DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)... ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (1) “Alhaji kabiru ga d’iyata nan samira kulawar ta na gareka yanzu, ka kula min da ita idan ta samu miji wanda yayi daidai da addini ka aura mata, kwanaki na basu da tsayi” Ya juya kan barrister usman “inason duk wills dina ka adana wa samira har se ta mallaki hankalinta kuma kaci gaba da juya kadarori na, na aminta da kai na kuma baka dukkan yarda ta” tarin daya si’ke shi ne ya kasa ‘karasa magana nan falon ya hautsine masu koke koke na yi masu addu’a na yi samira da dawo warta kenan daga skul ta fad’o falon a firgice daidai kansa ta tsugunne tare da sakin marayan kuka tana fad’in “Daddy um um daddy karka tafi ka barni, daddy idan ka tafi ka barni nima binka zanyi, kaga bani da kowa se ku gashi mummy ma ta tafi ta barni...” Hannun ta ya jawo dakyar ya d’ora kan na Alhaji kabiru maganar sa na fita dakyar yace “d....a..ga ya..u sh..ine daddy ki, Allah yay..i mi..ki albarka, ya shafo kanta yana salati, lokaci daya jikin sa ya saki idonsa a kanta rai yayi halinsa, gwaggo haulatu ta janyo samira jikinta tana sakin wani irin kuka me cin rai nan samira ta zube sumammiyya. Wani private hospital dake kusa dasu aka nufa da ita inda aka shiga bata taimakon gaggawa, yayin da a can gida kuma aka shiga shirya gawar Alhaji dan ‘kasa dan kaishi makwancin sa. Alhaji ibrahim d’an ‘kasa shahararren mutum ne wanda yayi suna ciki da wajen Nigeria, sana’arsa itace siyarda auduga se yan kananun abubuwa daya bud’e irin su kamfanin da ake yin designer jeans da ke carlifornia se gida je wanda yake bada haya a wurare da dama da kuma sauran kadarori wanda Allah yayi musu yawa, sai gonar nakin auduga masu yawan gaske. Asalin su mutanen mambila ne dake jihar adamawa su uku ne wajen mahaifansu wanda suka rasu tun suna matasa, gwaggo haulatu ce babba se daddy sannan alhaji kabiru, daidai gwargwado suna da rufin asiri dan mahaifinsu manomi ne ya bar musu dukiya me dama. Alhaji d’an ‘kasa yana da mata d’aya hajiya mariya da yarinyar sa d’aya samira wacce yanzu haka take shekara takwas a duniya, yarinya ce ta taso cikin gata cike da kulawar mahaifan ta duk wani jin dad’in duniya tana samu musamman da take ita kad’ai Allah ya mallaka musu. Dukiya irinta Alhaji d’an ‘kasa, da kuma ‘kafa da yake da ita a government yasa ake bashi tsaro har ita samiran dan ko makatanta zata se da securities su jira har ta tashi su dawo da ita. Samira na shekara bakwai hajiya mariya ta ‘bata a wata asabar ta shirya zuwa mahaifar ta bichi, kamar yacce ta Saba duk karshen wata, ita da amintaccen driver din alhaji me suna namadi har ila yau ba labarin su tun ana sa ran dawowar su har an fidda tun daga ranar Alhaji mai ‘kasa ya fara samun health deficiency wanda daga ‘karshe likitoci suka tabbatar da cewa yana da damuwa wacce yayi silar zuciyarsa ta samu matsala. *** “Mami na, mami na” Bud’e ido tayi ta kuma saurin rufewa ganin wani irin haske daya dabaibaye wurin, lalubar wurin ta shiga yi da hannu har tayi nasarar ri’ko wani lallausan hannu shima ya ri’ke ta gam, tsinto muryar daddy tayi yana cewa “Kar ki ta’ba bari ya kufce miki no matter what kar ki bari kiyi nesa dashi” Juyawa tayi dan ganin me hannun amma blank se wannan hasken murza idonta tayi wai ko ze washe but still hasken na nan, a hankali ta kuma lalubawa gabanta tana cewa “Daddy wanene wannan d’in da bana gani? Ku..ma kuma kai ma kana ina?” Ta ‘karasa with a shaking voice Dariyarsa taji, “mami na shi d’in haske ne *dabaibaye* da ke, don’t ever leave his sight” “Um..to kai fa??” Hawaye suka fara zubo mata Daga can nesa ta tsinkayo muryar shi “sai wata rana mami na, ki kasance me hakuri a duk yadda rayuwa tazo miki, Allah yayi miki albarka” Cikin lalube ta tashi zata bi hanyar da take yaqinin yabi taji an janyo ta da ‘karfi ta fad’a cikin wani faffad’an ‘kirji dake fidda wani sihirtaccen ‘kamshi wanda yabi ta hancinta ya shiga cancikin ‘kwa’kwalwarta ya zauna, ‘ko’kararin ‘kwacewa take bakinta na kwala kiran Daddy Daddy...tun ‘karfi. Girgizata suka shiga yi daga gwaggon har matashiyar yarinyar da baza ta wuce agemate din samira ba wani yin’kurawa ta kuma yi daidai lokacin ta bud’e ido Seda ta ‘kare musu kallo sannan ta fashe da wani sabon kukan, hannun gwaggo ta ri’ko “gwaggo na ki kaini wurin daddy na tun kafin yayi nisa kinji” Rungumeta tayi a jikinta tana share kwalla batare da ta bari ta gani ba, zuciyar ta cike da tausayin marainiyar Allah, kuka take bil hakki har se da likita ya zagayo ya mata allura. A hankali matashiyar yarinyar ta isa gaban gadon da yar uwarta ke kwance tana shafa mata gashinta dake barbaje bisa pillow idonta ya d’uru da ruwan hawaye ta d’ago kanta tana kallon gwaggo tace “Gwaggo yanzu haka Sam zata cigaba da kwanciya anan without us doing anything???, look how helpless she is, gwaggo dan Allah mu tafi da ita gidan mu se muke yin wasa tare tunda daddyn ta da mummyn ta basanan kinji” ta ‘karashe maganarta cikin kuka, “Aa mubina Samira wurin mu zata zauna ko daddy?” Juyawa sukayi dan basu ji shigowa ba, d’an lukutin yaron dake ri’ke da hannun alhaji kabiru yana washe hakwara ya watsa wa mubina harara Yace “kar na kuma jin kince gidan ku zata je that your tiny little home hahaha” Hura hanci tashiga yi ta taso a fusace tayo kansa gwaggo ta daka musu tsawa nan da nan suka kame kansu mubina da baki baya mutuwa a hankali tace “elephant kawai can’t you even say salam, ba wanda yaji abinda ta fad’a se yaron dan alhaji kabiru zama yayi suna gaisawa da gwaggo Hura hanci yayi yana kukkumbura ita kuma ta kuma sakar masa gwalo ai kuwa yayo kanta tana dariya ta shiga zagayen gadon da Sam ke kwance, Gwaggo ta kira sunan ta cike da warning duk suka kama kansu. Alhaji kabiru yayi gyaran murya yace “yaya inaga ya kamata kije gida ki huta yau haka” “To kabiru wane ze zauna da yarinyar?” “Um dama salamatu se tazo tunda likita yace ta farfad’o ‘kila zuwa gobe a bamu sallama” “Au to Masha’Allah, amma tunda gobe ake tunanin sallamar gara na zauna, ita salamatu me tsohon ciki Ina zata iya?” Ya jinjina kai “haka ne, Allah ya bata lafiya” ledojin daya shigo dasu ya ajiye gabanta “ga wannan fruits din zuwa dare zan dawo” “Allah ya kaimu, ka shirya wurin da zata zauna d’in?” “Eh! Na gyara mata d’akin kusa da nasu Amir har kayan ta duka an kai mata” “To madallah a ri’ke amana dan Allah” “Insha’Allahu yaya” Ta kalli yaron “kai ubana Ina zaka kai tsokar nan taka, ka samma mubina da Sam mana gasu nan kamar a bushe “ “Ba mubina tana tsokana na ba ni ba zan sammata ba se de Sam” “Kayi min daidai kuwa, kaga kwa rin’ka zauneta ai” “Eh mana murin’ka yi mata John cena” “Ni kuma nayi muku shoulder face” Dariya gwaggo tayi ta kalli alhaji kabiru Tana share kwalla tace “har na tuna yarintar ku da Ibrahim ke zaune ka” “Kai kai haba yaya dan Allah a bar tuno baya, ni kinga tafiyata ma” Tabishi tana ‘yar dariya, Amir na gaba yana baya suna fita ya waiwaya ya kalli d’akin yana me jinjina kai.... ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (2) ****** “Se umma! Allah yaja kwana uwarmu me share kukan mu” Kwafa tayi, “kaga habibii ka fita idona tun kan na sa’ba maka, tukunna ma tsaya meye duk ka damu da son komawa d’akin ne? Na zata kai da kan ka kace kafi son zama a na tsakar gida” Sosa ‘Keya yay “umma ki gane mana I wanna be close to you guys kin ga fa idan a waje ne kome ya shigo ta kaina ze fara amma idan Ina cikin gida I’m safe kuma dududu ma umma saura sati biyu na bar muku gidan ma duka,” “Se ya fara takan baba megadi kenan ko?, umm ai na ‘kagara ka tafi ma ko bakina ya huta da surutu, kai fa sokoncinka yawa gare shi zamani ya canja yanzu ‘yan fari suke da wayo amma kai kam kullum abin naka dad’a gaba yake, da Allah tashi ka bani wuri shashasha” “Me yaya na yayi?” Mai da kanta tayi hanyar shigowa, “a a Alhajina sannu da dawowa, shirmen da ya saba ne ” ta ‘karashe da fara’a Dariya yayi da cewa “Yawwa, sannu da gida ya jiki jiki”, ya zauna yana cire hula yana firfita da ita “Jiki kam se godiya” Yana kallan habibii yace “wai yaya na ka kira Umaru me gyaran AC kuwa, ko kayi halin naka na mantuwa” yace “Abba na kira shi tun ran da ka fad’a min ka sanshi da al’kawarin yan nepa, bari na kuma trying wayar” “Ya kamata” Amir dake jikin uwarsa a lafe ya shiga zayyana mata abinda ya faru a asibiti, tana dariya tare da tambayar me jiki da kuma gwaggo Habibii ya mi’ke tsaye yana faman mi’ka yace “bari na shiga d’aki na kwanta,” “Ya habibii na biyoka pls se muyi game?” “Aa sedai kai kayi, ni hutawa ta zanyi” Ya gyad’a kai “eh naji pls” Da hannu ya nuna masa hanya “muje to” A 360 yayi gaba habibii na biye da shi, Mi’kewa tayi ta samo masa ruwa ta kawo ya sha, hamdala yayi ya gyara zama “Salamatu jikin d’iyarki ya fara kyau sosai dan likita ma yace ‘kila gobe ya bamu sallama” “Allah sarki marainiyar Allah, wlh tausayi take bani ace a ‘kan’kantar shekarunta ta rasa mahaifanta duka” “To ya za’ayi abin Allah kenan ai, shi kad’ai yasan tanadin da yayi mata” “Um hakane Allah yayi musu rahma” “Amen, ina haladu azo a samo nama a zuba a freezer da duk abubuwan da aka san babu dan bana son ko alawa taji tana so ya zamana babu” “Gaskiya fa ai maraya hidimar sa daban take, gara mu fita hakkinta, oh Allah sarki yaya Ibrahim da mariya wai yau an wayi gari babu su, duniya labari “ Sallamar baba megadi ce ta katse su, yace ana sallama da Alhaji kabiru. **** Kwanan Sam bakwai aka sallameta lokacin mahaifinta na da kwana bakwai cif da rasuwa, gwaggo da kanta ta kai ta gidan Alhaji kabiru inda ta dam’ka amanarta a hannun umma salamatu, Dafarko ta d’anyi raku’be raku’be kasancewar bata saba da shiga cikin jama’a ba, kullum tana tare da mahaifinta indai ba makaranta ta tafi ba, se daga baya ta sake dake tasu tazo d’aya da Amir. Faran faran take da rana amma fa da ta shiga d’aki ta kwanta se tasha kukanta ta ‘koshi kan barci ya d’auketa wanda kuma kullum da kukan take tashi saboda mafarkin da ya riga ya zame mata jiki dan jazaman ne se tayi gashi har yau Allah be bata sa’ar ganin Daddy ba da kuma mutumin da kullum daddy ke kiransa da hasken ta. Duk wani jin dad’in rayuwa daidai gwargwado tana samu gidan baffa kabiru kullum iro driver dinta ke kai ta school se de tun bayan rasuwa ba a bata security ko d’aya a cewar Kawu kabiru iro kad’ai ma ya wadatar Kwanan Sam arba’in da bakwai umma salamatu ta sauka inda ta haifi ‘yar ta mace sak kawu se duhun fatar umma data d’auko, a lokacin nan abubuwa suka fara sauyawa Sam dan tunda akayi haihuwar nan ita ke taya uwani me girki hada hadar gidan kai har ta kai ita ke sharar gidan, ranar suna kuwa har zazza’bi tayi dan gajiya dama gashi ba sabo , yarinyar da aka haifa taci suna safiyya. Bayan shekara biyu Tashi tayi da salati a bakinta, ta fad’a toilet tayo alwala tayi salla da sauri sauri ta nufi falo dan gyarawa seda ta tattare komai sannan ta fad’a kitchen tana aiki tana kallon agogon bango gudun kar tayi latti bayan ta had’a komai ta jere bisa table sannan ta fad’a toilet dan yin wanka Kintsawa tayi cikin sabon unifoam d’inta na junior classes ta rataya sabuwar jakarta da aka bata a makaranta dan ever since daddy ya rasu komai kyauta hukumar makaranta ke mata. Kasancewar ta fara tasawa yasa wani ni’imtaccen kyau ya fara bayyanar mata idan ka ganta lange Lange kamar ka hureta amma kyau kam ko ‘yar uwarta mace ta kalle ta se takuma kallon ta. Muryar Amir taji yana kwala mata kira daga can sama kuma tana iya jiyo kukan safiyya, saurin fita tayi su kayi kici’bis da Amir yayi mata👌🏻Alamun tayi kyau ta turo baki tana masa hararar wasa yana faman tsokanarta iyeh kaga ‘yammatan j.s 1, dan alokacin shi j.s 3yake daidai ‘kofar fita tayi tuntu’be ‘kiris ya rage takai qasa ya taro ta, idanunta dake runtse ta bud’e a hankali suka sauka cikin na shi Cikin rawar murya ta furta “ya... ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (3) “Ya ha..habibii” Kanne mata ido yayi ” have I been missed?” yayi saki wata muguwar dariya “oya matsa daga gabana before na mangare ki” ya sake ta da sauri, Sum sum sum taja jiki gefe har tana neman fad’uwa, Amir da shigowarsa kenan yaga duk abinda ya faru ya ja hannunta a fusace suka nufi mota. Habibii ya bisu da muguwar harara, ya shige cikin gidan yana kwala wa umma Salamatu kira. **** “Sam muje wasa?” Girgiza kai tayi a hankali “um um sholey I can’t play now just go ahead “ “Why Sam ?” Yarinyar ta turo baki gaba alal dole ranta ya ‘baci , Mu’allim bello malamin islamic wanda yazo wucewa ya ji maganar tasu ya tsugunnawa Yace “meya samu samira naga tana ‘bata fuska ta manta yau kun shiga secondary” ya ‘karashe maganar idonsa kan fuskarta “Mu’allim tun safe haka take” Jinjina kai yayi idonsa kan ta, yace “Samira kina tuna daddy ne?” Kallonsa tayi idanunta cike da hawaye ya d’aga kai, “I miss him so much” Bud’e baki yayi zeyi magana wani security ya iso da sauri “mu’allim that your bossy brother yazo nemanka” “Ohhhhh, yanzu kuma” ya karashe da kallon agogon hannunsa kan ya juya ya nufi hanyar gate har yayi gaba ya waiwayo inda yaga idanunsu ‘kuri a kansa Yace” c’mon let’s go ” Kallon juna sukayi kan su bishi a guje, daka d’an nesa yace su jira shi ya nufi motar dake parking lot ya shiga, ya jima cikin motar sannan ya fito. Fuskar nan kadaran kadahan, har class ya raka su sannan ya koma office. **** Umma salamatu ta d’ago a fusace bayan ta tabbatar da yaran sun tafi makaranta cikin d’aga murya tace “Kagani ko ka gani ko, yau kwana tara kenan Ina bin kanka a tura Sa’idu (qaninta)can turkey yabi sakaran yaran nan to ga irinta nan, yanzu how sure are you manager din baze cuce mu ba bare yaga ba idon mu, nifa Ina tsoron mutanen nan, dukiyar maraya fa!” Ajiyar zuciya Alhaji kabiru ya sauke kan ya kalli habiibii yace “Kai na baka kwana biyu ka shirya ku koma tare da sa’idu, kaji dai abinda mahaifiyar ka ta fad’a “ Fuska a had’e ya amsa “naji Abba amma...” “Amma me? uban naka zaka kawo wa qabali da ba’adi? Eyeh? Fice ka bani guri” A fusace ya wuce, ta kalli Alhaji kabiru “nifa Abban yara inaga kaima se ka bisu kaje ka gano halin da ake ciki dan habibii yace wannan “Hidden” d’in sun aika musu da takarda kamar yacce suka tura wa ragowar kamfanonin” A rud’e yace “what!?” Ta kya’be baki “uhm duba ka gani” Amsa yayi yana shafa velvet bag d’in da aka rubuta ‘HIDDEN da manyan ba’ki bud’e jakar yayi ya fiddo takaddar da akayi rubutu da silver ‘make sure kun Adana every details’, “this is different from the others” “And that’s why nake so mu iya takun mu, and again ina buqatar kud’i dan zan aika ma c.i.d d’ina this time around inaso ya samomin gamsassun bayanai a kan ‘HIDDEN’ I want them to know they are dealing with d wrong people, Girgiza kai yayi ya wuce, ta bi bayansa da ido har ya fice ta d’auki wayarta ringing d’aya tayi aka d’aga “proceed as planned “ ta furta cikin kausashiyar murya **** Bayan wasu watanni Ta du’kufa sosai Amir yana koya mata maths dan gobe zasu zana jarabawar gama aji d’aya, “umma salamatu inaso ki tayani da addu’a gobe zamuyi maths” ta ‘karashe a shagwa’be, Shafo saman kanta tayi, “Insha’Allah habibty, Allah ya bada sa’a I trust you,and you never disappoint” Smiling tayi har beauty point dinta ya lotsa Amir ya zira biro ciki ta bige hannun tana dariya idonta kan umma salamatu wacce take kalla, Tsugunnowa tayi ta bata peck a chubby cheeks d’inta tace “concentrate habibty” Smiling tayi ta juya kan littafinta tana faman turo baki, sanin cewar dashi take ya ri’ko hannunta “am sorry baby sis ni ne ko bazan kuma ba kinji” Kallonsa tayi tare da nuna masa ‘karamin yatsanta tace “promise?” Ya sar’kafe cikin nashi “I promise”, suka cigaba da karatun su. Washegari Tafe suke zuwa office d’in mu’allim bello suna hirar yacce exams d’in tayi musu dad’i sunzo daidai sport center ball ta gangaro gabansu ‘Kiris ya rage sholey tayi tuntu’be Sam ta ri’kota, a fusace ta d’ago ta fara fad’a zabgegen yaron da ya zo d’aukan ball d’in ya tsaya yana huci fuskar nan a cusgune Sam da duk ta firgice ta hau Jan hannun sholey su tafi ‘ki’kam ta’ki tafiya ala dole ta saketa ta nufi office d’in mu’allim bello a guje daidai lokacin ya d’aga labule kanta ya bigi ‘kirjinsa ‘kamshin daya doki hancinta ne yasa tayi saurin d’ago kai idonta ya sauka kan... ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (4) Fuskarsa, “ya akayi cutie?” “Mu’allim sho..shole..y” ta ‘karashe murya na rawa tana nuna masa hanyar da hannu, gaba yayi da sauri ta mara masa baya daidai lokacin yaron ya d’aga hannu kenan ze doke ta, “Adnan!!” Mu’allim bello ya daka mishi tsawa, saurin sauke hannu yayi yana faman huci, kunnenshi ya ri’ko ya nufi office dashi su kuma sukayi zuru suna binsu da eyes, a hankali ta matsa kusa da sholey Tace “sholey are you okay?” Sholey da idanunta suka kawo ruwa ta girgiza kai da sauri ta fad’a jikin Sam “thank you for saving me” Hannu tasa saman gadon bayanta tana sama da ‘kasa dashi alamun rarrashi tace “its okay, afterall what are friends for?” Ta d’aga mata gira with a questionable look a fuskarta, murmushi sholey, “Good girl, let’s go home Mu’allim Bello will deal with him “ riqe da hannun juna suka nufi parking lots inda drivers dinsu ke jiransu. Aysha Aliyu shine asalin sunan sholey yarinyar Dr Aliyu da Barr. Badariyya, they are the family of four Affan shine babba wanda ya girmi sholey da kusan shekara bakwai, su biyu jal Allah ya mallakawa mahaifansu ‘yan boko ne sosai hakan yasa yaran su da wuya kaji suna wani yare wanda ba turanci ba banda shi kuwa se dai kanuri ko hausa Sholey sun had’u da Sam a lokacin zasu shiga primary one na makarantar capital school inda aka had’asu zama seat d’aya, tun daga wannan ranar suka ‘kulla aminta har kawo wa yanzu da suka shiga makarantar gaba da primary. **** Yau garin na kano an tashi da ruwan sama me qarfin gaske gari yayi sanyi ko ina kirif kirif yake haka zalika mutane tsilli tsilli suke waje, Sam na zaune a d’aki ita da mubina da tazo musu weekend suna kallon Aladin wanda hankalinsu rankatakaf suka maida can, turo ‘kofar da akayi ne ya ja hankalin su Murmushi ta saki ganin umma salamatu, “yammata na kallo ake?” “Uhm umma movie d’in nan yayi kyau am so sure you will like it, come and join us” “Oh Sam I will love to amma kinga fita zanyi” “Umma fita? Ina?” “Zan le’ka gidan sa’idu ne, bazan jima ba mubi na nan ku zauna yanzun zan dawo kinji” Fad’ad’a fara’arta tayi, “ok umma Allah ya dawo dake lafiya” Mubi ta d’aga mata hannu, ta fice. Bayan gushewar kusan minti arba’in suka ji bugun ‘kofa, “ina zuwa”Sam tace da mubi ta nufi downstairs, For kusan 20mins jin shiru Sam bata dawo ba despite kiran da take ‘kwala mata yasa mubina bin bayanta idan har kunnenta ba ‘karya suke mata ba tana iya jiyo muryar Sam na pleading daga can bayan gidan a guje ta nufi hanyar me zata gani? “Ya habibii? What are you doing?” Ta fad’a cikin kakkausar murya Ba zato yaji muryar ya waiwayo yana sakin wani yaudararren murmushi “oh mubina yaushe kika zo?” Kallon da take watsa wa hannun dake cakume da hannun Sam ne yasa shi saurin saki yana shafa kai “am umm...a..” A fusace ta janyo Sam suka nufi d’aki bayan ta zaunar da ita bakin gado tayi folding hannu “is he beating u” Cikin rawar murya tace “no, it’s just his natural way of treating me “ “What!? Amma meyasa baki fad’a ma umma ko baffa sunyi masa fad’a ba, can’t you ever stand for yourself kinga fa ya habibii is so mean” “Don’t worry mubi May be bayason zamana gidansu ne, afterall nan da kwanaki kad’an ze tafi, and I will be back to my normal self “ “Uhm, zo muje muyi game” “Wanne?” “X and O” Da fara’a ta girgiza kai suka nufi d’aki **** *Birmingham, London UK* Tsananin azaba da hucin sanyi yasa kowa ka gani sanye yake da cardigan babba da hular kai har dasu safar hannu dana ‘kafa, hakan take ga magidancin dake driving motor d’insa yana kuma ansa kira at thesame time Daga can ‘bangaren aka ce “uncle please kataimaka min na dawo ko da na wata d’aya ne AB machinaries need me, kaga nan tunda bro B yana nan....” Tun kan ya kai aya ya katse shi “hey mr Man oh let me call you with your name, Anwar bana san kame kame ka zama babban kwabo kenan tunda har ‘kaninka ze iya abu amma kai baza kayi ba, wannan ne taimakon da kake ta ikirarin zaka yi? Ko kuwa ka manta al’kawarin da kayi na DABAIBAYAR al’amuran nan, ka manta da Ammin ka...” “Uncle na kasa samun nutsuwata I don’t know what to do, amma Insha’Allah ko dan al’kawarin da na d’auka sai na cimma burina ko da zai zama aikina na ‘karshe a doron ‘kasa, but before that uncle inason hutawa inason ganin ammi na i missed her...” “...and AB machinaries ko?, kai wannan yaron da ace ba a nigeria aka haife ka ba da bansan yanda zakayi ba, zaka zo hutu amma na 2weeks kawai ka tattara komai ka barshi a hannun qaninka” “Yesss that’s my super uncle, I love you muah” ya manna wa wayar kiss ya shige gida. ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (5) Bayan wasu kwanaki... Firgigit ta tashi jin yadda ake buga ‘kofar d’akinta kamar za’a ‘balle, a iya ‘kiyasinta yanzu sha biyun dare ta wuce tabbacin kowa na gidan ya jima da kwanciya to wane haka? Ko de horror ne yazo cinye ni tunanin daya kuma rud’ata kenan har takai ga zubda hawaye jiki na makyarkyata, can ‘kuryar gado ta ma’kure kanta kira take “Daddy...wayyo umma na...um...” kan ta’karasa aka banko ‘kofar tun ‘karfi wanda yayi daidai da d’aukewar numfashin ta. Washegari Kwala mata kira ta ke tun ‘karfi amma shiru kakeji wai malam yaci shirwa, “kai yarinyar nan kuwa Anya lafiya? Baffa ya sauke jaridar dake hannunsa yace “kinsan fa yau saturday qila bata farka ba” “Haba Abban yara sha d’aya fa ta gota ri’ke min yarinyar nan kaga bara na dubo ta” Fad’owa yayi d’akin kamar wanda aka wurgo kallon sama da ‘kasa ta masa “Kai lafiya naganka a firgice?” Sana’ar tasa yayi ta susar kai yace “ko d’aya uwarmu kawai de...” “Kawai de me?, kai gafara da Allah naje gun d’iyata” fuu ta wuce sa, fuska a cakud’e ya isa gaban Abba ya zauna yana faman kukkumbura “ya dai yayana?” “Abba wai meyasa umma kullum take son min fad’a ni idan batason ganina ne ba se nayi komawa ta ba” Murmushinsu irin na manya yayi kan ya Kada baki yace “yayana kenan ka ta’bajin inda uwa ta guji d’anta?...” “To amma Abba baka ganin kullum kullum...” “Kayi haquri kasan umman taku gidan gargajiya ta taso har da kunya irin ta d’an fari yasa take maka haka bawai intentionaly bane,um?” “Abba shekarar ta nawa a birni nazata duk qauyencin mutum idan ya shekara arba’in ze dena amma...” A tsawace Abba yace “kai da Allah can banson sakarci mahaifiyar taka kake fad’ar haka a kanta, To lallai yau na kuma tabbatar da kanka yana da matsala dole mahaifiyarka take complain a kanka tashi ka bani wuri” ya ja tsaki rai a ‘bace, cikin tafiyar bouncing ya nufi hanyar waje “Ka kintsa dan jirgin ‘karfi biyar zaku bi” Wani qululu ya tokare mishi wuya a zuciye ya nufi waje dede lokacin da ihun umma Salamatu ya iske kunnansu A kusan tare suka fad’a d’akin, Amir ya tsugunna gabanta yana jijjiga ta “Sam Sam ki tashi! Sam wake up please” Umma salamatu dake a firgice ta nufi kawu “Abban yara Sam..Sam bata motsi” rasa abinyi yay kawai ya ciro hular kansa yana firfitu dan duk da AC dake d’akin d’igar gumi yake. Amir ne ya shiga girgiza sa “Abba muje hospital, Abba banson wani abu ya samu Sam” Aljihu ya shiga laluba fad’i yake “ina kake ina na ajiye “ ya d’ago kai yana kallon habibii “kai maza d’auko key “ ya cicci’be ta suka nufi parking lots inns salamatu na sa’be da safiyya kafad’a . *one hour later* Likita ya kalli Alhaji kabiru a fusace “malam anya kuwa yarinyar nan ‘yar kace kamar yanda ka fad’a yarinya qarama ace tana d’auke da hawan jini?” Murya na rawa umma salamatu tace “Ha..w..an jini likita?” Tare da dafe qirji “Kwarai kuwa hajiya, am sorry to say amma a gaskiya ku kiyaye dan bugun zuciyarta am ba daidai yake ba, ko zaku iya tuna wani abu daya faru da ita jiyan?” Umma tace “umm to gskya bama ce ba dan lafiya qalau muka rabu da ita ta shige d’aki ta kwanta” “Basu samu matsala ba, kuma ba wanda sukayi fad’a dashi cikin yara” ya nuna su Ameer da ya hannu, habibii kuma se dad’a had’e rai yake, umma ya kaikace tana duban sashen habibii “Umma” ameer ya furta yana kallonta yana girgiza kai ta juya gun doctor “babu” “Well To gskya de zan baku shawara ku rinqa bincikar a wani hali ‘yarku take ciki dan tabbas firgici ne yasata a wannan halin and again zan riqeta ta kwana biyu zuwa ta warware, “To bari muje mu dawo Ameer Kai se ka....” “Amm hajiya karki damu kanki, anan asibitin mutanen waje basa jinya munada wadatattun ma’aikatan da zasu kula da ita”, “Amma ta yaya...” Yana sakin murmushi yace “karki damu she’s safe with us” Kallon kawu tayi ya girgiza mata kai tace “To shikenan ma iya ganinta kan mu tafi” “Sure! Munirat munirat “ Wata matashiyar nurse ta shigo da sauri ya nunata “wannan ce zata zauna muku da ita zuwa lokacin da zata dawo daidai, ya kalleta take them to room no.18 VIP, “Yes sir” ya furta ta na me russunawa Kan tayi gaba su mara mata baya. Daidai shiga d’akin wasu matasan maza biyu suka fito daga ciki kasancewar bayan su a juye yasa Amir saurin cewa “who are those guys??” Nurse munirat tace “am.. ss..tudent ne suna bin rooms dan duba patient” “Students a private hospital?” Cewar habibii Duburburcewa tayi “am..a..” “Haba mana habibii kar ka rud’ata mana ba kaji me tace bane d’aliban lafiya ne, muje da Allah, kuyi tafiyar ku” ta qarashe zancen idonta a bayan matasan, gaba sukayi batare dako waiwaye ba. Kafad’a habibii ya d’aga irin ko a jikina, yayinda Amir ya riga kowa shigewa d’akin Kwance take sam’bal saman gado doguwar rigar baccin mark&spencer kalar pink tabi jikin nan ta lafe har kana iya gano ‘yan qananun boobs d’inta, gashinta dake barbaje saman pillow nurse munirat tabi ta kame gu d’aya tare da Jan farin quilt ya sakaya mata jiki, fuskar nan tayi kuyat takoma pink zirr abinka da farin mutum idanta dake luhu luhu har yanzu da d’igo d’igon busassun hawaye Hannunta d’aya an ma’kala drip yayin da d’ayan hannun ke manne cikin na Amir “Allah ya baki lafiya, Sam” “Amen, nifa Abban yara abin nan ya d’aure min kai shin me ya razana Sam har ya shiga wannan halin” “Ko dai mugun mafarkai take umma” “Banajin Amir, na fi ta’allaqa abin ga d’an uwanka Anya habibii ba kaine ka jef...” “Haba umman su, fisabilillahi ya kamata ki kawo maganar nan a nan, kai ku tashi mu tafi ma” “Abban yar...” “Kinga tashi muje kinsan halin da take ciki yanzu bata son hayaniya” Mi’kewa tayi tana fad’in “uhm yaushe ka zama likita kuma bansani ba?” Bece uffan ba ya nufi ‘kofa, yayin da umma ta matsa bakin gadon ta shafo sumar Sam, “Allah ya tashi kafad’unki” saman goshi ta sumbace ta, safiyya dake hannunta ta rinqa zillo tana son sauka gurin Sam. Nurse munirat dake gefe tsaye tace “hold on beauty yayarki bata da lafiya” Umma tayi dariya “ai akwai shaquwa tsakaninsu, nurse ga ‘yata nan a kula min da ita sosai dan Allah I can even give you some extra cash” “Kai haba hajiya bakomai ai aikinmu ne kuma ana biyanmu isassun albashi. Nagode” “Shikenan ya amanarta nan” ta fita Nurse munirat ta kalli gadon a fili ta furta “yacce kike me kyau am very sure haka zuciyar ki take” “Stop admiring her and do your work,” Saurin sunkuyar da kai tayi tana Sosa gefen wuya “am sorry sir” tayi saurin bi ta gefenshi ta fice, daidai lokacin akayi knocking bisa ‘kofar “Yes come in” “‘Daliban lafiya” ya furta cikin dariya Kanne masa ido babban yayi, suka tafa da likitan “Maza how far now? Kun ganta ba?” “Yeah...” “Ah ah fa Bro A wancan mutanen basu bari mun ganta sosai ba..” “Ha’a to gatanan ai se kaci gaba, doctor let’s go, meet me down there idan ka gama scanning d’in” ya furta cikin wata deep voice, suka fice Wanda aka kira da Bro B ya maida hankalin sa kan wayarsa dake hahhaska Sam tamkar me yin video, daya gama ya mayar aljihu ya Mara musu baya. Fitowa tayi daga inda take la’be tana tapping gefen bakinta da manuniya tana jinjina kai cike da tunani ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (6) Tayi saurin juyawa ta koma office d’inta, GET WELL HOSPITAL, asibiti ne da babban d’an kasuwa Alhaji Ammani ya ginawa babban d’ansa Hasheem bayan dawowar sa daga UK inda ya karanci gynecology wato likitan mata, asibitin be tsaya anan kad’ai ba akwai ‘kwararrun likitoci daga ‘bangarori da dama dake aiki cinkinsa tsaftataccen asibiti ne wanda ya gaji da had’uwa ta fannoni da dama kama ga ma’aikatan kiwon lafiyar, masu gyare gyare, wadatattun magunguna da dai sauran su Saboda sau’kin da asibitin ke da shi da kuma kwararrun likitoci ga kyakkyawar kulawa da ake baiwa majinyata yasa mutane ke tururuwa cikinsa. Wannan kenan, Alhaji ammani abokin Alhaji Ibrahim ne sosai hakan yasa alhaji kabiru ya bud’e family file a GET WELL gashi basu da nisa sosai. *** Tun kafin motar takai ya tsayawa ya dira yayi cikin gida direct d’aki ya shiga yana tattara kayan sa ya na tura su cikin akwati ya d’auko passport d’insa ya zira cikin Jakar dake goye a bayansa wayarsa dake hannunsa ya sa gaban aljihu ya nufi hanyar fita “Yayana ya haka?” “Abba zan wuce airport ne “ Ya kalli agogon hannunsa “airport by this time?” “Abba remain 2hrs fa” Umma tace “To ai ka jira abokin tafiyar taka yazo ko?” “Ya sameni a can” yayi gaba Baki, hanci, ido ta saki tana binshi dasu, A tsawace Abba yace “Yayana haka ya kamata kayi wa mahaifiyar ka magana?! Tamkar wata sa’arka!, ka dawo nan ko kuwa!” Cak ya tsaya, har seda Abba ya kuma cewa “ba da kai nake bane?” Dawowa yayi yana faman hura hanci, daf dasu ya tsaya, “idan har ka tafi ba tare da ka bawa mahaifiyar ka ha’kuri ba kai fa Allah!” Ya juya zuwa cikin gida. *** Dr Hasheem ya kallesu murmushi bisa fuskar shi “gaskiya you are a lazy being Anwar” Lumshe ido yayi kan ya bud’e su a kan hasheem “think whatever you want, bazan damu ba” ya cigaba da daddanna mini laptop d’in dake bisa stool, Girgiza kai Bro B yayi sanin cewar d’an uwan nasa baze kuma furta wata kalmar ba, ya kalli Dr yace “Allah da ace bansan Bro A ba zan iya ko bin hanyar da yake ba talkless of na mishi magana, kaga fa da muka shiga d’akin can ko kusa da gadon qin zuwa yayi, kamar wanda yaga trash” “Ai wallahi da zan samu uncle zance masa ne kai ya kamata kaje hutu shi ya zauna ya cigaba da aikin” Wani kallon karka fasa ya watsawa hasheem, hasheem ya kwashe da dariya yana fad’in “Allah kuwa kai da qasar haihuwar ka amma kabi ka tsane ta,” “Ka fad’awa wanda aka Haifa anan ba de Anwar ba!” Bro B yace “naji d’in and I’m proud to be a Nigerian” Harara daya watsa masa ne yasa shi saurin d’aga hannuwa “I’m sorry big Bro” Wayar dr hasheem ce ta katse su inda tashiga qara alamun kira dannawa yayi muryar wata nurse ya doki kunnuwansu “Dr room no.18” katse wayar yayi suka mi’ke a tare banda Anwar dake cigaba da latse latsen system, Hasheem ya kalli Bro B “ i think you should stay here gara naje naga halin da take ciki tukunna,” Nodding yayi shi kuma ya fice xua d’akin. Maida hankali yay kan d’an uwan nasa yace “Bro A do you think is a good idea ka tafi ka barni ni kad’ai anan?” Murmusawa yayi “kar ka damu I’ll soon be back afterall kasan hankali na baze ta’ba kwanciya ba matsawar kana cikin mugayen mutanen nan, so chill dana kwana biyu zan juyo, kar ka manta you are my only family now” Forming line yayi da baki, Bro A ya bashi assuring look tare da tapping kafad’ar shi , kiran dr hasheem ne ya shigo wayar Anwar, yace dasu suzo su same shi, tare suka jera zuwa d’akin Bro B ne ya fara sallama ya shiga, tayi waal da ido “Mu...Mu’allim Bello” Murmushi ya sakar mata sam ya jikin ki?” Gaza ansa shi tayi, tayi waal tana bin Bro A da ido ‘O’ shape tayi forming da bakinta, “Mu’allim is he your brother?” “Yeah...big brother” “Hello Mu’allim’s bro” ta d’aga mishi hannu. Blank look ya bata without saying a word ya maida hankalinsa kan waya. ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (7) Sam da bata lura ba ta cigaba da cewa “doctor dama ka san mu’allim B?” Kai ya d’aga, “he is nice right? U know what....” “Kaii!!...hasheem r u sure wannan ce yarinyar da bata da lafiya?” “Iya sani na idanunka garau suke so kar ka sa ni tantama” cewar hasheem a qafule dan zuwa yanzu ya fara jin haushin sabbin attitude d’in Anwar, Bro B yace “kana tunanin set up ne ko ya?” “Bro can’t you see tun shigowarmu take hayaniya ko mu bamu yi surutan da take yi ba, habaa make her stop or barshi am, bari na jira ku a office” fita yayi suka bishi da ido, Qasa qasa ya kalleta ganin yacce tayi kicin kicin da fuska yasa shi matsawa kusa da gadon tallafe da kafad’ar hasheem yace “Sam doctor hasheem aboki na ne, nazo gurin sa ne naga file d’inki shine na nemi alfarmar ganinki dan na tabbatar ke d’in ce” Murmusawa tayi had’e da lumshe idanu ta bud’esu saman nasa “nagode mu’allim, doctor hasheem is nice too just like you kasan me, he often give me some chocolates whenever muka zo nan and I share it with Ameer kamar yanda ka koya mana, kuma inace mishi thank you” Fad’ad’a murmushinsa yayi “that’s very good Sam keep it up” Gyaran murya hasheem yayi wanda yaja hankalin Bello ya girgiza masa kai, shi kuma ya amsa masa ta hanyar lumshe idanu, Saman kujerar dake kallon gadonta ya zauna “Sam how are you feeling now?” “Fine mu’allim” “Good, inaso ki nutsu ki zan miki wani tambaya but you have to promise me first zaki bani gamsashshiyar amsa” Da sauri tayi nodding “Anything for you mu’allim,” “Good, I want to know what exactly happens before you fainted?” ‘Dago kai tayi a firgice, hawaye suka hau shatatowa tamkar an bud’e fanfo, “U’ve already promised and kinsan lefin wanda ya karya alqawari” * Karkad’e rigan ta hau yi tare da gyara zaman talhar dake nad’e a wuyanta tana ganin fitowar sa ta mara mishi baya, Qare mishi kallo ta shiga yi daga baya, Ba’kin takalmin hamez sau ciki daya sakaye doguwar farar qafarsa ta fara kalla shigar baqaqen kayan sunyi mugun tafiya da imaninta baqin jeans da baqar riga me qaramin hannu shi ya kuma fito da haibarsa, kansa dake cike da baqar suma data dabaibaye fuskar had’e da saisayeyyen sajensa ya kuma dilmiyata a kogin begensa har tana jin inama ace yana mata kallo d’aya ya fad’a tarkon soyayyar ta kamar yanda ta kamu farat d’aya daga kallo d’aya. Jin taku daf dashi har ana neman ta’ba sahun sa yasa shi saurin waiwayo wa qiris ya rage goshinsu ya bigi na juna, direct idonta ya fad’a cikin nasa wanda yayi sanadiyyar tsayawar numfashinta na wasu sakanni, ga qamshin sassanyan turaren Ricci wanda ya had’u da versace da sauransu suka bugota har cikin qoqon hancin ta lumshe ido tayi ta bud’e cikin nasa tare da tallafar fuska da hannunta na hagu. ***’Baby ni dai ni dai se na bika um um”, kuka take har da su bubbuga qafa tamkar d’iyar goye, “habibty rayya ki bar ni naje bazan jima ba zan dawo kinji”, “To promise me ba zaka kalli kowace kucakar mace ba,” “na miki alqawari” “ba wani goodbye kiss,” “Kai baby baka da dama, To matso na baka”’*** Ba zato tasa hannu ta tallafo fuskarshi tana qoqarin manna bakinta saman nasa qiris ya rage su manne ya sakar mata lafiyayyun mari saman luntsuma luntsuman kumatun ta, zube wa tayi a qasa ba tare da ya kalle ta ba ya fad’a office d’in hasheem tare da bugo ‘Kofa da ‘karfi. * “Ya..yace idan na fad’a ze yimin irin yanda sukayi ma mummy nah...” Kallon juna sukayi da hasheem kan ya kalle ta “Sam kin manta yanda nayi punishing adnan da ya cilla wa sholey ball?” ‘Daga kai tayi yaci gaba, “I will deal with whom so ever he is kinji, feel free and tell me,” kula da yacce take a tsorace yasa shi cewa “trust me” Hanci ta ja ta fara da cewa “ bansan wane ba kullum dare idan su umma da kowa sun kwanta se yazo yayi ta buga min qofa to shine yau ma yazo” Kukan da yaci qarfin tane ya hanata wata sa magana, “Sam me yake miki?” “Yana ta’ba min jikina ku...kuma da zafi..” “Innalillahi....” Tashi yayi ya matso gabanta ya tsugunna idanunsa sun kad’a jazur muryarsa har bata fita sosai yace” Sam who is he?” “I don’t know, he cover his face with a lion mask” ta kuma fashewa da kuka, saurin kiran munirat hasheem yayi yace ta zauna gurinta su kuma suka yo waje “mu’allim umma na..ka kaini gurin umma na” Yana jinta ya share tare da fita daga d’akin da sauri. Jikin qofar ya jin gina qirjinsa na masa wani irin zafi... Hasheem ya ri’ko hannunsa yana bashi baki suka nufi office tun daga nesa ya hango mutum a yashe can bakin ‘kofa da sauri suka qarasa ya sa hannu jikin wuyanta da hannunta jin pulse d’inta na bugawa ya danna emergency button dai dai lokacin nurses biyu suka iso suka cicci’beta aka d’orata bisa gadon suka nufi wani d’aki dan bata taimkon gaggawa. Zaune yake yayi crossing qafafunsa bisa table yayi baya da kansa idanunsa a rufe sosai yayi nisa cikin tunani ba komai ke damunsa ba se waccan ficiciyar yarinyar da duk ta rud’a shi, a tunanin sa masifar daya zazzaga mata ze sa yaji sau’kin abinda ke damunsa se dai tamkar ya hurara ta cikin zuciyar sa ne, To shin damuwar ta meye? Bansan ta ba, hasali ma uncle aiki ya bamu a kanta and her stupid family, wait who the hell is she, what is so special about her da har uncle yasa muke wasting precious time d’inmu a kanta?! All this answers are to be answered by Bro B, jin zuciyarsa na tsananta bugawa tamkar zata ‘ballo mishi qirji ya dafe da sauri yana rintse ido “please wacece ke? Meyasa zaki min haka?”..numfarfashi ya shiga saukewa yana jin qirjinsa har ciwo ya fara saurin miqewa yayi dai dai lokacin suka turo qofar Neman fad’uwa yake Bro B yayi saurin riqosa “Anwar lafiya?” Girgiza kai yayi yana faman sauke numfashi batare daya furta ko kalma d’aya ba ya koma da baya ya zube saman kujera Bro B ya zo Yana gyara masa kwanciyar ya ri’ko hannunsa “Wacece ita?” “Wa kenan?” Fuska a murtuke hasheem yace “wacce ka wullar a bakin qofa?, wullahi baka da kirki Anwar....” Rufe ido yayi yanaji hasheem yana masa fad’a be hanashi ba har se da yaji shiru ya bud’e ido, yana me kallon Bro B yace “I need to know her more bro, yarinyar da uncle ya bamu aiki kanta” Baki ya bud’e ze fara magana ya katse shi “tashi muje gida, ba tare Daya kalli sashen da hasheem yake ba yace “se mun dawo!” Ya fice Bro B na biye dashi bayan sunyi musabaha da hasheem, batare da ya bawa asibitin 2nd glance ba ya figi motar qiris ya rage ya bigi security man din dake gate. Ranar duk samarin uku haka suka wuni sukuku Anwar Sam ce damuwar sa meyasa a duk sanda ya tuna da ita se gaban sa ya fad’i gashi Bro B yana ciwon kai be samu bashi labarin Sam ba! Bello a.k.a Bro B a.k.a mu’allim bello, yace da Anwar yana ciwon kaine kad’ai dan ya barshi ya sama damar tunanin yanda ze fidda Sam daga cikin wayan nan mutane ya yadda zata bar cikin su baki d’aya! Dan a yacce yake ji baze ta’ba samun kwanciyar hankali ba matswar tana rayuwa cikin iyalin Alhaji kabiru, after all ciwon da ake zargin wasu cikinsu sukayi still suna neman gurgunta rayuwanta, mene aibunta dan ta kasance cikinsu, mene aibunta dan ta aminta dasu d’ari bisa d’ari ya Allah wannan wace irin jarabawa kake yiwa baiwar ka, ubangiji ka tsare ta daga sharrinsu dan tsarewar ka. Da wannan addu’ar ya lumshe ido nannauyan bacci yayi awon gaba da shi. Can bangaren hasheem kuwa hankalinsa tashe yake dan yarinyar da suka samu sa’bani da Anwar ta’ki farfad’owa se bakinta dake furta Bro A wanda yake da tabbacin ji tayi Bello ya ambata, ba komai ke dugunzuma masa lissafi ba se tunanin cewar yau sukayi alqawari da iyalan me girma governor cewar ze sallami yarinyar su, gumin daya shatato masa ne yasa shi zaro handky daga gaban rigarsa ya share iska ya fursar ya nufi ‘kofa da niyyar zuwa d’akin rayya ya kuma bincikar halin da take ciki, sa hannunsa bisa handle kenan yaji an turo ‘kofar Wani kakkauran yawu ya had’iya a lokacin da sukayi ido biyu da firstlady hajiya maryam mainasara gefenta governor ne his excellency dr jamilu mainasara ne wanda suka rakiyar commissioners ne da S.A’s, har ‘kasa ya sunkuya dan basu girmamawa, tun kan ya furta wata kalma maganar firstlady ta doki dodon kunnensa “Dr hasheem don’t stress yourself please, zan fi so mu qarasa d’akin rayya tukunna, dan kaga taron nan duk nata ne. Yatsa yasa ya sharce zufar dake tsiyayo masa ta gefen kunne a zuciyarsa kuwa ba abinda yake se fad’in Anwar ka sakani yin qarya, ka sani jin kunyar dubbanin jama’a, na tabbata yacce sukayi gangamin nan to tabbas zan rasa kujerata a yau, ya kalli qanin mahaifinsa Commisioner of health Dr sufyan yana ta sakin fara’a, na tabbata fara’ar nan is going to be replaced by disappointment, Allahumma la sahla..ya shiga karanta wa a zuciyar sa har suka isa bakin qofar, bismillah yace da gov. Mainasara, yatsa ya girgiza masa da cewa “ah ah anan kaine jagaba doctor kai zaka fara shiga, Dariya yayi mai kama da yaqe kan ya wangale ‘kofar inda sukayi ido hud’u da d’iyar su kwance tayi male male mara lafiya Zam! Runtse ido yayi a zuciyar sa fad’i yake ta faru ta qare tun bare da ya bud’e ido sukayi ido hud’u da firstlady da ta kafa masa dara daran idanunta ‘Kasa yayi da kansa yayin da yaji mahaifan nata na ta qoqarin tashin ta, amma shiru maqatau kake ji wai maye yayi amarya. A d’an rud’e yaji muryar dr sufyan “hasheem ya haka?” Cijewa yayi ya d’ago kai “uncle b.....” “Suprise..” Sak ya tsaya da maganar da yake baki bud’e, tacigaba “mummy na” ta rungume ta ‘kaqam nan fa d’akin ya cika da shewa kowa na tofa albarkacin bakinsa, Hamdala hasheem yayi tare da kuma jingina jikin bango idonsa kafe bisa fuskar yarinyar dake ta faman zabgawa mahaifanta shagwa’ba su kuma suna biyeta ko dan itace ‘yarsu guda d’aya tal da Allah ya basu. “Alhamdulillah “itace kalmar data su’buce daga bakin hasheem, Dr sufyan dake gefen sa ya dafo kafad’ar shi tare da furta “Allah ya biya ka da gidan aljanna, she’s there source of happiness” Murmushi yayi tare da sosa qeya dan tabbas ya sani Allah ne ya cece shi se de me? Maganar da rayya ke fad’a ce ta sanya shi cikin wani d’an qaramin tashin hankali. “Mummy he is so handsome, ni dai Allah ina son shi idan ban same shi ba zan kashe kaina na mutu” “Doctor waye haka?!” Nannauyan numfashi ya sauke idonsa cikin na uncle d’insa ya furta “Anwar” Dr sufyan ya maimaita sunan cike da mamaki, “CEO AB MACHINARIES??, me yazo yi naija” “Whaat!!! Kana nufin yaron da na jima Ina nema wanda ya rinqa decline d’in requests d’ina, shine ya shigo garina?!” Maganar da ta fito daga bakin me girma governor kenan Bugun zuciyar sa ne ya tsananta, Anwar you are in hot pepper.... (Qarin haske😆 by next page qulle kan ya isa haka🤣, lol) ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (8) *NOT EDITED * Waiwaye~ Marigayi Amin Alfalla d’an asalin jihar kano ne qaramar hukumar dala , cikin unguwar lamido crescent GRA area gidan shi yake ya rasu a shekara ta dubu biyu da sha hud’u inda ya bar yara biyu uku tal a duniya tare da mata biyu duk da hajjo uwargidansa sunan ya aure tane kawai amma a UK take rayuwar ta dan can mahaifanta suke befi sau biyu ta ta’ba zuwa naija ba wic ko ‘yan uwanta dake maiduguri ba wani kyakkyawan sani tayi musu ba, gaskiyar sunan hajjo maryam yaranta biyu da marigayi alfalla Anwar da basheer se d’ayar matar sa sadiya wacce take yaren ibra ce, sun had’u da Marigayi ne sanadiyyar zuwan ta office d’insa na naija dake kano matsayin secretary d’insa inda ya d’auketa aiki har ta kai su ga qulla soyayya bayan auren su Allah ya azurta su da yarinya mace taci suna bilkisu , bayan rasuwar Marigayi ta d’auke d’iyarta suka tafi wanda har yau babu ita babu dalilinta, duk kuwa da duban da Barrister qanin marigayi alfalla yayi mata. Marigayi ya fad’i ya barwa yaransa d’inbin dukiya hakan yasa suke business ba kama hannun yaro inda sukayi naming businesses d’in nasu da AB....ma’ana Anwar bashir. AB MACHINARIES kamfani ne da yayi suna gun producing qualitative kaya hakan yasa qasashe da dama ke kwad’ayin yin business dasu se de qalubalen da suke fuskanta shine sam mamallakin kamfanin bawai da kowa yake mu’amala ba, za’a iya cewa kamar selecting yake. Game da maganar su da me girma gov. Kuwa akan wasu injina ne daya keso ya siya gurin su dan gyara shinkafar mu ta gida kamar yacce shugaban qasa yace akoma yi, se dai qiri qiri Anwar yayi ko oho da maganar daga baya ma se ya aika wa me girma governor cewa ya nema a wani wurin daban. Wannan kenan Dawo wa labari, “Doctor inason had’uwa da yaron nan within 48hrs, bawai Ina neman yardar sa bane, this is an order from me” cewar me girma governor ya juya ga P.A d’insa “ka samun cikin schedules, idonsa kan rayya yaci gaba, na miki alqawari ko ta halin qaqa se kin same shi kinji” Girgiza kai tayi cike da farinciki, “Amma your excellency..” “Kar ki damu kome ze zo mana da sauqi Insha’Allah “ ya qarashe a hankali zuwa can ya d’ago kai yana kallan dr sufyan yace “babban likita yaushe zaku sallame mu?” Waiwaya wa dr sufyan yayi zuwa sashen da hasheem yake yayi yace “Doctor yaushe zaka sallami patient Dinka?” “Yanzu am zata iya is wucewa gida zan aiko da magunguna zuwa anjima Insha’Allah” “Allah ya kaimu” cewar First Lady, bayan yan hirarraki da yan jaridu suka tafi, inda suka tafi suka bari hasheem da tunanin yacce zeyi ya kai Anwar wurin me girma governor yar dariya ce ta su’buce masa daya tuna yanda me girma governor ya rinqa alqawarin mallakawa yarinyar sa Anwar Mutumin da lafiyayyiyar mace ma ba ko wacce yake kulawa ba talkless of mara lafiya kamar Rayya. Lallai be san waye Anwar ba, mutumin da yake murd’ad’d’e, mutumin da idan kayi dama hagu yake yi, mutumin da yake wa fari kallon baqi. *Bayan wasu awanni* Anwar Alfalla shine sunan da yayi typing cikin system d’insa nan da nan ta bud’u yaci gaba da tura saqonni tare da acceptn wasu kwankwasa qofar da ake ne ya tsaida shi ba tare da ya d’auke idonsa daga kan computer ba ya bada izinin shigowa Babban mutum ne ya shigo, kallo d’aya zakayi masa kasan he’s in his early 60’s yana tafe yana gyaran babban riga, sallama yayi tare da jan kujera ya zauna. *Five minutes later* Duk inda quluwa takai ya gama quluwa alhaji me babura kenan wanda yayi tattaki takanas yazo wajen Anwar dan tattaunawa ta musamman, dad’a karkacewa yayi bisa kujerar yana hararar shi qasa qasa, ‘Dago kai yayi a nutse murmushi maqale a bakin shi, “barka da zuwa alhaji hope u didn’t find any difficulty coming in here?” Tambayar tazo mishi kamar da rainin hankali, basarwa yayi “ah Alhamdulillah, ya aiki naga kamar kana aikine ma” “Aa no karka damu nagama ai, if to say ban gama ba da zan sallame ka ne zuwa wani lokaci “ Jinjina kai Alhaji yay yaci gaba, “ko akwai wani abu da kake buqata?” “Sir Anwar kan maganar nan ce da mukayi a waya kan fitulun babura” Jimm yayi zuwa can ya sauke numfashi yace, “alhaji me babura ko?” “Eh eh ni ne” “Na tuna, amm bari muga..” Wasu takaddu ya janyo ya bashi yace gashi ya cike yayu transfer yanzu” Haka suka ci gaba da tattaunawa har Allah yasa aka dace suka rabu. *** Sam ta tashi a firgice tana qwala kiran Abbanta da umma har ma da Ameer nurse munirat ta fad’o d’akin a guje “Shhh calm down fine baby, menene ya sameki, gashi doctor hasheem ya fita wayyo” Marairaice wa Sam tayi “please ki kaini gurin umma na da Amir kinji kar su tafi su barni” kuka take bil haqqi, har da su majina “Okay ok kiyi shiru bari naje na d’auko waya na kira doctor” Girgiza kai tayi a tsorace, tunanin ta d’aya wannan mafarkin da tayi wai sun tafi sun Bart’s gashi tana ta neman su bata gan su ba” Wani sabon kukan ne ya su’buce mata, zuwa can bacci me nauyi yayi nasarar d’auketa. Munirat dake bakin qofa ta le’ko da farantin silver a hannunta me d’auke da allura ta shigo tayi mata. Tajima a tsaye tana kallon ta ba abinda take se qiyasta kyawu irin na Sam, zuwa can ta sauke ajiyar zuci ta fita tana gunaguni saboda wayar Doctor da taqi shiga *** Qarar bell ce ta tashe shi jin se dannawa ake ba qaqqautawa salati yayi tare da miqewa ya zauna hannu yasa ya murza idanu, ya kai hannu ya kunna bedside lamp idansa ya kai kan agogo 5:10am wane haka? Tashi yayi yana gyara zaman boxers d’insa ya nufi qofa, fridge ya tsaya yasha ruwa sannan ya nufi qofa ya bud’e, saurin juyawa yayi ya kalli time kan ya waiwayo ya kalle shi “Hasheem?!” Winking ya masa ya ra’be ta gefensa ya shige ciki, rufe qofar yayi ya biyo shi saman kujera ya zube yace “lafiya dai na ganka da asuba haka?” Dariya yayi, “ina neman rakiyar ka ne” “Rakiya yanzu?” “Taimaka min zakayi, nayi maka alqawarin daga yau bazan kuma takura ka ba bare ma tafiya zakayi zamu jima bamu had’u ba” Numfashi ya sauke yace “amma kasan yau by eleven jirgina ze tashi right?” “I promise you ba zamu jima ba” “What’s so important da gurin da zamu je kuma inane?” “Kasan dai ni ba d’an yankan kai bane” “Kana fad’a min magana ne? Zan fasa wullahi” Hannu ya had’e gu d’aya “yi hakuri yalla’bai ka shirya mu tafi” Hararan wasa ya yi masa ya shige d’aki . Se gurin 6:30am suka kama hanya, banda hamma ba abinda suke bugawa daidai wani tamfatsetsen gate yayi horn gate d’in ya bud’e ya nausa hancin motar ciki a harabar yayi parking suka fito wani matashin saurayi yayi musu sallama tare da yi musu iso zuwa bakin wani pool cikin wata bukka. Zaman su ke da wuya ya fito sanye da jallabiya hannunsa riqe da mug sallama yayi musu suka amsa, kiran sunansa da yayi ne yasa shi d’ago kai ko ba’a fad’a ba yasan wanene numfashi ya fusar tare da watsawa hasheem wani killer look. ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (9) *NOT EDITED* Sipping shayin yayi kan ya kada baki yace “Anwar Amin Alfalla, the young talented billionaire nasan za kayi mamakin ganina ko, well to clear your doubt ba abin mamaki bane duba da nan jihata ce, nakan san duk wani shige da fice da akeyi cikin ta” ya numfasa “well kuyi haquri na cika ku da surutu ban baku abin sha ba, duba da weather d’in garin nasan zaku fi buqatar me d’an d’umi” Basu kai ga yin magana ba ya bada order a kawo musu abun ta’bawa, maida idonsa yayi kan fuskar Anwar wearing a smile yace “Anwar ko kana da abin cewa?” Forming line yayi da bakinsa still idanunsa maqale kan hasheem kan yayi faking smile yace “ranka ya dad’e sir bani da abin fad’i, se abinda kace” Jinjina kai mainasara yayi “ok I think duba ga lokaci let’s just get straight to the point but kafin nan Anwar ko meye dalilinka na qin yin aiki dani? Ma’ana qin yimin abinda nayi requesting duk da cewar na had’a maka da deposit ne?” Murmusawa yayi yana me kuma sadda kai qasa yace “I’m sorry ranka ya dad’e amma inaga zefi cancanta muje kan maganar data kawo mu nan daga baya se muyi wannan” “Ko zan iya sanin dalilin da yasa kasan cewa ba maganar kenan data zaunar damu a nan ba” “Ranka ya dad’e akwai different companies da suke qwararru ta wannan fannin wanda suka dame ni ta ko ina kan meyasa akan ni kad’ai zaka damu?” Gyad’a kai mainasara yayi yana mamakin courage irin na Anwar ya d’age gira “maganar ka gaskiya ce, amma inaso ko dan gaba ka kiyaye, maganar mu ta gaba kuma..ko ka sanar dashi?” Ya karashe maganar idonsa kan hasheem “Aa ranka ya dad’e abinda ka aika ni yi kad’ai na aiwatar wannan hurumin ka ne” “Anwar! Ina neman alfarma a gurin ka” Mamaki ya cika shi cikin sanyin sauti yace “alfarma? A wurina kuma” Mainasara ya jinjina kai, daidai lokacin aka kawo musu abin ta’bawa aka zuba wa hasheem anwar kuma tea kawai ya kar‘ a shima d’in kad’an ya kur’ba “Anwar inason ka nemi auren yarinya ta Rayya..” maganar da me girma governor ya sashi wata muguwar qwarewa Tun qarfi hasheem ya shiga taping bayansa, bayan ya kar’bi gorar sassanyar ruwan sanyi ya tuttula masa a baki, sunkuyar da kai yayi na wasu sakanni kan yaja hanci ya mi’ke tsaye da sauri yana d’an sadda kai yace “with due respect ur excellency, I’m sorry for what I did a baya, amma idan kana son hukuntani ne dan Allah kayi ta wani hanya ba wannan ba” Dariya mainasara yayi “Anwar kenan” ya dafo kafad’ar shi “a kan wani dalili zan nema hukunta ka, kan rights d’inka? Aa bana haka, kuma hukunci da ‘yata how ridiculous! “ ya maida idonsa kan hasheem “dr ko zaka iya yiwa abokin ka bayanin rayya! I mean inda ta Ganshi” Gyaran murya yayi bayan ya kora ruwa ya kalli Anwar dake masa wani d’an banzan kallo “yarinyar da ta fad’i a bakin office d’azu” Kya’be baki yayi, ta ya suke expecting ze iya tuna wata yarinya! Wacce take asibiti ma mara lafiya, shirun da yayi yasa me girma governor dad’a watso masa tambaya, “ka tuna ta?” Girgiza kai yayi a qafule yace “I can’t remember her” “Whatever de Anwar wannan be maqasudin zaman nan namu, Ina neman alfarmarka da ka taimaka min, Rayya bata ta’ba neman abu ta rasa ba ko da kuwa Nisan sa yakai birnin sin, ga qoqon bara ta nan Anwar dan darajar Allah ka taimaka min” Kallon mamaki yabi governor dashi, soyayya? Shi ya so wata? Kuma wai da aure!” “Silence didn’t speak Anwar so zan baka dama kayi tunani amma kafin nan zanso ka ganta kan ka tafi dan abokin ka yace za kaje ganin gida” “Ye...yea..h, a zuciyarsa kuwa banda tafarfasa ba abinda take, shi yaso wata da zancen aure Ina yake da time ma, gskya ma he’s not ready kwata kwata, to speeds things up ya amsa da to, Nan da nan kuwa fara’ar me girma governor ta fad’ad’a inda yasa ayi ma firstlady magana ta sa Rayya ta kintsa, shiru be ya biyo baya har na wani d’an lokaci kan wayar dake gefen me girma governor ta d’au qara yana d’agawa ya sauke ya qwalawa wani magana inda ya umarceshi yaje government house ya d’auko Rayya, Tattaunawa suka cigaba dayi tsakanin me girma governor da hasheem inda nan take me girma governor yayi ma hasheem alqawarin alkhairi masu yawa saboda kawo mishi Anwar da yayi. Can gefen Anwar kuwa daddanna waya kawai yake amma hankalinsa kwacakon yana kan lokaci dan Allah Allah yake su tafi yaje ya fara shiri ya kuma ci mutuncin hasheem for bringing him to this hell To hell mana kai shifa ji yake kamar yana zaune a waya, horn d’in da suka ji ne yasa shi d’ago kai a nutse waze gani? Wannan fat mango d’ince, wacce ta nemi kissing virgin lips d’inshi, Idan be manta ba itace wacce ya hankad’e jiya, itace dama governor yake magana?, lallai dole yayi pleading dan Allah ne kad’ai yasan maza nawa taso raping, saurin kauda tunanin yayi jin maganar hasheem a kunnenshi “Look how breathtaking beautiful she is” Girar sama data qasa ya had’e ya watsa masa hararar kana da hankali kuwa, iska yaji fuuu ta doko shi before he knows se ganinta yayi tsugunne gabanshi ta tallafo chubby kumatunta ta tsare shi da ido, “Hey bro A meyasa kullum kake dad’a kyau ne” Saurin d’aga kai yayi yaga me girma governor bayanan ya maida hankalin shi kan hasheem ido waje Yana pointing d’inta da hannu alamun “is she d one?” Kai hasheem ya d’aga masa yayi baya yayi relaxing yana sakacen Haqori... (Ayimin afuwa yau ban samu damar typing da yawa ba. Tnc u) ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) Assalamu alaikum Ina neman afuwar jina shiru da ku kayi hakan ya faru sanadiyyar kakata da Allah yayi wa rasuwa, Ina barar addu’ar duk wanda ya karanta post d’in 🙏 nagode. (10) A nutse ya sauke kwayar idanunsa saman nata wanda hakan ya haddasa wa Rayya fad’a wa cikin shauqin bege, cike da izza yace “tashi a gaba na!” Ko d’ar bata yi ba sema koma wa da tayi saman side table ya zauna still idonta stick to him, numfashi ya sauke cike da rashin sanin yanda zeyi da fat mango (in anwar’s language 😆) kallon hasheem yayi yanda ya wani bararraje yana niqar abinci bayan ya jaju’bo masa wannan aikin, ‘kwafa yay tare da d’an sakin fuska ya kalleta ji yake kamar ya ham’bareta amma ya basar yana me faking smile “Hi beautifullll” ya wani ja word d’in, dariya ya sar’ke hasheem har be san lokacin daya fursar da ruwan bakin shi ba ya d’aga musu hannu “Sorry sorry pls” inda sukayi parking ya nufa yana dariya wanda sautin ta ke isa har kunnen Anwar, Fuska a d’an cunkushe ta juyo da kanta inda yake “wane wannan yake qoqarin spoiling mana special moments d’inmu, ko be ta’ba jin an fad’i haka bane” Mamaki maganar ta bashi, sosai ya fara doubting lafiyar yarinyar cikin kwantar da murya yace “baki san shi bane?...” ‘Dan jimm tayi alamun tunani, can ta d’aga kafad’a “not at all..” “Likitan ki ne..” “Likita? No! This is d first time I’m seeing this guy” “Is she suffering from..” “Alzheimer’s yes” Jinjina kai yayi idonsa a kan hasheem, tausayin yarinyar ya cikashi, a tausashe yace “Rayya wannan doctor d’inki ne, shine yake kula da ke kinji” Turo baki tayi “To amma ni ai lafiya ta qalau fa” Tsintar kansa yayi da murmusawa ya kalli agogon dake maqale a hannunsa a hankali ya furta I need to save a life, a fili kuma yace “Rayya will you like to join me for a ride?” Farinciki fal ranta ta yi nodding har da saurin miqewa, tsaye shima ya tashi ya kalli hasheem da ya ke kallonsa tamkar wani baqonsa ya kashe masa ido ya juya suka nufi mota, Hasheem tsabar mamaki ya gaza furta ko ‘A’ mamakin hali irin na Anwar yake, jin ana laluba masa aljihu yasa ya dawo present time Anwar ke neman key “Thank you” ya furta yana nuna masa muqullin ya koma motar a guje inda Rayya ke jingine tana jiransa... Wayar hasheem dake bisa table ne ta shiga ringing ya d’aga lokaci d’aya annurin fuskarshi ta gushe ya maida wayan cikin aljihu ba tare daya nemi sallama da me girma governor ba ya rubuta wani short notes ya bada a bashi ya fita ya shiga napep. *** Gwaggo ke ta kai kawo waya a kunne minti d’aya biyu taja tsaki, munu na zaune saman cushion ta shar’bar kuka cikin sheshsheqar kuka tace “gwaggo har yanzu bata shiga ba” Numfashi ta sauke “hmm, munu je d’aki ki d’auko min gyale mu kuma koma wa ko Allah ze sa sun dawo” “To gwaggo” ta shiga d’aki da sauri ta fito riqe da mayafin jikinta sanye da hijab ta mi’ka mata ta yafa suka rufe gidan suka fice *** A qagauce ya sauka a napep d’in ya fad’a asibitin straight d’akin ya nufa, bakin gado ya sameta tana ta gursheqan kuka bakin gadon ya tarar da ita zaune duk ta ciccizge carnula d’in hannunta tana ganin shi ta mi’ke tsaye “Doctor dan Allah ka kaini gurin umma na please doc..” Jirin daya kwasheta ne ya Hana ya ‘karasa maganar nurse munirat tayi saurin taro ta, riqe kanta tayi hawaye na bin kumatunta, gyara mata kwanciyar yayi tare da bata taimakon da tafi buqata nan da nan kuwa wani baccin ya d’auketa. Gefe ya matsa yana dialling number Alhaji kabiru, sake kira yayi for d 101 times amma shiru hakan yasa ya yanke hukuncin nufar gidansu yaji ko lafiya dan dole ya sallami yarinyar nan dan baze juri ganinta cikin wannan halin ba Motar sa qirar Honda 2008 wacce ke ajiye cikin garage din asibiti ya d’auka ya nufi gidan Alhaji kabiru *** Zaune yake gefen cashier yana kallon duk wani moves d’inta ta cikin mini TV we libgar kaya take da masu amfani da marasa amfani mutane se kallonta suke wasu ta danqara musu harara wasu ta ja musu tsaki ganin yadda lokaci ke ja yasa shi dakatar da ita hakanan, Marairaice fuska tayi “Bro A ice cream fa?” Iska ya fursar ya tsaya riqe da qugu “oya hurry up kar nayi latti kinji” Girgiza kai tayi ta juya ta d’auko cikin freezer har da dad’in chocolate shi dai yana ta bin kayan da ido mamakin inda zata kai uban kayayyakin yake wanda kwata da rabinsu kayan maqulashe ne Gida ya kai ta har qofar falon mahaifinta ta kira hadimin gida ya shiga da kayan agogon hannunsa ya kalla yace “To baqo zeyi halinsa ‘yammata na” Wal tayi da ido “ni nice ‘yammatan ka?” Kallon yacce take farinciki yayi yace “yes, and you are also my sister..” Ta katseshi “and..?” Ya gane abinda take nufi amma se yace “d’aya matsayin se idan kin min alqawarin kafin mu kuma had’uwa zaki rame” Kwa’be fuska tayi “why?” “‘Yammata na qiba is not good to your health” Shiru tayi kanta a qasa ya cigaba “in dai yammata na ta rage qiba I’ll surprise her” Da fara’ar ta tace “With what?” “Zan fad’a miki amma ba yanzu ba” Ta girgiza kai “Zan rage kaga dama mummy na bata so itama” “Very good yammata na, yanzu bari na tafi saura 2hrs jirgina ya tashi” ‘Kwal ‘kwal idonta ya kawo ruwa kula da haka yasa shi cewa “kinga bari naje na shirya se nazo muyi sallama ko” “To kayi sauri kaji” Ya d’aga kai “to shikenan” a hankali ta sauka a motar ya ja ya tafi, yana fita a gidan ya sauke relief sighs ya nufi gida. Qarfe 10:30 ya tura wa d’an uwansa text ya shiga jirgi suka lula gajimare. *** Lokacin da hasheem ya isa gidan Alhaji kabiru yayi daidai da isowar gwaggo daidai bayanshi ta tsaya lokacin da yake juyowa cike da tunanin mafita sukayi ido hud’u “Sannu bawan Allah, “ Kallonta shima yayi “sannu ina wuni” Cikin rawar murya tace “lafiya qalau, kai ma neman masu gidan kake yi ko?” “Eh amm nazo na tarar basa nan...” Wayarshi data shiga qara ne ta katse sa “Eh nazo gidan su yarinyar basa nan bello what’s happening?, Hello hello...mtsw poor network” ya maida wayar aljihu Gwaggo ta matso kusa dashi “Yaro ko kasan wani abu game da inda masu gidan nan suke ke?” Kallonta yayi ganin resemblance d’in yarinyar da Sam ya sa shi gyad’a mata kai. ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (11) *NOT EDITED * “Ina suka tafi, Ina d’an uwana ya tafi ka taimake ni ka bani amsa d’annan shi kad’ai ne dangina kaf fad’in duniyar nan ka taimake ni ka had’a ni dashi...” Tausayinta matar ya cika masa zuciya hakan yasa shi lumshe ido ya bud’e yace hajiya ni kaina tunanin inda mutumin nan ya tafi nake dan a jiya da safe ya kai yarinyar sa asibiti na da zummar a duba masa lafiyar ta se dai tun bayan barin su can ban kuma jin shi ba, ko wayar sa, hasalima da na kira ake rejecting daga baya kuma wayar a kashe na keji shiyasa nayi tattaki zuwa nan” “Samira kake fad’i? Samira na wurinka?” Ya d’aga kai “tabbas dan yanzu haka rigima take kan lallai se na kawo ta gurin umman ta, sai da nayi mata allura saboda ta samu nutsua sannan na samu na fito” “‘Dannan taimake ni ka kai ni gurin ta idan wani abu ya sameta bazan ta’ba yafe wa kaina ba..” Jikin hasheem yayi sanyi jin kalamin gwaggo hakan yasa shi saurin tare musu napep suka tafi, tare suka iso da bello wanda shima yayi parking motar sa kenan. gwaggo ya gaisar a tsatstsaye suka fad’a cikin asibitin duk irin gaisuwar da ake wa hasheem be tsaya ba se hannu kawai da yake d’aga musu, kai da ka gan su kasan suna cikin wani yanayi na tashin hankali, dai dai shiga d’akin suka jiyo ihu daga ciki, a qagauce suka fad’a nan suka ga an fice ta window da gudu se labulaye da iska ke kad’awa Maida ido sukayi kan Sam wacce ta ke a qaqqafe tamkar gawa baki bud’e ido a wawwangale kanta suka yi a rud’e su na jijjigata motsin da bakin ta ke yi Doctor ya bi, jin abinda tace yasa shi saurin waiwayawa baya daga lungun gado ya hango nurse munirat yashe cikin jini munu ta saki wani irin ihu tare da fashewa da kuka... *** *Birmingham, London UK* Zaune yake cikin wani tsadadden restaurants dake fidda wani tsadadden qamshin rose flower da ke tashi ta ko wani lungu da saqo na wurin, mata ne da maza baibaye da wurin ko wa na harkar sa, da yawan su masoya ne dan daga masu sarqafe da hannun juna se masu sumbatar juna wasu kam a rungume suke, kasancewar rayuwa irin ta waje ba wanda ya damu da abinda wani ke yi, Yayin da kowa ke harkar sa shi yana gefe ne rungume da magazine, duk da qarar takalmin da ta nufo shi, be hanashi qarasa abinda yake ba se ma d’aukar qaramin kofin whiskey dake bisa table yayi ya kur’ba, qamshin turaren Nina ricci daya bugo sa ne yasa shi sakin wani lallausan murmushin da ya fidda sirrin kyawun fuskar shi, a hankali ya d’ago ‘kwayar idonsa ya sauke saman kyakkyawar fuskar ta, “Kimberly” ya furta cikin sanyin sauti, tashi tayi da sauri ta fad’a jikin sa tare da sakin siririn kuka, “shhiiii ya isa haka kim pls ki bar kuka kar hankalin jama’a ya dawo kan mu” Bata kula shi ba se ma duka da ya Kaiwa faffad’an qirjinsa tana kuma shigar da fuskar ta jikinsa, ajiyar zuciya ya sauke he know hakan ze faru dama, tana d’aya daga cikin dalilin da yasa yake son dawowa, Be kuma furta ko kalma d’aya ba se hannu da yasa saman sumar kanta yana shafawa a hankali, Se da tayi kuka me isarta sannan ta d’ago idonnan nata yayi jaga jaga duk maskara ta ‘bata mata fuskar, powder tayi dabbare dabbare, janbaki kuwa duk ta goge saman ash rigar sa. “Mine ba zan kuma yarda kayi nisa dani ba ko da hakan na nufin rasa rayuwata ne , do you know d hell I went through duk sanadiyyar rashinka, mine yaushe zaka gane irin soyayyar da nake maka dukkan numfashi na yana fita ne da sunanka dan Allah kar ka kuma yin nisa dani idan ba haka ba zan kashe kaina” ta qarashe a marairaice Iska ya fursar daga bakinsa without saying a word ya d’auko tissue ya share mata fuska ya ja hannunta suka fita, a motar ta qirar Bentley dai dai gidan da ke street 11, average avenue suka tsaya, Sarqafe da qugun juna suka nufi cikin gidan kai kana ganin su kaga masoyan da suka jima cikin begen juna. *** Qarfe 6:35pm daidai agogon Nigeria aka idar da sallah a masallacin asibitin GET WELL, hasheem da bello suka jero a tare, qasan bishiyar zaitun suka tsaya bello ya kalli hasheem Yace “doctor muna stressing d’inka da yawa gaskiya” “Hmm..a da ba, amma yanzu inajin yarinyar nan tamkar wata ta jikina” Jinjina kai bello yayi “amma Doctor what’s your view akan case d’in nan? Kuma me kake ganin ya kamata muyi? Tsaya ma tukunna har yanzu securities basu samu wanda ya yiwa nurse d’inka illa ba?” “Well yace basu samu kowa ba, amma sun kuma tightening security, amm kagane ba ni a nawa tunanin babu yacce za’ayi ba wani notice nothing nothing mutanen nan suyi vanishing lokaci d’aya, kuma bayan sun san cewar yarinyar su na nan...” “Baka ganin suna gudun kar a ga gazawar su wurin kulawa da ita duba ga barazanar da ake wa rayuwarta a gidan?” “Well hakane, amma fa kar ka manta he’s d’an ‘kasa’s brother ...” Dariyar ‘keta bello yayi, “a naka tunanin baze iya cutar da ita ba” Ya d’aga kafad’a “it’s up to them all I know ni dai, we have to get justice for this young girl “ Wayar sa dake qara ya d’auko a aljihu, uncle U ya bayansa a screen d’in, a kunne ya saka “my one and only uncle” Daga can ‘bangaren ya amsa shi, ya jima beyi magana ba zuwa can yace “I’ll call him right away “ Hasheem da tuni mood d’insa ya canja yace “ni nasan dole se ya fara zuwa wurin baturiyar nan kan ya qarasa gida , Allah ya kyauta” ya ja tsaki ya bar gurin. Bello da ransa yayi mugun ‘baci ya shiga tattauna lips d’insa na qasa idonsa ya kad’a yay Jajir bango ya kai wa duka “Why Bro meyasa? Meyasa kake son lalata tarbiyyar da Ammi ta jima tana bamu, irin kalar sakayyar da zaka yi mata kenan???” *** “Wayyo umma na..ze kash..e..n...” tun qarfi gwaggo ta girgiza ta, ta farka, kalle kalle ta shiga yi zuwa can ta sauke ajiyar zuciya ta ruqunqume gwaggo hannunta cikin na munu fad’i take “Gwaggo kar ku bari yayi min, ze tsikara min allurar jikinsa, yaji wa nurse ciwo, yana ji min ciwo a jiki na wayyo qafana” munu da ta dafa qafar tayi saurin janye hannunta dai dai lokacin hasheem ya fad’o d’akin gwaggo na qoqarin gyara mata kwanciyar suka hango jini na biyo cinyar ta zuwa ‘kafar ta “Innalillahi wa Ina ilaihir raji’un” cewar hasheem wanda idonsa ya sauka kan jinin dake zuba... ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (12) *NOT EDITED * Wata nurse ya qwalawa kira aka ja gadon da take kai zuwa wani d’akin inda aka shiga bata taimakon gaggawa salati da salallami gwaggo ta shiga yi fad’i take “shikenan sun lalata mana ‘ya na shiga uku ni haule me zan ce ma ibrahim da mariya “ kuka tashiga yi bil haqqi munu dake gefenta itama nayi dakyar suka yi shiru. Wucewar awa d’aya da rabi doctor hasheem ya fito jiki a sanyaye ko d’ago kai ba yayi yazo wuce wa ta kusa dasu munu ta tare shi “Doctor ya jikin Sam?” A hankali ya d’ago kwayar idonsa ya sauke cikin nata dake cike da qwalla “ta..na nan lafiya bacci take” da haka yaja wata zuwa office, gwaggo tayi saurin zuwa qofar d’akin tana le’kawa ta wata ‘yar ‘bula, d’an guntun murmushi ta saki “dagaske yake bacci take munu” Murmusawa tayi hawaye suka biyo kuncinta tace “Alhamdulillah, gwaggo to muje mu ganta ko?”, girgiza kai tayi “aa munu I think zefi mu barta ta huta tukunna, zo mu jira a can” tayi pointing wasu kujerun qarfe. ~ Bello guri ya samu ya zauna har aka kira sallar isha bayan ya shiga yayi sallah ya fito ya zauna kan d’aya daga cikin kujerun shan iska dake harabar asibitin waya yake jujjuyawa a hannunsa amma zuciyarsa ta jima a duniyar tunani _Kimberly wata hatsabibiyar yarinya ce da tayi wa rayuwar Anwar shigar bazata, a lokacin da suke jami’a Anwar ya kasance d’aya daga cikin kwarin aji ma’ana wayan da kwakwalarwarsu tafi ta kowa ja hakan yasa da yawa d’alibai suke yawan zuwa gurinshi dan ‘karin haske, had’uwar su da Kimberly ya samo asali ne wani lokaci suna shekara ta biyu a jami’a inda tayi differing semester kuma ta kasance bata d’auka summer course ba da ta dawo, so da semester ta zagayo ne hasheem ya had’a ta da Anwar dan yake koya mata karatu, Sam Anwar be so hakan ba dan da farko ‘ki yayi se da yaga ran aminin nasa ya ‘baci ya amince, from the very first time da suka fara karatu Kimberly taji itafa ko da zata tafi tsirara se ta Mallaki Anwar tun daga nan fa tun Anwar na yakice ta har ya kyale inda ta kuma shiga jikinsa kai qarshema Allah kad’ai yasan iya abinda ke wakana tsakaninsu _ Iska ya fursar idanunsa a runtse yana jujjuya kai mafita kawai yake nema a gefe d’aya kuma yana mamakin abinda Anwar d’in yayi, wato dalilin komawar sa kenan?, hannu yasa ya cakud’a curly hair d’inshi, there’s only one way out ya ayyana hakan a zuciyar sa. Wata number yayi dialing “check your inbox” ya kashe wayar ya shige cikin asibitin, cikin reception ya hango su zaune gwaggo ta kafa tagumi munu kuma ta kwantar da kanta saman cinyarta, kai ya girgiza cike da tausayin su, ya nufi office d’in hasheem Handle d’in ya murd’a, daga ciki hasheem ya leqo ganin waye ya sashi bud’ewa, shiga yayi jiki ba ‘kwari ya shiga, saman doguwar kujera ya zube, shiru ya biyo baya ko wannen su da abinda yake qissimawa, hannu yasa ya shafo fuskarsa a hankali ya shiga karantowa bello abinda ya faru, Lumshe ido kawai yayi cike da tausayawa yarinyar kan ya miqe ya fita, wurin su gwaggo ya nufa ya tsugunna cike da ladabi “Hajiya kuyi haquri komai yayi zafi maganin sa Allah” d’aga kai tayi, ya cigaba “..amm hajiya nace idan babu damuwa zanso sanin alaqarki da Samira” Numfasawa tayi idonta quri a waje d’aya, ta shiga fad’a masa tsakanin su, cikin gamsuwa da bayanin nata yace “hajiya ni sunana bello Alfalla ni kuma malami ne a makarantar su samira haka kuma aboki ne ga likitan dake kula da lafiyar ta, ni Lauya ne me zaman kaina...ahh ya sosa kwantaccen sajen sa, ina miki wannan bayanan ne bisa wasu dalilai wanda na bar wa kaina sani which with time zaki sani Insha’Allah” Gwaggo dake jinjina kai tace “Allah sarki mungode da kulawa, Allah ya bada lada” “Amen, idan ba damuwa ko zan iya samun address ko dan gaba” “Anan muke sultan road Gidan alhaji Aminu” Noted, ya tafi bayan yayi musu sallama. Tashi gwaggo tayi zuwa d’akin Sam biye da munu, a lokacin wata nurse ta shigo ta duddubata murmushi d’auke a fuskarta tace “hajiya ‘yar nan taki is a fighter jikin ta yayi sauqi sosai zuwa gobe Insha’Allah zaku iya tafiya gida, let me go and give doctor hasheem the good news,” ta fita da sauri. Da azama Gwaggo ta nufi bakin gadon daidai lokacin Sam ta fara tari tun qarfi, munu ta taro ruwa a dispenser ta bawa gwaggo ta bata, a hankali ta shiga bud’e ido har ta wangale su duka “Gwaggo na” ta furta cikin rawar murya tare da fad’awa jikinta. *** “You mean sunyi qoqarin yi mata fyad’e?” Hasheem ya girgiza kai “haka ne, dan duk alamu sun nuna hakan” “Innalillahi...she need a very tights security, Bari na fad’a wa uncle” *** *8:00am Birmingham U.K* “Ammi na” ya shagwargwa’be mata tamkar yaron goye, duk ya kanainaye ta, shafa hannunsa ta cigaba da yi wanda suke sar’ke cikin nata , gyaran muryar uncle ce ta d’auki hankulansu inda ya tura kujerar da yake zaune baya, yana share bakinsa da tissue, wayarsa dake haske yayi picking yana duba saqo Yace “Anwar yaushe ka iso garin nan??” ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (13) Tari ne ya sarqe shi tun qarfi, Ammi da mom hajar suka tashi da sauri ko wa na qoqarin nema masa ruwa, cike da takaici uncle ke kallon su duka, guntun tsaki yaja ya tashi ya hau sama, kallon juna sukayi Ammi tayi wa mom hajar Alama da ido ta bishi, gyad’a kai tayi fuskarta d’auke da tausayin Anwar da take ta faman shafa bayan sa, hannunsa dafe da ‘kirji, da’kyar ya iya yiwa ruwan kur’ba biyu ya nemi Ammi ta rakashi d’aki dan hutawa. _Mom_hajar_ Zaune ta same shi bisa reading reading table yana gyara medical glasses dake maqale a idonshi, be ko waiwayo ba, yaci gaba da duba littafin Human values, lumshe ido tayi had’e da karya wuya gefe ta taka a nutse zuwa gabanshi, hannuwanta ta sa saman shoulder d’insa a hankali ta shiga massaging, lumshe ido yayi dan sakon ya isa inda ake buqata sosai tasan lagwan sa, she knows the right thing to do. Cikin kwantar da murya take fad’in “Ni dai nasan yalla’bai d’ina mutum ne me kula da nasa, baya ta’ba ganin wanin sa cikin wani hali ya yi ko oho dashi” ta sunkuyo dai dai kunnen shi “Ko zan san wanda ya ta’bo min soft heart d’ina?” Forming line yayi da baki, ya d’ora hannunsa saman nata dake kai komo saman ‘kirjinsa , zare glasses yayi ya d’ora saman littafin “Mata yaron ku d’innan yana caza min kai , na rasa ya zanyi, kina gani ke kika sa baki lallai na barshi ya taho amma daga zuwanshi kiga abinda yayi, ni nasan dama dalilin shed’aniyar yarinyar nan yasa shi cewa lallai ze zo har da yimin qarya! Wai ze zo ne inspecting company!” Gyara zaman ta tayi saman cinyar sa tare da kwantar da kanta saman kafad’ar sa hucin numfashinta na dukan dokin wuyansa ta furta “afuwa...afuwa yalla’bai na sani Ann be kyauta ba amma be kamata a halin da yake ciki ka tafi ba tare da nuna damuwar ka ba, a halin da ake ciki yanzu addu’ar mu yafi buqata” Ta d’ago kai, “um kaje ka duba shi idan jikin nasa da sauki ka nusar shi har fad’a ban hana kayi mishi ba, amma banda fushi kaji yalla’bai d’ina” Ido ya lumshe tare da bata peck saman goshi, har bakin qofa ta raka shi sannan ta zauna saman kujerar daya tashi ta shiga dialling number Bro B. ‘Dakin samarin ya nufa inda ya tarar dashi ya fito daga band’aki d’aure da towel a ‘kugu, tsayawa yayi fuskar nan a had’e, da sauri ya iso gabanshi ya tsugunna a qasa “Uncle...” hannu ya d’aga masa cikin Kausasa lafazi yace “Anwar komai kake yi kasani ubangiji yana kallon ka, kuma kowa yayi daidai lahirar sa ya gyara.” har ya juya ze fita ya tsaya “kar ka manta wata d’aya kawai na baka mu juya Nigeria tare” Ido ya wangale “uncle nige..ria?” “Yes...zan je da kaina wannan lokacin dan da alama abin ya fara fin qarfin ku” da haka ya fita daga d’akin inda ya bar Anwar da tunani. *** Washegari misalin qarfe sha biyu da rabi aka basu sallama direct gidan gwaggo suka nufa abinka da yaro tuni ta manta da abin da ya faru dan had’uwarsu da munu yasa ta shiga sabgar ta, da dare misalin takwas mu’allim bello ya kawo mata ziyara har da rakiyar sholey da yaje takanas har gida ya d’auko ta duk dan yasa Sam farinciki aikuwa ji tayi tamkar tafi kowa sa’a a duniya yau gata ga munu da gwaggo ga kuma sholey se wuraren tara mu’allim da sholey suka tafi bayan yayo musu shopping da dama. Bayan wata d’aya Hasheem ke zaune gaban firstlady Yana prescribing magunguna for Rayya bayan ya gama ya nemi izinin tafiya, har ya tashi tsaye ta fad’o falon kamar wacce aka jefo se haki take “W..ai..t doctor” Waiwayo wa yayi ya sauke idonshi saman nata, baki ta turo gaba“kai meyesa ne kullum kullum kake tafiya da wuri” bambarakwai yaji maganar, kallon firstlady yayi ya kuma maida idonsa kanta Taci gaba “ni ni Allah ka tsaya muyi hira tukunna ” ta shiga sharar qwalla, a fusace firstlady ta daka mata tsawa “ke! Ray...” Hannu ya d’aga mata ta gefe still idanunsa kan Rayya yace “I’m sorry ma, kina son yauma muyi hirar aboki na ba”ya nuna mata kujera bismillah, diddira qafa ta hau yi, “ni Allah ka dena min hirar wani da ban sani ba, I only knows you and you alone I want to spend the rest of my life with” saurin kallon ta yayi cikin fad’uwar gaba Sum sum sum ya nemi guri ya zauna without saying a word, hakan yasa firstlady hajiya maryam da muqarrabanta barin falon, Murmushi me kama da yaqe ya saki had’e dayin qasa qasa da idonsa yace “I’m at your service ma” Kunya taji ta kare idanunta daga mugun kallon da yake harba mata, yayin da reaction d’inta ke saka hasheem cikin wata duniyar ta daban. *Bayan wata d’aya* Malam aminu kano airport ya samu baquncin uncle usman da Anwar, inda Bro B ya taryo su a motar sa zuwa gidansu dake kwairanga road, shigar su befi da awa d’aya ba uncle ya yi shirin fita inda ya nemi rakiyar Bro B. 2:00pm Ringing d’in da wayar shi ce ta farkar dashi, hannu ya miqa yayi ya d’auki wayar ya qaga a kunne, cikin sleepy voice yace “inaji” “Tashi kaje sweet heaven high ka d’auko Samira, zan tura maka address d’in da zaka kaita” Kafin yace wani abu d’if wayar ta mutu, bud’e ido yayi ya kuma duba wayar ganin tabbas uncle d’inne yasa shi tashi ya shiga wanka. Farar top yasa mara hannu had’e da black three quarter ya feshe jikinsa da turaruka masu tsada sumar kansa da take kwance ya gyara ya d’auka car keys ya fice. Wayar bello ya kira yana d’agawa yace “Bro B kasa a fad’a ma yarinyar nan kalar mota Ina school premises kar ta wuce 2mins u know I hate waiting” ya katse wayar tare da gyara tsayuwar motar ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (14) *NOT EDITED * Tunda security man ya sanar da ita saqon mu’allim bello gabanta ke fad’uwa, tare suka taho da sholey har ta isa jikin motar sannan su kayi sallama, knocking window tayi jin qofar a rufe, shiru ba’a bud’e ba kuma qwanqwasawa tayi jin ba’a bud’e d’in ba yasa ta kara fuskar ta jikin window wai ko zata gano ciki, wur wur take da ido, jiki na rawa jin wani mugun fitsari daya cika mata mara gashi bata son shiga toilet d’in makaranta idonta ya cika da kwalla jin yana neman zubowa , kallon motar ta kuma yi gata dai se huci take amma ba alamun mutum cikin ta, juya wa tayi da niyyar nufar waje dan neman abun hawa, taku biyu zuwa uku taji ance “ke!” Banza tayi dan a tunaninta mazan makarantar ne jin ana ta cewa ke! har sau ba adadi had’e dayin horn yasa ta waiwayo a fusace tana faman matse ‘kafafu Wani irin bugu qirjinta yayi bazata ta’ba mance wannan fuskar ba ko da cikin mafarki wani nannauyan yawu ta had’iye a qafule ta watsa masa daradaran idanunta dake ta tsiyayar hawaye, komawa yayi cikin motar ya zauna yana qare mata kallo ta side mirrow badan tanaso ba se dan taimakon kanta kar tayi fitsarin wando yasa tayi saurin zuwa ta shiga tun kan ta qarasa rufe qofar ya figi motar su gateman da tsalle aka sha. Ido ta runtse tun qarfi hannunta bisa handle d’in qofa ta ruqunqume duk tabi ta firgita jin yacce yake manna gudu bisa shimfid’ed’iyar kwaltar sokoto road, qafar nan tata gam take dan qiris take jira fitsarin ya zubo, wani irin giya yaja aiko sam ta qwala qara tun qarfi tare da fad’owa jikinsa ta ruqunqume shi, ita duk a tunanin ta accident su kayi, a hankali ta shiga bud’e ido jin shiru ba ko motsi Idanunta suka fad’a cikin nashi hancinta dake bisa nashi ta janye da sauri kanta a qasa, “d’agani” Sassanyar muryarsa ta doki kunnenta, saurin kallon kanta tayi cikin zare idanu ta koma bisa seat d’inta, “Ke!!!! Fitsari kikayi min!!!!!” Wani irin bugu qirjinta yayi tamkar ze ‘ballo waje ta shiga kuka wiwi tana sheshsheqa tabbas fitsari tayi kuma a jikin sa innalillahi wa innalillahir raji’un, yau kam tasan wannan mutumin se ya kusan kasheta, Ji tayi ya ja motar ya kuma tsaya lokaci qanqani ta rikice ganin da tayi sun shigo wani gida murya na rawa tace “dan girman Allah kayi haquri kar kayi min komai wullahi zanyi duk abinda kace” kula da rud’ewar da tayi yasa shi sassauta abinda yayi niyyar yi mata, bud’e qofa yayi ya fita tare da fad’in “biyo ni” Ciki ba qwari ta bi shi a baya har zuwa wani tafkeken falo me d’auke da kujeru seti biyu, wata qofa ya nuna May da yatsa “shiga ki gyara jikin ki, akwai aerial cikin toilet yanzu zan kawo miki kayannan ki wanke min tass!” “Uhum” Yaja tsaki “dirty human being” ~~~~ 2 hours later Parking Bello yayi suka fito se fara’a suke shida uncle, “kaga abinda nake fad’a maka ko?” “Sosai uncle, nifa abin nan ya d’auren kai kana ganin zata yarda da maganar mu kuwa duba da ta manta abinda ya faru shekara ashirin baya?” Dariya uncle yayi “yaro yaro ne kai dai zuba ido ka gani,” “Su kuma su alhaji kabiru fa?...” Murmushi yayi “they are trapped” “Ban fahimce ka ba...” Shigowarsu falon ke da wuya wayar bello tayi qara “gwaggon samira ce” ya furta idonsa bisa uncle, “‘Daga muji” Answer wa yayi, suka gaisa tace “dama nace yau ko su sam nayin wani abu ne a school shiru bata dawo ba” Saurin kallon juna sukayi da uncle, cikin dabur dabur yace “ahh..ahh” uncle ya d’aga masa kai yace “eh nace ta jira na gama aiki ne se nayi dropping d’inta” “Ayya to shikenan, na yarda da kai bazaka ta’ba barin wani abu ya kusance ta ba” Girgiza kai yayi hannu a ka yace “insha’Allah nama gama yanzu zan kawo ta” “Allah ya kawo ku lafiya” ta ajiye, a fusace ya juya zuwa window yaga ali driver na wankin mota, d’akin Anwar suka nufa se de daidai shiga d’akin suka ji an yi atishawa cak suka tsaya, kuma yi akayi har sau uku, da sauri suka fad’a d’akin da suke kyautata zaton anan ne. Me zasu gani? Sam!!! Suka furta a tare, “mu...muallimmm sanyiiii” ta fashe da wani irin kuka me cin rai, juyawa yayi ya d’auko bargo cikin wardrobe ya lullu’beta fad’i yake “Shii shiii, babu abinda ze same ki kinji, trust me Sam, open your eyes please, ya kalli uncle, uncle kar ka bari ta rufe ido pls pls pls Sam say something,” tallafo ta yayi jikinsa yaji taja wani dogon numfashi har sau uku jikinta ya saki ‘Dora ta saman gado, wayar hasheem ya kira yana d’agawa ya fad’a masa tare da ce masa maza yazo yanzu. ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (15) *NOT EDITED* _afuwa na rashin jina on time_ 🙏 A fusace fad’a d’akin inda ya tarar da Anwar kwance yana bacci kashir’ban, hannu yasa ya yaye bargon ya cillar gefe, “Wullahi na rantse duk abinda ya samu amanata ka sani se na d’aure ka, d’aurewar da se ka gwammace mutuwar ka da rayuwar ka” ya qarashe maganar cikin qunar rai, Zaune ya tashi yana jinjina maganganun uncle, me yake nufi da yarinya? Wace yarinya? Ido ya zare da sauri ya miqe tsaye ya nufi falo, cikin tashin hankali ya nufi inda take kwance, “Malam kar ka qaraso mana nan!!!” Kallon bello yayi cike da mamaki jin yacce ya daka masa tsawa, “ni kake ma ha..ka!?” Gaza kallonshi bello yayi se ma juya baya da yayi, ya had’a kai da bango. Uncle ya kalla shima ya d’auke kai, sallamar hasheem ce ta sa su duka waiwayo wa, Goshin ya ya ta’ba da wuyanta, ya kara yatsansa a hancinta, “I think firgici be kawai de ko sanyi daya ta’bata,” warware bargon jikinta yayi, “we need to change this clothes, a kunna mata heater” “Ok ammm please ko zaki iya taimaka mana ki canza mata kaya” Rayya ta fito da ido waje, “waye ni?” Ta kalli hasheem cikin yatsinar fuska, d’aga mata kai yayi, turo baki tayi “ inane d’akin?” Nuna mata yayi bayan ya d’auko wasu riga da wando d’an daidai gwiwa sababbi ya bata. “Amma wullahi ka bani mamaki, qaramar yarinya me ta sani da zakayi mata wannan hukuncin dan kawai tayi maka fitsari?” Uncle yace “ai hasheem na rasa a ina yaron nan ya d’auko wannan mugun halin dan Sam ba haka nasan halin d’ana ba” Anwar dai bece komai ba se ido daya zubawa d’an uwansa jin yacce ya gasa masa magana d’azu abinda be ta’ba yi ba” Bello da hankalinsa kacokan ke d’akin da Sam ke ciki be san abinda suke tattaunawa ba, all he knows baze ta’ba yafe wa Anwar ba idan wani abu ya samu Sam” Wucewar mintuna talatin, Rayya ta fito a guje da qarfi take shaida musu ta farka, a tare suka nufi d’akin su bello tsabar sauri kamar ze kifa, Anwar jiki a sanyaye ya bisu a baya yana zulumin abinda ze gani. “Alhamdulillah jiki yayi kyau, sannu Samira” kallon rashin sani ta bishi dashi kan a hankali ta maida idonta saman na bello “mu’allim “ ta furta cikin sanyin sauti, tsugunnawa yayi a gabanta “Yes Sam ya kike jin jikin ki yanzu?” Bata bashi amsa ba hawaye suka gangaro “inason zuwa gurin gwaggo da munu” ‘Daga kai yayi, “yanzu zan kaiki kinji wipe away that tears, uhm!” Waiwaya wa yayi gun hasheem “Doctor yaya?” Matsowa yayi ya ta’ba kanta “well zafin jikin ya ragu zaka iya kaita gida idan yaso zan d’ora ta a kan magunguna , idan jikin yaqi kwana biyu se a kawo ta ko allura na bata” Kafad’a ta maqale “uhm uhm banaso mu’allim “ dariya sukayi duka, Rayya da duk ta qulu a tunaninta kan meyasa wannan yarinyar zata rinqa yiwa hasheem shagwa’ba se ciccin magani take Anwar da tun tuni yake jingine jikin qofa kuwa idonsa stick to Sam wacce ke sanye da oversized shirt and threequarter, ajiyar zuciya ya sauke lokacin daya ji bayanin hasheem yayi wa Allah godiya da babu abinda ya same ya, dan har ga Allah ba ze so ace ta sanadiyyar sa wani abu ya sameta ba, juyawa yayi jiki a sanyaye daga can yaji muryarta na furta “sorry..” kamar ya tafi se dai ya tsaya had’e da lumshe ido kan ya bud’e yacigaba da tafiya dai dai fita waje ya jiyo tana cewa “zan baka chocolates d’in da goggo ta siyo min kaji” One sided murmushi ya tsinci kansa da yi, kan ya waiwayo a hankali ya bata thank you look, ya sakai ya tafi, qasa mu’allim bello yayi da kanshi yana sakin murmushi wannan yarinyar wani irin zuciya take da, Samira halayyar ki na burge ni, ya ayyana hakan can qasan zuciyar sa. *** Munu dake zaune a qofar kitchen tana gyaran kayan miya ta kalli gwaggo tayi murmushi “gwaggo baki yarda da mu’allim bane?” “Ba haka bane munubiya, yarinyar nan amana ce a gareni taya kike expecting hankalina ze kwanta bayan bata tare dani” “Gwaggo nayi imani tunda tana tare da mu’allim she is safe, so ki kwantar da hankalin ki ‘yar ki zata dawo lafiya” Sauke tagumi tayi “Allah ya bi bakin ki” “Amee..” “Assalamu alaikum,” ta fad’o gidan tamkar wacce aka cillo “‘Yar halak” Gwaggo ta washe baki, “Sam yaki taho nan” ta janyo ta jikinta, rungume juna sukayi su gwaggo har da ‘kwalla, Munu ta tashi tana d’auraye hannu a gindin famfo tana fad’in “tabb aikuwa nima Allah dani za’ayi family hug d’innan” ta tafi a guje ta fad’a kansu “‘Yammata yi a hankali kar ki ‘balla mana gwaggon mu” Juyawa tayi ganin me maganar ta kare fuskarta da hannu “laah..haba mu’allim ni d’in nawa nake” “Ga ki nan duk qasusuwa “ Sam ta qarashe da yin gwalo Kwakkwa’be fuska munu tayi tana kallon gwaggo tace “wai gwaggo bana girmi yarinyar nan da kwana shida ba, Allah kice ta dena tsokana ta, ‘bakutu kawai” Ai Sam na jin haka se ta kwakka’be fuska ta saki kukan shagwa’ba, har da tashi a guje ta fad’a d’aki, dariya ya bisu dashi kan ya dawo da kallonsa gurin gwaggo dake sharar qwalla Cikin sadda kai tace “ina tausayawa rayuwar samira ba uwa ba uba, Allah ka bani ikon kyautata rayuwar ta” Numfashi ya sauke “Amen gwaggo, ni zan koma” “To madallah , Mun gode qwarai, yawwa bello niko nace ko za a iya samar wa munubiya gurbin karatu a makarantar ku?” “Eh me ze Hana sede yanzu kinga saura befi kwanaki ba su fara zana jarabawar shiga ajin gaba, amma wani aji take” “Aji d’aya suke da Sam” “To ba matsala se de nake ga idan babu damuwa ko a bari ta shiga bayan jarabawar kamar zefi” “Hakan yayi dama dan walwalar Sam nakeson su kasance tare” “Tom Insha’Allah zan fara processing “ “Nagode Allah yayi albarka” Sallama yayi mata, ta tashi “bari na d’ora girkin nan dan nasan tunda kuka had’u se ta Allah, fitowar ku ba yanzu ba. *** A can quryar d’aki kuwa Sam ce ta zage take ta bawa munu labarin abinda ya faru “Mutumin nan is so scary Sam, meyasa baki fad’awa gwaggo ba?” Ta girgiza kai “um um munu nice da lefi, pls kar ki fad’a mata” “What about this medicine??” “Wani magani ku ke magana ?” Cewar gwaggo data shigo d’aukan abu Kallon juna sukayi kan Sam tace “dama gwaggo bani da lafiya shine school doctor ya bani magani” Jin yacce maganar kefita daqyar yasa tace “meke damun ki” ta sa hannu a wuyanta da goshinta “Is just a minor headache and cold” “Minor? You are calling rashin lafiya minor ke ni bani medicines na kira hasheem ya tabbatar min da ingancin su” ta d’auki ledar maganin ta fita. Murmushi sukayi , a hankali munu ta d’ora hannuwanta saman na Sam “mu’allim na kula mana dake” Lumshe ido tayi had’e da jinjina kai Ta qarashe da cewa “Nima Allah yasa yake bani kulawa haka” Murmusawa su kayi a tare, ta kuma cewa “ba fa wani abu nake nufi ba, don’t think nagative “ Yanuwane face tayi had’e da d’aga kafad’a ta bud’e hannuwa, ta tashi ta shiga toilet dan d’auro alwalar magriba ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (16) *NOT EDITED * Da ya dawo daga masallaci be zarce ko ina ba se bakin shagon dake daura da gidan su, hira wasu Samaria biyu keyi da wasu daga ma’aikatan shagon hirar dai ta ball ce shi dai daga ya murmusa se ya d’aga musu kai idan an tambayesa abu dan Sam shi ba ma’abocin kallon kwallon qafa bane, wayar sa dake aljihu ya zaro ya shiga yanar gizo ba komai yana duba nasarorin da kamfanin sa ke samu a can qasar ta UK. Kewar kimberly ta tsargo masa, tsam ya miqe tare da zagawa bayan shagon dan kiranta sosai yake son jin muryar ta, Ilai kuwa tana d’agawa ta fashe masa da kuka, se dai tun kan ya samu damar rarrashin ta wata mota ta d’au hankalinsa wacce tayi parking daidai qofar gidan su, duk da irin kalar hello da take sirfa mishi be samu damar kulata ba, ya kashe wayar tare da seta wayar shi ya d’auki hoton plate number d’in, Tsayuwar shi ya gyara , ya shiga dialling number bello ringing d’aya tayi ya d’aga “kana ina” “‘Daki doing what suits me best” “Ok duba cikin wayar na turo maka saqo ka turawa dss bashari ya duba min” “Yes broseee” Kashe wayar yayi, ya cigaba da karantar motar zuwa can yaga anja an tafi, numfasawa yayi a hankali kan ya ja qafa ya koma cikin gida dan ji yayi komai ya sare mishi, me ke shirin faruwa kuma? Tambayar datayi crossing mind d’insa kenan. * Misalin 7:45 am zaune suke bisa dining table suna breakfast shiru ya ratsa, gyaran muryar uncle ce taja hankulan su duka, inaso wani cikin ku yaje gidan su Sam ya shaidawa gwaggo Ina willing kai yaranta boarding school saboda wasu dalilai nawa and bana so taqi aminta so kuyi duk abinda kuka san zaku iya saboda ta aminta” ya miqe dai dai lokacin shima anwar ya miqe “Uncle ni zanje na qarasa processing visa d’inka” Kallonshi yayi “Luke gidan tare idan ka dawo kayi wannan d’in daga baya” ya wuce ya barsu dariyar data kamo bello ya guntse ta dan yasan hanya hanya Anwar keyi dan kar su had’u da gwaggo domino uncle ya fad’a masa cewa ya shaida wa gwaggo abinda yayi wa ‘yar ta. *** Tafe suke a hanyar su ta dawo wa daga aiken da gwaggo tayi musu , munu ta dage se bawa Sam labarin da wani littafin hausa da wata ‘yar ajinsu ta basu take daf zasu tsallaka kwaltar titin gidan kawu kabiru ta hango wani mutumi ya shiga gidan, nuna wa munu tayi, “zo muje mu ga wane munu, kar ayi wa su umma sata” Bin ta munu tayi suka tafi a hankali suka karkata suka shige gidan sad’af sad’af yacce baza a ji takunsu ba falon farko suka shiga ba kowa nan suka lelleqa ko ina ba alamun mutum d’akin amir suka fad’a jin kamar takun mutum, can suka jiyo wata murya na waya “It’s cleared ma!” Daga cikin wayar suka jiyo ance “I am very sure zasu dawo ko ba dad’e ko ba jima just don’t forget to keep an eye” “Yes ma! Amma ya batun samira fa?” Dariya aka kyakyace da ita “wannan ka barta har zuwa lokacin da zata mallaki hankalinta shine take me amfani, yanzu ita da hoto basu da maraba” Firgici me sunan firgici ya kama Sam da munu suka ruqunqume juna har basu sani ba suka bigi wani flower vase ya fad’i qasa ai a guje suka maqale jikin bango se dai jinginar su ke da wuya bango ya juya dasu se gasu cikin wani tamfatsetsen closet wanda yasa lokaci d’aya Sam ta kurma wani uban ihu me tada hankali Munu dake a firgice tayi saurin d’ora hannunta a bakin Sam “shii shii...k...iy..I shi..ru kar ..a ji mu Sam” Ta fashe da kuka qasa qasa, hannun da Sam ke pointing tabi da ido bata san lokacin da ta fad’a baya ba har ta bige da bango, “Shish..shine...” Yawu munu ta had’iye da qyar idanunta kafe kan fuskar zakin dake kallo su, numfashi ta shiga saukewa a hankali ta taka a hankula zuwa wurin fuskar ta yaye saurin ja baya tayi ganin hoton ya habiibii, Saurin kallon juna sukayi cike da mamaki Sam cikin raunanniyar murya tace “dama shi..ne “ munu ta matsa kusa da ita tare da jan hannunta suka nufi wata qofa a hankali suka murd’a key d’in jiki se gasu a waje,wajen ma dai dai layin gidan gwaggo fita sukayi da sauri ba kowa se tsirarun mutane juyawa sukayi suna kallon qofar data rufe bazaka ta’ba cewa akwai wata qofa a wurin ba a kid’ime suka shiga zabga sauri zasu shiga gida kenan su mu’allim bello suka iso. A tsakar gida suka tarar da gwaggo suka fad’a mata suna kuka, duk suka rikita ta, menene? Me ya faru? Me ya same ku? Amma shiru ba wanda ya kulata, sallamar su Anwar ce ta sa su sassautawa “Yawwa ai gara da kuka zo, kun gansu sun tisa ni gaba se tambayar su nake ba wanda ya kulani, dan Allah kuntayani tambayar su, oh ni haulatu” Mu’allim bello yace “Sam, munu what’s wrong? Meke damunku?” Nan ma shiru ba amsa carpet d’in dake ajiye a gefe ya shimfid’a yana me kallon Anwar. Anwar da duk suka qular dashi jin yanda ake faman tambayar su basu amsa ba ya ce “Idan baku had’iye kukan nan ba, ni da ku ne” cikin kakausar murya, ‘Dif kake ji wai malam yaci shirwa, ashe wargi ma wuri ya samo “ku samu wuri” sum sum sum suka zauna kusa da gwaggo yaci gaba before the count of 3 ku fad’i abinda ke damun ku. Tar tar tar suka zayyano abinda ya faru hawaye na biyo baya tun bare Sam, hankali tashe gwaggo ta rinqa salati tana sallallami fad’i take “shikenan zaman mu a garin nan ya qare oh ni Allah ka bani ikon cin jarabawar nan taka, yanzu ace habibii ne dama ke qoqarin lalata miki rayuwa, kai duniya ina zaki damu” ta fashe da wani marayan kuka ta rungumo su jikinta “Ba kuka zaki yi ba gwaggo” “Me kake so nayi, bani da kowa bani da komai d’an uwana ya gujeni wannan yaran kawai nake gani naji dad’i to suma ana neman fara farautar su ina zanso kaina ni haulatu” Qwallar data ciko idanunsa ya share “gwaggo ku tashi mu tafi” Bello yayi saurin kallonsa, “ina?” Gidan mu “zaman su a nan ya qare” Ta girgiza kai “um um d’an nan wahalar se tayi yawa, ka bari zuwa gobe se mu koma can garin mu, inda muka fi wayo” “Gwaggo dan darajar Allah ki tashi mu tafi in yaso Mayi deciding step to take next” Kallonshi tayi ido a kod’e “kuj’e d’aki ku d’auko mana hijabai” Qulle gidan su kayi, suka d’unguma zuwa kwairanga road. ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (17) Tun daga nesa ya hango motar rannan a qofar gida, daga can baya ya tsayar da motar had’e da sauke wani gauron numfashi , “ya dai?” Bello ya tambaye shi, “ku sauka ku bi ta gate d’in baya” bello ya maida idonsa inda yaga Anwar d’in na kallo, wata baqar mota ya gani a qofar gidan wani mutumi jingine jikinta bayansa a juye, jikinsa ne ya bashi cewa ba lafiya ba, “su waye wad’ancan?” Ya furta a hankali, “abinda nake son sani kenan, har yanzu ba wani feedback daga wurin bashari ne ?”, “a a nasan da ya kira” girgiza kai Anwar yayi ya kalli su Sam ta cikin mirror had’e da sauke ajiyar zuciya a hankali yace “shiga dasu, zan bi bayan motar can” d’aga kai bello yayi ya juya baya “gwaggo bismillah muje mun iso ” Hanci taja, ta kama hannuwansu suka bi bayansa, tsawon mintuna sha biyar sannan mutumin ya matsa ya shige gida, motar taja. Ta wata kwana ya bi ya cimma motar a hankali yake binsu har zuwa commissioner road cikin wani tafkeken gida aka shiga, waige waige yayi unguwar shiru ba’a ji komai se kukan tsuntsaye, daga can baya kad’an ya hango wani me trader zaune yana quqqulla leda, parking yayi ya sauka zuwa wurin mutumin, Sallama yayi had’e da fad’in “Washh Allah baya na, na gaji” buzun dattijo ya d’ago da kanshi da hausa shi da bata fita dakyau yace “sannu bawan Allah” “Yawwa baba, dan Allah taimaka min da ruwa mana tun safiyar yau bansa komai a ciki na ba” “Kash se de fa kayi sa’a duk masu zafi ne “ ya miqa masa sachet d’in pure water Dariya Anwar yayi “nagode, amma baba daman talaka na samun abu me sanyi ne, rabo na da ganin ko qanqara na manta” Kallon sama da qasa mutumin ya mishi, “kai kuwa daga ina kake haka dan shigar ka da kamanninka sun nuna kai d’in babban mutum ne” Baki ya bud’e har da riqe ha’ba “wa d’in ni, tab lallai kace oga yayi aiki” “Kamar yaya ban fahimce ka ba” Gyara zama yayi, “ni sunana lawali nazo ne daga qaramar hukumar ajingi” “To to ko kai ne sabon direban hajiya” Jimm yayi zuwa can yace”..eh nine” Kallon da tsohon ya masa yasa shi shan ruwan jikinsa, “...amma..” “Uhm...riqe maganar ka inde gidannan ne wata biyu na baka zaka gudu kaima da qafarka” Ido ya waro waje “ko zan san meyasa kace haka?” “..kaje ka gani..” ya miqe tsaye bari na kewaya Binsa yayi da ido yana juya maganar, tashi yayi da zummar barin wurin ya hango wani ya leqo daga cikin gidan da motar nan ta shiga , bayan wata bishiyar darbejiya ya la’be, bisa mamaki sa se ganin wannan tsohon yayi ya fito shima yana waige waige har yana d’aga wa mutumin hannu Cikin d’aga murya mutumin yace “ina yake?” Dattijon dake leqe leqen neman Anwar yace “yanzu na barshi anan fa, wataqila gudu yayi” Cikin d’aga murya mutumin yace “dalla ware, ni dama nasan duk qarya ka shirya son shigowa kake, To hajiya tace ka cire wannan tsimman ka shigo ciki” Cikin d’aga murya dattijon yace “Kai dalla malam kasan yacce zaka rinqa min magana, ni ba sa’an ka bane” ya ja tsaki, hannu yasa ya cisge farin gashin bakin sa da na jikin gashin girar sa, “Ahhh yau tun a nan zaka tu’be, lallai kana had’uwar ka da hajiya ba zata yi kyau ba” saurayin da ada yake dattijo ya ja tsaki ya miqe tsaye tangar tamkar ba tsohon nan ba dake dunqufe se da ya kuma wawwaigawa gefe da gefe sannan yayi wuf ya fad’a gidan suka rufe. “Innalillahi wa inna’ilaihir raji’un” ya furta out of his breath, su wane wad’annan mutanen?, kuma wacece wannan hajiyar? Sad’ad’awa yayi ya fad’a mota ya tafi jiki a mace *** “Gwaggo ba wai uncle ze raba ki da su bane, kina ganin dai abinda ke faruwa boarding school d’in ita tafi dacewa da su” “Amma..” “Kar ki damu hajiya yaran nan tamkar yaran cikina suke, saboda gudun haka yasa na yanke hukuncin tura su can UK inda Iyalina suke tare da Anwar dan qarasa karatun su, Allah barshi ke kuma se ki zauna a nan tare da bello da kuma ni har Allah yasa mu warware wannan dabaibayin se mu koma can baki d’aya” Baki bud’e tace “barrister kaine?...” Ya murmusa “Ni ne gwaggo, na dawo da qarfina dan nemawa Samira haqqinta da ake qoqarin qwace mata” Gwaggo ta fashe da kuka “barrister ina cikin wani hali, a yanzu yaran nan sune kad’ai nake gani naji sanyi, idan sukayi nisa da ni ya...” “Gwaggo nima d’anki ne, Insha’Allah bazaki ta’ba maraicin rashin su ba” cewar bello Murmushi uncle yayi yace “nayi miki alqawari duk hutu zasu rinqa zuwar miki” Numfashi ta sauke “shikenan na amince nasan ba zaka ta’ba cutar damu ba, you are my last hope” Jinjina kai yayi, ta share hawayen fuskarta “Amma meye had’inka da su bello” Kafad’ar bello ya rungumo “ya’yan wa nane marigayi” “Allah sarki ‘yan albarka, Allah ya jiqan mahaifan ku” “Amen gwaggo” “kukan ya isa haka” suka jiyo muryar shi daga bakin qofa Kallon shi sukayi duka, gyara tsayuwarsa yayi tare da takowa jiki a mace ya zube saman kujera idonsa saman nasu Sam, “ku tashi ku bamu wuri, ya nuna musu qofar d’aki Bayan sun shige ya gyara zama had’e da tallafo fukarsa da hannayenshi, “Anwar lafiya” cewar uncle, girgiza kai yayi tare da miqewa ya rurrufe qofa da windows, suna binshi da ido kafin ya zauna ya zayyane musu duk abinda yafaru tun ganinsa na farko da motar, Cikin qunar rai uncle yace “yanzu kana nufin cikin yaran gidannan akwai wanda ke bada information a kanmu” “Yeah, akwai yaron su cikin mu” Bello ya kalli uncle “I think gara bro A ya tafi da yaran nan abuja gobe idan yaso suyi passport da visa kawai su wuce daga can” Jinjina kai uncle yayi idonshi kan Anwar “hakane ka shirya gobe ku tafe da safe tun kan garin Allah ya gama washewa” “Ni kuma..amma...” Barrister yace “uhm uhm ka koma bakin aikin ka se ka rinqa kular mana dasu, nayi magana da mss chloe kan makarantar da ka sauka ka je ka same ta” ya kalli bello “Kai kuma ka shirya dan muma da safe zamu tafi garin damagaran dake jamhuriyar nijar “ “Barrister ni kuma fa?” “Kar ki damu , bazan bar gidan nan ba face na bar miki yan sanda wanda zasu kula da lafiyarki ” Ta girgiza kai, “shikenan kai ni gurin yarana na kintsa su tunda fitar wuri zasu yi,” Bello ya taka mata, Anwar da uncle kua , kusan raba dare sukayi suna tattaunawa. 3:00am ‘Kishin ruwa ya farkar da Anwar, kasancewar dare ya tsala ba abinda kake ji se qarar haushin karnuka, qafafunsa ya fara s’aukarwa qasa daga bisani ya miqe tsaye seda ya duba fridge d’in d’akinsa babu ya nufi frdge d’in kitchen, “Gwaggo yinwa muke ji” muryar su Sam ta bigi kunnen sa, “To ya kuke so nayi muku, dan Allah ku daure zuwa gobe da safe se na bada a samo muku qosai da asuba” “Ni...ni dai Allah kinsan fa ba za’a samu da asuba ba, wayyo zan mutu” “Ke samira, kul kul na kuma jin kin ambaci mutuwa maza ku tashi ku d’auro alwala kuyi ta sallah yinwar zata ragu “ “What” ya furta a hankali bud’e warmers d’in dake saman dining yayi, ganin akwai abincin da cook ta dafa, tun na dare yasa shi yin hamdala saman trey ya jera har da plates da spoons ya nufi d’akin knocking yayi, daga ciki kallon kallo sukayi, gwaggo addu’a d’auke da bakin ta ta nufi qofar “Au Anwar kana tsaye dama, abin hannunsa ta kalla, “har da hidima haka da dare ai da ka barshi ma” a zuciyarta cewa take kar de yaji maganar da muke Murmushi yayi yana jinjina Kawaci irin na matar yace “aa bakomai” Hannu tasa zata kar‘ba yace “aa gwaggo barshi, kai maza kuzo ku kar‘ba kun tsare mutane da ido, munu ce ta fara zuwa ta kar‘ba, ita kuwa Sam dad’a sunkuyar dakai tayi tana dad’ matse cinyoyinta a qirji duk kunya ta kamata saboda rashin mayafi Kamar daga sama taji yace “Ke mara jin magana bazaki taso ba” rau rau tayi da ido idonta akan hijabinta dake jikin munu ta taso, a hankali ta isa gabanshi ido a runtse ta miqa hannu ta amsa plates d’in ta juya nan ma tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki, qofar yaja ya rufe ya jingina jikin bango ido lumshe Daqyar ya ‘bam’bare daga jikin bangon ya koma d’aki, fad’awa yayi saman gado had’e da ruqunqume pillow, ido ya rufe ba komai yake gani ba illa tafiyar Sam wacce duk takun da tayi yammatan qirjin ta ke motsawa kasancewar rigar baccin jikinta ce kawai tayi musu sutura, tsaki ya ja had’e da sakin guntuwar dariya yace “lemun tsami kenan” tashi yayi ya fad’a band’aki ya d’auro alwala ya shiga yin nafila ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (18) Abinci cike da baki ta watsa wa munu hararar qasan ido, tana fad’in “wlh tunda kika sa namiji ya ganni a haka se na rama,” a hankali munu tace, “To ba kece da gwaggo tace mu tashi muyi nafila ba, baki tashi ba, me kike dashi da zaki ‘boye masa..” ta qarashe da dariya Takaici ya cika Sam tayi qwafa, “To wayace ki d’aukar min hijabi ko bani da komai ai mu’allim bello yace duk namijin da ba baban ka ko qaninka ba ba muharraminka bane ka kasance me killace kanka...” qwarewar da tayi ne ya hanata qarasa maganar gwaggo data kishingid’a ta tashi a firgice tana shafa mata baya, munu kuma ta bud’e fridge ta d’auko mata ruwa, daqyar ta dawo daidai, abincin da bata qarasa ci ba kenan bacci yayi awon gaba da ita. Misalin 5:30, zaune suke suna hira Anwar yayi sallama, cikin qasaitaccen takun sa ya qarasa cikin falon daidai kujerar da gwaggo take ya tsugunna yana gaida ta, gaishe shi suma su kayi, ya amsa ba tare da ya kalla inda suke ba yace “Gwaggo akwai saqo na ajiye miki a d’aki,” jinjina kai tayi cike da tunanin ko menene? tace “To madallah angode Anwar” “Ku tashi muje ko” ya furta a hankali, gwaggo suka nufa ko wacce cikinsu ido ya kawo ruwa, amma ba damar kuka ganin yacce Anwar ke tsare gida, “Allah yayi muku albarka, kuji tsoron Allah, ku kuma riqe addinin ku, kar kuga bama tare bazan kwa’be ku ba, Allah na kallon ku kuma ku ze hukunta ku gwargwadon lefin da kukayi masa” ta kalli Anwar “a yanzu ragamar kula da ku su na hannunka, gasu nan amana” ta qarashe cikin rawar murya kallonsu tayi ganin yacce suke qiqqifta ido yasa ta shige d’aki da sauri, “Allah ya sauke ku lafiya” ta fad’a daga ciki. Da hannu ya nuna musu hanya, jiki a sanyaye suka nufi waje ko wacce na qunshe kukanta kar Anwar yayi musu fad’a, cikin wata golden d’in jibgegiyar motar Lexus Jeep suka shiga inda ya umarci d’aya cikinsu ta shiga gaba, munu tayi saurin shigewa baya ta bar Sam tsaye wacce kukan ta ya koma da biyu ga na rabuwa da gwaggo ga kuma na zama kusa da dodon ta, dan ita har firgita take idan taji koda motsin sa ne , inaga yau gashi gata?, “Ke ba zaki shigo bane,” Girgiza kai tayi ta bud’e ‘kofar a hankali zata rufe kenan se ga bello kamar wanda aka cillo yana haki alamun yasha gudu yace “hold on, taya zaku tafi ba sallama, ya miqa musu wasu manyan ledoji ga kaya nan idan kuka je abuja Bro A ze kai ku a d’inka muku kafin ku tafi, munu dake baya ta amsa su kayi Godiya, da baya ya koma yana Sarawa Anwar “Drive safely bro” Murmushi ya masa kan ya harba motar. *** Kusan minti biyar yana duba takaddar ba dan be fahimci abinda ke rubuce ba, se dan son tabbatar da abinda ke jiki shin ya take me?, wayar Anwar ya kuma trying for the fifth time in taqi shiga, bello ya fad’o masa a rai dialling wayarshi yayi ringing biyu ya d’aga “Babban likita na Rayya bada kanka a sare..” One sided murmushi yayi “Abokina Ina Yayanka?” Bello yace “yana daf da shiga Abuja” Duka ya kaiwa bango, yana to and Fro yace “ ya Allahu I really need to see him why did he left ba tare da sallama ba, when is he coming back?” “Well May be in a year or two” Da qarfi hasheem yace “what! Ze wuce UK ne, uncle ya sani?” “Yeah shi yace ya tafi da su Sam” “Sam kuma?! Ahhm ahh...is all right ina zuwa” yatsunsa biyu yasa saman goshi yana murzawa, kan ya zube hannuwansa saman table yana girgiza kai ya kalla agogo 11:45am key ya d’auka da wayoyinsa ya fita bayan ya barwa sakatarensa sallahun kowa yazo ace ya fita a dawo da yamma. *** Driving yake amma hankalinsa baki d’aya na kan wayar sa dake haske ba damar dauka. Juyawa tayi cikin lafiyayyen baccin da ya d’auketa tun barinsu kano, Mafarki take gata kwance saman gadon ta gefen ta daddy ne kwance yana kallonta a hankali tashiga bud’e ido “Morning daddy” ta furta murmushi d’auke a fuskarta, Gyara zaman medicated glasses din idonshi yayi Yace “morning mami” yayi pecking goshinta, hannu tasa ta maida cincinrindon gashin kanta baya, ta matsa kusa da shi tare da d’ora kanta saman kafad’arsa ta rungume hannunsa a jikinta, “Have you saw him?” ‘Daga ido tayi tana kallon fuskar daddyn tace “who?..” Murmushi yayi tare da Jan dongon hancinta yace “the one Mami” Jimm tayi tana kallon daddy tace “ he didn’t appear yet, ta turo baki gaba, daddy waye ne haka da ze shigo rayuwana? Bayan kowa guduna yake har dasu Abba, umma,Amir and that monster habibii “ Ta fashe da kuka Hannu yasa yana share mata hawaye still yana sakar mata murmushi yace “he will come, he will soon come” Cikin sheshsheqar kuka tace “daddy do you trust him?” Ya d’aga kai “Yes, he’ll bring no harm to you, he will be your guardian” ya tashi tsaye yana kallonta yana tafiya da baya da baya se da yaje daf qofa yace “se wata rana mami, Ina sonki “ Qwala masa kira tayi gashi ta Gaza tashi tamkar wacce aka danne. ~ Kuma rirriqe ta yayi da hannu yana qoqarin daidaita motar da d’ayan hannun, bugar bishiyar mangoron da yayi ne ya bashi sa’ar fusge hannunsa daga kan steering wheel ya fincikota had’e da zare mata idanu Cikin muryar bacci tace “i...a..m sorry.” Be kulata ba haka be sake ta daga ruqon ba, se bin jikinta da yake da ido har ta fara ruqunqume kanta taga yasa hannu ya had’a ta da jikinsa da qarfi har tana iya jiyo bugun zuciyar sa “U r safe”ya furta cikin sanyin murya, Ihun da munu ta saki ne yasa su d’agowa da sauri, ta zaro idanu had’e da rufe bakinta da hannu, maida idonsu sukayi ganin su saman wani tsibiri qwaqqwaran motsi idan su kayi zai iya ja motar ta hantsula Numfashi Sam taja tun qarfi lokaci d’aya ta fad’a saman qirjinshi a sume. ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (19) (For the 2nd time dirty human being kwance jikin Anwar😆) Ware ido yay waje yana kallonsu duka duk ya rud’e wannan shine ba’a motsi ranar mutuwa shin meye mafita? Hannu ya zira ta baya ya bud’e qofa, yace “ Ke d’auki kayan nan ki sauka a nutse” Munu kamar tsutsa ta shiga cilla ledar kayan su waje taja jiki ta sauka, bud’e qofar side din da suke ke da wuya motar ta shiga gilu gilu wanda yasa munu fashewa da kuka. Rintse ido yay yaja salati, a hankali ya matsa gefe ya fad’a waje wanda yayi daidai hantsulawar mota cikin tafkeken Ramin da ko qasansa ba’a gano wa. Numfashi ya sauke had’e da furta Alhamdulillah, qoqarin miqewa yake ya Gaza jin nauyi a jikinsa tun kan ya farga yaji muryar munu a kanshi Bro A, Sam ku tashi dan Allah, ku tashi kar suzo su same mu ta shiga jijjigasu tun qarfi Daga kwancen da yake ya d’aga kai daga can ya hango qatti kusan su biyar sun nufo su da sandina da wuqake ai be san lokacin daya ture sam daga kansa ba ya sa’ba ta a kafad’a tare da Jan hannun Munu suka yanka daji. Daga bayan tafkekiyar bishiyar da suka la’be suna iya jiyo hayaniyar qattin “Oga there are no where to be found may be sun fad’a tare da motor d’inne” Daga can mutumin yace “ John are you sure?” “Very, saboda mun duba duka wurin babu alamun su se kayan su” “Toh ku kwashe kayan kuje dasu banaso ku alamunsu a gani, duk nacin su kafin a neme su sun tafi barzahu” Dariya me firgitarwa mutumin yayi, yace “ok oga mungama aiki saura muji alert “ “Consider it done John kamanta ni ne?” Kashe wayar mutumin yayi, yace “we r done here let’s go “ Komawa Anwar yay ya jingina da bishiyar a gefe guda ya sauke idonsa kan Sam dake sume har yanzu a gefen ta munu keta zabga kuka, Gurin da suke ya shiga qarewa kallo daji ne sosai babu alamun ko bukka bare yasa ran ganin mutum, wayarsa ya d’auko da niyyar kiran waya ba network, dena jin sautin kukan munu da yayi ya tabbatar masa da tayi bacci Dad’a ‘karewa gurin kallo yayi babu alamar wani mahaluqi hakan yasa yaji baze yiwa su zauna a gurin nan ba, hannu yasa ya bubbuga qafar ta Munu ta bud’e ido cikin muryarsa da take a hankali yace tashi mu tafi, kai ta jijjiga, nan ya kuma sa’bar Sam suka shige dajin da Allah kad’ai yasan inda suke nufa. ***** Alwala ta d’aro tayi sallah tare da yiwa yaran nata addu’ar Allah ya sauke su lafiya sannan ta nemi makwanci daga kan bedside drawer ta hango farar envelop, se a lokacin ta tuna da saqon Anwar Hannu tasa ta bud’e damin kud’ad’e suka zubo had’e da farar takadda me d’auke da rubutu, “there are safe with me gwaggo 😊” Hawaye suka ciko mata ido a fili ta furta “Allah yayi maka albarka ya kare ku daga dukkan sharri” tattara kud’in tayi ta sa a qasan pillow ta kwanta bacci me nauyi ya d’auketa cike da mafarkin yaranta. A gefe guda kuma bello tun Bayan tafiyarsu ya Gaza samun nutsuwa gashi yana ta trying wayar Bro A bata shiga ga kuma wayar hasheem data sa shi a tunanin ko lafiya dan ba yacce ya Saba jin sa kenan ba, jallabiya ya zira saman boxers da vest d’in jikinsa ya d’auka key ya fita Fitowarsa ke da wuya ya hango mutum jingine jikin motar jiya, komawa yayi da baya ya la’be yana iya jiyo abinda suke cewa kasancewar yana kusa da gate ne, tabbas ya d’auki murya, jikinsa banda rawa ba abinda yake zufa ta shiga karyo masa ko ta Ina , jin shiru ya ratsa ya sashi leqowa qiris ya rage suyi gware da sauri ya d’ago kai “Uncle?” Cike da mamaki barrister yace “bello? Me kake yi anan” Baki ya bud’e ba tare da yace komai ba ya shiga wasi wasi a ransa yana addu’a Allah yasa mafarki yake, Barrister yacigaba da cewa “dama naji qarar mota ne shiyasa na leqo” ya qarashe maganar idonsa akan key d’in hannun bello, Sosa kai yayi, “ina za kaje haka kake sauri?” Ya kuma watsa masa tambaya “Uncle inason zuwa wurin hasheem ne” “Lafiya de ko?” “Inajin alamun zazza’bi ne, Zanje ya min da test” Hannu yasa saman goshinsa “subhanallahi, ai ko gashi se zufa kake, maza kaje Allah ya baka lafiya” “Amen” yace tare da fad’a wa mota ya nausa titi a gaggauce, d’an nesa da gidan ya tsaya yana mammaida numfashi, “Uncle wannan zufar da zafin da kaji a kaina na firgici ne, ya Allah kasa abinda nake tunani a kan uncle ba gaske bane” ya furta a fili Kwantar da kai yayi saman sitiyari game da lumshe ido, bayan wasu sakanni ya d’ago yana kuma trying wayar Anwar shiru taqi shiga dai dai lokacin wayar hasheem ta shigo, Daga can hasheem yace “Mu had’u a bristol palace” Kai ya d’aga kamar yana gabansa, yayi wa motar key. *** “Ka tabbata abinda ka fad’a haka yake?” Cewar hasheem in a serious tune ‘Daga kai yayi idanunsa na zubda hawaye “wullahil azim duk abinda na fad’a maka daidai ne, doctor yanzu haka wayar Bro A bata shiga mutumin da kaima sheda ne ko silent baya saka wayarsa bare ya kai ga kasheta” “Motar da yake ciki ba tracker ne?” “A...akwai” “Then what are we waiting for?, mu wuce wurin bashari” Fita sukayi da sauri, kai da ka gansu kasan ba’a nitse suke ba. ***farkawa tayi bakinta d’auke da salati , idonta ya sauka kan agogo ganin biyu saura yasa tayi saurin miqewa dan sauke farali “wani irin bacci nayi haka?” Ta furta a fili. Bayan ta idar da sallah ta kunna TV ta Kamo tashar sunna TV inda suka sako wa’azin malam Abdullah gadon ‘kaya me taken “tarbiyyar yaranmu a musulunci “ Idonta ya kawo ruwa lokacin da yaran nata suka fad’o mata hannu ta d’aga sama tana addu’a “ Allah kaine gatanmu Allah kana gani ba gazawa nayi ba, tafiyar tasu ce kad’ai mafita a gareni” ta shafa, zuwa can ta tashi ta leqa kitchen inda ta tarar da wata dattijuwa tsaye tana wanke kayan Miya suka gaisa ta sanar da ita sunanta lubabatu kuma ita keyin girkin gidan nan ta zauna suna ta’ba hira har lokacin sallar la’asar ta gabato. _Bayan kwana biyu_ Numfashi taja tun qarfi kan a hankali ta bud’e ido, kamo hannunta munu tayi “Sam Sam...Bro A Sam” ta rinqa qwala masa kira, Kasancewar dishi dishi take gani bazata iya cewa ga wanda ke tsaye kanta ba taji dai muryar munu kafin taga inuwar mutum biyu tsaye a kanta, Wata dattijuwar mace ta shigo d’auke da qwarya a hannunta ta tsugunna gefen Sam tana jiqa wani qaramin tsimma cikin qwaryar tana goga mata a fuska zuwa wuya, fad’i take “ “kai fillo bana fad’a maka ba ai wannan saiwar da ikon Allah mutuwa ce kawai bata magani yanzu ba gashi ba, kwana biyu tana kwance daga fara shafa mata magani yau ta tashi” Sanyin dake sauka a jikinta ne yasa ta wartsakewa idonta ya bud’e garau munu ta fara gani wacce bakinta ya Gaza rufuwa kafin ta maida idonta kan Anwar lokaci d’aya suka sauke ajiyar zuciya a tare, wanda yaja hankalin ‘yan d’akin suka shiga binsu da kallo Saurayin da aka kira da fillo yace “Ha’a yau tsohuwa ta zama likita” ya shiga taka rawa da sanda, basu ankara ba se ji suka yi muq dattijuwar ta maka masa sanda Fad’i take “yau naga mara kunyar fillo “ ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (20) NOT EDITED Gyaran murya yay game da kara hannunsa a baki, hakan yaja hankalinsu bece dasu uffan ba ya juya zuwa waje inda ya jingina da jikin katangar bukkar, d’ago kai tayi tana qoqarin zama, tsohuwa ta nufo ta da sauri “tashi a hankali jikinka ba qarfi” ‘Daga kai tayi da taimakon tsohuwar da mun ta zauna aka jingina ta da jikin tamusashshen pillow da aka nad’e saboda yayi tudu, “zauna kusa da ita bari naje na sa mata nono” cewar tsohuwar idonta a kan munu, ta fice Zama munu tayi a bakin gadon da aka shimfid’e da tabarma murmushi tayi har qwalla ta d’igo a idanunta tace “Sam sannu da jiki, yanzu meke damunki?” Murmushin ta mayar mata “bana jin komai se nauyi da kaina ke min” Hannu munu tasa ta kama kan ta tofa mata addu’a “sannu se a hankali ze sauka” lumshe ido tayi kan ta bud’e a kan qofa da take iya hango inuwar mutum a sanyaye ta furta “Is he mad at me?” Kallon qofar munu tayi “wh..why no! Ko d’aya tausayin halin da kike ciki yake bakya ganin yacce ya fita hayyacinsa ganin kinqi farfad’owa tsayin kwanaki biyu?” Numfashi ta sauke “bana jin zan ta’ba yin wannan matsayin a idon Bro A “ ta d’anyi yaqe kanta a qasa tana murza yatsunta tace “zan nemi afuwarka ko da baza ka kula Samira d’an ‘kasa ba hakan zesa naji na sauke wani bodem a kaina” “Magana kike yi ne?” Girgiza kai tayi tana bin d’akin da ido “a ina muke nan?” “Qauyen falalu kenan, hm ai Bayan accident d’innan Sam doguwar suma kikayi dan ni tuni na fidda rai a kanki Bro A ne kawai ke da hope dan shi ke ta bani baki cewar zakiyi making that you are a survivor” “Ya fad’i haka da bakin sa?” Tace cike da mamaki d’aga kai tayi, ta matsa kusa da ita, qasa qasa tace “har hawaye naga yanayi lokacin da kike sume fa” Ido waje Sam tace “he did c...” Hannu munu tasa ta toshe mata baki “shiiii...kar ya jiyo mu, amma duk abinda na fad’a miki dagaske nake wlh” murmushin gefen baki tayi had’e da juya idonta ta maida qofa lokaci d’aya ta had’iye abinda take qoqarin furtawa ganin sunyi ido hud’u dashi tsaye yake bakin qofa ya zira hannuwa cikin aljihu , seda ya numfasawa kafin ya tako ya zo gaban gadon, duk qasa sukayi da ido dan Anwar na d’aya daga cikin abinda ke firgita su, tun bare Sam da duk sanda ta ganshi se punishment d’in da ya ta’ba yi mata ya fad’o mata a rai “ ya kike jin jikin ki?” Muryarsa ta sauka cikin kunnen ta, “D..a s..au..qi “ tayi qoqarin furtawa a hankali murya na rawa, Kai ya d’aga, “d’an birni kazo na raka ka dutsen yin waya” maganar fillo ta katseshi Waiwayawa yayi ya kalli in da yaka daga waje ya girgiza masa kai, kan ya maida kanshi ‘bangaren da suke sun sussunkuyar da kai kamar wanda ke gaban siriki , ‘yar dariya yayi, “Hey’s ku bani few minutes, yayi pointing pink yatsansa ‘Daga kai sukayi, tare da bin bayanshi da ido, suka sauke idonsu kan na juna tare da sakin murmushi me sauti “Zaki iya tashi?” Munu ta tambaye ta ‘Daga kai Sam tayi a shagwa’be, hannu ta miqa mata ta kama, tana me fad’in “zo muje wurin tsohuwa da fillo” *** Bismillah yay ya danna number cikin ikon Allah wayar se faman ringing take ba’a d’aga ba , qiris ya rage ta tsinke aka d’aga daga can bello yayi saurin qagawa a kunne “Bro...A ya Allah bro ina kake? Ina ka ‘boye mana?” “Shiii...first ina wani gari me nisa da bazan iya fad’a maka yanzu ba, all I want you to know is that I’m perfectly fine, inaso ka sani na barka a hannun ubangiji, I trust no one..” Jijjiga kai bello ya yake hannunsa saman baki ya danne sautin kukan dake neman fitowa , yacigaba da saurarensa “..Bro B a situation d’in da muke yanzu inaso kad’a ka saki jiki da kowa ciki har da uncle saboda wasu dalilai dana barwa kaina sani, a qarshe ka turo min da isashshen kud’i yanzu ba anjima ba zan tafi can wani garin na shirya mu bar qasar nan” “Okay bro I’ll do that right away, ya..su Sam?” “They ar ok maza kayi abinda na saka, idan nayi settling zan kira ka” Hasheem dake ta kallon bello ya fisge wayar “Man where d f*ck are you???” Ya fad’a da qarfi Murmusawa yayi “somewhere..somewhere in the world, ka kula da Rayya,..” “Tsaya tukunna I’ve received another latter from ‘hidden ‘“ “What!?” “They said na fad’a maka no matter how far you are taking the treasure from them zasu nemo kuma they will hunt you down “ Lumshe ido yayi, “..Allah ya fi su doctor, se wata rana” Bello ya amshi wayar cikin zubda hawaye yace “Ammi? Me kake so nace mata?” “Kanemi abin fad’a mata, Ina sonka “ qitt ya katse wayar, Bello ya kalli time kan ya dubi hasheem yace “bari naje mayi magana” Kan hasheem ya iya furta wani abu tun ya ja mota, da qarfi yace “da me kake son naje gida?” Ya doki bango tun qarfi washhh ya hau yarfe hannu, tare da jan tsaki, ringing d’in wayar sa ne yaja hankalinsa ya duba Rayya ce, “Babe come and pick me at sardauna crescent SS office” be jira ansar ta ba ya katse, aikuwa ko minti biyar batayi ba se gata sallama yayi wa bashari ya tafi Hannu ta kawo zata ta’ba goshinsa cikin qosawa yace “babe sau nawa zan fad’a miki banason yawan had’a jikina da naki, Anya is kuwa kinje islamiyya?” Burki taja wanda kad’an ya rage motar bayansu ta goge su yayi saurin kai hannu ya jasu shoulder d’in titi daddage wa tayi ta fashe da wani ubansun kuka har taso firgita shi, hannu yasa ya cakud’a sumar kanshi a zuci ya furta Allah na gode maka, Facing d’inta yayi cikin karyayyiyar murya yace “babe I’m so sorry I don’t mean to hurt your feelings, soyayyar da nake miki ne yayi yawan da bazan iya jurar ganin kina yin wani abu ba batare da na tunatar miki ba, yayi shiru jin taqi kulasa sema turo baki da tayi Yaci gaba is da cewa, “I know my words are harsh, am sorry my love Insha’Allah bazan kuma ba” A shagwa’be tace “ya wuce amma meyasa kai kuma kake ta’ba wasu matan a hospital har da matan aure kuma” Lips d’inshi na qasa ya shiga taunawa duk gudun kar dariyar da yake qunshewa ta fito a zuci cewa yake “yarinyar nan akwai daru” Numfashi ya sauke a hankali yace “look at me Rayya” Maqe kafad’a tayi “har yanzu kina fushi da ni ko babe “ Ta girgiza kai yace, “am a Doctor my love, a gynecologist wanda dole nayi huld’a da mace” Cikin cool voice ya kuma cewa”but mind you duk huld’ar da zanyi dasu is different from yours, i love you from every drip of my blood” Jikinta yayi la’asar dan ko d’ago kai ta kasa se fuskarta data mamaye da murmushi wanda ke fallasa fararan hakwaranta, side mirror ta kalla game da nausa motar kwalta, shima sanin cewar bazata kulashi ba yasa shi komawa da baya ya jingina da seat idanunsa stick on her face cike da tausayawa condition d’inta tare da matsananciyar soyayyar ta a gare shi badan komai ba yana mata kallon tsintar dami a akala a ganinsa tafi qarfin ajinsa me zata yi da likita kamarsa tafi kalar manya, Lokacin data saukeshi a qofar gida ya leqo ta setin widow d’inta zan shigo anjima ki fad’awa mami zan ganta, drive safely ya ‘karashe da kallon ke kad’ai nake so, yau kam likita ya kashe bakin noisy Rayya dan har taje gida Gaza gane kanta tayi shin wani irin so take wa hasheem ne? Kai ta cusa cikin pillow tana imagining how her life will be without the hottest doctor, alarm na ya buga na lokacin shan maganinta ta tashi a hankali ta d’auki gorar ruwa dake saman bedside drawer tasha maganin kan ta miqe da niyyar zuwa wurin Mami dan sharia mata saqon likitan ta. *** Banki ya wuce direct inda ya ci sa’a qiris lokacin tashin su yayi amma ganin babban customer ne yasa suka shiga bashi kyakkyawar kula ganin irin maqudan kud’ad’en da yake nema, ba a wani d’auki lokaci ba transfer tayi ya tura wa anwar text da Done! Ina jiran call d’inka, Allah ya tsareka, ka kula da amana. Murmushi yayi lokacin da saqon ya iske shi, saukowa yayi tare da dafo kafad’ar fillo Yace “wani gari ne mafi kusa da nan?” Ha’ba ya kama alamun tunani kan yace “yawwa garin bununu, daga nan kuma idan ka haura ruwa zaka ‘bulla minna” “Kana nufin naija state” “Aa garin nufawa de” Numfashi ya fursar “zamu iya tafiya gobe da safe? Mu isa naija kan la’asar?” “Aa fa, saboda se an kwan biyu cikin ruwa” Ido ya fiddo waje “kwana biyu, babu wani alternative d’in, Ina nufin ba wata hanyar bayan wannan?” “Eh to akwai mamman me ice matuqin babbar mota ne idan zaku iya binsa se ya kaiku amma zuwa dare yace ze kama hanyar minna” Lips dinshi yayi nibbling kan yace “hakan za’ayi dan tafiyar tamu nada tsayi zo muje” Zaune suke tsohuwa na gyaran zogale tana basu labarin ta da rayuwar su ta da, suka shigo “tsohuwa mu zamu wuce” yace yana me tsugunno a gabanta” “Ku wuce? Ku wuce kuje Ina d’an samari?” Caraf fillo ya amshe “tsohuwa munje gurin me ice ne yace ze sauke su a minna, tunda a hanya suke” “Kai d’an samari babu inda zakuje da wannan yaron haka jikinshi ba qwari” Kallon sashen da suke yayi yace “tsohuwa Insha’Allah ba abinda ze sameta inaso mu tafi ne gudun kada mu shafa muku kashin awaki dan na tabbata mutanen nan dake farautar mu baza su gaji da bibiyar mu ba har se sun cimma burin su, a nawa tunanin barin mu qasar nan ne kawai mafita hakan ze faru ne idan mun yi katin shiga wata qasa” Had’e rai tayi, idonta kan ‘yammatan biyu da kwana biyu rak taji sun zame mata wani ‘bangare na jikinta tace “Tunda haka ne shikenan, ta nuna masa yatsa kayi min alqawari duk randa kuka dawo zaku kawo min ziyara?” Qasaitaccen murmushi ya saki “Insha’Allah tsohuwa ke da zaki min zaman d’aki ma” “Ja’iri” ta furta cikin sadda kai ta shige d’aki, can ta fitoya riqe da qwarya cike da damammiyar fura ta ajiye gabansu sam “maza ku shanye kar ku tafi da yinwa” Ta kalli anwar “zuwa qarfe nawa yace ku same shi?” “Bayan sallar magriba” “Madallah kafin nan kun huta ai” HANYAR MINNA Irin motar nan ce me rufaffen baya wacce ake safarar itatuwa daga wani gari zuwa wani gari kasancewar hayar motar su kayi ba komai a bayan se bencina biyu jingine da ko wani ‘bangaren motar Samira da Munu saman d’aya yayin da Anwar ke zaune saman wanda yake facing d’insu yana faman danna waya Munu da ta jima da yin bacci jingine take da ledar kayansu, yayin da Sam ta nad’e qafafunta a qirji fuskarta na kallon waje iskar Allah na kad’ata tana me bin duwatsu da bishiyu da ido tana jinjina baiwa da iko na ubangiji, iska ta fursar a hankali ta juyo tana me facing Anwar, a nutse ta d’ago kwayar idonta ta sauke a kanshi cikin zuciyarta tana mamakin yadda baya gajiya da latsa waya, mayan waya! ta harari side din da yake Murmushi ta saki a hankali ta lumshe ido se de tana bud’ewa de cikin hasken flash d’in waya “Maimaita abinda kika fad’a...” ya furta in a harsh tune. ©️Kdeey😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers ) (21) Jiki na rawa ta runtse ido har tana neman jirkitawa qasa, "Kayi...kayi hakuri bazan kuma ba dan...Allah" ta qarashe cikin rawar murya Shi dariya taso bashi ma se shegiyar tsokana ga tsoro daya yi mata katutu, yasa hannu yaja kunnenta "duk ranar da na kuma jin kin fad'i magana mara dad'i a kaina sena d'inke wannan qaramin bakin naki, silly girl" ya qarashe tare da d'allar lips d'in da hannu, har ya zauna be dena hararar ta ba, kula da hakan yasa ta qi bud'e idonta se ma jan jiki da tayi ta kwanta jikin munu har babban 'barawo yayi awon gaba da ita. 2:15am Suka isa garin minna, inda ya umarci driver da ya kaisu inda zasu samu makwanci yace masa wullahi iykar sa da minna tasha, gudun haduwa da yan sanda kada su kamashi a cewarsa, "Ba matsala idan kaga taxi ka tsayar mana se muje da ita" Hakan kuw akayi, dattijo ne me taxi din banda shegen surutu babu abinda yake ga wani d'an banzan kllo da yake wa Sam ta mirror, duk jinta take a takure, ta rinqa jan hijabinta ita a lallai se ta dad'a sakaya jikinta dan tamkar yana kallonta tsirara take ji "wannan wani irin bala'ine" munu da ta kula tace, surin girgiza mata kai Sam tayi alamar tayi shiru, ta gefen ido ta kalli Anwar daya toshe idonsa da baqin gilashi tayi da alama bema san abinda ke wakana ba, har gaban wani tangamemen hotel ya kaisu inda Anwar yayi masa kyakkyawar sallama har sun sauka sun fara tafiya ya tsaida me taxi d'in da cewar akwai ragowan kaya, se da ya tabbatar ya shigar dasu reception ya dawo se de da zuwansa ya bud'e qofar tare da janyo mutumin da hannu ya kai mishi kyakkyawan naushi har se da bakinsa yayi jini "Malam lafiya zaka doke ni" "Uban wa ya baka damar kallon mini mata, daka samu ma ban faffasa maka jiki ba! Get out of my side gara kawai" Ai kan kace meye wannan wuf ya fad'a mota ya tafi, anwar ya juya cikin hotel d'in rai 'bace, ba tare daya kalli gefen su ba yace "muje" a d'arare suka bi bayanshi dan sauri kamar zasu kifa. VIP room ya kama musu guda biyu ko wanne ciki da falo, se da ya rakasu har d'akin ya shiga y dudduba sannan ya ansa key ya basu bayan ya nuna musu nashi dake gefen nasu sannan ya tafi nemar musu abinda zasu ci. *Birmingham U.K* "Ah ah hajar wannan kayan da kike had'awa fa" cewar Ammi data leqo dan kiran ta suci dinner, hannu tasa ta kare idonta "Ammi dama d'azu ne barrister ya kirani yace na shirya kayana ze turo min da kud'in tafiya nigeria" "Zaman ya kama shi kenan?" "Eh haka yace ze kwana biyu, ni wlh har na fara kewar ki" tace game da shagwa'be fuska, Hararar wasa ammi tayi mata "kyaji dashi ja'ira, ni taso muci abinci bansan gulma" Ta bud'e fuska tana dariya tare da miqewa tace "Ammi me muka samu" "Abinda kika ce d'ana na kwad'ayi" "Cowleg" ta furta ido waje har da d'an tsallenta ta mara mata baya. *** Tun da yayi sallar asubahi ya nufi cafe din cikin hotel d'in cikin qoqarin tura saqo ta yanar gizo wato mail amma firr yaqi tafiya, wayar hashim ya kira bugun farko kuwa ya d'aga "Duk wani d'an iska ya biyo bayanka" "Tun da ka same ni a tsakiyar 'yan kan titi ba" ya bashi amsa, dariya hashim yayi suka gaisa cike da annashuwa yana tambayar jikinsa, Yace "Ya akayi kasan nine" "A halin da ake ciki yanzu duk baquwar number", Girgiza kai yayi yace "doctor wani taimako nake so kayi min" "Me kake so dani?" "Zan turo maka saqo ta mail da inda zaka tura min yanzu pls" "That is only if you tell me your whereabouts?" Gashin kansa ya shafo had'e da murza goshinsa yace "sai ka jini" ya katse wayar cike da tunaninka, ya san hashim for a lifetime, baze ta'ba barin ko quda ya cutar dashi ba se de a yanayin da ake ciki yanzu idan aka cire Ammi da bello bayajin akwai wanda ze yarda dashi. Qarar da wayarsa tayi yasa shi dawowa daga duniyar tunanin daya fad'a _Reply "done" from doctor_ Murmusawa yayi, ya tashi ya shiga restaurants d'in kusa dashi ya kar'bo breakfast d'in da yayi musu order, knocking yayi bisa door, "Waye" munu ta tambaya Cike da jin dad'in yacce ta tambayar yace"nine" bud'ewa tayi fuskarta d'auke da fara'a "ina kwana Bro A" "Lafiya" yace tare da handing mata leather bag d'in ya juya, har yayi taku biyu ya juyo zata rufe yace "wait, ina d'ayar take?" "Sallah take" tace a duburburce, gyad'a kai yayi badan ya yarda ba ta kuma cewa "sallar walaha" "Uhumm" kawai yace tare da d'aga girar sama ya tafi. Rufe qofar tayi tana me hamdala da be gano taba, ta ajiye ledar bisa table cikin d'aga murya tace "se ki fito dodon naki ya tafi" Sam dake bayan curtains ta fito hannu a saman qirji tana maida numfashi tamkar wacce tayi tsere "Ke lafiyarki" munu ta tambayeta "Baki ga abinda ya faru bane??" Munu ta kyabe baki tana fad'in "eh naga de kin 'buya bayan curtains sbda kar bro A ya ganki... sbda yana cinye mutane..ko?" Guntun tsuka tayi "ke dalla nifa tsoron wannan manyan idanun nasa nake bawai...." Dariya munu tayi "ke da shi maga wanda yafi wani ido" Turo baki tayi "tabb wlh gara nawa kina ganin nashi kamar na mujiya gashi yayi ta wani lumshe su kamar me jin bacci" "Ehhh lallai har kin manta warning d'in daya kafa miki jiya ko, maza ya jiki, ni dai taho muci abinci dan yinwa nake ji" Dad'a cuno bakin tayi ba tare da tace komai ba ta hau bud'e pack din abincin. Anwar da ke tsaye jikin qofar ya ji duk dramer da suke ya girgiza kai wato 'buyar mishi tayi, sbda idanunsa irin na mujiya ko? Zaki sani ne ya furta a fili. 3 weeks later Dawowar Ammi kenan daga raka mom hajar airport ko parking mota batayi ba wayar ta ta shiga qara alamun kira, d'agawa tayi had'e da yin sallama, aka ansa "Ann! Kaine? Inaka shiga hakane na dena samunka " tace a rikice "Ammi na lafiya ta qalau, inason fad'a miki ne ma in 3 days time zaki ganni, idan nazo zan fad'a miki duk abinda kike son ji, we wil talk later i love you" Tun kan ta samu sukunin amsa shi ya katse wayar se qarar message taji _reply "ammi kar ki sanar da kowa ina hanya, ki d'auki kayanki kije quarters d'in AB machinery zan same ki a can. Take care_ Tunani kala kala ta tsinci kanta dayi se de ta barwa kanta cewa anything has a reason baze ta'ba yin abu haka kurum ba. Ranar wata laraba misalin 3:30pm tayi musu cikin tafkeken kamfanin AB machinery ginin da idan ka shige shi zaka zata sace ka akayi, katangar sa kad'ai abar kallo ce me tsayin gaske ce ainun, ko ina cikin wurin zagaye yake da qayatattun flowers masu fidda qamshin dad'i ko ina ka kalla mutane ne birjik sanye da kaya kala d'aya wato blue colur daga bayan su tamfkeken A da B ne a had'e, duk inda motar da suke ciki ta wuce se kaga ana tafi fuskokin mutanen da kallo d'aya zakayi musu kasan turawa ne manne da murmushi wasu kuma dariya kai kan gani kasan farinciki suke, Maida idonta tayi inda yake tare da waro ido waje, dama yana fara'a haka? Hannu tasa ta dad'a murza ido wai kode mafarki take ganin tabbas d'in hakane yasa ta kuma leqawa ta kusurwar kujera inda har ta iya hango lotsawar man pride d'insa, Iska ce me d'umi ta doki spot d'in wuyansa har besan lokacin daya lumshe ido ya bud'e a hankali ba, jin abin na neman kashe masa ga'bo'bin jiki yasa shi waigowa a hankali sede tsayawar da motar tayi yayi daidai da komawar ta jikin window dan qarasa kashe kwarkwatar idonta "Sir mun qaraso" maganar driver ya d'au hankalinsa, daidai lokacin da yake shaqar wani ni'imtaccen qamshi, umartar sa yayi daya shigo da kayan shi kuma ya sauka ya tafi, ganin haka ta bud'e qofa tare da kamo hannun munu suka fito duk da son kalle kallen su basu samu daman yin hakan ba gudun kada ya 'bacewa ganinsu Gaban wata tafkekiyar wooden door suka tarar dashi tsaye yana danna door bell, wata baqar fata ce ta bud'e qofar tare da rissinawa "Welcome back sir" Be amsa ta ba ya wuce bayan tayi gaggawar kaucewa, suma suka bi bayan nashi tamkar jela, "Ammi na" ya furta cikin d'aga murya a lokacin daya dudduba d'akunan gidan Cikin gigin bacci ta daddafa ta fito, sama ta nufa kasancewar tana underground apartment, kiran sunanta da ya kuma yi ne yasa ta yin saurin haura benan "Ann my son" ta furta in a shaky voice wanda tuni hawaye suka hau ziraro mata, waigowar da zeyi ya hango ta tsaye da sauri ya isa gareta ya rungumeta dan yayi kewar Ammin nasa sosai "Ammi na" ya furta a hankali, sun jima a haka kan munu tayi gyaran murya game da fad'in "ina wuni", share hawayen tayi da hannu ta d'ago kai a hankali, ta amsa musu tare da qare musu kallo A nutse ta tako zuwa inda suke tana me dad'a fad'ad'a fara'arta tasa hannayenta ta shafo kawunan su dake sakaye cikin hijabi tace "sannun ku da zuwa yara na" hannu tasa ta d'ago ha'bar Sam tana kallon cikin qwayar idanunta, a hankali tace "Samira" Game da fashewa da kuka me tsanani wanda ya rud'asu duka, "Ammi ammi na lafiya me ya faru" Ita kuwa samira baya tayi had'e da sakin kuka wurjanjan, munu ta shiga bata baki yayin da Anwar ke lalla'ba mahaifiyarsa Hajjo wato Ammi ta d'ago tare da janyo samira ta rungume, idonta cikin na Anwar take cewa "She's her mothers child, she looks exactly like her, she's mariya's photocopy" ta qarashe maganar cikin hawaye had'e da fara'a "K..in..sa..n mummy na?" Lumshe ido Ammi tayi "'yar uwa tace ta jini.." *** A can gida nigeria kuwa uncle ya rasa gane kan bro B, gashi baya barin d'akinsa a bud'e , motar sa kuwa ta jima da barin gidan, kamar ko yaushe dawowarsa daga office kenan ya tararda gwaggo zaune a falo tana kallon labarai "A a barrister kaine haka da rana tsaka" "Wullahi fa yau Alhamdulillh aikin namu da sauqi" ya zauna saman kujera suka gaisa tace, " to madalla sannu bari na samo maka ruwa kan a qarasa abincin yau munyi ranar abinci" "Ai barshi gwaggo nagode, yanzu wani abokina da matarsa suka matsa seda naci a gidan su" "Ai kuwa yau abincin ka tayi tuwo da miyar agushi me tantaqwashi" "Atoh a ajiye min da dare ta dumama zanci" Hanyar kitchen ta nufa, "to bari na shaida mata kuwa" shi kuma ya haye sama. *** Tsaye yake bayan wata takekiyar daf dake ajiye gefen titi, seda ya gama qarewa samarin kallon tsaf kan ya danna Bluetooth dake maqale cikin kunnen sa, "na gama survey d'in" Daga can akace "Bello mutanen nan na da mutuqar hatsari, lallai ka kula" "Doctor insha'Allah zan kula, go and pamper Rayya not me" Daga ciki yana iya jiyo sautin murmushinsa, "to naji, ka gyara settings d'in glasses d'in?" "Eh" "Then you are good to go, take care" Kai ya d'aga, kan ya tsallaka titin zuwa gurin samarin dake zaune saman dakali. ©️Kdeey😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (22) Barka yace dasu game da d'aga musu hannu, kallons sukayi duka a kaikice cike da mamakin qarfin gwiwa irin tashi kul da yanda kowa ke shayin zuwa kusa dasu Cikin kakkausar murya d'ay cikinsu wato oga Nafi'u yace "kai yane?", shafa kansa yayi had'e da kunna Bluetooth dake maqale cikin kunnensa ta yacce ze iya jin maganar da dr ke mishi, Ya kada baki yace, "ahh sannunku fa, sunana buhari me dabaibayi nazo bautar qasa ne nan makarantar gomnati" "To se aka yi yaya.." cewar wani cikin zafin rai, hannu oga nafi'u ya d'aga masa, idonshi saman na bello "se aka yaya d'an bautar qasa" "Ina so ne idan babu damuwa nake zama cikin ku idan ina gida" Kallon juna sukayi, can d'ayan yace " me ze hana, sede idan ka yarda amma za mu rinqa qaruwa da kai ta wani fannin ko ya" Kai ya gyad'a "well inhar wannan ne me sauqi ne ai ina d kayan abinci, kayan kallo impact wancan shagon jikin makarantar can nawa ne" Nan d'ayannan daya d'au zafi ya washe baki da cewa "kai wancan kwftareren shagon, ah lallai mun samu mafaka, ni sunana rody" Ni kuma "aqilu" Cikin fara'a d'ayan yace "barka ni sunana salihu" Jinjina kai yayi, "da fatan zaku riqe ni da hannu biyu ku bani dukkan amanar ku" Dariya suka kwashe da ita tun qarfi kan wanda aka kira da salihu ya dafa kafad'arshi yace "zo muje abokina" Ba tare da wani tunani ba ya mara masa baya,suka nufi wani layi, "ina zamuje haka" "Gidan mu, inaso na nuna wa baba ta yau na samu kalar abokin da take fatan nake huld'a dasu" _kar ka bishi_ daga cikin Bluetooth doctor ya nemi dakatar dashi, gyaran murya yayi a wayance kan yace "salihu bari naje masallaci wani lokaci maje na gaishesu" 'Dan jimm yayi alamun beji dad'i ba, yace "shikenan ni bari na watso ruwa se mu had'u a can shagon" jinjina kai yayi ya juya ya nufi masallaci, Bayan an idar da sallah yace da salihu ya jira bari ya zaga band'aki, bayan wani incompleted building ya fake tare da danna wabi button jikin glasses dinsa wanda duk qura idonka baka isa ka gane akwai shi, fuskar hasheem t bayyana ta ciki, "Buhari me dabaibayi" ya bushe da dariya, dariyar shima yayi, "kayi scanning fuskokin su?" "Eh, gashinan computer na neman su" "Aha, bari naje" "Okay I'll keep you updated" Direct d'akinsa suka wuce daidai qofar shiga suka had'u dasu, oga nafi'u yace "abokin zamu fita aiki da Allah kad'an sama mana me maiqo odan mun dawo akwai naka kason" Rody yace "ahh oga kace yau akwai zuwa duniyar sama" "Wajibul manzil aboki naa" cewar aqilu cikin muryarsa ta riqeqqen d'an daba, gira ya d'aga da cewa dafatan ba zaku wuce goman dare ba dan ina kwanciya da wuri sboda zuwa aiki" Girgiza kai oga nafi'u yayi had'e da jinjina masa yace "se mun dawo" suka juya a tare, salihu dake baya ya d'ago masa hannu tare da sakar masa murmushi me kama da yaqe jiki a sanyaye, numfashi ya sauke bayan ya rufe qofar da key ya fad'a saman tamusashshiyar katifar dake qasan d'akin yana kuma qarewa shagon kallo game da jinjina kai yana mamakin ta yanda ake mutane ke iya rayuwa a irin wannan area, Seda ya tabbatar sunyi nisa da anguwar ya fito, ta wata boyeyyiyar hanya yabi dan zuwa gida can ya jangi driver zaune cikin mota ya shiga suka tafi yana shiga ya ciccire kayan jikinsa had'e da qullewa cikin leda, ya kishingid'a jikin leather seat tunanin Sam ya maye gurbin tunaninsa. *** Hawaye yaci gaba da zuba a idon Ammi yayin d take rungume da Sam a qirjinta, d'ayan hannunta kuma cikin na Anwar, saman kujera ta zauna tare da kuma kwanto da Sam kan cinyarta, shiru tayi kan ta fara magana da cewa " Alhaji muhammadu ningi shine sunan mahaifin mu ni da qanwata mariya tun ina shekara sha hud'u mariya na sha biyu mahaifiyarmu umma indo Allah yayi mata rasuwa hakan yasa jama'a matsantawa mahaifinmu qarin aure har yakai aka had'ashi da yarinyar kawunsa a cewarsu baze yiwu ya zauna hakanan da yara mata ba, Ina da kusanci sosai da mariya dan ta d'aukeni ne tamkar umma komai se ta tambaye ni ta keyi har wata ran hakan ke 'bata ran y Umma ramatu wato matar mahaifin mu, kula da hakan yasa nake takatsantsan, umma ramatu irin mutanen nan ne masu nunawa duniya tamkar su had'iye ka dan so a baya kuma sunfi kowa qinka , sauqin abun d'aya umma ramatu bata fiye zaman gida ba dan se yamma liqis take dawowa daga office inda take aiki a office d'in matar mataimakin governor, A shekarar dana gama secondary d'an abokin mahaifina ya ganni yace yana so, ba a d'au wani lokaci ba aka aurar dani gareshi ba tare da an duba wai ya kusan haihuwata ba duk da umma ramatu taso cusa wa babanmu ra'ayin hakan 'yan uwansa suka qi kuma Alhamdulillah naci ribar hakan duk da Allah da ya fini sonshi ya kar'bi abinshi se ya barni da gwarazan mazan da zasu sharen hawaye na, (ta shafo sumar Anwar) Mariya tayi aure a lokacin bello yana da shekara sha biyu a duniya, lokacin Alhaji amin alfalla ya zama Ambassador of nigeria to turkey dan gaba d'aya can muka koma da zama yayin da yara n kawo su nan garin karatu. Akwai wata rana da bazan manta ba mariya nada shekari goma da aure ta kira ni da daddare take shaida min gobe zataje ningi kamar yacce ta saba tana kai sadakar abinci da suturu ga mabuqata amma tanaji tamkar kada taje, meyasa na tambayeta, tace wullahi yaya inaji tamkar zanyi wani nisan zango ne, dariya nayi mata dan a tunani na shirmenta ne kurum, na kuma ce kada ta sake ta fasa zuwan, to dama gskya tun aurenta nada watanni ta fara fuskantar qalubale daga dangin mijinta har takai wani lokacin ta nemi tahowa turkey na bata baki, Barrister usman kuwa qanin mijina ne ubansu d'aya, nice na had'asu da maiqasa ganin yana neman lawyer da ze danqawa amanar wills d'inshi, Ranar da mariya ta 'bace a ranar na dira a nigeria dan duba mahaifina Allah barshi n qarasa kano na duba qanwata se mugun labari ya riske ni, gidan da ban samu zuw kenan ba na tafi kano, tun muna saka ran Allah ze bayyana ta har kwanaki suka shura aka tafi wata uku, Labarin rashin lafiyar me gidana yasa ni koma wa turkey inda isata asibiti keda wuya na tarar da gawar mijina wanda akayi poisoning a abinci, ranar nayi kuka tamkar zan mutu har ta kaini ga kwanciya a asibitin tsawon wata guda Duk abinnan dake faruwa ban yarda an sanar wa da yara ba, ni da kaina dana samu lafiya na tattara komai nawa na komo nan se da na tabbatar sunzo gurina hutu na fad'a musu zancen da har yau idan na tuna nake jin ba dad'i dan ni da kaina nasan ban kyauta musu ba ko ba komai zasu so ganin gawar mahaifin su. (Nan ma girgiza mata kai Anwar yayi tare da sa hannu ya share mata hawaye) Wannan shine gskyar labarin mu ni da 'yar uwata mariya, rasuwar mahaifinki kuwa barrister ne firr ya hanani zuwa, wanda bana ce ga dalilin hakan ba se de abinda na sani baze ta'ba yin abin da yasan be kamace ni ba" _kuyi manage da wannan insha'Allah zuwa anjima zaku sake jina_ son so🥰 ©️Kdeey😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (23) _this whole page is for you my wattpadians_ 💖 _jiddatul khair😍 thanks for your immense support_ 😘 ✨ ..hannu tasa ta share hawayen dake fita a idon sam ta d'ora da cewa "samira yanzu da Allah ya kawo ki garemu bazan kuma yarda ki bar ni ba, kece zaki maye min gurbin 'yaruwa ta a fuskarki zan rinqa ganin mariya ta, taja hanci tare da kamo hannun Anwar, insha'Allah bazaki kuma shedding tears ba while we are alive, Anwar is your brother and bello ma haka wic is younger to Anwar, Sam i never thought kece wacce suke kulawa da ita, but daga yanda naji labarin ki a bakin barrister yasa ni tausaya miki na kuma sa yarana lallai su taya uncle d'insu fighting dan wannan case d'in is not just for his carrier is a big goal in his own life and theirs, Ta kalli Anwar kan a kuma maida idonta kan Sam, "kiyi hakuri da maganganu na, na sani sunyi miki tsauri da nauyi a yanayin shekarun ki, but i know my baby has a deep understanding, kar ki ta'ba bari wani abu daga maganata ya ta'ba ki, kada ki damu kwatakwata i'm with you, your brothers are, uhm?" Ta qarashe da sigar tambaya, Jijjiga kai Sam tayi tare da dad'a ruqunqume Ammi cikin sanyin muryar kuka tace "i'm so happy Ammi, yau is one of the best days in my whole life, yanzu saura abu biyu buri na ya cika" "Abu biyu" suka kalli juna Ammi da Anwar Jinjina kai tayi "na farko Ammi inason mummy na ta dawo gare ni cox inaji a jiki na she's alive somewhere else in the world, na biyu kuma akwai haske na da nake kwana ina tashi dashi cikin zuciya ta, kullum daddy used to tell me kada na bari yayi nisa da ni" "What is that?" Ammi ta tambaya cikin bata hankalinta baki d'aya, "i don't know, since when daddy passed away na kasance cikin mafarki..." nan ta kwashe labarin tsaf ta basu cikin zubar hawaye, "Shushh...insha'Allah hasken nan naki ze bayyana gareki soon, ki kwantar da hankalin ki kinji,.." ta dad'a janta jikinta tana rarrashinta, Gyaran muryar da yay ne yasa su d'agowa cikin ciccin magani yace "Ammi bafa ita kad'aice a gabanki ba, gani ga munubiya but duk kinyi focusing kanta, how ridiculous" Hararar wasa Ammi ta mishi jin yana nuna kishinsa a fili, munu dake gefe tad'an dara a hankali kan ta kada baki tace "bro A are you jealous" Saurin shan mur yayi " am whaaat? N..no never da wannan yarinyar, malama tashi jikinta kuje kuyi sallah kuyi wanka se ku fito" Dariya reaction d'insa ya basu, Ammi ta d'ago kanta with a smile on her face tace "maza kuje wancan way d'in there is a room by your right hand side nan ne masaukin ku," tayi pecking forehead d'inta, "Ammi.." yace cikin ciccije lips, murmusawa sukayi duka sannan suka wuce yayin da shi kuma ya maye gurbinta, "ah ah kai ba masallaci zaka wuce bane" Tashi yayi "inason naji d'umin Ammina tukunna" Karan hancinsa taja, "bazaka ta'ba girma ba" "Not until i give you grandchildren" yayi winking eyes d'insa kan ya fita a guje, dariya tayi ta juya bedroom itama cike da farin ciki, bayan ta leqa kitchen ta shaida wa cook ya maza ya shirya table for four. Lokacin dinner Ammi ke tambayar sa school din da ze kaisu nan ya sanar mata boarding school ze kaisu kuma gobe, fork and table knife dake hannunta ta ajiye "Why boarding school?" Se da ya sauke numfashi, ya saci kallon su duk sun tsura masa ido yace "ku tashi ku bamu wuri" bayan sun tafi tace "Ann meke faruwa ne? Ko uncle ne yace kayi hakan?" Girgiza kai yay, cikin rawar murya yace "Ammi i'm afraid dont know who to trust" nan ya kwashe duk abinda ke faruwa kama da wannan motar dake kawo musu ziyara and basu san ko wane daga cikin gidan nasu ke huld'a dasu ba har zuwa neman halaka su da akayi, ya d'ora da cewa "na sani uncle will never do such thing but canjin makaranta daga wacce uncle yasa na kaisu d'in is the only way for their safety, na riga da nayi wa miss chloe magana kuma mun gama komai gobe zan kai su, in 2years time they will be graduates" yayi winking eyes d'insa tare da miqewa dan barin wurin Ammi da jikinta ke a mace dan sosai maganar tasa ta firgitar da ita, taja salati had'e da girgiza kai tace "yanzu cikin wannan yanayin kabaro min bello" Tsayawa yayi tare da waiwayo wa, "kar ki damu na bawa gwaggon munubiya amanar shi, she will look after him, hasheem too is with him all the time, and akwai SS kewaye da gidan, duk moves d'in kowa za a ke sanar dani, bara nayi sallah nazo yau kusa da Ammi na zan kwana" yace had'e da daga gira yana mata warm smile ya fice, Numfashi ta sauke tare da saurin maida hawayen dake qoqarin zubo mata, wannan wace irin rayuwa ce cike da qalubale who want to brings them them down, shin meye ribar ruguza farincikin marayun Allah, da wannan tunani Ammi ta qarasa d'akinta ta tada sallar magriba, A ranar kusan kwana sukayi hira ita da anwar dan tun 8 ya kora Sam da munu d'aki da cewar kada su kasa tashi gobe da safe, a zuciyarsa kuwa har da kishin yacce Ammi ke bawa Sam kulawa sama dashi😆. Washegari Tun 6 suka hallara saman table sede har yanzu basu fara cin breakfast ba sanadiyyar al'adar su ce sai kowa yazo ake fara cin abinci, hakan ya faru ne ta dalilin Sam da bata fito ba, "Anya kuwa Samira lafiya tun d'azu da kika kira ta tace gatanan amma shiru" Munu tace "Ammi haka take bata son cin abinci ko a gida haka gwaggo ke fama da ita" "To Ammi lets just start kafin tazo before na fad'i muku anan" ya qarashe had'e da turo baki, "Je ka kira ta" tace dashi "Me.." ya nuna kanshi da yatsa, ganin kallon da tayi mishi yasa shi miqewa ya nufi downstairs cike da qafuluwa ya shiga knocking bisa door, qofar ce ta bud'e alamun ba'a rufe take ba ya taka cikin d'akin daddad'an qamshi ne ya bigi hancinsa har be san sa'ilin da ya lumshe ido ba, d'akin neat yake tamkar ba'a ta'ba kwana cikin sa ba, tsintar kansa yayi da qarema d'akin kallo, numfashi ya sauke game da juyawa ze fita idonsa ya sauka bisa curtains da yaga suna motsi maida idonsa yayi view d'in d'akin ko alama be hango flowers na motsi ba bare yace iska ake, idonsa da sukayi qasa yasa shi gano sam'baleliyar farar qafa me d'auke da zara zaran fararen yatsu se mutsu mutsu suke, murmushi yayi me sauti ganin yacce take d'age qafafu ita a dole bata so a ganta, "Yaro yaro ne" ya furta a hankali, takawa yayi har gabanta yasa hannu ya yaye curtains d'in, tun daga idonta dake runtse ya shiga qare mata kallo zuwa kyakkyawar fuskarta dake sakaye da baqar talha zuwa shining pink lips d'inta ya gangaro saman qirjinta da tsabar bugu da yake har sama da qasa yake yi, wanda ya bada qaimi wajen tona albarkatun qirjinta da suka d'an girma, riga ce fara qarama daga ciki wacce tayi fitting dinta ainun akayi stalking cikin baqin wandon palazo, sosai shigar tayi mata kyau dan duk da girman wandon seda ya tona asirin dirin da Allah yayi mata, Ga sassanyan qamshin dake tashi cikin jikinta me d'ankaran dad'i wanda bawai turare bane kad'ai sabulu ne da toners masu d'ankaren tsada, lumshe ido yayi ya kuma bud'e saman fuskar tata wanda yayi daidai da bud'e idonta Cikin rawar murya take furta "ni banson zuwa boarding school,..." "Meyasa?" Ya tsinci kanshi da tambayar ta, idanunsa stick to her lips dake motsawa a hankali, "Banson na bar kusa da Ammi.." "She's mine Sssamm" ya qarashe da in-ina, "Nima ai tawa...cc.." Be bata damar qarasa maganar ba, cikin zare ido da qoqarin qwatar kanta ta shiga dukan qirjinshi tun qarfi, tsawon wasu sa'oi har ta fara yin laushi, oga Anwar kuwa hannu yasa had'e da tallafota jikin shi yana sakin numfarfashi out of control, Jin shiru yasa Ammi mara musu baya tunkan ta qarasa ta hango qofar a wangale amma ba alamunsa to ina Anwar yayi ta ayyana hakan se de sautin da take jiyo wa daga ciki yasa ta d'aga qafa tsugunnewa tayi a bakin qofa cike da tashin hankali dakyar ta iya d'aga murya Tace "Ann!!" _yanzun ma dai ba yawa pls bear with me, a tunani na da babu gara ko kad'an nake tsakuro muku, insha'Allah next update will be 10 read more💪🏻😉_ ©️Kdeey😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) _ina dad'a neman afuwa na jina shiru da kukayi hakan ya faru ne a bisa tafiya da nayi, nagode_ (24) Tamkar sukar aradu muryar tata ta doki kunnuwansa, daqyar ta tattara courage dinta t angije shi gefe tare da fad'awa jikin ammi had'e da sakin wani marayan kuka, a kid'ime Ammi ta d'ago kanta ta shiga duba ta tamkar me nemo wani abu, kan ta kada baki tace "maza share hawayenki yar albarka, ba abinda ze same ki kinji, makarantar da zaki ta qawata ce duk lokacin da kike kewata zansa a baku waya se mu rinqa jin lafiyar juna uhm?" Ta d'aga kai, "good, maza kuje nasa eliza tayi miki packing abincin cikin flask dan bazan so 'yata daga zuwa ta fara da abincin makaranta ba ko ya?" Nan ma kuma d'aga kai tayi , Ammi tasa thumbs d'inta biyu taja kumatunta, "oya give me that one in million dollar smile" Murmusawa tayi, had'e da kuma shigewa jikin Ammi, "wuce ka d'auko kud'i kuje ka saya musu suturu kafin kayi dropping d'insu" Ammi ta furta ba tare da ta kalli sashin da yake ba, Jiki a mace ya ja qafa tare da ra'bewa ya fita ta wani hanyar, saman sitiyari ya kwantar da kai, idanunsa a lumshe ya san cewa yana da yawan buqata amma be ta'ba expecting qaramar yarinya irin Sam zata iya jan ra'ayinsa har haka ba, shin meke faruwa ne? The feeling is so weirdo that he can't even imagine yanda akayi har ya isa gareta ya kuma mallaka mata bakinsa da ko kimberly da take fad'i tashi wajen ganin ta samu matsayin sumbata ba tayi nasara ba se kwailar yarinyar da bata yi wata cikakkiyar balaga ba, fursar da iska yayi lokacin daya jiyo sautin taku Dag can ya hangota kwance gefen kafad'ar Ammi munu na gefe suna murmusawa farinciki lullu'be da kowannen su, knocking da akayi bisa window yasa shi saurin sa hannu ya bud'e, "Maza ka sauke su ka dawo" tace game da juyawa ta koma, Forming line yayi da baki had'e da cije ha'koransa har ana iya hango yanda gefen goshinsa ke lo'bawa, shiru ne ya ratsa motar, munu dake a gaba tafi maida hankali wajen qarewa garin kallo yayin da Sam ke raku'be a kujerar baya, Sosai yayi musu siyayya kan ya je ya damqa amanarsu a hannun miss chloe inda aka wuce dasu d'akin kwanan su direct me d'auke da gadaje biyu gefe da gefe "Ya Allah" Sam ta furta ido waje munu kuma tace "Masha'Allah", rungume juna sukayi , idanunsu suka shiga roaming around d'akin bangon d'akin manne yake da stickers d'in sophia the first yayin da ko wani gado ke had'e da reading table se toilet madaidaici, kalar d'akin pink ne haka ma kalar curtains da carpet d'in duka, knocking da akayi bisa door ne yasa su dawo wa daga duniyar kallon da suke "Yes" suka furta a tare, wata dattijuwar baturiya ce ta leqo d'akin with a smile plastered on her face, "Wellcome to saint teresa college" Nodding sukayi game da fad'in "thank you" "I'm miss patricia, dafatan zakuji dad'in kasancewar ku a nan, ni ce shugabar d'akunan hostel d'inku hope you will cooperate with me" "Sure" suka ce tayi musu thumbs up ta tafi had'e da rufe musu qofa" "Saint teresa" munu ta furta cikin rolling eyes kan ta fad'a saman gado, dariya tayi ta juya ta nufi bathroom ta dauraye hannu ta fito gefen gadon ta zauna ta shiga bud'e flask dan kauda yinwar dake qwaqularta. ~ "Care to explain yourself?" Hannu sa daya d'ora saman handle ya janye game da waiwayo zaune take medicated glass maqale saman idonta tana duba jarida, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kan ya taka ya isa gabanta Daidai qafarta ya gurfana kansa a qasa tunda yake be ta'ba jin kunyar Ammi kamar ta yau ba, "Ina saurarenka" Muryarta ta katse sa, lumshe ido yayi game da bud'esu saman qafarta ya d'ora hannayensa a kai ya shiga mata matsa, ga mamakinsa se ta janye qafar cikin had'ewar fuska Tace "Ann kar ka maida ni babbar kurum mana , taya kake neman fito da sabbin d'abiu wanda ko a yahudu mara kunya ke yin hakan, kar ka bari na kuma tambayar ka" Rufe ido yayi, yace "...mata tace..." Cikin rawar murya tace "Ma..mata kace??" 'Daga kai yayi idonshi a qasa "Ammi banso kika yi pushing d'ina na fad'a miki ba, this is not the right time..." "..right time? Is this what you are suppose to say to me? Wait Anwar taya akayi Samira ta zama matar ka da yawun wa? Wane ya baka ita?" "...kawun tane, kawu kabiru," yace idonsa a lumshe, "Anwar yaushe ka fara qarya? Na zata kawunta an nemeshi an rasa, wait..don't tell me you are behind all this" "Not all Ammi.." "Ya isa.." ta d'aga masa hannu, tare da juy masa baya, rarrafawa yayi ya riqo qafarta jin tana sheshsheqar kuka, "Na rantse miki da Allah Ammi nayi hakan ne saboda farautar ransa da aka fara" Ta juyo hawaye na bin fuskarta "kanaso kace shima ana neman rayuwar sa ne?" "Hakane, ciki harda matar sa da yaronta" Cike da mamaki tace " ban fahimce ka ba" Gyara zama yayi, ya fara da cewa " wata rana na fita zagayen gari dai dai wani lungu a amadu bello way na hango wani saurayi na leqe hakan yasa naja gefe nayi parking dan ganin abinda zeyi bisa mamakina da yaga babu kowa se ya fito game d yafito wata babbar mace tazo suka fad'a wani d'an qaramin gida se da na tabbatar sun shige na fito , ta bayan wani window na tsaya dan naji meke faruwa a gefe guda kuma inason ne naji inhar barayi ne ko wasu masu tada zaune tsaye na kira 'yan sanda cikin ikon Allah se naji maganar mace na fad'in "Nace muku ki ida kashe shi kunqi wai shin ba kunyi min alqawarin kashe kabiru bane ko dai bakwa son kud'in ne! Kun kuwa san alqawari, dakanku kuka dafa qur'ani kuka kuma rantse zaku kashe mana shi, kai kuma Amir ina zancen fyad'en da zaka yi mata! Wai ku wasu irin daqiqai ne to billahillazi na baku kwanaki uku rak ku aiwatar da abinda nace muku in ba haka ba mu zamuyi da kanmu idan yaso kuyi biyu babu, haka itama uwar yarinyar mu kasheta dan mun gaji da ajiyar kayan da ba mamora.." Baya naja da jin haka, a take na bar wurin jiki na rawa na nufi makarantar da Bro B yake kula da Sam, na shaida masa duk abinda naji mummy wlh kuka nake daqyar na iya sanar dashi labarin tun daga wannan ranar muka saka ido kan shige da ficen su kwatsam a kwana na biyu sega shi an kawo Samira asibitin hasheem ganin haka nasa Dss bashari ya tura aka kama kafatanin gidan with d exception of shi uncle dinta da babban yaron ta na tura su nijar qarqashin kulawar aboki na shugaban qasar garin, Aurena da Sam kuwa ya faru ne dalilin ajiyeta a wurina da nace zanyi, kawu ya nemi tayina a kanta da farko naqi aminta sedai tsoron abinda ya faru da ita da Amir kada ya kuma faruwa da ita tunda ga habiibii yasa na yarda a ranar mutawakkilu ya amsa walicci na aka d'aura aurenmu bisa sadaki millon d'aya, wanda na bud'e acct da sunanta na ajiye a ciki da alqawarin duk sanda tasan gaskiyar lamarin zan mallaka mata haqqinta, sa'annan a tambayi ra'ayinta a kaina, Ba iya nan na tsaya ba dan nayi tattaki har turkey na damqa kamfanin dake can a hannun gomnati da taci gaba da kula dashi tare da basu 2 % na riba, a yanzu haka habibii wato d'an kawu kabiru na tura shi karatu singapore shi kuma kawu yana gidan mutawakkilu wato shugaban qasar nijar" Ammi durqushewa tayi hawaye nabin fuskarta, tace " Ann cikin labarinan wace uwar yarinya da aka gaji da ajiya", Murmushin da yafi kuka ciwo yayi yace "Ammi na mummyn Sam na raye..." Qirji ta dafe da hannh cikin kufcewar kuka take fad'in "um um um um Ann kada kayi min qarya! Ka fad'a min gaskiya dan yin hakan baze kwantar min da hankali ba sede ya tada min" Hannuwanta ya kamo cikin nasa "Ammi ki nutsu ki saurare ni yi miki qarya da wannan maganar babu riba a gareni mahaifiyata ki sani duk wannan fad'i tashin da nake saboda farincikin ki nake" Hannu tasa ta share hawayen fuskarta "Ann zan had'a ka da chief of army staff na nigeria madu Aliyu lallai inaso a kamo min matar kabiru dan tabbas tana da masaniyar inda mariya take" waya ta d'auka da niyyar kira yayi saurin cewa "Ammi zan fiso mubi komai a sannu, idan muka ce zamu bi abin sama ta ka abin baze zo mana da sauki ba, yanzu haka Bro B yana can kan binciken wanda suka kawo mana hari a hanya wanda nake kyautata zaton hakan will lead us to mutanen dake riqe dasu aunty mariya" Jimm tayi,can tace "Ann all this years ace mariya na raye? Shin wani irin hali take tsayin shekaru sha wani abu ba tare da taga wani nata ba?" Ta qarashe cikin tsananin kuka. Kwantar da kanshi yayi a qafarta shima yana zubda hawaye yace "Ammi na inaso kiyi min wani alqawari" yayi rigingine idonsa a kanta yace "you will never let Sam knows about this ciki harda zancen aure na dake kanta" Girgiza kai tayi cikin dashewar murya tace "meyasa.." "Hankalin ta baze d'auka ba, and nafison ta kammala makaranta tukunna" "Se idan ka iya d'auke idonka a kanta, dan idan har abinda ka aikata d'azun ya kuma faruwa to kuwa lallai ita da kanta zata kawo wani abu koda be danganci igiyar ka dake kanta ba" Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke had'e da jinjina kai cike da tunani bacci yayi awon gaba dashi , murmushi tayi cikin zubar hawaye ta d'aga hannuwa sama tana dad'a godewa Allah da kuma roqon Allah ya bayyana 'yaruwarta ya kuma kawo musu komai cikin sauqi, pillow ta janyo ta d'ora kanshi a kai ta d'auko blanket ta lullu'be shi, ta shige d'aki ta kwanta hawaye na zubo mata cike da tausaya wa rayuwar su, su duka, Bello ko a wani hali yake ciki? Tunanin hakan yasa tayi saurin kiran wayar bello, *** Cikin wani babban gida suka shiga bayan sun tabbatar da ba wanda ke ganin su, wata mata ta fito jikinta sanye da tsadadden leshi wuyanta da hannunta cike da gwalagwalai se d'aukan ido suke shigowarta cikin haske yasa hasheem da bello dake kallonsu tamkar a TV ta cikin camera da suka manna jikin salihu ba tare da sanin sa ba suka miqe a firgice... "Haj..iya mar...yam..mainasar" suka furta cikin rawar murya kallon juna sukayi a rud'e zuciyoyinsu na tsananta bugu, qurawa mini TV d'in ido, _Tafa hannu tayi "you guys did a very good job, you deserve a medal you know, tayi dariya kan ta hakimce saman kujera tayi musu alama da hannu cewar su zauna,_ _"Nafi'u kunyi qoqari mutuqa se dai naso ace ku da kanku kuka qarasa su, dake Allah na sona se ya kawo min komai cikin sauqi" ta kwashe da wata arniyar dariya lokaci d'aya kuma ta gimtse tamkar ba ita ba_ _Tace "naji ance baquwar fuska ta shigo unguwar ku" jimm sukayi cana rody yace "eh madam wani corper ne yazo serving anan makarantar arean mu"_ _"You know i hate new faces so ku iya takun ku" kai suka jinjina,_ _"Madam have u heard from lawalin nijar kuwa?" Cewar aqilu,_ _"Har yanzu ba wani labari, amma akwai tabbacin be fita daga garin ba"_ _"Partaining hajiya ya ake ciki akwai wani improvement?" Cewar salihu_ _Kafad'a ta d'aga "talking about waccan matar je kazo min da d'an iskan dattijon nan" ta furta hakan idonta saman wani qaton gardi dake tsaye a gefenta_ Sulalewa su bello sukayi , ganin an _shigo da wani dattijo hannunsa da qafafunsa maqale da ankwa jan qafa yake dan tafiyar ma ta gagare shi, shi da qashi marabar su qalilance se fata, janshi akayi har gabanta aka tunkud'ashi kansa se gilu gilu yake ko d'aga kai wannan ya kasa, qur suka zuba mishi ido sai salihu daya sadda kai,_ _"namadi" ta kira sunan sa tun qarfi, na rantse da wanda raina ke hannunsa idan baka fad'i inda diamond d'in nan yake ba, da kai da hajiya a yau kwanan ku ze qare"_ _dattijon da ta kira da namadi ya d'ago kai jiki ba qarfi cikin inda inda tamkar me koyon magana yace na rantse da Allah baki na baze ta'ba furta sirrin ubangida na ba koda zaku rinqa yankar nama na kuna zubar wa"_ _Miqewa tayi a fusace ta fisgo kulkin dake hannun nafi'u ji kake gamm! Ta buga masa a kai nan da nan kuwa jini ya hau zuba, saurin riqota akayi wani saurayi ne yace "mami ki barni dashi" cikin yaqunar fuska ya kalli namadi "na baka awa hud'u idan baka fad'i inda yake ba da kaina zan qarar da kwanakin ka da kai da ita so called hajiyar taka, ku d'auke shi_ _waiwayowa yayi yace "nayi magana da garwashi idan basuyi magana ba , da dare zamu kaisu baqin daji a harbe su duka, kukuma anan zaku tsaya har a qare aikin dan na gaji da magana d'aya kullum_ _ya kallo mahaifiyar tasa mami lets go kada daddy ya zama suspicious ya kama hannuta suka fice_ Tsakanin bello da hasheem rasa wanda ze tashi tsaye akayi duk idanunsu sun kad'a tamkar gauta ko wayanda suka shekara kuka, amma tsabar tashin hankali ne daya afka musu, bello ne yayi qoqarin sanar da dss bashari a kan plan din su hajiyar inda ya basu goyon baya hade da nema musu sojoji aqalla mota biyu zuwa uku, Hasheem kuwa kai ya sadda qasa cikin rud'ewa ba komai ke damunsa ba se tunanin halin da rayya zata tsinci kanta if she finds out about what her mothers doings, Ana cikin haka ne wayar bello tayi qara "Ammi" ya furta idonsa stick to hasheem's Daga can tace "my son ya kake?" Sama yayi da qwayar idonsa trying to maida hawayen dake neman zubo masa yace "am good ammin mu dafatan kina nan lafiya," Jinjina kai tayi cikin jan hanci tace " lafiya qalau ina tare da d'an uwanka with your cousin sis Samira" "Cous..in sis? Samira?.." Jinjina kai tayi tamkar yana kallonta tace "yes my son, ita d'in 'yar qanwata ce da ta 'bata mariya" Cikin zare ido yace "da..namadi?" "Yeah..shine amintaccen driver dinsu tare suka 'bata..." ta shiga yin kuka me cin rai, Numfashi ya sauke a zuciyarsa yana tunanin kenan itace ake cewa za a kashe tare da namadi anjima, wani kuzari yaji a jikinsa a fili yace "Ammi na ki tayani da addu'a dan 'yar uwarki ta kusa fita daga hannun mugayen nan, zata yi magana yace " Ammi zan kira ki anjima ki kular min da kanki, kice ma bro A i love him and tell Sam that i miss her" D'it wayar ta katse ido ya lumshe had'e da sakin murmushi, tsintar kansa yayi da farin ciki wanda be san dalili ba, tapping kafad'ar hasheem da ya zuba masa na mujiya yayi, "Lets go" Ya furta kawai ya nufi wane, cikin mota suka shiga basu tsaya ko ina ba se ofishin babban sona wato col. Kamal ibrahim (labarin aurena) inda suka zauna suna masu cigaba da kallon duk wani moves d'in jama'ar gidan through camera d'in jikin salihu. A can gefe guda kuma ss ke zagaye da ciki da wajen gidan governor dan kula da duk motsin hajiya maryam,. *** A can Birmingham cikin college Sam tun bayan zuwansu ke kwance ta gaza yin komai sa'ilin da munu ke kai kawo wajen shirya musu kayan su cikin wardrobe Kallon Sam tayi jin shirun nata yayi yawa tace "wai nikam meke damunki a tunanina dai tun ranar da muka baro kano kika gama kukan rabuwa d gwaggo, to yanzu kuma ko zan iya sanin abinda ke ja miki zubda hawaye?" Idanunta dake a lumshe ta bud'e tare da qoqarin zama cikin sanyin ta tace "munu bansan yanda zansa abinda nakeji into words ba, i can take the feeling away.." "Uhumm" munu tayi making sound with a questionable look Saukowa tayi daga gadon ta tsugunna a gaban munu "ina tsoron kada na saka zuciyata cikin hatsari" ta furta cikin damuwa "Subhanallahi hatsari fa, hatsari wani iri?" Cikin rawar murya tace "i have never been through this before, the only feeling da zan miki bayani ki fahimta is that of litattafen hausa da kike bani labari.." Kwashewa munu tayi da dariya pointing at Sam tace "Sam are you in love?" Jinjina kai tayi "deeply in love if i might say" Ihu munu tayi tana rawa tace "this is amazing sweetheart kinsan nima fa hakan ne ya faru dani na gaza furta wa ne dan kada kice am too young for it, kinsan dawa?..ko dake live it fara fad'a min naki? Tace sounding excited Sam ta girgiza kai, se na fara jin naki tukunna" "Tabb ai baki isa ba bayan kece kika fara yin zancen, dan Allah ki fad'a min kinji" A shagwa'be tace "munu manaaa" Hannu tasa ta kare idonta irin wai tanajin kunyar nan tace "Bro..B" Cakk duniyar ta tsaya wa Sam gabanta yayi wani irin bugu har seda ta dafe da hannu, tashi tayi da baya baya ta fad'a toilet, had'e da fashewa da kuka a hankali.. Can kum munu ta bud'e idonta se taga wayam Sam tashiga qwalawa kira "Shine kika gudu ko, zaki sameni ne inanan ina jiranki kizo ki fad'a min who the lucky champ is" Sosai ta jima cikin band'akin ko da ta fito ma sallah ta tayar da ta idar kuma ta rungume munu ta baya trying to act normal tace "nayi miki wayo, dama na kula tunda muka baro kano kike 'boyemin wani abu shiyasa nayi miki wayo" Ta juya a guje ta fita munu ta biyota suna dariya direct assembly hall suka shiga inda shugabar makarantar ke ma d'alibai barka da dawowa sabon term da kuma murnar zagayowa sabuwar shekara. To nima de kdeey ina taya dukkan masoya littafina dama kafatanin al'umma murnar sabuwar shekara *Happy new year 2020🥳🤸🏻‍♀💃🏻* ©️Kdeey😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (25) Iface ifacene ya maye gurbin maganar shugabar bayan data gama rattabo bayanai tare da kuma introducing malamai ga sabbin d'alubai, Haniyar da ta cika hall d'inne yasa taja gefen shiga corridor ta tsaya, kad'aici yasa ta tunanin abinda ya faru mintuna da suka shud'e "Bro..B" muryar munu ke mata yawo akai, taya akayi all this while bata fahimci inda 'yaruwar tata ta dosa ba? Hakan na nufin namiji d'aya suke so kenan, shin ya akayi na amincewa soyayyarka..bayan ni d'in banta'ba soyayyaba..,ido ta lumshe hawaye na cigaba da zuba, Gyaran muryar da akayi ne yasa ta bud'e idon a hankali, "handky" wata kyakkyawar yarinyar ta furta fuskarta d'auke da fara'a, kuma bud'e ido tayi dan kuma tabbatar da abinda take gani d'in shin dagaske ne? "Sholey" ta furta cike da mamaki da farinciki mixed together, jinjina kai tayi had'e da bud'e hannu tace "surprise" Fad'awa tayi jikinta cike da farinciki nan kuma kukan ya sauya zuwa na farincikin ganin qawartata. *** Bisa gadon ta suka zauna hannunsu a sarqe bayan fitar munu daga d'akin ta zayyana mata halin da take ciki, shiru sholey tayi kan tace "zaki yarda idan nace miki cikin labarin ki ba komai se zallar tausayawa da ganin qima? Sam you are just sixteen for goodness sake, kar ki bari wannan shirmummukan su kanainaye ki su tauyeki, yanzu ba lokacin soyayya bane, kiyi amfani da quruciyar ki kan tsufa yazo miki, nasani you are a human dole ki so opposite gender d'inki, amma b yanzu ba, Kuma ni duk cikin zantukan ki ba komai se zallar tausaya masa da kike saboda yanayin hidimar da yake dake, look we are in this environment to gain knowledge pn how to build our world nan da shekara biyu you will be freed up so lets use our time before its too late" ta qarashe da d'aga mata gira Kai ta d'aga a sanyaye kan ta sulale ta kwanta saman pillow, tabbas Bro B ya mata halacci a rayuwa tun da har ze iya kashe aikinsa ya koma kula da ita shin dagaske tausayinsa ne yayi rinjaye a gareta? Da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita. Sautin kiran sallar dake tashi a wayarsa ne ya tada shi daga nannauyan baccin da yake miqa yayi had'e salati idonsa ya sauka saman agogo dake maqale jikin bango, 2:00pm tashi yayi ya nufi d'aki yayi alwala yayi sallah sannan ya waiwayi office, *** Cikin ikon Allah suka isa gida sede shigar su keda wuya sukayi kici'bis da ita, ganin suna muzurai yasa tace dasu "mami, yaya kune yau a tare qarqashin inuwa d'aya, lallai za'ayi ruwa da qanqara" Hannu ya kai mata "ke dan ubanki ni sa'anki ne ko mami tsarar wasanki ce da zaki tsare mu da tambayoyi" Cuno baki tayi, "to ba gskiya bane abinda kullum fad'a kuke" hannu ya kuma kai mata da niyyar mangareta tayi saurin 'buya a bayan mami, Ya nunata da yatsa zan kamaki ne" Hararar sa tayi daga bayan mami bayan ya fice ta fito tare da zama kusa da mami tamkar zata shige jikinta, Tace "mami daga ina kuke haka jikin ki sanyi?" ta d'an d'ago tana kallon ta, d'auke kai hajiya maryam tayi cikin qoqarin kauda zancen tace "Rayya bansan tambayar kurum da Allah, daddyn ku ya shigo daga office?" Gyara zama tayi had'e da d'aga kafad'a "yeah...amma yana shigowa CP ya kirasa naga ya fita" "Ya fita? Shi da wa?" Tace cikin son ji, "Oh mami nifa ban sani ba, call and ask him" t tashi har ta fara tafiya ta waiwayo "yawwa i forgot mahaifan hasheem are coming" "Duk wani abu me muhimmaci is stick in here" ta nuna kanta da yatsa kan ta cigaba da cewa "so i see no reason da zan manta da neman auren 'ya ta" ta qarashe tana me d'aukar jaka ta shige d'aki. Halim ta kira tana kuma jaddada masa kan fitar su ta anjima da cewa ya shirya ta a sirrance, bayan ta ajiye wayar ta shiga to and fro a ranta tana ayyana cewa lallai ne su qarasa hajiya mariya da namadi a yau dinnan kan su maida hankali gun kabiru da yaronsa tun kan dss su gano she's behind all this, murmushi tayi me sauti a fili ta furta "lallai nasara na tare dani" ta bushe da wata iriyar dariya. Ita kuwa RayyaLumshe ido tayi game da kya'be baki ta wuce d'aki da niyyar kiran hasheem. ☆ Dss bashari, col. Najib (labarin aurena), tare da bello ne ke zaune a office d'in Najib suna shirya yanda operation d'in ze kasance, knocking a kayi bisa door "Yes" najib ya amsa, wata budurwa me matsakaicin kyau ta leqo "sir me girma governor ke neman iso" "Let him in×2" Suka miqe a tare dan girmamawa a daidai lokacin da jamilu mainasara ya shigo, sara wa najib yayi fuskarsa d'auke da murmushi, "your excellency sir" auka furta hakan a tare , da hannu ya nuna musu "pls have a seat" Sabuwar gaisuwa suka kuma yi, yace "Anwar right?" Yace idonsa kan fuskar bello, Hasheem ne ya amshe da cewa "qaninsa ne bello" "Uhum? Yeah se yanzu na kula wancan be kai wannan haske ba" "Yes sir " bello yace in a low voice. "Hasheem ya wajen manya" "Lafiya qalau sir" yace cikin shafar kai cike da kunya, jinjina kai yayi kan ya tattara hankalinsa kan col Najib, Yace "colonel akwai labari ne, dan daga ni had'uwar nan taku waje d'aya akwai magana" Dariya col najib yayi "we all went to thesame institute" Gira ya d'aga had'e da karkace kai yace "hmm, shi kuma wannan (hasheem) shine siriki na" Jinjina kai najib yayi "Masha'Allah Allah ya sanya alkhairi, hasheem nada kirki qwarai, se fatan Allah ya sa albarka" Cike da farinciki ya amsa da Amen×2. Shiru ne ya ratsa cikin nutsuwa col najib ya fara jawabi " your excellency sir ina me baka haquri a kan neman gaggawa da ka samu tare kuma da taso ka da mukayi cikin sanyin yamman nan dafatan za'ayi mana afuwa?" Girgiza kai gov jamilu yayi da hannu yayi masa alama ya cigaba ba komai, "ahm ur excellency sir wannan abokai nane bello da hasheem sunzo min da wani batu ne wanda ya shafeka hakan yasa naga abinda yafi kamata shine ka sani," 'Dan had'e fuska yayi had'e da jinjina kai yace "ina saurarenka" Nan suka zayyana masa duk abinda ke faruwa, lokaci d'aya gumi ya shiga karyo masa, fararen idanunsa suka kad'a zuwa ja, Murmushin daya fi kuka ciwo yayi "wato maryam bazata ta'ba canza hali ba" ya kalli najib da bashari Ni gomnati na bazata ta'ba d'aga qafa ga duk wanda ke neman kawo naqasu ga alummata ba saboda haka ina me umartar ku da kuje ku kama first lady da yaronta halim, inaso ku toshe kunnuwanku ga duk surutun da zeje yazo, haka kuma inaso hasheem ka tafi da motar ambulance a bawa mariya da yaronta taimakon gaggawa, kai kuma bello inaso ka kira min d'anuwanka da duk wanda kuka san maganar nan ta dangance sa dole a fasa kwai ko zuciyata ta samu sukuni" Ya tashi tsaye "inaso yanzu ba se dare ba a kamo duk wanda ke da sa hannu a alamarin nan" ya fice muqarrabansa suka mara masa baya, Ya bar su zaune cikin qullewar kai, hasheem da wayarsa ke ta haske ya duba ganin sunan Wife kamar yanda yayi saving yasa shi sauke ajiyar zuciya game da picking ya fita varender, Dss bashari ne ya fara miqewa yace "bari mu kamo 'yan daban can mu garqame se mu had'u a can gidan sirrin" "Hakan yayi, nima bari na sanar su shirya motoci" ya fita. Bello kad'ai ya rage zaune kansa yake murza wa dan ji yake yayi wa jikin sa nauyi, a hankali yasa hannu ya shiga dialling number Ammi *** "Bello lafiya naji muryarka haka" tace hannunta riqe da serving spoon da ta gama zubawa Anwar soup dashi, Kasa riqe kukan yayi har seda ya fito, cikin rawar murya yace "Ammi na mummyn Sam na raye..." Ludayin hannunta ne ya su'buce ya fad'i jiki na rawa tace "bel..lo me kake cewa?" Jinjina kai yayi "yes Ammi, ina da tabbacin hakan, yanzu haka a yau zamu qwato su daga hannun azzaluman da suka 'boye su" Wani marayan kuka ne ya kufce mata, Anwar yayi saurin amsar wayar yasa a kunnen sa, "Bro mekake cewa ne?" Fad'a masa yayi duk yanda sukayi, yace kuma yayi qoqari su taho nigeria cikin satin nan, haka kuma me girma governor yace a taho da dukkan wanda abin ya shafa. *** Sanye take da doguwar riga irin ta sudanese d'innan kalar ruwan qwai, kanta yane da mayafin kayan tayi turban yayinda kunnenta ke maqale da earpiece qira'ar sudeis ke tashi cikin suratul baqrah Ba bacci take ba, dan har tana iya jiyo hirar sholey da munu, gyara kwanciyarta tayi had'e da jan blanket ta rufe fuskar ta dan sam bata son sauraren zancen nasu. Wayarta da tayi haske ne yasa ta dubawa, _"tafiya ta kama mu, kiyi mana addu'a"_ _waye?_ tayi reply _mijin ki_ Taga an turo, had'e fuska tayi had'e da jan tsaki, ta ajiye wayar. Bubbuga qafarta sholey tayi, ta bud'e fuska, "Ke da wa kike jan tsaki haka?" "Nothing..is just that nagaji da zama kuma banjin karatu yanzu" "To kece ai kin wani kwanta, ki tashi muyi hira kin qi" "Sholey ba haka bane ke da munu baku da aiki se hirar soyayya, gara ke shattima yasan kina yi, ita kuma she's always day dreaming and i have no business with it all, hasalima ba saurayin nake dashi ba" 'Dala mata duka munu tayi tana dariya tace "Allah ya isa, insha'Allah wannan mafarkin da kike raina wa soon ze zamo gaskiya, ke kuma your husband will soon knock on your door" ta qarashe tana me kanne ido, Dariya sukayi duka, a shagwa'be tace "bazaku gane ba jikina ke min ba dad'i yau kamar wani abu na shirin faruwa" Sholey ta dakatar da ita da cewa "Heyy why bored bayan kina da ni, yalla ku zo muje yawo" Taja hannuwansu, "ina?" Sukace a tare, "school tour" ta amsa su riqe da hannun juna suka mara mata baya. *** "Meke faruwa ne your excellency?" Hajiya maryam ta furta a rikice "Take her away" yace ba tare da ya ko kalle ta ba, Macen soja ce ta matso kusa da ita "ur excellency please ki bamu had'in kai ta yarda komai ze zo mana ta sauqi" Hannu ta d'aga cikin zare idanu tana yin baya baya "keh kinsan kuwa ni d'in ko wacece i'm the firstlady of this state so babu wanda ya isa ya kamani" ta fad'a cikin karaji, "Maryam!" Gov jamilu ya furta a hasale "Ina me umartarki da ki basu had'in kai suyi aikinsu, kada ki bari nasa baki!!" Gaza furta komai tayi se rawar baki da take, daidai lokacin da Rayya ta fito, bin sojojin da sukayi cirko cirko da bindiga tayi a gefe guda kuma mahaifiyarta ke durqushe a qasa tana kuka, mahaifin ta kuma na tsaya can gefe daban ya juya musu baya ga halim sanye da ankwa hannu da qafa, A guje ta qarasa shigowa falon cikin inda inda ta rasa ma ina zata nufa, "daddy" ta dafa shi ta baya, waiwayo wa yayi yana me girgiza mata kai Yace "col kuje dasu, idan wayanda nake jira sun iso zan shaida maka, but please kamar yanda mukayi abinnan a sirrance inaso mu barshi a hakan" Sara masa col yayi tare da bada umarnin a tafi dasu, sede tun kafin su gama fita Rayya ta yanke jiki ta fad'i. Juyowa hajiya maryam tayi a guje tayo kanta, a tsawace gov yace " i said take her away" nan da nan akayi waje dasu, a take ya kira asibitin cikin gidan gomnatin aka shiga bata taimakon gaggawa, inda aka tabbatar da suma ce kawai nan da rabin awa zata farfad'o A can gidan barrister kuwa bello, barr, gwaggo da mom hajar ke zaune jugum jugum tun bayan da bello ya gama zayyana musu abinda ke faruwa ya kuma ce dasu nan da zuwa lokacin da me girma gomna ze neme su babu me fita daga gidan ciki har da yaran gidan. A can kuma hasheem ke zaune cikin motarsa gefensa ambulance d'in get well ce, daga inda yake yana iya jiyo qarar bindiga da qurar dake tashi zuwa can yaga ana firfito da mutane sanye d handcuffs, alamar da aka yi masa da hannu yasa shi bada odar a shiga da gado a fito da majinyata Cikin wani underground building cikin wani d'an qaramin d'aki me dubun gaske da yafi kama da cage aka zaqulo hajiya mariya wacce idan ka gani zaka rantse skeleton ce aka aza ta saman gadon aka fita da ita, namadi ma haka aka d'auko shi aka tafi dashi, Duk dauriya irin ta sojoji seda suka zubda qwalla ganin halin da suke ciki, haka ma hasheem dake basu taimakon gaggawa se faman shedding tears yake dan gaba d'aya ya kasa controlling hawayen. ©️Kdeey😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (26) _pray for me please ,..i'm sick🥺_ *kano state prison* Gidan masu laifi, wasu mata ke ta aiki a saman duwatsu, yayin da wasu ke zaune cincirindo guda suna hira wacce kashi 30/100 batsa ce, can gefe guda kuma wasu ke yashe a qasa irin wayanda idan suka jigata suka yanke jiki su fad'i saboda tsananin gajiya. Bulala ce riqe a hannun wata daga cikin masu basu tsaro tana shad'ad'a ma wasu daga cikin wanda ke yashe a qasa dan a ganinta qarya suke aikin ne basa so, Gefe guda umma salamatu ke zaune duk ta fita a hayyacinta wannan jikin duk babu d'an hasken ma yanzu babu shi se baqi da kayan qasusuwa, hannayenta tallafe da fuskarta hawaye na zuba daga idanunta girgiza kai tayi game da ajiyar zuci a fili take fad'in "oh ni salamatu×2 mahaifina ya yafe ni cikin yaransa tun sa'ilin da nayi wa matarsa dukan tsiya yace na bata haquri naqiya, mahifiyata shekararta shabiyar a cikin qasa, danginta duk sunqi waiwayo ni tun bayan da naci musu mutunci a tunanina tunda mijina nada arziqi to zan iya taka wuyan kowa, mijina maji'bancin al'amurana son duniya irin tawa yasa shi datse igiyar auremu d'aya , yaro na Ameer na d'ora shi bisa muguwar hanyata gashi ya 'bige a firsun, a yanzu haka banson a duniyar da yarana suke ba, ko hajiya maryam data yi ikirarin ganin bayan su taci nasarar hakan? Ko kuwa?, kaico na ni salamatu son duniya ya kai ni tashar dana sani" Wata iyamurar mata irin masu kula da masu laifi d'innan ta kalle ta tana girgiza kai dan taji duk abinda take fad'a, ciki da tausayawa Tace "dukkan ku da kike gani anan shed'an ke rinjayar ku, gara ma ke kinsan zaki fita, da yawa anan sede a fidda gawar su? Kinga meye ribar kenan? Ina me baki shawara duk da bansan kalar lefin ki ba, da ki amfani da lokacin ki anan ki nemi gafarar ubangiji dan rayuwa yanzu ba ta da tabbas, mutuwa kuma bata neman shawara" Kukan tane ya dad'u, cikin sanyin murya tace "nagode da shawara insha'Allah zanyi yadda kikace d'in", tun kan ta rufe baki aka shiga qwala kiran batch C grp dinsu kenan, kallon matar tayi had'e da miqewa ta nufi gurin aikin da Allah kad'ai yasan ranar gamawa. *** Hannunta biyu tasa tana jijjiga qofar cell d'in ciki karaji take fad'in "Ku bud'e min qofa nace! Tun kafin ku gamu da fishina, shin ko kunsan ni d'in wacece..." "Her excellency hajiya maryam jamilu mainasara..or let me just call you kidnapper..tsk tsk tsk uwardaba suits you best.." Ido, hanci, baki duk ta saki cikin rawar murya tace..." your excellency dan girman..." "...dakata maryam!! Wullahi tallahi bazan ta'ba yafe miki ba har gaban abada! Kuma ki sani bawai zan sawaqe miki bane i will keep you hostage sede ki sani le da dabba a wurina babu maraba! Ki shirya abinda zeje yazo" da fad'in haka ya juya ya fice cikin qunar rai, Allah kad'ai yasan meke zuciyar shi. Bayan kwana biyu... "Ammi duba yanda duk kika fita a hayyacinki dan Allah ki kwantar da hankalin ki..." "Ann...mariya...tana raye cikin qunci da wahalar da Allah kad'ai yasan adadinta for almost 13 to 14 years ya kake ganin halin da zamu same ta ciki..." "Ammi bro B yace she's fine and fine means fine insha'Allah, so please muje ki zauna a motor na janyo trolley mu tafi kada muyi missing flight" Cikin zubar hawaye ta girgiza kai, shi kuma ya koma ya janyo kayan, bayan yasa cikin booth ya nausa motar bisa kwaltar dake shimfid'e cikin company d'in. Hannu tasa ta d'auka wayarta dake vibrating mss patricia tagani nan da nan ta murmusa kan ta qaga a kunne had'e da sallama "Ammina.." ta furta in a shaky voice, "Sam my daughter, how are you?" "Good, ammi kina lafiya?" "Same here, i'm on my way to the airport" "Airport? Ammi ina zaki tafi ki barmu?" Ido ta lumshe cikin kukan zuci a fili kuwa cewa tayi "nigeria sweetheart zanje ganin bello i will be back in 2days insha'Allah" "Ammi kizo muyi sallama pls inaso na ganki" Hannu tasa ta matse idonta had'e da jan hanci ta kalli Ann, "can we make it? Ina so mubi ta saint teresa" Kai ya d'aga tare da juya akalar motar zuwa titin da ze kai ka makarantar, "Gamu nan zuwa" Kai ta d'aga kamar tana gabanta, ajiye wayar keda wuya munu ta fad'o d'akin, kallon mamaki ta bita dashi ganin tana ta faman cleansing face d'inta fara'a kwance saman fuskarta , tamkar ba ita ce ta bari kwance magashiyan ko lectures ta kasa zuwa. Kula da irin kallon da munu ke mata yasa ta juya qwayar ido tace "fine naji sauqin jiki na ne, and yes ina goge face d'ina coz banson Ammi ta ganni wani iri" Ido wide open munu tace "is she coming.." Kan ta bata amsa wayarta tashiga ringing nuna mata screen d'in tayi game da cewa "yes ta qaraso" light yellow veil kalar atamfar jikinta ta yane kanta dashi, tasa hannu ta amshe littattafen hannun munu ta ajiye game da jan hannunta sukayi waje. Tun daga nesa yake hango fararan hakwaranta garai garai tamkar qanqara, murmushi yayi me kamar ajiyar zuciya yayi crossing leg d'insa daga tsayen da yake kusa da kujerar Ammi ya rungume hannun hagunsa a qirji yayin da hannun damansa ke tallafe da fuskar sa yana tapping hancinsa da yatsa (manuniya), Na mujiya ya zuba mata from head to toe ya shiga qare mata kallo, takalmi ne flat sanye a qafarta shi ba lemon green ba haka kuma ba yellow ba, skirt ne pencil wanda ya fallasa dukkan wani curve na jikinta, yayin da idonsa ya sauka saman rigar jikinta kuwa taune lips d'insa ya shiga yi game da had'e rai, lips d'inta dake kyallin farin lipbalm kuwa seda ya sashi d'auke wuta na wani d'an lokaci, idanunta da sukayi d'an jaja-jaja ya qurawa ido ta rame shine abinda yayi crossing mind d'inshi bata da lafiya ne? Ba amsa , gaza d'auke idonsa yayi daga kanta sema gyaran murya da yayi yashiga amsa gaisuwar da suke masa, Rungume take jikin Ammi suna sallama, bayan ta d'agata karaf sukayi ido hud'u, tsintar kanta tayi da son kallanshi wanda hakan yayi mutuqar faranta ransa ko banza he will be able to look into those white and black balls she's the definition of beauty zuciyarsa ra fad'a masa hakan a tare suka d'auke kai, Ammi ta d'anyi dariyarsu irin ta manya, idonta a kan munu da itama ta kula da kallon kallo da suke, "Munu zo ki raka ni gurin mss chloe mu gaisa kada tace nazo ban leqata ba" Kai ta d'aga tana satar kallonsu, "Ammi bari na b..." "No kuje muna jiranku" yace his eyes still fix on her's, Tura baki gaba tayi idonta akan hanyar da suka bi, Yatsa ya d'alla mata saman lips ta saki wata kasalalliyar qara , cikin kunnenta yace "kinci sa'a Ammi is around da se nayi punishing bakin rashin kunyar" ido ya lumshe lokacin da hancinsa ya shaqi qamshin gashin kanta har be san lokacin daya furta "Wani irin turare ne wan..nan?" Dad'a runtse tayi kanta setin qirjinsa cikin sarqewar murya tace... ©️Kdeey 😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (27) "..ou..dul arab.." ta qarashe maganar cikin in-ina, girgiza kai yayi har sajen shi na gogar gefen fuskarta, jin da tayi kamar taku na tunkaro su yasa tayi saurin tura qirjinsa da hannu, taja baya tana sauke numfashi kanta a duqe tamkar mara gaskiya "Ann muje ko?" Numfasawa yayi game da bud'e lumsassun idanunsa, "yea, muje Ammi na" Murmushi tayi masa kan ta maida kallonta gurin Sam, miqa mata hannu tayi "muje ki rakani kinji samira na" Cikin sissinna kai ta zira hannunta cikin na Ammi suka nufi wurin mota, tsayawa tayi game da waiwayo wa cikin sakin qaramar dariya tace "munu wai meye sirrin ne naga se qiba kuke yi kamar ana hura baloon?" "Laa Ammi wlh babu komai, sede ko weather d'in garin ne ya amshe mu" "Shiyasa kuke qiba kenan?" "A a Ammi fa yinwar ganin kice ni dai take sani qiba" ta qarashe a shagwa'be, jan hancinta Ammi tayi "eh shiyasa naga kin tsaya gun d'anuwanki baki bini ba" Ji tayi tamkar qasa ta tsage ta shiga ga wani tsananin fad'uwar gaba da taji, 'ko de Ammi na zargin wani abu ya kuma faruwa tsakanina da bro A' rau rau idonta ya ciko da ruwa, jan hanci tayi idonta a qasa cikin muryar kuka tace "Allah Allah Ammi.." Gyaran murya yayi idonsa kan fuskar Ammi yace "mami mun kusa latti" Gyad'a masa kai tayi, kallon sam tayi cike da qaunar gudan jinin 'yaruwar tata tasa hannu ta goge mata fuska tana girgiza mata kai, Se da ta zauna tace dasu "to yanzu de na kauda yinwar ko, se ku maida hankali sosai a karatun ku dan mss chloe ta shaida min cewa soon zaku yi exam so ku dad'a riqe damtse kunji, make us proud uhm" suka jinjina kai "Insha'Allah Ammi" "Good, Allah yayi muku albarka" "Ameen" A sanyaye tace "Ammi.." "Uhm, samira na" "Bansan meyasa ba inajin wani iri tamkar wani abu na shirin faruwa, kuma kwana biyu bana mafarkin daddy na da haske" Jimm Ammi tayi cikin tunani kan tace "khairan insha'Allah, ki yawaita salati koma mene Allah ze maye shi da alkhairinsa, daddyn ki ma ki yawaita masa addu'a akan wacce kike masa" Kai ta jinjina, a tare sukayi musu addu'ar sauka lafiya, suna nan tsaye har seda motar ta 'bacewa ganinsu. *** Kimanin awanni biyar kenan da su kayi transit a Dubai, cikin wani restaurants dake cikin airport suke zaune Ammi is busy with her coconut milk shi kuma yana zaune ko kwanciya za'ace idonsa lumshe yana sipping watermelon drink Daga inda take zaune ta shiga leqen fuskar sa,"is everything okay Ann?" Firgigit yay, yana qarasa had'iye lemun bakinsa "bbbakomai.." Jimm tayi kan murmushi ya maye fuskar ta, "do you really love her this much?" Saurin kallonta yay tamkar wanda aka tsikara, kan ya hau kame kame irin na marasa gaskiya, qwayar idonsa ya sauke saman agogon rolex dake saqale da hannun sa yace "Ammi remain 20min jirgi ya tashi lets go" ya ajiye lemun yayi gaba da sauri yana susar qeya, bin bayansa tayi da ido murmushi maqale da fuskarta tana jin wani irin farinciki cikin ranta. *Kano Nigeria* Hannu biyu tasa ta tallafi wayar dake kunnenta, cikin muryar kuka take fad'in "doctor mami na,.." Hasheem dake tsaye jingine da qofar d'akinsa cikin tashin hankali yace "Rayya, calm down please kinsan condition d'inki..." "How the fuck do you want me to calm down bayan mahaifiya ta na cell.." "Babe tsaya ki saurareni ba nufi na kenan ba, i assure you mahaifinki baze ta'ba bari ta wuce daren yau ba.." "...kaima ka fad'a daren yau amma ta kwana a qasqantaccen wurin nan ai ko! Can't you get it! Damn it" ta katse wayar had'e da fashewa da marayan kuka, cikin kuka take fad'in "na zata kaine wanda zaka sharen hawaye na in my tough time ashe i am wrong, meke faruwa ne?" tashiga dukan goshinta da hannu. ~ Cirko cirko suke cikin cell d'in ko wannen su na hura hanci, aqil cikin qunar rai ya kaiwa salihu duka a hanci nan da nan kuwa jini ya hau zuba, Durqushewa yayi, kan ya d'ago shima ya kai masa dukan "me nayi maka da zaka kai min mazga" "Kana so kace ba kai bane ka nuna masa hideout d'inmu ba!" Nan f kokowa ta kacame tsakaninsu, Nafi'u ya daka musu tsawa, "dalla malamai bama san burr*uba, taya muna cikin wannan halin kuke neman yi mana hauka, wlh dan na katse muku rayuwa yanzu ba matsala bace a wurina, shashashai" "Oga na rantse da kabarin tsohona wannan shegiya ce, ba kiga yanda ya zama qawar corper ranan ba, he is the one that told him our secret, na tabbata" cewar rody "Kai dalla ware qasurgumin kafiri," salihu yace cikin zare idanu, kan su kuma cewa komai bello da bashari suka bayyana a gaban cell d'in Bro b yayi smirking game da tafa hannu, duk suka maido hankalinsu gareshi, cikin had'e rai yace "ku dena zargin d'anuwanku domin ni da kaina na gano kud'in su waye tun kafin nazo gare ku.." Dss bashari ya d'ora da cewa "and again idan kuka bari na qarajin muryarku sena sa an datse muku mafitsara" One sided murmushi bro B yayi suka bar wurin dan dama suna tattaunawa ne suka jiyo hayaniyar su, *** Washegari Gwaggo tace "hajar zaki iya fitar nan kuwa? Ko cikin ne mu tafi asibiti?" Girgiza kai tayi fuskarta kadaran kadahan, tace "a a gwaggo karki damu muje zan iya" Hannunta gwaggo ta kama suka shiga motar bello dake tsaye yana jiran su, ba wanda yace da wani uffan tun bayan gaishesu da yayi, "Ni kuwa bello lafiyar ka lau kuwa naga duk ka fad'a" 'Dan kallonta yayi cikin murmushi kan ya maida kansa titi yace "bakomai gwaggo kawai aiki ne da ya sakani gaba" "Ashsha shiyasa baka zama gida sosai, Allah ya dafa maka" "Ameen gwaggo, nayi kewar addu'oin ki" "Haba ai babu ranar da zan d'ora goshina a aqasa batare da na sakoku a addu'ata ba, Allah de yayi muki albarka" "Ameeen" yaja word d'in dai dai lokacin ya juya akalar motar zuwa state road, "Wash wash wash bayana" A firgice gwaggo ta waiwaya ganin yacce mom hajar ke botsare botsare ga gumi na karyo mata tako ina yasa ta cewa "bello inaga mu fara zuwa asibiti da alama haihuwa ce" "Wayyo gwaggo bayana, wayyo...dan Allah ku kira min bar..ris..ter" *** 'Dakin haihuwa aka shiga da ita, yayin da bello ya fita zuwa gida ya d'auko kayan da ta had'a dan zuwan wannan rana, be jima da kawo kayan ba ya fita ya taho da uncle, dan be fita da mota ba, gwaggo kuwa ta kasa zaune ta kasa tsaye dan tana iya jiyo ihu da salatin da take. Wucewar awa biyu kukan jinjiri ya karad'e harabar, ba a jima ba aka fito da baby nad'e cikin shawul, Cikin zubar qwalla gwaggo ta rungume shi a jikinta daidai lokacin da su uncle suka shigo, babyn bello ya kar'ba dan uncle d'akin da take kwance ya shiga dan duba lafiyar matarsa, "Gwaggo ki kalla kamarta d'aya da uncle sak" Kai ta jinjina, bari na gano lafiyar ta" kan ta rufe baki uncle ya fito a rud'e yace "hajar is no where to be found" "Kamar yaya?" Cewar gwaggo, kan ta fad'a d'akin a rud'e, har labule ta d'aga babu alamunta, daidai lokacin uncle ya umarci bello ya kira 'yan sanda dake kusa yanzu. *** Yatsa tasa ta d'auke hawayen idonta, game da kauda kai gefe, Hannu yasa ya riqo hannunta yace "Ammi.." Murmushi tayi "Ann rabona da garin nan tun lokacin da mariya ta 'bata" taja numfashi Tapping hannunta yay, ta kwanto da kanta saman kafad'arshi a hankali ta furta "nayi kewarta sosai" Smiling yayi tunawa da wayar su da bello kwana biyu da suka wuce. "Government house" tayi pronouncing a fili, kai ya d'aga yace "Ammi pls do me a favor" Kallon meyasa ta mishi, murmushi yayi "duk tambayar da zaki yi zaki samu amsar ta idan muka qarasa ciki" waya ya zaro a aljihu ya kira layin Bro B har sau uku be d'aga ba kasancewar ya barta cikin mota ya shiga police station. Hasheem ya kira, ya sanar dashi suna waje yace gashinan zuwa, Kan ya qarasa rufe baki yaji d'iff wayar ta mutu, ba sufi minti uku a wurin ba ya iso, Ammi ya gaida cike da farinciki" fad'awa yayi jikin Anwar game da fashewa da kuka, "I missed you, how have you been?" 'Dago shi yay "I'm fine, kamanta ina tare da Ammi" kai hasheem ya jinjina cikin share qwalla yace "lets go in" Cikin motar suka koma driver yaja su cikin gidan gomnatin, cikin babban falon baqi suka shiga "Ammi bismillah, yanzu ze fito" Gaza riqe mamakinta tayi tace "hasheem wai meke faruwa ne, me muke yi anan kuma wanene ze fito? Ina bello?" Kallon juna Anwar da hasheem su kayi kan su kai ga yin magana sallamar da akayi ta ja hankulansu suka amsa daidai lokacin data juyo da niyyar ansawa sukayi ido hud'u, Ido ta zuba masa tamkar me son karanto wani abu a jikinsa a hankali tace "Jamilu mainasara?" "Hajjo dafatan kina lafiya" "Kunsan juna ne?" Anwar ya tambaya cikin rawar murya Numfashi ya sauke , "ita d'in 'yar uwace ga matata" "Matar ka?" Ta kuma tambaya cikin mamakin da yaqi sakinta Murmushi yayi me kamar yaqe "matata wacce kuke mahaifi d'aya" Ido waje tace "kana nufin sadiyar inna ramatu?" Kai ya jinjina game da miqawa Anwar hannu "the great CEO AB machinery" Shaking hannu sukayi, "ya akayi hakan ta faru? Kuma a ina ka gano su dan iya sanina har mahaifinmu ya rasu ba a samu gurin da suke ba" Ammin tayi adding "Duk zan warware miki zare da abawa amma zanso mu fara dubo halin da patients d'inmu suke ciki, bismillah" Jiki a salu'be suka mara masa baya zuwa wani d'aki, da isar su jikin Ammi ya hau rawa da ta qarasa bakin gadon kuwa yanke jiki tayi ta fad'i.. ©️Kdeey😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (28) "Ammi!" Suka yo kanta a rud'e, ruwan dispenser hasheem ya tsiyayo cimin cup Anwar ya rinqa shafa mata samn fuska zuwa wuya, cikin hikimar ubangiji ta farka bakinta d'auke da sunan "mariya.." tashi tayi ta tsugunna setin fuskar ta, tasa hannu tana shafawa had'e da fashewa da kuka, "Yanzu wani mara imanin ne ya maida ki haka? Shine yanzu ina ribar take ? Innalilllahi wa inna'ilaihir rajiun" Kafad'unta ya riqo cikin kwantar da murya yace "Ammi ki bar kuka dan Allah mummy zata samu lafiya insha'Allah, ai duk wanda yaci zalin wani Allah ba ya barinshi, a yanzu haka mutanen da suka yi mata haka suna hannun hukuma, yanzu haka dalilin zuwan mu garinnan me girma gwamna ya nemi presence d'inmu dan warware abinda ya jima a rufe kamar yacce yace" With cold eyes ta kalli governor "jamilu who is behind all this?" * "Doctor i'm sorry to say dole zamu rufe asibitin nan har zuwa mu gama binciken mu, Alhaji kai kuma inaso kayi hakuri kje gida da jaririna nema masa abinci , ku saka mishi ankwa muje" "Wannn shine laifin banjiba ban gani ba, nashiga uku" cewar d'aya a ciki nurses d'in asibitin, "Ku dakata yalla'bai" Juyowa yayi "yes" "Amm i think i know where she is" Kallon kallo akayi, kan ya nuna mata hanya alamun muje to, nurse da doctor suna motar yan sanda yayin da bello a motar sa shi, uncle da kuma gwaggo ne se jinjirin dake hannun gwaggo. Tafiyar minti qalilan ya kaisu doctors quarters qwanqwasa qofa tayi daka ciki aka ansa da cewa ana zuwa, Wata dattijuwar mace ce da bazata wuce 50-60 b ta bud'e baki ta hangame, nurse d'in ta girgiza mata kai, kaucewa tayi gefe suka shiga, 'Daki nurse d'in ta shiga zuwa can ta fito hannunta riqe da mom hajar dake ciccije baki saboda ciwon jiki, Sairin miqewa uncle yayi ya nufo ta, "bawan Allah kada ka ta'ba ta dan kuwa kai d'in azzalumi ne!" Maganar nurse d'in ta razana zuqatan kafatanin mutanen dake falon, "sister nasira kinsan me kike cewa kuwa?" Doctor yace a tsawace, Idonta ta sauke bisa fuskar mom hajar tace "d'azu bayan an tafi goge baby _turo d'an teburin allura nayi zuwa bakin gadon da take, sannu nayi mata, na shiga zuqo ruwan allura d zummar nayi mata naji an riqo hannuna "kina buqatar wani taimako ne ko wani na damunki?" Girgiza kai tayi "inaso ne ki cece ni" "na cece ki" nayi mumushi kawai dan a tunani na ba'akan cikin hankalinta take ba, tsikara mata allura nayi bayan nagama dubata na juya zan fita ta riqo hannuna, "idan ban gudu daga nan ba kasheni zasu yi", "suwa?" , "mutanen da suka kawo ni, mijina d'an yankan kai ne, jira yake na haihu ya kashe ni saboda wai amfani na ya qare a wurinsa", "let me call the police", hanani tayi a cewarta megidan nata nada mutuqar hatsari na bari ta bar asibitin idan ta samu lafiya se nayi reporting, shine dalilin daya sa nayi snicking out da ita na kawo ta gidana_ wannan mahaifiyata ce dana ce tayi mata wanka kan na dawo musan abinyi, Qasa uncle ya durqushe, baki bud'e, gwaggo kuwa salati take da sallallami nan bello yayi musu bayanin yacce suke da ita har da irin sana'ar uncle d'in haquri aka bawa juna doctor da yansanda suka tafi, gwaggo ta matsa kusa da ita "Hajar a d'an zaman da mukayi zan iya rantsewa kina da hujjar yin wannan qaryar, sede ki sani qarya ba abar wasa bace tun bare irin wannan qazafin, bakya gudun abinda zeje yazo bare yanzu yanda duniyar take, 'barayi, kidnappers, masu garkuwa da mutane duk neman sunake ido rufe! Meyasa meye dalilin ki na yin hakan?" Kukane ya kufce mata me cin rai kan tace "na rantse da Allah gwaggo ba nayi haka bane dan cin zarafin barrister se dan kunyar abinda na aikata masa" Jimm gwaggo tayi kan ta kalli barrister dake tsugunne idonsa a kan hajar tace "shikenan inaga ya dace muje gida a qarasa maganar nan, ungo babyn nan kayi mata addu'a" A salu'be yasa hannu ya kar'beta "sedai ba dabino" yace "Kash kaga kuwa mantawa mu kayi ba mu saka ba" "Karki damu hajiya inada zamzam bari na kawo" "Ah zam zam? Dama ana iy amfani dashi madadin dabino?" Cewar gwaggo Bello ya gyad'a kai "eh, a littafin fada'ilu ma'u zam zam sahafi na 29 malamai sunce annabin rahma ya d'iga zam zam a bakin yaro, ko zuma a d'ugawa yaron a bakinsa ko a d'uga a bakin musulmi ya gauraya da yawunsa sannan a d'iga wa yaro" Gyad'a kai tayi game da cewa "akwai zumar addu'a cikin jakar ki hajar wacce na baki ki rinqa lasa ko" Mom hajar dke shedding tears tayi nodding kanta a qasa, jakar gwaggo ta janyo ta miqa wa barrister ya saka cikin bakinsa yasa wa yaran a baki, mulai mulai kuwa ya mamule, yay masa kiran sallah a kunnenta na dama game da miqata gurin gwaggo daidai lokacin da wayar bello ta karad'e falon da qara, Sunan Bro A yayi appearing saman screen d'in yay saurin answering, "Gamunan qarasowa" yace game da hanging off, "Ina ganin ya kamata mu wuce goverment house dan tuni su Ammi sun qaraso" Barrister ya kalli sashen da mom hajar take a hankali ya taka zuwa inda take "zaki iya bin mu ko hankalinki yafi kwanciya a nan" Girgiza kai tayi, game da d'aga kai tana kallon nurse "sister pls taimaka min da hijabi na a ciki" Kai ta d'aga tashiga wata qofa dake falon. Riqe da ita barrister ya zauna a baya ya kwanto da kanta saman qirjinsa zuciyarsa ciki da tunani dalilin matar tasa nayin hakan? Yayin da gwaggo ke gaba rungume da qawarta kamar yacce tace, bello kuma na driving hankalinsa baki d'aya naga kwaltar yana juya steering wheel cike da qwarewa. ♧ Hannun Ammi cikin na mummyn Sam dake bacci sanadiyyar allurar da akayi mata, Anwar ne yaja hannun hasheem suka fita daga d'akin "Ya dai ragowar mutuwa" hasheem ya furta cike da tsokana 'Yar qaramar dariya yayi, "bansan wulaqanci mijin fat mango" ya qarashe game da kanne masa ido d'aya, naushin wasa ya kai masa ya kauce yana fad'in "Wlh karka kuma zagar min mata ko mu hanaka zaman garin nan" Hannu ya had'a gu d'aya "ayi min afuwa masu gari, zo muje mu taho da baqin mu na nijar" Da motar hasheem suka tafi basu tsaya ko ina ba se gaban gidan senator asi'u, seda akayi musu iso suka qarasa ciki cikin tangamemen falon inda Alhaji tasi'u yake basu wani jima ba suka fito biye dasu wata baqar jeep ce inda bayan sun fara tafiya suka sa'ba hanya, Daga can kuma ss office a wata tinted mota aka sako hajiya maryam da d'anta halim ala nufo gidan gomnati dasu. *** Ta wutsiyar ido take kallonta dan ta kula tunda su Ammi suka tafi take wani sukuku ko suna hira bata jefo baki kaman yarda ta kanyi lokxi zuwa lokaci, Bakin gadonta munu ta zauna game da d'an jijjiga qafarta, idonta dake a lumshe ta bud'e suka sauka saman na munu, "Tashi muyi wata magana" munu tace, Kai ta gyad'a mata, tare da jingina bayanta jikin bango bayan tasa pillowfor support, "Sam inaso ki fad'a min gaskiya duk tambayar da zanyi miki pls" Sai da ta sauke numfashi tace "ina jinki," "Zaki iya fad'a min whats going on between ke da Bro B?" Baki ta bud'e ta katseta, "truth..i want the truth" "Munu is kind of weird! I don't know how to put it into words" Dariya tayi qasa qasa "ki fad'a min Sam zan fahimta, i saw the chemistry between the two you" "Dagaske?" Tace in a worry voice, "Hey chill, nice fa all i know is yana yawan kallonki a sace that is tun lokacin da muka koma gidan su ga yawan yi miki fad'a wanda ni a fahimtata yanason yake jin maganar ki ko da kuwa cikin kuka ne" Fuska ta yamutse "ke munu, ba novel kike karantawa ba all this signals..." "Oh! Ke a tunaninki abinda nake karantawa all na wash? To tsaya kiji duk abinda qwaqwalwa ta qirqira used to happen in real life" "Ahh" tayi making sound, "Baki yarda ba kenan?, shikenan, yanzu dai i need my answer" Gyara zaman Sam tayi had'e da crossing legs, nan ta zayyane mata tun first kiss d'insu har abinda ya faru ranar da suka zo yi musu sallama, "..munu wlh forcing d'ina yake abin nata damu na, kinsan yanda nake i usually bar magana a zuciyana...and i'm also scared to say it out especially to Ammi, dan Allah ki taimaka min munu.." ta qarashe cikin kuka, "Shiishh...is ok" tasa hannu ta goge mata hawaye tare da rungume ta, tunani ya cika kanta, Zuciyarta na bata lallai akwai de wata a qasa dan a yacce take ganin Ammi bayan kamasu cikin intimacy will never let go of it cikin sauqi dole akwai wata a qasa, da wannan tunanin bacci ya sace su kasancewar su duka ba sallah suke ba (they are on period). *** Tun bayan da suka isa gidan a ka bawa Ammi band'aki ta wanke mom hajar tas har da babyn ma, duk da cewa har kawo wa wannan lokacin tana zubda hawaye haka anyi anyi ta furta abinda ke zuciyarta taqi qarshema she insisted on lallai idan an zauna maganar data tara su zata fad'a idan kuma an takurata zata fasa maganar kuma she's going to live, hakan yasa aka bar yi mata maganar tun bare da suka samu ta shayar da baby teema wato fateema zahra kamar yanda barrister ya rad'a mata suna. ©️Kdeey😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (29) Sallamar sa ce taja hankalin bello dake hira da Ammi tsam ya miqe ya fad'a kan qirjinsa a tare suka saki wani silent kuka, "Bro B...dafatan kana cikin qoshin lafiya?" 'Dago kai yayi game da dafa kafad'arshi yace "yanzu kam dana ganka na tabbatar da lafiya nake, tun bayan daka tafi na kasance cikin fargaba da d'imauta, yanzu kam bazan yarda ka kuma yin nesa dani ba qafata qafarka" ya kuma rungume shi, d'an dukan bayansa Anwar yayi "nima bazan kuma yarda na barka cikin garinnan dake dabaibaye da abubuwan al'ajabi ba d'an uwana " Knocking akayi bisa door, inda me girma gomna ya bada umarnin a shigo, P.A d'in gomna ne, "Ya akayi Rabi'u?" Sai da ya sara cike da girmamawa yace "Sir, dss bashari yace a sanar maka da zuwansa" "Let him in" cewar jamilu mainasara Ya juya idonsa a lumshe ba tare daya furta uffan ga mutan falon dake ta'ba hira kad'an kad'an cike da alhini ba, Qarar qarafunan dake riqe da hannu da qafar halim ne yaja hankulansu kan masu shigowar, seda suka shigo falon sosai Ammi ta miqe tsaye sede kafin ta samu damar furta wata kalma muryar kawu kabiru ta daki kunnan gwaggo itama de miqewar tayi lokaci d'aya hawaye ya yanke mata, nan kuma isowar umma salamatu ta kuma saka falon a wani yanayin yayin da take hajiya maryam ta hau zantuttuka masu kama da sambatu cewar lallai se an fitar da umma salamatu daga falon firr ta rikice musu tamkar sabuwar ta'bi har seda kyautar lafiyayyan mari daga hannun me girma gomna ya sauka a kuncin ta kafin a samu weather d'in d'akin ta daidaita, nuna kanta tayi da yatsa cikin zare idanu take fad'in "Ni? Ni ka mara jamilu.." Dariya ya d'anyi me sauti, "kwarai maryam yau sunana jamilu...to Alhamdulillah tunda ke kanki kinsan ta faru ta kuma qare, a yau ina so ki sani duk wanda ya jira ganin bacci na to kuwa ze rasa nashi, maryam kin shani na warke inaso da bakin ki a gaban kafatanin mutanen falon nan or let me say family ki fad'i gaskiyar yanda al'amarin aure ya qullu tsakanina dake bayan 'yaruwar ki mariya da na nema?" Kallon kallo aka koma yi, cikin sauti me cike da d'imbin mamaki gwaggo tace "Me kake shirin cewa ranka ya dad'e?" Kai ya gyad'a idonsa saman fuskar hajiya maryam da yakejin tsanarta fiye da tunani yace "kar ki bari na fusata, dan al'amarin baze ta'ba yin kyau ba" 'Dit dit..qarar na'urar dake nuna fitar numfashin hajiya mariya ta karad'e kunnuwansu "ta farka" shine abinda wata nurse dake kula da lafiyar ta, ta furta cikin farinciki, cikin su rasa me bawa wani hanya akayi, Ammi dake gaba turus tayi data shiga dakyar ta iya jan qafa zuwa gaban gadon cikin zubar hawaye yayinda ta toshe bakinta da hannu.. Cikin murya me fitar da iska ta marasa lafiya tace "yaya...ha.j.j..o" ta miqa mata hannu, saurin kamawa Ammi tayi game da jinjina kai, "nice..nice mari.." Smiling hajiya mariya tayi, d'ai d'ai take binsu da ido kan fuskar jamilu mainasara ta tsaya, ta lumshe ido ta bud'e cikin qoqarin tashi, "Tsaya na taimaka miki jikin ki ba qarfi sosai" cewar nurse bayan da ta gyara mata pillow a bayanta ta yacce zata fi jin dad'in zama, murmushi ta mayar mata, kan ta waiwaya ta kalli yaruwar tata tace "tun bayan da labarin rasuwar daddyn Sam ya riske ni, nake mafarkin yaro me irin fuskarki yana bawa mami na kulawa yaya hajjo, se de mafarkina na jiya daban ne da sauran..shin dagaske ne Mainasara yasa an qwato ni ceto ni daga azabar da yaya maryam ke gana min na tsayin lokacin da Allah kad'ai yasan yawansu..yaya hajjo kin ta'ba jin labarin da mutum ke yiwa kansa fatan mutuwa?...to nayi wa kaina har wani lokacin nakan nemi kauce hanya, Tsayin wannan lokacin na kasance cikin wani cage da ko cikin dabbobi mafi qasqanci ake ajiyewa ciki, ba sallah, ba wanka se bayan wata take bani sitira na sauya, abinci sau d'aya a rana, bayan gida ina yinsa ne cikin ledar da kawo min abinci, ina shan ruwa sau biyu a rana, Bani da abin rufa cikin ko wani yanayi da ake ciki haka nake kwana, ga sauro dake addaba ta, kinsan me nake ce mata tun ina kwana d'aya a wurinta?" Ammi ta girgiza kai "..ina ce mata ne, yaya maryam ki taimakeni ki kashe ni idan bazaki iya ba ki bawa yaran ki su qarasa ni ko ki bani guba nasha..." ta qarashe cikin hawaye, Ammi ma cikin zubar hawaye tace "ya isa haka mari, duk ba mafarki kike yi ba, tabbas mainasara ya ceto ki daga hannun makirar can and he stands to get justice for you, ki bar zubar da hawaye kada kanki yayi ciwo.." "Yaya hajjo already na nakasa dan bazan iya bud'e idona duka ba saboda haske, i am used to duhu" Hannu ta d'aga sama "Allah na gode maka daka dawo dani cikin dangina" Gyad'a kai Ammi tayi fuskarta maqale da murmushi tace "Mari ki kwanta haka, idan kika huta zuwa anjima se muyi magana" Ido ta lumshe game da jinjina kai tace "i am thirsty.." Ruwa Ammi ta bud'e ta tsiyaya mata cikin cup ta d'ago kanta ta bata, a hankali tace "yaya hajjo yanzu shikenan gwaggo ramatu tayi sanadiyyar bazan kuma ganin daddyn Sam ba?" "wacece gwaggo ramatu Ammi?" Cewar Anwar, Numfasawa tayi tare da fad'in, "kishiyar babar mu ce kuma mahaifiyar maryam" "Amma ita d'in ai ta jima da rasuwa ko daddy?" Cewar Rayya, "Uhm, ta rasu ne a hatsarin mota daga jos adamawa zuwa jos wanda maryam ce ta haddasa hakan" "Daddyy?" Kai ya d'aga "at that time baki da lafiya Rayya bazaki sani ba, amma mahaifiyarki ta jima tana cutar da rayuwata har da ma taki..., kuje ku shigo min da ita" yace idonsa saman na securities dake tsaye bakin qofa, Ita ke gaba, halim a baya suka shigo kai a qasa, zama suka yi can gefe d'aya, bayan securities d'in sun fita ne, ya waiwayo game da zama saman kujerar dake tsakar d'akin yayi crossing legs "Inaso ku kad'e kunnenku dakyau dan jin yacce labarina ze faro" _tafe nake cikin garin bichi dake jihar kano se sauri nake na isa tashar jirgi dan tsaida masoyiyata da mahaifanta da zasu bar garin zuwa asalin garin mahaifinsu, duk wanda ya kalle ni se ya kuma kallo na ba dan komai ba se dan tsabagen dattin da nayi marabata da mahaukaci sabon ta'bi qalilan ce, dan dawowata daga kudu kenan na tarar da labarin tafiyar su,_ _Ranar seda na karad'e cikin jirginnan tsaf babu ko qurar su, nan na zauna cike da takaici har kusan awa uku sa'annan na koma gida, sede kafin na wuce gidan seda na tattambaya maqota ko akwai wanda yasan inda zasu daqyar na samu wata ta shaida min maiduguri suka koma inda yake asalin garin mahaifinsu,_ _Bayan qasa a gwiwa ba na shirya tafiya maiduguri bayan shan artabu da nayi da mahaifana a cewarsu tunda har kuka bar garin to kuwa lallai mahaifinku baze ta'ba yarda na zama sirikinsa ba haka suka hanani zuwa dana dage ma se mahaifina yace idan har naje ba da yawunsa ba,_ _Jin magana irin na yaran da yasa na haqura, har bayan kusan shekaru shida a lokacin na gama makaranta har ina aiki a gefe guda kuma ina siyasa, na hau jirgi zuwa maiduguri, bansha wahala wajen neman gidan ba kasancewar kakanku da yake sananne, ina isa na tarar da anyi rasuwa a gidan haka na zauna ba tare da na shaidawa mahaifinku dalilin zuwana ba daya tuntu'beni ma se cewa nayi ai nazo wani aiki ne,_ _Bayan sati biyu na lura cewa a duk sanda na shiga gida dan gaisawa da mahaifinku bana jin ko motsin mariya se gwaggo ramatu da maryam kad'ai hakan yasa nayi making up mind d'ina nayi masa magana, bud'ar bakinsa sai yace ai watan daya gabata aka d'aura auren mariya yanzu haka tana kano,_ _Kula da rud'ewar da nayi yasa ya rinqa ban baki, kwana uku bayan nan na shirya komawa gida, ana gobe zan tafi ina zaune a d'akin da aka saukeni naji yo hayaniya daga cikin gida, shiga nayi dan jiyo ihu, da isata na tarar da mahaifinku kwance rai yayi halinsa ga kuma mata na tofa albarkacin bakinsu_ _A lokacin nake jin labarin wai maryam ta haifo shege kusan shekaru biyu kenan a ranar kuma suka samu sa'bani da mariqiyar yaron shine ta tona mata asiri a gidan su har ma ta kawo yaron ta bata,_ _Wannan ne asalin yanda labarin ya faro, mahaifinku nada kwana arba'in cikin qasa kakanku ya nemi tayina kan na rufa musu asiri na auri maryam na tafi da ita,_ _A tunani na hakan kad'ai ne zesa a bar yada wa danginku magana yasa na amince, muka komo bichi tare inda nayi wa mahaifana qaryar bazawara ce na auro ta, da farko sun nuna sam basa sonta daga baya kuma suka aminta bayan shige da fice da maryam tayi ita da mahaifiyarta,_ _Idan bazan manta ba nasha kama maryam tana zuma mana magani a abinci ko tana binne abu kai har takai maryam idan mu kayi kwanciyar aure se ta lakaci ruwan maniyyi ta zuba cikin qaramar container,_ _Duk dan mu zauna lafiya ban ta'ba tambayarta dalilin hakan ba dan zuciyata na bani ba zata ta'ba cutar da ni ba, maryam ta fito da sabbin d'abiu na raini da kuma kalaman qasqanci ga mahaifana abin takaicin kuma bana iya yi mata fad'a bare kallon banza,_ _Ta ruguza soyayyar mahaifana a zuciyana haka ma 'yan uwana dan banda haihuwar Rayya, na jima ban nemi hanyar garin mu ba,_ _A wata rana muna hira da maryam muka d'auko hirar da inda nake sanar da ita cewa na gano gidan mijin mariya, nan ta nuna jin dad'inta har ma tace insha'Allah zata kai mata ziyara ashe bansani ba zuwa tayi aka binciko mata komai game da su har taci alwashin lallai se taga bayan su,_ _Ba mufi sati da maganar ba na tsinci labarin 'batan mariya, a d'aya 'bangaren kuma maryam bata nuna damuwarta game da hakan ba duk kuwa da cemin da take tana zuwa gidan har ma waya sunayi, banyi mamaki ba duk da banji dad'in yanda ta nuna ko oho ba sedai nayi shiru ne a ganina sun fi kusa,_ _A 'yan kwanakin na lura matata ta zama busy head ga wata iriyar waya da ta tsura mara amfani, hakan yasa na fara zargin akwai wata a qasa, nasa aka sa min ido akan dukkan wasu moves d'inta_ _cikin ikon Allah se muka had'u da ku (anwar, bello da hasheem) a asibitin getwell inda yarinya ta ke kwance kallo d'aya nayi muku nasan kud'in su waye duk da dama can arqalla ta ta'ba had'ani da Anwar, hakan yasa na rinqa cusawa Rayya soyayyar Anwar duk dan mu shiga jikinku dan shine abinda take lacking soyayyar 'yanuwan taka sede kasancewar rasgin lafiyarta bata fahimci hakan ba har se daga baya ta fuskanci soyayyarta naga doctor, Muna haka bello da hasheem suka zo min da labarin nan inda na basu goyon baya dan yaqi da makaman maryam, cikin ikon Allah ga inda muka tsinci kanmu,..all way leads to pure truth, "Na tsaneki×2 maryam" "Na shiga uku" ta furta game da fashewa da kuka, Adding yayi, "baki shiga uku ba tukunna dan har d'ari se kin shiga" "Bani da laifi jamilu.." Cikin girgiza kai Rayya ke fad'in " yanzu mummy rashin imanin naki yakai ki dauki ran d'an adam?? A gaskiya nayi takaicin kasancewar ki uwa a gare ni" "Um um Rayya nayi miki kama da wacce zatayi kisan rai?" Umma salamatu ta tashi tsaye a fusace tace "kwarai kuwa dan bada ban Allah ya kiyaye mu ba da tuni mun tafka babban kuskuren da kika so nayi ni da d'a na, kinsan mun zalunci yarinyar dake zaune damu tsakani da Allah, son duniya yasa kika kusa lalata wa yarona tarbiyyar sa, shin duk wannan abinda na lissafa kinaso kice duk ba yin kanki bane!" "Ko kuwa informations d'in da kike saina munafurtan mijina ina baki suma ba yin kanki bane.." mom hajar tayi adding a tsawace, "...you are all under gwaggo's spell !!!" "Mene?" Suka ce a tare, Kai ta d'aga, "mahaifiyata duk itace sila, wlh×2 ni aiwatar wace kurum tawa amma basirata bata kai nayi muku wannan DABAIBAYIn ba...na sani ba zaku yarda ba amma ko ni kai na bana sanin lokacin da nake yin wani abun har se na idar, a yanzu haka nasan bazan gaza kwana biyu a raye ba dan tasa nayi alqawari cewar duk ranar da na fasa qwai zan baqunci lahira... ©️Kdeey😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (30) _few pages left💃🏻🤸🏻‍♀_ ... Salati gwaggo tayi game da sallallami, "ke baiwar Allah amma baki ji dad'in halin ki ba sam" Cikin zubar hawaye mom hajar taja jiki gaban barrister "kaji dalilin da yasa nayi niyyar barinka...mijina sam ban san ya akayi na amshi tayin hatsabibiyar matar nan ba, a lokacin da muka zo gaisuwar Alhaji d'anqasa idan baka manta ba muna zaune aka kira ni a waya na fita dan ansa wa, baquwar murya ce ke sanar min na yar da passport d'ina a hanya kuma wai gata a location d'ina na fito qofar gidan Alhaji ibrahim d'an'kasa, ba tare da tunanin komai ba nayi yacce tace d'in, tun kallo d'aya da nayi mata naji gabana ya fad'i haka kuma naji bazan ta'ba iya musa mata duk abinda ta umarce ni da nayi ba, tun dga wannan ranar duk wani moves d'inka ina sanar mata, dan Allah ina roqonka da ka gafarce ni, ku gafarce ni nayi hakan ne ba a cikin hayyaci na ba" Tsam barrister ya miqe bayan ya bata baby shi kuma ya fita waje, Jamilu mainasara yayi 'kwafa, "Uhm kun ji ba?, yanzu me zaki ce akan wannan, kunsan Allah kada ku yarda dad'in bakinta yasa ku tausaya mata" ya waiwayo gare ta "..ko tunzurarren mahaukaci da yake mara lafiya baze ta'ba aiwatar da jahilcin kika yi ba!" Amshewa hajiya maryam tayi da cewa "Na rantse da wanda raina yake hannunsa asiri ne yake juya ni, dan sam qin aminta nayi da tazo min da shawarar a tunanina duk inda akaje aka zo su hajjo jinina ne..." Cikin gajiyayyiyar murya mariya tace "...idan har abinda kika fad'a ya kai zuciyarki to menayi miki da kika illata min rayuwa har haka, kuma meye laifin mijina a ciki?" A fusace hajiya maryam tace "Kasancewar sa me kud'i, k..ku..ma taya kike tunanin zan jure ganin kinyi aure kin barni ni da na girme miki da shekara kusan uku!..kinsan baqincikin hakan ne yasa ranar d'aurin aurenki na gudu bq d'in gidan kaka na 'buya ina kuka ashe a d'akin aka sauki baqin da suka zo d'aurin aure daga kano...daga cikin ma'boyata mahaifin namadi yaron Alhaji d'anqasa yana d'aya daga cikin wayanda aka sauka, daga ma'boyata na hangi shigowarsa ya shige band'aki fitowarsa tayi daidai da tashina zan fita naji ya janyoni na fad'a kansa a lokacin ya lalata min rayuwa...,tun daga wannan ranar na ci alwashin rama gi'bin da yayi min, a lokacin dana bincika naji labarin rasuwar sa yasa na maida hukuncin kan d'ansa namadi..shine dalilin da yasa na aikata haka..." Dariya jamilu mainasara yayi "to Alhamdulillah tunda har kin iya fad'ar dalilin ki amma ki sani ba wai mun yarda bane, na sani asiri gaskiya ne tunda har ya kama Annabin mu, amma maryam komai yana tafiya da hali ni kuma a gaskiya na gaji bazan iya zama da macen da take iya kisa ba saboda hak na yanke igiyar aure na biyu daga kanki kije su tafi dake ..." Rayya ta yanke jiki ta fad'i duk suka yo kanta harda hajiya maryam se de tun kan ta qaraso me girma gomna ya umarci CP ya shigo da mutanensa ya tafi da ita, Ihu hajiya maryam ta rinqa yi fad'i take abarta ta ga lafiyar 'yarta amma ko kallonta gomna beyi ba, sema barin d'akin da yayi. *** Haka rayuwa ta kasance yau dad'i gobe akasin haka, yau sati biyu kenan da fitowar su mummyn sam ba laifi ta samu lafiya se rashin qwarin jiki wanda hasheem ya tabbatar musu idan ta juri cin kayan gina jiki zata dawo daidai bada jimawa ba already yau kwanakin su biyu a gidan kawu kabiru wanda daqyar me girma gomna ya aminta suka tafi a cewarsa ai shima he is part of the family, sede tafiyar data kamashi zuwa france ne yasa ya yarda su tafi har ya damqa musu ragamar kula da Rayya dake kwance a asibitin hasheem dan sam jikin nata yaqi dad'i, duk wannan dramar da aka sha su Sam basu san abinda ke wakana kenan ba, kamar ko yaushe tafe suke su uku zuwa hostel ko wannen su da abinda yake tunani, numfashi sholey ta sauke bayan ta juya ta kallesu duka Tace "kunsan me?" Girgiza kai Sam tayi, munu tace "se kin fad'a" "'Dazu mami na ke fad'a min shatima ya kira ta wai zasu kawo lefe" "Ya fad'a mata ba ma ke ba?" Munu tace cike da mamaki, "Hmm, ance miki kunyarta yake wannan ta'b, ai yacce kika san ba yayar sa ba ko dan first cousins suke da ita, kuma kinsan yau sati d'aya bana picking call d'insa" Kafad'a munu ta d'aga "oho dai yaje tunda dai munayin sa ai shikenan" "Ke de bari qawata" cewar sholey suka tafa suna dariya, murmushi Sam tayi tace "congrats sweetheart" Rugumeta sholey tayi, "All thanks to you, tunda kece kika fargar dani na hango the Angel within him" "Group hug" munu tace tare da fad'awa kansu cikin dariya suka ce "wayyo zata karya mu" *** _Can't you call kiji ya muke silly girl_ Karanta message d'in ta kuma yi _silly girl_ mutum d'aya ke ya'ba mata kalmar nan, zaune ta tashi da sauri tana kuma maimaita kalmar bro A sunan yayi ringing cikin kanta, All this while dama shi ke tura mata saqo har yake kiran kansa da husband d'inta! unbelievable, baki bud'e ta koma tun farkon saqon daya fara tura mata tana karantawa. Saurin dialling number munu tayi dake sun fita shopping da sholey, tana ta ringing bata d'aga ba haushi yasa ta wurga wayar kan pillow game da kwantawa ta rungume qafafunta a qirji gabanta na wani irin bugawa "me bro A yake nufi...ya Allah kasa ba gaske bane na shiga uku na samu na cire bro B a raina kuma ga wannan! Innalilllahi, hawaye masu zafi suka siraro mata Thinking of him alone yana sa zuciyarta wani irin bugu, kenan shiyasa yake mata iskanci, ta waro ido waje game da fad'in wayyo! Ta jima a kwance zuwa can tasa hannu ta d'auko wayarta, ta shiga kiran layin Ammi a lokacin suna tare da mummyn Sam suna hira, Ammi na bata labarin auren Sam da Anwar, mummyn Sam tana kuka wanda kallo d'aya za kayi mata kasan kukan farinciki ne saboda murmushin dake manne saman fuskarta, Ringing d'in wayar yasa ta tsaya da cewa "Samira is calling.." Cikin rawar murya tace "Pls put it on speaker" Kai ta d'aga, "hello Ammi na" Zirrrr hawaye suka zubo wa mariya, "Samira na nayu fushi se yau kika tuna da ni" Cikin shagwa'be murya tace "Allah Ammi ba haka bane, mss paticia ce tasa mu kashe wayar dan kar tayi distracting d'in mu daga karatun exams" "Oh samira na wasa nake miki, how have you been, ya exams d'in?" "Alhamdulillah, nan da 4days zamu yi hutu gashi bakwanan" "Yea, Ann yace ba zaku zo gida ba har se kun gama session d'in baki d'aya," "Ammi.. yanzu..yaushe zaku dawo to?" Ta qarashe a shagwa'be kukan mummyn Sam ya d'an kufce dan har Sam se da ta jiyo, A rud'e tace "Ammi is everything okay?" Saurin riqo hannunta mariya tayi game da girgiza mata kai alamun kada ta fad'a mata,...jinjina kai tayi cikie da tausayin 'yaruwar tata tace "Lafiya, kin ga canjin weather yasa mura ke neman kama ni" "Ayyah sorry, yanzu when are you coming back" "Insha'Allah in two weeks time, akwai matar uncle d'in su Ann da muke zaune anan, ta haihu yau da safe so inaso ta samu qarfin jikinta sosai sa'annan mu dawo" "Okay Ammi, bara na barki" "Okay dear, ina 'yanuwanki" "They went for shopping" "Meyasa baki je ba?" "Period pain yasa ni gaba Ammi" "Have you take a medic?" "Miss patricia tace wai ba'ason ake shan magani" "Or sannu kinji make sure you relaxed kada kiyi motsi da yawa and drink some fruits uhm?" "Ok Ammi take care, i love you" "Bazaki ce na gaishe da brothers d'inki ba?" "..send my greatings to mu'allim bello" da fad'in haka tayi saurin ajiye wayar dan haka kurum taji fad'uwar gaba tun kan ta ambaci sunan Bro A. *** "Meyasa kika hanani fad'a mata, do you know how joyous she will be?" Cewar Ammi tana qoqarin ajiye wayar bisa bedside drawer, "..bana son ta shiga wani state ne, baki ji ba Sam d'ina ta girma har tana yin period" ta qarashe cikin dariya me had'e da kuka Kai Ammi tayi nodding, Muryar umma salamatu wacce shigowarta kenan ta doki kunnuwan su, "..she will be more than happy idan ta ganki a raye, she always says she misses you kullum dare se tayi kukan rashinku a gareta..nayi hasara rashin bata soyayyar uwa dan Allah ki yafeni mariya wullahi banyi hakan a sanina ba..Ameer yau satinsa guda baya ci baya sha duk ya fita hayyacinsa, yace lallai na nemo masa Samira ya nemi afuwar ta idan har ina son ya koma yanda yake, dan Allah ku agaza min" ta durqushe a gabansu cikin zubar hawaye, Kallon kallo sukayi tsakanin su, kan Mariya tace "muje na ganshi" Umma salamatu tayi leading d'insu har d'akin sa, inda yake kwance rigingine idonsa bisa sealing hawaye na zubo masa, babu me cewa shine Ameer d'in Sam d'innan me wasa da dariya, ya rame duk ya fita a hayyacinsa, Zama mariya tayi kusa da kanshi game da d'ora hannunta saman sumar shi, "Ameer d'an lukuti me qaton tumbi me kama da bulun boti..." d'ago kai yayi game da fashewa da kuka bayan ya kwanta saman cinyar mariya, "Itace waqar da take yi maka a duk lokacin da kazo gida back then can you remember? You are morethan a brother to her Ameer, duk abinda kayi wa Sam zata yafe maka, duk abinda ya faru kayi ba'a cikin hayyacinka ba, dole zata yafe maka uhm? Ka cire damuwa a ranka, inaji a jikina zata yafe maka" Cikin kuka yace "mummy kin tabbatar?" Kai ta d'aga "insha'Allah, maza zauna muci abinci kaji, yinwa nake ji and dont say no" ta nuna shi da yatsa in a playful way, Kallon ummasalamatu yayi kan yace "zanci nima" Nan suka zauna suka ci abincin ana ta'ba hira wacce take tun tada ce da haka har ya qoshi suka tafi suka barshi zeyi wanka ya fito falo, *** Bello da Anwar ke zaune suna hirar bayan saduwa cikin office d'in hasheem wanda ya tafi dubo lafiyar Rayya, "Kana son ce min first cousins muke da Sam all this while bamu sani ba?, Allah is great♡" cewar bello cike da farinciki mara misaltuwa Numfashi ya fursar tare da gyara zama ya had'e hannuwansa wuri d'aya bayan ya kuma kallonshi ya d'anyi one sided murmushi "Yeah, and Rayya too" "Alhamdulillah..you know what? Yanzu komai zaizo min cikin sauqi insha'Allah.." 'Daga gira Anwar yayi, "mene?" Ya tsugunna gabanshi "Bro A amanata, she's going to be mine, i'm willing to make her mine officially.." Duniyar yaji ta tsaya mishi cakk babu abinda yake iya jiyowa se sautin dariyar Bello game da hamdalar da yake...amanar sa??? Ya ayyana a ransa, kan ya jiyo shi yana fad'in "Yes Samira..i love her so very much..." ©️Kdeey😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (31) ..hawaye masu d'umi suka ciko idanunsa, yayi saurin sharesu da hannu kada bello ya gani, yayi saurin miqewa ya fice da sauri har suna neman yin karo da hasheem "Bro A" Yana iya jiyo muryar bello na kiransa but bashi da courage d'in fuskantar sa a halin da yake yanzu! There is only one way out! Bello be ta'ba neman abu ya rasa a wurina ba face nayi masa, se idan bani da halin yi, wu'ka da nama duk a hannuna suke, dole nasan abin yi, ya ayyana hakan a ranshi, Key yay ma motar sa ya nausa bisa kwalta, yana tafe yana zubda qwalla besan haka soyayyar Sam tayi mishi mugun kamu ba se yau da waninsa ya furta kalmar so a gareta, wanin ma d'an uwansa, steering wheel ya doka tun qarfi tare da fashewa da kuka hannunsa saman qirji yana duka fad'i yake "why why meyasa ki kai mana haka she's my heart and bello is my own blood" ya sauke ajiyar zuciya, da taimakon Allah ya isa gidan kawu kabiru. Cikin jerin motocin kawu ya ajiye tasa, da d'an saurinsa ya qarasa cikin gidan, ba me cewa ga halin da yake ciki saboda toshe idonsa da yayi da baqin gilashi, A falo ya had'u da umma salamatu da mummyn Sam cike da wani tsananin kunyar su ya sunkuyar da kai, har qasa ya tsugunna ya gaida su, cike da fara'a suka amsa masa umma salamatu na tsokanar shi "Haba Anwar a 21st century muke fa, surukuntaka is now old model, kai da za kazo mu zauna mu sha hirar mu " Key d'in hannunshi ya cusa cikin sumar kanshi yana susa game da kuma sadda kai yana murmushi, "Ammi fa?" Yace murya qasa "Au ja'iri bazaka kulani ba kenan, to kaje tana d'akin ciki daka hagu" Kai ya d'aga sum sum sum ya shige ciki, saman sallaya ya sameta zaune ta d'aga hannu sama tana addu'a, da azama ya isa gareta saman cinyarta ya kwantar da kanshi tare da sakin wani silent kuka wanda danshin ruwan da taji ne yasa data idar da addu'ar ta leqa fuskar sa, "Subhanallahi, Ann lafiya?" Kai ya girgiza "Ammi bro b.." A rud'e tace "Bello? Meya faru dashi?..d'agani muje na gani a ina yake?" Girgiza mata kai yayi a hankali ya tashi zaune fuskar nan tayi jaga jaga da ruwan hawaye "he..saidd..." gaza furta qarshen zancen yayi , A firgice tace "sunyi masa wani abu ne shima?" Ta tambaya "Ko d'aya Ammi,...Ammi kinsan cewar inason bro B sosai ko? Inason shi sama da yanda nake qaunar kai na..i can even sacrifice my own life in har tasa zata inganta," Cikin rawar murya tace "naji...naji fad'a min abinda ke faruwa mana" "...he is my only blood Ammi, i see Abbi when ever i look at him...Ammi soyayya batayi mana halacci ba" "Ka fahimtar dani Ann, ni-nifa bangane inda maganarka ta dosa ba" "Ammi zan iya bar mishi kowa, komai amma banda nan" ya nuna heart d'inshi da yatsa, ya cigaba da fad'in "...ita d'in zuciyata ce, rabuwa da ita tamkar rasa rayuwata ne,...meyasa ze ce yana son matata ta sunna!" Ji tayi d'if duniyar ta tsaya mata idanunta kan qofa inda bello ke tsaye tamkar ruwa ya cinyeshi. "Bel..lo!!!" Ta qwala kiransa on top of her voice, 'Dago kai yayi kan ya furta komai suka jiyo qugin mota tun qarfi, ai rasa me bawa wani hanya akayi tsakanin Ammi, umma salamatu da mummyn Sam, "Shin meke faruwa ne?" Suka furta kusan a tare idonsu bisa fuskarta, "Innalilllahi wa inn'ilaihir rajiun" ta furta a fili kan ta juya ta koma cikin gida suka mara mata baya, A daddafe ya fito falon, ya zube a gabansu, cikin sambatu yake fad'in bazan iya rabuwa da matata ba kuyi min rai, haka ya rinqa maimaita kalmar har bacci nannauya yayi awon gaba dashi, Cirko cirko sukayi a kanshi cike da tausaya masa, mummyn Sam ce tayi qarfin halin d'aukar waya ta kira bello, Wani irin rough driving yake cikin fitar hankali, yayin da a gefe guda kuma 'yan sanda ke biye dashi sedai duk qoqarin su basu cimma shi ba, yayi gaba ya barsu da cizon yatsa🤣. Shagon unguwar su salihu ya nufa dan yasan can ne ba wanda ya sani idan ka d'auke hasheem, wayarsa dake haske ya kashe ya kuma rufe kansa a d'akin, ruf da ciki yayi rungume da pillow yana kuka me cin rai, A fusace ya tashi zaune yana maganganu, "wallahi a a bayan na gama shukata qiris ya rage na girbe, Sam batayi deserving heartless miji irin ka ba, baka sonta lallai se ka datse igiyar auren nan ka bani ita domin ita d'in tawa ce, Nasha ganin soyayyata kwance cikin idonta, Sam bazata ta'ba amincewa da kai ba after dukkanin cin mutumcin da kayi mata, se yanzu da kaga ta isa ban ruwa...bazan ta'ba yarda ka mallaki abinda yake nawa ba, Sam Amanata ce, she's mine and i'm going to make her mine officially, dole ka sake ta na aura...!" Da haka ya silale bacci yayi awon gaba dashi. *** "Hasheem ya kake ganin lafiyar tashi" "Mummy damuwar da yake ciki na neman ta'ba mishi zuciya dan yanzu haka yana cikin maxim.." "Um um um um sam yarona lafiyarshi qalau..." "Only if you give him abinda ya ke so Am..." "Zo muje daga waje" tace dashi living mummyn Sam and umma salamatu behind. """ Tagumi ya kafa bayan gama sauraron abinda Ammi tace, "Ammi her love change d demon in him" "Pardon?" Jinjina kai yayi da cewa "tun sa'ada kuka zo na kula bai cika son magana ba kullum cikin kallon wayarsa which i definately know hotonta ne, he even day dream about her,..Anwar often smile amma yanzu his lips are always parted and spread kamar zasu ta'bo walls d'in kunnensa har hakwaransa ana gani yanzu" "...you observe all this ba tare da kasan da maganar nan ba? Dr kasan yarana sosai, cikinsu who deserve to be with Sam?" "Ammi Sam matar Anwar sunanta, kuma ba'a ta'ba canja wa tuwo suna Allah kad'ai yasan alkhairin da ya shirya cikin auren nan" "Bello fa?.." Gira ya d'aga game da cewa "well! Bello In my own observation tausayin Sam yafi rinjaye a zuciyarsa sama da soyayyar da yake ikirarin yana mata..." "Kamar yaya?" "Ina nufin tausayinta yake ji, be sani bane, but i'll make him understand" ya miqe tsaye, "Ina zaka je?" "Zanje na taho dashi" "..bazaka iya samun shi ba, wayarsa a kashe take.." One sided murmushi yayi "zan zo miki dashi yanzu Ammi" Cike da damuwa ta d'aga kai, da ido ta bishi har ya 'bace wa ganin ta. *** Abinci suke ci hakan yasa banda qarar spoon ba abinda ake ji, "kim" Saurin waiwayawa sukayi jin an qwala kiran hatsabibiyar yarinyar mss chloe kamar yanda suke kiranta dashi saboda rashin jin maganar ta. Daga wata qofa ta fito, tana girgiza tamkar bishiya idan ana iska, dama gata kamar ta karye tsabar rama, ido biyu suka yi da munu ai kuwa ta galla mata harara, Da turanci tace "ke wakike ma kallon banza" Munu tace "ke da wani idon kika ga na kalle ki?" Qwafa tayi cike da takaici can cikin zuciyarta kuwa haushi take ji da ba Sam bace, dan haka kurum taji batason yarinyar, yarinya tamkar ita ta halicci kanta, duk wani features da Anwar d'inta ke so na 'ya mace yarinyar nan me qwala qwalan ido tana dasu, abin takaicin kuma shine mom d'inta tace cousin sister d'in Anwar ce, Numfarfashi take tamkar wacce tayi tsere idanunta na faman harararsu, sede hausawa sunce harara a duhu...dan ita samira ko d'ago kai bata yi ba kanta a qasa tana cigaba da cin abincinta. Tsaki taja ta nufi wurin sakatariyar mahaifiyarta ta bata wata paper kan ta juya ta bar wurin cike da takaicin Anwar d'an uwan Samira ne. Nannauyan ajiyar zuciya Sam ta sauke bayan ta waiga taga fitarta, ta dawo da idonta kan munu, "Wai meyasa bakya shayin tsokanar matar nan ne? Bakya gudun ta fad'awa mamanta.." "Ta fad'a mana se me ai itama mss chloe tasan halin nata, kuma inada tabbacin mu zata mara wa baya" "Kinga kallon da tayi mana kuwa, Allah dakyar nake tura abincin nan dan qiris nake jira naga tayo kan mu nasa gudu" Dariya Munu ta kwashe da ita, "kice dama sadda kan da kikayi idonki na kanta?" "Ba dole ba kinga yanda take numfarfashi kamar tsohuwar guzuma" Dariya suka kwashe da ita, daidai lokacin suka jiyo ihun mss chloe tana masifar wa yace sakatariyar ta ta bari Kim ta tafi California ba tare da saninta ba, Kallon juna sukayi sum sum sum suka bar wurin zuwa sport complex. *** Daqyar ya iya cire jiki daga katifa ya nufi qofa jin yadda ake bugu, "Waye?" Ya tambaya in a sleepy yet cracky voice "Bello bud'e nine" Kamar ya share sede ya bud'e ya juya ciki, girgiza kai hasheem yayi bayan ya tura qofar, Komawa yay ya kwanta idonsa a lumshe, yayin da hasheem ke tsaye a kanshi hannunsa cikin aljihu yana karantar yanayin shi, Numfasawa yayi a hankali yace "Bello tashi muyi magana" "Ina saurarenka" yace ba tare da ya motsa ba, "Ka tashi ka zauna nace!" Yace in a commanding voice, Bello ya tashi zaune game da fursar da iska me zafi daga bakinshi, yace "ina jinka" "Menene dalilin da yasa baka ta'ba fad'amin labarin soyayyar da kake yiwa Sam ba, afterall ni da kai muke aikin nan tun farko, uhm?" "A lokacin she's such a baby and at that time i have no feelings for her,..." "Yaushe ka fara jin soyayyar a zuciyarka?" "The day Anwar punished her" "Uhumm?" "Tana kuka...helplessly... kallo d'aya nayi mata naga yarinyar need a shoulder to lean on, amma kaga yanda yayi treating d'inta idan ta zama under his custody me kake tunanin ze faru, shin waye ya bashi ita da har yake ikirarin matar shi ce?!" "Kawu kabiru, and it's official,..." "Official my foot! Doctor nasan Anwar abokin k..." "Anwar? Bello a kan mace kake kiran sunan d'anuwanka da raini? ka nutsu ka dawo hayyacinka fa, how sure are you ita yarinyar bata son auren? Or do you think 'yar qanqanuwar soyayyyar da kake ikirarin kanayi mata zata aminta da kai! Look idan rai ya 'baci be kamata hankali ya gushe ba, aure ba abun wasa bane kada na kuma jin kana cursing d'in shi in ba haka ba wullahi zaka gamu da fushin ubangiji, gara ka san abinda kake idan kuma kaqi tam! A yanzu haka mahaifiyarka na can hankali tashe kar ka bari ta dalilinka wani abu ya faru da lafiyar ta kamar yanda kayi sanadin ta d'an uwanka!" Da fad'in haka Hasheem ya fita a fusace cike da 'bacin rai. ©️ Kdeey😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (32) Qirjinsa ya tsananta bugu tsabar kad'uwa da firgicin abinda hasheem yace, mukullin mota ya d'auka ya fice da sauri daqyar ya iya tsayawa rufe qofar d'akin. Bumper to bumper suke tafiya dan ta side mirrow ya hango motar bellon, one sided smile yayi, bello will never choose anybody over d'anuwansa da mahaifiyarsa ya ayyana hakan, cike da farinciki ya juya akalar motarsa zuwa asibiti dan gano rigimammiyar tasa da taqi yarda ta koma gida, Da taimakon ubangiji ya isa gida, sede yana zuwa umma salamatu ke shaida masa sun tafi gidan barrister yanzu, can ya nufa zuciyarsa cike da tararradin a wani hali Ammi da Ann suke, A falo ya tarar da mom hajar zaune saman carpet tana pleading wa barrister, kallonsu yay cike da mamaki, "whats going on here?" Yace cikin rawar murya, Tasowa tayi da sauri ta kama hannun bello " B please taimake ni ka taya ni bashi hakuri yaqi saurara na tun ranar da abin nan ya faru, I'm fed up with his new attitude!" Ta qarashe maganar da kuka, Salati yayi game da dafe kansa, tamkar me koyon tafiya ya ja qafa zuwa kujerar da barrister yake, "Uncle..." "Shiiii.." yace game da d'ora yatsa saman lips, "But unclee.." "Wullahi na rantse da Allah na yafe mata, wannan halin tunanin da nake yi ba komai bane face tuna yanda na yarda da ita amma ta yaudare ni ta hanyar kwasar sirrika na ta yad'a a waje not thinking amanar da na d'auka na kula da dukiyar marainiyar Allah" "But uncle ka duba halin da take ciki she just gave birth, and..." Kai ya jinjina "bello kai yaro ne do you know what it takes to love a woman and to be betrayed by the same woman?, na yafe mata but dole tayi hakuri da sabbin halayen nan nawa dan baza su tafi lokaci guda ba" da fad'in haka ya bar falon zuwa sama, Idonshi ya maida kanta da ke qasa tana zabga kuka lokaci guda duk ta sauya mom hajar din da take 'yar gayu da 'kwalisa yanzu zaune take da riga da zani dabam dabam gashin kanta yayi buyu buyu, lallai tashin hankali bashi da rana! Daqyar ya samu ya lalla'bata game da bata baki kan komai me wucewa ne, nan ta shaida masa su Ammi sun tafi asibiti dan jikin Anwar yaqi dad'i, da haka ya bar gidan zuwa asibitin, room no 2 ya nufa kamar yanda nurse munirat ta sanar masa, Kwance ya hango shi saman gado, Ammi na gefen kansa ta kafa uban tagumi, yayin d gwaggo ke sallah saman sallaya, a hankali ya taka zuwa gaban gadon hawaye suka yanke masa cikin kukan zuci ya sumbaci goshin d'anuwan nasa dake kwance lokaci d'aya duk ya canza kamanni, duk ta dalili na? Ya tambayi kanshi, ganin dakyar numfashi ke fitar masa bakinsa a bud'e, da sassarfa ya qarasa gaban Ammi ya tsugunna game da kwantar da kansa saman cinyarta ya riqo hannuwanta cikin nashi tare da fashewa da wani marayan kuka yace "Ammi dan Allah ki yafe min, wullahi sharrin shaid'an ne banyi niyyar saka ku cikin qunci da tunani ba, hasalima bansan cewa Samira mata take ga Anwar ba, i'm just saying my mind out, dan Allah Ammi ki bashi haquri kice ya tashi ni na hakura bana sonta, i just come to realize that tausayinta nake ba so bane, Ammi kice wani abu pleaseee" Dafa kafad'arsa da akayi ne yasa shi d'ago kai ya rungume qafar mummyn Sam yana me cigaba da zubda qwalla "pls mummy talk to her taqi kulani kinji.." Kanshi ta shafo tan girgiza kai tace "ba qin kulaka tayi ba, ever since Anwar ya shiga wannan halin taqi yin magana kwata kwata" Cikin tashin hankali ya juyo gareta se gani yayi tana kallonsa idonta na tsiyayar hawaye, rarrafawa yayi gabanta, ta tallafo fuskarsa tana me share masa hawayen da hannunta game da girgiza masa kai a hankali ta furta "Allah ze baka wata mafi alkhairi kaji, kayi hakuri" Kai ya gyad'a a hankali yace "insha'Allah Ammi, Allah ya bawa Bro A lafiya" "Ameen" suka furta baki d'aya, nan dai suka had'u suka rinqa bashi baki har ya sauko suka shiga hira wace akasari ta Anwar ce da yanda auren su ya qullu. Satin Anwar d'aya ya samu lafiya, bello ya nemi yafiyarsa kan maganganun daya fad'a masa marasa dad'i, haka rayuwa ta kasance musu suna da wata biyar a nigeria suka fara shirin komawa dan Ammi tace hankalinta yayi kan su Sam da yanzu suke ajin qarshe a makaranta, Mummyn Sam kuma tace lallai da an koma a sanar mata abinda ake ciki dan ta gaji da ganin d'anta cikin damuwa, gwaggo ma dai wannan karan cewa tayi qafarsu qafarta dan tana son ganin lafiyar yaranta, Kawu kabiru ma shida iyalansa sun shirya tsaf dan kai wa Sam ziyara, a gefe guda kuma hasheem dake niyyar binsu dan yin wani course Rayya tasa rigima lallai se daddynta ya d'aura musu aure ta bishi dan bazata yarda yayi nisa da ita ba, hakan yasa akayi postponding tafiyar zuwa wata biyu masu zuwa, cikin wata guda aka shirya komai aka d'aura auren Rayya jamilu mainasara tare da angonta doctor hasheem se dai bazasu tare anan ba se ya dawo daga tafiyar da za su yi tare. Alhamdulillah komai yazo da sauki as expected! Sam ta had'u da mummynta, haka sun shirya da Ameer, after so many quarrels da su Mummy, gwaggo d umma salamatu suka yi mata ta aminta da auren Anwar duk da taqi sake wa dashi, dan ko an tura ta wurinsa idan yazo hira daqyar take zuwa wani lokacin har da kukan ta, Bello kad'ai ke iya lalla'ba ta ta saurari d'anuwansa, d'aki guda Anwar ya bawa hasheem da matarsa da za suyi zaman shekara d'aya da rabi a nan cikin gidansa na AB machinaries, Wani sabon al'amari daya 'bullo a gidan wanda ya ja hankulan kowa shine yanda bello ke nan nan da Munu, komai ita hatta abinci se yace ita zata zuba mishi, har tsokanar sa su Ammi keyi wai kodai akwai wata a qasa, baya ce musu komai se dai yayi dariya yace "she's my friend" Anwar nayin iya qoqari wajen ganin Sam ta sake dashi, amma abin yaci tura, sau da yawa yana jin yacce mahaifansu ke tata'burza da ita sede abinda ya lura tana da tsaurin ra'ayi, haka zalika tana da riqo which plays a very big role cikin qiyayyar da take nuna masa. *Bayan wasu watanni* "Special kunun aya" bello ya furta yana me jujjuya jug d'in hannunsa, Idanunsa dake a lumshe ya bud'e duk sun qanqance ya watsa masa harara, dakyar ya iya tashi ya nufi kitchen ruwan zafi ya tsiyaya a cup ya matse lemun tsami a ciki ya koma falon ya zauna yana kur'ba kad'an kad'an Hasheem yasa hannu ya d'auke cup d'in lemun tsamin ya zubar cikin sink d'in dining area, kallon juna suka yi da bello suka fashe da dariya, Anwar ya kalle su, "kun san Allah bansan iskanci ku bani abuna nasha dan Allahh" yana magana ne cikin ciccije baki game da rirriqe ciki dan be ma san sun zubar ba, "Kaga malam da matar ka da komai bazamu lamunci ka kashe mana yara ba kaje ka nemi magani a gonarsa" cewar hasheem yana gimtse baki cike da dariya, Wani juyi yayi a qasa yana jijjiga kai daidai lokacin da 'yammatan suka shigo, Rayya ce ta fara yin gaba ta fad'a jikin mijinta "wayyo houb na gaji sosai" Kanta ya shafo game da riqo hannunta "zo mu shiga ciki nayi miki massage babe d'ina" Bello kuwa nufar munu yayi "friend lets go outside kiga wani abu" ido ta waro waje dan mamakin da yake bata kwana biyu dad'a yawa yake kullum shine kiranta suyi hira ko suje shopping, Sam da ta rage ita kad'ai tsaye tayi saurin juyawa zata fita dan dama Rayya ce ta takura musu lallai sai sun rako ta, taji Anwar ya saki wani nishi tun qarfi ai bata san lokacin da ta juya ta nufi inda yake ba, Wani irin numfarfashi yake cikin rawar murya yake fad'in "r..u..wa.." Wawwaigawa tayi bata gani ba se ragowar kunun aya dake cup ta miqo masa kasancewar idonsa a rufe yake be lura ba ya kafa baki ai besan lokacin daya fursar ba ya shiga yin kuka, rasa abinyi tayi ta tashi da niyyar duba ruwan ya janyo hannunta ta fad'o kansa ya ruqunqumeta tamkar ze zira ta cikin jikinsa se zabga gumi yake, jin yanda yake tightening hug d'in kamar ze 'balla ta yasa ta fashe masa da kuka, ba tayi aune ba se jin saukar bakinsa tayi cikin nata . ©️Kdeey😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (33) Sumbatar ta ya cigaba dayi roughly har seda lips d'inta suka canza kala ya kuma cusa fuska cikin dokin wuyanta yana sakar mata love bites cikin wani qananun kuka kamar jinjirin daya jima be sha mama ba, hannunsa da taji yana karairina a ilahirin jikinta yasa ta kuma tsure wa har bata san lokacin da tace, "B..r..o..A da zafiii" A rud'e ya saketa game da kwantar da kansa saman qirjinta yana sakin numfarfashi tamkar wanda iska tayi ma kad'an, Sam de jikinta banda rawa ba abinda yake ga wani ubansun ciwon jiki daya damqeta, Wani sheshsheqar kuka ya sakar mata cikin kunne game da qananun sambatu cikin rawar murya yake fad'in "ho..ld me..h..old..mehhh"ya qarashe game da ruqunqumeta lokaci d'aya jikinsa ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, jin bata kuma jin motsinsa ba har kusan mintuna goma yasa tayi qoqarin tura shi gefe ta tashi gudun kada wani yazo ya same su a haka, Murya tamkar wacce aka qwato yace "Um um baby ki barni please" hawaye ne masu d'umi suka ziraro ta gefen idonta jin abinda yace, Cikin rawar murya tace " qirjina ciwo..kuma kar a shigo...please" Ji tayi yaja jiki gefe ya zauna game da dafe kai da hannayensa zuwa can ya miqe tsaye yace da ita, "come with me" ya miqa mata soft hannayen sa, da kamar ba zata kama ba ganin fuskar nan ba yabo ba fallasa yasa tayi gaba kurum, murmushi yabi bayanta dashi kan ya mara mata mata baya cikin tafiya kamar baya son taka qasa, turus ya tarar da ita a tsakiyar parlorn nasa, yace "shiga ciki mana" game da nuna mata d'akin da ya bud'e da hannu, kamar ta fashe da kuka haka take ji se de idan tayin wa ze lallashe ta?, Kaf mutan gidan bayan Anwar suke bi, Ammi ma da da bata damuwa yanzu ta fara had'e mata rai tana taya su mummy yi mata fad'a, tana tunanin nan bata san lokacin da har ya shiga band'aki ba se jin saukar ruwa tayi a jikinta. Firgigit tayi game da kallon sashen da yake ido ta waro waje ganin ba komai jikinsa sai towel d'aure a qugun sa, da qarami yana goge sumar kanshi Ihuu ta saki tun qarfi, yayi saurin toshe mata baki da hannu, kasancewar jikinsa babu qwari yasa su yin tangal tangal suka fad'a saman gado, Fuskar sa saman tata ba tare da ya sakar mata bakin ba in a low tune yace "ke meye haka? Kar kisa ayi zaton wani abu nake miki" Mutsu mutsu take na qoqarin qwace kanta daidai lokacin aka banko qofar d'akin "Bro.." maganar ce tayi saurin yankewa ganin halin da ya same su ciki, saurin ja yayi da baya game da rufe ido da tafin hannu "Please carry on banga komai ba" yayi saurin barin side d'in baki d'aya. Kuka tashiga yi bil hakki fad'i take "ka gani ba ka gani yanzu shikenan bro B ya gan mu dan Allah ka d'agani..wayyo mummy, wayyo daddy na" Shi kukan nata ma dariya yaso bashi yacce ta kwaye baki tamkar wata d'iyar goye wani hot kiss ya sakar mata tsayi wasu sakanni kan ya mirgine gefe yace "fita before i change my mind" Saurin miqewa tayi dan sauri kamar zata kifa seda ta je qofa tace "Allah ya saka min" ta fice a guje, dariya yayi game da sauke ajiyar zuciya a fili yace "you are indeed a blessing to me, Alhamdulillah" ♡ Kici'bus suka yi da bello tayi saurin sadda kai, "Amm ah..big sis munu is waiting for you outsi..." "Gani.." daga can inda take tsaye tayi waving, "Thank you" tace a hankali ta wuce, shi kuma ya tsaya leqen munu da ta 'buyar masa yana dariya tuno abinda ya faru da yayan nasa da sauri ya shige ciki, "May i come in?" Yace yana me knocking bisa door "Abinda ya kamata kayi d'azu kenan big head" Winking eyes yayi, "sorry bro..." Jan kunnen shi yayi, ya saki ihu cikin wasa, Anwar yace "this is for gani na da kayi da matata a yanayin da be kamata ba and for giving me kunun aya in form of lemun zaqi bayan kunfi kowa sanin matsala ta" Zeyi magana yace "shhh, duba min kayan da zan saka i need to go and talk to Ammi, inason tare wa da matata i can't wait any longer" Gira bello ya d'aga game da kwa'be baki yace "longing for ..." Nufo sa Anwar yayi da gudu ya fad'a closet yana dariya, shima Anwar d'in haka ya dafa kafad'arshi "What going on between you and munu ne uhm?" Ya d'aga masa kai da alamun tambaya, Dariya yayi game da rungumesa yace "wani hanin ga Allah baiwa ne bro, ina mutuqar son kasancewa da ita qarqashin inuwa d'aya, i..i deeply love her ina fatan ta zama mata a gareni" Tightening hug d'in Anwar yayi game da bubbuga bayan bello cikin muryar farinciki yace "i'm so happy to hear this , kasan kamar ka shiga zuciya ta tuntuni nake maka kwad'ayin ta, Allah ya tabbatar mana da alkhairi" *** Bangazar kafad'arta tayi "hey why are you blushing? Kamar wata sabuwar amarya, au ashefa itace" munu tace cikin dariya, Kwa'be baki tayi idonta ya kawo ruwa qiris take jira ta fashe da kuka, munu tayi saurin dafo kafad'arta "Sam is everything ok, ko keda angon naki ne, wullahi Bro A ya burgeni irin wannan nuna soyayya haka tun kan ku tare?" Cikin in ina tace "ke dalla nima bansani ba jikina ke min ciwo" Murmusawa munu tayi game da rausayar da kai tace "ayya sorry habibty muje gida ki amsa medicine gurin Ammi" Ta d'aga kai ido a runtse dan sosai take jin hannun Anwar har yanzu saman qirjinta da ke mata zafi, munu ta katse ta da cewa "Sam inason na fad'a miki wata magana but promise me bazaki fad'ama kowa ba tukun na" Kallon kamar ya tayi mata kan ta kada baki a sanyaye tace "Munu yaushe muka fara haka da ke?" Ido ta lumshe "is just that..hmm..okay,..am.you know ni da bro B.." ta had'e yatsun manunniyarta waje guda, Ido Sam ta waro waje game da cewa "Allahhhhh...har seda ta ja driver yaja birki dan firgicin yacce tayi maganan da qarfi, bubbuga seat d'in da yake zaune alamun yaja su tafi tayi, tace "kina nufin kin fad'a masa kina son sa?.." "Abin Allah, shi da kansa ya fad'a min ba tare dana 'bata lokaci ba na aminta, abinda na jima inaso na samu me zan jira" Dariya Sam tayi game da dukan hannunta "Allah ya shirye ki" "Ameen, yace anjima ze zo gida ya fad'a wa su gwaggo" "Allah ya kaimu" cewar Sam cike da farinciki mara misaltuwa *** "Mariya nifa hankali na ya kasa kwanciya har biyar da kwata yaran nan basu dawo ba anya lafiya kuwa?" "Ammi kenan su fa ba yara bane i'm very sure duk inda suke suna nan lafiya" Girgiza kai ammi tayi hannun ta riqe da waya "bari dai nasa Ann ya bincika min mall d'in da suka je", ringing biyu tayi ya d'aga, "Ammi na.." "Ann pls ka bincika min mall yaran nan sun fita shopping har yanzu basu dawo ba na kasa samun nutsuwa" "Oo Ammi na yanzu suka bar nan na tabbata sun kusa gida by now.." "Suka bar ina? Wane ya basu izinin zuwa gidan ka, zasu zo su same ni" ta katse wayar game da yin qwafa, Dariya yabi wayar dashi duk dan ni Ammi ke kaf kaf da yarinyar nan ever since ta gama makaranta, bata san yau na rage zafi ba, kuma tunda na d'and'ana naji dad'in abin bazan iya hakurin nisanta kaina daga gareta ba, lallai da daddare ma se na rage zafi, duk ranar da na d'ura mata 'ya'yana se ki tarkato min abata mu taho, da tunanin haka ya nufi parlour inda bello yake jiran sa, ♡ Sallamar su ke da wuya ta amsa su ciki×2 game da watsa musu kallon daya sagar musu da gwiwa, "Daga ina kuke?" Ta tambaya idonta saman akwatin talabijin, "Um..amm" Suka hau inda×2 A tsawace tace "Yaushe kuka fara yin gaban kanku ba tare da sani na ba?" Kiru kiru su kayi da ido "Ammi kiyi hakuri rayya ce tace mu rakata.." "Shine kuka zauna kuma?" Rau rau idanunsu suka kawo ruwa wannan ne karo na farko da Ammi tayi musu fad'a haka "Dan Allah Ammi kiyi hakuri baza mu kuma ba" cewar munu, "Ku wuce ku bani wuri"tace ba tare da ta kalli inda suke ba, da sassarfa munu tayi ciki, Sam kuwa jikin Ammi ta fad'a game da fashewa da kuka "Dan Allah Ammi kiyi hakuri bazan iya jurar ganin ki cikin fushi ba" "Haka kuke so ai" Girgiza kai tayi "um um insha'Allahu baza mu kuma ba kinji" Sallamar su Anwar ce ta katse maganar da suke, qasa×2 suka ansa Qirjinsa yayi wani irin bugu ganin Sam kwance bisa kafad'ar Ammi tana shar'bar hawaye tsintar kansa yayi da addu'ar Allah yasa ba fad'awa Ammi abinda ya aikata mata take ba, Qasa qasa yake kallonta se de fir taqi yarda su had'a ido se ma lumshe su da tayi, muryar Ammi ce ta dawo dashi daga balaguron daya tafi, "Soja ka zama ne da zaka tsaya mana a kai" Kai ya sosa game da matsawa jikinta ya zauna "barka da gida Ammi" "Barka ka dai, ina su hasheem da Rayya?" "Suna nan qalau mun baro su zasu fita" "Uhm Allah sarki" "Inasu mummy da gwaggo?" "Suna d'aki" ta bashi ansa "Bari mu gaisa"yace yana miqewa tsaye, seda ta tabbatar sun bar falon tace "Ammi bari na shiga d'aki na watsa ruwa" kai ta d'aga mata har ta fara tafiya ta jiyo muryar Ammi na cewa "zo ki je d'akina kiyi a can" haka kuwa tayi, 3hrs later Fitowarta daga wanka kenan sanye take da towel daidai cinya hannunta riqe da dryer tana drying gashinta aka turo qofa, "Ammi kinjini shiru ko wlh seda na tsaftace d'akin da band'akin shiyasa.." Jin da tayi an tsaya a bayanta yasa ta waiwayo gashinta ya mari fuskar sa ruwa ya shiga dripping saman fuskar sa, murmushi yayi mata game da matso da fuskarsa daf tata yace "ke haka ake zama a d'akin suruka baki da kunya dama?" Turo baki tayi gaba tare da saurin sakin dryer tana mammaqale towel d'inta, hannu yasa saman gashinta yace "meyasa kika wanke gashinki? Ko kema wanka ya kamaki kamar yanda nima nayi d'azu? Uhm" ya goga karar hancinsa saman nata, baby tamkar mayen qarfe nake a jikinki we r gleud" ya qarashe maganar yana manne jikinsa cikin nata tare da cusa hannuwansa ciki wet gashinta, "i adore you beautiful" ya d'an ciza lips d'in kunnenta, "i will never live your side till death do us apart " ya cusa kansa a dokin wuyansa giving her the best hickeys of her life, har bata san lokacin data lumshe ido ba tare da tallafo shi jikinta tana goga gefen fuskarta jikin lallausan sajen shi tasaka hannu ta rungumoshi jikinta, her lips are parted yayin da jikinta ya shiga maida masa martani, hannunta dake bayansa ta janyo har zuwa dokin wuyansa ta shiga shafowa zuwa sumar kansa "Ahhhh..." yayi making erotic sound dan yacce hannunta ke yawo wuyansa ba qaramin rud'ashi tayi ba. "Bro A kazo inji Ammi" daga nesa ta jiyo muryar bro B yana qwalo kiran, daqyar ta iya seta kanta tare da qoqarin d'ago kanshi, "ana kiran ka" tace cikin dashashshiyar murya, idanunsa da suka canza launi ya bud'e cikin nata har tana iya hango kwantacciyar qwalla daga ciki, dad'a lumshe ido yayi game da fad'in "i need you, pls ki tallafeni" gani tayi hawaye na biyo fuskar sa ba qaramin tashin hankali ta shiga ba har bata san lokacin data tallafo fuskarsa ba Tace "dan Allah ka dena kuka, zanyi maka duk abinda kake so kar Allah yayi fushi dani kaji" One sided murmushi yayi "wane yace miki haka?" "Gwaggo, tace idan har kace nayi maka abu naqi se Allah yayi fushi dani" Jimm ya d'anyi kan yace "sa kayan ki kizo muje wurin Ammi " "Ammi?" Ta tambaya "Yeah, kinji dai abinda gwaggo tace miki ko?" Ta d'aga kai "to maza shirya kizo kiji wata magana" Nodding tayi, ta shiga closet d'in Ammi tasa kayanta, sannan ta qarashe drying kanta, kula da cewa bata shafa mai ba se da yasa ta tu'be ya mulketa wanda ya d'auke su kusa rabin awa har seda ta fara yi masa kukan shagwa'ba, se da su kayi sallar isha suka fito falon. 8:00pm Jero wa suka yi har gaban dining table inda kowa ke zaune ana kwasar dinner ya ja mata kujerar kusa da bello ta zauna ya zauna opposite tata, tashi tayi ta zuzzuba musu suka fara ci ba tare da sunce uffan ba, d'ago kai yayi yaga kowa ya maida hankali kan abinci, gyara zama yayi game da miqe qafa ya zira ta ciki qarqashin teburin seda ya tabbatar ya ta'bo qafarta har ta d'an kallo shi, yayi murmushi Ya shiga yi mata tafiyar tsutsa a sangalelen ta, sede bisa mamakin sa ko kallo be isheta ba, sema dariya da take ita da munu yatsu ya had'e guri d'aya da niyyar mintsininta yaji qafa baibaye da gashi saurin maida idonsa yayi qasan table me ze gani, bello ya kalla yaga ya d'aga masa gira game da murmushi, haushi yasa shi kicking qafar har se da bello yayi ihu, ya miqe rai 'bace ze bar wurin Ammi tace "Ann samu wuri inason magana da ku" Zama yayi a salu'be tace "munyi magana da 'yanuwana nan da sati biyu zamu miqa maka matarka dan baze yiwu ku rinqa yi mana rashin kunya a gida ba, and again za'a daura auren bello da mubina (munu) a ranar asabar d'innan me zuwa..." bata kai ga qarasa maganar ba wayarta tayi qara, da hannu tayi musu alamar tana zuwa, qaga wayar a kunnenta ke da wuya ta sake ta game da yin salati... "Allah ya yiwa maryam rasuwa" ©️Kdeey😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (34) Rud'ewa falon yayi da koke×2, an rasa me lallashin wani 'yan mazan ne sukayi qoqarin basu baki, wayar sa dake haske ya d'aga ganin sunan hasheem yasa shi saurin picking daga can yace "Dagaske ne abinda nake ji?" "Yea...ina matar ka?" "Gamu a asibiti bata san wanda ke kanta ba" "Ka kula da ita bari naje na samar mana ticket" Sallama sukayi, gaban Ammi ya qarasa ya shaida mata fitar sa, nan ya bar bello wurin su. *** Bayan kwana hud'u ~Uncle ne ya tarbesu a airport d'in malam amin kano inda ya wuce dasu direct zuwa gidan gomnati dan can ake zaman makokin. Da isar su wuri ya kuma hautsinewa ganin Rayya kowa se gaisuwa ake musu, duk wani mahaluqin dake gidan se ya zubda hawaye idan ya kalli jamilu mainasara, duk ya rame ya qojale ya fita hayyacinsa to abune ya had'e masa ga abinda ya had'asu da Maryam, ga rashin d'iyarsa tilo data za'bi tabi mijinta ga musibar mutan gari da kullum ke yada mishi magana kan cewar ya zalunci matarsa cikin qaryayyakin da ake yad'awa ma har cewa akayi kamashi tayi da 'yar uwarta, yanzu haka yafi sati biyu kwance ba lafiya . Hasheem ne zaune gefen kanta hannunsa cikin nata ta hanashi matsawa ko can da nan, kusa da su Sam da munu ne sunyi jugum×2 su Ammi na can main parlor tare da manyan baqi dake zuwar musu gaisuwa daka gari×2, Da taimakon Allah da ma'aiki aka tashi zaman makoki lafiya, kwanan su biyu da zuwa aka je can family house d'in gidan baban su munu aka d'aura aurenta da bello bisa sadaki naira dubu d'ari biyar bisa waliccin qanin mahaifinta commissioner of agriculture Alh sabe doguwa, Duk wani abinda ya dace na al'ada anyi shi na daga zaman makokin hajiya maryam, duk wannan zama da ake Rayya taqi yarda ta had'u da mahaifinta duk ko da qoqarin da yake na ganin hakan ya faru, ko jin muryarsa tayi yanzu zata bar wurin, kasancewar rashin lafiyarta yasa su mummyn Sam suke lalla'bata sai de a ranar da suka cika sati uku aka sa hasheem ya kawo ta a zauna, A babban falon sirri na jamilu mainasara suka taru Ammi, mummyn Sam, gwaggo, mom hajar, barr, da me girma gomna ke zaune saman kujera yayin da duka yaran ke zaune qasa, Sam kusa da qafar mummyn ta, munu kusa da gwaggo yayin da hasheem, Anwar, bello ke jere a gefe d'aya, Rayya kuma na kwance gefen Ammi se ka rantse bacci take amma idonta biyu hasali ma hawaye ke zuba a idonta "Da sunan Allah me rahma me jinqai, me bayarwa me amshewa, na tara ku anan ne ba dan komai ba se dan ku tayani bawa d'iyata ha'kuri ku kuma tambayar min ita shin meye laifina a gareta? Mahaifana a late yanzu matata ma haka and wacce kawai zan kalla naji sanyi ta juya min baya, a yanzu ita kad'ai ce dangi na amma duk yadda naso ta saurareni abin yaci tura, to shine nake so ku taimaka min kuyi mata magana wataqil ku ta amsa ku" "La'haila ha ilallahu yau naga yaran zamani, ke rayya maza tashi zaune" cewar gwaggo tana tafa hannuwa, Ammi rai 'bace tace "haba jamilu 'yar cikinka ta gagare ka tanqwasuwa,..ke yanzu ba se anjima ba ki nemi gafarar mahaifinki! Yanzun nan!" Taqarashe a tsawace, Ajiyar zuci ta yi kan ta tashi zaune ta waiwaya sashen da suke cikin zubar hawaye tace "ku min afuwa iyayena na wlh ba ina yin haka bane dan na quntata ma mahaifina se dai na gaza sake wa ne saboda illar da mahaifiyata ta yi masa, a kullum na ganshi se mahaifiyata ta fad'o min, ku yafe min daddy" ta tashi ta je ta tsugunna kusa da qafarsa, "daddy i'm very sorry ka yafe min...and pls ka yafe ma mummy na.." tayi adding cikin zubar hawaye, Hannu ya d'ora saman kanta ya shafo, "ba kiyi min laifin komai ba Rayya, tsorona be wuce laifin da nayi miki ba abinda kika fad'a yanzu kuma ko waye a matsayinki abinda ze yi kenan, na yafe miki and pls be open to me banason shiru shirun nan da kike yi min uhm?" Kai ta d'aga, ya jata jikinsa ta kwanta, "to Alhamdulillahi" cewar Ammi, "Rayya mahaifinki a yanzu shi ze taka rawar mahaifiyarki idan kina da damuwa let him know duk abinda ya ke ze saurare ki, we all can come in your second option uhm?" Mummyn Sam tace looking at her, Kai ta d'aga with a smile plastered on her face kan ta kalli sashen da 'yan mazan suke tace "daddy nagode da afuwar ka a gareni but pls ina son kayi min wani abu in return" "Anything for you my daughter " "Idan duk ranar da mummy tayi 5 month zan fad'a maka, karka manta kayi min alqawari" "I promised" "Amm...i think ya kamata kafin mu tafi a tsaida ranar tarewar yaran nan dan bana son wata bidi'a ko ya kuka gani" Ammi ta qarashe idonta akan barrister da gomna Barrister ya jinjina kai "hakane nake ganin idan babu damuwa akwai gidajen su dake nan daura da nawa a gyara idan yaso su fara tare wa anan kafin mu koma" "Which means dole ayi d'an biki kenan idan ba haka ba mutanen mu su samu a bakin duniya" cewar gwaggo, dariya sukayi a take aka tsaida nan da sati biyu masu zuwa za a sha shagali. Ranar Biki Qoqarin kai hannu take ta ja zip d'in amma sam ta kasa cikin cuno baki take fad'in "ni ni ni Allah na gaji bazan ma fita ba, zir zir hawaye ya hau zubo mata, saman gado ta fad'a ta game da janyo wayarta tayi dialling number, bisa mamakin ta se jin ringing tayi a d'akin "mummy why do you left the fone here? Ta qarashe cikin chidish tune, Wayar ta cilla gefe jin da tayi an rufe qofa alamar an shigo ita a dile tayi fushi duk a tunanin ta mummy ce. Qamshin turaren TOBACCO daya bigi hancinta yasa ta sauke ajiyar zuci game da lumshe ido, she doesn't see dis coming, ta ina ya shigo cikin tarin jama'ar nan? Ta tambayi kanta Tafiyar tsutsan da yake mata yasa tayi saurin juyawa rigingine game da sakin dariya, "perfect" yace, qafafuns ya raba game da hawa samanta ba tare da ya ta'bata ba har seda fuskarsa ta daidaita da tata ya sakar ma kyawawan lips d'inta sumba kafin ya zira hannuwansa ta bayanta ya tallafo ta jikinsa, shiru ne ya biyo baya kan a hankali yace "nazo shirya amarya ta" Wal tayi da ido, ya kanne mata idonsa, dariya tayi tace "ina su mummy?" "Nace dasu su huta ni zan shirya abata" "Mene?" Yanda ta waro ido ya sa shi dariya, daidai lokacin suka ji knocking, " maza tashi ta qaraso" "Wa kenan" Miss dee from abuja na taso ta takanas saboda ta shirya min ke, qofa ya bud'e matar ta shigo kallo d'aya zaka mata kasan ta jiqu da naira ga uban gayu da take dashi cikin daddad'an muryarta data tsumu da turanci suka gaisa da Anwar kan ta maida idonta kan Sam game da furta kalmar "tubarkallah, amaryarka tamkar ita tayi kanta, she is the real definition of beautiful," Murmushi ya saki yana jin tamkar duk duniya ba wanda ya kai shi sa'a, miss dee ta kuma cewa "we are running out of time, oga sir ka bani aron amaryarka for just 3hours" Kai ya d'aga kan ya matsa jikin Sam ya bata peck a goshi "take care" ya furta cikin kunnenta da haka ya fita mutan gida ana tayi masa tsiya wai dududu awa nawa ya rage a kai masa ita, be kulasu ba se murmushi da yake saki har ya bar musu gidan baki d'aya, *** Few hour later Hawaye ne masu d'umi suka gangaro bisa fuskarta, "shiii kada ki 'bata mana shirin mu ango ya kasa biyana in ponds kamar yanda ya alqawarta" cewar mss dee Murmushi ya su'buce mata, still idonta bisa mirrow gani take kamar ba ita ba, sanye take da royal blue gown wacce take fitted se de ta bud'e daga qasa sosai har ta mamaye kusan rabin d'akin, sosi rigar tabi duk wani curve na jikinta ta kwanta showing her real figure 8 shape, fuskar nan tasha nude make up yayin da sumar kanta aka killace ta cikin royal blue head wuyanta da kunnenta se kyallin gold suke haka hannunta cike yake da kambunan gold, an sakaye qafarta cikin heel d'in dune yayin da clutch d'in hannunta ta zama ta kamfanin dune itama, duk inda ta motsa qamshin turaren khumra da tsadaddun designer turaruka ke tashi, wasu hawayen ne suka kuma yanko mata mss dee tasa tissue ta d'auke mata su, "wai su hawayen nan bazasu dena zuba bane" "I wish daddy na is alive to see this day" tace cikin muryar kuka "I'm sure he is watching from heaven" Murmusawa tayi kawai jin abinda matar ta fad'a daidai lokacin akayi knocking sholey ta shigo itama cikin ubansun kwalliya, "Hello besfrenn" tace cikin juyawa dan Sam taga kwalliyarta, a hankali ta karkato haba ai sholey daka tsalle tayi tana ihu "wow babe kinyi kyauuuu..."taja kalmar kan ta fad'a jikinta suka rungume juna ta d'auko wayarta qirar iphone 11pro ta d'add'ana mata pictures sannan ta fita dan kiran motar da zata d'auki amarya ta matso bakin qofar falon, Da taimakon mss dee ta tako d'as d'as zuwa waje sholey ta bud'e mata qofar baya ta shiga kan ta juya itama ta shige motar dake gaba, Hannu taji an zira cikin nata wanda ko ba'a fad'a ba tasan mamallakin su kasancewar motar da duhu yasa bata ganin fuskarshi sosai, daf da ita ya matso game da zira fuskarshi cikin wuyanta yayi kissing sannan ya miqa hannu ya kunna fitila, seda yayi blinking eyes sannan ya juyo da fuskarta setin da yake, "tubarkallah Masha'Allah" yace game da kashe wutar ya janyo ta jikinsa ya rungume haka suka zauna har seda suka isa harabar da zasu sauka wanda shima kan su saukan seda paparazzi suka gama buga musu hotuna har dai suka isa cikin hall inda tuni amare da angwaye sun hallara sune a tsakiya daga gefen hagu bello da munu ne daga dama kuma hasheem da Rayya dukkan ninsu sun sha kyau abun dai se Masha'Allah. Anci ansha an gintse, direct daga nan angwaye suka kwashi amarensu zuwa gidajensu kamar yanda gomna jamilu mainasara ya umarta. A gurguje🤸🏻‍♀ Yau watansu uku cif da tariya, wanda yayi dai dai da rasuwar hajiya maryam mahaifiyar Rayya, "Baby please mana..." cewar Ann dake zaune saman dining table yana cin gasashen naman rago" Sam dake tsaye gaban cooking gas tana juye irish a plate jikinta sanye da oversized shirt wacce ta sakkomata har rabin cinya , kallo d'aya zaka mata kasan ta Anwar ce tace "baby ni Allah se ka jira mun gama cia nutse sannan za muyi wanka baza mu fita da yunwa ba" "Baby cikina is full, kalla kiga yanda tumbi na ya girma" yace a shagwa'be "Ka bani minti kad'an kaji yanzu zan gama" Tagumi yayi with a pout on his face ya zura mata ido yana mamakin yacce kwana biyu kullum se tayi breakfast da irish take jin dad'i shekaran jiya daya hanata har da kukan ta, jira yayi har ta gama ya sa'bi abarsa zuwa band'aki inda suka sullu'bo wanka bayan ya nad'o ta cikin towel ya ajiye ta, suka mulke jikinsu da tsadaddun mayuka masu gyara fata sannan suka kimtsa suka fita zuwa gidan gomna. A tare suka jera zuw cikin falon kowa ya hallara su kad'ai ake jira, kallon juna sukayi sannin cewar sunyi laifi bayan sun gaida kowa taja jiki ta zauna tsakiyar munu da rayya shima gurin d'an uwansa da amininsa ya zauna , nan daddy ya kalli rayya yace "daughter bismillah yau zaman kinsan naki ne" Murmushi tayi wanda ya fallasa 'yan tageyen kumatun da tayi bayan sallama irin ta addinin musulunci ta kalli mummyn sam tace "mummy, nazo da qoqon bara ta da fatan zaki tallafa min?" Murmusawa mariya tayi " idan har ina da abin tallafa miki insha'Allah zanyi da dukkan qarfi na" Kai ta jinjina "daddy yau watan mummy 5 cif da rasuwa idan baka manta ba kayi min alqawari kuma yau nake son ka cika min" Kai ya d'aga, seda ta kalli mutan falon tsaf kan ta sauke idonta kan fuskar mijinta ya jinjina mata kai ta sauke ajiyar zuciya Tace"inason kayi replacing gurbin mummy da mummyn Sam" A birkice mummyn sam tace "what?!" Yayin da Sam ta miqe tsaye a firgice, Ammi kuwa hawaye game da murmushi ne suka maye fuskarta, kowa na falon ya cika da mamakin qarfin hali irin na Rayya, Sam ce ta fita daga falon a guje, mummynta ta bita, Anwar da Ammi ma bin bayansu sukayi, shiru falon yayi, hawaye suka ziraro a idon Rayya tana kallon mijinta tace"ka gani ko dama nasan baza su aminta ba" "Doctor jikin nata ya tashi ne?" Cewar mainasara, "Daddy...lafiyata qalau i know what i'm doing, na tabbata deep down inside you kanaso dan Allah kar kace aa i know mummyn sam too zata amince kar ka manta she's your first love inaso ka cika burin da ka jima kana mafarkin samu, this is d only way i can repay you kan 'bata maka rai da nayi lokacin rasuwar mummy please don't say no kaji.." "He won't say know.." waiwaya wa tayi ta kalli Ammi cike da mamaki, Ammi ta riqo hannun mariya tace "jamilu for the second time zan baka amanar 'yaruwa ta" Miqewa yayi game da d'an duqawa irin na girmamawa yace "nayi miki alqawari ko quda baze sauka saman fatarta ba without my permission" Sam dake tsaye ta bayansu tace "na yarda, Allah ya sanya alkhairi" ta qarashe cikin rawar murya sosai take jin kishin wani ze kasance da mahaifiyarta. A take me girma gomna yasa a nema masa zama da me martaba inda basu wani d'auki lokaci ba cikin satin aka d'aura aure, inda mummyn Sam ta tare a gidan gomnati matsayin firstlady, Bayan sati biyu, Ammi da iyalanta suka koma Birmingham inda zasu cigaba da zama lokaci lokaci zasu rinqa ziyartar qasarsu wanda Anwar yaci alwashin da ya gama ginin reshen AB machinries zasu dawo dun dun dun se ko idan ziyara, wanda hakan ba qaramin dad'i yayi wa Ammi ba, A gefe guda kuma a kullum jamilu mainasara cikin shiwa Rayya albarka yake, ganin tun lokacin daya auri Mariya yake samun cigaba ta ko ina, Bayan shekara hud'u "Kai ku d'agashi before nazo kan ku" Sam tace a tsawace, a firgice yaran suka fashe da kuka har suna sheshsheqa, Fuska shaye da toka yace "baby wai meke damun ki ne jiya mafa seda kika saka su kuka" "Oh shikenan kuma ban isa nayi ma yarana fad'a ba se ace meke damuna" fashewa tayi da kuka game da juyawa ta fad'a d'aki, "Innalilllahi" ya furta kan ya sa'bi twins d'in a hannunsa suka bi bayanta, kusa da kanta suka zauna ganin yaran na kya'be baki alamun suma zasu yi kukan yasa shi saurin dakatar dasu yace "heyys kuce we are sorry mami" Cikin gwaracinsu kuwa suka fad'a, tashi tayi zaune tana tura baki gaba ta janyo su duka jikinta tana kissing, jan jiki yayi zuwa gareta cikin kunnenta yace "nifa?" Hararar wasa tayi masa kan ta kwantar da kai saman qirjinsa tace "I'm pregnant" "Alhamdulillah" yace game da dira a qasa yayi sujjada, tayi rau rau da ido "are you happy?" Kallon ta yayi game da kallon twins dake lafe a jikinta bacci ya kwashesu ya amshe su d'aya bayan d'aya ya kwantar dasu a gadonsu kan ya zo ya jata jikinsa su kwanta hannunsa d'aya saman cikinta yana shafawa d'ayan kuma saman kanta yana mata susa, "I'm excited baby, kyautar mutum fa? Kinsan kullum addu'a ta itace Allah yasa na kasance cikin d'aya daga cikin wanda annabi zeyi alfahari dasu, baby Allah yasa yanzu ma ki haifar min twins" Dukan qirjinsa tayi, yace "yes kinga Afif da Affan sun cika 3years.." "Saboda kullum ku isheni da qiriniya ba uma su rinqa tumurmusheka" "Shine damuwar ki, shiyasa kike musu fad'a wlh baby idan ina tare dasu Allah kad'ai yasan irin farincikin da nake ace wai dukkan su jinina ne? Huh Allah is great" Jin da yayi tayi shiru ya leqa fuskarta yaga ashe she's fast asleep, a fili yace "wannan da rikici da kuma bacci kazo kenan" kissing d'in cikinta yayi tare da tofa musu addu'a duka shima ya shige jikinta lokaci d'aya bacci ya d'auke shi. _Tammat bi hamdulillah_ Na sadaukar da wannan littafin nawa ga duk wani masoyin rubutu na, sai kun jini cikin sabon littafina me suna ...DA CIWO A ZUCIYA TA Whatsapp only; 08148700538