chapter 1 *DAƊIN ZAMA🍁* Book 1 Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites* *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) *Disclaimer: Ban amince a sauya min littafi ta ko wace irin siga ko a ɗaura min a wani channel na youtube ba tare da izini na ba, yin hakan babban kuskure ne kuma zai sanya na ɗauki tsatstsaurar mataki domin haka a kiyaye* _Any resemblance to any figure or event, deceased or living is purely coincidental_ *Special thanks to* Addah Ramlah (Mai dambu) Lubna Sufyan Sanah S matazu And my pen sisters Janafty and Maryamkitty💕 *Sincerely, To Aunty Hauwa Yarima. Allah ya so ki da rahamar sa🤍* بسم الله الرحمان الرحيم *Ga wanda ya rayu a cikin kalamaina tun kafin na rubuta, wanda ya kasance tsakanin kowani layi na wannan labari. My dear Brother Muhammad Inuwa Ahmad, wanda Allah ya jarabta da nakasar kurmanta ba don bayi ƙaunar sa ba. You’ll always remain an irreplaceable treasure in our lives, a beloved person in our hearts* 01….Lokaci ne da rana ke baza hasken ta a sararin samaniya. Misalin Ƙarfe ɗaya da minti Arba'in. zafinta kuma ya sanya wa’inda Allah ya hore wa na’aurar sanyaya wuri a cikin motocin su kunnata, tare ɗage gilashin motar domin samun sauƙi. Saidai irinta dake cikin napep, da ma wa’inda suke kan mashina da kekuna a cikin cunkoson, har sai sun ɗaura hannu a fatar jikinsu sun sharce gumin dake tsatstsafowa, bayan zafin da abubuwan hawan su ya ɗauka a dalilin tsayuwa a ƙasan ranan na tsawon lokaci. Hayaniyar da ake yi na buɗe hanya bayi samun shiga kanta saboda damuwan da ya riga ya cika shi fall. Idanunta suna kafe a kan wasu yara da aka sallamo daga makaranta, suna tafe tana bin su da kallo yayin da suke hira da ƴan uwan su cikin nishaɗi da ƙoshin lafiya. Har saida suka ɓace ma ganinta, sannan ta mayar da ganin nata kan wani ƙaramin yaro dake sanye cikin sabon uniform riƙe da blue ɗin lunch box shima sabo, yana tsalle-tsallen shi a harabar ƙofar makarantar su. Murmushi ne ya suɓuce mata ba tare da ta sani ba, a hankali ta furta “kaman Muftee na.” tana da tabbacin ba zai wuce shekaru uku zuwa huɗu ba. Ta rungume envelope ɗin da take riƙe da shi a ƙirjinta, tana cigaba da kallon yaron cike da sha’awa har wani mutum ya nufo shi. Yaron kuwa yana hango shi ya fara murna da tsalle, daga inda take tana iya jiyo sautin ƙaramin muryar shi yana faɗin “oyoyo Abba!”. Mutumin ya ƙarasa ya ɗauke shi ya cilla shi sama ya caɓe farin ciki bayyane a kan fuskarsa. A gaban mashin ɗinsa ya ɗaura shi, yaron yana ɗaga hannu ma sauran ƴan makarantar su baban ya kunna mashin ɗin suka juya hanyar da zai kaisu gida wanda shi babu cunkoso a kai, suka tafi cike da farin ciki wanda zafin rana bai kai ya narkar da shi a cikin zuƙatan su ba. Ɗumin hawaye ta ji a kan fuskarta, bata damu ta goge ba ta maida dubanta gaba domin ganin yaya cigaban ɓude hanyar yake tafiya. Saidai cece-kucen da ake yi tsakanin mai babban motar da ya biyo hanyar da ba tashi ba da nufin sauƙe kaya a gaban wani babban shago, da kuma mai mashin ɗin da a garin kauce masa ya bugi napep ɗin wani har ya cire masa madubi bai nuna alamun mai sasantuwar yanzu bane. “Komai na rayuwar nan fa ɗan haƙuri ne. Da sun buɗe ma mutane hanya ne mu wuce uzururrukan gaban mu” “Hajiya toh ke zaki biya shi ne idan bai tsaya ya karɓi hakkin shi ba?” mai napep ɗin da suke ciki ya juyo ya fuskanci dattijuwar dake zaune a tsakiyar su yana sosa kunnen shi da wani ƙaramin kara da ya ɗauka a ƙasa. “Toh mu menene namu a ciki da za’a tare mana hanya?” ta mayar mishi da da martani. Budurwar dake ta ɗaya gefen dattijuwar kuwa hankalinta a kan wayar hannunta sai faman jero tsaki take yi. Rayuwa kenan, kowa da abinda ya dame shi. Ta sake maida dubanta kan envelope ɗin dake hannunta. Ita kuwa da sun san girman uzurinta, da shi kaɗai zai sanya su yayyafa ma zuciyar su ruwan sanyi su bude hanyar nan. Ba abin tace zata sauƙa daga nan ta ƙarasa da sawayen ta ba saboda akwai sauran tafiya a gabanta sosai. Kuma bata da kuɗin tare wani abun hawan a gaba, wannan ma saida ta haɗa da canjin hannun Khausar kafin ta samu wanda zai ishe ta zuwa da dawowa. Fatan ta bai wuce idan ta samu ganawa da wa’inda zata je wurinsu ba su amsa buƙatun ta. Da sun ceci rayuka har biyu kuma zata ƙare rayuwarta tana gode musu. Daga wani ɓangaren kuwa, akwai wanda da gaske yana da tabbacin cewa nashi uzurin, idan aka haɗa na duka mutanen dake da niyyar bin wannan hanyar a wuri guda, ba zai kai kaso ɗaya bisa goma cikin nashi ba. Shiyasa bayan faman danna horn da yake yi yana cika musu kunne, har wasu na haƙura da sanyin na’urar motocin su na ɗan lokaci su fito cikin zafin ranar domin ankarar dashi gajen haƙurin shi, ta hanyar rage nasu ɓacin ran a cikin muryoyin da suke ɗaga masa. Ko a jikin shi, domin ba jin su yake yi ba. kasancewar shima kamar su, gilashin motar shi a rufe yake. “Da ana filfili a wuce da baka saka wa taka motar fuka-fuki ba?” cewar wani yana ƙarasowa ɓangaren da yake saka ran hango matuƙin motar, ya ga wani mai ido da tozalin ne. A ɗan tsakanin aka samu nasarar lallaɓa masu rikicin da su koma gefe a sasanta, hanya ta fara buɗewa, wa’inda ke ta gaba-gaba suka fara kunna abun hawan su da shirin barin wurin da zaran sun samu dama. Saidai su jiran daman suke yi ya iso gare su da kan shi. Amma ga wanda yake ganin duk wani daƙiƙa da ya ɓata a hanyar tazara ne mai yawa yake ƙaruwa tsakanin shi da isa ga zaren da ya ɗinke rayuwar shi, ya hana shi yagewa filla-filla a lokacin da yake tunanin asirin shi ya gama tonuwa duniya ta yi mishi tsirara. Mutum irin wannan ƙirƙiran dama yake ma kan shi, koda kuwa a lokacin kowa ya tabbatar masa da ba zai yiwu ba. Hanyar da faɗinta ya bada damar wucewar mashina da kekunan yara ƴan makaranta ne kawai, ta cikinta ya hango faragar da shima Highlander ɗin da yake ciki zai wuce. Don haka bai yi shawara da kowa ba ya bawa motar wuta tare da matse horn, a lokacin da ya zugi gudu sauran ƙadan yayi ciki da mutumin da ya tunkaro motar, shikuwa ya saka kai ba ji ba gani. Ba zallan na tsakiyan cunkoson wa’inda har iskar wucewar motar tashi saida suka jita a fuskokin su, ga ƙirjin su dake luguden farbaga, da godiya ma Allah da ya sanya bai bi ta kansu ba. Har su da suke gafen hanya saida suka bi ƙurar da ya rufawa motar baya da kallo baki sake, tuni ya riga ya ɓacewa ganin su. “Ku ga wawa jahili” “ga wani banza mara hankali” Kaɗan kenan daga cikin kalmomin aibantawa dake fitowa daga bakin wasu kafin ƙurar ta kai ga lafawa. Amma marasa lokacin ɓatawa su ma sun bi jagorancin shi ne sau da ƙafa suka ɓulla hanyar da ya buɗe musu don ɗorawa a kan sabgogin rayuwar su bayan ɗan tsaikon da aka samu. Har zuwa lokacin da suka isa wurin da ta kwatanta mishi, bayan sun sauƙe budurwar nan a ƙofar wani shagon kwalliya, mai napep ɗin da ya ɗauko su bai fasa mita a kan motar da ya wuce su ɗazu ba. A ko wani layi na cikin zancen sa kuma sai ya zagi masu ƙudi da iskar da ya ɗebo su. Da a cikin nutsuwarta take, da ta ce mishi ba don wasu masu kuɗin ba, da wasu da yawa daga cikin wa’inda Allah bai horewa wata mafita ba baza su rayu ba. Irin su Muftee. Sauƙa tayi ta biya shi hakkin shi, kana ta juya ta nufi masu tsaron wurin da ya dace da kwatancen da aka yi mata, tana ƙoƙarin ciro takardan dake cikin envelope ɗin da tayi dakon shi. “Sannu da aiki officer” ta gaida su cikin girmamawa. Dukkan su suka amsa da “yauwa” kana suka bata hankalin su domin sauraron abinda take tafe da shi. Matsawa tayi wurin wanda ya fi kusa da ita, tana miƙa mishi ɗaya daga cikin takardun hannunta take faɗin “Hajiya Surayyah Kagarko nake son gani, tace in zo in same ta a nan” Duban takardan yayi a tsanake, takardan asibiti ne da bayanan lafiya na majinyaci mai suna Ibrahim Hashimu Baniza, mai shekaru huɗu. Ta ɗan cize leɓenta na ƙasa tana jiran amsar da zai bata, ko idan zai gane ƙarya take yi. Domin maƙwabciyar ta a children ward wanda itama take kwance da ƴarta a gadon dake gefen nasu, ita ta bata shawaran idan ta zo ta nuna cewa kiran ta suka yi ba niman allfarma tazo ba. Shiyasa ma ta bata sunan matar da tazo asibitin, a ranar da aka yi rashin sa’a ta tafi gida da muftee tayi mishi wanka ta samu ta huta kafin likitan shi ya zo duba shi da yammaci, saboda a ranan babu wani a kusa da shi bayan ita ɗin kuma an cire mishi ƙarin ruwa. Su kuma duk yanda aka yi dasu su saka ta a cikin list ɗin wanda za’a tallafawa da jinyan yaransu sun ƙi. Da cewar ba zasu yi amfani da information ba kawai ba tare da sun ga patient ba, sanin halin damfara na mutanen mu. Kafin a kirata ta dawo asibitin kuwa har sun tafi. Tun daga wannan rana take ta fafutukar yanda za’a yi su dubeta don tana buƙatar taimako matuƙa. Da tallafin su ne kawai muftee zai samu jinya mai kyau ya kasance cikin ƙoshin lafiya na tsawon lokaci. Har ɗan wani abu ta haɗa ta bayar wa mutanen da suka yi alƙawarin mata hanya zuwa ga masu A&I support organisation amma abu yaci tura, gashi gobe ake zancen zasu fara rabon tallafi. “Kin san inda zaki same ta ai?” tambayar tashi ya bata mamaki domin tayi tunanin zasu nemi ƙarin bayani kafin su barta ta shiga, shiyasa bayan addu’o’in da take ta nanatawa a cikin ranta take ƙoƙarin haɗa kalaman da zata gamsar da duk wanda ake buƙatar ta fuskanta kafin ta kai ga hajiya Surayyan. Sai ta samu kanta da gyaɗa mishi kai a lokacin da yake maido mata da takardan. Bata maraba da wani tsaiko da zata samu koda na daƙiƙa ɗaya ne idan ba ya zamo dole ba. Ta sani duk rintsi idan ta shiga wurin ta tambaya ba zata ɓata ba. Ya saka hannun shi ta baya ya tura ƙofar dake Jikin gate ɗin ya wangale mata “wuce Allah ya sawwaƙe ya bashi lafiya”. A lokacin da take amsawa da ameen tare da godiya tayi rabin ƙulewa ciki. Tsayuwa tayi tana ƙarewa harabar wurin kallo. yana da girma amma ba sosai can ba, kaman private school ko hospital. Ta juyar da duban ta daga jerin motocin dake fake a gefe guda zuwa ofisoshin dake ta waje kowanne da tambarin sunan shi a jikin ƙofar da yawanci a rufe suke. Sannan ta ɗaura idanunta a kan Babban ginin da yake tsaye curr a gabanta kaman mai jiran isowarta kawai, yana ɗauke da tambari wanda aka kafe a saman ginin da manyan baƙaƙe A&I SUPPORT ORGANIZATION. “A&I” ta maimaita harufan guda biyu a kan harshen ta a lokacin da wayar dake cikin ƴar purse ɗinta ya shiga ruri. Babban envelope ɗin ta mayar gefenta na dama ta riƙe a ƙasan hammatanta, kana ta buɗe purse ɗin ta ciro waya ƙirar itel mai keypad, madannin amsa kira ta latsa bayan ta karanta sunan mai kiran sannan ta ƙara wayar a kunnenta. “Hello khausar” “Na’am Aunty ILHAM.” dake wayar ba mai sirri bace sai amsar ɗaya ɓangaren ya fito tarr daga cikin ta. “Yaya aka yi?” “Kin samu zuwa ɗin?” ta furta dalilin kiran nata. “Eh, yanzu na iso, Amma ban samu ganinta ba tukunna. Yaya jikin Muftee?” Ta amsa da “da sauƙi.” sanna ta ɗaura da “ Toh Allah ya bada sa’a, yasa a samu abinda ake nima” Da “ameen” ta amsa tana mai jin daɗin addu’ar. “Bari na shiga, Sai mun yi magana. kice ma yaro na Mimi tana gaisuwa” “Ya samu komawa barci ma amma idan ya farka zai ji in sha Allah.” “Nagode Khausar. Allah ya biya ki da gidan aljannah” “Ameen Aunty” da haka ta katse kiran, ta mayar da wayan cikin purse ɗinta, kana ta durfafi wani mahaɗi na ƙaddararta da zai kamo baya da gaba ya ƙulle su a wuri guda ba tare da kowa ya taɓa tsammanin yiwuwar hakan ba. Har da ita kanta. A gaban teburin reception ta tsaya ta miƙa musu takardun hannunta kaman yanda tayi a gate, sannan suma ta sanar da su Hajiya Surayya Kagarko ne tace ta zo. Ba zallan hanta ba, harda hanjin cikin ta kaɗawa suke yi a lokacin da aka ɗaga waya aka kira ita Hajiya Surayya ɗin. “Yaya sunan ki?” receptionist din ya tambaya yana ɗan kawar da wayan daga kunnen shi. Da sauri ta amsa da “Amina Usman Jen. mother of Ibrahim Hashim Baniza” Ya mayar da wayan kunnen shi, ya maimaita duk abinda ta faɗa kana yayi shiru yana sauraron abinda ake faɗa na yan sakwanni, kafin ya amsa da “toh” ya ajiye wayar. “Ta ce ki jirata tana da baƙi” Hamdala tayi a zuciyarta, ta amsa a bayyane da “toh” tare da mishi godiya sannan ta nufi ɗaya daga cikin waiting chairs dake jere a reception ɗin. “Yi haƙuri malama akwai baƙin da zasu zo inspection yau, ki ɗan jira a waje.” Bata damu ba ta gyaɗa kai cikin fahimta. Dukda har ta fara jin daɗin sanyin AC dake aiki a cikin wurin saidai biyan buƙata ya fi dogon buri. Wajen ta fita, ta samu wuri mai inuwa a ƙasan wani bishiyar neem, kuma daga wurin zata iya hango mai fitowa da kuma mai shiga ciki. Awa ɗaya, biyu, uku… tun tana iya tsayuwa har ta nemi wuri a saman interlocking ɗin dake wurin ta zauna daɓas. A lokacin da kiran sallan la’asar ya shiga kunnenta sai ta miƙe ta sake komawa reception ɗin a ɗarare, da tunanin ko dai shanya ne aka yi mata. Receptionist ɗin yana shirin tafiya masallaci ta riske shi domin gashi tattare da alamun alwala. “Nace dan Allah bata fito ba?” ta tambaya tana matse fatar bakinta dake a bushe. Shi shaff ya ma manta da tana nan tana jira. “Meeting suke yi ne, shiyasa. Amma tunda lokacin sallah yayi na san ba zasu daɗe ba zasu fito” Ƙara kwantar da murya tayi tace “toh ni a ina zan yi alwala in yi sallah dan Allah?” “Bari na baki darduma, sai ki zaga baya daga ta waje akwai banɗaki da famfo.” “Toh Nagode” murmushi ya bayyana a saman fuskar da zafin rana da gararin rayuwa ya gama koɗarwa. “Ah babu komai” ya amsa tare da ɗauko mata darduman ta karɓa tana sake masa godiya sannan tayi kaman yanda yace, ta samu ta sauƙe farali. Da ta idar, sai ta cigaba da zama a kan abun ibadarta tana ƙara kai kukanta ma Allah da yi masa kirari, tare da roƙon cikin rahaman sa ya sanya abubuwa su tafi daidai. Wata farar mata, doguwa, mai ɗan jiki ta fara hangowa tana fitowa cikin hanzari da waya ƙare a kunnenta. Sannan ta hango wannan receptionist ɗin ya biyo ta a baya yana ta baza idanu a ƙoƙarin shi na hango ta. Ya kuwa yi sa’a idanun shi suka sauƙa a kanta daga inda take zaune. Da yatsa yayi mata nuni da matar da ta nufi ɗaya daga cikin motocin dake fake, bakin sa ya furta mata “ita ce.” ba tare da ya bari sauti ya fito ba. Aka ci sa’a kuwa ta fahimta, don haka tsugul ta miƙe ta durfafi matar kafin ta kaiga faɗawa cikin motarta, domin ta san daga wannan kuma shikkenan bata da wani daman. “Hajiya dan girman Allah ki taimaka mun yaro na” tace tana niman zubewa a kan guiwowinta tare da haɗe hannunta wuri guda cikin sigar roƙo. Matar da itama yanayinta yake nuni da damuwa ko tashin hankali tayi saurin ɗagota tana cewa “Baiwar Allah kiyi haƙuri nima emergency ne ya taso mun. Amma ki dawo gobe da safe ƙarfe goma. Nayi alƙwarin zan saure ki ko me kike tafe da shi” Da haka ta faɗa mazaunin driver tana mayar da wayar da daman ba katseta tayi ba a jikin kunnenta tana tambayar “A wani asibiti ne aka kwantar da ita?... Medi-plus?... gani nan zuwa” Bayanan da Ilham ta ji kenan kafin ta janyo ƙofar motarta ta rufe. MEDI-PLUS HOSPITAL, KADUNA. “Idan har bayan duk wani ƙoƙarina hakan zai faru to ina amfanin shi?” ya wasa kaifin tambayar tashi ta hanyar ɗaga hannu a iska, a hankali kuma idanun shi suke zagawa kan duk wani mai rai da numfashi dake tsaye a wurin, domin su fahimci amsa yake nima. Babu mai ƙwarin guiwar tanka mishi, dukda a wurin akwai wa’inda da kallo ɗaya zaka fahimci ba zallan rata na ƴan shekaru bane kawai a tsakanin su, a girme sun kai su haife shi. Saidai hakan bai basu ƙwarin guiwar cewa komai ba saboda ko sun faɗa ɗin ba jin su zai yi ba. Ba zai saurare su ba, zai yi amfani ne kawai da abinda kuturun zuciyar shi ta ayyana mishi, ko wani irin uzuri suka kawo suka tsayar a gaban shi in dai a kan Ikram ne ba zai kalla ba. Addu,a kala ɗaya yawancin su ke yi a cikin zuƙatan su, shine Allah ya kawo Surayyah da wuri don ita ƙaɗai take iyawa da shi wani lokacin. A yanda yake jin zafi a ƙirjin shi game da yanayin da Ikram ta kasance a ciki ɗazu a gaban idanun shi, babu wani abu da zai iya sirka wannan zafin a halin yanzu idan ba hannun agogo ne zai koma baya a samu wanda zai kare faruwar wannan hatsarin ba. Amma ganin yanda suka mishi shiru sai ya ƙara tunzura. “Idan ɗawainiyar mu ne yayi muku yawa sai ku faɗa mun in ɗauki ƴata mu bar muku gidan” “Wallahi da mun huta da bala’i da masi..” ɗane mata baki da matar dake tsaye a gefenta tayi da yatsar ta ya sanya tayi saurin haɗiye sauran zancen, ta kai hannunta wurin da zafi ya shiga ratsa fatar lebenta tana shafawa a hankali. “Ki bari ya gan ki mu shiga uku Huda” cewar matar cikin ƙasa da murya tana kare bakinta da tafin hannunta kada ayi katari ya hange ta ya fahimci abinda take cewa. Turo baki gaba Hudan tayi ta cigaba da sauraron masifan da yake zazzagawa a babin babu yanda ta iya. Don kowa ya sani bayan komai ya lafa idan ya fahimci akwai wanda bayi wurin a wannan lokacin tsaf zai iya saka ka a blacklist ya cire maka tallafi. Samm baya yi da duk wanda baya yi da Ikram. Hamdalan su saida ya fito fili a lokacin da suka hango Surayyah tana tunkaro su, Allah ya gani sun gaji da faɗan da yaƙi ci yaƙi cinyewa kaman cin ƙwan makauniya. Saida ta ƙaraso gaban shi ta tabbatar ya sanya ta a idanu kafin ta riƙo hannun shi biyu da suka yi ɗumi, fatar su ta tamke ga jijiyoyi sun fito raɗa-raɗa har zuwa wuyan shi da kan shi da babu hula, kuma a yanzu babu yawan gashin da zai ɓoye hakan. A hankali bakinta ya furta “kayi haƙuri Abdulhameed.” Ta sani a duk lokacin da ta riƙi hannun shi bayi iya ƙwacewa no matter what. Saboda a lokacin da yake tsananin buƙatar mai riƙon hannun nashi da ta kama bata sake ba har yau. “Aunty Surayyah yarinya guda ɗaya kawai, roƙo na guda ɗaya babu ƙari. Amma mutane kusan 20 sun gagara kulawa da yarinya guda ɗaya mai shekaru 3 da watanni 8 da kwana 4. Bayan lalular da Allah ya ɗaura mata sakacin mu ya ƙara mata wani. Shin mun yiwa mahaifiyar ta adalci?” Surayyah ta ji dogon tsakin da wani a cikin su ya ja, amma bata kula ba gudun kada shima hankalin shi ya tafi wurin ya fahimta, don haka ta ƙara ƙarfin ruƙon da tayi ma tsintsiyar hannun shi dukda tsawon yatsun ta basu kai su zagaye shi baki ɗaya ba. “Akwai sakaci tabbas amma wannan ma ƙaddarar ubangiji ne Abdulhameed. Ko da dukkan mu mun taru a kanta a wannan lokacin idan Allah ya riga da ya rubuta Kiki zata faɗi ta targaɗe a hannu to sai hakan ya faru. Kayi haƙuri don Allah” Tana kallo wani abu ya motsa a maƙogwaron shi, ɓacin ran shi yake ƙoƙarin haɗiyewa. A karo na babu adadi ya tabbatar mata da a duniyar nan wani yana cin albarkacin wani, sannan ɗan halak da ya amsa sunan shi bayi manta alkhairi. Kuma daga nan bai sake cewa komai ba, itama a hankali ta saki hannayen shi suka koma ma’ajiyin su a ɓangaren shi na hagu da dama. Sai kawai ya juya ya ƙarasa ƙofar ɗakin da ya baro cikin ta ba da daɗewa ba, ɗakin da aka kwantar da rabin ran shi cikin wani hali. Ya murɗa hannun ƙofar, ya tura a hankali, kuma yana shiga ya maido shi ya rufe saboda bayi buƙatar rakiyar kowa. Amma haƙuri tunda ta roƙa ya haƙura. Bayan shi aunty Surayyah dama sauran suka bi da kallo har ya ɓace ma ganin su, tana ayyanawa a ranta cewa Madaran waken suya ne ya siya mata wannan alfarmar. Madaran waken suya. `````` Seemahwrites ✨ . Chapter 2 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na’ibi Wattpad and arewapen *@Seemahwrites* #THE TRIO OF TALES _(Three minds, Three stories, One journey)_ Sincerely to Aunty Hauwa Yarima, Allah ya so ki da rahamar sa🤍 02… Sauƙa Ilham tayi daga bayan mashin ɗin da ya kawota. Ta zaro kuɗin da ya rage mata a cikin purse ɗinta sabuwar naira ɗari biyun da Khausar ta bata da kuma wata tsohuwar ɗari, ta miƙa wa mai mashin ɗin ya karɓa ya soke a aljihu sannan ya juya da kan mashin ɗinsa yayi tafiyar shi. Juyawa tayi ta fuskanci asibitin lokacin da ta shaƙi dogon numfashi, a hankali ta furzar kana ta sake jan wani. Nutsuwa ce take so ta sameta ko yaya ne, kada ta daburce idan Hajiya surayyah ta tuhume ta dalilin biyota da tayi. Girman asibitin da tsaruwar shi tun daga waje ya isa ya shaida mata asibitine ba na jinyar irin su ba, Allah yasa dai kada a tambaye ta abinda ya kawo ta don ta gaji da mako ƙarairayi. Ta fara takawa tana jin kaman a kan ruwa take tafiya amma wannan zaɓin kawai ita da Muftee suke da shi. Bata samu nutsuwa ba har saida ta hango kanta a farfajiyar asibitin. Abinda idanunta suka fara cin karo da shi kuwa motar Hajiya Surayyah ce fake a wurin da aka tanada domin adana motoci. Har murmushin jin daɗi saida ya bayyana a kan fuskar ta, sannan ta nufi inda ƙananun gravels suka lulluɓe ƙasan wurin cikin jin daɗi, sanin cewa idan ma ta shiga cikin asibitin ba sanin inda zata same ta zata yi ba. Amma babu yanda za’a yi tana zaune a wurin har ta fito ta tafi bata lura ba. Saima ta samu bakin interlock da aka kewaye shukokin dake zagaye da duk kusurwan asibitin ta zauna, bata damu da cewa matsugunin ya kasa ma mazaunanta ba tunda dai ta samu tana fuskantar motar hajiya Surayyan dake tsakanin wata baƙar highlander da jan honda. Ta shiga jira da daako cike da fata. Tabbas Allah bayi ɗaura ma bawa abinda ya fi ƙarfin sa, don haka tayi imani jinyar Muftahul khair bai fi ƙarfin ta ba, kuma zai kawo mata mafita. Abinda bata sani ba shine mafitar zuwan shi a kusa yake ko a nesa? Da sauƙi zaizo ko da sadaukarwa? Abu ɗaya kawai ta sani; zata iya yin komai a kan yaronta matuƙar ba saɓon Allah bane ba zata yi. Shiyasa bata gaji da jira ba har duhun maghriba ya lulluɓe gari sanin cewa indai hajiya Surayyah tana ciki to zata fito, amma tana tsoron ta matsa da niyyar gabatar da sallah ta dawo ta samu babu motarta. Shiyasa ta cigaba da zama har hasken solar ya maye gurbin rana wurin haske farfajiyar. Babu haske a wurin da take daɓashe, kuma a sannu sauro suka samu matattara a jikinta suna zagaye ta saboda duhun hijabinta har ma da fatar jikinta, kukansu suke rerawa a cikin kunnenta tare da kai mata cizo ɗaya bayan ɗaya. Lokaci ɗaya kiran sallan isha da ringing ɗin wayarta suka shiga kunnenta. Ta buɗe purse ta ciro wayan tana kallon ma’ajiyin caji da yayi jaa yana nuna buƙatar wutan lantarki da wayan yake da shi, kana ta mayar da dubanta kan sunan mai kira. Ajiyan zuciya mai nauyi ta sauƙe, ta ɗora murmushi a kan fuskarta kaman mai kiran na zaune a gabanta, sannan ta ɗauka ta ƙara a kunne. “Maama nah!” ta ambata tana kwaikwayon muryar ɗoki domin ta ɓoye mata damuwarta. “Na’am Fidela ta. kina lafiya” aka amsa cike da karsashi irin nata ta ɗaya ɓangaren. “Lafiya ƙalau maama. Ina Filiyan da Fitami.?” “Ihsan tana hostel, Jawad kuma zuwa yayi ya ajiye mun uniform ɗin shi mai datti shine ana kawo wutan nepa na saka ya ɗauka ya fita ya wanke.” ta ambaci yaran nata da inkiyar su na ainihi a maimakon na yare, kana ta ɗora da “yaya jikin mai gidan. Kin samu ganawa da mutanen kuwa, na ji shiru tun safe baki kira ba.” Jimm tayi cikin rasa tacewa. Ta ga ci ta ga rashi, ta kuma samun hope duka a yau kawai. Hala dai hajiya Surayyah ba mai fitowar yanzu bace ba ko kuma ma kwana zata yi a cikin asibitin tunda gashi dare har ya gama rufawa shiru. Awannin da suka rage mata basu wuce a ƙirga ba kafin a fara rabon tallaffin da safiyar gobe. “Rabon mutum bayi wuce shi Maama, zan jira idan rabon mu ne duk daren daɗewa Allah zai kawo shi gare mu. Ki mana addu’a” tayi maganar cikin karyewar murya. “Addu’a kullum a cikinta muke Fidela. Allah ya tallafa miki, ya tashi kafaɗun Ibrahim. Ke kuma Allah ya karɓa miki hakkin ki” Ji tayi kaman kuka zai ƙwace mata da zancen Maaman, saboda ta taɓo mata inda yake mata ciwo. “A ce ka haifi mutum amma ka gagara ɗaukan ɗawainiyar shi bacin kana da halin hakan Maama? Ya Hashim ko tausayin yaron nan bayi ji? Ni ba abun ya tausaya mun bane tunda ya san ba wani sana’a nake da shi ko wani hanyar samun kuɗi ba, amma ya sake mun jinyar yaron shi babu kunya ba tsoron Allah?. Wallahi da zan iya da bari zanyi Muftee ya mutu saboda uban shi ya gagara sauƙe hakkin da ya rataya a wuyan shi in ga yanda za’a yi. Amma ɗana shine zuciya da jini na, nima ba zan rayu ba idan babu shi” ta ƙarasa kukan na cin ƙarfin ta saboda ɗamewar da zuciyarta keyi. Ta ji lokacin da Maaman ta sauƙe numfashi kafin muryarta ya sake fitowa ta cikin wayar. “Kiyi haƙuri ki cire damuwar shi a ranki Fidela. Gani nan jira nake yi ɗaukan adashe ya juyo kaina in turo miki ki rage wani abun. Filiyan ma idan tayi hutun makaranta sai ta ɗan zo ta taya ki da ɗawainiyar asibitin kema ki samu ki huta” “A’a Maama, na san kema kina buƙatar kuɗin, tunda Allah ya ɗauke mana Taa bani da mai kula mun da ku yanzu. Ni daga wurina zan cigaba da ƙoƙarin wani abu har Allah ya kawo mana mafita. Amma kin yi naki ƙoƙarin Maama, baki haife ni ba amma ko kusa ban tashi da maracin uwa ba har bayan ran Taa kuwa, babu komai tsakani na dake sai addu’ar alkhairi da ƙauna mai tarin yawa. Shi kuma Ya Hashim Allah ba zai barshi ba, tunda bayi zalunci kuma bayi son mai yin ta, da taimakon shi ko babu Muftee zai rayu Insha Allah.” Rarrashin ta Maaman ta cigaba da yi da bata baki har ta rage kukan kafin tayi mata sallama da cewar duk halin da ake ciki ta sanar da ita. “Toh Maama na cinye miki kati ma” “Kin jiki.” Tace da sautin murmushi. Itama sai ta samu kanta da murmusawa. “Allah ya saka da alkhairi Maama ina ƙaunar ki” “A gaida mai gidana” “Zai ji in sha Allah” Da haka Maama ta datse kiran, sai itama tayi tunanin ya kamata ta kira taji jikin Muftee ɗin gashi Khausar tayi mata yakanar rashin kira ta tambaye ta lokacin da zata dawo. A agogon wayan ta ga lokaci karfe 8 har da minti 40. Ga jan layi na cikin akwatin cajin ma ya dauke ya dawo empty. Haka dai ta danna kiran layin Khausar ɗin da fatan katin wayan ya basu daman yin magana mai tsawo. “Hello Aunty Ilham.” “Khausar kun wuni Lafiya?” “Alhamdulillah aunty, an samu nasara?” “Tukunna Wallahi khausar, har yanzu ban samu ganawa da ita ba” Khausar ta amsa da “hasbunallahu wa niimal wakeel. Toh Allah yasa jinkirin ya zamo alkhairi” Jin ana mata kashedin ‘one minute remaining’ ya sanya ta cewa “ina yarona?” Bayan ta amsa addu'ar da ameen. “Gashi nan” cewar Khausar tana cire wayan daga kunnenta ta mayar nashi. “Mimi!” A wuni guda kawai da bata ji muryar shi ba a yanzu sai take jin kaman wani ɓari ne a jikinta da ya shanye ya dawo aiki da siririyar muryar shi ya shiga kunnenta. “Mufteen Mimi yaya jiki?” Ta amsa tana daɗa kwantar da murya saboda jikinta da take ji kaman ana zuba mata ƙanƙara. “Mimi kin….” Ɗiff taji maganar ta ɗauke. Ta ciro wayan daga kunnenta ta kawo shi gaban idanunta don ganin ko katin ne ya ƙare amma hasken wayan ya ƙi kawowa koda ta danna. Sai ta ji duniyar ta sake mata zafi, komai ya sake tsayawa, a hankali kuma fatan ta ya fara narkewa kaman daskararren kitse a ƙasan rana. …. Ƙarasowa tayi jikin gadon da ya kifa kan shi. A hankali ta kai hannunta ta taɓa saman kafaɗan shi don haka ya ɗago ya fuskance ta. A maimakon ta buɗi baki tayi magana sai ta nuna rigan jikin shi da yatsar ta, kana ta mayar da manuniyar kanta ta ware sauran yatsunta tana goga tafin hannunta sama da ƙasa a jikinta alamun ya je yayi wanka. Sannan tayi hand movement yanda mutum keyi idan zai cire riga kana ta haɗe tafukan hannayen ta biyu ta saka a ƙasan habarta na dama ta ɗan langabar da kanta ta ɓarin tare da lumshe idanunta na abinda bai fi daƙiƙa guda ba. Ya fahimci abinda take nufi tunda communication method ɗin shi ne dama. Amma ya fi fahimtar dalilin da ya saka tayi amfani dashi wajen isar da saƙonta, sanin cewa ya tsani ana mishi magana da sign language. Saboda Ikram dake barci ne, kada maganan su ya tashe ta, dukda kuwa bata sanye da hearing aid ɗinta amma sautin zai iya damunta. Da hannu shima yayi mata bayanin zai jira har sai ta tashi tukunna, domin sign ɗin da tayi masa na nufin yaje yayi wanka idan yana da niyyan kwana a asibitin ne. Ikram dake barci da ɗaurarren hannu ta nuna wannan karon sannan ta sake maido da hannun fuskarta ta ware idanunta kaɗan, ta bi ta nuna kirjin ta kana ta gwada kujeran da yake zaune a kai. Tana nufin zata zauna a nan har ya je ya dawo koda ikram ɗin zata farka. Tunani ya tsaya yi na ƴan daƙiƙu yana jin kaman ba zai iya ba dukda shima nauyin kayan jikin nashi ya dame shi, kuma tun safiya yake sanye da su, amma idan Kiki ta buɗe ido ta buƙace shi fa?. Wannan karon da baki ta ambata mishi “ina nan, ba zan motsa ba har sai ka dawo” maganar tata ya fita ba tare da sauti ba ko kaɗan amma tunda idanunsa na kan laɓɓen ta tana da tabbacin ya fahimta. Ya miƙe cike da sanyin jiki idanun shi a kan ƴar shi. Aunty Surayyah ta nuna kanta ta nuna shi kana ta nuna ƙofar fita ma'ana suje ta raka shi. Sai ya girgiza kai Alamar A'a. Ya gyara mata kujerar a gaban gadon ta zauna Sannan ya juya fita. Ya kuma yi namijin ƙoƙari da bai juyo ya sake kallon Ikram ba har ya janyo ƙofar a bayan shi ya rufe. Ƙaran shigowar saƙo da ya shiga kunnen Aunty Surayyah bayan fitanshi ne ya sanya ta miƙa hannu ta ɗauko wayan dake gefen flask ɗin ruwan zafi dake ajiye a saman drawer tare da magungunan Ikram. Wayan shi ne ya manta, amma ta san bai yi nisa ba idan tayi sauri zata cim mishi kafin ya bar asibitin. A saboda haka sai ta ɗauka ta fita daga ɗakin da sauri. “Yauwa kun gan shi, Wannan da ya wuce, shine sarkin masifan ɗazu da rana” wata nurse kenan take gwada ma ƴan uwanta Abdulhameed da ya wuce ta gaban su yanzu, domin su samu fuskar da zasu ɗora ma labarin da suka samu tun shigowar su dutyn su na night. “Haba! Gashi kaman ba zai yi magana ba ma” ɗaya a cikin su ke miƙa wuya kaman zata tsinke shi don ta samu idanunta su sake ɗauka mata fuskar Abdulhameed sosai. “Kutt kin ji bala’i? Ai yanda suka mayar da asibitin nan kaman gidan biki, shi kuma yana tsaye sai zazzaga yake yi kaman lawyern da aka bawa cin hanci” hannunta duka biyu a ƙugu tana ɗan girgiza take tabbatar musu da gaskiyar ta. “Uhmm ni naji ma wai wasu a cikin ƴan uwan nasu suna cewa wai Yarinyar Shegiya ce, basu yi aure da uwarta ba aka haifa masa ita.” “Ke haba?!” Suka riƙe baki cikin mamaki. “Walla….” “Ku gode ma Allah da baya ji, tabbas da kun gane kuran ku.” cewar Aunty Surayyah tana tsayuwa a gaban su. Sosai suka firgita har suna niman hanyar watsewa kowa taje ta kama abinda ke gabanta. “Gashi” Dake a tsarge suke, duka sai suka juyo a tare suna kallon wayan da take miƙo musu ƙirar samsung z Flip dake a rufe. “Karɓa ki kai mishi.” Ta bawa ta farkon sannan ta juya ta koma ciki. Da sassarfa ta bi bayan shi don har ya fice daga reception ɗin asibitin ya nufi wurin da ya faka motar shi. “Malam.. Hey… ka ji….” Irin kiran da take masa kenan tunda ba sanin sunan shi tayi ba har ta cim masa amma yana kan tafiya bai tsaya ba kuma bai waiwayo ba. Tunawa da tayi matar ɗazu tace baya ji ya sanya ta sha gaban shi tana fitar da numfashi. Irin kallon da yake mata gashi ya haɗe gabas da yamma yasa kawai ta miƙa mishi wayar ba tare da tace komai ba. Ya kalli wayan, kafin ya miƙa hannu ya karɓa ya buɗe ta. Hoton Kiki da ya cika screen ɗin ya tabbatar masa da nashi ne. Bai saki fuskar ba yace “Nagode” sannan ya raɓa ta ya cigaba da tafiya, ta bi bayan shi da kallo har ya buɗe ƙatuwar motar shi ya shiga sannan ta juya ta koma ciki kafin a nime ta. Kunna motar da yayi ya sanya hasken fitilun gaba da suka kunnu Suka dalle mata idanun da suka yi luhu-luhu ga hawaye dake kwaranya daga cikin su. Tayi saurin saka bayan hannayenta ta kare fuskarta. Saidai ya riga da yaga fuskar. Kuma ya gane ta. Ilham ce. A cikin kanshi sai yaji kamar an kirashi, da muryar nan "A Moher..." Muryar da itace karshe wajen kiranshi da wannan sunan. Akwai wasu mutane da kan shigo rayuwar mu kaman da kuskure. Wasu bayan kallo ɗaya ba zamu sake ganin su ba har ƙarshen rayuwar mu. Wasu kuma zamu yi ta gamuwa da su a hanyar wucewar mu na yau da kullum amma bamu taba magana da juna ba. Wasu wani abu zai haɗa mu na ɗan lokaci, daga nan kuma shikkenan anyi rabuwar karshe. Akwai kuma wa’inda a ajiye zancen sabo ma a gefe, su ɗin ɓarin rayuwar mu ne, ko bugun zuciyar mu, ko bangon jinginan mu madafan mu, ko kuma sune gishirin rayuwar tamu baki ɗaya da babu su babu ɗanɗanon rayuwa. Amma haka a lokacin da muke musu kallon ƙarshe a duniya sai muga kaman zamu sake. Su kuma wa’inda suka shigo rayuwar mu kaman da kuskure sai Allah ya ƙara haɗa mu da su a gaba, mu fara tunanin a ina muka san su?. Saidai Ilham tana cikin Ɓarin memories ɗin da ba zai taɓa mantawa ba har zuwa ranar da ƙasa zata rufe idanunsa. Kuma bayi fatan ya manta ɗin, bayi ƙoƙarin mantawar, saboda memories ne masu matuƙar ciwo da kuma muhimmanci a rayuwar shi. Daga wannan sati ɗayan ne ƙaddara tazo da bargonta mai nauyi ta lulluɓe shi, bata bar mishi ko ramin shaƙar numfashi ba. A sati dayan ne yake iya tuna farin cikin Nne, ɓacin ranta, tashin hankalinta, damuwarta, dariyarta da kukanta duk cikin sati ɗaya kacal. Kuma a lokacin Ilham ta faɗo ciki from nowhere, daga nan kuma bai sake ganinta ba sai a yau. Bayan tsawon shekaru goma sha biyu. ~•~•~•~•~•~•~• . chapter 3 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na’ibi Wattpad and arewapen *@Seemahwrites* #THE TRIO OF TALES _(Three minds, Three stories, One journey)_ 03... Haɗuwar Sati Ɗaya. KANO. *Talatin ga watan Maris, shekara ta Dubu biyu da sha huɗu(31/3/2014)* Riƙe take da tsintsiyar hannun shi, ruko tayi mishi sosai da iya karfinta idanunta yana maiƙon hawaye, amma sanin kanta ne bata isa ta buɗe baki ya ji kukanta ba, kasancewar itace dalilin da tasa aka ɗaga shi da sanyin safiya a lokacin da yafi jin daɗin barci domin ya rakata makaranta. Don haka bin takun dogayen sawayen shi take yi da gajerun nata, tana haɗawa da sauri-sauri gudu-gudu ta samu su daidaita tunda ba rage saurin tafiyan nashi zai yi ba. Tsoron ta ne ya ƙaru ganin sun fara hango gate ɗin makarantar. Dukda rakiyan yayan nata kuwa yanzu idan suka ga dama sai su saka ta wankin banɗakin su mai shegen wari da kashi a kasa kafin su bari ta shiga, kuma ta san shi ba cewa komai zai yi ba, Allah dai yasa babu prefects on duty kuma babu wasu ɗaliban da aka tsare idan kuma ba haka ba Allah ya Isa zata yiwa Addah Iman tunda ta san ta ɗan koma barci bayan an ɗaga su suyi shirin makaranta kuma har suka fita bata sake tashinta ba, gashi yanzu ta fito ko karyawa bata yi ba. Hanyar da suke bi a matsayin shortcut baya da faɗin da mota zai iya wucewa, mashin ma sai tuƙin kwararre a rakubewa ta gefen kwatami da buɗaɗɗen sokawe. shiyasa wani lokaci yake zama daba na yan shaye-shaye da masu busa sigari, domin sune zarnin fitsarin dake lungun bayi damun su. Har sun kusa fita bakin titi suka ji anyi Fiito daga bayan su tare da kwala kiran “Hey!" Shiga ukunta ya sanya ta waiwaya zuwa ga inda sautin muryan ya fito, idanunta suka shiga cikin nashi na tsawon daƙiƙa guda. Saidai kafin ta kai ga fayyace kamannin shi taci wawan tuntuɓen da ya sanya ta kusa kifawa. hannun yaya Aliyyu da take riƙe dashi ne abinda ya ceci haƙwaranta daga zubewa a kan dutsen da ta buge babban yatsar ƙafar ta a jiki Dukda saurin yake bunkawa kaman mai zuwa karɓan sadaka a masallaci. shima yatsar bai ɓata lokaci ba wurin aman jinin da ya rina jikin farin sock ɗin da yake lulluɓe a ciki. Ƙarar da ta saki cikin azaba ya sanya Ya Aliyyu da tsayawa da tafiyar, ya juyo ya fuskance ta yayin da ta durƙusa ta riƙo ƙafan tana baiwa ƙwallar da ya taru a cikin idanunta damar saukowa saman fuskar ta. Tsaki ya ja “Mtsww kina da azababben raki wallahi. Mu gani?” shima ya durkusa tare da amsar kafar daga rukonta ya zame sandal da safan jiki, ya shiga duba ciwon. “Farce na ya tumbuke ko?” ta tambaya cikin sheshshekar kuka “wayyo Allah na” Fatan yatsar ne kawai ya kuje sosai shine yake fitar da jini don haka yace “zaki tashi mu karasa ne ko kuma in yi tafiya ta?” Ta dago ta kalle shi tana ƙara kwabe fuska “Haba yaya Aliyyu! Ta yaya zan iya zuwa school a haka, ka kai ni chemist sai ka dawo ka fada musu na ji ciwo ba zan iya zuwa makaranta ba sai next week” ta ƙarasa tare da jan hanci. “Tuntube ne zai saka ki zaman gida har na tsawon sati guda Fidela?” ya tambaya yana tamke fuska. Ƙasa tayi da kai ganin mugun kallon da yake watsa mata tana kara matsar kwalla kana ta amsa da “shima tuntuben ana kamuwa da ƙwayar cutar tetanus aka fada mana a class din inter science” Ya jinjina kai, kafin ya mayar mata da martani sai ji yayi wani abu ya daki kafadan shi har saida yayi taku biyu da baya, kana ya samu ya daidaita tsayuwar shi ya dago duban shi don ganin menene. Idanun shi ne suka sauƙa a cikin na wanda ya daidata a cikin nashi kasancewar tsayin su ya kusan zuwa ɗaya. “Baka ji bane lokacin da na kira ka?” Duban shi na kan Aliyyu amma nata yana kan bakin shi da ya maƙale toothpick a tsakanin hakorin shi, wanda take da yaƙinin shine dalilin da ya sanya hausan nashi ya fito wani iri. Wani iri ba yana nufin babu dadi ba A’a, wani iri dai kaman daga bakin da bai saba da Hausar ba. Wani iri da bata san da cewa zai yi mata tasiri nan da shekaru masu yawa fiye mamakin da tayi a wurin ba kawai. “Ka kira sunana?” Aliyyu ya tambaya don sarai ya ji fiiton da yayi ɗazun. Bai amsa shi ba sai miƙa mishi sabuwar naira 500 da yayi yana masa alaman ya karba ya tafi da kai. Aliyyu bai karba ba, ba don bai fahimci nufin shi ba tunda ba yau bane gamuwar su na farko, sai domin yau ɗin bayi da niyyan aikata yanda yake so. “Ko na bata ne ta siyo a madadin ka?” ya tambaya ganin ba zai karba ba, lokaci daya yana dawo da dari biyar din gareta sannan duban shi ya biyo baya. Suka sake yin ido hudu, a cikin hausar tashi ya soma fadin “kara biyu zaki ce a bak..” Saurin wafce kudin da yaya Aliyyu yayi ya katse masa sauran zancen sa. ya dube shi da dan karamin murmushi tare da fadin “idan kaine kuma kwalin zaka karbo mun” Bai yi musu ba kaman yanda yayi tsammani, shiyasa da ya gan shi tare da yarinyar da yake da yaƙinin kusanci a tsakanin su yaji dadin kiran shi. Tunda yana sanye ne da uniform ɗin makaranta idan ya je ba zasu yarda su siyar mishi ba, haka itama yarinyar. Saidai yayi yunkurin tura ta ne don yayi mishi barazana kuma hakan yayi aiki. Ita dai dubanta ne yake yawo a tsakanin su bayan ta hadiye kukan ta, cikin rashin fahimtar abinda yake faruwa ko kuma abinda wannan yake nufi da ‘sanda biyu’ da kuma ‘kwali’ . “Tashi mu tafi” cewar yaya Aliyyu. Ta yunƙura zata dingisa ta jiyo shi yana fadin “ka barta a nan ka karbo mun sako na tukunna zan yi maka gadin ta.” Da sauri ta mike ta tusa kafar da babu safa cikin baƙin sandal dinta lokaci daya ta manta da raunin wanda jinin da ya fitar har ya bushe. “A’a Ya Aliyyu mu tafi dan Allah” tace tana komawa bayan shi ta ɓuya tare da sake riƙe damtsen hannun shi gamm. Sai ya taɓe baki kawai ya juya, hannun shi zube cikin aljihun wandon shi yake takawa ya koma dakalin kofar gidan da yake zaune dazun yayi zaman jiran dawowar su. Suna karasawa bakin titi Yaya Aliyyu yace ta tsaya daga inda zai iya hangotanta jira shi saboda babu yanda za’a yi ya je siyo sigari da ita. Ya karasa shagon da yake tsallaken makarantar su, akwai mutane biyu a gaban shi don haka ya jira saida aka fara sallaman su tukunna ya mika dari biyar ɗin yana fadan abinda za’a bashi. Mai shagon ya kalle shi a kaikaice. “Aliyyu kai da nakewa kallon mai hankali kai ma bushe-bushen zaka fara” Saurin kare kan shi yayi da “A’a malam Sama’ila ba nawa bane, aiko ni aka yi” “Waye ya aiko ka” “Uncle Rabe” ya samu kan shi da mishi karya don da kunya ya fadi ainihin wanda ya aiko shi kuma har ya yarda yazo. “Jiya-jiya na gama mishi gargadin kada ya sake aiko ku idan ba haka ba zan hada shi da baban ku. Bai ji ba kenan?” Aliyyu sai ya daburce ya fara kame-kame “D… daman fa.. Daman…” Ganin mutane suna tunkaro shagon, malam sama’ila ya amshi kudin ya fito da kwalin sigarin ta kasan kantan shagon ya dunkula masa a cikin hannun shi yana fadin “ka tafi, kada ka sake dawowa. Idan ba haka ba kuma a kunnen mahaifin ku.” Da sauri Yaya aliyyu ya bar shagon ya ƙaraso inda take yace su tafi. Da suka koma wurin mai fiito shima yace ta jira shi daga nesa, ya ƙarasa wurin da yake zaune sai taga ya dunƙula masa abinda ya siyo din yana waige-waige, alamun rashin gaskiya duk sun bayyana a jikin shi, ya dawo ya fisgi hannunta suka bar lungun. Chemist ya kaita aka wanke ciwon ƙafarta sannan suka koma gida fuskarta shabe-shabe da hawayen kukan shagwaba, don ta samu a lamunce mata ta sha zamanta a gida na tsawon sati guda kaman yanda ta kuɗurta a ranta. ….. *Abdulhameed* Duba agogon dake maƙale a tsintsiyar hannun shi yayi ganin tara da rabi ta gota, ya saka sigarin a cikin jakar makarantar shi tare da mikewa yana da yakinin zuwa yanzu Nne ta isa wurin aikinta. Ya saƙala hannun jakar shi ta saman kansa ya raba shi a kafadar shi na hagu kana ya gyara ma jakan zama a jikin kunkumin shi ta bangaren dama sannan ya karasa bakin titi ya tsari mashin ya hau. Da key din shi ya bude kofar dake jikin farin gate din ya shige tare da sake murzawa kofar key ta ciki ya rufe. Haka ma kofar parlourn yana shiga ya garkame. Durƙusawa yayi ya shiga warware igiyan cover shoes ɗinsa ya watsar da su a wurin kana ya karasa ya kunna socket ɗin Tv sannan da shi da jakan shi suka zube a kan dogon kujeran dake fuskantar talabijin. Lighter ya fara cirowa daga aljihun wandon shi, ya cire tsinken sakace hakorin dake bakin shi ya luma hannu a jaka ya fito da kwalin sigarin ya zari guda ɗaya ya makala a tsakanin labban shi ya kunna masa wuta. Kafin shirin da yake son kallo ya gama loading a DVD har ya zuke rabin kara hayaƙi ya buɗe madaidaicin parlon. A lokacin da ANIME mai taken BLEACH ya fara playing sai ya kishingida ya cigaba da zukan kayan shi hankali kwance. . . “Biko sir, ana m abia obere oge. I forgot some papers at home” A tsakanin kunne da kafadarta ta makala yar wayar da take magana a cikinta, yayin da take kokarin zura key a jikin kofar farin gate din da nufin bude shi. “Yanzun nan zan dawo nace maka mota na ma a kunne na barta” ta cigaba da faɗi cikin wayar tana shigewa ta cikin kofar bayan tayi nasarar budewa, bata tsaya ko tura shi tayi ba ta wuce cikin gidan tunda yanzu take saka ran fitowa. Kife murfin ƴar NOKIA ɗinta ja tayi bayan ta gama magana ta tusa cikin jakar hannunta, sannan ta canza makullin da take rike dashi cikin jerin gwanon mukullan tun daga na gate zuwa na gida, shima ta zura a ramin shi, ta murda, ta bude, tayi Shigewar ta ciki kanta tsaye, yayin da taja taci birki a tsakar parlon lokacin da idanunta suka sauƙa a kan abinda ya kaɗa mata hankali. “Nwam?!” ta kira cikin kaduwa. Kara hade fatar idanun shi yayi yana sauke numfashi a hankali kaman mai barcin gaske. Ita kuma ganin bai motsa ba ta sake kiran “Abdulhameed!” Tana karasowa kusa da kujeran da yake mike, hannun shi a saman kirjin shi da yake dagawa a hankali, ga plate din abinci da kwalban 7up da aka gama sha a wurin. “Nwam(my son).” ta kira a karo na uku tana dan bubbuga kafadan shi. “Hmm?” Sai a sannan ya bude idanun shi sannu a hankali yana mayarwa ya rufe kaman wanda barcin bai ishe shi ba. Bayan ƙaran bude gate dinta da yaji ne ya saka shi mikewa a gaggauce ya fincike igiyar wutan Tv da na DVD ya gyara ya kwanta, tunda ya san zata iya riskan shi idan yace zai kawar da plate din da yaci abinci sai kawai ya bar su a wurin. Cikin sa’a a kowani lokacin da zai sha sigari a gida yana gamawa yake ɗaga labule hayaƙin ya fita sannan yabi gidan da airfreshner baki daya, bakin shi kuma ya jefa masa alawar tom-tom. “Nne, ilotala (mama kin dawo?) ya tambaya cikin harshen Igbo yana hamma. “Abdulhameed mai kake yi a gida lokacin makaranta” ta mayar mishi tambayar da turanci. Dafe goshi yayi yana yamutsa fuska “headache Nnem.” ya bata uzurin da yake da yakinin shine kawai zai sanya yau ya sha a wurinta. Ya dora da “ina aji kan nata sara mun shine naje clinic aka mun allura aka ce na dawo gida na huta” bai ce magani bane saboda kada ta tambaye shi sauran wanda aka bashi. Hannu ta kai kan goshin nashi, babu wani zafin da ya wuce mizani amma dake zuciya irin ta uwa mai cike da ƙaunar danta ne ke bugawa a kirjin ta, take tausayin shi ya lullube ta. Ta sassauta murya tana mishi sannu da igbo shima sai ya dada narkewa har tana tambayan shi ko su je asibiti ne. “Naga likita ai a clinic Nnem. ta ce idan na samu isasshen hutu zan samu sauƙi” Sai ta jinjina masa kai fuskar ta lullube da damuwa. “Ina ba damuwar abinda nace jiya bane ya saka maka rashin lafiya?” Bai amsa ba sai mayar da kan shi da yayi yana kallon gefe. Don damuwa abinda ya dame shi kenan, shiyasa bai samu nutsuwa da safiyar yau ba saida ya bunka ma kan shi hayaki, kuma yaga babu amfanin zaman ajin da yake yi domin ya cika ma mahaifiyar shi burin ta, ya zama irin abinda take so, idan ita ba zata iya cika mishi nashi burin ba. Ɗofanuwa tayi a kujeran ta gefen kafar shi tare da shafo gefen fuskar shi cike da kulawa tana leka idanun shi, cikin murya mai taushi tace “Nwam. baban ka baya son waƙa, ka zabi wani abun daban ko menene shi ni zan tsaya maka amma banda waƙa tunda baya so. Nayi mishi alkawarin ba zaka yi waƙa ba.” Da ƙwallar da zancen ta na yanzu ya tara a idanun shi ya juyo ya dube ta. “Daman yana sona ne balle ya so abinda nake so?” Lumshe idanu tayi tana sauƙe numfashi cikin rashin jin dadin abinda ya fada. “Kada ka damu, ni na ishe ka rayuwa.” tace tana shafa gashin dake cike a kan shi wanda babu yanda ba’a yi da shi ya rage tsayin shi ba a makarantar su, amma askin punk yake so yayi na gayu da manyan mawaka wanda za,a aske gefe da gefe a bar mishi tsakiya shiyasa yake tarawa. Nokia mai murfin ta da ya shiga ringing ya sanyata mikewa tana cire makulli daya daga jikin mariƙin su ta mika mishi. “Gashi ka bude bedroom dina ka dauki wayan ka a bedside drawer duk abinda kake ciki ka kira ni. Idan kuma ka dan samu sauƙi kafin na dawo sai ka dauki kudi ka fita ka sayi abinda kake so.” “Okay Nnem. thank you” ya fada a cikin ranshi yana fama da matsanancin farin ciki. Daman siezing din wayar tashi da tayi ya zaunar da shi a gida amma yanzu tana fita shima ficewa zai yi. Ta sumbaci goshin sa hannunta a kan kumatun shi sannan ta fice daga gidan kafin wani kiran ya sake shigowa. Minti sha biyar a tsakani haka, bayan yana da tabbacin tayi nisa ya miƙe ya bude bedroom din. Wayar shi ƙirar blackberry ya fara dauka sannan ya bude ma’ajiyar kudinta ya zari dari biyar-biyar guda shida. Har ya fita ya janyo kofar dakin ko mai ya tuna? Sai ya koma ya kara guda biyu. Key din ɗakin ya ajiye mata a kan TV stand, bai ko sauya uniform din jikin shi ba ya fice daga gidan baki daya ya rufe da key din shi. Shagon unguwan su ya tsaya ya sayi katin dari biyu ya loda sannan ya kira numbern da yayi saving da “Fire”. “wassup Nigga” shine abinda ya shiga kunnen shi bayan an ɗaga kiran. Hannu ya saka ma mashin ɗin da yazo wucewa ta gaban shi Sannan ya amsa da “ka Same ni a studio yanzu. Kuɗin sun cika” “Weeehuu. Bari na kira ɗan Malam ya karɓo mana wancan saƙon toh” Bai amsa ba ya katse kiran sannan ya hau bayan mashin ɗin suka ɗau hanya yana mishi kwatancen wurin da ze kai shi. •~•~•~•~•~•~• Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin chapter 4 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites* *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) 04…“Subhanallah Fidela!” Maama ta ajiye wuƙar da take firan doya dashi ta miƙe, ganin yanda suka shigo tana ɗingishi, ga farin ƙyalle mai jini riƙe a hannun Aliyyu. “Yaya Ka kaini ciki” Ilham tayi magana tana numfarfashi kaman mai naƙuda a tsaye. Buge hannun da ta riƙe sa dashi yayi “dalla sake ni” yace yana watsa mata harara. Sai ta koma jikin Maaman ta lafe a jikin hannunta tana ajiyar zuciya. Maama da zuciyarta ke cike da zullumin abinda ya samu yarinyar da yanzu aka turata makaranta ta dubi Aliyyu tana tallafe Ilham a jikinta tace “me ya same ta ne?” Cike da takaici yace “Tuntuɓe fa tayi Aunty!.” sannan ya mayar da dubansa kan Ilham yana ɗaga hannu sama “Wallahi yanzu sai na kikkifa miki mari ki samu dalilin kuka da tushe.”ya jefar da farin socks ɗin a wurin, ɓacin rai ma ya saka ya manta ya wuce bai gargaɗeta kada ta labarta ma Maama abinda ya faru ba don ya san halinta da barbaɗen zance. Maama ta kalli safa mai jinin da ya jefar a ƙasa da kyau, sai a lokacin ta fahimci menene. ta sauƙe ajiyar zuciya domin tayi tunanin wani cutarwar ne mai girma ya samu Ilham. “Sauran kaɗan fa da na fasa kaina a jikin dutsen Maama, saboda yanda yake ja na kaman zai tashi sama. Kuma ciwon da zafi sosai ai kinga yanda yayi jini sosai ma” tayi maganar tana jan hanci tare da matsar ƙwalla. “Sannu ki shiga ki cire hijabinki ki kwanta, bari na soya doyan baban ku sai a saka miki”. Bata bari farin cikin da ya cika zuciyarta ya saka murmushi ya bayyana a leɓen bakinta ba, domin Maama tana ganin fara'ar ta fa toh shikkenan ta warke. Don haka ta fara ɗingisawa har ƙofar parlourn Maaman, tayi sallama ta ɗaga labulen ƙofar ta shiga sannan ta saki yanayin fuskarta. Dogon kujera ta ɗale ta miƙe a kai bayan ta zame hijabin wuyanta, tana jin wani yanayi mai daɗi yana shigarta jin yanda gidan yayi shiru kowa na makaranta, ba kamar kullum ba da su Ihsan ke takura mata. Har barci ya fara ɗaukarta zuwa garin nisa, ƙamshi ya ziyarci ƙofofin hancinta lokacin da Maaman ta shigo riƙe da ɗan bowl mai ɗauke doya, wanda aka dafa sannan aka naɗe shi a cikin ƙwai aka soya. Muƙut taji ta haɗiyi miyau, daman yunwa ya fara ƙwaƙular cikinta. “Fidela Tashi” Bata bari Maaman ta maimaita ba ta miƙe zaune ta saka hannu biyu ta karɓi bowl ɗin. Maama ta koma saman fridge ta ɗauko roban yaji sannan ta dawo tana faɗin. “Sauce ɗin da nayi bayi da yawa ne na juye ma Taa aka kai mishi office, ga yaji” Hannu ta saka ta karɓi roban tana furta kalmar Godiya, ga yawunta dake kan tsinkewa. Babu ɓata lokaci ta fara dandala ma doyan Yajin Maama mai ƙamshin tafarnuwa tana saita ma cikinta. “A wani chemist ne aka wanke miki ciwon?” Maama ta tambaya tana zama a gefenta, idanunta a kan yatsar dake naɗe da bandeji. Langabar da kai tayi “Na gefen makarantar mu, kuma Sunce wai kada nayi dogon tafiya sai nan da sati ɗaya” ƙaryar da ta gama shiryawa tun a hanyar dawowar su gidan ya biyo bayan amsar tambayar Maama. Maama ta jinjina kai “Allah ya sawwaƙe. Daga gobe sai Taa yana sauƙe ki idan zai wuce” Ta waro idanu “Maama tun kafin 7 fa yake tafiya, Taa da ko karyawa baya yi a gida?, idan naje makaranta ƙarfe 7 Wallahi saidai ayi ta saka ni shara tunda ba'a fara zuwa ba, kuma ma baya nan lokacin islamiyya, Gashi a lungun da muke bi shortcut Wallahi akwai ƴan shaye-shaye, yau har haɗuwa muka yi da wani ya tsare yaya Aliyyu ya bashi kuɗi ya siyo masa wani abu a shagon malam Sama'ila ya dunƙule a hannunsa ya koma ya bashi.” bata shaƙi numfashi mai tsayi ba saida ta samu ta dire. Kafin Maama ta gama sarrafa zancen a cikin ƙwaƙwalwar ta Aliyyu da ya dawo kashe wa Ilham warning ya faɗo ɗakin ko sallama babu. “Munafuka annamimiya, laifi na ne da na ɗauki kuɗina na bayar aka suturta kuturun ƙafar ki ban bari ya ruɓe aka guntule ba, amma babu damuwa akwai gaba. Kuma na siyo ɗin zo ki dake ni uwata, makira kawai.” Ya galla mata harara kafin ya saki labulen parlourn ya juya yayi tafiyar shi. Da ya shigo ko kallon Maama bai yi ba, amma a cikin kalaman shi ta fahimci saƙon da nata ne kuma ta ɗauka, don haka tunda ita ba uwar shi bace babu ruwanta da abinda yake yi ko menene. “Kinji shi ko Maama” Ta juyo ta kalli ƙwallar da ya taru a cikin idanun Ilham. “Kema ina ruwanki? Ba na hana ki shiga uku da faɗi ba'a tambaye ki ba?” Daman ta sani sai ita kaɗai Maama zata yiwa faɗa. Ko tayi daidai ko bata yi daidai ba idan ya shafi sauran yayyenta saidai tayi mata faɗa ita kaɗai su ba zata ce musu komai ba. Cikin kasashshiyar murya tace “Maama har bani kuɗi ɗan shaye-shayen yayi fa kafin yaya Aliyyun ya karɓa ya siyo masa” Ta waro idanu cikin tashin hankali tace “kuma kin karɓa?” Sauyawar yanayin Maaman lokaci guda ya sanya ta saurin ajiye bowl ɗin a gefe ta shiga girgiza kai da sauri. “A'a Wallahi ban karɓa ba” “Toh daga yau ban yarda ba ban amince ke kaɗai kina bin hanyar ba. Ko ki koyi shiryawa da wuri kina bin sauran ƴan uwan ki ko in faɗa ma baban ku.” zaburowa tayi ta riƙe hannunta tana ƙara girgiza kai “wallahi ba zan sake ba, dan Allah Kiyi haƙuri kada ki faɗa mishi” Yanayin kallon da take mata da wannan raunin a cikin idanunta ya tuna mata da shekaru tara baya, lokacin da aka kawo ta wannan gidan a matsayin amaryar mahaifinsu. Yayin da bata saka sauran yaran shi a cikin idanu ba sai bayan kwanaki, Ilham yarinyar shekaru uku a lokacin ne kawai tazo jikin gadon da take zaune a wannan daren, ta samu wuri ta zauna daɓas a saman carpet da aka lailaye ƙasan ɗakin da shi tana leƙowa ta kasan mayafin da aka lulluɓe ta, koda suka yi ido huɗu a lokacin da irin wannan kallon a fuskarta. Shiyasa bayan duk wani rikici da tashin hankali da ya biyo bayan karɓanta da tayi ta ƙi ta haƙura da yarinyar. Ba domin zallan jinta a rai da take yi kaman ƴar da ta haifa ba, harda dalilin raunin da take gani a cikin idanunta. ….. “Idan kuka samu abun nan yayi popular kuka san irin kuɗin da zaku samu?. Kuma daga nan baku buƙatar biyan kuɗin recording, saidai ma studios suna niman ku suna biyan ku tun kafin kuyi musu waƙan su sake ma duniya. Amma dubu goma zallan recording zai muku gaskiya, banda sabon sauti shima tunda kun ce tape har biyu kuke so.” Fire dake faman zuƙe sigarin da ya zara a aljihun wandon uniform ɗin Abdulhameed yana sirka musu iskan wurin da hayaƙi jira yake yi ya samu inda zai kashe wutar sigarin a goshi ko ƙeyar mai studio ɗinnan. “Amma yaya batun wanda kace idan muka haɗo kuɗin zaka haɗa mu yayi mana advertising na music tape ɗin?” Abdulhameed yayi tambayar cikin lalama, tunda ba zai fara waƙa bane don ya kunna a ɗaki yaji shi kaɗai. Yanda ake saka na wasu a Radio kowa yana ji haka yake so shima a saka nashi. Yana da burin har wata rana a haska shi a gidan talabijin domin haka gajen haƙuri ba nashi bane, sanin cewa waƙar su ba shi zai tallata kan shi ko ya siyar da kan shi ba sai sun kama ƙafar masana wa'inda suka fisu experience a music industry. Mutumin ya dube shi a cikin idanu “A moher! babu abinda baya yiwuwa idan akwai kuɗi. Kai idan kuɗin ka sun isa har Lil Wayne idan kana son gani zaku gana har kayi collaborating da shi ma. Don haka kuje ku ƙaro kuɗi ku dawo indai da gaske kuke kuna so ku zama manyan rappers a san da ku a ko ina.” Fire zai yi magana ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga mishi hannu. “Nawa zamu ƙaro?” Mai studio ɗin ya ɗan tsuke baki yana tunani kana yace “kun ga tunda ga na recording yanzu sai a samu na sound kaman dubu biyar na advertisement ma dubu biyar” “Amma hidiman ka akwai rainin hankali a ciki. Ba kai kace mana 10k zai yi mana komai da komai tunda ba babban production bane ba daga farko?” Cewar Fire a harzuƙe. “Abubuwa ne suka canza, idan ba zaku iya ba ga kuɗin ku kuje ku nemi wani studio” Fire ya miƙa hannu zai karɓi kuɗin. Lallai bai san yaya ma aka yi suka haɗa wannan ɗin a cikin kwana biyu kacal bane yake kawo musu wani maganar banza. Bayan Abdulhameed da yayi ƙuru ya haɗo dubu shida, ya san mahaifin shi na can yana niman sabon wayar shi da ya salwantar a dalilin sauran dubu huɗun da ya cika musu. Dakatar da shi Abdulhameed ya sake yi, shi ba mai zuciyar haƙura da abinda yake so cikin sauƙi bane. “Shikkenan, idan muka kawo wani dubu goman ka tabbata zaka cika alƙawarin ka?” Ya gyaɗa mishi kai yana lumshe ido cikin tabbatarwa da kuma jin daɗin damfaran samarukan da yake shirin yi cikin sauki. “Zamu kawo, ka cika alƙawari ko kuma zaman shagon nan ya gagare ka. Bani daba amma shi zai fara gwadawa a kan ka” ya ƙarasa magana yana nuna Fire wanda ya ɗaga rigan jikin shi karamin wuƙan da ya soke a kunkumin shi ya bayyana. Abdulhameed ya juya ya fice daga studio ɗin Fire ya rufa mishi baya bayan ya gyara zaman rigan shi. “A moher yanzu kam saidai mu fasa gari ayi a nemo kuɗaɗen nan” “Ba zaka yi abinda bayan mun shahara zaka ɓata mana suna ba.” Ya amsa da harshen turanci idanun shi kafe a kan baƙin canvas ɗin ƙafar shi. Tunanin ta inda zai fara yake yi, bai san ta ina zai fara nimo dubu goma ba tunda babu wani hanya na neman kuɗi da ya sani bayan idan yana da kowani irin bukata ya tambayi Nne ta bashi. Amma tunda ta nuna mishi bata amince yayi waƙa ba babu yanda za'a yi ta ɗauki har Naira dubu goma ta bashi, kuɗin school fees ɗinshi na term kenan, kuma makaranta mai tsada Nne ta saka shi a hakan. Ya luma hannu cikin gashin kanshi yana furzar da numfashi. Ba zai sake ɗauka mata kuɗi ba, wannan ma da amincewarta kuma bata masa iyaka ba shiyasa ya ɗauki daidai abinda zai biya mishi buƙata, amma ba zai taɓa yiwa Nne sata ba, bayan duk ƙoƙarin da take yi a kan shi. Ita kaɗai tana mishi gatan da masu uwa da uba basu dashi, ba zai mata sata ba bayan yasan irin wahalan da take yi a kansa shi kaɗai. Sai ya zaro blackaberry ɗin shi a aljihu ya miƙa ma Fire “Lukman nawa za'a sayi phone ɗin nan?” Karɓan wayan yayi ya jujjuya a hannun shi sannan ya mayar mishi yana faɗin, idan tayi daraja ne dubu 3, da kwalinta kuma zata iya kaiwa 3500 ko dubu 4 idan an samu mai so kai tsaye. Bayi da wani zaɓin da ya wuce ya tambayi Nnen dai, Ko wayar shi ya siyar ita ɗince zata nemi kuɗin siya mishi wani, kuma yana da tabbacin ta siye wayan nan ninkin kuɗin da zai siyar sau uku. “Ka san me? mu haɗu a wurin da muka saba, zuwa gobe zan yi ƙokari inzo da kuɗin.” …. Suna saka ƙafa a cikin gidan dariyar da Ilham take ƙyalƙyalawa ya fara shiga kunnuwan su, kafin suka hango ta zaune a kan farin kujerar roba ta ɗaure tray ɗin silver a kan cinyarta tana taya Maama tsintar wake. “Nidai ba zance a siyo kaji saboda ciwo a ƴar yatsa ba ahtoh, tunda ciwon bai kama bakin ki ba idan ya dawo sai ki faɗa mishi da kan ki” muryar Maama ya fito daga kitchen ɗinsu na tsakar gida wanda ta shiga ɗaura sanwan abincin dare. Saida Ilham ta ƙara ƙyalkyala dariya saboda son lallaɓa ta take yi kana tace “kema fa zaki ci idan aka yi farfesun Maamana” “Ba sai a hana ni ba?.” Tayi maganar lokacin da ta fito, sai taga Ilham ko rabin gama gyaran wake bata yi ba. “Har yanzu kuma baki gama tsince ɗan wannan waken ba Fidela?. Mijin ki sai ya fara gyangyaɗi kafin ki dinga kai mishi abinci ko?” Baki ɗaya hankalin su bai kai kan mutanen da suka shigo musu gidan kai tsaye babu sallama ba. Sai wucewarta suka gani fuuu janye da akwatinta bayan ta ja dogon tsakin da yayi nasaran tattaro duka hankalin su ya dawo kanta. Ita ta fara wucewa ɗakinta sannan masu rufa mata baya suka biyo sawu. “Duniya daɗi, tunda an samu an kori ƴar uwar mai gida sai bararrajewa kawai.” cewar ta biyun su tana ƙarewa simintin dake lailaye a tsakar gidan kallo yanda yake a share a wanke. Basu ishi Maama kallo ba sai karɓan tray ɗin hannun Ilham tayi ta koma ɗakinta dashi ta bawa Iska ajiyar su. Ganin haka Ilham ma ta miƙe zata bi bayanta. Ɗan ɗaɗin da take ji na yau hayaniyar gidan ya ragu na ɗan wani lokaci yana gushewa, daman su Iman da Ihsan suna dawowa daga boko basu daɗe ba lokacin Islamiyya yayi suka tafi banda ita, yayyenta maza kuma ba masu zaman gidan a ko yaushe bane dama, suna da wani matsugunin a family house ɗin Baniza. Shiyasa yanayin sosai yayi mata daɗi sai gashi wannan matar da idan ba'a ji muryar ta a maƙota a kowace rana ba bata jin daɗi ta dawo. “Ke! Baki iya gaisuwa ba ko? Saboda Jamila ta koya miki raina iyayen ki.” Ta ɗan turo baki “A fa fiyan goggo Fatu, a fa fiyan goggo Halima” ta gaida su ina wuni da harshen jenjo. Fatun bata amsa ta ba sai harara da ta watsa mata, tana riƙe da sabon kwali mai zanen keken ɗinki ta wuce ɗakin da matar farko da zura key ta buɗe daga gefen na Maama. “wuce muje ki taya mu shigo da kaya” goggo Halima ta umarta. Sai tayi saurin nuna mata yatsar ta “Ƙafa na akwai ciwo, Taa yace in huta shiyasa ko makaranta ban je ba yau” “Babu wanin nan lalaci kawai kike fama dashi, Ni zan so ganin wanda zai kai zuciya nesa ya tattare ki a ahalin Baniza” ta ja tsaki ta koma wurin shigo da sauran shirgin da suka zo dashi, itama Ilham sai ta saɓule jiki ta koma parlourn Maama ta cigaba da kwaciyarta. Duk kaiwa da komowa kuwa sai sun yiwa Maama habaici ta hanyar aibanta Ilham. Har yarinyar ta ƙare ta fara zubar da hawaye. Maama Bata kula ta ba saboda itama zuciyar ya iso wuya. Freezer ɗinta ta buɗe ta ɗauki ƙullin naman miya guda ɗaya wanda ta tafasa ta saka yayi kanƙara, sai kuma ta ƙara wani saboda Ilham da taji ciwon da take riritawa da kuma kishiyarta da ta dawo a yau tunda yanzu sanwar harda ita, ta haɗa da waken da ta ƙarasa tsincewa ta fita dashi. Kaya sosai suka baje a tsakar gidan har jikin bangon ɗakin Maama, A dakalin shiga parlourn Taa kuma suka samu matsuguni ana ta ɗaura sabon keken ɗinki. Tayi musu kallo daya ala dole sannan ta juya harƙan gabanta. “Ahalin Baniza dai muna da tushe da asali sai Usmanu mai idon gane-gane da ya je ya ɗibo mana tsintacciyar mage. Ina fatan dai kina kwana da tashi da sanin ko da aure ko babu Shafa’atu dai jinin Usman ce, duk aikin sihiri da tsafi baki isa ki raba su ba wallahi.” “Halima kin san dai ko bayan ran Usman baki da gado a gidan nan ko? Toh ɗaga hankalin na menene?” Ta tanka ganin shiru ba zai fishsheta ba tunda sun ƙare sun shigo da ita kai tsaye. “Au ke har ta rabon gado kike tun da rai da lafiyan shi shiyasa kika shiga kika fita sanda kika shiga tsakanin shi da Shafa ko?, toh da mu kike zancen Jamila dan Allah kada ki fasa” “Ku dai zauna ku tambayeta dalilin da yasa tayi yaji. Lokacin da suka warware abar su ina nawa ɗakin ina kula da tarbiyyan yara na, don na samu darasin cewa girma da hankali abubuwa biyu ne mabanbanta. Fidela kuma in sha Allahu rabbi yanda sauran ƴammata suke auren soyayya itama shi zata yi, ba wanda yaranku zasu dinga koro mana ita ko su gagara zuwa biko ba sai ta dawo da kanta” Idan sun jawo tayi musu gori Laifin su ne da basu bar rikicin su a iya tsakanin su yanda suka saba ba sai sun taɓa mata yarinya. “Wa ma zai ɗauki tsiyarki? Ai tun ranar da ta fara kallon ki a matsayin uwa muka cire ta daga cikin mu, bamu maraba da mugun Iri.” Sai yanzu Fatu ta magantu. Shafa da ta zare ɗankwalin kanta ta ɗora a ƙugu ta ƙaraso gabanta tana faman hura hanci “Kuma dai soyayyar ita ta sanya na shigo gidan nan ko shekara baki rufa ba gida ya dawo nawa yara suka dawo nawa. don haka duk wani taggu da munafurcin ki nan gani nan bari ɗumamen mayya, Usmanu ya ɗauko kainuwa dashen Allah.” Maama bata ji ko ɗarr da yanda take faman muzurai da hura hanci ba, domin idanma ta kai ga kacamewa Shafa’atu shaida ce a kan yanda zata ɗagata ta nana da ƙasa. “Ai soyayya idan ya wuce wanda yayi sanadin raba Usman da ahalin Baniza ƙarya ce” ta faɗa da murmushi a saman fuskarta, wanda yayi nasarar cusa ma Shafa takaici tayi kururuwa ta ruƙo wuyan riganta, suna shirin kaurewa suka jiyo muryan shi. “Kai! Kai!” Maama da take fuskantar ƙofar shigowa idanunta suka sauƙa a kan shi cikin fararen kaya da ya fita dasu a jikinsa riƙe da briefcase ɗin shi. Girma da kuma shekarun shi sun nuna ƙwarai a kan fuskar shi dake bayyana rashin jin daɗin yanayin da ya dawo ya riski gidan a ciki. Shafa da ta bashi ƙeya ta juyo ta fuskance shi a lokacin da zuciyarta ya shiga bugawa da karfi. Ya faɗa mata idan ta tafi kada ta dawo masa cikin gida tunda ita bata da sirri, kuma koda a waya bai taɓa kiranta ba tun bayan samun saɓanin su har zuwa yau, shiyasa da zaman jira ya isheta ta nema wa kanta mafita ta tattaro ta dawo in yaso sai ayi yanda za'a yi. “Sannu da dawowa” Shafa ta gaida shi kanta a ƙasa tana ƙoƙarin kada muryarta ya bada ita yayi rawa a gaban kishiya gashi ita ko iya gaishe shi bata yi ba sai wucewarta da tayi ta cigaba da harƙan gabanta. Koda ace ran shi ya ɓaci da banzatar dashi da Maama tayi toh bai gwada a kan fuskar shi ba, sai ma share gaisuwar Shafa da yayi, ya amsa nasu Fatu da “lafiya” kawai yana kallon yanda suka baje kolin su a hanyar wucewar shi sai ya wuce ɗakin Maama kawai ya duba Ilham da aka kira shi a waya aka sanar mishi ta samu rauni, dalilin shi na dawowa gida da wuri kenan. ```````````` . Chapter 5 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites* *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 05…“Abdulhameed!” Gyaran murya yayi daga cikin ban ɗakin, sai ta ɗaga murya tana faɗin “I'm going to make dinner, what do you want to eat?” Ya sake gyaran murya ta fahimci a inda yake, a ranshi yana ayyana koma menene ba za'a jira ya fito ba tunda ba'a kwana a toilet?. “You said?” Ta sake tambaya tare da ƙara sautin muryarta, sabila da haka bayi da zaɓin da ya wuce ya bata amsa da “Rice.” yana ɗaga murya yanda zata jiyo shi. “Kifi ko nama?” Ta tambaya cikin hausarta mai rauni. “Nne kowanne fah!” Ya amsa a ɗan hasale. Sauƙe numfashi yayi lokacin da yaji ta amsa da “okay” ya goga sabulu a hannun shi yana shirin kunna famfon sink ya sake jiyo muryarta tana tambayan. “Jollof or stew?” Da sabulun a hannun shi haka ya murɗa ƙofar ban ɗakin ya buɗe ya fito. Idanun shi suka sauƙa a kanta sanye da apron riƙe da muciya da kuma ludayi a hannayenta, wato cikin shirinta take. Ya sake mata murmushin da bata ɓata lokaci wajen maido mishi da martanin shi ba. “Nnem” ya kirata cikin taushin murya kana ya ɗaura da “duk abinda kika bani zan ci” Sai ta jinjina kai, cikin harshen Igbo tace “Na ɗauka baka da appetite ne saboda baka da lafiya, amma bari na yi mana stew da kifi toh” Gyaɗa kai yayi cikin nuna amincewa, shi ya manta yayi mata ƙaryan ciwo da safe ma. Har ta juya zata fita ya kira sunanta. Bai tantance ba a lokacin, na niman biyan buƙatar da yake shirin gabatarwa a gareta ne, ko kuwa abinda yake ji a zuciyar shi ne yake shirin bayyana mata… Amma da ta juya ta dube shi sai ya samu kanshi da furta “I love you” Lokaci ɗaya fuskarta ta haska da annurin murmushin da ya taho tun daga ƙasan zuciyarta sannan ta amsa da “I love you too Nwam” tare da huro masa kiss. Yana da tabbacin da a kusa da ita yake saidai ta janyo wuyan shi ya ranƙwafo ya daidaita da tsayinta sannan ta manna mishi sumbar a kuncinsa. Bayan ya gabatar da sallan Isha a ɗakinshi kaman yanda ya saba baya fita yin asuba da Isha a masallaci, sai ya fita zuwa kitchen ɗinsu a inda ya sameta gaban table gas tana juya tumatirin dake zaɓalɓaka a kan wuta tana yi tana waƙoƙin yare da ɗan girgizawa. Rayuwan da take yi a yanzu ita da ɗanta kawai yafi mata ƴanci da farinciki fiye da wanda tayi da ƴan uwanta na jini balle a sako zancen dangin mijinta, wanda take tuna rayuwar da tayi dasu kamar mummunan mafarkin da idan ta tashi ba zata bari ta sake komawa barci cikin sauƙi ba. Shiyasa duk son da take yiwa Muhammad tunda suka rabu bata sake waiwayan shi ba bayan ɗanta da taje ta ɗauko, kuma bata fatan bayan Abdulhameed a samu abinda zai sake shiga tsakaninsu har abada domin Zaman su bai yi daɗi ba sam, ƴan uwan shi ranta ne kawai basu rabata da shi ba. “Nnem.” ya kirata cikin taushin murya. Juyowa tayi ta dube shi, sai ya karya kai tare da kwaɓe fuska “can we talk? Please..” Ganin damuwa shimfiɗe a kan fuskar shi ya sanya babu ɓata lokaci ta kashe wutan miyan kada ya ƙone sannan ta ruƙo hannun shi. “Menene?” Da hannunta da ta riƙe shi, da shi yayi amfani ya janyota suka fice daga kitchen ɗin zuwa dining table ɗinsu mai kujera huɗu, yaja mata ɗaya ta zauna. Idanunta a kanshi, hannunta riƙe da nashi har shima ya samu matsuguni a gafenta sannan ya dubeta. “Nne I don't know where to start, amma kin san a duniyar nan bani da kamar ki right?” Jinjina kai tayi cikin tabbatarwa, tana ƙara bashi dukkan nutsuwa da hankalinta wanda bata raba da komai ba. Ya cigaba da cewa “that's why Duk abinda nake so da abinda zan yi ba zan taɓa samun nasara a kai ba saida amincewa da kuma taimakon ki. Nne ina son waƙa, ina son nayi waƙa, ina son in shahara Nnem. Ina son a lokacin da ɗaukaka yazo mun a dubeni ace ni ɗanki ne, kuma a sanadin ki ne na zama Abinda na zama.” Ɗan dakatawa yayi yana nazartan yanayinta, jikinta yayi sanyi kam amma babu alamun ta amshi zancen shi a kan fuskarta. Ba kuma ya zauna a nan don ya miƙe ba tare da amincewarta bane, idan yayi haka bai cika ɗa a wurin rai biyu masu masifan nacin da suka tsallake duk wasu iyaka suka rufe idanuwan su ga duk wani banbanci dake tsakanin su don kasancewa tare ba. “Mamana.” ɗagowa tayi ta dube shi da mamakinta ƙwalla ne ya taru a kwarmin idanun shi. “bayan gani a hoto ban san yaya kamannin Babana yake a zahiri ba. Bai tako yazo inda muke ya duba lafiyata ba, bani tunanin ko lambar wayata yana dashi, ya manta damu saboda ya samu wasu iyalan ya cigaba da rayuwa, toh meyasa ni zai datse mun rayuwata? Me ya bashi daman jayayya da Abinda nake so bayan kece kika sha wahalar ɗawainiya dani Nnem? Kece ya kamata ace kina da wannan zaɓin, kuma ina laifi a cikin waƙa?” Shirun da ya ratsa tsakanin su shiru ne wanda idan da Abdulhameed ya san abinda zai je ya dawo bayan shi toh da a tsakanin wannan shirun zai girgiza kan shi ne ya karkaɗe duk wani lissafi da yake ciki sannan ya dubi mahaifiyar shi ya shaida mata ya fasa shirin shi gaba ɗaya. Ya tabbatar da burin shi ya cika ne a lokacin da ta zaro wayarta daga aljihun dogon riga ƴar kanti dake jikinta, tun kafin ta latsa layin mahaifin shi yasan cewa duk wani rikicin da za'ayi abinda yake so ya riga ya samu. Kuma yana jin a lokacin da ta shiga jero masa kuɗurin ɗanta kaman itace daman ta tsara hakan tun farko bayan mahaifin nashi ya ɗaga kiran daga ta ɗaya ɓangaren. Tayi shiru tana sauraron yanda yake ɗaga murya yana tada jijiyoyin wuya da tabbatuwan kafuwar shi a kan hukuncin sa. “...Idan kuma ba haka ba, zan zo har inda kike in karɓi ɗana. Ba gazawa bane ya sanya na bar miki shi kuma ba don ina tsoron ki bane Amina Nkiru Eze.” “I dare you Muhammad Kagarko! I dare you please!. Wallahi a kan Abdulhameed zan baka mamaki tunda ai ba tare da kai muka yi naƙudan shi ba, ni kaɗai na san zafin kayana so don't try this nonsense with me Abeg.” Dogon tsakin da taja tana janye wayan daga kunnenta har saida ta latsa madannin katse kiran sannan yazo karshe. Ta ɗago ta dubi Abdulhameed “promise me ba zai taɓa karatun ka ba, idan har kayi ƙoƙari sakamakon jamb, waec da neco dinka suka yi kyau ni nayi alƙawarin tsaya maka a kan abinda kake so, Saboda kai ɗana ne!” Sai kawai ya ɗaga hannu yayi mata jinjinan ban girma kana ya fara kiɗa a kan teburin gaban shi yana mata waƙa da inyamuranci, cikin muryar shi dake kan ƙara zurfi yake mata kirari, ita kuwa ganin rawan ba zai yi mata a zaune ba sai ta miƙe tsaye tana rausayawa da faffaɗan murmushi a kan fuskarta, farin cikin ɗanta shine farin cikinta. …. “Miƙo mun dorinan nan Filiyan” Daman Ihsan Jira take yi saboda Taa ya tilasta musu jiranta su tafi tare gashi zata jawo musu dukan latti don haka harda ɗan haɗawa da gudunta ta koma ɗakin maama ta ciro zabgegiyar bulalan da take ratayewa a bango ta kawo. Ilham da ta baje a kan tabarman da suka karya tana matsar ƙwalla tayi saurin tashi zaune lokacin da Maama ta karɓi bulalan. “Kin tashi ko kuma?” “Wallahi Maama ba zan iya takawa idan na saka safa ba” “Sai ki saka ƙafa ɗaya tunda ɗaya ne mai ciwon” Tana hawaye da komai suka fita daga gidan sai gashi tana haduwa da ƙawayenta ƴan hanyar su ta share hawayenta suka cigaba da hira, tafiyanta take yi normal kuma don ta manta da zancen ɗingisawa. Maama bata tunanin ko rabin hanya sunyi lokacin da Hashimu babban ɗan goggo Fatu ya shigo gidan yana hargagi harda bulalan shi na jibgan Ilham wai tayi ma mahaifiyar shi rashin ɗa’a. . . . “kice Wallahi” Har wani kashe idanu take yi lokacin da ta amsa da “Wallahi tallahi, kunga a jikin wancan dutsen ne ma, hala har yanzu da jini na a jiki. kuma shima ɗan shaye-shayen a…” Maganarta ya katse lokacin da idanunta suka sauƙa a kan sigarin dake tsakanin yatsun shi biyu, yana fitar da hayaƙin da suke iya shaƙar warin shi daga inda suke. Kamar jiya, yauma sanye yake da uniform ɗin da ba zata iya tantance na wani makaranta bane, domin bata taɓa ganin mai irin shi ba a unguwar tasu. Idanun shi yana kan kuɗin da wani a gefen shi yake ƙirgawa, mikaƙƙun ƴan dari biyar-biyar da suka ƙara ma tsoronta tasiri lokacin da ya mayar da sigarin tsakanin leɓen shi ya karɓi kuɗin ya tusa a aljihun gaban wandon shi kana ya miƙe tsaye. Mantawa tayi da yanda ake numfashi yayinda idanun shi suka shiga cikin nata saboda tsaban kaɗuwa. Saidai ko sakwan guda bai gifta a tsakani ba ya juya ya rataya jakar shi ya ɗauki hanyar da zai fitar dashi daga lungun, ɗayan ya mara mishi baya. Duk tambayar da suka yi mata bayan nan basu samu wani amsa daga bakinta ba harda Ihsan mai son taji kanun labarai idan ta koma ta shaida ma Maama da ta bata aikin sakawa Ilham ɗin ido. Har suka isa gate ɗin makarantar bata sake ko tari ba, gani take yi kaman tana faɗan wani abu a kan shi dawowa zai yi ya sameta. A ɗarare ta biyo lungun a hanyar su na dawowa saidai bayi nan, har zuwan su da dawowan su daga islamiyya bata gan shi ba don haka ta saki ranta washegari. gashi ciwon ƙafanta har ya fara warkewa ta ɗaye bandejin abunta tunda bai yi nasarar hana zuwanta makaranta kaman yanda taso ba. A rana ta uku suna dawowa daga Islamiyya tare da ƙawayenta sai gashi nan zaune a wurinda ta saba ganinsa amma yau sanye yake da kayan gida blue din T shirt mai ratsin fari da baƙi da kuma wandon jeans. Babu sigari a hannun shi sai waya da yake latsawa ga kwalban limca da yasha kusan rabi a gefe da laidan biscuit dake a ɓare. Tana tafiya a tsakiyar su ne don ita take basu labarin aljanun wata da ya tashi ɗazu a gaban idonta lokacin da ake dukan latti, har mai aljanun ta cukumi wuyan ustaz ɗin dake dukan kuma itama tana cikin ƴan lattin amma hatsaniyar yasa ita da sauran ƴan baya suka tsira daga duka. Shewa da maganar da suke yi cikin ɗaga murya ya sanya ya ɗago kanshi daga screen ɗin blackberry ɗin da yake game a ciki ya ɗaura idanun shi a kansu lokacin da Ilham take ƙoƙarin komawa ta ɗaya ɓangaren, tana amfani da jakarta dake ɗauke da Al-ƙur’ani mai girma da sauran littattafan hadisai wurin kare fuskarta amma ya rigada ya ganta. Abinda bai tantance ba shine ma shine take ɓuya ko kuma hakan wani abun su ne na daban. Lokacin da ya mayar da idanunsa kan wayan shi “game over” ya gani rubuce, hakan ya saka yaja tsakin da ya sanya Ilham ƙara sauri ba waiwaye kada ace biyo ta yake yi. A washegarin ranan Abdulhameed suka yi nasaran zuwa studio suka yi recording ɗin waƙar su na farko shida Fire. ya rage saura ayi editing a naɗe musu shi a tape ya ɗauko ya kawo ma Nnem ta ji irin baiwar da Allah yayi mishi yanda zata ƙara samun ƙaimin tallafa mishi har yayi nasara a abinda ya saka a gaba. Bayan sun gama suka dawo lungun da suka saba zama saboda yana kusa da studio ɗin, Abdulhameed ya baiwa Fire kuɗi, ya siya ma kanshi awara a wani gida a lungun shi kuma ya siyo mishi cake da 7up a shagon malam Sama'ila saboda shi bai iya cin awara ba har yau. Suna ci suna hiran yanda abubuwa zai kasance ya fara ganin masu irin uniform ɗin islamiyyar su suna wucewa don haka ya baza idanu ko zai ganta, ko zai tabbatar da abinda ya gani jiya. Babu daɗewa sai gata nan a tsakiyan jama'a kamar ko yaushe tana tafe tana zuba choi-choi kaman kurna. Wannan karon da ya zuba mata idanu bai ɗauke ba har saida itama nata suka daidaita a cikin nashi. Lokaci ɗaya ta firgice ta fara ƙoƙarin ɓuya, kuma shi akwai abinda yake son tabbatar ma idanun shi don haka bai ɓata lokaci ba wurin saka yatsu biyu a tsakanin laɓɓan shi yayi fiiton da taji ƙaran shi har tsakar kanta. “Hey!” Ta sake jin muryar kaman na kwanaki huɗu da suka wuce. Bata san ta juya ta dube shi ba duk da zuciyarta dake mata kashedin ta gudu ko ta ɓuya. Saidai ba ita kaɗai ba, duk wa'inda suke tare ma abinda tayi shi suka yi, ciki harda ihsan kuwa. Sai ya nuna ta da yatsa ganin sauran ma sunyi zaton hankalin su yake buƙata. “You in the middle. What's your name?” Ita ya tambaya amma amsar ta fito daga bakin kowa banda ita saboda yanda cikinta yake hautsinawa. “Ilham” sauran suka bashi amsa a tare. “Zo” Bata taɓa sanin kalma guda ɗaya tilo yana da ikon jan linzaminta ba saida ta samu ƙafafuwanta suna kaita zuwa gare shi babu wani jayayya. Fire ya zuba mishi idanun mamaki yayinda shi kuma yake yiwa saman haɓarta kallon ƙurilla har tazo kusa ya samu yaga abun da kyau. Birth mark ne, abinda ake kira da tawadan Allah a hausance shine a ƙasan bakinta ta ɗan gefe kaɗan, amma ta saka wani baƙin abu ta zagaye shi ya kara turuwa da bayyana kuma kaman tasan yana yi mata kyau ne shiyasa tayi hakan da gan-gan. “Gani” ta maimaita cikin sanyin murya, hakan yasa ya dawo da idanun shi cikin nata. Gyara zama yayi yana gyaran murya sannan yace “ina Aliyyu?” Ta bashi amsa da “yana gidan su baban mu a Jakara” “Yayan ki ne shi?” “A hankali ta gyaɗa kai” “Idan kin je gida kice gobe ina niman shi” Sai ta amsa da “toh” “Jeki” ya sallameta tunda ya tabbatar da abinda yake ganin kaman idanun shi ne yake nuna mishi haka. Ya tsaya a kan hukuncin rabin fuskar Ilham ta ƙasa yafi kyau, domin ba yarinya bace da haka kawai idan ka kalleta zaka buƙaci ƙara wani. Amma idan tana magana ko dariya ga birth mark ɗinnan da take yiwa kwalliya ba zaka so idan ka ɗaura idanunka a kanta wani abu ya sanya ko ƙyaftawa kayi ba, saboda yanda fuskar tata take rikidewa baki ɗaya. Bata ɓata lokaci a wurin juyawa ta tafi ba kaman yanda yace. kuma hankalinta bai kwanta ba har saida ta saka kafarta a cikin gidansu. Ƙaran keken ɗinkin da ya cika tsakar gidan shi ya sanyata dakatawa ta furzar da numfashin ta tsira sannan ta dubi matar dake kan keken tana rage tsayinta kaɗan “A fa fiyan maman baba” ta gaidata. Idan ma shafa ta amsa gaisuwar toh bata jiba, saboda hankalinta ya tafi kan Ikram wanda ta shigo da gudu ta faɗa ɗakin maama. Ba sai an faɗa mata ba tasan zuwa zata yi ta shaida mata abinda ya faru tsakaninta da ɗan shaye-shayen nan bayan duk roƙonta da tayi har kaman zata durƙusa mata kafin su iso. Don haka ta rufa mata baya da sauri amma bata san yaya akayi bakinta ya furta sallama kafin ta shiga ba sai domin sabo da yinshi hala. “Maama wallahi…” “Koma kije ki gaisheta da gida mara kunya, kuma kika sake shigo mun ɗaki babu sallama sai na karya kafanki.” gargaɗin Maama da ya ceci Ilham kenan don Ihsan bata da zaɓin da ya wuce ta kame bakinta har sai tayi abinda aka ce. “Wa’alaikumussalam” ta amsa sallamar Iham tana miƙewa tsaye daga kujeran da take zaune tana kallon draman hausa a Tv don akwai wuta. Sai Ilham ta sake rusunawa, itama ta gaidata “ina wuni Maama nah, sannu da gida” Ta amsa da “lafiya Alhamdulillah Fidela. Ga abincin ki a kwanon filiyan na haɗa muku saboda an kai abinci maƙwafta a naki. Idan kun cire uniform ɗinku kuma kada ku fasa watsar mun a tsakar ɗaki, bari naje na kwaso shanya Almuru ta gabato.” da kalmar “toh” ta amsa hankalinta a kan ƙofar da Ihsan tayi sallama tana shirin sake shigowa ciki, saidai Maama bata saurareta ba tayi wucewarta hakan ya bawa Ilham daman ƙarasowa wurinta tana murmushi. “Ƴar ƙanwata, my Filiyan ƴar kyakkyawa.” tace tana riƙo hannunta. Ƙoƙarin ƙwace hannun tayi amma ilham taƙi sakewa “babu waninnan ai sanda tace idan baki ji gargaɗin da tayi miki ba in faɗa mata ta sanarwa Taa.” “Wallahi tambaya na yaya Aliyyu kawai yayi kuma ai kina gani ina bashi amsa na juyo, wallahi babu ruwana dashi, ɗan shaye-shaye ne fah!” “Toh sai idan kin yarda yau ke zaki wanke mana uniform sai ba zan bawa Maama Labari ba” Da sauri Ilham ta amsa da “na yarda!” “shikkenan, ki ɗauko plate ki zuba mana abinci toh.” shima ba musu ta amsa da toh tayi kaman yanda ƙanwarta da ta bawa shekaru kusan 4 tace. ```````` Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... JODA by Sadi-sakhna ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh DAƊIN ZAMA by Seemahwrites *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a turo shaidan biya ta 09039206763 Chapter 6 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites* *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) 06…. Sosai take farin ciki har ta gama shirin makaranta, saboda a safiyar yau Juma’a awara Maama tayi musu. Tana son awara sosai, gashi yau idan aka je makarantan boko ba za’a daɗe sosai ba kuma babu islamiyya, sannan da yamma zasu yi kwalliya su sanya kaya masu kyau suje yawon juma’a a basu kuɗin siyan wainar fulawa kuma maama ba zata hana su siya ba saboda yau juma’a ce, jumu’atu babban rana. “Maama zaki zuba mun wani in tafi da shi makaranta ina?” Ta tambaya daga bakin ƙofar kitchen lokacin da Maaman take miƙo mata kwanon na yayyenta maza ta kai musu ɗakinsu. Daga bayanta aka ce “Ƴan JSS suna zuwa school da lunch box ne daman?” Saida ta riƙe kwanon da kyau, saboda ta san idan tayi sake ta kifar da awaran nan a wurin ita da Maama ne, Sannan ta juyo tana hararar Ihsan. “Ni nace miki a lunch box za'a saka mun?!. Ni ko a laida ma inaso yanda zan ji daɗin faffasa shi idan zan ci.” Ihsan ta jinjina kai tare yin ƙwafa “Ni kike harara? In faɗa?” Da sauri Ilham ta shiga girgiza kai “A'a kiyi haƙuri dan Allah, ba zan sake ba” Maama sai ta tsaya kallon ikon Allah. “Menene zaki faɗa ɗin?” Tayi tambayar tana riƙe kwanon hannun Ilham kada ta samu ta gudu. Ganin yanda Ilham ɗin ta diririce ga ƙwalla da ya fara taruwa a idanunta sai Ihsan tayi murmushi tare da faɗin “babu komai fah Maama, wani wasan mu ne” ko babu komai zata samu Ilham ta dinga mata abinda take so. Ba don Maaman ta yarda dasu ba ta saketa ta tafi sai domin sun kusa yin lattin makaranta. Haka suka ƙarasa shiri suka fita bayan ta saka su sunyi addu'a. …. Kallon Fire dake faman bincika jakar shi yake yi jikin shi na tsuma. Kwana biyu kenan bai cika huhun shi da hayaƙi ba saboda ya faranta wa Nne kaman yanda itama ta faranta mishi, ta hanyar ɗaukan Kuɗi Naira dubu goma ta bashi ba tare da wani dogon sharaɗi ba don kawai yayi abinda yake so. Amma akwai wani abu a cikin hayaƙin dake saka mishi wani yanayi na musamman wanda bai san ta yaya zai yi bayanin shi ba, ba wai fita hayyaci bane saidai yana daga cikin abubuwan da suke daidaita mishi lissafi. Shiyasa zuwa yau yake jin kaman lissafin nashi yana niman ƙwacewa, gashi ba zai iya siyan sigari a unguwar su ba saboda kada wata rana labari ya koma wurin Nne. Sannan yanda yayi mata alƙawarin mayarda hankali a kan karatu musamman yanzu da yake ajin ƙarshe a secondary fashin makaranta ba nashi bane, daga ƙarshe kuma idan yaje siyan sigari shagon malam Sama'ila sanye da Uniform sai ranshi ya ɓaci kafin ya siyar mishi, idanma shiga ukun shi ya barshi kenan. A yanzu fata guda ɗaya yake da shi, ya samu na rage hanya a wurin Fire koda kara ɗaya. “Babu ko ɗaya?” ya tambaya hannun shi kaman zai shiga cikin jakan ya duba da kanshi, don gani yake Fire yana masa saiɓi. “Wallahi Old man ɗina saida ya caje ni tass kafin ya barni na fito. Kaga har na cikin jakan ma ya ɗauke” Abdulhameed yaja tsaki. “Yanzu yaya za'a yi?” Fire ya tambaye shi. Wani tsakin ya ƙara ja yana tunanin shagon da zasu samu a buɗe da sanyin safiyar nan a kusa. Son kuɗin malam Sama'ila yana iya barinshi fitowa shago da asubahi amma bai kai ya saka shi fita daga shirgin da ba nashi ba. Irin numfashin da ta haɗiya lokacin da ta hange shi da kuma yanda taja tunga ta tsaya ya tuna mishi da wacece ita. A jiya ya samu amsar tambayar ƙwaƙwalwarshi shiyasa tun daga lokacin ya manta da ita da ma wannan birthmark ɗinta mai sakawa tayi kyau ɗinnan. Tunawa da yayi yace mata ta kira masa Aliyyu jiya yasa ya ɗaga murya yanda zata jishi yace “Ilham… Zo.” Ga mamakin shi sai yaga ta dafe ƙirjinta da hannu bibbiyu tare da ƙwalalo idanu, a hankali kuma take juya kanta daga dama zuwa hagu zuwa dama. “Isn't your name Ilham?” ya tambaya ganin bata da niyyan ƙarasowa. Juyawa tayi ta dubi Ihsan da ta cije baki kamar ƴar dambe tana kallon ta. Sai tayi mata kallon ai ku kuka jawo, tunda jiya su suka sanar dashi sunan nata. “Wallahi kika je sai na faɗa ma Maama da Taa” Ihsan ta gargaɗeta cikin ƙasa da murya amma dake hankalin Abdulhameed yana kansu duka ganin yanda Ilham ɗin ta kiɗime sai ya fahimci barazana Ihsan take mata. “Kema zo. Ku zo dukkan ku biyu” Dake Ihsan gani take yi daga farko kaman ta tsira shiyasa hankalinta a kwance ta saka Ilham ɗin a gaba, amma yanzu da layin markaɗe yazo kanta a take cikinta ya ɗuri ruwa. Itace ɗan shaye-shaye yake kiranta? Ta haɗiyi miyau muƙut, Allah Sarki marigagiya Ihsan. “in ƙaraso in same ku?” yayi maganan idanun shi a kan Ihsan don haka ta riga Ilham ma ƙarasawa gaban shi. Murya na rawa tace “gani” Bai kulata ba saida Ilham ta ƙaraso, birthmark ɗinnan ya sake shiga idanun shi sosai kana itama ta amsa da “gani” cikin raunin murya. Koda yau bata yi dariya ba amma a haka uniform ɗin yayi mata kyau. A ɗan haduwar su na kwanakin da ba zasu haura 5 ba ya lura ko yaushe kayanta a wanke a goge yake kafin taje makaranta kuma haka take dawowa babu abinda ya canza a jikinta. “Ina yayanki?” Ya ƙare ya bayyana dalilin kiran. Saboda tasan cikin yayyen nata Aliyyu yake nufi yasa ta amsa da “bai dawo ba sai gobe” a ranta tana tambayar dalilin tsurar mata da ciki kenan dama? Shine ba zai tambayeta tun daga can nesa ta bashi amsa tayi tafiyarta ba?. “Amma kin sanar dashi ina niman shi?” Saida ta ƙara ƙasa da murya ta amsa da “ai bani da waya, kuma ina tsoron kiran shi a na Maama, dukana za'a yi a gida”. Ihsan dai tana ta tsilli-tsilli da ido. Ya muskuta ya ciro wallet ɗin shi a alijun wandon shi sannan ya buɗe ya ciro naira ɗari biyu ya miƙa mata. Saboda yanda ta tsorata da ganin kuɗin saida tayi taku biyu baya, da ace ta ƙara wani saidai ta jita fanjam a cikin kwatamin bayanta. Bai damu ba ya ƙara miƙa hannunshi don kuɗin ya isa gareta. “Me.. me zan yi da shi?” Ta tambaya ba tare da ta karɓa ba, ga jikinta da ya shiga rawa kaman mai jin sanyi. A zahirin gaskiya tunanin da ya zo kanshi a lokacin, ya gwada sa'ar shi da ita ne. wataƙil ita su yarda su siyar mata sigarin idan tace aikota aka yi amma sai ya samu bakinsa da furta abinda ya saɓa da tunanin da ƙwaƙwalwar shi ta bashi. “Tom-tom zaki siyo mun” “Na nawa?” “50 Naira” Sai ta gyaɗa kai “toh” ta saka hannu biyu ta karɓi kuɗin. Idan ba wani abu marar kyau bane ba zata ƙi zuwa ba tunda babba ne ya aiketa kuma ya san yayanta. Ta juya zata tafi ganin ƙaton jakar bayan da take goye dashi ya sanya shi sake kiranta da sunan da take ji kaman ba nata bane, domin cire H ɗin yake yi baki ɗaya yace “ILLAM” Ta juyo ta kalli hannun da ya sake miƙo mata “give me the bag, zan ajiye miki so that kiyi sauri” Babu musu ta zame jakan daga kafaɗunta ta miƙa mishi. Sai ya dubi Ihsan da take tsaye da nata jakan a baya, kusan girman shi daya da na Ilham, tayi tsuru-tsuru kaman kace Kyatt ta zura a guje. yace “je ki raka ta” Ta gyaɗa kai tare da amsawa da “toh” ta bi Ilham suka jera a tare kaman yanda suka fito tun daga gida. “Ka fasa sha kenan?” Fire ya tambaye shi da mamaki. Da “yeah” kawai ya amsa yana bude zip ɗin jakar Ilham yaga menene ya sanya shi nauyi haka. Text books ya fara cirowa har guda shida. English, maths, basic science, basic technology, social studies da civic education. Ya ajiye su a gefe sannan ya ciro Exercise books ɗinta duka, kusan guda goma sha biyu ne, ya jinjina ma ƙoƙarinta don shi ba zai iya dakon wannan shirgin ba, ina laifin taba ɗauko wanda zata yi amfani dasu a ranar kawai. Ya sake luma hannun shi a cikin jakar sai yaji ya taɓa wani abu mai laushi da ɗumi ga wani ƙamshi dake ziyartar hanci. Yayi saurin zaro shi don ganin menene sai ya yamutse fuska ganin awara ne ya mayar mata da kayanta yanda ya ɗauko shi yana jan ƙaramin tsaki. Buɗe littafin farko yayi wanda ya kasance na maths amma kansile-kansilen da ya gani ga assignment da aka yi mata marking taci 4 over 10 yasa ya rufe ya buɗe na gaba. Saidai shi tunda Nne ta haife shi bai taɓa ganin rubutu mai munin wannan ba, kaman tafiyan tsutsa da ake faɗa ɗinnan yau ya ganshi a rubutun Ilham. Ya rufe littafin yana karanta abinda ke jikin bangon littafin. Name: Amina Usman Jen…. Sunan Nne ɗinshi. Sunanta ɗaya da Nne. Wani abu yaji ya buɗe a ƙirjin shi kamar fure a lokacin da hasken rana ya bayyana, wani farincikin da bayi da dalili ya lulluɓe shi. Yana son duk abinda ya shafi Nnem ko menene. Sai ya cigaba da karanta abinda ke kasan sunan. Class: Jss 1 Subject: Islamic Studies Date: 4, March, 2014. Ya ɗaga littafin daga sama ya mayar dashi ƙasan sauran don ya samu daman ganin na biyun. Shima sunan irin na farkon ne, Amina Usman Jen. Hakan na nufin wancan ma littafinta ne tabbas ba na wata ba, sunan nata ne. Saidai bayanan da ya biyo baya yasha banban da na littafin farko. A wurin da aka rubuta Class: sai ta Rubuta ‘High Class’ a gaban shi. Subject: Ask the Teacher Date: Check the calendar Zai buɗe littafin yaga menene a ciki ya hango su suna dawowa, sai yayi saurin tusa shi ƙasan jakar shi dake ajiye a gefe kafin ta lura sannan ya fara ƙokarin maida mata sauran tarukucenta ciki. “Gashi” tace tana miƙa mishi laidan tom-tom ɗin da canjin. “open and take some” yayi magana yana zuge mata zip ɗin jakan. “No thank you” ta mayar masa da turanci itama. Sai ya tsaya da abinda yake yi. “ki ɗiɓa nace!” Haka saida ta ɗauka musu ɗaɗɗaya kafin ya bata jakanta suka tafi bayan sun mishi godiya. Ita dai daɗinta ɗaya anyi mata maganin bakin Ihsan tunda dai gashi yau tare lamarin ya ritsa da su, da bata san inda zata saka kanta ba idan aka je gida, hala saidai wata Fidelan bayan ita. ….. Haka ya gama gwaramniyan shi a ranan ya koma gida da littafin a cikin jakar shi. Saida yayi shirin kwanciya sannan ya fito dashi ya ɗale gadon shi ya buɗe shafin farko. Bismillah ne da Harshen Larabci aka rubuta shi babba da ruwan biro baƙi, wasalin jiki aka yishi da jan biro. Sai zanen hearts da taurari da jinjirayen wata manya da ƙanana aka yi da blue ɗin biro, baƙi da kuma ja ta cike sauran space ɗin dashi. Yayi mamaki da yaga rubutunta na larabci babu laifi. Ya juya shafin zuwa na gaban shi, shafin dake hagu wasu kalamai ne na hausa na soyayya da yayi mishi kama da waƙa. Harda gyaran Muryar shi yana ƙoƙarin rerawa amma ya kasa fasalta waƙan sai yana yinshi da rapping, wasu kalaman hausan ma ya gagara karantawa. _Madubi ke nai dubawa_ _Saurari bayani na_ _Soyayya linzami na_ Layi uku ya iya karantawa ya haƙura. Sai a can ƙasa bayan ta gama rubuta waƙar daga farko har ƙarshe tayi Scribbling harufan M&I ta zagaye shi da heart shape. Shafin dake bangaren dama kuwa waƙan Musulunci ne guda biyu, I pledge to Islam my religion da Rahman ya Rahman na Alafasy. Ya tsallaka shafi na gaba yayinda ya kasance kaman profile domin bayanan rayuwanta ne, sai wasu zanen flower da yake gani a hannun mata lokutan Eidi an zana musu da wani baƙin abu a bayan hannu, amma zanen nata yayi kyau sosai. I am Amina by name AKA Ilham AKA Fidela. I am 12 years old My tribe is Jenjo My favourite food is awara with sauce or yajin tafarnuwa. My hobbies are Sleeping, cooking, dancing and makeup. Ya murmusa, daman tayi kama da malalaciya, amma zaiso ya ganta tana rawa da wa’innan siraran ƙafafuwanta kaman tsintsiyan kwakwa. Haka yaci gaba da karanatawa. Kalan da tafi so, Kayan da tafi so, Suran da tafi so a cikin Alkur'ani, Ƙira’an Malamin da yafi burge ta, Subject ɗin da tafi so a makaranta, Jarumin da tafi so a film ɗin Hausa da na India, Mawaƙin da tafi so, Su nawa ne a gidan su, Maza nawa mata nawa, Yawan ƙawayenta dai yafi komai bashi mamaki. Da ya kai karshen bayanan sai yake jin kaman ya gama saninta, kaman ba haɗuwar hanya kawai suka yi ba. Kaman ya riga ya santa a zuciyar shi. Shafukan da suka biyo baya bayanan ƙawayen nata ne da bai damu da saninsu ba don haka ya dinga wucewa harda shafukan da an rubuta sunayen wa’inda zasu cika a sama amma basu kai ga cikawan ba. Saida ya isa shafin karshe ya tsaya domin abinda yake jiki ya banbanta da sauran. Ƙaton Heart ta zana da jan biro sai kifiya da ya ratsa ya raba heart ɗin gida biyu. A ta sama sai ta sake zana harufan M&I a ƙasan kuma sai ta saka cikakken Sunan MUHSIN and ILHAM. Sai wasu ƴan rubuce rubucen kalaman soyayya da tayi a gefe har ya tsinto kalmar “my handsome crush” A ƙasan zanen kuma waƙan Turanci ne na P Square mai taken ‘No one like you” ta rubuce shi. Takaici ya sanya shi wurgi da littafin ko kashe wuta bai yi ba ya ɗora kanshi a saman pillow ya rufe ido. ….. Duk inda take tunanin ta ajiye littafinnan ta duba amma bata ganshi ba. A sanadinsa ko yawon juma'a bata je ba haka ta birkita ɗakin Maama kaff tabi ta gyara shi tass amma ba littafi babu labarin shi. Dukda dai Allah ya taimaketa da bata je dashi makaranta ba da yau kashinta ya bushe. Saboda suna zaune sai gashi an shigo Inspection. Aka ce dukka ƴan ajin kada su ɗauki komai su fita gaban aji su tsaya perfects kuma suka shiga caje jakakkunan su suna seizing ɗin abubuwan da aka haramta zuwa da su makaranta. A cikin prefect masu inspection harda Health prefect Muhsin. A cikin abubuwan da aka haramta kuma harda slum book. Kuma slum book ɗin nata yana ɗauke da sunan shi. Haka kaman zata fasa ihu tana kallo yake bubbuɗe litattafan cikin jakanta yana dubawa, amma sai wani lipgloss ɗinta mai shining ya cire a matsayin yayi siezing ya mayar mata sauran littafanta cikin jaka ya rufe. Toh tun daga lokacin take niman slum book ɗinnan har dare bata samu ba, kuma duk wa’inda ta baiwa su cika a ajin ta tambaye su sun tabbatar mata baya wurin su. Har suka zo tafiya Islamiyya washegari da safe tana dame, da taje shima ta tambayi ƙawayenta na can suka shaida mata baya wurinsu suma. Sai a hanyar su na dawowa bayan la’asar ta tuna da cewa jiya da safe ya buɗe jakarta. Wannan ɗan shaye-shayen. Ta dubi wurinda ya saba zama. Babu shi a wurin sai abokinsa. Kaman ta haƙura sanin babu abinda zasu mata da littafi saidai ance matambayi baya ɓata. Kuma littafin sabone da ta siya da kuɗin break dinta da ta tara har naira 35, tare da biron cika slum book ɗin kala biyu kuma ya tashi Naira 60 ne. Kuɗin break ɗinta na wurin kwanaki uku kenan saboda a kullum Naira Hamsin Taa yake basu su raba ita da yayarta Iman wanda take hannun Shafa. Amma dake akwai rata sosai a tsakaninsu kuma Iman tana da ƙanne maza har guda biyu kafin azo kanta ya sanya babu wani shaƙuwa tsakanita da Iman sosai dukda uwa ɗaya ce ta haifesu, ba kamar ita da Ihsan ba. Ƙwarin guiwa ta tattaro ta ƙarasa wurin Fire, sauran ƴan hanyar su kuma suna jiranta daga can nesa tare da Ihsan. Sallama tayi mishi ya amsa Sannan ta nuna gefen shi da babu kowa tana faɗin “y..ya.. yana ina?” “Wane?” “Abokin ka” “A moher?” Sai ta gyaɗa kai dukda ba sanin sunan shi tayi ba daman. “Gashi nan” yace yana nuna bayanta da kai. Da sauri ta juya sai gashi tsaye ƙeƙam. Kafin tace wani abu kuma ya raɓata ya wuce, ta juyo lokacin da har ya samu wuri a gefen Fire ya zauna amma kaman bai fahimci wurin shi tazo ba sai ya ciro waya yana dannawa. “Nace ba…” bai ɗago ba. “Ka ji…” shima bai ɗago ba. “A Moher…” Saida ya ɗago ya sanya idanun shi cikin nata ya san yayi hakan. “Uhmm… dan Allah ka tsinci littafina jiya?” Tayi maganar tana cire idanunta daga cikin nashi ta mayar kan ƙasan hijabinta da ta riƙe da hannun dama tana nannaɗawa a jikin yatsar ta manuniya na hagu. Bai san amsar da zai bata ba, gashi bai zo da littafin ba balle ya mayar mata da kayanta. Lokacin da ya tashi da safe ya manta da ɓacin ran shi, da zai wuce banɗaki alwalan asuba sai kawai ya ɗaga littafin a ƙasa ya saka a drawern jikin madubin shi, bai kuma sake bi ta kai ba har ya fito daga gidan. Jin yayi shiru yasa ta sake ɗagowa ta dube shi, ganin ya mayarda hankalin shi kan wayar kaman bata wurin sai ta ƙaddara a ranta bai gani bane. Bata sake cewa komai ba ta juya ta koma wurin su Ihsan suka tafi gida. “Me yasa baka amsata ba?” Fire ya gagara haƙuri ya tambaye shi tunda yaga lokacin da ya ɗauki littafinta guda ɗaya jiya. “Kai meyasa bata tambaye ka ba?” Ya mayar mishi da tambayar don haka ya ja bakinsa yayi shiru. Jin an fara kiraye-kirayen Maghriba ya miƙe tare da jefar da sauran sigarin da ya gama sha ya bi da takalmin ƙafar shi ya murje shi don kashe sauran wutan da yake jiki, kana ya rataya jakar shi bayan ya saka tom-tom guda ɗaya a baki cikin sauran wanda Ilham ta siyo mishi jiya. “Lukman sai gobe” ya faɗa yana shirin daukar hanya. Da sauri Fire ya miƙe yana cewa “Ah ah, ba zamu je ɗin bane?” Ya ɗan yi zugum kana ya girgiza kai. “Nne Lukman, ina tsoron ɓacin ran Nnem” “Amma ai kace ta yarda, me yasa kuma ranta zai ɓaci?” Gyara tsayuwa yayi ya zuba hannayen shi cikin aljihu Sannan yace “Ta yarda in yi waƙa ba in yi tatoo a jikina ba. Su ɗin abubuwa guda biyu ne mabanbanta” Fire ya girgiza kai cikin rashin amincewa “ka taɓa ganin shahararren mawaƙin da bayi da tatoo?” A cikin mawaƙan da suke burge shi yake bin irin salon su kam bayi tunanin akwai wanda bayi dashi. Jin yayi shiru bai amsa ba Fire yace “toh ka gani!. Ba za'a yi maka kallon mawaƙi mai muhimmanci ba kaima idan baka dashi, kayi ko ƙarami ne ɗan na burgan aiki ɗinnan idan munzo yin video ya ɗan fito.” “Nnem nake ji Lukman” ya sake maimaitawa. ```````` Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA by Seemahwrites ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh JODA by Sadi-sakhna *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a turo shaidan biya ta 09039206763 Chapter 7 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites* *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely to Aunty Hauwa Yarima 🤍 UMMEE'S BAKING EMPIRE https://chat.whatsapp.com/L0WK91pLyVn8iQ6HjSwG8a?mode=gi_t *My Sister matso kusa ki ji.. Wannan cake ɗin da kike gani a online yake burge ki kin san inda zaki samu irin shi? Koko sha'awar glazed ko filled donuts kike yi? Ga plain ones for your Husband, father or boyfriend if they don't have a sweet tooth.* *Coming to you my brother.. kana iya bada kyautar nan mai sanya mace tsallen Murna? Ko Surprise ma abokai? For Eids, Anniversaries, birthdays, graduation or just to celebrate your girl or yourself? you can order a cake from us. Akwai crunchy cincin domin motsa baki ko a siya ma mama da baba su saka mana albarka.* *And don't forget about friendship or sibling bonds, You can always order a cake to celebrate their success or even to mock them with class😎, requesting captions that are satire and funny.* Muna siyar da: • Cakes na for every occasions ( birthday, graduation, anniversary dai dai sauran su) • Bento cakes • Cupcakes • Mouth watering brownies • Samosas • spring rolls • Glazed puffs • Filled, glazed and plain donuts. E.t.c *Ummee's Baking Empire –* *Making every Moment feels special. We always make sure that you recieved what you ordered 👌🏼💯* 📞 08173775170 📍 gwammaja, Kano 07…. Agogon dake manne jikin bango ya fara kallo lokacin da ya shigo gidan. Ƙarfe 9 da minti 17. Ya haɗiyi miyau yana damƙe hannun jakar shi, saidai zafin da yaji ya ratsa tsakanin yatsun shi ya tunasar dashi abinda ke wurin, don haka ya sake jakan yana yarfa hannu a hankali a yayinda yake baza idanu yaga ta ina mahaifiyar shi zata fito. Kitchen ya fara leƙawa bai ganta ba, sai ya dawo ƙofar ɗakinta ya ƙwanƙwasa “Nne, Enwere m ike ịbata?(In shigo?)” Ya ɗan jira yaji ko zata amsa shiru, ya sake ƙwanƙwasawa nan ma shiru, sai ya saka hannun shi na hagu ya murɗa handle ɗin ɗakin amma ya jishi a rufe. Toh ina taje a wannan lokacin? Wayar shi ya zaro a aljihu ya laluɓo lambarta ya danna kira, babu ɓata lokaci kuma aka sanar dashi ‘Line busy’ lokacin da ya ƙara wayar a kunne. Hankalin shi bai kwanta ba saida ya fito ya zaga ta baya inda take shanya kayan wanki da wasu abubuwa nan ma babu alamunta. Hankalin shi ne ya fara tashi sanin cewa Nne bata da wurin zuwa a garin Kano da ya wuce office sai gida, kuma ƙarfe biyar ɗin kowacce rana yana mata a cikin gidanta ne, bata taɓa bari tayi dare a waje saboda shi. Toh yau me ya faru? Ƙoƙarin sake kiran layinta yayi still yaji busy. Sai ya samu wuri ya zauna yana tunanin possibilities na wuraren da zata iya kasancewa a yanzu. Lokaci ɗaya kuma aka turo ƙofar parlourn, dake a ankare yake yayi saurin miƙewa a kan kafafuwan shi yana kallon fuskar mai shigowa. “Nwam” ta furta tana sauƙe ajiyan zuciya. Sai ya koma ya zuba a kujeran yana sauƙe ajiyar zuciya “Ina kika je Nnem? I've been calling your phone!” “Sorry ina waya da lawyer na ne….” bata rufe baki ba wayarta ya sake ɗaukan ruri kuma babu ɓata lokaci ta ɗaga, daman jiran kiran shi take yi ta ƙarasa zazzage shi. “You're very very stupid Muhammad Kagarko…” shine sallamar da tayi wa mai kiran wanda Abdulhameed ya gane ko wanene. Yana kallon yanda taja tunga daga bakin ƙofar saboda masifa ko rufewa bata yi ba gudun sauro. “.. Ni yanzu court ne kawai zata raba mu because I don't have time for your nonsense. Idan da kai mai hankali da tunani ne after all these years da baka waiwaye muba ba zaka kira Abdulhameed da ɗanka ba ma balle har ka gwada kana da iko dashi, Bayan ka zaɓi ƴan uwanka a kanmu Muhammad!. bayan azaban da ni da shi muka sha a gidan ku a gaban idanun ka, Idan na kwanta barci Fuskar ƙanwarka Surayyah ke firgita ni cikin dare. kuma sai in ɗauki ɗana in baka?! Over my dead body! Wallahi Idan kaga Abdulhameed ya dawo hannunka saidai a bayan raina! Tupu m eliwe n'ala, Tufia kwa!” tayi tofi tuff kana ta datse kiran tana huci. Abdulhameed kallonta kawai yake, saboda wannan ba shine karo na farko ba amma ya fara gajiya, girma ya fara kama shi meyasa wa'innan zuciyoyin biyu ba zasu yayyafa ma kansu ruwan sanyi ba su mayar da hankali wajen inganta goben shi?. Tun yana jin fitar numfashinta daga inda yake zaune har ta fara ƙoƙarin daidaita kanta saboda kada ta cigaba da ɗaga mishi hankali. Ta ƙaraso inda yake zaune ta samu matsuguni a gefen shi. “I'll protect you with everything I have Nwam, so kada ka damu kaji?” tayi maganar tana ɗora murmushin dole a saman fuskarta tare da riƙo hannunshi duka biyu cikin nata. Ƙaramin ƙaran da ya saki tare da saurin zame hannun shi na dama daga cikin nata ya sanya ta dubi hannun cike da damuwa. “Ciwo ka ji?” Girgiza kai yayi, yana ƙokarin mayar da hannun bayansa ta riƙe, ta sake janyowa gaban idonta don taga menene. Daga gefen yatsar shi manuniya da ya kumbura yayi ja ta hango wani baƙin zane. Ya sake ƙoƙarin zame hannun kafin ta fahimci menene amma ruƙon da tayi mishi ba na wasa bane. Ta tsura ma abun ido a ƙoƙarinta na gano ko menene. “Tatoo kayi Abdulhameed?” Ta ɗago tana kallon shi da matsananciyar mamaki. Tun lokacin da aka fara yake nadama, tun kafin ya gama shanye raɗaɗin da yake da tabbacin Nne zata ji ninkinsa a cikin zuciyarta. “Tatoo Abdulhameed!” Tayi maganar wannan karon da tabbatarwa. Sannan ta saka hannunta tana shafa sunan “A Moher” da take gani a rubuce taji ko ba tatoo ɗin bane, ko zane ne da tawadan da idan ta murza zai goge. Ƙaran da ya saki wanda yafi na ɗazu ya tabbatar mata da ba kuskuren fahimta tayi ba. “Sakayyar da zaka yi min kenan? After all I've been through to take care of you and protect you, is this how you'll repay me Abdulhameed?” Kafin zancenta su kai ga taɓa zuciyar shi, hawayen da ya gani suna zuba daga idanunta ne suka yi matuƙar ɗaga masa hankali. Ba zai iya tuna ranar da ya taɓa ganin Nne tayi kuka ba. Macece ita mai ƙarfin guiwa da taurin zuciya, mace jajirtacciya, mace mai kamar maza wanda ta zamo masa uwa da uba ita kaɗai ba tare da taimakon kowa ba. Sauƙe kai yayi cikin jin kunya da nadama, yana jin ko hakuri ne ya kamata ya bata amma bakinsa yayi mishi nauyi. Ta miƙe tsaye ba tare da ta sake cewa komai ba saboda kuka dake niman kufce mata. Abubuwan da ta tara a ƙasan zuciyarta na tsawon shekara goma sha takwas ne yake niman tasowa shiyasa kawai ta shige ɗaki ta rufo ƙofa tunda a yau kam ba zata iya danne su ba. Yana zaune a wurin ya fara jiyo gunjin kukanta, abinda ya ƙara ɗaga mishi hankali yayi saurin tashi ya ƙarasa ƙofar ɗakin yana jijjigawa ta buɗe mishi. “Nne kiyi haƙuri ki buɗe please, ki daina kuka don Allah” muryar shi ta fito da kauri saboda yanda maƙoshin shi ya cunkushe. “Nnem ba zan sake ba. I promise. Ki gafarceni ki buɗe dan Allah.” Yana daga cikin dararen da suka yiwa Abdulhameed tsawo a rayuwar shi. Yayi magiyan, ya bada haƙurin, ya ɗauki alƙawari, ya zubda hawaye amma a ciki babu abinda ya sanyanta ran mahaifiyar shi, haka suka yi kwana zaune da ƙofar parlour a buɗe. Da gari ya waye ganin zata yiwa kanta illa da yunwa don ta faɗa masa shi ɗinne bata son gani sai ya shirya ya fice ya bar mata gidan. ….. ILHAM “Har yanzu baki samu littafin ba?” Ihsan ta tambayeta bayan sun isa Islamiyya ta sake tambayan wasu ƙawayenta da basu zo jiya ba. Girgiza kai tayi damuwa shimfiɗe a fuskarta. “Sai kiyi haƙuri ki sake siyan wani toh, amma ni ina da yaƙinin shi ya ɗauka” “A moher?” Ta tambaya tunda shine mutum na farko da yazo kanta itama. “Eh mana, idan ba haka ba ai littafin yana nan kafin ya karɓi jakan ki” Ta jinjina kai don ba karamin mamaki tayi ba lokacin da Muhsin ya duba jakan bai gani ba, sai tayi tsammanin yayi nufin rufa mata asiri ne, saboda saida ta tabbatar littafin yana jakarta kafin ta fito daga gida domin akwai ƙawayenta da suka dameta ta basu su cika. “Amma kin gani ai na tambaye shi baice yana wurin shi ba” “Daman ɓarawo yana faɗan abinda ya sata ne? Kuma ƴan shaye-shaye dukkan su ɓarayi ne musamman shi da yake bada manyan kuɗi a siyo mishi abu, kina gani kinsan kuɗin sata ne” “Ko satan yake yi mai zai yi da littafi?” Ihsan ta buɗe baki tana kallonta “Addah Fidela kare shi kike yi?” Tayi saurin girgiza kai “kawai dai naga ko siyarwa yace zai yi tunda da rubutu a jiki babu mai siya, saidai idan wa mai ƙosai zai kai” tayi maganar karshen saboda ta ƙaryata tunanin Ihsan na kare shi. Tana iya tuna komawar su gida jiya, da ta samu Yaya Aliyyu ta sanar dashi saƙon A Moher na niman shi da yake yi tasha faɗa kaman zai ari baki wai kula shi take yi shiyasa har yake bata saƙo ta faɗa. Kuma bai haƙura ba saida ya haɗata da Taa ya saka ta Kneel down, kaman zai saka bulala ya zaneta ma Maama ce ta bada haƙuri ta lallashe shi. Tayi kuka kaman mene amma tayi mamakin yanda duk inda aka kaɗa aka rawa Ihsan taƙi cewa komai a matsayinta na wanda suke tafiya suke dawowa tare, haka aka saka su kneel down da ɗaga hannu tare a ƙasan hasken wata da sauro. Shafa tayi ta habaicinta wai yaran Maama suna neman lalacewa, har bakinta yayi tsami babu wanda ya kulata a gidan. Sai bayan awa ɗaya Taa ya turo yaya Aliyyun yace musu su tashi suje su kwanta. A nan ne yaya Aliyyu ya zaunar dasu a ɗakin Maama ya sake musu faɗa da gargaɗi sannan ya shiga musu nasiha sosai. Yana sanar dasu irin illar shaye-shaye da hulɗa da masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, yanda suke ƙarewa a wulaƙance da yanda rayuwar su ke lalacewa. Ya basu labarai kala-kala a kan wa’inda suka yi shaye-shaye a baya yanzu sun ƙare a gidan mahaukata ko a bola ko a gidan gyaran hali kuma sun tsorata sosai. Shi da idanun shi bai taɓa ganin A Moher yana maye ba amma ya gargaɗesu a kanshi sosai, daga ita har Ihsan yace duk wacce ta sake zuwa inda yake sai ya saka dorina ya zane su gaba da bai. A lokacin kuma da Ilham ta ɗauko fuskar A moher a cikin kanta ta haɗa shi da wannan yanayin da yaya Aliyyu ya fasalta sai tsananin tausayinsa ya kama ta. Yanayin bai dace da shi ba. “Ai ko dan ya kaiwa mai ƙosan ma kinga zai iya sacewa” “Haka ne” ta amsata kawai tana tusa lomar taliyan murji a bakinta. Kafin a tashe su da yamma shaff ta manta da tunanin A Moher ko littafinta, dan haka ta cigaba da hidimarta da ƴan makarantar su, har suka ɗau hanyar komawa gida tana tsakiyar su kamar kullum tana bada labarikan dake sanya kowa dariya harda ita kanta. Yana zaune yana kallon su amma yau ko da kuskure bata dubi inda yake ba. Yana kallon yanda take dariya cike da nishaɗi yayinda zuciyar shi take ƙara motsewa a ƙirjin sa. Har sun wuce ya ɗaga murya ya kirata “Ilham!” Suka waiwayo baki ɗayansu suna kallon shi. Sai ya ɗaga mata littafinta a hannu daya, ɗayan kuma da shi ya kai sigarin da yake sha bakin shi ya sake zuƙa tare da fesar da hayaƙin. “Kada ki je” Ihsan ta riƙe hannunta tana girgiza mata kai. “Littafina kawai zan karɓa Filiyan, dan Allah” ta zare hannunta sannan ta tunkari inda Abdulhameed yake zaune warin taban shi na ƙara ƙarfi a cikin hancinta har yana saka ta tari, amma a haka ta ƙarasa. Tana zuwa kusa ya miƙa mata ba tare da yace komai ba. Ta saka hannu biyu ta karɓa tana duba sunan jiki ta tabbatar nata ɗinne. “Na gode” ta faɗa murya a shaƙe tana saka hannunta a kan hancinta Saboda warin yana damunta. Ya ɗaga kai ba tare da ya dubeta ba. Ta juya da nufin tafiya, taku ɗaya… biyu… sai ta sake juyowa. Saida ta haɗiyi miyau kana ta kira shi “A Moher” Ya juyo ya saka idanun shi cikin nata da yake iya hango wani yanayi mai zurfi a cikinsu. “Dan Allah ka bari” shine abinda tace na gaba dubanta yana komawa kan sigarin hannunshi wanda ko rabi bai zuƙe ba. Amma wannan shine zai zamo karan ƙarshe da zai riƙe a hannun shi da wannan nufin. Karo na ƙarshe kenan da zai sha sigari a rayuwar shi. Kuma ba domin Ilham bane. Ba don tace ya bari ba. Saidai akwai wasu abubuwa a ƙaddara da sukan zamo mana sanadi na sauyawar rayuwar mu. Wannan sanadin ba Ilham bace gaba dayan shi, amma ta kasance wani ɓari na cikinsa wanda ba zai manta ba. Saboda ita kaɗaice ta taɓa duban shi a garin Kano ta bashi shawarar da zai amfane shi dukda tsoron da ya gani a yanayinta. . . . “Alhamdulillah” tace tana juya littafin a hannunta da faffaɗan murmushi a fuskarta ganin babu abinda ya same shi sannan ta sake buɗewa tana duba ciki. Komai lafiya, domin bata lura da shafin farkon ba har saida ta tafi na ƙarshe inda tayi zanen M&I a cikin heart. Ta daɗa matso da littafin kusa da idanunta dukda lafiyan su ƙalau kuma zanen ba ƙarami bane Amma tana son tabbatar da abinda take gani ne. M&I ɗinta ne ya rikiɗe ya koma A&I. Correcting fluid aka saka aka ɗauke M ɗin gaba ɗaya aka sauya shi da A. Mamaki ya daskarar da ita a zaune. Saboda meyasa?. Waye yayi mata wannan aikin a cikin wa'inda ta basu littafin nan?. Da ta duba wurinda ta rubuta Muhsin Vs Ilham kanma babu sunan gaba ɗaya an rufe shi da farin fenti tass kuma ba'a musanya shi da komai ba. Hankalinta samm bai bata zai iya kasancewa aikin A Moher bane. Saidai hala a cikin wa’inda littafin ya taɓa shiga hannun su akwai mai Crushing a kan Muhsin itama shine tayi mata wannan aikin. Ta juya littafin ya koma shafin farko inda ta rubuta M&I ƙarami a Ƙasa shima ya koma A&I. Waye yayi mata wannan aikin fisabilillahi?. Ko lokacin da ta baiwa class monitor ɗinsu namiji ya cika ne aka samu wani mai Crushing ɗinta ya karɓa daga hannun shi? Tunda shi sunansa Zulƙarnaini ba daga A ya fara ba. *Monday 7th, March, 2014* Bumm… aka banko ƙofar dakin sannan ta faɗo ciki. “Abdulhameed! Abdulhameed tashi… tashi Abdulhameed!” Zame bargon da ya rufe har kansa dashi yayi. A hankali ganin shi ya daidaita da hasken da ya gauraye ɗakin lokaci ɗaya, sannan ya tashi zaune yana hamma. “Sauƙo Nwam, we have no time to waste, ka shirya mu tafi yanzu” tayi maganar tana birkito da kayan cikin wardrobe ɗinshi mai ƙofa huɗu, tana zaɓan wanda suka yi mata tana zuba su a cikin madaidaicin akwatin da ta buɗe. Ya haɗiyi miyau, Lokaci ya sake zagowa kenan. Lokacin tafiyar da babu waiwaye. A yau ma bayi da zaɓin da ya wuce na barin kano, tafiya ta har abada. Bayi da wani zaɓi bayan ya bar karatun shi, abokan shi, waƙar shi, rayuwar da ya saba da ita ya sake komawa inda zai shimfiɗa sabuwa. Yanzu kuma Ina suka nufa? Bayi da ƙwarin guiwar yi mata wannan tambayar tunda ya sani ba zai canza komai ba. Bayan komawan shi hannunta yana da shekaru shida, a Maiduguri suka fara zama na tsawon shekaru uku kafin rana ɗaya suka tashi irin wannan tafiya. Faɗi ƙasa yayi yana bori yana kuka amma bata kula shi ba, haka da zata saka shi a mota kaman ɗan da ta sato aka fito ana kallonsu saboda a lokacin a compound suke zaune. Daga nan suka wuce Bauchi, tsawon shekaru biyar har ya samu shiga Jss two, suka sake tashi rana ɗaya bayi mantawa shikam tafiyan dare suka yi tun yana kuka a mota har barci ya dauke shi, sai buɗe idanun shi yayi a garin Sokoto. Yayi ƙoƙarin ganin bai bari ya saba da garin ba wannan karon, yaƙi yin abokai, ko yaran unguwan su yaƙi kulawa sanin cewa zaman su ba mai ɗorewa bane. Amma ganin har sun shekara huɗu sai ya fara samun fata, wataƙil shikkenan yazo ƙarshe, wataƙil zuciyar shi zata samu mahuta a nan. A wannan karon dai ta sanar dashi kafin ranar da zasu sake nausawa gaba saboda ya shirya a tsanake. Ya sauƙa a saman guiwowin shi yana roƙonta ta haƙura su zauna saboda lokacin girma da hankali sun riske shi shekarun shi goma sha bakwai. “Nwam I work with the NGOs, aiki na ba na zama a wuri ɗaya bane, kayi haƙuri inda zamu je ma zaka saba” shine amsar da ta bashi shekara ɗaya kacal daya wuce. Amma bayan yazo kano ya haɗu da Lukman abokin da bai taɓa samun kamar shi ba, wanda suke da buri da mafarki iri ɗaya, sai lokacin nan ya sake zagowa a kurkusa ba tare da ya shirya ba. . Ta bar abinda take yi ganin har yanzu yana zaune, ta ƙaraso jikin gadon ta kamo hannun shi harda mai tatoo ɗin amma ba shi bane damuwar ta a yanzu. Saida ta jawo shi ya miƙe tsaye sannan ta fara tura shi hanyar bathroom dake ɗakin “Kayi brush kawai mu tafi, bamu da lokacin wanka babanka ya riga da ya iso Kano tun jiya” ta tura shi banɗakin ta rufo ƙofa kana ta cigaba da haɗa abubuwan da take da tabbacin zai buƙata, in yaso sauran sai ta turo a kwashe daga baya. Bai ko yi sallan asuba ba, don gari bai gama wayewa ba tukunna. Yana iya kallo daga ɗan windown dake banɗakin yanda waje yake da duhu har yanzu., amma ya san ba zata jira shi yayi raka'a biyun nan ba don haka yayi brush kawai kaman yanda tace ya wanke fuskar shi sannan ya cire rigan jikin shi ya jefa a laundry basket dake toilet ɗin ya fito daga shi sai sweatpants ɗin barcin sa. Da sauri ta nufo shi da rigan dake hannunta ya ɗan ranƙwafa ta zura a wuyansa sannan ya miƙe tana taya shi zura hannuwan. “Ka ɗauki wayanka da duk wani abinda zaka buƙata ka zuba a cikin wannan jakan” tace tana miƙa mishi wani backpack. Bai ce komai ba ya karɓa ya ƙarasa gaban madubin shi yana tattara su mai da turarensa yana zubawa a ciki. Ta ɗebo boxers ɗinsa da singlet ta zuba a ciki tana cewa “kayi sauri Abdulhameed kada yazo ya same mu a gidan nan, dan ba zan iya bashi kai ba koda na minti ɗaya, idan Muhammad yayi nasara a kaina zuciyata zata buga!” Ta karɓi jakan ta zuge zip dinshi sannan ta koma ta bayan shi ta goya masa. “Muje” tace tana riƙo hannunsa. “Headphones ɗina” yace yana juyawa jikin drawern gefen gado ya ciro baƙin headphone din ya lanƙaya a wuyan shi bayan ya rufe yalwataccen gashin kansa da hulan baƙin hoodie ɗin da ta saka mishi. Suka fito harabar gidan yana janye da akwatin shi itama tana gara nata a kan tayoyin su, ga iskar asuba mai sanyi dake kaɗawa. Motarta ƙiran 406 ash colour ta fara kunnawa yayi warming a yayinda ta dawo ta taya shi jera kayan a booth suka rufe a tare. Ita ta buɗe masa mazaunin mai zaman banza ya shiga ta saka masa seatbelt da kanta ba don bai iya ba. sannan ta dauko mishi biscuit da 7up a back seat sai yaci idan yana jin yunwa, taje ta buɗe gate kana ta koma mazaunin driver ta fice da motar daga gidan. Gari na dusu-dusu suka harba titi, kuma yanda take jin daɗin zabga gudu yana da alaƙa da kasancewar babu yawan abubuwan hawa a kan hanya sai ɗai-ɗai. . . . “Maama wai Addah Fidela bata da lafiya” Rufe tukunyar abincin karyawan yara da ya kusa nuna Maaman tayi, don dukda kasancewar Shafa ce da girki yau saidai yaran su tafi da yunwa ko suyi latti amma ba zata tashi tayi musu abun kari da wuri ba kuma har da nata yaran a masu zuwa makarantar. “Salon Ƙin makarantarta kala-kala ai, kice ta tashi tayi wanka kafin na shigo ɗakin nan” Daga inda take kwance a kujera a parlour tana iya jiyo kalaman Maaman yayinda take juyi riƙe da mararta. Jin gyaran muryan Taa da ya shigo gidan a lokacin tun bayan fitan shi sallan asuba ya sanya ta daddafa ta miƙe ta shiga banɗakin Maama ta watsa ruwan da Ihsan ta rage mata. Sai kuma taji daɗin jikinta. Don haka da ta shirya cikin riga da wandon uniform ɗinta ta fito sai Maama ta tabbatar karyan ciwo ne kawai. Tana jin ciwon maran sama-sama amma saboda Taa yana nan har yanzu ta daure suka karya, kuma shi da kanshi ya sauƙe su a ƙofar makaranta da motar shi ranan. . . . “Nwam.” ta kira ba tare da ta rage gudun da take fantsamawa a kan titi ba, don gashi har sun ɗau hanyar barin gari sun nisa ƙauyuka. Bai juyo ba amma yana jinta. Ya toshe kunnen shi da headphones ɗinshi saidai bai kunna komai ba a ciki. “Abdulhameed kayi haƙuri, Please” Ya juyo da mamaki ya dubeta yayinda itama ta juyo tana sake mishi murmushi. Wannan murmushin. Wannan fuskar. Wannan rayuwar. A cikin sakwan ɗaya kacal duk suka haska a cikin idanun shi lokacin da ƙarar horn ɗin tankar mai ta shiga kunnuwansu, juyawan da zasu yi har ta haɗe da gaban motar su sun zama abu guda. Fashewar gilashin gaban motar da ya watsu daga fuska zuwa jikin su, huruwar balon-balon Iska da ya bugo ƙirjin Nne wajen kareta daga buguwa da gaban motar saboda a lokacin da ta tuna da sakawa danta seatbelt ta manta da saka nata ita, da kuma zafi da raɗaɗi da ya ziyarce shi ta ko ina duk cikin sakwan guda ne kacal. Daga nan babban motar taci gaba da tura motar tasu baya da ƙarfin tsiya kaman yanda suka zo da gudu haka yake mayar dasu tunda girma da nauyin ba ɗaya ba. Zuciyar shi yake ji kaman zata fasa kirjin shi ta fito saboda yanda take luguden tashin hankalin da bai taba jin koda labarin kwatankwacinsa ba. cewa da ake yi mutum na ganin mutuwa ya haska a cikin idanun shi, toh da ya haska a cikin na Abdulhameed sai yaƙi dauke hasken da wuri. A cikin wannan yanayin, a cikin wannan azaba da tashin hankali Nne ta sako hannunta ta danne ƙirjin shi da jikin kujeran a yunkurinta na kare shi daga cutarwa ko yayane. Salati kawai take yi a bakinta a lokacin da suka tunkuɗa daji motar su ta shiga gudundule yana rotsewa ta ko ina, headphones ɗin kunnen shi ya daɗe da faɗi. Sai a lokacin suka samu rabuwa da babban tankar da tayi gefe itama ta cigaba da karo da bishiyoyi da duwatsu don control ya riga da ya kwacewa matuƙin ta. Sai wani irin ƙaraa, ƙara mai disashe sauraro da yafi tashin hankalin shi tsanani ya biyo bayan hantsilawar da babban motar tayi, ya shiga cikin kunnen shi ya ratsa shi kaman mashi mai tsananin kaifi, wanda yasa yaji kaman wani abu ya tarwatse a cikin kanshi. A hankali kuma jini ya fara gangarowa daga cikin kunnuwan shi. Daga nan Abdulhameed bai sake sanin inda yake ba, azaba ya sanya ƙwaƙwalwar shi niman hutu na wucin gadi. . . . “A ɓalla kofar, kuyi sauri ku ɓalla” Hayaniyan da ya kamata ya farkar dashi kenan. Amma ko lokacin da mutane suka zagaye motar ana ƙoƙarin ceton rayukan da basu da sani a kan masu ita, bugun zuciyar shi ne ya farkar dashi. Saidai sauƙin da ya samu na ɗan lokaci ya mantar dashi azabar da yake ciki, don haka da ya buɗe idanunsa sai yaji kaman a wani wurin yake daban da gidan duniya. Bai taɓa sanin ana jin raɗaɗi irin wanda yake ji ba, ga kunnuwan shi da yake jin kaman ana kaɗa mishi ƙararrawa a cikin su babu ƙaƙƙautawa bayan zogin azaba da suke masa, kaman ya mutu kawai ya huta. amma idanun shi yana kan Nne wanda kanta yake kife a kan steering da airbag ya fasa shi ya fito, a yanzu ya gama aikin shi ya sace, saidai ko ina a jikinta jini ne. Jini a goshinta, jini a fuskarta, jini a ƙirjin ta da gaba ɗaya kayan jikinta. Gabaƙi ɗaya motar ya ɓaci da jini. Jini kawai. “N..n..nem” ya san ya kirata amma bata ji kiran ba tunda bata amsa ko ta buɗe ido ba. Saidai shima bai ji sautin kiran ba, la’alla saboda ƙararrawar da ya cika mishi kunne ne. Saboda haka ya tattaro duk wani juriya yanda yake jin kaman maƙogwaron shi zai tsinke banda nauyi da ya danne ƙirjin shi ga bakin shi a fashe ya sake kiranta da yunƙurin da yafi na da. “Nne ki buɗe idanun ki, please” Ya rintse idanun shi yana jin kaman zai sake ficewa cikin hayyacin shi. A hankali hawaye wanda yake gauraye da jini yake gangarawa saman kuncinsa. Hamdala da mutane keyi na hango shi ya buɗe ido yana motsi, da shawarar da suka yanke na a fara taimakon shi kafin mahaifiyar shi duk bai ji ba. Sai ji Yayi an sako abu ana yanka Seatbelt ɗin dake jikin shi Sannan aka fara ƙoƙarin janyo shi ta cikin window, ashe har sun ƙarasa cire gilashin duk bai ji ba. . . . “Maama, Maama jini. Jini Maama” Zuciyar Maama da ya kusa faɗowa daga ƙirjinta ta dafe tare da miƙewa tsaye tana kallon Ilham wanda suka shigo tare da Ihsan, kana ganin idanunta zaka san taci kuka ta ƙoshi. “Jini a ina?” Ta tambaya ƙirjinta na bugawa fatt-fatt. Sai Ilham ta juya bayanta yanda ƙasan rigan uniform ɗinta mai haske ya rine da jan kala. “Ina zaune ne a waje kafin a shiga aji, ina tashi kawai naga jini a jikina” Ta sauƙe ajiyar zuciya na samun nutsuwa kaɗan, girma ne yazo ma Ilham da wuri. “shiga banɗaki ki jira ni ina zuwa.” Ta juya kan Ihsan ”Ke kuma ki kwantar da hankalin ki ba wani abu bane, zata samu sauƙi”. ```````` . Chapter 8 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites* *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) 08… KADUNA 2026. Sallamar da ta shigo gidan da ita ne ya katse lokacin da ƙafarta ya shiga cikin plate ɗin da aka gama cin abinci aka ajiye daga bakin ƙofa. Ta ɗaga dubanta daga kai bayan ta tabbatar bata fasa ba sannan ta shiga kallon parlourn wanda kaman anyi wasan dambe a tsakiyar sa. Yana da ɗan girma amma Babu komai na kayan ƙawa a ciki, Daga labulen dake maƙale a bango don suturta mata ɗakin sai carpet ɗin tsakiyar ɗaki da take da tabbacin ta ƙalƙale shi kafin ta fita asibiti jiya, amma yanzu wari yake yi. Ba sai ta nemi dalili ba don ga kofin ruwa dake kife a wurin. Gefen shi kuma farin singlet ne, daga inda take tsaye kuma tana iya hango stain ɗin manja a jiki, sai rigan jamfa light brown da baƙin boxers yashe a hanyar da zai sada ta da bedroom. Bata ji komai a ranta ba domin wannan yanayin ya riga ya zame mata jiki, rashin lafiyar muftee ne dai ta gagara sabawa dashi har yau. saidai shima ɗan kukan da ta samu tayi yau ya sanyaya mata rai kaɗan, kuma gobe sammako zata yi ma Hajiya Surayyah Kagarko tunda tayi mata alƙawari. Tsugunawa tayi ta haɗa kwanukan a wuri guda sannan ta tattara kayan a hannunta ta nufi uwar ɗaka da su, tana daff da shiga ta fara jiyo murya na magana ƙasa-ƙasa. “Uhmm baby nah?... Rowan ganinki kike mun ina?.... Toh yaushe zan zo?” Ta sauƙe numfashi kana ta ɗaga labulen ɗakin ta kutsa kai. Hango shi tayi kwance yayi ɗai-ɗai a tsakiyar gadon wanda shimfiɗin shi yake a yamutse kaman wanda take da wasu yaran masu hawa suyi birgima a kai, yana sanye da wandon jamfar da ta tsinci rigan shi a parlour. Ta kalle shi sau ɗaya ta wuce jikin buhun da suke tara kayan wanki daga ƙofar banɗakin su ta zuba kayan hannunta a ciki, tare da zame hijabin wuyanta shima ta jefa don tun shekaran jiya take yawo dashi har tsami yake yi. Tana jinsa yana cigaba da wayan shi hankali kwance ba don bai lura da ita ba sai domin sanin babu abinda zata iya aikatawa a kan hakan. “Me yasa zaki dinga zama da yunwa?... Ba nace bani so ba?” ya ƙara kashe murya yana karkaɗa ƙafan da ya daura ɗaya bisa ɗaya. Ita sai yanzu ta tuna da rabonta da abinci tun safiya, hala shiyasa ma take jin ta jigata sosai duk jikinta ciwo yake yi yanzu haka musamman ma mazaunanta. Cikinta ne taji yayi wani irin ƙugi lokacin da ya ambaci “toh yanzu me zaki ci? Shawarma?.... Da me kuma?” Wanka taso shiga amma sai ta fasa, gwamma ta zauna ta jira shi har ya gama, sanin ƙaramin aikin shi ne cikin ƴan mintuna zata fito ta samu ya kwanta ya rufe idanunsa, kuma duk yanda zata yi ba zai kulata ba tunda ya san farkon wata ne zancen baya wuce na kuɗi, Idan ta matsa kuma yayi fushin gan-gan ya naɗa mata na jaki a cikin daren nan. Haka suka gama tsinke furen su da koma wacece bata damu ba. Ita dai fatan ta ɗaya Allah yasa ta samu wani abu a wurin shi ko na abun hawan sintirin asibiti ne ta rage. Ta fi minti 30 tana zaune a wurin tana tunanin sallolin dake kanta ga alƙawuran ƙarya da yake ta shirgiɗa ma ƴar mutane dake shiga cikin kunnenta. Mutumin da ya gagara riƙe mata ɗaya da ɗa ɗaya shine yake mata alƙawarin aure kwanan nan take yarda?. Taɓe bakin da yaga tayi tare da sakin ƙaramin murmushi yasa yayi ma budurwar sallama ya katse kiran da suke yi ta WhatsApp cikin tsarguwa. Tayi saurin gaida shi da “A fa fiyan Ya Hashim (ina wuni ya Hashim)” Saida ya tsare gida sannan ya fara da faɗin “sai yanzu kika ga daman dawowa daga gantalin taki ina?” Da ace baya cikin hankalinsa ne sai tayi tunanin bai san daga ina take ba, amma sanin niman wani abu take yi daga gare shi ya sanya ta karya murya kana ta amsa da “Jikin Muftee har yanzu babu daɗi, kuma babu kowa a jikin shi balle in samu in sato jiki in dawo, yanzu ma da na koma can ɗin Khausar ce tayi mun alfarmar kwana tare dashi in zo in huta.” Shima ya san da hakan, shiyasa ya baje kolin shi a gidan da tunanin ba zata dawo ba saida safe “Daman ai ke kullum kina da tacewa, ba'a kada ke a baki. Amma wallahi ki bari na cigaba da tara ki Ilham hukunci zan ɗauka da hannuna ba tare da mun dangana da wurin Baba babba ba ma, ni Hashim na isa in yi maganin ƙaramar mara tarbiyya irin ki, tashi ki bani wuri.” Ya yunƙura ya kai mata dukan da ba don ta saba da saurin hannun shi ta ƙware a kaucewa dukan da yake kawo mata a kowani lokaci ba da tabbas ya same ta. Ta miƙe a kan ƙafafunta tana ganin yanda yake watsa mata mugun kallo mai cike da tsana, wanda ita kanta ta shiga kokwanton ko akwai lokacin da Hashim ya taɓa kallonta da ƙauna a idanunsa, kaman ba'a yi lokacin da yake nuna mata soyayya gabanin rasuwar mahaifinta ba. Ta haɗiyi miyau ko wani abu mai zafi da ɗaci da take ji a maƙogwaronta zai samu ya wuce amma abun bai matsa ko nan da can ba. Ko kuɗin da zata hau napep ta tafi asibiti gobe babu, babu abinci a gidan bayan garin masara da bai wuce mudu biyar ba da shinkafar da bata saka ran zai kai mudu ɗaya, babu manja ba mangyaɗa balle a je zancen maggi da kayan miya, kuma ya sani tunda wata ya ƙare har an shiga sabuwa bai siyo ba bai bata kuɗin siya ba, kuma ya san tana tafiya da abinci asibiti tunda ɗan shi ne kwance a can yau fari gobe tsumma. Ya ja dogon tsaki tare da juya mata baya yana mai cigaba da danna dalleliyar wayar shi wanda bata ma san wacce ƙira bace domin bai daɗe da siya ba kuma bata da ikon kai hannunta jiki. Ta buɗe bakin da yayi mata nauyi saboda kukan da ya fara zuwa mata, daman ba wai ta ƙoshi da shi bane ɗazu, haske mata fuskar da aka yi da lantarkin mota ya sanya ta haƙura ta share hawayenta ta ɗauki hanyar komowa babban asibiti da sawayenta tunawa da cewa bata da ko sisi. Murya na rawa tace “Baban Muftee babu abinci a gidan nan. Dan Allah ka taimaka kayi mana cefane ka ɗan bani wani abu ina yin na adaidaita dashi, sai in ji da na asibitin da sauran abinda ba’a rasawa” Wani ƙundumemen ashar da ya juyo ya watsa mata ya sanya ta rugawa da gudu ta shiga banɗakin ta rufo ƙofar tare da saka sakata ta ciki domin tana da tabbacin da ta bari ya riƙeta toh fa saidai hala idan shine zai je zaman jinyar Muftee da kanshi gobe. Hannu ta saka ta dafe kunnuwanta lokacin da ya tokari ƙofar da ƙafar shi kaman bai san tsakar dare bane. “Shegiya tsinanniya! Dan abu ta kazan uban ki babu abinda kika iya sai buɗe bakinki mai shegen wari kiyi ta ci gashi dai ko nunawa baya yi a jikin ki domin ni ba gane komai nake yi ba, da wani shegen baƙi kaman zunubi! Idan jinyar tsakani da Allah ne ba gashi masu maganin gargajiya suna bada maganin da yake warkar da sickler ɗin ba? Kawai Kina yawon banzanki kin fake da asibiti sai lale mun aljihu kuke yi Munafuka! Ko nine na ɗora mishi rashin lafiyar?” Hawaye take zubarwa tana durƙushe a gaban shaddan da aka yi amfani dashi ba tare da an damu da a kora da ruwa ba. Hawaye ba na zagi da kushewar halitta da yake yi mata ba, wannan ya zamo mata kaman ruwan sha. Hawayen zagin mahaifinta da yake cikin ƙasa da kuma na danasanin kasancewar ɗanta matsayin jinin Hashim a karo na barkatai take yi. Ya dauki lokaci yana mita da zage-zage don saida ya tabbatar bai bar mata ƙofan da zata sake tambayar shi wani abu a kwanan nan ba sannan ya koma gado yayi kwanciyar shi, chatting ɗin ma ya haƙura dashi. Saida taji shiru kaman na mintuna 20 zuwa 30, ta tabbatar cewa ya kwanta, sannan ta miƙe tsaye ta kwaɓe kayan jikinta. A hankali yanda ba zata yi ɓuruntu da yawa ba ta kora shaddan kada ace ba barci yayi ba ya ƙara samun dalilin sababi, ga banɗakin yayi kaca-kaca, ta saka ma ranta dai saida safe kafin ta wanke shi, amma koda ta duba bata ga omo ko sabulu da zata wanke jikinta dashi ba ko ɗanɗani. Ɗan kilin da ta siya na ɗari da hamsin jiya ta ajiye daga windown toilet ɗin ya ƙarar dashi tass sai laida ya bar mata. Ruwa mai sanyi ta fara jiƙa jikinta dashi sannan ta jijjige laidan klin ɗin ta zuba ɗan ruwan kumfan a jikin sosonta ta cuɗe jikinta dashi kana tayi alwala ta fito cikin sanɗa, har ya fara sake minshari kuwa. Ta siɗaɗa zuwa ghana must go ɗin kayanta ta ciro wata shuɗiyar atamfa rubber ɗinkin doguwar riga da hijabi tiyebo ja, ta janyo darduma daga kan ƙofa ta fita parlour ta shimfida ta tada sallan Maghriba da Isha dake kanta. A kowani sujjada idan ta saka goshinta a ƙasa sai ta rasa me ɗaya zata roƙi Allah ko kuma ta ina zata fara domin komai ma baya mata daɗi, amma sai ta samu kanta da yi mishi godiya tana zubda hawaye saboda akwai masu son irin rayuwanta da yawa kwance a gadon asibiti, indai zasu kasance cikin ƙoshin lafiya kamarta tabbas zasu so ace da sune a matsayinta. A kan darduman da tayi sallah tayi kuka a wurin gajiya ya rako barci suka saceta dukda yunwa dake ƙwaƙular hanjinta. …. Agogo ya kalla lokacin da ya fito daga bathroom ɗaure da farin towel a ƙugun shi, jikinsa yana fitar da tiririn zafin ruwan da yayi wanka dashi. Ƙarfe sha ɗaya har ta gota, yayi saurin tsane jikin shi ya laluɓo baƙar jallabiya da gajeren wando ya saka. Ba zai taɓa iya zama babu turare ba balle ya fita a haka shiyasa har ya iya tsayawa ya shafa designer Oil perfume ɗinsa na Bakhoor by Seemah(08021689184) sannan ya ɗauki wayan shi da agogon hannun shi ya fita bayan ya kashe wutar ɗakin. Driver dake zaune a cikin mota yana jiransa daga mashigar ɓangaren yana hamma tare da kare bakinsa da bayan hannun shi na hagu ya gyara zama yana wartsakewa da ganin fitowar Abdulhameed. Yayi ƙoƙarin yaƙi da duk wani barci da ya fara kawo masa ziyara saboda ba zai yi gangancin sake ɓata mishi rai ba, musamman a yanayin da yake ciki. Tare suka fita da safe, ya kaishi wurin ganawar da suka yi da kamfanin da zasu basu wasu daga cikin kayayyakin amfanin marasa lafiya, kuma ganawar tasu a ɗauki tsawon lokaci shiyasa da lokacin Sallah yayi ya rufe highlander ɗin da suka fita a cikinta kasancewar ya kai ɗayan motar wurin wanki, yana idarwa kuma bai tsaya dogon addu'a ba ya fito sanin cewa shima ubangidan nashi zai iya fitowa a kowani lokaci, amma sai riskar shi yayi a jikin motar yana ƙwala masa kiran da ko shi ya amsa ba ji zai yi ba. Da sassarfa ya ƙarasa wurin, Kuma Abdulhameed bai tsaya tambayan shi inda yaje ba ko yayi mishi bayanin abinda yake faruwa, ya wafce key ɗin motar daga hannunsa ya faɗa ciki, ya zugeta a ɗari ya bar shi a wurin. Sai da ya koma gidan yake jin cewa ai Ikram ce ta faɗi a kan keke ta samu targaɗe a hannu, har an kwantar da ita a asibiti. Abdulhameed ya fi zama a gaba ko ina ne zasu je amma a yau tunawa da hatsarin da suka yi da Nne da yayi, ya sake ganin komai a cikin idanun shi kaman jiya ne ya faru, ya sanya shi buɗe back seat ya shiga. Saida drivern ya kunna fitilun motar da zasu fita a gidan ya tuna da ganin Ilham da yayi ɗazu da ya dalle mata idanu. A lokacin da ta kare idanunta daga hasken, Reverse yayi, amma idanun shi a kanta har saida ya juyar da kan motar, hasken da suka bayyana mishi ita suka koma kan gate ɗin asibitin. Ya sake juyowa yayi mata kallon ƙarshe a cikin duhun, yana daɗa samun tabbacin ita ɗin ce tabbas saboda Birthmark ɗin ƙasan bakinta. Wannan birthmark ɗin da yake mata kyau a lokacin baya. Amma yayi mamakin yanda ta canza tayi baƙi ta koma wata iri. Bai tsaya mamakin abinda ya kawota asibiti ba sanin cewa ba zai wuce dalilin da ya kawo shi ba shima, ma'ana rashin lafiyar wani nata. Kuma kukan da yaga tana yi ya saka mishi yaƙinin mai jinyar na da kusanci da ita sosai, domin shima da ance mishi idan yayi kukan Kiki zata warke da tsaff zai yi. Shiyasa a yanzu ma yayi ƙoƙarin cireta daga cikin tunanin shi har suka isa Medi-plus hospital yaje yaji da abinda ya dame shi. Yana isa ya samu Aunty Surayyah zaune a gaban gadon Ikram tana cin tuwo a plate. Ya manta da ana jin yunwa ma dukda kasancewar rabon shi da abinci tun breakfast da suka yi tare da Kiki. Shima ƙarewa yayi a lallaɓata ta samu ta saka wani abu a nata cikin saboda kukan ciwon kai da take yi mishi, shiyasa ma bata je makaranta ba, ya fita ya barta da Nanny ɗinta. Aunty Surayyah tayi mishi alama da har yanzu bata farka ba tun kafin ma ya tambaya, ya gyaɗa mata kai yana zama a bakin gadon tare da leƙa fuskar Kiki da yake ganin kaman har ta rame a wuni guda kawai. Juyowa yayi ya fuskanci Aunty Surayyah yana mata alamun kai cokali baki sannan ya nuna Ikram da yatsa yabi ya ware hannun. A matsayin tambayar ita Kiki mai zata ci idan ta tashi. Nuni tayi mishi da tuwon da take ci a plate sannan ta buɗe baki can ƙasa da murya tace. “Da ɗumi tuwon, ɗazun nan na saka aka tuƙo shi daga gida domin zai fi mata sauƙin ci. Kaima ka samu ka saka ko kaɗan ne a cikin ka” Ya girgiza kai yana yamutsa fuska, samm baya son tuwo ko miyar menene, musamman tuwon shinkafa dama-dama semovita, rabon shi da na gari kuma ana niman shekaru uku da ƴan kai. Saida ta haɗa mishi tea ya sha ya taɓa bread ɗin da ta tura aka siyo slice biyu, sannan ta yarda ta tafi gida ta huta kaman yanda yace. Haka ya koma gaban gadon yana kallon Kiki kawai don tsoron taɓata yake ji kada ya fama mata ciwo a rashin sani. ….. ILHAM Dake yunwa ba ƙanin ubanta bane ƙarfe uku da Arba'in na dare sai gata tana haɗa garin kwaki. A cikin drawern kayan Muftee kuma ta samu wani ɗan ƙullin sugar da ta ɓoye. Hashim ya buɗe baki yana ta sharar bacci har ta wanke garin a banɗaki ta wuce shi ta koma bai ko motsa ba, haka ta zauna ta saka sugarn da bai ishi garin ba amma daɗin shi take ji har maɗiga saboda yanda taji yunwa. Da tayi sallar asuba ta so sake komawa ta kwanta ta daɗa huta gajiya amma bata son yin lattin zuwa wurin Hajiya Surayyah musamman yanzu da bata da kuɗin napep ɗin zuwa A&I, idan takawa zata yi a sayyada kuma dole sai tayi sammako ta samu isa a kan lokaci. Wayanta ta fara jonawa a caji don har lokacin akwai wutan nepa, ta naɗe carpet ɗin parlorn ta fita ta shanya shi a garu iska ya ɗauke warin, da sanyin asubahi ta fara sharan tsakar gidan, ta dawo ta gyara parlon tass sannan ta ɗaura mishi ruwan wanka a kan murhun gawayi ko zata samu dalilin da zai tashi ya bata wuri ta gyara uwar ɗakin don idan ta tafi ta bar mishi ma ba gyarawa zai yi ba. Sauran shinkafar da ta rage musu ta juye a farantin silver ta gyara, idan masu shagon unguwan sun fara fitowa sai ta karɓi bashin mangyaɗa, maggi da barkono ta haɗa dashi a lallaɓa. Da ruwan ya tafasa ta fara shiga ta kora banɗakin da ruwa da tsintsiya tunda ba omo, kafin ta sirka mishi ruwan a bokitin plastic ta koma tashinsa a barci yana ƙunƙuni kaman wani ƙaramin yaro, haushi kaman ta kifa masa mari da zata iya. Tana cikin kaɗe zanin gadon ya leƙo kanshi daga banɗaki. “Ilham ina sabulun wanka?” Sai ta kalle shi sheƙeƙe “ai ya ƙare ya Hashim, nima jiya a haka nayi wankan” Tsaki yayi “Shiyasa ai ba zaki daina wari ba” ya sake jan wani tsakin. Ya fito ƙofar banɗakin inda ya jefar da wandon da ya kwana dashi a jikinsa ya ɗauka ya mayar sannan ya duba rigarta da ta gama yamutsewa a cikin kayan wanki ya saka yana ƙwafa “ina ƙyashin wanda kike sakawa nake amfani dashi kike ji? Wallahi zaki ga baƙin hali, dani kike zancen” ya fice daga ɗakin ita kuwa ta cigaba da abinda ke gabanta gashi ƙarfe 7 ta gota. Kafin ya dawo ta gama da abinda zata iya a ɗakin taje ta sauƙe shinkafar da ya gama nuna. Shikuwa ganin tukunya a kan murhu da zai wuce sai yayi zaman jiranta ta kawo masa abin karyawa bayan ya gama shirin fita. Wanda zata kaiwa Muftee da Khausar da kuma wanda zata ci da rana ta fara zubawa a babban cooler ta yaryaɗa masa man da ta soya ko albasa babu, da yajin da ta daka a turmi tana zaune a wurin, ta samu laida ta ƙulle kwanon a ciki ta ɓoye, sauran kuma ta zuba a faranti ta barbaɗa mishi maggi rabi sannan ta saka cokali, ta shiga dashi ciki wurin Hashim dake zaune a saman darduma da ya shimfida a kan tiles ɗin ɗakin, cikin shigar shi ta kamala sanye da yadi mai kyau da ya sha ɗinki harda hula, sai zuba ƙamshi yake yi hankalin shi na kan wayan da yake dannawa. Kallonta yayi bayan ya ɗago idanunshi daga kan shinkafar da bai san ko mai ma babu a cikinta ba, amma ya tabbata yaji lokacin da take daka yaji shiyasa ya tsaya yayi manejin koma menene take dafawa da saidai yayi karyawan shi a waje. ````````` Seemahwrites ✨ Chapter 9 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites* *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 09… Ilham?!” Ya kira sunanta da mamaki. Rage tsayinta tayi a gabansa kada yanzu ya miƙe ya haɗa kanta da bango, ta amsa da “Na'am ya Hashim” “Menene wannan farau-farau ɗin? Shine abinda zanci?” “Abinda muke dashi kenan a gidan, maggin ma fita nayi na karɓo bashi a shago.” A hasale yace “bana son rainin hankali, yanzu fah ina jinki kina daka a waje..” Tayi saurin amshewa da “Maggin ne yayi tauri saida na saka a turmi na faffasa, gashi nan na barbaɗa maka.” ta ƙarashe tana matse baki saboda murmushin da yake niman ƙwace mata, ta ɗan ji sanyi a cikin zuciyarta da tayi mishi hakan. Saidai yanda ya yunƙuro ya sanya tayi saurin ja da baya tana kare fuskarta da hannuwanta a tunaninta marinta zai yi. Hasken da ta gani yasa ta sauƙe hannun ta buɗe ido, sai ganinshi tayi ya ɗaga labule yana saka takalmin shi daga bakin ƙofa, ko waiwayenta bai sake ba ya sake mata labulen yayi gaba. Tana sauraron takun shi har ya ƙarasa ya wangale ƙofar dake jikin gate ya dawo ya kunna mashin ɗin shi ya hau ya bar mata gidan, a ranshi yana jinjina girman wulaƙancin da zai yi mata. Bai yi niyyan siyan shawarman jiyan nan ba, ya faɗa ne kawai saboda daɗin zance, amma duk yanda ake siyarda shawarma da safiyar nan a garin kaduna sai yaje ya nemo. Taɓe baki tayi ta miƙe da farantin shinkafar a hannunta, rufe mishi zatayi idan ya dawo sai ya ɗauka yaci, bai ajiye cefanen da zatayi miya ba balle ta damu kanta ta ɗauko hanya tun daga asibiti ta zo ta tuƙa masa tuwon dare. Bata da lokacin sake yin wanka, sai kawai ta ƙarasa kimtsawa ta mayar da hijabinta da tayi sallah dashi, ta cire wayanta daga jikin caji ta kulle gidan bayan ta ɗauki abubuwan da zata buƙata ta miƙa key ma maƙwabtansu idan ya dawo bata nan ta san zai tura yara su karɓa masa. Idan tayi sauri kuma har zata samu isa asibitin ta bawa su Khausar abin karyawa kafin ta tafi wurin Hajiya Surayyah Kagarko, ta san khausar ɗinma ta gaji don zaman ba na daɗi bane, idan tana son tafiya gida babu damuwa tunda gari ya waye, ai ma tayi mata ƙoƙari, kuma itama tana fatan ba daɗewa zata yi ba zata dawo jikin yaronta. A hanya ne kiran Khausar ɗin yake shigowa wayarta, ta ɗauka tunda ita ba kati take da shi ba gashi ta ƙure limit ɗin bashinta. “Aunty Khausar ayi haƙuri gani nan zaki ganni nan da ƴan mintina” tace da sautin murmushi bayan ta kara wayan a kunne. “Lah Aunty Ilham ki bari kawai ki fara zuwa wurin su kada kiyi latti, za'a kawo mana abin karyawa yanzu daga gida nida Muftee” Ta kalli kwanon dake ƙulle a cikin laida mai fari da baƙi da ta rungume. “Allah sarki Khausar kiyi ma umman ku godiya sosai don Allah” “babu komai Aunty sai kin dawo, Allah ya bada Sa'a” da haka ta katse kiran daga bangarenta. Wannan ya bawa Ilham damar kasancewa a cikin A&I Support Organisation da karfe 9:23 na safiya, rungume da envelope a hannu ɗaya kwanon abinci a ɗayan. Da murmushinta ta gaida receptionist ɗin jiya, shima ya amsa mata da murmushin kana ya sanar da ita cewa hajiya Surayyan bata shigo ba tukunna amma yau ya bata matsuguni a ɗaya daga waiting chairs ɗin wurin ta jira isowarta. AC ɗin wurin yana ratsata take fatan Allah yasa yau ta taho a kan alkhairi. ….. Fitowa tayi rataye da jakarta, ta zura ƴar makullinta a cikin raminsa ta murɗa shi sau biyu ta garƙame ƙofar ɗakin, sannan ta juyo ta kalli tsakar gidan tana gyara zaman yalwataccen mayafinta. Ƙarfe 8 da rabi na safiya amma yanda ta dawo ta same shi a daren jiya har yanzu ma a haka yake kaca-kaca kaman babu mutane a gidan, ga shinkafar da yara suka ci suka zubar tun jiya da rana har ya bushe a wurin. “Hudah! Hudah!!” Ta kira cikin ɗaga murya. Jin ba'a amsa ba ta mayar da kiran zuwa “Ameerah! Zakiyya! ɗaya a cikin ku tazo” Yanda kasan bayan ita babu wani mai ji da magana a gidan, ko samun mai faɗa mata idan ma basa kusa ne ba'ayi ba. Sai ta ƙarasa ɗakin dake gefen nata ta ɗaga labule tare da yin sallama domin ƙofar ɗakin a buɗe yake already. Matar dake zauna a jikin socket ɗin da ta jona dutsen guga, ta baza darduma da kaya a kai tana gogewa ta amsa mata sallamar. “Ina kwana Maman Ameerah, ina su zakiyya?” ta haɗa mata gaisuwan da tambayar wuri guda lokacin da idanunta suka sauƙa a kan Ameerah dake kishingiɗe a kan dogon kujera hannunta riƙe da remote ɗin TV tana kallon Series, da ta san Aunty Surayyan leƙowa zatayi da ta tashi ta gudu cikin ɗaki don ai taji kiran taƙi amsawa, babu wanda ya isa ya saka ta aiki da safiyar nan. Tace “Ameerah Gidan nan babu mutane ne kuka bar tsakar gida tun jiya da datti ba zaku saka tsintsiya ku share ba kuna ƴammata?” Saurin miƙewa zaune tayi tana kare kanta ta hanyar faɗin “Yau fa Zakiyya ce mai dutyn shara da wanke-wanke aunty Surayyah, nawa sai jibi idan Hudah tayi gobe, ai kinsan ni bani ƙin yi.” “Ina Zakiyyan?” “Ta tafi Makaranta, kuma ta san itace zata yi ta tsallaka ta tafi” “Toh yanzu sai ta dawo kenan za'a share gidan?” Da mamakinta sai cewa Ameerah tayi “Ai zuwa ƙarfe biyu za'a tashe su, daman na faɗa mata haka zata dawo ta same shi yanda ta bari” Aunty Surayyah ta tsaya kallonta galala, mahaifiyarsu da tayi kaman bata ɗakin sai a lokacin ta buɗe baki tace “Ai itama tace ba zatayi bane saboda kema baki yi naki ba jiya, sai kananun yaran nan ne na saka su suka tattara wurin sama-sama kafin su wuce Islamiyya” Ta turo baki cikin ƙunƙuni tace “Toh umma ba wunin asibiti ba muka yi ba jiyan a jikin Kiki?. ko sai in dawo daga asibiti da almuru kuma in kama shara don Allah” Aunty Surayyah dai ta sake musu labulen ta bar kofar ɗakin amma maganganun da suke musaya a tsakanin su bai bar shiga kunnenta ba, a inda maman Ameeran ke cewa. “Ai da kin yi da safen babu wanda zai ce miki kiyi shara da daddare, gashi kin jawo min magana har ɗaki ina zaman zamana” Allah sarki mahaifiyar Abdulhameed, ita kawai ta tuna a lokacin, da irin zaman da suka yi da ita shekaru 30 baya. Kaman yanda rana yake fitowa yake faɗuwa babu fashi haka itama ta ɗauki hidiman gidan a wuyanta ko ruwa ko iska bai saka ta fasa ba, domin koda ta riga ta tsaftace gidan idan aka yi ruwan sama ko iska mai karfi ya shigo da datti sai ta sake fitowa ta share, saboda a rayuwarta bata son ƙazanta bata jin daɗin zama a cikinta shiyasa ta ɗaura ma kanta alhakin gyarawa a kowani lokaci. Amma hakan bai saka ta iya tsallake ma zagi da cin fuska daga mazauna gidan ba, suna iri-iri babu wanda ba'a kiranta dashi, da wanda bata ganewa saboda Hausan ta bai yi ƙwari ba daga farko harda wanda zai yi daidai da iliminta. Gashi ta haɗu da tsangwaman uwar miji don mahaifiyar su bata sonta ko kaɗan kasancewarta inyamura, har kafurta ta anyi saboda gani suke yi musuluncinta bai cika ba tunda bata bin Al’adun malam bahaushe. Ba da son ran mahaifiyar su Muhammad ya auro Amina ba sai don iko da mahaifinsa ya nuna a kanta lokacin, shiyasa ta bada dama ma kannensa suka rainata matuƙa gaya, bayan Muhammad ɗin Shine babba a gidan baki ɗaya. Idan tayi sharan haka za'a ɓata ta sake sharewa, a ci abinci a tara mata wanke-wanke kamar ƴar aiki, tukunyar abincinta kuwa kaman na runduna, a ciki da ƙwaryan ƙannen shi maza har lokacin da take ɗauke da tsohon cikin Abdulhameed a jikinta. Sannan ita kanta Surayyan bayan ƙananun sharri da munanan ƙazafi da ta dinga binta dasu har dambe sun taɓa yi a lokacin ƴammatancin ta a gidan. Tana da tabbacin hakkin Amina shi ya hanata jin daɗin Zaman Aure, ga kishiyoyi da suka kusan kasheta da asiri, tayi ta dogon jinya kaman ba zata rayu ba, har ta ƙare ta haƙura da auren baki ɗaya, tunda har ta gama zaman gidan mijin na shekaru goma bata taɓa ko ɓatan wata ba bayan kishiyoyinta suna haihuwa lafiya lau, kaman gasar haihuwar ma suke yi duk shekara saboda mijin su yana da rufin asiri sosai. Sai kuma gashi kafin ta kaiga niman yafiyar Amina Allah ya ɗauki ranta ba tare da ya bari sun sake ganawa ba. Itama mahaifiyarsu da ta fara assasa abun gashi Allah ya ɗauketa ya bar Abdulhameed ɗin da basu saka shi ma a cikin lissafi a lokacin. Shiyasa ta zaɓi ta ƙare sauran rayuwarta wajen kula dashi da kyautata masa ko Allah zai tausaya mata ya yafe mata kura-kurenta ba sai an isa filin ƙiyama ya tsayar da ita a gaban shi tare da Amina ba. Ba don haka ba da ba zata zauna a gidan har ƴaƴan cikinta su taso suna abinda bai dace ba kuma bata da bakin magana ba, amma yanzu sune masu gida tunda ba da daɗewa ba Abdulhameed ya saka kuɗi ya mallaka ma ubansu gidan, ita alfarma yayi mata ya bar mata ɗakin da ya kasance na mahaifiyarta ta cigaba da zama dukda ya biyata kuɗin shi hannu da hannu. Juyawa tayi zuwa ɗakin mai gidan a yanzu, Yayanta Muhammad, ta same shi zaune a parlour mahaifiyar Hudah tana zuba mishi abinci a plate. “Ina kwana yaya” ta gaida shi tana zama a gaban shi a saman tsohon carpet ɗin dake baje kan tiles din dake walwalin sabunta yana ɗaukan ido. Gidan sabone dall Abdulhameed bai shekara biyu da yi musu renovation ba, a lokacin da ya sayi gidan maƙwabtan su zai fitar da nashi ɓangaren daban saboda Ikram, saboda bata samun kulawan da ya dace a tare da su, sai ya saka aka rushe gidan gaba ɗaya aka ɗaga sabon gini na zamani amma haka mahaifin shi ya dawo da tsoffaffin kayan ɗaki saboda a cikin ƴaƴansa da ƙannensa an rasa wanda zai canza masa carpet ko kujera koda mai sauƙin kuɗi ne, suna jira saidai shi Abdulhameed ɗin yayi. Gyaɗa mata kai yayi saboda be kai ga haɗiye ƙosan da ya tura a baki ya kora da kunu ba. Ta juya wurin maman Hudah ta gaidata tana amsawa ciki-ciki saboda wani dalilinta. “Yaya nace an kwantar da yarinyar Abdulhameed a asibiti jiya, ta faɗi ne ta samu rauni a hannu, duk munje asibitin mun dubota a jiyan” Saida ya ƙarasa tauna ya haɗiye, yabi ya sake kurɓan kokon shi, sannan ya dubeta a tsanake. “Wata yarinya kenan Sharmama?” “Yarinyar shi Ikram jikar ka” Ƙosai guda biyu ya sake ɗauka a hannunshi ya tunkari bakinsa dasu yana faɗin “Ni ai cikin Jikoki na babu mai suna Ikiram” ya cusa ƙosan a baki ya fara taunawa yana kallonta kaman mai niman ƙarin bayani da gaske.” “Haba yaya, sau ɗaya kawai, ko text kayi mishi a waya ka tambaye shi jikinta, zai ji daɗi Wallahi saboda ya damu sosai” Sai ya girgiza kai yana murmushi, ya haɗiye ƙosan ba tare da ya kora ba, kana ya gyara zama ya jingina da jikin kujeran bayansa . “Sharmama abun duniya ba zai taɓa rufe mun idanu na karɓi abinda yake ba daidai bane. Ban amshi wannan al'amarin ba lokacin da Abdulhameed baya da komai, ba zan karɓa ba don kawai Allah ya kawo mishi wadata.” Cikin yanayin damuwa tace “Yaya wannan maganar ta wuce ai” “ke kinsan ba mai wucewa bane, idan kuma na bari ya wuce a wurina yaya kike so in taya shi bayani a wurin Allah tunda na bashi goyon baya da nakasar shi yaje ya haifo mun ƴar gaba da fatiha ya kawota ƙarƙashin kulawana” Ta kalli maman Hudah da tayi kaman an mannata a wurin da super glue ta kasa tashi ta tafi, sai ta shiga zuba wani ƙosai da kokon tana turowa gaban Aunty Surayyah don kawai ta cigaba da zama ta saurari gulma. Akwai abubuwan da ta so ta tunasar dashi da yawa, yawan nasu laifukan a wuri Allah da ma hakkin Amina da ɗanta Abdulhameed dake wuyan su, amma sai ta fasa saboda maman Hudah, tace “wannan tsakanin shi da ubangiji ne, bamu san menene matsayin shi a wurinsa ba, idan yaga dama sai ya yafe masa. Amma ita Ikram menene laifinta? Haka zata girma ta fara fahimtar ita wacece daga wurin mu? Kada muyi sanadin rayuwarta ya shiga garari don Allah”. Ta lura da yanda kalamanta suka shiga jikinsa amma sai yayi ƙarfin halin taɓe baki, ya karkaɗa mata hannu ta tashi ta bashi wuri. Haka yake da tsananin kafiya da ƙi faɗi, tana fatan dai ba zai bari lokaci ya sake ƙure masa ba a wannan karon ma kafin ya juyo ya fuskanci gaskiya. Kitchen ta koma ta ɗauki kwandon abincin da ta haɗa na asibiti kafin ta koma tayi wanka ta shirya. Ta so tayi ma mutanen gidan tayin zuwa asibitin sai ta rage musu hanya amma dake ranta a dagule yake sai kawai ta saka kwandon a seat ɗin baya ta shiga ta tada mota ta bar gidan. A waje take haɗuwa da ƙanin Abdulhameed ɗin na uku Mukarram, ta tsaya suka gaisa sai ya buƙaci su tafi asibitin tare bayan ta sanar da shi can ta nufa. Izini tayi mishi ya shiga seat ɗin gaba suka ɗau Hanyar Medi-plus hospital. . . . Da shigar su ɗakin da sallama suka hango shi tsaye rungume da Ikram wanda ta lafe a kafaɗar shi tana ƙananun kuka, shi kuma sai aikin jijjigata yake yi yana shafa bayanta kaman wata jaririya. Yana ganin Aunty Surayyah ya sauƙe numfashi. “Aunty taƙi cin abinci tana ta kuka” yayi magana kaman zai fasa Ihu. Ƙarasawa tayi ta karɓeta dukda yarinyar tana da zuri amma haka ta ɗauketa tunda mara lafiya ce. Mukarram dai ya ajiye basket ɗin abinci ya koma gefe yana kallo. Aunty Surayyah ta ɗago fuskar yarinyar da take nan fara tass, gashin kanta da parking ɗinshi ya warware mai tsananin laushi ya sauƙo har saman fuskarta. “sorry Kiki kina son indomie?” Girgiza kai tayi idanunta a rufe tana ƙara kukanta na shagwaɓa. “Eggs fah? Na kawo miki banana ma.” Tayi maganan tana murmushi don haka yarinyar ta buɗe fararen idanunta ta zuba mata su. Ƙarasawa jikin gadon ɗakin Aunty Surayyah tayi ta ajiyeta sannan ta shiga buɗe abubuwan da tazo da su ta fara zuba mata farfesun kaza da romo mai ɗan yawa kana ta tsoma soyayyan ƙwan a ciki tana yanyanka komai da cokali daidai bakin Ikram ɗin. Tana kallonta saida ta gama ta dawo gefenta ta zauna zata fara ciyar da ita saboda hannunta sannan ta kawar da kai tana noƙewa. “Uhm-uhm.. Daddy nake so ya bani” Aunty Surayyah ta miƙe, tunda dai zata ci ai shikkenan. Abdulhameed ne ya maye gurbinta a gefen Ikram ɗin yana bata abincin a baki yana bata chivita orange da ya tsiyaya mata a cup ta kora har saida ta kawar da kai ta ƙoshi tana ɗan ƙaramin gyatsa lokacin ta kusan cinye abinda ke cikin bowl ɗin kafin ya ajiye ya bata ruwa ta sha. Sai a lokacin ma ya lura da Mukarram dake zaune a bakin ɗayan gadon dake ɗakin, aunty Surayyah kuma tana ta kimtsa musu wurin. Mukarram yayi mishi jinjina da hannu kawai yana ƙaƙalo murmushi. Da mamakinsa sai Abdulhameed ɗin ya mayar masa martani domin har cikin ransa ya ji daɗin ganinsa. Ikram na jikinsa yana shafa kanta a hankali Aunty Surayyah take masa bayanin abubuwan da zasu wakana a safiyar yau na rabon magunguna da zasu yi ma marasa lafiya, sai kayan abinci da kuɗin jinya ma masu ɗauke da manyan cututtuka masu wuyan magancewa irin su cancer, sickler, Aids da sauran su, sai kuma wheel chairs da hearing aids ga masu nakasan ji da tafiya harda test da za'a yi wa masu ciwon zuciya kyauta duka a bisa tallafin da suka karɓo daga gwamnati da kuma kungiyoyi masu zaman kansu ciki harda World health Organisations WHO. Kuma bayan sun gama shirya yanda komai zai tafi wa’inda suka ɗora a kan abun da masu saka ido akan tabbatar da wanzuwar shi cikin gaskiya da amana jiran lokaci da umarni kawai suke yi su fara aikin su. “Mun yi meeting da su sosai jiya kuma duk wani bayani da iyaka da ya kamata ayi musu nayi musu” Ya jinjina kai “Komai yayi, Allah yasa mu fara lafiya mu gama Lafiya” Ta amsa da “ameen” tana ajiye wayan da take karanto masa sauran tsare-tsaren da ta ƙarasa a daren jiya, sannan ta miƙe don lokaci ya tafi. “Na gode Aunty Sharmama” ya furta ba tare da ya kalleta ba, idanun shi a kan ikram da ta fara gyangyaɗi. don haka babu amfanin amsawa tunda ba zai san ta amsa ɗin ba, sai kawai ta fice daga ɗakin Mukarram da ya samu ya karya yayi tamm cikin abincin da suka zo dashi ya rufa mata baya. …. Tana zaune har 10:22am, har sanyin AC ɗin ya fara mata yawa kafin Aunty Surayyah ta iso. Ilham tayi saurin miƙewa tana gaidata. “Oh kece, biyo ni office” ta wuce ciki bayan ta karɓi wasu takardu a wurin receptionist. Suna tafe Ilham tana ƙarewa cikin Organisation ɗin kallo. Ko ina fess ga shiru mai sanya nutsuwa da kukan tsuntsaye mai daɗi, sai ofisoshi da yawa a jejjere kuma a jikin kowanne akwai shuke-shuke da fulawowi, ga wasu matasan bishiyoyi da suka yi rumfa ma tsakiyar wurin ko ina abun sha'awa har suka shiga office ɗin Hajiya Surayyah mai ƙamshin daɗi Saboda turaren office na Bakhoor by Seemah(08021689184) da take yawan amfani da su. “Zauna Malama” ta bawa Ilham matsuguni bayan ta zaga table ɗinta ta zauna itama. “Ki sanar dani me yake tafe dake?” Ilham tana rawar jiki ta ciro takardun dake cikin envelope ɗin ta miƙawa hajiya Surayyah, ta saka hannu ta karɓa tana dubawa kafin Ilham ta fara mata bayani. “Daman yarona ne, sickler ne, ciwon nashi ya tashi sosai muna kwance a asibiti, kuma babu kuɗin magani Hajiya, alluran da ake masa ba zamu iya siya ba, shine nake roƙon tallafinnan da aka ce za'a bayar dan Allah a taimaka a saka damu, dan girman Allah Hajiya” ta saka hannunta daya cikin ɗaya tana ƙanƙan da kai cikin roƙo. Hajiya Surayyah ta nisa tana kallon Ilham, kafin kalmar da ta san Ilham ɗin ba zata so jin shi ba ya fito daga bakinta. “Kiyi haƙuri.” ``````` Seemahwrites ✨ . Chapter 10 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Arewapen & Wattpad @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 10… ƙirjinta yayi mummunan bugawa, a lokacin duk wani lissafi da ta gama haɗawa a cikin kanta na yanda abubuwa zasu yi mata sauƙi da take zaman jiranta a reception ya shiga warwarewa. Ta zame daga kujerar da take zaune tana tura shi baya domin ta samu isasshen wurin da zata sauƙa a kan guiwowinta yayinda hawaye suka fara gudu a saman fuskarta. “Hajiya don girman Allah. Na roƙe ki Hajiya dan girman zatin ubangiji..” ta shiga roƙo da magiya tana kuka shar-shar. Miƙewa Hajiya Surayyah tayi da sauri ta zaga teburin ta nufo Ilham dake roƙonta tana kuka kaman ranta zai fita. Ta yi ƙoƙarin ɗagata ta mayar da ita mazauninta na farko Amma yanda jikin Ilham ya ɗauki rawa ya ƙara bata tausayi. Kuma bata yarda ta miƙe ba, a ganinta idan ta miƙe kafin buƙatarta ya biya gani Hajiya Surayyah Kagarko zatayi kaman tana da wani zaɓin bayan wannan. Tabbas Hajiya Surayyah ta tausaya mata, kuma ta yarda da duk bayanan da tayi mata amma Ilham ba ita bace ta farko. Mata da suke cikin yanayi irin nata suna da yawa a faɗin Nigeria, kuma suna samun da yawa wa'inda suke zuwa gare su da ƙoƙon bara irin nata a kullum. Suna iya ƙoƙarinsu ne kawai amma sun kwana da sanin cewa ba zasu taɓa iya yiwa kowace uwa maganin damuwarta ba saidai su rage na ɗan wani kaso daga cikinsu, amma idan suka ce kukan kowacce uwa da ta tsaya a gabansu zasu share toh nauyin zai rinjayi kafaɗunsu ne, aikin su zai koma babu tsari kaman yanda aka saba yi a ƙasar, saboda dole su koma bangaren masu kawo koken su a maimakon wa'inda suka duba suka ga cancantar a basu taimako. “Malama Ilham tallafin da kike magana a kai yanzu haka rabo yayi nisa, tun ƙarfe 9 da rabi suka fara kinga babu yanda za'ayi in saka ki. Kiyi haƙuri zuwa wani jiƙon in sha Allah zan yi ƙokari na tabbatar kin samu” Gaba ɗaya gaban hijabinta ya jiƙe da hawayen da ke ɗiga a kai da kuma zufan dake tsatsafowa a jikinta kaman ba ɗazu ne take rawar ɗari a reception ba saboda AC “Hajiya ki dubi girman Allah, kaman yanda ya taimaka miki Hajiya dan Allah ki taimaka mana, Wallahi bani da yanda zanyi, na gama iya ƙoƙarina, abinda mara lafiyan zai saka a bakin shi ma wani lokaci gagara na yake yi”. Hajiya Surayyah ta lumshe idanunta. Duk lokacin da taji rayuwa tayi mata ƙunci ko kuma kaɗaici ya lulluɓeta irin wa’innan mutanen take tunawa taji sanyi a ranta “Shikkenan naji tashi” tace da Ilham, sai kuwa ta miƙe ɗin tana share hawaye don tayi tunanin ƙoƙon bararta za’a amsa. Ta koma jikin jakarta da ta shigo dashi ta zaro saɓɓin ƴan dubu-dubu guda biyu ta dawo ta riƙe a hannunta na hagu sannan ta miƙawa Ilham wayarta dake hannun dama. “Gashi saka min lambar ki, nayi miki alƙawarin da wani abu ya tashi ko ba irin wannan ba zan san yanda za'a yi a maƙala ki a ciki. Koda a cikin satin nan ya samu zaki ga kirana in sha Allah” Da alama ta ƙure gwajin sa'ar ta, kuma tunda ta ƙwanƙwasa ta sake ƙwanƙwasawa babu ƙara toh ba zata samu karɓuwa ba, daman Hajiya Surayyah alƙawarin sauraronta tayi mata jiya kuma ta saurareta ɗin. Sai ta ɗauki dangana ta rubuta mata lambar tana yi tana jan hanci, ta mayar mata da wayar bayan tayi saving da ‘Amina Usman Jen’. Dubu biyun da Hajiya Surayyah ta ɗauko ta mayar hannunta na dama sannan ta miƙa ma Ilham “gashi kiyi kuɗin mota, sai kinga kira na” Ta rage tsayinta kana ta saka hannu bibbiyu ta amsa tana zuba godiya kaman wanda ta bata dubu goma, hakan ya ƙara ma Hajiya Surayyah tausayinta, don saida ta rakata har reception suka sake sallama tana kallonta ta ɗauki laidan da kwanonta yake ciki ta rungume tare da purse ɗin da ta saka dubu biyun a ciki da kuma envelope ta sake musu godiya ta fita bakin hanya niman mashin, a ranta tana sarewa don ta san idan hidima suka sha kan hajiya Surayyah ba zata tuna ta kirata ba, ta bata tabbaci ne kawai don taji sanyi a ranta kuma taji ɗin, in sha Allah hanyoyin Allah da yawa suke. Khausar ta fara hangowa zaune a kujera da isarta pediatric ward ɗin, tana juya abu a cikin kofin roba tana magana da dariyar dake bayyana wushiryarta. A lokacin da idanunta ya shiga cikin na Ilham dake ƙarasawa jikin gadon su kuma sai ta taɓa ƙafar yaron dake zaune a saman gadon tana cewa “Muftee ga Mimin ka” Yaron yayi saurin juyowa ya kalleta a lokacin ta iso wurinsu tana ɗora murmushin dole a kan fuskarta. “Babana ka tashi? Ina kwana” “Mimi ina kwana. Jiya inata jiran ki har nayi barci Mimi” Ya ɗan kwaɓe fuska yana kallonta. Sai ta bishi da kallon tausayi, ga canular maƙale da ɗan hannunshi, ramar da yayi ya nuna har a fuska. Ganin ƙasusuwan ƙirjin shi kaman babu tsoka a zagaye da su kuma na yawan saka ta zubar da ƙolla. Amma yanzu sanye yake da tsohuwar rigan sanyin da ta siya mishi a gwanjo last year, dake shi ɗaya ne kacal kamar tsoka a miya saidai a cire a wanke yasa duk kalan rigan yabi ruwa. “Ina kwana Aunty Ilham” Khausar ta gaidata da faffaɗan murmushi a saman fuskarta. Ilham ta ɗaga idanunta daga kan Muftee ta dawo dasu zuwa ga khausar a inda take ganin kunun gyaɗa ne a cikin kofin don gashi fari tass. “Lafiya Aunty Khausar, yaya gajiyan ki? Na gode fah, na gode sosai Allah ya biya ki da gidan aljannah ya baki miji na gari” Khausar ta duƙar da kai a kunyace tana amsawa da ameen. Saida Ilham suka gaisa da sauran majinyatan dake ward ɗin suna gwada mata kayan alkhairin da aka ajiye musu niƙi-niƙi, wasu har sun fara tafiya da kayan abincinsu gida, tayi musu murna ta dawo jikin gadon yaronta. “Aunty Ilham ina kin samu muma sun saka mu?” Ta numfasa ta girgiza kai kawai, sai ta samu wuri ta ajiye kwanon da tazo dashi, ta zauna a gefen Muftee tana zura hannu ta cikin rigan shi taji ko jikin shi da zazzaɓi. “Ga abinci ko zaku ƙara ne” tayi maganar tana kallon Khausar wanda ta girgiza kai har yanzu murmushi bai bar fuskarta ba. “Da abun daɗi muka karya wanda In-law ɗinki ya kawo mana, ko Muftee nah?” Ta ƙarasa tana jijjiga ƙafar yaron, ya ɗan yi dariya mai sauti. Har cikin ranta Ilham take jin daɗin yanda Khausar take taya ta son Muftee, “iye, shine sirikin nawa bai tsaya mun gaisa ba?” “Ai ko shigowa bai yi ba Aunty Ilham, daga waje ya tsaya saboda yayi lattin zuwa wurin aiki. Amma yace da yamma zai dawo ya duba jikin Muftee ɗin” tace tana miƙewa da kofin hannunta ta ajiye, ta ƙarasa saman drawern asibitin ta dauko wata farar laida mai tambarin wani wurin shawarma ta miƙa mata. “gashi kema mun ajiye miki naki” Ta karɓi laidan ta buɗe tana leƙawa, ɗan gutsurin shawarma ne naɗe a cikin takarda, ga ƙamshin dake shiga hancinta yana sakata haɗiyar yawu don ta daɗe bata ci wannan abun ba. “har dani Aunty Khausar? lallai wannan siriki nawa dole inji dashi.” Ta ciro ta gutsura, daɗi yana ratsa duk wata kusurwa na bakinta zuwa jijiyoyin kanta har maɗiga, daman bata karya ba, dan haka ta koma gutsiran shi kaɗan-kaɗan kada ya ƙare da wuri, Khausar kuma tana baiwa Muftee kunun da ta samu ya huce a baki suna taɓa taɗin yanda abubuwa suka kasance a asibitin da kuma A&I. Ƙarfe sha biyu Khausar tayi mata sallama zata je tayi wanka, kuma zata kawo saurayinta ya gaida Ilham da yamma kaman yanda tayi mata alƙawari. Ilham tayi mata godiya sosai kuma taƙi barinta ta tafi saida ta karɓi kuɗin napep kuma ta biyata ɗari biyun da ta karɓa aro jiya, ya rage a cikin kuɗin da Hajiya Surayyah ta bata sauran naira dubu da ɗari uku. ….. Da misalin ƙarfe uku na yamma Hajiya Surayyah ta koma Medi-plus kai ma Abdulhameed abincin rana, Saboda saida ta koma ta dafa abincin da kanta, domin sa’ilin da ta koma gidan ta samu abincin da tace maman Hudah ta zuba na asibitin bata zuba ba. Haka ta yayyafa ma zuciyarta ruwan sanyi bata ko kulata ba ta ajiye mayafi ta shiga kitchen tayi jollof rice a gaggauce wanda yaji kifi da yawa sai kuma cabbage da Cucumber da ta yayyanka a ɗan bowl ta lulluɓe da farin laida. tayi wanka ta saka dogon riga da hijab sannan ta fita ta kai masa abincin. Yana zaune a kujera ya ɗora Ikram a cinyar shi yana riƙe da tab ɗin da take kallon Omar and Hanna da hannu ɗaya, ga hearing aids wato Na’urar taimakawa sauraro maƙale a kunnuwanta dukka biyu. ɗayan hannun shi kuma yana riƙe da wayan da yake ƙoƙarin rubuta saƙo. Bai san da shigowarta ba dukda tayi sallama, har saida Ikram ɗin ta taɓa shi ta nuna Aunty Surayyan sannan ya juyo ya dube ta. “Good Afternoon” yace da ita yana ajiye wayan. “Afternoon Abdulhameed, yaya mai jikin?” Sai ya leƙa fuskar Ikram yana tambayarta “How are you feeling Kiki?” Ta ɗago ta dubi Aunty Surayyah tana kwaɓe fuska. “Har yanzu da zafi hannun” “Kiyi haƙuri, zai bari a hankali.” Sai ta gyaɗa kai tana mayarda hankalinta kan cartoon ɗinta. “Yaya aiki Aunty?” Abdulhameed ya tambaya yana maido da hankalin shi gareta. Ta ajiye basket ɗin tana amsawa da “alhamdulillah, an gama rabon yau cikin nasara in sha Allah, sauran na gobe shi kuma babu yawa daman” “Masha Allah, sannu da ƙoƙari” Ta amsa da yauwa, ta zuba mishi abincin tare da ƴar shi a dalilin sun saba ci a plate ɗaya. Amma shi kaɗai yaci shinkafar, haka ya ɓata hannunshi wajen cire ma Kiki ƙayan kifin yana bata a baki, har saida ta koshi kafin yaje ya wanke hannunshi a sink ɗin toilet ya dawo ya saka spoon ma shinkafar da ta gama sanyi, da taimakon cabbage ɗin kai ya samu yaci da ɗan yawa. “Sun yi muku zancen sallama kuwa?” Aunty Surayyah ta tambaya bayan wani lokaci. “Yes, but I asked them to extend it. Na fi son sai jikinta ya ƙara kyau tukunna. Ki cika mun casual leave a office please” Ta cika mishi casual leave ta miƙa ma wane kuma tunda daman office dinshi ne suke processing?. Amma sai ta amsa shi da toh kawai suka cigaba da tattaunawa sama-sama har aka kira la’asar, da ya fita masallaci yin Sallah sai ta shiga da Kiki toilet ɗin ɗakin ta kunna ruwan zafi tayi mata wanka cikin kiyaye ɗaurin hannunta. Saida ya dawo bayan ta shirya ta cikin riga da wando baƙaƙe ta tufke mata gashin kanta sannan take sanar dashi zata wuce gida ta huta dan tabbas akwai gajiya a jikinta. Ta ɗauki basket ɗin da ta kawo abincin safe tana masa sallama, sai yace kawai ta bar abincin dare zai yi order, ya sake mata godiya. “babu komai. Allah ya ƙara sauƙi, saida safe” Har ta juya ya sake kiran sunanta. “An sama mata wata Nanny ne? Because when I resumed work zasu dinga tashi a school ni kuma ban koma gida ba.” Ta jinjina kai “za’a samu kafin nan in sha Allah. Criteria da ka zana ne kawai zai yi wahalar samun wacce ta cika shi duka, yawanci sai ƴammata dake zuwa daga ƙauye ake samu sai kuma Christian mothers” Ya girgiza kai “Kiki is still young Aunty Surayyah, akwai abubuwan da yaro ba'a koya mishi a makaranta sai a wurin uwa, Islamiyya karatu kawai zasu koya mata amma aiki da shi sai a gida, so idan na ɗauki Christian ba zata samu wannan ba. And sanin zafin yaro sai wacce ta haifa itama taji, I won't tolerate anyone maltreating my child please” Ta sani, shiyasa ya haƙura da nannies guda uku da aka taɓa samarwa Kiki. Ta farkon yarinyace da ba zata wuce shekaru 15 ba, tayi ƙoƙarin kula da ita sosai amma bata iya girki ba, kuma kikin ba komai take iya ci ba koda taje ta karɓo mata a cikin gidan, watarana ma sai ace mata babu. Gadan-gadan Ikram ta fara zabgewa ga yawan rashin lafiya shiyasa ya sallameta. Ta biyun kuma Christian ce da ta dan manyanta tana da wasu yaran ma. Saidai ba'a ɗora sati ba Aunty Surayyah taji Ikram tana kiran Jesus sama jesus ƙasa ko tuntuɓe tayi saidai kaji tace “Jesus!” A maimakon ta ambaci sunan Allah, ai Aunty Surayyah bata ma bari Abdulhameed ya fahimta ba ta sallame ta. Haka ma ta ukun da ya taɓa dawowa ya samu tana ɗaɗɗauke masa fuskar yarinya da mari wai ta zubar da abinci a ƙasa, kaɗan ya rage ta kwana a station, saida Aunty Surayyah tayi kaman zata je ƙasa tana roƙon shi kafin ya yarda ya haƙura. Shiyasa yanzu da yace baya son makamantan su ta fahimta. “Za'a cigaba da dubawa in sha Allah.” Ya sake yi mata godiya sannan ta buɗe kofar ɗakin ta fita. Bata bar haraban asibitin ba sai ga alert na 200k ya dira a account ɗinta. …. Ƙarfe huɗu daidai Khausar ta kira ta sanar ma Ilham suna ƙarasowa tare da saurayinta amma har wajajen biyar shiru. Haka ta canza ma Muftee kaya ta gyara wurin don yazo ya gansu fes-fes. Tana cikin waya da Maama ta hango fuskar Hashim yana tunkaro ta, Hashim da tun washegarin ranar da aka kwantar dasu bai sake tako kafar shi asibitin ba shine take hangowa sanye da kayan da ya fita dasu ɗazu da safe a jikin shi, bayan sa kuma Khausar ce riƙe da basket ɗin abinci. “Aunty Ilham” Khausar ta wuce shi ta ƙaraso jikin gadon da fara'a tana ajiye kwandon abincin a ƙasa. Gaban Ilham ya yanke ya faɗi!. Mijinta Hashim, da Khausar?... Kai ina?!. Tayi tsammanin duk wanda Khausar ɗin take soyayya dashi sananne ne a wurinta don Ahalin Baniza basa auren bare, amma tunda Khausar ɗin bata taɓa ambatan sunan shi ba hala bata san shi bane, ko itama zata yi irin na Taa ɗinsu da ya kafa record ɗin wanda ya fara auren bare kuma wata ƙabila daban lokacin da ya auro Maama, kuma daga kan shi ba'a sake ba. Muryar Khausar ne ya katse mata tunani “kinga na daɗe ko? ina ta tsaye ban samu abun hawa bane kuma ni bana hawa mashin shine na haɗu da Baban Muftee ya kawo ni” ajiyar zuciyan da tayi a lokacin ya ɗarsa mata kwokwanton kishin Hashim take yi ne dama? ko kuma kasancewar Khausar ce yarinyar da yake kulawa abin bai mata daɗi ba saboda kusancin da ke tsakaninsu?. Amma koma menene yanzu ta wanke mata zarginta daman ta san hakan da kamar wuya kawai shaiɗan ne yaso sakata waswasi. “Allah sarki. Toh ina In-law ɗin nawa?” Tace tana ɗaga idanunta daga kan Hashim don bai kula halittarta ba sai wucewa da yayi ya ɗauki Muftee a hannun shi yana masa magana. Khausar ta murmusa itama tana ɗaga idanunta daga kansu ta mayar kan Ilham. “Sai wani lokaci yace, yau ɗin wani abu ne ya taso masa” “Allah sarki. Toh Allah ya nuna mana” Ta amsa ta Ameen, sai ta matsa jikin Hashim tana saka Muftee dariya shima Hashim ɗin yana biye mata dukkan su uku suna ƙyalƙyalawa an bar Ilham rakuɓe a gefen gado kamar itace baƙuwa a duniyarsu. *Kabilar Jenjo* Ƙabila ce da ake kiran mutanenta da Jenjawa, ƙabila ce mai daɗaɗɗen tairhi wato tsohuwar ƙabila da ake samunsu ta yankunan arewa maso gabashin Nijeriya Musamman Adamawa da Taraba state. Masana na kallonsu ne a matsayin kabila mai tsohuwar al'ada da harshen kanta saboda sun mallaki yare da suke magana da junansu da ita. Ƙabila ce masu tarin zaman lafiya, sun kuma kafu ne ta yankin Karim Lamido LGA a karkashin karamar gari da ake kira JEN, Dukda akwai kauyuka da dama da jenjawa suke zaune tare da Yaruka daban daban kaman su Fulani, hausa da sauran kabilu. Kusan duka jenjo kusan kowa ya san kowa ne saboda yadda abubuwansu kan wakana a tsakaninsu kaman aure da sauransu, sannan sun kasu kashi uku akwai Christians akwai Musulmai akwai kuma masu bautan dodo. An fi sanin jenawa da Noma, kamun kifi, saƙa da kuma kasuwanci. Ana kiran yarensu da jenjo language ko a ce yaren jenjo. Suna da daɗin zamantakewa amma kuma mafadata ne wa’inda ba'a taɓa su su kyale, suna da haɗin kai ta yadda ko faɗa ne wani jenjo ya zo ya tarar ana yi da ɗan uwansa jenjo zai shiga sai an gama dambatuwa tukuna ya tambayi dan uwan me ya haɗa faɗan? Kowa ya san kowa saboda rashin yawansu hakan ya sa suke da kyamar aure daga waje ko wata kabilar a kokarinsu na kare harshensu da al'adarsu. ```````` Seemahwrites ✨ . Chapter 11 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites* *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 11…. Malam Mahmoud Ibrahim Baniza. Manomi ne wanda tun a zamanin samartakan sa ya gwada yana sha'awar noma, sai mahaifinsa Ibrahim Jen ya yanka masa fili a cikin gonan shi ya bashi iri a matsayin jarin da yakan bawa kowani ɗan shi idan zai fara sana'a ya duƙufa aikin gona. Da ya samu Allah ya saka masa Albarka sai gashi kaka tana zagayowa yayi Aure da ƴar maƙwabtansu mai suna Amina. Watan Amina tara cuss a gidan shi ta haifa masa ɗa namiji wanda yaci sunan mahaifin shi Ibrahim, wata shekarar tana sake zagowa ta sake haifan Namiji mai suna Umar. Ganin bajintan da Mahmoud yayi a ranar sunan umar ya kusa yafi wanda yayi a haihuwar Ibrahim ya sanya ƴan suna tsokanarta a lokacin da suke ɗaga zannuwan da ya kawo mata cikin sabon akwati haka ma kayan jariri. “Amina Allah ya sake dawo damu baɗi muga abin arziƙin da yafi wannan kinji?!” Shine abinda ƴan gidan su Mahmoud da sauran abokan arziƙi suke faɗa tana murmushi daga ƙuryar gado. Saidai koma bakin su ne ya kamata bata sani ba Amma ba'a rufa shekara ba ta sake haihuwar ƴarta mace wacce suka sakawa Sahura, saidai daga haihuwarta lafiya ya gagari Amina. Haka suka dinga ziryan asibiti daga Jen zuwa cikin taraba kuma tayi jinya sosai kaman ba zata tashi ba har saida ta koma gidansu. Mahmoud kuma Ya kaiwa mahaifiyar shi Sahura ruƙon yaran a lokacin, a ganin shi ɗawainiya ne zai yiwa iyayen Amina yawa idan ya ɗebi yara har uku ƙanana ya kai musu bayan suna fama da jinyar ƴar su, sai gashi ƴan uwa sun saka shi a gaba da zuga na ya ƙara aure ya samu wacce zata riƙe masa yaran da amana, mahaifiyar su girma ya kamata ba zata iya raino ba. Da ƴar ƙanwar mahaifiyar shi aka haɗa su mai suna Dijengala. Suka saka auren wata guda kacal daman iyayen Dijengala a shirye suke su mata aure miji kawai ake jira kuma an samu. Amma Mahmoud ya rasa yaya zai yi ya sanar da Amina da iyayenta. Kullum idan yaje dubata sai ya buɗi baki zai yi maganar auren, idan yaga yanda take kallon shi cikin azaban ciwo tana cije baki rike da cikinta ko tana washh sai yaji ya kasa. Saida za'a shiga satin bikin da yaga babu sarki sai Allah yake faɗa mata. Bata ce komai ba har ya tashi ya tafi amma ranar ɗaurin aure a asibiti yayiwa Mahmoud saboda Amina da akewa aiki a ciki. Kuma daga nan shikkenan ta fara samun sauƙi a sannu. Dijengala bata haura wata biyu a gidan ba ma Amina ta dawo kan yaranta don jikinta yayi kyau sosai. Haka akayi zaman da daɗi da dambe sai gashi Amina ta sake samun wani cikin, Dijengala shiru, Amina ta haifi ɗanta namiji da suka sakawa Usman. A ranar suna, wannan karon ba Mahmoud bane yayi bajinta, saboda ƴan kuɗaɗen shi sun ƙare a kan auren Dijengala da kuma rashin lafiyan Amina. Kayayyaki aka kawo masu kyau da tsada tun daga garin kano. Sai a lokacin itama Amina take jin cewa ashe ma wani Alhaji dake siyan amfanin gonansa yayi wa takwara, shine yaji daɗi ya zuba musu kaya haka harda kuɗi ya baiwa Mahmoud kyauta. Abinda ya tsayawa Dijengala a rai kenan bayan watanni itama Allah yasa ta samu ciki, tun daga nan ta duƙufa da addu'ar Allah yasa namiji zata haifa kuma da ta haifa ɗin saida ta tursasa Mahmoud ya sanya mishi Usman shima, amma abinda take nima ɗin bai samu ba don kafin saƙo ya kaiwa alhajin tafiya ta kama shi kuma bai dawo ba sai bayan watanni huɗu. sai ya zamo Usman sun yi biyu a gidan kuma suna linzami idan ka kira kowannen su zai amsa, don haka aka koma cewa ɗan Dijengala Ussy. Da Amina ta sake haihuwar mace Halima sai ta rufe haihuwa saboda yanayin jikinta. Dijengala kuma ta ƙara da Rabi'u wanda ake kira da Rabe sai Aliya da Laweeza. Rasuwan mahaifin Mahmoud ya kawo zancen rabon gado wanda a ciki harda gonan da Mahmoud ɗin yake samun abinda yake ci da iyalansa ya biya sauran bukata na rayuwa, kuma yana da ƴan uwa da yawa, har su 17 a wurin mahaifin su. Suka yanke shawarar kada a siyar da gonan, a barshi ma Usman yana biyan su kuɗin haya amma sai yaƙi amincewa gudun matsala da ɗaukan hakkin wa’inda zancen bai kwanta musu ba danne su aka yi. Aka ɗauki gona aka sayar aka bashi rabon shi na gado ya nausa Kano wurin Alhaji Usman niman arziƙin shi a can. Kaman da wasa ya fara gini a Jakara a filin da uban gidan shi Alhaji Usman ya siyar mishi daga gefen gidan shi, ya dawo da iyalan shi ciki. Lokacin da Alhaji Usman zai tashi a Jakara ya koma sabon ginin da yayi sai Mahmoud ya shawarci ƴan uwan shi da suke ɗaki ɗaya da su haɗa kuɗi su sayi gidan sai su dawo kano da zama su shiga harƙan kasuwanci. Suka aminta da zancen ganin yanda shima samun shi ya ƙaru don haka suka tattaro ƙwan su da ƙwarƙatan su suka dawo gidan da aka san shi da gidan Baniza a yau. Kuma har suka kafu a garin Kano yaransu suka girma suka mallaki hankalin kansu basu taɓa bari wani bare ya shiga cikin zuriar su ba, sun gwammace su koma Jen su sama ma yaran su abokan rayuwa. har manyan ƴaƴan Malam Mahmoud suka yi aure aka zo kan Usman a wannan tsarin ake. Usman ya fito ya shaida musu akwai wacce yake so Jamila kuma bafulatana ce, a ranan irin marukan da ya ɗiba a wajen mahaifiyar shi Amina saida ta kwana tana ciwon hannu. Amma dake soyayyar tazo da zafi sai gashi ya tubure a kan ra'ayinsa babu shiri aka nimo yarinya a dangi mai suna Aisha aka aura masa sai shiga ɗakinsa kawai yayi bayan ya dawo daga interview ɗin niman aiki yaga mace a lullube. Fatattakan Aisha yayi waje ya rufe ƙofar shi ya kwanta haka aka dinga bugawa Sahura da sauran ƴan uwan shi suna sababi ko a jikinsa har suka gaji suka kama Aisha dake kuka wiwi suka mayar da ita ɗakin mahaifiyar shi. Saidai abu kaman almara sai gashi cikin ƙanƙanin lokaci Aisha ta fara tara masa zuri'a, ta haifa masa Abubakar, Iman, Ahmad sai Aliyyu daga nan ciwon ƙoda ya sakata a gaba kafin Allah ya ɗauki ranta bayan ta Haifi Amina wacce akewa laƙabi Ilham da shekaru biyu. Sosai mutuwar Aisha ya taɓa Usman, daman shine mafaɗaci fiye da ƙanin shi Ussy don shi babu ruwan shi Rabe nema yake taɓa rashin ji. Amma haka ya dawo sukuku abin tausayi kaman shima maraicin yake yi tare da yaran shi. Bai sake dawowa cikin zaamar shi ba saida ƙaddara ta sake haɗa shi da Jamila a shagon yayan shi Umar tazo siyan yadin Hijabi shi kuma yaje shan iskan yammaci a wurin. Daga nan suka sake jamewa, musamman da yaji duk bayan tsawon lokacin nan bata yi aure ba, sai yake ganin kaman sanadin shi ne hakan ya faru don duk shi ya kora mata maneman ta. Aka tada tsohon zuma ya sake mata alƙawarin aure wanda ta jishi ne kawai amma ta san abu ne da ba zai yiwu ba. Usman ya samu magabatan shi da zancen Auren Jamila don mahaifin su ya rasu a tsakanin nan. Daga farko basu aminta ba suma amma ganin yanda ya matsa yasa suka ce yaje ya nemi amincewar Mahaifiyarsa. Dake matar Mutum kabarin shi, Jamila ta shiga ɗakin Usman sai dai ba na gidan Baniza ba, Bayan sharaɗin da suka kafa mishi na cewa bayi da matsuguni a gidan har sai ranar da ya rabu da Jamila. Bayan auren ko gaida mahaifiyar shi yaje yi sai ta juya ta bashi ƙeya ya gama bada hakurin shi ya tashi ya tafi, takwaranta Ilham ma da ta samu labarin Jamilan ta karɓeta zata riƙe tace a daina kawo mata yarinyar. Saidai ganin shekara ta zagayo babu alamar Usman zai saki jamila sai ma tsohon ciki da take dashi yasa mahaifiyar shi yanke shawarar ta saka shi ƙara aure da ta bar Jamila tayi nasara a kan su, suka aura mishi Shafa’atu. Bai so Shafa kaman yanda ya samu kansa da son Aisha ba saboda bata da hali, amma haka yake haƙuri da ita alfarmar mahaifiyarsa da take ci. Da Jamila ta haihu sai ta zaɓi ta sanya ma yarinyarta suna Ihsan don ta faranta ma Usman Saboda ta lura mahaifiyar Ilham duk sunan yaranta mata daga I ya fara na maza kuma daga A. Shafa ganin ta fara haihuwa da yara maza sai kanta ya ƙara faɗi, ɗanta na farko aka saka mishi Mahmoud shiyasa ake kiranta da maman baba, a lokacin da Jamila wato Maama kaman yanda yara suke kiranta ta haifi ƴarta na biyu wanda taci suna Islam shima namiji shafa ta sake haifa, sai a haihuwa na uku suka yi kunnen doki wajen haihuwan maza dukkan su, yaron Maama yaci sunan mahaifinta Ahmad amma dake akwai wani ahmad ɗin a gidan sai ta zaɓi ana kiran shi da Jawad daga nan haihuwan ya tsaya mata. Khausar kuma ƴar kawu Rabe ne ƙanin mahaifinsu da suke uba ɗaya dashi wato ɗan Dijengala, so cousins suke da Ilham da Hashim. samun aiki da babansu yayi a wani kamfani a kaduna yasa ya tattaro iyalansa daga gidan Baniza ya dawo dasu kaduna sai gashi sun zamo ma Ilham zallan ƴan uwan da take dasu a kurkusa dukda ma su khausar ɗin sun jima a nan. ***** “Aunty Ilham bari na tafi, sai gobe ko jibi zan dawo” muryar khausar ɗin ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula. Cikin sanyin jiki tace “toh Aunty khausar nagode” Ta langabar da kai “ayyah babu komai fah” “Ki gaida su mama” ta miƙe zata raka ta sai taga Hashim ma ya juya zai tafi. Ta bude baki zata yi magana yayi saurin katseta da “zan ajiye ta ne in wuce gida in huta, tasowata kenan daga aiki na gaji” Abinda ya ƙara bata mamaki shine basket ɗin da Khausar tazo dashi sai gashi ta ɗauka zata tafi dashi. “Daman kada Mu bari a jikin mashin ne mu koma mu samu babu shiyasa muka shigo dashi, amma zan kawo miki naki gobe Aunty Ilham, wannan na yaya Hashim ne ya kira maman mu yace a zuba mishi yana jin yunwa” ta koro bayani kaman wanda aka tambaye ta. “Muje da’alla muna ɓata lokaci” cewar Hashim yana ciki-ciki da murya kaman wanda yayi ajiyan miliyoyi a asusun bankin sa. Ilham Sai ta hangame baki kawai tana kallon bayan su yanda suka jera kafaɗa da kafaɗa har suka bar ward ɗin. ````````` . Seemahwrites ✨ Chapter 12 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites* *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 12…. A wurin da suka yi parking Khausar ta tsaya tana saka hannu biyu ta riƙe basket ɗin da kyau kada kwanukan su tankware abun ciki ya zuba. Hashim ya zura key yana buɗe kan fara mayyan shi da ya rufe kada brothers ɗin da suka fishi so suyi mishi gaba da ita. “Amma Ya Hashim ka sa naji kunya yau” “Koh?” Ya ɗago ya kalleta da murmushi a saman fuskarsa sannan ya mayar da hankali akan abinda yake yi. Cikin muryar da ta ƙara matseta saboda yanga ta cigaba da cewa “wallahi ƙirji na sai bugawa yake yi har muka fito, naji tsoro sosai” Miƙewa yayi yana gyara zaman rigan jamfan shi da wadataccen murmushi a kan fuskarsa “tsoron me kuma? ba ita tace miki tana son ganin saurayin ki ba? Toh gani nazo mun gaisa” ya hau ya kunna mashin ɗin ta ɗauki diri sannan yayi mata alamu da kai tazo ta hau. Ta taka a yangance ta miƙa masa basket ɗin, a wurin karɓa ya haɗa da hannunta da gangan. Duk da tayi saurin janyewa amma ya riga ya ji abinda yake son ji. Laushin hannunta. Laushin da babu irin shi a hannun Ilham, don zai iya rantsuwa nashi hannun yafi tata taushi tsaban surfe da wankin jama'a da ta ɗaura ma kanta ana bata canjin da bai taka kara ya karya ba. “Yaya Hashim mana!” ta turo baki cike da shagwaɓa tana mishi hararar wasa. Ya lashe leɓen bakin shi yana dariya mai sauti “watanni nawa ne suka rage yarinya? Kinga hau mu tafi in mayar dake wurin mama lami lafiya.” Dake makirci ne abun dama sai ta dafa kafaɗan shi da hannu ɗaya ta hau, suka juya suka hau titi suna hirarsu ta soyayya babu ma wanda ya sake tunawa da wata Halitta mai suna Ilham a cikin su. Ita kuwa tana ciki tana tunanin yanda zata fidda wando ta ka, bata yi tsammanin Hashim zai shigo har asibitin ya fita ba tare da ya basu ko sisi ba. Ƴan canjin hannunta daga sayi Detergent sayi bleach ya dawo sauran Naira ɗari takwas, ta kasa haƙuri saida ta siya ma muftee ayaba da lemu na ɗari uku a bakin asibiti ya ci ya ɗan samu kuzari a jikinsa. Amma sai gashi zuwa dare zazzaɓi ya rufe shi, dole ta siya mishi paracetamol ta bashi, tana zaune tana kallon yanda ƙirjin shi yake ɗagawa yana sauƙa a hankali bayan ya samu barci hawaye suna bin kumatun ta. Ji take yi kaman ƙaddara ta katangeta a wani ɗaki mai tsananin duhu da babu wani taga da haske zai shigo ko kuma ƙofar da zata buɗe ta kuɓuta. Ji take yi kaman zata ƙare rayuwarta ne tana lalume a cikin wannan duhun har mutuwa tazo ta risketa. Amma muftee take tausayi, shine a ranta shiyasa ta kasa hakura ta daina lalumen. Ciwon shi ba na warkewa gaba ɗaya bane, dukda babu cutar da Allah ya sauƙar a duniya ba tare da ya fara sauƙar da maganinta ba. Amma ilimin na cutar sickler har yanzu bai gama bayyana ba, kuma ma bata da halin da zata fita tayi fafutukar niman shi. Kuka tayi sosai ta bai wa uku lada, tana danne nadamar da yake tasowa daga ƙasan zuciyarta. Nadamar da shaiɗan yake saka mata na haihuwar Muftee. Amma nadamar komawa gidan Hashim bayan sakin da yayi mata a shekaran auren su na farko bata yi ƙokarin yaƙi dashi ba. Wataƙila da yanzu akwai wani ɗan haske a rayuwarta ko yaya ne. ….. *2:40am* ABDULHAMEED “Turn around dear” A hankali ta juyo ta saka fararen idanunta da baƙin cikin su ke ƙyallin hawayen da suka gama zuba daga ciki a cikin nashi. Ya sakar mata murmushi mai taushi, ya saka hand shower da yake riƙe dashi ya ɗauraye mata kumfan jikinta. Saida ya tabbatar ta wanku tass sannan ya ciro pink towel ɗinta dake rataye a hangern banɗakin ya naɗeta a ciki kana ya raba ta da ƙasa suka koma cikin ɗakin tana kwance a kafaɗarsa, ya kwantar da ita a saman gadon da ya sauyawa bedsheet ya sake rufa mata ƙaramin blanket ɗinta saboda sanyin da daren ya saka. Dake barci ba isarta yayi ba daman babu ɓata lokaci ta mayar da barcin, sai ya koma toilet ya ɗauraye kayanta da zanin gadon da kashin da tayi a jikinta ya ɓata su sannan ya jiƙa su a cikin ruwan comfort ya fito. Lokacin har ƙarfe uku da rabi na dare ta gota amma haka ya fita sanar da nurses ɓacin cikin da Kiki ta samu saboda suyi mata abinda zai magance shi kafin ya galabaitar da ita. Tare suka dawo ɗakin da Nurse dake ɗauke da tray ɗin da ta ɗora alluran da za'a yi ma Kikin da kuma ruwan da za'a ƙara mata. Ba don ran Abdulhameed ya so ba ya sake tashinta daga barci a lokacin da zai saka mata riga kafin a ɗaura mata drip, kuma saida tayi kukan da yaji kaman ya taya ta a lokacin da ake saka mata Canular. Ya san ba zai iya mayarda barcin ba sai ya ɗauro alwala yazo ya fara gabatar da nafila kaman yanda Mahaifiyar Kiki ta shawarce shi da yi a lokacin da damuwa yayi mishi yawa. Yana kan darduma har gari yayi haske, sai a lokacin kuma ɗan nutsuwar zuciya da ya samu da kuma ganin Kiki bata sake farkawa ba ya baiwa barci daman zuwa ya sace shi. Da tunaninta a ran shi ya rufe idanunsa, don haka yanzu ma ita yake gani, ita yake gani tana murmushi kaman bata da wani damuwa a duniya. Sai tayi mishi nuni da takardar da ta ajiye masa tare da biro a saman desk ɗinsa, ta shiga yi mishi bayanin da bai fahimta ba da hannu. Amma ganin sunaye da yawa rubuce a saman takardan yasa ya fahimci nashi sunan take son ya rubuta. Sai ya juyar da kan shi ta daya gefen ya sake kwantar da kanshi a saman desk ya bata ƙeya. zafin da yaji a bayan ƙeyar tashi yasa shi saurin dagowa tare da fitar da sautin “Ah” yana sosa wurin, sai a lokacin ya lura da plastic ruler dake hannunta. Ta tamke fuska irin babu wasa ɗinnan tana sake nuna mishi takardan da rulern da take riƙe da shi. Sai kawai ya miƙe tsaye a kan ƙafafun shi ta gane tsayin su ba ɗaya bane don ya lura ta zo da raini. Daga nan kaman wanda yake kallon film a TV haka scene ɗin ya ɗauke zuwa wani wuri daban amma gata tsaye a gabansa. Saidai a maimakon murmushi hawayene ke bin kumatunta tana kallon nashi ƙwayan idanun cikin wani yanayi. “Please Abdulhameed, Please!!!” Ta riƙo hannunshi na dama cikin nata biyu tana magiya. Ya ɗaga idanunshi daga kan fuskarta don ma kada ya fahimci abinda take nufi zuciyarsa ta cigaba da karyewa sannan ya kwace hannun shi daga ruƙonta. “Please Go Ikram” ya faɗa ba tare da ya kalleta ba tunda yanzu ta warke ya san zata jishi. Sai ta shiga dukan ƙirjin shi da hannayenta tana kuka mai gunji, dukan da yake jinsa kaman a kan zuciyarsa take yi kai tsaye. Hannunta ɗaya ya riƙe ya juyo ya kalleta da idanunsa da suka fi gauta jaa sannan cikin kaushin murya yace “Nace ki tafi! Bana son ganin ki” Bai rufe baki ba ta ɗauke shi da mari da ɗaya hannun. “Allah ya Isa. Allah sai ya saka mun Abdulhameed. I hate you!” Buɗe ƙofar da akayi yasa ya buɗe idanunsa, ya sauƙe su a kan Aunty Surayyah da ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama, hannunta riƙe da basket ɗin abun karyawa da kuma jakan ƙarin kaya da yace a kawo musu tun jiya don ba zai na iya barin kiki ita kaɗai ya tafi gida wanka da shiryawa ba, kuma Aunty Surayyah da yake ganin zai iya aminta ya barta jikin Ikram aiki yayi mata yawa. Ya amsa mata yana miƙewa tsaye ya duba Ikram ɗin. Aunty surayyah da itama hankalinta ya koma kanta ganin ƙarin ruwa a hannunta yasa ta taɓa shi ya juyo sannan take tambayan shi abinda yake faruwa. “She got sick last night, kinga da mun tafi gida da bansan halinda zata shiga ciki ba kafin mu dawo” Ta jinjina kai cikin yarda da zancen shi sannan ta tofa ma Kikin addu'a don shine kawai abinda zata iya mata a halin da ake ciki. “Yaya zancen Nanny? An samu?” shine tambayar da yayi mata na gaba damuwa bayyane a yanayin shi. “Nayi magana ana kan dubawa, kafin satin ya ƙare in sha Allah za'a samu, kada ka damu” Ya jinjina kai sannan suka mayar da akalar zancen su ya koma kan aiki, har zuwa lokacin da aunty Surayyah tayi masa sallama zata tafi office, sai a lokacin Ikram take farkawa, ya saka musu abincin suka ci tare bayan ta gama kukan ɓacinta. ….. Saida ta duba ta tabbatar sauran Shinkafar bata ɓaci ba sannan ta bawa Muftee ya ci, tare da kunun da ake basu sadaka kullum da safe, don haka ta tafi da ɗan nutsuwa a ranta saboda yana ƙoshe, Inda ta hau mashin da sauran canjin ɗari biyun hannunta, suka yarda suka kaita gida da ƙyar da magiya a kan farashin. Kamar kullum Hashim yayi ɗai-ɗai da gidan, ga kulolin da khausar ta kawo masa abinci wanda ya cinye sauran da ya rage kafin ya fita aiki ya bar mata kwanukan a wurin da ƙasusuwan da ya tattaune su har ɓargo ta tattara masa. Ta gode ma Allah ma da bata same shi a gidan ba, don haka cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ta shiga tattarawa ta share ko ina tayi wanke-wanke da sauran Omon da tazo dashi daga asibi ta ɗan rage wanda zata yi wanka don bata samu na wanke banɗaki ba ma ga wari da zarnin fitsari da yake yi, sai ruwa ta sake zubawa ta wanke da tsintsintsiya, ta ci Sa'a ma da yau bai yi mata ajiyan da ya saba a cikin seater ba. Bayan tayi wanka ta ɗauro alwala tazo tana gabatar da sallan walha dukda lokacinta har ta kusa ƙurewa, ta cigaba da roƙon Allah ya kawo mata mafita a cikin kowani hali. Ta miƙe tana naɗe darduma saboda ta san nayi, yanda za'ayi ta samu kuɗin da zata yi abincin da zata tafi musu dashi asibiti, don ta ƙudura a ranta ko tayi ba zata ajiyewa Hashim ba. Wayarta ne ya shiga ruri. Ta duƙa da darduman a hannunta ta ɗauka a ƙasa tana duba sunan mai kiran. ‘Yaya Haidar’ ta gani kaman yanda tayi saving. Sai ta latsa madannin amsa kira ta ƙara a kunnenta tare da sallama. “A jifa’en Yaya Aliyyu (ina kwana yaya Aliyyu)” ta gaida shi. “Fidela wai ke kika ce yaran nan su zo? Kina fama da majinyaci zasu ƙara miki wani nauyin iye?” Ya fara da tuhumar ta yana share gaisuwan da tayi mishi. Tayi saurin Amsawa da “Eh Yaya, saboda hakane ma nace Filiyan tazo, yanzu ma da zan dawo gida yin wanka babu kowa a jikin shi” Tana jin yanda ya sauƙe ajiyan zuciya, daman yaya Aliyyu ba dai zuciya da faɗa ba, halin mahaifinsu gare shi sakk, don har tayi aure tana matuƙar Shakkan Taa, shiyasa take mamakin yanda a lokacin baya A Moher ɗinnan yake iya aikan yaya Aliyyu siyo sigari kuma ya je. “Toh Islam kam damuwa kawai zata zama miki, Ihsan ɗin tazo ita kaɗai” Ta kwantar da murya “Allah sarki Yaya nayi kewar su ne wallahi.” “Ai zaku zo taron shekara nan bada jimawa ba, zaki ganta a sannan, idan kika matsa kuma Ihsan ɗinma sai tayi zamanta” Jan bakinta tayi ta saka mishi sakata, sai shine ya sake cewa “ki tura min account numbern ki in saka miki abinda ya samu, sai a cigaba da haƙuri har zuwa lokacin da Allah zai ƙara buɗa mana.” Haka yake, yana da wannan ƙokarin na taimaka mata da abinda Allah ya hore mishi lokaci zuwa lokaci, ba kaman sauran yayyenta biyu ba da ko kiranta suka gani basu ɗauka, koda gaisuwa ne kawai tunda sun gaji da roƙonta, kuma Yaya Aliyyu ba aiki yake yi ba saidai buge buge, duk da ya samu ya kammala degree ɗinsa da kuɗin gadon da suka samu wanda ita nata ya ƙare a jikin jinyar Muftee don karatu ya daɗe da fita daga cikin lissafinta. Kaman tace masa Opay ne saboda bata da ko katin tura masa saƙo amma gudun ɓacin ransa sai ta shiga godiya sosai cikin farin ciki da jin dadi. Bai amsa ba ya katse wayar daga ɓangaren shi dan haka da sauri ta fita ta shiga makwabtan su ta karɓi aron waya ta tura masa. Tayi tunanin dubu biyu dubu ukun da ya saba zata gani amma sai ga alert ɗin har naira dubu biyar. Bata san tayi tsalle ta dire a wurin ba saida matar da ta bata wayan take tambayanta menene sannan ta shiga godiya ma Allah ta labarta mata itama ta taya ta murna sannan ta shiga ta siya katin ɗari uku daga cikin account ɗin wanda suka kwashe dari biyun da suke binta bashi a take ya koma sauran ɗari. Ta danna kiran yaya Aliyyu dominn tayi mishi godiya amma har ya gama ringing bai ɗaga ba. Sai tayi godiya wa matan ta tafi shagon dake kusa dasu tayi masa transfer ɗin sauran kuɗin, idan ya cire kuɗin da yake binta bashi sai ya bata sugar da maggi, omo, manja da mangyaɗa ya bata sauran canjin. Sai gashi kuɗi ya koma dubu uku dukda ma bai karɓi charges ba. Ta bi ta sayi busashshen tattasai da tumatir domin fresh ones yafi karfin ɗan talaka a yanzu, ta haɗa da ɗan nama na ɗari biyar a wurin mai tukubar unguwan saboda muftee da ya daɗe bai ci naman ba har yana ce mata wai haƙorin shi na ƙaiƙayi. Sai gashi dubu biyar ta koma dubu ɗaya da ɗari biyar. Amma nauyin laidan da ta shiga dashi gida da nutsuwar da zuciyarta ya samu ya biya. Don haka tayi musu tuwon gari miyan kuka mai lafiya da nama kuma gobe in sha Allah taliya da miya zata yiwa Muftee. Da azahar ta koma asibitin ta bashi abincin yaci da yawa kuwa domin yayi mishi daɗi, sai taji ta ƙara samun ƙwarin guiwar cigaba da fafutuka saboda farin cikin yaronta. ….. Bayan kwana biyu aka sallami Ikram daga asibiti har ma an cire mata cast ɗin hannunta don shima da sauƙi sosai. Ya kasance ranar Alhamis ne, Abdulhameed ya fito ɗauke da ita a kafaɗa, ɗayan hannun shi riƙe da jakan kayan su, Aunty Surayyah na biye da sauran shirgin su har jikin mota inda ya saka Ikram a back seat ya saka mata seatbelt, suka zuba kayayyakin a booth sannan ya shiga gaba Aunty Surayyah ta shiga mazaunin driver suka dauki hanyar zuwa gida. “Yauwa zancen Nanny ɗinnan…” ya fara magana sai ta bashi hankalinta da ta raba da tuƙin da take “... Wanda kika yi zancenta, mai yaro mara Lafiya, a ɗauke ta indai zata iya” ```````` Seemahwrites ✨ . Chapter 13 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites* *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 13…. “However, A faɗa mata bana son wasa, bana son fashi, bana son latti, bana son ƙazanta and I absolutely don't tolerate anything that will harm my daughter, kada tayi saken da ko ƙwaro ne zai cije ta under her watch.” Da zuciyar shi ɗaya yayi maganan amma sai ya ga Aunty Surayyah tayi murmushi tana gyaɗa kai. Da ace Abdulhameed kaman sauran maza yake haka ma Kiki kaman sauran yara take, da ta faɗa mishi duniyan nan gabaki ɗayanta ƴar haƙuri ne. Abinda yake nima a wurin Nanny da babu abinda ya haɗa ta da ƴar shi bayan albashin da za'a dinga biyanta duk wata, ko uwar da ta tsuguna ta haifa masa yarinyar ba zata iya ba. Amma sanin wanene shi da irin gwagwarmayar da yayi a rayuwa tun da ƙananun shekarun shi yasa zata cigaba da mishi uzuri ta bi shi a yanda yake har lokacin da komai zai wuce kaman bai taɓa faruwa ba. “Yaushe zata fara zuwa?” ya tambaya lokacin da suka yi parking a gaban ɓangaren shi, ya sake ɗaukan Kiki a hannun shi wanda iskan mota yasa ta koma barci. “Ban kirata ba tukunna, na fara niman amincewar ka ne, but I'll call her now” “Okay, thank you so much Aunty sharmama” Bayi gajiya da mata godiya, kuma yana jin kamar duk godiyan da zai yi mata bai isa ba, don haka zai cigaba da mata godiyan ne koda hakan zai nuna mata irin darajar da take dashi a idanunsa. “Babu komai” tace tana juya kan motan ta koma office. Kwana huɗu kawai amma sai yake ganin gidan yayi mishi ƙura sosai. Ya kwantar da kiki a kan gadon shi sannan ya fita zuwa store ɗin kitchen ya ɗauko tsintsiya da mopper. Babu ɓata lokaci ya shiga yin shara, ya ƙwalƙwalo ko ina ya zuba dettol a ruwa yayi mopping, ya bi ya ɗauko napkin ɗin goge-goge. Ko ina shiru, duniyar shi ta riga da ta saba da wannan shirun, don ya manta da yanda hayaniyarta yake baki ɗaya. Amma yanzu tunani daban-daban ne suke karakayya a cikin kan shi, saboda kwanan nan yana yawan mafarkin Ikram da tunaninta. Ikram mahaifiyar ƴar shi Ikram kaman yanda ya mayar ma abinda ta haifa sunanta saboda hakan ne kawai daidai. Ya kwana biyu yana Tunanin gaskiyar da ba kowa ya sani ba bayan su uku, sai kuma Ubangijin da ya halicce su duka. Ya kuma ɗau Alƙawarin ba zai taɓa bari Kiki tayi rayuwa irin ta mahaifiyarta ba. Zai yi iya ƙoƙarin shi a matsayin shi na uba wajen ganin ya kareta daga dukkan cutarwa. Kafin wani lokaci ko ina yayi fess sai kamshin air fresheners dake tashi. Yayi musu ordern abinci, ya koma ɗakin shi da Ikram ke kwance ya shiga bathroom yayi wanka da ruwa mai zafin da ya narka duk wata gajiyan dake tattare da shi kana ya shirya cikin navy blue shirt da dogon wando fari tass. Tunanin yanda Kiki zata ɓata mishi wandon da abincin da zata ci yasa ya canza ta zuwa gajeren wandon khaki, in yaso idan suka gama sai ya cire ya mayarda wanda yayi niyyan sakawa tun farko. Da abincin ya iso saida ya jirata ta tashi da kanta lokacin ma biyu ta gota. Da yunwa ta farka kaman wanda aka yiwa yasa a ciki, kuma saida ya yanka mata apple taci bayan ta karya kafin su baro asibitin, sai suka fita dining ya fara bata abincin a baki kafin ya shiga da ita ya wanke ta tass itama. Daɗewan da yayi bai koma jikin wayan shi da ya ajiye ba yasa yaci karo da saƙonni barkatai lokacin da ya ɗauka. A ciki har da missed calls guda biyu daga wani number da yayi saving da “Excellency” A take yanayin fuskar shi ya sauya. ….. Zaune take a waje da sanyin safiya, tana wankin kayan shi da ya gaji da ganinsu a zube ya siyo sabulu ya bata, sai gashi yazo zai kunna mashin ɗin shi zai fita daga gidan ba sannu ba madallah, ko kallo bata ishe shi ba, don kallon nata ma ɓacin rai yake ƙara masa. “Baban Muftee” Ta miƙe tana tsane hannunta daga ruwan kumfan. “Yaya akayi kuma? Kina ganin dai wurin aiki zani ko!” Ya tambaya yana muzurai kada taga daman tambayan shi wani abu ganin ya sayi sabulun wanki. Shima yanzu haka kuɗin yake nima, da zata bashi karɓa zai yi yayi mata godiya, dan albashin ya ƙare tass tun wata bai je ko ina ba saboda hidiman da ya saka a gaba. Sai ta sunne kai tana mutstsuka hannun nata cikin fargaba tace “Daman Filiyan ce zata zo mun gobe” Yamutsa fuska yayi “wacece Filiyan?” ya tambaya kaman da gaske bai sani ba. “Ƙanwata Ihsan” ta bashi amsa. “ƴar Jamila?” Gyaɗa kai tayi amma bata amsa ba, don yanda Maama take mata matsayin uwa, kuma ta riƙi ɗan shi a matsayin jikar ta, ya kamata ace ta samu girmamawa daga gare shi. “Toh yanzu niman izini kike yi ko kuma sanar dani kike?” “Ɗan zaman asibitin ne zata taya ni na wani lokaci tunda bamu san zuwa yaushe zasu sallame mu ba.” “Idan dai izini na ake nima toh ban yarda ba, idan kuma gidan naki ne ai sai tazo mu gani Ilham” Ya faɗa yana nuna ta da key din mashin ɗin shi, ya ja dogon tsaki ya kama hanyar shi ya fita yana mitar da ta zame masa jiki. Ta dai jishi amma har duniya ta naɗe bata jin zata iya hana Ihsan zuwa inda take, kuma taimakon da zata mata Hashim ɗin bai nemo wanda zata mata irin shi ba. Ko babu komai zata samu lokacin da zata cigaba da ƴan sana’o’inta a cigaba da samun na rufin asiri, tunda gashi ta samu kanta a zamanin da mata su ke kula da kansu a gidan aure. Ƙarasa wanke kayan tayi tass ta dauraye su, wasu saida ta shanya a jikin garu, saboda yawa igiyan shanya bai ɗauke su duka ba. Ganin ba damina bane tayi shirinta na tafiya asibiti idan ta dawo sai ta kwashe lokacin sun bushe don idan ta Hashim ne saidai su kwana a wurin. Bashin Ƙarago ta karɓa taje musu da shi asibitin suka sha tare da kunun sadaka ita da Muftee suka yi tamm, amma tun a nan ta fara tunanin dabaran da zata yi su samu na abincin rana, gashi ɗan abinda sauran suka tarfa mata cikin kayan tallafin da suka samu har ya ƙare daman ba yawa. Ta yi tagumi tana kallon matar dake canza ma jaririyarta da bata da lafiya pampers, ga yarinyar ƴar ficiciya, har oxygen aka saka mata duk abun tausayi. Wayanta dake gefen Muftee ya shiga ruri, tayi saurin ɗauka kada ƙaran shi ya damu majinyatan dake ward ɗin, ta ma manta ne da ta iso bata saka a silent ba. “Hello” tace bayan ta ƙara a kunnenta ganin babu suna a kan lambar, ma'ana bata yi saving ba. “Malama Ilham ina kwana, Surayyah Kagarko ce” Tsugul ta miƙe tsaye kaman wanda aka tsikara da allura. “Ina kwana Hajiya!” Ta amsa da “lafiya ƙalau. Zaki iya zuwa ki same ni yanzu? Kaman yanda nayi miki alƙawari wani abu ne ya samu amma ba irin wancan bane” Hannu ta saka ta kare bakinta cikin tsananin farinciki, tayi ƙoƙarin daidaita kanta tana faɗin “gani nan zuwa yanzu Hajiya, na gode, na gode sosai” “Saii kinzo” Hajiya Surayyah ta katse kiran, Ilham sai ta shiga hamadala ma Ubangiji, don duk abinda za'a ce maka ya samu in sha Allah alkhairi ne duk da ma bata san menene ba tukunna. Zata ɓata lokaci idan tace zata tafi da ƙafa, dan haka ta roƙa aron naira ɗari uku a wurin matar da suka fi shiri da ita a ward ɗin. Har ta danna kiran Khausar ya shiga, mai ta tuna sai ta katse kiran, kawai tace ma mutanen ward ɗin su ɗan saka mata idanu a kan Muftee dan Allah bari ta je ta dawo. “Mimi ki siya min minti” shine abinda yace mata da zata tafi. “In sha Allah yaron Mimi” ta sake mishi murmushi, suna daga ma juna hannu ta tafi. Babu ɓata lokaci sai gata a cikin A&I Support Organization, kuma kai tsaye aka kaita ofishin Hajiya Surayyah, ta rage tsayinta ta gaida matar mai mutunci sannan ta zauna a kujeran da ta nuna mata. “Kaman yanda na faɗa miki ba tallafi bane irin wancan, aiki ne na samu mai kyau shine zan miki tayin shi idan zaki iya” Aikatau shima ba baƙonta bane, tayi aiki a gidajen masu kuɗi saidai idan jikin Muftee ya kwantar dasu a asibiti na tsawon lokaci tana komawa sai ta samu an kawo wata a madadinta a bata haƙuri. “In sha Allah zan iya Hajiya, a ina ne?” “Toh ai baki ji wani irin aiki bane ba” Aunty Surayyah ta faɗa da murmushin ganin ɗokinta, sai ilham ma ta murmusa ta gyara zama tana sauraron ta. “Aikin raino ne, yarinyar ɗan yayana, ta kusan cika shekaru huɗu” “Na kwana ne Hajiya?” ta tambaya damuwa yana maye gurbin farincikin da take ciki, kada ace zata sake ganin samu ta ga rashi ne. “A'a daga safiya ne ƙarfe 7 zuwa 5 na yamma a ranakun mako, kuma banda weekend” Ta ɗan yi jigum tana tunani. Yaya zata yi da Muftee yanda bata da mai zama mata a jikinsa? Filiyan zata zo amma hutun ta na ƙarewa zata koma BUK. “dubu dari ne albashin” muryar Hajiya Surayyah ya ratsa dodon kunnenta. Ta waro ido tare da dafe ƙirji “Dubu ɗari Hajiya?!” Aunty Surayyah ta jinjina kai. “Shiyasa na kira ki saboda alƙawarin da nayi miki” Tana jujjuya kai tace “zan iya hajiya, in sha Allahu zan iya” Koda aikin dubu biyar zuwa goma ta samu indai kuɗi zasu shigo hannunta zata yi, balle aikin dubu goma sau goma. “Amma bayi da Mata a halin yanzu, saidai duk a gida daya muke rayuwa ɓangarensa ne kawai daban, kuma da kin zo kin shiryata ta tafi Makaranta shima zai fita aiki sai ki samu fili ki kimtsa gidan, idan an tashe su zaki je da driver ku ɗaukota ki sake mata wanka ki bata abinci, toh yana dawowa zaki iya tafiya gida abun ki.” “Zan yi hajiya, wallahi zan yi, yaushe ake so na fara zuwa?” “ko gobe ma, ina kina da mai zama miki a jikin yaron ki?” Ta ɗan sosa ƙeya ta cikin hijabinta “A dan yi mun alfarma zuwa jibi Hajiya, ƙanwata zata zo daga kano zata taya ni” “Shikkenan Allah ya kaimu jibi ɗin. Idan kin shirya sai ki kira ni in yi miki kwatancen gidan.” “In sha Allah Hajiya, Nagode fah, Allah ya saka da alkhairi ya ƙara girma” Bata bar A&I ba saida naira dubu biyu a cikin purse ɗinta kamar wancen ranar. Saboda farin ciki bata bari ta koma asibitin ba Ta kira Maama ta sanar da ita. A yanda tayi ta mata addu'an Allah yasa ya zame mata alkhairi ta bata shawaran ta kula ta riƙe amana kuma Ilham taji ɗauka. “In sha Allah Maama na, zan kiyaye” “Yauwa Fidela, hidiman yara kuma saida haƙuri, dukda kema kina dashi amma ba zaki haɗata da wanda kika saba dashi ba, kuma sai kin bata matsayin ƴa a wurinki kafin ta ɗauke ki a matsayin uwa sai kuji daɗin zaman. Kada ki dinga duba kuɗin da zaki na samu kinji? Amana ne aka baki wanda Allah zai tambaye ki a kanshi ranan ƙiyama, dan haka kiyi ƙokarin cika shi da zuciya ɗaya. Allah ya kaɗe fitina” Saidai abinda Ilham bata sani ba shine; kamar yanda kuɗin aikin nan yake da yawa haka ma wahalar shi, haka ma ƙaddarar da zata datse mata farin ciki ta saka ta zubar da hawaye mai tarin yawa. Yanzu dai abinda ya rage shine yanda zata sanar da Hashim, dan idan ya samu labarin kudaɗen da zasu fara shigo mata shikkenan zai sake janye jikinsa daga sauƙe hakkokin da suka rataya a wuyan shi, na Muftee da ita kanta. . . . Banbanin da ya shigo yana yi ne ya saka ta tsumewa a daƙin har saida ya ƙaraso ciki, ya sameta durkushe da dutsin guga a hannunta tana danne kayan shi da ta wanke da safe. “Kina jina kika yi mun banza ko? Mara godiyan Allah!. Har ki samu wacce zata ɗaura ma kanta dawainiyar ki kice mata bakya so? Ina saboda nace kada Ihsan tazo mun gida ne nima zaki raba ni da ƴan uwana?” Ta dora dutsen a kan kifaffen kwanon samira sannan ta miƙe tsaye. “Idan zancen khausar kake yi da tazo cemun tayi tana da wurin zuwa shine nace ta tafi kawai, daman bisa kuskure ma na kirata, amma ban yi tsammanin zata haɗa mun munafurci a wurinka ba” Marin da ya ɗauketa da shi yasa saida tayi baya saboda ya shammaceta, ƙafarta ya ture dutsin guga da samiran, garwashin ciki ya zube a saman tiles din wurin. Raɗaɗi ya ziyarci fuskarta a inda yatsun shi suka sauƙa da kuma dunduniyar kafarta. “Yaya Hashim, yau a kan Khausar ka mareni?. Khausar din da nice na jawota jikin mu?” “An mare kin. Idan kina da ƙarfin ramawa bismillah. Kuma dan Allah wata tazo mun gida ta gani, dukkan ku sai na baku mamaki tunda na lura ba fasawa kika yi ba, toh mu cigaba da zubawa mu gani waye zai kwashe.” *Washegari* Ƙarfe 12 da rabi na safe Ihsan ta sauƙa a garin Kaduna, Ilham kuma ta shirya mata dambun tsaki da jollop ɗin taliyan murji na manja da wake, ya ji daddawa kaman yanda ta san Ihsan ɗin tana so. ```````` Seemahwrites ✨ . Chapter 14 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Wattpad and Arewapen @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 UMMEE'S BAKING EMPIRE https://chat.whatsapp.com/L0WK91pLyVn8iQ6HjSwG8a?mode=gi_t *My Sister matso kusa ki ji.. Wannan cake ɗin da kike gani a online yake burge ki kin san inda zaki samu irin shi? Koko sha'awar glazed ko filled donuts kike yi? Ga plain ones for your Husband, father or boyfriend if they don't have a sweet tooth.* *Coming to you my brother.. kana iya bada kyautar nan mai sanya mace tsallen Murna? Ko Surprise ma abokai? For Eids, Anniversaries, birthdays, graduation or just to celebrate your girl or yourself? you can order a cake from us. Akwai crunchy cincin domin motsa baki ko a siya ma mama da baba su saka mana albarka.* *And don't forget about friendship or sibling bonds, You can always order a cake to celebrate their success or even to mock them with class😎, requesting captions that are satire and funny.* Muna siyar da: • Cakes na for every occasions ( birthday, graduation, anniversary dai dai sauran su) • Bento cakes • Cupcakes • Mouth watering brownies • Samosas • spring rolls • Glazed puffs • Filled, glazed and plain donuts. E.t.c *Ummee's Baking Empire –* *Making every Moment feels special. We always make sure that you recieved what you ordered 👌🏼💯* 📞 08173775170 📍 gwammaja, Kano 14…. Wallahi nayi kewar ki sosai ƴar ƙanwata” Cewar Ilham idanunta suna tara ƙwallan farinciki, suka sake rungume juna suna murna a tsakar gidan zuciyoyinsu na shawagi, kusan shekaru biyu kenan rabon su da saka juna a idanu. Last Year da aka yi taron family Muftee ya ɗan taɓa pnuemonia, amma ta jinkirta kaishi asibiti ganin idan suka je gida zasu ɗan kwana biyu in yaso sai ta kaishi asibitin Malam Aminu Kano, don likitan da ya fara ganin shi ma lokacin da aka gano shi sickler ne Kafin su koma kaduna da zama yana can. Amma Hashim bai tashi faɗa mata ba zai tafi da su ba, saida ya bari ta gama shirya musu kayan su tsaff ta haɗa ɗan tsarabar da zata kai gida don shi ba baƙon zuwa wa mutane hannu na dukan cinya bane ko lokacin da yake niman aurenta. Duk da ya san ba son shi take yi ba a lokacin, kuma ta gwada mishi hakan a aikace, amma ko ma wa’inda suka yarda aka haɗa auren bai taɓa ruƙo komai ba, haka zai zo hannu rabbana ya cikata da surutu a Falon Taa ɗinsu tana kuɗundune cikin hijabi tana gumm da baki har ya gama ya tafi babu wani ɗan ihsani. Ihsan ta ɓamɓare jikinta daga na Ilham tana yamutsa fuska “Yunwa nake ji Addah Fidela! Kin san idan zan yi tafiya bani iya karyawa in ba haka ba sai nayi amai a mota” “Yi haƙuri acici mala’ikun tauna” Ta kama hannun akwatin Ihsan ta raba shi da ƙasa don babu taya guda ɗaya a jiki balle ta ce zata ja shi. “Kai-Kai Filiyan?! garin Kano kika ɗauko kika zo dashi ne?” tace jin nauyin akwatin yayinda Ihsan ta ɗauki buhun da take da tabbacin yafi akwatin nauyi suka shiga parlorn Ilham ɗin da ta ƙalƙale shi harda maƙala turaren tsinke sai ƙamshinsa ke tashi. “Fidela ina kayan ɗakin ki?” Shine sallamar da Ihsan ta shiga dashi. Ilham tayi murmushin yaƙe “wani kayan ɗaki kuma? Kin san daman ai tunda na siyar da kujeru na da zamu bar kano ban sake siyan wasu ba” “Toh ina TV da fridge ɗinki? Babu komai a parlorn ki sai carpet da wani yamutsolon labule?” “Suma ba don kada sanyi ya kama Muftee na ba da ba zaki zo ki same su ba. Ni zauna in baki abincin kafin kice wa Maama nah na barki da yunwa.” Ta ja hannun Ihsan din suka zauna a gaban tray ɗin da ta shirya mata abincin cikin wani koɗaɗɗen food flask da kwanon samiran da yasha lamba har ya godewa Allah. Ƙamshin taliyan ya tuna ma Ihsan yunwar da take ji don haka ta mayarda hankali a kan abincin da ta tursasa Ilham saka hannu suci tare har saida suka ga bayan shi tass, daman babu yawa sosai ne Ilham ɗin taƙi ci don gani take yi Ihsan ba zata ƙoshi ba. Sai gashi Allah ya saka masa albarka dukkan su sunyi tamm suna hamdala. Ihsan ta tashi ta nufi inda suka jingine buhun sannan ta fara firfito da kayan ciki. Ƙullin shinkafa da flour kusan mudu biyar biyar a cikin laida mai yellow da baki ta fara direwa a gaban Ilham, sannan laidojin taliya guda huɗu, macaroni huɗu, goran faro mai cike da mangyaɗa guda biyu na manja guda ɗaya. Laidan maggi guda biyu, omon wanki babban jaka da sinkin sabulun wanka ga na wanki ma harda man shafawa babban roba, da doya guda biyu a ƙasan buhun. Saida ta gama fitowa dasu ta dubi Ilham da hawaye ke gangarawa saman Fuskarta, tace “toh gashi in ji Maama. Ita ta saka yaya Ahmad ya baki shinkafa babban yaya kuma ya kawo doya.” “Allah sarki Maama, Allah sarki Maama nah” Ihsan taƙi kallonta kada itama zuciyarta ta karye, ta sake miƙewa ta kwantar da akwatin kayanta, ta ciro wani laida da aka samu da ƙyar ya shiga cikin akwatin ta miƙawa Ilham. Share hawayenta tayi da bayan hannu ba don sun daina zuba ba ta warware ƙullin laidan don ganin abinda ke ciki. Kaya ne, riguna da wanduna na yara gumama da yasha wanki da guga suka fito tass fiye da wasu na kantin ma don masu kyau ne sosai. Har set guda uku haka ta ciro su tana da tabbacin kuma na Muftee ne. Bayan haka ga safan ƙafa har guda uku da na hannu guda ɗaya, da hulunan sanyi guda biyu. sai kuma rigan sanyi mai kauri guda ɗaya da mara kauri mai hula da dogon hannu duk na Muftee. Itama Maaman bata barta haka ba, an saka mata dogayen riguna irin marasa nauyin nan guda biyu, sai riga da skirt kalan purple mai matuƙar kyau. “Allah ya saka da alkhairi Maama nah, Allah ya biya ki da gidan aljannah, Allah ya bani abinda zan biya ki dashi” Ihsan ta amsa da “Ameen ya rabbi, sai ki tashi ki gwada mu gani” Ganin sabon kaya a jikinta kawai ya sanya ta farincikin da bayi misaltuwa, sai juyi take a gaban fasashshen madubin da ta jingina a jikin windown parlourn tana karewa kanta kallo. Ihsan dai kallonta kawai take kaman ba ita bace ta zuba uban ƙiba lokacin da ta haihu ba, har Taa ɗinsu yana tsokanarta da wai ta dawo cin-cin saidai tayi ta murmushi don basu saba yana zolayar su ba. Amma yanzu ta zabge tass ta ƙare, har haiban da take dashi a da yanzu babu, kamar ba ita ake kira da ‘Ƴar ƙwalisa’ lokacin ƴammatancinta ba, har sunan gidan su a unguwan ya koma gidan su ƴar ƙwalisa dake tayi sana'ar kitso da zana baƙin lalle dayis, kana zuwa niman kwatance ka faɗi wannan sunan za'a kaika har ƙofar gidan su. Ga farin jini da Allah ya bata ba ga zallan maza ba har mata kowa yana yin Ilham saboda Ado, kwalliya da kuma fara’arta. Amma duk da yanzu sanye take da rigan da Ihsan har tana harsaso irin kyan da zai yi ma Ilham ɗin lokacin da aka siya sai taga bai yi mata kyan ba. Kaman ba Fidelan da suka tashi tare bane wannan, kaman an canza ta da wata matar da ta girmeta nesa ba kusa ba. Rayuwa kenan. Ta ɗauke ƙwallan dake kwarmin idanunta a fakaice tare da ɗora murmushi a saman fuskarta “Yayi miki kyau” Ilham ta juyo da murmushin da duk yanda kamanninta ya kaiga canzawa, da yin duhu, bai hana shi mata kyau ba, ga birth mark ɗinta dake ƙara bajewa a sanadiyar hakan. Tayi ma Ihsan fari da ido tana rangwaɗa tace “wani abu sai nayi kwalliya ma.” Sai kuma ta tuna ko powder bata dashi amma ta san ba zata rasa samu a wurin Ihsan ba. Ta ɗora da cewa “Allah sarki Islam, Yaya Aliyyu ya hanata zuwa” “Kuma ta saka rai ba. Ta yi kuka sosai da aka ce ba da ita za'a taho ba, saida ya ɗauke ta suka je Cravings ya siya mata ice cream kafin ta haƙura. Kuma da gaskiyan shi idan muka zo har mu biyu zamu cika muku gida ne mu takurawa ya Hashimu” “Toh tabbata zaku yi a nan ɗin? Abu na ɗan lokaci?” Ilham ta harareta. “Zaki sani ne” Ihsan ta mayar mata da hararar sai kuma aka jawo wani hirar aka ɗora. Hankalinta a kwance tunda Khausar da bakinta ta amince zata zauna a jikin Muftee har sai ta dawo bayan tazo tana kukan da yayi ma Ilham kama da abinda ake kira Munafurci, musamman da take mayar mata yanda ta kasance tsakaninta da Hashim a daren jiya, tana ƙara ƙarfafa zargin da Ilham ɗin take yi a kansu. Amma Ba ita ta kira ta ba don haka bata ji nauyi ba ta tattaro ta dawo, bayan ta bata shawaran da take ganin zai fishsheta albarkacin zaman tare da kuma ƙaunar da ta nunawa Muftee koda kuwa na riya ne. “Idan soyayya kika tsaya yi da Ya Hashim zan baki shawara khausar, idan kina da tsayayyen manemi ki bashi dama ya fito kiyi auren ki don ya Hashim bai shirya yin aure yanzu ba” Warewa idanunta suka yi cikin tashin hankali tace “soyayya kuma Aunty Ilham? Na shiga uku!” ta ɗora hannu a ƙirji. “In rasa da waye zan yi soyayya sai mijinki? Ai sai na zama butulu. Wallahi saboda ke nake girmama shi amma babu wata soyayya a tsakanin mu.” Ilham dai ta jita ne, amma ai ita ba yarinya bace. Ko dan bata nunawa Khausar din ita take kula da kanta da ɗanta bane take tunanin wani abu Hashim ɗin yake dashi saboda yana saka kaya masu tsada yayi ado ya fita?. Sai dai bata sake cemata komai ba ta barta da halinta ta dawo gida tana zaman jiran isowar Ihsan. …. ABDULHAMEED “Daddy…” Ta dago Jin bai amsa ta ba. Idanun shi na kafe a kan wayan shi da yake karanta saƙon da ya shigo masa yanzun nan. Sai ta saka hannunta biyu, harda mara lafiyan da tace ba zata iya riƙe cokali da shi ba ta tallafo fuskar shi. Ajiye wayar yayi yana maido da duban shi kanta. “Daddy.” Ta sake kira. “Yes my Kiki” ya amsa yana bata sauran hankalin shi. Sai ta saki fuskar tashi ta mishi nuni da plate ɗin plantain and chips dake tsakanin su. “Oh sorry” ya ɗauki fork ɗin da ya ajiye ya soka plaintan ɗaya da dankali ɗaya sannan ya haɗa da scrambled egg dake gefe ya kawo bakinta, ta wangale mishi ya saka a ciki. Ganin saƙon Excellency ne ya mantar dashi cewa abinci yake bata. Girman abinda saƙon ya kunsa kuma ya sanya shi karantawa yana sakewa don ya samu ya fahimtar da ƙwaƙwalwar shi abinda sakon ke nufi. Kuma tsawon layi guda gare shi amma yana niman hargitsa masa lissafi. “I'm going to run for governorship” Shine abinda saƙon yace. Toh shi meye nashi a ciki?. Da sign language Ikram ta tambaye shi wani abu, sai ya girgiza kai cikin rashin amincewa “No, sai kin warke tukunna” Ta sake daga hannu zata roƙe shi da sign language ya riƙe hannun don bayi so. Bayi son ta tashi a matsayin nakasashshiya bayan kunnuwanta suna iya ji da taimakon na'ura, kuma akwai yaƙinin aikin da za'ayi mata a kunnen idan ta fi haka zai iya dawo mata da jinta kaman yanda ya dawo da na mahaifiyarta. Amma bayi son sign Language ne Saboda yana tuna masa da Mahaifiyarta Ikram, His ‘I’. Itace sanadin da ya yarda ya fara koyon sign language. Ita ta saka yaji yana nan a matsayin ɗan Adam kamar kowa bayan ya riga da ya rasa komai. Ita ta bashi kwarin guiwa ya dage yayi karatu har ya samu yanda zai yi ya kula da Kiki a yanzu. “It's dangerous, so we're not going to the park until you've fully recovered” Ta riga da ta saba da komai take so sai yayi mata koda kuwa yaƙi amincewa daga farko. Sai ta zame daga kan kujurar dining ɗin da take zaune ta kwanta da bayanta tayi flat a ƙasa sannan ta shiga ihu tana birgima. Ba jin ihun nata yake yi ba, amma ya san yana kama ne da ƙaran da yake ji a kunnen sa a duk lokacin da ya gwada amfani da Hearing Aid ɗin shi. Bayi kawo masa komai sai ƙara, ko sau nawa zai shiga workshop ɗinsa ya gyara, ko sau nawa zai canza samfurin shi bayi iya jin komai bayan wannan ƙaran. Sauƙowa yayi, ya durƙusa a kan guiwar shi ɗaya ya rike kafaɗunta da hannu biyu kada a garin haka ta fama ciwon nata da yake tsoro. “Okay okay, we're going shikkenan?!” Ta bar birgiman tana gyaɗa kai. Zaunar da ita yayi ya ɗauko serviette a saman table ɗin yana share mata hawaye. “Ohh Kiki you're a handful!” Sai tayi masa murmushi, murmushin da ya ɗauke shi ya kaishi wasu shekaru can baya. JAPAN 2017. . Babu kowa a ajin sai shi kaɗai kaman ko da yaushe, domin tun da aka kawo shi makarantar bayi zuwa ko ina daga Hostel sai class da ake masa dole, sai dining hall tunda ya daɗe da fahimtar yunwa ba ƙanin uban kowa bane. Amma duk wani extracurricular activities da za'a yi bayi shiga. Daga inda ya kwantar da kan shi a kan desk ɗinshi dake jikin windown bayan ajin kuma yana iya kallon abinda ke faruwa a filin. Babban filin wasa da ya haɗa kalolin mutane a cikinta, baƙaƙe, farare, Larabawa, chinese, turawa, indiyawa da sauran yaruka daban-daban har da hausawa irin shi, duka a cikin filin wasan The PEN international Academy Dake ƙasar Japan. Saidai dalili ɗaya ne duka ya tara su a wurin. Kasancewar su nakasassu a cikin Al’umma. Ya cigaba da kallon yanda suka rarrabu. Masu lalurar gani sun taru a wuri guda da malaman PE ɗinsu, masu lalurar tafiya kowa a kan keken shi, haka masu lalurar ji da magana suma a wuri guda… Kuma a cikin su ne ya hango ta, cikin uniform dinta na sport fari mai ratsin ja da kuma farin hula a kanta. Gudu take yi tana bin wani ƙwallon kafa har sai da ta samu isa gareshi ta buga, sai dai a maimakon ya shiga cikin raga sai ya bi ta bayan ragan. Ya ɗauka zaiga damuwa a yanayinta amma dariya take yi sosai harda riƙe ciki. Sai ya fara tunanin menene abun daɗi da har zai saka mutumin da bayi ji bayi magana kaman sauran mutane dariya haka?. zuciyar shi ta shiga angiza shi da yaje filin shima. Ya tashi riƙe da zoben Nne wanda yazo dashi tun daga Nigeria, ya sauƙa ƙasa har filin wasan. Amma a maimakon ya shiga cikin su sai ya samu wuri a kujerun ƴan kallo kusa da inda zai ga abinda suke yin da kyau don ba ma sport wears bane a jikinsa. Ko minti biyar bai yi a wurin ba sai ga wani ya bugo ƙwallo daga ta bayanta, ita kuma ta saka kai gaba dan haka bata gani ba. Yayi saurin miƙewa yana ƙwala kiran “Hey!” da nufin ta kaucewa ƙwallon. A karo na farko da ya buɗe baki yayi magana tun bayan zuwan shi. Mantawa da itama bata ji kamar shi. Har saida ƙwallon yayi nasaran samunta a kai sannan ta juyo tana matse fuska tare da sosa ƙeyarta. Sai ya samu kanshi da murmusawa ko babu komai an rama mishi dukan shi da tayi a ƙeya da ruler last week. Saka idanunta da tayi cikin nashi yasa dariyar tashi ta ɗauke, ganin ta ƙura masa idanu sai ya tsuke fuska ya kawar da duban shi daga gareta. Yana tunanin tashi ya bar wurin sai gata tsaye a gaban shi riƙe da ƙugu tana huci. Magana tayi mishi da sign Language. Bai gane ba saboda bai iya ba, bai taɓa koyan koda abu masu sauƙi ne da sauƙin ganewa ba, don haka ya shareta ya cigaba da murza zoben a hannunshi. Sai kawai ganin wasu ƴan fararen yatsu yayi sirara sun gifta a gaban idon shi, ya duba sai yaga zoben Nne dake hannun shi babu. Ɗaga idanun da zai yi kuwa Ikram ta arci na kare tayi cikin filin, ai babu ɓata lokaci yabi bayanta da ɗan iskan gudu. . ƙoƙarin kawar da tunanin yayi daga cikin kan shi don yana kara masa damuwa. Ya dauki Kiki ya mayar da ita saman kujera ya cigaba da bata abinci har saida ta ƙoshi don kanta kafin ya shiryata suka fita amusement Park kaman yanda ta buƙata. ….. ILHAM Labulen da aka ɗaga lokaci ɗaya kaman ana yaƙi ya katse hirar da suke yi a tsakanin su. Idanun Ihsan dake zaune a kan carpet kanta a buɗe da kuma Ilham da ta saka karamin kujera a bayan Ihsan ɗin ta zauna tana kitsa mata gashin kanta suka sauƙa a kan Hashim da ko shigowar shi gidan basu ji ba tsaban hira tayi daɗi. Aka tsaya kallon-kallo na minti guda curr. Ita Ilham jikinta ne yayi sanyi saboda kashedin da yayi mata jiya. Ihsan kuma kallon cikin idanun shi take yi kai tsaye babu wani girmamawa ko tsoro, shi kuma idanun Ihsan din ne suka sanya guiwowin shi suka yi sanyi a kan rashin mutuncin da yazo yiwa Ilham. Don khausar ta tabbatar masa da Ihsan tana hanyar zuwa masa gida yau, kuma ta labarta masa abinda Ilham ɗin ta faɗa mata a kan shi. “Sannu da dawowa baban Muftee” Ilham tace daga zaune gudun kada ta ƙarasa ya ci mutuncinta a gaban ƴar uwarta. Sake labulen yayi ba tare da yace komai ba yana shigowa ciki. “Filiyan ba zaki gaida shi bane?” Ilham ta buga mata ƙasan kifiya a tsakar ka ganin har zai wuce ciki tana gumm, kuma shima ya gagara cewa komai. “wash!! Shine sai kin dake ni? Ai jira nake yi yayi mana sallama ki gani ko ba zan gaida shi ba” Hashim bai ce komai ba, Siɗif-siɗif ya ƙara sauri ya shige ciki yana jin dama tun farko juyawa yayi ya fice a gidan. ```````` Seemahwrites ✨ . Chapter 15 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Wattpad and Arewapen @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 15… Ilham ta miƙe zata bi bayan shi Ihsan ta ruƙo rigan jikinta, tana tilasta mata maido da hankalinta da ya gama tafiya uwar ɗakin da Hashim yake ciki zuwa gare ta. “Menene?” Ta tambayi Ihsan da ta ƙura mata idanu, tana riƙe da ita kuma bata ce komai ba. “Mun gama kitson ne?” Ta tambaya tana shafa rabin kan da yake har yanzu a tsefe da ɗaya hannunta. “Baki ga baban Muftee ya dawo bane? Zan dawo in ƙarasa miki ai” “Kina dai ganin maghriba ta gabato, kuma Maama ta sha mana faɗan kitso ko tsifa da Almuru, kuma ba zan kwana da rabi da rabin kai ba gaskiya.” Danƙwale tayi mata “kin ci gidanku Filiyan. Ba nayi miki zancen Almurun ba ki bari sai gobe kika ce a fara a haka? Ai nace yanzu zan dawo”. Ta ƙwace riganta daga riƙonta, ta karasa jikin ɗakin tayi sallama kana ta ɗaga labule ta shiga tsoro yana daɗa mamaye zuciyarta. Yanzu idan Hashim ya sake jaddada mata hukuncin shi a kunnen Ihsan fah? Koma ya zo ya koreta a gidan da kan shi, Ina zata saka kunya da nauyin Maama?. “Sannu da dawowa” tace tana tsaye daga bayan shi a lokacin da yake cire riga ya jefa mata a kan gado idan taga dama ta ɗaga. Bai kulata ba ya shiga kunce mazargin wandon shi, shima ya zame shi a ƙasan wurin ya tsallaka shi ya raɓata ya wuce hanyar ban ɗaki. Ganin haka Ilham ta fita ɗauko mishi dambun tsakin da Ihsan bata ci ba, ta saka a kan tray da jug ɗin ruwa a gefe ta dawo ɗakin. Ko idan ta bashi zai huce ya hakura da nunawa duniya irin zaman da suke yi. Tana da tabbacin ba baƙon abu bane a wurin duk wanda yake kusa da su amma sirri komin kashin sa sirri ne, ko da ita bata da rabon hankalinta ya kwanta tana fatan kada damuwarta ya cigaba da damun zuciyoyin Ihsan da Maama. Ganin toilet ɗin a wanke ga sabon sabulu yasa ya yanke shawarar yin wanka bayan ya gama abinda ya shigar da shi. Tana zaune a gaban tray ɗin bayan ta tattara kayan da ya watsar Ya fito sanye da gajeren wandon da lokacin canza shi bai yi masa ba tukunna don sai yayi kwana huɗu zuwa sati yana maimaitawa, idan ɗoyin shi ya fara shiga masa hanci tukunna yayi tunanin lokacin canza wani yayi. Tayi tsammanin zata samu sauƙin shawo kan shi idan yaga kwanon abinci, amma ko kallo bata ishe shi ba haka ya wuce zuwa akwatin kayan shi da ta jera a gefen ghana must go ɗinta, wanda na lefenta ne ya mallake tun bayar da ta siyar da wardrobe ɗinta tayi jinyar Muftee da kuɗin. Yana jin yunwa amma gidan su Khausar ya nufa da sunan lallashi, ya san kuma zasu tarbe shi da abinci mai rai da lafiya shiyasa bai kula tsiyan dake cikin samiran Ilham ba, ya shirya cikin jamfa ruwan goro ya kafa hula. “Baban Muftee abincin fah” ta tambaya ganin yana shirin fita. “Kiyi yanda kike so dashi tunda ban Isa da gidana ba Ilham” Hararan da ya watsa mata tare da wucewa ya hanata sanar da shi aikin da ta samu na raino wanda zata fara zuwa gobe. Ya fita parlourn da sallama a bakinsa inda Ihsan ke zaune ta lulluɓe kanta da mayafin kayanta tana danna waya. Yayi tunanin zata gaida shi yanzu amma kaman bata san da halittar shi ba saida ya zo fita yaji tace “Uhm”. Tuƙuƙin baƙin ciki yazo ya tsaya mishi a wuya kuma babu yanda ya iya da ita, don idan yana dukan Ilham yana kwana lafiya yana tsoron Ihsan da idanunta ke a tsakar ka tsaff sai ta iya ramawa. Amma duk zai yi maganin su ne ita da Ilham ɗin. “Wallahi baki da kunya yarinyar nan” Ilham ta girgiza kai tana komawa matsuguninta a bayan Ihsan. Ta yatsina baki tana kashe wayan ta ajiye. “Wallahi ina da kunya nikam, marasa mutunci ne bani gani da gashin ido.” Ilham ta fisgo gashin kanta bayan ta zame mayafin “dalla rufa mun baki, ko baya aure na kin san dai yayan ki ne” Jin Ilham ta saka kibiya tana tsaga gashinta yasa ta koma ƙunƙuni kawai kada ta soke ta da shi idan ta cigaba da magana. Da suka gama Ihsan ne ta fara miƙewa ta shiga banɗakin yin fitsari tare da alwala amma da ta haɗu da ajiyan Hashim da aroma ɗin shi ya cika banɗakin babu shiri ta fito. “Kambu Aunty Ilham kashe ni kuke son yi?” Ilham ta tsaya da alwalan da take yi a bakin rariya. “Lafiya?” “Haka kuke amfani da toilet ɗinku? Toh gaskiya ba zan iya ba motan dare zan bi in koma kano.” Da sauri Ilham ta miƙe tunawa da Hashim ya shiga banɗakin bayan ta wanke kuma ta san halin shi. Bata ce komai ba ta wuce ciki tana jin Ihsan na faɗin “Haka kawai ana zaman lafiya? Ni ba haka ake ba a garin mu wallahi” kunya ya hana ta tankawa saida taje ta tsaftace banɗakin ta bar ƙofa a buɗe iska ya kora warin kafin ta ce Ihsan ta shiga. Kuma dake da gajiya a jikin Ihsan kafin Hashim ya dawo gidan har tayi barci a parlor inda Ilham tayi musu shimfiɗi a ƙasa, daman ta saba da kwanan parlour idan tana gudun kada takaicin Hashim ya ƙarasa ta, sai yau yayi mata daɗi ganin gata ga rabin jikinta. Kiran sallan asuba ta tashi, ta shiga hidiman hura wuta da sharan tsakar gida kaman kullum saboda ta samu tayi sammakon zuwa asibiti. Sai gashi Ihsan tana gama karatun Alqur'ani da azkhar ɗinta itama ta fito ta saka mata hannu don haka babu ɓata lokaci suka gama suka soya doya a matsayin abun karyawa, ba don Ihsan ta so ba aka zuba ma Hashim. Kuma har suka ci suka fita bai farka ba kasancewar yau Lahadi. Asibiti suka fara zuwa su biyun. Ta tambayi wacce ta yarda zata dinga duba mata jikin Muftee yanda ya kwana, ta tabbatar mata da sauƙi kafin ta kira Hajiya Surayyah tayi mata kwatance ta tafi ta bar shi da Ihsan. …. 8:51am Mai gadi ne ya wangale mata gate bayan ta sanar dashi wurin wacce tazo. Bata tsaya mamakin irin girma da kyawun gidan ba ganin kuɗin da suka ce zasu dinga ɗauka suna bata duk wata. don haka ta kutsa kai cikin ƙaramin ƙofar da ta gani a buɗe ta shiga. akasin yanda ta samu harabar gidan ta waje ƙal-ƙal, tsakar gidan kaca-kaca yake, ga taliya da shinkafa a barbaje kaman wanda aka zubawa kaji, ga miyan kuka da aka zubar a wurin har ya bushe ba'a samu mai saka ruwa ya wanke ba, ƙudaje kaman a gidan gandun ƙauye. Ta buɗe murya ta sake sallama ganin babu kowa a tsakar gidan, sai wata budurwa ta fito daga kitchen hannunta rike da farantin da indomie da wainar ƙwai yake tururi a kai. “Baiwar Allah daga ina?” Cewar Hudah” “Ina kwana” Ilham ta fara gaidata, kana ta ɗora da “nazo wurin Hajiya Surayyah ne” Hudah ta kalleta sama da ƙasa tana yatsina baki sannan tace “Babu Hajiya Surayyah a gidan nan” Bata rufe baki ba ƙofar ɗakin aunty Surayyah ya buɗe ta fito sanye da farin hijabi har ƙasa. “Malama Ilham bismillah” shine kawai abinda tace ma Ilham da ƙaramin murmushi a saman fuskarta ko inda Hudah take bata kalla ba. Itama Hudan ta buga tsaki ta bar wurin kafin Ilham ta iya jan ƙafarta zuwa inda ɗakin yake. Saida ta shiga ciki taga girman shi, gashi ko ina ya wadata da hasken lantarki ga sabon fenti da yake nan ƙal ba kaman na tsakar gidan ba da yara suka zane shi da chalk da gawayi. Sai Hajiya Surayyah ta ƙara burgeta ganin kaman yanda ta haɗu a karan kanta muhallinta ma ya haɗu, banda ƙamshin turaren wuta mai daɗin da yayi mata kama da wanda Maama take yawan amfani dashi na Bakhoor by Seemah (08021689184). Ta fara dauko mata ruwan gora mai sanyi a fridge ta ajiye a gabanta, kana ta zauna a kujeran dake kallon inda Ilham ke zaune a saman carpet. “Sannu da zuwa Malama Ilham” “Ina kwana Hajiya, yaya aiki” ta gaidata tana ƙasa da kai cikin girmamawa. “Lafiya Alhamdulillah. Yaya jikin yaron ki” “Da sauƙi Hajiya” “Masha Allah. Bari a kawo miki abun karyawa” Tayi saurin girgiza kai “ A'a na karya kafin na fito Hajiya, Nagode” Hajiya Surayyah ta gyaɗa kai “Toh madallah. Yanzu kafin in nuna miki inda zaki fara aikin akwai abubuwan da nake son jan hankalin ki a kai” Ilham ta gyara zama ta bata dukkan hankalinta, don bata son ta baɗa ma hajiya Surayyah ƙasa a idanu bayan ta zaɓi ta taimaka mata. “Na farko sai kin yi haƙuri Malama Ilham…” Haƙuri.. Haƙuri… ta daɗe tana jin kalmar nan daga bakin mutane daban-daban. Kuma a kowani lokaci akwai nauyin da kalmar yake tafe da shi. Na farko da aka faɗa mata a ranar da aka ɗaura mata aure da Hashim ne, kuma ya zo mata da baƙin ƙaddarar da har yanzu take cikin duhun shi ta gagara kuɓuta. Na biyu an faɗa mata shi a ranar da ta rasa bangon jinginan ta, ranar da mahaifinta ya bar duniya, kuma daga nan ta san ainihin abinda ake nufi da maraici. Na uku shine ranar da likita ya miƙo mata takardar genotype ɗin Muftee da yake rubuce da harafin ‘SS’. Kuma daga nan ya fara rashin lafiyan da Allah ya barwa kansa sanin ranar da zai samu sauki. Toh wannan shine karo na huɗu. Daga bakin Hajiya Surayyah Kagarko. Kuma bata san da me yake tafe ba, amma tana fatan yazo mata da sauƙi. “... Yarinyar da zaki kula da ita tana da lalurar ji don haka tana bukatar kulawa ta musamman, shiyasa sai kin yi haƙuri sosai kin kai zuciya nesa. Ki tausaya mata kaman yanda kike tausayin naki yaron, Yanda kika durƙusa a kan guiwowin ki kina magiya a kan rai da lafiyan shi yasa naga dacewar ki da wannan aikin, saboda tana buƙatar kulawar uwa irin ki. Don Allah ki jata a jiki Ilham kuma shima mahaifinta sai kin yi haƙuri da shi saboda ita kaɗai gare shi kuma laluran su kusan iri ɗaya, kin san kurame da faɗa. Bani tunanin akwai wani abu mai tsayi ma da zai ke haɗa ki dashi amma idan an kai ga haka ki kalle shi ki bashi hakuri ni sai ki sanar dani a shawo kan lamarin kin ji ko?” Ilham ta jinjina kai ta amsa ta “in sha Allah Hajiya” tana jin nauyin ƙirjinta na raguwa jin girman Haƙurin bai kai sauran na baya ba. In sha Allah zata iya, indai a kan Muftee ne babu abinda ba zata iya ba. Hajiya Surayyah ta ɗora da “Masha Allah. Sai kuma a kula da tsafta, da aiki mai kyau dan Allah banda amaja. Kiyi girki daidai gwargwadon da zai ishe ku kema ki ci ki ƙoshi, a dinga gyaran ɗakinta da gidan kullum duk wani abinda ake buƙata kuma kai tsaye ki zo nan ki same ni idan lokacin aiki ne kuma ki kira ni a waya.” Shima ta amsa da “toh Hajiya” Sannan Aunty Surayyah tace su je ta zaga da ita ko ina a ɓangaren, ta nuna mata abubuwa kafin su Kiki su tashi daga barci tunda yau weekend babu makaranta babu aiki. Tana tafe Ilham na binta a baya, tunanin dattin dake tsakar gidan tsaye a ranta tana ji dama zata bata minti goma zuwa sha biyar zata share shi ta wanke tass ko zai yi mata yanda take so. Har suka isa ƙofar flat ɗin kafin ta ajiye tunanin ta ɗago ta dubi ƙofar shiga, lokaci guda taji ƙirjinta na bugawan taraddadin abinda zata riska a ciki a lokacin da Hajiya Surayyah ta murɗa hannun ƙofar ta tura. Ya kai hannu zai buɗe ƙofar daga ta ciki kenan yaga ana turowa daga waje, don haka ya matsa baya yana jiran ƙofar ya gama buɗewa idanun shi a kan mai shigowa. Kaman yanda yayi tsammani Hajiya Surayyah ya fara gani don ita kawai ke da lasisin shigo mishi part kai tsaye a cikin gidan. Amma da idanun shi suka mata kallon sakwan biyu sai suka fahimci ba ita kaɗai bace, A hankali kuma suka ɗaga daga kanta suka sauƙa a kan wacce ke tafe tare da ita. ILHAM. ``````````` Seemahwrites ✨ ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh  JODA by Sadi-sakhna  DAƊIN ZAMA by Seemahwrites  *A whatsapp  One 1k Two 1800 Three 2400*   *Telegram  One 700 Two 1200 Three 1500* Account details  0545475847  Gt bank  Fatima Muhammad Gurin Sai a turo shaidan biya ta 09039206763 Chapter 16 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Wattpad and Arewapen @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 16…. A karatun da ake musu a Islamiyya, akwai babin da idan aka zo ita da ƙawayenta sai su jawo wuyan hijabinsu su rufe fuskarsu suna dariya ƙasa-ƙasa. Shi kuma malamin da yake warware musu zare da abawa kan hukuncin da addini ta yanke a kan wacce ta taka wa’innan matakan suna mishi kallon ɗan Iska. Sai gashi bata iya dariya ba lokacin da ta taka mataki na farko wanda ke tabbatar mata na biyu ma yana tafe wata rana. Maama ne ta zaunar da ita ta jaddada mata daga wannan lokacin an buɗe mata littafin ayyuka, duk abinda tayi mai kyau ko akasin shi za'a cigaba da rubutawa har zuwa ranar da zata koma wurin mahaliccinta, makomarta kuma zai kasance bisa sakamakon da ta samu a wannan littafin. Haka ta wuni jikinta sukuku, tana kwance tana juya maganganun Maama da na malamin su a kanta. Zata iya cewa daga Ranar da ta fara jinin Al’ada rayuwarta ya fara canzawa. Kaman labarin da aka gama karanta babi na farko aka miƙa zuwa na biyu kai tsaye. Wasu ɗabi’unta na banza ko na shirmen ƙuruciya Maama ce ta sakata ta sauya su ta hanyar Nasiha da gargaɗi, wasu kuma a karan kanta ta ji ya kamata ta bari. A cikin sauyin da ya sameta lokaci guda ba tare da tayi tsammani ba kuma harda shi. Harda A Moher. Daga ranar da tayi masa magana a kan shan Sigari bata sake ganin shi ba. Kullum suka zo wucewa suna hira kaman ko yaushe, sai ta samu bakinta da yin shiru idanunta kuma su tafi zuwa inda suka saba ganinsa yana zama amma babu shi babu dalilinsa, Sai abokinsa da wasu matasan da suka maye masa gurbin A Moher. A hankali kuma ta fara mantawa dashi, rayuwa ta cigaba da tafiya har ta taka mataki na biyu wanda shine aure. Amma a yau da ta saka mai kama da A moher a cikin idanunta, sai take sanin ashe akwai wani ɗan ƙaramin gurbi da zuciyarta ta tanada masa a cikinta, wanda ke cike da ƙwaɗayin sanin yanda rayuwar shi ta kasance bayan rabuwar su. Ko yanzu yana ina? Ya bar shaye-shaye? Da idanunta take yiwa Abdulhameed wa’innan tambayoyin duk da ta san bayi da amsar su. Shima ya kasa cire nashi idanun cikin nata, a cikin kan shi yana jinjina ma lamarin ƙaddara wacce bata gajiya da baiwa ɗan Adam mamaki a kan yadda take tafiyar da rayuwar shi. Ilham ce tsaye a gaban shi. Ilham da ya barta a rayuwar shi na baya. Itace ƙaddara ta sake ɗaukowa ta kawo mishi. “Abdulhameed wannan itace sabuwar Nannyn Ikram, Sunanta Ilham.” Aunty Surayyah tayi magana jin shirun yayi yawa sai tayi tunanin ita ya kamata ace ta gabatar da su ma juna. Abdulhameed!. Ta maimaita sunan a cikin kanta. Bata taɓa sanin ainihin sunan A Moher ba, haka ma bata san menene ma'anar A moher ɗin ba, ita dai ta san ta kira shi da sunan ya ɗago ya dubeta. Amma yau sai taji dama ace koda sau ɗaya ne ta taɓa jin ainihin sunan shi da zata iya banbanta shi da na wannan. Ilham tayi ƙoƙarin ɓanɓare idanunta daga cikin nashi ta rage tsayinta tana gaida shi. Bai kaiga amsawa ba wayar shi yayi vibrating a aljihun wandonsa don haka ya ciro yana dubawa. Saƙon Excellency ne kaman yanda yayi tsammani don shi ya ɗaga shi da sanyin safiyar nan duk da gajiyar dake cin jikinsa, bayan sun gama karaɗe gari tare da Kiki jiya har wurin taran dare driver na ta yawo da su, shiyasa yaso yayi barci sosai ya samu hutu yau kafin gobe ya koma aiki tunda leave ɗin da ya ɗauka ya ƙare. Cikin seconds ya rubuta reply “on my way” ya tura sannan ya maido dubansa ga Aunty Surayyah. “I'm in a rush, please take care of Kiki, idan na dawo we’ll talk Aunty Sharmama” Ya raɓa ta gefen Ilham ya wuce ba tare da ya bari idanun shi dake cike da tarin tambayoyin yanda aka yi rayuwarta ta sake tsayar da ita a gaban shi sun sake shiga cikin nata ba. “Muje ko?” Muryar Aunty Surayyah ta dawo da ita daga kamanta muryar shi da take yi da na A Moher. Sun so suyi kama, amma akwai wani zaƙi a bayan muryar A Moher wanda babu a cikin Muryar Abdulhameed. Sai wani amo da idan ya shiga kunnenka duk yawa da ƙarancin shekarunka, walau mace ko namiji dole sai ka waiwayo ka kalle mai shi, shiyasa itama ta bi bayan shi da kallo har ya nufi motar da driver ya fito musu da shi harabar gidan. Gyaɗa ma Hajiya Surayyah kai tayi sannan ta shiga binta sau da ƙafa. Suna shiga parlorn sanyi AC ya buge ta, ta shiga juye-juye tana baiwa idanunta abinci. Komai na parlorn Fari ne da ruwan ƙasa mai haske sosai, daga kan labulaye, kujeru, carpet, center table ga wasu manya manyan windows da suka baiwa hasken rana damar shigowa sosai dukda gilasan a rufe suke. Babu datti ko ƙazanta ko ƙanƙani, komai yana tanade ne a wurinda ya dace har throw pillows ɗin kujera suna jere reras kaman ba parlorn namiji ba. Suka wuce parlorn zuwa kitchen bayan Aunty Surayyah ta gama mata bayanin yanda zata ke gyara shi a kullum. Sun daɗe a kitchen tana gwada mata yanda ake tanada komai kaman yanda Abdulhameed yake so da kuma inda kayayyakin da zata dinga abinci da su suke, ta shigar da ita har store ɗin dake haɗe da kitchen ɗin a inda Ilham ta ga kayan abinci kaman a shago, kaman ta ɗauka ta kai nata gidan suyi ta ci tare da Muftee. Hajiya Surayyah tana tsaye a kanta ta shiga sharan gidan da take ganin a share yake amma abinda aka sata shi zata yi babu musu, har ɗakin Ikram suka je saidai babu yarinyar a ciki sai tarin kayan wasanta da duk gidan masu kuɗin da ta taɓa aiki bata taɓa ganin kamar su ba. Ɗakin babba ne a karan kansa amma tarukucen ciki ya saka girman nashi ya ragu sosai. Suma kayan wasan haka ta gyara musu zama bayan ta share ɗakin ta shiga ta wanko banɗakin dake haɗe dashi. Ta saka mopping mist ta goge gidan har kitchen banda ɗakin da aka ce Mata na Mahaifin yarinyar ne. sannan ta shiga haɗa musu abun karyawa. Aunty Surayyah ta taya ta da wasu abubuwan kasancewar yau ne rana na farko kuma Ilham ɗin bata san kan cimar mutanen gidan ba, suna aikin tana mata ƙarin bayani har suka gama, lokacin ƙarfe sha ɗaya ta gota. Suna fitowa daga kitchen zasu jere abincin a kan dining sai ga kukan Ikram na daga Fitowa daga ɗakin Abdulhameed. Aunty Surayyah ta bar Ilham ta ƙarasa, ta wuce ɗakin da sassarfa sai gata ta fito da wata sangamemiyar budurwa a hannu, don wannan tafi Muftee ɗinta kumari nesa ba kusa ba. Bata gama mamaki ba sai gashi ta iso inda take tsaye ta saka mata yarinyar dake kukan sakalci a hannu. Suka kalli juna ita da farar yarinyar kafin ta buɗe ƙaramin bakinta ta saka ihun da ya saka Ilham rintse idanu, sauran ƙiris ta sake ta a ƙasa aunty Surayyah tayi saurin saka hannu ta karɓeta. “Kiki Aunty ce da zata dinga miki wanka tana baki abinci” Zillon da take yi tana birgima yasa itama Aunty Surayyan ta sauƙeta a ƙasa kafin ta faɗo. Kaman jira take yi ta kwanta tana bori kukan yanzu harda hawaye tana kiran Daddynta. Aunty Surayyah ta kalli Ilham wacce jikinta yayi sanyi tace “sai haƙuri fah Malama Ilham, a hankali zaku saba in Allah ya yarda” Ta haɗiyi miyau tare da durƙusawa a kan guiwowinta ta shiga lallashin Kiki saidai kaman wanda take ƙara Volume haka suka sha fama da ita na wurin minti 30 kafin da ta gaji tayi shiru don kanta, shima taƙi zuwa wurin Ilham firr sai Aunty Surayyah ce ta ɗaura ta a cinya ta bata abinci tayi mata wanka, Ilham ta dauko kaya aka saka mata. …. ABDULHAMEED Ya ɗauki kusan minti uku yana jira bayan ya turawa Excellency saƙon isowarshi kafin wani mutum ya fito sanye da ƴar shara da hula dara a kan shi, yayi masa iso cikin gidan. Yayi tunanin su biyu zasu gana kaman yawancin lokutan da Excellency yake zaɓan suyi magana cikin sirri, amma a yau sai ya ci karo da baƙin fuskoki guda uku zaune a manyan royal chairs dake zagaye da babban parlourn. A tsanake ya bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya don ya san da su waye zai zauna a ƙasan inuwa guda. Ya gane fuskar mutum ɗaya a cikin su bayan yayi masa kallo na biyu amma sauran yana da tabbacin bai taɓa ganin su ba a rayuwarshi. Wanda ke Hakimce a dogon kujeran dake kallon ƙofa ya ajiye tumbinsa ɗan dadai ya yafato Abdulhameed ɗin da hannu sannan ya bubbuga space ɗin dake gefensa ma'ana ya zo ya zauna. Kan shi ya kulle gaba ɗaya, amma bai bari hakan ya nuna a fuskar shi ba ya ƙarasa ya zauna da ƙwarin guiwa. Excellency yayi murmushi yana kallon mutanen dake parlourn, su kuma nasu duban na kan Abdulhameed ko zasu gano Abinda ke tattare da shi na musamman. “Wannan da kuke gani shine tsanin da zamu haura zuwa ga nasara in sha Allah” cewar Excellency ba tare da ya bari Abdulhameed ya fahimci a kanshi suke magana ba. Ɗaya a cikinsu ya gyara zama cikin rashin fahimta yace “Excellency, ga wa’inda suka goge a mulki suka daɗe ana damawa da su a siyasar ƙasar nan bamu riƙe su ba sai wani saurayi guda ɗaya rakk?” Ya gyara zama a kujeran yana shafa gashin bakinsa murmushin kan leɓen shi yana ƙara faɗi, idanun shi a kan Abdulhameed da ya saka hankalin shi gaba don burin shi su gama abinda zasu yi su watse, Excellency ya sanar dashi dalilin kiran da yayi mishi na gaggawa ya samu ya koma wurin Kiki, shiyasa bai ma saka hankalin shi ya karanci abinda suke cewa ba. “Baku san me nake hangowa game da shi bane. Su wa’inda kuke magana a kan su idan muke je musu da buƙatar mu ba zasu bamu goyon baya ɗari bisa ɗari ba har sai sun tabbatar sun kwashe kaso mai girma a cikin tafiyar nan, amma wannan sai yanda nayi da shi, wannan alƙawari ne a tsakanin mu.” Mutumin da ya shigo da Abdulhameed ya dawo da tray mai ɗauke da ruwan gora a hannunsa ya ajiye a gaban shi sannan da hannu yayi mishi alaman ya zuba ya sha ruwan. Yayi hakan a maimakon ya zuba masa da kan shi ne saboda ya isar ma sauran mutanen wurin saƙon Excellency na dalilin da yasa ya zaɓi yayi amfani da shi. Saboda Nakasarsa. ….. Zuwa Azahar daga ita har Hajiya Surayyah jikin su yayi laushi saboda yanda kiki take walagigi da rayuwar su, ta yi nan ta yi can, ta ce tana son kaza sai an yi mata tace ba shi ba. Gashi ko kallon arziƙi Ilham tayi mata sai ta saka ihu tana niman Daddynta. Don haka Ilham ta shafa ma kanta lafiya ta tafi ɗakin da Aunty Surayyah tace zata iya hutawa a ciki tayi alwala tayi sallah Sannan ta wuce kitchen ta daura sanwan abincin Rana lokacin ƙarfe biyu ta kusa. Shinkafa basmati ne tayi jollop ɗinsa ya sha carrot, green beans da peas tunda ta gansu a wadace a cikin fridge. Tana yayyanka Albasa round-round zata zuba a kai lokacin ya kusa nuna sai ga Aunty Surayyah ta shigo. “Ina fatan ba a kan abincin zaki saka wannan albasan ba Ilham” Ta tsaya da yankan ta ɗago idanunta da suke tsiyayan hawayen yajin da albasan ke da shi tana jan hanci tace “a kan shi ne hajiya.” “Ai Ikram bata cin yankakken Albasa, kuma tare suke cin abinci da babanta, ki bar shi a haka kawai” Ita kuwa ina fasalin Jollop rice babu albasa a kai? Amma babu mai niman ra’ayinta don haka ta amsa da toh. Sai ta ajiye albasan a gefe ta ƙarasa girkin ta zuba musu a food flask ta kai dining. Hajiya Surayyah ma ta saka mata a plate dukda bata tambaya ba amma ita san ya kamata ganin yanda suka wuni tare a cikin gida. Da zata ci sauran wanda rage a tukunyan sai ta zuba albasan duka ta ci kayanta tana santi, sannan ta wanke komai a take a take ta kimtsa kitchen ɗin tass tana yi tana lissafin yanda zata kasafta Naira dubu ɗari nan da kwana talatin a cikin kanta. Fitowarta daga kitchen ta hange su zaune a dining shi da Ikram, plate ɗin shikafan da ta dafa a gaban su yana ta cire carrot da green beans ɗin da ta zuba a ciki yana mayarwa gefe saboda kiki ta ce bata so. Ta taɓe baki ganin samun wuri irin na ɗan Adam gashi ita tana niman kayan gina jikin ma mara lafiya amma bayi samuwa. Bata ga Hajiya Surayyah a parlorn ba don haka ta ƙarasa kusa da table ɗin ta durƙusa kana ta gaida Abdulhameed da “Ina wuni” Bai ji gaisuwan ba, har saida yaga alaman mutum a gefe kafin ya ɗago daga abinda yake yi, ya juya ya dubeta. “Sannu ko” Muryar shi ya sake shiga kunnuwanta yana sanyata lumshe idanu tare da buɗe su a kan hannayenta dake bisa cinyarta, har yanzu da damshin ruwan da ta gama aiki da shi a jikin su basu gama bushewa ba. Ta amsa tana sake gaida shi. Ya ga dai alamun tana magana amma bata kallon shi. Ya ajiye cokalin hannun shi ganin hankalin Kiki ya koma kan TV dake nuna kids show da ya saka mata, kuma ta ɗan ci abincin da yawa. “Look at me” Bata san da ita yake yi ba, muryar tashi ce kawai ta sanya dole ta ɗago ta kalle shi amma sai ta samu shima ita yake kallo. “Amina Usman Jen.” Ya kira cikakken sunanta. “Are You married?” ```````````` Seemahwrites ✨ ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh JODA by Sadi-sakhna DAƊIN ZAMA by Seemahwrites *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a turo shaidan biya ta 09039206763 Chapter 17 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Wattpad and Arewapen @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 17… Babban kuskuren da ya taɓa yi a rayuwar shi shine kula matar Aure. Ya bari matar aure ta raɓe shi, suka keɓe wuri guda tare da matar Aure. A sanadin haka ne kuma Kiki take zaune a gaban shi yanzu haka, dalilin da yasa ya sadaukar da rayuwar shi wajen Kula da ita, amma a haka yake tsoron ta girma ta dube shi da kuskuren da ya aikata wanda bai taɓa tsammanin girman sakamakon shi zai kai haka ba. Bayi jin zai taɓa danasanin haɗuwa da Ikram a rayuwar shi, amma a kowace safiya yana buɗe idanunsa ne cike da nadamar sake Kulata da yayi da Auren wani a kanta. “Kina da Aure?” Ya maimaita tambayar shi cikin harshen da zai fi yiwa Ilham sauƙin fahimta. Ba zata iya jure kallon cikin idanun shi ba, don haka ta sauƙe kanta ƙasa kafin ta amsa da “eh”. “Look at me. I can't hear you if you don't look at me. Kunnuwana basu aiki” Tabbacin da ta samu kenan a kan wannan ba A Moher bane. kama ce kawai da Ubangiji yake sanyawa a tsakanin wasu daga cikin halittun sa, amma a iya saninta babu wani dalili da zai saka kunnen A moher su daina aiki bayan garau yake ji da su a lokacin baya. Ajiye tunanin A moher tayi a gefe ta buɗe baki tace ma Abdulhameed “Eh, ina da shi” Ya furzar da Numfashi. Shikkenan babu ruwan shi. Duk abinda take ciki babu ruwan shi, ba zai yi gangancin sake maimaita kuskuren shi ba, ba zai ƙetare iyakar shi ba, zai tsaya ne a iya iyakar abinda ya sake haɗa su. Haɗiye duk tarin tambayoyin dake kan harshen shi yace “We're done eating” Ta miƙe da nufin tattara kwanukan abincin sai ya mayar da idanun shi kan program ɗin da Kiki take kallo kada ma ya sake kallonta. Saida yaga ƙulewarta kitchen sannan ya tashi daga kan dining ya ɗauki kiki suka koma light brown couch dake fuskantar TVn suka zauna. Ilham ta dauko Tupperware a cikin cabinet ɗin da aka gwada mata ta juye sauran abincin sai kawai ta yanke shawaran ɗaura abincin dare ɗiyanin. Sanwan tuwon semovita ɗinta da miyan taushe suna zaɓalɓaka ta fita don ta gabatar da sallan La’asar, bata ga Abdulhameed ko Ikram a parlor ba da zata wuce, sai TV dake ta ɓaɓatun sa shi kaɗai da kayan wasan Ikram ɗin dake barbaje. Ta ƙarasa ta kashe musu TVn ta kimtsa wurin Sannan ta wuce, amma har ta idar ta koma ta tuƙa tuwonta ta kwashe ta sake jere musu a kan dining bata ji ɗuriyar su ba. Ganin biyar ɗin da suka yi yarjejeniya a kai da Aunty Surayyah yana niman wucewa yasa ta jawo musu ƙofar gidan ta koma wurin Aunty Surayyah don ta sanar da ita zata wuce asibiti. Tayi sa'ar ganin an share tsakar gidan, amma maiƙon abincin na nan ƙudaje suna kan bi, ta ɗauke idanunta tana gaida manyan matan da taci karo da su a wurin har ta isa ɗakin Aunty Surayyah ta ƙwanƙwasa. “Bismillah shigo” Muryar Aunty Surayyah ya fito daga ɗakin. Ta tura ƙofar ta shiga da sallama a bakinta. Ilham ta rage tsayinta a gaban kujeran da take zaune da takardu a kan ƙaramin teburin da ta ajiye a gabanta tana rubutu a kai. “Hajiya na gama komai kaman yanda kika ce” “Sannu da aiki Malama Ilham” Hajiya Surayyah ta ajiye biron hannunta ta miƙe tsaye ta shiga ciki sannan ta dawo da farin envelope a hannunta ta miƙa mata. Gashi, dubu talatin ne a cikin kuɗin aikin ki zan fara baki tunda kince kina da mara lafiya a asibiti, sai ki fara rage wani abu kafin a cika miki sauran idan lokaci yayi. Kyautatawa yana da daɗi koda a kan hakkinka ne, musamman idan aka maka shi a lokacin da ka fi buƙata. Ta saka hannu biyu ta karɓa idanunta na tara hawayen murna, sai taga kaman kyauta ne aka ɗauka aka bata. “Hajiya Nagode, Nagode Hajiya Allah ya saka da mafificin alkhairi Allah ya jiƙan magabata” Ta amsa da “Ameen, Babu komai, sun cinye abincin da kika zuba musu da rana ne?” Ilham ta girgiza kai “A'a na juye sauran a roba mai murfi na saka a fridge.” “Ki je ki ɗauka ki tafi da shi. Idan sun rage abinci kina tafiya da shi ko ki bayar ma masu buƙata” Ta amsa da “toh” ta miƙe tana sake godiya. Sai ta shiga bangaren ta ƙofar baya dake kitchen, ta juye shinkafar a laida ta wanke roban ma, ta fito zata fita ta ƙofar parlor saboda zai fi mata sauƙin fita gate, amma sai idanunta suka sauƙa a kan damatsen Abdulhameed dake waje saboda baƙin singlet ne kawai yanzu a jikin sa da gajeren wando, ya baiwa ƙofar kitchen ɗin baya. Shima ganin lokacin tafiyar nata yayi sai yayi tunanin ta tafi, kuma idan yana son hutawa sosai, ko in aiki suka yi mishi yawa yana son yayi ya gama da wuri, ya fi jinsa a sake idan babu nauyin kaya a jikinsa. Bata bari Kiki dake buga Ball a tsakar parlorn ta lura da ita ba ta lallaɓa ta koma ta inda ta fito. Napep ta hau tunda akwai isasshen kuɗi a hannunta. Bata taɓa ɗokin ganinta a asibiti ba kaman na yau. Tana isa ta fara gwada ma Ihsan kuɗin da aka bata, ta juye musu abincin da ta dawo da shi a plate tace su ci kafin ta je ta siyo magunguna da alluran Muftee ta dawo ta bata labarin duk abinda ya faru. Suna cikin hiran wayan Ilham ya fara ruri, da ta duba sai taga babu suna, amma sai ta ɗaga kiran ta ƙara a kunne tare da yin sallama. “Waalaikis salam, Fidela ina kwana” Jin sunan da aka kira ta dashi ya saka ta ɗan yi shiru tana ƙokarin ɗago muryar waye. Da hakan ya gagara sai ta amsa da “lafiya” “Yaya gida, yaya jikin Baban mu” Ta sake amsawa da “ da sauƙi alhamdulillah” sannan ta ɗora da “amma ka gafarce ni ban gane waye nawa ba” “Sageer ne” ya amsa kai tsaye. Saida ta ɗan ƙara wasa ƙwaƙwalwarta kafin ta tuna shi. Ɗan yayan baban su ne, baffa Umar, wanda daga mahaifin Hashim sai shi. “Ayya yi haƙuri yaya Sageer, ka san an dade ba'a gana ba shiyasa muryar ya kwanta mun” Dogon tsakin da Ihsan ta ja jin ta ambaci sunan yasa Ilham ta kalleta. Nan ta ɗago dalilin kiran da sageer ɗin yayi mata don ta so tayi mamakin yanda ma aka yi ya samu numbernta. Sageer yace “Gaskiya ne, kuma ban kyauta ba na sani amma in Allah ya yarda daga yanzu zan gyara, duk sati zan dinga kira ina jin lafiyar baban mu” Ilham ta murmusa “Haba duk sati? Sau ɗaya ma a shekara ya isa.” “haba auntyn mu kada kiyi Fushi mana.” “Ni nace maka nayi fushi? Ba gashi yau ɗin ka kira ba” Ya ɗan yi murmushi “Toh idan tana kusa dan Allah a ɗan bata” “Wacece?” Ta tambaya kaman bata fahimta ba. “Filiyan. Dan Allah” Ganin yanda Ihsan take girgiza kai kaman ƙadangariya saida ta ba ma Ilham dariya. Ta gimtse tace “toh gata nan” tana cire wayan daga kunnenta ta miƙawa Ihsan. Saida ta harari Ilham kaman idanunta zasu faɗo ƙasa kafin ta karɓi wayan ta ƙara a kunne. Kaman wanda aka cusawa tsumma a baki haka tayi sallama. Kuma duk abinda Sageer ɗin zai ce mata daga ta amsa da Uhm, sai Uhm-uhm, tana yi tana murguɗe-murguɗen baki, har ta gaji da sauraren shi ta datse kiran ba tare da sun yi sallama ba. “Baki da kirki yarinyar nan” cewar Ilham tana ɓare lemon ɓawo da yatsunta. “Wallahi bana son haka Aunty Ilham bana so! Ai na san abinda nake yi na ƙi ɗaukan wayar tashi. Ko so kike yi nima in shiga wannan azababben familyn in ɗora daga inda kika tsaya?” Saboda ta tsokane ta Ilham tace “kin san dai duk inda kika je kika dawo auren dangin nan dai shine, ko wa kike dashi kike ruɗin kanki dole haka zaki dawo gida ki samu mijin aure, gwamma ma ki samu mai son ki mai lallaɓa ki zai fi miki” “Allah ya kiyaye! Ni da Ahalin Baniza saidai alaƙa ta jini da babu yanda ka iya da shi amma ba zan taɓa aure a cikinsu ba tunda mai tilastawan yanzu babu shi sai inga wanda zai min dole” Ilham tayi murmushi, tunawa da yanda suka so Juna ita da Muhsin, kaman ba zasu rabu ba. Haka ta dinga koran maneman ta wa’inda suka zo da shirin su na Aure Saboda lokacin Muhsin yana karatun shi na likitanci, sai a shekaran da zai kammala ta tsinci kanta a ɗakin wani da ba shi ba. “Ki ce In sha Allah” Kaman ba zata faɗa ɗin ba sai kuma ta maimaita har sau biyu. Ilham tayi murmushi ta mika mata rabin lemun da ta gama barewa, ta cire tsala daya a cikin ɗaya rabin ta saka a bakinta kafin ta saka sauran a hannun Muftee. …. Saida ya je masallaci ya gabatar da sallan Isha kafin ya ɗauko Ikram a kafaɗan shi zasu ci abincin dare, ya ja kujeran dining ya zaunar da ita shima ya zauna sannan ya shiga buɗe kwanukan abincin da Ilham ta ajiye musu. Ganin miyan taushe a flask ɗin farko yasa jikin shi yayi sanyi tun kafin ya buɗe tuwon semovita dake ƙyalli a cikin laidan da aka ɗaure su zam-zam. A cikin sharuɗan da ya zayyana ma Aunty Surayyah ya manta bai lissafo abubuwan da baya ci ba. Sai dai daman mai raino ya ɗauka ma Kiki ba wai mai aiki ma kan shi ba, tana girki ne a gidan saboda Ikram ta ci ba don shi ba, bai ma taɓa ɗaukan nannyn da ta taɓa girka abinci ya iya ci ba sai Ilham. Shi dai burin shi kawai a cika mishi cikin ɗiyar shi, in yaso shi yana fita yana niman abinda zai saka a nasa cikin ko kuma yayi ordering takeout ya ci a gidan. Amma da ya buɗe kwanon shinkafan rana da nufin zubawa Kiki, tururin ƙamshinsa ya bugi hancinsa, sai ya samu kansa yana ci shima har saida ya koshi, shiyasa yanzu ma yayi tsammanin ta dafa abinda zai ci ne. Ganin bai fara zuba musu abincin ba Kiki ta taɓa shi “Daddy yunwa” ta ɗaura hannu a saman cikinta tana yamutsa fuska. Tuwon ya saka guda ɗaya a plate da miyan kaɗan sai naman da yake saka ran shi zai iya taɓawa. A lokacin da suka tashi daga table ɗin sauran kullin tuwo guda ɗaya a cikin huɗun da Ilham ta saka a cikin food flask ta rufe. Kuma ba zallan Kiki ba har Abdulhameed ya ji daɗin cikan da cikinsa yayi damm. *Washegari* Ƙarfe 7 na Safiya ya yiwa Ilham a gidan, ko karyawa bata yi ba don mai mashin ma yana jiranta a waje ta samu ta miƙa ɗanwaken da tayi ma su Ihsan a asibiti suka juyo. Amma saida ta shiga ta gaida Aunty Surayyah kafin ta shigo ɓangaren Abdulhameed dake a buɗe, ganin babu kowa a parlor sai ta wuce kitchen kanta tsaye ta. Ta sha mamakin ganin har plates da cups ɗin da ta ajiye musu tare da abinci jiya a wanke an tanada su a inda ya dace, babu wani abu mai datti a cikin sink. Ta buɗe fridge da tunanin abinda ya kamata ta dafa musu na karyawa sai taga sauran tuwon da ya rage da miya an tanada shi a cikin takeaway daban-daban. Abun ya burgeta sosai, don ko lokacin da take da fridge duk yawan abinci idan ta zuba ma Hashim yaci ya bari haka zai barshi ya kwana a cikin kwano yayi yauƙi, sai dai da safe idan ta dawo daga asibiti ta zubar ba kuma wai don sun wadata da abincin ba. Ta ciro ƙwai uku da kayan miya ta ajiye kana ta ɗauki doya ta fere ta zuba a tukunya non-stick da irin su kawai ta gani jere a kitchen ɗin, ta zuba ruwa da gishiri ta kunna mishi wuta, kayan miyan kuma ta markaɗa shi baya-baya a grinder. Mantawa da zancen yarinyar bata cin yankakken albasa da Hajiya Surayyah tayi mata jiya, sai ta ɗauko karamin tukunya ta zuba mangayada a ciki ta yanka albasa mai yawa ta zuba ta dan fara juya shi kafin ta zuba sauran kayan miyan a kai. Cikin kanƙanin lokaci ta kammala sauce ɗinta ta kashe masa wuta, sannan ta koma kan doyan da yayi laushi ta kaɗa kwai ta soya shi. Saida ta jera komai a kan dining sannan ta wuce ɗakin Kiki don tayi mata wanka da shirin makaranta. Ihun da yarinyar ta dinga zundumawa kafin ta gama shiryata da kokuwa ba tare da Abdulhameed ya leƙo ba ko sau ɗaya ba, ya tabbatar ma Ilham kunnuwan shi basa aiki. Faran fuskar nan tata tayi jaa lokacin da suka fito suka samu Abdulhameed cikin shirin fita aiki sanye da navy blue shirt da baƙin wando. Ta zame daga jikin Ilham da gudu ta ƙarasa ta faɗa jikin shi tana sabunta kukanta. A kiɗime ya ɗago fuskarta yana tambayan abinda ya sameta, fitowa da yayi yaga an shirya abinci a dining ya fahimtar dashi Ilham tana gidan, shiyasa ya zauna yana jiran ta fito da Kiki don bayi son ko karo suna yi da juna a cikin gidan. Cikin sheshsheƙan kuka tace “Ha…ha.. hannuna Daddy” tana ɗaga mishi hannun da ta targaɗe a jiki. Ya ɗago ya kalli Ilham dake tsaye daga gefe tana kallon taɓara, nata yaron bai isa yayi mata abinda Kiki take yi ba tare da ta gyara masa zama ba. “Ba’a faɗa miki hannunta na ciwo bane?” ya tambaya. Sauƙe idanunta tayi daga kan Kiki zuwa ƙasa, sannan ta gyaɗa kai a hankali jin yanda yayi maganan da faɗa. “Look at me and talk to me Ilham!” Ta ji yanda ya cire H ɗin cikin sunan nata, kaman yanda A Moher yake yi, amma dake ba abinda yake gabanta ba kenan sai hakan bai bada wata ma'ana ba a cikin kanta har ta ɗago ta kalle shi kaman yanda yace. “An faɗa mun, amma ban taɓa mata ciwo ba” Hasalima ko soso bata saka a hannun ba da zata yi mata wanka, daga kafaɗanta zuwa guiwan hannunta kawai ta wanke ta ɗaurayeta, kuma ko da take riƙeta tana tirjewa ta mayar da hankali wajen ganin bata taɓa hannun ba saidai ta riƙeta da ɗayan. “Idan baki taɓa mata ciwo ba bazata ce kin taɓa mata ciwo ba” Ƙarya kenan zata yi ma Kiki?, da girmanta zata yi ƙarya ma ƴar cikinta?. Tunawa da Huɗubar Hajiya Surayyah yasa tace masa “Kayi Haƙuri” kawai. Ya haɗiye rabin ɓacin ransa ganin wannan shine karo na farko, zai gwada yi mata uzuri. “Be extra cautious next time, please” yace yana maida nasa idon kan Kiki da ya ɗaura ta saman cinyar shi yana share mata hawaye da handkerchief. Ganin haka ta fahimci ya sallameta sai ta juya ta koma kitchen, sauran doyan da ya rage ta zauna ta ci. Ta fara da wanke-wanke da sharan kitchen kafin ta fito ta samu babu su parlor, ta duba kwanon da ta saka musu abinci babu komai a ciki harda sauce ɗin albasan sun cinye tass. Ita sai a lokacin ta tuna ance yarinyar bata cin yankakken albasa. Tayi murmushi kawai ta kwashe kwanukan ta kai sink. ``````````` Seemahwrites ✨ ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh JODA by Sadi-sakhna DAƊIN ZAMA by Seemahwrites *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a turo shaidan biya ta 09039206763 Chapter 18 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Wattpad and Arewapen @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 18… Idanun shi ita suke kallo, tana zaune daga gefen shi a gidan baya, a cikin seat ɗin da ya katange ta da seatbelt, Amma zuciyar shi ta koma nazarin abinda ya faru ɗazu a tsakaninta da Ilham. Kaman yanda yace, har cikin zuciyar shi ya yarda Kiki ba zata yi ma Ilham ƙarya ba tunda ya fi kowa saninta a duniyar nan, tun tana cikin tsumma yake kula da ita har zuwa yanzu. Amma sai yake jin kaman wani dunƙulen abu ya tsaya a ƙirjin shi tunda Ilham ta buɗe baki ta bashi haƙurin nan, kuma duk yanda ya kai hannun shi ƙirjin ya shafa inda yake jin abun ya gagara bajewa. “Kiki” Ta buɗe idanunta da suka fara lumshewa a kan shi, kukan banzan da ta gama sha ne yasa taji jikinta yayi laƙwas. Sake tambayarta a kan taɓa mata ciwon da tace Ilham tayi yaso yayi, amma da wa’innan manyan fararen idanuwan suka shiga cikin nashi, sai yaji wannan shine mafi girman rashin adalcin da zai yi ma kanshi, idan har zai yarda da baƙuwa a cikin rayuwar su fiye da yarinyar da yasha kwana da yunwa saboda ita ta ƙoshi. “Kada kiyi barci school zaki je” Muryar shi tana sauƙa ne ko ta tashi da control ɗin emotions ɗinsa. Kaman yanda ji yake taimakawa yanayin fitar sauti daga bakin mutum mai cikakkiyar halitta shi zuciyar shi ne take wannan aikin a maimakon kunnuwan da suka mutu suka barshi a tsaye. Shiyasa idan ranshi ya ɓaci sai muryar ta fito da ƙarfin da ya wuce ƙima, haka ma idan yana cikin nutsuwarsa sai muryar ta fito da taushi kaman yanda yayi magana da Kiki a yanzu. Sai ta kwaɓe fuska ta cigaba da ƙananan kuka. Da ya barta ta fara baccin ta san saidai ta buɗe ido ta ganta a kujeran office ɗin shi ya saka an fasa zuwa makarantar sun tafi tare. Fitowa yayi riƙe da pink schoolbag ɗinta bayan sun yi parking a gate ɗin makarantar, ya zago ta bangaren ta ya buɗe mata ƙofa, ya ranƙwafa ya cire mata seatbelt ɗin kana ya miƙa mata hannu, ta maƙe kafaɗa tana narai-narai da idanu. “Zan dawo miki da ice cream. I promise” yace yana ƙara miƙa mata hannun shi. Sai yaga ta kama shi da hannunta na dama ta fito a cikin motar. Kanshi ya sake kullewa. Hannu mai ciwon da ta kawo ƙaran Ilham ta fama mata kenan, wanda ta samu targaɗe a jiki. Ya rage tsayinsa ta hanyar durƙusawa a gabanta yana kallonta, amma ya kasa cewa komai, saboda fuskar mahaifiyarta yake gani a duk lokacin da ya kalleta, macen da a duk lokacin da ta aikata ba daidai ba a wurin shi take samun mafaka koda ya san da abinda ta aikata. Jakan ya rataya mata a bayanta ya gyara mata zaman hearing aid ɗinta sannan ya shafa gashin kanta da Ilham ta tufke mata shi. Yana kallo har ta wuce cikin gate ɗin tare da sauran ƴan makaranta sannan ya koma cikin motar drivern shi ya ja suka ɗauki hanyar A&I. 9 ta gota da ƴan mintuna lokacin da ya shiga cikin office ɗinsa. Ga mutanen da suke zaune a waje suna jiran shi, ga tarin takardu a kan teburin shi harda na aikin da suka fara last week da kuma wanda ke zuwa a gaba. Nutsuwan da ya samu ɗaya, bayi bukatar nan da wasu awanni ya sake fita dauko Kiki daga makaranta tunda tana da Nanny yanzu, sannan makarantar tasu da nisa sosai saboda saida ya nemi inda ake bawa yara abinci mai kyau da inganci ya sakata tunda ba iya haɗa mata lunch box kullum zai yi ba. ….. ILHAM Jiya ta daɗe a asibiti suna hira da Ihsan, tana bata labarin irin abubuwan da ta gani a gidan da take aiki har suka gangaro kan abinci, tana mafarkin itama ace wata rana gidanta ne ya wadata da kayan abinci da abubuwan sarrafa shi irin haka, a ce komai tana da shi a cikin store ko a kitchen cabinet ko a fridge, ita da yaronta su ci abinda suka so a lokacin da suka so kuma mai daɗi mai ƙara Lafiya. “Idan kuma rabona na gidan duniya bai kai haka ba ina miki fatan Allah yasa ki samu filiyan. Ko ba miji mai tarin dukiya ba Allah ya baki miji mai zuciya wanda ya fi ƙarfin Abinda za'a ci a gidansa” Abinda tace ma Ihsan kenan jiya. “Shine kuma kike mun fatan Auren Sageer Umar Baniza a hakan?” Ihsan ta kalleta a kaikaice. Ilham tayi murmushi “Ai ƴan familyn Banizan ba taruwa suka yi suka zama ɗaya ba, tunda mahaifin mu ma mutum ne mai ƙoƙari, sai kiga shima ya riƙe mana ke da amana” “Allah ya kiyaye wallahi” ta ja tsaki tana juyo ma Ilham fuskar wayanta dake kan wani shafin girki ta gwada mata wani fried spaghetti da meatballs. “Gobe kiyi musu irin wannan abincin ki kawo mana sauran” “AL Mayya’u” Ilham ta kai mata dukan wasa kafin ta karɓi wayan tana kallon yanda aka haɗa. Saida ta kalli video ɗin sau uku ta tabbatar ta haddace yanda aka haɗa da abubuwan da aka zuba sannan ta wuce na gaba, haka tayi ta kallon girke-girke, Idan lokacin Sallah yayi ta tashi tayi ta dawo ta cigaba da kallo har saida datan Ihsan ya ƙare ta haƙura. Ta bata dubu biyu a cikin kuɗin da ya rage ta sayi Datan a ciki, tunda ga zaman wuri ɗaya sai ta ɗan samu na kashewa a hannunta sauran kuma zasu dinga amfani da shi wajen zirga-zirga. Yau bayan su Abdulhameed sun fita sun bar mata gidan sai ta shiga gyara shi tana yin faɗa ma kanta a kan Kiki tunda gashi har an fara samun matsala a rana ta biyu, zata yi ƙoƙarin binta a yanda take a zauna lafiya, ba zata yi saken da zata rasa aikin da har ya fara rufa mata asiri ba. Da ta gama ta dawo kitchen haɗa abincin rana kafin lokacin da aka faɗa mata zasu je ɗauko ta a makaranta yayi sai tayi karambanin haɗa spaghetti da meatballs ɗinnan, bayan ta gama ta yi juice ɗin kankana ta saka a fridge yayi sanyi sannan ta shirya ta samu driver a waje yana jiranta. Gaban motan ta shiga, bayan ta gaida shi ta ja bakinta tayi shiru tana kallon hanya. Yau a mahanga daban take kallon mutane, saboda bata cikin wa'inda ke tafe a kan sawayen su cikin zafin rana ga tarin damuwa, sai taga garin yayi mata daban, gashi tafiya kawai suke yi sumul ko ƙaran tafiyan motan bata ji sai sanyi da ƙamshi mai daɗi dake ratsa ta. Ta ɓalle marfin motan ta fita ta ƙarasa wurin masu tsaron makarantar bayan sun isa, “Sannun ku da aiki nazo ɗaukan Ikram Abdulhameed a Nursery One” Saida ta jira a ƙofar wurin aka kawo mata Kiki wanda ta fito da murnanta a tunaninta daddynta ne yazo daukanta, amma ganin Ilham sai ta ɓata fuska kuma taƙi zuwa. Da ƙyar drivern ya lallaɓata ya dauketa ya saka a bayan mota, bai manta kashedin Abdulhameed a kan saka mata seatbelt a koda yaushe ba kafin Ilham ta koma gaban motan suka dawo gida. Ilham tana cire mata seatbelt ta bangaje ta tayi cikin gidan da gudu tana niman babanta, saida ta gama dubawa bata gan shi ba ta dawo wurin Ilham. “Fitsari” tace tana rawan mazari. Ilham ta riƙe hannunta zata kaita toilet ta tirje a wurin. “Ni ki ɗauke ni” Haka ta sunkuya ta ɗauketa har kofar banɗakin sannan ta ajiyeta a kan tayi addu'a ta shiga da kafar hagu sai kawai ta shige da gudunta bata yi addu'an ba ta ɗaga skirt ɗin uniform ɗinta ta zame farin leggings da pant dake ƙarƙashin sa tayi abinda yake gabanta tukunna tace Ilham tayi mata tsarki. Haka da ta canza mata kaya ta zuba mata abinci zata bata a baki kaman yanda taga ake mata sai taƙi amsa, ta karɓi fork ɗin a hannunta na hagu tana ci tana zubarwa. Ganin ba zata iya cigaba da shiru ba tace “Kiki ba kiyi bismillah ba” Bakinta a cike da dunƙulen naman da ta tusa tace. “Bismillah. Ina daddy na?” “anjima kaɗan zai dawo” “Ni ki kaini wurin shi” “Sai idan kin gama cin abinci” ta amsa ta tana tsince taliyan da take zubarwa kan table ɗin tana mayar mata cikin plate ɗinta. Saida ta cinye abinda ke kan Plate ɗin tass tace a ƙara mata, kwatsam sai ga Abdulhameed ya faɗo cikin gidan babu notice, ko sallama bai yi musu ba, don yana so ne yaga yanda Ilham zata ke kula da kiki a bayan idon shi. Ilham dake zaune a kan kujeran dining da yake gefen na Kiki sai ganin shi kawai tayi a kansu, bata ma ji lokacin da ya buɗe ƙofar shigowa ba. Tayi saurin miƙewa tsaye tana kallon shi, ta ma rasa me zata yi, Allah dai ya taimaketa da hijabi a jikinta sanin ba gidanta bane bata da hurumin cirewa. Kalmar “sannu da dawowa” ta laluɓo a kan harshenta, sai ya gyaɗa mata kai fuskar shi a sake, babu wannan ɓacin ran da ya fita da shi da safe. Kiki ta sauƙa daga kujeran murna duk ya cikata, zata yi kan shi da gudu Ilham tayi saurin ruƙota ta dawo da ita sannan ta zari tissue ta goge mata maiƙon bakinta kafin ta saketa ta ƙarasa gudun da ta fara ta rungume ƙafafun Abdulhameed. Ajiye laidan hannun shi yayi a ƙasa ya ɗauketa. Ganin haka Ilham ta ɗauki hanyar komawa kitchen ta basu wuri, sai ya kirata. “Ilham” Ta tsaya cakk amma bata juyo ba. Muryar ta canza amma yanda yake kira iri ɗaya ne. Iri ɗaya da A Moher, anya ba shi bane wannan?. Ya ƙara cewa “ki ɗauki ɗaya” Da ta juyo sai taga laidan da ya shigo da shi yake gwada mata. Ganin ba zata ƙarasa ta ɗauka din ba sai ya sunkuya riƙe da kiki ya ciro roban Ice cream guda ɗaya daga cikin laidan, ya bayar ma Kiki ta riƙe tana ta murna sannan ya miƙa ma Ilham laidan da sauran abinda ke ciki. Ta tako kusa da su kaɗan ta rage tsayinta Sannan ta tallafe ƙasan laidan da hannayenta biyu. “Na gode Allah ya saka da alkhairi” Ya sake mata laidan yana juyawa riƙe da yarinyar shi a cikin ran shi yana fatan idan ta sha Ice cream ɗin ya sanyanta mata zuciya a kan faɗan da yayi mata ba tare da laifinta ba. Ko yanzu saida ya sake taɓa hannun Kiki da tace yana ciwo amma ko lura bata yi ba, kuma da shi ta karɓi roban ice cream ɗin da ya bata. Sauran abincin da Ihsan take zaman jiran a kai mata bai samu ba, haka Ilham ta sake ɗaukan kwanon dake kan dining bayan sun gama babu komai a ciki, sai sauran ice cream zata kai musu ta rarrasheta da shi. Isanta ke da wuya ta samu Khausar tana zaune da basket ɗin abinci a gabanta, Ihsan tana daga gefe tana danna wayanta ta bar Khausar ɗin tana tsuru-tsuru kamar marainiya. “Aunty Ilham” ta kirata da wannan muryar da a da yake mata kama da na marasa wayo ashe na Munafurci ne. “Sannu khausar” tace da ita tana ƙarasawa ta kusa da gadon. “Spaghetti da meatballs ɗin kenan?” Ihsan ta wafce laidan hannunta fara'arta yana dawowa saman fuskarta, daman ba shiri suke yi da khausar ba tun da kuma bata jin zasu fara a yanzu shiyasa da suka gaisa sama-sama sai ta kama kanta. Ilham ta barta saida ta buɗe taga abinda yake ciki sannan tace “Ai daman ban ce miki zaki samu ba” Ƙwafa tayi kawai saboda Khausar dake zaune a wurin ta ciro Ice cream ɗin ta fara sha. “Ki rage ma Muftee amma sai ya narke sanyin ya fita kafin a bashi” Ta juya wurin khausar dake dogon wuya tana leƙa abinda ke cikin robar “ko zaki sha ne Aunty Khausar?” Dariyan yaƙe tayi, “A'a wallahi nagode, ai ina ta jiran ki ne nima na cika alƙawarin da na ɗauka, na musamman nayi miki girki yau” “Ayyah Nagode, gashi ina ƙoshe ni, saidai Filiyan su ɗiba in kai sauran ma Ya Hashim, mun gode sosai” Ta saki wani murmushi kaman na dole, gabaki ɗaya a tsarge take tunda Ilham ta iso amma ta gagara tashi ta tafi, ganin ta kasa kunnuwa tana son ta ji gulma yasa ko Ihsan ta ɗauko hiran gidan aikinta sai ta kawar da zancen kafin Khausar ta rigata kai ma Hashim labarin ta fara aikatau. Ana kiran sallan Isha ta ɗauki kwandon abincin tace Khausar ta taso su tafi, ko babu komai ta hutaceta komawa ta daura tukunya. Suka shiga napep ɗaya aka fara sauƙe khausar a gidan su kafin aka wuce da ita. Har saida ta gyara ɗakin da Hashim ya gama wargazawa tayi wanka ta fara hutawa kafin ya dawo. Ganin yau ya shigo yanayin shi babu laifi yasa tana gabatar mishi da abincin Khausar ta zauna a gaban shi ta tanƙwashe ƙafafu. “Baban Muftee daman aiki ne na samu” “Aiki? Yaushe aka fara daukan jahilai aiki? Ko kina da kwali ne da ban san da shi ba?” Bata san a wani bangare na jikin shi furta kalma mai daɗi yake gutsuran shi ba. “A wani gida ne na samu” “Bauta dai zaki ce ba aiki ba” A cikin ranta tace ai gwamma shi akwai sakamako mai kyau duk wata. A fili kuma cewa tayi “Eh shi” “Toh yanzu izini kike nema ko sanar da ni kike yi?” Ya maimaita mata irin tambayar da yayi mata lokacin da ta sanar da shi zuwan Ihsan. Saboda a zauna lafiya tace “Izini nake nima” “Toh ban yarda ba” ````````` Seemahwrites ✨ ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh JODA by Sadi-sakhna DAƊIN ZAMA by Seemahwrites *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a turo shaidan biya ta 09039206763 Chapter 19 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Wattpad and Arewapen @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 19… Kallon shi take yi da idanunta da suka fara tara ƙwalla ba tare da ta sani ba saida yawan hawayen ya fara disashe kallon mamakin da take mishi. Bata taɓa tunanin akwai wani hanyar samu da zai taɓa zuwa mata Hashim yayi yunƙurin datse mata shi ba, shi dai ba zai bata ba amma ba zai hanata nemowa ba koda naman jikinta ne zata ke gutsura tana siyarwa ko kuma ta tafi har bangon duniya ta dawo wannan ba damuwan shi bane, amma bata taɓa sanin muguntar shi ta kai haka ba. Yawan dalilan da yasa take buƙatar aikin saboda gazawar shi da suka zo kanta idan tace zata fara zayyano masa su daga ita har shi a wurin zasu kwana. “Meyasa?” shine kalmar da a hanyar shi na gangarowa ya biyo kan harshenta, sauran kuma zuciyarta suka wuce suka taru a kan sauran nauyin da ke kanshi suka ƙara matse shi a ƙirjinta. “Saboda haka naga dama Ilham. Saboda na Isa!” Yayi maganar cikin isan da ya san yana da shi. Ta rufe idanunta hawayen ciki suna samun daman gangarowa saman kuncinta, ji take yi kaman idan ta buɗe su ta ganta a wata duniyar daban da wannan, ko wannan ɗinma tana so idan babu Hashim a cikinta. “Ko kuma ki zaɓa tsakanin tura ƙanwar ki gida da bautan da kike son zuwa, dole zaki haƙura da ɗaya” yayi magana yana ɗauraye hannun shi a cikin kwanon da ya gama cin abinci, hawayenta ba damun shi yake yi ba, shi dariyarta ma a yanzu ya fi bashi haushi. Ta yaya zata iya zuwa aikin a yanzu ma bayan Muftee na kwance a asibiti idan babu Ihsan?. Zuwanta ne yasa har ta ji ƙwarin guiwar amsawa Hajiya Surayyah cewa zata yi, har tunanin ƙarewar hutun makarantar Ihsan ɗin take yi ba tare da an sallame su ba, saidai idan zata dinga barin Muftee shi kaɗai kenan ta je nima masa kuɗin magani da abinci. “Dan girman Allah ka yi haƙuri kayi ma ɗana rai ya Hashim. Duk abinda nake yi ka san saboda shi ne, idan ba haka ba kuma ka karɓi ragamar jinyar shi sai in saka Ihsan ta koma gida, nima na gaji!” …. A Rana ta uku kawai, tun ba'a je ko ina ba Ilham ta fara makara, bayan duk gargaɗin da ya saka aka yi mata kafin a ɗauke ta, gashi ta jawo masa latti daga shi har Kiki, domin da ya san zata kai har wannan lokacin bata zo ba da ya shirya Kiki tun da wuri ya haɗa mata abinda zata ci. Cire agogon hannun shi yayi ya naɗe hannun rigan jikinsa, ya riga da ya gama shiryawa cikin shirt kalar green mai duhu da wando ruwan madara, ya tuɓe Kiki yayi mata wanka ya saka mata uniform amma har suka fito parlor babu alamun Ilham. Ɓacin rai ne ke niman kama shi, yana fatan tana da uzurin da zata tsayar a gaban shi mai girma, idan ba haka ba kuma zai haƙura da ita a sake niman wata. Cereal ya haɗa ma Kiki ta sha, ya zuba mata cookies da chocolate a cikin jakarta sanin ba zai riƙe mata ciki na tsawon lokaci sosai ba. Yana durƙushe a gabanta yana saka mata takalmi ita kuma ta dafa shi kada ta faɗi aka turo ƙofar tare da sallama. Abinda yake yi ya cigaba tunda bai ji ba, har saida Kiki ta taɓa shi tayi masa nuni da inda Ilham ke tsaye sannan ya juyo ya dubeta, ya miƙe tsaye yana kallonta ba tare da ya gama saka ma Kiki takalmin ba. Fuskarta da ta duƙar yake kallo, yana ƙoƙarin tabbatar da abinda yake gani idan ba idanun shi ne suke masa gizo ba. Bruises. Gefen bakinta kusa da birthmark ɗinnan a fashe yake, kumatun ta kaman wanda tayi hatsari ta faɗo a kan mashin, ga idanunta ɗaya da ya kumbura har bata iya buɗe shi da kyau. Leɓen bakin shi ya ciza ƙwallan ɓacin rai na taruwa a cikin idanun shi. “Who did this to you?” Ya tambaya cikin wata iriyar murya bai ma lura da haƙurin da take bashi na makaran da tayi ba, da uzurorin da take ta haɗawa tun fitowarta daga gida ko zata samu ya aminta. Yau ko abincin asibiti bata kai ba ta ƙaraso nan, bata ma jin zata iya dafa abincin don duk jikinta ciwo yake yi. Ta ɗago idanunta ta ɗora a kan fuskarsa, ɓacin ran da ta gani a cikin idanunshi saida ya bata tsoro. Shi kuma Ikram yake kallo. Ikram Aminu Yashi. Tsaye a gaban shi da kwatankwacin bruises ɗin dake kan fuskar Ilham a yanzu. “Duka na yayi Abdulhameed. Duka na yayi” Ya Lumshe idanun shi da nufi kawar da wannan hoton daga cikin kan shi, Ilham ce yanzu tsaye a gaban shi ba ita ba, Bruises ɗin fuskarta ne damuwan shi. “Babu kowa” ta amsa kafin ya kai ga sake tambaya. Ta ɗora da “don Allah kayi haƙuri ba zan sake kaiwa iwar haka ba” Babu kowa da tace ya bashi amsar da yake nima, ya kawar da kan shi gefe yana furzar da Numfashi, leɓen bakinsa dake rawa yake kan cizawa ya samu ya daidaita kansa. Wannan ba huruminsa bane, shiga cikinta yana nufin ƙetare iyakar da ya saka tsakaninsa da Ilham kasancewarta matar aure. Saida ya ɗau lokaci mai tsawo yana danne zuciyar shi, ƙwaƙwalwar shi na tuna ma zuciyar abinda ya faru shekarun baya da abinda zai cigaba da faruwa a dalilin hakan, kafin ya samu ta haƙura ta fara hucewa a sannu. Ya katse shirun da faɗin “Okay” Ya juya wurin Kiki da ta samu wuri ta zauna ta ciro laidan chocolate daya a cikin jakarta ta buɗe tana ci. Ya ƙarasa saka mata takalminta ya ɗauke ta da schoolbag ɗinta, duk Ilham tana tsaye a wurin a tunaninta haushin rashin zuwanta a kan lokaci ne yasa tana wurin yake ƙarasa shirya ƴar shi da kan shi. Saida yazo wuceta zai fita yace “don't do anything, ki huta kawai, zan saka a kawo abinci you don't need to cook” Bai jira cewarta ba suka yi gaba suka bar mata gidan tare da jawo ƙofa a bayan shi ya rufe. Sai ta zube a ƙasan parlon kawai ta shiga rera kukan da bata samu ta iya yi ba tun jiya, sai sauƙe ajiyan zuciya ta dinga yi bayan Hashim ya gama jibgan ta kaman ƙato ɗan uwan shi. Babu wanda zata kai mishi kuka ya share mata hawaye, daga wa’inda ko sun sani babu abinda zasu iya a kai banda ta ƙara musu damuwa sai kuma wa’inda ko gawanta aka ɗauka aka kai musu aka ce gashi Hashim yayi ajalinta sai sun samu dalilin da hakan ya zamo laifinta. Kuka take yi mai zafi da gunji, tana jin ba don yaron da zai shiga mawuyacin hali a bayan ranta ba da ta mutu ta huta. …. Ran Abdulhameed a dagule suka sauƙe Kiki a makaranta ya wuce office. Ko da aiki sun ƙara mishi yawa saboda komawan da yayi gida jiya lokacin tashin sa bai yi ba amma yau ya kasa taɓuka komai sai tunanin halin da yaga Ilham a ciki ke masa yawo a kai. Da ya kasa haƙuri ne ya ɗaga waya yayi text ma Aunty Surayyah. Office ɗin shi babu nisa da nata amma yana jin nauyin zuwa ya sameta a kan wannan maganan, sai yake jin kaman hakan bai kamata ba, Saboda Ilham matar Aure ce, saidai tunda tana aiki a ƙarƙashinsa hakki ne a kan shi ya kula da ita. Ita ma Aunty Surayyan da taga saƙon shi sai bata zo office ɗin shi ba ta wuce gida kai tsaye. Bata samu Ilham a parlor ba da ta isa, ta duba ɗakin da aka bata nan ma bata ganta ba sai ta shiga kitchen. Tana baje a kan tiles ɗin ƙasan kitchen ɗin idanunta a rufe Hajiya Surayyah ta shigo, tsoro ya kamata ganin kaman babu rai a tattare da Ilham, da azama tayi kanta tana jijjiga ta. Ganin ta buɗe idon Aunty Surayyah ta sauƙe gauron ajiyan zuciya. “Ƴar nan mai ya same ki haka? Tashi mu tafi asibiti.” Ta tallafota suka fita har cikin jan motarta dake mashigar gidan daman ko kasheta bata yi ba saboda yanda Abdulhameed yayi mata bayanin halinda Ilham ɗin take ciki. Private hospital mafi kusa ta kaita aka yiwa Ilham dressing ɗin ciwukan jikinta, aka haɗa mata da magani tare da allurai, Sannan suka koma gidan, Aunty Surayyah tace ta kwanta a kan gado tayi barci har sai ya isheta. Wannan taimako da kulawan da ta samu ya saka ta ji sanyi sosai a ranta, ɗacin da take ji a zuciyar ta ma ya ragu, ga alluran da aka yi mata ya rage mata raɗaɗin ciwukan jikinta. …. ABDULHAMEED Ordern abinci yake yi a website ɗin wani restaurant bayan ya idar da sallan Azahar lokacin da saƙon Excellency ya shigo wayan shi cewa yana son ganin shi. Ya so ace ya je ya ɗauko kiki daga makaranta ne ya kawota office ɗin ta ƙarasa wuninta a nan su bar Ilham ta huta sosai, amma akwai yarjejeniya mai ƙarfi tsakaninsa da Excellency wanda yafi duk wani schedule dinsa muhimmanci, don haka yayi text ma Hajiya Surayyah ya roƙeta ta taimaka mishi ta ɗauko Kiki daga school akwai inda zai je. “No problem” shine reply ɗin da ta rubuto mishi. Sai ya koma cikin office ɗinshi ya ɗauki mouth spray ɗinsa da wallet ya rufe office ɗin ya bada makulli ma secretary ɗinsa ya tafi wurin Excellency. . . . Kallon Mutumin yake yi, kallo na tsanaki. Yana so ya bayar ma abinda yake faɗa muhimmanci amma ma'anar shi ta gaza haɗuwa a cikin kansa, bai fahimci dalilin ma da yasa ya same shi da zancen ba, amma ya zauna yana karantan abinda yake cewa daga farko har zuwa inda Excellency yake tunanin bayanin da ya kamata yayi ma Abdulhameed ta cika. “.... Kai kuma nayi maka alƙawarin zaka ƙara samun damammaki, hanyoyin samun ka zasu ƙaru, idan mulki ya shiga hannun mu ma kaga sai yanda muka so, rayuwar ka da na wanda suke jikin ka zai ƙara kyau ko ba haka ba?” Yayi ƴar ƙaramar dariya yana kallon Abdulhameed ɗin tare da shafa tumbinsa. Saida ya nisa cikin yanayin rashin fahimta yace “Allah ya saka min albarka a abinda nake yi sir, har muna samu mu taimaka ma wasu, kuma mutane sun yarda damu da abinda muke yi muna samun tallafi a kai a kai.” “Yauwaa kaga dalilin da yasa na zaɓi muyi amfani da hakan mu jawo mutane kenan, saboda sun yarda da kai. Idan ka cika min alƙawarin da ka ɗauka ni kuma ina tabbatar maka baka buƙatar tallafi daga wurin kowa” “A&I ƙungiya ce mai zaman kanta Sir, ina ganin kaman idan aka yi yanda kace ta koma ta gwamnati” Ganin Excellency yayi shiru yana kallon shi kawai da mamakin amsar da ya samu a wurin shi sai ya miƙe tsaye. “kaman yanda na ɗauki alƙawari duk wani abu da zaka saka ni a karan kaina zan yi maka shi duk wahala da hatsarinsa. Amma A&I Support organization bayi cikin yarjejeniyar mu. Zan je in duba yarinyata, na barka lafiya” Ya juya ya ɗauki hanyar fita sai ga mutumin da a ko yaushe da riga ƴar shara yake ganinsa da hula dara ya sha gabansa, fuskar shi a tamke ya buɗe hannunshi wajen Kare Abdulhameed daga ƙofar fita parlon. Fahimtar cewa Excellency ne bai gama magana da shi ba sai ya juya ya sake fuskantar shi ya ji abinda ya rage kuma. “Yarinyar wajenka… zan taimaka maka ka bata kariya na dindindin idan ka amince. Idan ba haka ba kuma wata rana ina tabbatar maka zasu dawo, zasu dawo da nufin karɓanta kuma babu yanda ka iya, duk wani wahala da sadaukarwa da kayi zai tashi ne a banza.” …. Da Aunty Surayyah ta ɗauko Kiki daga makaranta, ta shigo ma Ilham da abinci, kuma ta saka ta a gaba saida ta ci ta sha magani. Duk wani motsi da Aunty Surayyah zata yi wajen taimaka mata da wani abun sai tace “Nagode Hajiya” “Haba godiyan ya Isa haka na gaji da ji, ki bari bakin ya huta ko zai samu ya warke da wuri” Ilham ta ja bakin ta ɗinke. “Ki kalli yanda ya canza miki kamanni” Sai tayi ƙasa da kanta a kunyace. “Kuma zaki sanar da iyayen ki ne ko zaki yi shiru ya samu ƙwarin guiwar sakewa? Kafin yayi miki illa kinji..” “Iyaye na sun rasu” Ta samu kanta da bata amsa. Sai faɗan da Aunty Surayyah ta faro ya tsaya. “Magabata fah, waliyyi, wani babba wanda zai tsaya miki ya karɓa miki ƴanci baki da shi?” Ta ja hanci saboda kukan dake zuwa mata. “Iyayen shi sune magabatan nawa Hajiya, baban shi shine babban yayan su baban mu. Kuma ma shi suke bayar da goyon baya a duk abinda zai faru tsakaninmu” “Innalillahi wa inna ilaihirraji'un. Toh Allah ya Isa miki” “Ameen” tace tana share hawayenta da bayan hannu a ƙoƙarinta na kada ta sake fama ciwon idonta, Amma ta san Allah baya zalunci kuma baya son Azzalumai, tabbas zai saka mata wata rana. ````````` Seemahwrites ✨ ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh JODA by Sadi-sakhna DAƊIN ZAMA by Seemahwrites *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a turo shaidan biya ta 09039206763 Chapter 20 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Wattpad and Arewapen @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 20… Ganinshi kawai suka yi a tsaye, bai shigo ba amma babu wani shamaki a tsakaninsu dake ƙofar ɗakin a wangale take, maganar da suke ya saka babu wanda ya ji sallamar da yayi daga farko, shi kuma bai sake yin wani ba. “Daddy..” Kiki ta sauƙa daga kan cinyar Aunty Surayyah tayi kan Abdulhameed da gudunta. Idanun shi a kan Ilham lokacin da ta rungume mishi ƙafafu, suma shi suke kallo ita da Aunty Surayyah, sun riga da sun san shine kawai mai shigowa gidan kai tsaye amma ganin lokacin da yake dawowa bai kusa yi ba yasa suke kallon shi kaman baƙo. Nutsuwa kaɗan ya samu ganin idon Ilham ɗin ya saɓe gashi har ta buɗe tana kallonsa da shi, an rufe raunin kuncinta da bandeji, na gefen bakinta kuma an sakaye shi da wani magani mai kalan da ba na jini ba, ba kalan da a duk duniya ake amfani da shi matsayin alamar zafi, hatsari ko tashin hankali ba. Don shima nashi tashin hankalin yana da wannan kalan. Ga kuma wani ƙarin zafin kai dake tunkaro shi, wanda ya gama sakankancewa a kai har saida Excellency ya tunasar da shi. Ganin Ilham ta cire idanunta daga cikin nashi shima sai ya sauƙe su a kan Kiki dake faman washe masa haƙora ya mayar mata da ɗan ƙaramin murmushi Sannan ya sunkuya ya ɗauke ta. Saida Aunty Surayyah ta jira ya sake ɗagowa ya kalleta tace “Abdulhameed ka dawo?” Ya jinjina kai fuskar shi babu annuri “Yes Aunty Sharmama, I have something to do outside of the office…” Har ila yau Hausa ba ya gama zama a kan harshen shi bane, tunda bai gama ƙwarewa a kanta ba ya daina jin yanda ake furta sauran kalmominta balle ya riƙe su a cikin kansa yana amfani da su. Shiyasa bayi iya dogon magana ba tare da ya sirka da turanci ba, ya dai yi ƙoƙarin barin inyamuranci don ko yayi ma a cikin mutanen da yake rayuwa tare da su a yanzu babu mai ganewa sai ya fassara. Ya ƙarasa da “Shiyasa na taso da wuri” Iyaka ƙoƙarin shi yana yi wajen ganin bai sake ɗora idanun shi a kan Ilham ba duk da zuciyar shi dake ingiza shi, don gani yake yi kaman idan ya sake kallonta zai ga wani abu ya canza a fuskar tata, zai ga babu wannan raunin duk sun ɓace. Amma Kiki saida ta kamo haɓar shi cikin ɗan hannunta, ta karkata fuskar shi ya tsaya a kanta kafin take nuna Ilham da yatsa tana cewa “Daddy wancan matar ta ji ciwo” Ya ja dogon numfashi ya furzar a hankali yana kallon yarinyar, bai ga abinda a duniyar nan zai iya rabata da shi ba, shiyasa ya rufe ido ya amince da buƙatar Excellency. “Kin ce mata sannu Allah ya sawaƙe?” Gyaɗa kai tayi, kuma shi a karan kan shi ya san ƙarya Kiki take yi ba sai an faɗa ba amma tunda nashi gaisuwan ya shiga kunnen Ilham shikkenan. Yace “welldone Aunty, bari na tafi da ita ku huta. Thank you” Godiyan da yayi a kan taimakawa Ilham da tayi ne amma bayi son ita Ilham ɗin ta fahimci ya bayar ma lamarinta muhimmanci ko kaɗan, daga haka ya juya ya bar ƙofar ɗakin. Yanda suke zaune a bakin gadon cinyar su na gogan na juna ita da Aunty Surayyah duk ya gama takurata, kuma ta ji rashin dacewar ganin su a haka da Abdulhameed yayi a matsayinta na wacce take aiki a ƙarƙashin su, amma ta kasa motsawa har saida Aunty Surayyan ta miƙe. “Nima bari na baki wuri, ki kwanta kafin la’asar tayi, idan kin yi sallah sai ki je gida” Ilham ta miƙe tsaye. “Hajiya idan babu wani abinda zan yi, tunda ya dawo nima zan tafi” “Gaggawan me kike yi? Ko wani dukan za'a sake miki idan baki koma da wuri ba?” Da sauri ta amsa da “A'a asibiti zan je wurin yarona, yau ban je na duba shi bane” Ta ɗan tsura mata ido cike da tausayi. “Kin tabbata baki buƙatar a haɗa shi da hukuma? Ni zan tsaya miki, kuma za'a hukunta shi daidai da laifinsa” Ta shiga girgiza kai idanunta a rufe, a cikinsu ganin irin masifa da bala’in da zata ƙara gayyato ma kanta take yi, Idan labari ya isa familyn Baniza na ta haɗa Hashim da hukuma sai ta gwammace kiɗa da karatu. Ai idan dukanta ne ba yau ya fara ba, kuma bata jin yau ɗin zai kasance karo na ƙarshe koda kuwa zata cigaba da yin kaman yanda yake so a gaba, amma ba'a taɓa samun wanda yace mishi meyasa ba balle ace ya bari, saidai ita a hore ta da gujewa bacin ransa. “A'a Hajiya dan Allah, ki rufa min asiri kawai in cigaba da lallaɓawa, wata rana zai wuce” “Allah yasa” cewar Aunty Surayyah tana sauƙe numfashi. “Muje in ajiye ki a asibitin” Har ciki suka shiga da ita ta duba jikin Muftee ta ajiye musu 5k sannan ta zaga ta gaida sauran majinyata kafin ta tafi. “Addah Fidela na tambaye ki a ina kika ji ciwo haka kin yi mun banza?!” Ihsan ta tunkareta bayan ta dawo daga raka aunty Surayyah mota, tana taɓa mata wurin a hankali don gani take yi kaman ba da gaske ba, jiya-jiya suka rabu garas ɗinta. Ta cire hannun Ihsan a fuskarta don tana jin zafin raunukan har yanzu. “Hatsari muka yi nida mai mashin da safe, amma da sauƙi sosai kada ki damu” Ta wuceta ta ƙarasa ta ɗauki kofi mai murfin da suke ajiye ruwan sha a ciki ta buɗe murfin ta kafa a bakinta, tunanin yanda zata fara faɗawa Ihsan zancen zamanta da ta hakura da shi kawai ya saka ta ji maƙoshinta ya bushe matuƙa, kafin ma a zo kan yanda zata yi da Muftee idan ta tafi ɗin, gashi da suka haɗa ƙarfi da ƙarfe wurin bashi kulawa har ya fara farfaɗowa yayi haiba. Saida ta shanye ruwan tass, ta sauƙe kofin tana kallon cikinsa. “Filiyan ki haɗa kayan ki kawai kiyi kuɗin mota da dubu biyar ɗinnan gobe ki koma wurin Maama ki ƙarasa hutun ki a can tunda kinga yanzu da sauƙi kwanan nan zasu sallame mu in sha Allah” Ihsan ta yamutsa fuska tana kallonta a kaikaice. “Ban gane ba? Dududu yau kwana huɗu da zuwana idan ma zaki kore ni ai sai ki bari ko sati na cika.” Ta ɗago idanunta da suka tara ƙwolla take ƙoƙarin mayar da su tace “Allah ya baki haƙuri ni ba koran ki nake yi ba, zaman asibiti ne babu daɗi na sani” “Toh ace ma na yarda zan tafi yaya zaki yi da aikin ki? Kawai ki faɗa min ainihin abinda ke faruwa malama” Ta saka hannu ta tallafe goshinta hawayen idanunta suna gangarowa kan fuskarta. “Cewa yayi in haƙura da aikin ko in hakura da zaman ki a nan Ihsan. Ba zan iya haƙura da aikin ba domin abincin da kika kawo mana wata rana zai ƙare, haka jikin Muftee wata rana zai sake tashi a sake kwantar da mu a asibiti. Kuɗin Ya Hashim ma jikinsa da cikinsa yake kashewa da sauran bukatunsa amma hakkin mu dake wuyan shi bai ɗauke shi a bakin komai ba, kinga dole in dage in nemi kuɗi, shiyasa na zaɓi aiki na a kan taimaka mun da kike yi, Allah ba zai hana ni inda zan yi ba.” da ƙyar ta samu ta kai ƙarshen zancenta don jin maƙoshinta take ya sake bushewa ƙadagas kalaman suna fitowa da zafi. “Innalillahi wa inna ilaihirraji'un. Amma wallahi Yaya Hashimu bayi da mutunci ko kaɗan, bayi da imani bayi da tausayi” ta ja tsaki tana karasawa ta karɓi wayanta a hannun Muftee da yace ta kunna masa game, amma shima tunda yaga fuskar Ilham jikin shi yayi sanyi. Ilham ta riƙe wayan a tsorace “me zaki yi?” “Maama zan kira, wallahi babu inda zan je” “Dan Allah kada kiyi mata zancen hatsari na, hankalinta tashi zai yi” Kallonta kawai Ihsan tayi tana kokwanton abinda Ilham din ta ɗauketa da ba zata fahimci ainihin abinda ya sameta ba daga bayanin da tayi yanzu. “Naji, ba zan faɗa ba” Ganin da gaske take yi Ilham ta maida mata wayan. Har Ihsan ta laluɓo layin Maama sai kuma ta fasa ta danna kiran numbern da tayi saving da ‘Yaya Zaki’. Bai ɗauka a kiran farko ba saida na uku ya kusan tsinkewa kafin ta ji sallamar shi yana ƙarawa da “ko bani da hankali idan nazo naga missed calls guda biyu kin san zan biyo. Sallah nake yi Filiyan!.” “Kayi haƙuri yaya Aliyyu wallahi Addah Fidela ce dama” ta yi saurin katse shi don idan ya fara masifa bayi gamawa da wuri. “Me ya sameta?” Tana jin yanda muryar shi ya canza yayi ƙasa in all seriousness. “Wallahi mijinta ne yace wai saidai na bar masa gida, kuma jikin Ibrahim har yanzu, gashi tana zuwa gidan aiki kullum tun safiya har dare shine ta zauna take ta kuka” “Me kika yi masa?” Kaman yana gabanta ta zaro idanu tace “Ni kuma? Kwana na ɗaya a gidan kacal fah, kuma banda wanka babu abinda yake kai ni can, sannan bani zuwa ma lokacin da yake nan balle in yi karo da ajiyarsa” Bai fahimci zancen ajiyar da tace ba kuma bai maida hankali a kai ba sai cewa yayi “shikkenan bari na kira shi mu ji, idan kuma kin je ne kika tada mata husuma a cikin gida ki kuka da kan ki” “Ni wallahi babu abinda nayi, wa ma yake da lokacinsa banda ita Fidela ɗin?” ta turo baki tana ƙunƙuni lokacin da ya kashe wayan shi. Ta riƙo hannun Ilham da ta ƙame kamar sabuwar soja duk tsoro ya gama kamata, tana jin gwara ta haƙura ita ta cutu a kan abinda zai biyo baya idan ta shigo da wasu cikin lamarin nan, wasun ma mutum mai zuciya da Fushi irin Aliyyu. “Ki zauna ki kwantar da hankalin ki babu inda zan je kuma babu abinda zai faru, ai ko ce mishi aka yi an jefo ki duniya ne daga sama cin kashin ya isa haka.” …. A parlorn mahaifin su khausar suka saba zama suyi hira, kuma Hashim bayi zuwa sai da daddare, saboda yanda yake son a rufe zancen auren har sai lokacin da yaga ya kamata ya fito ya bayyana da kansa. Ya sani babu mai goya mishi baya idan aka ji ya rakito ƙarin aure bayan ga ɗan shi kwance a asibiti, kuma hakan zai bawa Ilham daman yin ƙorafi a saurareta, amma idan ya bari sai bayan an sallami Muftee daga asibiti ya ɗago zancen babu mai ganin laifinsa tunda ba a kan shi aka fara mata biyu ba a family. shiyasa ba zai bari Ihsan ta ɓata masa shiri ba. Ya dubi Khausar da ta rakuɓe daga cikin soron gidan su, rashin jin daɗin tsayuwar ya nuna a kan fuskarta amma baffa Umar yana cikin gidan kuma yana da baƙo wani abokin shi ya kawo masa ziyara. Cikin taushin murya da ƴammata kawai yake lallaɓawa haka yace “na faɗa miki nayi wa tufkar hanci, idan Ihsan bata bar kaduna a yau ba gobe a kano zata kwana, yanzu menene damuwar?” “Ai ni kawai cewa nayi kada ka bari Aunty Ilham ta faɗa mata zancen ta je ta sanar a family house, ba cewa nayi ka koreta ba, yanzu ka sani ma ko ɓacin rai yasa ta faɗa mata a je ayi ta yawo da ni a baki ban ji ba ban gani ba?.” Ta kwaɓe fuska tana shirin masa kuka rurin da wayar shi ya ɗauka ne ya katseta. Ganin sunan Aliyyu a matsayin mai kiran yasa cikin shi ya bada sauti Ƙulululu, ya tsani hidima da wannan ɗan balaja’un, don bayan mahaifin su mai rasuwa a saboda shi kawai yake ɗagawa Ilham ƙafa wani lokaci, domin ɗanyen kan Ihsan ba komai bane a gaban nashi. Ba don ya so ba ya ɗaga kiran ya ƙara a kunne tare da yin sallama Muryar shi yana fitowa da rawan rashin gaskiya. “Baban Muftahu an wuni lafiya, yaya mai jiki” Bai taɓa kiran shi ya jajanta mishi rashin lafiyan Muftee ba sai yau, shiyasa ya amsa da tsoron abinda aka kira aka faɗa masa. “Lafi… Au da Sauƙi alhamdulillah.” “An sallamo su daga asibitin kenan?” Aliyyu ya tambaya. “A'a ba'a sallame su ba tukunna, ka san samun lafiya sai a hankali dukda ma ita wannan cutar bamu san ƙarahenta ba, gashi nayi-nayi da ita a gwada na gida tunda ana dacewa taƙi ita sai na asibiti” ya ƙarasa da ɗan dariya kada Aliyyu ya fahimci maido da laifin kan Ilham yake son yi yanda za'a ce ita taƙi jin maganar shi. “Hakane, ita Kuma Filiyan laifin me tayi aka ce ta dawo tunda naji na ita Fidelan, daman ba jin magana take yi ba na sani, in yaso ni sai in zo in taya ku ɗawainiyar asibitin tunda idan ba Ihsan ɗin ba sauran daga manya sai ƙanana sosai ba iyawa zasu yi ba saidai Ni” “Hasbunallahu wa niimal wakeel!” Hasim Ya miƙe daga jinginen da yake yana dafa ƙirji. Ai gwamma ace Ihsan ta dawo da zama dindindin da ace Aliyyu ne zai zo yayi ma Ilham zaman jinya. “Kada ka damu zata zauna kawai har ranar da taga daman dawowa don kanta” Aliyyu yace “toh madallah, sai a ƙara haƙuri ka san mata ne rauni gare su kuma marayu ne, idan aka zalunce su sai Allah ya kama mutum yayi mishi ɗaurin da ba zai taɓa samun hanyar warwarewa ba. zan yi mata magana ta koma gidan baffa Rabe da kwana, Allah ya shige mana gaba” Ƙittt, ya katse kiran ya bar Hashim da Khausar suna kallon-kallo. An faɗo daga sama an faɗa rijiya. …. Tunda ya samu aka fara program din da Kiki take so sai ya tashi ya barta a jikin TV ya shigo ɗan ɗakin da ya mayar da shi workshop ɗinsa na haɗe-haɗe da gyare-gyaren na’urar taimakawa ji. Mafarkinsa kenan, ya zama babban Engineer ta wannan fannin, Amma abinda yake yi a yanzu, A&I mafarkin Ikram Aminu Yashi ne, saidai shine kawai zaɓin da ya rage masa a lokacin da ya siyar ma Excellency patent ɗin sabon samfurin hearing aid ɗin da ya ƙirƙiro don ya ba ma Kiki ingantacciyar rayuwa. Saidai har yau Excellency bai yi amfani da patent ɗin ya bayar ana ƙirƙiran Hearing Aids ana siyarwa yana samun riba ba, ko ya siyar ma manyan kamfanunnuka, duk da sun tsaya ne a kan zai riƙe a wurin shi amma idan Abdulhameed ɗin ya biya shi ta wani hanya zai dawo mishi da patent ɗinsa. Kuma tunda ya bashi ya daina amfani da samfurin kwata-kwata, har Kiki ba da irin shi take amfani ba, don yana so ne alaƙar shi da Excellency ya tsaya a iya patent kawai amma kaman hakan ba zai yiwu ba. Drawer ya buɗe ya ɗauko wani case kaman na Airpods ya dawo ya zauna a gaban table ɗin da ya baza kayan aikin shi, ya ciro abun ƙananu guda biyu sannan yayi pieces-pieces da su kafin ya fara gyarawa. Ya ɗauki lokaci yana tunanin abubuwan da zasu canza idan jin shi ya dawo, irin rayuwan da shi da yarinyar shi zasu yi a gaba, kuma babu buƙatar Excellency yayi amfani dashi wajen samun goyon bayan talakawan ƙasa a siyasa tunda shima yanzu yana ji kaman kowa. Ya daɗe yana taɓe-taɓe kafin ya mayar da abubuwan ciki ya haɗa su kaman yanda suke daga farko, saidai akwai abubuwan da ya gyara daga ta cikin wanda shine yake fatan zai kawo sauyi a rayuwar shi. Fata a karo na babu adadi. `````````` Seemahwrites ✨ ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh JODA by Sadi-sakhna DAƊIN ZAMA by Seemahwrites *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a turo shaidan biya ta 09039206763 Chapter 21 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Wattpad and Arewapen @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 21… Ya riƙe Na’urar guda biyu a hannun shi na hagu da dama. A hankali ya kai jikin kunnuwan shi, ya tusa a cikin ramin kunnen saboda ƙanƙantan shi ya shige sosai yanda ba za'a iya hango shi daga waje ba sai an saka lura. Komawa yayi ya jingina bayan shi da jikin kujeran da yake zaune a kai, yana ji a jikin shi wannan karon ma ba zai yi aiki ba, amma zuciyar shi tana faɗa mishi ba haka ba, yana jin kaman the result will be different this time, kaman daga wannan, rayuwar shi zata koma yanda take kafin Accident ɗin da ya sauya komai. Ya kai hannu ya danna makunnin abun sannan ya zauna yana jira. Ya cigaba da jira.. saidai shiru. Shiru babu komai, ko da wannan ƙaran da yake ji a duk lokacin da ya gwada. Hasken da wayar shi yayi ya rushe fatan da ya samu na cewa na’urar tayi masa aiki, shirun ɗakin ne yayi yawa. Saboda bai ji ƙaran shigowar saƙon ba. Bayi manta ranar da suna meeting a A&I. Ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya kan mai yin presentation yana reading lips ɗinsa don ya gane abinda yake faɗa idan akwai abinda yake so a canza ayi nan take ba sai daga baya yayi zaman duba meeting Minutes ba su ma ya mayar da su baya. Wayar shi dake kan table yana ta ringing kowa yana ji amma banda shi, har mai presentation ɗin ma saida ya tsaya saboda ƙaran yayi yawa. Aunty Surayyah ta ɗauki wayan ta miƙa masa lokacin kiran ya dawo missed call tare da saƙon da aka ajiye masa. Saida aka tashi a meeting ɗin take ce masa ya bata wayan ta rufe masa muryan. Ya girgiza kai. “Ina so in sani lokacin da ji na zai dawo koda ni kaɗai ne” A yanzu ma bai ji ƙaran shigowan saƙon ba. Sai ya cire Na’urar kawai ya mayar cikin gidan shi, ba yau ya fara gwadawa ba balle ya gagara jure zafin da yake ji a ƙirjinsa. Ya dai ɗauki tsawon lokaci bai gwada ba kafin yau, kuma dalilin yana da nasaba da maganar da Excellency yayi masa a kan Kiki da kuma… ya rintse idanu yana girgiza kai lokacin da ƙwaƙwalwar shi ta hasko masa fuskar Ilham a ganin da yayi mata da safiyar yau. Ya buɗe su a kan wayan dake saman table a gefen case ɗin hearing aids ɗinsa, ya ɗauka ya kawo shi kusa da fuskarsa yana duba saƙon da ya shigo. Saƙon guda biyu ne, na farko alert ne na shigowar kuɗin cikin asusun bankin shi, da ya fara ƙirga Zeros ɗin dake bayan lambar farko ya kai guda shida sai ya bar sauran kawai ya buɗe saƙo na biyu dake gwada sunan Excellency a kai, domin ya riga ya san kuɗin na menene. ‘Come in tomorrow and sign the contract. Da zaran ya cika mun samu abinda muke nima zan maido maka da patent ɗinka’ Ya miƙe tsaye yana zura wayan a aljihu ba tare da yayi reply ba tun da dole duk yanda Excellency yace haka zai yi. parlour ya koma wurin Kiki, sai ya samu har tayi barci a kan kujera ga laidan sauran biscuit mai filling ɗin dabino da ta gama ci a matsayin abincin dare a gefen ƙafar ta, yau daga ita har shi sun gagara cin abincin da yayi musu order sai kame-kame. Kewar abincin Ilham yake yi, wannan spaghetti da meatballs ɗin, jollof rice ɗin da ta fara girka musu, harma da tuwon da tayi ya ci ba don ran shi ya so ba, idan da zai samu yanzu zai sake ci. Amma a yanayin da ta bar gidan zata kwana biyu kafin ta samu sauƙin dawowa bakin aikinta. ….. ILHAM Tare da Ihsan suka koma gidan zata tattara kayanta ta mayar gidan su Khausar, kaman yanda Yaya Aliyyu yace bai yarda wani abu nata ya sake kwana a gidan Ilham ba bare ita kanta. Saida ta gyara ma Ilham gidan tass tana tilasta mata ta zauna ta huta kawai, sannan ta shiga haɗa kayanta a cikin akwati. “Filiyan kiyi haƙuri dan Allah” Ilham dake zaune a gaban akwatin da Ihsan ta kwantar tana naɗe kayanta masu datti da bata samu daman wanke su ba tana zubawa a ciki ta ƙare tayi magana, bayan dogon shirun da ya ratsa a tsakanin su. “Meyasa zaki bani haƙurin laifin da ba naki ba? Na san a sanadi na aka sauya miki kamanni, kuma Wallahi ko wuƙa za'a saka ma Ya Hashimu a wuya ba zai iya kawo dalilin da yasa yayi mana wannan wulaƙancin ba, amma ya jira, kwanan nan zan bashi dalili in sha Allah don wallahi sai kin bar gidan nan, ai mutum ce ke mai rai da hankali ba dabba ko itace ba” Ilham ta girgiza kai “Ki bar maganan nan dan Allah, bayi da amfani. Duk abinda zan faɗa miki ba zaki gane ba Filiyan, don ni da wanda ke cikin hali irin nawa ne kawai muka san me muke ji” “Sai kuma aka ce miki zama dashi dole? Tunda Allah ya haɗa ki da Azzalumin miji ba sai ki ƙara gaba ba? Ko mutuwa zaki yi idan kika rabu da shi?” “Idan ni ban mutu ba Muftee fah?” “Oh daman shi yake busa mishi numfashi? Ko akwai uban abinda yake tsinanawa Muftee ɗin a yanzu?” tana huci ta wurga pink ɗin Polo shirt ɗinta da ta gama linkewa a cikin akwatin har saida ya warware. Ilham tayi shiru ganin ranta ya ɓaci sosai. “Ki zauna ya kashe ki kinji” ta ja tsaki tana cigaba da abinda yake gabanta. Murmushin da yafi kuka ciwo Ilham tayi tace “Na faɗa miki ba zaki gane bane Filiyan. Amma ba'a bazawari sai bazawara, ma'ana babu wanda yake kallon laifin namiji a mutuwar aure. Kece kawai mutuncin ki zai zube a idanun jama'a, haka za'a yi ta ganin ki da laifin kashe auren ki da kika yi duk inda kika ratsa ana yamaɗiɗi da ke, shiyasa aure rufin asiri ne” “Wani auren ba? Banda irin naki wallahi. Auren da akwai mutunci da kwanciyar hankali a cikinsa ne ake kira da Auren rufin asiri, amma idan ta bakin mutane zaki bi ranan da aka kawo gawan ki sai sun yi ƙorafin ta hanyar da kika mutu bai yi musu ba.” Ta sani daman duk bayanin da zatayi ma Ihsan ba zata fahimta ba, amma ita ta san abinda take hangowa. Ta yi shiru tana sauraron Ihsan ɗin tana ta zazzageta kaman itace gaba da ita har ta gama haɗa komatsenta zata tafi ta fito rakata sai ga Hashim ya shigo gidan da laida a hannun shi. Ilham kaman ba zata yi masa magana ba, don bayan sallama ko sannu da dawowa bakinta yayi mata nauyin furtawa, shi kuma ya musu tsaye bai kauce ya basu hanya ba kuma bai ce komai ba, yana riƙe da baƙin laida a hannu. Ta ƙare tace “Ga Filiyan ɗin zata tafi” “Ai mun gama magana na fahimta da Aliyyu kuma na yarda ta zauna” Da shirinsa na ya lallaɓata ta cigaba da zama ya zo a fasa zancen zuwanta gidan su Khausar. “Eh shine yace ta tafi gidan Baffa Rabe, zata bar mana gidan ka sha iska daman mun takura ka” Ya kalli Ilham da mamaki jin maganan da ta yaɓa mishi amma kwantacciyar wutar da ya gani a cikin idanunta ya saka yayi shiru, don sai yaga kamanta da Ihsan ma ya ƙara fitowa duk da gefen fuskarta na lulluɓe cikin farin bandeji. Ya dubi Ihsan da ta saka ma bakinta sakata saboda kawai a zauna lafiya, ya ƙaƙalo murmushi yana miƙa mata laidan hannun shi. “Har kuwa na yo miki tsaraba” “Tsaraba ya wuce wanda nake samu a toilet da ƙamshin sa yake cika ko ina? Wancan ma ya ishe ni Nagode sai anjima” bata tsaya jiran rakiyan Ilham ba ta kinkimi akwatinta tayi gaba suka yi mata rakiyan idanu. Ƙafa ta saka ta hankaɗa ƙofar tana ficewa ta sake hankaɗo shi ji kake yi Bammm. Ilham ta lumshe idanunta da hawayen ciki zuwa yanzu sun fara kafewa, kamar zuciyarta Ihsan tayi wa wannan bugun haka ta ji, babu shakka Hashim yayi nasaran samar da giɓi a tsakaninta da ƴar uwarta mai sonta da fahimtarta tun da gashi sun gagara samun daidaito a kan shi. “Kin gani ko? Kin ga dalilin da yasa nace Ƙanwar ki sai ta bar min gida? Wallahi baku da tarbiyya, ban san menene baffa Usman ya gani a jikin Jamila ba, gashi ta zo ta ɓata mishi gid…” “Ya Isheka zagin Maama nah Hashimu! Ya isheka Wallahi. Ina so ka sani ba don Maama ba, ba don ta hore ni da yiwa mahaifina biyayya ba da ba zaka ganni ba balle kayi mun Abinda ka ga dama.” Baki a buɗe ya saki laidan hannun shi a ƙasa tsaban kaɗuwa,sai ga yalon bello da ayan ruwa da ɗinya suna gudundule a tsakar gida. Bai taɓa tunanin ko a zuciyarta Ilham zata iya faɗa mishi magana irin haka ba balle a gaban idanunshi. “Me nayi maka? Me nayi maka ka tsane ni haka? Idan Muftee ne ba ni kaɗai na haife shi ba. Da ace jininka ba irin nawa bane da lafiya ƙalau zamu haife shi, bayan wannan da muka yi tarayya a ciki sai ka faɗa mun menene laifina na musamman?” Yatsar shi yake kaɗawa yana gwada ta dashi cikin rasa ta cewa. “Gajiyan da na tara miki bai ishe ki ba ko?” ya samu bakin shi ya buɗe yana muzurai. murmushi mai sauti tayi. “Don Allah ka kashe ni ka huta ko Ahalin Baniza zasu baka kambun jinjina, daman sun baka wani a ranan addu'an ukun Taa(babana) sai su ƙara maka wani” Ta ja tsaki ta juya ta bar shi a wurin da shi da su yalon bellon shi. ….. Rabe ɗan sha'ani, baka faɗa da kowa sai ɗan sa Ido. Wannan shine taken mahaifin Khausar tun a zamanin samartakan shi. A cikin yaran dijengala idan ka cire Ussy da sauƙin kai yake a halittar shi, shine kawai bai ɗauki ƴan ubanci ba don dukda baya jin magana a lokacin amma shi ya fara zaman gidan Baniza tare da yaran Amina. Haka zai dinga tura yaransu su siyo masa sigari ko maganin mura, idan iyayen yaran suka tunkare shi da maganan sai ya sauƙe kai ya basu haƙuri amma gobe ma sai ya sake. Shine yayi sanadin farkon haɗuwan Abdulhameed da Aliyyu. A shekaran da Abdulhameed ya haɗu da Ilham Aliyyu yayi paper, shi kuma A Moher canje-canjen makaranta ne ya maida shi baya amma ya bashi kusan shekara biyu. Ranan da Rabe ya fara aikan Aliyyu siyo masa sigari, Aliyyun ya je ba don ran shi ya so ba sai domin yanda Rabe ɗin ya dinga roƙon shi kaman ƙanin shi. Yanda ya karɓi kwalin da malam Sama'ila ya lulluɓe masa a cikin baƙin laida tare da gargaɗi mai yawa na kada ya sake dawowa idan ba haka ba zai faɗa ma mahaifinsa, juyawar da zai yi, Abdulhameed dake tsaye a bayansa sanye da Uniform ɗin makaranta ya saka hannu ya karɓe laidan Sannan ya miƙa mishi Naira ɗari biyar sabuwa ya sayi wani. Banzan kallon da Aliyyu ya bisa da shi ya tabbatar masa kaurewa ne abinda zasu yi na gaba. “Na san gidan ku, na san babanka da inda yake aiki, and I can tell him if I want” A cikin faɗan malam Sama'ila ya samu abinda yayi masa barazana da shi, amma ko wuƙa aka saka mishi aka ce a arean ya gwada ina ne gidan su Aliyyu saidai a cire mishi wuya. Kuma tun daga ranan ne ya samu daman aikan Aliyyu in dai yana sanye da Uniform ɗin makaranta har zuwa ranar da ya gan shi tare da Ilham. . Da kan shi Baffa Rabe ya fita ya shigo ma Ihsan da akwatinta yana share mitan da Maman Khausar take yi a kan ya kawo mata ƴar Jamila, ya kai mata kayan har ɗakin da Khausar ke kwana tare da ƙanwar ta. Duk butulcin sa ba zai manta da halaccin mahaifin su Usman a gare shi ba, shine ya tsaya masa ya samu aikin da ya rufa ma kan shi asiri har zuwa yanzu. Ihsan ma tunda ta gaidata ta nemi wuri a ɗakin ta zauna, zata jure duka wannan a kan Ilham, saboda tana da tabbacin Ilham zata iya mata fiye da haka idan itace ta samu kanta a cikin halin da take ciki. Saida aka kira isha ta fito zata yi alwala sai ga baffa Rabe ya shigo mata da laidan awara mai zafi da Cway peach mai sanyi sosai har ya fara ƙanƙara. Daman cikinta yana kiran chiroma domin yau abincin ƙofar asibiti ta siya suka ci ita da Muftee ganin har rana tayi sosai Ilham bata zo ba. Saida ta gabatar da sallanta sannan ta zauna a nutse ta cika cikinta, ta cigaba da amsa waya tana ganin kiran Sageer dake shigowa lokaci bayan lokaci yana jinta on another call, ba zata yi blocking ɗinsa ba idan ya gaji ne zai ƙara gaba. Sai wuraren ƙarfe 10 Khausar ta dawo ɗakin, kuma har kowa tayi barci a cikinsu babu wanda tace ma ƴar uwarta ƙala. …. 7:18am. A sannu yake takawa zuwa ɗakin Kiki, yana sanye da kayan barci shirt da dogon wando baƙi mai laushi da yayi complimenting fatar jikinsa, takalmin ƙafar shi ma na kayan ne. Yana so ne ya fara shiryata kafin yayi wanka idan ba haka ba sai ta ɓata masa kaya. Ya murɗa handle ɗin ƙofar ya tura a hankali, idanunshi suka fara sauƙa a kan Ilham dake zaune a bakin gado kafin Kiki dake tsaye a gabanta sanye cikin uniform, gashin kanta rike a hannun Ilham ɗin tana taje mata. Sai ya tsaya kallon su da mamaki kaman yanda suma suke mishi. “Meyasa kika zo?” fatar girarsa ta tattare lokacin da yayi mata wannan tambayar. Har zata sauƙe kanta don ba zata iya cigaba da jure kallon cikin idanunsa ba sai kuma ta tuna da abinda ya faɗa mata. “Ba zan sake latti ba ayi haƙuri dan Allah…” “Nace ma Aunty Sharmama a bari ki samu sauƙi kafin ki dawo bakin aikin ki” ya katse ta. ko bayi da imani ba zai koreta a kan abinda ya faru jiya ba, kuma a hakan ma saida tazo. “Na samu sauƙi, Nagode” Sai ya koma da baya kawai ya jawo ƙofar ya rufe musu ya koma yayi shirin office. Indomie da dafaffen ƙwai tayi musu a matsayin abun karyawa kuma ya ji daɗin da bata ce zata wahalar da kanta ba. Saida ya saka ma Kiki hearing aid dinta ya fita daga gidan ya bar Ilham tana saka mata takalmi, ganin ta fara yarda da ita sai ya ƙara samun nutsuwa, ya zauna a mota yana jiran su. “Kiyi Addu'a” tace ma kiki lokacin da zasu fita daga cikin gidan. Sai ta ɗago ta kalleta tana yamutsa fuska “wani addu'a?” “Addu'an fita daga gida” “Ni ki barni in tafi” ta fara ƙoƙarin kwace hannunta da take rike da shi Da ta dage mata sai tace “bismillah” kawai. “Tawakkaltu…” Ilham ta cigaba don ta bi bakinta ta ƙarasa. Daga yanda Kiki ta maimaita kalmar Ilham ta fahimci bata saba da furtawa ba. “Wa la haula…” “Nikam ki kaini wurin Daddy na gaji” ta fara mata rashin kunyar da Ilham tayi tunanin mantawa tayi. Sai ta ƙarasa addu'an kawai ta tofa mata, Abdulhameed yana kallon su ta cikin tinted glass ɗin motar har suka ƙarasa Kiki ta buɗe ƙofar ta ɗaya gefen da yake zaune ta shiga driver ya ja suka barta tsaye idanunta suna yiwa motar rakiya. ````````````` Seemahwrites ✨ ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh JODA by Sadi-sakhna DAƊIN ZAMA by Seemahwrites *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a turo shaidan biya ta 09039206763 Chapter 22 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Wattpad and Arewapen @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 22… Saida ta ga fitan su ta juya ta koma cikin gidan ta fara aikin gyara ko ina. Ita kaɗai take ta kaiwa da komowa, ko ina yayi shiru sai ƙamshin Diffuser da sanyin AC, ga wadataccen hasken hantsi dake ratsowa ta gilasan winduna bayan fararen ƙoyayen wuta da suke a kunne suna ƙara fito da kyawun gidan. Wani nutsuwa da yake zuwa mata a irin wannan yanayin ya samu wuri a ƙasan ranta ya kwanta. Ba gwamma da tazo ɗin ba?! idan ta zauna a wancan gidan ma zuciyarta ne zata cigaba da ƙonewa da baƙin cikin Hashim har sai ta murmushe ta dawo toka, amma a nan bayan ta samu nutsuwar jiki da na zuciya zata samu abu mai daɗi ta kai ma yaronta da Ihsan da ta baro su tare. Da sassafe Ihsan ta zo ta karɓeta a asibitin da ta kwana tare da Muftee don haka rabonta da Hashim tun jiya da yamma. Ta gama su shara da goge-goge ta gyara ɗakin Kiki ta wanke toilet ɗinta, sannan ta dawo kitchen tana tunanin abinda zata dafa. Akwai abubuwa da yawa da suka zo mata a kai amma babu kayan haɗawa a cikin store ɗin gidan. A cikin abubuwan harda awara da idan an soya shi ake haɗa sauce a zuba a ciki a gwamutsa. Ga su masa, zoɓo, kunun aya da na gyaɗa, dambu, tuwon shikafa miyan kuka ko kuɓewa, biski da sauran abinci masu daɗi, duk babu kayan haɗa su sai abincin kwali da kayan flour. Ta ci Sa'an samun wake amma ɗan turmin dake kitchen ɗin zata iya riƙe shi a cikin tafin hannunta, sai ta fita ta ƙofar kitchen ta shiga bangaren sauran mutan gidan da nufin aro turmin da zata surfe waken a ciki, ta san ba zasu rasa ba. Tsakar gidan yana nan kaman yanda yake, ta ɗaga idanunta daga kan interlocks ɗin da suka yi duhu kaman sun shekara goma sha ana taka su tsaban dauɗa. Ƙofar farko shine Aunty Surayyah tace mata na kakan yarinyar da take raino ne, wato mahaifin Abdulhameed, na gefen shi kuma yana rufe don haka ta wuce wanda ke kallon na farkon. Sallama tayi ba'a amsa ba, kuma tana jin motsi da ƙaran TV don haka ta sake yin wani sallaman. “Waye wai?” Wata siriryar murya ta fito daga cikin ɗakin. “Nanny ɗin Ikram ne” Ilham ta bata amsar da zata iya ganewa. Tana tsaye tana jiran a mata izini ta shigo ko ta faɗi abinda ya kawota sai ganin budurwar tayi ta fito kaman an wurgo ta, da Ilham bata yi saurin yin baya ba ma gware zasu yi. Yanda take ƙare ma Ilham kallo daga bandejin fuskarta har ƙafa haka itama take ƙare mata. Ba fara bace amma bata da duhu sosai, wankan tarwaɗa ce irin Abdulhameed, ya dai fita hanci, cikan gashin gira da na ido da tsawon fuska saboda dogo ne sosai, dogo irin wanda basu da yawa a cikin dogaye, amma sauran kamanninta duk irin nashi ne. Sai da ta gama ƙare mata kallo itama kafin tace “yaya aka yi?” A cikin ƙannenta Ilham ta fara tunanin wanda zai yi Sa'a da ƴammatan, idan kuma ta canka daidai toh Islam ne, ƙanwarta na uku. Ilham tace “aron turmi nake son a bani dan Allah” Ta harɗe hannunta a kirji “Turmi? Me zaki yi da shi” Koda ace ma wani taji Islam tana yin magana da wannan tone ɗin tabbas sai ta gurje mata baki, amma wannan ba Islam bace, nima take yi a ƙarƙashin ɗan uwan su. “Surfen wake zan yi” “Ku baku da turmin ne a…” “Zakiyya!!” Matar da ta fito daga cikin ɗakin tana ɗaura ɗankwali ta tsawatar mata. Saida ta ƙulle ɗankwalin a kanta ya zauna sannan ta nuna Zakiyyan da yatsa. “Mun samu lafiya na kwana biyu kina niman sake rakito mana masifa ko?” Ta juya ta dubi Ilham “malama ga kitchen ɗin can ki shiga ki ɗauki Abinda kike so. Daga yanzu kina wucewa kan ki tsaye ba sai kin zo mana nan ba” ta ja hannun ƴammatan suka koma ciki. Taɓe baki Ilham tayi ta ɗauki hanyar kitchen ɗin, ko sati bata cika a gidan ba amma duk wanda ta taɓa haɗuwa da su sai sun nuna mata halinsu. Saida ta ratsa tsakanin kwanukan wanke-wanke dake baje a tsakar wurin ga kwando a gefe ba'a tara a ciki ba, shima turmin saida ta duba ciki ta ga da sauran kayan miyan da aka daka ba'a kwashe ba, amma tsami yake yi. Ta samu plate ta juye musu a haka, ta ɗauki turmin da taɓaryar shi ta koma wurin aikinta. Yau ma da ita aka je ɗauko kiki daga makaranta. Kuma a yau ne ta fara sanin yarinyar magananniya ce gashi bata damuwa ko babu mai kulata haka take biya karatun da aka musu a makaranta da waƙe-waƙe tiryan-tiryan, idan ta tsaya haɗiye yawun bakinta kafin ta ɗora sai ta tambaye su daddynta su kaita wurin shi. Da suka yi parking Ilham tayi sannu ma driver, ta fita ta buɗe ma Kiki ƙofa ta cire mata seatbelt sannan tace ta fito su shiga ciki. Maƙe kafaɗa tayi “Ni ki ɗauke ni” Ita kuwa bata ga dalili ba da zata yi ta dakon jibgegiyar yarinya irin wannan da lafiyanta. “Kin ga ina da ciwo Kiki, ba zan iya ɗaukan ki ba” “Toh a ina kika ji ciwon?” “A hanya” “Da me kika ji?” “Faɗuwa nayi” “Toh yaushe zaki warke ki ɗauke ni?” Saida ta rufe idonta ta ja dogon numfashi ta furzar sannan ta buɗe su ta sake kallon yarinyar. Ɗan ƙaramin fuskarta abin sha'awa amma tana da yaƙinin da mahaifiyarta take kama ko da bata taɓa ganinta ba. Don bayan yalwar gashin ido da na gira sai dogon hanci babu wani abinda ta ɗauko a fuskar Abdulhameed ga farinta sosai har tana yellow-yellow. “Nima ban sani ba kiki, mu je in baki juice mai daɗi a ciki” Sai gashi ta sauƙo daga cikin motar ta kama hannun Ilham suna tafiya, bata bari sun shiga ba ta sake ce mata “kiyi addu'a” Ta yamutsa fuska kaman yanda tayi da safe “Ke ni fah ban iya ba” “Sunana ba ke ba! Mimi zaki ce” Sai ta turo baki. “Ni toh ban iya ba” Kice “bismillahi..” Tayi mata shiru. “Zan shanye juice ɗina ni kaɗai idan baki faɗa ba” “Toh bismillahi” muryarta ta fito da alaman tana shirin kuka. Ta so ta rabu da tarbiyyan Kiki tayi abinda aka sakata kawai amma ba zata iya ba saboda itama uwa ce, ta haifa, kuma ba zata so a bayanta a bar ɗanta da halinshi ba. Idan yayi laifi zata so a samu mai tsawatar mishi, idan bai san abu ba a koya mishi, idan yayi kuskure ayi mishi gyara. Amma tana tsoron faɗan Abdulhameed da fushin sa, bata son abubuwa marasa daɗi suyi ta haɗa su har ya ƙare ya sallameta. “Walajna” ta ɗora tana kawar da tunanin a ranta tunda da kyakkyawar niyya zata yi. Kiki ta maimaita. Sai tace “kiyi ta maimaitawa zuwa gobe idan kin iya zan baki abun daɗi” “Menene abun daɗin toh?” “Sweet” ta bata amsa, tunda shine abinda zata iya siya. Ta miƙo mata ƙaramar yatsanta “promise?” Saida Ilham tayi murmushi sannan ta maƙala nata ƙaramin yatsan a jikin na yarinyar tana maimaita Kalmar “promise” Alalen laida da tayi ta gutsutstsura mata ta saka mata sauce ɗin hanta da ta haɗa tare da shi sannan ta zuba mata juice ɗin Cucumber da tayi. Har ɗan ƙaramin gyatsa kiki tayi lokacin da ta gama cinyewa, Ilham tayi murmushi “kice Alhamdulillah” Shi kam bata yi musu ba ta faɗa. Ilham ta sake maimaita mata addu'an shigowa gida har saida ta riƙe kusan rabi, ta taya ta tayi assignment ɗin da aka basu a makaranta kafin ta tashi ta ɗaura sanwan abincin dare tana haɗawa da alwalan la'asar. “Kiki zo muyi Sallah” tace lokacin da ta dawo parlourn. “Ina kallo ne” ta bata amsa idanunta kafe a kan cartoon ɗin da ake nunawa a TV. Sai ta ƙarasa ta kashe TV ɗin, ai kuwa ta zube a wurin kaman gwate tana birgima, saida Ilham ta haƙura ta kunna mata TV ɗin kafin ta miƙe ta share hawayenta ta koma ta zauna ta cigaba da kallonta. Lokacin da Abdulhameed ya dawo har ta kammala abincin dare, alalen da tayi kuma ta ɗibawa Aunty Surayyah a wani food flask. Saida ta fara miƙa ma Aunty Surayyah abincin, ta mayar da turmin da ta wanke shi tass kitchen ɗin da yake cikin yanayin da ta barshi da safe, sannan ta ɗauki Abinda ya rage ta tafi da shi bayan tayi mishi sallama kuma ya bata ɗaya daga laidojin da ya shigo da su tayi godiya. Saida ta isa asibiti ne suke duba abinda ke cikin laidan ita da Ihsan saboda a hanya kayan hannunta sun yi yawa. Kayan marmari ne, kama daga Apples jajaye da koraye, transparent takeaway na inabi da na strawberry sai abarba da ayaba. Ihsan harda takawa saboda murna, suka ci suka sha suka sammar wa maƙwafta, sun ma manta da shirgin Hashim har saida ya kira wayan Ilham bayan Isha yana tambayanta yaushe zata dawo yana jin yunwa. ….. ABDULHAMEED Ya daɗe yana tunanin abinda zai yi mata ba tare da ya ƙetare iyaka ba, yana da kuɗi mai yawa amma bayi da hujjan bawa Ilham kuɗi haka kawai tana matar wani, kada yaje garin taimako ya saka ta a masifa. Suna hanyar dawowa daga Gidan Excellency ne bayan ya je ya saka hannu a kan takardar sabon yarjejeniyan su, idanun shi a kan hanya zuciyar shi kuwa ta nisa kan maganar da suka yi da lawyern Excellency a kan Kiki lokacin da ya hango masu fruits a gefen hanya. Har sun wuce yace ma driver yayi reverse, ya fita da kan shi ya zaɓi abinda yake so a bashi, saida ya karɓi laidan farko yace a sake saka wani irin shi don kada Ilham tayi tunanin na musamman ya siya mata, kuma ya sanma Kiki zata ci wasu abun a ciki. Card ɗin shi ya miƙa musu suka cire kuɗin su bai tsaya duba ko nawa bane ya karɓa ya tafi, kuma ya ji daɗin da ta karɓa tayi godiya duk da fuskarta bai gwada wani abu ba yana da tabbacin dai bata yi misunderstanding good intentions ɗinsa ba. Wanka ya fara yi ganin yanda Kiki take walwala ya san babu yunwa a cikinta, ya fito sanye da gajeren wando brown da farin T shirt, ya ƙarasa jikin dining da yake hango kulolin abinci har guda huɗu a kai da jug ɗin da raɓa ya lulluɓe jikin shi saboda sanyin abinda yake ciki, dan saida ta saka juice ɗin yayi ƙanƙara sannan ta fito da shi kafin ya zo sha ya narke. Ya buɗe food flask ɗin farko suka yi ido huɗu da alale. Shi kam ya saba ci a wurin Nne don yana daga cikin favourite foods ɗinta, amma shikafan da Ilham ta niƙa a Grinder ta turara shi kaman biski ba don rayuwar da yayi a gidan mahaifinsa kafin tafiyar shi Japan ba da bai san menene shi ba, amma ya sha cin na garin masara ko miya babu. Haka ya raba plate ɗinsa gida biyu ya zuba kowanne a gefe ya fara ci, fuskar shi da murmushin jin daɗi don bai yi tsammanin zai samu damar cin wannan girkin a yau ba, amma gashi har kala biyu. Kiki ma ta sake cin abincin kafin su kwanta, yace ta kawo assignment ɗinta suyi sai tace sun yi da Ilham, cikin jin daɗi ya miƙe ya juye abinda ya rage ya saka a fridge kamar kullum ya wanke komai tass saboda bai yi imani da kwanan kwanuka a cikin sink ɗinsa ba. …. Jollof ɗin macaroni na manja tayi ma Hashim da kayan abincin da aka kawo mata daga gida, ya dai siyo kayan miya harda kifi. Bata kula abincin ba domin a ƙoshe take, ta shiga banɗaki ta watsa ruwan ɗumi a jikinta don ta gaji sosai sannan ta samu wuri ta kwanta. Bata san ƙarfe nawa bane lokacin da taji ana taɓa ta, ta dai san barcinta yayi nauyi domin da ƙyar ta iya buɗe idanunta a kan Hashim dake tsaye a kanta daga shi sai boxers. “Tashi mana” ya sake ranƙwafowa ya bubbuga kafaɗanta. Sai ta zuba masa idanun da suka gagara buɗe girman su gaba ɗaya amma mamakin dake cikin su ya fito. Ta buɗe baki da ƙyar tace “Haba kai kuwa!” Shima saida ya ji ɗacin dake cikin muryarta amma bai san yaya aka yi ba yau yake jin yana buƙatar ta bayan tsawon lokacin da ya ɗauka bai nimeta ba, fiye da watanni huɗu. Kaman dai akwai wani abinda ya canza a jikinta, kaman ita ɗince ta canza masa yake mata kallon sabuwar Ilham ba wanda ya gama kashe kishirwar shi ya watsar da shirginta ba. Idan ba ta ɓata lissafi ba ma ovulation take yi, kuma rabonta da pills ɗin planning ya jima tunda babu abinda yake haɗa su, amma yanzu idan ta zaɓi ta sauƙe hakkin da Allah ya ɗora a wuyanta ta sake samun ciki suka haifi wani SS ɗin fa yaya zata yi?. Ta yiwa kanta adalci bayan shi ko ita abinda zata haifa da zai ƙare a wahale kaman Muftee? . . . 6:30am. Yau jikinta a mace take jinsa gaba ɗaya, bata ƙi ta kwanta ta sake hutawa ba, da ace babu wani abu mai muhimmanci dake jiranta, da barci zata ƙara har sai ta ji ya isheta kuzarinta ya dawo. Amma haka tayi abinda zata iya a gidan, ta haɗa abun karyawa ta ajiyewa Hashim dake barci har yanzu, sauran macaronin jiya kuwa ya rufe shi a kwano zafi ya saka ya buga sai zubarwa tayi ta wanke coolern ta saka abincin asibiti a ciki ta tafi da shi. Yau bata ga Abdulhameed ba har saida ta gama shirya Ikram ta kawota dining sai gashi a zaune cikin irin shigan da ya saba fita da su, amma yau rigan shi kalan Olive green ne da grey ɗin wando. Ta gaida shi ya amsa sannan ta tafi ta basu wuri su yi breakfast. “Kiki baki biya mun karatun da nayi miki ba jiya” cewar Ilham lokacin da suka zo fita daga gidan. Ta kwaɓe fuska “Toh ai baki bani sweet ɗin bane uhmm…” “Mimi” Ilham ta ƙarasa mata. “Ai baki bani sweet ɗin bane Mimi” “sai kin fara biya mun kafin in baki” ta nuna mata laidan minti mai tsinke da ta siyo mata a shagon asibiti kafin ta zo. “Idan kuma baki yi ba shikkenan sai in shanye kaya na” Sai gashi ta karanto addu'an tiryan-tiryan sai gyaran da ba za'a rasa ba, Ilham ta rage tsayinta a gabanta tana murmushi ta miƙa mata sweet ɗin. “Masha Allah kan ki yana ja my dear” Kiki ta karɓi laidan mintin tana washe baki. “Mai kika ce?” ta tambaya jin ta karɓa tayi shiru. Kiki ta kalleta da iya gaskiyarta tace. “Babu” Ilham ta girgiza kai “Thank you zaki ce” Gilashin motan a rufe suke duka, amma kaman a cikin kan shi yake jin maganar da Ilham take yi da Kiki saboda yana iya kallon motsin leɓenta daga inda yake zaune. Lokaci yana tafiya, wataƙil Ilham ta manta da haka ne. Amma bai yi interrupting ɗinsu ba har saida Ilham ta gyara ma Kiki kusren da take yi sannan ta ƙarasa mata addu'an shiga gida da alƙawarin zata ƙara mata wani sweet ɗin idan ta iya duka. Abinda yake so kenan, wannan part ɗin da ba zai iya cikewa Kiki ba ya samu wanda zata kamanta hakan. Ta shafa kan yarinyar tana saka mata albarka, sai a sannan ya bada driver daman yayi musu horn Kiki ta zo su tafi. ````````````` Seemahwrites ✨ ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh JODA by Sadi-sakhna DAƊIN ZAMA by Seemahwrites *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a turo shaidan biya ta 09039206763 Chapter 23 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Wattpad and Arewapen @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 23… bata da amsar bayarwa idan aka tambayeta a kan tafiyar ƙaddararta. Ya cigaba da gudu ne ko yana tsaye a wuri guda? wannan Allah ne ya bar ma kansa sani. Amma idan aka barta sai tace kamar da baya yake komawa ba gaba yake yi ba, idan kuma ba tafiyan ƙaddararta bane yake hakan toh Hashim ne da ya ɗauketa matsayin bolar kasuwa yake sakawa take jin haka. A daren jiya bayan ya ɗagata daga barci, daga alamun shi ta fahimci abinda ya kawo shi. Ba'a kwana biyu ba da yayi mata lilis kaman zai aikata lahira, tun yana kutubol da ita tana ihu har ta fara neman hanyar guduwa daga gidan ganin bayi da asara idan ya rabata da ranta,. Sai gashi ko zafin raunukan da ya bar mata bata gama ji ba ya lallaɓo yana niman wani abu a wurinta saboda son zuciya. “Haba kai kuwa!” Saida ta buɗe baki tayi magana ta ji inda zuciyarta ke zafi har zuwa maƙoshinta. “Ban gane ba! bani son rainin hankali fah Ilham. Don kin samu sake kina abinda kike so ba yana nufin zaman kanki kike yi ba Yauwa! Zaman aure kike yi kuma gidan nan ba da kuɗin ki nake biyan haya ina ajiye ƙatuwar banza da ba zata amfane ni da komai ba.” Allah ya gwada mata lokacin da zai zo tayi wata guda babu sabon baƙin cikin Hashim dake ƙara taruwa a tsakanin ƙirjinta ya sakata taji kaman zai fasa haƙarƙarinta ya fito. Bata sake cewa komai ba, ta tsaya jiran yayi yanda yaga dama da ita, amma bata cikin yanayin da zata iya masa wani abu. Tsamin jikinsa na ranan da ya gama kwasowa ya sakata rintse idanunta, tana imagining yanda gobe zai yi wanka ya saka turare ya kaiwa mutanen waje da ƴammata ƙamshin, ita kuwa an barta da na boxers ɗinsa da idan tazo wankewa sai tayi masa saɓi biyu. Bata san me ya faru ba, amma a hankali ta ji warin dake shiga hancinta na raguwa, da ta buɗe idonta sai taga baya tsaye a wurin, kafin ta ji motsin shi a bayanta, tana juyawa sai taga ya kwanta a ɗaya ɓangaren gadon ya juya mata baya. Salum-alum ta ɗauki pillownta ta bar mishi gadon ya bararraje, daman wayan da yake yi a parlo lokacin da yake cin abinci da wani murya mai bata haushi yana tauna cafal-cafal baki a buɗe kaman rago yasa ta shiga ta kwanta a gadon har barci ya ɗauketa. Ta koma parlo tayi kwanciyarta shine da ƙyar ma ta iya tashi tayi sallan asuba a kan lokaci, ta wuce shi yana ta minshari ta shiga banɗaki, har ta ɗauro alwala ta fito ta ɗauki zani da hijabi bai farka ba. Ringing ɗin wayarta ne ya dawo da ita cikin nutsuwarta, ta mayar da mopper da take goge ƙasan kitchen dashi cikin bokitinsa sannan ta ɗauko wayan a saman fridge tana duba sunan mai kira. Ƙaramin tsaki tayi ganin Sageer Baniza ne, itama ya fara addabanta zuwa yanzu tun da in dai ya kira Ihsan bata ɗauka ba sai ya kirata ta haɗa su. Kaman ba zata ɗauka ɗin ba ta dai kai zuciya nesa. “Assalamu alaikum” “Addah Fidela ina kwana” “Ba zaka bar addan nan ba ko Yaya Sageer?” Ta faɗa da ɗan murmushin da bai kai zuci ba. Shima murmusawa yayi “Ai ni yanzu bani da wanda ta wuce ki” Tace “Lallai kam” tana taɓe baki “gashi kuma bani tare da Filiyan ɗin, ka san na faɗa maka ina zuwa aiki” “Ai nima ba saboda ita na kira ba yau, daman na faɗa miki duk sati zan dinga kira muna gaisawa. Yaya jikin Baban mu” “Da sauƙi Alhamdulillah” “Toh Allah ya ƙara sauƙi. Yauwa an dawo da taron shekara nan da sati uku, saboda akwai bikin ƴar wajen baffa Ussy da ɗan Inna Sahura, sannan ba'a so ya kai cikin damina saboda ruwan sama” Bata samu labari ba ko a wurin Addah Iman tunda ta san yayyenta maza ba kiranta zasu yi su faɗa mata ba, Maama kuma ba lallai ta sani ba. Ko da yake idan ta ga Imam ta kirata toh wani magana taji yana yawo a family a kanta sai ta kira tayi mata faɗa koda kuwa jita-jita ne kawai. lokacin da suke zaune a kano ma har wanke ƙafanta take yi ta zo kuma duk yanda zata yi mata bayanin gaskiyan lamari ba zata saurara ba, idan kuma tayi Sa'a ta saurareta ɗin haka zata nemo duk inda rashin gaskiya yake ta ɗora mata. Shiyasa rashin shaƙuwar su ya ƙara tsamari gashi ita ce kawai yayarta mace, ta gwammace idan abun kuka da jajantawa ya sameta ta kira ƙanwarta Ihsan su raba damuwar tare, ita da ba ciki ɗaya suka fito ba. “Toh Allah ya nuna mana lokacin” Sageer ya amsa da “ameen, ai zaku zo wannan karon ko?” “In Allah ya yarda zamu zo” Tana fatan ta je ta ga Maama da sauran ƙannenta harma da yaya Aliyyu, amma Allah yasa zuwa lokacin an sallame su daga asibiti kuma Allah yasa Hashim ya yarda su tafi tare, zata biya ma kanta kuɗin mota har da shi idan yana so, don abun ya zo mata a daidai, nan da sati ukun zata ɗauki albashinta na farko sai ta roƙi hutun sati ɗaya ta je ta dawo. “Allah ya yarda, sai ki ɗan faɗa ma Filyan dan Allah tun da bani da ƙimar da zata dinga ɗaukan kira na, a ce ina gaisheta” Toh Allah yasa dai Ihsan ba miji mai haɗa wuri zata aura ba. A bayyane ta amsa addu'ar da tayi a zuciyarta da “Ameen” Sageer ya ɗauka tashi addu'ar ta amsa. “Na gaishe ki Addah Fidela, a gaida yaya Hashim sai anjima” ita ta kashe wayan ta maida shi inda yake, ta cigaba da aikinta tana ƙira’ar suratul Kahfi daga kanta tunawa da yau juma'a ne, zata samu lokacin kula da Muftee gobe da jibi kasancewar su weekend sai Ihsan ta huta. Ƙarfe sha biyu aka tashi Kiki daga makaranta suka je suka ɗaukota, kuma Abdulhameed ma daga masallacin juma'a gidan ya dawo. Ya samu tana kan aikin haɗa abincin dare, Kiki sai binta take yi ƙafa da ƙafa ta hana ta sukuni a kitchen ɗin. A haka ta ƙarasa koya mata Addu'an shiga da na fita daga gida har suka fara na shiga banɗaki kafin ta kammala dakan sakwaran da kiki ta gama tsoma hannayenta a ciki sauran kaɗan ta daka mata ƴan yatsu, kafin ta gama yarinyar duk ta cika mata ciki. Yau ma ta ɗebi sakwaran ta kai ma Aunty Surayyah da zata mayar da turmi, ganin mutan gidan a waje ta rage tsayi ta gaida iyayen su suka amsa da ƙyar amma yaran bata ishe su kallo ba, ta miƙe ta wuce ɗakin aunty Surayyah. “Sannu da aiki fa Ilham, Allah ya bada lada” Ta amsa da murmushi a saman fuskarta don Tana jin matar a ranta sosai. “Yauwa Hajiya nace za'a ɗan masa magana ne ya siyo Shinkafan tuwo da waken suya da gyaɗa a ɗan samu sauyi a abincin? Wani lokaci ina rasa abinda zan girka saidai maimaici” “Abdulhameed baya cin tuwo ai shiyasa kika ga babu ɗin, hakama awara nake gani” Mamaki ya saka tayi shiru kana tace “sau biyu ina yin tuwo a gidan fa Hajiya, kuma bai yi mun magana a kai ba” “Amma ya ci?” Itama Aunty Surayyah mamaki ne ya kama ta. Ilham ta gyaɗa kai “yawan wanda na bari Kiki ba zata iya cinyewa ita kaɗai ba” Aunty Surayyah tayi murmushi mai sauti tana tuna shi a wani lokaci da ya wuce kaman bai taɓa faruwa ba. Wahala da daɗi suna canza mutum tabbas. “Shikkenan, ki yi list ɗin duk abinda kike son a siyo ki ba ma driver ɗin shi, da abinda babu da wanda ya kusan ƙarewa ma duka ki rubuta zai siyo” Ta amsa da toh tayi mata sallama ta fito, sai bata sake cewa mutanen wurin komai ba tayi wucewarta. A cikin asabar da lahadi ɗin da suka wanzu a rayuwarta, wannan suna cikin masu daɗin da suka zo mata a garin Kaduna. Ita kanta ta san jikin Muftee ya fara kyau don har a fuska yayi haiba gashi ɗan walwala ya dawo mishi, idan ta tuna ƙiriniyar Kiki dai sai ta ji tausayinsa ya kama ta, yanda yake abu da sanyi-sanyi kaman wani babba mai cikakken hankali. Haka Ihsan zata zo su wuni suna hira sai dare ta tafi don zaman gidan Baffa Rabe ma da babu gwamma ba daɗi ne, har take ma Ilham taɗin kaman shirin auren Khausar suke yi don taga yanda mahaifiyarta take ta siye-siye. Ta kwana biyu ma bata ga Khausar ɗin ba, ba kaman a baya da idan bata zo yau ba zata zo gobe, amma tun bayan zuwan Ihsan ta Janye jikinta. Tana mata fatan alkhairi don idan haka ne ta ji shawaranta kenan ta rabu da Hashim ta kama dahir. Da safiyar litinin tayi karo da abubuwan da ta lissafo an siyo an jibge su a store ɗin gidan, babu ɓata lokaci ta shiga haɗa awara, ta dafa shi mai laushi sosai bata zaƙe masa wurin saka tsami ba, ta saka a kwando ya tsantsame lokacin da take dafa zoɓonta mai kayan ƙamshi, ta soya shi tayi mishi lafiyayyen sauce sannan ta haɗe su wuri guda, lokacin da take tasting kaman zata sulale a ƙasan kitchen ɗin tsaban daɗi. Da ta zuba ma Kiki ma saida ta ƙara mata a cikin na Abdulhameed bayan ta cinye. Sai ta zaunar da ita bayan sun gama ta kitse mata gashin kanta tass saboda ta gaji da ganin shi a haka, kuma dake hannunta babu zafi rikici kaɗan kiki tayi, tayi shiru tana sauraron tatsuniyar da Ilham take mata har ta gama mata cuku guda 16 ta tufke mata jelar su, sai gashi sun fito rass a farin kanta sun yi mata kyau. Ta gama shirinta na tafiya bayan dawowan Abdulhameed sai ga Kiki ta shigo. “Mimi wai ki zo in ji daddy” ta faɗa daga bakin ƙofa. Kirjin Ilham ya buga dummm. Ko magana bayi mata idan ba ya zamo dole ba, kiran menene yake mata yanzu?. Tana taraddadi a cikin ranta taje, yana zaune a dining da food flask ɗin da ta zuba masa abinci a gaban shi, saida ta rage tsayinta a wurin kafin ya ɗago ya kalle ta. “Do you have something else please? Bana cin wannan” ya nuna awaran da ya fara zubawa a plate don yayi zaton wani abu ne daban. Ta ware ido tana masa kallon rashin yarda. Daman akwai wanda baya son awara a duniyar nan balle ace baya ci gaba ɗaya? Ai awara ne ya kamata ma ya zama abincin duk duniya kowa yana ci kaman shinkafa da kuma buredi. Kaman ya karanci abinda ke zuciyarta yace “da gaske bana ci, ko Lukman ya sani, da ina ci da lokacin da na dauki littafin ki na ɗauki wanda ke cikin jakar ki saboda shima ƙamshin sa kaman wannan, amma ba zan iya ci ba” Girman idanunta ne suka ƙaru fiye da na da, kaman zasu faɗo ƙasa. Bata san bakinta ya furta “A Moher?” ba tare da sauti ya fito ba. Saida ta ji muryar shi a cikin kunnenta “Abdulhameed Muhammad Kagarko. Not A Moher, he's gone” Shine. Ta tuna lokacin da yake miƙa mata laidan ice cream ɗinnan, ta ga wani baƙin abu a jikin ƙaramar yatsar shi ta ciki. Da yake miƙa mata laidan fruit kuma sai ta saka ido ta fahimci tatoo ne amma ta kasa karanta abinda yake rubuce saboda mayar da hannun da yayi bayan ta karɓa. Sai yanzu ta gane menene a rubuce. A Moher. Ainihin sunan shi kuma Abdulhameed Muhammad. Shine wannan. “Ko oats ne a bani please, ba zan iya jiran isowan delivery ba and I'm starving” ya sake magana. Ƙafafuwanta da take jin su kaman igiyar lilo ta samu ta miƙar dasu ta koma kitchen ɗin. Saida ta ɗauko wata jibgegiyar tukunya ta kunna gas zata ɗaura sannan ta ankara ta mayar ta ɗauko karami ta zuba ruwa da oats ɗin a ciki. Mamakin da take yi ba wai na kasancewar shi wanda take tsammani tun daga farko bane sai inda rayuwa ta kawo shi. A tsawon shekarun da suka shuɗe bayan ganin da tayi masa na ƙarshe ta samu kanta da tunanin kalan rayuwar da yake ciki yafi sau nawa. Amma bata taɓa hango shi da wani halitta a jikinsa da ya daina aiki ba, bata hango shi yana kula da ƙaramar yarinya shi kaɗai ba saboda bai yi mata kalan wanda zai yi aure ba ma, bai yi mata kalan mazan da har zasu ɗauki kafar su suje niman aure a ɗauka a basu ba, ya dai fi kalan mayaudara masu wasa da zuciyar ƴammata. Amma yau A Moher ne ya koma haka?! Allah mai iko. Oats ɗin ta juye a bowl bayan ya gama, ta fasa madaran gwangwani guda ɗaya ta juye a kai sannan ta kai mishi ya saka sugar da kan shi. “gashi” Ta dubi kuɗin da yake miƙa mata da ido. “Kuɗin kitson Ikram ne, Nagode” Girgiza kai tayi, “ka bar shi kawai” muryarta ya fito a hankali saboda har yanzu mamakin da ya kamata bai saketa ba. Amma ba tayi ma kiki kitso don ya biyata bane. Sai ya mayar da kuɗin wurin Kiki dake zaune a gefen shi tana kallo a wayar shi, ya karɓi wayan ya bata kuɗin yace “sauƙa ki miƙa mata” Ta karɓi kuɗin ta sauƙo ta kawo ma Ilham inda take durƙushe. “Nima sai ki sake siya mun sweet ɗinnan” Tayi mata murmushi tana saka hannu biyu ta karɓi kuɗin. Daga kaurin su ta san da yawa, a ina ake biyan kuɗin kitso kamar haka?” “Sai kina mata Please, zan dinga biyan kuɗin shi separately” Godiya kawai tayi, kuɗin da ya bata yanzu kawai zai kai na kitson Kiki duk sati na rabin shekara. Kuma ranan da tunanin shi ta kwana, har tayi ma Ihsan taɗi itama ta dinga mamaki. “Wa ya sani ma ko shine ya canza miki initials ɗin Slum book ɗinki ya koma A&I? da kin tambaye shi ai” Ihsan ta ƙarasa da dariya tana tofe yatsuntsa suyi damshin da zata ji daɗin ƙirga kuɗin da ya ba ma Ilham. “kuɗin kitso ya cika Naira dubu ashirin cuss, nima dai kitson nan zan fara a kan yaran masu kuɗi daga gobe, har da ƙunshi ma sai su cika mun ya kai hamsin abuna” Ilham ta kai mata dukan wasa suka bushe da dariya dukkan su. Daman Allah yayi alƙawari ma duk wanda yayi imani, dukkan tsanani yana tare da sauƙi. Kuma itama ta fara ganin sauƙi a abubuwa masu yawa. A faro daga kan Hashim. Bai sauya sheƙa ba, yana nan da dunƙulallen hannu, amma cikin ikon Allah ya daina mata ajiya a cikin toilet tun bayan habaicin da Ihsan tayi mishi, wani lokaci ko ya manta ya fito sai ki ji ya koma yana korawa. Babun da take fama da shi ma yayi sauƙi sosai, yanzu bata rasa taro da sisi a hannunta, ga kawo kaza siya kaza da ake mata a asibiti bata rasa yanda zata yi da su ba, kuma abubuwan da suke samu daga gidan aikinta suke ci har su rage yasa bata buƙatar yin cefane saidai ta je ta jalafta ma Hashim abinda ya samu idan yaga dama ya siyo abinda zata haɗa ta dafa masa yayi daɗi. Seemahwrites ✨ ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh JODA by Sadi-sakhna DAƊIN ZAMA by Seemahwrites *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a turo shaidan biya ta 09039206763 Chapter 24 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Wattpad and Arewapen @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 UMMEE'S BAKING EMPIRE https://chat.whatsapp.com/L0WK91pLyVn8iQ6HjSwG8a?mode=gi_t *My Sister matso kusa ki ji.. Wannan cake ɗin da kike gani a online yake burge ki kin san inda zaki samu irin shi? Koko sha'awar glazed ko filled donuts kike yi? Ga plain ones for your Husband, father or boyfriend if they don't have a sweet tooth.* *Coming to you my brother.. kana iya bada kyautar nan mai sanya mace tsallen Murna? Ko Surprise ma abokai? For Eids, Anniversaries, birthdays, graduation or just to celebrate your girl or yourself? you can order a cake from us. Akwai crunchy cincin domin motsa baki ko a siya ma mama da baba su saka mana albarka.* *And don't forget about friendship or sibling bonds, You can always order a cake to celebrate their success or even to mock them with class😎, requesting captions that are satire and funny.* Muna siyar da: • Cakes na for every occasions ( birthday, graduation, anniversary dai dai sauran su) • Bento cakes • Cupcakes • Mouth watering brownies • Samosas • spring rolls • Glazed puffs • Filled, glazed and plain donuts. E.t.c *Ummee's Baking Empire –* *Making every Moment feels special. We always make sure that you recieved what you ordered 👌🏼💯* 📞 08173775170 📍 gwammaja, Kano 24… Daga inda Abdulhameed ya saka kujera ya zauna da coffee table a gaban shi, ya daura laptop da takardu a kai, yana iya hango Kiki dake karaɗe harabar gidan a kan kekenta. Tun kafin a sallame su daga asibiti ya ɗaga keken a inda zata iya ɗaukowa, kuma bayan abinda ya faru bai yarda yana barinta ta fito waje wasa ita kaɗai ba, sai yau da ta saka mishi bori shine ya ɗauko aikin da yake ƙarasawa suka fito tare. Rabin hankalin shi na kan abinda yake typing a cikin laptop ɗin rabi yana kanta lokacin da saƙo ya shigo wayar shi. Kafin hankalin shi ya kai kanshi wani saƙon ya sake shigowa, kuma sai a lokacin ya lura. Ya bar abinda yake yi, ta cikin akwatin bayan wayan yaga an rubuta ‘2 Unread messages’. Ya ɗauki wayan a cikin hannun shi na dama, da yatsar shi babba ya buɗe shi, haske ya cika screen ɗin yana bayyana masa hoton wacce ya fi ji a kusa da zuciyar shi a yanzu. Tun tana shekara biyu yayi mata hoton a gidan zoo da ya kaita taga namun daji. Yana iya tuna yanda take dirin murna tana nuna mishi biri da ƴar yatsarta tana cewa “daddy monkey” sai kuma ta shafa overall ɗin jikinta tana washe haƙora don overall ɗin monkey ɗin ya saka mata mai kunnuwan biri a jikin hulan rigan harda bindi ta baya, farin cikin da ya lulluɓeta yasa ya saita cameran wayan shi ya ɗauketa a hoto, kuma ko da ya tashi canza waya hoton ya mayar a kan lock screen ɗinsa, kuma shine har zuwa yau. Ya jawo notification bar don ya duba wanda ya turo saƙon, idan ba mai muhimmanci bane ya bari sai Kiki ta sauƙa daga kan keken nan da yake ganin kaman zata sake faɗi ta sake jin wani ciwon. Number ya gani babu suna, saboda bai yi saving ba, ko kuma yace ya dawo ya goge bayan yayi daga farko, saboda bayi buƙar kusancin mai lambar da su a yanzu. Shigowar saƙo a karo na uku yasa ya danna abinda aka rubuto ya bayyana. ‘Na sani I'm asking for too much, amma ka taimaka min na ganta ko sau ɗaya ne’ ‘please Abdulhameed’ ‘Dan Allah’ Yana gama karantawa kuma saƙo na hudu na shigowa. ‘rabona da saka ta idanu na fi shekara, kamanninta zai ɓace a cikin kaina’ Sai saƙo na biyar ‘sau ɗaya kawai Abdulhameed. Dan Allah!!!' Fita yayi daga kan saƙon baki ɗaya ya rufe wayan ya mayar da shi ya ajiye. Bayi da lokacin ta. Ya mayar da hankalin shi kan yarinyar dake zagayawa a kan kekenta pink colour mai tayoyi uku daga baya ɗaya a gaba. Daga shi har ita sun samu nutsuwar da basu da shi kafin shigowar Ilham Rayuwar su. A kallo ɗaya zaka gane haka a jikin Ikram, Da walwalan ta, da ma ɗabi’unta. Shi kuma a zuciyar shi yake jin akwai wani kaso mai girma na nauyin da ya ragu masa. Kaman yanzu yana da wani assurance ne na komai zai tafi lafiya a tare da yarinyar shi, tunda Ilham tana nan. Basu koma cikin gida ba saida Maghriba ta gabato, ya shiga da ita bathroom ɗin shi zai yi mata alwala ganin ta fara son sallah amma sai tace zata yi da kanta. Famfon cikin tub ya kunna mata saboda na sink yayi mata tsayi. Kuma ta kamanta yin alwalan dukda ba a jere ta yi komai ba don da fuskarta ta fara, ta wanke ƙafa sannan ta dawo ta kuskure baki ta wanke hannu. Ya dai samu tayi ɗin kuma haka yayi masa daɗi, dama ganin ta yi ƙarama ma fara Sallah yasa ya sakankance bai fara koya mata komai ba. Gyalen wani abayanta yayi ƙoƙarin tukuikuya mata saboda bata da hijabi, da tace da ƙafarta zata tafi sai ya saka mata takalmi, suka shiga part ɗin mahaifinsa yana riƙe da hannunta har ɗakin Aunty Surayyah saboda idan ya je masallaci sai yayi Isha yake dawowa. Ya haɗu da mahaifiyar Hudah tana alwala a ƙofar ɗakinta da zasu wuce, amma yanda bata ɗaga ido ta dube shi ba haka shima ko sannu bai ce mata ba, bai kuma umarci Kiki ta gaida ta ba suka wuce abinsu. Kiki tayi ta dungurawa a darduman Aunty Surayyah bayan ya tafi ya barta, sai ɗauko wani darduman Aunty Surayyah tayi ta bar mata wancan. ….. “Ba zaki ci abincin ba?” Tambayar da Hashim ya tsareta da shi kenan bayan ta tashi zata bashi wuri. Juyowa tayi ta sake kallon abincin kaman ba ita ce ta dafa ba. Shinkafa ce ƴar gida da miyan busasshen tumatir, ita kuwa basmati ta ci da nama zuƙu-zuƙu a cikin miyan da haɗaɗɗen coleslaw ya ji ƙwai da mayonnaise harda wake da masaran gwangwani. Ta taɓe baki ba don ta raina abincin ba, sai don Hashim ɗin ya fi ƙarfin wannan cimar a gidan shi, shinkafar ma wanda aka kawo mata daga wurin Maama ne kayan miya kawai ya kawo. Mutumin da albashinsa babu laifi kuma ba nauyin kowa yake da shi a wuyansa ba bayan nasu da ya gagara sauƙewa, ita bata san ma me yake yi da kuɗin ba bayan siyan tsadaddun sutura ma kan shi da kashewa ƴammata. Ta girgiza kai “Alhamdulillah. Na ci abinci a gidan aiki na” “Muftee fa? Banga kin ɗiba zaki kai mishi ba” “Shima yaci” “Na gidan aikin?” Ta gyaɗa kai. “Gaskiya ne, zo ki rage tsayin ki a nan” ya cire cokalin da yake motsa abincin da shi ya nuna mata inda yake son ta zauna da shi. Da tayi kaman yanda yace sai ta ɗago tana kallon shi. Ya kalli cikin idanunta da kyau, sosai yaga ta canza masa, ba kamanninta ba, amma akwai wani abu da ya canza a game da ita a kwanan nan. Har yanda take kallon shi, akwai wani abu da ya ɓace a cikin idanunta. Wannan raunin nata yau bai gan shi ba, kuma hakan bai yi masa daɗi ba. “A gidan aikin naki ne suke baki abinci har ki kai ma ɗan ki?” Da “Eh” ta amsa cikin tabbatarwa. “Aikin me kike yi?” Sai yau yaga daman tambaya? Ta bashi amsa da “Gyare-gyaren gida ne da girki sai rainon yarinya.” “Kuma kina da majinyaci a kwance kike zuwa kiyi duk wa’innan abubuwan?” Shiru tayi ta sauƙe kanta ƙasa, don wannan ba tambaya mai niman amsa bane, accusation ne, so yake yi tace wani abu ya samu dalilin mata wani wulaƙancin amma ba zata ce komai ba, ta riga da ta san halin shi maganin zama da shi zata cigaba da haɗiya. “Nawa ne suke biyan ki da kika zaɓi ki kai ƙara na don nace ki bar aikin, kika zaɓi ki kori ƴar uwar ki a kan ki ji magana ta?” Da sauri ta sake ɗagowa tana kallon shi da mamaki kaman ba shine ya bata zaɓin hakan ba amma ya dawo da komai kanta. Yanzu idan ta faɗa masa gaskiyar nawa ake biyanta abubuwan da take samu tayi da kuɗin ba zai yiwu ba. Don ko lokacin da take ɗaukan dubu goma sai yace tayi cefane ko wani buƙata idan ya taso mata a cikin kuɗin zai bata daga baya, shikkenan kuma ya wuce ba zai bayar ɗin ba, idan tayi magana kuma cibi ya zamo ƙari. Don haka da ta buɗe baki sai harshenta ya furta “Dubu Talatin da biyar” Ta ƙara biyar ɗin a kai ne saboda lissafin zai fi zama masa. Kuma ya yarda daga ganin yanda ya waro ido “Kaii. Da gaske?” Ta jinjina kai “Masu rufin asiri ne sosai kuma suna ci daga dukiyar da Allah ya hore musu” Maimakon ya gane magana ta faɗa masa sai ya girgiza kai “Dole ki daina cin abincin gidan nan kam. Kin samu Capacity Hajiya Ilham, Allah dai yasa ba da kuɗin haram ake biyan ki ba, ko wata rana a haɗa dake a siyar a ƙara yawan dukiya” Bata san meyasa maganar tashi ta bata dariya ba, amma ta ga mamakin murmushin da tayi a kan fuskar shi. Ya ɗaura da “Toh daga yanzu dai sai a sakar mun wuya in sha ruwan sanyi tunda na barki ki nemi na kan ki, idan ma wani abu daban kike yi ake baki wannan kuɗin ke kaɗai zaki san nayi randa ta kwaɓe miki” Bayan yawan kuɗin da ta ɓoye mishi, akwai abinda bata fito ta sanar da shi ba. Kasancewar ma single father take aikin, saboda ta san ba zai fahimta ba, koda tayi masa bayanin yanda abin yake ba zai fahimta ba. “In sha Allah sai alkhairi, Nagode sosai” daga haka ta miƙe ta fita ta kimtsa inda ta gama dafa abincin don barci take ji tun goma bata cika ba. …… 7:20am Kayan da zai saka yake dubawa, kullum sai ya zo irin haka yake lura da yawancin wandunan shi farare ne ko kuma kala masu haske. Amma idan ya je siyan kaya kaman ya manta sai ya sake debo irin su, kuma bai iya saka manyan kaya ba, bai saba da sakawa ba tun tasowarsa, takura sosai yake yi idan ya saka har sai ya dawo ya cire ya ji sakat, shiyasa wata rana idan yazo niman abinda zai suturta jikin shi sai ya daɗe yana lalumen wanda zai banbanta da sauran wanda ya sanya a cikin satin, don sai ayi tunanin kaman kaya ɗaya yake maimaitawa. Farin wandon ya haƙura ya ɗauka ya haɗa shi da farin riga mai laushi, sai ya ɗora baƙin open suit a kai kada yayi kaman gawa a cikin likkafani. Yana maƙala agogo a tsintsiyar hannun shi saƙonta ya sake shigowa. Bai ji tsaƙin da ya ja a cikin kunnen shi ba amma ya san yayi. Tun jiya ta dame shi, messages kusan 20 a tsakanin yammaci zuwa safiya duk ya share amma bata haƙura ba. Ya saka wayan a aljihu ya feshe jikinsa ta turaren Amouage king Blue, sannan ya kashe wutan ɗakin ya fito. Kiki na zaune a kujeran dining, Ilham na ɗaukan wani round abu da fork tana saka mata a plate amma daga wurin ƙamshin abun yana shiga masa hanci duk da suma na turaren shi ne yasa duk suka juyo suka dube shi, Kiki ta sauƙo da gudu ta zo ta rungume ƙafafuwan shi kaman yanda ta saba. “Daddy kazo Mimi ta saka mana abinci” ta ja hannun shi zuwa teburin, kuma Saida ya ƙarasa kusa ya gane menene, masa ne, abinda bayan a dalilin yunwa da ta kusa masa illa bai sake ci ba. Ai kuwa jiya yaga shinkafan yin masan da ta jiƙa, sauran kaɗan ya zubar da yazo wanke kwanukan da suka ci abincin dare don ya ɗauka ruwan datti ne, har ya fara juye farin ruwan a cikin sink yaga shinkafa a ƙasa sai ya sake zuba wani ruwan a kai ya bar mata kayanta, ashe ma sune zata markaɗa ta soya ta basu su ci. Saida ta ƙarasa zuba yanda plate ɗin zai ɗauka ta lulluɓe sauran da baking sheet da ta saka saboda tururi kada ya jiƙa shi, ta mayar da murfin ta rufe kana ta buɗe kwanon miyan shima ta zuba yanda zai ishe su su biyu. Kuma bai samu ƙwarin guiwar cemata baya cin abinda ta dafa yau ba ma don yaga alamun abun bai yi mata daɗi ba last week da tayi awara bai ci ba. Bayan ta wuce da ya ɗauki fork ya gutsiri ɗaya ya dandala masa miya ya kai baki sai ya gyara zama ya zaƙe yana ci sosai. Vibration ɗin da wayan shi ya cigaba da yi yasa ya dakata ya ciro wayan ya duba. ‘Abdulhameed’ Ita ɗin ce dai. ‘Na dawo Kd. Zan zo in ganta please, sau ɗaya kawai” “Pleeeesee” Kaman zai share saƙon sai dai kuma bai san me zata aikata ba don ya lura halin su kusan ɗaya da ƴar uwarta, duk abinda suka ga dama suke yi a lokacin da suka yi niyya. Ya saita cameran wayan a fuskar Kiki dake fama da wani ƙashi tana ta gwaigwaya, bakinta duk miya, ya ɗauketa a hoto ba tare da ta sani ba, ya tura ma wannan numbern. Sannan ya shiga cikin gallery ɗin shi, ya ɗauko wanda yayi mata ranar da zata fara zuwa makaranta, da uniform a jikinta, jaka goye a bayanta, tana ta murna kafin ta je ta dawo da kuka, shima ya tura mata kana ya shiga rubuta reply. ‘She’s Healthy and Happy’ ‘Kada ki zo mun gida.’ ‘Don't you dare come to my house’ Daga nan kuma sai ba'a sake turo komai ba har ya ƙammala shirin barin gidan. Da ɗan dama Ilham ta haɗa ƙullin masan don tana son zuba ma aunty Surayyah ga kuma wanda zata ci, dukda ta so tafiya da shi ma Ihsan amma sauran babu yawa sosai, saboda wanda ta cika food flask ɗin da shi a kan idan suka rage zata ci Kiki tace ta saka mata a kwano ta tafi da shi makaranta. Tana cikin soya wanda ya rage ɗin bayan sun tafi, sauran ita kaɗai a part ɗin ta fara jin knocking a ƙofar parlour. Ta juya masan ta rage wutan ƙasan kaskon kafin ta fita ta duba wanene. Ɗaya daga cikin yaran gidan ne, amma bata san sunanta ba, ita ce dai ranan tace mata babu Hajiya Surayyah a gidan. Suka tsaya suna kallon kallo an rasa waye zai fara gaida wani a cikin su. “Yaya Abdulhameed yana nan?” Huda ta tambaya bayan saida ta tabbatar da baya nan ɗin tazo. Ilham kaman zata bata amsa daidai da tambayarta tunda sun fita sanin yana zuwa aiki amma sai tace “baya nan” “Okay daman yunwa nake ji, shine na zo ki saka mun abinci.” Daga yanda Hudan tayi magana har yanda ta coge da hannunta goye a kirji, ko ita ce take biyan Ilham kuɗin dafa abincin albarka. Amma a wannan gidan bata da ta cewa ne, sai ta ce mata “toh ina zuwa” ta koma ciki. Ba zata so su kai ƙarar ta wurin Abdulhameed ta hana su abinci ba, bayan ita ƴar aiki ma yana gani take tafiya dashi bai hana ta ba. Sauran duka ta kwashe daga cikin kasko don ya soyu, ta zuba mata a plate da sauran miyan sannan ta rufe da wani plate ɗin ta fito da shi, a parlour ta samu Hudah zaune a kujera ta ɗora daya kan ɗaya tana jiranta. Ta ƙarasa ta miƙa mata, kuma babu sannu balle na gode ta karɓa tayi tafiyarta. Ƙofar da ta buɗe ta wuce ta ciki ma ta bar ma Ilham ɗin ne tazo ta rufe. ```````````` Seemahwrites ✨ ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh JODA by Sadi-sakhna DAƊIN ZAMA by Seemahwrites *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a turo shaidan biya ta 09039206763 Chapter 25 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Wattpad and Arewapen @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 25… Ba'a rufa kwana biyu ba sai ga wata daban ta zo. Ita dai ta Iya gaida Ilham kana ta gabatar mata da kanta da sunanta Ameerah, kuma ƙanwar Abdulhameed ce sannan ta faɗi abinda ya kawota. Haka ta sake zuwa ta juye musu abin karyawanta, ta jira har saida ta gama abincin rana kafin ta samu abinda ta saka a cikinta mai nauyi. Kaman da wasa sai suka maida hakan dabi'ar su, haka zasu zo su karɓi rabonta a barta da kame-kame, kuma tana tsoron taɓa sauran abubuwan da ba'a mata izini a kai ba ta koma ɓarauniya. Ranan Alhamis da tayi chips and eggs na karyawa, bata jin motar su Abdulhameed ya bar unguwan Hudah ta zo ta karɓa, hakan bai yi musu ba, tana gama vegetable couscous da rana sai ga zakiyya da Ameerah sun zo a tare, ko su wanda ta dafa abincin domin su basu kai ga ci ba suka shigo har cikin kitchen ɗin kowa da plate ɗinta da suka ɗauka a cikin wanda ta wanke ta jera su a dish rack, suka ɗebi abinda yayi musu a cikin wanda tayi niyyar ɗiba ma Hajiya Surayyah da wanda zata kaima Ihsan da Muftee. Bata jinjina ma lamarin su ba saida ta fito parlour ta same su sunyi ɗai-ɗai, sun kunna TV suna ci suna kallo, ga lokacin tashin su Kiki a makaranta yayi. Ganin abin nasu na niman wuce gona da iri gashi duk gyaran da tayi ma wurin sun ɓata shi, couscous har kan carpet, sai ta kasa haƙuri ta je kansu ta tsaya “Bayin Allah zan rufe gidan mu je ɗauko Ikram daga school” Wani wulaƙantaccen kallo kawai Ameerah ta watsa mata, sai Zakiyya ne tace “kiyi tafiyar ki mana ai muna nan, mun faɗa miki mu su wayene, me ma zamu ɗauka a gidan toh da sai kin rufe?” “shikkenan bari na kira Hajiya Surayyah in sanar da ita tunda amanar gidan aka bani.” Ta juya zata koma kitchen ta ɗauko wayarta, da hanzari dukkan su suka miƙe. “Laa daga ita har shi ba'a musu gwaninta kin ji, gwamma ma ki daina zaƙewa domin idan ya juyo ta kan ki kema ba daɗi zaki ji ba” cewar Zakiyya. Ameerah ta fisgo hannunta “da’alla yi mata shiru kizo mu tafi” Suka tsallake plate ɗin sauran abincin da wurin da suka ɓata suka tafi suka bar mata. Saida ta koma ta sake ɗauko tsintsiya ta shiga tattara wurin, tana durƙushe da kitchen towel a hannunta tana goge jikin kujerar da suka shafawa maiƙo, gani tayi kaman idan ta bari sai sun je ɗauko Kiki sun dawo ba zai fita ba. A ɗan razane ta miƙe lokacin da aka turo ƙofar parlour, haka kawai jikinta ya bata Abdulhameed zata gani sanin cewa tayi ba daidai ba. A maimakon shi ɗin sai ta ga yarinyar shi tana shigowa, biye da ita kuma Aunty Surayyah ce. “Mimi oyoyooo” Kiki tazo da gudunta goye da jakan makaranta ta rungume kunkumin Ilham da ta bushe a tsaye. Aunty Surayyah ta ƙaraso idanunta a kan tsintsiyan da aka ajiye a gefe da fakan da bata kai ga zubar da dattin da ta kwashe a ciki ba. Cikin muryar da bai yi kama da na tuhuma ba take tambayarta “Sai yanzu kike sharan gidan Ilham?” “Hajiya kiyi haƙuri, su Ameerah ne suka ci abinci shine nake share wurin, amma yanzu nake shirin zuwa in ɗaukota” Fatan goshin Aunty Surayyah ya tattare lokacin da ta tsuke fuska tana yi ma Ilham kallon mamaki kaman bata yarda da abinda tace ba. “Su Ameerah? A cikin gidan nan?” ta tambaya yatsarta na nuni da ƙasan parlourn. Ilham ta sauƙe kanta don bata da amsar bayarwa. “Toh ke kuma abincin wa kika dauka kika basu?” Kanta a ƙasa tana kallon cikin idanun kiki dake rike da ita har lokacin tace “sauran wanda ya rage ne suka ci” “Sauran wanda ya rage ko kuma abincin ki? Idan ba zasu ci abinda iyayen su suke dafwa ba basu da hannu ne zasu zo wurin ki su karbi abinci? Ko sune suka ajiye ki?” Ilham bata taɓa jinta tana faɗa ba, ko yaushe suna haduwa ne da fara'a a fuskar Aunty Surayyah, tana faran-faran da Ita, matsalan da take gujewa gashi nan saida yayi mata dabaibayi, saboda da ta haƙura ta basu ma ba tsira tayi ba. Ta rage tsayinta ta hanyan sauƙa a kan guiwowinta ta daidaita tsawonta da na kiki tana sauraronta. Jin ta sake yin shiru Aunty Surayyah sai ta cigaba da faɗa. “Banda iskanci wani kalan kayan abinci ne bayi siya ya jibge musu sai sun zo nan sun karɓa? Da abinda yake ci da wanda bayi ci duka yake cika musu store da shi ko wani wata. Kuma da kema baki basu fuska ba sun san basu isa su fara ba, amma sarai sun san gamuwan su dashi ba daɗi” Saida ta tabbatar ta kai aya tace “Kiyi haƙuri Hajiya, ba za'a sake ba in sha Allah” amma ta sani idan aka faɗa ma Abdulhameed sabon faɗan da zata sha sai yafi wannan. A hankali kuma ta zame ma yarinyan jakan bayanta tare da cire mata takalmin da ta shigo ciki da shi. Ta shafa kitson Kiki da har yayi sako-sako saboda laushin gashinta, tana ɗorawa da “Kuma ban san an daɗe da tashin su ba ganin lokaci bai tafi ba, tattara wurin kawai naso yi mu tafi” Numfashi Aunty Surayyah ta sauƙe kafin ta miƙo mata takardan hannunta. Ilham ta saka hannu biyu ta karɓa. “Kira na aka yi a makarantar tasu zasu yi talent show shiyasa na je da kaina suka yi mun bayani muka dawo tare. Na kira in sanar da ke ban same ki ba, amma na faɗa ma driver idan kin fito ya faɗa miki” “Ayyah wayan na ajiye shi a saman fridge a kitchen ban gani ba, kiyi haƙuri dan Allah hajiya” Aunty Surayyah ta amsa da “babu komai, ki duba Idan akwai abinda zaki iya taimaka mata da shi toh, ko kuma ni da mahaifinta muga yanda za'a yi a weekend tunda abun sai ranan talata” Ta buɗe takardan dake ɗauke da tambari da kuma adireshin makarantar a sama tana duba abinda ke ciki. Jeren gwanon abubuwan da yaran zasu zaɓa ne kusan guda goma, kama daga Creative art, story telling, cultural dance harda waƙoƙin yara Nursery Rhymes, da kuma kwanan wata da lokacin da za'a yi taron. Wanka ta fara yiwa kiki ta bata abinci sannan suka zauna tana tambayarta ko tana son ta koya mata tatsuniyar da zata je ta bayar a makaranta, sai ta girgiza kai wai za'a mata dariya, kuma bata iya zane sosai ba tunda tana ganin yanda take yi idan zata taya ta homework, idan aka samu wa’inda suka fita iyawa zata faɗi tunda abun kaman gasa ne, sai gashi sun tsaya a kan cultural dance don shi Kiki ta fi so, amma bata sani ba ko babanta zai yarda. Saida Abdulhameed ya dawo, Aunty Surayyah ta shigo ta ƙofar baya ɗauke da ƙaton cooler tace Ilham ta ɗauka ta tafi da shi abincin ranan ta ne, bayan kuma ta riga da ta ɗebi na dare. Mamaki da damuwa yasa ta buɗe kwanon tana kallon taliya da miyan jajjage yana tururi, Aunty Surayyah girki kenan ta je tayi mata? ta ɗauka wancan maganan ya wuce ai, ta yi tunanin shikkenan ta fasa faɗawa Abdulhameed tunda ta mata faɗa kuma ta bata haƙuri. Sannan a lokacin da tayi musu sallama zata wuce tana jin Aunty Surayyah tana mayar masa da abinda ya faru tiryan-tiryan, shi kuma ya bata hankalin shi ɗari bisa ɗari, idanun shi kafe a kan fuskarta yana karantar abinda take cewa a hankali kuma ɓacin rai yake bayyana a tashi fuskar, ko lura da Ilham bai yi ba har ta wuce. Ƙarasa wuninta tayi a cikin zullumi bayan ta koma asibiti, aiki dai gashi kaman da sauƙi tunda ta fara gane kan komai amma matsaloli kala-kala sai tasowa suke yi duk ƙoƙarin da take yi na gujewa hakan. Saidai washe gari tun tana saka ran Abdulhameed zai ce wani abu har ya fita da safe ko kallonta bai yi ba. Bayan misunderstanding da suka samu a kan Ikram, ya ƙudurta a ran shi ba zai sake tuhumarta da laifin da bayi da tabbaci a kan itace mai laifin gaba ɗaya. Shiyasa yayi ma tufkar hanci a inda yake ganin ya dace. Saboda ya gwada rashin jin daɗinsa a kan abinda yake ganin anyi ba daidai ba, Mahaifinsa ya sake yin iyaka ma mutanen gidan da abinda ya shafe shi. “Shikkenan yara ba zasu yi laifi a tsawatar musu ba Yaya?” “Kiyi mun shiru Surayyah!” Ya daka mata tsawa wanda Abdulhameed ne kawai bai ji sautin shi ya shiga kunnuwan shi ya ratsa jijiyoyin jikinsa kaman sauran mutanen wurin ba amma ya gani a yanda jikin mahaifin nashi yake tsuma. “idan abinci ne ya daina saya ya gani ko iyalaina ba zasu rayu ba. Uwar shi ma ni na ciyar da ita har ya samu yazo duniya balle yayi tunanin lalacewa na ya kai ya goranta mun” Daman a haka aka fara, kuma a haka tafiyan yake cigaba har zuwa yau. Ya fara ƙin mahaifin shi ne da danginsa saboda Nne bata son su, amma sai bayan ya dawo cikinsu a lokacin da ya rasa ta ya fahimci dalilin da yasa ta nesanta shi da su. Ƙaddara da soyayya ne ta haɗa duniya biyu mabanbanta. Rayuwa, yau da gobe da kuma banbancin yanayi ya hana kowanne samun sukuni a cikin inuwar ɗaya. Amma da yana da wurin zuwa, da dangin mahaifyar shi sun kalle shi a matsayin jinin su, a matsayin ɗa tilo a wajen ƴar uwar su ba ɗan bahaushe ba, da babu abinda zai kawo shi kusa da Kaduna ko arewacin Nigeria gaba ɗaya. Ilham ta yi murmushi lokacin da Kiki ta ƙarasa addu'an da ta koya mata daidai babu kuskure ko ɗaya. Ta rataya mata jakanta da water bottle, suna ɗaga ma juna hannu ta shiga mota suka tafi. Da taji knocking bayan tafiyar su har ta saka ma ranta yaran gidan ne suka sake dawowa, ta je ta buɗe tunda yanzu ta san nayi da su, sai ta ga Aunty Surayyah da shirinta na fita, ga jaka rataye a kafaɗanta key ɗin motar ta a hannu. “Ilham zo muyi magana” tace tana shigewa ciki. Ilham ta tura ƙofan ta mara mata baya, da Aunty Surayyan ta samu kujera ta zauna sai ita ta nemi matsuguni a ƙasa daga gefen kujeran tana sauraronta. “Daga yanzu idan kina buƙatar wani abu kawai ki kira a waya ki sanar dani ba sai kin shiga ɓangaren mu ba, ko Kiki zaki iya faɗa mata ta sanar da mahaifinta idan na gaggawa ne ko baki same ni a waya ba. Idan kuma akwai wani abun daban ni zan zo da kaina, ko abinci ne zan zo in ɗauka amma bani son ki sake shiga wurin su tunda suma an yi musu iyaka da nan dan Allah” Abdulhameed bai ce komai ba, ba don babu abinda ya faru ba, kawai bai ce mata komai bane wannan karon. “In sha Allah Hajiya.” ta amsa kanta a ƙasa. …. Tun ganin da yayi ma wata budurwa a wurin dinnern abokin aikin shi kwanaki uku da suka wuce bai yi tsammanin idan yayi mata magana zata kula shi ba saboda haɗuwarta, ya san tafi ƙarfin aljihun shi, amma yana daga cikin jerin mazajen da abu mai kyau ko kwalliya yake ɗaukan idanun su, shiyasa bai yi ƙasa a guiwa ba ya gwada sa'ar shi, sai gashi bayan lambar waya har adireshin gidan su dake unguwan Rimi ya samu. Babu ƙarya ya ɗauki wanka a taron, har kaman zai fasa zuwa event ɗin saboda damuwan shi a yanzu shine ya ƙarasa haɗa lefen Khausar ne, kuma ya san ita da mahaifiyarta sun saka buri shiyasa yake son yayi mata mai kyau. Sai gashi ya samu aron kuɗi a wurin ogan shi ya samu ya ɗinka babban rigan da abokai suka saka ya siya da sabon takalmi sai yayi aron hula. Shiyasa da ya tashi zuwa gidan ma bai je mata a kan mashin ba, ya roƙi wani abokinsa mai hidiman ƙarya ma ƴammata irin shi amma shi yana da mota domin daga babban gida ya fito, wani ɓangare na halayen su da yazo ɗaya yasa abokantakan sun yayi ƙargo. Suka shirya kaman mutanen arziƙi suka ɗauki hanyar Unguwar Rimi. Kyau da sabuntakar motar da tazo wucewa a lokacin da suke ƙoƙarin gano gidan da zasu je yasa Hashim ya bi motar da kallo. Gilasan motar a sauƙe suke don haka ya samu damar ganin wanda yake zaune a ɓangaren mai zaman banza, a lokacin da mutumin ya juyo alaman magana yayi da wanda ke zaune a gidan baya, sai ya ɗaura guiwar hannun shi dake maƙale da agogon fata a daidai inda sleeve ɗin baƙar rigar shi ta tsaya a jikin window ya ɗan dafe kan shi. Kallon sakwan guda kawai ya samu yayi mishi, amma ya hango abubuwa da yawa da shi bayi da shi a wurinsa, abubuwan da kallo ɗaya zaka yiwa mutum fahimci suna tare da shi, cikin su harda kuɗi. Bai fara lissafin abinda suka biyo baya ba, idanun shi suka sauƙa a kan wanda take gidan baya. Daga kalan kayan jikinta, sarƙan dake manne a wuyanta, mayafin da ta lulluɓe kanta da shi, duk sun isa su tabbatar masa ba ita bace, amma raunin da ya ji mata a fuskarta shi yayi mishi rana. Tabon wannan raunin na idonta da kuncinta shi ya haska masa Ilham ya ganta ya ganeta. Sai kuma faffaɗan murmushin da ya wadaci fuskarta. `````````````````` Seemahwrites ✨ ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh JODA by Sadi-sakhna DAƊIN ZAMA by Seemahwrites *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a turo shaidan biya ta 09039206763 Chapter 26 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Wattpad and Arewapen @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 26…. Rayuwa tana da wani hanya na ba ma ɗan adam mamaki, mamaki a kan kanshi. Sai kaga mutum ya daɗe yana burin zuwan wani dama ko lokaci saboda abinda yake so ya aiwatar a cikinsa, amma idan lokacin ya riske shi sai ya gagara aiwatar da abinda yake buri, saboda wannan daman babu ita, ko kuma yanayin ya sha banban da tunaninsa. Kaman yanda ta daɗe tana kokwanto a kan A Moher, sai gashi a yanzu ko kallon shi ta kasa yi da tunanin dake ranta, nashi kallon ma ta fara kasa jurewa, wanda yana tsananta shi ba da wani nufi bane sai don ya fahimci komai da kowa da idanunsa. Amma ita kunya take ji, ba kunyar shi kawai ba. Harda kunyar kanta. Shi da take tsammanin zai zamo abun Allah sarki a nan gaba, sai gashi ko da Allah ya tauye masa wani ɓari na jikinsa amma ita ce ke nima a ƙarƙashin sa. Kuma ya gane ita wacece, ya bayyana mata hakan. Haka kuma yanayin da yake kallonta da shi a cikin idanunsa kafin ko bayan nan bai canza ba, yana kallonta ne kaman ɗaya daga cikin miliyoyin mutane da Allah yake haɗa hanyar su da taka a tsawon rayuwarka. Ta banbance hakan ne da yanda ta ga yake kallon wa'inda suke da muhimmanci a rayuwar shi, kaman Kiki da Aunty Surayyah, yana Kallon su ne da zuciyarsa a maimakon idanuwa. Babu kusancin da ya wuce abinda yake kawota gidan a tsakanin su, daga ranan da awara ya bayyama mata shi wanene kuma sai ta ɗauki matakan ƙara nisanta kanta da shi. Banda ranan da ta makara saboda tuyan masa yana da ɗaukan lokaci, da safe kafin ya fito zata gama shirya musu abun karyawa a dining table ta zuba ma kiki nata ta bar wurin, tun da ta lura cin abincin da ya fara hucewa ba damunsa yayi ba, ko ta zuba da zafi ma sai ya jira ya huce ya fara ciyar da kiki kafin ya kai nasa bakin. Haka da yamma idan ta gama yiwa Kiki abinda ya dace zai dawo ya samu abincinsa, kuma kafin ya gama ci ya huta ta gama na dare saidai tayi masa sallama ta wuce. A bisa roƙon Aunty Surayyah ta nimawa Kiki kayan Fulani na talent show ɗinsu. “Daman babanta bafulatani ne?” Ilham ta samu kanta da tambaya don Abdulhameed bai yi mata kalan Fulani ba, Hausa ma idan yana yinta kaman wanda ya koya ne kawai saboda zama cikin hausawa. “A’a yace wai mahaifiyarta ce bafulatana” Ta ji maganar a wani iri, kaman itama Aunty Surayyan bata da tabbacin yaren matar da suka zauna da ita a gida ɗaya, duk da ma zuciyarta ta daɗe tana tambayar mahaifiyar Kiki tana ina ne a halin yanzu? amma bata bari tambayar ya iso kan harshenta ba. Ta fi dai kyautata zaton mutuwa tayi, ko hala rabuwa suka yi, domin bayan a kan zancen kayan fulanin bata taɓa jin wani a cikin su ya ambace ta ba. Akwai gidan da ake bada hayan kayan fulani a unguwan su, kuɗin da Aunty Surayyah ta bata kuma ya kai a siya sabo harda canji, shiyasa ta ba ma matar kuɗin kawai tace ta taimaka a siyo ma Kikin harda sarƙa da awarwaron murjani, ƙwarya, ludayi da kuma faifayi. A weekend ta karɓi kayan ta wanke ta goge mata tare da kayan Hashim da ya tara da ma nata saboda yanzu bata samun lokaci sai weekends ɗin, sai kuma na Muftee da na Ihsan. Gajiyan wanki da gugan yasa da wuri ta kwanta ranar asabar bayan ta ajiye ma Hashim taliya da manja da yaji. Fitsari ya tashe ta ƙarfe ɗaya na dare, ta kunna tocin wayanta tana haskawa saboda nepa sun ɗauke wuta, ta ci karo da kwanon abincin a inda ta ajiye mishi, da ta shiga ciki ma gado yana gyare tsaff, mai birkitawa da juye-juyen danna wayarsa baya kai. Ta kaikaita murfin abincin kada yayi tsami ta gyara tayi kwanciyarta don ya sabar mata da haka, bata da ƙimar da ko wani uzuri ne ya riƙe shi ya kirata ya sanar da ita, balle ma idan wani abun ne yake yi shi ya sani, bata da nutsuwar da zata saka damuwar shi a cikin kanta, bata jin kishin Hashim a ƙirjinta ko me zai yi, gargaɗin da tayi ma Khausar ma Saboda ita ne, saboda ta san ba kowace mace bace zata iya irin zaman da take yi. Da asuba kuwa da zata shiga yin alwala sai gashi nan kwance cikin wata sabuwar shadda yana ta minshari, ga sabon hula da takalmin da ya cire su a inda ya jefar da babban rigan kayan, sai takardan cupcake da takeaway ɗin da ya gama cinye abun ciki har ƙashin saida ya tattauna cokali kawai ya bari, sai goran soft drink. har tayi shirin fita asibiti kuma bai farka. Ranan talata ya kama ranan da za'a yi talent show ɗin su Kiki, kuma kowani yaro ana bashi pass guda uku ne na iyayen shi biyu da sibling ɗaya idan an fi haka yawa kuma saidai ku bada kuɗi ku siya wani pass ɗin. Sai gashi guda ukun da aka bayar ma Abdulhameed ya rasa yanda zai yi da su, Kiki bata da kowa sai shi, kuma shima tun da ya rasa Nne yake jin shi kaman bayi da kowa, sannan mura mai zafi ya kama Aunty Surayyah ko A&I bata iya zuwa ba ranan Monday, ba zai so ace Kiki ne kawai bata da familyn da zata nuna ma sabbin ƙawayenta da malaman su ba. Da ya samu shiga yi mata ya jiki bayan ya dawo daga sallan asuba ta amsa da “Jiki da sauƙi Abdulhameed, tun jiya ma naso na karɓi pass ɗinmu, toh ciwon kai ne ya hana ni fitowa” “Har zaki samu zuwa Aunty Sharmama?” Cike da ƙwarin guiwa tace “In sha Allahu, mura ce fa kowa yana yi, zan sha magani in saka takunkumi ai ba zamu barka kai ɗaya ba.” “Guda biyu ne” yayi maganan yana mata kallon tambaya. Cikin fahimtar abinda yake nufi tace “zamu je da duk mai niyya, ko mu biyu ma mun isa idan ta fito mu tafa mata, kada ka damu” Ita ta saka shi ya shiga ya gaida mahaifinsa kafin ya koma ɓangaren sa. Yanda ya sauƙa a kan guiwowin shi, har ya miƙe ya juya ya tafi Mahaifin shi bai ɗago ya dube shi ba, balle ya sani ko ya amsa gaisuwan ko bai amsa ba. Itama Aunty Surayyah da ta gama ƙoƙarinta kowa a gidan ya dinga kawo mata uzurin da zai hana su zuwa sai ta dawo wurin Ilham dake goge kwanukan da ta gama wankewa tana jerawa a dish rack da kitchen cabinet. “Ilham kina ganin zaki iya zuwa ma Ikram talent show din da za'a yi a makarantarsu” Da hanzari ta amsa da “Eh Hajiya, zan je” murmushin jin daɗin tayin da aka mata ya bayyana a kan fuskarta, ta dunƙule farin kitchen towel ɗin a hannunta ta tana fara'a sosai. “Toh ba sai kin sake ɗora abinci ba, idan kin gama abinda kike yi sai ki zo ɗaki na mu shirya kada mu makara” Ta gyaɗa kai tana amsawa da “toh hajiya” Bata fara tunanin zuwa da kayan jikinta ba saida ta je ta samu Hajiya Surayyah cikin dogayen rigunan saudiyya masu manyan mayafai ɗinnan orange colour da fari-fari a jiki. Sai agogo, abun hannu da zobe da ta jera a hannunta amma tayi ma Ilham kyau ba na wasa ba. Ana ganinta da Hajiya Surayyah a haka a waje za'a gane ƴar aikinta ce, wataƙil ayi tunanin ma ba a birni ta faro rayuwarta ba saboda yanda rayuwa ya maida ita. “Na duba miki kayan da zai yi miki saboda babu lokacin da za'a je nema miki koda abaya ne saidai wannan, amma shi bayi da hijabin da zai shiga da kalan, saidai gyale, amma babba ne. Idan an gama sai ki tafi da su gida ki cigaba da sakawa” Bata jin tana da wani zaɓi ko ta cewa a kan abubuwan alkhairin da Aunty Surayyah bata gajiya da mata, kuma bata ba ta damar tsayawa ta ɓata lokaci wurin mata godiya ba ta umarceta ta sauya kayan jikinta zuwa wanda ta bata sannan ta zaɓo mata sarƙa da ɗan kunne, takalminta ne aka yi rashin sa’a yayi ma ilham yawa sosai, duk da skirt ɗin kayan ma saida ta hauro da shi har cikinta kafin tsayin yayi mata kuma saida a aka kame kunkumin da clip Saboda a tsayi da garin jiki ma Aunty Surayyah tayi mata fintinkau. Sai Aunty Surayyah ta kira Mukarram ƙanin Abdulhameed dake zama a shagon siyar da takalma yana samun na kan shi, tace ya nema mata baƙin takalmi size 38 ya ba ma masu delivery su kawo yanzu. Saboda tsananin daɗewan da tayi rabonta da kafa ɗauri da ƙyar ta samu ɗankwalin yayi mata yanda take so a kanta, kaman ba ita bace ko biki suka je a family haka ƴammata da ma matan Aure zasu yi ta layi da ɗankwalayen su a hannu idan suka ga irin wanda tayi a kanta. Da Ilham ta ɗan goga powder da man leɓe ta yafa gyalen sai taga ta fito daban, kaman Fidelan Maama da Taa, wanda duk wani abun kwalliya ko na yayi idan suka gani sai sun siya mata saboda tayi farin ciki, saboda ado yana sakata farin ciki sun sani, kuma sun bata goyon baya da aljihun su. Duhun fatar yana nan, canzawar kamannin yana nan, amma ta daɗe bata ga ita da kanta tayi ma kanta kyau ba sai yau. Aunty Surayyah ta kalleta daga sama har ƙasa lokacin Mukarram ya kawo takalmin da kan shi, da yaji inda zasu je sai yace shima zai bi su idan babu damuwa. “Kinga yanda kika fito?. Masha Allah” Ilham ta kasa danne Murmushinta saboda ta san ba daɗin baki bane zalla. “Murmushin ki yana da kyau” Tace lokacin da Abdulhameed ya rufo gidan ya ƙaraso ya same su a jikin mota. Daga nesa ya hangota tana murmushin, bai sake kallonta ba har ya zo ya wuce su yana faɗin “mu je” tunda ya san zasu ji shi, amma ya ɗan yi mamakin ganin da ita zasu tafi. Mukarram ne ya shiga mazaunin driver, Abdulhameed a gefen shi. A gidan baya kuma Aunty Surayyah ce zaune a bayan seat ɗin mukarram Ilham tana bayan na Abdulhameed. “Mukarram kashe AC ɗinnan kafin mu isa ina yoyon hanci” cewar aunty Surayyah tana maƙala takunkuminta tun lokacin jin yanda motan ya ɗauki ɗari. Mukarram da Ilham suka murmusa jin abinda tace, Abdulhameed kuma bai san me aka ce ba sai ganin glass ɗin window suna sauƙa kawai yayi. Ya juya yana kallon mukarram ko wani matsalan ne sai yayi masa nuni da Aunty Surayyah da babban yatsar shi a baya don haka ya juya yana kallonta. “Lafiya dai?” ya tambaya ganin takunkumi a fuskarta. Saida ta sauƙe tunda ba zai ji abinda zata faɗa ba kafin tace “Kada in yi na yara ne a samu mai kora ni gida, shiyasa nace a kashe AC ɗin” Dariya ya kufce wa Ilham, ta mayar da kanta jikin windown gefenta tana yi shi kuma sai ya amsa ma Aunty Surayyah da “Allah ya sawaƙe” kawai ya juya ya fuskanci gaban shi tare da ɗora guiwar hannun shi dake maƙale da agogon fata a daidai inda sleeve ɗin baƙar rigar jikin shi ta tsaya a jikin windown da aka buɗe, ya ɗan dafe kan shi. Suna taɓa hira sama-sama a tsakanin su ukun banda wanda bai san me ake cewa ba ma, har suka isa ƙofar hall ɗin da za'a yi show din, suka nemi masu siyar da pass aka siya ma Mukarram kafin suka shiga ciki. Suna jin ance masu cultural dance zasu shigo suka daɗa mayar da hankali. Abdulhameed, Aunty Surayyah da Mukarram suka saita Cameran da zasu yi recording Ikram. Sai kuma ita dake zaune a can baya saboda bata son ɗaya daga cikin su ya lura da ita Musamman shi Abdulhameed ɗin da kan shi. Kiki suna shigowa kan stage ta fara baza idanu saida ta hango daddynta ta ɗaga mishi hannu tana dirin murna, har saida ƙwaryan kanta ya kusan faɗowa malamar su tayi saurin riƙewa. A lokacin da suke yin rawar kuma Ilham ta ji inama itama tana da waya mai yin video da ta ɗauka ta ajiye. Da suka gama aka yi musu tafi sosai, wa'inda suke gaba da su suka zo suka gabatar da nasu category ɗin kafin aka zo bada kyauta ma wa'inda suka yi shura a cikin kowanne. Saidai su ƴan Nursery duka an basu kyauta don haka kiki ma ta samu. An yi hakan ne maganin rikicin ƙananun yara kuma yayi aiki, don da murnanta ta fito aka fara ɗaukan su a hoto. “Ayi mun da Mimi” Ta ƙaraso jikin Ilham ta riƙeta. Sai Ilham ta sunkuya ta ɗauketa a hannunta ayi musu hoton a haka. “Kun shirya?” Mukarram ya tambaya yayinda ya saita cameran wayan Abdulhameed a kansu domin yafi fito da hoto. Kiki ta jingina kanta a jikin na Ilham a lokacin da ya ɗauka ya sake wani a take, sai mamaki ya bayyana a idanun Ilham a na farko a na biyu kuma murmushin jin daɗinta ne ya fito. …… 6:06pm “Sannu Filiyan” Ilham ta ƙaraso inda Ihsan ta kifa kanta a jikin gadon Muftee, shi kuma yana shafa mata kan a hankali da hannun shi mai maƙale da Canular. Ta miƙe zaune jin muryar yayarta daman ba barci tayi ba, hannunta yana kan mararta dake ciwo sosai sai faman cije baki take yi. “Ko zamu je wurin likita mu roƙe shi ya rubuta miki magani ne mu siyo, ko yayi miki allura?” ta tambaya cike da kulawa. Ihsan ta girgiza kai “A'a dan Allah, idan na sha burufen ma zai bari, period cramps ne” likitan dake on duty a lokacin har sun yi exchanging numbers Saboda yanda ya matsa mata, kuma idan ya kirata wani lokaci tana ɗagawa, sai yanzu kawai su je wurin shi ace tana period ya bata magani?. “Toh mu je in siya miki maganin sai ki tafi ki huta ni zan kwana a nan” Ihsan tana cikin zafin ciwo amma saida ta tambayeta game da suturar da ta gani a jikinta duk da Ilham ta mayar da hijabinta a kai ta saka gyalen da takalmi a cikin laida, ta labarta mata duka abinda ya faru kafin su rabu sannan ta dawo ɗakin yaran. Nurse ta gani riƙe da hannun Muftee mai canular tana tsirga mishi ruwan allura a ciki. Ta ƙarasa da sassarfa tana cewa “Nurse an yi mishi alluran shi fah!” Ihsan ta jaddada mata hakan kafin ta tafi. Ko arziƙin kallo Ilham bata samu ba saida ta gama abinda take yi sannan ta juyo tayi mata kallon hadarin kaji a daƙile tace “malama zaki gwada mun aiki na ne?” Ilham tayi shiru bata amsa ba har ta bar wurin. “Mimi yaushe zamu je gida?” Muftee ya tambaye ta lokacin da ta zauna a gefen shi yana shigewa jikinta. “Likita yace mun kusa in sha Allah, kayi ta addu'a ka ji, bari na zuba maka abinci” Ta fito d takeaway ɗin haɗaɗɗen shinkafa da coleslaw da kaza ta buɗe musu suka ci, daman souvenir biyu aka bata har da na Abdulhameed da yace bayi buƙata shine ta ba ma Ihsan ɗaya ta tafi da shi, ga su samosa da springrolls, donut da cupcake duk a ciki da suka yi matuƙar daɗi, ta duba sticker ɗin dake manne a jikin containern ba don tana da kuɗin siya ba sai don ta ga sunan wanda Allah yayi wa baiwar iya small chops har haka. Ummee’s Baking Empire (UBE) ta gani da lambar waya kamar haka 08173775170 kuma abin mamaki location ɗinta a kano ne, kenan tun daga kano aka yi ordern su har KD? Ko da yake inganci da daɗin shi ya biya buƙata sosai. Basu daɗe da cin abincin ba Muftee ya fara mata gyangadi, ta zaunar da shi a jikinta kada ya kwanta cikinsa ya ɓaci, sai kuwa ya tashi mata da safe babu wani kuzari a jikin shi. Abun har ya fara bata tsoro ganin ko magana baya yi sai wani nishi kaman wanda aka dannewa ƙirji. “Ibrahim. Ciwo ne kake ji?” Ya lumshe idanun shi ya buɗe ya sake lumshewa, tsoro ya ƙara kama ta. “Muftee, yaya ne?” Still ba amsa. A hargitse ta ƙarasa tayi ma Nurses ɗin da suke cikin ward ɗin magana. Kuma da wanda tayi mishi allura jiya ta sake mishi sai gashi har abinci ya ci ya sha kunun gyaɗa kafin Ihsan ta dawo ta karɓeta ita kuma ta tafi. Saidai ta riga da ta makara. Ta makara a laraban da ya canza ƙaddarar rayuwarta gaba daya. Ta makara a laraban da bai nuna kyawun da juma'arta zata yi ba. Da taje gidan ta samu Kiki saboda an basu hutun kwana ɗaya su huta bayan taron da aka yi jiya, amma Abdulhameed har ya tafi wurin aiki sai Aunty Surayyah ta tarar don itama muran ba wai ya saketa bane. Wajajen Goma da rabi wayan Ilham ya shiga ruri, har yayi na farko ya tsinke bata ɗauka ba kasancewar a kitchen take barin shi ita kuma ta raka Kiki toilet. Da ta koma jikin wayan ganin missed calls guda 12 daga Ihsan, 5 daga Maama, 20 daga Aliyyu sai 15 daga Addah Iman yayi matuƙar tsorata ta. Abu ɗaya ta kawo ma ranta. Muftee ne ya rasu. Amma kiran yaya aliyyu da Addah Iman fah?, Abinda ya faru ya fi haka girma tabbas. Kiran Ihsan na 13 ne ya shigo wayan tayi saurin ɗauka, sai kuka kawai ta ji Ihsan tana yi ba tare da tace komai ba. A take taji zufa yana yanko mata, kirjinta ya shiga dukan uku-uku, fargaba mai tsanani ya rufeta. Ta fito parlo da sauri zata bar gidan idanunta suka sauƙa a kan Kiki. Sai ta rasa yaya zata yi da yarinyar. “Kiki zo mu je wurin Aunty Surayyah ki zauna kafin in dawo” Ta kalleta tana turo baki “ina zaki je?” Bata kulata ba ta ruƙo hannunta suka fita ta jawo ƙofar kawai domin babu key a jiki, ta ƙarasa da Kiki har jikin ƙofar da zai sada ta da ɗaya ɓangaren gidan sannan ta sake ta. “Je ki wajen Aunty Surayyah maza, yanzun nan zan dawo” Ta ga yanda yarinyar ta kwaɓe fuska tana shirin kuka amma sai ta juya kawai da sassarfa ta bar gidan. Bata sani ba ashe kiki biyota tayi. Mai gadi sai yayi tunanin tare suke kuma ba da nisa zasu je ba don haka bai dakatar da ɗaya daga cikin su ba har suka fice ya rufe ƙofa. Cikin Sa'a Ilham tana fita ta samu napep, ko faɗa mishi inda zata je bata yi ba ta shiga suka fara tafiya, idan ma ba hanyarta suka nufa da wacce take cikin napep ɗin ba sai ta sauƙa a bakin hanya ta shiga wani. Gudun da zuciyarta ke yi, da kuma hayaniyar da ƙwaƙwalwarta yake wajen canko mata abinda ya faru ya saka har suka wuce bata lura da Kiki dake ƙarasowa jikin napep ɗin ba. Tana ganin sun tafi sun barta kuwa ta fara kuka. Kafin wani a unguwan ya jiyo kukanta wata baƙar mota mai bakin tinted tayi parking, farar matar dake sanye da baƙin shades a idanunta ta fito daga mazaunin driver ta zagayo ta tsaya a gaban Kiki da murmushi a fuskarta. “I finally got to see you my Little angel” ta zare gilashin idanunta kana ta miƙa ma yarinyar hannu. “Zo, zo na kaiki wurin Daddyn ki” Babu musu Kiki ta kama hannunta, matar ta share mata hawayen idanunta sannan ta ɗauketa ta saka a cikin motar dake ƙyallin sabuntaka ta saka mata seatbelt sannan ta zaga ta shiga suka bar unguwar. ```````````` Seemahwrites ✨ ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh JODA by Sadi-sakhna DAƊIN ZAMA by Seemahwrites *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a turo shaidan biya ta 09039206763 Chapter 27 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Wattpad and Arewapen @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 27… Ihsan ta sake kira bayan sun ɗauki hanya, ba zata iya jira sai ta isa ta ji ko ta ga me yake faruwa ba, gwamma ta fara faɗa mata sai ta san wani irin shiri zata yi ma zuciyarta kada ta kasa jurewa ta tarwatse. “Filiyan mai ya faru?” Cikin muryar kuka ta kira sunanta “Addah Fidela…. Mu.. Muftee.. ne” Sheshsheƙar da take ya tabbatar ma Ilham Mutuwa yayi, amma sai bata sare ba ta tambayeta “mai ya same shi?” hawaye suka fara bin kuncinta tun kafin ta ji amsar tambayarta. “Muftee ya…” ɗiff wayan ta katse, ta ciro daga kunnenta ko kuɗinta ne ya ƙare ta duba ta gani akwai saura, ta sake maida ma Ihsan kira zuciyarta na tsere fiye da na tayoyin napep ɗin da take ciki, bata ƙi ta rufe ido ta buɗe ta ganta a gaban gadon yaronta ba. Ba'a amsa kiran ba har ya yanke, tana ƙoƙarin sake maida wani sai ga kiran Maama ya shigo. Da ta ɗaga bata san meyasa ta saka mata kuka ba, kukan da bata da tabbaci a kan dalilin yinsa, amma ta san tana bukatar tayi kukan kafin komai. “Fidela ki riƙe addu'a, Innalillahi wa Inna ilaihiraji'un da hasbunallahu wa niimal wakeel su zaki riƙe kiyi ta maimaitawa ba kuka ba, dukkan tsanani maganin shi Allah, kuma shine kawai zai tsaya miki” Tabbas Muftee ne ya rasu, bata hango wani dalilin da zai saka Maama take faɗa mata irin wa’innan kalaman ba bayan haka. Sai kuma tayi sa’ar yin kaman yanda Maaman tace, bata samu bakinta ya ambaci sunan Ubangiji ba sai yanzu, tana farawa sai taji tunaninta na haɗuwa wuri guda, ba don ta samu mafita ba sai domin tana jin akwai wanda yake da ƙarfin iko da buwaya a tare da ita kuma yana sane da lamarinta. “Zan turo yayanku ya dawo da ku idan kun shirya, amma kada kiji komai, Allah na nan, kaman yanda ma'anar inkiyar ki yake nufi ɗiyata, kuma yana tare da mai gaskiya.” Lallashin da Maama take mata ƙara karya mata zuciya yake yi. Ta riƙe wayan tana kuka har suka isa asibitin kafin ta sauƙa ta bada mai napep abinda yake hannunta tayi ciki da sassarfa. A waje ta hango Ihsan tana ta matsar ƙolla, da alamu dai jiranta kawai ake yi a bata gawan yaronta, ta ji guiwowinta kaman an kwaɓe mata su, tun daga cikinta kuka yake taso mata amma ta danne ta isa ga ƴar uwarta ta. “Filiyan ya rasu ko?” Ta yi tunanin ta gama shirya ma abinda zata ji zuwa yanzu sai gashi tana niman zubewa a jikin Ihsan da tambayar ya fito daga bakinta. Ihsan tayi saurin ruƙota tana girgiza kai kukanta yana ƙaruwa. “Bai mutu ba Addah, Muftee bai mutu ba amma yana cikin mawuyacin hali, jijjiga yake yi yana suma, har yanzu likitoci suna kan shi” A hakan ma ta ji sanyi, tun da ba rasa shi tayi baki ɗaya ba da sauƙi. Ta saka hannu ta share hawayenta da yaƙinin Allah zai ɗaga mata kafaɗun shi kaman lokutan baya da yake shiga yanayin da sai ta gama yanke tsammani ya tashi ya samu sauƙi. “Shine zaki tsinka mun zuciya Filiyan? Da kin faɗa mun tun a wayan ai, zan iya jurewa” Ba shi kenan ba, ba iya abinda yake faruwa ba kenan, amma ba zata iya ƙara mata wani baƙin albishir ba, wannan ma daurewa take yi ta sani. “Likitan ne ya ƙwace wayan, lokacin ina ciki tare da su” “Babu komai in sha Allah, idan Allah ya yarda zai tashi, babu komai” Duk wanda yayi tawakkali Allah zai kawo mishi mafita, ta tilasta ma kanta haƙuri cike da wannan yaƙinin. Wayan hannunta ya sake ɗaukan ruri, Addah Iman ne take kiranta, saida taji wani daɗi da ta fahimci dalilin kiran a yanzu, tun ma kafin ita ta sani ta zo gashi har ƴan uwanta dake wani gari sun fita damuwa da damuwarta, don bata taɓa tunanin ko menene zai faru Aliyyu zai taɓa ajiye mata missed calls ɗin da suka wuce 3 ba balle guda 20. Ta ɗaga kiran da nufin ta kwantar ma Addah Iman da hankali, Muftee ba mutuwa yayi ba. Babu ko sallama Iman ta fara da faɗin “Ilham baki da hankali ashe? da auren ki ga ɗanki rai a hannun Allah amma hakan bai ishe ki ishara ba kike yawon barbaɗe mutuncin ki a gari kike ɓata mana suna saboda asara? Ke wace irin shashasha ce? Yanzu da kika kashe auren sai ki ji daɗin yin yanda kike so, jaka wawuya kawai” Ta saba Idan ta kirata tana gama faɗin kalaman bakinta zata kashe wayanta, saidai ita ta kira idan tana da kalaman kare kanta. Yanzu kuwa bata jin koda Iman ta tsaya saurarenta tana da amsar da zata bata, saboda bata ma fahimci ina zancenta ya nufa ba. Wani yawo take yi na zubda mutunci ita da take niman hanyar cire wando ta ka? Wani auren ta kashe? Nata da Hashim?. Ita ko tunanin sanar da shi halinda ake ciki bata yi ba, babu amfanin da sanar da shi ɗin zai yi mata, kuma ba zata manta ranar da ya buɗi baki yace mata Mutuwar Muftee hutu ne a gareta ba, don kawai a lokacin ta yi ƙoƙarin raba damuwarta da wanda take ganin shima abun ya shafe shi kai tsaye kamarta. Tayi ma Ihsan dake tsaye a gabanta kallon niman ƙarin bayani “Filiyan…” Ihsan ta sake fashewa da kuka ta juya ma Ilham baya ta haɗa hannunta a saman fuskarta ta kifa kanta a bango tana matsar ƙolla. Ilham ta haɗiyi wani iska mai zafi a cikin maƙoshinta dake a bushe ƙamas, ta bi bayan kiran Yaya Aliyyu hannunta yana ɓari. “Fidela.” Ya kirata muryar shi a dake. Shiru tayi ta kasa cewa komai, tabbaci take nima amma bata da tambayar da zata iya mishi. Jin tayi shiru sai ajiyan zuciyanta da yake ji daga wurin, yace “Ina hanya, amma kafin na iso ki tabbatar kin tanadi amsar da zaki bani domin na baro haƙuri na a gida. In Allah ya yarda Ibrahim zai tashi, muna ta mishi addu'a Allah zai bashi lafiya” Ya ƙare da tausarta kafin ya katse kiran. Ta ruƙo Ihsan ta zaunar da ita a dakalin barandar asibitin itama ta zauna a gefenta, tayi shiru tana kallon ƙasa ta rasa wani abu ɗaya zata riƙe tayi masa kuka. Haka lokaci yayi ta tafiya suna zaune a wurin, likitoci sai zirya suke yi tare da nurses, amma babu wanda ya neme su, koda wani abu ne babu wanda yace su je su siyo su kawo. An kusa fitowa daga sallan azahar kafin likitan da suka fara soyayya da Ihsan ya ƙaraso inda suke zaune yayi musu sallama. Ihsan ta miƙe tsaye, Ilham kuwa ido kawai ta iya ɗagawa ta dube shi. Fuska ba yabo ba fallasa yace “zaku iya shiga ku duba shi” Shi da kan shi yaji akwai buƙatar ya musu ƙarin bayani, ma'ana ya faɗa musu laifin waye abinda ya faru, saidai ɓacin rai kawai zasu samu tun da ko mutuwa Muftee yayi babu abinda zasu iya saidai su ɗau dangana, amma tunda an samu ya tashi, manyan sa sunce shikkenan su zasu hukunta Nurse ɗin da tayi mishi alluran da ba nashi ba har double dose kuwa, ba sai iyayensa sun ji ba. Ya ciro wayan Ihsan a cikin aljihun shi ya miƙa mata ya wuce ya barsu. Ganin fuskar Muftee maƙale da oxygen mask da suka shiga ya sake sanyata a juyayi. Ta zauna ta zuba masa rinannun idanunta, so take ta samu ko a cikin zuciyarta ne ta tsayar da addu'a taji an kira sunanta. “Ilham!” Kaman muryar Hajiya Surayyah. Da ta ɗago sai taga ita ɗin ce tsaye a kanta. Aunty Surayyah bata ba ta sakwan biyu da zata ƙare mamakinta ba tace “Ina Kiki?” A tunaninta ma kowani uzuri ne ya taso ma Ilham ɗin ta tafi ba tare da ta sanar da kowa ba suna tare da yarinyar, tunda mai gadi da yaga sun daɗe basu dawo ba yayi azancin kiranta ya tabbatar mata a tare suka fita, shiyasa bata tsaya ɓata lokacin kiranta a waya ba ta biyo sawunta ta ɗauki ƴar Abdulhameed ta maida mishi ita gida kafin ya samu labari, kuma ta canka daidai da ta fara zuwa asibitin da ɗan Ilham yake kwance, amma bata ga Ikram ba. “Ina Kiki?” ta sake tambaya tashin hankali na bayyana a fuskarta ganin Ilham tayi shiru. “H.. Hajiya na tura ta wurin ki ai kafin na fito” “Innalillahi wa Inna ilaihiraji'un!” Sai ga Aunty Surayyah ta ɗaura hannu a ka. “Ilham tare aka ce kun fita, dan Allah tana ina in mayar da ita gida?kiyi tunani dan Allah, ko kin kaita wani wurin kafin ki zo” Ilham ta mayar da dubanta kan yaron da bayi iya shakar numfashi da kan shi, bai ma san a ina yake ba amma kafin ta zo gare shi itama Kikin ce damuwarta, babu yanda za'ayi ta fito musu da yarinya haka kawai tazo asibiti da ita. “Wallahi har ƙofan ɓangaren ku na rakata nace ta je wurin ki kafin na fito, babu wani wuri da nake da shi da zan kaita Hajiya” “Shikkenan, bari na koma na sake duba cikin gidan sosai, Allah yasa tana can ɗin, yaron ki ma Allah ya bashi lafiya” Ta amsa da “ameen” dake dukkan su babu nutsuwa a jikin su Aunty Surayyah ta juya da sauri ta fita ba tare da tayi mata sallama ba itama Ilham tana zaune bata miƙe da nufin rakata ba. Parlour, kitchen, toilet, store, har filin ta bayan gidan saida Aunty Surayyah ta duba amma babu kiki babu labarinta, ɗakin Abdulhameed kuma a garƙame yake da makulli. Da abun yafi karfinta ne ta kira Mukarram yazo suka fara knocking gida-gida suna tambayar ko sun ga ƙaramar yarinya fara mai shekaru huɗu tana sanye da simple gown yellow da kitso mai beads a kanta amma har ƙarfe huɗu shiru, kuma halin da ta baro Ilham a ciki yasa bata sake tuntuɓarta ba, amma yanzu ya zamo dole ta shigo ciki a bincika tare da ita tunda ita ce mutum na karshe da aka bari tare da Kiki. Ilham jin shirun yayi yawa yasa tayi tunanin ko an ga Kiki ne, ganin kiran Aunty surayyah ƙarfe 4 da minti 12 ya ɗaga hankalinta matuƙa, gashi har lokacin Muftee bai motsa ba. Haka ta tsallake ta bar shi da aka sanar da ita ba'a ga Kiki ba har yanzu, ta ɗale mashin zuwa gidan a fujajan. Kuma da gaske babu Kiki, abun kamar Almara, sauran mutan gidan ma sun shigo parlourn yana cike kowa tana tofa albarkacin bakinta, Aunty Surayyah kuwa ta fice a hayyacinta zuwa lokacin, tunaninta ko menene ya faru ita ce mai babban laifi tunda ita ta kawo Ilham. Ana cikin tuhumar Ilham ta faɗi inda yarinya take ya shigo gidan. Ya ja tunga daga bakin ƙofa kawai yana kallon su, Ba’a taɓa masa irin wannan cikan a gida ba zai kuma so sanin dalilin na yau. A hankali yake takowa ciki idanun shi na niman wanda zai samu amsan tambayar shi a wurinta. “Aunty Sharmama” ya kira da ya hango ta zaune a farin one seater ta zamo gaba ta ɗora guiwar hannunta na dama a kan cinyarta sannan ta saka tagumi da shi. Ta miƙe tana kallon shi, wannan nutsuwar da ta gani a fuskar shi ya kusan bacewa tana da tabbaci. “Kiki ce Abdulhameed. Bamu ganta ba” ta sanar da shi kai tsaye sanin ɓoye-ɓoye ƙara tunzura shi zai yi. “Tun yaushe?” Ya tambaya idanun shi a kan Ilham dake durƙushe a gefen kujeran Aunty Surayyah hawaye na bin fuskarta. Ta ɗago ta kalle shi da rinannun idanuwanta “yaro na ne jikin shi ya tsananta da safe, shine aka kira aka..” “Da safe? Amma sai yanzu ake sanar da ni?” Ya ɗago hannun shi na hagu yana duba ogogon dake jiki. “past 4:30pm, sai yanzu ya kamata na sani?!” sautin muryar shi ya fara tashi, sai gashi masu tofa albarkacin bakin su ma sun yi muƙus. Ilham ta miƙe a kan kafafuwanta. Murya na rawa ta fara mishi bayani da fatan zai fahimci ba laifinta bane “Kira na aka yi a asibiti, yarona ne…” “SHUT UP!!” Ya daka mata tsawan da saida hanjin cikinta suka kaɗa. “Idan wani abu ya samu ƴata I'll sue you! Wallahi tallahi I'll make sure you rot in prison if anything happens to her, ki fita ki nemo mun ita yanzun nan ko kuma Shari'a ce zata rabani da ke, Get Out of My House!” ta rintse idanunta ta tsame a wurin bata ko motsa ba banda kakkarwa da jikinta yake na tsananin tashin hankali. “Get Out I said!!!” Ya sake daka mata wani tsawan yana mata nuni da hanyar fita kafin zuciyar shi ta saka shi ya angiza ta. Kuma sai a lokacin ne Ilham ta san nauyin dake tafe da Haƙurin da Aunty Surayyah ta bata a ranar zata ɗauketa aiki. Ɓatan yarinya sukutum. Ita ina zata saka kanta?! Da ta ja ƙafarta ta bar gidan ta daɗe a bakin titi tana tunanin inda zata yi. A ina zata fara neman Kiki a yanzu? Ina yarinyar ta shiga ko kuma su waye suka saceta? Sai ta ji damuwar lafiyar Muftee da zuwan Yaya Aliyyu ya dawo ba komai ba a gaban wannan. Idan ya tabbata ba'a ga kiki ba ta shiga uku ta lalace. Saida wayanta yayi ƙara ta san ashe har lokacin tana riƙe da shi, ta ɗago ta kawo saitin idanunta da ƙwallan dake kwance a ciki yasa take gani dishi-dishi, ta saka hannu ta ɗauke su kafin ta iya ganin message din da aka turo daga lambar da tayi saving da ‘Baban Muftee’. Wasu maganganu ne da Ƙwaƙwalwarta ta gaza fahimta a yanzu, saidai kalmomi huɗun karshe wanda shine yasa taga wuri yayi mata duhu lokaci ɗaya kafin ta daina ganin komai. “Na sake ki, Fasiƙa” ````````````` Seemahwrites ✨ ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh JODA by Sadi-sakhna DAƊIN ZAMA by Seemahwrites *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a turo shaidan biya ta 09039206763 Chapter 28 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Wattpad and Arewapen @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 28…. Saitin kayan shafa shine kusan abinda ya ragewa Hashim kawai a haɗa lefen Khausar saboda ya daɗe da fara shiri, a ranar da suka dawo kaduna da zama suka sauƙa a gidan baffa Rabe ya ɗora idanun shi a kanta ya ji a ran shi ya samu mata, ganin yanda ta girma ta cicciko. Da inner wears da night gowns ya fara haɗa kayan, a wurin wata abokiyar aikin shi da suka yi saving numbern juna tana saka irin kayayyakin a status ɗinta, ya fara siya da ɗaɗɗaya yana ajiyewa ganin yanda Ilham ta lalace a yanzu albarkatunta duk sun lamushe, ko ta saka ba zata mishi kyau ba balle ta dauki hankalin shi, gwamma ya samu sabon jini yanda zai more kuɗinsa. Mahaifinsa Ibrahim Baniza da ƙanin shi Umar Baniza sune suka shige masa gaba a kan zancen auren Khausar kuma Rabe ya basu domin idan ya hana zasu iya cewa don shi da su ba ƴan ɗaki ɗaya bane ba. Aka saka aure watanni huɗu, kuma hakan yayi ma Hashim, yanda zai samu isasshen lokaci ya ƙarasa shiri a tsanake. A lokacin da yake shirin sanarwa sauran dangi kwatsam cutar sickler ɗin Muftee ya motsa, yanzu kusan watanni biyu kenan suna kwance da Ilham a asibiti, Shiyasa zancen auren ya koma sai wanda suka ji kawai, gashi sun haɗa kai wurin ɓoyewa yaran marigayi Usman Jen kada suce ba'a kyauta ma ƴar uwar su ba. Shi a karan kan shi ma zai fi so ya ba ma Ilham mamaki da auren, ya ƙara gwada mata iyakar ta. Sai gashi kafin ya kai ga ida nufinsa ita ta shayar da shi mamakin da saida ya bugar da shi, domin haka ya bi motar nan da kallo bakinsa a buɗe cikin tsananin kaɗuwa. Ilham dai da yakewa kallon banza ashe ta fi shi sanin gari, nata iskancin ba da irin shi take yi ba sai masu manyan motoci. Sun yi ƙoƙarin bin bayan su shi da abokinsa amma inaa, sun daɗe da yi musu nisa. Haka ya haƙura suka ƙarasa inda suka nufa, bai shirya asarar kuɗin man da suka ƙona ba. Yana ganin gate ɗin gidan su yarinyar da ya je wurinta ya fara hamdala a cikin zuciyar shi, kakan shi ta yanke saƙa. Hudah ta fito cikin ƙwalliya ta burgewa, Hashim yana ayyana kuɗin leshin jikinta don ya kasa sakawa Khausar irin su saboda tsadan shi. Ɓangaren Abdulhameed ma ta shigar da su, sanin ya fita kuma ba dawowar yanzu ba. Ta shimfiɗa musu carpet a inuwa da ƙaryar daddyn su yana da baƙi a parlour ne, tayi nuni da part ɗin Abdulhameed dake a rufe. Saida suka fara gaisawa ta shiga jere musu kalolin abincin da ita da mahaifiyarta suke ta kiciniyar haɗawa tun farar safiya. Hudah ta faɗa mata akwai maiƙo a jikin Hashim daga gani, shiyasa zasu yi masa tarban bajinta. Ta basu wuri suka ci suka gyatse sannan ta dawo suka taɓa hira sai burga yake mata ita kuwa tana ta murmushin jin daɗin ta samu miji. Saida taga an yi azahar har biyu tayi basu tashi tafiya ba tace masa zata koma ciki kanta yana ciwo, kafin Abdulhameed, Aunty Surayyah da ma sauran wa'inda suka tafi talent show ɗin Kiki su dawo su riske su. Haka Hashim ya miƙe ya kaɗe rigarsa, ba don kada ajinsa ya zube ba da yace ta saka mishi sauran abincin a takeaway ya tafi da shi, amma ko sile biyar bai ajiye mata ba suka juya suka tafi. Ayyanawa yake a ran shi Idan ya samu ya auri Khausar ya riƙe wannan ƴar masu kuɗin a hannunsa shikkenan ya huta da takaicin duniya. Ilham ce kawai zata zamo masa cikas, kuma a yanzu ya san ta yanda zai yi ainihin koya mata hankali. Daman tunanin inda zai ajiye Khausar yake ta yi, gidajen haya sun yi mahaukacin tsada yanzu, idan ya buga mata red card shikkenan babban matsalar shi ta kau. A yammacin ranan ya haɗa kayan shi cikin jaka, Ya kira office ɗinsu ya ɗauki excuse da ƙaryan Mahaifiyarsa ce babu lafiya zai je dubota a garinsu. Tattaki zai yi har Gidan Baniza ya samu magabatan su tunda yanzu yana da hujja ƙwaƙƙwara na rabuwa da Ilham ba tare da wani ya ga baƙinsa ba. ….. Kai tsaye asibiti Aliyyu ya nufa da isowar shi Kaduna, ɓacin ran da yazo da shi kuma ba kaɗan bane, har ƙananan ƙannen shi da mahaifinsu ya mutu ya bari bayi tausayin su kaman yanda yake tausayin Ilham, saboda yanayinta ga kuma irin abokin rayuwar da Allah ya haɗa ta dashi. Ashe ba mutunci gareta ba. Idan ya tabbata tana abubuwan da Hashim ya lissafo yau sai yayi mata dukan mutuwa saidai su koma da gawarta kano. Ran shi ya ƙara ɓaci da ya samu babu ita a jikin yaron da aka sakawa bututun numfashi, ya tasa Ihsan a gaba ta kawo shi gidan da aka ce tana aiki, tun da koda bata taɓa zuwa ba ya san Ilham zata kwatanta mata unguwan, idan ma suka je basu gane gidan ba tambaya zasu yi ta yi har sai sun samu, ya shiga yaci ubanta a can. Hangota da suka yi tsaye a gaban gate ɗin wani gida yasa Aliyyu ya dakatar da mai napep ɗin da ya kawo su a gefen wata bishiyar neem, suka fito ya biya shi kuɗin shi ya tsaya ya karyi reshen bishiyar ya figeta, Ihsan tana ta kuka tana bashi haƙuri ya shareta ya nufi Ilham gadan-gadan. Ba zai yi mata magana ba saidai ta ji tsumagiya a gadon bayanta, amma kafin ya ƙarasa gareta yaga tayi luuu zata fadi, ya jefar da reshen bishiyan da ɗan iskan gudu yayi kanta. Sai dai ya makara, ta rigada ta kai ƙasa. …. Har bayan Isha Abdulhameed da Aunty Surayyah suna yawon neman Kiki, sun je har school ɗin su da A&I koda ace wasu sun tsinceta tayi musu kwatancen can sun kaita, haka suka gama zagawa a banza duk ya rasa mafita, gaba ɗaya idanun shi sun gama kaɗawa sai zafin rai yake tayi, nutsuwar da ya samu na yin Sallah ma ba mai yawa bane. Aunty Surayyah da Mukarram sun tafi kai cigiya masallatai da gidan Radio kuma har an fara watsa hotunan Kiki a social media, shi kuma yana police station zaune a kujeran gaban DPO dake ɗaukan bayanan da zasu yi amfani dashi wurin nemota da kan shi. Ya tambayi Abdulhameed ko akwai mutanen da yake tunanin zasu iya ɗaukar ta ba tare da sanin shi ba, sai ya fara tunanin shima wa yake dashi a yanzu balle Ikram? Tun da Nne ta rasu ƴan uwanta suka juya mishi baya, tun da ya zama nakasasshe mutane da yawa suka cire shi a cikin lissafin su, amma ita Ikram tun farkon rayuwarta bata da kowa, da tana da shi da ba'a damƙa mishi ita tana cikin tsumma ba tare da damuwa da rayuwa ko mutuwarta ba, to waye zai ɗauke mishi ita yanzu idan ba mai fatan raba shi da sauran farin cikin shi ba?. Ya tsayar da ƙafar shi na dama da yake girgizawa yayinda ya zurfafa tunani, yace “Babu, amma akwai wanda I'm sure tana da masaniyar inda take, saboda ita ce last person da na bari a tare da ita, maybe idan ku ne kuka tambaye ta zata faɗa muku inda yarinyata take.” Iya lokacin da zai iya ɗiba ma Ilham ya cika, idan kuwa yau ba zai koma gida tare da Kiki ba toh kwanciyar hankalin da ba zai samu ba itama sai ya haramceta. Cikin zaƙuwa DPO yace “Toh me muke jira? Faɗa mana wacece a je a kawota sai ta bamu amsar tambayoyin mu” Aka kawota suka lagabtar da ita tuni zata warware musu komai, Idan hakane solving case ɗin zai zo musu da sauƙi, kuma zai samu alkhairi sosai a wurin Excellency tunda shine ya ɗaura shi a kai ya jaddada masa muhimmancin Abdulhameed a gare shi kada ayi wasa da lamarinsa. Abdulhameed ya sauƙe gajeriyar numfashi tunawa da kallon da yayi ma Ilham ɗazu. Ya ga damuwa matuƙa a cikin idanunta, ga yanda ta dinga zubda ƙolla. Ya ciro wayan shi ya kunna, ya dubo text message ɗin su da Aunty Surayyah na wata ɗaya da ya wuce, kana ya miƙa ma DPO wayan ya saka hannu ya karɓa. “Nanny ɗinta ce, ga Address ɗinta” DPO ya jinjina kai yana mayar masa da wayan kafin ya bada umarnin a je a taho da Ilham yanzu-yanzu. Abdulhameed ya cigaba da zama a ofishin na kusan mintuna talatin, babu inda yayi saura da zai je neman Kiki shiyasa kawai ya zauna ɗin, kaman yace a fasa ɗauko Ilham a motar ƴan sanda ya tura a ɗaukota a mutunce idan ba zata yi gardama ba, amma idan ya bita a lalama ba zata faɗi inda Kiki take ba. Bayi so ya fara saka tunanin haɗa baki aka yi da ita aka yi garkuwa da Kiki a cikin kan shi, sai dai ya karanta labarin faruwar irin haka sau da dama, ya gagara yaƙi da shaiɗanin da yake kissima masa yiwuwar hakan. Ƙarfe 9 dai-dai wayar shi tayi vibration ɗin shigowar saƙo. Ganin numbern ta ya saka gaban shi faɗuwa matuƙa, shin cireta a cikin lissafin shi da yayi har yayi tsananin da bai yi tunanin zata iya ɗauke Kiki ba duk tsawon lokacin nan?. Ta faɗa masa tana cikin Kaduna. Ta faɗa masa zata zo ta ganta. Amma bai zarge ta ba sai Ilham. Cikin sanyin jiki ya buɗe saƙonta, ya ci karo da abinda bai bashi mamaki ba, amma ya kai maƙura wurin ɓata mishi rai. ‘ta ƙi yin barci tana ta kuka, Muna gida na dake Millenium City.’ Sai a lokacin ya ga saƙon da ta turo mishi tun ƙarfe uku na rana. ‘Na tafi da baby zata kwana mun, gobe da sassafe kafin lokacin school zan dawo da ita.’ Ya rufe idanun shi ya buɗe a kan message ɗin. Ilham tayi ƙoƙarin yi masa bayani bai saurareta ba. Kaman yanda shima ba'a saurare shi ba lokacin da yaje da Kiki gidan su tana da kwana uku kacal a duniya. Bai duba rashin lafiyar ɗanta yayi mata uzuri an bi komai a hankali ba, kaman yanda shima ba'a duba nakasar shi an sassauta masa ba. Bai duba yanda take kaffa-kaffa da kanta da ma hidimar su ba ya tura mata ƴan sanda su je su zubar mata da mutunci. Lallai ya kwafsa. He messed up big time!. Ran Abdulhameed ya gama ɓaci yayi baƙi. Ya miƙe tsaye yana huci, jijiyoyin jikinsa sun tashi, a daƙile yacewa DPO da ya ɗago yana kallon shi. “An sameta. Ilham bata da laifi, a rabu da ita” Ya juya ya fita, kiran da DPO yake masa da tambayar inda take a banza tun da bai ji ba. Minti 18 tsakani driver ɗin shi yayi horn a gaban gidan da suka iso bisa kwatancen Abdulhameed. Bai tsaya an buɗe musu ƙaton gate ɗin ba ya ɓalle marfin motan ya fita, ya shige ciki ta ƙofar dake gefe kai tsaye. Sai yaga gidan ya ƙara masa girma da isa inda take tsaye tana jiran shi, sanye da hijabi light brown iya guiwarta, daga ƙasa kuma wandon kayan barci ne mai faɗi ya sauƙa har ƙasa, kafafunta a cikin farin crocs. Ita shirin barci take da shi kenan bayan ta gama ɗaga masa hankali?. Fuska a tamke yake takawa inda take idanun shi a kanta. “Tana ina?!” Ya tambaya cikin hargagi. Da ace ya iya ɗaga hannu ma mutane zai iya kifa mata mari saboda yanda ran shi yake tafasa. Ta dubi security guards dake kai kawo a harabar gidan, Ameer ne ya ajiye su don kare lafiyanta amma ta san akwai masu leƙen asiri ma babanta a cikin su. “Mu shiga ciki” tace tare da juyawa sanin zai biyo bayanta tunda linzamin shi yana hannunta a yanzu. Saida suka shiga cikin makeken parlorn da ya jinjina ma girma da tsaruwan shi a baya kafin ya ja ya tsaya. “Mardiyya! Ina yarinyata?” Ta dakata da tafiya, ta juyo ta dube shi. “Tea tace zata sha, shine na haɗa mata a upstairs, tana gama sha barci ya ɗauketa, da ban ɗago ka da tsohon dare ba” Murmushi yayi da bayi da haɗi da nishaɗi, “Are You kidding me? Ki ɗauke mun yarinya kizo kina faɗa mun maganar banza? I was searching all over Kaduna for her!..” Ganin zai tara mutane ta katse shi da faɗin “I Texted you Abdulhameed! Na faɗa maka na ɗauke ta, banda ma ni ɗin ce da cigiyar gaskiya zaka yi saboda a waje na sameta tana kuka. And na dawo kaduna ne musamman saboda ku, saboda na sanar da kai a kan shirin su na karɓanta.” “What?” Ya tambaya muryar shi yana sauƙowa. Gyaɗa mishi kai tayi “Yes Abdulhameed, sun damƙa maka ita ne saboda gudun ɓacin sunan su a siyasa, yanzu kuma lokacin zaɓe ya sake ƙaratowa sun fahimci zata musu amfani tunda kaima ka fara yi ma wanda zai fito takaran gwamnan Kd, zasu karɓeta Abdulhameed very soon” Kaman wanda aka watsa masa ruwan ƙanƙara haka jikinsa yayi sanyi. “Bata cika shekara huɗu a duniya ba Mardiyya” Lokaci ɗaya Idanunta suka tara ƙwalla “Ba a kanta suka fara sadaukarwa ba ka sani. Da ni suka fara.” Ya shafa kanshi da yanzu bayi tara masa gashi yana furzar da numfashi. “I'll not allow it. Never. Ki je ki ɗauko mun ita mu tafi” Bata musa ba ta juya zuwa matakalan da zai kaita sama, ya bi bayanta da kallo yana tunasar da zuciyar shi wacece Mardiyya. Amma ko sunanta ba zai taɓa zuwa kan shi ba tare da ya fara Tuna Ikram ba. Ikram Aminu Yashi. JAPAN 2017 Ganin yana niman cim mata yasa ta tsaya da gudun da take falfalawa tayi surrender. Saidai duk yanda yayi ƙoƙarin cin burki lokaci guda abu yaci tura saida yayi ciki da ita dukkan su biyu suka zube a ƙasa warwas gefen jikin shi a kan nata. Ƴar ƙara ta saki na bugewar da tayi, ga nauyin shi ya danneta, amma Abdulhameed bai ji ba saida ta taƙarƙare ta ture shi daga jikinta tana kwaɓe fuska. Ya ɗago guiwar hannun shi da ya kuje a Yashin dake gefen Filin yana nuna mata ganin ita ta takalo shi kuma wai ranta ya ɓaci. Ta turo baki tana watsa mishi harara ta saka hannu ta gyara zaman farin hulan kanta, ta rufe gashin dake kwance luff a goshinta sannan ta yunƙura zata tashi ta bar shi a wurin, yayi saurin jawo hannunta ta dawo ta zauna daɓas. “What's your name?” Ya tambaya. Tafin hannunta ta juya mishi alaman mai yake faɗa? Ita ba iya reading lips take ba kuma bata ji kwata-kwata. Ya nuna ƙirjinta shima yana juya mata nashi tafin hannun da ƙura ya gama buɗe shi. Idanu ta waro ta saka hannayenta ta kare ƙirjinta tana masa wani irin kallo. Shi hankalin shi ma bayi kan abubuwanta da basu kai sun kawo ba banda yanzu da ta saka ya ankara. Tsaki ya ja ya saka yatsar shi manuniya ya rubuta mata tambayar a ƙasa. Saida ta karanta ta saki ƙirjinta sannan ta saka hannu ta share tambayar itama ta saka yatsarta ta Rubuta mishi. Ikram Aminu Yashi. Ya ɗago ya dubeta lokacin itama shi take kallo. Ya gwada ta da yatsa yana faɗin “Ki kiyaye ni.” Sai ta sake masa murmushi. ````````````` Seemahwrites ✨ ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh JODA by Sadi-sakhna DAƊIN ZAMA by Seemahwrites *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a turo shaidan biya ta 09039206763 Chapter 29 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Wattpad and Arewapen @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 29… Tafin hannun shi ya buɗe mata da nufin ta saka mishi zoben Nne a ciki. A tunaninta taimaka mata zai yi ta miƙe don haka ta goge ƙuran hannunta a jikin farin sweatpants ɗin jikinta sannan ta saka nata tafin hannun cikin nashi ta yunƙura zata miƙe tsaye. Sake janyota yayi da ƙarfi ta dawo ta zauna daɓas, ta yamutsa fuska tana kallon shi saboda buga mazaunanta da tayi. Yayi mata alamar yanda ake saka zobe da cirewa a jikin yatsar shi sannan ya sake buɗe mata tafin hannun shi ta saka mishi a ciki. A razane ta ware ido tare da dafe ƙirji, ita ta manta dalilin da yasa yake bin ta a guje kenan, sai ya mata kaman tsere ne suke yi kuma ta haƙura ta sadaƙar masa ya ci. “Chukwu m! (My God)” Abdulhameed ya furta a hankali ganin ta fara dube-dube. Tun tana yi daga zaune har ta miƙe tsaye tana juye-juye ko zata hango ƙyallin zoben azurfan da ta jefar. Shima ya miƙe tsaye ya ruƙo hannunta ta juyo ta fuskance shi kafin ya sake gwada ta da yatsa. “Wallahi ki kuka da kan ki idan baki samo mun ring ɗina ba Ikram” Bata ji me yace ba, amma ta gane gargaɗi yayi mata wannan karon. Tashin hankalin da ya gani a cikin idanuwanta yasa da ta cigaba da bin hanyar da suka wuce tana dubawa shima ya fara taya ta. Har tsakiyar filin da koren ciyawa yayiwa ƙawanya saida suka durƙusa suka duba babu zobe babu alaman shi, gashi almuru ta gabato wuri ya fara duhu sai ƙoyayen fitila da suka maye gurbin rana wurin haska makeken filin. P.E teacher ɗin su ta haɗa kan sauran student ɗinta masu matsalar ji irin su sannan ta zo tayi musu alaman suma su zo su tafi saboda kowa ya watse, sai Ikram ta miƙe tsaye da sign language tayi mata bayanin da sha'awar fahimtar abinda take cewa ya kama Abdulhameed. Malamar ta taɓa agogon hannunta sannan ta haɗa yatsar ta babba da manuniya sau biyu, ma'ana ta basu minti ashirin su shigo ciki sannan ta juya ta tafi da sauran students. Zuwa lokacin hankalin Abdulhameed ya fara tashi, amma ganin yanda fuskar Ikram yayi kaman zata fasa Ihu yasa bai sake cemata komai ba suka cigaba da kewaye filin. Can kaman wanda aka tsikara yaga ta miƙe tsaye. Ya tsaya da abinda yake ya ɗago yana kallonta, sai yaga ta luma hannunta a aljihu ta fito da shi a dunƙule. Ya miƙe tsaye yana fatan abinda yake tunani ne. Tana buɗe tafin hannun nata kuwa sai ga zobe a ciki. Ashe yana cikin aljihunta duk tsawon lokacin nan. Sai ta fashe da dariya kaman wanda taga wawan zama. Saida ya saka hannu na ɗauki zoben daga cikin nata kafin ya dunƙule ɗaya hannun shi ya kifa mata ranƙwashi. Mugun kallon da ya watsa mata yasa ta haɗiye kukanta tana ƙifi-ƙifi da idanu. “Wuce muje” yayi magana yana tura ta gaba don ba wai ya huce bane, lokacin Sallah ne yayi idan basu je masallaci ba har aka idar kuma hukunci zai hau kansu. Ta ɗaga idanunta sama tana kallon yanda sararin samaniya ya koma kalan orange saboda rana dake hanyarta na faɗuwa. Abdulhameed ma ya ɗaga kan shi yana kallon yanda yayi kaman ranan ta bayan ginin makarantar su zai ɓuya, fiye da wata guda da gwamnatin tarayya na Nigeria ta ɗauki nauyin kawo shi makarantar ta hanyar scholarship ɗin STEM training amma sai yau ya taɓa lura da kyawun shi. Ya sauƙe numfashi yana cigaba da angiza ƙeyar Ikram har masallaci, sai gashi tana wanke kwanuka yana ɗaurayewa a kitchen ɗin cafeteria bayan an gama cin abincin dare a matsayin punishment na makara Sallah da suka yi. A wurin ma garin rikici saida suka fasa kofunan glass har guda biyu, saboda gani yake yi ƙiraren hannayenta basu da ƙwarin da zasu yi masa sauri yanda yake so, ita kuma tace ba zata yi ɗauraya ba domin idan ta gama sai ta saka kitchen towel ta goge su duka ta jera. Sai goma na dare ya samu komawa ɗakin su a gajiye, daman baya kula kowa yana hawa gado sai barci. Ya ɗauka daga nan shikkenan abinda ya haɗa shi da ita ya raba, sai gashi tare da ita a wajen class ɗinsu sun yi kneel down washegari, a dalilin lattin zuwa aji da suka yi, kuma gajiya da yaci jikin kowannen su jiya ya sanya barcin su yayi nauyi. Kaman bata lura da shareta da yayi ba ta rarrafo kusa da shi ta jingina da jikin shi, barcin ba wai ya isheta bane ba har yanzu, idan ta samu dama zata ƙara ko kaɗan. Shi tunda yazo bai ga wanda ke shiga mishi hanci da ƙudundune ba kamar wannan yarinyar. Ya saka yatsar shi manuniya a goshinta, ya tura kanta baya dashi, sannan ya sake bada tazara a tsakanin su ta hanyar matasawa gefe yana kallonta a fuska a tamke. Turo baki tayi ta jingina da bangon class ɗin ta cigaba da gyangyaɗinta. Ya juya kan shi baki ɗaya daga kallonta yana sake tuna accident ɗin da suka yi da Nne kamar yanda yake yi a kullum. Shekaru uku kenan amma har yanzu rayuwar shi bata dawo daidai ba. Shi da ya kamata ace yayi nisa a jami'a a shekarun shi 21 da haihuwa amma gashi nan a cikin shirmammun yara. Ya juya ya dubi Ikram yana jan tsakin da babu wanda ya ji sautinsa harda shi kanshi balle Ikram da idanunta ke a rufe, dara-daran lashes ɗinta sun rungume juna. Saida malamin dake cikin ajin ya gama zai ɗauki attendance ya fito yayi musu alamar su shigo da hannu. Sai gashi ita ce mai zagawa da takardar da kowa yake rubuta sunan shi a kai, yayi mamakin yanda aka yi duk cikin masu dama-dama a ajin wannan ƴar yarinyar ce mataimakiyar shugaban aji. Da yaga ta nufo desk ɗin shi sai ya harɗe hannun shi a ƙirji yana hararar ta. Ganin ta yi kwana bata ƙaraso ba Ya jinjina kai tare da mayar da hankalin shi kan abinda malamin ya rubuta a kan allo kafin ya fita. “100 days to exams” Tun Kafin su zo an riga an sanar musu duk wanda bai ci jarabawa ba gwamnati zata dakatar da biya musu kuɗin makaranta saidai su dawo gida, saboda duk wani international student sai yaci jarabawar da ake kira da EJU kafin ya samu gurbin karatu a jami’o’in ƙasar. Yana da tarin tambayoyi amma bayi tunanin akwai wanda zai iya tambaya balle ya samu amsa. Ya ɗora hannun shi biyu a saman desk ya kwantar da kan shi yana kallon Ikram zaune tana rubutu a seat ɗin dake row ɗaya da nashi amma kujeru biyu sun shiga tsakanin su. Ba zaice taƙamamme ina ne wurin zamanta ba a ajin, yau zai ganta a gaban aji gobe ya ganta a tsakiya jibi tana baya. Sai gashi lura da ita da Abinda take yi ya zamo masa ɗabi'a, koda bai so ba sai ya kama idanun shi a kanta ko ita ta kama shi yana kallonta, sai ta saki lallausan murmushi a saman fuskarta tare da ɗaga masa hannu, borin kunya ya saka shi haɗe rai ya juya. Idan ta tara mutane a kanta tana bayani da hannunta da sauri-sauri kuma, sai ta tuna mishi da surutun Ilham. Zai iya cewa a lokacin da yake tunawa da ita kenan kawai, amma rayuwarta da alƙiblar da yake tafiya ba damuwar shi bane. Kawai dai idan ya tunata sai ya tuna da birthmark ɗinnan na ƙasan bakinta. Ba'a fi kwanaki da haka ba, a ranar lahadi, ya gama bin layin karɓan breakfast a dining hall kenan, yana shirin samawa kan shi wurin zama yaji mutum ya faɗo jikin shi, ba don ya riƙe tray ɗin da aka ɗora plate ɗin abincin nan da kyau ba a jikin shi zai kifar, a haka ma tea ɗin da ya haɗa a kofi ya zube duka a cikin abincin da zai ci. Ta koma ta baya ta rungumo kunkumin shi a ƙoƙarinta na ya zamo mata kariya. Fararen hannunta da suka zagaye cikin shi Abdulhameed ya kalla, ya ɗago yana kallon gayen dake ƙokarin zagawa ya cafkota daga bayan nashi. Bai san mai yake faruwa ko kuma abinda tayi musu ba, amma ya san ita ce bata da gaskiya ba don haka ba ba zata gudu ba, saidai ta tsaya ta kama ɗan ƙugunta duk tsawon mutum tayi mishi rashin kunya. Ya ajiye tray ɗin a kan table ya ɗauki chopsticks ɗin ƙarfe guda biyu da aka saka masa ya ci abincin da su, suna ɗigar da ruwan shayi ya saita su a fuskar saurayin kaman zai ɓula mishi idanu. Da sauri yayi baya ya shiga yima Abdulhameed bayanin abinda Ikram ɗin tayi mishi da sign language. Bai barshi ya gama ba dukda ba fahimta zai yi ba ya sake yunƙurowa kaman zai dake shi, hakan ya sa ya haƙura da kai mata hannu tunda Abdulhameed ɗin ya fishi a tsaye. Da ya je ya kai ƙarar su, shi da ita basu karya ba aka saka su wankin banɗaki, kafin su gama su dawo an gama rabon abinci har sauran ɗalibai sun watse ana goge wurin. Yana zaune a staircase tazo rungume da wasu manyan biscuit guda biyu da madaran kwali harda straw, ta miƙa mishi komai ɗaya. Da bai karɓa ba, ta ɗora mishi a kan cinyar shi ta koma gefe ta ɓare laidan nata biscuit mai dabino a ciki ta fara ci. Kafin ta gama shima yayi rabin nashi don har ƙullewa hanjin cikinsa suke yi saboda lokaci ya ja sosai. Yunwar da yaji a yau, ya tuna masa da irin rayuwar da yayi a gidan mahaifinsa. Sai yaji yana son cigaba da zama a Japan, yana buƙatar yayi nesa da Nigeria na tsawon lokaci. Madaran ya zuƙa ya ajiye kwalin a gefe sannan ya taɓata, ta juyo ta bashi hankalinta tana tauna a hankali. Ya ɗaga hannun shi yana so yayi mata magana amma ya rasa yanda zai bayyana kalaman bakin shi da yatsunsa. Sai ta ɗaga mishi yatsar ta ɗaya sannan ta tashi da sassarfa ta haura saman matakalan babu ɓata lokaci ta dawo riƙe da ƙaramin jotter da pountain pen ta bashi. Idan ba ɓata gani yayi ba sai yaga kaman sunanta ne rubuce a jikin biron, rubutu tun daga kamfani. A maimakon ya fara zancen abinda ya dame shi sai ya rubuta mata tambayar ma'anar ‘Yashi’ dake jikin sunanta. Ya san family ɗin yashi, kaɗan daga ciki ƴan Nigeria sun san ƙauyen yashi dake ƙaramar hukumar alƙaleri a garin Bauchi, amma kowa ya san family ɗin yashi wanda suke da nasaba da garin, saboda dukiya da Allah ya wadata musu, suna da kamfanunuwa da gidajen mai a yawancin jihohin Nigeria, saidai Ikram bata yi masa kama da yaran masu kuɗi ba, shiriritan ta yayi yawa. Kafin ya gama tunani ya ganta tana dawowa hannunta ɗaya a dunƙule, kafin ta nuna mishi ƙasan da ta ɗebo a ciki. Ya kalleta ya sake kallon yashin da babu inda zata iya samun shi a cikin makarantar saidai filin sport dake ta baya, shi bai ma lura da tashin ta a gefen shi ba, lokacin tunanin shi yayi zurfi. Ya gyaɗa kai cikin fahimtar abinda take nufi, bata da alaƙa da wancan yashin. ya ɗauki jottern da ta ajiye ya rubuta mata. “Je ki zubar ki dawo” Idan ba haka ba yanzu sai a saka su share matakalar baki ɗaya, domin ko ina an ɗauki tsafta da muhimmanci a ƙasar musamman a makarantu. Ta je ta zubar ta dawo lokacin ya sake wani rubutu ya bata ta karanta. “yaya zan yi in ci jarabawar da za'a yi?” Ta ɗauki lokaci tana rubuta amsa, har saida yaji ƙirjin shi yayi nauyi da tunanin darussan da ake buƙata suna da yawa fiye da na Jamb da waec, kafin ta miƙo mishi tare da ƙura mishi idanu a lokacin da yake karantawa. “dole kana buƙatar cin Maths, Japanese language da Sign language, Sai sauran subjects ɗin major ɗin da kake son zaɓa. Amma ni community Health nake son karantawa saboda ina son buɗe NGO a Nigeria ina taimaka ma masu disabilities da basu da halin zuwa makaranta da marasa lafiyan dake kwance a asibiti da ƙananan yara.” Abinda bai tambayeta ba yafi yawan abinda yake son ji a cikin bayaninta. Ya rubuta mata “who ask you?!” Da ta karanta sai yaga tayi murmushi sannan tayi rubutu ta miƙo masa. “Zan koya maka Sign language da japanese language, shekaru na 6 a nan duka na iya” Kaman ta san abinda zai roƙa kenan a gaba amma yana gudun raini, kada ta samu fuskar sake mishi irin na ranan. Sai ya rubuta mata “okay” kawai ko godiya babu. “kai kuma zaka koya mun maths” Harara ya watsa mata ya rubuta amsa “No” ya mayar mata. Sai ta ruƙo hannun shi tana kwaɓe fuska alaman roƙo. Saboda kada ta dame shi ya gyaɗa kai ya samu ta sake shi. A sannu Abdulhameed ya fara koyan Sign language, ya fara amfani da shi, ya fara fahimtar mutanen da yake tare da su, sai yaji kaman yanzu duniyar ba shi kaɗai bane kaman yanda yake ji a baya tun bayan da ya rasa kunnunwansa. Daga wannan rana kusancin su ya ƙaru da Ikram saboda lokacin da suke ɓatawa a tare da juna wurin karatu, da ma hira da take yi mishi koda baya so, sai ta gwada mishi shima darasi ne da zai saka ya ƙara gogewa a sign language, kuma hakan ya sanya ba tare da yayi aune ba ta shige jikin shi, ya saba da ita. Kwanakin da aka fara ƙirga su tun daga ɗari a kwana a tashi suka ƙaraso, aka rubuta jarabawa saura sakamako, amma yana ji a jikin shi alaƙar shi da Ikram bata da ranar ƙarewa. Saboda ita ce mutum na biyu da ta taɓa shiga ran shi haka bayan mahaifiyar shi, ta zamo wani ɓari na rayuwar shi da baya jin zai iya haƙurin rashinta. Result ya fito kuma shi da ita sun samu abinda ake buƙata, don haka course ɗin da ya cika ‘Biomedical Engineering Technology’ ma ya samu. Bayan ya ji burin Ikram sai ya fahimci nashi bai wuce ya ƙirƙiri abinda zai dawo mishi da jin shi ba, saboda bai cire rai wata rana zai koma dai-dai ba. Ranar Entrance ceremony ɗinsu sai ga Mardiyya, ƴar uwar Ikram uwa ɗaya uba ɗaya. Sosai Ikram tayi murnan ganinta saboda bata yi tsammanin akwai wanda zai zo mata daga gida ba, amma duk yanda Mardiyya ta so Abdulhameed ya shiga hoton da za'a yi musu tare Ikram ta ƙi. Bai ɗauki abun da zafi ba koda tayi mishi bayanin ƴan gidan su ne bata son su san shi tukunna, tunda ko ba daɗe ko ba jima matuƙar suna son juna da gaske dole watarana ya dangana ga wurin iyayenta. Shikkenan kuma bayan Mardiyya babu wanda ya sake leƙo Ikram, shikam dama bai saka ran ganin kowa ba. Akwai likitocin dake zuwa duk shekara su duba su, wanda suke da chance ɗin sake ji idan an taɓa kunnen su ko da taimakon hearing aid ne sai Organisation ta ɗauki nauyin surgery ɗin su. Da shi aka fara, saboda nashi hatsari ne ya jawo mishi Lalacewar Inner Ear hair cells ɗin shi, shiyasa yake iya magana domin abun bai shafi ƙwaƙwalwar sa ba, ba kaman Ikram da aka haifeta da nakasar ba saboda gado tayi a wurin kakanta ta ɓangaren uwa. Ita kaɗai ta raka shi har ƙofar ɗakin tiyata tana bashi ƙwarin guiwa, a shekaran da aka yi nata bayan nashi yayi failing, da hatsarin idan aka sake taɓa kunnen za'a sake jawo masa wani matsalan, shima ita ke bashi ƙwarin guiwa yayin da ake gungura ta a gadon marasa lafiya. Shi kaɗai ya zauna jira har aka gama aka fito da ita, har ta farfaɗo, amma saida aka tabbatar cochlear implant da aka yi mata is successful sai ga Aminu Yashi tsaye a gaban Abdulhameed, yazo tare da mahaifiyarta da Mardiyya. Idan kuma aka ce tsakanin rabuwar shi da Ikram zai ƙirga toh daga wannan ranan zai fara har zuwa ranar da suka zauna tare da Mardiyya tana faɗa mishi ko da iyayensu sun yarda zasu bashi Ikram ba zai iya bata rayuwar da ya dace da ita ba, shi ba kowa bane bayi da komai, ita kuma iyayenta suna da burika masu yawa a kanta. Kuma duka abinda ta faɗa gaskiya ne. Bai ajiye ba bai bawa wani ajiya ba, ko a yanzu da suke shirin kammala karatun su idan aka ce ya fito ya auri Ikram ba zai iya ba, tun da ba zata iya rayuwa da shi a gidan su ba, Musamman a yanzu da yasan ita wacece, ya san wani Yashi ne maƙale da sunanta. Shi ya fara jan baya da ita lokacin da take undergoing therapy, sai ta buƙaci ya rakata kaman yanda suka saba yaƙi zuwa, har ya ƙare ya fito ya nuna mata bayi ra'ayinta a yanzu, duk saboda ta samu kyakkyawar rayuwa. Amma bayan tayi aure da wani ba shi ba, haɗuwar su a Nigeria ya zame masa darasin da har zuwa yau bai sake taɓa macen da ba muharraman sa ba da gangan. . . . Abdulhameed ya miƙa hannu ya karɓi Kiki a hannun Mardiyya ya raɓa ta a kafaɗar shi, ba tare da ya sake ce mata komai ba ya juya ya bar mata gida. `````````` Seemahwrites ✨ Chapter 30 *DAƊIN ZAMA🍁* Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites) Wattpad and Arewapen @Seemahwrites *Women of Words Writers* #THE TRIO OF TALES (Three minds, Three stories, One journey) Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍 30… Aliyyu yana zaune yana jira saida Ihsan ta taimaka mata ta zauna da kyau tare da saka mata pillow a bayanta sannan yace ma Ihsan ɗin ta fita ta basu wuri suyi magana. Sun yi Sa'ar samun ɗakin da babu kowa, kafin Ya cicciɓo Ilham ya kawota aka sallami wanda ke ɗaya gadon. Saida ya ji ƙaran jan ƙofa da rufeta da Ihsan tayi kafin ya tattara hankalin shi gaba ɗaya a kan Ilham da bai san zabgewar wuni ɗaya bane tayi ko na tsawon lokacin da ya ɗauka bai saka ta a idanun shi ba. Bayan gungun tashin hankali da suka yi mata rubdugu harda rashin cin abinci a cikin sanadin rashin samun kuzari a jikinta, kuma bayan ta farfaɗo zuciyarta bata huta ba, musamman da taga Yaya Aliyyu a gabanta. “Fidela” ya kira sunanta yana tsareta da idanuwa. Kai a ƙasa ta amsa da “Na'am” kan kace mene hawaye sun sake samun hanyar gangarawa fuskarta. Ba zallan Rashin lafiyan Muftee ko ɓatan Kiki ba, ƙazafin zina da aurenta da hashim ya jefe ta dashi shine ya fi bata tsoro, amma zata yi ƙarya idan tace sakin da yayi mata bai girgizata ba. “Ki buɗe baki kiyi mun bayanin abinda yake faruwa idan kina son in saurare ki da kunnen fahimta, da zaran mun koma kano ba lallai ki samu wannan damar ba” Da wani abinda yake faruwa ɗaya zata fara? “wallahi Allah shine shaida na, bayan fafutukar da nake yi da izinin shi da amincewar shi, ban taɓa tsallake iyakata a wurin nema wa kaina mafita ba” Ta fahimci da abinda yake so ta fara kuwa, hujjan da Hashim ya riƙe yake so ayi mata hukunci da shi ba tare da an ji ta bakinta ba. “Shi kuma wanda yace ya gan ki a mota ke da shi da idon shi shekaran jiya da misalin ƙarfe 11 na safe fa? Da suturar da ba taki ba a jikin ki Ilham?” Ƴan gidan su basu kiran sunanta sai sun saka ta ji bugun zuciyarta ya tsananta, saboda babu wasa ko wargi a tare da hakan koda daga bakin Ihsan dake matsayin ƙanwarta ce kuwa. Hawayen dake ɗiga daga idanunta yasa take jin hancinta ma kaman zai taya shi ɗiga, saida ta ja hanci kafin tace “taron makaranta zamu je suka bani kyautar sutura shine na saka a jiki na, kuma wallahi ba mu kaɗai bane a cikin motar, akwai ƴan uwan shi guda biyu mace da namiji da suka mallaki hankalin su a tare da mu…” “Tambayar ki nayi wanene shi?” Aliyyu ya katseta idanun shi a lumshe, yankan jiki da tayi ta faɗi ya ɗarsa masa tausayinta a zuciya, amma bayi so ta ƙure ɗan sauran haƙurin da ya samu a sanadin haka. “Mahaifin yarinyar da nake raino ne.” “Yarinyar da aka sace?” Ihsan ta faɗa mishi komai kenan, babu amfanin ɓoyewa. Ta gyaɗa kai. “Duk ke kaɗai Ilham?! Yayi kyau. Ina fatan kin tanadi kuɗin da zaki yi belin kanki tun da gashi can ya tura ƴan sanda gidan ki a kama ki” A zahiri shi take yiwa kallon mamaki baki a buɗe hawaye na wanke mata fuska amma Abdulhameed take gani a baɗini. Shi take kalla da mamakin da ya hana ta ko motsin kirki, shi da ta karɓi lamarin shi da zuciya ɗaya ta hidimta ma yarinyar shi fiye da yanda take yiwa nata yaron bayan yana cikin halin buƙatar kulawa na musamman. Ya san bai yarda da ita ba yake barinta da yarinyar su biyu a gida babu idanun kowa a kansu? Da tana da niyyar cutar da ita da tuntuni bata yi amfani da wannan damar ba? Abdulhameed bai duba wannan ba, cin mutuncin da yayi mata a gaban ƴan uwansa bai ishe shi ba sai ya tozarta ta a idon duniya. Ta haɗiyi wani abu mai ɗaci a maƙogwaronta sannan ta tsinkayo muryar Yaya Aliyyu yana cigaba da magana cikin faɗa. “Me yasa baki sanar ma Maama cewa wanda zai ɗauke ki aiki bayi da mata ba? Ƙofar zargi komin kashin sa kin san hatsarinsa Ilham? Neman kuɗi hauka ne? Ko akwai wanda yace miki lallai sai kin ɗorawa kan ki abinda yafi ƙarfin ki? Da kika ga ba zaki iya ba meyasa baki bar masa ɗansa kin dawo gida ba?” Tun da tayi shiru har ya bar ɗakin bata sake cewa komai ba, bayan fitan shi Ihsan ta dawo, ta saka mata ruwa a buta tayi alwala da Sallah, ta koma gadon ta zauna tana jin yanda ƙirjinta ya riƙe. Ta kasa cin komai a daren ta kasa barci tana tunanin abinda wayewar gari yake tafe da shi. Hala yanda ta kwana a gadon asibiti yau gobe saidai kwanan police station. Sai taji duniyar duk tayi mata zafi. . Duk yanda taso ta cigaba da kwanciya da safe saida ta tashi ta je duba Muftee saboda Ihsan tace ya farka wajajen ƙarfe huɗu na asuba kuma idan jikin shi ya ƙara kyau zasu cire mishi oxygen ɗin. Yaya Aliyyu ta hango tsaye tare da likitoci uku, hankalinta ya sake tashi kada wani abune ya sake faruwa. Kaman cece-kuce suke yi. Majinyata da yawa sun bar gadajen yaran su sun zo jin kanun labarai. “Zo nan Fidela” ya yafato ta da hannu lokacin da ya hangota. Likitocin sai tausan sa suke yi amma fafur ya ƙi sauraren su. Cike da sanyin guiwa ta taka ganin manyan likitoci ne a wurin, ƙaraminsu a matsayi shine wanda suke soyayya da Ihsan, Dr Bello. Aliyyu ya fara mata bayanin abinda yake faruwa dalla-dalla. Dawowar shi jikin Muftee bayan yayi sallan asuba ne ƙus-ƙus ɗin da nurses suke yi a kan Crises ɗin da Muftee ya samu, dalilin alluran mara lafiyan gefen gadon shi ne aka yi mishi. Shine ya tada rikicin ba zasu yarda ba, duk da sun tabbatar mishi zasu sallami nurse ɗin a asibitin ko a bata suspension mai tsayi. “Ai zai tashi ko?” Ta tambayi wanda take tsammanin zai faɗa mata gaskiya cikin sanyin murya. Dr Bello ya gyaɗa kai tare da cewa “in sha Allah, ya riga ya fita daga cikin danger” “Shikkenan, babu komai ku barta a bakin aikinta, ta taimaka ma mutanen da suka fi yawan wanda aka samu kuskure a kansu, Allah ya kiyaye na gaba” Idan bata yi mata uzuri ba, bai dace tayi tsammanin ya kamata Abdulhameed yayi mata uzuri ba itama. Babu ɗan adam ɗin da ya wuce kuskure. ….. A gadon shi ya kwantar da Kiki ya rufa mata bargo iya cikinta, sannan ya jawo kujera ya ajiye a gaban gadon ya zauna. Saƙo ya rubuta ya turawa Excellency, yau ya kasance rana ta farko da ya fara yi masa tuni a kan alƙawarin su shi da kan shi. Saboda Excellency ya san zai neme shi ɗin yasa tun bayan da aka sanar da shi Abdulhameed yace an samu yarinyar bai sake tuntuɓar shi ba. Saboda ya san bai wuce dangin mahaifyar ta bane suka ɗauke ta. Indai haka ne kuma zai neme shi. “Da safe ƙarfe 10” shine reply ɗin da ya samu daga Excellency na dogon saƙon da ya tura mishi. Ya ajiye wayan yana kallon rigar jikinta kalan pink da Mardiyya ta saka mata, har kitson kanta sun sake mata, yanzu rabin kitson an tufke mata ne a tsakiyar kanta sauran an sauƙo dashi gefen fuskarta, har beads ɗin da aka saka mata a jiki ba wanda ta fita dashi daga gidan bane. A wuni guda kawai ya ji kaman har an fara nesanta shi da yarinyar. A wannan karon ba zai bari lokacin da zai fara ƙirga tsakanin rabuwar shi da Kiki ya zo ya riske shi yana zaune ba, tun da wuri zai dauki mataki. 7:03am Yana kitchen yana soya ƙoyin da zasu haɗa da dankali ta shigo tana murtsuka idanu. Ta ƙarasa wurin shi ta taba shi ya juyo sannan tace “Daddy ina Mimi?” Ta zuba mishi idanu tana jiran amsa saboda yanzu ta saba kusan kullum Ilham take samu a kitchen ɗin. Sai ya rasa me zai ce mata, ita kanta Ilham ɗin idan ya ganta yanzu bayi da abinda zai ce mata. Tayi haƙuri? Abinda yayi mata ya fi ƙarfin kalmar haƙuri. Ƙaurin kwan da ya shiga hancinsa yasa shi saurin kashe gas ɗin kafin ya saka majuyin hannun shi ya juya ɓangaren ƙwan da ya fara baƙi ya dawo sama. Mai kyau ɗin da ya fara soyawa ya saka mata ya saka ma kan shi ƙonannen sannan ya ɗauki plate ɗin, ya riƙe hannunta zuwa dining. Abincin bai yi mata daɗi ba kaman yanda na Ilham yake, idan tayi musu dankali irin haka sai ta haɗa musu da sauce ɗin albasa ko na hanta a maimakon Ketchup da suka saba dashi a da. Ya shiga damuwa ganin bata ci dankalin da yawa ba. “Kiki Aunty da ta ɗauke ki jiya tayi miki wani abu ne?” Gyaɗa kai tayi, tace “Ta cire mun kaya da pant ɗina tayi mun wanka. Kuma Mimi tace duk wanda ya cire mun kaya ko pant in faɗa maka” “Kin yi daidai. Mimi ta faɗi daidai” yayi murmushi yana shafa kanta. Alkhairin Ilham a gare shi mai yawa ne, abinda tayi masa a wata ɗayan nan bayi da abinda zai iya saka mata da shi, sai gashi yayi mata halin ɗan Adam, kuma tun ba'a je ko ina ba ya fara ganin gurbinta. Saida ya sauƙe Kiki a school kafin driver ya wuce da shi gidan Excellency. A wani wuri da aka yi kejin adana tsuntsaye kala daban-daban ta bayan gidan ya same shi yana zuba ma wasu fararen baru tass abinci, irin foreign breed manya masu yawan gashi ɗinnan. Ya tsaya a lokacin da wanda yayi masa Iso ya sanar da Excellency zuwansa kafin aka bashi damar ƙarasawa. Saida ya gama abinda yake yi kafin ya juyo ga Abdulhameed. “Karfe 10 nace” yayi magana yana kallon Abdulhameed bayan ya duba lokaci a jikin agogon shi. “Kayi haƙuri, ba zan iya jira ba” Ya ɗauka parlourn shi zasu shiga suyi maganar saboda muhimmacinta, ko wanda bai kai shi ba ma basu yin shi a waje, ko baƙi yazo gidan ya tarar sai Excellency yasa an shiga da shi private parlour ɗin shi ya jira shi. Amma yau a tsakar fili suka zauna suna fuskantar juna. Waya Excellency ya ciro ya kira lawyer ɗinsa da ya ɗora a kan case ɗin Abdulhameed. “Yaya ake ciki?” Abdulhameed ya karanta kalmar da lips ɗinsa suka furta. Sai yaga Excellency ɗin yayi shiru yana sauraro kawai. Bai shiga waswasin dalilin da yasa Excellency ya ƙi haɗa shi da lawyern kai tsaye ba saidai komai za'a yi ya zamo shine a tsakani. Saboda ya san waye Excellency. Ɗan siyasan da ya fara gwagwarmaya tun a jami'a, ya riƙe muƙamai tun daga ƙananu har zuwa SUG president, a lokacin ne ya samu sunan Excellency a bakin ɗalibai ƴan uwansa. Daga nan kuma har matakin sanata ya riƙe, yanzu yana shirin fara niman kujeran gwamna, kuma ranan da ya kira Abdulhameed suka zauna cikin sirri yana bashi labarin yana da burin yayi har shugabancin Nigeria gaba ɗaya bai san amfanin mene sanin hakan tun da wuri zai yi masa ba. Amma ya fahimci dalilin da yasa Excellency yake son juya mutane suyi yanda yake so, saboda cikar burin shi dole sai da taimakon mutane. Saida ya katse kiran ya dube shi. “duk yanda zamu yi ba zamu samu takardun nan cikin sauƙi ba. Idan muka ce da kuɗi zamu yi amfani sun fimu kuɗi ka sani, kuma muka ce zamu saka gaggawa a ciki muka yi saken da zasu gane shirin mu komai zai lalace, suna da tarin hujjoji bamu da komai, zan sama maka duk irin flight ɗin da za'a samu nan da kwana biyu ku bar Nigeria” Abdulhameed ya ja numfashi a sannu ya furzar kana yace “Sabon contract ɗinmu fah?” Bayi taɓa saka hannu a jikin ko wani irin takarda ba tare da ya duba dokokinsa ba. Kuma sharuɗan da Excellency ya gindaya ma wanda aka samu tangarɗa daga ɓangaren shi kuɗaɗe ne da yawansu ya kai ya tattara dukka abinda ya mallaka kafin ya iya biya. Idan ya amince da hakan kuma yaya za'ayi ya iya cigaba da kula da Kiki banda ɗaruruwan mutanen da lafiya da ilimin su ya dangana da A&I support Organisation?. Idan kuma Excellency bai ce sai ya biya ba, toh zai kawo masa wani sabon sharaɗin da zai saka ya ji kaman yana ɗaya daga cikin tsuntsayen dake kulle a cikin kejin nan. “Idan na koma da ita Japan, zasu binciko mu duk inda muka shiga muka fita, akwai ƙasashen da alaƙa na da ita ya saɓa ma dokokin su musamman ace babu mahaifiyarta a tare da mu. Sannan bani so in yi breaching contract ɗinmu, so zan cika maka alƙawari kafin in tafi, ina fatan bayan nan I'll gain my freedom, ina buƙatar in yi protecting abubuwan da suke da muhimmanci a wurina da kaina. Ba tare da kutsen kowa ba.” Excellency yayi murmushi. Daman ya san daga lokacin da wani abu ya samu Kiki, toh ko Abdulhameed ya daɗa depending da shi ne ko kuma yayi mishi tawaye. Amma lokaci ne zai bayyana komai. “We shall see” ….. Ganin zuwa dare Muftee har yana karɓan abinci yasa suka fara shirin barin Kaduna, saboda yanda Ilham take jin bata iya numfashi da kyau a garin, yanda take ganin yayi baƙi a idanunta, dalilin da ya kawota kuma Allah ya kawo ƙarshen shi. Duk da Yaya Aliyyu ya tabbatar mata Hashim ya kwana a kano kafin shi ya taso amma Bata iya sake taka ƙafarta a gidan Hashim ba sai Ihsan ne ta je ta haɗo mata kayan sawanta. Ta so tayi mamaki da bai tafi da key ba ma ya mayar gidan da suke bada ajiya, a jikinta take jin akwai Abinda Hashim yake shiryawa da bata san menene ba. Ranar juma'a da hantsi suka dangana tasha. Aliyyu yana rungume da Muftee a haka yake ta musu cuku-cukun samun mota da biyan kuɗi daga aljihun shi. Wani yanayi da a cikin shekaru biyar da ta ɓata da Hashim bata taba samun kanta a makamancin shi ba. Har Ranar da zasu dawo Kaduna da zama daga aljihunta ta biya kuɗin motar da ya tattaro kayan ɗakinta, shiyasa ma bata zo da kujeru ba ta zaɓi ta siyar ta sayi wani a nan, amma a haka kuɗin ya lalace. Da akwatin su da Muftee kuma haka ta dinga tiƙi-taƙa da su, damuwan shi kan shi kawai. Kuɗin seat ɗinta ma da ƙyar ya biya domin daga farko dagewa yayi ya kashe kuɗi da yawa saidai ya biya mata rabi ko ta jira sai ya samu tazo. Kunyar idon Maama da ta rakota har tasha daga fitan ta daga takaba yasa suka wuce salum alum. “Yaya akwai kuɗi a wurina” tace ma Aliyyu tana bashi katinta na opay. Jiya ma ta ga dubu ɗarin da Hajiya Surayyah ta turo mata tare da dogon saƙon ban haƙuri bayan ta kira ta bata haƙurin har tana cewa zata zo Ilham tace ba sai tazo ba, tunda an samu Kikin falillahil hamd. Ko kallon katin bai yi ba yace “ki bari zaki buƙaci kayan ki daga baya” yayi gaba ya samu drivern motan da zasu shiga yayi mishi magana a basu seat ɗin da Muftee ba zai wahala ba. Isar su cikin garin Kano bayan sallar Juma'a yayi daidai da ɗaurin Auren Hashim Ibrahim Baniza tare da Amaryar shi Khausar Rabi’u Baniza. …. *Hmm Wasa farin girki.* *Hashim da Khausar Alƙawari ya cika.* *Ilham ta bar Kaduna ma Abdulhameed* *Zawarcin da take tsoro, gudun abinda mutane zasu ce, akwai wanda zata iya tare ma kanta a halin yanzu?* *Mu haɗu da ku a littafi na biyu domin cakwakiyar yanzu aka fara. It will be available on arewapen by 17/09 Telegram and WhatsApp by 20/09.* *Sneak peak* “Na dawo Ilham, I am back once again” Kallon shi tayi daga ƙasa har a kaikaice. Ya sake canzawa. Saida ta kalle shi a cikin ido kafin cikin gatse tace “ka dawo daga ina?.” Zuciya ɗaya ya amsa da “Na kai Kiki an yi mata a aiki a kunne. Ta samu Lafiya yanzu, she doesn't need hearing aids anymore” Har cikin zuciyarta zancen yayi mata daɗi amma sai ta taɓe baki tace “yayi kyau, matsa mun a hanya Abdulhameed, ana jira na” UMMEE'S BAKING EMPIRE https://chat.whatsapp.com/L0WK91pLyVn8iQ6HjSwG8a?mode=gi_t *My Sister matso kusa ki ji.. Wannan cake ɗin da kike gani a online yake burge ki kin san inda zaki samu irin shi? Koko sha'awar glazed ko filled donuts kike yi? Ga plain ones for your Husband, father or boyfriend if they don't have a sweet tooth.* *Coming to you my brother.. kana iya bada kyautar nan mai sanya mace tsallen Murna? Ko Surprise ma abokai? For Eids, Anniversaries, birthdays, graduation or just to celebrate your girl or yourself? you can order a cake from us. Akwai crunchy cincin domin motsa baki ko a siya ma mama da baba su saka mana albarka.* *And don't forget about friendship or sibling bonds, You can always order a cake to celebrate their success or even to mock them with class😎, requesting captions that are satire and funny.* Muna siyar da: • Cakes na for every occasions ( birthday, graduation, anniversary dai dai sauran su) • Bento cakes • Cupcakes • Mouth watering brownies • Samosas • spring rolls • Glazed puffs • Filled, glazed and plain donuts. E.t.c *Ummee's Baking Empire –* *Making every Moment feels special. We always make sure that you recieved what you ordered 👌🏼💯* 📞 08173775170 📍 gwammaja, Kano