'amuranta. A kusa da Dada ji ya zauna, don babu ƙarya ya yi kewar mahaifiyar tasa. 'Yan matan ba su zauna ba, sai da suka yi serving na kowa kafin suka ja kujera suka zauna. Duk yadda Sultanah ke ƙoƙarin ta jure, ba ta din ga satar kallon Abdoul ba, hakan ya gagara, ta kasa daurewa. Don haka a ɗan fuzge ta din ga satar kallon shi, cike da fatan kar ya kama ta, ko kuma Yah Tareeq ya gan ta, ya tuna be yi mata faɗa a kan abin da ta yi ba. Don kuwa tun da ta ga ya kalli saƙon be ce komai ba, ta san tabbas wani abun yake shiryawa, dalilin kenan da ya sa take jin jikinta a matuƙar sanyaye. Ita dai Jawahir sai sakin murmushi take yi, saboda yadda Ummanta ta sanar da ita Maama ta tabbatar mata da za ta isar wa da Abeey maganarta ita da Tareeq. Ita kuma dama ba ta da wani buri illa na mallakar Tareeq ɗin. Ba tun yau ba, kyawunsa ke matuƙar kashe ta, tana ƙaunarsa ainun, tana matuƙar son kallon kyakkyawar fuskarsa, da kuma irin ƙirar da Allah Ya ba shi. Sai bayan sun gama cin abincin sannan suka koma palourn Dada ji, nan aka cigaba da hira sosai. Sai dai idan dai har abin ya shafi Maama, toh ba za ka ji Maami ta ce komai ba. Don ita hirar ta ta fi kasancewa ne tsakaninta da Hajiya Zulai, da kuma Alhaji Bashir. Duk abin da take Dada ji na lura da ita, ta yi dai kamar ba ta gani ba ne. Don ita kam har ta gaji da yi mata magana a kan halayenta. Maamin wata irin mata ce da lokuta da dama ka kan kasa gane kanta. Ban da haka idan hali mai kyau ne Maama ta fi ta. Amma kuma ita burin ta kawai kowa ya yi harkarsa, ba ta son wani abu ya haɗa ta da abokiyar zaman nata kwata-kwata. Sai ka ce masu zaman gaba, wanda ita Dada ji ba za ta ɗauki hakan ba. Duk da hakan ya fi saka wa su zauna lafiya, amma kuma babu yadda za a yi su zauna babu magana, bayan suna zaune ne cikin gida ɗaya, ƙarƙashin mutum ɗaya. Kuma hakan ya samo asali ne, tun wani ɗan tashin hankali da ya faru tsakanin su, Dada ji ɗin da kanta ta shirya al'amarin, ta ce babu ruwan kowa da kowa. Shi kenan Maami ta riƙe wannan maganar, a cewar ta ai an ce da ita babu ita babu Maama. Ya yin da ta ɓangaren Maama, duk wani abu da ya shafi Maami babu ruwanta da shi, amma tabbas idan suka haɗu za ta mata sallama, da sauran su. Girgiza kai Dada ji ta yi. 'Mace sai ka ce mai zuciyar kafirai, kina abu tamkar ƙaramar yarinya. Toh ai ga mijin naku nan ya dawo, sai ki ci gaba da gaba da abokiyar zaman naki' Ta raya hakan a ranta. Kallon Tareeq Abeey ya yi da ya miƙe yana gyara tsayuwarsa hannunsa ɗauke da waya. "A'ah, Tareeq ina za ka je ne?" Ɗan murmushi ya yi a kan laɓɓansa kafin ya ƙarasa gaban Abeeyn ya tsuguna a gefen kujerar da yake kai ya ce a nutse "Abeey, ina buƙatar fita ta gaggawa." Daga haka suka ɗan yi magana ta tsawon mintina biyu a hankali, wanda babu wanda ze ce ya ji abin da suka faɗa. Kallan Tareeq Abeey ya yi, kana ya ce "Ubangiji Allah Ya tsare, zuwa gobe ma samu mu tattauna." Abeey ya faɗa yana ɗan kafe shi da idanunsa, saboda tabbatar da abin da idanun nasa ke ganar masa a fuskar ɗan nasa. "Ameen Abeey." Ya faɗa yana miƙewa. Sallama ya yi da duka mutanen ɗakin kafin ya fice. Kai tsaye sashensa ya wuce, ya ɗauki abin da ze ɗauka ya fice daga gidan. Ba shi ya dawo cikin gidan ba, sai bayan ƙarfe 12pm. Don haka ruwa kawai ya watsa ya kwanta don yadda idanunsa ke buƙatar bacci. ... "Idan da zaɓi za ka ba ni, toh tabbas zan nemi soyayyar Hidaya ne, saboda Sultanah mahaifiyarta duk da kasancewarta aminiyar Ummeey ina shakkar ta wallahi." Abdoul ya ƙare yana shafa kansa. Dariya Tareeq ya yi jin abin da ya faɗa. Ya ja siririn tsaki kafin ya ce "Amma dai ka ba ni kunya Abdoul.. Amma dai ba wannan ba, ni nan ni ne amininka, kuma ina mai ba ka shawara da ka nemi Sultanah saboda ta fi Hidaya sauƙin kai. Abeey dai shi zai aurar da Sultanah ba Maami ba, idan kuma ba shi ba ni ne. Don haka kar ka ji komai, duk da ma Maami na da kirki wani lokacin, amma fa idan ka fahimce ta." Jinjina kai Abdoul ya yi irin a yatsinen nan, cike kuma da rainin hankali ya ce "Ehh, haka fa." Wani murmushi Tareeq ya saki ba tare da ya ba wa yanayin Abdoul ɗin muhimmanci ba ya ce "Uhmm." Gyara zama Abdoul ya yi, bayan ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Ka tabbatar?" Jinjina masa kai Tareeq ya yi ba tare da ya ce komai ba. Don haka Abdoul ya ce "Shi kenan, zan gwada.. Allah Ya ba ni sa'a." Ya ƙare irin a marairaicen nan. Cike da jin daɗin yadda burin ƙanwar tasa ke neman cika ya janyo wayarsa cikin basarwa ya ce "Bari na soma sanar da ita, don ta fi ɗaukar abin da muhimmanci." Da sauri Abdoul ya riƙo hannunsa yana girgiza kai ya ce "A'ah kar ka kira ta, kar ya zamana hakan ya koma tirsasawa, gwara ka bar ni da kaina na yi mata magana, na san duk wani abu da ke ranta za ta fito ta faɗa mini ba tare da wani shakku ko tsoro ba, tun da ba zan nuna mata ta hanyarka na biyo ba." Sauke ajiyar zuciya Tareeq ya yi, irin 'Shi kenan toh' ɗin nan, kafin ya ce "Allah Ubangiji Ya tabbatar da alkhairi. Amma tsaya ka tabbatar ba karɓar tayin nan ka yi saboda mutuncinmu ba? Za ka so ƙanwata kamar yadda nake fatan ita ma za ta so ka? Ka san ba na son a wulaƙanta mini er'uwa." Dariya sosai Abdoul ya yi, kana bayan ya dena ya soma faɗin "Tareeq manta wane ne kai kake a wajena, ka manta duk wani abu da ya shafe ka dole ne a wajena na so shi? Toh ka manta da wannan son, ba irin shi zan yi wa Sultanah ba, nata na daban ne, matuƙar dai ta amince da ƙudurin da zan je mata da shi." Wani irin sanyi ne ya ji yana ratsa shi, ya lumshe kyawawan idanunsa yana jin har cikin zuciyarsa farin ciki mara misaltuwa. Wato har abada ba zai daina alfahari da kasancewar Abdoul amininsa ba. Fata yake hakan ya zama silar farin cikin er'uwarsa na har abada. Yana fatan hakan ya zama dalilin sake ɗorewar zumuncinsu da su Abdoul na har abada. Yana fatan wannan abu ya zama ɗaya daga cikin abin da zai zama cikin tarihin gidan Iyalan Dikko na sama-sama. .. Washe gari ma suna tashi da safe a wajen da suka kwana jiya, Ameer ya yi sallama da Daneen ya tafi inda ya sami aikin. Ita kuma ta ci gaba da zama a wajen, saboda gurin ya fi security, kuma babu mutane da yawa, can kuwa maza ne kawai, kafin ka ga mace ma aiki ne. Shi ya sa ya ce ta zauna, idan ya gama aikin sai ya dawo. Ranar ma be dawo da wuri ba, sai da ya kai kamar jiya sannan ya dawo da abinci mai rai da lafiya. Kamar jiya ma cikin farin ciki ya kawo wa 'yar'uwar tasa abincin, ɗan kuɗin da ya samo suka yi amfani da su wajen abubuwan buƙata, ya yin da Daneen ta ɗauki wani abun ta ajje musu, wanda za ta din ga ɗauka kullum ta ajiye har su kai adadin wanda suke buƙata su nufi ƙauyensu. Haka Daneen da Ameer suka ci gaba da kasancewa a wannan wajen. Da safe bayan sun gama abin da za su yi Ameer zai tafi wajen aiki, ita kuma ta ci gaba da zama a wajen har ya dawo. Sai dai ga mamakin Daneen, sai ta lura da tun ranar da Ameer ya samu aiki, da kuma washe gari da yake dawowa cikin matuƙar farin ciki, be sake dawowa kamar haka ba. Tun daga ranar duk lokacin da ya dawo jikinsa a matuƙar sanyaye yake. Babu wannan nishaɗin, sai tarin damuwa da kuma tunani. "Wai Ameer me kake ɓoye mini? Me yake faruwa?" Daneen ta faɗa tana kallansa, cike da sake nazarinsa. Da sauri ya ɗaga idanunsa ya kalle ta a nutse kafin ya buɗe baki ya ce "Babu komai Adda.. Wani abun kika gani?" Girgiza kai ta yi cikin ɗan faɗa ta ce "Shi kenan, amma ka sani daga yau ba za ka sake zuwa wajen aikin nan kai ɗaya ba. Idan ba haka ba kuma sai dai ka dena zuwa gaba ɗaya. A haƙura da tara kuɗin kawai." Be san lokacin da ya ɗaga idanunsa ya kalle ta ba, daidai lokacin da ƙirjinsa ya wani mahaukacin bugawa. Sai ya shiga girgiza kai kamar wani ƙadangare kafin ya ce "A'ah Adda, kin san gidan biredi babu mata, ba ze yiwu ki ce za ki din ga zuwa ba. Idan ba haka ba za su kore ni gaba ɗaya." "Eh, gwara su kore ka, idan dai har za ka ci gaba da dawowa da damuwa." Sauke numfashi Ameer ya yi, ya lumshe idanunsa masu kama da na Daneen, ya rasa me yake damun ƙwaƙwalwarsa. Gaba ɗaya kansa a hargitse yake. Idan da zai dena zuwa da sai ya fi kowa farin ciki. Sai dai kuma yadda yake ji tamkar ana azalzalarsa da zuwa wajen ya ji kwata-kwata ba ze iya daina zuwa ba. Kai ko da ma Daneen ɗin ce ta ce ya dena zuwa, a yadda yake jin gaba ɗaya tunaninsa da nutsuwarsa ta tafi can ɗin ba ya tunanin zai iya amincewa da hakan. Sai dai kuma gefe guda yana ji shi kansa da zai iya hana kansa dena zuwa da ya dena. Wannan dalilin ne ke sanya shi jinsa tamkar wani zautacce, saboda yadda tunani da ra'ayi biyu ke ta masa yawo a cikin kwanya, kwanyarsa shi ɗaya. Kuma duka hankalinsa ya kwanta da su. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 17 Ƙura masa idanu Daneen ta yi, tana so ta ga ko za ta iya karantar abin da yake ɓoye mata, don tabbas tafarar ɗaya ta fahimci hakan. Sai dai ba ta ce masa komai ba, har zuwa lokacin da ya dawo daga mara armashin tunaninsa ya sauke idanunsa a kanta. Duk kuma sai ya so ya duburbuce saboda ganin tana masa wani kallo da ya fi kama da na tuhuma. "Adda." Ya faɗa a sanyaye. Da sauri ta girgiza kai "Kar ka kira sunana, kawai ka buɗe baki ka faɗa mini abin da ke faruwa, idan ba haka ba na faɗa maka ba za ka sake zuwa ba." Ta ƙare maganar da iya gaskiyarta har lokacin tana kallon sa. A sanyayen dai ya sake faɗin "Ki yi haƙuri Addatah, shi kenan ki shirya mu din ga tafiya tare ai shi kenan koh?" Sai a lokacin ta yi murmushi kafin ta ce "Toh damuwar ta mene ne?" "Gajiya ce fa kawai." Ya faɗa bayan ya langaɓar da kansa. "Ai dai mun kusa koma wa wajen Innarmu In Sha Allah." Jinjina kai Ameer ya yi yana murmushi, sai dai bai ce komai ba. Kamar yadda ya faɗa kuwa, washe gari tare suka tafi wajen aikin shi da Daneen. Suna tafe suna hira, tana kallon duk inda suka wuce, saboda ita ba ta taɓa zuwa wajen ba. Don iyakincinta cikin kasuwa, idan suna buƙatar wani abu ta shiga ta siyo musu, daga nan ta koma inda suke ta zauna. Sun yi tafiya mai ɗan tsayi kafin Ameer ya kalle ta ya ce "Ki zauna a nan, kin ga cikin layin nan a nan gidan biredin yake, zan je idan na gama sai na fito mu tafi." Kallon layin ta yi kamar mai son hango gidan biredin. Sai dai ba ta hango ba, amma ko babu komai nan ɗin zai fi mata kwanciyar hankali tun da tana kusa da ɗan'uwanta. Don haka ta gyara tsayuwarta ta ce "Toh shi kenan Ameer, Allah Ya ba da sa'a, ina jiran ka fa." Ta ƙare a hankali tana kallon sa. "Toh Adda bari na je." Ya ƙare yana ɗan murmushi, wanda ya yi nasarar lulluɓe tulin damuwar da ke danƙare a zuciyarsa. Wadda ta hana zuciya da ƙwaƙwalwarsa sukuni. "Allah Ya tsare." Ta sake maimaitawa tana bin sa da kallo har ya bar wajen a sanyaye. Sai da ya ɓace mata da gani sannan ta dena kallon sa, gaba ɗaya wani burinta ya tafi kan yadda za su yi maza su koma wajen Innarsu. Ba za ta sake barin ɗan'uwanta ya din ga aikin wahala ba. Tana fata ta yi kuɗi a rayuwarta, Ameer ya ji daɗi. Haka zalika Innarsu ma ta ji daɗi. Gaba ɗayansu su dena aikin wahala. Zama ta ci gaba da yi a wajen, ta yi shiru tamkar mai tunani. Sai dai zuwa can idan ta gaji sai ta ɗaga kai ta kalli abin da ke faruwa a gefenta sai kuma ta maida fuskarta kan cinyarta. A nan ta yi sallah, ko bi ta kan wani abinci ba ta yi ba, ta ci gaba da jiran Ameer. Zuwa can kuwa sai ga shi ya dawo. Ya wanzar da murmushi a kan fuskarsa da ta sauya daga da, wadda take koyaushe cikin matuƙar annushuwa, zuwa wata daban. Sai dai duk iya ƙoƙarinsa yake don kar Addar tasa ta fahimci wani abin. Duk da ya san hakan ma ba mai yiwuwa ba ne. Sai dai inda Allah Ya taimake shi, yadda damuwar da ke shimfiɗe a kan fuskarsa ta ta'allaƙa ta da gajiyar aiki kamar yadda ya sanar da ita. Ko minti 2 ba su ƙara ba, suka yi gaba zuwa wajen da suke zama, suka kuma saba. A nan suka ci abinci sannan suka ci gaba da zama. A 'yan kwanakin da suka biyo baya, sosai al'amuran Ameer ke ci gaba da sauyawa, ba shi da aiki sai tunani da kuma damuwa. Har ta kai yanzu ba ma ya iya ɓoye damuwar a gaban Daneen ɗin saboda yadda ya gajiya. Duk wani ƙwarin gwuiwarsa ya ƙare. Ji yake kamar ƙwaƙwalwarsa za ta yi bindiga idan ya cika tunani. Dare ne, domin kuwa wajen ƙarfe 10pm ne. Daga shi har ita babu wanda ya soma ƙoƙarin neman wajen kwanciya. Ita ta yi shiru ne kawai tana kallon sa, mamaki take yadda take ganin shimfiɗaɗɗiyar damuwa a kan fuskarsa amma ya ƙi faɗa mata. Bayan hakan ba halinsa ba ne. Ta rasa gane abin da ke damun Ameer ɗin, wanda ya sauya shi cikin kwanaki kaɗan haka. Ta rasa yadda za ta yi, don haka kawai sai ta zuba masa idanu ta ji ko zai sanar da ita damuwarsa. Sai dai abin da ma ta lura da shi, tamkar hakan ƙara ba shi lasisin yin tunani ne ta yi. Don kuwa kwantar da kansa ya yi jikin wani gini da ke gefensa ya yi shiru. Daga inda take zaune take ci gaba da kallon sa, tunani barkatai cikin ƙwaƙwalwarta. Ba tun yanzu ba take hango shi yana gyara zamansa, daga baya ma sai ya tashi daga inda yake ya sauya waje. A hankali ta miƙe jin da ta yi gabanta ya ɗan faɗi, kai tsaye ta ƙarasa inda yake. "Ameer." Ta faɗa bayan ta dafa hannunta a kan kafaɗarsa. Ɗaga jajayen idanunsa ya yi ya kalle ta hannunsa dafe da cikinsa. Ta bi hannun nasa da kallo ba tare da ta lura da idanunsa ba ta ce "Me yake damun ka Ameer?" Ta faɗa a ɗan gigice da muryarta da ke rawa. Girgiza kai ya yi kafin ya ce "Adda cikina ke ciwo." "Cikinka kuma?" Ta faɗa tana riƙo hannun nasa. Jinjina kai ya yi yana sake dafe cikinsa. Cikin matuƙar ruɗewa da rashin sanin abin yi Daneen ta ce "Me ka ci Ameer? Me ya sami cikin naka?" "Babu abin da na ci fa." Ya faɗa har lokacin hannunsa a kan cikinsa. Da sauri ta shiga girgiza kai, daidai lokacin da idanunta suka cika taff da ƙwalla ta soma faɗin "Me ya sa kake mini haka ne Ameer? Me na maka? Me ya sa kake ta ɓoye mini abubuwa da dama? Me ya sa ka tsiro da wasu halaye bayan da ba haka kake ba? Idan wani abu ya same ka me zan faɗa wa Inna? Ba za ka buɗe baki ka yi mini magana ba Ameer?" Ta ƙare maganar lokacin da wasu kyawawan hawaye suka sauka a kan kuncinta. Abin da ya matuƙar ba wa Daneen mamaki shi ne yadda Ameer ya fashe da kuka, kuka kuma ba irin na wasa ba, kuka sosai tamkar wanda ake duka ko ake yi wa wani mummunan abu. Maimakon ta ɗan ji sassauci, sai kukan nasa ya sake dugunzuma mata hankali, cikin rawar murya ta ce "Na shiga uku Ameer, faɗa mini abin da ya faru? Cikin ne?" Ta tambaya a ruɗe tana sake riƙo hannun da ke riƙe da cikinsa. "Ki yi haƙuri Addatah, ki yi haƙuri kin ji?" Shi ne abin da ya faɗa har lokacin yana kuka tamkar mace. Cikin ƙanƙanin lokaci jikinta ya ɗauki rawa, muryarta da ta shige ta yi ƙoƙarin janyo ta wajen faɗin "Sanar da ni abin da ke faruwa Ameer, na shiga uku." Ta faɗa tana jin yadda wani bala'in tashin hankali ke ci gaba da rikito mata. Sai da ya sake girgiza kai, idanunsa da suke a lumshe ya buɗe, ya ɗora su a kan Daneen, ya sauke hannunsa da ke kan cikinsa, duk da yadda yake jin cikin nasa tamkar ba a jikinsa yake ba, amma ya yi ƙarfin halin kamo hannayenta duka biyun. Muryarsa har wani sarƙewa take yi lokacin da ya soma faɗin "Adda ki yi haƙuri, na rasa yadda zan yi, ban san ya zan yi na raba kaina da mutanen nan ba, ban san tsautsayin da ya haɗa ni da su ba. Ban san abin da ke damun ƙwaƙwalwata ba. Ni dai kawai na ji ba na son rabuwa da su, ko da zan yi ƙoƙarin hakan ma ba zan iya ba. Adda maza ne su ba mutum ɗaya ba ba biyu ba, kullum sai sun yi amfani da ni Adda. Ba su taɓa ce mini kar na sanar wa da kowa ba, amma tamkar an rufe bakina na kasa faɗa miki, na kuma kasa hana kai kaina inda suke. Na kasa barin ki ki san inda nake zuwa Adda, ina tsoron kar ki hana ni zuwa kuma in ƙi hanuwa. Don ji nake yanzu haka in da zan wayi gari cikin ƙoshin lafiya toh zan koma wajen nasu. Kullum cikin kuka nake Adda cikin dare. Na rasa yadda zan yi, na rasa mene ne mafita. Na rasa abin da ke mini daɗi. Ina jin tamkar ƙwaƙwalwata ba ta jikina, ina ji tamkar wani noti da ke kaina ya kwance. Adda na rasa abin da ke mini daɗi. Ni da kaina fa nake kai kaina wajen su, me yake damu na? Anya kuwa ni ɗin ne? Ya zan yi ne ni kam? Na rasa abin da ke mini daɗi. Na rasa ya zan yi, don Allah Adda ki yi haƙuri ki sanar da ni abin da zan yi, ki yi haƙuri kar ki ɗauki matakin da ba zan iya jurewa ba. Zuciyata zafi take mini, ina ji ina numfashi da ƙyar. Ki yafe mini Adda." Ya ƙare maganar yana sake fashewa da wani marayan kuka. A hankali ta shiga zame hannunta daga cikin na Ameer, idanunta da suka ƙafe ƙaff, babu hawaye ko ɗigo a kan fuskarsa. Kallon sa kawai take yi tamkar wadda ta soma ganinsa a yau ɗin nan. Wani irin gudu zuciyarta take, wanda ya mugun wuce ƙa'ida. Don kuwa idan da za ka kalli ƙirjinta a lokacin, za ka iya ganin yadda zuciyarta ke bugawa a haukace. Kallon sa kawai take yi, shin da gaske abin da take ji daga bakin Ameer gaskiya ne yake faɗa mata? Ameer Ameer dai nata shi ne yake faɗin wasu maza suna amfani da shi? Idan dai har ta fahimci abin da yake nufi kenan wasu sun yi lalata da shi? 'Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un' Ta ambata a fili muryarta na wani irin karkarwa tamkar yadda jikinta ke wani mahaukacin ɓari tamkar wadda ke shirin zube wa a ƙasa. Dalili kenan da ya sanya Ameer ya ɗaga idanunsa da suka yi jajur, har sun yi wani luhu-luhu ya kalle ta, ita ma shi take kalla. Ya girgiza mata kai kafin cikin sanyi ya furta "Ba laifina ba ne Adda." Maganar da ya yi, ita ce ta ba wa kukan da ya maƙale mata damar fitowa, ta shiga rera shi kamar za ta shiɗe. Zube wa ta yi a kan ƙafafunta ta shiga rera shi kamar ranta zai fita. Ita kam wannan wace kalar baƙar rana ce a wajenta? Wace kalar mummunar rana ce wannan? Wanne kalar bala'i ne wannan ya shigo cikin rayuwarsu ita da ɗan'uwanta? 'Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un' Ta sake maimaitawa, daidai lokacin da Ameer ya ƙaraso inda take zaune ya zube shi ma a kan ƙafafunsa. A karo na barkatai ya sake furta "Ki yi haƙuri Addatah, ban san yadda aka yi hakan ta faru ba. Kin fi kowa sanin halin ɗan'uwanki." Maganarsa da ke fita a wani hahharɗe ta daki dodon kunnenta. Sai a lokacin sannan ta samu ƙwarin gwuiwar soma magana. "Me ya sa za ka mana haka Ameer? Me ya sa ba ka bari mun mutu da yunwa da rashin gata ba, a kan wannan abin. Iyee Ameer? Ba gwara mu mutu ba, da ka jefa kanka cikin wannan ɗabi'ar. Ameer me ya sa ka yi mana haka? Me ya sa ka canja daga Ameer ɗina da na sani? Me ya sa haka Ameer?" Ta ƙare hannunta a kan kwalar rigarsa tana ja kamar za ta cire rigar. Tun daga ƙasan zuciyarta maganar take fitowa, muryarta cikin kuka tamkar ba za ta iya ƙarasa maganar ba. Yanzu kam kukan Ameer babu sauti, sai hawayen da ke ta tsere a kan kuncinsa. "Ki kashe ni kawai Adda, ko na dena jin zafin da nake ji a cikin zuciyata. Ki ɗauki wani abun ki caka mini a ƙahon zuciyata Adda, na san tabbas zan ji sassaucin abin da nake ji a zuciyata. Ni kaɗai na san me nake ji, ni kaɗai na san irin raɗaɗi da zafin da nake ji Adda. Don Allah ki kashe ni ko na huta, ke ma ki huta da wannan baƙin cikin da na ja miki, ko hakan ze sa Inna kar ta ji labarin nan." Ya ƙare a raunane yana jujjuya kansa idanunsa na wani irin lumshewa kamar me shirin yin bacci. "Haɗuwata da su kawai zan iya tunawa. Ban san abin da suke yi ba, har na tsawon kwana biyu. Sun ce mini aikin biredi ne zan din ga yi. Tun daga ranar kamar an sauya ni, shi ne suka soma amfani da ni, ban san yadda aka yi na kasa ƙin komawa gobe ba. Duk da yadda zan ji a zuciyata Allah zai kama mu, zai kuma yi mana azaba, hakan ba ya hana ni zuwa wajen su kullum. Kuma kullum cikin kuka nake Adda, amma ni.. na rasa ma me zan ce." I zuwa lokacin ta dena kukan kallon sa kawai take tana nazarin maganganunsa. Lokacin da ya kai ƙarshe, sai ta ji wasu guntayen hawaye sun sauko mata a kan fuskarta. Ta ja ɗan'uwanta ta rungume tana jin wani sabon kukan na taho mata. Ko babu komai ta san zai samu sassauci a kan abin da yake ji, ko babu komai ze yi kuka a kan kafaɗar 'yar'uwarsa ya ji tabbas fa yana da wajen da zai iya ɗora kansa ya yi kuka. Ai kuwa sai ya lumshe idanunsa yana barin hawayen na sauka a kan fuskarsa tamkar za su ƙare. Sun shafe wajen mintina goma a haka kafin ta ji yana sauke numfashi da gudun gaske. Ta yi azamar sanya hannu ta ɗago shi tana kallan sa. "Ameer." Ta faɗa ganin yana ci gaba da lullumshe idanunsa. Fahimtar abin da take nufi ne ya sanya shi faɗin "Cikina, da ƙirjina Adda.. Ina ji tamkar za su bar jikina. Wani abu nake ji ya tokare mini numfashina." Ya faɗa yana ci gaba da kokawa da numfashinsa. Da sauri ta gyara zamanta tana faɗi cikin rawar murya "Kar ka damu, za ka samu sauƙi. Kwanta ka yi bacci kaa ji?" Ta faɗa tana taimaka masa, ta kwantar da kansa a kan cinyarta. Runtse idanunsa ya yi ruff, hannunsa na kan ƙirjinsa da yanzun ya fi masa ciwo a kan cikinsa. Ji yake tamkar duk wasu abubuwa da ke cikin ƙirjinsa suna dab da fitowa fili saboda wani irin yanayi da tun da Inna ta haife shi bai taɓa jinsa ba. Shiru Daneen ta yi tana kallon yadda yake sauke numfashi a wahalce, ta runtse idanunta da hawayen suka ƙeƙashe, suka ƙafe gaba ɗaya. Haƙiƙa yau ɗin wata rana ce wadda ba za ta taɓa mantawa da ita ba, yau ɗin wata rana ce da ta kafa musu mummunan tarihi cikin tarihin rayuwarsu. Abin da suke ji a nesa da su sai ga shi ya faru a kan ƙaninta, rabin jikinta. Su kuwa waɗannan mutanen su waye su? Waɗanne irin mugaye ne su, da suka rasa wanda za su lalata sai ƙaramin yaro Ameer? Daga zuwa neman aikin yi don su samar wa kansu abin da za su ci da wanda za su yi guzurin tafiya ƙauyensu? Don mugupnta da rashin tsoron Allah sun lalata mata rayuwar ƙani? Ba sau ɗaya ba ma har fiye da a ƙirga? Sun kuma yi amfani da wani abun can wajen rufe masa baki da jan hankalinsa zuwa wajen, duk da wayo da takatsantsan irin na Ameer? 'Hasbunallahu wa ni'imal wakeel' Ta faɗa a kan laɓɓanta tana runtse idanunta har lokacin bugun zuciyarta bai koma daidai ba. Lallai ko ma mene ne har abada sun gama neman aiki daga ita har ɗan'uwanta, gari na wayewa za su ɗauki hanyar tafiya ƙauyensu da ƙafafunsu, idan ya so in Allah Ya yi su isa suna a raye, idan kuma bai ƙaddara ba Allah Ya ji ƙan su. Haka wannan baƙar ranar ta ƙare suna zaune a wajen, ko wajen da take kwana ba ta koma ba, haka ta ci gaba da zama, kan Ameer na kan cinyarta har zuwa wayewar gari. Sai dai kafin gari ya gama yin haske jikin Ameer ya yi wani irin mahaukacin zafi, ban da karkarwa babu abin da yake yi, da ƙyar yake iya buɗe idanunsa saboda zafin ciwo. Zuwa lokacin Daneen ta gama ruɗewa, tun tana ƙoƙarin danne kukan da ke taho mata har ta kasa. Ta bar shi ya fito saman fuskarta da ke shimfiɗe da damuwa fall. "Sannu Ameer." Ta sake faɗa a karo na barkatai. Da kansa ya yi amfani wajen ɗaga mata alamar ya ji ta. Sai dai jikinsa babu abin da ke sake yi sai ɗaukar uban zafi mara misaltuwa. "Adda ina ji kamar ana daddatsa mini ƙashi, zuciyata ta yi mini nauyi." Ya faɗa a sanyaye har lokacin idanunsa a lumshe. "Sannu Ameer, ko dai mu je asibiti ne?" Ta yi maganar kamar mai tambaya, sai dai kuma a zahiri ba jiran amsar wani take nema ba. Wannan ne dalilin da ya sanya ta miƙewa cikin mutuƙar rikicewa ta nemi taimakon wasu don a ɗaukar mata Ameer ɗin ta kai shi asibiti. Kwata-kwata hankalinta bai kawo mata abin da asibitin za su iya nema ba, ita dai kawai ta ga Ameer ɗin a asibiti a duba shi a ba shi magani ya warke shi ne burinta, inda kuma hankalinta ya tafi. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 18 Da taimakon wasu bayin Allah aka saka mata Ameer cikin napep ɗin da aka tarar mata. Ta yi saurin faɗa wa ciki tana jin gaba ɗaya jikinta na ci gaba da rawa, tamkar ma ƙafarta ba za ta ɗauki nauyin jikinta ba. Babu ɓata lokaci drivern ya ja motar suka soma tafiya ba tare da ya jira jin ta bakinta ba. Saboda ko ba ta masa bayani ba, ya san idan ba asibiti ba babu inda za su tunkara a yanzu. Don haka ya yi hanyar asibitin da ya san ya fi kusa da inda suke. Yadda numfashin Ameer ke wani irin rikicewa, yana kai masa cafka cikin ficewar hayyaci, shi ne abin da ya sake tsorata Daneen. Ta rungumo shi cikin jikinta hawaye na gangaro wa a kan kuncinta, cikin wata dashashshiyar murya ta furta "Don Allah Ameer kar ka yi mini haka.." Ta kai ƙarshen maganar tana sake sauke idanunta a kan fuskarsa da idanunsa ke kusan a rufe, hannunsa ɗaya na sautin zuciyarsa, ya yin da numfashinsa ke ci gaba da ƙoƙarin barin gangar jikinsa. Abin da ya sanya mai napep ɗin ƙara gudu kenan, don ƙoƙarin ganin sun isa asibiti a ceci ran wannan bawan Allahn da shi kansa yake ganin tamkar abubuwan da yake na fitar rai ne. A haka suka ƙarasa cikin asibitin, Ameer na rungume jikin Daneen, gaba ɗaya ta rasa sukuni, daga zarar ta janyo wannan addu'ar sai ta ji ta kufce mata, hawaye kuwa har ta gaji da tsaida su, ban da sauka kan kuncinta babu abin da suke yi. Zuciyarta na ci gaba da bugun da take ji tamkar za ta faso ƙirjinta ne ta fito. Mai napep ɗin da kansa ya sauka ya ɗaukar mata Ameer da har lokacin ba ya cikin hayyacinsa. Wani irin numfashi yake yi a wahalce, idan ka gan shi ma ba za ka ɗauka yana da rai ba, saboda yadda gaba ɗaya jikinsa ya saki. Sai dai idan ka kalli fuskarsa, ko kuma ka ƙura wa ƙirjinsa ido, shi ne za ka ga yadda yake ɗagawa a wani irin hankali. Bayansa Daneen ta bi da sauri, kamar yadda shi ma yake saurin. Tana tafe tana goge fuskarta da hannayenta, ba tare da ta san abin da take furtawa ba take ci gaba da faɗin abin da ya zo mata a rai. "Ameer kar ka yi mini haka.. Ka tashi ka warke mu koma wajen Innarmu don girman Allah." Ire-iren maganganun nan take ta furtawa tana bin bayan mai napep ɗin. Har zuwa lokacin da suka isa emergency. Cikin gaggawa aka karɓi Ameer saboda yadda jikinsa ya yi mugun tsamari. Daneen ta zube a kan gwuiwoyinta tana sake fashewa da wani sabon kukan. Ta jima a wajen, ba tare da ta san abin da ya ci gaba da faruwa ba. Ita dai burinta ɗaya ta ji halin da ɗan'uwanta yake ciki. "Ki yi haƙuri, In Sha Allah zai samu sauƙi. Addu'a za ki yi masa ba kuka ba." Ta jiyo muryar mai napep ɗin nan yana faɗa mata. A hankali ta ɗan ɗaga jajayen idanunta ta kalle shi, da ƙyar cikin dashashshiyar murya ta ce "Na gode sosai, Allah Ya saka maka da alkhairi." Ta faɗa tana lumshe idanunta. "Babu komai." Ya faɗa, kafin ya gyara tsayuwarsa ya ce "Bari na wuce, Allah Ya ƙara sauƙi. In Allah Ya yarda zuwa an jima zan shigo." "Toh." Ta faɗa a sanyaye. Ko minti 5 bai yi da tafiya ba, aka nemi ganin waɗanda suka kawo Ameer. Da wani irin sauri Daneen ta miƙe ta shiga office ɗin likitan. Gwaje-gwaje aka ba su rubuce a takarda. Ita dai Daneen ba wannan take buƙatar ji ba. Don haka ta luma ƙwayar idanunta cikin na likitan ta ce "Don Allah ya jikin ƙanina?" Sai da ya kalle ta, ya ɗan yi jimm kafin ya ce "In Sha Allah zai samu sauƙi. A je a kawo gwajin nan yanzun nan, za mu san abin yi ne bayan an yi su." Cikin sauri ta jinjina kai, ba ta sake cewa komai ba ta fice daga office ɗin. Sai kuma da ta fito ɗin sannan ta dakata tana kallan takardar tamkar idanunta za su faɗo. Sai a lokacin ƙwaƙwalwarta ta tuna mata babu ko sisin kwabo a jikinta, ba kuma ta da wanda za ta tunkara ya ba ta kuɗin yin gwajin. Ta lumshe idanunta tana ambatar sunan Allah daidai lokacin da ƙirjinta ya wani irin bugawa. Buɗe idanunta ta yi, ta shiga jefa su cikin asibitin kamar mai neman wani abu. Cikin rashin sanin abin yi ta shiga taka ƙafafunta, tunani birjik cikin ƙwaƙwalwarta, mafita kawai take nema, mafita kawai take so. Ameer take so ya sami lafiya, toh amma ta ya ya? Tana ci gaba da waɗannan tunanukan sai tsintar kanta ta yi cikin harabar asibitin. Ta sake wuwwulga idanunta tana kallon mutanen da ke zaune, wasu na tsaye, wasu kuma na hira. Kai tsaye ta soma takawa, ba ta jira komai ba, ta tsuguna har ƙasa lokacin da ta isa dab da wata mota, wadda wani babban mutum ke tsaye, gefensa kuma wata mata ce, ya yin da wani saurayi da a ƙalla zai yi shekaru 30, ke kusa da mutumin. "Don girman Allah ku taimaka mini da kuɗin gwajin waɗannan, ƙanina ne ba shi da lafiya, kuma ba ni da komai, don Allah ku taimaka mini." Ta yi maganar idanunta a kan mutumin. "Ka ga halin mutanen koh? Har sun fara." Matar ta faɗa tana jan tsaki a ƙarshen maganar tata. Kallon Daneen mutumin ya yi, kafin ya maida dubansa kan matarsa ya ce "Idan ma ba su fara ba ba ni da nutsuwar saurarar kowa a yanzu.. Kai Yohanah ina jiran ka, kar ka ƙara ko da minti 10 ne a kan lokacin da na ba ka. Na dai faɗa maka, ka kuma kiyaye." Ya ƙare maganar yana kallon saurayin da ke gefensa, wanda ke sanye cikin wata riga da wando crazy. Kansa da wani banzan aski, ya yi cibiri-cibiri a tsakiyar kan. "Toh sai na ƙaraso." Ya faɗa da gurɓatacciyar hausarsa, da tun daga fara maganarsa za ka fahimci ba bahaushe ba ne. Ko da yake fuskarsa ma kaɗai ka kalla za ka iya fahimtar hakan, daga zarar kuma ya yi magana shi ne za ka tabbatar. Bai jira wani ya sake cewa komai ba ya faɗa cikin motar, matarsa na gefensa ya ja ya fice daga asibitin. Daneen ta bi su da kallo tana jin wata faɗuwar gaba na kama ta. A hankali ta ɗan sake runtse idanunta tana miƙewa a kan ƙafafunta, har lokacin idanunta na bin ƙurar da mutumin nan ya bari. "Nawa kike buƙata?" Ta ji an ambata daga bayanta. Da sauri ta juyo har tana ƙoƙarin yin tuntuɓe ta kalli matashin saurayin da a kira da 'Yohana'. Kawai sai ta miƙa masa takardar. Maimakon ya kalli takardar, sai ya ci gaba da bin ta da kallo, tun daga sama yake kallon ta har ƙasa, wanda har hakan ya ɗan so ya sa ta tsargu, har ta kai ga ta soma janyo addu'a cikin zuciyarta. Sai ya maida dubansa kan takardar ya shiga karantawa. "Mu je." Ya ambata yana yin gaba. Babu musu Daneen ta soma binsa. Hausarsa kwata-kwata ba ta da daɗin saurara, saboda yadda bai iya ta ba, kawai dai yana kwaɓawa ne. Dukkan kuma wasu alamu sun nuna yarinyar nan da ke gabansa ba lallai ta iya turanci ba. Don haka suna ci gaba da tafiya ya ce "Kina son taimako a kan duk abin da kike so na yi miki?" Duk da ya yi maganar a juye, amma tabbas ta fahimce shi, dalili kenan da ya sanya ta jinjina kai tana faɗin "Ehh don Allah." Ajiyar zuciya ya sauke, kafin ya ce "Alright, I will help you, but ke ma za ki taimaka mini a kan wani abu. Get it?" "Zan taimaka maka idan dai har ka taimake ni, ni dai burina kawai ɗan'uwana ya samu lafiya." "Ohk don't worry, he will be fine soon." Duk da ba wani turanci ake yi musu a makarantarsu ba, amma tabbas ta fahimci abin da yake nufi, don haka ta jinjina kai kawai. Har bayan shuɗewar wasu awanni Daneen na tare da Yohana, bayan an yi wa Ameer gwaje-gwajen da likita ya buƙata. Kuma da taimakon Ubangiji, taimakon gaggawar da aka ba shi ya taimaka masa matuƙa, wanda har bayan dawowarsu daga gwajin ya samu wani wahalallen bacci ya ɗauke shi. Sosai Daneen ke ci gaba da jajanta kirkin Yohanah, don duk wasu alamu sun nuna ba musulmi ne ba. Abin da ya sa kuma ta ƙara tabbatarwa, shi ne da lokacin Sallah ya yi ba ta ga ya tashi ya yi ba. Sai dai taimaka matan da ya yi, ya matuƙar yi mata daɗi, ta kuma gode wa Allah da ya kawo mata shi a irin wannan lokacin da ta ke buƙatar taimako. .."Zuciyarsa ta yi raunin da ana buƙatar a yi masa aiki, idan ba haka ba a kowanne irin lokaci za a iya rasa shi." Likitan ya faɗa yana kallan Yohanah. Dama ya san da wuya idan ba haka ne zai faru ba, saboda yadda shi kansa da ba likita ba ya ga yanayin Ameer ɗin, da kuma gwajin da aka masa. Hannu ya miƙa wa likitan suka gaisa kafin ya fita daga office ɗin. Kamar yadda ya tsammata kuwa, Daneen na ƙofar tana jiran sa. Kallon sa kawai take yi, tana jira ta ji abin da zai ce. Fahimtar hakan ya sanya shi faɗin "Ana buƙatar a yi masa aiki a zuciya." Wani irin jiri ne ya kwashi Daneen, lokaci guda wani duhu ya zo ya mamaye ganinta. Ta yi gefe za ta faɗi, duk da yadda take ƙoƙarin ganin ba ta zube ba. Dalili kenan da ya sanya Yohana kai hannunsa ba tare da wani tunani ba ya riƙo ta. Wani irin runtse idanunta ta yi, tana komawa kan ƙafafunta, ta yi maza ta buɗe a kan hannunsa da ke kan nata hannun, sai kuma ya yi saurin janyewa yana furta "Sorry girl, Sorry please." Ya faɗa saboda yadda ya ga tana bin sa da wani irin kallo. Ba tare da ta bi ta kan abin da yake faɗa ba, ta zube a kan ƙafafunta tana jin yadda bugun zuciyarta ya ƙaru. 'Aiki a zuciya?' Shi ne abin da take ta maimaitawa, hawaye tuni sun cika mata idanunta. "Stop crying Cutie. Ki tashi mu samu mafita." Ya faɗa yana kallan yadda take kuka kamar Baby. Duk wasu alamu sun nuna yadda take matuƙar ƙaunar ɗan'uwanta. Gaba ɗaya aikinta da kuma maganganunta sun nuna shaƙuwa da kuma tsananin ƙaunarta da ɗan'uwanta. 'Me hakan ke nufi?' Ya tambayi kansa. Sai kuma ya yi gefe, ya fito da wayarsa daga cikin aljihu ya danna wa wata number kira. "What's going on?" Ya faɗa bayan an ɗaga wayar. Shiru ya yi na ɗan wasu sakanni, yana saurarar abin da ake faɗa masa daga can ɓangaren, kafin ya ce "Ya yi, send me the address now! I will call you later." "Ohk." Ya sake faɗa bayan wasu sakanni. Jefa wayar ya yi cikin aljihu kafin ya koma inda ya bar Daneen, da ke zube a wajen tamkar wadda aka dasa. "Tashi mu tafi." Da sauri ta ɗaga idanunta ta kalle shi. Ya jinjina mata kai kana ya ce "Ehh, asibiti za mu sauya.. Za ki iya sadaukar da wani abin da kika mallaka saboda ɗan'uwanki." "Matuƙar dai zai samu lafiya." Ta faɗa tana jinjina kai. "Ohk let's go. But let me go and meet the doctor, I will explain everything to him. Wait for me here." Daga haka bai jira ta ce komai ba ya faɗa cikin office ɗin. Wajen minti 20, sai ga shi ya fito, tana tsaye kamar yadda ya bar ta. Ya miƙa mata takardun hannunsa kafin ya wuce ɗakin da Ameer yake. Runtse idanunta Daneen ta yi tana sake gode wa Allah. Ba don Allah Ya kawo mata Yohanah ba, da ba ta san yadda za ta yi ba. A bayan motar Yohanah ɗin aka kwantar da Ameer, da na'ura ke taimaka masa wajen numfashi. A gaban motar Daneen ta zauna, ya yin da shi kuma ya zauna wajen mai tuƙi. Babu ɓata lokaci ya ja motar suka fice daga cikin asibitin. Suna tafiya Daneen na juya wa baya ta kalli Ameer, sai kuma ta dawo ta ci gaba da kallon titi. Ganin abun take tamkar a mafarki, tamkar ba Ameer ɗinta ba. Har suka yi tafiya mai nisa ba ta daina tunane-tunane ba. Tun daga bakin asibitin za ka fahimci lallai babban asibiti ne, babban ma irin babban da ya amsa sunansa babba. Hamshaƙi, haɗaɗɗe wanda kallo ɗaya za ka masa, ka san ya lamushe kuɗaɗe da yawa wajen gina shi. Idan kuwa aka shiga ciki ba za ka taɓa zata a cikin Nigeria kake ba, saboda matuƙar haɗuwa da ya yi. Kai tsaye a inda aka tanada don ajje motoci Yohanah ya yi parking na motarsa, Daneen kuwa ban da ci gaba da kallon cikin asibitin babu abin da ta yi, mamaki take toh me ya kawo su nan ɗin? Saboda yadda duk wasu alamu suka nuna nan ɗin bai yi kama da inda za a taimaka wa talaka ba. Ita tun da take ma, ko kuma ta ce tun da suka shigo garin Kano ba ta taɓa ganin waje mai kyau da tsaruwa irin wannan ba. Sai dai da yake gaba ɗaya hankalinta yana kan Ameer ya sa yana ida yin parking ta sauka daga motar ta koma inda Ameer yake. Shi ma saukar ya yi. Cikin ƙanƙanin lokaci aka shigar da Ameer cikin asibitin, da cikinsa ya fi harabarsa tsaruwa nesa ba kusa ba. .. "Akwai wani cikin asibitin nan, mahaifinsa mugun mai kuɗi ne. Ƙodarsa ce ta lalace, ana buƙatar a sauya masa wata. Saboda haka idan dai har kika sadaukar da ƙodarki ga ɗansa, toh tabbas ko ma nawa ne, ko nawa ake buƙata, zai biya a yi wa Ameer aiki. Zai iya fitar da shi ma waje ƙwararrun likitoci su yi masa aiki. Ƙodarki guda ɗaya kawai za ki bayar, daga nan ki saka a ranki ɗan'uwanki ya samu lafiya." Tun da Yohanah ya fara magana Daneen ke kallonsa, tana rarrabe duk wata kalma da ya faɗa. Har bayan kusan minti ɗaya da gama maganar ba ta ce komai ba. Sai zuwa can sannan ta ce "Ka tabbatar zai biya a yi wa Ameer aiki? Ko da an yi aikin kuma na mutu idan na bar Ameer a hannunka za ka kai mini shi wajen mahaifiyarmu?" Daneen ta faɗa cikin sanyayyiyar muryarta. Murmushi Yohanah ya yi, yana ɗan shafa gefen kumatunsa. Sai da ya soma girgiza kai sannan ya ce "Nothing will happen. Just pray as much as you can, za a yi komai cikin nasara. Za ki samu lafiya, ɗan'uwanki ma haka." Ya yi maganar a nutse saboda ya ba ta ƙwarin gwuiwa. Ganin ta sake yin shiru ne, ya sanya shi faɗin "Za ki iya zuwa ku yi magana da doctor, zai yi miki bayanin komai himself." Ajiyar zuciya Daneen ta sauke, kafin a hankali ta buɗe baki da ƙyar ta ce "Na amince." Ba ƙoda ba, ko da zuciyarta ce za ta iya sadaukar wa a kan ɗan'uwanta, matuƙar zai samu lafiya. Ballantana ƙoda da aka ce mata guda biyu ce. Ubangiji Allah Ya dubi zuciyarta Ya ba wa ɗan'uwanta lafiya, da ita kanta da za a ciri wani abu daga cikin jikinta. Shi kuma wanda zai siya ƙodar tata Allah Ya sa ya ji tausayinsu, ko da kuɗin da ake buƙata wajen yin aikin, ya fi kuɗin da ya yi niyyar bayarwa, ya taimaka ya biya gaba ɗaya. Ya kuma saka a yi aikin cikin nasara. Wani irin murmushi Yohanah ya saki, yana sauke ajiyar zuciya. Kai tsaye ya shiga office ɗin likitan don yi masa bayanin abin da ya kawo su cikin asibitin. Duk da da farko ba su nuna ba, don sai da ya bari aka karɓi Ameer tukunna, bayan ya ajje kuɗi masu ɗan tsoka kamar yadda yake a tsarin asibitin. A sanyaye Abeey da ke sanye cikin wata bluen shadda, ɗinkin babbar riga, ya ke takawa zuwa cikin ɗakin. A hankali ya ɗora hannunsa kan hannun ƙofar ya tura. Har lokacin Maama na zaune kusa da ɗanta hannunta na cikin nasa. Yana kwance kan gadon, rabin jikinsa lulluɓe da bargo, ya yin da idanunsa ke a lumshe tamkar mai yin bacci. Ɗaga idanunta Maama ta yi ta kalli Abeey, bayan ta amsa sallamarsa. Ya ƙarasa cikin ɗakin, idanunsa na kallan fuskar ɗan nasa da ta yi fayau, ya ce "Sannu Tareeq." Ya faɗa yana kallansa cike da tausayawa. A hankali ya shiga buɗe idanunsa da suka masa nauyi. Ya sauke su a kan Abeeyn, yana sauke numfashi a hankali kamar wanda ya yi aikin wahala. "Sannu." Maama ta faɗa a hankali. Sai ya jinjina kai yana ƙaƙalo murmushi ya wanzar a kan fuskarsa kafin ya ce "Yawwah." Ya ƙare har lokacin da murmushin ƙarfin hali a fuskarsa. "Yanzu dai ba ka isa ka ce mini ka warke na yarda ba. Ka ma daina mini wanna yaƙen. Ni na fi so ko me kake ji ka sanar da ni Tareeq. Ba garin wannan ɓoye abin da ke damunka ɗin ba ne ya janyo haka ba. Ni dai Abeey ka faɗa masa ya daina wannan ɗab'iar tasa, idan da wani abun ya same shi kafin mu ankare fa? Ko kuma abin da ke damun nasa bai fito fili ba ya ci gaba da cin sa a cikin jikinsa fa?" Ta ƙare maganar tana kallan Abeey. Murmushi Abeey ya yi kana ya ce "Ya isa haka, shi kenan faɗan ya isa haka. Yanzu dai ki yi haƙuri ki.." Kafin ya kai ga ƙarasa maganar, wayarsa ta ɗauki ruri. Ya zube idanunsa a kan wayar, ganin doctor ke kiransa ya sanya shi saurin ɗagawa. Shiru ya yi na tsawon mintina yana saurarar abin da likitan ke faɗa. Suka ɗan yi magana kafin ya ajje wayar. Ya kalli Maama murmushi na tashi a kan fuskarsa ya ce "Tun kafin a je ko'ina, har an samu yarinyar da za ta sadaukar da ƙodarta gun yaronki." Da matuƙar mamaki Maama ta ce "Da gaske Yallaɓai? Ita kuwa me take buƙata a rayuwarta wanda za mu iya biyan ta da shi?" Ta tambaya wani irin murmushin farin ciki na tashi a kan fuskarta. "Abin mamaki, Likitan ya sanar da ni ba ta buƙatar komai." Shiru Maama ta yi tana kallon Abeey cike da mamakin jin furucinsa. "Ba ta buƙatar komai kuma?" Jinjina kai Abeey ya yi kafin ya ce "Ya ce ta bayar da ita ne saboda a yi wa ɗan'uwanta da ke kwance cikin asibitin nan addu'ar Allah Ya ba shi lafiya. Ban da wannan ba ta buƙatar ko sisi." Littafin DANEEN na kuɗi ne, a kan 500. Sai dai daga farko har ƙarshen Book 1 free ne, Book 2&3 shi ne na kuɗi kuma duka a kan 500. Har yanzu kuma muna cikin Book 1 ne, wato (Free pages). Waɗanda za su fara payment yanzu, su tuntuɓe ni ta 08124818273. Waɗanda kuma sai mun gama Book 1 ne za su yi payment, zan saka muku yadda za ku yi a last page na Book 1. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 19 Jinjina kai Maama ta yi cike da mamakin jin abin da Abeey ya faɗa. Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce "Allah Sarki! Amma abin kam da mamaki. Allah Ubangiji Ya saka mata da alkhairi, Ya ba wa ɗan'uwanta lafiya." "Ameen." Abeey ya amsa da hakan, har lokacin annurin fuskarsa yana nan. Tun da Abeey ya fara magana Tareeq yake kallon sa har ya ƙare. A hankali ya ɗan gyara kwanciyarsa lokaci guda yana lumshe idanunsa. Da sauri Maama da ta lura da shi ta taso tana faɗin "Me ya faru?" Girgiza kansa ya yi lokaci ɗaya yana buɗe idanunsa. A hankali ya soma faɗin "Abeey wace ce ita? Ina son ganin ta tukunna." Ya faɗa cike da ƙarfin hali. "Oh Yah Ilahy Tareeq, ka samu ka samu ka yi bacci kafin mu ji abin da Likita zai faɗa." Girgiza kai Tareeq ya yi kafin ya ce bayan ya riƙo hannun Maama. "Maama ki bar ni na ga wadda za ta ba ni ƙodarta ba tare da wani dalili ba. Ina buƙatar ganin wace ce ita tabbas." Tun kafin ya ƙarasa Maama ta katse shi da faɗin "Rashin yardarka ya yi yawa Tareeq, har a kan lafiyarka ma?" Ta ƙare tana kallon sa. Iska ya fesar daga bakinsa, ganin da ya yi kwata-kwata Maaman ta ƙi fahimtarsa, lokaci ɗaya kuma yana mayar da jikinsa ya kwantar a kan gadon, har lokacin idanunsa a lumshe. "Ya isa haka Fatima. Kin fi kowa sanin halin ɗanki, ina ga kuma hakan ba laifi ba ne. Amma dai a halin da kake ciki ka fi buƙatar hutawa, so ka kwanta ka samu ka yi bacci zuwa an jima. Ni da mahaifiyarka za mu yi magana da yarinyar." Jinjina kai kawai ya yi daga inda yake kwance ba tare da ya ce komai ba. Maama ta bi shi da kallo cike da tausayawa. Hannunta ta kai a hankali ta taɓa wuyansa, jin da ta yi zafin ba sosai ba ya sanya ta sauke ajiyar zuciya har cikin ranta tana jin daɗi. Saboda yadda kwana biyu Tareeq ɗin ya din ga fama da matsanancin zazzaɓi mai zafin gaske. Babu daɗewa aka turo ƙofar ɗakin, Sultanah ce da Hidaya cikin dogayen riguna kusan iri ɗaya sai dai ba kala ɗaya ba ne. Da sauri suka ƙarasa inda Tareeq ɗin yake, kowacce jikinta a matuƙar sanyaye. "Sannu Yah Tareeq." Suka kusan haɗa baki wajen faɗin hakan. Ɗan lumshe idanunsa ya yi kaɗan kafin ya ce "Yawwah." "Wai Yah Tareeq dama ka san da wannan ciwon?" Hidaya ta faɗa kamar za ta yi kuka. Girgiza kai ya yi, yana ɗan ƙaƙalo murmushi a hankali ya ce "Kaɗan kaɗan.. Ban san abin ya kai haka ba, duk da ina karɓar gwajin lafiyata a kai a kai, ban san lamarin zai yi tsamari har haka ba." Ya ƙare a ɗan gajiye. "Wallahi Yah Tareeq mun fi ka kula da lafiyarka. Kai dai kawai ciwon a jikinka yake, amma mun fi ka damuwa da shi." In ji Sultanah tana kallon sa. Yanzu kam sai da ya ɗan yi dariya, daidai lokacin da Abeey ya miƙe yana faɗin "Ya kamata mu yi waje fa haka." Cikin girmamawa duk suka amsa da "Toh." Ba su ɗauki lokaci mai tsayi ba gaba ɗaya suka fice suka bar shi shi ɗaya zuciyarsa cunkushe da tunane-tunane. Cikin ikon Allah aka gwada ƙodar Daneen, kuma za ya iya cira a saka wa Tareeq. Don haka Likitan ya tsayar da washe-gari a matsayin ranar da za a yi aikin. Gaba ɗaya jikinta a matuƙar sanyaye yake, lokacin da take taka wa tana bin bayan wani da zai raka ta ɗakin da Ameer yake ciki. Sai da ya tura ƙofar ɗakin sannan ya juya ya bar wajen. Daneen ta bi shi da kallo kafin ta maida idanunta cikin ɗakin. Runtse idanunta ta yi, tana jin yadda zuciyarta ta karye, saboda hango ɗan'uwanta da ta yi kwance, har kuma lokacin ba ya iya numfashi shi ɗaya sai da taimakon na'ura. Kamar wadda ke tsoron taka ƙasa haka take takawa zuwa cikin ɗakin idanunta a kansa. Ta zuba wa kyakykyawar fuskar Ameer idanunta lokacin da yake bacci kai sai ka rantse cikin kwanciyar hankali yake, babu wani abu da ke damunsa. A nutse ta kai hannunta ta riƙo hannunsa cikin nata, tana jin wata irin ƙwalla na tarar mata. Idanunsa ya shiga buɗewa a hankali kamar ya san wadda ke tsaye a wajen. Sai dai shi ma cike yake da fatan a ce ya buɗe idanunsa ya ga 'yar'uwarsa a gefensa. Aikuwa cikin ikon Allah yana buɗe su ɗin kuwa ya sauke a kan Daneen. Runtse idanunsa ya yi kafin ya buɗe a hankali daidai lokacin da wasu kyawawan ƙwalla suka zubo daga cikin idanunsa. "Ameer." Ta faɗa, tana kai hannunta kan bakinta ta toshe don kar kukan da take ta riƙewa ya fito. "Adda." Ya yi ƙarfin halin faɗa. Rasa abin da za ta yi ne ya sanya ta zube wa a wajen kawai, ta kifa kanta a kan gadon ta shiga raira kukanta a hankali. Hannunta da ke kusa da na shi ya riƙo sosai, dalili kenan da ya sanya ta saka hannunta ta share fuskarta kafin ta miƙe tsaye tana kallon sa. "Kin ga abin da na ja mana koh?" Ya faɗa a raunace. Girgiza kai ta yi tana barin hawayen cikin idanunta damar zubowa. "Ka dena mini irin wannan maganar Ameer, ba ka ja mana komai ba. Duk abin da ka ga ya faru dama rubutacce ne. Bawa kuma ba ya taɓa wuce wa ƙaddararsa." Murmushin yaƙe Ameer ya yi, yana sake jin yadda gaba ɗaya duniyar ta fice masa a ransa. Ji yake tamkar zuciyarsa za ta yi bindiga saboda tsananin ciwon da yake ji a cikinta. Cikin sanyi da ƙarfin hali ya soma faɗin "Adda ba na tunanin zan rayu kowanne irin aiki aka yi mini. Ni kaɗai na san abin da nake ji. Bayan zuciyata Adda cikina na yi mini wani irin ciwo da na kasa fahimtar wane iri ne shi. Idan na mutu ki nemar mini yafiya gurin Innarmu, duk abin da ya faru ni na jawo. Sai da kika ce mini kar mu baro ƙauyenmu amma na kafe, yanzu ga abin da ya faru." Ya kai ƙarshen maganar yana sauke wani numfashi a mugun wahalce. "Ameer ba na so, ka dena na faɗa maka. Ba za mu koma wa Inna a wani irin hali ba, In Sha Allah za mu koma mata ne a yadda muka baro ƙauyenmu. Za ka warke da yardar Ubangiji. Na kuma roƙe ka da ka cire wannan damuwar da kake ɗora wa kanka ko don samun lafiyarka, Ameer ka san lafiyarka ita ce tawa don Allah." Daneen da muryarta ke fita da ƙyar cikin kuka ta faɗi haka. Girgiza kai kawai ya yi ya ce "Toh Adda na dena, na dena.." Ya faɗa yana wani lumshe idanunsa. Sai da ya yi bacci tana cikin ɗakin sannan ta fice ƙwaƙwalwarta fall tunani kamar za ta tarwatse. ..Tana nan zaune inda Yohanah ya bar ta, bayan ya ba ta uzurin zai je ya dawo. Ta zauna ta yi shiru cikin rashin sanin abin yi. Ita kanta tunani nema yake ya yi wa ƙwaƙwalwarta yawa, sai dai babu yadda ta iya. Haka nan take zaune, a ido tana wajen amma a zahiri ita ce zaune a wajen kawai, amma gaba ɗaya hankali da duk wani tunaninta yana wani wajen daban. "Doctor na son ganin ki." Shi ne kawai abin da ta ji, wanda ya yi nasarar dawo da ita daga dogon tunanin da ta tafi. "Na'am?" Ta ƙare maganar da alamar tambaya tana kallon wadda ta yi mata magana. A karo na barkatai ta sake maimaita mata saƙon Likitan tana nazarinta. Miƙewa Daneen ta yi tana faɗin "Tohm." Daga haka ta bi matar a baya zuwa office ɗin Likitan. A bakin wani ɗaki suka rabu, ya yin ita matar ta kalli Daneen ta ce "Ki shiga." Kallon ta Daneen ta yi tamkar mai neman ƙarin bayani, sai dai kuma ba ta ce komai ba, illa jinjina kai da ta yi. Daga haka matar tayi gaba ya yin da ita kuma ta tura ƙofar ɗakin da sallama ɗauke a kan laɓɓanta. Kusan a tare suka amsa sallamar, dukkan su idanunsu a kanta. Kasancewar ba ta san za ta yi ido huɗu da wasu fuskokin ba, ya sanya ta yin turus tana ɗauke kanta daga kallon su. "Ƙaraso mana." Maama ta faɗa har lokacin idanunta a kan Daneen. Cike da sassarfa Daneen ta ƙarasa cikin ɗakin tana jin bugun zuciyarta na ƙaruwa. "Taho ki zauna a nan." Maama ta faɗa, ba tare da jin komai ba ta ja hannun Daneen ɗin ta yi mata mazauni a gefe kaɗan da ita. Babu musu Daneen ta zauna hannunta ɗaya cikin ɗaya, zuciyarta fall tunanin shin su waɗannan ɗin su waye su? "Ina wuni?" Ta yi ƙarfin halin faɗa a hankali. "Alhamdulillahi, ya jikin ƙanin naki?" Maama ta faɗa. "Alhamdulillahi." Ita ma Daneen ta ba ta amsa a sanyaye. Hidaya da ke gefen Maama ta ce "Wai ita ce za ta ba wa Yah Tareeq ɗin ƙoda?" Jinjina kai Maama ta yi tana murmushi. Cikin matuƙar farin ciki Hidaya ta miƙe ta koma kusa da Daneen, tana jin wata irin ƙaunarta lokaci guda. Tun shigowar ta take yaba irin kyawun da Allah Ya ba ta, sai dai da yake ba ta san wace ce ba ya sanya ta kama kanta. "Amma na ji daɗi, Allah Ya ba ki abin da kike nema duniya da lahiya, Allah Ya biya miki buƙatunki na alkhairi." "Ameen." Sultanah ta amsa addu'o'in Hidaya tana murmushi. "Ya sunanki?" Hidaya ta faɗa tana kallon Daneen da murmushi a kan fuskarta. Sai da ta ɗaga kyawawan idanunta da suka ƙanƙance sannan ta ce "Daneen." "Woww, suna mai daɗi. Sannu Daneen." In ji Hidaya tana murmushi. Godiya sosai suka ci gaba da yi wa Daneen, suna kuma yi wa Ameer addu'a. Abin da ya matuƙar faranta ranta kenan. "Sultanah ku je gida tare da ita ta samu ta yi wanka ta yi bacci ta huta kafin goben da za a yi aikin." Maama ta faɗa bayan ta miƙe tsaye. Da sauri Daneen ta kalli Maama tana girgiza kai. Tana kai wa ƙarshen maganarta ta soma faɗi cikin sanyayyiyar muryarta. "A'ah, ba zan iya tafiya in bar ƙanina ba. Ki yi mini afuwa don Allah ba zan iya ba." Kallon ta su duka suke yi, abin bai ba su mamaki ba, don duk tana hakan ne a kan ɗan'uwanta. Su ma kuma sun san me ake nufi da ɗan'uwa. "Shi kenan, ki je zuwa an jima sai ku dawo idan kin huta." Kamar za ta fasa kuka haka ta ji. Tabbas matar ta yi mata kwarjini amma duk da haka ba ta ji ko nan da can za ta iya matsawa daga asibitin, bayan Ameer na ciki a kwance. Don haka cikin girmamawa ta ce "Don Allah ki yi haƙuri ki bar ni wajen ɗan'uwana." Ta faɗa lokacin da ƙwalla ta cika cikin idanunta. Cike da tausayawa Maama ta ce "Babu damuwa. Allah Ya ƙara lafiya, Ya kuma saka miki da alkhairi." Wata ƙatuwar ajiyar zuciya Daneen ta sauke, tana jin wani sanyi na ratsa ta. Haƙiƙa ta ji daɗin kai ƙarshen maganar da matar ta yi, don da ta ci gaba da cewa ta je ɗin ba ta tunanin za ta iya ci gaba da yi mata musu. A sanyaye ta amsa da "Ameen." Daga haka suka yi sallama da Daneen suka fice daga ɗakin. Ita ma ba ta ƙara wasu mintina ba ta fice zuwa inda take zaune ɗazun. Washegari ita ce ranar da za a yi wa Daneen aikin cire ƙoda, ya yin da za a yi wa Tareeq na dashen ƙodar. A kuma safiyar ranar ne Yohanah ya je ya biya duk kuɗaɗen da ake buƙata na aikin da za a yi wa Ameer. Cike da mamaki Likitan ke kallon sa, ya ce har lokacin ya kasa dena tantamar anya kuwa Yohanahn kafiri ne da gaske? "Amma me zai hana ka nuna fuskarka wajen Alhaji Alhassan. Alkhairinka yawa gare shi wajen iyalinsa." Murmushi Yohanah ya yi kafin ya ce "Babu damuwa, ina yin komai ne saboda Allah, kuma ba na so ya sani. Akwai dalilin yin hakan, ina so ne na rama abin da ya yi mini. Kamar yadda yake taimakawa mutane a bayan ido, shi ya sa nake so na rama masa ba tare da ya sani ba." Jinjina kai Likitan ya yi, bayan ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Duk da haka, ko da sau ɗaya ne ka bari ya ganka ya gode maka. Ka samo wadda za ta ba wa ɗansa ƙoda. Duk da a matuƙar buƙatar kuɗi take, hakan bai sa ka bar ta da shi ba. Ka kuma ƙi barin Alhaji Dikko ya biya kuɗin aikin a matsayin kuɗin ƙodar yarinya, shi ma ka ɗauke masa. Kuma duk da haka ba ka so ya sani, bayan kai ɗin na daban ne, mai ɗumbin alkhairi a gare shi." Kafin Yohanah ya ce komai wayarsa ta shiga ringing, ya kalli mai kiran nasa, kawai sai ya tura ta cikin aljihunsa kafin ya ɗaga idanunsa ya maida su kan Likitan ya ce "Please doctor a yi abin da na ce. Ita yarinyar babu damuwa za ta iya haɗuwa da shi, amma ni babu buƙatar hakan kamar yadda na faɗa maka." Yohana ya ƙare maganar yana sakin wani murmushi, lokaci ɗaya yana kai hannunsa guda ɗaya ya shafa haɓarsa har lokacin idanunsa a kan Likitan. #YOHANAH #KIDNEY #DANEEN #TAREEQ #AMEER *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 20 Jinjina kai Likitan ya yi kafin ya ce "Shi kenan, Allah Ya saka maka da alkhairi. A madadin Alhaji Dikko, ina sake miƙa godiya gare ka." Ba tare da Yohana ya amsa ba ya miƙa wa Likitan hannu har lokacin fuskarsa da murmushi suka gaisa. Daga haka ya yi waje, Likitan ya bi shi da kallo yana ci gaba da mamakin kyawawan halaye irin nasa. Cikin nasara, ikon Allah da kuma tarin addu'o'i daga bakunan iyalan Dikko aka yi wa Daneen da kuma Tareeq aiki. .. "Sannu yaron nan." Dada ji ta faɗa tana kallan Tareeq cike da tausayawa. Jinjina kai ya yi daga inda yake kwance, yana sake lumshe idanunsa. Shafa goshinsa Maama ta yi tana jin wani irin tausayin ɗan nata, saboda sanin halinsa da ta yi, idan dai har ka ga ciwo ya kayar da shi, toh da gasken ciwon nan ya shahara. Ba ta ce komai ba, sai neman waje da ta yi ta zauna, daidai lokacin da aka turo ƙofar ɗakin. Sultanah, Abdoul da Hidaya, su ne suka shigo. Idanunsa a kan Abdoul ya sauka, cike da mamakin yadda suka shigo tare da su Sultanah. 'Ko dai har abin nasu ya ɗore haka?' Ya raya hakan a ransa, yana fatan a ce da gasken haka ne. "Tare kuke ne?" Dada ji ta yi tambayar tana kallon Abdoul, tambayar da take ta masa yawo cikin kai. Don haka sai ya maida duban sa kan Abdoul don jin amsar da zai bayar, cike da fatan Allah Ya sa burin ƙanwarsa ya cika. "A'ah, a cikin asibitin muka haɗu." Ya ba wa Dada ji amsar cikin girmamawa. "Ayyah." Ta yi maganar a taƙaice. Daga haka ya gaishe ta, kafin ya gaisa da Maama. Sai kuma ya ƙarasa inda abokinsa yake. "Sannu! Ya ƙarfin jiki?" Ya tambaya cikin kulawa. Sai da Tareeq ya lumshe idanunsa kafin ya ce "Alhamdulillahi." "Allah Ya ƙara sauƙi, sannu." Yanzu kam jinjina kai kawai ya yi yana sake lumshe idanunsa don so yake ya ɗan sake runtsawa, don jin sa yake tamkar an canja ji. Wani daban yake ji tun bayan da aka yi aikin. Sai dai shi a karan kansa ya matuƙar jin daɗin jikinsa, wanda ya yi kwana da kwanaki rabon da ya ji irin hakan. Su ma Hidaya da Sultanah gaishe da yayan nasu suka yi. Zuwa can Abdoul ya ce "Maama zan so na ga wadda ta sadaukar da ƙodarta a kan Tareeq ɗinmu, ko don in yi mata godiya." Da sauri Dada ji ta kalle shi ta ce bayan ta soma tafa hannunta. "Kaa ga aikin shiririta, daga zuwa ɗazu tana bacci babu wanda ya sake komawa. Ke maza ku tashi mu je wajen baiwar Allah ɗin can." Ta ƙare maganar tana miƙewa tsaye. Babu musu dukkansu suka miƙe. Maama ta kalli Tareeq, ganin da alama kamar bacci ya ɗauke shi ne ya sanya ta bin bayan su Dada ji da suka yi waje. "Allah kuwa Yah Tareeq yana jin jiki, wallahi duk jikina a sanyaye yake." Hidaya ta faɗa a marairaice, tana hango fuskar yayanta da ta ɗan sauya, kamar ba shi ba. "Wallahi ke kam.." Ita ma Sultanahn ta faɗa a sanyaye. Hidaya ce a gaba, don haka ita ce ta yi amfani da hannunta wajen tura ƙofar ɗakin. Sultanah, Maama da Dada ji suka bi bayanta. Sai Abdoul da ke a ƙarshe, wanda sai da Maama ta ce ya shigo sannan ya bi bayan su. Gaba ɗayansu idanunsu na kan gadon. Tana kwance har zuwa lokacin tana bacci, duk da yadda take bacci hakan bai hana bayyana yadda idanunta suka ɓurma suka yi ciki ba. "Allah Sarki baiwar Allah." Dada ji ta faɗa tana kallan innocent face ɗin Daneen, wadda yarintarta ta gama bayyana ko daga kallan fuskarta. Tun kafin su kai ga zama, Daneen ta wani irin zabura daga baccin da take, a firgice ta furta bayan ta tashi daga kwanciyar da take. "Ameer!" Gaba ɗaya idanunsu sai suka sake koma wa kanta. Tarr ta buɗe idanunta cikin ɗakin, sai ta shiga rarraba manyan idanun nata, tana kallon duk mutanen da ke ciki. "Ameer." Ta sake faɗa a kan laɓɓanta har lokacin ba ta daina kallon su ba. Hidaya ce ta tashi ta ƙarasa inda take, ta nemi waje ta zauna kafin ta kalli Daneen da ke takure waje ɗaya ta ce "Sannu." Kamar sai da ta ce sannun sannan ta tuna abin da ya faru, saboda yadda ta kai hannunta ƙirjinta ta dafe. A hankali ta buɗe baki ta ce "Tohm." "Ya jikin?" Sake dafe saitin ƙirjinta ta yi tana sauke wani numfashi kamar wadda ta yi tsere, ba tare da ta ba wa tambayar Hidayan muhimmanci ba ta ce "Ƙanina.." "Hidaya taimaka mata ta gyara jikinta, sai ta je ta ga ƙanin nata." Maama ta faɗa. Da "Toh." Hidaya ta amsa, kafin ta miƙe tana kallon Daneen ta ce "Mu je koh?" Babu musu Daneen ta soma ƙoƙarin saukowa daga kan gadon. Da sauri Hidaya ta riƙo ta saboda ganin yadda ta yi ta koma baya da sauri. "Sannu." Ta sake furtawa cike da tausayin Daneen ɗin. Kusan a tare duk 'yan ɗakin suka sake faɗin "Sannu." Ya yin da Abdoul ya ɗora da faɗin "Bari na je waje Maama, zuwa an jima sai na shigo." Babu musu ta amsa da "Toh." Daga haka Abdoul ya saka kai ya fice daga ɗakin, Sultanah ta bi shi da kallo tana murmushi. Hidaya ce ta taimaka wa Daneen sosai wajen yin komai, don har cikin ranta tausayi take ba ta. Sun kwashe fiye da rabin awa kafin suka dawo ɗakin. Nan ma dai ta taimaka mata ta sake kwanciya, saboda yadda ta fi jin daɗinta. Don ita kanta ji take kamar ba ita ba. Wajen da aka mata aikin kuwa babu laifi yana mata ciwo, amma dai ita wannan ɗin bai ɗaɗata da ƙasa sosai ba, duk kuwa da cewar ba zafi ne normal ba, tana jin zafin har cikin jikinta, amma kuma ba ta ɗauka hakan da muhimmanci ba. Don gani take duk wani zafi da za ta ji, toh zai biyo bayan zafin da take ji na ganin ɗan'uwanta cikin halin ciwon da sanadiyyar wasu suka jefa shi. Sai a lokacin sannan suka gaisa, dukkansu suna yi mata ya jiki. "Alhamdulillahi." Shi ne abin da take amsawa da shi kawai, don ita dai gaba ɗaya hankalinta yana kan Ameer. "Mun gode sosai, Allah Ya saka miki da alkhairi, Allah Ya biya miki buƙatunki na alkhairi, Allah Ya ba wa ɗan'uwanki lafiya." Dada ji ta faɗa tana jin har cikin ranta abin da yarinyar ta yi musu yana ɗaya daga cikin alfarmomi masu matuƙar muhimmancin da har abada ba su taɓa mantawa da shi ba. Ba kuma za su taɓa iya biyanta abin da ta musu ba. "Ameen, ina so na ga ƙanina." Ta faɗa a narke tana kallon Dada ji. Ajiyar zuciya Dada ji ta sauke tana kallon Maama ta ce "Anya kuwa za su bar ta ta fita?" Kallon ta Maama ta yi kana ta ce "Hakan ba damuwa ba ne, amma kuma ai jikinta za a duba. Ki bari idan kin ɗan ƙara jin dama-dama ko zuwa gobe ne sai ki je ki gan shi." Maama ta ƙare maganar tana kallon Daneen. Runtse idanunta Daneen ta yi tana jin yadda take bugun zuciyarta ya ƙaru. Ta yaya ma za ta iya haƙura ba tare da ta ga ɗan'uwanta ba? Ba ta san lokacin da ta miƙe ba, duk da yadda wajen ciwonta ya amsa, amma hakan bai dame ta ba. Sai dai ta runtse idanunta na tsawon sakanni kafin ta buɗe. Ta ce muryarta na karkarwa. "Don Allah ki bar ni na je na gan shi kin ji? Zan iya tafiya, zan iya komai ma kin gani?" Ta yi maganar tana soma miƙewa tsaye. Da sauri Hidaya da Sultanah suka miƙe, suka riƙo ta. "Maama don Allah ki bar ta ta je, tana so ta gan shi ne." Hidaya ta faɗa fuskarta a narke tana kallon Maama. "Toh shi kenan, ku je ke da Sultanah ku raka ta. But u should go and ask doctor Adam, za ta iya fita?" Jinjina kai Hidaya ta yi tana sakin Daneen a hankali ta fice daga ɗakin. Daidai lokacin da wayar Maama ta yi ƙara. Ta kalli mai kiran kafin ta ɗaga. Sai da suka gaisa kafin daga can ɓangaren Umman Jawahir ta ce "Ya mai jikin?" "Alhamdulillah, jiki da sauƙi." In ji Maama. "Wallahi na ƙagu mu dawo in ga jikin yarona. Kin ga musamman ma dai Jawahir duk ta bi ta ɗaga hankalinta. Tun da aka kwantar da shi a asibitin nan ta ɗauki damuwa ta ɗora wa kanta, yanzu haka ma kin ganta kuka take, don Abbanta ya ce ba gobe za mu taho ba." Murmushi Maama ta yi, a ranta tana ji idan Allah Ya yarda yaronta ya samu mace mai sonsa tsakani da Allah kenan. "Ayyah Allah Sarki Jawahir. Ai babu komai me ye na damuwar? Jikin nasa kuma da sauƙi ai, ki ƙara rarrashinta." "Ni ma haka nake faɗa mata. Kin ji koh Jawahir?" Umma ta ƙare maganar tana kallon Jawahir da ke gefen ta. "Yawwah." Maama ta faɗa. "Toh Allah Ya ƙara afuwa. Kuma In Sha Allah muna dawowa nan za mu taho babu ɓata lokaci." "Allah Ya yarda." Daga haka suka yi sallama. Ba ta daɗe da ajiye wayar ba Hidaya ta dawo cikin ɗakin. Ita da Sultanah suka taimaka wa Daneen wajen kai ta ɗakin da Ameer yake. A bakin ƙofar suka bar ta. "Bari mu jira ki a nan." Hidaya ta ƙare maganar tana sakin murmushi. Ita ma murmushin ta ƙaƙalo kafin ta jinjina kai. Daidai lokacin da Yohanah ya fito daga cikin ɗakin, yana shirin rufe ƙofar ya ga Daneen. Sai ya saki murmushi yana faɗin "Ke ce?" Jinjina kai Daneen ta yi hannunta dafe da gefenta don ta fi jin daɗin tsayuwar. "Ki ƙara gode wa Allah, saboda da alama an yi aikin nan cikin nasara. Ameer na dab da samun lafiya." Ba ta san lokacin da wani murmushi ya suɓuce mata ba, sam sai ta kasa amsa wa Yohanah maganarsa, ban da ƙarasawa ciki da ta yi don ta gane wa idanunta. Shi ma bai damu da amsar tata ba ya wuce ta gaban su Hidaya da babu wadda ta kalle shi har ya bar wajen. Cike da sassarfa take ƙarasa wa cikin ɗakin idanunta a kan Ameer da idanunsa ke a lumshe. "Ameer." Ta faɗa tun kafin ta ida ƙarasawa inda yake. Kamar a mafarki ya ji muryar 'yar'uwarsa, don bai taɓa tunanin zai sake buɗe idanu ya ga wani ɗan'adam ba, a lokacin da za a masa aiki. Sai ga shi da alama an gama masa aikin, ga shi kuma zai ƙara ganin 'yar'uwarsa. Abin da dai bai sani ba kawai shi ne, shin zai sake ganin Inna-wuro? "Ameer." Daneen ta sake faɗa tana riƙo hannayensa. Wasu irin ƙwalla ne suka sakko daga cikin idanunsa zuwa kan kuncinsa. "Addatah." Ya faɗa muryarsa a wani irin cunkushe. "Na'am Ameer, ka warke koh?" Ta tambaya tana jin wani irin farin ciki na ziyartar ta. Murmushin yaƙe Ameer ya yi kafin ya ce "Ba na tunanin har abada zan warke Addaneen. Ina ji a jikina kamar ba zan ƙara ganin Innarmu ba, duk da yadda nake son ganinta. Na so a ce na ga babanmu kafin na tafi na bar ki Addatah. Ban san zuwanmu garin nan shi ne silar rugujewar farin cikinmu ba, da ban matsa mun taho ba. Ban san neman kuɗin koma wa ƙauyenmu zai sake zama wani ɓangare na wargajewar farin cikinmu ba, da ban nema ba. Na yi nadama matuƙa, na janyo wa kaina. Kalli yadda mutanen nan suka lalata mini rayuwa, zuciyata kuma rauninta na da yawa shi ya sa ta kasa daurewa. Adda kin san su ɗin su waye?" Kallon sa kawai take yi tun da ya soma magana har ya dakata, ji take gaba ɗaya maganganun kamar ba na Ameer ba, kamar ba Ameer ɗinta ƙaninta mai tarin ƙuruciya da shiririta ba. Sai ta ji maganganun da suke fitowa daga bakinsa tamkar wanda wani babba yake yin su. 'Shin me yake shirin faruwa?' Ta tambayi kanta tana maida dubanta kan Ameer. "Ni na faɗa maka ina buƙatar sanin su waye su Ameer? Wanne irin maganganu ne suke fito wa daga bakinka Ameer? Ba ka da hankali ashe dama?" Ta faɗa tana jin yadda ilahirin jikinta ke karkarwa tamkar mazari. Girgiza kai Ameer ya yi, ya yi nasarar kamo hannun Daneen cikin nasa ya ce "Ban sani ba ko Allah zai sa ki samu dama ki shigar da su ƙara Addah, ban sani ba ko bayan raina za ki buƙaci sanin sunan mutanen da suka datse mana farin cikinmu, suka yi mana katangar ƙarfe da rayuwarmu mai daɗi, suka kuma zamo sanadiyyar rabuwarki da ɗan'uwanki." Wani mari Daneen ta kai wa Ameer a gigice tana jin yadda jikinta ke ci gaba da ɗaukar rawa. Tuni idanunta sun soma zubar da hawaye. Jin maganganun Ameer ɗin take har cikin kowacce gaɓa ta jikinta. "Ameer ba ka da hankali? Ba ka da hankali ashe dama? Ashe ba ka sona Ameer? Ashe ka tsane ni Ameer ban sani ba? Wasu irin maganganu kake faɗa haka mara sa daɗin ji? Toh ko dai so kake zuciyata ta tarwatse?" Ta tambaya cikin kuka tana kallon yadda ya runtse idanunsa. Duk da yadda ya ji zafin marin, amma hakan bai sa ya ji ya karaya ba. Shi kaɗai ya san me yake ji yanzu haka a cikin gaba ɗaya jikinsa, wasu abubuwa yake ji waɗanda ko za a kashe shi ba zai iya kwatanta su ba. Hannunsa ya saka da iya ƙarfin da yake da shi ya janyo Daneen ɗin, idanunsa a lumshe ya saka bakinsa saitin kunnenta ya soma faɗi a wahalce, sannan kuma a rarrabe, a kuma hankali. "Ki yi haƙuri Adda, ko da za ki buƙaci sanin su waye su.." Sai ya dakata a nan yana sake riƙe hannun Daneen da masifar gaske. "Ki fara shari'a da yaron gidan Alhaji Dikko, shi ne shugaba kuma ogan duk waɗanda suka yi amfani da.." Maganar da ta kasa fita kenan, saboda wani yunƙuri da ya yi. Cikin second ɗaya ya saki hannun Daneen, wanda hakan ya tilasta mata saurin kallon fuskarsa. Numfashinsa ne yake fita da wani irin sauri, tuni idanunsa suka soma ƙaƙƙafewa, ya yin da ya fara wata irin shaƙuwa. Wani mahaukacin karkarwa da jikinta ke yi shi ne ya sanya ta runtse idanunta. Ta buɗe su a kan Ameer da ta ga yana wasu abubuwa waɗanda ba ta taɓa ganin irin su ba. Don haka ta yi saurin riƙo shi tana faɗin "Ameer." Ta faɗa da ƙarfin gaske, tana ci gaba da kallon yadda yake kokawa da numfashinsa. Kwata-kwata tunaninta bai kawo mata ta je ta kira likita ba, don saboda tsananin ruɗewa, kawai kiran sunansa take. Sai zuwa can da ta ga dai babu sauƙi sai a wajen Allah, hakan ne ya sanya ta sakinsa, ta sake sauke luhu-luhun jajayen idanunta a tsakiyar kyakykyawar fuskar Ameer daidai lokacin da ya ja wata ƙatuwar ajiyar zuciya, ta juya don zuwa kiran Likita. Sai dai a maimakon ɗazu da sautin fitar numfashin Ameer ya cika dodon kunnenta, sai ta ji shiru. Cakk ta dakata tana buɗe idanunta da har wani rufewa suke don kansu saboda tsabar kukan da suka sha har suka gaji. Fata take a ce numfashin nasa ne ya daidaita, ya kuma daina duk wasu abubuwa da ta ga yana yi waɗanda ba ta taɓa gani ba. Sai dai wata daƙiƙiyar faɗuwar gaba da ta ji ita ce ta sanya ta sake runtse idanunta na tsawon sakanni, kafin ta buɗe a hankali ta juya idanunta a kan gadon da Ameer ke kai. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 21 Ƙura masa kumburarrun idanunta ta yi tana kallon yadda gaba ɗaya ya wani miƙe a kan gadon, gaba ɗaya sautin nan nasa da take jiyo wa ta daina ji kwata-kwata. Maimakon ta ji farin cikin fahimtar numfashinsa ya daidaita, sai ta ji wata irin faɗuwar gaba ta ziyarce ta, wadda ta sanya ta saurin runtse idanunta. A hankali ta shiga taka wa zuwa kan gadon, har lokacin idanunta a kan Ameer. Hannunta duka biyun ta saka ta riƙo fuskarsa, a sanyaye ta furta "Ameer." Ta ƙare sunan da ya gama fita da sautin bugawar zuciyarta. Shiru babu amsa. Ba tare da kawo komai cikin ranta ba ta sake kiran sunansa a karo na biyu, nan ma dai shiru, bai kuma motsa ba, haka zalika bai kalle ta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci jikinta ya ɗauki rawa. Ta sake yin amfani da duka hannayenta biyu wajen riƙo shi, ta shiga jijjiga shi a haukace tana faɗin "Ameer ka tashi, Ameer ka tashi mana. Meye haka kake yi Ameer? Ameer.." Ta ƙare maganar cikin ɗaga murya. Dalili kenan da ya sa Hidaya da Sultanah da ke waje saurin shigo wa cikin ɗakin. Ko sanin sun wanzu cikin ɗakin ba ta yi ba, a haukace ta ci gaba da faɗin "Ameer ka tashi mana Ameer ka tashi don girman Allah." Ta faɗa muryarta na wani irin sarƙewa. A tsorace suke kallon abin da ke faruwa tsakanin Daneen da Ameer, gaba ɗaya tashin hankali ne ya bayyana a kan fuskarsu. Sultanah ta kalli Hidaya, murya can ƙasa ta ce "Sisi je ki kira Likita." Sai da Hidaya ta lumshe idanunta tana jin wani irin tausayin Daneen ɗin na kama ta kafin ta fice daga ɗakin. Babu daɗewa suka shigo tare da Likitan, har kuma zuwa lokacin Daneen ba ta haƙura ba, ci gaba take da jijjiga Ameer tana kiran ya tashi, ya buɗe idanunsa. Hidaya ce ta ƙarasa ta riƙo Daneen tana faɗin "Bari Likita ya duba shi." Hannu Daneen ta saka tana shirin ƙwace jikinta a lokaci ɗaya tana furta "Kin gan shi fa ba ya motsi." Ta ƙare tana nuna Ameer ɗin da hannunta ke wani irin karkarwa. Riƙe ta sosai Hidaya ta yi tana faɗin "Ehh, ki bari ya duba shi." Ta faɗa cikin rarrashi tana rungumo Daneen ɗin. Tun kafin ta kai ta jikinta take iya jiyo sautin bugun zuciyarta da yake fita da wani mahaukacin gudu. Gaba ɗayansu ƙura wa Likitan idanu suka yi, suna kallon lokacin da ya fara gwada Ameer. Daneen ta kafe shi da jajayen idanunta tana jira ta ji abin da zai faɗa. Zuwa can sai ta ga ya zame abin da ya saka a kunnensa, ya kuma ja zanin da ke a iya cinyar Ameer ya rufe masa fuska, ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa, kafin ya juyo a sanyaye idanunsa a kan Daneen da ita ma shi take kalla tamkar idanunta za su faɗo. "Ameer ba ya tare da mu, Ki yi haƙuri Allah Ya karɓi abinsa." Ya faɗa a sanyaye, don shi kansa ya matuƙar gigita da mutuwar Ameer ɗin, saboda yadda bayan an gama masa aikin ya gwada masa komai ya ga normal, kuma suke saka masa ran samun lafiya da yardar Ubangiji cikin ƙanƙanin lokaci, sai ga shi cikin awannin da ba su da yawa Allah Ya karɓi abinsa. Kwata-kwata ma ba ta ji abin da ya faɗa ba, saboda yadda hankalinta ya koma kan Ameer da ta ga Likitan ya lulluɓe. "Me ya sa za ka rufe shi? Kar ya kasa shaƙar iska." Daneen ta faɗa bayan ta yi nasarar fusge hannunta daga cikin na Hidaya, ta ƙarasa tana ƙoƙarin buɗe Ameer. "Ki yi haƙuri Ameer ya koma wajen mahalliccinsa." Likitan ya faɗa don ya ga alama ba ta fahimce shi ba. "Ƙarya kake yi Ameer ɗina bai mutu ba, Ameer bai mutu ba, Ameer ba zai taɓa iya tafiya ya bar ni ba." Ta ƙare cikin ɗaga murya tana kallon Likitan. Kafin ba tare da ta bi ta kansa ba, ta saka hannu ta yaye lulluɓin da ya yi masa, ya zamana tana iya kallon fuskar Ameer, ta ce tana bubbuga fuskar tasa. "Ameer ka tashi ka ƙaryata abin da mutumin nan yake faɗa, ka tashi ka yi mini magana Ameer. Ameer don Allah kar ka tafi ka bar ni, kar ka yi mini haka Ameer. Ya ya zan yi da rayuwata idan ya zama babu kai? Mai zan koma na cewa Inna idan ka yi mini haka? Don Allah idan wasa kake yi ka tashi Ameer. Me ya sa zuciyarka ba ta da juriya ne Ameer, me ya sa ka koyi rashin juriya bayan a da kai ne me juriyar. Yanzu ni za ka yi wa haka Ameer? Tafiya ka yi ka bar ni a wannan duniyar Ameer?" Daneen ta faɗa cikin gigitaccen kuka tana girgiza kanta. Idanunta har wani hazo-hazo take gani saboda tsabar kuka. "Ka tashi Ameer, ni ce fa nake ce maka ka tashi, wai so kake su sake ce mini ka mutu? Ameer me ya sa za ka yi mini haka?" Ta ƙare maganar tana kifa kanta a ƙirjin Ameer, ta shiga girgiza kanta tana fidda wani irin sautin kukan da ke fitowa tun daga can ƙarƙashin zuciyarta. Hannu Hidaya ta kai ta riƙo Daneen, duk da yadda ta kasa ko gezau ne ta ƙi ɗaga jikin Ameer, hakan bai hana Hidaya yin iya ƙoƙarinta ba wajen ɗago ta. Sai kuwa ta faɗa jikinta tana fashewa da sabon kuka, mai tsuma zuciyar mai sauraro. Kuka take irin kukan nan da ke fita haɗe da zafin da ɗan adam ke ji a cikin zuciyarsa. "Kin ga ya ƙi kula ni koh? Ya ƙi yi mini magana don in yarda da abin da wancan mutumin ya faɗa. Me ya sa Ameer zai mutu ya bar ni? Bai san yadda nake ƙaunarsa ba ne?" I zuwa lokacin Hidaya kasa jurewa ta yi, kawai ita ma sai ta fashe da kukan tana saka hannunta ta dafe kan Daneen da ke kan kafaɗarta. Wani irin tausayin Daneen ɗin na ci gaba da ratsa ta. Nauyin da ta ji ne a jikinta ya sanya ta kai hannunta ta goge hawayen kan fuskarta, daidai lokacin da Sultanah ke faɗin "Hidaya kamar ta suma fa?" Ta ƙare maganar kamar mai tambaya. Likitan da kansa ya yi kiran nurses aka zo aka fitar da Daneen ɗin da ta fice a hayyacinta gaba ɗaya daga cikin ɗakin. Duka suka bi ta da kallo ba tare da kowa ya ce komai ba. Lokacin da su Maama suka ji labarin rasuwar Ameer ba ƙaramin tashi hankalinsu ya yi ba. Kusan gaba ɗaya suka ɗauki salati, cike da tausayin Daneen ɗin da wasu daga cikinsu ke kallon ta tamkar 'yar'uwarsu, tun lokacin da ta sadaukar da wani abu daga jikinta zuwa Tareeq. "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Tareeq ya faɗa yana runtse idanunsa. Haƙiƙa tabbas ya ji mutuwar yaron, duk da bai taɓa ganinsa ba sai labarinsa. Ita kanta wadda ta ba shi ƙodar har yanzu bai taɓa ganinta ba, duk da yadda yake so ya haɗu da ita ya ga wace ce ita, sannan kuma ya yi mata godiya a bisa wannan sadaukarwar da ta yi. Sai ga shi lokaci guda ana faɗin ɗan'uwan nata da take komai saboda shi ya rasu. "Ubangiji Allah Ya gafarta masa." Ya faɗa yana jin har zuciyarsa babu daɗi. "Ameen Ya Rabbi. Allah Sarki yarinyar nan, wallahi tausayi take ba ni, tana matuƙar ƙaunar yaron, ko awa ɗaya ka zauna da ita sai ka fahimci irin ƙaunar da take wa yaron. Ashe ɗazun sallama ta je su yi, kai ya ilahil alameen ka gafarta wa yaron nan, wai ƙaramin yaro da ciwon zuciya." Dada ji ta faɗa jiki a sanyaye. "Ciwon zuciya?" Tareeq ya faɗa cike da mamaki. Jinjina kai Dada ji ta yi kafin ta ce "Wallahi kuwa, ai a kan hakan ma aka yi masa aiki. Ashe ashe ma ba zama zai yi ba." "Ikon Allah! Allah Ya gafarta masa." Tareeq ya faɗa shi ma jikin nasa a sanyaye. Hidaya ce take zaune a ɗakin da Daneen ke kwance, ta kwashi fiye da awa uku kafin ta farka. "Ameer." Nan ma da abin da ta farka kenan. A kan laɓɓanta Hidaya ta furta "Ya Allah." Tana miƙewa ta ƙarasa kan gadon. "Me nake a nan? Ina ɗan'uwana yake?" Ta faɗa a zabure tana kallon gefe da gefen ta. "Ki yi haƙuri ki zauna Daneen, don Allah ki yi haƙuri." Girgiza kai Daneen ta shiga yi, daidai lokacin da wasu sabbin hawaye suka fara zubowa sharr sharr a kan kuncinta. "Shi kenan Ameer ɗina, zuciyata zafi take yi mini, ina jin tamkar za ta fito daga ƙirjina, ta ya ya zan iya jure rashin ɗan'uwana rabin jikina? Wai Ameer ne ya rasu? Ameer fa, ya rasu? Ya tafi kenan ya bar ni? Ba zan sake ganinsa ba, ba zan sake jin maganarsa ba? Ba za mu sake zuwa makaranta tare ba? Ba za mu sake fita kasuwa tare ba? Dada ba za ta sake saka mu aiki tare ba? Ba za mu sake yi wa Innarmu aiki tare ba? Ba zan sake ganinsa yana dariya ba? Ba zai sake zama kusa da ni yana ba ni labari ba, ba zai sake ɗora kansa a kan kafaɗata ya yi kuka ba, ya sanar da ni matsalarsa, ya kira ni Addarsa. Ashe ɗumbin ƙaunar da nake masa ta ƙanƙanin lokaci ce, ashe ba za mu daɗe da shi ba? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Ya Allah Ka sassauta mini abin da nake ji, zuciyata za ta iya tarwatsewa. Wayyo Ameer ɗina." Ta ƙare maganar lokacin da wani sabon kuka ya ƙwace mata. Jikin Hidaya ne ya ƙara yin sanyi, ta shiga share hawaye saboda yadda maganganun Daneen ɗin suka sake jefa ta cikin tausayinta matuƙa. "Ki yi haƙuri." Shi ne abin da ta iya faɗa a sanyaye. Daidai lokacin da Likitan ya ƙaraso cikin ɗakin, ba tare da ya ce komai ba, ya ƙarasa haɗa allurar hannunsa. Ya yi wa Hidaya alama da kansa, miƙewa ta yi ta ƙarasa inda Daneen take ta riƙe ta, da taimakonta ya yi wa Daneen wadda ke shirin soma magana allura. Wani irin runtse idanunta ta yi na tsawon sakanni, maganar da ta kasa fitowa kenan. Kawai sai ta koma ta kwanta a kan gadon numfashinta na fita da sauri da sauri, A hankali ta ji wani irin bacci na fizgarta, lokaci guda tasirin baccin ya yi nasarar danne duk wani abu da take ji, don haka cikin ƙanƙanin lokaci wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita. Kusan a tare Doctor Adam da Hidaya suka sauke ajiyar zuciya, ya kalli Hidaya ya ce "Na yi mata allurar bacci don tana buƙatar ƙwaƙwalwarta ta huta, idan ba haka ba za a iya samun matsala. Ki kula da ita." "In Sha Allah." Hidaya ta faɗa tana jinjina kai. Daga haka ya fice daga ɗakin, ya yin da ta ci gaba da zama idanunta a kan Daneen ɗin cike da matsanancin tausayinta. ... "Daneen." Hidaya ta faɗa da sauri tana ƙarasawa inda Daneen ɗin ke tsaye, bakin ƙofa tana ƙoƙarin fita daga ɗakin. "Ina za ki je?" "Wajen Ameer." Ta ba ta amsar tana kallon ta. "Ya Ilahy." Hidaya ta faɗa tana dafe goshinta. "Ina so ne kawai in sake kallon fuskarsa, duk da na san ba magana zai yi mini ba." Sai a lokacin sannan Hidaya ta sauke ajiyar zuciya jin abin da Daneen ɗin ta faɗa. "Amma dai ya kamata ki je ki ɗan huta tukunna." "Uhmm.. uhmm." Ta faɗa tana girgiza kai, ta lumshe idanunta tana jin yadda kanta ke juyawa kamar zai rikito ƙasa. Ganin haka ne ya sa Hidaya ta bi bayanta. Har ɗakin da Ameer ke ciki Daneen ta shiga, sai dai ga mamakinta babu kowa a ciki, ta ƙarasa tana sake duddubawa hankali a tashe. "Ina suka kai mini ɗan'uwana?" Ta tambaya a razane, lokacin da ƙwalla ta kawo idanunta. "Bari na kira miki Likita." Hidaya ta faɗa tana ficewa daga ɗakin. Bin ta da kallo kawai Daneen ta yi kamar wata doluwa, har zuwa bayan wasu mintina Doctor Adam ya shigo cikin ɗakin. Muryarta har rawa take lokacin da ta furta "Ina Ameer? Ina ɗan'uwana yake?" "Ɗan'uwanki Yohanah ya karɓi gawarsa. Mun yi duk wasu abu da ya kamata lokacin kina bacci, ba zai yiwu kuma a jira ki ba saboda ba bacci ne mai ƙarewa da wuri ba, shi ya sa ma ya karɓe shi kawai." Wani irin bugawa da zuciyarta ta yi, shi ne ya sanya ta saurin kai hannunta kan ƙirjinta tana lumshe ido, kawai sai ta koma ta yi yaɓar a kan gadon, daidai lokacin da wani irin jiri ya soma ƙoƙarin kayar da ita, duk kuwa da a zaune take. "Thank god, zo ka yi magana da ita." Doctor Adam ya faɗa yana kallon Yohanah da ya shigo cikin ɗakin. Babu ɓata lokaci kuma ya fice bayan sun gaisa da Yohanah. "Daneen." Yohanah ya faɗa yana ƙarasawa inda Daneen take, sai a lokacin ta iya ɗaga idanunta da suka yi mata wani irin nauyi ta kalle shi, tun kafin ya ce komai ta ce "Ina ka kai mini ƙanina?" Sai sa ya fesar da iska daga bakinsa sannan ya ce "An binne shi." Amsawar da ciwonta ya yi, shi ne ya tuna mata akwai ɗanyen aikin da ba a daɗe da yi mata shi ba. Ta runtse idanunta tana girgiza kai. Kafin a hankali ta ɗaga su ta kalle shi, muryarta na karkarwa ta ce "Ameer musulmi ne, kai kuma ba musulmi ba ne." Girgiza kai Yohanah ya yi kafin ya ce "Kar ki damu, wajen wani maƙocina na kai shi, shi ya yi masa komai na musulmai." Kukan da take ta ƙoƙarin dannewa shi ne ya ƙwace mata, ta zube a wajen tana soma raira shi. Shi kenan Ameer ya tafi ya bar ta, shi kenan da gaske ita da Ameer sai dai a lahira. Kwata-kwata ta kasa cewa komai, sai kukan da take gaba ɗaya jikinta na wani irin rawa. "And har Alhaji Dikko ma ya samu damar halartar jana'izar." Ya ƙara mata bayani a kai, don cire shakkun da ya gani a tare da ita lokacin da yake magana. Cakk kukan da take ya tsaya, ƙirjinta ya buga a lokaci guda, hawayen da suke sintiri a kan kuncinta suka dakata. Har ba ta san lokacin da ta miƙe a kan ƙafafunta ba, tana kallon Yohana ta ce cikin dakushashshiyar muryarta. "Waye Alhaji Dikko?" Da mamaki Yohana ke kallon Daneen, ganin da gasken ƙarin bayani take nema ya sanya shi faɗin "Mahaifin wanda kika ba wa ƙodarki.." Cikin wani irin tashin hankali, ruɗu ta ƙarasa kusa da Yohana, tana kallon cikin idanunsa ta furta "Ɗansa na ba wa ƙoda?" Ta tambaya a gigice. Jinjina mata kai ya yi alamar tabbatarwa. Ta runtse idanunta, tana buɗewa lokaci guda a kan Yohanah. "Shin ka san kuwa dalilin mutuwar Ameer?" Nan ta shiga sanar da shi abin da ya faru da Ameer, da kuma ambatar ɗan gidan Alhaji Dikko da Ameer ya yi, kafin ta ɗora da faɗin "Yanzu kuma kana mini wata magana da na kasa fahimtar ta. Me kake so ka faɗa mini? Me kake so ka ce mini? Faɗa mini tun kafin zuciyata ta buga, ƙaryata abin da zuciyata ke hasaso mini don Allah kar ka ce na ɗauki wani sashe na jikina na sadaukar da shi ga wanda ya zama silar mutuwar ɗan'uwana." Ta ƙare maganar jajayen idanunta da suka kumbura sosai kamar mai ciwon ido a kansa. Sai da Yohanah ya lumshe idanunsa, ya dafe ƙirjinsa yana sauke ajiyar zuciya, saboda shock ɗin da abin da ke fito wa daga bakin Daneen ya shigar da shi, kafin ya soma faɗin. "Alhaji Dikko dai ɗaya ne cikin garin nan, wanda kowa ya san shi. Kuma ɗa namiji ɗaya gare shi, shi ne kuma wanda kika ba wa ƙodarki." Yohana ya ƙare maganar yana gyara tsayuwarsa, idanunsa a kan Daneen. Ameer! Ya Allah 😭 Ina miƙa saƙon ta'aziyyata zuwa gare ku, Allah Ya ji ƙan Ameer. A yi haƙuri da abin da aka gani, kar a cinye ni ɗanya. 😂 Dama haka rayuwar take, dukkanmu abin da muke jira kenan, sai dai fatan Allah Ya sa mu cika da kyau da imani. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 22 Wani irin dumm ta ji kunnenta ya yi, jirin da ta ji yana neman kada ta ya sanya ta saurin yin baya ta zube a kan ƙafafunta. Idanunta a rufe suke lokacin da take sake jiyo kalaman Yohana a cikin kunnuwanta, tamkar wanda ke maimaita mata su. Kallon gefen sa Yohana ya yi ko zai samu ruwa ya ba ta ta sha, ko ta ɗan ji sassaucin zafin da ko ba a faɗa ba ya san abin da take ji kenan. Musamman kuma da saboda tsabar ruɗewa hawaye ko kaɗan ya ƙi sauka a kan fuskarta. "Bari na samo miki ruwa." Ya faɗa yana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin. Da sauri ta girgiza kai, lokaci ɗaya tana buɗe idanunta da suka sake haɗewa suka yi wani irin mahaukacin ja. Ta kafe shi da su tamkar mai neman ƙarin bayani. Fahimtar abin da take nufi ne ya sanya shi jinjina kai, kafin ya ɗora da "Abin da na faɗa haka yake. Amma ki kwantar da hankalin ki, komai zai zo cikin sauƙi." Cikin wani irin zafin nama ta miƙe tsaye a kan ƙafafunta da suke rawa, amma ba ta damu da hakan ba, tsananin tashin hankalin da take jinta a ciki ya sanya duk wani abu da take ji ba ta damuwa da shi. Wani irin huci take fitarwa, gudun numfashinta ya ƙara sauri, ya yin da zuciya da komai nata suka ƙeƙashe. "In kwantar da hankalina kake faɗa mini? Shin ka manta abin da ya faru ne? In ɗauki ƙodata in sadaukar da ita gurin wanda ya zama sanadin mutuwar ɗan'uwana sannan ka zo kana ce mini in kwantar da hankalina? In kwantar da hankalina ta ya ya? Ta ya ya zuciyata za ta sami sukuni, bayan ƙodata na can jikin makashin ɗan'uwana? Ta ya ya zan kwantar da hankalina bayan wanda ya yi silar mutuwar Ameer na ci gaba da rayuwa ne a dalilin taimakon da na masa. Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Ta faɗa tana dafe kanta da duka hannayenta biyu saboda wani irin juyawa da yake mata. Iska Yohanah ya fesar daga bakinsa, ya jinjina kai kafin ya sauke ajiyar zuciya, cikin kwantar da murya, saboda yadda ya ga yanayin Daneen ɗin ya sauya cikin ƙanƙanin lokaci ya ce "Nemi waje ki zauna." Idanunta ta ɗaga ta watsa masa, ya dafe goshinsa kafin ya ce "Ki zauna ki ji abin da zan faɗa miki." Nan ma dai ba ta motsa ba, bai kuma ga alamar za ta zauna ba. Don haka sai ya ƙarasa kusa da ita, a hankali ya soma faɗin "Ban yi niyyar sanar da ke komai a yanzu ba. Sai dai bisa ga dukkan alamu ƙudirinmu zai iya zama iri ɗaya. Shin kin shirya ɗaukar wa ɗan'uwanki fansa? Idan ehh ne amsar, toh ki zauna mu yi magana." Tun da ya fara maganar take kallon shi har ya dakata. Ta runtse idanunta tana jin yadda kwata-kwata numfashinta ya ƙi saituwa. Tunanin ɗan'uwa rabin jikinta ya tokare mata komai, uwa uba kuma wannan mummunan al'amarin da ya faru, ta rasa inda za ta saka kanta ta ji daɗi. Kukan da take ta ɗan ji sanyi a ranta yanzu ta kasa, ta kasa kwata-kwata, ban da wani irin abu da ya tokare mata ƙirji ya hana ta sakat, babu abin da take ji. Ajiyar zuciya Yohana ya sauke a karo na barkatai lokacin da ya ga Daneen ta zauna, ta shiga jinjina kanta kafin a fili ta ce da dashashshiyar muryarta. "Zan iya komai saboda ɗan'uwana. Ƙalilan abu ne ba zan iya ba.." Kafin ya ji ta ambaci abin da ba za ta iya ɗin ba, ya katse ta ta hanyar fara faɗin "Kar ki damu, ki yi shiru kawai ki saurare ni." Ya ɗan dakata a nan kafin ya ci ga da faɗin "Wato a zahirin gaskiya, ni ɗin nan da kika gani, ban saka hannuna dumu-dumu cikin sha'aninki da ɗan'uwanki haka kawai ba, sai saboda wata manufa. Manufar kuma ba komai ba ce, yanzu za ki ji ta. Na kawo ki asibitin nan ne saboda ki bayar da ƙodarki ga Tareeq, wanda na samu labarin rashin lafiyarsa a wajen wani abokina da yake bibiyar mana rayuwarsa. Na sanar da ke su ne za su biya kuɗin aikin, saboda kar ki saka wani abin a ranki, ina tsoro kar ki saka shakku a kaina, har idan an zo gaɓar da nake so in faɗi ba tare da na yi nasara ba. Sai dai a zahirin gaskiya ba su ne suka biya kuɗin aikin Ameer ba, ni ni ne nan na biya kuɗin, ya yin da su kuma aka sanar da su kin bayar da ƙodarki ne kyauta ga ɗansu ba tare da kina buƙatar ko sisinsu ba. Na san za ki yi mamakin dalilin da ya sa na yi hakan, toh ba komai ba ne face saboda sanin halin Alhaji Dikko da na yi. Idan dai har daga ƙarshe ya fahimci wace ce ke, zai iya ɗaukarki zuwa cikin gidansa, a matsayin wadda kika ba wa shalelen ɗansa ƙoda ba tare da buƙatar ko sisin kwabo ba. Ni kuma dama abin da nake so kenan. Na san idan dai har na ce ki je ki ba su ƙoda a baki kuɗi, daga baya ko da wani abu ya faru, ba lallai su kalle ki ba, tun da zai iya yiwuwa ma daga lokacin da suka ba ki kuɗin ƙodarki shi kenan sun gama da ke. Ko kuma ma ba lallai su haɗu da ke ba, ƙila a yi komai ta hannun likita. Ni ɗin nan da kike gani, fansa nake so na ɗauka a kan Tareeq, shi ya sa na so amfani da ke wajen tura ki cikin gidansu, aikina ba mai wahala ba ne, zan iya cewa naki ma ya fi shi wahala. Idan dai har ki amince sai na sanar da ke abin da za ki yi mini. Sai dai abu ɗaya nake so ki tuna shi ne, ke ɗin kin sani ba kowa ba ce, ba za ki iya yin shari'a da ɗan gidan Alhaji Dikko ba, saboda ba wannan karon ne farko da wasu da dama suka yi yunƙurin yin hakan ba. Ki sani idan dai har kika amince kika aiwatar da abin da zan sanar da ke, toh ki kwantar da hankalinki, ni da kaina zan yi amfani da duk wata dukiya da nake ita, in taimaka miki wajen shigar da Tareeq ƙara, kuma ba zan haƙura ba har sai an ƙwato wa ɗan uwanki haƙƙinsa. Amma fa duk hakan ba za ta yiwu ba, sai kin san yadda kika yi kika shiga gidan na Alhaji Dikko, kika yi duk abin da zan faɗa miki. Daga nan sai ki koma wajen mahaifiyarki ku taho a fara shari'ar mutuwar Ameer. Dukkanmu abu ɗaya ne a ranmu, FANSA! Saboda haka za mu haɗa hannu mu yi aiki tare." Shiru Daneen ta yi na tsawon mintuna bayan da ta gama jin maganganun Yohana. Maganganun da suka shigar da ita cikin duniyar tunani, haɗa su take sake yi waje ɗaya tana ci gaba da fahimtarsu. Zuwa can ta sauke ajiyar zuciya tana kai hannunta saitin zuciyarta da ke ci gaba da bugawa ta dafe. "Ki yi magana please." Ya faɗa yana kallan ta, a ransa yana fatan Allah dai Ya sa ba ƙin amincewa za ta yi ba. Ba tare da ta damu ta ji dalilin Yohanah na ɗaukar fansa a wajen Tareeq ba, ita dai kawai tun da ta san za ta ɗauki fansa ne a kan ɗan'uwanta shi kenan. Don haka ta buɗe bakinta da ya yi mata nauyi ta ce "Na amince!" Ta faɗa don tabbas duk wasu abubuwa da Yohanah ɗin ya faɗa ya yi mata. Ta kuma amince da shi ɗari bisa ɗari. Wata gauruwar ajiyar zuciya ya sauke kamin ya ce "Za ki iya zuwa ki huta, za mu ƙarasa maganar." Miƙewa ta yi ba tare da ta ce komai ba, duk da yadda ta ji jiri na shirin mayar da ita, hakan bai sanya ta komawa ta zauna ba, ta soma takawa a hankali tana runtse idanunta lokaci bayan lokaci. "Amma kar ki sake ki sanar da su kina da iyaye a can wani waje. Ka da ki sake ki nuna musu kina da iyaye, na sake maimaita miki. Idan har da gaske a kan ɗaukar fansar ɗan'uwanki za ki je gidan yi, toh kar ki sake su san da wannan maganar. Ki bari tukunna sai bayan komai ya kammala sai ki koma wajen mahaifiyarki da zancen mutuwar Ameer, sai dai kuma tare da kyakykyawan labarin kin ɗauki fansa a kan wanda ya yi sanadin mutuwar ɗan'uwan naki." Maganganun Yohana suka daki dodon kunnenta. Ta ɗan dakata kaɗan, amma ba tare da ta juyo ba. Kenan hakan na nufin za ta ci gaba da zama tare da su ba tare da ta koma wajen Innarta ba? Ko da yake lokaci ne ƙanƙani, daga zarar ta samo wa Yohana abin da yake so, shi kenan Tareeq ya shiga hannu, kamar yadda ya sanar da ita, ta kuma san lokacin ne hukuma za ta ƙwatar wa Ameer haƙƙinsa. Don haka kawai ta jinjina kai, a kan laɓɓanta ta furta. "Toh." Wanda ita kanta ba ta da tabbacin ya ji ta ko bai ji ta ba, don ita kanta ba ta ji sautin maganar tata ta fita ba. Tamkar wata er maye haka ta ci gaba da takawa don isa ɗakin da aka kwantar da ita. Duk kuwa da irin yadda jiri ke ci gaba da kwasarta, yana ƙoƙarin kifar da ita hakan bai sanya ta dakatawa ba. Gaba ɗaya zuciyarta ta bushe, ta ƙeƙashe, Fansar nan dai ita kaɗai ke yawo a cikin zuciya, ruhi da ƙwaƙwalwarta. Numfashi Yohana ya fesar lokacin da ta ida ficewa daga cikin ɗakin, ya fito da wayarsa yana sake fesar da iska daga bakinsa, har lokacin idanunsa a kan wayar. "Kai baba shege ne wallahi, ka fiya takura. Toh yanzu ga shi garin abin da na yi da kake ta kushewa ya janyo mana wata hanyar mafi dacewa. Ga shi nan yanzu mafita ta same mu cikin sauƙi. Ya kamata ka sara mini, don wallahi kaina na wuta, ka jira ni gani nan zuwa, idan na zo zan yi maka bayani." Daga haka ya katse wayar yana miƙewa, ba tare da ya bi ta kan kowa ba ya fice daga asibitin. ... Sun fi awa cikin asibitin, amma ta kasa matsa wa ko nan da can ne daga kusa da Tareeq ɗin. Duk da wanzuwar Maama, Ummanta har ma da Abeey hakan bai dame ta ba. "Ya kamata fa a yi maganar auren yaran nan Yaya." Umman Jawahir ta faɗa daga inda take zaune tana kallon Jawahir. Shi ma Abeey kallon su ya yi kafin ya ce "Kar ki damu, daga zarar yaron nan ya samu lafiya, za mu yi magana da mahaifin Jawahir a tsayar da ko sati ɗaya ne. Ban ga amfanin ɓata lokacin ba, saboda haka ku ma ku fara shiri." Cikin wani irin farin ciki Umman Jawahir ta ce "Alhamdulillahi, Allah Ya ƙara girma Yaya, Ya kuma tabbatar mana da alkhairinsa." Murmushi ya yi kafin ya amsa da "Ameen." Daidai lokacin da Dada ji ta shigo cikin ɗakin, Maama da ba ta daɗe da fita ba na bin bayanta. Ta nemi waje ta zauna lokaci ɗaya tana amsa sannu da zuwan da suke mata. "Alhassan har yanzu fa sau ɗaya matarka ta zo duba yaron nan." Dada ji ta faɗa tana kallon Abeey. Sai da ya ɗaga kai ya kalle ta sannan ya ce bayan ya sauke numfashi kaɗan "Ki bar ni da ita Dada ji, babu damuwa." Girgiza kai ta yi ta ce "A'ah, kar ka yi mata komai. Na tambaya ne dai in ji ko ba ka sani ba, toh amma tun da ka sani ɗin bar ta. Ta ci gaba da duk abin da ta ga shi ne daidai, babu damuwa." Dada ji ta ƙare maganar tana irin murmushin nan na gefen baki. "Ai Dada ji da kin bar Yaya ya yi mata ko ma mene ne, ban da iskanci kuna cikin gari ɗaya, gida ɗaya a ce wai sau ɗaya ta zo ta duba Tareeq duk uban jikin da yake sha? Mu kan mu da ba ma garin gaba ɗaya hankalinmu na nan, ba shi ne dalilin da ya sa muka dawo yau ba. Ai da ba yau za mu dawo ba. Amma ita ki ga abin da take fa." "Ummu Kulsum ki yi shiru ki bar mutum da halinsa, akwai ranar ƙin dillanci." Dada ta katse ta da faɗin hakan. Jijjiga kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba. ... Tun da ta shigo Hidaya ke kallon ta. Ta tashi da sauri don ta taimaka mata saboda yadda ta ga tana tafiya tana wani rangaji, sai Daneen ta yi amfani da hannunta wajen dakatar da ita kafin a fili ta furta can ciki. "Zan iya." Hidaya ba ta takura mata ba, ta koma ta nemi waje ta zauna, ya yin da ita kuma Daneen ta ƙarasa kan gadon ta kifa kanta a kan gwuiwarta ta runtse idanunta. Sai a lokacin sannan ta ji wannan abin da ya tokare mata ƙirji ya soma warwarewa, lokacin da wasu hawaye suka taru a cikin idanunta, kafin ka ce mene wannan sun soma sintiri a kan kuncinta. Wasu zafafan hawaye ne, da suke sakkowa da zafin su, wanda kuma ba na komai ba ne sai na nadama, takaici, da kuma baƙin cikin ba da ƙodarta ga mugu, azzalumi, wanda ba ya tsoron Allah!! "Yah Tareeq!" Hidaya ta faɗa tana miƙewa bayan ta amsa sallamarsa. "Wai da kanka?" Ta ambata tana kallonsa murmushi fall kan fuskarta. Shi ma murmushin ya ɗan yi kafin ya jinjina kai kawai. "Alhamdulillahi, sannu, ka ƙaraso Yaya." Babu musu ya ƙarasa shigewa cikin ɗakin a nutse cike kuma da takatsantsan. Ya nemi waje ya zauna kan wata kujera, idanunsa a kan Daneen da ake iya jiyo sautin shashsheƙarta. Sai da ya ɗaga kai ya kalli Hidaya kafin ya ce bayan ya ɗan ƙanƙantar da kyawawan idanunsa. "Subhanallahi! Har yanzu ba ta bar kukan ba?" Sai da Hidaya ta rausayar da kanta kafin ta ce "Wallahi kuwa, na rasa yadda zan yi." Hannu ya saka ya ɗan murza goshinsa, har ga Allah ya ji mutuwar yaron nan, ba kuma zai so a ce wadda ta zama silar ci gaba da rayuwarsa tana zaune cikin wannan halin ba. Don haka cikin muryarsa mai daɗin saurara ya ce "Sannu.." "Daneen.. Yah Tareeq.." Hidaya ta faɗa tana murmushi. "Ohh.." ya faɗa yana ɗage girarsa ɗaya. Kamar daga sama ta ji sunan Tareeq da Hidaya ta ambata, sunan da tun da Yohana ya sanar da ita shi ne ɗan gidan Alhaji Yohana ta ji ta tsani jin sunan, ballantana kuma a kai ga ganin mamallakin sunan da ba ta taɓa ganinsa ba. Sai dai tarin abin da ya bar mata danƙare a cikin zuciya na da yawa. Har ba ta san lokacin da ta ɗaga jajayen idanunta ta sauke su a kan Tareeq ba. Karo na farko da ta fara ganin kyakykyawar fuskar Tareeq, wadda a gare ta baƙa ƙirin ce, fuska mafi muni a rayuwarta, fuskar mutumin da ya zamo silar wargajewar farin cikinta. Shi ma wannan ne karo na farko da ya soma ganinta. Idanunta cikin nasa suka faɗa, saboda yadda ta ɗago ba tare da ta shirya ba. Duk da tsananin tasirin da idanun Tareeq ke da shi, hakan bai sanya ta ko da ƙoƙarin janyewa ba ne, sai ma ci gaba da jefa masa wani mummunan kallo da ta yi, tana jin yadda zuciyarta ke ci gaba da zafi, wata uwar wutar fansa na sake ruruwa a ƙirjinta. Cikin basarwa, duk da yadda ya tsargu da irin kallon da take bin sa da shi, sai dai ƙaryar mutum ya fahimci hakan, ya ɗan gyara zamansa kaɗan kana ya ce "Ya ƙarin haƙuri? Ki yi haƙuri Allah Ya gafarta masa, Ya sa can ta fiye masa nan. Ke kuma Allah Ya saka miki da alkhairi. Na gode sosai, na kuma yaba da ƙoƙarinki." Runtse idanunta Daneen ta yi tana jin yadda kalamansa ke ratsa kunnuwanta, jin tasirin su take tamkar ana soka mata mashi a ƙirji. Jin su take kamar yana watsa mata ruwan zafi tafasasshe. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 23 Har kusan bayan minti ɗaya da gama maganar ba ta ce komai ba. Shi ma kuma bai damu ba, don ko shi wani lokacin ya kan tsinci kansa cikin rashin son yin magana. Musamman ita kuma da take cikin wannan hali, dole ne ya yi mata uzuri. A nutse cike kuma da takatsantsan ya miƙe tsaye ba tare da ya sake kallon inda Daneen take ba ya dubi Hidaya, kafin ya ce komai ta ce "Yaya sai haƙuri, mutuwar ta taɓa ta sosai wallahi. Tun kuma da aka ce an fitar da gawarsa daga cikin asibitin nan abin ya sake yin gaba. Ka ga duk ta takura kanta, tun ɗazu ba ta umm ba ta umm umm. Kawai dai a takure take." Ta ƙare maganar a dame. Ɗan lumshe idanunsa ya yi, yana buɗe su lokaci guda. A nutse ya ɗan juya ya kalli Daneen kafin ya juyo bayan ya ɗan sauke numfashi. Sai da ya kai hannunsa saitin ƙirjinsa kafin ya ce "Allah ne Ya sa zan rayu, amma ta sanadin yarinyar nan, saboda haka ki kula da ita tamkar yadda za ki kula da kanki Hidaya. Ko da yaushe ki din ga tuna akwai muhimmiyar tsokarta a jikina, wadda nake tsaye a nan saboda ita." Murmushi Hidaya ta yi, saboda yadda ta ji matuƙar daɗin yadda ya nuna damuwa da kulawa a kan yarinyar da bai taɓa ganinta ba sai yanzun. "In Sha Allah Yah Tareeq. Ko ba ka faɗa ba wannan ya zame mini dole." Jinjina kai ya yi yana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin, Hidaya ta yi saurin faɗin "Bari na taka maka." Daga haka suka jera suka fice daga ɗakin. Tun lokacin da ta ji wannan kalaman nasa ta ji wasu irin hawaye sun tarar mata cikin idanu, sai dai ga mamakinta wannan raunanniyar zuciyar tata, sai ta neme ta ta rasa, kawai dai wani irin zafi take ji da kuma raɗaɗi mara misaltuwa. Maganganun nasa sun matuƙar ɓata mata rai, wato nuna wa yake shi ɗin mutumin kirki ne. Abin da ya fi komai tsaya mata a rai, shi ne maimaita yana rayuwa ne ta dalilinta. Idan ta tuna ta sadaukar da ƙodarta ga mutumin da ya zama silar mutuwar Ameer ɗinta, ji take gaba ɗaya ta tsani kanta, ji take da tana da hannun dawo da agogo baya, da ta dawo da shi, ta ƙi ba shi ƙodarta. Tana nan zaune har zuwa lokacin da Hidaya da Sultanah suka shigo. Ko ɗaga kanta ba ta yi ta kalle su ba, don gaba ɗaya ba ta ƙaunar ganin su. Duk da yadda zuciyarta ke raya mata ba su san waye ɗan'uwansu ba, amma yau dole ta bi abin da wani sashe na zuciyarta ke raya mata. Ci gaba da kaɗaicewa ita ɗaya shi ne mafita. Su ma ba su takura mata ba, suka ci gaba da zama kawai. Bayan kwana bakwai. Abubuwa da dama sun faru a cikin kwana bakwai, ciki kuwa har da ci gaba da kula da lafiyar Tareeq da kuma Daneen. Ta kowanne ɓangare Alhamdulillah ana samun ci gaba. Sai dai Daneen da kullum tamkar ana ƙara mata kewar Ameer ne. Duk lokacin da kewar ta tashi, sai dai ta zauna ta yi kukanta ta gode wa Allah. Don ma dai in da aka samu sauƙi, tana jin sassauci idan ta tuna abin da ya ci gaba da zaunar da ita cikin asibitin. Duk da ba ta da tabbacin idan ta koma ƙauyensu za ta tarar da Innarsu, amma dai tabbas daga zarar komai ya kammala can ɗin za ta nufa. Kullum sai Tareeq ya zo duba ta, ta ɓangaren ta ban da wutar fansa da ke ci gaba da ruruwa a cikin zuciyarta babu abin da zuwansa ke haifar wa sai hakan. Dalili kenan da ya sa ta ga alamun zai shigo za ta fake da bacci ko dai wani abun, wanda zai sa ba za ta haɗa ido da shi ba, saboda yadda take jin wata irin tsanarsa a can ƙarƙashin zuciyarta. Ta ɓangaren sa kuwa, samunta tana bacci ko wani abun bai taɓa damunsa ba. A wajensa ma ya fi son hakan, ko babu komai za ta sake warwarewa sosai. Ya kuma san a cikin kwanakin dole ne ta ci gaba da kewar ɗan'uwanta. A lokacin ne kuma aka sallame su su duka, da niyyar za su din ga dawowa ana duba su lokaci zuwa lokaci. ... "Doctor Adam ya sanar da ni Yohana ɗan'uwanki ne wanda kike da shi shi kaɗai yanzu bayan ɗan'uwanki da kika rasa. Sai dai yau kuma na ji wani batu daban, ya ya abin yake kenan?" Abeey da ke zaune kan kujera ya faɗa yana kallan Daneen da ta yi shiru ita ma tana zaune, kanta na kallon ƙasa. Sai da ta runtse idanunta sannan ta buɗe, ta tuna maganar da suka gama da Yohana yanzu, inda yake jaddada mata kada ta manta, kada ta taɓa ambatar tana da iyaye, idan har da gaske tana son ɗaukar fansar ɗan'uwanta. Don haka ta ɗan sauke numfashi kafin ta soma faɗin "A wajen kishiyar kakarmu muke, wadda ta haifi Innarmu, ita ce ba ta sonmu, kullum cikin muzguna mana take. Ameer da kansa ya ce mu gudu mu bar mata gidan kafin ta ƙara yi mana wani abun. Shi ne ma dalilin da ya sa muka baro ƙauyenmu. Muna so ne mu gina rayuwarmu kafin mu koma mata." Jinjina kai Abeey ya shiga yi kana ya ce "Iyayenku fa..?" Wani irin bugawa ƙirjin Daneen ya yi, sam-sam ƙarya ba halinta ba ne, ba ta saba yi ba kwata-kwata, shi ya sa take ta kame-kame. Yanzu kuma ga shi ya yi mata tambayar da ba ta tunanin za ta iya amsa ta. Ta ya ya za ta buɗi baki ta kashe iyayenta? Innarta fa? "Ayyah, ba dai sun mutu ba?" Ta jiyo muryar Abeeyn kamar ya san me take tunani. Jiki a saluɓe ta ɗaga kai ba tare da ta kalle shi ba, don gani take kamar idan ta ɗaga kai ta kalle shi zai karanto ƙaryar da ta masa. "Ya Salaam.. Allah Ya gafarta musu, Ya sa sun huta." Ba ta iya amsawa ba, sai shi ya amsa abarsa da kansa. Bai kuma damu da hakan ba, don ya san wataƙila ta tuna da iyayen nata ne. Don haka ya gyara zamansa kafin ya ce "Ki kwantar da hankalinki, In Sha Allah daga yau kin zama ɗiyata. Zan ɗauke ki na tafi da ke gidana a matsayin 'yata albarkacin wannan alfarmar da kika yi wa shalelena. Za ki rayu a gidana ba a matsayin wata daban ba, a'ah kamar yadda na faɗa miki daga yau ke ɗin 'yata ce. Zuwa nan gaba kaɗan, In Sha Allah ni da kaina zan kai ki ki ziyarci ita kakar taki, ba kuma da niyyar in mayar mata da ke ba. A'ah, zan kai ki ne kawai ku gaisa, don za ki zauna tare da ni ne In Sha Allah har Allah Ya kawo miki mijin aure." Ɗaga raunanan idanunta Daneen ta yi ta kalli Abeey cike da mamakin jin abin dake fito wa daga bakinsa. Lallai wannan mutumin akwai karamci. Duk wasu alamomi kuma sun nuna bai san waye ɗansa ba, bai san abubuwan da yake aikatawa a ɓoye ba. Sai da ta harhaɗa kalmomin da za ta faɗa sannan ta buɗe baki da ƙyar ta furta "Na gode sosai, Allah Ya saka da alkhairi." Cike da yabawa da hankalin 'yar ƙaramar yarinya mai juriya ya ce "Allah Ya yi miki albarka, Ameen." Daga haka ya miƙe tsaye yana gyara zaman babbar rigarsa. Kafin ya kai ga ci gaba da tafiya ya ce "Ki shirya duk abin da kike buƙata, za a shigo a ɗauka, sai ki fito da su Hidaya mu wuce." "Tom." Nan ma ta faɗa a sanyaye. Sai da ya fice daga ɗakin sannan ta miƙe tsaye, idanunta a lumshe take hango yadda za ta kasance cikin gidan na Alhaji Dikko, da niyyar ɗaukar fansa. Kamar daga sama ta jiyo jagwalgwalalliyar hausarsa lokacin da yake faɗin "Na gode wa Allah." Dalili kenan da ya sanya ta buɗe idanunta da sauri ta sauke a kansa. Hannunsa ya zura a aljihu ya fito da wata babbar waya ya miƙa mata. Bin wayar ta yi da kallo, kafin ta ɗaga kai ta kalle shi. Ya jinjina kai yana nuna wayar da bakinsa. "Karɓi ki ji mana." Ya faɗa a ɗan dame. Hannunta ta saka ta karɓi wayar, daidai lokacin da ya soma faɗin. "Ki riƙe wayar nan, zan din ga kiran ki a cikinta lokaci zuwa lokaci. Ki kasance ko da yaushe kina kusa da ita, kar ki yi nisa da ita, saboda yadda zan din ga jin duk abubuwan da suke faruwa. Kar ki yi wasa don Allah. Kusanci kawai nake so ki samu da 'yan gidan, daga nan zan sanar da ke abin da za ki yi mini." Jinjina kai Daneen ta yi, kafin da muryarta da har lokacin ba ta koma ainahin tata ba ta ce "Ban iya amfani da ita ba." "Riƙe, zan sanar da ke yadda za ki yi amfani da komai. Na saita miki komai, idan kuma na kira, za ki ga wajen accept nan za ki danna." Jinjina kai dai Daneen ta kuma yi ba tare da ta ce komai ba. Ya juya baya da sauri jin kamar motsi. "Bari na tafi, don Allah ki yi komai cikin takatsantsan, don kada a fahimci abin da ya kai ki cikin gidan." Daga haka bai jira ta ce komai ba ya fice daga ɗakin. Wayar hannunta ta bi da kallo na tsawon sakanni, kafin ta juya ta ta shiga kallon bayanta, sai kuma ta matsa ta ja wasu kaya da ta ga Hidaya ta haɗa ɗazun, wanda da alama nata ne ta jefa wayar ciki, bayan ta nannaɗe cikin wani ɗan kwali. Lokacin da Abeey ya sanar wa da Dada ji hukuncin da ya yanke a kan Daneen, murmushi ta yi ta ce "Haba kai kuwa Alhassan, kana tsammanin zan ce ban amince ba? Ni kuwa da wace irin uwa ce? Yarinyar da ta ɗauki ƙodarta ta ba wa Tareeq don ka ce za ka ɗauke ta cikin gidanka sai in hana?" Ta dakata a nan tana girgiza kai, kafin ta ci gaba da faɗin "Ina maraba da ita ɗari bisa ɗari. Allah Ya sa zaman ta alkhairi ne a cikinmu." "Ameen." Ya amsa yana murmushi. Duka a harabar ƙaton haɗaɗɗen asibitin suka haɗu, sai a lokacin Daneen ta nutsu tana ƙarewa wannan waje da ake kira da wai asibiti, wannan kyakykyawan waje kallo. A mota suka ɗunguma, inda driver ke jan su. Dab da za su fita daga asibitin ta ji wani irin hawaye masu zafin gaske sun sauka a kan kuncinta. Sun shigo tare da Ameer, sai ga shi ta fita ita kaɗai ba tare da Ameer ba. Lamarin da tun da take ba ta taɓa zata ba. Ba ta taɓa tsammanin akwai ranar da za ta zo su rabu da Ameer ba, rabuwa ma irin ta har abada. Wani sabon miki ne yau ɗin ya tayar mata a zuciya, kewar ɗan'uwanta ta dawo mata sabuwa. Don haka ta shiga rera shi, tana ji ina ma ina ma a ce mafarki ne take yi, ko kuma wani wajen Ameer ɗin ya tafi zai dawo su ci gaba da rayuwarsu. Har suka isa gidan na Alhaji Dikko ba ta daina kukan da yau ɗin ya dawo mata sabo ba. Tun kafin su sauka, masu aiki suka ƙaraso suka soma kwasar kaya suna shigar da su cikin gidan. Ko samun nutsuwar kallan irin ɓarin kuɗin da aka yi a ginin gidan ba ta tsaya yi ba, don gaba ɗaya hankalinta ba ya wajen. "Sultanah ku je da ita ɓangaren ku." Abeey ya faɗa yana kallan su. "Toh." Sultanah da Hidaya suka amsa kusan a tare. Sai a lokacin suka kalli Daneen, wadda duk suna sane da ita, sun ƙyale ta ne ta yi kukan, don sun san dole ɗan'uwanta ta tuna shi ya sa take kuka. "Su kai ta ɓangaren su kuma kamar ya ya?" Maami da ke ƙarasowa wajen ta faɗa tana bin Daneen da wani irin kallo, tamkar ita ce mai gidan. Da mamaki Abeey ya kalle ta ya ce "Asma'u.." Ya ambata yana kallon ta da matuƙar mamaki shimfiɗe a kan fuskarsa. Sai da ta girgiza kai sannan ta ce "A'ah, ai wai tambaya ce." Girgiza kai Abeey ya yi ba tare da ya ce komai ba, ya ja siririn tsaki yana barin wajen. "Toh ita ce yarinyar da ta ba wa Magaji ƙodarta." Muryar Dada ji ta katse mata saƙe-saƙen da take a zuciyarta. Ta san da biyu ta faɗi hakan, don ta san ba ta ƙaunar ta ji ta kira Tareeq ɗin da Magaji. Abin da ba ta iya ɓoyewa kenan har a kan fuskarta. Sai da ta ɗauke kai tana kai wa iska harara, ba tare da ta bari kowa ya ganta ba sannan ta ce "Amma don kawai ta ba wa Tareeq ƙoda, hakan ba shi ke nuna za a shigo mana da ita har cikin gida ba tare da mun san wace ce ita ba." "Aou kawai ne ma Asma'u? Ehh lallai.." Dada ji ta faɗa tana jinjina kai. Ɗauke kai ta yi tana jefa wa Sultanah da ke ta narke fuska, tana yi mata alamun ta bari don Allah harara. Ita kuwa ko a jikinta, don ita dai haka nan kawai tun kallo ɗaya da ta yi wa yarinyar ta ji kwata-kwata ba ta kwanta mata ba. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 24 Murmushin yaƙe Tareeq ya yi, wanda ya tsaya iya kan laɓɓansa. Ya girgiza kai, mamakin halin Maamin na kama shi. Ta yadda ita kwata-kwata ba ta iya ɓoye abu, sai ta amayar da abin da ke ranta sannan take samun nutsuwa. Har Dada ji ta buɗe baki za ta sake yin magana, sai kuma ta fasa, ta juya ta kalli su Hidaya ta ce "Ke Hidaya ku wuce da ita sashenku. Zuwa an jima idan Allah Ya kai mu za mu haɗu." Babu musu Hidaya ta amsa da "Toh." Daneen da ta fahimci da ita ake, sai ta bi bayan su Hidaya. "Ki huta lafiya Dada ji, bari na raka Tareeq sashensa." Maama ta faɗa ba tare da ta kalli inda Maami take ba. Murmushi Dada ji ta yi kana ta ce "Tareeq ɗan gatan Maama. Allah Ya ƙara lafiya." Ta haɗe maganar lokaci ɗaya. Ɗan lumshe idanunsa Tareeq ya yi kafin ya yi murmushi ba tare da ya ce komai ba. Dada ji ta wuce sashenta, ya yin da Maama da Tareeq suka wuce sashen nasa. Da kanta ta buɗe ko'ina. Tamkar suna cikin gidan, babu wani abu na datti, ko kuma wanda zai nuna an daɗe ba a shiga ɗakin ba. Saboda kullum duk da ba ya cikin gidan, sai Hidaya ko Sultanah, ɗaya daga cikinsu ta zo ta gyara ɗakin. Har bedroom ta kai shi, sai da ya nemi waje ya zauna sannan ta ce "Ka samu ka yi wanka, ka yi bacci ka huta sosai yau ɗin nan." Ta faɗa don ta san halinsa sarai. Jinjina kai ya yi yana ɗan murza goshinsa ya ce "In Sha Allah Maama." Murmushi ta yi, tana jin farin cikin yadda ta ga jikin yaron nata ya yi matuƙar kyau, wanda hakan ke nuna yadda ya samu lafiya. Sai da ta miƙe sannan ta ce "Bari na wuce." "Toh Maama." Daga haka ta fice daga ɗakin. Sai da ya tabbatar ta fice daga sashen sannan ya sauke ajiyar zuciya, ya dawo da dubansa cikin ɗakin, idanunsa a kan laptop ɗinsa da ke ajje gefe guda. Ya ɗan fesar da iska daga cikin bakinsa kafin ya miƙe. Kai tsaye toilet ya faɗa, ya yi wankan da ya kwana biyu bai yi irinsa ba da ruwa mai matuƙar ɗumi. Ya kwashe kusan awa guda sannan ya fito, yana jin iska na ratsa ko wacce kafar gashi ta jikinsa. Kai tsaye gaban mirror ya nufa, ya shiga taje kwantacciyar sumar kansa. Ya taje ta tsaff, sannan ya shafe jikinsa da turarukansa masu matuƙar daɗin shaƙa. Cikin wata doguwar rigar jallabiyya ya shirya, wadda kalarta ta karɓi kalar fatarsa. Tattausar fatar jikinsa ban da sheƙi babu abin da take yi. Key ya ɗauka ya ƙarasa ya kulle ƙofar gaba ɗaya, sai ya bar key ɗin ma a jiki. Kai tsaye ya wuce kan gadonsa, ya zauna. Ƙafarsa ɗaya na tankwashe a kan gadon, ya yin da ya saukar da guda ɗaya ƙasa. Ya saka hannunsa ya ja laptop ɗin da ke ajiye ya kunna ta. Kamar yadda ya tsammata ayyuka ya tarar jingim a gabansa. Ya lumshe idanunsa yana tunanin ta ina zai fara. Ɗaya bayan ɗaya ya din ga bin komai da ya kamata ya duba. Har zuwa bayan wani lokaci. Ya fito da wayarsa da tun da ya kwanta a asibiti bai sake bi ta kanta ba ya kunna. Tun kafin ya kai ga buɗe ta kira ya shigo cikin wayar. Ya fesar da zazzafar iska daga bakinsa yana kallan mai kiran nasa. A nutse ya amsa wayar, ya shafe wajen rabin awa suna magana kafin ya katse, ya kira wata number. Daga can ɓangaren aka ce bayan sun gaisa "Yallaɓai za ka iya shigowa kuwa? Abubuwa da yawa suna jiran ka." Sai da ya ɗan yi jimm kafin ya ce "Zan yi ƙoƙarin shigowa, ni kaina na yi kewar komai, ba kuma na son abubuwa su haɗe mini, saboda haka zan shigo gobe idan Allah Ya kai mu, ka tura mini duk wani abu da ya kamata na sani kafin na zo." Daga haka ba su daɗe ba ya katse wayar. Haka ya din ga yin waya a daren kusufa-kusufa. Daga wannan sai wannan, wani su daɗe suna wayar, wani kuma ba sa wuce mintina kaɗan. Ranar dai gaba ɗaya haka ta ƙare ba tare da ya rintsa ba. Domin kuwa bayan ya gama abin da zai yi, sai yi shiga yin sallolin da ya saba duk dare, bayan ya idar kuma ya shiga muraja'ar Al Kur'ani. ... Tun da suka shigo ɗakin take kallon sa, ita dai i zuwa yanzu ta daina mamakin irin waɗannan tanƙama tanƙaman ɗakunan na alfarma. Wani irin ƙaton ɗaki ne da ya ji kaya masu kyau matuƙa. Komai a wataye yake ba tare da takura ba, abubuwa kala-kala masu ƙawata ɗaki duk ɗakin ya ji su. Komai biyu ne cikin ɗakin, wanda hakan ke nuna kowa na da mallakinsa. Ta ɗaga kai a hankali tana kallon wani waje da tabbas ya fi yi mata kama da banɗaki, don i zuwa yanzu ta soma fahimtar abubuwa da yawa tun bayan shigowar su cikin garin Kano. "Ki shiga ki yi wanka." Ta jiyo muryar Hidaya. Da sauri ta kalle ta, sai kuma ta jinjina kai tana ƙaƙalo murmushi. Kawai sai ta yi gaba, wannan ledar da take ta fata a ce an shigo da ita ta hanga, don haka kai tsaye can ta nufa don ɗauke wayar da Yohana ya ba ta. "Akwai komai na buƙata a ciki, bari mu je mu dawo." Hidaya ta sake faɗa. Sai da ta lumshe idanunta tana jin daɗin hakan, sannan ta ce bayan ta juyo "Tohm." Daga haka suka fice daga ɗakin a tare. Sauke ajiyar zuciya ta yi, kai tsaye ta nufi jakar nan, ta yi saurin ciro wayar ta riƙe a hannunta. Juya ta ta shiga yi, don kamar yadda ta faɗa masa kwata-kwata ba ta san yadda za ta yi amfani da ita ba. Kamar jira yake, sai ta ji hannunta yana girgiɗi, ta yi saurin kallon wayar ganin dalilin girgiɗin hannun nata daga wayar ne. Sai ta ga number na yawo a kan wayar. Ƙura wa wayar idanu ta yi kamar mai jiran wani abu, sai kuma ta kai hannunta, tana tuna abin da ya faɗa mata. Don haka ta danna 'Accept' tana kara wa a kunnenta. "Daneen." Ta ji an ambata daga can ɓangaren. "Na'am." Ta ambata tana gyara tsayuwarta, don ko ba a faɗa ba, ta san shi ne. "Kun isa gidan?" Ya tambaya. Jinjina kai ta yi tamkar yana gabanta, sai kuma ta buɗe baki a hankali ta ce "Ehh." "Madallah, kamar yadda na faɗa miki ki yi takatsantsan da wayar nan. Zan din ga kiran ki a kai a kai. Yanzu ma kuma na kira ne don na sanar da ke, kar ki ce za ki din ga zama cikin ɗaki, a'ah.. ki din ga ƙirƙiro duk wani abin da zai sa ki din ga ganar mana takun Tareeq. Duk wani takunsa ya kasance kina sane da shi, kina kuma sanar mini, ta hakan ne kawai zai sa mu cimma abin da muke so." "Tohm." Ta amsa masa bayan ta gama jin bayanin nasa. "Ya yi kyau." Ya faɗa daga can ɓangaren, daidai lokacin da ta sauke wayar daga kunnenta. Ta yi shiru kamar mai tunani, sai kuma ta sake sauke ajiyar zuciya, kai tsaye ta wuce banɗakin. Sakin baki ta yi tana kallon banɗakin da ya gaji da haɗuwa tamkar ba banɗaki ba. Kai idan ba don ta fara wayewa ba, da yau ne farkon zuwanta garin nan cewa za ta yi ba banɗaki ba ne. Don kuwa tsaff za ta samu wajen kwanciya, tsaff za ta iya yin shimfiɗa ta kwanta abin ta ba tare da ta san cikin banɗaki take ba. Haka dai tana ta kalle-kallenta da mamakin yadda masu ginin gidan 'yan birnin nan ke zama su tsara ko'ina, ciki kuma har da toilet. Ita dai ruwa ta tara a bokiti ta yi wankanta kamar yadda ta saba a gida. Zuwa can ta fito bayan ta mayar da hijab ɗin jikinta. Doguwar rigar abaya ta tarar a kan gadon, ta ɗauka tana kallon ta. Sai kawai ta zumbula ta, ba ta bi ta kan mayafin ba, ta mayar da hijab ɗin. Sai ta cusa wayar cikin kayan da ta cire, ta ninke su waje guda. A ɗakin ta ci gaba da zama, wani sashe na zuciyarta na faɗa mata ta fita, saboda ta din ga ganin motsin Tareeq, ya yin da wani sashen ke raya mata da kar ta yi gaggawa. Yau ne ranar ta farko cikin gidan, don haka ta bari zuwa gobe sai ta fara aiwatar da abin da ya kawo ta. ... Washegari da safe tun da suka fita ba ta sake jin motsin su ba. Saboda sun san da baƙunta, nan suka ajje mata abin karyawa, suka kuma bar ta ta sake sakewa ita ɗaya kafin baƙuntar ta sake ta. Ba ta san me za ta faɗa wa Yohana ba idan ya kira ya tambaye ta yadda ake ciki ba. Don haka kawai ta miƙe, gwara a yi komai da wurwuri, ko zuciyarta ita ma za ta samu sassaucin abin da take ji. Cike da takatsantsan take takawa, tana yi tana duba gefen ta don kar ta haɗu da wata. Cikin sa'a kuwa har ta fito palourn Maama ba ta ga kowa ba. Don haka a gaggauce ta fice daga palourn. Daidai lokacin da shi kuma yake ƙoƙarin wucewa. Da sauri ya yi baya, saboda yadda ya lura sam ba ta san da tahowar wani ba. Cike da mamaki yake bin ta da kallo. Rashin tsammanin ganinsa ya sanya ta ji ƙirjinta ya wani irin bugawa. Sai ta runtse idanunta da sauri ko za ta samu ta ji nutsuwa ta zuwar mata. "Ina so.. ne na je na.. gaisar da Kaka." Ta faɗa cikin inda inda. Shiru Tareeq ya yi yana kallon Daneen na tsawon sakanni, kafin ya ɗauke kyawawan idanunsa daga kanta. Ba tare da ya nuna ya ji abin da ta faɗa ba ya ce "Kin tashi lafiya? Ya jikin naki?" Runtse idanunta Daneen ta sake yi a karo na biyu, ta tsani ta ji ya yi mata wannan tambayar, kai gaba ɗaya ma ba ta son wata magana ta haɗa ta da shi. Ji take kamar kar ta amsa, ji take kamar ta yi wucewarta ba tare da ta tanka masa ba. Sai dai kuma ta san hakan ka iya zama abu na farko da zai kawo cikas na zamanta cikin gidan. Ta san hakan ka iya janyo zargi a wajen kowa ma ba shi kaɗai ba. Don haka cikin dakiya ta furta "Alhamdulillah." "Ma Sha Allah, Allah Ya ƙara afuwa. Hope dai kin ji daɗin gidan namu?" Ya faɗa ba tare da shi kansa ya yi tsammanin hakan ne zai fito daga bakinsa ba. Don tabbas da wani ɗan gidan nasu na wajen shi kansa sai ya yi mamaki. Ko da yake magana fa ake a kan wanda ta ba shi ƙoda. Shi ma kansa hakan ya ɗauka a matsayin dalilin da ya sa yake son jin lafiyarta a ko da yaushe. A yanzu kam har cikin zuciyarta shiru ta yi niyyar yi, ta damƙe hannunta ɗaya da ke cikin ɗayan. Da ƙyar, kamar wadda aka yi wa dole ta ce "Ehh." "Madallah." Ya faɗa, daga haka bai sake cewa komai ba ya wuce parking space a gaggauce. Ɗaga idanunta da har kalarsu ta sauya ta yi ta bi shi da kallo, zuciyarta ban da harbawa babu abin da take yi. Tana kallon yadda yake ɗan waige-waige lokaci zuwa lokaci. 'Duk wasu alamomi sun nuna ba ya son kowa ya lura da fitar tasa, wata ƙila ma wajen fasiƙancin zai nufa, shi ya sa ba ya so a sani.' Ta raya hakan a ranta, daidai lokacin da Ameer ya faɗo mata cikin rai. Ta yi yaƙe tana fesar da iska daga bakinta, don hana kukan da ta ji ya taho mata fitowa. Kawai sai ta juya da sauri ta koma cikin ɗakin da aka sauke ta. ... "Huh Hidaya Yah Abdoul ne, wallahi Yah Abdoul ne Hidaya. Ina zan saka kaina don daɗi, karanta ki gani fa, neman amincewa ta yake a kan soyayyarsa. Ina zan saka kaina don daɗi Sisi?" Sultanah ta faɗa lokacin da Hidaya ke a jikinta ta ruƙunƙume ta kamar za ta ɓalla ta. Dariya mai suna dariya Hidaya take yi, don babu ƙarya ta taya 'yar'uwarta murna ainun. "Na gani Sisi, Alhamdulillah, Alhamdulillah Alhamdulillah." Hidaya ta faɗa tana murmushi. Sai a lokacin sannan suka koma suka zauna. Daneen da ke gefe kwance kamar mai bacci tana jin duk abin da suke cewa. Sai dai ba za ka taɓa zata ba, duk da kwanciyar da ta yi ba irin ta bacci ba ce, amma za ka yi tsammanin baccin ne ya kwashe ta ba tare da ta sani ba. "Mu tashi Daneen ta ci abinci tun kafin Maama ta shigo ta ci mana mutunci." Hidaya ta faɗa tana kallan Daneen. Girgiza kai Sultanah ta yi kafin ta ce "A'ah, bar ta ta yi baccin, idan ta tashi sai ta ci. Yanzu dai mu yi magana a kan abin farin cikin da ya same mu. Ya kike gani? In faɗa wa Maami?" Waro ido Hidaya ta yi ta karɓi wayar hannun Sultanah ta ce "Hajjaju, ki ba shi amsa tukunna. Maami kuma ba yanzu ba gaskiya, mu bari sai komai ya kankama tukunna." Ta ƙare tana murmushi. Jinjina kai Sultanah ta yi kafin ta ce a sanyaye. "Ga shi dai cikin farin ciki nake ji na Sisi, amma ban san me ya sa nake jin wata irin faɗuwar gaba ba. Na kasa gane dalili." Murmushi Hidaya ta yi tana kamo hannun 'yar'uwar tata ta ce "Cikin farin ciki kike jin ki fa Sulty, ina da tabbacin hakan na da nasaba da farin cikin. So ki kwantar da hankalinki, burin ki ya kusa cika In Sha Allah. Yah Abdoul zai so ki fiye da yadda kike son shi." "Ina fatan hakan." Sultanah ta faɗa a sanyaye. "Ya kamata mu je gidan Umma, kin san dai halinta da na Jawahir ɗin kanta. Biki yana ta matsowa." Ajiyar zuciya Sultanah ta sauke kafin ta ce "Wato Hidaya mu sake gode wa Allah da Ya ba mu ɗan'uwa irin Yah Tareeq wallahi, har abada zan ci gaba da alfahari da shi, ki ga dai yadda silar sa nake ta farin ciki. Bikinsa kuma nan da sati biyu, ai dole ne mu tashi tsaye. Daɗin abin kuma Jawahir ce matar. Allah dai Ya tabbatar da alkhairinsa." Taɓe baki Hidaya ta yi kafin ta ce "Ameen dai, duk da dai ni wallahi ban wani so haɗin nan ba." Duka Sultanah ta kai mata a kan yatsun hannunta ta ce "Ke Sisi." "Yoh Allah kuwa." Motsin da Daneen ta yi ne ya sanya Hidaya kallon ta. Ta dubi Sultanah ta ce "Kin ga kar mu tashi baiwar Allah, zo mu fita mu ba ta waje." Ta faɗa tana jan hannun Sultanah. Babu musu Sultanah ta miƙe a nutse suka fice daga ɗakin. Wani irin gumi ke tsatstsafowa Daneen tun da ta ji abin da suke faɗa. Ta kai wajen mintina goma tana sake tauna maganganun nasu, kafin ta miƙe ta ɗauko wayar nan daga inda ta ɓoye ta. Hannunta har karkarwa yake yi, lokacin da ta ke nemo number Yohana cikin karambani. Sai kuwa ga shi ta gano ta, ta danna masa kira tana jin wani irin zafin zuciya. Idan har Tareeq ɗin ya yi aure ya bar ta cikin gidan me kenan? "Daneen." Ya ambata tun kafin ta ce komai. Ba tare da ta amsa kiran sunanta da ya yi ba, ta soma faɗin "Yanzun nan na ji ƙannensa na faɗin aurensa nan da sati biyu. Na rasa me ma zan ce ne ni kam." Cikin wani irin tashin hankali Yohana ya miƙe tsaye, idanunsa har wani ƙanƙancewa suke yi. Ya kai wajen mintina biyu bai ce komai ba, kafin daga baya ya buɗe bakinsa ya ce "Ya zama dole mu tashi tsaye.. Kamar yadda yake, har yanzu babu abin da ya canja a ƙudirinmu, sai dai a yanzu sati biyu ne da mu ni da ke. A cikin kuma sati biyun ne za mu yi duk abin da ya kamata. Ki shiga cikin jerin abubuwan da suke kan wayar, za ki ga Whatsapp, ki shiga ciki zan tura miki wasu hotuna, ki duba ki karanta da kyau. Zan yi miki bayanin komai ta can. Abin da kawai nake so na tunasar da ke, dole sai kin dage, sai kin cije, kin saka wa kan ki jarumta. Kin ji kowacce kasada ce za ki iya don samun damar cika burina, da kuma naki. Hakan ma ya yi daidai, ko babu komai idan muka san muna da ƙayyadaddun kwanaki, za mu fi yin aikin da sauri. Ki ajje wayar yanzun nan ki shiga abin da na faɗa miki." Daga haka ya yi mata bayanin yadda za ta hau online ɗin yana jiran ta. "Kar ki manta sati biyu ne kawai da mu." Ya sake maimaita mata kafin ta katse wayar. Tamkar yana gabanta ta jinjina kai, tana jin ko ma wacce irin kasada ce za ta yi domin cikar burinsa, daga nan kuma ya samu ya shigar mata da Tareeq ɗin ƙara, a ƙwatar wa Ameer haƙƙinsa. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 25 Kamar yadda ya kwatanta mata haka ta yi, kamar wadda ya koyawa ga ta ga shi, sai ga shi har ta gane duk abin da ya koya matan. Maganarsa ce kaɗai cikin Whatsapp ɗin, don haka kawai sai ta taɓa sunan nasa da ya yi saving da YOHANA B. Tarin messages ne, duka daga shi ɗaya. Har bayan ta shiga ma wasu ba su daina shigowa ba. Tsayawa kawai ta yi tana kallon ikon Allah. Duk da ya yi mata bayanin komai, amma a wannan karon kuma ba ta san mai za ta yi ba. Amma dai sai ta shiga karanta saƙonnin da suke a rubuce ɗaya bayan ɗaya. Daidai lokacin da wayar ta soma ƙara kenan. Yanzun ma dai shi ke kira, don haka ta ɗaga tana kara wa a kunnenta. "Kina ji na?" Shi ne abin da ya faɗa. Ta jinjina kai tamkar tana gabansa. Sai kuma tunawa da ta yi ba ya ganin ta ya sanya ta buɗe bakinta ta ce "Ehh.." Nan da nan ya shiga yi mata bayani tamkar ɗazun. Ta yi shiru tana saurara, da kiyaye duk abin da yake faɗa mata. Wajen mintina 20, sannan suka yi sallama. Sai a lokacin ta koma cikin Whatsapp ɗin suka ci gaba da magana ta nan. Ƙura wa wayar idanu ta yi tana kallon takardun da ya turo mata. Ta iya karatu daidai gwargwado, saboda haka ta shiga karanta duk abin da ta gani rubuce a jikin takardar. Wasu abubuwan ta fahimci me ake nufi, ya yin da wasu suka yi mata tsaurin fahimta. Hakan ne ya sa maimakon ta fahimci abin da take karantawa, sai ya zamana kawai karantawar take yi ba tare da tana fahimtar komai ba. Don inda ba ta fahimta ba, ya fi inda ta fahimta sau fiye da biyar. Taɓe baki ta yi, tana mamakin dalilinsa na son nemo masa irin takardun. "Ashe ma shi duk a kan takarda yake wannan abin." Ta raya hakan cikin zuciyarta tana ɗan juya manyan idanunta. Shiru kuma ta yi na tsawon mintuna, kafin murmushin gefen baki ya ɗan bayyana a kan laɓɓanta, murmushin da yanzun ya maye gurbin murmushinta tun bayan mutuwar Ameer. Ba ta taɓa tunanin bayan ganin gawar ɗan'uwanta za ta iya ci gaba da walwala ko murmushi ko da kuwa na yaƙe ne ba. Ba ta taɓa tunanin idan Ameer ya rasu za ta iya ci gaba da rayuwa ba. Sai ga shi ta iya rayuwar, har ma ga shi tana iya murmushi. Ta ɗan lumshe idanunta da lokaci ɗaya kalarsu ta sauya daga fari zuwa ja. "Toh ko dai ya yi haka ne duk saboda ni?" Ta sake raya hakan a ranta. Cikin ƙanƙanin lokaci ta ji tabbas haka ne, idan ma ba haka ba ne, toh ko ma waɗanne irin takardu ne suna da muhimmanci, duk da ita ba ta ga wani muhimmancinsu ba. Don haka ko ma mene ne za ta yi yadda za ta yi ta ɗakko masa takardun. 'Don dai takarda?' ta furta hakan a kan laɓɓanta. Lokaci guda tana lumshe idanunta. A ranta tana sake jinjina kirki irin na Yohanah. Gefe guda kuma tana tuna yadda daga zarar ta ɗakko masa takardun, nan ba da daɗewa ba za ta ga Tareeq a gaban kotu. Asirinsa ya tonu a idon duniya. Sannan kuma a yanke masa hukunci. ... "Ba kwa jan yarinyar nan a jiki, shi ya sa kullum take zaune ita ɗaya. Kada dai shiririta ta mantar da ku alkairinta gare ku." Maama ta faɗa tana kallon Hidaya da Sultanah. Tareeq da ke zaune ya kalle su a ɗan fuzge kafin ya ci gaba da danna wayarsa. Ita kanta Maama da take zaune ba ta yi tunanin yana da abin da zai ce ba, sai lokacin da ta ji ya buɗe baki ya ce "Kuma ina yawan ba su amanarta ba." Ya faɗa ba tare da ya kalle su ba. "Yah Tareeq Allah kuwa muna kula da ita. Yanzu haka ma barin ta muka yi ta yi bacci." Hidaya ta faɗa bayan ta karyar da kanta gefe. "Ke Sultanah maza je kira mini yarinyar nan." Da "Toh." Sultanah ta amsa tana miƙewa. Kai tsaye ta wuce ɗakinsu. Cigaba da zama suka yi cikin ɗakin, lokaci zuwa lokaci Maama kan jefo wata maganar, shi ko Hidaya wani ya amsa ta. Har zuwa lokacin da Sultanah da Daneen suka shigo ɗakin, Daneen na sanye cikin hijab ɗinta kamar koyaushe. Don ko a cikin gidan ma da aka tashi yi mata siyayyar kaya, har hijabi suka kawo mata da yawa. Ba ta sani ba ko gani suka yi tana son shi ko haka nan ne kawai, ita dai ba ta sani ba. A hankali take takawa cikin ɗakin, kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki. Abin da ya ƙara wa tafiyar armashi kenan, sai ta zama kamar tana tafiyar ƙasaita ne. Ƙasan kujerar da Maama ke kai ta nema ta zauna, a nutse ta ce "Barka da rana." "Barka ka dai, ya jikin naki?" In ji Maama. "Alhamdulillah." Daneen ta faɗa har lokacin a sanyaye. Tun kafin ta iso cikin ɗakin ta tabbatar da wanzuwarsa ciki. Sai kuma da ta yo kusa-kusa, sai ta ji duk ya cika ɗakin. Sai dai kuma gefe guda, ita kaɗai ta san abin da take ji. Ta kuma saka ranta ba za ta gaishe shi ba. Akan me ye ma za ta gaishe shi? Waye shi ɗin? Mutumin da ya yi sanadiyar mutuwar Ameer shi za ta gaisar? Lallai kuwa da ta cika cikakkiyar mara lafiya. "Toh Alhamdulillahi, Allah Ya ƙara afuwa. Sannu kin ji Daneen?" Maama ta faɗa tana murmushi. Ita ma ɗan murmushin ta ƙaƙalo tana gyara zamanta. Kamar ya ce mata ya jiki, ko kuma dai wani abun, sai kawai ta gintse, duk da ya san da wanzuwarta cikin ɗakin, amma bai nuna ba. Don kuwa ci gaba ya yi da danna wayarsa kamar bai san ta shigo ba. Tun da har ba ta san ta gaida babba ba, bari ya kama kansa, ko ita ma ta saita nata. Dakatawa kuma ya yi da danna wayar, ya ɗan yi shiru sai dai har lokacin idanunsa na kan wayar ne. Amma kuma idan ya yi hakan ya yi daidai? Yarinyar da ta ba shi ƙoda ba tare da wani dalili ba fa? Ya ɗan runtse idanunsa hannunsa a kan goshinsa yana murzawa. "Na bar muku sashena a buɗe, wata a cikin ku ta ɗan je ta gyara mini. Zan ɗan fita ne." Da mamaki Maama ta kalle shi ta ce "Unguwa kuma Tareeq? Ina za ka je?" Sai da ya ɗan gyara zamansa sannan ya sanar da ita inda zai je. Ta yi masa addu'ar Allah Ya tsare, ƙannensa na amsawa da Ameen sannan ya fice daga ɗakin. Ta lumshe idanunta tana jin wani irin daɗi na ratsa ta, 'Sashensa a buɗe?' Ta sake tuna hakan cikin zuciyarta tana ji kamar ta tashi ta taka rawa. Ba ita ta bar palourn ba sai da Maama za ta wuce ɗaki ta ɗan yi bacci. Ta yi sallama da Maaman, don dama ɗazun su Hidaya sun fita. Daga haka Maama ta wuce daƙinta, ya yin da Daneen ta wuce nasu ɗakin. Babu ɓata lokaci ta kira Yohana ta sanar da shi abin da ke faruwa. Ya yi shiru yana saurarar ta har ta gama, sannan ya ce yana murmushin da har a cikin muryarsa kana iya ji. "Da gaske?" "Ehh.." Ta amsa masa a taƙaice, kamar yadda ya taƙaita tambayar tasa. "Yanzun nan zai fita? Yawwa toh ki yi amfani da wannan damar wajen shiga sashen nasa, kar ki yi sanya. Na san ba yanzu zai dawo ba. Don haka ki yi abin da na sanar da ke. Sannan kuma tsaya, ki sake tabbatar mini da yanzun zai fita." Ba tare da kawo komai ba ta jinjina kai, kafin ta buɗe baki ta ce "Eh, yanzun nan ya fita." "Toh shi kenan zan ajje waya. Ki yi duk abin da ya dace ina jiran kiran ki." .... A fuzge ya kalli wayarsa da ta shiga ringing. Ya ɗauke kai yana maida hankalinsa kan driving ɗin da yake, Abdoul da ke gefensa ya kalli mai kiran. 'Jawahir' Shi ne abin da ya bayyana a kai. "Ba za ka ɗaga ba ne?" Abdoul ya faɗa yana kallonsa. Lumshe manyan idanunsa ya yi kafin ya ci gaba da driving, kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya sanya hannunsa ya ɗauki wayar. Bai kai ga ɗagawa ba ya ce "Haka na faɗa maka?" Ya faɗa bayan ya juya ya jefa masa harara. Murmushi kawai Abdoul ya yi, saboda ganin da ya yi ya kara wayar a kunnensa, alamar ya ɗaga. Ajiyar zuciya Jawahir ta sauke kafin ta ce "Har na cire ran ba za ka ɗauka ba wallahi." "Saboda haka ne halina?" Ya faɗa cikin basarwa, lokaci ɗaya yana sauya hannun da ya riƙe wayar da ɗayan hannun. Duk sai ta dabirce, ba wai don wani abu ba, sai don yadda ya yi magana ya dake ta, har sai da ta ji wani yarr. "A'ah.. fa.. ba haka.. nake nufi ba." Ɗa. Jinjina kai kawai ya yi a hankali kafin ya ce "Toh yanzu dai ya aka yi? Ina driving ne." Ya yi maganar a haɗe. "A'ah babu komai, kira na yi kawai na ji muryarka, sannan na sanar da kai yadda na yi kewar ganin kyakykyawar fuskarka." Ta ƙare maganar tana ɗan sauke numfashi gami da murmushi. Ɗan sauke wayar ya yi daga kunnensa, yana jin waɗannan kalmomin nata sun daɗe da ginsarsa. Ko ba ma haka ba, ya daɗe da daina jin wasu abubuwa da suka shafi soyayya za su birge shi. Sai dai kuma ita burinta kullum ta faɗi yadda take ƙaunar ganin kyakykyawar fuskarsa, abin da ba ya so kenan, amma ta kasa ganewa. "Toh ya yi, zan samu na shigo." Ya faɗa kamar a gajiye. Murmushi ta yi tana faɗin "Yawwah sai ka zo Habiby." Daga haka ya sauke wayar ya ci gaba da driving ɗin da yake. "Aboki Allah Ya sa sau kana son Jawahir." Abdoul ya faɗa yana kafe shida idanunsa, kamar mau son gano gaskiyar abin da zai faɗa. Tareeq bai kalle shi ba, illa ci gaba da abin da yake yi da ya yi. Bayan shuɗewar minti ɗaya, wanda sai ka ɗauka ba zai amsa ba ne sannan ya ce bayan ya sauke gajeriyar ajiyar zuciya "Idan dai har na aure ta zan koyi sonta. Abin da na sani kenan." Ya yi maganar kamar ya gama kenan, sai dai kafin Abdoul ya ce komai ya cigaba da faɗin "Amma idan dai har halayenta sun yi mini." Da mamaki Abdoul ya kalle shi cikin rashin fahimta ya ce "Ban gane ba? Idan kuma halayen nata ba su yi maka ba fa?" "Za ma su yi mini, tun da har na amince da ita yanzun." Jinjina kai Abdoul ya yi yana murmushi kafin ya ce "Toh Allah Ya tabbatar da alkhairi. Ameen." Ya yi addu'a da amsar duka a tare, don ya san halin mutumin nasa ba lallai ya amsa ba. Ko zai amsa ma sai dai ya amsa a zuciya, wanda shi ba zai gane ya amsa ɗin ba. "Sauke ni nan Tareeq." Abdoul ya faɗa yana kallon inda suke ƙoƙarin wucewa. Babu musu Tareeq ya gangara gefen titi ya tsaya. Suka yi sallama da Abdoul sannan ya tashi motar ya bar wajen. Sanye cikin hijab ɗinta take ci gaba da tafiya, ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ba ta waige-waige saboda kar a gano ta. Dab da za ta isa sashensa, ta yi kiciɓus da Sultanah da riƙe da waya a hannunta. Dakatawa ta yi tana jin zuciyarta na harbawa, ita ma Sultanah dakatawa ta yi tana kallon ta da murmushi a kan fuskarta ta ce "A'ah, Daneen.. me ya fito da ke?" Wani daƙiƙin murmushi Daneen ta ƙaƙalo tamkar za ta fashe da kuka. "Ko kin gaji da zaman cikin ne?" Sultanah ta katse ta da faɗin hakan a daidai lokacin da take tsaka da lalubo abin da za ta faɗa. Har wata ajiyar zuciya ce ta suɓuce mata, sai kawai ta shiga jinjina kai tana murmushi. "Allah Sarki mu je in taka miki." Lokaci guda gaba ɗaya murmushin ya ɗauke. Ta yi maganar tana soma takawa. Kamar ta rusa ihu haka ta ji, sai dai babu yadda ta iya, haka ta bi bayanta suka soma tafiya. Tun kafin su yi nisa, wayar Sultanah ta shiga ƙara. Daneen ba ta ji abin da aka faɗa daga can ɓangaren ba, ta dai ji Sultanah ta ce a sanyaye "Toh Maami." Daga haka ta sauke wayar daga kunnenta. Ta kalli Daneen a nutse ta ce "Ki ƙarasa kawai 'yar'uwa, bari na je ciki, Maami na kira na." "Tohm." Daneen ta faɗa tana jin wani irin farin ciki na mamaye ta. Sai dai ba ta nuna a kan fuskarta ba, saboda yadda take ji a ranta ya zama dole ta saita kanta, ta sauya takunta, idan ba haka ba a ramfo ta. Sai da ta daina gano Sultanah sannan ta ci gaba da tafiya, addu'a take a ranta kada Allah Ya sa ta sake haɗuwa da kowa har ta je inda za ta je. Addu'ar tata kuwa ta karɓu, don har ta ƙarasa inda yake da tabbacin nan ne sashen Tareeq ba ta haɗu da kowa ba. A wannan lokacin ma sai da ta ɗan tsaya ta dudduba, ta ga babu kowa sannan ta wuce cike da sassarfa, har tana ji kamar za ta kifa. Wata kasalalliyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta buɗe idanunta da ke a lumshe a kan ƙofar sashen nasa. A hankali ta saka hannunta ta tura. Kamar yadda ta tsammata kuwa, a buɗe take. Ta ji wani sanyi ya ratsa ta, ta saki murmushi tana saka kanta cikin sashen nasa. Sai dai yaɓe-yaɓe! Don kuwa tana taɓa ƙofar ɗakin ta ji ta ɓame da mukulli. Dakatawa ta yi tana jin yadda zuciyarta ke bugawa. 'Anya kuwa a kullen take?' Ta raya hakan a ranta tana kallon ƙofar ɗakin. Sai kawai ta sake saka hannunta da ke ɗan rawa kaɗan da niyyar turawa, nan ma dai shiru. 'Kenan ƙarya yake, da ya ce sashen nasa a buɗe yake?' Ta tambayi kanta har lokacin idanunta a kan ƙofar. Shiru ta yi na tsawon sakanni, 'Toh ko dai yana nufin sashen ne kawai a buɗe ban da ɗakunansa' Cikin lokaci ƙanƙani wannan tunanin ya faɗo mata. Tunanin da ɗazun kwata-kwata bai kawo mata ba. Saboda yadda ta ƙagu da neman hanyar shiga sashensa kafin cikar sati biyun nan. Cike da ɓacin rai ta fito daga sashe. Ko dubawa ma ba ta yi ba ko da wanda ke kallon ta. Ta ci gaba da takawa gaba ɗaya fuskarta a cakuɗe, jikinta a sanyaye ya yin da take taku cike da sassarfa kuma a hanzarce. A haka har ta ƙarasa sashen Maama. Kamar wadda ba ta da laka, haka taka takawa cikin sashen, zuciyarta gaba ɗaya a cunkushe. Ta ma rasa wanne tunanin za ta ba wa zuciyarta haɗin kai su yi? Ita dai ta san burinta ɗaya ta samu damar shiga ɗakin Tareeq. Don haka dole ne ta miƙe tsaye, ta samo ɗin ko a yi a wuce wajen. "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Shi ne abin da kunnuwanta suka soma tsinto mata lokacin da take dab da shiga ɗakin. Ta dakata tana jin yadda zuciyarta ta harba lokaci guda. "Hatsari kuma? A ina? Tareeq? Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Maama ta faɗa cikin wani masifaffen tashin hankali. Cikin sakannin da ba su wuce goma ba, jikin Daneen ya ɗauki rawa ba kaɗan ba. Ta runtse idanunta tana ci gaba da jin yadda kalaman Maaman ke mata amsa-kuwwa a cikin kunne. Ta kai wajen minti 5 a hakan kafin ta buɗe idanunta. "Yanzun nan zai fita? Yawwah ki yi amfani da wannan damar wajen shiga sashen nasa, kar ki yi sanya. Na san ba yanzu zai dawo ba. Don haka ki yi abin da na sanar da ke. Sannan kuma tsaya, ki sake tabbatar mini da yanzun zai fita." Maganganun da suka koma yi mata amsa-kuwwa kenan a maimakon na Maama. Tuni ɓarin jikinta ya ƙaru, gumi ya shiga tsatstsafowa daga ko'ina na jikinta. Ta runtse idanunta a karo na barkatai tana tunanin shin me yake faruwa ne? Afwan da ji na da kuka yi shiru kwana biyu. Na ɗan yi busy ne a kwana biyun, saboda ba na gida. Amma In Sha Allah daga gobe shi kenan. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 26 Duk da yadda take jin ƙirjinta na bugawa ba a daidai ba. A hankali yake bugawa, sai dai da wani irin ƙarfi, hakan bai hana ta yin kasada ba, kawai ta runtse idanunta sannan ta faɗa cikin ɗakin. Daidai lokacin da Maama da idanunta suka yi jajir take faɗin "Dada ji Tareeq ne wai ya samu hatsari." Yadda ƙafar Dada ji ta yi ƙass ne, tun farkon da ta ji Maama ta ambaci sunan Tareeq ya sanya ta saurin koma wa ta zauna hannunta a kan ƙafar tata. Sai dai cikin tashin hankali take faɗin; idanunta a kan Maama "Hatsari? Ya Hayyu Ya Qayyum." Ta faɗa har lokacin hannunta na kan ƙafarta. Duk da yadda take jin tana mata zafi, amma tashin hankalin da ta ji kanta a ciki na hatsarin Tareeq ɗin ya danne komai. Ɗaukar mayafi kawai Maama ta yi tana shirin yin waje, Hidaya ta shigo cikin ɗakin. Haka kawai ta ji zuciyarta ta buga tun kafin ta ji abin da ya faru. Kamar kar ta tambaya saboda duk wasu alamu sun nuna ba lafiya ba. Amma kuma hakan ba za ta yiwu ba, don haka ta ce bayan ta ɗan lumshe idanunta "Maama me ya faru?" "Hidaya zo ki taimaka mini in miƙe mu tafi. Yayanku ne ya samu hatsari yanzun nan." Wani irin harbawa da ta ji zuciyarta ta yi, shi ne abin da ya sanya ta saurin kai hannunta saitin zuciyarta ta dafe. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunta suka tara hawaye fall. Kwata-kwata ma sai ta kasa furta komai. Ficewar da Maama ta yi ita ta dawo da ita daga hayyacinta. Kawai sai ta fashe da kuka, daidai lokacin da ta ƙarasa inda Dada ji take. Ta sanya hannunta da ke karkarwa ta taimaka mata ta miƙe. "Ya isa, kukan ya isa haka Hidaya. In Sha Allah ba wani abu ne babba ba." Cikin muryar kuka ta furta "Ameen." Tana kai hannunta kan fuskarta ta share hawayen. A ranta kawai hasaso ɗan'uwanta take. Fata take Allah Ya sa ba wani abu babba ne ya samu ɗan'uwan nata ba. A tsaye kawai take kamar wadda aka dasa, ban da karkarwa babu abin da jikinta yake yi. Sai da suka fice daga ɗakin gaba ɗaya sannan ta ƙarasa shigewa ciki. Kawai sai ta zube a kan kujerar tana sauke numfashi. Ta kai wajen mintina biyar, kafin ta miƙe ta faɗa cikin ɗakinsu. Ba ta yi wata-wata ba, wajen danna wa number Yohana kira ba. Ringing 1 ya ɗaga wayar, yana shirin fara magana ta katse shi da faɗin "Me ye alaƙarka da hatsarin da Tareeq ya yi?" Cikin wani irin amo Yohana ya furta "Hatsari kuma? Yaushe? Ina Tareeq ɗin yake?" Cike da tsoron kar abin da take zargi ya tabbata ta ce cikin dakiya. "Kar ka nuna kamar ba ka sani ba mana." Ta faɗa da gaba ɗaya gaskiyarta, bayan ta yi ƙoƙari wajen danne duk wani tsoro da fargabar da take ji. "Amma ba ki kyauta mini ba Daneen, kuma a gaskiya zan faɗa miki ban ji daɗi ba. Me ya sa zan saka hannu wajen yin wani mummunan abu a kan Tareeq? Bayan dukkanmu so muke a hukunta shi a hukumance. Na ɗauka na tura miki abin da nake so ki samo mini a wajen Tareeq, takardu ne fa kawai. Ban da su babu komai. Ke ce fa mai fansar da ta fi muhimmanci da kuma girma, so kike a ɗaukar miki fansar ɗan'uwanki. Kuma shi ne dalilin da ya sa na dage, nake kuma son ke ma ki dage. Amma idan kin ga ba za ki iya ba, ko kuma za ki saka zargi a cikin ranki, toh ina ga babu amfanin ci gaba da zaman ki cikin gidan nan, kawai ki fito ki koma ƙauyenku, ki sanar da su mutuwar Ameer kawai. Idan ya so sai ku nemi wata hanyar da kuke ganin za a iya hukunta Tareeq ɗin." Ya ƙare maganar cikin wani irin yanayi, da ke nuni da yadda ya ji babu daɗi da gaske. Shiru Daneen ta yi, tana jin yadda jikinta ke ƙara yin sanyi. Sai da ta daure, ta yakice komai, sannan ta iya yago magana ta ce "Toh amma me ya sa ka din ga tambaya ta da gaske yanzu zai fita?" Ta tambaya a sanyaye. "Kawai so nake na ji, saboda ki je sashensa. Shi ne kawai dalilin da ya sa na tambaye ki. Ban da haka ina ruwana da inda zai je da kuma yake? Duk fa saboda ke ne. Ki yi tunani mana." Shiru Daneen ta yi tana nazarin duk maganganun da ya faɗa. Wajen minti 2, sannan ta sauke ajiyar zuciya, wadda shi kansa sai da ya jiyo sautinta. Ya gyara zamansa daga inda yake zaune kafin ya ce "Ban ji daɗin yadda zargi ya shiga tsakaninmu ba." Ya faɗa a hankali. Wata ajiyar zuciyar Daneen ta sake saukewa kana ta ce "Ka yi haƙuri, na kasa ƙaryata abin da zuciyata ke ta hasaso mini ne." Daga haka kawai sai ta ajiye wayar ba tare da ta sake jin wani abu da ya ce ba. Ta zauna yaɓar a kan gadon ɗakin zuciyarta na wani irin zafi. Wata irin kewar Innarta ta ji tana ratsa ta, gefe guda kuma tunanin Ameer ɗin da kullum yana cikin mafarkinta. Ta ƙagu komai ya kammala ta gan ta a kusa da Innarta. Ko ta samu ta ɗora kanta a kan kafaɗarta ko cinyarta su yi kukan rashin Ameer tare, su yi wa Ameer addu'a tare, su kuma tuna shi tare. Miƙewa ta yi a hankali ta shiga zagaye ɗakin, hannunta duka biyun cikin na juna. Gaba ɗaya kwanyarta ta cushe da tunanunnuka kala-kala. Tsoron ta ɗaya kada a ce Tareeq ya rasu a asibiti yanzun. Ba ta so ya mutu ba tare da an hukunta shi ba, ba ta so ya mutu ba tare da an masa hukunci daidai da muguntar da ya yi wa ɗan'uwanta ba. Don haka za ta yi ta masa addu'ar ya rayu, ko don ya karɓi kashinsa a hannu. Tana ci gaba da zagaye ɗakin Sultanah ta shigo da sauri. "Sister shirya mu wuce asibitin da aka kai Yah Tareeq. Yah Tareeq ne ya yi hatsari." Sultanah ta yi maganar, gaba ɗaya yanayinta na nuni da yadda take cikin tashin hankali. Bin ta da ido kawai Daneen ta yi, ita ma duk nata hankalin a tashe yake. Sai dai ba na komai ba ne face kar ta je Tareeq ya mutu ya bar ta da fansar da ba ta ɗauka ba. Dogon hijab ɗinta Sultanah ta ɗauka ta saka a gaggauce, sai da ta yi hanyar fita sannan ta ce "Ki fito mu tafi." Daga haka ba ta jira Daneen ɗin ta ce komai ba ta fice daga ɗakin. Babu musu Daneen ta bi bayanta, gwara ta kasance tana kusa, ko babu komai za ta din ga sanin a halin da Tareeq ɗin yake ciki. ... Lokacin da suka isa, an daɗe da shigar da Tareeq emergency, saboda mummunan raunin da ya samu a ƙafarsa. Babu wanda ya samu damar ganinsa. Dukka sai suka yi cirko-cirko suna jiran jin halin da yake ciki hankali a tashe. Sai dai kowannen su addu'a yake, Allah Ya sa ko ma mene ne zai zo ya zo da sauƙi. "Ubangiji Allah Ya ba ka lafiya yaron nan." Dada ji ta faɗa a sanyaye. Sultanah ce ta iya amsa wa da "Ameen." Ita ma jiki a sanyaye. Ita dai Daneen sai raba ido take. A zahiri ita kanta ma neman lafiyar tasa take, sai dai abin nasu ya fita daban. Don su suna so ne ya samu lafiya kawai, ya yin da ita kuma nata son ya samu lafiyar saboda fansarta ne. A nan suka ci gaba da zama har zuwa shuɗewar wasu lokuta masu tsayi. Zuwa lokacin har Abeey ma ya iso shi da babban amininsa Alhaji Abubakar. Abdoul ma tuni ya iso, don har ya riga ma su Abeey zuwa cikin asibitin. ... Kansa a kwance yake a kan pillow, ya yin da hannunsa ɗaya ke kan fuskar tasa, idanunsa a rufe. Turo ƙofar da aka yi ne ya sanya shi buɗe lumsassun idanunsa da kalarsu ta ɗan sauya. Bai yi yunƙurin tashi ba, duk da ba ya iya ganin mai shigowar. Sai dai tun kafin ta ƙaraso ya fahimci wace ce, don haka a hankali ya shiga miƙewa zaune. Da sauri Maama ta ƙarasa ta gyara masa zaman. Ya zube idanunsa da suka faɗa a kan Maaman yana jin wani irin rauni na kama shi. Ita ma shi take kallo ba tare da ta ce komai ba. Ta ma rasa me za ta ce, ko kuma ta ina za ta fara. "Maama ni kuma ƙaddarata a ciwwuwwuka take. Ina ta saka ku cikin fargaba koh? Ni kaina ba na jin daɗin hakan. Amma ya zan yi Maama?" Ya ƙare maganar a sanyaye. Kafe shi da idanunta Maama ta yi, tuni fuskarta ta ɗinke tsaff. Kamar ba za ta ce komai ba, sai kuma ta girgiza kai ta ce "Ga ka dai a haka kamar ka girma ka yi hankali, har kana da ƙannen da za ka tsawatarwa, ashe ba haka ba ne. Tareeq yanzu ni za ka kalla faɗa wa wannan maganar? Waye yake ɗora cuta? Akwai wanda haka kawai yana sane zai ɗora wa kansa cuta? Allahn da Ya jarabce ka da ita shi zai yaye maka In Sha Allah. Za ka samu lafiya cikin yardar Ubangiji." Lumshe kyawawan idanunsa ya yi a hankali kamar mai jin bacci, ya buɗe su a kan Maama kafin ya ce "Ki yi haƙuri Maama. Amma kuma kina tunanin wannan ƙafar za ta warke kuwa?" Ya ƙare maganar idanunsa a kan ƙafarsa da ke ajje kawai a nannaɗe. Shi kaɗai ya san azabar da yake ji daga cikinta, tamkar ana daddatsa ta da wuƙa irin kakkaifar nan. Ita ma kallon ƙafar tasa ta yi da jajayen idanunta, ta kai wajen minti 1 tana kalla kamar mai nazarin wani abu, sannan ta buɗe baki a nutse ta ce "Ai Allah na ce." Jinjina kai kawai ya yi, yana koma wa baya, ya jinjina da pillow. A hankali ya ɗan fesar da iska daga bakinsa, kamar wanda ke shirin sake cewa wani abun. Sai kuma ya tsuke bakinsa ya yi shiru. Maama ta nemi waje ta zauna tana kallon ɗan nata cike da tausayawa. ...."Alhamdulillahi, cikin ikon Allah abubuwa da dama da sauƙi. Sai dai kuma.." Likitan ya ɗan dakata a nan yana girgiza bironsa a kan takardar gabansa. Jinjina kai Abeey ya yi alamar yana tare da shi, hakan ne ya sanya shi ɗan ajiye numfashi kafin ya ci gaba da faɗin "Ƙafarsa.. Gaskiya ƙafarsa ta samu mummunan rauni sakamakon yadda ta maƙale cikin motar sosai, da ƙyar aka iya zaro ta. Kamar yadda aka sanar da ni kenan. Wannan ne dalilin da ya sa.." Sai ya sake dakatawa a nan. "Ya Hayyu Ya Qayyum." Abeey ya faɗa a fili idanunsa a lumshe. A ransa yana ji lallai lokaci ya yi da Tareeq zai ajiye ko ma mene ne, ya tsayar da hankalinsa a kan kasuwanci kawai. A hankali ya juya ya kalli likitan, yana jin yadda ilahirin jikinsa ya yi matuƙar sanyi, sannan ya ce "Kaa ga kada ka ɓoye mini komai. Tareeq ɗana ne, saboda haka ka sanar da ni komai a kan matsalar ƙafar tasa." "Ba zan ɓoye maka ba Ranka ya daɗe, fatanmu na warkewar ƙafarsa har ya miƙe ya ci gaba da tafiya ba shi da yawa. Ƙafarsa ta samu mummunan rauni kamar yadda na faɗa maka, wanda zai iya taɓa lafiyar tafiyarsa. Ba ma fata, ba kuma za mu cire rai ba, In Sha Allah za mu yi masa aikin da idan Allah Ya yarda za a dace. Amma sai dai ka yi haƙuri Yallaɓai, don hakan ba lallai ba ne." Likitan ya ƙare maganar a sanyaye, saboda yadda ya ga yanayin Abeey. Ya san yadda yake matuƙar ƙaunar yaransa, musamman ma kuma Tareeq. Sai dai ga shi Allah Ya fi jarabtarsa da ciwuka. Bai ga kuma amfanin ɓoye masa komai ba, tun da da kansa ya nemi ya sanar da shi hakan. Gwara ma ya sanar da shi gaskiyar, ba su da tabbacin za a samu nasara a aikin, saboda kar sai an yi ba a dace ba, a zo ana wallahi tallahi. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 27 Ɗan jimm Abeey ya yi na tsawon minti ɗaya ba tare da ya ce komai ba. Kafin zuwa can ya sauke ajiyar zuciya, a hankali a kan laɓɓansa ya furta "Ya Ilahy." Kafin ya maida dubansa kan Likitan ya ce, ilahirin jikinsa a sanyaye. "Na gode." Shi ne abin da ya iya furtawa kawai, daga haka ya miƙe ya miƙa masa hannu kana ya juya ya fice daga office ɗin. Bin sa da kallo Likitan ya yi, yana jin wani irin tausayinsa da na ɗan nasa na kama shi. Kai tsaye Abeey ɗakin da Tareeq ke ciki ya nufa. A hankali ya tura ƙofar ɗakin har lokacin jikinsa a matuƙar sanyaye. Har zuwa lokacin Maama tana zaune gefen ɗan nata. Ya ƙarasa a sanyaye bakinsa ɗauke da Sallama, ya ja kujera ya zauna daidai lokacin da Maama ke amsa sallamar tasa. Gaba ɗaya idanunsa na kan Tareeq da sai a lokacin ya amsa sallamar Abeeyn, saboda yadda hankalinsa ya ɗan yi wani wajen. "Tareeq." Abeey ya ambaci sunansa. "Na'am Abeey." Ya amsa yana kallon sa. Sai da ya kalli ƙafarsa kafin ya ce bayan ya maida duban sa kan Tareeq ɗin. "Ya ƙafar taka? Ya kake jin duka jikinka?" Shiru Tareeq ya yi na ɗan wasu sakanni, yana nazarin abin da ya kamata ya ce. Don kuwa idan har gaskiya zai faɗa, toh ba zai iya kwatanta abin da yake ji a cikin ƙafarsa ba. Ya ɗan sosa goshinsa a nutse kafin ya ce "Alhamdulillahi Abeey, da sauƙi." Murmushin yaƙe Abeey ya yi, a ransa yana ji ina ma a ce hakan ne. Domin kuwa, daga yanayin yadda Tareeq ɗin ya yi magana za ka fahimci kawai ya faɗa ne. "Allah Ya ƙara lafiya Tareeq. In Sha Allah za ka samu lafiya, kamar ba ka taɓa yin ciwo ba." Jinjina kai ya yi yana murmushi, lokaci ɗaya yana gyara zamansa saboda ciwon da ƙafarsa take ya ɗan motsa. Maama ce ta amsa da "Ameen." Ya yin da shi kuma ya sake kwantar da kansa gefe idanunsa a lumshe. .... Kallon ta kawai Umma take, duk lokacin da ta shigo ba tare da ta ce da ita ko uffan ba. Ita ma ba ta ce wa Umman komai ba, fita kawai take yi, ta ɗauko kayan ta shigo da su sai kuma ta sake fita. Har zuwa lokacin da ta dawo cikin ɗakin ta zauna jagab a kan kujera tana faɗin "Washh.." Ta yi maganar tana zame hular kanta idanunta a lumshe. Sai a lokacin sannan Umma ta ce, bayan ta ɗauke duban ta daga kan kayan zuwa kan Jawahir. "Jawahir, waɗannan kayan fa?" Ta faɗa tana nuna su. Buɗe idanunta Jawahir ta yi ta kalli kayan, sannan ta gyara zamanta a kan kujerar ta ce "Umma kayan kitchen ne fa." Ta ƙare maganar tana turo baki. "Iyeeee, yau na ga ikon Allah. Wai Jawahir me ye haka ne? Ba za ki iya haƙuri cikin satin nan na je na siyo miki duk abin da kike buƙata ba?" Sake tura bakinta ta yi kafin ta ce "Toh Umma ba ga shi na rage miki wasu abubuwan ba. Kuma ma na ga har yanzu kin ƙi zuwa, bayan bikin saura 'yan kwanaki." Dariya Umma ta yi tana girgiza kai. 'Wato a kan Tareeq Jawahir ba ta da kunya.' Ta raya hakan cikin zuciyarta. Ya yin da a fili kuma sai cewa ta yi "Toh ya yi, sai ki tashi ki shigar da su ciki ki wuce mu je mu duba jikin Tareeq." A razane ta ce "Jikinsa kuma? Me ya faru da Yah Tareeq ɗin?" Ajiyar zuciya Umma ta sauke kafin ta ce "Ba ki ga missed call ɗina a wayarki ba? Wallahi ya samu hatsari ne." "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Na shiga uku? Amma dai babu abin da ya same shi?" Ta tambaya a ruɗe idanunta a kan Umman. "Tashi mu je." Umma ta faɗa tana miƙewa. Ko sake bi ta kan kayan ba ta yi ba, ta ɗauki jakarta ta zura a hammata, har tana riga Umman ma ficewa daga ɗakin. A cikin satin aka yi wa Tareeq aiki a ƙafarsa, aikin da cikin ikon Allah aka dace matuƙa yadda ba su yi tsammani ba. Don haka cikin farin ciki Likitan da ya jagoranci aikin yake miƙa wa Abeey hannu fuskarsa ɗauke da murmushi yake faɗin "Congratulations Sir, an yi aiki cikin nasara In Sha Allah." Cikin wani irin farin ciki Abeey ya miƙa masa hannu suka gaisa, fuskarsa na nuni da irin farin cikin da yake ciki. "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah." Shi ne abin da Abeey ya din ga faɗa. Likitan bai tari numfashinsa ba, sai da ya gama sannan ya ce "Sai dai za a ɗan ɗauki lokaci gaskiya kafin ya iya taka wa da ƙafar tasa. Ina nufin za a samar masa kujera ne ya din ga duk wasu abubuwa da zai yi a kai. Aikin ƙafa kam an yi nasara, amma ba yanzu zai iya takawa ba, sai zuwa lokacin da Allah Ya nufa, amma fa a yadda muka ga ƙafar tasa, muna kyautata zaton nan ba da daɗewa ba ne In Sha Allah." Jinjina kai Abeey ya yi, duk da yadda ya ji jikinsa ya yi sanyi. Amma kuma idan ya tuna inda Allah Ya taimake su aka yi aikin lafiya sai ya ji sanyi a ransa. Godiya sosai ya yi wa Likitan da ya yi ta sinnar da kai cike da kunyar jin Alhaji Dikko guda na yi masa godiya haka tamkar wanda ya yi masa wani babban abu na musamman. Ta ɓangaren Daneen kuwa abubuwa sun cakuɗe mata, domin kuwa idan dai har tana lissafi daidai, yanzu haka saura sati ɗaya bikin Tareeq. Don haka gaba ɗaya ta ruɗe, duk wata hanya da za ta sada ta da ɗaki, wajen ajiyar kayan Tareeq kawai shi take nema. Sau da dama ta kan faki idanun mutane ta je sashen nasa, sai dai kamar kodayaushe a kulle dai. Ga shi kusan kullum suna asibiti. Babu damar ta ce ba za ta je ba, don tana tsoron kar a zargi wani abun. .... "Sannu Yah Tareeq." Hidaya ta faɗa a karo na barkatai. Murmushi Tareeq ya yi har fararen jerarrun haƙoransa na bayyana kaɗan. "Hidayaaaa.." Ya ɗan ja ƙarshen sunan, jin yadda motsi kaɗan sai ta ce masa sannu. Murmushi ta yi kana ta ce "Na'am Yah Tareeq." "Na warke fa." Ya faɗa yana ɗan gyara zaman ƙafarsa. "Allah Ya sa." Ta faɗa a sanyaye. A hankali ya ɗan kalli gefensa kafin ya maida duban sa kanta ya ce "Ina Daneen?" Da mamaki shimfiɗe a kan fuskarta ta ɗaga kai ta kalle shi. Tana matuƙar mamakin yadda yake iya kula da rayuwar Daneen ɗin, sosai da sosai yake barin ta da mamaki ya kusan kashe ta. Yadda ya haddace sunanta cikin ƙanƙanin lokaci, yana ɗaya daga cikin abin da ke matuƙar ba ta mamaki. Sai dai abin da ba ta sani ba, kula da rayuwar Daneen ya zama dole a wajensa. Ko babu komai yanzu haka rayuwa take a cikin gidansu. Ya zama dole ya saka wa duk wani takunta ido. Duk yadda aka yi ma Hidaya manta halinsa ta yi. Gefe guda kuma take-taken yarinyar bai yi masa ba. Dalili kenan da ya sa yake lura da duk wani motsinta. "Yah Tareeq.." Ta ambata cike da mamaki ba tare da ta ba shi amsar tambayar da ya yi masa ba. Sarai ya fahimci abin da take nufi, don haka ya saki wani miskilin murmushi da ya matuƙar ƙawata fuskarsa kafin ya ce "Ba ni amsa ta." Ya faɗa cikin basarwa. Kafin ta kai ga cewa komai, Daneen ta yi sallama cikin ɗakin kanta a ƙasa kamar wata munafuka. Dukkan su suka bi ta da kallo, kafin Tareeq ya janye nasa idanun. Ga maɗaukakin mamakinsa, abin da bai taɓa ji daga bakin yarinyar ba, sai ga shi ta ce "Barka da wannan lokacin." Kusan a tare shi da Hidaya suka sake kallon kyakykyawar fuskarta da har zuwa lokacin ba ta ɗaga ta ta kalle su ba. A karo na biyu ya sake janye idanunsa yana ɗan taɓe bakinsa, kamar ba zai amsa ba sai kuma ya ce "Barka dai. Ya jikinki?" Har ta ɗaga kai za ta kalle shi, sai kuma ta fasa, don so take duk wani zargi da ta fara karanta a kan fuskarsa ya fice masa a rai. Don haka so take ya ɗauka kunya ce da rashin sabo ke hana ta gaishe shi, ko kuma yi masa ya jiki, duk da yadda shi ba ya gajiya, a kullum idan za su haɗu sai ya yi mata ya jiki, duk kuwa da ta warke, sai ɗan abin da ba a rasa ba. "Alhamdulillah. Ya jiki?" Ta yi ƙarfin halin faɗar hakan, a yanzu tana kallonsa. Ba tare da ya kalle ta ba ya amsa da "Alhamdulillah." Daga haka gurin ya ɗauki shiru. Ita dai Hidaya kallon su kawai take yi su duka kamar ta samu T.V. Sai zuwa can sannan ta ce "Sister ki zo ki zauna mu yi hira." Murmushin nan na yaƙe, wanda ake cewa ya fi kuka ciwo Daneen ta saki tana girgiza kanta. Da ƙyar ta iya furta "A'ah, bari na ɗan je waje." Ta yi maganar tun kafin ma Hidaya ta ce komai ta fice daga ɗakin. Hidaya ta bi ta da kallo tana murmushi kafin ta maida duban ta kan Tareeq. .... Shiru Maama da Dada ji suka yi, bayan da suka gama sauraron bayanin Abeey duka. Bayan wajen shuɗewar mintina biyu sannan Maama ta ce "Yanzu ya za a yi kenan?" Ta tambaya a sukwane. Ajiyar zuciya Abeey ya sauke kana ya ce "Toh! Ni dai ban yanke komai ba. Amma abin da yake akwai kawai shi ne aurensa da Jawahir za a yi cikin satin nan kar a fasa. Idan ya so kin ga faɗuwa ta zo daidai da zama, sai ta ci gaba da kula da shi. Amma ya kika ce Dada ji?" Cikin na'am da zancen Abeey Dada ji ta ce "Tabbas zancenka ya yi Alhassan, kuma In Sha Allah hakan shi ne mafita. Ko babu komai Jawahir 'yar'uwar Tareeq ce, kuma tana son shi, kula da shi a yanayin da yake ciki In Allah Ya yarda ba zai zama matsala ba. Abin da nake so da ku kawai, ku fara shirye-shiryen aure, domin kuwa kamar yadda aka tsaida shi sati mai zuwa, ba za a daɗa ba, ba za a rage ba. Za a ɗaura shi In Sha Allah. Allah Ya sa hakan ne mafi alkhairi, Allah Ya ba su zaman lafiya, Ya ba wa yarinyar nan ikon kula da Tareeq har zuwa lokacin da zai warke." "Ameen." Dukkansu suka amsa da hakan, cikin na'am da maganar Dada jin ɗari bisa ɗari. .... A karo na barkatai ya sake kallon kyakykyawar matarsa da ke zaune a kan kujera. Sai dai ta kwantar da kanta a kan hannun kujerar da take kai ne, hannunta ɗaya yana gefenta kan kujerar, ya yin da ɗayan yake lilo kusa da kanta. Idanunta a lumshe suke, sai dai duk da haka, hakan bai hana ƙwalla sauka a kan kyakykyawar fuskarta ba. Cike da tausayawa yake kallon ta. A kullum a kodayaushe yana rasa ta ina zai soma rarrashinta? Ta ina zai ba ta baki a kan yanayin da ta tsinci kanta? Yana ji a jikinsa tamkar shi ne sila, shi ne silar rugujewar farin cikinta. Sai dai duk da haka, ya zai yi? Ta ya ya zai iya jure ci gaba da kallon ta cikin wannan yanayin? Tunani ya yi wa ƙwaƙwalwarta yawa, a kodayaushe tunani take. Idan aiki take tunani take, idan ta zauna ta yi shiru tunani take, idan bacci take ma duk mafarkin abu ɗaya take, haka zalika ko magana suke, sai dai ya ji shiru, idan ya kalle ta kawai sai ya ga alamar ta faɗa wata duniyar tunani. Wataran kuma sai dai kawai ta zauna ta yi ta kuka, musamman ma idan ba ya kusa da ita, shi ya sa kwata-kwata ba ya son yin nesa da ita. Don ba ya so abin ya yi yawa, kar ya janyo mata babbar matsalar da ta fi wadda take ciki a yanzun wato Depression. "Fatoum.." Ya faɗa a sanyaye kamar yadda ya saba kiran ta da hakan. A karo na farko ba ta ji ba, sai da ya sake maimaitawa sannan ta buɗe idanunta da sauri ta tashi zaune sosai tana kallon sa da jajayen idanunta. "Na'am." Ta faɗa tana yin amfani da hannunta wajen goge fuskarta. "Ba za ki yi ƙoƙari wajen rage damuwar nan ba koh? Kin manta abin da Likita ya faɗa koh? Ki yi haƙuri don Allah ko da ba za ki daina duka ba, don na san hakan abu ne mai matuƙar wahala, amma a ƙalla ki rage don Allah. Ko da ni ma zan samu salamar zuci. A kullum idan na kalle ki cikin irin wannan yanayin, ina ji tamkar ni ne sila, kai ba ma tamka ba, ni ɗin ne dai sila. Don Allah ki yi haƙuri Fatoum ki fawwala wa Allah komai, za mu dace In Sha Allah." Duk tsayin maganar nan da ya yi, murmushi kawai ta yi idanunta na kallon wani wajen ta ce "Uhumm." Ta faɗa tana girgiza kai. Shiru ya yi yana kallon ta, ya sauke ajiyar zuciya kafin a sanyaye ya sake kiran sunanta a tausashe. Sai a lokacin tamkar wadda ta dawo daga tunani sannan ta kalle shi, a hankali ya ɗaga mata kai kafin ya ce "Ki yi mini magana mana." Tamkar jira take, sai kuwa ta shiga girgiza kai, tana jin ɗacin kalaman da take tattarawa za ta faɗa. Tun kafin fitar su ma tana jin ɗacinsu ballantana kuma ta faɗe su. Sai dai duk da haka, hakan bai hana ta soma faɗin "Na rasa yadda zan yi, ban san me zan yi in ji daɗi ba. Tunanin nan da nake zaunawa na yi shi kaɗai ne mafita ta. Duk da yadda nake ji tamkar ƙwaƙwalwata za ta tarwatse. Amma ba zan iya hana kaina tunanin yarana ba. Ni idan da mutuwa ne ma suka yi, zan haƙura, na san zuciyata za ta fi samun salamar suna can cikin kwanciyar hankali In Sha Allah. Amma yanzu fa? Ban san inda suke ba, ban san suna cikin wane irin hali ba. Shin a wane waje suke rayuwa? Shi ma ban sani ba. Yaushe ne Allah zai haɗa mu? Duk ban sani ba. Yallaɓai ina ji tamkar zuciyata za ta faso ƙirjina ne ta fito ta tarwatse, ina ji kamar ƙwaƙwalwata za ta fashe idan ina tuna su. Ina iya ƙoƙarina wajen ganin na bar wa Allah komai, amma na kasa daina tunaninsu. Kullum suna cikin ko'ina na jikina a manne, komai nake su ɗin ne dai a raina. Shin ya zan yi ni kam da raina? Ina zan ga yarana?" Ta yi maganar a raunace. Ajiyar zuciya ya sauke, yana jin daɗin yadda yau ɗin ta amayar da abin da ke cikin zuciyarta. Ba kamar sauran ranaku da ta fi son ta yi shiru, ko kuma ta yi guntuwar magana ba. Ya runtse idanunsa yana ji da gasken gaske shi ne sila! Shi ne silar raba wannan uwar da 'ya'yanta. Shin me ya sa ma ya shiga rayuwar Fatima? Tabbas da ya san haka ne zai faru, da bai yi yunƙurin neman auren Fatima ba. Ko kuma ma tun farko ya yi fatan kar Allah Ya haɗa shi da Fatima. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 28 Ya shafe kusan mintuna biyu ba tare da ya ce komai ba. Kallon ta kawai yake yi cike da tausayawa, zuciyarsa kuwa wani irin raɗaɗi yake ji, raɗaɗin kuma ba na komai ba, sai na zamowarsa silar rugujewar farin cikin Fatimarsa. "Ki yi haƙuri, in sha Allah yaran nan suna cikin ƙoshin lafiya, kuma za su dawo miki cikin ƙoshin lafiyar. Abin da nake so da ke kawai ki ci gaba da addu'a, sannan ki rage wannan damuwar da kike yi. Kada ki manta da shawarwarin likita da ya ba mu. In Allah Ya yarda nan ba daɗewa ba za mu samu labarin inda suke, tun da har yanzu ban daina cigiya ko Allah zai saka a dace ba. Ki yi haƙuri ki yi shiru." Ya ƙare maganar cikin rarrashi da taushin murya. Hannu Inna-wuro ta saka ta goge fuskarta a nutse, idanunta a lumshe tana ci gaba da jin bugun zuciyar da take fama da shi kusan kowanne lokaci. A hankali ta buɗe baki da ƙyar ta furta "Allah Ya sa." Ta faɗa tana maida bayanta ta kwantar kan kujerar da take kai cikin rashin sanin abin yi. Bin ta ya yi da kallo ba tare da ya ce komai ba. Ya rasa ta inda zai ɓillowa wannan al'amari. Shiru kawai ya yi ya ci gaba da kallon ta yana tunanin hanyar da zai bi wajen tsananta bincike ko Allah zai sa a dace su sami inda yaran nan suke. ... Turo ƙofar da aka yi shi ne ya sanya Maama ɗaga ido ta kalli mai shigowar. Umma da kuma Jawahir suka ƙaraso cikin ɗakin. Da murmushi ta miƙe tana faɗin "Lale marhaba." Maida mata da martanin murmushin suka yi kana Umma ta nemi waje ta zauna. Ya yin da Jawahir ta tsaya a gefen kujerar Umman tana sunnar da kai ƙasa. Gaisawa Umma da Maama suka yi, Umman na tambayar jikin Tareeq. "Jiki Alhamdulillahi wallahi, zuwa gobe ma idan Allah Ya kai mu, muke saka ran sallama, kamar yadda suka faɗa." "Kai Alhamdulillah, Alhamdulillah. Ashe ƙafar ta yi sauƙi ke nan, ko ma in ce ta warke?" Umma ta faɗa tana murmushi. Sai da Maama ta kalli ƙafar Tareeq ɗin da idanunsa ke a lumshe kamar mai bacci kafin ta ce "Alhamdulillah kam, ta warke za a ce. Sai dai... Ba ku yi magana da yayan naki ba ne?" Ta ƙare maganar da sigar tambaya. Girgiza kai Umma ta yi tana faɗin "A'ah, ba mu yi ba kam. Amma yau sun haɗu za su yi magana da Abban Jawahir." "Barka da wannan lokacin Maama." Jawahir ta faɗa tana murmushi. Amsa mata gaisuwar Maama ta yi cikin sakin fuska, har ranta tana ji in Allah Ya yarda ta yi sa'ar suruka. Sun kwashe wajen minti 20, kafin Tareeq ya buɗe idanunsa. "Sannu Tareeq." Umma ta faɗa tana kallon sa. Sai da ya ɗan saki murmushi kaɗan, wanda ya ƙawata kyakykyawar fuskarsa sannan ya ce "Yawwah, Barka da wannan lokacin." Ya yi maganar a haɗe. "Barka dai, ya jikin?" Sai da ya jinjina kai sannan ya amsa da "Alhamdulillahi." Nan ta sake yi masa fatan samun sauƙi, Maama ta amsa da "Ameen." "Yah Tareeq ina wuni?" Jawahir ta faɗa tana satar kallon wannan kyawawan ƙwayar idanun nasa. Ta kafe shi da idanunta, tun kafin ma ya ɗago nasa ta kasa kalla. A hankali ya ɗaga nasa idanun ya kalle ta, ya ɗan lumshe su, lokaci guda yana buɗewa ya ce "Alhamdulillah Jawahir, kina lafiya?" Ya yi ƙarfin halin faɗin hakan. Sai da ta gyara tsayuwa tana jin wani irin farin ciki na mamaye ta sannan ta ce "Lafiya ƙalau." Daga haka ta sake mazewa a gefe ba tare da ta zauna ba. Hannu Maama ta saka ta yafito ta tana faɗin "Kin ga ni ba na son wata kunya zo ki zauna. Baƙuwarki ce ni?" Ta ƙare maganar tana dariya. Ita ma Umman dariya ta yi, ya yin da Jawahir ke ta murmushi kawai. Kamar yadda Maaman ta faɗa, don haka ta nemi waje ta zauna kuwa. Bayan shuɗewar wasu mintuna aka fara kiraye-kirayen Sallahr Maghrib, duk suka yi alwala suka dawo cikin ɗakin. Maama ta kalli Tareeq ta ce "Za ka yi alwalar ne?" "Ehh.." Ya amsa mata da hakan. Ƙarasawa ta yi keɓantaccen wajen da aka ajje masa kujerar da ba a daɗe da kawo ta ba, ta ɗakko ta, ta ƙaraso da ita inda yake. A hankali ta shiga taimaka masa don ganin ya zauna a kan kujerar. Wani irin ƙwarewa Umma da ta zuba ruwa a tambulan tana sha ta yi, ruwan da ta ji ya shige mata har tsakar ka. Ta saka hannunta ta shiga bubbuga kanta har lokacin idanunta a kan Tareeq. Har ba ta san lokacin da ta furta "Ba ya iya tafiya ne?" Ta faɗa tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki na bayyana cikin muryarta. Ba tare da kawo komai a ranta ba Maama ta ce "Wallahi kuwa, kin ga dai ikon Allah." Wani irin bugawa zuciyar Umma ta shiga yi fat!fat!fat! Ba za ta iya jurewa ba, don haka jiki duk a sanyaye ta ce "Kenan har tsawon wane lokaci zai ɗauka yana zama kan kujerar nan?" Tana ci gaba da taimaka masa ɗin dai ta ce "Har zuwa lokacin da Allah Ya nufa. Su kansu likitocin ba su sani ba, sun dai ba mu tabbacin idan Allah Ya yarda watarana zai iya miƙewa a kan ƙafarsa. Shi ne ma dalilin da ya sa Abeeyn Tareeq yake so a yi auren daga zarar an sallame shi, kin ga daga an ɗaura aure sai Jawahir ta ci gaba da kula da shi." Wani irin kuka mai ƙarfi Jawahir ta fashe da shi, tana jin yadda ilahirin jikinta ke karkarwa. Kawai sai ta zube a kan gwuiwoyinta tana ci gaba da raira shi. Maama ta kalle ta cike da tausayi, don ta san kukan na tausayin halin da Tareeq ya tsinci kansa a ciki ne. Duk da ba ta sake jin wata magana daga bakin Umma ba, ba ta damu ba, ta shiga tura Tareeq zuwa toilet don ya ɗauro alwala. Shi dai bai ce komai ba, bai kuma nuna alamar yana tare da su ba, duk da yadda cikin zuciyarsa yanayin yadda Umma ta yi magana ya shigar da shi wani yanayi na kokwanto da kuma fargaba. Komawa Umma ta yi kawai ta zauna a kan gado idanunta a kan Jawahir. Shiru ba tare da ta ce komai ba, take ci gaba da kallon ta. Ta kasa furta komai, ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ne. Ita ta haifi Jawahir, ta kuma fi kowa sanin halinta. Wannan kukan da take, daga ita Jawahir ɗin, sai kuma ita suka san na mene ne. Suna yin Sallahr Maghrib suka bar asibitin, bayan sun yi sallama da Maama a gaggauce. Shi dai Tareeq bin su kawai ya yi da kallo, don ba ƙaramin mamaki yanayin yadda suka fita daga asibitin ya ba shi ba. Ita kuwa Maama ba ta kawo komai a ranta ba, ta ci gaba da harkokinta. ... "Toh shi ke nan, amma kin san abin da za a yi?" Maami da ke riƙe da waya kare a kunnenta ta faɗa bayan ta nemi waje ta zauna. Daga can ɓangaren aka ce "A'ah." "Kin san halin 'yar taki, ba za ta taɓa yarda da auren haɗi ba. Saboda haka ki turo yaron ya zo da niyyar ya zo gaishe ni, daga nan zan san yadda za a yi su haɗu. Bayan ya tafi sai na sanar da ita ya nemi da a ba shi numberta. Kin fahimci fa'idar yin hakan?" Jinjina kai matar ta yi kamar Maamin na gabanta kafin ta ce "Ehh, na gane. Hakan kuma ya yi matuƙa, Allah Ya haɗa mana kansu." "Ameen." Maami ta amsa da hakan. Daga haka ba su ƙara wasu mintuna masu yawa ba, suka yi sallama. Murmushi Maama ta saki tana kallon Maman Abdoul da ke zaune kujerar da ke kusa da tata. "Barkan ki da wannan lokacin Madam." "Barka dai Hajiyata.. Wai Sultanah ake nema wa abokin haɗi?" Ta haɗe gaisuwar da tambayar ta yi su lokaci guda. Jinjina kai Maami ta yi kafin ta ce "Ita fa. Amma ki yi a hankali kar ta ji. Kin san halin Sultanah." "Na sani kam. Amma me zai hana tun da ga na gida a tafi wani wajen? Wallahi da mun haɗa ta da Abdoul. Ina son yarinyar wallahi, ko don nutsuwarta." Girgiza kai Maama ta shiga yi kana ta ce bayan ta yi murmushin yaƙe "A'ah ke kam, wani irin haɗi kuma tsakanin Abdoul da Sultanah?" "Wallahi kuwa ƙawata, na ɗauka kamar sai ya fi koh?" Sake girgiza kai Maami ta yi ta ce "Toh ai kin ga mun riga mun gama magana da Hajiya Ati, da ba mu yi magana ba sai a yi yadda kika faɗa ɗin." Ɗan jujjuya kanta Maman Abdoul ta yi sannan ta ce "Toh hakan ma ya yi. Allah Ya tabbatar da alkhairi." Sai a lokacin sannan Maami ta saki murmushi tana faɗin "Ameen, ƙawata." ... Gyara zamansa Abeey ya yi, kafin ya ɗan sauke ajiyar zuciya. Dukka hankalin 'yan ɗakin sai ya dawo gare shi. Sai da ya gabatar da addu'a sannan ya soma faɗin "Wato dalilin haɗa wannan taro da na yi ba komai ba ne, face don na sanar da ku ɗaurin auren Tareeq da za a gabatar da shi ranar juma'ar nan mai zuwa idan Allah Ya yarda. Ba kuma shi da kowa ba face 'yar'uwarsa Jawahir. Muna fatan Allah Ya tabbatar da alkhairi, Ya kuma kaɗe dukkanin abin ƙi. Idan wani na da magana zai iya yi." "Toh, Allah Ya amsa addu'o'in nan, sannan kuma Ya yi muku albarka gaba ɗaya. Ni kam me ya kamata na ce? Bayan godiya ga Allah. Tun da ga shi jikokina biyu suna ƙoƙarin auren junansu. Allah Ubangiji Ya sanya albarka." Dada ji ta faɗa, har cikin muryarta farin cikin da take jin ta ciki na bayyana. "Ameen." Maama ta faɗa tana murmushi. Wani banzan kallo Umma take watsa wa Jawahir daga inda take zaune. Duk da sanin halin 'yar tata, amma ko babu komai ta san za ta ji kunyar buɗe baki ta yi magana, musamman saboda kwarjinin Abeey. Amma ya za su yi? Ya zame musu dole su magantu. Ita dai Jawahir ta rasa ta inda za ta fara. Shin me za ta furta kai tsaye ba tare da wani kwane-kwane ba, wanda ko ba ta yi bayani ba za a fahimci abin da take nufi? Tabbas ta san tana son Tareeq, ba kuma don komai ba sai don kyawunsa, kyawun surar da Allah Ya ba shi. Tafiyarsa, komai nasa su ne suke burge ta, ko kuma ta ce su ne take so. Toh yanzu kuma ga shi babu ƙafa, yana zaune ne a kan kujera, ya zama gurgu, mara ƙafa. Kenan me za a kira shi? 'Musaki?' Ta ji zuciyarta ta yi saurin ba ta amsa. Ta runtse idanunta tana jin yadda zuciyarta ke ci gaba da bugawa. Ke nan duk yadda ta tsarawa rayuwarta hakan ba zai yiwu ba? Wato suna nufin ta auri Tareeq a yadda yake a yanzun, ke nan me za ta je yi gidan auren? 'Bauta' Ta sake jiyo hakan a cikin kwanyarta. Tuni har ta fara hasaso kanta a cikin gidan Tareeq. Duk da kayan alatun da ke gidan, ta san muddin ta shiga gidan nan tata ta ƙare. Sai dai ta lalace a banza a wofi wajen kula da nakashashshshen mijin da ake ƙoƙarin liƙa mata. Ita ba ta san da gaske ba shi take so ba, ƙirar jikinsa take so ba sai yanzu. Yadda kuma ta ji zuciyarta ta yi na'am da hukuncin da suka yanke ita da Ummanta ya ƙara tabbatar mata da hakan. Don haka cikin ƙarfin hali, ta tattaro jarumta ta afawa kanta. Ta haɗiye tsoron da take ji, kafin ta runtse idanunta na tsawon wasu sakanni, kana ta buɗe. A hankali ta buɗe bakinta da ƙyar ta soma faɗin "Abeey don Allah ka yi haƙuri, amma ba zan iya auren Yah Tareeq a halin yanzu ba." Gaba ɗaya mutanen ɗakin kallon ta suke yi cikin matuƙar tashin hankali, idan ka cire Umma. Cikin matuƙar mamaki Maama ke ci gaba da kallon ta, tana jin abin kamar wani wasan yara. Cikin ƙarfin hali ta furta "Jawahir, kin san me kike faɗa kuwa?" Ta faɗa jikinta a matuƙar sanyaye, wanda ya ja har muryarta ma a sanyayen take. Shiru Jawahir ta yi, ta kasa ɗaga ido ta kalli Maaman. Sam Maama ba ta yi tunanin za ta sake jin wata magana daga bakin Jawahir ba, duk kuwa da ita ta tambaye ta. Amma sai ta ji ta ce "Eh Maama. A yi haƙuri don Allah." Wani irin kallo Sultanah da Hidaya suke bin Jawahir da shi. Gaba ɗayansu sun kasa furta komai. Ganin abin suke kamar almara, ko kuma shirin film. Anya kuwa Jawahir ɗin ce? Jawahir dai Jawahir masoyiyar Yah Tareeq? Cike da ƙarfin hali, da kuma ƙaryata abin da kunnuwanta suka jiye mata Dada ji ta ce bayan ta sauke duka idanunta a kan Umma. "Maimunatu, kin ji abin da yarinyarki take faɗa kuwa?" Ɗaga idanunta Umma ta yi ta kalli Dada ji. Karo na farko da ta fara kallon Dada ji ɗin ba a matsayin mahaifiyarta ba, bayan tsawon shekaru masu yawa. Ba za ta iya bari a ce tana ji tana gani, duk yadda ta ci buri da 'yarta a ce ta ƙare a auren nakashashshshe, musaki, mara ƙafa ba. Wanda ko likitoci ba su da tabbacin zai warke ko kuwa nan gaba kaɗan za a yanke ƙafar ne idan ta daina aiki. Daga lokacin kenan sunan ɗiyarta zai tashi daga Jawahir ya koma 'Matar Gurgu' Abin da ba za ta iya jurewa ba ke nan. Tabbas ta matuƙar so haɗin Tareeq da Jawahir, ko don yadda Jawahir ɗin ke son shi. Ita kuma tana matuƙar ƙaunar abin da ɗiyarta ke so, shi ya sa ta yi ta fafutuka wajen ganin auren nan ya yiwu. Amma fa a lokacin ba ta taɓa tunanin Tareeq ɗin zai tashi daga cikakke kuma lafiyayyen mutum zuwa nakashashshshe ba. Don haka ba za ta iya jure ganin 'yarta ta ƙare rayuwarta wajen kula da miji ba, a banza a wofi ta lalace. Kullum babu hutu, sai dai kula da nakashashshshen miji. Ina za ta iya zuba ido ta din ga kallon shalelen 'yarta cikin wannan hali? Hakan ne ya sanya ta ɗan jan wani numfashi, tana ji ya zama dole ta buɗe baki ita ma ta magantu ko da hakan na nufin rugujewar zumuncinsu. *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 29 "Ki yi haƙuri Dada ji, ban san me zan yi mata ba." Shi ne abin da ta faɗa, ba tare da ta bari sun haɗa ido da ita ba. Kallon ta kawai Dada ji take yi cike da tsananin mamakin da ya hana ta furta komai. Ji take kamar ba gaske ba ne, waɗannan maganganun ba daga bakin Maimunatun suke fitowa ba. "Jawahir har cikin zuciyarki kike faɗar wannan maganar?" Abeey ya faɗa bayan ya kalli Jawahir ɗin. Kasa haɗa ido ta yi da shi, kawai ta ci gaba da kallon wani wajen kana ta buɗe baki da niyyar soma magana, Abeey ya katse ta da faɗin "Ɗaga idanunki ki kalle ni sannan ki tabbatar mini da abin da kika faɗa." Kamar ba za ta ɗaga idanun nata ba, haka dai ta daure ta kalli Abeeyn a ɗan tsorace. Ba ta buƙatar ƙarin bayani, don ta san abin da yake buƙatar ta ce, don haka ta buɗe baki ta ce "Eh Abeey a yi haƙu..." Ɗaga mata hannun da Abeey ya yi, shi ne ya sanya ta katse maganar da ta fara, ta yi saurin yin ƙasa da kanta. Tun da ta fara magana ya ɗaga lumsassun idanunsa ya kafe ta da su, ba ya buƙatar wani ƙarin bayani daga Jawahir. Domin kuwa, duk wani bayani da yake so ya sani ya fuskance shi daga cikin muryarta. Ya san Jawahir tana son shi, bai kuma taɓa tunanin tana son shi don ƙirar jikinsa ba, duk da yadda ya kamata ya fahimta, ko don yadda maganganunta da yawa ba sa wuce a kan kyawunsa ne da sauran su. Amma bai taɓa barin hakan ya yi tasiri a zuciyarsa ba. Sai ga shi yanzun ƙiri-ƙiri ta bayyana ba za ta iya aurensa ba, ba kuma don komai ba sai don nakasar da ya samu a ƙafarsa. A hankali ya lumshe idanunsa yana jinginar da kansa kan kujerar da yake kai ba tare da ya ce komai ba. Dubansa Abeey ya maida kan Umma ya ce "Maimunatu kin amince da abin da yarinyar nan take faɗa?" Ya ƙare maganar har lokacin yana kallon ta. Shiru ta yi na tsawon sakanni kamar mai tunani, kafin ta gyara zama ta ce "Toh ya zan yi da ita Yaya? Ita ta ce tana so tun farko, yanzu kuma ta ce ba ta so saboda wani dalili. Sai nake ganin kamar babu abin damuwa, tun da dai ra'ayi ne. A yi haƙuri kamar yadda ta faɗa ɗin." Tun da ta fara magana Abeey ke kallon ta har ta ƙarasa. Ya yi matuƙar mamaki, maganar Umma da ita kanta Jawahir ɗin sun ba shi mamaki. Ya kuma jefa shi cikin shakkun halayya da ɗabi'un mutane da ka iya sauyawa cikin ƙanƙanin lokaci. Bai taɓa tunanin haka daga Umman Jawahir ba. Bai taɓa tunanin akwai ranar da za ta zo, don Tareeq ya samu nakasa a ƙafarsa ta bi bayan ɗiyarta na ƙin aurensa ba. Ta ɓangaren Dada ji kuwa shiru ta yi tana kallon Maimunatun. Lallai duk inda aka ce ɗa ba naka ba ne, wani lokacin sai hakan ya bayyana. Tun da ta ɗauki Maimunatu take riƙe da ita tsakani da Allah ba tare da ta taɓa nuna mata wani bambanci tsakaninta da Alhassan ba. Duk wanda ma bai sani ba, ba zai taɓa cewa Umman ba 'yar Dada ji ce ba. Don kuwa tun da take ba ta taɓa buɗe baki ta ce ba 'yarta ba ce. Kullum burin ta ma kar wani ya gane ba ita ta haife ta ba. Duk wata kulawa da ya kamata uwa ta ba wa ɗiyarta ta ba wa Umma. Babu abin da ta rage ta da shi wanda uwa za ta yi wa ɗanta. Sai ga shi lokaci ɗaya ta guji jininta, don kawai Allah Ya jarabce shi da ciwo. Ciwon da suke fata da addu'ar Allah Ya yaye masa, Ya sa ya warke. Amma ita da ɗiyarta sun juya masa baya, sun nuna ba su yarda da ƙaddara ba, sun fito fili sun nuna dalilin da ya sa suke son Tareeq, ba tare da tunanin yadda hakan zai janyo tangarɗa wa zumuncinsu ba. "Za ku iya tafiya. Allah Ya saka da alkhairi." Abeey ya faɗa yana jin yadda zuciyarsa ke zafi. Ya fi jin zafin ƙanwar tasa a kan ɗiyarta, domin bai taɓa zaton haka daga gare ta ba. Ba su ce komai ba dukkansu suka miƙe, ba tare da sun kalli kowa ba, suka fice daga ɗakin. Daidai lokacin da suka fito daga ɗakin, ita ma Maami ta fito daga nata sashen. Ta kalle su saboda yadda ta gan su kamar a birkice. Ba wani mutunci suke yi da Umman ba, amma yau ɗin sai ta ji ina ma a ce suna yi, ko don ta ji abin da ya faru, saboda yadda yanayin Umman ya nuna kamar ba lafiya ba. Kamar ba ita ba, ta ce bayan ta ɗan rage tazarar da ke tsakanin su "Lafiya me ya faru?" Ta faɗa tana ƙare musu kallo, kallon da a idanunsu ya fi kama da na rainin hankali ko wulaƙanci. Wani banzan tsaki Umma ta sauke tana jan hannun Jawahir, kamar ba za ta ce komai ba, don kwata-kwata ba ta yin Maamin, amma sai ta ce "Ban sani ba. Idan gulmar kike so, me ya hana ki zuwa taron da Yaya ya shirya? Ba fa na son iya-shege." Umma ta ƙare maganar tana jefa mata wani banzan kallo. Daga haka ba ta jira ta ce komai ba, ta ja hannun Jawahir suka wuce suka bar ta a wajen. Bin su ta yi da wani wulaƙantaccen kallo, tana ji yau ɗin gaba ɗaya ta gama muzanta. Me ya sa ma ta yi mata magana bayan dama tun can ba shiri suke yi ba? Ta ja tsaki tamkar za ta tsinka harshenta. Baƙin ciki ya bi ya cika mata zuciya. Kawai sai ta juya ta koma sashenta ranta a mugun ɓace. A ɗaya ɓangaren kuwa tun bayan da suka fita shiru ne ya biyo baya na tsawon mintuna masu yawa. Babu wanda ke da niyyar cewa komai, saboda yadda dukkanninsu kowa da abin da yake saƙawa. Sosai zuciyarsa ke masa wani irin zafi. Wanda rabon da ya ji shi tun bayan rabuwarsa da Diyana. Me ya sa ba shi da sa'a ne shi kam? Sun yi soyayya da Diyana kamar babu gobe, sai dai ashe gaba ɗaya tana son shi ne don dukiyarsa, dukiyar da ta yi ƙoƙarin mallake ta tun kafin ta kai ga shigowa gidansa. Ba domin ikon Allah ba da tuni wani zancen ake ba wannan ba. Bai so Jawahir ba, amma kuma ya amince da aurenta, ita kuma ga abin da ya faru. Kenan shi ƙaddararsa a kan soyayya take? Ko kuwa ya kira ta a kan mace ne? Macen ma wadda sai yana dab da aurenta? "Hidaya." Da kaushashshiyar muryarsa ya ambaci sunan, bayan ya buɗe idanunsa da suka rine daga fari fat, zuwa ja. Shi kaɗai ya san irin zafin da yake ji a ƙirjinsa. Ba ya tunanin zai iya ci gaba da zama cikin ɗakin, gwara ya samu ya keɓance kansa ko ya ji sukunin abin da yake ji. "Na'am Yah Tareeq." Ta faɗa a matuƙar sanyaye tana kallon ɗan'uwan nata cike da tausayawa. Tun kafin ya yi magana ta fahimci abin da yake nufi, don haka ta miƙe, kai tsaye ta ƙarasa bayansa ta shiga tura shi. Daidai suna dab da gifta Maama ta yi ƙarfin halin faɗin "Ba na son tunani Tareeq. Ka samu ka yi bacci, za mu yi magana zuwa safiya. In Sha Allah hakan ne mafi alkairi, kar ka saka wa kanka damuwa. Hakan ma taimakonmu Allah Ya yi, ta hanyar nuna mana masoyanmu na gaske da kuma waɗanda ba na gaske ba." Shiru ya yi yana saurarar abin da Maaman take faɗa, bai ce komai ba kawai ya jinjina kansa, suka wuce. Ita ma Dada ji bin su ta yi da kallo cike da tausayin jikan nata. ... "Wai me kike jira ne? Ko dai kin haƙura kin fasa ɗaukar fansar ɗan'uwan naki? Ko dai ba kya so a hukunta Tareeq ne?" Maganganun da Yohana ya faɗa mata ke nan, waɗanda suka saka ta yin shiru kamar mai nazari. Kafin ta kai ga cewa komai ya sake faɗin "Anya kuwa kina lissafin ragowar kwanakin da muke da su? Cikin sati biyu kwana nawa muke da shi? Ki faɗa mini idan kin fasa ne in daina damun kaina." Sai a lokacin sannan ta sauke ajiyar zuciya, ta buɗe baki da ƙyar ta soma faɗin "Ina nan ina iya ƙoƙarina. Na matuƙar gode da kulawa, kuma in Allah Ya yarda za ka ji ni zuwa gobe. Na gaji da zaman gidan nan kwata-kwata, ba na son ci gaba da kasancewa gida ɗaya da mutumin nan. Ba na son ganinsa ko kaɗan, duk lokacin da na gan shi kewar ɗan'uwana dawo mini take. Ina jin zuciyata na mini zafi, wani irin abu ke tokare mini a ƙirji ya din ga tokare mini numfashi. Ba na son ganin sa ko kaɗan. Zan yi ƙoƙari in Allah Ya yarda a cikin kwana biyu in san yadda zan yi in shiga ɗakinsa." Jinjina kai Yohana ya yi kafin ya ce "Yawwah, ki ƙoƙarta. Kar ki manta har yanzu ruhin ɗan'uwanki na can cikin rashin salama. Gwara a yi maza a hukunta shi ko ruhinsa ya samu salama." Jinjina kai kawai Daneen ta yi kamar yana gabanta. Soma fahimtar halinta da ya yi ne ya sanya shi fahimtar ta ji abin da ya faɗa. Don haka bai sake cewa komai ba, kawai ya katse wayar. Daidai lokacin da aka turo ƙofar ɗakin aka shigo. Ita ma kuma daidai lokacin ta fito daga cikin toilet. Hidaya da Sultanah ne, suka sakar mata murmushi kusan lokaci guda. Maida musu da martanin murmushin ta yi, kana ta ƙaraso cikin ɗakin. "Ohh, kwata-kwata ba na jin daɗin jikina yau ɗin nan wallahi." Sultanah ta faɗa tana ɗan dafe kanta bayan ta zube a kan luntsumemen gadonsu. "Ke dai malama kawai ki ce Yah Abdoul bai kira ki ba." Hidaya ta faɗa tana dariya. Harara Sultanah ta jefa mata kana ta ce "Lallai ma Sisi, wallahi ba ki da dama. Toh ko damuwar Yah Tareeq ai ta isa ta hana mu walwala daga ni har ke ɗin." Cikin na'am da zancen Sultanah Hidaya ta kwantar da kanta kan pillow kana ta ce "Wallahi ke kam ki bari kawai. Duk jikina a sanyaye yake tun jiya wallahi." "Daneen." Hidaya ta faɗa tana kallon Daneen da ta yi shiru tana kallon wani wajen kamar mai tunani. Da sauri ta kalli Hidayan ba tare da ta ce komai ba. Cikin mamaki ta ce "Lafiya kuwa?" Ɗan murmushin yaƙe ta aro ta yafa a kan fuskarta kafin ta ce "Babu komai." "Kin tabbatar 'yar'uwa?" Hidaya ta sake tambaya cikin kulawa. Jinjina kanta ta yi tana miƙewa. Ta ce bayan ta kalli Hidaya "Bari na ɗan fita." Jinjina kai Hidaya ta yi tana faɗin "Tohm." Daga haka Daneen ta fice daga ɗakin, ya yin da Hidaya da Sultanah suka bi ta da kallo har ta fice. "Ba ta da walwala gaba ɗaya, kamar akwai wani abu da ke damun ta." Sultanah ta faɗa har lokacin ba ta daina kallon inda Daneen ta ɓace wa ganinsu ba. Cike da amincewa da zancen nata Hidaya ta jinjina kai kana ta ce "Na gani fa.. Ga shi ba ta saurin sabo. Ta ƙi sakin jikinta kwata-kwata ballantana mu shiga jikinta." "Wallahi, abin na ba ni mamaki." In ji Sultanah. A hankali take taka wa cikin palourn, sanye take cikin doguwar rigar atamfa, da kuma dogon hijabin da ya wuce har ƙasan gwuiwarta. "Ohk." Shi ne kawai abin da ta ji, wanda hakan ya matuƙar tsorata ta, don ba ta yi tsammanin akwai wata halitta cikin ɗakin ba. Domin dai kuwa ita ba ta gani ba. "Wayyo Allah na." Ta faɗa bayan ta dafe ƙirjinta, maganar tata ke nan da ta ɗauki hankalinsa. Ya ɗaga kai ya kalle ta, daidai lokacin da ita ma ta sauke nata a kansa. Sam ba ta yi tsammanin ganinsa a wannan lokacin ba. Kafin haɗuwar idanunsu waje ɗaya ta yi saurin janye nata tana sakin ajiyar zuciya, lokaci guda rashin annurin fuskarta na sake bayyana. Wani irin ɓacin rai tuni ya mamaye ta. 'Kar ki kwafsa' Ta ji wani ɓangare na zuciyarta ya gargaɗe ta. Ji take kamar ba za ta iya ba, amma haka ta daure, ta cije, ta kuma yi iya bakin ƙoƙarinta wajen haɗa kalmomi ta ce "Barka da wannan lokacin." Shiru ya yi yana nazarinta na tsawon sakanni. Kamar kuma ba shi ba, sai ya janye idanunsa kafin ya ce "Barka dai. Ina za ki je?" Ya ji tambayar da yake tsarawa cikin ransa ta yi masa katsalandan wajen fitowa. Har ta ware idanunta da niyyar kallon sa, sai kuma ta fasa, don ba ta so kallon fuskarsa ya tuna mata da waye shi. Dalili ke nan da ya sanya ta faɗin "Na ga su Hidaya suna hutawa, shi ne na ce bari na tambaye ka ko za a gyara maka ɗaki ne." Ta ƙare maganar ita a karan kanta tana jin wani banbarakwai. Shiru ya yi na tsawon sakanni ba tare da ya ce komai ba. Har ta cire ran zai amsa, ta kuma ji haushin kanta sannan ta jiyo muryarsa can ƙasa ya ce "Yanzu dai ba na buƙata kam." Ya dakata a nan. Bai yi niyyar sake cewa wani abu ba, sai dai ko babu komai ita ɗin mace ce mai muhimmanci a rayuwarsa, bayan haka kulawa ce ta nuna a gare shi, yana da kyau ko ya ya ya nuna ya yaba. Don haka ya ce "Amma idan ina buƙata zan yi miki magana. Kira mini Sultanah ko Hidaya." Ya yi maganar lokaci guda. Cike da takaici da haushi ta juya ba tare da ta ce komai ba. Ya ɗan lumshe idanunsa na tsawon lokaci yana saƙe-saƙe a cikin zuciyarsa. Har bai san lokacin da Sultanah ta ƙaraso cikin ɗakin ba. Sai da ya ji hannunta saman kujerar da yake kai sannan ya ankara. "Yah Tareeq." Ta faɗa tana kallon yadda duk wasu alamomi suka nuna ya dawo daga tunani ne. Ba tare da ya amsa kiran sunansa da ta yi ba ya ce "Kai ni ɗakin Maama." Ya faɗa kai tsaye. Babu musu ta tura shi har zuwa bedroom ɗin Maaman. Daga haka ta juya. Maama ta kalle shi tana faɗin "A'ah, ƙarasowa ka yi kenan." Jinjina kai ya yi kana ya ce "Ehh Maama, wata muhimmiyar magana nake so mu yi." "Toh! Ikon Allah! Me ya faru kai kam? Sanar da ni." Maama ta ƙare tana gyara zamanta. Ya yi shiru yana nazarin ta inda zai fara maganar, duk da yadda duka jikinsa ya yi na'am da abin da ya yanke. Bai san ya daɗe cikin ɗakin ba tare da ya ce komai ba, sai da Maama ta ce "Tareeq!" Ta kira sunansa cike da mamakin yadda ta ga ya faɗa duniyar tunani. Duk da ta ga tarin damuwa a kan fuskarsa, sai dai hakan ba abin mamaki ba ne, duba da abin da ya sake faruwa tsananinsa da Jawahir. A hankali ya ɗan lumshe idanunsa a nutse kana ya buɗe su a kan Maama. Cikin nutsuwa ya soma magana, kamar wanda ba ya so a ji abin da yake faɗa. "Maama.." *♡☆DANEEN☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) Mikiya Writers Ass.. Book 1 Pg 30 "Ina ganin idan har kin amince da abin da zan faɗa, toh na samu mata." Ya ƙare maganar yana kallon ta. Cike da mamaki wanda ya bayyana a kan fuskarta, Maama ke kallon sa. Jin abin take kamar a mafarki. Ya samu mata fa yake faɗi? Ta yaya? A ina? Yaushe hakan ta faru? Anya kuwa ma Tareeq ɗin ne? Duka waɗannan tambayoyin ita kaɗai take yi wa kanta cikin zuciyarta, sai dai har lokacin idanunta na kansa. Bayan wajen shuɗewar sakanni talatin sannan ta ce "Mata kuma Tareeq? A ina? Wace ce ita? Yaushe kuma kuka haɗu har ka ji ta kwanta maka a rai, har za ka iya auren ta? Faɗa mini Tareeq." Ta yi maganar cike da zaƙuwa da jin amsar da za ta fito daga bakinsa. Hannunsa ya kai a hankali ya ɗan murza goshinsa, kafin ya lumshe idanunsa a nutse yana jin wani irin nauyi cikin ƙirjinsa. Ta ɗauka hakan da ya yi yana nuni ne da ya haƙura da yin maganar saboda yadda ya ga tsananin mamaki a kan fuskarta. Sai dai ga mamakinta sai ji ta yi ya ce "Maama idan dai har kin amince, zan auri Daneen, idan ita ma ta amince." Wani irin kallo Maama take bin Tareeq da shi, kallon da lokaci guda ya fassara shi da 'Anya kana da hankali?' Bin sa da kallo Maama ta ci gaba da yi ba tare ta ce komai ba. Cikin zuciyarta addu'a take yi, Allah Ya sa ba ƙwaƙwalwar yaronta ce ta taɓu ba. Daneen fa? Cike da fargabar da ta zo ta yi mata dirar mikiya lokaci guda ta ce "Tareeq." Ta faɗa bayan ta sake kafe shi da idanunta. Saukar da kansa ƙasa ya yi, jikinsa a matuƙar sanyaye. Bai yi tunanin samun cikas tun a wajen Maama ba, shi ya sa ma ya fara yi mata maganar. "Ka san me kake cewa kuwa? Daneen ce matar da kake nufi ka samu? Da gaske kake yi?" Ta faɗa cike da tashin hankali. A nutse ya ɗan sauke ajiyar zuciya, yana jin har cikin ransa daɗin tambayar da Maaman ta yi masa. Ko babu komai zai fayyace mata komai, dalilansa na son auren Daneen ɗin. Ya ɗan ja numfashi kaɗan yana ajiyewa, kafin ya buɗe baki a nutse ya soma faɗin "Maama na yi tunani, na yi tunani har na gaji. A zamanin nan ban san kuma wace mace ce za ta so ni tsakani da Allah ba. Na gwada ta waje, ta ba ni kunya. Kun gwada 'yar'uwa, ita ma ta ba mu kunya. Toh a duk tunanin da na yi, na ga babu wadda ta dace in aura da ta wuce Daneen." Daga haka ya ɗan dakata bayan ya sauke gajeren numfashi a hankali. Ba ya buƙatar jin wani abu daga bakin Maama a kan maganar da ya yi, don haka ya ci gaba da faɗin "Yarinyar nan ta ɗauki ƙodarta ta ba ni, ba tare da sanin waye ni ba. Ba tare da buƙatar komai ba Maama. Ba kya tunanin ta cancanta na aure ta?" "Idan kuma da wata manufar ta bayar fa?" Maama ta yi saurin katse shi da faɗin hakan, tun kafin ya ida sauke maganar. Lumshe idanunsa ya yi a hankali, yana buɗewa lokaci guda. "Ba haka ba ne Maama, hakan ne amma kuma har yanzu ba mu gane ta ba? Ko ma hakan ne ƙoda fa ta ba ni Maama, idan dai har dukiyata take so, ba ma sai ta yi abin da Diyana ta yi ba, wallahi zan iya mallaka mata. Wanda ba na tunanin ma hakan ce a ranta. Idan kuma za ta ƙi ni ne saboda wani abu, ina ganin a yau ɗin nan zan fahimta. Don kuwa idan har kin ba ni dama, toh zan je in same ta ne da maganar a yau ɗin nan. Ina so ranar da su Abeey suka shirya ɗaura aurenmu da Jawahir, a ɗaura a ranar kar a fasa, idan dai kun amince." Ya ja wata ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa cike da gajiya da dogwayen maganar da yake ta yi, wanda za ka iya fahimta ta cikin muryar tasa. "Ko dai da ma tuntuni kana sonta ne?" Maama ta faɗa idanunta a kansa. Ɗan murmushin gefen baki ya yi kafin ya ce "Maama, a jiya na yanke shawarar auren ta, da ba a fasa aure na da Jawahir ba ba zan yi wannan tunanin ba. Hakan na nufin akasin abin da kika faɗa kenan?" Ya ƙare maganar kamar mai neman amsa, sai dai ba amsar yake so ba, don haka ya ɗora da faɗin "Amma dai tabbas na amince zan aure ta, a matsayin mace mafi muhimmanci a rayuwata. Wadda ta sadaukar da wani sashe na jikinta ta ba ni. Sannan kuma ta amince da aure na, duk da yadda 'yar'uwata ta ƙi ni saboda ƙafata." "Idan ta amince ke nan?" Maama ta yi masa wannan tambayar. Sai ya jinjina kai kawai a nutse. Maama ta gyara zaman ta kana ta ce "Ba mu san wace ce ita ba, ba mu san zuciyarta ba. Saboda haka sanar da ni, auren naku na tsawon wane lokaci ne? Abin da kake nufi, za ka aure ta ne har zuwa lokacin da za ka warke ko kuwa me kake nufi?" Cike da mamaki yake kallon Maaman, bai taɓa tunanin waɗannan maganganun daga bakinta ba. Sai yake ganin kamar ba Maamansa ba. Anya kuwa ita ɗin ce? Ya tambayi kansa. Sai dai abin da bai sani ba, tsantsar soyayyar ɗanta ce ke nema ta rufe mata idanu. "Ke nan hakan na nufin in aure ta saboda wata manufa Maama? Idan na yi hakan na yi wa kaina adalci kuwa? Muna tare da Jawahir da Umma tun yarinta, amma ba mu taɓa sanin abin da ke zuciyarsu ba sai yanzun. Kin ga ke nan rashin sanin wace ce Daneen ba komai ba ne. Amma Maama ki faɗi duk abin da kike so na aikata, In Sha Allah ni mai biyayya ne a gare ki." Shiru Maama ta yi na tsawon mintuna ba tare da ta ce komai ba. Bai ma yi tunanin za ta kuma cewa komai ba, sai zuwa can ya ji ta soma faɗin "Shi ke nan Tareeq, ina addu'a a kan duk abin da ya zama alkairi a gare ka ya dawwamar da shi. Abin da ba shi da alkairi ya nesanta mini kai da shi. Duk da ban ji hakan ya kwanta mini ba, amma kuma kai ya kwanta maka, na kuma san ba za ka zauna haka ba tare da neman zaɓin Allah ba. Don haka na amince ɗari bisa ɗari, Allah Ya tabbatar da abin da ya fi alkairi." Lumshe idanunsa ya yi yana jin nauyin da ke ƙirjinsa ya ɗan ragu, ya kai wajen minti ɗaya a hakan, kafin ya buɗe idanunsa a kan Maama. "Na gode sosai Maama, Allah Ya saka da alkairi." Ba ta iya amsawa ba, sai murmushi kawai da ta yi a hankali. ... Da mamaki take kallon Hidayar da ta shigo ɗakin tana faɗin wai Maama na kiran ta. Ta tashi zaune daga kwancen da take, idanunta sun sauya kala kamar wadda ta yi kuka. "Maama na kiran ki." Hidaya ta sake maimaitawa ganin da ta yi kamar ba ta fahimci abin da take faɗa ba. Jinjina kai ta yi tana faɗin "Toh." Daga haka ta miƙe jiki a sanyaye ta bi bayan Hidayan. "Ɗiyata, ki bi Hidaya, Yayanku na jiran ki za ku yi magana." Shi ne abin da Maama ta ce bayan sun je inda take. Da sauri ta ɗaga kai ta kalli Maama cike da mamaki. A kan laɓɓanta ta furta 'Yayanmu?' Har cikin zuciyarta tana jin wani banbarakwai, kuma da gaske wallahi ba ta gane abin da take nufi ba. Ita ma Hidaya da ba ta san dalilin kiran Maaman ba, ya sanya cike da mamaki ta ce "Yah Tareeq?" Ta faɗa bayan ta buɗe manyan idanunta irin na Tareeq. "Shi." Maama ta faɗa tana jinjina kai. Kiran sunansa da Hidaya ta yi, shi ne ya ƙara mata haske a kan maganar Maaman. Nan take duk wani ragowar annurin fuskarta ya ɗauke ɗiff, take ta ji wani irin bugun zuciya. Toh ke nan me ye dalilinsa na son ganin ta? Wace magana za su yi? Ita kwata-kwata ba ta da buƙatar ganin sa, ballantana kuma har wata magana ta haɗa su. "Maza Hidaya ki raka ta." Shi ne abin da Maama ta faɗa da ɗan murmushi a kan fuskarta. Kamar wata saƙaguwa, haka ta soma tafiya, zuciyarta cunkushe da tunanunnuka kala-kala. Gaba ɗaya kuma fuskarta a cunkushe. Dab suke da ƙarasowa inda yake, daga nesa tana iya hangen sa daga kan kujerar da yake kai. Ba ka iya ganin komai na jikinsa sai baƙar kwantacciyar sumar kansa, da ke ta sheƙi. 'Babu yadda za a yi ma ka ƙare rayuwarka da ƙafa, mugu kawai. Allah ne Ya fara nuna maka iyakarka, sakayya ka fara gani tun kafin a je ko'ina. Ka kuma jira hukuncin da alƙali zai yanke maka daga zarar na gama abin da ya kawo ni cikin gidan nan' Abin da take raya wa a cikin zuciyarta ke nan, zuciyarta na mata wani irin zafi. "Yah Tareeq ga ta in ji Maama, bari na koma." Hidaya ta faɗa tana murmushi. Ɗan gajeren murmushi ya maida mata, kana ya jinjina mata hannu, alamar girmamawa. Ta yi dariya kafin ta wuce daga wajen. Ci gaba da tsayawa ta yi a wajen kamar wata saƙaguwa. Ba tare da ta kalle shi ba, don ba ta so ƙoƙarin wanzar da murmushi a kan fuskarta da take ta yi ya gagara. Bayan wajen minti 2, don har ta gaji da tsayuwar, sannan ta jiyo muryarsa a nutse "Ki zauna mana." Runtse idanunta ta yi tana ji kamar ta buɗe baki ta ce 'Ba zan zauna ba' Sai kuma ta cije, ta daure ta ɗaga ƙafafunta da ƙyar ta nemi waje ta zauna. Ajiyar zuciya Tareeq ya sauke yana tunanin ta inda zai fara. Idan ya ce zai fara ne ta gabatar da kansa kamar hakan ɓata lokaci ne, idan ya ce zai gabatar da kansa a matsayin masoyinta, nan ma tabbas ya yi ƙarya. Hakan ne ya sa bayan shuɗewar wasu mintuna sannan ya ce "Daneen." Ya kira sunan da wani irin sauti, da duk da ya saba faɗin sunan ba ta jin ya taɓa faɗa da irin wannan sautin. Dalili ke nan da ya sa ta ɗan shiga ruɗani, kada dai ya gano ta? Kada dai ya gano wace ce ita? Kar dai ya gano dalilin zuwan ta gidan? Wannan ruɗewar da ta yi, ita ce dalilin da ya sanya ta ɗaga raunanan idanunta ta kalle shi, sai dai ko sakan 10 ba ta yi ba ta sauke tana jin yadda zuciyarta ke bugawa, so take kawai ta ji ya ambaci abin da ya sa aka kira ta. Sai da ya ɗan yi shiru, yana tunanin ta inda zai fara, don sai yake jin abin wani banbarakwai, kamar yana shirin aikata saɓo. Amma sai ya fesar da iska daga bakinsa kafin ya soma faɗin "Na san za ki yi mamakin sakawa da na yi aka kira ki. Toh a zahirin gaskiya dai ina ganin babu amfanin kwane-kwane, duk da cewar ke yarinya ce, amma idan aka yi duba da nutsuwarki, hankalinki, hangen nesa da sauransu In Sha Allah hakan ba abin damuwa ne." Ban da bugawa babu abin da zuciyar Daneen ke yi, wannan zagaye-zagayen da yake ta yi babu abin da yake sake jefa zuciyarta sai tsoro. Kamar ya san me take tunani, sai ya ci gaba da faɗin "A taƙaice dai, idan har kin amince na zo da ƙoƙon barar neman auren ki cikin ƙanƙanin lokaci." A razane Daneen ta ɗaga narkakkun idanunta ta zube a kansa, daidai lokacin da shi ma ya ɗaga nasa idanun ya kalle ta. Hakan ya ba wa idanunsu damar sarƙafewa cikin na juna. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunta suka soma sauya kala, duk da yadda idanunta ke cikin nasa, hakan bai sanya ta janyewa ba. Duk kuwa da matuƙar tasiri da kuma kaifin su. Sosai ƙirjinta ke wani irin zafi, zuciyarta na ci gaba da bugawa tamkar za ta faso ƙirjinta. Maimakon ya janye idanunsa sai ya ji yana so ya ci gaba da kallon ƙwayar idanun nata, saboda ya karanci wasu abubuwan daga cikinsu. "Allah Ya kiyaye ni auren mugu, fasiƙi, wanda ba ya tsoron Allah." A zahiri abin da ya kamata ta furta ke nan, sai dai bugun da zuciyarta ke yi, ya tabbatar mata ba ta amince da hakan ba. A karan kanta ma sai take ji idan har muggan kalamai suka fito daga bakinta zuwa Tareeq ɗin, shi ke nan ta kwafsa komai. Komai ya ruguje musu. Toh amma kuma idan ba ta ce hakan ba, me za ta ce? Za ta buɗe baki ne ta ce ta amince da aurensa ko kuwa? Kusan mintuna biyar a haka, kafin ta sauke idanunta bayan sun yi wani irin ja. Shiru Tareeq ya yi na tsawon mintuna yana sake faɗaɗa tunaninsa a kan irin kallon da ya ga Daneen ɗin na yi masa. Sai dai kafin ya ida tunanin, ya tsinto muryarta tana faɗin "Ba zan iya ba. Ni ba kowa ba ce, face wadda ke zaune a cikin gidanku saboda alfarma. Kar ka ce za ka saka mini ba ka ƙoda da na yi ta hanyar aure na. Ba zan iya ba." Ta ƙare maganar tana fashewa da kuka. Duk da ba har zuciyarta take faɗar hakan ba, kawai ta faɗa ne don kare kanta, saboda yadda ta lura da kallon tuhuma ɗin da yake bin ta da shi. Doguwar ajiyar zuciya Tareeq ya sauke mara sauti. Ko babu komai wannan maganganun da ta faɗa sun ruguza wannan karyayyen tunanin nasa da ya fara. "Kar ki yanke hukunci cikin gaggawa. Ki je gaba ɗaya yinin yau ki yi tunani. Abin da nake so da ke kuma, ki cire wannan tunanin na cewar zan aure ki ne saboda in biya ki ƙodarki da kika ba ni. A'ah." Ya faɗa yana girgiza kai. "Har abada ba zan iya biyan ki ba." "Ba zan iya ba." Ta faɗa da ƙarfin gaske, tana jin wata irin wutar ƙiyayyarsa na sake ruruwa a cikin zuciyarta. Wannan wace irin rana ce? Wanda ya zamo silar mutuwar Ameer shi ne yake neman da ta amince ta aure shi? Wane irin sakaci ita kuwa ta yi? Ta yaya ma za ta iya aurensa bayan ta shigo gidan ne da niyyar ɗaukar fansa, ba kuma a kan kowa ba face shi? Ta aure shi ta ce ta auri me ke nan? "Saboda yanzu ba na taka wa a kan ƙafata?" Ya jefa mata tambayar muryarsa a dake. Da sauri ta ɗaga idanunta ta kalle shi. Ya jinjina mata kai bayan ya ɗan saki wani murmushi ya ce "Duk abin da kika yanke ki sanar da ni. Amma ki sani, idan ba ki amince ba, zan ɗauki hakan a matsayin saboda abin da ya sami ƙafata ne. Ko da yake, babu damuwa za ki iya tafiya." Ai tun kafin ya dire maganar ta soma barin wajen cike da sassarfa, haɗa hanya kawai take yi, kamar za ta kifa. A haka dai har ta ƙarasa ɗakinsu. Zubewa ta yi a kan gadon tana fashewa da wani kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Yau ɗin wata irin kewar Ameer ce ta dawo mata sabuwa, sai take ji tamkar yau ne Ameer ɗinta ya tafi ya bar ta. Sai take ji tamkar a yanzu ne suke magana ita da Ameer, maganar tasu da ta zamo ta ƙarshe. Ta cure cikin bargo waje ɗaya tana ci gaba da sheshsheƙar kuka cike da kewar Ameer da Innarsu. Ji take kamar ta watsar da komai ta koma ƙauyensu. Toh amma kuma ba ta da tabbacin idan ta koma ƙauyen ma za ta sami Innarsu, uwa uba kuma idan har ta bar gidan, ke nan hakan na nufin ruhin Ameer ya tafi a banza ke nan? Bayan ga shi tana da damar da za ta iya yin wani abu, wanda har zai kai su ga samun nasara. Wannan dalili, shi ne kaɗai abin da ya sa ta ji zuciyarta ta yi na'am da ci gaba da zaman ta cikin gidan, daga nan sai ta bazama ƙauyensu don biɗar Innarsu. Ta shafe fiye da awa ɗaya a wajen, kafin kamar wadda aka mintsina ta sakko daga kan gadon, kai tsaye toilet ta faɗa, ta rufe shi, sannan ta danna kiran Yohana. Jin tana neman katsewa kafin ya ɗaga ne ya sanya ta faɗin "Ka ɗaga mana, ka ɗaga mana.." Daf da za ta tsinke ɗin kuwa ya ɗaga, ta sauke wata ƙatuwar ajiyar zuciya. "Daneen." Ya ambata kamar yadda ya saba kullum saboda tsaro. "Na'am." Ta ambata da muryarta da ta fara dashewa saboda kukan da ta sha. "Oh my gosh! Me ya faru Cutie?" Ya faɗa cike da mamakin yadda ya ji muryarta ta sauya. Sai da ta ja wata ajiyar zuciyar kafin ba tare da ɓata lokaci ba ta shiga kora masa duk wasu abubuwa da suka faru. "Puhahaha..." Ya sheƙe da wata mahaukaciyar dariya, wadda ta matuƙar ba wa Daneen mamaki, wanda har hakan sai da ya bayyana a kan fuskarta. Ya kai wajen minti ɗaya kafin ya ce hallau dai cikin gurɓatacciyar hausarsa. "Buɗe kunnenki da kyau ki ji. Wannan wata dama ce muka samu. Sanar da shi kin amince da aurensa, da ma ba hanyar shiga ɗakinsa muke nema ba? Idan kika aure shi ai dole ki shiga ɗakinsa, ko ma in ce dole a kai ki ɗakinsa. Kin ga damar da muke so ta samu, a cikin kwana biyu za ki iya samar mana abin da muke buƙata, kin fahimta? Saboda haka kar ki damu, aure ne kawai da za ku yi na kwanaki ƙidayayyu, daga zarar kin samo mana abin da muke nema shi ke nan sai ki nemi takardar saki." Tun da ya fara magana take jin zuciyarta na wani irin harbawa kamar za ta fito daga ƙirjinta. Ita dai haka nan kawai take jin tsoro na shigar ta, duk da kamar yadda ya faɗa ɗin hakan shi ne mafitar su, toh amma ta yaya za ta yi aure ba tare da sanin Innarta ba? "Kuma ko an ce za a je ƙauyenku don sanar da kishiyar kakarku kamar yadda kika faɗa wa Alhaji Dikko, ki san yadda za ki ki hana, saboda kar a kwaɓa mana aiki." Ta jiyo muryar Yohanan kamar ya san abin da take tunani. Ta sake yin shiru na tsawon wasu sakannin kafin ta buɗe baki da ƙyar ta ce "Toh." Daga haka ta katse wayar, ta yi shiru tana sake nazarin abubuwan da ya faɗa. Tabbas idan dai har mafita suke so, toh abin da Yohana ya faɗa shi ne daidai. Sai dai kuma idan ta haƙura da ɗaukar fansar ne. Abin da kuma ba ta ji zuciyarta ta yi na'am da hakan ba. Ran ɗan'uwanta fa, Ran Ameer ɗinta fa. Ta runtse idanunta a hankali zuciyarta a cunkushe, wanda ta rasa dalilin hakan. ... "Sultanah ina yi miki magana kin yi shiru, wai ma ni sa'ar ki ce ne?" Maami ta faɗa a fusace tana kallon ta. Runtse idanunta Sultanah ta yi cikin rashin sanin abin yi, ta rasa me Maamin take nufi da ita. Ruwan da ke gaban ta Maami ta ɗauka ta kai bakinta ko za ta daina jin zafin da take ji cikin zuciyarta. "Maami ba zan iya auren wani idan ba Yah Abdoul ba. Ban taɓa faɗa miki ba ne, amma na daɗe da soyayyar Yah Abdoul danƙare a cikin zuciyata. Kuma maganar da nake miki yanzu ma haka mun yi nisa ni da shi, har ya ce ma nan da lokaci kaɗan zai sanar wa da Abbansa." Wata daƙiƙiyar ƙwarewa da Maami ta yi, ita ce ta sanya Sultanah tana kai ƙarshen maganar da ta ɗauko ta yi shiru. Ta miƙe da sauri tana faɗin "Sannu Maami." Ta faɗa bayan ta zuba ruwa cikin tambulan ta miƙa mata. Hannu Maami ta saka ta karɓa kawai, sai dai maimakon ta sha ruwan sai ta ci gaba da tarin har zuwa lokacin da ya yi sauƙi ba tare da ta sha ruwan ba. Kallon ta kawai Sultanah take yi, tana fata ta kalle ta da idon rahama, ta kalle ta da idon tausayi irin na mahaifiya. "Wanne Abdoul ɗin kike nufi?" Wata irin ajiyar zuciya Sultanah ta sauke, tana jin daɗin tambayar Maamin. Ta yi murmushi kana ta ce "Maami Yah Abdoul fa namu, Yah Abdoul na Yah Tareeq." Ajiye kofin hannunta Maami ta yi, duk wani tashin hankali ya gama bayyana a kan fuskarta. Sai dai cikin dakiya ta ce, duk da yadda harshenta ke ƙoƙarin bijire mata wajen yin maganar, amma haka ta daure, ta cije ta yi iya bakin ƙoƙarinta. "Na riga na zaɓa miki miji Sultanah." Shi ne kawai abin da ta iya faɗa. A take idanun Sultanah suka tara ƙwalla, ban da bugawa babu abin da zuciyarta ke yi. Cikin tashin hankali ta ce "Maami ki yi mini afuwa. Ina son Yah Abdoul, wallahi ina son shi matuƙa, zuciyata za ta iya bugawa idan ban same shi ba. Maami taɓa ki ji yadda zuciyata ke harbawa, ban san halin da zan tsinci kaina ciki ba idan maganar da kike faɗa ta zama gaskiya. Maami Abdoul fa abokin Yah Tareeq, ɗan gidan aminin Abeey, kuma ɗan gidan amiyarki. Ki yi mini wannan alfarmar don girman Allah Maami." Ta ƙare maganar tana fashewa da sabon kuka. Kukan da ke fitowa tun daga ƙasan zuciyarta, wadda ke mata wani irin zafi, zafin da rabon da ta ji shi tun kafin Abdoul ya zo mata da tayin soyayyarsa. Ta daɗe rabon da ta ji shi, har ta fara sabawa da farin ciki, sai ga shi rana ɗaya, Maami na neman tarwatsa mata wannan farin cikin. Don kuwa ta san raba ta da Abdoul babban abu ne, wanda ba ta sani ba ko zuciyarta na da ƙarfin ɗauka. Ganin da ta yi Maami ta yi mata shiru ne ya sanya jikinta ya ƙara yin sanyi. Ta girgiza kanta tana jin yadda lokaci guda ya yi mata wani gingirin. "Maamina ki ce wani abu mana don Allah." Ta faɗa cikin kuka. Sai bayan shuɗewar wasu sakanni masu yawa, sannan Maami ta miƙe, cikin ƙarfin hali ta ce "Gwara ma ki cire ranki, don wallahi ba za ki auri Abdoul ba. Ke kika ce za ki ɗaga mini hankali wallahi sai na tsine miki a banza. Ki kama kanki, idan ba haka ba ran kowa ya ɓaci. Idan na ce kowa ina nufin kowa." Ta dakata a nan sannan ta ci gaba da faɗin "Kuma idan kika sake kika fita daga cikin ɗakin nan za mu haɗu da ke. A nan za ki kwana daga nan har zuwa lokacin da za ki amince da ƙudirina." Daga haka ta bar wajen cike da sassarfa ta shige ɗakinta. Runtse idanunta Sultanah ta yi tana jinginar da kanta a kan kujera, yau kam wace irin baƙar rana ce a gare ta? Me Maami take faɗa haka? Shin da gaske abin da yake faruwa gaskiya ne, ko kuwa wani mummunan mafarki ne take yi, wanda ke neman datse mata farin ciki? Sai a lokacin sannan ta iya fashe wa da wani marayan kuka, ta cure waje ɗaya tana kifa kanta a tsakiyar gwuiwoyinta, ta shiga raira shi, cikin rashin sanin abin yi. ... Jinjina kai Dada ji take yi cike da mamakin wannan al'amari na Ubangiji, wato ba ta taɓa kawo wa har cikin ranta Tareeq ɗin zai yi wannan tunanin mai matuƙar amfani ba. Sai ga shi da kansa ya samar wa kansa mafita. "Wato ina ga na fi kowa farin ciki da wannan abu ya faru, Ubangiji Allah Ya tabbatar da alkhairi, Ya yi muku albarka. Alhassan." Ta ƙare maganar tana kallon Abeey. Cikin girmamawa Abeey ya ce "Na'am Dada ji." "Ina ganin a gobe goben nan, ba sai wata rana ba, a ɗaura auren nan kowa ma ya huta." Cikin na'am da zancen Dada ji Abeey ya ce "In Sha Allah Dada, duk yadda kika faɗa haka za a yi." Ya faɗa har cikin muryarsa za ka iya fahimtar yana cikin farin ciki. Don kuwa tabbas ya yi farin cikin matuƙa. "Amma ina so da kaina na ji daga bakin yarinyar, kafin nan sai na san abin yi." Jinjina kai Dada ji ta yi kafin ta ce "Gaskiya ne wannan, hakan na da kyau." Wayarsa Abeey ya ɗauka ya kira number Hidaya. "Turo mini Daneen yanzu." Kasancewar ta san inda suke ya sanya ta amsa wa da "Toh Abeey." Daga haka ta miƙe ta je ta kira Daneen ɗin, a ranta tana fatan Allah Ya sa abin da take tunani ne yake shirin kasancewa. Har ƙofar ɗakin Abeey ta raka ta, tana shirin juyawa Daneen ta yi saurin riƙo hannunta tana faɗin "Hidaya." "Na'am." Hidaya ta amsa bayan ta kalle ta. Narkar da fuska ta yi, kamar wadda ke shirin yin kuka ta ce "Tsoro nake ji, ba zan iya shiga ni kaɗai ba." Hannunta Hidaya ta kama tana murmushi "Toh mu je in raka ki." Ajiyar zuciya Daneen ta sauke, kana ta bi bayanta suka shige ɗakin Abeeyn. Sai da suka gaisar da kowa, sannan wajen ya ɗauki shiru na tsawon mintuna. Zuwa can Abeey ya soma faɗin "Ɗiyata Daneen, shin kin amince da auren Tareeq kamar yadda ya sanar da ni?" Runtse idanunta Daneen ta yi na tsawon sakanni, kafin tun kafin ta kwafsa, kawai sai ta ɗaga kanta a sanyaye. "Ma Sha Allah! Alhamdulillah." Dada ji ta faɗa cikin wani irin farin ciki. Shi ma ajiyar zuciya Tareeq ya sauke, yana ji bayan wani lokaci yau ga wata mace ta amince da aurensa, ba don dukiyarsa ba, ba da niyyar mallake masa dukiya ba, ba kuma don ƙirar jikinsa ba, ba kuma don tana son shi ba. Sai kawai don kimarsa da darajarsa a wajenta. Lallai kuwa Daneen ɗin za ta ci gaba da kasancewa mai daraja da kuma ƙima a wajensa. Bayan wajen shuɗewar mintuna goma Abeey ya ce "Zan ɗauke ki mu je ƙauyenku saboda sanar da mariƙiyarki batun aurenki da za a gabatar a gobe." Tun kafin ya ƙarasa maganar ta ji zuciyarta ta buga. Don haka yana ida wa ta fara faɗin bayan ta ɗaga kanta karo na farko ta kalli Abeeyn. Sai a lokacin ne ma sannan ta fahimci Hidaya ba ta cikin ɗakin. "A'ah kar ka je don Allah. Za ta iya yin duk wani abu don kar a yi auren nan. Ka yi haƙuri kar ka je." Ta faɗa har lokacin tana girgiza kai ƙirjinta na ci gaba da bugawa. Cike da tausayawa Tareeq ke kallon Daneen, lallai tabbas rayuwar yarinyar nan akwai tarin ƙalubale a cikinta. Gaba ɗaya 'yan ɗakin ma da kallon tausayin suke bin ta da shi. Abeey ya sauke ajiyar zuciya tausayin yarinyar na sake kashe masa jiki. "Kar ki damu, kar kuma ki yi kuka. A yanzu ɗin nan mu ne iyayenki In Sha Allah. Ba ma za ta ji labarin ba ballantana ta hana." "Alhassan kamar yadda ta faɗa ɗin a bari idan babu damuwa. Idan komai ya lafa shi Tareeq da kansa sai ya ɗauke ta ya kai ta can ƙauyen nasu wajen kishiyar kakar tasu." Dada ji ta faɗa. Jinjina kai Abeey ya yi kana ya ce "Abin da nake nufi ke nan ni ma Dada." Ya dakata a nan kafin ya maida duban sa kan Maama ya ci gaba da faɗin "Saboda haka ku fara shirye-shiryen duk wasu abubuwa da suka dace, In Sha Allah gobe ne ɗaurin auren. Duk wasu abu da ake buƙata a yi su daga baya." ... Tsaki ya ja a karon farko yana kallon mai kiran nasa. Kamar kar ya ɗaga, sai kuma ya tamke fuskarsa, yana shirin ɗagawa kiran 4ps ya shigo wayar. Sai ya sauke ajiyar zuciya, duk da ya san shi ma ɗin ba lallai ne su kwashe ta da daɗi ba. Kara wayar ya yi a kunnensa bayan ya ɗaga, daga can ɓangaren Pops ya ce "Yohana." "Yes, Pops." "Kana ina?" Pops ɗin ya faɗa, cikin muryarsa babu alamun wasa. "Me ya faru?" Ya katse shi da tambayar hakan. "Ka zo ka ɗauke ajiyar ka." "Amma Pops.." "Na dai faɗa maka, barin garin ma za mu yi gaba ɗaya. Idan kuma ba ka yi hakan ba za ka ga ba daidai ba." Numfashi ya sauke yana jin ransa na ɓaci, be ce komai ba ya datse kiran yana jan tsaki. Har wani huci yake fitarwa saboda tsabar ɓacin rai. Wato Babansa na son ya kwaɓa masa aiki. Ya dafe goshinsa yana tunanin ta ina zai fara? ... Tun ɗazu yake ganin wayar tana kawo haske babu ƙaƙƙautawa. Alamar kira ne ke ta shigowa. Don haka ya ɗan ja gajeren tsaki, kafin ya janyo wayar. Ganin sabuwar number ce ya sanya shi jefar da wayar ya kwantar da kansa kan bangon gadon idanunsa a lumshe. Zuwa can sai ya ji alamar shigowar saƙo, ya ɗan gyara zamansa kana ya janyo wayar ya buɗe saƙon, cikin zuciyarsa yana mamakin yadda ya ji ya zaƙu da son karanta labarin tun da ya ji alamar shigowar saƙo. "Shege, wai har ni za ka nuna wa ba ka gane waye ni ba? Duk iya shegen nan fa mu ma mun iya shi, ka fi kowa sanin hakan. Shi ya sa na yi yadda zan yi na nemo number ɗinka, na kikkira kuma ka ƙi ɗagawa. Dalili kawai nake so na ji na abin da ka aikata. Amma dai kar ka manta duk iya shegen nan ni ma na iya fa, musamman ma kuma yanzu da na ƙaro wani." Ya karanta message ɗin ya kai sau biyar, kamar wanda ke shirin haddace duk wani rubutu, da kuma wasalin da aka yi amfani da su wajen rubuto saƙon. Ya yi shiru yana jin yadda zuciyarsa ke ɗan bugawa, wanda hakan ya tilasta masa lumshe idanunsa. A hankali ya sake kwantar da kansa jikin bangon gadon, yana jin yadda saƙon ke ci gaba da yi masa amsa-kuwwa cikin kunnuwansa, tamkar wanda ake sake karantowa. Ba ya fatan abin da yake tunani ya tabbata. Ya fi awa ɗaya a hakan, yana ci gaba da saƙawa da warwarewa, zuciyarsa tamkar za ta yi bindiga. 'Ko kuwa dai batun aurensa ne ya zagaya har inda ba su yi tunani ba, wanda hakan ka iya janyo tabbatuwar tunaninsa?' Ya tambayi kansa, duk da ya san babu mai ba shi wannan amsar. ... Washe-gari ta kasance ranar Juma'a, wato ranar da za a ɗaura aure. Bayan an yi Sallahr Azahar, a babban masallacin Dikko da ke cikin unguwarsu, Abeey da ya zama waliyyin amarya, ya karɓi sadakinta a hannun Alhaji Abubakar (Mahaifin Abdoul) wanda shi kuma ya zamo waliyyin ango. Cikin ƙanƙanin lokaci dubban mutane suka shaida ɗaurin auren DANEEN da kuma angonta TAREEQ ALHASSAN DIKKO. Ɗaurin auren da duk da ba a wani shirya masa ba, amma manyan mutane da dama sun samu halartar ɗaurin auren. Kafin ka ce mene ne wannan, tuni maroƙa sun fara shela, ta hanyar faɗin "Allah Ya nufa. Tabbas Allah Ya nufa. Aure ne irin na girma, an ɗaura auren Shalele, ɗa ga Alhaji Dikko, Tareeq, tare da amayarsa Daneen. Alƙawarin Allah Ya cika." Maganganun da suka tilasta shi runtse idanunsa ke nan, wani babban al'amari da bai yi tsammani ba, shi ne bugun zuciyar da ya ji ya ziyarce shi. A nutse ya buɗe bakinsa, a kan laɓɓansa ya shiga furta. "Ya Hayyu Ya Qayyum." Alhamdulillah! A nan na kawo ƙarshen littafin DANEEN Book 1. Mai son ci gaba da karanta DANEEN Book 2 har zuwa Book 3, zai tura ₦500 ne ta.. 8124818273 Zahra'u Yusuf Ishaq Opay Shaidar biya ta wannan number 08124818273 Ko kuma kai tsaye a tuntuɓe ni ta 08124818273.