[05/12 à 16:45] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9QNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780252 05/12/2024 *Page 01* Inalilahi wa ina ilaihi raju'un! Na sake maimaitawa a karo na ba adadi, radaɗin da nake ji a cikin zuciyata ya girmi tunanin duk mai tunani. Idanuna na rufe kwala na ci gaba da yi min tsiyaya kamar ana ruwa da bakin ƙwarya. Ganin dai zaman ba yi min zai yi ba sai na tashi na shige toilet ɗin ɗakina na sake yin wani wanka domin zafin da zuciyata ke yi irin shi sai nake ji a jikina. Ina fitowa daga wanka na shiga zaɓar kayan da zan saka tuni kuma na share hawayena na aro jarumtar duniya da wani kayatacen murmushi na ɗaura akan fuskata. Ta baya na ji an rungume ni sai na ture hannun na ce"Qalbi kaya nake sakawa" juyo da ni ya yi ya ce"An ki a saka kayan" murmushi na yi mishi na ce"Haba nawan a yi min afuwa na saka ko da riga ce" na faɗa ina haɗawa da yar shagwaɓa wadda na riga na san tun ba yau ba tana tafiya da duk wata nutsuwarshi. Saki na ya yi kamar dai yadda na sani Ni kuwa na dauki riga ta na saka na shafa mai na ce"Qalbi office fa?" Girgiza kai ya yi ya ce" Yau fa ba zan je ba" gyara tsayuwata na yi a daidai lokacin da na gama gyara rolling ɗin babban mayafina na ce "To Qalbi ni kam zan tafi idan ka gama hutun ka same ni a can" bai amsa min ba wannan ya bani tabbacin yau yan miskilancin sun motsa sai na ɗauki key din motata da Jakata na fice daga ɗakin. Ƙasa na sauka na tarar da ahalin gidan na fama yin breakfast sai na karasa na gaishe da iyayen har ƙasa amsa min suka yi kafin na fice zuwa office. Ina ba falon baya Mama Sa'a ta ja tsaki ta ce"A haka kuma a ce ana neman aljanna, ko mijinka ba ka damu da shi ba bare kuma ka tsaya kula da shi sai yawon gantalin zuwa office" dariya Rumana ta yi ta ce"Ke ma Mama da wani zance to ba sai mutum ya sami tarbiyya ba zai san mene ne hakkin miji ba" caraf Jidda ta amshe zancen da cewa"kar fa ku manta yar mace ce a ina za ta sami tarbiyya bayan ba su da uba" haka suka yi ta cirawa suna mayarwa har suka gama cin abincinsu. Sai da suka gama ne masu aiki suka shiga kwashe kayan abincin kafin Abdallah ya sauko ƙasa bin falon yake da kallo a cikin ranshi kuma yana tunanin kenan da gaske ne Sumayya office ɗin ta tafi ta bar shi. Taɓe baki ya yi kafin a fili kuma ya ce"Kin ga abin da zan yi miki" kafin ya ƙarasa fakon ya gaishe da Mama da ke zaune tana faman kallon TV kafa daya kan daya. Ta ce"Ya aka yi ba ka tafi office ba Abdallah?" Sosa keya ya yi ya ce "to da ba zan je ba amman kuma na ga gara kawai na je zan rage wani aikin" murmushi ta yi ta ce"Gaskiya kam Gara ka tafi , don mai kirjin na iya ɗin can har ta tafi kar ka je ka na zaune a nan ta sace maka kuɗi" kicin-kicin ya yi da fuska ya ce"Dan Allah Mama ki daina, bana son jin ki na zagin Sumayya don sai babu yadda zan yi ne" wani irin uban ihu ta yi har dankwalin kanta na kunce wa ta shiga tafa hannu tare da yin salati ta ce"Allah mai iko kai Abdallah yanzu Ni kake faɗa wa wannan magana, ba shakka biri ya yi kama da mutum" shiru ya yi yana jin babu daɗi abin da Mama ke faɗa kuma ta bangare ɗaya yana ji a cikin ranshi babu daɗi idan ya ci gaba da zuba ido kullum tana zagin Sumayya ɗin. Tashi ya yi ya bar wajen tare da nufar office. Yana fice wa Rumana da Jidda wanda tashin su daga barci kenan suka iso falon suka tarar da Mama tana ta bambamin masifa. Rumana ta ce"Me kuma ya faru?" Kwalla ta fara matso wa tana fadin "Ba Abdullah ba ne yau kam ya nuna min Sumayya ta fini a cikin gidanan, wai fa ce min ya yi na daina zaginta" wani uban ashar Jidda ta yi ta ce"Dama ba faɗa miki ki bari mu ɗauki mataki akan wannan yarinyar amman kika ki duba fa dan Allah yanzu har yaya Abdallah ya kai matakin da zai riƙa mayar miki da magana Duk a kanta" tsaki Mama ta ja tana mai ci gaba da kokarin ɗaura dan kwalinta da har yanzu ta gaza ɗaura shi ta ce"Ni fa tun farko da na san haka za ta kasance Allah ne shaida ta da ba zan bar wannan auren ya kasance ba" ita da ƴaƴanta suka ci gaba da jefa maganganunsu wadda duk rabi suna zagin Sumayya ne da su.. Ina zaune a office aka turo ƙofar tare da shigowa ban dago ba saboda na riga da na san idan dai ba Abdallah babu wanda da zai yi wannan ɗanyen aikin. Sai da ya ja kujera ya zauna kafin na ɗago da murmsuhina na ce"Yanzu sallamar ma wuya take yi wa wasu" bai yi magana ba sai ma watsa min wata tambaya ya yi "Me kika yi wa Mama tun safe take faɗa?" Girgiza kaina na shiga yi don tun tuni hawaye sun cika min idanu duk da kuwa idan dai da sabo ya dace a ce na saba da wannan hali na mijina a duk lokacin da ƴan uwanshi ko mahaifiyarshi za ta ce na yi mata wani abu wuni zai yi yana yi min faɗa yana cin magani sai na ce"Ni kuwa Qalbi gani nake wannan maganar ba ta dace a yi ta a nan wani zai iya jin mu idan muka koma gida sai mu tattauna a cikin nutsa ina ganin hakan zai fi" bai sake wata magana ba ya tashi ya fice daga office ɗin. Girgiza kaina na yi kafin na ci gaba da aikin gabana. Tun la'asar na haɗa komatsaina na nufi gida bayan na yi wanka na yi salla sai na sauka kitchen don haɗa abincin dare. Bayan na gama na jera a dinning kafin lokacin cin abinci ya yi don gabadaya a nan muke taruwa mu ci abincin. Ko da Abdallah ya shigo gidan ko kallon wajen da nake bai yi ba ya haura sama abin shi. Ko da lokacin yin dîner ya yi a falonmu na tarar da shi yana aiki a laptop ɗinshi zama na yi na ce"Qalbi ka yi hakuri ka san ba na iya ƙurar fushinka a kaina, da ka yi fushi da ni gara a yi min bulala ɗari da hamsin" sai na ƙara marairaice fuska na ce"Dan Allah ka yi hakuri Qalbi" sai yanzu na samu na ga ɗigon rahama a fuskarshi ya buɗe baki da niyyar ya yi magana sai Mama ta banko kofar falon tare da shigowa kamar an cilo ta daga sama ta ce"Ke munafuka algunguma tashi ki bani waje ina son ganawa da ɗana" ban tanka ba sai miƙewa da na yi na nufi ɗakina na zube akan gado tare da rafka wani uban tagumi *Assalama'aleikoum Allah ya sake haɗa mu a wani sabon labarin, ina fatan za ku bi shi domin daukar darasi da dama a cikinshi* [06/12 à 00:19] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 *Page 02* Bayan na shigo ɗakin na rafka uban tagumi sai ga Abdallah ya shigo ɗakin, zama ya yi a bakin gado ya watsa min manyan idanunsa masu rikitar da ni da sauri na kawar da nawa idon na fara wasa da yantsuna ina jiran jin abin da zai fara da shi sai kuma na yi shiru na tsawon lokaci. Na ɗago da idanuna sai kuwa ya sauka akan nashi don dukan alamu shi ɗin ma Ni yake kallo. Ya ce"Sumayya!!" Da wata irin murya mai nuni da gargaɗi, tuni na sha jinin jikina na ce"na'am Qalbi" "Sumayya me kike son zama ne a cikin gidan nan? Rigimar safe daban ta rana daban" idanuna tuni sun kawo kwalla ina gab da fara kukan da idan da sabo ya ci a ce na saba da shi na ce"Qalbi me ya faru? Ko ma mene abin da na aikata ina son ka yi min uzuri ka saurari nawa jawabin" wani tsaki ya ja wanda har cikin raina na ji shi sai ya ce"Ina son daga yau ki shiga hankalinki ba na so Mama ta kuma kawo min ƙara akan kin yi mata wani sai na yi mugun saɓa miki, kin ji ko?" Gyaɗa kai na yi kamar wadda ke tsoron magana na ce"Allah ya huci zuciyarka Qalbi" bai ko sake sauraren maganata ba ya bar ɗakin. Tashi na yi na yi wanka na fara nafila ina jero addu'oi wadda idan da sabo tun tuni na saba, Allah ne kaɗai gatana ba ni da wani wanda ya fi shi na riga na miƙa gabadaya lamurana a hannunsa. Ban san lokacin da barci ɓarawo ya ɗauke ni a wajen ba sai da na ji an fara kiraye-kirayen sallar asuba kafin na tashi na ɗauro alwala. Ina gama salla na fara aikin gyaran bangaren nawa. Ko da na isa ɗakin da Abdallah ya kwana na tarar bai dawo daga masallaci ba. Aikin gabana na ci gaba da yi har ya shigo ɗakin, har ƙasa na tsuguna na gaishe shi amsawa ya yi cikin fara'a kamar babu abin da ya faru a daren jiya, babban dalilin da ya sa nake ƙara jin kaunar shi a cikin raina bai kasance mutum mai riƙo ba duk abin da ya faru da an ɗauki lokaci zai sauko kamar ba a yi ba. Rungume ni ya yi tsam a jikinsa ya ce"Babe, fatan kin kwana lafiya?" Murmushi na yi na ce"Lafiya qlau Qalbi ina fatan kai ma haka" da kai ya yi min alamar lafiya qlau kafin ya ce"Ki je ɗakin Mama ki yi mata shara da mopping idan kika gama aikin da kike yi" idanuna na ɗago daga kan kirjinsa na ce"Amman Qalbi masu aikin gidan fa" yatsarsa ya saka akan lips dinsa alamar na yi shiru sai na yi gum da bakina na fice daga ɗakin. Ƙasa na sauka na shiga kitchen na fara haɗa kayan da za mu yi breakfast da shi. Dakin Mama na shiga da sallama a bakina tana zaune akan bed dinta tana faman jan carbi ta amsa min, har ƙasa na tsuguna na gaishe ta ba ta ko kalle ni ba ta amsa min daƙyar sai na ci gaba da cewa"Mama dama na zo ne don gyara miki ɗakin ne" tana cin magani ta ce"Sumayya tashi zan yi don ki share ɗakin" girgiza kai na yi na ce"A a Mama amman ki yi min uzuri na gyara kin ga zan je office" tsaki ta ja ta ce"Sai ki tashi ki tafi idan na gama abin da nake yi zan yi miki magana sai ki gyara ɗakin" kamar yadda ta faɗa ban ƙara furta wata kalma ba na bar ɗakin. ★Abdallah★ Tunda ta fice daga dakin na zauna tare da rafka tagumi tunani nake a raina ina zan samu mafita, bana da burin da ya wuce a rayuwa na ga Sumayya cikin farin ciki da kwanciyar hankali sai dai kuma hakan ta gagara kullum cikin musguna mata nake rana ba ta fito wa ta faɗa ba ta zubar da hawaye a kaina ba, ina zani da wannan alhakin? An ya zan iya kwanciyar kabarina da alhakin Sumayya a kaina kuwa? Ire-iren tambayoyin da nake jefa wa kaina a duk lokacin da zan kasance ni ɗaya a zaune sai dai kuma kash ba ni da amsar su. Ban ma san abin da yake hana ni saka matata a cikin jin daɗin duniya ba, duk maganar da aka faɗa min daram nake hawa kan ta na zauna, wannan lamari zai haifar min ɗa da ido kuwa? Turo ƙofar ɗakin ta yi har yanzu fuskarta dauke da mutmushi wanda idan ba ni da na yi mata farin sani ba na san sarai wannan murmushi ne mai kama da kuka ne take yi, sai da ta ƙaraso wajen da nake zaune kafin ta zauna akan cinyata ta ce"Qalbi mutanen gidan ba su tashi ba, na kawo maka breakfast ɗin ka nan ne?" Gyaɗa mata kai na yi alamar e mutmushi ta kuma yi kafin ta ce"Yau kam da ƴan miskilancin muka tashi" daga nan ta fice zuwa kitchen da dukan alamu. Ina zaune a wajen jim kaɗan sai ta dawo ɗauke da katin plate mai kayan breakfast a ciki. Ba ta damu da sakawa a cikinta ba haka ta zauna tana bani a baki ina ci har na koshi kafin na riƙe mata hannu tare da girgiza mata kai alamar ya isa haka. Ajiye cokalin ta yi ta shiga goge min baki sai na ce"Kin yi abin da na saka ki?" Girgiza kai ta yi ta ce"Mama ba ta tashi ba ta ce min idan ta gama za ta kira ni" ban ce mata komai ba sai gyaɗa kaina na yi kafin na zame ta daga jikina na nufi toilet. ★Sumayya★ Kayan breakfast ɗin na kwashe na kai kitchen haushi Qalbi duk ya mamaye min zuciya kenan bai gamsu da bayanin da na yi mishi ba ne ko mene ne da zai wani ture ni ya fice zuwa toilet. Ban damu da cin wani abinci ba ne haka na haura ɗakina na yi wanka kafin na yi shirin zuwa office. Ko da na gama ban kuma bi ta kanshi ba don na tabbata ya bar gidan na sauko ƙasa na dauki motata na nufi office ɗina. Da yamma ko da na dawo gida ina buɗe kofar falon da Mama Sa'a na ci karo ta watso min wani kallo wanda ko sallamar da na yi ba ta amsa min ba. Gaishe ta na yi duk dai na san babu tabbas ɗin amasarta sai na fara kokarin haura steps don zuwa ɗakina ta ce"Ke Sumayya zo nan" juyawa na yi na je na ce"Mama gani" tsaki ta ja ta ce"Ni sa'ar ki uwarki ce da za ki tsaya min a ka kikam" zama na yi akan cafet ɗin fakon ba tare da na yi magana ba ta ce "Ɗazu da safe ba na ce miki ki jira ni zan yi miki magana akan gyara min ɗaki shi ne tsabar isakanci kika fice daga gidan don ban isa da ke ba ko?" Girgiza kai na yi na ce"Mama ba haka ba ne na ga zan makara ne shi ya sa na tafi" wani kallon mai saman ruwa take yi min ta ce"To ai yanzu kin dawo tashi ki je gyara min" tashi na fara kokarin yi ina faɗin "To zan kai canza kayana sai na zo na gyara yanzu" girgiza kai ta yi ta ce"Ajiye jakar ki je ki yi min abin da na saka ki" ban kuma tanka mata ba don na san idan na tanka ma a kaina za ta ƙare, kawai sai na cire mayafina da jakar na zubar da su akan kujera har wayata da makulin mota na nufi ɗakin Mama. Mama Sa'a na ganin Sumayya ta shiga ɗakinta don gyara shi sai ta ja tsaki a ranta a fili kuma ta ce"Shegiya mai sunan mage" zama ta yi don ci gaba da kallon tv sai kuma hankalinta ya sauka a kan handbag ɗin da Sumayya ta ajiye ta shige ɗaki. Nan ta buɗe ta ido ta zaro tozali da idanunta suka yi da bandir ɗin ƴan jika goma sababi a miƙe. "Tabdi, wannan yarinyar a ina ta samu kuɗi haka?" Ta faɗa tare da ciro kudin ta shiga juya su a hannunta "wannan kudin kam idan dai ba a office ɗin Abdallah ta sato su ba, zuwa ta yi ta budé wa wani gardin kafa ya bata su, jika ɗari (200k) ne fa" ta faɗa tana ƙara karewa kudin da ke hannunta kallo ji take kamar ta ɗauke su ta ɓoye ko kuma ta mayar da su cikin jakar Sumayya. Daƙyar ta yaƙi zuciyarta ta amince mata akan ta mayar da kudin cikin jakar da ta ɗauko su. Haka kuwa ta yi ta maida su ciki kafin ta yi wani murmushin mugunta don ita ɗaya ta san irin makircin da za ta ƙulla wa Sumayya akan kuɗin, kila ma silar su ta bar mata gidan ko ta huta da jaraba... Ko da na gama gyara ɗakin na saka turaren wuta na fito falon na ce"Mama na gama" da ka ta amsa min, na kwashi kayana na bar falon a cikin raina ina cewa "Wannan miskilancin na Qalbi da dukan alamu wajen Mama ne ya gado shi" ina shiga ɗakin na ajiye duk abin da ke hannuna na kuma sauko wa kasa don girka abincin dare. Ya riga ya zama kamar wata ibada ne a kaina, ni zan yi girkin safe na kuma yi na dare ko kuwa na je office safe da yamma duk masu aikin gidan a banza suke baya da haka ma Rumana da Jiddah da ke zaman banza babu abin da suke yi sai dai su wanke goma su tsoma biyar amman duk da haka ko tsinke ba sa iya ɗauke wa a cikin gidan. Ina gama abincin na koma ɗakina na yi wanka tare da yin kwaliyya don tarbar Qalbina ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba kuwa sai gashi ya shigo gidan rungume shi na yi ina yi mishi oyoyo kamar dai wata ƙaramar yarinya. Shi ma biye min ya yi a haka har ya gama wanka ya tafi masjid don yin sallar magariba da isha'i. Ni ma tawa sallar na yi ina zaune a kan tapis har ya dawo gidan zama ya yi ya ce"Babe dan Allah a ban abin da zan ci don yunwa nake ji" murmushi na sakar mishi kafin na tashi na ce"To mu je dinning sai ka ci ka koshi ko" kamar wani karamin yaro ya maƙale min kafaɗa ya ce"Ni a nan zan ci" girgiza kai na yi na ce"Dama da safe a nan ka yi breakfast tashi mu tafi falon don kar Mama ta damu ta yi tunanin ko babu lafiya ne" tashi ya yi ya bi bayana muka sauko ƙasa don cin abincin dare. ★Mama Sa'a★ Ji nake yi tamkar na shaƙe wannan yarinya Sumayya ta mutu ko na huta da bakin cikinta wannan yarinya tun ranar da aka kawo ta wannan gidan na tsane ta sai dai kuma babu wata hanya da ban bi ba don ganin na saka ta bar min gida amman a banza har yanzu shiru kake ji malam ya ci shirwa. Wani shu'umin murmushi na yi tunawa da na yi yau kam kashinta ya bushe don da dukan alamu yau ranar sa'ata ce domin yau na ɗauki alwashin sai ta bar mana gida ko na huta da ganinta munafukar banza munafukar wofi. Mutmushi da ke fuskata ne ya ƙara yalwatuwa ganin sun sauko daga ɓangarensu ita da Abdallah sai da suka zo daidai wajen da nake na ce"Ke Sumayya kira su Jiddah mu ci abinci" sakin hannun Abdallah ta yi wanda tun fitowar su falon yake sarke cikin na juna sai na raka ta da harara tamkar idona zai faɗo. Jim kaɗan sai ta dawo tare da su Jiddah. A dinning muka haɗu gabadaya don cin abinci yau kam har da Malam mahaifin su Abdallah wani daɗi nake ji yana ziyartar ko wane sashe na jikina. Sai da na tabbatar fakon gabadaya ya yi shiru sai na ce"Sumayya wani mutum ya kawo saƙon kudi ya ce a baki ɗazu da na saka ki aiki, kuma ya ce kar ki manta da jini za ku haɗu a wajen da ya ce miki, na saka miki kudin a cikin karni" gabadaya idanun mutanen fakon na kan Sumayya wadda da dukan alamu har yanzu ba ta fahimci abin da nake nufi ba. "Wane ne ya zo neman ta?" Na jiyo muryar Abdallah yana watso tambayar. "ka ji ka da wani zance daga ungo kai, shi ke nan sai ka san ya wa aiko da su" sai yanzu ta yi magana duk ta ruɗe ta ce"Mama ina ga fa babu wanda ya zo nema na gidan nan" fashe wa na yi da kukan munafurci na ce"Sumayya ai nafi karfin na yi miki ƙarya bare kuma yau na fara, idan ƙarya ne a duba jakarta mana ai za a ga kudin da na saka a ciki" Tun kafin na gama rufe bakina tuni Rumana ta tashi ta nufi hanyar ɗakin Sumayya don ɗauko jakar ni kuwa raina fari tas kamar farar takarda. *Cmnts nd share* [06/12 à 12:50] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 *Page 03* Da ido na kafe Sumayya ina sakin murmushi a ƙasan zuciyata wanda a zahiri kuwa duk na yi kicin-kicin da fuskata alamar ban ji daɗin abin da yake faruwa ba. Miƙo min jakar Rumana ta yi ta ce"Mama ga jakar ki duba" wani shu'umin murmushi na yi na ce"Ba Abdallah, shi ne mijinta shi ya fi dace wa da ya buɗe don gani da idonshi" karbar handbag ɗin Abdallah ya yi ya shiga buɗe ta ya fara fito da kayan ciki. Sumayya kuwa ta yi tsaye tana kallon shi har yanzu abin da nake burin gani bai faru ba don na matsu na ga hawaye suna zuba daga wannan kyakkyawar fuskar ta Sumayya. Kuɗin ya ciro ya shiga juya su a hannunsa fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce"Mama mutumin da ya kawo kuɗin nan bai faɗa miki sunansa ba?" Girgiza kai na yi na ce"A a kawai dai ya bani sakon da zan faɗa mata ne kuma na faɗa mata" sai yanzu Malam ya yi magana ya ce"Sumayya ƴata me ya faru? Kin san mutumin da ya kawo kuɗin nan?" Saurin amshe zancen na yi ta hanyar cewa "Ku ji malam da wata magana, kenan ni ba ku yarda da abin da na faɗa ba shi ne sai ka ji ta bakinta" "To Sa'a ai ba haka ake shari'a ba, ko ba komai kin tsaya mu ji abin da yarinya za ta faɗa don sanin gaskiyar magana kila rashin fahimtar zancen mutumin ne kika yi" har na buɗe bakina don yin magana sai na ji Abdallah na faɗi "Babe, ke muke jira mu ji wane ne ya kawo miki kuɗi har gida?" A ɓoye na sauke wata ajiyar zuciya don ganin yadda ran Abdallah ya ɓaci yau kam babu shaka sai Sumayya ta tafi gidansu. ★Sumayya★ Da mamaki nake bin su da kallo, raina ya kai kololuwa wajen ɓaci, wani irin ɗaci nake ji a cikin raina wanda na rasa ta ina zan fara kwatanta shi. Da ido nake bin hannun Abdallah da kallo yadda har yanzu yake juya kuɗin yana wani zare ido tamkar bai san daga ina kuɗin suka fito ba. Daƙyar na iya daukar dutsen jarumta na ɗaura akan bangon zuciyata wajen hana hawayen baƙin cikin da ya yi kawanya a cikin zuciyata zubo wa a gaban idonsu. "Ke fa muke jira ko" Muryar mijina ta daki kunnena buɗe bakina na yi daƙyar na ce"Ba abin da kuke tunani ba ne, kuma kuɗin da ake magana akan su tun daga office na zo da su" wani tsalle Mama ta yi tare da fashewa da wani irin kuka wanda za ka iya rantse wa da Allah naman jikinta ake yanka ta ce"Sumayya yanzu ƙarya zan yi miki kenan? Ba laifinki ba ne idan da ni na haife ki ai ba za ki kalli idona ki ce na yi karya ba, amman sanin ba ni da daraja a idanun ki dole ki faɗi haka" Tuni hankalina ya ƙara tashi don na san a kaf duniyar nan idan akwai abin da yake ɓata ma Abdallah rai ya ga mahaifiyarsa cikin damuwa, musamman da yanzu da ba lafiyar kirki gare ta ba "Mama ki yi hakuri ba abin da nake nufi ba..." Ban ƙarasa maganar da na fara ba Abdallah ya ɗaga min hannu ya ce"Babe je ki ɗaki ina zuwa" ban kuma ƙara faɗar wata magana ba na bar dinning din don zuwa ɗakina. Isa ta ɓangarena ban yi tsinke ba sai a ɗakina na zube a tsakiyar gadona tare da fashewa da kuka wanda ya riga ya zamar min abin yi. Na dauki lokaci mai tsawo a wajen kafin Abdallah ya turo ƙofar ɗakin ya shigo tare da sallama, ban samu damar amsa wa ba don har yanzu hawaye na zarya daga idanuna ga bangaren kaina na dama da ya ɗauki wani uban ciwo kamar ana buga min guduma a wajen. Zama ya yi a bakin gadon tare da ajiye handbag ɗin da na baro musu ita a falo, hannu ya saka ya fara share min hawaye ya ce"Ki yi hakuri Babe na yarda da ke ɗari bisa ɗari sai dai kuma kin riga da kin san ba zan iya ƙaryata mahaifiyata ba a gaban idonta kuma a gaban ƴan uwana" rinanun idanuna na watsa mishi na ce"To na ji, amman ko ba komai bai dace ka yi min tsawa akan laifin da ban aikata shi ba" tausasa muryarsa ya yi ya ce"Na sani amman a lokacin na rasa abin yi ne, amman don Allah ki yi hakuri ki min afuwa kin ji matata" gyaɗa kaina na yi na ce"Ya wuce, amman ina son ka fice min daga ɗaki zan yi barci" "yau a nan zan kwana" ban ko kalle shi ba na ce"ga waje nan sai ka kwanta" ina gama maganar na shige toilet a can ɗin ma sabon kukan da babu mai rarrashina na kuma ɗaura shi daga inda na tsaya. Ganin dai Sumayya ba ta niyyar fitowa daga toilet din sai ya tashi ya tafi ɗakinsa ya canza kaya kafin ya dawo ɗakin sumayya ya bi lafiyar gado. Washegari ban yi la'akari da abin da ya faru a daren jiya ba, na fito zuwa kitchen don girka abin da za mu ci, yau cike da mamaki nake bin Mama da ƴaƴanta da ke zaune a falo suna ta faman hira da kallo. Gaishe ta na yi kafin na juya na fara kokarin barin falon don yin abin da yake gabana sai Jiddah ta ce" Anty Sumayya a cikin kuɗin da saurayinki ya ba ki jiya ki bani 20k mana", babu kunya babu tsoron Allah ta ƙarasa maganar tana wani juya idanu ko kallo ba ta ishe ni bare kuma ta saka ran zan amsa mata na bar falon ban ce ko uffan ba. Ko da na gama aikin gabana na haɗa abincin Abdallah don kai shi ɗakinmu har zan wuce Mama ta ce"Idan ba za ki zauna ki ci abinci kamar kowa a dinning ba kar ki kuskura ki ƙara shigar min da abinci zuwa ɓangarenku" ban yi magana ba na koma na ajiye kwanukan akan dinning kafin na haura sama na tarar da shi har ya gama shirinsa da dukan alamu ni ɗaya yake jira. Zama na yi a bakin bed na gaishe shi na ce"Qalbi yau kam ka sauka ƙasa ka yi breakfast" yana gyara zaman rigar suit ɗin da ke jikinsa ya ce"Akan wane dalili bayan kin san sarai na fi son na yi breakfast ɗina a falona" murmushi na yi na ce"Haba Qalbi iya na yau ne fa kaɗai, gobe ma idan Allah ya kai mu a nan za ka ci ka ƙoshi" "to shi kenan na amince amman na yau kaɗai" gyaɗa kaina na yi a cikin raina na ce"yau ɗin idan na guje wa masifar Mama ai na isa barka" da sauri na ɗago kaina don jin Abdallah yana magana sai na ce"Idan ka gama mu je ka karya ko?" Sai da ya bi ni da kallo tun daga ƙasa har sama kafin ya ce"Ban fahimta ba za ki je office ba ne yau ko mene ne?" Girgiza kai na yi na ce"Me ka gani, zan je mana" "don na ga ba ki shirya ba har yanzu" "mu je idan ka gama cin abinci zan dawo sai na shirya" Ƙasa muka sauko har mun fara taka steps ɗin gidan ya ce"Wai da yaushe kike breakfast Babe? Kullum sai dai ni na ci ke ba za ki ci abin da kika girka da kanki ba" murmushi wanda ya fi kuka ciwo na yi don jin maganar Mama Sa'a ta wancan ranar na yi daram a cikin kwanyata. "Babu abin da kika iya daga ki ci sai dai ki kai toilet ki zubar, shekara uku da aure amman shiru malam ya ci shirwa ko ɓatan wata ɗaya babu" jin Abdallah ya dafa kafaɗa ta ne ya saka na dawo daga duniyar tunanin da na lula na ce"Ina cin abinci mana kawai dai ba na son yin breakfast ɗin ne tun safe don kar na je office na yi barci" gyaɗa kai ya yi bai ce komai amman alamun shi sun nuna bai yarda da abin da na faɗa ba, ni kuwa han wani damu ba na ja shi muka ƙarasa dinning din na zuba mishi abinci ya shiga ci. Yana gama wa ya shiga ɗakin Mama ya gaishe ta kafin ya fito ya same ni a wajen da ya bar ni, ya ce"Babe kuɗin da na gani jiya a wajen ki nake son ki bani aron su" gyara zama na yi na ce"Kai kuwa Qalbi me za ka yi da kuɗi har kake kokarin cin bashi?" Sosa keya ya yi ya ce"To dama Mama ce ta tambaye ni kuɗin kuma kin ga wata ya yi nisa" "Nawa kake bukata" na tambaye shi don kar ma ya tsira wani dogon surutu don na riga na san da wata manufar a kasan zuciyar Mama shi ya sa ta tsiro da ya bata kudi "E to ko 100k za su isa" "Kuɗin su na wajen da ka bar su jiya" murmsuhi ya yi ya ce"Dan Allah ki kai mata su kin ga ni na makara" gyaɗa kaina na yi na ce"To zan kai mata" shi kuwa ya fice daga gidan. Tashi na yi na shiga ɗaki na yi wanka na shirya don zuwa office sai na ciro da kuɗin na je kofar ɗakin Mama na kwankwasa ta bani izinin shigowa. ★Mama Sa'a★ Faɗar baƙin cikin da na kwana da shi a daren jiya ɓata baki ne Allah ne shaida ta ban so ko kaɗan Sumayya ta sake kwana a cikin gidan nan ba, Allah ya sani so na yi ta kwana a gidansu sai dai kuma duk wani shirina ya wargaje ya tashi a tutar babu. Amman idan ta san wata ai ba ta san wata ba na yi alkawari sai ta bar min gidan ɗa ko na yar da ɗan mangwaro na huta da ƙuɗa. Yau tun safe na kira Jiddah ɗakina na ce"Ki na ji ko Auta" gyaɗa min kai ta yi alamar tana saurare na, sai na ci gaba da cewa"Idan Sumayya ta fito daga ɗakinta ki ce da ita a cikin kuɗin jiya ta baki jika ashirin" "To Mama har ta fito ɗin" haka na tasa keyar su gaba muka nufi falo zaman jiran fitowar Sumayya. Ga mamakina ko tanka ma Jiddah ba ta yi ba, bare kuma mu saka ran za ta bata kuɗin ko kuma ta faɗi wani abin da zai sa na yi mata masifa tun safe, amman ko kallon arziki ba mu samu daga gare ta ba. Ganin haka ya sa na dawo ɗakina na zauna bayan na hana ta tafiya sama da abinci duk da kuwa na san ba ita za ta ci ba don ta kai wa Abdallah ne, na yi haka ne kawai don ransa ya ɓaci. Lokacin da ya gama cin abincin ya shigo ɗakina kallon shi na riƙa yi don na ga ko da ɗan ɗigon baƙin ciki ne a fuskar shi na alamar Sumayya ta ɓata mishi rai akan ta ƙi kai mai abinci ɗakinsa. Sai dai kuma shiru babu wani abu da ke nuni da hakan tsaki na ja a cikin raina don wannan lamari ya fara ɓata min rai duk ta inda zan fito sai ta samu hanyar canza akalar abin da na shirya mata. Murmushi na yi a lokacin da ya tsunguna har ƙasa ya gaishe ni. Cike da fara'a na amsa kafin kuma na ce"Tun ba yau ba na so yi maka magana amman kuma sai na ga yadda kake kokari da mu kar dawainiya ta yi maka yawa" ɗago kansa ya yi cike da biyayya ya ce" Mama me ya faru?" Gyara zamana na yi na ce"Ina son na tambaye ka kuɗi ne amman ina jin nauyin ka" murmushi ya kuma yi min ya ce"Mama idan ba ki tambaye ni na yi miki ba ina anfanin neman da nake yi? Kar ki damu Mama ai kin fi ƙarfin ki bukaci wani abu ki rasa idan dai ina da sauran numfashi a duniya, nawa kike bukata?" Murna fal raina na ce"Jika ɗari nake so" "To Mama zan bada in sha Allah" yana gama faɗa ya tashi don tafiya office. Da gangan na bukaci haka don na ga kudin da ke hannunta tabbas na san su zai kawo min don da wannan safiyar babu shaka na san ba shi da wannan kudin a hannunsa amman na tambaye shi su. Bayan kamar minti talatin da fitar Abdallah sai Sumayya ta turo ƙofar ɗakin sallama ɗauke a bakinta ta ce"Mama ga wannan kudin Qalbi ne ya ce na kawo miki su" karɓar kudin na yi ita kuwa ba ta ƙara furta wata kalma ba ta bar min ɗakin. Ina ganin ta fice na tashi tsaye tare da sakin guɗa kamar wadda aka yi wa albishiri ɗin kujerar Makka rawa na fara takawa na ce"Kai ni dai Sa'a na ci sunana wannan uwar sa'a haka abin kam sai godiyar Allah." Ni ɗaya na ci gaba da shagalin murna na raba Sumayya da kuɗin da ban san daga gidan uban wa ta samo su ba. Amman ni dai burina ya cika kuɗin sun dawo mallakina. Hakika raina kan yi baƙi a duk lokacin da na wayi gari na ga Sumayya da wani abu a hannunta, bana son ko kaɗan irin uban kuɗin da Abdallah yake kashe mata, ni da na haife shi ma ba ya min irin wannan hidimar da yake yi wa ƴar gwal ɗin matarsa. *Cmnts nd share* [06/12 à 21:33] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 *Page 04* Ina isa office na tarar har sun fara meeting wanda Allah ya sani tsabar abubuwan da suka yi min yawa a kaina ya sa na manta da maganar wani meeting. Ganin tabbas dai sun fara ba tare da ni ba sai na shige office ɗina na zauna. Na fara duba wasu files sai bayan sun gama Abdallah ya turo ƙofar office ɗin ya shigo, ɗago kaina na yi na ce"Qalbi kenan dai ba za ka bar shigo min office babu neman izini ko?" Murmushi ya yi ya ce"Ni da office ɗin matata ai babu shamaki a tsakani na da shi" ya faɗa tare da jan kujera ya zauna "Kin ba Mama kuɗin da na ce?" Gyaɗa kai na yi na ce"E na bata" "idan aka yi albashi zan yi miki transfert" "Allah ya kai mu lokacin, Amman Qalbi ba ka ganin wasu ɗawainiyar sun yi maka yawa, ka riƙa rage wa, ka riƙa la'akari da abin da gobe za ta haifar don babu wanda ya san goben sai Allah" ɓata fuska ya yi ya ce"Ban gane ba, Babe me kike nufi? Kuɗin da na ba mahaifiyata shi ne kika fara ƙyashi yanzu kuma?" Girgiza kaina na yi na ce"Allah ya tsare ni yin ƙyashi da matar da take matsayin uwa a wajena" "Idan ba kishi da ƙyashi ba ne ki ke yi da ita, to mene ne?" "Allah ya huci zuciyarka, ban faɗi haka da wata manufa ba illa ma fadar hakan da na yi sai don gobenmu ta yi kyau da ni da kai har da ita Maman" tsaki ya ja kafin ya miƙe tsaye zai bar office ɗin, file ɗin da ya shigo da shi a hannunsa ya ajiye min kafin ya ce"Ga shi nan ki duba idan kin ga dama" ya juya ya bar office ɗin. Aikin gabana na ci gaba da yi kafin na fara duba file ɗin meeting ɗin da suka yi ba tare da ni ba" duk raina a jagule nake jin shi. Ina cikin aikina sai wayata ta ɗauki ƙara janyo ta na yi ganin sunan jumelle/Twins da alamar Heart/cœur a jiki ya saka na ɗaga tare da yin murmsuhi kamar tana gabana na ce"Madame, ba ki san lokacin aiki ba ne yanzu" daga can bangaren aka amsa min da "Lokacin aiki ai ku ya dama masu Company ba mu ba yan kasuwa" dariya na yi na ce"Kai wannan kasuwancin da a kullum ake yi mana tutiya da shi mu ma shi za mu fara" dariya Rumaisa ta yi ta ce"Mu gani a ƙasa in ji kare" ni ma dariya na yi na ce" ke ma ai yanzu kin faɗa, ya gidan ina princesse?" "Tana lafiya, ina Abdallana?" "Ke kam Rumaisa ba a raba ki da shiririta, yanzu idan Mustapha ya ji ki me za ki ce mishi?" Dariya ta yi ta ce"Ni fa kiranki na yi don na ce miki yau zan zo" "To Allah ya kawo ki lafiya" muka yi sallama na kashe wayar tare da fara haɗa kayana don barin office ɗin. Sakatariyata na kira a waya bayan ta ƙaraso na ce"Ki cire duk wani meeting ɗina na yau ba zan samu damar zuwa ba" da to ta amsa min kafin ta fice daga office ɗin. Ni ma gida na yi wa tsinke ina shiga falon na tarar da Mama a zaune a falo ko sallamar da na yi ba ta amsa ba ta ce"To daga ina kuma? Wannan tafiya dai ba za a ce daga office ba" na ce"Daga office nake Mama" fashewa ta yi da dariya ta ce"Ki nemi karamin yaro ki sanar da shi, don ni dai da hankalina don ba yarda zan yi ba kuma ina sha Allah nan ba da daɗewa ba Abdallah zai gane ainihin fuskar matar da ya aura, wa ya sani ma ko a yawon ta zubar ɗin kika cire mahaifarki ki ka siyar da ita tsabar son abin duniya" tana jan bakinta kafin ta ci gaba da watso min maganganunta masu kama da saukar gwarwashin wuta a cikin zuciyata na fice daga dakin na nufi ɗakina. Ko da na cire kayana sai na sauko ƙasa na shiga kitchen na haɗa duk wani abun bukata don yin girki na nufi kitchen ɗin da ke bangarena da shi. Sai da na kai kitchen ɗin na manta da ban ɗauko maggi ba ƙasa na kuma sauko wa na ɗauko har na fara taka steps mai zuwa ɓangarena Mama ta ce"Ni kam yau wane irin munafurci ne ake shirin yi da girkin ma ba za a yi a kitchen ɗin falon ba" "Mama zan yi ɓaki ne" "Su waye za su zo? In ce dai ba wannan gayar ɗangin naki ba ne za su zo su cinye wa mutane abinci bayan ga ƴarsu nan a gida da ita da babu duk ɗaya" murmsuhina da ya fi kuka ciwo na yi na ce"A a ba su ba ne za su zo" "To ko da na ji da sauƙi tunda dai ba su ba ne" ɗakina na koma cike da jin haushin maganganunta amman sai na yi kamar babu abin da ya faru na ci gaba da aikin gabana. ★Mama Sa'a★ Yau kam ina falon nan sai na ga munafikin da zai zo gidan ɗana ya ci amanarsa har gida, don wannan munafurcin na Sumayya ban yarda da shi ba idan dai ba yan uwanta ba ne za su zo gidan to kawai kwartonta ne za ta kawo gidan. Ni kuwa ba zan taɓa barin hakan ta faru ba da ya zo gidan zan yi sauri na kira Abdallah ya zo ya ga abin da na daɗe ina faɗa mishi amman ya ƙi yarda da maganata. Channel ɗin Tv na canza na ci gaba da kallona har Rumana ta shigo falon don sai yanzu ta tashi daga barci na ce"Ke dai Rumanatu kin ji kunya ina dalilin wannan barcin, sai na yi wa ƴaƴanku magana ya samo miki ko da ɗan aiki ne a Companysu" miƙa Rumana ta yi ta ce"Gaskiya dai kam Mama kawai ki yi mishi magana kin ga ni ma zan fara yin ado irin na Sumayya na zama kyakkyawa" wani kallon ba ki da hankali na yi mata kafin na ce"Sai yanzu na san ba ki da hankali ke kam, tsakaninki da Allah ina wani abin mangari da burgewa a jikin Sumayya?" "Tab Mama ai kuwa dai tana da kyau babu laifi" "Ke don Allah shashar banza da wofi da dukan alamu wajen bokan da ta kai Abdallah har da ke suka kai" tashi ta yi ta bar falon tana ta faman yin gunguni. Ban wani kula ta ba na ci gaba da abin da nake yi wato kallon tv da kuma jiran kwarton da Sumayya za ta kawo har gida. Can aka turo ƙofar falon da sauri na ɗago kaina don ganin mai shigo wa, da ido biyu muka yi da Rumaisa matar Mustapha shi ɗin cousin ɗin su Abdallah ne ta ɓangaren mahaifinsu. Ita kuwa ƴan biyun Sumayya ce da ka ganta ka ga Sumayya kamar an tsaga ƙara, amman ita ko babu komai ta san ciwon kanta. Da sauri na kauda tunanin da yake raina na ce"Maraba, maraba sannu da zuwa" karasowa ta yi cikin falon ta ce"Mama Sa'a barka da wannan lokaci" kafin ta zauna akan daya daga cikin kujerun falon na ce"Yauwa Rumaisa ƴar albarka, ya gidan ina mai babban suna?" "Tana lafiya tana tare da mahaifinta, ina Sumayya?" "Tana ɗakinta" na faɗa ba don na so ba. Miƙe wa tsaye ta yi ta ce"To Mama Sa'a bari na je mu gaisa" daga nan ta fice zuwa sashen Sumayya. Tsaki na ja a raina na ce"Aikin banza da na san Rumaisa ce bakuwar ai ba zan zauna na ɓata wa kaina lokaci wajen korar sauron da ke shige da fice" ina gama maganar zucina na bar falon zuwa ɗakina na bi lafiyar gado. Don shi kaɗai ne aikin da zan yi a yau dai, Sumayya ta ci albarkacin Rumaisa ni fa da an yi min shawara da cewa zan yi Abdallah ya auri Rumaisa saboda ko babu komai ita ta haifa wa mijinta ƴa kowa ya san ba juya ba ce ya aura sai ni ce dai aka haɗa da jaraba da wannan mai sunan mayun. ★Sumayya★ Ina cikin girkin na ji an buga kofa da karfi alamar rufe ta aka yi, fito wa na yi daga kitchen ɗin na ce"Ikon Allah Rumi ni ban san ranar da za ki zama babba ba" zama ta yi akan sofa ta ce"Kin san Allah ba wani fi na ƙi ka yi ba to ki yi min a hankali" kitchen na koma na ɗauko mata drinks kafin na dawo na ajiye a gabanta. Zama na yi kafin na ce"To mutun dai ko da minti ɗaya ya riga ka zuwa duniya ya girme maka kuma yin biyayya dole ne" bayan ta ɗauki cup ɗin drink din ta ce"Wannan shari'a ina ga sai an je gaban Ummi ita ɗaya ce za ta faɗa miki cewa ni ce babba ki yarda" dariya na yi na ce"To ki saka rana sai mu je gaban Alkali mai girma ummi" drink ɗinta ta shiga sha ni kuwa na koma na duba girkin da na ɗaura kafin na dawo falon wajenta. "Ina princesse ya aka yi ba ki kawo min ita ba?" "Tana wajen Mustapha mana tare suka tafi office ai" kallonta na yi na ce"Ikon Allah yau kuma sunan mijin kai tsaye aka kira babu ko kara, faɗan min laifin me kuma ya yi?" Don duk ranar da Rumaisa za ta kira sunan mijinta haka kai tsaye babu shakka ya yi mata wani abin ne, taɓe baki ta yi ta ce"Ya fara sha min kai ne da maganar haihuwa ni kuma gaskiya ba kaza ba ce, duka ma shekarun Aisha nawa ne?" Ajiyar zuciya na sauke kafin na matso kusa da ita cikin sigar rarrashi na ce"Haba Rumi kar ce haka mana, wasu fa neman haihuwar suke ido rufe ba su samu ba, ki tsaida shan maganin haka tunda dai har mijinki ne ya bukata" wani kallo ta yi min kafin cikin halin ko in kula ta ce" To sai ce miki aka yi haihuwar banza ne?" Girgiza kai na yi alamar a a sai ta kuma cewa "Don ba ki san zafi da radaɗin da ake ji tun daga daukar ciki har haihuwa ba ne shi ya sa za ki ce na bar shan magani na haihu, ko da yake ma ta ina za ki san ciwon haihuwar bayan kuma ko ɓatan wata ɗaya ba ki taɓa yi ba" kamar dirar wani mashi mai dafi na ji maganganun ƴar uwata a cikin zuciyata, idona taf da hawaye amman sai na yi saurin dakatar da su na ce"Haka ne kam, to ki bari ki huta kafin nan" tsaki ta ja ta ce"Haka kawai duk dawainiya ta yi maka yawa, zan je Dubai sarin kaya next week zan kawo miki Aisha ta yi miki kwana biyu ko ba komai Abdallah zai rage zafin rashin haihuwarki" gyaɗa kai na yi na ce"Allah ya kai mu sati mai zuwan" kitchen na tashi na shige a ɓoye na saka bayan hannuna na share hawayen da ya zubo min duk kokarin ɓoye su da nake yi amman a banza. Falon na koma na tarar da ita wannan karan tana waya zama na yi sai da ta ƙare kafin na ce"Less ɗin da na tura miki pics ɗinsu wancan watan sun ƙaraso?" "A a sai dai gobe za su iso amman fa sai kin ƙara 200k" "Ke Rumaisa ki ji tsoron Allah duk wannan uwar dibar" dariya ta yi ta ce"Matar Abdallah idan fa ba ki bani 200k wani zan siyar wa da su" girgiza kaina na yi ina mamakin hali irin na yar uwata na ce"To zan yi miki transfert amman sai an yi albashi" dariya ta yi ta ce"Ko ke fa Hajiyata na fi son haka ai" shiru na yi mata ban kuma amsa mata ba sai ta ce"Ina maganin da na turo miki last week ba ki ban labarin abin da ya faru ba, Abdallah ya yi ihun daɗin kamar yadda Mustapha ya yi?" Girgiza kai na yi ina mamakin wannan lamari babu abin da ya dame ta za ta yi iya yi min rahoton mu'amalar aurenta ko ɗan ɗigo ɗaya ba za ta manta ba ita wannan bai dame ta ba na ce"To ai ban yi anfani da shi ba" "Ke wallahi sake gare ki" dan murmsuhi na yi irin na ba za ki ji komai daga gare ni ba na ce"Ba sake ba ne lokaci ne ba mu samu ba" ido ta zaro ta ce"Ci gaba da zama ba za ki biya masa bukatarsa ya nemo wata sai ki huta" dariya na fashe da ita na ce"Rumaisa idan fa ta zo ba a kaina za ta zauna ba da halinta za ta zauna" tsaki ta ja a fili kafin ta ɗauki wayarta ta fara cire code ɗin ta ce"Nake ɓata raina a banza ma ni na manta da ba ki san ciwon kanki ba" tashi na yi daga kan kujerar da nake zaune na ce"To uwargidan Mustapha da ta san ciwon kanta bari na zubo miki abinci" "yi sauri kam don dama na yi missing ɗin girkinki" kitchen ɗin na nufa ina yi mata dariya sai dai kuma zuciya fal hawayen baƙin ciki ne ke zuba daga cikinta. *Cmnts nd share* [07/12 à 19:02] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 *Page 05* Falon na fito ɗauke da tray ɗin abinci na dire shi a gabanta, na shiga zuba mata kamshi ne ya daki hancinta kafin ta ce"Sumy kin samu wasu sabin spices da alamu?" Gyaɗa kai na ce"To Rumy ba dole ba, su fa maza sai a na kula da cikinsu" "E to kuma fa kin yi gaskiya gara ki riƙa yin girki mai daɗi da kamshi ko babu komai Abdallana ba zai ƙara miki kishiya ba" baki na saki ina kallon ta "Ke Rumy wai mene ne matsalarki da kishiya? mene ne abin da ta yi miki?" Zamanta ta gyara tana wani cin magani ta ce"Ni fa ba iya a kishiya matsalata take ba, duk wani wanda ya ce yana son abin da nake so sai inda karfina ya ƙare wajen daukar mataki" dariya na yi na ce"Allah ya shirye ki Rumy, Allah ya sa mai babban suna kar ta yi halinki" ido ta zaro ta ce"Wace ni ta yi halina ai wallahi sai dai irin halin juyar uwarta ko babu komai na san ba za ta sha wuya a duniya ba muddin ta yi irin halinki" kamar saukar aradu na ji zancenta sai dai kuma sanin wace ce Rumaisa sai kawai ban ɗauke shi a wani abu ba muka ci gaba da hira har yamma ta yi. "Shi Abdallana har na gaji da jiran shi bai zo ba ga yamma ta yi" na ce"Ikon Allah kenan dama zaman jiran Qalbi ki ke yi ba don ni ki ke zaune ba" ido ta zaro ta ce"Tab ke wa? Wannan ziyarar ai ta rabin rai ce" "yar rainin hankali ai da office za ki je ki tarar da shi ko" "kwantar da hankalinki tashi zan yi yanzu na tafi, idan na ganshi kin ga sai in ji daɗi zuwa gidana ko?" "Haka ne kam tashi ki tafi tun kafin dare ya yi miki" Hira muka ci gaba da yi har yamma lis kafin ta yi shirin tafiya, ƙasa na yi mata rakiya ba mu tarar da Mama Sa'a ba sai ta ce"Idan Mama Sa'a ta fito ki ce mata na tafi" da kai na amsa mata don duk abin da ya shafi Mama Sa'a tsoro yake bani ni kam don yanzu za ta yi maka wulaƙanci babu abin da ya dame ta. Sai da Rumaisa ta ɗauki motarta ta bar harabar gidan har zan juya sai kuma na ga mai gadi yana sake buɗe get da alamun Abdallah ne ya ƙaraso gidan. Tsayawa na yi jiran shi. ★ABDALLAH★ Tunda na bar office ɗin Sumayya raina ke yi min zafi, haƙiƙa a can baya ba ta taɓa nuna ƙyashin na yi wa wani daga cikin dangina hidima yau ne za ta fara kuma ma a kan mahaifiyata abu ne da ba zan lamunta ba a cikin gidana. Yau duk wuni ranar da wannan tunanin na wuni a cikin raina matakin da zan ɗauka a kan ta amman da na yi nazari sai na ga rashin jin daɗin da na nuna mata tun a office ɗinta ma kaɗai ya isa ta gane kuma ba za ta kuma ƙara tafka wannan Kuskuren ba, Sumayya ta kasance mutum ce da ba ta da matsala ko kaɗan a rayuwarta da ka yi mata nuni da Kuskurenta ba za ta ƙara aikata irin shi ba wannan na ɗaya daga cikin dalilin da ya sa nake ƙara kaunar ta a cikin raina. Ko da na je office ɗinta ba ta nan handle ɗin kofar na kama na ji a rufe, a raina kuma sai nake tunanin ina ta je ba ta sanar da ni ba. Motata na dauka na nufi gida. Daidai bakin get na haɗu da Rumaisa, glass ɗin motar na sauke na ce"Uwargidan Mustapha barka da wannan lokaci" murmsuhi ta yi ta ce"Ban gane uwar gida ba kar dai ka ce min ɗan uwanka aure zai ƙara?" Hannu na tafa kamar yadda mata ke yi na ce"Tabdi kar ki ce min ba ki sani ba" girgiza kanta ta yi alamar ba ta sani ba na ce"To kuwa idan kika je gida ki tambaye shi" "wata tambaya, da na je zan ce ya bani takardar saki , kuma sai na ce mishi ai kai ka ce min ya yi amarya" dariya na yi wannan karon domin kowa ya san halin Rumaisa na kishi akan abin da take so ko a gaban waye kuwa babu ruwanta tsaf za ta nuna kishinta, kuma kan abin da take so sai dai karfinta ya ƙare sai na ce"Kai mistake ne fa na yi, ina son cewa uwar gida kuma amaryar Mustapha ai daga ke babu ƙari" sai yanzu ta yi murmushi ta ce"Yanzu kam hankalina ya kwanta" gaisawa muka yi kafin ta tafi ni ma na figi motata sai cikin gida. Ina gama parking da sanyin idanuna na yi tozali, motar na kashe na fito, da gudu ta ƙaraso ta rungume ni a kunne ta raɗa min "oyoyo Qalbi" wani irin sanyi ne yake ratsa ni a duk lokacin da na ji muryarta tana kira na da wannan sunan. Wayar hannuna ta amsa kafin ta zare makulin motar daga jikin motar. Sai da na ƙare mata kallo kafin na ja hannunta zuwa cikin gida. Kai tsaye bangarenmu na yi wa tsinke don yau ko zuwa gaishe da Mama ban yi ba. A kan kujera na zaunar da ita kafin na haɗa hannayenta guda biyu na riƙe su game a nawa hannun na ce"Babe" ɗago idanunta ta yi ta sauke su a kan fuskata na ci gaba da cewa"Me yake damun ki? Ina hango damuwa a cikin kwayar idon ki" girgiza kai ta yi ta ce"Babu abin da yake damuna" "Babe kar ki fara ɓoye min damuwar ki , ina son ki sanar min abin da yake cikin ranki kin ji matata" ta buɗe baki da niyyar ta yi magana Mama ta turo ƙofar ta shigo falon ta ce"To hamshakiya, ɗan nawa ma ba za a bari da ya dawo daga office ya fara tozali da mahaifiyarsa ya kwashi albarka ta ba, an wani jawo shi an shigo ɗaki da shi za a fara yi mishi zanen ƙarya da gaskiya ko?" Ɗago kaina na yi na kalli Mama na ce"Ba laifinta ba ne, ni na bukaci na fara jin matsalarta kafin na je na gaishe ki" ido Mama ta zaro ta ce"Babu shakka an wanke an zuba ma a baki ka sha ko?" Ta ƙasan idon nake bin Sumayya da kallo wadda har yanzu ba ta ce uffan ba, tamkar wata yar tsana haka take zaune a wajen Mama ce ta ci gaba da cewa. "Tashi to mu je ɗakina don ina son ganin ka" gyaɗa kai na yi na ce"To bari na watsa ruwa sai na zo" "yanzu nake da bukatar ganin ka idan kuma ban isa ba sai mu gani" tashi na yi ba dan raina ya so ba na fice daga falon Mama na biye da bayana. ★SUMAYYA★ Fashewa na yi da kuka zuciyata kamar za ta fasa kirjina ta fito haka nake jin zafi rana zafi inuwa ƙuna ba ni da wani madogara face Sarkin sarakai Ubangijin da ya halicce ni. Ina zan saka kaina ga baƙin cikin dangin miji akan abin da ba ni na ɗaura wa kaina ba, babu wanda zai saurare ni bare kuma har na samu mafita. A wajen na ci gaba da kukana ina tunanin mafita, mahaifiya da ke zama bango, babban jigo a rayuwar ƴaƴanta ni tawa fushi take da ni babu ruwanta da lamurana idan zan shekara goma ina sanar da ita damuwata babu abin da ya dame ta da matsalar da nake ciki. Ta yi fushi da ni ta ɗauki karan tsanar duniya ta ɗaura min bayan ba ni da laifi, ba yin kaina ba ne son mijina da son ɓoye sirrin aurena su ne suka jawo min duk abin da ke faruwa da ni a halin yanzu. Ban san lokacin da barci ya ɗauke ni a wajen ba sai buɗe idona na yi na tsinci kaina a tsakiyar gadona duk da na san aikin Abdallah ne. Haka na tashi na yi wanka na ɗaura alwala na yi sallolin da suke kaina ban gushe a wajen ina rokon Ubangijin samai ya kawo min mafita a rayuwata ya kawo min haske kafin na koma gare shi. Yau kam da wani irin ciwon kai na tashi wanda na daɗe ban yi irin shi sai yau shi ya sa na nema wa kaina salama ko office ɗin ma ban tarki zuwa ba. A nan kan tapis na ci gaba da kwanciyata ban san iya adadin lokacin da na ɗauka a wajen ba a kwance sai da na ji kamar ana shafa gashin kaina. Ido na buɗe na sauke su a kan Abdallah murmushi ya sakar min ya ce"Baiwar Allah duk barci ne har yanzu" tashi zaune na yi na fara ƙare mishi kallo na ce"Karfe nawa ne yanzu" don har ya shirya tsaf a cikin suit ɗinshi don zuwa office. "Karfe takwas fa har da rabi" dafe goshina na yi na ce"Ya Allah, bari na haɗa maka ko da ruwan tea ne ka sha kar ka fita haka ba ka ci komai" girgiza min kai ya yi ya ce"Ki bari kawai tunda dai kin makara idan na je office na yi oder abin da zan ci, ko na je cantine" girgiza kaina na yi na ce"Don Allah ka yi hakuri wallahi kawai barcin ne ya fi karfina" "Babu komai Babe, tashi ki shirya mu tafi ko" girgiza kaina na yi na ce"Ba zan iya ba kaina ke ciwo idan ka je ka ce da secrétaire ɗina ta turo min aikin da zan yi yau ta email" gyaɗa kai ya yi ya ce"Tashi to ki sha ko tea ne sai ki sha magani" "Zan sha ba yanzu ba sai zuwa an jima" miƙe wa ya yi ya ce"To ni zan tafi idan ba ki ji sauki ba ki kira ni sai na kai ki asibiti" da kai na amsa mishi kafin ya ja kofar ya fice daga ɗakin. Ni kuwa kan bed na koma na dasa sabon barci wanda sai da karfe goma ta yi na tashi, yanzu kam na ji sauƙin ciwon kan sai kawai na shiga toilet na yi wanka na canza kaya sai kuma a lokacin nake jin wata irin yunwa. Ba na son na sauka ƙasa na haɗu da Mama Sa'a sai na shiga kitchen ɗina neman abin da zan saka a cikina amman babu, dole uwar na ƙi na nufi ƙasa. Na yi sa'a ba ta falon har da murna na nufi kitchen na soya kwai da dankalin turawa kafin na haɗa tea mai kauri na jera a plate na ɗauko su don zuwa ɗakina. Ina shigo falon sai na hangi mutane biyu mata a zaune na gaishe su ban tsaya ba na ci gaba da tafiya don isa ɗakina. Sai na ji murya Mama Sa'a tana kira na ajiye plate kan ɗan tebur da ke karshen falon na yi sai na juya na koma cikin falon na ce"Mama ga ni" taɓe baki ta yi ta ce"ba ki ga baƙi ba ne?" Girgiza kai na yi na ce"Mama na gansu" "ba su kai matsayin da za ki gaishe su ba kenan, saboda ba ki samu tarbiyya mai kyau ba ko?" Ƙasa na yi da kaina cike da jin kunya na ce "Mama ai na gaishe su lokacin ba ƙƴa nan ne" hannunta ta shiga tafawa ta ce"Yanzu kuma ina magana ki na magana?" Ɗaya daga cikin matan da ke zaune ce ta ce"Haba dan Allah Sa'a ki rabu da ita mana ai ta gaishe mu" ɗayar kuma ta ce"Wace ce wannan ɗin Sa'a?" murmushi Mama ta yi ta ce"Ai matar Abdallah ce, kuma juya ce ba ta haihuwa" salati matar ta saki ta ce kuma ki ka ci gaba da zama da ita, ai kawai ko Abdallah ya sake ta ko kuma ki mutu ba ki ga jikokinki da za su fito daga tsatson Abdallah ba" shiru Mama Sa'a ta yi alamar tana nazari sai ta ce"Kuma fa kin yi gaskiya, zan san abin yi kuwa, ke tashi ki bar wa mutane falon" ban jira ta sake fadar wata magana ba na ɗauki kwanon abincina na haura sama. Ina hawaye domin tun da na zo duniya ba a taɓa yi min irin wulaƙanci da Mama Sa'a ta yi min yau ba. *Cmnts nd share* [08/12 à 22:45] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 *Page 06* Ina komawa ɗakina ko da wasa ban sake gigin sauko wa ƙasa don gudun abin da zai je ya dawo sai kawai na yi zamana a ɗakina. Har yanzu Ban ji sauƙin ciwon kan da ke damuna ba wayata na ɗauka na kira likitan da ke kula da duk wanda bashi da lafiya a Companymu, ban so kiran Abdallah dan kar na ɗaga masa hankali. Ko da ya ɗaga kiran cikin mutunta juna muka gaisa. "Madame Abdallah lafiya dai ko ?" Kamar yana gabana yana kallona na girgiza kai na ce"Docteur wallahi da wani irin ciwon kai na tashi kuma har yanzu da na sha magani bai daina" shiru ya yi yana ɗan nazari kafin ya ce"Iya ciwon kai ne?" Na amsa masa da "shi kaɗai ne" "Kawai défense ne kike yi, ki cire duk wata damuwa a ranki sannan ki kwanta ki huta zuwa gobe idan ba ki ji sauki zan zo Company na duba ki" godiya na yi mishi tare sallama na kashe wayar. Kamar yadda ya ce na yi haka kuwa na yi rage gudun ac falona na yi na dauko pilow daga ɗakin na kwanta a kan kapet. Kamar daga sama na ji ana kiran sunana buɗe idona na yi na sauke su tas a kan jiddah. Ina shirin yin magana ta ce"Mama tana kiran ki" daga nan ta juya ta fice ta bar falon. Tashi na yi na wanke idona kafin na sauka ƙasa don amsa kiran Mama Sa'a, ina zuwa na lura da matan ɗazu har yanzu ba su tafi ba sai na je kusa da Mama na ce"Mama gani" wani kallon sama da ƙasa ta yi min kafin ta ce"Ba shakka kin samu duniya Sumayya, ke yanzu har damar barci ki ka samu ko?" Girgiza kaina na yi na ce"Ba na jin daɗi ne" wata uwar harara ta jefo min kafin ta ce"Yaushe rabon ki da ki yi jini" Wata irin kunya ce ta kama ni tamkar kasa ta buɗe na shige ciki nake ji, na ma rasa abin da zance saboda ban shirya jin irin wannan tambayar daga gare ta ba. Ko mahaifiyata zan ji kunyar wannan tambayar daga gare ta bare kuma uwar mijina. "Haba Sa'a wannan wace irin tambaya ce haka?" Daya daga cikin kawayen Mama Sa'a ta faɗa. "Ba fa wani abu ba ne Larai, kawai don na tabbatar ko ciki gare ta" Mama Sa'a ta bata amsa cikin halin ko in kula don ita fa ba ta ga wani laifin tambayarta ba. Ɗayar matar ce ta ce"Ke ma dai Sa'a da son saka kai uku kike to ai wannan tunda dai tun farko ba ta haihu ba, ba fa yanzu ba ne za ta ɗauki ciki har ta haihu. Idan ma kin shirya neman mafita gara ki nema idan kuma ba haka ba ki zauna ki ci gaba da kallon ruwa har kwaɗo ya yi miki ƙafa" Wannan cin mutuncin da me ya yi kama shiru dai na yi ina kallon su domin lamarin nan ya wuce tunanina sai na tsinkayo muryar Mama Sa'a daga cikin duniyar tunanina tana cewa "Kin wani yi min kikam a ka, je ki ɗaura mana girki saboda rana ta fara" duk da ba ni ke girkin rana ba a gidan amman wannan dama da Mama Sa'a ta bani ta barin fakon har sai da na sauke ajiyar zuciya da sauri na juya har doguwar rigar da ke jikina tana faman harɗe ni na nufi kitchen ɗin. Sumayya na barin falon Larai ta ce"Maganar gaskiya Sa'a wannan abin da kike yi wa ƴar mutane ba yi ba ne don Allah idan ba ta haihu ba laifin na waye, Allah da ya baki haihuwar shi ne dai ita ma zai hore mata, amman ki saka ta gaba ki na yi mata cin kashi har a gaban baki idan ki ka yi ba abin kirki ba ne, kar ki manta ki na da ƴaƴa mata kuma ita ma ba don mahaifiyarta ba ta son ta ba, kamar yadda kike son naki bakya son ayi musu irin wannan cin kashi to ita ma ki daina yi mata" Baki galala su Mama suka buɗe suna kallon Larai kafin Mama ta ce"To fa Larai ai dole ki kare ta don ke ɗin ma da kaɗan ki ka fi juya. Don ɗa ɗaya ki ka haifa a shekara biyar da aure" da mamaki Larai take kallon Mama ta ce"Babbar magana yaro ya tsinci hakorin babansa ke yanzu tsakani da Allah ni ce yau za ki yi wa gori daga na faɗa miki gaskiya. Kar ki damu ba zan faɗi a ƙasa kamar ki ba amman a juri zuwa rafi watarana dole tulu zai fashe" tana gama kai wa nan ta dauki mayafinta ta nufi kofar falon. Ɗayar matar ce ta ce"Haba Larai ai ba za a yi haka ba dawo ku sasanta" banza Larai ta yi mata ta fice daga gidan. Tsaki Mama ta ja ta ce"Aikin banza kawai, to ita ina ruwanta ma da lamarin nan ni dai na ga ba maganar ɗanta ake yi ba" Ita ma kawarta shiru ta yi da bakinta don ta ga Mama ba ta son ana yi mata kutse a cikin lamarunta. Ina shiga kitchen na saka bayan hannuna na share hawayena daidai mai aiki gidan ta shigo don ɗaura girki ta ce"Hajiya yau ba ki je office ba" gyaɗa mata kai na yi sai ta ce"Me za a dafa yau?" Girgiza kaina na yi alamar ban sani ba sai kuma na ce"Jiya me aka dafa?" Amsa ta bani sai na ce"To ɗauko doya ki fere min" Sai da na gama girkin tas na jera a dinning na je falon na ce"Mama na gama girkin" ba ta ko kalle ni ba ta ce"Allah ya sa dai ba ki cika min gishiri ba" girgiza kai na yi na ce"A a Mama ban cika ba" gyaɗa kai ta yi ta ce"Sai ki bani waje ai" ban jira wani abu ba na bar falon ko abincin ban zuba ba na koma ɗakina. Wayata na tarar tana ringin na ɗaga tare da sallama Rumaisa ta ce"Ke malama a yi ta kiran ki amman a banza" dan guntun murmushi na yi saboda Rumaisa kullum cikin mita take ban san ya Mustapha ke iya zama da ita ba na ce"Baiwar Allah ina kitchen ina girki ne" "Tab ai da na san ba ki je office ba da na zo na ci abincinki mai daɗi" "Yanzu ma ai dare bai yi miki ba" dariya ta yi ta ce"Dare ya yi min yanzu kam sai dai ki girka dîner da rabona zan turo Mustapha ya amsar min" "To babu damuwa Allah ya kai mu daren lafiya" "Dama mai delivry ne zan ba kayanki shi ne na ce bari na ji ki na office ko gida" "Ina gida kam yau ki aiko shi kawai" daga nan muka yi sallama na ɗauko laptop dina na fara duba sakon email ɗin da sakatariyata ta turo min. ★Mama Sa'a★ Bayan Sumayya ta bar falon na ce"Balki mu je mu ci abinci ko?" Tashi muka yi muka nufi dinning ɗin sai na tura mai aikina ta kira su Rumana. "Tabdi wannan abincin ai daɗin ya yi yawa idan ka biye wa daɗin ai ba za ka koshi ba" Balki ta faɗa tana mai kai loma bakinta. Dariya na yi amman ban ce komai ba saboda a rayuwata ina son jin an yaba abin da ya fito daga gare ni. "To gaskiya Sa'a wannan yarinyar ta iya girki maganar gaskiya kar ki yi sake da ita domin wannan daɗin haka ai da wuya a yaran zamanin nan ka samu wanda ya iya girki kamar ita" murmsuhi na yi na ce"Balki ki daina wannan santi ki ci abinci" kamar an yi ruwa an ɗauke kuwa ya ja bakinta ta yi gum ta ci gaba da cin abincinta, wanda ni kaina na san ya yi daɗi. Ko da muka gama ɗaki muka shiga muka yi sallah kafin muka dawo falo muka zauna. Can aka fara buga kofar falon kiran mai aiki na yi na ce"Ke buɗe kofar nan" bayan dan lokaci sai ta daow ɗauke da wata leda mai kyau ta ce"Cewa aka yi na Hajiya Sumayya ne" cike da wani irin zafin nama na amshi ledar na ce"Mene ne ki ka tsaya min kikam a ka, wuce ki bani waje" Ledar na shiga buɗe wa nan fa idona ya fito fili kamar za su faɗo kasa tozali da na yi da wasu rantsatun less masu matukar kyau wanda ko ban san kudinsu ba na san suna da tsada. A hankali na fara fito da su ina rafka salati. "Balki taya ni figa uwar miji ta zama kaza, duba ki ga wannan uwar siyayar da aka yi da kuɗin dana, yau Allah na tuba tunda nake ban taɓa saka irin wannan kayan masu uwar tsada har haka ba" na faɗa ina juya less ɗin a hannuna. Balki ta ce"Gaskiya Sa'a kayan sun yi kyau sosai" ɗaya da ciki na ɗauka na miƙa mata na ce"Ga wannan ki dangwali arziki ke ma" hannunta na rawa ta amsa tana cewa"Alhamdulilah, kai Sa'a na gode sosai Allah ya sa ki fi haka Allah ƙara arziki" da amine na amsa. Ni ma na zaɓi guda ɗaya kafin na shiga kiran Sumayya don ta zo ta ɗauki sauran kayanta. ★Sumayya★ Ina daga falona na ji Mama tana kirana da sauri na tashi gabana na dukan uku-uku don har na fara tunanin ko wani laifin na yi mata. Ina isa cikin falon idona suka yi tozali da less ɗin da na yi oder tun wancan watan a wajen Rumaisa. Ga kuma ledar da ke dauke da tambarin shagon Rumaisa din a ajiye a ƙasa. Mama ce ta ce"Zo ɗauki sauran kayanki na zaɓi guda biyu ni ɗaya kawata ɗaya" wani irin bacin rai ne ya taso ya tsaya min a makwoshi sai kuma ta ce"Ko ban isa na dauka ba ne? Ai dai na ga kayan nan kuɗin ɗana ne, kenan ni ma ina da iko a kan su idan ki na da wata magana kuma to sai ki faɗa" girgiza kai na yi na ce"Mama ba ni da abin faɗa" "Ko da na ji ɗauki ledarki ki fice min daga nan" ledar na ɗauka na bar falon. Raina a mutukar bace amman ban ce komai ba na shiga ɗakina tare da ajiye ledar ina bin ta da ido. *Cmnts nd share* [09/12 à 22:07] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 *Page 07* Baƙin ciki duk ya ishe ni, babu yadda na iya haka na buɗe sauran less ɗin ina bin su da ido. Ajiye ledar na yi na nufi toilet na yi wanka na canza kayana kafin na sauko ƙasa, yanzu kam Mama ba ta nan da dukan alamu ma kawarta ta tafi. Kitchen na shiga na fara kokarin ɗaura tuwon shinkafa da miyar kuɓewa don tun da Rumaisa ta furta cin abinci da na girka yau kam sai ta ci ko Mustapha ya shiga uku a wajenta. Sai da na gama na jera na su Mama a dinning kafin na haɗa na Rumaisa a cikin babban basket. Na kwashi kayan abincin Qalbi don yau yadda nake jin raina a bace ba zan iya zama tare da su Mama don cin abinci a falon ba. Yadda raina ke min ƙuna na ma rasa me zan yi don jin sauƙin abin da Mama ta yi min. Allah ne shaida ta na ko da na yi order ɗin less ɗin na dauri niyyar na ba Mama Sa'a ɗaya na kaiwa Ummina guda biyu sai na ɗauki guda biyu. Tsaki na ja a cikin raina a fili kuma sai na tashi na shiga wanka domin tsara kwaliyya kafin zuwan Abdallah. Bayan na gama shirin na sauko ƙasa sai ga kiran Rumaisa bayan na ɗaga ta ce"Ke Malama kin yi girkin da rabona?" Kamar tana gabana na gyaɗa kai na ce"Na gama ma madame turo Mustapha ya amsar miki" dariya Rumaisa ta yi ta ce"Ke ma Sumy yo zancen yaushe kuma ai Mustapha ya daɗe da ya ɗauki hanya" dariya na yi na ce"Don Allah Rumy ki rage kwadayin nan haka" "Sai dai ki faɗi duk abin da ki ka ga dama Malama don babu hakurin da zan yi musamman idan abincin gidanki ne" sallama muka yi na kashe wayar. Sai na zauna a falo ina jiran zuwan Mustapha domin yanzu da na tashi na bar falon idan ya zo sai abin ya zama abin faɗi. Da sallama ya shigo falon hannunsa ɗaya riƙe da princesse Aysha ɗayan hannun kuma dauke da kwanukan abinci. Da gudu Aysha ta yi kaina, ɗaga ta sama na yi na rungume ta tsam a kirjina ina sauke ajiyar zuciya don an kai sati uku ban saka ta a idanuna ba ta ce"Momy" cire ta na yi daga jikina ina duba ta sai na ga kamar ta rame sai yanzu na ɗaga kai na kalli Mustapha na ce"Ba ta da lafiya ne?" Girgiza kai ya yi ya ce"Sumayya ina wuni" sai da wata kunya ta kama ni, ba na son ko kaɗan na ji wani abu ya faru da Aysha. Ɗaure wa na yi na ce"Mustapha zauna mana" Waje ya samu ya zauna sai na shiga kitchen na haɗo masa drinks na kawo. Duk inda na saka ƙafa Aysha tana biye da ni, sai da na dauki kwanukan na kai kitchen kafin na dauko ta a hannuna muka dawo falon na zauna na ce"Mustapha ya aiki?" "Alhamdulilah Sumy, Abdallah bai dawo ba har yanzu?" Girgiza kai na yi na ce"Bai ƙaraso ba har yanzu, don Allah Mustapha me yake damun Aysha?" Shiru ya yi kamar ba zai yi magana ba ya ce"Sumy ba na son na ɗaga miki hankali amman maganar gaskiya Aysha ba ta samun kulawar da ta dace a wajen mahaifiyarta" ban yi mamaki ba sanin halin Rumaisa sai na ce"Mustapha ka yi hakuri don Allah, in sha Allah zan same ta na yi mata magana" gyaɗa kai ya yi ya ce"To na gode sosai Sumy Allah ya saka da alkairi" Aysha da ke ta faman kallon cartoon ɗin da na saka mata na zuba wa idanu ina kallonta sai na ji Muryar Mustapha yana cewa "Da a ce ke ce mahaifiyarta da ta ji daɗin rayuwarta don ko ba komai za ta samu kulawa" girgiza kai na yi na ce"Kar ka ce haka Mustapha, ka san sarai halin Rumaisa da an yi mata magana za ta gyara" bai ce komai ba sai can ya ce"Ina Mama?" "Tana ciki, bari na kira ta ku gaisa" ina tashi da niyyar tafiya Aysha ta sauko daga kan sofa ta rike min riga. Jan hannunta na yi muka nufi dakin Mama da sallama na tura kofar ɗakin daƙyar ta amsa min amman ganin Aysha sai ta saki murmushi. "Maraba da mai babban suna, Hajiya Indo ina Mamanki?" Ta faɗa tana miƙa ma Aysha hannu alamar ta zo gare ta. Takawa ta yi har ta ƙarasa bakin gadon nan ta shiga yi mata magana kamar babu ni a wajen. "Mama, Mustapha yana falo yana son ku gaisa" na faɗa ina ɗari-ɗari gudun abin da zai je ya dawo. Ai kuwa ta ce"To baƙar manafuka sai yanzu da ki ka gama ƙare min kallo ki ka tuna da wani Mustapha ko? To je ki ce ina zuwa" miƙa wa Aysha hannu na yi na ce"Zo mu je" Mama ta yi saurin janye Aysha ta ce"Aikin banza idan ki na son ki yi iko da ƴa ki haifi taki kafin ki tsira yin iko da ita don wannan dai da uwarta, kuma abin farin cikin ma duk duniya sun shaida Mustapha bai auri juya ba sai Abdallah da ya yi zaɓen tumun dare ko ɓari ba ki taɓa yi bare kuma a kai ga haifo santala-santalan yara" shiru ban ce komai ba sai juya wa na yi da niyyar barin ɗakin. Ina ƙarasawa cikin falon ya yi daidai da shigowar Abdallah falon. Zuwa ya yi ya rungume ni ya ce"Babe babu oyoyo?" Da sauri na haɗiye kukana na ce"Sannu da zuwa Qalbi" Cikin falon muka ƙarasa sai Mustapha ya ce"Ba shakka ita soyayyar a gaban idonmu ma ba a jin kunya ko?" Da sauri na ɓoye kaina a kirjin Abdallah sai Mustapha ya fashe da dariya ya ce"Aikin banza ki ka yi Sumayya ai kin gama yin rashin kunyar ma" cire ni daga kirjinsa ya yi ya ce"Ke Babe rabu da shi, ina wani rashin kunya ke da mijinki" Zame jikina na yi kafin na tsiyaya drinks a cup na miƙa masa, amsa ya yi ya ce"Tanks you Babe" sai ya zauna suka fara tattaunawa maganar office da Mustapha. Falona na koma ni ma na ci gaba da aikin gabana. Bayan wani lokaci sai ga kiran Rumaisa ina ɗaga wa ta ce"Malama ina mijina?" Ido na zaro cikin wasa na ce"Kar ki ce min bai dawo gida ba har yanzu?" Rumaisa da ke kwance a kan sofa tana jiran zuwan Mustapha don wata irin yunwa take ji kuma ta riga ta ɗaura ran cin abincin Sumy yau ɗinan, ta yi saurin tashi zaune ta ce"Tsakani da Allah Sumy Mustapha ba ya gidanki?" Girgiza kai na yi kamar tana gabana na ce"Da gaske nake yi miki Hajiya Rumy" tashi ta yi ta figi gyalenta da makulin motarta ta ce"wallahi sai Mustapha ya faɗa min wajen yar iskar da ya je, kuma ma tsabar rainin hankali har da ƴata zai tafi hira" Fashe wa na yi da dariya har da riƙe ciki na ce"Allah ya shirye ki Rumy da wannan uban baƙin kishin, Mustapha yana falo tare da Qalbi, bari na je na bashi abinci ya kai miki gimbiya" wata ajiyar zuciya ta sauke wadda har ina iya jiyo sautinta daga cikin wayar. Falon na sauko na tarar su na shan hirarsu na ce"Qalbi ka yi hakuri ka saki mijin wancan matar hakan nan, don wallahi yanzu muka gama waya tana masifa" tsaye Mustapha ya tashi kamar wanda aka tsikara ya ce"Allah na gode maka kin ga fa Abdallah ya rufe ni da surutunsa da ba ya ƙare wa har na manta da sauraniya ce ta aiko ni" dariya na yi na ce"Duk wannan ɓarin jikin na tsoron Rumy ne?" Dariya Abdallah ya yi ya ce"Babe dan Allah bashi abin da aka aiko shi ya amsa. Idan ba haka ba kin san sarai zane shi za a yi" Kitchen ɗin na nufa na ɗauko kayan abincin da na haɗa a basket na kawo mishi Qalbi ne ya ce"Ikon Allah wai dama kai abinci aka aiko amsa" kamar wani maraya Mustapha ya saki tausayi ya ce"Don Allah Abdallah kira min Mama na yi mata sallama na tafi gida" dariya na yi na ce"Kai kam Rumy ta saka ka uku, amman ka bar min princesse yau gobe idan Allah ya kai mu zan kai ta gida" amsa min ya yi da to kafin Mama ta fito suka yi sallama na ja hannun Aysha muka nufi ɗakina har da bye bye take yi wa Daddynta. Bayan Mustapha ya tafi Abdallah ya shigo ɗakin yana dariya na ce"Qalbi ka daina yi mishi dariya fa, don kai ma ba a san ya kake yi idan matarka ta aike ka" girgiza kai ya yi ya ce"To ai ni matata ƴar aljanna ce ba ta yi min irin faɗa da Rumy ke yi wa Mustapha" Ni ma dariya na yi na ce"To kai ina évidence ɗinka a kan Rumy tana yi mishi faɗa, kawai tsoron kar ya ɓata mata rai ne yake yi" murmushi ya yi ya ce"Yau kam na san ba za a bani abinci a baki ba tunda dai ga princesse" "daɗi na da kai Qalbi ka na saurin gane abubuwa" Wanka na yi wa Aysha don dama akwai wasu kayanta a gidan kafin na kwantar da ita tare da yi mata addu'a na dawo falo na tarar da Qalbi na zauna a kusa da shi ina yi mishi hira kamar babu abin da yake damuna. *HAJIYATA KI NA INA NE? AI DAI BA KI MANTA LABARIN tura ta kai bango BA DA KUMA LABARIN Kuskure.* *To zo yau ga labarin DA WATA KUSAN... Wadda bahaushe ke cewa gara nesa.* *Labarin ya fara daukar zafi fa, Hajiya ki biya kudin karatunki kawai sai mu haɗu a Paid Group* Only 500 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange. *Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252* [10/12 à 23:02] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 🔥FREE PAGE🔥 *Page 08* Bayan na zauna a kusa da shi ne na ce"Qalbi ya aiki?" Murmushi ya yi ya janyo ni jikinsa ya ce"Hum yau ba kin ƙi zuwa office ba ai kin kyauta" girgiza kai na yi na ce"To Qalbi kai da ka bar ni a nan a kwance ba lafiya" da sauri ya dafe goshinsa ya ce"Ya Salam wallahi na manta da kin ce ba ki da lafiya" wani irin takaici ne ya rufe ni jin wai ya manta ma da ba ni da lafiya. Wannan wata irin rayuwa ce tashin hankali daga na uwar miji sai na mijin ni yanzu ya zan yi da raina, ganin idan na nuna ɓacin raina ma a banza sai na yi kwafa na share abin da ya faɗa tare da dane kululun baƙin cikin da ya tokare min wuya, amman duk da haka sai na yi shiru ban amsa mishi ba, sai ya kuma cewa"Ya jikin yanzu?" "Na gode wa Allah" dan shiru ne ya biyo ba sai kuma ya ce"Duk da ba ki da lafiya har da girki ki ka yi" kai na gyaɗa mishi na ce"ai bin da ya zamar min dole ne, ko ban yi don kaina ba za a saka ni na yi" "Kai Babe idan da ɗan ni ne ai da kin bari ko?" Girgiza kai na yi na ce"Ta ina zan fara bari bayan kuma na san ko breakfast ba ka yi ba da za ka fita, to wai ma me ya hana ka dawo gida da rana?" "Kin san sarai aiki ne ya yi min yawa idan ba dan haka ba ai da na dawo tunda dai na riga na san ki na gida" "To ai ka ci aikin ka koshi a office ko" gira ɗaya ya ɗaga ya ce"Sosai ma na ci na ƙoshi, yanzu kawai sai barci zan yi" ya faɗa yana wani kumshe ido kamar da gaske barcin yake ji. Tashi na yi na bar falon ɗakina na shiga na ɗauko ledar less ɗin na dawo falon na miƙa mishi na ce"Qalbi ga shi" karɓar ledar ya yi ya ce"Wannan fa daga ina?" Zama na yi na ce"Oder da na yi daga wajen Rumy ce ta ƙaraso" buɗe ledar ya yi ya fara kallon kayan ya ce"Ban fahimta ba, ba ce min ki ka guda biyar ki ka siya ba?" Gyaɗa kai na yi na ce"E biyar ne" "Amman a nan guda uku na gani ko kin kai wa Ummi ne" girgiza kai na yi na ce" Ta ina zan je gidan Ummi ban sanar da kai ba, Mama ta ɗauki guda ɗaya ta ba kawarta ɗaya" ido ya zaro kamar za su faɗo ƙasa ya ce"Ban fahimta ba a kan me Mama za ta ɗauki abin da ki ka siya da kuɗinki har kuma ma ta yi kyauta da shi" "Ba a kan komai ba, ta yi haka ne don ta isa da ni duk abin da yake nawa kamar dai mallakinta ne ai"na faɗa duk da dai raina bai so faɗin hakan ba.ta ina zan fara faɗa mishi ban ji daɗin abin da mahaifiyarsa ta yi ba, ai ko ba komai a na barin halak don kunya, tashi ya yi ya fice daga falon na kuwa san ɗakin Mama Sa'a zai je. Tsaki na yi a raina na ce"Ya rage naku less kuwa yanzu na fara siye a gidan nan" Abdallah yana fita daga ɗakin ya nufi ɗakin Mama Sa'a tare da su Jiddah ya tarar da ita Jiddah ce ta gaishe shi Rumana tana faman latsa wayarta ya ce"Ke marar kunya ban isa ki gaishe ni ba ko?" Da sauri ta ajiye wayar ta ce"Ka yi hakuri yaya Abdallah ina yini?" Banza ya yi mata bai amsa ba Mama ta ce"To mene ne kuma ƴar gwal ta ce mun yi da za ka zo ka sauke masifar a kan ƴata?" Bai bi ta kan abin da ta ce ba sai ya ce"Mama me ya sa ki ka ɗauki less ɗin Babe?" Tashi Mama ta yi zaune tana ɗaura dan kwalinta ta ce"Ban fahimta ba ita Sumayya ce ta ce maka na ɗauki kayanta" zama ya yi ya ce"Mama maganar gaskiya nake yi bai dace ki yi haka" "Oho kenan ni karya nake yi ko, matarka ita ce mai gaskiya ko ubana? Yanzu faɗa min abin da ya dace na yi, to na je na ɗauka ku yi abin da za ku yi daga kai bar ita, to in banga lalacewar zamani Abdallah yaushe ka yi girman da za ka tsaya min a ka saboda matarka" tashi ya yi ya bar ɗakin bai kuma cewa komai ya koma ɓangarensu. Yana shigo wa ya nufi wajen da sumayya ke zaune tun fitar shi ya ce"Don Allah Babe ki yi hakuri, idan na samu kuɗi zan siya miki waɗansu" girgiza kai na yi na ce"Ba na bukata Qalbi, kar ka damu kuma ina son ka bar zancen maganar ta wuce shi kenan" Washegari tunda safe Aysha ta tashi da wuri don tare da ita na yi girkin breakfast sai surutu take yi min. Bayan na gama girkin na shirya tsaf na yi mata wanka ita ma ina fita zuwa falo ta jawo kwalin madarar da ta sha tun juya sauran da na ajiye a kan mirror ta ɗauko ta yi zaman dirshan ta shiga sha. Ina dawo wa na ce"Allah mai iko na manta sam da wannan madarar da ba zan bari ki ɓata jikinki ba" daukarta na yi na goge mata jiki kafin na ɗaura ta a kan bed ɗina, daidai kuma Abdallah ya shigo ɗakin ya ce"Babe barka da safiya yau dai Aysha ta kwace min ke" dariya Aysha ta yi kamar wadda ta fahimci abin da yake nufi. Kan bed ɗin wajen da take zaune ya je ya rungume ta ya ce"Princesse bonjour/good morning" cikin hausarta da ba ta gama zama cikakkiya ba ta amsa. Nan suka hau hira ni kuwa ina gyara wajen da ta gama shan madara duk ta zubar da ita a ɗakin, don a garinta haka ta riƙa kwasa tana zuba wa a baki. Ya ce"amman yau Aysha ba ta sha madara ba ko?" Wata uwar harara na watsa mishi na ce"Ba ta sha ba kam tunda dai idonka sun makance" sai ya fashe da dariya ita ma dariya ta yi ganin Abdallah na dariya. Tsaye na yi a wajen ina kallon su ina fatan Allah ya kawo ranar da ni ma zan samu yara wanda zan yi alfahari da su kamar ko wace uwa, ni ma na ga ranar da zan wuce gorin da Mama Sa'a take yi min a gidan nan. Ban san hawaye na zuba daga idanuna ba sai jin hannun Abdallah yana share min su sai da ya gama share min hawaye ya ce"Babe me ya faru kuma kike kuka?" Girgiza kai na yi na ce"Babu komai fa" "ke Babe babu komai kike hawaye kuma?" Gyaɗa kai na yi kafin na bar wajen domin aikin banza ne idan na sanar da shi damuwa ta ba shi da maganinta Allah da ya halicce mu shi kaɗai ne zai iya kawo min mafita a halin da nake ciki a yanzu. Bayan mun gama shirin mu tun tuni Abdallah ya wuce zuwa office, ni ma hannun Aysha na kama muka sauka ƙasa inda muka tarar da Mama da ƴaƴanta suna breakfast har mun kai bakin kofa Mama ta ce"Ke sumayya tare da Aysha za ki tafi yawon gantalin?" "E Mama zan kai ta gida ne" "E to gara dai ki mayar musu da ƴarsu kar maitarki ta motsa cikin dare ki tsotse mata jini kamar yadda ki ke tsotse na ƴaƴan Abdallah, don ke kam baƙin ciki ya yi wa rayuwarki kamun kazar kuku babu abin da za ki bari wani ya samu ko wannan ɗan aikin da Abdallah yake yi don na tsaya ne ina addu'a da tun tuni kin saka an kore shi mai farar ƙafa kawai" sai da ta gama maganganunta na ja hannun Aysha muka nufi mota. Sai da ta zauna ta ce"Momy za ki kai ni gida?" "E princesse zan kai ki gida, ko bakya son zuwa" "A a Momy ni ba zan je ba" "me ya sa, daddynki zai yi missing ɗinki fa" "To ai Momyna ba ta yi missing ɗina ba" girgiza kai na yi na ce"Ki bar faɗin haka Princesse Momynki time ne ba ta da amman idan ba haka ba ta yi missing ɗinki sosai" gyaɗa kai ta yi kafin ta ci gaba da wasa da wayata da ke hannunta. Sai da na biya office na ba secrétaire ɗin aikin da na yi jinya kafin na fito na nufi gidanmu. Da sallama na shiga dakin bayan mai gadi ya buɗe min gate ɗin gidan ina riƙe da hannun Aysha. Ummi da ke zaune a dakin ta ɗago ta amsa. Littafin da ke hannunta ta ajiye tare da rungume Aysha ta ce"Ga kishiya ta zo har gida" zama na yi na ce"Ummi ina kwana?" "A gidanki Aysha ta kwana?" Gyaɗa kai na yi ina jin zafi a raina don babu shakka ba dan Ummi ba ta ji gaisuwa ta ba ne sai dai kawai ba ta yi niyyar amsa min ba ne. Tsawon shekaru huɗu kenan da Ummu ke fushi da ni har yanzu ina jin ɗacin abin a cikin raina sai dai kuma duk da haka ban bar bata kulawa kamar yadda na dauki lokaci mai tsawo ina yi. Sai yanzu na dawo daga duniyar tunanina na ce"E Ummi jiya Mustapha ya je da ita sai ya bar ta" "Ina ita Rumy take?" "Ba mu haɗu ba, ni ma yanzu daga office nake zan kai Aysha gida ne" "Ai yanzu kin san sarai Rumy ba ta gida" wasa na fara da yan yatsuna na ce"E dama sai da yamma zan kai ta za mu zauna a nan ne" "Ki bari zan kira Rumy ta zo ta ɗauke ta za ki iya tashi ki koma bakin aikinki" murya na ɗan rawa na ce"Ummi ina mai ƙara ba ki hakuri a kan Kuskurena amman zuciyata ba za ta iya ci gaba da ɗaukar irin wannan hukunci da kike yi min Ummi ke uwata ta ce kaf duniya ba ni da wanda ya fi ki. Na san na yi kuskure dan Allah Ummi ki yafe min" ɗaga min hannu ta yi ta ce"Sumy ya isa haka idan ba ki da abin cewa ina son ki kama gabanki, tabbas dan na san muhimmancin bakin uwa da tasirin da yake yi a kan rayuwar ƴaƴanta idan ba haka ba da na daɗe da cire ki daga cikin ƴaƴana, ba zan yi miki mugun fata ba kamar yadda nake sanar da ke a kullum sai dai na yi miki fatan shiriya" idanuna tun tuni sun cika da hawaye ajiye ledar less ɗin da zan kawo mata na yi kafin na ajiye mata kudi da za su kai jika ɗari biyu na ce"Ummi Allah ya huci zuciyarki, ko ki na bukatar wani abu?" Girgiza kai ta yi ta ce"Babu abin da nake bukata za ki iya tafiya" miƙe wa na yi sai na sumbaci Aysha a goshi kafin na fice daga falon. Ina shiga motata sai na haɗe kaina da sitiyarin motar na fashe da kuka mai tsuma zuciya, tsawon shekaru huɗu kenan ina abu daya, tsawon wannan lokaci a duk sanda zan zo ganin Ummina zan nemi yafiyarta a kan laifina sai dai kuma har yanzu jiya-i-yau ba ta ma kallona bare har na saka ran za ta saurare ni har ta yafe min laifin da Allah ne kaɗai masanin abin da ke ɓoye. Sai da na yi kukana mai isa ta kafin na share hawayena na yi wa motar key sai office ɗina domin ban san inda an nufa ba kamar yadda na yi wa Mustapha alkawarin yi wa Rumy magana ban iya zuwa shagonta ba domin bana cikin nutsuwar da zan iya fahimtar da ita Kuskurenta. ★Only 500 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange *Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252* *Cmnts nd share* [11/12 à 22:44] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 🔥FREE PAGE🔥 Only 500 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange. *Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252* *Page 09* Ko a office ɗin ma haka na yini cikin rashin sukunin da rashin madogara. Duk abin da nake yi maganganu Ummina su na maƙale a cikin zuciya ta. Na rasa yadda zan yi don Ummina ta yafe min kuskuren da gabadaya duniya ke kallona da shi. Abdallah ne ya shigo office ɗin yau kam ya yi sallama kuma ko da ma bai yi ba yau ba zan tanka mishi ba. Zama ya yi ya ce"Kin je ganin Ummi?" "E na ja ban ma karasa ba wajen Rumy Ummi ce ta ce na bar Princesse a wajenta" shiru ya yi yana bin fuskata da kallo ya ce"Ki yi hakuri Babe duk wannan abin da yake faruwa ni ne na ja miki shi idan da a ce ban bi son da zuciyata ke yi miki ba da yanzu duk haka ba za ta riƙa faruwa ba" da sauri na saka hannu na rufe mishi baki. Cikin Muryar kuka na ce"Hakika Qalbi soyayyar da muke yi wa junan mu ba za ta zama zunubi ko kuskuren da wadannan abubuwan suke faruwa ba, duk wani abu da ka gani Allah ya riga ya saka shi a cikin kundin kaddararmu ne babu yadda za mu yi da shi sai dai mu yi addu'a kuma mu zuba wa sarautar Allah ido" shiru ne ya biyo baya na wani dan lokaci. "Babe ki ba ni dama na sawake miki, domin ina son ganinki cikin farin ciki ina son ganin kin yi rayuwa kamar kowa, ki amince min na sake ki sai ki auri wani" na ji muryar Abdallah kamar saukar guduma a tsakiyar kunnena bayan shiru ya biyo baya na wani dan lokaci. Cikin hanzari na ce"Hakika ba ni da wani miji a wannan duniyar idan ba kai ba, muddin ka ga na kasance da wani ɗa namiji to sai dai idan babu kai maganar saki ka cire ta daga tunaninka. Ranar da Allah ya ƙaddara karshen aurenmu tabbas na san zai dauki ran daya daga cikinmu ne" na faɗa ina ci gaba da zubar da hawaye tabbas na san rabuwar mu shi ne mafita a gare mu amman tabbas soyayyar da muke yi wa juna idan har muka yi kuskuren rabuwa to babu shakka karshen farin cikin da za mu yi kenan a wannan duniya. Mu ɗin mun zama hanta da jini rabuwar mu zai yi wuya, domin kuwa mun rasa wani bangare ne na jikinmu. Shiru ne ya biyo baya na tsawon wani lokaci duk da dai ban san me Abdallah yake tunani ba na san ba zai wuce mafita yake hango mana a rayuwar aurenmu duk da dai na dogara akan babu mai yi sai Allah, ido kawai na zuba mishi ina jiran jin ranar da zai yi niyyar katse tunanin da yake don yi min magana. "Babe ko za mu sake komawa asibiti ne? Kin san fa an ce shi magani katari ne sai ki ga kuma an dace da samun waraka" ya faɗa yana kokarin janye idanunsa daga kaina don da dukan alamu kunya ce ta kama shi. "koma wa asibiti ba mafita ba ne a gare mu, wata asibitin ce ba mu je ba? Qalbi sanin kan ka ne kuɗin da muka kashe akan matsalarmu Allah ne kaɗai ya san adadin su, sun ishi wani mai karamin karfin ci da sha har da sana'a" shiru na yi na dan lokaci amman ganin ba shi da niyyar amsa min sai na ci gaba da maganata "Kamar yadda na faɗa maka, Allah shi ne mai saukar da cuta, mai kuma bada lafiya a lokacin da ya so, mu tattara duk lamuranmu mu saka su a hannunsa tabbas shi ɗin mai ji ne kuma mai gani ne ya fi mu sanin halin da muke ciki sannan ya fi mu sanin tanadin da ya yi wa rayuwarmu a nan gaba, kila ma duk wannan burin samun lafiyar da gare mu akan matsalar da ta adabe mu sau ka ga mafitar ba alkairi ba ce" A hankali ya tashi daga kan kujerar da yake zaune ya nufi inda nake zaune ya rungume ni yana mai share min hawaye ya ce"Hakika Babe na yi dacen samun ki, kuma na san Allah ne ya yi min alfarma ya bani ke ba wai tsumina ko dabarata ba ne, ina fatan mutuwa in bar ki Babe don tabbas idan ki ka mutu ki bar ni na zama maraya na har Abada" rungume shi na yi ni ma a jikina ina mai ci gaba da zubar da hawaye wanda suka zamar min kamar wata kankara da ke sanyaya zuciyata. Zame jikinsa ya yi daga nawa ya saka hannunsa yana goge ruwan hawayen da ya ɓata min fuska. Kofar aka kwankwasa na bada izinin shigowa. Mustapha ne ya shigo da sallama ya ce"To tantabaru ku yi mana uzuri dan Allah don a office kuke ba a bedroom ɗinku ba" murmushi na yi don idan da sabo mun saba da halinsa Abdallah ya ce"Kai malam ba ka je office ba?" Girgiza kai ya yi ya ce"Daga can nake, Sumy wajen ki aka aiko ni" dariyata na kunshe don ganin irin rainin hankalin Rumy ta ina za ta fara aikin shi bayan kuma ta san lokacin yana office. "To me aka ce na yi?" Na faɗa ina bin shi da kallo "Ta kira wayarki ne tun ɗazu ba ta same ki ba, ta ce kar ki kawo princesse yau ki bar ta sai weekend" "To ai an yi aikin banza don har na kai ta gida wajen Ummi kuma ta ce za ta kira ta don ta zo ta ɗauke ta" girgiza kai ya yi ya ce"Ni kam yanzu ban san yadda zan yi ba" Abdallah ne ya ce"Ka koma bakin aikinka zan je na ɗauko ta zuwa an jima" murmushi ya yi ya ce"yauwa haka ya yi na gode sosai brother" a tare suka bar office ni kuma na fara tunanin akan wane dalili za ta ce kar a kai yarinyar gida bayan kuma ita tana nan ba komai take yi ba. Wayata da tun bayan barin gidan Ummi take cikin mota na sauka ƙasa parking Space na dauko ta. Kiran Rumy na gani babu adadi kiranta na yi ringin biyu ta ɗaga na ce"Rumaisa akan wane dalili ki ka ce kar a kai Princesse gida" cikin halin ko in kula ta ce"Tafiya zan yi zuwa wani taron kasuwanci" rai a bace na ce"Rumy zaman aure da kike gani ba abin wasa ba ne, ko sati biyu ba a yi ba da kika dawo daga yawon ki yanzu kuma za ki koma. Haba dan Allah ko ba ki ji tausayin Mustapha a matsayinsa na mijinki ba ya dace a ce kin ji tausayin Aysha a matsayinta na ƴarki mai ƙananun shekaru wannan sam ba halin uwa ta gari ba ce" "ke dan Allah Sumy tsaya ke kin san mene ne uwa ma bare kuma har ki ce wa wani shi ba uwa ta gari ba ce, ke da kike ta garin ina ƴaƴanki suke? Ina son ki sani ba ki fini son Aysha ba don ko babu komai daga tsatsona ta fito ni na yi rainon cikinta. Idan kin ga kin iya riƙe ta har na dawo to idan ba za ki iya ba kuma zan bar ta a wajen mahaifinta. To in ban da abin ki ai ni taimakon ki ne zan yi yadda ba ki da wanda za su ɓata miki ɗaki shi ne na baki aro amman ki zo ki dame ni da wata nasiha ban ci ban sha ba. Ki ji da matsalar gabanki mana ki ji da matsalar rashin haihuwar da ta yi miki kamun kazar kuku" daga nan ta kashe wayar kit. Da mamaki nake bin wayar da kallo, tamkar wani audio haka maganganunta suke dawo wa a cikin kunnena. Na rasa ma abin da yake min daɗi ko office ɗin ƙasa komawa na yi na figi motata na nufi gida. Ina isa gidan kai tsaye dakina na nufa ban tsaye bin ta kan Mama Sa'a da ke falon ba tana yi min magana. Kwanciya na yi akan gadon ina tunanin rayuwar da muka yi a baya. Rumaissa na kashe kiran da ta yi wa Sumayya dai ta kira wata number wadda da dukan alamu ba ma ta Niger ba ce. Rai a matukar ɓace ta fara magana mai kama da faɗa "Kin ga abin da ƴar gwal ɗinkin ta yi min ko?" Daga can bangare aka amsa mata da "Me kuma ya faru? Mene ne abin da Sumayya ta yi miki yanzu?" Kamar wadda za ta mangare mutum ta ce"Ta fara yi min katsaladan ne a cikin rayuwar aurena, wallahi ki faɗa mata hawainiyarta ta kiyayi rama ta to kin san sarai ba ni da mutunci" cikin kwantar da murya matar ta ce"Rumaissa ki yi hakuri idan dai Sumayya ce zan yi mata magana kuma in sha Allah ba za ta sake saka baki a cikin lamarin aurenki ba, haka ya yi miki?" Gyaɗa kai Rumy ta yi ta ce"E hakan ya yi mu kwana lafiya" tana gama maganar ta katse kiran. Tunani matar ta shiga yi akan wane irin laifi ne kuma Sumayya ta yi da har Rumaissa ta kawo kashe, don ita rabon da ta ga kiran Rumaisa har ta manta. Tsaki ta ja tana cewa "kila ma ba wani abun a zo a gani ta yi mata ba amman kuma ta ɗaga wa mutane hankali a banza" Na yi nisa cikin tunanina na ji wayata tana ringin ɗaga kaina na yi sai na ga number anty Maryam yayarmu ce ita ce ta farko a cikin ƴaƴan Ummi tana ƙasar Canada da mijinta da yaranta guda biyu. Da sauri na ɗaga kiran tare da yin sallama na ce"Anty ina yini?" "Lafiya qlau, Sumayya ya aiki?" "Aiki kam da godiya, ya yara?" "Duk suna lafiya, me ya faru tsakaninki da ƴar uwarki?" Da sauri na tashi zaune daga kwanciyar da nake don na yi mamakin tambayar da ta yi min. "Anty me ya faru? Wani abu aka ce na yi?" Na faɗa da sauri don har na matsu don jin amsar da za ta bayar don ban san abin da Rumaisa ta ce na yi ba. "Rumaissa ta ce min ki na yi mata shiga hanci da ƙudundune a rayuwar aurenta bayan kuma ban san ki da saka kanki a cikin abin da bai shafe ki ba shi ya sa nake son jin gaskiyar lamarin?" Na shiga uku ni Sumayya wannan wata irin rayuwa ce laifin me na yi wa Rumy har take tunanin na shiga rayuwar aurenta ni kuma. "Anty wallahi ba haka ba ne kawai don na faɗa mata gaskiya ne akan yawan yawon da take yi ba ta tsayawa ta kula da ƴarta da mijinta shi kenan na yi mata laifi" na faɗa wannan karon har da hawayena ina jin wani iri a cikin raina, yau ko wani na ga yana shirin shiga rayuwar aurenta ai zan hana shi bare kuma a ce ni da kaina zan shiga har na yi mata katsaladan abin da cin rai yake. "Sumayya kin san sarai tun ba yau ba na shiga tsakaninku da Rumaisa, ki fita harkar ta mana idan ta bukaci wani abu daga gare ki sai ki yi mata idan ba haka ba kuwa ki kawo ido ki zuba mata kin fi kowa sanin yadda take wata irin mutum ce ita da ba za ka taɓa fahimtar abin da take so idan ba ta faɗa maka, tunda dai har gyara kayanka ya zama sauke mu raba zuba mata ido akwai ranar da za ta fahimci don ki na masoyiyarta ne kike faɗa mata wasu abubuwan ba masu kyau ba ne ta daina aika su. Shi kuwa namiji duk yadda ya kai ga son ka idan ba ya samun kwanciyar hankali dole ne wata rana ta zo da zai daina son ka" hawayen baƙin cikin da suka zubo min na share na ce"Shi kenan anty babu komai zan bar faɗa mata gaskiya tunda ba ta so" "Yauwa Sumayya hakan zai fi kawai, ya maganar neman maganin ke da Abdallah" cike da kunya da kuma jin nauyi saboda idan har ba da Abdallah ba ne, ba na son yin maganar rashin haihuwa da kowa. Ɗaurewa na yi na ce"Mu na kan neman magani har yanzu" ajiyar zuciya ta sauke ta ce"Allah ya kai mu ranar da zai ba ku na ku ƴaran kuma ku huta" da amine na amsa sai kuma shiru ya biyo ba can ta ce"To ki gaida Abdallah sai kwana biyu in sha Allah" kashe wayar ta yi sai na bi wayar da ido ina mai nazarin lamarin yar uwata Rumaissa. *Cmnts nd share* [12/12 à 18:45] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 🔥FREE PAGE🔥 NA KUSA GAMA FREE PAGE HAJIYA ME KIKE JIRA BA KI BIYA KUDIN KARATUNKI BA? Only 500 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange. *Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252* *Page 10* Ganin dai babu sarki sai Allah, sai na tashi na shiga toilet na yi wanka na fito na tada sallah. Bayan na gama sallar sai ga Abdallah ya shigo ɗakin hannunsa ɗauke da Aysha, da sauri ta sauko daga hannunsa ta yo wajena. Ni ma miƙewa tsaye na yi ina naɗe abin sallah ina faɗar "Oyoyo oyoyo princesse ta dawo" zuwa ta yi inda nake tsaye tana nuna min hannunta mai ɗauke da chocolat na ce"Wa ya ba ki abin daɗi haka?" Da hannu ta yi min nuni da Abdallah da ke tsaye a bakin kofa har yanzu bai motsa ba bare kuma ya yi magana na ce"Ni ma uncle a ba ni chocolat" da sauri ta ɓoye nata a bayanta ta ce"Momy babu" dariya na yi na jawo ta jikina na rungume ta. Duk wani kunci da damuwar da nake ciki sai na ji kamar an yaye min shi babu ko ɗaya sai wani daɗi da nake ji domin murmsuhin Aysha yana saka ni farin ciki fiye da misali. Har yanzu murmsuhin kan fuskata bai gushe ba sai na kalli Abdallah na ce"Qalbi sannu da zuwa ina chocolat ɗina?" Karasowa ya yi cikin dakin ya ce"Ba a ba manya iya na yara ne" girgiza kai na yi na ce"To ai ni ma yarinya ce, ko Aysha?" Da sauri ta girgiza kai ta ce"A a Momy ba yarinya ba ce" dariya Abdallah ya yi ya ce"To kin ga ni ko Aysha ai ta san ke ba yarinya ba ce, kin ga kuwa ai ba za ki samu chocolat ba" Dariya na yi na ja hannunta ina cewa"Mu je a yi wanka tunda dai an gama kwadayin" da gudu ta ruga ta ɓoye a bayan Abdallah tana noke kafaɗa "Ikon Allah wannan duk gudun wankan ne?" Da sauri ta gyad'a kai tana ta dariya. Sai da na haɗa da wayo kafin ta yarda ta bi ni zuwa toilet don yi mata wanka. Ko da na gama na canza mata kaya na shafa mata mai da turare sai na bata wayata na nufi dakin Abdallah, akan gadonsa na tarar da shi yana zaune ya rafka uban tagumi toilet dinsa na wuce kai tsaye na haɗa mishi ruwan wanka na zo na zauna a kusa da shi na ce"Me yake damunka Qalbi, wannan uban tagumi da ka rafka?" Girgiza kai ya yi ya ce"Babu komai Babe" kasa na yi da murya na ce"Ai banza ba ta kai zomo kasuwa, sai dai kuma idan ita damuwar ta kai girman da ba za a iya sanar da ni wanzuwarta ba" shiru ya yi bai ce min komai. Na kuma cewa"Tashi ka je ka yi wanka Allah ya yi maka maganin damuwarka" Tashi ya yi ya nufi bathroom ni kuwa na koma ɗakina na shiga ba Aysha abinci don na san daga wannan game ɗin za ta bige da yin barci. Ina gama bata abinci a baki tana ci tana zuba min shagwaɓa har ta gama na yi mata brush ta dawo kan bed ɗin ta zauna. Cire mata game ɗin na yi daga wayar na saka mata application ɗin da aka tanada domin yara don su koyi addu'oi. Rufe kofar na yi kafin na koma dakin Abdallah. "Qalbi mu je ƙasa ka ci abinci mana" lura na yi da bai ma san ina yi ba har sai da na karasa gaban shi na saka hannuna ɗaya a tsakiyar sumar kansa na fara shafa wa a hankali. Sai yanzu ya ɗago kai ya kalle ni ya ce"Babe yaushe ki ka shigo?" "Tun ɗazu na shigo ina yi ma magana sai na lura ka yi nisan kiwo" shiru ya yi bai ce min komai ba sai na kuma daurewa na ce"Dama ina yi maka magana ne akan ka zo mu ci abinci" Buɗe bakinsa ya yi da niyyar ya yi magana sai kuma ya fasa, lura da kamar akwai abin da yake son sanar min da na yi sai na zauna a bakin gadon na haɗa hannunsa guda biyu a cikin nawa a hankali na fara matsa masa su. Na dan ɗauki lokaci ina yin haka kafin na ce"Qalbi ni fa rufin asirinka ce idan ba ka faɗa min abin da yake damunka ba wa za ka faɗa wa?" Ɗago idonsa ya yi ya sauke su a kaina sai da ya ƙare min kallon don har na yanke shawarar watsar da makaman yaƙina na ƙyale shi saboda ba karamin yaro ba ne shi ɗin da zan zauna ina ta faman rarrashin shi akan abin da yake damuwarsa ce, a iya sani na da shi ban aikata mishi laifin komai bare kuma na zargi kaina da cewa na yi mishi laifi. Sai dai kuma kwatsam a lokacin da ban yi zato ba na ji ya ce"Babe ina da wata ƴar bukata ce a wajenki" ido na zuba mishi ina bin shi da kallo kuma na buɗe kunnena da kyau. "Yaya Hisham ne aka kora daga gidan da yake haya shi da matarsa, to kuma nan za su dawo da zama" Da ido kawai nake bin shi da kallo don ban ma amsa ba, ban ma san mene ne amsar da ya dace na bashi ba don wannan maganar tashi ta fi kama da sanarwa akan neman izini ko babu komai shawara tana da daɗi sai a yi min shawara amman haka kawai a ce min za su dawo gidan ai ba ni da ta cewa tunda dai har sun riga da sun yanke hukuncinsu. Sai kuma na ji yana cewa"Bai biya kuɗin hayar wata uku ba mai gidan ya ce zai kai shi kotu idan bai biya shi ba zuwa karshen wannan satin, ina son ki bani aron jika ɗari biyar don Allah Babe, ba zan so a kai shi kotu ba saboda matsalar kuɗi" gyaɗa kaina na yi na ce"Allah ya kai mu gobe zan maka transfert" da sauri ya rungume ni ya ce"Babe na gode sosai Allah ya bar kauna" ban amsa mishi don gaskiya ban ji daɗin abin da ya yi min ba. "Tashi mu je ka ci abinci" miƙe wa ya yi ya kama hannuna muka sauka ƙasa don cin abinci. A dinning gabadaya jama'ar gidan suka haɗu don cin abincin dare. Bayan na zuba ma Abdallah na zuba na Mama da na Baba sai na zuba wanda zan ci na zauna akan kujera na fara ci. Sai na ji Mama tana cewa Baba"Mun gama magana da Hisham ɗin gobe idan Allah ya kai mu za su taho nan ɗin" ni dai ban tanka musu ba na yi shiru na ƙyale su ina ci gaba da cin abincina. Sai Mama ta ce"Sumayya gobe idan Allah ya kaimu su Hisham za su dawo nan da zama gobe idan Allah ya kai mu sai ki share musu wancan ɗakin" da sauri na dago kaina ina bin yatsarta da kallo sai na ce"Ai gobe zan je office ne" Wani banzan kallo Mama ta watso min ta ce"Aikin banza wane ne ya damu da zuwa office ɗinki babu wani office da za ki je muddin dai ba ki gama aikin da na saka ki ba" tashi na yi na bar dinning ɗin ganin wanda nake zaune don shi bai damu ya saka baki ba a cikin lamarin ba. Ina shiga ɗakina na yi wanka na yi addu'a tare da yi wa Aysha na kashe wayata da take ta faman karatun addu'a don tun tuni Aysha ta yi barci. Kafin Ni ma na kwanta na rufe idona ta tunanin mafita don na fara gajiya da wannan cin kashin da ake yi min a gidan mijina. Washegari ko da na farka breakfast na daura har yanzu Aysha ba ta farka ba shi kuwa Abdallah ko ta kanshi ban bi sai da na gama duk aikin da zan yi na haɗa breakfast ɗinsa na kai mishi ɗaki sai a lokacin na ce"Qalbi barka da safiya" "Jiya ko da na shigo kin yi barci ko?" Gyada kai na yi na ce" gajiya ce ta saka ni gaba, ga abinci ka ci don kar ka yi lati" Zama ya yi ya fara cin abincin ya ce"Yana na ga kin shirya yau ba za ki je office ba ai ko?" Da mamaki na kalle shi na ce"Akan me ba zan je office ɗin ba?" Cikin halin ko in kula ya ce"Ai umarnin Mama ne ba ta ce kar ki je ba ki zauna don gyara wa su yaya ɗaki ba?" Wani shu'umin murmushi na yi na ce"E kuma haka ne, bari na je na duba Aysha ko ta farka daga barci" ɗakina na shiga ina saka yadda zan yi kafin na dauki Aysha na kaita toilet na zuba mata ruwa a hankali a fuska. Tashi ta yi ta buɗe ido tare da fashe wa da kuka na ce"Zan yi miki video na ce da uncle kukan wanka kike yi" sai ta yi shiru da bakinta na ce"Ko ke fa yarinyar kirki" wanka na gama mata na shirya ta na bata abinci ta ci kafin na ja hannunta muka sauko ƙasa don na dauki aniyar ba zan zauna a gidan ba don na yi musu tunda dai ba baiwa ba ce ni ɗin. Ina saukowa kasa wannan ya tabbatar min da har yanzu Abdallah bai bar gidan ba amman ban damu ba na saka Aysha a mota na yi ma motar key muka bar gidan. Abdallah ko da ya gama breakfast ɗinsa ya shiga dakin Sumayya amman bai tarar da ita ba da mamaki ya fara tunanin to ina ta je. Bai tsaya wani tunani ba ya nufi office a parking Space ya hangi motar Sumayya tunani ya fara kenan ba ta bi umarnin mahaifiyarsa ba ta saka ƙafa ta bar gidan tabbas sai ya ɗauki mataki akan Sumayya don ba zai yarda da wannan halayyar ta raini da take don tsirowa ba musamman zuwa ga mahaifiyarsa. Kwafa ya yi tare da shige wa cikin Company ya nufi office ɗinsa kai tsaye. Da yamma ina gama aikina sai da na biya wani supermarket na yi wa Aysha siyayar kayan sawa da kuma biscuit da chocolat. A hanya sai surutu take tana ta faman kiciniyar buɗe ledar na ce"Princesse don Allah ki yi hakuri da buɗe ledar nan sai mun je gida" "Na ajiye Momy" ta faɗa kafin ta daina taɓa ledar. Ina isa gidan na yi parking na fito da ledar kafin na kama hannunta muka nufi cikin gida. Mama Sa'a da tun safe bayan ta gama breakfast take jiran saukowar Sumayya amman shiru har ta gaji da jiran gawon shanu ta kira Rumana ta ce"Ke Rumanatu je ki kira min Sumayya" da mamaki Rumana take kallon Mama ta ce"Wata Sumayyar bayan tun ɗazu ta tafi office, ina ta jikin window ɗakina na hango ta" "kan bala'i wallahi wannan yarinya ta yi mugun raina min wayo, idan ba rainin wayo ba jiya sai da na ce ta tsaya ta yi shara amman sam ta ƙi Allah sai na ɗauki mataki akan wannan yarinyar. Idan ba jaraba irin ta Abdallah ya sawake ma wannan juyar mana ko mun huta amman kullum abin ƙara gaba yake na yi masifar na yi nasihar na yi makircin amman har yanzu ina ci gaba da bulayi bara a kufe" ita dai Rumana shiru ta yi tana ci gaba da zuba wa Mama ido da kunne don saurarenta. "Je ki kira Jiddah ku gyara musu ɗakin kafin su iso" wani kallon mamaki take bin Mama da shi ta ce"Wa wai ni ? Wallahi ba zan yi ba a saka masu aiki ko kuwa jiddah idan ta ga za ta iya sai ta yi ɗakin da a shekara ɗaya ma ba a buɗe shi ba shi ne za ki ce wai mu share" tana kaiwa nan ta fice daga falon. Baki Mama ta saki tana kallon Rumana don dama ta san za a rina wai an saci zanin mahaukaciya, ya lafiyar kura bare tana zawo a banza ma Rumana ta yi ma mutum rashin kunya bare kuma an saka ta aiki. Dole uwar na ƙi Mama ta kira mai aiki ta saka ta aikin gyaran ɗakin da babban ɗanta zai zauna da matarsa. Zama ta yi tana faman jiran dawowar Sumayya don ta sauke mata abin da yake cikinta don ba za ta dauki wannan sabon salon iskanci da Sumayyar ta tsiro da shi ba. *Cmnts nd share* [16/12 à 19:45] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 🔥FREE PAGE🔥 NA KUSA GAMA FREE PAGE HAJIYA ME KIKE JIRA BA KI BIYA KUDIN KARATUNKI BA? Only 500 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange. *Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252* *Page 11* Ta riga ta saka a cikin ranta sai ta yi maganin Sumayya duk rashin kunyar da Rumana ta yi mata ba ta gabanta sai rashin kunyar Sumayya ce take gani. Ai dama an ce laifi tudu ne sai ka hau naka ka riƙa hango na wani. Tana zaune a wajen tana ci gaba da saka da warwara bayan an gama share ɗakin da ta saka mai aikin gidan ta share, sai aka turo kofa Hisham ne da matarsa Umaimah suka shigo da sauri Umaimah ta karaso inda take zaune ta rungume Mama ta ce"Mama na yi kewarki sosai" murmsuhi Mama ta yi ta ce"To ai dama Umaimah sai da na faɗa wa Hisham ya dawo da ke gidan nan amman ya ƙi ai gashi yanzu kun dawo" ita ma murmushin ta yi ta ce"Yanzu kam Mama ai na dawo ko zan ci gaba da zama a kusa da ke" Daidai Hisham ya karaso ya ce"Mama barka da safiya" zama ya yi akan capet kusa da kafar Mama ta shafa gashin kansa ta ce"Hisham sannu da kokari, wannan abu da ya faru sam ban ji daɗi ba, amman yanzu ai shi kenan ka bar musu gidansu sai ku zo ku rayu a gidan ɗan uwanka lafiya qlau babu wanda zai dame ka da ka biya haya" gyaɗa kai ya yi ya ce"Haka ne Mama mun gode sosai da wannan dama da ki ka ba mu" "haba haba ai babu zancen godiya ku ɗin ƴaƴana ai, ku tashi ku shiga daga ciki ku ɗan kimtsa" tashi suka yi suka nufi dakin da aka ware musu nan suka shiga gyara kayansu. Umaimah tunda ta auri Hisham Mama ta dauki son duniya ta ɗaura mata, tun bayan aurensu yanzu shekara biyar amman sau uku tana haihuwa ƴaƴan su na mutuwa wannan ne ya ƙara ma Mama Sa'a soyayyar Umaimah a cikin ranta saboda yadda take jin tausayin Umaimah ɗin wannan dalilin ne ya sa wutar tsanar Sumayya ta ƙara ruruwa a zuciyar Mama Sa'a domin ita a ganinta ai gara Umaimah ko babu komai ita tana haihuwa Allah ne bai bar mata ba amman ita Sumayya ko ɗan ɓarin nan ma da mata ke yi ita bata taɓa yi ba. Ganin Umaimah ta samu fada a wajen Mama sai take cin karenta babu babbaka a cikin gidanta wani lokacin ko Hisham bai isa ya taka mata burki ba idan tana wani abin saboda da ya ce zai yi mata magana sai ta kira Mama ta sanar mata ita kuwa Mama ta rufe shi da faɗa daga karshe dai ita Umaimah za ta samu damar yin abin da ta ga dama Mama ta daɗe a wajen a zaune har aka yi sallah ta tashi ta yi sallah ta dawo zaman jiran gawon shanun da take yi wa Sumayya. Can kuwa sai ga Sumayya ta turo kofar falon da sallama a bakinta hannunta kuma riƙe da Princesse Aysha da ledar siyayar da suka yi a super market. ★SUMAYYA★ Da sallama na shigo gidan sai na lura da Mama zaune a falo na ce"Mama ina yini?" Wani kallon mai akan ruwa ta yi min nan na fara tunanin abin da na yi mata ni kuwa magana na ji tana yi wa Aysha "Mai babban suna ina Mamanki?" Aysha ta amsa mata "Momy tana gida wajen Daddy" na ce"Aysha mu je a yi wanka ko?" Har mun fara tafiya na tsinkayo muryar Mama tana cewa"To marar mutunci banza shasha da bata san ciwon kanta ba, a haka dai za a ƙare a rainon ƴaƴan wasu kai ba ka da naka" ban ce komai ba idan a ce ana yin sabo da mugayen maganganu ni kam da tun tuni na yi sabo da wannan cin kashin na Mama. Sai dai kuma ita zuciya ba ta da ƙashi tsoka ce, duk wannan abin da Mama take yi min na kasa kauda kai sai ta ci gaba da cewa "Tsabar isakanci irin naki da na saka ki aiki sai ki ka figi wannan kafafun naki masu kama da karas ki ka bar gidan nan ko? Wallahi ki kiyaye ni ki fita nesa da ni na faɗa miki, wannan ya zama karo na farko kuma na karshe da zan saka ki wani abu a gidan nan ki saka ƙafa ki shure shi sai na yi mugun ɓata miki rai wallahi. Ina dalilin wani aiki, aikin banza aiki wofi, kullum mutum yana saka wasu ɗangalalun kaya ya bar gida da sunan wani aiki ko. To ki yi a hankali don ina gab da hana yin wannan aiki sai dai ki zaɓa zama da Abdallah ko kuwa aikinki" shiru na yi ina nazarin amsar da zan bata amman sai na rasa abin faɗa sai na bi jikina da kallo doguwar rigar atanfa ce a jikina ta buɗe sosai har tana sharar ƙasa ga wani babban mayafi da na saka kuma a haka za a ce dangalalun kaya ne, kawai na gyaɗa kai na ja hannun Aysha muka bar falon don zuwa shashena Ina jinta tana ci gaba da bambamin faɗanta amman ban tanka mata ba. Ina shiga dakina Aysha ta ce"Momy ina jin yunwa" gyaɗa mata kai na yi na ce"Za ki ci indomie?" Da sauri ta girgiza min kai ta ce"A a Momy ba na so" shiru na yi ina nazarin abin da zan sama mata ta ci yanzu-yanzu saboda Allah ya sani a gajiye nake sosai. Ganin dai babu sarki sai Allah sai na ce"Bari na dauko miji madara ki sha kafin na gama girki" sai ta fara dariya har da tsalle don murna. Cire kayan jikina na yi na saka wasu na ja hannunta muka sauka ƙasa zuwa kitchen don na haɗa dinner sai ita kuma na bata madara ko na samu sallama don da an jima za ta fara yi min kukan yunwa take ji. Muna shiga kitchen na dauko mata madara na daura ta akan kujera na shiga store don duba abin da zan girka. Jiddah ce ta shigo kitchen idonta ya sauka akan Aysha da take shan madara har ta fara ɓata rigar da ke jikinta ta ce"Kan uba ashe ba ki da mutunci wannan yarinyar to uban waye ya baki madarar har da za ki ɓarnatar da ita" Aysha kam sai yanzu ta ɗago kai ta kalli jiddah ganin ta fara zaginta tuni har idonta ya fara kawo kwalla ta ce"Momy ce ta ba ni" hannu ta saka ta kwace cup ɗin da Sumayya ta zuba mata garin madarar a ciki ta ce"To dan uwarki ba za ki sha ba je ki gidan ubanki sai ki sha a can tunda dai wannan babu kudin uwarki a ciki" fashe wa Aysha ta yi da kuka. Daidai na bude kofar store ɗin na fito don duk abin da jiddah ke faɗa akan kunnena sai kuma na yi mugun ganin tozali da na yi da jiddah tana zungurar mata goshi. "Jiddah lafiya me ta yi miki haka?" Na tambaye ta don jin ba'asin dalilin da ya sa ta shiga haƙƙin yarinyar da ba komai ta ce mata ba. "Kawai na ce madara ce ba za ta sha ba don ba uwarta ta siya ba" wani mamaki ne ya kama ni tunda nake a cikin gidan nan jiddah da Rumana ba su taɓa faɗa min wata magana ba ni da su kare ba zan baka ba kuma ba zan kore ka ba. Ko gaisuwa ba ta haɗa mu sai wasu ƴan maganganu masu muhimmanci kadai ke shiga tsakanin amman yau shi ne har za ta faɗa min magana ba sai na ce"Jiddah ke ki ka siye madarar da Aysh take sha?" "Ba ni na siya ba amman yayana ya siya kin ga na fi ta iko da madarar" kwace cup ɗin na yi daga hannunta na ce"Idan yayanki ya zo ki turo shi ya kwace madarar daga hannunta wannan na san mai iko da abin ne ba ke ba karan kaɗa mita kawai" dariya ta yi ta ce"To juya ma ta fara magana, don Allah ki ji da abin da ya dame ki na rashin haihuwarki zai fi miki" da ido na bita har ta bar kitchen ɗin ban so na tanka mata ba amman abin nata ya wuce makaɗi da rawa wajen da Aysha ke zaune na je na shiga share mata hawaye na ce"Ki yi hakuri princesse ki rabu da jiddah sha madararki kin ji" girgiza min kai ta yi ta ce"Ni ice cream zan sha" dare goshina na yi don kaina bala'in ciwo yake min na ce"To ki sha madarar idan muka gama cin abinci dare zan siyo miki ice cream ɗin" gyaɗa kai ta yi kafin ta karbi cup ɗin ta shiga sha ni kuma na fara kiciniyar girkin abincin dare. "Sumayya! Sumayya! Sumayya ashe ba ki da mutuncin ban taɓa sani ba sai yau, to uban me Jiddah ta yi miki da za ki dake ta ke ki ka haifar min ita ne?" Da mamaki na kalli Mama da yanzu ta shigo kitchen ɗin sai masifa take kamar ta ari baki na ce"Mama me aka ce na yi kuma?" "Au, ba ki ma san abin da ki ka yi ba kenan" girgiza kai na yi alamar ban sani ba ta ce"To uban wane ne ya daki jidddah?" "Ni kam ban sani ba don ban dake ta ba" "To karya za ta yi miki ne? Na ce karya za ta yi miki?" Abdallah da tun shigowar Mama yake tsaye a bakin kofar kitchen ɗin duk abin da ya faru akan idonsa amman bai yi magana ba sai yanzu ya ce"Mama rabu da ita zan yi mata magana" juyo wa Mama ta yi ta kalle shi kafin ta ce"To dai ka gani yanzu isakanci matarka har wanda ku ka fito ciki ɗaya da su yi wa take yi" kafin ta fice daga kitchen. Wajen Aysha ya karasa ya ce"Princesse ki bani madarar mana" ba ta yi musu ba ta miƙa mishi cup ɗin ya yi mamaki don ya san sarai Aysha ba ta kyautar madara sai ya ce"Yau kuma ƴan kyautar ne kenan?" Girgiza kai ta yi ta ce"Ni ice cream nake so" "to ki gama shan madara sai mu je mu siyo" nan ma girgiza kai ta yi ta ce"Ni dai yanzu nake so" sai lokacin ne ya kalle ni ya ce"Ki canza mata kaya za mu fita" daga nan ya fice daga kitchen ɗin. Ni kuma mai aiki na kira na ce ta duba min tunkuyar da na daura sai na je na canza wa Aysha kaya Ina shiga falon na kai ta ɗakina kafin na shiga dakin Abdallah na ce"Qalbi sannu da zuwa, ya aikin?" Bai ko kalle ni bare kuma na saka ran zai amsa min sai na kuma cewa"Qalbi lafiya kuwa?" Wani kallo ya watso min da idanunsa wanda nake hango tsantsar bacin rai a cikinsu sai da gabana ya fadi don a wannan karon ban san abin da na yi ba, murya na rawa na ce"Qalbi magana nake" sai yanzu ya shirya yi min magana ya ce"Zauna" guri na samu a kusa da shi na zauna tare da zuba mishi idanu ina jiran jin abin da ni Sumayya na aikata. "Babe mene ne matsalarki ke kam? Jiya Mama ta saka ki aiki ba ki yi sai ki ka share umarninta ki ka fice daga gidan nan ko?" An zo wajen yanzu kam sai ya ci gaba da cewa"Na zuba miki ido don ganin gudun ruwanki amman yau ma kuma sai na tarar da ke kin kuma ɓata mata rai, Babe ba na son wannan sabon halin da ki ka tsira. Mahaifiyata tamkar mahaifiyarki take don haka dole ne ki yi mata biyayya kamar yadda za ki yi min kuma ki yi ma mahaifiyarki" gyaɗa kai na yi na ce"Qalbi na fahimta sosai kuma in sha Allah za a gyara, amman maganar ɗazu guguwar fahimta ce ka yi wa lamarin don ni sam ban daki Jiddah ba" hannu ya ɗaga ya ce"Ya isa Babe, Mama ce ta yi ƙarya ko kuwa ya maganar take? Wai me kike son zama ne yanzu?" Buɗe bakina na yi da niyyar yin magana sai dai ya yi saurin ce min tashi ki je ki shirya Aysha za mu tafi siyan ice cream" Tashi na yi kamar yadda ya bukata na bar dakin. Kaya na ciro da Aysha na shirya ta kafin na ce"Je ki Uncle yana dakinsa sai ku tafi" bye bye ta yi min kafin ta fice daga ɗakin, zama na yi a bakin gadona na fashe da kukan baƙin cikin da yake cin raina *Cmnts nd share* [17/12 à 22:46] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 🔥FREE PAGE🔥 NA KUSA GAMA FREE PAGE HAJIYA ME KIKE JIRA BA KI BIYA KUDIN KARATUNKI BA? Only 500 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange. *Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252* *Page 12* Sai da na yi kukana mai isata kafin na share hawayena na sauka ƙasa don ci gaba da girkina ko da na sauko ƙasa babu kowa shiru kamar an yi ruwa an ɗauke daidai zan shiga kitchen ɗin muka yi kicibis da Umaimah na ce "Anty Umaimah sannu da zuwa" wani banza kallo ta jefo min kafin ta ce"Juya ashe ki na gidan?" Tamkar saukar wata guduma haka Muryarta ta daki kunnena da kuma zaginta a gare ni ban ce komai ba sai na matsa mata daga hanya sai da ta fice daga kitchen kafin ni kuma na shiga. Abdallah kuwa bayan sun fita daga gidan tare da Ayhsa parking Space ya nufa inda ya ɗauki motarsa ya buɗe wa Tasha gidan gaba kafin ya shiga shi ma. Sai da ya fara driving sai Tasha ta ce"Uncle ka na son na faɗa maka wani abu?" Gyaɗa kai ya yi ya ce"Princesse ba ni labari abin da ya faru" murmsuhi ta yi kafin kuma cike da yarinta ta ce"Ɗazu anty Jiddah ya karɓe min madarata da Momy ta ba ni kuma ta ce ba zan sha ba tunda dai ba uwata ba ta siya" wani ras gabansa ya fadi daƙyar ya iya daure wa ya ce"Ita anty jiddah ta ce haka?" "Kwarai kuwa daddy har da haka ta yi min" ta faɗa tana zungurin kanta da yatsarta "kuma ta ce wai ai ba Momy ba ta siya yayanta ne siye madarar" ransa ya kai kololuwa wajen ɓaci kenan dai wannan dalilin ne ya saka Mama zuwa wajen Sumayya tana yi mata faɗa kamar ta ari baki. Ya ce"ki yi hakuri princesse ba za ta ƙara yi miki haka ba ita jiddah" gyaɗa kai Aysha ta yi ta ce"To uncle wane ne yayan anty jiddah?" Wani iri ya ji tambayar kamar wanda wani babba yake yi jera mishi wasu tambayoyi sai dai ya ce"Ni ne yayanta princesse" sai ta ce"Uncle to ka bari na sha madara tunda kai ka siye ta ka ji" da sauri ya gyada kai ya ce"To princesse idan ki na so ma ki shanye duka kuma yanzu ma zan siyo miki wata" ihun murna ta fara. Kafin suka yi parking a bakin shagon da ake siyar da ice cream suka shiga, tunani ne fal ransa sai dai kuma duk hankalinsa ya bi ya tashi domin gani yake yi sam bai yi wa Sumayya adalci ba tunda dai bai barta ba har ta kare kanta daga zargin da ya kafa mata ba amman kuma yana son mahaifiyarsa fiye da duk tunanin mai tunani shi ya sa idan dai akan ne ba ya tsayawa wani dogon nazari zai hukunta duk wanda ya shiga gonarta. Sai da suka biya wani katoton mall ya siya mata madara kafin suka nufi gida. Isar su gida ke da wuya aysha ta kwasa a guje sai cikin gida duk kiran da Mama take yi mata ba ta bi ta kansa ba sai da ta isa har dakin Sumayya. Ina zaune a bakin gado don ni ma yanzu na shigo dakin sai ga Aysha ta shigo da gudu tana ta murna na ce"Princesse mene ne ya zo garin wannan uwar murna haka?"Da murna ta ce"Momy kalli uncle ya siya min" da sauri na amshi ledar da ke hannunta na buɗe sai na ce"Princesse cewa uncle ki ka yi ya siya miki?" Ta girgiza kai ta ce"Momy na faɗa mishi abin da anty Jiddah ta yi min ne" girgiza kai na yi cike da alhini na ce"to zauna ki sha ice cream ɗin" tana zama ni kuwa na tashi na nufi falo daidai shigowar Abdallah Yana karasowa na ce"Qalbi sannu da zuwa" sai da ya zaune kafin ya ce"Yauwa Babe ya gidan?" Da lafiya qlau na amsa sai ya ce Babe ɗazu me ya sa ba ki faɗa min abin da ya faru tsakaninku da Jiddah har ta daki Aysha" girgiza kai na yi na ce"Ai ba ka bukaci sanin abin da ya faru ba saboda ka ce na rufe bakina" shiru ya yi kamar ruwa ya cinye shi ya ce"Ina mai baki hakuri akan abin da na yi" haushin shi ma nake ji yanzu kam amman sai na daure na ce"babu komai ai ya wuce" tashi ya yi ya sauka a ƙasa ya shiga kwala kiran Jiddah. Tana fito wa ya zuba mata ido tare da cewa"Uban me Aysha ta yi miki har ki ka dakar musu ƴa" Mama da yanzu ta fito daga dakinta ta yi saurin amshe zancen "To shanyaye an zana maka ƙarya da gaskiya ka hau kai ka zauna ko tsabar rashin tunani" cewa ya yi "Mama babu wanda ya zana min karya da gaskiya sai dai iya tsagwaran gaskiyar aka faɗa min" ido Mama ta zaro ta ce"Sakaran banza ni wannan duk ihun da kake yi fa akan mace ne, ina dalili kira wancan matar taka ta mayar da yarinyar gidan ubanta ai ba dole ba ne ko zaman nata a nan gidan" Baba ne yanzu ya shigo gidan ya ce"Ke Sa'a ba ki da mutunci ashe to yarinyar da ake magana a kanta ko babu Sumayya a nan gidan ta kai matsayin da zai riƙe ta saboda ƴarsa ce halak malak" "Tab ƴar Mustapha dai to ai Abdallah juya ne kamar matarsa" Umaimah da fitowar ta kenan daga ɗaki ta faɗa tana mai fashe wa da dariya ganin wani irin kallo da Mama ta yi mata sai ta y saurin cewa"Mama ina nufin ai shi Abdallah ba shi da ƴa kin ga kuwa ai wannan ba za a ce tasa ba ce yarinya ta koma gidan ubanta zai fi" wata ajiyar zuciya Mama ta sauke kafin kuma ta ci gaba da cewa" gobe idan Allah ya kai mu kar a maido yarinyar nan gidan nan ta tafi gidansu" tana gama magana ta bar falon ba to ko bi ta kan abin da baba ke faɗa ba. Ita kuwa jiddah tuni ta sha jinin jikinta don ta san sarai mai raba ta da Abdallah a gidan nan sai ya dage juyo wa ya yi cike da masifa kanta domin fara yi mata balbalin bala'i. Tun farkon dambarwar su har zuwa yanzu Sumayya na tsaye daga gefen corridor tana kallon su sai yanzu ta fito daga maɓoyarta. A hankali na karasa tsakiyar falon na ce"Qalbi ka rabu da ita gobe idan Allah ya kai mu zan mayar da Aysha gidansu" ina gama magana ba juya na bar falon ban tsaye sauraren abin da Abdallah zai ce min ba. Ina shiga falo na yi zaman jugum ina tunanin ta ina zan fara kiran Mustapha har na ce ya zo ya ɗauki ƴarsa bayan kuma ina da tabbacin Rumy ba ta dawo daga yawonta, na shiga tashin hankali don wannan shi ake cewa ga mutuwar uwa ga soyen nama. Ga masifar mutane gidan nan akan zaman aysha ga kuma ina jin nauyin mahaifinta. Ban san Qalbi ya karaso cikin falon ba sai da ya taɓa min kafaɗa na dago na kalle shi ya ce"Ki yi hakuri Babe amman ba na nufin na amince akan ki kai Aysha gida domin na san yadda kike jin farin ciki idan ki na tare da ita ba zan so na zama sanadiyar da zai datse ba" murmushi da ya fi kuka ciwo na yi na ce"ka kwantar da hankalinka zan kai ta gida kamar yadda Mama ta bukata idan ina bukatar ganinta don na yi farin ciki zan je gidansu" daga haka na tashi na bar mishi falon zuwa ɗakina. *SAURA PAGE UKU MU GAMA FREE PAGE* *Cmnts nd share* [18/12 à 21:46] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 🔥FREE PAGE🔥 NA KUSA GAMA FREE PAGE HAJIYA ME KIKE JIRA BA KI BIYA KUDIN KARATUNKI BA? Only 500 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange. *Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252* Saura page biyu na gama free page ki hanzarta biyan kudin karatun ku *Page 13* Zama ya yi a wajen tare da zabga uban tagumi shi kansa ya san abu ne mai wuya Mama ta saka Sumayya musamman a yadda Sumayya ke son Aysha sannan take jin nauyin Mustapha ba za ta iya kiransa akan ya ɗauke ƴarsa ba. Ya daɗe a wajen a zaune yana saƙa da warwara har wani barci ya fara kokarin dauke shi sai ya tashi ya nufi ɗakinsa. Yau kam ko ta kan abincin da Sumayyar ta girka basu bi ba su Mama ne kaɗai suka zauna suka ci iya cikinsu kafin suka bar shi a nan. Washegari tun bayan da Abdallah ya tashi ya ma ƙasa haɗa ido da Sumayya don wasan ɓuya ya shiga yi mata wani bala'in kunyarta yake ji bai ma san ta ina zai fara tunkarar ta amman kuma ya san babu shakka sai Sumayya ta cika umarnin da Mama ta bayar don ko shi bai isa ya tsallake umarninta ba. ★Sumayya★ Ina tashi daga barci bayan na yi sallah da addu'oina na shiga wanka sai da na yi wanka kafin na sauka ƙasa don yin breakfast Mama na tarar a falo tana faman kallon tv cikin raina na ce"Ikon Allah ko dai a falo ta kwana yau?" Ganin babu mai bani amsa sai kawai na ce"Mama ina kwana ?" Ɗago kai ta yi ta lalle ni ta ce"To mai sunan mayu an tashi kenan" gyaɗa kai na yi alamar haka ne sai ta ce"Allah na tuba yo ke sumayya ai mantawa nake yi duk wannan abin da Abdallah yake na riga na san ba yin kansa ba ne shi da ya auri mayu ai sai abin da aka gani, kuma fa ni haihuwar ma na fara zargin idan ba ke ce kike sadaukar da yaran tun suna gudan jini kafin su zama tsoka ga aljanunku na mayu don maye kam abin tsoro ne" tashin hankali daga tashi na daga barci ko wanda na zo gidan don shi ban gani ba amman na fara breakfast da mugayen maganganu sai kuma ta ci gaba da cewa"Wannan karon dai don Allah idan kin samu ciki ki yi hakuri kar ki kai musu ki bar mana shi muna bukatarsa" tashi tsaye na ina jin hawayen bakin ciki su na son zubo min sai dai kuma alkawari na ɗauka akan ba zan taɓa barin Mama Sa'a ta ga hawayena ba har ta yi tunanin ta yi galaba ne a kaina sai dai kuma ba a san maci tuwo ba ba zan taɓa karaya har ranar da Mama Sa'a za ta daina yi min cin fuskar da take yi min a gidan nan. "Na shiga uku don na fahimci ke maya ce da sunan mayu shi ne ki ka tsura min ido ni ma za ki zuƙe min jinina ta hanyar maitar ido ko? To sumayya a hir din ki kurwata ba abin wasan mayu ba ce, to idan ba lalacewa irin ta duniya ba don tsabagen jaraba jinin surukarki za ki sha yanzu kuma" murya Mama Sa'a ce ta katse min tunanin da na yi nisa a cikinsa sai da ta kai aya a maganarta kafin na mike na nufi kitchen don ɗaura abincin safe yau idan da ba uwar mijina ba ce ta yi min kazafin maita da babu shakka kotu ce za ta raba mu da shi amman ita Mama ta zama kuturwar uwa zama da ita dole ne. Bayan na bar falon hawayen baƙin ciki suka kuma zubo min amman sai na share na shiga girkina. Ina cikin aikin gabana sai ga Umaimah ta shigo kitchen ɗin ta ce"Barka da Safiya Hajiya Sumayya" dan murmushin takaici na yi na ce"Barka da asuba Umaimah" sai ta fara yan dube-dube a kitchen ɗin na ce"Umaimah me kike nema ne haka?" Shiru ta yi min ba ta amsa min ba ni kuwa sai na ja bakina na yi shiru domin kar na jaza wa kaina da wannan safiyar. Sai da ta gama dube-duben amman ba ta samu abin da ta zo nema ba kamar an yi mata dole sai ta ce"Juya ba ki ga sugar ba?" Ni ɗin ma banza na yi mata kamar yadda ta yi min ɗazu ta kuma cewa "Juya magana nake yi miki fa" sai yanzu na juyo na kalle ta na ce"Umaimah a iya sani na ba sunana ba juya, sannan kuma idan kin kira ni da juya ke kuma a kira ki da me? Me lalataciyar mahaifa ko da wane suna ki ka ga ya dace a kira ki? Ba zan zauna ki saka ni gaba ki na zagina ba bayan kuma Ni ban ga yaron da aka nuna aka ce wannan Umaimah ce ta haife shi ba ni kuwa tunda dai har ban ga na ki ba gabadayanmu juya muke babu wani bambanci". Fice wa Umaimah ta yi daga kitchen ɗin tare da fashe wa da kuka. Mama ta fito da sauri har tana tuntuɓe ta ce"Subhanallah Umaimah me yake faruwa?" Cikin kuka Umaimah ta ce"Mama wallahi Sumayya ce ta shiga zagina da farar safiyar nan" cike da masifa Mama ta gyara ɗaurin dankwalinta ta ce"Me ta ce miki wannan matsiyaciyar kuma" tana mai ci gaba da kukanta ta ce"Mama yau Sumayya ta yi min gori akan haihuwa" carab Mama ta ce" ku ji gorin daura karfin zuciya to ita ɗin idan ba juya ba ce da wane suna za a kira ta, Allah na tuba tun da ta zo gidan nan ta taɓa yin ɓarin ciki ne ko kuma ta haifa ya mace ne? Babu ko ɗaya kenan kuwa ba ta isa ta ce miki juya ba don ita ta fi uwar juya ma ke ni fa ina ga tsabar son kuɗi irin nata siyar da mahaifarta ta yi ga shi yanzu Abdallah ya auro mana jaraba da kuɗinsa" Tun farkon maganganunta har ta kai karshe ina daga jikin kofa ina jinta ina zubar da hawaye baƙin ciƙin zagin da Mama take jero min hannu na saka na goge hawayena sai kuwa muka haɗa ido da Mama ta ce"To baƙar munafuka mai baƙar aniya kin gama zagin ta kuma kin zo ki na yi mana laɓe, to fito ki faɗa min akan wane dalili za ki zage ta ke uban wa ya zage ki? Na riga na san Sumayya ba ki gadon mutuncin ba kuma wallahi ina daidai da duk wani iskanci da ki ka tsiro da shi a gidan nan, kenan tunda dai ba ki sami damar zagina shi ne ki ka ɓiye a bayan Umaimah kike zagar min ita ko?" Da sauri na girgiza kaina sai kuma ta ja tsaki ta kama hannun Umaimah kamar wata karamar yarinya suka bar falon, kitchen na koma na ci gaba da aikin gabana. Bayan mun gama breakfast na shirya Aysha muka sauko ƙasa don zuwa office sai muka haɗu da Mama a falo ta ce"Mai babban suna yau za ki tafi gida ko?" Da sauri Aysha ta girgiza ta ce"A a ni a wajen Momy zan zauna" murmushi Mama ta yi ta ce"Hum yau kam sai kwana a gidan Momy Rumaisa" fashe wa Aysha ta yi da kuka ita kuwa Mama ta fara dariya na ja hannunta muka fito waje na ce"Princesse ki daina kuka wasa ne Mama take yi miki fa" maƙale kafaɗa ta yi ta ce"Ni dai a a" na ce"Da gaske fa ba ki ga ko kayanki ba mu ɗauko ba?" Sai ta gyaɗa min kai na ce"To share hawayenki babu inda za ki je ki na tare da Momynki kin ji?" Da sauri ta gyaɗa min kai tana murmushi kuma tana saka hannu tana goge hawayen da ya zubo mata. Shiru na yi ina bin ta da kallon tausayi gani a tsaka mai wuya ko ita Ayshar ba ta son zuwa gidansu bare kuma ni da ta zamar min sanyi idaniya sai da ta ce"Momy na bar kuka mu tafi office yau zan taya ki aiki" motar muka shiga har na fara driving sai ta ce"Momy Ni ma zan je makaranta" na ce"To ki bari sai kin kai shekara biyar" da yatsunta ta yi min nuni ta ce "shekara haka?" Na girgiza kai na yi mata nuni da alamar biyar da hannuna na ce"A a shekara haka" sai kuma ta yi shiru har muka karaso bakin office ɗin, ina kokarin shiga cikin Company wayata ta ɗauki ringin ɗaga wa na yi tare da sallama Mustapha ne na shiga gaishe shi na ce"Ina Hajiya Rumy ya dawo ne?" "A a ba ta dawo ba dama ta ce ne mu zo mu same ta a can" cike da mamaki na ce"Ban gane ba idan ka tafi aikinka fa?" "Wallahi na faɗa mata amman ta ce babu ruwanta tana bukatar ganin mu" "idan tana bukatar ganinku ta dawo gida mana" shiru ya yi na ce"Mustapha wallahi rayuwar aure ba za ta yi a haka ba kai ne namiji a gidan kai ya dace ka riƙa bada umarni ba wai a riƙa baka ba" "Sumayya ya zan yi?" Tsaki na yi yadda ba zai ji Ni ba na ce"To wai kai Mustapha ina dalilin wannan rayuwar da ka ɗaura kan ka a cikin ta? Rumy ma haihuwarta aka yi ba ita ta haifi kanta ba ka je ka sanar da Ummi abin da yake faruwa mana" shiru ya ɗan yi alamar yana nazari ya ce"Ina tsoron sanar da Ummi ne kuma a yi mata faɗa ba za ta ji daɗi ba" taɓe baki na yi na ce"Zauna a haka to, yaushe za ku tafi" "Yau jirginmu zai tashi zan zo na dauki Aysha" gyaɗa kai na yi na ce"Muna office sai ka zo, zan je gidan na haɗa mata kaya zuwa an jima ka ba mai gadi key din gidan da na ɗakinta kuma" da to ya amsa kafin muka yi sallama na kalle ta na ce"Kin yi missing ɗin daddy ko?" Ɗaga min kai ta yi alamar haka ne sai na ce"Daddy zai zo ya ɗauke ki ku shiga jirgi" ido ta zaro ta ce"Momy zan je" na yi murmushi na ce"To shi kenan sai daddy ya zo bari mu je mu yi aiki a office kafin daddy ya iso" wata irin ajiyar zuciya na sauke don ganin na samu hanyar da zan kai aysha wajen mahaifinta ba tare da raina ya ɓaci ba ko kuma na ji kunyar Mustapha. Ina ɗan rage aikin gabana na sauki Aysha muka nufi gidan Mustapha key na amsa a wajen mai gadin kafin na shiga gidan dakinta na shiga na fara haɗa mata kayanta da na ɗauko sai ta ce ba ta son wannan daƙyar na samu na gama duk na bi na gaji. Sai ga kiran Mustapha ya shigo wayata tambaya ta ya yi ina office na ce"A a gamu a gidanka na gama haɗa kayan princesse" "To shi kenan gani nan zuwa don yanzu zamu wuce" jan hannunta na yi muka fito bakin get na ce"Princesse yanzu daddy zai zo ku tafi" gyada kai ta yi daidai Mustapha ya yi parking motarsa a kofar gidan yana fitowa da gudu ta je ta rungume shi ta ce"Daddyna" shi ma rungume ta ya yi yana murmushi cike da tausayi nake kallon su. Karasowa ya yi wajen da nake tsaye muka kuma gaisawa kafin na ce"To Allah ya tsare hanya Ni zan koma office" murmushi ya yi ya ce"Na gode sosai Sumayya da wannan karamci da kike yi min a wannan rayuwar" "babu komai Mustapha yi wa kai ne kuma ma ai Aysha ni ma ƴata ce" kai ya gyada ya ce"Duk da haka Sumayya kin kai abin a jinjina miki" na ce"Princesse kin kawo min tsaraba ko?" Ciki da murna ta ce"E Momy zan kawo miki mana" rungume ta na yi na yi mata kiss a goshi na ce"Allah ya tsare hanya ki gaishe da Mama Rumy" sallama na yi musu kafin na shiga motata na bar kofar gidan. *Cmnts nd share* [19/12 à 22:38] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 🔥FREE PAGE🔥 NA KUSA GAMA FREE PAGE HAJIYA ME KIKE JIRA BA KI BIYA KUDIN KARATUNKI BA? Only 500 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange. *Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252* Gobe zan gama free page in sha Allah. Ku biya kuɗinku don a yi wannan tafiyar da ku. *Page 14* Sumayya na barin wajen Mustapha ya ja hannun Aysha suka shiga gida. Kayan da Sumy ta haɗa mata ya ɗauko da kuma na shi kayan kafin suka fito ya rufe gidan ya ba mai gadi keys ɗin. Napeep suka shiga don zuwa airport ya yi ta kiran number Abdallah don ya zo ya kai su airport ɗin amman bai same shi ba har ya hakura ya kira ɗan sahu. Sai da suka kisa isa aysha ta ce"Daddy ni ba zan je ba" rungume ta ya yi a jikinsa ya ce"Me ya sa ba za ki je ba princesse?" "Ni dai Daddy zan koma wajen Momy ne" da mamaki ya ce"wata Momyn?" Ta ce"Momyna mana" girgiza kai ya yi ya ce"Haba princesse ki yi hakuri kin ji idan muka dawo an kai ki wajen Momyn" sai yanzu ta saki ranta suka shiga jirgin don tarar da hajiya Rumaisa. ★Sumayya★ Ina baro wajen su Mustapha na ji wata kwalla ta zubo min ta rashin Aysha da zan yi a kusa da ni kwana biyu, sai dai kuma ta wani bangaren ina jin wani farin ciki don na san zan tsira daga masifar Mama kwana biyu. Office na nufa kai tsaye bayan na gama aikin da yake gabana na nufi gida ina shiga gida ila haɗu da Umaimah ban ko kalle ta bare kuma ta saka ran zan amsa mata na nufi hanyar bangare na sai ta ce"Juya sannu da zuwa" murmushi na yi na ce"Na'am yar uwa juya sannu da gida da zaman kashe wando" da mamaki ta ce"Sumayya ni ce mai zaman kashe wando kuma? Gyada mata kai na yi na ce"To ai babu bambanci ke da su" shiru ta yi ba ta ce komai ba ganin haka sai na ja ƙafafuna zan bar wajen. "Sumayya ina son za mu yi magana" gyaɗa kai na yi na ce"To ina sauraren ki" kamar ba za ta ce komai ba ta ce"Ki je ki cire kayan jikinki zan zo sai mu yi maganar" "To shi kenan sai kin zo" ina gama magana na fice zuwa ɗakina. Wanka na yi kafin na yi sallar la'asar da ban samu na yi ba ina ta tunani a cikin raina wata magana ce haka Umaimah ke son mu yi da ita. Rumaissa tun barinta gidanta hankalinta kwance yake babu wani taron kasuwanci kawai dai ta yanke shawarar barin gidanta ne don ta sha iska a rayuwarta ta duniya mutum ce ita mai don tafiye-tafiye sai dai kuma shi Mustapha babu ruwan shi da irin wannan tafiye-tafiye shi ya sa a koyaushe ta shirya za ta bar gidan ba tare da sanin kowa ba shi kuwa Mustapha ba ya iya yi mata magana saboda ba ya son bacin ranta sanadiyar son da yake yi mata kwata-kwata ba ya iya taka mata burki. Ina gama wankan Abdallah ya shigo ɗakin ya yi murmushi ya rungume ni ya ce"Babe ya aiki?" "Alhamdulilah Qalbi ya ka yini?" "Lafiya qlau ina princesse Aysha ?" Ido na zaro na ce"Ban fahimta ba, ba cewa kuka yi na kaita gidan ubanta ba? To na kai ta"dafe goshinsa ya yi ya ce"Kai kar ki ce min haka ki ka kaiwa Mustapha ita? To me ki ka ce mishi?" Zare jikina na yi daga riƙon da ya yi min na ce"Abin da ku ka ce na yi shi na yi" zama ya yi a bakin gado ya ce"ya Salam wane irin rashin hankali ki ka aika haka Babe?" Ɗage kafaɗa ta ɗaya na yi na ce"ko ma dai wane irin rashin hankali ne abin da ku ka ce na yi shi na yi" daga nan na nufi wajen dressing mirror na shiga shafa mai sai ya ce"Babe me ki ka ce da Mustapha?" Ya yi maganar cikin ɓacin rai na ce"Ka kira shi ka tambaye shi tunda dai ka na da numbersa" haushi ne ya mamaye Misira zuciya da kuma fargaba kar a ce Sumayya ta sanar da Mustapha abin da suka ce shi da Mama akan zaman Aysha a gidan. Wayarsa ya ɗauka ya kira number Mustapha sai dai kuma ba ta shiga sai kuwa ya ƙara shiga tashin hankali marar misali ya ce"Babe kin ga abin da ki ka ka mana ko?"cikin halin ko in kula na ce"Babu abin da na ja muku illa abin da ku ka ce na yi biyayya kaɗai na yi muku kamar yadda ku ka bukata" ina gama magana ya nufi hanyar fita ya ce"Wallahi Babe sai na ɗauki mataki akan wannan abin da ki ka yi yau" yana kaiwa nan ya buɗe kofar ya fice tare da buga ta da karfi. Ni ma ci gaba na yi da abin da yake gabana Ina gama sa kaya na zauna a bakin gado na ɗauki wayata na kira Ummi bugu biyu ta ɗaga na ce"Assalama aleikum ya Ummi" amsa min ta yi na ce"Ummi barka da gida fatan ki na lafiya?" Ummi'' da ke zaune a bakin gadonta ta ce"Ina lafiya Sumayya ya gida?" Da murna na ce"Lafiya qlau Ummi" "Lafiya me yake faruwa?" Cike da mamaki na ce"Ummi me ya faru?" "Babu abin da ya faru ina tambayar ki ne ko akwai abin da kike bukata" girgiza kai na yi kamar ina gabanta na ce"A a Ummi'' babu komai" "To sai an jima ki gaida mutanen gidan" kafin na yi magana ta katse wayar bin wayar na yi da kallo idanuna suna ciko wa da kwalla wannan wata irin rayuwa ce Ni Sumayya da wata Muryar zan yi magana na sanar da mahaifiyata ba ni da laifi ni ɗin ban aika ta wani laifi ba, sai dai kuma wannan gaskiyar ta yi min nisa faɗarta kamar ciro wuƙar yanka naman jikina ce. Na daɗe a zaune a wajen cike da zulumin da kuma mafarkin ranar da mahaifiyata za ta dauke ni a mutum ta bar kallona da da idon aibu Tashi na yi na sauka ƙasa sai yanzu muka haɗu da Mama na ce"Mama ina yini?" "Lafiya qlau mai sunan mayu ya aiki?" Mamaki ne ya kama ni na ce"Lafiya qlau Mama" murmushi ta yi ta ce"Yauwa mai sunan Mayu dama ina son ganin ki akwai wata yar bukata gare ni" ɗago kaina na yi na kalle ta kuma na mayar da su ƙasa na ci gaba da kallon yatsun kafata sai ta ci gaba da cewa"An yi min haihuwa ne kuma ba ni da abin da zan bayar sannan kuma na tambayi Abdallah ya ce min sai dai na jira karshen wata kuma Ni gaskiya ba zan iya ba" murmushin takaici don da ma na san wannan magana da wannan doguwar gaisuwar ba a banza ba Mama take yi min ita daƙyar na fi ƙarfin kwanyata na fito daga duniyar tunani na ce"Mama me kike bukata?" Washe haƙora ta yi ta ce"Yau ina son turmin atanfa guda biyu da kuma yan kuɗin da zan hau napep da kuma wanda zan bayar na biki" shiru na yi ina nazarin mene ne Mama take son maida ni a gidan nan amman sai ta ce"Ko ba zan samu ba?" Girgiza kai na yi na ce"A a Mama za ki samu" "Yaushe za ki ba ni?" Ikon Allah kenan har lokacin da zan bayar ma sai na faɗa sai na ce"Idan sallah ya kai mu gobe ina dawowa daga office zan kawo miki" sai yanzu ta kuma sakin fuskarta ta ce"To mai sunan mayu Allah ya kai mu gobe lafiya" da amine na amsa kafin na wuce zuwa kitchen. Sai ga Umaimah ta shigo kitcten ɗin ta ce"Na so zuwa shashenku sai na ga Abdallah ya shigo sai na hakura" ban juyo na kalle ta ba sai na ce"Ai da kin zo ma babu damuwa" "A a gara dai da na yi hakuri sai kin sauko yanzu ai zan iya sanar da ke" gyaɗa kai na yi 'a ce"Eh za ki iya sanar da ni" dan sosa kai ta fara alamar tana jin nauyin maganar amman kuma ya zama dole sai ta furta maganar sai ta ce"Ba ni da lafiya ne kuma kin san halin da muke ciki daga Ni har Hisham, to idan ba za ki damu ba ina son Aron wasu ƴan kudi domin zuwa asibiti" da kallo na bita sai yanzu na lura da sak irin yadda Mama ta yi tambayar nata kudin ita ma ta wannan hanyar ta biyo sai na ce"Allah ya ba ki lafiya idan Allah ya kai mu gobe ki shirya sai ki je asibitin zan kawo Miki kudin idan na koma daki" godiya ta min kafin ta bar kitchen ɗin Ni kuma na bi ta da idanu. *Cmnts nd share* [20/12 à 21:24] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 🔥 KARSHEN FREE PAGE🔥 Only 300 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay Yan Niger kuma 300f ta wannan number +22780416252 *Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252* *Page 15* Bayan na gama girki na nufi ɗakina ina ta tunanin wannan bakon lamari da su Mama suka ɓulo da shi su na shirin maida ni saniyar tatsa sun ajiye banki a gida. Jakata na buɗe na ciro da yan jika goma guda biyu daidai zan fito daga ɗakin muka haɗu da Abdallah ya ce"Babe ina za ko je da kudi a hannu haka" na yi niyyar tafiya ba tare da na ce mishi komai ba ya kuma cewa"Babe magana nake yi miki' kamar ba na so na ce"Zan kai wa Umaimah kuɗi ne" "kuɗin me za ki kai mata?" Murmushin takaici na yi na ce"Ba ta da lafiya ne shi ya sa zan ba ta kudin zuwa asibiti" wani irin kallo ya yi min ya ce"Ke ce Hisham ba?" "Ka fi ni sanin ba ni ba ce Hisham amman ko ba komai ka san sarai Hisham ba shi da aikin yi bare kuma ya bada kuɗin da za ta je asibiti" gyaɗa kai ya yi kafin ya matsa min daga hanya ya ce"Je ki kai mata" fice wa na yi daga dakin ina jan ɗan tsakin na sauka ƙasa na tarar da Umaimah na miƙa mata na ce"Ga wannan Allah ya sa dai sun isa" wani kallo ta watsa min ta ce"Haba Sumayya ya za a yi 20k su ishe ni zuwa asibiti" da kallon mamaki nake bin ta galala nake kallon ta wannan shi ne a baka ɗauki ka tambaya wa ya gutsiri nan na ce"Iya abin da gare ni ne yanzu idan kin ga sun ishe ki to idan ba za su ishe ki sai ki bi wani alazin ki nemi ƙari ke ya dama" ina gama faɗar haka na juya zan tafi sai ga Mama da kallo take bin hannun Umaimah ta ce"Sumayya ni ina abin da na tambaye ki?" Wani haushin ta ne ya kama ni na ce"Sai gobe idan Allah ya kai mu Mama, sai na tafi office zan biya na siyo miki atanfar" gyada kai ta yi ta ce"To shi kenan Allah ya kai mu goben amman dan Allah kar a siyo atanfar ƙarama a siyo min manya" wani haushi ya kama ni na ce"To Mama Allah ya kai mu goben zan kawo manyan" Ɓangarena na koma na tarar Abdallah ba ya falon sai na shiga ɗakinsa, a zaune na tarar da shi na ce"Qalbi ka na bukatar wani abu?" Girgiza min kai ya yi alamar ba ya bukatar komai, sai na buɗe drower ɗinsa na fara haɗa kayan wanki sai ya ce"Kun yi waya da Mustapha?" Na girgiza kai na ce"A a ba mu yi ba" "Rumaissa fa?" Ya kuma watso min tambayar "Ita ma dai Rumy" ɓata fuska ya yi cike da damuwa ya ce"Bari na je gidan na ji ko lafiya" ya faɗa tare da ɗaukar key ɗin motarsa, sai da ya kai bakin kofa zai buɗe na ce"Ba sa ƙasar sun yi tafiya" turus ya ja birki ya tsaya yana watso min shanyayun idanunsa ya ce"Tsakanin ki da Allah Babe sai yanzu za ki faɗa min Mustapha ya yi tafiya?" "To ai ba ka tambaya ni ba, yanzu ma bakina na ne ya kufce na faɗa maka" a hankali ya tako zuwa bakin drower ya tsare ni da manyan idanunsa ya ce"Babe yaushe raini ya shiga tsakanin mu da ke?" Girgiza kai na yi cike da fargaba na ce" Ba fa raini ba ne Qalbi" cike da tsawa ya ce"To mene ne?" Shiru na yi ina kallon yatsun ƙafata ya ce"Na ga yanzu har da wasu maganganu kike faɗa min" "Qalbi ka yi hakuri ba zan sake ba in sha Allah" gyaɗa kai ya yi ya ce"Shi kenan kar ki sake" daga nan ya fita zuwa falo ni kuma na ci gaba da aikin da yake gabana. Washegari tun safe Umaimah ta shirya ta tafi asibiti gwajin farko likita ya shaida mata tana ɗauke da juna biyu tsawon wata biyu murna a wajen Umaimah ba a magana ko sauran gwaje-gwajen ma ba a gama ba ta fito ta tare mai napep sai gida. Tana shiga gida ta fara kwala kiran sunan Mama da gudu Mama ta fito daga ɗaki ta ce"Umaimah lafiya me yake faruwa kuma?" Da gudu ta je ta rungume Mama ta fara ihun murna, Mama kuwa baki ta saki tana kallon Umaimah tana jiran ta faɗa mata abin farin cikin da ya samu haka. "Mama, mun kusa samun ƙaruwa, ina da ciki" wata irin guɗa ta murna Mama ta rangaɗa wanda ya yi ya saka Jiddah da Rumana fitowa daga dakinsu suka yo falon Mama ta ce"Kai ma sha Allah alhamdulilah kai Allah shi ne abin godiya abin farin ciki ya same mu" Rumana ce ta ce"Me yake faruwa wa ya samu kujerar Makka?" Mama ce har tana haɗa kalmomi wajen faɗi "Ba fa kujerar Makka ba ce aka samu Umaimah ce ke ɗauke da juna biyu" ihun murna Rumana ta saka ta ce"Anty Umaimah congratulations na ta ya ki murna wannan abin farin cikin da ya same mu" ita ma jiddah ta ce"Allah ya raba lafiya Anty Umaimah Allah ya kai mu babbar rana mu sha shagali" zama suka yi suka shiga hira. ★Sumayya★ Duk da wayar da muka yi da Mama bai ishe ni ba sai na je super market na yi mata siyaya kafin na nemi izini a wajen Abdallah akan zan je gaishe da Mama bai ko yi musu ba ya amince min tare da cewa idan na je na gaishe da Mama. Kashe kiran na yi bayan mun yi sallama na ɗauki motata na nufi gidan Mama, isa ta gidan na tarar da ita a zaune mai aikinta na matsa mata ƙafa da murmushi akan fuskata na ce"Kande ba ki je hutu ba?" "E anty Sumayya ban je ba sai wani watan an tashi lafiya?" Ta faɗa tana kokarin miƙewa don kawo min drinks na ce"Lafiya qlau ya aikin?" Tana tafiya ta amsa min da lafiya qlau sai na juya na kalli Ummi na tsunguna na ce "Ummi barka da safiya" "Barka Sumayya babu aiki ne yau?" Zama na yi akan kujera na ce"A a Ummi akwai aiki na ce dai bari na zo na gaishe ki" "To kin zo, sai ki faɗa min abin da ya kawo ki" girgiza kaina na yi na ce"Babu komai Ummi kawai ina son ganin lafiyarki ne" wani kallo ta watso min ta ce"Sumayya ba ki damu da lafiyata ba, ba ki damu da farin cikina ba hakika da kin samu da ni ba za ki buɗewa wani layin banza ƙafa a titi ya ɓata miki rayuwa bayan kuma ba mijinki ba ne. Farin ciki ya yaye daga cikin zuciyata tun ranar da na yi ido biyu da wannan farin tissu ɗin babu ɗigon jinin budurcinki a jikinsa" idanuna sun fara zubar da hawaye tunda daga farkon maganarta cikin kuka na ce"Ummi ba abin da kike tunani ba ina son ki saurare ni don jin gaskiyar lamarin" hannu ta ɗaga min tana girgiza kai ta ce"Sumayya ki yi min shiru da bakinki me za ki faɗa min? Lokacin da ki ka yi yawon ta zubar ɗinki a kasar waje ko kuma ranar da ki ka rasa budurcinki? A ciki wane ne za ki sanar da ni tashi ki kwashe tsimokaran ƙafafunki ki bar min gida" Kamar yadda ta yi min umarni haka na tashi na bar falon ledar da na kawo mata ma sai mai gadi na ba ya shigo da ita. Driving nake hawaye yana rufe min idanu ba na ma ganin gabana Allah ne ya kawo gida lafiya sai da na yi parking ba saka wani tissu na goge hawayen da ya bata min fuska duk kwalin da na saka ya zubo min, na shiga gyara fuskata sai yanzu na tuna da ban siyo atanfar da Mama Sa'a ta ce na siyo ba. Wayata na ɗauka na kira number Rumaissa wadda ba ta Niger ba tana ɗagawa ta yi sallama ta ce"Hajiya Sumayya uwar princesse dan princesse ta yi missing ɗinki shi ne ki ka kira ki ji to ga ta nan cikin koshin lafiya" dan murmushin takaici na yi na ce"Ba ma ɗan ita na kira ba ina son ki saka daga shago a aiko min da atanfa turmi biyu" "Sai ki ce magana ake ta ƴaƴan banki, wace iri kike so?" "Ni kam ban sani ba Mama Sa'a ce za ta yi biki da su" "To shi kenan yanzu za a kawo sai dai ban ji kash ba" murmushi na yi ina tuna irin amanar da ke tsakanin Rumy da kuɗi na ce"To nawa ne kuɗin yanzu zan saka su" sallama muka yi kafin na shiga cikin gida zuciyata sai zafi take yi min Ina shiga cikin falon na yi kicibis da maganganu Mama Sa'a a daidai lokacin da muka haɗa ido da ita tana cewa..... *Abin ya zo in ji mai tsoron wanka, Hajiyata ki na son sanin abin da ke luluɓe a cikin wannan labarin ne? To hanzarta biyan kudin karatunki* Don jin shin laifi da Ummi take tuhumar Sumayya da shi mene ne dalili, shin Sumayya nada hujja ko a a? A cikin Sumayya da Abdallah wane ne mai matsalar haihuwa? Ya karshen Mama Sa'a zai kasance Na san za ku so sanin mene ne asalin hujjar kafuwar labarin akan kalmar *DA WATA KUSAN...* MU HAƊU A PAID PAGES +22780416252