[10/10, 2:55 PM] 💘: DAMUWATA. (Sanin abin adona) By Mrsjmoon *EXQUISITE WRITER'S FORUM ( EWF).* Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai. Allahumma salli ala sayyidina Muhammadu wa ala alihi  ada-da mafi ilmi salatin da'imatan bi du'a'un Janna. S.A.W. *Sharhi.* Labarin (DAMUWATA) hak'k'ina ne ban yarda a juyamin shi ta wani siga ba ko yimin iko da shi ta hanyar had'a document ko makamancin haka sannan ba kyauta ba ne amma da pages masu zuwa domin farin cikinku masoya. Allah ya sa mu amfana da darasoshin da ke cikinsa na khairan, muyi watsi da kishiyar shi Allahumma amin. *Jimlar littafan marubuciyar:* Free books. Mabrukha Ra'ayi Rayuwar Bahijja. A tunanina Ruwan dare. Paid books. Bak'on lamari Rashin jituwa Banyi zato ba Rabi'atul Addawiyya Rumasa'u Mutunci Madara ne Doctor Laylah. *Baki d'aya shafin sadaukarwa ne ga Aunty Maijidda Musa (Aunty Jidda) Allah ya albarkaci rayuwarta tare da zuri'arta biy jahiy Nabiy S A.W.* Page 01. Cikin talatainin dare wanda masu iya magana kan kirasa da suna mahutar bawa. Ni kam a gareni kiran shi na yi da lokacin gadin kaina domin zaune na ke a gefen katifana ba komi ke damuna ba sai barci wanda yake d'ibana ina korarsa da k'arfi da yaji domin bazanyi sakaci ya d'auke ni ba ya zamo rayuwata ta shiga garari. Abinda na kasa fahimta a rud'ad'd'en lamarin shi ne saceni ake sonyi ko kuwa b'atamin rayuwa. 'Sai dai b'ata miki rayuwa domin alamu sun nuna hakan.' Sosa gefen wuyana na yi cikin aminta da amsan da zuciyata ta bani. "Oh ni Deejah me ke shirin faruwa da ni ne? Waye wannan mutumin dake son dasamin bak'in tabbo mara b'acewa a jiki da ruhi? Ya Allah ga baiwarka Nana Khadijatu ka dubeni duban da batasan ya yake ba sai kai da ka halicceni, d'aukinka ya zamo jagoran yayewar duhun nan da na ke ciki." Ruwan dake d'iga a bayan hannayena ya ankarad da ni kuka na ke yi mara sauti. " Hak'ik'a DAMUWATA na dabanne da sauran mutane. Shin wai ahaka zan cigaba da rayuwa ban samun barci?" Amsan da ban samoshi ba kenan tun soma fuskantan barazanar shigomin d'aki cikin dare har zuwa yanzu da na ke mai-maita shi. Sake sosa wuyana na yi cike da tausayin kaina. "A kwanaki biyun nan har na rame, samun barci alamun natsuwa ne dan haka rashinsa dole ya sakawa mutum ciwo, ya Rabbi ka bayyanamin abinda ke cikin duhun nan batare da hankalin Mamana ya tashi ba." Motsin da na jiyo a bakin k'ofa yasa na zabura na koma bayan k'ofar na manne, jikina na mazari cikin bugawar k'irji, ina jin ana kici kicin bud'e k'ofar, ba jimawa akayi nasarar  bud'ewa tare da turota a hankali, na d'auke numfashi ina kallon inuwar mugun sadda ya doshi saman katifana a cikin d'an hasken da ya shigo d'akin ta glob din waje, sam ban tsaya tantance ko waye ba  duk da burina kenan gano shed'anin da ke lalibeni idan ina barci wanda na ke kwatar kaina da k'yar. Ganin ya dage da neman inda na ke sai na silale cikin sand'a na fice daga d'akin zuwa mafakana wato d'akin tumakan Mama, wurin dana gyara tun da yamma dan b'oyewa saboda shigana makewayi ya sakani jin tsoro. Na tsuguna a cikin dabbobi jikina na cigaba da rawa, damuwa ya kuma lullub'eni, sai lokacin naji dama na tsaya na kunna wutan d'akin naga fuskan mugun. "A sannu zan gano ko waye insha Allah." Na furta cikin matse gefen wuyana cikin nauyin idanu alamun kwanciya kawai na ke muradi. 'Deejah zurfin ciki banaki ba ne ki sanarwa Mama kada ya sami nasara akanki ya kaiki ya baro, ki jefa Mamanki cikin damuwa da ke kanki.' "A'a ba zan iya wannan zancen da Mama ba, ina jin nauyin furta shi ga wanima balle Mamana." 'Zurfin ciki nan sam baiyi ba Deejah.' "Na san da haka amma to ya zanyi?" 'Ki koreshi domin samun 'yancin furta matsalarki gudun cutuwa.' Jinjina kai na yi domin na amince da wannan shawarar da zuciyata ta bani. Na jima tsugune zuwan na ji wani abu mai sanyi na bin k'afana ya sa na mik'e, na kuma jin ya nad'emin dika k'afafun, aikam na daka uban tsalle na fad'a cikin tumakai, atake suka soma ihu sabida na firgitasu, bashiri nayo waje a guje na shige makewayi ina haki, muryan Mama da Baba na jiyo suna salati na fito da gudu a rud'e na rungume Mama ina mai danne kukana kada ya baiyana ta ritsani da tambayoyin dalilin yinsa alhali bani da amsa, sai na matse bakina da hannu d'aya ina lek'en abinda sukagani suke yiwa salati. Maciji ne k'ato ya nad'e k'aramar tunkiya zare idanu na yi jikina na kuma d'aukan rawa ganin tunkiyar a wurin dana tsugunna d'azun ta ke kwance. 'Wato shi ne abinda d'azun ya nad'emin k'afafu?' Tuno hakan ya sa na kwalla ihu ina tsalle tamkar macijin ne yazo ya sake nad'eni, a rud'e Mama ta kamani ta soma tofamin addu'a. Tsaki Baba ya ja yasoma fad'a. "Ga Tunkiyanki nan cikin hatsari kin biyewa wannan sokuwan da batasan komi ba sai janyo miki asara." "Uwata tafi min dik abinda na mallaka Malam dan haka bai dace ka had'ata da dabba ba domin darajar bil'adam mai girma ne sama da dukkan halittun duniya sannan Uwata kam bazata tab'a janyomin asara ba sai alkhairi, nasha sanar da kai wannan zancen amma ka kasa daina jinginamin ita da kalman k'an-k'anci." Wani tsakin ya kuma ja tare da cewa "Ai sai ta korar miki macijin in gani tunda tafi ni amfani da daraja." "Ni da kaina zan koreshi Malam domin lafiyar Uwata yafi nawa muhinmanci a yanzu kuma ni bance tafika amfani ba, dan Allah ka rika fahimtana." "Ai sai kiyi tunda d'iyar t... "A kul! Malam ka tsaya daganan kada ka furta abinda zai zamo sanadin rabuwarmu, da fatan ka tuna me na ke nufi?" "Ke! Hurera kifita idanuna in rufe wallahi akan wannan yarinyar mai bak'i jini zan ci miki mutunci matuk'a." Ina gani Mama zata sake magana na kulle mata baki ta kalleni na girgiza mata kai. Shiru ta yi ranta amugun b'ace, Baba ya buga babban rigarsa a fusace ya koma d'aki. Da kallo Mama ta raka shi zuwa can ta janye jikinta zuwa cikin dak'in tumakan, na biyo bayanta cikin rik'o hannunta ina cewa "Dawo Mama kada ya illamin ke na shiga uku na lalace." "Insha Allah bake ba shiga uku Uwata balle lalacewa indai ina numfashi " "Mama to ki... Maganar ta mak'alemin ganin babu macijin ba sanmatarshi sai tunkiyan kwance ta mik'e bisa alamu ta mutu. "Muje ki kwanta zuwa gobe mai cire maciji zaizo a fidda shi a inda ya b'oye." "Mama ina ya je?" "Ai dama ba zai tsaya ba tunda yaji motsin mutane." "Mama kada yazo ya cutar damu muna barci." "Wanda ya dogara ga Allah to Allah zai bashi kariya batare da saninsa ba, ki dage da mik'a lamuranki gare shi domin shi mai amsa buk'atun bayi ne." Motsa kai nayi alamun gamsuwa da zancen. Har d'akina ta kawoni wanda ta kunna fitillar dana kashe ina ganin zata fita na rik'ota bance komi ba kaina sunkuye motsa kai ta yi cikin fitar murmushi ta je ta kulle k'ofa tare da zubawa wurin da aka jijjije da k'arfi ido." "Waye gwanin lalata miki k'ofa Uwata?" "Nima ban sani ba Mama." Na ambata cikin rawar murya. "Uwata sanarmin da damuwanki." "Lafiyalau na ke Mama." "Ban yarda ba maza sanarmin kinsan ina jin dirin Damuwarki a k'irjina ko da baki furtamin ba wanda na tabbata kwanaki biyu nan duk kinyisu cikin damuwa ce musanman cikin dare kamar bakya samun ishashshen barci dubi da yarda kike tashi amakare kuma idanu kumbure." "Kiyimin addu'a kawai Mama wata k'ila wasi-wasin shed'an ne ke hasko miki ina cikin damuwa." 'Uwata na san zurfin cikin ki dan Allah ki sanarmin da abinda ke damunki inyi maganinsa tun bai girma ba." "Mama ki amince ina cikin walwalata ba abinda ke damuna." "To Allah ya sa hakan ne dan nasan zurfin cikinki yafi k'arfinki Uwata, abinda na ke nusar da ke aitaka  hakan ba abu mai kyau ba, dan Allah ki gyara kada wata rana ya cutarmin da lafiyarki." Bance komi ba illa na kuma narkewa a kafad'arta ina lumshe ido alamun jin barci. "Ina jin b'arayi sun soma harin gidan nan dan ko jiya najiyo motsi kamar ana gudu ko da na fito sai na samu Malam na dubawa, wata k'ila waken suyar da na yi cikonsa sukeyiwa fako." "Allah ba zai basu sa'ar d'aukan komi ba." "To Allah ya sa hakan." "Amin." "Mama kada ki tafi tsoro nakeji." Na furta da sauri ganin ta janye jikinta daga nawa. "Ba zan tafi ba Uwata mu kwanta a nan, Allah ya tsaremu da mugun ji da gani." "Amin Mamana." Na amsa cikin k'an-k'ameta domin a zahiri tsoron maciji ya danne bargaban da na ke ciki na azzalimin da ke kawomin hari a cikin gidanmu ba tsoron Allah. Washe gari bayan na kammala tilawar karatun qur'ani kamar yarda na saba na fito na isa k'ofar Mama dan gaisar da ita domin tunda subahi ta koma d'akinta, sai dai kafin inyi sallama najiyo maganar Baba cikin d'aga harshe. "Wallahi Hurera duk ranar da kika kuma zuwa d'akin Uwani kika kwana sai na sab'a miki kuma in had'aki da mai sakamako wato Allah." Banjiyo me Mama ta ce ba sabida muryanta ya yi k'asa. "Na dai sanar miki in har ina gidan nan ban yafe ba kika kuma kwana da baliga alhalin ga mijinki na buk'atarki dan kuyi aikin lada amma sabida rashin hankali kikayi watsi da shi kika manne a jikin 'yar... Ban tsaya jiyo k'arshen kalaman Baba ba na bar k'ofar jikina na rawa domin na san k'arshen kalman yafi duk kan kalamansa muni. D'akina na koma na tura k'ofar da ta kusa fad'i k'asa na zauna gefen katifa cike da damuwa hawaye na bin kumatuna. 'Anya Baba shi yayi sanadin kawoni duniya kuwa? Ko dai da gaske ne da Maman su Khamila ke ambatamin 'yar karere? kai ban amince ba kawai salon kishinta ne na fitina ke kaita da yin kalamin wanda ko su Maman Anas bata bari ba.' "Uwani!." Najiyo sautin kiran da Baba ya kwallamin da k'arfi, ban samu amsawa ba ya kuma kwad'amin wani kiran da yafi na farkon k'ara, da sauri na fito ina hard'ewa. "Dan Uwarki ki amsamin kinfi k'arfi?" "Kayi hak'uri Baba." "Dalla rufemin baki sokuwa kawai wacce bak'in jini ya k'are akanta ba mashin-shini, ai wallahi sai kin tsufa a gaban Uwarki ba aure tunda ta zab'i b'atamin rai a kanki." Wani kuka ne ya zomin domin na tsani a hantareni, dik da na nasaba da hantarar Baba hakan baisa ya zamemin jiki ba dan kullum ya tozaratani sai na zubda jirwaye. "Au ban ci Ubanki ba kikemin kuka sabida Hurera ta gama sangartaki?" Matsawa gefa na yi  da sauri saboda nasan yanzu zai iya kawomin duka. "Tashi ki wanke wake alale nakeson karyawa da shi yau saura kuma ki tsaya sanyin jikin nan da kika kwaso a can duniya dan Hurera kam ita macece mai zafin jini." Tashi na yi ina cigaba da kuka mara sauti. "Uhm ko da ya ke meye gamin kifi da kaska da za... "Ya isheka haka nan Malam, maza tafi Uwata kije ki kwanta dan ina jiyowa a jikina barcin nan bai isheki ba." "Mama aiki zanyi in na gama sai in kwanta " "Na ce ki tafi zanyi masa dik abinda ya keso domin samun ladar aure." Ban sa ke magana ba na bar wurin amma ba d'aki na koma ba kamar yarda Mama ta umurceni, wake na tafi na d'ebo na jik'a na d'auka na koma can wurin rijiya sabida bana son jin zancen da su Mama zasuyi wanda bana dad'i ba ne kuma nasan duk a kaina ne. "Wallahi bana son wannan takun sak'ar da sukeyi sabida ni, anya zan gama lafiya kuwa idan har ban kawo k'arshen samun sab'anin mahaifana a kaina ba? Tabbas dole na san abinyi dan kawo k'arshen rashin jituwarsu ta sanadina." Ina wanke waken sai sabbatu na ke yi cikin muryan kuka domin ta wannan haryar nafi jin dad'in amayar da dukkan DAMUWATA. **** Malam na sha gayamaka bana son abinda kakeyiwa Uwata, raina na b'aci ainun, wallahi duk in ka tozarta Uwata ji na ke tamkar ni kake tozartawa afakaice saboda baka tashi zaginta sai in munsami sab'ani." "Au Allah." "Eh, ina jin zafin abin matuk'a." "To yanzu kika fara ji kuwa." "Malam kenan, wallahi Allah kaji rantsuwar d'an musulmi, inda ace igiyar aure nan a hannuna ya ke na rantse da girman Allah da tuni na sallameka na huta da ganin tashin hankalin Uwata ta dalilinka." "Duk sabida na tab'a Uwani kike yimin wannan kalaman Hurera? Shin ke da Uwani ina ce duka mallakina ne? "Naka ne amma sai ka gyara mu'amalanka da ita sannan zan amince da kalamanka." "Ya yi kyau Hurera, zan d'au mataki na k'arshe in Allah yaso." "Malam tafi ka cigaba da laziminka kafin ka fito na tabbata Uwata ta gama alalen." Mama ta sauya zancen domin tasan nacin mijinta, sam bai gajiya da ririta zance. Shi kam jifarta kawai ya ke yi da mugun kallo ba tare da ya sake yin magana ba. Aikam kafin ya furta kalma ta bar masa wurin zuwa d'akin tumakanta ta janyo wacce maciji ya halaka daren jiya ta fito da ita waje ta koma d'akinta ba jima tafito rik'e da mayafi ta dubi Baba da ke tsaye har lokacin na harare-harare ta ce "Zan lek'a gidan Malam Habu mai macizai dan yazo ya ciremana kada ya dawo daga baya ya illatamu." Bai tanka ba itama bata jira amsawarsa ba ta fice, tana shigewa zaure ya gyad'a kai cikin jan k'wata ya shige d'aki a fusace. *** Kafin k'arfe Takwas da rabi na kammala dafa Alalen itama Mama ta gama dama kunun tsamiya tana soya fanke saboda Bata cin Alale dan yana b'ata mata ciki. Muna gama karyawa Malam Habu ya iso cikin mintoci goma da shigowarsa ya kama macijin kato da shi, duk tsoro ya maga cikani dan yinin ranar manne da Mama na yi domin Baba ya koma d'ayan gidansa sai na sami sakewa na yi ta zuba mata shagwaba tamkar k'aramar yarinya, ita kuwa ta yi ta biyemin tare da bani labarai masu saka nishad'i. Ni da Mamana aminan juna ne DAMUWATA na ta ne haka nima damuwarta nawa ce. A ranar Mama ta sanya aka cire k'ofar d'akina da aka karya aka sanja wani mai k'arfi tare da inganci sannan ta sanya aka soma ginamin k'amin bayi na wanka ta waje wanda za'a shigo da shi cikin d'akina. Da yake ta saki kud'i kafin yamma angama ginin floor da sauran gyaran bayi ya rage wanda suka ce washe gari zasuzo su k'arasa. Washe suka dawo suka kammla komi bayina k'arami mai kyau dan har da tayis aka sakamin a k'asa da jikin bango tare da yimin cabinet na ajiye kayan wanka. Iya farin ciki nayisa, k'awata Fanta na ta tsalle tare da janyoni wai sai na taka rawa ni kuma ban iya rawa ba sam, Mama na gefe sai dariya ta ke yi mana ganin yarda Fanta ta dage tana ta kwasan rawa wai Mama ta maidani yar gayu, kuma Abin k'arin farin ciki har aka gama aikin nan Baba bai lek'o mu ba, faruwar hakan yafi komi farantamin rai sama da ginin bayin, rashin sanya Babana a ido yafimin kwanciyar hankali da samun natsuwar ruhi dan ko Mama na fahimci tafi sakewa idan bai ziyarcemu ba. Sanjamin k'ofa ya bani damar samun barci cikin natsuwa batare da fargaban komi ba, damuwata ya zamo tarihi indai akan gadin kaina ne yayin da d'aukakin bil'adam ke samun hutu wato cikin dare. Sannan na lura Mama ta sanya ido a game da shiga da fitar masu kawo mana ziyara musanman 'yan samarin unguwarmu masu shigowa siyan Zob'o da kunun Aya wanda ta ke yinsa duk ranakun Litini da Labara dan takance jiki da jini Uwata dole mu huta tunda Allah ya bamu rufin asiri dai-dai misali. Duk in ta ambaci haka na kanyi murmushi. Hak'ik'a Mama jarumar uwa ce mai kula da kiyon da Allah ya bata akan 'ya'yansu, shi yasa alfaharina da ita ba mai musaltuwa ba ne, abinda na sani dai ina k'aunar farin cikinta matuk'ar k'auna. Bayan sati biyu. Sai murmushi na ke dokawa Mama na gefena tana dura kunun Aya a robobi. Ina lura da kallon da ta ke saukemin na son jin abinda ke sanyani murmushi amma dai bata tofa ba, sai lamarin ya k'ara sakani nishad'i na yi ta doka murmushina tare da motsa kai lokaci zuwa lokaci tamkar mai sauraren wak'a. Ba komi ne ya sanyani farin ciki nan ba sai ganin mun sami sati biyu cif Baba bai zo gidanmu ba wanda muka sami labarin wai ya yi tafiya zuwa maiduguri ta'aziyyar Malaminsa da ya rasu ta bakin babban yayanmu Auwalu. 'Allah yasa ya yi wata biyuma a can mu huta da sababinsa.' Na ambata cikin raina ina mai cigaba da murza Fulawa wanda zanyi meetpie sabida bikin yayen Haddar alqur'anin aminiyata Fanta da za'a yi ranar Asabar. "Uwata ko na samu suriki ne?" Da sauri na kalli Mama ta motsa kai cikin murmushi tare da cewa "Ina burin jin wani yazo sallama da Uwata, ko nima na jiyo k'amshin samun jika na yi ta masu tawai." Samun kaina na yi da rashin jin dad'i, sai na maida kaina k'asa hawaye na taruwamin domin abu kad'an ke sakani kuka. "Uwata ka da ki damu komi lokaci ne, wata rana sai labari, wasa na ke yi miki amma ina son sanin abinda kike nazartawa da ya sakaki nishad'i." Numfashi na sauke cikin rawar murya na soma maganar abinda ke cin raina kullum. "Mama na soma tsorata da lamarin, yanzufa shekaruna ashirin da hud'u zan shiga da biyar watan gobe amma ko da wasa wani namiji bai tab'a cewa yana sona ba hatta da k'awaye in aka cire Fanta ba wacce ke k'awance da ni, hakik'a zuwa yanzu na'amince maganar Baba gaskiya ne ni d'in mai bak'in jini ce na k'arshe." "Kul! Uwata kada ki sake ambatar haka in baso kike kiyiwa Allah butulci ba, komi ya faru da bawa cikin k'addararsa ne, bawa bai isa ya tsarawa kansa rayuwa ba fa ce wanda da ya haliccesa wanda baya kuskure cikin mulkinsa, jalala da buwayarsa masu fad'i ne wanda sanin hak'ik'aninsu sai shi kad'ai dan haka bai manta da ke ba yana sane da ke in lokacin zuwar mijinki ya yi zaki had'u da abokin rayuwarki batare da zatonmu ba." "Haka ne Mama amma fa ki duba ki gani Khamila k'anwan bayata ce sosai dan kince na bata shekaru bakwai amma gashi saura watanni bikinta ni kuwa ko wanda zaice ina son ki Kha... Sai kuma na kasa k'arasawa sabida ni d'in mai yawan jin kunya ce. "Ina Uwata ta ke?" "Gani Mamana." "Maza bani hankalinki." "To." "Ina son ki nemi zab'in Allah sai kiga Allah ya kawo miki miji d'aya tamkar da dubu ba yawan damuwa ba domin ba zai k'areki da komi ba sai shiga matsala sannan miji irin na Khamila wake burin d'iyarsa ta auri irinsa? Wanda kowa ya shaida baida halin kirki yawo da wuk'a yakeyi, me za'ayi da makashin mutane da tare hanya ya kwace musu hak'k'insu, insha Allah mijinki sai yazamo alfaharin dangi gabas da yamma kudi da arewa, wanna shi ne addu'ar da na ke yi miki duk in na kai goshina k'asa." "Ba Amin ba!, har abada ita da samun mijin da kikeyi mata fata wannan a rubuce yake." A razane muka kalli k'ofar shigowa, bakin Mama na rawa ta ce "Malam!" "Na'am Hurera." "Shin kai wani irin Uba ne?" "Uba kuma?" Mik'ewa Mama ta yi ta shige d'akinta da sauri batare da ta amsa masa ba, rufa mata baya ya yi yana gyara babban rigarsa cike da fitina. Gabana ne ya fad'i na dafe kaina da ke barazanar rabewa biyu domin yin ido biyu da Baba ya d'aukemin farin cikin da na wayi gari da shi, cikin k'arfin hali na k'arasa mulmula meetpie d'in na tashi zuwa d'akina ina hard'ewa amma jiyo muryan Mama cikin kuka yasa na dakata a bakin k'ofarta, samun kaina nayi da yi musu lab'e abinda ya zamo bak'on lamari daga cikin halayyana. *Ya kukaji Fans? Shin Labarin zai kayatar da ku kuwa?* *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a (domin k'an-k'aro martaban aure.) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/11, 11:39 AM] 💘: DAMUWANA (Sanin abin adona) By Mrsjmoon. EWF. *Shafin sadaukarwa ne ga Zarah d'ansauka (Mom Jasrah) Allah ya yiwa rayuwa albarka.* Page 02. "Malam ya isheka! Wallahi Allah kana daf da kaini bango wanda zan ajiye komi a gefe na kwatarmana 'yancinmu dan haka ka bari kawai cikin girma da arziki ko in shayar da kai ruwan mamaki, Uwata tawa ce ni kad'ai, eh na amince hakan sai ka barmin d'iya ta shak'i iskan 'yanci kamar ko wani yaro tunda ka nesanta kanka da ita." Dafa bago na yi idanu waje domin jin yarda Mama ke magana ya jefani cikin rud'ani. "Kingama d'iban albarka naki?" Na jiyo Baba ya furta a hankali wanda na shiga cikin mamakin jin  muryan nasa cikin sanyi tamkar banasa ba, domin zan iya cewa tunda na taso ban tab'a jin maganarsa a hankali irin wannan ba. "Da saurana" Mama ta ambata muryanta na rawa alamun ta soma kuka. Dafe goshina na yi cike da damuwa domin wata rana bana jin dad'in yarda Mama ke amsawa Baba zantuka kai tsaye ba ladabi irin na Mata zuwa ga Mijinta. "Ina saurarenki isash-shiya." Wannan karan cikin masifa Baba ya ambata lamarin da ya kuma sanyamin jiki kenan na sake lafewa sosai dan in jiyo zantukan da kyau, zuciyana sai harbawa ta ke yi tamkar zata fito daga ma'ajiyarta. "Malam kaji tsoron Allah wallahi saninka bai amfana maka komi ba tunda kake kan cutar da mutanen da basu san ta ina aka hau ba balle su san inda za'a sauka, kafi kowa sanin li'irabi akan k'addararren al'amari amma saboda son zuciya irin naka ka bi ka ta ke ka juya masa baya to wallahi ka sani laifi kake aikatawa mai girma wanda Allah sai ya tambayeka kiwon mu da ya baka a matsayinka na shigabanmu kuma Malami wanda ke koyar da mutane bin haryar sanin Allah da Manzonsa." Lumshe ido na yi cikin jin k'arin mutuwar jiki, kalamn Mama suna amsa kuwwa a cikin kunnuwana. 'Uwata ta wace ni kad'ai' shi ne kalman da ke maimaita kansa a cikin brain d'ina. Gyara tsayuwa na yi cike da burin sanin fassaran kalman. Shiru ban sa ke jin motsin komi ba dan ko tari ban jiyo Baba ya yi ba haka Mama ta daina shesshekan kukan, jikina ya sake macewa, kwakwalwata ta d'auki zafi ainun, kukan da najiyo Mama ta fashe da shi mai sauti kamkar wacce aka duka yasa na zabura kamar zan shiga cikin d'akin sai kuma na tsaya cak ina jan numfashi sai nima na fashe da kukan cikin rashin fitar sauti, jikina sai rawa yakeyi. Jin alamun tafiya za'a fito sai na koma mazaunin da Mama ta tashi da sauri na soma juya kunun ayar tare da sauke kaina k'asa hawaye na d'iga saman zanin jikina. Inaji a jikina kallona Baba ke yi sadda ya fito, ban d'ago ba balle in gaishesa kamar yarda nasaba, kimanin mintoci biyu zuwa uku ya bar wurin batare da yaja min tsakinsa da ya saba ba. D'agowa na yi na rakashi da ido daf da zai shiga zauren ya waigo muka had'a ido ya juya da sauri ya fice na sake ware manyan idanuna da sukayimin nauyi, cike na ke da mamakin sauyawarsa lokaci d'aya daga mai sababi zuwa mai sanyi domin tunda na mallaki hankalina Baba bai tab'a shigowa ya fice batare da ya zagi Uwana da Ubana ba ko da kuwa barci na ke yi ya shigo gidan tabbas kafin yafita sai ya zo inda na ke ya zunbud'amin zagi sannan zai tafi, abin har ya zamemin jiki shi yasa yau da baiyi sabon nashi ba na shiga mamaki. Da tunanin sauyin nasa na tashi na shiga d'akin Mama bata a falo kai tsaye na shiga uwar d'aka na hangota kwance saman gado ta juyawa k'ofar shigowa baya tana kuka cikin k'aramin sauti a sanyaye na hau gadon na kwanta a jikinta na fashe da kuka mai k'arfi, a rud'e ta juyo ta rungume ni tana shanye kukanta amma yak'i shanyuwa ba yarda ta iya dole ta biyemin muka cigaba da kuka tamkar wad'anda aka yiwa dukan tsiya. Zuwa wani lokaci Mama ta tsaida kukan ta soma shafamin baya alamun rarrashi amma ban san tanayi ba sabida a lokacin ma naji wani sabon kuka na zuwamin, na ko b'are baki na yi ta yi cikin sark'ewar tari. "Ya isa haka nan Uwata, bakiga nima da kike tayawa na hak'ura ba, bakomi haka Allah ya nufemu da zama a k'asan jagora mara fahimta kinga kenan hak'uri ya zame mana dole." "Mama ba rashin fahimta ba ne tsabar rashin adalci ne a matsayinsa na Malami amma sam bai aiki da saninsa, wallahi wani zubin in ya aikata abu tamkar ba mai koyar da d'aliba ilimi ba." "Uwata kalamanki akan hanya suke Malam baiyi mana adalci ko kad'an, bai aiki da sanin da Allah ya hore masa haka bai duba sadaukarwan da muke kanyi masa domin hakkinmu da ya rataya a wuyarsa bai saukewa, ban tab'a damuwa ba saboda ina da rufin asirina wanda har wasu na ke taimakawa amma a hakan ban tsiraba saima biyoni da tijara da ke kanyi akan abinda yasan rayuwa ce ba wanda yafi k'arfin fuskantan irinta." "Mama muyi ta hak'uri wata rana sai labari." "Shi ne abinda na ke nusar da ke amma ki sani da gajiya fa." "To ya zamuyi da shi?" "Uhm a kwai Allah ai kuma kinsan dan yasan ke ce lagona shi yasa ya ke b'ata miki domin raina ya b'aci, tun kina k'ara yake min wannan d'abi'ar amma zuwa sadda kika girma sai ya sanja salo da yawan ambatarki da sunar asara alhalin ke d'in arziki ce mai tarin yawa domin wani daga cikin dukiyar da na ke tak'ama da shi har shima ya ke cin moriyarta ke ce silar albarkansu." "Ni kuma Mama?" "Eh ke ce Uwata domin bayan na sayi idan nan mun tare sai b'arayi suka shigo suka sacemin abinda ya ragemin na kudi wanda na b'oye zanyi jari, anyi abin da kwana biyu kika shigo da kaza budurwa makwafciyata marigayiya Iya Mai Kunu ta baki dan kiyi kiwo to itace tayi ta zuba mana 'ya'ya na saidasu ma siya miki tunkiya da matashin rago wanda Hajiya Inna ta cika kud'in domin ita ta siyo a k'auye da haka suka cigaba da hayayyafa ta hanyar saida raguna ina k'aro tumakai, kajin suma ina saidawa tare da tara kudad'en cikin amincin Allah a shekaru uku zuwa hud'u nasiya firjin wanda yanzu muke kan samun abin rufin asiri da shi." "Ikon Allah Mama a she ina da k'ashin arziki haka amma Baba ke kirata da suna mara albarka?" "Uwata kenan wannan halin Malam ne tijara dik wanda ya tsana ko da kuwa kullum zai kwanta ya bi ta kansa ya wuce ba zai daina aibatashi ba, ni kaina bai barni ba duk da ranar da na yi masa wanda ya ke fankama shi mai dukiya ne yafi k'arfi wulak'anci." "Mama wai me yasa ya tsaneni to?" Shiru Mama bata amsamin ba sai na Kuma jefo mata tambayar da ke cimin rai. "To Mama ko dai nid'in ba d'iyarsa ba ce kamar yarda Maman su Khamila ta ke ambatamin kalman karere?" "Yau she ta kiraki da wannan sunar?" "Tunda nayi hankali ta ke ambatamin sunar shi yasa bana son zuwa gidan ke kuma sai ki matsamin akan sai naje munyi zumunci da 'yan uwana." Shiru Mama ta yi na zuba mata ido cikin fad'uwar gaba. "Mama gaskiya ta ke fad'a ko?" "Uwata ke d'in ba karere ba ce domin ita da d'iyoyinta arzikinki suke kan ci dan da kud'inki mijinta ya sami bud'i har ta zama haka ta sami bakin kiranki da sunar banza amma zanyiwa tufkan hanci daga yau bata sake ambatamin ki sunar." "Mama wai kina nufin Baba Usman ke ce kika ranta masa kud'in da keyin sana'a shi ne dalilin da dik sati ke kawo miki riba?" "Eh, jari na bashi dik in aka sami riban sati sai ya raba uku ya bani kaso d'aya ya rik'e kaso biyu." "Ikon Allah Mama kina da hali mai kyau shi yasa muke ganin haske a lamuranmu." "Dik ke ce sila Uwata." "Uhm Mamana ta kaina." Na ambata cikin murmushi domin labarin ya farantamin rai ainun. "Uwata in har ina numfashi bazakiyi kukan damuwa ba sai bisa rubutaccen al'amari." "Allah ya amince hakan Mamana." "Amin." "Yawwa Mama wai me a baya jama'a sun nunamin kulawa da k'auna kamar yarda na ke gani anayiwa yara?" "Sosai kuwa an nuna miki k'auna Uwata, dan a yarintarki ke d'in mai masoya ne domin Allah ya hore miki farin jini na ban mamaki, ga samun kyauta a wurare da dama." "To Mama me yasa yanzu sai naga kamar suna k'yamata?" Na cillo Mata tambayar cikin tsareta da idanu. Kauda kai naga ta yi zuwa can najiyo muryanta cikin rawa. "Uwata kinfi gaban a k'yamaceki duk da ta... "Duk da me ne Mama?" "Tashi muje mu kammala aikinmu tambayoyin sun isa haka Uwata." "To Mama amma dan Allah kidaina yiwa Baba kuka sabida yanajin dad'in ganin hawayenki abin da na lura da shi kenan." "Na bari Uwata, taso muje muna aiki kina bani labarin yarda d'alibanki ke amsan karatu." Mike'ewa na yi ina maijin natsuwar ruhi ganin Mama tana walwala. "Ina sonki Mamana." "Uwata ni baki ba zai iya d'aukan furucin son da na ke yi miki ba saboda akan ki na fuskanci rayuwa kala-kala shi yasa na ke jin dirin duk abin da ke damunki a ruhina." "Mamana hoo ni kam a bakinki na tab'a jin ana jin damuwar wani zuciya cikin wata zuciyar." "Uwata kenan." "Mama kina da abinda kike son sanarmin amma kina kauce masa, dan Allah meye shi? Kuma aina danginki suke nima nasoma zuwa garesu ina yin hutu kamar yarda Aminiyata Fanta ke tafiya Maiduguri hutu." "Kome kike son sani game da ni zan sanar miki amma ba yanzu ba." "Sai yaushe Mama?" "Ranar da zaki bar gabana zuwa gidan mijinki." "Taf! Mama ba rana kenan tunda Baba ya ce ba zan... "Zancen Malam ba fad'ar Allah ba ne, ki d'aukeshi tamkar holok'o wanda akeyiwa lak'abi da hadarin Kaka  wanda bazai tab'a zubda ruwan sama ba duk kuwa bak'in da ya yi sannan Malam cewa ya yi bazaki samu mijin da na ke yi miki fatar samu ba, ba wai bazaki tab'a yin aure ba." "Mama ni da shi ya ambatamin hakan wai sai dai in k'are a gyaran d'akin dabbobi ba dai zama inuwar aure ba." "Shi Malam d'in?" "Eh Mama." "Yaushe ya furta miki wannan alkaba'in kalma?" "An kwana biyu, dan kawai Anas ya zageni na buge masa baki akan idonsa shi ne yazo ya ke ambatamin wai ba zanyi aure ba balle na haihu sai dai in k'are a kwashe kashin dabbobi." "Ta Allah ba tashi ba, wuce muje na gaji da jin zancen Malam raina kuma b'aci ya keyi." Fitowa na yi na hura gawayi na d'ora mai a wuta saida na soma suyar meetpie sannan Mama ta fito na kalleta ta sakarmin murmushi na taso na mik'o mata robar meetpie d'in dana kwashe na ce "Mama ci kiji yayi dad'i kuwa?" D'auka ta yi ta gutsira cikin gyad'a kai "Kai Uwata yafi sama da abinda ake buk'ata, gobe zakiyi mana sai mu ajiye muna sha da tea." "Mama dik santin ne haka har kika manta gobe ina wurin hayaniya kuma jibi zanje wurin babban hayaniya mai lasisi." "Oh na tuna gobe kuna wurin yayen Fanta, Lahadi da laraba kuma kina wurin samun lada na kyau." "Uhm Mama wallahi ba dan kin nuna kina son ina zuwa koyarwan nan ba wallahi da hak'ura na yi saboda hayaniyar yaran kad'ai ciwon kai ke sakamin sannan gashi ba wanda ke hurd'a dani makar mujiya na ke zama, abin haushi Malaman makarantar suyi ta bina da kallo tamkar mai d'auke da nak'asa, Allah nagaji Mama ki amince na zauna gida tare da ke kawai yafimin samun natsuwar ruhi." "Uwata ki daina hasko wani mugun abu a tare da ke kawai komi zakiyi ki yisa dan Allah insha Allah nasara na tare da ke." "To Mamana." "Da kyau Hafizan Uwata." Murmushi na yi na maida hankali kan aikina ina mai jan istiggifari a asirce domin tuba ga laifukan da na aikata natare da na sani ba. Mama kuma ta zauna ta cigaba da d'ura kunun aya a robobi, tana gamawa k'awata Fanta ta shigo da k'awayenta su biyar had'i da ita, ban sansu ba amma na hango duk suna kama da juna, sai k'amshin turare suke bugawa na lumshe ido domin naji dad'in shak'ar k'amshin kasancewata ma'abociyar son k'amshi. Suka zube suka gaida Mama cikin girmamawa kamar yarda sukaga Fanta ta yi. Kunun ayar mai sanyi Mama ta basu tare da d'iban musu meetpie ganin tana shirin rabe musu Fanta ta d'auke robar tana cewa "Mama wallahi ya ishesu haka kuma sunci wanda zan basu gobe ehe." Dariya na soma k'awayen na tayani tare da dawowa kusa da ni suka kewayeni kamar zasu fad'omin cike da nuna k'auna a idanuwansu, kallonsu na yi sai naji wani dad'i na ratsani domin wannan shi karo na farko da k'awaye suka nunan kulawa batare da watsamin kallon banza ba ko jamin tsaki da zarar munyi ido biyu da su. "Deejah kawo in tayaki soyawa." Cikin 'yanmatan wata ta ce da ni, kafin inyi magana Fanta ta zabga ashar cikin cewa. "Kan uban can! Bintu kurance zaki bawa suyar abina wallahi baki isa ba bani wurin in zauna tunda ladar ya isheki kuma kowa ta koma gefe ko in watso mata ruwan mai ta koma gida sa tanbo." Me zasuyi in ba dariya ba, Mama kam barin wurin ta yi dan lamarin Fanta yafi k'arfinta. "Fanta ke dai kin fiye rowa da alama zan koma k'awance da Deejah na barwa su Fiddausi ke." "Kai nima da Deejah zanyi tunda gidansu ana raba kunun aya mai dad'i." "Fiddausi uwar kwad'ai to ba mai kwacen k'awa, domin Fanta a kayi Deejah ita kad'ai dan kusani ehe." Dariya muka saka. A haka na kammala suyar muka shiga d'akina na shiga wanka bayan na shirya na d'auko mana abinci tare da kayan sanyi muka baje muna ci ana hira. A nan Fanta ke sanarmin daga inda k'awayenta sukazo wato daga asalin garinsu Maiduguri wanda na gano 'yan uwan juna ne dan tushensu d'aya suka fito. Sai kallonsu na ke yi wayayyu da su ko wacce da babban wayarta tana latsawa sai a nan na hango ta Fanta sabuwa dal na zare ido ta kwashe da dariya tana cewa "Uncle ya bani gift d'azun da safe naso shigowa na nuna miki amma Aunty masifa ta hanani fita, zan baki tsohuwar tawa ki shigo gari tunda kin zama 'yar k'auye Mama ta ce zata siya miki kince a'a haddar Qur'ani kike son had'awa, kin had'a Haddar kince ta barshi ba kyaso, Allah yanzu komin k'auyancinki sai kin bari na koya miki har kan arziki ki bar yawo da rakata kashi, gidan layi, haba K'awata ga aji ga komi kina yin abu tamkar wacce batayi jami'a ba." Murmushi kawai na yi ina yabawa iya surutun Fanta, ko yamu bata had'iyewa. Su kam dariya suka sanya suna taya Fanta cashemin, littafi addu'o'i na d'auko na soma dubawa dole suka rabu dani dan nak'i tofa kalma. "Wai Aunty Nafisan ce Aunty masifa Fanta?" Bintu ta ambata cikin tsare gira wanda hakan da ta yi na hango kamarsu da Aunty Nafisa sosai sama da Fanta. 'Wata k'ila uwa d'aya suke.' Na ambata cikin raina. "Eh ita fa, ko kema kin san sunar ya dace da ita wallahi ba dan ina jin tausayin halin da Deejah zata shiga ba na kewata da tare da ku zan tafi na huta da sababinta kamar tsohuwar makauniya." Duka Fiddausi ta taska mata a cinya cikin cewa "Shegiyar gora Allah k'ara bana ban zuwa ba kika ce ni ce banson amoreni zaki zo, to madallah da kiga ganewa idanunki, halinta na 'yammatanci na nan ba abin da ya sanja." "Aikam dai Aunty Nafisa ta shiga uku da fad'a kowa yazo wurinta sai ya gudu shi yasa Momy ke yawan ambatar hak'urin Fanta data iya zama da ita na tsawon shekaru biyar bata kawo k'orafin fininarta ba." "Au har da ke Sakina kina biyewa sharrin su Fanta?" "Kinga Bintu zamu kwashi jakar uba da ke idan baki daina kirana ina yiwa Nafisa sharri ba." Hangame baki mukayi jin ta kira Aunty Nafisa ba sakayawa. "Kunga dik abinda Fanta ta ambata gaskiya ne dan kowa a cikinmu yasan halin tijararta dan haka a binda yafi mu bita da addu'a kawai ba zaman cin mananta ba." "Maganarki gaskiya ne Beebah." Fiddausi ta ambata ahankali sai lokacin na tsoma baki kuma a karon farko dana na yi magana tun shigowarsu, domin sam na shafa'a ko gaisawa da juna ba muyi ba. "K'awata tunda kinsan halinta abinda yafi kici maganin zama da ita kawai, domin wasu haka Allah ke yo su masu fad'a batare da anyi musu laifin komi ba." 'Kamar Baba kenan.' Na ambaci hakan a raina cikin lumshe ido wanda suke cike da jin barci. Ihu da naji sun saka yasa na bud'e ido da sauri, Fanta ta kyalkyale da dariya tana cewa "Bana sanar muku cewa muryanta mai dad'i ba ne, shi yasa take rowarsa dan sai ku d'auki sama da awa kuna zaune batayi magana ba sai murmushi kamar gonar auduga idan kunji tana surutu to da Mama ce ko ni idan nataki sa'a." "Kai Fanta banda sharri dai." Na ambata ina shafo wuyana. Wani ihun suka kuma sakawa na bisu da kallo ina hango yarintarsu sabida bisa alamu na girmesu duk da sun kaini girma da cika domin ko Fanta na bata shekaru kusan uku, su d'inma baza su wuce age mate dinta ba, Beebah ce kawai na hango zamu iya zuwa sa'anin juna dan ko kamewa tafi su haka itama na lura miskila ce dan bata cika magana ba. Tundaga lokacin suka cikani da tambayoyi dan kawai inyi magana ni kuma na biye musu dik da takuranin da sukayi. A ranar bak'in cikin da Baba ya sanyamin zuwan su Fanta ya sa na manta farin ciki ya maye gurbinsa. Sai da muka sallaci isha'i suka tafi bayan munci tuwon dare wanda ni da su muka yi aikin. Bayan sun wuce sabon hira muka b'ud'e da Mama mai cike da farin ciki sai misalin sha d'ayan dare na kwanta a d'akinta ina saman gado ita kuma tana zaune saman sallaya tana jan carbi. Kamar a mafarki na jiyo hayaniya ko da na bud'e ido Baba na hango ya wani shak'ure Mama a lungu, cikin magagin barci na sakko zan iso wurin tunanina dukanta yakeyi na bashi hak'uri amma muna had'a ido da shi ya saukemin mugun kallo da jajayen idonsa wanda hasken da bai wadaci d'akin ba ya haskomin fuskansa, na koma saman gado da sauri dafe da k'irji sabida a yawan shekaruna na fahimci sunnah Baba ke son ya yi da Mama cikin k'arfi. Wani sarawa kaina ya yi sakamakon jiyo kalaminsa gareni. "Koma ki kwanta ki saurari abinda kike burin ji da gani wanda shi ne ya ya janyoki d'akin kwana alhalin kinsan girkinta ne." "Wallahi Baba... "Kwanta abinki Uwata kunyarsa ba naki ba, maza ka haik'emin a gabanta Malam tunda burinka kenan taga tsiraicinmu." "Haka kika ambata ko Hurera? Zanko shayar dake mamaki yau Hurera." Ya amabata cikin wani nishi da ya gigitamin natsuwa, a kuma lokaci d'aya Mama ta rafka salati mai k'arfi. Ban san sadda na diro ba na fice zuwa d'akina na kulle k'ofa na jingina da shi na saki kuka jikina na mazari tamkar wacce aka watsawa ruwan k'an-k'ara. *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure.) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/13, 10:47 AM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Mrsjmoon *Shafin sadaukarwa ne ga Rahma Kabir (Mom Sultan) Allah ya albarkaci rayuwarki tare da zuri'arki baki d'aya, Amin.* Page 03. "A wacce duniya na ke ni Nana Khadijatu? Wacce kalan rayuwa ce  haka? Wani irin bak'i dare na fad'o cikinsa mai mugun duhu? K'alu innalillahi wa Inna ilaihin raji'un!, Allahumma igfirli war hamni. Lahaula waka quwwata illa billahil aliyul azim. Shin Baba wani kalan mutum ne? Shin haka keyiwa sauran d'iyoyinsa ko ni kad'ai ya ke b'e ke yiwa hakan? Hakik'a Baba bakayimin adalci ba, ba ka kyautata min, ka tozartani tozarci mafi muni, wallahi  na tsane... "Allaha natuba ka yafemin fushin zuciya ne amma bazan tab'a tsanar wanda ya yi silar kawoni duniya ba." Na ambata tare da tura kaina tsakanin cinyoyina ina girgizawa, kuka na kuma fashewa da shi cike da jin matsanancin tausayin kaina tare da Mama, kimanin mintoci goma shabiyar saanna na tsagaita da kukan domin ya kasa yimin maganain zafin da na ke ji a ruhina sai ma k'aramin rad'ad'i sa ke yi. Cikin layi na mik'e zuwa toilet na d'auo alwalla na zauna saman darduma domin bazan iya tsayuwar gabatar da sallar nafila ba. Istiggifari na soma ja batare da nasan yawan adadinsa ba domin saida nayi iya yina sannan na koma kan yiwa Annabi S.A.W salati shima nayi bakin yarda ya samu sai na cike da hailalah, na d'ora da ambatar sunar Allah AL-DAFI'U. Na sami awa biyu a zaune cikin amincin Allah na somajin natsuwar jiki da ruhi na samuwa gareni, Alhamdulillah na kama ambata a fili ina jan hanci ruwan hawaye kuwa wannan ba'a maganarsu domin jin natsuwa ya soma rab'ata sai wani rauni na daban ya nashe ruhinta tare da k'arin zubar ruwan jurwaye, tausayin kaina na ke ji tamkar irin wacce ta rasa kowa a duniya. Gyara zama na yi na soma tashibi na musanman ga Allah S.W.A dan samun cikar mizani da ayyukan alkhairi ranar sakamako wato _Subbahanallahi wa bi hamdihi wa Subbahanallahil azim._ Ban san adadin carbi nawa na ja ba amma na san dai natsuwa ya gama nashe ruhina da dukkan gab'b'aina. Samun kaina nayi da sakin murmushi, idanu na lumshewa cike da jin matsanancin barci. Barcin ne ya soma fizgata na tsuke baki na cigaba da ambaton addu'ar tafiyar da k'uncin zuciya a'a asirce duk dan na k'ara samun natsuwa, ba jimawa kuwa barci ya d'aukeni batare da na sani ba. A firgice na farka jin muryan Mama na kirar sunana. Rik'eni tayi ganin yarda nake zaro idanu cike da tsoro. "Uwata koma barcinki banzo dan na tasheki ba, nazo duba yarda kika kwana ne, kuma alhamdulillah tunda alamu ya nuna kin sami barci mai dad'i." Shafo fuskata na yi na ce "Mama rana ta fito banyi sallar subahi ba." "Garin ya hakan ya faruwa uwata?" "Mama bari inyi sallah dai." "To maza tafi kiyi dan yanzu kusan k'arfe takwas na safe muke ciki." Da sauri na mik'e na fad'a bayi. Bayan na idar da sallah Mama ta sake shigowa d'auke da jug tare da cup ta ajiye a kusa dani ta kuma fita ta dawo rik'e da madaidaicin kula, murmushi na yi na rik'o hannunta na ce "Mamana Allah ya biyaki da dubun alkhairori, ina sonki Mamana sama da son da na ke yiwa kaina." "To Uwata nagode, yanzu maza ki karya kizo ki wuce wurin walimar Fanta dan ta shigo har sau biyu duk kina barci." Idanu na zaro domin na manta da saukar Fanta. A hanzarce na kammala karyawa inda banci wani abin kirki ba duk kuwa da magiyar da Mama keyimin da na cinye. Wanka nayo na shirya dik a cikin gaggawa na fice da d'an gudu Mama ta rakani da addu'an alkhairi. Ina fitowa waje Baba na isowa, wuce shi nayi tamkar ban gansa ba duk kuwa da na gansa tare da abokinsa hakan bai sa na tsaya gaisar da su ba saboda hakanan naji tsanarsa danake kaucemawa ya dira a ruhina, mutuncinsa na son samun nak'asu a idanuwana. "Malam wancan ba Khadija ba ce ta gidanka?" "Ita ce." "Yaushe ta koma mara tarbiyya da har zata iya wucemu bata gaishemu ba." "Mallam Ilya wannan ba komi ba ne da alama hankalinta ne bai wurinmu." "Anya kuwa?" "Malam Ilya shigo kayi aikin dana rok'i arziki kawai yafi wannan zantukan d'iyoyin zamanin wanda in baka dasu a gidanka to danginka basa rasawa." "Oh to yanzu na gane gori kake son yimin akan... "Walalhi Malam Ilya ka yarda ba gori na ke yi maka ba kuma dan girman Allah ka bar zancen nan kada ta koma ta wani sigan da rayuka zasu ba'aci." Daga gaka Malam Ilya bai sake furta kalma ba ganin haka sai Baba ya ja hannunsa suka shige cikin gidan domin bawa Mama hak'urin abin kunyar da ya aikata daren jiya wanda son zuciya yayi masa jagora, shi ne dalilin gayyato abokinsa. **** Ina shiga gate d'in gidan su Fanta na hango Aunty Nafisa tare da Uncle sun jero cikin shigar alfarma, da alama wurin walimar zasu tafi. Na k'arasa na russuna cikin ladabi na gaisar da su. Uncle ne ya amsa tare da tambayata dalilin da yasa na makara zuwa wurin taron. Kasa amsa mishi na yi saboda da yarda jikina ya d'auki rawa sakamakon ganin yau ya tsaya yimin magana mai tsayi abinda baitab'a yimin ba tun sanin da na yi masa, maganarsa gareni bai wuce amsa gaisuwa shima atak'aice. "Oya taho muje dama can muka nufa." "No, bata kudin Napep kawai Abban Hafiz ta wuce" "Ba zan bata ba." "Me ye haka Abban Hafiz?" "Mele ne, kuma ki fita idanuna wallahi ko ranki yafi na d'azun baci, kin daiji na gaya miki, sokuwar banza kawai wacce ta girma amma tamkar ana k'ara mata rashin tunani, mitchew!!" Ai ko da Uncle zai duba na kusa kaiwa k'ofar k'aramin gate domin ina jin kalma Aunty Nafisa na bar wurin a hanzarce dan na san waye ita ba abin damuwarta ba ne ta rufeni da duka ta barni da ciwon jiki dan tasha dukan Fanta a gabana shi yasa na ke jin tsoronta ainun. Ina tsoron dik abinda zanyi atabamin lafiyar jiki shi yasa ita kanta Mama bata iya duka ba sam. Sai dai duk abin da Uncle ke fad'awa Aunty Nafisan sun shigo kunnuwana saboda ya bud'e murya, jin fad'arsa ya kuma rud'ani na k'ara sauri. "Khadijatu!" Na tsikayi muryansa na kwalamin kira ai a guje na fice wajen gate, cikin sa'a ina fitowa Napep na sauke fasinja na fad'a tare da sanar da shi inda zai kaini. Shima ganin yarda na ke bai tsaya b'ata lokaci ba ya fizga Napep d'in muka tafi. Sai sauke numfashi na ke yi tamkar wacce ta yi gamo da dodo sai lamari ya bani dariya na sunkuyar da kai na yi ta sauke murmushi. Taka burki da mai Napep ya yi ba shiri ya saka na d'ogo a  hanzarce cikin ambatar sunar Allah AL ALIMU. "Fito na ce ko in sab'a miki!." Fitowa na yi jikina na rawa zatona marina zaiyi sai ya nunamin motarsa na tafi cikin sanyin jiki na bud'e gidan baya na zauna tamkar munafuka. "Malama ki saki jikinki kada wannan munafuncin naki ya kuma janyo hankalinsa kanki abinda faruwar hakan zai iya janyo miki matsala da ni." D'agowa nayi ina kallon cikin idanun Aunty Nafisa tako zabgamin harara murmushin yak'e na sauke mata tare da maida fuskata gefe. "Wallahi sai naci ubanki bokan nan." Da sauri ya kalleta, ta kuma gabgamin harara, na b'ata rai tare da cewa "Babana ba boka ba ne." "Ubanki! Me ye shi, in ba Boka ba?" Sunkuyar da kai na yi sabida ban saba maidawa wanda ya girmeni da magana ba amma na k'udurta zanyi mata nasiha akan kada ka sake ambatawa mahaifina kalman Boka. Motsin tafiyar motar ya sanar dani Uncle ya shigo motar. "Khadija idan nakuma baki umurni kika tsallake to har gaban Malam zanje na baki kashi." "Kayi hak'uri Uncle." Bai tankamin ba sai nima na tsuke bakina ina cigaba da kallon gefen titi sannan inaji a jikina Aunty Nafisa kallon banza take watsamin tamkar yarda ta saba yiwa kowa. "Ke da Fanta abu d'aya na ke d'aukanku, wato k'annin matana dan haka kada ki sake aikata min abinda Fanta bazata iya yimin ba." "To Uncle, inshs Allah zan kiyaye." "Hakan yafi." "Abban Hafiz wai... "Nafisat idan kinsan kalman ki ba ta arziki bace to ki barta a ranki zaifi." Kallonsa na yi fuskan nan tasa a had'e tankar yarda na sanshi a baya. Ware min idanu ya yi ta mirror alamun me ye? Na sunkuyar da kaina k'asa a hanzarce cike da jin kunyar abinda na aikata wato kallo abin da na tsani ayimin. Daga haka ba wanda ga sake magana har muka iso harabar makarantar. Na kama k'ofa zan fita na tsinkayi muryansa cikin kaushi "Wait! Khadijatu." Komawa na yi na zauna ina wasa da zobben azurfan dake yatsana. Magana naji yanayi a waya bisa alamu da malamin makarantar ne, yana ajiye wayar nawa ta d'auki k'ara fito da ita nayi daga cikin pose d'ina mai kyau ainun wanda Mama ta yomin tarabar shi data shiga kasuwa. Mama ce ta ke tambayana yarda na isa na tabbatar mata da lafiyalau. Ina sauke wayar a kunnina idanunmu ya had'u dana Uncle samun kaina na yi da kallon cikin idanunsa tamkar yarda ya ke kallon nawa, musmushi ya yi tare da juyowa ya kalleni sosai na yi hanzarin sunkuyar da kai ina latsa gidan layina fad'in Fanta. "Nafisat dama k'anwar taki bata da waya baki sanarmin ba?" Yarda ya yi maganar ba wanda zaice shi ne ke fad'a d'azun. "Wa kenan? Ta ambata a dak'ile hankalinta na kan wayarta. "Nana Khadijatu." "Yau she na ke da k'anwa mai wannan sunar Abban Hafiz?" "Oh ya rabbi, a gaskiya baki da kirki Nafisat, yanzu k'awar Fanta ai k'anwarki ce inda kara." "Idan kuma babu karan fa?" Kafin ya bata amsa Abokinsa da ya kira ya iso dan haka sai ya bud'e k'ofar ya fice sun sami mintoci biyu zuwa uku sannan Uncle ya umurcemu da mu fito inda muna fitowa sukayi gaba muka rufa musu baya. Wannan damar Aunty Nafisat ta samu ta yi min gargad'i akan fita harkan mijinta. Ni sai lamarin ya zamomin wani kala domin tun tasowata bantab'a cin karo da wata nayimin gargad'i akan mijinta ba ko saurayinta. Haka nan kawai naji wani nishad'i na ratsamin ruhi a maimakon shiga k'unci domin Aunty Nafisat ta sokamin maganganu masu zafi wanda zasu k'ona min rai ta hanyar kiran Baba da Boka abin da ta hango na tsani jin kalman shi yasa a zantukan nata ta yi ta kiran Bokan Ubanki, amma sam basu k'onamin rai ba kamar yarda ta ke da buri. Daf da zamu isa wurin muta be na kalleta cikin murmushi mai sauti ta ware ido na kuma murmusawa tamkar zanyi magana sai kuma na tsuke baki hakan kuwa ya b'ata mata rai dan hannu ta d'aga zata zabgamin mari na yi saurin sunkuyawa ta sami iska wanda ya jata ta tafi zata fad'i na yi hanzarin tareta cikin ambatar sunar Allah RAHMAN. Da sauri Uncle ya juyo tare da abokinsa. "Lafiya?" "Normal Dear kawai d'an tuntub'e naji." Ta bawa Uncle amsa cikin tureni daga rik'on da nayi mata. "Allah ya kara kiyayewa." Abokin Uncle ya ambata. "Amin." Na amsa tare da gaisar da shi ya amsa cikin kauda kai gefe yana mai gaisar da Aunty Nafisat. Tamkar mai ciwon hak'ori haka ta amsa Uncle ya ja dogon tsaki ya yi gaba dan yaji haushin abinda tayiwa abokin nasa. Wuri na musanman Malamin ya kaimu wanda baida nisa da inda ya ajiye Uncle domin wurin maza daban mata daban. Hak'ik'a wurin ya tsaru matuk'a dan wurin manyan bak'i ne, lumshe ido na yi ina hasko sadda na zauna a cikin taro irin haka. "Alhamdulillah, ya Allah da ka bani ilimin addini da na zamani dai-dai misali, Ya rabbi ka bani ikon aiki da su ta hanya na gari." Na furta a hankali. Tsakin da Aunty Nafisat ta ja yasa na bud'e ido duk sai naji na takura sabida yarda Aunty Nafisat ke zabgomin harara da kuma idanun mutane da ya dawo kaina, murmushin yak'e na yi ta yi ina kallon idanunta ta kuma jan tsaki mai sauti sama da na farko sai na kauda fuska na yi kamar badani ta ke yi ba zuwa can na fakaici idanun Uncle na sulale zuwa wurin su Bintu wanda tun ganina suke ta d'agomin hannu. "Ayya Deejah kinyi kyau sosai." Suka ambata a tare. "Nagode, kuma kunyi kyau." "Deejah k'awarki tayi fushi da ke." "Safeena a tayani bata hak'uri, jiya na raya daren ne da yiwa Annabi salati shi yasa na tashi a makare." "Masha Allah, rayuwarki na kan burgeni matuk'a." "Uhm." Na ambata cikin sosa gefen idona. Haka suka yita min hira ina biye musu cikin jin dad'in kulawar da suke bani. 'Karfe goma dai-dai aka soma kiran masu saukan suna yin karatu. Masha Allah shi ne abin ambata domin kowa a ka kira zaiyi karatu cike da kwarewa, Fanta harda kuka sadda akazo kanta lamarin da ya ja hankalin mutane sukayi ta sanya mata albarka tare da yi mata lik'in kud'i ciki har da ni da su Bintu, Uncle kam mu da muka rufeta ya yi ta zubawa 'yar dari biyar-biyar sabbi fil. 'Karfe biyu da mintoci goma sha biyar aka tashi taron cike da farin ciki. Muna isa gida sallar azuhur mukayi. Ni da Beebah muka hau hidima da tulin 'kawayen Fanta zuwa la'asar dik sunka watse, muna zaune a d'akin Fanta sai hayaniya sukeyi na koma gefe na sami gefen gadon Fanta na zauna ina duba wayarta domin soma gane yarda ta ke saboda daga jiya zuwa yau na ji son rik'e babban waya. Maganar Aunty Nafisat na tsinkaya cikin hargajinta na fama. "Ke! dalla ta so ki dafamin abinci." Tsit d'akin ya d'auka na d'ago na bi su da kallo sai naga ni suke kallo sai na maida kai ga abinda na ke yi. "A haka Abban Hafiz ke ambatarki da k'anwata, inayi miki magana kin bawa banza ajiyata, uhm yayi miki kyau, labari zai isa kunninsa domin na san ke ba K'awata ba ce." Da sauri na d'ago har ta juya zata bud'e k'ofa na ce "Ayya Aunty ban san dani kikeyi ba, kiyi hak'uri muje na dafa." Batare da ta juyo ba ta amsa "Ban son gulma kawai in zakizo kizo ba sai kin cikamin kunni da karad'i ba." Baki bud'e na raka bayarta da ido cike da mamakin k'arfin halinta tare da nunan iko alhalin bai zama dole inyi mata aikin ba. Tsaki Beebah ta doka ta fice fuww, Bintu ta rufa mata baya Fanta ta janyo hannuna cikin cewa "Ba girkin da zakiyi mata dan ke ba 'yar aikinta bace." "Wallahi Deejah kada kiyi tunda bata san yarda zata nemi arzikin ayi mata abu ba." Fiddausi ta furta cikin fad'a. "Uhm nikam na tafi gidan Mama nasha kunun aya. " Safeena ta ambata tare da ficewa. "Jirani mu tafi dan nasan halin k'awata sai tayi girkin ni kuma ban shirya ta yata ba." Rik'o hannun Fanta na yi ta fizge ta fice da gudu Fiddausi ta rufa mata baya da gudu itana. Girgiza kai na yi na fito zuwa d'akin Aunty Nafisat hayaniyarta najiyo cikin muryan fad'a sai ban shiga ba na juyo zuwa kitchen na samu ta fitarmin da dik abinda zan buk'ata. Aiki na somayi cikin kwarewa domin amfani da kayan wutar baizamemin abin wuya ba dan nasaba taya Fanta girki da su sannan girki wani sashi ne na rayuwata domin idan ina yinsa har wani nishad'i na ke samun kaina ciki, lokuta da mada Mama kan kirani da Uwata sarauniyar girki, jin hakan na k'aramin k'aimi wurin ganin na dafa abinci mai rai da lafiya. A cikin awa biyu na kammala dafa jelop rice wacce ta ji kayan lambu da yankakkun Hanta tare da had'in zobo drink. Ina goge hannuna da towel najiyo k'amshi wani turare mai shegen k'amshi, juyowa na yi cikin lumshe ido sakamakon kasancewata mai son k'amshi, "Sannu da Aiki." Na bud'e idanu da sauri jin muryan Uncle wanda ke tsaye a bakin kofar kitchen hannayensa zube cikin aljihunsa. Kunya ce ta ziyarceni ganin ya ganni babu hijab, kai na sunkuye na ce "Yawwa, barka da yammaci." Banji ya amsa ba kuma ina ji ajikina kallona ya ke cigaba da yi sai na janyo hijab d'ina dake rataye saman k'ofa na sanya na d'ago muka had'a ido ya murmusa kad'an tare da shigowa ya nufi wormers dana zuba abincin ya bud'esu ya maida ya kulle ya d'auki cup k'arami ya zuba zobo drink dana  jefa k'an-k'ara cikinsa, ya d'auki sanyi. Gyashi na ji ya yi tare da hamdala duk a lokaci d'aya. "Dama ke Nafisat ta saka aikin dana sanyata?" Ban amsa ba sabida ban san amsar sa zan bashi ba sabida kada na ambata eh ya zamo na yi laifi a wurin aunty Nafisa. "Thank you Khadijatu, me kike so na baki amatsayin tukuici? Saboda kin farantamin rai ta hanyar fitar da ni jin kunyar abokan kasuwancina." Still ban ce komi ba dan wani yanayi na fad'a domin wannan shi ne karo na biyu tun zamowata budurwa da namiji ya tab'a yabamin har da neman zab'ina akan wani abu da zaiyimin na farantawa. "Uhm ina saurarenki." Muryansa ya katsemin tunanin dana fad'a. Kallonsa na yi kad'an sai naga ya cikamin ido kuma na kasa furta kalma. "Bakiji maganar da nasanar miki d'azun ba ko Khadijatu?" "Kayi hak'uri Uncle." "Oya na ji sarkin tuba, zama sanar da ni abin da kike so." Motsa yatsuna nayi cikin saita harshena na ce... *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure.) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/14, 2:40 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Mrsjmoon. EWF. *Shafin sadaukarwa ne ga Ramlat Mai Dambu (Mom muwaddat) Allah ya yi wayuwa albarka tare da raya zuri'a cike da ni'imominsa. Amin.* Page 04. "Babu tukuici a tsakaninmu Uncle, dan kawai na yi aikin da ya zamamemin abin alfahari, Ni tamkar d'iya ce ko ince k'anwa a gareka." "Nasan da wannan just ina son jin ra'ayinki akan abinda na k'udurta yi miki ne sabida yarda kika farantamin ta hanyar fitar da ni kunya da abinda na nemi alfarma matana da ta yimin amma tak'i sai ta sanyaki gashi kinyi abinda nasan bazata iya shi ba, kinga kin cancanci a faranta miki ta hanyar rukuici." "Uncle ka gama faranta min tunda ka ya bi aikina." Na amsa cikin fitar da siririyar dariya domin ainun naji dad'in yabon da ya yi min. "Wato bazaki fad'aba kenan ko?" "Please Uncle ka amince komi na yi a gidan nan nayisa ne domin Allah, badan abiyani ba, ka tuna fa kace nid'in tamkar Fanta ka d'auke ni, kaga kenan yarda bazaka biya Fanta ba nima ba zaka biyani ba." "Allah ya yi miki albarka." Ya furta hakan a hankali. "Amin." Na amsa da sauri ina sakin murmushi domin ina son jin an ambatamin kalmar albarka a rayuwata shi yasa kusan kalaman Mama gareni albarka ce mafi yawa. Murmushi na ji yayi mai sauti ya rab'a gefena zai wuce, daf da kunnina naji ya ce "Ki dafamana ruwan Lipton mai kayan k'amshi tare da yangen na'a-na'a, yarda dai zai fito da k'amshinsa mai gamsarwa." Ban amsa ba saida na ji ya kai k'ofar fice kitchen d'in sannan na ce "To Uncle." Juyowa ya yi na yi saurin juya masa baya. "Muna da yawa Nana Khadijatu dan haka a cika fulas kamar biyu." "Insha Allah Uncle." "Very good." Ya ambata tare da barin wurin na raka hanyar da yabi da ido cike da mamakin sakewarsa dani yinin yau lamarin da ya zomin a bak'on lamari dan sam ban d'auka haka ya ke da sauk'in hali ba tare da iya mu'amala mai kyau da wanda basu ishesa kallo ba tamkar ni. Bayan wucewarsa da mintoci na yi tsam ina nazarin lamarin sai kawai wani nishad'i ya ziyarce ni na cigaba da aikina cikin kuzari inayi ina ambatar sunayen Allah a zucci sabida yin hakan ya zamemin d'abi'a na musanman. Tunanin soya naman kaza ya zomin domin su k'ara da shi, ta ke kuwa na soma aikin cikin hanzari. Na kammata kenan ina tsaftace wurin Aunty Nafisa ta shigo cikin jifana da kallon da na tsana wato na wulak'anci. "Abban Hafiz ya shigo nan ne?" "Eh." Wani ashar na ji ta antayo wanda ya sakani tsayawa tsak da abin da na keyi jikina na rawa saboda da yarda na tsorata. "Uban me ya sanar miki?" "Babu komi Aunty kawai ya umurceni da in dafa masu ruwan Lipton ne sai naga dacewar in soya musu kaji domin karrama bak'in." Saukan mari na ji a saman fuskata kafin indawo hayyacinsa ta sakarwa cabinet duka a take man gyad'an danayi amfani da shi ya watso na d'aka tsalle gefe amma duk da haka sai da ya zubomin a yatsun k'afa cikin gigita na kwalla ihu Aunty Nafisa ta kuma d'aukeni da tagwayen mari tare da d'ora kafarta ta ta ke yatsun da man gyad'an ya tab'amin na kuma fasa ihun da yafi na farko k'ara ta k'ara danne yatsun aikam ban san lokacin dana kai mata duka ba na sameta a kusa da ido ta fasa ihu tare da janye jikinta na zube saman guiwayona ina kuka cikin ciccira saboda yarda na ke jin zafin na ratsamin brain yafi gaban kwatance. Ban san me ya faru ba sai jiyo muryan Uncle na yi cikin k'araji na cewa "Nafisat! kul kika soka mata wuk'ar nan,shin kin hauka ce!?" Ina jin kalman wuk'a na mik'e a guje zan bar kitchen d'in Uncle ya nemi rik'eni na hankad'ashi gafe na fice sai dai kafin in fice falon ya kamani ya rik'e gam a jikinsa. "Please Uncle ka sakeni intafi wurin Mamana kada ka kashe mata ni, wallahi ba zan sake shigo mata gida ba, kace tayi hak'uri saboda Fanta na ke zuwa dama kuma daga yau ban sake zuwa." Ganin yarda na ke magana kamar bana hayyacina sai ya soma jijjigani yana ambaton sunana da k'arfi, still ban daina son kufcewa ba tare da jadda masa bazan sake shigowa gidan ba, gyara runguman da ya yi min ya yi tare da cewa "Please calm down Deejah, no one can harm you again, I'm with you." Cak na dakata ina gwama numfashi, jin yarda hannunsa ke yawo a gadon bayana Kimanin mintoci biyu zuwa uku sannan ya sakeni na zube saman kneel d'ina ina cigaba da kuka mai sauti domin zugin da yatsun keyimin bana wasa ba ne. "Kalla kigani Nafisat, shin wannan shi ne sakamakon da ya dace kiyiwa wacce ta faranta miki ta hanyar fitar da mijinki kunyar idanun abokansa? Haba Nafisat, daga taimako sai ki nemi halakata? To wallahi kinji na rantse wannan shi ne karo na farko kuma na k'arshe da zaki sake aikata wannan rashin hankalin a gidana, yanzu da banzo ba soka mata wuk'ar zaki yi ko me?." "Da ka bari kaga me zanyi mata da wannan tambayar 'yan sandan naka?" "Nafisat kina son in fusata na sauke fushina akanki ko?" "Sakina zakayi Abban Hafiz ko me?" "Ko me zanyi idanunki zai ganemiki." "Wai me nufinka a kan wannan shegiyar yarinyar?" "Abinda zuciyarki ta karanta miki kuna ita ba shegiya ba ce kinsan waye mai sunar." "Na rantse da tsarkin mulkin Ubangiji baka isa ka tijarani gaban wannan mai suffan aljannun ba dan zan iya yin ajalinta wallahi dan haka tun wuri ka dawo hayyacinka ko in... "Mahaukaciyar banza da wofi wacce girmanta ya zama na iska, dalla rufemin baki mai bak'in hali kawai wacce ko jininta bata kyale ba, Allah ya kawo miki sauk'in wannan jarabar " "Ni d'in Abban Hafiz?" "Yes ke!, Ko da abinda zakiyi ne?" "Na rantse sai naci Uban Aljannan yarinyar nan." "Kidai ci naki!" "Muhseen! Ni kake zagi a gaban wacce ta isa ba?" "Ba zagi ba, ina daf da nad'a miki duka billahil azim Nafidat!" Ina jin yarda Uncle yayi furucin cikin mugun fushi na ji wani k'arfi ya zomin na tashi na fad'a d'akin Fanta na kulle tare da zare key na fad'a saman gado na tura kaina cikin filo na fashe da kuka mai fitar da hucin yaji a ruhi. Na d'auki lokaci ina yin kukan kafin ciwon da marata keyi ya dakatar da ni na koma juye-juye ina ambaton sunar Allah. Jin ya lafamin sai na tashi da k'yar ya bud'e bedside drawer na d'auko tablet na b'alli really extra tare da maganin ciwon mata nasha na koma na kwanta ina mai addu'ar samun sauk'i a cikin raina. Zuwa can na kuma tashi zaune na tsirawa yatsun k'afana ido sunyi bororai,biyu cikinsu sun fashe sakamakon murjesun da Aunty Nafisa ta yi. "Oh ni Deejah wai me nayiwa wannan baiwar haka da zafi ne?" 'Bakiyi mata komi ba tsabar mugunta ce irin nata wanda har jininta bata bari ba.' "Na yarda mugunta ne kuma insha Allah bazata sake ganina a gidanta ba balle ta nemi kasheni. I'm sorry Fanta nasan hakan bazaiyi miki dad'i ba amma dole ne na yi nesa da 'yar uwanki tun batayi ajalina ba." Komawa nayi na kwanta inajin tsigan jikina na tashi alamun zazzab'i zai kamani, tun ina karanta wasik'an jaki har barcin wahala ya d'auke ni batare da na shirya ba. Jin ana tab'amin k'afa yasa na farka nayi arba da Beebah rik'e da almakashi tana bud'e bororan, su Fanta sun kewayeta, ganin na tashi sai duk suka soma jeromin sannun amsawa narik'ayi a hankali cikin dushewar murya. "Uwata sannu kinji?" Na tsinkayi muryan Mama daga nesa. "Mama kinga yar... Sai kuma na fashe da kuka batare da na fad'i abinda nayi nufin fad'a ba. "Please Khadijatu kiyi shiru yanzu Beebah zata gyara wurin ki sami sauk'in zafin." Motsawa Uncle kai nayi ina mai rintse ido jin yarda ciwon ke yimin zafi. Tabbas badan ganin Uncle a wurin ba da ihu zanyi ta zabgawa domin nasan ina da raki, abu kad'an ke sakani kuka haka ciwo komin k'ank'antarsa ina iya yi masa kuka. Kunyar idanun Uncle ya taimaka nayi jarumta amma duk da haka saida nayi k'anin kuka wato kwalla. Bayan Beebah ta gama gyaramin k'afar Uncle ya fita ba jimawa ya dawo tare Aunty Nafisa ta isa gaban Mama ta gaisheta cikin girmamawa wanda na bawa zuciyata cewa Uncle ne ya sakata yinsa dole. Inda na ke ta iso ta yi k'asa da murya tamkar mai rarrashina ta ce "Banyi nadamar k'onaki ba saima nishad'i da na wadata shi, tamakr irin haka zan cigaba da baki assignment har ki gane bakin rijiya ba wurin wasar makaho ba ne." "Nagode Aunty, Allah yayi miki abinda kikayi min." Na ambata yarda kowa zai jiyoni sab'anin nata. "Amin." Su Fanta suka amsa domin d'aukansu addu'a Aunty Nafisa keyimin yayin da a gefenta ta ware ido tana kallona na sakar mata murshi tare da yunk'urawa na mik'e Mama tayi hanzarin rik'oni. "Mamana zan iya takawa fa." "Nasani Uwata, muje  ahakan kawai kinsan bazan barki ki tafi da kanki ba." D'ora kaina nayi saman kafad'unta cike da shagwab'a har da wani tale baki irin na yara. Aikam su Fanta suka saka dariya ina kallo shima Uncle saida ya murmusa ya yin da Aunty Nafisa ta zabgomin harara cikin dibara. Har gida su Beebah suka rakomu tare da Uncle wanda wannan shi ne shigowarsa karo na farko. Har na yi wanka na ci abinci kad'an bisa turasawar Mama tare da shirin barci duk su Fanta na nan basu da niyyar tafiya gida. Duk da inajin barci sabida maganin da nasha har da na sa barci amma sai na zauna ina sauraren hirarsu wanda baki d'aya yake gudana akan bak'in halin Aunty Nafisa. Zuwa can Fiddausi ta kalli agogo ta ce "Kuzo mu tafi dare ya yi kuma gashi gobe zamuyi asubanci." "Gobe zaku koma?" Na cillo mata tambayar. "Eh amma Kano zamu tsaya muyiwa k'anwar Momy kwana biyu sai mu wuce sabida ankoma makaranta musanman sister Beebah da ta ke aikin taimakon al'umma." "Masha Allah sister Beebah ina godiya da kulawarki sosai." "Bakomi Deejah sai dai muna son sanin abinda ya faru kika k'one." "Tsau-tsayi ne kawai, na gama soya kaji na ajiye maid'in, sam namanta da shi kusa dani sai kawai na shuresa shi ne ya zubemin a yatsu." "Ikon Allah, wallahi sadda Uncle ya sanar da cewa tsau-tsayi ne jinsa kawai na yi dan d'aukana aunty masifa ce ta k'onaki ya b'oye gaskiyan dan nasan zata aikata hakan dubi da yarda ta tsaneki babu gaira babu dalili." "Kai Fanta banda k'azafi dai." "Bintu wallahi dan baki san muguntan Aunty Nafisa ba ce shi yasa na ce tare da ku zan koma, na shak'i 'yanci." "To karatun naki fa?" "Wallahi dan shi ne amma ina kammalawa zan dawo gida nagaji da masifa wanda duk girmana wata rana dukana takeyi." "Duka fa!?" Bintu ta ambata idanu waje. "Sosai kuwa dan kawai yanzu Uncle ya saka mata doka ne mai tsauri shi yasa ta daina amma ko 'ya'yan bata barinsu Shan iska da bala'inta." "Ikon Allah amma in haka ne Aunty Nafisa ta fiye fad'a tare da saurin hannu." "Kema kya dai dawo rakiyarta domin ni ce zan bada shaidan haka saboda har yanzu bayana da shedan dukanta." Dik shiru sukayi suna kallon Beebah domin sun tuno lokacin da abin ya faru. Numfashi na sauke a hankali idanuna kulle domin magan-ganun nasu ya isheni saboda bana son kojin sunar Aunty Nafisa balle labarin muguntarta. Jin sun cigaba da tattauna zancenta sai na haye katifana na juya musu baya cikin fatar samun barci ya d'aukeni. Ba jimawa Mama ta shigo ta sanar musu da sutafi gida dare yasomayi, sallama sukayi mata tare da yimin addu'ar samun lafiya suka fice. Jin fitarsu na tashi zaune na tsirawa yatsuna ido ina jin kwallah na cikomin. "Aunty Nafisa bakiyi ba wallahi, Uncle Muhseen bakayi dacen mata ba, Allah ya had'aka da ta gari." "Amin ya rabbi, wata k'ilama kece." Kallon k'ofa na yi idanu waje, Beebah ce tsaye ta sakarmin murmushi tare da k'arasa shigowa ta zauna gefena ta ce "Nadawo in kwana da patient d'ita ce." Kauda kai nayi ina hasko rashin tabbaci akan zance ta. "Hak'ik'a abinda na fad'a bashi ne dalilin dawowata ba, sanin dalilin da ya saka Aunty Nafisa ta k'ona ki ya dawo da ni dafatan zaki sanarmin da gaskiya ba dan na isa ba sai girman Allah." "Waya sanar miki da cewa ita ce ta k'ona ni?" "Babu kowa amma na rantse da girman Allah ko kaffara bazanyi ba ita ce sanadin k'onewar yatsun k'afafunki, in kuma ba ita bace kema ki rantse da girman Allah kamar yarda na yi." "Ita ce, shi kenan kin samu amsan?" Na ambata da sauri cikin kauda kai gefe. "No, ina son sanin dalilin faruwar hakan daga nan ni kuma zan sanar miki da abinda na hasko har ya janyo afkuwan lamarin." Tsirawa Beebah idanu na yi na wasu dak'ik'u, ita kam sai dokamin murmushi ta ke yi, zuwa can na sauke numfashi ta tashi ta isa bakin k'ofa ta kulle tare da tofa addu'a ta juyo muka zubawa juna idanu. "Sanar dani sanadin Deejah." Labari na bata daga sadda suka fice ni kuma na tafi d'ora girki har zuwa inda na farka na sami Beebah rik'e da k'afana. "A she abinda na hasko gaskiya ne to in haka ne ina addu'ar Allah ya tabbatar da shi ko Aunty Nafisa ta yi hankali sanadin rab'arta da zakiyi, dan walalhi Allah d'abi'unki sun burgeni, musanman rashin son hayaniyarki ga uwa uba aiki da ilimi, shi yasa na ce bazanbi su Safina Kano ba zan zauna tare da ke suje su dawo ta nan sai mu wuce gida." "Kai amma nagode da wanna k'auna." Na ambata cike da murna matsananci, wanda naga mamakin faruwar hakan a fuskan Beebah. "Sister Beebah dole inyi murna da ganin mace 'yar uwata a karo na biyu tun mallakan hankalina ta nunamin k'auna cikin kulawa managarci." "Ban gane ba Deejah." "Beebah, idan aka cire Mamana da zuri'ar Baba Umaru to Fanta ce ta farko da na had'u da ita ta k'aunace ni ba tare da yimin kallon banza ba tun mallakan hankalina a matsayin mace baliga haka ita ce ta bar abu mai mahinmanci na rayuwarta sabida ni, kamar yarda kika bar zuwa ziyara domin ki kasance tare da ni, kai wallahi nagode sosai, Allah ya faranta miki sama da wanda kika yimin." "Amin, amma kalamanki sun sakani a duhu zan so sanin labarinki." "Wannan a bayyane ya ke Sister." "To ina saurarenki." Zama na gyara tare da rungume filo sannan na soma cewa... *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/15, 4:59 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin a dona) By Mrsjmoon EWF. *Shafin naki ne Dear Khadija candy  Allah ya tabbatar da nasarori a duk kan lamuranki, Amin.* Page 05 "Gani nan kin ganni gaban Mamana da Babana sai dai ina da 'yan uba masu yawa dan haka 'ya'yan Baba mun kai ashirin da shida amma maza sunfi yawa, mata mu hudu ne kacal kuma dik sunyi aure saura ni na rage banyi ba. Baba na da gida wanda ya kasance na gado inda sauran matarsa biyu suke zaune tare da matan k'aninsa Baba Usman. Nan gidan mallakin Mamata ce domin ta sanarmin ita ta siya kayanta domin gujewa tashin hankali da abokanan zamanta. Na taso cikin so da k'auna musanman wurin mahaifiyata sannan ba abinda na nema na rasa amatsayina ta d'iyar talakawa masu rufin asiri. Na kasance bana da k'awa tun bayan shigata S.S 1 domin a lokacin na soma sanin ciwon kaina kuma a lokacin na soma kasancewa cikin damuwa domin dik wata k'awa ko aboki dana ke dasu a primary zuwa j.s 3 sai suka gujeni suka daina kulani batare da munyi fad'a ba, haka nan kawai suka daina yimin magana sai bisa dole, sun maidani tamkar mai d'auke da cuta, hatta da malamai da suke ji dani saboda hazak'ana sai suka koma rashin sakewa dani sai dai na rik'a kamasu suna satan kallona wanda hakan ke jefani cikin damuwa, na rik'a tunamin cutar da na ke d'auke da shi wanda jama'a suke gudun kada in shafa musu. Na kanyi kuka duk in na keb'e kaina musanman lokacin break inda zan hango 'yan ajinmu na harkokinu da juna amma ni a ware gefe kamar mayya. A cikin wannan hali na kammala secondary school bana da k'awa ko aboki sai wanda karatu ya had'amu ko wanda suke cewa na koya musu abinda basu fahimta ba, suma basa yarda muyi hira ta nishad'i, iyakata dasu yimusu bayani abinda basu gane in nagama suyimin godiya su tafi. Faruwar hakan ya k'ara sanyawa na zamo mara son magana da haniya dukda dama can ina da kayana amma rashin rayuwa da k'awa ko aboki ya taimaka ainun wurin mai dani miskila domin ko a cikin unguwa bana da k'awa, ako da yaushe zaki ganni ni kad'ai ko tare da Mamana, domin hatta da 'yan uwana wanda muke uba d'aya da su basu shiga sabgata wanda wannan bai dameni ba sam saboda zaman doya da manjan da ke tsakanin mahaifanmu na tabbatar ya haifar da hakan. Baiwata na fahimtar karatu tun daga kan na addini har zuwa na boko domin duk ajin dana shiga ni ce agaba da kowa, wannan baiwar ya taimaka sosai wurin d'aukemin yawan DAMUWATA domin duk kad'aicin da na ke ciki bai raunatamin hazak'ata ba saima sake zaburar da ni da ya yi wurin zamemin abokin d'ebe kewa. Na shiga jami'a da burin samun sauyin rayuwa ta fannin samun k'awa ko da d'aya ce tilo domin cikar buruna samun k'awa ko aboki, sai dai anan shima bata sanja zani ba abinda na baro a secondary school da islamiyya shi ne na tarad a nan wanda zance na Jami'ar har yaso fin na can domin a nan ina fuskantan harara tare da tsaki duk in muka had'a ido da mace 'yar uwata musanman irin masu ji da kansu d'innan d'iyoyin masu fad'a aji, duk in hakan ya faru da ni murmushi na ke yi amaimakon b'ata rai hakan kuwa na tunzirasu suyi ta son na kulasu dan su tijarani a bainar jama'a ni kuma da nagane ta ke ta kensu sai na bawa banza ajiyarsu, na zame musu tamkar kurma wacce bata fahimci manufarsu ba sai dai abin na k'onamin rai. Sai dai game da samari wannan fannin ina samun sassauci domin basamin mugun kallo sai kallo na k'urillah wanda natsaneshi ainun, wanda na ke ambatarsa da kallon hango munina domin kallo ne irin na cutarwa wanda musulinci ta yi hani da shi domin ina muzanta duk in naci karo da sunayimin sannan takaicin bazasu tab'a yimin magana ba sai isata da kallo, na kansamu wasu su rakani da murmushi wasu kuma kallon ne tsabarsa kamar tsoffin mayu. Duk wannan Damuwar da na ke ciki na kad'aici ban zauna na sanar da Mamana ba saboda na san tafi ni Damuwa da DAMUWATA ma'ana in har na sanar mata zatafini shiga damuwa sannan idan na dawo gida tana bani lokacinta wanda ya ke wankemin Damuwar da na d'ebo a waje. Mamana itace ta zamemin k'awa, abokiyar d'emin kewar rashin k'awaye da dukkan budurwa ke burin samunsu a rayuwa. Sadda Fanta ta shigo rayuwata sai na kuma samun k'awa abokiya ta gari duk da tasha wuya kafin insoma kulata wanda mukan had'u a hanyar zuwa islamiyya da Tahfiz, ta yi ta jana da hira ina amsawa cikin rashin sakewa har a k'arshe muka d'inke gam kamar yarda kika gani. Lokacin dana fahimci Fanta nayimin k'auna wanda na rasa abaya wato k'awa na shiga nishad'i ainun, wanda a dalilin hakan yasa na sanar da Mama dukkan DAMUWATA tun daga lokacin dana soma fuskantan rashin abokan mu'alama a waje da makaranta sai dai abin da na ke gudu shi yafaru domin Mama tashiga damuwa inda ta d'auki kwanaki tana maganar lamarin wanda na yi danasanin sanar da ita domin ban cika son mai-maita zance ba, idan abu ya wuce to ya wuce kenan a gareni. K'aunata da Mamana na daban ne wanda zance banga wata d'iya da Mahaifiyarta ke jiyo DAMUWATA ko farin cikinta ba kamar yarda Mamana ke jiyo nawa. Lokuta da dama na kan zauna ina nazarin faruwar hakan amma a k'arshe sai na d'inauce na rasa gano dalilin. Hak'ik'a nima ina son Mamana domin ita ta koyar dani k'aunarta tun bansan kaina ba tamkar yarda ta zamo ita ce malamata na farko a fannin ilimin addini." "Masha Allah da samun managarciyar uwa kamar Mama." Beebah ta ambata cikin murmushi. "Godiya nake sister." "Mention not dear cigaba ina saurarenki." Gyaran murya nayi na d'ora "K'awancenmu da Fanta hak'ik'a ina alfahari da shi domin a lokacin na gano samun abokin hira sa'anka na sanya natsuwa sama da komi. A haka na cigaba da rayuwa cikin godiyan Allah domin a yanzu bana tare da Damuwar rashin abokin tattauna lamurana tunda na samu Fanta dik da ba komi na ke iya sanar da ita ba makar yarda bana iya sanar da Mamana dik kan DAMUWATA har kwanar gobe lamarin da ta ke kan yimin fad'a da in daina domin bai da kyau sam. A yanzu haka na kammala Jami'a inda na samu Degree d'ina akan harshen turanci haka na yi bautar k'asa na kammala cikin nasara sannan na yi saukan Al'qur,ani mai girma tare da haddarsa da kuma wasu littafai na addini wanda Mamana ta jagoranci karantar da ni tun ina k'arama daga bisani na k'ara gogewa a gaban malamai. Mamana nada ilimin addini sosai da na boko daidai misali, shi yasa muke rayuwa cike da wayewa. Baba kuwa na addini gareshi domin shi malamin zaure ne wanda bai barin d'iyoyinsa yin karatun boko mai zurfi dan Mata daga Primary suke tsayawa Maza kuwa daga secondary domin suna kallamawa suke kama sa'anar hannu dan ba wanda yanemi gadar Baba a fannin malumta sai babban yayanmu Auwalu. Ni ce kad'ai na samu yin karatun Boko mai zurfi har zuwa matakin Jami'a, wanda bansan dalilin faruwar hakan akaina ba sai dai wani lokacin ina danganta rashin jituwana da Babana na da nasaba da zurfin karatuna tunda kaf d'iyoyinsa ba mai ilimina maza da matan, ba alfahari ba har zuwa na addini ba wanda ya kaini domin ni ce kad'ai na haddace Al'qur,ani cikinsu amma Mazan unyi sauka a gabansa Matan kam ko saukan basa samun damar yi ya keyi musu aure. "Ikon Allah amma kin more kam Allah yayiwa iliminki albarka." "Amin tare da naki." Na amsawa Beebha cikin murmushi. "Amma sai dai ban gane Rashin jituwar dake tsakaninki da Mahaifinki ba?" Shiru na yi ina lalibo amsan da zan bata domin ciki ba anyisa dan cin abinci bane kad'ai har da ma'adanar ajiye sirruka. "Ok just ignore it." Na yi Beebah ta ambata a hankali. Ajiyar zuciya na sauke cikin jan hamdala a ruhina dan ko Fanta da ta ke ganin komi a idanun ta ban tab'a yin maganar da ita ba haka itama bata tab'a tambayar dalilin faruwan hakan ba. "Uhm Nana Khadijatu fad'in Uncle Muhseen." Na kuma tsinakayar muryanta daf da kunnina murmusawa na yi tare da cigaba da cewa "Na yi training a catering school inda na samu kwarewa a fannin girkin zamani da had'a snacks dan na gargajiya wannan Mamana itace malamata tun inayi bai nuna har na zamo gwana." "Masha Allah, a fannin aiki fa?" "Nasoma karantarwa a wani Privet Shool amma yanzu na bari, sakamakon 'yar tsaman da mukeyi da yaron mai makarantar yasa na ajiye masu aikinsu. Haka nan mutumin ya d'uaki karan tsana ya d'oramin domin ko magana bai had'amu amma a kullum zak'ulo laifina ya keyi yana tozartani a bainar jama'a, gani da saurin kuka, da girmana na yi ta zubda hawaye d'alibai nayimin dariya akan haka Mama ta maramin baya na bar musu aikinsu. Kuma tunda na bar makarantar ba wanda ya waiwayeni da ban hak'uri akan haka naji banson sake yin wani aiki ko wani iri ne duk da ina da takardu masu kyau, idan nace zan nema bazan rasa ba. Yanzu dai ina koyar da karatun Hadda a makarantar Tahfiz da na yi bisa tursa-sawan Mama wai wannan ta addini ne zan sami lada tunda Malaman suka biyoni gida to in je. Ba dan nasoba na soma zuwa, shi bana fuskanta matsala illa ta kallon nan da maza keyimin tamkar mai d'auke da lalura sannan muna hira da malamai jefi jefi, abu d'aya ke damuna a makarantar yawan hayaniyar yara domin abinda na tsana na farko kenan hayaniya dan na sakamin ciwon kai mai zafi, haka zalika kallon banza da mata keyimin duk in na shiga taro ko had'uwa da su a wani sabgar bai sanja ba, ako da yaushe DAMUWATA shi ne sanin dalilin faruwan lamuran biyu da suka kewayeni wato kallon da Maza keyimin na k'urulla da kallon da Mata keyimin na wulak'anta, shi yasa sadda ku ka shigo gidanmu na hango kulawanku gareni nashiga nishad'i ainun sannan gashi yanzu kin kuma tabbatarmin da hakan ta hanyar nunan k'auna tamkar yarda Fanta ta nunamin a baya." "Ikon Allah hak'ik'a rayuwarki Deejah da a baben mamaki cikinsa sannan ina hasko lauje cikin nad'i amma ko meye shi ina rok'on Allah yasa khairan ne domin ba kyau danganta lamari da wani abu daban wanda ba khairan ba ne sabida wani abin daga Allah ne." "Ina godiya da addu'a tare da nasiha akan yarda da k'addara mai kyau ko kishiyarta." "Bakomi sister, Allah ya shige mana gaba." "Amin." Munyi shiru na wasu mintoci sannan Beebah ta kuma cewa "Deejah kin gama bani labarinki a tak'aice amma har kika kammala banji kin ambaci Saurayinki ba." Idanu waje nake kallonta ta kyalkyale da dariya na yi hanzarin kulle mata baki ina kallon agogo cikin cewa "Sister dare fa ya yi." Motsa kai ta yi cikin murmusawa ta ce "Ina saurarenki." "Wai Beebah ke yar jarida ce ko marubuciya?" "Babu ko d'aya." "To in haka ne dan Allah ki rabu dani da wannan tanbayoyin naki, kuma wannan uban surutun da kika sakani na yi shi ne kike kira da tak'aitaccen tarihi." "Eh mana domi in nasoma baki nawa sai mun kwana munyini ban gama ba." Sa ke ware idanu na yi ta kawo yatsarta kamar zata sakamin a cikin ido na kulle da sauri, mukasaki murmushi a tare. "To bani naki ina saurarenki." "Wasa na keyi miki ni bani da labarin komi sabida komi na ke muradi na sameshi abokai maza da mata, 'yan uwa na gari tare da iyaye masu k'aunar farin cikinmu. A ittifak'i Aunty Nafisa ce kawai ta fita zakka a zuri'armu dan ita ta taso da fad'a tare da kyashi, hakan nan ita mai... D'aga mata hannu na yi da sauri ta dakata tana kallona, juya kai gefe na yi "Dan girman Allah kada ki sake yimin maganar Aunty Nafisa saboda a duniya itace ta biyu da naji banson ko jin muryanta balle sunarta." "Waye na farkon?" "Sirri na ne dear Beebah." Na ambata cikin dafa kafad'arta. "Ok nadaina sonji kuwa." "Godiya na ke da hakan." "Uhm da wayau dai kin kori zancen Saurayinki ko Deejah?" "Bani da shi kuma ban tab'a yinsa ba." "Ban yarda ba kawai kina b'oyemin ne domin Fanta ta sanarmin bakya da sabo haka kina da zurfin ciki wanda har Mama kina yiwa." "Eh na amince duk abin da kika ambata halina ne amma ki sani ke banyi miki ko d'aya ba, in baki yarda ba gobe ki tambayi Fanta idan na tab'a sanar da ita wad'an nan labaran duk dad'ewarmu da ita." "No basai na tambayeta ba, na yarda kin bani matsayi na daban a rayuwarki kamar yarda nima na baki dan hak'ik'a ina k'aunarki Deejah k'auna irin ta tsakani da Allah." Rungumeta na yi da sauri ina jan siririyar dariya, itama dariyar ta keyi. Mun raba dare da Beebah muna shan hira, barcin dake damuna tuni ya tafi kam dole. Bayan ta idar da Sallar subahi domin ni ina fashin sallah, na dubeta cikin hasken da baiwadaci d'akin ba na ce "Sister sanar dani abinda kika hasko jiya wanda ya saka Aunty Nafisa ta k'onani." Tasowa tayi daga saman sallayar ta dawo kan katifa ta rik'o hannuna ta ce "Na hasko Uncle Muhseen na sonki shi ne dali... "So! Kuma? Wacce irin so?" Na katseta da sauri idanu waje. "It's may be na au... "Dan girman Allah Beebah mubar maganar, rik'e abinda kika hasko a ranki na fasa jinsa." Ina ambatar haka na zame na kwanta tare da juya mata baya, k'irjina kuwa sai harbawa ya keyi. "Tabd'i jan kishi da Aunty Nafisa, ai abinda ma ba zai yiwu ba ne, ya Allah ka tsareni ji da ganinsa." "Ba amin ba." Jin maganar Beebah yasa na gano zancen da na keyi a zucci ya fito fili kenan. Shiru na yi tamkar mai barci alhalin idanuna biyu. Saukan hannun Beebah a bayana yasa na sauke numfashi ta rik'e arm d'ina ta soma magana cike da natsuwa yarda ko banso dole su shiga kunnuwana. "Khadija wallahi Allah na hango k'aunarki a idanun Uncle Muhseen, kuma na yi murna sosai domin na sha jin Momy na addu'a akan Allah ya shirya mata Nafisa tare da bawa mijinta mafita akan bak'in cikin da yake kwasa akanta, nima danaji haka sai na soma tayata addu'a saboda na tsani mugun hakinta na rashin jituwa da dangin mijinta. Wannan dalilin ya sanya tun jiya dana hango kin fito daga motarsa tare da yarda fuskan Aunty Nafisa ya koma na amincewa ruhina kece mafitarsa kuma addu'ar mu ta karb'u." Na juyo zanyi magana ta d'agamin hannu tare da cigaba da cewa "Ina mai baki shawara da ki amince da zarar ya ambata miki asirin ruhinsa, sannan idan har Allah ya nufa kika zamo matarsa wallahi kinyi miji na kere sa'a son dukkan d'iya mace ta sameshi a matsayin bokin rayuwar duniya har da lahira saboda yarin nagartansa a fili suke, na tabbata kema kin sansu." Lumshe ido na yi ina jin tsigan jikina na tashi, abin mamaki sai naji tamkar in bud'e ido na yi arba da Uncle a zaune gabana kamar yarda Beebah ta ke yanzu. "Deejah kince baki son sanin labarin Aunty Nafisa da na baki labarin fitinarta wanda ya kai mutanen gida basa murnan zuwanta ziyara itama hakan da ta lura da shi yasanya bata zuwa sai bayan shekara-shekara amma kinga Uncle yana zuwa dik k'arshen wata ko sati biyu sabida harkan kasuwancinsa yana da k'arfi a Maiduguri, haka yana kawo yaransa su Hafiz ganinmu duk in an sami hutun makaranta, yana da kyaky-kyawan fahimta da danginmu sama da jininmu Nafisa. Na ji kakarmu Hajiya Babba na cewa Aunty Nafisa irin mutanen ne da Allah ya halitta tsiya na ganiyar shed'ancinta dole muyi hak'urin zama da ita a haka." Ban san sadda na kyalkyale da dariya ba jin abinda Hajiya Babba ta ambatawa Aunty Nafisa. Ita ma Beebah dariyar kyalkyale da shi "Madallah da wannan safiya mai cike ni'ima." Muka tsinkayi muryan Mama daga bakin k'ofa, cikin murya mai cike da nishad'i na ce "Amincin Allah ya tabbata ga Mamana, abin alfaharina." "Amin Uwata farin cikin Hureratu." Sakkowa na yi na yaye labulen na rungume Mama wacce ke tsaye a bakin k'ofa tana jiran fitowana domin lokuta da dama haka takeyimin, ta kance koyarwar Ma'aikin Allah S.A.W ta ke bi na neman izini shiga wuri kafin bayyana. "Ina kwana Mama?" "Muntashi lafiya Habeebah?" "Lafiyalau Mama." "Masha Allah, ya kuma gajiyar hiran jiya? Dan najiyo Uwata batayi barci da wuri ba." Kulle baki Beebah tayi tana dariya k'asa-k'asa. "Uwata ya k'afafun?" "Sunyi sauk'i sosai Mama." "Masha Allah, nagode Habeebah da taimako." "Kai Mama ai Deejah tamuce tunda masoyiyar Fanta ce." "Haka ne, Allah ya biyaku da khairan ita kuma Nafisa Allah ya shiryata." "Amin." Beebah ta amsa yayin da ni kuma na jefowa Mata tambayar "Mama wa ya sanar miki da itace ta k'onani?" "Mijinta kuma darajarsa taci wallahi da sai na koya mata hankali, ina da hak'uri amma akanki ban san kalmar ba, gidanta dai kingama shiga insha Allahu." "Ayi hak'uri Mama kada Aunty Nafisa ta raba zumuncin nan tasu da Fanta." "Wannan ne kam bata isa ba Habeebah, Allah da ya had'asu shi ya isa ya rabasu ba ita ba." "Yawwa Mamanmu haka na ke son ji." Murmushi Mama ta yi tare da ficewa, muka biyo bayanta ta shige kitchen ni kuma na soma gyara gida Beebah na tayani, muna gamawa muka koma kitchen muka amshi Mama aikin had'a abin k'aryawa. Kafin bakwai da rabi mun gama komi, mukayi wanka, na bawa Beebah kayana sabbi ta saka sannan muka zauna karyawa inda ruwan tea kawai nasha saboda ban son karyawa da sas-safe ya yin da Beebah ta baje ta cika tumbinta ba wani bak'unta. Sake yimin dressing d'in ciwon Beebah tayi tare da matsamin nasha magani dan cewa na yi tunda ya soma k'ak'ewa ba zan sha ba. Misalin k'arfe tara saura kwata na shirya dan zuwa makarantar Tahfiz inda na ke koyarwa, Mama taso hanani dubi da ciwona na nuna zan iya zuwa, Beebah ta biyoni muka fito muna hira cike na natsuwa. Kafin mukai Bintu ta kirata ta sanar mata da cewa sun wuce Kano ta yi musu fatar dawowa lafiya ta bani wayar nima nayi musu addu'a. Muna shiga makarantar abokin koyarwana kuma classmate d'ina dan tare mukayi karatun hadda amma ya girmeni sosai wato Aliyu Muktar, shi ne ya dubeni cikin murmushi ya ce "Malama Deejah yau da bak'uwa kika zo mana?" Kallon shi na yi kamar zan amsa masa sai na sami bakina da yin nauyi, jin haka sai na wuce na bar Beebah tsaye da shi. *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/16, 11:08 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) Mrsjmoon EWF. *Shafin na my Billy Galadanci ne, Allah ya bar zumunci tare da yalwatuwar nasara agareki mara iyaka, Amin* Page 06. "Kayi hak'uri haka Deejah ta ke sam bata da sabo musanman ga Maza." "Ni ne shaida akan wannan halin na Khadija, tsawon shekaru da muka shafe muna karatu a cikin aji d'aya amma bamu tab'a maganar da ta wuce na mintoci biyu ba sai ko in karatu ne ya had'amu shima sai wurin muraji'a ko amsarwa juna hadda." "Lallai kai ne ya dace ka sanar da mutane rashin sabonta ba wai asanar da kai ba." "Uhm k'awar malama Khadija na tsareki da surutu, gashi har ta b'ace miki." "No bakomi, dama rakiya nayo yanzu dai ka bani wurin zaman da zan dakaci fitowarta." "Ok muje daga can in ban takuraki ba na tayaki hira kafin lokacin shiga darasina ya yi." "Aikam ina godiya da karamcin nan, abokin Deejah." "Aboki kuma?" "Eh." "Ina, ai ban isa na zamo abokin Malama Khadija ba saboda ita d'in kayan manya ne irin Sarakuna d'in nan masu fad'a abi dole ko da rai bai so ba." "Kai Abokin Deejah, duk ita kad'ai." "Allah kuwa Khadija ta da bance, samun irinta cikin Dubban Mata sai antona domin sauraren kalaman da suke fitowa daga bakinta kawai zai bawa mutum amsar cewa ita d'in ba sa'ar zancen yara irinmu ba ce ko manyanma sai wanda Allah yayiwa gamdakatar." Dariya sosai Beebah ta sanya wanda hakan ya janyo hankali wasu malamai tare da d'alibai. "K'awar Malama muk'arasa wurin kada nasamu kira daga hukumar makaranta ace ina zance cikin tsakiyar makaranta." Motsa kai ta yi tana d'auke dariyar, suka jera cike da wayewa. Aliyu ya dubeta kad'an ya ce "Sunana Aliyu Muktar." "Masha Allah, ni kuma Habeebah." "Wow my Aunty, domin sunar babban yayarmu ce wacce muke Baba d'aya. "A she ina tare da k'anina" Motsa kai ya yi batare da ya furta kalma A k'asar bishiyar magoro ya yi musu masauki saman kujerun roba, ganyen bishiyar na kad'awa cikin fitar da iska mai gamsarwa, hira suka cigaba da yi cike da sakewa tamkar sun jima da sanin juna. *** Misalin k'arfe shabiyu saura mintoci goma na kammala koyar da aju-juwan danake shiga, na fito ina raba ido dan neman inda zan hango Beebah. "Malama, Malam Auwal yana kiranki." Idanu na zubawa matashiyar yarinyar tamkar ban gane abinda ta fad'a ba. "Malam Auwal ne ya ce in kira masa ke, yana office d'insa tare da su Malam Bashir." Motsa kai na yi, yarinyar ta bar wurin, najima tsaye batare da na motsa ba. "A'a Malama Khadija kina lafiya kuwa?" Saida nayi gaba kad'an sannan ta amsa "Ina lafiyalau Malam Hassan, dafatan kaima haka?" "Alhamdulillah" Ya amsa cikin nufar office d'in shugaban makarantar tamkar badani yake maganar ba alhalin shi ya soma.kulani, tsaki na ja a cikin raina tare da nufar office d'in nima ina k'issima dalilin kiran da a keyi min. Office d'in cike da malamai na samu domin malamai shida ke ciki gami da shugaban makarantar bakwai, na zauna tare da gaisar da su a jam'i suka amsa, shiru ya ratso wurin zuwa can na tsinkayi muryan mataimakin shugaba Malam ishaq ya kira sunana, ban amsa ba illa idanu da na d'ago na zuba masa gabana na fad'uwa. Sake kiran sunana ya yi alamun yana buk'atar amsawana, amsawar na yi a hankali, ya yi gyaran murya tare da cewa "Shugaba Malam Auwal ya kiraki ne domin ya nemi alfarman da ki cigaba da koyarwa regular saboda wasu daga cikin malamanmu sun sami takardan cigaba da karatu a k'asar misra, idan sun tafi zamu fusakanci karancin Malamai shi yasa mukaga dacewar ki dawo koyarwa full, dafatan zaki amsa k'ok'on bararmu da hannu biyu?." Wani dim na ji saboda burina na bar koyarwan baki d'aya sai ga wani batu sabo. "Dan Allah Malama Khadija ki amince sabidya muna da bukatarki ainun, d'alibanmu na gane koyarwanki haka iyayensu na alfahari da hakan makarantarmu na samun d'auka ta wannan fannin, dan Allah kada ki watsa mana kasaya idanu." Shiru na yi ina sauraren magan-ganun Malaman wanda duk kaninsu saida suka tofa albarkacin bakinsu ta hanyar rok'on amincewana a k'arshe suka tsuke bakunnansu suna dakacen amsana. Na d'auki mintoci kusan uku kafin na ce "Zanyi shawara da mahaifiyata." "Allah yasa muji alkhairi." Shugaba Malam Auwal ya furta cikin saukemin kallon k'urillah wanda na tsana. "Amin." Duk suka amsa. Sallama na yi musu na fito sai dai ban ga Beebah a inda na barta d'azun ba, tsayawa na yi ina nazarin inda ta shiga, maganar Malam Hassan ya sa na juyo ina nemo amsan da zan bashi akan tambayar da ya yi min. 'Me yasa bakya alfahari da abin adonki Malama Khadija?' Tambayar nasa na sake maimaitawa a raina ina son sanin ma'anar kalman ABIN ADO daya ambata. Tamkar kuwa ya shiga raina najiyo yana yimin fashin bak'in manufarsa "Manufata shi ne me yasa ba kya danganta kanki da Mahaifinki sai dai a koyaushe Mahaifiyarki kike ambata a muhallin Mahaifinki alhalin ita d'in k'asa ta ke da shi ta kowani fuska tun daga halitta har zuwa girman matsayi wanda Allah ya bashi akan sama da nata dan mace bata tab'a jagorancin d'iyoyintaba sai da tsayayyen namiji." "Malam Hassan kana da k'arancin sani akan muhimmancin Mahaifiya ga d'iyoyinta, tabbas Allah ya S.W.A ya fifita halittar Namiji akan Mace amma a wurin girman matsayi ta fannin biyayya sai ya fifita halittar Mace domin sai da ya ambata da abita sau uku kafin ya ambaci uba kaga kenan ba'aibu ba ne dan na ce zanyi shawara da mahaifiyata, ka san ko masu iya magana sunce ciwon 'ya Mace na 'ya Mace ce." "Haka ne, kina da hujja mai k'arfi Malama Khadija amma kisani ba kowa ne zaiyi tunanin karatun da kika tunasar dani yanzu ba saboda bayan fitarki k'orafin yarda kike yawan ambaton Mahaifiyarki akan lamuraki sama da Mahaifinki alhali shi d'in jagoran al'umma ne, masanin ilmomin islama abin alfaharin dukkan 'ya'ya a ce shi d'in mahaifinsu ne, wannan dalilin yasa na ce zanyi miki tambaya kuma na gamsu da bayanenki Allah yasa mugama da mahaifanmu lafiya, musanman Uwa." "Amin." Na amsa a tak'aice tare da barin wurin cikin jin wani yanayi na rashin jin dad'in cece-kucen da sukayi akaina bayan fitna. 'Dole in bar makarantar nan dan bazan juri gulma ba.' Cikin zancen zucci na isa bakin gate batare da na nemo inda Beebah ta mak'ale ba. "Kinganni zaune anan ina dakon fitowarki domin Aliyu ya sanarmin da kin gama darasinki." Kallon inda ta ke zaune na yi gefen bencin mai saida kayan fruits, da hanzari ta taho ta rik'emin hannu cikin rawar murya ta kuma cewa "Ke da waye Deejah?" Girgiza mata kai na yi ta motsa hannuna da k'arfi, na kulle ido ina jan hailalah a cikin ruhina. "Oya tell me! Waya tab'aki? In tafi na ci masa k'aniya." "Ba kowa Beebah kawai gajiya ne, mutafi gida kada mutane su taru kinsan abin kallo baiyiwa jama'a wahala." "Ki sanarmin da damuwarki K'awata."  Ta ambata amma cikin rad'a. Dukan kafad'arta na yi cikin sauke mata murmushin yak'e sabidya yarda ta yi maganar takomamin sak Aminiyata Fanta, mai damuwa da DAMUWATA. "Jini baya b'uya." Na furta mata a hankali, ta murta dan ta fahimci inda zancena ya dosa. Hannunta na ja muka isa wurin mai saida fruits, yana ganina yasoma zubawa a leda murmushi ne ya kubcemin ganin abinda keyi wanda faruwan hakan ya tabbatarmin ya gama gane abubuwan da na ke siya duk in na shiga makaranta. "Gashi Malama." Amsa nayi tare da bashi kud'insa ya duba ya gyad'a kai, Beebah ta amshi ledar muka nufi bakin titi. Muna cikin Napep Beebah ta cikani da labarin Aliyu Muktar na dubeta kad'an ina k'unshe dariya saboda na san abin da zan fad'a dole yasanya ta barmin kunni ya huta. "Nafahimci Aliyu ya mallake zuciyar 'yar mutanen Barno." Aikam d'if ta d'auke zancen na saki siririyar dariya ina kallon idanunta ta had'e rai, sai na juya kaina gefe ina kallon titi domin haka na ke so. Bayan mun watsa ruwa muka isa farandan Mama ta gabatar mana da abincin, shinkafa mai miya da salad, mukaci sosai tare da korawa da kunun aya mai sanyi. Tashi na yi zuwa d'akina Beebah ta rufamin baya, ina zama gefen katifa ta janyo kujerar kwalliya ta zauna tana wani cin magani dariya na kyalkyale da shi. "Wato na zame miki mahaukaciyar ko Deejah?" "No K'awata, kawai nagani ne fushin sam baiyi kyau da kyak-kyawar fuskanki ba." Murmushi ta saki na jinjina mata hannun ta kama ta rik'e gam tare da cewa "Aliyu Muktar ke yake so ba ni ba." "So?" "Eh so tare da k'auna, Aliyu keyi miki kuma na gamsu da halayyansa d'ari bida d'ari dan haka ina baki shawara da ki amshe-shi a matsayin your first love, insha Allah bazakiyi da kin sani ba." "Yaro ne shi Beebah, bana son b'atawa kaina lokaci." "Kada ki butulcewa rahman Allah Deejah, domin Allah ne ya amshi rok'onki a yau kika sami wanda ya ambata miki kalman So wanda kike muradin jinsa da jimawa." "Nagodewa Allah, Allah ya sanya khairan a tarayyanmu." "Amin ya rabbi, haka ya kamata ki ambata ba wai zancen yarinta ba." Sosa tsinin gancina na yi tare da gyara zama na ce "Beebah ya akayi Aliyu ya sanar miki da yana So na?" "Labarin tsarin rayuwarki mukeyi wanda ke burgemu musanman rashin hayaniyarki da gudun abin magana, shi ne ya sanarmin da sirrin ruhinsa akanki wanda ya ce kusan shekara d'aya kenan yake burin ya sanar miki amma kwarjininki na yi masa shamaki sai ya kasa tunk'ararki da zancen, ganina tare da ke ya bashi kwarin guiwar sanarmin." "Kwarjini kuma?" "Yes Deejah, kina da kwarjini na ban mamaki wanda shi ne dalilin da ya sanya maza ke shakkar tunk'ararki da kalman So dan ba Aliyu kad'ai ke shakkar furta miki kalman ba hatta da shugaban makarantar tare da mataimakinsa dama wasu malaman duk sun kasa kallon idanunki su ce suna sonki." "Ikon Allah, to ke wa yasanar miki da wad'annan bayanan?" "Aliyu, dan ya ce da kunnuwarsa yaji suna tattauna zancen, lamarin da ya sanyashi k'amar jinya amma ganin lokaci ya ja bawanda ya iya tunk'ararki sai ya sami natsuwar ruhi, shi ne yau ya sanarmin domin inyi masa jagora da ki kulashi ko da cikin tsokali ne." "Uhm to zan kulashi amma dai ina jiyowa ajikina kamar lamarin ba zai d'ore ba." "Saboda me yasa kike son jifan lamarin da mugun fata?" "To na yi shiru." "Hakan ya kamaceki dama." "Aliyu ya sami 'yar campaign a bulus." "Eh naji dai kome zaki ce." Juya kai na yi inajin natsuwar ruhi na ganin a she bana da cutar komi tunda gashi an sami wanda ya furtamin kalman k'auna abin da najima ina tsumayen jinsa a bakin Namiji. "Aminiyar Fanta ko bakya son Aliyu ne?" "Ta ya zan iya amsa miki wannan tambayar alhalin ni ban san ya kalman ta ke ba tun tsawon rayuwata." "Deejah zaki sani da yardan Allah domin na hango tarin k'aunarki mara algus a idanun Aliyu." "Uhm Allah ya sa hakan ne." "Amin." Lumshe ido na yi cikin son yin barci amma sai maganar da mukayi da Malam Hassan ya bijiromin na bud'e ido da sauri Beebah ta sakarmin murmushi cikin cewa "Yanzu bakiji kunya ba da kika ce Aliyu yayi miki yaro?" Kulle ido na kumayi cikin murmushi batare da nace komi ba. "Aliyu ba yaro ba ne, ya sanarmin shekarunta talatin da uku, shi ne babba a d'akinsu, yana da k'anni uku mace d'aya maza biyu da kuma wata wacce suke abokan wasa da Hajiyarsu ta rik'e amma ita ta yi aure. "Tabbas nasan lokacin aurenta, dan naso zuwa Allah bai nufa ba." "Kinga kenan inda a k'auye ne da yanzu ya kusa ajiye suriki." Duka na kai mata jin sharrin da ta zabgo. Dariya muka sanya. Zuwa can ta mik'e ta dubeni na d'auke kai. "Malama ta so muje na gaida Aunty Nafisa kada ta kai k'arata fadar Momy ko Alhaji Babba." "Sai kindawo amma ni Deejah na gama shiga gidanta insha Allah." "A she zancen bai wuce ba kenan?" "Ya wuce amma dai yatsuna har yanzu zugi sukeyimin, kinga ko da ya wuce a raina to a cikin fatana da sauran miki." "Kina da gaskiya Deejah kuma kin burgene da kika zamo mai fad'ar gaskiyan ruhinki, bari in tafi zuwa dare zan dawo, me kike son in dafo miki?" "K'awata Fanta da mai da yaji." Dariya ta kyalkyale da shi ta fice tana dariyar, murmusawa na yi na koma na kwanta na tsirawa ceiling ido, zuwa can na kulle su. Cikin barcin da yasoma d'aukana najiyo sababin Baba na bud'e ido da sauri tare da tashi zaune ina jan hailalah jin muryansa ya nufo k'ofar d'akina. Ina sauke kallona kan bulalan dake hannunsa na daka tsalle sai cikin toilet kafin in kulla ya ritsani ya rizgoni na dawo tsakiyar d'akin, wani tsalla na kuma dakawa na fad'a jikinsa na cukui-kuyeshi. Gam na ji ya rungumeni har ina jin numfashi nayimin wuyar fita. "Malam!" Na tsinkayi muryan Mama cikin tsawa. Tureni ya yi da sauri tare da daga bulalan zai zubamin Mama ta rik'e cikin wani lakan murya wanda bansanta da shi ba ta ce "Ficemin a gida na barka bari na har abada Malam, sadakinka zan bawa Baba Umaru ya baka kamar yarda ka bashi ya bani. A yau na tsaneka Malam tsana mafi mu... Kullewa Mama baki na yi jikina na rawa ta ture hannuna abakin nata, kafin ta sake furta kalma na kuma kulle mata baki cikin cewa "Baba shima abin adona ne Mama ki barshi ya hukuntani wata k'ila laifi na yi masa." "Malam ba abin adon ki ba ne Uwata, Ni ce abin adonki kuna ki barni na kwatar nama 'yancinmu, wallahi na gaji da lamarinsa, daga yau nagama aurensa." "Mama ki daina fad'ar haka dan girman Allah." Na ambata cikin matsanancin kuka. "Na daina, kuma na hak'ura saboda kwanciyar hankalinki Uwata." Rungume Mama na yi cikin jan hanci ita kuwa ta soma shafan bayana tamkar tana rarrashin yarinya 'yar yaye. "Nagode Hurera da kalan halaccinki, nagode k'warai." Muka tsinkayi muryan Baba ya ambata cikin shak'ewar murya. Da kallo muka rakashi har ya fice d'akin. "Mama me na yi masa ya tsaneni?" "Zan sanar miki da mafarin komi Uwata, wanda baici ya zama hujja ba ga mutum mai hangen nesa ." "Ina saurarenki Mamana." Shafo fuskana ta yi cikin b'oyemin b'acin ranta wanda ni kuma na karantosa amma sai na nuna  bangane ba, na sake shigewa jikinta ina sauke numfashi, a haka ina manne a jikinta muka fito daga d'akina zuwa d'akinta. *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/17, 3:35 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Safiyya (Mrsjmoon) *Shafin na d'aukakin masoya labarin DAMUWATA ne, Allah ya biya muku bukatunku na alkhairi ya baku yalwan arziki daga cikin tarkokin arzikinsa. Ina sonku har cikin Ruhina.* 07 "Uwata ki k'ara zamowa mai juriya akan lamuran Malam, insha Allah zai zame miki alkhairi." "To Mamana amma sanar da ni mafarin da Baba ya tsaneni." "Kibar zancen Uwata wata rana ba sai kin tambayeni ba zan sanar miki." "Mama dan Allah ki fitar da ni a duhu game da lamurana da Baba." "Uwata kinsan na sanar miki zan baki labarin kaina ko?" "Eh Mama." "To mafarin tare suke da labarina" Shiru na yi alamun ina son sani na dai k'yale ne kawai saboda bana cikin masu naci akan abu. "Ina rok'onki Uwata ba dan ni sai dan wanda ya yi halittarmu cikin isa da mulkinsa wato Allah S.A.W da ki bar zancen nan in lokacin ki sani ya yi zansanar miki batare da kin nemi sani ba, ko d'azun natsuwarki na ke son gani shi yasa na ce ki taho kiji amma ba manufata na sanar da ke abin da kike burin sani ba, dafatan zakiyi hak'urin zuwar lokacin dana d'iba?" "Shikenan Mama abin da kikace shi zanbi kuma zan dakaci zuwan lokacin da yarda Allah." "Da kyau Uwata alfaharin Mamanta." Murmushin na yi ganin yarda Mama ta yi maganar ta sigan wayon da ake yiwa yara dan su manta da abu. Dik yarda ran Mama ya b'aci haka nan ta danne ta soma yimin hira mai sanya nishad'i, nima ganin hakan sai na sake na nuna mata bana tare da damuwar komi sannan wannan damar nabi na sanar da ita abin da ya faru game da buk'atar malamai na son in koma koyarwa kullum amaimakon a sati sau biyu dana ke zuwa. "Uwata inaga ki sanar da su kin k'ara kwana d'aya akan kwanaki biyun da kikeyi sai ki koma shiga sau uku a sati Asabar, Litini da Laraba." "Wallahi nima hakan na raya a raina Mama." "To kingani, dama na hango rashin son hayaniyar da bakiso ne, haka zanso ki huta ba wai ace kullum kina zaryan fita ba." "Mamana ta kaina, kina son Deejah ta huta alhalin itad'in ba 'yar hutu ba ce." "Inji wa ya ce miki ke ba 'yar hutu ba ce?" "Ni na fad'awa kaina." "To ki sanar da kanki ke 'yar hutu ce domin baki nemi komi kin rasa ba." "Haka ne Mama, a kullum Ina alfahari da samunki a matsayin mahifiya domin kin gama sharemin hawayen babu akan duk kan komi, wallahi sosai nake sonki Mamana." "Ina godiya Uwata. Allah ya nunamin aurenki k'asa bai rufe idanuna ba." Sunkuyar da kaina nayi ina murmushi tare da amsawa da Amin a cikin raina. So na ke na sanar da ita yau wani ya furtamin kalman so amma inajin nauyin ambata. "Duk ranar da za'a kaiki gidan miji a ranar zan sanar dake abinda ya shige miki duhu Uwata, kada ki saka damuwa akan lamarin ked'in d'iyarmu ce abin alfaharinmu." "Allah ya kaimu lokacin lafiya Mama, nima ina alfahari da ku." "Muna godiya da hakan." "Mamana kiyi hak'uri dan Allah ki sanarmin laifin da nayiwa Baba yau har ya tunzurashi yazo dukana dan in kiyaye sake aita laifin." "Uhm Uwata bakiyi masa komi ba fad'ar ni da shi ne, to ganin ban kulashi mun raba hali ba shi ne ya d'auko doriga ya huce akanki tunda ni bazan doku masa ba sannan ya tabbatar in ya tab'aki zan kulashi." "Mama kema kiyi ta hak'uri da lamuran Baba insha Allah watarana sai labari." "To Uwata Allah ya cigaba da bamu hak'uri." "Amin." "Mamana wai meye abin adona?" "Uwata baki san abin adonki ba?" Shiru nayi zuwa can na amsa "Na sani kawai ina son k'arin baya ni ne." "To sanarmin inji in kinsani." "Ke ce abin adona Mamana domin hakan d'azun na sanarwa da Malam Hassan da ya sanarmin cewa wai Baba ne abin adona sannan naji d'azun kin ce shi ba abin adona ba ne sai na k'ara tabbatarwa da ke d'ince abin adona." "Eh gaskiya Malam Hassan ya fad'a miki, Uba shi ne abin ado Uwata, daga yau duk wanda ya tambayeki abin adonki ki sanar masa da cewa Mahaifinki shi ne abin adonki, saboda duk tink'ahon 'ya ko d'a to da Uba suke ado domin shi ne haskensu a idanun al'umma ko da aya suke kuwa sune dai tink'ahonsu domin baki tab'a jin ance Mace ta zamo waliyyiya a wurin d'aurin aure ba sannan zancena na d'azun bacin rai ne ya sa na furta hakan amma Babanki shi ne abin adonki ta ko wani fuska." Idanu na tsira mata ina auna zantukan saman harshenta zuwa cikin ruhinta sai na ji baya rasa nak'asu ganin a yarda ta dage tana mai-maita zantukan tamkar wacce aka tursasa. "Ki cire shakku Uwata haka zancen ya ke har zu... "Kina nufin duk takun sak'an dake tsakanina da Baba shi ne abin adona ba ke ba?" Na katse mata abin da ta yi niyyar ambata. "Tabbas Malam abin adonki ne Uwata haka nima abin adonki ce." "Shi kenan Mama na amince zan rik'esa na d'an lokaci zuwa sadda zanyi aure amma ke zan rik'eki  na har abada." "A'a Uwata ki rik'emu abin adonki na har abada kinji." "Kiyi hak'uri Mamana haka nan kawai na ji zuciyata takasa amincewa da in rik'e Baba na har abada kamar yarda na aminta na rik'eki." "Lallai zuciyarki ta sanar miki da karatun gaskiya Uwani, kada ki sake ki rik'e ni abin adonki koda na minti daya ne domin bazan rufe miki cinya ba yayin da kika zo d'aura zani." Idanu na zubawa Baba dake tsaye bakin k'ofar shigowa d'akin barcin Mama. Sai na sami kaina da jin fad'uwar gaba duk da ban gama fahimtar zancensa ba amma na hasko har cikin ruhinsa zancen ya fito. Motsa min kai ya yi alamun tabbatar da kalamansa fuskan nan nasa kamar dare saboda yarda ya d'aureta babu alamun rahma. "Ki rik'eni ayar zuciyarki ta amince miki Uwani domin bazata sanar dake k'arya ba." Ya furta cikin halin ko in kula. Lumshe ido na yi ina hasko Baba a wani muhalli na daban wanda ya haddasa k'arin bugun zuciyana. "Hurera ina son yau ayita ta k'are tsakanina da ke." Jin abinda ya furta yasa na bud'e ido da sauri na sauke kan Mama wacce tayi k'asa da kai hakan danagani ya kuma jefa zuciyata cikin rud'ani matsananci. "Kin amince na baki takardan sakin da kika nema yanzu?" Da sauri na kalli Baba ya watsomin harara da jajayen idanunsa. Girgiza masa kai na yi cikin zubar hawaye na isa gabansa, ina bud'e baki zanyi magana kuka ya kufcemin sai na kife fuskata a saman k'afafunsa na soma rerawa cikin fitar sauti. Na sami wasu mintoci inayin kukan wanda bai k'areni da komi ba sai janyomin k'arin k'unci a zuciya zuwa can na tsagaita, cikin rawar murya na d'ago na kalli Baba na ce "Ba dan na isa ba sai dan martaban Manzon Allah S.A.W kada ka saki Mamana, ta tuba ga dukkan laifin da ta aikata maka cikin sani da rashinsa kuma bazata sake aikata abinda zai sosa maka raiba insha Allah. Ka hukuntani Baba idan yin hakan zai wanke maka b'acin ran da kake ciki, ka dukeni iya yarda ranka yaso ni d'in abar ikonka ce amma kada ka saki Mamana dan girman Allah." Tsit d'akin yayi sai sautin kukana kawai ke tashi. "Kinji abinda Uwani ta rok'a miki ko Hurera? Shin kin amince bazaki sake yimin rashin d'a'a ba tare da nunan iko akanta?" "Eh na amince amma bisa sharad'in zaka dawonin da dukiyata da ke hannunka kafataninsu." "Me ye! haka kikeyi Hurera!? Shin soyayyar d'iyarmu har ya kai wannan matakin ban sani ba?" "Kafi kowa sanin abinda na keyi Malam kuma daga yau zuwa gobe na baka dan ina son ganin dukiyata a kammale tamkar yarda ka amsa domin kwandala ban amince ta yi ciwon kai ba, sannan ka aikata duk abin da kake ganin ruhinka na k'issima maka akan ni da Uwata ban hanaka ba amma ka sani ka tab'amin shaksiyyanta billahil azim sai na yi shari'a da kai wannan a rubuce ya ke bazan d'aga maka k'afa ba a game da dagulawa Nana Khadijatu lissafi, dafatan ka tuna zantukanmu na gaban Baba Umaru?" Mama na gama ambatar haka ta mik'e ta janyo hijab d'inta ta zira ta fice batare da ta bari idanunmu ya had'u ba gudun kada in hanata aikata k'udirinta. Kallona na maida kan Baba wanda zufa ke ta tsats-tsafo masa a saman goshi. "Me ke faruwa Baba? Fitar da ni a duhu dan Allah." Na jero masa tambayar jikina na rawa. Abin maamki sai naga Baba ya sunkuyo gabana ya kamo hannuna ya matse gam a cikin nasa, ya yi k'asa da murya cikin cewa "Uwani ki taimaka ki bawa Mamanki baki da tabar maganar dukiyan nan sabida wallahi bani da hanyar samosu." Shiru na yi ina cigaba kallonsa, sake yin k'asa da murya ya yi ya ce "Idan kika sanya baki nasan zata hak'ura bazata kuma tada zancen ba sannan kin taimaki Mahaifinki ga kub'uta daga tozarcin duniya idan mamanki ta k'wace dukiyanta da ya zamo rufin asirinsa." "Baba idan na yi hakan zaka dawo yin mu'amala dani mai kyau kuma zaka amince kai d'in abin adona ne?" "Zan daina hantararki Uwani idan kin cika alk'awari." "Zamowa abin ado fa?" "Kada ki damu Uwani aike d'iyata ce, ni dai burina ki tursasa Hurera data ya femin dukiyanta dake kaina yafiya kuma na har abada." "To zaka janye zancen sakinta har abada kaima?" "Wannan zancen an barshi Uwani, ni da Hurera aurenmu  mutu ka raba takalmin kaza sunarsa da yardan Allah." "Ina godiya Baba." "Bakomi Uwani fatana dai ki cika alk'awari." "To Baba amma shin kud'in ya kai... "Uwani ke yarinyar kirkice mai hankali gami da natsuwa, Allah yayi miki albarka." Shiru na yi ganin ya datsemin abinda zan furta da yimin yabo abinda ya zamemin sabon abu daga gareshi. "Uwani ke haske ce a rayuwarmu ni da Hurera dan haka ki kuma zamowa haske wanda bai yankewa a gareni ta hanyar yimin wannan alfarman." "To Baba amma ka amsa... "A'a Uwani kada ki yimin tambaya wanda samo amsarta zai zamemin babban aiki." "Shikenan Baba na bar tambayar, insha Allah Mama zata mallaka maka." "Da kyau Uwani, Allah ya rayaki rayuwa mai albarka." "Amin ya rabbi Baba." "Zan tafi amma dan Allah kada ki muna mata ni na tursasaki da ki rok'armin yafiyanta, kawai ki nuna mata ra'ayinki ne aikata hakan." "Zan kiyaye baiyanar sunarka Baba." "Madallah d'iyar arziki." Da kallo na rakashi har ya fice, cikin tutani na shiga sai kuma na murmusa cikin jin natsuwar ruhi. "A yau ranace da bazan manta da ita ba, Aliyu ya aikomin da sak'on yana so na, Baba yayimin magana cikin lumana har da sanyamin albarka, tabbas gobe zan tashi da azumi  domin nuna godiyata ga Allah akan wannan rana da ya nufeni da ji tare da ganinsa" Da sauri na tashi na soma gyara d'akin Mama duk da baya da datti. Ina gamawa na fito waje nanma na gyarasa tsaf sannan na shiga kitchen na d'ora girkin dare. Ina kammala zuba a bincin a kula na tsinkayi sallaman Fanta cikin karad'inta na fama, da sauri na fito muka rungume juna cike da murna, idanu muka had'a da Beebah na saki Fanta da sauri na nufeta ina doka murmushi. "Ke dai tafi ku gama ganin juna da aminiyarki tunda abin 'yar wariya ce." "Affuwan my Beebah." Na furta cikin rungumota. "Uhm ni sakeni ki tafi wurin Fanta ta baki sak'on farko daga Uncle wanda ya ce tukuici ne kafin ni kuma na baki ta biyu wacce tafi na farkon muhinmanci." Kallon Fanta na yi ta zira hannu cikin hand bag ta fiddo leda fara sol ta mik'omin amsa na yi batare da na fidda abinda ke cikin ledar ba. "Ciro da bissmillah Aminiyata domin mallakinki ne." Fanta ta Umurceni. "Tura hannu na yi na ciro abin da ke ciki d'auke da basmallah, ware ido na yi suka sanya dariya, bud'e kwalin dana ciro nasomayi jikina na rawa na cikaro da dalleliyar waya k'iran sumsung, takardan da ke d'auke da kudin wayar na kalla sai na ajiye wayar a k'asa ina kallon su Beebah idanu waje hannayena dafe a k'irjina. "Ba'a maida hannun kyauta baya, ki amsa tare da godiya domin mallakan waya mai daraja irin wannan rabonki ne ya tsaga." "Amma Fanta wayar sama da dubu d'ari tafi k'arfina." "Idan ta million ce batafi k'arfinki ba Deejah domin na tabbata in kika ce kina so Mama zata siya miki dan haka ina had'aki da Allah ki amshi kyautar nan tare da yiwa Uncle godiya, ya tabbatar min ke tamkar ni ya d'aukeki kinga kenan shi yasa ya siyo mana wayoyi iri d'aya illa bambancin kala." "To Fanta nagode sosai kuma a mik'amin godiya a garesa kafin inzo da kaina." "Masha Allah, zaiji K'awata." "Uhm!." Beebah tayi gyaran murya, muka maida hankalin gareta, ta rausayar sa kai cikin kashe min ido d'aya sannan ta ce "Sak'on Uncle na biyu ita ce samun wuri na musanman a ruhinki." "Banfahinceki ba." "Zanyi miki dala-dala k'awar Fanta, ke dai bini a sannu kawai. Zama na yi suma suka zauna, sallaman Mama ya dakatar da zancen sa Beebah ke shirin sanar da ji, mukayi mata sannu da zuwa ta amsa a hankali tare da shigewa cikin d'aki. "Mama bata da lafiya ce?" "Eh " Na amsawa Fanta domin bana da amsar da tafi wannan." "Allah ya bata lafiya." "Amin." Bari mu tafi zuwa anjima zan dawo sai muyi maganar amma kafin nan zan turo miki sak'o domin ki soma shirin burge Uncle d'inmu." Tagumi na zabga saboda zantukan sun jefani cikin tunani, aikam a tare suka kyalkyale da dariya ganin yarda na yi tamkar mara lafiya, harara na cilla musu suka sake kwashewa da dariya tare da nufar hanyar fita gidan, ina kallonsu suka tafi na tashi jikina a mace na shiga kitchen na d'auko abincin, ina fitowa Mama na sanyo kai kitchen d'in sai na koma da baya ta shigo ta kama kafad'una ta rik'e gam, na rintse ido ina karanto addu'an samun kariya daga musiba sabida yarda naga idanun Mama ya tsoratani. "Uwata kiyi hak'uri da rayuwa domin kowa da kika gani da abinda ya zame masa k'alubale duk kuwa muk'aminsa ko sarautarsa." "Haka ne Mama shi yasa Annabi S.A.W ya umurcemu da mu zamo masu yarda da k'addara ta khairan ko kishiyarta." Rungumeni Mama ta yi tana sauke ajiyar zuciya, mun jima a haka kafin da sakeni tare da rik'o hannuna muka fito na ajiye kulan abincin, zama mukayi a shinfid'ar da na yi domin cin abinci, sai lokacin idanunta ya sauka kan kwalin waya tare da wayar da suke a jiye gefe. "Wa ya baki?" "Uncle Muhseen ya aiko su Fanta su kawomin wai tukuicin dafawa abokansa abinci da na yi ranar Dana k'one." "Allah ya biyasa da dubun alkhairori." "Amin." "A she abinda zai siya miki kenan d'azun ya shigo neman izini." "Ya shigo wurinki Mama?" "Eh ya zo shida Fanta ya sake bani hak'uri akan abinda ya faru sadda zai tafi sai ya ce yana neman izinin da in bashi dama ya rik'a kula da lamuranki kamar yarda yakeyiwa Fanta, na kuma bashi dama saboda na hango gaskiya a tare da shi gami da uwa uba natsuwa." "Ikon Allah Uncle na da abin mamaki, a da fa ko na gaisheshi bai amsawa sai yaga dama amma daga jiya zuwa yau ya sanjamin matuk'a." "Uwata hoo, to kika sani ko yana ciki ne?" "Cikin me Mama?" "Manema aurenki mana." "Innalillahi! Bana fatan faruwan hakan Mama, dan Allah ki daina zancen nan bana so, wallahi bazan iya zama da matarsa ba." "Uwata natsu dan Allah, nifa hasashe na ke yi ba zahiri ba ne da zaki rud'e haka kamar zaki zauna da mala'ikan d'aukan rai." Mik'ewa na yi nufin yi dan gujewa zancen, Mama ta maidani na koma zaune ba shiri, cikin tsare gira ta dubeni na sunkuyar da kai. *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/19, 4:58 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Mrsjmoon E.W.F *Shafin na ku ne 'yan uwa rabin jikina, Yaya Sadiya (Mmn Ihsan) tare da Yaya Amina (Mmn Ganar) Alkhairori marasa iyaka su dawwama a gareku bi jahiy Nabiy S A W. Amin.* Page 08. "Uwata me ke damunki? Da kike son maida wata d'abi'a mara kyau ya zamo naki. Ni ce fa na ke yi miki magana amma kikayi nufin tashi ki bani wuri, innalillahi wa Inna ilaihin raji'un, yau wacce kalan rana ce tazo gareni ni Hurera." "Rabbi igfirli. Na tuba Mamana kiyi hak'uri bazan sake aikata makamancin haka gareki ba." Na ambata cikin rawar murya. "Uwa banyi fushi da ke ba kuma da yardan Allah bazan tab'ayi ba." Fad'awa jikinta na yi ta rungume ni, a hankali take shafan suman kaina zuwa bayana, nayi lamo ina jan hailalah domin samun nutsuwar ruhi. "Uwata." "Na'am Mama." "Shi me ya kamata kiyi a daren wannan ranar wanda kika tsinci kanki da d'a namiji ya aiko miki da kyau mai matuk'ar amfani?" "Zan rayata da nafilfili sannan na wayi gari da Azimi domin nunawa Allah godiyata akan faruwar hakan." "Masha Allah, Uwata tafi na kowa hangen nesa." Murmusawa na yi tare da sark'e tafin hannunta cikin nawa na ce ,"Mamana a yau abubuwa uku sun riskeni kuma dik a kusan lokaci d'aya, dan haka kema ki tayani nuna farin cikin ta hanyar raya daren da salloli tare da tashi da Azimin nafila." "Wannan a rubuce ya ke Uwata amma zanso sannin ragowar abubuwa biyun dan nasan na farkon dai kyautar waya ce daga makwafcin arziki." "A'a kyautar waya ita ce cikon na ukun." "To ina saurarenki Uwata kuma Aminiyar Mamanta." Manna jikina na sake na yi da nata  sannan na sunkuyar da kai domin ina jin kunyar zancen farko, a hankali na ce "Mama a yau abokin karatuna ya aikomin da sak'on yana sona ta bakin Beebah haka a yau Baba ya... Hamdalah da Mama ta sanya mai k'arfi ya sanya na dakata da zancen na kamo hannunta na kife fuskata a kai ina dariya k'asa-k'asa. "Uwata insha Allah sai kin tara masoya masu yawa, kin zab'a kin darje, ina fatan ki samu nagari maiyi miki k'auna ta hak'ik'a,." "Allah ya nufa hakan Mamana." "Amin, ai ina jiyo jinkirin nan naki alkhairi ne." Ina kallon idanunta na cigaba da cewa "Mamana abu na biyu shi ne Baba ya sanya min albarka ya sanarmin ni d'in yarinyar arziki ce kuma haskenku ce ni, ya amince shi abin adona ne, ya tabbatar min bazai sake hantarata ba, mu'amalar arziki zai kasance tsakaninmu." Kallon da Mama ke bina dashi yasa jikina ya yi sanyi sai na kamo hannunta na rik'e gam na ce "Dan Allah Mama ki yafe masa du... "Uwata tashi muyi haraman sallah idan mun idar ina son yin magana dake sannan ina tayaki murnan abinda Malam ya ambata miki na albarka, ina addu'ar yasa har cikin ransa haka zancen yake ba don cikar wani buri nasa ya sanya shi yin furucin ba." Kasa amsawa na yi da Amin sabida yarda jikina ya yi lakwas jin Mama ta harbo jirgin. "Uwata ko har yanzu yatsun suna yi miki ciwo ne naga fuskanki ya sanja?" Kallon yatsun k'afata na yi sannan na girgiza kai. "Sun k'ame banjin ciwo sosai sai abinda ba'arasa ba kamar k'ai-k'ayi na warkewa." "Hakan na ke son ji, maza tashi muyi sallah a cikin lokacinta." Mik'ewa na yi na shige d'akina. Saida na saka sabuwar wayata a chargy sannan na fad'a toilet. Ko da na idar da sallah sai na koma na yi suddaja na rok'awa Uncle Muhseen rahamar Allah tare da neman alkhairi a lamarina da Aliyu a k'arshe na rok'i Allah ya sanyawa Mama sanyi da ta yafewa Baba dukiyanta kamar yarda ya ke buri. Bayan mun sallaci isha'i muka fito baranda muka zauna, abinci Mama ta umurta da mu soma ci bayan mun gama sai muyi zancen. Kamar ko da yaushe ban wani ci abin kirki ba sai kunun Aya dana cika cikina da shi. Bayan na wanke kayan da muka b'ata na dawo na zauna na tsirawa Mama ido murmushi ta sakarmin tare da tashi ta nufi zaure ba jimawa ta dawo. "Na kulle gidan ne sabida na fahimci yanzu Malam ya koma yimana lab'e." Kauda kai gefe na yi batare da na ce komi ba. "Uwata kinajin haushina akan lamarinmu da Malam ko?" "A'a Mama kawai dai raina baya son tanki in tanka da kukeyi ne akaina." "Uwata bana iya jure ganin Malam na tab'amin ke ce." "Shi d'in mahaifina ne Mama ki barshi ya rik'a hukuntani kamar yarda yakeyiwa d'iyoyinsa idan sunyi masa ba dai-dai ba." "Ke kina da bambanci da su domin bakya k'yetare umurninsa kamar yarda sauran sukeyi masa, sam ba kyayi masa laifin da zai hukuntaki dan haka bazan bari ya zakunceki ba." "Zalinci kuma Mama?" "Eh." "Shifa Uba yake gareni, abin ikonsa ce ni." "Nasan da haka amma ki sani akwai hakkin d'iyoyi akan mahaifansu dan haka yi miki hukunci batare da kin aikata laifin komi ba wannan zalinci ne kuma ba zan tab'a lamunta ba." "Nidai Mama ki koyi hak'uri akan duk wanda ya tab'ani domin wata rana sai labari, ko ance su tab'ani bazasu iya ba." "Allah ya kaimu wannan lokacin Uwata k'asa bai rufe idanuna ba." "Amin Mama." "Uwata natsu da kyau ki saurari maganar da zan sanar miki." "To Mama ina saurarenki." "D'azun dana fita gidan Baba Umaru naje, mun gama magana akan aurena da Malam, zan bashi sadakinsa shi kuma zai bani takardata tare da dukiyata." "Innalillahi wa Inna ilaihin, Mama dan girman Allah ki bar maganar rabuwa da Baba domin yin hakan tamkar kin maidani marainiya ce dan na tabbata Baba ba zai barni na zauna tare da ke ba, zai gwadamiki karfin ikon da mazaje ke gwadawa matayensu da zarar sun rabu da su." "Ki rubuta zamanmu dake aure ne kawai zai rabumu amma ba k'arfin ikon Malam ba saboda ke d'iyata ce da na ke da iko ita ko ta wani fuska." "Mama nidai ki janye maganar rabuwan nan dan girman Allah." "Uwata in kinga na janye sai Malam ya bani dukiyata dama Baba Umaru ya ce idan ya dank'amin hakkina in janye maganar saki idan kuma shi ya bani takardana kamar yarda yake shiri to shi kenan ba kare bin damo." "K'alu innalillahi wa Inna ilaihin yanzu aina Baba zai samo miki kudinki alhalin kinfi kowa sanin baya da hanyarsu." "Yana da shi Uwata, mugunta ce irin tashi ya ke son dannemin gadon da mahaifina ya barmin wanda yasha wuya wurin tarasu." "Mama nikam ina rok'on da ki yafe masa dan girman Allah da Manzon sa." "Uwata Malam ne ya rok'eki da ki nema masa affuwana kika amince shi ne ya ke saka miki albarka tare da yi miki alk'awarin daina hantararki." Shiru na yi domin idan na amsa da eh, na karya alk'awarin da nayiwa Baba akan bazan bari sunarsa ya fito ba in kuma na ce a'a nayi k'arya, shirun danayi shi ne mafita." "Uhm Uwata kenan har yanzu baki gama sanin duniya ba to bazan bar masa ba wallahi tallahi kinji na rantse to ko baya sallah sai ya biyani hak'k'ina." Tsirawa Mama ido na yi cike da ruwan hawaye. "Uwata kada ki sakawa kanki damuwa, zamu warware da Malam saboda yana da gidan gona wanda ya bunk'asashi da dukiyana. Kuma kema kin san sagonsa na saida kayan hatsi, yana kuma da filaye kinga kenan yana da hanyar biyana dukiyata kuma ba da jimawa ba zakiga hakan domin Baba Umaru tsohon alk'ali ne zai amsarmin kayana kamar yarda ya amsa a hannuna ya mik'a masa bisa shaidun lauya da wasu dattawa." "Nidai Allah yasa kada kuyi rikici a binda ke tadamin da hankali kenan." "Bazamuyi ba Uwata dan haka ki kwantar da hankalinki idan ya tambayeki yarda mukayi kice masa kin sanarmin ban amsa miki ba." "To Mama." "Gobe da safe zamu shiga muyiwa Alhaji Muhseen godiya." "Tare da ke Mama?" "Eh domin nafiki jin dad'in kyautar nan." "Uhm Mama kenan, Allah ni kad'ai zanje in yaso idan kun had'u kyayi masa." "Nima na ambata ne dan naji na bakinki Uwata." Murmushi na yi ganin Mama na son maidani yarinya k'arama. "Uwata wallahi ina farin ciki da tarayyanku da Alhaji Muhseen sama da yaron nan Aliyu da kika sanarmin." "Mama shifa Uncle bai furta yana sona ba kawai hasa-shenki ne abinda bana fatar ya tabbata." "To shikenan Uwata Allah ya zab'a miki mafi alkhairi cikinsu." "Wayyo Mama shin wai da wanda ya furta da wanda bai furta ba wanne ne dahir?" "Wanda ya furta." "To Mama Aliyu shi ne dahir d'ina." Kallon da Mama ke yimin yasa na tashi da gudu na fad'a d'akina. Bayana ta biyo ta zauna gefen katifa ni kuma na koma k'asa na zauna kaina sunkuye. "Uwata dik abinda kike so shi na ke so amma ki sani ke d'in allurar cikin ruwa ce mai rabo ka d'auka dan haka na ke baki shawara idan Alhaji Muhseen ya furta miki kalman so da ki amince kada ki duba kina da Aliyu, kinji ko?" Gyad'a kai na yi alamun amsawa amma a k'asan raina addu'ar kada Allah ya bashi damar furtamin na ke yi. "Uwata kada kiga ina ta ambatar Alhaji Muhseen kiga kamar dan yana da kud'i ne na ke kwadayin da ki aureshi sam ba haka bane ina dai duba natsuwarsa ne tare da sanin darajar makwataka da uwa uba ilimin addini da ta zamani da ya mallaka sannan ke shaidace yana aiki da iliminsa yarda ya dace." "Haka ne Mama." "Da kyau sannan shi managarcin namiji ne wanda duk kan uwa ta gari zata so d'iyarta ta zamo k'ark'ashin ikonsa wato ta aureshi a game da kyautatawa iyali kuwa wannan ke ce zaki bada shaidan shi d'in jarimi ne ta kowani fuska ga iya mu'amala da mutane da sanin hak'k'in makwaftaka, kinga ko dan wad'an nan abu-buwa zanso ace ya zamo surikina, Uwata ta sami kwanciyar hankalin da na ke yi mata addu'ar samu." "Mama dan Allah kiyi shiru haka nan wallahi kina yin maganar k'irjina na harbawa sam bana son maganar." "Shi kenan Uwata na yi shiru amma zan cigaba da yi miki addu'ar samun miji na gari ko da kuwa ba Alhaji Muhseen ba ne ko Aliyu." "Nagode Mamana ta kaina." "Uwata abin alfaharin Mamanta, za'a soma soyayya." Tura fuskata na yi tsakanin cinyoyina, ina jin ta mik'e tare da shafo kaina sannan tafice. Tashi tsaye na yi na soma kai kawo domin magan-ganun Mama sun tsayamin a rai. "Tabbas Uncle mijin aure ne amma matarsa abar tsoro ce." Na furta a hankali cikin jan karan hancina. Hangowa wayata na haske yasa na isa na d'auka tare da sallama muryan Aliyu Muktar ya doki kunnuwata sai na daburce domin ban saba waya da maza ba in ba Kawu Habibu ba. Dariyar da najiyo yanayi k'asa-k'asa yasa na saita kaina har da wani tsare gira tamkar yana gabana na amsa sallaman tare da tambayar shi lafiyarsa. "Lafiyalau, alhamdulillah matar Ali." Ware idonu na yi jin sunar da ya rad'amin, dariyarsa na kuma jiyowa amma irin mai fitowa cikin iska d'in nan. "Ina son Nana Khadijatu ainun shi yasa na kirata da Matana kai tsaye dan inaji ajikina ke d'in mallakina ne, uwar 'ya-'yana." "Uhm, ya su Mama da sisters." Na samu kaina da ambatar haka duk kuwa da naji dad'in kalamansa. "Suna lafiyalau, Salma ta ce agaisheki kafin ta zo gida." "Wacece ita?" "K'anwarmu ce yanzu ta shiga S S 1." "Masha Allah ina amsawa, sai tazo ina zuba ido." "Ai tare zamuzo gobe da hantsi insha Allah." "Gobe!" "Eh ko bakya nan ne?" "Ina nan sai kunzo." "Insha Allah kafin mu taho zan sanar miki." "To." Mukayi jim zuwa can ya kira sunana cikin wani siga, ban amsa ba sai gyaran murya da na yi, murshinsa najiyo nima sai na murmusa. "Yimin hirar k'auna dan bazan tambayeki amincewa da k'auna ta ba saboda tunda kika d'auki wayar najiyo amon amincewarki na amsa kuwwa a kunnuwana da tsokar zuciyata." Dariya ce ta kufcemin ba shiri. Shima dariyar ya sanya daga nan yasoma yimin kalaman k'auna wanda bansan da su ba a rayuwata, ni dai iyakata da shi eh, a'a, uhm domin bansan taya zan maida masa da martanin ba. Muna tsaka da wayar Beebah ta shigo da sallama yana jin na amsa sallama sai yayimin sallama, na ajiye wayar ina kallon cikin idanunta. "Soyayya da dad'i, wata yarinya ta fad'a a cikinsa." "Baki da dama Beebah." "Ina da ita fa sai dai inayin dana sanin yiwa Aliyu jagora zuwa gareki." "Ban fahimceki ba." "Zaki fahimta tunda gida bai k'oshi ba, ba za'a bawa dawa ba." "Matsalata da ke kenan iya salon magana wanda bancika fahimta ba." "Kina Bahaushiya amma d'iyar Kanuri tafiki jin Hausa." "To ya zanyi?." "Ki koma School ki yo degree a fannin Husa." "Aiki ja, ban iyawa kam." Dariya muka sanya. "Ina wayarki?" Nuna mata na yi da yatsa, ta iso ta cirota a chargy ta sanya layukan MTN da GLO ta soma latse-latse tun ina kallonta har na gaji na kwanta barci ya d'aukeni dama shi na ke ji sosai. Washe gari ina kammala azkar na fito waje da Baba na yi arba zaune a baranda yana jan tsarbi, gabansa na isa na gaisheshi ya amsa cikin gyaran murya na koma d'akina batare da na shiga d'akin Mama ba. "Jiya Uncle ya kira wayarki kinyi barci." Ware idanu na yi cikin jin fad'uwar gaba. "Na tabbata zai kuma kira." "Dan girman Allah ki kashe wayar." "Saboda me?" "Bana son na yi magana da shi ta waya ne sai bayan na yi masa godiya baki da baki." "Kinyi magana kam amma ba za'a kashe ba, kidai hanzarta zuwa yi masa godiya kafin ya kira." "Insha Allah zanje." "Good." Shiru ya ratsa wurin zuwa can na katse shirun da cewa "Kince zaki sanarmin da wani sak'o daga Uncle." "Zan sanar miki Aunty Deejah." "Aunty kuma?" "Eh." "Uhm kin fiye neman zance kam." "Muje na gaisar da Mama tare da kammala ayyukan gida idan mun gama sai muyi maganar." "Motsa kai ta yi ta fice ni kuma na yi hanzarin kashe wayoyina gudun kiran Uncle sannan na biyo bayanta. *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/20, 12:07 AM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Safiyya (Mrsjmoon) E.W.F *Shafin na aminai ne My Jamee, (Mom Aysar), dear Mamie waru, Mom sayyid, my sis VC, Oum Abdul A'had, My Fauxah and Dear Safiyya Abbas Gambo (Maman Mama) Allah ya bar k'aunarmu tare da albarka ga zuri'a duniya da lahira. Amin.* Page 09. Ko da na fito har Beebah ta shige d'akin Mama rufa mata baya zanyi Baba ya kirani da hannu na isa gabansa na durk'usa. "Wannan wacece mara tarbiyya ce?" Ya ambata cikin rad'a. "Yayar K'awata ce Fanta." "Shi ne Fanta tafita aiki da hankali?" Shiru na yi dan bansan abinda Beebah ta aikata masa ba. "Tana kallona ta kasa gaisar dani ta shige d'akin Hurera sabida da ita fitsararra ce, ni da gidana wata 'yar zamani ta shigo ta maidani ni da banza duk d'aya." "Kayi hak'uri Baba taga kana lazimi ne." "Bata dai da tarbiyya kuma zanci mutuncinta domin bata isa ta shigo muhallina ta wulak'antani ba." "Bazata sake ba insha Allah Baba." "Naji amma magiyanki bai isa dakatar dani daga k'udirina ba dan sai na cimata mutunci domin gaba ta kiyaye aikatawa wani irin hakan." 'Ya Salam Baba bazai tab'a sanjawa ba dai.' "Ya kukayi da Hurera jiya?" Da sauri na kallesa sabida hankalina ya nausa cikin zancen zucci. "Na ce ya kukayi da Mamanki akan maganar yafemin dukiyanta?" Ya sake cillomin tambayar ganin na k'i cewa komi. "Bata kulani ba." "Kamar ya?" "Ko da na yi mata magana kallona ta yi batare da ta ce komi ba." "Hurera akwai bala'in wayau, ta gano ni na tursa-saki kenan? Shi kenan muzuba mugani shege ka fasa kud'i dai nacisa ba zan biya ba." "Kudai sami masalaha Baba." Harara ya cillomin na sunkuyar da kai. "Iskancin banza, ko in na biyata uban wa zai gajesu in bani ba." "Me kace Baba?" A hanzarce ya kalleni sai kuma ya watsomin harara na yi saurin matsawa ya nunoni da yatsa cikin muryan gargad'i "Wallahi kika kuskura naji zancen nan a bakinta sai na lahira yafiki jin dad'i dan sai na il... "Wallahi Baba ba maijinsa." Na katseshi jikina na rawa. 'Dagamin hannu ya yi alamun in tashi, na mik'e nashige d'akin Mama da sauri. Beebah na hango tana gyarawa Mama zaman labule ita kuma Mama na zaune ta jingina da kujera tana karanta Hisnul Muslim. Wurin Beebah na nufa nasoma tayata ba jimawa muka kammala gyara d'akin ciki da falon sai lokacin Mama ta idar da karatun ta kirani na iso na zauna gabanta tare da gaisheta, amsawa ta yi cikin kallon Beebah. "Sannu Habiba Allah ya baki miji nagari." "Amin Mama." "Baki da kunya Beebah." "A'a Uwata barta ta amsa a fili domin addu'ar alkhairi abar amsawa kowa yaji ne." "Mama ki rabu da ita, k'ila kowa irinta ce mai kunya har dana rashin hankali." "Lahaula... Kinjita ko Mama? Kunya adon Mata ne kuma tana daga cikin Imani." "Ya isa haka nan d'iyoyin albarka, ku muje ku samawa kanku abinda zakuci  ni kuma nayiwa Malam abincin gargajiya." "Me zakiyi dafa masa Mama?" "Tuwo miyar kuka." Matsawa kusa da kunninta na yi na ce "Wai Mama me ya kawosa gidan nan alhalin ba girkinki ba ne?" D'an tureni ta yi Beebah ta sanya dariya b'ata rai na yi tare da ficewa suka rufamin baya suna dariya. Kafin k'arfe Takwas ta yi mun kammala komi na shiga wanka ina fitowa Beebah ta shiga, ko mai ban shafa ba na zira doguwar rigar shadda na fito na sami Mama zaune a baranda tana cin tuwon da tayiwa Baba. "Mama kice dama ke ce zaki ci tuwon ba wani Baba." "Gaskiya ne ni ce na yi marmarinsa amma ganin Malam yazo sai na ce bari inyi mana sai gashi ya fice batare da yaci ba." "Mama dama ba'a nan ya kwana ba?" "Eh, ina fitowa bayi dan yin alwalaln subahi na tsinkayi bugan gidansa." "Ikon Allah Baba kenan sanin halinsa sai shi kad'ai." "Zauna ki karya dan zaki rakani gidan Baba Umaru." "Aikam dama na kwana biyu ban kai musu ziyara ba, dik na yi kewar Hajiya Inna." "Itama ta yi kewarki, shiyasa na ce muje tare sabida jiya ta yi ta fad'a wai ban barinki kinayin zumunci da su kodan basu suka haifeni ba." "Kai Hajiya Inna ba ruwanta da b'oye-b'oye." "Hakan shi ne dai-dai Uwata, a duk inda kike to ki zamo mai gaskiya da fad'ar gaskiya komin d'acinta, domin gaskiya ita ce jigon tsanin ginuwar Imani a Ruhi." "To Mama, Allah ya kara mana Imani." "Amin Uwata." "Mama bamu sami damar yin Azimin ba." "Zamuyi dama kinsan komi nufin Allah amma tunda munyi alk'awari zamu cikashi insha Allah." "Allah ya bamu iko gobe mu wayi gari da shi." "Amin." "Insha Allah zan tayaku domin aikin neman lada ba'a sanyin jiki." "Godiya muke Habibatu." "Mama babu godiya tsakaninmu sai sanya albarka domin tamkar Deejah na ke gareki." "Madallah to Allah ya yi muku albarka." "Amin." Muka amsa a tare. Muna kammla karyawa Beebah ta koma d'akina ta kwanta ni kuma na fice zuwa yiwa Uncle godiya. Ina zuwa bakin get d'in gidan naji k'irjina ya harba wani tsoro ya jiyarceni sai na soma karanto addu'a, na koma da baya na zauna a k'asar bishiyar dake fuskantan gate d'in na tsirawa bencin da Baba maigadi ke zama ido, tunanin yarda Aunty Nafisa taza kalleni na ke yi saboda babban abinda na tsana kallon banza wanda ya zame mata tamkar ibada. Kimanin mintoci goma ina zaune cikin nazari sai kawai na tashi cikin kuzari na doshi gate d'in domin yanzu na sami natsuwa sama da d'azun. Ina tura k'amin k'ofa Mai gadi na bud'ewa Uncle gate ganina sai ya fasa fita ya kashe motar na k'araso na russuna gefen da yake zaune na gaisheshi, bai amsa ba ya bud'e motar ya fito ya jingina da jikin motar, kallonsa na yi ta gefen ido, idanunmu ya had'u da juna sai na yi sauri sa ke russunawa kafin inyi magana na tsinkayi muryansa. "Lafiyalau Khadija mai gudun makwaftanta." Murmushi na yi tare da cewa "Naga sak'o nagode sosai, Allah yasa kafi haka, ya jik'an mahaifa, ya yiwa zuri'a albarka ya kayi dace da gidan Aljanna mad'aukakiya." "Amin ya rabbi tare da ke." Motsa yatsuna na yi suka bada sauti, ya ja fasali tare da cewa "Duka sak'on sun sameki?" "Eh." "Har na wajen Beebah kin karb'a da hannu biyu?" Shiru na yi bugun k'irjina ya dawo sabo. "Da alama Beebah bata sanar miki da sak'on nan ba ko Khadijatu?" "Eh bamuyi maganar ba amma nasan zata sanarmin." "Ok, shigo ki rakani yiwa su Bintu tsaraba." "Mama zata aikeni ne Uncle." "Ok, tafi gani nan shigowa neman alfarman ta aramin ke." "A'a Uncle muje sai na sanar mata a waya " "Bani number wayar nata." Karanto masa na yi, ina tsaye ya kirata sun jima suna magana sannan sukayi sallama ya kalleni na sunkuyar da kai. "Khadijatu mai kunya ce." Ya ambata cikin dariya, murmusawa na yi. Da kansa ya budemin kusa da driver na zauna sannan ya shiga muka fice. Tafiya mukeyi tamkar kurame sannan tuk'in a hankali yakeyi na gane hakan ne jin yarda ake zabga mana horn amma baisa ya k'ara gudu ba, wani d'an a daidaita sahune yazo gefena ya zabgo masa zagi, na rafka salati tare da neman masa shiriya wurin Allah. Wani ajiyar zuciya na ji ya saki tare da k'ara gudu yana kallon titi ya ce "Ke d'in Uwa ce ta gari Khadijatu mai nemawa d'iyoyinta falalar Allah tun kafin su iso duniya." "Uhm." Kawai na iya ambata tare da maida fuskata gefe. "Kina da bambanci mai tazara tsakaninki da Nafisa domin da ita ce maida masa da martani zatayi harma da k'ari dan ta iya manyan zagi tamkar jikar maguzawa." "Ai Uncle ba kowo ne ke iya mallakan hankalinsa ba ya yin da wani ya zagesa, banga laifin Aunty Nafisa ba dan ta ramawa mijin zagin da akayi masa." "Khadijatu shi komi na duniya d'an hak'uri, zagin nan fa bai mannewa a jiki balle ace zai zama tambo, idan kabar wanda ya aikata da halinsa kansa ya zaga kamar yarda kika aikata sai zagin ya koma masa ke kuma kika sami lada yayin da kikayi masa addu'a." "Allah ya k'ara mana hak'uri." Na ambata ahankali domin zantukansa gaskiya ne. "Amin." Shiru ya ratsa zuwa can na tsinkayiaganarsa. "Ina neman alfama idan Beebah ta sanar miki da sak'ona ki amince ba dan na isa ba." Shiru na yi gabana na fad'uwa, nidai ban k'aunar jin sak'on nan sam. Latsa horn ya yi na kalleshi da sauri ya saukemin murmushi, ya maida hankali kan titi ya cigaba da cewa "Bazan takuraki ba Khadijatu, na bar miki zab'in ranki, dik abinda kika zanta da ruhinki ki sanar mata domin lamari ne dake buk'atar amincewar ruhi da ruhi." Still ban ce komi ba shima ganin nak'i tankawa sai ya sauya zancen da jefomin tambayoyi game da rayuwar yau da kullum, ina bashi amsa dai-dai fahimtana, kuma na fahimci yana gamsuwa da bayanen. Da k'arfi da yaji dai Uncle ya maidani masuraciya domin bai bar bakina ya huta ba har muka iso babban kanti. *** *** Dai-dai sadda Uncle ya bud'ewa Deejah k'ofa tashige, Nafisa na isowa volcany sam bata hango Deejah ba amma ta shiga tunanin da wanda mijinta zai fita. Ta ke zuciyarta ya hasko mata da Beebah ce ko Fanta. "Kai amma ai ba zai bud'e musu mota ba." Jim ta yi cikin jin fad'uwar gaba, sai ta sakko zuwa wurin Baba Mai gadi, sadda ta jefo masa tambayar rud'ewa ya yi, tsawa ta daka masa tamkar yaronta alhalin ya yi jika da ita. "Hajiya da Khadijatu ce." "Khadijatu kuma? Wacece ita?" "K'awar Fanta." Wani ashar ta zabga wanda ya firgita Baba maigadi ya ja da baya ta nunosa da yatsa idanu jajur cike da tarin masifa, kafin ta zabga masa zagi ya shige d'akinsa da sauri ya kulle k'ofa domin da jimawa kallon mara hankali yakeyi mata tun sadda ta tab'a rufeshi da fad'a har da daga hannu kamar zata dukeshi dan kawai ya bar yaronta Hafiz ya fita waje wasa da yaran unguwa bisa tsautsayi mashin ya bugeshi yasami gobcewar gashi a hannu. "Gara Alhaji ka auro mai hankali da da sanin darajar bil'adam ko wannan sokuwan ta yi hankali ta gane me duniya ke ciki. Zan cigaba da yi masa addu'a akan Allah ya bashi Khadijatu amatsayin mata, tabbas da kagama hayewa kam, yarinya mai hankali da aiki da ilimi, hak'ik'a gidan zai gyaru idan hakan ya kasance." Haka dai maigadi ya yi ta zancensa shi kad'ai kulle da d'aki. Nafisa kam a tsiyace ta koma cikin gida direct d'akin Fanta ta shiga ta sameta kwance tana amsa wayar saurayinsa Abul Abbas. "Ke tashi in aikeki wurin Uwar Deejah." Mik'ewa tsaye ta yi jikinta na rawa tare da datse wayar, tama kasheta baki d'aya ta dubi Aunty Nafisa idanu waje. "Yes wurinta zan aikeki, ki ce mata na ce ta datse banzan alak'ar da ta k'ulla tsakanin d'iyarta da mijina tun kafin na d'auki mataki wanda ba mai dad'i ba ne dan zan iya kashe 'yarta har lahira in har ta sa ke ta auremin miji." Lumshe ido Fanta ta yi ta koma ta zauna gefen gado ta yi tamkar ba ita Aunty Nafisa ke bawa umurni ba. "Fanta ko dai da had'in bakin ki cikin lamarin ne?" "To Aunty ai ban fahimci inda zantukanki suka dosa ba ne, Deejah dai kinfi kowa sanin ta kwana biyu bata shigo gidan nan ba balle su had'u da Uncle haka kinfi kowa sanin ingantaccen tarbiyyanta amma sai naji kinzomin da zancen cin mutunci, to a gaskiya bazanje ba, kina da k'afa kije mana amma kafin nan ki sani Mama bata d'aukan raini, idan kikayi mata fitsara zata ladaftar da ke kuma ki tuna kina da tambo a wurinta, kika kuskura kika taka mata gida da tijara komi zai iya faruwa wanda na rashin dad'i ne haka Uncle ya sami labari kinfi kowa sanin abinda zai faru, at end sai ince Allah kaiki lafiya ya dawo da ke da idanu lafiyayyu." Abin mamaki duk zancen da Fanta keyi mata kasak'e Nafisa ta yi tana kallon bakinta har ta dasa aya bata motsa ba. Ganin haka sai Fanta ta fad'a toilet da gudu domin ta kwana da sanin shirunta ba alkhairi ba ne. "Shegiya da dai kin zauna kallona wallahi dana illata miki bakin rashin kunyar." Ta ambata ganin Fanta ta nemi mab'oya, ficewa ta yi cikin nazarin zantukan. "Maganar Fanta da k'amshin gaskiya fa na san wacece Mama zata iya nad'amin duka in har na rattafa mata sak'on da na bawa Fanta, yanzu me ye abinyi? Bari in jira dawowar Abban Hafiz naji abinda yake nufi da fita da d'iyar makwafta unguwa alhalin gani matarsa ta sunnah bai fita da ni ba. Kai wallahi namiji munafuki ne yanzu ya rasa abinda zai sakamin da shi sai neman wannan 'yar banzan yarinyar mai siffan munafukai. Oh ni Nafisa ina ta murna ta tsorata ta daina shigomin gida a she suna manne a waje, kai wallahi ko me zai faru sai dai ya faru amma sai na yiwa uwarta da bokan ubanta kashedi akan mijina dan su rabashi da d'iyarsu." Tana ambatar haka ta janyo dogon hijab ta jira ta sakko k'asa cikin had'a matakala bibiyu ta fice harabar gidan a tsiyace. Bawan Allah maigadi na hangota ya kuma d'iba da gudu ya shige d'akinsa ya kulle, ganin haka suma sauran ma'aikatan, masu kula da fulawa tare da mai wanki da guga suka kwasa da gudu suka nemi mab'oya dama maigadi na tsakiyan basu labarin abinda ya faru ne d'azun sai gata da fito a fusace." Ita kanta lamarin ya bata dariya, ta murmusa ta fice tana tsine musu a zuciyarta ganin sun maida ita mahaukaciyar karfi da ya ji. *** "Kin ga ne Khadijatu fito mu shiga ki zab'i abinda kike so kawai na maidaki gida in yaso idan sun dawo sai suzo da kansu su zab'i abinda ransu ke so." Na tsinkayi maganar Uncle, sadda ya yi parking a harabar Babban Kantin. "Nikam ban son komi, nagode mutafi gida kawai." "Ko turaruka ba kya so?" "Uncle d'awainiyar ta yi yawa, mutafi kawai." "Na san ke d'in mai son k'amshi ce dan Fanta tasha sanarmin da na siyo mata turare duk in na yi tafiya wanda zata baki gift lokacin birthday naki dan haka ki amince na zab'o miki." "Shi kenan Uncle zab'o d'in." Na furta kaina sunkuye. "Thank you Nana Khadijatu." D'agowa na yi na zubawa bayansa ido har ya shige cikin Kantin, sauke ajiyar zuciya na yi inajin wani kalan natsuwa na ratsa ruhina. "Uncle ya san kansa matuk'a dole matarka ta yi kishinka." Na ambata cikin rad'a tare da bud'e kofar motar na fito na jingina ina kallon mutanen da ke kai kawo. Lumshe ido na yi ina shakar iskan bishiyoyin da suka k'awata harabar Kantin. "Wow gaskiya na ji wani nishad'i a ruhina tunda na doso Kantin a she dai zanyi gam da takar ne wato gamo da matar A... Da sauri da d'aga masa hannu, na hanashi k'arasawa, langab'e kai ya yi na sauke masa murmushi. "Ina godiya da wannan kyauta Malama Khadija." "Na me fa?" "Na sadakan murmushi da kikayimin yanzu." Nuno shi na yi da yatsa ya mik'o hannu tamkar zai kama yatsar na janye ya sanya dariya, na girgiza kai tare da gyara tsayuwa a jikin motar. "Aliyu kana da ban dariya wanda a da ban lura da hakan ba sam." "K'auna kansa ka soma lura da d'abi'un mosoyi." "Uhm ka ganka ko da iya salon zance." "Gaskiya ne Deejah, ni kaina ban san kina magana mai tsayi irin haka ba sai yanzu." "Banda sharri dai Yallab'ai." "Allah ki yarda kawai." "To naji amma yarda bai zama do... Bud'e k'ofar motar da Uncle ya yi da k'arfi ya katsemin abinda zan furta. Na kalli Aliyu shima ni yake kallo cike da tambayoyi sai na yi masa bye da hannu na shiga motar, ina zama Uncle ya fizga motar a guje ya bud'e Aliyu da hayak'i, waigawa na yi na hangosa yana karkad'e fuskansa sai na ji raina ya b'aci, na juyo muka had'a ido da Uncle shima fuskansa a had'e, tura kaina na yi tsakanin cinyoyina k'irjina na harbawa da sauri da sauri. *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/21, 2:16 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Mrsjmoon. E.W.F. *Shafin na ku ne 'yan uwa, abokai na gari, dukkan daukakin yan EXQUISITE WRITER'S FORUM. Allah ya bar k'auna mara algus. Amin ya rabbi.* Page 10. 'Me hakan ke nufi, na jin harbawan zuciya dik in na had'a ido da Uncle? Please zuciyata kada kiyiwa first love d'ina haka, wallahi ina son Aliyu.' "Shi ne wane?" Maganar Uncle ya dawo dani duniyar zancen zuccin dana afka, d'agowa na yi na kalleshi kad'an sannan na amsa a ladabce. "Classmate d'ina a tahfiz kuma abokin koyarwana duk a can." "Only wad'annan ne alak'arku?" "Yana s... Sai na yi shiru na kasa k'arisawa. Shima bai kuma cewa komi ba ya cigaba da gudu saman kwalta sai da muka sauka titi muka shigo layin unguwarmu sannan na kuma tsinkayar maganarsa. "Yana sonki ko kina son shi?" Idanu na tsira masa batare da na amsa ba, shima kallona ya yi ya sauke murmushin gefen baki. "Naji dad'i da ya kasance fagen ina da d'an takara domin hakan ya alamtamin cewa mallakan Nana Khadijatu ba abu mai sauk'i bane, sai an zage dantse, sai anyi kamar anayi sannan tamkar fad'a ce a filin daga inda kowa zaiso ya sami narasa akan abokin karawarsa, dan hakan zan zamo jarimi ta ko wani fuska domin hanin na yi nasarar sunkuce Nana Khadijatu amatsayin mallakina." Bugun numfashi ya k'aru, innalillahi wa Inna ilaihin raji'un kawai na ke ja dan ban zaci Uncle zai iya ambatamin wad'annan kalaman ba ido na ganin ido. "Ina neman alfama da kiyimin girki dan na yi kewar abincinki, shin Zan samu?" Motsa kai na yi kawai saboda yarda bakina ya yimin nauyi. "Nagode." Ya ambata cikin fitar murmushi mai sauti. Horn ya yi a gate d'in gidansa na dubesa da sauri. "Dan Alalh ka bari in sauka a nan." "Ba'a nan na d'aukeki ba." Ya bani amsa a d'an fusace. Yana gyara Parking Aunty Nafisa na isowa wurin. "Kagani ko Uncle da ka saukeni a bakin gate na tafi amma yanzu gashi nan matarka zata kuma il... "Kiyimin shiru Deejah ko ranki ya b'aci." Tsuke bakina na yi tare da zamewa na kwanta cikin seat, ina ambaton sunar Allah. "Malama ki fito kije kiyimin abinda na ce." Fitowa na yi jikina na rawa aikam Aunty Nafisa takawomin cafka na kwalla ihu tare da komawa cikin motar na kulle. "Nafisa wallahi zan sab'a miki gaban ma'aikatanki.." "Wallahi baku isa ba ku ci amanata ace bazanyi magana ba sabida mulkin mallaka, na rantse yau sai na lahira ya fita jin dad'i." "Kika sake magana billahil azim saina baki mamaki, in kuma kince wasa ki sake furta kalma kigani." A fusace Aunty Nafisa ta bar wurin. "Fito muje ciki." "Uncle dan soyayyarka da Manzon Allah ka barni inyima girkin a gidanmu." Shiru ya yi na sakonnni sannan ya ce "Ok fito ki tafi can d'in." Motsa kai na yi tare ficewa rik'e ledar da ya siyomin turaruka da wasu kayan da banfahimci meye su ba. "Bakiji ba." Cak na tsaya. "Ki had'omin da zob'o drink d'in nan mai d'and'ano kinji?." "Insha Allah." Ina amsawa na yi gaba dama ban juyo ba koda na tsaya, ina ji ajikina kallona ya keyi shi yasa har na fice ban waigo ba. "Tana da kyawun sura dana zuciya da yardan Allah ke d'in uwar 'ya'ya na ce." Ya ambata cikin murmushi, ya juya ya nufi ciki, kafin ya shiga falon ya sauya yanayinsa zuwa fuskan shanu saboda tuno 'yar darun matarsa. Nafisa na tsaye goye da hannayenta cike da masifa tana jiransa, yana shigowa kuwa ta nufesa cikin da baka'i ya yi hanzarin d'aga mata hannu cak ta tsaya tana kallon fuskansa sai jikinta ya yi sanyi bai kalleta ba haka bai furta mata kalma ba ya haye sama cikin sar-sarfa. "Thank you Beebah da kika kawomin shawara mai kyau, insha Allah Azumin bana dake zamu tafi Umrah dan kin can-canci tukuici." "Wato da jinina ka had'a baki ake son ganin bayana ko Abban Hafiz?" "Zato zunubi koda ya zamo gaskiya dan haka ki kyautatawa 'yar uwanki zato." "Bazan kyautata ba, wallahi sai naci ubanta shi yasa ta maida gidan tamkar gidan Ubanta a she tasan munafuncin da ta ke k'ullawa kenan? Shi yasa d'azun ta yi ta bani hak'uri to yanzu bata isa hanani zuwa na tijara Uwar Deejah ba, munafukan banza da wofi masu shiffan 'yan wuta kawai." Ta kai k'arshen maganar cikin sauke nunfarfashi tamkar wacce ta yi gudu. "Nafisa wallahi tallahi kinji na rantse idan kika kuskura kika fita gidan nan bada izinina ba sai kin tafi Maiguduri komin dare a yau d'in nna." A razane ta ja baya tana kallon idanunsa ya kuma zare matasu cike da b'acin rai, kafin ta furta kalma ya shige bathroom tare da bugo k'ofar. "Me suka bawa mijina ya daina lallab'ani? Me na ke shirin ji da gani idanuna biyu ba mafarki ba? Kalman saki fa ke shirin samuna dik akan wannan shegiyar yarinyar wacce bata isa komi ba. K'alu innalillahi wa Inna ilaihin raji'un!  Kishiya ni Nafisa zan zauna da ita? Kai wallahi sam ba zai yiwu ba, dik abinda zanyi sai na yi dan ganin ban zauna kishi da ko wacce d'iya mace ba." A fusace ta fito d'akin ta shiga nata ta kulle ta d'auki waya rubutu ta yi na sakonnni ta tura tana ganin ya tafi ta cillar da wayar gefe ta mik'e tsaye ta soma kai da kawo tamkar mai nak'uda. "Kai Nafisa matsala ce na yarda da zancenki Beebha ita d'in zuma ce shanta saida wuta, daga yanzu na sanja miki Nafisa, dik kika b'atamin zan rama dai-dai da abinda kikayimin na daina yi miki uzuri wanda sam bai amfanamin komi, ina kuma gode miki Beebah dan kin haskamin hanyar dawo da 'yar uwanki tunaninta." Yana maganar ne cikin fesa turare a kan yallabiyarsa, yana gamawa ya sakko falon k'asa ya kunna TV ya kamo world sport, kwallaon da suke haskawa ya d'auke masa hankali, ya gyara zama cike da jin natsuwa domin ya sami bakin kashe rigimar Nafisa cikin ruwan sanyi. *** Ina shiga gida kiran Aliyu ya shigo wayana da kallo nabi number har ya tsinke ban d'aga ba, wani ya sake shigowa sai na maida wayar silent, na iso gaban Mama na russuna wacce ke yanka alaiyahu. "Sannu da dawowa Uwata." "Yawwa Mama sannu da aiki." "Yawwa." "Ina Beebah?" "Daf da zaki shigo ta fita." "Ok, bari in hanzarta na samawa Uncle abinci dan ya rok'eni da in dafa masa wani abu." "Me zaki dafa masa?" "Ban sani ba Mama sai na shiga kitchen d'in tukunna zan duba." "In zaici Tuwon Shinkafa da miyar Agushi da sai ki d'iba masa wanda na ke yi." "Zaici bari in watsa ruwa nazo, zuwa lokacin miyar ta yi ai." "Insha Allah ta kallama kam." Daga haka na shige d'akina. "Uwata manya, komi naki a tsare yake, rayuwarki abar koyi ne ga dibban Mata, Allah ya zab'a miki miji na gari wanda zai baki kulawa fiye da wanda na ke yi miki fatan samu." Mama ta ambata cikin murmushi. Saida na gabatar da sallar azuhur sannan na zauna shafa mai, na yi kyalliya kamar ko yaushe mai sauk'i na sanya gown na yi rolling da k'aramin gyale na fito na samu Mama ta kammala har ta killace na Uncle a kula mai kyau, jug na d'auka na zuba masa zob'o wanda Mama ta dafa ta saka a fridge kafin ta zuba a robobi. Kayan da zai k'ara masa d'and'ano na zuba na jerasu a kwando. "Mama bari in mik'a masa." "Tam ki dawo lafiya." Baba maigadi na bawa ya tafi kai masa, ina tsaye ya dawo na yi masa godiya na juyo idanuna ya sauka kan Aliyu zaune a saman lipan d'insa sabuwa dal, nuno shi na yi da yatsa ina murmushi ya ko zabgomin harara dafe bakina na yi ina dariya k'asa-k'asa. "Nagode Khadija." Da sauri na kalle shi jin voice d'insa irin na mai fushi. "Na kiraki baki d'auka ba, na zo gidanku kin sanyani gaba kina dariya saboda ni talaka ne banda mota da kyau, balle uwa uba kud'i to nago... "A'a Aliyu kada kayimin wannan fahimtar tun bamuyi nisa ba." Na katse shi cikin tsare gira. "To wacce kike so inyi miki Khadija?" "Ta karamci mai cike da yarda, ban son sake jin ka ambatamin kalamai masu nuni da bambanci tsakanin talaka da mai kud'i saboda ka san dukkanninsu bayin Allah ne, ba wanda yafi wani a gurinsa sai wanda yafi jin tsoronsa. Sannan kiranka na gani ban d'auka ba ne sabida ina son kammala aikin dake gabana yanzu kuma ina yiwa fushin da kayi dariya ne sabida baiyi maka kyau ba amma duka Ina neman affuwa insha Allah zan kiyaye gaba." Murmushi Aliyu ya saki cike da samun natsuwar ruhi. "Ya wuce dama ruhin Aliyu batayi fushi da abincinta ba." "Ka ganka da iya tsokana." "Ba tsona ba ce Matar Ali ke abaincin ruhina ce." "Uhm ka dai bani kunya please." "Kunya adon Mata, right?" Harara na cilla masa batare dana amsaba. "Affuwan na daina baki kunya kinji matar Ali?" "Aliyu bakajin magana ko?" "Bari in wuce zuwa yamma zan dawo dama yanzu na biyo zuciyata ce kuma na gamsu da abinda nagani, bye." Da kallo na raka shi har ya b'acewa ganina. "Uhm Aliyu kenan, shima salonsa kusan d'aya ne da Uncle, oh ni Nana Khadijatu ta haka soyayyar ta zomin? Allah ka zab'amin mafi khairan cikinsu." "Amin Aminiyata." Na tsinkayi muryan Fanta daf da kunnina, juyowa na yi ta saukemin duka a shoulder cikin cewa "Baki da kirki Deejah." "Me na yi kuma?" "Wato maimakon ki kawoma Uncle abinci da kanki sai kika aiko masa Baba maigadi." "Fanta tsoron had'uwa da Aunty Nafisa na ke yi." "To ai ko yanzu baki tsira ba dan shi ya aikoni da kizo da kanki." Idanu na zare ta kwashe da dariya. "Dalla matsoraciya, Allah ya ceceki ni Baba ya gani na amsa na kai masa falonsa saida na zuba masa ya soma ci sannan na fito." "Nagode Aminiyata." "Bakomi, muje na ci nawa dan ina zubawa Uncle ina had'iyar miyau." Murmusawa na yi muka jera, muna shiga da Beebah mukayi arba zaune saman tabarma tana cin tuwo. "Dama ba gida kikaje ba?" Na jefo Mata tambayar. "Eh naje layin baya ne na siyo mana fruit, ai ina kallonki kina soyayya na yi hanzarin shigewa gida dan bansan ya ganni." "Saboda me?" Cigaba da cin tuwonta ta yi kamar batajini ba. Wanke hannu Fanta ta yi da zauna sai nima na wanko, Fanta ta zubo mana muka soma ci, ina hankalce da Beebah yarda ta ke kallona ta gefen ido tana sakin murmushi. "Da alama sister Beebah na son in daina kulata." Na ambata cikin doka mata harara. Dariya ta kyalkyale da shi wanda ya janyo hankalin Mama tafito a hanzarce. "Me ya faru Habiba?" "Mama bakomi kawai nishad'i na ke ji." "To Allah k'aro nishad'i mai sanya nutsuwan ruhi." "Amin Mama." Fanta da Beebah suka amsa yayin da ni kuwa na yi tamkar bana wurin. "Uwata ya dai?" "Lafiyalau Mama." "Anya? Nasan kina tare da damuwa." "Mamana ina sonki matuk'a." "Uwata kenan mai wayon sha-shantar da abinda na ke son ji." Tashi na yi na kama hannunta muka shige d'akinta, cikin bedroom muka nufa na zaunar da ita a bakin gado ni kuma na janyo stool na zauna a gabanta, na marairaice fuska sannan na soma magana "Mamana bisa alamu hasashenki akan Uncle zai tabbata, ina jin tsoron abinda zai biyo baya gashi ruhina ta kamu da son Aliyu kuma bana son in bijirewa buk'atan Uncle ko dan tarin alkhairorinsa garemu sannan ina matuk'ar tsoron zaman kishi da matarsa. Mama dan Allah ki taimakeni ki sanar da Uncle ya yi hak'uri, nasan idan kika fad'a masa zai fahimta sama da ni." Tsawon mintoci uku Mama ba ta yi magana ba. "Mama nasan tunaninki Uncle zaifi Aliyu rik'eni tunda ya fisa sanin waceceni sai dai ina son kiyi nazarin rayuwar da zanyi a gidansa na rashin 'yanci da tarin fargaba." "Uwata ko shi Alhaji Muhseen baisan komi akanki ba, abinda na ke so da ke shi ne ki barwa Allah zab'i wata k'ilama ba mijinki cikinsu. "To Mama." "Uwata ki kulasu duka, ki basu soyayyarki dai-dai misali, kada ki zafafa son wani cikinsu wanda rabuwarku zai zame miki k'alubale. Aliyu da kike ambata kina sonsa ban amince ba." "Mama ban fahimta ba." "Nufina ban yarda kiyi masa wannan k'aunar da na gani a idanuwanki ba tun bai soma takowa k'ofar gidanku zance ba sannan bama shi ba kowaye ya furta miki kalman k'auna ban amince ki zurfafa son sa ba, kiyi masa dai-dai misali da fatan kin fahimce ni?" "Eh Mama." "Da kyau tashi kije wurin su Fanta kada abarsu su kad'ai." Fitowa na yi na samu sun gyara wurin sun shige d'akina, ina shiga Fanta ta rangad'a gud'a na ja baya idanu waje suka tafa ita da Beebah, tsaki na ja cikin raina na janyo stool na zauna na zuba musu ido, iska Beebah ta huramin na kullesu da sauri. "Wani sak'o Uncle ya sanarmiki ki fad'amin?" "Yana muradin da ki zama matarsa ta sunnah uwar d'iyoyinsa, kin amince?" Numfashi na sauke ahankali. "Zanyi tunani." "Ai baki isa ba, eh kawai na ke son ji yanzun nan ba sai anjima ba." "Kina farin ciki da ayiwa yayarki kishiya kenan?" "Eh." Ta amsamin kai tsaye. Murmushi na yi dan sam banji mamaki ba. "To ni ina tsaron kishi da ita, ki sanarwa Uncle da haka." "Ma'ana dai kin amince zaki auresa Aunty Nafisa ce matsalarki?" Dan Allah Beebah ki fahimceni mana, ke fa Aliyu ya aiko amma yanzu kinayi tamkar baki san komi ba." "Ke d'in allurar cikin ruwa ce mai rabo ka d'auka dan haka Deejah sanin mijin sai Allah, wata k'ila daga Aliyu har Uncle ba mijinki cikinsu sai dai abinda na ke son ki sani shi ne mace bata tsaida mutum d'aya ta ce shi zata aura, tana iya yin samari sama da biyar kuma sai kiga wani daban ya fito ya aureta, yanzu dai ki nemi zab'in Allah cikinsu dama wanda zasuzo nan gaba." "Tabbas maganar Sister Beebah gaskiya ne insha Allah Deejah sai kin had'a goslow a k'ofar gidan nan masu gulman kin rasa masoyi suji kunya." "Uhm Fanta kenan, kidai tayani addu'ar samun miji nagari kawai, masu gulma kuwa banda lokacinsu, su aiki ya sama." "To Allah ya bamu baki d'aya." Beebah ta ambata a hankali. "Amin." Muka amsa atare da Fanta. "Deejah wallahi inajin murna ainun ganin yarda kika soma tara masoya damuwarki akan rashinsu ya zamo tarihi." "Nagode Beebah, ni kaina ina cike da mamakin lamarin." "Komi fa lokaci ne K'awata." "Haka ne kam Aminiyata." "Aha ansoma nuna wariyar ba." Beebah ta ambata cikin zabgo musu harara. Dariya muka sanya har ita. "Yau su Bintu na hanya ya kamata in dafa musu abincin tarba." "Yes Deejah tafi mu san abiyi musu dan yau Aunty Nafisa bata cikin kuzarin dafa komi shi yasama inaga Uncle ya ce kiyi masa girki." "Sabida ta ganni tare da shi ko?" "Oho mata dai." Fanta ta amsamin cikin zunkud'a shoulder. Kafin in sa ke magana ta fice. Beebah na kalla ta saukemin murmushi ta ce "D'azun Aunty taga fitarku ta yi nufin zuwa ciwa Mama mutunci kafin ta iso Fanta ta kirani sai na tareta a waje na maidata gida amma dan Allah kada hakan ya baki tsoro domin hausawa sunce auren da aka soma samun rikici yafi k'wari." "Uhm wannan kawai zance ne ba tabbas a cikinsa." "Ni dai na rok'eki domin Allah da Manzonsa kada ki bijirewa muradin Uncle." "Beebah na rasa gano abinda yasa kuna 'yan uwa na jini ga Aunty Nafisa amma kuke goyon bayan mijinta da yayi mata kishiya." "Tashi muje idan su Bintu sun iso sai muyi maganar a gabansu kiji kalamin bakin kowa akai, ina ganin zakifi gamsuwa." Tashi na yi muka fito daidai lokacin Baba na shigowa, dank'e hannuna Beebah ta yi jikinta na rawa, kallonta na yi na kuma sauke idanu kan Baba wanda ya shigo a fusace "Innalillahi wa Inna ilaihin." Na ambata a hankali. "Ubanki kika tsaya kallo mai siffan aljannu?." Na tsinkayi muryan Baba saman kaina, ja baya na yi cikin girgiza kai. "Hurera!" Ya kwallawa Mama kira. Bata amsa ba ya kuma kiranta, sai da Baba ya kirata sau hud'u sannan ta fito tana murza ido bisa alamu barci ta soma, kallon da Mama ta saukemin yasa na ja hannun Beebah muka shige kitchen wurin Fanta. *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/23, 2:05 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Safiyya (Mrsjmoon) E.W.F. Page 11. "Kiyi hak'uri Deejah amma mahaifinki ya cika fad'a, wallahi tsoro ya bani ganin yarda ya shigo a fusace sannan d'azun da safe na sunkuya ina gaisheshi amma ko kallo ban isheshi ba, na yarda wannan halayyan nashi ya sanya baku jituwa." "Sister Beebah halayyan Baba halitta ce dan koni ada tsoronsa na ke ji amma tunda na fahimci haka Allah yayoshi sai na saba kamar yarda Aminiyata ya bi jikinta." "Uhm ku mumaida hankali a kan aikinmu kunsan kowa abin da tafi so za'a dafa mata." Na datse zancen saboda yarda na ke jin b'acin rai kuma ban son su gano hakan. "Hakan ba zai yiwuba kawai muyi musu girki d'aya wanda zasuci baki d'ayansu." "Nima hakan naga yafi Sister." "Ki tafi ku huta insha Allah kafin su iso na kammala komi." Na kuma ambata cikin tsare gira. "Baza'ayi haka ba Fanta tafi ki d'ebo komi a gida kizo ayi amfani da shi." "Idan ta d'ebo kada tazo dashi gidan nan, insha Allah bazamu rasa abin yin amfani ba duk da muna talakawa." "Ya Salam, please Deejah ki fahimce ni mana." "Beebah dan Allah kiyi shiru muyi abinda ya kamata dan banjin ina da natsuwar fahintarki ba." "Tam na yi shiru Aunty." "Ko ba Aunty ba." Dariya suka kyalkyale da shi ganin yarda na tsuke fuska. "Fushin baiyi miki kyau ba Aminiyata." Murmusawa na yi. "Yawwa ko ke fa sai annuri na kuma cika kyak-kyawar fuskanki." "Ban da zagi fa Aminiyata." "Allah ba zancen zagi domin ke kanki kinsan mai kyauce tamkar tauraruwa cikin dubbab taurari." "Kinyi na kud'in ki wallahi." "Ai gaskiya Fanta ke fad'a ke d'in tubarkallah masha Allah, tamkar 'yar buzaye ko Shuwa Arab." "Eh wallahi Sister Beebah." "Dan Allah ku barmin kunnuwa su huta." "Ank'i sai kin sanar da mu nasabanki daga wani yare kika fito." "Yaren Baba mana Hausa Fulani." "Amma kinsan Allah ko a farce baki kama da Baba haka 'yan uwanki duk kinfisu kyau duk da suma da farare cikinsu amma naki hasken na dabanne." "To ni bakuga yarda Mama ke da haske ba, ita na d'auko." "Eh gaskiya hasken Mama kikayo aminiyata amma duk da haka kinfita fari." "Eh nafita kam amma ai munyi kama." Karkacewa Fanta ta yi tana k'aremin kallo na kai mata duka ta ja baya cikin cewa "Kuna kama a halittan idanunku da kyawun diri amma in banda nan ban hango ta inda kukayi kama ba." "Kai Fanta ki duba dai da kyau hatta madai-daicin bak'insu iri d'aya ne." "Kai Beebah a she haka kika k'arewa Mama kallo?" "No a photonku na tantance." Banza na yi da su ganin in na biye musu ba zamuyi abinda ke gabanmu ba. Bintu Alale, Firdausi jelop d'in macaroni jelop sai Safina shinkafa da miya. Komi dai-dai mukayi yarda bazai zamo anyi albazaranci ba. Mun jere abincin a d'akina muka zauna muna hira Fanta ta kalli Beebah ta langab'e kai. "Me ye malama?" "Dan Allah Sister idan ya iso ki kulashi kinga domin ke zaizo" "Wai Yaya Abdallah zai kawo su?" "Eh." Dogon tsaki Beebah ta ja tare da mik'ewa zata fice. "Kada ki yi haka sabida ance bak'onka Annabinka." "Fanta wallahi inda na san munafuncin da kuka k'ulla kenan tabbas da bazan jirasu ba zan wuce amma ko yanzu ba zaku sami abinda kuke so ba na rantse." "Eh mun yarda amma dan Allah ki kulashi cikin walwala in ya wuce sai kiyi mana duk masifar da kika so." Shiru ta yi, Fanta ta janyo hannunta ta zaunar gefen katifa tana yi mata magana a kunni, tagumi ta zabga na yi gyaran murya ta kalleni na girgiza mata kai, murmushi ta saukemin wanda a fili na dole ne saboda hakan ya bayya a saman fuskanta. "Me ke faruwa, kuke 'yan b'oye-b'oye?" Na cillowa Fanta tambayar duk da shiga lamarin rayuwar mutane ba halina ba ne. "Gata nan kiyi mata nasiha ta daina wulak'anta mana Yaya, saboda shi tak'i bin su Bintu sada zumunta shi ne ya biyosu domin ya ganta dan ta yanke alak'a dashi tsawon wasu watanni, ta daina d'aukan wayarsa tayi blocking nasa a k'arshema ta saka shi a black list, in kuma ya kirata da wayar Mamansa ko k'anninsa tana jin muryansa zata kashe wayarta baki d'aya." "Innalillahi, me ya yi zafi haka?" "Wai bazata auri mai mata ba saboda tana tsoron jarabar matarsa mai hali irin na Aunty Nafisa sak." Wani zabura Beebah ta yi tayo kan Fanta, ita kam ta kwasa da gudu ta fice zata rufa mata baya na rik'eta cikin tsare gira na ce "Ke kin gujewa auren tashin hankali amma ni kin dage sai na yi?" Numfashi ta yi ta saukewa cikin alamun fushi, zuwa can ta yi gyaran murya sai lokacin na saki hannunta dana kama. Ruwa ta d'auka ta sha sosai sannan ta k'ara yin gyaran murya ta soma magana cikin natsuwa. "Duk abinda Fanta ta sanar miki gaskiya ne illa abu d'aya shi ne da ta ce halin Mas'uda d'aya da na Aunty Nafisa, sam halinsu ya sha bamban saboda Aunty Nafisa bata tsafi haka tana shakkar Uncle Muhseen sakamakon da ita Mas'uda mijinta bai isa da ita ba hatta da mahaifiyarsa sai taso yake zuwa gaisar da ita, k'anninsa kuwa ta haramta musu zuwa gidanta, tun abin na damunsu har yanzu ya daina. Shin ta ya ina kallon wannan lamari zan amince na zama matar shige wacce bata tab'a yin daraja." "A gaskiya Mas'uda bata da hali amma duk da haka ina ganin aurensa zai baki damar kwatosa daga halaka, domin zaki nusar da shi hakkin uwa kan d'iyoyinta, kiga kenan tamkar kinyi jihadi ne." "Ada naji zan iya yin hakan amma tunda na had'u da burin zuciyata duk da shima tamkar son maso wani na keyi masa wanda masu iya magana kan kirasa da k'oshin wahala, naji gara in hak'ura da shi na kama na gasken a haka nan." "Son maso wani bana gaske ba ne Sister, kidai yi hak'uri ki kama Yaya Abdallah please." "Ko mu biyu muka rage a duniya ba zan aureshi ba." "Me ya yi zafi?" Banza ta yi da ni na rik'o hannunta "Beebah walalhi Abdallah ya bani tausayi yana cikin matsalar rayuwa gashi kin kasa fahimtarsa." "Shi kuma baisan da yana cikinta ba domin duk wanda ya nusar da shi illar rayuwar da a keyi a gidansa sai ya k'ulla gaba da shi nima dan na nuna masa illar watsi da goggo da ya keyi shi ne ya soma zagina tamkar ya sami d'iyarsa har da cewa bashi bani shi ne na nuna masa nid'in 'yar halas ce na datse dik wani hanya da zai sadani da shi domin na fahimci gani yake bazan iya rabuwa da shi ba saboda kud'insa tare da kyawun da Allah ya bashi sai dai ya makaro domin ni una sonshi ne domin Allah badan wani abu nasa da Allah ya yi masa baiwar samu ba kuma kinji na rantse wallahi har ya koma ba zaiga dariyana ba, zai san ya zageni, zai san ya kirani da wawiya, banza, wofi mara tunani." Innalillahi wa Inna ilaihin, a gaskiya Yaya Abdallah bai kyauta ba, zagi na zubda mutunci duk kuwa yarda kake d'aukan mutum." "Ai kam ya zubar masa a idanuna, zubewa na har abada." "Please Beebah ki sassauta hukuncin da kikayi masa, ki tarbesa in yaso da ya tafi ki watsar da shi." "Ai na rantse kuma bazanyi kaffara ba, walalhi zai san ni 'yar hakas ce gaba da bayana." "To Allah ya kyauta, abin ya girmama." "Amin." Shiru mukayi zuwa can na ce "Tashi kiyi wanka tunda kin koramin Aminiya, idan kin fito sai inyi." "Na fasa." "Duk saboda jin Ab... "Deejah dan girman Allah kibar zuciyata ta sami natsuwa da kiramin sunar mara hankalin nan." "Na shiga uku ni Nana Khadijatu." "Ki tafi kiyi wankanki." "Ok bari na fita na samo musu drinks saboda ba abasu Zobo da kunun Aya kawai ba tunda gasu tafe da babban bak'o." Harara ta zabgomin na murmusa tare da ficewa. "Walalhi sai na ciwa su Safina mutunci musanman Bintu dan nasan itace uwar kaud'in ingizashi ya zo." "Ba ita bace sister Beebah, goggo ce da kanta ta ce ya dawo dasu kuma shi ba danke zaizo ba ni ce na ambaci hakan amma dan Allah kiyi hak'uri bansan haka ranki zai b'aci ba." "Bakomi Fanta ya wuce." Ta ambata cikin sakin fuska tamkar ba ita ce ta murtukesa ba. Murmushi suka sakarwa juna. Tafi na soma daga bakin k'ofa sannan na shigo muka had'a ido da Fanta na kanne mata ido d'aya ta yomin jinjina da babban yatsarta amma a wayance gudun kada Beebah ta harbo jirgin domin plan muka had'a dan ta sakewa Abdallah fuska. "Kin san Allah Deejah sister Beebah tana da gaskiya dan Yaya Abdallah mijin ta ce ne na gaske, hatta da unguwa in zaije idan matarsa bata gamsu ba fasawa yakeyi wai baya son barinta cikin tunanin inda ya je." "Ikon Allah amma kam ta sami miji mai gaskiya." "Uhm na banza da wofi ba tunda na b'atawa mahaifiyarsa raina akanta." "Kuyi masa addu'a wata rana sai labari." "Idan sister Beebah ta amincewa aurensa ba." "Ba sai Beebah ce zata saitashi ba ko matarsa zata iya nusar da shi illar b'atawa iyaye rai." "Banjin hakan zai faru ba tunda akanta komi ke faruwa, ita ce silar faruwar komi dan ance tunda ya soma neman aurenta halayyansa na kirki suka sanja zuwa na tsiya." "To Allah ya shiryata." "Amin, shi yasa na ke ya bawa Uncle wallahi domin shi jajirtacce ne domin duk son da ya keyiwa Aunty Nafisa tana sab'awa umurninsa zai hukuntata musanman da yanzu sister Beebah ta kuma d'orashi akan hanyar saita mata tunani wanda muke fatar halin rashin kirkinta ya zamo tarihi." "Ku ne kuka ambata masa ya nemi aurena kenan? Shin kuna tunanin tahanyar yi mata kishiya ce zai dawo da ita hanyar gaskiya?" "A'a shi da kansa ya ambata yana sonki wanda najima da fahimtar d'abi'unki na burgesa bai furta miki kalman k'auna ba ce sai yanzu, kinsan komi lokaci ne. Sannan Aunty Nafisa kuwa muna fatar ta dalilin zama dake ya saka ta yi koyi da halinki nagari ta dawo mai kyakkyawar mu'amala da kowa musanman mu jininta." Shiru na yi na kasa sake cewa komi saboda yarda nake jin fad'uwar gaba. Gyaran muryan Beebah ya sanya muka gane ta fito wanka, da sauri Fanta ta shige toilet dan gabatar da wankan itama. "Insha Allah tsoron da ke ranki zai zamo tarihi sabida muna kanyi miki addu'ar samun rayuwa mai inganci a gidan Uncle." "Ke da su wa?" "Mama da Sisters d'ina." "Shin da gaske su Bintu sun san da maganar nan?" "Eh dan aminiyarki ta fesa musu kuma sunyi na'am da lamarin saboda zamansu da ke na kwanaki biyu sun fahimci bakya da matsala zaki iya hak'uri da halayyan 'yar uwanmu." "Uhm har yanzu kuna kan bani mamaki wai ace kuna 'yan uwar Aunty Nafisa na jini amma kuna murnan da ayi mata kishiya." "Ke ba kishiya ba ce Deejah, abokiyar zamace tagari mai tarin nagarta wanda muka tabbatar bazata iya bin hanyar banza ba dan ta cutar da 'yar uwanmu sabida kina aiki da iliminki kuma kin gama samun tarbiyya daga uwa ta gari wato Mama." "Nagode da wannan yabawan, insha Allah zan nemi zab'in Allah cikin shi da Aliyu, duk wanda ya zab'amin zan amshesa da hannu biyu tare da mik'a godiya gareshi." "Uwata neman zab'inki ya kasance na kan kowa da kowa ne ma'ana ki nemi zab'in Allah akan duk inda mijinki yake yazo gareki bisa amincinsa idan kuma yazo to ki amshesa da hannu biyun da kika ambata domin yanzu bana goyon bayan Alhaji Muhseen ko Aliyu saboda zab'in Allah shine sama da komi haka yardansa babban alkhairi ne ga rayuwar bayinsa dan haka ked'in alluran cikin ruwa ce mai rabo ka d'auka, ina fatar managarci, jajirtacce, mai tsoron Allah S.W.A da son Manzon Allah S.A.W zai d'aukeki ku rayu cikin inuwar aure na har abada." "Amin ya rabbi Mama." Beebah ta ambata cikin rawar murya saboda kalaman Mama sun shigeta ainun, ita dai zuwarta garin Kaduna tana ta samun natsuwar ruhi ta kalaman Mama masu cike da fikra. Ni kam zubewa na yi gaban k'afafun Mama ina jan numfashi. Kamo ni ta yi ta rungume tana bubbuga bayana. "Habibatu aramin ita muje unguwa, inaga sai bayan isha'i zamu dawo sai ku kula da gidan." "Tam Mama kudawo lafiya." "Allah ya so hakan." "Amin." Daga haka muka fice Mama na rungume da ni, a d'akinta na yi wanka na shirya. "Uwata gidan Baba Umaru zamu saboda lamarin Malam yasoma bani tsoro kada wata rana ya kasheni ya maidake marainiya ya mallake dukiyar da ke zalama akan shi." "Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un, Mama me ya kawo wannan magan-ganun? Dan Allah kidaina ambatarsu dan suna sanyamin shakku." "Shakkun me ne Uwata?" Shiru na yi ganin haka sai ta ja kunnina da k'arfi na sanya k'ara ta kuma mud'ewa rik'e hannunta na yi cikin cewa "Shakkun ganin kamar ni ba d'iyar Ba... "Nana Khadijatu!!." Kiran sunana da Mama ta yi da k'arfi ya sanya ni yin dif da maganar ina girgiza kai. "Wuce muje kuma kada na sake jin wannan banzan kalamin ya kuna fitowa a bakinki.' "Kiyi hak'uri Mamana." "Na yi, wuce muje magriba na kawo jiki." Tafe muke a cikin Napep ina nazarin yanayin Mama, na hango tana tare da damuwa amma tana k'ok'arin b'oyemin sai na samu kaina da jin b'acin rai abinda na ke korerarsa kullum yana neman samun muhallin zama a ruhina wato tsanar Baba domin na tabbata shi ne silar faruwar b'acin ran Mama ta dalilin shigowarsa d'azun. Sadda muka isa gidan Baba Umaru suna gabatar da sallar magrib muma alwalla mukayi muka gabatar inda bamu tashi ba muka cigaba da azkar zuwa lokacin sallar isha'i domin tarbiyyan zuri'ar Baba Umaru idan anyi sallar magrib ba'a tashi sai an sallaci isha'i sai bisa babban dalili, hatta da yara k'anana 'yan shekaru Tara zuwa sama sun san da d'abi'an, 'yan k'asa da sune kawai zakaji karad'insu suma da zarar Baba Umaru ya shigo zasu natsu saboda baison hayaniya sam amma fa ya iya jan jikokinsa da sawa kamar yarda yakeyimin. "Jikalle kuma takwarata kin b'uya ko kuma ince Hurera ta b'oyeki, sam bata bari kiyi zumunci da mu." "Ayi hak'uri Hajiya Inna, ai gani yau nazo a gadonkima zan kwana." "Kamar gaske." Murmushi na saki ina kallo idanun Mama da itama ke doka murmushin. Surikan gidan ne sukayi ta shigowa d'akin Hajiya Inna suna gaisar da Mama ni kuma ina gaisar dasu cike da kunya saboda yarda suke ta k'orafin na daina zuwa gaishesu. "Zata rik'a zuwa duk ranar Juma'a insha Allah." Mama ta ambata cikin 'yar dariya. "To Allah ya nufa hakan." Hajiya Inna ta amsa. "Amin." Suka amsa tare da ficewa. "Taho muje mu gaisa da Baba naji shigowarsa." Mama ta ambata cikin tashi tsaye. "To." "Hurera abi komi a hankali banda gareje kinji?" "To Inna." "Alhaji ya soma sanarmin da lamarin, ina ta yaki addu'ar Allah ya rayaki ku jima da Nana Khadijatu." "Amin ya rabbi Inna." "Sannan kiyi tunani akan zuwa wurin danginki domin shekara ashirin da d'aya ba kwanaki ashirin da d'aya ba ce." "Insha Allah Inna zanje domin har da maganar nazo sanarwa Baba amma sai na soma zuwa Kwara naga zuri'ar Baba Abdul Ganiyu." "Masha Allah Allah ya ida nufi." "Amin." Ina tsaye ina saurarensu farin ciki ya gama cikani jin zamuje wurin dangin Mamana abin da najima ina mafarkin zuwan lokacin. "Uhm inda rai da rabo." "Tabbas haka nr Uwata." Kallon Mama na yi a she zancen zuccin da na yi ya fito fili. "Idan kin gaisar da Baba ki fita in mungama zan kiraki." Ta sanarmin daf da zamu shiga falon Baba Umaru. "To Mama." Da sallama muka shiga falon dattijon ya amsa mana tare da cillomin tsokana irin ta jika da Kaka. "Matar b'oye yau ta bayyana to ki koma bana yi dan ban rasa mai neman ladar ba, gasunan buhu-buhu sai wanda naga damar ansawa gaisuwa tare da sakawa aiki." Dariya na sanya saboda yarda yake maganar cikin zare idanu cike da barkwanci. "Alhamdulillah yau na saka mai fuskan shanu dariya." Nan ma wani dariya na kuma sanyawa cikin kulle bakina, hatta da Mama dariyar ta ke yi. Bayan mun gaisheshi na fito na bar Mama zaune gabansa cike da ladabi. D'akin Hajiya Inna na dawo muka soma hira cikin maida zancen halayyan Baba wanda na fahimci na b'ata mata rai ainun. K'aran wayata ya katse mana hiran ganin Aliyu ne sai na kalleta ta sakarmin murmushi tare da mik'ewa ta fice tana cewa "Takwarata ba dai kunya ba to na bar miki d'akin, a ci soyayya lafiya." sunkuyar da kai na yi, ina jin ta fice na gyara zama tare da d'aukan wayar wanda kiransa na biyu kenan, yi masa sallama na yi cikin laushin murya fiye da wanda Allah ya horemin. *Affuwan 'yan uwa l ina cikin uziri ne shi yasa jiya kuka jini shiru.* *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/24, 11:20 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Safiyya (Mrsjmoon) E.W.F. Page 12. "Kayi hak'uri mantawa na yi in sanar maka da mun fita tare da Mama." Na ambata masa bayan ya amsa sallamar. "Kada kidamu Habiba ta sanarmin yanzu suka shiga gida ai sun fansheki musanman Fanta da ta ce zatayi miki hiran tare da yin recoding idan kinzo ki saurara." Dariya muka sanya daga nan muka cigaba da hira inda na dage ina maida masa da martani amma duk da haka wani kalman tanayimin nauyin ambata. Kimanin mintoci goma shabiyar muka d'auka sannan mukayi sallama, sosai zantukan Aliyu suka sakani cikin nishad'i. Kwanciya na yi a saman kushin ina doka murmushi. "Hak'ik'a ina sonka Aliyu." Na ambata a fili sai kuma na yi saurin kulle bakina tare da kife fuskata a filon kujerar saboda da yarda kunya ya ziyarce ni. Misalin k'arfe tara da mintoci bakwai kiran Mama ya shigo wayana ban d'auka ba sai na tashi na nufi falon Baba Umaru dan nasan tafiya zamuyi. Ina shiga idanuna ya sauka kan Kawu Habib b'ata rai na yi cikin kauda kai aikam ya kyal-kyale da dariya su Mama na tayashi dan sunga abin da na yi. "Ko kuka kika fasa ba zai hanani na kiraki da Dije ba." "Ni ba Dije ba ce, Hajiya Inna kina jinsa na b'ata miki suna ko?" "To Takwara ya zanyi da d'an neman zance, ai inda kara ke d'in Mama ya kamata ya kiraki." Kallonsa na yi ya murgud'amin baki kamar mace sai na sanya dariya ya ko taho kamar zai dukeni na manne jikin Hajiya Inna. Gaisar da shi na yi ya amsa cikin kamala tamkar bashi ba. "Khadijatu Mamanki ta yi miki kyauta amma ta ce kada a sanar miki yanzu amma dai mune shedu dan haka ki kasance wurin yi mata addu'ar gamawa lafiya domin samun uwa kamarta sai antona." "Nagode Mama Allah ya sa kifi haka, Allah ya baki kyautar Aljanna ranar sakamako." "Amin ya bamu baki d'aya Uwata." "Amin." Habibullah tashi ka maidasu gida tunda hanyarka ce." "To Baba." "A'a Baba kabarshi ya tafi wurin iyalinsa sabida zan biya gidan Malam kafin mu isa gida." "Yaya Hurera muje in kaiku inba dai kina son bambance matsayina gareki ba ne." "Shi kenan Habibu muje, dafanta zakayi dariya ka daina cin maganin." Ficewa ya yi cikin murmushi. Muma sallama mukayi da su Baba muka sameshi har ya kunna motar. "Dije zaki zo taron suna gobe ko?" "Sunar wa?" "Kar dai ince bakijemin barka ba?" "Ya Salam Aunty Zainab ta haihu ne?" "Uhm ba laifinki ba ne na mamanki ce, yanzu na yarda da zancen Hajiya Inna sam baki d'aukemu a danginki ba kamar yarda muka d'aukeke." "Habibu kayi hak'uri ni kaina banje barka ba dan namanta amma zamuje taron suna insha Allah." "To, Allah baku iko. Shiru ya ratsa motar zuwa can na ce "Kayi hak'uri Kawu Mama zata zo   goben amma ni bayan sunar zanzo." "Saboda me?" "Kasan Uwata kifin rijiya ce data shiga taro sai taga kamar ita kowa ke kallo shiya bata son shiga taron jama'a sai dole." "Da gaskiyanta tana da abin kallo musanman ga maza." Da sauri na kalleshi ya murmusa tare da maida hankali kan titi." "Habibu kaifa Kawun Uwata ce amma na lura kana son maida ita abokiyar wasanka." "Yaya Hurera wallahi gaskiya na ambata Deejah na da abin kallo kamar ilimi, hankali, natsuwa da uwa uba hak'uri, shi yasa mazaje zasu so mallakanta a matsayin uwar 'ya'yansu, na tabbata duk wanda ya aureta ya yi babban dace tare da rabon na samun mace ta gari wanda Manzon Allah S.A.W ya ce dace da samunta shi ne mafi jin dad'in duniya." "Zancenka gaskiya ne Habibu." "Kinga kenan dole ta rik'a killace kanta ba ko wani kucaka da gara ya kamata suna kallonta arhaba." "Kai Kawu dan Allah kadaina fasamin kai." "Yabon gwani ya zama dole Deejah, ke dai ki godewa Allah da kika tara baiwa wanda ba kowa yake samunsa ba." "Nagode Kawu." "Godewa Allah 'yar Kawu." "Habibu hoo, ba dai tsokana ba." "Yaya haka Allah ya halicceni ya zanyi." "Sai hamdala ga Allah." Na ambata a hankali. Sadda muka isa k'ofar gidan Baba k'arfe tara da rabi saura mintoci biyar. "Ku shiga ina jiranku." "A'a Habibu ka wuce kada mu b'ata maka lokaci." "Bakomi ina jiranku." Shigewa mukayi ina jan addu'a saboda nasan ba zamu fito lafiya ba batare da an b'atawa Mama rai ba. "Mama wai me yasa ba mu bari mun zo da safe ba?" "Yanzu Allah ya nufa muzo. Kayan auren Khamila aka kawo." "Oh an dai-daita kenan?" "Oho musu nidai an sanarmin an kawo kayanta bisa alamu wani ne dan wancan anmaida masa nasa tunda makashin mutane ne." "To Allah sanya khairan." "Amin." Dun zancen cikin rad'a mukeyinsa har muka shigo tsakar gidan inda muka sami mutane cike ana ta kallon kayan cikin mutunci Mama ta gaisar da su suka amsa nima na gaishesu suka amsa tare da zubomin idanu abin da natsana kenan shi yasa ban son zuwa gidan sai suyi ta kallona tamkar sunga sabon halitta. Baya na juya musu ina latsa wayata inda na ke hira da su Beebah a wani group danaga an sakani. "D'iyar golden ko sai yaushe mijin da ake jira zai fito?" "Lokaci dai, zab'in Allah bana mutum ba na nan tafe." Juyowa na yi jin amsar da Mama ta bawa Uwar gidan Baba mai suna Asabe. "Uhm wai ba, ko sai an tsufa ba zab'in Al... "Kada ki sake kiyi sab'o Asabe domin shi zab'in Allah ba wanda ya san sadda zaizo saboda cikin rashin tsammani ke zuwa dan haka ki sanya ilimi kafin ki furta kalami." Tsit wurin ya yi zuwa can jama'an wurin suka soma yiwa Asabe fad'ar rashin dacewar abinda ta yi tare da bawa Mama hak'uri, ganin abin na son zama rigima babba sai Mama ta yi musu sallama tare da yiwa maman Kamila fatan alkhairi muka fito Kawu Habibu ya ja muka tafi amma ina lura da yarda Mama ke ta sauke ajiyar zuciya alamun ranta ya b'aci hatta da Kawu ya fahimci bata cikin wal-wala shi yasa bai nemi maganaba har muka isa gida. Abin mamaki Aliyu na gani zaune saman lifan nasa, yana ganinmu ya diro ya zube gaban Mama ya gaisar da ita cikin girmamawa sannan ya koma wurin Kawu ya gaisar da shi. Sunarsa Kawu ya kira ya amsa yana sunne kai. Mama da Kawu ciki suka shiga ni kuma natsaya wurinsa. "Dare fa ya yi Yallab'ai." "Alk'awari na yi sai na gaisar da Mama yau tunda kuma na cika burina  sai ince Allah tashemu lafiya." "Amin, nagode da k'auna." "Ba godiya tsakaninmu Matar Ali." Girgiza kai na yi, ya kunna mashin d'in ya tafi cikin d'agamin hannu. "Dujengala kice in-law shi ne jarimin?" Kauda kai na yi, ya sanya dariya. "Sai da safenku Yaya." "Aha mungode Habibu, agaida masu jegon kafin muzo." "Zasuji." "Allah kaika gida lafiya Kawulle." Na furta masa cikin tsokana. Duka ya kawomin na gofce ina dariya dan nima na sami sunar kiransa. "Wannan yarinya zata haukatani fa, to na wuce dai." "Da dai ka zauna neman magana." Cikin dariya ya fice na kalli Mama ta nunamin d'akina "Tafi ki huta da safe zamuyi magana nasan son sanin inda Habibu ya san Aliyu kike son ji." Da sauri na fad'a d'akina, ina jiyo dariyarta. "Sannu da dawowa Aunty Deejah." Idanu na ware jin sunar da Beebah ta ambatamin. "Eh ke Auntynmu ce tunda Uncle Muhseen ya fad'a fagen yak'in nemna mallakan ruhinki." Toilet na fad'a batare da na biye mata ba, dariyar danaji an kwashe da shi yasa na fito da sauri Bintu ce kwance saman katifa sam ban lura da ita ba. "Ke ma kina bayansu Fanta ko?" "Eh kuma ki sani har k'anwar Uncle ta Sami labari cikin satin nan zata shigo Kaduna may be time d'in mun wuce dan jibi kamar yanzu kowa na kwance saman gadonsa yana huce gajiya." "Nikam me yasa kukeyimin haka ne? Yanzu kunsa zata zo idan ta sami labarin ba haka bane me zaku ce da ita?" "Nufinki wancan yaron kike so wanda bai wuce sa'arki ba?" "K'anina ne kin manta." "To wallahi kada ki bashi lokacinki a banza da wofi domin baku dace ba sam." Banza na yi da ita na koma toilet. Har na kwanta na jiyo maganar Bintu. "Deejah kada kiyi Wasa da damarki domin samun miji kamar Uncle Muhseen rabo ne, tun kafin kuyi nisa ki sallami Aliyu dan wallahi indai muna raye baki da miji sai Uncle Muhseen." "To Baba da Mama." "Zancen gaskiya ne dan nasan Baba da Mama suna ganin Uncle wanda ya mallaki komi bazasu amince su bawa wanda ke neman na siyan sutura ba." "Kinga Bintu ki kyaleni inyi barci tam." "Bazan bar kiba sai kin san waye Uncle." Banza na yi da ita, Ina jin Beebah na dariya k'asa-kasa bisa alamu ita ta kunna wutan ta koma gefe. "Ai kin shiga uku tunda Bintu ta ke yin lamarin fiye da kowa." Tashi zaune na yi na zubawa Beebah idonu ta gyara zama cikin cewa. "Ni da Bintu da Aunty Nafisa dakinmu d'aya. Fanta d'iyar k'anwar Momy ce. Safina da firdausi su kuma d'iyoyin yayyun Momy ce. Iyayenmu kansu had'e shi yasa muka taso da son juna dan duk gidan da mukaje ba'a nuna bambanci, abu d'aya muke." "Da kyau." Na ambata tare da komawa na kwanta. "Kada ki yi mamakin yarda dukkanmu muke son ki auri Uncle sabida ke ce zaki iya zama da 'yar uwanmu ba cuta ba cutarwa." "Ni kuma ta cutar da ni ko?" "A'a fa, Uncle zai baki kariya fiye da tunaninki." "Shi kenan na amince soyayyarsa amma bance zan auresa ba saboda zab'in Allah na ke kan nema." "Masha Allah, yanzu kuwa zan sanar masa dan ya soma zuwa zance Kai tsaye kafin Malam Ali ya mallake zuciyarki." Bance komi ba haka banji fad'uwar gaban da na ke ji ba dyik in anayimin zancen auren Uncle Muhseen. Wayata ce ta yi k'ara na duba sak'o ya shigo. "Ina godiya da wannan aminci." Kallon Beebah na yi ta jinjinamin kai. "Tukuicina kujerar Umrah a wannan Azimin ya tabbatarmin na can-canci hakan saboda na d'orashi akan hanyar gyarawa matarsa zama tare da yi masa jagorar mallakan tauraruwan taurari Nana Khadijatu." Ware ido na yi. Ta tashi ta soma rawa cikin ambatar "Khadija haske ce a ko ina." Abinda ta yi ta ambata kenan Bintu na tayata, saida suka gaji sannan suna zube suna maida numfashi. "Deejah Uncle maraya ne Babansa ya rasu tun yana d'an shekaru biyu. Mamansa ta raine shi na shekaru uku k'anin Babansa ya amshe shi lokacin yana da shekaru biyar kenan, kulawansa ya dawo hannunsa inda ya fuskanci k'alulabe da mafi aka  sarin marayu ke fuskanta ko ince wad'anda suka taso ba tare da maifiyarsu ba.  K'an warsa Hafsat mamansu ne d'aya, tana tare da k'anwar Mamanta a garin Abuja saka makon rasuwa da mahaifiyarsu ta yi sanadin haihuwar k'anin Hafsa wanda shina kwanarsa biyu a duniya ya bi mamnsa. Su biyu  ne rak mamansu ta Bari wato Hajiya Madina. Muna da dangartaka da Uncle dan sadda yazo neman auren aunty Nafisa aka gano mahaifin Mamansa abokin kakarmu ne, dan 'yar Maiduguri ce ita Babansa ne d'an Kaduna. Numfashi na sauke cike da jin tausayin Uncle. "Uncle yana da burin k'anwarsa ta zauna a gidansa amma halin Aunty Nafisa ya hanata zama, duk da bata dukanta bata zaginta amma fad'a da sanya aiki kawai sun isheta ko Fanta dan tana da hak'uri ne wallahi da tuni ta gudu." Juya baya na yi sabida har ga Allah yanzu bana son ana ambatar sunar Aunty Nafisa a gabana. "Muna da yak'innin idan kina tare da ita zata soma koyi da halinki na hak'uri da kirki har gidan Uncle ya zamo yarda yakeso wato jama'a su cika shi ana kaida kawo cikin kulawarsa." "To Allah yaso hakan." Na ambata a hankali. "Amin." "Idan momy ta sami labarin nan zatafi kowa jin dad'i domin tafi kowa sanin kishin Aunty Nafisa wanda idan taga abokiyar zamanta na yin abin alkhairi itama zata aikata fiye da nata musanman intaga Uncle na yabawa aikin 'yar uwan zamanta to zata zabura ta aikata ko dan ya yaba mata, kinga kenan anjefi tsun-tsu biyu da dutse d'aya ." Numfashi na ja a hankali ina k'ara fahimtar dalilin da ya sanya su Beebah ke goyon bayan aurena da Uncle sabida halaiyan 'yar uwansu ya bak'anta ransu. 'Uhm ni dai gani ga Allah, ban san me ya zab'amin ba.' Na ambata cikin raina, a fili kuwa na ce "Ya Allah ina fatan samun zab'inka mafi alkhairi a rayuwata." "Insha Allah Uncle d'inmu zai zab'a miki." Suka ambata a tare, ido kawai na zuba musu. Ina saurarensu sai ambatar halin karamcin Uncle sukeyi  suna k'ara na-natawa. A makare muka tashi saboda muka idar da sallar subahi barci muka koma. Mama ta kammala duk aikin gidan dan haka wanka mukayi muka karya na wuce Tahfiz a gaggauce dan lokacin shiga ajina ya kusa. Sadda na shigo gate ina kallon Aliyu daga nesa tsaye bakin wani aji amma ban nuna na gansa ba na shige ajin da zan soma da shi. "Ba ko gaisuwa matar Ali." Sak'on na karanta na maida wayar silent batare da na bashi amsa ba. Ina tsakiyan k'arin hadda ya shigo da sallama, yaran ne suka amsa masa nikam a zucci na amsa na cigaba da karatuna, tsaye ya yi yana bina da kallo dakatawa na yi na tura masa sak'on dan Allah ya fita, maimakon ya fita kamar yarda na nema sai ya tako zuwa gabana ya tsaya mik'ewa na yi ina kallon yaran na ce "Yau Malam Aliyu yazo tayamu karatu ya kamata kuyi masa wuri." Dariya suka sanya, shima darawan ya yi ya tafi gefen wani yaro ya zauna. "Oya ayi mana karatun." Murmushi na yi na koma na zauna na cigaba da karatu amma duk sai naji na takura saboda yarda idanunsa ke kaina. Aya na sanya ma dubeshi kad'an sannan na ce "Dan Allah Malam ka k'arasa musu ni bari in tafi d'ayan ajin da na ke son yi masu gwaji." Ban jira amsarshi ba na fice. Daga Ajin da na ke ina yiwo karatunsa cikin d'aga murya, murmushi na yi ta dokawa kawai ina yabawa k'aunata dana hango a idanunsa. Koda lokacin tafiyana gida ya yi Aliyu na  ajinsa dan haka baisan na wuce ba. Ina shiga gida saiga kiransa, d'auka na yi ya rufeni da tulin k'orafi akan tafiyata ban jirasa ya kawoni ba. "Aliyu mu kame kanmu mu sani makaranta muke ba filin masoya ba, ka daina biyoni gaban d'alibaina kada su rainamu kasan sun soma girma tsaf zasu fahimci inda muka dosa, ka amince mu kasance tamkar bakomi tsakaninmu amma da zarar mun bar kamaranta mu nunawa juna k'au... Sai kuma na yi shiru ina 'yar dariya. "Uhm k'arasa mana Matar Ali." Shiru na yi. "Na amince da zancenki dear ko dan gudun sa'idanawa masu neman abin fad'a batare da ankasa da su ba." "Nagode da fahimta." "Ni ke da godiya, ki jirani bayan la'asar zanzo da sister na." "Ok sai kunzo." "Love you always Matana." "Me too." Dariyan da ya kyalkyale da shi yasa na datse kiran na kife fuskata a tafukan hannuna. "Uwata kin dawo lafiya?" Da sauri na d'ago Mama ce tsaye k'ofar kitchen, kallon da takeyimin ya tabbatarmin da ta ji wayar da na ke yi. Da gudu na kwasa zuwa d'akina. Dariyar Mama na jiyo har da tafa hannaye. "Ikon Allah, wannan wani irin kunya Allah ya baki Uwata?" Cukuikuye fuskata na yi da bedsheet, ina sauraren zantukan Mama. Duk yarda taso in tashi nak'i sai kawai ta fice tana dariya mai sauti. Nima dariya na sanya ganin yarda Mama ke farin ciki yafi komi sanyani nishad'i. "Da alama Aliyu kai alkhairi ne a rayuwata." Na furta a hankali. "Uhm." Beebah ta yi gyaran murya, harara na cilla mata ta kwashe da dariya cikin girgiza sumar kanta dake d'igan ruwa. "Malama ina Yaya Abdallah?" "Ya koma garinsu tun d'azun." "Ayya bana nan bamu had'uba." "Nima tun isowarsu har ya wuce bamu sake ganin juna ba." "Saboda me ne?" "Babu." "Anya kin kyauta masa kenan? Ko ba dan alak'ar k'auna ba ai kya bashi kula dan zumunta." "Deejah me kike so inyi masa? Ya zo naje mun gaisa na zauna cikin dangi yana hira da kowa bandani to akan me zan cusa kaina ya zo ya tozartani dan na hango take-takensa kenan." "To Allah ya kyauta." "Amin." "Uncle yana ta kiranki, shin me yasa baki daga ba?" "Tana silenta ne." "To ki kirasa kafin ki kwanta dan na sanar masa da zaki kirashi idan kin dawo." "Nikam kunyarsa na ke ji, please ki sanar masa na yi barci." "Jibi kamar yanzu ina gadon Momyna, maga wanda zakiyiwa salo." "Wayyo kewa zai kasheni." "Ina kika san kewa, ai sai muntafi da aminiyarki." "Kuna nufi Fanta daku zata wuce?" "Insha Allah, amma zata dawo." Kwalla naji sun cikomin na yi saurin juya mata baya. "Mu muka matsa ta biyomu saboda ku sami fahimtar juna da Uncle batare da Aunty Nafisa ta sanya zargin cewa Fanta ce ke rura lamarin ba." "Kuna ganin wannan matakin shi ne mafita?" "Eh domin bazan b'oye miki ba hankalin 'yar uwanmu ya tashi duk yarda muke goyon bayan lamarin tabamu tausayi d'azun da ta ke kuka a gabanmu amma mun nuna mata Uncle mijin mace hud'u ne ta yi addu'a akan lamari shi yafi akan tada hankalinta, da alama ta d'auki nasihohinmu musanman na Safina saboda ita malama ce kamarki sannan Allah ya yi mata baiwar iya lwantarwa da mutum hankali." "Uhm nidai dan girman Allah ku barni da Fanta." "Kiyi hak'uri itama tana son kai ziyara taga dangi." "Shi kenan Allah ya dawo da ita lafiya." "Amin." Wanka na shiga na d'auro alwallah na sallaci shafa'i da wutri na yi shirin barci. Kwanciya na yi cike da sake-saken yarda al'amuran rayuwata yasoma sauyawa da salo mai cike a bababen mamaki. 'Wai ni ce wacce ada maza ke k'in kulawa amma yanzu sun soma cajamin kwakwalwa.' "Inkon Allah kenan." Na ambata a fili. "Sai ji da gani ba" Na tsinkayi muryan Beebah ta amsamin. Sai da safe na yi mata, itama ta shiga toilet tajima sannan ta fito bisa alamu wanka ta yi. Tsakiyar dare na farka sakamakon jin motsin ana tab'amin k'ofa, gabana ya fad'i tuno rayuwata na baya wanda na ke gadin kaina a duk tsakiyar dare. Addu'a na soma ja inda ya taimakamin na samu kuzarin mik'ewa na nufi k'ofar. Ina bud'ewa Mama ta fad'omin a jiki tana nunfarfashi tare da nunamin hanyar k'ofar d'akinta da yatsa dan takasa yin magana. *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/25, 11:01 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Safiyya (Mrsjmoon) E.W.F. Page 13. Rungumota na yi ina salati tare da janyota ciki na maida k'ofar na rufe, addu'a na soma tofa mata hankalina a tashe. Saukan fitar numfashinta da sauri da sauri ya tashi Beebah daga barci ta iso gabana tana jeromin tambayoyi ganin ban amsa mata ba sai addu'a na ke aikin tofawa Mama cikin sauri-sauri sai ta zubo ruwa a kofi ta zauna ta rik'e babban yatsar k'afar Mama da kyau ta soma tofa addu'a a ruwan hannunta, tana gama tofawa sai ta guntsa da fesa aikam ta ke Mama ta ja numfashi mai k'arfi, Beebah ta k'ara guntsan ruwan sai dai kafin ta fesa mata akaro da biyu tari ya sark'eta kofin da ruwan addu'ar ke ciki ya kufce a hannunta ya zube a k'asa. Sannu na yi ta jera mata har zuwa sadda tarin ya lafa ta matso muka cigaba da tofawa Mama addu'a. Tsawon rabin awa muna fama da Mama kafin mu samu ta dawo hayyacinta ta soma ambatar Hasbunallahu wal ni'imal wakil, da k'arfi ganin haka muma muka somabinta, zuwa wani lokaci sai ta rufe da salati. Gumi sai b'ulb'ulowa ya keyi daga sassan jikinta, gamin haka sai muka samu madai-daitan towel muka soma goge mata, lumshe idanu ta yi tana mai ambatar albarka a garemu. Bayan munga ta sani natsuwa sai muka kamata zuwa saman katifa, ta dubeni cikin tarin rauni ta ce "Uwata akwai damuwa a gidan nan, hak'ik'a da idanuna naga wani halitta mai kama da maciji na son hayomin gado shi ne ya firgitani wallahi ji na yi kamar zuciyata zata fito sabida tsoron halittar, tabbas da yazo da ajali da yanzu zuciyana ta buga na zamo gawa, kin koma marainiya na hak'ik'a." "Mama kwanta ki huta gobe da safe sai muyi maganar kuma in Allah yaso kinfi k'arfi dik kan abin sharri daga jinsin mutum da aljan, insha Allah burinki sai ya cika a kaina k'asa bai rufe idanunki ba." "Allah yaso hakan Uwata." "Amin." Muka amsa tare da Beebah. Maganin ciwon kai ta nemi in bata ta sha, Beebah ta b'allo Boska d'aya Sudrex d'aya ta bata, tana sha bajimawa barci ya d'auketa cikin fitar murmushi mai cike da natsuwa. Kasa komawa barci na yi sai na d'auro alwallah nasoma jera nafil-fili cikin kaiwa Allah kukana da ya karemu daga dukkan sharrin abin cutarwa na fili da b'oye, Beebah itama maramin baya ta yi, haka muka kwana addu'o'i. Bayan mun idar da sallar Subahi muka shiga d'akin Mama a tsorace bakinmu d'auke da addu'a, bamuga komi ba, Beebah ta ce mu bincika ko ina amma Mama ta hana ta ce mai cire maciji zaizo ya cire shi. Hak'ik'a abin ya tab'a min zuciya ganin yarda Mama ta koma kamar yarinya domin da taji motsi zata zabura ta k'ank'ameni ko Beebah, sukalewa na yi na shiga bayin waje na  kulle kaina na yi ta kuka cikin rashin fitar sauti, bayan na rar-rashi kaina na fito cikin k'ok'arin sanya wal-wala a fusakata gudun sake dagulawa Mama lissafi. Ko abinci ba wanda ya ci dan ko abin karyawa bamu sami damar had'awa ba saboda halin da mukaga Mama ya gama kashe Mana jiki domin da gari ya yi haske ta garas sai ta rik'a sunbatu tamkar wacce brain d'inta ya ke son tab'uwa, da mun had'a ido hawaye ke zubomin amma bana bari ta gani Beebah ce ta fahimta tasoma yimin nasiha a hankali gudun kada Mama taji ta k'ara bircikewa. Haka muka kasance da Mama mun kasa dawo da ita asalin natsuwarta. Da hantsi mai cire maciji yazo ya gama hayak'insa da bincikensa baiga komi ba ya tafi, Beebah ce ta sanarwa da Uncle halin da ake ciki yana zuwa bai jira komi ba ya kira wani Malami da d'alibansa suka zauna danyin saukan alqur'anin a gidan, mu kuma ya ce mu tafi da Mama asibiti ganin yarda ta ke yin abun tamkar rud'ad'd'iyar tsohuwa, shima lamarin ya firgitashi. Kwatanta damuwan dana shiga ba mai misaltuwa ba ce, na yi kuka har na ji zuciyata na son samun matsala ta hanyar jin ina fizgar numfashi da kyar tare da jin tanayimin zugi, kan dole na rarrashi kaina da kaina tunda nak'i jin ban bakin su Beebah. Babban DAMUWATA shi ne na rashin sanin halin da Mamana ke ciki tsawon awanni shida da muka kawaota domin mun kawota da mintoci goma sha biyar Likitoci suka shige da ita wani d'aki sai dai inga sun fito sun shiga ba labarin komi, lamarin ya k'ara d'agamin hankali kenan nakasa sauraren ban bakin kowa hatta kuwa da Uncle domin gani na ke basu san kalan damuwarta da na ke ciki ba ne shi yasa suke cewa na daina kuka dan inda banyi kukan ba tabbas da nima ina kwance a gadon majinyata. Bayan na gabatar da sallar magriba na dawo bak'in k'ofar da ka saka Mama na kife fuskata a jikin bangon na kuma fashewa da kuka mara sauti saboda tuni muryata ta dushe. "Dan girman Allah kiyi hak'uri Aminiyata, ki tuna falalar mai yarda da k'addara ta khairan ko kishiyarta, kina da sani akansa shin me yasa bazaki zamo cikin masu mik'a lamuransu ga Ubangijin da baya barci balle gyan-gyad'i ba? Ki yi hak'uri irin wacce Allah ya umurci bayinsa mumunai da su aikata idan jarabawar rayuwa ta riskesu, ki sani Allah da ya jarabci Mama da lalura nan ya fiki sonta sannan faruwan hakan alamun tana cikin bayinsa salihai ne wanda ke dorawa cuta domin gwada imaninsu tare da shafewar zunubai." Rungume Fanta ya yi tsan-tsan ina kuka mai ciccira. "Insha Allah Mama zata warke jinkirin bayyanar halin da ta ke ciki alkhairi zai zamo biy jahiy Nabiyyi S.A.W." "Allah ya so hakan, nagode sosai Aminiyata." Na ambata batare da tunanin tajiyoni ba saboda yarda muryan ke fita can a mak'oshina. "Ku tafi da ita gida ta huta." Na tsinkayi muryan Uncle daf da ni. Da sauri na juyo na rik'o hannunsa batare da tunanin komi ba saboda natsuwana ya yi balaguro. "A'a Uncle ba zan iya hutawa ba alhalin Mamana na cikin wannan halin, ka barni har zuwa sadda zan san halin da ta ke ciki." "Wani hali ta ke ciki?" Ya cillomin tambayar tamkar bai san komi da ke faruwa ba. Maimakon amsa masa sai na saki hannunsa na koma jikin Beebah na kwantar da kaina a kafad'arta na  fashewa da sabon  kuka. "Beebah ku tafi da ita gida na ce." "Ba zanje ba!." Na furta da k'arfi. "A haka kike son Mama ta yi ido biyu da ke? Kin koma tamkar wacce ta yi amai da zawo, oya ki tafi gida ki huta  wannan shi ne umurnina na k'arshe akanki." Ban sa ke magana ba kuma ban daina kuka ba, hawaye na bin cheek d'ina tamkar an bud'e famfo na motsa masa kai alamun cika umurninsa. Jan hannuna Bintu ta yi na kalleta naga itama kukan ta ke yi. "Kunga idan kuka zaku koma kunayi banga amfanin had'aku da ita ba." "Sorry Uncle mun bari." Fanta ta ambata cikin muryan kuka. "Ku tabbatar da ta ci abincin kafin in iso." "To." Beebah ta amsa a hankali. "Yaya me yasa bazaka barta ta shiga ta ganta ba? Tana fa cikin yanayi mai kyau itama burinta ta sanya d'iyarta a ido." Wata murya mai sanyi naji ya ambaci haka, ai banjira amsawan Uncle ba na juyo da gudu caraf Uncle ya kamani ya matse hannuna gam. Runtse ido na yi saboda da yarda rik'on ya ratsa sassan jikina. "Ki tafi gida idan kin dawo zaki ganta." "Dan soyayyarka da Ma'aikin Allah ka barni inga halin da Mamana ke ciki kafin in tafi." Sakina ya yi wani hannu mai mugun d'umi sama dana Uncle ya kamani haka nasoma binsa tamkar jela a k'ofar wani d'aki ya tsaya ya juyamin baya dama banga fuskansa ba, ban kuma damu da sai nagani ba. "Ki shiga tana ciki amma idan kika d'aga mata hankali da wannan kukan naki tabbas da kaina zan fito da ke." Motsa kai na yi tare da tura k'ofar d'akin na fad'a ciki da sauri dan gani na ke tamkar Uncle zai hanani duk da baibiyo bayanmu ba. Mama ce zaune saman gado, nurse na bata tea a baki. Da sar-sarfa na isa bakin gadon sai kuma na tsaya tsak ina sauke numfashi hawaye na bin kumatuna. "Uwata taho kusa naji d'uminki." Da sauri na k'arisa na zauna tare da mannuwa a jikinta. "Mamana in na rasaki nima binki zanyi." "Ki godewa Allah shi ne abin buk'ata kafin furta komi Uwata." "Alhamdulillah ala kulli halin." "Masha Allah." "Mamana ta ya... "Kiyi hak'uri da duk kan tambayoyinki yanzu tana cikin hutu ne ba'asonta da yawar magana." Motsawa nurse din kai na yi ta murmusa tare da mik'amin kofin tea d'in. "K'arasa bata ina son gabatar da sallah." "To." Na amsa tare da komowa inda ta tashi  na zauna. Da ido muke magana da Mama muna saukewa juna murmushi. Bayan ta gama shan tea d'in ta kwanta ina rik'e da hannunta barci ya d'auketa wanda nagano anyi mata allurar barci ne kafin in shigo. "Taho ku tafi suna jiranki." Idanu na zuba masa yana kama da Uncle sosai tamkar 'yan biyu sai dai wannan yafi Uncle jiki da tsawo domin shi irin mutanen nan masu girman jiki yayin da Uncle ya ke cikin matsakaita. Duk a d'an kallon dana k'are masa na gano ba wani mai shekaru ba ne girman jikin ne kawai. "Idan kin gama kallon munin nawa sai ki sanarmin da abinda ya fi burgeki ko baki tsoro a halittana." Ware idanu na yi baki bud'e. "Dalla wuce ki bani wuri mummuna kawai, wallahi Yaya na cikin wahala da yake sonki domin ba abinda zakiyi masa sai shirme da uban kallo kamar yar daji, wata k'ilama gara sakaryan matarsa na gida da ke." Juyawa na yi jiki a sanyaye na sumbaci goshin Mama bayan na tofa mata addu'a, nazo na wuce ta gefensa kaina sunkuye. "Haramun ne saka turare mai janyo hankali dan haka ki kiyaye saboda cika sharud'an addininki." Ban kula zancensa ba na yi gaba ina maijin haushinsa haka nan naji baimin ba. Naso tambayar su Fanta d'an fiti nan mai kama da Uncle amma gudun kada su juyamin zancen da tsokana sai na tsuke bakina sai dai kalamansa na k'arshe sai amsa kuwwa sukeyumin a kunnuwa domin ban saka turare ba sam amma dan neman magana ya ke yimin wa'azi, siririn tsaki na ja wanda nikad'ai najiyo kayana. Har muka isa gida bandaina zantukan zucci. Cikin  sakin fusaka na yo wanka tare da cin abinci wanda muka siyo a hanya. Sai tsokanata Fanta keyi da nuna irin kukan da na yi Bintu na karemin. "Ki kyaleta Bintu ai itama ta yi kukan." "Aikam kowa ya yi kuka hatta da aunty Nafisa ta shiga damuwa sadda ta sami labari." "Anya Sister Safina hakan ne kuwa?" "Gara dai ki tambayeta kam domin mun san ta shiga damuwa ne saboda mijinta na tare da ke." "Kai Sister Beebah wai me yasa kike yin haka ne?" "Safina k'arya ko da wasa haramun ne, kinsan da haka to me zaisa ki fad'a abinda ba haka ba ne? Ko Deejah ta aminci Aunty Nafisa ta shiga damuwa saboda ciwon Mama na tabbata a fatar baki ne amma a cikin zuciyarta ba aminta ta yi ba domin zan iya cewa tafimu sanin halin yar uwarmu saboda nuna mata halayarta da ta gamayi." "Haka ne sister Beebah nima ban san me ya janyo na kama sunarta Aunty Nafisa ba." "Is ok Sister Safina an kulle babin yanzu kuzo muyi addu'ar dorewar samun lafiya ga Mama." Firdausi ta ambata. Zama mukayi a carpet Beebah ta jero addu'a tana gamawa na soma ina gamawa Safina ta d'auka haka mukayi har zuwa kan Fanta, Firdausi da Bintu sannan muka shafa, bayan munyi tawasaali da addu'o'in akan Allah ya bawa Mama lafiya mai d'orewa. "Gobe zaku wuce gida ko?" Na tambayesu cike da jimami. "Sai munji daga Uncle." Bintu ta amsamin. "Uhm nikam zaku barni da kewa." "Fanta na tare da ke dan Uncle ya soke tafiyarta tare da mu saboda ya ce kewar zaiyi miki yawa." "Allah sarki Uncle, mutumin kirki." "Kina son shi ko?" Kallon Fanta na yi kawai batare da na ce komi ba." "Fanta shiru alamun amincewa ne." Bintu ta amta cikin kannemin ido. Murmushi na yi kawai domin har yanzu damuwar laluran Mama bai sakeni ba. "Muna sonki tsakani da Allah Deejah shi yasa bamu taya yar uwarmu kishi ba saboda mun san kyawun halinki bazaki tab'a cutar mana da jini ba, muna bayan aurenki da Uncle d'ari-bisa d'ari." Safina ta furta hakan cikin sanyin murya mai cike da natsuwa abin da ya janyo shigar zantukan cikin kowani kofa na jikina kenan. "Kuma muna fatan itama bazata cutar da ke ba saboda abin da ta tsana a rayuwarta shi ne bin bokaye da mugayen malamai sannan masifarta zamu tayaki da addu'a Allah ya sanya sanyi a lamarin ku zamo abin alfaharin mijinku, inuwa mai kore masa dukkan damuwa." Kallon Beebah na yi sadda ta rufe baki, kwalla ne suka cikomin saboda kalamansu ita da Safina sun jefani cikin wani hali wanda na ke hango bijirewa auren Uncle tamkar watsa musu k'asa a idanu ne tare da yi masa butulci. 'Mama da ku kun sakani a tsakiya amma bakomi na amince hakan kaddarata ce, Allah ya baki ikon faranta muku tamkat yarda ku ke kan farantamin.' "K'awata insha Allah zakiyi alfahari da wannan auren, ina ji ajikina jinkirinki alkhairi ne tunda gashi tashi d'aya Allah ya baki miji d'aya tamkar da dubu, irin Uncle. " "Allah ya amince hakan Fanta" Na ambata a hankali. "Amin." Suka amsa a tare cike da wal-wala. "Hak'ik'a bazan manta da samuwarku cikin rayuwata ba, kun ciremin kokwanton dana ke ciki na ganin ko bak'in jini na ke da shi da k'awaye basa hurda da ni." Dariya suka kyal-kyale da shi jin kalamaina cikin k'ok'arin fitar da murya. Sallaman Uncle yasa suka natsu ya daga labulen ya ce "Ki taho muje ku kuma ku kwana a gidan sabida kada abarshi ba kowa." Suka amsa da to cike da ladabi, na yi musu sallama muka fice. "Baba ya sani kuwa?" Na cillowa Uncle tambayar sadda muka hau titi. "Eh, yanzu haka a can na baroshi tare da matansa." "Uncle ance tana buk'atar hutu kada su dameta da hayaniya." "Sa'ad zai kula da lamarin." "Likita ne shi?" "A'a." Shiru na yi ina hasko surar mai kama da shi wanda nabawa suna da d'an fitina. Runtse ido na yi da sauri hasko matar da zai aura wacce zatayi aiki da masifarsa tamkar yarda Mama ke kan hak'uri da sababin Baba. "Aikam ta gamu da aiki babba." "Wa ne?" Kama baki na yi jin a she zancen zuccin ya fito fili ban sani ba. Gyaran murya ya yi ganin banda niyyar amsa masa. "Mama jinnu suka bata tsoro amma masu karatu sun saita lamarin dan malamin ya sanarmin wai turensu akayi mata sai akayi dacen ta rik'e azkar domin anso ta haukace ne Allah ya bata kariya sai abin ya tsaya a rud'ewa na d'an lokaci." "Allah ya k'ara karemu." "Amin." Zuwa can na kuma jin muryan Uncle. "Su kuma Likitoci sunce ta kamu da hawan jiki shima sunyi nasarar saita komi sai ki dage da yi mata addu'ar samun kariya har da ke kanki, gobe Malamin zaizo dubata a Asibiti zaiyi magana da ke dan na ce ya taimaka ya baki addu'o'i tare da wasu nafil-fili saboda na fahimci Baba na da sakaci akan bawa iyalansa kariya daga miyagun lamura duk kuwa da matsayinsa na nasanin ilmin addini." "Uncle nagode sosai Allah ya biyaka da khairan." "Amin." "Banso sanar miki ba amma ya kamata ki ji ne sannan banso Mama ta ji, lamarin ya tsaya tsanina da ke da kuma Baba da ya furta kalamin." "Me Baba ya ambata maka Uncle?" "Idan Mama ta dawo gida zan sanar miki." Shiru na yi amma a zahiri naso jin abinda Baba ya ambata masa. "Kina son saurayinki Aliyu ko?" Da sauri na kalle shi ya gyad'an kai sai na girgiza masa nawa murmushi ya yi mai sauti na juya fuskata gefe ina jin fad'uwar gaba saboda zuciyata Aliyu ta ke so domin shi ne first love d'ina, shi ne mutumin da bazan tab'a mantawa da shi ba wanda ya kawo iyakar DAMUWATA na rashin masoyi. 'Ba zan iya furtawa Uncle ina son Aliyu ba.' "Ina kuma rok'on a bani gurbi ko da d'an mitsi-tsine wanda idan na kira waya a amsa min ko da ba'a bani damar soma zuwa zance ba." Nok'e kai na yi ya ja jelar kitsona da ya fito waje sai na tura kai tsakanin cinyoyina. Sai da na ji ya kashe motar sannan na d'ago na tsirawa harabar Asibitin ido. "Sarkin kunya muje ko?" Wani kunuyar ne ya sa ke kamani, ficewa ya yi yana 'yar dariya, nima dariyar na sanya amma a tak"aice  wanda ban bari Uncle ya jiyo ba, saida ya k'wan-k'wasamin galass sannan na fito ina nok'e kai. "Nana Khadijatu sarkin kunya, Allah ya yi miki ludifin da ya tanadar masu kunya wato ya k'ara wadata k'irjinki da Imani mara iyaka." "Amin ya rabbi " *Masoya kunsan tafiyata a hankali ne, duk wanda ya ke bin books d'ina zai tabbatar da hakan, bana rushing haka bana yanke labari ko aya yake so dan Allah ku cigaba da bina a yarda na tsara labarin domin bazan yanke ba haka ba zan tafi da gudu ba dan tafiyar mai dogon zango ne gami da fad'i, nasan kun fahimci hakan tun a shafin farko na labarin, masu k'osawa da jin asalin Deejah kada su damu lokaci dai fad'in Mama Hurera. A dukkan komi a kwai sanadi to sanadin asan Deejah bai zo ba, aci gaba da gashi fans. Allah ya k'ara mana kwarin idanu, amin.* *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/26, 10:33 PM] 💘: DAMUWATA BY MRSJMOON E.W.F. Page 14. A tare muka jera zuwa cikin asibitin duk kuwa da yarda naso ya yi gaba na biyo bayarsa ya k'i. D'akin ba kowa sai wata nurse domin na yi zaton zan sami su Baba a ciki. Nurse d'in na ganin mun shigo ta mik'e ta fice, na matsa ina lek'en fuskan Mama wacce  har lokacin barci ta ke yi, a kwana da yini har ta rame sosai sai dogon hancinta tare da fuakanta suka k'ara tsayi, haske kam wannan ba'a magana domin sai ta koma tamkar balarabiya wanda da ganinsa kasan bana lafiya ba ne. Sumba na sauke mata a goshi ina maida kwallan da ke neman zubomin. "Ya rabbi ba dan halina ba ka bawa baiwarka lafiya alfarman Annabin karfo da k'arshe." "Amin ya rabbi, insha Allah zata sami sauk'i burina ki cire damuwa domin ita kanta bazata so ta farka ta ganki cikin yanayi mara kyau ba." "To Uncle zanyi k'ok'arin cirewa." "Hakan ya kamata." Shiru ya ratsa na minti biyu zuwa uku. "Da alama wannan d'an ka iyan bai bar kowa ya shigo ba sai Malam." Uncle ya ambata yana waige-waige kamar mai neman wani abu. "Har shi ban bari ba." Muryan d'an fitinan ya ratso, na juyo da sauri na tsira masa ido ya sanja sutura zuwa manyan kaya akan d'azun da ya ke sanye da k'anana. "Kai wallahi Brother over acting d'in ka ne wata rana ke sanya mu b'ata da kai, yanzu har mijin nata ka hana shigowa ya ganta? To me kenan kayi fisabilillahi?" "Eh fa har shi d'in banbari ba saboda kiyaye dokan Likita kuma a gabansu ya zo ya kuma tabbatar musu da kada wanda ya shiga ko waye nata." "Wannan plan d'inka ne Brother domin nafi kowa sanin waye kai, inaga makaranta zaka koma ka zamo Likita akan Engineer tunda ka shiga rigarsu ta zartar da hukuncin da ko su basa yinsa wato hana murarrami ganin halalinsa." Dariya ya fashe da shi yana rawa da kai na kuma zuba masa ido ina kallon dimful nasa da suka lotsa duka biyun. "Yaya wallahi na yarda kafi kowa sanin halina shi yasa Abba ke had'ani da kai dan gano gaskiyan abinda na b'oye a ruhina." "Ba dai ka kyauta ba Brother, a ce har mijinta ka hana shigowa ganin iyalinsa, haba dan Allah me yasa wata rana lamuranka baka sanya tunani cikinsa?" "Kaima zaka fita idan ka cigaba da mita." "Au har da ni?" "Eh har dama Matarka mai kallon tsiya kamar goyon k'auyawa." Uncle ya kalleni na juya baya ina mai maijin kunya. "Kaga Brother zanci gidanku in ka ce zaka sanyawa iyalina ido." "To ka sanar mata ban son kallo in ba haka ba zan tsire mata idanu sai ka zamo d'an jagora." "Amsa naka na ce Sa'ad." Jin Uncle ya ambaci sunarsa yasa na juyo da sauri na kuma tsira masa ido kamar mai son gano tawayarsa. 'Dama shi ne Sa'ad d'in?' "Khadijatu meet my blood brother Sa'ad." Maganar Uncle ya katsemin zancen zucci, kauda kai gefe na yi tamkar banji me ya ce ba saida ya sa ke mai-maitawa. "Ok, ina yini?" Na furta ina kuma kallon cikin idanunsa. "Fine mai kallo k'urillah." Murmushi na yi dan nafahimci yana da son raha kuma shima ya tsani kallo kamar yarda na tsana amma sai gashi yau ina yi har ana sanarmin da ba'aso lamarin da ya zamo karan farko cikin rayuwata. "Kaga Brother zan sanya Abba ya yi maka aure da yar daji mai tallan Nono in har baka daina takurawa iyalina ba." "Wallahi na bari Yaya domin ban shirya kashe 'yar mutane ba, good night, iyalin big brother Allah tashemu lafiya.." Ya fice da sauri, kallon Uncle na yi ya girgiza kai tare da janyo kujera ya nunamin da yatsa na zauna ya dawo bayana ya dafa kujerar na kalleshi ya jinjinamin kai tare da cewa. "Kinga na kori mai takura miki cikin ruwan sanyi." Shiru na yi tare da kallon hawa da saukan numfashin Mama. "Alamun ta samu lafiya kenan insha Allah wani abin cutarwa ya bar k'ara shigowa gidanku balle ya nemi tab'a ku." "Allah ya amince hakan Uncle." "Amin iyalina." Murmushi mai sauti na yi saboda tun d'azun sunar ke bani dariya. "Insha Allah ke iyalina ne Khadijatu." "Uncle ka tafi gida kaga dare ya soma yi." Na sauya akalar maganar saboda yarda ke bani kunya. "Tare zamu kwana." Idanu waje na ke kallonsa. "Ko tun yanzu kina son nunamin Maman ke kad'ai ke da ita?" "A'a fa kawai hakan bai kamata ba ne dubi da kana da iyali kuma na tabbata suna can suna dakon dawowar ka musanman ganin baka saba kaiwa dare a waje ba." "Sun san inda na ke to ba damuwa." "Uncle dan Allah ka tafi kada fa ka zamo mara adalci tun ba'ayi nisan zango ba." "Oh da haka Kuma fa, nagode da tunatarwa, na tafi ki kula da kanki tare da Mama dan Allah." Kai na motsa ina kallon fuskansa ya yi da ya ke tafiya da baya da baya saida ya kai bakin k'ofa ya d'agamin hannu  cikin cewa "Good night Iyalina." Da kallo na raka bayarsa ina hasko wal-walar da ke kwance saman fuskansa abinda ya sanyani murmusawa tare da jin sanyi na shiga cikin ma'adanar halittar zuciyana. "Uhm Uncle manya, sam baya duba girmansa sai ya yi tayimin abinda matasan samari ke yiwa 'yan mata." 'Shi ne So wanda ake kira mai maida tsoho yaro.' "Aikam in haka ne to So babban kalubale ne a cikin rayuwar bil'adam, tunda yana maida mai natsuwa zuwa kishiyarta." 'Ke dai Deejah ki taka a sannu ka da reshe ya juye da mujiya.' Idanu na zaro ina jinjina amsan da zuciyata ta bani. Gyara zama na yi cikin k'ok'arin kauda tunanin tun ban soma zamowa mahaukaciya ba. Sai dai abin mamaki fuskan Uncle da na d'an fitina su ne ke tamin gizo a idanu duka na kaiwa goshina ta ke na saki yar k'ara ina liliya wurin saboda zafin da na ji. Cool music na jiyo nesa da ni mai taken soyayya, inda wayar ke haske na tsirawa ido saboda tun daren jiya rabona da ita. "Uncle yazomin da ita kenan ko wa?" Ringing wayar ta kuma na tafi da sauri na d'auka duk kuwa da bak'uwar number ce. Sallama na yi maimakon a amsa sai saukar ajiyar zuciya akayi tare da datse kiran baki d'aya. "Wa ye?" Ganin zan sanyawa kaina ciwo akan son gano ko waye sai na watsar da lamarin na koma gaban Mama na zauna na tsirawa hawa da saukan numfashinta idanu tamkar mai irgawa. Addu'a na yi ta karantowa Ina tofa mata zuwa wani lokaci barci ya soma kamani na tashi na kulle k'ofar tare da tofe ko wani sak'o na d'akin da  Ayatul kursiyu na haye gado na kwantar da fuskata a kirjin Mama ba jimawa barci ya d'auke ni. *** Uncle Muhseen ko da ya isa gida bai shiga gidansa ba a k'ofar gidan su Deejah ya tsaya ya kira wayar Beebah bata daga ba ya nemi na Bintu a kashe , sai da ya kira duka wayoyinsu duk ba wanda ya yi dacen an d'aga, fitowa ya yi ya tura k'ofar gidan ta bud'e ya yi jim saboda tunaninsa a kulle zai sami k'ofar. Hasko shi akayi da filita mai mugun haske ya kare fuskansa hucin duka ya jiyo ya sunkuya da sauri hakan ya yabawa mutumin damar ficewa gidan a guje bayansa Uncle ya biyo amma ya nemesa k'asa ko sama ya rasa, kirjinsa na dukan uku-uku ya nufi cikin gidan, d'akin Deejah ya shiga ya samesu suna ta barci ajiyar zuciya ya sauke ganin babu alamun an tab'a su, ya fito waje yana haskawa da fitilar wayarsa buhunan waken suya ya ciki karo da buhunan waken suya an fito da su an jera. "Ikon Allah wato barawo ne ya shigo sata, to wa ya bud'e masa gidan? Domin na tabbatar su Bintu sun kulle gidan tunda suka kwanta barci." Komawa d'akin ya yi dai-dai lokacin Fanta ta tashi zatayi fitsari ganinsa saida ta tsorata dan batayi zaton ganin mutum ba, kiranta ya yi da hannu suka fito waje saida suka kai zaure ya ce "Kulle gidan ki tofa addu'a na shigo duba ku ne." "To Uncle amma ta ya ka shigo alhalin mun kulle k'ofa?" "Nima abude na gansa shi yasa na shigo duba ku." "A bud'e kuma?" "Kinga kulle ki tafi ki kwanta securities zasu zo gadinku insha Allah bakomi sai khairan." "To Uncle saida safe." "Ok mu kwana lafiya." Yana tsaye ta kulle gidan shi kuma ya kira waya kimanin mintoci goma shabiyar 'yan sanda uku suka zo a mashin sun jima suna magana kafin ya barsu ya shiga motarsa zuwa gidansa. Sallama ya yi a falon duk da yaga da duhu alamun babu kowa amma bai sanya ya shigo kai tsaye ba. Makunnin wutar ya latsa haske ya gauraye falon zama ya yi cike da gajiya ga yunwar da ta addabesa, mik'ewa ya yi dan samawa kansa abinda zai kori yunwar. Ja baya ya yi cikin razana da ganinta domin sam bai jiyo takunta ba sai gaminta ya yi tsaye gabansa. "Dole ka razana mana saboda ka san baka da gaskiya, wallahi Abban Hafiz wutar Allah sai ta cika in har ka ce wannan mugun halin zaka tsiro da shi na yanke zumunci tare da munafunci. Wai ina matarka baka damu da ni ba kamar yarda ka damu da d'iyar makwafta, na rantse da Allah ba zan tab'a yafewa aljanan yarinyar nan Deejah ba domin ta rabani da dangina tare da mijina to wallahi Allah sai ta biya dan bata ci banza ba, zan nuna mata ainihin kalata wanda ta ke da duhun kai akansa Dan sai na wulak'antata da duk kan gatanta, sai ta yi kukan jini bana hawaye ba, billahil azim kukan da ta sakani sai ta yi ninkin baninkin nasa indai ina numfashi, sanann kaima ban ya... "Ke! Banson sokanci da rashin natsuwa maza b'acemin da gani tun kafin ranki yafi dare duhu." Ganin magan-ganun Nafisa bana k'are ba ne shi yasa ya dakatar da ita cikin fushi amma hakan baisa ta tsagaita da tijarar ba saima haukacewa da ta yi cikin daga murya tana kuka tana fallasa mygayen alwashinta akan Deejah muryanta sai sark'ewa keyi tamkar zatayi amai. Shiru ya yi yana kallonta domin yasan ya tab'ota, bai kyauta mata ba saboda tunda ya fita sadda Beebah ta sanar masa da halin da Mama ke ciki bai kuma waowayen gida ba ko kayan da ya sanja Sa'ad ya turo ya d'aukan masa kuma ya tabbata sunyi halin nasu da ita saboda basa zama inuwa d'aya dalilin kenan da baya zuwa gidan saida babban dalili. "Kiyi hak'uri Mom Hafiz, yanzu hutu na ke buk'ata, tafi ki samomin abinda zanci wallahi yunwa ke damuna." Ya yi furucin cikin laushin murya saboda maganganunta na daf da sanya masa ciwon kai, dole dibarar lallab'ata ya zo masa. "Ai da ka dauko dadiron naka ta huce maka gajiyan kuma ba mai sakani shiga cikin da wannan daren salon in d'auko aljannu ka barni da wahala, ai saidai ita d'iyar Bokann tazo ta dafa maka abin da zaka ci amma ba dai Nafisatu ba jinin bare-bari." Runtse ido ya yi yana jan addu'ar samun nutsuwar zuciya saboda kada ta tunzirashi ya aikata abinda zai damesa, musanman kalman dadiro da ta ambata "Abban Hafiz yau fa sai ka zab'a ni ko d'iyar makwafta domin nagaji da hak'uri akan cin kashin da kakeyimin akanta, wallahi yau sai ka sanarmin da hakikanin alak'ar dake tsakaninku." "Fine, kina son sani ko?" Ya furta cikin wata murya mai kaushi daga ji ranta ya kai k'ololuwar b'aci. "Eh." "Iyali ta ce." "Me!?" "Ban hanya in wuce ko in aikata abinda ba zaiyi mana dad'i ba duk kanmu." Fad'awa kujera ta yi jikinta na rawa saboda yarda ta hango komi na iya faruwa idan har bata kauce ba. "Na shiga uku ni Nafisa d'iyar Boka ta gama min da miji, shi da ke rarrashinna idan na tubure masa irin haka yau shi ne ya komamin horror,  Allah ya isa tsakanina da ke Deejah wallahi sai na koya miki hankali, saina b'ata miki fuskan nan mai kama da ta aljannu inga ta inda zaki kuma d'aukan hankalin mijina." "Aikata hakan dai-dai ya ke da yanke alak'ar aurenmu da ke na har abada sannan ko da habaici kika tozarta min Khadijay ban yafe miki ba." Yana ambatar haka ya haye sama ranta tamkar wuta, yunwarma da yakeji nemarta ya yi ya rasa, sai bugawa zuciyarsa keyi da k'arfi. "Hak'ik'a Aurenki shi ne kaddarata Nafisa, ya Allah ka bani ikon cinye jarabawan nan ka kuma yimin dacen samun mace ta gari mai kwantarmin da hankali ko da ba wacce raina ke burin mallaka ba ce." Hawaye ne masu dumi suka zubo masa burinsa ya jiyo muryan Deejah wannan dalilin ya sa ya kirata da number da bata san shi da shi ba tana d'auka ya datse kiran. Abin mamaki yana jin sallamarta cikin taushi ya sami kansa cikin nutsuwar ruhi, hamdala ya yi tare da cigaba da ambatar sunar Allah AL-GAFURU. A haka yana zaune saman kujera barci ya soma kamasa sai kawai ya gyara kwanciya. *** Kiran sallar asalatu ya farkar da ni na sauka a hankali na ji Mama ta rik'eni da sauri na kalleta ta sakarmin murmushi a hanzarce na koma jikinta na rungumeta k'am-k'am ina dariyar murna. "Uwata Allah ya yi miki albarka mara iyaka, Allah ya inganta rayuwarki, Allah ya rabaki da ganin tijarar rayuwa Gabas da Yamma, Kudu da Arewa." "Amin ya rabbi Mamana." "Tafi kiyi nafila idan kin sallaci subahi sai ki taimakamin inyi wanka." "To Mamana." Ina idar da sallah aka kwan-kwasa k'ofa, na bud'e cikin jin faduwar gaba, Baba ne tsaye fuskan nan kamar an aiko masa da sak'on mutuwa. Russunawa na yi na gaisar da shi ya amsa a dak'ile na maida k'ofar na kulle na koma saman sallaya na cigaba da jan carbi amma hankalina na kan su Baba wanda na fahimci Mama bata so ganinsa domin yana ta kiran sunarta tak'i amsawa, ta yi kamar mai nisan barci alhalin ganin shi yasa ta koma kwance. "Ke! Uwani tun jiya bata farka ba ne?" "Ta farka." "Da yaushe?" "Tsakiyar dare." "Alluran hutun suka sa ke yi Mata ko me?" "Magani dai suka bata inaga shi ne ya kuma sakata nauyin barci." "Me suka ce na damunta?" "Hawan jini." "Kin gani ba, ai dama na sanar mata indai tana tare da ke sai ta gamu da ciwon zuciya bama hawan jini ba." "A'uzubillahi! Baba ni d'in?" "A'uzubillahi akanki shegiya mai bakin jini gayyar ta zu... Tarin da Mama ta sark'e da shi yasa Baba dakatawa da yimin tijara. A guje na hau gadon na kamota ina kiran sunarta bata amsa ba amma ta daina tarin. Kallon Baba na yi ya zabgomin harara kwantar da ita na yi na sauka na fice zuwa kiran Likita. Tare muka dawo da Likita tare da nurses biyu, cewa sukayi mu basu wuri, muka fito ni da Baba sai zagina ya keyi zuwa can ya koma kam Uncle na antayo masa zagi tamkar ba malamin ilimi ba. "Alla wannan munafukin Alhaji Muhseen ya ke ko wa, k'ara zan shigar da shi akan shigamin safgar iyali kai tsaye batare da neman izinina ba, duk kudinsa idan na saka masa ido wallahi sai ya koma mai gyaran talkalmi ya fisa arziki, muzuba mu gani shege ka fasa ba dai aurenki ya ke son yi ba, Uhm." Nidai kai na juya gefe ina saurarensa hakalina na ga halin da Mamana ke ciki. Ban aune ba na ji an zabgamin carbi a kai na kwalla ihu wasu nurses suka taho wurin a guje ganinsu Baba ya bar wurin tamkar bashi ya aita dukan ba. "Kiyi hak'uri Mamanki zata sami lafiya kinji." Motsa kai ba yi domin d'aukansu halin da Mama ke ciki ne ya sanyani ihu, su suka kamani na zauna saman bencin da Baba ya tashi sai bani baki sukeyi, muna a haka Likita ya fito tare da nurses ya dubeni ya ce "Ina Babanki?" "Ya tafi ya dawo." "Ok shiga tana son ganinki amma ki kula kada ki yarda maganar bacin rai shiga tsakaninku saboda zuciyarta na daf da samun matsala." 'Shi kenan bakin Baba zai tabbata.' "Tana son hira mai sanya nishad'i dan haka ki lula sosai." Maganar Likita ya dawo dani tunanina. "To." Na amsa cikin rawar murya. Ina shiga Mama ta d'agomin hannu na isa da sauri na kama. "Malam ya tafi ko?" "Eh." "Kin sanarwa da Baba Umaru kuwa?" "A'a." "Maza kiramin shi." "To." Na tafi in d'auko wayar inda na barta jiya babu ita ba sanmatarta, shiru na yi ina nazarin inda na jefata. "Uwata." Mama ta kirani cikin wata murya mai kama da ta yara masu tsamin baki. Da hanzari ya juyo wurin batare da na amsa ba sai dai abinda na yi arba da shi ya kusa sanya zuciyata bugawa. Mama ce ke d'agomin hannu cikin son furta kalma tamkar ba yanzu ta kirani da muryan yara ba. Kallon yarda bakinta ya koma gefe na ke yi jikina na rawa, ga wani irin jijjiga da ta soma ruwan kumfa na fitowa daga bakin tamkar wacce taci guba. "K'alu innalillahi wa Inna ilaihin!." Kalmar da na ambata kenan da k'arfi ina mai nufar Mama da wani irin k'arfi na cukumeta ina zabga ihun kiran Likita da muryana wacce ta soma dawowa hayyacinta daga dushewa, nurses suka shigo a guje wanda na ke zaton dama suna hanyar zuwa d'akin ne saboda muna da tazara da inda suke. Cikin dibara sukayi nasarar rabani da jikin Mama. Na juya musu baya ina wani irin kuka wanda na ke jin zafin fitarsa har cikin tsokar naman zuciyata. "Mama kada ki tafi ki barni wallahi ba zan iya rayuwa babu ke ba, in kika tafi zan biki ne a birnemu tare, wayyo Allah rayuwata!. Hasbunallahu wal ni'imal wa kil!, La'ilaha illa anta subbahanaka inni kuntu minal zalimin!." Na zame k'asa na zauna dirsha ina cigaba da mai-maita addu'o'in cikin k'araji. Saukan hannu naji a saman kafad'ana yasa na tsaya tsak tare da kallon wanda ya dafanin, zubawa Likitan ido na yi wanda ban san sadda ya shigo ba. "Kiyi hak'uri duk mai rai... Ban gama jinsa ba wani sautin dim ya sauka cikin kunnuwana abinda ya haifar da toshewarsu kuma alokaci  d'aya idanuwana suka daina ganin komi, duhu ya mamayesu, ji na yi tamkar ina yawo a sararin samaniya, zuwa can naji kamar ana janyoni zuwa k'asa al'amarin da ya sanyani jin ina fizgar numfashi da k'yar kenan daga haka ban kuma sanin me ke faruwa ba. *Zaku iya soma booking kafin zuwan k'arshen free pages, send #300 only a 0468069082 Haruna Safiyya GTbank, aturo shaidan biya ta 08132166848.* *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/27, 8:16 PM] 💘: DAMUWATA BY MRSJMOON E.W.F. PAGE 15 K'arfe biyar da mintoci goma Sha biyar Alhaji Muhseen ya fito zuwa masallaci kamar yarda ya saba saboda shi mutum ne mai rik'o da addini in kaga jam'in sallar subahi ya kubce masa to baida lafiya ne ko ya fita k'asar. Fitowarsa ya tuna da police da ya d'auko gadin su Bintu. Wurinsu ya nufa suka gaisa tare da tabbatar masa da babu wanda ya dawo dan yunk'urin shiga gidan, godiya ya yi musu suka jera zuwa masallaci saboda musulmai ne, bayan an idar da sallah suka fito har cikin gidan ya yi musu jagora suka ga abin da akazo sata suka kuma duba ko ina ko zasu sami shaidan da zaisa agano barawon amma basuga komi ba, sallamarsu ya yi ya dawo cikin gidan ya sami su Fanta tsai-tsaye cike da tsoro jin barawo ya shigo suna barci. "Ku shirya ku kulle ko'ina ku dawo gida 'yan sanda zasu cigaba da saka ido a gidan daga nan har zuwa sadda masu gidan zasu dawo." "To Uncle." Suka amsa atare. Ya fice cikin tako mai cike da natsuwa. Yana shiga gidansa mota ya d'auko ya nufo Asibiti cike da burin son sanya Deejah a idanunsa, yana sanyo hancin motarsa a cikin Asibitin Baba na fitowa, horn ya yi masa dan ya tsaya su gaisa amma yana kallonsa ya kauda kai gefe ya yi gaba tamkar zai kifa saboda sauri. Raka bayan Baba da kallo ya yi cike da mamakin baudadden halinsa na rashin fahimta. "Ikon Allah sai kallo da alama taimako na son zama matsala, ko jiya badan na kai zuciya nesa tare da tuna cewa ni ke neman had'a ziri'a da shi ba tabbas da mun raba abin kallo a bainar jama'a." Ya ambata cikin dafe gefen kansa da ke yi masa ciwo tun daren jiya. Ya jima zaune cikin motar kafin ya fito jikinsa a sake ya nufo ciki. Nurses din da ya gani sun shige d'akin da Mama ke kwance a guje yasa shima d'iba da gudu ya rufa musu baya. Saidai kafin ya isa sun kulle k'ofar wayar Deejah ya kira tana ringing ba'a daga ba ya sake kira akaro na biyu ya ji akashe. "Me ke faruwa?" Fitowar Likita daga d'akin ya yi hanzarin shan gabansa. "Dr. Jalal me ke faruwa?" "Biyoni office Yaya, dama kai zan kira yanzu." Saida Dr. Jalal ya b'acewa ganinsa sannan ya bi bayansa. "Yaya Muhseen yarinyar nan tana cikin wani hali domin ta shiga coma farfad'owarta zai d'auki d'an lokaci saboda firgitan da ta yi da ganin halin da Mamanta ke ciki." "Jikin Maman ya kuma tashi ne?" "Eh dan har munyi zaton rai ya yi halinsa wanda ya kai Dr. Salim ambatawa Khadija rasuwarta dalilin fad'awarta doguwar suma kenan." "Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un." "Relax Yaya insha Allah ba zata wuce sati d'aya ba zata farfad'o." Dr. Jalal DAMUWATA Mahaifiyarta ce kadaiga halin da ta ke ciki shin ya zata koma idan ta sami labarin?" "Zanyi mata bayanin yarda zata fahimta, insha Allah abin da kake gudu bazai tab'a faruwa ba." "Allah ya so hakan." "Amin." "Ina ita Khadijatun?" "Tana nan a cikin d'akin." "A sanja mata daki please." "Hakan dama zamuyi, mun barta ne zuwa anjima." "Dr. A sanja mata yanzu dan Allah." "Shi kenan bari in sanarwa Nurses su kaika private room." "Yawwa, nagode Doctor." "Bakomi Yaya, fatarmu dai su sami lafiya." "Allah ya basu lafiya." "Amin." *** Uncle Muhseen ne zaune gaban gadon ya tsira mata ido hankalinsa ya yi nisa  cikin tunani, sam baiji motsin bud'e k'ofa ba sai maganarsa ya ji. "Yaya tunani ba shi ne mafitar lamura ba, kayi musu addu'a shi ne sukafi buk'ata." Ajiyar zuciya ya sauke tare da mik'ewa ya rik'o hannun Sa'ad. "Nagode da tunatarwa Brother." "Bakomi magajin Abba." Murmushin ya ke ya yi tare da komawa ya zauna a inda ya tashi ya dora hannunsa kan na Deejah ya kalli inda Sa'ad ya ke tsaye. "Brother ka zamo shaidana akan k'aunar da na keyiwa Nana Khadijatu, wallahi ina sonta, so mai tsafta wanda na ke hasko kwanciyar hankali a cikinsa domin ina fatar zamanta a karkashina ya sanya gidana ya gyaru wanda dangi zasu cikamin shi ta hanyar sada zumuntar da suka yanke saboda mugun halin Nafisat." "Allah ya cika maka wannan burin." "Amin." "Yaya Abokina Dr. Jalal ya sanarmin dalilin tashin ciwon Mamanta guba aka shafa mata a lips domin sunyi buncike sun gano hakan amma bai shiga bakinta ba ya k'i sanar makane saboda yarda yaga kana cikin damuwa." "Innalillahi wa Inna ilaihin, waye ya shiga d'akin bayan Khadijatu?" "Bansa ni ba kam." "Zauna da ita ina zuwa." Yana ambatar haka ya fice Sa'ad ya rakashi da ido daga bisani ya zauna ya kafe Deejah da ido cike da tausayi, siririn tsaki ya ja tare da mik'ewa ya fito ya kira Nurse ta kula da ita. "Abokina ya kamata ku gano wanda ke son kashe matar can." "Engineer lamarin a rikice ya ke kaga dai d'aga yarinyar sai Babanta suka kasance a cikin d'akin kaga ba wanda zamu zarga cikinsu." "Haka ne." "Sannan matar kamar lamarinta da junnu dan ko su zasu iya had'a wannan kaidin dan su had'a rigima domin a d'orawa wani laifin su koma gefe suna dariya." "Eh da wannan kuma dan a yarda aka kawota alamominsu ya nuna duk da hawan jini shima na sanya fad'awa yanayin." "Haka Engineer kuma mai shirin zama Likita." "Be serious Malam." "To Yallab'ai yanzu abinda zamuyi shi ne hana kowa ganinsu sai wanda aka yarda da shi kuma tare da amintattun Nurses wanda zasuyi masu rakiya har zuwa sadda zasu fito." "Good job Abokina, Allah ya k'ara fasaha." "Amin." "Bari in koma gida domin daga Masjid na taho nan." "Allah sarki, hak'ik'a Engineer kai da d'an uwanka kuna da hali mai kyau, Abba ya yi dacen samun 'ya'ya masu albarka." "Uhm abin da Momy ta kasa ganowa kenan." "Kai ne ka kasa fahimtarta Abokina." "Jalal me kake son inyi wanda zata fahimceni?" "Nuna mata ka daina aikata sab'on Allah tare da bin umurninta kuma ka amince da zab'in ta." "Ban aikata komi Abokina, nasha sanar da kai amma ka kasa aminta." "Wallahi na aminta abin da Momy ke zargi ba gaskiya ba ne domin Abokina tsoron mata ya keyi." "Uhm nagode da fahimta kuma abin da na aikata ai kuskure ne sannan natuba ina da tabbacin Allah ya yafemin." "Insha Allah Abokina." Furzar da iska ya yi idanunsa jajur. "Sorry Yallab'ai, abu d'aya na ke so kayi yanzu shi ne ka amince da zab'inta tunda kai ka lalata hanyar to ya zama dole ka gyara ko dan rufuwar asiri." "Bazan amince ba." "Abokina zab'in Momy ne fa." "Ko zab'in Abba ne banga mai sanyani na amince ba dan haka kada ka sake yimin zancen banzan nan sannan ka sani Momy bata da wani zab'i sai takura dan haka ka kiyayeni da kalamin nan tun ranka baifi nawa b'aci ba." "Affuwan Yallab'ai sarkin hawa tamkar garin kwaki." "Ai saikayi, kuma kada ka sa ran sake ganina nan kusa a Asibitin nan." "Kaga matsalata da kai kenan saurin fushi." "Shi yasa zan d'auke kafa ka daina ganin fushin." "Zauna Abokina muyi magana na fahimta domin bana son fushin mahaifiya ya tab'a min kai." Wani dogon tsaki Sa'ad ya ja tare da ficewa ya bugo masa k'ofar office d'in da k'arfi wanda saida ya razana. "Kai anya Sa'ad shi kadaine kuwa? Tabbas ruwa baya tsami banza, saurin fushin nan ya yi yawa ga rashin fahimta, hak'ik'a bai rama mutsa-mutsai saman kansa." Dr. Jalal ya ambata cike da damuwa. *** Gidan malamin da ya yi saukar Alqur'ani Uncle Muhseen ya nufa sun jima suna magana kan lamarin inda ya yi ta bashi labarin yarda mugayen aljannu suke had'a fitintunu tsakanin al'umma a rasa gano kan lalura, domin kai tsaye ya karyata zancen guba, ya ce siddabarun mugayen aljannu ne da akayi mata turensu suka juya lamarin da guba dan had'a fitina asoma zargin da babu makama. Uncle kam ya gamsu da bayanan, a k'arshe suka fito tare zuwa Asibitin. Sun sami Baba da matarsa kewaye da da Mama, k'iri-kiri Baba ya hana su isa wurinta duk kuwa da suna kallonta tana magana akan ya barsu amma ya rufe ido ya yi ta fesa bala'i tare da ik'irarin samuwar alkaba'i ga Uncle wanda tashin harshensa ya janyo Likita ya shigo ya koresu tare da bawa Uncle damar ganinta shi da Malam wannan abu da Likita ya yi ya bakanta ran Baba ainun inda ya k'ara kullatan Uncle domin bai jira komi ba ya fice tare da matarsa suka bar Asibitin baki d'aya, ya tarar musu Napep suka tafi gida shi kuma ya nufi gidan Baba Umaru wanda har zuwa lokacin bai sami labarin lalurar ba. Saida suka tabbatar Baba ya b'ace sannan suka juya da mai Napep zuwa Asibitin suka sallameshi suka shiga suka zauna suna raba ido, zuwa can suka tambayi wata Nurse d'akin da Deejah ta ke ba tare da tunanin komi ba ta yi musu jagora zuwa d'akin. Zama sukayi a kujerun roba da suka samu a cikin d'akin suka tsirawa Deejah ido, suka kalli juna sai suka kyalkyale da dariya har da yin k'aramar gud'a cike da nishad'i. Bincike suka somayi ko zasu sami abin kwalam amma basu sami komi ba cike da jin haushi Asabe ta nufi inda Deejah ke kwance ta falla mata mari wanda saida yatsunta suka fito ta kai hannu ta shak'e mata wuya da iyakacin k'arfinta duk, ita kam Deejah bata san anayi ba. "Kul! Yaya barta kada ki k'arasa gawar da banaki ba." Cikin huci ta juyo "Wallahi Hinde ji na ke tamkar in kashe su na wataya cikin  dukiyar tumakan can wanda kullum sake tunbatsa sukeyi, hassada da kushe basayi musu komi sai ginuwa" "Wallahi Yaya nafiki bak'in ciki da ganin albarkansu haka nafiki son Hurera da wannan shegiyar su mace muci gado a bulis." "Ki bari kawai Hinde ai ni a duk kwanar duniya sai na yi fatar samuwar sanadin macewar tumakan nan da lalacewar duk k'addarorin Hurera amma abin takaici tamkar taki ake yayyafa musu, ni lamarin har tsoro ya ke bani." "Ai itama a tsaye ta ke bata gidan Boka bata gidan mugayen Malamai shi yasa duk asiran da muke b'atar da kud'ad'e wurin yi mata ya kasa tasiri akanta." "Ai yanzu gashi muna zaune tasu tazo k'arshe, insha Allah Hurera bata warkewa haka wannan shegiyar daga wannan sumar sai dai ta jita cikin k'abari, rayuwar barzhu ya tabbata garesu." Wani shewa suka tare da tafawa suka juya suka buga duwawo cike da farin ciki. "Ai Yaya suna mutuwa kafin a kaisu zan tura Anas ya sungumomin uwar garken in kaita k'auye wurin Kaka na yi ta cin amfaninta hankali kwance." "Nikam buhunan waken suyar nan na ke hari dan ko daren jiya na tura Kamalu ya haura ya satomin su sai wannan banzan Alhaji Muhseen d'in ya zo ya kwafsa dan iya mugunta har da saka 'yan sanda gadi wanda har yanzu zancen da na ke miki basu bar gidan ba." "Oh ni 'ya su kajimin dan wahalar makwafci dai, ko ina ruwansa da lamarin gidanta?" "Oho masa, amma ai ya tab'o Malam, ina mai tabbatar miki sai yaga bayarsa, duk dukiyarsa sai ya zamo tarihi, kuma ina bayarsa ya makashi a Kotu tunda banga dalilin shiga lamarin iyalinsa da ya yi ba yana k'aton baligi." "Uhm Yaya ina tsoron kada Malam ya janyo mana fitina muna zamanmu lafiya kinsan dai yafishi kud'i da sanin manya." "Ke dalla can matsoraciya kawai wallahi ni burina a kulleshi tare da manna masa kazafin yana lalata da Deejah kinga tunda yana da mata jefeshi za'ayi mu kuma mu tik'i rawarmu da shewa." Wani dariya suka kuma kwashewa da shi tamkar tab'abbu. Turo k'ofar akayi suka juyo idanu waje, tsira musu ido ta yi duk sai suka daburce, rashin gaskiya ya baiyana karara a tare da su "Nagode zaku iya tafiya tunda kun gama nishad'in." Hijabansu suka sanya suka fice kansu k'asa irin na munafukai. "Mama wad'an nan mutane basu da gaskiya, rawa da guda fa nagansu ta window sunayi tamkar suna gidan biki, dalilin da yasa kenan na kirawoku dan ku gani." Nurse da ta rakosu ta ambata cike da takaicin. "Bakomi sunma kansu ne ai ciwo na kan kowa." "Allah dai ya kyauta, wallahi dana san ba mutanen kirki ba ne bazan yi musu jagorar zuwa ganinta ba." "Kada ki damu, koma bakin aikinki sai dai gaba a kiyaye wad'anda zasu nemi ganinta." Uncle ya ambata a hankali. "Insha Allah, Dr. Jalal ma ya saka wanda zasu kula da wanna gefen." "Da kyau, hakan ya makata kam." Kujera Uncle ya matsawa Mama da shi bakin gadon ta zauna idanunta cike da hawaye. "Kada kiyi kuka addu'ar samun waraka zakiyi mata kamar yarda ta rik'a yi miki sadda kike kwance." "To Alhaji amma kukan ne yakeyin kansa duk yarda na koreshi yak'i tafiya." Ta amabata cikin muryan kuka. Sauke kai kasa Uncle ya yi yana jin wani kalan tausayinsu na kuma nashe kirjinsa. "Komi mai zuwa da wucewa ne Hajiya, ki daure kina ambatar addu'ar dana sanar da ke d'azun insha Allah dakiya zai rab'eki." "To Malam, hak'ik'a bani da bakin gode maka sai dai na dauwama cikin nemawa rahmar Allah har zuwa ranar da ruhina zai bar gangar jikina zuwa ga mahaliccinsa." "Ina godiya da wannan karamci, Allah ya sa damu da Rahmar Allah baki d'aya." "Amin." Uncle ya amsa ahankaki idanunsa na kan Deejah. "Na k'ara yarda da addu'a takobin mumuni ne domin a dazun idan ancemin zan iya takawa da kafafuna zuwa nan zan musanta amma da zuwar Malam bayan ya gama yimin addu'a ina shan Zam-zam d'in nan sai narika jin tamkar ana kwanceni daga mugun d'auri, cikin amincin Allah na rikajin kuzari na kuma nashe duk kan gab'b'aina, kai madalla da samamuwarka cikin rayuwarmu, ina mika dubun godiya a gareku Allah ya rubuce zuwa gaban Ma'aikin Allah." "Amin." Suka amsa shi da Uncle. "Itama yanzu zan jaraba sa'ata insha Allah bazata kai kwanakin da Likitoci suka ambata ba duk da nata ba nindaren aljannu." "Allah ya taimaka." "Amin Mamanmu." Kallon Uncle Mama ta yi sai taji kunyar sunar ta sauke kai k'asa, shima kunyarta ce ta kamashi ya juya baya yana sosa sajensa. Malam ya matsa gaban gadon Deejah ya ja addu'a mai tsawo ya tofa a robar Zam-zam ya guntsa ya fesa mata a fuska, bata motsa ba ya kuna fesawa duk bata motsa ba haka ya cigaba da yin addu'a yana fesa mata ruwan Zam-zam a fuska har sau bakwai sannan ya dakata yana sauke numfashi tamkar wanda ya yi gudu zuwa 'yan sakonni sai ta d'aga hannunta na dama da k'arfi ta maida ta kuma motsa kai cikin cije leb'e daga haka bata k'ara motsi ba, ta koma yarda ta ke tamkar gawa. Hamdala Malam ya yi, ya  juyo ya fuskanci su Mama da jikinsu ya gama yin sanyi da lamarin. "Alamun masara kenan dama k'a'idar addu'ar idan ta motsa aiki ya yi kyau idan kuwa bata motsa ba har tsawon mintoci goma to koda ta tashi zata iya gamuwa da wani lalurar daban to sai gashi ta motsa ko minti d'aya ba'a samu ba, tabbas dole mu k'ara godewa Allah, domin mun rok'esa kuma ya amsa mana nan ta ke, Allah Alhamdulillah." "Alhamdulillah." Mama da Uncle suka ambata a tare. "Hajiya anjima bayan la'asar Alhaji zaiyimin jagora zan shiga gidanki in sake yin saukar Alqur'ani da yarana sai mu rufe da rokon Allah akan ya baku kariya daga duk kan sharrin jinsin mutum da aljan duk da munyi hakan to zamu karayi akaro na biyu bayan kwana biyu sai mu zauna zama na k'arshe wato na uku inda zamuyisa kafin a sallamoku. Da yardan Allah kunyi ban kwana da duk kan sihirce-sihirce da akeyi muku a gida kuma idan Khadijatu ta warke zan rubuto  mata addu'o'i wanda zaku rik'ayi bayan sallar subahi da magriba domin kara samun kariya daga mugaye." "Nagode Malam, Allah ya biyaka da khairan." "Amin." Rakiya Uncle ya tafi yiwa Malam abinda ya bawa Mama damar yin kuka, ta kife kuskanta a tafin hannun Deejah ta saki kuka mara sauti, ji take tamkar ta dawo da laluran kanta. "Allah ya tashi kafadarki Uwata, ina da buri mai yawa akanki, ina son naga Aurenki tare da zuri'arki, na goyasu tare da yi musu tawai, zuri'ar da ban samu ba ina burin na samesu ta fanninki, ki haifamin na gansu suna kiriniya a gabana, ya Allah ka saukar da salama zuwa ga baiwarka Nana Khadijatu ba dan halinta ba." "Amin ya Allah Mama." Dagowa ta yi Fanta ta fado jikinta tare da sakin kuka mai sauti. Isowarta kenan da abinci Uncle ke sanar da ita. "Fanta DAMUWATA mai tarin yawa ne, idan na rasa Uwata bansan ya zanyi ba, ita ce bangon dafawana, ita na ke kallo na sami farin ciki, hak'ik'a in ta tafi ta barni nima zan bita ne domin banga amfanin rayuwa babu ita ba." Rufe mata baki Fanta ya yi tana girgiza nata kai hawaye na kuma b'ulb'ulo mata. "Barni in fitar da DAMUWATA Fanta ko ya taima na sami sauk'in malolon da ya tokaremin k'ahon zucci." "Mama ki ambaci sunar Allah shi ne maganin damuwarki sannan ki kwanta ki huta domin surutun sake jefaki cikin damuwa zaiyi gashi dama ba lafiya ce ta wadaceki ba." Hannu ta kai fuskan Fanta tana share mata hawaye cikin motsa mata kai alamun aminta da kalamanta. "Nagode Mama." "Hak'ik'a kunyi tarayya wurin halayya sa Uwata shi yasa k'awancenku ya yi k'arko." "Mama dan Allah ki taho ki kwanta a nan ki huta." Ta ambata tare da nuna mata gefen gadon Deejah, tana mai zaunar da ita a wurin cikin lallab'awa, sai lamarin ya bawa Mama dariya ta murmusa ta damk'e hannun Fanta ta d'ora a saman na Deejah, ta tsirawa hannayen idanu cikin sauke numfashi zuwa can ya ce "Ko da na rasa Uwata dan kiyimin alk'awarin zamemin tamkar ita." "Na yi miki wannan alk'awari Mama." "Nagode, Allah ya yi miki albarka." "Amin." Ta amsa cikin sakin kukan da ta ke cijewa kada ya kufce. Rungumeta Mama ta yi tana sauke ajiyar zuciya saboda sunar Allah As-saburu da ta soma ambata cikin ranta ya taima wurin sanya mata jarumtar da batayi zaton samunsa ba. *Duk wanda ya rik'e Allah tabbas shi kuwa zai ishe masa ga duk kan damuwarsa, mu daure muna mik'a lamuranmu ga Ubangiji mabud'in taskan Alkhairori. Allah ya yayemana dukkan damuwarmu alfamann Manzon Allah S.A.W* *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/28, 1:52 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Mrsjmoon E.W.F. https://youtu.be/v9iNYDvS8JM Pls kiyimin subcribe a YouTube channel d'ina.🖕 PAGE 16. "Muyi hak'uri dai Fanta kuka baya maganin damuwa sai ma k'ara wa, ki tuna abinda kika sanarmin yanzu, shin me yasa zaki maida hannun agogo baya?" "Mama Deejah ce kwance kamar gawa? Jiya fa muna tare lafiya lau, shi ne abin da ya bijiromin na kasa daurewa." "To ya zamuyi da k'addarar Allah? Sai hak'uri kawai tare da mik'a lamarin garesa domin samun d'aukinsa ba dan iyawarmu ba." "Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un." Fanta ta ambata tare da sake k'amk'ame Mama, lamarin da yaso karyamata zuciya amma sai ta soma addu'a cikin fitar sauti a hankali. "To zaki wuce gida kuwa in har kuka zakizo kina sanya mutane." "Uncle na kasa daurewa ne." "Ki cigaba da ambatar addu'ar da kika sanarwa da Mama har ta sami jarumta." Motsa kai ta yi tare da janye jikinta ta koma gefen Deejah ta wurin kanta ta zauna bakinta na motsi alamun addu'ar ta ke yi hannunta na yawo saman sumar Deejah. *** "Yaya ka kwatantamin gidansu sai inje na dubo maka ita." "K'anwata kinfi kowa sanin tsaron Hajiya." "Zance mata zani gidan Aunty Zainab ce." "Tsakanin gidan su Deejah da gidan Zainab da tazara mai nisa kafin kije ki dawo na tabbata Hajiya zata kira taji idan kinje kuma in kika soma zuwa gidan Zainab kina fita zata kira Hajiya ta sanar mata da kin fito kinga kenan lamarin ba mai sauki ba ne." "Yaya yanzu ya za'ayi?" "Bari ruwan ya kare sai in lallab'a na tafi da kaina." "Bazaka iya ba Yaya, jikinka bai warke ba, kallifa yarda kake magana kana hutawa." "Buguwar da na yi a hakarkari na ne keyimin zafi amma banjin ciwon komi bayan shi." "Ka dai samo wani dibaran domin kaima na tabbata Hajiya baza ta barka ka fita a haka ba." "Bari in sake kiran K'awarta ko zanyi dacen ta d'auka tunda ita nata wayar a kashe ya ke." "Ok jaraba mugani " Cikin jan tsaki ya jefar da wayar gefe. "Bata dauka ba ko?" "Ina cikin damuwa wallahi, narasa wanda zan kira na sami labarin Khadija." "Mijin Aunty Zainab mana tunda kace, ka ganinsu tare." "Kuma hakan ya kamata, nagode k'anwata." Kiran number ya yi aka d'auka bayan gaisuwa sai ya rasa abinda zaice masa. "Ya dai Aliyu?" "Yallab'ai dama zance ya wurin su d'iyarka?" "Oh Khadija?" "Eh." "Wallahi yanzu Baba ke sanarmin Mamanta bata da lafiya tana Asibiti." "Ya rabbi, shiya ban samun wayarta kenan?" "Eh zaiyiwu hakan ne." "Allah yabata lafiya." "Amin." "Wani Asibiti ne?" "Ban sani ba dan nima yanzu zan tafi na d'auki Baba mu tafi amma in na isa zan kiraka." "To nahode." Ok bakomi." Sauke wayar ya yi tare da lumshe ido. "Itama bata da lafiya ne ?" "Mamanta ne a ka kwantar." "Ayya Allah ya sa kaffara ce." "Amin." "Amma Yaya kana son janyowa kanka ruwa fa." "Kinga kada ki sake maganar sokuwar nan ya hadamu." "To ai bance komi ba " "Gara dai haka." "Salma fito hakanan ki barsa ya huta." "To Hajiya." Gyad'a mata kai ya yi ta fice tana murmushi. *** Habibu ya cika fam da takaicin Baba akan zagin dake da durawa Uncle duk kuwa da bai sanshi ba amma ji yake tamkar d'an uwansa ake zagi ga shi Baba Umaru na ji amma bai ce kanzil ba hasalima wani littafin addu'o'i ya bud'e yana bita. Zuwa can Habibu ya ce "Haba Malam Hadi kana Malami amma ake jin wannan ashariyar abakinka dan kawai makwafci ya nuna kulawa ga iyalinka abinda na yi imani kai bazaka iya yimusu ba." "Kai Habibu ban son rashin ta ido kaji ko? Shin kasan muhinmancin iyali kuwa?" "A'a sai ka koyar da ni irin yarda ka san naka." "Akul Habibu, kada na kuma jin bakinka." "To Baba." "Baba wallahi mutumin nan ya rainani, dan Allah kayi masa iyaka da iyalina, kwata-kwata ban son su sake mu'amala da shi domin ina jin ana maganar arzikinsa bana halas ba ce wata kilama so ya ke ya shanyemin jininsu, ya kaini ya baro." "A'uzubillahi! Me ya kawo wannan maganar kuma Hadi?" "Baba wallahi lamarin ne ya kasa kwantamin dubi da yarda yake kashewa Uwani kud'i duba fa ka ga wayar dubbunnan kud'ad'e da ya mallaka mata tamkar bai san zafin nemansu ba." Mik'a hannu Baba Umaru ya yi ya amsa wayar ya jefa a aljihu batare da ya duba ba. Hararan gefen ido Baba ya maka masa domin yaso saida wayarce shi yasa ya d'auke amma azal ya sanyashi yin maganarta ta zamo haramiyarsa. "Hadi duk yarda makwafci ya ce shi d'in d'an uwa ne saboda shaidansa kad'ai zai iya kaika gidan Aljanna, ina tunasar da kai abinda ka sani kake takewa shi ne ka kyautatawa makwafci zato tare da rufa masa asiri musanman ga wanda ya bada kula ga iyalinka." "To Baba amma ai musulinci bai bashi damar shigamin gida lokacin da bana nan ba, ko dan gudun gudun zargin mutane." "Abinda na ke tunasar da kai kenan cewa ka kyautata masa zato kuma zanyiwa tufka hanci akan irin haka bazai sake faruwa ba tunda ya wuce iyaka, shiga gida yana baligi." "Yawwa Baba kaima dai kagani." "Zan bincika lamarin tundaga farko kafin in yanke hukunci." "Ai wallahi ko da ka ja masa kunni sai na makashi a kotu." "Kotu!?" Habibu ya amtaba batare da ya sani ba. "Eh can zan kaishi kuma sai ya gane shayi ruwa ne, dani yake zancen." "Wato in na fahinceka dama can kuna da jika'kkiya kenan?" Baba Umaru ya furta cikin shakewar murya domin ya soma gajiya da rashin kangadon Baba. "A'a kawai shiga lamarin iyalinsa da ya yi na ke son ayi masa iyaka da su." "To ba amfanin sakani cikin lamarin da kayi kenan?" "Da shi mana Baba, kawai rubdugu zanyi masa ya gane ba da wasa na ke yi ba." "Hadi in kanayiwa Allah da mahaifanka ka janye maganar kai makwafcinka kotu." "Baba ka... "In har na isa da in sanya baki cikin lamarin to ka janye." "Shi kenan amma wallahi sai ya fita harkan iyalina." "Naji zai fita." Daga haka shiru ya ziyarci motar, Habibu ya ja tsaki kad'an cikin zabgowa Baba harara ta mirror, dak'uwa Baba ya auno masa batare da ya bari Baba Umaru ya gani ba, wani hararan Habibu ta bunko masa tare da cije lips. "Kayi koyin halin girma tamkar mahaifinka." "Kafi kowa sanin hakinsa kaf na kafe saidai kayiwa kanka wa'azin kula da iyali." "Baba yaushe Habibu ya koma mara kunya haka?" "Habibu ban son na sake jin amonka." "To Baba." Ga masifa a bakin Baba amma Baba Umaru ya katange damar amayosu saboda bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne. Koda suka isa Asibitin Uncle ya koma gida Baba ya yi ta hura hanci Baba domin bai so hakan ba, Baba Umaru dai na kallonsa cikin nazari ya yin da Habibu ke ta zabga masa harara cike da takaicin hanashi maganar da Baba ya yi da sai ya wanke Baba tas da ruwan kalamai. Abin mamaki ko sannu da jiki Baba baiyiwa Mama ba da ya iso ya sameta cikin k'oshin lafiya sama da d'azun da ya barta cikin godiyan Allah, balle kuma ya yiwa Deejah da ke kwance tamkar gawa. Halin ko in kulan da ya nuna ya tab'a zuciyar Mama amma ganin su Baba Umaru sai ta kauda duk bacin ranta saboda matsayin su na da banne. Addu'a Baba Umaru ya ke ta tofawa Deejah yana rik'e da hannunta na dama cike da tarin damuwa zuwa can ya juyo ya tambayi Mama yarda lamarin ya kasance. Abinda Likitoci suka sanar mata ta fad'a masa ya jinjina kai ya sake tambayarta yarda ita kuma ciwonta ya sameta nanma abinda ta sani da wanda Uncle ya bata labari ta fad'a masa tare da taimakon Malamin nan duk ta sanar da shi sai dai bata tona tijarar da Baba ya yi ba. "Alhamdulillah zanje gidan Malamin na yi masa godiya domin ya taimakeni wurin bawa amanata kariya, Allah ya biyashi da gidan Aljanna." "Amin ya rabbi." Habibu ya amsa da sauri yana aunawa Baba wani kallo. K'ara hade rai Baba ya yi tamkar wanda aka aikowa da sak'on mutuwa. Kallonsa Mama ta yi ta ce "Kaima Malam ka je ka gode masa domin ya taimakemu iya taimako." "Zanje, ko ba Malam Isuhu mai gudun duniya ba?." "Eh, haka fa sunarsa ya ke." "Au a shema  d'ana ne, kai masha Allah, ai ya yo gadon sanin lak'anin korar shed'anu wurin mahaifinsa Malam Hassan, madallah da d'an arziki irin albarka." "Baba ka sanshi kenan?" "Eh na sanshi Hurera, mahaifinsa mutumina ne kafin Allah ya yi masa rasuwa." "Allah sarki gaskiya ya zamo Malami na gari." Da sauri Baba ya kalleta ta sauke masa murmushi ya kauda kai yana tsinewa Uncle da Malam Isuhu cikin ransa. Ni zan koma na aiko Habibu da sak'o wanda idan ta farka shi zata soma sha, insha Allah jikinta zai dawo dai-dai batare da firgicin komi ba balle kufcewar tunani." "To Baba, nagode." "Ke ma ki sha idan ya kawo sannan Hajiya zata zo bayan sallar magriba ta kwana da ku saboda kema ba lafiyar ce ta wadaceki ba." "To Baba, Allah ya k'ara girma." "Amin, Allah yasa kaffara ce." "Amin." "Hadi zamu barka a nan ne?" "Eh Baba." "To ayi ta hak'uri kada ka tada zancen nan a Asibiti saboda jama'a, idan sun dawo gida zanzo da kaina mu zauna kuma ka tabbatar ka bawa Malam Isuhu hadin kai anyiwa gidan nan addu'o'in da ya kamata dan na fahimce akwai damuwa cikinsa." "To, za'ayi." "Madallah, nabarku lafiya." Suka fice da Habibu Baba ya rakasu da mugun kallo tamkar zai cinyesu da idanu. "Malam uban nawa kake harara?" "Kinga Hurera ki fita idona in rufe." "Allah baka hak'uri amma ka sani ba zan tab'a hararan naka mahaifan ba." Tana ambatar haka ta juya masa baya tana mai ambaton sunar Allah dan samun rinjaye akan zuciyarta domin kallon da ya raka Baba Umaru da shi ya sosa ranta. "Ke! fice ki bamu wuri munafuka banza kawai, 'yar rahoto." Da sauri Fanta ta fice tana sharan hawaye dan tana kwance gefen Deejah. "Hurera kin san Allah na kara ganin Alhaji Muhseen a Asibitin nan sai ranki ya b'aci." "Malam wai me kake nufi ne? Yanzu Uwata na kwance tamkar gawa amma ka kasa yi mata sannu da jiki balle addu'a amatsayinka na Malamin addini?" "Uwanki kika ce ko uwata?" "Tawa ce ba taka ba." "To sai ki tsukemin bakinki mai kama da Asusu ki saurari kashedina wanda ke makwafin wajibi a bishi in ana son ganin dai-dai." "Malam dan Allah ka tafi kaina ya somin ciwo." "Yanzu kika soma ganin ciwon kai in dai bazaki bi abinda na ke so ba." "Me kake nufi?" "Abin da tunaninki ya baki." "Kai ne sanadin ciwo na kenan?" "Wannan kuma kanki akeji nidai na sanar miki kada Alhaji Muhseen ya sake shigamin lamarin iyali." "Yanzu kuwa yasoma shiga saboda wata rana surukinka ne shi." "Au Allah?" "Insha Allah." "Zamuga ni." "Insha Allah khairan gamu gani." "Shi kenan Hurera ki nunawa duniya ban isa da ke ba kinji?" "Malam kayi nazari domin wallahi Alhaji Muhseen mutumin kirki ne, kai shaida ne domin kafin zuwar lokacin nan kasha sanarmin da cewa baka tab'a ganin mai kud'i mara girman kai da sanin darajan makwafci irin shi ba." "Au saboda yana da arziki shi yasa kike son ya auri Uwani?" Shiru Mama ta yi bata amsa ba. "Shi ne irin mijin da kikeyi mata addu'ar samu kenan?" Ya furta cikin cillowa Mama kallon banza. "Eh." Ta ambata kai tsaye. "To ina tayata murna." Kafin Mama ta san abin cewa ya buga babban rigarsa ya fice. Dafe goshinta ta yi saboda jiri da ta soma gani. Ba dan Fanta ta shigo ba tabbas da fad'owa k'asa zatayi daga saman kujerar da ta ke zaune. Cikin sa'a Nurse ta shigo ita ta taimwa Fanta suka dorata gefen gadon Deejah, cikin gaggawa aka kawo wani dago d'akin aka maidata kansa, Likitoci biyu suka rufu kanta, cikin mintoci da basu gaza goma ba ta samu barci. Fad'a Dr. jalal ke yi tamkar zai ari baki a k'arshe ya bada umurnin kada a sake barin Baba shigo masa Asibiti, har masu gadi ya sanarwa wannan kashedi. *** Kamar yarda Malam Isuhu ya ambata  bayan sallar la'asar ya iso gidan Uncle ya fito suka shiga cikin gidan su Deejah suka raba Qur'ani har da Uncle suka soma karatu da ya ke suna da yawa awa d'aya da rabi suka kammala suka soma jero addu'a d'aya bayan d'aya suna daf da kammalawa Baba ya fad'o gidan afujan-jan. Duk yarda yaso yin tijara kasawa ya yi darajar gamin Al-qur'ani sai ya sami kansa da zama aka shafa addu'ar da shi. Kallon da Malam Isuhu keyi masa ne ya yasa jikinsa k'ara yin sanyi. Uncle ne ya mik'awa Malam hannu sukayi musabaha tare da mik'a godiya, ya dubi Baba ya russuna cikin ban girma ya gaisar da shi ganin karramashin da Uncle ya yi sai ya saki rai ya soma washe bakin dole. Haka d'aliban suka soma gaisar junarsu ta hanyar musabaha daga k'arshe suka russunawa suka gaida Malaminsu da su Uncle, daga nan suka fice gidan ya rage saura su uku. "Malam Yusuf ga mai gidan nan ni albarkacin makwaftaka ya sa na jagoranci lamarin." "Malam Hadi kai ne maigidan Hajiya?" "Eh, Hurera ba, ai bataje Hajji ba Malam." "Inda rai da rabo Baba." Uncle ya mabata cikin murmushi. Tsaki Baba ya ja ya juya zai fice sai dai maganar Malam Isuhu ya dakatar da shi ya juyo a hanzarce. "Me ka ce?" "Cewa na yi na kudiri aniyar maidawa wanda ke son cutar da Hajiya aniyarsa." "Haba Malam Isuhu kana masanin addini amma kana son saka sharri da sharri, ka da fa kamanta yin hakan d'aukan zunubi ne domin ba lallai ne ya sauka kan wanda ya aikata d'in ba." "Idan na aikata tabbas sai ya sauka kan wanda ya yi tare da wanda ya yi sanadiin aiki." "Kuma dai?" "Eh, saboda rama mugunta ga macuci ba laifi ba ne." "Kagane Malam Isuhu mubar maganar zanzo gida na sameka sai muyi maganar anatse mai cike da fahimtar juna." Kallon k'urillah Malam Isuhu ya kafeshi da shi sai kuma ya murmusa tare da motsa kai ya kalli Uncle ya ce "Insha Allah sauka na k'arshe Malam Hadi zai jagoranta shi da d'alibansa." "Malam da ka cikashe aikinka kawai." "Alhaji ai tare dani za'a yi har da kai tamkar dai yarda mukayi wannan tare manufata shima Malam Hadi ya kamata ya taimaka da irin nasa baiwar tunda shi ne jigon gidan." "Haka ne, to Allah ya kaimu lokacin." "Amin." Uncle ya amsa Baba kam kai ya wuya gefe zuciyarsa tamkar wuta saboda takaicin ya sa tijarar da ya zo da shi. Sake yin musabaha da Baba Malam Isuhu ya yi Uncle ya rufa masa baya suka bar Baba tsaye tamkar an dasashi. "Ya kamata in san inda kaina keyimin ciwo tun kafin gwad'o ya yi min k'afa." Baba ya ambata cikin zare idanu, ganin Uncle ya dawo sai ya dai-daita natsuwarsa tare dajin wani kalan tak'ama ya ziyarce shi. "Baba dan Allah kayi hak'uri akan laifin dana aikata maka na shiga lamarin iyalinka kai tsaye batare da na nemi izininka ba, hakan ya faru ne saboda halin dana ganta a ciki wanda tunanin nemanka ya b'acemin sai bayan na kaita Asibiti amma insha Allah hakan ba zai sake faruba, ka ya femin dan Allah." Shiru ya yi yana kallon Uncle a d'age cikin hura hanci. "Ni makwafci na gari ne ban aikata hakan don muzguna maka ba sai dan taimako irin ta makwafci na kwarai." Ya sake ambatar haka a ladafce. "Shi kenan ya wuce amma ka sani daga yau ban amince na sake ganin kafafunka a cikin gidan iyalina ba tunda ba gidan gala ba ne." "Insha Allah zan kiyaye." Tsaki ya ja, Uncle ya kalle shi da sauri domin tsaki nadaga cikin abinda ke fusatashi. "Tunda kai kayi kid'an to kai zakayi rawar ba ruwan Hadi ciki." "Ban fahinceka ba Baba?" "Munufata tunda kai ka kaisu Asibiti ba zanyi asarar ko taro ba, kai da kaja ruwar kai zai duka." Murmushi Uncle ya yi cikin jinjina halin Baba wanda samuwar lamarin yasa shi ganewa. "Wannan ba komi ba ne Baba ai yiwa wani aka ce yiwa kai ne." "To madallah, zaka iya ficemin a gida." Wani murmushin Uncle ya kuma yi, ya karkace a ya tura hannu a aljihu ya ciro kud'i yan dari biyar biyar masu yawa ya russuna ya mik'awa Baba, wani kallon banza ya saukewa kudin amma a zahiri godiya ya ke gabga masa cikin ransa ya yi hakan ne dan kare marbata. "Na me ye wannan?" "Ihisanin dai dana saba yi maka ne na aiwatar amma ba dan wani manufa na daban ba." "Nagode, Allah ya rubuce " Ya furta cikin damk'e kud'in. "Amin Baba." Sukayi sallama cikin wal-wala lamarin da ya yi ta bawa Uncle dariya. 'Wato kudi masu sayo martaba da k'arfi da yaji.' Cikin ransa ya ambata yana kuma murmusawa. "Halayyan Baban Khadijatu nada ban mamaki, gashi dai masanin ilimin addini amma in ya kwab'a wani abin tamkar bai tab'a zuwa makaranta ba balle ace yana koyarwa." Ya furta cikin ransa. Su Bintu ya gani suna shiga mota wanda ya tabbatar Asibiti zasu, ya k'arasa wurin cikin wal-wala amma ganin yarda fuskansu ya ke cikin rashin wal-wala sai ya tsare gira, duk suka fito suna gaisar da shi bai amsaba sai idanu da ya zubawa Nafisa wacce ke hakimce a gidan baya bata fito ba. "Ina zaki je?" Ya jefo mata tambayar. "Asibiti." "Kai waye ba lafiya?" Ya maido da tambayarsa kan su Beebah da ke tsai-tsaye "Mama da Deejah." Safina ta amsa masa. Ya juyo kan Nafisa kafin ya bud'e baki ta rigashi cewa "Makwafci ko me ya yi maka na aibu ya kamata ka saka masa da khairan dan koyi da halin Manzon Allah." "Sallallahu Alaihi Wasallam." Ya ambata tare da su Beebah. "Abban Hafiz ina fatar daga yau fushin ya k'are?" Ta ambata a hankali wanda da alama shi kad'ai ya jiyo saboda ya matso jikin motar ya bawa su Bintu baya. "Allah ya kiyaye hanya." Ya ambata tare da mik'a mata kudi "Ku saya musu kayan marmari." "Ok." Ta amsa tana kallon cikin idanunsa, murmushi ya sauke mata ta maida masa da martani. Yana tsaye suka fice inda Beebah ce ke jan motar. "Allah yasa tuban gaskiya kikayi dan na san waye ke Nafisat idan kin so shirya tsiya." "Alhaji gashi inji wani mutum ya ce abaka idan ka dawo." Mai gadi ya ambata cikin miko masa Emblem. Amsa yi ya ya nufi cikin gida yana kallon agogon da ke d'aure a tsin-tsiyar hannunsa na hagu. *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/30, 9:42 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Mrsjmoon. E.W.F. https://youtu.be/v9iNYDvS8JM Pls ku dannamin subcribe a YouTube chennel d'ina.🖕 *Alhamdulillah. Masha Allah. Congratulations Sister Aisha (Neesha). A yau Asabar anshiga daga cikin, matakin cikar kamala ya kammalu tsaf, Allah ya sanya khairan tare da dauwaman zaman lafiya, samuwar albarkan zuri'a d'ayyiba tare da so da k'auna mara iyaka, Allahumma Amin🤲.* Shafin na ki ne baki d'ayan shi, Amarya 'yar shagali😍. Page 17. *Aliyu.* "Yaya kayi kyau." "Wani kyau ga bak'in fata." "Ai su ne asalin kyawa-wa." "Fad'arki ba." "Da gaske Yaya bak'in fata na da kyau kuma ina son bak'in mutum." "Saboda kinganki fara ba." "Allah ba haka ne, nidai ina son bak'in abu shi yasa ko a kala ne nafi zab'an bak'i." "Ke ni rabani da surutu, sanarmin da gaisuwarki zuwa ga My Deejah." "Au batare zamu tafi ba?" "Ki rufamin asiri kada Hajiya ta hana fitar baki d'aya." "Kasan Allah Yaya yau sai naga Khadija ido da ido." Zama ya yi gefen gado ya tsira mata ido. "Zan fita yanzu a cewar zani gidan su Alawiyya amso Note book d'ina sai ka fito mu wuce." Kallonta dai ya ke yi batare da ya yi magana ba, ganin haka sai ta fice tana dariya. "Salma matsala in ban barta taje ba bazata barni na huta da uban mitaba." Ya ambata tare da mik'ewa ya k'ara fesa turare, ya fito ya sami Hajiya ya russuna cikin tarbiyya ya yi mata sallama ta rakashi da addu'ar dawowa lafiya. Tafe suke a Napep sai runtse ido ya keyi saboda yarda keken ke motsi yana jin inda ya bugu na yi masa zafi. "Sannu Yaya, jikin ko?" Da kai ya masa yana cije lips. "Ba dan soyayya ba na tabbata ba mai fito da kai waje ko zuwa gobe ne saboda son jikinka ko mace albarka." "Kin raina ni ko Salma?" "Sorry big Brother." "Idan kinga Mall mu tsaya asiya musu wani abu." Ya ambata tare da kulle ido. "To mijin Khadija." Kunninta ya ja ta k'ank'ame hannunsa cikin yin k'ara. "Idan mun koma gida ki tanadi abin fad'awa Hajiya domin ba ruwana ban san inda kikaje ba." "Bakomi zanyi mata bayanin gaida maman surikarta mukaje." "Da na yanke bakinki kuwa." "Wai Yaya me yasa bazaka sanar mata da ka samu Mata ba?" "Zan sanar mata amma ba yanzu ba." "Uhm wallahi ina guje maka samun matsala tunda gida bai... "Idan kina son komawa gida da lafiyayyun hak'ora kada ki sake maganar Amira ya had'anu." "Insha Allah bazan sake ba" "Hakan ya fi Miki." "Yaya ka... "Keep silent Salma, surutunki ya yi yawa." Cikin hanzari ta kulle bakinta, girgiza kai ya yi tare da lumshe ido surar Deejah na yi masa gizo. 'Ina son Khadija haka ina jin dirin k'aunarta har cikin tsokar zuciyata.' Ya ambata cikin zuciyarsa fuskansa cike da murmushi. Salma dai idanu ta tsira masa ga magana tana son yi ba halin furtawa sai ta kuma gyara zama tana k'arewa duk kan motsinsa kallo cikin yabawa tare da addu'ar itama Allah ya had'ata da maiyi mata k'auna na hak'ik'a irin wannan. Ajikinsa ya ji kallonsa ta ke yi ya bud'e ido ta yi hanzari kauda kai rankwashi ya sauke mata ta kyal-kyale da dariya, shina dariya lamarin ya bashi, hatta da mai Napep sai da ya dara duk da bai san abin da sukeyiwa dariya ba. *** Aunty ga mai fruits in tsaya a siya ne?" Beebah ta ambata cikin kallonta ta mirror. "Ki dai tsaya ki d'auki mai saida fruits din duka yafi" Dariya su Bintu suka kwashe da shi. "Kun soma haukacewa ne!?" Nafisa ta daka musu tsawa. Tsit sukayi, kowacce na tura baki cikin k'un-k'uni. "Kufuto fili ku zagene da wannan na zuccun da kukeyi." Ba wanda ya amsa mata ta ja dogon tsaki tare da cewa "Bazan siya musu komi ba wanda ya basu maula ya wadatar." "Maula kuma?" "Eh maula, ko kuna zaton ban san komi ba ne?" "Baki sani ba gaskiya." Bintuvta amsa kaitsaye. "Uwar kini-bini to sanar da ni." Yi ta yi tamkar bata ji ba. Ya ja kwata cikin watsowa Beebah harara "Saura kuma inji gulman ban siya ba tare da kalman maula wallahi inci uban mutum ba mai hanani." "Amma Aunty ba girmanki ba ne hakan, tunda Allah ya hore miki ko Uncle bai bada kudi ba ke ya kamata ki siya da naki." Fiddausi ta ambata cikin tsare gira. "Na ce bazan siya ba da baki kamar siyad'in!." "Jikin ya motsa kenan." "Wallahi Beebah zan ci k'aniyarki domin ba ki wuce in lakad'a miki duka ba kin dai san dai wacece ni, wato ga mmahaukaciya ko?" "Uhm Aunty Nafisa kenan ni bakiji na kiraki da kalman hauka ba." "Kina buk'atar dukan kenan?" "Uhm gaibu." "Zaki ramane in na bugeki?" "Ni bance ba amma duka yanzu ai sai su Hafiz." "Au kinfi k'arfin hukuncina kenan?" "Ni bance ba fa." "To me kike nufi da kalamanki?" "Dan Allah Aunty Nafisa kiyi hak'uri tunda dai kince bazaki siya ba ai shike nan." Safina ta ambata a hankali. "Eh bazan siye d'in ba, munafukan banza kawai, ai wallahi da Kaka Alhaji zan had'a ku duk ya cimin k'aniyarki." "Damu kayi miki me?" "Kinga Safina idan kika sake yin magana wallahi sai na sumar da ke." "Abin azimun ne." Firdausi ta furta tana kauda kai gefe. "Wai kuna son maidani mahaukaciya ce ko me?" Shiru ba wanda ya tanka mata, tsaki ta ja Mai sauti, har suka iso Asibitin fad'a ta ke yi. Gyara parking Beebah ta yi ta dubi Bintu ta ce "Idan da kud'i a hannunki ki samo masu fruits a bakin gate bama shiga hannu sake ba domin ba girmanmu ba ne." "Babu sister." "Muje da shi a wurina." Firdausi ta furta tare da bud'e k'ofar motar ta fice "Wallahi kuka siyo sai na ci ubanku." "Wai Aunty ina ruwanki ne? Ba fa kud'inki zasu tab'a ba." "Eh ko ba nawa ba ne ai na isa in bada umurni abi." "Idan ya kaucewa shari'a, Allah da kansa ya yi hani da bin umurnin na gaba." "Beebah billahil azim zanci Ubanki a motarnan." "Allah huci zuciyarki Aunty, uwar gidan Uncle mai kirki." Tana ambata ta fice da sauri Safina ta rufa mata baya tana dariya ya yin da su Bintu suka wuce bakin gate batare da sun saurari masifar Nafisa ba. "Wallahi yaran nan duk saina gyara muku zama ba dai ni kuke wulak'antawa kan wata banza ba, uhm ai zaku gamu da Kaka Alhaji ni kad'ai nasan tuggun da zan k'ulla muku, duk ku bar garin nan ba shiri." Tana nan tsaye jikin mota su Bintu suka dawo. Ba suyi mata magana ba suka wuceta tamkar basu santa ba, bayansu ta bi tana zabga musu harara. 'Idan na b'atawa wanda kuke rawar k'afar nunawa k'auna sama da jininku fuska da ruwan batir ta koma dodanniya abar tsoro ga kowa ai kwa dawo hayyacinku, shegun yara kawai.' Murmusawa ta yi cike da jin kwarin guiwar aiwatar da k'udirinta wanda shi ne dalilin zuwarta Asibitin. *** *Baba Umaru.* "Baba ga wata shawara akan zantukan Malam Hadi." "Ina saurarenka Habibullah." "Idan zaka yanke hukunci ka saurari duk bayanen kowa sannan kayi nazarin dukkansu sai ka yanke hukunci bisa tunaninka ba na wani gefe ba." "Hakan na ke da niyyar aikatawa Habibu." "Yawwa Baba kuma wallahi na gano rashin gaskiya a lamarin Malam Hadi." "Habibullah kenan, wani haline na Hadi zaka tusamin da ban sanshi ba? Ai ina kallonsa ne kawai domin na gano Alhaji Muhseen yana taimakon Hurera ne shi ne ya ke bak'in ciki amma na tabbata da zarar ya manna masa kud'i zaiyi tsit kasan indai akan kud'i ne komi zai iya aikatawa." "Allah ya shirya shi kam." "Amin. Amma ina cikin nadamar amincewa da auren Hurera ga Hadi, aure rai ne da shi da kuma Allah na fushi da mai guntileshi amma da wallahi Hurera bata kuma zama da Hadi." "Muyi ta binta da addu'a Baba domin aurenta ya zamo auren k'addara." "To Allah ya iya mana dace da khairan ba dan halinmu ba." "Amin Baba." "Bari inje na gaida Hajiya Inna tare da sanar mata ta shirya cikin lokaci." "To madallah hakan ya yi, ka sanar mata ta yiwa Hurera abu mai laushi da mara lafiya ke buk'ata." "To Baban Hurera." Dariya Baba ya sanya tare da watsowa Habibu dakuwa, shi kuwa ya fice yana dariya. *** *Hinde da Asabe.* Yaya nikam da zaki amince munbi Juma inda ta ke amso sa'a har ta mallake kowa na gidan ba wanda ke tsallaka kara duk in ta sanya, kinga da sai mu jefi tsun-tsu biyu da dutse d'aya, mu mallake Hurera da Malam hankali kwance in yaso in munje wurin sai mu raba ni na Mallaki Hurere ke kuma ki mallaki Malam." "Zancen bur inji tusa. Kinga Hinde ki fita ido ko kin dawo miki Asabena ta zamanin baya." "To Yaya me na yi kuma daga shawarar arziki sai tijara ya biyo?" "Son kai dai shawarar arziki ba" "Ta ina naso kan nawa?" "Ta mallakan Hurera ni ki mannamin Malam mai mugun tsari a jikinsa, kinga garin neman gira sai in rasa ido a k'arshe na haukace yazamo kinci duniyarki da tsinke, to wallahi aniyarki ta biki, muguwar banza kawai wanda bak'in hali ya gama yiwa sutura." "To ya isheki haka nan Yaya, kada abin ya koma cin zarafi." " Bai isa ba, muguwar banza da wofi kawai." "Duk mugunta na ban kama ko farcenki ba tunda ban tab'a yin kisan kai ba." "Hinde! wa ya yi kisan kai?" Muryan Baba ya ratso kunnuwarsu. Tsit sukayi, ya k'arasa cike da masifa, suka ja baya ya nunosu da yatsa yana tattare babban rigarsa ya ce "Munafukai zaku sanarmin da wanda ya aikata kisan kai ko sai na maidaku b'eraye? Kun k'are a sata cikin kasuwa." "Tsafi ka koma Malam?" "Ke Hinde! Shiga hankalinki ko in sab'a miki matuk'ar kika nemi kawomin wargi, kindai san halina ciki da bai." "Allah huci zuciyarka." "Amin, maza sanarmin da wanda Asabe ta kashe tun ban mik'aku ga hukuma ba." "Hukuma kuma?" Asabe ta ambata idanu waje. "Eh, in kaiku kuyi bayani a can ko ba dan Allah ba sai dan bak'ar azaba  domin sanyawa zanyi suyi muku dukan jakuna masu d'iban yashi da duwatsu." K'iftawa Asabe ido Hinde ta yi ta karkace ta ce "Malam abinda ya faru kusan shekaru ashirin meye na son ta tado da shi?" "Ban fahimceki ba uwar salo tamkar d'iyar marok'a." Murmushin yaudara da cilka masa ya maka mata harara ta kuma murmusawa cikin cewa "Manufata Nuhu almajiri da ka duka har ya zamo sanadin barinsa gidan duniya shi ne muke maida zancen har na ke cewa itama tana da alhakin kisan kai tunda ita ya yiwa laifi ta sanar maka kai kuma ba bincike hau dukan... "Dalla can rufemin baki, sokayen Mata kawai da iya janyo masifa ana zaune lafiya, maza ku kama aikin gabanku ban son munafunci da maido zancen da ya wuce sabo." "Had'a idanu sukayi suka murmusa batare da Baba ya gansu ba. Sab'a babban rigansa ya sake yi ya shige d'akinsa yana cewa "Gidan Hurerama zan kwana saboda b'arayi sun soma kaiwa dukiyarta hari, makwafcin kirki ta samu ya sanya makatan tsaro amma yau na koresu ni zanyi gadin dukiyar iyalina." "Aikam ka kyauta." Suka ambata a tare. "Ko ban kyauta ba matsalarku ba ce, mahassada kawai, ai duk kallon munafuncinku na ke yi dan nasan komi amma duk ranar da kuka kaini bango wallahi sai kunga tijara ganin idanunku." "Malam me mukayi mata kuma?" "Farin ciki da ciwonta Mana." "In wannan ne ai ba wanda ya kaika murna." "Me kike nufi da zantukanki Asabe!?" Ya furta cikin fad'a tare da fitowa waje. Ja baya sukayi ya watsa musu mugun kallo ya koma d'akin yana ta sababi wanda basa fahimtar me ke cewa. Jan hannun Asabe, Hinde ta yi suka shige k'uryan d'akinta gudun kada ya jiyo abinda zasu tattauna. "Yaya wallahi ki daina kaini bango kada wata rana na tona asirin dake birne." "Hinde wai har sai yaushe zaki daina yimin barazana kina doramin alhalin mutuwar Jaririn da tuncan a matacce ya iso duniya?" "Yaya wallahi ke kika kashewa Hurera d'a dan najiyo kukansa amma kafin in shigo kin aikata mugun nufinki." "Ikon Allah, a she har yanzu sharrinki bai ragu ba Hinde saima k'aruwa?" "Sharrinmu dai zaki ce." "To naji nina kashe Jaririn Hurera amma aikema kinyi mata asirin da bazata sake haihuwa ba tare da sanyawa Uwani bak'in jinin rashin mijin aure." "Au haka bokanki ya sanar miki da ni ce na aikata wad'an nan aiyukan?" "Ko me zaki ce na tabbata ke ce kikayi su." "Bilahil azim ban shiga lamarin Uwani ba na sandai na kashewa Hurere kwayoyin halittar haihuwa." "Oh a she kema kin aikata kisan kan kenan?" "Ni kam Yaya ba wannan zancen ya sa na janyoki muyi ba dan Allah mu rufe babinsa tunda duk munsan gaskiyan muna yiwa Hurera zagon k'asa tsawon shekaru kuma har yau bamuyi nasarar ganin bayanta ba." "Naji, ina sauraren dalilin janyoni k'uryan d'akinki ya ke jikan iblis." Dariya Hinde ta yi sai kace wacce aka ambatawa sunar arziki ta ce "Yaya matso ki ji abinda na shirya a game da zancen zuwar Malam gadin dukiyan Hurera." Da sauri Asabe ta kai kunninta daf da bakin Hinde, zuwa can suka shek'e da dariya tare da tafawa. "Hinde a gaskiya ke d'in shu'uma ce ta k'arshe." "Kiyi shiru kawai mu jira baiyanar sakamako wanda zamu kwashi rawar d'aga buje, muci kaji mu more a cikin dukiyar bulus, bamu tara ba amma munfi mai ita cin moriyarta." Wani shewan suka kuma sakawa har da daka tsalla tamkar yara. *** Iya gigicewa Aliyu ya yi ganin halin da Masoyiyarsa ke ciki tsakanin rayuwa da mutuwa. Sai kallon na'urar da ke nuna tana da rai ya keyi tamkar ya tafi ya latsashi ta dawo hayyacinta. Mama sai kallonsa ta keyi tana tantance natsuwarsa. 'Shi da Alhaji ko wa ye mijin uwata cikinsu oho?' Ta ambata cikin ranta. Kasa jurewa ya yi ya fice daga d'akin, ya zauna gefe ya dafe kansa, Salma tazo ta tsaya gefensa saboda itama lamarin ya tab'a ranta. Beebah ce ta matsa daf da shi wacce ta biyo bayansa ta ce "Duk halin da muke ciki kenan Aliyu, kayi hak'uri insha Allah zata dawo hayyacinta." "Allah ya amince hakan." "Amin." "Na yi ta kiran wayarta bai shiga naki kuma baki d'auka." "Wayarta ba asan inda ta ke ba nawa kuma na dakinta an kulle." "Ayya nima na sami k'aramin hatsari ne jiya da Rana." "Sannu Allah ya baka lafiya." "Amin." "Zan wuce." "Ok Agaida Hajiya" "Zataji." "Sister sai anjima." "To Allah ya kara musu lafiya." "Amin, mungode." Beebah ta dawo d'akin jikinta a sake saboda hango k'aunar Deejah mai tsanani a idanun Aliyu da ta yi. 'Allah ya baki lafiya Deejah.' Ta furta cikin ranta. Aunty Nafisa kam jikinta ne ya yi mugun sanyi dan ita sam bata kawo haka jikin ya yi tsanani ba, mugun nufinta kauda shi gefe ta yi ta ja kujera gefe da zauna tana nazarin rayuwa. Su Bintu ba su bar Asibitin ba sai bayan sallar magriba lokacin da Hajiya Inna ta zo. A hanya ba wanda ya yi magana hatta Aunty Nafisa ta kame bakinta. Sai da suka shigo layin gida sannan Beebah ta ce "Ita dai rayuwa wata aba ce mai ban mamaki yanzu ka ke mutum anjima ka zamo gawa dan haka mu aikata khairan domin bamusan aya mutuwa zata riskemu ba." "Zantukanki abar yin nazari ne sister, Allah ka sanya-ya mana zuciya." "Amin Fanta." Suka amsa Banda Aunty Nafisa da ta yi nisa cikin tunanin yarda zata raba mijinta da Deejah cikin ruwan sanyi. Uncle suka samu zaune a falo tare da yara wanda sukayi barci a saman jikinsa. Duk a falon suka zauna tare da gaisar da shi ya amsa cikin tambayarsu jikin Deejah. "Da sauk'i amma na musulinci." Fanta ta ambata cikin rawar murya. "Insha Allah zata tashi cikin lafiya." "Allah ya so hakan." Suka amsa masa. Siririn tsaki Nafisa ta ja suka kalleta sai kuma suka mik'e a tare suka bar falon. "D'auki yaran nan ki kaisu d'akinsu." Banza ta yi da shi ta mike ta haye sama. Girgiza kai ya yi yana jan Mata shiriya cikin ransa, yaran ya d'auka ya kai d'akinsu. Har ya kwanta ganin Aunty Nafisa ta shigo sai ya sauka ya fice d'akin da sauri ta biyosa amma kafin ta cinmasa ya fice falon baki daya. "Me hakan ke nufi? Abban Hafiz na nufin na zamemasa dodo kenan?" 'Ga alamu nan kin gani.' "Wallahi bai isa ba." Ta bawa zuciyarta amsa cikin fushi. Da takaicin ya isheta sai ta zube saman kujerar falo ta fashe da kuka mai sauti wanda har su Fanta na jiyota amma ba wanda ya yi yunk'urin fitowa. Uncle  kuwa ficewa daga gidan ya yi baki d'aya saboda baya muradin sauraren zantukan Nafisa wanda ke saka masa ciwon kai. Daga inda ya ke tsaye yana hango duk abin da ke faruwa a k'ofar gidan su Deejah. "Wallahi ina tausayin halin da kike ciki Khadijatu, Allah ya tashi kafadarki lafiya alfarman Manzon Allah S A.W." Ya furta a hankali. Wayar Dr. Jalal ya kira sun jima suna tattauna yarda jikin nata ya ke. Ya kashe wayar ya juya zai shiga gida yajiyo tsayawar mota waigowa ya yi samari biyu ya hango sun fito a cikin motar na d'aukan kaya wato mai budadden baya wacce ake kira da akori kura. Gidan su Deejah suka shiga ya ware ido yana mamakin daga inda suka zo. Kimanin mintoci biyar da shigarsu suka fito kowa d'auke da buhun waken suya a bayansa da alamu a kwai wanda ya d'ora musu aciki. Gyara tsayuwarsa ya yi cikin sake shiga mamaki, yana nan har suka gama zuba buhunan waken wanda suka cika motar taf. Ganin zasu tafi ya isa wurij da hanzari duk suka sakko suna kallonsa cikin alamun rashin gaskiya. Sallama ya yi musu suka amsa cikin muryan mashaya. "Wa ya turoko d'aukan kayan?" "Mamallakinsu." Suka amsa a tare cikin cijewa na 'yan daba. "Wa kenan?" "Mai gidan." "Baba ko Mama?" Nan fa sukayi shiru zuwa can dayansu ya amsa "Mama." "Ok kud'an bani mintoci biyu." "Muna sauri ne Malam bazamu iya jiranka ba." "Ok to zaku iya tafiya amma ba da kayan ba." "Yallab'ai me kake nufi?" Cigaba da danna wayarsa ya ke ta yi wanda tun soma yi musu magana ya fara. Kallon juna sukeyi sai suka koma saman motar tare da bawa driver umurnin tafiya. Yana kunna motar wata mota ta gyara parking a gabansa, kafin samarin su san abinyi 'yan sanda sun kamasu sun tura cikin motarsu har da drivern. Hannu Uncle Muhseen ya d'agawa 'yan sanda dan su tafi saboda ya sami wayar Dr. Jalal. "Kaiwa Mama please." "Ok ganima tare da ita nazo bata magani." "Had'ani da ita." "To gata." Gaisheta ya yi cikin girmamawa ta amsa itama cikin girma. "Mama kinyi magana ne azo a kwashe waken suyar da kika ajiye?" "A'a." "Ok to ya jikin naki?" "Alhamdulillah." "Na Khadijatu fa?" "To angode Allah dai." "Insha Allah muna tare da nasara." "To Alhaji, nagode sosai da kulawa." "Bakomi Mama masu iya magana sunce yiwa wani yiwa kai." "Haka ne, Allah ya rubuce." "Ami, sai da safe." "Allah ya tashemu lafiya." "Amin." Wayar Mama ta tsirawa ido. "Tabbas da abinda ke faruwa amma tunda ya nuna bai son fad'amin na barwa Allah lamarin, Allah yasa khairan ne." "Amin." Dr. Jalal ya amsa. "Likita wai me ye ma'anar wannan k'aran da wancan na'urar keyi wanda kika sanyawa Uwata?" "Shi ke nuna tana da rai." "Ikon Allah sai kallo." "Kuma idan kin lura da kyau zakiga tana sauke numfashi sai dai in ta yi d'aya tana d'aukan sekonni kafin ta k'ara amma duk ba matsala ba ne insha Allah zata tashi cikin k'oshin lafiya." "Allah ya nunamin wannan lokaci." "Amin." Shigowar Hajiya Inna ya bawa Dr. Jalal daman barin d'akin. K'aramin Qur'ani Hajiya Inna ta mik'awa Mama ta amsa tare da yi mata godiya. "Ya zamo shi ne abin yin bitarki Safe, Rana Dare domin duk kan waraka yana cikinsa, duk in kin idar da karatun kiyi tawassali da sunayen Allah d'ari ba d'aya ki rok'a mata sauki, insha Allah zakiga rahma na samuwa gareta tare da ke kanki." "Nagode Inna, wallahi kunyimin duk kan komi, bazan tab'a mantawa da ku ba cikin farihin rayuwata, Allah ya saka muku da gidan Aljanna." "Amin, kada ki samu ke d'iyarmu ce tamkar Habibu haka muka daukeki." Kuka Mama ta fashe da shi Hajiya Inna ta matsa ta dafa kanta ta soma tofa mata addu'a, rungumeta Mama ta yi ta cigaba da kukan wanda damuwar halin da Deejah ke cike ne jigon yinsa. Uncle Muhseen kam suna gama wayar ya kira wasu matasa suka maida waken ciki ya sallamesu ya koma gidansa ya d'auka kwad'o ya kulle gidan inda anan yaga wanda suka yanke da zarto. Tuno yarda sukayi da Baba yasa shi kiran number da ya amsa wurin Mama sai dai ya kira wayar nasa har sau biyar ba'a d'aga ba kallon agogon wayarsa ya yi yaga k'arfe Sha d'aya saura. "Dare ya yi dana tafi gidanka na sanarma da abin da ke faruwa amma insha Allah gobe da subahi zan isa masallacin da kake limanci muyi maganar dan bana son muna samun sab'ani a matsayinka na mahaifin wacce na ke burin ta zama uwar 'ya'yana nan gaba." Ya ambata cike da damuwa ganin dare na k'arayi sai ya koma gida cike da takaicin rashin aikinyin da ke jefe matasa cikin halin sace-sace gami da shaye-shaye. *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure.) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/31, 9:28 PM] 💘: DAMUWATA. (Sanin abin adona) By Mrsjmoon. E.W..F. Page 18. K'arar na'urar da ke nuna Deejah na da rai shi ne ya tashi su Mama barci a dai-dai lokacin kuma anata kiraye-kirayen sallar subahi. Dr. Jalal tare da Nurses ne suka shigo a hanzarce sakamakon jiyo k'aran na'urar. Fita su Mama sukayi suka tsaya bakin k'ofar cikin jan addu'o'i nasara. Bayan wucewar wani lokaci Doctor ya fito da sauri Mama ta sha gabansa murmushi ya sauke mata ya nuna mata d'akin da hannu. "Tafi ta ganki dan itama ke ta ke ta ambata." "Da gaske Likita?" "Eh Mama." Cikin rawar jiki Mama ta fad'a d'akin ta yi ido biyu da Deejah jingine da gado Nurse na wanke mata baki. Kulle ido na yi na bud'esu kan Mama wacce ke tsaye hawaye na bin kumatunta. "Mamana kina raye dama ban saraki ba?" "Alhamdulillah." Shi ne abinda Mama ta furta a maimakon bani amsa. "Gawa ta k'i rami ya jikin naki?" "Hajiya Inna taho taji d'uminku." Da sauri suka iso tare da rungumeni. Murna kam naganshi wurin Mama, ni kaina farin cikin da na samu kaina ciki na ganin Mama a raye ba mai misaltuwa ba ne. "Ina Baba Umaru?" Ta ambata saboda shi kawai na ke son sanyawa a ido. "Yana Jigawa." "Lafiya ko?" Mamata ta ambata cikin sauri idanunta zube kan Hajiya Inna. "Sai ya dawo muji saboda bayan na taho Habibu ke sanarmin sun tafi." "Allah yasa dai lafiya wannan irin tafiya cikin dare." "Amin." "Mama muma mutafi dan Allah naga Dattijon kirki wanda bakya gajiya da bani labarin karamcinsa gareki." "Uwata insha Allah kina warkewa zan shirya mana tafiya." "Da fatan har Sokoto zakuje?" "A'a Inna kowanne tafiyarsa daban zan shirya masa da yarda Allah." "Allah ya amince." "Amin." "Mama ki saka mana ranar zuwa dan Allah, ina son ga nina cikin dangi masu yawa, naje can gidan naje can." "Kin ganki Takwara da salo tamkar abin da kike ambata zaki iya aikatawa, ke da kike kifin rijiya sam ba kya son jama'a." "Allah Hajiya Inna ina son ganina cikin dangi irin masu yawan nan." "Uwata bari in had'o miki tea ki Sha." Mama ta kauda maganar. "To amma wanda na ke son yi jikina duk ciwo keyimin." "Ai kam dole ki jiki ba dai-dai ba, kwanaki biyu a kwance ba motsi dole gab'b'ai su amsa." "Hajiya Inna wai dogon suma na yi ko me?" "Eh fa, irin wanda ke kama, coma inji turawa." Shiru na yi ina tuno kalaman da suka shigo kunnuwana lokacin. "Uwata sannu kinji? Allah kada ya k'ara nuna mana irin wannan lamari." "Amin Mamana." "Hajiya Likita ya ce abata abu mai d'umi sai ta sha magani kada abarta ta yi tafiya ita d'aya saboda jikinta ba kwari." "To nurse zamu kiyaye." "Nikam wanka na ke sonyi in rama sallolin da ke kaina." "Ki bari ki warware ai ya shigo babin lalura Takwara." "Hajiya Inna to a barni inyi wanka na sanja tufafi." "Anfa samu lafiya kenan agwa-gwa sarkin wanka." Murmushi na yi tare da komawa na kwanta. Duk yarda su Mama suka so nasha tea na kafe sai na yi wanka. "To ki jira gari ya gama wayewa sai su Fanta su d'auko miki kayan da zaki sanja." "To zanyi fitsari." "Sakko na rik'eki Uwata." "A'a yi zamanki Hurera, ke da baki da k'oshin lafiya." "Hajiya Inna ce ta rakani, ina jin fitarta na tub'e kayan jikina na hau watsa ruwan sanyi, ba sabulu na yibta tirje jikina dukbda jirin da na ke gani haka kan na dafa bango ya kammala wankan na d'auro zani na fito sumata na d'igan ruwa, baki suka bud'e ganin wayon da na yi musu. "Uwata halinki sai ke, narasa inda kika samo wannan tsafta." "Wurin Kawu Habibu." "Aikam sai wurin d'an ka iya." "Zanyi sallah Mama." "To cire ganin jikinki ga wankakke da Hijab." Sanjawa na yi na hau sallaya saidai nakasa tsayuwa sakamakon rawar sanyin da na ke yi. Ai kam Hajiya Inna ta balbaleni da fad'a tamkar zata ari baki ya yin da Mama ta ruga kiran Likita. Kafin likita ya iso Hajiya Inna ta cic-cib'eni ta d'ora a gado ta rufeni da bargo tana ta tofamin addu'a sai duk suka bani tausayi na soma nadamar yin wanka da ruwan sanyin. Ina jin Likita ya shigo ya dubani tare da yimin allura wanda ban jima ba na mance abinda ke faruwa sakamakon barcin da ya d'auke ni. *** Kamar yarda Uncle ya k'udurta yana idar da sallah ya nufi masallacin  da Baba ke bada sallah. Na'ibinsa ya samu bayan sun gaisa ya tambayesa Baba ya sanar masa baizo sallah ba, cike da mamaki ya juya sai ya tsinkayi muryan Na'ibin. "Amma ga babban d'ansa nan ka sanar masa da sak'on insha Allah zai isar zuwa ga reshi." Kallon wanda aka kira babban d'an Baba ya yi a ta ke ya aminta saboda kamannin da ya gani. "Biyoni." Abinda Uncle ya furta kenan tare da yin gaba. "Bishi Auwalu kaji da abinda yazo." "To Baba." Uncle Bai sanar da Auwalu komi ba har saida suka iso k'ofar gidan su Deejah sannan ya dakata ya kalle shi a natse ya labarta masa abin da ke faruwa. "Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un." Auwalu ya ambata cikin sanyin murya wanda ya ja hankalin Uncle har ya zuba masa ido yana mamakin sanyinsa tamkar ba jinin Baba mai zafi ba. 'Tabbas su Kamalu ne da wannan aikin bisa hud'ubar su Inna, da gaske kenan Baba ya sha furan mai maganin barci? In ko haka ne Innar su Anas bata kyautawa Baba ba.' "Malam Auwalu tunda kaine magajin Baba zuwa anjima kazo muje police station d'in ka gansu tare da bayanin dalilin zuwarsu yin sata." "Alhaji Baba yana cikin gidan nan, maganin mura ya sha barci mai nauyi na daukesa shi ne suka sami nasarar aikata satan." Ya ambaci haka saboda kunyar tonawa Matar Babansa asiri. "Me ye hujarka?" "Jiya da dare ni na kawosa gida kuma ya sanarmin zaisha maganin mura." "Ok bari mu dubashi." Suna shiga da Baba sukayi arba zaune saman buzu ganinsu yasa shi sallame lazimin ya nuna Auwalu da yatsa "Uban wa kabarwa tsaron tsangayar?" "Antashi lafiya Baba?" "Ban sani ba, amsamin tambayata kafin gaisuwa ya biyo baya." "Baba Na'ibi zai kula da su." "To lafiyalau, me kazo yi?" "Alhaji zai sanarma, nabarka lafiya, Alhaji sai wani lokacin." "To Malam Auwalu ga wanna ka hau abin hawa." "Hannu ya mik'a ya amshi kudin tare da yin godiya, suna had'a ido da Baba ya girgiza masa kai tare da cije leb'en k'asa, murmushi ya yi kawai ya fice yana tir da halin mayintar kud'i irin na Baba. "Halin Baba sai shi, sam ba'a yiwa mutum kyauta ya kauda idonsa a kai." Ya furta a hankali. "Alhaji me ke faruwa?" Gyarar murya Uncle ya yi sannan ya jero masa duk abinda ya faru. "Wallahi saina shukawa Hinde rashin mutunci saboda ita ta bani fura mai kayan maye na yi ta shek'a barci wanda ya janyomin asarar sallah cikin Jam'i, ga shi har b'arayi sun shigomin gidan iyali." "Baba ko dai maganin muran da ka sha ne ya haifar da nauyin barcin?" "Uban wa ya sanarma na sha maganin mura?" "Auwalu ne." "Oh yanzu na gane daga inda iskanci ya fito wato shima ya lalace kenan shi yasa ya siyamin lemu ya zuba kwayoyi shi ne zai ce maka ina mura to billahil azim sai na... "A'a Baba banda saurin rantsuwa a matsayinka na shugaba kuma jagorar dubannin al'umma." "Allah ya yi maka albarka Abdul Muhseen dan ka tunasar dani kiyaye harshena." "Amin Baba." "Yanzu zamu tafi naga shegun ne ko ya?" "Sai zuwa hantsi zamuje, insha Allah." "To amma ka sanar da a sanja musu kamannin ko?" "Eh, dan yanzu haka ance sun sanar da wanda suka turosu, kafin mu isa za'a kamosu." "Yawwa hakan ya kamata a had'asu a ci k'aniyarsu yarda gaba ko sunar b'arawo aka kira zasu bar wurin a guje." Murmushi Uncle ya yi yana k'ara yabawa fitinar Baba. Bayan tafiyar Uncle Baba ya nufi kitchen yana surutai zuwa can kuna ya soma yabon Mama. "Allah ya biyaki da khairan Hurera da kina nan sai abinda na so ci zaki dafamin, ina ci ina tura mikin masifa amma bazaki d'aga kai ba saboda sanin darajar aure, shi yasa duk rintsi ba zan rabu da ke ba sai na binne gawarki da hannayena biyu kafin nan tuni Uwani ta dad'e da zama yar gari a barzahu domin wannan sumar batashi zatayi ba." Shi kad'ai ya yi ta zuba surutu har ya samu ya gama soya kwai tare dadafa ruwan zafi ya had'a tea mai kauri ya tafi ya kulle k'ofar gida ya dawo ya zauna saman buzunsa ya korawa hakali kwance. "A she ban manta rayuwar almajiranci ba inda muke satar kwan kajin Malam dana makwafta mu tafi bayan gari mu d'iba girki mai rai da lafiya. Ya Allah ka yafe mana laifukanmu domin munyi cuta iya cuta na cinyewa kaji kwai da zabbi." Sai ya kwashe da dariya. Yana kammala shan tea ya kulle gidan ya nufo gidansa cike da tarin masifa, duk wanda ya gaisar da shi hannu kawai ya ke d'aga masa sai in anyi masa sallama ne ke amsawa saboda sanin muhimmancinta. Kafin ya isa gida Uncle ya kirasa ya sanar masa da farfad'owar Deejah wani burki ya ja ya yi dif, Uncle ganin kamar da matsalar network sakamakon jin shiru ba amsa sai ya datse kiran da nufin anjima zai sake kiransa. "Wanna d'iya anyi mai taurin ran tsiya, bari in hanzarta zuwa Asibitin kada Hurera ta mannamin hauka ta ce ina farin ciki da ciwon ne dan na hango abin da ta ke burin ambata kenan gaban jama'a." Ya tari mai Napep tare da sanar masa da inda zaije. Ana Napep d'in sai tsaki ya ke ja. *** Aliyu. "Aliyu ka natsu ka san inda kanka ke ciwo." "To Hajiya na ce zan duba buk'tarki." "Bana son ka duba Aliyu, burina ka tafi zance gidansu saboda ita mai sonka ne da gaskiya domin da bakinta ta furta tana son ka aureta." "Hajiya ina da fa wanda na ke so." "Wacece ita?" "Khadija." "Wacce Khadija?" "Wacce mukayi walimar haddar Qur'ani da ita." "Oh jikan Alhaji Umaru surikin Zainab?" "Au Hajiya a she kin san Khadija na da alak'a da su Yaya Habibu?" "Sosai kuwa domin lamarin aurensa da Mamanta akayi mace mai karamci." "Shi kenan fad'uwa tazo dai-dai da zama." "A'a bata zo ba saboda gida bai k'oshi ba'a kai dawa ba sannan ka tuna Amira k'anwar Zainab ce ta jini dan haka batun Khadija babu shi kaji dai na gaya maka." "Hajiya dan Allah ki... "Zancen kake so Aliyu." Tana ambatar haka ta bar mishi wurin. "Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un, wallahi ina son Khadija DAMUWATA duk na mallaki Khadija ce, ya Allah ka kawomin mafita cikin sauk'i." "Amin Yaya." "Salma kina jinmu da Hajiya ko?" "Eh Yaya amma ina baka shawara da ka nuna tamkar ka amince amma a wurin Amira ka sanar mata da gaskiyan zuciyarka insha Allah zata fahimta tunda nasan tasha jin labarin illar auren mijin da bai son mace." "Nagode k'anwata." "Bakomi damuwarka tawa ce Yaya." "Anjima zan lek'a Asibiti." "Zan bika." "Islamiya zaki sarkin yawo." "Kai Yaya ziyarar maralafiya zani ba yawo ba." "Baza ki je ba." "To shi kenan ranar alhamis na je." "Yawwa na amince da wannan kam." "Yaya Deejah na da kyau tamkar shuwa ko 'yar k'asar turawa." "Tubarkallah Masha Allah." Dariya Salma ta kyal-kyale da shi, ya murmusa tare da ficewa. Gyara d'akin ta soma yi tana 'yan wak'e-wak'enta cike da nishad'i. *** Hinde wai lafiya kuwa su Kamalu shiru basu dawo ba?" "Nima zancen da zanyi miki kenan Yaya." "Kada fa mafarkina na jiya ya tabbata." "Na me fa?" "Wai gini ya fad'o ya halaka su Kamalu, aka kawo mana su cikin jini tare da rakiyar 'yan sanda." "Innalillahi, aiko da wuya ba an kamasu ba ne domin tun daren jiya gabana ke fad'uwa, wallahi cike na ke da fargaba kada asirinmu ya tonu abin da bamu samuba ya tabbata wato amsar takardan saki. "Haba Hinde wai me yasa duk zantukanki ba na arziki ne ciki? To wallahi mugun bakinki ya k'are a kanki." "Yaya wallahi ina jiyowa a jikina ba nasara a wannan tafiyar nasu." "Bazan gani ba, mai bakin baki kawai." "To shi kenan Yaya na yi shiru." "Shi dai yafi." Suka cigaba da aiyukansu na safe duk jikinsu a sanyaye. "Hinde wai in tambayeki, da wa Kamalu suka tafi?" "Kinsan Anas bai da lafiya shi ne K'asimu ya ce zai bishi sai shima Garba ya ce zaije naso hanashi amma ya kafe sai ya je, Kamalu ya cemin zai d'auki Isyaku Jagwa tunda yana da motar d'aukan kayan sai su loda a ciki." Wani ihu Asabe ta kwalla wanda saida Hinde ta zabura. Wani mugun ashariya ta watsowa Hinde tare ta cukumeta, suka soka kokuwa fad'i Asabe keyi "Kin kasheni da raina Hinde, duka 'ya'yana kika tura yo sata, wallahi mai rabani da ke sai Allah." "Usaman (k'anin Baba) da matarsa suka zo rabo. Suka saki juna suna huci tamkar zakaru. "Me ye haka kukeyi dan Allah, haba Innar Kamalu da Innar Anas, kunfa girma, kuna da surukai amma baku daina d'abi'an yara ba, to wallahi wannan abin Yaya kuke zubdawa da mutunci ba kowa ba a matsayinsa na babban Malami a garin nan." "Usman wallahi wani abu ya sami 'ya'yana sai naga bayan Hinde koda zan tafi tsirara ne." "Zakuwa ki tafi tsirara domin inda kika kwana na wuce da tafiya mai nisa" "Haka kika ce?" "Hak'k'un domin nasan da b'acin ranar nan na turasu kinga na rama lak'awa Kabiru satan kwan kajinki da kikayi shekaru goma da ya wuce inda kika janyo Malam ya illata masa kunni d'aya ya zamo baijin magana da shi." "Tana nan dama kika b'ullo min Hinde?" "Eh, dan ki sani yanzu raina tangaran." Wani duka Asabe ta kaiwa bakin Hinde ta ke leb'enta ya fashe. Cikin gigita ta rarimi murfin tukunya ta wurgo mata ya sauka a gyeyar Usman wanda ya nemi janye Asabe. Ihu ya kwalla ya zube k'asa dafe da wurin, kuru-ruwa Matar ta sanya tayo kan Hinde suka rintsab'e da dambe. "Innarmu! Ga 'yan sanda nan cikin mota tare da K'asimu fuskanci duk ta kumbura." Atiku yaron Hinde ya shigo a guje yana fad'a. Tamkar walk'iya haka Usman da Matarsa Mairo suka b'ace zuwa sashinsu ya yin da Hinde ta ruga d'akinta Asabe ta biyota ganin haka ta tureta da k'arfi ta fad'i k'asa ta kulle k'ofar da sakata. Asabe ta mik'e cikin zundumawa Hinde zagi, ta nufi kofarta sai dai tana  saka k'afarta a d'akin ta tsinkayi muryan K'asimu na cewa "Ga d'aya can." Da sauri ta waiwayo ta yi arba da macen 'yar sanda, K'asimu d'aure cikin ankwa. Cikin zafin nama tayo kan 'yar sandan ta cukumeta da dambe bisa tsautsayi tAsabe ta ture 'yar sandan da k'arfi sai ko ta zame ta yi cikin rijiya wanda ke tsakar gidan. Sautin ihunta tare da ba  fad'awarta ya janyo hankalin 'yan sandan da ke waje suka shigo a guje, Hinde da su Usman suma suka fito suna rafka salati jin abin da K'asimu ke ambata cewa Innarshi ta jefo 'yar sanda a rijiya. *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [11/1, 9:32 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Mrsjmoon E.W.F. https://youtu.be/v9iNYDvS8JM Pls 'yan uwa ku dannamin subcribe a YouTube d'ina. Page 19. Sadda na farka jikina ya yi k'arfi sosai sai dai yarda na hango idanun Mama sai na saka kuka dan sun kumbura suntum, damuwa ne kwance saman fuskanta abin da ya taimaka wurin karyarmin da zuciya. Jin kukana Hajiya Inna ta somamin fad'a, tsit na yi ina sauraren sababinta mai kama da na Baba saidai ita nata akan gaskiya ne sab'anin na Baba. "Inna kiyi hak'uri." "Bazanyi ba Hurera, shin abin da ya kamata ta yi kenan ko godiya ga Allah?" "Hajiya Inna to na yi shiru dama Mama ce na hango cikin damuwa sai kuka yazomin." "Duk shiri-ritanku iri d'aya, abu ba abu ba kuyi ta b'aran baki tamkar saunoni." Murmushi na yi ta dunguremin kai, na kama yatsar zan tura a baki ta fizge tana dariya "Mamana." Na kira sunar cikin rauni ta taho a hankali ta kama hannuna kafin ta yi magana aka turo k'ofar Uncle ne da su Fanta suka shiga cike da farin ciki dan ko samun damar gaisar su Mama basuyi ba suka nufoni kowa na son isa inda ni ke. Hak'ik'a farin cikin da suka nuna na ganin samuwar lafiyana yafi gaban kwatance Mama sai sanya musu albarka ta ke yi bakinta har kunne Hajiya Inna kam fatar samun mazaje na gari ta yi musu, shi kuwa Uncle addu'ar da sukeyi masa na daban ne. Sun sakani a tsakiya sai tsokanata sukeyi kamar yarda suka saba, duk rashin son maganarta yau kam na biye musu sai doka murmushi na ke yi cikin bawa kowacce amsa a hankali saboda yanayin k'arfiin jikina, lamarin da ya sake jefa Mama cikin farin ciki kenan domin ina hango motsa kai da ta ke yi cike da nishad'i. Uncle na tsaye gefe daga bakin k'ofa Dr. Jalal na yi masa k'arin bayani game da lafiyar Deejah. Saurarensa kawai ya keyi ba tare da yana fahimtarsa ba saboda hankalinsa na kan masoyiyarsa shima sai murmushin ya ke dokawa yana jin natsuwa na daban na kuma nashe ruhinsa. 'Ina son yariyarnan matuk'ar so, ya Allah ka mallamin ita idan har hakan alkhairi ne.' "Yaya inaga ka taho muje office zakafi fahimtar zantukana." Kallon Dr. Jalal ya yi sai kunya ta kamashi ya wuce gaba da sauri Dr. Jalal ya sanya dariya mara sauti ya nufi wurin Deejah ya yi k'asa da murya ya ce "Ki rik'esa amana wallahi yana sonki da gaskiya." Juya kai gefe na yi saboda zancen ya bani kunya. "Dan Allah kubarta ta huta haka nan aminanta." Dr. Jalal ya furta cikin sigan wasa. Dariya suka sanya ya fice yana murmushi bayan ya saukewa Fanta kallo na daban wanda faruwar hakan yasa ta rakashi da ido baki bud'e. "Da magana a cikin kallon nan kenan ko sister." Da sauri ta maida dubanta kan Safina. "Eh da magana kam domin na hango k'auna a cikinsa." "Kinga sister bana son kwashe-kwashe." "Likitan ne kwashe-kwashe?" "Ban sani ba." "Aikam dole ki sani K'awata." Na ambata cikin dariya ganin yarda ta tsare gira. "Deejah har da ke ko?" "A'a fa kawai dai naga ya kamata ki sani ne duk da ni fadar Abdul Abbas na ke." Mik'ewa ta yi Bintu ta janyo hannunta ta koma zaune. "Kinga idan kina sonshi ki bada kai muna bayanki saboda wannan gayen samunsa sai mai sa'a." "Ban son shi, shi kenan zaku bar kunnuwana su huta?" "Eh amma sai na sanar da Uncle kin kamu da son k'aninsa." "Wa kenan?" "Sa'ad." Kama baki ta yi cikin ambatar Innalillahi. Aikam na fashe da dariya mai sauti, su Bintu na tayani. "Kinga k'awata ki daina dariyar nan domin baiyi miki kyau ba, gara kiyi murmushin da kika saba." "Alamun samun natsuwar ruhi kenan Fanta " Beebah ta ambata hankalinta na kan wayarta domin ko murmushi batayi ba tun soma hirarmu. "Wai ita nan zata layance ne ta kori zancen Sa'ad." Fad'in Safina ckin dariya. "Ai sai kiyi ta yi tunda kin sami karatun sallah." "Kinga malama bamu san gulma, ko ba maganarsa kika ishemu da shi jiya ba, to zamuce Uncle ya had'a zumunci, hakan ya yi miki ko?" Cewar Fiddausi. "Wallahi zan kai k'ararku wurin Uncle in baku daina yimin sharri ba." "Ya isa haka, kun cika mana kunne da hayaniya alhalin ance mu bar Deejah ta huta." "K'yalesu Sister Beebah, lamarin na bani nishad'i ainun." "To nikam sun dameni." "Munyi shiru Babban Yaya." Fiddausi ta ambata cikin murgud'a baki. Beebah ta kawoma bakin duka ta sunkuya, suka sanya dariya. Shigowar Baba yasa duk suka natsu saboda sun sanshi yanzu sai ya korasu waje. Suna gaisar da shi ko kallo basu ishe shi ba, ya buga babban rigarsa ya nuna Mama da yatsa cikin tijararsa na fama ya ce "Hurera in na isa da ke ki tashi yanzu mu tafi gida tunda kun sami lafiya kuma in Allah ya so ba mai sake zuwa wannan matsiyacin asibitin ko da ciwon mutuwa ne ya kamaku gara ku mace ina kallonku da dai zuwa shegen Asubiti nan mai kama da na yahudawa." "To ta Allah ba takaba ciwo da mutuwa na kan kowa kuma Asibitina ba matsiyaci ba ne balle ya zama na kafurci saidai kai ne matsiyacin, fitinannen mutum kawai, Malamin bai kaiba, wanda baisan darajar iyalinsa ba, zalaman kawai ya ajiye, mai fuska biyu kawai. Wallahi ba dan Yaya Muhseen ba da banga wanda ya isa yasa ka sake shigomin Asibiti ba." "Jalal ban isa da kai ba ko? Shin ba na ce kada ka sake magana ba?" "Kayi hak'uri Yaya amma wallahi wannan makwafcin naka ba dan arziki ba ne saboda na gano yana da sa hannun a ciwon matarsa har da 'yarsa, shi ne ke son kashesu lokacinsu baiyi ba." "K'alu innalillahi wa Inna ilaihin raji'un! Ni Malam Hadi zakayiwa kazafi Likitan fanko? To wallahi bani yarda sai na d'au mataki ba dai tak'amarka jama'ar da sukeyima tururuwa ba to sai ka koma kare bai... "Dan soyayyarka da Ma'aikin Allah Baba kada tayi masa baki, shi d'in mai taimakon al'umma ne." Na furta cikin kuka. Kallona ya yi sai naga ya tako ya iso daf da ni cikin cewa "Uwani ke ce haka cikin k'oshin lafiya, murya ras?" "Eh, Baba." "To madallah, sannu fa, kin tsallake rijiya da baya domin irin wannan ba'a cika tashi da lafiya ras irin haka ba." "Ita dai sumul ta tashi soi fatan samun kwarin jiki wanda shima zuwa anjima zata koma tamkar taba tab'a kwanciya ciwo ba." "To Hurera da fatan kema kin gama warwarewa?" "Alhamdulillah ala kulli halin." "Da kyau." Kowa sai kallon Baba ya keyi tamkar ba shi ne ke fesawa Doctor Jalal ruwan bala'i ba, ya koma kamar wanda junnu suka shafa yana masifa lokaci d'aya ya koma maganar arziki. "Baba kayi hak'uri yarinta ce ke damun Dr. Jalal kuma bai san alak'arka marasa lafiyan ba sai yanzu amma da duk haka bata faru ba, dan Allah ya ci albarkacina ka mance lamarin ya zamo tamkar bai tab'a faruwa ba." Uncle ya katse shirun da rarrashin Baba. "Alhaji Muhseen ban sanka da k'arya ba amma sai gashi yau kana yimin ba kunya balle tsoron gamuwarka da mahaliccinka, yaron nan ne baisan alak'ata sa iyalina? Sai dai ka fad'awa yaron goye amma ba Abdul Hadi ba mai hak'ora talatin da biyu cik." Wani kunya ne ya kama Uncle ganin yarda kallo ya dawo kansa sai kawai ya juya ya fice batare da ya sake furta kalma ba. "Amma kai ba mutumin arziki ba ne, to ka sani hukuma ce zata rabani da kai ba dai haka ka ambata cewa kare ba zan sake gani a cikin Asibitina ba, ni kuma zan nuna maka ni d'in jinin malamai ne kuma wanzamai masu tutuniya da yardan Allah ba bokanci da buge-buge k'asa ba, ni Abdul Jalal sai na baka mamakin da duk wani bil'adam bai tab'a baka shi ba tsawon rayuwarka, mu zuba mugani shege ka fasa." Dr. Jalal na gama ambatar haka ya fice a fusace. D'akin ya Kuma yin tsit baka jin motsin komi sai sautin kukana saboda lamarin ya b'atamin rai ainun. "Ka kyauta Hadi sai ka tafi tunda abinda kazoyi ka gama." Kallon Hajiya Inna ya yi wacce ke zaune gefe d'aya a saman sallaya, sai ga Baba ya sunkuyar da kai domin sam bai lura da ita ba saida ta yi magana. "Ayi hak'uri Hajiya wallahi rai na ne ya b'aci na ganin da girmana da komi masu gad'i sun hanani shigowa duba iyalina har saida na kira Alhaji Muhseen sannan suka barni na shigo sai ga wannan yaron ya tareni da zantukan banza har da zagi tare da mannamin k'azafin iska da wofi." "Ko me ya yi maka kaika siyo da kudinka Hadi." "To Hajiya ayi hak'uri dai." "Ni bakayimin laifi ba amma dai zan baka shawara agame da wannan halin naka wallahi ka kiyayi furta kalamai marasa dad'i a duk yarda suka zo maka domin in kasan wani baka san wani ba sannan ik'irarinka na alkaba'i ka bari ko masifun da kake ambatawa mutane ya koma kanka." "Insha Allah zan kiyaye." "Allah yasa mudace." "Amin." "Takwarana daina kukan nan kada kanki ya yi ciwo, kinba ba gama samuwa kikayi ba." Sakkowa na yi zuwa gaban Hajiya Inna na russuna kafin in furta kalma ta janyoni zuwa jikinta ta kai bakinta kunnina tana mai cewa "Kada ki furta komi ni ne maganin Babanki ki zuba ido kiyi kallo domin na fahimci shi d'in zuma ne shansa saida wuta." Motsa kai na yi, ta d'ago fuskata ta soma sharemin hawaye wanda tana sharewa wasu na biyowa. Uncle ne ya dawo ya sanar da ansallameni, su Beebah suka soma tattara kayanmu, Baba na tsaye yana kallosu takaicin Dr. Jalal da Hajiya Inna cike da ransa domin nasihar da Hajiya Inna ta yi masa ya d'aukeshi cin fuska ne ba komi ba, kawai ya bada kai ne saboda girmanta da ya ke gani. Uncle na kalla na langab'e kai ya kirani da hannu batare da kowa ya lura ba, ya fice waje na rufa masa baya ina jin kaina tamkar zai rabe biyu. "Khadija ina rokonki da kizo muje ki bawa Dr. Jalal hak'uri saboda in har ya sakawa Baba ido lamarin bazaiyi kyau ba dan nasan wayeshi akan 'yancinsa sannan yana da k'anin Baba wanda in ya kai sunar Baba wurinsa abin sai addu'a kawai zance." "Dama abinda na ke son in aikata kenan Uncle, kaini na rok'eshi domin bana son Baba ya sami matsala ta sanadin zuwarmu Asibitin nan." "Ok kinyi tunani mai kyau Iyalina." Kauda fuska na yi saboda bana cikin good mood d'in da zanyi masa murmushi wanda na fahimci shi ya ke son gani. Yana gaba ina binsa a hankali saboda jiri da na ke gani, muna shiga office d'in na jingina da bango sakamakon jin da na yi zan fad'i, ido na ke son bud'ewa amma sai naji sunyi min nauyi sai na hak'ura na sake rintsesu, na mik'o hannu naji an kama, Dr. Jalal na ambatar sunana a hankali saidai na kasa amsawa saboda nauyin da harshena ya yi tamkar yarda idanuna sukayi. Daga nan ban sake sanin ya akayi ba nadai farka ne na ganni kwance saman gado, d'akin ba haske sosai amma na hango Hajiya Inna zaune saman sallaya. Salati na soma yi da k'arfi na jiyo muryan Mama na kiran sunana sai dai a dushe ya ke muryan nata wanda ya tabbatarmin da kuka ne ya haifar da hakan. "Sannu Uwata, Allah dai yasa kafface, sannu kinji, jarabawar rayuwa ce ta zo mana da sauyi mai firgitarwa." "Yawwa Mamana, zansha ruwa." Hajiya Inna ce ta kamani na tashi zaune, Mama ta bani ruwa nasha mai yawa na koma na kwanta ina ambaton sunar Allah Al-hamidu a cikin raina domin shi ne kad'ai ya can-canci a gode masa a dukkan halin da mumuni ya riski kansa ciki. Cikin daren Dr. Jalal ya dubani sosai bayan ya matsamin saida na sha tea, ina gamawa ya kama hannuna na kalle shi ya motsa kai cikin cewa "Khadija rayuwarki tamkar rayuwar mutane masu yaww like Mama, Yaya Muhseen, su Hajiya Inna da ma k'awayenki su Fanta tare da al'uman Annabi irinmu masu tausayin halin da kika sami kanki ciki na rashin lafiyar jiki d'an haka na ke baki shawara da ki jajirce wurin kauda damuwa a zuciyarki, ke malama ce kin san kalolin addu'o'i na tafiyar da duk kan damuwar jiki da ruhi, to ki sanya su zamo aminan zuciyarki wurin tuno da su ta hanyar ambatarsu, kada ki sake bari damuwa ya kwantar da ke akaro na uku domin banjin zaki tashi da lafiyar tunani ba ko na jiki. Dan Allah da Manzon Allah ki bamu hadin kai aikinmu ya sami nasara, lafiya ya wadaci jiki da ruhunki baki d'aya." "Insha Allah Doctor zanyi bakin iyawata na ganin damuwa bai yiwa rayuwata illa ba." "Masha Allah, ina rok'on sauk'i a gareki dama duk kan masu fama da rashin lafiya." "Amin. Nagode." "Ki kwanta ki huta kinji?" "Insha Allah." Bayan fitarsa Hajiya Inna ta zo ta zauna saman kujera ta dubi Mama dake manne da ni ta ce "Hurera ku kwanta ku huta dan kema ba lafiyar ce ta isheki ba." Ba musu Mama ta kwanta gefena sai na kwanto rabin jikina a saman nata na lumshe ido ina mik'a godiya ga Allah da ya bani mahaifiya irin Mama mai damuwa da dukkan DAMUWATA. Karatun Qur'ani Hajiya Inna ta soma cikin harshen karatun zaure saboda shi ta iya, na yi tsam ina saurarenta domin naji dadinsa har ina burin iyashi, natsuwar huri ya wadacemu baki d'aya barci ya daukemu batare da mun sani ba. Hak'ik'a samun ilimim addani musanman na Alqur'ani babban falala ce, gashi haske ne ga dukkanin duhu. *** Baba gidan ya koma cike da fushin yarda Mama tak'i yi masa magana tunda ta kulashi sau d'aya bata sake nuna tana wurin ba wannan abu da ta yi ya k'ona masa rai. Wanka ya yi da ruwan sanyi saboda ranar da ya kwaso tare da tiri-rin da zuciyarsa keyi masa. A baranda ya zauna yana bincikensa, sai tsaki ya ke ta dokawa saboda ya kasa gane komi, zuwa can ya ture mazubin k'asar gefe ya zabga tagumi. K'arar da wayarsa ta yi ne ya katse masa tunani ya d'auka da hanzari ganin sunar Babban yaronsa Auwalu ya bayyana. Sallamarsa ya amsa bai tsaya amsa gaisuwarsa ba ya  rufeshi da fad'a akan kiransa da ya yi. "Kayi hak'uri Baba matsala ce babban yasa dole sai na kiraka." "Me ye shi?" "Innar su Kamalu da Innar su Anas na wurin 'yan sanda." Tsaye Baba ya mik'e yana cewa "Me! suka janyowa kansu ni Hadi?" "Wallahi Baba ban san ainihin  abinda ya faru ba amma dai Baba Usman ya sanarmin wai Innar su Kamalu ce ta jefa 'yar sanda a rijiya daga tazo da K'asimu cikin ankwa." "Innalillahi! Yau na shiga uku da wad'an nan matan jaraba, to yanzu anciro 'yar sandan ko kuwa?" "Eh ancirota amma da wuya ta rayu saboda ance bata motsi yanzu dai an wuce da ita Asibiti dan a tabbatar da rayuwarta." "Kai kana ina ne yanzu?" "Ina bawa d'alibai karatu." "To ka sallamesu ka tafi ofishin 'yan sanda idan an tamabayeka inda na ke ka ce na yi tafiya yau da subahi ban san komi akai ba saboda ba a gidan na kwana ba." Jim Auwalu ya yi amma tsawar da Baba ya daka masa sai ya amsa jikinsa na rawa. Ka she kiran ya yi yana share gumi. "Amma anyi shegun nata masu janyomin bala'i ina zaman lafiyana, wallahi ba mai kaini belinsu, su da suka janyo masifar ya k'are akansu, yanzu bari in nemi Alhaji Muhseen muje wurin 'yan banzan yaran can a zabgawa iyayensu tara na samu na sakawa a aljihu domin walalhi cewa zanyi sun kwashe rabin waken sun siyar sun dawo kwashe sauran ne Allah ya toni asirinsu aka kamasu kuma sai anbiya ninkin kud'in, duk buhu d'aya a sittin da biyu zai tashi na ce buhu ashirin da biyar suka sace, iyayensu sayi maganin shed'ancinsu domin sunji a jikinsu." Murmushi ya yi jiyo k'amshin zuwar kud'ad'e a bulus. Cikin gaggawa ya shirya ya fito yana sab'a babban riga ya doshi gidan Uncle dan ya tabbatar zuwa yanzu ya baro Asibitin. Mai gadi ya aika ba jimawa sai Uncle ya fito cikin shigar kamala sai k'amshi ya ke bugawa. gaisar da shi Uncle ya yi amkar wani abu mara dad'i bai faru ba. Suna tafiya cikin mota Baba na sanar da shi yarda yatsara za'a amsa wurin iyayen yaran shi dai Uncle baice uffanba saboda ya san darace zataci gida domin tuni ya sami labarin 'ya'yan Baba ne b'arayin. Suna isa 'yan sanda suka kewaye Baba zasuyi masa tijara, Uncle ne ya yi musu magana tare da tunasar da su girman rawanin da ke kansa. Baba kam sai zare ido ya ke yi jin abin da 'yan sandan ke fad'a. ' Yanzu b'arayin nan ashe su Kamalu ne? Iyayensu suka turo su? Kenan na shigo hannu duk boren danayi bazanyi asarar kud'i ba a she sai na yi dai, kai anyi sokayen mata marasa sanin ciwon kai, inbanda b'atan basira ta ya zasu shigo sata gidan Hurera, gidan da akayi saukan Alqur'ani mai girma cikinsa, to wallahi zanyi belin ku amma zan baku mamaki matuk'ar mamaki, zaku san kun zubdamin da martaba.' "Baba muje ciki." Ya tsinkayi muryan Uncle daf da shi wanda ya taimaka wurin katse masa zantukan zuccin da ya ke yi. Wani kallo ya saukewa Uncle tare da girgiza kai. 'Kome ya faru kai ne sanadi da baka kira masu babbak'un kaya ba da banga zubewar mutunci ba, wallahi ni kad'ai nasan tsiyar da zan shuka maka.' "Baba ka natsu ba wanda ya isa ya kulleka tunda ina wurin kuma belin matarka zanyi shi insha Allah tunda anyi sa'a 'yar sanda da ta jefa rijiya bata mutu ba haka bataji babban ciwo ba balle buguwa mai wuyar magani firgicin ne ya sanyata dogon suma amma yaran sai sunje gidan yari domin gaba suji tsoron aikata sata." "Nagode Alhaji." Abinda Baba ya iya ambata kenan shima jin ba shi ne zai kashe kud'in belinsu Asabe ba amma ba dan ya daina jin haushin Uncle ba Duk wani kace na ce Uncle ne ya shige gaba har aka basu belin su Hinde wanda suka sha dukan tsiya fuskansu dik ya bumbure sakamakon sanadin jefa 'yar sanda rijiya da Asabe ta yi shi yasa ana kawosu 'yan uwan aikinta mata suka rufesu da dukan kawo wuk'a. Hinde kam ta tsinewa Asabe ba iyaka ya yin da Asaben ke saurarenta ta kasa ramawa saboda tafi buguwa. Kallonsu Baba ke yi a tsiyace ba d'igon tausayin halin da suke ciki ya yin da su kam sun kasa had'a ido da shi, ko wacce cike ta ke da farban makoman aurenta domin sunfi kowa sanin masifar Baba barinma da duka zubar masa da mutunci aka kawosu gidan masu babbak'un kaya, gidan da keyiwa tofin Allah tsine ba gaira ba dalili. *** Sadda na farko gari ya yi haske, Mama na hango rik'e da Alqur'ani tana bita a sirrance, ban nuna mata na tashi ba sai na lafe tare da lumshe ido ina kallonta ta k'asar gashin idanu cike da k'auna mara misaltuwa. Hajiya Inna ce ta matso kusa da Mama ta yi k'asa da murya bayan ta saukemin kallo na seconni. Samun kaina na yi da bud'e kunnuwa da kyau domin jiyo zancen da zatayi wanda na raya a kaina ne sai dai sab'anin zargina sai na ji ta soma cewa "Hurera su Babanki zasu dawo gobe insha Allah sannan ya ce in sanar miki da ki zauna cikin shiri na tafiya duba Alhaji Abdul ganiyu domin tafiyar gaggawan da ya yi sanar masa akayi ya rasu shi ne ya tafi domin ya sami jana'iza sai ya samu dogon suma ya yi." "Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, Insha Allah da Uwata ta sami sauk'i zamu tafi Inna, dama ina shirin tafiyar ne lalura ta samemu." "Hakan ya kamata, sannan Alhaji ya sanarmin shi Alhaji Abdul ganiyu na son magana da ke baki da baki." "Ayya Baba ai da ya sanarwa da Baba Umaru sai ya sanarmin." "Ba zai rasa sanar da shi ba amma dai yafi buk'atar ya yi maganar da ke ido da ido." "To ina nan tafe da yardan Allah." "Madallah, sannan ina baki shawara idan kun baro kwara to ku sauka a Sokoto sada zumunta, ki watsar da duk abinda ya faru abaya inda hali ki yafe musu domin kema Allah ya yafe miki." "Inna ban jin zan iya yafewa dangin mahaifina, sannan bazan tab'a waiwayansu ba, yarda suka bawa Duniya ni to zan tabbatar musu ni d'in ta Duniya ce domin na gamu da ku masu karamci fiye da su marasa adalci." "A'a Hurera ki zamo mai yafiya sannan idan kika aikata haka mahaifinki ba zaiji dad'i ba domin duk tunk'ahon d'a ko 'ya da asalinsu suke tutiya ko da kuwa a ya suke su ne dai ababen adonta duniya da hahira" "Allah sarki Babana mai sona tare da damuwa da duk abinda ya shafeni, da shi na saba saboda mahaifiyata banyi wayon saninta ba amma yarda ya ke bani labarinta sai na ke ji tamkar na rayu da ita sannan indai sune zanyi tink'ahon da su wallahi gara na dauwama ba dangi tunda ina da sanyin idaniyata Nana Khadijatu." "Allah ya gafarta musu da Rahma, amma Hurera ya kamata ki rage zafin nan da kika d'auka ki tuna bawa bai tsallake zanen k'addararsa domin lamari ne da Allah ya samar da shi tun kafin tsiron halittar bayi." "To Hajiya Inna zan duba." "Hakan na ke son ji domin rik'o bai da kyau." "Nagode Inna." "Bakomi, sannan abu na gaba dole ki sanar da Khadija... "Dan girman Allah Inna mu bar wannan maganar." "Saboda me kike b'oye gaskiyan alhalin lokacin abayyana ya yi?" "Bana son damuwarta saboda DAMUWATA ce." "Wannan ba hujja ba ce Hurera." "Hajiya Inna dan girman Allah na ce ki bar magana zamuyita gaba." "To ai shi kenan tunda kinga hakan yafi miki." "Dan Allah kiyi hak'uri Inna." "Bakiyimin komi ba Hurera dama shawara ce na kawo tunda kince sai nan gaba ina yi miki fatar kaiwa lokacin cikin rayuwa." "Allah ya amince." "Amin." Daga haka suka sanja labari zuwa zancen mugun halin Baba wanda banso hakan ba. "Bisa alamu Mama na da babban damuwar da ta ke b'oyemin." Na furta hakan wanda fitar sautinsu suka tsaya a iyaka saman lab'b'ana. *Munata gangara izuwa k'arshen free pages dai.*😍 Pay 300 to 0468069082 Haruna Safiyya GTbank. Send the evidence to WhatsApp number 08132166848. *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [11/3, 11:29 PM] 💘: DAMUWATA ( Sanin abin adona) By Mrsjmoon E.W.F. https://youtu.be/v9iNYDvS8JM Pls 'yan uwa ku dannamin subcribe a YouTube d'ina, nagode. Page 20. Tsam na yi ina nazarin zantukansu tare da son gano abinda Mama ke b'oyemin amma iya hangena na kasa gano abin, lamarin da ya sanya sanjawan bugun numfashina ya soma fita da sauri batare da na san dalilin faruwarsa ba, na yi hanzarin kulle bakina gudun kada sautinsa ya bayyana su gano na farko har na jiyo hirarsu tunda na gano basa so inji. Hakan danayi ya sanya na sark'e cikin fitar da tari mai k'arfi. A tare suka iso gareni, Mama ta soma shafamin baya cikin jeramin sannu Hajiya Inna kuwa ta kafamin kofin ruwa a baki, bayan tarin ya tsaya sai na tsirawa Mama ido ta ware nata na lumshe nawa tare da motsa leb'b'ana. "Me kike son sanarmin Uwata?" "Godiya na ke son yi muku." Na furta duk da ba shi ne a raina ba. "Da akayi me?" "Kula da ni batare da gajiyawa ba." "Wannan hakkin mu ne Uwata dan haka babu godiya a tsakaninmu, kinji ko?" Motsa kai na yi ina saukewa Hajiya Inna murmushi wacce ke binmu da kallo cikin sigan tausayi. 'Da magana a bakinki Hajiya Inna kuma zan jiyo shi da yardan Allah.' Na ambaci hakan a raina tare da zamewa dan in kwanta saidai Mama ta hanani hakan inda ta umurceni da in sauka in d'auro alwalla inyi Sallar Subahi. Na sakko ina cije baki saboda jirin da baigama sakina ba. Ita ta taimakamin na shiga toilet, tana tsaye na yi tsarki tare da d'auro alwalla muka fito saboda ta san halina da son wanka ina iya k'ara sanyawa jikina ruwan sanyi da zarar ta bani wuri. A Zaune na gabatar da sallah a cikin sujata na k'arshe na rok'i Allah da ya bayyanamin abinda Mama ke b'oyemin ko da jinsa ko ganinsa zai zamo ajalina ne. Na yi wannan addu'ar ne saboda yarda na ke son sanin lamarin. Haka nan kawai naji b'acin rai ya kanai-naye ruhina cikin sekonni bayan na d'ago daga sujjadar, koda na sallame sallar sai na koma saman gado na kwantar tare da juyawa su baya. "Uwata jikin ne?" "A'a." Na amsa a tak'aici abinda ban tab'a yi mata ba kenan bata amsa cikin rashin girmamawa. "To tashi kisha tea kafin Likita ya shigo." "Barci na ke ji Mama." Wannan karan cikin rawar murya na amsa mata. Hannunta na ji cikin sumata sai na sake lafewa batare da na juyo ba. "Uwata na san kina tare da damuwa b'oyenmin kike yi." Tashi zaune na yi cikin son dai-daita fuskata zuwa wal-wala. "Kada ki wahalar da kanki Uwata wurin layancewa domin na jiyo dirin damuwarki a k'irjina, oya maza sanarmin da shi tun ban sab'a miki ba." Dariyar dole na sanya duk dan in nuna mata ban tare da damuwar komi na d'aga yatsa na nuna Hajiya Inna wacce ta bud'e baki tare da zaro idanu jin abinda Mama ta ambata ina cewa "Kalli Hajiyarki k'uda na shirin fad'awa bakinta." Harara ta zabgamin na kamo hannayenta na rungume a k'irjina ina doka murmushi. "Harbawan me zuciyarki ta ke yi haka da sauri?" "Wai tana neman ki aminta da kalaman d'iyarki ce na bata tare da damuwan komi." "Na amince Uwata bata cikin damuwa tunda muna tare da ita a ko da yaushe kuma zamu cigaba da kasancewa da ita har zuwa sadda k'asa zai rufe idanunmu tare da burin had'uwa da juna a gidan Aljanna." "Allahumma Amin Mamana." "Wannan k'auna taku Hurera na bani tsoro anya lamarin nan kuwa mai b'ullewa ce?" "Inna bakomi sai khairan, wannan shi ne ni'imar da Allah ya dasa a cikin shayar da 'ya'ya nono ko da ba... Sai kuma ta yi shiru tare da mik'ewa ta nufi hanyar toilet. "To Allah ya tabbatar da khairan mara iyaka Hurera." "Amin tsohuwar su Mama." Na amsa cikin tsokana. "Fad'i ki k'ara da ihu tsohuwar su ce ko wani ya ce taki ce?" "Eh kince dole sai na kiraki da Inna kinga kenan kin saka dole kin zama tsohuwata." "Takwara ciwon nan naki yazo miki da son surutu." Lumshe ido na yi bance komi ba itama daga haka bata sake magana ba. Ganin Mama ta ji bata fito ba sai Hajiya Inna ta hadamin tea mai kauari ta tsareni saida na shanye. Lokacin dMama ta fito kanta k'asa dan tak'i kallona saina nuna tamkar ban lura da b'oyemin fuskanta da ta ke yi ba na d'auko apple na soma gutsira cikin zantukan zucci masu yawa a game da bak'on lamarin da na kasa gano kansa balle tushensa. "Kunga tafiyata na koma gida na huta tunda duk kun warke." Hajiya Inna ta ambata cikin kallon Mama wacce da alama ta yi nisa cikin tunani bata jiyo maganar ba. "Ayya Hajiya Inna ki jira mu tafi tare tunda zamu sami sallama yau insha Allah." "Takwarata su Malam na kan hanya dawowa to ina son zan sama musu wani abu kafin su iso." "To tafi na baki izini tafi." "Ja'ira kin samu lafiya fa bakin ya bud'e da tsokana kala-kala." "Eh dai tafi sai nazo kwance jikka." "To amma dai ki tabbatar kin maida jikinki saboda Malam bai sakewa ramamman mace fuska dan na tabbata wannan manya idanun naki da suka sake fitowa zasu firgitamin miji tsaf." Kafin in bata amsa ta fice da sauri tana dariya Mama na tayata domin ta maido da hankalinta kanmu. "Hajiya Inna kenan ta san kan iya tsokana." "Uwata ke ce Inna ke sakewa irin haka duk cikin jikokinta saboda bata yarda da wasan jika da Kaka ba gudun rashin kunya irin na wasu jikokin sannan wasan kansa wasu Malaman sunce baya cikin musulinci." "To Mama me yasa ni kad'ai takeyiwa?" "Ita zata amsa miki wannan tambayar kam." "Mama wai me... Dawowar Hajiya Inna yasa ban furta abin da na yi niyya ba, muka zuba mata ido ta iso ta ja hannun Mama suka fice zuwa can ta dawo ita d'aya tare da d'aukarwa Mama hijab shima bata jima ba ta dawo ta zauna saman kujerar roba a gabana muka zubawa juna ido, numfashi ta ja ta soma magana "Nana Khadijatu Allah ya jarabceku da rayuwa k'ark'ashin baudd'en mutum sam Malam Hadi bai aiki da saninshi a matsayinsa na babban Malamin da ake ji da shi." "Me ya faru kuma?" "Ina fita na had'u da Alhaji Muhseen yazo tafiya da Mamanki wai ya tsayar da matarsa a waje sai sun nemi gafarar Hurera kafin kafafunsu ya shiga masa zauren gida sannan ya tara mutanen unguwa nata fesa musu lamarin da bai kamata ba domin ance duk wanda ya rufawa wani asiri to Allah zai rufa masa." "Duk me ya janyo hakan Inna?" Tsit na yi jin bak'in labarin abin kunyar da matar Baba tare da 'ya'yansa suka tafka. "Dan rashin kyautawa kam sunyisa Takwarata amma ai fad'ar cikin gida ne bai kamata ya bari na waje su ji ba ko dan mumbarin da ya ke hawa bada sallah." "Abin kunyar ce kam hakan Inna kuma ina tabbatar miki da wata manufa nasa yasa shi kiran Mama." "Abinda itama ta ke sanarmin kenan dan ta nuna bazata je ba na bata kwarin guiwa." "Ko me ye dai Allah na tare da masu neman taimakonsa." "Wannan haka ya ke Khadijatu, masu neman taimakon Allah cikin lamarinsu basa tab'a ganin bak'in cikin ratuwa." "La shakka babu Inna." Munyi shiru zuwa can Hajiya Inna ta soma yimin hira inda yawancinsa akan yarda rayuwa ta ke juyawa al'umma ce musanman wad'anda suka d'auki duniya da fad'i. Knocking a kayi Inna ta amsa da a shigo matar Kawu Habibu ne tare da Aliyu Muktar, ware ido na yi shi kuwa ya tsaya a k'ofa yana jefomin murmushin k'auna, sunkuyar da kai na yi jin Zainab na tsokanarsa, bai kulata ba ya iso gaban Hajiya Inna ya sunkuyar har k'asa ya gaisar da ita ta amsa cikin tambayar sa mahaifiyarsa. "Hajiya ya mai jikin?" "Gatanan ta warke tunda bakiyi tunanin zuwa cikin lokaci ba sai da kikaji mijinki zai dawo gudun kada ya saukemiki halin nasa yasa kika zo to angode amma ki sani shi kyautatawa abune mai kyau kuma lalura na kan kowa dan Khadijatu bata zo miki barka ba bai zama hujjar da zaki riketa ba domin kinfi kowa sanin halinta na rashin son jama'a." "To Hajiya ai duk rashin son jama'arta sai ayi mata fad'ar rik'o da zumunci tunda duk abu d'aya muka aikata har gara ni da ita." Shiru Hajiya Inna ta yi cike da takaicin domin abinda ta tsana kenan ta nunawa mutun kurensa ya k'i amsa. "Hajiya Inna a yi hak'uri idan na k'ara samun sauk'i zanzo ganin Baby  musanman tabbas na san ban kyautaba, Ina neman affuwan Matar babban mutum mai halin girma." "Allah ya yi miki albarka Takwarata." "Amin." Muka amsa tare da Aliyu wanda ya koma gefe yana saurarenmu tunda ya gama gaisar da Inna. "Bari in lek'a gida Takwara." "To Inna sai kin dawo." "Aha, ke kuma idan kinga dama ki zauna da ita kafin wani cikin ni da Hurera ya dawo." "Agaskiya ba zan zauna ba saboda jego na keyi nadai zo  dubata kada ya zamemin abin magana wanda duk da hakan gashinan ban tsira ba saida akayimin luguden labba." "Matar Kawu ki iya bakinki fa, Inna ba sa'ar yinki ba ce dan haka ki tauna kalaminki kafin ki furta in har kina son gamawa lafiya." "Idan ank'i yin hakan fa?" Bud'e baki na yi zan bata amsa Inna ta d'agamin hannu tare da komawa ta zauna. "Zaki iya tafiya tunda kin gaisar da itan." "Ok na barku lafiya, Allah ya k'ara affuwa." Banza mukayi da ita ta fice abinta ba damuwar komi. "Hajiya dan girman Allah kiyi hak'uri, halin Zainab sai ita sam bata san ya kamata ba ko a family haka ake fama da ita bata da kunyar gayawa babba duk kalamin da ya fito bakinta." "Kada ka damu Aliyu, wannan ba sabon abu ba ne, Allah dai ya ganar da ita." "Amin." Ya matso daf da gadon ya ce min "Na yi kewarki, Allah yasa kaffara ce." "Amin." Kud'i mai yawa ya ciro yan dari bibiyu sabbi fil ya ajimin saman cinya sannan ya fice bayan ya sake bawa Hajiya Inna hak'uri. "Me ke tsakaninku da shi Takwarata?" Shiru na yi tare da kulle fuska da tafukan hannayena. "Oh na fahimta, to ba damuwa za'a kuma yayibo irin rashin d'a'a ba." "Hajiya Inna me ya yi?" "Jinin Zainab basu k'ara shigomin ahali da yardan Allah dan haka tun kafin ki haukace a shiriritan so dinan ki koreshi." Idanu na zare ta zabgomin harara. "Inna wai ya suke da matar Kawu?" "Abokik wasanta ne domin da babanshi da Mamanta uwarsu d'aya ubansu d'aya kuma yayarshi wanda suke uba d'aya abokin Habibu ne, agidansu Habibu ya had'u da ita dan Mamanshi ita ta rik'eta har zuwa aurenta." "Ikon Allah amma duk shekarun da muka kwashe da Aliyu ban tab'a sanin hakan ba." "To ina kike zuwa balle ki had'u da 'yan uwansa sannan shima Aliyun bai zuwa gidan Habibu sai hab'o." Shiru na yi ina nazarin wannan lamari, ta ke naji duk damuwar da na ke ciki ya koma ba komi ba saboda tuno mugun halin Zainab da tasha gwadamin wanda nashajin Hajiya Inna na cewa d'aukosa ta yi wurin uwar goyonta. 'Wato mahaifiyar Aliyu bata da kirki kenan? Aikam na hak'ura da kai domin ina burin aure na ke inda Zan sami kwanciyar hankali ba kishiyarta ba.' "Ban son shiga dogon tunani saboda lalurarki." Na tsinkayi muryan Hajiya Inna daf da ni. Kallonta na yi har lokacin bata cikin walwala. "Kiyi hak'uri Inna." "Ya zamamin dole Khadijatu sai dai DAMUWATA shi ne na yarda surikata gudan jinina d'aya tilo zata zamemin abokiyar gaba." "Ban gane ba Inna? Kina nufin su Mama Indo ba surukanki ba ne?" "Surukaina ne amma duk kan mazajensu 'ya'yan uwar gidan Alhaji ce wacce ta rasu ta barmin su duk suna k'ananu, Habibu shi ne yarona na shida kuma shi ne ya rayu har naga aurensa domin yayunsa da k'anninsa daga sun taso suke mutuwa domin babban yayarsa na daf da yin aure ya sami hatsarin mota ya mutu nasan kin tuna lokacin." Eh na tuna da kawu Hamza, Allah ya ji kansu da Rahma " "Amin. "To yau kinji yarda na ke da su Balarabe." "Allahu albar, sannu Inna, lallai ke ta daban ce, Allah ya biyaki da khairan." "Amin ya rabbi." "A gaskiya su Mama Indo nada ladabi sama da Zainab sam ba wanda zaice ba ke ce kika haifi mazajensu ba." "D'iyoyin tarbiyya kenan, sannan sun samu mazaje tsayayyu masu jajircewa akan abin da suke so dole abi ba irin Habibu ba da gata ya yiwa yawo ya ke ganin matarsa ba komi ta ke yimin ba saima ganin ni ce nacika fad'a da saka ido." "Shi Kawun ke kallonki da hakan?" "Ya wuce kokwanto Khadijatu domin yanzu indan da gabansa hakan ya faru wallahi tsaf bayar matarsa zaibi ya yi ta k'unci na tozarta masa iyali gaban mutane." "In haka ne kam da sake wallahi, ai lamarin uwa sama da komi ya ke, gashi wayayye da ilimi amma bai aiki da shi." "Ki bari kawai Khadijatu, shi yasa na kance da shi halinsa d'aya da Hadi." Kulle baki na yi idanu waje na ke girgiza mata kai murmushi ta yi kad'an ta ce "Na tabbata ko halinsu bai zo d'aya ba a wani abin zaizo domin ya yi nisa akan lamarin figaggiyar matarsa mai zubin zabbin daji da kanta kamar k'ullin maganin sanyi." Dariya na kyale-kyale da shi tana tayani. Daga haka muka saki zancen domin nagano ta sanyo mana raha ne saboda bata son acigaba da zancen. *** Ina cin abincin rana faten Irish ne ya ji hanta da ganyen ugun wanda su Fanta suka kawomin, sai hira mukeyi hankali kwance domin Hajiya Inna ta sami wucewa gida tunda ta ga isowarsu. Mama ce ta shigo Uncle na biye da ita tare da Baba a bayansu. K'irjina ne ya harba ganin Baba domin na tabbata sai ya b'atamin rai kafin ya tafi. "Kai dalla! Ku fice ku bata wuri ta sha iska, kunzo kun nanuk'eta da tik'a-tik'an jikinku ba mijin kwasa ko da ya ke duk jirgi d'aya ya kwasoku da ita ga kyau da wayewa ba mashin-shini, kai tir muku!." Tashi su Fanta sukayi duk suka fice jikinsu a sanyaye, na kalli Uncle wanda na hango b'acin rai a idanunsa kwance sai kawai na fashe da kuka mai sauti ina kaiwa k'arfe gadon duka wanda ke nuni da takaicin da na ke ciki. *TALLA.* *Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:* Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka) *Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [11/4, 5:42 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Mrsjmoon E.W.F. https://youtu.be/v9iNYDvS8JM Pls 'yan uwa ku dannamin subcribe a YouTube d'ina, nagode. Page 21. "Ke! Kuma me akayi miki kika b'are baki kamar faranti kina kukan iyashege, to maza ki rufe mana baki ko ingamu da ke ba ciwo ba ko mutuwa kikeyi zan iya taka gawarki na wuce ta kai ba ruwana." Shiru na yi amma badan tsoron dukansa ba sai dan takaicin halinsa tare da tunanin yin kukana baida amfani. "Dan an kira k'awayenki tik'a-tik'a shi ne abin yin kuka saboda Hurera ta gama sangartaki, ke yanzu dan Allah ko kunya bakiji kamarki kina kuka, inda a k'auye kike da yanzu kina da 'yay'ya bakwai zuwa goma amma dubeki zaune makar gar, to wallahi ki sani kwanaki kad'an ya rage in zar... "Dan Allah Malam kayi shiru haka ban muji da abinda ya damemu tunda kai haka Allah ya yika baka gajiya da sababi mara ma'ana da ke janyo jin kunya." "Hurera ni... "Dan soyayyarka da mahaliccinmu ka daina fad'ar nan haka, haba dan Allah kai ko gajiya bakyayi da zance a gaban idanun kunya." Tsuke baki ya yi yana aunawa Mama mugun kallo, kunya ce ta rufeni ganin yarda Uncle ya ke binsa da kallon banza, tabbas kallon ya haskomin karatun ruhinsa wato takaicin Baba mai jin tamkar a rufe rufeshi da duka. "Uncle nagode da tarin d'awainiya Allah ya jik'an mahaifa ya kuma shirya maka zuri'a tare da gamawa lafiya cikin samuwar babban rabo ranar lahira." Sai da ya yi gyaran murya sannan ya amsa lokacin har Mama ta amsa ya yin da Baba ya tsare giran sama da k'asa yana zabgomin harara. "Bari inga Dr. Jalal." Uncle ya furta batare da ya jira amsawarmu ba ya fice. "Munafukin banza wai shi nan ya ji haushi na kori k'aninsa, to an koresun in zai iya ya rufeni da duka yaga inda tsiya ke zamaninta wallahi." "Allah ya yi mana tsari da ganin tsiya." "Amin." Na amsa da sauri. "Ya jikin naki?" Baba ya ambata cikin taushin murya. Ban dauka da ni ta keyi ba shi yasa bance komi ba. "Au dan kin samu na tambayi ciwon karyan da kikayi shi ne zaki maidani sokon banza?" Kafin inyi magana Mama ta rigani da cewa "Gata nan ta warke ganin idanunka sai kuma me uban 'yan sababi." "Hurera me yasa sam baki san darajar aure ba ne?" "Sabon karatun sanin darajojin aure zamu koma makaranta muyo tare da kai domin kome ka kirani kaine malamina." "Zan sab'a miki fa Hurera ba ruwana da Asibiti ne nan." "Maza aikata abin yamad'i-d'i karo na biyu a safiyar nan a samu masu d'oraka a yanar gizo da bugawa a jaridu kaga ka zama dan wasan kwai-kwayo na zahiri kamar yarda sabon sunarka ya koma a unguwarka yanzu." "Ni Malam Hadi kike kira da d'an drama?" Banza Mama ta yi da shi, nikam tuni na juya baya tare da tura yatsuna cikim kunnuwana saboda na gaji da sauraren sababin Baba. "Sai mun had'u a gida zan nuna miki nafi gaban iskancinki sannan kada kiga na d'aga darajarki a gaban abokan zamanki d'azun ki d'auka kin sameni ne a'a biyana zakiyi dan wallahi sai naci buhunar wake biyar domin na saka buri akan wanda sukayi satan sai reshe ya juye da mujiya dan haka sai ki shirya bi... "Allah ya ganar da kai hanyar gaskiya." Mama ta ambata tare da shigewa toilet ta barshi tsaye da baki bud'e, dariya ce ya zomin na kife fuska gudun kada ya jigoni na shiga uku K'aran buga k'ofar ya sanarmin da Baba ya fice, numfashi na sauke ina auna lamuran Baba wanda na yanzu na ke d'orasu a mizanin rashin hankali. "Astagafirullah." Na ambata a hankali. Shigowar Doctor, Uncle da su Beebah biye da su ya yi daidai da fitowar Mama daga toilet. Ya bani sallama tare da shawarwari agame da daina barin damuwa ko tunani na takuramu ni da Mama saboda su ne babban matsalolinmu. Sosai Mama ta yi masa godiya, su Fanta suka tattara mana kaya muka fito. Ni da Mama tare da Bintu motar Uncle muka shiga ya yin da su Fiddausi suka shiga wanda suka zo a ciki Beebah ta ja, ta yi gaba Uncle ya rufa mata baya, akan hanya ya kira Hajiya Inna ya sanar mata da an sallamemu. "Yawwa Alhaji sanar da Malam kada ya zama abin laifi duk da yasan za'ayi sallaman." "To Mama." Ni ya mik'owa wayar batare da ya furta kalma ba. Sunar da naga an sanya Baban Nana na kira har ta tsinke ba'a d'auka ba, haka na yi ta kira sau ba adadi a k'arshe sai aka kashe wayar. Mik'awa Uncle wayarsa na yi ya amsa batare da ya cemin uffan ba haka nima ban tofa ba. "Mama dan girman Allah kiyi ta hak'uri da Baba insha Allah hakurinki babban riba ne saboda halinsa ba ke kad'ai yake yimawa ba, na fahimci haka Allah ya yo shi mafad'aci ga saurin hasala akan abin da bai kai ya kawo ba." "To Alhaji Allah ya k'ara mana hak'urin baki d'aya." "Amin." Muka amsa. Wayar Bintu na amsa na turawa Aliyu sak'o. Ina kallon Uncle na hararan hannuna ta gefen ido sai lamarin yabani dariya na murmusa har sautin na fitowa ya kalleni ido cikin ido na lumshe nawa. "Ina wayarki?" Ya furta cikin rad'a. "An sace wayar." "Inji wa?" Wannan karan ya bud'e murya. "To Uncle nazo da ita Asibiti ba'a ganta ba." "Ok za'a siya wani." "A'a kada a siya tana wurin Baba Umaru, Habibu ya sanarmin da sun dawo daga tafiya za'a kawo mata." "To Mama." Ya amsa cikin girmamawa. Wayar hannuna ta yi k'ara number Aliyu ya baiyana sai na maida silent tare da maidawa gefe na ajiye, ina kallo kira ya yi ta shigowa ban d'auka ba saboda idanun Uncle wanda yanzu k'imarsa ya kuma ninkuwa a gare ni ainun. "Ki d'auka wulak'anci bai da kyau Khadijatu." Cikin rad'a ya ambatamin haka, kallonsa na yi ya jinjinamin kai maida kai gefe na yi batare da na bi umurninsa ba. Muna isa gida su Beebah suka gyaramin d'akina dana Mama cikin a binda baifi awa d'aya da dawowarmu ba gidan ya koma fes har girki sun d'ora, wanka na yi muka zauna a baranda saman babban tabarma Fanta na yi min fifita sakamakon zafin da na ce yana damuna, shi yasa na sanya riga mai yankakken hannu da siket mara nauyi sai na sanya k'aramin hijab wanda ya tsayamin iya wuya. Aunty Nafisa ce tare da yaranta suka shigo mun gaisa cikin mutunci Mama ta sake yi mata godiya akan d'awainiyar da Uncle ke kanyi mana. Muna tare da ita har dare sannan tsawon lokacin ban hango tijara a idanunta ba domin duk had'a idanun da zamuyi bata yimin mugun kallon da ta ke bina da shi a tun sanina da ita. Sai bayan isha'i ta wuce tare da su Bintu, su kabar Beebah da Fanta. Ina sallah na jiyo shigowar Baba Umaru Ina idarwa na tafi muka gaisa sai tsokanata ya keyi da gawa tak'i rami, Kawu Habibu na taremin. Shigowar Baba yasa na bar wurin da sauri ina jin Kawu Habibu na k'orafin sababin Baba dan ganin yarda na tsorata da shigowarsa. Ba jimawa na jiyo muryan Uncle inda na fahimci masalaha akazo samu bisa jagorancin Baba Umaru. "Aliyu ya na k'ofar gida fa." Idanu na zubawa Beebah, ta gyadamin kai "Tun kina wanka ya zo kuma ya kamata ki fita." "A gaban su Baba Umaru zan fita zance?" "To me ye? Kinga ba sai Baba ya gane muna da masun-sunar da ya yi mana gorinsu ba." Sunkuyar da kai na yi saboda yarda ta yi maganar na gano zagin da Baba ya yi musu d'azun ya b'ata ranta. "Uhm wallahi badan mahaifinki ba ne Deejah na rantse da d'azun bansan kalan maganar da zanyi masa ba dan har zagi zai iya masa amma sai ya zamo ya haifeki 'yar albarka." "Aunty Beebah ba Uncle ya ce maganar ta wuce ba." "Ya wuce Fanta kawai dai har yanzu haushi lamarin ya ke bani barinma dana jiyo muryansa yanzu." "Kiyi hak'uri nima d'iyarsa bai bari ba, kin dai gani da idanunki." "Ya wuce yanzu tashi ki tafi wurin masoyinki." "Dan Allah ku fita ku wakilceni domin bazan iya tsallake taron can ba." "Fanta tafi ki sanarmasa tasha magani jiri ta ke gani ya shigo su gaisa." "A'a kada ya shigo." "Me kike nufi?" "Ya tafi sai da safe ya dawo." "To baki isa ba sai ya shigo tunda dubiya yazo ba soyayya ba." Tab'e baki na yi jin abinda ta ce idanu ta zaro na zabga mata harara tare da hayewa saman doguwar kujera na kwanta. Fita sukayi tare da Fanta zuwa can na jiyo sallamar Aliyu da sauri na tashi na jira hijab na cure wuri d'aya. Duk Ina jin sadda ya gama gaida kowa su Beebah suka yi masa jagora zuwa d'akina na sha mamaki da banji Baba ya yi sababi ba amma tuno da Baba Umaru a wurin sai na barshi saboda ganinsa sa ne ya tsuke baki. Tashi zaune na yi muka gaisa daga nan shiru ya biyo baya, su Beebah dai na zaune saman gado kowacce na latsa wayarta basu da niyya bamu wuri sai hakan ya yimin dad'i saboda har cikin raina banda kalman furta masa.. "Allah ya k'ara lafiya." "Amin, nagode." "Bakomi ke matar Ali ce insha Allah." Da sauri na kalleshi ya dokamin murmushi sunkuyar da kai na yi. "In Allah ya kaimu gobe Hajiyana tare da Salma zasu zo dubaki." "Ok Allah ya kaimu." "Amin." Ya mik'e ya fice Fanta ta rufa masa baya. "Ke matar Muhammad Muhseen ne ba Ali ba." "Uhm Beebah hoo naga dai ke ce duk kikayi kid'a da rawar nan fa." "Shi yasa na ke son goge zunubina." Dariya ta bani sosai na dara tana tayani. "Allah Deejah kafin in bar garin nan sai kin rabu da Aliyu." "Saboda me?" "Haka nan naga yanzu baku dace da juna ba, farar mace sai farin namiji kamar Uncle zubin labarawa." "Kinyi kuskuren fad'ar karin.maganar Malama cewa akayi farar mace sai bakin namiji, farin namiji kuwa sai farar mace tamkar yarda Uncle suke da Aunty Nafisa ita chocolate shi fari, my Ali baki ni 'yar fara kad'an." "Ko ba 'yar fara kad'an ba." Ta furta cikin kawomin duka na gofce tare da komawa serious na ce "Bazan auri Aliyu ba saboda da wasu manyan dalilai wanda zan sanar da ke kafin ku tafi." "Zanso jinsu yanzu saboda tafiyarmu zai iya yiwuwa gobe ne." "Gobe kuma?" "Eh saboda Aunty Nafisa ta had'a mana gurmi wurin tsoho mai ran k'arfe ya kira Uncle lallai mu taho gobe ko ya iso garin Kaduna da kansa ya d'aukemu musanman ni da ke aikin taimakon al'umma." "Wayyo zansha kewa." "Muma haka amma tafiyar banda Fanta saboda muna da biki watan gobe zasuzo da fatan zakiyi mana kara kizo?" "Insha Allah zanzo duk da muma zamuyi tafiya amma nasan kafin bikin mundawo." "Dan Allah kizo." "Insha Allah." "Ok." "Bikin na miji ko mace?" "Babban yayarmu baki d'aya shi ne zaiyi aure." "Masha Allah." "K'aton tazuru ne fa duk k'anninsa sunyi aure da 'ya'yanzu shi kuwa ya tsaya bautawa boko, da kiranye ya dawo Nigeria, baki gansa ba tamkar bature." "Ikon Allah, lokacin auren nasa ne baiyi ba sai yanzu." K'asa ta yi da murya sannan ta ce "Ina son shi fa insha Allah zanzo a ta biyu shi yasa na yakice Yaya Abdul da k'arfi da ya ji." "To wata sabuwa inji 'yan ca-ca." "Ki bari kawai dear ni kad'ai na ke kidana da rawana sannan in banda ke ba wanda ya sani." "To ta ya za'a yi auren kenan?" "Ta yarda akeyi." "Zanso ganin wannan soyayya wacce ta ke ma kauniya." "Ki bari kawai Deejah ni kaina na bata wannan sunar amma ina fatar ta sami ido bada jimawa ba domin ba zan iya bawa kowa ruhina ba sai Yaya Mubajjal." "Wow suna mai dad'i ga tarin ma'ana." "Duk mai sunar ya tarasu wallahi ya san kansa baruwansa kowa na sa ne, kinga tunda ya dawo duk jikokin gidan shi ke d'awainiyar karatunsu hatta da mu da muke jikokin d'iyoyi mata ya d'auki nauyi sai d'an abin da ba'arasa ba iyayenmu keyi mana, kud'i ya ke samu tamkar yana hak'osu a k'asa saboda a can turai ya ginu har kamfanoni ya ke da su tare da turawa." "Masha Allah, matarsa ta yi dacen miji mai son zumunci." "Wallahi fa ta yi dace kuma ta tsinci dami akala domin d'iyar kawunsa zai aura itama yar boko ce lecturer ce sai dai yafita kyau da aji nesa ba kusa ba." "To ke Beebah ba sai ki cire kanki a lamarinsa ba ki fidda masu sonki tunda shi ya sami mata." "Bazaki gane wani kalan so na keyi masa ba wallahi ba dan kudi da kyawunsa ba ne na kamu da k'aunarsa, tun ranar da nagansa naji fad'uwar gaba kuma tundaga ranar duk in mun had'u sai na shiga yanayin daburcewa, tun ban gano dalilin ba har nagano sonsa na ke yi." "Ikon Allah sai ji da gani." "Kin nan me?" "Sai kin fad'a." "Duk cikinmu yafi yimin magana ko yanzu mafi yawancin shirye-shiryen bikin shi Momynmu zatayi wanda ni ya d'ora a kai na nemi shawararta ta ce in bar mata komi a hannunta daga nan fa ya maida gidanmu wurin zuwarsa ni kuma anan na kuma kamuwa da kaunarsa matsananci saboda yarda ya ke shigemin ko nak'i fitowa idan ya zo sai yanemi izinin momy ya biyoni d'akina shi yasa na daina gudu duk in ya zo sannan gashi ya iya tsokana irin ta abokannan wasa sai dai in yana yimin daburcewa na keyi sam ban iya maida masa da martani inda zai ta kirana da 'yar k'auye mai kunyar maza, wani zubin Momy ce zatayi ta taremin." "To shima yana sonki kenan?" "Ko d'aya, haka yakeyiwa dukkanmu sai dai kafin ya kirasu ne ya kirani sau ba adadi." "Amma naga ko sau d'aya banga kunyi wayata ba." Nunomin wayarta ta yi naga Miss call barkatai. "Kullum sai ya kirani wani in amsa wani in share saboda haushin auren da zaiyi." Dariya na kyale-kyale da shi ta tale baki tamkar zata fashe da kuka. "Sorry dear in baki shawara?" "Eh." "Ki rik'a amsa kiransa inda hali ke ce zaki soma kiransa sannan ki b'oye kishin nan ta gaibu domin wanda kikeyi bai sani ba, ki nemi zab'in Allah ba son zuciyarki ba, in har mijinki ne da kansa zai furta miki k'auna." "Nagode da shawara amma da kamar wuya hakan ya faru kawai ni ce zan ambatawa Kaka ina son shi na tabbata aurenmu zai k'ullu cikin ruwan sanyi " "Ban amince kiyi haka ba saboda naji masu iya magana sunce matar shige bata daraja, gara ya furta da kansa." "D'an boko ne da makar wuya ya zauna da mata biyu." "To ki hak'ura da shi mana ki rik'e Yaya Abdul." "Wannan kam ko mu biyu muka rage a duniya ba zan tab'a aurensa ba, nayiwa kaina wannan alk'awarin." "Tsana in ya yi yawa mafi lokuta  k'auna ke komawa, to dan Allah ki barwa Allah lamarin sai ya zab'a miki mari alkhairan." "Insha Allah zan mik'a lamarin ga mai zab'awa bayi duk abinda yafi zama alkhairi a garesu." "Da kyau tawan." Murmushi mukayi tare da tafawa. Gyaran murya Fanta ta yi muka kalleta tsaye bakin k'ofa ta kafe Beebah da ido. "Me ye?" "Kin tsargu ne? To babu komi sai dai ni ce ta uku wacce ta san makauniyar soyayyar nan." Dak'uwa ta yo mata muka fashe da dariya. "Wallahi Aunty Beebah da a ce Yaya Mubajjal zai aureki da zance kunfi dacewa akan Aunty Hajara nan mai k'aton goshi da uban salo wai ita 'yar boko." "To sannu 'yar son kai." "Serious aunty Beebah, kun dace da juna kuma zan tayaki addu'ar Allah ya baki shi a matsayin miji." "Amin 'yar uwa nagode." "Sai dai wani hanzari ba gudu ba maganar fidda miji da Dady ya yi miki yana nan fa ba d'aga k'afa, shin ya zakiyi?." "Ki bari kawai 'yar uwa babban  DAMUWATA yanzu wannan maganar ce ga Momy ta goya masa baya shi yasa na ke jin tamkar kada in koma." "Ga shawara ki kira Yaya Mubajjal ki sanar masa tare da neman shawararsa ko ki nuna masa ya nema miki alfarma wurin Dady da ya k'ara miki lokaci tunda kuna d'asawa ba zai juya miki baya ba." "Good idea Aminiyata." Na ambata cikin jinjinawa Fanta. "Kuna ganin in aikata hakan?" "Eh amma shawarar k'arshe na ya nema miki alfarma Dady ya k'ara miki lokaci kawai zakiyi masa. " "Tam shi kenan, anjima zan sanar masa naji abin da zaice." "Allah ya sa ya ce zaki aureni Habibatu." Rungumeni ta yi cikin cewa "Da na kwana yi miki addu'ar gamawa lafiya da barin miki kyautar Umrar da Uncle ya yi min." "Oh Aunty Beebah ba kunya." "Amsa naki Fanta." Ta watso mata d'ak'uwa cikin tsare gira. Dariya muka sanya cike da nishad'i. *** Washe gari tunda subahi kiran Uncle ya tashemu inda ya sanar da Beebah ta shirya shi zai kaisu. Ina azkar duk jikina a sanyaye na jin zasu tafi. Sabo akace turken wawa to hakan ya faru gareni domin yinin ranar ko murmushi banjin na yi ba tun Mama da d'aukan abin da wasa har ta ga da gaske na ke sai ta koma bani baki amma duk da hakan  ban dawo wal-walata ba na dai rage tsare gira. Fanta dama tunda taga ina hawaye ta fice ban sake sanyata a ido ba. Misalin k'arfe uku na rana muna zaune saman tabarma Mama na damamin furar Tamba wanda Hajiya Inna ta aikomin da shi, muka tsinkayi sallama atare muka amsa wata Mata mai jiki tana da haske dai-dai misali ta shigo tare da matashiyar budurwa wacce kallo d'aya na yi mata na gano k'anwar Aliyu ce saboda kamarsu da juna har ya b'aci duk kuwa da tana fara shi kuwa bak'i. Cikin girmamawa Mama ta basu wurin zama yarinyar ta zauna ta gaisar da Mama tare da yimin ya jiki na amsa cikin murmushi saboda naji dad'in ganinsu. Matar kam tsaye ta yi k'erere tana jifana da wani kallo wanda ya saukemin kasala tare da bugun k'irji, gaisuwar da na ke nufin yi mata nakasa aiwatarwa, alokaci d'aya na nemi farin cikin ganinsu na rasa. Mama da bata lura da kallon ba ta tafi d'auko musu abin motsa baki. "Ina yini?" Na furta cikin jajircewa. "Mahaifiyar Aliyu ce dafatar ya sanar miki zuwana?" Ta maidomin da amsar gaisuwar ta bayyanamin kanta. "Eh, kunzo lafiya?" "Ba damuwarki ba ne wannann." Da sauri na kalleta ta zaromin manyan idanunta kauda kai gefe na yi ina jan addu'ar duk da yazo bakina. "Na zo yi miki kashedi ne a kansa, ki rabumin da d'a ba zai aureki ba na zab'a masa wacce ta dace da shi domin auren zumunci zaiyi da d'iyoyin ar... "Akul! kika nemi aibatamin d'iya akan idona Hajiya Asiya, tunda dai kin fad'i abin da ya kawoki to fice min a muhalli tun ranki baifi nawa b'aci ba." Cikin fushi Mama ke maganar wanda na hango mamaki a idanun wacce ta kira kanta da mahaifiyar Aliyu jin kalamin Mama "Ni kike kora a gidanki?" "Ya wuce kokwanto, maza ficemin ko in sanya afitar da ke kuma idan kin isa da d'anki kada na sake ganinsa a k'ofar gidana balle ya shigomin muhalli." "Haka kika ce?" "Eh." "Kin tabbata d'iyarki ta rabumin d'a kenan na har abada?" "Ko a lahira bana fatar Uwata ta had'u da d'anki." "Masha Allah, abu yazo cikin sauk'i, nabarki lafiya." Banza Mama ta yi da ita illa nuna mata hanyar ficewa da ta yi. "Hajiya ba haka kukayi da Yaya ba dan Allah ki ba su hak'uri dan d'anki zaifi cutuwa." "Zaki tashi mu tafi ko sai na sab'a miki?" Da sauri Salma ta mik'e suka fice na kalli Mama ta watsomin harara sai na tashi da sauri na shige d'akina ina jin zuciyata tamkar zata fad'o k'asa. *Assalamu alaikum. Shahararren kamfanin nan na oriflame na yin registration kyau a wannan wata duk mai burin a dama da ita a harkan siye da siyarwa na kayan kamfanin ko yin amfani da kayan domin jin dad'inta to wannan babban damace a gareki ki garzayo ayi miki register kyauta kafin wata nan ta November ya k'are domin in ya k'are sai kin biya kusan 5k kafin ki samu damar zama 'yar kamfanin mai 'yanci dan haka ki taho ki zama .ai 'yanci a kyauta. Dan k'arin bayani ku tuntub'i wannan number 08131166848.* [11/5, 1:15 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Mrsjmoon E.W.F. https://youtu.be/v9iNYDvS8JM Pls 'yan uwa ku dannamin subcribe a YouTube d'ina, nagode. Page 22. "Dan Allah ki fito waje zuciyata na koma ga mahallicina ko na huta da wannan rayuwa mai cike da damuwa kala-kala, shin wai meye dalilin zamowata mara sa'ar rayuwa ce? Ina burin gabatar da rayuwa mai cike da kwanciyar hankali tamkar sauran mutane? Wayyo ni Nana Khadijatu ina zan saka kaina? Mahaifina bai bar ruhina ya sami natsuwa daga wasi-wasin shi d'in uba na ne ko zaman agolanci na ke yi a k'ark'ashinsa ba sannan ga saurayin da na sama bayan tsawon lokacin dana kwashe ina geben samun abokin rayuwa Mahaifiyarsa ta jagoranci rabuwarmu duk da na soma fidda shi a raina amma banso rabuwarmu  ya zo ta wannan sigan ba. Ina da tulin tambayoyi a gareki Mama dan Allah ki amsamin su ko natsuwar da na ke nema ya rab'eni. Ya Salam, ya rabbi ka kawomin d'auki badan halina ba. K'alu Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, Allahumma ajirni fi masibati wa khalifni khairan minha." Sune kalman dana rik'a ambata cikin matsanancin kuka hannayena duka biyun dafe da k'irjina wanda na tabbatar bana rabuwa da Aliyu ba ne domin ina jin wani sabon lamari na daban zai sameni wanda zanyi kukan shi yasa na bud'e baki ina yinsa tamkar wacce aka aikowa da sak'on mutuwar Mama. A k'arshe zamewa na yi na kwanta saman sallaya ina cigaba da kuka amma mara sauti saboda yin mai sautin zai janyo hankalin Mama saidai duk da rage sautin bai hanata jiyowa ba. Ina jin shigowarta nak'i motsawa tana d'ora hannunta a gadon bayana sabon kuka ya kubcemin na fashe da mai k'arfi sosai cikin jijjiga. Hannunta ta soma yawo da shi a bayana a hankali ba tare da ta yi magana ba, ina ji a jikina itama kukan ta keyi mara sauti, d'if na d'auke nawa tare da tashi zaune da hanzari na fad'a jikinta ina cewa "Natuba Mama dan Allah ki yafemin ba burina kenan ba na sakaki kuka lamarin ne ya dameni dole saina zubda jirwaye zan sami natsuwar jiki da ruhi, dan Allah kada kiyi fushi da ni, natuba Mamana, kiyi shiru dan girman Allah, zubar hawayenki dafi ne a gareni dan Allah kibari kada wani abu mara kyau ya sameni sanadin kukan nan." "Banyi fushi dake ba Uwata kuma ba kuka na ke yi ba fatana ki sanya salama cikin ranki dan samuwar lafiyarki sannan kada kiyi zargin na jagoranci rabaki da mosayinki ne saboda da wata manufa tawa a'a sam ba haka ba ne ina dai burin kiyi rayuwa ce mai cike da 'yanci wanda zaki sakata ki wala a gidan aurenki ba wanda zaki dawwama cikin k'unci ba bisa takurawar uwarmiji wannan dalilin yasa na datse alak'arki da Aliyu kuma idan har na isa na fad'a ki ji to daga yau babu ke babu Aliyu har abada sunarsama bana son ki sake ambata koda a cikin zuciyarki ne, burina ki kasance tamkar baki tab'a sanin shi ba balle ki tuna kun tab'a musayan kalaman k'auna." "Mama... "Uwata hakan na ke buk'ata da ke, hatta da makaranta da kuke had'uwa kin daina zuwarsa kenan domin na tsani mahaifiyarsa da shi kansa tunda ta sanya Uwata zubda hawaye a kan idona sannan ta nemi aibatamin ke da kalma mafi muni da natsani jinsa." "Mama na hak'ura da shi tun kafin zuwar wannan lokaci kuma insha Allah zan ciresa a babin rayuwata sai dai ina rok'on da ki janye kalman tsana ga Aliyu saboda baiyi komi ba ko ba komi ya so Nana Khadijatunki da zuciya d'aya, ya karya bak'in tarihin nan na tana da bak'in jini ta rasa mai furta mata kalman so." "To Uwata na jenye harma da Mahaifiyar masa duk na yi hak'uri irin wanda Allah da Manzonsa duke son mumunai nagari sunayi wato hak'uri mai kyau." Sunkuyar da kai na yi ganin tana kallona cikin murmushi ga hawayenan cikin kwarmin idanunta suna daf da zubowa. Ban d'agoba na mik'a hannu na share mata hawayen, ta rik'e hannuna gam na d'ago da sauri ta motsa kai, matsowa jikinta na yi ta saki hannuna na samu damar shigewa na lafe, bubbugamin baya ta soma tamkar uwa na rarrashin 'yar yaye. "Mama tun jiya na soma cire Aliyu a ruhina saboda... Na sanar da ita duk abin da ya faru zuwar matar Kawu Habibu dubani da zantukan da mukayi da Hajiya Inna. "Alhamdulillah, Allah ya zab'a miki mafi alkhairi." "Amin Mama." Na amsa a hankali cike da kunya ta shafi sumar kaina cikin cewa "Taho muje ki tayani aiki domin zama wuri d'aya na janyo tunani mara tushe da fatan ban takura Uwata ba?" "Mama kekoh." Na ambata a shagwab'e. Hanncina ta ja na d'auke numfashi cikin sigan wasa ta saki da sauri na fashe da dariya tana tayani. "Allah ya cigaba da albarkatan rayuwarki Khadijatu." "Amin Mamana." Fitowa mukayi Mama ta yi ta yimin hira mai sanya mantawa da duk kan damuwa. "Uwata yau Litini insha Allah jibi laraba zamu tafi Kwara dubo jikin Babana." "Allah ya kaimu Mama." "Amin." "Gobe zamuje yi masu tsaraba da fatan zaki iya shiga kasuwa?" "Zan iya Mama." "Madallah, anjima Habibu zaizo muje shagunana domin ina son saidaasu na had'esu ya zama babba guda d'aya kamar super market." "Masha Allah, Allah ya taimaka." "Amin, zan dank'a a hannunsa dan hakan zai fi akan yawo da hankalin da masu hayan keyimin ko ba komi shi nawane, da wasu su cinyemin gara shi ya ci ya more." "Hakan ya yi Mama, Allah ya yiwa nema albarka ya taya Kawu Habibu rik'o." "Amin." "Jiya an sami masalaha tsakanin Alhaji Muhseen da Malam ina fatar nadamar da na hango a idanun Malam ya zamo na gaskiya ne." "Amin ya rabbi." Shiru ya ratsa wurin na dubeta kad'an ta motsa kai alamun tana saurarona. "To Mama kin hak'ura da zancen dukiyanki na wurin Baba ko?" "A'a bazan hak'ura ba dan zaman jiya har da shi aka tsaida maganar ina dawowa daga Kwara zai dank'amin kayana domin lokacin yin amfani da su ya yi dama an bashi ne ya ajiye amatsayinsa da shugabana sai ya nemi a bashi damar ya juya zuwa sadda za'a nema to lokacin neman ya yi." "To Mama idan baya da shi fa?" "Na sanar miki yana da gidan gona wanda da kud'ina ya mallaka haka ya siya gonaki duk da kud'in yanzu haka takardun gonakin jiya Baba Umaru ya amsa daga hannunsa gidan gonar kuma zaiyi masa kud'i Habibu zai siya sai a had'a da gonakin a lissafa in sun kai adadin kud'ina in kuma sun wuce sai abashi ragowar hakk'insa." "Kuma duk Baba ya amince cikin ruwan sanyi?" "Eh saboda Baba Umaru ba sa'ar wasanshi ba ne sannan komi da akayi anyisa ne a rubuce tare da shaidu. Idan komi ya kammala filin da ke kan layin su Baba Umaru za'a siya a gina babban Mall wanda zai kasance babu ce kawai ba'a siyarwa." Dariya na sanya cike da jin dad'i na ce "Da sai in zama shuga mai bada umurni." "Allah dai ya cika mana burinmu Uwata domin komi da kikaga inayi to dan ingantuwar rayuwarki ne, kada k'asa ya rufe idona Malam ya handame komi ya koramin." "Godiya na ke Mamana amma dan Allah ki kyautatawa Baba zato." "To naji amma ki sani ba godiya a tsakanin Uwa da 'ya sai addu'ar samun babban rabo ranar lahira." "Allah ya biyaki da gidan aljannatul firdausi." "Amin ya rabbi." "Yawwa Mama wai ya muke da Baba Abdul Ganiyu nan?" Shiru ta yi har na cire rai da jin amsar tambayar sai kawai na kamo hannunta na langab'e kai cikin sanyin murya na ce "Kiyi hak'uri Mama idan sanarmin zai takuraki wallahi na fasa jin nasabanmu da shi." "Zan sanar da ke amma a takaice domin zuwa yanzu ya kamata ki soma sanin ya ni ke da duk wanda kika ganmu tare." "To Mama Ina saurarenki." "Kinga Baba Abdul Ganiyu abokin mahaifina ne na k'ud da k'ud amma shi bayarbene ya yin da Mahaifina Abdullahi ya zamo Hausa Fulani d'an asalin garin sokoto. Sadda Allah ya nufa zan zo garin Kaduna da zama Baba Abdul Ganiyu ne ya had'ani da Baba Umaru wanda shi kuma ya zamo abokin kasuwancinsa daga arewa zuwa kudu. Baba Umaru ya rik'e ni tamkar shi ya haifeni dan haka wad'an nan mutanen biyu bani da kamarsu in kika cire mahaifana, Abdaullahi da Hadiza da kuma ke 'ya ta." "Allah ya kai haske k'abarinsu." "Amin." "To Mama ina danginmu na Sokoto?" "Suna nan." "Me yasa ba... "Uwata kada ki tsananta bincike domin na yi miki alk'awarin sanar da ke komi idan lokacin ki sani ya yi." "To Mama na kame bakina." "Da kyau, idan zaki sha furanki tana cikin fridge." Murmushi na yi jin ta sauya akalan zancen. "Ko sai zuwa dare zaki sha?" "A'a zan sha yanzu, bari in d'ibo kad'an." "Aha, sai ki zuba zuma zaifi dad'in d'and'ano akan saka siga." "To Mamana." Ina shan furar na dubi Mama wacce ke gyara zogale zata dafa mana wanda Hajiya Inna ta aikomin da shi domin na ce kwad'onsa na ke son ci da dare. "Ya dai Uwata?" Lashe lips na yi na amsa da "Ina burin na ganni cikin danginmu duk da bana son hayaniyar jama'a amma son ganina tsakanin kakanni, iyaye da abokanan wasa maza da mata wannan babban buri ne da ya jima a ruhina sai dai idan na nutsa cikin tunani sai wani lamari da na rasa gane kansa ya zo ya shafe burin ta hanyar jefani cikin fargaba har sai na ji ban son ganina cikin dangin baki d'aya sai na rik'a jin dama banzo duniyar ba." Banza Mama ta yi da ni domin tunda na fara maganar bata nuna zata furta kalma ba. Na matso jikinta na jingina ina sauke numfashi, still bata kulani ba sai na gyara zama a gabanta na ce "Zanso idan mun dawo Kwara mu tsaya a Sokoto inda halima ki barni a can na zaga dangi na birni da karkara dan samun ladar zumunci." "Allah ya kaimu lokacin amma zuwa Sokoto ba yanzu ba saboda ko wani tafiya nasa daban na ke son yi." Jinjina kai na yi ina wasa da ganyen zogalen da ta tsinke. "Uwata da magana a bakinki ko?" Kallonta na yi ta waremin idanu cikin jiran abinda zan fura sai na girgiza kai tare da tashi na shige d'akina ina murmushi. "Nana Khadijatu kenan, Uwata ta kaina, nasan damuwarki bai wuce zantukan da kika gamayi na yi banza da ke, affuwan Uwata bana da jarumtar biye miki ne." Mama ta furta tare da mik'ewa ta shige madafi. *** *Asabe da Hinde.* Asabe ce zaune a k'ofarta ta tsefin kai wanda da kyar ta ke kamo bindin korar saboda tsabar tsufar da ya yi gami da datti, Hinde kuwa tana nesa da ita tana gyaran gyad'an miya. "Hinde wallahi duk tijarar da na gani gami da iziya a hannun masu babbak'un kaya ban saduda ba ko misk'ala zarratin domin sai naga bayan Hurera kafin k'asa ya rufe idanu zanji dad'in a raina." "Yaya tamkar kin shiga zuciyata, tunanin da na keyi kenan yanzu, wallahi da abin na ke kwana na ke tashi musanman mijin da Uwani zata aura, gashi mutumin kirki sam abinsa bai rufe masa idanu ba da ganinsa ya san abinda yakeyi, hak'ik'a zataji dad'in zama da shi, Hurera zata huta fiye da zatona, zata tabbata cikin jin dad'i mu kuma 'yan maula domin ko Malam sai yarda ta yi da shi dama ya lafiyar giwa balle ta yi hauka." "Hinde kin sosamin inda keyimin k'aik'ayi, billahil azim ji na ke tamkar in wayi gari acemin Alhaji Muhseen ya mutu na rantse da sai na yi rawa da juyi dan Hurera taga samu taga rashi kenan a lokaci d'aya." "Ai idan zaki bani had'in kai na rantse sai dai ya auri wata amma ba Uwani ba, domin nafi jin takaicin ni'imar da zata shiga muna kallo tamkar tumakai." "Ina tare da ke 'yar uwa, tunda mun samu ya yi mana yayyafin naira muyi jari to mu had'esa kaf mu fantsama neman sa'ar datse wannan bak'ar alak'ar domin ba zan kirashi da fari ba." Wata dariya Hinde ta b'arke da shi wanda ya bawa Asabe tsoro ta shige d'akinta da gudu biyo bayanta Hinde ta yi tana cigaba da dariyar tamkar ta sami tab'in hankali nanko ras ta ke tsabar jin dad'in kalaman Asabe ce. *** "Yaya Aliyu kabi umurnin Hajiya domin ta yi rantsuwa ba zaka auri kowa ba sai Amira." Numfashi ya sauke ya kafe Salma da ido "Me Hajiya ta aikata a gidan su Khadija wanda ya janyo ta sakani a black list ko na kirata bai shiga na ganta a online na yi mata magana ta yi blocking d'ina na sanja layi na kirata tana jin muryana ta kashe na tura sak'o ta wayar K'awarta Fanta ta k'i dawomin da amsa, maza sanarmin da abinda Hajiya ta aikata musu da ya janyo na fuskanci wannan lamarin. "Kayi hak'uri Yaya ba zan iya sanar maka ba saboda nayiwa Hajiya alk'awarin kame bakina." "Zanje gidan yau da kaina in yaso zanji komeye a bakinta." "Kada kaje saboda Mamanta ta fusata zuwanka zai zamo zubewar mutuncin Hajiya ce domin ta ce idan ta isa da kai ta hanaka zuwa gidan, kenan zuwanka tamkar Hajiya bata isa da kai ba ne." "Duk me ya kawo wannan zantukan daga zuwa dubiya?" "Wanna tambayoyin Hajiya ke da amsoshinsu kuma ya kamata ta amsa maka domin ina zargin da abinda ta ke b'oye mana wanda ya shafi Khadija domin da kunnuwana na ji aunty Zainab na yi mata rantsuwa akan wani abu na so jin abin amma Hajiya ta sauya zancen tare da rufeni da fad'a dan na nemi k'arin bayani." "Zainab zan sama naji munafuncin da ta k'ulla domin tunda ta gano Khadija ce wacce na ke so na hango tsanar lamarin a idanunta, kuma wallahi idan ta yi sanadin rabani da wacce na ke so rayukanmu zasu b'aci matuk'ar b'aci." "Kabi komi a sannu Yaya amma ina ji a jikina Deejah ba matarka ba ce." "B'acemin da gani ko in nad'a miki duka! Wawiya kawai wacce ba'ajin alkhairi abakinta sai sharri." "Ni d'in Yaya?" "Zaki fice ko sai na zubda miki da hak'ora?" Cikin fushi Salma ta bar d'akin tamkar zata saka kuka. "Ina cikin tsaka mai wuya ni Aliyu." Ya furta tare da sake dialing number Fanta haka ya gama ringing ba'a d'aga ba, kwanciya ya yi na cigaba da kiran wayar amma baiyi dacen an d'auka ba balle ya rok'eta ta had'ashi da Deejah. "Why Hajiya? Kin san yarda na ke jinta a ruhina kuwa? Wallahi ba zan auri wacce kike muradi ba domin ban tab'a kallonta a matar da zan aura ba sai k'anwa." "Zakata tabbata ba aure kenan in har baka auri d'iyar d'an uwana ba wallahi ba zanyi kaffara ba kai da aure sai in anayi a lahira sai dai kuma in zakayi ba da sa albarkana ba wannan kam sai ince na barwa duniya kai babu ni babu kai har abada." "Hajiya me yasa kika sanja daga mai k'aunar farin cikin 'ya'yanki zuwa kishiyarsa?" "Son k'ulla zumunci ya sanjani kuma ba zan tab'a dawowa ba dan haka zab'i ya rage ga mai shiga rijiya, walau kayimin biyayya ka auri jininka Amira ko ka band'aremin na barwa duniya kai tare da yima tofin jeka ka gani." "Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un! Hajiya wai me ye haka kikeyi?" "Idan ka gama yanke shawara ka sanarmin wallahi ba zan matsa maka sai ka so cikar burina ba amma dai ka tuna zab'i biyu na baka kuma duk wacce ka d'auka zan amsa da hannu biyu." Tana fad'ar haka ta fice daga d'akin. Kuka ya fashe da shi mai sauti baya ko jin kunyar k'anninsa su jiyo shi. "Zainab!." Ya ambata cikin kaushin murya. Wayarsa ya laliba ya doka mata kira bugu d'aya ta d'auka cikin karad'in cewa "Angon Takwara my in-law kana  lafiya?" "Abinda kikayimin Allah ya yi miki fiye da shi, Allah ya sanyo k'unci a ruhinki sama da wanda kika jagoranci dasamin, Allah ya kawo sanadin da mijinki zai gano b'oyayyen halinki na raina masa Mahaifiya, Allah ya karya k'adarinki ki gamu da gamonki ta hanyar da bakiyi zato ba." "Me ke damunka Aliyu?" "Allah ya isa tsakanina da ke kuma k'anwarki ba dai taji dad'in zama da ni ba, wawiya kawai bulutu mai saka khairan da sharran." Kafin ta sake furta kalma ya datse kiran. Sai numfashi ya ke saukewa cikin furzar da huci, key d'in mashin nasa ya d'auka ya fice tamkar zai kifa. Zainab kam kuka ta fashe da shi cikin durawa Aliyu zagi tamkar ba yayata ba, ganin hakan baiyi mata ba ta kira Hajiya ta rattafa mata k'arya da gaskiya. Shiru Hajiya ta yi bata da niyyar cewa komi saboda yarda ranta ya b'aci. "Hajiya wallahi in wani abu mara kyau ya sameni bakin Aliyu ne." "Zaizo har gida ya baki hak'uri d'iyata, ki daina kuka insha Allah ba abinda zai sameki sai alkhairi." "To Hajiya nagode." "Na ce ki daina kukan nan." "Na bari." "Da kyau, ki shafamin kan jikalleta." Bata amsa ba Hajiya ta kashe wayar tare da neman Aliyu aka sanar mata wayar a kashe ne. Tsaki ta ja ta cije leb'en k'asa cike da takaicin rashin samunsa. Aliyu kam na fita gidan su Deejah ya nufa sai dai ya aika yara har uku ana dawo masa da amsar bata nan alhalin duk in ya tambayi yaran sun ganta suna amsa masa da ita ce ta ce a ce masa bata nan. Garin yaji na juya masa ya samu dakali ya zauna ya tsirawa bishiyar ced'iya da ke nesa da k'ofar gidan ido tamkar mai irga rassanta nan kuwa lulawa ya yi cikin tunani. "Kai! Me kakeyi a nan?" Muryan Baba ya katse masa tunani. Firgigit ya yi tare da zubewa yana gaisheshi. "Lafiya, daga ina?" "Abokin karatun Khadija ne." Ya sami kansa da furta hakan. "Oh bari aturo maka ita dan nasan kazo gaisheta sa jiki ne ko?" "Eh, Baba." "To jirata." Da idanu ya raka Baba yana zabga masa albarka a cikin ransa. Yana tsaye na fito fuska a had'e. Wawan ajiyar zuciya ya sauke ya taho da hanzari tamkar zai rungumeni na koma da baya cikin zaure da sauri ya rufa min baya, ganin zan koma cikin gida sai ya rik'o hijabina na juyo idanuna na zubar hawaye na had'e hannayena alamun rok'o na ce "Dan soyayyarka da fiyayyen halitta Aliyu ka rabu da ni rabuwa ta har abada." "A'a Khadija, kada kiyimin haka, ruhunanmu bazasu d'auka ba dan Allah ki saurareni." "Aliyu lamarin mahaifiya dabanne da na kowa dan haka na ke baka shawara da kayi mata biyayya tamkar yarda na yiwa tawa Mahaifiyar na tabbata zamuga haske cikin rayuwarmu." "Khadija kin amince zaki iya rabuwa da ni?" Shiru na yi masa saboda bakina ya yi nauyin amsawa Amma ba wai dan bazan iya amsawa da a'a ba ne sai dan ina ganin cin kuska ne na amsa masa kai tsaye. "To ni bazan iya hak'ura da ke ba ki rubuta da k'aunarki zan koma ga mahaliccinsa." Kuka ne ya kufcemin ganin yarda ya ke furta kalamin da iya kacin gaskiyarsa. "Koma ciki kai kuma tafi kayiwa mahaifiyarka biyayya dama Uwani ba sa'ar aurenka ba ne Allah ne ya baka ita har ta soma kulaka sai kuma somuwar Uwarka ta yi sanadin b'ata komi saboda son zuciya." Tsit mukayi muna kallon Baba da ya shiga tsakiyarmu ya raba tsakaninmu yana mazurai. Hannun na d'aga masa alamun bye na shige gida da gudu shi kam zubewa gaban Baba ya yi ya ce "Baba kayi wani abu akai wallahi jna sonta, itama tana sona." Mik'a masa hannu Baba ya yi Aliyu ya zaro idanu kai Baba ya gyad'a. "Ban fito da kud'i ba Baba kayi hak'uri zan kawo maka." "Zaka iya tafiya kuma wannan shi ne rana ta k'arshe da zaka sake zuwamin k'ofar gida tunda matsiyaci ne kai." "Baba kayi hak'u... "Kaci Uban Uwarka mataccen nan na ce kaji ko?" Baba ya gabgowa Aliyu zagi cikin nad'e hannun riga, alamun zai bugeshi. Da gudu Aliyu ya fito zauren ya kunna mashin d'insa ya bar unguwar amma yana jin aransa ba zai iya rabuwa da Deejah ba. *Assalamu alaikum, 'yan uwa Barkanmu da warhaka ga wata dama ta samu mai burin dogaro da kansa. Shahararren kamfanin nan na oriflame na yin  registration kyau a wannan wata duk mai burin a dama da ita ko shi a harkan siye da siyarwa na kayan kamfanin a samu riba Mai yawa ko yin amfani da kayan domin jin dad'in rayuwa to wannan babban damace a gareku, maza ku garzayo ayi muku register kyauta kafin wata nan ta November ya k'are domin in ya k'are sai kun biya kusan 5k kafin ku samu damar zama 'yar kamfanin masu 'yanci dan haka ku taho dan zama masu 'yanci a kyauta. Domin k'arin bayani ku tuntub'i wannan number 08131166848.* [11/7, 2:06 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Safiyya (Mrsjmoon) E.W.F. Page 23 "Ina uwani ta ke? To maza kizo ki bud'e kunnuwanki da kyau ki saurari kalamina akan matsiyacin yaron can." Ina jiyo Baba daga cikin uward'akan Mama amma ban motsaba saboda wani haushin shi na ke ji duk kuwa da yarda na ke korar lamarin amma sai k'ara nitsawa ciki raina keyi. Jiyo sabon hargaginsa yasa na tashi daga kwancen da ni ke na tallabe kumatuna hawaye na cigaba da wankemin fuska tamkar an fud'e famfo. "Narabaki da wannan matsiyacin yaron na fad'a na k'ara tabbas na rabaki da shi domin baida komi sai k'wambon banza da k'arya da ganinsa ba zai iya rik'eki ba balle har mu sami ihsani daga gare shi, d'an gidan matsiyata ne wanda ke neman cin yau babu na gobe dan haka nima ina bayan Mamanki ki fita sabgarsa ki auri mai arziki wanda zan fanshe rainonki da na yi, a yau ina bayan cikar burin Hurera wato auren mijin da ya kerewa sa'a wato d'aya tamkar da million ba dubu ba, kamar dai Alhaji Muhseen ko ma wanda ya zartashi inda darajana zai k'ara hauhawa duk inda na ratsa ayimin fad'anci tamkar basarake dan ina da suriki ishasshe wanda ya kama k'asa, gagara badau wanda arziki ya yiwa mayafi ya barranta da talauci." "A'uzubillahi! Malam me kake ambata haka? Dama jari muke nema da ita ko me? Wani talauci garemu da zamu jira sai mijin Uwata ya bamu abin duniya? Malam dan Allah ka sanja sam wannan son abin duniyar naka bai da kyau, ba haka musulunci ya tsara mana da mu nemi duniya ba, wallahi ina jiye maka fad'awa halaka akan wannan makauniyar d'abi'a naka wanda baka bar kowa ba tamkar ba masanin illimin addini ba." "Na fahimci bak'in cikin da kikeyimin ya wuce iyaka Hurera, bayan kina son amshe dukiyanki ki mallakawa Uwani ta yi arzikin da kikeyi mata fata shi ne ni kike son na talauce tamkar b'eran masallaci, to wallahi baki isa ba, kinyi kad'an ki zamenin inuwar giginya na nesa kasha dad'i, na rantse da Allah sai Uwani ta zamemin jari kamar yarda ta zame miki hanyar bud'ewar k'ofofin samu tun bata san kanta ba wanda kike neman maida mata da kayanta na koma a huhun ma'ahu, ba wan ba wan karatun d'an kama, na yiwa duniya zuwar zomo yarda na zo a guje na koma a guje, to da sake wai anyiwa mai dami d'aya sata, dole ne ki sanja tsari a game ta amshe dukiyanki ko kuma Uwani ta zamemin jari ko zab'i na k'arshe shi ne na tafi masallaci na yi shela ga mai son sadakar aurenta na bawa ko waye ko da kuwa Makaho ne, Kuturu ne, Gurgu ne, Bebe ne kai ko duk wanda ya had'a duka nak'asar ne indai ta zamo rabonsa zan bashi ita Sadakarta." "Malam! Kana cikin hankalinka kuwa?." "A'a sama na ke cizo." "Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un, wai shin har sai yaushe zamu sami kwnaciyar hankali daga sababinka ne Malam? Shin son kud'i hauka ne?" "Kanki akeji Hurera abinda na sani ne indai ni Uban Uwani ne dole ki barni na yi duk yarda naso da ita tunda bak'in jininta ya ta'azzara ta zama uwar mata a gabanmu muna ta ibada da haramtacce ruwa." "Me ka ke nufi da kalamanka Malam?" "Abin da jahilan farko sukayi ittifa'i." "K'alu innalillahi wa inna ilaihin raji'un! Kana nufin ka zama irinsu kenan?" "Ke! Hurera shiru-shiru fa ba hauka ba ne, kada kiga na baki dama kina jefomin tambayoyi ki d'auka na zama mijin ta ce ne to ina nan a tsayena tamkar Nonon maza ban rankwafa ba ko na kafan allura dan haka wallahi ki shiga hankalinki da ni ko allura ta tono garma, sirrin b'oye ya fito fili a yi walk'iya kowa ya ga zahiri, idan kuma kin musanta to ki cigaba da tsayawa a gaba kina furtamin duk kalaman da suka zo bakinki ni kuma zan shayar da ke zumar mamaki ba Madara ba domin terere zanyi ma'ishi ban da abin kaico." "Allah ya shirya ka." "Amin, yin la'asar yafi miki ko inyi bankad'a, kuma dole ki bani wani kaso a dukiyarki domin dogaro da kaina ko in hau munbari na fed'e biri har wutsiya, in na ce har wutsiya to tundaga salsalan zan soma tareda bada damar duk wanda bai fahimta ba yazo na yi masa bayani gamsas-shiya." "Malam me ka sha ne yau?" "Abin da tunaninki ya baki." Shiru Mama ta yi jikinta asake hakan da Baba ya hango ya sake bud'e mata wuta da barazana ta wani sigan mai tab'a zuciya wanda ya sanyani fitowa idanuna cike da hawaye na russuna gabansa na ce "Dan Allah Baba kayi shiru kaga makwafta na iya jiyo harshenka sannan ni ta kace tayimin duk hukunci da kaso ba mai hanaka dama kyawun mijin d'iya na farko ya zamo zab'in mahaifinta ne, na amince Baba ka yi sadaka da ni ga kowa zaka sameni mai biyayya ga zab'in ka ni dai fatana rashin jituwar da ke samuwa tsakaninka da Mama ya zo k'arshe, hankalin mahaifana ya dawo wuri d'aya yarda zasu kashe su rufe ba mai ji." "Uwata ta shi ki koma d'akin ki bana son shirme." "Mama kiyi hak'uri yau komi yazo k'arshe walallahi bana son wannan rayuwar da mukeyi na sababin Baba." "Na ce ki koma d'akin ki ko ki tafi wurin Fanta." "Da dai kin barta taji komi saboda lamarin ya shafeta kinga daga nan za... "Malam na rantse da wanda ya haliccemu zan wulak'an... "Mama ki bari, miji darajarsa daban ya ke nasan kin sani to dan darajar mai daraja Manzon farko da k'arshe ki daina d'aga harshenki sama da nasa domin hukuncin Allah zai sauka kanki kai tsaye batare da duban 'yancinki kike karewa ba." "Allah ya yi miki albarka Uwata, nagode ainun da tunasarwa, maza tashi ki tafi wurin Fanta ina son samun masalaha da Malam." Kallon Baba na yi ya zunkud'a kafad'a sai na maida kollon kan Mama ta murmusa tare da bani umurni da hannu wato na tashi. Mik'ewa na yi na koma d'akina na fito da hijab na yi waje amma ba gidan Uncle na nufa ba, titi na mik'e ina zantukan zucci ganin ina ta tafiya mutane na rakani da ido sai na tsaida mai Napep na sanar masa da inda na nufa wato gidan Baba Umaru domin kalaman Baba sun tsayamin a rai ina burin sanin fashin bak'insu a bakin Hajiya Inna domin na tabbata ta san komi. 'Fed'e biri har wutsiya, tereren bankad'a, abin b'oye ya fito fili, allura ta tono garma.' Sune kalaman da na ke ta maimaitawa a cikin zuciyana, ina mai burin jin fashin bak'in su. *** Deejah na fita Mama ta nuna Baba da yatsa cikin b'acin rai ta ce "Duk abin da ka shirya Malam tafi kayi amma ka sani hukuncin mai karya alk'awari zai hau kanka kuma zan kai k'ararka wurin wanda baya barci balle gyan-gyad'i wato Allah sannan ka tuna Allah na amsar addu'ar wanda aka zalunta nan ta ke, a k'arshe ina yima albishi da cewa Aurenmu guntilalle sunarsa dan na fahimci ka manta yarjejeniyarmu sanan kamar yarda ka tonamin asiri nima zan tona naka, muzuba shege ka fasa d'an halas sai yanka, zamuga wanda zaifi kunyata a idon duniya." Baki bud'e Baba ke kallonta har ta dasa aya. "Sharri zakiyi min ko me Hurera?" "Au sharri ko? Tam ga fili ga mai doki ai wanda ya fasa aikata nufinsa ba d'an hakas ba ne." "Hurera kinfi kowa sanin banda tambon abin ash-sha dan haka ki gama borin kunyarki ki dawo kan hanya domin ba mai hanani samun rabo a cikin dukiyarki." "Sai Allah da ya haliccemu, shi ne zai hakana samun rabon nan." Mama ta bashi amsa idanu soye cikin rashin tsoro na ban mamaki. "Shi kenan muzuba mugani." Ya ambata cikin buga babban rigansa. Har ya juya zai tafi Mama ta bi bayarsa da sauri ta rik'o babban rigarsa ya juyo a fusace sai ta fad'a k'irjinsa ya ko rungumeta tsan-tsan yana sauke numfashi saboda duk tsiyarsa yana son Mama matuk'a, sun jima a haka sannan ya d'agota ta k'ara lafewa tare da yin d'age ta kai bakinta cikin kunninsa ta yi masa rad'a lamarin da ya sanya shi tureta yana gwama numfashi cikin nunota da yatsa sai dai ya kasa furta kalma saboda nauyin da harshensa ya yi. Barin masa wurin ta yi jikinta a mugun sanyaye. 'Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un, Malam, a she dai shi d'in ne ba wani bare ba, wayyo ni Hureratu naga takaina, wannan wacce irin rayuwa ce na ke kan fuskanta? Ba laifi na ba ne, tun daga tushe bansan ta inda aka hau balle saukan amma k'addarar bata sanja zani ba, Allah Astagafirullah.' Sune zantukan zuccin da Mama ke ambata har ta isa d'akinta ta yi masauki a bakin dago tallabe da kumatunta duka biyun, hawaye na bin samansu.   Baba kam zama ya yi a k'asa dab'as kamar kayan wanki dafe da k'irjinsa wanda ke bugawa da k'arfi, addu'a ma ya kasa ambata haka kunnuwarsa sun kasa yarda da abinda Mama ta furta masa, ya jima zaune sannan ya tashi tsaye ya k'urawa hanyar zaure idanu zuwa can harshensa ya motsa. 'Ta ya hakan zai faru? Kai dole na san inda kaina ke ciwo, wallahi ko zan rasa rayuwata ba zan bari Hurera ta fidda bak'in labarin nan ba, Anya Hurera bata da shafan shed'anu kuwa?.' Amsar da baibawa zuciyarsa kenan ba ya zabura ya fad'a d'akin Mama a fusace. Tana ganinsa ta mik'e ta bi gefensa ta fice zuwa d'akin Deejah ta murza key saboda in har ta tsaya za'a iya haifar d'a mara ido dan ta tabbata yarda ta kekijin zugi a zuciyarta abin da bai tab'a faruwa da su ba shi ne zai afkuwa wato fad'a da duka. *** Ina isa k'ofar gidan Baba Umaru kiran Mama ya shigo wayana na d'auka tare da sanar da ita inda na tafi. "Uwata kada inji zancen komi ya fito abakinki idan har kina son zaman aurena da Malam ya yi k'arko." Shiru na yi zuciyata na kuma d'aukan zafi. "Idan kinsan ba wanda ya ganki to ki juyo domin kina shiga Hajiya Inna zata gano da matsala ta sanarwa da Baba shi kuma ya yi alk'awarin raba aurenmu duk in wata matsala ya kuma fillowa a tsakaninmu, na san kinfi kowa son zamammu da Malam ya d'ore." A jiyar zuciya na sauke tare da cewa mai Napep "Juya dani inda ka d'auko ni." "Allah ya yi miki albarka." "Amin." Na amsa cikin rawar murya. A kwanar fita layin motar Kawu Habibu ya sha gabanmu, k'iris ya rage  bamu fad'a masa ba salati muka ambata da k'arfi, ni da mai Napep "Kalli wani banza dai." "Yi hak'uri Malam Kawuna ne." "Amma dai bai da lafiya ne ko?" Ban amsa masa ba na hango fitowar Kawu, yana isowa ya mik'awa mai Napep dubu d'aya tare da cewa "Sauketa, Allah bada sa'a." Godiya ya yi masa amaimakon zagi dana zata zai auna masa tamkar yarda ya soma ' Kud'i kenan, masu gidan rana.' Na ambata cikin raina sannan na fito na shiga motar, maimakon mu nufi hayar gida sai ya juyo dani gidan Baba Umaru. "Ka kaini gida ne Kawu." "Hajiya Inna ta umurceni da in kawo mata ke domin Annur yaron Yaya Shafi'i ya sanar mata da zuwarki tare da komawarki batare da kin taka k'ofar gidan ba." Lumshe ido na yi ina tunano abin da zansanar mata domin kare martaban auren Mama wanda na ke burin ganin ya inganta har zuwa mutuwa. "Ina son Mata mai halayyaki Khadija." Ban bud'e ido ba amma na tabbata kallona Kawu keyi. "A yau kuma a yanzu na k'ara nutso da son k'ara aure da mai kamanninki sak ko da ta hayayyane ba sai lalai mai siffarki ba." Zillo zuciyana ta yi na bud'e ido da sauri na kafeshi da su. Dariya ya kyalkyale da shi tare da dukan steering, na yi kwal-kwal da ido zan fashe da kukan dama na ke cikinsa, ya yi saurin kunna wayarsa karatun Qur'ani ya bayya cikin sural Ankabut. Lum na yi ina bin karatun cikin raina ina maijin natsuwa na rab'ata. Sautin fitar murmushinsa yasa na kalleshi ya motsamin kai "Duk kan damuwa maganinsa na cikin sauraren zancen Allah ko tilawarsa dan haka kada ki sake damuwa ya yi sanadin rayuwarki abanza batare da kin cikawa Mamanki burinta ba na yiwa 'ya'yanki tawai." "Nagode Kawu da kayi sanadin natsuwa ya nashe ruhina." Jinjina kai ya yi tare da yin parking a k'ofar gidan sannan ya maido hankalinshi kaina ya ce "Ba Hajiya Inna ta ce in daukoki ba ni da kaina naga zuwarki tare da komawarki shi yasa na dawo da ke domin inji dalilin zuwarki sannan kika koma batare da kin shiga cikin gida ba." "Kawu yawan bincike haramun ne to ka barshi a sirri ne." "Shi kenan Dije na bar kaza cikin hashinta domin kada in figeta na gano kwarangwal ce." Murmushi na yi jin yarda ya yi zancen cike da tsokanar da ya saba. "Yanzu taho muje ki gaida su sai in maidaki gida." "Hajiya Inna zata tambayi inda muka had'u kuma kasan ban iya k'arya ba." "Haka ne shi yasa na ke k'aunarki tamakar rai da ajali." "Kawu dan Allah ka bari wallahi zanyi maka kuka." "Oya maza kiyimin kukan tsun-tsu Kanari ni kuma na shagala da saurarenki na yi ta dilalan yamu tamkar dolo." Da sauri na bud'e k'ofar na fice ina murmushi ya biyo bayana yana dariya muka jera ya yi k'asa da murya "Kada kiyi magana ko ta tambayeki daga inda muke, ni zan amsa domin na iya girba k'arya tamkar kud'in duba, right?." Ware ido na yi ya kauda kai gefe cikin cewa "Zanyi Istiggifari da dare kinsan Allah gafurilul rahimun ne." Ban tanka ba ya mintsili fatar wuyana na kwabe fuska ya kyalkyale da dariya domin shi mutum ne wanda dariya baya yi masa wuya ga tarin tsokana duk da ina jin kunyarsa amma haka nan ke takuramin da tsokana duk in mun had'u. "Wa na ke gani da darenan kamar Mariliya?" "Ita ce fa Inna gata nan Gawa tak'i rami ba, na tsinto miki ita a gaban tukuban mai tsire wai kwad'ayin cin nama ta ji ta fito batare da Yaya Hurera ta sani ba, bata ko jin tsoron 'yan iskan gari suyi wuf da ita mu shiga gararin nemanta har birnin sin." "Amsa naka Habibu wai meyasa ka maidamin da Takwara abokiyar wasarka ce?" "To Inna ai kyawun Uba ya sake da d'iyoyinsa ba yawan sababi ba, dake janyo tsana a tsakani." "Kawu ka bar cimin fuska dan Allah, shima Baba zai daina sababin insha Allah." "Kingani ko Inna? To na kame bakina mai Baba sarkin sababi har da na sari." Duka na kawo masa ya gofce Hajiya Inna ta nuna masa k'ofar fita ya taho kamar zai fad'a jikinta ta rafka salati ya dawo da baya ya zauna saman Cushing yana kyal-kyalan dariya, nima dariya lamarin ya bani na murmusa. Gaisar da Hajiya Inna na yi ta amsa cikin wal-wala tare da tambayata lafiyar Mama. "Alhamdulillah." "To masha Allah." Abinci ta kawomin tuwon shinkafa da miyar yauk'i sai farfesun k'ashin Akuya mai taushi sai k'amshin kayan k'amshi ya ke fitarwa. Tare da Kawu Habibu mukaci tuwon a kwano d'aya saboda ina cikin ci ya tsoma hannu duk maganar da Hajiya Inna keyi masa bai kulata ba, sosai lamarin nasu ya burgeni sai naga tamkar ni da Mama masu fahimtar juna. Gyaran muryan Baba Umaru ya ratso kunnuwaemu, duk muka natsu tare da zubawa hanyar idanu. "Habibullah Kawun kawai, to maza taso inbaka sak'on Malam Isuhu kada in manta." "To Baba dama ina son magana da kai domin na yi Mata kuma mai hanani aurenta sai mutuwa ka zamo shaida tamkar yarda na sanar maka a garin Kwara." "To Habibullah, Allah yasa abokiyar arzikinka ce dan nafi kowa farin ciki da lamarin." Sark'ewa na yi Hajiya Inna ta mik'omin ruwa na sha, ta rufe Kawu da fad'a shi kuwa ya soma zabgomin harara fuska a had'e, Baba kam girgiza kai ya yi tare da barin k'ofar ganin haka sai na rufa masa baya da hanzari ina cewa "Muje in gaisar da tsohon arziki Uban Mamana." Kawu Habibu ya tashi tsaye zai biyo bayana Hajiya Inna ta daka masa tsawa ya koma ya zauna cike da ladabi ya tsira mata ido ba k'iftawa lamarin da ya razanata domin ta hango gaskiyan kalamansa cikin idanunshi. Alhamdulillah anan muka kawo k'arshen free pages. Kamar yarda na sanar daku zaku sami ruwan kyautar pages to gasu nan da fatan sun sanyaku nishad'i fiye da zato na. *Mun soma dai jin tsokacin labarin DAMUWATA to gundarin labarin na nan tafe  cikin cigabansa sai dai babban DAMUWARMU shi ne sanin waye mijin Deejah. Aliyu, Uncle ko Habibu ne? Uhm ba zance komi ba domin Deejah allura cikin ruwa ce mai rabo ka d'auka sannan mai rabon zai bada mamaki. Tambayar a nan shi ne ta ya hakan zai faru? Shin me ye sirrin da Mama ke adawa da fitowarsa fili? Ina labarin k'azamin nufin su Hinde da Asabe? Ina k'udirin Nafisa na b'atawa Deejah fusaka? Shin addu'ar Aliyu na tab'a Zainab kuwa?Duban tambayoyi gami da amsoshinsu masu tarin yawa duk muna dakon jinsu abakin Mama da ma wasu jama'ar da bamu kai ga jiyo sunayensu ba. Labarin DAMUWATA ba damuwar Deejah kad'ai ke d'auke da shi ba, damuwoyin mutane masu yawa ne masu halayyar mabam-banta tare da soyayya mai tafiya cikin salo na daban da sauran da kuka sani.* *Duk mai son cigaban labarin pay #300 to 0468069082 Haruna Safiyya GTbank or MTN card. Send the evidence via 08132166848. Update ba delay da yardan Allah S.W.A. Thank you fans, ina girmamaku iya girmamawa domin da bazarku na ke taka rawa. On 13 insha Allah zamu cigaba da posting ba kama hannun yaro. Bissalam sai mun had'u a paid group 😍* [11/7, 2:09 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) BY Safiyya (MRSJMOON) Labarin DAMUWATA: Labari ne mai nisan zango domin komi da mafarinsa dan haka warwaransa zai zamo mai fad'i ne. K'aunar uwa da 'yar ba kara zube ya ke ba da mafarinsa wanda ya kasance fansa ce ga wata rai mai tasiri a jiki da ruhi. (Ba'asan ta inda aka hau ba balle saukan) Kalma ce mai buk'atar li'irabi, gamsas-shiyar amsarta yana cikin Labarin DAMUWATA. Labarin DAMUWATA ba damuwar Deejah kad'ai ke d'auke da shi ba, damuwoyin mutane masu yawa ne kana masu halayyar mabam-banta kuma da soyayya mai tafiya cikin salo na daban da sauran da kuka ji da gani. Labarin DAMUWATA: Akwai wani zanen k'addara wanda ya ke tabbatacce daga Allah. Labarin DAMUWATA: Ya k'unshi abubuwa masu ban al'ajabi, takaici da nishad'i. Salon labarin na dabanne, tafiyar k'uran na cike da fikrah, kudai ku garzayo ku samu damar kantashi cikin 'yanci. Kada dai ku manta marubuciyar ta goge wurin warware zare da abawa tamkar dai a yarda ta saba tubka kuma ta war-wareshi tsaf a cikin littafanta kamar su: Rabi'atul Addawiyya Rashin jituwa Mutunci Madara ne Bak'on lamari Rumasa'u Mabrukha Dr. Laylah da sauransu masu matuk'ar fad'akarwa gami da nishad'antarwa. Pay #300 to 0468069082 Haruna Safiyya GTbank or MTN card. Send the evidence via 08132166848. Update no dealy on 13 insha Allah.