[9/28, 3:25 PM] Khadija Candy🥰: 16 Tun ina kuka muryata na fita har takai baka iya jin kukan nawa hawayen ma suka daina zuba sai ciwon idon suke min, bana iya ganin komai domin bana iya daga idon na kalli kowa, iyakar abun da zan iya shaida shi ne hankali ne be bace ba, domin ina jin lokacin da Mama da Yaya Maryam suka rika ni suka fito da ni mutane sai Allah ya ba da hakuri wasu na addu'ar Allah ya jikansa, ban tabbatar da mota muka shiga ba har sai da na ji muryar Mijin Yaya Maryam da kuma karar rufe motar da ta yi, ta zagayo ta dayan gafen ta shiga ta kwantar da ni jikinta. “Kanwata ki yi hakuri kin ji? Allah baya barin wani dan wani, da yana barin wata rayuwa saboda wata, da ya bar uwar da mutuwa ta dauke ta bar jariri, ita mutuwa tana kan kowa, ke kanki idan lokacin tafiyarki yayi babu wanda ya isa ya tare, ke da kika rasa uba? Ai ke kin san zafin mutuwa Zahra, mun rasa uban tun ba mu mu mallaki hankalin kanmu ba balle yanzu da kika yi aure? Inda sabo ai ya ci ace kin saba da mutuwa ko? Ki yi hakuri ki dauki halin Annabawa, ki yi ta maimaita Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, yanzu addu'a da neman yafiya Deen yake nema ba kukanki ba, ki yi imani da Allah Zahra ki bar masa komai, Manzo Allah Sallalahu Alaihi Wassalam yace baya tare da mu wanda idan masifa ta same shi yake marin fuskarsa, yake kururuwa irin ta lokacin jahiliya wato mutun ya rika fadin ya bani ya lalace ya shiga uku da wasu maganganu da basa nuna cikar imanin bawa ga Ubangijinsa, yake keta tufarsa ko ya aske gashin kansa, sai kuma Annabi yace ka yi bushara ga masu hakuri wadanda idan masifa ta same su sai su ce mu a gurin Allah muka fito kuma a gurinsa za a mayar da mu, wato Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un hakika suna da yabo mai girma daga Ubangijinsu da kuma kyakkyawan sakamako” Na daga mata kai kamar zan iya, cikin iyawar Allah ya yardarsa kamin mu isa gida bakina ya bude na yi ta nanata Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Yaya Maryam na rike da ni har muka isa bakin kofar shiga gidana, a lokacin ne na ji wani abu ya taso ya tunkari zuciyata ya tokare kahon zuciyata, a yau zan shiga gidan da Deen ba zai sake shiga ba har abada, zan rayu ba tare da mijina ba. Wasu hawayen suka zubo min, haka muka shiga cikin gidan da har mutane sun fara taruwa a ciki, domin an sanar da rasuwarsa tun muna asibitin kuma abokinsa ya karbi makullin gidan ya bude saboda su suka zo da gawarsa da kuma mahaifinsa. Duk makota na da suka shigo cikin gidan suna ganina sai hawaye wadanda zuciyarsu bata da karfi kuma suka saka kuka mai sauti, abun da ban sani ba, ashe an yi masa wanka anyi masa sutura, ina dosar falona sai mutane suka rika cewa kar a bar ni na shiga saboda ka yi kuka. “Ba zan yi kuka ba ku bari na ga fuskarsa dan Allah” Babu wanda ya bada goyon bayan a bar ni na ga gawar, ciki kuwa har da yan'uwansa da kuma nawa yan'uwa ciki har da Mama da ta iso yanzu bayan shigowa ta, domin a asibitin muka baro ta tare da Hajiya da aka sakawa drip. Hankalinta zai tashi be kamata a barta ta gani ba, zata yi kuka, kowa da dai da abun da yake fada. “Ba zan yi komai ba, na san ni ai ba kowa ba ce tun da ban tare ransa na hana shi fita ba, na karbi wannan kaddarar da hannu biyu kuma na shirya rumgumarta kuma da yardar Allah sai na cinye ta, dan Allah ku bar ni na masa gani na karshe wannan ce kadai dama ta” Na fada cike da gwarin guiwa, wata kila sun yardar da ni, ko kuma kalamai na ne suka karya musu zuciya, sai aka amince min na shiga na ga mijina. Daga bakin kofar Yaya Maryam ta sake ni na karasa cikin falon da kafafuwa da bake jin sun yi min nauyi har jini ya fara saukowa domin sun dan kumbura. A cikin karaga na hango shi kwance an masa sutura da farin lailai wanda shi ake yi ma kowa sutura talaka da mai kudi, bafada da Sarki, yana kwance a mike gurin daya babu motsi, a yau jikinsa na zama ba na shi ba saboda rai ya bar jikin, a yau sai dai a juya shi ba dai ya motsa ba, hakika na tabbatar da rayuwa ba komai ba, a jiya yana raye a yau kuma gashi a kwance. Na karasa kusa da shi na zauna na kai hannuna cike da imani na yaye likkafanin iya fuskarsa, sai na yi arbar da kyakkyawar surarsa fuskarta na ta haske kamar na kira shi ya amsa min. “Ya masanin yau da gobe da jibi da anjima, ya buwayi gagara misali, ya mai rayawa mai kashewa, ya Ubangijina wanda kai kadai nake yi ma bauta, Allah ka sani na yi zama na amana da soyayya da mijina, ni da shi duka bayinka ne Allah masu yawan tsaba maka, Allah a yau ina son ka shaida na yafewa mijina duk abun da yayi min wanda na sani da wanda ban sani ba, da wanda ya sani da wanda be sani ba, ya Allah ina roka masa gafararka rahmarka da jinkanka, domin kai mai yawan yafiya ne mai yawan gafara, Allah a yau mijina ba shi da gata sai naka, Allah ka isar masa ka dauke masa tsoro da azabar kabari da na alkiyama, Allah ka sani Deen ya kyautata irin kyautatawar da miji na gari zai yi ma matarsa ya samu aljannarka, ya Allah ka bashi, yadda ya tsare mutunci ya tsare ci da sha na, Allah ka tsare shi daga azabar wutarka, Allah ka sani yayi min muhalli yayi min sutura Allah ka yi masa muhalin da sutura a aljanna, Allah ka yafe masa zubansa wanda ya aikata maka akan kuskure ko ganganci, wanda ke tsakaninsa da bayinka ka daukar masa, Allah ka lullube shi da rahmarka” Na shafa addu'ar da na yi tare da hawayen da suka sauko min, sannan na yunkura na daga na sumbanci goshinsa. “Ina son ka mijina, amman Allah ya fi ni sonka, fatar da ka yi ta haduwa da ni a aljanna Allah ya tabbatar mana sai wata rana Deen” Na maida likkafanin ina masa bakwana na har abada, duk yadda kuka ya so ya ci karfina sai na danne domin kukan ba zai dawo da rayuwarsa ba, haka ma kuka ba zai canja abun da Allah yayi niya ba, kuma idan har ban yi hakuri na ci jarabawar nan ba, toh zan yi hakuri don dole ne a inda hakurin ba zai min rana ba. Na mike tsaye ina ta kallon gawarsa sannan na juyo na fito cikin karfin hali da ni kaina ban saka ran zan iya ba, kusa da Mama na je na zauna mutane sai kallona suke hawayen kuma sai suka tsaya min cak kamar an yi ruwa an dauke, gidan yayi tsit kamar babu kowa a ciki. Wata a cikin makotana ta miko min carbi na karba na yi ta nanata Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un. Har maza suka shigo suka shiga har cikin falona suka dauko gawar Deen suka fito da ita, ina ji ina gani aka fice da gawarsa fita ta har abada, lumshe ido na yi na kwanta jikin Mama tana ta kuka ita da Yaya Maryam da Bahijja da har rike ta ake ana rufe mata baki, ni kuwa Allah ya dauke min kuka sam bana jinsa a kusa da idona. Kudin da suke hannumu wadanda muka fara tarawa na aikinsa kamin na samu wata mafita su aka karba aka yi ta biya masa bashi da ya fada, wasu kuma sai su ce sun yafe, wadanda suke nesa kuma Baba ya dauke nauyin bashin a kansa.   A wajen gidanmu aka yi masa sallah, sannan aka dauki gawarsa zuwa gidansa na gaskiya, kamin a isa da shi gafara kawai nake nema masa har aka rufe shi aka dawo, masu amsar gaisuwa suka zauna a waje wato maza kenan, mata kuma na ciki gida tare da ni, duk wanda ya shigo ya kalleni sai ya zubar da hawaye, ba dan ina kuka ba sai dan kukan da na sha dazun da jiya ya saka fuskata ta canja kamarba tawa ba, kowa ni yake tausayawa domin duk wanda ya san mun yi aure da Deen ya san irin soyayyar da muke nunawa juna, musamman yan'uwa da kuma makotanmu domin baya jin nunawa duniya ni kuma baya shayin nuna soyayyata a ko'ina.   Sai dare aka ta ho da Hajiya a lokacin Mama na ta son tirsasani na sha furar da aka kawo daga makota, domin sun mana kara sun kawo abinci kala kala da botoci da tabarmi, suna ta tambayar lafiyata hakan kadai ya isa ya nuna maka yadda zama da makota yake da dadi. A nan ta bude wani sabon babin kuka mutane na ta bata hakuri, domin ita ma kanta abar tausayi ce kasancewar daga Deen sai Bahijja ta haifa, saboda wabi take (Mutuwa yayanta suke idan ta haifa) ni kam ina rike da carbina ina da ambaton Allah, can bayan gama sallah Isha'i mutane na ta shigowa wasu wadanda ba su samu shigowa ba da rana ba,  wasu kuma makotanmu ne da suka shigowa su sake duba ni. A cikin mutanen da suka shigowa gaisuwa har da Jamila uwar dan da zan haifa ko ya, yanayin surarta da kamshin turarenta irin na manya masu kudi ya banbanta ta da sauran bakina masu rufi asirina wasu kuma ma talakawa ne talaf, fuskarta kuma ta fita kar a idona duk sa kasancewar babu wuta sai fitilu da aka kunna, kuma ai ba zan taba manta fuskar matar da ya siye abun da zan haifa ba, idan m nace na manta na yi karya, ta kusa ta ratsa mutane ta zauna kusa da ni da katon cikinta kamar nawa. Gaisawa muka fara yi sannan ta yi min rasuwar rashin Deen kana ta dora da wa'azi da nasiha. “Ki bar wa Allah komai Inshallah Allah zai miki sakamako mai kyaut na abin da kika yi, dan Allah karki saka damuwa a cikin ranki abun ya zo ya taba lafiyar da abun da ke cikinki, kin san ba a son mace mai ciki da yawan tunani ko kuka saboda zai iya shafar lafiyar yaro” Na kalleta da kyau sai na ga kamar magana take min saboda zafin yayi min yawa. “Ya akai yi kika san gidan nan?” “Dr Hamid ya sani, shi ya kawo ni suna tare da Barrister a waje za su miki gaisuwa” Na yunkura na tashi tsaye domin na kagara ta bar gidan, haka nan nake jin kamar na tsane ta a yau. Sai ita ma ta mike tsaye tana tambayar mahaifiyata  ni ban amsa ta ba sai Yaya Maryam dake rike da Husna. “Ga ta can, Mama za a miki gaisuwa” Ta karasa tana nuna mata Mama tare da kiran Mama, sai Mama ta taso ta karaso kusa da mu Jamila ta yi mata gaisuwa ta ciro kudin da zai kai 20k ta mika mata Mama ta karba tana godiya tare da addu'a, Yaya Maryam kuma ta bi Jamila da kallo na mamaki, kamin ta juyo kaina. “Ina zaki je Zahra?” “Waje Kanena ne zai mata gaisuwa” Jamila ta amsa da kanta, sai Yaya Maryam ta sauke Husna daga jikinta ta mike tsaye. “Muje na rakaki” Ban musa mata ba, sai dai na lura kamar Jamila bata so haka ba, mu muka fara fita sannan ta fito mun dan yi nisa da gidan kadan zuwa inda muke hango mota a fake Jamila tana bayanmu domin ta fini nauyin jiki, Dr Hamid na hango ni sai ya bude motar ya fito tare da Barrister suka rufe motar suka jingina suna jiran karasowarmu, Yaya Maryam na ta haska min hanya har muka isa, sannan Jamila ta iso daga baya Yaya Maryam na ganin Dr Hamid ta gane shi. “Wannan ba likitan da ya duba Deen ba ne” “Ni ne, ya hakuri?” Ya amsa mata da kansa. “Alhamdulillah” “Allah ya jikansa yayi masa Rahma, Zahra ya hakuri” A lokacin ne hawaye ya cika idona tunawa da yadda na salwantar da rai saboda wani rai da ban samu abun da nake so ba. “Alhamdulillah” Barrister ma ya dora min da tashi gaisuwar na amsa hawaye na sauko min. “Na san zaki yi mamakin yadda na san gidanki ko? Akwai addireshin a file din mijinki, kuma dazun tare da mu aka masa sallah dazun har aka kai shi Allah dai ya masa Rahma” “Ameen Allaah ya bada lada” Yaya Maryam ta fada ni kan ban da hawaye babu abun da bake. “Ki yi hakuri duk mai rai mamaci ne, kuma Inshallah zaki samu kyakkyawan sakamako a gurin Allah” “Na gode” Na furta daker sannan na juyo da zimmar tafiya sai Jamila ta kira ni na juyo. “Please take care of yourself” Kallonta kawai nake na kasa ce mata komai, har sai da Yaya Maryam ta dafa ni. “Zahra” Sannan na juyo muka nufo gida ni da ita. “Ya kyauta da wasu likitocin suna da tausayi, wannan matarsa ce?” Na girgiza mata kai kawai sai kuma na yi saurin daga mata kai, idan na ce ba matarsa ba ce to wacece ita? Kamar na san zata tambaya sai na ce. “Mun taba haduwa da ita asibitin ina tunanin yar'uwarsa ce” “Allah sarki ita ma ciki ne da ita, Allah ya sauke ku lafiya” Wani sabon kuka na ji ya zo saboda na san idan na haihu baby ba nawa ba ne, amman ai aikin da aka yi ba a samu rayuwarsa ba? Hakan na nufin jarjejeniyar ta fasu kenan? Na share hawayena da sauri ina jin kamar na juya na kira Dr na yi magana da shi, wata kila ma zuwan da yayi magana yake son yi da ni, haka dai muka shigo cikin gidan zuciyata da tunani kala kala. ABIEY POV. A hankali yake saukowa downstairs din yana gyara hannun rigarsa, Ammy dake zaune a kasaitacciyar kujera ta dago tana dubansa. “Sai ina?” Ya dan yi shiru kamar mai tunani. “Wai zan je na yi ma Mai Martaba bakwana gobe zan wuce” “Ka kyauta, ka gaishe shi amman ga breakfast din nan yana jiranka” Ammy ta fada tana murmushi. “Maybe zan karya a gurin Anty but yanzu bana jin zan iya cin komai” “Why” “Just” Ya daga kafadunsa shi kansa ba zai iya fadar abun da yake damunsa ba, kawai dai yana jin jikinsa ba dadi haka ma ransa a bace yake for no reason, sai ta nuna masa guri kusa da ita “Zauna Aliyu” Ba musu ya zauna ana sauke ajiyar zuciya a sirrance. “Me yake damunka?” “Wallahi Ammy ban sani ba, kawai dai na farka na ji ni wani iri, and ina son na tambaya ke kika ba Zahra kudin aikin ne?” “Aa ba mun yi da kai cewar zaka saka a bata ba?” “Yeah Sauban ya fada min ko da yaje biyan kudin ya tararda wani ya biya, na kira Dr da Anty sun ce duk ba su suka biya ba” “Toh ni ma ban biya ba, maybe Allah ya kawo mata wata mafitar ne” “Maybe” Ya fada yana mikewa tsaye. “Ka gaishe shi” Ammy ta sake fada sai ya juyo yana kallonta da murmushin da be san inda ya samo shi ba. “Yau kuma ke da kanki” “Ranar na masa rashin kirki shiyasa” Murmushi yayi ya juya ya nufi kofar fita, da dan kuzarinsa ya sauko entrance din ya nufi motarsa tun kamin ya karasa ya danna key hannunsa sannan ya bude ya shiga motarsa yayi reverse. Cikin natsuwa yake driving har ya fice daga gidan, be yi nisa da unguwar ba PA ya kira shi sai ya bude Bluetooth din dake cikin motarsa yayi connecting. “Ranka ya dade komai ya zama ready karfe biyar za su tashi gobe” “Okay” Ya amsa sannan ya yanke wayar yana jin kamar ya fasa tafiyar, yana faka motarsa harabar masarautar Zahra ta fado masa a rai, ya kan irin wannan yanayin da kuma tunaninta a duk lokacin da take cikin wata matsala ko damuwa, wayarsa ya dauko kamar ya kira Sauban sai kuma wata zuciyar ta hana shi, a ganinsa hakan be dace ba why zai yi ta neman shiga rayuwarta? Bayan tana matar wani? Ya bude motar ya fito da kafa ya taka har bangaren Anty, yana kokarin ya kai hannunsa ya bude kofar falon Aisha ta bude ta fito tare da kawarta, cike da murna ta tarbe shi. “Oyoyo Big bro daman ina ta nemanka, yau ma zan buga maka waya” “Akwai wata matsala ne?” “Eh Babba” Ya kalli kawarta dake gaishe shi ya amsa sannan ya sake kallonta. “Je ki dawo sai mu yi magana” “Okay Ya shiyasa na ke sonka” Ta fada cikin murna da jindadi, ya sakar mata murmushi kadan ya shiga cikin falon, kai tsaye ya nufi upstairs kasancewar babu kowa a falon sai Ac da plasma, Bedroom din Anty ya fara knocked sai da ta yi masa izinin shiga sannan ya tura ya shiga, idonta na yin arba da shi sai fuskarta ta cika da kyakkyawan murmushi. “Maa Shaa Allah kamar ka san ina nemanka” Ya zauna saman kujera yana kallon yadda ta canja tsarin furniture din. “Aisha tace min akwai matsala? Miya faru?” “Matsala ba yar karama ba, amman dai yanzu ka fara zuwa ka gaisa da Mai Martaba sai ka dawo mu yi magana” “Daman bankwana na zo masa, gobe zan wuce Abuja daga can zan hau jirgin England” “Hutu zaka je?” “No akwai wasan da zamu buga ne, kuma daman ina bukatar barin kasar nan” “Amman dai ba zaka dade ba ko?” “Ban sani ba for now, wasan dai zai dauke mu for 3 days ban san adadin kwanakin da zan kara ba” “Allah ya ba ku nasara ya sa ayi a sa'ah” “Ameen” Ya mike tsaye ya fice daga dakin, sai da ya leka dakin Narji duk da ya san ba lallai ne ace tana ciki ba a irin wannan lokacin saboda tana zuwa makaranta, ko bayan haka Narjin ba irin yan matan nan ne masu son zaman daki ba. Ta cikin kofar falon ya kunna kai zuwa bangaren Mai Martaba, samun kofar yayi a rufe, hakan na nufin Mai Martaba ya fita daga turakarsa kenan yana fada ko kuma falonsa da yake ganawa da baki, a dole ya juya ya dawo ta cikin falon Anty, ya fita ta kofar falon ya fita daga bangaren gaba daya ya shiga bangaren Mai Martaba, jerin motocin Mai Martaba ya tarar a harabar fadar ko ba a fada masa ba ya san Mai Martaba fita zai yi ko kuma ya dawo daga wani gurin. Yadda fadawa da dogarai suke mika masa gaisuwar suna zubewa kasa sai ka rantse da Allah shi ne dan sarki na fari ko kuma wanda ya fi kauna. Be shiga fadar ba saboda hangota ta yayi a rufe sai ya nufi masaukin bakin Mai Martaba. “Idan kuma ya disgani a gaban mutane fa?” Ya ayyana a ransa a tunaninsa zai tararda baki ne a falon, sai dai yana tura kofar falon ya shiga sai ya hango Mama Lami zaune a kujerar dake kusa da ta Mai Martaba sai wata matashiyar yarinya da zata tofi Aisha kadan tana zaune daga kasa sanye da abaya ash colar sai madaidacitar jakata a gabanta dayan hannunta rike da tabarau. Ba al'adarwa ba ce yin sallama idan ya shiga bangaren Mai Martaba saboda ya san Mai Martaba ba zai amsa masa ba, domin baya amsa sallamar kowa idan yana cikin mutane sai dai fadawansa su amsa, idan kuma daga shi sai iyalinsa ne ya kan amsa wani lokacin musamman idan zaman be wuce na mutun biyu zuwa uku ba, ko kuma matansa, sai da ko daga shi sai Mai Martaba ne a gurin Abiey yayi sallama Mai Martaba ba zai taba amsa masa ba saboda tsana. “Wa'alaikassalam” Mama Lami amsa masa sallamar da be yi kamar da gayya, kallonta kawai yayi ya risina har kasa da gaishe da mahaifinsa, be amsa masa ba sai ma dauke kai da yayi ya maida wani gefen kamar wanda yayi arba da makiyinsa, Abiey be damu ba daman inda sabo ya kamata ace ya saba da wannan yanayin. “Daman na zo ne na yi maka bankwana za mu tafi England gobe da yardar Allah” Nan ma Mai Martabarta be ce masa komai ba, sai Mama Lami ce ta amsa masa. “Maa Shaa Allah, Allah ya tsare ya kaiku lafiya kuma ya bada nasara” “Ameen” Ya amsa da kamar dole. “A tashi lafiya” Na fada yana kokarin tashi sai Mama Lami ta ce “Abiey baka gane wannan ba?” Ya kalli matashiyar budurwar da Mama Lami ta nuna masa sai ta dago ta kalleshi da manyan idonta, baka ce wulik sai dai irin bakin nan mai kyau mai shining irin na yayan manyan masu kudi. “Ban santa ba” Ya amsa a takaice. “Ummiter ce kanwar Engr ce” Cewar Mama Lami. “I thought ba Engr data muke da shi a Kano ba” “Engr Bashir Alkali Auta daya ne dai a Kano” Mama Lami na fadar haka sai matashiryar da aka kira da Ummiter ta gaishe shi. “Good afternoon” “How are you” Ya amsa mata ba tare da ya jira ita ko Mama Lami sun sake magana ba, ya kalli Mai Martaba yana dan rankwafawa cikin girmamawa ya ce. “Ammy ta ce a gaishe ka” Sai a lokacin Mai Martaba ya daga masa hannu ya daga masa kai a lokaci daya alamar yana amsawa, Mama Lami ta dan sauke kai kasa Abiey kuma yayi murmushi kadan sannan ya ya juya ya fice. Mama Lami ta bishi da kallo kamin ta kalli Ummiter. “Tashi ki tafi tun da kun gaisa, daman dai tace duk zuwan da take bata taba ganin Mai Martaba ba shiyasa yau ta zo ta kana nan na ce ta zo ta gaisheka” Ya mike tsaye tare da jakarta ta yi ma Mai Martaba a tashi lafiya sannan ta fice. Wannan karon a karamin falo ya samu Anty zaune tana jiransa ita da Aisha, sai da ya karewa fuskokinsu kallo sannan ya zauna. “Ka yi breakfast ma kuwa?” Anty ta tambaya sai ya girgiza mata kai alamar aa, tun kamin tace komai Aisha ta tashi ta fito daga falon fa nufi dinning. “Kun gaisa da shi?” Ya daga mata kai, shi kansa haka yake wani lokacin idan jinin sarautar ya motsa sai dai yayi ta maka magana da kai sai ta kama dole zai bude baki yayi magana. Bayan ya sha farfesun kayan ciki ya ci soyayar plantain Aisha ta fara koro masa matsalarta. “Kiri kiri matar nan ta hana Mai Martaba ya fitar da mu waje karatu Fisabilillahi adalci ne? Yanzu kuma na je na yi ma masa magana akan motar da yace zai siya mana yace na bashi lokaci zai nemi ni amman yanzu sai ta zo da wata magana a jiya wai kara dai ya bari sai idan zai aurar da mu ni da wadanda be bawa ba, kuma yayanta manya duk an ba su wadanda take cewa a bar mu sai zai aurar kanana ne fa, kuma idan aka yi haka ai ita riba biyu zata ci, saboda zata iya cewa a siyawa su Murshida idan za a musu aure bayan kuma yanzu ya siya musu” “Shi ne kawai matsalarki?” Ta daga mashi kai. “Kuma ina son na yi Masters dina a waje” “Sai kuma me?” “Shikenan zan yi magana da PA sai kuje da shi ki zabi motar da kike so, kuma ki fada masa inda kike son yi da Masters din sai ya nema miki” Amaimakon ta yi murna sai ta bata rai domin ba haka take so ba. “Ai ko yanzu ta samu yadda take so, saboda kao ka biya min ba Mai Martaba ba, kuma motar ma kai ka siya min” “Toh ya kike so yayi? So kike ke da shi Mai Martaba ya tsine muku? Kin san dai ba sauraren Abiey yake to miye na kawo karar Mai Martaba a gurinsa” Anty Amarya ta fada tana kallon babbar yar tata. “Haba Anty haka zamu yi ta zama ana nuna mana banbanci a gidan nan? Komai sai a ware mu dabam kamar ba haihuwarmu Mai Martaba yayi ba, tsakani da Allah na gaji ni wannan tsoron da kike nuna musu yana cutar da mu” “Ammy ma da take magana idan Mai Martaba yayi abu ya sa ya canja ne daga abun da yayi niya?” Abiey ya fada sai ta mike tsaye a fusace tana fadin. “Ni dai ba kai nake son ka yi min ba, ina da gata kuma ni ma yarsa ban san banbancina da sauran yayansa ba da zai rika ware mu dabam” Daga Anty har Abiey binta suka yi da kallo, Abiey ya dauke kai yana fadin. “Allah sarki Aliyu bawan Allah” Domin shi abun da Mai Martaba yake masa ya fi na kowa. Anty ta yi murmushi tana maida dubansa gurinsa. “Sai kuma matsalar Narjis, Mama Lami ta yi mata miji ita kuma tace bata sonshi” Abiey ya wara ido yana kallon Anty da mamaki. “Ta mata miji kamar ya?” “Dan gidan Justice Umar ne, shekaranjiya ta same ni da maganar amman tace bata fada ma Mai Martaba ba” “Miyasa ba zata bawa yarta ko yar Hajiya Kilishi ba sai Narji?” “Cewa ta yi wai shi ya ganta yace yana so” “And sai ki fada musu bata son shi” “Shi ne ba zan iya ba Abiey, kuma ka san idan Maganar ta kai gurin Mai Martaba zai iya cewa ya amince tun da komai suka ce shi ake yi, ita kuma ta zo ta nuna masa bata so wata matsala ta taso” “No kin ga banbancin Ammy da ke, ke tsoronsu kike so ta halin yaya Ammy kuma bata sharkar kowa a cikinsu har Mai Martaba, akan me zaki amince ma from place yaron nan fa mashayi ne, kuma kamin Narji ai Aisha ce babba why not ita ba a kawo mata shi ba sai Narji da suka raina?” Anty ta yi shiru fuskarta na nuna tsananin damuwa domin ita ma kanta har ga Allah bata so sai dai bata iya musawa Mama Lami duk abun da tace shi za'ayi, tana matukar tsoron ta kamar uwarta. “Toh ni yanzu da kika fada min me kike so na yi? Na cilasta Narjis auren wanda bata so saboda tana jin magana ta? Ai ba ma mutuncin gidan nan ba ne da masarautar nan ace yar masarautar da ta auri dan Justice Umar, ba kudi muke nema ba balle ace zata auren shi saboda kudinsa, ba zan cilasta ba kuma matukar bata so Wallahi ba za'ayi ba, na san ni ba kowa ba ne a gurin Mai Martaba amman wannan karon abun ya isa haka” Yana fadar hakan ya mike tsaye ya fice daga falon a fusace. ZAHRA POV. Duk yadda zan bayyana yadda mace take ji idan ta rasa miji sai na ga kalmomin kamar ba za su hadu su wadatu na isar fassarar yanayin ba, shiyasa wasu suke cewa mutuwar miji ta fi ta uba ciwo, sai dai ni a yanzu na kasa banbancewa tsakanin rashin uba da muka a shekarun baya da kuma rashin miji da na yi a yanzu. Musamman da dare yayi zan kwanta sai yanayin yadda muke kwance ya dawo min a rai, ko tufafinsa na kallo wani abun nake ji yana ta so min, sai dai fa kam hawaye Allah ya dauke min su, ba sakafai suke zubo min a ido ba idan dare yayi bana kwana sai na tashi na raya dare da addu'a ina rokon Allah ya yafewa mijina ni kuma ya bani juriyar cin jarabawar da na fada. A haka dai har aka yi sadakan uku a ranar kan na shiga tashin hankali sosai domin na tabbatar Deen ya tafi ya bar ni kenan har abada, ba laifi mun yi ta samun abinci daga abokansa yan'uwa da makota kowa yana ta kawo mana daidai gwargwadon hali, har mai gidan da muke haya sai da ya kawo mana abinci kuma yace idan muna bukatar wani abun na fada, duk wata soyayyar irin ta bahaushe da kuma dangantaka ta musulunci an nuna min ita sosai kuma na yaba domin ba ko wane musulmi ne yake samun irin gatan da na samu ba a cikin yan'uwan miji da makota na nesa da na kusa. Washe garin ranar da aka yi sadakan uku Jamila ta sake dawowa gidanmu, ban yi mamakin ganinta ba daman ta fada min zata dawo, yau kan gidan daga ni sai Bahijja ne a waje, Mama na daki tare da Yaya Maryam suna kintsa min dakin, Hajiya kuma tana gidansu gurin danginta saboda jinyar da take har yanzu jikin be saki da kyau ba,hakan yasa ana gama amsar gaisuwa sai yan'uwanta suka maida ita kusa da su saboda kar damuwar ta yi mata yawa.... Yau kan Hijab ta saka har kasa sai dai kamshin turaren da ta saba yi be canja kala ba, tun kamin ta karaso Bahijja ta janyo tabarmar dake kusa da mu ta shimfida mata sai ta zauna fuskarta da murmushi. “Ya hakurin hakuri Zahra?” “Alhamdulillah” Ta kalli Bahijja. “Wannan kanwarki ce?” “Aa kanwar mijina ce” “Allah sarki ya hakuri?” “Alhamdulillah” Bahijja ta amsa, sai shiru ya biyo baya idonta na kan cikina ni kuwa nawa suna kasa ina ta tunanin yadda zan fara yi mata magana. “Allah yasa tare da Dr kuka zo” “Aa ni kadai na zo, kina son magana da shi ne?” “Aa” Na amsa saboda kar Bahijja ta zargi wani abu, sai ta kalli Bahijja ta kalleni. “Mama na nan zan gaisa da ita” “Bahijja kira mata Mama” Na fada ina shafa wuyata da kassafan wuyan suka gama fitowa. Bahijja ta tashi ta shiga falon, sai Jamila ta yi saurin matsawo kusa da ni. “Me kike son magana da Dr akwai wata matsala ne?” “Gani na yi an yi aikin ba a yi nasara ba, abun da ake kokarin cin ma be samu ba, ran da anke son na ceta be tsaya ba, hakan na nufin yarjejeniyar bata zauna ba tun da be rayu ba” A take yanayin fuskarta ya canja tana min wani irin kallo na mamaki da rainin wayo. “Lallai baki da hankali, ko mijinki ya rayu ko be rayu ba yarjejeniya ta zauna saboda kudi ya fita daga hannuna yaje asusun asibiti, kuma bari na tunatar da ke, karki kuskura ki bari wani likita ya duba ki ba Dr Hamid ba, haka ma karki yarda ki haihu sai a hannunsa, idan kuma kika saba yarjejeniya kin san abun da doka tace” Hawaye na zubo min sai na yi saurin sauke kaina kasa, ita kuma ta daga da hikima tana kallon Mama da Yaya Maryam. “Ashe kuna ciki” Suka amsa mata suka zauna aka gaisa sannan ta yi musu sallama ta tashi har ta fice tana fadin Allah ya kara hakuri. “Gaskiya Likitan nan yana da kirki ina jin shi ya turo ta yace ta zo ta duba Zahra, ya nuna tausayawa sosai” Mama ta fada cikin jindadin yadda aka nunawa yarta kulawa, Yaya Maryam kan bata ce komai ba sai wani kallo take min mai kama da harara, na saka hannuna na share hawayen sannan na mikar da kafafuwana da suka kumbura. ABIEY POV. Be dawo gidan ba sai dare. Ko da ya shiga bedroom dinsa ya samu Ammy tana ciki tana kimtsa masa kayan da zai tafi da su. “Yanzu da kana da mata ba ita za ta yi wannan aikin ba?” Yayi murmushi yana zaunawa kusa da mahaifiyarsa. “Ki yi addu'a Allah ya kawo” “Addu'a ai kullum ina yinta, kuma ya kawo sai dai idan ba so” Yayi murmushi. “Matar ce ta aure har yanzu bata zo ba shiyasa ban ga wanda ta yi min ba, idan lokaci yayi ko wacece sai na aura” “Toh Allah yasa, amman lokaci tafiya yake yi Aliyu baya jiran kowa kuma idan ya wuce ba zaka iya dawowa da shi ba” “Haka ne, amman na Tambaye ki mana” “Ina ji” Ta fada ba tare da ta kalleshi sai kokarin rufe traveling box din take. Sai yayi shiru domin tambayar tana da nauyi sosai ko a gurinsa balle kuma a gurin Ammy. “Wane irin tsabani kuka samu da Mai Martaba... Har ta kai ga kun rabu...? Kuma miyasa kuka tsani juna ke da shi?” Juyowa ta yi ta kalleshi a take yanayin fuskarta ta canja. “Miyasa ka yi min wannan tambayar Aliyu?” “Wata kila amsar tana da nauyi ko Ammy?” “Kai ne mutun na biyu da yayi min wannan tambayar bayan Zahra” Ya furta cikin yanayi na rashin jindadi sannan ta mike tsaye ta fara takawa zuwa gurin kofar, Abiey ma ya mike tsaye. “Tsawon shekarun nan da na dauka na girma ne a hannunki ban tana kauna ko soyayya ta mahaifi ba, ban san abun da kika masa ba har ya tsane ni, be taba kula da ni ba balle ya damu da ni, idan kuma na tambaya sai ki ce ban masa komai ba, na kasa fahimta Ammy miyasa uba zai tsani dansa ba tare da ya masa komai ba? Tsana kuma irin wanda ban taba ji ko gani ba, har yanzu ba ki taba fada min abun da ya raba ki da Mai Martaba ba...” Yana kai aya ta juyo ta wanke masa fuska da mari mai kyau, sai ya lumshe ido ita kuma ta juya ta fice rai bace. Sai da ya ji karar rufe kofar dakinsa da ta yi sannan ya bude idon ya zauna bakin gadonsa, yana kokarin gano kuskurensa a cikin kalaman da yayi ma Ammy, haka nan dai yake jin kamar ba magani ne kadai abun da ya saka Mai Martaba ya tsane shi ba, idan har magani ne Anty ma ai ba za su bar yaranta a banza ba amman shi yadda Mai Martaba yake dauke kai a lamarinsa abun yayi yawa. “Zahra ta san dalilin da ya saka Mai Martaba ya tsane ni da yawa kenan? Kuma ta san dalilin rabuwarsu da Ammy?” Ya furta sannan ya mike tsaye ya nufi gurin madubi yana kallon kansa, fuskarsa sak irin ta mahaifinsa balle ya ce ko shi din ba shi ne mahaifinsa ba. Haka dai ya kwana da tunani kala kala har bachi ya dauke shi yana tashi da safe kuma ya dasa da wani, sai dai ya lura da yanayin Ammy gaba daya ya canja. Bata fasa yi masa abun da take masa ba sai dai fuskarta babu annuri, tana aje masa kofin tea ya kalleta ya ce. “Ba ki saba fushi da ni ba Ammy, idan maganar da na yi miki jiya ta bata miki rai ki yafe min dan Allah, ba zan jure ki yi fushi da ni ba” Dagowa ta yi ta kalleshi sai yayi arba da hawayen idonta. “Kai kadai ne na yi raino ba tare da iyaye da mahaifi ba, ba dan kuma naka uban ya mutu ba sai dan kiyayya kuma ka zama abun da ka zama a yau duk ta dalilina, yaya hudu na haifa amman na fi son ka fiye da sauran, ina son alakarka da mahaifinka ne saboda ina son ka samu aljannarka a karkashin kafarsa da tawa, zuciyarka ta daina raya maka komai Aliyu” Ya daga mata kai cike da gamsuwa. “Inshallah” Daga haka be sake cewa komai ba, bayan ya gama karyawan ya fita zuwa office din Sauban suka dade a a tare suna hira, har la'asar suna tare daman dai idan ba dayansu yana wani abun ba basa rabo da juna kusan ko da yaushe suna tare, most hiran da za ayi Sauban ne mai surutun Abiey shiru yake sai dai yayi dariya ko murmushi a wani gurin, idan ma yayi magana ba da yawa sosai ba. Suna kokarin rabuwa kira ya shigowa Sauban, kamin ya daga sai da ya fadawa Abiey cewa mutumen da ya saka yayi bincike akan ciwon Deen ne har yana fadin. “Bari mu ji ko ya samo mana labarin wanda ya biya kudin ne” Abiey ya maida hankali sosai yana kallon Sauban da ya amsa kiran. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, yaushe? Ya Sallah ya masa Rahma” Ya fada sannan ya sauke wayar yana kallon Abiey. “Wai yanzu aka kira shi aka fada masa mutumen da ya zo yana neman details dinsa jiya ya rasu yau” “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un” Abiey ya furta da karfi yana dafe kanshi zuciyarshi ta buga da mugun karfi. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un” Ya sake furtawa be taba tsammani zai ji wani abu akan mutuwar Deen ba, can kuma ya dago ya sake duban Sauban. “Da gaske ya rasu?” “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un” “Yes amman ai miye na mu a ciki mu? Kai da ya kamata ka yi murna?” “Haba Sauban miye abun murna a mutuwar wani?” “No Haba Abiey this is your turn fa da zaka gyara tsakaninka da Zahra, kasan daman ance mai hakuri mawadaci” “Wane hali Zahra take ciki yanzu?” Abiey ya tambaya yana tuna yadda zata shiga tashin hankali. “Shi ne mai muhimmanci ba mutuwar Sauban ba” “Ko dai miya aikata min dai ai musulmi ne, so ya kamata ka san abun da zai fito bakinka kai na fa musulmi ne” “Toh Allah ya masa Rahama” Ya fada ba dan yayi niya ba, Abiey be ce masa komai ba ya bude motarsa ya shiga, da tausayin Zahra ya iso gida ya san yadda take kuka babu kakkautawa idan wani abu ya same ta, balle kuma wannan sai a yanzu yake jin rashin jindadin bata taimakon da be yi ba akan lokaci. Labarin mutuwar Deen ne abun da ya fara labartawa Ammy, ita kanta ta kadu matuka da jin mutuwarsa, ta aje spoon din hannunta ciki yanayi ya tausayi ta ce “Allah sarki Zahra zaki sake shiga cikin wani tashin hankalinka kuma” Ya shafa kansa cikin damuwa ya ce. “Ammy kina ganin akwai wata hanya da zan iya taimaka mata ne?” “No kar ma ka soma, kana yin wani yunkuri za a ce ka jidadin mutuwarta, mu ma ba zamu je mata gaisuwa ba sai an kwana biyu” “Amman zan bincika na ji idan tana cikin wata matsala maybe we could help” Ammy ta dafa shi tana murmushi. “No karkayi gaggawar aikata komai Aliyu, na sa kana son Zahra amman ka dan dakata na lokaci, yanzu ka shiga ka yi wanka ka shirya jirginku zai tashi 5pm ka sani kuma yanzu 4:37” Ya daga mata kai cike da gamsuwa, sannan ya mike tsaye ya nufi upstairs. 5pm daidai ya isa Airport sai dai har biyar da kwata, suna cikin jirgin be tashi ba saboda passengers ba su gama shiga ba. An kawata gurin kamar ba cikin jirgi ba, domin ga bakwaye sai yayi zaton wani kasaitaccen falo ne da ba shi da girma sosai, wasu passengers suna gaba gurin zaman mutane uku uku su kuma suna VIP, ya maida fuskarsa kusa da window, ya dora kafarsa daya saman daya gaba daya hankalinsa da tunaninsa yana gurin Zahra ne, me zai fara mata? Me ta fi bukata? ‘This time around i won't let you down Zahra i promise, zan kula da ke irin kulawar da baki taba mafarki ba, i will be right beside you, i will guide you ba zan taba bari hawayenki su zuba ba akaina i....’ Matashiyar budurwar dake tsaye tana sanyi da uniform din masu aikin jirgin ta katse masa alkawarin da yake dauka a zuciyarsa. “Hi kamar Abiey” Ya daga mata kai, sai ta sakar masa murmushi. “Ka gane ni kuwa?” Ya sake dubanta. “Kamar mun hadu” Ya amsa fuska ba yabo ba fallasa, sai ta sake yin murmushi. “Ummiter” Ta fada masa tana kokarin tuna masa sunanta kamar ance mata neman sani yake, be ce mata komai ba ya sake dauke kai zata sake wata maganar wata ma'aikaciyar da ba zata wuce sa'arta ba ta shigo gurin tana nemanta. “Ummiter Ya Bashir yace idan mun sauka mu kira shi akwai kayan da Anty Jamila zata zaba sai a zo mata da su” Ummiter ta yi murmushi. “Okay” “Will you guys excuse me please i have something important to think about” Abiey ya fada yana kallonsu with serious face, yan matan masu kama da juna suka kalli sunan su sannan suka juya a tare suka fice. *Littafin nan n kudi ne, biya ki karanta cikin aminci, pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 and send the evidence of payment to 08036126660* [10/1, 5:16 PM] Oum_Nuwaira🥰: 1️⃣7️⃣ https://arewabooks.com/book?id=62d7b1c97fc1109aa61b7fca MARUBUCIYAR LITTAFAN 1. ZAGON KASA 2. HAFSATU MANGA 3. ZAKI 4. FULANI 5. CIWON SO 6. BAKAR WASIKA Duk zaku iya Samun waƴannan ne a Arewabooks, Ga link nan a sama👆🏻 Ayi following nawa da kuma comments. *Littafin nan n kudi ne, biya ki karanta cikin aminci, pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 and send the evidence of payment to 08036126660* ZAHRA POV. Bayan Jamila ta fita na kwanta saman tabarma na dora hannuna daya saman cikina ina jin wani irin kaunar ďa ko yar da zan haifa, ban taba jin sonsa da kaunarsa irin na wannan karon ba, ashe ba zan iya cika alkawarin Deen na kula masa da abun da na haifa ba? Da kuma saka masa sunansa ko sunana idan mace ce, na sani da ace Deen ya san da cewar na siyar da cikin nan da sai yayi fushi da ni saboda yana so na balle kuma abun da zan haifa masa, not just Deen Hajiya da Mama ma ba za su yafe min ba, miyasa na aikata? Ka yafe min Deen ina kokarin ceto rayuwarka ne rayuwar da ba zata tsaya ba, kuma ban yi nadama ba aikata hakan ba saboda na yi saboda masoyina. “Anty Zahra kuka kike?” Maganar da Bahijja ta yi min ne ya saka na taba fuska sai na ji hawaye ya sauko ta gefen idona. “Da Ya Deen ya san zaki yi kuka da yawa bayan mutuwarsa, da ya rokeki kar kika yi ko dan abun da yake cikinki, kuma kin sani Ya bayan son kukanki, ba kuma ke kadai kika yi rashi ba na fiki jin yadda kike ji” Na kwalleta daga kwance dake yayinda take zaune bakin kofar falona, sai na tashi zaune. “Ba ki fini jin komai ba Bahijja, ke dan'uwa kika rasa zaki iya aure mijinki ya maye miki gurbinsa, mace ko uba ta rasa aka ce idan ta yi aure ta tashi daga marainiya saboda mijinta ne zai rika kula da ita, ni kuwa mijin na rasa kacokan kin kuwa san zafin rashin abokin rayuwa Bahijja, miji ko kuntata maka yake wata rana sai ka yi marmarinsa balle kuma ni da Deen be min komai ba sai kyautatawa, ba zan taba samun miji irinsa ba, wannan kadai ya isa ya bani gwarin guiwar rike alkawarinsa na kin yi aure har karshen rayuwata” Na karasa hawaye na sauko min biyu biyu, ni kadai na san yadda nake ji a zuciyata sai kuma mata irina da suka rasa na su mazanjen, na shafa cikina. “Deen ya dade yana kwallafa rai a cikin nan, ashe Allah ya kaddara ba zai ga abun da zan haifa ba” Bahijja ta hada kai da guiwa ta fashe da wani irin kuka mai taba zuciya, wanda ya saka Mama da Yaya Maryam fito da sauri sai dai ganin nima ina kuka sai fahimtarsu dalilin kukan na mu gaba daya. “Haba Zahra mamaci fa addu'ah yake so ba kuka ba, na san zaki ji ba dadi kuma dole ki ji damuwa, amman idan kin ji haka ki rika furta Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un” Mama ta sai na maimaita hawaye na sauko min. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Mama mutuwa tana da ciwo Mama ni kadai na san abun da nake ji, shikenan Deen ya tafi kenan?” Mama kanta sai da na saka ta kuka ita da Yaya Maryam, Bahijja ma daker aka samu ta yi shiru balle kuma ni mai gayya mai aiki, tabbas mutuwa akwai da ciwo, mutuwa baki da tausayi, babu ruwanki da soyayya, idan na kalli fadin gidan nan ace babu Deen a ciki sai na ji zuciyata ta yi min wani iri, yadda muke mu'amala zamantakewarmu, rayuwarmu da yadda yake min idan ya shigo, idan zai fita ma, sai abun ya tsaya min a rai, minti daya biyu sai na sauke ajiyar zuciya nake iya samun numfashina ya daidaita. Da taimakon Yaya Maryam na koma bedroom dina na kwanta ina kokarin rufe ido na ji ta ce. “Ina son magana dake Zahra” Na kara bude idon da ban gama rufewa ba na kalleta. “Miya faru?” Ta nufi jakata data saka karkashin gado ta janyo ta bude tana ciro takardar yarjejeniya na tashi zaune babu shiri ina kallonta gabana na mugun faduwa. “Miye wannan?” Na kura mata ido na ma kasa kallon takardar data nufo ni da ita, tsabar tsoro da tashin hankalin ganin takardar da Yaya Maryam ta yi a lokaci na tabbatar da za a daka min tsawa zan iya faduwa na suma. “Na yi ta karantawa na maimaita amman ban gane inda kan rubutun ya nufa ba duk da kasancewar da hausa aka rubuta shi” “A ina kika gan shi?” Na tambaya hawaye na sauko min. “A cikin jakarki” “Mama ta gani?” “Bata gani ba, amman yanzu zata gani kuma ta ji komai” “Fada mata kamar kin kara jefani a cikin matsala ne kawai, ni kuwa a yanzu mafita nake nema” Sai ta matso kusa da ni. “Kar dai da gaske kin aikata Zahra?” Na sauke kai kasa ina hawaye. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Zahra me yake damunki? A ina kika hadu da wadannan mutanen? Taya ma aka yi suka dora ki a wannan hanyar? Anya kina cikin hayyacinki kuwa? Kin kuwa san abun da ake nufi da ďa? Ko dan baki haihu kin ji abun da ake ji ba? Zahra ina ganin kamar kin yi hankali ashe har yanzu hauka da kurciya suna nan tare da ke?” Na yi mata alama da ta yi shiru saboda ina gudun kar Mama ta ji. “Kina tsoronta kika aikata abun da kika aikata?” “Ba zaki fahimce ni ba Yaya Maryam, ba zaki fahimci yadda nake ji ba” Na fashe da kuka marar sauti, sai ta matsa kusa da ni sosai ta zauna fuskarta cike da tausayina ta ce. “Da gaske kin aikata Zahra?” Na daga mata kai still ina kuka, sai ta dafe kai ta fara ambaton Allah. “A lokacin idona a rufe yake ina neman mafitar yadda zan yi na samu mafitar kudin da za'ayi ma Deen aiki” “Toh gashi an masa aikin be rayu ba, sai yaya? Dole ne a kama wannan likitan” “Ki rufa min asiri dan Allah, karki bari kowa ya ji maganar nan idan yarjejeniyar ta fita sai na biya naira miliyan ashirin” “Ba zaki biya ba, kuma dole za a barki da danki ko yarki, sai ma a kama su ita ce wannan matar data zo dazun ko?” Na daga mata kai. “Ni daman zuciyata ta daya ba zuwan banza take ba, Zahra na za mu cigaba da rufe maganar nan ba dole ne kowa ya san da wannan saboda a sama miki mafita” Na rike hannunta da sauri ina girgiza mata kai. “Aa Wallahi idan maganar nan ta fita wata matsalar zan sake shiga.” “Miyasa kika aikata Zahra miyasa?” “Ba ni da wata mafita, kuma ba zan iya kallon mijin ya mutu ba tare da na yi wani kokari na ceton ransa ba” Na fashe da kuka mai karfi wanda ya saka muryata fita, har sai da ya rumgume ni, domin ita ma kanta tasan ina cikin mawuyacin hali a yanzu, rufe min baki ta yi tana kuka kamar yadda nake, Mama ta shigo da sauri tana kallona cike da tausayawa. “Haba Zahra, wannan abun da kika ba zai dawo da Deen ba, kuma sai ki jawa kanki wani ciwon ai miye haka kamar na musulma ba? Haba Zahra? Dan Allah ki yi hakuri” Ta karashe maganar cikin muryar kuka domin tuni hawaye suka wanke mata fuska. A ranar na ci kuka irin kukan na na rashin madafa irin kukan da babu mai cetonka kuma baka da wata mafita sai addu'a. Da yamma Mama ta dama min koko na sha domin shi na ji ina kwadayi sai ta aika makota aka siyo mata kamu ta dama min ta saka min suga da madara, na sha kumun sosai daman na dade ban sha kunu mai dadi irim yau ba, bayan na gama sha Yaya Maryam ta dauke kofin dana bata sannan ta aje min kwanon abinci. “Ga wani nan ki kara” “Ba zan iya ci ba” Bata ce min komai ba ta bude abincin ta fara ci, sai da Mama ta tashi sannan ta matsa kusa da ni. “Yanzu idan kika haihu sai ki yi yaya? Mama da Hajiya su ga ba ďa?” “Likitam yace zai bani matacce wanda zan nuna a matsayin dan da na haifa babu rai, kuma yace daga yanzu kar na sake zuwa asibiti sai dai na kira shi idan ina jin wata matsala, kuma yace a gurinsa zan haihu” Ta sauke ajiyar zuciya. “Kin yi kuskure Zahra” “Yaya Maryam dan Allah ki min alkawarin babu wanda zai ji maganar nan dan Allah, in ma zaki fada ki bari sai na mutu” “Haba Zahra wannan karon wace irin magana ce, na miki alkawari babu wanda zai ji maganar nan har sai idan ke kika bukaci haka, amman dai ki yi tunani” Na daga mata kai ina share hawayen ido, ni kaina ina jin kamar ba zan iya bada abun da zan haifa ba ga wata macen da ban sani ba, sai idan ban bada ba ina da wata mafitar ne? Ana daf da sallah magariba Yaya Maryam na zancen tafiya gida ni kuma ina kokarin tashi na yi alwala domin tuni Mama ta yi nata, Bahijja kuma tun da yamma tace zata je ta leka Family house dinsu gurin Hajiya ta duba jikinta. Sai muka ji sallama wata bakuwar murya ce kuma bakuwar fuska da ban wayance ta ba, ko ma na ce ban taba ganinta ba. Mama da Yaya Maryam suka amsa mata sai dai idonta a kaina yake kamar ta san ni sai murmushi take. “Sannu ya hakuri” Duk muka amsa mata har ni, sannan ta kalli Mama ta ce. “Sunana Sadiya gidanmu na ta can baya, sai jiya Mama take fada min an yi rasuwa a nan har sun zo gaisuwa lokacin ina makaranta” “Allah sarki, Allah ya saka da alheri” Mama ta fada s zuciyata bata yarda da ita ba, na lura Yaya Maryam kallon rashin yarda take mata. “Zo ki zauna” Na fada domin na lura akwai magana a cikin cikinta, ashe kuwa abun da take nema kenan sai ta zauna, ni kuma na nufi butar da Mama ta aje na dauka na shiga bandakin tsakar gidan na yi fitsari ko da na fito na samu Mama ta shiga ciki Yaya Maryam kuma tana daga zaune bakin kofar dakin ta tsare budurwar da ido. Sanin Yaya Maryam ta san komai ya saka na kalleta na ce. “Dan Allah Yaya Maryam dan ba mu waje” Sai da ta sake kare mata kallon tun daga sama har kasa sannan tashi ta shiga cikin falon, na kalli yarinyar da sauri. “Fada min waya turo ki?” “Dr Hamid ne da Jamila suna son magana dake a waje” “Su suka turo ki?” Ta daga min kai. “Ba zan iya fita na yi magana da su ba, saboda ina takama idan mutane suka gan ni a waje zai zama abun magana kuma ko ba takaba ina da tsohon ciki be kamata na fita waje na yi magana da wani a waje ba ina matar aure” “Magana ce mai muhimmanci, da dai kin daure ba kowa zai san alakarki da su ba balle har a zargeki” Ta fada min da sauri tana kallon kofar falon kamar mai tsoron kar wani ya fito. “Tashi ki tafi zan fito” Ta mike da sauri ta saka talkamin cikin sanda ta fice daga gidan, ni kuma na kira Yaya Maryam sai ta fito da sauri kamar daman jiran take na kirata. “Wai Dr ne yana waje da matar za su yi magana da ni” “Toh su shigo cikin gidan mana” “Ba zai yiyu ba saboda Mama tana nan zata iya ji, kuma Bahijja zata iya dawowa ta tararda da mu” “Gaskiya ba zan bari ki fita waje ba, na san me suka zo miki da shi” “Ba zai wuce mu yi magana ba, kuma ba zan dade ba ni dai ki dauke min hankalin Mama please kar ta gane na fita” Ba dan ranta ya so ta shiga falon ta dauko min hijab dinta. “Zan kai buta bandaki idan kin dawo sai ki rataye Hijab din a waje ki shiga ki fito da butar” “Toh Mama fa?” “Zan tsayar da ita a falo ba zan bari ta fito ba sai kin dawo” “Toh” Na karbi Hijab din na saka da sauri sannan na saka talkamina na fice cikin sanda kamar yadda wacan bakuwar ta yi, kusa da kofar gidanmu na sami motar Dr Hamid. Yana ganina sai ya bude min gidan baya, ni kuma na girgiza mashi kai. “Aa ba sai na shiga ba” Sai ya bude motar ya fito, ita kuma ta sauke gilashin motar idonta sanye da katon tabarau irin wannan mai batar da kama. “Ki shigo cikin mota zai fi sirri” “Kuna son sirri kuka sako wannan matar a ciki” “Bata san komai ba, kawai dai na fada mata yadda zata yi ne idan ta shiga gidan, kuma tana fitowa na sallame ta ta tafi” Dr Hamid ya fada muryarsa kasa kasa. “Me kuke kirana? Kuma ku daina yawan zuwa saboda mutane za su saka ido kuma mahaifiyata zata iya ganewa” Na tambaya, sai ta bude motar ta fito, Dr Hamid ya kalleta sannan ya sake kallona ya ce. “Dazun Jamila ta je min da wata magana cewar kin ce yarjejeniya ta fasu saboda mijinki ya mutu?” Na kalleta sai dai ban ce komai ba. “Ba a haka Zahra a ka'ida kudi ya riga ya fita daga hannun Jamila kuma an yi ma mijinki aiki kin ga da anyi nasara da yanzu yana nan raye rashin nasarar kuma ba zai canja komai ba saboda kudin an riga an yi amfani da su” Nan ma shiru na yi hawaye suka fara cika min ido. “Idan kuma kina son rike cikinki ne zaki ba mu naira miliyan ashirin, kuma ki sani ba ni kadai zan shiga a matsala ba idan ma kin fallasa har da ke sai kin shiga, saboda ke kika siyar a ra'ayin kanki ba cilasta ki aka yi ba, kin ga da ni da ke sai duk mu amsa tambayoyi yan jarida” Jamila ta fada, a karo na uku da na kasa bude baki na furta komai sai ruwan hawaye nake. “Ba haka ya kamata ki yi mata magana ba, ke da ita duka taimakon juna kuka yi, ita ta taimake ki ke kuma kin taimaketa, kuma magana ya kare na zo nan ne saboda na fahimtar da ita saboda na daga mata hankali ba” Bayan Dr Hamid ya gama fadar hakan ya dauke idonsa daga barin kallon Jamila ya sake kallona. “Sai abu na biyu kuma Mijin Jamila ya ce be yarda matarsa ta haihu a kasar nan ba sai a waje, saboda haka muka zo neman alfarma idan zaki iya bin mu waje ke ma ki haihu can” Na girgiza kai da sauri. “Ba mu wannan cikin yarjejeniya ba, ba zan bar garin nan zuwa ko'ina ba” Sai ya daga min hannunsa. “Shikenan babu dole daman roko kuka zo ba cilasta ki zamu yi ba” “Amman Dr idan ba wannan ba bamu da wata mafita can ma din zai fi nan sirri kuma kasan yadda mijina yake ji da cikin nan ba zai taba yarda na haihu a nan ba” Sai ya juya ya kalli Jamila wanda ta yi maganar. “And we can't force her, idan bata ra'ayi babu dole, ke sai ki san yadda zaki yi janyo ra'ayin mijinki ya yarda ki haihu a nan” “Ko kuma ka bata dama ta yi tunani ba, domin gaskiya na san Miji ba zai yarda ba” “Kuma ba zamu cilasta ba, tun da har ta furta cewar ba zata je ba ki kyale ta kawai dan ba zan saka ta dole ba” “Amman Dr... ” Ta daga tana kokarin daga murya sai ya daga mata hannu. “Ba sai kin daga mata muryar ba because she's pregnant women ba ayi ma mata masu ciki tsawa saboda ta yi yarjejeniya ba kanta ta siyar ba saboda haka tana da yancin ta yi abun da take so” Wani kallo ta yi masa. “Ni ma ai cikin ne da ni be kamata kana bari raina yana baci ba” “Yours is fake tana kuma na gaskiya ne” Maganarshi ta tsoke ta irin sukan da ya bayyana a fuskarta, bata sake cewa komai ba ta bude motar ta shiga, sai ya juyo ya kalleni. “Zahra ki kwantar da hankalinki a nan zaki haihu da yardar Allah, kuma ina kara tunatar da ke cewar daga yanzu awon cikinki har zuwa ki haihu ya dawo hannuna” Na daga masa kai. “Zan shiga ciki kar kanwar mijina ta same ni a nan” “Okay” Na juyo da saurina na dawo na nufo gida, sai da na fara lekawa na ga babu kowa aje sannan na shiga na cire Hijab din na rataye na shiga bandaki na sai na tararda butar da Yaya Maryam tace zata aje min. Jinginawa na yi gurin hawaye na sauko min na kai hannuna na dafe zuciyata dake min zafi. ‘Ba zan iya bada cikin nan ba, ba zan bada wannan cikin ba’ Na fada a raina ina sulalewa kasa na zauna ina kuka marar sauti, ban fito bandakin ba sai da na ji muryar Yaya Maryam tana fadin. “Zahra har yanzu kina bandaki gashi har hudu ya sauko? Ba a son jimawa a bandaki fa” Share hawayena na yi na fito daga bandakin rike da butar dake kokarin zamewa a hannuna ta fadi, har ta yi kamar zata nufo ni sai ga Mama ta fito a dole ta tsaya inda take ni kuma na nufi magudanar ruwa na duka na fara alwala ina ta kuka tun ina yi cikin karfin hali har ta kai bana iya boyewa sai da kuka ya fito, Mama ta rafka tagumi tana ta kallona a zatonta kukan rashin Deen kawai nake, sai dai ba kukan rashinsa kawai ba har na kuskuren dana aikata wanda yanzu ya dawo ya dame ni. Yaya Maryam ce ta zo ta rika ni na mike tsaye sai ta rumgume ni. “Ki yi ta fadin Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un” Na daga mata kai, sai dai kuka baya bari na furta, ina rike da ita har muka shiga falona da babu komai saboda an siyar da kujerun gurin neman maganin Deen, uwar daka ta shiga da ni ta zauna saman sallayar da Mama ta gama sallah da ita. “Me aka miki Zahra?” “Yaya Maryam ba zan iya bada cikin nan ba, ina som abuna kuma matar da zan ban san wacece ita ba, idan na bata ya zama nata har abada kuma ban san wane hali zai kasance ba” “Toh ya zaki yi Zahra? Kin riga kin aikata kuskure, ni da zaki dauki shawarata da sai ki fada kowa ya sani idan ma shari'a ta kama ayi sai ayi” “Aa matsala zamu shiga idan aka yi haka” “Yanzu me suka ce miki?” Na fada mata komai, a take ta harzuka. “Wallahi babu inda zasu je dake, waya san ma ko so suke su kasheki idan kin haihu saboda asirinsu yayi ta rufuwa babu wanda ya sani” A take hankalina ya tashi, domin zuciyata bata raya min haka ba sai a yanzu da Yaya Maryam ta yi wannan maganar. “Balle sun ga kin fara nuna musu cewar kina son danki” “Yaya Maryam ko dai na gudu?” “Ki je ina? So kike hankalin Mama ya tashi? Kuma ki shiga a bakin duniya? Zahra ki rika tunani idan zaki yi abu” Na fara yawo da idona ina ta tunanin mafita. “Na tafi ruga gurin su Hajjo, kin ga babu wanda zai san ina can ma” “Zahra kina da hankali kuwa? Me zai kaiki can? Garin da ko nepa babu komai na jindadin rayuwa? Kuma tafiyar kwana uku? Idan ma kin tafi shi zai warware wannan matsalar ne? Zaki kara saka Mama da Hajiya a tashin hankali ne kawai” Na sauke ajiyar zuciya, a zahiri na nunawa Yaya Maryam ba zan je ba, sai dai zuciyata bata daina raya min tafiyar ba. “Guduwa ba ita ce mafita ba, dan Allah karki tafi” Na daga mata kai. “Ba zan je ba, amman dan Allah karki fadawa Mama komai ciki har da maganar nan da muka yi” “Na miki alkawari ba zan fada ba, tashi kije ki yi sallah kar ayi Isha'i” Na tashi kamar yadda ta bukata na shiga bandakin bedroom dina na yi alwala na fito da tunani kala kala, na yi ta rokon Allah a cikin sallah ta, tsakanin guduwa da kuma zamana, domin zuciyata ta fi natsuwada tafiyar, idan na gudu ai ba za su san inda nake ba, balle har su takura sai sun karbi babyn da zan haifa, amman kuma idan na tafi wa zai yanka min rago a can? Suma ai dole za su yi mamakin zuwana da tsohon ciki, mutanen karkarar mutane ne masu kara da girmama wata kila za su iya yanka min daya daga cikin dabobinsu idan ma ba su yanka min ba, sai na tafi da kudi na yanka nawa. Sai da duhu ya soma yi sosai sannan Abban Husna ya zo ya tafi da Yaya Maryam, sai dai ba mu rufe gidan ba saboda tunanin Bahijja zata dawo, amman shiru hakan ya saka Mama ta kira waya ta tambaya ko lafiya sai aka ce mata lafiya kalau a can zata kwana, a daren daga ni sai Mama muka kwana a gidan, washe na farka da dan kuzarina na share dakina Mama ta dumamana mana shinkafar jiya kuma ta dama mana sauran kamun da aka siyo min jiya, Yaya Maryam kuma bata iso gidan ba sai 12 na rana tare da duka yaranta kasancewar yau weekend babu makaranta, kusan yanzu a nan take wuni kullum saboda ta rage min kewa da katuwar kular abincin suka zo, ta yi mana tuwo a gidanta miya kawai ta girka a gidan. Ana kiran sallah azahar muka ji tsayawar mota a kofar gidan, da farko na yi tunanin Dr Hamid ne mo Jamila suka sake zuwa, ba ni kadai ba yar Yaya Maryam dake zaune muna cin abinci a tare na lura hankalinta ya tashi da jin tsayawar motar musamman da muka ga an dauki lokaci ba a shigo cikin gidan ba, yara ta ma duk abinci suke ci balle na ce su leka waje domin su ga ko waye. “Waye a waje? Na ji kamar mota ta tsaya kuma har horn an yi” Mama na rufe baki wani namiji maji karfi ya shigo dauke da buhun Shimkafi na jefar a bakin kofar gidan mai binsa ma ya aje saman wanda wacan ya aje suka sake fita suka shigo da mai da kayan tea suka jera mana a gurin aiko yaran Yaya Maryam da gudu suka tashi suka fita ganin wanda ya aiko kayan da kuma inda suke dauko su, suna fita Dr Zainab ta shigo Ammy na bayanta sai wata bakuwar fuska da ban sani ba, Ammy na sanye da yadi da farin mayafi Dr Zainab kuma ta saka abaya kanta da hula ta rike dankwalin abayar a hannunta, bakuwar dake tare da ita kuma tana sanye da atamfa sai mayafi da ta rufe kanta zuwa bayanta da shi. “Assalamu Alaikum” Kusan a tare suka min hada baki gurin yin sallamar, sai na sauke kaina kasa na samu kaina da kasa amsa musu, Yaya Maryam da Mama suka amsa suna kallonsu, tun kamin ayi musu izinin zama Dr Zainab ta nufi wata kujerar zama ta mata ta dauko ma Ammy ta aje mata, Mama ta tashi ta shiga falo ta dauko tabarma ta shimfida musu Dr Zainab da Matar suka zauna a kai, har suka gama gaisawa da Mama da Yaya Maryam ban dago ba sai da Ammy ta kirani da sunan da ta saba kirana da shi. “Zahra autata har yanzu fushi kike da Ammynki?” “Ammy kina tunanin zan manta da abubuwan da suka faru ne?” Na amsa mata ba tare da na kalleta ba, har yanzu ina tuna yadda ta tsaya kai da fata ta rantse danta ba zai aure ni ba. Dr Zainab ta ce “Haba Zahra ashe ba zaki iya shafe abun da ya faru ba ki manta da komai” Na kalleta. “Da zan iya shafe wani abu, da na shafe tahirin saninku da na yi a rayuwata...” “Ke Zahra... ” Mama ta daka min tsawa sai na dube ta. “Mama mutanen nan sun wulakanta, idan ku kun manta ni ban manta ba” “Daman gaisuwa muka zo Allah ya jikansa ya bada hakuri ya sauke ki lafiya, Ammy tashi mu tafi” Dr Zainab ta fada a fusace tana mikewa tsaye, ashe sanin da na yi mata na saurin fushi bata canja. “Ayi hakuri Zahra rashin fahimta ne aka samu, kuma abubuwa sun biyo ta hanyar da ba mu yi zato ba” Ammy ta fada sannan ta saka hanunta jaka ta ciro kudin da zai kai 50k ta aje kusa da Yaya Maryam. “Zamu tafi Allah ya bada hakuri” “Amin Allah ya bada lada” Mama ta fada, sannan suka fice ba tare da na sake kallon inda suke ba. “Zahra ba a haka gaisuwa suka zo be kamata ki nuna musu wani hali ba” “Mama kamar kin manta mutanen nan? Allah kadai ya san dadin da za su ji da suka san Deen ya mutu ko ma waya fada musu ya mutu? Allah na gode maka da ya kasance ba sakina Deen yayi ba sai da mai rabawa ta raba balle ayi min dariya” Na fada hawaye na sauko min. “Ko kunya ba su ji ba” Na sake fada ina turo baki gaba cike da jin bakincikin gaisuwar da suka zo min, ni da Yaya Maryam muka yi ta zancen abubuwan da suka faru muna jin bakinciki, idan na tuna Abiey sai na ji kamar ba ni da wani makiyi da ya kai shi, and the most annoying thing is memories rayuwar da muka yi cikin farincika ya dawo fara dawo min a rai zuciyata ta fara nuna min his ugly happy face, na yamutsa fuska kamar zan yi amai, gaba daya ma sai na ji abincin ya fita a raina. Wasa wasa kwanaki suka fara mikawa aka share sati daya da kwana biyu da rasuwar Deen, kullum cikin yi masa addu'a nake zuciyata kuma tana ta begen masoyinta, ga kuma tunanin rabuwa da cikina da ya saka ni gaba, na rasa makama zuciyata na ta raya min ba ni da wata mafita data wuce guduwa, ga shi alamun haihuwa sai kara bayyana suke, cikina ya kara nauyi yayi min kasa sosai, zaki sai zuba yake min saboda Mama ta jika min zobo ina sha, Hajiya kuma ta aiko min da kayan jike jike da ake sha na mai ciki, duk bayan kwana biyu kuma sai ta zo ta duba ni, ko kuma ta kira waya ta tambaya me nake son ta girka min, wannan gatan da soyayyar da suke nuna min saka ko na yi unkurin guduwa sai na yi tunanin wane hali zan saka su idan suka wayi gari babu ni? Ni ma idan na gudu wahala zan sha saboda cikin nan, ta inda na samu kwanciyar hankali Dr Hamid ko Jamila babu wanda ya sake zuwa gidanmu, sai dai yanzu Mama ba kullum take kwana da ni ba, Yaya Maryam ma tun da aka yi sati daya sai ta daina zuwan dake tana min wuni sai an kwana biyu, daga ni sai Bahijja sai wata kanwar Kakata da bangaren uba muke koma kwana a gidan. *LAHADI 5:39pm* Ina zaune rike da carji ina ja Bahijja na zauna kusa da ni tana fadin na yi rama sosai ni da Hajiya bata san wanda yafi wani jin zafin mutuwar Deen ba. Kamar daga sama muka ji sallama daga kan da zan yi na yi arba da Jamila tana sanye da katon hijab har kasa sai bakin tabarau da facemask dake fuska ta rufe ko'ina ruf domin har hannunta sanye yake da safa, sai wata kudaddiyar yarinya tana rike da jakarta kana ganinta kasan yar aikinta ce, wani irin faduwa gabana yayi domin wannan karon ta tararda ni tare da Bahijja ne ga kuma Kakata dake taya ni kwana. “Wa'alaikissalam” Na amsa mata daker, sai ya karaso inda muke ta yi tsaye ganin hakan ya saka Bahijja tashi ta dauko mata tabarma. “Ai ba zama zan yi ba, daman na zo ne kawai na duba lafiyarki, ya hakuri” Ta fada fuska ba yabo ba fallasa, ban yi mamakin ganin fuskarta a haka ba wata kila bata huce daga kin amincewa na bita a waje da na yi. “Lafiya ta kalau hakuri kuma mun gode Allah” “Maa Shaa Allah, Allah kara hakuri ya saukeki lafiya shin yaushe ne edd ki? Kila mu haihu tare” Wannan karon da dariyar yake ta karshe maganar saboda kallon mamaki da Bahijja take mata, wata kila bata son Bahijja ta zargi wani abu. “Sun ce May 23, ke fa? Ko da yake haihuwa sai lokaci yayi” Na fada mata ba kamar yadda yake rubuce a takardar scanning dina ba. “Ni ai na shiga wata ba, ashe baki shiga wata takwas ba ma ke, toh Allah ya raba lafiya daman dai nace bari na biyo ne kawai saboda zan tafi tare da miji Abuja” “Allah sarki Allah ya tsare” Ta amsa da Ameen sannan ta juya sai kuma ta sake juyowa. “Wai babu wayar da za a iya kira a same ki ne? Ya kamata ace kina da waya fa” “Toh ki saka min number ki a nan, kuma ki siya da wuri please” Ta fada tana saka hannu ta ciro tsadaddiyar wayarta ta miko min, ba musu na karba na saka mata numberta sannan na mika mata wayarta, sai da ta yi mana sallama sannan ta fita, zuciyata na tsaka da raya min cewar da biyu ta zo, Bahijja ta jefo min tambaya. “Anty Zahra wacece wannan?” “Kawata ce amman ta bani shekara biyar gaskiya can suke sama” Na amsa mata, sannan na sauke ajiyar zuciya, a ranar kamin dare yayi har na matsu, suna sallah Isha'i na bude jakar da Mama ta saka mana kudin da muka samu da kuma wadanda muka rage na aikin Deen da muka samu na dauki kudin da zai kai dubu dari na saka a jakata ba tare da na bari Bahijja ko Daada sun lura ba, a yadda muka saba dukanmu a daki muke kwana amman a yau sai na zabi kwana a falo saboda na samu mafita a abun da nake shiryawa, a falon na kwana har safe washe gari na fito harabar gidan na yi alwala na shiga falo na shimfida dankwalina na yi sallah, Bahijja da Daada suna daki suna na su Sallah na dauki handbag dita na fito waje kamin na kai bakin kofar fita gidan har hawaye sun wanke min fuska, bayan na bude gidan na juyo ina kallon gidan, sannan na fito kamin na isa titi ma na gaji sosai ga shi safiyar ma bata gama waye ba, haka na isa titi ina yi ina waigawa gabana sai faduwa yake kamar zai fasa kirjina ya fito. Na isa titi ina ta rabon ido daker na samu wata Napep shi ma da wani mutum a ciki sai da na fara shiga sannan na fada masa inda zai kai ni. [10/3, 4:49 PM] Oum_Nuwaira🥰: 1️⃣8️⃣ Ko da tara tayi na safe na hau motar Zaria domin ya fi min kusa fiye da ace na tafi garin Mama tafiyar kwana uku wata kila ma kamin na kai za tararda da domin na fadawa Yaya Maryam kuma be zama lallai ta boye ta ki fadawa kowa ba, kusan duk wanda ke cikin motar kallona yake saboda yadda nake hawaye kamar zan karar da hawayena ga kuma katon cikin dake jikina numfashina har wahalar ita yake. Ba ku dade ba muka isa Zaria kasancewar daga Kano zuwa Zaria babu nisa, na sauka ta shar sai na ji dabam ina tajin kamar ace na taho da mask dina ko Niqab, cikin tashar na kusa na nemi shagon da ake siyar da kayan ciye ciye provision na siya mask a gurin da biscuits ya miko min lemu mai gas sai na tuna Deen ya hana ni shan abu mai gas. “Malam ba ni mai madara” Na mayar masa sai ya miko min mai madara ya bani canjina kasancewar dubu daya na bashi ya kuma miko min leda na saka, sannan na kama hanya ina tunanin ko zan iya gane Kauyen su Hafsat, wata tsohuwar kawata ce da muka taso tare tun muna yara yar zaria ce sai dai tana zaune a kano ne a unguwar mu hannun yayarta kamin ayi mata aure da wani dan'uwanta a kawo ta Zaria, sai dai iyayenta suna kauyen Kalbana (sunan kauyen Kalbana na kirkira ne). Kai tsaye na nufu inda ake faka motocin kauyen na taba zuwa sau daya lokacin da tana Kano na saci kafa na tafi ba tare da sanin Mama ba, aiko ranar da na dawo na sha duka a gurin Deen kamar zai kashe ni domin a tunaninsa lokacin na je gurin wani saurayi ne. Ina isa na tararda mutun mutun biyu kawai ake jira a take na biya kudin mutun biyu saboda na samu wali kasancewata mai ciki. A cikin motar na bude lemun da biscuits ina ci, wani dan tsoho mai zubin mayu sai kallona yake, ni ko na daddage ina ta karanto addu'a, idan ma mayen ne sai dai ya ci kasan, daman ance mayu sun fi son mace mai tsohon ciki ko amarya ko mai jego ta fi saukin kamawa a garesu domin jikinta a sake yake kurwarta kuma a kasa take ba kamar sauran da kurwarsu take tashi ba. Ina fara karanta wa'inyakadun lazeena kafaruu.... Har zuwa karshe sai ya fara tsarguwa ya juya fuska be sake kallon inda nake ba har motar ta isa da ni yar karamar kasuwar da ake hawan babur a isa kauyen Kalbana. Na fito na dauki jakata na rayata na kara gyara mask dina da na yi kasa da shi saboda biscuits din da na ci, na nufi gurin da babura suke fake wasu tuni ma sun nufo motarmu da ta tsaya domin aikinsu kenan daukar passengers zuwa cikin kauyen ko kuma gaba da kauyen domin babu titi mai kyau idan da mota za a je za a sha wahala sosai saboda rashin kyaun hanyar, na fada ma mai achaban inda zai kai ni sai ya fada min kudin zuwa can, a take na hau ya fara tuka babur din muka dauki hanyar kauye mai cike da albarkar Manoma. Tafiya ce mai dan karen nisa domin ta dauke ni awa daya da rabi kamin mu isa, aiko kafafuwa kamar na fasshe da kuka abun cikin na sai motsi yake daga ni har shi ko ita mun matsu. Babban family a kauyen domin gidan irin gidan nan ne na gado irin wanda kowa ke ware na shi bangare ya gina nasa a ciki, kuma mahaifinta shi ne sarkin majema na yankin kamin Allah yayi masa rasuwa. Ina tsaka da tambayar wani matashi gidansu sai mai achaban yace min ya sani. “Ai da kin yi magana da can zan sauke ki, waye be san gidan Margayi Musa Sanga ba” A haka na koma kan achaban muka sake wata tafiyar ta minti ashirin sannan muka iso kofar gidan, na sauka na biya mai achaban na doshi gidan ina kallon yadda yanayinsa ya canja domin a can da gidan kasa ne gaba daya yanzu kuma na ga gaban gidan da wani bangare ginin bulo ne na zamani, sai dai ba ayi filista ba balle fenti. Na shiga cike da tsoro irin na bakunta waya sani ma mahaifiyarta tana nan ko ta rasu ko zan iya gane bangaren da take ba, wani gidan na fada na fada musu wanda nake nema. “Inno Mamansu Hafsat wanda ta yi zama a Kano” “Oh ga bangarensu can” Matar mai goyon ta nuna min, sai na juya na nufi bangaren, na shiga da sallamata ina ta karewa bangaren Kallo. “Wa'alaikissalam” Muryar Hafsa na ji ta amsa ta juyo daga wankan da take yi ma yaro ta kalleni mamakin ganinta ya saka na tsaya cak domin a iya sanina ta yi aure irin auren da ake yi ma yarinyar tun bata gama makaranta ba a lokacin muma ss1 aka cireta aka mata aure, ita ma mamakin ganina ya saka ta tsaya a gurin kamar hoto. “Uwani...” Ta furta haka take kirana tun ina complain har na gaji na rika amsawa kasancewar ina da sunan mahaifiyarta ne. Da gudu ta iso gareni sai kuma ta ja ta tsaya tana kallon cikina. “Allahu Akbar Uwani rai kan ga rai? Ashe Allah be kare ganawarmu ba” Kallona take irin na canjawa da nayi nima ina mata kallon yadda ta yi rama ta kara baki kamar ba ita ba, a take hawaye ya cika idonta ta rungume ni tana murna tana kwalawa mahaifiyarta kira. “Inna fito ga takwararki” Inna ta fito da sauri tana kallona irin kallon nan na baka wayanci mutum ba, har sai da Hafsat ta yi mata bayani. “Allahu Akbar yar nan? Allah sarki sannu da zuwa sannu da zuwa” Kamar su hade haka suka rika murnar ganina. A take aka yi min shimfida aka bani ruwa da filo ta cire kudi tace a siyo mata taliya da kifi ta daba min, abun ka da mutanen kauye masu karamci da kara kamin azahar har gidan ya cika da kwanon abinci, domin duk mutanen gidan da suka dafa abinci sai da suka kawo min suna ta min marhabun, har na rasa wane zan fara ci, Hafsat kam sai tambaya take idan akwai wani da nake so ta siyo min, mun sha hira duk da bana jin sakewa sosai amman a dole na washe damuwata ta ragu sai dai faduwar gabana be daina ba na halin da Hajiya da Mama za su shiga. Can da hira ta yi dadi take fada min aurenta ya mutu, sam ban jidadi ba ganin tana da kurciyarta gashi har sun haihu biyu. “Ni kam yi mamakin ganinki gida, amman ban dauka mutuwar aure ba ne, Hafsat miya faru?” “Mi ya faru kuwa Uwani mazan yanzu mutunci ne da su, auren zamani ya zama abun da ya zama aure zai kara saboda arziki ya fara samuwa yana zuwa onisha kai kayan masarufi yana samun kudi sai maganar aure ya shirya ma Amarya daki ciki da falo a kusa da nawa ni kuma kin san daki daya da ni ko da yake baki taba zuwa ba, nawa dakin dai daya ne kuma indai har ga mutunci da adalci kamata yayi ya gyara min nawa ko kuma ni da ita duk ya gina mana sabon daki, daga na yi magana sai ya fara masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, daman gaba daya ya canja sai rawar kafa yake zai yi amarya, yan'uwansa suka hau zuga shi wai na cika mugun kishi daman mahaifiyarsa ce take so na domin ita ta hada auren yanzu kuma bata raye, daga yar magana nan sai ga saki abun haushi kuma ba saki daya ba har biyu ya karbi yaron sa babban wannan karamin ya kai wa yayarsa kawai ya bar min” “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un wannan mutuwar auren har da ku?” Na furta cike da bakin ciki. “Hmmm ai auren yanzu idan kin yi dace ki gode Allah, ba kafi ba na dara ko'ina fama ake mazan ne kamar an kwashe na kwarai, yanzu kuma baka san inda zaka fada ba” “Hafsat ba za a shirya ba? Tun da har ga yara?” “Tun da ya sake ni har yau be tako kafarsa gidan nan ba, Baba Halilo har aikawa yayi nemansa amman bai zo ba, kuma yana zuwa cikin garin nan tun da yan'uwansa ai duk suna nan kalilan ne a Zaria, ďan da ya karbe ma yana nan garin hannun yayarsa, mazan yanzu ba su da mutunci Uwani, Allah yasa dai ke kin dace” “Na dace sosai domin mijina irin mazan nan ne masu wuyar masu kuma na san har abada ba zan taba samun irinsa ba, amman na rasa Hafsa saboda ya rasu” Ta daki kirji da karfi ta dora hannun saman kai. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un Uwani Deen ya rasu?” Na daga mata kai ina hawaye. “Ashe kin san shi na aura” “Eh Anty Samira ta fada min tace Zaharadeen kika aura” Ta karasa ita ma hawaye na sauko mata. “Wayyo Allah Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Sannu Uwani Allah ya masa Rahama” “Ameen” “Yaushe ya rasu?” “Yau kwana goma sha uku” Ta share hawayenta tana min kallon mamaki sai ta waiga ko'ina ta matso kusa da ni. “Uwani? Takaba kika yi kika zo?” Na daga mata kai sai ta rufe baki da sauri. “Lafiya?” “Ba lafiya ba ke ma kin san lafiya ba zata saka na bar gida na dawo nan a cikin yanayin da nake ba” “Miya faru” “Zan fada miki amman ba anan ba, kuma ba yanzu ba, dan Allah karki ba Inna ta san ina takaba kuma karki fadawa kowa abun da zan fada miki” “Inshallah na miki alkawari babu wanda zai ji” Ta yi shiru tana kallona can kuma ta ce. “Yanzu babu wanda ya san kin zo nan?” Na daga mata kai “Amman hankalinsu ba zai tashi ba Uwani?” Na yi masa da kai ina hawayen da su kadai suke iya fadar halin da nake ciki. “Idan ban gudu ba, ba ni da wata mafita” “Saboda me?” “Saboda za a raba ni da abun da yake cikina” “Kamar ya? Ban gane ba” “Siyar na yi saboda rashin lafiyar Deen...” Ban karasa ba ta saka hannunta ta rufe min baki tana kallon kofar dakin Inna. “Bar maganar nan Uwani ba ri sai gobe mu yi ta, idan zan je mu je aikin gona sai mu tafi tare ai zaki iya ko?” “Ba nisa bana iya tafiya mai nisa yanzu ban san miyasa ba” “Cikin da kike da shi ne hala kin shiga watan haihuwarki ne?” “Aa wata takwas ne da kwana sha shida yanzu” “Kina kusa Allah ya sauke ki lafiya.” “Ameen” Na amsa ita kuma tana ta kallona cike da tausayawa. ABIEY POV. Kwanansa takwas a England suna buga wasa sannan ya dawo gida, a karo na hudu kenan da ya sauka a Masarautar be sauka gurin Ammy ba, daman ya kan kwatanta yin haka lokaci lokaci saboda Anty Amarya da kuma Mai Martaba da Ammy ta nuna masa yin hakan zai kara gyara alakar dake tsakaninsu. Anty ta san da zancen dawowarsa hakan ya saka ta shirya masa abinci mai kyau ita da yayanta duk kuwa da ta san ba lallai ne ya ci ba, idan ma ya ci wani ba zai ci wani ba, but ta saba a duk lokacin da yayi tafiya kuma ta san da zancen dawowarsa tana shirya masa abinci da kayan tabawa, already yana da direban dake dauko shi daga airport hakan yasa be kira Anty ya fada mata ya sauka airport ba, sai ganinsa ta yi cikin falon Narjis tana tsaye daga gafensa tana murnar ganinsa shi kuma waya makkale a kunnensa yana fadawa Ammy isowarsa. “Barka da zuwa mutanen turawa” Ya yi murmushi yana sauke wayar. “Anty” “Na'am ďana ya hanya?” “Alhamdulillah” Sai ka fara wanka ko abinci zaka fara da shi. “Food first” Ya fada yana cire jacket din dake jikinsa kana ganinsa kasan damuwarsa ta dan ragu domin fuskarsa a sake take. Anty ta yi mamakin ganinsa a haka rabon da ta ganshi haka an dade, sai dai bata ce masa komai ba sai kallonsa take har ya iaa dinning din tare da kanwarsa ta fara bude masa abinci. “Wannan ni na yi maka ni kadai” “Bari na dandana hmmmmm hmmmm dadi” Ya fada yana kara kai yayinda ya kai cake din a bakinsa. A dinning ya baje hajarsa ya ci ya koshi yayi nas sannan ya tashi yana jin cikinsa kamar zai fashe ya nufi dakinsa, kamin ya shiga ya ja ya tsaya jin kamar muryar Aisha tana dagawa saman ta Anty da alama wata gardamar suke, fasa shiga yayi dakinsa ya nufi kofar dakinsu su Aisha ya tura ya kofar ya tsaya daga bakin kofar yana kallonsu, Anty na tsaye Aisha na zaune fuskansu babu annuri a fuskokinsu. “Lafiya....” Ya tambaya har Aisha ta yunkuro zata fada masa sai Anty ta yi saurin dakatarta ita. “Babu ruwanki a ciki, idan ke ba a isa da ke ba shi an isa da shi” “What's going on here?” “Aure za a mana ni da Narjis sun gaji da ganinmu a cikin gidan nan” This time around abun dariya ya bashi domin murmushi yake mai sauti. “As how” “As ni an min miji” “Ke ko Narjis” “Ni din dai, wai be kamata ace za'ayi auren Narjis ni a bar ni ba, saboda haka ta hada ni da kanenta kamar ance mata na rasa miji ne, babu ranar da zan fita wani be gan ni yace yana so ba, ba za a min magana ace na fito da miji ba sai kawai ace ta hada ni wani kanenta kamar na yi kwantai yana da mata fa, ni a tsarina auren mai mata baya ciki, kuma na yi magana Anty tace zata ga laifi? Na rasa gane wane irin mulkin mallaka ake mana a gidan nan domin ba a banbanta mu da bayin cikin gidan nan ba” “Anty you can't force her idan bata ra'ayi” Abiey ya fada, sai Anty ta juyo ta kalleshi. “Idan bata ra'ayi sai ta bi ta hanyar lalaba a rabu lafiya, ba wai ta rika nuna kamar ta fi karfin ayi mata haka ba, har fa ikirari take idai sai ta aure shi to sai dai Mai Martaba ya koreta wannan magana? Su su yi min, sannan yanzu kuma ita ina kokarin taro ta tana subucewa” “Yes da na auri zuri'ar Lami kara na mutu ban yi aure ba, kara Mai Martaba ya koreni ba zan taba hada jini wannan Azzalumar matar ba” Aisha ta fada da iyakar gaskiyarta domin ta tsani abokan zaman mahaifiyarta. “Yanzu ki gabatar min da wanda kike so, idan na yi bincike na ga ya cancanta zan gabatar da shi gurin Mai Martaba” Abiey ya fada mata sannan ya kalli Anty ya ce. “Anty yanzu an daina zancen auren dole, please ki kyale su su zabi wanda suke so mana” Ya saki kofar dakin ya juyo zuwa dakinsa yana fadin. “Shiyasa bana son zuwa gidan nan kullum da kalar matsalar da take bullowa” Wani kamshin dadi mai kwantar da hankalin mai shakarsa dakin yake saboda turaren da Anty ta saka, saboda ta san danta mai son kamshi ne sosai. Sai da yayi wanka ya fito ya shirya kansa ya sannan ya hau saman gadon ya kwanta ya dauki wayarsa ya kira Sauban suka gaisa, sannan ya kashe ya kira yayarshi Dr Zainab yana tambayar ko sun ce gaisuwa. “Mun je mun kai mata abinci Ammy kuma ta bata kudi” “How is she?” “Lafiya kalau, amman ta so fada min magana.....” Murmushi yayi lokacin da Dr ta fada masa abun da Zahra ta yi masa. “Za ta yi saurin yafe mana ba, i hope dai baki fada mata wata maganar marar dadi ba?” Ta hade yawun bakinta. “Ban fada mata ba” “Thank You” Ya sauke wayar yana murmushi babu abun da idonsa suke nuna masa sai fuskar Zahra. Bayan Sallah La'asar ya shigo bangaren Anty ya shiga har dakinta ya zauna a saman kujera yayinda take zaune kasa tana cin abincin da bata samu ci ba da rana. “Mai Martaba zai dawo da wuri yau?” “Wallahi ban sani ba, da dai ka shiga bangaren Mama Lami ka bincika domin ita ke da girki yau” “Anty ke ma kin san ba zan shiga 6angarenta na tambaya ba, ina son magana da shi ne face to face” “To yau da gobe duka girkinta ne, kuma yau ina tunanin suna da wani taro da za'ayi na masu cutar shanyewar jiki da kungiyar unicef ta shirya har da Governor na ji ance zai je gurin” “Okay, zan tafi gurin Ammy Maybe gobe na shigo da wuri sai na yi magana da shi” Ya fada yana Mikewa tsaye. “Abiey karka aikata abun da zai bata tsakaninka da mahaifinka, Mama Lami tana shirya komai ne saboda tana son a samu matsala na fahimci shiyasa na so ku bi abun a hannu, idan ma yaron ya zo ta nuna masa bata sonsa a fuska in dai yana da hankali ai ba zai dawo ba” “Amman kika san abun da aka shirya a tsakaninsu? Ba lallai idan ta nuna masa yar fuska ya guje mata ba, ke dai kin Mama Lami ba zata aura mata kenanta haka nan kawai ba dan Aisha ta jidadi sai dai idan kanen ba mutumen kwarai ba ne ko kuma akwai abun da take hari” “Duk da haka dai ku bi abun a sannu, sun san yadda suke su gyara kansu gurin Mai Martaba hakan ya saka basa taba laifi a gurinsa, makirci sun iya shi har sun gaji, dan haka ku bi a sannu” “Inshallah” Ya fada sannan ya fice daga dakin, dakinsa ya shiga ya dauki keys dinsa ya sauko da kuzarinsa yana dialing number Sauban. Yana fita falon Sauban na picking call din. “Ya....” “Gida nake son a samo min?” “Gida kuma? Wane iri?” Sauban ya tambaya with confused din da ya bayyana har a muryarsa. “Irin wanda zan iya zama, gidan dake kusa da na iyayen Zahra, but don't let any body knows ni na siya gidan, idan ma babu babban gida a gurin ka siya min kanana sai a rushe su a gina upstairs ta yadda zan a iya hangen cikin gidansu” “Wait... Abiey mi zaka yi?” “Zama mana” “Why?” “Why? Idan ana maganar Zahra har kana tambayar dalilina na aikata abu? Kai kana ganin yanzu zan iya yin wasa na bari ta subuce min? No” Ya fada yana yi ma motar keys da hannunsa daya. “To amfanin me siyen gida a gurin zai maka?” “I want Zahra to be last thing da zan gani kamin na yi bachi, kuma i want her to be first da zan haifa fara gani idan na farka, duk yadda zan fada maka ina son Zahra ba zaka gane ba, Sauban ina son Zahra wani irin da wata kila nan gaba sai ka rabu da ni akanta, ni kaina ban san wane irin so ba ne” “Toh Aĺlah ya kawo maka sauki yasa Zahra alheri ce a rayuwarka, kuma ya baka ita yasa ta fahinceka” “Ameen Sauban baka taba burgeni irin yau ba thank you Dude” Ya sauke wayar tare da danna horn, wa motar dake gabanshi. “I can't wait Zahra na labarta mayuyacin halin da na shiga bayan rashinki i will tell you all about it, i love you more than i did before, i miss you just because i don't ses your face nothing change no one can take your place” Ya kai hannu ya shafa fadaddan kirjinsa yana murmushi. ZAHRA POV. A gidan na kwana sai na fi jin dadi bachi ma fiye da gida, domin a gadon karfe na kwana mai lilo, bayan na yi sallah na sake komawa bachi mai kama da na wahala, ban farka har sai da Hafsat ta tashi ni da kanta na sauko ina tambayarta inda zan samu brush da man goge baki sai ta kira wani yaro ta ba shi kudi ya siyo min na wanke bakina na wanke fuska na dawo dakin Inna na sha kuku na dora da dumame, duk abun da nake hankalina yana gurin su Mama, ko a wane hali suke yanzu? Sai dai idan na tuna dalilina na guduwa sai na ji kamar na tsira. Misalin tara muka kama hanyar gona ni da ita muna ta tafiya a hankali saboda cikin dake jikin Inna ma sai da ta so ta hana ni zuwa sai dai ganin na dage akan ina son zuwa da kuma Hafsat da ta saka baki ya saka ta bar ni muka tafi. Wadanda suke zuwa tare tuni sun yi gaba domin sun bakwai wasu takwas ba safe suka tafi ita ma saboda jira na ne ya saka bata yi sauri ba. Ba mu yi wata tafiya mai nisa ba na samu gurin na zauna ina hutawa sai wai na ke fadi saboda gajiya. “Anya kuwa zamu iya tafiyar nan dake Uwani?” “Akwai nisa sosai?” “Da dai mun fita da wuri da sai mu je gonar kusa amman yanzu kan sai mun yo yar tafiya kamin mu isa na san gonar dan Ali an cika ta yanzu sai dai mu tafi ta Idi dan bana son gonar da aka yi ma taro” “Amman dai ki rika min ruwa kar muje na fara jin kishin ruwa” “Bari na koma na siyo miki na leda” Ina zaune a gurin ta koma ta siyo min ruwa ta dawo sannan muka kama hanya, muna tafe ina mata labarin yadda komai ya faru har muka isa, ita kanta da nake ba labarin hawaye take balle kuma ni mai bada labari domin abun sai ya dawo min sabo na samu guri na zauna ina ta rusar kuka. “Ki yi hakuri Uwani, kuma ki zauna a nan har ki haihu amman kinsan mutanen karka ba kamar na birni ba ne, dole za ayi gulma duk da ba su sanki ba ace kin zo kin haihu a nan, kuma kin san idan ana takaba ba a kwaliya ba a zuwa ko'ina sannan zaki bar su Mama cikin tashin hankali da tunanin inda kike” “Na sani, wannan ma lalura ce ni dai idan zan tsira da abun da yake cikina ban zan damu da maganar mutanen gari ba” “Amman idan zaki bi shawarata ki samu wata wayar sai ki aika musu sako cewar kina cikin koshin lafiya kar su damu” Na daga mata kai ba dan na gamsu ba, domin asiri zai iya tonuwa idan na yi haka za a iya gane inda na ke. Mun yi tafiyar da ban zata ba sannan muka isa cikin katuwar gonar da ni dai ban ga iyakarta ba, karkashin wani ice na shimfida dankwalina na zauna ita ta kallon yadda suke aikin gonar ita da sauran matan da suke gonar, rayuwar karkara tana da matukar burgewa suna ta aikinsu suna hira kamar babu damuwa a tare da su suna cikin farinciki abu kadan sai dariya ga kokari ko wace mace na iya kokarinta dan kar wata ta fi wata, akwai rijiyoyi da yawa a gonar inda ake debo ruwa ga mai bukatar sha ko yin wani abu da su, sai dai rijiyoyin ba su da marafe a sake suke. ABIEY POV. A gidansu ya kwana uku sai washe garin rana hudu ya shirya da wuri ya dawo Masarautar saboda yana son magana da Mai Martaba, he got lucky lokacin Mai Martaba be fita ba sai dai yau din ma ba girkin Anty ba ne na Hajiya Kilishi ne, be shiga bangaren shi kadai ba sai da ya saka Anty a gaba, daman can ba saba zuwa yayi magana da Mai Martaba daga shi sai shi ba sai Anty ta masa iso, wannan ne karo na farko da zai saka bakinsa a alamurran gidan domin duk abunda ake babu ruwansa a ciki saboda Mai Martaba ya ware shi dabam, sai this time yana jin ba zai kyale ayi am Kanensa auren dole ba. A karamin falonsa suka zauna Anty akan kujera shi kuma a kasa, Mama Lami ce ta fara fitowa sannan Mai Martaba tana takawa a hankali tana washe hakoranta da ta kawata da hakoran zinari na Makka guda biyu, daman haka take yar barikin macece indai Mai Martaba yana nan to bata da gurin zama sai inda yake kullum tana can tare da shi ta kalallame kamar ta fi kowa sonsa da tausayinsa ko da kuwa ba girkinta ba ne, wani lokacin ta kan dagawa Anty Amarya kafa saboda tana nuna mata bata so, ba kamar Hajiya Kilishi dake mata kawaici ba saboda kansu a hade yake. Sai da ya zauna sannan ta zauna tana tana kallon Abiey domin sun gaisa da Anty tun shigowarsu kamin ta kira musu Mai Martaba amman Abiey be gaishe ta ba daman kuma be saba gaishe ba. Abiey ya masa kusa da Mai Martaba ya kwashi gaisuwa Mai Martaba be masa komai ba be kuma yi wata alama dake nuna ya amsa gaisuwar ba. Har Abiey yayi kamar ya ce da Mama Lami ta bashi guri zai yi magana da mahaifinsa sai kuma wata zuciyar ta raya mishi yayi maganar a gabanta domin ita ma ya shafe ta. “Allah ya kara maka lafiya magana nake son na yi, shawara ce wanda nake ganin kamar ita ce mafita a gurin Aisha da kuma mu gaba daya” Mai Martaba ya dan karkato kadan ya kalleshi. Abiey ya dora daga inda ya tsaya. “Mai Martaba kai uba ne ga kowa balle kuma a garemu mu da ka haifa, kuma na san ko ni da baka kauna ba zaka zaba min abun da zai cutar da ni ba balle kuma sauran yan'uwana” Sai da Mai Martaba ya hade yawu a lokacin da Abiey yake furta kalmar ko ni da baka kauna.... Ya sauke numfashi a hankali “Mai Martaba akan kawo maka karar wani ka yanke hukunci balle kuma cikin gidanka, daga wani gurin wata yar zata iya zuwa ta kawo maka koke kuma ka duba mata, Mai Martaba a game da mijin da aka zaba ma Aisha da Narjis ne dukansu basa so, Aisha tana da wanda take so Narjis kuma ba ma aurene a gabanta ba yanzu, na san ni ba kowa ba ne a gurin Mai Martaba amman hakan ba zai hana na fada maka wani bangare na abun da na fahimta akan abun da ake kokarin hadawa ba, ba wai ina ganin rashin dacewar hakan ba ne kawai ina ganin kamar a bawa ko wace hakkinta shi ne mafita kuma za a samu zaman lafiya” Mai Martaba ya kalli Mama Lami sai dai kamin yayi magana ta yi dariya ta kalli Anty ta ce. “Zuwarai kenan, yanzu wannan maganar ce ba zaki iya yi tsakaninki da Mai Martaba ba har sai kin sako Abiey a ciki? Haba dai wai yaushe zaki waye ne sai kace Mai Martaba wani dodonki ne” Anty ta kalleta. “Ba zan iya musa hukunci Mai Martaba ba shiyasa ban tukare shi da maganar ba, shi ma sun kuka masa ne shiyasa yayi shahadar yin haka” Mai Martaba yayi gyaran murya. “Ban cilastawa kowa a cikin yayana auren wanda basa ra'ayi ba, kuma ba zan cilastawa kowa ba shawara ce da Hannatu ta kawo ban kuma ce a cilastawa daya daga cikinsu ba, Narjis ance shi mutumen ya ga yarmu ne yana so Aisha kuma ita ta Hannatu ta kawo shawarar kuma ina tunanin kamar hakan zai dace, amman idam har basa ra'ayi ba zan cilasta musu ba” A take fuskar Anty ta cika da farinciki Mama Lami ma haka sai dai kowa ya ga nata ya san na bakinciki ne. “Allah ya saka da alheri, abun ai be kai ce da kin same ni da maganar ma da mun warwareta tsakaninmu” Mama Lami ta fada Anty dai bata ce komai ba, bayan tabe baki da ta yi Abiey ma farinciki yake domin be yi zaton jin haka daga gurin Mai Martaba ba. “Kai ma ai ya kamata ka fito mana da matar aure ka girma Abiey” Mai Martaba ya fada ba tare da ya kalleshi ba, kusan a rikice Abiey ya dago ya kalli Mai Martaba yana jin kamar ba daga bakin Mai Martaba maganar ta fito ba, not just him Anty da Mama Lami ma mutuwar zaune suka yi mamaki ya cika su. Sai dai hakan be hana Mama Lami karfin halin furta. “Gaskiya kam ni ma na so na yi magana domin na lura Zuwaira kamar abun be dame ta ba” “Ina masa maganar ai matar ce har yanzu be rika ba, kin san ďana babu ruwansa da sha'anin kula mata ba shi da wata wanda yake so a yanzu” Anty ta fada baki har kunne saboda jindadin Mai Martaba yayi maganar Abiey. “Ga yan'uwa ga mata a gari ai sai a nema masa, ko yarinyar da ta zo nan kwana kin baya ai sai a nema masa ita idan yana so yar gidan Mr Bashir Auta” Abiey ya kalli Mai Martaba baki sake yana kokarin ce masa akwai wanda yake so, sai dai wa? Ai ba zai ina cewa Zahra ba domin takaba take, sai dai space din yatsun hannunsa da na zuciyarsa na Zahra ne kawai saboda haka dole ya sama wa kansa mafita kamin Mama Lami ta kulla masa wani sherin. “Akwai wanda nake so” Anty ta kalleshi da mamaki Mama Lami kuma ta yi murmushin yake. “Maa Shaa Allah yar dangi ce ko daga nesa aka dauko, ashe ko zama be gan mu ba Abiey ya sake yin budurwa” Sai ya samu bakinsa da furta sunan yarinyar da be hada komai da ita ba. “Yasmin” “Maa Shaa Allah aiko ka zabo mai tarbiya Wallahi, dan Yasmin tana da mutunci” Wannan karon Anty ce ta yi maganar sannan ta fara yi ma Mai Martaba bayanin din Yasmin din da Abiey yake nufi domin kar Mai Martaba ya dauka Yasmin yar dan'uwansa, Anty ta ji dadi sosai daman ta lura kamar suna shan inuwa daya da Yasmin da Abiey, tun bayan rasa Zahra sai a yau Abiey ya furta yana son wata macen. “Zamu nema maka aurenta da yardar Allah” Mai Martaba ya fada, Abiey be san lokacin da ya kai hannunsa ya dafa kafafuwan Mai Martaba ba not because of yace zai nema mashi auren Yasmin, saboda ya nuna mashi kulawa wanda be taba nuna mashi ba. “Allah ya kara maka lafiya, na gode kwarai da kulawa” Mai Martaba ya dauke kai fuskarsa a hade kamar ba shi yayi furucin ba. Abiey da Anty suka fito bangaren Mai Martaba cike tsananin farinciki da suka dade ba su samu kansu a ciki ba. “Ban sha fada maka ba Abiey wata rana komai zai wuce Mai Martaba zai kaunace ka kamar sauran yan'uwaka koma fiye da sauran daman can ni na san Mahaifinka yana sonka, na tabbatar da ba kai ka yi masa maganar su Aisha ba wata kila da be saurari kowa ba, domin zai ga kamar an same shi da maganar ne kai tsaye ba tare da an raba ta gurin matansa ba” Abiey yayi murmushi yana kokarin zaunawa kan royal cushion din Anty. “Ban yi zaton haka da sauri ba” “Ba'ayi sauri ba Abiey shakara nawa ka yi a duniya kamin Mai Martaba ya kalleka ya furta maka wata magana mai dadi?” “Tun da aka haife ni sai yau, kuma dukan abun da ya faru a yau ya faru ne saboda ke da Ammy, Thank you so much Anty you're such a wonderful mom beautiful wife” Anty ta yi murmushi tana saka hannu ya tare hawayen daya cika idonta ganin hawayen Abiey dake sauka, ta kwalawa Aisha kira. “Humaira fito yayanki ya miki yaki” Abiey yayi saurin mikewa tsaye ya share hawayensa, sai ga Aisha ta fito da gudunta, Anty na labarta mata abun da ya faru ta rumgume Abiey cike da murna da farinciki. “And abun farinciki na biyu Abiey ya fitar da matar da yake so” Aisha ta nufo Anty cikin murna. “Wacece Anty?” “Yasmin step sister din Dr Zainab” Aisha ta daka tsalla ta dire tana ihu, sai Abiey yayi saurin sakatarda ita. “No.... Wallahi babu komai a tsakanina da Yasmin kawai na fadi sunanta ne saboda na kare kaina gudun kar Mama Lami ta min jaye jaye” “Amman a gabanka fa Mai Martaba yake fadar za a nema ka aurenta Abiey? Be kamata ka yi haka ba, bayan ka fadi kana sonta sai kuma ka zo yanzu kace mana ba haka ba, shi ma ai ba zai jidadi ba” “Kwantar da hankalinki Anty zan samu Yasmin zan yi magana da ita, na san yadda zan shirya komai lemme go and Ammy abun da Mai Martaba ya min a yau, jiki da zuciyata Zahra nake ajewa nata ne ita kadai” “Allah ya baka Zahra nan Anty ta fada min mijinta ya rasu” Aisha ta fada sai ya amsa yana jindadin addu'arta. “Amin My Sweet Sister” Cikin farinciki da mamaki Abiey ya bar gidan, kamin ya isa gurin Ammy har ya motsu saboda daddadan labarin dake bakinsa, daf da entrance din kofar falon Ammy ya faka motarsa ta miliyoyin nairaro ya fito ya shiga falon, Zaune akan laulausan center carpet ya hango Ammy plate din guava a gefenta, Jummai na zaune nesa da ita suna hira, da sauri karasa kuaa da ita ya kwanta a gurin ya dora kansa akan cinyarta, Jummai na ganin haka ta tashi ta ba su guri. “Me ya same ka na farinciki yau?” “Ammy yau Mai Martaba yayi abun mamaki” Tun kamin ta tambaya ya labarta mata, sai hawayen jindadi ya cika idonta. “Mahaifinka yana alfahari da kai Aliyu, kawai ba zai iya fada maka ba ne, Mai Martaba mutum ne mai son ya ga dan'uwa yana son Yan'uwansa Allah ya maka albarka kuma na ji dadi na yi murna da na ji kana son Yasmin I'm very happy” “No... kawai na yi kariya da ita na ni ban taba jin komai akan Yasmin ba” “Then why do you mentioned her name?” “Saboda na kare kaina ne mana, zan yi magana da Yasmin ai zan fada mata idan an tambaya tace bata so” Ammy ya shafa kansa tana murmushi wani irin son ďanta take fiye da sauran, ta kai hannu ta dauki wani bangare na guava da take ci ta saka masa a baki, sai ya lumshe ido yana taunawa a hankali. Kamar an tsikare shi sai ya tashi zaune da sauri gabanshi na mugun faduwa irin faduwar nan ta faruwar wani abu da ba alheri ba. “Lafiya?” Ammy ta tambaya tana kallonsa. “I don't know, gabana faduwa yake sosai look at this” Ya nuna mata hannunsa tsikar jikinsa har tashi take. “Something is wrong somewhere i hope Zahra is Safe” Ammy ya girgiza kai. “Zahra ko da yaushe Aliyu? What if a cikin yan'uwaka ne ma? Allah dai ya tsare ka yi ta ambaton Allah” “Ammy i used to feel this duk lokacin da wani abu ya faru da ita” Ammy bata ce masa komai ba, domin ya fara isarta da zancen Zahra yanzu kam. ZAHRA POV. Tun suna aikin ina kallonsu har bachi yayi gaba da ni, daman can ni da bachi ba ma rabo, bachin nawa be yi nisa ba na soma jiyo ihu da karar wani abu mai firgitarwa kamar cida, ina bude ban ga kowa ba a cikin matan da suke aikin kowace ta kama gabanta suna gudun ceton rai, ta inda nake jiyo karar na kalla wato samaniya, wani katon abu ne mai kama da karamin jirgi ya zo da gudu ya fado cikin gonar kamin na yi wani yunkuri har ya kai kasa, gudu nake son na yi amman tashin nawa ma sai ya zama aiki, irin jirgin nan ne mai kama da na yawo domin na sha ganin irinsa idan muka je dauko Abiey daga Airport, daga inda jirgin ya fadi zuwa inda nake kwance babu nisa sosai na samu kaina cikin wani irin tashin hankali marar misaltuwa, musamman hango mutumen da na yi yana kokarin ceton ransa wani bangaren na fiffiken jirgin ya danne, ga kuma wata na kokarin kamawa. Ba zan iya ganin rayuwa na bukatar taimako na kasa taimawa ba hakam yasa duk wani nauyin jiki da ciki da nake ji sai na neme shi na rasa da guduna irin na masu ciki na isa gurin ina jin abu na sauko a tsakanin cinyoyina zuwa kasan kafata kamar ruwa, dukawa na yi na saka iya karfin da nake tunanin ina da shi fifffiken sai dai abun ka da marar karfi ga kuma ciki ban iya dagawa yadda ya kamata ba sai dai na taimaka masa ya samu fitowa, yana fitowa ni kuma na fadi zaune a gurin ina wani irin uhu na fitar hankali domin cikina nake jin kamar zai bar jikina da karfin tsiya, mutumen da na taimaka ma ne ya saka hannunsa ya daga ni sama yana janye jikina kusa da jirgin saboda ya fara kamawa da wuta, be iya daukata gaba daya ba sai ya jani har kusa da wata rijiya ya aje kamar jiran ake ya yanje ni sai ya jirgin ya kama gaba daya da wuta mutanen karkarar da suka nufo inda jirgin yake suka koma da gudu ganin wuta, ni kuwa har lokacin ihu nake jinin kuma be daina min zuba ba.... [10/4, 9:55 PM] Oum_Nuwaira🥰: 1️⃣9️⃣ ABIEY POV. Da tunanin hakin da Zahra take ciki ya wuni ya kwana kuma ya tashi, gaba daya zuciyarsa ta ki natsuwa, so yake ya san halin da sahibar tashi take ciki kuma babu hali, duk wani tunani da yayi da wata hanya da yake ganin zai bi ya san halin da take ciki ko zai iya taimaka mata ta tashe masa. Suna fitowa sallah Isha'i wata dabarar ta fado masa, sai ya dauki keys din motarsa ya fice ba tare da ya fada ma Ammy gun da zai je ba, bata san fitarsa sai da ta ji tashin motarsa. Tafiyar minti ashirin ta kaishi gidan Dr Zainab, a bude ya tararda gate din gidan ita kuma tana tsaye tana jikin motarta tana magana da Babbar yarta Aslamiya. “Is like fita zaki yi” Ya fada bayan ya fito daga motarsa. “Aikin dare nake” “Uncle...” Aslamiya ta fada tana mika masa hannu suka yi shaking. “Go inside zan yi magana da Dr” “Okay idan ka koma kace ina gaida Ammy” Na daga mata kai yana murmushi, sai da ta shige falon sannan ya fuskanci Dr. “Ina son ki min favor” Ta kalleshi not saying anything. “So nake kije ki duba Zahra” “Seriously? Na ce mata me? Abiey yace na zo na dubaki? Da wani idon ma zata kalleni? Ka san yadda yarinyar ta tsane mu kuwa?” Ya sauke ajiyar zuciya. “Cikin hikima zaki yi, i just want to make sure she's fine jikina na raya min ba lafiya ba” “Abiey listen to me...” Kamin ta karasa ya tare numfashinta. “No Dr this will be the last favor please” Ta ja dogon numfashi ta sauke ba dan ranta ya so ba. “Zan je da safe” “No yanzu please kamin ki wuce gurin aikin, idan kin gani ko ji wani abu sai ki fada min a waya, but hankalina ba zai kwanta ba yanzu har sai na san halin da take ciki” “Kai ba mala'ika ba kai ba aljani ba kai ba kowa ba sai ka rika cewa kaji kaza kaza Zahra bla bla haba” “Ciwon so kenan mai hana mai yinsa zama lafiya” Na fada yana murmushin dake nuna shi kadai ya san abun da yake ji. “Amman zuwa gidan mutane da dare?” “Ya fi sirri ai, kuma kin ga yanzu ba zan iya bachi ba sai na san halin da take ciki” “Zan biya ta can kamin na je asibiti” Ta fada tana bude motarta ta shiga, shi ma ya juya ya koma gurin motarsa ya shiga sai suka fita a tare sai dai direction din kowa dabam. ZAHRA POV. Ban sake sanin inda kaina yake ba, ban kuma san iya dakiko ko mintuna da na dauka a haka ba, wata kila ma nayi awanin da yawa. Sai farkawa na yi na ji akan wani gado mai yawo ina bude idon sai na ji bana gani da su da kyau, can sama sama nake jin yaniyar mutenen da wasu yareka da ba zan iya shaidar turanci ko hausa ko larabci ko kuwa wani taren ne na dabam duk ba zan iya ganewa ba a wannan lokacin, iyakar abun da na sani kamshin iskar da nake shaka ya sauya zuwa wani daban da bana so, ga wani irin zugi da murdawa da marata ke yi kamar abun cikina zai fito, na dan motsa saboda azabar ciwon da nake ji sai na ji wata muryar da ban sani ba sunan kiran. “Malama Malama Malama” Kalmar nake ji yana ta maimaitawa, kwakwalwata na ta hadawa amman na gagara fahimtar ma'anar kalmar da kuma yaren da yake magana da shi. “Jini fa take bukata ta zubar da jini mai yawa...” Na sake jin wata maganar da ban fahimci me take nufi ba, can kuma na ji wani ya ce “Ku gwada jinina mana idan zai yi sai a saka mata” Nan ma van fahimci abun da suke fada ba, ni dai taimako kawai nake nema idan suka ce zasu raba ni da abun da ke cikina ma zan yarda saboda azabar da nake ji, na maida idon na rufe ina numfashi kamar ba ni ba, bana jin kuzari ko kadan sai azabar murdawar mara, ina jin lokacin da aka daura min wani abu a hannuna aka buga hannu aka shafa min wasu ruwa sannan aka soka wani karfe a cikin jijiyata aka cirewa, komai kamar mafarki nake ganinsa. “Hankali ba zai kwanta ba sai matar nan ta tashi she saved my life” Wannan karon da yare biyu akayi magana sai dai hakan be saka na fahimci komai ba. “Muje a gwada jinin” Shi ne last sentence da kunnena ya jiyo min, sai kuma numfashin ya tafi dan sauran hankalin daya rage min ya cire gaba daya. Wannan karon na bude ido da dan kuzarina idon nawa kuma nawa kar ina ganin komai farin ceiling na fara arba sa shi fanka na juyawa a hankali, can kuma na juyo idona gorar jini ce abun da na fara yin karo da ita kamin na kalli hannuna da jinin ke shiga ciki, sai kuma na juya dama da ni na kalli Hafsat dake kwance tana bachi, da alama dare ne sosai domin alamu ya nuna haka yanayin yadda na ji tsit ta ko'ina ga kuma hudun da nake hangowa ta windows, na kai hannuna na taba cikina sai kuma na dan dago na kalli cikin, wata katuwar rigar ce a jikina sai kuma zanen da aka rufe min kafafuwana da shi. “Alhamdulillah” Na furta cike da nauyin baki, ina tabbatar da godiya ta ga wanda shi kadai ke kashewa ya raya, na yunkura ina rika karfen gadon na tashi zaune na mika hannu zan riko gorar ruwa sai gora ta fado kasa wanda hakan yayi sanadin tashin Hafsat. “Uwani.... Sannu ya jikin” Na daga mata kai ina nuna mata ruwa. “Aa likitoci sun ce kar a baki komai sai an cire jinin” “Ina jin kishin ruwa sosai” “Ki yi hakuri kin ga dare ne, ba zai yiyu na kira likita ba tun da jinin ma be yi nisa ba gora ta biyu ce aka saka miki, kuma na karya alkawarin da na daukar miki na ji tsoro sosai saboda jinin da yayi zuba na dauka mutuwa zaki yi, na kira Anty na ce ta fadawa Mama kina nan gurina kuma muna asibiti dake” Ban ga laifinta ba, domin ko nice a halin sa take ciki abun da zan aikata kenan. “Na ma dauka haihuwa ce sai suka ce ba haihuwa ba ce wai matsala dai kika samu” Na koma na kwanta na lumshe ido sai hawaye suka ce sallamu alaiki, idon da ban sake budewa ba kenan har safe, shi ma saboda na ji ana kokarin cire robar jinin dake hannuna ne. “Sannu Madam” Likitan ya fada yana sakar min murmushi sai na amsa masa da kai na tashi zaune. “Likita za a iya sallamata a yau?” “Aa gaskiya muna bukatar mu tabbatar da kin samu lafiya sosai” “Ba ni da kowa a nan likita ina son na koma Kano gurin mahaifiyata a can ma za a iya kula da ni” “Baki da wanda zai zo zaria yayi jinyarki?” “A zaria nake?” Na tambaya ina kallon Hafsat sai ta daga min kai. “Eh ke da shi nan aka kawo ku saboda a baku taimakon gaggauwa, amman shi mutune na ji ance ya koma kano tun jiya saboda ba wani ji rauni sosai ba” Na kalli likitan. “Ka taimaka min da Allah, hankalin mahaifiyata zai tashi idan ba a kano nake ba” “Toh indai haka ne sai dai mu miki transfer daga nan zuwa asibitin dake Kano” “Eh na yarda hakan zai fi min sauki ma” Da wannan ya yarda sai ya fita ya bar wata nurse tana balla magani ta bani, sai na karba na aje har sai da na karya da lafiyayyen abinci da aka kawo mana daga wata babbar hotel dake zaria sannan na sha maganin, ina gama sha likitan ya shigo tare da Nurse din dazun ya mika min takardar transfer. “Gashi sannan maganinki idan aka miki allura ba zaki sha magani ba, kuma ki tabbatar kije aaibitin da muka turaki, sannan Alhaji Bashir yace idan kika farka a asanar masa, na fada masa kin farka har kin nemi transfer yace a miki kuma ya vada umarnin daukar nauyin duk wani ciwo na ki, saboda haka na kira likitan dake Aminu Kano na sanar da shi komai idan kin isa sai ki nemi Dr Hassan ki ba shi wannan file din wannan kuma number wayarshi ce” Ya karasa yana miko min number da kuma file dina. “Na gode Likita” Har ya juya sai kuma ya juyo ya kalleni. “Uhm yace ki dan jira za a kawo miki sako kamin ki tafi” Na daga masa kai. “Allah ya bada lafiya, ko da yake dai mun yi solving din komai sai dai dan a kara tabbatarwa” Wannan karon Hafsat ce ta yi masa godiya, ya fice tare da nurse din yana murmushi, kana ganinsa kasan irin likitocin nan ne masu saukin kai. Yana fucewa na kalli Hafsat na ce. “Ina jakata?” “Gata nan na aje miki karkashin gado, daman na zo da ita ne da tunanin ko za a kashe kudin magani sai gashi mutumen ya dauki nauyin komai ba a taba kudinki ba” “Dan Allah ki raka ni na hau mota kin ji” “Kin ji fa abun da likitan ya fada yace mutumen yace ki jira za a kawo miki sako, kuma ba ki sani ba ko su Mama suna hanya” “Mama ba zata zo nan” “Saboda me?” “Na san wacece mahaifiyata Hafsat, ba zata zo nan ba, muje ki raka ni na hau mota” Na share hawayena na tashi tsaye tare da gyara daurin zanen dake jikina. “Tufafinki fa suna gida na bada a wanke saboda zanen duk ya lalace da jini, amman ga hijab dina nan na kawo miki” “Na gode” Na furta ina jin wani abu kamar kwallo yana min yawo a zuciya, duk yadda Hafsat ta so na tsaya dan karban sakon da likitan yace za a kawo ban tsaya ba, saboda zuciyata ba a can take ba, kuma ban san wane kalar sakon ba ne. Ina takawa a hankali har muka fito cikin asbitin tun daga yanayi da tsarin aaibitin ya isa ya sanar maka cewar asibitin ta kudi ce irin wannan mai zaman kanta, domin an tsara asibitin da kyau kai kace ma a garin Abuja kake ba Zaria ba, muna fitowa Hafsat ta tare min mai Napep ta saka yan komatsan data kwaso na tabarma da sauran abincin da muka rage da kuma yan kayanta, sannan na shiga ita ma ta shiga ta fadawa mai Napep din inda zai kaimu, yana fara tafiya na bude jakata na kirga 5k a cikin kudina na mika mata. “Ga wannan ki bawa Inna” Na sake kirga 5k na mika mata. “Wannan kuma na ki” “Haba Uwani ni ban baki ba kuma zan karba?” “Da bani da su ai ba zan baki ba” “Na gode Allah ya saka da alheri, kuma dan Allah ki yi hakuri da kiran Mama da na yi na rikice ne shiyasa” “Ba ki yi laifi ba ni ma abun da zan aikata kenan idan kika samu kanki a cikin wannan halin na gode da kulawa kuma ki min godiya a gurin Inna” “Me muka miki na godiya, ai kin fi haka idan ma mun yi” Muna isa tashar na fita, sai ita ma ta fito. “Ki koma Hafsa ai zan iya shiga mota da kaina na gode” Bata ce komai ba sai ta rumgume ni ta fashe da kuka. “Allah ya yaye miki damuwarki kawata ya miki mafita” “Ameen” Na furta ni ma cikin kuka sannan na sake ta. “Sai wata rana Hafsat idan muna da rabon ganawa” “Nan da kwana biyu zan zo Kano na dubaki da yardar Allah, Allah ya kaiki lafiya” Na ciro kudin mai napep na mika masa sannan na nufi gurin da aka faka motar Kano. Mun kusa awa daya a gurin sannan motarmu ta daga zuwa Kano, muka isa cikin lokaci ina fita motar sai gabana ya soma faduwa, sai na fito bakin tashar motar sannan na tari napep na hau na fada masa inda zai kai ni, kamin mu isa ina ta saka yadda zan fara yi ma Mama bayani amman na rasa mafita, domin har yanzu ban san me zan rika na yi amfani da shi a matsayin dalilina na guduwa ba, haka dai na fito Napep din ina jin kamar ace zan gudun ba, domin abun zai zame min matsala ne a yanzu, dari biyu na bashi sannan na juya ina tafiya kamar wanda bata son takawa na nufi kofar gidanmu, na kusan minti hudu a tsaye sannan na aga kafata na shiga cikin gidan cike da nauyin baki, ban san ta inda zan fara sallama ba. Kamar rai ya ga mutuwa haka na ji lokacin da na yi arba da Mama a zaune tana gyaran wake, sai ta dago ta kalli kofar domin ganin wanda ya shigo muna yin ido hudu sai annurin fuskarta ya canja ya maida kanta gurin gyaran wanken da take ta cigaba ba tare da ta ce da ni komai ba. Ni kuwa na yi tsaye a gurin kamar an dasani na san halin Mama idan ta yi fushi bata da kyau ba kasafai take saukowa da wuri ba. Na cira kafata na fara takawa sai ta dakatar da ni. “Tsaya nan karki karaso nan, me zaki zo ki min?” “Ki yi hakuri Mama dan Allah” Na furta hawaye na sauko min muryata kamar mai koyon magana. “Kin san da hakuri kika tsallake kika bar dakinki zuwa wata uwa duniya? A tunaninki idan kin gudu mutuwa zan yi? Na rasa uwa ban mutu ba, na rasa uba ban mutu ba, na rasa mahaifinku tun kuna kanana na rayu da ku babu taimakon kowa sai Allah kuma ban mutu ba, sai dan kin gudu ke kaidai zai saka na fadi na mutu? To na yafe ki kije duk uwa duniyar da zaki je, abun magana ne daman kin ja ma kanki kina takaba kin gudu an rasa inda kika yi” Na saki jakar hannuna ban damu da cikina ba na durkusa kasa na hade hannayena ina kuka. “Mama dan Allah ki yafe min ban yi haka dan na bata miki rai ba, Mama baki san abun da ya saka na gudu ba...” “Na sani, Maryam ta fada min komai tashi ki fita...” Ta amsa min tana mikewa tsaye ta nuna min kofa. “Mama dan Allah....” “Ki fita na ce karki bari na maimaita kalmar nan a karo na uku Zahra...!” Na tashi tsaye da sauri domin har yanzu ban daina tsoron dukan da Mama take min lokacin da ina budurwa ba idan ta fara bata min da sauki sai an kawo min agaji. “Ki tafi duk inda zuciyarki ta raya miki ki gani ni mutuwa zan yi” Na dauki jakata ina hawaye na fice daga gidan ina tafiya kamar zan fadi haka na nufi titi, wata zuciyar na raya min na tafi gurin Yaya Maryam ko Hajiya, sai dai me? Za su karbe ni ko kuma kyarata za su yi kamar Mama? Kara ma Yaya Maryam amman Hajiya da wane idon ma zan kalleta? Na yi tafiya mai nisa a fada ina tafe ina hawaye da nadamar abun da na aikata tun da fari, sannan na samu gindin wata bishiya na zauna na huta sannan na matsa kusa da wani mai shago na siye ruwa na sha na nufi titi na tari adaidata sahu na hau na fada masa unguwar da zai kai ni. Har kofar gidana ya sauke ni na bashi kudi ina ta jin kunya kar na gada ido da mutanen unguwar domin ban san ta ina zan fara amsa tambayoyinsu ba, bayan na sallame shi na karasa na taba kofar gidan sai na jita a rufe, ji na yi kamar na fadi a gurin saboda damuwa da ta taru ta tsaya min akai, sai dai babu dama saboda unguwarmu ne kuma mutanen unguwar za su sani za su fito su tambaye ni me yake faruwa. Haka na juya na koma titin na tari wani Mai Daidaita na hau ya mayar da ni gidan Mama, shi ma na sallame ni na nufi kofar gidan da tunani da kuma addu'ar Mama zata hakura ta yafe min ta karbe ni. “Au dawowa kika yi?” Shi ne abun da ya fara fitowa daga bakinta a lokacin da ta yi arba da ni. “Mama na je gidan a rufe yake, dan Allah ki yi hakuri ki bar na zauna nan ba ni da inda yafi min nan” “Kin san da wannan kika kama kafa kika maida gaba gabas kika gudu? Kina takaba da tsohon ciki?” Ta tashi ta shiga dakinta bata dade ba ta fito ta jefo min makullin gidana. “Ashe kin san da gidan kika bar shi kika tafi, to ga makulli nan dauki ki juya” Na duka na sauka wasu irin hawaye masu zafi suna sauko min. “Mama na tafi?” Na tambaya ina jin kamar tace min aa Zahra dawo ki zauna. “To har sai na fada miki? Kin manta halina wai?” Na juya na fara tafiya kamar bana son fita na bar gidan, kamin na isa titi ma wata uwa da ga duniya ce, haka na sake tare wani mai daidaita na shiga ya maida ni gidana, na saka makullin na bude na shiga ciki ina ganinsa kamar kangon gida, tsaye na ji a tsakar gidan bayan na tura na kara kofar ban rufe ba, ina kallon kofar falona, ji nake kamar na bude baki na ce Deen na dawo ya amsa min, ji nake kamar ya fito ya rumgume ni yana murna da ganina, amman babu hali saboda babu shi a tsaye. Na karasa na bude falon na shiga na zauna sai na rasa ta ina zan fara kuka, ina zaune har aka kira zahar na tashi na yi alwala na yi sallah na yi ta ambaton Allah har wata sallah ta tararda ni, na gabatar da ita na kwanta a gurin ina jin yadda yunwa ke neman dauki a cikina, amman bana da kuzarin yin komai sai kuka. Har aka kira magariba babu wanda ya shigo gidan saboda babu wanda ya san na dawo sai Mama ira kuma na san ba fadawa kowa za ta yi ba saboda tana fushi da ni, kuka kan a ci shi har na koshi daker na samu na lallaba na yi sallah magariba a zaune na kwanta ina da tunani can na ji an kira isha'i na tashi na yi, sai zuciyata ta cika da kewar mijina mutumen da baya barina da yunwa no matter how yake fushi da ni, mutumen da komai zan masa a duniyar nan baya iya barina cikin bakinciki da damuwa. Tashi na yi na bude jakar da tufafinsa suke ciki na fiddo wani fari yadi nasa da yake yawan sakawa ranar jumma'a na dauki filona dake kan katifa na saka masa rigar na kwantar da fito sai na dora kaina ina ta jin kamshin jikinsa, halshen dake cikin bakina har rawa yake saboda kukan da nake jikina na amsawa ta ko'ina. A rayuwa babu bakincikin da ya kai na miji ya tafi ya bar matarsa tana begensa, abun nan yana da matukar zafi da ciwo, ka tuna cewar ba zaka kira mutun ya amsa maka ba ba zai san halin da kake ciki ba, kuma ba zai taba dawowa ba sai dai taka zuciyar tai ta begensa. “Tafiyarka ce ta haddasa komai Mijina, mutuwar ta yaye farincikina ta gusar da hasken da yake zuciyata, ina ma ina ina ma ka dawo Deen ga Zahra na ta begenka” Na karasa ina fashewa da wani irin kuka mai taba zuciya da dan kuzarin da ya rage min, ina cikin wannan hali wutar unguwar ta dauke gaba daya. Can na ji an turo kofar gidan ana haska ko'ina da fitila mai haske. “Sallamu Alaikum” Wata murya da nake jin kamar na sani tana ta doko sallama, sai dai ba ni da kuzarin amsawa sai na kuka, har cikin falo aka shigo wannan karon sunana ake kira sai na gane mai muryar tun kan ta karaso cikin dakina. “Zahra...” Ta haska ni da fitila bana iya komai sai kuka. “Subhanallahi” Ta furta tana karaso kusa da ni da sauri. “Miya faru kika zauna ke kadai kuma cikin hudu babu ko haske” Na mika mata hannuna sai ta miko min sannan nata ta tashe ni zaune ta haske fuskata da kyau, sai ta yi saurin aje wayarta akan tafitar ta rumgume ni. “Na gode da kika zo Anty Zainab, na gode...” Na furta cikin wani irin kuka ina kankanmeta... *Allah yasa ba ni kadai Zahra ta tabawa zuciya a yau ba* 😪 [10/6, 2:52 PM] Oum_Nuwaira🥰: 2️⃣0️⃣ Kuka na yi sosai a kafadarta sannan ta dago ni ita ma idonta na zubar da hawaye ta ce. “Miya same ki Zahra? Miya kike wannan kuka haka?” Na yi shiru domin ban san me zan fada mata ba. “Kina zaune ke kadai acikin duhu daman ke kadai kike kwana a gidan?” Na girgiza mata kai. “Guduwa na yi sai yau na dawo, kuma Mama ta ki ta karbe ni” “Amman miyasa kika gudu?” Na kalleta kamar na fada mata sai kuma na ga fadin ba shi da amfani saboda ba zata sama min mafita ba, kuma dan'uwanta ma ba zai min ba domin be taimake ni a lokacin da nake bukatar taimakon ba balle yanzu, kuma fada mata zai kara bayyana sirrin dake rufe ne, a tonawa kaina da ita kanta Jamila asiri. “Babu komai” “Babu komai zaki gudu? Look Zahra na san kina jin haushina ni da dan'uwana amman wannan matsalar da kike ciki ba abu ne da ya shafe ni ko ya shafe shi ba, ki kawar da komai a ranki ki fada min damuwarki wata kila zamu iya samun mafita?” Na girgiza mata kai. “Ba komai, me kika zo yi nan?” Ta yi murmushi ta kai hannu ta shafa fuskata. “Ba komai na zo na duba lafiyar Kanwata ne kawai zan je gurin aiki sai kuma na tsaya ta nan na dubaki” Na sauke kaina kasa. “Yanzu fada min kina son Mama ta dawo ta zauna ne ko kuwa kina son ki koma gurinta ne da zama?” “Zan koma gidanta” “To taso muje” “Tace ba zan zauna ba, fushi take ni” “Zan mata magana kuma zata ji i promise” Na sauko saman katifar na dauki hijab dina na saka na dauki makullin gidan, a tare muka fito ita ta rufe min gidan ta saka ni gaba har gurin motarta ta bude min gaba na shiga na zauna sannan ta zagaya ta shiga ta tashi motar, har muka isa gidan Mama hawaye na ke ga idona ciwo yake saboda kukan da na yi, ko da muka doshi kofar gidan sai na tsaya daga baya tana ganin haka sai ta riko hannuna ta wuce gaba sai da ta yi sallama aka amsa mata sannan ta shiga cikin gidan. Mama ta fito daga daki tana kallonta da ni kamin ta ce. “Sannu da zuwa” “Mama ina wuni?” “Lafiya kalau” Ta amsa da muryar da ke nuna har yanzu bata sauka daga fushin ba. “Mama zamu iya zama?” Anty Zainab ta fada sannan Mama ta dauko tabarmar dake jingine ta shimfida mata muka zauna kaina na kasa. “Mama na taso zan je gurin aiki sai na tsaya ta gidan Zahra da zimmar na duba halin da take ciki, sai na same ta tana zaune ita kadai a dakina tana ta kuka idonta har ya kumbura, ga hudu babu wuta a gidan na tambaye ta abun da ya faru bata fada min ba, sai tace kin ce ba zata zauna a gidanki ba haka ne?” Mama ta kalleni sannan ta amsa mata. “Haka ne” “Ban san girman laifin da Zahra ta aikata miki ba, amman a yanzu Zahra bata da wani gata sai na ki bata da wanda zai tsaya mata sai ke, tun da mijinta baya raye mahaifinta ma baya raye duka duka yaushe Deen ya rasu? Bata gama fita daga jin zafin rashin mijinta ba sai kuma ace ta fuskanci wata damuwa daga gareki? Ke fa uwace Mama kuma kin san yadda mace take ji idan ta rasa miji domin ke ma kin rasa mahaifinta, idan kika ce Zahra ba zata zauna tare da ke ba gurin waye kike son ta je ta zauna? Dan Allah ki yafe mata idan wani abun ta yi miki ki tausaya mata ki dubi halin da take ciki, ta ya zaku barta can ta zauna ita kadai kamar wanda ta rasa kowa?” Mama ta sauke ajiyar. “Shikenan ya wuce na gode” “Yanzu zata iya zama a gurinki ko? Ko kuma zaki koma can inda take ne ki zauna?” “Aa sai dai ta zauna a nan” “To na gode Mama Allah ya saka da alheri” Sai a lokacin na dago na kalli Mama Anty Zainab kuma ta mike tsaye ta yi mana sai da safe ta fice. “Mama kin yafe min?” “Idan ban yafe miki ba tsine miki zan yi Zahra?” Na tambaya kuma ta amsa min da muryar kuka. “Akan me zaki aikata wannan abun? Yanzu da kin jefe kanki a wannan halin ya kika ji? Ke idan zaki yi abu ba ki san ki yi tunani ba? Akan me zaki siyar da abun cikinki akan mutunen da be cancanci haka daga gareki ba? Ina kika taba jin an siyar da cikin? Sai kasashen inyamurai” Kalmar akan mutumen da be cancanci haka daga gareki ba ya fi komai tayar min da hankali. “Mama Deen din ne be cancanci haka daga gareni ba? Ko dai kin manta waye Deen?” “Na san waye shi mana ai yana kaunarki yana sonki amman ba so da kauna na gaskiya ba, idan yana sonki akan me likitoci zasu ce ya ke6e kansa daga kusantar ki amman be yi haka ba? Kuma mahaifaiyarsa ta san da wannan ta kyale ku? So yake ke ma ki kwashi ciwon ki wahala ko? Sannan da zai rasu ma cewa yayi ki masa alkawarin ba zaki taba auren kowa ba har ki mutu wannan ma duk soyayya ce” Na girgiza mata kai hawaye na sauko min. “Mama baki fahimta daidai ba Deen yana so na sosai” “Toh Allah ya bar kauna Laila matar Majnoon” Tana fadar hakan sai ta mike tsaye ta shige cikin dakinta ta bar a gurin ina ta aikin rusar sabon kuka, gaba daya sai zuciyar ta ki yi min dadi gaba daya na ji ina ma a can na zauna ni kadai ban zo gidan ba, da ban ji wata magana marar dadi a akan Deen ba. Dayan dakin da na saba kwana lokacin da ina budurwa Mama ta gyara min na shiga na kwanta rai babu dadi har safe. Bayan na gama sallah asuba na koma na kwanta amman na kasa bachi har Mama ta gama shirya abinci safe ta shigo ta kawo min, sai na tashi da sauri ina gaisheta. “Ina kwana Mama” “Lafiya kalau, Zahra ki yi hakurin da maganar da na yi miki jiya kin ji? Tuntuben halshe ne da rashin fahimta” Ta fada min fuska a sake sai na daga mata kai jina a sanyeye, zauna ta yi kusa da ni tana sauke ajiyar zuciya. “Ban zan miyasa kika aikata haka ba tare da neman shawarata ba, Zahra ni mahaifiyarki ce kaf duniyar nan baki da kamar ni, kowa ya so ki to a bayana yake kuma ba zan taba son abun da zai cutar da ke ba ko ya jefaki a cikin wata matsala” “Mama na yi tunanin idan aka yi ma masa aikin zai rayu ne, kuma na san idan na fada muku zaku iya hana ni” “Ba zan bari ki aikata ba tabbas da kin fada min, domin ransa ba a hannunki yake ba a hannun Allah yake, amman yanzu kin riga kin aikata da zaki ji shawarata da na shawarce ki da shawarar da zata fidda ke da mu” Na kalleta. “Wace Shawara ce Mama?” “Ki dauki kaddara wanda ita ta saka kika amince da wannan abun tun farko, kin riga kin yi alkawari tun farko kuma karya alkawarin na nufin bada wani adadi na kudi da ko an hada ni da ke an siyar ba zamu yi wannan kudin ba, kuma zaki jawa kanki abun magana ne kawai yan jarida su taru akanki ana miki tambayoyi haka kuma kutu zata hukuntaki, idan kuma kika gudu zaki iya jefa kanki a cikin hadari ne irin wanda kika saka kanki a yanzu” “Mama na bata cikin kenan?” Ta daga min kai. “Shi ne kawai mafita ni da ke” Wani abu na ji ya tsaya min a zuciya na juya kaina na juyo na rasa ina zan saka kaima na ji sanyi, ina zan jefa rayuwata na samu sassauci. “Shikenan Mama zan bata” Na amsa ina hawaye ita ma hawayen take tana kallo. “Da kin shawarce ni tun farko da baki aikata wannan abun ba, da yanzu baki jefa kanki a cikin wannan halin ba” Ta rumgume ina ta kuka babu kakkautawa. Misalin sha daya Yaya Maryam ta zo gidan ita kanta na lura tana cikin damuwa musamman da na fada mata shawarar da Mama ta ba ni. “Mama ba zata baki shawarar da zata cutar da ke ba, ki yarda ki bada ďan karki sake aikata abun da zai saka ta yi fushi da ke, domin ranta ya bace sosai da na fada mata shiyasa ta yi fushi ko a lokacin da aka kira aka fada mana halin da kike ciki cewa ta yi ba zata je ba kuma ni ma ba zan je ba” “Na aminta Yaya Maryam zan ba au duk abun da na haifa Allah yasa hakan shi ne mafita a gareni” “Ameen yar'uwata” Na kwantar da kaina jikinta ita kuka ni kuka, Mama ma dake zaune bakin kofar dakinta ina jiyo shisshikar kukanta wata kila ta ji abun da muke tattaunawa. “Yaya Maryam dan Allah zaki je asibitin ki karbo min number likitan?” “Saboda me? Me zaki yi da ita?” “Na fada masa cewar ina nan, kuma na fada musu edd na domin wacan da na fada mata ba na gasken ba ne” “Zan je na karbo miki Inshallah” Da taimakonta da karfafa guiwa na ci abinci, ina gamawa sai ga Hajiya da wasu yan'uwanta da Bahijja gaba daya Hajiya ta canja kamar ba ita ba domin tana da jiki amman yanzu duk ta zube.ta rame sosai, ta nuna min damuwarta na tafiyar da ni bada sanin kowa ba, sannan ta karfafa min guiwa yadda zan sarrafa rayuwa na samu sukuni saboda Mama ta musu karyar cewar na kasa zama gidan ne saboda Deen baya ciki. “Daman na sani sai kin shiga damuwa, amman ki bar wa Allah komai Zahra shi zai miki mafita ya yaye miki komai” Hajiya ta fada, a gidan suka wuni har dare sannan suka tafi, lokacin da mijin yaya Maryam ya zo sai suka tafi gidana ita da shi suka kwaso min tufafina na sakawa suka kawo min sannan suka wuce. Washe gari bata dawo gidan ba sai da number likitan ta fada min a gurinsa ta karbo da kanta, sai an saka line a wayar Mama na saka miki number na kira shi be daga ba har ta yanke ina kokarin kiransa na biyu sai gashi ya kira. “Hello....” “Zahra ya kike?” “Lafiya Kalau” “Maa Shaa Allah, wannan line ki ne?” “Eh nawa ne” “Wanda ta zo karbar numberki ta fadi min cewar yayarki ce hope dai bata san da maganar komai ba?” Na dan yi shiru sannan na amsa. “Ta sani” “Haba Zahra ya zaki yi haka? Abun da ya kamata ace sirrinmu ne? Ta ya zaki sako wata a ciki?” “Yar'uwata ce idan bata sani a taya zan kiraka ka karbi haihuwa ta? Dole sai wani na kusa da ni ya sani bayan ita babu wanda ya sani” “Amman kamata yayi kamin ki sanar da ita ki fara shawartarmu saboda wannan abun da kike ganin sai iya jefa mu a matsala mu duka” “Ni dai na kira na fada maka cewar edd da na fada ma Jamila ba daidai ba ne, na duba takardar zan haihu nan da sati uku Inshallah” “Amman miyasa kika canja da farko?” “Ba canjawa na yi ba, na fada ne ba tare da na duba ba ashe ba daidai na fada ba” “Shikenan zamu shirya komai kamin lokacin, amman zan zo na karbi takardar anjima” “Amman bana gida ina gidan mahaifiyata zan aiko maka addireshin yanzu idan mun gama waya” “Amman ba matsala idan na zo?” “Ka kira ni kamin ka zo sai na san yadda zan yi na fita” “Okay” Ya kashe wayar. Dare na yi sai ga kiranshi ya shigo na yi zaton da Jamila zai zo sai yace min “Ga almajiri nan zan aiko idan ya shigo bara ki kira shi kamar zaki ba shi sadaka sai ki ba shi takardar ya kawo min” “Toh” Na amsa sannan na tashi na shiga daki na dauko takardar na rike a hannu, almajin na yin bara na kira shi ya shigo na mika masa takardar ba tare da nace masa komai ba shi ma ya karba ya fice be ce min komai ba. Fitarsa da kamar minti goma Dr Hamid ya kira ni. “Na karba, amman ya kamata idan zaki haihu ki kasance ke kadai sai wannan yayar taki da ta san komai so that mu samu yin aikin ba tare da sanin kowa ba” “Toh” “Sannan na ba Jamila number wayarki zata kira ki” “Tace min zata yi tafiya” “Eh taje Abuja kwananta daya ta dawo saboda wata yar matsala da mijinta ya samu, zamu shirya haihuwarta kamin taki haihuwar saboda komai ya zama daidai” “Toh” “Kuma idan kina jin wata matsala ki fada min mu tari abun da wuri” “Bana jin Matsalar komai” “Yaushe zaki koma awo?” “Ranar Laraba na dade ban je ba amman zanje wannan larabar” “Shikenan idan an fada miki wata matsalar ki kiri ni ki fada min” “Toh” Na amsa sannan ya kashe wayar, tun daga wannan ranar ban sake lafiya ba awon cikin ma da nace zan je ban je ba saboda ciwon zuciya da ya matsa min kuma ban fadawa kowa ba saboda kar a matsa min da zancen zuwa asibiti, ni kadai na san halin da nake ciki, kuma a kullum sai Dr ya kira ni ya tambayi lafiyata na amsa masa da bana jin komai a lokacin da ya tambaya ko naje awon sai na amsa masa da eh sun ce komai lafiya yake, na kwashe kusan sati daya kullum a daki nake bana fitowa sai idan zan yi fitsari so alwala wani lokacin ma sallah a zaune nake yinta saboda cikin ya kara yi min kasa a yanzu, ga tunanin da nake ya haifar min da rama sai cikin ya janye ni na koma kamar wata yar tsana. Ranar wata jumma ina kwance daki rike da carji sai ga kira ya shigo wayata da bakuwar number, na dade ina kallon number har kiran yana daf da katsewa sannan na amsa na kara wayar a kunne. “Hello” “Zahra ce?” Na ji muryar Jamila “Eh ni ce ina wuni” “Lafiya kalau, Dr ya fada min abun da kika yi na shigowa da yar'uwarki cikin maganar nan, Zahra kina ganganci da rayuwarki kuma kina kara jefa kanki a cikin matsala ne, domin na rantse miki da Allah idan maganar nan ta fita sai na aikata miki abun da baki yi tunanina ba, kin san wacece ni? Kin san su waye dangina? Kin san waye mijina? Kin san yan'uwan mijina? Fitar sirrin yana nufin rasa aurena rasa gatana kin kuwa san idan na rasa daya daga ciki sai na aikata miki abun da baki taba zato ba, kin san ba zaki iya ba waya cs ki fara? Ki gargadi yar'uwarki karta kuskura fadawa kowa? Kuma karki kuskura cewa zaki yi wasa da hankalina ko na Dr kika fada min fake date na Edd dinki sai yanzu zaki fada mana na gaskiya? Wani abu kike shiryawa ko? Sai na baki mamaki Zahra kina fama da talaucinki kin samu an taimaka miki kike kokarin jefa ni a matsala, wannan ya zama na farko kuma na karshe da wani zai ji zancen nan? Kuma da zarar kin mallaka min ďana ko ƴata ki manta da ni a rayuwarki dan kar zuciyarki ta raya miki wani abu” Bata jira ta ji amsa da zata fito daga bakina ba ta kashe wayar, ni kuwa na tashi zaune ina mamakin karfi hali da karfin duniyar da ya rufe mata ido take fada min magana son ranta, rushewar wani abu na ji kamar gini hakan yasa na tashi da sauri na fito ashe zan iya gudu da tsohon cikin idan wani abu ya same ni, domin a tunanin wani bangare na ginin gidan mu ne ya fadi. Ko da na fito na tararda Mama har ta kai waje gurin kallo ni ma lekowa na yi sai na ga ba mu kadai ba har da makotanmu sun fito kallo, wani kangon gida ne dake kusa facing din gidanmu aka rushe da motar rushe gidaje. “Abun ba ko sanarwa ni Wallahi na tsorata” Wata makociyar su Mama ta fada kowa sai ya dora da na shi, ni dai ban ce komai ba na juyo na dawo cikin gidan na zauna tunanin gobena. ABIEY POV. Dr na barin gidan ta kira shi ta fada masa hakin da ta samu Zahra. “Amman ke a fahimtarki me yake damunta?” “Wallahi ban fahimci komai ba, kuma na yi tambayarta bata fada min ba, sai dai kasan duk abun da zai saka Mamarta ta yi fushi da ita ba karamin abu ba ne” “Gashi bata da wata kawa ta kusa balle na bincika ko zan sani” “Abiey ka bi komai a hankali” “Shikenan, Thank you so much Dr Zainab kin min abun alheri da ba zan manta ba na gode da kila kula min da Zahra” “Anything for you” Ta fada fuskarta da murmushi sannan ya kashe wayar, ya mike tsaye ya nufi windows dakinta yana kallon backyard. “I wish na san minene matsalarki Zahra” Ya furta yana murza yastun hannunsa. The following day ya tafi gidansu Momy domin yin magana da Yasmin ko da yaje ya samu tana makarantar Islamiya haka ya zauna ya sha hira da Momy kamin ta dawo, abun da ya dade be yi ba ita kanta Momy ta lura da yadda Abiey yake cikin farinciki a yau sai dai bata tambaye shi komai ba, domin aganinta ba huruminta ba ne, har 6pm yana zaman jiranta Yasmin bata dawo ba sai 8pm kasancewar weekend ne ranar assabar da lahadi suna hadda har 8 na dare suke kaiwa wani lokacin. “Amman dai maganar da zaka yi da Yasmin tana da muhimmanci sosai ko?” Momy ta tambaya ganin yadda ya bata lokacin tun 2pm yana jiranta har 8pm, da wani abun ne dabam sai dai yace zai je ya dawo ko kuma yayi waya da ita, amman ya tsaya sai yayi magana da ita face to face, shi dai be ce ma Momy komai ba bayan murmushin da yayi. Yana kishingida jikin kujerar falon Yasmin ta shigo da katon hijab dinta hannunta rike da jakarta ta makaranta, tashi yayi zaune yana kallonta suna hada ido sai ya sakar mata murmushinsa mai kyau ita ma murmushin ta yi masa sai dai ganin Momy yasa ta yi saurin gusar da murnushin ta karaso cikin falon da sallama. [10/6, 8:31 PM] Oum_Nuwaira🥰: 2️⃣1️⃣ “Barka da dare” “Welcome” Ya amsa mata a takaice, sannan ta kalli Momy ta gaishe ta. “Barka dai yan makaranta an dawo, tun dazun Abiey ke jiranki” “Ni” Ta nuna kanta, sai Momy ta tashi zaune tana fadin. “Ke fa” “Momy bari ta ci abinci tukuna” “No ai kara dai ta saurareka yanzu daga baya sai ta ci abinci bari na baku guri” Sai da Momy ta shige dakinta sannan Yasmin ta zauna a inda Momy ta tashi tana kallon Abiey. “Allah yasa ba laifi na yi ba” Yayi murmushi domin ya kura tsorone a tare da ita. “Ba ki yi laifi komai ba, wani taimako nake son ki yi min” “Taimako kuma na minene?” “Zaki min idan na fada” “Zan iya maka abun” “Zaki iya” “Ka fadi ko minene babu wani abu da zaka nema daga gareni da zan kasa yi maka shi matukar ina da iko” Yayi murmushi. “Thank you, uhm shekaranjiya ne..... ” Tun da ya soma bata labarin bata ji komai ba har sai da ya kawo gabar da ya ambaci sunanta, sai ta ja wani irin numfashi da karfi shi kansa sai da ya ji. “No you don't have to worry, kawai na yi haka ne saboda na samu mafita daga gurin Mai Martaba, da kuma Mama Lami idan ban yi haka ba za su iya zaba min wanda bana ra'ayi” “To miyasa ka ce ni?” “That's the point, na san Mai Martaba zai aiko a tambaya masa aurena gurinki da su Momy idan ya gama bimciken da zai yi, idan an zo ina son ki amsa musu cewar ke baki so na kina da wanda kike so, already na yi magana da Ammy ta sani na san kuma zata sanarwa Momy shiyasa ban mata maganar ba” Yawu ta hade a hankali gabanta yayi mugun faduwa, ta kasa dauke ido daga barin kallonsa. “Yasmin...” Ya kira sunanta sannan ta sauke idonta kasa tana jin wani zafi na taso mata. “Can you” Ta sake kallonsa irin duban da ita kanta bata san tana masa shi ba, sai kuma ta yi saurin maida kanta kasa. “Yes” Ta amsa sai ta tashi da sauri ta bar shi a falon zaune, binta yayi da kallon mamaki da shakkun yadda ta yi masa. “Is she okay?” Ya tambayi kansa, sai kuma ya ta tabe baki ya mike tsaye yana kiran Momy. “Ba dai har kun gama ba” Shi ne abun da Momy ta fito tana fada. “Eh daman magana ce zan yi da ita ba mai tsawo ba zan wuce sai da safe” “Toh Allah ya bamu alheri ka gaishe da su Ammy” “Za su ji” Ya fice daga falon kuzarinsa, Momy ta bi shi da kallon kamin ta juya zuwa dakin Yasmin. Bayan ya dawo gida yake fadawa Ammy yadda suka yi, sannan ya kira Sauban ya labarta masa abubuwan da suka faru kusan ya fi kowa farincikin da jin abun da Mai Martaba yayi ma abokinsa. “Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba aje ba in ji hausawa, amman kana ganin Yasmin zata maka haka?” “To zai hana? Ba abu ne mai wahala ba, ya maganar gidan? Ina son na zauna kusa da Zahra ko dan na rika sanin halin da take ciki” “Ana nan ana bincikawa yawancin wadanda ake samu bana kusa da gidansu ba ne, amman akwai wani gida da aka fara gini aka bari shi kuma be da girma sosai gaskia” “Idan zai yiyu a siye na kusa da shi mana sai a hada in ya so sai a ninka musu, idan kuma haka be samu ba sai a siye shi nan ayi gidan sama” “Amman kai kana ganin zaka iya zama a nan Zahra bata gane ka” “Ba zan taba bari ka gane, i just want to be close to her” “Shikenan zan bincika mana, Allah yasa Mai Martaba ya barka ka aureta kar wata matsala ta ta so kuma” “No no kar ma kasa wannan a ranka, kar zuciyarka ta sake raya maka zan rasa Zahra” “Ba fata nake ba, kawai ina sasashe ne” “To ka daina wannan hasashen” Ya sauke wayarsa cike da rashin jindadin kalamin da Sauban yayi. ZAHRA POV. TWO WEEKS LATER... Wani irin murdawa na ji marata na yi ta saba min haka sai dai  ba irin na yau ba yau kan ta tsananta min sosai, kusan jin nake kamar bayana zai balle gabana kuma kamar zai zazzago kasa ya cire gaba daya, a wahala na rarrafo zan fito saboda fitsarin da nake ji sai Mama ta rike ni. “Ina zaki?” “Fitsari zan yi” “Aa ba a hawan shadda (Masai) idan ana nakuda balle gashi har kin fara zubar da jini, ki yi fitsarin a nan zan gyara” Tana gama fadar hakan ta tashi ta cire ledar tsakar dakin ta maida gefe daya ta dauko wani katon tsohon zane ta shimfida. “Yi fitsarin ki dawo nan ki zauna” Na saki fitsarin a nan Mama ta dauko ruwa zata min tsarko na rike da sauri na karba na yi tsarkina ina ta karewa kar Mama ta gan ni, da taimakonta na isa gurin da ta shimfida min zanen na kwanta, sai tace na tashi zaune na bude kafafuwana. “Aa ni ba zan bude kafafuwan ba haba Mama ai da kunya?” “Kunya? Ni na haife ki fa? Kuma ranar haihu mace har tana jin kunya ne? Ai sai daga baya dai ko?” “Ni dai gaskiya ba zan iya ba, ni tafi dakinki zan haihu da kaina” Murmushi ta yi. “Ai ko da sauran nakuda bata taso miki gaba daya ba shiyasa har kika da bakin fadin haka” Haka ne kuwa duk wani rufe kafafuwa da nake ina jin kunyar Mama na farko farko ne ina jin azabar ta asali ban san lokacin da na walgare kafafuwan ba na kwala ihu. “Mama ciwo nake ji na shiga uku” Na fada ina jin wani irin azaba da ban san yadda zan kwatanta ba, a take na ji fitsarin sun kara taruwa a marata. “fitsari nake ji” “Ki yi su a nan, kuma ki rika ambaton Allah” Na yi yunkurin fitsarin sai na ji sun ki fitowa ashe ba fitsari ba ne tsabar azabar ciwo ne, na kai hannu na cire dankwalin kaina saboda wani zafi da nake jin ya baibaiye jikina, na kai hannu na fara tsife kitson dake kaina can kuma na mari cinyata. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un Mama mutuwa zan yi, mama ku cire min abun nan Mama ki kira likita Mama ki kira shi ki fada masa ina nan ina shan azaba wayyo Allah” “Ki bari sai idan kin haihu sai a kira shi” “Ba zan bari ba ba zan bari ba, ai ba jikinki ba ne baki san yadda nake ji ba, cikina fashewa zai yi marata ciwo take kasana ma barkewa zai yi, wayyo Allah marata” Murmushi kawai Mama ta yi ta cigaba da tufa min addu'a a kofi bayan ta gama ta ba ni na sha, ta shafa min ragowar a cikina. “Allah ya sauke ki lafiya, ki yi ta ambaton Allah” “To wai ba addu'a kika ga ina yi ba, ni dai ki kira likita wayyo Babana” Na fada da karfi ina kuka ji nake kamar na tashi na tafi har asibitin gurin likitan, wayarta ta dauka ta kira Yaya Maryam ta sanar da ita halin da muke ciki bata gama wayarba amai ya cika min baki na fara amai kamar ba gobe, lokacin na tabbatar da uwa uwa ce  babu kyama ta rike ni tana ta tausayina idan naje rufe kafafuwana sai ta bude, mikewa na yi tsari na fara yawo cikin dakin ina karanta duk addu'ar da ta zo kaina. “Yanarukuna bardan wassalamu ala ibrahim.... Ya hayyu ya kayyun... Ya Allah na ya gwanina Allah ka kawo min sauki, wannan mutuwa da zan yi a yau ka kawo min saukinta” Mama ta rike ni ta zaunar sai na kai kaina na leka ina kallon yadda na komai ya canja. “Mama haka kika ji da zaki haifi Zahra? Mama ki yafe min Mama na yafe miki, da na san haka abun nan yake da ban yarda na raini cikin nan ba, na shiga uku na lalace, wayyo duniya wayyo lahira” Sai da na yi awa daya a haka sannan Yaya Maryam ta zo, tana isowa ta sanar da Mama tare take da Dr Hamid sai na mike tsaye jiki ba tufafi zan fita na tafi waje gurin Dr Hamid din sai da Mama ta rike ni. “Ke babu tufafi a jikin ba” “Mama ina ruwana da tufafi wai? Kowa ya gan ni mana, ke dai baki san yadda nake ji ba” Na fada ina son na kwace kaina domin jin nake kamar da naje gurin likitan cire min cikin zai yi an samu sukuni. Yaya Maryam ta daura min zane ta saka min Hijab. “Yace a fito da ita ba a nan zata haihu ba?” “To ina zai kaita?” “Ni dai be fada min ba, amman yace na fito da ita mu tafi wani gurin” “To kuwa da ni za a tafi, ba zan bari ku tafi ku ka dai ba da yata a wannan hali” A take na sako fitsari mai tare da jini, Mama ta rika ni ta dayan bangaren Yaya Maryam ta rika dayan bangaren muka fito sai da aka sani ni motar Dr Hamid din sannan Mama ta koma ta rufe gidan sai Dr ya kalli Yaya Maryam. “Da ita zamu je?” “Eh” Kamar yace wani abu sai kuma ya zagaya ya shiga mazaunin direba Mama ta shiga baya tare da ni yaja motar kamar zai tashi sama, kamin mu isa inda zai kai ni na fara rokon Mama yafiya ina bar mata wasiya. “Zahra hakuri ake duk haka muka ji” Yaya Maryam ta fada ban san lokacin da na kai mata duka ba. “Karya kike ba haka kika ji ba, muguwa ni kadai na san me nake ji, Wayyo Babana Wayyo Deen” Mama addu'a kawai take tana tofa min, wata private hospital muka nufa, ko da muka isa mun tararda an aje kujerar daukar marar lafiya, da alama ya shiryawa komai tun kamin a kawo ni, Mama da Yaya Maryam suka dora ni kan kujerar wata nurse ta turawa da gudunta, su Mama suna biye, wani katon daki aka shiga da ni, aka dora ni saman gado aka janyo wani karfe aka dora kafafuwana a kai. Matar ta cire zane na ta dauko wani ta dora ta rufe min kafafuwan zuwa cikina, sai ga Dr Hamid ya shigo cikin shiga irinta ta masu shiga tiyata ya rufe fuskarsa da mask hannayensa kuma da safa, ya daura drip ya saka min a hannu sannan yayi allurar a cikin ruwa, ya kalli Mama da Yaya Maryam yace su fita. “Ku fita please” “Aa ni babu inda zan je sai ta haihu” “Mama babu abunda zai faru, dan Allah ki fita dan ma yana private hospital ne da asibitin gwannati ce ba za a bari ma ku shigo nan ba, dan Allah ki fita” Daker da sudin goshi Yaya Maryam da nurse din suka lallaba Mama ta fita bayan ta bugawa Dr Hamid warning cewar idan na mutu ta rantse masa da Allah sai ta yi shari'a da shi. Hannunsa ya fara saka min a ciki sai wani ruwa ya fashe da karfi ya watso masa har a jiki da karfi yayi tsalle yayi baya sai dai haka be hana ruwan bata masa jiki ba. “Sannu sannu” Shi ne abun da yake ta fada. “Ki yi nishi” “Ya kare nishin” “Be kare ba daure ki yi kin ga kan babynki yana kusa na fara jinsa” Sai na yunkuro zan kai hannu na taba ni ma naji abun da ya ji sai nurse din ta maida ni ta kwantar. “Push Zahra ki yi nishi” Na yi nishin sai na ji kan wani abu ya tsaya min a gaba kamar ya tare kofar, ga wani azaba da nake ji a gurin kamar an yanka ni. “Da kyau yi nishi” Na sake gwada nishin sai na ji ba zan iya ba, gaba daya na gaji karfina ya kare, sai na kwanta a gadon kamar tsumma, duk wata dabara da Dr zai min na yi nishi yayi idan na yunkura na yi nishin sai na ji ba zan iya ba ko kuma na yi kadan. “I can't breathe I'm so weak ” Na furta ina tuna yadda Deen yace zai zo ya rike ni idan zan haihu, kuka nake sosai, can sai ga wani irin karfi ya zo min na nisa sai na ji abu ya fara fitowa ashe nishin haihuwa ba mutum yake yinsa karan kansa ba Allah ne yake kawo masa wannan karfin, ina sake nisawa a karo na biyu sai kukan abun da na haifa hawaye na sauko min Dr ya saka hannu ya karasa cire shi ya dago shi haka nan da jini ya doro min saman kirji. “Kin haifi ďa namiji Zahra Congratulations” Sai na fashe da wani irin kuka marar sauti ina kallon yadda idonsa yake rufe yana ta rusar kuka, fari ni sol kasancewata ni da mahaifinsa duka farare ne, sai dai ba zan iya shaida waya biyo ba domin babu kamanin kowa a fuskarsa, sai dai kyakkyawa ne mai dogon hanci sosai. Nurse din ta daga shi saman jikina ta yanke masa cibiya ta goge masa jiki ta mikawa Dr Hamid ita kuma ta fita ta karbo kayan jarirai, wasu tufafi ne ta shigo da su masu matukar kyau wadanda na san ba nawa ba ne domin ba mu zo da kayan jariri ko daya ba, ta saka masa ta dora shi akan wani tawul mai laushi sai Dr ya karba ya doro min saman jiki, ina ta kallon fuskarsa shi kuma yana ta aikin kwashe min jini, sai da suka gama komai suka tsabtace ni sannan ya kalli nurse din yace. “You can go, ki ce Mama a yayarta su shigo” Nurse din ta fice, sai ga Mama ta shigo tare da Yaya Maryam dukansu hawaye ne a fuskarsu sai ya mika musu ďan. Na tashi zaune ya cire drip din da ya saka min ina jin kamar ba zan iya zamaba saboda azabar ciwon da gurin yake min, audugar masu haihu ma da ya bani na saka sai na ke jin kamar ban zaka ta daidai ba. Ficewa yayi ya bar mu mu kadai a cikin dakin. “Mama duk wannan wahalar da na sha bada ďan nan zan yi?” Na tambaya ina kuka. “To ya zaki yi da kaddara Zahra” Mama ta amsa ni tana kallon yaron, sai ta mikawa Yaya Maryam da ita ma kuka take Yaya Maryam ta miko min shi na saka hannu biyu na karba na kai bakina na sumbanci goshinsa, na yi sauri na bude nono na zan saka masa a baki sai Mama tace. “Zahra ana son a fara bawa yaro danino da ruwan zanzan kuma sai an wanke nono ake ba shi” “Mama barta ta bashi dan Allah” Yaya Maryam ta fada ta saka hijabinta ta goge min nono na saka masa a baki a take ya daina kuka ya kama ya fara sha, sai na ji wani irin ciwo kamar na cire nonon daga bakinsa. “Rada mishi suna Zahra ki yi masa huduba a both kunensa ki rada masa sunansa” Yaya Maryam ta fada, sai na cire nonon daga bakinsa na yi masa huduba sannan na rada masa nunan masoyina, na maida masa da nonon a bakina ina kuka. Dr Hamid ya turo kofar ya shigo rike da kwali yana ganin ina ba yarona nono sai yayi saurin dakatar da ni ya aje kwalin da sauri ya karaso ya karbe shi. “You shouldn't” Ya matsa da shi baya ya juya zai fita. “Dan Allah ka bari na sake kallonshi” Ya juyo ya dawo min da shi sai na kalleshi. “Allah ya maka albarka” Na furta sannan na sumbance shi, ya karbe shi na rumgume shi ina jin kamar kar a raba ni da shi. “Wane suna kika zon a saka mashi Zahra?” “Zaharadeen...” Na fada muryarta na rawa saboda kukan da ke son ya ci karfina, sai ya karbe shi ya daga min kai hawaye na sauko masa ya fice da shi. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un” Shi ne abun da na ke ta furtawa na koma saman fadon na kwanta ya lumshe ido, sai Mama ta zo kusa da ni ta tsaya. “Zahra” Na bude idon na kalleta. “Tashi” Na tashi sai ta rumgume ni, wani irin sanyi na ji sai zuciyata ta samu sassauci na fashe da kuka da nake ta dannewa. Dr be dade ba ya dawo ya bude kwalin daya aje dazun ya dauko wata matacciyar jaririya a cikin zane ya mikawa Yaya Maryam. “Nurse zata zo ta kaiki dakin hutawa, so that ki samu bachi kamin ku wuce gida” Ya fada sannan ya karbi jaririyar ya maida cikin kwali ya dauki kwali gaba daya ya mikawa Yaya Maryam. Ina ji ina gani aka raba ni da ďana na fito dakin ina ta kuka zuwa wani dakin da aka tanadar min zuciyata kamar ta cire, ina jin kamar na yi ihu ga kukan da nake ma jin nake kamar be ishe ni ba, wani abu nake ji kamar na yi ihu. “Zahra” Muryar Anty Zainab muka ji wato yayar Abiey, sai Mama ta juya ta kalleta ita ma hawaye take haka ma Yaya Maryam. “Lafiya?” “An haihu ne abun da ta haifa be zo da rai ba” Mama ta amsa mata. “Ayyah Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un Wayyo Allah” Zuwa ta yi ta rumgume ta gabana tana sanye da rigar likitoci a iya sanina ba wannan asibitin Anty Zainab take aiki ba, wata kila wani abun ne ya kawo ta na dabam. Fashewa na yi da kuka sosai na kankame ta ina jin kamar na fada mata damuwata amman ba hali, sai kiran nake ďana ďana har ta kalli Mama tace. “Namiji ne?” “Mace ce” Mama ta amsa sai ta sake ni ta bude kwali ta kalli jaririyar. “Allah sarki” Ta dawo ta sake rumgume ni, ita kai ni dakin da zan huta maimakon na zauna saman gadon sai na zauna a kasa na takure kuri daya ina jin wani jiri yana daukata. Ta yi bani hakuro har ta gaji ta fita ban daina kuka ba, bayan fitarta wata nurse ta shigo tare da magani ta Mama tace likita yace bani, Mama ta kalli Maryam. “Ki tafi da jaririyar a gida a rufe ta, zan kira Hajiya na fada mata muna asibiti Zahra ta haihu abun da ta haifa be zo da rai ba, ki aje uwar sai na zo ayi gina a rufeta, zanen kuma ki wanke mata ki gyara gidan” “Toh Mama” Ni kuma na shura kafa a kasa ina kuka “Ni mai rai na haifa....” Mama ta yi saurin rufe min baki. “Zahra ki dawo hayyacinki so kike ki jefa kanki a matsifa ne” Na cije bakina ina kuka sosai, su Hajiya ma suna isowa kukan suka kasa Bahijja har da dora hannu akai, a tare da su kuma koma gida domin ban iya yi bachin da ake son na yi ba, ban kuma yarda na bari yayi min allurar da ya nufo ni da ita ba, shayin da aka hada min ma ban sha ba, bana bukatar komai a lokacin sai mutuwa, nakudar da na yi da wani azabar ciwon da na ji sai na manta da komai ďana kawai nake gani a idona, dama ace mutuwa yayi da hankali zai fi kwanciya fiye da ace yana hannun wata da bata san zafin daukar cikinsa ba balle haihuwa. ABIEY POV. Zaune yake kan machine din motsa jiki yana motsa jikin da be samu yayi da safe ba, Bluetooth a kunnensa yana kallon katuwar plasma dake gabansa, ya hada gudu kamar wanda yayi gudun fanfanlaki. Wayarsa dake kan dayan machine din a aje ta yi vibration sai ya danna Bluetooth din kunnensa. “Hello” “Abiey kana ina?” “Ina gida gurin Ammy ya akai?” “Na shiga ban ganka ba” “Bari na fita ina dan motsa jiki ne” Ya tsayar da machine din sannan ya sauka ya dauki wayarsa ya fito daga dakin na motsa jiki ya bullo cikin babban falon Ammy, be samu kowa a falon ba hakan yasa ya wuce kai tsaye dakinsa sai da yayi wanka ya shirya cikin kananan kaya ya feshe jikinsa da turare sannan ya fito ya tura kofar bedroom din Ammy. Sai da ya fara karewa Dr Zainab kallo sannan ya kalli Ammy. “Lafiya?” “Wai Zahra ta haihu abun da ta haifa be zo da rai ba” “Ohh....” Ya furta not happy not sad, Dr ta juyo ta fuskance shi. “Another news yaushe ka aika neman auren Yasmin ba ni da labari?” “Plan ne kawai ba na gaske ba ne” Ya amsa yana zaunawa kusa da ita wato kan doguwar kujerar da take zaune. “Toh Momy ta kira ni tace Mai Martaba ya tura manyan mutane nema maka aurenta” “Eh Anty ta yi waya da ni kamin su tafi ai yace a tambaya ko Ammy zata bada wani daga Familynta” “Amman baku fada min Anty ta kira ba” “Ba auren gaske ba ne kawai haka hakan ne saboda ya kare kansa, shiyasa ni ma ban bada kowa a cikin dangina ba” Wannan karon Ammy ce ta amsa mata. “To zai zama na gaske kuwa domin an tambayi yarinya ta amsa tana sonka kuma iyayenta sun baka, Momy ta kira ta fada yanzu nan ina kan hanyar zuwa” Dr Zainab ta karasa tana murmushi, Abiey ya mike tsaye da sauri yana kallon yar'uwarsa, kusan a lokaci daya wayarsa ta yi ringing kiran Anty ya shigo ya amsa kiran da sauri. “Hello Anty” “Abiey ba ka yi magana da Yasmin ba ne?” “What happen?” “Toh iyayenta sun ce sun baka yarinya ta amsa tana sonka” “What.....!!!?” Ya furta da karfi baki sake zuciyarsa na bugawa da mugun karfi. [10/9, 10:54 PM] Oum_Nuwaira🥰: 2️⃣2️⃣ Ya cije lips dinsa ya sauke wayar ba tare da ya sake cewa Anty komai ba. “Taya yarinyar nan zata min haka?” “Miyasa ka saka ta a ciki tun farko?” Dr ta tambaya, ya kalleta. “Saboda ina tunanin mafita ce, i thought zata taimaka min” “What if tana sonka?” “No my body my wealth my heart is only for Zahra and her alone” Ya fada yana nuna kansa, Ammy ta ce. “Wata kila bata fahimci abun da kake nufi ba” “Okay bari na same ta yanzu na yi magana da ita” Yana fadar hakan ya nufi kofa kamin ya fita Dr ta ce. “Yasmin is innocent Abiey ka yi magana da ita yadda zata fahimta don't hurt her feelings, tana zaman zamanta ka saka ta a cikin maganar nan yarinyar nan marainiya ce please ka bita a hankali” Juyowa yayi yana mata kallon mamaki. “Ita ta saka kanka, taya an tsara yadda za'ayi yarinya ta zo ta canja magana” Ya juya ya fice rai a bace. Dr Zainab ta kalli Ammy tace. “Ina ganin kamar Yasmin tana son Abiey” “Na dade da fahimtar haka, taya mace zata ga kyakkyawan saurayi kamar ďana bata ce tana so ba, mutum ga kudi ga daukaka ga kyau ga sarauta” “Yasmin ma ba zata duba wannan ba idan zata so shi, kawai dai tana sonsa ne, idan ba haka ba babu abun da zai saka ta amsa haka bayan yayi magana da ita” “Kuma son Aliyu indai ba shi ya gani ya ce yana so ba, wahalar da kai ne, domin hankalinsa gaba daya baya gurin kowa sai Zahra” Dr ta motsa kanta a hankali. “Yeah she deserves Zahra And Zahra deserve someone like Abiey wanda ya kula da ita sosai domin yarinyar nan tana cikin damuwa sosai, ina tuna lokacin da aka yi wasa da rayuwar mijina yadda na ji balle kuma ace na rasa shi, ita kuma ta rasa mijin yanzu kuma ta rasa babynta so sad” Ammy ta sauke ajiyar zuciya. “Babu yadda Allah baya ikonsa, sai hakuri mutuwa babu yadda ba a ganta ba” Mikewa tsaye Dr ta yi ta cire labcot din jikinta. “Bari na sauka na ci abinci” ABIEY POV. Tafiyar minti shabiyar da kai shi gidansu Yasmin wato gidan Momy, ko parking din kirki be yi ba ya fito ya nufi kofar gidan, kamin a bude masa kofar falon yayi knocked ya fi a kirga. Momy ta kanta ta bude masa kofar “Aliyu” Ba karamin jihadi yayi ba na danna fushinsa ya dan saki ransa ya gaisa da Momy, sannan ya karaso cikin falon ya zauna ba tare da yace da Momy komai ba. “Gurin Yasmin ka zo?” Momy ta tambaya sai ya daga mata kai da sauri. “Wata yar matsala aka samu Momy...” “Na san da komai ai Ammy ta yi min bayani, yanzu haka kamin ka zo fada da nake mata kenan” “Momy zan iya magana da ita” “Bari na kira maka ita” Momy ta tashi ta nufi dakin Yasmin, bata dade ba ta fito ta dawo ta zauna. “Gata nan fitowa” “Okay” Ya amsa yana wasa da keys din hannunsa, shiru shiru babu Yasmin babu labarinta, hakan yasa Momy ta aika mata da kira daga inda take zaune. “Yasmin.... Yasmin....” Bata amsa ba sai kara rufa kofa suka ji an saka makulli, Momy ta tashi ta nufi kofar tana tabawa ta jita a rufe gam babu. “Yasmin ki bude kofar nan kar ranki ya bace miye haka?” Wani gumi ya karyowa Abiey ya mike tsaye ya nufo kofar. “Yasmin bude kofar magana kawai zan yi da ke kinji” A hankali yake maganar yana kokarin kwantar mata da hankali, Yasmin dake cikin dakin ta rufe idonta dake zubar da hawaye ta jingina da kofar ta sulala kasa, ita kanta bata san dalilinta na yin haka ba, kawai ta samu kanta da amsa musu da eh ne a lokacin kanen mahaifinta suke tambayarta. “Momy ko zaki tafi ina son na yi magana da ita” Momy ta amsa masa da kai ta juya ta nufi kitchen, sai da Abiey ya ga ta shige sannan ya kwankwasa kofar. “Yasmin... Bude mu yi magana ta fahimta da ke kinji” Ta girgiza kai kamar ance mata tana ganinsa. “Yasmin dear please karki jefa ni a matsala, i face a lot of challenge bana son wata damuwa a yanzu i just want to focus on Zahra and her alone, ban san dalilinki na yin haka ba, wani ya cilasta ki ko kuma kuskuren fahimta aka miki ko bakinki ya subuce ce, amman na san kina daga cikin mutanen da suka san halin da nake ciki, ba za ki yi wani abu da zai kara jefa ni a damuwa ba” Ya sake murda kofar. “Yasmin bude kofar kin ji” Haka yayi magana ya gaji da tsayuwa Yasmin ta ki ta bude kofar, har sai da Momy ta dawo gurin. “Bata bude ba” “Momy ko dai tana da aljannu?” Momy ta yi murmushi. “Yasmin da magana ma be ishe ta ba, babu wani iska sai iskanci irin na yaran zamani” “To na ga mun yi magana da ita lafiya lafiya sai kuma na ji magana ta canja” “Karka damu zan yi magana da ita, maybe tana jin kunyar abun da ta yi maka ne a yanzu shiyasa ba zata bude ba, amman ko da ita bata musu magana ba ni zan yi magana da su kanen mahaifin nata Inshallah” “Okay thanks” Ya fada sannan ya saki kofar ya juya tana tafiya a hankali har ya fice, sai a lokacin Yasmin taja numfashi ta aje tana jin yadda kamshin turarenta ke kara sa zuciyarta tana bugawa da karfi. ZAHRA POV. Makota da yan'uwa suna ta zuwa yi mana gaisuwa, Mama ta saka dankwali ta daure min cikina daman can ta tanadar min da wasu abubuwan da zan bukata a jego. A aka dora ruwan zafi da sunan na yi wanka Hajiya ta siyo min nama ta dafa min a gidan Mama saboda na ki cin komai, bana aikin komai sai kuka tun ana bani hakuri har aka hakura aka saka min ido. Ina zaune daki bayan na fito daga wanka Mama ta balla maganin da likita yace a bani ta miko min. “Karbi ki sha” “Ni bana son wannan maganin” “Shi zai taimaka miki ya tsayar miki da zubar nonon” “Ni bana so ni ki kyale, ba zan sha ba” “Aiko kara ki sha zai taimaka miki, idan ba haka ba nonon zai dade yana miki ruwa kuma sai ta yi miki ciwo, tun da ba wani zai tsosa miki ba Allah ya riga da yayi ikonsa” Hajiya ta fada. “Ni Wallahi mai rai na haifa” Na fada ina hawaye sai Mama da daka min tsawa da sai da jikina ya dauki rawa. “Wallahi Zahra idan bakinki ya sake furta magana nan sai na bata miki rai fiye da yadda kike zato, ke kika fi kowa rashin yarda da kaddara ne? Ko kin taba ganin an yi ma Allah haka? Wawuyar banza kawai” A take na fashe da wani irin kuka da sai da Hajiya ta rika ni ta zaunar. “Duk yadda kike ji ba ki kai ni Zahra, kin gan ni nan haihuwata goma sha daya amman biyu kawai Allah ya bar min ya karbi sauran, Allah kadai ya san yadda na so ganin ďan Deen ko ba komai zan ji sanyi amman babu yadda zamu yi da ikon Allah, ki yi hakuri kinji” Hawaye ya sauko mata, sai na kwantar da kaina jikinta ina kuka Mama kuma ta watsar da maganin ta tashi ta fice ta bar mana ďakin. “Indai ba zata iya hakurin zama da ke ba, sai na maidaki gurina har ki gama wanka abun kadan sai ta rufe ki da fada” Na kara fashewa da kukan tausayin kaina da kuma ita a lokaci daya. The following day Hajiya ta koma gidanta, aka bar ni daga ni sai Mama sai kuma Yaya Maryam dake zuwa ta wuni ta koma, ita take ta ba ni magana tana kwantar min da hankali amman ina na kasa samu kwanciyar hankali ďana kawai nake gani sai na kara ramewa daman bana wani iya cin abincin kirki, babu ranar da bana kuka haka babu daren da zai zo ya wuce ban yi kewar mijina ba, sai abun ya zame min biyu na rasa inda zan ji sanyi, na koma kamar wanda bata da kowa a duniyar nan. “Allah kadai ya san wane hali yake ciki, ko sun saka masa sunan ko kuma wani za su saka” A zatona a cikin raina na yi maganar ashe a fili na yi, sai jin na yi Mama ta amsa min. “Sunan da suka ga dama mana shi za su saka masa, ki cire ranki a tunanin yaron nan dan Allah Zahra ni kaina ina cikin damuwa kara daga min hankali kike” “Mama yanzu idan aka ce wata uwa ta dauke miki ni ko Yaya Maryam ya zaki ji?” Ta dago daga gyara wutar da take ta kalleni sai ta sauke ajiyar zuciya. “Mutuwa kadai ke iya raba ďa da uwa, kuma abun da kika aikata kamar mutuwa yake, idan baki daina tunani ba za ki iya jawa kanki wata matsala” “Babu abun da nake so a yanzu Mama sai mutuwa, domin ita ladai ce mafita a gare ni, idan na mutu zan manta da komai ciki har da kuskuren da na aikata” Tasowa ta yi ta dawo kusa da ni ta zauna. “Kin ga duk rayuwar nan da kika ganin kina cikin tsanani? Wani na can yafi ki shiga matsala, da za a baki irin kaddararki da sai ji sanyi, ke ma na ki zai zama tarihi kamar ba ayi ba” “Haka dai kika ganin kamar zai wuce Mama amman ba zai taba wuce ba, na rasa Deen kenan har a bada kuma ga ďana” Kama kaina ta yi ta kwantar saman kafadarta. “Zai wuce Zahra komai zai zama labari” “Mama” Na kira sunanta a hankali sai ta amsa min. “Na'am” “Ina son zan je na yi magana da Dr Hamid” “Maganar me? Idan zai yiyu na maida masa da kudinsa na karbo babyna” Dago ni ta yi daga kafadarta ta kalleni. “Ina zaki samu kudi mai yawa haka?” Na yi shiru sai kuma na fada mata abun da nake ganin shi ne mafita. “Wata kila Abiey zai taimaka min ko?” “Uhmmm yaro man kaza, yar dawowar da yayarsa ta yi tana nuna miki kulawa ta karya har kin fara yarda da ita? Kin manta duk abun sa suka miki suka mana?” “Mama ni yanzu mafita nake nema” “Kuma kina da tabbacin Abiey zai sama miki ita? Waya sani ma ko yayi aure wata kila ba baya kasar, ko da ace yana nan ke yanzu har zaki iya tunkararsa da wata magana ta neman taimako? Bayan ya gama watsa miki kasa a ido? Sai ya dauki kudi mai yawa haka ya biya miki bukatarki saboda farincikin da ya kasa sama miki shi a can baya? Ki kaddarar ma ya baki kudin a ganinki ita matar zata yarda ta baki ďanki? Ta cewa mijinta da yan'uwanta me? Ai ba zata kyale ki ba, kuma kin ga bamu san Wacece ita ba, macen da zata bada miliyan bakwai da wani abu a take kuma ta saka miki diyar miliyan ashirin idan kin karya alkawari ai kin san ba karamar mace ba ce, shi kan shi mijinta babban mutun ne shiyasa har take son haihu da shi, sannan idan maganar nan ta fita har ta kaiku kotu to ke da ita duk sai an hukuntaku” “Toh Mama zan yi magana da shi ya taimaka min na sake ganin yaro ko da sau daya ne” Ashe na yi sara akan gaba domin kuwa ina rufe baki, kiran Dr Hamid ya shigo wayar Mama da na saka line ne, jiki na rawa na dauka. “Hello” “Zahra ya kike” “Alhamdulillah” “Ya kamata na kira na tambayi lafiyarki ko na zo, sai dai na daga miki kafa ne saboda ki samu relief kar ganina ya sa ki rika tunani, ya karfin jikin na ki” “Na gode Allah” “Maa Shaa Allah akwai abun da kike bukata ne?” “Eh ina son magana da kai” “Okay ina saurarenki” “Ba a waya ba, a fili maganar mai muhimmanci ce” “Allah yasa ba akan yaron nan ba?” “Aa akan lafiyata ne, akwai yan matsalolin da nake ji ina son na ganka face to face” “Ba zai yiyu na zo gidanku a yanzu ba, amman ke zaki iya yin dabara ki same ni a asibiti sai mu yi magana” “Da yaushe zan same ka?” “Kin ga ai ga waya sai ki kira ni kamin ki zo” “Zan iya zuwa yanzu?” Yayi shiru kamar ba zai amsa ni ba har sai da na dauka kiran ya yanke ne. “Hello” “Ke da wa zaki zo?” “Ni kadai” “Ki same ni a Favor Hospital, asibitin da kika haihu, idan kin zo sai ki kira ni” “Toh” Na amsa da sauri sannan na share hawayena na sauke wayar na mike tsaye da sauri. “Mama zan je na yi magama da shi zan roke shi ya bar ni na ga ďana” “Zahra wa kika taba ganin tana jego ta fita? Jegon ma haihuwar fari?” “Maman zan fita da sunan zuwa asibiti ne, dan Allah karki hana ni ina son na ga little Deen ne, wata kila shi na dama ta karshe da na ke da ita ta ganinsa” Hawayen da suka sauko min kadai sun isa su saka Mama ta tausayawa min balle kuma har na hada da magiya. “To bari na tashi mu tafi tare” “Aa idan ya gan ni da wani ba zai yarda ba, ki bar ni na tafi ni kadai” Daga bakina da nake magana da shi har jikina rawa yake, kana ganina kasan ina cikin yunwar son ganin ďana. “Toh Allah ya tsare” “Ameen” Na shiga daki da sauri na dauki hijabi na saka na fito rike da yan canji a hannu na hawan napep na nufi kofar fita ina kokarin ficewa ba tare da na ce da Mama na tafi ba, sai ta yi saurin rikoni. “Zahra kina cikin hayyacinki kuwa? Haka zaki fita kafarki babu talkami? Kuma da wace waya zaki kira shi? ” Sai a lokacin na kalli kafata ashe ban saka talkami ba, kuma ban dauki wayar kiransa. Mama da kanta ta dauko min talkamin sannan ta mika min wayar, na saka talkamin na karbi wayar na fice ina jin kamar na runtse ido ya bude na gan ni a aibitin gaban Dr Hamid. ABIEY POV. “Mai Martaba zai ga rashin kyautawarka fa, ya kamata ka je ka yi masa godiya” Anty ta fada sai ya dago daga barin kallon agogon hannunsa na miliyan hudu ya kalleta. “Godiya kuma?” “Yes ko da ace ya saba yi maka ya kamata ka gode masa balle kuma yayi maka abun da be taba ba, kuma ya tsaya tsayin daka har sai da aka baka Yasmin” Ya busar da iskar bakinsa. “Yarinyar ina ganinta kamar Allah ashe tantiriya ce, tun lokacin da abun nan ya faru ta ki yarda mu yi magana da ita face to face, first day na je gidansu ta ki fitowa, na sake zuwa aka ce tana Islamiya na tafi har islamiyarsu amman yarinyar nan bata fito ba” Anty ta yi murmushi. “Yasmin fa sonka take, shiyasa ta amsa a lokacin da aka tambaye ta” Kamar wanda aka tunawa da wani abu sai ya mike tsaye da sauri. “Bari na yi tafi gidan Momy” “Gurin me?” “I need to talk to her” “Toh Allah yasa ta baka hadin kai, idan ba haka ba kam zata jefaka a matsala, ka san dai ba zaka fara zuwa ka fadawa Mai Maetaba cewar baka sonta ba, kuma idan ba daga gareta aka ji wata matsalar ba Mai Martaba ba zai taba magana biyu ba” Ya amsa mata kai, sannan ya fice sai kamshin tsadadden turare yake zubawa, taku yake irin na yayan manyan sarakai taku mai cike da kasaita da isa irin ta masu arziki da yake magana da kansa a jikinsu da kuma sarauta da ke cikin jininsu, one step yayi saura ya sauka daga entrance din Anty sai ya ji wata familiar voice ta kira sunansa. “Abiey....” Ya daga kai ya kalleta doguwar rigar abaya ce a jikinta sai wata yar karamar jaka makalle a hammantanta. “Hi...” Kamar wanda be ji abun da ta fada ba, ko kuma be san da yaren da take magana ba haka yayi mata ya cigaba da takunsa har ya isa gurin motarsa a daidai lokacin ne ita ma ta karaso. “Hi” Ya mata banza kamin ya kare mata kallon tun daga saman kanta da rabi ke waje saboda ya sha gyara har zuwa kafafuwanta, if he can remember ita ce yarinyar da ya gani a fadar Mai Martaba kuma ita ce ya gani a cikin jirgin lokacin da zai je Abuja, ba tare da ya ce da ita komai ba ya bude motar ya shiga yayi reverse ya fice daga gidan. “Do i look ugly?” Ta tambayi kanta tana karewa kanta kallo. A waje ya faka motarsa saboda gudun kar ya shigo da ita ciki Yasmin ta gani ko ta ji karar tsayawar motar ta gudu ta boya, slowly yake tafiya har ya iso kofar falon yayi knocked and he got lucky Yasmin ta bude masa da kanta. Wani irin bugawa zuciyarta ta yi da mugun karfi shi kuma ya tsare da ido fuska ba yabo ba fallasa. “Can we talk now?” Ta saki kofar ta dawo ta zauna rike da littafinta na islamiya da take home work, ya zauna a kujerar dake facing dinta. “First of All Yasmin miyasa kika min haka?” Ta kasa dagowa ta kalleshi gabanta sai faduwa yake kamar zai cire. “Why? And kika maida ni kamar wani dan'iska kullum idan na zo sai ki boye” Hawaye ne ya fara mata zuba. “Talk to me ba kuka na zo ki min ba” “Ban san miyasa na aikata hakan ba” “As how baki san miyasa kika aikata haka ba? Hankalinki ya gushe ne?” Ta girgiza masa kai. “To ta ya? Zai da muka yi magana da ke ta fahimta tun kamin Mai Martaba ya aiko, amman kika lalata komai” Wannan karon da fada yake mata magana saboda ta bata masa rai sosai. “Fine abun da ya faru ya faru, yanzu zaki iya gyara ki fadawa iyayenki cewar ke kin janye ba ni kike so ba kinji?” Ta dago ta kalleshi tana sauke wani irin wahalallen numfashi. “Kin ji?” Ta amsa masa kai hawaye na sauko mata sosai. “Good girl, daman ni na san indai ba sherin shedan da zugar zuciyata as pretty as you are me zaki yi da ugly man like me, yadda kika da natsuwa ai you deserve someone better than me, ni kuma sai na je na ji da Zahra ta” Ya karasa yana murmushi yana kallon fuskarta babu abun da take sai hawaye kamar ruwa, kamar ya tambaye wani abu sai kuma zuciyarsa ta hana shi. “Now zaki iya min alkawarin zaki fada ma iyayen ki haka?” Ta daga masa kai. “Good Thank you, ina Momy?” Bata iya amsa masa sai girgiza masa kai ta yi alamar Momy bata nan. “Okay kar ma ki fada mata na zo” Ta daga masa kai sai da ya sake kallonta sannan ya nufi kofar fita sai ta juya ta bi bayansa da kallona zuciyarta na mata mugun zafi. A compound din gidan ya ciro wayarsa ya kira Dr Zainab sai dai ba ta yi piciking ba har sai da ya sake kira. “Hello aiki fa nake yi?” “I need to see you kina ina?” “Asibiti ya aka yi” “Okay” Ya sauke wayar ya danna key hannunsa ya bude motar sannan ya shiga yayi mata key heading to Favor Hospital gurin Yayarsa. [10/9, 10:54 PM] Oum_Nuwaira🥰: 2️⃣3️⃣ Ban san gurin da zan same shi a aibitin ba, hakan ya saka lokacin da na shigo na kira shi a waya sai yace min na samu guri na zauna a daya daga cikin kujerun da suke ward din female surgical ward na jira shi, ba musu na zauna, jiki babu karfi ina ta kallon mutane, wasu da suke zaune kusa da ni suna ta hira kamar ba su da damuwa a tare da su masu tafiya ma kallonsu nake, ni kuwa tawa zuciyar kunshe da bakinciki da tunani kala kala, na zauna a gurin for moren 3 hours ina jiransa, na sake kiransa sai yace min na jira shi aiki yake, da na gaji da zama a ciki sai na fito waje ina zagayawa rumgume da hannayena, a wajen ma na yi awa daya ina jiransa be kira ni be kuma fito ba, hakan yasa na kira kiransa sai ya sake ce min aiki yake na jira shi. Na kusan awa biyar a aibitin ina jiransa be fito ba kuma be kira ni ba, wannan karon da na gwada kiran wayarsa sai na same ta a kashe, a take idona ya cika da kwalla, na gane idan kana nema a gurin wani kai ne abun wulakantawa, a yau saboda ni nake nema yaki ya bani lokacinsa wata kila saboda ya san dalilina na zuwa gurinsa, domin ba za a ce ya rasa lokacin kula da ko da 30min ne ba. Komawa na yi ciki ina tambayar mutanen ciki na fadi sunansa da kuma asibitin da yake aiki kamin wannan har na nuna musu numberta, sai wata yar albarka mai far'a a cikin mutanen tace bari ta duba min shi. “Biyo ni mu je....” Na bita muna ta tafiya har muka isa wani bangaren na dabam, sai ta saka na tsaya daga waje ta shiga ciki ta masa magana, kusan a tare suka fito yana ganina ya hade fuska kamar ba shi ba domin ban taba ganinsa a cikin wannan yanayin ba. “Je ki jira a inda na ce zan fito” “Toh” Na amsa na juya na fice na dawo inda na tsaya dazun a nan ma sai da na gaji na fito harabar asibitin ina dan zagaya idona na zubar da hawaye sannan na hango shi ya fito zan tako na iso gareshi sai yayi min alama da na jira shi a nan, haka na ja na tsaya har ya karaso yana kallona. “Ina wuni ya aiki?” “Lafiya kalau, me kike so?” Sai na samu kaina da nauyin baki na kasa furta komai, wata kila har da fuskarsa da na gani a hade. “Zahra me kike son zama ne? Kin san da cewa zaki saka kanki a cikin matsala ne kawai idan kina kokarin tuntubata? Tun muna yin abu a sirrance har wani ya ji?” Na sauke kai kasa hawaye na zuba. “Me kike so?” Na kasa magana, ya sake tambaya na kasa magana sai hawaye nake yanayin yadda ya zo min na san abun da zan tambaya ba zai samu a gurinsa ba. Tsaki yayi ya juya zai koma sai na kira sunansa. “Dr Hamid” Be juyo ba ya cigaba da tafiya sai na yi saurin binsa ina. “Magana kawai nake son yi da kai” “Wato na gane kina da matsala Zahra, karki saka kanki a matsala kuma ki saka ni ba zaki iya daukar wannan” Ya fada a tsawa yana nuna da yatsa. “Heyyyyyy kaiiiiiii” From nowhere muka ji muryar da ba zan taba iya mantawa tana dira a kunnuwanmu kamar saukar aradu, wanda hakan ya saka mutane da yawa kallon inda muryar take fitowa ciki kuwa har da ni da Dr Hamid, na tabbatar be ji abun da muke fada ba, sai dai ya fahimci akwai rashin jituwa ne saboda nuna da yatsa da Dr Hamid yayi da kuma hawayen da suke min zuba. “Be careful, you have no idea who this woman is” Ya fada a lokacin da ya karaso kusa da mu, Dr Hamid ya kalleni “Who's this” Ni kaina na san ba tambayar waye yake ba, tambayar sanin matsayinsa yake a gurin. “Ban san shi ba” Na amsa ina amsa wani irin kallona na tsana. “Malam Lafiya?” “Zaka san lafiya idan ka sake nuna mata yatsa” Dr Hamid ya tambaya sai Abiey ya amsa masa. “Please tell me shi ne dalilin kukanki” Ya tambaya yana kallona, wannan karon zubar hawayen da nake ba na komai ba ne sai na bakinciki ganin Abiey. Dr Hamid be ce komai ba ya juya ya bar mu tsaye a gurin. “What now Abiey.... Sai me?” Na tambaya ina masa kallon da shi kansa ya san ba shi da na biyu a mutanen da na tsana a duniyar nan. “You called my name Hiayatee.. You say Abiey...” The name part ‘Hiayatee’ ya fi komai kona min rai fiye da ganin fuskarsa a yau, haka yake kiran a wacan gurbatacccen lokacin da muke tare, domin a gurina gurbatacaccen lokaci ne wanda na bata shi a banza a wofi. “Me kike nema a gurin mutumen nan Hiayatee? What do you want?” Wani kallon nake masa zuciyarta na tafarfasa gabana na duka uku uku. “Ka san abun da na ke so? Na daina ganin wannan mummunar fuskar taka, kuma na daina jin sunanka ko wani mai irin sunanka har karshen rayuwata” Share hawayena na yi na juya taku daya biyu ban yi na uku ba ya sha gabana yana min wani kallo na tausayin munafurci. “How are you now? Do you need someone to talk to? I know how you felt” “No you don't... Karya kake yi baka san yadda nake ji ba, baka taba rasa kowa ba balle ka san yadda nake ji, kuma ka ci min fuska a lokacin da naje neman taimakonka and how you're standing in front of me kana tambayar how i feel? Ko kake na fada maka irin zafin da nake ji a cikin zuciyata na rasa masoyi da na yi so that ka yi celebration ranka yayi sanyi?” Guntun murmushi na ga yayi ya sauke kansa kasa ya busar da iskar bakinsa ya girgiza kai at the same time. Na wuce shi na yi gabana. “Sorry about your lost...” Na juyo. “Mijina ba ya bukatar addu'arka” “Not for him, for your baby i just want to let you know that idan kina bukatar wani abu ko wani taimako I'm here for you” “Allah ya raba ni da neman taimako gurin wulakantacen mutun irinka, na yi na daya kuma ba za sake ba har abada” Na juya na cigaba da tafiya zuciyata na mini wani irin zafi marar misaltuwa, haka na bi hanya ina tafiya ina hawaye daga asibitin zuwa gidanmu akwai nisa sosai amman a kafa na taka har gida saboda bakincikin da ya zame min biyu a yau, bakincikin rashin saurare da Dr Hamid yayi da kuma ganin Abiey da na yi a yau wanda shi ya fi ko wane bata min rai. Kamar wanda talauci yayi ma mugun kamu haka na shigo gida domin na rame sosai ga lafiya bata isheni ba ga kuma kuka da na sha, ga kuma tafiyar kasa da na yi sai kashi ya game min. Ina shigowa na fadi kwance saman tabarma sai hawaye suka fara taruwa a idona. Mama na ganin haka ta taso daga inda take zaune tana alwala ta karaso kusa da ni ta taba ni. “Zahra?” “Mama ban samu magana da Dr Hamid ba, tun a lokacin da na tafi be saurare ni awa biyar da ni ina jiransa daga karshe da ya fito ma rufe ni yayi da fada” “Saboda?” “Ban sani ba, be ma saurare ni balle ya ji abun da ke tafe da ni” “Zahra...” Na kalleta sai ta ce. “Tashi zaune” Na tashi zaune sai na jingina da kujerar dake bayana ta zaman tsakar gida. “Kin san dai ni mahaifiyarki ce ko? Ba zan baki gurbatacacciyar shawara ba?” Na daga mata kai. “Ki yi hakuri ki karbi wannan kaddara da hannu biyu, ki barwa Allah komai, da be rubuto miki haka ba da komai be faru ba, ki cire yaron nan a ranki” “Mama so nake na sake ganinsa ko sau daya ne, wata kila shi ne ganina na karshe” “Ki cire wannan a ranki, ka rasa rai ma ka hakura balle wannan da kika san yana raye? Kuma a inda zai samu kulawa mai kyau? Dan Allah ki kwantar da hankali ni ma nawa hankalin ya kwanta kin ji Yata” Na daga mata kai na lumshe ido ina hawaye. “Zan gwada Mama Allah yasa zan iya” Ya rumgume sai na fashe da wani irin kuka mai taba zuciya. “Mama na ga Abiey” Na fada cikin kukan da nake. “A ina?” “A can Mama na tsane Shi” Bata ce min komai ba ta cigaba da rarrashina har na samu natsuwa. ABIEY POV. “Ka yi magana da ita?” Dr ta tambaye ayayinda suka jero suna tafiya. “Yeah but...” Sai kuma yayi shiru. “Ni fa tun dazun kai na tsaya jira and you keep telling me kana cikin asibiti nan all this while baka shigo ba” “Ina shigowa na zan wuce na hangota tana ta safa da marwa i hide somewhere ina ta kallonta you have no idea i feel right now God i love that girl, i love her so much...” Dr ta girgiza kai tana murmushi. “She even called my name Abiey.... And she nailed it” “Just like that tace Abiey” “Tace what now Abiey? But tana cikin damuwa sosai na ga damuwa a idonta kuma na ga kaunata a idonta” “Idonka sun maka karya bana tunanin zaka ga kaunarka a idon Zahra a halin yanzu ban sani ba dai ko gaba maganar damuwa ita kam na yarda 100% tana ciki saboda ta rasa mijinta couple months yanzu kuma ta rasa babynta” “He's not more her miji, kuma wannan tsanar da kika ganin Zahra na min soyayya ce and her first love, Zahra ba zata taba manta rayuwar da muka yi ba, ba zata taba son wani kamar yadda take so na ba, na yarda tana son Deen but not as much as she love me” Wannan karon Dr tsayawa ta yi kallonsa sai yayi murmushi. “Ina son sanin wanene likitan nan kuma me take nema a gurinsa har yake nuna mata yatsa” “Wane likita?” “Ban san shi ba, ban ma taba ganinsa ba sai yau” “Don't tell me you're jealous?” “I have a right to, but it's not about that it's about pointing his finger on her face” “To sannu baban soyayya, yanzu fada min miya kawo ka a gurina?” “Daman ina son na ce ki je ki bincika min lafiyarta ne, but yanzu ba zan sake saka kowa ba i will go by myself, saboda na gane zuciyata tana kirana izuwa gareta ne kai tsaye, abu na biyu na yi magana da Yasmin amman ina son ke ma ki yi na san tana jin maganarki kuma zata fi fahimtarki, so nake tsakanin yau zuwa gobe a lalata maganar nan” “Bata saurareka ba ne?” “Ta saurare ni mana na shiga gidan....” Dr ta yi murmushi bayan ta gama sauraren yadda Abiey yayi da Yasmin. “Zan yi magana da ita you can rest now” “Thank you” Ya furta sannan ya saka hannunsa aljihu yana lalaba keys dinsa, a gurin ya barta tsaye ya nufi gurin da ya faka motarsa domin gurin da nata motar yake aje daban da inda kowa ke ajewa. Farinciki ganin Zahra da yayi a yau ya saka shi manta duk wata damuwa da yake ciki. “You look beautiful when you are looking at me” Ya furta yana murmushi kallon tsana take masa amman a gurinsa kallo ne mai muhimmanci da ace bata kaunarsa da yanzu ta manta komai da ya faru ta masa magana kamar ba au taba samun matsala ba, but ta kasa mantawa saboda ta kasa cire sonsa a zuciyarta. “Let give love another life” Ya furta yana shafa kansa, a maimakon ya tafi gida sai ya juya motarsa zuwa unguwarsu Zahra, ya faka motarsa nesa da gidansu sosai ta jingina da kujerar motar yana hangen gidansu sai ya samu kansa da murmushi yana tuna lokacin da yake fakawa ta fito da gudu wani lokacin saboda ta saci kafa ta shige motarsa ya dauke zuwa wani gurin ko gurin Ammy. “I missed those days, i miss you Zahra so much” Sosai ya kurawa kofar gidan ido yana jin kamar ya sallama ta fito. Ya dora hannunsa kan karjinsa saitin da inda zuciyarsa take yana sauraren yadda take buga masa. Ya dade a gurin kamin ya hango ta ta fito ta hanyar dake facing din inda ya aje motarsa sai dai bata san shi ba ne saboda bata san shi da wannan kalar motarta, gaba daya kuma hankalinta baya jikinta balle zuciyarta ta raya mata zai biyo har ta tsaya kallon ko'ina ta hango shi, tashi yayi zaune da sauri yana kallonta har ta shige cikin gidan. “Bukata ta biya” Ya furta kana ya yi reversed ya juya motar ya fita daga unguwar ya dauki hanyar gidansu Ammy. ZAHRA POV. Bayan sallah Isha'i ina zaune bayan Mama dake sallah Baba ya shigo, na gyara zama na gaishe shi ya amsa ya zauna kusa da ni yana aje ledar dake hannunsa. “Lemu ne bude ki gani idan zaki iya sha” Kallonsa na fi sai na yi murmushi duk da kasancewar ba lallai ne ya gani ba, domin babu nepa a gidan sai hasken fitilar da aka juya kanta zuwa kofar waje. Hausawa suka ce kamar kumbo kamar korensa, salinsa sak irin na ďansa haka Deen yake min baya som shigowa gida ba tare da ya riko min komai ba, ban ankara ba na ji hawaye suna sauko min. “Sannu da zuwa” Na ji Mama ta fada sai na share hawayena na ina jin zuciyata tana min wani iri. “Na gode Baba, ya Hajiya?” “Lafiya kalau take, na yi magana da wanda zai kawo rago jibi idan Allah ya kai mu mahauci shi zai yanka ya gyara...” Yana rufe baki wayar Mama ta yi ringing alamar kira, sai na ga Mama ta yi saurin yanke kiran. “Zahra ina kawarki Hameeda ce ta yi flashing duba ki ga idan akwai kudi sai kirata” Na karba ba dan na san ina da kawa Hameeda ba kuma ban fahimci Dr Hamid ne ya canjawa suna ba har sai da na duba kiran. “Eh bari na kirata” Na tashi da sauri na nufi daki na bar Mama da Baba a waje, ina shiga na kuma can karshen dakin na zauna a kasa na rage muryar wayar sosai kuma na yi kasa da tawa muryar saboda kar a aji na kira shi. Ringing daya yayi picking. “Hello” “Hello” Ni ma fada ba tare na san da wace kalmar zan biyo baya ba, domin shi ya kira ni ba ni na kira ba ban kuma manta da wulakancin da yayi min dazun ba. “Zahra” “Na'am” “Ya gida?” “Lafiya Kalau” “Na kira kika yanke” “Eh wayar ta Mama ce daman line na na saka a ciki, kuma ka kira a lokacin akwai mutane shiyasa aka yanke kiran” “Yanzu fa? Allah yasa ke kadai kike” “Na kebe ni kadai a yanzu” “Ki yi hakuri da abun da ya faru a dazun, ina cikin bacin rai ne sosai shiyasa” Magana yake min ba kamar ba shi ne ya fusata sosai dazun ba akan abun da ban san dalili ba “Amman ya kuke da Abiey?” “Ka san shi ne?” “Fitaccen mutum ne, zai yi wahala wani yace miki be san shi ba” “Mun yi zama makota da shi ne” “Kawai?” “Eh” “Okay....” Ya amsa kamar be yarda ba, sai kuma ya ce. “Anyway dazun me kika zo yi a gurina” “Ba komai” Na amsa domin ban ga amfanin fadin matsalar a yanzu ba. “Am.. Uh.... Yaron nan... Idan aka ba shi nono yana saka shi ciwon ciki...” Faduwa gabana yayi sai na mike tsaye da sauri ina dafe da kirjina. “Miya faru? Miya same shi?” “Ina son na tambaya ko ki bashi wani abu ne lokacin da na bar miki shi a asibiti?” “Wallahi ban masa komai, taya zam cutar da ďana” “Ba maganar cutarwaba ce ina nufin ko kin ba shi wani abu da zai saka shi gurbacewar ciki?” “Ban masa komai ba” “Idan kin san kin yi ki fada so that a samu mafita tun wuri karki je ki kashe shi” “Ban masa komai, dan Allah ka fada min miya same shi? Me zai saka na yi ma masa wani abu?” Na tambaya wani kuka mai karfi na zo mini, gaba daya jikina yayi sanyi gabana kuma sai faduwa yake. “Babu.. Abun da ya same shi... da farko mun dauka ko matsalar daga rashin kyau nonon Jamila ne... Amman an gwada ba shi nonon wata wasu matan har biyu shi ma ya saka su ciwon ciki, kuma ana bashi madara ita ma tana ba shi matsala” “Ban masa komai ba ka bincika nononta wata kila ba shi da kyau” “Nononta lafiya kalau yake, kuma ba nononta kadai ke saka shi ciwon ciki ba, so ki fada tun wuri idan kin san da wata matsalar” “Ban san da matsalar komai ba, da na sani da fada ko dan a ceto rayuwarsa” Ya sauke ajiyar zuciya ina jin kamar akwai abun da yake boye min, sai ya sauke wayar ba tare da yace min komai ba, ni kam tuni hawaye suka wanke min fuska ina jin kamar ďana mutuwa zai yi a hannun wata wanda ba mahaifiyarsa ba. Fitowa na yi dakin na ajewa Mama wayarta na nufi dakin da nake kwana tana tambayar na gama waya da Hameeda kai kawai na iya daga mata na shige, ina shiga na maida kofar na rufe na kife saman katifa sai kuka, shi na kwana yi har safe daman ni da kuka mun dade da kullo abota tun a lokacin da Deen ya fara yin bakwana da duniya ban san wata rana sa zan ce farinciki ya rabe ni ba. Ana gama sallah asuba Mama ta dora min ruwan zafi, daman can da zarar ta gama sallah azuba take dora min ruwa idan ya tafasa sai ta dama min kunu sannan ta zuba min na wanka. Sai da na fito daga wankan na sha nunu sannan na fito waje na aje kofin da na sha da shi da zimmar na hada sauran kayan na wanke. “A a ban saka ki ba, tashi ki je ki kwanta jiya ba ki samu bachi ba” Ya daga kai na kalleta mahaifiyata ce ko ban fada ba zata iya fahimtar halin da nake ciki domin idanuwa da fuskata sun nuna haka, sai dai na san bata son ta yi min maganar saboda Baba yana cikin gidan. Tashi na yi na koma dakina na kwanta sai kuma na ji katifar bata min dadi, na tashi zaune na ranka tagumi ina tunanin anya ban zalinci ďana ba? Da kuma ni kaina? Sai dai wata zuciyar kokarin nuna min take ba ni da laifi na aikata abun da na aikata ne saboda neman mafita, tashi na yi na fito waje na karbi wayar Mama na dawo dakin na kira number Dr Hamid be daga ba sai na ji wani zazzabi ya sauko min, gaba daya na rasa abun da ke min dadi. Na sake kira be daga ba sai na yanke shawarar kira Jamila kai tsaye domin zuciyata ta kwadaitu da son sanin halin da ďana yake ciki, kowane ringing daya tare da bugun zuciyata yake shiga, tsoro nake kar ta ki dauka ta dayan bangaren kuma ina fargabar abun da zan fada mata idan ta daga kiran. “Ya aka yi?” Jikina ya hau rawa na tsoronta can kuma sai na samu kaina da murmushi hawaye na sauko min sakamakon jin sautin kukan ďana da na yi yana fitowa daga cikin wayar. “Ina jinki?” Na kasa magana sai hannu na saka na dafe kirjina. “Mtssssss” Taja guntun tsaki zata yanke wayar sai na yi saurin dakatar da ita. “Daman tambayar jikinsa zan yi” “Shi wa?” “Dana.....” “Danki babu ko kunya babu tsoron Allah? Wato Dr fada miki abun da ya ke ko? To bari na gargade ki idan baki da hankali zan miki shi, daga yau sai yau karki kuskura kiran ďana da sunan ďanki, and daga karki sake kiran wayata sannan idan wani abu kika masa dake saka shi ciwon ciki idan ya kama nono to ki fada tun wuri, domin Wallahi zan iya shari'a dake akan ďana, idan wani abu ya same shi ba zan barwa Allah ba” “Ban masa komai ba, ina rokon alfarmar ki dan Allah ki taimaka min ki rufa min asiri ki bari na ganshi ko sau daya ne” “Baki da hankali Zahra” “Ki kira ni da ko wane kalar suna, ki wulakanta ni yadda ranki yake so zan dauka saboda na ga....” Na kasa karasawa saboda kar na furta kalmar ďana ranta ya bace. “Danki... Dan Allah ki min wannan lamanin dan alfarmar da Allah yayi miki, ki taimaka ki cece rayuwata wata kila ba zan yi tsawon ran da zan sake saka shi a idona ba, waya sani ko nonon mahaifiyarsa yake so?” “Dana ba shi da wata uwa sai ni, ki daina yin abu kamar kin fini sonsa kuma na fada miki tun wuri idan kin san wani abu kika masa ki fada tun wuri, daman can zuciyata bata natsu da baki shi da aka yi kika gani ba har na tsawon lokaci, Allah ya saukewa ďana ya sha nononki ko zai mutu ba zai taba shan nononki har abada...!” Sai da na zabura a lokacin da ta yanke kiran, sai ya rumgume wayar ya runtse ido ina kuka marar sauti saboda kar Baba ya ji ni. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un.... ” Na furta ina jin ina ma ban aikata ba, ashe haka ko wace uwa ke ji idan ďanta yana kuka hankali ya tashi matuka da jin kukan ďana da na yi, ina jin kamar na ruga naje agareshi a guje na bashi abun da yake bukata. “Na cutar da kaina na cutar da jaririn da be san komai ba.... Na saka Hajiya ta yi zaton bata da jika... Na yi dalilin fitar jinin Deen a hannuna, na rasa Deen na rasa ďana wayyo Allah” Wannan karon da da ihu ya ambaci Mahallincina ina jin kamar na yi hauka kuka na zo ta ko'ina Mama ta shigo ďakin da sauri. “Lafiya?” Sai na tashi da sauri na rumgume ta ina jin kamar ita ce zata min maganin matsalolina na fashe da wani sabon kuka wanda ya saka Baba shigowa yana tambayar ba'asi. [10/10, 2:55 PM] Oum_Nuwaira🥰: 2⃣4️⃣ *Littafin nan na kudi ne, karanta na sata daukarwa kanki hakki ne, domin sauke nauyi biya ki karanta cikin aminci, pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 and send the evidence of payment to 08036126660* “Yarinyar nan tana cikin damuwa” Shi ne abun da ya fito daga bakin Baba a tunanin Baba ina kuka ne saboda rashin Deen da baby kawai, Mama dai bata ce komai ba ta yi ta rarrashina har sai da na samu sukuni sannan ta fita ta bar ni a dakin ina ta faman sauke ajiyar zuciya, sai na yi kamar na dauki wayar na kira Dr Hamid sai kuma wata zuciyarta ta hana ni wata kila shi ma idan na kira ya fada min magana marar dadi ko ma ya rufe ni da fada kamar Jamila. Sai da Mama ta sallami Baba sannan ta shigo dakin ta tambaye ni abun da ya faru tun jiya har kawowa yau. Damuwa na gani karara a fuskarta wanda hakan ya saka hankali ya kara tashi. “Mama mutuwa zai yi ko?” Ta sauke ajiyar zuciya ta kalleni. “Babu wanda ya san mutuwar wani sai Allah, ina tunanin na ce ki cire yaron nan a ranki, karki sake kiran wani daga cikinsu da sunan tambayar lafiyarsa, indai na isa na baki shawara ki ji” Na daga mata kaina da ke min wani mugun ciwo sannan na lumshe idona na kwanta. Nan da nan bachi ya dauke ni ban farka ba sai da na ji muryar Yaya Maryam da kuma hayaniyar yaranta ita ta farkar da ni, na taso na fito waje na zauna kusa da ita sai ta kalleni tana murmushi. “Ya jikin Zahra?” “Alhamdulillah” Na amsa da muryarta da bata fita sosai. “Kin ci abinci?” “Eh na sha koko da safe” “Ga danwake na miki na san kina son shi” Ban ce mata komai ba na kwantar da kaina jikin kafadarta sai na ji wani sanyi. “Mama ta fada min abun da ya faru ki barwa Allah komai kin ji Zahra ki saka ma ikonsa da sarautarsa ido, yadda Allah ya so haka yake kasancewa” Na daga mata kai, ina kallon yaranta dake wasa a tsakar gida gwanin sha'awa, sai gani ina murmushi a da can mi ba gwanar son yara bace amman daga daukar cikin nan da na yi zuwa haihuwa Allah ya saka min son Yaya sosai. Ban daga jikinta ba sai da aka kira sallah azahar sannan na daga ta tashi ta yi alwala ta dawo kusa da ni ta yi sallah ta dauko plate ta zuba min danwaken Husna ta dauko min spoon amman sai na samu kaina da kasa ci. “Ki daure ko ci mana, idan kina zama da yunwa zaki jefa kanki cikin wani hali ne kawai sannan hakan yana nuna baki yardar da kaddarar da Allah ya dora miki ba” “Ina jin tausayin yaron nan, ina jin tsoron hakkinsa da Allah zai tambaye ni” Na dauki spoon na na debi ďan waken na kai bakina. “Yau da safe Abiey ya zo gidanmu” Kasa tauna ďan waken na yi na kalleta. “Gurin me? Cewa yayi yana son magana da ni amman kamin yayi magana da ni sai da ya fara yi da Abban Husna” “Maganar me?” “Kawai dai ya tambaye ni ne damuwarki, yace ya gan ki asibiti jiya tare da wani likita, yana son ya san ko akwai wani abu da kike bukata ne” Kamin na ce komai Mama dake daki ta ja tsaki ta ce. “Abiey dai be san kunya ba, ni abun da yake a yanzu shi da yan'uwanshi har mamaki yake ba ni, kawai dai bana nuna musu komai ne saboda hali da tunani ba daya ba, kuma tun da har abun ya wuce kara a bar shi ya wuce kawai” “Ban san manufarsa a yanzu ba, ko da zan nemi taimako zan nema a gurin sa a yanzu? Bari na fada muku abun da na boye lokacin da Deen yake cikin ciwon nan sai da naje neman taimako gurin Abiey amman be taimaka min ba, sai ya nuna be ma san ni ba” Ina rufe baki Mama ta fito daga dakin tana fadin. “To ke miya kaiki a haka kuma kike zancen sake neman taimakonsa kwanakin baya? Har kike tunanin zai iya daukar miliyan ashiri ya baki?” “Miliyan ashiri na me?” Yaya Maryam ta tambaya, sai Mama ta fada mata tana kokarin zaunawa. “Wai ta fanso ďanta, mutumen da ya so saka mu a kunya a ranar daurin aurenki kike tunani zai miki haka? Yanzu ma ban zan abun da yan'uwansa suke nufi ba ai Wallahi amanar Zahra sai ta fita a gurinsa” “Wata kila kuma duk ba mu fahimci abun ba Mama” Daga ni har Mama kallonta muka yi. “Kamar ya?” Mama ce ta tambaya ni kam kasa cewa komai na yi. “Wani lokacin abubuwa suna zuwa ba ta yadda muka tsammani ba, kuma gaskiyar mutum ba zata iya fitar da shi ba sai da hujja” “Ni fa ban gane wannan abun da kike kokarin fada ba?” “Mama Abiey ya shigo har cikin gidana tare da mijina mun yi magana ta fahimta da shi, farkon abun da ya kawo shi a gurina na bincikar lafiyar Zahra ne da kuma bata taimako idan tana bukata, sai da ya fadada min abun ya kwance sirrin dake boye ya cire ni daga cikin hudun da nake ciki” Na aje spoon din hannuna. “Ya dai shimfida miki karya ya shirya yadda zai wanke kansa ya samu karbuwa a gurinki, saboda amana ta kama shi kuma yana son ya sake cutar da ni” Mama ma dariya ta yi. “Maryam kina da karamar kwakwalwa, maganar wuni daya ta saka kin manta da duk abun da ya faru?” “Maganar wuni daya tana iya wanzar da zaman lafiyar da aka shekara dubu ba a samu ba, wuni daya na iya warware yakin da aka dade ana yi, kuma tun lokacin da abun nan ya faru ba mu ji bangaren Abiey ba, ba mu taba tsayawa mun saurara ba, sannan Mama akwai wasu abubuwan da ya kamata hankali ya fahimta” “Da alama Abiey yayi miki biya mai kyau kudi ya baki ko ya miki alkawarin wani abu ne? Shiyasa har kika zauna kina tsara wannan maganar” Sai ta kalleni tana murmushi. “To ni waye sai siye saboda na wanke shi? Wanke shi a gurinki ba ina nufin ki so shi ba, kawai dai ina fadar abun da na fahimta wanda shi ne gaskiya” “Kamar ya?” Ta kalli Mama. “Mama baki yi tunani ba lokacin da Ammy ta rantse da Allah Abiey ba zai auri Zahra ba? Kuma ta ce idan har ya aureta zata tsine masa albarka? Da ace bata son Zahra tun farko ba zata bari ayi baiko ayo lefe a biya sadaki ba” “Ai sheri suka mata alhalin karya ne” “Dr Zainab ce ta shirya haka saboda bata da wata mafita a lokacin sai wannan, amman abu ai ya kamata ace mai hankali yayi tunani ace duk soyayyar da Abiey yayi da Zahra sun rabu a ranar daurin aurensu? Kuma tun lokacin Abiey be yi aure ba dace yaudararta yake son yi da yanzu yayi aurensa shi ma har ya haihi ko ya kusa haihuwa, bayan kuma duk abun da ya faru yanzu ya dawo yana bibiyarta shi fa saurayi ne a yanzu ita kuma ta yi aure har ta haihu, idan ba kyau ba me ye Zahra take da shi da zai saka Abiey ya dawo yana neman sulhuntawa da ita har yana damuwa da damuwarta, yana da kudi iyayensa suna da kudi yayi suna da zai iya neman auren yar kowa ya a bashi, amman duk ba yi ba” “Karya yake yi ya yaudare ni ne kuma amanata ta fara fita shiyasa yanzu ya dawo yana neman inda zai fake” “Fada min Zahra kamin yanzu Abiey ya taba nemanki da iskanci?” Na girgiza kai. “Be taba ba ai be ga fuska ba” “Shi na san akan ce idan namiji ya kwanta da mace ba zai aureta ba, ya yaudare amman ke ya rasa ranar da zai miki haka sai ranar da za a daura aurenku? Alhalin ba ki tana masa komai ba?” “Daman Deen ya taba fada min ai yayan manyan mutane ba sa auren yayan talakawa, haka baya faru a zahiri sai a littafai ko a fina fina kuma na yarda tun da gashi anyi min” “That's the point Deen ba shi ya lalata duk wata alaka a tsakaninku, ke kanki kin san son da Abiey yake miki ba na wasa ba ne kuma babu abun da zai saka yayi miki haka..” Mikewa na yi tsaye na shuri da plate din danwaken da ta kawo min. “Ban taba jin na tsaneki ba sai yau, Deen ya gama min komai Maryam tun da ya cire kunya a ranar da Abiey ya so saka ni, kuma ya rike ni amana har karshen rayuwarsa, Wallahi babu wani abu da zaki fada da zai saka na ga hasken Abiey ko da digo daya ne, babu wani abu da zaki yi ki saka na ga laifin Mijina sai dai na ke ki bata kanki a gurina, mijina yayi mutuwa kyakkyawa babu wanda zai bata masa suna” Mama ta mike tsaye ta rike ni domin fuskata da hawayena sun nuna maganar da nake da gaske nake yinta. “Maryam be kamata ki yi wannan maganar ba haba?” “Wallahi Mama dan baki san gaskiya ba ne, daman zuciyata ta dade tana raya min abubuwa kawai dai ban ce komai ba, amman ki duba yadda lamarin nan ya faru kina gani kin san akwai lauje cikin nadi, sannan ki duba yadda Deen yake cewa ta masa alkawari bayan mutuwarsa ba zata auri wani ba, ciwon nan nasa ma fa son yayi ta dauka kawai dai ba a son ana fadar abubuwan marar kyau akan mamaci ma amman Wallahi Deen din nan ba mutumen kirki ba ne ni daman ban so aurensa da Zahra ba” Ban san lokacin da na nuna da yatsa ba. “Karya kike yi Maryam Deen mutunen kirki tun da be taba kashe kowa ba, kuma be sace abun kowa ba kuma ba zaman banza yake ba yana da sana'a, Deen ya gama miki komai a rayuwa tun da ya rufawa yar'uwarki asiri ya aureta a lokacin da wani banza ya so ya tona mata asirin, kuma daga yau sai yau karki sake furta wata kalmar akan mijina” “Dole ne na fada miki gaskiya saboda ni yar'uwarki ce...” “Na datse zumuncin dake tsakanina dake daga yau, indai saboda yan'uwantaka zaki fada min wata magana marar dadi akan mijina to daga yau karki sake kirgawa da ni a cikin yan'uwanki” “Saboda wani banza zaki....” “Mijina ba banza ba ne ban yafe miki ba Maryam” Mama ta rike domin kokarin kai mata hannu nake duk kuwa da na san bana iya dukanta. “Ya isa haka haba Maryam, ko Deen be auri Zahra ba be dace ki masa haka balle ya auri yar'uwarki” Fashewa na yi da kuka sai Mama ta rika ni ta saka ni ďaki, Yaya Maryam kuma ta dauki jakarta ta fice tare da yayanta ko sallama bata mana ba, bana taba jin bacin irin na yau ba, ban tana jin na tsani Maryam irin yau ba, ashe a cikin yan'uwanka ma akwai makiyanka, ko kadan bana son na ji wata magana marar dadi akan Deen domin be rage ni da komai ba, kuma na san Abiey karya kawai yake masa. A yau na tabbatar da wani bacin rai yafi gaban kuka domin ina shiga dakin hawaye suka daina min zuba sai bugawa kirjina yake kamar ya fado, lallai a yau na kara tabbatar da Abiey ba mutumen kirki ba ne kamar yadda Deen ke fada min. “Ka yi gaskiya baka raye amman yana maka kazafi saboda ya bata ka a gurin mutane, mugun halinsa na ta kara bayyana, na so ace kana raye Deen ka ga wannan ranar kunnuwanka su ji maka abun da makiyina yake fada bayan ranka, mutum mugun ce dan'adam butulu” Na fada ina murmushin takaici. “Yau da yar'uwata za a zauna a zagi mijina? Wannan bakinciki yayi min yawa da wannen zan ji? Rashin mijina ko na ďana ko kuma na abun da Maryam ta yi min a yau” Na fada daman can ko lokacin da ina budurwa idan muka samu matsala da ita bana kiran da Yaya Maryam sai dai Maryam kai tsaye. “Mama wai ki ji wannan abun? Allah ma ya isarwa Deen” Mama dai bata ce min komai ba, ni ka dai na yi ta mitata har na yi na gama ban ji bakinta. “Zahra kin ga mutumen nan yana ta kira amman bana son ki dauka” Na fito da sauri daman tun dazun nake ji wayarta tana ringing sai dai ban maida hankali a gurin ba saboda raina a bace yake. ‘Wata kila fada zai yi yace miyasa na kira Jamila?’ Wata zuciyarta ta raya min sai dai hakan be hana ni picking ba. “Hello” “Zahra ya gida?” Na ji muryarsa tsabanin yadda na yi zaton zan ji ta. “Lafiya kalau” “Am na yi magana da Jamila akan matsalar yaron nan muna son zaki matsa nononki mu gwada ba shi mu gani saboda mu na son mu gano inda matsalar take” Na kai hannuna a kirjina ina jin wani irin sanyi marar misaltuwa, sai dai ban yanke hukunci kai tsaye ba. “Zan yi shawara da Mama tukuna idan na yanke hukunci zaka ji ni” Ina fadar hakan na yake wayar na zauna kusa da Mama da sauri ina fada mata. “Amman ke zaki iya kina matsar nononki kina bashi?” “Eh mana Mama tun da har akwai ruwan nonon mai zai hana na yi haka, kuma gwadawa za'ayi aga idan shi ma be saka shi ciwon Cikin ba” “Ina tsoron kar asirinmu ya tonu Zahra? Saboda idan kina ba shi nono wata rana za a gane, kuma duk ranar da asirinki ya tonu zaki sha magana a gurin mutane Hajiya kuma ban san da wane idon saki kalleta ba” “A boye zan rika ba shi babu wanda zai sani da yardar Allah” “Shikenan, amman karki saurin nuna masa kin amince tun da gashi har sun fara zarginki” “Toh Mama” Ban kira shi a lokacin ba duk da kasancewar na samu goyon Mama kuma abun ne da zuciyata take so, haka na daure har sai da ya sake kirana da kanshi shi ma kuma ba kai tsaye na nuna masa amincewata ba sai da ya hada da magiya. Da yamma lis ya aiko yaro ya lunch box na yara, na karba ina budewa sai na ga wata yar karamar gora a ciki, na sallami almajin ni kuma na shiga daki na fara matsa nonon da ya kusan dankarewa saboda rashin tsotson, ban tana sanin akwai azaba a matsar nono ba sai a ranar idan na matsa sai na runtse ido na bude da taimakon Mama na samu na yi rabin karamar gorar daker sannan na kira shi a waya na fada masa ya aiko almajiri, bayan kamar mintuna biyar muka ji sallamar almajiri Mama ta amsa ya ce “Wai wani a waje ya ce a bada sako ” Mama ta rufe lunch box din ta kai masa, ba ayi minti talatinba zazzabi ya rufe ni Mama ta dauko min magunguna na sha kamin ta dauke ledar maganin muka ji sallamar Hajiya da yan'uwanta. JAMILA POV. Expensive white curtains din falon kawai zaka kalla kasan mutanen da suke rayuwar a cikin gidan ba su darajar nera ba, balle kuma ka sauke idonka akan set 3 na mayan kujerun da suka kawata falon, ko wane corner na katon falon air conditioner ne a tsaye, komai na falo fari ne ciki har da dinning din da aka yi ma area dabam, daga cikin falon kana iya hango wani kasaitacen falo madaidaici da aka kawata komai na sa blue, dama da falon wani katon stairs da mutum biyar za su iya jerawa su hau ko su sauko a tare, an gawata ko wace kusurwa ta falon kamar ba a mutu ba, Jamila ce zaune a rumgume da jaririnta a daya daga cikin set din kujerun da suke falon fuskarta a hade tana juya gorar nonon dake hannunta. “Idan ya sha be yi ciwon ciki ba hakan na nufi wani abu ta yi ma masa kenan?” Dr Hamid ya aje numfashi a hankali. “Be zama lallai ba, saboda nonon ki ba ainahin na haihuwa ba ne sai da aka hada wasu abubuwan sannan ruwan nonon ya zo” “To madarar dake saka shi ciwon kiki fa?” “Daman ba kowane cikin jinjiri ke daukar shan madara ba, kawai mu yi fatan idan ya sha zai samu lafiya ba zai saka shi komai ba” “Me hakan ke nufi?” “Sai a rika karbo masa mana, ko kuma ta dawo nan ta zauna har zuwa lokacin da zai fara cin abinci sai a yaye shi” Ta yi wani shu'umin murmushi. “Ba dan kana dan'uwana ba da sai na ce Zahra hada kai ta yi da kai saboda ta samu abun da take so” “Jiya ta same ni office na mata abun da be kamata na yi mata ba, saboda na samu ta rika nisanta kanta da ni gudun kar ta ja mana matsala, sai dai ganin ba mu da wata mafita ya saka na yi bita da lalama ina tambayar dalilin hakan yasa ta kira shi saboda ta ji lafiyar yaron nan, idan har ya tabbata nonon mahaifiyarsa yake so to dole za a rika ba shi shi domin shi ne rufin asirinmu” “Ban taba ganin jaririn da aka haifa ace idan an bashi nono ko madara yana saka shi ciwon ciki ba sai wannan, waya sani ko wani abu ta yi masa lokacin da ka bar mata shi mutane fa sai Allah zata iya ba shi wani abu ko ta shafa masa” Dr Hamid yayi shiru yana nazari. “Mai yiyuwa amman bana tunanin haka” “Ni kam ko da nononta ya ba shi lafiya ba zan yarda ta cigaba da ba shi nono ba” “Zaki iya rasa shi, domin dole ne a dakatar da bashi wannan nonon da madara idan kuma baya cin komai kin san ba zai rayu ba, sannan kin ji yanzu mijinki yana maganar fitar da shi waje, idan kika yi sake aka zurfafa bincike za a iya Mijinki zai iya gano cewar ba ďansa ba ne saboda blood type din yaron nan ba irin na mijinki ba ne, ya kamata ki yi taka tsantsan domin ba ke kadai ce a cikin matsala ba har da ni” Ta daga kanta sama ta sauke ajiyar zuciya. [10/12, 9:15 PM] Oum_Nuwaira🥰: 2️⃣5️⃣ Ya saka dayan hannunsa ya dauki daya daga cikin tawul din dake nade a durowar ya goge fuskarsa zuwa kansa, sannan ya fito dayan hannunsa rike da wayar dake jone a kunnensa. “Idan ma abun da kake fada haka ne, ai ba wannan hanyar ya kamata ta biyo ba” “Bata da wata hanyar ne sai wannan a yanayin yadda Yasmin take da kunya da zata iya fitowa kai tsaye ta nuna maka ba, wannan ce kawai damarta kuma kai da kanka ka samar mata ita” “Ban yi dan nasan zai kawo min matsala na, da ace na san Yasmin zata min haka da zan saka sunanta a ciki ba, kuma wannan abun ma ai rashin kunya ne, zata raba min hankali biyu ni kuma ina son tunani ya tsaya akan Zahra ne kawai” “Dole ne ka yi taka tsantsan kuma la bi Yasmin a hankali domin idan ka ce zaka mata jan ido zata iya bata lamarin” “Mun kusan kawai a haka ai, matukar ba ta yi abun da na roke ta” “Amman Abiey kasan zaka iya hadawa biyu? Ga Zahra ga Yasmin?” “Nonono kasan mata basa son kishiya and i think Zahra tana daga ciki, ko da ma ace tana so ni a karan kaina ba zan iya hada soyayyarta da wata ba” Ya fada yana kallon kanshi a madubi. “But ka san minenen? Ni Wallahi at first na dauka kana da feelings akan Yasmin ne” Guntun murmushi yayi. “Wani lokacin tana min yanayi da Zahra ta hanyar magana da mu'amala amman hakan ba shi ke nufin ina son Yasmin ba” “Buddy i hope Zahra zata fahimci wannan soyayyar da kake mata ba tare da ka wahala ba” “ni ma fatana kenan, sai dai kasan turawa sun ce what come easy won't last and what last won't come easy, Deen ya riga ya bata komai wai lasan mugun nan har cewa yayi ta masa alkawarin ba zata auri wani namijin ba bayan mutuwarsa?” “What!? Da gaske? Kai a ina ka ji wannan maganar?” “Yayarta take fada min” “Yayarta fa ka ce? Taya?” “Yes na na je asibiti saboda na yi magana da Dr akan Yasmin sai na samu Zahra a aibitin, ta kusan bata awa hudu ko biyar a gurin tana jiran wani likitada karshe da ya fito ma sai ya rufe ta da fada ita kuma ta fara masa kuka, ban san abun da take nema a gurinsa ba amman dai na fahimci akwai damuwa a tare da ita sosai, a talk to her bata saurareni ba, that's why na je kai tsaye gurin Yayarta at that time na shirya fuskantar duk wani lokaci da yayarta zata min damuwarta ce ta dame ni, na karanci damuwa a idonta sai dai ba lallai ne ta ba ni damar yaye mata damuwar cikin sauki ba, haka yasa na tafi gidan Yayarta na saka aka min sallama da mijinta na fara magana da shi sannan na min izinin ganin matarsa, na zauna na gaisa da ita the first da ya fara fitowa bakinta wai ban ji kunya  ba na zo gurinta bayan duk abun da na yi?” Ya juya ya ba madubin baya. “Ka ce mata me?” “Na shimfida mata duk abun da ya faru, kuma na jidadin yadda ta fahimta daman sai da na fara fahimtar da mijinta, a lokacin ne take fada min cewa yace ta masa alkawarin ba zata auri kowa ba bayan ransa, and ya cigaba da mu'amalarta after likitoci sun ce ya kebe kansa, ina mamakin wane irin so yake mata ne? Wannan ba so ba ne, sam mun dai gode Allah ya mutu da wuri” Sauban yayi dariya. “Ya cika zafin kishi Gaskiya” “It's not about kishi wannan ba so ba ne kai baka gane ba? Idan yana sonta ai ba zai mata haka ba” “Allah ya kyauta yanzu dai you got lucky Yayarta ta saurareka, sauran Mamanta da Zahra, sai dai zaka sha wahala kamin Zahra ta fahimta saboda tana son Deen sosai” “Sometimes Sauban kana abu kamar baka san waye ni ba, taya zaka bude baki kai tsaye ka fada min Zahra taba son Deen sosai, kamin Zahra ta so Deen wa ta fara so? I'm her first love duk wanda Zahra zata so bayana yake Wallahi tana son Deen ne by force saboda tana ganin ya taimake ta a lokacin da na gujeta bayan kuma shi ya shirya komai” “Easy Men... Yanzu yaushe zamu je mu yi mata gaisuwa?” “Shi ne matsalar ai amman dai zamu je i will call you back” Ya sauke wayar tare da ajiyar zuciyar da har wani zafi take masa saboda Sauban yace Zahra tana son Deen sosai. Windows din dakinsa ya nufa ya bude yana hango kasan benen wani iska mai dadi na ratsa shi. “Zahra bata taba son Deen sama da ni ba never” Ya karasa furucin da karfi, can kuma ya juyo ya fito dakin zuwa dakin Anty a hankali ya tura kofar dakin ya shiga, Anty dake aikin nade wani farin lace ta kalleshi fuskarta da murmushi. “Angon Zahra na Yasmin” Murmushi ne ya cika fuskarsa sai ya ji kamar Anty ta yaye masa damuwarsa saboda kirarin da ta yi masa. “Angon Zahra din dai ya wadatar” “Ita Yasmin din ta fasa ne?” Wani guntun murmushi ya yi mai hade da mamaki. “Anty ya kike magana kamar ita ce namiji ni ne mace” “A matsayin da kake a yanzu ai kai ne mace ita ce namiji domin idan har bata ce ta fasa auren ba, kasan Mai Martaba ba zai aminta matsala ta fito daga gurinka ba, kuma zai dauka kana wasa da hankalinsa bayan an je an tambaya aure sai kuma ka ce ba ka son yarinya a yanzu, kar fa ka manta wannan ne karo na farko da Mai Martaba ya nuna damuwarsa akan lamarin ka har ya shiga ciki, aiko ka ga wannan amaryar mai tsada ce” “Na yi magana da ita tun shekaranjiya kuma na samu Dr ita na mata magana na san zata yi mata magana” “Zauna Abiey” Ya zauna yana kallonta. “Wata Dr ko Ammy ko ni ko Momy ba za mu iya canja ra'ayin Yasmin akanka ba matukar tana sonka, amman kai zaka iya canja ra'ayinta ko da kuwa tana sonka” “Anty na yi magana da ita, kuma ina tunanin ta fahimta in dai ba jan ido take son na yi mata ba” “Ba maganar jan ido ka zaunar da ita ka fahimta da ita cikin hikima ku yi magana ta fahimta ta yadda zata fahimce ka kai ma kuma ka fahimce ta, a tunani zata yi ta amsa maka da to ne kawai amman ba zata taba aikata hakan ba” “Shikenan zan sake magana da ita, amman shi ne na karshe idan ba ta yi ba zan samu Mai Martaba da kaina na fada masa cewar bana ra'ayinta” “Karka aikata haka kara dai ka hakura matsalar ta fito daga gurinta” “Okay... Anty yaushe zaki je yi ma Zahra gaisuwa?” “Tare da kai ya kamata mu tafi kafata kafarka kai ma ya kamata ka fara motsawa ai, duk dai be dade da rasuwa ba, amman ya kamata ka fara nuna mata kulawa ta san da cewar har yanzu kana kaunarta” Anty ta fada tana murmushi. “Zamu je tare da ke da su Aisha sai ku shiga ciki ni zan tsaya daga waje, idan ta ga tana ra'ayin gaisawa da ni zata fito” “Shikenan to ka saka mana rana” “Gobe” “Allah ya kai mu” Ya amsa da Ameen, sannan ya mike tsaye yana shafa aljihun wandonsa ya fice daga dakin. Dakinsa ya koma ya dauki one of his car keys sannan ya nufi downstairs ya sauko yana kallon Aisha dake cin salad ya mayar mata da murmushin da ta yi masa sannan ya nufi kofar. “Abiey ina zaka je?” Ya dawo baya yana kallonta. “Ke ba uwata ba, ke ba matata ba ki tsayar da ni haka nan kawai da tambayar inda zan je? Kin fi kowa sanin na tsani tambayar nan carefully next time” “Sorry..” Ta fada tana kama kunnuwanta be sake ce mata komai ba ya fice, few steps suka isar da shi gurin motarsa tun kan ya karasa ya dannan keys din hannunsa ya bude motar ya shiga. Tun kamin ya isa yake ta tsara kalaman da zai samu Yasmin da su, but before yayi magana da Yasmin ya kamata yayi magana da Dr so that ya san yadda suka yi, kamar ya dauko hanyar gidanta sai kuma wata zuciyar ta raya masa ya fara kiranta. Wayarsa ya dauka yayi dialing mumber ta ringing daya ta yi piciking. “Hello Abiey yanzu fa nake kokari kiranka” “Miya faru? Kin yi magana da Yasmin?” Dr ta juya ta kalli Yasmin dake zaune a kusa da ita sannan ta amsa masa. “Eh amman zai fi kyau ka same ta ta kanka akwai abubuwan da take son fada maka” “Kamar ya?” “Tana gidana yanzu haka, saboda na kirata na yi magana da ita” “On my way” Ya yanke kiran sai sake kiran Sauban. “Sauban ya maganar ginin gidan nan?” Shi ne abun da ya fara tambaya lokacin da Sauban yayi picking call din. “Yana nan ana kan shi abu yayi nisa ma” “Thank you, and you too ya kamata ka samu time ka je gaisuwa” “Idan ka shirya sai mu tafi tare” “Zamu je da Anty gobe” “Okay kira ni idan kun tashi” Da haka suka rabu, sannan ya rike wayar a hannunsa ya cigaba da tukin da dayan hannu har ya isa gidan, ya dade cikin motar domin ba kasafai yake son shiga cikin gidan ba gudun kar mijin Dr ya same shi a ciki domin ba sa jituwa da juna tun daga lokacin da aka fasa aurensa da Zahra. Har ya daga waya ya kira Dr yace mata yana waje sai kuma ya fasa ya bude motar ya fita ya nufi cikin gidan. Sau daya ya taba door bell din ya ja ya tsaya yana kallon harabar gidan, Dr ce da kanta ta bude masa. “Welcome” Ya shigo ba tare da ya amsa ba, idonsa be sauka gurin kowa ba sai Yasmin dake zaune a kujerar dake facing din kofar idonta yayi ja sosai har ya kumbura. Juyowa yayi ya kalli Dr sannan ya sake juya ya kalleta. “Yasmin?” Ta sauke kanta masa wasu hawayen na sake taruwa a idonta, sai ya sake kallon Dr a karo na biyu irin kallon nan mai alamar tambayar, kafada ta daga masa ta rufe kofar ta nufi kitchen tana fadin. “Ka sauke ta gida” Yasmin ta mike tsaye ta dauki yar karamar rigarta ta gyara mayafinta kamar daman can shi take jira, Abiey can't tell why yake jin rashin dadi na ganin hawayen Yasmin duk kuwa da be san dalilin zubarsu a idonta for now. Da kansa ya bude mata front seat ta shiga ta zauna sannan ya rufe ya zagaya driver side ya shiga yayi ma motar key, the whole journey is full of silent words, ko da abun da yake tunani kuma yake sakawa a zuciyarsa. Sai da suka kusan isa gidan Momy sannan Abiey ya kalli Yasmin da har lokacin hawaye take sharewa ya ce. “Are you okay Yesmin? Can we talk?” “Me zamu yi magana akai? Rabuwarmu?” “Mu ba masoya ba ne, balle ace zamu rabu” Ya fada yana wata yar siriyar dariya. “Anty Zainab ta yi requesting wani abu a gareni mai matukar tsada da wahala, Momy ma ta yi kai ma kai yi saboda na su san abun da nake ji ba, amman ina son na tambaye ka?” “Uhmm” Ya maida dukan hankalinsa gurinta. “Ya aka ji a lokacin da ka rasa Zahra?” Ya tsayar da tukin da yake ya samu gefen titi ya faka motarsa. “Kamin na fada miki abun da na ji, ina son ki shirya ki tafi gidansu Zahra ki tambaye ya taji a lokacin da aka fasa aurenmu? Ya take kallona? Wane irin hali ta shiga? Daga lokacin zaki fahimta ki yanke hukunci akan dalilin daya saka nake ta rokon ki sa a fasa baikon nan da kanki” ‘Miyasa ka koya min sonka?’ Ta tambayi kanta tana kallonsa wani irin kaunarsa na fisgarta kamar ta bude zuciyarta ta saka shi ciki ta rufe, can kuma sai ta lumshe ido ta hade yawu a hankali, ya kalleta sannan ya cigaba da tukin har suka isa gidan be sake ce mata uffan ba, sai dai hawayen da take sun saka shi jin babu dadi. ZAHRA POV. Nasiha sosai Hajiya ta yi ta min tana kwantar min da hankali, ban taba ganin wata sarakuwa mai son matar ďanta kamar yadda Hajiya take so na ba, tun kamin na auri ďanta bata taba nuna min banbanci da yarta Bahijja ba balle kuma yanzu da nake ganin kamar ma tafi so na fiye da yarta, farfesun kan rago ta kawo min yan'uwanta da suka zo tare da ita kuma kowa ya dauki kudi ya bani sai bayan sallah magariba suka tafi. A daren ranar da tunani biyu na kwana a raina, tunanin abun da Yaya Maryam ta fada akan Deen da kuma nonon da za a baiwa yarona ina ta addu'ar Allah yasa kar nonon ya saka shi ciwon ciki. Washe garin bayan na yi wanka na shirya Mama ta kawo min abun karyawa, a yau kukun mai kayan sabe sabe tayi min wato na gyaran nono daman tun da asuba na ji ta tana aikin daka kayan da muke da su sai dai ban yi zaton ni zata damawa ba. Ban kuma yi mamakin ganin haka ba saboda na san ta yi min ne saboda nono na yayi kyau. Da rana ma tuwo ta yi min da miyar shuwaka da kifi, ba laifi na ci tuwon sosai kamar ba ni ba, domin na dade ban sake jiki na ci abinci mai yawa haka ba. “Zahra kin san abun da kika yi ma yayarki ba ki kyauta ba?” Ina daf da gama sudar yatsun hannuna Mama ta yi min wannan maganar. “Amman Mama ita baki ga abun da ta yi min ba? A kaddara ma da gaske Deen ya aikata abun da take fada, ai be dace ta zo tana fada ba a yanzu saboda baya raye, kuma akwai ďana a tsakanina da shi ba zan jidadin ta aybanta uban ďana ba, Mama Wallahi ko da ace Deen ya aikata hakan da gaske to na jidadi domin shi yake nuna cewar kaunar da yake min mai kyau ce marar algus, domin ya rike ni amana ya nuna soyayya da kaunar da na san har na mutun ba zan sake samun irinta ba, a tsawon zaman da muka yi Deen be taba daga min murya da sunan zai min fada ba ko kuma ya nuna ni da yatsa balle har ta kai ga ya doke ni, mahaifiyarsa bata taba nuna min banbanci da yarta ba, shin hakan be isa ya saka na so Deen ba? Miya laifinsa idan ya yaki kowa akan abun da yake so? Da ace Abiey yana so na da gaske da be guje min ba ko da kuwa mutuwa zai yi a ranar, balle ma na san karya take ita ma kuma ba laifinta ba ne laifi Abiey ne shi ya shirya wannan saboda ya wanke kansa kuma ya sake dawowa ya cutar da ni” Mama ta gyada kai. “Gaskiya ne, idan na gaske ya aikata to ya rike amana irin rikon da ko wace uwa take son ayi ma yarta, Allah ya masa Rahma” “Ameen” Na amsa ina jindadin addu'ar da Mama ta yi masa, ni kam na san indai ba a yabawa masoyina ba to ba za a zage shi ba. Bayan sallah La'asar kiran Dr Hamid ya shigo wayar Mama da gangan na ki dagawa har sai da kiran ya yanke, fargaba nake kar a fada min cewar jajarin yayi ciwon ciki bayan ya sha nonona, yana sake kiran wayar gabana ya fadi sai da na yi Bismillah sannan na daga kiran na kai wayar a kunne ina kallon Mama. “Hello” “Zahra ya gida?” “Lafiya Kalau” Sai shiru ya biyo baya ni da shi babu mai cewa uffan har na kusan dakika ashiri. “Hello” “Yeah ina jinki daman na kira na fada miki za a sake gwada ba shi nononki a karo na biyu daga nan sai mu bincika mu gano daga ina matsalar take” Lumshe ido na yi na kai hannuna kirjina ina jin wani irin sanyi a raina, domin ko be fada min ba na san nonona be saka ďana ciwon ciki ba. “Ban fahimce ka ba” “Zan kawo miki goro ne sai ki sake matsa nonon naki ki ba shi” “Aa gaskiya” Na amsa kai tsaye kamin na dora da cewa. “Yawan matsar nonon zai iya sakawa mutane su gane, kuma ni ina jin zafi ba zan iya cigaba da yin hakan ba” “Sai ya kenan?” “Idan tana son na bashi nono sai dai ta kawo shi ya rika sha idan ya koshi sai a maida shi gurinta, shi ma kuma a bisa sharadi” “Wane irin sharadi?” “Zata biyani na shayar da yaronta, domin hakkin shayar da shi a yanzu ba a kaina yake ba” “Zahra ya kike magana kamar ba ke ba? Ko kina ganin kamar kin samu wata damar da zaki wasa da hankalin mutane ne?” “Ina zancen wasa da hankali a muhalin da zan taimaka muku? Ban ce dole ba fa idan kun ji kuna iyawa ne kawai” Wani uban tsaki yaja ya kashe wayar. Sai na yi murmushi Mama ta kalle ni tana fadin. “Miyasa kika yi haka?” “Mama ai maganin biri karen maguzawa, idan ban musu haka ba ni za su fara disgawa a yanzu ma ai be nuna min nonon ya karbe shi ba sai cewa yayi wai za su kara gwadawa ba, kin ga ta nan zan gane idan ta gaske tana son yaron nan ko ba komai zan samu kusanci da shi, ina kallon wannan abun a matsayin wata mafita da Allah ya kawo min” “Ina ji miki tsoron kar hakan ya janyo miki wata matsala a nan gaba” “Babu wata matsala da zai janyo min da yardar Allah ke dai kawai ki taya ni da addu'a” “Idan kuma ta yardar ki cigaba da zuwa kina shayar da shi, ba ki tunanin asirinta zai tonu? Kuma ke ma naki zai tonu? Domin mutane za su yi mamakin ace kina yawan fita zuwa wani gurin ga shi ko arba'in ba ki yi ba” “Mama maganar mutane baya saka ni yin abu ko ya hana ni a yanzu, matukar kin amince bana shayin kowa lokacin da zan rasa mijina mutanen suna ina? Miyasa ba su kawo min dauki sun hada min ko da rabin kudin na yi magani ba? Sai yanzu za su fara magana? Maganar su ba zai dame ni ba” “Tun yanzu dai sai ki tanadi abun da zaki fadawa Hajiya ba sai gaba ba, domin ina hango abun da tunaninki be baki ba a lamarin nan” Na yi shiru ina sauke dogon numfashi. [10/14, 8:36 PM] Oum_Nuwaira🥰: 2️⃣6️⃣ Ta mike tsaye da sauri ta sha gabansa. “Haba Hubby miyasa kake da saurin fushi ne? Abu kadan sai ka hau ka fara fada ba zaka ma tsaya ka saurareni ba?” “Me zan saurara? You're just try to kill my son, yaron nan baya samun lafiya idan ya sha nononki amman kin ki yarda kowa ya duba shi sai ďan'uwanki tun da kika samu cikin nan ba ki yarda da kowa ba sai ďan'uwanki har sharadi na gindaya miki cewar ba a nan zaki haihu amman kika bijire kika dauki kawarki kuka je asibiti sai kirana ka yi aka fada min kina gurin haihuwa, waya sani ko haihuwar da kika yi a nan ne ya janyo masa matsala?” Ta yi murmushi duk wani abun da Mr Bashir zai fada ko ya nuna akan ďanta zata masa uzuri saboda ta san yadda yake son haihuwa tun kamin yau. “Haihuwa a nan ba zai saka ya kamu da wani ciwon ba, ai da Hamid ya fada mana, kuma ba wani dalilin ya saka na ke son Hamid yana duba shi ba sai dan ganin na gida ne shi kuma kwararen likita ne, and duk wani bincike da ya kamata ayi akan nonon nan an yi ba a gano wata matsala ba, saboda har madara tana saka shi ciwon cikin nan ka ga ba daga nono ne kawai ba kuma jiya ma da ya sha be yi ciwon cikin ba na so mu dan jira mu ga idan abun ya bi haka ai mun fita ba sai mun fita waje ba” “Duk kwarewar Dr Hamid akwai likitan da ya fishi kwarewa, kuma ba zai yiyu ace yaro idan ya sha nono ko aka ba shi madara yana ciwon ciki kuma ace babu matsalar komai ba, dole akwai matsala, so iya na yau ne idan yaron nan ya sake shan nono yayi ciwon ciki ni da kaina zan kai shi asibiti” “Na yarda, amman idan ka akai shi na kowa ne likita zaka yarda da duba shi bana son likitan da be san kan aiki ba ya taba min yaro ka fi kowa sanin yadda na ke son ďan nan, kukan shi ma jinsa nake kamar na yi kuka” Yayi wani kasaitaccen murmushi ya kai hannu ya taba fuskarka. “Ke ma kenan da zan iya mutuwa ki auri wani ki samu haihuwa, balle ni da na san idan a yau na fadi a mutu ba ni da ďan da za a kasa dakiyar nan tawa a bashi kasonsa? Kin san iya kimarki da darajarki da kaunarki da ta karu a zuciyata saboda haihuwar nan da kika yi? Da ace wata uwar ce ta haifa min yaron nan ba ke da da kaunar da zan nuna mata zata saka na manta da ke na saboda soyayya da kaunar da na ke yi ma yaron nan, yanzu kuma da ya kasance ta dalilinki na samu yaron bana ganin kowa a gabana sai ke da ďanki, duk wata kauna da soyayya da na nuna miki a baya, sharar gafe ce kuma wasa ce” Ya rumgume shi cike da jindadi ta lumshe ido, bayanta ya shafa yana jin wani irin kaunarta marar misaltuwa na kara tsarashi, shekara tara yana neman haihu Allah be bashi ba sai wannan karon. “Lokacin da na fara jin kukan yaron nan sai da na fashe da kuka na farinciki, wai ďana ne na jinina nake jin sauti muryar kukansa, yaya rahama ne tabbas kuma ba zaka tana sani ba sai ranar da ka rasa ko ďaya, ko ba komai na san zan mutu na bar wanda za a kalla a tuna da ni” Dagowa ta yi ta kalleshi sai ta yi arba da hawayen da suka cika idonsa har suka sauko masa, hannu ta kai ta share masa hawayen nata idon ma cika da hawayen tausayin mijinta, ba da yan furta cewa zai mutu sai dan tausayinsa na sanin cewar ďan da take ikirarin nasa ba jininsa ba ne, ita kanta da take ba ďanta ba ne. Wayarsa dake ringing ya ciro daga aljihunsa yana dubawa. “Su gwaggo ne wata kila sun iso bari na tare su” Ya fada fuskarsa da annashuwa domin ya san saboda a taya shi farinciki yan'uwa na nesa da kusa suke ta zuwa yi masa barka wasu ma suna tare a gidan, ta sake tana murmushin karfin hali sai da ya shafa bayanta sannan ya fice ita kuma ya juya ta nufi gurin gadon jaririn tana takawa a hankali har ta karasa kusa da shi ta tsaya tana kallonsa. “Allah ya ba ni komai ban da haihuwa, na san mijina zai kaunarci yaron nan kamar ďansa alhalin ba ďansa ba ne, Allah ka yafe min wannan zunibin da na aikata da kuma wanda zan aikata nan gaba, ka rufa min asiri kar a gane komai har yaron nan ya girma” Wannan karon hawayenta tare da murmushi suke, tabbas tana jin rashin kyautawa a abun da ta aikata sai dai bata da wata mafitar ne sai wannan, idan har ba ta yi haka ba ta san Mr Bashir zai iya auro wata kamar yadda ya sha yi a baya kuma su zo su haihu ya juya mata baya shi da yan'uwanshi, kuma a raba gado ba zata tashi da komai ba sai hakkin wanka kamar an fada mata shi zai rigata mutuwa, tana duba yadda yake da tarin dukiya ace idan ya fadi ya mutu bata da komai sai hakkin wanka, amman a yanzu fa? Yan'uwanshi za su kaunace ta daga ita sai ďanta, kuma mijinta ma dole ita kadai zai so haka kuma zata samu kaso mai yawa idan ya mutu domin namiji ne ďanta. Kusan a firgice ta juyo ta kalli kofar ďakin yaron da aka turo, domin tun kamin ya zo duniya mahaifinsa ya ware masa ďaki daya a cikin ďakunan dake kusa da nata kuma aka kawata shi da duk wani abun bukata irin na yayan turawa, a part dinsa ma sai da ya shirya masa wani dakin da yafi wannan da yake a ciki tsaruwa da kyau. Da karfi ta hade yawu ta kai hannu ta share hawayenta tana jin rigar tsadadden lace din dake jikinta yana sukarta. “At least ya kamata ki yi knocked kamin ki shigo Ummiter” “Shekaranjiya da na yi knocked na shigo kika ce zan tashi yaro yana bachi, yau kuma kin ce ya kamata na yi knocked, Anty Jamila ya kamata ki san ni fa ba yar aiki ba ce you can't just treat me anyhow just because kina matar yayana” Hajiya Jamila ta yi wani gutun murmushin tana rausayar da kai. “Ashe ma kin san matar yayanki ce, matukar kina son girmama ďan'uwanki dole ni ki bi ni sau da kafa, ban san abun da kike son yi a bangare na ba, bayan kuma mijina yayi muku part din dabam saboda kun zama abokan zamana” “Na shigo nan ne saboda na dauki ďana domin danginmu suna bukatar ganinsa kakaninsa da suka zo, sannan nan gidan ďan'uwana ne ina damar na zaga duk inda nake so a lokacin da nake so, ba uwa ba uba wa kika tunani zai rika mu bayan ďan'uwanmu?” “Saboda na zama kishiryarki mana, shiyasa ba ki yarda ki tare a ko'ina ba sai gidan nan” Ummiter ta karaso kusa da ita tana fadin. “Kwarai da gaske, Yayana zai iya canja mata be canja yar'uwarba ina fatar kin san da wannan! A tunaninki mugun halinki zai hana mu zama a gidan ne? Kamar yadda ya hana sauran matan da yake aurowa zama? Kin dai tsira tun da kin haifo mana ďa ba dan haka ba da babu abun da zai hana ďan'uwanmu kara aure a karo na biyar” “To sai ayi mu gani, matsalar haihuwar ai ba ni kadai ba ce har da ďan'uwanki, ke ma kuma ba ki wuce matsayin ba” Hajiya Jamila ta fada cike da zafin rai sannan ta fice a fusace ta bar Ummiter a bedroom din, harara Ummiter ta bita da shi ta ja tsaki. “Duk abun da kike so akaina ba zaki taba samu ba, ni ba irin Imaan ba ce da zan yi zuciya na bar miki gidan ba, nan da ke idan kika ga na bar shi to aure na yi” Ta saka hannu tare Bismillah ta dauki jaririn tana murmushi. “My sleeping handsome, da ama ace ba ta cikin wannan wicked matar ka fito ba, but hakan ba zai hana mu nuna maka kauna ba Habibi” Tana fada tana kallon kyakkyawar fuskarsa. “Ni Wallahi ban so yaron nan ya dauko hasken matar nan ba, na so ace bakin mu ya dauko ayi baki mai kyau Allah yasa ka zama baki kamar ni” Haka dai ta yi ta maganarta tana takawa a hankali gudun kar ya farka ta fice da shi. *** *** *** Tana shiga dakinta ya cire ďankwalin kanta ta wulgar da shi saman gado. “Wannan yarinyar ko? Idan ban mata sanadi da gidan nan ba, ba zata bar ni na zauna lafiya ba, ta hana ni jindadin gidan mijina” Ta nufi wayarta tana kai hannu ta dauka kenan sai ga wata gwaggon Mr Bashir ta shigo bakin har kunne tana mata barka, wani irin yauki take gwaggon bata fita ba Sister din Jamila ta shigo da wasu bakin, daman tun da ta haihu babu ranar da ba a zuwa yi mata barka daga bangarenta har zuwa bangaren mijinta, da kuma abokan arziki da makota wasu ma tun da ta haihu suka tare a gidan bayan sabin yan aikin uku da mijinta ya daukar mata, sai dai be yarda daya daga cikinsu ta taba masa yaro ba. A dole ta hakura da wayar da zata yi har sai da ta gama sallamar bakin sannan ta dauki wayar ta fita daga dakin zuwa can wani dakin da ba a shiga ta turo kofar ta shige bandaki sannan ta kira Dr Hamid. “Yarinyar nan gani take tana iya wasa kada a tsakiyar ruwa?” Ta fada bayan ta gama sauraren bayanin da Dr Hamid yayi mata na abun da Zahra ta shar'anta masa. “Saboda tana ganin an zo nema a gurinta ne, mu kyale ta na kwana biyu idan ta ga ba mu sake yi mata magana ba zata tuntube mu” Ya cije lips dinta tana jinjina lamarin. “Ba zan taba yarda yarona shiga wannan kazamin gidan na su ba, shan nononta ma saboda ya zama dole ne, gashi mijina yace daga yau zuwa gobe idan ya sake jin kukan yaronsa da kanshi zai kai shi asibiti” “Amman ban baki shawarar ki dauki yaron nan ki kai mata ta shayar da shi ba, zata ma iya guduwa, ko kuma ta samu damar aikata wani abu, kin san kuma ba ke kadai ce a matsala ba har da ni” “Ko da wasa ba zan yarda a fitar da shi ba tare da ni ba, domin hakan zai janyo min matsala kuma dole wata rana asirina zai tonu” “To ya zamu yi yanzu?” “Ka fada mata zata dawo ta zauna a gidana ta cigaba da rainon ďana har zuwa lokacin da zai samu lafiya” “Hakan zai kara tona asirinmu ne, saboda mutane za su fara lura wata kila m iyayenta ba za su yarda ta dawo ta zauna a nan ba, kuma a nan yau da gobe dole gaskiya zata fito” “Ba zan taba bari a gane ba, kuma ita ma dole ta yi taka tsantsan domin ta san har da tata rayuwar tana cikin matsala, Dr Hamid yaron yana nufin komai na rayuwata ka fi kowa sanin yadda na sha wahala kamin na samu yaron nan, da asirina ya tonu a yanzu kara na rasa igiyar auren dake tsakanina da Mr Bashir, idan kuwa har zan iya yarda na rasa igiyar aurena ka san yaron nan yana nufin rayuwata ne ina nufin rayuwata gaba daya!” “Kaina wannan abun ya saka ni a cikin matsala, ban taba aikata ko da zubar da ciki ba balle wannan! Idan gaskiya ta bayyana da wani ido zan kalli mijinki? Kuma sunana zai bace i think auren yarinyar nan zan yi idan ba haka ba zai zama kamar na kashe maciji ne ban tsare kan ba” “Kama ganin haka zai zame mana mafita?” “Shi kadai ne mafita” “Karka aureta, ni na san wata mafitar amman a yanzu ina son ta zauna a tare da ni a gidana, zata dawo da zamanta a nan ne gaba daya har zuwa lokacin da ďana zai samu lafiya” “Zan yi magana da ita” Ta sauke wayar tana kashe ido. “Kina wasa da rayuwarki, baki san Wacece Jamila ba, ke dai na taimaki rayuwarki yanzu kuma kina son wasa da damarki, hmmm yaro be san wuta ba sai ya taka, da na rasa igiyar aure ko ďana sai dai ke ki rasa farincikinki ko ma rayuwarki gaba daya” ZAHRA POV. Sai da na fara share ďakin da nake kwana na kwashe sannan fara share waje, kamar daga sama na ji sallamar Anty sai na dago na kalli kofar shigowa cikin gidanmu. Na kuwa can ka daidai domin Anty ce tare da yaranta biyu Aisha da Narjis ban amsa sallamar ba kuma ban fasa sharar da nake ba, sai na yi kamar ban san da shigowarsu cikin gidan ba. “Zahra shara ake yi?” Na dago na kalleta kamar na amsa kiran sunan da ta yi sai kuma wata zuciyar ta hana ni, domin kazafin da Abiey yayi ma Deen a yanzu ya saka na kara tsanar Abiey ba shi ka dai ba har da yan'uwansa da duk wani da yake da alaka da shi. Mama ce ta tashi tana mata maraba daman can Mama bata iya fushi ba ko da ka bata mata rai zata iya nuna maka ta huce sai dai ta bar abun a zuciyata, amman a gurin wasu a gurin yayanta kam kamar ni da Yaya Maryam idan muka bata mata rai a take muke sani domin fushi take da mu mai tsanani kamar bata san inda muka fito ba, musamman ma ni da take cewa na fi kowa rashin jin magana. Mama ta dauko tabarma ta shimfida musu ni kam ko inda suke ban sake kallo ba. “Zahra ko baki gane ni ba?” “Na gane ki mana Anty, ai ba zan manta fuskarki ba, da kuma dalilin da ya saka na san ki ba” Ta yi murmushi. “A yayyafawa zuciya ruwan sanyi, zo ki zauna mu ba bakin zafi ba ne gaisuwa muka zo” Kamar na musa mata sai kuma na aje tsintsiyar hannuna na nufi inda take na zauna. “Zahra kin dauki zafi da yawa, kuma kina da yancin nuna bacin ranki amman a rika sassautawa, kuma abun da ya wuce ayi hakuri a bar shi a matsayin abun da ya wuce” “Har abada abun da Abiey yayi min ba zai taba wuce ba, kuma ba zan taba mantawa ba, kuma ba zan fasa rokon Allah ya saka min ba” Ta yi shiru kamar ba zata ce komai ba, sai kuma ta juya gurin Mama ta yi mata gaisuwar sannan ta dora da cewa. “Muna tare da Abiey yana waje yana son ya shigo yayi muku gaisuwa idan da hali” “Ya shigo mana, bari na dauko mayafina” Mama ta tashi ta shiga daki ta dauko mayafi ta rufe jikinta, ni kam daman da hijabi nake zama a yanzu saboda Mama tace ba a son mai jego na sakin jikinta any how. Sam ban jidadi da Mama ta amsa kai tsaye tace ya shigo ba, sai dai ba zan iya hanawa ba. Anty ta kalli yarta ta ce “Narjis je ki ce ma Yayanki ya shigo” Ina jin haka na tashi na shige dakin Mama na zauna zuciyata na wani irin tafasa, sallamar ma shi ma da naji sai da na ji kamar na saka reza na yanke kunnuwana, ga wani matsifafen turare daya saka da ke ta tsokata ta har cikin dakin Mama da nake zauna. “Mama Zahra fa...?” Ya tambaya bayan ya gama yi ma Mama gaisuwa, wani kololon bakinciki ne na ji ya taso min ya tsaya min a kirji, har sai da na sauke numfashi sannan na samu sukuni. “Zahra.... Zahra...” Mama ta kara ni har sau biyu ba ta yi na uku ba na amsa na taso na fito, zaune yake kusa da Anty ya sadda kanshi kasa yana motsa keys din hannunsa a hankali. Zaunawa na yi kasancewar tabarmar irin mai fadin nan ce da zata wadaci mutum biyar ko fiye ma, ya dago ya kalleni da wasu mayun idanuwanshi dake kara saka ina jin haushinsa. “Zahra ya hakuri?” “Baka ji kunya ba Abiey? Kai da kanka zaka tako ka iso har cikin gidanmu da sunan gaisuwa?” Ya sauke kansa kasa yana murmushi. “Subhanallahi ya kike magana kamar ba musulma ba” Na kalli wanda ta yi maganar. “Na san me na ke yi Anty, kuma ke ma kin san babu irin wulakancin da Abiey be yi min ba” Na juya gurin Abiey “And lemme warn you karka sake fadin wata mummunar kalma akan Mijina, Deen ya gama lafiya ya rabu da kowa lafiya, karka sake samun yar'uwarta da wani zancen banza akan mijina, macuci mayaudari kawai azzalumi so kake ka bata kanka Deen a gurin mutane? To Allah ya fika kuma Deen yayi maka nisa Abiey kuma ka karasa kanka tsana a zuciyata ka yafawa kanka bakin fentin da ba zai taba goguwa ba” Ima kai aya Mama ta daka min tsawa. “Aa... Zahra kanki ďaya kuwa?” Ya dago ya kalleni ya fara min magana kamar da rarrashi. “Barta ta fadi abun da take ra'ayi Mama, saboda Deen ya dorata a gadar da ba zata iya fahimtar komai ba, amman ki yi tunani Zahra a Wallahi tallahi ban guje ki haka nan kawai dam na yaudareki ba Deen ne ya shirya komai...” Ban san lokacin da na yunkura daga inda nake zaune har tafin hannuna ya kai a fuskarshi ba. “Allah ya waddaranka Abiey, ka zo da sunan gaisuwa kuma ka zauna a cikin gidanmu kana aibanta mijina...” Ji na yi an taba ni ina juyowa kanwarshi da suke uba daya Aisha ta dauke ni da mari. “Kazama dake har kin isa ki daga hannu ki mari Babban mutun kamar ďan'uwana, kin san yadda yake fama saboda ke amman yau ki siffanta shi da wasu munanan kalmomi kuma ki daga hannu ki mare shi? Waye ubanki duk garin nan? Kiyayya ba hauka ba bace Zahra ďan'uwana baya neman komai a gurinki ba ki da abun da zai saka ya yaudareki, macucin mijinki ne ya shirya komai ke kuma da yake wawuyace kin kasa fahimta, Anty tashi mu tafi” Ta mike tsaye ni kuma na bita da kallo baki sake hawaye na sauko min na zafin kalaman da ta jefeni da su. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un” Anty ta fada Mama kam zaunenta take tana kallon ikon Allah, kuma na san ba zata rasa dora min laifi ba wata kila shi ya saka bata ce komai ba. Abiey ya mike tsaye idonsa har sun kada sun yi ja kamar ba na shi ba cikin wata irin muryar da ban taba sanin yana da ita ba ya fisgo Aisha ya dawo da ita baya. “Duka ki bata hakuri Aisha” “Amman....” Kasa karasawa ta yi sakamakon wani mugun kallo da ya watsa mata. “I'm sorry” Ta furta. “Kneel down” Ya fada tsabar bacin rai jikinsa har rawa yake, sai da ta aje numfashi da karfi sannan ta durkusa kasa guiyoyinta tana watsa min harara ta ce “Sorry” Tsakamin mikewarta tsaye da wanke mata fuska da yayi da mari biyu ma su kyau ban san wanda ya riga wani ba. “How dare you raise your hand on her face? How dare you Aisha...” D muryar dake nuna tsananin bacin ransa ya furta hakan yana kallon Aisha dake dafe da gefen fuskarta tana kuka domin a gefe daya ya sauke mata marin har biyu. Sannan ya kalli ya Mama ya ce “Mama ayi hakuri dan Allah” Ya juya ya fice Aisha ta bi bayansa tana kuka. “An yi na farko an yi na karshe Zahra da yardar Allah indai akan Abiey ne” Shi ne abun da Anty ta fada min sannan ta mike tsaye ta fice daga gidan Narjis na take mata baya, ni kuma kalli Mama ina kuka. “A gaishe ki dai Juliet, matar Deen ma'asumin da ba shi laifi, ke ke ke Zahra ba wata ba sai Ciwon son Deen ya kashe ki, mahaukaciyar banza marar tunani ai ni Wallahi wannan bata burge ni da bata miki mugun duka na fitar hankali ba” Runtse ido na yi jin kalaman dake fita daga bakin Mama, sai kuka yace min ta ho mu hade, tashi na yi da sauri na shige daki na kwanta saman katifa rike da hannun da na mari Abiey, marinsa da na yi a yau ya fi komai yi min zafi har ga Allah ban jidadin aikata abun da ban taba zaton ko a mafarki zan aikatawa Abiey shi ba, duk kuwa na san da cewa ya cancanci haka. [10/16, 5:39 PM] Oum_Nuwaira🥰: 2️⃣7️⃣ Sauban dake driver side ya bude motar ya fito hango Aisha da yayi ta fito tana kuka kamar karamar yarinya, kamin ya kalli Abiey dake gabanta fuskarsa babu annuri. “Miya faru?” Abiey ya jingina da motar yana sauke ajiyar zuciya ba tare da ya amsa masa ba, cikin kuka Aisha ta ce “Marina yayi” Sauban ya kalli Abiey da sauri. “Marinta ka yi?” Abiey be ce komai ba ya zagaya dayan side din ya shigo, Aisha ta bude back seat ta shiga Sauban na kokarin komawa cikin motar ya zauna sai ga Anty ta fito tare da Narjis, wannan karon be ce uffan ba har sai da suka shiga motar shi kuma ya fara driving. “Abiey indai na isa da kai... In dai zan fada maka magana ka ji to daga yau kar na sake jin sunan yarinyar a bakinka, kuma karka sake takurawa kanka da tunaninta” Abiey ya juyo ya kalli Anty dake maganar. “Amman Anty ba zaki ga laifin Aisha ba? Ita ta fara marinta fa? Akan me zata daga hannu ta mari Zahra tsakani fa da Allah” “Lallai so hana ganin laifi, yanzu duk darajarka da kimarka da yarinyar ta keta ta daga hannu a gaban kanenka kuma a gabana ta mareka baka ga laifinta ba? Abiey ka girmi yarinyar a shekaru a matsayin ba dan kaddara ta so ba da babu abun da zai saka ka kalleta ma, amman a haka ta daga hannu ta mareka, ta kiraka da kalmomi marar dadi a gaban idona agaban kanenaka saboda abun da bata san gaskiyarsa ba? Ai ko karya kake yi ba zaka zauna a gaban mahaifiyarta ka zagi Deen ba” “Anty dan Allah maganar nan zata iya tsayawa a tsakaminmu?” “Ba zata tsaya ba” “Anty kin fi kowa sanin Ammy bata da hakuri” “Dole sai ta ji abun da ya faru, kuma ni da ace zaka ji magana ta Wallahi da ka yafe yarinyar domin ta fice min a rai, kuma baikonka da Yasmin ba za a fasa ba” Uffan Abiey be sake cewa ba, balle kuma Sauban da tun da aka fara maganar ba saka bakinsa ba, Anty kuma bata fasa fada ba tana ta munana masa Zahra, har suka isa masarautar Sauban ya faka daidai entrance din shiga part din Anty, Narjis ta bude ta fita tare da Aisha da fuskarta ta kumbura saboda marin da Abiey yayi mata da kuma kukan da ta sha. Sai da suka shige ciki sannan Abiey ya kwantar da kujerar motar ya kwanta ta runtse ido, Sauban na ganin haka yayi reverse ya bar gidan yana tukin a hankali. “Abiey I'm your friend, dole ne na fada maka gaskiya ko da zata maka daci” Abiey yayi saurin bude idonsa ya kalli Sauban. “Karka fadi wata magana da zata bata min rai a kan Zahra, ina son yarinyar Sauban ko da zata saka wuka ta yanyanka ni, ina sonta kuma ina son na tabbatar mata da haka” “Amman ka daina zuwa da yan'uwanka a gurinta” “Zan kiyaye, sauke ni gurin Ammy” Sauban ya kalleshi cike da tausayi sannan ya sauke ajiyar zuciya. Babu wanda ya sake magana a cikinsu har aka suka isa gidan Ammy, Abiey ya bude motar ya fita, a hankali yake takawa har ya isa bakin kofar falon hannunsa ya kai ya tura kofar ya shiga. At first yayi tunanin zai same ta a falo, domin tana jiransa a duk lokacin zata yi masa fada ko kuma wata magana. Sai dai be samu kowa a falon ba cikin har da Jummai mai aikin Ammy, kai tsaye ya nufi upstairs yayi knocking kofar ďakin sannan ya tura ya shiga, Ammy da plate din zogale ki kan cinyarta ta dago ta kalleshi, sai ya tsaya jikin kofar kamar mai jin tsoron karasowa. “Anty ta kira ki?” Ta tambaya yana ala ala tace masa aa sai ya fara tarar abun tun kamin Anty ta shimfida mata komai. “Eh yanzu muka gama waya, kuma ta fada duk abun da Zahra ta yi daman ďan talaka be iya samun guri ba, saboda ka kai kanka ka nuna kana son ta shi zai saka ta daga hannu ta mareka? Waye ubanta duk garin nan....” Da fari cikin lalama Ammy ta fara maganar kamar abun arziki sai kuma ta karasa a tsawace alamar ta fusata sosai. Abiey yayi saurin sakin kofar ya karaso kusa da ita ya zauna. “Ammy karki zafafafa please” “Kar na zafafa? Wata banza yar banza da bata wuce auren direban gidana ba ta daga hannu ta mareka? Saboda ta samu dama ka furta kana sonta?” “Ammy tana cikin bacin rai ne bata gama fahimta ba” “Bata gama fahimta ba? Mi zata fahimta? Kana sonta? Idan baka somta zaka koma gurinta ne? Ka kwana ka tashi da son yarinyar nan kamar ibada yanzu kana zuwa yi mata gaisuwa ta mare ka kuma ta kira da azzalumi macuci ai ko dan sanin Zuwaira matar Mai Martaba ce ya kamata ta daga maka kafa ta ji kunyar wulakanta ka, balle kuma har ta san da cewa kai ma ďan Sarkin ne, ta manta yadda take zuwa ta hau saman gadona ta kwanta? Yau zata daga hannu ta mari ďana? Alhamdulillah da baka aureta ba, kuma ko ita kadai ta rage ya mace ka hakura da ita kenan” A razane ya mike tsaye. “Ammy? No no no no no no! No please na san ranki daman zai bace amman bana son ki sake cewa komai zamu yi magana daga baya” Be jira abun da zata fada ba ya fice daga dakin da saurinsa, jikinaa har rawa yake numfashinsa na fita da karfi tsabar tashin hankali kansa har tsarawa yake. ZAHRA POV. Hannuna na dora akan filo ina da rutsar kuka, ina jin kamar wani ya zo ya bani hakuri ya fada min cewar abun da na yi daidai ne. Amman ko Mama da muke gida daya bata shigo dakin ba ta kyale na ci kuka har na kusa cinye kaina ina ta jin kamar na yanke hannun nawa da na mari Abiey da shi na jefar. Can bayan sallah Magariba na fito waje na zauna na rumgume hannayena ina ta kallon tsakar gidanmu, har lokacin Mama bata ce da ni na yi daidai abun da na aikata ko akasin haka ba, ina jin yadda wayarta ke ta ringing bata daga ba kuma bata ce min na zo na karba ba, har sai da na gaji na tashi na nufi inda take zaune tana cin tuwon da bata min tayi ba na dauki wayar na duba sai na yi arba da ni number Dr Hamid. “Dr ne yake kira” Na fada mata kamin na amsa sai ta amsa min da kamar tana fushi. “To ni yake kira ko ke?” Na juya ya shiga dakinta sannan na amsa kiran, bayan mun gaisa ya fada min bukatarsa na cewar sai dai na koma gidan da aiki. “Ba zai yiyu ba, ina danyen jego na tare a gidan wasu dole mutane za su yi zargi kawai idan kana bukatar nonon a rika kawo shi yana sha” “Gaskiya Mahaifinsa ba zai yarda a fitar da shi ba” “Ai ba dole sai kun yi yadda zai gane ba” “Idan har kina gudun tonon asirinki ne, ai kawo shi a gurinki yana shan nono shi ne babban tonon asirin ma, idan har ba zaki yarda da zama a can gaba daya ba zaki iya zuwa kina ba shi nono kina dawowa a matsayin kina kula da shi, amman babu wanda zai san da hakan sai ni da ke” Na yi shiru ina nazari, daman can babu wani dalili da zai saka ni yin yin haka sai dan na rika ganin ďana, kuma yana da gaskiya yawan kawo shi zai janyo min matsala. “Na amince” “Good, zan zo na dauke ki a yau kin ga dare ne ma babu wanda zai sani sai ki shayar da shi zuwa safe sai na dawo da ke ko kuma cikin daren ma idan kina so” “Shikenan” “Ki shirya kamin na zo” “Toh” Na amsa sannan na kashe wayar na fito waje ina labartawa Mama yadda muka yi amman ban yarda na fada mata cewar zan kwana a can ba domin na san ba zata aminta ba. “To ai sai ki yi yadda kika ga dama saboda ke kike da iko da kanki, da ubanki na raye zaki yi abubuwan da kike yi ne yanzu? Ni ai saboda kin rai na ni ina mace ko?” Na kalleta da mamakin furucinta. “Mama sai da fa muka yi magana dake kamin na aminta zan rika shayar da shi” “Toh Allah ya baki sa'a, kin san ke yanzu idan mutum ya hana ki yin abu makiyinki yake zama” “Mama saboda na mari Abiey ne kike ta wannan fushin da ni? Shi baki ji abun da yake fada akan Deen ba” Na fada cikin kuka daman bani da wahalar kuka ko da bana da gaskiya balle a inda na san ina da ita. “To waya sani ko gaskiya yake fada, ai da karya da yanzu ya kama gabansa kamar yadda Maryam ta fada, ke kuma baki tsaya kin yi bincike ba kawai ki daga hannu ki mareshi ke ga matar Deen” “Amman taya Deen zai hana aurenmu Mama? Taya? Yayarsa fa da kanta ta zo ta mana gwaji ta ce ni nake dauke da cuta mai karya garkuwa jiki saboda a fasa auren kuma akan karya, a gaban kowa mahaifiyarsa ta ce ba zai aureni ba, idan ya aureni sai ta tsine masa albarka, ba dan Deen ya aure ni a ranar ba wata kila da bakinciki be bar ni na kawo yau ba, Deen be duba ciwon da aka ce ina dauke da shi ba, be duba kowa ba be damu da komai ba ya amince ya aureni, idan har da gaske ne Deen shi ya shirya haka miyasa ba su fada ba tun a wacan lokacin sai yanxu? Kuma taya Deen zai shiryawa Anty Zainab haka ina ma zata gan shi, daman tun gabatowar auren na lura gaba daya sun canja min, amman duk baki gani ba Mama sai ni kike ganin laifi na” “Ko miye yayi miki be cancanci ki dauki hannunki ki mareshi ba, ko ďanki sai abun da ya kai ya kawo ake duka balle babban mutum kamar wannan wanda a yau idan suka so mu bar garin nan Wallahi dole mu bar shi” “Mama ko lokacin da Deen ba shi da lafiya Hajiya tace na je na nemi taimako a gurinsa kuma na je da ace ya taimaka min da yanzu ban rasa ďana ba, ko da kuwa ace Deen din ya rasu, amman be taimaka min ba, kuma a haka yake ikirarin yana so na” “To wai idan ba sonki yake ba, yanzu me ya dawo da shi gurinki? Rai kike da shi da zaki ba shi? Ko kuma gafara zaki masa ki yaye masa zunubai” “Amana ta ce ta kama shi, waya sani ma ko yayi aure matar ta yaudare kamar yadda yayi min shiyasa ya dawo neman gafarata” Duk a cikin kuka nake maganar, sai dariyar Mama na ji ta tsude hannunta ta mike tsaye.. “Kuma sai yayi ma Deen shari? Akwai kamshin gaskiya a maganar shi kuma ba mu saurare shi ba balle mu ji, dan haka ni ba zan iya yanke hukunci ba” “Ai saboda ba shi da rai zai iya fadar komai akansa” “To Allah ya sauwake, indai har abun da yake fada gaskiya to ina ji miki tausayin ranar da zaki gane haka, domin lokaci ya kure miki a wannan lokacin” Na share hawayena. “Dr yace zai zo ya dauke ni” “Allah ya kiyaye” Na mike tsaye na shiga daki na canja tufafina na saka hijab, sannan na fito waje na zauna Dr Hamid be zo ba sai tara da rabi, ya kira Mama ta miko min wayar na karba ya sanar min yana waje, sai na aje mata wayar na fita jikina har rawa yake saboda na san zan je na ga ďana ne ban taba sanin haka uwa take ji idan ta rasa ďanta a kusa da ita ba sai a yanzu da na matsu na yi arba da fuskar ďana. Nesa da gidanmu ya aje motarta saboda kaucewa idon mutane, ina isa na bude front seat na shiga da sauri na zauna shi kuma yaja motar kamar mun yi sata haka ya fita daga unguwar, sai da muka hau titi sannan ya kalleni yana murmushi. “Ya gida” “Lafiya Kalau” Na amsa ba tare da na kalleshi ba. “Dan za aje ganin baby har da kwalliya ake?” Na dan dago na kalleshi kadan na maida kaina kasa, domin na san ban yi kwalliya ba bayan tufafin dana canja ko man shafi ban shafa ba balle na hoda, da ma dai cewa yayi ina da kyau wannan kam ba zan musa ba, bana bukatar ma a fada min haka ni kaina na san ina da kyau irin kyau na yi mai daukar hankali hakan yasa nake da farinjini ko a lokacin da ina budurwa har Deen ya kan ce duk masu so na saboda ina da kyau ne, da ace ni mummuna ce da ba za su so ni ba, na kuma gasgata hakan domin shi kadai ne ya aure ni ba tare da ya taba furta min kalmar so ba, kuma ba dan komai ba sai dan ya cire ni daga kunyar da Abiey ya zo jefani, to taya wai ba zan so Deen? “Kin yi shiru Beauty” Ya katse min tunanin da nake, wannan karon da mamaki na kalleshi domin na lura ya zo min da wasu bidi'o'in da ban san da su ba, domin babu wasa a tsakaninmu kuma be taba nuna min fuskar hakan ba. “Gidan yana da nisa?” Na tambaya domin na fara jin takura a zaman da na yi a motar ba dan babu enough space ba sai dan kallona da yake ta yi. “Ko da tafiyar a kusa ne, ai tsawaita ta zan yi saboda na yi ta kallon kyakkyawar fuskar nan taki mai daukar hankali, tsakani da Allah kin yi kyau ba wasa nake miki ba” “Na gode, amman zan fi ganin mutuncinka idan baka sake furta min kalamai irin wadannan ba” Murmushi yayi mai sauti, sannan ya hanna horn a gaban wani katon gate, wasu mazaje majiya karfi suka leko sannan suka bude gate din. Da ace a bachi na farka na samu kaina a cikin gidan nan da babu abun da zai hana sake komawa domin zan yi zaton mafarki nake. Dare ne amman ba zaka iya gane hakan ba saboda fitilu da suka haske ko'ina na gidan sai idan ka daga kanka sama zaka ga hudu da tausarari, kowane bangare na furannin gidan fulfular da ruwa yake kamar wata kasar da ba nigeria ba. Harabar gidan ma ba interlock ba ne wani abu ne mai kama da tiles kuma kamar an zuba ruwa a kasa. Lallai hausawa sun yi gaskiya suka ce masu layya na cin nama, wani wan wani, baba da babansa, yau na ga arzikin ko kuma na ce gyaran gidan da ya ci ubansu na Abiey. Anya mutanen cikin gidan nan sun yarda da mutuwa kuwa? Na tambayi kaina ina kallon windows din da suke sama na wani farin karfi mai kama da silver. Kofar da Dr ya dosa da ni ma kadai abar kallo ce ta cika idona ta ko'ina. Door bell ya fara dannawa babu jimawa aka bude mana kofar sai kamshi yayi mana lale marhabun ina kokarin cire talkamina sai Dr yace. “Shigo da su, akwai gurin da ake aje talkami ai” Na dago kafata na shigo cikin falo sai ya nuna min inda zan aje talkamin kafata, na nufi gurin na cire talkami sai ya nuna wadanda zan saka na taka zuwa cikin falon, abun ka da bakauya kai na daga sama ina karewa katon falon mai kama da wata karamar fada kallo, sam ban lura da mutane na dake falon ba har sai da Dr ya ce. “Ki gaishe da mutane mana Zahra” Na bisu daya bayan daya da kallo falon na kasu kusan hudu, kowa da inda ya hakimce kana ganin jama'ar cikinsa kasan mutane ne masu ji da kansu, na gaisa su wasu sun amsa wasu kuma ba su amsa min ba, a cikin wadanda suka amsa har da matar nan da Ammy ta taba zuwa da ita gaisuwa wata kila tana da alaka da yan gidan ko kuma wani ta rako oho. Ina kokarin zama a inda Dr Hamid ya nuna min sai na ji muryar Hajiya Jamila dake sauko downstairs tana min magana cikin tsawa. “Aa aa zauna a kasa dai” Na kalleta kamar na ce wani abu sai kuma na zauna a kasan kamar yadda ta umarta, ta sauko tana ta wani yatsina fuska kamar wanda ta yi arba da abun kazanta, ban yi mamaki ba daman wadanda ba su kaita arziki ba ma sun yi wulakancin balle ita da zata yi kashi ta goge da dala idan ta ga dama. “Ina wuni” Na gaishe ta cikin girmamawa sai ta amsa min kamar bata son magana, ashe ganin da nake mata ba ina tunanin kamar tana da saukin kai ba haka take ba. “Wai sabuwar mai kula da baby ce zamu dauka” “Eh aiko zaki samu mai kula miki da shi yadda ya kamata, amman dai ayi bincike mutane sai a hankali” Wata mai tsinin baki ta fada, ina kallonta sai ta yi min kama da masu neman gindin zama a gidan masu abun lasa. “Eh sai da muka yi bincike ai” “Dr wuce ciki bari na gabatar da ita gurin Hubby” Ina jin tacewa Dr Hamid dake hakimce yana latsa waya haka na san akwai alaka mai karfi a tsakaninku ba wai ta iya taimako ba ne kawai kamar yadda ya fada, daman kuma ina ganin kamaninta a fuskarta sai dai ban zargi komai ba sai a yanzu. Tashi yayi ya nufi katon upstairs din da ban tana ganinsa a fili ba sai a tv ya haye sama ita kuma ta mike tsaye tana yauki ta nufi wata kofar. “Biyo ni” Na mike tsaye na bi bayanta, tana gaba ina biye har muka isa wani katon corridor a kawata dama da hagunsa da fulawoyi sai kamshi ke tashi ga sanyin ac da ban san ta ina yake bullo ba, lallai na yarda a duniya ma akwai wata karamar aljanna. “Jira ni a nan” Ta fada sai na yi karaf zan yi magana ta yi min alama da na yi shiru, ta matso kusa da ni. “Bari sai mun shiga dakina mu yi magana, akwai security cameras da yawa a gidan nan ki yi taka tsantsan” Na daga mata kai sannan na ja na tsaya, ta shiga wata kofar, bata dade ba ta fito ta shiga dayar dake kusa da ita sannan ta fito ta yi min alama da na shigo, ban sam miyasa ba sai na samu kaina da faduwar gaba katon daki ne da babu komai a cikinsa ai kayan motsa jiki. Wani bangare na dakin ta nufa ni dai ina biye sa ita har muka shiga. “Hubby motsa jiki da dare? Na shiga dakinka baka ciki” “Na ci abinci da yawa ne, kuma kin san idan ban motsa jikin ba ba zan jidadin bachi ba saboda ban samu na yi da safe ba” Ya amsa ni dai kaina na kasa kar na kalli mijin mutane. “Waya kawo maka tea, ai da ka kira sai na kawo maka” “Ummiter, na ga kina jego ne you need to rest ai tea ne ba wani abu ba” “Any way i have a surprise and request for you, na san zaka ji ba dadi saboda baka son maid amman wannan zata taimaka min ne na kula da Babynmu” Na dan dago na kalleshi na yi zaton tsoho zan gani ko dattijo, amman sai idanuwana suka yi arba da wanda ba zan iya kiransa da tsoho ba kuma ba yaro cancan ba, zai girmi abi wata kila da shekara hudu ko biya ko sama da haka kadan, fuskarsa ta yi min kama da wani wanda na sani amman a ina? Kuma waye? Shi ne ba zan iya tunawa ba, fajamas ne jikinsa sai dai gaban rigarsa a bude yake kana iya hango yadda kirjinsa ke cike da kananan gashi, hannunsa na rike da kofin da ya kira da na tea kana ganinsa kaga irin kirar mazan nan yan hutu ga kowane bangare na jikinsa ya amsa kirarsa irin wanda mata da yawa suke son ganin a jikin namiji wata kila saboda motsa jikin da yake. “Amman kamata yayi ki fara magana dani ba wai ki gabatar min da ita kai tsaye ba” “Na san idan na fada maka zaka ce aa ne shiyasa, amman ka yi hakuri, bata da yara ko daya mijinta kuma ya rasu tana bukatar aikin ne, kuma ka ga nima zan samu sauki idan mutane sun rage tun da ni kadai za a bari sai Yasmin kuma kaga Yasmin tana zuwa gurin aikinta ba kullun take zama ba” Ta fada tana karasawa kusa da shi. “And i promise you kula da Baby kawai zata yi ba zata yi girki ba, na san baka son girkin kowa sai nawa” Magana take masa shi kuma kamar mai tunani, na sauke kaina kasa saboda kallon da yake min da nake jin kamar ya wuce kima. “Ke ya sunanki” Ya tambaya sai na amsa masa cikin girmamawa. “Zahra yallabai” “Zahra ko? Zo nan” Na taho kamar yadda ya bukata ba tare da na kawo komai a raina ba. “Zauna” Ya nuna min kujerar dake kusa da wanda yake zaune a kanta, a maimakon na zauna a kai sai na zauna kasa na sadda kaina kasa. “Zahra dago ki kalleni” Gabana ya fadi zuciyata na raya min kamar kure karyata zai yi, Hajiya Jamila kuma ta yi shiru tana kallonmu kamar bata gurin. Na dago na kalleshi sai na yi arba da kyau da kuma kwarjini da Allah yayi masa duk kuwa da kasancewar shi baki, sai dai be kai wacan mugun Abiey kyau ba, kuma Abiey zai fi shi kurciya. “Kin san fuskar nan tawa?” Na kalli Hajiya Jamila sannan na girgiza masa kai. Hajiya Jamila ta kalleshi da mamaki ta “Hubby lafiya?” Ya daga mata hannu. “Zaki iya tuna wani lokaci da jirgi ya fadi a wani kauye?” Na dago da sauri na kalleshi ina daga masa kai. “A ina?” “A wani kauye dake zaria muna cikin gonar ni ina kwance sauran mutanen kuma suna aikin gona sai jirgi ya fado har har har...” Gurin saurin fada maganar ta lake min sai na kara tuna fuskarsa tabbas shi ne, ban san lokacin da na nuna shi ba. “Kai ne wanda karfin jirgin ya fadawa... Kai...kai...” Ya daga min kai yana murmushi. “Ni ne” “Ban fa gane ba miya ke faruwa” Sai ya kalleta ya ce. “Wannan yarinyar da kike gani ita ta ceci rayuwata ba dan ita ba da yanzu takaba kike, zaki iya tuna yarinyar da na ce miki ta taimaka min lokacin da jirgina ya fadi? Har na aika mata da hukunci a asibiti aka ce ba a same ta ba? To ita ce wannan” Kamar a rude Hajiya Jamila ta nuna ni. “Wannan? Ita din ce dai ko kama?” “Ai ba zan taba iya mantawa fuakarta ba har a bada, badan yarinyar nan ba da yanzu bana duniya, domin da mai tsaron lafiyata da direban jirgin duk wutar ta kone su sun mutu, amman ita wannan yarinyar ita ta janye min karfin nan na fito lokacin tana da tsoho ciki” “Damkari....!” Hajiya Jamila ta fada tare da kaiwa zaune, sai ya kalleni ya kalleta yana murmushi. “Abun mamaki ko? Kin ga Allah ya kawo mana ita har gida” “Aiko ni na ga mamaki Hubby, ni san mamaki hmmmmm.... ” Ta karasa tana girgiza kai, kana ganinta kasan mamaki ne ya cika ta, kamar yadda ni ma ya cika ni domin ban taba zaton mijinta ne ba, ban kawo a raina cewa zan taba haduwa da wanda na ceta ba. “Ina cikin?” “Na haihu be zo da rai ba yallabai” “Subhanallahi Allah yasa ba sanadin abun da ya faru ba?” Na kalli Hajiya Jamila sannan na kalleshi na amsa min. “Sanadin haka ne” “Daman sai da na ji tsoron haka, saboda kin zubar da jini da yawa a lokacin nan, kuma na san nawa da aka saka miki a lokacin ba zai isheki ba a lokacin I'm sorry...” Na sauke kaina kasa ba tare da na amsa ba. “Welcome Zahra....” Ya fada yana murmushin dake nuna ya jidadin ganina. “Damkari...! Makari....!” Hajiya Jamila ta fada tana kallona sai na dago nima na kalleta wata kila mamaki ne be gama fitarta ba. ____________ #Team Deen #Team Abiey [10/19, 5:23 PM] Oum_Nuwaira🥰: 2️⃣8️⃣ “A ina take da zama?” Ya tambayi Hajiya Jamila sai ta kalleni. “A nan take Kano” Ya juyo ya kalleni. “Wani abu ya kai ki a can kauyen ne” “Na tafi gurin kawata ne” “Allah sarki, na aika miki da sako a lokacin sai aka tarar baki nan a asibitin, kuma na saka a bibiye ki aa ce ba a san inda za a same ki ba” Na sauke kaina kasa. “Zaki iya aikin kula da Baby?” “Haba Hubby sai da na yi magana da ita kamin na kawo ta nan, sai da na bincika komai” “To Maa Shaa Allah, Allah ya bata ikon rike mana Babyn da amana, nice to meet you” “Inshallah, na maka alkawari zan kula da Baby kamar ni na haife ta, ba zaka taba samuna da wata matsala ba” Hajiya Jamila ta sauke numfashi da karfi sannan ta mike tsaye. “Tashi mu shiga ciki” Na mike tsaye kamar yadda ta umarta ta juya ta wuce gaba na bi bayanta, muna fitowa dakin sai ta tsaya tana kallona kamar bata taba ganina ba, sannan ta juya ta cigaba ta tafiyar ni kuwa me zan yi idan ba binta ba. Sai da muka fito falon sannan ta nuna min raben wata kujera. “Je can ki zauna ki jirani zan nuna miki ďakin da zaki zauna” “Ba zuwa na yi na zauna gaba daya ba, kawai na zo na bashi nono ne na koma” “Ban gane ki ba shi nono ki koma? Dr Hamid be fada miki abun da na ce ba?” “Ya fada min, ni kuma na fada masa ba zan zauna a gidanki ba, sai dai na rika ba shi nonon ina komawa” “Ke Zahra kalleni da kyau, ke kin san ba dan kaddara ba baki isa ma ki tako kafarki a cikin gidan nan ba balle har ki saka min sharadin abun da zan yi da wanda ba zan yi ba” Tana gama fadin haka ta wuce a fusace zuwa upstairs din a raina sai addu'ar Allah yasa ta fado nake. ***   ***    *** Sai da ta maida kofar bedroom din ta rufe sannan ta juyo ta kalli dan'uwanta dake rike da waya yana tabawa. “Dr kasan wai mun yi kitso da kwarkwata?” Ya dago ya kalleta. “Miye?” “Wai zaka iya tuna wani hadari da Mr Bashir ya samu kwanan baya jirginsu ya fada a wani kauye?” “Yes” “Matar da ta taimaka masa har na fada maka yana ta nemanta” “Yes you even told me idan kika ganta zaki mata kyauta mi ta yi?” “Yarinyar nan ce...! Wai ita ce” Dr Hamid yayi saurin aje wayarta hannunsa gefen kujerar da yake zaune. “Wasa dai kike” “I swear to God, yanzu nan ya ganta ya tabbatar da ita ce kuma ita ta fadi cewar shi ne?” “Wow....” Dr ya fada kamin ya kyalkyale da dariyar ba zata. “Ba abun dariya ba ne Dr ina cikin matsala” A kokarinsa na gintse dariyar ya daga mata hannu. “Sorry i mean...” Sai kuma ya sake fashewa da dariya. “Na rantse abun ne ya bani mamaki dariyar ce take zuwa min a ba zata, so that's mean mun kawo masa ita har gida?” “Shi ne abun da yake fada” Dr Hamid yayi gyaran murya still dariyar bata gama fitarshi ba. “Yanzu yaya kenan?” Hajiya Jamila ya zauna bakin gadonta tana sauke ajiyar zuciya duk sanyin ac dakin be hana ta jin zafi ba. “Ina jin tsoron kar ya mata kyautar da zata iya juya tunaninta ta ce zata karbi ďanta, secondly yanzu take fada min cewar wai ba zata zauna a nan ba sai dai ta rika zuwa tana ba shi nono kuma hakan tonon asirina ne, bayan kuma na riga na fada masa cewar a nan zata zauna gashi Ummiter tana gidan idan tana zuwa tana komawa za a iya samun matsala amman idan a nan zata zauna har sai yaron yayi wayo ka ga kullum tana tare da shi babu wanda zai zage nono take ba shi” “Yeah ta fada min cewar ba zata zauna zaman gaba daya ba” “Amman baka fada min haka ba, da ban bari ta zo ba har na gabatarda ita gurin Mijina, bana son na yi magana da ita a cikin mutane ne kar ta fara min hauka dan haka ka yi magana da ita ka fada mata a nan zata zauna” “No idan tana ra'ayin zama a nan har na wani lokacin zata zauna, idan kuma bata ra'ayi ba dole ba ne” Dr Hamid ya fada with serious face din dake nuna ba da wasa yake ba. “Ban fahimta ba” “Ba hakkinta ba ne shayarda yaron nan, ra'ayinta ne idan tana sha'awa dan haka be zama lalle mu cilasta ba” “Ra'ayinta zamu bi kenan?” “Yes” Wani kallon mamaki Hajiya Jamila ta yi ma dan'uwan nata. “No please kar ma ka nuna mata haka, ita kuma ya kamata ta bi mu dole abun da na ce shi za'ayi kar ma ka barta ta dauka kamar tana da wata damar ba mu umarni mu bi, a nan zata zauna and that's final” Dr Hamid ya mike tsaye. “Jamila miyasa kike abu baki tunani ne ko tausayi? Yarinyar nan fa ďanta aka raba ta da shi ďan ma ďan fari a haka ta hakura, yanzu kuma mun je neman ta shayar da yaron nan sai ki fara saka mata wani sharadi, yanzu ita ya kamata saka kuma dole mu bi, dazun ma ina ganin kina fada mata ta zauna a kasa kamar idan ta zauna akan kujerun wani kazanta zata saka musu, ba baiwai ba ce kuma ba aiki take nema ba, shayar da yaron nan kawai zata yi, amman baki fahimci halin da take ciki ba saboda baki taba haihuwa ba baki san yadda uwa take ji ba” Hajiya Jamila ta hade abu da karfi ta dafa zuciyarta. “Yau ni kake yi ma gori Yaya? Saboda wata banza? Wata da bata kai ta daga kai ma ta kalleni ba?” “Ba gori nake miki ba, ni ma uba ne yarana biyu na san yadda take ji, yarinyar nan karamar yarinya ce ta rasa miji kuma yanzu ta rasa ďa hakan kadai be isa ya saka a tausaya mata ba? A haka kuma ta kawo kanta ta shayar da yaron nan amman kina kokarin wulakantata?” Hawaye ne ya sauko a fuskarta Hajiya Jamila tana kallon Dr Hamid da ke tsaye ransa a bace kamin ya duka ya dauki wayarsa. “Zata kwana a nan ta shayar da yaron da safe zan dawo na maida ita gidansu, zan yi magana ta fahimta da ita idan ta yarda ta zauna, idan kuma ta ce ba zata zauna ba i won't force her” Yana kaiwa nan ya fice daga dakin ya barta tsaye hawaye na sauko mata. Tun da take a rayuwarta bata taba jin zafin gorin haihuwa ba irin na yau, Ummiter ta sha yi mata gori haka daidaikun mutane daga familyn mijinta amman ba a taba yi mata gorin haihuwa yayi mata zafi kamar na yau ba, wata kila saboda Dr Hamid dan'uwanta ne na jini, faduwa ta yi kwance saman gadon ta fashe da wani irin kuka har lokacin tana dafe da kirjinta. “Yau ni Ya Hamid yake yi ma gorin haihuwa saboda wannan jahilar yarinyar, da ta san ciwon ďan zata siyar da shi ne, tun tafiya ba ta yi nisa ba an fara haka, ba zan bari ta zauna a garin nan ba, yarona na yin wayo dole za su bar garin nan gaba daya” Sai kuma ta tashi zaune tana kallon kofar dakinta. “..... Ko kuma.... ” Sai kuma ta yi shiru bata karasa ba ta  cige baki. Shigowar Ummiter ne ya saka ta yi saurin share hawayenta ta juya fuska. Ummiter ta dan tsaya jikin kofar tana son fahimtar kuka take ko akasin haka. “Anty Jamila..” Ta kira sunanta, sai hakam be saka Hajiya Jamila ta juyo ba domin ta san yadda Ummiter ke mata gulma ko abun da be kai kawo ba balle wannan da zata iya zuwa ta fadawa yayanta cewar ta ganta tana kuka, ko kuma ta jidadin ganinta a halin damuwar saboda ba kaunar juna suke ba ita da Ummiter. “Anyway Yaya yace Yarinyar da kika dauka aiki ita ce ta taimaka masa lokacin da jirginsu ya fadi, ita na zo gani” Nan ma Hajiya Jamila bata juyo ba kuma bata ce mata komai ba, Ummiter ta tabe baki ta juya ta fice tare da ja mata kofar ďakin. ZAHRA POV. Ina tsaye a inda ta bar ni har ta haye sama, bayan wani lokaci na ga Dr Hamid ya sauko da saurinsa ba dan dai kar ace na yi gulma ba da sai na ce ransa kamar a bace yake wata kila fada suka yi ko kuma wani abun ta fada masa marar dadi oho domin na lura ita ma ba wani dadin zama ne da ita ba. Ina ganin na doshi kofar fita ya fice daga falon na yi hanzarin cira kafa na taka na bi sawunsa, ko da na fita yana daf da bude motarsa sai na kira shi muryar kasa kasa. “Dr Hamid” Ya juyo ya kalleni sai ya sakar min murmushi ya rufe motar ni kuma na taka a hankali na karasa kusa da shi. “Tace wai dole sai na zauna a gidan” Kai na ga ya daga sama yana kallon ko'ina sannan ya matso kusa da ni kamar zai taba ni. “Shiga mota mu yi magana gidan nan zagaye yake da security cameras” Na daga kai ina kallon ko wane kusurwa ta gidan amman ban ga wata alama ta camera ba, na lake kafada alamar ba zan shiga ba, sai yayi murmushi ya kara matsowa kusa da ni ni kuma na dan matsa baya. “Idan baki bukutar zama ba zan cilasta ki ba, kin fada min ai ba zaki zauna ba ko?” Na daga masa kai. “Okay zaki ba shi nonon ne kawai gobe zan zo na maida ke gida, amman dai zamanki zai fi a nan Zahra saboda rufin asirinmu mu duka” “Jego fa nake yi, sai kuma na bar gidanmu na zauna a nan ai mutane za su min gulma kuma zasu iya ganewa” “Shikenan idan an yi sati fa? Ko kwana goma?” “Ni dai ban sani ba” Na fada ina hade hannayena, murmushi ya sake yi. “Shikenan idan kin yanke shawara zaki iya fada min a waya ai, and ki yi hakuri da abun da Jamila ta yi miki dazun, ta yi hakan ne saboda muma gaban mutane kuma ta riga ta gabatar da ke a matsayin yar aiki kinji” Na daga mishi. “Kin yafe mata” “Ba wani abu ba ne, daman masu kudi suna hantarar talaka ai, kuma basa son rabarsa talaka kuma ya saba da wannan rayuwar so it's not a big deal” “Some... Rich people... ” Ya furta sannan yayi one two three step backwards yana murmushi ya saka hannunsa aljihu yana kallona. “Good Night” “Good night” Na mayar masa sai ya bude motar da baya baya kamar baya son daina kallona sannan ya juya ya shiga, ni kuma ina tsaye har ya tashi motar ya juya ya fice daga gidan, ko bayan fitarsa na dade a tsaye ina ta kallon dukiyar da aka narka a harabar gidan sannan na juyo kamin na kai kofar falon aka bude daga can ciki wasu daga mutanen da na tarar dazun suka fito mata hudu sai dayar dake rike da yaro, matar da na taba gani tare da su Ammy tana daga cikin mutanen da suka fito kamar dazun yanzun ma kallona kawai take, da alama suna da alaka mai karfi tsakaninsu da Hajiya Jamila domin ta yi musu rakiya har bakin kofar falon. Gefe na ja na tsaya har sai da suka fice sannan na shiga cikin falon akan kujera na zauna ina jin sanyin ac kamar yayi min yawa, kasa kasa nake kara karewa daular falon kallo lallai mai gidan nan be san zafi dukiya ba sam, idan ba haka ba wannan gyara da falon ya sha kamar ba za a mutu ba, Allah yasa ma duniyar ta Allah ce... “Zahra...” Ina tsaka da gulmar zuci Hajiya Jamila ta kirani a tsawace, ai ko a razane na juyo na kalleta. “For the last time karki sake zauna min akan kujera, ya zama na karshe da zan sake miki magana” Na kalli wata tsohuwa da kuma wani matashiyar yarinya da zan kanwa ta uku da ita da suke falon sannan na sauke kaina kasa na sauka daga kan kujerar. “Toh Hajiya” Na amsa zuciyata na sosuwa domin ko kadan ban jidadin yadda ta yi min a yanzu ba, idan a dazun saboda mutane ne yanzu kuma fa? “Ta so mu je” Ta saks fada a tsawace, sai na mike na bi bayanta domin tuni ta yi gaba abun ta, inda muka bi dazun muka sake bi sai dai wannan karon dakin dake kusa da ke kusa da na dazun ta shiga na bi bayanta sai na tsinci kaina a cikin wani daki mai cike da kayan wasa yara an kawata ko'ina kamar yadda ake yi ma ďakin yaran turawa yaran ma yan gata, wutar ďakin ma wata kala ce mai kama da blue da ratsin pink a ciki, Wani karami gado na hango jaririn kwance yana ta sharar bachi, na dunkule shi da kayan sanyi irin masu tsadar nan. “Shiga bandakin nan ki wanke hannunki” Ta fada tana nuna min bandaki fuska babu annuri kamar wanda ta yi arba da makiyiyarta. Kamar na ce wani abu sai kuma na nufi bandakin na bude na shiga, ashe a nan din ma wata duniyar ce mai abun kallo da mamaki, domin ban ga wani mai na wanke hannuna ba sai tawul ko gurin da ruwa zai zuba ban gani ba, hausawa sun ce ďan hausa ba bobawa ba, dan sink din da na gani na duka ina karantawa sai na ga an yi hoton omo a na farko a na biyun kuma ruwa, latsawa na yi a zatona zai zubo min detergent din ne, amman shiru hakan yasa na kai hannuna kasa da zimmar latsa kasan sai kawai na ga sabulun ya zubo, tsabar mamaki ban san lokacin da na bude baki ba. “Laaa....” Na janye hannun na murza sabulun na wanke sannan na tara inda aka yi hoton ruwa sai ruwa suka zubo a hannuna na wanke sannan na saka tawul din na goge na fito. “Dauko shi a hankali” Wani irin shauki na ji ya kamani, jikina rawa na mika hannu na dauko ďana ina kallon fuskarsa zuciyata na kara cika da kaunarsa, ji na yi kamar na rumgume shi a kirjina amman ba dama dogon hancinsa be yi min kama da na rowa ba sai Deen, a take idona ya cika da hawaye har suna kokarin zubo min, juyawa ta yi ta fice ba tare da tace min komai ba, sai na bi bayanta a lokacin ne na samu damar sumbantar ďana. Muna fitowa mu ka kusa cin karo da wata budurwar da ba zata wuce sa'a ta ba idan kuma ta dara ni kadan tana sanye da doguwar rigar da tafi kama da bachi, sai ta nuna ni tana murmushi. “Ke ce Zahra ko?” Na kasa amsa hawayen da suke makalle suka zubo min a fuska. Hajiya Jamila ta juyo ta kalleni. “Ita ce ya aka yi?” “Yaya yace na kirata zata gaisa da su Gwaggo” Budurwar ta fada tana yatsina ma Hajiya Jamila fuska, sai da Hajiya Jamila ta kalleni daga sama har kasa sannan ta mika hannu zata karbi yaron. “Zan iya zuwa da shi” Na fada da sauri ina kauce domin ji nake kamar kar a raba ni da shi. “Ki je da shi gidan uban wa? Dallah ba ni yaro na” Ta karbeshi da karfi wanda hakan yayi sanadiyar tashinsa daga bachi ya fara mika da hannayensa dake sanye da safa, na saka hannu na share hawaye sannan na kalli yarinyar wasu hawayen na sauko min, Hajiya Jamila kuma ta ja tsaki ta wuce ta bar mu a tsaye black beauty din ta bita da harara tana tabe baki, sannan ta rika hannuna ta nufi wata hayar da ni, sai da muka fita daga corridor sannan ta sake tana fadin. “Ai wacan matar sai kin yi hakuri da ita, bata da halin kirki sam, ni ma nan karfen kafa na zame mata da yanzu ta kare ni kamar yadda ta kori yar'uwata” Na saka hannuna na dama na share hawayen sai dai ban ce mata kofar ba har muka isa gaban wata kofar bude kofar ta yi sai gani a cikin wani madaidacin falo mai kyau ga sanyi kamar kasar turawa, sai da ta kai farkon falon ta bude wata kofar muka fita waje, a nan ma wani bangare ne na harabar gidan iska sai kadawa yake saboda hadarin dake haduwa a samaniya, wani apartment din muka nufa da be yi girman wanda muka fito ba, sai da ta yi knocking sannan ta tura sai da ta fara shiga sannan na bi bayanta. Madaidacin falo ne mai cike da kayan kallo da kujeru sai dai be yi kyau sauran ba, Mijin Hajiya Jamila na zaune a kasa kusa da wata tsohuwa, sai kuma wasu manyan mata su hudu suna zaune saman kujera, budurwar ta karasa kusa da matan tana fadin. “Gata nan” Na zauna daga nesa da su a kasa, sai Alhajin ya ce “No ta so ki zauna kan kujera” “Aa nan ya isa” Na fada ina maida kaina kasa. “Allah sarki yarinya mai hankali, ya sunanta” “Mama ce amman dai ita Zahra ake ce mata” Alhajin ya amsa mata da muryar da nake iya karantar murmushi yake yi. “Allah sarki Fadimatu ce, an gode kin ji Allah yayi albarka ya kawo miji na gari idan kuma akwai ya bada zaman lafiya” “Jamila tace mijinta ya rasu, lokacin da abun ya faru tana da ciki ina tunanin na fari ne ko?” Na daga mashi kai sai ya dora da “Sanadin abun da ya faru yasa ta rasa ďan saboda ta zubar da jini da yawa sosai gaskiya” “Eyyah Allah ya jikan mijinki ya baki wani mai albarka kinji, an gode an gode Alhaji yana ta nemanki ashe zaki tararshi har gida ba in ji Allah” Daya daga jikin matan dake zaune kan kujera ta fada sannan sauran ma suka min addu'a. “Yaya yanzu ita zata rika kula da Babyn kenan?” Budurwar ta tambaya tana sotsan kanta da babu dankwali. “Eh Haka Jamila tace, zata dan taimaka tana rika mata shi kamin yagi gwari” Ya amsa sannan ya kalli budurwar mai kama da shi ya ce. “Ummiter rakata ta koma daman dai zaki gaisa da iyeyena ne” Wannan karon yana kallona ya karasa maganar, sai na mike tsaye wanda aka kira da Ummiter ta biyo bayana muka fito. [10/19, 8:50 PM] Oum_Nuwaira🥰: 2️⃣9️⃣ *Littafin nan na kudi ne, karanta na sata daukarwa kanki hakki ne, domin sauke nauyi biya ki karanta cikin aminci, pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 and send the evidence of payment to 08036126660* ABIEY POV. A hankali ya busar da iskar bakinsa ya gyara zaman hannunsa na hagu dake aljihu, hannunsa na dama kuma na rike da kofin ruwa. Can kuma ya ciro hannun ya duba agogon dake daure a hannunsa. “9:13pm” Ya furta sannan ya aje daga kai yana kallon harabar gidan tare da kurba ruwan, ajiyar zuciya ya sauke ya sunkuya ya aje ruwan ya dauki keys dinsa dake kan mini center tebur dake gurin ya juyo ya fito daga backyard din ya dawo cikin dakinsa, kai tsaye ya zarce zuwa kofar fita dakin kamar an korashi haka ya sauko stair ba karamin dadi ya ji ba ganin falon ba kowa, balle ya tsaya amsa tambayayiyin Ammy na ina zai je. Yana isa gurin kofar falon ya bude ya fita be san key din wace motar ce a hannunsa ba har sai da ya latsa key din wata kafirar BMW ta yi kara, sai ya zagaya tsakamin motocin ya nufi inda take ya bude ya shiga yana reverse ya kunna kai daman masu kula da shiga da ficen gidan tuni suka wangale masa gate. Driving kawai yake yana tunanin yadda zai wanke Zahra a gurin Ammy da Anty, musamman ma Anty da yake ganin ta fi kowa daukar abun da zafi. In 35min ya iso kofar gidansu Yasmin horn yayi aka bude masa sai ya samu guri a harabar gidan ya faka, hakan nan kawai yake jin baya bukatar shiga ciki daman ba gurin Momy ya zo ba balle yace zai shiga ya gaishe ta, wannan zuwan na Yasmin ne kawai, wayarsa ya ciro dake aljihu ya kiran number Yasmin kamar ba zata dauka ba sai kuma ta yi picking. “Fito gani nan waje” Jimmm ta yi kamar ba ta ji abun da ya fada mata ba. “Toh” Ta amsa ya yanke sannan ya maida dubansa gurin kofar falon yana jiran fitowar Yasmin. After like ten min aka bude kofar ta fito tana sanye da doguwar rigar atamta sai mayafin da ta rufe jikin, bude motar yayi ya fito yana jiran karasowarta ita kam bata yarda ta kalleshi ba har ta iso inda yake tsaye. “Barka da dare” “How are you?” Ya bukata kamar an masa dole sai a lokacin da kalleshi hawaye na sauko mata wasu kuma na taruwa a idonta. “I'm not fine” “Me too” Ya furta yana dauke kansa ya kalli sararin samaniya da iskar hadari ke kadawa. “Na zo na yi magana da ke ne akan maganar mu shiyasa ban shiga ciki na gaisa da Momy ba” Yana maganar tana masa wani irin kallo kamar ta hade shi. “Na yi magana da Abbah Musa na fada masa ina son a fasa zancen baiko...” Sai kuma ta yi shiru, Abiey ya tattara dukan hankalinsa da natsuwarsa ya mika mata zuciyarsa na wani bugawar dadi. “Ahen... Ina jinki” “Ya ce ba zan raina musu hankali ba, ban isa na zubar musu da mutunci ba, miyasa ban fadi haka tun kamin su amsawa Mai Martaba ba, sai bayan sun amsa zan taso musu da wata maganar, wai ban isa na maida su kananan mutane ba, ba za su yarda matsala ta taso daga garesu ba, kuma babu fashin aure sai idan kai kace ka fasa....” A take annashuwa da farincikin dake tare da Abiey suka gushe. “What...! What do you mean? Yasmin ya zaki saka ni a matsala... Ya salam.. ” Ya fada yana juyawa ya daki motar da mugun karfi, kana ya juyo ya rika hade kafadunta yana jijjigata da karfi. “Yasmin ya zaki min haka? Tun abun na sabo da kin yi abun da na fada miki da yanzu haka be faru ba! Miyasa zaki saka mi a matsala?” Sai ta amsa masa cikin kuka. “Kai ka saka kanka a matsala Abiey, miyasa zaka saka zobe a yatsan da ka san idan har za a cire shi sai dai a gutsure shi? Miyasa zaka ambaci sunana a bagirin da zuciyata ta dade tana nema? Na sani ba zaka taba so ba Abiey ni kuma ban isa na bude zuciyata na cire soyayyarka ba....!” Sakinta yayi ya matsa baya ya nuna kansa with shock, sai ta daga masa kai ta saka hannayenta biyu ta rufe fuskarta ta fashe da kuka. Baya baya Abiey yayi har sai da ya jingina da motarsa ya dafe kanshi ya duka a gurin yana jin wani zazzabi na taso mashi. “Na shiga uku... Yau na ga Idi zigidir” Sai kuma ya mike tsaye yana girgiza mata kai. “Yasmin ba zaki iya zama da ni” Ta cire hannayenta daga fuskarta tana kuka. “Zan iya” “Zuciyata babu wanda take so sai Zahra da Zahra ita kadai...” “Zan roka maka Allah ya sassautawa maka son Zahra Abiey” Addu'ar da tace zata yi ta yi farraku tsakaninsa da Zahra sai ya saka a take ya ji ya fara tsanarta. “Amadadin kin min addu'a ki raba ni da Zahra, me zai hana ki yi ma kanki addu'a so na ya fita daga zuciyarki?” “Kamin yau... Na roka a dare mabanbanta, ka min a kawo yanzu na roka amman ba a amsa min ba sai ma aka kara kawo kusanci a tsakanina da kai ta inda ban zata ba” “Yasmin indai kina so so na hakika to ba zaki so na shiga matsala ba, kuma zaki so abun da na ke so” “Indai har da gaske kana son Zahra to zaka fi kowa fahimtar halin da nake ciki, Ciwon So masifa ne Abiey da ace ina da iko da ban bari Son ka ya shiga zuciyata ba” Ta fadi durkushe kasan guiwoyinta tana kuka, ita kadai ta san abun da take ji, ita kadai ta san halin da take ciki akan Abiey kuma tabbas da zata iya da ta cire soyayyarsa a zuciyarsa, gana daya sai jikin Abiey yayi sanyi, durkusawa yayi kasa ya rika hannunta sannan ya matsa kusa da ita sosai ya rumgume ta a hankali. “I'm sorry....” Lumshe ido ta yi tana jin kamar ta saka wuka ta tsaka kirjinsa ta shiga cikin jininsa ta kwanta, sai da ya tabbatar ta samu natsuwa sannan ya mike tare da ita tsaye. “Ki shiga ciki ki huta zamu yi magana daga baya okay” Dagowa kai ta yi ta kalleshi sannan ta daga da ga jikinshi tana jin kamar ta rayu a kirjinsa rayuwa ta har abada. “Ka yi hakuri idan na bata maka rai...” Ya hade yawun bakinsa. “No dukanmu ba ma iya sakawa junanmu abu kuma ba ma iya cirewa, ko wace zuciyata tana juyawa bisa ga ikon da Ubangiji ya bata, da ace dan adam zai iya wani abu, na tabbatar da yanzu Zahra ta cire so na a zuciyarta, amman ta kasa saboda bata da iko akan komai, abun da ta yi min dazun yanzu ya kara tabbatar da da har gobe Zahra tana kaunata” Yasmin ta yi murmushi irin murmushin nan da hausawa ke cewa ya fi kuka ciwo. “Zahra ta yi dace Abiey ka rayu da soyayyarta na tsawon lokaci” “Yasmin.... Zahra ta so ni ba dan wani abu nawa ba, ni da ita mun kamu da kaunar junanmu ba tare da mun sani ba, sannan Zahra ta cika duk wani sharadi da na ke so a mace, ko kadan bana son na auri mace da ita take so na ni bana son ta, saboda zan iya cutar da ita, Yasmin na shiga a zuciyar Zahra na nuna mata kauna kamin abubuwa su canja mana, ba zan manta lokacin data durkusa har masa tana rokon kar na fasa aurenta ba amman ban iya yin komai ba saboda Deen ya shiryar mana gadar zare, wannan ce damar da nake da ita wanda zan nuna Zahra cewar ina kaunarta irin kaunar da babu wanda ya taba yi mata irinta, ina son na rayu da Zahra fiye da yadda kike jin kina son rayuwa da ni....!” Yana kaiwa nan ya bude motarsa ya shiga ya yi mata key ya bar Yasmin a tsaye ta bishi da kallo. “Ciwon so yana dawainiya da kai Abiey, ni kuma be bar ni ba, ‘So’ baka kyauta mana ba” Yasmin ta fada tana hawaye jikinta sai kamshin turaren masoyinta yake. *** *** **** Tuki kawai yake yana jin kamar bata son komawa gida, kuma be san inda zai je ba da ma ace irin da ne da Sauban be yi aure da a gurinsa zai tare. “Miyasa abubuwa suke tasowa su shiga tsakanina da ke Zahra! Why why...” Ya buga sitiyarin motar da mugun karfi. “And kullum daga gurina matsalar nan take tasowa why me?” Kamar mahaukaci haka yake fada da kanshi tana jin wani kalar bakinciki marar misaltuwa. Daker ya kalli wayarsa dake ringing ba dan Sauban ne mai kiran ba da ba zai taba dagawa ba. “Miye?” Shi ne abun da ya fada bayan ya amsa kiran. “Are okay” “I'm not” “Okay maybe later” “Fada min yanzu minene?” “Nuratu ce tace min ta ga Zahra a gidan yayarta wai an gabatar da ita a matsayin yar aiki” Guri ya samu ya faka motar sannan ya gyara zaman wayar a kunnesa. “Zahra tawa?” “Eh yanzu ta dawo daga gidan take fada min” “Zahra fa? Anya ta san Zahra da kyau kuwa?” “Ta santa mana kasan da ita suka je yi mata gaisuwa tare da Ammy da Dr, kuma na nuna mata hotonta a waya tace min ita ce” “Wait.. kana da hotunan Zahra a wayarka?” “Amman dai ka san ba wani abu ke tsakanina da ita ba ko?” “Ina aka ce maka an ganta?” “Tace gidan yayarta ubansu daya da ita, tace tana zaune aka gabatar da Zahra a matsayin wanda zata rika kula da babyn da yayar ta haifa” “Me Zahra ta rasa da zata je ta yi aiki a gidan wani? Ina raye?” “Ni ma abun da nake tunani kenan, tace yanzu haka tana gidan” “Ina ne gidan?” “Me zaka yi?” “I need to see her” “No idan ma magana kake son yin da ita ka same ta a gidansu zai fi” “Zan tabbatar ne idan ita din ce, fada min wace area ce?” “Zan maka text din address din, maybe ma ka san shi wani Alhaji Bashir mai kudi ne sosai kwana baya ma yayi hadarin jirgi, kuma ance be taba haihuwa ba sai wannan karon” “Ban san shi ba, amman turo min address din” Ya sauke wayar da matukar mamaki. “Mi zai saka Zahra aiki a wani guri?” Tambayar da yayi ma kansa kenan har lokacin be daina mamaki ba. Few minutes later Sauban ya turo masa sakon address din, da hannu daya Abiey yake driving dayan hannunsa kuma rike da waya har ya isa unguwar. Tun daga yanayin area kasan area ce da manyan mutane masu fada aji kuma wandanda suka taka nesa da kafafuwansu suka tsaya, babu gidan da be nuna isar mai shi a unguwar titi ma tsif yake kamar an yi ruwa an dauke baka jin komai sai motsi dogayen itatuwan dake kadawa saboda hadarin da ha hadu a samaniya har ya rufe taurari. Police din da ya gani a kofar gidan da ya banbanta da saura ya tabbatar masa da cewar gidan ne, kai tsaye ya isa gaban gate din ya danna horn sai police suka taso shi kuma ya sauke glass din motarsa. “Sannu da zuwa” “Yauwa Mai gidan yana ciki?” Police dake son tantance fuskar Abiey ya ce. “Kana da appointment da shi?” “Yeah ka fada masa Abiey ne Mai Martaba ya turo ni” “Allah sarki ni kam na ce kamar Abiey sannu da zuwa ranka ya dade” A take suka bude masa gate din ya kunna kai cikin gidan mai kama da wata masarauta a gurin da aka tanada domin aje motoci ya nufa ya faka motarsa yana tsara yadda zai amsawa Mai gidan idan ya tambaye dalilin zuwansa, mutumen da ya gani a kusa da motarsa ya saka ya sauke gilashin motar. “Ya aka yi?” “Sai ka juyo da motar ranka ya dade masaukin bakin ta can yake” Abiey ya bude gurin da yake ajiyar kudi a cikin motar ya dauko bandir din 500 ya mika masa. “Shiga cikin gidan nan gurin matansa ka ce Abiey yana sallama da Zahra” Mutumen ya saka hannu biyu ya karba jiki na rawa yawu ma magana. “To ranka ya dade” ZAHRA POV. Da hannu Ummiter ta nuna min ďakin Hajiya Jamila sannan ta juya tayi tafiyarta, a lokacin falon babu komai amman gudun yin laifi ya saka ban hau stairs din ba na dawo na zauna a kasa har na tsawon lokaci. Ganin bata fito ba kuma wani wanda zan iya cewa yayi mata magana be fito ba yasa na tashi na fara taka stairs din har na haye sama tsintar kaina na yi a wani guri mai kama da karamin falon sai dai wannan dakunan ne a jere wasu kuma suna kalon juna, daki na biyu na nufa kamar yadda ta fada sannan na kwankwasa ban ji an amsa ba, hakan kuma be saka na kasa kwankwsawa a karo na biyu ba haka na kwankwasa har sau uku jin ba a amsa min ba ya saka na murda kofar dakin na shiga da sallama. “Ba a shigo min ďaki Zahra sai na bada izini” “Na yi ta kwankwasawa ba amsa min ba” “Tun da kika ji ban amsa miki ba ai kin sa ina uzuri” Na yi shiru ban ce mata komai ba, a yadda na lura Hajiya Jamila na da wani irin izza da nuna isa da son wulakanta mutane. Haka ta bar ni a tsaye a jikin kofar har sai da na gaji da tsayuwa na juya zan fice sannan ta yi min magana. “Ina zaki je? Ki zo ki ba shi nono mana” Na juyo na dawo kusa da inda take zaune, na karbi yaron na zauna kan kujera na bude nono na saka masa rigar baki tare da Bismillah, wani irin dadi ne ya ziyarce ni sam yau ko ciwon da nake ji idan ina matsa nono ban ji ba, tashi ta yi ta rufe dakin da key sannan ta juyo ta kalleni “Idan kin gama bashi nono ki dora shi akan gado, ga blanket nan a kasa ki shimfida ki kwanta” Na kalli blanket din dake aje a kasa na kalleta. “Ko dai baki san inda na fito ba be kamata ki wulakanta ni ba” “Au to da miye nufinki? Ki hau saman gadon miliyan uku ki kwanta? Ni na kwanta ke ki kwanta?” “Kudi ba hauka ba ne Hajiya Jamila, kuma ni ba aiki na zo yi miki ba taimako kika nema kuma na yi miki, na fi karfin wulakanci” “Alhamdulillah tun da har kin san ina da kudin, taimako kuma ke ake yi ma alfamar” “Ni dai na ke muku alfamar ko ba komai kin ci amfanina tun da na baki abun da kudin da kika takama da su ba su ba ki ba” Ina ganin yadda ta bata fuska na san kalamaina ba su yi mata dadi ba. “Kudi sun biya bukata domin sun siya min abun da baki san kimarsa ba, kin zubar da darajarki ta uwa, kara ni neman haihu ya saka ni aikata abun da na aikata ke kuma fa?” Na sauke kaina kasa ina jin rashin kyautawar abun da na aikata. “Ba a haife ki ba Zahra, ba ayi wata ďiya mace da zata tako har cikin ďakina ta fada min bakar magana ba, aje min yaro karki shayar da shi bakin nononki” Ta furta da karfi sannan ta nufi wayarta ta dauka ta kira Dr Hamid tana ta masifa a waya har da su rantsuwar ba zan kwana a gidan ba. Ni ko sai na ji kamar na ce ta yi hakuri saboda na samu kasancewa da ďana. Tana gama wayar ta jefar da ita kan gadonta ta nufo ni ta karbe yaron da karfi bana son na yi kokuwa da ita ďana ya ji ciwo hakan yasa na sakar mata ta cire bakinsa daga nono sai ya fashe da kuka. “Fice daga ďaki.. Wawuyar banza kazama” “Kazamar da ta yi miki amfani ba, wawuya kuma bata wuce ki ba wanda ke wulakanta matar da ta taimaki rayuwarta ta rufa mata asiri” Na fada a fusace sannan na juyo na nufi kofar na bude na fito, ban san miyasa Hajiya Jamila ta son wulakanta ni ba, daga taimako sai kuma abu ya koma da cin mutunci kamar wata Kishiyarta. Falo na dawo na zauna sai da na zabi kujerar da nake kyautata zaton tafi sauran tsada sannan na zauna zuciyata har bugawa take saboda bacin rai, ba dan kura ta yi lafiya ba karnuka har sun isa su yi mata haushi. Ina zaune akan danna door bell din falon sai na tashi da sauri na isa gurin kofar a zatona Dr Hamid din na da ta kira ya iso, sai dai ina budewa sai na yi arba da wani mutumen da ban sani ba. “Barka da dare dan Allah ki ce ma Hajiya wai Abiey yana sallama da Zahra” Da mamaki na kalli bayan mutumen sai dai ban hango kowa ba. “Ina yake?” “Yana ta can gurin motoci” Na kara bude kofar na saka takalmina na fito ina da mamakin waya fada masa ina? Miya zo? Anya ni Zahra? Kuma Abiey dai wanda na sani ko wani. Bayam mutumen na bi sai ya nuna min inda wata bakar mota take fake, tsaye yayi na ki na karasa ina ta kallon motar sai gashi ya bude motar ya fito fuska ba yabo ba fallasa ya doso inda nake, be karaso ba yaja ya tsaya yana kallona. “Da gaske ke ce?” Na kalli ko'ina na gidan tunawa da na yi da Dr Hamid yace min akwai camera a gida na karasa kusa da shi. “Me kake yi a nan?” “Ke zan tambaya? Miya kawo ki nan?” “Ba ruwanka, ka fita sabga ta” Na juya sai na ji an riko dantsen hannuna an jiyo da ni da karfi. “Zahra saurareni mana, mi zai saka ki zo aiki a gidan nan? Me kika rasa?” “Ban sani ba, and for your information karka sake zuwa gidan nan” “Sai kuma me?” Na kalleshi da kyau sannan na furta. “I hate you” “And...” “I hate you na tsane ka” “And...” Na rasa kalmomin da zan hada na fada masa maganar da zata masa zafi domin na lurar wadandan basu jika shi yadda na ke so ba. Muna cikin wannan halin aka haske mu da mota kamin daga bisa aka kashe fitilar motar mai motar wanda Dr Hamid ne ya faka a kusa da inda muke tsaye har lokacin Abiey na rike da cinyar hannuna dake cikin hijabi. “Lafiya?” Shi ne abun da Dr Hamid ya fara tambaya a lokacin da ya fito motar, sai Abiey ya sake ni ya kalleshi. “Okay kai ka kawo ta nan kenan?” Dr Hamid ya kalleshi irin duba na tsanaki sannan ya kalleni. “Wuce mu je ciki Zahra” “To ta shiga mu gani” Abiey ya fada yana hade fuska kamar ba shi ba, haka nan kuwa na samu kaina da masa juyawa na koma cikin gidan kamar yadda Dr Hamid ya bukata. “Shiga mota” Dr Hamid ya fada, nan ma ina cira kafa Abiey ya ce. “Karki shiga motar nan” Ni dai kam na yau san Abiey ba a banza ya zo min ba, sai da yayi min asiri domin umarninsa na bi na kasa shiga motar. “Miye tsakaninki da shi?” Dr Hamid ya tambaya. “Karka sake tambayar abun da yake tsakanina da ita, and karna sake ganin inuwarka a inuwarta, ke kuma tun har kin fi son haka mu zuba zuwa ni da ke i will show you my other side” Ya karasa yana kallona babu wasa a maganar shi kamar yadda fuskarsa ma ta nuna. “Shiga mota mu je” A nan kam Allah ya ba ni ikon karya sihirinsa na ki bin umarninsa amman ban iya furtawa ba sai hade hannu da na yi na juya na nufi gate ina takawa da kafafuwana a lokacin har an fara yayyafi, haka na isa gate din suka bude min na yi tafiyata na bar su can a tsaye sai da na yi nisa na fara jin tsoro ga ruwa ya fara karfi kamar na juya na koma sai ga motar Abiey ta faka gabana, bude motar yayi ya fito ya nufi bayan motar ya bude ya dauko hula da wata jacket ganin haka yasa na ja na tsaya ina kallonsa har ya karaso kusa da ni ya dora min jacket din saman hijab hular sanyin dake kansa hannunsa ya saka min a kai. “Wuce mu tafi Malama” “Ni ba zan shiga motar ba” “Waya ce ki shiga?” Ya nuna min hanya sai na wuce gaba yana bayana, ina ta jiran ya fara rokona na shiga motar ya kai ni gida amman be yi ba har na wuce motar ina jin lokacin da ya rufe ta ya biyo bayana muka fara takawa a kasa ga ruwa sai karfi yake karawa, na san kuma idan na yi tafiyar lafa ni da isa sai Asubahi domin ni ba gwanar tafiya a kafa ba ce ga unguwar babu mutane sai mu kamar mayu. “Na fiki zama bad boy ai, idan arziki be miki ba ai tsiya zata miki” Na juyo a fusace. “Ina ruwanka da ni wai? Na tsane ka Abiey ka fita daga rayuwa” “Ba zan fita ba” Ya amsa min kamar zai doke ni yana matsawo kusa da ni har muna shakar numfashin juna ni da shi... ABIEY POV. A hankali ya busar da iskar bakinsa ya gyara zaman hannunsa na hagu dake aljihu, hannunsa na dama kuma na rike da kofin ruwa. Can kuma ya ciro hannun ya duba agogon dake daure a hannunsa. “9:13pm” Ya furta sannan ya aje daga kai yana kallon harabar gidan tare da kurba ruwan, ajiyar zuciya ya sauke ya sunkuya ya aje ruwan ya dauki keys dinsa dake kan mini center tebur dake gurin ya juyo ya fito daga backyard din ya dawo cikin dakinsa, kai tsaye ya zarce zuwa kofar fita dakin kamar an korashi haka ya sauko stair ba karamin dadi ya ji ba ganin falon ba kowa, balle ya tsaya amsa tambayayiyin Ammy na ina zai je. Yana isa gurin kofar falon ya bude ya fita be san key din wace motar ce a hannunsa ba har sai da ya latsa key din wata kafirar BMW ta yi kara, sai ya zagaya tsakamin motocin ya nufi inda take ya bude ya shiga yana reverse ya kunna kai daman masu kula da shiga da ficen gidan tuni suka wangale masa gate. Driving kawai yake yana tunanin yadda zai wanke Zahra a gurin Ammy da Anty, musamman ma Anty da yake ganin ta fi kowa daukar abun da zafi. In 35min ya iso kofar gidansu Yasmin horn yayi aka bude masa sai ya samu guri a harabar gidan ya faka, hakan nan kawai yake jin baya bukatar shiga ciki daman ba gurin Momy ya zo ba balle yace zai shiga ya gaishe ta, wannan zuwan na Yasmin ne kawai, wayarsa ya ciro dake aljihu ya kiran number Yasmin kamar ba zata dauka ba sai kuma ta yi picking. “Fito gani nan waje” Jimmm ta yi kamar ba ta ji abun da ya fada mata ba. “Toh” Ta amsa ya yanke sannan ya maida dubansa gurin kofar falon yana jiran fitowar Yasmin. After like ten min aka bude kofar ta fito tana sanye da doguwar rigar atamta sai mayafin da ta rufe jikin, bude motar yayi ya fito yana jiran karasowarta ita kam bata yarda ta kalleshi ba har ta iso inda yake tsaye. “Barka da dare” “How are you?” Ya bukata kamar an masa dole sai a lokacin da kalleshi hawaye na sauko mata wasu kuma na taruwa a idonta. “I'm not fine” “Me too” Ya furta yana dauke kansa ya kalli sararin samaniya da iskar hadari ke kadawa. “Na zo na yi magana da ke ne akan maganar mu shiyasa ban shiga ciki na gaisa da Momy ba” Yana maganar tana masa wani irin kallo kamar ta hade shi. “Na yi magana da Abbah Musa na fada masa ina son a fasa zancen baiko...” Sai kuma ta yi shiru, Abiey ya tattara dukan hankalinsa da natsuwarsa ya mika mata zuciyarsa na wani bugawar dadi. “Ahen... Ina jinki” “Ya ce ba zan raina musu hankali ba, ban isa na zubar musu da mutunci ba, miyasa ban fadi haka tun kamin su amsawa Mai Martaba ba, sai bayan sun amsa zan taso musu da wata maganar, wai ban isa na maida su kananan mutane ba, ba za su yarda matsala ta taso daga garesu ba, kuma babu fashin aure sai idan kai kace ka fasa....” A take annashuwa da farincikin dake tare da Abiey suka gushe. “What...! What do you mean? Yasmin ya zaki saka ni a matsala... Ya salam.. ” Ya fada yana juyawa ya daki motar da mugun karfi, kana ya juyo ya rika hade kafadunta yana jijjigata da karfi. “Yasmin ya zaki min haka? Tun abun na sabo da kin yi abun da na fada miki da yanzu haka be faru ba! Miyasa zaki saka mi a matsala?” Sai ta amsa masa cikin kuka. “Kai ka saka kanka a matsala Abiey, miyasa zaka saka zobe a yatsan da ka san idan har za a cire shi sai dai a gutsure shi? Miyasa zaka ambaci sunana a bagirin da zuciyata ta dade tana nema? Na sani ba zaka taba so ba Abiey ni kuma ban isa na bude zuciyata na cire soyayyarka ba....!” Sakinta yayi ya matsa baya ya nuna kansa with shock, sai ta daga masa kai ta saka hannayenta biyu ta rufe fuskarta ta fashe da kuka. Baya baya Abiey yayi har sai da ya jingina da motarsa ya dafe kanshi ya duka a gurin yana jin wani zazzabi na taso mashi. “Na shiga uku... Yau na ga Idi zigidir” Sai kuma ya mike tsaye yana girgiza mata kai. “Yasmin ba zaki iya zama da ni” Ta cire hannayenta daga fuskarta tana kuka. “Zan iya” “Zuciyata babu wanda take so sai Zahra da Zahra ita kadai...” “Zan roka maka Allah ya sassautawa maka son Zahra Abiey” Addu'ar da tace zata yi ta yi farraku tsakaninsa da Zahra sai ya saka a take ya ji ya fara tsanarta. “Amadadin kin min addu'a ki raba ni da Zahra, me zai hana ki yi ma kanki addu'a so na ya fita daga zuciyarki?” “Kamin yau... Na roka a dare mabanbanta, ka min a kawo yanzu na roka amman ba a amsa min ba sai ma aka kara kawo kusanci a tsakanina da kai ta inda ban zata ba” “Yasmin indai kina so so na hakika to ba zaki so na shiga matsala ba, kuma zaki so abun da na ke so” “Indai har da gaske kana son Zahra to zaka fi kowa fahimtar halin da nake ciki, Ciwon So masifa ne Abiey da ace ina da iko da ban bari Son ka ya shiga zuciyata ba” Ta fadi durkushe kasan guiwoyinta tana kuka, ita kadai ta san abun da take ji, ita kadai ta san halin da take ciki akan Abiey kuma tabbas da zata iya da ta cire soyayyarsa a zuciyarsa, gana daya sai jikin Abiey yayi sanyi, durkusawa yayi kasa ya rika hannunta sannan ya matsa kusa da ita sosai ya rumgume ta a hankali. “I'm sorry....” Lumshe ido ta yi tana jin kamar ta saka wuka ta tsaka kirjinsa ta shiga cikin jininsa ta kwanta, sai da ya tabbatar ta samu natsuwa sannan ya mike tare da ita tsaye. “Ki shiga ciki ki huta zamu yi magana daga baya okay” Dagowa kai ta yi ta kalleshi sannan ta daga da ga jikinshi tana jin kamar ta rayu a kirjinsa rayuwa ta har abada. “Ka yi hakuri idan na bata maka rai...” Ya hade yawun bakinsa. “No dukanmu ba ma iya sakawa junanmu abu kuma ba ma iya cirewa, ko wace zuciyata tana juyawa bisa ga ikon da Ubangiji ya bata, da ace dan adam zai iya wani abu, na tabbatar da yanzu Zahra ta cire so na a zuciyarta, amman ta kasa saboda bata da iko akan komai, abun da ta yi min dazun yanzu ya kara tabbatar da da har gobe Zahra tana kaunata” Yasmin ta yi murmushi irin murmushin nan da hausawa ke cewa ya fi kuka ciwo. “Zahra ta yi dace Abiey ka rayu da soyayyarta na tsawon lokaci” “Yasmin.... Zahra ta so ni ba dan wani abu nawa ba, ni da ita mun kamu da kaunar junanmu ba tare da mun sani ba, sannan Zahra ta cika duk wani sharadi da na ke so a mace, ko kadan bana son na auri mace da ita take so na ni bana son ta, saboda zan iya cutar da ita, Yasmin na shiga a zuciyar Zahra na nuna mata kauna kamin abubuwa su canja mana, ba zan manta lokacin data durkusa har masa tana rokon kar na fasa aurenta ba amman ban iya yin komai ba saboda Deen ya shiryar mana gadar zare, wannan ce damar da nake da ita wanda zan nuna Zahra cewar ina kaunarta irin kaunar da babu wanda ya taba yi mata irinta, ina son na rayu da Zahra fiye da yadda kike jin kina son rayuwa da ni....!” Yana kaiwa nan ya bude motarsa ya shiga ya yi mata key ya bar Yasmin a tsaye ta bishi da kallo. “Ciwon so yana dawainiya da kai Abiey, ni kuma be bar ni ba, ‘So’ baka kyauta mana ba” Yasmin ta fada tana hawaye jikinta sai kamshin turaren masoyinta yake. *** *** **** Tuki kawai yake yana jin kamar bata son komawa gida, kuma be san inda zai je ba da ma ace irin da ne da Sauban be yi aure da a gurinsa zai tare. “Miyasa abubuwa suke tasowa su shiga tsakanina da ke Zahra! Why why...” Ya buga sitiyarin motar da mugun karfi. “And kullum daga gurina matsalar nan take tasowa why me?” Kamar mahaukaci haka yake fada da kanshi tana jin wani kalar bakinciki marar misaltuwa. Daker ya kalli wayarsa dake ringing ba dan Sauban ne mai kiran ba da ba zai taba dagawa ba. “Miye?” Shi ne abun da ya fada bayan ya amsa kiran. “Are okay” “I'm not” “Okay maybe later” “Fada min yanzu minene?” “Nuratu ce tace min ta ga Zahra a gidan yayarta wai an gabatar da ita a matsayin yar aiki” Guri ya samu ya faka motar sannan ya gyara zaman wayar a kunnesa. “Zahra tawa?” “Eh yanzu ta dawo daga gidan take fada min” “Zahra fa? Anya ta san Zahra da kyau kuwa?” “Ta santa mana kasan da ita suka je yi mata gaisuwa tare da Ammy da Dr, kuma na nuna mata hotonta a waya tace min ita ce” “Wait.. kana da hotunan Zahra a wayarka?” “Amman dai ka san ba wani abu ke tsakanina da ita ba ko?” “Ina aka ce maka an ganta?” “Tace gidan yayarta ubansu daya da ita, tace tana zaune aka gabatar da Zahra a matsayin wanda zata rika kula da babyn da yayar ta haifa” “Me Zahra ta rasa da zata je ta yi aiki a gidan wani? Ina raye?” “Ni ma abun da nake tunani kenan, tace yanzu haka tana gidan” “Ina ne gidan?” “Me zaka yi?” “I need to see her” “No idan ma magana kake son yin da ita ka same ta a gidansu zai fi” “Zan tabbatar ne idan ita din ce, fada min wace area ce?” “Zan maka text din address din, maybe ma ka san shi wani Alhaji Bashir mai kudi ne sosai kwana baya ma yayi hadarin jirgi, kuma ance be taba haihuwa ba sai wannan karon” “Ban san shi ba, amman turo min address din” Ya sauke wayar da matukar mamaki. “Mi zai saka Zahra aiki a wani guri?” Tambayar da yayi ma kansa kenan har lokacin be daina mamaki ba. Few minutes later Sauban ya turo masa sakon address din, da hannu daya Abiey yake driving dayan hannunsa kuma rike da waya har ya isa unguwar. Tun daga yanayin area kasan area ce da manyan mutane masu fada aji kuma wandanda suka taka nesa da kafafuwansu suka tsaya, babu gidan da be nuna isar mai shi a unguwar titi ma tsif yake kamar an yi ruwa an dauke baka jin komai sai motsi dogayen itatuwan dake kadawa saboda hadarin da ha hadu a samaniya har ya rufe taurari. Police din da ya gani a kofar gidan da ya banbanta da saura ya tabbatar masa da cewar gidan ne, kai tsaye ya isa gaban gate din ya danna horn sai police suka taso shi kuma ya sauke glass din motarsa. “Sannu da zuwa” “Yauwa Mai gidan yana ciki?” Police dake son tantance fuskar Abiey ya ce. “Kana da appointment da shi?” “Yeah ka fada masa Abiey ne Mai Martaba ya turo ni” “Allah sarki ni kam na ce kamar Abiey sannu da zuwa ranka ya dade” A take suka bude masa gate din ya kunna kai cikin gidan mai kama da wata masarauta a gurin da aka tanada domin aje motoci ya nufa ya faka motarsa yana tsara yadda zai amsawa Mai gidan idan ya tambaye dalilin zuwansa, mutumen da ya gani a kusa da motarsa ya saka ya sauke gilashin motar. “Ya aka yi?” “Sai ka juyo da motar ranka ya dade masaukin bakin ta can yake” Abiey ya bude gurin da yake ajiyar kudi a cikin motar ya dauko bandir din 500 ya mika masa. “Shiga cikin gidan nan gurin matansa ka ce Abiey yana sallama da Zahra” Mutumen ya saka hannu biyu ya karba jiki na rawa yawu ma magana. “To ranka ya dade” ZAHRA POV. Da hannu Ummiter ta nuna min ďakin Hajiya Jamila sannan ta juya tayi tafiyarta, a lokacin falon babu komai amman gudun yin laifi ya saka ban hau stairs din ba na dawo na zauna a kasa har na tsawon lokaci. Ganin bata fito ba kuma wani wanda zan iya cewa yayi mata magana be fito ba yasa na tashi na fara taka stairs din har na haye sama tsintar kaina na yi a wani guri mai kama da karamin falon sai dai wannan dakunan ne a jere wasu kuma suna kalon juna, daki na biyu na nufa kamar yadda ta fada sannan na kwankwasa ban ji an amsa ba, hakan kuma be saka na kasa kwankwsawa a karo na biyu ba haka na kwankwasa har sau uku jin ba a amsa min ba ya saka na murda kofar dakin na shiga da sallama. “Ba a shigo min ďaki Zahra sai na bada izini” “Na yi ta kwankwasawa ba amsa min ba” “Tun da kika ji ban amsa miki ba ai kin sa ina uzuri” Na yi shiru ban ce mata komai ba, a yadda na lura Hajiya Jamila na da wani irin izza da nuna isa da son wulakanta mutane. Haka ta bar ni a tsaye a jikin kofar har sai da na gaji da tsayuwa na juya zan fice sannan ta yi min magana. “Ina zaki je? Ki zo ki ba shi nono mana” Na juyo na dawo kusa da inda take zaune, na karbi yaron na zauna kan kujera na bude nono na saka masa rigar baki tare da Bismillah, wani irin dadi ne ya ziyarce ni sam yau ko ciwon da nake ji idan ina matsa nono ban ji ba, tashi ta yi ta rufe dakin da key sannan ta juyo ta kalleni “Idan kin gama bashi nono ki dora shi akan gado, ga blanket nan a kasa ki shimfida ki kwanta” Na kalli blanket din dake aje a kasa na kalleta. “Ko dai baki san inda na fito ba be kamata ki wulakanta ni ba” “Au to da miye nufinki? Ki hau saman gadon miliyan uku ki kwanta? Ni na kwanta ke ki kwanta?” “Kudi ba hauka ba ne Hajiya Jamila, kuma ni ba aiki na zo yi miki ba taimako kika nema kuma na yi miki, na fi karfin wulakanci” “Alhamdulillah tun da har kin san ina da kudin, taimako kuma ke ake yi ma alfamar” “Ni dai na ke muku alfamar ko ba komai kin ci amfanina tun da na baki abun da kudin da kika takama da su ba su ba ki ba” Ina ganin yadda ta bata fuska na san kalamaina ba su yi mata dadi ba. “Kudi sun biya bukata domin sun siya min abun da baki san kimarsa ba, kin zubar da darajarki ta uwa, kara ni neman haihu ya saka ni aikata abun da na aikata ke kuma fa?” Na sauke kaina kasa ina jin rashin kyautawar abun da na aikata. “Ba a haife ki ba Zahra, ba ayi wata ďiya mace da zata tako har cikin ďakina ta fada min bakar magana ba, aje min yaro karki shayar da shi bakin nononki” Ta furta da karfi sannan ta nufi wayarta ta dauka ta kira Dr Hamid tana ta masifa a waya har da su rantsuwar ba zan kwana a gidan ba. Ni ko sai na ji kamar na ce ta yi hakuri saboda na samu kasancewa da ďana. Tana gama wayar ta jefar da ita kan gadonta ta nufo ni ta karbe yaron da karfi bana son na yi kokuwa da ita ďana ya ji ciwo hakan yasa na sakar mata ta cire bakinsa daga nono sai ya fashe da kuka. “Fice daga ďaki.. Wawuyar banza kazama” “Kazamar da ta yi miki amfani ba, wawuya kuma bata wuce ki ba wanda ke wulakanta matar da ta taimaki rayuwarta ta rufa mata asiri” Na fada a fusace sannan na juyo na nufi kofar na bude na fito, ban san miyasa Hajiya Jamila ta son wulakanta ni ba, daga taimako sai kuma abu ya koma da cin mutunci kamar wata Kishiyarta. Falo na dawo na zauna sai da na zabi kujerar da nake kyautata zaton tafi sauran tsada sannan na zauna zuciyata har bugawa take saboda bacin rai, ba dan kura ta yi lafiya ba karnuka har sun isa su yi mata haushi. Ina zaune akan danna door bell din falon sai na tashi da sauri na isa gurin kofar a zatona Dr Hamid din na da ta kira ya iso, sai dai ina budewa sai na yi arba da wani mutumen da ban sani ba. “Barka da dare dan Allah ki ce ma Hajiya wai Abiey yana sallama da Zahra” Da mamaki na kalli bayan mutumen sai dai ban hango kowa ba. “Ina yake?” “Yana ta can gurin motoci” Na kara bude kofar na saka takalmina na fito ina da mamakin waya fada masa ina? Miya zo? Anya ni Zahra? Kuma Abiey dai wanda na sani ko wani. Bayam mutumen na bi sai ya nuna min inda wata bakar mota take fake, tsaye yayi na ki na karasa ina ta kallon motar sai gashi ya bude motar ya fito fuska ba yabo ba fallasa ya doso inda nake, be karaso ba yaja ya tsaya yana kallona. “Da gaske ke ce?” Na kalli ko'ina na gidan tunawa da na yi da Dr Hamid yace min akwai camera a gida na karasa kusa da shi. “Me kake yi a nan?” “Ke zan tambaya? Miya kawo ki nan?” “Ba ruwanka, ka fita sabga ta” Na juya sai na ji an riko dantsen hannuna an jiyo da ni da karfi. “Zahra saurareni mana, mi zai saka ki zo aiki a gidan nan? Me kika rasa?” “Ban sani ba, and for your information karka sake zuwa gidan nan” “Sai kuma me?” Na kalleshi da kyau sannan na furta. “I hate you” “And...” “I hate you na tsane ka” “And...” Na rasa kalmomin da zan hada na fada masa maganar da zata masa zafi domin na lurar wadandan basu jika shi yadda na ke so ba. Muna cikin wannan halin aka haske mu da mota kamin daga bisa aka kashe fitilar motar mai motar wanda Dr Hamid ne ya faka a kusa da inda muke tsaye har lokacin Abiey na rike da cinyar hannuna dake cikin hijabi. “Lafiya?” Shi ne abun da Dr Hamid ya fara tambaya a lokacin da ya fito motar, sai Abiey ya sake ni ya kalleshi. “Okay kai ka kawo ta nan kenan?” Dr Hamid ya kalleshi irin duba na tsanaki sannan ya kalleni. “Wuce mu je ciki Zahra” “To ta shiga mu gani” Abiey ya fada yana hade fuska kamar ba shi ba, haka nan kuwa na samu kaina da masa juyawa na koma cikin gidan kamar yadda Dr Hamid ya bukata. “Shiga mota” Dr Hamid ya fada, nan ma ina cira kafa Abiey ya ce. “Karki shiga motar nan” Ni dai kam na yau san Abiey ba a banza ya zo min ba, sai da yayi min asiri domin umarninsa na bi na kasa shiga motar. “Miye tsakaninki da shi?” Dr Hamid ya tambaya. “Karka sake tambayar abun da yake tsakanina da ita, and karna sake ganin inuwarka a inuwarta, ke kuma tun har kin fi son haka mu zuba zuwa ni da ke i will show you my other side” Ya karasa yana kallona babu wasa a maganar shi kamar yadda fuskarsa ma ta nuna. “Shiga mota mu je” A nan kam Allah ya ba ni ikon karya sihirinsa na ki bin umarninsa amman ban iya furtawa ba sai hade hannu da na yi na juya na nufi gate ina takawa da kafafuwana a lokacin har an fara yayyafi, haka na isa gate din suka bude min na yi tafiyata na bar su can a tsaye sai da na yi nisa na fara jin tsoro ga ruwa ya fara karfi kamar na juya na koma sai ga motar Abiey ta faka gabana, bude motar yayi ya fito ya nufi bayan motar ya bude ya dauko hula da wata jacket ganin haka yasa na ja na tsaya ina kallonsa har ya karaso kusa da ni ya dora min jacket din saman hijab hular sanyin dake kansa hannunsa ya saka min a kai. “Wuce mu tafi Malama” “Ni ba zan shiga motar ba” “Waya ce ki shiga?” Ya nuna min hanya sai na wuce gaba yana bayana, ina ta jiran ya fara rokona na shiga motar ya kai ni gida amman be yi ba har na wuce motar ina jin lokacin da ya rufe ta ya biyo bayana muka fara takawa a kasa ga ruwa sai karfi yake karawa, na san kuma idan na yi tafiyar lafa ni da isa sai Asubahi domin ni ba gwanar tafiya a kafa ba ce ga unguwar babu mutane sai mu kamar mayu. “Na fiki zama bad boy ai, idan arziki be miki ba ai tsiya zata miki” Na juyo a fusace. “Ina ruwanka da ni wai? Na tsane ka Abiey ka fita daga rayuwa” “Ba zan fita ba, kuma idan an sake ganinki da wani namijin sai na ba ki mugun mamaki ” Ya amsa min kamar zai doke ni yana matsawo kusa da ni har muna shakar numfashin juna ni da shi... [10/21, 8:03 PM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣0️⃣ Kansa ya daga sama ya sauke sannan ya matsa baya. “Kana tunanin karfi zai saka na manta abun da ka yi min Abiey? Ko kuma cilasta ni zaka yi na yafe maka” Ina rufe baki sai ya daka min tsawa ya sake matsowa wannan karon kamar zai doke ni. “Ba yafiyarki na ke so ba Zahra..kuma ba rokon na ke ki so ni ba, ki cire wannan a ranki” “To me kake so? Dawowa ka yi ka takurawa rayuwata?” Na tambaya hawaye na sauko min, sai na juya ba tare da yace min komai ba ya koma gurin motarsa ya bude ya shiga yayi mata key sannan ya jan motar ya karaso inda nake ya faka bude min front seat. Wannan karon bana bukatar ya fada min na shiga, domin ina jin tsoron tafiya a hanya ni kadai ko mu biyu domin hudu yayi, shiga na yi na zauna sai ya fisgi motar kamar zai tashi sama. “I'm sorry i don't mean to be rude to you, ke din ce wani lokacin sai...” “Sai me?” Na tambayana ina kallonshi. “Zahra ta ya zaki manta duk rayuwar da muka yi, ko da ace da gaske na yaudareki ya kamata ace kin yafe min mana” “Ba da gaske ba ne a Abiey?” “I don't want to say this Deen ya shirya komai, kin kasa fahimta kin kasa ba ni damar da zan wanke kaina” “Tun a lokacin da abun ya faru ya kamata ka wanke kanka ba wai yanzu! Kuma da zaka rabu da ni da ka rabu da ni kamin ranar da ka so ka kunyata wata kila da yanzu na manta da an taba halittarka, kuma baka bar ni ba sai da ka yi min kazafi, ban taba Zina ba Abiey amman ka ce ina da hiv kuma ta hanyar sex na samu taya zan manta wannan ranar?” “Deen yayi kidnapping Mijin Dr Zainab and he force her ta shirya haka, saboda a fasa aurena da ke, and Ammy support her saboda yayi mata rantsuwa da al'kur'ane idan aka dauren auren nan zai kashe mijinta, he already told her ya san rayuwar shi ba mai tsawo ba ce so be damu ya rasa ransa akanki ba, after the wedding kuma babu damar mu kama shi saboda za ki iya cewa ana binsa da shi ne, besides ba mu da wasu evidence a lokacin, and hana su yin komai ne saboda ke kar a daga miki hankali a lokacin da kika aure shi, amman ban gujeki ba Zahra ban yaudareki babu dalilin da zai saka na yi haka, yanzu ma ba ki san halin da nake ciki all because of you, Mai Martaba ya tambaya min auren Yasmin ina ta kokarin na yi cancelled abun and you slap me in front of my Step Mom, ranta ya bace sosai ta je gida tana ta masifa Ammy ma ranta ya bace” Tun da ya fara maganar bance masa uffan ba, hawaye kuma ba su daina min zuba ba jiki ya mutu na kasa yarda da abun da Abiey ya ke fada a yanzu, kuma na rasa courage din karyata shi, but deep down inside my heart wani irin yaki ne tsakanin zuciyata dake karbar sako da kuma kaina da ke aikawa. Har kofar gidanmu ya faka motar sai na cire rigar da ya saka min na mika masa na cire hular kaina na mika masa, na kai hannu na bude motar ya kira sunana. “Zahra...” Sai na juyo na kalleshi hawaye na sauko min kamar ba gobe. “Abiey i need some space, i need to think kaina a kulle yake a yanzu ina bukatar hutu...” Na fada muryarta a sanyeye sai ya daga min kai. “I understand i just want you to know that i love you and if you need anything I'm here for you” “I need some space...” Na sake maimaitawa sannan na bude motar na fita, kamar zan fadi haka na isa kofar gidanmu kafafuwana babu karfi, ina tabawa na ji kofar a rufe daker na daga hannu na kwankwasa kofar kamar daman can Mama na tsaye jikin kofar tana jirana sai ji na yi  bude da sauri. “Zahra ina kika je kika zauna haka?” Na shiga cikin gidan ba tare da na amsa mata ba, da ace Abiey be bani labarin nan ba wata kila da yanzu ina da labarai da yawa da zan bata, a yanzu kam ya katse duk wani hanzari nawa tunanina ya tsaya cak. “Lafiya kika kuka? Miya faru?” Ta tambaya bayan ta yi arba da hawayena. Sai na sauke kaina kasa ina rike da hannayena. “Mama Abiey ya fada min wata magana a game da abun da ya faru ina son na tabbatar ta ina son na san gaskiya, amman ban san ta ina zan fara ba” Mama ta dafa ni domin ta fahimci akwai damuwa sosai a tare da ni. “Ina kika hadu da Abiey? Me ya fada miki?” “Gidan Su Hajiya Jamila” “Shiga ciki ki zauna” Na nufi dakin da nake kwana ita kuma ta rufe gidan, ko da ta shigo dakin ni har na kai zaune ina hawaye, sai ta zauna kusa da ni. “Miya faru Zahra” Maimakon na fada mata sai kawai na fashe da kuka na kwanta a kafarta. “Ki fada min abun da ya faru mana, ya akai ya same ki a can? Ko kin fada masa abun da yake faruwa ne?” “Aa ban san yadda aka yi ya ji ina gidan ba kawai ya same ni a can ne...” Cikin kuka na fada mata abun da ya faru, sai ta cika da mamakin zuwansa gidan ni kuma zuciyarta tana cike da damuwar abun da Abiey ya fada min. “Wata kila yana da alaka da mutanen gidan ne shiyasa har ya san da haka, da ace ya san da wani abun bayan wannan da yanzu yayi miki magana, ki kwantar da hankalinki be san komai ba” “Amman Mama da gaske Deen ya aikata abun da Abiey ya fada min?” Na tambaya ina kallonta domin shi ne abun da na fi damuna. “Akwai kamshin gaskiya a ciki amman ba zamu tabbatar ba har sai kun yi bincike” Na mike tsaye da sauri ina tambayar Mama wayarta, ji nake kamar ba zan iya kwana ba sai na yi magana da Hajiya. “Me zaki yi da wayata?” “Hajiya zan kira ina son na tambaye ta” “Ko da ace ta sani ai ba zata fada miki gaskiya ba, balle kuma be zama lallai ace ya aikata hakan da saninta ba” “Mama ina son na ji ta bakin Hajiya, Deen ba shi da abokin shawara sai Hajiya indai har da gaske ne mahaifiyarsa zata sani” “Ko ta sani be zama lallai ta fada miki ba” Na koma na zauna ba dan na gamsu ba, sai dan bana son musawa Mama a yanzu. “Idan har da gaske ne, Deen ya cutar da ni kuma ya cutar da Abiey ya kuma saka na cutar da Abiey...” Sai kuma na kalli Mama da sauri zuciyata na karyata abun da Abiey ya fada min. “Allah yasa ba gaskiya ba ne Mama Deen ba shi da mugun hali har haka” “Ameen” Ta amsa sai na hau saman gadon da Hijab na kwanta na nade guri daya ina jin wani sanyi na taso min, bachin da ban yi ba kenan har safe kuma daren yafi ko wane dare yi min tsawo a rayuwata. Kamar ko yaushe Mama ta shirya min ruwan wanka ta dama min kunu sannan ta dumama tuwon jiya ta kawo min, sai da na fara yin wanka sannan na dauki kunun na sha kadan shi kam dumame ban iya ci ba, har zuwa yanzu kuma ban labartawa Mama wulakancin da Hajiya Jamila ta yi min ba, haka ma ban fada mata cewar mijinta ne mutumen da na taimakawa lokacin da hadarin jirgin nan ya faru ba, jiya ma labarin zuwan Abiey a gidan kawai na fada mata domin hankalina baya gurin gaba daya, natsuwata da muradina yana gurin abun da Abiey ya fada min, ina son na dauki permission gurin Mama na fita amman na san ba zata bari ba. Ina cikin wannan halin muka ji sallama kofar gida muryar namiji ne da zan iya kira magidanci duk kuwa da kasancewar ban ga fuskarsa ba. Mama ce ta amsa sannan ta tambaya waye. “Dahiru ne, Ammy ce ta aiko ni Mahaifiyar Abiey tace na zo na dauki Zahra tana son magana da ita” Mutumen ya amsa daga can wajen da yake, a take gabana ya fadi faduwar da ban san ta minene ba. Taso na yi na fito waje na kalli Mama dake aikin gyara tsintsiya. “Allah yasa lafiya” “Ameen, lafiya zan yi?” Na tambaya sai ta daga min kai. “Eh ai ki tafi kiji dalilin nemanki da take” Na juya na koma ciki na canja hijab din jikina na saka takalmi na fito ina jin sallamar Yaya Maryam Mama dake tsakar gidan ta amsa mata, ni kuma na sauke kaina kasa ina jin kunyar hada ido da ita. “Masu jego ina zuwa” Ta fada tana kunno kai cikin gidan, yayinda ni kuma na ke kokarin fita, sai Mama ta amsa mata. “Zahra” Ta kira bayan Mama ta fada mata inda zan je, sai na juyo sai ban kalleta ba. “Zaki iya zuwa ke kadai ko na raka ki?” “Zan iya” Na amsa muryarta na isar da damuwata. “Lafiya kika yau?” Ban amsa mata ba na juya na fice, ko da na fito Direban mai manyan shekaru yana tsaye kofar gidan yana jirana, sai na gaishe shi ya amsa min sannan ya wuce gaba na bi bayansa, kamin na isa gurin motar har ya bude min gidan baya, shiga kawai na yi na zauna ya rufe motar sannan ya shiga mazaunin direba yaja motar. Ina ta kallon titi da daidaikun mutane har muka isa kofar gidan sai da yayi horn sannan aka bude masa gate din ya ja motar zuwa cikin gidan har gaban Entrance din gidan ya faka motar ina ganin haka na bude na fita ban jira an yi min iso ba na doshi kofar daman gidan ba bakona ba ne. Door bell na fara dannan sannan na murda kofar sai na same ta a bude da alama an shiryawa zuwan nawa domin ban san Momy da barin kofar falo a bude ba da safe. Sai da na jefa kafata ciki sannan na yi sallama muryata kasa kasa, Jummai da Ammy dake tsaye gurin dinning suna magana suka juyo suna kallona, Jummai ta amsa min a yayinda na ga sauyin fuska a gurin Ammy domin a take murmushin da take ya gushe, hakan kuma ba karamin faduwar gaba ya saka ni ba. “Bismillah Zauna....” Daga can inda take tsaye ta min nuna da kujera, sai na karasa gurin kujerar na zauna maida kaina kasa, sai ta karaso kusa ta zauna a kujerar dake facing din wanda nake zaune sai da ta gama kallona sannan ta juya ta yi magana da mai aikinta. “Jummai dan ba mu guri zamu yi magana” “Toh Hajiya” Ta amsa sannan ta nufo kofar fita falon ta bude ta fice ta rufo kofar. “Kin san dalilin da ya saka na ce a dauko min ke?” Na girgiza kai alamar aa ba tare da na kalleta ba. “Gargadi nake son na yi miki, ke kin sani ba kyau kika fi sauran matan duniya ba, balle ki ce idan Aliyu ya rasa ki ya rasa kyakkyawa mace har abada, ba asali kika fi su, ba ku da arzikin da ďana zai rika bibiyarki akansa, so ne kawai da Allah ya dauka ya saka masa a zuciyata, kuma mun yi miki duk wani hallacin tun kamin abubuwa su lalace, ko da ace da gaske Aliyu ya fasa aurenki ya kamata yanzu da ya dawo neman yafiyarki ki yafe masa, amman jindadi ya saka ki daga hannunki ki mari ďana saboda ya nuna yana sonki? Zahra ke fa bazawara ce a yanzu ďana kuma Saurayi ne, Ciwon So ba Ciwon Hauka ba ne, kuma mai son ka baya ganin ramarka da ace kina son Aliyu kamar yadda yake son ki da yanzu ke kike rokon ya dawo ku yi soyayya da juna ko da kuwa ya yaudare ki, son nan da kika masa zai rufe miki ido ki kasa ganin laifinsa, amman Alhamdulillah ina yi ma Allah godiya da ya saka Aliyu be aureki ba, domin lokuta da yawa mutum yana son abun da ba alheri ba ne a gurinsa, na tabbatar ke da Aliyu babu alheri a zamanku shiyasa har Allah ya kawo abubuwan da suka faru aka fasa auren” Na dago na kalleta ina jin wani ruwa mai kama da hawaye suna taruwa a fuskata. “Na kira ki a nan ne saboda na shaida miki cewar Mai Martaba yayi ma Aliyu mata yarinya mai hankali mai tarbiya kuma yar gidan manyan mutane, ke kin fi kowa sanin takun sakar da suke da Mai Martaba yanzu kuma Allah ya kawo daidaito a tsakaninsu, dan Allah dan darajar mahaifinki karki zama silar da zata rusa auren Aliyu da Yasmin domin suna son junansu, jarabawar son da Allah ya dorawa Aliyu kuma muna nan muna addu'a muna nan dake zai warke kamar be taba yi ba, ki kwantar da hankali daga yau inda Aliyu ďana ne ni na yi cikinsa na haife shi na shayar da shi na raine Shi har ya girma kuma zan fada masa magana ya ji, to ba zai sake bibiyarki ba balle har ki jidadin wulakanta shi, Zahra ko ke kadai kika rage mace a duniyar nan to mun yafe ki Aliyu zai mutu be yi aure ba” Gyaran zamanta ta yi sannan ta kalleni. “Saboda ke Aliyu ya dauki tsawon lokaci yana fada da yar'uwarsa, wata kila za a iya fada da yar'uwa a kwashe lafiya, amman ba za ayi da uwa a kwashe lafiya ba, haka ma ba za ayi da mahaifi a kwashe lafiya ba, saboda haka ina son ki tsaya da Aliyu irin tsayin da zai san da gaske kika, kuma ki yi masa kalamin da zai fahimci gaskiyarki, Zahra bana son wata alaka ta sake shiga tsakaninki da ďana, bana son na sake jin sunanki a bakin Aliyu! Sabanin haka zai janyo matsala ni a tsakanin Aliyu da mahaifinsa haka ma da sauran yan'uwansa da kuma ni da ma haife shi, mun riga mun san baki son Aliyu, to ina mai tabbatar miki Aliyu ba zai sake wahala akanki ba har abada...!” Da wani irin karfi na hade yawun bakina, hawaye kam ban san adadin wadanda suka min zuba ba, tun suna zuba da sanyi a ciki har suka koma zuba da zafi kamar za su kona min fatar fuska. “Zaki iya tafiya....” Ta nuna min kofa, sai na mike tsaye ina jin kamar na fadi nufi kofar ina takawa a hankali jiri na daukata, zuciyata ta cika fam kamar zata fashe kaina kuma ina jin kamar babu komai a cikinsa. Ban san na iso gate din ba har sai da na ji daya daga cikin masu gadin wanda ya sani yana salati sakamakon buguwa da kaina yayi da gate din. “Subhanallahi Zahra lafiya” Ya kalli saitin inda kofar take sai dai hawayen dake min zuba ba su bar ni na ga kofar da kyau ba, sai na kai hannu na lalaba na fita tafiya kadan na yi na samu guri na zauna ina jin kamar ban taba shiga tashin hankali irin wannan ba, miyasa abubuwan nan za su zo min a lokaci daya? Na runtse ido da mugun karfi sannan na saka hannu na share hawayena na bude idon na mike tsaye na fara tafiya, sai da na yi nisa na isa titin sannan na samu Napep na hau sai da ya fara tafiya sannan ya tambaye inda zai kai ni, sai na fada masa unguwa uku gurin Hajiya. Ban sauka ba sai da isa har kofar gidan. “Malam bari na shiga na fito ka kai ni gida” Na fada masa saboda babu kudi a hannuna, sai ya kashe sautin wakar dake tashi ya kashe napep din ni kuma na shiga cikin gidan dake bude. Bahijja na fara cin karo da ita tana bakin kofar dakinsu tana goge wandonta na makaranta da dutsen goge tufafi na gawayi. “Sallama Alaikum” Na yi sallama bayan na kusa isa kofar dakin. “Wa'alaikissalam” Ta amsa da mamaki na san ba zai wuce na ganina da ta yi ba kamar daga sama bayan kuma ta san ina jego ban isa fara fita ba, yanayi na kuma be nuna zuwan nawa na lafiya ba ne. “Ina Hajiya?” “Tana daki Lafiya?” Ban sake ce mata komai ba na nufi dakin na shiga sai na kusa cin karo da Hajiya da ke kokarin fitowa. “Zahra Lafiya?” “Ba lafiya ba Hajiya, zuwa na yi na tambaye ki kuma ina son ki fada min tsakani da Allah, idan kin boye min ba zaki boyewa Allah, kuma duk ranar da na gane gaskiyar ba zan taba jindadin boyen min da kika yi ba” “Miya faru Zahra?” Kamin na ce komai Mai Napep din dake waje yayi horn. “Bahijja je ki sallame shi” Kamar umarni take jira sai ta tashi da sauri ta shiga daki ta dauko kudi ta fita waje, Hajiya kuma ta kama ni ta karasa shiga da ni dakin ta zaunar. “Tambaye ni abun da kike so Zahra na miki alkawari matukar na san gaskiya zan fada miki” Na kalleta idanuwa na cika da wasu hawaye daman can ba su cire jan da suka yi na kukan da na yi. “Hajiya da gaske Deen yayi garkuwa da Mijin Yayar Abiey saboda a fasa aurena da Abiey? Da gaske Deen shi ya shiga tsakanin Soyayya ta da Abiey?” Wani dauke numfashi ta yi ta sauke ajiyar zuciya sai ta amsa min kai tsaye amsa da mamakinta ya kusa saka ni suma. “Gaskiya margayi ya shirya komai saboda ya bata alakarku da Abiey kuma saboda a fasa aurenku” Baki sake nake kallonta sai ta fara hawaye. “Amman be fada min yayi garkuwa da mijin Dr Zainab ba sai bayan da aikata, ki yi hakuri Zahra ki yafe masa ya aika abun da ya aikata ne saboda yana sonki...” Na girgiza mata kai hawaye na sauko min. “Wannan ba so ba ne, son kai ne... Idan har da gaske yana so ne, to zai so abun da nake so ne, ba ya jefani a halin da na shiga ba, Hajiya kuma kin san da wannan kika bar ni na tsani Abiey? Bayan shi yake da gaskiya? Wace irin uwa ce ke?” “Wata uwa ce Zahra mai son abun da ďanta yake so, Zaharadeen be san komai ba a rayuwarsa sai shaye shaye, amman sanadin ki ya rage har ta kai ga ya daina gaba daya, shin miya ba zan so haka ba?” Ta tashi daga inda take zaune ta nufi karkashin gadonta ta janyo wani akwaitin karfe ta bude ta dauko wani kwali ta miko min. Kamar ba zan karba ba sai kuma na saka hannu ya karba na bude farar takardar na fara yin arba da ita sai na saka hannu na dauka na bude takardar. _Zuwa ga wanda zata karanta wasikar nan zuciyata tana mai sosuwa da abun da na aikata, amincin Allah ya tabbata a gareki Zahra na sani a lokacin da zaki karanta wasikar nan bana raye domin rayuwata gajera ce shiyasa na zabi rayuwa da ke kamin mutuwa ta dauke ni. Na aikata abun da na aikata ne Zahra saboda ina kaunarki tun daga lokacin da na fara saka ki a idona zuciyata ta kamu da son ki, sai dai ba ni da halin nuna miki saboda hankalinki ba a gurina yake ba, kuma na san idan na nemi aurenki ba za a ba ni ba saboda ba ni da aiki bana sana'ar komai, gashi rayuwata ta lalace tun ina da kananan shekaru na girma da shaye shaye sanadiyar aike da ake ina soyawa, a lokacin da na ankara na gane illar abun da lokaci ya riga da kure min domin kuwa har shaye shayen ya yi min illa, sai dai son ki ya saka na fara boyewa Zahra, na fara kokarin sauyawa saboda na same ki, kamin zuciyata ta daya min cewar ba zan tana samun aurenki ba, saboda hankalinki gaba daya yana gurin Abiey ko bayan Abiey kina da wasu samarin da suke sonki wandanda suka fi ni komai, da za su siye soyayyarki a gurinki ko a gurin iyayenki, a ranar da aka yi miki baiko da Abiey Zahra ban dauka zan kai safe ba saboda bakinciki da ciwon zuciya, amman kowa be fahimci haka ba, daga lokacin ne na daura damarar ko ta halin yaya sai na aureki domin likitan da nake zuwa gurinsa yana duba ni ya tabbatar min da cewar na kamu da ciwon hanta mai hatsari, kuma idan har ban dauki mataki ba zan iya rasa rayuwa, a lokacin ba ni da wani buri da ya wuce na ga na mallakeki Zahra hakan yasa na boyewa kowa maganar kuma na aikata abunda na aikata saboda na san rayuwata ba mai tsawo ba ce, soyayyar da nake miki ta saka bana iya dauke hannuna daga jikinki balle har na nisance ki. Abiey yana da komai Zahra ni kowa ba ni da komai a zuciyata sai kaunarki kuma na shirya mutuwa a lokacin saboda ke, da gaske da ace Dr Zainab bata aikata abun da na umace da shi ba, babu abun da zai hana na kashe mijinta a lokacin, domin ina jin idan har ban same ki ba rayuwata bata da amfani, ina kaunarki Zahra fiye da yadda Abiey yake Sonki sai dai bana da wasu hujjoji da zan gamsar da ke akansu saboda na boye soyayyarki ne a cikin raina, kuma ba ni da wasu qualities da zai saka ke ko danginki su kauna ce ni, saboda na lalata rayuwata da shaye-shaye, amman Abiey mahaifinsa Sarki ne, mahaifiyarsa kuma mai kudi ce, shi ma sanannen mutum ne yana da kudi kuma baya shaye shaye ba kamar ni ba, ba zan iya kara da shi ba, gashi yayi min shigar kutso ya riga ni furtawa, na sani idan na furta cewar ina son ki a lokacin ba za a saurare ni ba, kuma ba za a bani ke ba, wata kila ma ace hassada na ke miki, ke ma kuma ba zaki kalle ni ba._ _Na sani abun da zamu haifa mace ko namiji biyu uku ko daya ba za su alfahari da ni ba, amman ni ina alfahari da ke da duk abun da za ki haifa min, kuma ina sonki kar tsanata ta saka ki kyamace yayana, kar tsanata yasa ki kyamaci mahaifiyata domin zaki karanta sakon nan ne bayan bana raye Zahra mahaifiyata kuma bata da kowa a lokacin sai Bahijja sai ke da abun da muka haifa, ki yafe min Zahra ki yafe min ki yafe min Ciwon so ne ya saka ni aikata haka, dan Allah kar abun da na aikata ya saka ki ji kin tsane ni ne, kuma har hakan ya saka ki manta da ni daga masoyinki mai kaunarki har abada.... DEEN_ Shakaf takardar ta jika da hawayena ina dagowa Hajiya ta miko min hotunana da suka dade da bata. “Ga hotunanki, ajiya ta kare mai su ya tafi Zahra....” Hajiya ta fada tana kuka, jimke hotunan na yi na lumshe ido, sai na ji Bahijja ta fashe da kuka. [10/25, 12:25 PM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣1️⃣ ABIEY POV. After like awa daya da fitar Zahra Abiey ya sauko falon yana sanye da kananan kaya, kai tsaye dinning ya nufa inda mahaifiyarsa take zaune tana shan tea ya ja kujera ya zauna kusa da ita. “Good Morning Ammy” “An tashi lafiya” “Alhamdulillah” Ya amsa yana sauke ajiyar zuciya sannan ya dauki karamin tea cup ya aje gabansa. “Bari na boiling ruwan tea” “Jummai ba ta dade da zuba su a flask ba, na ce kar ta zuba da wuri saboda baka son ya dade a aje” Kallonta yayi fuskarsa da murmushi ya mike tsaye. “Ammy bari dai na tafasa shi da kaina” Tabe baki ta yi ta girgiza kai tana kurba tea din. “Aliyu” Ya juyo “Na'am” “Idan ka dora ruwan ka zo ina son magana da kai” “Okay” Ya amsa sannan ya shiga kitchen ya dauki kettle din dake wanke aje ya sake wankewa sannan ya kunna tap ya zuba ruwan ya gona, kana ya juyo ya fito daga kitchen, a inda ya zauna dazun ya sake zama ya bude coolar dake gabansa ya dauki plantain ya kai bakinsa. “Jiya ka dawo late kuma baka kwanta da wuri ba, domin ka kai har 1am a balcony, kuma na san dakin ka ma baka samu bachi da wuri ba, shiyasa ka fara late” Ya dan yi jimmm sai kuma ya daga mata kai yana tauna plantain din a hankali. “Why?” “Jiya dai na je na yi magana da Yasmin, after that Sauban ya fada min Matarsa tace ta ga Zahra a wani gidan an gabatar da ita a matsayin yar aiki, to i went to that house na yi magana da ita na dauke ta na kaita gida, bayan na dawo kuma sai tunani ya hana ni kwantawa da wuri” Ammy ta aje kofin tea dake hannunta tana kallonshi da irin duba na fahimta. “Aliyu, ko ka lura yanzu zamani ya canja da za'ayi irin soyayyar da kake yi ma Zahra?” “Ban fahimta ba” “Shin baka taba tambayar kanka miyasa kai kadai kake son Zahra ita bata son ka ba?” “No Ammy Zahra tana so na mana... ” Ya amsa mata yana murmushi mamakin jin abun da ke fita bakinta. “Me Zahra ta yi wanda zai tabbatar maka da haka? Da ace Zahra tana son ka kamar yadda kai kake son ta na tabbatar da yanzu ta bar komai ya wuce, shin fada idan kai ne zaka iya daukar fushi da Zahra na tsawon lokaci ko da ace ita take da laifi?” “Ammy hankalin mace ba daya ne da na namiji ba” “Haka ne, shiyasa ta zo har nan ta yi min warning cewar bata son ďana ya sake shiga lamarinta bayan ta mareka a gidansu ta ci mutuncinka, kuma ta tabbatar min da cewar ita tana da wanda take so” Ya gyara zamansa da sauri. “Zahra ta zo nan Ammy?” “Eh ba ta wuce awa daya da fita ba” “Kuma da gaske ta fadi abun da kika fada min yanzu?” “Zan fara yi maka karya ne akan Zahra?” A sauke kanshi kasa zuciyarshi na wani irin halbawa da mugun karfi. “Aliyu ba zan cilasta rabuwa da Zahra ba, amman zan baka shawara a matsayina na mahaifiyarka idan zaka ji ka cire yarinyar nan a ranka ,wata kila ba alheri ba ce a gurinka shiyasa Allah be baka ita ba, kuma iya kar soyayya ka nuna mata Allah ma ya sani” “Deen ya ci nasara...!” Ya furta yana runtse ido tare da murmushin takaici. “Wani lokacin kuma har da son zuciya, da ace Zahra na maka Kwatankwacin son da kake mata da yanzu ta yafe maka ko da kuwa ace ka aikata mata hakan da gaske, dan haka nake son ka bawa zuciyarka hutu ka saurara mata da zancen Zahra har na wani lokaci, shawara ta biyu kuma karka lalata zancen baikonku da Yasmin saboda Mai Martaba, kuma na tabbatar yarinyar nan tana sonka idan kuwa haka ne ya kamata ka duba mata domin ka fi kowa sanin yadda Ciwon So yake, wata kila ma sanadin haka Allah ya dube ka ya baka Zahra, Kuma Yasmin tana da tarbiya tana da hankali amman ita kuma kyakkyawa ce kamar Zahra” Ya kalli Ammy da sauri. “Ammy bana son Yasmin ban taba jin ina Son Yasmin so na aure ba ko soyayya, kawai dai ina mata kallon yar'uwa ne duk kuwa da kasancewar ban hada komai da ita ba, kuma tsakani da Allah zuciyata babu wanda take so sai Zahra, and Ammy kin sani mata basa son Kishiya ni ma kuma kaina ban shirya aje mata biyu ba...” Yana kai aya Ammy ya mike tsaye a fusace ta daki dinning din. “Toh sai ka je ka ji cigaba da son Zahra har sai son nata ya kashe ka sai a nada kambu a baka, amman bari ka ji na fada maka karka sake min maganar yarinyar a cikin gidana, kuma ina mai tabbatar maka matukar baka auri Yasmin ba, ba zan taba goya maka baya ka auri Zahra ba, ko da ta dawo maka, yarinyar nan bazawara ce ba budurwa ba kai kansa kasan abun magana zaka ja a gurin familyn mahaifinka amman a haka na goya maka baya saboda ina tunanin yarinya ce mai hankali, amman yanzu na gane kalarta kuma saboda ita ba zan yarda ka lalata auren da Mai Martaba ya nema maka ba” Kamar ta jefar da kujerar bayanta haka ta ja baya da karfi ta fice daga dinning, Abiey ya bita da kallo yana mamakin yadda ta dauki zafi sosai akan Zahra. Mikewa yayi tsaye ya nufi upstairs dakinshi ya shiga ya dauko keys dinsa da wayarsa ya fito, sai da ya fice daga falon sannan ya kira Sauban ya labarta masa abun da ya faru tsakaninsa da Ammy. “Abiey ni ma da zaka dauki shawarata da ka hakura da yarinyar nan ko da na dan lokaci ne, domin abun da ta yi bata kyauta ba yanzu kuma ace duk bayan cin mutuncin da ta yi maka a can gidansu kuma ta biyo Ammy har gida ta fada mata haka? Tsakani da Allah ko wace uwa ce dole ranta ya bace, and yes ni da Ammy duk ba zamu fada maka abun da zai cutar da kai ba so nima shawarar da zan baka ka auri Yasmin idan ya so Zahra sai ta zo a ta biyu” “Ko na auri Yasmin ba zata jidadin zama da ni ba, saboda zuciyata kwata kwata bata gurinta” “Koya zaka yi har ka saba, Abiey ya kamata ka tausayawa yarinyar nan, kai ka jefata a cikin wannan halin idan baka aureta baka mata adalci ba, yanzu kuma ni na zan baka shawarar ka ce ma Mai Martaba cewar baka son yarinyar nan ba” Ya shafa kansa ya jingina jikin motarshi yana sauke ajiyar zuciya. “Me zan yi Sauban? Na yi shiru kawai na saka ido ina kallon yadda abubuwa suke wucewa?” “Abiey ba ko yaushe ake kwana akan gado ba, be zama lallai abun da kake so ka samu ba, baka san tsarin da Allah yake maka ba” “Duk da haka dai i need to talk to Zahra maybe zata ba ni dama ta saurareni” “Allah yasa ta saurareka din” “Ameen” Ya amsa sannan ya sauke wayar ya bude motar ya shiga, be tsaya ko'ina ba sai da ya isa unguwar su Zahra, da fari nisa da gidan ya faka kamin ya karaso gaban gidan daidai inda ake gina masa nasa gidan ya faka motarsa yana kallon kofar gidansu, tunanin yake yadda zai fuskanci Zahra, ajiyar zuciya ya sauke ya kwantar da kujera ya jingina. Daga kwance da yake ya hangota ta sauka Napep ta shiga cikin gidan sai kuma ta fito ta sallami Mai Napep din ta koma ciki, ajiyar zuciya ya sake saukewa a karo na barkatai. ZAHRA POV. Jin hawayen ba za su kare min ba yasa na bude ido na aje hotunan da suke hannuna na mike tsaye. “Zahra tafiya zaki yi?” Hajiya ta tambaya sai na daga mata kai har lokacin hawaye nake. “Ba zaki ce komai ba?” “Da ace Deen yana raye da na yi magana da yawa har sai kalamaina sun kare, amman a yanzu babu abun da zan fada domin ba shi da muhimmanci, sai dai ki sani ke da Deen kun cutar da ni cutarwa mai girma, kin san abun da ďanki ya aikata amman kika rufe baki fada min ba” “Wace uwar ce zata so ďan wani fiye da nata? Zahra duk abun da Margayi ya aikata ya aikata ne saboda yana sonki kuma yana ganin ba shi da wata hanya da zai mallakeki sai wannan” “Wannan ba so ba ne, miyasa be fada min ba? Ko da zan ki shi ya kamata ya furta min, ba ya lalata soyayyar wani ba, kuma da kazafi mafi muni ya kuma saka na tsani wanda shi yake da Gaskiya” Na furta ina jin kamar na dora hannu a kai na yi ihu. Bahijja dake kuka ta taso ta rike hannayena. “Dan Allah karki furta wata mummunar kalma akan yayana, da kin san yadda yake son ki da baki ji haushin abun da ya aikata ba” “Gaskiya ne, saboda baki taba soyayya ba, baki san zafin da ake ji idan aka rabu da masoyi na gaskiya ba” Na fisge hannayena na fice daga gidan ina jin wani irin kuka da bacin rai, lokaci zuwa lokaci nake yarfar da hannun da na saka na mari Abiey da shi. “Ka yafe min Abiey ka yafe min dan Allah” Na furta ina jin kamar ace yana tsaye a gabana na durkusa har kasa na nemu yafiyarsa, sai kuma maganar Ammy ta dawo min a zuciya gargadin da ta yi min da kuma irin fusatar da ta yi, yanzu na fahimta tana da gaskiya abun da na yi ban kyauta ba sai dai na aikata hakan ne a cikin rashin sani, na bata hakuri? No ba lallai ne ta fahimta ba wata kila idan na nunawa Abiey na fahimci gaskiya zai iya fasa auren Yasmin matar da Mai Martaba ya zaba masa hakan kuma zai haifar da matsala a tsakaninsu, bayan kuma na san da akwai rashin jituwa a tsakaninsa da Mai Martaba. Har na iso gida tunani nake kala kala wata zuciyar na ce min na nemi yafiyar Abiey a yayinda yar'uwarta take kokarin hana ni. Sai da na shiga gida na karbi kudi gurin Mama sannan na bawa mai napep din na koma jiki babu karfi idon kam idan akwai abun da ya fi kumbura yayi ga wani ja da yayi min kana ganina kasan na yi kuka. Dakin Mama na shiga na zauna akan ledar tsakar dakin na sauke kaina kasa for the first time na ke jin wani irin kunyar Yaya Maryam da kuma jin rashin kyautawar abun da na yi, hannuna na hadu na saka ina matsa na daman. “Me ya faru?” Mama ta tambaya sai na dago na kalleta wasu hawayen na taruwa a idona. “Ammy ta min gargadi akan Abiey, tace Mai Martaba ya masa mata bata son na zama silar rusa auren kuma ta ce idan har zata masa magana ya ji ba zai sake zuwa gurina ba” Ina rufe baki Mama ta taba hannayenta. “Haka na ke so, ta kyauta yanzu kan ba kare bin dabo, kin ga kin hita wulakanta mutumen da ya fiki komai kuma ya dawo yana bibiyarki saboda Deen” Na runtse ido sosai ina jin kamar kuka zai kubuce min. “Mama na yi magana da Hajiya kuma ta tabbatar min da abun da Abiey ya fada min da gaske ne Deen ya shirya komai saboda ya bata alakata da Abiey” Yaya Maryam ta kai hannu ta dafa ni. “Mahaifiyarsa ta sani kenan?” Na daga mata kai sai na rika hannun nata da ta dafa ni da shi. “Ki yafe min na aikata furta miki kalmomin da ba su dace na yi ba saboda ina cikin fushi kuma ban fahimci komai ba” Na fada ciki kuka na tausayawa kaina da kaina. “Tun tuni ina ta nuna miki baki fahimta ba, tun da daga lokacin da likitoci suka ce ya kebe kansa ya boye miki ya kamata ki fahimci cewar ba son gaskiya yake miki ba” “Ban gane ba, saboda ina masa kallom jarumin da ya ceci rayuwata a lokacin da Abiey ya yaudare ni, yanzu ban san abun da zan yi ba Tsanar Deen ko kuma kaunarsa? Na nemi yafiyar Abiey? Ko kuma na nuna masa cewar na fahimci ba shi da laifi? Kaina a kulle yake” Na furta ina fashewa da kuka. “Karki tsani Deen Zahra, shi a yanzu baya raye kuma akwai ďa a tsakaninku, kuma bayan Deen ya aureki be cutar da ke ba, be taba dukanki ba, be tana hanaki abinci ba, be taba son bata ranki ba, ba zai aikata miki wani abu da gangan saboda ki shiga damuwa ba, wani lokacin zuciya tana kai bawa ga halaka domin tana raya masa abubuwan da aikata su haramun ne ko kuma saka kai a damuwa ko kunci, saboda kar hankalinki ya tashi ya saka ya boye miki ciwonsa, mahaifiyarsa ma bata taba nuna miki kiyayya ba sai kauna, Deen yana sonki so mai tsanani wanda ya haddasa kishi mai zafi a zuciyarsa da har yake ganin idan kika dauki cutar zaki mutu da wuri ba tare da kin rayu da wani namiji ba, sannan mutum ne mai tsananin son kanshi shiyasa ya aikata abun da ya aikata saboda ya same ki, tabbas da ya nemi aurenki a halin da yake ciki ba zan taba bashi ba, ko da kuwa kin nuna kina sonsa amman ya canja saboda ke Zahra, idan har ba zaki iya yafe masa ba be cancanci tsana daga gurinki” Na daga kai na kalli Mama da ta jero min kanli da bad'adin da ya kamata ya hana zuciyata tsanar Deen. Shiru ne ya ciki ďakin baka jin tashin komai sai sautin kukana. “Allah ya kyauta” Mama ta fada sannan ta tashi ta fice daga dakin, sai na saka hannayena na dafe kaina ina jin yadda yake sara min kamar zai cire.  “Ki yi hakuri Zahra, ta kuka kuma yanzu ai ta kare tun da Deen baya raye, godiya ya kamata ki yi ma Allah da ya saka Abiey be daina kaunarki ba har yanzu” Kallonta na yi zuciyata nayi mini wani irin zafi. “Yaya Maryam kin san zafin da mace take ji idan mijin da bata so ya kusance ta? Kin san yadda na sha wahala kamin na koyawa kaina iya zama da Deen? Ba karamin yaki na yi ba na yi ba da zuciyata kamin ta aminta da Deen a matsayin mijina, a duk tsawon zaman da muka yi ban taba jin son Abiey ya fita a rayuwata ba sai dai na ji na tsane shi saboda abun da ya aikata ba, a duk tsawon lokacin nan ina kallon Deen ne a matsayin mai gaskiya Abiey kuma mayaudari, ban taba jin ina kaunar Deen ba ko da na rana daya amman a haka na koyawa kaina sonsa har nake jin na fi ko wace mace dace da miji, miyasa ba zai gina tashi soyayyar a muhallinsa na dabam ba? Miya zai saka na tsani mutum da zuciyata bata san kaunar kowa ba sai shi? Akan me zai bar ni ina kallon wani a matsayin mayaudari? Wane irin kalami ne ban yi ma Abiey? Wane irin cin mutunci ne ban yi ma yan'uwansa ba? A kowace sallah sai na roki Allah ya saka min akan abun da Abiey yayi min duk saboda abun da Deen ya shirya Yaya Maryam, rayuwar da nake mafarkin ginawa da Abiey ta rushe saboda Deen...!” Yaya Maryam ta sauko ta zauna kusa da ni ta rumgume ni sai na kwanta a kafadarta ina kukan da nake jin kamar na mayar da zuciyata na huta. Muna haka yaro ya shigo da sallama Mama dake waje ta amsa. “Wai ance ana sallama da Zahra a waje” Da sauri na dago daga jikin Yaya Maryam da nake kwance ina kallon kofar waje kasancewar labulen kofar ďakin a dage yake, zuciyata bata raya min kowa ba sai Abiey. “Je ka ce waye” Na fito na kalli Mama da sauri. “Wata kila Abiey ne” “Bari dai ya dawo mu ji” Na share hawayena da sauri ina jin kamar kukana ya kare. “Wai yace wani ne” Yaron ya fada bayan ya dawo, sai na kalli Yaya Maryam wanda ta fito wajen na kuma sake kallon Mama na ce. “Wata kila yana tsoron yace shi din ne na ki Fitowa, bari na je na duba Mama” Ina cira kafa sai Yaya Maryam ta rike ni. “Zahra be kamata kina fita any how ba, haihuwa fa kika yi, mutane ma ai sai su yi ta magana” “Magana kawai zan yi da shi dan Allah ku bari na fita” “Sake ta, ai yamma bata yi ba babu mutane safiya ce” Tana saka ki na juya da sauri kamar baiwar da ta samu yancin, ina zura talkami na fice da saurina zuciyata na wani irin bugawa da karfi. Tsaye na yi cirus ina kallon Dr Hamid dake sanye da farar shadda tsaye daf da kofar gidanmu, a take na kunshe zumudi da nake na sauke kaina kasa daga barin kallonsa da nake na kusan dakiku goma na lumshe ido. “Ba gaisuwa ba sallama kar dai fushin Jamila ya shafe ni” Ya fada yana dan murmushi sai a lokaci na tuna da yadda muka rabu gaba daya na manta da lamarinta sai a yanzu, a sanyaye na gaishe shi ina bude idon. “Barka da safiya” “An tashi lafiya?” “Alhamdulillah” Ya leki fuskata “Miya samu idon nan na ki?” “Ciwo suke min” “Kuka kika yi? You don't need to hide na san abun da Jamila ta yi bata kyauta ba, kuma na yi magana da ita on behalf of her ina mai baki hakuri ina neman yafiyarki” “Babu komai dama ta samu ita ma ban ga laifinta ba, kasan hausawa sun ce idan ka samu rana ka shanya garinka” “No bata kyauta ba tsakani da Allah, kuma ba a haka shiyasa ban kira ki na zo kai tsaye na san idan na kira ba lallai ki dauka ba, idan ma kin dauka be zama lallai ki fito ba” “Komai ya wuce Dr Hamid ba zata sake ganina ba, ni ma kuma bana fatar na sake sakata a idona, it over” Na furta cikin wani yanayi da nake jin kamar zuciyata ba zata iya yafe ďana ba. “Ba fahimta ba...” “Ba zan sake shayar da shi ba, ku nemi wani nonon ku bashi” “Fushin ne haka?” “Zahraty ban san mai halinki da daukar zafi ba” “Da gaske na ke yi, i need to move on, akwai abubuwa sa yawa da ya kamata na canja a rayuwata, na yi sadaukarwa a muhallin da be dace na yi ba, ďana be yi min komai ba, amman uba ďana....” Jikina ya fara rawa kamar ba zan iya tsayuwa ba ina kokarin dukawa a kasa sai Dr Hamid ya dafa kafaduna ya rike ni. “Are you okay.?” Na daga mashi kai ina kokarin daidaita natsuwata na hana kaina kukan da yake son kubuce min. Kamar ance dago kai ki gani ina kallon gurin motar da ban lura da ita ba sai yanzu kuma a zatona Dr Hamid ne ya zo da ita, kwasam na yi arba da Abiey a tsaye jikin motar yana kallonmu fuska ba yabo ba fallasa. Wani irin numfashi na ja na aje da karfi har sai da Dr Hamid ya juya ya kalli inda nake kallo, sannan ya juyo ya kalleni sai ya saki kafadata. “Mutumen da ya hana ki shiga motana ne ko?” Sarai na ji tambayar da yayi min sai dai hankalina baya gurinsa gaba daya imanina ya tafi gurin Abiey da shi ma kallona yake yi. Ya sake juyawa ya kalleshi sannan ya kalleni. “Miye alakarki da mutunnan ne ni kam?” Sai a lokacin na kalleshi. “Labari ne mai tsawo da ba zai fadu a lokaci daya ba” “Allah yasa be san abun da yake tsakaninmu ba, domin na yi mamakin ganinsa a gidan “Be sanin abun da ke tsakaninmu ba yayi abun da yayi jiya ne saboda yana tunanin akwai soyayyar a tsakaninmu” “I'm glad, bana son kowa ya san da maganar nan Zahra dan Allah ki rike mana amana, ki bari yayi ta tunanin soyayyar ce kawai kamin Allah ya yayi mana mafita” Ya fada sannan ya kama hannuna na dama ya kai bakinsa ya sumbanta. “Bari na barku wata kila akwai abun da zaku tattauna, zan kira ki” Kasa ce masa komai na yi na bishi da wani irin kallo na mamaki da ya kamani. Be juyo ya kalleni ba sai da ya isa gurin motarshi da sai a lokacin na lura da ita, murmushi kawai yayi sakar min ya bude motar ya shiga sai ya bar gurin sannan na juyo da kallo gurin Abiey. Ga mamakina sai ya tako ya karaso inda nake tsaye bakin kofar gidanmu yana wani irin kamshi mai tayar da hankali da saka faduwar gaba. “Hi” Wani irin kallo nake masa kamar a yau na fara ganinsa, wani irin kallo ne da yake kara fito min da tsantsan kyansa da martabarsa a yau. Sai yayi murmushi ya saka hannayensa aljihu. “Yaushe kika lalace har kika bar maza na taba ki any how?” Na yi murmushi ina tuna lokacin da yake kai hannu zai taba ni sai na ce masa ni ba yar iska ba ce. “Zahra you don't need to hurt yourself just to make me feel like an idiot, baki bukatar ki ari dabi'un da ba naki ba saboda kawai ki ba ni haushi” Ya sauke numfashi sai na sake kallonshi hawaye na sauko min. “Abiey...” Be bari na fadi abun da zan fada ba ya tari numfashina. “I know ina takura miki, i just come to talk you, Ammy ta fada min kin je har gida kin fada nata cewar akwai wanda kike so shi ne wannan?” Sai na samu kaina da kasa furta komai, na karyata mahaifiyarsa ne? Na fada masa gaskiya cewar ita ta kira ni da kanta? Ko kuma na yi shiru. “Wannan din ma ba son shi kike ba, kamar yadda kika kara tabbatar min da cewar ba son Deen kike ba, da kina son shi tsakani da Allah da baki isa kula wani ba bayan mutuwarsa da dan lokaci kadan, wannan din ma na san kina kula shi ne saboda na yarda da cewar kina son shi na kyale ki” Ya jingina da ginin gidanmu sannan ya cigaba. “Zahra Wallahi zan jurewa zuciyata matukar daina zuwa gurinki zai kawo miki farinciki, kuma idan har ta tabbata wannan mutumen kike so zan kyale shi da shi muddin zaki samu farinciki a zamanki da shi, amman hakan ba yana nufin na daina son ki ba har abada ba zan taba iya daina son ki ba, ko da ba zaki aure ni ba, ina fatar ki fahimci cewar ni Aliyu ban ci amanarki ba, ban san yadda zan miki ki fahimta ba amman tabbas ban ci amanarki ba Zahra kuma ban yaudare ki ba” Na sauke kaina kasa ina murmushi hawaye na ta tsiyaya. “Secondly kar haushi da kike je ya saka ki rika neman cin mutuncin iyayena ko cin fuskarsu, ba sai kin je kin samu Ammy da magana marar dadi ba akaina, kina shuka kiyayya ne a zuciyarsu, duk abun da zaki yi ki yi min ni kadai” Zubewa na yi kasan guiwoyina na saka hannu biyu na dafa kafarsa na runtse ido. “Abiey......” Sai kuma na kasa furta komai sai kuka nake, matsawa yayi baya baya yana kallona, na mike tsaye na matsa kusa da shi na kama hannunsa na mari fuskata da shi zan sake marin a karo na biyu sai ya fisge hannun. “Subhanallahi” Ban tsaya komai ba na saka nawa hannun na mari kaina kamin na yi na biyu ya rike hannuna. “Miye haka Zahra” “Wallahi da zan iya Abiey da na cire hannunan na jefar domin da shi na aikata abun da a yanzu yake damuna, baka cancanci komai gurina ba sai girmamawa da mutuntawa” Ya sake hannuna yana kallona, sai na sake durkusawa kasa na hade hannayena. “I'm sorry” Ya girgiza min kai ya matsa baya. “Abiey i love you more than i did before, no one can take your place Abiey no one, babu abun da ya canja daga kaunar da nake maka babu daren da zuciyata baka begenka amman gadar da Deen ya gina mana ya saka na ke maka kallon mayaudari, you're here in my heart...” Na taba saitin zuciyata, sai ya daga kansa sama da sauri ya dantse baki ya rufe ido kana ya jumke hannunsa, sai kuma ya bude idon ya kalleni hawaye dake makkale suka zubo masa ya juya ba tare da yace min komai ba ya nufi motarsa ya bude ya shiga ya bar ni gurin ina kuka. [10/29, 10:48 AM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣2️⃣ Ammy ta sauko a hankali tana kallon Abiey da ya hade kai da guiwa, da fargaba ta karaso inda yake zaune ta dafa shi. “Aliyu...” Dagowa yayi ya kalleta sai kuma ya mike tsaye da sauri ya rumgumeta, daman yana bukatar ya rumgume wani saboda farincikin da yake a ciki. “Alhamdulillah Ammy tafiya mai nisa ta yanka min a yau” Ammy ta dan yi dariya sannan ta kai hannunta ta shafa bayanshi. “Alhamdulillah” Ta furta duk da kasancewar bata san dalilin farinciki nasa ba, kuma ta yi ta ayyanawa a zuciyarta bata canka ba. Sakinta yayi ya kama hannayenta ya rike. “Rabon da na ga ďana a cikin irin wannan farinciki har na manta” Ya daga kansa sama wani wata kalar dariya kamar ba shi ba. “Guess what Ammy” Ammy ta yi shiru alamar tunani sannan ta girgiza masa kai. “Ba ni da wannan basirar fada min kawai” Zaunar da ita yayi sannan ya zauna gefenta. “Ammy yau Zahra ta durkusa gabana tana neman yafiyata, ita da kanta take fada min cewar tana kauna a yanzu fiye da yadda take kauna ta a ada?” “What do you mean?” “Ammy ta gane gaskiya” “Just like that” “I don't know how amman tabbas ta gane gaskiya, ban san ma me zan ce mata ba kawai na baro ta a can na dawo gida, ina ganin kamar mafarki na ke yi” Ammy ta rika kallonshi with confused gabanta na faduwa. “Ammy are you not happy?” Ta yi saurin yin dariyar da bata kai zuci ba ta. “Of cause I'm happy Aliyu ka samu abun da kake so me zai saka ba zan yi farincikin ba, amman ka lallabata ne ko kuma me? A ina ka hadu da ita?” “Gidansu na je” Ya furta yana ciro wayarsa dake ringing a aljihu ya mike tsaye yana amsa kiran Sauban ya nufi kofar fita. Ammy ta bishi da kallo har sai da ya fice sannan ta juyo da kanta tana mamakin yadda zai fada mata cewar Zahra ta yafe masa? Saboda maganar da tayi mata ne ko kuma wani abu take shirya masa? Ammy ta mike tsaye ta nufi upstairs tana tafe tana tunani har ta shiga dakinta ta nufi gefen gadonta ta dauki wayarta. Number Dr Zainab ta fara dialing ta dora kafa daya kan daya. “Daman na ce sai Ammy ta yi missing dina” Shi ne abun da Dr Zainab ta fada a lokacin da ta amsa kiran “Amman ko a waya ai ya kamata ki kira ko?” “Ammy kiran waya ma sai kana da time fa, kwana biyun nan aiki yake min yawa, gashi yara sun koma school shiyasa bana samun zuwa” “Zaki samu shigowa yau?” “Miya faru? Na ji muryarki wani iri” Ammy ta sauke ajiyar zuciya. “Aliyu ne ya zo min da wata magana mai nauyi kuma mai wuyar fassarawa” “Kamar wace irin magana?” Ammy ta nisa sannan ta bata labarin da Abiey ya bata, sannan ga dora mata na abun da ya wakana tsakaninsu da Zahra. “Ammy ina ganin maganar da kika mata ne ya saka ta natsu, kin san mace tana da wani abu daya, tana aikata abun da take so idan aka lallabata sai dai daga lokacin da ka fara yi mata wuta to zata yarda a zauna lafiya” “Hakan na nufin Zahra ta san Aliyu bw yaudareta ba kenan? Amman ta kyale shi yana ta bibiyarta? Har ta ci mutuncinsa a gaban yan'uwansa?” “To wata kila kuma ta gane gaskiyar ne” “Ko kuma tana son ta yi amfani da damarta ta cutar da shi ba” “Kamar ya?” “Zata iya nuna masa cewar ta gane gaskiya saboda ta raba shi da Yasmin kuma ta hada shi da Mai Martaba, daga karshe tace ba zata aure shi” “Bana tunanin haka, yanzu dai abu mai muhimmanci musan ta ya aka yi ta fahimci gaskiya?” “A kaddara ta gane gaskiya ne, gane gaskiyarta zai haifar da matsala, domin abu ne mai wahala Aliyu ya auri Yasmin, sannan Yasmin ko iyayen ta ba za su yarda wani matsala ya fito daga bangarensu ba, na kuma san waye Mai Martaba ba zai taba yarda a rushe maganar auren ba, kin ga hakan zai iya haifar da matsala a tsakaninsu” “Ba zai ji dadi ba, amman zai fahimta mace ma yanzu ba a mata auren dole balle kuma Namiji” “Ba lallai ne ya fahimta ba, Dr ina jin tsoro kar haka ya saka Aliyu da Mai Martaba su samu matsala, domin ba lallai ne Mai Martaba ya yarda Aliyu ya auri bazawara ba, kara ma a da lokacin da aka ta hidimar auren yanzu be ce komai ba kuma be saka kansa a ciki ba, saboda a lokacin be kula da Aliyu ba, yanzu kuma ya kula har yayi magana” “To Ammy ya zaki yi yanxu? Kin san dai ba zaki ce Abiey ya daina son Zahra ba ko kuma ya ki aurenta ba zai ma saurareki ba, kin kuma san ba zai sake sakacin yarda ya rasa Zahra a karo na biyu ba, ba kuma zai auri Yasmin ya auri Zahra at the same time ba” “Miyasa ban masa magana ba, ni sam zuciyata bata yarda da cewar yarinyar da zuciya daya take sonshi ba a yanzu, amman zan yi magana da Zuwaira” “Ammy kar garin neman gyara gira ki rasa ido, karki aikata abun da zai saka Abiey ya yi ta kallonka da wata fassarar ta dabam” Ammy ta sauke ajiyar zuciya. “Zan yi tunani akai” Ta sauke wayar sannan ta kashe tana kallon wani bangare na ďakinta, sai kuma ta mike tsaye ta nufi gurin windows dinta ta bude tana hango Abiey da har lokacin waya take makkale a kunnensa yana jingine jikin mota. Ammy ta maida dubanta gurin wayar hannunta ta shiga contact list dinta ta yi dialing number Anty Amarya ringing daya ta yi picking. “Yanzu fa nake kokarin kiranki, Abiey ne ya fada min wata magana yanzu, wai Zahra ta nemi yafiyarsa” “Haka yace min ni ma yanzu, amman ina son ki zauna da shi ki nuna illar rashin auren Yasmin, idan yaji zai hada biyu ruwansa ne, amman ni dai bana son ya fasa auren nan” “Ni ma na yi wannan tunani, saboda Mama Lami da Hajiya Kilishi za su samu hanyar bata shi a gurin Mai Martaba, shi kan shi Mai Martaba zai ga kamar Abiey ya dauke shi karamin mutum ne, domin shi ya furta yana son Yasmin din a lokacin, ina ganin idan har zai fuskanci Mahaifinsa da maganar sai dai ya roki alfarma a amince masa ya hada da Zahra din” “Ki yi magana da shi, ni ma zan nuna masa haka, ko dan ita Yasmin din domin na lura ita ma tana son shi” “Inshallah” Da haka suka rabu. Abiey ya dade a waje yana waya da sauran kamin ya kira Anty ya fada mata da Dr Zainab da kawarshi Safeena. “Oh Congratulations finally zaka samu waraka daga ciwo kenan, kuma zaka farfado daga dogon suman da ka yi” Safeena ta fada sai yayi dariya. “Allah kadai ya san yadda na ke son yarinyar nan, ba ni da wani buri a yanzu bayan wannan” “Ita ma kuma zata yi dacen miji Abieu ko da ace mace kaunarka take ka zauna da ita zata ji dadi balle kuma ace kai kake kaunarna, ai ko na so na ga fuskar Zahra yau, kuma na so na jidadin da ya ta fahimta yanzu har take neman yafitarka” “Ni ma ina son jin haka, I'm out of worlds best out of control shiyasa ban ma iya tsayawa na yi magana da ita ba, komai ya zo min kamar mafarki sai kawai na bar gurin, but zan koma anjima da dare zan yi magana da ita” “Okay idan ta labarta maka ni ma ka fada min, and ka fada mata Safeena na gaishe ta sosai da sosai” “I will tell her Safeena, i will” “Hmmm Happy Boy Congratulations once again” Yayi dariya sannan ya sauke wayar. ZAHRA POV. Tashi na yi na dawo cikin gidan sai na zube a tsakar gidan ina jin kamar na narke a gurin saboda kuka da tashin hankali Abiey ya tafi be ce min komai ba, Mama na tambayar abun da na faru na zazzaga mata komai ina kuka. Yaya Maryam ta kama ni ta zaunar kan tabarmar da Mama ta shimfida sannan ta rungume ni. “Haba Zahra ke ma kin san Abiey zai dawo mana, wata kila mamaki ne ya saka shi yin haka, amman wanda yake neman a hudu balle kuma yanzu da ya samu aka hasko masa, zai dawo ki kwantar da hankali komai ya zo karashe ai, daman bawa baya wuce kaddararsa da baki auri Deen ba” Haka ta yi ta lallaba ni da kalamai masu dadi tana kokarin kwantar da min da hankali, cikin ikon Allah sai na samu sa'ida kuka da nake ya tsaya har muka dauko zancen wani bangare na rayuwar mu da Abiey. Ana daf da sallah azahar sai ga Hajiya ta zo gidan, Mama dai bata fasa halinta ba na tarbonta da far'a tana mata sannu da zuwa, ni dai kasa daga kai ma na yi na kalleta, sai dai duk da haka na lura Yaya Maryam ta fi ni daukar zafi domin tun da Hajiya ta dauko maganar Yaya Maryam bata ce komai ba, kara ji na kan jefa wata kalmar jefe jefe saboda na nuna mata ban jidadin abun da ďanta yayi min ba. Mama kuma tana nuna mata kamar Deen be aikata wani laifi ba saboda ya rike ni irin rikon da ko wace mace take so, tabbas ban san komai ba a tsawon zamana da Deen sai gata da soyayya, sai dai a yanzu na na kasa yafe masa saboda ya saka ni da Abiey mun mutu akan abun da ba shi ne gaskiya ba. “Ban taba sanin haka kike Zahra sai yau, lallai ďana yayi hakurin zama da ke, ashe akwai abun da zai saka ki manta waye Margayi a gurinki? Ina soyayyar da kike masa? Ashe duk ta karya ce? Na gode Allah da ya nuna mana halinki tun yanzu, ashe da Margayi ya rayu ya kawo yanzu da ya wahala domin kiyayyar da zaki nuna masa ba kadan ba ce, Zahra kin yi ba zata” Na dago na kalleta. “Hajiya ba zaki ga laifin...” Ban karasa ba Mama ta daga min tsawa hakan ya saka na ja bakina na yi shiru. Har ta gama abun da zan iya kira da borin kunya ta tafi ban sake ce mata uffan ba. “Tsakani da Allah Hajiya ta raina mana hankali, ta ya ďan ka zai aikata abu bayan kuma an gano gaskiya ka ce ba za a ga laifinsa ba? Da saninta ya aikata duk abun da ya aikata, yanzu take son ganin Laifin Zahra” Yaya Maryam ta fada sai Mama ta nuna ta da yatsa. “Ke ma ki iya bakinki, har gobe Hajiya Mamanki ce ko ba dan Abiey ba miji daya muke aure, kuma har gobe Zahra bata isa ta goge kanta daga kasancewa matar Deen ba, dole sai an fadi cewar ta taba aurensa, saboda haka ku dauki wannan abun a matsayin kaddara” Ajiyar zuciya na sauke Yaya Maryam kuma ta kalleni ta dauke kai ba dan bata da abun fada ba, sai dan na san ita din mai jin maganar Mama ce ba kamar ni ba. Tafiyar Hajiya da kamar awa biyu sai ga Baba ya shigo fuska babu annuri har wani bude hanci yake yana hararata kamar ya dake ni, sannu da zuwa da muka masa ni da Yaya Maryam ma be amsa ba, Mama ta tashi ta karbi yar jakar hannunsa sai ya nufi kofar daki kamar zai shiga sai kuma ya juyo ya kalleni. “Ke ashe Zahra baki da mutunci?” A take gabana ya yanke ya fadi, Yaya Maryam ta kalleshi kamar yadda ni ma nake kallonshi. “Tun da mahaifinku ya fadi ya mutu waya zame muku gata bayan ni, waya kula da ku cikin abokan Aminu bayan ni? Amman yau ace zaki kalli Idon Hajiya Balkisu ki zagi ďanta tass, saboda abun da be taka kara ya karya ba? ďana ba shi a duniya amman ki kalli idon mahaifiyarsa ki ci mutunshi?” Mama ta fito daga dakin rike da jakar ta tsaya bakin kofar tana kallon yadda Baba ke tayar da jijiyar wuya. “Babba be taba zama kamar Karami ba Malam da dai ka zauna ka huta sai na koro maka bayanin abun da ya faru” “Bayanin me zaki koro min? Lokacin da take aibata ďana ya kamata ki saka baki yi magana ba yanzu ba, daman ai duk lalacewar da Zahra ta yi ke ce sanadi yarinyar nan tun tana karama baki san ki mata fada ba ko kuma ki hana ta aikata abu, haka ta tashi bata jin maganar kowa” Yaya Maryam ta mike tsaye jikinta har rawa yake. “Baba kai uba ne a garemu, ko da ace ba ka auri mahaifiyarmu ba ka cancanci girmamawa a garemu, saboda ka zauna da mahaifinmu kuma kasan ciki da wajensa, balle kuma ace kana auren Mama, wata kila Hajiya bata fada maka yadda zaka fahimta ba” Ya nuna Yaya Maryam da yatsanshi hannunshi har rawa yake kamar mazari. “Ke kama bakinki, yau nake zaune tare da Hajiya da zata fada min karya? A can da bata fada min ba sai yanzu? ” Yaya Maryam zata sake magana Mama ta daga mata hannu. “Ban koya miki wannan tarbiyar ba, ko dukana kika ga yana yi ban ce ki saka hannu ki tare ba, saka talkaminki dauki mayafinki ki tafi gidan mijinki ina gaishe da yara” “Toh Mama” Ta amsa a ladabce sannan ta nufi dakin Mama ta dauko mayafinta ta saka da jakarta ta saka talkaminta ta nufi kofa, binta na yi da kallo har ta fice sannan na juyo na kalleshi. “Idan har zaka yi adalci karka ga laifina Baba, idan kuma ta kama dole sai ka gani to ka kalli abun ta fuska biyu ta bangarena da kuma bangaren Deen” Da hannu ya watsar da ni yana wani yatsina hanci, cikin tsawa yace. “Rufe min baki wawuyar banza, ko dan irin zaman da Zaharadini yayi da ke ai be cancanci ki bishi da wani kalamin ba saboda son zuciya, da ace ke din kina da hankali da tunina ai da kin gane cewar abun da ya aikata be aikata laifi ba, saboda duk abun da ya aikata ya aikata ne saboda ke, amman ace mutum baya raye kina son a dole sai kin dora mashi laifi? Mahaifiyarshi bata gama warkewa daga zafin ciwon rashinshi yanzu kuma ki kara mata wani, ai ina tunanin ko wani ki ga yana zagin Zaharadini sai inda karfinki ya kare balle kuma har ace kin zage shi da gaske” “Wallahi zuciyata bata tana raya min cewar da saninka Deen ya aikata abin da ya aikata ba” “Ai da nasan ke ce da na hana shi, domin duk mutumen da zai zauna bayan idonka ya zage ka, to ba masoyinka ba ne, abun da aka ce mamaci idan ya bar duniya ba a fadin aibunsa idan ma yana da balle kuma ke da kika matarshi, Zaharadin be barawo ba ne, ba ya fashi da makami baya kashe mutane, kuma duk abun da ya aikata ya aikata ne saboda ke, kuma inda mutumci ko da be aikata abun da ya aikata ba idan ya ce yana sonki ya cancanci a bashi ko dan ni, wane irin gata ne Margayi be miki ba? Na tabbatar da ubanki na raye ba zai wuce aura miki Zahraddini ba” Na mike tsaye zuciyata na bugawa da mugun karfi. “Da ace Deen ya nemi soyayya ta ruwan sanyi ba zai yi laifi a gurina ba, amman ya aikata abun da be dace ba, kuma ya bar ni cikin duhun rashin sani, miyasa ba zai fada min gaskiya ba, a haka kuma baka ganin laifinsa, da ace ba Abiey ya aikatawa abun da ya aikata ba, wata kila da yanzu yana gidan Yari domin abun da ya aikata babban laifin ne da za a iya daureshi har na tsawon shekaru wata kila ma har karshen rayuwarshi” Mama ta daka min tsawa ta nuna min ďaki. “Zahra wuce ki shiga ďaki?” “Wane ďaki? Ta gama cin mutunci ďana a gaban idona ta ci mutuncinshi a gaban mahaifiyarsa kuma ki ce ta wuce ta shiga ďaki, ta ci abincina ta kwana a muhallin? Ai yau kin nuna min budulci Zahra yau kin ba ni mamaki, Wallahi a lokacin da Hajiya ta fada min maganar nan na yi zaton zata fada min cewar kin tausaya masa, ashe kara da baya raye da yau ya ga bakinciki Allah ya waddaranki Zahra, shi ma wannan na tabbatar da ya aureki da yanzu yana nan yana nadama” Ina bude baki na sake magana Mama ta sake daka min tsawa a karo na biyu. “Na ce ki shiga daki ko?” “Aa barta ta gama, ai daman rashin kunya ne ta iya har ta siyarwa” Ba karamin jihadi na yi ba na hade maganar da ta taru a baki, domin na san idan na sake cewa tak sai Mama zata iya cewa zata doke ni, a tarihin rayuwarta ban san Mama ta yi sa'in sa da Baba ba, a iya tsawon rayuwar da na yi tare da ita ban san wata rana da ta taba mayar masa da magana ba, ban kuma san wata rana da ya bata umarni ta ki bi ba, tsantsan biyaya Mama ta yi masa, duk da ban san irin zamantakewar da ta yi da mahaifina ba, domin na taso ne ba tare da na taba ganinsa ko sau daya ba, mutumen da nake kira da uba a yanzu shi na sani a matsayin mahaifina. Hawayen da suka cika idona na share na nufi hanyar ďakin shi kuma ya juya ya fice kamar zai balla kafafuwansa ya tashi sama. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un” Mama ta furta ni dai ban juyo ba har na shige ďakin, tun da na shiga ban fito ba sai abincin dare ma Mama da kan ta shigo ta kawo min, har lokacin kuma bata ce min komai ba. Ana sauka daga sallah Magariba Baba ya shigo gidan ina jin Mama na sama sannu da zuwa ya amsa mata sama sama, ďaki ya fara zama kamin Mama ta yi masa shimfida a waje ya fito ya zauna kasancewar an dauke wutar nepa a lokacin. Ko da na fito na zagaya bandaki ina jin yana murda radio shi, da ada ne zan masa sannu da zuwa ya amsa, yanzu kuma ban ji ina iya mashi ba, be ma zama lallai idan na mashi ya amsa ba. Bayan na fi fitsari na dawo dakin na dauki carbi na hau katifar na kwanta na fara zikiri, sai kuma tunanin đana ya fado min a rai, ko a wane hali yake a yanzu Allah masa ni, wata kila yana can yana fama da ciwon cikin. Na girgiza kai ina kokarin ganin ban saka abun a raina ba, amman na kasa wani irin kaunarsa nake ji tana kara fisgata. Sosai nake son sanin halin da yake ciki tashi na yi na fita dakin zuwa gurin Mama dake zaune kan tabarma tare da Baba kamin na yi magana wayarta ta yi kara. “Daman wayarki zan ce ki ara min” “Gata can daki tana ringing” Na juya ba tare da na ce masa komai ba, sai ya kira ni. “Zahra yanzu idan mahaifinki ne zaki zo nan ki tsaya baki gaishe shi ba? Wato yanzu isa zaki fara nuna a cikin gidana ko? Ke kuma kina kallo baki ce mata komai ba” Na juyo tun kamin Mama tace komai na ce. “Baba barka da dare” Ban jira ya amsa ba na sake juyawa na shiga dakin ina jin Mama ba ce mashi “Yaran yanzu ka haife su ne ba ka haifi halinsu ba Malam” Ni dai ban maida hankali a akan maganar da su ke ba kara inda wayar take na dauka ganin Mama Hanne ce ya saka na kawo ma Mama wayar da sauri na tsaya jiran ta gama wayar ta ara min na kira Dr Hamid na ji halin da ďana yake ciki. Sai ga yaro ya shigo da kuzarinsa. “Sallamu Alaikum wai Abiey yace ana sallama da Zahra” Mama dake waya ta dago ta kalleni nima kallonta na yi kamin na kalli yaron sai muka hada baki ni da Baba gurin furta kalmomi mabanbanta. “Ka ce gata nan zu... ” “Ka ce bata nan” Na kalli Baba da sauri. “Baba magana kawai zan yi da shi dan Allah” “To ki tafi ki fada masa kar ya sake zuwa kofar gidan nan” Mama ta sauke wayar da sauri ta kalleshi. “Malam Aliyu ne fa dan Mai Martaba” “Ko ďan Sarkin Saudiya ne be dame ni ba, kuma ba shi zaiba shi damar shiga cikin gidana yayi yadda yake so ba, bana son na gan shi kofar gidana, idan ya sake zuwa Zahra ta fita to ta fita kenan ba zata dawo min a gida ba” “A dai yi hakuri a rika kai zuciya nesa, ban san iya abun da Hajiya ta fada maka da yasa ka hau da wannan zafin ba, amman yana da kyau idan ana sara a rika duba bakin gatari” Mama ta fada tana kokarin saukar da shi akan hawan da yayi da yawa na fushi, sai ya taso mata kamar yana jiranta. “Ba za a ayi ba, kuma na fada miki idan ya sallamo Zahra ta sake fita ta fita kenan sai dai ta nemi wani gidan” “Zahra kam ba, bata da inda ya fiye mata gurin da nake zaune, idan har ta bar gidan nan to aure ta yi ko kuma ta bar shi tare da ni, domin idan bana har kace zaka kori Zahra a gidan nan to kamar ka kareni ne tare zamu tafi” “Ruwanki, ni dai kin ji na fada miki gidan ba ta sha ba ne da za a rika zuwa ana faka min da motoci ban san su waye ba, ai duk abun da kuke a bayan idona mutanen unguwa suna fada min” Ya fada yana daga kafadunsa, Mama ta kalleni. “Saka Hijab ki tafi” Na juya ina jin yadda zuciyata ke tafarfasa na shiga dakin na dauki Hijab dina na saka na fita, kasancewar babu wuta a line kuma motar tashi baka ce ban iya fahimtar inda ya faka motar ba har sai da ya kunna hasken motar, sannan na karasa sai ya bude motar ya fito ya kunna fitilar wayarsa ya haska fuskata. “I miss this face, da a kebe muke Zahra da na rumgume ki na ji sanyi” Na sauke kaina kasa ina murmushi. “Ji annurin fuskarki the smile your pretty face i miss you a lot” Na dago na kalleshi duk da kasancewar bana ganin fuskarsa da kyau saboda hudun yau da babu ko farin wata. “I miss you more Abiey” Ya jingina da motarshi ya daga kanshi sama yana murmushi mai sauti. “Wow....” Na kuma na gyara tsayuwata hango Baba tsaye kofar gida, yana ďan haske haske da fitilarshi. “Abiey...” Ya dago kamar zai kai bakinsa saitin kunnensa. “Hiayatee...” Na dan matsa baya kadan. “Ina son zan saka maka number Mama idan zaka zo ka kira ni sai a fada maka inda zamu hadu” “Miyasa?” “Ba komai mutane suna saka ido a nan kuma Baba baya son haka” “Amman akwai inda zamu hadu da ne da yafi kofar gidanku?” “Akwai dalili, yanzu ma ina son na koma ciki” Na karbi wayarsa na saka mishi number Mama sannan na mika nasa sai ya hada da hannuna ya karba. “Look Zahra idan akwai wata matsala ki fada min, karki boye min komai, ina son na yi magana mai yawa mai tsawo da ke amman na lura kamar baki cikin natsuwa, ki fada min idan akwai wata matsala” Na zare hannuna. “Ba komai, zan shiga ciki sai da safe” Na fara tafiya da sauri gabana sai faduwa yake gani nake kamar Baba zai iya zuwa yayi masa cin mutunci, ni kuma ba zan yi farinciki da hakan ba domin ko kadan a yanzu bana son abun da zai bata ran Abiey. [10/30, 11:42 PM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣3️⃣ A kofar gida na wuce Baba na shigo ciki, sai ya biyo bayana. “Na fada miki ko? Kar na sake ganinsa kofar gidan nan, idan kuma ya sake zuwa kuma kika fita to kin fita kenan” Na dan juyo kadan na kalleshi sai dai ban ce na nufi dakin da nake kwana, ina shiga sai na jingina na lumshe ido har lokacin kamshin turaren Abiey be fita a hancina ba, samun kaina na yi da murmushi ya lumshe ido ina jin wani irin kewarsa da annashuwa da na dade ban ji irinta ba. “Zahra” Kiran Mama ya dawo da ni daga duniyar tunanin da na tafi sai na amsa na fito. “Karbi ga waya” Na karaso na mika hannu na karba, da fari na yi zaton number Dr Hamid zan gani sai dai ganin number da na kasa cireta a kaina ya saka na kara jin wani farinciki ya lullube ni, sai da na shigo cikin ďakin sannan na kara wayar a kunnena. “Hello” “Hiayatee...” Na yi murmushi ina jin sunan har cikin raina. “Murmushi kike yi” Na yi saurin daga maishi kai kamar yana gabana. “Yanzu kuma kin daga kai...” “Ka fara duba” Na tambaya ina nufar katifar na zauna. “No na san ki dai in and out me kike yi yanzu?” “Komai kawai ina zaune dai” “Kawai ina zaune dai...” Bayan kalmar farkon ta karshen a tare muka karasa ta saboda ya san abun da zan fada kenan, mun saba idan ya kira ni zai tambaye me na ke yi, idan ina wani aiki na kam fada masa, amman da zarar na ce komai to kalmar da zata biyo bayan kawai ina zaune dai... “I know everything about you Zahra, abun da kike so da wanda baki so, abun da yake saka ki a cikin bacin rai ko damuwa da kuma wanda ke faranta miki rai, ban manta komai ba kuma ban goge komai daga rayuwar da muka yi a baya ba” Yayi shiru yana sauraren numfashi dake sauka a sauri sakamakon zuciyata dake bugawa da karfi. “I miss you i mean i miss you so much, ban yi zaton wata rana zata zo min da wuri haka da zan sauraren muryarki ko na yi magana ki saurareni ba, kyautar ganin fuskarki da kika min a dazu ta fi duk wata kyauta da za ayi min a duniyar” Ya sake yin shiru sai kuma yayi murmushin da sai da na ji sautinsa a kunnensa na dama. “Rayuwa bata da sauki idan babu ke Zahra, na saka budewa ko wace mace zuciyata na kasa yarda akwai wata mace da tafi kyau natsuwa hankali, balle har zuciyata ta raya min na so ta, ba zan ce na gaji ba, amman jiki yai sanyi kuma zuciyata ta yi rauni bayan na rasa ki, har nake ganin kamar ba zaki dawo a gareni ba, but wani abu ya tsayar da ni cak kuma ya kasan zaka ni farinciki idan na tuna shi, kin san me ye?” “Aa Abiey...” Na fada da sautin dake karantar da shi kuka nake kamar kama da na farinciki da kuma kewar juna. “Idan na tuna cewar kina farinciki a inda kike, wannan abun ya kan saka na ji hankali ya kwanta, as long as zaki samu farinciki zan iya jure ko wace kalar rayuwa, matukar ke zaki samu farinciki, but Zahra duk tsawon kwanakin nan zuciyata soya take ni kadai na san halin da nake ciki, na kasa daina dorawa Dr Laifi, every minutes every seconds yana tuna min da ke, idan na ga wata mace ke kike fado min a rai, kuma a haka ban tana kawowa a raina wata rana zaki tsaya ki saurareni ba” Na runtse ido ina kai hannuna saitin zuciyata na hawaye na sauko min wasu kan wasu. “Rayuwata bata da sauki Zahra, ga tsanar Mai Martaba ga rashinki na sha wahala a zuciyata ban san wani lokaci da na yi farinciki na tsawon sati ba, ban san wani abu da ya faranta min rai irin yau ba, Allah da ya dora min kaunarki shi kadai ya san yadda nake son ki Zahra, and i know kin yi rayuwa da tsanata a ranki and that's the most painful part” Ya karasa yana dariyarsa mai kyau sai ya kai hannu na share hawayena, sannan na bude ido ina shan jan dake taruwa a hancina. “Kuka kike yi? Don't make make me cry, if not i will knock your head saboda kin san hawaye ya fara taruwa a idona” Kusan a tare muka numfasa sai dariyar data fito bakina da wanda ta fito bakinsa suka yi tarayya da juna gurin fitar a tare. “Ni ma na wahala kamin na saba, na sha da ci kamin na fara dandanar zakin zaman aure, da fari na yi zaton ba zan iya ba, duk wani motsi da Deen zai yi zai tuna min da kai ne, wani lokacin na kan kirashi da sunanka, a haka dai har ya koya min yadda zan manta da kai, bayan zuciyata ta dade da karbar tsanarka, amman na kasa goge komai naka duk da kasancewar na sabawa zuciyata tsanarka” Ina jin lokacin da ya busar da iskar bakinshi. “Ya aka yi kika aminta da ni a yanzu Zahra? Taya kika gane gaskiya?” “Ta hanyar fada min da ka yi, miyasa baka fada min haka ba tun da?” “Ada can ba ni da hurumin magana da ke balle na fada miki ki fahimta, secondly ba mu da wani evidence da zan iya yin shari'a da Deen akansa, thirdly na san idan na maka shi kotu zan daga miki hankali ne kuma zan karawa kaina tsana a zuciyarki ne, amman kin ga yadda Allah yake ikonsa” Na yi shiru zuciyata na min wani iri. “Hiayatee...?” “Na'am” Na amsa da wani irin siga da ban san taya lafazin bakina na sallace da shagwaba ba, duk kuwa da irin nauyinsa da nake ji na abubuwan da suka faru. “Ahhh Awwww i miss this Shagwababbiyar yarinya ji fuskarta” Na yi dariya shi ma dariyar yake. “Na zo na ganki?” “Ba yanzu ka tafi ba?” “Ban isa gida ba ai, na kasa hakuri ne shiyasa na kira na sake jin muryarki and i need to see again and again and again and again and again” “No ka ga yanzu ina bukatar hutu, kuma mutanen unguwa za su fara saka mana ido, shiyasa bana son ka zo har sai ka kirani, after that yaushe na haihu? Ai ya kamata na dauki lokaci kamin ace ina tsayuwa da wasu” “Okay Babe amman Wallahi i need to see your face again ga wannan wayar babbar waya ce da zan iya kiranki mu yi video call” “No karamar waya ce” “Na siyo miki babban wayar yanzu?” “No wannan ma ta isa zamu iya magana ai” “Okay Zahra duk yadda kika ce haka zan yi, kamin na manta Safeena tace na gaisheki” “Safeena na duniya daman?” Daga haka muka shantake da labarin rayuwar baya, daga bisani ya bijiro min da tambayar yadda aka yi na fahimci gaskiya, sai na fada masa sai dai ban yarda na labarta masa abun da Baba da Hajiya suka min ba. A daren ranar da waya na kwana a kunnena tun yana min magana ina iya ji na amsa wata na yi murmushi ki dariya a wata maganar har bachi ya sace ne. ABIEY POV. Murmushi yayi yana sauraren yadda take shigar da numfashi da fitarwa irin na wanda bachi yayi masa nauyi. “I miss you...” Ya furta har lokacin murmushi yake sai ya juya daga gefen da yake kwance ya saka wayar a hands-free ya sauka kan gadon ya nufi bathroom. Sai da ya raba jikinshi da tufafi sannan ya isa gaban shower ya kunna ya rufe ido, ta fara jika kanshi ruwan na sauka a jikinshi, ba zai iya kwatanta farinciki shi a yau ba, bayan godiya ga Ubangijinshi babu abun da yake sai da ko'ina na jikinsa ya san da farinciki zuciyar dake raba masa jiki da kaunar Zahra a yau, yana murza shower gel yana murmushi annurin fuskarshi na kara bayyana, sai da ya tabtace jikinsa ko'ina fes sannan ya kashe shower ya dauki karamin tawul ya daura ya fito rike da dayan yana goge jikinsa. Gaban katon madubu ya tsaya a zahira zaka yi tsammanin kyakkyawar surar jikinsa da mazantakar da Allah yayi masa yake karewa kallo, a baďini kuma tunanin rayuwarsa da Zahra yake, har ya shafa mai ya fesa jikinsa da turare ya nufi closet ya dauko pajamas ya saka be daina murmushi ba, shi kansa ya san ya kusa tabuwa a yau, domin ji yake ya cike wani gurbin wani karon rami dake zuciyarsa sai yake jin kanshi cikakaken namiji a yanzu. A inda ya aje wayar ya nufa ya dauka ya matsar da ita kunnensa har lokacin Sahibarsa bachi take tsalle yayi ya fada kan gadon yaja filo ya rumgume ya kara wayar a kunnensa ya rufe ido yana jin kamar Zahra na kusa da shi. “Sleep tight Hiayatee... You have everything now” Ya fada sannan ya kashe yanke wayar yana jin kamar ya dawwama yana sauraren numfashin bachinta. Ji yake kamar ba shi da damuwa kwata kwata a rayuwarshi a yau. Baka bukatata a yau, bachi ya fada masa shi kuma sai ya amsa masa da yes domin juyi ya rika yi kan gadon ya kasa bachi farinciki dake ransa da zumuncin sake saka Zahra a idonshi a gobe be bari bachi ma ya zo kusa da shi ba, ashe ba kowa bachi ke iya sata ba domin a yau Abiey ya tabbatar da haka, farinciki ya hana shi bachi ya rufe ido amman ya kasa bachi, da ya gaji da juyi akan fado ne ya tashi ya fito dakinsa ya sauko falon ya nufi kitchen ruwan zafi ya fara tafasawa yana ta kallon kitchen din kamar yau ya fara shiga. “Abiey...” Ya juyo yana jin kamar a lokacin Zahra take kiranshi, saitin inda take tsaye a wacan lokacin yake kallo tana rike da cinyar naman kaza. “Zan cinye wannan sai ka cewa Ammy kai ka ci” “Ba zan ce ba saboda ba ni na ci ba” “Ni kuwa zan fadawa wannan yarinyar gaskiya na ce mata ba aurenta zaka yi” Ya daga kafadunsa. “I don't care idan na rasa mata, ke ma ba zaki samu miji ba” A shagwabe ta murguda mishi baki ta harareshi ta sude hannunta tass sannan ta nufi kofa ta fice tana watso mashi harara. Juyawa yayi yana kallon kofar yana murmushi kamar dai wacan lokacin da komai yake faruwa. Ajiyar zuciya ya sauke ya dauki ruwan da ya gama tafasa ya zuba a cup ya fito ya dawo dinning. Zallar tea ya hadawa kanshi da two cube sugar ya matsa lemun tsami ya saka kayan koli sannan yaja kujera ya zauna ya fara motsawa, sai da ya rage zafi sannan ya fara kurbawa sai a lokacin ya tuna cewa be ci komai ba a yau kaunar Zahra kuma bata bari ya ji yunwa ba. A hankali yake kurba tea yana ajewa har yayi rabi sannan ya kwantar da kansa kan kujerar dinning din yana kallon Pop. ZAHRA POV. Ban san iya awanin da wayar ta dauka a kunne bayan nayi bachi, ni dai na farka na fa wayar a can gefe ni kuma ina karshen katifa rabon da na yi bachi mai dadi haka har na manta, duk kuwa da kasancewar babu komai a cikin mafarkina sai ďana. Bayan sallah asuba da kaina na fito na kunna wutar da Mama ta saba kunnawa na dora tukunya ita kuma ta zuba ruwan zafi sannan na koma na kwanta ita kuma ta yi alwala ta shiga ďaki ta yi sallah. Misalin bakwai na safe aka yanka ragon da Mama ta bada kudi aka siyo, na yi tunanin Baba zai shige gaba ayi komai da shi kamar yadda ya shige gaba gurin siyo ragon, amman sai abun ya sha banban domin saka talkamin shi yayi ya fice daga gidan bayan ya karya da dumamen tuwon da Mama ta yi, Sai da Mama ta nemo wani makocinmu ya yanka mata ragon aka gyara aka yi komai, sannan aka shigo dashi ciki gida, abun ka da kai mutane arziki kam la'asar ta yi har an gama gyara naman an soye shi rumus, sannan ta debar musu wanda zata ba su ta kara ta shigo min da nawa ta dauki nata. A ranar na yi waya da Abiey ya fi a kirga, each and every minute sai ya kira ya ji lafiyata da muryarta, kinnci abinci? Me kike so? Me kike ji? Akwai abun da yake damunki? Su ne abun da yafi tambayata kamin ya roki a bar shi ya zo ya gan ni, ni kuma bana son na samu da Baba hakan yasa ban ba shi dama ba, ko baya ga wannan akwai mutane da yawa a gidan mu a yau da suka taya Mama aiki be dace su gan ni na tsaya da wani ina magana ba, wannan dalili ya saka Dr Hamid ma daya kira ni ya sanar min cewar yana kofar gidanmu yana son ganina ban fita ba, har ya gaji ya tafi, sai dai na wuni da rashin jindadin ďana a kusa da ni musamman soya naman nan da akayi sai a lokacin na ke kara ganin laifin abun da na aikata domin na yi sadaka a inda be kamata ba, Hajiya Jamila bata da kirki bata cancanci ďana ba, haka ma Deen be cancanci na siyar da rai saboda na ceto ranshi ba... Da haka na kwashe kwana hudu ko kofar gidan ban je ba, a tsawon kwanakin nan kuma babu komai a zuciyata sai farinciki na kulawar da Abiey yake ba ni duk kuwa da kasancewar a waya ne kawai muke iya kasancewa tare da juna, ta dayan bangaren kuma ina tunanin ďana zuciyata na raya min kamar ba lafiya ba, musamman kwana biyun nan da Dr Hamid ya matsa min da rokon yana son na je gidan na bawa yaron Nono ko kuma na matsa a kai masa sai na ki yin ko daya, wani lokacin ma idan ya kira ni ba zan daga ba domin na san maganar da zai min kenan. A Ranar da Mama ta karbi girki Ina zaune tsakar gidan ina wanke under wears dina ya shigo da cefane be yi sallama ba daman kwana biyun nan gaba daya ya canja daga shi har Hajiya domin ko naman da Mama ta aika musu kin karba ta yi, Baba ma da Mama ta ba shi na shi be karba ba, sai wani shan kamshi yake idan ya shigo cikin gidan, idan kuma yayi arba da ni kamar ya ga wata makiyiyarsa wani lokacin har mamakinshi nake, yadda ya take gaskiya idonsa suke nuna masa karyar a matsayin gaskiya.. “Sannu da zuwa” Be amsa min ba, hakan yasa ban samu kuzarin na tashi na karbi ledar hannunshi ba. Har sai da ya karasa inda Mama take zaune tana gyaran shimkafa. “Sannu da zuwa Ya kasuwar?” Ita kam ya amsa mata shi ma ciki ciki kamar baya son magana, daki ya shiga be dade ba ya fito ya fice daga cikin gidan. Be dawo ba sai bayan sallah Isha'i yau ma a waje Mama ta yi mashi shimfida saboda ya bukaci haka duk da kasancewar akwai wutar nepa a dare. Ina jin yana kokarin kama Bbc ni kuma na gyara kwanciyata wayar Mama na gefena domin a yanzu kullum da wayarta nake wuni na kwana saboda yawan kiran Abiey. Abun ka da ďan halak hausawa suka ce kak'i ambato, ina tsaka da tunaninshi a raina sai kiranshi ya shigo, sai na yi murmushi sannan ya dauka. “Guess what?” Na ďan yi shiru alamar nazari sannan na ce. “Ka siye wani abu?” “No wrong... Ina kofar gidanku” “Wasa kake?” “I'm serious” Na tashi zaune da sauri. “Amman Abiey na fada maka idan zaka zo ka kira ni” “Na gaji ne Zahra kullum idan nace ina son ganin fuskarki sai ki kawo min wani uzuri, ki hana ni zuwa kin san kuma yadda nake marmarin ganin fuskarki” “Shikenan zamu hadu a wani gurin amman ba gidan nan” “Saboda me? Don't tell me mutane kike tsoro? + inda nake a yanzu mutane ba za su gan ni ba, kuma babu ma mutane da yawa a unguwar kin ga garin akwai hadari yawancin masu iyali duk sun shige gida” “Abiey ba zai yiyu na fito ba” “Ki taimaka min ko kofar gida ne ki tsaya ma ga fuskarki sai ki koma Wallahi Zahra na yi missing dinki tun ranar nan ban sake saka ki a ido ba” “Akwai wata yar karamar matsala ne” “Wace matsala?” “Baba baya son ina kula mutane a yanzu sai nan gaba” “Fuskarki kawai nake son gani Zahra please” “No Abiey ba zan iya fitowa ba” “Fine zan kwana a nan, ko kuma na yi sallama na shigo cikin gidan ki zabi daya” “Ba zan iya zaba ba Abiey dan Allah ka tafi” “Ba zan tafi ba sai na ganki Zahra” “Kai ma ba girmanka ba ne a rika ganinka a unguwarmu” “You think wasa nake ba zan tafi ban ganki ba? Trust me Zahra ba zan tafi ko'ina ba sai na ganki” Na kashe wayar gaba daya gabana na mugun faduwa, domin har ga Allah bana son tashin hankalin Mama a yanzu, ga furucin da Baba yayi bmna cewar idan har na sake fita na fita kenan babu dawowa, na san kuma Mama ba zata yarda da wannan ba, hakan kuma ba karamar matsala zau haifar musu ba. Ina tsaka da neman mafita na ji sallamar yaron da zaton almajiri ko ďan makocin yana fadin. “Wai Abiey yace yana sallama da Zahra a waje” Yaron na kai aya Baba ya kwala min kira, sai na dora hannu na toshe kunnuwana ina jin kamar kar na amsa domin yanayin yadda ya fisgi murya gurin kirana kadai ya isa ya sanar min da bacin ranshi. “Na'am” Na amsa gabana na faduwa ina ta sake saken abun da zan ce mashi, ina fitowa ďakin tun kamin na karaso inda yake ya jefeni da tambayar da ban san ta ina zan amsa ta ba. “Ban fada miki kar yaron ya sake zuwa ba? Ko ban fada miki ba” “Ka fada min Baba amman....” Sai maganar ta makale ko me zan ce ma oho gaba daya ji anke kamar kalmomina sun kare. “Amman saboda kin raina ni shi ne zaki bari ya sake zuwa ko? To bari na fita na mashi magana da kaina” Ya fada yana kokarin mikewa tsaye, sai Mama ta ce. “Haba Malam wannan ba mutuncinka ba ne, be dace ba ko da ba Abiey ba ne balle kuma ace shi? Kamar baka san su ke da garin nan ba?” Wani uban tsaki yaja ya mike tsaye sai na yi sauri na karasa na rike rigarshi. “Baba dan Allah karka yi, bari na yi magana da shi zan fada masa kar ya sake zuwa” Ganin yayi shiru be ce min komai ba ya saka na juya na koma daki na dauko Hijab na fice, a gaban wani gida dake fuskantar na mu da ake gyara ya faka motarshi, yana ganin na fito ya bude motarsa ya fito yana shouting. “I knew it...” Na karasa kusa da shi tashin hankali dake tare da ni yana kara bayyana a fuskata. “Abiey dan Allah ka daina zuwa a nan idan ma ka matsa kana son ganina zamu iya haduwa a wani gurin amman ba a nan ba” Ya matso kusa da ni sosai yana kallon fuskata sai ka rantse da Allah be taba ganin kyakkyawar mace irina ba, murya can kasa kasa irin ta masu neman kwantar da hankalin yaro ya ce. “Okay, amman ki daina daukar lokaci mai tsawo ban saka ki a ido ba Zahra, ji nake kamar na sace ki na gudu Wallahi” “Na ji yanzu ka tafi” Ya daga min kai yana yawo da idonsa a kan fuskata, juyawa na yi na kalli kofar gidanmu sai kuwa na juya a daidai domin Baba ne ya fito ya nufo inda muke tsaye, juyowa na yi da sauri na kalli Abiey dake ta kallona kamar zai lashe. “Abiey ka tafi yanzu” A maimakon ya amsa min sai ya daga kai yana kallon Baba da ya doso mu gadangadan, baya bukatar na fada masa matsayin Baba a gurin, haka zalika ya san Baba ne mahaifin Deen tun kamin Deen ya aureni. Baba na isowa yayi masa sallama Abiey be amsa ba kuma be daina kallonshi ba. “Malam dan Allah ka kama mutuncin ka bana son ganin kowa a yana zuwa sallama da Zahra” Na juyo da sauri na tari numfashi Baba. “Baba dan Allah...” “Rufe min baki fitsarariyar yarinya” “Please control your tongue, at least ya kamata ka yi magana da girmamawa ka san waye ni?” “Ina ruwana da waye kai? Kudinka ko sarautarka bata dame ni ba, kaje can ka yi shashanci ba kofar gidana ba, dan haka ya zama karo na karshe da zan sake ganinka a nan” Baba ya fada cikin daga muryar dake kokarin tara mana jama'a, Abiey ya saka hannayenshi aljihu yana kallon Baba da murmushin takaici a fuskarshi. “Kamar kumbo kamar korenta...” “Abiey dan Allah ka tafi” Na roka ina hawaye. “Zan tafi Zahra amman ki fada masa gobe zan dawo jibi ma zan dawo” “Aa Dan Allah kai baka gane ba ne, Baba baya son zuwanka ya min gargadi akan idan ka sake zuwa na fita zai koreni dan Allah ka tafi Abiey...” Abiey ya kalleni sannan ya kalli Baba har ya juya sai kuma ya juyo sakamakon wadansu kalamai da Baba yake fada marasa dadi “Idan ba iska ce yarinya ko arba'in bata yi ba ka fara zuwa kana mata sallama, kowa ya ga Zahra ya ganka ya san ba aurenta zaka yi ba, dan haka kar na sake ganinka kofar gidana” A yadda na lura kamar da gayya Baba yayi maganar cikin daga murya saboda hankalin mutane ya dawo kan mu, kuma ya samu domin tuni daidaikun mutane da suke nan suka fara kallon inda muke tsaye. “Baba dan Allah ka bari dan Allah” Ina rufe baki ya wanke min fuska da mari mai kyau. “Ai duk ke kika ja min ba a taba jina da kowa ba unguwar nan sai yau, da baki kula shi ba da be samu wannan damar ba, kuma na fada miki idan ya sake zuwa nan sai dai ki bishi” Wani abokin Baba ne ya zo yana ba shi hakuri, mamaki ya fara kama mutane ganin cewa Abiey wanda fuskarshi sananniya ce, kuma Baba yayi ne saboda ya tozarta shi da ni. “Simple...” Abiey ya fada naman fuskarshi na rawa alamar ranshi ya bace sosai. Ni kuma na dafe fuskar na juya da gudu na shiga cikin gida ina kuka... [11/1, 7:25 PM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣4️⃣ Da kuka na shigo gida na fada jikin Mama ina labarta mata abun da Baba yayi min, mikewa ta yi tsaye kamin Baba ya shigo cikin gida har ta kagara. Be shigo da sallama ba, ahasali ma yana shigowa ya hau Mama da fada. “Na fada miki bana son ganin kowa kofar gidan nan ko?” “Gaskiya Malam abun da kake yi be dace ba, na san kai uba ne a gurinsu amman kana wuce gona da iri, Zahra ko yar makota ce ta zo ta tsaya kofar gidanka be kamata ka yi mata wannan cin mutuncin ba balle kuma ace yarka” “Aa ni ba yata ba ce da yata ce ai da ta ji magana ta, da bata tsallake sharadin da gindaya mata ba, kuma ke ma da baki tsaya a gabana kina sa'insa da ni ba akan ta” “Wallahi ko ban san inda Zahra ta fito ba, dole na yi magana balle kuma ace tana yata, mutumen da ya zo gurinta ba mutumen banza ba ne balle ka ci mutuncinta saboda shi, har kana neman tara mata jama'a, wannan abun sam be dace ba” “Oh yanzu ko kunya baki ji ace yarki na fita waje tana magana da maza? Yaushe mijinta ya rasu? Kuma yaushe ta haihu? Da har zata fara kula su? Kuma mutanen arziki ne za su kula mace mai biki?” “Malam kana abu kamar baka san waye Abiey ba!” “Toh waye shi? Dan yana ďan sarki? Ko kuma ďan yana da kudi? Sai aka yi me? Kofar gidana ya zo ba ni naje gidanshi saboda ina da ikon nace bana bukatar ganinsa a gidana, kuma daman na fada miki idan Zahra bata ta sake kula shi zata fitar min a gida, yau ma na sake nanatawa kar na sake ganinsa a karo na uku” “Wannan dokar ta yi tsanani Malam” “Idan ta mata tsanani ai sai ta san inda dare ya mata tun wuri, kin ga ba kare bin damo, daman ta saka kin fara sa'insa da ni a gabanta, nan gaba kuma ban san iya inda abun zai kai ba” Yana rufe baki na mike tsaye ina mashi wani kallo mai kamada da harara. “Ko a gidan nan aka halittoni Baba ba zan kwana a cikinshi ba yau” “Zahra.... Babu ruwanki a wannan maganar” Mama ta fada min cikin tsawa. “Mama ba zan zauna a gidan nan ba, korata yake duk abun da yake yana yi min ne saboda na takura” “Rufe min baki wuce ki shiga ďaki” “Aa kar ta shigar min ďaki sai idan kayanta zata kwaso domin ba zata kwanar min a gida ba, ni zaki nunawa fitsara?” “Zahra ba zata je ko'ina ba Malam, idan har Zahra zata bar gidan nan sai dai mu tafi tare” “To saka mayafi ki bita, daman ai ke kike daure mata gindi tana yadda take so” Mama ta kalleshi tana girgiza kai kamin ta ce komai muka ji an banko kofar gidan da mugun karfi kamar za a balla kofar manyan zaratan sojoji ne kusan su shida suka shigo cikin gidan, ni dai faduwa na yi durkushe jikina na rawa zuciyata kuwa kamar zata fasa kirjina ta fito saboda tsoro, Mama nata nanata Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Baba kuma ya ranta a na kare sai ďakin Mama, aiko sojojin suka bishi da gudunsu har cikin ďakin suka kamo shi kamar wata bankarariyar kaza haka suka fito da shi kafafuwanshi na lilo, sai kuka yake yana ba su hakuri. “Ku yi min rai, ku yafe min dan Allah, me na muku? Ku tausaya min ina neman abun da na ci” Mama ma ta shiga ba su hakuri tana hadda hannayenta biyu guri daya, ni kuwa da na lura ba gurin kowa suka zo ba sai Baba sai na hankali ya dan kwanta daman na san za a riba daman can kare yana da haushin kura balle kuma yanzu da Baba ya ci mutuncin Abiey. Wani mahaukacin mari da suka mashi sai ya saki fitsari ni kuma na dafe kuncina biyu ina jin kamar ni aka mara, ganin suna kokarin fita da shi ya saka Mama ta bisu tana tambayar “Ina zaku je da shi? Dan girman Allah ku yi hakuri” Ko kula ta ba su ba suka fice da shi, ba dan hawayen da na ga yana zuba a idon Mama ba da sai na zuba ruwa kasa na sha domin murna. Ko ba a fada min ba na san Abiey ne ya aiko a tafi da shi hakan kuma yayi min daidai domin maganin biri karen maguzawa. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, abun da nake ta nunawa Malam kenan ya ki ya gane, wani talakan ma ba a taba shi a zauna lafiya balle kuma ďan sarauta ina dadin haka?” “Mama mu ai babu ruwanmu korar mu ma yayi a gidan ai” “Ke da yake baki da hankali ba, ai idan wani abun ya sake shi ta dalilinki za a ce, gashi kuma sojoji basa da imani kar su je su kashe shi nake tsoro” “Ko ma me aka mashi Mama ai shi yaja wa kanshi” “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, zama be gan mu ba” Ta fada tana dora hannu saman kai har lokacin kuka take, kan kace kwabo makota sun cika gidanmu suna ta jajatawa Mama, tana ta kiran mutane a waya tana fada musu, ciki har da Hajiya. Babban tashin hankali Mama na rashin sanin inda za a kai shi ko suka tafi da shi. “Zahra ki kira Abiey ki yi magana da shi dan Allah ko kuma ki kira shi sai ki ba ni wayar” “Toh” Na amsa mata ba dan komai ba sai dan bana son musa ba, amman ba dan haka ba da ba zan kira shi din ba domin ni yayi min daidai. Wayarta na karba na koma ďakin da nake kwana na nemo number Abiey a call list na kira shi sai da wayar ta kusa yankewa sannan yayi picking. “Hello” “Hey Beautiful” Na yi murmushi kamar yana gabana. “Mama tace na tambaye ka mutanen da saka su tafi da Baba ina, za su kai shi?” Sai yayi shiru kamar be fahimci tambayar tawa ba, wata kila kuma ni din ce ban fada da sigar da zai fahimce ni ba. “Abiey” “Hiayatee tambayar shi kawai za su yi su dawo da shi” “Kamar ya tambayarshi? Kana ina?” “Gida” Na zauna ina ambatar sunanshi. “Abiey idan wani abu ya samu Baba ba zamu ji dadi ba, domin yana a matsayin uba ne a gare ne, kuma. Mijin mahaifiyata ita kanta ba zata so wani abu ya faru ba, yanzu haka kuka take ta yi” “Mama?” “Ba ki fada mata abun da yayi ba?” “Na fada mata, har korar mu ma yayi saboda zuwanka amman duk da haka hankalinta a tashe yake sai kuka take ita ce ma ta ce na kiraka na yi magana da kai ko kuma na bata ta yi magana” “Zan saka su kawo shi” “Amman kar su mishi wani abu dan Allah” “Okay” Ya amsa min muryarshi kasa kasa kana jinshi ka san ranshi a bace yake. ABIEY POV. A fusace ya fita daga unguwar irin fusatar da ace za a tara mashi Baba a gaban mota zai taka shi ne ya wuce, hakan ya saka be tafi gurin Ammy ba sai kawai ya nufi Masarauta gurin Anty Amarya, har daf da entrance din kofar falonta yayi parking ya fito yana jin wani zafin azaba da zuciyarsa ke masa saboda bacin rai, har wani huci yake a lokacin da ya shigo falon. Aisha da Siyama yar Hajiya Lami dake zaune a kujera ďaya suna duba wani lace suka masa sannu da zuwa amman be amsa musu ba sai ya zauna ya daga kanshi sama, sai kuma ya saka hannunshi aljihu ya ciro wayarshi, contact list dinshi ya shiga rabon da ya kira babban Yayanshi su gaisa har ya manta wani lokacin ma har shi yayan ke kiranshi su gaisa idan aka dauki lokaci domin ya san halin kanenshi. Amman a yau ya ji yana bukatarshi domin shi ne kawai zai yaye mashi damuwar da yake ciki a yanzu, ya san idan ya fadawa Mai Martaba wata kila zai masa fada ne idan kuma be mashi fadan ba zai saka bakinsa a ciki ba, wayar bata dade tana ringing ba yayi picking cikin barkwanci kamar yadda suka saba. “A.B yau ka tuna da ni” “Kanal dole ce ta saka wani abu bake son ka saka yaranka su yi wani aiki a nan” “Kana magana kamar kana bani umarni who's the elder?” “Come on Bro I'm not in the moon mutumen ya bata min rai over” “Yayi maka?” Abiey ya gyara zamanshi ya busar da iskar bakinshi, Aisha da Siyama sai kallonshi suke ba ma kamar Siyama da ta samu abun labartawa Mahaifiyarta, Aisha kuma na damuwa da halin da ďan'uwanta yake ciki ne domin ta lura da hakan tun farkon shigowarshi. Kamar mai rubuta labari haka Abiey ya fada ma Yayanshi abun da ya faru, kasa kasa Aisha ke satar kallon Siyama da idonta yake kan Abiey kamar zai fado tsabar gulma da maida hankali tana saurarenshi. Abiey ya busar da iskar bakinshi ya dora kafa daya kan daya. “Darasi kawai nake son a koya masa kuma yau din nan ba sai gobe ba” “Shikenan ka turo min address din, but ka kiyaye shiga irin area nan, that's why ba kowa namiji yake son neman aure a karamin gida ba” “I don't care as long as ina son yarinya su waye iyayenta be dame ni ba, i will text the address” Ya sauke wayar yana cika ma bakinshi iska, Aisha ta kalli kanwarta Siyama. “Siyama ki tafi da lace din, idan kawo mana ni da Narjis” “Okay” Ta amsa sannan ta mike tsaye ta fice tana ta waigen Abiey. Aisha kuma ta tashi ta nufi ďakin Anty Amarya. Yana sauke wayar ya aika mashi da address din, sannan ya kishingida jikin kujerar ya rufe ido, ba dan Zahra ba da Allah kadai ya san yadda zai yi da mutumen nan, domin a yau ya bata mashi rai fiye da ďanshi. “Abiey....” Ta kira sunanshi tana saukowa stairs din da saurinta Aisha na biye da ita, gyara zamanshi yayi ya kalli Anty yana jin kamshi na sarawa. “Me ya faru? Aisha ta ce ka shigo cikin bacin rai” Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya labarta mata abun da ya faru. “Da alama dai gaba dayansu ba su da mutunci” “Ba shi ya haifi Zahra ba, ba su hada komai da shi ba sai abokantakar da yake da Babanta sai kuma auren mahaifiyarta da yake yanzu” “Abiey ka saurare ne” Ya juyo yana fuskantar ta. “Ka dagawa area kafa ita kanta Zahra ka bata time na san a yanzu kuna son juna kai da ita, amman ka sani abu kadan zai iya ja maka matsala kuma kasan waye mahaifinka ya kamata ace kana barin wani abun ko dan wani” “Babu abun da zai taba mutunci ko martaba a nan balle har ya shafi Mai Martaba, kawai dai bana son Ammy ta hana ni aikata abun da na yi niya ne shiyasa ban je gida a haka ba” “Yana da kyau duk abun da zai zubar maka da mutunci ka kiyaye Abiey, ba dan yau ba tun ranar da ka fada min cewar Zahra ta yarda da kai ina son na yi magana da kai ya kamata ace kana tunani idan zaka yi abu” “Anty kin san yadda nake son Zahra bana son ki fada min wata magana marar dadi akan ta please” Ya fada ta sigar da zata fahimta ita kuma bata da wata mafita sai ta hakura ta kyaleshi domin ta fahimci ba zai gane karatun ta a yanzu ba. Mikewa yayi tsaye “Zan tafi sai da safe” “Allah ya ba mu alheri” Ya amsa da Ameen sannan ya fito cikin gidan ya nufi motarshi, da fari da ya shiga motar sai ya kwantar da kujerar ya kunna motar ya kara gudun ac har lokacin ji yake kamar hukuncin da ya saka ayi ma Mahaifin Deen be wadatar ba. “ƙut” Yayi kwafa sannan ya tashi zaune yayi reverse ya fice daga gidan gaba daya. Kamin ya isa gidan Ammy Zahra ta kira wayarshi, sai da ya hade yawu sannan ya yi picking. ZAHRA POV. Haka muka kwana cikin zullumi da tunani halin da Baba yake, washe gari ana saukowa daga sallah asuba Yayan Baba ya kwankwaso mana kofar wato Baba Mani domin Mama ta kira tun cikin daren ta fadawa Matarshi sai dai be samu zuwa ba sai yau. Da ni ya fara gaisawa kasancewar ni na fara bude mashi kofar gidan ya amsa min hankali a tashe irin na dan'uwa mai damuwa da dan'uwanshi. “Ina Maman ta ki take?” “Tana ciki” Na amsa mashi sannan na nufi dakin Mama kamin na karaso sai gata ta fito sanye da Hijab idonta a kumbure carji na rike a hannunta. “Yaya Mani ne?” “Eh an tashi lafiya” “Alhamdulillah Ammy Bismillah” Gaba dayan mu muka dunguma muka shiga dakin, ni na zauna a kasa ita kuma ta zauna kan gadon Baba Mana ma kasa ya zauna kasancewar babu wani abun zama kuma ba zai yiyu ya zauna kusa da Mama ba. “Jiya ko da kika kira ji ina hanyar dawowa daga Kwarzo, kuma ban shigo da wuri ba shiyasa ban samu na zo ba” Mama na matsar kwalla ta labarta mashi abun da ya faru, sai ya girgiza kai yana. “Subhanallahi abu be yi dadi ba, Shi ma dai ai ba a haka talaka ma ba zaka taba wani ba ka zauna lafiya balle masu gari, yanzu ga abun da ake gudu kenan ai” “Kuma ba abun da ya fi daga min hankali kamar rashin sanin inda aka kai shi” “Shi yanzu mutumen ina za a ganshi? Sai a bashi hakuri ko zai ji ya hakura ko kuma ki yi mashi magana Zahra” Ya karasa yana kallona. Sai na dago na kalleshi for the first time a yanzu na ji rashin kyautarwar abun da Abiey yayi domin Mama na ta damu kuma na san sauran yan'uwanshi ma za su damu, kuma kowa laifina zai gani domin a dalilina komai ya faru. Kamar Baba Mani ya san tunanin da nake kenan sai na jinkayo muryarshi yana fadar “Amman tsakani da Allah Zahra bata yi dadewar da za a ce ta fara kula maza ba a yanzu, kuma indai a kan haka ne yayi magana yana da gaskiya domin Zahra ni kaina ya ce a gurina balle kuma shi, ya kamata Mutumen nan ya girmama shi a matsayinshi na magabacin Zahra” Na sauke kaina kasa, Mama ta kasa cewa komai sai dai ina karantar kunnar ranta da ya nuna a fuskarta, lokaci daya muka mike tsaye cikin tashin hankali kowa da kalar salatin da yake ni kuma na dora hannu saman kai na duke kasa saboda mugun karar da na sake ji mai kamar jirgi ya fado. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un” Mama ta fada sannan ta riko hannuna muka fito daga ďakin, sai muka tsinci kam mu a tsakar mai kamar da tsakar fili, domin an rushe katangar dake gaban mu wanda ta tare da kofar gidanmu, an kuma rushe wanda ke gefen gidanmu. “Su waye wadannan? Me muka musu?” Mama ta tambaya hankalinta a tashe. Baba Mani ya nufi ind dayar motar dake rushe gini take aje domin jin ba'asi, dayar motar kuma ta nufo inda muke tsaye gadan gadan kamar mu ma zata kwashe mu da gudu muka bar gurin ni da Mama, Mama ta nufi gurin su Baba Mani ni kuma na dawo gurin dayan dake kokarin rushe mana gini ina mashi hannu amman be kula ni ba, cikin bulon da suka rushe nana na gini na dauki wasu na fara jifar motar ta su da duk kalar duwatsun da na samu kamar wata mahaukaci haka na zama har sai da na kashe motar bayan ya riga ya rubar da ginar dakin Mama ya fito ya nufo inda nake tsaye. “Ke baki da hankali ne?” “Ba ni da hankali, Azzaluman banza me muka muku da zaku rusa mana gida?” “Abiey ne ya saka mu yi mu umarni kawai muke cikawa” “Abiey...!” Mutumen ya fada min sai na maimaita sunan ina mamakin yadda Abiey zai saka a rushe gidan da muke kwana, bayan kuma ya san ba ni da inda zan raba da yafi min nan. Na nufi inda Mama da Baba Mani suke tsaye kamin na karasa Mama ta nufo ni sai muka hadu a tsakiyar gidan da zan iya kira da fili wannan karon hawaye shar nake gani a idon mahaifiyata har sautin kukanta yana fita, kukan da na dade ban gani ba, mutane sun zagaye mu sai kallo suke an rasa wanda zai saka baki yayi magana. “Zahra sun ce Abiey ne ya saka su rusa gidan, ki kirashi ki ce yayi hakuri dan girman Allah, mu zai saka a matsala ba Malam ba, dubi mutanen da suka mana taro kowa so yake ya samu abun gulma kuma kowa mu zai dorawa laifi” Sanyin saukar hawaye na ji a kumatuna, zuciyata na raya min kamar Abiey ba zai yi haka ba, sai na samu kaina da kasa cewa eh ko aa, domin ba ni da tabbacin shi din ne ko akasin haka, idan ma ba shi din ba ne to waye ne? Ai jiya shi ya aiko aka tafi da Baba kuma na yi magana da shi miyasa be hakura har sai ya turo an rusa mana gida? Duk cikin fushin ne?amman ban san Abiey da irin wannan zafin zuciyar ba. “Kayan mu” Mama ta fada tana kallon motar da mutumen da yayi min magana ya kunna ya nufi dakinta, ni da ita muka ruga a aguje domin kwashe wasu kayan kamin a rusa mana dakin, matan makota da a yanzu suka fara fitowa suka biyo bayanmu mazan da suke abokanin Baba kuma suka nufi motar domin sake yin magana da dayan mai rusa gidan, gurin da Mama take aje kudi ta fara lalabe sai dai yadda suka nufo mu da motar na tabbatar idan suka tararda mu taka mu zasu yi da motar domin ba da wasa suke aikinki ba. Hakan yasa na ja Mama muka bar kayan a nan mutanen da suka fara taya mu diban kayan su ma suka gudu, haka muka tsaya a gefe muna ji muna gani aka rusa ko wane bango na gidan saka mai da shi fili, wani bangare na ginin har ya sauka kan ginin makotanmu. “To miye amfanin haka? Wannan ma ai ya zama zalumci taya zaka rusa gidan mutum bayan ka kama shi ka boye Allah kadai ya san abun da zai saka ayi masa, waya sani ma ko ya kashe shi” Shi ne abun da Baba Mani yake fada kamin ya fara labartawa makotanmu abun da ya faru, daman jiya a gaban idon wasu komai ya faru. “Mama bari na kira Abiey” “Ki kirashi ki ce mashi me? Aikin gama ai ya gama, wayar ma ban san inda take ba” Mama ta fada tana share hawaye, sai wata makociyar mu ta bukaci mu shiga gidanta mu zauna domin a inda muke tsaye fili ne ba gida ba. [11/2, 12:20 AM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣5️⃣ A lokacin da ya isa gidan be fada ma Ammy komai ba, sai dai be isa ya boye mata damuwarshi ba domin abun a bayyane yake a fuskarshi, tea da yake sha ma wani lokacin idan kwanta yau be sha ba yana shigowa ya shiga ďakinshi ya kwanta. Hakan kuma ba karamin mamaki ya bawa Ammy ba, domin ta san ďanta tsakanin jiya da shekaran jiya zuwa yau yana cikin farincikin da ya dade be samu ba. Sai da ya gaji da kwanciya ya shiga bandaki ya watsa ruwa ya fito ya yayi abun da ya zame masa wajibun wato saka turare sannan ya saka karamin wando ya kwanta ruf da ciki ya yi dora kanshi akan fili ya rutse ido, kamar an tsikare shi sai ya tashi zaune ya dauki wayarshi ya rike a hannun ya kama number Mama da Zahra take kiranshi da ita yana ta kallo kamar ya kira kuma yana ganin haka be dace ba, saboda abun da ya faru a yau. Ya busar da iskar bakinshi ya koma ya kwanta ya dora wayar a kirjinshi, kamin ya dago ta ya kira yayan shi, ringing biyu ta yi be daga ba, be kara mashi kira na uku ba ya aika mashi sako. _Ya Auwal ka sa a saki mutunen nan kuma kar su illata shi please_ Yana gama tura sakon ya ja blanket ya lullube ba dan yana jin bachi ba, babu abun da ke yawo a kwakwalwarshi sai tunanin Zahra, he wanted to call her so badly amman yana shakar yin haka saboda Mahaifiyarta. “I shouldn't” Ya furta yana rufe ido kamar mai bachi. “But mutumen nan ya wuce gona da iri ai, ďan shi yayi min yanzu kuma shi? No i can't tolerate it” Ya sake fada still idonshi a rufe, Ammy ce ta turo kofar ďakin ta leko tana kallon ďanta, already ya ji motsin murda kofar dakin da Ammy ta yi ta bude, kuma jikinshi ya ba shi cewar ana kallonshi hakan ya saka ya dago har ya kalli kofar. Ammy na ganin haka sai ta karaso cikin ďakin ta zauna kusa da shi tana kallon kamshi. “Aliyu ka samu matsala da Zahra ne?” Ya tashi zaune yana kallonta. “Ko da Mai Martaba?” Nan ma be ce komai ba kamar mai tsoron fada mata. “Ko kuma a bangaren kallon ne wane abu ya faru? Ko ka yi fada da wani ne?” “Babu ko daya Ammy zan kwanta ina jin bachi” Ya amsa mata a tunaninsa be dace ya fada mata haka a yanzu ba, domin kuwa baya son Ammy tana jin wani bad abu yana faruwa bangaren Zahra. “Okay Good Night ka yi addu'a kamin ka kwanta” “Okay” Ya fada yana komawa ya kwanta Ammy ta bishi da kallon dake nuna cewar akwai abun da Abiey yake boye mata, ta dade zaune a ďakin har sai da ya fara runtse ido sannan ta tashi ta fice, tana fita ya bude idon ya kwanta rairai yana kallon ceiling, sai da yayi yakin gaske sannan bachi ya dauke shi be farka ba sai Asuba, sai da ya fara rage ace dakin sannan ya shiga bathroom yayi alwala ya fito ya gabatar da sallah Asuba a dakin, bayan ya gama ya dora da karatun Alkur'ane, sai da rana ta fito sannan ya rufe karatun ya maida kur'anen a muhalinsa ya bude windows rana ta hasko ďakin na shi sannan ya koma kan gadon ya kwanta ya mika hannunshi ya dauko wayarshi, ba tare da tunanin komai ba ya kira number Mama da zimmar zai gaisa da Zahra, ko kadan jin wayar a kashe be mashi dadi ba har ga Allah muryarta ya so ya fara ji, domin rabin mafarkinsa nata ne. Aje wayar yayi a gefe ya koma bachinsa na safe da yafi ko wane bachi yi mashi dadi. Kamar mataccen haka ya rika sharar bachi mai nauyi ko motsawa baya son yi, daman dabonshi da bachi mai nauyi irin haka har ya manta. Daker Ammy ta tashe shi, shi ma sai da ta hada da girgiza shi. “Aliyu” “Na'am” Ya amsa kana ya motsa ba tare da ta bude ido ba. “Wannan wane irin bachi ne? Tun safe har 10 na safe” “Ten ta yi” “Har ta gota, ka tashi ka shirya kana da baki” Ya bude idonshi da ya takure saboda bachi ya kalleta. “Guest?” “Yeah” “Kuma ni suke son gani?” “Eh yan jarida ne” Tashi yayi zaune. “Yan jarida? Me zai kawo su gurina?” “Kana magana kamar baka san waye kai ba? Maybe suna son tatattaunawa da kai ne akan wani abu” “Ba a tattauna sa ni haka nan Ammy har sai an rubuto min takardar da neman izini idan na amince na bada dama ake yi amman ba haka nan kai tsaye ba” “Idan kuma wani abu ne da ya shafi aikinsu fa? Domin ba ďan jarida daya ba ne” Abiey ya sauka saman gadon da sauri ya nufi gurin windo dake fuskantar harabar gidan ya leka sai dai be iya hango kowa ba. “Da gaske Ammy?” “Karya zan maka Aliyu? Tun jiya na lura baka cikin natsuwa idan akwai wata matsala ka fada min” “Matsalar dake akwai bata kai yan jarida su ce za su yi hira da ni ba, waya ma ya ba su izinin shigowa?” “Ni” “Suna ina?” “Kofar falo” Bathroom ya nufa ya wanke bakinshi a gurguje ya fito ya be damu da canja jallabiyar dake jikinshi ba wanda yayi sallah da ita da asuba ba ya nufi kofa ya fice kamin ya sauko downstairs, Ammy ta tsaya tsakiyar stairs din tana kallon Abiey da ya nufi kofar fita falon. Hannu ya kai ya bude kofar falon ya fito waje yana kallon mutanen da sai a yau ya taba ganin fukokinsu su kusan shida biyar maza mace daya, ganinshi yasa suka mike tsaye suka karaso inda yake tsaye yana kallonsu da saurinsu two of them na dauke da camera yayinda biyun kuma suke rike da microphone one of them kuma tana rike da pen da abun rubutu. “Safiyar yau aka wayi gari da sabon labari cewar ka saka an rusa gidan wani magidanci sakamakon gargadin da yayi maka cewar baya son ganin ka kofar gidan, har wasu na cewa ka saka an sace mutumen ba a san inda yake ba a halin yanzu” Abiey ya kalli mai mashi tambayar yana mamakin yadda yake kirkira marar karya kuma ya jefe shi da tambayarta. “Da gaske ne kana neman yar gidan ko kuma rade rade ne?” Mace ta tambaya a nan ma juyowa yayi ya kalleta. “Gaba dayanku ba ku iya aikinku ba, ba kananan yan jarida ke hira da ni ba manya” Yana gama fadar hakan ya juya ya bude kofar falon ya koma ciki, gurin da Telephone din falon take ya nufa na kira masu kula da gate din. “Karka sake bari wani ya shigo cikin gidan nan da sunan aikin Jarida, idan na sake ganin yan jarida a gidan nan to a bakin aikinku” Ya maida wayar a muhallinta sannan na nufi stairs da tunani kala kala da mamaki, mi zan saka yan jarida su yi mashi irin wannan tambayar idan babu rame mi ya kawo maganar rame? And waya gayyoto yan jarida a gurin ma abun da ya faru da dare? Yana tsaka da jerawa kanshi tambayoyi Ammy ta jefo mashi wata. “Me ka aikata Aliyu?” Ya tsaya daidai inda take tsaye a lokacin da ya jingina. “Ammy ban yi wani abu ba, abun da na sani kawai mun samu matsala da mahaifin Deen a jiya” “Mahaifin Deen? Miye hada ka da mahaifinshi?” “Na je ina son zan yi magana da Zahra ne sai ya fito ya fara fada min magana yana cewa kar na sake zuwa gurin a gabana ma ya mari Zahra” “Ni ban gane wannan maganar ba” “Ammy kin san Mahaifin Deen shi ke auren mahaifiyarta maybe yana jin haushi ne, ni kuma da ya min haka sai na kira Ya Auwal na fada mishi abun da ya faru kuma na bukaci ya saka a kama mahaifin ayi masa duka, na tura mashi address din kuma ina tunanin ya aikata, but kamin na akwanta jiya na fada shi ya sa a sake shi” “Yankin Kano ba hurumin shi ba ne, miyasa zaka saka shi ya aikata ta haka? Aliyu ina ta hango maka matsalolin da suke tattare da yarinya gashi tun yanzu abubuwa marasa dadi sun fara faruwa, ka san kuma mutane abu kadan suke jira su fara yadawa gashi muna zagaye da makiya ta ko'ina, abu kadan na samun ka dadi za a ji, jiya jiya da faruwar abu ace yau har yan jarida sun shigo gidan nan neman karin bayani? Idan wannan labarin ya samu Mai Martaba ya kake tunanin zai ji?” “Ammy ki daina zafafa abu dan Allah, wannan abun har wata magana ce da zata je kunnen Mai Martaba? Idan ma ta je i can explain...” Ammy ya sakar mashi ido irin kallon nan na mamakin yadda yake maida komai ba komai ba. “Me ka fadawa yan jaridar?” “Ban yi magana da su ba” Ya amsa mata ya sannan ya fara takawa ya karashe hayewa Ammy kuma ta bishi da kallo har ya shige ďakinshi sannan ya sauko falo ta zauna ta dialing number babban ďanta,tana kwalawa Jummai dake kitchen tana wanke wanke kira “Jummai” “Na'am Hajiya” Jummai ta fito da sauri tun kamin ta karaso Ammy ta ce. “Fruits zaki yankawa Aliyu, maybe ba zai karya da ruwan zafi ba yau ki kai mashi ďakinshi kamin ya fito” “Toh Hajiya” Jummai ta amsa sannan ta juya da sauri ta koma kitchen din, Ammy kuma ta dauki remote ta rage volume din plasma tana amsa sallamar da Ya Auwal. “Wa'alaikassalam” “Ammy an tashi lafiya” “Lafiya kalau ya iyali?” “Alhamdulillah, har na ji kunya sosai Wallahi.ya kamata na kira aiki ne yake saka mu gaba” “Wane irin aiki ne da zai saka ka manta da iyayenka, kai da ďan'uwanka halinku daya, shi da yake ba ya kasar sai dai mu gaisa da chat” “Ammy Wallahi abubuwan ne ba daya ba, kuma kin san daman kusan karshe karshen shekarar nan aiki ya kan yi yawa, amman da zan mun samu natsuwa ina son zan dauki hutu na dawo gida na yi wata daya” “Hmmn yanzu dai ba wannan ba, na kira ne akan maganar Aliyu yace ya saka ka kama wani” “Eh yau da safe ma na ga sakon shi cewar a saki mutunen kuma na fada musu za su kai shi har gida” “Me yace ayi mashi?” “Kawai dai ya nuna min yana son ayi mashi horo ne kawai” “Okay da mijina” “Zai ji, akwai wata matsala ne Ammy” “Aa Allah ya muku albarka ya shirya zuri'a” “Ameen na gode Ammy Allah kara miki lafiya” “Ameen” Ta amsa sannan ta yi mashi sallma ta sauke wayar, ta dago tana kallon Abiey da ya sauko cikin shiga ta shadda kanshi da sauran ruwa, da alama wankan kawai yayi be tsaya shafa komai ba ya saka tufafinshi ya fito uzurce keys din mota a hannunsa dayan hannunshi kuma rike da waya. “Ina zuwa?” “Gidansu Zahra i need to see her” “Breakfast fa?” “Maybe sai na dawo” “Na saka Jummai ta yanka maka Fruits” “Ba zan iya cin komai a yanzu ba Ammy sai na dawo” Ya amsa ta yana duba wayarshi dake ringing, be bata lokaci ba ya amsa kiran. “Sauban” “Abiey me yake faru?” “Ban gane ba” “How online zan turo maka wani labari da wasu gidan jaridu online suka buga” Abiey ya kai zaune tare da sauke wayar gabanshi na mugun faduwa, data ya kunna tunani kala kala suna bijiro mashi, sai da sakwanin da aka turo mashi suka fara shigowa sannan na Sauban yayi appearing sama. Da kamar tsoro ya taba chat din ya bude sai idanuwanshi suka fara arba da wasu hotuna da jaridun online suka wallafa. *Fitaccen Jarumin kwallon kwando Aliyu Abubakar Aliyu da aka fi sani da Abiey ya rusa gidan wani magidanci saboda ya hana shi magana da agolarshi* “Abiey ya saka an rankadawa wani magidanci doka, kuma ya rusa gidanshi a dalilin wata yarinya dake zaune a gidan* *Da gaske dan Sarkin Kano kuma fitaccen jarumin wasan kwallo kwando Abiey ya doki wani tsoho saboda budurwar da ake riko a gidan?* *An rusa gidan wani magidanci saboda mace...* *Fada tsakanin talaka da mai kudi, Abiey ya rusa gidan su talaka saboda ya hana shi mu'amala da yar da yake riko* *Me yake faruwa da ďan Sarkin kano?* Ko wane gidan jarida da kalar kanun labaranshi da suka buga labarin da shi, sun yi ado da katon hoton Abiey, wasu sun saka a inda yake sanye da kayan aikinsa wato na buga wasan kallonn kwando, wasu kuma manyan hotunanshi masu zafi dake trending a instagram suka dauka suka saka. Gidan jarida biyu ne suka saka hoton gidan da aka rusa, suka saka hotonshi a gefe. Abiey ya mike tsaye da sauri ya shiga kiran number Mama sai ta ji ta a kashe kamar dazun. “What is happening here? Waya yayi wannan aikin? Why? Who do this?” Ya fara safa da marwa a falon yana sake gwada number Mama, but still switch off. Jumma ta karaso inda yake tsaye ta janyo karamin tebur ta dora mishi plate din fruits. “Gashi ranka ya dade” Be kula ta ba balle ma plate din, sai kallon wayarshi yake da kiran Anty Amarya ke shigowa, kiranta na yankewa na Dr Zainab ya shigo nata ma na yankewa na Sauban ya sake shigowa, haka aka rika jero mashi kira har da old friends ďanshi da suka jima ba su kira shi ba, kuma ya kasa picking call ko daya, da sauri ya saka wayar aljihu ya nufi stairs din da kamar gudu ya shiga dakinshi ya bude gurin da yake ajiyar mask ya dauko baki ya saka ya bude gurin ajiyar glasses dinshi ya dauko kato wanda ke batar da fuskar mutum ya saka ya fito, kamin ya sauko downstairs Ammy ta kai tsaye waya a kunnenta dayan hannunta kuma dafe a kirji. “Ina zaka je?” “Someone is behide this Ammy, jiya jiya da faruwar abu amman har gidajen jaridu sun buga labaran karya, kuma ni ban saka a rusa gidansu ba, dole akwai hannun wani a cikin lamarin nan” “Don't tell me rubbish...” Ammy ta daka mishi tsawa, sai ya ja ya tsaya a gurin kamar hoto yana kallon yadda ran mahaifiyarshi ya bace, ta dayan bangaren kuma kiran Aisha na shigo wayarshi. JAMILA POV. Tana da safa da marwa da a dakin hawaye na mata zirya sai aikin jijjiga Amir take dake kafadarta yana rusar kuka kamar zai mutu, tun kamin suna rabon shi da shan nonon Zahra, ranar da aka yi sunan ma ya wuni a wahale da ciwon ciki ga daukar da ya sha a gurin mutane, domin an yi taron da har bata iya gane wasu mutanen, an kashe dokiya kamar domin ranar aka tanade ta, ga kyaututuka da ta samu daga manyan mutane da matansu, kawayenta yan'uwan mijinta da kuma makota da abokan kasuwanci, Sunan mahaifin Mr Bashir yaron ya ci wato Ibrahim sai aka yi masa lakani da Amir, yaro ya samu soyayya ta ko'ina a gurin danginta ba ba a gurin dangin mahaifinshi ba sai ka rantse da Allah akan ta aka fara haihuwa kuma sai bne ďa na karshe da za a sake haihuwa a duniya. Sai dai da haka hankalinta ba a kwance yake ba saboda kukan da Amir na ciwon ciki, har yanzu cikinshi ka ki ya saba da noninta, balle kuma madara da ake kadawa na ba shi, duk wani abu da take ganin mafita ne ta gwada be yi ba, har nonon wasu matan an gwada bashi amman abun be karbe shi ba, yaron sai rama yake yana yawan kuka saboda ciwon ciki, ita kuma har ga Allah bata son sake waiwayar Zahra, duk kuwa da irin damun ta da Mr Bashir yake da tambayar Zahra, tun bayan da ta yi mashi karya cewar mahaifiyarta bata yarda ta yi aikin ba, da ya nemi sanin inda take kuma sai ta nuna mishi ita ba bata san inda Zahra take rayuwa ba, kuma matar da ta kawo mata ita ma bata sake zuwa ba, gashi ba su da number juna, sam bata yarda ta nuna mishi cewar Yayanta Dr Hamid ne ya kawo ta ba, hakan kuma be yi ma Mr Bashir dadi ba domin yayi niyar kyautata mata iya kar kyautatawa. A razane ta juyo ta kalli kofar dakin da aka turo, wani mugun faduwa gabanta yayi a lokacin da ta yi arba da wata likitar dake tare da mijinta. “Bismillah Dr Zainab” Ta aje Amir a gadon da aka tanadar mashi na yara tana kallon mijinta kamar idonta zai fado. “Sannu” Dr Zainab ta ce da Jamila tsabar hankalinta baya gurin bata iya amsawa ba sai kallon mijinta take. “Baka fada min zaka zo da likita ba” “Wata kila idan na fada miki zaki kawo wata shawarar ne, idan na ce ki je asibiti ba zaki je ba yaro sai cutuwa yake, baki yarda kowa ya duba shi ba sai dan'uwanki kuma be zama lallai ya san komai ba domin komai da muhalinshi” Ta hade yawun bakinta tana jin yadda makoshinta ya bushe kamar bata taba jika shi da yawu ba. “Duk likita likita ne Hubby, bana son a matsawa yaron nan ne, ni kadai na san wahalar da na sha kamin na same shi ni kadai na san yadda nake jin yaron nan a raina, amman tun da ka matsa zan kai shi asibiti yanzu nan” Ya kai hannunshi ya dafa ta domin ya lura da damuwar da matarshi take ciki ga hawaye har yanzu basu daina mata zuba ba, dazun na tausayin Amir ne yanzu kuma na tashin hankali ne da faduwar gaba wato tsoro. “Ki kwantar da hankali wannan kwarariyar likita ce, Alhaji Habibu ne ya hada ni da ita kawai ki yi fatan Allah ya ba shi lafiya” “Ameen Allah” Ta fada tana kallon yadda Dr Zainab ta dago shi tana dubawa. “Wannan ba abu ne da za'ayi a cikin gida ba, na san ku manya ba ku son kwantawa asibiti amman dole ne wannan saboda ayi wasu gwaje gwaje kuma mu gano daga ina matsalar take, domin mu bincike abun da yake yawan saka shi ciwon cikin kuma miyasa nonon mahaifiyarshi ma yake saka shi yin haka? Duk muna bukatar sani idan ta kama har nono zamu gwada” “Ba matsala mu dai batan mu ya samu lafiya” Dr Zainab ta maida yaron a inda yake kwance ta nufo Jamila dake tsaye. “Idan ya sha nono yana amai? Kuma kina daukar awa nawa kamin ki bashi nonon?” Amaimakon ta amsa sai kawai ta fashe da kuka ta fice daga dakin, Mr Bashir ya kalli Dr Zainab yana murmushin karfin hali ya ce. “I'm sorry hankalinta duk ya tashi akan ciwon yaron nan, kuma ban fada mata zan zo da ke ba, domin bata son a taba yaron nan ko kadan lemme talk to her” Dr ta mayar mashi da murmushin da ya bata sannan ya juya ya fice ita koma ta maida hankalinta gurin yaron. [11/3, 7:43 PM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣6️⃣ Ya nufi kujera ya zauna ya aje wayar a gefe. “Yaushe ka lalace har haka Aliyu? Akan me zaka saka a dauke tsohon mutane? Wannan abun ya zama hauka, baka san yana da ikon a kan Zahra a matsayinshi na aminin mahaifinta? Ko ka manta da mahaifiyarta yake aure? Wannan abun da ka aikata ya gyara abun ne ko kuma ya kara bata shi?” “Ban yi da nufin komai ba, sai dan bata min rai da yayi, Ammy wannan abun yayi yawa ďan shi yayi shi kuma yanzu yace zai dora?” “Kasan ba zaka iya ba ka fara? Akan me zaka dauki halin da ba naka ba ka ratayawa wuyanka? Wannan abun ya tashi daga soyayya kuma ya zama wani abun na dabam, domin gashi ya taba Martaba gidan nan ya taba kimarka ya taba kimar Mai Martaba domin dole za a ce ďanshi ne, da wans idon zaka kalleshi ma? Daman can ba jutuwa kuke samu ba balle kuma yanzu? Miyasa idan zaka yi abu baka tsayawa ka yi tunani?” Ya tashi daga inda take zaune ya karso kusa da ita ya tsaya. “Ammy ki saurareni dan Allah, ban saka a rushe gidansu yarinyar nan ba, me zai saka ma na yi mata haka, ni kawai na ce a dauki mutumen nan a yi masa horo so that ya san ba a bata mutane irin a zauna lafiya” Ammy ta nuna shi da yatsa. “Kai ka karya mashi dokar gida, saboda haka yana da ikon ya hukunta ko yace ka daina zuwa kofar gidanshi, arziki da sarauta da daukaka ba hauka ba ne, maganin kar ayi kar fara idan da baka je kofar gidanshi ba da be ganka ya wulakanta kaba” “Ammy ba gurinta naje ba gurin Zahra...” “Ya isa haka wai Zahra ce kadai mace a duniya da idan baka same ta ba zaka mutu a gwaro? Ina ce Mai Martaba ya tambaya maka Yasmin? Ko ka manta? Yanzu me zaka fadawa duniya? Zargin da aka fara yi a kanka zai iya fin haka ma, daman mutane kadan suke jira, ka kyale yarinya Aliyu bana son na sake jin sunanta a bakinka na gaji” Kanshi ya sauke kasa yana jin wani yanayi marar dadi. “Na ji na yi kuskure amman ba ni na saka a rusa gidan da suke ciki ba” “To waya saka? Waya san ka dauke shi? Dole akwai mai bibiyarka, yanzu kuma an samu damar tun da ka bada kofa, daman be kamata kana zuwa gidansu yarinyar nan ba yaushe mijinta ya mutu? Da har zata fara kula wasu? Kuma macen da ta yi haihuwa? Allah kadai ya san abun da wasu jaridun za su buga nan gaba” “Ammy ina son na yi magana da ita” “Na fada maka ka dauke kafarka daga gurinta? Yanzu ba matsalar da ta faru nake kokarin solving ba? Shi zaka taka kafa kaje gidan? Mutanen unguwar su saks ganinka?” “Ammy idan an rusa gidan da suke zaune ai dole na nema mata wani da za su zauna” “Ba yanzu ba, ka bari mu gama da wannan matsalar tukuna” Ammy na fadar haka ta kalli wayarta dake ringing. “Mai Martaba...” Abiey ya kalleta da sauri cikin matukar tashin hankali, sai da Ammya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta amsa kiran ta kai kunnenta gabanta na faduwa. “Assalamu Alaikum” Tarar dakiku goma ya bada sannan ya amsa mata. “Wa'alaikissalam ďanki yana kusa?” “Eh yana kusa Mai Martaba” “Ki turo min shi yanzu nan” “Toh” Ta amsa sannan ta sauke wayar idonta na duban Abiey. “Mai Martaba yana nemanka, sai ka tanadi irin amsar da za ka ba bashi” Kanshi ya daga sama ya sauke ajiyar zuciya. “Karka yarda da amsa cewar ka saka a kama shi, amman ka fada mashi ka je kofar gidan idan ya tambaye ka dalili ka fada mishi cewar yarinyar da aka fasa aurenka da ita ce, ai ya san lokacin sai dai ace be santa ba” “Amman Ammy mi zai saka na ce ba ni na sa aka kama Baban ba bayan kuma ni ne?” “Idan ka amsa cewar kai ne, zai iya yarda kai ne ka rusa gidan, amman idan kofar gidan kawai ka je babu wata hujja dake nuna haka, kuma karka nuna mashi ka yi sa'insa da shi” Ya daga mata kai alamar gamsuwa, kana ya cira kafa ya taka zuwa kofa, kamin ya fice kira ya sake shigowa wayarshi, da mamakin shigowar kiran ya janyo kofar falon ya rufe yana picking call din. Daga shi har ita aka rasa wanda zai ce fara magana, sai da ta kira shi take jin nauyin yi mashi magana, shi kuma ya gagara cewa komai jira yake ya ji abun da zai fara fitowa bakinta. “Idan baki da abun fada zan kashe wayar i have something important to do” “Na kira ne kawai na ji lafiyarka” Ba kira ne neman jin lafiya kadai ba domin bata taba mashi makamacin irin wannan kiran ba, labarin abun da ake zargin ya aikata ya je mata a kunnenta sai dai bata san taya zata fuskance shi da maganar ba, me zata ce mashi? Zuciyarta na raya mata Abiey ba zai iya aikata hakan ba musamman a lamarin abun da ya shafi Zahra, to waya aikata? Kuma miye dalilin aikatarwa? Sosai take jin damuwa domin hakan ya taba martabar gidansu da kuma kimarshi, duk wanda ya aikata haka yayi ne domin neman bata mashi suna da taba darajar gidansu, lura da yadda kowace gidan jarida suka yi na su shimfidar labarin, comments din mutane kowa da kalar fararsa da yake mashi har da masu cewa Zahra kasuwarshi ce, wasu kuma su ce neman lalata mata rayuwa yake, sam abun be mata dadi ba. “Lafiya ta kalau na gode da kulawa” Ya amsa mata bayan yaja dogon numfashi ya sauke. “Mu wuni lafiya” Ya kasa furta komai har ta yanke wayar. “Oh Ya Rabbi Allah” Ya fada yana jin ina ma be aikata ba, yanzu a wane hali Zahra take ciki ita da mahaifiyarta? Nunberta ya sake gwadawa aka tabbatar mashi da wayar a rufe take har lokacin, hakan ya saka shi yanke shawarar kiran Dr Zainab yayinda yake kokari kunna motar. Ringing biyu ta yi kamin ta yi na uku ta dauka. “Abiey na kira baka daga ba kana da abun da yake faruwa kuwa?” “Na san komai Dr” “I don't want to ask you amman...” “Ban aikata ba, all what i know is na saka a kama mutumen yau da safe kawai sai ga yan jarida a gidan nan suna min tambayoyi Sauban kuma ya turo min hoton da ake ta yadawa a media, ban san wanda ya rusa gidan ba, ina ta kiran number Maman Zahra bata shiga, that's why i call you alfamar nake son ki yi min ki je gidansu ki bincika min saboda Ammy tace kar na je da kaina” “Ni ma ina gidansu Mr Bashir Auta idan na fito gida zanje, amman zan bincika gurin Zahra” “Thank You” Ya saka wayar aljihunsa sannan ya yi ma motar key, tun kamin ya isa masarautar gabanshi ke mugun faduwa kanshi har sarawa yake. Lokacin da ya isa masarautar bangaren Anty Amarya ya fara shiga yana kokarin hawa upstairs ya ji motsinta a kitchen tana magana da Aisha, sai ya sauko ya nufo kitchen din bakin kofa ya tsaya ya jingina da kofar, Anty dake aikin gyara allayahu ta juyo ta kalleshi cikin yanayi na damuwa. “Ina ta kiranka baka daga ba” “Anty idan na daga ma ban san me zan ce ba” “Mai Martaba yana son magana da kai” “Ya kira Ammy” Anty ta matsa kusa da shi. “Ka yi hakuri da duk abun da Mai Martaba zai fada maka, kuma karka musa mashi, kuma ina fatar baka aikata” “Ban rushe gidan ba, amman na saka an kama mutunen” “Wani lokacin muka bukatar taka tsantsan saboda mutunci da kimarmu, Abiey da zaka hakura da yarinyar nan wata kila shi zai fi zama alheri, ina ta son na maka magana akan karka tunkari Mai Martaba da maganar nan har sai abubuwa sun daidaita sai gashi wannan abun ya faru” “Ko da ba yanzu ba dole ne na sanar da Mai Martaba, ni kaina ban jidadin yadda labarin zai riskeshi a yanzu ba, amman dole zai sani domin aurenta nake son yi ba zaman banza ba” “Yanzu dai mu tafi kar yace ka bata mashi lokaci domin dazun a tare ya tara mu gaba daya yace na kira ka yana son magana da kai” Aisha dake gafe tsaye ta tabe baki. “Allah kadai ya san wanda ya isar wa Mai Martaba da labarin nan, kuma wannan abun ma akwai wanda ya shirya haka” Anty Amarya ta juyo ta kalleta. “Ko ma dai minene ya riga da faru, sai a kiyaye gaba, amman Abiey ka yi maganar nan da wani ne?” Anty ta karasa tana kallon Abiey. “Babu wanda na fadawa sai ke, Ammy ma sai a yau take samun labari Sauban ma ban fada mashi ba” “Ni fa gani nake kamar Siyama ta fitar da labarin nan, saboda lokacin da ka shigo ka zauna kana magana a waya tana falon nan muna duba Lace din angon Zubaida, na lura hankalinta gaba daya yana kanka kuma ta ji komai” “Ko da ta ji ai sai dai ta kai labari” Anty ta kalleshi tana murmushi. “Baka san halin makiyi ba Abiey, za su iya riga Malam Masallaci su aikata saboda a bata tsakaninka da Mai Martaba kuma a bata maka suna, daga Mama Lami har Hajiya Kilishi sun san gidansu Zahra kuma sun san abun da ke tsakaninka da Zahra” “Amman ba su san Zahra bata da aure ba” “Ai kamar ka bata labari ne, saboda ka yi maganar a gaban Siyama kuma mai son abun ka ya fika dabara, kai ma kuma an koya maka darasi domin ba a magana a gaban makiyi musamman irin wannan” “Ban kula ba ne saboda na shigo raina a bace, kuma ban yi tunanin wannan maganar zata saka ayi wani abu ba” “Ko daga yanayin yadda aka rubuta labarin ai kasan biyansu aka yi kuma am ba su labarin abun da ya faru ne, idan ba haka ba daga faruwar abu jiya jiya ace yau har ya shiga media” Hannayenshi ya saka Aljihu ya juyo suka fito tare da Anty suna tafi suna maganar har suka isa bangaren Mai Martaba, zaune suka same shi karamin mayafi a kafadarshi kanshi sanye da tsadadiyar hula ya dora kafafuwanshi akan tuma kasa (Titimi) kofin Shayi na gafenshi hannunshi kuma rike da waya har biyu. As usual Anty ta yi sallama, Mama Lami dake zaune kusa da kujerar Mai Martaba ta amsa mata, kallo daya Abiey yayi mata ya dauke kai ya zube a kasa ya kwashi gaisuwa Mai Martaba ko kai be dago ba balle ya amsa mashi, Hajiya Lami ta mike tsaye sai Mai Martaba ya daga mata hannu yayi mata alama da ta zauna, sannan ya kalli Anty. “A kira Hajiya Kilishi” “Toh” Ta amsa sannan mike tsaye ta fice, Abiey dai yana zaune a gurin kanshi a kasa. Anty bata jima ba ta dawo tare da Hajiya Kilishi suna tafe suna hira sama sama, a kujera daya suka zauna daga Hajiya Kilishi har Mama Lami kallon Abiey suke suna kallon junansu alamar gulma na cinsu Anty kuma idonta na kansu. Mai Martaba ya dauki tsawon lokacin ba tare da yace komai ba, har sai da ya gama abun da yake da wayarshi sannan ya mikawa Abiey wayar, Abiey ya kalleshi tare da mika hannu ya karbi wayar, hotunan labaran abubuwan da suka faru ne da hotunanshi. “Miya kai ka unguwar?” Kamar saukar aradu haka Abiey ya ji saukar tambayar Mai Martaba a kunnenshi, be taba jin tsoron amsa wata magana kamar yadda yake ji a yanzu ba. “Akwai wata yarinya da na yi nema shekara biyu da suka wuce, an mana baiko da ita domin ka san da maganar sai dai lokacin kana fushi da ni shiyasa baka saka hannu a ciki ba, sai su Baba Waziri ne suka yi komai, to mijin da ta aura ya rasu tana gidansu a yanzu shiyasa na je” Hajiya Kilishi da Mama Lami sun kalli juna. “Kana da wata alaka da yarinyar ne?” Abiey ya hade yawun bakinshi. “Ina son.. Ta... Ne Mai Martaba kuma ina fatar aurenta” “Ita ce yarinyar da muka nema maka aurenta?” “Allah ya baka yawan rai, ba ita ba ce amman ita ce yarinyar da na ke so?” “Ita kuma wacan fa?” Sai ya sauke kai kasa ya kasa amsawa, wata kila idan yace yayi haka ne saboda kar Mama Lami ta hada shi da yarinyar zai bata ran Mai Martaba domin zai ce yayi wasa da hankalinshu ne. “Magana fa ake maka Baba” Cewar Hajiya Kilishi, Anty ta kalleta tana dan murmushi domin ta san an sosa mata inda yake mata kaikayi ne. Abiey ya dago jiki a sanyaye “Mai Martaba Zahra ce yarinyar da nake so kuma nake fatan aure” “Ita kuma wacan ba aurenta zaka yi ba kasa na nema maka aurenta? Ko kuma zaka auri mata biyu ne dayar a boye?” “A gafarce ni Mai Martaba na yi kuskure kuma ina son na fada maka maganar Zahra ban samu dama ba ne” Mai Martaba ya gyara zama fuskarshi babu annuri ya ce. “Soyayyar ta ce ya saka Mahaifinta yace ka daina zuwa kofar gidan har ka rusa mashi gida kuma ka saka a ka hukunta shi? Ko kuma saboda ka bata sunan masarautar nan ne?” “Ba mahaifinta ba ne, mahaifinta ya rasu mijin mahaifiyarta ne kuma daman can baya so, kuma Wallahi ban rusa musu gida ba, ban yi sa'insa da shi ba, ban kuma saka a kama shi ba akwai dai wanda ya shirya duk wannan abun” “Kamar wa kenan?” Abiey ya kasa cewa komai ya sauke kai kasa. “Zan maka wani gargadi karo na farko kuma na karshe” Wani irin faduwa gaban Abiey yayi numfashinsa na fita da karfi. “Kar wata alaka ta sake hadaka da yarinyar nan, domin ba zaka maida mu mutanen banza ba, ka zubar mana da kima kuma ka janyo mayo mana surutu a gurin jama'a, abu na biyu bana son na sake jin labarin zaka buga wata wasa ko ka buga, akwai kamfunan da zaka iya kula da su, zan nema maka aiki a duk inda kake so, amman bana son maganar wasanka, na uku nan da wata biyu za a nadaka Galadiman, zaka daina yawo kai kadai sai tare da fadawa, kuma surarka da mu'amalar da zata canja daga yanzu, ka kiyaye duk wani abu da zai zubar da mutuncin Masarautar nan, karka sake janyo mana wata magana ” Kamar a mafarki haka Abiey ya ke jin dokokin Mai Martaba yana kallonshi baki da kunnen a sake ido kamar yayi magana. Mai Martaba yayi gyaran murya sannan ya kalli matanshi ya ce. “Ku kuma na tara ku a nan ne saboda na sanar muku cewa na saka auren Abiey nan da wata uku masu zuwa, idan iyayen yarinyar ba su shirya aurar da ita a yanzu ba, zamu nema mashi wata” Kusan a rude Abiey yake Kallon Mai Martaba kamin ya juya ya kalli Anty baki a sake. “Maa Shaa Allah ya kai mu ya sanya alheri” Hajiya Kilishi ta fada cikin rashin jindadi rai domin ba wannan hukuncin suke son Mai Martaba ya yankewa Abiey ba, son so ya tsaurara fiye da haka, musamman nadin sarauta da Mai Martaba ya shirya yi masa. Kusan a tare Hajiya Kilishi da Mama Lami suka mike tsaye suna tafe suna yabawa da Allah kyauta gaba, Anty kuma na zaune kamar ďanta Abiey, sai da suka fice sannan Anty ta kalleshi ta ce “Mai Martaba da dai ka duba dokokin nan ka saussauta wasu, Abiey yana son yarinyar nan sosai kuma abun da ya faru kuskure da dukanmu ba mu san waye ya aikata ba” Mai Marataba ya daga mata hannu. “Hukunci ne na riga da na zararta idan har akwai abun da yake son fada shi zai fada ba ke ba” “Allah ya baka hakuri ya huci zuciyarka a gafarce ni” Anty ta tashi jiki a sanyeye ta fice, tabbas ta jidadi da Mai Martaba be tsaurara ba kamar yadda suka so kuma nadin sarautar da zai masa yayi mata dadi, sai dai hukunci da ya yanke na shiga tsakanin Abiey da Zahra be mata dadi ba. After fitar Anty Abiey ya daga kanshi cikin nauyin kirji ya kalli Mai Martaba. “Mai Martaba na gode da karamci da ka yi min, kuma da yardar Allah zan kiyaye wannan ma kuskure ne aka samu kuma ban aikata ba, sai dai na san ba lallai ne ka yarda da ni ba, amman ina rokon wata alfarma ka duba hukuncin da ka yanke na raba mi da Zahra, Wallahi Mai Martaba ina son Zahra irin son da uwa zata iya mutuwa idan aka raba ta da ďanta, saboda ita na dauki lokaci” “Miye dalilinka na gabatar mana da wata ba ita ba?” “Saboda a lokacin bata gama takaba ba, kuma bana son a bani wata amadadinta” “So kake mu zama kananan mutane mu fasa wacan auren saboda kulla wani?” “Mai Martaba ko kadan bana son Yasmin” “To ka koyi sonta tun a yanzu, domin babu abun da za a canja ko da bana raye” “Ka gafarce ni Mai Martaba Wallahi ban ba zan iya son wata ba bayan Zahra, ka taimaka min wajen bin umarni Mai Martaba na san ba zaka so ni fiye da sauran yayanka ba, a haka na ke rokon alfarmar ka tausaya min akan abun da nake so dan Allah kar na kasa bin umarninka” “Bana saka doka a karya, bana bada umarni a musa ko a gurin jama'ar gari balle a cikin gidana, amman kai ka yi ka tabbatar ďan Uba biyu Umaima ta gurbata min zuri'a, har yanzu ina kyamar abun da Mahaifiyarka ta aikata da ya saka wani kaikayi a zuciyata, idan har ba zaka iya bin umarni na to sai ka bi zabi zuciyarka, amman fa ka sani zan cire hannayena a duk wani lamari da ya shafe ka” Abiey ya runtse ido yana jin jiri na dibanshi daga zaunen da yake, gaba daya duniyar ta juye masa kasan ya dawo sama saman kuma ya koma kasa, dan haske da farincikin da yake hangowa a gurin Zahra ya fara sauya masa zuwa duhu, kofar ta kulle gaba daya wani kalar nauyi kanshi yayi zuciyarshi kuma na aiki raba jiki kamar jikin zai fasa fasa jijiyarshi ya fito. [11/3, 11:29 PM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣7️⃣ Meaning of POV 👉 point of view HAJIYA JAMILA POV Cikin kuka ta shigo dakin ta fada kan gadonta tana jin wani sabon kukan marar misaltuwa na tunkaro ta, ta san idan har wannan likitar tace zata zafafa bincike akan ciwon Amir asirinta zai iya tunowa, idan kuwa har asirinta ya tono, ta rasa Mr Bashir kenan kuma ta rasa duk wani abu da take mafarkin mallaka ta dalilin shi da ďan da take ikirarin na shi ne, kuma ta jefa ďan'uwanta cikin matsala. Har ta unkura ta tashi zaune sai ta ji ana murda kofar dakinta hakan yasa ta kara lafewa ta cigaba da rairai kukan. Mr Bashir ne ya shigo dakin ya karaso har kusa da gadon ya zauna ya kai hannunshi ya shafa bayanta a kokarin shi na dagota ya ce. “Madam ki kwantar da hankalinki ba wani abu za'ayi ma Amir ba, ke ma kin san idan zai cutu ba zan ba kira wata likita ba, duk wani tunani da kike ko ganin kamar za su janyo mashi wata matsala ba haka ba ne, ita ma wannan kwarariyar likita ce ta san aikinta kawai ki yi fatan ya samu lafiya” Ta kwantar da kanta jikinshi. “Tsoro nake Hubby kar na rasa ďana ko kuma su ce min wata matsala ce da maganinta ba nan kusa ba” “Babu abun da zai faru Ki kwantar da hankalinki duk yadda kike son yaron nan na fiki son shi” “Shikenan Allah yasa sikar samun lafiyarshi kenan” “Ameen haka nake son ji” Ya sake shafa bayanta yana murmushi zuciyarshi cike da kaunarta da kuma tausayin yadda take son ďanshi. “Bari na je na yi magana da ita” Ta daga mishi kai kana ta bishi da kallo har ya fice, da sauri ta tashi ta nufi inda wayarta take aje ta dauka ta shige bandaki ta saka key duk kuwa da ta san da cewar abu ne mai wahala Mr Bashir ba zai dawo ďakin domin ya fi son zama a bangarenshi balle kuma yanzu da take kyautata zaton yana can tare da Dr Zainab. ZAHRA POV. A gidan makota da muka shiga wasu suka shigo suna mana jaje wasu kuma na shigo gulma domin na san abun da yake kawo su kenan. Sai da aka kira sallah azahar sannan muka koma gidan tare da taimakon jama'a muka kwashe kayan da za su kwasu Mama ta saka maza suka dauke mata gadonta da katifa suka kai mata makota. Na san abun da Baba yayi mashi be kyauta ba, kuma na jidadin da ya saka aka kama Baba duk kuwa da ban san kalar hukuncin da zai mashi ba, amman hakan zai koyar da shi darasi, domin ni ma ban jidadi ba, kuma iya hakuri Abiey yayi domin yana da karfin iko da dukiyar da zai iya daure Deen a wacan lokacin be yi ba, a yanzu kuma ace mahaifinshi yana kokarin cin mutuncin shi? Ina laifi yayi masa gargadin cikin mutunci ba ta hanyar tara jama'a ba, wata kila kuma Abiey ya zafafa domin ban san zafin zuciyar Abiey ya kai har ya saka a rushe gidan da shi ne rufin asirin mu ba, gashi a yanzu muna tsakiyar fili muna kwasar kaya mutane sai kallonmu suke makiya na mana dariya, na san ko ba a fada a gabana ba za a fada bayana cewar saboda ni aka yi kuma ni ce silar komai, hakan kuma ba zai min dadi ba kamar yadda rushen gidan be mana dadi ba dukanmu. “Abiey mu ya wulakanta ba Malam ba, domin mu muke rabe a nan” Mama ta fada tana kwashe spoons din ta dake cikin ginin bulo. “Mama ina jin kamar ba Abiey ne ya aikata mana haka ba” “To waya aika? Me muka tarewa wani balle a rushe mana muhallin ai shi ya kama Malam wannan aikin ma na shi ne” Na yi shiru domin bana son musa mata kuma bani da hujja, sai dai na kasa yardar Abiey zai aikata haka, ko da yake hausawa na cewa wanda be fushi ba idan ya fusata be iya ba, idan har ta tabbata shi ya aikata be kyauta ba, domin laifin Baba be kai ya rusa mana gida ba. Abun da ba mu sani ba ashe labarin abun da ya faru ya kadare social media, a gidan da Mama take kai ajiyar kaya muka samu labari amayar gidan ta nuna min yadda aka watsa labarin a facebook mutane na ta yi mana fassara kala kala su kansu wadansu gidajen jaridun yanayin yadda suke buga labarin kamar suna cewar ni din karuwar Abiey ce, wasu kuma kamar suna kokarin taba martabar gidansu ne da na Mahaifinsa, a lokacin ne na tabbatar lallai abun da Abiey ya aikata babba ne domin kokarin bata mana suna yake daga ni har shi. Sosai da sosai na ji ina son magana da Abiey sai dai babu dama domin wayar Mama ta lalace daker ma muka ganta a cikin gini, gashi be zo ba kuma ba zai yiyu na je gidanba domin ban san halin da yake ciki ba, kuma ban san irin kallon da za'ayi min ba, kuma be zama lallai Mama ta bar ni na tafi ba. A gidan muka yi sallah azahar sannan muka hau Napep zuwa gidan Kawun mahaifiyata wanda kaka ne a gurina, sai muka sha banban muna isa aka ce yanzu ya fita bayan ya fada musu cewar gurin mu zai je saboda ďanshi ya fada mishi abun da ya gani a media yana yawo, kuma ya kira wayar Mama be samu ba, shimfida matarshi ta yi mana muka zauna ita da surukarta suka kawo mana abinci kasancewar tana gida daya da suke da ita. A nan Mama ta labarta musu abun da ya faru ni dai ina zaune waje daya jiki ba kwari na kasa ganin laifi Abiey kuma ba ni da hujjar wanke shi, Matar Kawu ce ta kira Kawu ta fada masa cewar ni da Mama muna gida, sannan na saka number Yaya Maryam na yi mata flashing, after few seconds ta kira na labarta mata abun da ya faru bayan na fada mata cewar muna gidan Kawu. Ana daf da sallar La'asar Yaya Maryam ta shigo gidan tare da fuskarta babu walwala kamar yadda ta mu take, ita kan bata bawa ko wane bangare gaskiya ba, ta nuna abun da Baba yayi be kyauta ba, haka ma abun da Abiey yayi be kyauta ba, musamman Abiey da take ganin kamar ya zafafa da yawa. “Ni sai nake ganin kamar ba shi ya aikata ba” Na fada jikin sanyi jiki har bana son kallon fuskar Mama saboda yadda damuwa ta cita har ta cinye. “Be zama lallai shi ya aikata ba, domin Abiey yana da hankali da tunani, kuma lokacin da Deen yayi masa sharri ma be yi komai ba balle yanzu da yake ganin ya same ki” Cewar Yaya Maryam sai Sa'adatu wato matar Kawu ta ce. “Ko kuma fansa yake dauke? Kin san wasu mazan basa yafiya, wata kila duk kaunar da yake nuna miki a yanzu yana neman wanke kanshi ne da kuma son rama abun da kika mashi wasu mazan fa ba su da kyau” Yaya Maryam ta girgiza kai. “Da dai ace Zahra yar wani hamshakin mai kudi ce, ko kuma yar sarautar zan iya yarda da haka, amman idan har Abiey zai rama ba sai ya tsaya bata lokacin shi ba, kuma ban ga abun da aka yi mashi da zai ce sai ya rama, burin shi a kullum Zahra ta fahimce kuma ta fahimta, tsakani da Allah abun da Baba yake yi a yanzu ko ni nake da ikon da yake da shi abun da zan aikata kenan” Mama ta ce. “Tunaninku karami ne, komai Malam yayi muku yayi muku alherinsa fiye da haka, shi ya aurar da ku, kuma tun bayan mutuwar Babanku waya ke kula da mu idan ba shi ba? Ko da a munafurce yayi ni ya biya ni, yanzu ma saboda abun da Zahra ta yi ne akan Deen ya fusatashi da kuma wasu abubuwan da Hajiya ta fada masa, kuma da ace an bi abun ta siga mai kyau zamu iya daidaita komai amman wannan abun da Abiey yayi ya kara bata abin ne kawai, kuma idan mijinku ko masu neman auren Zahra suka wulakanta Malam kamar ni suka wulakanta saboda ni yake aure, kuma abokin mahaifinku ne, ya isa ya ce ayi ko ya hana” Mama Sa'adatu tace. “Ni fa abun da nake ganin yafi ki shirya ki tafi gidan Hajiyar ki bincika ko an dawo da shi” “Wallahi nauyin zuwa nake ita kanta Hajiya ta dauki zafi a lokacin kamin Malam, yanzu kuma na san zata kara fusata ne ni ban san ma me zan ce musu a yanzu ba” “Mama ko ki siyo sabuwar waya ki saka line ki?” Na fada domin na matsu na ji daga bakin Abiey, muna saka da tattauna wanda zai je siyen wayar sai ga Kawu ya shigo, sai aka dawo da labari kasa a nan yake labarta mana cewar yaje gidan ya samu guri ya zama fili daga can kuma ya tafi gidan Hajiya ya samu Baba a can an dawo da shi daga chemist fuskarshi ko'ina a kumbure, ba karamin tashi hankalin Mama yayi ba lokacin da ta ji halin da Baba yake ciki sai ya tashi da sauri ita da Yaya Maryam da matar Kawu suka saka mayafai suka nufi gidan Hajiya domin duba Baba, ni kuma Kawu ya saka ni a gaba yayi ta yi min masifa kamar ni na umarci Abiey ya aikata abun da ya aikata, ni dai ban ce Uffan ba daman can na san ni za a dorawa laifi domin ta dalilina komai ya faru, Kawu sai kumfar baki yake har da fadar na hakura da Abiey domin ko an yi aure matsaloli za su yi ta biyo baya kuma zai zaman babu shiri ko ganin mutunci juna a tsakanin shi da Baba, wata kila ma Baba yace ba zan aureshi ba kuma idan ya fadi haka yana da hujja be kamata na musa mishi ba. Ni dai kaina na kasa har ya ci ya shude ban ce eh ba balle aa, sai da ya fita sannan ya shiga bangaren surukarshi na ari wayarta na saka line Mama kamar jira ake ina sakawa kiran Hajiya Jamila ya shigo wayata mamaki ne ya kamani ta kira ta tabbatar da abun da yake faruwa a media ko kuma dai nata kiran na dabam ba, da fari kamar ba zan dauka ba, sai kuma wata zuciyar tace na daga na ji uzurinta. “Hello” “Hello Zahra ina wuni” Ta amsa min ta dayan bangaren muryarta masa kasa har da wata uwar gaisuwa kamar ta Allah. “Lafiya Kalau” Na mayar mata ina jiran tace min na ga abun da yake ta yawo a media da gaske ne, sai na ji wata maganar ta dabam tsabanin abun da zuciyata take raya min. “Zahra ke kadai kike? Magana nake son mu yi akan Amir” Har an rada mashi suna kenan tun da har na ji tana mashi alkunya da Amir. “Ina saurarenki” “Ina son na zo na yi magana da ke face to face inda hali” “Aa wayar ma ta isa ai, zamu iya yin magana” “Da fari dai zan fara da baki hakuri akan abun da na yi miki Wallahi ba halina ba ne ban san abun da ya zo kaina ba, ban san abun da ya same ni ba a lokacin har na aikata abun da na aikata” “Babu komai ya wuce, daman ance ido waye ka raina yace wanda nake gani kullum” “Ba haka ba ne, Zahra taimakonki nake nema, na san kin taimaka min da farko, kuma na gode a yanzu ma ina kara neman taimakonki?” “Ashe ina da rana da har Hajiya Jamila zata nemi taimakona ikon Allah” “Dan Allah Zahra ki bar komai ya wuce mana, yaron nan Zahra ke ma naki ne idan kika taimaka ni da ke kamar mun ceci rayuwarshi ne” “Ni ban gane abun da kike magana a kai ba” “Zahra ki taimaka min dan Allah kar na rasa ďa na ki dawo gidan nan ki zauna zan ware miki ďaki daya ki rika kula da ďanki kina ba shi nono dan Allah” Shiru na yi duk kuwa da irin tashin hankali da nake ji a tare da ni na fada min cewar ni da ita kamar mun ceto ďan mu ne hakan na nufin rayuwarshi tana cikin mawuyacin hali kenan? “Ba ni da ni wani abu da zan yi iya yi ma ďanki a yanzu, na siyar kuma kin siya ya fita daga hakkina” “Na sani amman duk da haka ina son ki cigaba rainonshi ne ki cigaba da ba shi nono dan Allah ki taimaka min Zahra, idan ma biyanki zan yi Wallahi zan iya” “Sai na yi tunani akai kuma zan yi shawara da mahaifiyata” “To na gode sai na jiki ki badi ko nawa saki shayar da shi zan biya ki” Ban sake ce mata komai ba na yanke wayar. Hajiya Jamila da hawaye suka samu girbi a idonta ta saka hannunta ta share hawayen idonta tana wani sabon tashin hankali daya tunkaro ta a yanzu wanda ya saka ta neman mafita a gurin Zahra ido rufe, a ganinta idan ba ta yi haka asirin ta zai iya tonuwa, idan dan'uwanta ya bata hadin kai ba zama lallau sauran likitocin da bata sani ba su rufa mata asiri amman idan Zahra ta dawo ta cigaba da bawa yaron nono asirinta zai rufu. Tana dora hannun a ta fara murda key din kofar bathroom din ta fito ta ji kamar an taba kofar dakinta, da sauri ta karasa budewar ta fito ta nufi kofar gabanta na faduwa ta bude ta leka bata ga kowa ba, ajiyar zuciya ta sauke ta dawo cikin dakin ta aikawa Dr Hamid kira, cikin matukar damuwa irin ta neman mafita take labarta mishi abun da ya faru. ABIEY POV. Tsakanin apartment din Anty Amarya da na Mai Martaba babu nisa ba musamman idan ka bi ta cikin falon ba kamar na sauran matanshi domin ya gina shi ne saboda Ammy a wacan lokacin kamin ya maye gurbinta da Anty Amarya. Tafiya ce da idan ka so sauri cikin dakiku ma zaka yi ta ka iso bangaren Anty ko na shiga bangaren Mai Martaba, amman a yau corridor yayi ma Abiey tsawo da ya dauke shi kusan minti talatin be iso part din Anty ba, idan ya cira kafa daga kamin ya daga yar uwarta wani yaki ne na duniya saboda tarin gumurzun dawakain tashin hankalin dake ranshi, idanuwanshi sun kada sun yi ja sai ka rantse da Allah baya iya gani da su, saboda yadda tashin hankali ya canja masa halitta a take. Bayan umarnin da Mai Martaba yayi mashi na rabuwa da Zahra, maganar karshe da mai Martaba yayi masa ta matukar daga mashi hankali daman ya dade zuciyarshi na raya mashi ba magani ne kadai abun da ya saka Mai Martaba ya tsare shi ba, me yake nufi da cewar Ammy ta bata mashi zuri'a? Daman ta taba tambayar Ammy ta nuna mashi bata son tambayar kuma ta fada mishi daga ita sai Zahra suka san dalili, ya san ba za a kalleshi ace ba Mai Martaba ne mahaifinshi ba, domin duk a cikin yayan Mai Martaba babu wanda ya fi biyo shi kamar Abiey. Idan zuciyarshi ta aika mashi tambaya sai ruhin dake can tare da Zahra ya jefo mashi ta shi tambayar ta ya zai rayu babu Zahra? Haka ya shigo cikin falon be ko san ya iso ba har sai da Anty ta dafa kafadarshi sai ya kalleta yana kokarin dawowa hayyacinshi. “Abiey... Ka kwantar da hankalinka zN yi magana da Mai Martaba idan mun keba” Ya kasa ce mata to ya kasa ce mata aa kuma ya kasa daga mata kai, kallonta kawai yake irin kallon dake nuna tunaninshi da hankalinshi ba akanta suke ba. “Abiey....” Ta sake girgiza shi sai ya kalleta a nan ma be ce komai ba ya nufi kofa, ita kima ta bishi da ido har ya fice, da sauri ya shiga motarshi yadda ya juya motar ma wani abun kallo ne domin wasa yake da rayuwarsa kamar an fada mashi bayan wannan ran akwai kyautar wasu da za a yi mashi, yadda yake gudu da mota kadai ya isar ya nuna yadda ba shi tsoron rasa rayuwarshi. Kamar zai tashi gidan haka ya rika danna horn masu bude gate din suka bude jiki na rawa, kamar mai gasar tsere haka ya faka motar ya fito ya nufi entrance din falon Ammy, yana murda kofar ya ji ta a rufe sai ya kwankwasa kuma ya danna door bell da mugun karfi. “Aliyu...” Ammy ta fada bayan ta bude kofar tana kallonshi, damuwa ce da tashin hankalin da ba zai kirgu ba a fuskarshi. “Aliyu...lafiya? Mai Martaba yayi maka wata maganar ne? Ya ci mutuncinka a ciki jama'a ko?” Ta tambaya dan ta san abun da tsohon mijinta zai iya yi ma ďanta ne. Abiey ya dauke kanshi daga barin kallonta ya shigo cikin falon ya nufi first set na cushion ya zauna, ganin haka ya sa ta rufe kofar ta dawo kusa da shi ta zauna ta shafa kanshi kamar wani karamin yaro. “Aliyu talk to me mana wani abun Mai Martaba yayi maka ne?” Ba tare da ya kalleta ba ya ce. “Tun da na taso na bude ido a rayuwata ban san wani abu soyayyar mahaifi ba, amman na san ta mahaifiya, ban san kulawa da uba na amman na san ta uwa, Mai Martaba be tana kirana ya tambayi lafiyata ba be taba cewa min Aliyu ko Abiey ka ci abinci? Kana ina yanzu? Ina zaka je? Ka ci gasa ina taya ka murna, amman ke har yanzu kina min wannan tun tasowa ta har zuwa girma na, kina son abun da nake so kina kin abun da zai bata min rai ko ya saka ni a damuwa, hakan yasa nake son ki sama da yadda kowane ďa yake son uwarshi a duniyar nan, amman a yau Mai Martaba ya ambaci sunanki ya ce kin gurbata mashi zuri'a” Ta dauke hannunta daga kanshi ta kalli wani bangare na ďakin ta lumshe ido. “Zuciyata ta dade tana raya min cewar ba saboda magani kawai Mai Martaba ya tsane ni ba, kuma ba zan cilasta ki fada min ba, amman ina son ki tabbatar min shim da gaske kin aikata wani abu da ya saka kai kayi a zuciyar Mai Martaba ya kasa mantawa da shi har ya tsane ni?” [11/5, 2:07 PM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣8️⃣ Ammy ta tashi tsaye da sauri tana kokarin hana idanuwanta tara hawaye. “Wayata tana ringing?” Ta nufi upstairs, Abiey ya bita da kallo har ta fice sannan ya sauke kai yana furta. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un” Ammy na shiga ďaki ta maida kofar ďakin ta rufe ta nufi gadonta ta zauna sai ta bashe da wani irin kuka da ita kanta ta dade bata yi shi ba, hannayenta ta saka ta rufe bakinta saboda kar kukan ya ci karfinta ya fita, bata bi ta kan wayar dake ringing ba har sai da ta samu sukunin zuciya, bathroom ta shiga ta wanke fuskarta sannan ta nufo wayar ta dauka missed calls din Anty Amarya ne da na Momy mahaifiyar Yasmin, Anty Amarya Ammy ta fara kira ta dawo ta zauna saman gadon wayar a kunnenta tana gyara murya so that kar a fahimci kuka ta yi ko kuma tana cikin damuwa. “Salamu Alaiki Ammy” “Na'am Zuwaira ya gida?” “Abiey ya fada miki abun da ya faru?” Gaban Ammy ya fadi. “Aa be fada min komai ba...” “Ya dawo gurinki?” “Eh amman be ce komai ba” From a to z Anty ta labartawa Ammy hukuncin da Mai Martaba ya yanke akan Abiey Ammy tana ta saurare ta ji cewar ko a gaban Anty Mai Martaba ya furta cewar ta gurbata mashi zuri'a amman bata ji Anty ta fada ba. “Na taso na bar su a can, ban san abub da suka tattauna ba amman na ga Abiey ya fito rai a bace kamar ma baya cikin hayyacinshi” “Zan yi magana da shi kuma zan yi magana da Mai Martaba” “Toh Allah ya kyauta” “Ameen” Ammy ta amsa sannan ta sauke wayar ta kalli kofar ďakinta Dr ce ta shigo riga da Lab coat a hannu dayan hannunta kuma rike da handbag. “Ammy Lafiya na ga Abiey a damuwa?” Ammy ta ja dogon numfashi ta sauke. “Kin san ďan'uwanki kullum yana cikin damuwa, yanzu ma wata matsalar ce ta sake bullowa” “Ni ma abun be min dadi ba, amman yace be aikata ba yanzu haka ma daga gidansu Zahra na ke na samu gidan ya zama fili kuma babu kowa a gurin na tambaya aka ce tace za su je gidan kawunsu amman su makonta ba su san ina gidan yake” “Mai Martaba ya saka auren Aliyu da Yasmin nan da wata uku, kuma zai nada shi a matsayin Galadima nan da wata biyu, sannan ya ba shi umarni aje wasan kwallon kwandon da yake a gafe zai hannata mashi wasu kamfanonu da zai kula da su, kuma ya ce baya son ya sake maganar Zahra” “Amman Ammy wannan hukunci be yi tsari ba? Kin san yadda Abiey yake son kwallo fa kuma kin san abu ne mai wahala ya iya rabuwa da Zahra” “Mai Martaba baya son wasan da Aliyu yake yi kuma yana daya daga cikin dalilin da ya saka tsabani a tsakaninsu, zancen aurenshi da Yasmin kuma ya min daidai, kuma shiga tsakakaninshi da Zahra ma ya min daidai, domin hakura da juna shi ya fi, amman zan yi magana da Mai Martaba ya hakura ya bar shi ya cigaba da sana'arshi ta kwallo” “Ammy kina ganin Abiey zai iya hakura da Zahra?” “Ke kuma kina ganin zan iya bari tarensu da Mai Martaba ta lalace? Wannan hukunci ma da ya yake na san ba zai musu dadi ba, domin ba haka suka so, ko ba komai Mai Martaba ya nuna mashi kulawa a yanzu abun da ya kasa ba shi can baya, a yanzu da girma zai kama Aliyu da Mai Martaba ba zan yarda abubuwa su lalace ba” “Ina tausayin Abiey sosai Ammy da dai za ku hakura ku kyale shi da Zahra” “Be zama lallai tarayyarsu ta zama alheri ba, so da tari zaka so kuma ya zama rashinshi shi ne alheri, idan ba ayi ma tukfar hanci ba nan gaba ba mu san iya abun da zai faru ba” “Haka ne, Allah ya zaba mana abun da ya fi zama alheri a tsakaninsu” “Ameen” Ammy ta amsa sannan ta mike tsaye. “Tsaya a nan zan yi magana da shi” “Okay” Ammy ta bude kofar ta fito har ta sauko downstairs idonta na kan ďanta da ya soke kai yake zaune a inda ta bar shi har lokacin. Kusa da shi ta zauna sai ya dago ya dubeta. “Aliyu karka yi maganar nan da Yayarka kuma karka yi ta da kowa domin babu wanda ya san komai daga ni sai Allah sai Mai Martaba sai kuma Zahra da na taba fadawa, bana son ka tattaunar maganar nan da kowa saboda karka sakawa kowa hakku a rai” Ya daga mata kai alamar gamsuwa yana jika makoshinshi daya bushe da yawun bakinshi ya runtse ido. “Allah ya maka albarka” “Ammy zaki iya roko min Mai Martaba ya bar ni da Zahra? Saboda ina son ta sosai kuma bana son tsaba Umarninsa, bana son na janyo abun da zai zame mana abun magana” Ya fada ba tare da ya bude idon ba. Ammy tana ta kallon ďanta kamar ta yi mashi wata maganar sai kuma ta amsa mishi “Zan yi magana da shi” Abiey ya bude ido ya mike tsaye ya nufi ďakinshi, sosai hankalin Ammy ya tashi ganin yadda ya koma jiki a sanyeye saboda damuwa. Tashi ta yi ta shiga nufi upstairs, Dr dake kwance kan gadon ta tashi zaune, Ammy bata ce mata komai ba ta dauki key din motarta da mayafinta “Ammy ina zuwa?” “Gurin Mai Martaba” “Amman kina ganin zai saurareki?” “Sosai kamin ya min yanzu ba ni kadai nake tafiyar da rayuwar ďana ba?” Ta  fadar haka ta dauki wayarta Dr ma ta tashi suka fito tare Ammy ta sauka downstairs ita kuma ta shiga ďakin Abiey. Kwance ta same shi idonshi a rufe fuskarshi na fuskantar ceiling. “Abiey?” Ya bude ido ya kalleta. “Magana nake son yi da kai” Sai ya tashi zaune ita kuma ta karaso ta zauna saman gadon tana kallonshi cike da tausayawa. “Abiey ka yi hakuri da duk yadda rayuwa zata zo maka, wani lokacin sai an jarraba bawa sosai kamin a bashi abun da yake so, na san kana son Zahra kuma baka son Yasmin tonka roki Allah ya saka maka kaunar Yasmin idan har aurenta alheri a gareka, kuma ya cire maka son Zahra idan ita din ba alheri ba ce a gareka, kuma ka yi hakuri” Ya daga mata kawai alamar gamsuwa, it's just like kamar kalmomin bakinshi sun kare, tunaninshi ya tsaya guri daya damuwa na neman maida shi kamar lokacin da ya taba rasa Zahra. “Na je na bincika ban samu Zahra ba, kuma na tambaya makota sun ce taje gidan kawun mamarta amman ba su san gurin ba, amman na samu an maida gurin fili” Nan ma kai ya daga mata ya koma ya kwanta ya runtse ido, Dr ta sauke ajiyar zuciya kana ta tashi ta fice daga ďakin. Wannan karon Ammy bata tsaya jiran ayi mata iso ba, domin kuwa tun kamin ta isa Masarautar ta kira Mai Martaba a wayarta ta sanar mashi tana tafe, hakan yasa ta faka a harabar apartment dinshi ba na Anty ba kamar yadda ta saba, ta fito ta nufi katuwar kofar kusan ko wace kowa a bude ta same ta har kofar falonshi da yake ciki yana hutawa. Da sallama ta shiga sai ya dago ya dubeta Mama Lami ta kalleta ba tare da ta amsa ba. “Wa'alaikissalam” Mai Martaba ya amsa mata da kanshi, da mamaki Mama Lami ta kalli Mai Martaba sannan ta sake kallon Ammy tana dariyar kyaƙe. “Sannu da zuwa Hajiya Umaima” “Sannu dai Lami ya aikin kula da Mai Martaba?” “Alhamdulillah sai kace karamin yaro” Cewar Mama Lami tana dariya sai Ammy tace “Ai a gurinki ba, ba mu guri zan yi magana da Mai Martaba” Mama Lami ta kalli Mai Martaba sannan ta mike tsaye ta fice tana jin kamar ta tsaya sauraren dalilin zuwan Ammy sai dai ba dama domin Ammy ba kanwar lasa ba ce ba irin Anty Amarya bace, duk da dai ta san maganar ba zata wuce ta hukuncin da Mai Martaba yayi ma Abiey ba. Ammy ta tsaya kallon Mama Lami har sai da ta fice sannan ta juya ta fuskanci Mai Martaba dake kokarin cire gilashin dake sanye a idonshi. “Ina son mu yi magana ne akan Aliyu” Ta hannu yayi mata nuna da kujera sai ta nufi kujerar ta zauna, Mai Martaba ya tattara dukan hankalinshi ya mika mata, daman haka yake indai Ammy na a guri Mai Martaba baya sauraren kowa sai ita. “So nake ka duba, a cikin hukunci da ka saka ma Aliyu ka sausauta ma shi wasu, na san kana da iko akanshi na aiwatar da duk wani abu, amman akan duba masalahar abu” “Maslahar ce na duba shiyasa na yanke wannan hukunci” “Ranka ya dade a dai duba dai, Aliyu baya son yawo da kowa, ka san kuma babu ruwanshi da sarauta kuma kace zaka nada shi ina ganin haka kamar tawaya ne a gurinshi, sannan tun tasowar shi ya tashi da sha'awar kallon hakan yasa na bashi duk wani goyon baya har ya kai inda yake a yanzu, rana tsaka sai kace ya daina?” Tana maganar Mai Martaba yana kallonta har ta kai aya sannan ya dora kafa daya kan daya. “Na yi hakan ne saboda bana so, abun kunya ne ace ďan sarki ya taso yana buga kwallon wannan ba al'adarmu bace zamani ne ya canja mana wasu abubuwa kuma dole ta saka muka karbe su, yanzu kuma ina son ya daina umarni ne wannan” Yayi shiru yana cigaba da kallonta damuwar dake tare da tsohuwar matarshi yake ta karanta. “Nada shi a matsayin Galadima zai taimaka masa gurin shiga cikin harkokin Masarautar nan, zai canja mu'amalar shi da jama'a ko dan ya kiyaye janyo mana abun magana, sannan ina son ďana a kusa da ni...” Ammy ta duba shi duba irin na mamaki. “Yau kai da kanka kake fadar haka Mai Martaba?” “Umaima ko na ki ko na so Abiey jini na ne, ko da ba jini na ba ne ba zan ki abun da ya fito a cikinki ba, balle kuma ace jinina ďana” Idon Ammy ya cika da hawaye. “Ka san da wannan amman kake kokarin hako abun da na dade da binnewa? Miyasa zaka ce na gurbata maka zuri'a a gaban shi? Har ka zo ya zo yana tambayar dalili? Kasan zafin da make ji? Ka san irin zuriyar da na yi kamin na gina rayuwar ďana? Na jure na jajirce kamin ya kai yanzu, saboda na san bashi da laifi, na raini ďana saboda kar ya tashi ace mashi shege...” “Abiey ba shege ba ne yana da uba” Ammy ta mike tsaye hawaye na zuba a idonta. “Karka cilasta mashi abun da be saba ba, domin be girma a tare da kai ba, ba san abun da yake so da wanda baya so ba, kar neman kusancin ka da shi ya bata tsakanina da ďana...” Tana kai wa nan ta juya ta nufi kofa. “Babu wata dokar da zan canja, idan har Abiey be yarda da bin umarnina ba to sai dai ki canja mashi wani uban” Juyowa ta yi ta kalleshi tana share hawaye ba tare da tace da shi komai ba ta fice, kamar yadda bata shiga bangaren Anty Amarya ba lokacin da zata shigo haka ta fita ba tare da leka apartment dinta ba, domin tana cikin damuwar da bata bukatar kowa ya ga fuskarta. Sai dai bata tsira ba domin ta tararda gidanta da wasu yan'uwa da suka ji abun da ya faru suka kira wayarta bata daga ba, musamman mukusanta sai dai zuwansu ya saka ta dan ji sakewar zuciya saboda hirar da aka sha, sai dai bata fada musu Abiey yana cikin gidan ba shi ma kuma be fito ba har dare azahar la'asar da magariba duk a cikin dakin yayi idan ya gama sai ya hau gadonshi ya kwanta. After ya gama sallah isha'i ya hau saman gadonshi ya dauki wayarshi yayi trying number Mama, dazun ya samu number a bude amman ba a daga kiran ba daga baya aka kashe wayar sai ya aika mata da sako, a yanzu din ma wayar a akashe take, ajiyar zuciya ya sauke gaba daya bashi cikin natsuwa domin be san halin da Zahra take ciki ba, kuma be san inda take ba, zancen da Mai Martaba yayi mashi ba ya hana shi samun natsuwa, so yake ya san abun da Ammy ta aikata sai dai be san ta ina zai fara ba, baya son ya tambayeta ko ya matsa mata Ammy ce ta turo kofar dakin ta shigo sai ya dan dago ya kalleta ya koma ya kwanta. “Me za a hada maka? Baka ci komai ba tun safe” “Bana jin yunwa” Ya amsa, kusa da shi Ammy ta zauna tana kallonshi cikin damuwa. “Aliyu kana cikin damuwa” Ya tashi zaune. “Ammy ai dole na damu kin san yadda na ke son Zahra, a yanzu da nake ganin na samu dama sai kuma Mai Martaba ya bullo min da wannan? Sannan yace ya saka date din aurena da Yasmin? Ammy bana son Yasmin ko kadan Wallahi” “Amman baka tsanar ta ai” “Eh bana tsanarta amman ba zan iya zaman aure da ita ba” “Kuma kasan Mai Martaba ba zai canja kudinshi ba, tun farko kai ka daure kanka da kanka, dazun naje na yi magana da shi ko zai sauko sai ya nuna min idan har ba zaka iya bin umarninshi ba sai dai na nema maka wani uban, ni kuma bana son abun da zai shiga tsakaninka da Mai Martaba Aliyu bana son ku samu matsala” “Kema kin goyi bayanshi kenan? Na hakura da Zahra kike nuna min” “Aliyu Zahra ba numfashi ba ce da zaka ce idan ka rabu da ita mutuwa zaka yi, ba addini ba ce balle ka ce idan ka barta kafirta ka yi, ni din nan da na haife ka zan iya mutuwa kuma ka cigaba da rayuwarka balle Zahra da ta hadu da kai daga baya” Ta yi shiru kamin ta sake kallonshi tace. “Idan ka yi mata bayani ai zata fahimta, ta san kana son ta yanzu ma abubuwa ne suka zo ta hanyar da ba ayi zato ba you can talk to her, Sauban ya zo yana falo” Ya mike tsaye ta nufi kofa sai ya daga kai ya kalleta. “Yeah i did... Amman ba akan wannan maganar ba akan abun da kike boye min Zahra told me everything” Cak Ammy ta tsaya ta juyo cikin matukar tashin hankali ya bugun gaba ta kalleshi, gaba daya sai jikinta ya dauki rawa a take mokoshinta ya bushe idanuwanta suka fiffito suka cika da kwalla kamar marar gaskiya Abiey kuma karantar abun da ta aikata yake a fuskarta daga zaunen da yake yana zuciyarshi na raya mishi abun da Ammy ta aikata ba karami ba ne. Kwakwaso kofar ďakin aka yi Sauban ya murda kofar ya leko Ammy ta juyo ta kalleshi hawaye na sauko mata sai kuma ya kalli Abiey dake zaune. “I'm sorry... Ban san magana kuke ba daman Zahra ce ta zo” Abiey ya mike tsaye da sauri. “Zahra? Ina take?” “Tana falo” Sauban ya saki kofar ganin Ammy ta doso kofar da zimmar ficewa, sai ya kauce ta fito daga dakin tana share hawaye, Abiey yaje ya fito Sauban ya maida shi ciki ya shiga ya turo kofar ďakin. “Taya zaka saka mahaifiyarka kuka Abiey? Kana da hankali?” “Ba akan Zahra ba ne” Abiey ya fada yana kokarin bude kofar ya fito, da saurinshi ya nufo downstairs zuciyarshi har wani fisga take ta hango masoyiyarta. ZAHRA POV. Bayan sallah la'asar Mama ta dawo daga gidan Hajiya tare da Yaya Maryam da Matar Kawu dukansu fuska babu annuri, Mama da Yaya Maryam ina kallonsu na san kuka suka yi musamman ma Mama da idonta har kumbura yayi, ina ta tambayar abun da ya faru kowa ya kasa amsa min sai hankalina ya tashi. “Ko dai Baba ya mutu ne?” Na tambaya ina kokarin fashewa da kuka domin hankalina a matukar tashe yake. “Be mutu ba yana nan da ranshi, amman auren dake tsakanina da shi ya mutu” Mama ta amsa min, hannu na do saman kai na rufe ido sai hawaye suka fara min sallama a saman fuska, auren mahaifiyata ya mutu saboda ni, bayan mutanen da na zan za su magana ita kanta mahaifiyar tawa ya zata ji? Idan ta kalleni ai ba zata iya mantawa ba, a ina zamu zauna yanzu? Gidan gadon su Mama da yan'uwanta suka maye suka zauna zamu raba ko kuma gidan gadon mahaifinmu da na aka siyar saboda neman kudin maganin aikin Deen? Ko kuma haya zamu kama mu zauna? “Wannan abu dai be yi dadi ba, dukansu ba su yi tunani ba kamin aikatawa musamman shi mai son Zahra saboda Malam kamar uba ne a gurin ta komai yayi mashi ya kamata ya hakura, shi ma Malam be kamata yayi masshi cin mutunci ba ko dan kasancewar shi babban mutum, amman ya biye zuciya yana taya ďanshi kishi” Matar Kawu ta fada, Mama dai bata ce komai ba, Yaya Maryam ta ce. “Ni gani nake sila yake nema saboda ya fara canjawa tun daga lokacin da aka ce Deen ya aikata ba daidai ba kuma Zahra ta ga laifinshi, kenan goyon bayan ďanshi yake yana ganin kamar abun da ya aikata ba laifi ba ne kuma be kamata a ga laifinshi ba, Wallahi Abiey ma yana da hakuri da wani tuni ya aikata musu rashin mutunci” Ni dai shiru nake bana iya cewa komai, domin a dalilina komai ya faru duk wanda za a ga laifinshi a bayana yake. [11/5, 11:41 PM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣9️⃣ Muna zaune a gurin Surukar Mama Sa'adatu ta kawo min wayarta da na saka line na wai an turo min sako. Mama kallona kawai ta yi ta dauke kai na mika hannu na karba, ban san ta cire line a airplane mode ba domin na yi haka ne saboda kar ya sake kirana kamar yadda ya kira dazun. “Zahra idan kin ga sakona ki kirani dan Allah ina son magana dake, Zahra idan ya wuce yau ban saka ki a ido ban yi magana da ke ba, zan saka a gano min inda kike” Na goge sakon bayan na gama karantawa ni kaina ina bukatar magana da Abiey sai dai bana son silar daukar wayar Abiey ya tambaye ni inda nake balle har yace zai zo, bana son Mama ta sake ganin laifi hakan kuma ba yana nufin na hakura da Abiey ba, amman a halin yanzu ya kamata mu nisanci juna har zuwa lokacin da Mama da Baba za su huce. Muna cikin wannan halin Kawu ya dawo yana samun labarin abun da ya faru ya rufe ni da fada kamar zai doke ni, ni dai ban da aikin kuka babu abun da nake yi Yaya Maryam na rarrashina ita ma ya rufe ta da fada yana fadin ita ke goyon bayana. Ina kwance jikinta wayar dake hannuna ta yi ringing kiran Dr Hamid ya shigo. “Wayar waye? Waya kira ki?” “Dr Hamid ne...” Na amsa cikin kuka ina da tabbacin rashin amsawar zai iya saka Kawu ya doke ni ma domin ranshi ya bace sosai. “Ba ni wayar” Na miko min hannu sai na mika mashi wayar jiki na rawa, bude bayan wayar yayi ya cire karamin batir din ya cire line biyu daya Mama daya kuma na Surukarshi sai ya saka su duka biyun a baki ya taune ya jefo min wayar. “Allah yasa na ga kin sake kiran shi ko kin kwatanta mashi kofar gidan nan ki ga yadda zan karyaki” “Gaskiya kam yanzu ina amfanin haka auren uwa ya mutu, ke ma ai ba jindadinki ba ne” Mama Sa'adatu ta kara da nata, aiko kamar ta sosawa Kawu inda yake mashi kai kayi sai ya ce. “Bar marar hankali ko sunanshi na sake ji a bakinki sai na kusa halaka ki” Haka dai na wuni cikin takura da fadan Kawu, bayan sallah Magariba Mama da ni muka kama hanyar zuwa family house dinsu, daman Yaya Maryam tun da yamma ta hau napep ta koma gidanta, ko da muka je can sai hankalinsu ya tashi, wai suna ta kiran wayar Mama ba su samu ba tun a lokacin da suka samu labarin abun da ya faru a media kuma sun je can ba su samu kowa ba, abun ka da gidan taro maganar kawai suke ta yi sai dai su ba kamar Kawu ba basa dora min laifi wasu ma basa ganin laifin Abiey sai na Baba, manyan gidan suka ce ai sasantawa za'ayi amman sai nan da kwana biyu idan ya huce tukuna. Dakin wani Yayanta muka zauna ni da ita suka kawo mana abinci, ni kam dai ko kallon abinci ban yi ba domin ba shi ne a gabana ba, Mama dai ta ci kadan ta wanke hannun sai na miko mata ruwan sha da aka aje mana ta karba ya sha. “Mama na ce ko naje na ba Baba hakuri akan abun da ya faru?” Shiru ta yi alamar nazari sannan ta kalleni. “Idan kika ba shi hakuri a yanzu zai yi tunanin saboda ya maida aurena ne” “Idan kuma aka dade ban san iya abun da zai biyo baya ba, kuma idan ma yayi wannan tunanin ba laifi ba ne, ko da na yi wayo na bude ido da aurenku na ganku be kamata saboda ni aurenku ya rabu ba, na san abun da Abiey yayi be kyauta ba amman na tabbatar be yi haka dan ya tozarta ni ko kuma ke ba a matsayinshi na mijinki sai dai ya kalli abun ne ta wata fuskar ta dabam wato ta bangaren Deen shiyasa ya aikata abun da ya aikata, Mama ki ba ni dama na je na bashi hakuri ai shi ubana ne kamar yadda kika ce” “Shikenan amman ki bari sai da safe” “Da dare ya fi sirri Mama, kara na tafi tun a yanzu ba sai gobe ba” “To ki dawo da wuri kar a fara tanbayar ina kika je, idan kuma kin hadu da wani ya tambaye inda zaki je da dare ki ce kaya zaki dauko a gida” “Toh, amman Mama ya zamu yi da gurin da aka rushe?” “Haya zamu kama Zahra, wannan neman aure na Abiey ya zame mana fitina tun farkonshi har kawowa yanzu” Na yi shiru ban ce komai ba, daman me zan ce kare Abiey zan yi? Ko kuma Mama zan shigarwa mu taru ni da ita mu zagi Abiey, idan har akwai mai laifi to Deen domin shi ya haddasa komai. Da sanďa na fita gidan da sunan zuwa gurin Baba sai dai ni zuciyata tana a gurin Abiey ne, musamman cewar da yayi zai saka a nemo ni kuma na san zai iya, ni kuwa ba jindadi ba ne ace ya zo gurin a wannan, shi kanshi ban san halin da yake ciki ba kuma ba san yadda yake so zai shiga damuwa be ji daga gareni ba, kamar yadda ni ma bake son tambayar shi wasu abubuwan. Amman ya zan yi? Gidan zanje? ‘No be kamata ki je ba, duk bayan gargadin da Ammy ta yi miki? Idan ma kin je me zaki ce? Gani kin zo ganin Abiey?’ Wata zuciyar ta fada min, hakan yasa na cire abun a rai na, ina isa titi na fara taron Napep biyu da suka wuce cike suke da mutane hakan yasa ba su tsaya ba, ina kokarin na tari ta ukun da zata wuce na ga wata mota da ta wuce ni ta dawo baya ta tsaya daidai inda nake, kokarin kaucewa na yi sai matukin motar ya sauke gilashin motar ya kira sunana. “Zahra...” Tsayawa na yi sai dai ban dawo ba, sai ya kara yin baya da motar ya tsaya daidai inda zan ganshi ya kunna wutar motar na ga fuskarshi sannan ya bude motar ya fito ya zagayo inda nake tsaye. “Zahra ina zuwa haka cikin dare?” “Wani guri zanje” “Ina wayarki?” “Daman ba ni da waya ta Mama ce nake saka line na kuma gini ya fado mata ta lalace” Ya sauke ajiyar zuciya. “Zahra na ji abun da ya faru abu be yi dadi ba, amman ina da tabbacin aboki ba zai saka a rushe muku muhallin ba, shi kanshi abun ya dame shi yanzu haka Ammy ta kira ni wai tun da ya shiga ďaki fito ba har yanzu and i know damuwarshi ba zata wuce abun da ya faru yanzu ba, kin yi magana da shi?” Na girgiza kai alamar aa ina waige waige kar wani ya gan ni a gurin. “Family house din Mamana a nan yake za a iya ganinmu” “If ba matsala zamu iya shiga mota mu yi magana, na ga ma kamar fita zaki yi” Ya sake waigawa ko'ina sannan na bude front seat na shiga na zauna shi kuma ya zagaya ya shiga side dinshi yayi ma motar key muka hau titi. “Da zaki min dadin rai da na kira Abiey kun gaisa ko kuma na kai ki gidansu domin yana can kwance babu lafiya” A take hankalina yayi matukar tashi. “Ba sai na je gidan ba, amman ya jikinshi?” “Da sauki za a ce, amman Zahra gidan ai ba bakonki ba ne, idan ma baki son shiga ciki zaki iya tsayawa a waje sai na kira shi, tsakani da Allah ba zai jidadi ba idan na fada mashi na hadu dake ban kawo ki ba, idan kuma kin yarda ki fada min gidan da kike zan dauko shi na kawo shi a halin rashin lafiyar da yake ciki” “Aa bana son ya san gidan” Na fada ina jin tausayinshi na kara cika min zuciya. “Okay amman zaki yarda ki mu je gidan? Na san Abiey yana son magana da ke sosai, ke kanki ba zaki rasa abun da zaki tattauna da shi ba” Na yi shuru ina nazari, wannan ce kadai damar da nake da ita da zan yi magana da Abiey, kuma idan ban aminta na hadu da shi a yanzu ba, wata kila Sauban zai iya takurawa sai ya san inda nake zama a yanzu, wanda hakan ba alheri ba ne a gareni a yanzu, domin Kawu da Mama da sauran yan'uwanta za su yi zaton kamar abun da ya faru be dame ni ba ne, ni ma kuma ina son ganinshi ko dan sanin halin da yake ciki so that na samu peace of mind. “Amman ba zan shiga cikin gidan ba” “Yeah ba sai kin shiga ba zan iya fada mashi sai ya fito” Kusan zan iya cewa kamar Sauban yayi min dole ne, domin har muka isa gidan ban daina wasi wasin zuwa ko akasin haka ba, na samu kaina da tsananin faduwar gaba a lokacin da aka bude mana gate din gidan. “Na ce maka ba zan shiga ciki ba” “I thought can cikin gidan kike magana gurinsu Ammy, nan ai harabar gida ne, kuma zai fito sai ku zauna a mota ku yi magana” Ya fada mini amman hakan be saukar min da natsuwa ba, sai a yanzu nake ganin rashin dacewar zuwa na, da dai a da ne da Ammy bata min cin mutunci ba, ko da yake wacan karon ma fusata ta yi na marin da na yi ma ďanta, na san kuma ko ba ita ba ko da wata uwar ce abun da zata aikata kenan. Wayarshi ya dauka ya fara kiran Abiey sai da ya jera mashi 3 Missed calls Abiey be daga ba, sannan ya kalleni. “Bari na shiga na yi magana da shi” “Amman dan Allah karka bari Ammy ta san muna tare” “Okay amman saboda me?” “Be dace na zo ba, kamin Ammy ta yi min gargi akan Abiey” “Abiey ya fada min amman wacan lokacin ai saboda kin nunawa Abiey tsana ne yanzu kuma kauna kika nuna mashi, dadi ma zata ji kuma zata san a yanzu babu komai tsakaninku sai soyayya, Zahra yadda kike da Ammy be takama ace yanzu wani abu ya shigo ciki ba, ko da wani abun kika yi kamata yayi ki nemi yafiyarta” “Na ji amman ba yanzu ba Sauban” “Shikenan bari na shiga na yi mashi magana” “Toh” Na amsa gabana sai faduwa yake ina jin kamar na fita motar na yi tafiyata. Ina ji ina gani ya fice shi kanshi waigena yake. Ban san kalar maganar da yayi da Abiey ba, ina jiran na ga fitowar Abiey sai na hango Sauban ya fito ya bude motar da nake zaune. “Zahra Ammy ta ce ki shigo” Gabana yayi dukan uku uku, taya Ammy da kanta zata ce na shigo? “Aa ni ba zan shiga ba, dan Allah Sauban ka maida ni gurin da ka dauko ni” Na fada muryata na rawa domin tsoro ne ya kama ni a lokacin, ni kaina na san wani lokacin bana tunani idan zan aikawatar da abu, da tun farko ban biyo shi na shigo cikin gidan ba. “Abiey ne ba zai iya fitowa ba, shiyasa tace ki shigo” “Ba shi da lafiya ne sosai?” “Eh, kuma Ammy ba da wata manufar tace ki shigo ba” Ban san lokacin da na sauko da Kafafuwana daga cikin motar ba na fito jin cewar masoyina babu lafiya, daman can gidan Ammy ba bakona ba ne, sai dai a yanzu da abubuwa suka faru marasa dadi. Bayan na fito ya rufe motar sannan ya wuce gaba ina bayanshi kafafuwana sai hadewa suke ina tafiya kamar zan fadi zaune. Sai da ya fara shiga cikin falon sannan na mika kafata ni ma ba shiga, babu kowa a falon ko tv da ake bari a kunne a yau kashe na same shi. “Zauna bari na yi magana da Ammy” Na zauna ba dan na so ba, sai dai babu yadda zan yi domin ni na kawo kaina, idanuwana na kasa har sai da na ji motsin saukowar mutum a stairs, sannan na dago ina kallon Ammy dake saukowa da kuzarinta, ba zan ce ranta a bace yake ba haka kuma ba zan ce tana murna da ganin ba, sai dai na lura da damuwa karara a fuskarta, mikewa na yi tsaye ina kallonta har ta sauko ta nufo inda nake. “Ban gargade ki akan Aliyu ba Zahra? Ban fada miki cewar Mai Martaba yayi mashi mata ba? So kike ya tsabawa umarninmu? To idan har Aliyu ya zabi cigaba da zama dake ko kuma ya dage akan sai ya aureki to sai dai ya zaba tsakanin mu da ke, na fada miki a baya kuma a yanzu zan fada miki babu ke babu ďana har abada...!” Magana take hawaye nake ina jin kamar kafafuwana ba za su iya daukata ba, Abiey ne ya fara saukowa da saurinshi Sauban na bayanshi. “Ammy dan Allah ki yi hakuri....” Kamin na karasa fadar abun da zan fada Ammy ta dauke ni da mari. “Munafuka, na yi nadamar saninki da na yi Zahra kuma na yi nadamar fada miki sirrina, tsintacciyar mage ada can na yi tunani ke yarinyar mai kirki da zata iya rike min sirri ta ji tausayin ďana amman kalle ki saboda ke komai ya lalace, Mai Martaba ya saka auren Aliyu da Yasmin nan da wata uku saboda haka ina gargadinki da ki rabu da ďana tun wuri” Abiey zuwa yayi ya shiga tsakiyarmu ya tare ni daga kalaman da Ammy take min. “Haba Ammy haba” “Ki yi hakuri ko yafe min na miki alkawari hakan ba zai sake faruwa ba” Na fada sannan na juya sai Abiey ya sha gabana. “Ina zaki je?” Na kasa amsawa saboda kukan da ya ci karfina. “Zahra miyasa kika zo a yanzu?” “Ni na cilasta ta zo i just wanted to surprised you ban yi zaton abun da zai faru kenan ba” Sauban ya fada cikin damuwa da rashin jindadin abun da Ammy ta yi, ni dai ban iya sake furta komai ba na nufi kofar na bude na fita sai Abiey ya biyo bayana yana min magana kamin ya sha gabana. “Zahra ki saurare ni mana” “Abiey...” “Na'am” Ya amsa tare da saka hannayenshi biyu ya tallafo fuskata. “Ba zan yarda na zama silar lalata alakarka da Mai Martaba ba, ba zan bari ya kai mu ga zabe tsakanin ni da iyeyenka ba” Ya fara share min hawayen da ba su gama sauko min ba, ban kuma san ranar da za su gama ba. “Ammy ta fusata ne kawai amman zata sauko kin ji zan yi magana da ita” “Wannan ba abu ne da yake tsakanin ni da kai kadai ba, a tsakaninmu ne mu duka Abiey, ni ma Iyayen sun samu matsala saboda ni ba zan bari ka samu matsala da iyayenka saboda ni ba, ba zan iya daukar nauyin ba, kuma ba zan iya bari ka tsaba ma umarnin Mai Martaba ba, magana ce ta gaskiya da gaskiya Abiey dan Allah ka nuna min kaunar da kake min kuma ka tabbatar min da ita ta hanyar hakura da ni a rayuwarka, inda har son da kake min na gaskiya ne to ka auri Yasmin kuma ka bi umarnin Ammy da Mai Martaba ta haka zan tabbatar da kaunar da kake min ta gaskiya ce” Lokaci daya ya dauke hannayenshi daga fuskata yana kallon kwayar idona dake yawo cikin tashi. “Komai zai daidaita Zahra” “Komai zai daidaita idan muka hakura da junanmu, ba ko wace soyayya ce take nufin aure da kasancewa a tare ba Abiey, kuma ba duka masoya ne suke samun cikar buri ba, ka nuna min kauna na sani amman hakan ba zai gamsar da ni ba har sai ka bi umarnin Ammy, ina son ka Abiey amman soyayyarka bata yi tasirin da zata hana ni bin umarnin iyayena ba, iyayenka da nawa sun samu matsala saboda mu miyasa ba za mu hakura mu so farin cikinki su ba Abiey” Na durkusa kasa na hade hannayena ina rokonshi. “Ka dubi girman Allah ka tabbatar min da kaunar da kake min ta hanyar kaurawa min, ina nufin kauracewa ta har abada...!” Ya dukoso ina kallona hawaye na gani suka sauko a kyakkyawar fuskarshi. “Hakan zai tabbatar miki da ina kaunarki Zahra?” Na daga mishi kai ina jin zuciyata kamar zata fado saboda bakin ciki da kuka da yake cina, mikewa yayi tsaye ya fara tafiya sai ni ma na tashi tsaye na juya ina kallonshi. “Abiey kai ka saka aka rushe mana gida” Tsayawa yayi cak ya juyo ya kalleni. “Ba ni ba ne, amman zan nema miki gurin da za ku zauna a duk inda kike so” “Bana son ko tsinke daga gareka, kawai ina son na ji daga bakinka ne saboda zuciyata ta kasa yarda kai ka aikata” Na juya na cigaba da tafiya. “Tafiya zaki yi Zahra” Ban juyo ba, kuma ban fasa tafiyar da nake ba har na fice daga gidan. Sai da na yi nisa da tafiya sannan na duke kasa ina kuka kamar marar gata, sautin takunshi na ji a bayana da kuma kuma kamshin turarenshi. “Miyasa zaki cilasatawa kanki abun da ba zaki iya ba? Taya kike kokarin raba zuciyarki da abun da idan babu shi ba zata rayu ba” Na mike tsaye na kalleshi a fusace na ce “Karya zuciyata take Abiey tace idan babu kai ba zan rayu ba, kamin na san da kai nake rayuwa kuma zan cigaba da rayuwa ko bayan babu kai, karya so yake yace zai tsaka ka tsaba umarnin iyayenka ko kuma ni na tsabawa nawa babu wannan ranar Abiey, kuma karya so kake min idan har ba zaka iya aiwatar min da abun da na roka ba. Hakan na nufin ba zan taba iya banbance soyayyar gaskiya da ta karya ba, ba zan iya banbance tsakanin kai da Deen ba dukanku kanku kawai suka sani ne kuma kuke so...” Na juya tare da share hawayen da karfin tsiya na fara tafiya, sai na ji ya rumgume ni ta baya. “Zan bi umarnin Mai Martaba Zahra kuma zan bi umarnin Ammy, zan tabbatar miki da cewar ina kaunarki irin kaunar da wani ďa be taba yi miki ba, amman hakan ba yana nufin na rabu da ke rabuwa ta har abada ba...! Ina mamakin yadda zuciya take iya bari bakinki ya furta min kalma rabuwa Zahra ba san yadda nake ji a zuciyata ba ba kuma zaki taba sani ba” Ya sumbanci gefen fuskata. “Na riga da na sani Deen ya yaye miki kaunata a zuciyarki Zahra, amman har gobe ina kaunarki i want to you haka kuma ina farinciki da ke Zahra, maybe today is the last of our lives or our memories, ina son ki sani a kusa ko a nesa ina tare da ke, idan kina bukatar tsaro ko taimako ki fada min i will be right beside you i still love you Zahra ki saka wannan a zuciyarki if you ever need save just called me” Ya sake ji ya juyo da ni ya kama duka hannayena ya sumbanta sannan ya kai hannunshi ya taba fuskata, dayan hannuna kuma ya shafi fuskarshi a fuskarshi har cikin zuciyata nake jin sanyin hawayenshi da hannuna ke tabawa ya sumbaci cikin hannuna sannan ya saki hannayen nawa ya juya ya fara tafiya ba tare da ya juyo ba. [11/7, 8:11 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣0️⃣ Ban iya tafiya gidan Baba ba sai nufo gida cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara zuciyata kamar zata cire, kirji na wani irin zafi kamar an saka min garwarshin wuta. Daidai gurin da Sauban ya dauke ni a gurin mai napep ya aje ni sai na fita na mika mashi duka kudin da ke hannuna ba tare da na ce komai ba na juyo ina tafiya sai ya kira. “Malama ga kudinki” Ya miko min dariyar ya dauki dari biyu daman dari bakwai ne Mama ta ba ni, ban iya tsayar da kuka na har na shiga cikin gidan, na samu unguwar babu wutar nepa hakan ya taimaka min na shiga cikin gidan ba tare da kowa ya lura da halin sa nake ciki ba. Ina shiga dakin na samu Mama tana sallah isha'i sai na zauna a kusa da kofa na jingina da ginin na dafe zuciyata ina jin kamar na mutu na hutu, ji nake kamar na yi bankwana da Abiey kenan bankwana irin na wanda zai mutu ya barka, kuka na ke sosai marar sauti numfashi na yin sama kamar zai rabu da jikina, ba hawaye ba har majina zuba take min balle hawayen da nake jin kamar domin ranar yau kadai aka yi min su. Mama na gama sallah ta dauki fitila ta haska fuskata. “Zahra lafiya?” Na kasa magana sai kuka nake marar sauti ina jan nunfashi da mugun karfi. “Mi Malam yayi miki? Wata maganar ya fada miki?” Na kasa magana domin na tabbatar idan har na bude bakina kuka ne kawai zai fito min. Mikewa ta yi ta dawo kusa da ni tana kallon fuskata. “Fada min mana, wannan abun ya isa haka, ba zan dauki cin mutunci ba saboda yana a matsayin magabacinku ba shi yake nufin ya wulakanta ku ba” Ta mike tsaye ko bata fada min ba na san ba zai wuce tace zata tafi gurinshi ba, sai na rike kafarta ina girgiza mata kai domin abun da zan iya yi kenan a lokacin nan, dokowa ta yi ta rika fuska. “Bude baki ki yi min magana” “Ba... Ba... Ba... ” Na kasa fada kuka ya ci karfina jikin ko'ina rawa yake, sai da na yi da gaske sannan na iya furta “Abi....ey ne....” Maganar na yankewa kukan yana karuwa. “Mutuwa ya yu?” Na girgiza mata kai alamar aa, zaunawa Mama ta yi kusa da ni ta rumgume hakan ya bude min kofar wani sabon kuka marar misaltuwa, har wani kara numfashi yake gurin fita, a daren kam kuka be tausayawa idona ba tun ina yi da kuzari har na ji jikina ya zama kamar kaďa. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un Allah ya dauke miki wahala Zahra ko na mutu iyar kukan da zaki yi kenan” Mama ta fada tana kokarin tare nata kukan daman tuni hawaye suka wanke mata fuska, sai da na yi kukan sosai na gaji sannan ta daga ni jikinta ta fita ta debo ruwa ta saka cire min hijab ta cire dankwalin kanta ta saka cikin ruwan ta matse ta daga rigata ta saka min saitin zuciyarsa sai naji rahama, ta sake natsewa ta saka min goshi sannan ta share min majinar ta share hawaye. “Zahra na hada miki ruwa ki yi wanka?” Na daga mata kai na kara matsawa kusa da ita na dora kaina saman cinyarta na runtse ido zuciyata na min ciwo sosai, sai da bachi ya fara daukata sannan ta dauko filo ta saka min a kasan kai ta tashi ta fita, can cikin bachi na ji Mama na tashi na sai na bude idona da suka kumbura na tashi zaune. “Ga ruwan zafi can na dora miki a gidan Maman Mufeedat kuma na bada an siyo miki tea ki sha kin ji Auta ta” Ta miko min kofin shayin sai na karba na kafa kai na sha, sannan na cire tufafina na daura zane na fita na dauki ruwan dake da ďan dumi na shiga bandaki na yi wanka, ko da na dawo Mama ta zuba min shimkafar sai dai ban iya ci ba kaina sai ciwo yake kamar zai tsage, ban iya bachi ba har sai dai Mama ta fita ta samo min magani na sha. Nan da nan bachin wahala yayi gaba da ni, ban farka ba sai safe shi na sai da Mama ta tashe ni, wanka na fara yi sannan ta zuba min kokon da aka kawo mana, na sha kadan Mama kuma ta ci dumame, abun da ya faru ya zame min kamar mafarki. “Ko na siyo miki tea” Na turo baki gaba na kwanta jikinta cike da shagwaba. “Ni bana ci” “To ya jikin na ki?” “Da sauki” Ta kai hannu ta taba ni. “Miya samu Abiey?” “Ba Abiey ne...” Na fada a shagwabe ina kokarin dora mashi laifi kamar ba ni na bukaci haka ba. “Miya faru?” Kamin na gama bata labarin ma wani aiki ne domin kuka ya gama cin karfina har ya tafi da kuzarina. “Indai saboda ni ne Zahra da baki aikata haka ba, na san mutane za su yi gulma kuma dole a dora miki laifi amman idan bera da sata daddawa ma sa wari, laifin ba naku ba ne ku kadai har da na Malam sai dai dole ne a fi dorawa Abiey laifi domin shi kamar suruki yake a gurinmu dole ne ko zaginshi muke yi kullum idan yana kaunarki ya hakura ya jure, sai dai ina ganin kamar abun be kai ki yankewa kanki wannan hukuncin ba, saboda zaki iya cutar da kanki kuma shi ma zaki cutar da shi domin na tabbatar yana kaunarki sosai” Na gyara hancina wasu hawayen na sauko min. “Ba saboda ke da Baba kawai na yanke wannan hukunci ba, har dan saboda Ammy da Mai Martaba, tun kamin na fahimci gaskiya Ammy ya fada min cewar Mai Martaba ya zaba mashi mata, kuma jiya ma ta kara tabbatar min da haka, Mama na san irin yadda Mai Martaba ya tsani Abiey Abiey kuma yana ta neman mafitar da zata aadashi da mahaifinshi, yanzu kuma ya samu har Mai Martaba ya nema mashi aure da kanshi ba zan yarda na zama sanadiyar lalara wannan alakar ba, kuma Ammy tace min idan har ya zabi zama da ni su kuma za su yafe shi, Mama bana son na zama silar shiga tsakanin ďa da uwa, kuma ban ga laifinta ba, domin kowa uwa tana nemawa ďanta mafita ne da farinciki ina ganin kamar idan mun auri juna ba lallai mu samu farinciki ba, saboda akwai rashun jituwa tsakaninshi da Baba ni kuma zan samu tsakani da Ammy ina ganin kamar hakura da juna shi ya fi” Mama ta yi murmushi ta shafa fuskata. “Kin yi tunani mai kyau Zahra, kuma fatar hakan ya zama silar samuwar farincikinki, Allah ya sa haka shi ne alheri a tsakaninku kuma yayi muku mafita dukanku” “Ameen Mama” Na fada ina kara fashewa da kuka, nan wata duniyar kukan na gina sai da Mama ta rarrashe ni sannan na yi shiru na kwanta akan tabarmar da muka kwana a jiya. Misalin tara na safe Yayanyun mahaifiyata da kanenta suka shigo na gaishe su na koma na kwanta, ina ta sauraren hirar da suka da Mama yawancin su Abiey suke dorawa laifi wasu kuma Mama domin a ganinsu ita ta bar ni na fita alhalin ina cikin jego. A nan take labarta musu cewar tana son zata kama haya babu wanda ya bata goyon baya suna ganin kamar be dace ta bar gidan ta je ta kama haya a wani gurin ba. “Ba zan kama inda zan zauna ni kadai ba, amman dai na fi son na kama hayar ko dan Zahra da bata gama wanka ba, ba zan zauna ace kullum sai na je kofar wasu na dora ruwan zafi ba, ko kuma idan zan dafa wani abu ko ita na dafa mata sai na je wata kofar ba, kuma ďakin nan ba gyaren ba ne bandakin ma sai ka zagaya a na mutane ai dai ba haka ake so ba, kenan miji ya fi miji kyau” “To ai zaman da zaki yi ba wani mai dade ba ne, domin fatan a gyara muke ba wai a yi ta zama a haka ba, na san idan an kwana biyu ya huce zai nemi ki” Cewar wani kanenta sai ta yi murmushi ta ce. “To ko da za a koma din ai ka ga na samu muhallin zama, ba sai yayi wahalar nema ba, ni dai kam da zaku yarda ku bar ni da na saba da wacan unguwar sai na kama hanya a can mu zauna” Ganin ta dage yasa suka amince mata ta kama hayar a can, ni kaina zan fi jindadi zama a can sama da irin wannan gidan da yake na iyalai wani lokacin akwai ganin laifi da gulma kara dai gurin da kake zaune kai kadai ko kuma da wasu da ba yan'uwanka ba. Sun dade suna hira sannan suka fita Mama ma fita ta yi ta shiga bangaren Matar kanenta ta yi wanka ta dawo ta shirya a dakin. “Akwai abun da za a dauko miki a can? Zan tafi na dauko wasu kayan na mu kuma na fadawa Malam Zubairu ya nema mana gidan haya a can unguwar” “Babu abun da za a dauko min” Na fada ina ta jin haushin mutane da zarar na tuna abun da ya faru a daren jiya sai na ji kuka na kwankwaso min kofa, sai faman sharar hawaye nake musamman ma da Mama ta fita sai ya zamana ni kadai ce a dakin hakan ya bani damar fashe kurjin kukana na tausayawa kaina, idan na ji motsin matan gidan kamar za su shigo sai na fake na yi kamar bachi nake. Daga Maman Mufeedat har Matar Kawu Bala da suka kawo mana abincin rana ba su ga fuskata ba. Mama kuma bata dawo ba sai kusan la'asar ina jin sallamarta na tashi zaune ina jiran ta shigo na yi mata nata kukan na tafiya ta bar a ni kadai a ďakin domin a yanzu laifin kowa nema nake na rasa abun da yake min dadi. “Zahra kina nan ďaki har yanzu” Sai kawai na fashe da kuka. “To Mama ba kin tafi tun safe sai yanzu kika dawo kin bar ni ni kadai kuma kin san ba wani guri nake zuwa ba kuma ba sabawa na yi da gidan nan ba” Tsayawa ta yi tana kallona daman can ta san ni da shagwaba sai dai bayan na yi aure Shagwabar ta koma gurin Deen. “To ba ni kadai na dawo ba, tashi ki wanke fuskarki” “Da wa kika zo?” “Hajiya Jamila gata nan kofar ďaki” Ban san lokacin da na zabura na tashi tsaye ba. “Mama Hajiya Jamila kuma? Mi ta zo yi a nan? Mama kin san gidan family ne fa miya sa zaki zo da ita?” “Na je can ina cikin unguwar sai gata ta zo, kuma ta matsa tana son na kawo ta gurinki na nuna mata ba zan yi haka ba, amman ta dage tana son ta yi magana da ke” “Mi zan mata?” “Shiyasa na zo da ita, sai ki ji bakinta” Mama ta leka ta ce ta shigo, sai ga ta shigo dakin tana sanye da dogon hijab har kasa fuskarta da mask hannunta rike da makullin mota, hannu ta saka ta cire mask din tana kallo na fuskarta abun tausayi idonta har ya fada kamar wanda ta yi kuka ko kuma ta kwana da ciwo. “Zahra...” Ta kira sunana ban amsa ba. “Na san zaki yi mamaki ganina a nan ko?” “Ki yi saurin fadar abun da zaki fada a gidan taro muke kuma wannan ya zama karo na karshe da zaki shigo gidan nan” “Toh daman na zo ne akan maganar mu” Yanayin yadda take maganar sai ka rantse da Allah masinja ne yake magana da ubangidanshi. “Na ce zan yi shawara ai” Ta matso kusa da ni sosai ta kama hannuna sai ta fara hawaye. “Zahra ina cikin babbar matsala, asirina zai iya tonawa idan baki koma kin cigaba da shayar da yaron nan, akwai barazanar rasa rayuwarshi, kuma asirina yana gaf da tonuwa, tonuwar asirina na nawa ba ne ni kadai har da ke da Dr Hamid” “Miya hada ni da tonuwar asirinki?” “Saboda Mai gidana ya dage yana son a kai yaron asibiti a duba lafiyar shi, kuma hakan zai iya sakawa a gane cewar ba ďanshi ba ne, idan kuma ya gane gaskiya zai iya hukunta ni da ke da Dr Hamid, sannan aurena mutuwa zai yi kuma shi ma yaron zamu jefa rayuwarshi cikin wata matsala, mijina ma zai shiga damuwa sosai, amman idan kika yarda kika koma a gidan ki ka cigaba da shayar da shi babu wanda zai gane, kuma kin ce ci rayuwata da ta mijina da taki da ta yaron da kuma ta Dr Hamid...” Na kalli Mama sannan na sake kallontabna girma mata kai ina bude baki kamin na ce komai ta yi saurin durkusawa masa ta kama kafafuwana tana kuka sosai. “Ki taimaki rayuwata Zahra dan Allah ki rufa min asiri ki fada min ko nawa kike so zan biyaki, dan Allah ki taimaka min, Ki tausayawa yaron nan shi kanshi abun tausayi ne ya zai ji idan ya bude ido ya ga abun da muka aikata? Da wane idon zaki kalleshi? Kuma dukanmu zamu jefa rayuwarmu cikin hadari kuma duniya zata ji abun da muka aikata, za mu kunyata Zahra karshenta mu kare rayuwa a gidan yari, Mama ki sa baki dan Allah” Ya juya gurin Mama tana kuka sosai kamar ba ita ba, daga ni har Mama mamanki ta muke. “Idan na koma a can me zan fadawa mutane? Ba zan iya ba gaskiya” “Babu wanda zai gane a yanzu saboda gidanku da aka rusa Mama ta fada min abun da ya faru, ina son ku koma gidana da zama a akwai BQ zaku iya zama a can kin ga mijina ma ba zai gane ba, kuma nutane ba za su yi zargin komai ba, na miki alkawari idan kika gama shayar da yaron zan siya miki gidan da za ku zauna, kuma zan baki enough kudin da zai taimaka muku, kuma ki fadi ko nawa kike so a yanzu zan baki” “Duk da haka dai ina bukatar shawara” “Zan barki ki yi shawara Zahra, amman ba tafiya zan yi mai nisa ba, zan je na zauna a mota na jiraki dan Allah ki tausaya min kar na rasa ďana da mijina” Wani irin kuka take sosai har gabana faduwa yake kar wani ya ji kukanta ya leko ya same mu a wannan halin. “Dan Allah ki tashi ki tafi kar wani ya shigo ya same ki a nan” “Idan ma ba a same ni a nan yau ba, za a same ni a gobe da jibi har sai Allah ya saukar da tausayi a zuciyarki kin amince da bukatata, Wallahi da kin san mawuyacin halin da nake ciki da kin tausaya min, rashin haihuwa masifa ne shi yaja min komai” Ta mike tsaye tana share hawayenta ta fice, daga ni har Mama da kallo muka bita, ko da karya Hajiya Jamila take ta yi nasara akaina domin kuwa tausayinta ya kama ni, kamar yadda na ga tausayinta a fuskar Mama. “Mama ban san miyasa kika kawo a nan ba, yanzu damu na zata fara yi har sai asirina ya tonu” “Irin magiyar da take miki yanzu tana kuka irin ta ta yi min a can kofar gidan mutane, tausayinta da kuma gudun zargin mutane ya saka dole na amince na kawo ki gurinta, kuma idan har baki son tonon asiri dole ne ki amince da abun da take rokonki domin idan mijinta ya gane gaskiyar siyen yaron nan ta yi zai daureku daga ke har ita, kamin ayi bincike a gano mai gaskiya har a fitar da ke kin kunyata a idon duniya kuma kin yi zaman gidan yari, Hajiya da duk wanda be san komai ba zai sani, kuma ba za su dubi abun da kika yi a matsayin taimako da ceto rai ba, za su ce da gangan kika aikata, labarin ki zai yadu a ko'ina wata kila har ya shafi Abiey, kuma idan kika taimaka ke ma kin ceto rayuwar ďanki ba wai ita kadai kika taimakawa ba, kuma a irin wannan lokacin kike da damar taimako domin idan har muka riga muka kama haya ba zai yiyu mu bar gidan mu koma wani guri da zama ba, kuma zai yiyu ki koma can da zama ba, amman a yanzu babu wanda zai zargi wani abu domin kuwa rufin asirin ba nata ba ne ita kadai har da ke, a halin yanxu idan asiri ya tonu daga Malam har Hajiya sai sun maka ki kotu akan kin siyar musu da ďa kin musu karyar ya mutu” Na kalli Mama cikin yanayi na damuwa. “Idan kuma muka koma gidan wata matsala ta faru fa?” “Ba na fatar haka, kuma ina fatar nan ba da jimawa ba Allah ya baki mutumen kirki ki aura ki cigaba da rayuwarki a gidan mijinki ita kuma ta cigaba da na ta rayuwar” “Amman yanzu me zamu fadawa mutane?” “Mai sauki zan ce wata mata yayar kawarki ce da ta ji abun da ya faru sai ta ba mu muhalin zama a gidanta kenan babu wanda zai makuri ni akan sai na fadi gaskiya, amman ba zan cilasta ki ba idan har kina ganin zaki takura kanki ne ko kuma saka kanki a cikin wata matsalar karki amince, ni ma na fada ne kawai saboda ina ganin hakan shi ne mafita a gurin gaba daya” “Amman Mama idan aka shirya aurenki da Baba ya zamu yi? Kin san ba lallai ya yarda ya zauna a can ba” “Idan ma be zauna acan ba, ai dole ya kama min haya domin ba shi da wani gida da zai aje ni a yanzu sai wanda yake ciki tare da Hajiya shi ma kuma na haya ne ba na shi ba, idan ma na dawo mun zauna a wani gurin shi ma mafita ne domin a gidan Hajiya Jamila zan barki ki cigaba da zama har sai yaron yayi kwari albashi idan mutane suka tambaya sai na ce ita Hajiya Jamila ta bukaci na barki a can, ko ya ta kama mafita ce a garemu Zahra” Na zauna akan tabarmar ina nazarin maganar Mama, tabbas tana da gaskiya ta wani bangare amman ina tsoron halin Hajiya Jamila tun tafiya bata yi nisa ba ma ta fara wulakanta ni a gidanta balle kuma ace nan gaba! Na san tana cikin matsala sosai tun da har ta iya dukawa har kasa tana rokona tana kuka, idan ma zan yarda na zauna a gidan sai da sharadi da kuma yarjejiyar abubuwan da tace zata yi min kuma ba zan shayar da yaron a kyauta ba sai ta na yanka mata albashin da zata rika biya duk karshen wata. [11/7, 11:12 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣1️⃣ Ban yi zaton da gaske take a waje zata jiramu har mu yi shawara ba sai da na ga ta dawo cikin gidan. Wannan karon idonta a kumbure yake sosai da alama zaman jiran mu da ta yi a motar ma kuka ta yi, yadda ta shigo cikin ďakin sai ka rantse da Allah ba za a saka mata yatsa a hannu ta ciza ba sumi sumi da ita abun tausayi. “Allah yasa kar na yi mummunan ji dan Allah Zahra ki amince da kudirina ki taimaki rayuwata dan girman Allah” Na kalli Mama Mama ta kalleni sannan ta kalli Hajiya Jamila ta ce. “Zauna Hajiya” A take Hajiya Jamila ta zauna kamar daman can umarni kawai take jira, hankali a tashe take kallonmu na san fargabar ta ba zai wuce na tsoron kar mu ki aminta da kudirinta ba. “Na yi magana da Zahra ko kuma na ce mun yi shawara kuma Zahra ta amince da bukatarki, amman bisa wasu sharuda da zan gindaya miki yanzu nan” Hajiya Jamila ta tattara hankalinta gaba daya ta maida gurin Mama ni kaina kallon Mama nake domin ban san sharudan da take magana akai ba, na sai dai na ce ni ma ina da nawa sharadin amman ban fada mata ba a zuci na yi maganar. “Ina jinki Mama” “Na farko ba zan dauki ki wulakanta min ya ko ki ci mutuncinta ba, na biyu a duk lokacin da yata tace zata daina shayar da ďanki zata daina ko da kuwa ba ki so haka ba a wannan lokaci, abu na uku Zahra zata shayar da yaron ne a matsayin yar raino saboda haka dole ne duk wata ki biyata naira dubu ashiri, babu barazana ko kulla wani makirci a tsakaninki da ita” “Shikenan sharadin ki Mama?” “Eh kuma zamu yi haka ne a rubuce kamar yadda kika wacan yarjejeniyar a rubuce” “Na yarda” Ta fada da sauri tana kama hannun Mama tana mata godiya har da kukanta. “Na gode Allah ya biya muku bukatunku na alheri ya raya” Ta taso ta rumgume kamar zata hadeye ni a cikinta tsabar murna. “Amman dan Allah ina rokon wata alfamar ku yarda ku koma gidana a yau din nan ko kuma gobe idan da hali” “Yau kuma?” Ta amsa min da sauri Mama ta ce. “Kin yi magana da mijinki ne?” “Aa be san komai a kai ba, mijina baya son mai aiki amman na san zai amince da Zahra a matsayin mai aiki saboda ta taba taimakonshi, yanzu ma zan mashi karyar cewar an rusa gidanku ne ba ku da gurin zama shiyasa na baku bq ku zauna, idan na fada mashi kamin ku dawo zai iya cewa na bari a siya miki wani gidan, domin yana neman hanyar da zai saka miki da abun da kika mashi ne shiyasa yake ta yawan tambaya ta ke da inda za a same ki ni kuma na mashi karya cewar matar data kawo min ke bata sake dawowa ba, kuma ban san halin da kike ciki ba na fada mishi cewar kin tafi zaki dawo amman baki dawo ba, kuma zuwanki a yau ko gobe zai taimaka min a fasa zuwa asibitin” “Sai dai zuwa gobe, amman yanzu zan shiga da ke ki gaishe da mutanen gidan su sanki kuma na fada musu kudirinki tun a yau” Mama ta fada a take kuwa ta amince bayan ta fada mana cewar zata aiko mana da motar da zata kwashi kayanmu. Babu inda Mama bata zagaya da ita ba cikin gidan ta fada musu abun da ta yi mana cewar ta ba mu gurin zama a gidanta, sai dai Mama bata fada musu ko matar waye ba, su ma kuma ba su santa ba domin ba fita take ba kuma ba wata fitattaciyar mace ce ba da za a ce kowa ya sani, mijinta ne fitacce shi ma kuma wasu sunanshi kawai suka sani ba su san fuskarshi ba. Abun mamaki tun a ranar Hajiya Jamila ta aiko da motar aka kwashi kayan mu da suke can unguwar da aka rusa mana komai aka kai gidanta aka zube, sai dai ni da Mama ba zamu koma ba sai gobe da safe kamar yadda ta bukata bayan ta tsara mana yadda zamu yi idan mun shiga gidan, kowa da irin zaton da yake mana musamman makonta mu domin wasu sun yi tunanin mutumen da yayi fada da Baba ne ya bamu wani gurin wasu kuma suka ce yar uwarshi ce wasu kuma sai su tambaye mu wacece ita. Haka dai aka taya mu kwashe kayan muna mikawa mazan suna saka a mota ana ta mana tambayoyin gulma, ni dai bana iya cewa komai sai ta kama dole Mama ce take da karfin halin amsa musu ni kuma ina fama da wani irin ciwon kirji da ban taba jin irinshi ba kuma ban fadawa kowa ba. A daren daker bachi ya dauke ni saboda tunani da kukan rabuwata da Abiey wanda na tabbatar hakan shi ne alheri, bana da tsarki balle na ce zan raya daren da sallah, sai dai na dauki carji ina ta salati da istigifari har garin Allah ya waye ban samu bachi ba gashi numfashi ma ji nake kamar ba ya wadatar min yadda ya dace, sai dai bana son fadawa Mama kar na kara tayar mata da hankali tana cikin nata tashin hankalin. Da safe bayan na yi wanka Mama ta saka Maman Mufeedat ta hada min tea amman ban iya sha ba, zuciyata sai zafi take kai kuwa kamar zai rabe gida biyu saboda ciwon da yake, ruwan sanyi na aika aka siyo min na sha na kwanta, sai ga yaro ya shigo wai ana sallama da Maman Zahra a waje, Mama ta yafa mayafinta fita bata dade ba ta dawo tace min na tashi na kintsa. “Amman Mama mutane ba za su yi wani tunanin ba? Kowa tun da farar safiya? Ba tare da rakiyar kowa ba?” “Ba zamu ce musu komawa zamu yi ba, zan fada musu cewar zamu je mu ga gurin ne idan mun yi magana da shi ya amince sai mu dawo mu fada musu cewar zamu koma a can din albashi idan suna son raka mu sai mu tafi tare” “Toh” Na amsa ina jin kaina na min wani irin tsara jiri har kwasata yake saboda ciwon da kan nawa yake, Mama ta sake fita ni kuma na tashi na dauko hijab dina na saka na saka talkamina na jingina da kofar ďakin ina jin kamar na yi ta ihu. Ganin idona a rufe yasa ta kira sunana. “Zahra” Na bude idon na kalleta da sauri. “Lafiya?” “Lafiya Kalau ina jiranki ne” “Tunani kike yi?” Kamar tace min fadi ki yi ta kukan rashin masoyinki haka na ji a take idona ya cika da hawaye, ai dole na yi tunani domin ina son Abiey musamman ma a yanzu, na fada a zuciyata a zahiri kuma sai na ce “Aa kaina ne yake dan ciwo kadan” “Bari na baki magani ki sha, ba ki ma ci komai ba Zahra” “Ba zan iya ci ba, maybe sai mun dawo maganin ma ina jin kamar idan na sha zan iya yin amanshi ki bari sai zuwa anjima idan na ci abinci sai na sha” Bata ce min komai ba, sai kallona take cike da damuwa. “Mu tafi” Na shiga gaba ta fi bayana ko da muka fito mun samu wani dan'uwanta a kusa da motar yana jiran fitowarmu ba karamin faduwa gabana yayi ba, ita kanta na tabbatar ta tsorata da ganinshi musamman da ya furta cewar zai bi mu mu tafi tare ne. “Da dai ka hakura muje mu ga muhallin kasan masu kudin nan ba son jaye jaye suke ba, idan muka ga guri sai mu dawo a tafi tare gaba daya” Da wannan Mama ta yi nasara ya yarda muka shiga bayan motar ni da Mama ya rufe mana direban da ta aiko jiya tare da Mai diban kaya yaja motar muka fara tafiya, kwantar da kaina na yi jikin Mama sai na ji hawaye suna min zuba, har yanzu zuciyata bata yarda ta dauki kaddarar rabuwa da Abiey ba, ban kuma san ranar da zata dauka ba, rabuwa da wanda kake so ba shi da sauki musamman ma ace mutumen yana raye, zafin rabuwar mu da nake ji a yanzu yafi wanda na ji a lokacin da ya fasa aurena, domin a wacan karon ina mashi kallon mayaudari ne a dole na koyawa rayuwata rashinshi wannan rabuwar kuma mai zafi ce wanda ta fi garwashin wuta, da zarar na tuna cewar Abiey yana raye an gina mana katanga a tsakaninmu ne sai na ji kamar na hade zuciya na mutu, da ace na san irin wannan wahala ake sha a so irin wannan zafin ake ji idan an rabu da ban yarda na karbi soyayyar Abiey ba tun farko wata kila da abubuwan da suka faru ba su ba faru ba, da yanzu ban ji wannan radadin da nake ji ba, zai dauke ni yaushe kamin zuciyata ta aminta da kadararta? Tsawon wani lokaci zan dauka kamin na saba da rashin Abiey? “Ba zan sake son kowa ba, ba zan sake bari zuciyata ta kamu da kaunar kowa ba, ba zan yarda na sake kula kowa ba” Na yi zaton a badini nake wannan zacen har sai da Mama ta yi magana sannan na ankara da zahiri ne. “Hakuri ake Zahra kowa da kalar kaddararshi, ke na ki son a haka ya zo wasu a gurinsu dadi ne kuma waraka ce, ke kuma a gurinki ciwo ne” Na fashe da kuka na saka kaina a jikin Mama, har muka isa gidan kuka nake, gidan ba bakona ba ne domin kuwa ba wannan ne zuwana na farko ba, hakan yasa ban maida hankali gurin tsari da kyau gidan ba, hankalina da tunanina sun ni nisan zango a duniyar damuwata, zuciyata ji nake kamar ta tsaya gurin daya ba bata motsa min, kaina sai sarawa yake kamar a ciki ake yakin duniya direban da ya kawo mu ne ya shiga cikin gidan be dade ba ya fito yace da mu shigo ciki, cikin karfi hali na daga kafana na fara takawa jiri na daukata har muka shiga cikin falon. “Sannunku da zuwa ku karaso nan” Na kalli saitin gurin da suke zaune ita da mijinta da kuma wata budurwa da ba zata wuce sa'a ta ba, wacce ta taba kai ni gurin yan'uwan mijin Jamila. Duk mutum daya a mutun hudu nake ganinshi saboda jirin dake daukata takawa nake ina tafiya amman ji nake kamar ina nutsewa a cikin ruwa, tafiya nake har muka karasa inda suke zaune a inda Mama take ganin ya kamata mu tsaya ta ja ta tsaya ni kuma na cigaba da tafiyar kamar zan fada kansu har sai Mama ta riko ni. “Zahra lafiya kike?” Na juyo na kalleta ita ma a mutun hudu nake ganinta bakinta ma dake motsi hudu nake ganinshi, zaunar da ni ta yi a kasa kamar yadda na ta zauna ta gaishe da mijin Jamila da Hajiya Jamilar kanta da kuma budurwar da ba zan iya shaidar sunanta ba. “Yanzu nake mishi bayanin abun da ya faru na rushe muku gida da aka yi, na fada mashi jiya ma kun zo nan tun safe kuna jiranshi har yamma be dawo ba” Cewar Hajiya Jamila cikin muryar magiya da tausayi irin na masu neman mafita Mama ta dora da “Eh mun zo shiyasa ma tace zata aika yau a dauko mu idan kana gida kasancewar yau weekend, Alhaji a taimaka mana dan Allah a ba mu gurin da zamu laba cikin suturar da Allah yayi maka” Cikin jindadi na ji muryar Alhaji Bashir yana fadar “Karki damu zan baku BQ ku zauna kamin a siyo muku gurin da zaku zauna saboda Zahra babu abun da ba zan iya ba, yarinyar nan ta taimaki rayuwata kuma na jidadin haka fiye da zatonku ba dan Allah ya bata iko ta taimaka min da yanzu wani labarin ake ba wannan ba, kuma na jidadin da kika tuna da ni a lokacin wannan matsalar ta same ku kuma kuka nemi taimako na” Magana yake kallonshi nake amman bana ganin mutun balle wani abu dake cikin falon gaba daya hudu ya baibaye idona maganar shi kawai nake iya ji da kuma na yarinyar dake tambayata. “Wai daman labarin da ya karade media akan Abiey ke ce yarinyar da ake fada?” Juyawa na yi na yi na kalli inda nake jin sautin muryarta na fitowa, da kuma ta Alhaji Bashir dake tambayar matarshi. “Ba kin fada min cewar mijinta ya rasu ba? To wanene wannan?” “Wannan kuma sai dai mu ji daga bakinta Hubby ni kaina ban san alakarsu ba...” Ita ce amsar da Hajiya Jamila ta bashi kuma ita ji sautin murya ta karshe da na ji daman na dade da rasa ganina halshena kuma yayi nauyin da ba zan iya daga shi na furta ko da A ba, da wani irin karfi aka fisgi numfashina har sai da na mike tsaye na saka hannuna a kirjina ina wani irin kugi ina jin hannayen mutun biyu a jikina masu kokarin rike ni amman hakan be hana ni kai wa kasa ba ina ta kokuwa da ran dake neman barin jikina, kamar an yaye min hijabi haka ganina ya dawo farat daya wata kila ina rabon na yi ma Mama ganin karshe ne domin fuskarta na fara arba da ita tana ta jijjigani tana kuka kamin wani duhun yayi min sallama numfashi ma ya tafi ban sake sanin komai ba. ABIEY POV. Banbanci shi da mai jinya asibiti kadan ne, mai jinya asibiti yana samun kulawar likita a yayinda shi kuma ya kulle kanshi ciki ďaki yana jinyar zuciyarshi ba tare da samun kulawar kowa ba, domin ya ki yarda da sake da Ammy ma balle ya karbi kulawarta tun a shekaran jiya da Zahra ta yi masa furucin rabuwa, sosai yake son ya tabbatar mata cewar yana kaunarta kuma akwai banbanci a tsakanin soyayyar da yake mata da kuma ta Deen, sai dai ta dayan bangaren yana jin kamar ba zai iya ba, domin a yanzu ya fi kaunar Zahra fiye da da, sonta na fisgarshi kamar zai raba zuciyarshi da gangar jikinshi. Kamar jiya da shekaran jiya ya wuni a ďaki yau ma a dakin ya kuduri aniyar wuni, yana kwance saman gadonshi Ammy ta shigo cikin yanayin na damuwar da ya gagara boyuwa a fuskarta, bakin kofar dakin ta tsaya tana kallonshi. “Aliyu ka daina fitowa cin abinci, idan an kawo maka haka za a fita da shi lemu kawai kake sha sai ruwa, so kake ka jawa kanka wani ciwon ne?” “Bana son abinci ne shiyasa ko ina son na ci bana iya ci” “To ka tafi asibiti mana” “Zan tafi gobe” Har ta juya sai kuma ta juyo. “Yasmin tana garden tana jiranka” Ya daga mata kai cike da ladabi. “Zan fito yanzu” Sai da ta sake kallon kyakkyawar fuskar ďanta sannan ta juya ta fice. Mikewa yayi tsaye ya zura talkaminshi tare da daukar wayarshi ya rike a hannu ya bude kofar ya fice, kai tsaye garden ya nufa har ya isa gurin da Yasmin take zaune be kalleta ba ita ma kallo daya ta yi mashi ta dauke kai gabanta na faduwa, zaunawa yayi a dayar kujerar ita da shi aka rasa wanda zai fara yi ma dan'uwanshi magana, can dai ta daure tana wasa da hannun Hijab dinta ta ce. “Ammy ce tace a dauko na zo na duba ka baka da lafiya” Be ce mata komai ba sai yawo yake da idonshi a swimming pool din dake gabansu. “Ya jikinka?” Sai a lokacin ya kalleta “Babu sauki kuma babu ranar warkewa, idan har zaki biye Ammy to zaki ta ta zuwa duba lafiyata ne har zuwa lokacin da za'ayi auren sai ki cigaba da jinyata har ki rufe gawata” Ta sauke idonta kasa. “Daman na yi zaton rashin lafiya ce irin ta mutane I'm sorry” “You shouldn't ba laifinki ba ne, but I'm telling you this saboda ki saba tun yanzu” “Sabawar ba mai wahala ba ne, yardar ce mai wahala, ka jefa mu a cikin matsala musamman ni zan cutu da yawa Abiey” Tana fadar haka ta mike tsaye hawaye sai zuba suke mata ta fice daga gurin, shi kam binta yayi da kallo har ta bace mashi sannan ya cire key wayar dake hannunshi ya kira line Sauban. Yanayin yadda Sauban ya amsa wayar ya isa ya sanar da Abiey cewar Sauban yana tare da matarshi ne. “Abiey?” “Sauban ina son ganinka ni zan zo ko kuma kai zaka zo?” “Kana ina?” “Garden din Ammy” “I will be there soon” Abiey ya dauke wayar daga kunnenshi yana ta kallon harabar gurin da tunani kala kala a zuciyarshi, cikin mintunan da ba su wuce salatin ba Sauban ya iso gidan yana faka motarshi ya nufi hanyar garden din dake ta bude kasancewar hanya biyu ce za a iya shiga garden ta harabar gidan kuma za a iya shiga ta cikin falon Ammy. Abiey kallon abokinshi yake har ya iso ya zauna a inda Yasmin ta tashi. “Gaba daya ka canja Abiey ka ga yadda ka rame wai? Jiya baka kai yau rama ba gobe kuma ban san ya zaka zama ba, ya kamata ka dauki kaddara baka san me Allah yake nufi da ku ba” “Ina ta kokarin haka Sauban” Ya fada sannan ta tashi zaune daidai yana aje numfashi a muhalin da ba nashi ba. “Akwai wata matsala ne?” Sauban ya tambaya domin ya ga alamar hakan a fuskar abokinshi kuma ya san Abiey ba zai bukaci ganinshi haka nan kawai ba tare da wata matsala ba, kamar yadda shi ma idan wani abun ya ta so shi gaba yake neman Abiey su warware. “Sauban so nake na je ka nemi auren Zahra...” Abiey ya fada mishi kai tsaye babu alamar wasa ko zolaya a tare da shi, mutuwar zaune Sauban yayi wanda ta fi ta tsaye tashin hankali da mamaki. “Wh... Wha... What...” Har furta har sau biyu sai a na uku ya iya hada kalmar. Wayar Abiey ce ta yi ringing da kamar izza Abiey ya kalli wayar ganin number yayarshi ce Dr Zainab ya saka shi amsa kiran. “Hello” “Abiey yanzu aka shigo da Zahra asibitin nan gurin abokin aikina wanda ka taba ganinsu a tare wai zuciyarta ta buga, Mamanta sai kuka take” A firgice Abiey ya mike tsaye be san lokacin da ya saki wayar ba ya mikawa Sauban hannu. “Ba ni key din ka” “Lafiya” Sauban ya tambaya, Abiey be tsaya ba shi amsa ba ba ya fisge key din hannunshi ya fice Garden din da gudu. [11/8, 9:35 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣2️⃣ Kamar mahaukaci haka ya isa asibitin tun suna cikin mota Sauban ke tambayar Abiey abun da ya faru amman ya kasa magana ka kasa ce mashi komai, sai gudu yake har suka isa asibitin. Kamar an koroshi haka ya fito daga motar Sauban ma saurin sauka yayi ya zagaya driver side ya kashe motar ya rufe sannan ya bi bayan Abiey, Office din Dr Zainab Abiey ya shiga hankali a tashe ita kanta Dr Zainab sai da ta tsorata da yanayin yadda ya shigo office din. “Ina take?” Dr dake magana da wani abokin aikinta ta mike tsaye tana kallon shi. “Da sauki fa ka kwantar da hankalinka” “Wane ďakin take?” Abiey ya sake tambaya a daidai lokacin da Sauban ya shigo office din. “Follow me” Dr ta fada sannan ta wuce gaba suka bi bayanta shi da Sauban kamin ta kai shi ďakin da Zahra take har jin yake kamar ya kara mata saurin kafafuwa, suna isa bakin kofar ďakin Dr Hamid na fitowa tare da wani likitan da nurse, Abiey be tsaya komai ba ya mika kafa zai shiga ciki sai Dr Hamid ya tara mashi hannu a bakin kofar. “You're?” Abiey yayi mashi wani banzan kallo. “Abiey” Sauban ya amsa mashi sai Dr Hamid ya kalli Sauban. “Alakarsu nake magana ba sunanshi ba” “Dr please bar shi ya shiga, hankalinshi ba zai kwanta ba har sai ya ga yarinyar nan” Dr Hamid ya dauke hannunshi yana kallon Dr Zainab zai bar Abiey ya shiga ne kawai saboda shi ma yana son yayi requesting wani abun a gurin Dr Zainab ba dan wannan ba da sai ya wulakanta Abiey a gurin. “Amman karka tashe ta bachi take bukata, domin zyciyarta ta yi bugawar da ba dan tsarin Allah ba da yanzu an rasa ta” Abiey ya shiga ďakin da sauri, sai Dr Hamid ya kalli Sauban ya ce “Zaka iya jiranshi a waje” Sauban ya kalli Dr sai ta daga mishi kai, hakan yasa ya juya domin komawa gurin motarshi zai fi mashi ya jira shi a can sama da ya jira shi a nan. Sai da Sauban ya wuce Likita da Nurse din dake tare da Dr Hamid suka fice daga gurin sannan Dr Hamid ya jero tare da Dr Zainab yana tafiya yana labarta mata a halin da ya samu Zahra. “Subhanallahi Allah ya tsare gaba” “Ameen, Dr akwai rokon da nake son na yi miki” “Ina saurarenka” Ta furta a yayinda ta ja ta tsaya ta hade hannayenta tana kallonshi. “Akan maganar yaron kanwata ne Amir ďan wajen Alhaji Bashir shekaranjiya matarshi take fada min cewar mijinta ya zo da ke akan Matsalar yaron na rashin shan nono” “Eh an yi haka yau ma na ce ta zo asibiti mu fara auna nononta” “Eh haka tace amman akwai maganin da na dorata a kai ne wanda muke fatar zai karbeta ko kuma ya karbi jaririn, sai dai mijin nata ne ba shi da hakuri kin san be taba haihuwa ba sai wannan karon shiyasa ya daga hankalinshi sosai akan lamari, rokon da nake son na yi miki shi ne ina son ki kara min time nan da kwana biyu mu ga yadda maganin zai karbe ta, sai dai bana son ki fada mashi ko kuma ki nuna mashi wani abu, saboda zai iya nuna rashin yarda ko kuma ya ga kamar bana son a kawo yaron gurin wani likitan ne” Cikin Mamaki Dr Zainab ta ce. “Daman kanwarka ce?” “Eh uwarmu daya uba daya, ai tana fada min sunanki ta siffanta min ke sai na gane ki domin ita ma kanta tace ta fara ganin sauki amman mijin nata ne be yarda ba, ita kuma bata son abu ya zama biyu duk wani bincike da ya kamata mu yi mun yi amman yana ganin kamar dai ban yi abun da ya dace ba” “Allah sarki shiyasa na ga ta fita ďakin tana kuka, ba matsala, zan daga kafa Inshallah kasan mai neman haihu kamar mutuwa tana neman rai ne ko'ina shiga yake” “Haka ne ni ma ai ban ga laifinshi ba.... ” Haka suka jera suna tafe suna hira har suka isa gurin da za su rabu kowa ya nufi gurin aikinshi. ABIEY POV. Yana tura kofar ďakin ya hangota kwance an saka mata oxygen an daura mata drip, babu kowa a dakin sai ita kayan da tukunyar oxygen da kuma machine din dake nuna yadda numfashinta ke tafiya, karasawa yayi kusa da ita ya tsaya kanta yana ta kallon fuskarta da wani irin tausayi, ya dade a haka sannan ya zauna yana kallon dayan hannunta dake karamin yatsanta ke sanye cikin wani karamin abu mai kamar zobe, ya sake kallon fuskarta dake ta haske dogon hancinta na kara fitar da kurciyarta da kyau da Allah yayi mata. “Na fada miki Zahra ba zamu iya ba, ko mutuwa na yi ina da tabbacin za ki wahala kamin zuciyarki ta karbi wannan kaddarar balle kuma ace ina raye kin san da ina rayen kuma zan rayu da wata ba ke ba” Yayi murmushi idonshi na cika da kwalla zuciyarshi cike da rauni. “Ina kishinki yake? Taya zuciyarki zata iya daukar rashina a karo na biyu? A farkon ma ya kika kare balle a yanzu? Abubuwa da yawa sun lalace Zahra we can't fix it, wata kila da yanzu muna a matsayin mata da miji amman ji yadda kaddara ta yi da mu” Ya shafa hancinsa iyakar kokarinsa yayi na hawayenshi zuba. “Da farko Deen, yanzu kuma Ammy Mai Martaba, Step Fasher dinki, ban san abun da Allah zai mana nan gaba ba amman Zahra ni ma ina jin kamar rayuwata ba zata yi tsawon da zan dade ina rayuwa da wata macen da ba ke ba, rabuwar mu ta farko ta maida ni kamar mahauci kuma na kamu da ciwon zuciya a lokacin da kika sake dawowa rayuwata i thought na warke ashe ba haka ba, silar karuwar ciwon ne” Yayi shiru ya sauke kanshi kasa hawayen da yake ta kokarin hana su zuba suka sauko mishi. “Kowa da kaddararshi ni ban rasa uba amman na rasa gatanshi, ban rasa uwa ba amman na rasa farinciki” Ya dago yana kallon pretty face dinta. “Wasu mutanen za su yi mana kallon wawaye, miyasa za ki fadi ki suma saboda da ni ko su ce miyasa ni wani abun zai same ni saboda ke, amman soyayya wani abu ne mai asali tsakanin bawa da Ubangijin ma akwai soyayya balle kuma tsakanin dan'adam da ďan'adam, to ina kuma ga mace da namiji, first love wani ciwo ne da ba a taba warke shi har a bada no matter how bad it hurts, ba ki fi Yasmin da sauran matan duniyar nan kyau ko asali ba Zahra, Allah sai ya saka min son ki ke kadai Zahra ba dan kina autar mata ba, be bude min zuciya saboda na so wata macen bayan ke ba Zahra, kuma sai ya kawo wata katanga yayi mana tsakani da ke abubuwa marasa dadi suke ta faruwa Allah shi ya bar wa kansa shi sani wata ni da ke mu samu farinciki a gaba” Ya mika hannunshi ta shafa gefen fuskarta. “Idan kuma be hukunta na mukasance a nan a tare ba, Allah ka min kyautar wannan kyakkyawar halitar taka a aljanna a matsayin mata, Allah kai ka saka min kaunar Zahra kuma ka sani ina kaunarta ya Allah idan har ba zamu rayu tare a duniyar nan ba, ya Allah ka mantar da ita soyayyata ta yadda zata samu sukunin rayuwa da wani cikin aminci, Allah karka azabtar da ita da kaunata, ni kuma ka bar min kaunarta ta yadda zan samu salama ko da mai irin sunanta na ji” Ya mike tsaye ya yana cigaba da kallon fuskarta, dayan hannunshi ya saka ya share hawayenshi. “Mun fada kaunar juna a lokacin da ba mu san minene so ba, kuma ba mu san komai zai faru ba, so be dubi cewar ke har talaka ce ni ďan mai kudi ya hada mu, haka so yake be duba kalar fata ko asali, so na gaskiya babu ruwanshi da komai... Pretty i'm broken deep down Zahra kaunaki kullum karuwa take a zuciyata” Yayi baya baya yana kallonta da murmushi a fuskarshi. “Get well soon Babe, I love you” Ya furta yana jin kamar kar ya tafi, ya dade tsaye bakin kofar yana kallonta sannan ya bude kofar ya fice ya zuba hannayenshi aljihu tashi zuciyar na mashi ciwo sosai kamar yadda ta saba, shi kanshi ya tabbatar ya fi Zahra juriya ne kawai ba dan haka ba shi da a yanzu yana kwance fiye da ita. Sauban na hangoshi ya yi ma motar key ya bude mashi front seat, Abiey ya shiga ya zauna yana kallon harabar asibitin kallo daya zaka mashi ka fahimci yana cikin damuwa. “Ta samu sauki?” Abiey ya kalleshi. “Mai irin wannan ciwo baya taba warkewa Sauban you got lucky baka taba rasa masoyiya ba, matar da kake so take son ka ita ka aura, that's why you will never understand how painful it's” Sauban ya juya motar suka fara tafiya. “Wai daman can Zahra tana da ciwon zuciya?” “Tana da ciwon so dai, irin wannan abun idan wata fargaba ko rashi suka same mutun shi yake sakawa zuciyarshi ta buga wani lokacin ma ana rashi shi gaba daya” Abiey na fadar haka ya juyar da fuskarshi yana kallon titi da motoci kamar ba shi yayi maganar ba. “Sauban ina son ka nemi auren Zahra” Sauban ya kalleshi daman be gama mamakin furucinshi na dazun ba aka kira waya maganar su ta yanke. “Wasa dai kake yi ko?” Abiey ya kalleshi. “Ka taba ganin na yi wasa akan wani lamari da ya shafi Zahra? I take everything about her serious” “Taya zan nemi auren Zahra Abiey ya kake magana kamar baka cikin hankalinka” “Na san abun da nake yi, wannan ce kadai mafitar da nake da ita da Zahra zata samu relief, and i believe zaka iya min abun da na bukata” “No ba zan iya ba, idan ma wasa kake yi ka daina joke a part, taya zaka nemi auren yarinya ku rabu baka samu aurenta ba yanzu kuma ka ce na nemi aurenta? Na ji na nemi aurenta idan kuma na nemi aurenta ta amince fa?” “Shi ne abun da nake so ai, amincewarta ko da bata amince ba ina son ka shiga ka fita har sai ta amince ta aureka” Cikin tsananin mamaki Sauban yake kallon abokinshi. “Abiey wai da gaske kake ne?” “Yes and i mean it, ina jin ban taba rokon wani abu a gurinka ba, wannan ne karo na farko kuma karo na karshe matukar ba ka amince min ba” “Abiey ka san fa na yi aure kuma ina son matata muna zaune lafiya, sai kawai na zo mata da maganar aure a yanzu? Duka duka yaushe ma aka yi auren to? So kake ka haifar min da fitina a zamantakewar mu?” “Idan ka ga dama zaka iya haifar da kanka fitana, idan kaka dama ka barta ta sani idan kaga dama ka boye neman auren da yin auren gaba daya” “Ai dole labari zai kai mata, kuma mutane ai sai su zarge ni” “Ka aje zancen zargi a gafe, karka kalli nutane da kyali kyalin duniya idan zaka yi taimako, Sauban ba zaka ce min aa ba, kana ganin halin da yarinyar take ciki i care about her so much, i feel her pain i laugh when she's laugh, idan wani abu marar kyau ya sake samunta i won't forgive myself, Zahra tana so na amman ta zabi ta hakura da ni saboda farincikin iyayena, akwai soyayyar da ta wuce wannan ne ta aure mutumen da be dace ya zama mijinta da farko yanzu kuma ba mu san iya abun da zai faru ba, Zahra need someone to talk to, wani wanda zai fada nata cewar komai zai wuce zai zama tarihi, wanda zai kwantar mata da hankali ya saka ta samu natsuwa” “Mutane za su kallon na ci amana Abiey kuma ita kanta Zahra ba zata aminta da ni ba” “Kai zaka saka ta aminta da kai Sauban dole ne ka min wannan, for the sake of our friendship” “Abiey yadda kake da kishi kake zaunar Zahra har zaka iya cewa na nemi aurenta?” Abiey ya hade yawu a yanzu din ma da yake gabatar mashi da bukatarshi wani kishin ke fisgarshi. “Dole ce ta saka” “No ba zan iya ba” Sauban ya amsa mashi a fusace, kallonshi Abiey yayi ya dauke kai. “That's means you end our friendship....” A firgice Sauban ya kalli Abiey kamin ya juya ya cigaba da tukin da yake he never thought Abiey da gaske yake sai yanzu, sai dai shi baya jin cewar Abiey yana cikin hayyacinshi yake mishi wannan maganar, har suka isa gida Sauban be sake cewa Abiey komai ba, Abiey kuma be sake kallon side da Sauban yake ba. Rai a bace Sauban yayi reverse ya bar gidan ba tare da ya shiga ya gaishe da Ammy ba kamar yadda ya saba. Abiey kamar wanda aka cirewa lakka haka ya hau entrance din Ammy ya murda kofar falon da ya samu a bude ya shiga ciki sam be lura da Ammy da bakuwarta dake zaune a wani bangare na falon ba domin hankalinshi ba ya gurin kowa sai Zahra dake can kwance. “Aliyu” Ammy ta kirashi sai ya juyo ya kalli saitin inda take zaune. “Ina ka je? Na ga fitarka a firgice kuma na kira wayarka baka daga ba” Sai a lokacin yana tuna da ya saki wayarshi a Garden. “Na barta a Garden” “Ina ka je?” “Asibiti na duba Zahra bata da lafiya” Ya fada cikin yanayi na damuwa, Ammy ba yarda ta sake yi mashi maganar abun da ya shafi fitarshi ba balle har tace mashi ya jikin Zahra. “Ba ku gaisa da Hajiya Asma'u ba” Ya Abiey ya cira kafa ya karasa kusa da su ya gaishe da Hajiya Asma'u ta amsa mashi cikin far'a tana mashi ya aiki. “Alhamdulillah” Ya fada sannan ya juya ya fara takawa. Ammy ta ce “Yasmin tana ďakina tana jiranka zaka kai ta gida” “Okay let me get my keys” Ba tare da ya juyo ba ya fadi haka ya cigaba da taciyarshi har ya haye sama ta tura kofar ďakinshi ya shiga, kamar yadda ya fada gurin da yake ajiyar keys din ya nufa ya dauki na motar da yafi yawan hawa ya fito ya nufi ďakin Ammy. Yasmin na ganinshi ta yi saurin gyara zamanta ta sauke kai kasa. “Mu je na sauke ki gida” Ba musu ta mike tsaye shi kuma ya juyo sai ta biyo bayanshi, yana gaba tana kallon yadda yake sauka stairs din kamar mai kirga step dinshi, yana sauka ya nufi kofar fita ita kuma ta nufi gurin su Ammy ta yi musu sallama sannan ta fice daga falon, ko da ta fito Abiey na tsaye bakin kofar Garden rike da wayarshi yana jiranta, tun da ta fito yake kallon lafiyarta har ta iso. “Ki yi hakuri da abun da na yi miki a dazun” “No ba sai ka ba ni hakuri ba, ba ka yi laifi a abin da ka aikata ba, kuma kana bukatar ayi maka uzuri idan ma ka yi laifin” He smile in pain. “Har zuwa yaushe zaki yi ta min uzuri?” “Har zuwa lokacin da Allah zai cire min son ka” He smile again. “Idan kuma be cire ba fa?” Ta kalleshi. “Ban roka ba ma ya ba ni ya kake gani idan na roka?” “Ashe son da kike min ba mai karfi ba ne tun da har zaki iya rokon Allah ya cire miki so na a zuciyarki” “Mu musulmai be Abiey mun yarda da kaddara mai kyau da marar kyau, kuma ko da yaushe muna neman zabin Allah a cikin lamurranmu ne, ina addu'ar ne da neman zabin Allah idan alheri ne ko akasin haka” Da hannu yayi mata alama da ta wuce gaba sai ta jera da shi suka nufi motar a tare, shi ya fara shiga sannan ta bude ta shiga tun da yayi ma motar key be sake kallon gefen Yasmin ba kuma be sake ce mata komai ba, ita ma bata ce mashi ba sai dai tana satar kallonshi jefi jafi har suka isa gidan. “Na gode” Ta fada tana kokarin bude motar ta fita. “Mai Martaba yace zai saka lokacin aurenmu nan da wata uku” Juyowa ta yi ta kalleshi. “Wata uku kuma?” Ya daga mata kai har lokacin be kalleta ba. “Wata uku ai yayi kusa, yaushe muka fahimci junanmu ma? Ya kamata ace musan wane irin zama zamu yi idan muka yi aure” “Karki damu zan iya iya kokari na ga ban cutar da ke ba, zamu aure saboda cika umarnin Mai Martaba, kuma saboda Zahra ta bukaci haka?” “Me kake nufi? Ita kuma ta yi Yaya?” “Ammy ta ce ba zan aureta ba, Mai Martaba ma be goya min baya ba saboda abubuwan da suka faru, and na samu matsala da iyayenta dalilin wannan an kulle mana kofar da muke ganin kamar idan mun bita zamu mu bulle” “Ina Zahra take a yanzu?” “Asibiti an kwantar da ita” “Saboda kai?” Ya kalleta ya daga mata kai. “Kai da Zahra kun cancanci juna Abiey, ba zan iya shiga tsakanin wannan soyayyar ba, saboda ni ba zaka rasa wanda ka mutu kana so ba, a dalilina Zahra ba zata rasa ka ba” “Babu yadda zamu yi, mun saka kanmu a sarka ne domin Mai Martaba ba zai yarda a fasa auren nan ba, kamar yadda iyayenki ma ba za su tunkari Mai Martaba da zancen ba ki nuna so na ba, domin sun fada tun farko ba za su zubar da kimarsu ba” Bata sake ce mashi komai ba ta fice daga motar, binta yayi da kallo har ta shige cikin falon Momy sannan ya jinginar da kanshi jikin kujerar motar ya sauke ajiyar zuciya ya runtse ido yana jin yadda zuciyarshi ke mashi mugun zafi da radadi kamar an saka wuka an yanka ta an saka mata barkono a ciki tsabar ciwon da take mashi. [11/10, 4:58 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣3️⃣ “Sannu...” Na ji wata muryar da ban gama tantancewa ba, a hankali na bude idon sai na yi arba sa kyakkyawan murmushin dake shimfide a fuskar Dr Hamid. “Sannu Zahra” Na dauke kai daga barin kallonshi na kalli Mama da fuskarta ta fada saboda tashin hankali, sannan na kalli Yaya Maryam ita ma sannu take min. “Mi ya faru?” Na tambaya gaba daya jin nake kamar babu kwakwala a cikin kaina na kasa tuna komai right now miyasa aka kawo ni a nan miya faru kamin a kawo ni daga ina aka kawo ni nan duk ban tuna ko daya ba. “Ya jikin na ki?” Dr Hamid ya tambaya sai na unkura na tashi zaune cikin rashin kuzari. “Alhamdulillah” Na amsa ina hade yawu, sau Dr Hamid ya matso ya rika fuskata ya bude idona yana kallo. “Kina jin wani abu yanzu?” “Aa bakina da ba dadi” “Zai daina” Na daga mashi kai. “A bata abinci ta ci babu matsalar komai yanzu da yardar Allah idan ta gama sha zan shigo na bata magani” “Toh an gode” Mama ta fada sannan ta bude manyan kulolin da na san gidan Dr Bashir suka fito ko Dr Hamid domin kulolina da ni na san ba za mu iya siyensu ba. Lafiyayen abinci ne har kala biyu dafadukar shinkafa da kayan ciki sai kuma tuwon semo miyar agushi da ta ji kifi da nama sai kamshi mashanu take. Tuwon Mama ta zuba min domin ta san na fi son shi ta dora min plate din akan gado sai na sauko da kafafuwana cikin rashin kuzari. “Ina zaki?” Dr Hamid ya tambaya. “Bandaki” “Zaki iya zuwa ko a rika ki?” Ya amsa min da kai sannan ya juya ya fice ni ma na taka na shiga bandakin, ina kunna tap sai abubuwan da suka faru suka dawo min a kai. Bakina na wanke na wanke fuskata sannan na yi fitsari na fito na dawo saman gadon na zauna. Kasa cin tuwon na yi sai ruwan tea Mama ta hada min na sha. Bayan kamar mintuna asirin Dr Hamid ya dawo dakin sanye da safar hannu fuskarshi sanye da farin gilashi. “Madam ya jikin?” Ya tambaya da murmushi, sai Mama ta amsa mishi. “Da sauki dai a yadda muka gani yanzu” “Allah kara sauki ta ci abinci?” “Aa gashi nan na rufe bata ci ba, tea kawai ta sha” “Okay” Ya nufi akwai da aka jera magani yana fadin. “Mama ko zaku dan ba mu guri” “Toh” Mama ta amsa sannan suka tashi tare sa Yaya Maryam suka fice, sai da suka rufe kofar sannan ya turo akwatin maganin ya karaso inda nake zaune ya cire safar hannunshi ya mika hannu ya bude plate din tuwon da Mama ta rufe ya zauna saman gadon ya aje tuwon tsakiyarmu. “Ko wani abun kike so a siyo miki?” “Aa bana jin cin abincin ne” “Idan ba ki ci abinci karin damuwa ne, ba ki son ki warke da wuri ne?” Na yi shiru ina sauke kai kasa. “Zahra” Ya kira sunana sai na dago na kalleshi kadan shi ma kallona yake. “Mama ta fada miki abun da yake damunki?” Na girgiza kai. “Zuciyarki ce ta buga, irin wannan yana faruwa idan wani abu ya faru kamar mutuwar wanda baka zata ba, ko rabuwa da wanda kake tsananin kauna sai kuma zuciya ta kasa jurewa, ba ko wace zuciyata take jure daukar wahala ba, wanu lokacin kuma kamar idan mutum yana da hawan jini ko damuwa irin wannan yana faruwa” Ta saka hannunshi ya dauki spoon din dake cikin tuwon ya gutsara ya kai min saitin bakina. Kasa ce mashi aa na yi kuma na kasa bude bakin na karba har sai da ba bani umarni. “Bude bakinki” Na bude bakin kadan sai ya saka min karamar lomar mai kamar ta jarirai. “Ban san wacece ke ba kamin yanzu, saboda haka ba zan yanke hukunci akan rayuwarki, wane irin kalubale kika fuskanta kamin ki kawo yanzu, a yanzu din ma wane kalubale kika fuskanta” Ya sake dibar tuwon ya kai min a bakina na karba na fara taunawa, sannan na debi kifi ya kai a baki. “Idan wani ya tambaye ni wacece Zahra? Amsar da zan bashi ita ce Zahra wata yarinyar ce mai karancin shekaru kyakkyawa mai saukin kai mai hankali mai tarbiya wance take rayuwa tare da mahaifiyarta da yayarta” Wannan karon ma be cigaba ba sai da ya sake kamin lomar tuwo a bakina, sannan ya dauki kofi ya bude ruwan roba ya zuba ya dauka da hannunshi ya kai min a baki na sha kadan ya aje ya sake daukar spoons din ya cigaba da ba ni abincin da na tabbatar da be yi feeding dina ba ba zan iya ci ba. “Ban san wani abu na rayuwarki ba bayan wannan, wace rayuwa kika yi kamin yanzu asalinki wacece ke ban sani ba, kuma ina bukatar sani amman kamin nan na san ina daya daga cikin mutunanen da suka saka zuciyarki ta buga ko kuma suka hanaki farinciki a baya bayan nan wanda hakan ya haifar miki da damuwa” Na kalleshi cikin yanayin damuwa yake min maganar yana cigaba da ba ni abinci. “A lokacin da Jamila ta kira ji cikin tashin hankali tana fada min cewar gani nan kin fadi a kasa kin suma, hankalina ya tashi sosai na fada mata ta saka ki a mota ta turo ki asibiti a motar mijinta aka kawo ki asibitin kamin a iso da ke na shirya komai, sai dai na tsorata sosai a lokacin na fahimci cewar zuciyarki ce ta buga” Na kawar da kai daga spoon din da yake kokarin saka min a baki. “Na koshi” Sai ya dauki ruwa ya mika min na saka hannu na karba, yana kallon gefen fuskata ya ce. “Zahra da ace faduwar nan da kika yi baki farkawa ba, wata kila da hakkinki be bar mu ba, musamman ma ni, i know da amincewar ki na aikata but still zalinci ne saboda ke kina neman mafita ne da ace wani nace ki kashe zaki iya kasheshi saboda ki taimaki rayuwar mijinki, if i could turn back the clock zan dauki kudin nan ne na biyawa mijinki a kyauta, ko da zai rayu ko ya mutu” Ya mike tsaye ya fara kankara maganin yana miko min. “Zahra zan fada miki wani da na boye miki, ni da Jamila uwa daya uba daya muke kanwata ce, shekararta tara da aure wannan ce ta goma, ta shiga damuwa sosai domin mijinta yana son haihuwa gashi ya tara dukiya amman Allah be ba shi haihuwa ba, ita da shi duk suna son junansu ya kara aure ba sau daya ba sau biyu matan suna fita, sun yi ta neman magani na asibiti da na hausa amman shiru, daga baya sai ta fahimci hankalin mijinta ya tashi sosai saboda rashin haihuwar da kuma tsana ta yan'uwan miji da suke nuna mata ita kanta tana son ganin jininta, a shawarce ta shawarce shi akan a ciri kwanshi a ciri nata a dasa a cikin wata amman be yarda, sannan ta yi mashi magana akan ya bada kwanshi a hada da bata a raini ďan ko yar a cikin machine irin yadda wasu turawan suke a waje shi ma be yarda ba, duk wata shawara da zata kawo zai ce aa” Na karbi maganin na sha sai ya karbi kofin ya aje. “Tausayin halin da take ciki yasa na kawo mata shawarar mu busa cikinta idan zata haihu sai mu samu cikin wata mu siya, sai kuma muka yi sa'a da ke a lokacin daman can mun fi a samu irin wannan ďan naki saboda ya zamana na sunna ne ba na banza ba, Zahra karki so ganin farinciki a gurin mijinta da yan'uwanta da kuma yan'uwan mijin a lokacin da aka bada sanarwar tana da ciki, wannan abun ya kara min kwarin guiwar cigaba da abun da muke har muka samu wannan nasarar” Ya tura akwatin maganin zuwa inda ya dauko shi dazun. “But then i realized mun cutar da ke, haihuwar fari muka karba kuma ta mutumen da kike tsananin kauna wanda ya mutu ya barki kina bukatar ďanshi iyayenshi ma suna son ganin jinin jikansu ke ma na ki iyayen suna son ganin ďanki, yanzu kuma mun saka ki gaba akan muna son ki shayar da shi, na san ďanki amman ba hakkinki ba ne, ban san Jamila taje ta same ki tana ta magiya ba, sai a jiya da ta fada min dazun ma kamin ki farka ta kira ni tana cewa idan kin farka tana son an sallamo ki ki dawo cigaba da zama gidan saboda ki shayar da yaron, mijinta da tun a jiya wata tafiyar ta kama shi ya kira ni ya ce duk abun da ya kamata na yi miki shi zai biya na san yayi hakan ne saboda kin taimaki rayuwarshi a lokacin da hatsarin jirgin nan ya faru kamar yadda Jamila ta fada min, you saved him and now you saved his wife you're such a wonderful soul Zahra, precious, humble and beautiful” Ya tako ya karaso kusa da ni yana kallon fuskata ni kuma na sauke nawa idon kasa. “You deserve happiness Zahra, na miki alkawari zai na cire duk wani ciwo da yake damunki sai na kuranye miki duk wata damuwa i promise you this i will fix what is broken zan cire abun da yake ciwo ne a rayuwarki” Ya durkusa a gabana yana kallon hawayen dake zuba a idona. “That's why nake son sanin wacece ke, wace kalar rayuwa kika yi kamin yau akwai labari mai yawa a cikin sumanki da kuma hawayen da kiks zubar ba a yanzu Zahra, N miki alkawari ba zan sake bari abu ya takura miki ba, ba zaki sake tsintar kanki cikin damuwa ba...” Turo kofar ďakin aka yi daga ni har shi muka juya muka kalli kofar Sauban ne tsaye bakin kofar ďakin yana kallonmu hannunshi rike da manyan ledodi yana sanye da kananan kaya kamar abokinshi. Dr Hamid ya mike tsaye ni kuma na saka hannuna na share hawayena. “Ya kamata ka kwankwasa kamin ka shigo Malam” “Nan asibiti ba gida ba Dr ina fatar ka san haka” Dr Hamid ya nuna mashi kofa duk kuwa da kokarin da yake na kunno kai cikin dakin. “Tana bukatar hutu you can leave” “Only if she says so...” Sauban ya fada a yayinda ya karaso kusa da ni ya aje manyan ledodin a gurin da aka tana da domin dora kaya. Dr Hamid kamar zai sake mashi magana sai kuma ya kalle ni na girgiza mashi alamar aa hakan ya saka shi juyawa ya fice ba tare da ya sake cewa komai ba. “How are you Dear” Na kalli Sauban da sauri ‘Dear’ Kalmar da be taba fada min ba ko a wacan lokacin da nake wasa da shi balle kuma yanzu, ban amsa ba na kalli kofa. “Ba mu zo tare da Abiey ba” Ya fada da murmushi a fuskarshi kamar ya san tunanin da nake kenan. “Da zo jiya kina bachi, dazun ma na zi kina bachi ya jikinki?” “Na ji sauki” Ya dauko ledar ďaya ya bude babu komai a ciki sai tarin chocolate wani ma har na manta rabon da na ci irinshi domin a wacan lokacin da muke tare da Abiey yana siya min chocolate masu tsada sosai bayan rabuwarmu kuma Deen ba shi da karfin siya min. “Na san za a kawo miki abinci so i brought some chocolate for you hope you like it” Na kalleshi na kalli chocolate's din. “Ya aka yi ka san ina asibiti” “Ina tare da Abiey a lokacin da Dr Zainab ta kira shi ta fada mishi cewar an kawo ki asibiti, sai yace Allah ya baki lafiya” “Shi ya ce ka zo ka duba ni?” “No” “Why are you here” “Because i care for you” Na kalleshi magana yake kamar ba shi ba, ban samu saba makamancin wannan da Sauban ba, kuma be tana min irin wannan game din ba kamar yadda ban ga alamar da zolaya yake wannan maganar a fuskarshi ba. “Care for me?” “Yeah” Ya sauke ajiyar zuciya ya busar da iskar bakinshi yana kallona da duba ba na wasa ba. “Zahra you go through enough, kin dade kina ba ni tausayi sosai saboda na san zaki fuskancin irin wannan kalubalen a duk lokacin da kika gane gaskiyar cewar Deen yaudararki yayi, amman ban dauka bayan haka wata matsalar zata iya kunno kai a tsakaninku ba, the way da kuke son junanku na tausaya muku sosai musamman ma ke, kuma Inshallah zan yi iya kokarin na ganin komai ya daidaita a tsakaninku” Na sake kallonshi. “Ni da Abiey mun yanke wannan shawarar ne saboda muna ganin kamar hakan shi ne mafita a tsakaninmun, bana son wani abu da zai shiga tsakanin Abiey da iyayenshi musamman Mai Martaba, kuma ya kamata dukammu mu yardar da kaddara mu ta mu kaddarar kenan” “Duk da haka Zahra kina bukatar kwanciyar hankali, idan Abiey yana da Yasmin da zata kawar mishi da damuwarki ke wa kike da shi? Ina fatar shawarar da kuka yanke ba zata shafi alaka ta da dake ba, even though we're friends amman ina son ki aje kallona a matsayin abokin Abiey, ba ina tausayinki kawai saboda wata manufa ba, no ko da ace ban san ki ba iyakarcin tausayin da zan miki kenan, tun daga lokacin da na samu labarin abun da Abiey yayi na san za a samu matsala amman ina son ki dauki wannan a matsayin kaddararki kamar yadda kika fada ki ma jajirtacciyar mace Zahra” “Deep down i know one day things will change, ba zamu dawwama a haka ba Sauban, wata rana komai zai zama labari idan muna raye wani lokaci kamar haka mun manta da komai, ina son na tafiyarda rayuwata kamar Abiey be taba rayuwa a cikinta ba, not because of bana son but because of kaddararmu, kuma idan har ina son na manta da Abiey dole ne chanja komai na rayuwata mu'amala ta zamantakewa, abokanin mu'amala so that i can move on i have to believe in myself” Na fada hawaye na sauko min. “Hakan yana da kyau” Ta furta a gajarce yayi shiru, jikina ya ba ni cewar kallona yake, a yayinda nake ta aikin sharar kwalla. “Am... Ban san ko akwai abun da kike so na zo miki da shi idan zan dawo” “Ba sai ka dawo ba Sauban na gode da kulawa” Na fada mishi ina kallonshi. “Zan yi ta zuwa Zahra har zuwa lokacin da zuciyata zata samu natsuwa cewar kin samu kwanciyar hankali, ke din abar tausayi ce duk wata kulawa da zan baki ko na nuna akanki zan yi saboda Abiey i know you need him” Ya dauke numfashi na tsawon dakika biyar sannan na numfasa na kwanta saman gadon. “Karka fadawa Abiey ka zo nan” “Kamin na zo nan sai na fada mashi zan zo, ba ce karka je ba kuma be ce ka je ba sai dai na san ya jidadi saboda ba zai iya komai a kai ba, ke kanki kin sani da ace babu wata matsala da ta shiga tsakaninku da yanzu yana nan tare da ke, please let me do his duty ko ba komai hakan zai san yaya mashi” Ban san me zan sake ce mashi ba, a iyakar sanina akwai alaka mai karfi a tsakaninsu wanda ta wuce da aboka sai dai a kirata da yan'uwanta domin tun kamin na san Abiey ko na hadu da shi suke tare da Sauban Abiey ya taba fada min a tare suka ta so, saboda bana tunanin Sauban zai nuna min kulawa da wata manufa sai dan tausayi kamar yadda ya fada da kuma nunawa Abiey ya damu da damuwarshi. “Karki cika kanki da tunani kuma idan kina bukatar wani abun ki fada min” “Na gode” Na fada ba tare sa na sake kallonshi ba har ya bude kofar ya fice. Sai tunanin Abiey ya dawo min sabo na san a duk inda yake a yanzu baya cikin kwanciyar hankali da natsuwa domin ni ma na kasa jurewa balle kuma shi, sai dai ina addu'a da fatan hakan ya zame mana alheri a tsakaninmu. Wata kila a cikin maganin da Dr Hamid ya ba ni akwai na bachi domin fitar Sauban da kamar minti goma bachi yayi gaba da ni ban farka ba sai da aka kira sallah La'asar shi ma kuma hayaniyar hirar da Mama take da Hajiya Jamila ne ya tashe ni, kamar zata hadeye haka ta rika murna da farkawata tana ta min sannu da jiki idan Mama ta dauko abu zata ba ni sai ta karba ta mika min, abinci kadan na ci ina ta kallon Amir dake dunkule a cikin kayan sanyin a hannun Mama, bayan na gama ta karba ta aje ta dauki ruwa ta miko min na karba na sha, sannan ta matso kusa ni tana kallona kamar mai tsoron yi min magana, sai kallon Mama take hakan ya karantar da ni akwai magana a bakinta. “Mama lafiya?” “Wai so take ki bawa yaron Nono” Na kallin yaron. “Muna asibiti fa wani zai iya gani” “Zan tsaya jikin kofar sai ki ba shi idan na ga wani sai na fada miki, wallahi rabon shi da abinci tun jiya madarar nan tsoron ba shi ita nake saboda tana saka shi ciwon ciki kuma Dr yayi magana da likitan da mijina ya kawo tace ta ba shi kwana biyu idan ya samu lafiya shikenan idan kuma be samu ba zata fara nata bincike, Dr Hamid na fada mata cewar yana kan wani aikin ne na magani kuma ba wani magani da yake kawai dai mun dogara da ke, jiya ma na yi magana da Dr Hamid yace min za a iya sallamarki a yau saboda jikin na ki da sauki albashi sai a cigaba da kula da ke a gida” Hausawa suka ce ďan halak kaki ambato tana rufe baki Dr Hamid ya shigo dakin rike da wasu files. “Yauwa gashi nan ma ya zo” Ya kalleta sannan ya kalleni. “Minene?” Ta kora mishi bayani da kamar magiya. “Na ce za a iya sallamarta amman ban ce ki yi magana da ita ba” Ya fada yana kallona. “Na ji ka ce ta ji sauki, zuwan nan ma saboda ta bashi nono ne idan Hubby ya san na fita zai yi fada saboda baya son ana fita da yaron nan” “Eh ta ji sauki hakan ba yana nufin ta cigaba da abun da kike so ba, ki tafi gida zan yi magana da ita” Ya fada a tsawace ba ita ba ko na na yi mamakin yadda ya yi fusata har yake daga murya ranshi a bace. Bata sake cewa komai ba ta mika hannu ta karbi Amir ta fice. [11/10, 9:30 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣4️⃣ Bayan ta fice daga ďakin ya juya shi ma ya fita be dade ba ya dawo ya kama hannuna ya saka min abun auna jini sai Mama ta ce. “Doctor idan Zahra ta samu lafiya zamu iya komawa gida ta cigaba da bashi nonon saboda ita ma ta cigaba da wankan ruwan zafinta kar jikinta ya danyence” Cikin mutuntawa Dr Hamid ya ce. “Amman Zahra ta samu lafiya, amman ba za a cigaba da yi mata suraci ba, wankan ruwan zafi ne dai ba zan hana ba, kuma zancen ta koma a gidan nan wannan ra'ayin Zahra mu bar ta har sai ta zaba” “Ba ni da matsala Dr indai zan iya komawa ni a shirye nake” “Karki yi wani abu saboda ni ko saboda Jamila ko saboda wani dabam, always listen to your heart, baki san kina da hakkin ki ba? Karki gina kanki da rayuwarki akan ra'ayin wasu” Ya fada bayan ya duba jinin nawa ya cire min abun a hannu. “Ba ni da matsala ni akwai wanda bana son ya sake zuwa ya same ni a nan indai zan iya cigaba da shan maganina ina son a sallame ni” Murmushi yayi. “Mutumen dazun ko? Any way daman idan abun ya zo da sauki ba ma rike mutum a asibiti mu kan sallame mutum mu dora shi akan magani da kuma dokoki idan zaki iya kiyaye zamu iya sallamarki, kuma abun ya zama na gida zan cigaba da dubaki” “Inshallah zan kiyaye” “Good, idan zan wuce gida zan tafi da ku” He said with light smile on his face. Na amsa mishi da kai sai da yayi wasu rubuce rubuce sannan ya dauki kayanshi ya fice. Yaya Maryam duk abun da ake bata ce komai kamar bata cikin dakin, ta taso ta dawo kusa da ni ta zauna. “Wai Zahra anya Likitan ba ďan'uwan matar nan ba ne, suna yanayi sosai kuma yanayin yadda ya daka mata tsawa idan be isa da ita ba ba zai mata haka ba, saboda kawai yana likitanta ba zata dauki wannan daga gareshi ba” “Yace min kanwarshi ce uwa daya uba daya” “Ah no wonder ni kam abun ya ba ni mamaki sosai na ga kama a fuskarsu yau” Mama ma ta cika da Mamaki ita da Yaya Maryam, kamin daga bisani Yaya Maryam ta dauko zancen abun da ya faru ciki har da rabuwar mu da Abiey da kuma zancen komawarmu gidan Hajiya Jamila. Har suka ci suka sude ban ce komai ba domin hankalina da tunanina ya tafi wata duniyar, muna haka yan'uwan Mama suka yi ta shigowa duba ji suna min ya jiki na bangare Baba na na sun shigo sai dai ba su kai na Mama ba, Dr Zainab ma ta shigo sai dai bata dade ba ta fita. Misalin 6 na yamma Dr Hamid ya dawo ďakin bayan ya kammala aikinshi, sai da ya kara auna ni sannan ya saka ma'aikatan asibitin dake share share suka kwashi kayanmi zuwa gurin motarshi. Mama da Yaya Maryam da babban ďanta Abdulkareem suka take musu baya mi kuma na jero tare da shi ina takawa a hankali yana ta yi min hirar asibitin yadda aka tsara gurin da ya fara aiki kamin daga bisani ya dawo nan. Muna isa yayi saurin bude min gaban motar. “Bismillah Zahra” Ban kawo komai a raina ba na shiga na zauna ya rufe, sannan su Mama suka bude baya suka shiga, tun da muka kama hanya ban kalli inda yake ba balle wata kalmar ta fito daga bakina zuwa gurinshi, shi ma kuma be sake ce min komai ba wata kila saboda su Mama suna cikin motar ne. Sai da muka isa bakin gate din gidan sannan ya kira Hajiya Jamila ya sanar da ita cewar mun iso sannan ya danna horn masu gadin suka leko ganinshi ne yasa suka koma suka bude gate din shi kuma yaja motar zuwa cikin gidan, na yi zaton a harabar gidanta zai faka gurin da nake hango manyan motoci na alfarma, sai ya faka a gurin da na ke kyautata zaton BQ ne domin yanayin gurin ya nuna haka, Mama ta fara budewa sannan na bude na fito sai hango Hajiya Jamila muka yi ta nufo inda muke da saurinta. “Maa Shaa Allah kun dawo” “Allah ya nufa” Mama ta amsa mata, sai ta wuce gaba muka bi bayanta zuwa cikin bq din mai kama da wani karamin gidan Mai kudi domin har da ac aka saka a dakunan gudan biyar bayan an kawata ko wace kofar ďaki da fulawoyi, yadda gurin yake tass sai ka rantse da Allah akwai mutane a gurin domin an share ko'ina an goge ba datti ko kadan. “Wane ďakin kuke so?” Dr Hamid ya tambaya yana kallona da murmushi a fuskarsa. “Ba mu da zabi” Na amsa mishi ina dauke kaina daga barin kallonshi. “Duka ďakunan iri daya ne babu banbanci, sai dai na ga kamar kuma da kaya da yawa zaku iya rabawa ku saka wasu kayana a dayan dakin dayan kuma sai ya zama na kwanaku” Cewar Hajiya Jamila, Mama kam tuni ta fara duba ďakunan har zuwa kitchen din dake can gefe, bandakin kuma yana cikin ďakunan tare da su, dakin farko muka zaba mai binsa kuma Mama tace zai zama na saka sauran kayanta. “Amman dai ba dake za ayi aikin nan ba Zahra ki shiga ciki ki zauna idan gama gyara sai ki dawo” Dr Hamid ya fada ganin Mama da Yaya Maryam sun fara daukar wasu kayan suna sakawa ciki. “Ba wani gyara zamu yi sosai ba saboda dare ya fara, sai dai mu saka wasu mu bar wasu” “Kamar gado da katifa da wardrobe ku bar masu aikin gidan nan su saka muku sai ku nuna musu gurin da za su aje bari na musu magana” Kamin mu ce komai Hajiya Jamila ta fita daga gurin, jiki na rawa suka iso suka fara kama kayan suna sakawa ciki ni kuma Dr ya cilasta min shiga cikin gidan wai har sai sun gama, a tare muka jera da shi muna takawa har muka isa gurin na mika hannu na taba kofar shiga falon sai ya riga ni ya rike hannun kofar. “Kamin ki shiga Zahra ina son ki yi hakuri da duk yadda zaki samu rayuwa a nan gaba ko kuma a yadda kika same ta a yanzu, lokuta da dama abun da muke so ba sai da mike samu ba, kuma kin ga yanayin jikinki dole be ki kawar da damuwa a ranki da duk wani abu da zai kawo miki bacin rai, karki yarda ki rika zama ke kadai ki rika samun wani abu da zai dauki miki hankali kuma ki daina bari idonki na ganin abin da zuciyarki bata so, hakan zai taimaki lafiyarki kuma zai taimaka miki sosai ta bangaren rayuwa da kuma mu'amala da mutane, and you have to be very careful da duk wani abu da zaki yi ba sai abun da ya shafi tsakaninki da Jamila ba, ko da tsakaninki da yan'uwanki ne saboda akwai security camera ko'ina a gidan nan, ki kula da shan maganinki akai akai” “Inshallah na gode sosai Allah ya saka da alheri dawainiyar da kai da ni Allah ya biyaka” “Wannan kuma Mijin Jamila zaki yi ma godiya shi ya dauki nauyin komai” Na daga mishi kai sai ya bude min kofar. “Ki fada mata na wuce” “Ba zaka shiga ciki ba?” “Mijinta yana ciki” Kamar ya san zan tambaye shi ba ka ce yayi tafiya sai yace min “Yayi tafiya amman ya dawo dazun da zamu shigo na kirata take sanar da ni” Na daga mishi kai sannan na shiga cikin falon na alfarma yaja kofar ya rufe daga can waje, a karo na biyu bayan shigowar da na taba yi a gidan yau na sake daga kai ina kallon kyakkyawa falon da masu shi ba su san darajar naira ba. “Sannu da jiki Zahra” Kamar daga sama na ji muryar Mr Bashir da sauri na dawo da dubana gurin kujerun dake dama da ni sai ganinshi na yi zaune sanye da Jallabiya Ash color wani dan karamin teburi a gabanshi ya dora system dinshi a gaba. Da sauri na durkusa ina gaisheshi daga inda nake tsaye be amsa min ba sai yayi min alama da na zo da hannu, abun ka da talaka sai na tashi jiki na rawa na karasa inda yake zauna na duka kasa. “Barka da yamma yallabai” Ya dade yana kallona kamin ya amsa min da wata siga ba zan iya karantar halin da yake ciki ba, damuwa ko. akasin haka? Ba zan ce farinciki ba dai domin ban ga annashuwa ko nishadi a tare da shi ba. “Yauwa ya jikinki?” “Alhamdulillah, na gode sosai da dawainiyar da kai da ni Allah ya saka da alheri” “Ameen, Dr yace zuciyarki ce ta buga haka ne?” “Eh haka ne” “Kina da wata damuwa ne?” “A yanzu dai babu” “Kamim yanzu fa?” Na yi shiru kaina a kasa. “I know be kamata na shiga cikin rayuwarki ba, but ya zama dole ko dan na san wacece uwar ďana....” A firgice na dago na kalleshi gaba na mugun faduwa irin faduwar da na tabbatar idan aka auna jinina a lokacin za a ce ya kai 1000 dubu ba ma dari wani abu ba, yawun bakina suka tsarke ni a take na fara tari, wani kallo yake min kamar mai karantar abu a fuskata. “Uwar ďan...ďan...ďan... ka kuma?” Yayi murmushi ya dauki kofin dake kusa da shi ya kai bakinshi. “Mai kula mai ďanka ai kamar mahaifiyarshi ce, be kamata ace na yanke miki hukunci kai tsaya ba ba tare da sanin wacece ke ba, gudun kar wani abu ya faru nan gaba mu koma da na sani, ya kamata mu san da wa muke zaune” Ya karasa yana daga kai ya kalli Hajiya Jamila dake saukowa downstairs din da mamakinta. “Hubby yaushe ka shigo falon?” “Yanzu nan, ina yi ma Nanny ya jiki ne” Na kalli Hajiya Jamila idona kamar za su yi magana ita ma kallona take cike da fargaba. “Zahra yanzu kika shigo?” Kai kawai na iya daga mata na mike tsaye sai na ji kafafuwa kamar ba za su dauke ni ba. “Bari na je na duba su Mama ko sun gama” “Ai da kin ce kin duba Amir yana ďakina” Ko bata fada min ba na san ba zai wuce idan na shiga dakin tace min na bashi nono ba, fasa fitar na yi sai na nufi inda ta sauko zuciyata na raya min abubuwa da dama jikina na rawa kamar mai jin sanyi, any Mijin Jamila be gane gaskiya ba kuwa? Amman kuma idan ya gane ba zai saka mana ido mu yi ta wasa da hankalinshi ba. Daf da zan shige na juyo sai muka hada ido domin ni yake kallon irin duban da ba zan iya fassarawa ba, ita ma Hajiya Jamila kallona take tana rike da hannun mijinta. ABIEY POV. Ya aje spoon din hannunshi ya dauki ruwa ya sha sannan yaja kujerar baya ya mike tsaye. “Aliyu” Ya kalli Ammy “Zauna” Ya koma ya zauna, Dr kalli Ammy ta kalli kanenta. “Dazun na duba jikin Zahra ta ji sauki sosai” Ya daga mata hannu. “Yasmin kuke son na aura kuma zan aureta, dan Allah ku daina min zancen Zahra ko wani abun da ya shafe ta” Dr Zainab da Ammy suka hada. “Aliyu ba mun hana ka auren Zahra ba ne saboda wani ra'ayi na karan kaina, sai dai tunanin haka shi ne mafita a gareku, bana son abun da zai bata tsakani ka da Mai Martaba, kai ka sani na fi kowa son farincikika kuma ina son abun da kake so wannan ya saka tun kamin ya furta cewar kana son Zahra na ke girmama ta ina kaunarta, ko a yanzu idan Mai Martaba ya yarda ka aureta ni ba ni da matsala” “Mai Martaba ba zai yarda na aureta ba, saboda ina son ta kuma na san matanshi za su iya zuga shi su nuna mashi illarta, saboda haka ba ni da wani zabi da ya wuce auren wanda kuke so, da farko ni na cutu, yanzu kuma yar mutane za a cutar” Ya mike tsaye ya fita daga dinning area din Ammy da Dr suka bishi da kallo. “Ammy ni kan da zaki iya lallaba Mai Martaba da an bar Abiey ya auri Zahra saboda yana sonta sosai kuma ita ma tana sonshi” “Na yi magana da shi amman be saurare ni ba, kuma ya tabbatar min idan har Aliyu zai bi zabin ranshi to shi kuma zai yafe shi, na san ďana mai biyayya ne ba zai iya musu mana ba shiyasa ya amince amman ni ma bana son aurenshi da Zahra yanzu” “Saboda me?” “Zai zama abun magana a cikin dangi kuma a duniya kasancewarshi sanannen mutum za ace ya auri bazawara a cikin dangin ubanshi ma zai zama abun magana shi kanshi Mai Martaba bana jin zai yarda ya barshi ya aureta” “Da wannan dan wannan amman da zai yarda sai yayi ta biyu da ita” Ammy ta yi shiru bata sake cewa komai ba, ta san ďanta yana son Zahra sai dai ita kuma a yanzu bata son aurenshi da ita ko dan sirrin da take kallon Zahra ta fallasa a gurin Abiey wanda tana da tabbacin da shi Abiey yake kallonta, kuma ba zai daina kallonta abun da ko da ta mutu, kawai dai ya kasa nuna mata komai ne saboda kunyarta da kuma irin tarbiyar da ta yi mashi ba zai iya nuna mata komai ba. Harabar gidan ya fito ya saka hannayenshi aljihu yana kallon ma'aikatan gidan dake aikin yanke gyara fulawa zuciyarshi na raya mishi wani abu da yake fatan ba gaskiya ba ne, ringing din wayarshi ya katse mashi tunanin da yake sai ya ciro wayar ya kalli screen din. “Sauban” Ya furta sannan ya amsa kiran. “Ina jinka” “Na je na duba Zahra dazun” Abiey yayi murmushi. “Ka yardar kenan?” “I can't say no to you as long as haka kake so zan yi” “How is she?” “Jikinta da sauki sosai amman dai tana cikin damuwa Abiey kuma yarinyar nan tana kaunarki you make the right decision, na same ta tare da likitan nan da ya hana ka shiga ranar yana gabanta a kasa ita kuma tana zaune saman gado tana kuka ban san abun da suke tattaunawa ba amman dai kuka take” “Next time idan zaka je ka yi min recording so that i can trust you more, and ka bincika gida mai kyau ka siya mata idan kuma wannan take so sai a gyara mata, if kuma tana son wannan gidan da aka gina sai a bar mata shi” “I will ask her” “Thank You” Ya mashi godiya sannan ya juyo ya maida wayar aljihunshi ya juyo gurin kofar falon ya murda ya bude ya shiga cikin falon, Dr Zainab na rike da jakarta tsaye tare da Ammy tsakar falon suna magana sai dai ganshi ya saka sun katse maganar suka juyo suna kallonshi, be ce musu komai ba y nufi wata doguwar cushion ya zauna ya maida hankalinshi gurin tv ke aiki, Dr Zainab ta nufi kofar fita falon Ammy ta yi mata rakiya. Ammy ta rufe kofar falon ta dawo cikin falon ta zauna kusa da Abiey tana kallonshi “Aliyu” Be amsa mata ba kuma be bari ta fada mishi abun da ke bakinta ba ya ce. “Ammy zan tambaye ki tsakani da Allah this time daga bakinki nake son jin amsar nan” Runtse ido ta yi ta bude ta sadda kanta kasa kamar mai kunyar hada ido da shi. “Aliyu karka tambaye ni abun da ba zan iya amsa maka baki da baki ba, karka kalleni da abun da Zahra ta fada maka, na aikata abun da na aikata ne saboda juya min baya da Mai Martaba yayi a wacan lokacin saboda shiga tsakanina da shi da kai, miyasa ka dame kanka har ka san abun da ba zai amfana maka komai ba sai dai ya haifar maka da damuwa da bakinciki, ni ma kuma ya haifar min ka san irin zafin da nake ji idan na tuna abun da ya faru tun kana karami balle kuma a yanzu da ka girma? Mai Martaba ya barranta kanshi da ni irin barrantawar da har abada ba zamu sake kasancewa tare ba, ba dan babu aure a tsakaninmu ba sai dan abubuwa da suka faru, na rai ne ka tun daga haihuwarka har zuwa girmanka ni kadai Aliyu, hakan ya haifar da zargi da yawa a zuciyar mutane amman na gode da Allah a yanzu hankalin Mai Martaba ya karkato gareka ya fara nuna maka kauna kamar sauran yayan da ya haifa, shiyasa ba na son wani abu ya shiga tsakaninka da shi da zai lalata mu'amalarku, domin abun zai fi yi maka zafi a yanzu fiye da rasa Zahra” Kamin Ammy ta gama fadar kalaman da ta kumsa a bakinta hawaye da ya zuba a fuskarta ya fi a kirga kana kallonta ka san tana cikin wani irin magagi na bakinciki marar misaltuwa.. “Ashe da gaske tsanar da Mai Martaba yayi min ba ta asiri ba ce kawai tana da dalili” Ya lumshe idonshi da suka cika da hawaye ya bude. “Na bude ido ina kallon Mai Martaba a matsayin mahaifina sai dai tsanar da yake nuna min wani abun tambaya ne da na dade ina yi ma kaina, kuma. Zuciyata ta kasa natsuwa da shi Ammy miyasa kika boye min wannan?” “Saboda alkawari ne da muka yi tsakanin ni da shi cewar babu wanda zai taba sani komai har kasa ta rufe Idon mu, hakan kuma be canja komai daga kasancewarka ďanshi ba domin har gobe kai jininshi ne...” Abiey ya mike tsaye cikin wani irin yanayi na mamaki da bugawar zuciya yana kallon Ammy duk wata maganar da ya furta a yanzu ya furta ne kawai saboda ya samu amsar tambayar dake mashi yawo a zuciya a yanzu kuma ya samu ta inda be yi zato ba a take hawaye na wanke mashi fuska. #Team Abiey #Team Hamid #Team Deen #Team Bashir #Team Yasmin #Team Zahra [11/12, 3:11 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣5️⃣ “Na rayu a gidan Mahaifinka irin rayuwar da babu wata mace a duniyar nan da zata gwada min gata a gurin miji, ni ce mace mafi soyuwa a gurin Mai Martaba irin soyayyar da baya iya yin adalci a tsakanina da abokan zamana, wannan abun ya tsokane musu ido ciki har da yan'uwan mahaifinka da iyayenshi, akan ce na yi magani na mallake shi alhalin ban taba kai nera biyar gurin wani na ce yayi min magani na mallake Mai Martaba ba, ni na san babu wata mace da zata rayu a zuciyar Mai Martaba ya nuna mata kauna kamar yadda ya nuna min, wannan soyayyar da ya nuna min ita ta cutar da ni ita ta haifar da duk abun da ya faru a yanzu, duk wata hanya da za a bi a raba ji da mijina sai da aka bi kuma aka yi nasara, sherin kishiyoyi be bar ni na zauna lafiya ba, zaman da na yi a gidan na shekara daya ne kawai saki daya ya gagara gyaruwa a tsakanina da shi, na dawo na zauna a gidan nan na rayu da kai da sauran yarana har zuwa yanzu ban sake sha'awar sake yin aure ba, saboda mahaifinka ya maye gurbina ya auri Zuwaira (Anty Amarya) kuma na san har yanzu bata iya maye gurbin nawa ba, mahaifinka ya nunawa Zainab kauna irim wanda be taba nunawa yayan shi ba duk da kasancewarta agola amman yana sonta saboda kasancewar yata...” Abiey ya koma ya zauna yana kallon Ammy dake kuka kamar ranta zai fita, be ce mata komai ba ita ma kuma bata sake furta wata kalmar ba sai sharar hawaye take kamin ta mike tsaye ta nufi upstairs da kallo ya bita har ta haye sannan ya saka hannu ya share na shi hawayen ya mike tsaye ya fita falon, bakin kofar ya tsaya yana kallon harabar gidan. “Ba zan yi irin kuskuren da kuka yi ba, ba zan tsufa na kasa samawa zuciyata abun da yake so ba, Zahra is my destiny and she's here in my heart nothing can keep us apart” Magana yake da kanshi yana taba sautin inda zuciyarshi take, ya saka hannunshi aljuhu ya ciro wayarshi ya kira Yasmin buga daya ta daga muryarta a sanyaye. “Hello” “Yasmin kina gida?” “Eh” “Gani nan zuwa” Ta yi shuru tana saurare har ya kashe waya bata sake cewa komai ba, a tunaninta zai zo ne saboda wata maganar ko wani abun kamar yadda ya saba, tana dauke wayar daga kunnenta ta sanar da mahaifiyarta cewar Abiey yace zai zo. “To tashi ki shirya mashi wani abun ke ma kuma ki gyara” Ta kalli Momy da ta yi maganar ta ce. “Ina tunanin akwai abun da zai kawo shi ba zuwa ne gurina kai tsaye ba kawai” “Duk da haka dai ki shirya ya same ki cikin kwaliya shi ya fi” “Toh” Ta amsa sannan ta tashi ta fice daga dakin zuwa dakinta wanka ta fara yi tana fara shafa mai ya sake kiran wayarta jiki na rawa ta yi picking. “Hello” “Hey Beauty ina waje” She take a deep breath kamin ta dauke wayar daga kunnenta ta kalli sunan Abiey dake rubuce a wayarta ta sake maida a kunnenta tana ganin kamar ba shi ya kira ta da suna mai dadi like ‘Beauty’ ba wani ne mai irin muryarshi kuma mai kama da shi. “Ka dan jira ni kadan gani nan zuwa, ko kuma ka zauna a....” Kamin ta gama ya tari numfashinta. “No zan jira ki a mota” “Okay” Ta sauke wayar tana ji sani abu mai kama da faduwar gaba da sanyi jiki saboda kiranta da Beauty da Abiey yayi. Sama sama ta shirya ta dan shafa power kadan ta saka green abaya sai mayafin abayar da turaren da ta bata kamar zata tashi garin kano da kamshi, a dakin ta bar wayar ta fito ta nufi kitchen ta bude fridge ta dauko lemu da ruwa ta dora a tray da cups sannan ta rufe ta fito ta nufi kofar fita falon gabanta sai faduwa yake zuciyarta na raya mata Abiey ya zo mata da wani dadin bakin ne da zai yi amfani da shi ya roke ta ta sake cewa iyayenta ta fasa aurenshi, wata kila kuma Mai Martaba ya amince mashi da fasa auren ne ko kuma wata mafitar ya samu oho, ta tunani kala kala ta doshi inda motarshi take. Abiey da ya kwantar da kujerar motar ya kwanta ya juyo yana kallon Yasmin dake takuwa zuwa gurin motarshi kamin ta iso ya mike hannu ya bude mata front seat sai ta shiga ta zauna ta sauke idonta kasa ta kasa ce mishi komai, murmushi yayi ya tashi zaune da kyau yana kallonta. “Na dade ban ga wata mace da ta yi kwalliya ta yi kyau kamar yadda kika yi ba Yasmin you look beautiful” Ta dago ta kalleshi da tsananin mamaki. “Yau da wacce ka zo?” Yayi murmushin dake kara mashi kyau da kwarjini ya mika hannu ya dauki gorar ruwan dake saman tray dake rike a hannun Yasmin ya bude ya sha. “Wani abun aka min da ya bata min rai, shiyasa na zabi zuwa gurinki na wanke zuciyata ko zan samu sa'ida” “Idan akwai abun da kake so zaka iya fada ba sai ka yi gwaiďanci ba” Wannan karon murmushin da yayi mai sauti ne, ya kara kurba ruwan. “Ba ki yarda da ni ba kenan, Wallahi babu abun da ya kawo ni gurinki kawai rai na ne a bace kuma na ga babu gurin da zan je na wanke zuciyata sai gurinki” “Abiey baka shan wani abu balle....” Bata karasa ba saboda tana ganin kamar kalmar ta yi tsauri, sai ya karasa mata da murmushi a fuskarshi. “Bana shan komai amman na sha giyar kaunarki ita ce ke juyana ni” Ta dauke kai daga barin kallonshi ta sauke kafafuwanta kasa zata fice daga cikin mata domin gaba daya ita bata gane kan Abiey ba yau, sai ya riga bude side dinshi ya fita ya zagaya ya sha gabanta. “Yasmin ba ina miki kalaman nan saboda na yaudare ki ko kuma ina neman wani abu daga gareki ba, no ina tunanin ya kamata mu watsar da komai a yanzu mu fuskanci rayuwa aure fa zamu yi idan ba mu fara fahimci juna a yanzu ba yaushe zamu fahimta? Ya kamata mu bar komai ya wuce ai” “I know you are doing this just to make me happy, ba dan kana so na ba” “Wa ya fada miki? A gurin wa kika ko yi wannan?” “I know” “No ina son ki Yasmin amman ba irin son da na ke yi ma Zahra ba domin ba zan miki karya ba, bana son wata rana ki tuna ni ni ce Abiey be taba so na ba amman ni na so shi sosai, dole ne na koyi kaunarki saboda kar na cutar da ke hakan ya saka ki tsani yayan da zamu haifa da ke nan gaba, kar wata ayi magana ta ko kuma ki tuna da ni ki yi nadama, a lokacin da bana raye” Ta duka ta aje tray hannunta sannan ta dago ta dube shi. “Wani ya fada maka zaka mutu ne?” Sai yayi murmushi ya shafa kanshi. “Yasmin mutane irin mu ba sa rayuwa mai tsawo a duniya, idan har zamu rayuwa mai tsawo to So zai mutu, idan kuma so zai rayu to mu muke saurin mutuwa, ni kuma na tabbatar da so ba zai taba mutuwa a zuciyata ba, ina son na gyara komai before it too late, idan har zan ji kamar na yi hauka akan Ciwon son Zahra to ni na fi kowa cancantar na san yadda wasu suke ji akan So, Yasmin ba zan bari Ciwon so na ya cutar da ke ba, na yafe Zahra ko now amman ke ba zan yafe ki ba” Ta sauke kanta kasa idonta na cika da hawaye, tausayinshi ta ke ji da kuma tausayin kanta a lokaci daya, shi ya rasa wanda yake so ita kuma ta san ba zai so ta kamar Zahra ba, kawai dai zai so ta ke saboda ya rasa Zahra kuma saboda kar ta shiga wani mugun hali a dalilinshi. “Juya gefenki na dama kadan ki wata yarinya kyakkyawa mai kama da ke” Ya fada domin ya lura da hawayen da suke sauko mata, ta dago ta juya a hankali dama da ita inda motarshi take ta kalla. “Yi kasa da idonki kadan” Ta yi masa da ido sai ta yi arba da kyakkyawar fuskarta a jikin bakin gilashin motar bata san lokaci da murmushi ya subuce mata ba. “Kin fi kyau da murmushi ki daina kuka please” Ta kalleshi ta kai hannu ta share hawayenta. “Shiga ciki ki aje tray kuma ki gaishe da Momy sannan ki dauki permission ina son ki raka ni wani guri” “Toh” Ta amsa still tana murmushi, sannan ta duka ta dauki tray ta ya kauce mata ta wuce. Sai da ta shiga cikin falon sannan ya saka hannunshi aljihu ya ciro wayarshi ya kira Sauban. “Ya jikin Zahra” Shi ne abun da ya fara tambaya a lokacin da Sauban ya karba kiran. “Sun ce ta ji sauki an sallame ta amman ban ganta ba” “What do you” “Na shigo asibiti amman ban ganta ba, sun ce likitan ya sallame ta kuma na je can unguwarsu ban same ta ba” “Dole ne ka binciko inda take mana Sauban, ka sama mata muhallin ka rika kula da ita but make sure ka saka recording idan zaka je gurinta so that i can trust you more” “Abiey kana son ka jefa ni a matsala Wallahi, ban san yadda zan yi ma na shiga jikin yarinyar nan har ta saba da ni ba” “Always remember ba saboda kanka kake wannan ba saboda ni, and i know you're willing to do anything for me you can do this Sauban you can help your friend wannan kadai damar da na ke da ta wannan hanyar ne kawai zan iya samun cikar burina” “Shikenan zan bincika inda take kuma zan yi duk abun da kake so” “Thank You” Ya kashe wayar ya dago yana kallon Yasmin da ta fito rike da yar karamar jakarta da wayarta, kara bude mata kofar gaban motar yayi ta shiga ta zauna ya rufe sannan shi kuma ya zagaya ya shiga yayi ma motar key. A gidan Dr Zainab suka fara zuwa sun dade a can ita kanta Dr ta yi mamakin ganinshi da yasmin musamman yadda ya sake kamar daman can yana son ta sosai ta zo ta kebe da shi ta yi magana amman bata samu dama ba domin be yarda ya tashi ya bar Yasmin ba a falon suka tsaya kuma be yarda ya tashi ya barta ba, a gidan suka yi sallah Isha'i sannan ya dauko ta ya dawo da ita gida, a daren ranar Yasmin ji ta yi kamar an biyata hajji domin ta kwana da farincikin da take ganin bata taba yin irin shi ba, ko da a munafunce Abiey ya nuna mata kauna ita dai ya biyata tun da har ya iya danne zuciyarshi ya bata kulawar da ta kamata, kuma tana da tabbacin daga haka zai kamu da tsananin kaunarta ba tare da ta sani ba. Tun daga lokacin sai Abiey ya sabawa kanshi da kirata da safe ya ji ya ta tashi da rana ma su kan dade suna waya ko da bashi da abun fada mata zai ce ta ba shi labari idan kuma ya samu time zai dauke ta su fita ko kuma ya zo gidan su yi hira, duk abun da yake yi yana yi ne saboda ya sabawa zuciyarshi da ita kuma ya kori zama da ita kamin lokacin da zaman zai kama su domin ya san idan har ya ce zai koyi zama da ita bayan ta zama mata a gidanshi zai cutar da ita ne kuma ya cutar da kanshi, amman idan ya fara tun a waje zata san wa ta aura kuma ta koyi hakuri da zama da shi kamar yadda shi ma zai koyawa zuciyarshi hakurin zama da ita ba dan yana kaunarta. A iya tsawon kwanakin da ya kwashe yana bawa Yasmin kulawa be taba jin zai iya mantawa da Zahra ba idan ya kare waya da Yasmin sai ya kira Sauban ya tambaye shi lafiyar Zahra wani lokacin kamin ya kira Yasmin sai ya fara kiran Sauban sai ya hada conference duk wata hira da Sauban zai yi da ita Abiey yana saurare. Ba tare da sanin Sauban ba Abiey ya dauki wayarshi ya saka wani code da zai rika yi ma shi forwarding duk kira shi da Sauban zai yi da Zahra, wani time din kuma shi zai turawa Sauban sakon da zai aikawa Zahra tun abun yana damun Sauban har ya fara sabawa. Tun daga lokacin kuma Abiey be sake tambayar Ammy ko neman sanin komai akan silar lalacewar alakarta da Mai Martaba ba ba dan baya bukatar sanin ba sai dai lura da yayi da halin da ta shiga a wacan lokaci da ta soma ba shi labarin wanda ya kai bata ma iya cin abincin ta koshi kuma tana kunyar hada ido da shi ta kasa sakewa ta koma kamar yadda take da shi a can da. ZAHRA POV. Ina shiga ďakin na samu Amir a kwance saman gadonta hannu na saka na dauke shi na zauna bakin gadon ina kallon fuskarshi sai wani irin kaunarshi ta kamani na ji kamar ace mallakina ne, kyakkyawa ne sosai kasancewar ni da ubanshi duk ba a baya ba gurin kyau da hasken fata. Hannu na kai na shafa fuskarshi a hankali sai ya motsa ya kalleni idonshi fari kal kamar madara, murmushi na yi na kai bakina na sunbanci goshinsa. Har na saka hannu na ciro nono na bashi sai kuma wata zuciya ta raya min idan akwai camera a dakin fa? Ai za a iya gani domin Dr Hamid ya fada min cewar na yi tsaka tsantsan akwai camera ko'ina a gidan, saurin dauke hannuna na yi ina tuna kalamin da mijin Jamila yayi min dazun cewar yana son wacece uwar ďanshi. “To ko dai ya ga ina aikata wani abu ne?” Na tambayi kaina kamin na samu mai ba ni amsa Hajiya Jamila ta shigo dakin ta rufe kofar da makulli. “Kin ba shi nono?” “Aa ina jin tsoro ban san ko akwai camera a ďakin ba kar mai gidanki ya gani” “Babu camera a ďakuna sai dai a wajen gida da kuma ďakin yaron nan amman ďakina da ďakin mijina da falo duk babu camera” Jin haka yasa na daga hijab dina na saka hannu ya ciro nono na saka mashi a baki, sai ya karba da sauri ya fara tsosa da karfi ya dade yana tsutsa sannan ruwan nonon ya kawo. “Me Hubby ya tambaye ki?” Ina tsaka da ba Amir nono ta yi min wannan tambayar, ba tare da na kalleta ba na amsa mata. “Ya tambaye abun da ke damuna ne sai kuma yayi min ya jiki” “Okay duk tambayar da zai miki ki san irin amsar da za ki ba shi karki yi subutar baki” Na daga mata kai. Sai bayan sallah isha'i na fito daga bangarenta na shiga BQ ko da na shiga na samu su Mama sun jera komai sun gyara daki yayi kyau tare da taimakon masu aikin da Hajiya Jamila ta yi ma magana su kama musu gyaran haka ya taimaka abun yayi sauri. Sai tara mijin Yaya Maryam ya zo ya dauke ta bayan ya shigo cikin gidan ya duba gurin har ya saka mana albarka. Misalin tara da rabi Hajiya Jamila ta aiko mana da abinci da na tabbatar hotel aka siyo shi domin be yi kama da abinci da aka girka ba ya fi yanayi da abincin siya. Na dan ci kadan Mama ba bata wani ci sosai ba domin ba son shimkafa take da dare ba, bayan mum gama zan kwashe kayan Mama tace na bari ta kwashe domin jikin nawa babu karfi sosai har lokaci, kwashe kayan ke da wuya muka ji sallamar Dr Hamid da sauri na tashi na dauki Hijab na saka Mama ta leka waje sai suka gaisa ina jin lokacin da yake tambayar Mama ni sai tace bari ta yi min magana. “Tashi ki je Dr Hamid ne” “Me zan ma shi?” “Ya za'ayi na sani ni? Ki leka wata kila magana yake son yi da ke” Cikin rashin jidadin zuwanshi na tashi na fita na taka inda yake tsaye yana wasa da keys din hannunshi na tsaya ba tare da na kalleshi ba. “Zahra ya karfin jiki?” “Alhamdulillah” “Kin ci abinci?” “Eh” “Zan wuce gida ne na ce bari na sake biyowa na duba lafiyarki maybe ma ba ki sha maganinki ba” Na yi murmushi domin kuwa yayi sara ne a kan gaba, ban sha maganin ba sam na manta da wani zancen shan magani ma Mama ma ina jin kamar ta manta bata tunatar da ni shan maganin ba, wata kila kuma tana jiran sai zan kwanta ne. “Zan sha idan zan kwanta” “Daman ai na sani saboda ba son magani kike ba, je ki dauko ki sha agabana” Na yi wata yar siririyar dariya marar sauti. “Zan sha Allah ka yarda” Ya dade yana kallona da murmushi a fuskarshi sannan ya duba agogon hannunshi. “Shikenan bari na tafi, idan akwai abun da kike bukata ki yi magana da Jamila gobe za a kawo muku abinci da gas din girki” “Har da dawainiya haka mun gode Allah ya saka da alheri” “Ameen na yi magana da ita ne ta waya dazun sai take fada min cewar mai gidanta yace gobe za a kawo muku” “Mijinta yana da kirki sosai” “Yana da kirki gaskiya taimako da jin kai halinshi ne, yana da tausayi” Haka muka yi ta yar hira har goma ta gota sannan yayi min sallama ya tafi. Ina komawa ciki na sha magani na kwanta kamar na labarta Mama abun da ya faru tsakanina da mijin Jamila sai kuma na ake ganin kamar abun be kai na bada labari ba. [11/12, 7:44 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣6️⃣ Washe gari aka kawo mana kayan girki da kuma gas kamar yadda Dr Hamid ya fada, Mama ta jidadi sosai mutanen da suke zuwa duba gurin da muka dawo ma suna ta taya mu murna wai mun yi dace da mutanen arziki, a anan na gane ashe mutane da yawa sun san shi babban mutum ne mu dai da ba mu da alaka da shi kuma ba mu da shige shigen bin gidanjen masu arziki yasa ba mu san waye shi ba sai sunanshi, shi ma ta hanyar gidajen radio muke ji, domin ni dai ban taba ganin fuskarshi ba balle na shaidi cewar shi din ne. Duk wanda ya zo ya ga gurin da muke zaune sai ya ta ya mu murna domin guri da mai kama da gida gashi an kawata gurin ga kuma ac da aka saka a ko wane daki. Sai da mutane suka watse sannan mana ta dora min ruwan wanka suka tafasa sai ta ba ni tawul na saka na yi wanka da shi domin babu itacen dogon yaro a gidan da zan iya amfani da shi, duk itacen da suke Garden din gidan daga na ayaba sai na lemu sai guava da mangoro da kuma sauran kayan marmari, bayan na yi wankan ta dama min kunun kayan safa safe irin na mai jago da zai karamin ruwan nono sannan ta dora girki. Da yamma can sai ga Dr Hamid wai ya zo mu gaisa ya kara abincikar lafiyata ya auna jinina ya ce yanzu ya zama normal zan iya daina shan maganin saboda kar yayi kasa sosai ya zama wata illar, mun dan taba hira kadan sannan yayi min sallama ya tafi. A kullum idan zan kwanta sai na bawa Amir nono da safe ma sai na shigo bangarenta na shayar da shi haka ma da rana sai dai ta tabbatar da cewar idan na samu kuzarin Amir din zai koma hannuna ne a matsayin Nanny ina kula da shi sai idan dare ya raba zan kawo shi a gurinta, ni kuma hakan yayi min dadi domin ina son na samu lokaci da yarona ina son na kebe da shi musamman ma da na lura da yana son hannuna domin komai kukan da yake idan na dauke shi zai daina. Kwana biyu da na yi a gidan ina shayar da yaron sai ya samu lafiya yana walwala, sai dai ni kuma na rasa walwalar ta dalilin tabbatar da rasa masoyina da na yi, ina ta kokarin mantawa da shi amman na kasa each and every minute sai na tuna da Abiey, a yanzu kaunarshi ta fi azalzalata fiye da ko yaushe, wannan na saka bana iya zauna na ci abinci yadda ya kamata bana iya sakewa na yi hira da ko da Mama ne. Ranar da na muka kwana biyar a gidan Dr Hamid ya zo tare da Dr Zainab a lokacin Amir yana hannuna mun gaisa da ita ina ta jin tsoro domin kallon da take min ya wuce ka'ida kamar mai zargi haka take ta kallona, hannu ta kai ta karbi yaron daga hannuna tana mashi wasa. “Dr yace min ya samu lafiya” Dr Zainab ta fada tana juya shi a kafadarshi. Hajiya Jamila ta ce. “Gaskiya ya samu lafiya, daman ko da Hubby yayi miki magana yana kan wani magani da Dr Hamid ya dora shi akai, shiyasa ya roki ki daga mashi kafa kar abun ya zama biyu” “Na ga alama ai daman Dr ba baya ba gurin kwarewar aiki” Ta amsa idonta na kaina. “Sannu Zahra ya lafiyar jiki?” “Alhamdulillah” Na amsa kamar munafuka bana son na hada ido da ita, Hajiya Jamila ta kalleni ta kalleta. “Daman kin santa ne?” “Eh makotan mu a inda muka taba zama” Ta amsa mata jikina na ba ni cewar har yanzu ni take kallo, ina dago kai muka hada ido sai na yi saurin sadda kaina kasa. “Oh Allah sarki” Cewar Hajiya Jamila sannan ta mika hannu ta karbi yaron. Dr Zainab ta mike tsaye still idonta na kaina. “Toh ni zan tafi daman dai na ce zan zo na duba yaron ne saboda kar mijinki yace ban sake zuwa ba, daman dai na fada mashi cewar mu bada kwana biyu mu ga idan yaron be samu sauki ba sai a fara mashi wasu gwaje gwaje” “Aa ya samu sauki sosai Wallahi mun gode” Hajiya Jamila ta fada da sauri, Dr Zainab ta sake kallona ta ce. “Kin dawo da zama a nan ne Zahra?” “Eh muna tare da Mama” “Okay” Daga haka bata sake ce min komai ba har ta fice daga gidan, harabar gidan Dr Hamid ya rakata ya dawo falon ya same ni tare da Hajiya Jamila. “Thank you Zahra” Ya fada min yana kallona Hajiya Jamila dai bata ce komai ba sai tashi ta yi tare da ďanta ta nufi hanyar dakinta. Sai da ta shige sannan Dr Hamid ya kalleni “Zahra matar nan yayar Abiey ce right” “Ka san Abiey ne?” “Not much, amman labarin abun da ya faru ya karade ko'ina kuma na san cewa Abiey dan'uwan Dr Zainab ne” “Mutane sun rubuta Labarai marar dadi da yawa akan mu” “Musamman ke abun zai fi effecting dinki sama da shi, duk dai ban san alakarku ba amman ina kallon kamar ya yaudareki ne ko? Guy nan is very arrogant ya cika jin kanshi and kin san cele din nan ba su da tausayi da damuwa da kowa sai kansu wannan yasa be taba burge ni ba” Na yi murmushi ina sauke kaina kasa na saka hannu daya cikin dayan. “Abiey ba haka yake ba, mutum ne mai sauki ga ga wanda ya fahimce shi, kuma be yaudare ni ba kawai dai kaddararmu ce a haka” “Maybe dai yana kusa da zuciyarki ne sosai shiyasa kike fadar haka ba zaki gane abun da nake nufi ba” “Ba ka yi karya ba Abiey yana kusa da zuciyata sosai irin kusancin da idan zan numfasa sai na tuna shi ina kwana da shi a raina na tashi da shi” “Amman Zahra kun yi soyayya a tsakaninku ne a can baya? If i may ask” A take na ji idona ya cika da hawaye, na mike tsaye da sauri. “Bari na tafi ko akwai abun da zan rikawa Mama” “Okay” Ya nuna min kofa sai muka tako a tare muka fito haka ya rokoni har gurin BQ na shiga sannan ya koma. Ana sukowa daga sallama magariba mai gadin gidan ya sallama mana a BQ wai ana sallama da ni a waje, gabana na fadi sosai Mama ma ta yi mamakin domin ba mu san wani da zai iya zuwa ya sallama min a wannan lokacin ba. “Toh ko dai Abiey ne?” Mama ta fada a take na ji zuciyata ta yi wani zillo kamar ta bar jikina ta tafi ta gana da masoyinta. “Ya fada maka ko waye shi?” Na tambayi mai gadin gidan. “Aa be fada ba” “Dan Allah ya kamaninshi suke?” “Fari ne haka dogo yana cikin mota, ya ce ya mana kin san da zuwanshi” “Ka ce ga ni nan zuwa” Ya juya ya fita ni kuma na cire hijab din jikina na dauki wani na saka na tambayi izninin Mama. “Tafi wata kila wata maganar zai fada miki” Na saka talkamina na fito ina jin kafafuwana na min nauyi, ina fitowa sai na same mota harabar gidan an faka, kai tsaye na nufi gurin kamin na isa aka bude motar ga mamaki Sauban ne fuskarshi da murmushi kamar an masa bushara. “Ki ce gidan na ku haka yake da tsaro sai an bincike mutum tsab sannan ake bari ya shigo cikin gidan, ba dan ina son ganin ki i swear da fasawa zan yi” Na yi murmushin da ya same min na dole ina mamakin zuwanshi gidan, ko da yake ba abun mamaki ba ne domin Dr Zainab ta zo dazun ta same ni a gidan wata kila ta hanyarta ya samu labarin cewar ina zaune a nan, sai dai kuma me ya kawo shi gurina? Kamar ya san amsar tambayar nake nema sai ya ce. “Na san zaki yi mamaki abun da ya kawo ni ko? Na zo na kara duba lafiyar ki ne, kin bar asibiti ba tare da kin sanar min ba, i hope ba laifin abokina ya shafe ni ba” Na girgiza mashi kai. “Ko kadan mu ma sallmar ta zo mana an a bazata” “Amman duk da haka ai ya kamata ki sanar min ko a waya ne, na yi ta yawom zuwa asibitin nan kuma kin san dan iskan likitan nan ya hanani ganinki yace be san inda kike ba, number Mama kuma idan an kira bata shiga, ina ta nemanki amman ban samu ba na sha wahala sosai fa, sai dazun Dr Zainab ta fada min inda zan same ki domin ita ma na yi ta bincikar tace min bata san inda kike ba” “Ba ni da waya yanzu” “A nan kike zaune?” Ya bukaci sani yana karewa BQ din kallo. “Eh tare da Mama” “Allah sarki ki min magana da ita mu gaisa” “Da Mama?” “Eh ko akwai matsala ne?” Na girgiza kai alamar aa na juya sai ya kira ni. “Zahra” Na juyo bude motar yayi ya dauko kwalin sabuwar wayar da sabon line ya dora min saman wayar. “Ga wannan ki samu wayar da zaki rika magana da mutane, ga kuma sabon line ba lallai kowa ya san kina da shi ba sai wanda kika aminta kika bawa number” Kallon wayar na yi sai na ke jin kamar yana min maganar Abiey. “Aa bana son rike waya a yanzu” “Kin fi son idan zan zo na rika aikawa ana kiranki ko da yaushe? Kuma idam ina son na gaisa da ke sai na zo” “Aa ba lallai masu gidan su rika bari kana zuwa ba” “That's why nake son ki karbi wayar nan i promise you ba zan bawa Abiey number ba, you can trust me” Na dade ina tunanin karba sannan na mika hannu na karbi wayar na yi mashi godiya, sannan na juya na shiga ciki na sanar da Mama ta ba shi izini sai ya shiga ya gaisa da ita ya bata hakurin abun da ya faru har yayi ikirarin siya mana gurin zama. “Aa nan ma ya ishe mu ba sai an nema mana wani gurin ba, amman dai idan da hali ina son ka je ka samu shi Malam ka bashi hakuri kuma ka biyaki kudin gidanshi idan kuma yama bukatar a gina mashi wani ne sai ka gina mashi saboda an shiga hakkinshi” “Wallahi Mama ba Abiey ya saka a rushe gidan nan ba, amman dai za a yi haka saboda kowa yana kallon mu muka aikata kuma shi ma ba zai fahimta ba zan bashi hakuri da yardar Allah” “Toh Allah ya bada iko mun gode” “Akwai wani gida da yake gabanku sabo ne da ake ginawa na yi maganar shi idan zai muku sai a siya muku shi” “Aa nan din ma wadatar karka bata kudinka mun gode Allah ya kara rufa asiri” Duk inda ya taro akan siya mana gida sai Mama tace mashi aa da haka dai ya hakura yayi mata sallama bayan ya aje mata kudin da zai kai 100k ya taso na rakoshi muka dawo gurin motar. “Ke da Mama halinku daya na kawaici idan ance za a muku abu sai ku ce aa” Na yi murmushi, sai ya bude motar ya dauko wata karamar leda ya miko min. “Ga chocolate na siyo miki karki ce aa please shaidan kawai ake yi ma kyauta ya ce aa” Da wannan furucin ya daure sai na saka hannu biyu na karba ina mashi godiya. “Yanzu kuma sai yaushe?” “Shikenan mana ba sai ka sake zuwa ba” “Korata kike yi?” “Aa ka ga nan ai ba gidan mu ba ne, ba kowa zai dauka a rika shigo mashi a gida kai tsaye ba” “Shikenan idan akwai waya ai ba zan rika takura miki da yawa ba zan san halin da kika ciki so that na tabbatar da lafiyarki” Da wannan muka rabu, sai dai hakan be saka ya daina zuwa ba ya maida kiran a waya kamar wani abinci da safe zai kira ya tambaye lafiyata da yadda na tashi haka ma da rana da dare ma idan zai kwanta sai mun yi waya, tun abun na damuna ina kin sake jiki har na ya fara same min jiki abun ka da mai bukatar abokin hira ya kan cire min kewa shi da Dr Hamid dake zuwa lokaci lokaci wani lokacin kuma sai na wuni a falon Hajiya Jamila ina kula da Amir ina kallo, domin na fara sabawa da gidan da kuma ma'aikatan gidan sai dai na ki yarda na sake jiki da kanwar Mr Bashir saboda ta cika saka min ido da yawa ga yawan tambaya kamar yar jarida a wata daya da na kwashe a gidan har yanzu ban gama karantarta ba idan bata garin saboda yanayin aikinta na zuwa kasashe da garuruwa har sakewa nake ita ma kanta Hajiya Jamila bata sakewa idan bata cikin gidan, sai dai na lura Ummiter yarinya ce mai son mutane da hira, kawai dai basa jituwa da Hajiya Jamila ne domin idan muka zauna a falon daga ni sai ita zata yi ta zagin Hajiya Jamila ne a gabana ni kuma wannan yasa bana cewa komai gudun kar ta kara gaba da ni tace na ce alhalin ban ce ba. Ba a iya kiran waya Sauban ya tsaya ba har sakon karta kwana turo min yake wani lokacin na kan tsaya na karanta wani lokacin kuma bana karantawa na ke gogewa, a sati sau daya yake zuwa mu gusai ina kallon kamar Abiey ne ya saka shi yi min haka wata zuciyar kuma na raya min kamar Sauban yana son ya maye min gurbin Abiey ne, duk kuwa da kasancewar be nuna min ko ya furta min yana so na ba amman yanayin yadda yake kula da ni da yawan waya akai akai abun ya daure min kai, idan na yi mashi magana sai ya nuna ba saboda Abiey yake yi ba, ita ma kanta Mama ta fara zargin Sauban so na yake, duk zuwan da Sauban yake gidan be taba haduwa da Mai gidan ba, domin ya fi zuwa da rana shi kuma mai gidan baya zama sai da dare ko da safe, idan ma yana nan kullum yana bangarenshi ba kasafai yake shiga bangaren Hajiya Jamila ba, idan ma yana shiga bana gani domin ta gargade ni cewar idan yana cikin gidan kar na shigo sai ya fita bangarenta, ko Amir take son a goya wani lokacin sai dai ta dauko shi ta kawo min BQ a nan zan ba shi nono na goyashi. Kamar ko wane sati muna jingine jikin motar Sauban muna gaisawa muka ga an bude gate da sauri motar mai gidan ta kunno kai, daga ni har Sauban kallon motar muke har ta karaso inda muke tsaye ta faka aka sauke gilashin motar, tsabar faduwar gaban da nake kaina har wani tsarawa yayi. “Sannu na zuwa” Na daga ina dan risinawa sai da ga karewa Sauban kallo sannan ya kalleni. “Waye wannan?” Na kalli Sauban na rasa ta ina zan fara. “Ah... Ah... Ah” Maganar ta ki fita na rasa kalar karyar da zan yi. “Idan kin sallame shi ki same ni a bangarena” “Toh Yallabai” Na fada sannan ya wuce da motarshi ni kuma na kalli Sauban da tsoro na ce. “Ka ga abun da na ke gudu ko? Ka tafi dan Allah daman irin mutanen nan ba sa son ganin kowa cikin gidansu” “Zan tafi amman zan dawo, dole yayi hakuyi saboda ya aje ki a gidanshi” Kamar na yi kuka haka na ji kamin Sauban ya bar gurin har gumi ya tarar min. Yana wuce na shiga BQ na fadawa Mama abun da ya faru da kuma son ganina da Mijin Jamila yace yana son yi. “Daman can ni zuwan da yake ba son shi nake ba, saboda zai haifar da matsala ne kawai a tsakaninku kin san ba zai yiyu ki ce zaki aure shi ba yana a matsayin abokin Abiey, kawai dai bana son na hana shi zuwan ne ya ga kamar ina korarshi ne” “Ni ma ai ba son zuwan shi nake ba shi ne yake zuwa ai” Na fada ina kuka daman tuni na fara kukan. “Toh yanzu sai ki tashi ki je ki ji abun da zai fada miki” Na mike tsaye ina jin kamar na ce Mama ta raka ni mu je, cikin rashin kwarin guiwa na fito BQ na nufi apartment dinshi kai tsaye domin a can ya ce na same shi be ce bangaren Hajiya Jamila ba, kamar kazar da kwai ya fashewa haka na isa kofar na kwankwansa shiru ba a ce min komai ba na sake kwankwasawa sai sharar kwalla na ke nan ma ban ji ance ki shigo ba, sai na murda kofar na tura a tare ta bude sai da na fara lekawa kamar wanda zata yi sata karaf muka hada ido da bawan Allah dake zaune kan cushion hannunshi rike da waya, da sauri na koma na rufe kofar sai na ji wani sabon kuka ya taso keyar ido na gaba, ko kadan bana son na yi laifi da zai saka ya ga kamar na taka mashi dokar gida ko kuma yace zai sallame mu daga gidan domin zai zame min wahala ne a yanzu saboda na saba da ďana. Na kwankwasa ba a ce min komai ba sai na sake bude kofar na shiga na kuma ki yardar na kalli inda yake zaune. “Karaso nan” Sai na ji kamar yace zo nan na dake ki duk da na san na wuce duka a yanzu, haka na tafi ina ta kuka kadan kadan na zauna a kasa ina yarfar da hannu, shiru ban ji yace min komai ba dago kai na yi na kalleshi sai na ga ni yake kallo a take na fara ba shi hakuri. “Dan Allah ka yi hakuri.” “Dukanki aka yi” Na girgiza kai alamar a a. “Marinki aka yi?” Nan ma kan ma girgiza mashi. “Toh miye na kuka?” “Fada zaka min” Na fada cikin kuka marar sauti, murmushi na gani a fuskarshi. “Miye alakarki da wannan mutumen ina yawan ganinshi a gidana” Ban yi mamakin ya ce yana ganinshi na daman Dr Hamid da Hajiya Jamila sun fada min akwai camera ko'ina a gidan. “Ba ni da wata alaka da shi” “Karki min karya Zahra i respected you so much ina kamar ba laifinki ba ne, wannan ya sa na ke daga miki kafa” “Kawai abokin tsohon saurayina ne” “Tsohon saurayinki ko tsohon mijinki?” “Saurayi dai” “Mutumen da ya saka aka rushe muku gida?” Na daga mishi kai. “Anyway bana son na sake ganinshi a cikin gidana karka sake ganinki tare da shi har sai kin bar gidan nan, karki koya kanki tsayuwa da maza kala kala ďanki ya bude ido ya fahimci mahaifiyarshi na da samari barkatai” idona kamar za su yi magana haka suka yi bayan wacan lokacin a yau ma mijin Hajiya Jamila ya sake min wata magana mai fasa kwakwalwa. “Dana kuma...” Na tambaya hantar cikina na kadawa. “Ina nufin Amir” “Ba ni na haifi Amir ba Yallabai” “Ni ma ban ce ke kika haife shi ba, haka dai nake ganinshi kamar ďanki saboda kina kula da shi kuma kuna kama sosai” Na sauke kaina kasa ina jin hawayen idona na kafewa saboda tsoro, ashe ba komai ake iya yi ma kuka ba, muna a wannan halin Hajiya Jamila ta shigo dauke da tray ta aje a gaban mijinta. “Na fada miki ki rika hutawa mana, wani lokacin ki rika bari Zahra tana girkawa ko tana wata hidimar so that ke kuma ki samu hutu idan kuma wata mai aikin za a dauko miki sai a karo” Kallon da yayi kama da na mamaki ta yi mashi. “Hubby kai da na san baka son mai aiki?” “Na lura kamar Zahra tana da tsabta ba kamar yadda nake tunanin sauran yan aiki suke ba” Na dago na kalli Hajiya Jamila. “Aikina kula da Amir ne kawai ban zan iya wani aikin bayan wannan ba, ni ban ma iya girki ba” Hajiya Jamila ta kalleni ta sake kallon Mai gidanta. “Hubby wani laifi ta yi aka kirata nan?” “No na kira ne na fada mata cewar ina son gobe ta je asibiti a auna jininta saboda an ce hepatitis ya kashe mijinta so that mu tabbatar bata dauke da shi kuma bata sakawa Amir ba” Da ace dan'adam zai iya shiga zuciya ya ga tashin hankali da take ciki wata kila da za a ga tashin hankalina da na Hajiya Jamila zai iya cika duniyar nan, musamman ni da nake ganin kamar na fi kowa laifi domin ita zai iya yi mata da sauki kasancewarta matarshi tsabanin ni, Hajiya Jamila ta zauna kusa da shi da sauri ta dafa shi. “Amman Hubby kamin a kawo ta nan sai da na bincika komai nata lafiyarta, wacece ita da duk wasu abubuwan bata dauke da cutar komai” “Ina son na kara samun natsuwa da ita ne, gobe likita zai kaita asibiti a duba lafiyarta daman can ya kamata na yi haka tun kamin ta fara kula da Amir” “Haka ne wannan ba matsala ba ne zan kira Dr Hamid na sanar mashi” “Dr Hamid is not our family Doctor, Dr Zainab zata duba su” “Su? Ita da wa?” “Ita da Amir” Ya fada kai tsaye yana kallonta tashin hankalin dake fuskarta irin shi a fuskarta jiki yayi sanyi gaba daya. “I thought i didn't tell you that, Zahra don't tell har kun yi shakuwar da zaki zauna kina ba mijina labarinki da rayuwarki” Ta tambaya tana kallona kamin na ce komai ya amsa mata. “Na dan tambaye ta few things ne ta fada min you can go Zahra” Na mike tsaye ina kallon yadda ya daure ni a gaban matarshi da cewar na fada mashi cewar mijina yana da hepatitis alhalin ban san inda ya samu labarin ba, Hajiya Jamila kuma ta watso min wata uwar harara da na tabbatar idan muka kebe ba karamin cin mutunci zata min ba. [11/14, 7:36 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣7️⃣ Ina shiga BQ kamin na labarta ma Mama komai na dauki wayata na kira Sauban na sanar da shi gargadin da Alhaji Bashir yayi min. “Miye matsalarshi da zuwa na gidan?” “Baya son ganin kowa a gidan shi daman na fada maka ai masu kudin basa son shisshigi, daman ina ta jin tsoro gashi nan kuma ya gani har yayi min magana” “Saboda ya gani ko yayi magana ba zai saka na daina zuwa gidan ba, Zahra idan kika ga na dauke kafata a gidan to kin bar gidan ne” Na mike tsaye ina nuna gina kamar yana gabana. “Sauban bana son matsala na gargade ka tun yanzu, ina ce saboda ni kake zuwa yanzu kuma bana son zuwanka ai akwai waya” “Waya ba zata wadatar ba Zahra dole sai ma ganki” Na kashe wayar na kalli Mama girar sama da ta kasa a hade. Kamin na ce komai wayar ta yi ringing da sauri na yi picking ganin Sauban ne. “Ki fada mashi idan baya son ganin baki a gidanshi to ya sallame ki” “Bana son abotar na fasa” Na fada ina zare ido sai ji na yi ya saka dariya. “Now i understand why Abiey yake son ki, dan zaman da na yi da ke na fahimci abubuwa na rayuwarki” “Ni dai na fada maka kuma ka zo ka karbi wayarka idan har ba zaka ji magana ta ba” “A matsayinki na wa zan ji maganarki? Kin ba ni shekara nawa?” “A matsayina na kawarka” “Ai kin ce ba ki son abotar ko kin manta? Kuma zan so na karbi wayata da duk wani chocolate da na taba baki” Na yi shuru ina tunanin da gaske yake ko wasa dai. “Ai ba ni nace ka ba ni ni ban taba cewa ka bani abu ba, dan haka ba zan biya ba” Na kashe wayar, na kalli Mama dake kallona da mamaki a fuskarta. “Ke dai kam ba zaki girma ba Zahra, sai na ga kamar kin yi wayo kuma ba wayon kika yi ba” Na turo baki gaba na zauna kusa da ita. “Toh Mama ba ki ga mijin Hajiya Jamila yana min fada ba wai kar ya sake ganina da kowa a gidan nan, kuma har yace wai zamu je ayi gwajin jini ni da ďanshi Mama ke kika fada mishi na aure mai hepatitis?” Mama ta bude baki tana kallona. “Ikon Allah Zahra Ina zan ga mijin Hajiya Jamila har na fada mashi haka? Ba dan dake da wautarki ba, kuma dai ko na ganshi sai na zauna na bashi labarin abun da ya kashe mijinki?” “To a ina ya ji?” “Waya sani, amman yana babbar magana ce ina ya ji labarin nan? Ko dai ita Jamilar ce ta fada mashi” “Ba ita ba ce kuma ya hada ni fada da ita yace da ita wai ni na fada mashi, yace gobe zamu je gwani ni ba zan je ba, idan anje gwaji aka ce jinina daya da ďanshi sai ya saka a kamamu” “Toh ko dai ya gane gaskiya ne?” “Idan ya gane Mama ba zai bar mu ba, da yanzu ya rufe mu, amman dai ina ganin mu gudu kamin ya gane” “Mu gudu muje gurin uban waye? Duk ba rashin tunaninki ne ya janyo komai ba, ga makiya ki sake saka mu a cikin wata masifar kin san dai Hajiya da Malam ba za su kyale ki ba” Na dora hannu a saman kai. “Ni dai yau na shiga uku, Mama ya zan yi to?” “Ya zaki yi dole ki je a dauki jini ainita Jamilar dole ta nema muku mafita, wata kila ma yayanta zata saka ya auna jini” “Tace haka yace mata aa wai Dr zata auna” Har lokacin kuka nake ba hawaye tashin hankalin dake zuciya ya cika har yayi yawa, haka dai muka yi ta tattauna maganar da Mama har muka ji sallamar Hajiya Jamila jikina na rawa hantar cikina na kadawa na fito domin bayan ta yi sallama sunana ta kira bata shigo dakin ba, a tsaye na same ta tana jirana ina isowa kusa da ita ta kama hannuna ta matsa nesa da kofar BQ din wata kila bata son Mama ta ji. “Akan me zaki fadawa mijina cutar da ta kashe mijinki? Tambayarki yayi? Kuma ko tambayarki yayi ai kamata yayi ki boye, ba wai ki sake baki kina ta zuba ba, gashi nan yanzu kin janyo mana wata matsala” Ni dai na yi shiru to me zan ce, ko da na fada mata ba lallai ta yardar ba kuma ba zan iya karyata mijinta ba, haka dai na yi shiru ta yi ta fadanta har ta gaji ta yi shiru, bayan ta gama fadanta ta shige bangarenta ni kuma na dawo BQ a nan kuma Mama ta rufe ni da wani fadan wai miyasa ban fada mata gaskiyar cewar ba ni na fadawa mijinta komai ba. Haka na kwana cikin bacin rai washe gari ma ana gama sallah asuba muka ji an bude gate din gidan, ni dai ban leko ba domin ba aikina ba ne kula da wanda zai shigo ko ya fita, ba a dade ba na ji muryar Dr Zainab tana mana sallama a dayan bangaren kuma tana hira da mijin Hajiya Jamila, ina jin sallamarsu na koma bachi karya Mama ce ta amsa ta tashi ta leka waje ta gaisa da shi. “Zahra na nan?” “Eh ranka ya dade amman bachi” “Yauwa haka na ke so, a tashe ta please” Ina jin haka na yi zumbur na tashi zaune. “Mama dan Allah ki ce na suma” Na roka kamar na yi kuka. “Tashi ki je ana kiranki ba zan yi karyar komai ba, ki daina jin tsoro idan ma kina da laifi ai ita Hajiya Jamilar ta fi ki laifi, wata kila ma wannan ta san Dr Zainab zata iya rufe mata asiri tare take da ita saboda haka ki tashi kawai ki tafi” “Amman Mama Dr Zainab zata fada ma Abiey kuma zata san gaskiya” Ina maganar hawayena na zubar min a ido, haka na tashi cikin tsoro cikin kuka Mama na min fada na natsu na daina kuka amman ko saurarenta ban yi ba na fita a haka. “Lafiya kike kuka?” Dr Zainab ta tambaya. “To ba jinina za a dauka ba na sani ai” “Daukar jinin shi ne abun kuka kamar za a cire ranki” A cewarta tana dariya, ni dai kukan kawai nake, Mijin Hajiya Jamila kuma na tsaye gefe daya ya maida hannayenshi baya yana kallona uffan be ce ba. “Na rantse da Allah an auna ba ni dauke da cutar Wallahi Wallahi” Har kasa na kai ina mashi rantsuwar an gwada ni ba ni dauke da cutar. “Zahra ba wai yace kina dauke da ita ba ne, kawai za a sake gwadawa ne, daman yana da kyau ko baka dauke da cuta ka je a gwadaka, kuma be kadai za'ayi ma wannan ba, kin ga jinin ďanshi da na matarshi ma an dauka, daman an fi son kamin a ci komai” A nan na gane ba ni da wani iko sai na mika hannu aka daura min rowa aka dauki jini ina kuka sosai, wata kila Dr Zainab da shi mijin Jamila su zata kukan daukar jinin nake sai dai ni kukan watan tonon asirina da ya kama ne nake yi, gashi ya biyo mana ta hanyar da ba mu yi zato ba, yace zamu je asibiti ashe zuwa zata yi gidan kuma tun da asubar fari kuma har da na matarshi aka dauka bayan na danshi. “I trust You Dr Zainab” Ya fada mata bayan ta dauki jini ta yi mana sallama, ita kuma ta daga mashi kai tsaye na yi ina kallonsu har suka fice daga BQ din ina jin kamar na bita na roke ta kar ta auna jinin ko kuma idan ta auna ta boye result din. Bayan mun shigo dakin tare da Mama na ji wani sabon kuka ya sake rufe ni “Mama ko dai na tafi gidan Dr Zainab na roke ta kar ta tona mana asiri” “Karki kuskura ki dai ki mikawa Allah komai ki yi ta addu'a kawai, Allah ya dubi zuciyarmu ya rufa mana asiri ba mu yi haka dan mu cutar da kowa ba, Allah ka da ka kunyata mu a cikin makiya ya Allah” Mama ta rufe da addu'a ita ma tana hawayen domin ni da ita duk tsoron abun da zai biyo baya ya gama cinye mu. ABIEY POV. 6pm Abiey na zaune bayan motarshi Sauban na jingine da motar yana kallon wani gurin fuskarshi da murmushi bayan ya gama labarta mashi yadda suke yi da Zahra a jiya da dare har yanzu abun be daina saka shi dariya ba, abun da be sani ba Abiey na tsare da shi da ido yana karantar yanayinshi da nishadin dake bayyana a fuskarshi tun kamin ya zo a yau ya labarta mashi abun da ya faru Abiey ya ji komai a waya, code da ya saka a wayar Sauban duk wani kira da Sauban zai yi tsakaninshi da Zahra zai ji sai dai shi Sauban be san da wannan ba. Abiey tun jiya zuciyarshi ke tafasa daman can idan ya saurari wayar da Sauban yake da ita ko kuma Sauban ya bashi labarin cewa ya tafi gurin Zahra Abiey sai yayi da gaske yake iya cin abinci saboda wani bakin ciki da ke rufe, a jiya zuciyarshi tafasa take a yanzu kuma soyuwa take na ganin murmushi a fuskar abokinshi sanin silar murmushin na shi. Sauban ya juyo still yana murmushi ya kalli Abiey ya ce “Zahra tana da wauta sosai some time the way she act tana burge ni” Abiey ya watsa mashi wani kallo yana jin wutar kishi ya azalzalarshi. “Sauban control your tongue taya zaka fada min acting din Zahra na burge ka? Remember aikinka kawai ka dauki hankalinta har ta aminta ta aure ka ba wai ta burge ka ba ko kuma ka so ta” “Subhanallahi Abiey ba zan iya tarayya da kai a soyayya ba kar Allah ya nuna min wannan ranar, saboda na ce acting dinta na burge ni ba shi ke nuna ina son Zahra” “I think ya kamata ka daga mata kafa for now ka daina zuwa gurinta har sai na bukata” Har Sauban ya bude baki yayi magana sai kuma wata zuciyar ta hana shi ganin ran Abiey a bace, sai kawai ya nufi motarshi ya bude ya shiga yayi mata key da wani kallo Mai Kama da harara Abiey ya bishi haka kawai yake ta jin haushin shi kamar ba shi ya shirya masa neman kusanci da Zahra ba. “Mtswwwww” Yaja wani dogon tsaki zuciyarshi na buga da mugun karfi har saman T-shirt din dake jikinshi ana gani, da ace na Sauban ne yayi masa wannan maganar ba da mai raba shi da wanda zai kalli tsabar idonshi yace Zahra na burge shi sai Allah, yana jin wayarshi na ringing amman bacin rai ya hana shi saka hannu aljihu ya dauko wayar ma balle har ya iya amsawa, sai tsaki yake ta yi sai da ya gaji da zama a harabar gidan sannan ya sauka baya motar ya nufo cikin gidan ko kadan bs damu daya duba mai jero mashi kiran ba haka ya shiga falon mahaifiyarshi fuska babu annuri, Ammy dake kokarin tashi jin an fara kiran sallah a masallacin gidan ta kalleshi sai kuma ta yi saurin dauke kai domin bata son su hada ido a yanzu tana matukar jin kunyar shi. “Aliyu Dr ta kira ni tace ta kira wayarka baka daga ba” Abiey dake kara bata fuska yana jin kamar Ammy ta kara mashi bacin rai ne ya ce “Ni ta bar ni da abun da ya ke damuna ni” Ammy ta bishi da kallo har ya fara taka stairs din. “Aliyu” Ya juyo ya kalleta, sai dan sauke idonta daga barin kallonshi. “Akwai abun da yake damunka ne? Na ga ranka a bace kuma gashi har ka furta abar ka da abun da yake damunka? Me ke damunka?” Kokarin kirkiro murmushi yayi. “Ahh.. Ba komai Ammy bari na yi alwala an fara kiran sallah” Ya juya da sauri ya haye sama gaba, ko da ya sauko Ammy bata falon yana sauke nadin hannun rigarshi ya nufi kofar fita da kuzarinshi, yana daf da isa kofar masallaci Dr ta sake kiranshi haka ya amsa kiran kamar na mashi dole. “Haba Dr tun da har kika kira ni ban daga ba ai kin san bana cikin yanayin amsa kiran ne kuma yanzu masallaci zan shiga” “Wani abu na gani mai matukar daga hankali da tausayi Abiey” “A ina?” “Zahra ta aikata ta jafa kanka ciki mawuyacin hali mai fitar da ita a yanzu kuma sai Allah” Abiey ya tsaya cak tun daga lokacin da sunan Zahra ya daki dodon kunnenshi. “Miya faru da ita” “Ba magana ce da zamu yi a waya ba, idan ka gama sallah ka same ni a gida kamin Abbansu ya dawo” Abiey ya sauke wayar yana kallon ma'aikatan gidan dake shiga masallacin sai dai a badini zuciyarshi tana can gurin tunanin maganar Dr Zainab ta fada mashi. “Miya samu Zahra?” Ya tambayi kanshi gabanshi na faduwa domin baya son abun da zai daga hankalin masoyiyarshi a yanzu balle har ya taba ta. ‘Ko saboda zuwan Sauban ne?’ Wani bangare na zuciyarshi ya raya mashi, kamin ya sake jefawa kanshi wata tambayar. “Ko wani abun suka mata? This time around idan mutanen nan suka taba ta ba zan kyale su ba, and if aka sake shirya wani makircin i will face Siyama kai tsaye” Ya fada yana tuna maganar da Aisha ta yi mashi cewar tana ganin kamar Siyama ce ta fada ma Hajiya Kilishi da Mama Lami har aka shirya rushe musu gida da sunan shi ya aikata, sai da ya yaki shaidan da zuciyarshi sannan ya shiga masallacin ya fuskanci alkibla tare da mamu ya bi jam'i aka gabatar da sallah Magariba tare da shi. Ana sallame sallah shi ne mutum na farko daya fara fita masallaci cikin gaggauwa abun da be saba ba, domin idan an gama sallah ya kan tsaya har sai yayi tasbihi yayi addu'o'i sannan ya fita. A uzure ya shigo falon Ammy ya har zai nufi upstairs sai idonshi suka kai gurin key motarta dake aje a inda ta zauna dazun da sauri ya dauki key din ya juya ya fice, tun kamin ya isa gurin motar ya daga murya yana cewa masu gadin da suka fito masallaci a yanzu su bude mashi gate, kamar wanda aka cewa ga Zahra can zata mutu haka ya shiga motar yayi mata key ya fisgeta da karfi ya fice daga gidan daman tuni suka karasa gate din da gudu suka bude mashi, kamin ya isa gidan yar'uwarshi har jin yake kamar ya kirata a waya ta fada mashi ko minene daker ya daurewa zuciyarshi ya karasa gidan, gudun kar mai gadin gidan ya bata mashi lokaci ya saka shi fakin a bakin gate din gidan ya yi knocking din karamar kofar gate din gidan Mai Gadin ya leko ta yar karamar hanyar ido domin duba ko waye yana ganin Abiey ya bude kofar da sauri yana mashi barka da zuwa. “Yauwa sannu” Ya amsa sama sama sai zuba sauri yake, entrance din kofar falon da kamar gudu ya hau shi ya kwankwasa kofar ya danna door bell at the same time. Yarta ce ta bude mashi ta tarbe shi da murna tana. “Uncle Welcome” “Thank You where is your Momma?” “Tana dakinta” “Je ki fada mata na zo” “Okay Uncle” Yarinyar ta zuba da gudu zuwa dakin Dr Zainab, kanenta suka taso da murna suna mashi welcome sai ya mika musu hannunshi yana shafa kansu yana murmushi. “Sorry ban zo da chocolate ba” “Uncle Momma tace ka shigo” Ya saki hannun yaran da sauri ya nufi dakin da yarinyar Dr Zainab ta fito yana isa ya tura kofar dakin ya shiga, zaune ya same ta kan carpet sanye da Hijab da alama yanzu ta gama sallah Magariba domin tasbihi take har ya samu guri ya zauna yana kallon fuskarta dake dauke da damuwa. “What happen?” Ta mike tsaye ta cire Hijab dinta ta aje gefe ta nufi gurin da jakarta take aje ta dauko wasu takardu da suke hade gudu biyu ta mika mashi, kallon takardun ya rika yi kamin ya mika hannu ya karba. “Miye a ciki?” “Gwajin jini ne da Alhaji Bashir ya saka na yi na shi da na ďanshi da na matarshi da kuma na Zahra” “You mean mutumen da Zahra take zaune gidanshi?” “Eh wannan na Zahra da ďanshi ne” Abiey ya bude takardun da sauri yana dubawa, ba shiri ya mike tsaye yana kara karantawa. “What this mean?” Ya tambaya domin karanta tabbatarwa ba dan be fahimci turancin dake jikin takardar ba. “Jinin Zahra da yaron nan Amir daya ne, kuma jinin yaron da na mahaifinshi da mahaifiyarshi ya banbanta” Ta sake nufar jakarta ta dauko wasu takardu ta mika mashi, ya karba da sauri yana dubawa. “Taya kika gano haka?” Ya matsa baya ta zauna saman gadonta. “Tun a kwanan baya da wani aikinshi da nake kula da familynshi ya hada mu yace yana son na zo na duba ďanshi akan idan ya sha nono yana saka shi ciwon ciki, na je gidan na duba yaro na lura kamar mahaifiyar yaron bata jidadin zuwa ba domin tun a gaba ta fara kuka, sai dai yaje ya rarrasheta yace hankalinta ne ya tashi saboda bata son ana yawan taba yaro, ni kaina nayi zaton ko dan saboda bata tana haihuwa ba ne kamar yadda ake ta fada, sai after na tafi sai Dr Hamid ya same ni da zancen ma bashi kwana biyu saboda yana kan yi ma yaron wani maganin ne baya son a samu matsala, a lokacin da zuciyar Zahra ta buga a lokacin ne ya roki wannan alfarmar, ni kuma na amince mashi ba tare da tunanin komai ba, ban kawo komai a zuciyata ba a zatona da gaske ne, ashe wani abu suke boye min” Abiey ya koma ya zauna yana kallonta cike da tashin hankali. [11/14, 10:03 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣8️⃣ Ta numfasa sannan ta cigaba. “The following day ya sake kirana a waya yace min be ji daga gareni ba, ni kuma na sai na mashi karya cewar na dora shi akan wani magani da na bawa matar ta bawa yaron idan ya samu sauki shikenan idan kuma be samu ba zan cigaba da bincikar Matsalar, har yake ce min yana son na auna jinin yaronshi na hada a cikin file din yaro idan na kammala bincike na yana son zai gani, sai dai zan cen ya kau saboda na fada mashi cewar na dora yaron akan magani, shi kuma ya yarda daga haka muka shashartar da zancen, sai shekaran jiya ya kira ni yace min yana son na gwada jinin matarshi da yaron shi da kuma Nannyn yaronshi da na shi jinin shi kanshi, ya bukaci na zo gidanshi na dauki jinin na su kuma ya dankamin amana kar na zance mashi komai ko da matarshi ko wani ya bukaci haka, duk ban fahimci komai ba har sai da na je daukar jinin yadda matarshi ta rika dari dari ya bani mamaki, sai kuma da muka je gurin Zahra tana kuka sosai na debi jininta, bayan mun fito yace min Dr ina cikin wata matsala da kwankwanto wani da nake fatar ya kusance ba gaskiya ba, amman na yardar dake na san ba za a hada kai da ke a cutar da ni ba, kuma ina son ki yi gwajin nan a sirrance a wani asibitin da ba za a iya canja komai ba” Ta kalli kofar ďakinta jin hayaniyar yaranta kusa da kofar, Abiey kuma ya sake maida dubanshi gurin results din yana dubawa. “After na baro gidan da minti ashirin Dr Hamid ya kirani yace ana son ya hadu da ni, babu irin hakurin da ban bashi ba akan ya jira na fito aiki amman yace ba zai iya ba magana ce ta gagawa, a dole na fada mashi meet point muka hadu sai ya fara karanta min halin da yar'uwarshi take ciki kamin daga bisani ya roki na bashi gwajin jini i refuse sai yace zai ba ni miliyan ashirin saboda na bashi jinin yaje ya yi gwajin idan ya gama zai kawo min results sai na bawa mijin kanwarshi nan ma na ki, a dole ya fito ya fada min gaskiya kuma ya roki na rufa mashi asiri na rufawa kanwarshi da kuma ita kanta Zahra, duk da haka ban yarda ba na dawo gida na shirya na tafi wata private hospital aka gwada jinin results din da ya bada kenan, Wallahi yau kasa aikin komai na yi a office saboda magiyar da Dr Hamid yake min da kuma ganin wannan results din” Ta mike tsaye ta bude wardrobe dinta ta dauko wata bakar jakar ta kawo gaban Abiey ta aje. “Miliyan hansi ne a cikin jakar nan a lokacin da nake ta kiranka baka daga ba har na kira Ammy na ce ta sanar da kai magana ce mai muhimmanci a lokacin ne Dr Hamid ya kawo min kudin nan har cikin gidan nan yana rokon na canja results din nan, fitarshi da minti talatin Alhaji Bashir ya kira ni yace min yana son ganin results din tsakanin yau da daren nan zuwa gobe” Ta karashe maganar cikin wani irin damuwa na rashin makama, Abiey ya ce “Har yanzu ba ki kai gurin da nake so na ji komai ba” “Abiey baka taba mamakin dalilin Zahra na zuwa a gidan matsayim yar aiki tun a lokacin da ka fada min cewar Nuratu ta ganta a gidan ba? Ni kaina na tabbatar da haka ne a lokacin da na sake komawa gidan tare da Dr Hamid ka tuna lokacin da na fada maka cewar Zahra tana gidan?” “Yeah amman zuciyata bata raya min wani bad abu ya kai Zahra gidan ba, she even told Sauban cewar matar gidan ta tausaya musu ta ba su gurin zama ita kuma tana kula da babynta, Sauban ma be taba fada min komai ba?” “Wata kila shi ma be sani ba” “That's mean Zahra ta siyar da yaronta?” Dr Zainab ta daga mishi kai. “Tun yana ciki domin har takardar yarjejeniyar na gani a hannun Dr Hamid da kudin ta biyawa Deen kudin aikin da aka mishi” Abiey ya runtse ido da sauri ya cige bakinshi. “Ohhhh nooooo Zahra why?” “Bata da yadda za ta yi ne a lokacin domin tana neman mafita ne, sai suka yi karya cewar abun da ta haifa ya koma, ko a lokacin da ta haifi yaron na shiga dakin ina mata sannun sai cewa take ita mai rai ta haifa a cikin kuka sai a yanzu na gane abun da take nufi, Zahra ta jefa kanta a matsala gashi yanzu ta koma ta tare a gidan tana shayar da yaron saboda nonon matar ba shi da kyau kuma cikin yaron yaki karbar nonon kowa sai na Zahra” “Yanzu na fahimci dalilin alakar Dr Hamid da Zahra wata kila ma ita ta sska a rushe gidansu Zahra saboda ta dawo gidanta ta zauna, why on earth Zahra zata siyar da cikinta saboda ceton rayuwar da bata cancanci cetonta ba?” “A cikin takardar yarjejeniya Zahra ta saka hannu akan cewar idan har ta tsaba daya daga cikin dokokin zata biya naira miliyan ashirin, daman ina ta mamakin ina Zahra ta samu kudi haka ashe ta wannan hanyar ta same su” Abiey ya mike tsaye kallon yayarshi. “Sun yi haka ne saboda suna ganin bata da mafitar kudin kuma babu inda zata samu, what if i pay the price?” Dr Zainab ta mike tsaye ita ma tana kallonshi har lokacin da damuwa a fuskarta. “Ba biyan price din ne matsala ba, zaka iya biyan fiye da haka ma, fuskarta Alhaji Bashir a fada mishi gaskiya ne Matsalar abu ne mai wahala ya kyale ta wata kila zai iya cewa zai dauki matakin shari'a ka ga kenan Zahra ce a cikin matsala da kuma Dr Hamid” “Don't make the same mistake twice, idan wacan karon tsoron rasa rayuwar mijinki ne ya saka kika canja results yanxu kuma son kudi ko kuma rufawa abokin aikinki asiri? Taya zaki ci amanar mutumen da yarda dake ya baki amana? Ki bashi results dinshi ya karanta ya san halin da yake ciki ki maida ma matarshi da Dr Hamid din kudinsu” “Zahra fa...” “Let him face her... Let him know the truth...Zahra bata da laifi nema suka yi ita kuma tana neman mafita shiyawa ta siyar, idan duk abun da na tara a duniyar nan zai kare kowa ya tsane ni ba zan bari wani ya nunawa Zahra yatsa a gaban goshinta balle ya ce zai hukunta ta” “Idan su ba su yi ba baka tunanin mahaifan Deen za su iya ce za su hukuntata?” “A nan zan nuna musu inda talauci ya banbanta da arziki, na saka a daure uwar da uban akan laifin da ďansu ya aikata domin da saninsu ya aikata trust me Dr this time around I'm joke about her idan har zan iya yarda na rasa raina to zan iya yardar na rasa Zahra a karo na biyu Zahra is innocent put this in your mind” Ya juya ya fara tafiya ta rike shi domin ta lura ba da wasa yake furta kowane harafi ba. “Abiey karka ayi abun da zai daga hankali Ammy karka kuma ka aikata abun da zai bata tsakaninka da Mai Martaba ka manta gargadi da yayi maka ne?” Dawowa yayi ya kalleta. “Idan har uwa tana son ďanta cilas ne ta so abun da yake so, kuma abun da yake saka shi a farinciki, apart from Mai Martaba kuma he's no longer my father...” Ba shiri ta saki rigarshi baki sake tana mishi wani irin kallo na na tsananin mamaki, a gurin ya barta tsaye da mamaki ya fice daga dakin, a falon ma kamar guguwa haka ya fita yaran na mashi sai da safe be kula su ba, yana ya ari kafa haka yake tafiya har ya fice daga cikin gidan gaba daya ya nufi inda ya faka motar Ammy ya bude ya shiga yayi mata key kamar wanda baya son ranshi haka yayi reverse yana dukan sitiyarin motar. “Why Zahra Why.......” Ya furta da karfi kamar ya cire makogaronshi tsabar daga murya yana yamutsa gashi dake kanshi. “Be cancanci kan akaifarki ba Zahra akan me zaki salwantar da rai?” Ya runtse ido ya bude yana jin karin wata tsanar ta Deen, ga kuma tausayin Zahra a gefe da ya lullube shi. “Allah Baiwar Allah, Allah kadai ya san irin hawayen da kika zubar a kan wannan abun how i wish kina kusa da ni Zahra you need a hug” Wayarshi ya ciro ya kira Sauban few ringing Sauban yayi picking murya kasa kasa domin ranshi ya bace da abun da Abiey yayi mashi a dazun. “Hello” “Sauban kana ina?” “Gida” “Ka tafi gurin Zahra yanzu meet her face to face talk to her in a code way tell her ka san abun da take boyewa and if tana son mafita kuma tana son sirrin nan ya cigaba da rufawa ta amince da wani abu daya da zaka roka a gurinta, idan ta tambaye minene ka ce fada mata cewar ta amince da zance aurenka” “What...!” Sauban dake zaune Nuratu na kwance a cinyarshi ya daga ta jikinshi da sauri. “Ka san abun da kake fada kuwa” “Na sani just go wannan lokacin ne ya kamata mu aiwatar da komai” “She even warning me kar na sake zuwa gidan fa” “Duk yadda zaka yi ka shiga cikin gidan ka sani ba Sauban, saboda matarka tana da alaka da matar gidan that's why na samu kwarin guiwa abun da kake yi, na san ko da za a hana kowa shiga cikin gidan ba za a hana ka” “Yes tana da alaka amman bata taba ganina gidan ba, kuma ita ma bata san ina zuwa ba duk zuwan da nake ban taba yarda mun hadu da ita ba, mijinta ma sai jiya muka hadu i thought ko zai tuna ni ya gane fuska ta saboda mun taba haduwa amman be yi ba, i don't know ko da gangan ya aikata haka oho” “Please kar ma ka kirata ta hana ka zuwa just go meet her face to face ka fada mata abun da na fada maka yanzu” “And wane irin secret ne? Ban san komai akai ba” “Just go zamu yi magana daga baya” “Okay” Sauban ya amsa sannan ya mike tsaye da mamaki, Nuratu ta kalleshi ta kira shi da sunan da ta suka saba kiran juna. “Pyar (Love in indian language) lafiya?” Ya kalleta a gaba daya ya manta da a gabanta ya amsar wayar Abiey ma sai lokacin. “Ba komai wani business ne da muke wata yar matsala ta taso bari naje na dawo” “Na raka ka?” “No zauna abin ki i will back soon” Ya sumbance ta sannan ya dauki makullin motarshi ya fice, ta tunani kala kala ya isa unguwar, tunanin yadda zai shiga cikin gidan har ya samu Zahra ta kula shi da kuma tunanin maganar da zai fada mata domin ya lura akwai wani abu a kasa da Abiey be fada mashi ba and ya yanke shawarar da zarar ya bar gidan gurin Zahra zai tafi gurin Abiey ya ji ko ma minene, horn yayi masu aikin kula da gidan suka bude mashi after sun leka sun ta tabbatar da shi din ne, suna recognized fuskarshi na saboda zuwan da yake gurin Zahra shi ma ta dalilinta ya dan saba da su har yake musu yar kyauta time to time, domin be taba zuwa gidan ba sai a wannan lokacin da zama ya dawo da Zahra a gidan duk da kasancewar matarshi tana da alaka da matar gidan, sai dai ita ma kanta matar ta shi ba yawan zuwa take ba domin daga lokacin da aka yi aurensu zuwa yau zuwanta gidan sau biyu ne kawai daga time din da Hajiya Jamila ta yi rashin lafiya ta zo dubiya sai kuma haihuwar da ta yi, a ranar sunan yaron ma bata samu zuwa ba domin ita ma tana ta fama da nata laulayin, Sauban ma be taba sanin suna da alaka ba sai after an daura musu aure. A inda ya saba aje motarshi ya faka ya kira daya daga cikin ma'aikatan gidan ya aika a kira mashi Zahra, sai ga mutumen ya dawo ya sanar mashi Zahra bata nan. “Amman dan Allah bata nan da gaske ko kuma dai tace maka haka?” “Toh gaskiya na ganta domin ita ta amsa min da na yi sallama tana zaune waje ma tace ace bata nan” “Okay na gode” Ya fada sannan ya bude gurin da yake ajiyar kudi ya tsakuro wani abun ya mika mashi. “Ga wannan ko” “Na gode sosai Allah ya kara rufa asiri” “Ameen” Bayan mutumen ya wuce ya dauko wayarshi ya kira number Zahra tana fara ringing aka yanke kiran, ya sake gwada kiran sai ya ji wayar a kashe. Kallon hanyar BQ din yayi yana ta tunanin abun yi, can kuma ya sake kiran Mutumen dazun ya sake aika shi gurinta wai yace mata ta fito magana ce mai muhimmanci, kamar dai mutumen ya dawo mashi da amsar bata nan. “Okay thanks” Ya bude motar ya fita da kanshi ya nufi BQ din, nesa da kofar ya tsaya yana ta doka sallama ana ki amsa mashi sai can Mama ta amsa mashi ta fito sanye da Hijab dinta. “Sauban ne” Ya risina da sauri ya gaishe ta. “Eh nine Mama barka da dare” “Ya gida ya iyali?” “Lafiya Kalau Mama Zahra fa?” “Zahra tana bachi” “Mama da an taimaka min a tashe ta akwai maganar da nake son na fada mata ne mai muhimmanci” “Da dai ka yi hakuri, kanta ya wuni yana ciwo yau daker ma bachi ya dauke ta” Ba ya son yayi ta magiya sai ya mike tsaye yayi mata sallama ya fice shi dai ya san Zahra bata bukatar ganinshi ne kawai idan ba haka ba ko sallah Isha'i ba'ayi ba Mama ta ce mashi Zahra ta yi bachi. Motarshi ya shiga ya juya zuwa main house din domin akwai yar tafiya tsakanin BQ da kuma babban gidan, a harabar gidan ya faka ya bude motarshi ya fito ya doshi kofar dake rufe ya kwankwasa. Ba a jimawa Ummiter ta bude mashi kofar “Sannu” “Yauwa Sannu” “Hajiya Jamila na ciki?” “Eh tana ciki” “Ki ce mijin kanwarta ne Nuratu” “Okay Bismillah” Ta bude mishi kofar da kyau, daman tana ganinshi ta ji kamar ta taba ganin fuskarshi sai a yanzu ta gane waye shi domin taje bikin auren kuma ta ga calender auren a hannun matar yayanta. Cikin falon ya shiga ya zauna ita kuma ta nufi upstairs domin kiran Hajiya Jamila, an dauki dogon lokaci kamin Hajiya Jamila ta sauko a lokacin Ummiter har ta manta da taje kiranta daman can haka take indai kai kake nemanta ko nema a gurinta sai na sha rana zata kulaka, balle ma dai yau da take a firgice firgicin da ya kasa boyuwa a idanuwanta da fuskarta. Ta zauna a dayar kujerar rumgume da ďanta suka gaisa da Sauban sannan ya gabatar mata da abun da ke tafe da shi. “Daman ina son na yi magana da Zahra ne, so bana son na yi kai tsaye ne shiyasa na shigo nan idan da hali ina son a sallamo min ita” Kallon mamaki Hajiya Jamila take mashi Ummiter kam ta dade tana satar kallon matar yayanta daman tun da ta dawo daga gurin aiki a yau ta lura gaba daya Jamila bata cikin hayyacinta. “Zahra? Wace Zahra?” Hajiya Jamila ta tambaya kamar bata san wace Zahra yake magana akai ba. “Zahra dai da suke zaune a BQ” “Daman ka santa ne? Ko kuna da alaka?” “Aa na san ta dai, akwai wanda ya aiko ni a gurinta ne” “Wani waye wannan?” Sauban yayi shiru kamar ba zai amsa ba. “Sirri ne maganar da zan yi da ita bata wuce minti uku ba zan tafi” Hajiya Jamila ta hade yawun tashin hankali ta juya dama da hagu ta ce. “Babu wanda zan iya aikawa ya kira maka ita a yanzu gaskiya, kuma ba ni da number wayarta” Sauban ya kalli Ummiter da ta yi kamar kallon Plasma take da gaske ya kirata. “Hey Sis” Ta juyo tana wani yauki irin wanda ta saba. “Ummiter by name” “Okay Ummiter zo ki ji please” Ta taso ta zo kusa da shi ta tsaya daman tana neman yadda zata kara kusanci da su ta ci abun da suke tattaunawa. “Please BQ za ki je ki taimaka ki yi min sallama da Zahra amman ki ce Hajiya Jamila take nemanta” Hajiya Jamila kamar ta bude baki tace karki ce haka Ummiter sai kuma Allah ya rike mata baki ta kasa cewa komai har Ummiter ta fice daga falon. Ummiter na shigowa tare da Zahra cikin Hajiya Jamila ya duri ruwa a zatonta wani abun zai faru, ganin Sauban ya mike tsaye ya kara daga mata hankali. “Zahra ni nake sallama dake zamu iya zuwa waje mu yi magana” Zahra ta daga idonta da yayi jajir kamar an zuba mata ruwan barkono a ciki ta kalli Sauban sannan ta kalli Hajiya Jamila, sai ta juya ba tare da tace komai ba Sauban ya bi bayanta suka fice daga falon. Gurin da Sauban ya faka motarshi ta tsaya, Sauban ya kura mata ido yana kallon yadda fuskarta ta kumbura da alama ta ci kuka da ya fi karfinta. “Zahra are you Okay?” Sai kawai ta fashe da wani irin kuka ta bi jikin motar ta sulala kasa ta duke tana ra rusa kuka kamar ranta zai fita, gaba daya sai jikin Sauban yayi sanyi shi ma risinawa yayi a gurin yana kallonta sautin kukanta na taba mashi zuciya, wayarshi ce ta yi ringing mikewa yayi tsaye ya matsa can gefe inda ba zata ji shi ba ya amsa kiran Abiey. “Ka yi magana da ita?” Shi ne abun da Abiey ya fara tambaya. “No ba zan iya magana da ita a yanzu ba?” “Kuka take yi she's crying so hard” “Karka da mu ka yi magana da ita kawai” “No Abiey ba zan yi haka, what if abun da zan fada mata zai kara daga mata hankali ne? Tana cikin damuwa ba zan fada mata haka a yanzu ba i can't kai baka da tausayi ne, taya zan fada maka kuka take ka ce na yi mata magana a haka” Sauban ya yanke wayar a take cikin fusata da halin Abiey yana kallon Zahra dake can duke tana ta rusar kuka har lokacin. Abiey ya dauke wayar a kunnenshi yana kallon screen din wayar. “How dare you Sauban you end my called, ka fini sanin MATATA ne!” Abiey ya daga kafarshi ta dama ya buga a kasa da mugun karfi, zuciyar na suya tana tafasa tana kuna a lokaci daya. _________________ Ni kam na ce ikon Allah sai kallo 🤔 Anya bilu ba zata ja bau ba kuwa? Su waye team Abiey ni dai har gobe ina team Deen 😍 [11/15, 9:53 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣9️⃣ Abiey na fita Dr Zainab ta dauki wayarta ta kira mijinta kamin ya daga kiran kafarta ta gama zagaye dakin jikinta har rawa yake. “Assalamu Alaikum Madam” “Ranka ya dade kana kusa?” “Lafiya?” “Ba lafiya ba, wani aikin ne ya taso na gaggawa ina son idan kana kusa ka raka ni mu tafi tare idan kuma baka kusa ina son ka yi min izini na tafi?” “Ina? Wane irin abu ne haka?” “Ba zan iya maka bayani a waya ba, bana son a kwana ban aiwatar da abun nan ba, domin ba ni tabbaci zan kai safe na san rai a hannun Allah yake amman wannan case na san za a iya aikata komai domin ganin maganar ta rufe” “Gani nan zuwa yanzu, idan kin san you're not safe ki bari na kira police, and ki rufe gidan nan kar yarana su fita ko'ina” “Okay amman karka fadawa police komai ka dawo da yanxu please” “On my way” Ta sauke wayar, sannan ta kira Ammy ta nufi karshen gadonta ta zauna, Ammy ta amsa wayar da sallama. “Wa'alaikissalam Ammy barka da dare” “Barka dai Dr ya yaranki?” “Alhamdulillah Ammy ke kadai kike?” “Kullum a gidana ni kadai nake ai, sai dai idan na yi baki miya faru?” “Wani abun na ke son na tambaye ki amman ban san yadda zaki ji kuma ban san ta yadda zaki fahimci abun ba” “Miya faru Zainab? Fada min mana” Dr Zainab ta yi jimmm na dan lokaci sannan ta numfasa ta ce. “Abiey ne yanzu ya fita daga gidan nan, ina mashi magana akan Mai Martaba sai yake ce min Mai Martaba is no longer his father abun ya ba ni mamaki kuma ya ba ni tsoro ta ina Abiey ya samu wannan magana haka? Ko dai sherin su Hajiya Kilishi ne ko kuma tsanar da Mai Martaba yayi mashi ne yake ganin kamar ba Mai Martaba ya haife shi ba?” Ammy dake zaune rike da plate din apple ta mike tsaye da sauri plate din dake cinyarta ya fadi kasa. “Waya fada mashi wannan magana?” “Ban sani ba ban kuma san dalilinshi na yin wannan tunanin ba” “Ina yake?” “Ya fita ina zaton gida zai zo” Ammy ya sake wayar daga kunnenta ta katse kiran da sauri ta kira line Abiey, da farko line busy ta ji wayar daga baya kuma ta sake kira aka sanar mata mai number yana kan amsa wani kiran ta jira, ta katse ta sake gwada kiran be amsa ba sai a karo na hudu. “Hello” “Aliyu kana ina?” “Ina compound” “Shigo yanzu cikin ďakin na ka same ni” “Toh” Kamin ya hau sama ya shigo dakinta har ta matsu, ita da kanta ta sauko kasa sai kuka hadu a falo, tsayawa yayi yana kallonta. Ammy da hawaye suka cika idonta har suke zuba ta tambaye shi. “Why did you learn this?” “What?” “Cewar ba Mai Martaba ne mahaifinka ba? Waya fada maka haka? Zahra?” “Zahra bata fada min komai ba, ban tambaye ta komai ba kawai na bi ta salo ne da hikima na gane komai” Ammy ta dafa shi ta shafa kanshi tana kuka sosai kamar ba ita ba. “Na rantse da sarki Allah kai ďan Mai Martaba ne jininsa ne kai, amman babu yadda zan iya wanke kaina domin na riga na dabawa kaina wuka, amman ka yarda da ni uwa da uba ne suka kawo ka duniya, dan halak ne kai ďan sunna” Ta sake shi ta juya mishi baya tana kuka sosai. “Toh mi ya saka Mai Martaba ya tsane ni? Me kike boyewa?” “A yanzu ka fallasa yar'uwarka ma da bata san komai ba ka fada mata a yanzu, sauran duniya ta ji amman ina fatar kamin lokacin ajalina ya riske ni ta yadda zan samu na manta da komai kuma yaya ba za su kyalle ni su ji kyamar ganina ba” Cikin kuka ta karashe maganar, Abiey ya taka ya shiga gabanta. “Me mika aikata Ammy?” Ta nuna kanta. “Taya mahaifiya zata iya bawa ďanta labarin abun da ta aikata Aliyu? Taya kake tsammanin zan baka iya baka labarin abun da na san ba zai taba iya fita daga kwakwalwarka ba? Abun da zaka dade kana kallona da shi?” “Idan baki fada min ba? Waye zai fada min? Mai Martaba da kanshi? Ko kuma Zahra? Ko kuma so kike na yi ta zama cikin kwankwaso da tunani kala kala? Idan kuma na yi zato ki ce ba haka abun yake ba? Babu dalili da zai saka Mai Martaba ya tsane ni tsana irin wannan idan har ni ďanshi ne, idan kuma da hanyar halak kika same ni Ammy duk wani abu da zai biyo baya mai sauki ne, kaddara ma da ba hanyar halak kika same ni ba ina da wani abun da zan yi ne? Zan iya canja abun da ya riga da ya faru ne? Haka kuma ba zai saka na tsane ki ba ko kuma na juya miki baya domin ke uwata ce kin dauki cikina tun ban san da zan zo duniya ba har kika haifo ni, Ammy har na girma ban san wani abu gatan mahaifi ba na ki na sani, to akan me zan tsane ki ko da kuwa ta hanyar banza kika same ni?” Ammy ta kalleshi da duba irin na uwa mai alfahari da samun ďa mai tunani da tarbiya irin nata, rikata yayi ya zauna a kujerar dake kusa da su. “Ba zan cilasta ki ko fada min ba, amman ba zan taba samun salama ba har sai na san komai, domin kin raba min tunani gida biyu ne a yanzu” Ya saka hannunshi ya share mata hawayenta. “Ko na kasa da ni ba zan bari ya zubar da hawayen bakinciki saboda ni ba, balle kuma mahaifiyata dan Allah ki yi hakuri ki daina kuka Ammy” Ya mike tsaye ya nufi kitchen ta dauko ruwan da cup ya dawo kusa da ita ya zauna ta zuba mata ruwan ya mike mata ta karbar ta sha sannan ta share ragowar hawayen dake zubo mata, ya karbi cup din ya aje bayan ta sha ruwa sannan ya mike tsaye rike da ita suka haura sama har dakinta ya shiga da ita ta zauna saman gado shi kuma ya duka ya dauki plate din apple din da ya fadi dazun ya fara tattara apple din. “A wani kokaci can baya, na yi soyayya da mahaifinka soyayya sosai kamar ba za a rabu ba, sai dai Allah be kaddara aure a tsakaninmu ba, kasancewar al'adar masarautarsu ďan sarauta ko yar sarauta ba sa zabar abokan zama, sai dai a hada dan wannan masarautar da wacan ko kuma ďan cikin masarautar, amman ba sa yarda a auro musu bare na hadu da Mahaifinka a gidanmu domin kakanta da mahaifina abokan juna ne, ta wannan hanyar muka san juna har muka kulla soyayya, ya sani a dokar masarautar ba a auren bare a wacan lokacin ni ma kuma na sani kowa ma ya sani amman a haka muka cigaba da son junanmu, kwatsan wata rana sai mahaifina ya shigo gida ya sanar da Umma ma yace ta sanar min cewar ya ba da ni ga abokinshi, mahaifinka kuma aka yi mashi mata a masarautar wato Hajiya Kilishi yar Sarki Rano a wacan lokacin” Ammy ta saka hannu ta share hawayenta, Abiey kuma ya dago ya kalleta bayan ya gama tattara apple din. “A wacan lokacin mu yaran da, muma da tsananin biyayya ga iyaye, ba ko wace budurwa ake bawa damar zabar miji ba sai dai iyaye su duba wanda ya dace su aura maka, mu kuma biyayya da kawaici ba zai iya bari mu tsabawa iyayenmu ba, ko da baka son mutum idan iyaye suka zaba maka shi zaka amsa ne kawai ka yi na'am, to haka ce ta faru da ni ban iya musawa mahaifina ba har aka daura aurena da abokinshi, ba zan iya kiran mahaifinsu Zainab da tsoho ba kuma ba zan ce da shi yaro ba, iyakar abun da na sani shi din abokin mahaifina ne sosai ni kuma ni ce ta biyu a gurin mahaifina, a wacan lokacin ana mana aure ne da kananan shekaru ba kamar yanzu ba, na yi sa'ar aure duk da kasancewar bana son shi amman Alhaji Falalu Na'ala mutum ne mai matukar adalci da tsanin ya kamata da mutunci, ya rike ni amana ba zan iya tuna wata rana da ya bakanta min ko kuma ya musguna min, sai kuma na yi sa'a da abokiyar zama ta gari mai saka ni a hanyar kwarai, mahaifiyar Yasmin ta rike ni kamar kanwarta bata taba nuna min tsana ba, bata taba nuna min cewar ni kishiyarta ce ba, sai dai ta kira ni da kanwarta duk wani zuga da taegumi bata dauka ba, muka zauna a gidanshi kamar yaya da kanwarta, Alhaji Na'ala babban mutum ne mai arzikin da abu ne mai wahala ka lissafa mutun biyar a masu kudin kudin arewa baka saka da shi ba a wacan lokaci, na zauna a gidan babu tashin hankali babu tsoron komai sai gata da girmamawa ya rike ni amana kamar yadda yayi wa mahaifina alkawari, mahaifinka kuma ya zauna da matarshi Hajiya Kilishi be dade ba ya auro Mama Lami wanda ita ma yar sarautar ce a lokacin ne mahaifinshi ya kwanta dama sai a ba shi sarautar garin Kano, aka nada shi a matsayin sabon Sarkin Kano, lokacin da na haifi ďana na farko Auwal yana yaya hudu a lokaci domin sai da na shekara biyu sannan na haihu shi kuma matanshi biyu kuma suna haihuwa kamar suna gasar juna, na yi na biyu mahaifin Zainab ya saka mishi sunan mahaifinsa waton Muhammad Sani, daga lokacin haihuwar sai ta dauke mana ni da Momy abokiyar zamana, daman na tararda ita da yaranta biyu a lokaci, ita ma yarinyace kamar ni domin ba ita ce matarshi ta farko ba ,sai dai ta zama kamar ita ce uwargida kasancewar matar da ya aura da fari ta rasu ta bar mashi yara uku duk maza” Ammy ta daga kai ta kalli air-condition dake ďakinta. “Ita dai bata sake haihuwa ba, ni kuma na sake samun cikin Zainab a haifeta lafiya kalau tana da shekara uku mahaifinta ya rasu ya bar mu da yara, bayan na cika idda mutane suka ta aikowa suna sona wasu kuma suna nunawa da yawan wasu na san suna kallon dukiyar da mijina ya mutu ya bar mana ne ni da yarana wanda na tabbatar ba zamu taba iya cinyata mu kadai ba duk da kasancewar an raba gado an bawa kowa na shi, a cikin mutanen da suka ta so neman aurena har da mahaifinka ba wani wata wata ba na amince aka daura mana aure ba wata da wata matsala ba sai dai na shiga gidan cikin rashin sa'a saboda yan'uwanshi ko kadan basa so na, saboda ni ba yar sarauta ba ce kuma suna ganin be kamata ace yana matsayin Sarki ya auro mazawara mai yaya uku ba, Mahaifiyar Yasmin bata bar ni na tafi da Auwal da Muhammad Sani ba, sai ta kama su ta rike daman ba ni da haufi na san ba zata cutar da yayana ba, sai na tafi da Zainab kadai, aiko sai Mai Martaba yace wa yake son a cikin yaya ba ita ba, kaunar da yake nunawa Zainab be taba nunawa yayanshi ba, na rayu a cikin wata soyayya da mulki Mai Kulki Martaba ba baya shawara da kowa sai ni, har mantawa yake yana da wasu matan komai dai Umaima zamanshi Umaima tashinshi Umaima, komai aka kawo sai yace a kawo gurina, idan na ce abu baya tsallaka ba hakan yasa kowa yake zargin wani magani na yi mashi, alhalin ban taba zuwa gurin kowa na roki ya ba ni magani da zai kara kaunata a zuciyar shi ba, mu yi zama na rashin dadi tsakanina da matanshi mun yi ta samun tsabani, suna magani kala kala ni kuma bana yin komai sai dai na san abu daya, bana wasa da addu'a kuma a lokacin da mahaifinta tana raye ta rubuta min Bismillah dubu na sha, sai dai bakina yana min yaki sosai domin idan aka min abun da ban gamsu ba ko ban jidadinshi ba a take nake fara masifa kuma idan ya zo ni zai shigarwa ko da kuwa ba ni da gaskiya har muka kai wani matsayi da Mai Martaba baya iya kwantanta adalci a tsakanina da sauran matanshi, kamin ya aureni yayi alkawarin cewar ba zai taba yarda a sakawa ďanshi ko yarshi sunan iyayenshi ba, amman ni shi da kanshi ya fada min cewar idan na haifi namiji sunan mahaifinsa sai saka mashi wato Aliyu idan kuma mace na haifa sunan mahaifiyarshi zai saka Khadija, idan kuma na haifa mace da namiji duka zai saka sunan iyayenshi, ai kuwa sai yan'uwanshi suka ce ba su da makiyiya abar tsana sai ni, duk kuwa da irin kyautata musu da nake da kuma nake sakawa yayi musu, sai dai akwai wani kanenshi Margayi Surajo wanda Waziri ne a wacan lokacin kamin ya rasu ubansu daya da Mai Martaba shi kam yana so na sosai ba kamar sauran ba, da tsanar ta yi yawa sai Mai Martaba ya kamin min gida dabam” Ammy ta ja dogon numfashi ta sauke tare da tashi tsaye da sauri ta shige bathroom tana hawaye, sakamakon shigowar yaran Dr Zainab, Abiey ya tashi tsaye yana musu murmushi yaja su suka fice daga ďakin rike yana musu wasa dayan hannunshi rike da da plate din apple da ya kwashe. ZAINAB POV. Ba a dauko dogon lokaci ba Mijinta ya shigo, a tsanake ta yi mashi bayanin komai sannan ta kora mashi da abun da take ganin shi ne mafita a gareta a yanzu. “Ina son na hadu da shi na bashi nono results din ya san gaskiyar komai, bana son ya kai gobe domin ba mu san abin da zai iya faruwa ba, wacan karon ma saken da na yi na ya haifar da matsala har Deen ya samu damar da ya samu” Engr yayi shiru na dan lokaci yana nazari. “Amman kina ganin zaki samu ganinshi a yanzu?” “Zan fara kiranshi” “Kira shi to, ki fada mashi za ku hadu wani guri safe da ba gidanshi ba” Yana rufe baki Dr ta dauki wayarta ta kira Mr Bashir be daga ba, sai ta yanke shawarar tura mashi sakon kar ta kwana. “Salam, ina son hadu wani guri da ba gidanka ba ina son na baka results din da ka bukata a yau din nan, kuma akwai magana mai muhimmanci da nake son mu tattauna” Tana tura sakon ta dauke hannunta sai ga kiranshi ya shigo, jiki na rawa ta yi picking. “Hello ranka ya dade” “Dr kina lafiya?” “Alhamdulillah ka karanta sakona” “Shiyasa na kira ki ai, zaki iya zuwa ki same ni a Mr Bashir Auta Estate?” “Eh ranka ya dade amman zan zo tare da mijina” “Ba matsala i will text the house number” “Okay” Ta kalli mijinta bayana ta kashe kiran. “Yace mu same shi a Auta Estate” “Tashi ki saka mayafinki i will drop the kids gidan Ammy zai mu je mu ganshi domin a can zasu fi samun tsaro idan mu ka bar su nan ba su musan me zai faru ba” Tashi ta yi ta dauki mayafinta ta saka da jakarta da results din yake ciki, mijinta kuma ya saka yaranshi a mota duk da kasancewar akwai mai gadi amman hankalinshi be natsu da shi ba domin ba manta yadda aka taba shigowa cikin gidan aka tafi da shi ba. Sai da suka fara sauke yaran gidan Ammy suka tabbatar sun shiga cikin falon sannan suka juya ba tare da su sun shiga ba, suka dauke hanyar Estate din Mr Bashir wasu manyan gidane ne da ya gina na alfamar yake badawa haya ga wandanda suka ci suka koshi, domin Estate ne ba babu ta biyunta a garin Kano, komai na bukatar rayuwa a saka a unguwar babu abun da za su fito su nema sai dan ra'ayi ba dai da rashi ba, tun daga gurin hutawa har shopping da makaranta da police station da private hospital. Suna tafe suna hirar abin da da yadda suka kallon lamari har suka isa gaban wani wangalelen gida da number shi take rubuce a jikin screen din wayarta da Mr Bashir ya turo mata da kanshi. Sai da ta kira shi ta sanar mashi suna waje ya aiko manyan bodyguards din da zaka iya rantsewa da Allah naman mutan suke ci tsabar girma da karfi fukarsu babu annuri, suka shiga da su ciki su kansu sai da suka tsorata, ko'ina na gidan cameras din tsaro ne ga kuma police daga ciki suna gadin gidan, Dr ta san da unguwar amman bata taba sanin yana da gidan da yake zama a ciki ba sai yau. Hankalinta be kwanta ba har sai da suka shiga cikin gidan ta yi arba da shi ya tarbe su da far'ah sannan ta samu natsuwa har ta zauna suka soma gaisawa, Engr ma hannu ya mika mashi suka gaisa sannan ya samu guri ya zauna kusa da matarshi. “Dr Allah yasa results din ne?” “Ranka ya dade results din ne, amman kamin na baka akwai abun da nake son na fada maka, kuma akwai rokon da nake son na yi maka, ina fatar zaka saurare ni kuma zaka duba abun da zan fada ko na gabatar da idon basira” Mr Bashir ya kalli Engr duba na natsaki sannan ya kalli Dr Zainab ya gyara zama. “Ina saurarenki” Dr Zainab ta sauke ajiyar zuciya ta kalli mijinta sannan ta fara magana cikin natsuwa. [11/16, 4:39 PM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣0️⃣ “Na san ba hurumi na ba ne shiga cikin rayuwarka ko yin magana akan wani abu da ya shafi iyalinka, sai dai a matsayina na wanda ka yardar da ni kuma a matsayina na musulma ina da hakki na lurar da kai ga wani abu da be zama lallai idonka ya kai can ba, bana son ka ce na maka katsalandan a al'amurra...” Bata karasa ba ya daga mata hannu. “Dr... Zainab ina tunanin kin san da cewa akwai likitocin da suka fiki gwarewa a aiki, kuma akwai likitoci da yawa a kasar nan har wajen kasar nan, amman yarda da ke da abokina da wanda ya hada ni dake yayi ya sa na aminta da ke na dauki ragamar aikin nan na danka a hannunki, ina fatar ba wata matsalar kika samu ba, and you can go ahead kai tsaye ba sai kin tsaya rabe rabe ba, kuma idan da dama mijinki ya ba mu guri a iya sanina dokar aikinku sirrin majinyaci da likita sirri ne” “Haka ne, amman na shigo da shi ne saboda na yardar da shi kuma shi ma yana daga cikin wani bangare na labarin da zan baka, kuma ina son ka aminta da ni ne ka san da cewa bayan shi da kanena babu wanda ya san da wannan labarin, kuma babu wanda zai taba sani ko da za a dora min wuka a wuyana” Dr Zainab ta fada sannan ta saka hannunta cikin ta dauko results din ta rike. “Bana son ka dauki abun da zafi ne, Dr Hamid ya same ni gida ya ba ni tukicin kudi naira miliyan hansi akan na canja results din dake cikin takardun nan, amman ban aminta da yin haka ba domin ba zan iya lalata aikina ba kuma ba zan iya cin amanarka ba, amman ina son zan roki alfarma karka yanke hukunci a cikin fushi ka tsaya ka yi nazari kuma ka yi adalci karka dubi cewar wannan matar ka ce wannan kuma baka da alaka da ita” Ta mike mashi results din sai ya mika hannu ya karba zuciyarshi na bugawa da mugun karfi bugawar da ya wuce misali bugawar da zai iya haifar mashi da matsala a take, sai ya gama zagaye katon falon da ido sannan ya sauke akan takardun dake nade, ya saka dayan hannunshi ya warware ya fara dubawa, sai ga naman fuskarshi na rawa kamin ilahirin jikinshi ya karba duk sanyi dake falo sai da gumin bakinciki ya karyo mashi. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un” Ya furta yana murmushi tare da wasu hawaye masu matukar zafi, ya saka hannunshi ya rufe idonshi ya cize bakinshi yaja wani kalar numfashi mai wahalar saukewa, daga Dr Zainab har mijinta sai da tausayin Mr Bashir ya kama su. “Alhamdulillah da Allah ya nuna min haka da wuri, daman zuciyata bata natsu da Jamila ba, tun daga lokacin samun cikinta har zuwa haihuwar da ban so ta yi ta a nan ba bata yarda da kowa ba sai ďan'uwanta, Ummiter ma tana min complain amman na taka mata burki saboda na yardar da matata 100%, sai dai daga baya bayan nan na ga wasu abubuwa a camera tsaro na gidana, ta fada min cewar wata ce ta kawo Zahra sai ga shi na ga farkon shigowarta tare da Dr Hamid, sai dai ban yi tunanin matata zata iya cutar da ni ba duk wani abu na jindadin duniyar nan na mallaka mata shi na yarda na zauna da ita saboda ina tunanin ni da ita zamantakewarmu a tare jarabawa ce...” Yana magana hawaye na sauko mashi. “Wata kila ta yi haka ne saboda ta faranta maka rai, domin ita ma wanda ta siyar da ďan ta ta siyar ba dan bata son shi ba sai dai ta ceto rayuwar mijinta” “Zahra...” Ya tambaya hawayen dake sauka a idonshi sun ki tsayawa shi kuma be fasa sharewa ba, bakin cikin dake zuciyarshi ya kusa saka shu hadeye zuciya. “Ita Dr Hamid ya nuna min komai na yarjejeniyar da suka yi....” A tsanake Dr Zainab ta labarta mashi komai ciki har da bangaren da mijinta ya shigo ciki, sai yayi murmushi ya girgiza kai still hawaye na sauko mashu har lokaci be taba jin bakinciki rashin haihuwa irin yanzu ba, farinciki da ya ginu saboda ďan da yake tunanin na shi ne ya rushe a yanzu. “Na gode Likita a yanzu ma ina son ki sake taimaka ki min wani jihadi” “Kamar me ranka ya dade” Wayarshi ya dauka ya hoton results din sannan ya mikawa Dr Zainab original din. “Ki koma da results din nan, ki bawa Dr Hamid yayi abun da yake so ya baki wanda yake so sai ki kawo min, kuma ki dauki kudin da suka baki ni ma kuma zan miki wani tukicin mai tsoka” “Amman hakan ba zai haifar da matsala ba?” “Babu matsalar da zai haifa, sai dai ya taimaka min ke ma kuma ya taimake ki saboda rayuwarki zata zama kamar a cikin hadari idan baki aikata abun da suke bukata ba” Ya amsa mishi da kai, hannunshi ya kai ya dauki wani tissue ya goge hancinshi. “You can go ki kammala komai cikin lokaci, kuma ina son maganar nan ta tsaya iya tsakanina da ke” Nan ma kan ta daga mashi, sannan suka tashi suka mishi sallama ita da mijinta suka fice, after fitarsu ya mike tsaye yana jin kamar zaman kujerar ba ya mashi dadi, zagayawa ya fara yi a cikin falon yana sauke ajiyar zuciya daker wani irin daci yake ji a cikin ranshi dacin da ya bayyana dannano har a halshen bakinshi, a takw ya ji kamar fever na neman kai shi kasa gurin windows din falon ya nufa ya zanye curtains din yana kallon waje. Tunanin matan da ya rabu da su yake saboda farinciki Matarshi, yar'uwarshi ma Imaan wanda yaya ce a gurin Ummiter ya bar gidanshi saboda Jamila, runtse ido yayi yana jin yadda duniya da abunda ke cikinta yake juya mashi a kai. A iya kar tunaninshi da hangenshi be hango wani good reason da zai saka Jamila ta yi mashi haka ba, duk da juriya irin nashi sai da ya zauna saman kujerar yayi ta kuka kamar wanda aka yi ma mutuwa. “Allah ka ba ni komai kuma na gode maka da haka, Allah ka ba ni jarabawa guda biyu ta arziki wanda zaka tambaye ni a ina na samo kuma ta ya na kashe ta, sannan Allah ka yi jarabawa mafi girma ta rashin ďa ko ya, ya Allah ya dube ni da Rahma lallai kai mai yawan rahama ne mai jinkai, ya Allah ka saukar min da ijaba ya Allah, Ya Ubangijina karka karbi rayuwata har sai na ga sanyi idanuwana, ya Allah ka ba ďa ko ya ta ta tsabbaciyar hanya, idan kuma ba ni da wannan robon na samu haihuwa a duniya ya Allah ka saka min juriya da hakuri da dangana a zuciyata domin ka fini sanin abun da zai zama alheri a gareni kuma ka fini tausayin kaina tabbas kai gwani ne kuma kai fi kowa sanin abun da ya dace da ba yinshi” Ya shafa addu'a tare da ruwan hawayen dake saukar mashi, can kuma ya girgiza kai. “Rashin ďa bala'i ne tsarki ya tabbatar maka ya Allah” Ya saka tafukan hannayenshi biyu ya rufe fuskarshi yana kuka irin kukan da bakinciki baya bari sautinshi ya fita. *** *** *** A mota suka yi ta tattauna maganar ita da mijinta kamin su isa gidan Ammy domin daukar yaransu, duk tsawon lokaci da suka dauka a gidan Mr Bashir Ammy na bandakin tana rutsar kuka abun da ta aikata ya dawo mata sabo fil tana ganin kamar ta aikata shi ne a gaban yayanta. Jin shiru yayi yawa ya saka Abiey ya hauro sama ya shigo dakin sai ya samu bata ciki sai dai ya ji motsin ruwa a bandaki, zuwa yayi ya tsaya bakin kofar bathroom yana ta jiran firowarta, shiru bata fito ba ga motsin ruwa yana ji hakan ya saka shi kiran sunanta. “Ammy....” Sai ta kasa amsa mashi tana kokarin tsayar da kukanta hawayen kuma suka ki bata hadin kai, tura kofar yayi ya shiga ciki a hankali tana jin motsin shigowarshi sai ta tara hannunta tana ta watsawa fuskarta ruwa babu kakkautawa, karasawa Abiey yayi kusa da ita ya rumgume mahaifiyarshi ta baya kukanta na taba zuciyarshi. “Ammy are you still crying? Haba Ammy ke fa mahaifiyata ina kaunarki no matter what you did, no matter how bad you're daukar cikina kawai da kika yi zuwa haihuwata hakki ne balle kuma na girma a tare da ke na rayu da ke har yanzu i love you so much Ammy” Hawaye ne suka zubo mashi har cikin kahon zuciyarshi yake jin kaunar mahaifiyarshi irin kaunar da yake da tabbacin Ammy bata da ta biyu a gurinshi ko da kuwa ace ta kashe kowa dake duniyar nan ta aikata duk wani abu da zai saka ta zama bad mother, da ace Ammy ta haife shi ta hanyar da bata aure ba hakan zai yi effecting dinshi ya saka shi damuwa amnan ba zai saka ya tsana ta ba ko ya juya mata baya because he know what MOTHER means. Ammy ta juyo ta rika fuskarshi tana kallonshi “Allah ya maka albarka Aliyu ya baka yayan da za su maka biyayya kamar yadda kake yi min” “Ameen Ammy” Ya amsa da murmushi a fuskarsa, sannan ya saketa yana kokarin Juyowa suka juyo muryar Dr Zainab ta shigo dakin Ammy, kamin Abiey ya isa bakin kofar fita bathroom din Dr ta iso ganin kofar a bude ta tsaya tana kallonsu. “Lafiya?” Abiey ya juya ya kalli Ammy sannan ya sake juyawa ya kalli yar'uwarshi. “Lafiya Kalau” Shigowa ta yi katon bathroom din mai kama da wani karamin ďaki ta nufi Ammy da sauri hankalinta a matukar tashe. “Wane irin lafiya kalau Ammy miya faru” Abiey ya juyo yana kallonta. “Dole ne sai kin san abun da ya faru tsakanin ďa da uwa?” “Is not about ďa da uwa kuka fa Ammy ta yi kalli idonta” “Akan maganar da na yi ne” “Ba laifinka ba ne laifi na ne da na fada mata, miya saka ka wannan tunanin ma tun farko?” Abiey ya dan tabe baki yana kokarin boye abun da yake nan. “Saboda na ga Mai Martaba ya tsane ni da yawa ne, i thought ko haka ne ashe na yi kuskure” “Amman Abiey zai ka zargi Ammy akan haka? Be kamata ka yi haka ba tun farko...” “Komai ya wuce Allah ya muku albarka dukanku” Ammy ta fada, sai Dr Zainab ta rumgume ta. “Ameen ya bar mana ke Ammy” Abiey yayi murmushi, sai da Ammy ta gyara sannan ta fito suka gaisa da mijin Dr Zainab, da za su tafi gida Dr da Abiey suka taka zuwa gurin gate suna tafiya tare tana labarta mashi abun da ya faru tsakaninta da Mr Bashir Mijinta kuma ya ja motar ya fita da ita waje ya jira tare da yara har sai da suka gama tattauna da dan'uwanta sannan ta shiga front seat yaja motar suka wuce. ZAHRA POV. “Zahra...” Ina jin Sauban dake duke gabana yana leken fuskata yake kirana amman na kasa amsawa balle ma na dago. “Subhanallahi Zahra kina cikin wata matsala ne ko kuma kiran da na yi miki ne ya kara saka ki cikin damuwa?” Nan ma ban amsa mishi ba ban kuma san ranar amsa mishi ba. Jinginawa yayi da motar ya zauna kusa da ni sai na dago kadan na kalleshi tausayina na gani a cikin idanuwanshi. “Zahra miya faru?” Ina shisshikar kuka na bude baki sai na kasa cewa komai. “You don't have to tell me idan kina ganin kamar be kamata na ji ba, amman bari na tambaye ki akwai wani abun da zan iya yi na taimaka miki?” Na girgiza mashi kai alamar aa. “Okay amman akwai abun da zan iya yi na tsayar da zubar hawayen nan na ki?” Nan ma na girgiza mashi kai, sai ya mikar da kafafuwanshi ya zauna da kyau ya daga kanshi sama yana kallon taurari. “Zahra wani lokaci kaddara tana zuwa ma bawa ba a yadda ya so ba, sai dai ta yadda Allah ya so, ban san miye damuwarki ba, ban san ta ina zan iya shiga rayuwarki na miki maganin matsalarki ba, amman zan roka miki Allah ya yaye miki damuwarki kuma yayi miki mafita ya tsaya miki a ko miye ke damunki and i promise you zan raya dare ina roka miki Allah ya yaye miki danuwarki” Ni ma kaina na daga ina kallon samaniya. “Wata rana kamar haka zaki hango damuwarki, ki zauna da wani kina bada labari cewar a da can na yi kaza na shiga hali kaza da kaza” “Ina fatar haka” Na furta cikin hardewar halshe, sai ya kalleni yana dariya. “Kamar ban taba ganin kina kuka ba sai yau, ashe kina kyau da kuka” Ya ciro wayarshi ya fara daukata hoto ina wani gurin ina hararar camerar wani kuma ya dauke mu tare. “Ki taimaka min ki yi murmushi ko kadan ne” Ya bukata yana kallona lips dina. “To ina kuka zan yi murmushi kuma?” “Kadan za ki yi, saboda tarihi” Haka dai ya takura ni na yi murmushin kadan na yi zaton hoto yake ashe video ne, sai jin na yi ya tintsire da dariya sosai. “Zahra idan ba ke ba, wa za a cewa yayi dariya yana cikin kuka kuma ya aminta yayi?” Murmushi na yi na rufe fuskata ina jin kunya sosai, na dade a haka sannan na dago sai na ga idonshi yana kaina fuskarshi cike da annashuwa. “Na yi farinciki da na ga murmushi a fuskarki Zahra baki san abun da na ji ba a lokacin da na ga kina kukan nan Wallahi na ji kamar ace zan iya saka hannu na cire miki damuwarki a take” Na sauke idona kasa domin wani kallo yake min na kurrilla. “Tashi tsaye” Na mike tsayen kamar yadda ya bukata shi ma ya mike tsaye yana cigaba da kallona. “Promise me ba zaki sake kuka irin na dazun ba, kin karya min zuciyata sosai, kin ba ni tsoro” Sai na ji kamar ya tuna min da dalilin kukan ne a take na sake jin wani sabon kuka na dusaso duniyata, domin na san watan kuka na ne ya tsaya, ba ni da wata mafita a yanzu domin Hajiya Jamila ta kasa fada min cewar ta bawa Dr Zainab kudi amman har yanzu bata aminta ta ba su result din ba, hakan na nufin zata bar Mijinta ya san gaskiya kenan kuma ita ma zata sani wanda hakan zai haifar min da matsala, ba ta bangaren mijinta kadai ba har ta gurin Hajiya da Baba kuma mijin Hajiya Jamila ma zai iya daure mu ni da Mama. “Zahra...” Ya kira sunana jin na yi shiru ina tunanin makomata. “Sauban ina son na shiga ciki” “Okay, amman zan iya sanin dalilin kukanki? A yanzu ma ina karantar damuwa a fuskarki” “Bada maka ba shi da amfani domin ba zaka min magani ba, kuma matsalata bata shafe ka ba, kar ma ka saka kanka a ciki da haifar maka da matsala” Ya rumgume hannayenshi. “Indai ya shafe ki ya shafe ni Zahra, amman ba zan cilasta ki fada min ba, hakan kuma ba zai hana ni aiwatar da abun da na yi miki alkawari ba zan yi ta roka miki Allah sauki har sai ya samu a rayuwarki” Na daga mishi kai ina share hawayen da suka fara min zuba. Ina kokarin ce mishi ya tafi kar Mai gidan ya sake zuwa ya tarar da shi sai kawai na ji an bude gate din gidan da gudu, ba ni tabbacin mijin Hajiya Jamila ne ko wani ni sai dai yanayin yadda suka bude motar da gudu ya nuna haka. “Ka gani ko? Mai gidan ya dawo kuma yace min kar ya sake ganina da kai gashi ina cikin wata matsala zan haifar da kaina wata, yau dai na shiga uku” Na fara kuka Sauban ya juyo yana kallona, iyakar abun da na sani ya bude baki zai yi min magana amman ban tsaya sauraren abunda ya fada ba ko zai fada na ranta a na kare kamar wata aljana haka na isa BQ da guduna ina haki, yadda na fada dakin da guma ma sai da hankalin Mama ya tashi. “Lafiya” Sai kawai na fashe da kuka. “Mai gidan ne ya dawo ya same ni da Sauban? Na shiga uku” “Sauban kuma?” “Eh ashe ba Hajiya Jamila ce take kirana ba, shi ne amman a falon Hajiya Jamila na same shi” Na fada jikinta na kara fashewa da kuka, dazun dai kukan rashin mafita da tsoron tonuwar asirina nake yanzu kuma na amsa tambayoyin mijin Hajiya Jamila nake, Mama sai aikin ba ni hakuri take can kuma ta rufe da fada wai ai ni na bashi fuska tun farko gashi nan yanzu abu yana son ya zame min matsala. “Kuma da kika je kika ga ba Hajiyar ke kiranki ba, ai sai ki dawo ki bar shi a can amman kika tsaya tuntuni har Mai gidan ya same ki...” Mama na rufe baki na karawa kuka nawa mai, haka muka kwana cikin zullumi da tunani ni da Mama, ko iska ya kada sai na ji kamar wani ne zai zo yace min min mijin Hajiya Jamila na nemana. Misalin karfe bakwai na safe Mama na shirya mana abun karyawa ni kuma ina kwance saman carpet din da na yi sallah ina tunani muka ji sallamar Ummiter da sauri na tashi na koma saman katifa na kwanta na fara bachin karya gabana sai bugawa yake jinina na yawo kamar zubar ruwa tsabar tsoro. Haka Mama ta shigo tana tashina domin ta san ba bachin gaske nake ba. “Zahra tashi ki tafi yana nemanki” Da gangan na ki motsa na yi samo kamar mai bachi gaske. “Kin san dai jinkirinki zai kara bata mashi rai ne kawai ko?” “To ni Mama me zan ce mashi?” “Ya zan yi na sani, ki tashi ki tafi kika sani ko ya yanke shawarar korarmu a gidan ma mu huta” A dole na tashi na fito daman ban ban cire hijabin da na yi sallah ba, ko da na fito na samu Ummiter sanye da uniform dinta na aiki yayi matukar yi mata kyau duk da kasancewar ta baka. Tana gaba ina biye cikina sai kuka yake na tsoro har muka shiga bangarenshi. [11/16, 8:51 PM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣1️⃣ Na kara samun kaina cikin tashin hankali a lokacin da na ga muna nutsawa cikin falon shi da ban taba shiga ba. “Ummiter” Na kira sunanta ta juyo. “Idan bachi yake karki tashe shi ki kyale shi kawai sai zuwa anjima” “Wani irin bachi kuma? Ba shi yace a kira ki ba” Na yi shiru ta dan tabe baki sannan ta juya ta cigaba da tafiyar, ni kuma a cilas na bi bayanta muka doshi falon. ‘Idan ya tsiye ni da tambaya zan ce mashi ba ni ba ce Mama ce ta fito ta yi magana da Sauban’ Na ayyana a raina ina ta nemawa kaina mafita, can kuma wata zuciyar ta raya min wata kila ba akan ganina da Sauban zai yi magana ba, wata kila ya gano gaskiyar abun da muka aikata ne, domin da maganar Sauban ne da tun a jiya yayi min magana ba sai an kwana ba, a take na ji cikina ya murda da karfi har na ji kamar zawu zai zubo min, sai da na karanta Bismillah ba adadi kamin na shiga falon gumi har ya samu hanya a jiki, ni da Ummiter kusan zan iya cewa idon mu sun yi bakin gani, domin Hajiya Jamila muka gani akan kafafuwan Mijinta tana dariya kamar wanda bata da damuwa shi ma murmushin yake kana ganin fuskarshi ka san yana cikin farinciki, da sauri ta tashi saman jikinshi ta zauna gefe. “Haba Ummiter ba ko sallama” “Ban san kina ciki ba ai, dazun da na fita Yaya kawai na bari” Ummiter ta fada sannan ta kalli mijin Hajiya Jamila tace. “Yaya ni na wuce” Kai ya daga mata alamar okay, Hajiya Jamila kuma ta bita da harara na yi mamakin karfi hali irin na Hajiya Jamila kamar wanda ta shiga tashin hankali a tsakanin shekaranjiya da jiya ba, musamman jiya da ni kaina sai da nawa hankalin ya tashi sakamakon kin karbar kudin da aka ce Dr Zainab ta yi, amman gata a yau har su dariya ko da yake wanda ya iya ya huta da ni ce da tuni na gudu na bar gidan, jiya ma na so mugu sai dai Mama bata ba ni hadin kai ba, wai a cewarta guduwa ba mafita ba ce idan ma mun gudu ina zamu je, ko da mum samu mafaka zai iya nemanmu kuma ya samu. “Lafiya ka kira Zahra?” Ta tambaya tana kallona “Lafiya Kalau, akwai wanda na ce bana son na sake ganinshi a idan nan kuma jiya na gansu tare” Hankalina ya dan kwanta jin cewar ba magana ce akan ďanshi ba. “Oh Okay daman akwai mai zuwa gurinta ne? Ban sani ba wake zuwa gurinki Zahra?” Yanayin yadda Hajiya Jamila ta yi tambayar sai ka rantse da Allah ba a gabanta Sauban ya aika aka kira ni ba jiya, sai dai be zama lallai ace ta san zuwan da yake ba, domin bata da alaka da camers din gidan balle na ce ta gani kuma bata taba fitowa ta gan mu a tare ba idan ba jiya ba. Kaina na kai kasa ina murza yatsun hannuna kamin na ce komai mijinta ya karbe. “No bari na yi magana da ita, dan ba mu guri” Ya dauki kofin dake gefenshi ya shanye abin da ke ciki gaba daya, kamar an cilasta haka ta tashi ta fice daga falon ni dai ban yarda na kalleta ba har ta fice ina jin karar rufe kofa gabana ya kara faduwa, hausawa suka ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake tun kamin yace min komai na dago na kalleshi ina kuka da turo baki. “Wallahi bana son zuwanshi kuma na fada mishi cewar baka so amman be daina ba, kuma jiya ma da ya kira ni ban fito ba shi ne ya shiga falon Hajiya yace a kirani kuma da na zo shi ne yayi dabara yace mu fito waje” Kallona kawai yake be ce min komai ba har na kai aya na yi shiru dan kaina sai dai ban daina kukan ba domin na san hukuncin da zai min a yanzu babba ne domin yayi min gargadi tun a farko ni ce ban ji ba, ya dauki tsawon lokaci yana kallona ba tare da ya ce komai ba. “Miye alakarki da shi?” “Babu alakar komai” Na amsa mashi da sauri. “Babu alakar komai yake zuwa gurinki?” Na nuna bayana. “Abokin Abiey ne, Abiey tsohon Saurayina” “Kin taba fada min haka” Na yi shiru na bata fuska sosai alamar ina daf da fashewa da kuka. “Wannan ne karo na biyu da zan tambaye ki wacece ke Zahra, ina son sanin wani abu daga tahirin rayuwarki wata kila hakan zai amintar da ni ga wani abun da nake ji a zuciyata game da ke, kin yi min abun da ba kowa yake iya yi ba, kuma har gobe ba zan manta da ceton rayuwata da kika yi ba ko kadan bana son na saka miki da mummunan abu” Na hade hannayena guri daya ina yawo da su hawaye na sauko min, to ni na ina zan fadi wace ce ni. “Ni.... Ni... Ni kawai wata yarinya ce da bata jin magana, na ta so a hannun Mamana na bude ido da ita ban san mahaifina ba, Mama ta fada min cewar tun ina ciki ya rasu, sai dai na san abokinshi domin shi ya auri mahaifiyarmu bayan rasuwar babanmu ya rike mu ni da yar'uwarta Maryam kuma shi yake juya mana duniyar da mahaifinmu ya bar mana, yana da wata mata daya muna kiranta da sunan Hajiya tun daga lokacin da dan'uwanta ya kaita makka tana da yara biyu Zaharadeen da muke kira da Yaya Deen a wacan lokacin da kuma Bahijja da ba zata wuce sa'a ta ba, haka na taso na gan mu kamar yan'uwa, Hajiya bata nuna mana banbanci da yarta wani lokacin ma sai ta yi min abu ba ta yi ma yarta ba, idan kuma muka yi laifi ni da ita Deen ne yake mana hukunci musamman ma ni domin ita tana jin magana ba kamar ni ba, mu biyu Mama ta haifa sai dai ni ce marar jin magana idan an hana ni abu sai na aikata idan kuma aka ce na yi ba zan yi ba. Ba ni da kawa sai Hafsat wata yar Kaduna ce kanwar makociyarmu ce da yayarta ke rikonta a gidanta da take a aure a nan Kano, a rayuwata na tsani zuwa makaranta sai dole sai dai Hafsat tana cilasta min zuwa domin ita tana son zuwa makaranta ba kamar ni ba, wani lokacin sai Deen ya ba ni kudi ko kuma ya kai ni makarantar wani lokacin kuma zai je ya dauko ni, wani lokacin kuma idan na dawo daga makaranta gidansu nake tafi na wuni idan na yi wani laifin ma can na ke guduwa sab, wata rana mun dawo daga makaranta muna tafiya tare da Hafsat muka biyo ta gurin masu siyar da kayan marmari, daman mun saba mu kan biyo ta gurin mu tsinci wanda suka zubar wanda zamu iya sha mu sha wanda ba zamu iya ba kuma sai mu zubar. Bayan mun gama tsinta muka nufi gida muna tafe ina sha ita dai Hafsat bata sha saboda tan mata fada a gida cewar ta daina cin abun a hanya, ni ma kuma an yi min hudubar sai dai bana jin magana balle na daina kuma ni a ganina ba komai ba ne cin abinci a hanya, sai da muka shiga unguwar sannan kowa ya nufi gidansu, a zauren gidan mu na ci karo da Deen ya fito daga cikin gidan, ina ganinshi na yi saurin boye lalatacciyar kwakwar dake hannuna a bayana na turo baki gaba. “Zahra me kike ci?” “Ba komai” Na amsa a shagwabe ina kara cinno bakin gaba kamar zai fado. “Sau nawa za a fada miki cin abinci a hanya babu kyau?” “Da na shigo cikin gida ne nake ci” Hannunshi ya saka ya kama bakin Hijab dina ya goge min bakina da fuskata. “Dan Allah ki zaina cin abinci a hanya Zahra ba kyau, kuma wannan fruit din da kuke tsinta fa ya lalace wanda ba a so ne kike dauka kina sakawa a cikinki, irin shi sai ya saka miki ciwon ciki ai” “Ni dai ina so haka nan” Na fada a shagwabe ina karasa taune kwakwar dake bakina. “To Allah ya sauwake” Ban damu da na amsa da Ameen ba na wuce cikin gidan shi kuma ya bini da kallo har na shige, da sallama na shiga Mama ta amsa min waya a kunnenta tana watsar hakora da alama da mutum mai muhimmanci take wayar, hannunta na rike da iv da ledar cingan, hannu na saka na karbi cingan din na bare na fara ci na zuba ragowar a jakata tare da kwakwar dake hannuna. “Mama bikin waye za'ayi” “Karanta ki ga ni mana ba yar bako ba ce ke?” Na karbi katin na fada dubawa sai gani tsaye ina tsalle da murna bikin da muka dade muna jira ya zo wato bikin yar wan babanmu. “Mama kin ga har bikin ya zo amman baki min ankon ba” “Ai na fada miki ba ni da kudin yi miki ankon yanzu, kina da tufafinki goge ki saka, mutanen da ba su damu da ku ba, bikin ma sai da ya rage sauran kwana uku sannan aka kawo iv, ina cingan din ma” “Gashi nan na zuba a jakata amman gaskiya Mama sai kin min ankon nan” Na dauko cingan daya na mika mata. “Ba fa ke kadai aka kawowa, ke da yar'uwarki kara ma ita sai ta shirya ta tafi tun da tana da aure ke ko ba kije ba baki da laifi ai” “Mama bari na shirya na tafi na kai mata ko?” “Ga abincin ki can” Na tashi na shiga dakin da saurina daman akan yawo ba ni da na biyu, a gaggauce na ci abinci na shirya na sai na dauki hijabin Mama na boye a cikin nawa hijabin sai da na kai zaure sannan na cire hijab dina na jefo cikin gida na saka nata ina jin tana kirana na fice a 90 ina dariya, na san idan na dawo karbe Hijab din zata yi domin sabo ne ta dinka bata taba saka shi ba, ina isa titi na yi sa'ar samun abu hawa na hau, dan napep din da na hau mai far'a ne da son mutane abu ka da mace mai farin jini sai hira ta kaure tsakanina da shi, can na hango wani tsaye a gefen titi yana siyen kayan marmari a gurin da na saba cintar na kasa. “Wallahi idan zan samu sa'a sai na sace ledar can” Na fada ba tare da tunanin komai ba, mai Napep din dake jana ya juyo ya kalleni sannan ya kalli gurin da nake kallo. “Idan har zaki iya satowa ni kuma zan kaiki” “To idan aka kamamu fa?” “Ba za a kama mu, gudu zan yi da Napep din kuma kamin ya shiga mota ai mun nisa” “Ai to mu bar gurin” Na fada ina lakawa domin mun yi nisa sosai da gurin. “Zan iya komawa ai” “Koma dan Allah” Kamar wasa sai rage gudu ya yi kwana muka juya, sai dai mun yi latti muna dawowa mutumen na shiga motarshi. “Ba mu yi sa'a ba” Na fada ina dariya shi ma dariyar yayi, muka juya motar na gaban mu muka cigaba da hirarmu, kwatsan muka ka hango Mai Motar yana kokarin fakawa a gaban wani katon super market, aiko sai mai Napep din ya bishi muka faka bayan motarshi, muna zaune a ciki har sai da ya fito sai Mai Napep din ya juya Napep dinshi zuwa titi ni kuma na fita daga cikin Napep din na doshi inda yake tsaye yana kokarin bude motarshi ina ta saka yadda zan fisge ledar na gudu sai dai ina isa gurin sai zuciyata ta karaya na kasa yin komai sai tsaye na yi ina kallonshi ina kallon ledar hannunshi, fasa shiga motar yayi sai ya juyo yana kallona can kuma ya daga kai yana kallon harabar ko zai hango idan ina tare da wani ne. “Kina son wani abu ne?” Ya tambaya da muryarshi mai dadi sauraro, kai na girgiza mashi sai yayi murmushi ni ma na mayar mashi da murmushin na juya na fara tafiya. “Excuse me kina bukatar wani taimako ne?” “Aa kawai dai na ga kamar na san ka ashe ba wanda na sani ba ne” Na amsa ba tare da na juyo ba, bina yayi da kallo har na shige Napep din na leko shi sai ya dago min hannu ni ma na daga mashi ina jin kunya, can kuma na kyalkyale da dariya. “Ba ki karbo ba?” “Ai ina ganin zubanshin na san da cewar idan na mashi sata ba zan kwanshe lafiya ba, kai kana ganin wacan ka san ďan masu kudi ne” “Indai haka ne ai ba zai biyoki dan kin karbo ledar hannunshi ba, ni sai yayi min kama da wani dan kwallo ma Wallahi” Na yi dariya, muka cigaba da hira har ya kai ni kofar gidansu Yaya Maryam, sai da na fita cikin napep din sannan na tambaye shi nawa zan bashi. “Bana son ko asisi amman dai ina son ki taimaka min da number wayarki” “Wallahi ba ni da waya” “Kina budurwa ace baki da waya ba zan yarda ba” A take na daga mishi hannuna na nuna mishi. “Ka gani da gaske na ke Wallahi babu waya a hannuna” “To ta ina samari suke kiranki” “Wasu dai ina ba su number Mamana amman tana min fada” “To ki ba ni a haka ko kuma ni na baki tawa” “Aa sai dai na baka ta Yayana idan ka kira sai kace mashi Zahra kake nema” Ya miko min wayar na karba na saka number Deen daman ina da number a kaina na saka mashi number yayi saving. “Allah yasa dai idan na kira ki dauka kin san masu kyau ba kowa suke sulawa ba” Na yi dariya. “Wallahi zan dauka” Da haka muka yi sallama sannan na shiga cikin gidan, na tafi sa'a ko da na shiga tana gurin wanka gashi yaronta baya nan domin a lokacin danta daya tana da cikin na biyu, kulolin abincinta na bude na dauki plate na zuba na fara ci dan naman miyar na tsame na cinye ina ta sauri na cinye kamin ta fito, sai dariyarta na ci. “Kamar na san zaki zo na dauke abincin mijina na boye, yarinya da ta zo bata aikin komai sai bincike” Na yi dariya ina tsude hannuna. “Hala na muku albashi? Na ga daman da yawa kuma cin ce kin cire na mijinki” “Ina ruwanki, muguwar yarinya ina Mamata” “Tana can gida Hijabinta ne ma na saka, ga kuma cinga tace a baki na bikin Anty Maimuna” Ta dauko mai ta shafa shafawa tana fadin. “Ikon Allah ashe bikin ya tashi” “Eh kuma ban yi anko ba, Mama tace ba zata min ba” “Mama ai tana iya kar kokarinta komai kika kwaso ita” “To wa zai min idan ba ita ba?” “Ina da 3k bari na baki idan kinje can ki saka mata kuka dole ta cika miki ki siya atamfar 3500 take ai sai ta baki na dinki” “Jibi za a fara bikin ma” “Ki siye atamfar da wuri ki kai dinki zan cika miki 3500 din” Da sauri na tashi na rumgume ta ina murna. “Na gode Yaya Maryam wai kin karbo atamfarki gurin dinki ko na je na karbo miki” “Na karbo kuma Wallahi karki satar min abu ki saka” Ta yi min gargadi domin ta san halina na saba daukar tufafinta na saka sai na gama yawo na dawo mata da shi, wani lokacin ma bata sanin na dauka har na dawo mata da shi. Kyalkyale na yi da dariya, ban bar gidan ba sai da yamma lis ina ta jiran mijinta ya dawo ya ba ni kudin Napep domin na saba idan na tafi gidan shi ke ba ni na komawa shi kanshi ya san da wannan dokar da kudin atamfar na fita daga gidan a nufin gidan Hajiya, ana kiran Sallah Magariba na isa gidan ko da na shiga Hajiya na gaban murhu tana tuka tuwo Deen kuma na alwala ba karamin dadi ba na tararda shi da na yi daman zuwan nawa kusan saboda shi ne. “Ina kika fito Zahra da Magariba?” Na karasa inda yake alwalar na zauna. “Daga gidansu Yaya Maryam, so nake ka rakani gida saboda na saka Hijab din Mama zata iya cewa zata dake ni saboda sabo ne” Hajiya dake kwasar tuwo ta juyo. “Kin san sai ta dake ki kuma dole sai kin aikata? Ke dao ba zaki taba jin magana ba” Na cinno baki gaba. “Kuma Yaya Deen wani zai kira ka yace yana nemana to ni na bashi number ka” Ya tsayar da alwalar da yake ya kalleni. “Wanene?” “Wani Mai Napep daya dauke ni dazun yace na bashi number na fada mashi ba ni da waya Mama kuma fada take min tana cewa ina raba mata number shi na na bashi number ka” Mama ta saka dariya. “Zahra mai farin jini kullum sai kin yi sabon saurayi” Deen kuma ya mike tsaye ya nuna ni da yatsa. “Duk kika kuskura ya kira ni sai na miki mugun duka, akan me zaki bada number ta har da wani zuwa ki fada min ke yar son maza, kullum kika fita sai wani ya biyo ki ke kuma gani sakarya sai kin tsaya kamar gareki farinjini ya yanke saka” Haka ya rufe da fada har ya kammala alwalar ni dai sai turo mashi baki nake ina hararshi kasa kasa. “Kuma ba zan raka ki gidan ba sai dai Mama ta kashe ki” Na fada min kamar zai doke ni, Hajiya sai dariya take mana, ni kuma na tashi ina mita na dauki buta na zuba ruwa na fara alwala. “Wallahi idan be raka ni ba sai dai na kwana nan” “Zo dauki ga tuwonki ki ci” “Ni ba zan ci tuwo ba” “Sai me?” “Indomie na ke so” “To bari Deen ya zo shi da ya daukar miki wannan sai ya siya miki ni kam ba zan iya ba, zo dauki ga na shi tuwon ki kai mashi a ďakinshi” Na aje butar bayan na gama alwalar na dauki tuwon na kai mishi dakinshi, kwalbar Coca-Cola da na gani aje gefen kujera na dauka na shanye ragowar lemun ciki sai na ji test din shi kamar ba irin na lemun gora ba, ban fadawa kowa ba ban kuma nuna na sha ba, na fito na kuskure bakina na shiga dakin Hajiya na yi sallah sannan na fito na zauna waje, shiru shiru ban ga ya dawo ba hakan ya saka dole na dauki tuwon na saka a gaba na fara cin ina mita kamar ance dole sai na ci, can na fara jin kaina na juyawa wani abu mai kamar bachi kamar ba shi ba yana son daukata kuma be dauke ni ba, na ji yawun bakina na tsinke kaina yaki tsayawa akan wuyana, ina bude baki na kira sunan Hajiya sai na ji sunan yana ja muryar na min nauyi sosai. “Hajiya.... ” Na daga kai daker na kalli sama sai taurarin dake sama suka fara hadewa da juna, na sauke kaina kasa tsoka biyu dake cikin miyar ya suka fara tsalle kamar ana ball da su, kwanon tuwon kuma sai yawo yake, na kalli yatsu hannuna sai na ga sun zama goma goma sabanin da da suke biyar biyar. [11/18, 10:04 PM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣2️⃣ Na kwala mata kira da wata muryar da ke jinta kamar ba tawa ba. “Hajiya” Ta fito da sauri tana dubana. “Zahra” “Hajiya kin taba ganin nama na tsalle?” “Aa” “To wannan naman tsalle yake, kalla ki gani” Ta duba ko bata duba ba shi ne ban sani ba, nidai idona suna kan naman dake ta aikin tsalle a idona, can na ji Deen ya shigo yana tambayar ba'asi. “Ban san miya faru ba ta kira ni wai na fito na ga nama yana tsalle, sai kuma na same ta a wannan halin” Na daga kai daker na kalli Deen shi ma tsalle na ga yana yi. “Eh nama yana tsalle kai ma kana tsalle” Can kuma na ga ginin gidan shi ma yana dagawa. “Gini ma tsalle yake, ka gani ko tukunyar tuwo ma tsalle take” Ya diko daidai inda nake zauna yana kallon fuskata, can na ga idanuwanshi suna ta yawo hancinshi na juyawa. “Kin shiga dakina?” “Eh na sha lemu, na shanye dika” “Kin shawa kanki bala'i, dole sai kin yi bachi zai sauka” “Yau ba zan yi bachi ba, a haka zan zauna har a bada komai tsalle yake Hajiya ke ma tsalle kike” Na fada ina kallon Hajiyar dake aikin tsalle kamar zata je sama, wani abu mai kama da bachi ya fara zuwa yana jana ban sake sanin inda nake ba. Asubar fari na ji saukar ruwa a jikina aiko na zabura na tashi da sauri ina kallon Hajiya kamin idona ya sauka akan Deen daya bata fuska alamar be jidadin ruwan da Hajiya ta zuba min ba. “Da kin barta idan bachi ya sake ta farkawa za ta yi, gashi nan kin jikata kuma sanyi fa ake Hajiya” “Ina san ko ba zata farka ba yarinya tun jiya da aka kwantar da ita bata motsa ba kamar gawa, na sha maka magana Deeni bana son abubuwan nan da kake ajewa a cikin gidan nan idan abun ya zama maka dole ka rika zuwa can waje ka nayi abun ka ba sai ka shigo min cikin gida da wani kayan ba” “Lemu ne fa kawai, kuma ita ma kwadayinta ne ya kai ta ai” Ya miko min hannu na rika hannunshi na mike tsaye sannan na fashe da kukan jika min tufafi da Hajiya ta yi. “Daga bachi dazu dazun ban ko dade ba kin jika min tufafi yanzu da wanne zan je gida kuma Mama tace zata min masifa” “Mamar da aka kira aka fada mata a nan zaki kwana” Na gwalo ido domin na san halin Mama bata yarda na kai dare wani gurin ma balle na kwana, ya aka yi aka yi convinced dinta ta yarda ma wani abun mamaki ne a gurina. “Hajiya ashe ko yau sai ta soya namata, bari dai na yi sauri na tafi kamin a gama sallah Isha'i” “Isha'i ki dai jira safiya ta yi asuba ce” Kamar almara haka nake ganin komai, sai dai na lura da Deen da zarar ya kalleni sai yayi murmushi, Bahijja kuma dariya ma take min kai tsaye sai da Hajiya ta yi da gaske sannan ta shafa min lafiya. Ban iya cin komai a gidan ba saboda tsoron abun da zai biyo baya daga bangaren Mama, Deen ya aro babur din abokin shi ya goyani muka dauki hanyar gida yana fada min yadda suka yi da Mama. “Na fada mata kanki ke ciwo ba zaki iya zuwa ba, saboda haka idan kin je gida haka zaki fada mata” “Toh amman ka ji ta yi fada a waya” “Tace ko kanki zai tsage ki dawo gida sai Hajiya ta roke ta ta barki ki kwana a nan domin gidan ba bakonki ba ne” Na yi shiru ina ta kallon hanya, can ya jefo min tambaya. “Waya baki kudi Zahra?” Sai a lokacin na tuna da kudin ankon da Yaya Maryam ta ba ni. “Laa Yaya Maryam ce ta ba ni na ankon Anty Farida, saboda Mama ta ce ba zata min ba sai ta ba ni 3500 tace na nemi na dinki” Ya san ba zan mashi karya ba, domin karya ba halina ba ne ban saba yi ma mutum karya ba ko da kuwa za a yanka ni. “Nawa ne na dinki?” “2k suke cewa amman ka ga lokaci na kure bikin fa jibi ne ba za su karbi haka ba sai yayi tsada” Be ce min komai ba, ni ma ban sake ce mashi ba har muka isa gida. Sai da ya fara shiga sannan na bi bayanshi, sai da yayi ta bawa Mama hakuri yana rokon kar ta dake ni sannan na yarda na shiga cikin dakin, Mama na ganin ya fita ta shigo dakin ta bulalarta data saba duka da ita, can saman gadonta na hau na fara ihu kamar zan tashi gidan. “Mama dan darajar iyayenki ki yi hakuri” “Oya shirya ki tafi makaranta ba san abun da zaki yi ba idan kin wuni a gidan” Tana rufe baki na nufi inda na jefar da uniform dina na dauka na saka su haka domin dawowar da na yi jiya ban wanke su ba ban ma wuni a gidan ba balle na wanke, da sauri na saka tufafin na dauki jakata ta makaranta na nufi inda talkamina suke na saka, sai da na kai bakin kofa na juyo ina fada mata cewar ban ci komai ba. “Ita Hajiyar bata baki abincin ba?” “Ta ba ni amman ban tsaya na ci ba saboda ina tsoron kar na zo ki dake ni” “To ba zaki tsaya cin abinci ba ki yi latti, wuce ki tafi a haka, tun safe Hafsat ta biyo ki amman kina can gurin shashancinki” Na san idan na kara wata maganar zata iya cewa zata dakeni, ba dan haka ba ba ba zan tafi makarantar ba sai na ci abinci ko kuma ta ba ni kudin makaranta, haka na fito cikin gidan fuska a narke kamar na yi kuka, na san idan na ce zan tafi makaranta a yanzu zan sha doka ne kawai a makarantar wata kila ma a hana ni shiga domin na yi latti sosai. Hakan ya saka na nufi gidan Makotanmu daman na saba idan bana son zuwa makaranta ko kuma na yi ma Mama wani laifin gidan na ke guduwa na boya ba tare da Mama ta sani ba, babban gida ne da nake kyautata zaton masu shi ba su san darajar nera ba, domin an kawata ko'ina na gidan masu gadi har mutum biyu duk wani kayan alatu dake akwai a duniya akwai shi a gidan, ba abun da nake ji ma dadi kamar kasancewar matar gidan ta dauke ni kamar yarta, na kan zauna na yi hira da ita tana ba ni kyauta abubuwa sosai musamman idan zan tafi makaranta idan na leka gidan ta kan hada min tsarabar tafiya makaranta. Ammy mace ce mai far'a da son mutane ba kamar wasu masu arzikin da zaka tarar suna da izza da daukar kai ba. Ba wuce kwana biyu da tarewa a unguwar ba na leka gidan na gaishe tun daga lokacin sai na zama kamar yar gidan, sai dai ita bata taba zuwa na mu gidan ba Mama ma bata taba zuwa na su ba, a unguwar kam bana jin akwai mai shisshigin shiga gidan kamar ni, ni ma kuma ba wai ina zuwa saboda Allah ne ba, sai dan abubuwan dadin da nake tararwa a gidan da kuma alherin da take min. Gate din na fara kwankwasawa dayan mai gadin ya bude min karamar kofar yana ganin ni ce ya fara tsokata irin yadda ya saba. “Sarkin latti kullum sai ta yi lattin zuwa makaranta” “Eh na ji kai kana zuwa makarantar ma, ai kara ni” Na rama ina dan hararashi na nusa kai cikin gidan ba tare da fargabar komai ba, na bar shi yana dariya yana cigaba da tsokana ta. Karo na farko na tararda kofar falon a bude domin ba al'adar Ammy ba ce barin kofar falonta a bude, bakin kofar falon na tsaya ina cire talkamina ina kallon Ammy dake zaune a kan center carpet din falon wani katon namiji na kwance a cinyarta. “Ni fa bana son yarinyar nan Ammy matse ni take idan ina magana da ita tun kamin na tafi yanzu kuma waya san yadda ta zama” “Ita kuma Raliya fa?” “Raliya ma Wallahi tattaba ni take idan muna hira Ammy lalata ni za su yi fa ni bana sonsu duka gaskiya” Shi ne abun da namijin da nake kyautata zaton akwai alaka mai karfi a tsakaninsu yake fada a shagwabe gwaninn ban haushi, shiga na yi cikin falon ina gwalo ido da mamakin yadda mace zata lalata namiji. Motsin shigowata ce ya saka Ammy ta dago kai cike da far'a tana kallona hannunta na jikin fuskar namijin da ban san waye ba domin ban ga fuskarsa ba. “Zahra” Sai a lokacin na tuna ban yi sallama ba, komawa na yi na sake shigowa da sallama, sai ta saka dariya namijin ma tashi yayi zaune yana kallona, ina yin arba da fuskarshi gabana ya fadi mutumen da na tashi yi ma sata a super market, amman miya kawo shi nan? Kamar ya san zance sa na ke a zuciyata sai ya sakar min wani tattausan murmushi. “Na hadu da yarinyar nan jiya” Ammy ta kalleshi. “A ina?” “Na fito siya ma yaran Dr Zainab alawa, kin tuna?” Ya karasa yana daga min gira kamar yana magana da wanda suka saba fuskarshi da murmushi, ni ma dan murmushi na yi na haye kujera na zauna daman can bana jiran ace min na zauna idan na zo gidan. “Ammy good morning” Na gaishe ta ina tunanin alakarta da wannan katon saurayi, ko tace min ďan ta ne ba zan yarda ba domin ban taba ganinshi ba kuma be yi kama da ita ba, bayan Dr Zainab ban san Ammy na wani ďa ko ya ba, ko da yake ban taba zauna na yi hirar iyalinta da ita ba. “How are you Zahra ba ki tafi makaranta ba?” Na cinno baki gaba domin ta tabo min gun da bana so. “To Ammy ba na yi latti ba, kuma Mama tace sai na je saboda kawai na je na kwana a gidan Hajiya” “Wacece Hajiya?” “Kishiryar Mama ce kuma bachi ne ya sace ni ban samu na dawo gida ba, sai da safe shi ne wai sai na tafi makaranta” Na shagwabe nake maganar kamar na fashe da kuka. “Ahh kin yi laifi gaskiya akan me zaki tafi ki kwana a wani gurin ba gida ba?” “Ammy it wasn't intentionally ai ban saba kwana a wani gurin ba” “Ko dai baki saba ba ya zama na farko kuma na karshe, duk abun da iyaye basa so idan mutun ya aikata shi ba wata riba zai gani ba sai faduwa da bacin rai, karki sake kin ji? Ba kin fada min Mamaki ku biyu kawai ta haifa ba?” Na daga mata kai. “Kuma kin ce yar'uwarki ta yi aure, ke da kika rage kamata yayi ki zama mata sanyin idaniya kin ji? Kuma ki daina wasa da makaranta karatu shi cigaban mutum a yanzu” “Toh, amman dai ba zanje ba yau na yi latti dukana za su yi, har ma manta kudina na anko a can gidan Hajiya” “Biki zaku yi?” “Eh...” A take na kwashe labarin komai na bata, tun daga kan alakata da amaryar da yadda mahaifinta ya wofintar da mu da kuma ankon da Mama tace ba zata min ba. “Yanzu dai tashi ki shiga kitchen ki duba idan akwai ragowar abinci ki dauka ki ci” “Toh” Na mike tsaye a take na cire Hijab din makarantar na aje akan kujera tare da jakar makarantar na fara nufar dinning domin a nan na san tana girke abincinta, bina yayi da kallo kamin ya juyo gurin ina jin lokacin da yake tambayarta wacece ni, sai ta yi dariya “Zahra yar makontanmu ce ita ma auta ce kamar kai, sai dai ta fika saukin kai da son mutane, ban san iyayenta ba amman ita na santa kana kallon yadda take mu'amalarta kamar yar gida, ka san ni kuma da son yara sai kuma zama daya” “She's so pretty Ammy, so friendly” Har cikin raina na jidadin furucinsa domin ina jin dadin ace min ina da kyau, sai dai ban yarda na juyo ba balle har na nuna jindadin nawa. “Ammy ba komai a nan kin cinye” Na fada ina jin kamar na fashe da kuka domin ban samu komai a cikin kulolin ba. “Kitchen na ce ki duba ai ba dinning ba” Na nufi kitchen din kai tsaye, a nan na samu kayan karyawa irin na masu alfamar wani hadin ma ban taba ganin Ammy ta yi shi ba sai yau, wata kila bakonta ta shiryawa shi. Tray na dauka na zuba duk wani abun da raina yake son ko wane gefe gefe sannan na hada tea mai kauri na saka a tsakiyar tray na dauko na fito falon na nufi kofar fita. “Zahra ina zaki je?” “Waje zan je na ci” Na amsata ina kallon bakon nata da ya kasa dauke ido a kaina. “Aliyu tashi ka bata guri zata ci abinci” “Kunyata take ji?” Ya nuna kanshi har lokacin idon na kaina kamar zai cinye ni. “Ta saba zaunawa ta ci abincin ta anan ba dan kunyarka ba zata fita waje ba” Yayi murmushi ya mike tsaye yana wani irin kamshi ya nufi daya daga cikin dakunan Ammy. Zuwa na yi na zauna kusa da ita na saka tray a gabana. “Ammy wannan waye wai ya cika kallo” Murmushi ta yi “Aiko kin yi sa'a ďana babu ruwanshi da kallon mata ma” Na yatsina fuska ina kai lomar nama a bakina. “Danki? Amman ba ke kika haife shi ba ko?” “Ni na haife shi mana ba ki san shi ba ne, saboda ba mu dade da dawowa unguwar nan ba kuma lokacin da muka dawo yana waje gurin harkokinshi na kwallo shi ma be san wannan gidan ba wacan da ake gyara ya sani” Na tsude hannu. “Ammy yanzu wani gida zaku koma kenan?” “Eh wanda muka baro ba, ana mana gyara ne za a maida shi gidan sama, idan an gama gyara, a can zamu zauna mun dawo nan ne saboda ana gyara can” “Ammam kuma da gaske wannan ďanki ne?” “Ban da abinki Zahra zan miki karya ne? Shi yake bin Zainab amman baya zama a nan yana zama kasashen turawa ne” “Ikon Allah amman baki yi kama ba, Ammy ya fiki kyau” “Eh mana saboda yana saurayi ai dole ki ce ya fini kyau” Ta amsa ni data dariya, ashe da biyu ta yi maganar ni kuwa a bakin gaskiya nake fada. “Ammy kenan shi ne auta?” “Eh amman yanzu ke ce auta ba shi ba” Na yi dariya ina kwasar garar da na tabbatar bakina ya dade be hadu da ita ba, haka na zauna na ci na koshi na yi nas na nemi leda na saka sauran sannan na hau kan kujerarta na kwanta. “Ba a bachi akan kujera, Shiga ďaki ki kwanta” “Dakinki?” Na tambayar da mamaki sai ta daga min kai. “Eh amman na wanda nake kwana ba, dayan ďakin dai” Na tashi na nufi dakin dana ga namijin da Ammy ta kira da ďanta ya shiga, zaune na same shi bakin gado yana dannar wayar, sai dai shigowata ta saka ya dago kai yana kallona. “Ammy ce ta ce wai na shigo na kwanta bachi nake ji” “Okay” Ya amsa ni with so much respect ya mike tsaye ya fice daga ďakin tare da ja min kofar a hankali. Farkon abun da na fara yi shi ne na nufi makunne ac dakin na duba ban ga gurin da ake karawa ko rage sanyin ba, garin kalle kalle idona ya kai gurin remote din ac, cikin farin na dauka na karanta komai na kure sanyin ac na sake na kunna fankar sama na kunna na kasa dake aje sannan na haura saman gadon na kwanta. Wani kalar sanyi ne an musamman ya rika ratsa fatata yana shiga cikin kashina kamin bachi ya dauke ni jikina har rawa sanyi yake amman ban yarda na kashe ac ba, domin babu shi a house a nan kuma banza ta samu ai kara a sha kamin a mutu. Ban farka sai kusan azahar, a kashe na ga ac da ceiling fan din da kuma standing fan din da na kunna, ni kuma an lullube ni da blanket, ko waye da aikin na san ba zai wuce Ammy ba. Gurin da na ga kofa na nufa na bude sai na tsinci kaina a wani bandakin da ban taba shiga ba tun da Mama ta kawo ni duniya domin ko bandakin gidan Yaya Maryam da nake ganin mijinta ya gyara mata, be kai wannan kyau da tsaruwa ba, bana jin kashi amman a haka na kirkiro shi na yi na danna ruwa suka wuce da shi, na wanke hannuna na yi alwala na tsaya na kalli kaina a madubi sannan na fito. Blanket din na fara nadewa na aje a saman gadon sannan na bude kofar na fito falon ban samu kowa a falon ba na nufi gurin da jakata ta makaranta take na dauka na yi sallah azahar a gurin sannan na dauki jakar na goya na nufi kofa na bude na fice abina ban tsaya neman inda Ammy ta shiga ba. Ina tsaka da saka talkamina na makaranta na ji irin kamshin turaren dazun na bakon Ammy domin zuciyata bata natsu na kirashi da ďanta ba. “Where are you going?” “Home” Na amsa ina kallon kitson dake kamshi gashi dai kyakkyawa amman yayi kitso a kai kuma shi ba mace ba, hannu ya saka aljihu ya ciro kudi ya miko min. “Ammy tace idan kin tashi a baki, na shiga na samu kina ta bachi har lokacin baki tashi ba” Sai da na karewa kudin kallo sannan na tambayesa. “Na minene” Cikon kudin ankon da kike nema, cikin farinciki na saka hannu na karba ina godiya [11/19, 1:46 AM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣3️⃣ Baki har kunne na isa gida ina jin kamar an biya min kujerar hajji domin dubu biyar da Ammy ta bani a yanzu idan na hada da 3500 da Yaya Maryam ta bani zai wadace ni na dinka atamfar har na siye mayafi ma. Ina isa na samu Mama ta yi wanke da shinkafa, dacan ba shiri nake da wake da shimkafa ba sai na shige dakinta na bude jakata na dauko ragowar nama da na ci gidan Ammy na bude na cinye ragowar na tsude ledar, na jefa mata ledar karkashin gado na shafe bakina na fito. Ruwan zafin da Mama da dora min na dauka na sirka ma shiga bandaki na yi wanka, tun kamin na fito na ji muryar Deen yana magana da Mama, ina fitowa wankan ya bini da kallo idonshi zai fado, ba wani baya ni da ni ba balle na ce su yake kallo haka ma kirjina be gama girma ba shi ma balle na ce mamana yake kallo sai dai ko farin fatata da kuma kyau da Allah yayi min. “Laa Yaya Deen yaushe ka zo” “Yanzu” Ya amsa min fuskarshi ba yabo ba fallasa daman can a iya sanin da na yi masa ba mutum ne mai yawan dariya ba. Daki na shiga na shirya da atamfa na dauko hijab din islamiya na saka na dauko jakar na fito. “Mama makaranta zan tafi” “Ba ki ci abincin rana ba?” “Mama ai kin san bana son shinkafa da wake kuma kika girka” Mama ta riko hannuna tana lallabani. “Yi hakuri daure ki ci, kamin ki dawo sai na girka miki wani abun me kike so?” “Indomie ki saka min kwai” “To je ki ci shimkafar da safe ma baki ci komai ba, shiyasa kullum gaki nan sai rama kike kamar marar lafiya” “Sai dai ki ba ni kudi na siya a makaranta” “Ki siye kayan kwadayi ki zuba a ciki anjima ki dawo kina cewa ciki na miki ciwo ko?” Na turo baki gaba. “To ni dai Mama zan tafi a haka idan ba zaki ba ni ba, na wuni da yunwar” “Je ďaki ki dauko 100” “150 dai Mama kin san fa ina jin yunwa sosai” Ta amsa min da kai, cikin murna na koma dakin na dauko 150 na fito na tsaya kusa da Deen. “Ya Deen ina kudin anko da Yaya Maryam ta ba ni? Zaka raka ni kasuwa na siyo ankon please sai ka sauke ni a makaranta” “Ba da babur na zo ba, mu je dai na tara miki napep” Ya mike tsaye, ni kuma na sake komawa dakin a karo na biyu na dauko kyalen ankon na fito ina labartawa Mama kudin da Yaya Maryam ta ba ni, sai dai ban fada mata cewar Ammy ta ba ni wasu ba. A zaure na samu Deen tsaye yana jiran fitowa ta, 3500 din ya fara ba ni sannan ya miko min wasu 3k dabam. “Wannan zai isa a miki dinkin?” Cikin murna na karba. “Na gode Ya Deen, ka ga wasu nan ma Aliyu ya ba ni dazun sai na hada na siye mayafi da sabon jaka ma” A take na ga yanayin fuskarshi ta canja, dan matsawa na yi baya domin ya saba dukana idan na karbi abu hannun saurayi, Mama kuma bata cewa komai balle ta hana shi. “Wane Aliyu” “Wani bakon gidan Ammy ne yace Ammy tace na cika kudin ankon?” “Wacece Ammyn” “Wannan matar da na taba fada maka tana ba ni kayan dadi, wadanda suke bayanmu” “Miye alakarki da Aliyun da zai dauki kudi ya baki? Nawa ne?” “5k ne yace Ammy ta ba ni” “Ba ni kudin” Ya miko min hannu fuska kamar bakin hadari, hannu na maida baya na lake kafada, na san matukar na bashi kudin ba zai dawo hannuna ba. “To ai Ammy ce ta ba ni..” Ina ruwa baki na yi arba da wasu taurari masu kyale har guda hudu, ba shiri na saki kudin tare da jakar makarantar da kyalen ankon na dawo cikin gidan da gudu ina kuka Mama ta mike tsaye da sauri tana ta rika ni. “Lafiya?” “Ya Deen ya mare ni wayyo idon” Ji nake kamar idon ya tsiyaye tsabar azaba domin hanninshi har cikin idona ya shiga, ina ganin ya shigo cikin gidan na boya bayan Mama ina kuka sosai. “Mama ta fada miki an bata kudi?” “Kudi kuma? Waya bata kudi” “Wai wani Aliyu na gidan Ammy” “Ban san shi ba, amman dai na san Ammy makociyarmu ce ita ma kuma ina jinta ne a bakin Zahra, ka san duk kofar gidan masu abun hannu ta sani, amman bata fada min Aliyu ya bata kudi ba” “Amman Mama taya Zahra zata samu kudi baki sani ba, abun nan fa yana yawa” “Ban da abinka Deeni taya zan san ta samu kudi, tun da bata nuna min ba kuma yaron yanzu ka haife shi ne baka haifi halinshi ba, ina kudin yake” Ya mikawa Mama har da wanda Yaya Maryam ta ba ni, Mama na jugowa ta cire talkaminta ta fada duka na da shi ina kuka sai ga ni na gudu na neman mafaka a gurin Deen din, daker na sha a hannu Mama daman irin wannan duka biyun bana tsira a gurin Deen idan ma Mama bata min ba shi zai min idan kuma Mama na yi min ba zai ceto ni ba, sai idan na wani laifin ne. Islamiyar da ban tafi ba kenan na yi yammaci ina kuka har kaina yayi ta ciwo, Mama kuma ta yaga katin auren ta kona bayan Deen ya ce ba zan yi ankon ba. Bakinciki kona iv da Mama ta yi sai ya fi min ciwo fiye da karbe kudin da aka yi da kuma hanani anko. Da dare ma daker bachi ya dauke ni sakamakon tsamin da jikina yayi domin ba dan kankanen duka na sha ba a hannun Mama, jiki kuma irin na yayan manya ne da baya son wahala sai hutu. Tun daga ranar ko kofar gidan Ammy ban sake be bi ba domin Mama ta yi min gargadi cewar kar na sake zuwa gidan, ba wai na ji gargadin ba ne kawai dai na daga kafa ne na kwana biyu domin bana son na tafi gidan da tabon hannun dukan Deen da yayi min kamar dunkulen jini a ido. Irin shiriritar da muka saba ita ka yi a a yau ma sai da muka bi gurin masu kayan itatuwa muka debi na diba muka kamo hanyar gida, a hanya muka rabu da Hafsa ta nufi gidansu ni ma na nufi na mu gidan, ina sallama Yaya Maryam ta amsa min tana gyara daurin dankwalinta. “Oyoyo yar kanwata” Na fada jikinta ina shagwaba daman na saba yi mata haka wani lokacin, lura da na yi da ita ma son da take min ba na wasa ba ne wani lokacin har ta fi Mama tausayina ma. “Yaya Maryam kudin da kika ba ni na anko Mama ta karbe kuma Ya Deen har da dukana yayi” Ya dafa ni ta kalli Mama. “Mama saboda me?” “Bata jin magana, zuwa ta yi ta karbi kudin wani, kin san abun da ke hada ta da Deeni kenan, kuma yana da gaskiya Zahra tana wuce gona da iri” “To ina ruwanshi da ita wai? Haka fa yake dukanta idan ya ganta da wani bana son wannan halin na shi Wallahi, Zahra bata isa ta tsaya da saurayi ba ne? Ko kuma baiwar gidamsu ce ita, kuma idan ma haka ne shi ma ai sai a hana shi tsayuwa da ita” Na karbe ina kara karfafa abun. “Kuma Wallahi Mama Bahijja tana hira da samari har sallama ake mata, amman ni sai ya riga min fada yana dukana saboda baya kaunata be son cigabana, hassada yake min so yake kanwarshi ta yi aure ta bar ni a nan” Dariya Mama ta yi, Yaya Maryam tace. “Mama Gaskiya ki yi mishi magana ko kuma ki saka Baba yayi mashi magana tsakani da Allah be dace yana saka mata hannu yana dukanta ba ba fa yarshi ba ce” Na yamutsa fuska “Har da wani cewa ba zan je biki ba” “Aifa ba zaki je ba saboda yace ba zaki ba, ba zan barki ki tafi ba sai ace na goyi bayanki ai, daman can ba son zuwanki nake bikin nan ba” Na tashi kamar buzuzu na shige daki ina fatali da uniform din makarantar. “Wallahi sai na je” Na fadawa kaina ina jaddada zuwan nawa, musamman da na ji Yaya Maryam a zancen yau ake dinner. Ima fita gidan da sunan zuwa islamiya gidan Ammy na wuce, wannan karon ban tsaya kula wasa da Mai gadin yake min ba, na karasa harabar gidan da Ammy take zaune tare da Anty Zainab da Aliyu fuska kamar ace min kyas na fashe da kuka. “To Autar Ammy yau da me aka zo?” Anty Zainab ta fada tana tsokana, daman can ta saba tsokanata tun ba yau sake da ita ba har na saba, saboda girmamawa an zauna a kasa gurin kafafuwan Ammy ina ta tabe baki. “Ammy barka da yamma” “Barka dai Autata kwana biyu na daina ganinki miya faru?” “Ai ranar da kika ba Aliyu kudi ya ba ni, ina nunawa a gida shi kenan sai Ya Deen ya mare ni ya saka Mama ta dake ni kuma aka ce ba zan je bikin ba” Aliyun da tun da na shigo idonshi yake kan wayarshi ya dago ya kalleni. “Saboda me?” Anty Zainab ta tambaya. “Wai miyasa zan karba kudi hannum wanda ban sani ba, kalli idona har yanzu akwai jini a ciki” Na kwale mata ido ina nuna mata gurin da tabon jini ya kwanta a ciki. “Waye wannan Deen din Yayanki?” Aliyu ya tambaya, sai na girgiza mashi kai. “Aa komai ba mu hada ba fa, agola mu ne” Ya kalli Mahaifiyarsa. “Ammy miye agola?” “Step brother” “Just” Ya tashi zaune da kyau yana mamaki. “Ya saka mata hannu ya dake ta? Ji yadda jini ya kwanta a idonta fa? I swear da a waje wannan sai an kai shi Kotu, katon banza da shi ba zai doke maza ba sai ya samu karamar yarinya ya saka mata hannu, gaskiya ya kamata ki yi magana da iyayenta wannan ya tsaba doka ai” Daga Ammy har yayarshi da nake kira da Anty Zainab dariyarshi suke. “Abiey nan fa ba kasar waje ba ne, mu a nan musulmai ne kuma musulman ma a arewa, iyayenta da duk wanda ke da iko da ita zai iya hukuntata idan ta yi ba daidai ba” “Amman wannan ko a musulunci be dace ba, ta ina aka yarda namiji ya saka hannu ya doke mace, ke kina ganin jikin wannan kin san ba irin wanda ake duka ba ne idan suka mata wani dukan ai za su iya karyata ma, i can talk to her parents” Ammy ta mike tsaye tana fadin. “Babu ruwanka Aliyu sai ka je gidansu mutane ka ce cewa iyayenta kai ne wa? Ni din dai ya kamata na shirya na shiga na gaisa da iyayenta su san ni na sansu, amman kai ina dalili” “Hakkin makotaka mana ai tana da hakki, matsalar Africa kenan ba ku sam hakkin dan'adam ba sam idan ba haka ba taya step brother zai dake yarinya a saka mashi ido” A bakin gaskiyarsa yake magana domin alamun shi sun nuna haka, Ammy dariya kawai ta yi ta shiga cikin gidan ta bar mu wajen. “Kin dinka ankon?” Aliyun ya tambaya sai na girgaza mashi kai. “Kina so?” “Eh amman yau ake dinner ba zai yiyu na saka ba” Ya kalli Anty Zainab. “Wane tela kika san zai iya dinka mana kaya yanzun nan” Anty Zainab ta rausayar da kai. “Kana ji fa ance ba zata je bikin na ba” “Ba Mamanta ga hana ba fa, shi ya hana ta imagine” “Idan ka janyo mata wani dukan fa?” “Zaki min ko na kira Sauban?” “Babu ruwana a ciki” Ta mike tsaye ni da shi muka bita da kallo har ta shige, sannan muka dawo kallon junanmu kusan a tare muka sakarwa juna murmushi na sauke kaina masa ina jin nauyinshi shi kuma ya maida idonsa gurin wayarshi can kuma ya kara wayar a kunne ya kira macen da na ke kyautata zaton budurwashi ce. “Safeena kina kusa?” Ban san me wanda aka kira da Safeenar tace ba na ji ya amsa da. “Da yauwa lace zan siyo mai kyau please ina son ki bada a dinka min shi yanzu nan karki damu da ko nawa za'ayi” “Okay” Ya sake amsawa kana ya mike tsaye ya nuna min mota, da sauri na tashi na nufi motar, shi kuma ya shiga cikin gidan be dade ba ya fito rike da keys kamin ya karaso har na gama kallon fuska a jikin madubin motar, front seat ya bude min na shiga motar ta alfarmar na zauna shiga kuma na zagaya mazaunin direba yayi ma motar key, wani kalar rawa nake takawa a cikin zuciyata na dade ina addu'ar shiga kahirar mota amman bata karbu ba sai yanzu, ga sanyin ac ga motar tayi sama sauran motocin sai hangosu nake kamar kananan motoci tsabar dadin zama da sanin drajar naira baka jin motsin tafiya sai dai ka ga mutane ta cikin gilashi da kuma camerar dake cikin motar. Shopping mall ya faka ya bude ya fita ni kuwa na hakimce a cikin motar har sai da ya bude min sannan na fito na bar jakar makarantar a cikin motar muka jera muka shiga ciki, line masu lace muka tsaya ya bani damar zabe mi kuwa sai da na duba na dubo na ga dan ubansu sannan na dauko, ya shiga da ni gurin masu mayafai na dauko wanda zai shiga da lace din, talkami ma zabowa na yi sannan muka nufi gurin biya kudi. ATM dinshi ya mika ina gafe tsaye dadi kamar ya kasheni tsabar murna bakina baya rufuwa. “Yarinyar can kallona kawai take ko ta san ki ne?” Bakinshi kusa da kunnena yake fadin haka, na kalli saitin gun da yarinyar take tsaye, tabbas shi take kallo kallo kuma bana wasa ba. “Aa ni ban taba zuwa nan ba, bata san ni ba sai dai ko idan tana sonka ne” Na fada kaina tsaye domin haka zuciyata ta raya min kamar yadda idanuwana suka gani, murmushi yayi ya mike tsaye straight ya saka hannayenshi aljihu. “Je ki min magana da ita” Na daga kai na kalleshi sai na ga shi ma ita yake kallo, tafiya na fara sai da ma yi rabi sai kuma na dawo da gudu ina tambayarshi. “Ya sunanka Abiey ko Aliyu? Na ji Anty Zainab tace Abiey Ammy tace Aliyu” “Ammy ce kawai take kirana da Aliyu amman kowa Abiey yake ce min” Na juya na koma ina ta tsara yadda zan yi magana da budurwar har na isa. “Sannu sis” “Yauwa sannu” “Wacan Yayana ne sunanshi Abiey yace na karbo masa number ki” “Ni da gaske Abiey ne? Wallahi I'm confused ashe shi din ne” Ta fada tana daka tsalle sai ta bar ni tsaye a gurin ta tafi gurinshi ta gaisa da shi ta dauki hoto da shi, ina nan tsaye wasu mazan ma suka zo suka yi hoto da shi, ni kam kadan ya rage mamaki be kashe ni ba. Bayan mun shiga mota na kalleshi na ce. “Miyasa mutane suka daukar hoto kai?” Sai yaja zirin hancina “Saboda ina tare da ke mana, ina yarinyar da na ce ki min magana da ita” “Ba ta zo ba miyasa baka mata magana” “Ban iya magana da mata ba, ban san yadda zanyi na yi hira da su ba irin na saurayi da budurwa” “Da gaske?” “Yes zaki koya min” “Eh mana idan zaka je gurin budurwarka ka rika kirana zan fada maka me ake cewa” “An gama” Matar dazun ya sake kira ta kwakwanta mashi wani gurin muka dauki hanyar janbulo. Wani shagon dinki ne ko da muka isa mun tararda wata mace a gurin daga ita sai karamin mayafi tana ganin motar Abiey ya bar motarta ta nufo mu suka gaisa sannan ta karbi lace din ta ce na fito muka shiga ciki aka auna ni, sannan na dawo cikin motar na zauna ita kuma ta shiga gidan baya, ina jin suna ta hirar kasashen duniya tun ina saurarensu har na fara jin bachi, kwantar min da kujerar motar yayi na kwanta abina kamar ina cikin motar ubana. Cikin kankanen lokaci aka gama dinka lace din doguwar riga aka yi min ba mai mai doguwar kwaliya ba a wuya kawai aka saka bakin lace din sai a hannu. Tsabar farinciki ji na yi kamar na rumgume shi. A motar da muka tafi muka dawo ita kuma Safeena ta shiga motarta dabam, ban bari ya shiga cikin gidansu ba na ce ya sauke ganin magariba ta gabato. “Amman Mamanki tace ba zaki je ba ko shi step brother dinki” Na yi kamar ban ji ba na bude motar na fita. “Kin gurin da ake dinner ne?” “Eh na sani gidan Baba Dattijo aka saka” “Akwai wanda zai kaiki?” “Aa” “Idan kin shirya ki zo na kaiki” “Toh na gode sosai Abiey” Na dauki jakata ta makaranta sai kuma na juyo na kalleshi. “Ko dai na bar kayan a nan kar Mama ta yi min fada? Kuma Ammy zata maka fada kai ko?” “Karfe nawa zaki je?” “8:30pm” “Zan jira ki a kofar gate” Hakan ya min dadi, sai ta taimakamin na isa gida cikin salama, Mama na tambayar dalilin dadewa a islamiya yau gashi har an kira sallah nace mata haddata ce ban iya ba. Ana gama sallah Isha'i sai na dauko wando da riga da nake bachi da su na dauki tufafina mai datti na saka a ciki yayi kamar ni din ce a kwance na lullube shi da zane, daman yau ba a dakin Mama zan kwana ba saboda yau girkinta ne Baba a dakinta zai kwana ni kuma na kwana a dayan daki. Ina ganin Mama ta fara sallah na fara samame na fito gidan cikin tsanda. Ina yin nisa na falfala da gudu sai da na kusa isa gidan Ammy sannan na fara tafiya normal. Na dan dade a gurin sannan Abiey ya fito da motarshi ina ganin ya faka na nufi motar sai ya bude min na shiga shi kuma ya fito waje a cikin motar na shirya shiri irin na canja tufafi ba na kwalliya ba domin ko man ban shafa ba balle hoda haka kuma be hana kyau na haska blue lace din ba. Shi kanshi sai da ya yaba da yadda kayan suka karbe ni, be san garin sosai ba dan haka ni na taimaka mashi gurin kwatance har muka isa unguwar da ba ni da tabbacin ita din ce. “But Zahra i feel like kamar ba abun kirki muke ba, i don't ko Mamanki tace ba zaki je ba” “Already na zo kara kawai ayi hakuri sai na dawo” Ni kaina na san ba karamin duka zan sha ba idan na dawo, sai dai a lokacin ina ganin idan bukata ta biya komai zai faru ya faru ba matsala ba ce. “No gaskiya be kamata ba lemme take you back” Ganin zai canja shawara na bude motar da sauri na sauka, kamin ya bude side dinshi ya zagayo ha shige wata corner da na gani a kusa da gurin, ashe hanya ce sai dai mota ba zata iya bi ba, hadawa na yi da gudu ta yadda zan mashi nisa ko da ya biyo sawuna, wata budurwa da taci kwalliya na gani na bita ina tambayarta gidan Dattijo. “Ke dan Allah kin san gidan Dattijo inda ake bikin dinner yau” “Biki?” “Eh” “Biyo ni muje” Ba musu na bita har ina mata godiya, kamar abun arziki tun ana tafiya ina da saurana har na fara gajiya sannan muka iso wani katon guri da aka kawata ga mutane sosai a gurin sai rawa ake ta yi ana cashewa. A lokacin da na duba da kyau sai na ga ba Amaryar da nake nema ba ce wata Amaryar ce, sai dai babu yadda na iya aci kada kudi ya bace inji buzu da ya cinye lipton din shayi, gefe na koma na tsaya wata zuciyar na raya min na koma na nemi amaryar sai dai ina jin kamar ba zan gane hanya ba ga shi kafafuwan sun fara ciwo. Budurwar da muka zo tare da ita ce ta zo ta ja ni muka shiga tsakiyar filin da ake rawa ni ma na fara takawa domin har ga Allah kidan yayi min dadi, da rawa ta yi rawa ni ana baje na fara takawa da karfi can na fara hango kafafuwan masu rawa suna komawa kamar kafafuwan doki wato da kofoto amman jiki da kai na mutane, tun ina gani daidaiku har abun ya fara yawa. Abun ka da mai yawo sai na janyo hannun budurwa na fito da ita filin. “Ke zo mu tafi, ba wannan amaryar nake nema ba” Bata musa min ba ta biyo ni, ina ganin mun yi nisa kadan na rike hannunta gam na jata muka fara gudu sai da muka yi nisa sosai sannan na sake ta ina fadin. “Ke wannan bikin fa ba na mutane ba ne, Wallahi bikin Aljanune ke baki ga kafafuwansu ba irin na dawakai da kofotai” Dariya ta yi ta dago min kafarta daya sai na yi arba da kafar dokin ita ma. “Irin wannan?” Ziippppp fisari suka zubo min, hanji suka fara kuka hawaye sallama alaikum jiki sai rawar sanyi yake, dukawa na yi a gurin na rike kafar na fashe mata da kuka. “Ki taimaka dan Allah ki yi hakuri, Wallahi kuskure aka samu ba bikinku na zo ba bikinmu ne zan zo, kuma subutar baki na yi, ki yafe min ya ke wannan aljana” Kamar na rike doke haka na ke jin fatar kafarta da gashi da kofoto, kamar ance na dago sai na hango Abiey yana haske inda muke da waya. “Zahra gurin nan fa daji ne miya kawo ku nan? Na kasa na natsuwa na tafi na barki ne, na tambaya aka ce an ganki da wata kun biyo hanyar nan” Waiga na yi ina karewa gurin kallo ashe kuwa daji ne mai kama da tsohuwar unguwa, yana karaso kusa da ni na mike tsaye da sauri hawaye sharrr. “Miya same ki? Shiyasa na kasa tafiya idan wani abun ya faru ni za a dorawa laifi, baiwar Allah miya faru” Ya karasa yana kallon budurwar sai na ji wani sanyi sanyi a raina, ashe ba ni kadai nake ganinta ba, matsawa na yi baya ina son fada mashi cewar ba mutum ba ce kuma bana son ta gane. “Kofotosss kofotossss kofotossss” “Minene wai? Are you okay?” Da na fahimci ba ganewa zai yi ba, sai na risina cikin hikima na cire talkamina na saka hannuna na dauka na mike tsaye na watsa da gudu. “Wallahi ba mutum ba ce kofoto gareta kafafuwan doki, ka shiga uku Abiey....” Na fada da karfi ina gudu kamar mai gasan tsere, wata kila ya kalli kafafuwan nata wata kila kuma kalamai na ne suka tsorata shi sai hango shi na yi ya wuce ni a guje @360 ko waigo ni be yi ba, a nan ni ma na watsar da talkamin hannuna na ce kafa miye na ci ban baki ba, yau ga ranarki. [11/20, 9:09 PM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣4️⃣ Murnushi yake kamin dariya ta subuce masa sai ya saka hannunshi ya kare bakinshi yana girgiza kai, ni ma murmushin na yi na sauke kaina kasa ina wasa da yan yatsun hannuna, jin karar taba kofa ya saka na dago na kalli kofar, Hajiya Jamila ce ta shigo rike da Amir tsaye ta yi cirko tana kallonmu musamman ma mijinta da har yanzu yake dariya, a take murmushin da ke fuskata ya gushe na nemi natsuwata na maida ta a jikina. “Lafiya kuke dariya?” “Na ke yi dai...” Ya amsa mata still dariyar bata gama saukar masa ba, sai ta shigo tana kallona. “Miya ya saka dariya Hubby?” Ya daidaita natsuwarshi ya nuna mata wayarsa dake kusa da shi. “Wani labari na karanta” Ta kalli wayar ta sake kallona kamar mai zargi ta nufo ni da Amir. “Karbi yaron nan Zahra” Na mika hannu biyu na karba shi sannan na mike tsaye. “Yaron nan yana kama da Zahra ko kin kula da haka” Da sauri ta kalleshi da duba irin na firgici da tashin hankali. “Kama kama kama da Zahra kuma? Miye hadinshi da ita da zai yi kama da ita?” Yayi murmushi yana kallona hankali kwance. “Kin ga ita ma fara ce da ta dauki yaron nan sai ma yayi mata kyau” Ta sake kallona ta dauki lokaci tana ba idonta abinci a jikina sannan ta ce min. “Zahra ki tafi falo ki rarrashi Amir yayi bachi” “Toh” Na amsa mata sannan na juya na fice zuwa falonta, safa da marwa nake ta yi a falon ina shafa bayan Amir, tunawa da Abiey ya saka ni murmushi. Ina zaune a dakin har Amir yayi bachi sai na haura sama na shiga dakinta na kwantar da shi a hankali na sumbaci goshin ina kokarin kai hannu na shafa kanshi na ji ta ce. “Karki sake, sumbartansa ko shafa jikinshi ko yi masa duk wani abu da zai sanya kusanci a tsakaninku aikinki a gidan nan bashi nono ne kawai, abu na gaba kuma karki sake kebewa da mijina ya zama na farko kuma na karshe, ke mai kula da yaro ce kawai ki saka wannan a zuciyarki” Mikewa na yi tsaye cike da mamakin furucinta da yanayinta ta ya sauya a take. “Lafiya Hajiya?” “Lafiyar ce ta kawo haka you can go” Da mamaki na fito dakin har na isa bq tunanin be ayyana min komai daga canjin fuskar Hajiya Jamila ba, zuciyata bata raya min kishi take ba domin ban ga dalilinta na kishi ba ta fi ni nesa ba kusa ba, ita a yanzu matarshi ce tana da kudi kuma tana da jiki mai kyau, ni kuwa idan aka cire kyaun fuska miye na ke da shi da Alhaji Bashir zai duba yace yana so na, domin ko yar kibar nan ta matan aure ni Allah be bani ba yadda na ke lokacin da ina budurwa a yanzu ma haka nake a bushe musamman kwana biyun nan da nake cikin tashin hankali da rashin natsuwa. Mama ma tayi mamakin furucinta a domin da na labarta mata abun da Hajiya Jamila ta yi min, sai dai ita ta dora awon a misalin kishi ne, ni kuma ina ganin kamar ba kishi ba ne bakin hali ne kawai irin nata, daman can farko ta nuna min daga baya kuma ta dawo neman taimakona har tana rokona tana kuka, wata kila tana ganin a yanzu ta wadatu da abun da take nema a gurin shiyasa ta fara neman hanyar wulakanta ni, a daren na kwana da begen Abiey a raina labarin da na tsakurawa Alhaji Bashir ya saka ni nisawa a duniyar begenshi. Washe garin bayan na yi sallah na yi karatun kur'ane rana ta fito sai na kwanta kamin mu kulla alaka da bachi wayata ta yi ringing, kiran Sauban ne kai tsaye for the first time na ji ina bukatar amsa kiran cike da nishadi. “Zahra” “Na'am An tashi lafiya” “Ba lafiya ba, domin ban san yadda kika kwana ba, shiyasa na ce ba zan turo miki sako ba sai dai na kira na ji muryarki” “Na kwana cikin tunani da begen abokinka, Sauban kana da hotonshi ka turo min” Shiru yayi har sai da na dauka kiran ya tsinke ne, na cire wayar a kunne na duba sannan na sake maida. “Hello” “Ina jinki, bana son na ce miki ba ni da shi ne, na san idan na ce haka ba zaki yarda ba, kuma idan ma na hana ki zaki iya samu amman Zahra ki natsu akan abun da zai faranta ranki ya kwantar miki da hankali, i think tunanin Abiey ko kallon hotonshi ba zai kara miki komai ba sai damuwa, a yanzu babu abun da nake so kamar kwamciyar hankalinki” Samun kaina na yi da murmushi ko a munafurce Sauban yake nuna min kulawa ya damu da ni kuma hakan ya faranta min rai a yau, ko ba komai ya nuna min kauna da hanyar nuna kulawarshi a kaina. “Zan yi kokarin kiyayewa” “Good ya kika tashi? And tell wannan mutumen ya miki fadan ganinmu da yayi a tare?” “No be yi min ba” “He got lucky da ace yayi miki fada ba za mu kwashe lafiya ba, domin ba zan yarda kowa ya rika saka min ke kuka ba” Na yi murmushi. “Yana da kudi fa ai ba zaka ita masa fada ba, kuma ya fika gaskiya domin kai ka tarar da shi a gidanshi kuma ka karya dokarshi” “Idan baya son ganina a gidanki ya sallame ki mana dokarshi dokar banza ce tun da har ya aje kyakkyawar mace irinki” Murmushin da ya kusan zama dariya na yi, ina ta saurarenshi har ya gama maganar da zai yi yayi min sallama, kiranshi na sauka na Dr Hamid ya shigo sai da na gyara kwanciyata sannan na amsa kiran sai ya sanar min cewar yana bangaren Hajiya Jamila na same shi a can, kamar wanda bata son motsa jiki haka na aje wayar na sauko saman katifar na fito waje, Mama na fadin na tsaya na karya na fada mata cewar ba zan dade ba. A bude na tararda kofar part din da alama an shiryawa zuwa, abun ka da marar gaskiya kamin na shiga cikin falon tsoro ya kamani domin na san ni da shi da Hajiya Jamila duk muna cikin wani yanayi ne mai kama da kwai da zarar ya fashe zamu kunyata ba mu san iya abun da zai biyo baya ba. Murmushin sa ne abun da na fara yin arba da shi, Hajiya Jamila tana zaune a kujerar dake fuskata ta shi fuskarta ba yabo ba fallasa. “Karki tashi hankalinki ba laifi kika yi ba, na ga tsoro a tare da ke wani albishir na ce ni zan miki shi da kaina” Cikin rashin fahimta na karasa na zauna. Sai da ya waiga ko'ina na falon ya tabbatar mu ne kadai a falon sannan yayi kasa da murya ya ce. “Dr Zainab ta mince ta karbi kudin kuma ta ba ni takardun yau zan maida nata da su, bayan na canja shiyasa na ce ni da kaina zan miki wannan albishir din kin ga sai ki kwantar da hankalinki ki sake yadda kike so a yanzu” Ya san kwanciyar hankalin nawa domin wannan maganar na daya cikin abun da ya kwantar min da hankali a yanzu, fargaba be wuce ace watan tonuwar asirina ya kama ba, amman amincewar da ta yi zai sanya salama a zukantan mu, sai dai ban san miya na kasa murna da haka ba ina ta jin kamar ba mu aikata abu mai kyau ba. “Ko ba ki yi farinciki ba ne Zahra?” “Na yi murna mana na ji dadi” Na fada ba domin na ji dadin ba sai domin na kare kaina, idon Hajiya Jamila yana kaina wani kalar kallo take min da ban san na minene ba, har sai da na soma tsawalla ina unkurin tashi na musu sallama Dr Hamid ya riga ni. “Bari na tafi saboda ina da aiki da yawa yau kuma ya kamata na maida takardun hannun Dr Zainab kamin lokacin ya kure” “Amman Yaya da zaka dan dakatar da zuwa domin na kura idon Hubby kamar yana kan mu bana son ya kula da yawan zuwanka ko kuma yawan kebewa da Zahra” Dr Hamid ya kalleta. “Ya miki wata maganar ne?” “Aa lura dai na yi da hakan, ya kamata mu yi taka tsantsan dukanmu” “Yeah you're right, zan kiyaye see you later” Ya karasa yana kallona tare da sakar min murmushi, kofar da Dr Hamid ya rufe bayan ya fita falon bana tunanin ta gama rufuwa aka bude yar'uwarta dake can kusa da stairs. Mijin Hajiya Jamila ne sanye da kananan kaya da suka karbe domin ni ma kaina sai da na yaba yadda kyaushi ya kara bayyana a tufafi balle kuma ita da take matarshi. Da sauri ta mike tsaye ta nufi shi sai dai hakan be hana shi barinta ya karaso gurin Set din kujerun da muke zaune ba zauna a kujerar da Dr Hamid ya tashi, cikin hanzari na mike tsaye ina mika masa gaisuwa. “Ina kwana Yallabai” “An tashi lafiya” “Lafiya kalau” Na juya da zimmar ficewa sai ya kira ni. “Zahra” Na juyo sai dai ban yarda na kalleshi ba, duk kuwa da jikina ya ba ni cewar shi din kallona yake. “Madam me kika shirya mana na breakfast?” Hajiya Jamila da a yanzu ta karaso kusa da mijina ta amsa tana kallon yadda yake kallona. “Mun makara ba mu barka da wuri ba, shiyasa ban dora komai ba Ummiter ma yau ba zata je aiki ba kai ma i thought bachi kake yi shiyasa ban girka komai ba, amman zan dora yanzu” Ya daga mata hannu yana kallona ni ma kallonshi nake a munafunce ina dauke ido. “No no ya kamata ki huta, bari Zahra ta shirya mana abun karyawa, Zahra kin iya girki?” A take ido suka rain fata a duniyar nan ba abun da na tsana kamar ace min na yi girki ba dan bana son girkin ba sai dan ban iya ba, gudun na kunyata kaina ya saka na daga kaina har sau uku a na hudu na samu na iya furta. “Eh na iya” “Good the kitchen is yours now ki girka mana farfesu sai ki soya mana dankali bana cin kwai amman Matata tana ci ke ma idan kina ra'ayi zaki iya soyawa Ummiter ma tana so, and Wife ina ganin a maida girkin su tare da na mu gaba daya ba dole sai sun girka na su dabam ba” Karashe maganar yayi yana kallonta kamar mai neman shawara. “No ba zan iya ba, girkin mutum uku na ya nake yinsa balle na mutun biyar? Already ka zuba musu abin ci a store to miye na neman a hade abinci da masu gida?” “Idan ba zaki iya ba Zahra sai ta cigaba da girka mana” Ni kaina mamakinshi na ke balle kuma ita da mamakin ya bayyana a fuskarta. “Excuse me, Hubby baka cin abincin masu aiki fa?” Kallona yayi sai na yi saurin sauke ido kasa ina jin bugawar gaba. “Wannan tana da tsabta kuma na ga kin aminta da ita, daman ni kazanta ce bana so a kula da tsabta kin ji Zahra” Na daga mashi kai sannan na juya na nufi kofa sai ya sake kirana ina juyowa ya nuna min kitchen. “Ki girka mana abu na ce” Kamar a rikice na nufi kitchen din ina jin wani abu mai kama da kuka na neman hanya a idona, katon kitchen da komai a akwai a ciki wani abun ma ban san amfaninshi ba ban kuma san abun da ake da shi ba balle na san yadda ake kunnawa ko kashewa, ba abun da ya tsaya min a rai kamar dafa farfesu, har ga Allah ban san yadda ake yin farfasu ba domin ban taba yi ba, a gidan Ammy ma na ga ana yi ban tana tsayawa na kalli yadda ake ba, haka ma Mama da take girkawa wani lokacin ban san yadda take ba sai dai idan ta girka ta na ci. “Farfesun ma na miye zan yi?” Na tambaya kaina da muryar da kuka ke son ya ci karfinta, dankalin na fara gyarawa na kunna gas sannan na dora fraying pan na bude cabinet ina dubawa sai ko zan ga mai, daker na gano inda take aje mai na dauka an zuba, da na lura ba rawa ba tumame sai na cire hijab dina na aje gefe daya na takarkade ina ta soya dankalin sai da na yi kwasar farko, sannan na leka falon ban ga kowa ba daga ita Hajiyar uwar izza har mijin nata, sai dai idona ya sauka akan wayar dake hannun kujerar da Alhaji Bashir ya zauna, kafafuwan na sauko na fito daga kitchen din ina kallon stairs na karaso gurin wayar kamar na kai hannu na dauka sai kuma tsoro ya kamani, na juya na koma kitchen din cikin tsanda. “Idan ban dauko wayar ba kuma da me zan yi farfesun? Ko kuma na ce musu ba iya ba? Ai kuma dai da kunya ace ban iya ba, to ko dai na tafi na dauko tawa wayar? Kuma ai ba ni da data, ko kyma na kira Mama ta zo ta girka musu?” Haka dai na yi ta magana da kaina, saga karshe na yanke shawarar dauko wayar da nake kyautata zaton ta Alhaji Bashir din ce ya manta na duba yadda ake farfesun. Kamar wanda zata yi sata haka na dawo falon ina ta waige waige har na samu nasarar kai hannu na dauki wayar, tun da nake a rayuwata ban taba daukar wayar na ji tana neman subucewa a hannuna ba irin wannan saboda sulbin da take da shi, lallai kayan kamfani daban da na shago abun manya na manya ne a duk inda yake, maida kofar kitchen din na yi na rufe a hankali ba tare da na bari kara ta fito ba, sannan na taba wayar hoton Amir ne a gaban wayar yana bachi, a take tausayin Alhaji Bashir ya kamani ,domin yana kallon Amir a matsayin ďanshi ne alhalin ba jininshi ba ne, a yanzu kam ina jin rashin kyautawa a abun da na aikata, ko da yake ni dole ce ta saka amman Hajiya Jamila ta yaudari mijinta yaudara mai girma kuma yaudarar da babu wanda zai san gaskiya sai Allah. Na raba kaina da ďana zai girma be san ni a matsayin mahaifiyarshi ba, ban san Mama a matsayin kakarshi ba sai wasu familyn na dabam a matsayin familynshi, anya hakkin yaron nan ba zai kamani ba? Da kuma amanar Alhaji Bashir din na hada baki da ni a zalinci mutun da na lura babu komai a tare da shi sai alheri da son kyautatawa? Na share hawayen da suka zubo miki na nisa ina taushe wani numfashi mai wuyar zama a masarafarsa. “Ban yi da mugun nufi ba Amir, kuma ban aikata hakan saboda bana sonka ba, sai dai na ceto rayuwar mahaifinka rayuwar da bata tsaya ba” Na aje wayar na dora hannuna akan sink hawaye wasu na rigan wasu sauko min, ina matukar jin kaunar yarona kalaman da Deen ya taba yi min da kuma wasikar da na karanta a gidan Hajiya suka tsaya min a rai. ‘Ki kula min da abun da zaki haifa ko da bana raye ki tarbiyantar da shi’ ‘Karki tsani yayana saboda abun da na aikata’ Kuka na yi sosai sannan na share hawayena na wanke hannuna da fuskata a jikin fanfon kitchen ko na kwashe dankalin daya soya, na rage wutar gas din na maida hankalina gurin wayar sai a lokacin tunanin pin din wayar ya zo a kai, ga mamakina ina taba samn wayar sai ta bude ashe babu password a jiki, ba karamin dadi hakan yayi min ba a take na kunna data wayar na saka wayar a silent na shiga cikin ina dubawa har na gano YouTube, kai tsaye na shiga na rubuta farfesu, a take aka nuna min video kala kala, farfesun kaza na kifi na kan garo na kayan ciki and so on. Freezer na nufa na bude na ina dubawa, babu komai a cikin sai kayan marmari, rufeta na yi na nufi dayar dake kwance na bude sai na yi arba da nama kala kala. Da taimakon video dake playing na yi musu farfesun nama zallarshi, yadda na ga suna zuba abubuwa haka na yi sai dai ban saka kayan kamshi ba domin ban ga ko daya ba, sinadarin dandano ma daker na ganoshi, sai da na gama na sauke sannan na fasa kwai na soya, ban yi tunanin dandanawa na ji yadda girki yake ba domin na gama girkin ne cikin rashin natsuwa ina ta fargabar kar Hajiya Jamila ko Mijinta su shigo su same ni da wayar, wannan yasa idan na kalla sai na boye wayar a cikin zane, domin idan wani ya same ni da ita ban san me zan ce ba musamman ma shi wata kila zai ce sata na yi, sai dai cikin hikimar Allah babu wanda leko kitchen din har na gama girkin. Manyan kuloli na dauko na zuba komai a dabam dabam sannan na dauka na nufi dinning na jera sannan koma kitchen din na dauki wayar na da na aje bayan cups na yi clearing video din da na kalla na rufe data na fito ina ta kalle kalle har na yi nasarar aje wayar a gurin da na dauke ta, wani wawan tsalle na daka ina jindadin yadda na shirya komai ba tare da kowa ya gane komai ba, ba tare da tunanin komai ba na haura sama ba kwankwasa kofar dakinta tun kamin, daga inda nake tsaye ina jiyo sautin Ummiter, hakan ya fahimtar da ni hira suke mai cike da nishadi, ashe kuwa na canka a daidai domin dariyar dake take yi a yanzu ya tabbatar min da haka. “Zahra” “Na'am Hajiya tana ciki” Na amsa ba tare da na gaishe ta ba daman can zuciyata bata taba raya min na gaishe ta ba, taya zan gaishe da matar da bata wuce sa'a ta ba. “Eh tana ciki” Ta bude kofar dakin gaba daya, hakan ya bani damar hango Alhaji Bashir dake zaune kan kujera Hajiya Jamila kuma tana zaune kusa da shi, sai dai na ga tsabanin abun da na gani a fuskar Ummiter da Alhaji Bashir, ita kam sam babu ko kufan murmushi a tare da ita balle dariya har ya kaita ga nishadi. [11/21, 10:53 AM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣5️⃣ Bayan na sanar musu cewar na gama na sauko na daya a dayan set din cushion din domin bana son na tsaya a kusa da inda ya zauna dazun yayi zaton ko na taba mashi waya, babu mai iya sanin farincikina sai Allah da ya amince min na girka wannan breakfast a yau na shirya komai ba tare da sanin kowa ba, balle a gane cewar ban iya ba. Ummiter ce ta fara saukowa jikinta sanye da tufafin bachi wando da riga ta nade kanta da wani abun da nake kyautata zaton tawul ne. Alhaji Bashir ne na biyu sannan Hajiya Jamila, a duk lokacin da muka hada ido harara take aiko min da ita, mijinta kam ban da murmushi babu abun da yake, ba na ce ina ganinshi kullum ba balle na ba da shaidar kyakkyawan murmushin sake fita tsakanin kumatunshi amman tabbas tsakanin jiya da na fara bashi labarina zuwa yau na lura nishadin shi dabam yake. “Kin cire na ki ko?” “Aa ban zuba ba” “Ke da girki, mu da fara ci zo ki zuba na ki mana” Na dauki plate din da yake nan na bude cooler na zuba, na sake daukar dayan na zuba dankali da kwai, sannan na dauka zan tafi. “Tea fa?” Na juyo na kalleshi sai kuma na kalli Hajiya Jamila wacce ta hade min fuska. “Aa wannan ya isa” Ban jira ya sake cewa wani abu ba na fito falon da saurina, kamin na karasa bq na tsaya na dandana abinci domin tun a cikin yawuna ya tsinke, saranda na yi ina fidda ido waje, anyi ba'ayi ba kenan ni kaina ban taba cin girki marar dadi irin wannan gashi dai be nuna ba kuma ga rashin dadi wani gurin ma kamar gishiri ya zarce. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un” Na fada cikin tashin hankali, da gudu na karasa bq din a waje na aje plates din hannuna na dawo da gudu zuwa main house din jikina har mazari yake, ala ala nake idan ba su ci ba ina shiga cikin falon muryar Hajiya Jamila ta dira a kunne “Ni gaskiya ba zan iya cin wannan abincin ba” Ummiter kuma sai kwasar dariya take, tsaye na yi jikin kofar falon irin yadda yara suke idan sun yi laifi fuskana na bayyana rashin jindadin abun da na aikata, sai suka dago suna dubana, Alhaji Bashir da fuskarsa take sake har yanzu ya ce. “Zahra karaso mana” Kamar ance karasa ki jr ga ajalinki haka na ji, sai na samu kaina da kara matsawa baya na kwalla sharrr daman can haka nake zarar zan aikata laifi to kuka ne zai biyo baya tun kam ayi min hukunci. “Dan iskanci kin san baki iya girki ba kika karba kika yi? Shi wannan abinci mai kama da guba da kika girka mana so kike mu ci mu mutu ne?” Na girgiza kai daga inda nake tsaye, sai Alhaji Bashir yayi alama da na zo da hannu, cikin karfin hali na taka na karasa gurin ina mai tsananin jin kunya taya mace kamar ni ace ban iya girki ba, ai da kunya ba ma karama ba. “Kiriniya bata barki kin tsaya kin ko yi girki ba ko Zahra?” Na sauke kai na kasa ina jin sautin murmushinsa. “Video da kika gani a waya suna tsallaken time ne ke kuma kin yi amfani da yadda suke kika girka mana wannan ba ki yi la'akari da haka ba” Wata kunya ce ta kama ni, ya aka yi ya san na dauki wayar har na duba?ko dai akwai camera a falon da kitchen din ne? Wata kila Hajiya Jamila ta boye min ne saboda na saki jiki na aikata wani abun ta gani, wannan maganar da mijinta yayi ya tabbatar min da akwai camera a falon ba kamar yadda Hajiya Jamila tace min a waje kawai aka saka camerar tsaron ba. Yanayin yadda muryarsa ke fita ya isa ya karantar da ni cewar ranshi be bace ba, musamman da na daga kai na kalli fuskarsa sai na yi arba da murmushi irin na mazan dake da kokarin fin karfin zuciyarsu ko da an musu ba daidai ba su kasa nunawa. Ummiter kallon mamaki take min tana yi ma Alhaji Bashir sai kuma ta kalli Hajiya Jamila da ta kusa mutuwa tsaye. “Ba ki iya girki ba Zahra?” Ya tambaya, sai na daga masa kai ina dan turo baki ji nake kamar ya muzantani a bainar nasi. “Ya kamata ki koya ko dan gaba, maza suna son mace da ta iya girki misali irina ina son mace mai girki kala kala, kuma ya kamata ki koyi amfani da wasu abubuwan like wannan dankali akwai inda ake soya shi ba sai an saka cikin ruwan mai ba, Wife ina tunanin catering school zamu nema mata what do you think?” Ya karasa yana kallonta wata uwar harara da ta jefo masa ni kaina sai da na nemi natsuwata na rasa, Ummiter kam abun da take nema ne ya bude mata kofa wato gulma har bakin Alhaji Bashir dake motsi kallon take balle kuma reaction dina da na Hajiya Jamila. “Hubby ina son magana da kai” Tana fadar haka ta mike tsaye har wani hura hanci take kallo daya zaka yi mata ka fahimci ranta a bace yake, daman kuma na lura da hakan tun a jiya. “Okay gani nan shigowa” Amsa mata yake amman idonshi akai yake kamar zata wulgar da kujerar data zauna haka ta jata baya ta bar dinning a matukar fusace, a take na karanci jindadi a fuskar Ummiter sai kallona take da mamaki. “Ummiter shiga kitchen ki shirya mana wani abun da zamu ci” “Okay dan'uwana Yayana” Ya mike tsaye tare da jan kujerar a baya a hankali ta sauka dinning din ta shiga kitchen. “Zauna” Yayi min nuna da kujerar da Hajiya Jamila ta tashi. “Yallabai...” Ban karasa fadar abun da zan fada ba ya daga min hannu. “Ki ce Bashir idan yayi miki nauyi ki kira da Mr Bashir” Sai da na ji faduwar gaba for no reason. “Hajiya Jamila zata iya fada, tace kar na sake kebewa da kai” Murmushi yayi ya dauki dankalin ya kai bakinshi. “Ina ta karanta abubuwa akanki, har yanzu akwai kurciya da wauta irin ta yan auta a tare da ke, taya Jamila zata yi miki magana cewar karki sake kebewa da mijinta kuma ki fada min? Dazun ma zuciyarki bata raya miki da sanina na bar wayata akan kujera ba? Ba ki yi mamakin wayar babu password ba? I expect ki dauka ki duba wani abu kuma kin yi” Risinawa na yi kasa ina kuka. “Wallahi ba bincike na yi maka ba video kawai na duba na abinci” Da hannu yayi alama da na tashi tsaye. “Kina tauye kanki kuma ba ki iya tsayawa ki yi tunani Mai Kyau kamin aikata abu, ya kamata ki fito kai tsaye ki fada min ban iya girki ba, daman na saka ran haka yara irin da basa jin magana ba komai suka iya ba, sai kuka da shagwaba, i wonder how mijinki ya iya zama da ke?” Yanayin yadda ya karashe maganar ya nuna tambaya yake da neman sani, sai na share hawayena. “Daman ai ya saba da halina tun a gida” “Shi Abiey?” “Aa Deen” Yayi murmushi. “Shi ma kin taba masa kenan? Zauna ki tsakura min ya kuka kare da Abiey?” Na kalli hanyar stairs yan hanjin cikina na kadawa ba dan tsoron Hajiya Jamila ba sai dan gudun bacin rai, kallon stairs din yayi ya kalleni “Look Zahra daga Jamila har abun da yake karkashinta iko na ne mallakina na ne, saboda haka ki natsu kuma ki bi duk umarnin da zan baki wata kila hakan zai goge shafukan laifukan da kike da su a gurina” Zaunawa na yi idona na kanshi irin na marasa gaskiya. “Waya ce na ni wani abu? Wani laifin aka ce na maka? Ko kuma na aikata cikin rashin sani ne?” Kallona yake yana zagaye fuskata da idonshi can ya sauke gurin bakina yana kallon lips dina. “Fada min ya kuke kare da Abiey? Ina son sani abubuwa akanki, saboda ina son zuciyata kara natsuwa da ke” Na ware hannuna ina tabawa sai idonshi ya koma gurin tsiraran yatsun hannuna. -Gudu muka rika yi ina ta kiranshi amman be juyo ba kuma ba tsaya min ba har sai da ya ji na fara kuka, na fadi a gurin ina ta kiran Babana da Mama sannan Abiey ya dawo ya kama hannuna yace “Ki tashi mu gudu mana, bana tunanin a nigeria muke fa, duba wannan dajin babu kowa babu haske, kuma tafiyar da na yi be wuce daga nan zuwa can ba ina nemanki sai hango ki na yi a tare da matar nan amman duba gudun da muke amman har yanzu ba mu kai gurin mutane ban ga alamar titi ba” Kuka na fara yi domin na gaji sosai. “Ni ba zan iya gudi ba na gaji da yawa” “Haka zaki daure waya ce ki kawo mu nan, tun da nake a rayuwata ban taba shiga hatsari irin wannan” “Ai kai ka kawo mu kai ka yi min dinki da baka dinka min wannan lace din ba da yanzu ina can gida ina bachina, amman kai ka dinka min ka kuma ka kawo nan” “Laifin ki ke kika ji maganar iyaye ki ai, da kin ji maganarsu da duk haka be faru ba” “To waya ce na bijire musu ba kai ba, kai ka dinka min kaya kuma ka dauko ni ka kawo gurin bikin aljana Allah ka dai ya sani gaskiya wata kila kai ma aljanin ne” “Amman da na kawo ki ai na ce ki tashi mu tafi kika ki ko? Kuma da kin fada min cewar Mamanki ta hana ki zuwa ba zan yarda na kawo ki ba, gashi nan abun da kika ja mana ai” Na fisge hannuna. “Abiey mu ga kafarka” Tsaki yayi ya mike tsaye ya fara tafiya, sai na saka kuka ina ihu idan na yi ihun sai murta ta amsa amo, da sauri ya dawo ya fara kokarin rufe min baki. “Ki yi shiru Zahra karki ja mana wata matsalar haba, kina jin yadda muryarki take amsawa kin san ba a duniyar mutane muke ba” “Ban yarda da kai ba, mu ga kafanka” Ya daga wandonshi da sauri ya haska kafar da wayarshi, farar fata na gani irin ta mutane amman ban gansu ba har sai da na kai hannu na taba, ban ji gashi irin wanda na ji a gurin wacan yarinyar Aljanar mai kafafuwan doki ba, hakan kuma be kara gamsar da ni ba sai da na dankara mashi kwanta har sai da yayi kara. “Miye haka?” “Tabbatarwa na yi, yanzu me zan fadawa Mama? Kuma na san Deen sai ya kusa kashe ni idan na koma gidan” Na fada cikin kuka ina tuna irin azabar da Deen yake ba ni idan ya ga na tsaya da wani balle kuma ace na bi namiji na shiga motarshi. Ya sake kama hannuna. “Yi hakuri ta so mu tafi” Na mike tsaye muka cigaba da tafiya cikin tsoro yana rike da hannuna gam. “Karki juya, ba a son tafiya ana juyawa” Da dukan alama shi ma tsoron be gama fita cikinshi ba, idan ba haka ba taya zai ce min wai kar na waige ba a son waige idan ana tafiya. Kyalkyalewa na yi da dariya sai yayi saurin sakin hannuna. “Zahra ke ce?” Ina jin haka na san tsoro yake ji sai dariyar ta kara taho min. “Ban taba ganin namiji mai tsoro ba irinka, ashe ma kai matsora ci ne” “It's not funny Zahra baki da hankali ashe, now i understand why ake dukanki a gidanku taya zaki fara mana dariya muna cikin wannan halin” “Haka ka wuce ni fiuuuuuu kamar iska” Na nuna yadda yake gudun ina cigaba da dariya, sai gashi shi ma yana dariyar, tafiya muka cigaba da yi har muka gaji muka samu gindin wani ice muka zauna ni da shi, sai ya jinginar da wayar tsakiyar mu nan tsoron ya sake dawo min. “Ka kira waya mana ka fadawa Babanka ko Ammy, ni tsoro nake ji” “Network din ya dauke ai, da tun kamin ki fada na kira” “Yanzu ya zamu yi?” “Waya sani kin janyo mu kin kawo a nan, Allah yasa idan kika koma gida ayi miki shegen doka” “Kai ma Allah yasa idan ka koma Babanka yayi maka shegen duka” Ya kalleni. “Da ace Babana zai doke ni ko ya hukunta idan na yi masa laifi da zan fi kowa farinciki da jindadin haka” “Saboda?” “Saboda mahaifina ba kamar mahaifinki ba ne, ni nawa mahaifin babu ruwanshi da ni, idan na ci ko ban ci ba, ba damuwarshi ba ne idan wani abun zai same na fadi na mutu ma ba zai damu ba” “Ka masa laifi ne?” “Ban masa laifin komai ba domin na tashi ban san wani abu soyayyar mahaifi ba, ko riga daya be taba siya min na saka ba, a gidan Ammy na bude ido ita ce uwata ita ce ubana, ita take hukunta ni idan na yi laifi kuma ita take cilasta min zuwa gidan mahaifina daga ita sai matarshi ta uku Anty Amarya ita ma tana so na sosai kuma tana nuna min kulawa tana neman duk wata hanya da zata shirya tsakanina da mahaifina” “Fada kuka yi?” “Ba mu yi fada ba Zahra, ko da na bude ido haka na samu kaina cikin tsanar mahaifina ban san dalili ba, amman abun nan yana min ciwo sosai, amman kin yi dace ba kamar ni ba Babanki yana son ki” “Ka fini sa'a domin kai ka ga mahaifinka, ni kuma ban san nawa uban ba, Mama ta fada min tun ina ciki ya rasu ban taba ganinshi ba sai a hoto, sai abokin shi na sani wanda shi yake auren Mama ta a yanzu” Kamin na karasa maganar hawaye regen regen sauko min yake, domin ni ma ina da wannan tabon na rashin sanin mahaifin ko sau daya ban taba jin muryarshi ba, balle na yi rayuwa da shi. “Allah ya mishi Rahma” “Ameen” Na share hawayen sai ya rika kaina yana kokarin kwantar da ni kan kafadarshi na buge masa hannu. “Kai wai miyasa kake taba ni be kamata ba fa, ni dai ba yar iska ba ce” “Ni kuma dan iska ne ga iskanci nan rubuce a goshina, daga taimako, ai gashi nan kin jefa mu cikin wannan halin” “Ai nima bana son taimakonka daga yau, ba ni ba kai daman ba san haka za a fada min a gida, kuma zan fada musu cewar sace ni ka yi?” “Ya aka yi na sace ki? Ai babu wanda ya gan ni gidanku kuma ban san hanyar gidanku ba” Ina ganin ya mike tsaye ni ma na tashi sai ya dauki wayarsa ya matsa daga kusa da ni, binsa na yi da saurina. “Kin ce ba ni ba ke” Ban sake ce masa komai ban kuma daina binsa ba, har muka samu wani fili muka zauna a guri ni dai kamin wani lokaci bachi yayi gaba da ni, ban farka sai da safe ina bude ido na zabura na tashi zaune ina waige waige can na hango shi zaune yana ta daga waya sama da alama network yake nema, da sauri na tashi na karasa inda yake zaune. “Ka kira gida ne?” “Network din ne sai ya kawo ya dauke gurin nan ba network daman ke na ke jiran ki farka mu tafi” Na waiga ina kallon ko'ina na dajin, irin dajin nan ne mai kama da tsohuwar gona idan an cire amfanin gonar babu komai a ciki sai haki da ciyayi. “Abiey a ina ka kawo ni?” “Ya za'ayi na sani? Ki kabe kanki akwai kasa” Na kabe dogon gashina da ya gama hautsinewa saboda wahala dankwalin da mayafin ma ban san inda suke ba daga ni sai doguwar rigar lace din da aka dinka min jiya, kama hanya muka yi muna ta tafiya cikina sai kukan yunwa yake min ga gajiya, daker da tsudin goshi muka fara hango mutane, kamin mu karasa gurinsu na yi kuka har Abiey ya gaji da ba ni hakuri ya saka min ido. Mutanen kauyen mutane masu karamci da son mutane sosai sai da suka fara ba mu abinci da ruwa, Abiey yayi fir shi ba zai ci ba, ni kan na zauna kamar a gidan mu na kwashi tuwona na ci na koshi ba wani kyama na sha ruwa sannan suka ba mu guri muka yi na yi sallah, bayan na gama na dawo kusa da shi na zauna. “Abiey ka je ka yi sallah?” “Na yi sallah tun a inda muka kwana na yi taimama a gurin na yi sallah, yanzu kuma na kira Ammy na fada mata muna garin Bagar (Fake name)” “Ya aka yi ka san sunan garin?” “Mutanen garin suka fada min, kuma na yi browsing na gani” “To yanzu tafiya zamu yi?” “Aa a nan zamu jira su har su zo” “Amman dan Allah idan mun koma gida ka je gidan mu kace musu sace ni ka yi ka ji?” Ya wara ido yana dariya. “Na saka kaina a bala'i kenan? Ya aka yi ma muka zo nan? Ko ina motata?” “Waya sani, ashe kenan wannan yarinyar da muka bi tafiyar da ta yi da ni har mun iso nan kenan? Kai kuma ya aka yi ka zo?” “Shi ne abun tambayar ai” Na waige na kalli mutanen da suka ba mu masauki a gidansu, sannan na juyo na kalli Abiey na ce. “Idan sun tambaye ka kai mijina ne ka ce musu eh, ni ma idan sun tambaya zan ce musu kai mijina ne ni matarka ce” “Saboda me?” “To ai idan ba mu fadi haka ba, za a mana kallon yan iska ne ace miya kuka zo yi ba miji da mata ba” “Ni kin min kankanta ba zan iya aurenki ba, kuma ban shirya auren yanzu ba ma” “Ni ma ba da gaske na ke ba, saboda na kare mutuncina ne, kar ayi min kallon yar iska” Na fada ina zare masa ido yo ina ruwana da mukaminsa ko wani kudinsa ko girma na da yayi to me age it's just a number. [11/21, 4:26 PM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣6️⃣ Da Ammy aka zo daukar mu, ta yi musu godiya sosai ta yi musu alheri sannan muka shiga motar da direbanta tare da wani dan'uwanta yake ja, muka kama hanyar gida. Babu kalar fadan da Ammy bata mana ba a motar musamman ma Abiey shi ta fi dorawa laifi, muna isa gidan ta ba ni bandaki na yi wanka ta dauko min wata doguwar riga da ta yi min yawa na saka. Sannan ta kawo min abinci na zauna a kasa ina ci ina kuma tana zaune a saman gadonta tana min wani sabon fadan. “Yanzu kin tashi hankalin Mamanki Allah kadai ya san halin da ta shiga, tace karki je biki amman kin kama kafa kin tafi konda yake ba lafinku ba ne laifin Aliyu ne” “Ato ai na fada masa laifinshi ne amman be yarda ba, ai da be kai ni gidan ba da ba haka be faru ba” “Kun tashi hankalinmu na kira wayarshi a kashe, yau da safe kamin mu tafi ma Mamanki ta aiko gidan nan gurin neman ki na fada mata cewar ba ku ma garin nan” “Ammy dan Allah ki rufa min asiri karki ce ni na taho da kafafuwana, ki ce Abiey sato ni yayi” “Aa akan me zan lakawa ďana sata? Ke kika aikata ai dole a miki hukunci” Duk yadda na so Ammy ta shirya karya ta yadda za a wanke ni a gurin Mama Ammy bata yarda ba, haka ta saka ni gaba muka tafi har gidan ita ta fara shiga, ina lafe kofar gidan sai ga Deen ya fito da saurinsa yana ganina ya dafa zuciyarsa ya zauna a dankali dake kofar gidan ya rufe ido ya dafe kai. “Zahra kin daga min hankali” Na matsa baya, na san hukunci mai kauri ne ban daga masa hankalin ba ma ya hukunta ni balle kuma na daga masa hankali. “Ina mutumen nan ya kaiki? Miya faru?” “Babu abun da ya faru, hannuna kawai ya rike sau uku be amman babu abun da ya faru” Ya mike tsaye a fusace ni kuma na fada masa gaskiyar ne saboda ban iya karya ba, kuma kar yayi tunanin ko wani abun ya faru yace zai min hukunci mai tsauri. “Wuce mu shiga cikin gida” Da gudu na shiga cikin gidan, sai na samu gidan na mu cike da Uncles dina da Hajiya da kuma Yaya Maryam, juyawa na yi zan koma saboda mugun kallon da Mama take min sai Deen ya riko ni riko bana wasa ba ya saka kafarshi ya buge nawa kafafuwan na fadi kasa ba kwari sai ihu ya biyo baya, a take ya cire belt dinsa ya fara dukana da shi aka rasa wanda zai ce uffan ko ya ta so ceceni a hannunsa sai Ammy dake kokarin tara jikinta ta maida ni bayanta “Haban bawan Allah wannan mugun dukan kamar wanda ta yi kisan kai, wannan ai sai ka ji mata ciwo” Deen kamar jiranta yake sai yayo kanta yana kokarin sauke haushin ďanta a kanta. “Ina ruwanki lokacin da zata bi ďanki miyasa ba ki hana ba? Yarinya kamae Zahra ace ta iya bin namiji suje su kwana a wani guri?” Ammy ta kalleshi da kyau ta girgiza kai. “Daga ganin idonka yaron nan baka da tarbiya, taya zaka kalli idona ka fada min wannan maganar? Ai ko ban san Zahra ba idan na ga zata yi abun da be kamata ba ba zan barta ba balle kuma ace da ďana zata aikata haka?” Sai da Hajiya ta taso ta shiga tsakani sannan Deen ya shafa min lafiya, Ammy ta fice rai a bace, daga ranar ban sake zuwa ko'ina ba kullum ina gida gidan na daga ďaki sai daki idan na fito waje to fitsari zan yi ko na zagaya bandaki, Mari Deen ya saka min saboda kar na sake zuwa ko'ina ba sai dai idan zan yi fitsari ko bayan gidan Mama ta kan bude ni naje na yi idan na dawo sai na miki mata kafafuwana ta saka min. Wata rana ina sanye da marin ina alwala kawata Hafsat ta shigo muka sha hira da ita da zata tafi bata sakon gaisuwar yan makarantar mu na Islamiya da kuma boko, har ina fadar na yi marmarin makaranta. Bayan ta tafi na tashi ina tsalle cikin marin na shiga daki na yi sallah, sai na kwanta a gurin na yi shiru ina ta tunanin abun da na jawa kaina da ina da yanci na je duk inda nake so amman ban da yanzu da aka saka min mari a cikin gidan ma ba ni da wani walwala, gashi babu mai cewa komai babu saka baki ya ba da hakuri yace a cire min. Ina tsaka da kukana Deen ya shigo da yar ledarshi kamar yadda ya saba min idan zai shigo ya kan shigo min da wani abun ci saboda ya san ni da kwadayi gashi kuma ya saka an saka min mari bana da gurin zuwa. “Kuka me kuma kike?” “Na gaji da wannan marin Yaya Deen dan Allah ka cire min, Wallahi zan rika jin magana ka yi hakuri dan Allah” Fuskar damuwa yayi yana kallon fuskata dake zubar da hawaye. “Ni ma bana jindadin ganinki cikin marin nan Zahra, amman rashin jin maganarki ne yake damuna, bana son yadda kike shigewa Maza, wani zafi zuciyata take min idan ana kallonki ma balle kuma ace alaka ta shiga tsakaninki da wani” “Ba zan sake ba, idan na sake ka fille min kai, dan Allah ka cire min wannan abun ya ishe ni” Yadda na marairaice fuska kadai ya isa ya saka shi tausaya min, daman can kuma na san akwai tausayina a tare da shi. “Zan cire miki, amman zaki min alkawarin babu ruwanki da kowa dan Allah duk rashin da zaki yi ki yi amman ban da kula maza” “Toh ba zan yi ba, cire min” Na janye zanena na mike masa fafaren kafafuwana, ina jin motsin Mama na yi saurin janye kafafuwan domin fada take min idan ina sakin jiki a gaban Deen. “Deeni ne?” “Eh Mama ya gida?” “Lafiya Kalau ina su Hajiya” “Suma suna lafiya, suna gaisheku” “Ina amsawa” “Mama na ce yanzu kam za a cirewa Zahra marin nan mu ga ko zata natsu ” “Na natsu ma Wallahi ba zan sake ba” “Allah yasa” Mama ta fada sannan ta tashi ta dauko makullin ta bude min da kanta, wani tsalle na yi ina murna ina jindadi, Deen kallona kawai yake yana murmushi, a ranar na wuni cikin yanci sai dai haka be saka Mama ta bar ni na tafi ko kofar gida ba, washe gari ma Deen ya zo gidan daman kusan kullum yana gidan mu saboda ni, sai dai hakan be taba sakawa na ayyana a raina cewar so na yake ba, tunani be bani wannan ba. Da zai fita na bishi ina masa magiyar ya kai ni gidan Yaya Maryam. “Idan nace za tafi Mama ba zata bari ba, kuma idan muka tafi tare ma wani ba zai min magana ba” “Je ki fadawa Mama ki dauko Hijabinki” Da sauri na koma cikin na sanar da Mama sai tace ba zan bishi ba. “Yadda kike ganin idan kin keba wadanda zai miki fada yana nuna miki ba daidai ba ne, haka shi ma ba muharramin ki ba ne ya kamata ki san da wannan bana son shege masa da kike” “Wayyo Mama ina son zuwa dan Allah” “Bari sai ya tafi zan baki kudin napep ki tafi ke kadai” “Toh” Hakan da Mama ta yi ba karamin dadi yayi min ba, daman bana son da shi sai dole domin takura min yake idan muna tafiya a tare ko kallon maza na yi sai yayi ta min fada. Zuwa na yi na sanar masa cewar ba Mama ta hana ba zan tafi ba, sai ya shiga da kanshi yayi mata magana amman bata amince ba a dole ya ba ni hakuri yace na bari sai nan gaba kadan idan ta yardar zai tafi da ni. Sai da ya wuce na je na shirya Mama ta ba ni kudin Napep tana min nasihar cewar na natsu na daina abun da abun da nake. “Kina kallona idan ana dukanki ko kasheki za ayi babu wanda zai ce ayi hakuri, shi kuma idan ya tashi dukan na ki be san yayi miki da sauki ba, ke kuma zaton kike dadi nake ji idan yana dukanki, ko baka son ďanka ai baka son ana dukanshi balle kuma kana kaunar abun ka, dan Allah ki zama mai jin magana Zahra” Tana rufe baki Baba ya shigo cikin gidan da sallama, ni da Mama muka amsa masa na karbi kayan hannunshi na kai daki sannan na fito na saka talkamina. “Ina zata je?” “Gidansu yayarta na aike ta ta karbo min sako” Mama ta fadi haka ne saboda ta kare ni, domin ta san Baba zai iya cewa ba zan je ba. “Amman dai kin san halin yarinyar nan, yaushe aka cire nata marin nan ma yanzu kuma zaki aiketa” “Baba to ai ba dade zan yi ba, kuma ka san ni marainiya ce Baba ya ba ku amana ta yace duk abun da nake so ayi min” Na fada cikin yanayin da ke nuna yana hana ni fitar zan saka masa kuka. “Ba dadewarce matsalar ba, rashin jin maganar ne matsalarki, kuma ni babanki be bar min amanarki ba ban sani ba dai ko ya barwa Mamanki, hakan kuma ba zai hana idan kika yi laifi na hukuntaki ba ko na saka Yayanku ya hukunta ki” “Yanzu ai na shiryu baba, ba zan sake yin komai ba” “Toh gamu gani ai, muna nan dake ba sai an yi nisa ba yarinyar nan zata je ta dauko mana abun magana” “Malam ayi ta mata fatan shiriya, abun da take ba dadi yake min ba kuma yara ne sai da addu'a” “Toh Allah ya shirya, zuba min ruwanka ki kai min bandaki kamin ki wuce kafar yawo” Na dauki bokitin wanka da sauri na cika shi da ruwa na kai masa bandaki sannan na fice gidan zuciyata fes, rabon da na ga kofar gidan yau kwana tara kenan, sai da na bi ta gidansu Hafsat muka fara shiriricewa a can sannan na fito na kama hanya, ina tafiya na ci karo da yara suna jan mahaukaci ni dai ba mahaukaciya ba ce balle na biye musu hakan kuma be hana mahaukacin biyo ni su suke jan shi amman ni yake bi, Mama ta fada min ba a yi ma mahaukaci gudu hakan yasa ban yi gudu ba duk kuwa da bina da yake sai dai na hade masa fuska saboda kar ya ga dama ta. Shuuuu na ji saukar bulala mai shegen zafi a bayana, wani tsalle na yi na fashe da kuka kamar na ce masa kara min sai ya kara auna min ta biyu har zuwa ta uku, duken da nake na yi cikinsa na kwashi kafafuwansa na mike tsaye sai gashi a kasa kamin ya tashi na yi hanzarin cire talkamina na kwada masa a kai sannan na juya na ranta a na kare, ina gudu yana bina ni, har muka iso gida da mugun gudu talkamina a hannu na shigo gidan ina fadin. “Mahaukaci mahaukaci” Mama ta tsallake kwanon abincin da Baba ke ci ta fada ďaki da gudu ta rufe, ni ma dakin na nufa sai dai rufewar da Mama ta yi yasa dole na na shige bandaki daman ya fi kusa, na san Baba da nauyin jiki wata kila be yi hanzarin tashi da wuri ba ne ko kuma mahaukacin ya rike shi oho Allah kadai ya sani, ihunshi kawai na ji yana fadin. “Ka dubi girman Allah Bawan Allah ka yi hakuri ban maka komai ba, ka dubi rahmar Allah ka yi hakuri ban maka komai, na tuba ka yi hakuri dan Allah wayyo jama'a a kawo agaji” Daker muryarsa take fita da dukan alama shakure wuyan Baba yayi ko kuma ya danne shi, daman mahaukacin irin manyan mazan nan ne masu kirar samudawa. “Dan Allah ka yi min rai, ni na jaka ba, Zahra ce ba ni ba ne ba a nan gidan ta shigo ba, kalli sama kalli sama gata a can sama tana maka magana, Zahra idan ba ki fito ba sai na halakaki, Malam ka dubi girman Allah ka tafi gata a can bandaki tana maka gwalo, Malam ba a nan ta shigo ba, na rantse da Allah da Al'kur'ane ban san ta, na rantse maka da Allah ban san ta ba, ba yar gidan nan ba ce, shiga uku zai kashe ni, ban maka komai ba, Zahra idan baki fito ba sai auren uwarki ya kare a gidan nan” Ina jin haka na rufe baki daman jikina mazari kawai yake, ruwan wanka da na kai ma Baba dazun kamin na fita na zubar na kife bokitin na daka na taura katangar bandakin daman bandakin mu irin wannan ne da baya da mufi a sama kuma gunin bashi da tsawo sosai domin irin na bayan gida ne dake tsakanin bayan gida da wani bayan gidan daga tsakiya an yi hanyar ruwa, ina hawan ginin na dire ta baya na auna da gudu na fita ta gaban wani gidan na fita ta wata hanyar, gidansu Abiey ya fi kusa hakan yasa ina fitowa kwararon na kwankwasa kofar gidan aka bude. “Oyoyo Zahra yaushe rabonki da gidan nan” Na watsawa Mai gadin harara na murguda masa baki na wuce cikin gidan kamar wata yar gidan, a bude na tarar da kofar falon sai na aje talkamin da suke hannuna a bakin kofar na shiga da sallama ina haki kana ganina kasan akwai abun da ya faru. “Maraba da Autata oyoyo na yi missing dinki” Ammy ta ware min hannayenta sai na karasa kusa da ita na rumgume irin side hug din nan, sannan na zauna a kasa. “Ammy ya gidan” “Lafiya Kalau Zahra Aliyu yana ta damuna da nemanki, ya damu naje na duba masa ke” “Amman baki je ba ai” “Bana son Mamanki ta ga laifina ai, kin ga zata ga kamar mu muke kara dora ki a hanya, kuma abun da yaron nan yayi min ban jidadinshi ba” “Ki yi hakuri Deen haka yake yana da saurin ido sosai, Ammy ina Aliyun?” “Yana garden yanzun ya gama matsa min Kafafuwana dake ciwo” Na tashi na fice daga falon ba dan na san inda Garden din take ba, sai dan na san abun da ake kira da haka, gurin da nake hango itace na nufa ina shiga na same shi yana waya a daya daga cikin kujerun da suke gurin na zauna ina kallonshi murmushi ne kwance a kyakkyawar fuskarsa gashi fari tass hanci kamar na ara masa idanuwansa da haske sosai gashin kansa ma yayi baki wulik ya kwanta gwanin sha'awa. Sai da ya gama wayar ya dube ni “Kana da kyau Abiey” Na fada masa a bakin gaskiyata domin ko mace na gani mai kyau zan iya fada mata cewar tana da kyau domin ni a gurina fadar haka ba komai ba ne. “Na yi kyaunki?” “Zolayata kake ko?” Ya daga min gira daya. “Ya kike Zahra? Ina son Ammy taje ta duba min ke amman bata je ba, ta fada min tun tana cikin gidan nan mugun ya fara dukanki ko? Wallahi yayi sa'a da sai na hukunta shi ko dan abun da yayi miki da Ammy amman Ammy ta hanani daukar mataki” “Har da mari ya saka min sai jiya aka cire min, bana zuwa ko'ina yayi min duka sosai” “Mari kuma? Wannan mutumen ba shi da kirki duk da dai ban taba ganinshi ba, son ki yake ne?” “Aa Wallahi, babu komai tsakanina da shi” “Amman yanzu ba a sani ba kika zo gidan nan ko?” Na daga masa kai ina dariya idona ya kai gurin icen mangoro. “Abiey zaka ciro min mangoro daya” Na kalleshi ashe kallona yake har lokaci be kuma dauke idonsa. “Miye?” “Kallonki dadi yake min silly girl, babu ruwanki yadda ta nuna miki haka kike yi i like your style” Na rufe fuskata ina dariya na dade a haka kamin na bude idon still idonsa na kai. “Kina da saurin sabo da mutane Zahra, shiyasa mutane suke binki shi kuma wannan mahaukacin yake ta hauka” Kalmar mahaukaci da ya fada ta saka na tuna da mahaukacin da ya biyo ni yanzu, sai na kyalkyale da dariya ba bashi labari shi ma dariyar yayi sosai. “Kin ja masa kamar yadda kika min, har mafarki sai da na yi bayan na dawo fa” Na cize baki ina kallonsa. “Abiey ka cire min mangoro daya mana” Wannan karon a shagwabe na yi maganar ina son masa kuka. “Okay bari na dauko abun cirewar, ko na kira Haruna mai aiki ya cire miki saboda akwai zuma a gurin sai an yi a hankali” Ya tashi ya fita daga gurin, ni kuma sai zuciyata ta kwadaita min son ganin zumar, sai ko na tashi na karasa gurin icen na daga kai sama ina kallon, katon gidan zuma na gani a gurin. “Laaaa” Na fada ina mamaki ashe haka take yin katon guri, kuma Mama ta taba fada min cewar idan aka taba ta tana bin mutane, domin na tabbatar da gaske ne ko karya na dauki katon dutse na jefa mata be kai gurin ba ya fadi sai na sake dauka na sake jefawa haka na yi ta yi har sai da na same ta, aiko sai ta yi runduna ta nufo ni kuma na auna da gudu na fice Garden din amman zumar nan da karfi hali bata fasa bina ba, da gudu na shiga falon Ammy ina fadin “Zuma zuma zuma...” Abiey dake tsaye ya fadi kwance kamar wanda ya ga yan bindiga, Ammy kuma dake complain din ciwon kafa sai ga ta tsalleke Abiey ta haye stairs da gudunta tabur tabur domin mace ce mai jiki, ta banko kofar dakin gam.... Ni kuma na nufi kitchen da sauri na rufe aka bar Abiey shi kadai a falon, tab na kunna na jike jikina da ruwa na cire hijab dina na fara korar sauran zumar da ta biyo ni sannan na nufi kofar baya na bude na fice da gudu. [11/21, 7:28 PM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣7️⃣ Gurin Haruna mai gadin na tafi shi ya karasa korar min zumar sannan na fita babu ko talkami a kafata haka na na tari abun hawa na hau na fada masa gurin da zai kai ni. “Amman lafiya kafarki ba talkami kuma ba ki yi kama da masu tabin hankali ba” “Wallahi zuma na jefa ta biyo ni sai na bar talkamin a can” Dariya ya fara yi, shi da mutumen dake cikin napep din da alama shi ma guri daya za a kai mu. “Shiyasa kika jika kayan? Daman kyakkyawan mata basa jin magana kina daya daga cikinsu da alama” Mutumen ya fada sai na yi dariya na rufe fuskata, muna kai wa kusa da wani shago ya bukaci mai nepep din ya tsaya sai ya kalleni. “Size nawa kike sakawa?” “37” Ya fita, be dade ba sai gashi ya dawo da wasu talkamin roba masu kyau ya mika min na karba cikin jindadi da murna na saka ina masa godiya, daidai kofar gidansu Yaya Maryam aka sauke ni sai ya karbi number wayar Mama da nufin zai kira ni ni kuma na fita na shige cikin gidan, ina shiga na samu Mijinta a waje suna cin abinci tare. “Iyeee masoya” “Bismillahi yanzu zaki dagula mana lissafi” Mijinta ya fada sai na saka dariya na nufi kitchen dinta na dauki plate na zuba abinci. “Auta kin samu yanci? Ina kika fito da jikanken tufafi?” Ban fada mata ba saboda ina tsoron kar taje ta fadawa Mama wata rana, bayan na gama cin abincin mijin Yaya Maryam ya ara min wayarsa na yi ta game har sai da na gaji. Da yamma ba yi sallama da gidan na mijinta ya bani kudin napep bayan na sato mata sabuwar atamfar da bata saka na boyeta a hijab na fito kamar ban dauki komai ba. Idan na yi laifi bana tafi gida kai tsaye musamman idan na san Mama ko Baba na yi ma laifin na kan saka Deen agaba ne domin yana hana Mama dukana, idan har ya saka hannu ya dake ni to abun da ya shafi samari ne, ban tafi gidan kai tsaye ba sai na nufi gidan Hajiya. Ko da na shiga na tarar Hajiya ta gama soya kaji tana kasawa. “Laa mu kan Baba be kai mana ba” Shi ne abun da na fara fada farkon shigata gidan, ko sallama ban yi ba daman tun daga zauren gidan nake jiyo kamshi. “Ni ma ba kawo min Yaya ba, Yayana ya aiko min da abuna Wallahi, na san halinki zaki iya tafiya ki fada mata cewar an kawo mana nama ki hada fada” “Ke ma Hajiya ai kin san sai na fada Wallahi” “To ko Wallahi ba zan yi kashin nan dake ba, ba ke dai ba kya jin magana ba, to ai sai ki yi mu gani” Ban dauka da gaske Hajiya take ba har sai da ta kasa naman ta bawa Bahijja nata na Deen kuma tace a kai masa dakinshi ta dauke nata ta shige daki. Abun ka da marar zuciya kuma kwadayayyina haka na je na zauna gindin murhun nan ina lasar tukunyar data soya kazar da ita. “Zahra me kike nan” Deen da fitowarshi kenan daga wanka ya tambaya, juyowa na yi na kalleshi sai na yi dariya ina kallon kirjinsa dake kara fitarta mazantakansa wato Muscle, a zatonsa wani bangaren na jikinsa nake kallo domin yana daure da tawul ne, a take ya hade fuska. “Miye haka Zahra? Me ke damunki ne?” “Jikinka nake kallo fa na ga irin na masu daukar karfi ne” Ya kalli jikin nasa sannan ya sake kallona. “Ya aka yi kika fito? Ba Mama tace karki fita ba?” “Na bata hakuri ne sai tace na tafi, kuma a hanyata ta tafi na ga mahaukaci ya bini shi ne nake son ka rakani gida” “To tashi a nan” “Mai nake lasa, Hajiya bata ba ni ko tsinke daya ba wai saboda na ce sai na fadawa Mama an siya mata nama” Dakin Hajiya ya nufa ya dage labulen ya leka. “Hajiya ina nama na?” “Yana dakinka” Ta amsa mishi tana cin naman, sai ya saki labulen ya juyo ya kalleni. “Je ki dauki nawa ki ci” Na mike da sauri na nufi dakin na dauki na san inda ake aje masa abu sai na nufi gurin na dauki kwanon naman na hado da wata yar karamar leda dake gurin, sai da na fito sannan ya shiga ya shirya ni kuma na saka naman a gaba ina ta ci na boye ledar da na dauko ina lalabawa na ji abu mai kamar haki a ciki. Hajiya na fitowa ta same ni ina cin naman sai ta fara fada wai shi yake daure min ina kara lalacewa. “Haba Hajiya ya za'ayi ki bani nama Zahra tana gidan nan kuma ki yi tsammanin zan iya cinsa na hanata? Ai kara ki bata abu ki hana ni da ki ba ni ki hanata, bana son abun da zai taba yarinyar nan Wallahi” Shi ne abun da Deen ya amsawa Hajiya da shi, sai ta bude wani sabon babin na fada “To yayi kyau sai ka cigaba da yi ai, gashi nan sai kara lalacewa take kuna goya mata baya” Yana ganin na bata fuska zan yi kuka yayi hanzarin janyo kofar dakinsa ya rufe. “Tashi muje” Haka na fito da robar naman sai da muka kawo zaure ya cire dankwalin kaina ya goge min bakina ya gyara min fuskata. “Yaya Deen ka siya min lemu dan Allah idan na je gida zan fi jindadin cin nama” Ya amsa min da kai fuskarsa babu yabo ba fallasa daman can be fiye dariya ba, na bude naman na ci na mika masa ragowar. “Ka ci wannan” “Ba ni na bakinki” Ya fada yana kallon yadda nake tauna naman a bakina dariya na fara yi domin ban dauka da gaske yake ba, har sai da ya kai hannunshi cikin bakin nawa ya ciro naman ya saka a bakinki. “Baka kyama?” Na tambaya ina yatsina fuska domin kazantar hakan nake ji. “Ina yi mana, amman dai ke bana kyamarki” Da murmushi yayi min furucin sannan ya wuce gaba na bi bayansa. Sai da muka iso titi ya bukaci na tsaya zai tsallaka ya siyon min lemun, sai na matsa jikin wata transformer na tsaya shi kuma ya tsallaka titi, gefena na ji ana sallama sai na juyo a hankali na kalli mutumen dake sanye da rigar wandon jean da T-shirt, sanin Deen zai iya hango ni ya saka na matsa gefe ba amsa masa ba, sai ya sake matsowa wannan ya sake min sallamar. “Wa'alaissalam” “Sannu yan mata ya kike?” “Yadda kake” Na amsa ina ta son nayi yanga kuma ban iya ba, dariya yayi ya juya ya kalli wata motar sojoji dake can gefe sannan ya sake kallona. “Bana son na tsaya magana dake a hanya, ina ne gidanku? Ko kuma number waya zaki ba ni da zan kira ki” Kamin na amsa masa har Deen ya karaso gurin yana zuwa ya fara hararata. “Ke baki da hankali ko? Ko wane kare da mussa ya tare ki sai kin tsaya ne? Malam tafiya?” Mutumen mai kirar masu karfi ya kalleshi. “Waye kai?” “Ina ruwanka da waye ni? Ku da kun ga mata sai neman musu magana kamar kun haukace” Mutumen ya kalleni. “Miye alakarki da shi” “Ba mu da alakar komai” Mutumen kamar jira yake ina rufe baki, ya dauke Deen da mari, cikin zafi nama Deen ya rama marin har ya kara masa da gyara, kamar kyabtawa da Bismilla haka motar sojojin dake fake gefe ta karaso kusa da mu sojiojin ciki suka zagaye mu ashe akwai wata motar ma dama da ni ban lura sai a lokacin da suka suka karaso suka zagaye mu, Deen na ganin haka ya durkusa kasa kamar mai neman gafara. “Dan Allah ka yi hakuri, mahaukaci ne ni Wallahi sam sam sam ba ni da hankali dan Allah ka yi hakuri, idan ni din ba mahaukaci ne ba Allah ya tsinen” Mutum ya dauke Deen da mari, jikin Deen sai rawa yake kamar ba shi ba. “Ke na san ki ma?” Deen ya tambaye ni yana kanne min ido daya alamar yana son na amsa. “Aa baka san ni ba” “Ka gani ko? Idan ba mahaukaci ba waye zai yi haka?” Ba su saurare shi ba suka fara dukanshi duka bana wasa ba, a take hankalina ya tashi sosai na fara kuka ina ba su hakuri sai mutumen ya ce su kyale Deen. “Tashi ka tafi” Deen ya tashi ya fara tafiya mutane sai kallon mu suke, sai da yayi nisa da su sannan ya daga muryar ya ce. “Allah ya isa yan iska yan shaye shaye, mazinatan banza” Har sauran za su bi bayanshi wanda ke tsaye da ni ya hana su, ya kalleni yana murmushi da zai kwantar min da hankali. “Ba wani abu za a yi miki ba, ina ne gidanku” “Gidanmu yana gida” Yayi dariya yanayin yadda na amsa masa shi ma ya san tsoron nake ji. “Zo ga motata cen shiga na kaiki gidan” Ya nuna min wata motar dake fake gefen inda sojojin dazun suke tsaye, bana son na masa gardama yace ni ma zai dake ni, kusan zan iya cewa cilas ce da tsoro ya saka ni aminta na wuce gaba muka isa gurin motar, ya shiga ni ma na shiga muka dauki hanyar unguwarmu ina nuna masa ina share hawaye, har muka isa mutane na ganin motar sojoji har biyu aka watse kowa mamakin ganin motocin sun tsaya kofar gidanmu ake, na ina fitowa cikin motar idon kowa sai yayi kaina gashi har lokacin na kasa daina hawaye domin tsoro ya kamani sosai. “Shiga gida ki min sallama da Babanki ko Mamanki” Na nufi cikin gidan ina kuka ina daga bakin kofa na tsaya ina rike da kayan Yaya Maryam dana sato da kuma dan kullin ledar da na dauke dakin Deen na ce. “Baba wai sojoji sun ce suna sallama da kai a waje” Baba dake kwance da dauri a kafa da hannu ido daya ma an rufe masa da bandeji da alama mahaukacin nan na dazun ba karamin duka ya sha a hannunshi ba, ya kwalo idon daya ya kalleni. “So....” “Joji” “So...” “Joji gasu nan a waje har mota uku” Sai ya fashe da kuka. “Na shiga uku na lalace ba ni da haihuwa ba ni da shan azaba, ki fita ki fada musu Babanki ya dade da rasuwa, ki ce kakanki ne kawai a gidan kuma tsoho ne ba zai iya fita ba, ni dai Na shiga uku Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un” Na juya na koma ina hawaye na cewa sojan. “Wai yace na fada muku Babana ya dade da rasuwa, kakana ne kawai kuma tsoho ne yana kwance ba zai iya fita ba” Sojan yayi murmushi. “Shiga ki ce masa to ya mana izini ni zan shigo” Na juya na koma cikin gidan na tsaya daga bakin kofar gidan na fada musu sakonsa, sai ga Baba dake kwance ya tashi zaune daga nan sai ya mike tsaye da kariyar a kafa ya rika bin gini yana fadin. “Aniyarki ta biki Zahra, wahalarki sai dai ta ganki ke kadai” Dakin Mama ya shige ya rufo kofar ya saka sakata, Mama da babu abun da take sai ambaton Allah ta tashi ta shige bandaki tana kuka. “Yariya kamar yar aljannu ki dauko wannan ki dauko wancan, to na gaji ni ma kin dan san su waye sojoji amman kika je kika taba su, ko sun zo ba zan fito ba Wallahi sai dai na kwana a bandakin nan” Haka suka bar ni ni kadai a bakin kofar...” “Zahra....” Ban kai aya ba Hajiya Jamila ta kira sunana a tsawace, kamar wanda aka sakowa rai haka na zabura saboda tsorata da na yi na kalli upstairs din da take tsaye fuska babu annuri. Da sauri na mike tsaye jikina sai bari baya na yi zan fadi har sai da Mr Bashir dake dariyar labarin da na bashi ya riko hannuna sannan na samu na tsaya daidai. “Ban miki kasheda da kebewa da mijina ba? Ban gargade ki akan mijina ba?” Mr Bashir ya daga mata hannu wannan karon murmushi yake, Ummiter ma dake kitchen sai da ta leko tana kallonmu. “Wife listen ba abun fada ba ne magana ce kawai nake da ita” Saukowa take kamar ana turo ta. “Daga jiya zuwa yau ban gane maka ba Hubby wannan abubuwa da kake yi ba hakinka ba ne, kuma ka san zuciyata zata iya cewa bugawa akan haka” Wani shu'umin murmushi na gani a fuskarsa ya kalleni ya kalleta. “Matar nan da kike gani, ta taimaki rayuwata kamar yadda ta taimaki rayuwarki a yanzu take kula da ďanki, saboda she deserved respect daga garemu” “Hubby aikin Zahra kula da Amir ne kawai, ya kamata ka san da wannan” Magana take hawaye na sauko mata kana ganin ta kasan mace ce mai zafin kishi da bata iya controlling kanta. Barin dinning din yayi ya matsa kusa kusa da ita ya kai hannunshi ya dafa ta. “Haka kuma Zahra ba baiwa bace, saboda na zauna na yi Magana da ita ko na taimaka mata ba wani abu ba ne, ya kamata ki san da wannan” Yaja ta jikinshi ya rumgume yana murmushin da ban gama fahimtar manufarsa ba. Ita kuma sai wani gunji take kamar wata zakanya. “Ummiter idan kin gama ki zubawa Zahra da Mama na ta, mu kuma ki kawo mana na mu” “Toh” Ta amsa tana kallon da mamaki sannan ta juya ta shiga kitchen, shi kuma ya kara rumgume matarsa yana aiko min da sakon kyakkyawan murmushi. Ina tsaye a gurin Ummiter ta zuba min nawa ta kawo min na karba da hannu biyu na fice jiki a sanyaye. ABIEY POV. “Really Sauban” Ya fada bayan ya gama sauraren wayar da Sauban yayi da Zahra dazun da safe, bacin rai na biyu kenan Sauban ya saka masa bayan na farkon da ki yarda ya bi umarninsa har yake nuna masa kamar ya fi damuwa da Zahra, gashi har yanzu be kira shi ba be kuma zo ya same shi, and now ya saurari yadda yake kokarin tunkude shi a gurin Zahra. Can kuma yayi murmushi kalaman Zahra sun masa dadi cewar ta kwana da begensa a ranta. “Soon dear soon zaki zama tawa” Ya mike tsaye ya fito daga dakinshi ya sauko kasa, Dr Zainab da Ammy dake zaune a kujera daya suka dago suna kallonshi. “Ammy akwai yadda za'ayi a matso da auren mu da Yasmin kusa?” Da mamaki Dr Zainab ta ce “Da gaske?” “Yes, ina son a rage wata daya din nan a saka shi time din da Mai Martaba yace zai nada ni sarautar Galadima” “Kana sonta kenan?” Ammy ta tambaya, sai ya daga kafadunsa ya nufi kofar fita yana amsa mata. “Daman bana kinta” Da kallon mamaki suka bishi har ya fice, kai tsaye gurin motarshi ya nufa tun kan ya karasa ya matsa key hannunsa ta yi horn hakan ya sanar da masu gadin gidan fitar gaggawa zai yi, kamin ya juyo har an bude masa gate din yana isa ya fita @360 ya kama hanyar gidan Sauban, ya san by time shi da Sauban basa nisa da gida idan basa tare to ko wannensu yana gida. Abiey na isa gidan Sauban aka bude gate din Sauban ya fito. Sai suka samu gurin gaban gidan suka faka motocinsa, Abiey dake ji da isar Izzar bs fito cikin motar ba sai Sauban ne ya fito ya same shi a motar. “Gurinka zan tafi” Abiey be ce masa komai ba, sai kallon gidajen dake gaban na Sauban yake. “Ban yi abun da ka bukata ba saboda tana cikin damuwa sosai” Nan ma Abiey be ce masa uffan ba. “I think something is wrong amman bata fada min ko miye ba” Abiey ya hade yawu ba tare da ya kalli Sauban ba ya ce. “Yaushe zaka mata magana?” “I need to know minene za a mata Barazanar da shi tukuna because bana son na zama silar tashin hankalinta, and ka daina yin abu kamar kana ba ni umarni I'm your friend Abiey not your boy, I'm just helping you” Abiey yayi wani dan iskan murmushi. “Idan haka ne ka bi umarnina kawai, so nake a daura auren cikin satin nan” “Ko da an daura aure akan kudirinka, idan Zahra bata so dole a rabu” Sai a lokacin Abiey ya kalleshi. “I have dia every day waiting for this, and you look in to my face and telling idan Zahra bata so dole a rabu?” “Yes saboda ka yi amfani da ni ka yaudareta, ni zata kalla a matsayin mayaudarin ba kai ba, domin zaka cika na cilastata amincewa ta aure ni a bisa shadin neman mafita i think ba dan tana so na ba” “Daman ai ba zata so ka ba, Zahra ba zata taba son wani ba sai Abiey da Abiey da Abiey and Abiey only, Man get out of my car” “You forced me to do this, and now kana kishi? I understand why ka rasa ta da farko because of your foolishness” Sauban na fada masa haka ya bude motar ya fita, Abiey ya daga kai sama ya runtse ido ya cije baki ya girgiza kai, kamar wanda ya shiryawa mutuwa haka ya fisgi motar ya isa gida cikin bacin rai, ya fito motarsa a daidai lokacin da Dr Zainab take kokarin bude tata motar ta shiga. “Are you okay?” Ya nufi inda take tana fadin. “Wai ni Sauban zai kalla yace min na rasa Zahra because of my foolishness?” Dr Zainab ta rufe motarta tana kallon bacin rai da kishin dake cin kanenta. “Maybe he's right, sai da na so hukunta Deen a wacan lokacin ka hana haka ka zuba ido har suka yi zaman aurensu, and now ka dauki kishin Sauban ka saka a zuciyarka bayan duk abun da Sauban yake yi yana yi saboda kai, Abiey karka bari mace ya shiga tsakanku, saboda kar Sauban yayi aure ya barka ka shiga damuwa ya saka yin auren da wuri, kullum cewa yake kai yake jira har sai ka mu matar da kake so, daker familyn suka yi convinced dinsa ya yarda yayi aure, and now ka kawo shawara kana ganin hakan mafita ne a gare but kana son dora masa laifi” Wani irin numfashi yaja ya sauke yana jin zuciyarsa kamar zata rabu biyu, akan Zahra baya ji baya ganin duk wani abu dake gabansa, wani azababben kaunar Zahra ce ta motso masa har take kokarin neman ciwon da yake jin kamar ya matsa matsa kawana biyu wato ciwon zuciya... Da sauri ya bar gurin ya shiga falon Ammy cikin azabar ciwo ya haura sama ya shiga dakinshi ya nufi bandaki kai tsaye. Tarin jini yayi ya zubar tara hannunshi ya wanke bakinshi da fuskarsa, a hankali ya sulale ya zauna kasa yana maida numfashi, ko kadan baya son zama da Yasmin a matsayin mata sai dai baya iya karya alkawarin Zahra na cewar da tayi ya nuna mata son da yake mata na gaskiya ne ta hanyar auren Yasmin shi kuma yayi mata alkawarin tabbatar mata da hakan, ga wasan kwallon da Mai Martaba yake son raba shi da ita is one of his favorite, thirdly baya son sarauta ko kadan, but ya bar komai a zuciyarsa ya daurewa kansa ya yarda ya rasa na shi farinciki su samu na su cikar burin... [11/22, 9:05 PM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣8️⃣ Abiey ya dade zaune a bandakin sannan ya fito ya tsaya gaban madubi yana duban kanshi, idan ka kalleshi zaka yi zaton mutum ne mai kwanciyar hankali, musamman yadda natsuwa irin ta masu maida komai ba komai ba ta sauka a fuskarsa. “Alhamdulillah” Ya furta yana kara jaddada godiyarsa ga Allah, abun da ya dace ga musulmin kwarai mai hankali da aikata a lokacin da yake cikin kunci da kuma farinciki. Hannunshi ya saka aljihu ya ciro wayarsa ya dannawa Sauban kira, bayan Sauban ya karba kiran ya gyara tsayuwarsa gaban madubi yana kallon kansa cike da tarin tunani kala kala. “Na kira ne kawai saboda na baka hakurin abun da ya faru I'm sorry” “Ni ma na yi unkurin kira sai ka rigani, I'm sorry” Sai duk suka fashe da dariya. “Kana ina yanzu ina son magana da kai” Abiey ya daga kanshi yana karewa dakin da ba bakonshi ba kallo. “Ina gida ina dakina” “Okay gani nan zuwa” Aje wayar yayi ba tare da ya sake furta komai ba, ya zauna kan gadonsa idonsa na duba agogon dake hannunshi, kafin zuciyarsa ta ayyana masa karanta rubutun da yaki yardar ya bude tun bayan da ya karbi files din ya dauko pen ya saka hannu a duk inda ya kamata sannan ya maida takardun ya aje ya yana busar da iskar bakins. Ammy ce ta leko dakin ta tsaya daga bakin kofa tana kallon yanayin ďanta “Aliyu” Ya dago idonsa da kwalla ya tara har ya kwanta ya kalleta, cike da karfin hali irin na masu juriya ya sakar mata murmushi ya sauke kansa kasa, ba karamin tashi hankalinta yayi ba ganin danta a cikin damuwa ma wani babban abun tashin hankaline a gurinta balle kuma ace ta yi arba da kwalla a idonsa. Karaso ta yi kusa da shi ta zauna cikin murya irin ta masu rarrashi ta ce. “Ina tunanin baka da wata abokiyar shawara ko wanda zaka fadawa damuwarka idan wata matsalar ta same ka a duniyar nan sama ni, fada min Aliyu me yake damunka?” Babban dan yatsansa ya saka ya tare hawayen idonsa ya juyo yana murza idon. “Abu ya fada min a ido yanzu” “Idan akwai abun da na tsana a duniyar nan to ganin hawayenka ne Aliyu, ace yau na ga hawaye a idon ďana kuma na gagara sharesu, ka fada min danuwarka dan Allah” Cikin wani irin rudu da rigici na uwar da ta damu da danuwar danta Ammy take tambayarsa muryarta na rawa kamar zata saka kuka. Yayi saurin juyowa ya kalleta tana murmushi “Ammy ba komai i promise” “Saboda Mai Martaba ko? Na san ya tsaurara zan kuma sake yi masa magana idan ma rabuwa zai yi da kai fine” “Subhanallahi, shekara talatin kika yi Ammy kina jiran ranar da Mai Martaba zai kula da ni ya nuna damuwarsa a kaina, a yanzu Lokacin ya zo sai kuma ki nemi bata lamarin? Ke kika yawan fada min cewar na bi Mai Martaba ko dan saboda na samu aljanna, taya yanzu kike nuna min hanyar bijeri masa? Yardar Allah tana tare da yardar iyaye haka yardar iyaye tana tare da yardar Allah, ana bin umarnin Allah sama da na kowa kuma Allah shi yace abi iyaye, sannan ana bin umarnin Iyaye matukar be tsaba umarnin Allah ba, umarnin da Mai Martaba ya ba ni be tsabawa unarnin Allah ba, kuma ina tunanin haka ne saboda kara martabar gidansa da kuma tawa, abun da nake ganin ya fi kawai ki taya ni da addu'a Allah ya ba ni ikon jurewa da karfin halin bin umarninsa” Hawaye ya cika idon Ammy har ya sauko masauki a kumatunta, babu komai a zuciyarta sai tausayin ďanta, tun tasowar Abiey be san wani abu farinciki mai daurewa ba, ya taso cikin bakinciki da wulakancin da Uba yake masa, after that ya samu Zahra daga bisani ya rasata ya shiga wata sabuwar damuwar, yanzu kuma ya sake samunta wani abun ya shiga tsakani ga Mai Martaba zai nada shi Sarauta abun da baya so, kuma ya hana shi wasan da yake, daman can Mai Martaba baya son ace jinin sarauta na abun da ya sabawa addini da al'ada. “Da gaske zaka duk wannan Aliyu? Ni ma ba wai bana son aurenku da Zahra ba ne, matsalar da kuke yawan samu da kuma abubuwan da suke faruwa ne bana so, sannan sanadin ta ka san abun da na shekara da shekaru ina boyewa” Hannayenta ya kama ya rike irin yadda yara suke idan suna bukatar abu cikin lafazi mai dadi da kokarin fahimtar da mahaifiyarsa ya soma wanke masoyiyarsa. “Wallahi Ammy Zahra bata san da wannan maganar ba, duk abun da na fada miki na fada ne kawai saboda na samu labarin komai, amman Zahra bata fada min komai ba, dan Allah karki dora mata laifi kuma karki tsane ta akan haka” “Ina fatar hakan” Ta kai hannu ta share hawayen da suka zubar mata. “Yanzu Zuwaira ta kira ni tana min maganar ya kamata a fara hada maka lefe na zancen aurenka da Yasmin” Ji yayi wani abu ya daki kahon zuciyarsa kamar mashi, saurin dauke kai yayi ya sauke numfashi ba tare da ya bari Ammy ta fahimta ba. “Okay ku hada duk abun da ya kamata Ammy, zan baki ATM dina” Ya mike tsaye a kokarinsa na avoiding maganar. “Tace Mai Martaba zai bada kudi, yace komai ake bukata ayi masa magana” Murmushi ne ya subuce masa. “Yasmin ta yi sa'a ta zo a daidai lokacin da zata ji dadi rayuwa, na rayu da Zahra ta so ni ba dan wani abu nawa ba, daga baya kuma ta rasa ni bata taba so na saboda wani abu da nake da shi ba” “Yasmin ma bana tunanin tana sonka saboda wani abu naka Aliyu, yarinyar tana da tarbiya idonta be yi budewar da abubuwan duniya za su fara kawatuwa a zuciyarta ba balle har su yi tasiri” “Amman Zahra tana son abun da zai kawo min kwanciyar hankali, ko kuwa tashin hankali ne ita a gurinta, any way Allah ya zaba mana abun da ya fi zama alheri ina tunanin Sauban yana waje yana jirana bari na same shi” Kamin Ammy tace komai ya nufi kofar fita dakin ta bude ya fice. Sun samu awa daya a tsaye shi da Sauban yana labarta masa abubuwan da suka wakana tsakaninsa da Dr Zainab, halin da Zahra take ciki da kuma abun da yake tunanin shi ne mafita a garesu a yanzu. Sauban ya gyara jinginar da yayi mota yana kallon Abiey ya ce. “Amman kana ganin wannan abun ya isa ya saka Zahra ta amince da aurena kai tsaye?” “Tun farko zuwa ba zaka je mata ta siffar rarrashi ba ne, kai tsaye zaka tafi mata da barazanar hakan zai tsoratar da ita ta amince, sai dai bayan ka yi magana da ita ni da kai da Dr Zainab ina son zamu je mu samu mahaifiyarta mu yi magana da ita” “Ina fatar hakan ya zama mafita, amman zata yi mamakin yadda aka yi na ji” “Zata yi mamaki, sai dai zamu batar da mamakin nata, kuma mahaifiyarta zata taimaka mana ina tunanin, domin idan muka fito mata kai tsaye ba zata yardar ba, zata fara baka wasu sharudai akaina da kuma mutane kamar yadda ta baka da farko” Sauban kallon shi kawai yake yana maganar har ya kai aya, sannan ya jingine maganar ya dauko wata. “Abiey ina fatan hukuncin nan da Mai Martaba ya yanke maka be yi sauri ba” Abiey dake faman maida numfashi ya ce “Yayi Sauban, amman ina fatar samun sauki a gaba kuma ina fatar hakan ya zama silar warware abubuwa da dama, ina son na yi masa biyayya ne saboda Ammy da Zahra kuma ina son ni ma idan na sake bijiro masa da tawa bukatar ba zai ce min aa ba” “Muna wannan addu'a, Allah ya yaye maka damuwa Abiey” “Amin thank you” Ya amsa da murmushi yana jin dadin yadda abokinsa ya zame masa kamar dan'uwa. ZAHRA POV. Bayan gama sallah azahar ina zaune ina nazarin gargadin da Mama ta yi min na cewar na kauce kuma na dauke ido akan mijin Hajiya Jamila tun da har ta fara nuna min bata tun kamin lamarin yayi nisa, sai dai na rasa yadda zan yi na kaucewa hakan domin duk wata hanyar da zan hango ina ganin kamar mafita sai na ga ba mafitar bace, domin Mr Bashir ba zai aiko yana kirana na ki zuwa ba, na zai tambaye wani abu na ki fada masa ba. “Amman Mama kin san ba zan masa ba zan je ba idan ya kira ni, ni ban san ya zan yi ba” Mama ta matsar da plate din abincin dake gabanta ta ce. “Anya Mutumen nan be gane gaskiyar abun da ke tsakaninki da Jamila ba? Ina ganin kamar yana gwara kanku ne ke da ita” Na bude baki irin na mamaki. “Kai... Ai da ya gane da yanzu ya rufe mu, musamman ni kara ita matarsa zai iya daga mata kafa amman ni ina dalilinsa na rufa min asiri? Da ya gane da yanzu wani case din ake ba wannan ba, ai da ba zai tsaya yana min dariya ba” “Idan kuwa ba haka ba ne, to ina tunanin ya fara sonki, cikin biyu dole ayi daya, idan ba shi ba me zai saka yace a hade abinci a can kuma har ya bukaci ki yi musu girki daga karshe yace za a nema miki makarantar koyon girki?” “Hmmm Mama Wallahi kara ma ki tubarwa Allah miye Mr Bashir zai yi da ni? Kalleni fa” “Abiey ma da ya fisa kurciya ya so ki balle shi, kuma shi farin jini ba daga nan yake ba, zaki ga mutum mummuna amman ana sonshi wani kuma ga kyaun ga farin jini, wani kuma ga kyaun ba fari jini, amman ke kina da wannan baiwar yana da wahala ki shiga guri ki fita wani be ce yana sonki ba, yanzu ba ki lura da yadda Sauban ya rufe ido ya take abotar dake tsakaninsa da Abiey ba ya dage yana sonki? Haka nake tunanin Alhajin nan ma ya fada” “Tabb ai Wallahi Hajiya Jamila zata iya kashe ni, daga ganin wannan matar tana da zafin kishi sosai” Ashe sara na yi akan gaba ina rufe baki Hajiya Jamila ta banko kofar dakin ta shigo babu ko sallama, daga ni har Mama kallonta muke, a take kirjina ya hau bugawa domin alamunta sun nuna ba da alheri ta shigo ba, Mama ce ta yi karfin halin yi mata magana. “Hajiya Allah ya sa lafiya?” “Ina lafiya, yarki na kokari kwace min miji? Ai baki fada min cewar haka yarki take ba da ban aje mu a gida ba, daman dan adam haka yake ka yi masa rana yayi maka dare” Mama ta yi murmushi irin na manyan mutane masu tsayawa su yi tunani kamin yanke hukunci. “Hajiya Jamila bana son ranki ya bace akan abun da ya faru, kuma bana son ki yanke hukunci cikin fushi, kishi gaskiya ko wace mace dole ta yi kishi akan mijinta balle kuma ke da kike da miji kamar Alhaji Bashir babban mutun, amman idan kin duba a halin da Zahra take ciki a yanzu ba soyayya ce a gabanta ba” “Ba zan iya gane wannan ba, ke da ita ban san abun da kuke shiryawa ba, so kuke ku mayar da ni shashasha yarki ta aure min miji ku mallake shi saboda na kawo ku a babban gida ido ya bude, to Wallahi tun wuri ki jawa yarki kunne bakin rijiya ba gurin wasan makaho ba ne, akan miji zan iya komai Wallahi ban yarda wata mace ta zauna da miji ba ko na minti daya, daman ai talaka be iya samun guri ba daga kawo ki sai ki saki jiki kina masa magana kala kala har da wani tahirin mijinki ya mutu ciwon hanta ne ya kashe shi? Wai ke ala dole ya kula ki....” A fusace na mike tsaye ina kallonta rai a bace. “Ya isheki haka Jamila, kar fa ki manta ke kika nemi mu dawo gidan nan mu zauna saboda bukatarki, kuma a cikin sharudan da muka gindaya miki kika dauka babu cin mutunci ko cin zarafi a ciki, kuma wannan fadan mijinki ya kamata ki yi ma shi ba mu ba, domin idan be kira ni ba, ba zan je ba kuma idan be tambaye wani abun ba ba zan fada masa ba, kishi ba hauka ba ki daina yarda zuciyarki tana fin karfinki akan abun da be taka kara ya karya ba” “Ke har kin isa ki fada min abun da zan yi da wanda ba zan yi ba akan mijin? Waye ke? Ke kama kanki saka masa gishiri langaɓu tsada yake, na fi karfin ki yi min wannan Wallahi, kuma na miki kadaidi na farko kuma na karshe akan mijina, ko ido kika sake dagawa kika kalli mijina sai na baki mugun mamaki” Na kada ido na rausayar da kai ina mata kallon rashin mutunci da tsageranci na ce. “Ko yanzu mijinki ya aiko kirana sai na tafi, idan har kin isa da shi miyasa baki hana shi ba, sai mu da kika raina zamu zo kina mana masifa kamar wasu bayinki? Taimako kika nema kuma aka yi miki ba bara ko roko muka zo gidanki ba, kuma ke arziki yake tsokarewa ido har kike gani wata zata iya neman shiga gurin mijinki saboda ta samu aurensa akan dukiyarsa, dukiyar da saka kika saye dan wani a matsayin nasa, ni kudi baya burge ni” “Karki kike, kudin da kika siyar da rayuwa saboda shi zaki ce baya burge ki? Kudin da suka saka aka rushe gidan da kuke zauna sanadin haka aurem uwarki ya mutu na buku umarni kuma kuka bi kuka dawo gidan nan da zama saboda kudi? Kudin da ya saka kika zauna a kujerar dinning dina a dazun kina maganar da ban san ta micece ba da mijina? Ko kike cewa ba ki son kudi? Bari ma miki gargadi na karshe akan mijina zan iya hada yakin duniya na uku Wallahi, babu mace da ta isa ta zauna da mijina matukar ina numfashi, ba dan rainon wayo ba taya zaki zauna a kujerata kina fuskartar mijina kina masa labari ke wai tsaya ma me kuke tattauna ne?” “Yadda zan fitar da ke a gidan na shiga na zauna, ba mallake duk wani abu da kike takama da shi, Jamila ko da kika dauko ni ba a talauci kika gan mu ba” Na bata amsa cikin tsiwa ina girgiza jiki kamar gaske. “Karya kike Wallahi, ke kin san matan da na zauna da su suka bar min miji balle ke? Maganin da kika yi ma Sauban mijin kanwata ya kama shi ni ba zai kamani ko ya kama mijina ba, sannan ina son ku tattara komai na ku ku bar gidan nan kamin dare, taimakon na fasa tun da abun ta zama iskanci” Magana take tana hakki Hajiya Jamila irin matan nan ne marasa mutunci, irin matan da suke manta alheri a take, jikinta har rawa yake tana matso ni kamar zata kai hannu ta dake ni, kuma da zata taba ni da zata iya kai ni a kasa ta danne domin tana da lafiyayyen jiki irin na manya mata, ba kamar ni ba da za a iya sacewa a gudu. Mama ce ta yi hanzarin shiga tsakiyarmu. “Barin gida Hajiya Jamila zamu bar shi, amman ina son ki tuna cewar ke kika nemi taimakon Zahra ba mu muka nemi haka ba” “To yanzu bana bukata, waya sani ko wani asirin kuka ma yaro yaki ya kama nonon kowa sai na Zahra, da yardar Allah babu abun da zai same ni, ki ja yarki ku bar mana gida tun wuri” “Zamu tafi, amman kar wani abun ya same ki ce zaki waiwaye mu, ba ke ba yata daga yau” “Daman ai hanyar motar dabam da jirgi dabam” Ta juya a fuce ta fice daga dakin, ni kuwa na hade hannu cikin isa na ce. “Babu inda zamu je, sai a yanzu da take ganin ta gama amfana da ni zata ce ta wulakanta mu” “Saboda me? Ai gidanta ne ita ta kawo mu, yanzu kuma ta bukaci mu bar mata gidanta a dole mu bar mata gidanta, amman ki sani baka maciji baya cizon mumini a rame daya har sau uku, ta yi na farko an yi mata uzuri ta yi na biyu mun tausayawa mata to ba za'ayi na uku ba” “To yanzu Mama ina zamu koma Fisabilillahi, kina ganin Baba har yanzu be sake waiwayarmu, kuma mun yi ma mutane karya cewar ta ba mu guri mu zauna sai kuma yanzu mu ce ta koremu” Mama ta fita dakin ba tare da ta ce min komai ba, kayan da muka bata na abinci ta hade guri daya, ta dawo ta shiga bandaki ta wanke jikinta ta fito ta shirya ta saka hijabinta ta dauki jakarta sannan ta kalleni ta ce. “Ki zauna a dakin nan karki je ko'ina ko ta sake dawowa tana miki masifa karki kula ta” “Ina zaki je Mama?” “Gurin yan'uwana zan tafi, sai na dawo” “Allah ya kiyaye” Na mata addu'a ba dan daina ya so tafiyar tata ba. Bata wuce minti talatin da fita ba na dauki waya na kira Sauban na sanar masa ina son ganinsa. “Amman idan ka zo karka shigo cikin gidan ka tsaya daga waje, zan fito na same ka” “Amman lafiya?” “Ina son mu yi magana ne akan wani abun” “Ni ma ina son magana dake, gani nan zuwa” “Sai ka iso” Na dauke wayar daga kunne ina jin bakincikin amincewa da na yi muka dawo gidan da zama tun tashin farko, iyakar kokari mun yi na bin dokarta sai dai na lura Hajiya Jamila mace ce mai son milkin kowa ta juya kowa yadda take so kuma ta murje ido kamar ba ta yi ba, alkwarin da ta dauka da dokokin da muka gindaya mata da yarjejeniyar da muka yi kamin na dawo gidan da zama a yau duk ta matasu. [11/24, 7:23 PM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣9️⃣ A waya ya sanar da ni cewar yana waje, sai na saka hijabina na janyo kofar na rufe na fito ina ta tararar bangaren Hajiya Jamila, masu gadin shka bude min kofar na fice. Nesa da gidan ya faka kamar yadda na fada masa tun kamin na karasa inda motar take fake ya bude min front seat. Ina zaunawa sai ya kalleni da murmushi a fuskarsa. “Kullum kyau kike karawa ban san miye sirrin ba” Ban shiryawa murmushi ba wannan yasa ban yi murmushin ba, domin ba shi ne a gabana ba yanzu, sai na nade hannayena na juyar da fuska ina kara bayyana fushi. Leko fuskata yayi sai ya aje wayar hannunshi ya gyara zama. “Zahra akwai wata matsala ne?” Na daga masa kai ina mara turo bakin gaba. “Ba Hajiya ba ce ba” “Wace Hajiya?” “Jamila mana ba ma zan sake cewa Hajiyar ba” Yayi murmushi. “Lemme touch kayan Abiey” Sai hannunsa na ji a fuska ya juyo da fuskar tawa yana kurawa bakina ido kamar idon nasa za su yi magana. “Miya faru?” Hannu na saka na dauke hannunsa kan fuskata. “Jamila ce tace mu bar mata gidanta” “Saboda me?” Daki-daki na tsara masa abun da ya faru, kallona ya sake yi da murmushi a fuskarsa. “Mijinta yake sonki ne?” “Ina fa, kawai tana da karamin kai ne bata gane komai idonta rufewa yake” “Idan ba sonki yake ba mi zai saka yayi haka a gabanta” Na kalleshi. “To ko so na yake?” “Ke baki sani ba ya za'ayi wani ya sani? Amman ina ji miki tsoron ranar da zai gane gaskiya bana tunanin zai kyale ki, abun da nake ganin ya fi tun a yanzu ki yi aure inuwar aure zata baki kima da martaba, kuma kin ga ita kanta Jamila hankalinta zai kwanta dake kuma mijinta ma dole ya kyaleki” Magana yayi min mai halshen damo, kamar ya idan ya gane gaskiya? Gaskiyar me? “Ni ban shirya aure yanzu ba, yaushe aurena ya mutu da zan ce na yi wani, kuma ba ni da wani da zan iya aure a yanzu” “Baki san musulunci ya yarda aurenki ya mutu da safe idan kin cika idda da rana a daura miki aure da dare ba? Musamman irin aurenki da haihuwa ce iddarki, karki damu da abun da mutane za su fada karki haramtawa kanki abun da Allah ya halal ta miki” Shiru na yi ina kallonshi har yanzu mamakin furucinsa na dazun nake. “Me kike tunanin ina zuwa yi gurinki? Me yake kawo ni? Kula dake right?” Na daga kai. “Bayan wannan zuciyarki bata raya miki wani abun ba? Miyasa yake kula da ni, wannan kulawar ta yi yawa” “Ka ce saboda na rage damuwa” “Yeah saboda ki rage damuwa amman ai ba kekai kike cikin damuwa ba, miyasa ban kula wasu ba sai ke? Akwai wadanda suka fiki shiga matsala” “Miyasa ni kake kula ni?” “Saboda ina sonki...” Ya fada min kai tsaye murya kasa kasa yana matso da fuskarsa kusa da tawa. “Sauban ni ce fa” “Na sani, na dade ina jiran zuwan wannan ranar ranar da zan fada miki gaskiyar abun da yake zuciyata, Zahra na dade da kaunarki a cikin zuciyata, sai dai ba ni da wata damar nuna miki saboda hankali yana gurin Abiey a da na hakura dake saboda abokina, sai dai kaddara ba barku kun zauna da juna ba, na san Abiey zai iya yin sakarcin hakura dake ya barwa Deen da ban bari soyayyarku ta yi karfi ba, and now Deen ya mutu Ammy da Mai Martaba sun shiga tsakaninki da Abiey, and now ga wannan matsalar ta taso kina tunanin kina da wanda zaki aura sama da ni” “Sauban ko wani abu ka sha? Kai fa abokin Abiey ne?” “Idan ni abokin Abiey ne dai na haramtawa kaina abun da Allah ya halatta? Karki damu da idon da zan kalli abokina da su ko ya mu'amalarmu zata kasance, kamin na fara zuwa gurinki sai da na sanar da Abiey, after mun fara shakuwa da juna na sanar masa kudina saboda bama boyewa juna sirri ni da shi, kuma ya nuna min ya jidadin haka, har ya fada min zai fi kowa farinciki idan Zahra ta yarda da aureka, ko ba komai kusancimu zai karu kuma na san zaka rika ta tsakani da Allah” “Wata kila ya fada maka haka ne, saboda yana kaunarka a matsayinsa na abokinka, baya son ya nuna maka damuwarsa ranka ya bace, amman na tabbatar Abiey yana so na, kuma dole zai ji kishi idan aka ce muna soyayya ma balle kuma ace na aure ka, ba zan iya haddasa masa bacikin ba, ba zan iya cin amanarsa ba” Na fada hawaye na rige rigen sauko min, lallai na yarda dan'adam butulu ne yanzu duk amincin dake tsakanin Abiey da Sauban ace Sauban zai iya tunkarata kai tsaye ya fada min cewar yana kaunata wane irin so ne wannan da zai saka ka manta aminci da abotar dake tsakaninka da amininka ka murje ido ka aure budurwarsa. “Ki tsaya ki yi tunani Zahra karki yanke hukunci cikin bacin rai, kuma ki duba halin da zan shiga idan kika amsa min da a'a” “Babu wani hali da zaka shiga domin babu komai a zuciyarka sai tsantsar budulci, karka sake ganinka a kusa da ni, kuma kar ka sake kiran wayata ko ka bi a gurin da na bi, idan ka sake min wata maganar sai na sami Abiey da kaina na sanar da shi abun da kake shiryawa” Na bude motar na fice a fusace, sai ya bude bangarensa ya fito. “Kamin ki sanar da ni abun da kika shirya zan riga ki sanar da Mr Bashir abun da kika shirya ke da matarsa, sannan na sanar da Mahaifan Deen abun da kika boye musu” Cak na tsaya gabana yayi dukan shida shida, na juyo a matukar firgice na kalleshi. “Kin siyar da ďan cikinki saboda ki ceto rayuwar Deen, kin hada kai da matarsa da yayan matarsa kin mallaka masa ďanki a matsayin nasa, ya kike tunanin zai ji idan ya gane gaskiyar dan da yake alfahari da tutiya ba nasa ba ne? Wane irin hukunci kike tunanin zai yanke miki? Idan ma ya kyale ki yan jaridu da Mahaifan Deen za su saka miki ido ne? Kin ga daga lokacin kin bata sunanki da sunan danki kuma kin yankawa kanki tikitin zuwa gidan yari, wata kila ma zuciyar Mr Bashir ta buga ya mutu a daureki” Na tako na dawo a inda yake tsaye hawaye na sauko min kamar ba gobe. “A ina ka ji wannan?” “A gurin wanda kuka nemi ta rufa muku asiri ta boye sirrin, wannan abun da kika aikata ya saka Abiey da Ammy da ita kanta Dr Zainab suna murna da yi ma Allah godiya da baki auri ďansu ba, idan kika san yadda Abiey ya tsane ki a yanzu saboda abun da kika aikata sai kin gode Allah da ya saka ba ku ganin juna a yanzu” “Ba da son raina na aikata hakan ba, talauci ne ya saka ni haka” “Yan jarida zaki yi ma wannan bayanin, rai ya fi rai ne da zaki da zaki siyar da ran da be miki komai ba, tun kamin ya zo duniya? An fada miki talauci hauka ne? Talauci ke saka rai fita daga jiki ne? Ko kuma kina tunanin arziki zai hana mutuwa aiwatar da aikinta ne? Da kika samu kudin kika biya ya tsaya ne? Sai kika yi biyu babu da ace kin yi tawakkali ki bar wa Allah komai da yanzu ba ki shiga wannan halin ba” Ba ni da wata dabara sai ta kuka har numfashina yana kokarin fin karfina, cikin saldewar halshe na ce. “Sauban baka da wannan kusanci da zaka nemi wargaza rayuwata ko da Mr Bashir akan abun da be kamata ya shafe ka” “Da gaske? Baki san ina da kusanci da mutanen gidan ba? Ranar da na shiga cikin gidan na zauna a falo har na aika aka kiraki ba ki yi mamaki? Jamila yaya ce a gurin matar da nake aure a yanzu, ko Matata kadai na sanarwa zata iya ruguza komai naki, saboda haka ina baki shawarar ki yi tunanin abun da zai zame miki mafita tun wuri wanda zai fitar da dake daga taskon dana sani, kwana biyu na baki ki yi shawara” “Ba zan aikata abun da kake bukata ba, ba zan yarda na yi butulci ba” Na bashi amsa da kakkausar murya sannan na juya na nufi kofar gidan na shiga na bar shi a tsaye. Ina shiga daki sai an samu yancin yin kuka yadda raina yake so, ina nadamar abun da na aikata, gashi sanadin haka na jefa mahaifiyata cikin tashin hankali ni ma kuma na jefa kaina, har ana min bazarana da shi, a cikin kalaman da ya fada min ba wanda ta fi daga min hankali da saka ni bakinciki kamar cewar da yayi Abiey ya tsane ni saboda abun da na aikata. Na yi zaton Sauban zai sauya shawara ya kyale ni amman sakon karta kwana na gani ya shigo a wayata da sunansa. “Ki yi shawara da zuciyarki, karki yarda ko Mama ta san da wannan maganar, Wallahi Zahra kin ji na rantse miki da Allah ko? Son da nake miki zai iya sakawa na aikata komai a yanzu, fiye da abun da Deen ya aikata ya shiga tsakaninku da Abiey, kuma ina mai kara tabbatar miki kwana biyu na baki karki yarda ki bijirewa umarnina, idan ba haka ba zaki jefa kanki a babbar matsala” Ban yi zaton wata matsalar zata bullon min a bayan wannan da nake ciki ba, da san abun da Sauban zai zo min da shi kenan da ban yarda na kira shi ba, kuma a lokacin da ya zo da ban yarda mun hadu ba. Ko da Mama ta dawo ta tararda ni kwance galala na ci kuka har na gode Allah idanuwana sun yi sundun sundun, daman can bana dauka abu da wasa balle kuma wannan, yaushe Sauban ya lalace ya fara gurbata tunaninsa har zuciyarsa ta daya masa yayi min bazarana da wannan, da gaske zai aikata abun da yake da kudiri akai idan na ki amincewa ko kuma dai ya fada ne! Na rasa amsar tambayar tunani da tashin hankali suka ki sakin kwakwalwata, duk juyin duniyar da Mama ta yi na fada mata dalilin kuka ban fada mata ba, a lokacin da na lura da ta damu sai na fake da cewar korar da Jamila ta yi mana ne ya saka ni kuka, Mama ta yi ta tausasar zuciyata sannan ta yi min albishir da cewar gobe zamu koma gidansu da zama wato family house dinsu da muka baro, kamin a samu gidan haya. Ana gama sallah Magariba sai ga Dr Hamid ya shigo gidan, kamin ya shiga bangaren Hajiya Jamila ya kira ya sanar da ni yana waje kuma yana son na nema masa izini gurin Mama zai shigo yayi magana da ita. Na sanar da Mama ta bada umarni sannan na fada masa sai yace na fito na yi masa iso, ba tare da tunanin komai ba na saka mayafina na fito, sai na same shi a inda ya saba tsayawa, cikin rashin kuzari irin na wadanda suka rasa madafa na karasa gurin na yi sallama ya amsa min, muka gaisa sannan ya mika min ledar hannunsa. “Aa na gode” “Allah yasa ba laifin da kanwata ta yi zai shafe ni, na kira na sanar da ita cewar ina nan zuwa sai ta fada min irin kwabar da ta yi” “Tana da gaskiya wani gurin ai, ko ni ce ba zan yarda mijina ya kula wasu ba” “Ashe ke ma kina da kishi kenan, ki ce na shirya wa kishinki ba sauke kenan” Na sauke kai kasa cike da tunanin manufar furucinsa, dariya ce ta biyon bayan maganar da yayi sannan ya dara da cewa. “Ko ma dai minene bata kyauta ba, kuma ba ta yi abun da ya dace ba, ai hallacin da kika yi mata ko da mijinta kika ce kina son auren be kamata ta daga ido ta kalleki ba balle har ta nuna kishinta akai, amman dai na yi mata fada sosai kuma na nuna mata illar abun da ta aikata, na kwantar mata da hankali na fada mata cewar kina da wanda zaki aura Allah yasa ban yi karanbani ba” Wannan karon da kamar zolaya yake maganar, ni kam tawa ma ta isheni yanzu ba zancen tashin gidan ko wulakancin Jamila ne a gabana ba, matsalar Sauban ce data kunno min take chaja min kwakwalwa a yanzu. “Zahra kamar akwai damuwa sosai a tare da ke” “Ba komai” Na amsa ina saka hannu na share hawayena. “Ki kwantar da hankalinki ba, zamu cigaba da zama nan na wani lokaci kawai ba sai an dade ba” “Ba zai yiyu mu zauna ba, Mama ta riga ta yi magana da Yan'uwanta za su sama mata gurin da zamu zauna na gode da kulawa” “Shiyasa nake son na yi magana da ita, wata kila zata fiki fahimta da saurin saukowa” Na daga kai na kalleshi a kaikaice. “Na yi nadamar duk wani abu da na yi Dr Hamid, da ban yarda zan iya ceton rayuwar da ba a hannuna take ba da yanzu ban shiga duk wannan halin ba, na kasa ganewa talauci ya saka na aikata abun da na aikata ko kuma wauta da rashin yardar da kaddara” “Idan har magana kike ta yarda da kaddara to ya kamata wannan kadarrar ma ki yarda da ita ki watsar da komai ki dauka haka Allah ya hukunta miki a yanzu ma ki rumgumi komai da hannu biyu, kuma ina mai tabbatar miki komai zai wuce nan ba da jimawa ba” “Ina fatar haka, ni kadai na san abun da nake ji a zuciyata, ji kadai na san halin da nake ciki, na rasa abubuwa da suka kamata su kasance da ni, na ruguza farincikina da kaina, na rasa makama, da ban aikara abun dan na aikata ba da kanwarka bata zarge ni akan mijinta ba” Na durkushe a gurin ina jin zuciyata na mini wani irin zafi da zogi na azabar bakincikin da nake ciki. “Ba ke kika bukaci zama a gidan nan ba, Jamila ta janyo ki saboda haka babu laifinki idan mijinta ya nuna miki kulawa, kuma ai ita da bakinta ta fada cewar mijinta yana neman hanyar da zai saka miki da abun da kika masa, shin tana tunanin zai rika daure miki fuska ne ko kuma ya kareki? Daman can Mr Bashir mutum ne mai son mutane, kar abun da ta yi ya dame ki” A tunaninsa ina kuka ne saboda abun da Jamila ta yi min ne kawai, na haka na kaune kashina daya tsaya min a wuya na share hawayena na masa iso gurin Mama, a gaban ya aje ledar hannunsa sannan na durkusa har kasa yana bata hakurin abun da kanwarsa ta yi, wata kila ya cilasta shigowa bangarenmu ne domin yana tsaka da bata hakurin Hajiya Jamila ta shigo ita na ta soma bata hakuri sannan ta dawo kaina tana neman yafiyar abun da ta yi min. Uffan ban ce mata ba domin bata da kimar da zan iya yi mata wani furucin a yanzu, Mama ma ina tunanin ta hakura ne kawai saboda Dr Hamid dake ta yi mata magiya, sai dai hakurin da ta yi ba yarda ta zauna a gidan ba ne ta tabbatar musu da cewar ta hakura amman zancen tashi yana nan domin ta sanar da yan'uwanta. “To ko dai sai na kira Mijina ya baku hakuri ne” “Baki bukutar haka ranki ya dade, ai na riga da na hakura, amman idan na ce zan zauna a yanzu ai abun ya zama da rainin hankali yan'uwana ma za su ga kamar na mayar da su kananan mutane” “Zan iya zuwa da mijina mu ba su hakuri” “Hajiya ba sai kun yi haka ba, zuwan ku zai kara bata lamarin ne kawai domin ban fada musu cewar kin kore mu ba, kawai dai na fake da cewar ina son na bar gidan ne saboda tsare tsaren gidan basa min dadi” “Mama idan haka ne ai zamu iya zuwa mu baku hakuri mu ce su lallaba ku zu zauna, ni kaina ba wai ina son ku zauna na lokaci mai tsawo ba ne, zaman ku a nan ba zai wuce wata daya ba, na miki alkawari Mama zan sama muku gidan da zaku zauna na kanku, ko bayan ni Mr Bashir ma bana tunanin zai barku haka” Da ďaďan kalamai da kallamewa da komai suka tirsasa Mama da amince da zama a gidan, bayan Dr Hamid yayi alkawarin zai dauki yar'uwarsa su tafi har gurin dangin Mama su ba su hakuri da neman su barsu su cigaba da zaman gidan. Kamar yadda ya fada washe garin ranar Dr Hamid da Hajiya Jamila suka saka mu a mota ni da Mama zuwa family house dinsu, su kansu su yi na'am da Dr Hamid da kuma kanwarsa a tunaninsa tana son mu ne tsakani da Allah ba dan wata manufa ba, sai bawa suke suna saka musu albarka. Goma ta arziki Dr Hamid yayi musu sannan muka fito gidan, a hanyar mu ta dawowa gida na ke jin Jamila na fadawa Dr Hamid cewar mijinta yayi balaguron wani aiki na kwana biyu, da muka dawo gidan yana ta kara bawa Mama hakuri, ni kam na zama kamar wani hoto domin babu wata wadatacciyar walwala a tare da ni, hirar da zan iya cewa ma tursasa ni yayi ma tsaya ina yinta ba dadi take min ba. Ban dauka da gaske Sauban yake ba har sai da na lurar da barazanarsa na kokarin yin yawa, domin kullum sai ya turo min sako yana kara jaddada min kudirinsa, idan na koshe wannan line sai ya aiko min da wani, daga baya sai na kashe wayar gaba daya na aje, da ya fahimci na daina amfani da wayar sai ya koma aiko min sako ta hanyar masu gadin gidan, kamar wani dan'adan haka Sauban ya rikide min ina ta mamakin abun da ya same shi har haka. [11/24, 10:14 PM] Oum_Nuwaira🥰: 6️⃣0️⃣ Na dauki damuwa da tunanin abun na saka a raina har ta kai bana iya zaunawa na ci abinci yadda ya kamata, ga kuma tsutsata da Amir yake sai ya kara sakawa na zama wata yar tsana daman can ba wani abun kwarai ke a jikin ba balle kuma yanzu da bana da wani abun yi sai tunani da neman mafita, idan kuma na nemi shawarar zuciyata sai ta fada min na amince da kudirin Sauban gudun kar na sake jefa kaina da mahaifiyata a cikin wata damuwar, Dr Hamid ma yayi ta neman sanin abun da yake damuna amman na gagara sanar da Mama ma balle kuma shi da nake ganin ba shi da wata alaka da ni. Sati daya na sakwana bana komai sai addu'a da raya dare da sallah nafila ina neman Allah ya kawo min mafita sai dai ban ga alamar bullowar wata hanyar ba. Ranar da muka cika kwana takwas da maganar Sauban ya sake zuwa gidan ya faka a harabar gidan ya aiko yana min sallama, ina jin sunansa gabana ya fadi domin na san ba alheri ne ka kawo shi a yanzu ba, tun daga wacan lokacin da yayi min barazana zuwa yau idan ya sallamo a gidan sai na ji kamar na haka rame na binne kaina na huta, a yau sai na kekashe kasa na ce ba zan fito ba. “Saboda me? Tun farko ba sai da na gargade ki akan zuwa gidan nan da yake ba? Da mai gidan yayi miki magana kika masa magana a wajen gidan kuke tsayawa, yanzu kuma ya riga ya shigo cikin gida ki ce ba zaki fito ba?” Na yamutsa fuska cike da damuwa, kalaman na ratsa ni. “Idan ma baki son zuwan gidan nan sai ki je ki sallame shi daga yau sallama ta har abada, kin ga daga nan zai daina zuwa, daman can na fada miki ba son zuwanshi nake ba” Na nisa ina tunanin tafiyar tawa, domin ban san da wacce ya zo ba tun da har ya iya shigowa cikin gidan kai tsaye bayan kuma na fada masa ba sau daya ba cewar Mai gidan baya son ganinsa a cikin gidan. Tashin hankali da ba a saka masa rana inji hausawa, sai kawai na ji sallamar Sauban a bakin kofar dakinmu, da sauri na dauki Hijab na saka domin kokarin shigowa yake tun kamin a masa izninin shiga. Mama ma ta tashi ta sauri ta gyara zamanta daman bata rabo da hijabi tun da muka dawo gidan. “Wa'alaikassalam” Mama ta amsa masa, hakan ya bashi damar matsowa sosai kusa da labulen kofar yana tambayar. “Mama barka da dare, ko zan iya shigowa” Cikin sauri na girgiza mata kai alamar ta ce aa amman ba yi min yadda nake so ba, sai ta bashi umarnin shigowa. “Eh Bismillah” Sallama yayi ya shigo cikin dakin ya zauna kusa da kofa ya gaisa da Mama. “Sauban ka tafi gani nan zuwa” “Wannan zuwan ba naki ba ne ke kadai, na zo ne har saboda Mama, saboda na gaji da yawo da hankali da kike min” A kaikace na kalleshi ina mamakin yadda zai buga min wata kwallo a ragar da ban san da zamanta ba. Kamin na yi wani unkuri ya fara shimfidawa Mama karyar da ta daure ni da manyan tsarkoki da ba zan iya kwance kaina ba. “Mama ina son magana dake ne saboda abun da Zahra ta yi min, kuma ina son ki yanke hukunci tsakani da Allah karki duba kusanci da Zahra ko rashin alakarki da ni” Yayi shiru ni kuma na zuba masa ido domin na ga iya gudun ruwansa, Mama kuma ta gyara zama ganin babu wasa a tare da shi sai zallar tausayi da ke fita a muryarsa. “Mama tun ba yau ba mun yi magana da Zahra, magana kuma ba ta soyayyar ba ce ta aure ce, kuma da farko ta nuna min kamar babu matsalar komai, sai daga bayan nan take nuna min kamar ke ce baki son tarayya ta da ita, ni kuma a ganina ba haramun ba ne idan kin amince kin bar Zahra ta aure ni, saboda Abiey yayi sonta shi yake nuna ni ta haramta a gurina ba, kuma Mama ba mu san inda Rana zata fadi ba, lokuta da yawa abin da ba a so shi ne alheri wanda kuma ake so sai ya zama ba alheri ba, kwana biyun nan gaba daya Zahra ta canja min hakan ya haifar min da damuwa ba yar karama ba, kullum da kalar dabarar da take bullo min da ita, tace na bata dama ta yi shawara na bata daga karshe sai ta nuna min ita yanzu matsala ba daga ita ba ne daga gurinki ne, shiyasa na zo da kaina na roki alfarma a gurinki ki dube ni a matsayin ďanki, ya zaki ji idan aka ce wata mace ta yi min alkawarin aure kuma har na sanar da iyaye akan Zahra har matsala sai da muka samu da Matata, na san zaki dubi kamar kusancina da Abiey be dace na yi haka ba, amman Mama so ya wuce nan, Abiey ya riga da ya kama gabansa a yanzu an saka masa ranar aure da Yasmin, ko wannan kadai be isa ya saka Zahra ta nemi rufawa kanta asiri ba? Shi kansa mai gidan nan da yake saka mata dokiki kamar yarsa da ace tana da miji ai ba zai fara mata haka ba” Da dai ace gasa ake ta marubuta tabbas Sauban zai karbi Awards a yadda ya tsaya ya marairaice fuska ya kuma shake murya ya tsarawa Mama zancen da ba ne ba. Kamar wata kyanwa haka na zama na lafe jikin ginin dake kusa da katifa ina tunanin yadda zan warware wannan mugun kullun da Sauban yayi min, muna hada ido da Mama sai ta watsa min harara irin wanda ke nuna ko dukana zata iya yi idan Sauban ya bar dakin. “Sauban, Zahra ba ita ke aurar da kanta ba, tana da magabata bangaren uwa da uba, kuma ba wai bana son ka aureta ba ne, aa ina duba abun da zai fi zama masahala ne a tsakaninku kai abokin Abiey ne be kamata ace ka auri Zahra ba, amman tun da har ta nuna tana sonka kuma ta fada maka ni bana da matsala, indai kun sasanta kanku kuma kin ji cewar za ku iya jurewa da maganganun jama'a na wa fatan alheri kawai sai Allah” Mama na rufe baki sai ga Sauban ya kai goshi a kasa yana sujudar godiya, ya dago yana kara yi ma Allah godiya. “Duk da haka dai, a kara tunani Sauban bana son ku jefa rayuwarku cikin matsala, domin Zahra bata da wayo da tunani wani lokacin” “Inshallah Mama na gode Allah ya saka da alheri, kin gani ko Zahra daman ina ta fada miki Mama bata da matsala ke ce dai kika gagara tsayawa ki yi mata bayanin yadda zata fahimta ne kawai” Cikin wasu ruwan hawaye da ban san lokacin da suke kwararomin ba na ce. “Sauban kana tunanin yin haka zai saka na aureka da karfi ne? Na fada maka ba zan iya cin amana ba, ba zan abun da zai zame min ciwo daga baya ba, akan me zaka zo ka shimfidawa Mama abun da ni da kai mun san be faru ba? Ya kake abu kamar yaro karami?” Sakin baki yayi yana kallona kamar da gaske shi ne mai gaskiyar ni ce mai karyar, Mama ta masa nuna taja dogon numfashi ta sauke ta ce. “Sauban je ka waje zata zo ta same ka” “To Mama, amman ina fatar ban haddasawa Zahra matsala ba?” Mama ta yi murmushi ta girgiza kai. “Ba komai shashashanci ne kawai irin na ta” Cike da nuna damuwa ka ya tashi daga dakin, kusa da Mama na dawo na zauna sai na rasa kalaman da zan hada na wanke kaina, harara kawai Mama take watsa min irin wanda na manta rabon da na aikata wani abu da ya bakanta ranta kamar wannan, cikin karfi hali irin na marasa madafa na dago na ce “Mama Wallahi....” Tassss na ji sauka tafin hannun Mama a fuskata, marin da da sai da shatin yatsunta ya kwanta a farar fatar kumatuna. “Shashashar banza wawuya, idan ma bana son alakarki da shi dole sai kin fada masa? Sannan ke ba zaki iya tunanin abu mai kyau ba? Yadda zuciya ta raya miki haka kike? Ina ganin kamar kin yi hankali kin san abun da kike ashe haukarki ma karuwa take? Akan me zaki masa alkawari cewar zaki aurenshi bayan kin san alakar dake tsakaninsa da Abiey? Oh yanzu na gane shi ne dalilin shiga damuwar da kika yi ko abinci ba ki iya ki ci?” Na girgiza kai zan sake magana Mama ta buge min baki. “Rufe min baki, ba dai kin masa alkawarin aure ba? Kuma kika kawo ni a tsakiya kika manna? Amman a nan idan na nuna miki bana son zuwanshi cewa kike ke ma ya zame miki dole ne, ashe kina can kina tsara masa aurensa za ki yi har kina dora laifin a kaina? Tabbas na isa na hana aurenku, daman abun da nake hango miki matsala ne da yadda mutane za su kalleki, amman tun ke baki san Annabi ya faku ba sai ki je ki yi duk abun da kika tunanin mafita ne a gurinki, tashi ki je ki same shi” Na runtse ido na bude ina jin yadda duniya da lamurran cikinta suke yamutsa tunani, kamar tsumma a cikin ruwa haka na mike tsaye jiki ba kauri zuciya babu karfi na fice daga dakin. A lokacin da na hango Sauban jikin motarsa yana jira na fitowata sai na ji kamar ace da bindiga a hannuna na halbe shi ko na huce wannan cikin da ya saka min a yanzu. “I'm sorry, na yi hakan ne saboda na taimaka miki wajen shigar da ni gurin Mama, kuma idan har ba ki son kowa ya san Auren dake zamu iya yinsa a sirrance ba tare da Abiey ko wasu sun sani ba, ni dai ina son kasancewa da ke ne ko da na kwana daya ne” Na data kai na kalleshi da idanuwan da hawaye suka ci karfinsu, daman na dade da lura kamar ba so yake min irin na Allah da Annabi ba domin a cikin sakwannin da yake aiko min ya fi yawan jaddada cewar yana son ya kasance da ni ne ko da na kwana daya ne kamar yadda ya fada a yanzu. A iya tunanina Abiey ba mazinaci bane balle na ta kai ga na zargi Sauban, sai dai baka iya shaidar kowa a wannan zamanin sai kanka, wata kila akwai wani abu da yake burge Sauban a jiki da ya kasa hakura har ya kwadaitu da son kasancewa da ni kamar yadda ya fada, ya sani sarai idan ya zo min da maganar banza ba zan amince ba, shiyasa ya bullo ta wannan hanyar. “Iya barazanar da ka yi min bata wadatar ba? Har sai ka biyo ta wata hanyar da ba zata bulle da kai ba? Da farko na yarda da kai Sauban ban yi zaton zaka zo min da wani wasa ta yara ba, abun da ka aikata a yanzu ba abu ne ya burgewa ba, kuma idan kana tunanin ka yi wayo ne to baka yi, kuma wannan be isa ya saka na amince da mugun kudinka ba” Dariya yayi. “Zahra kenan, wato barazana kika dauki abun da na fada miki ko? To na rantse miki da Allah zan aikata matukar baki amince da kudina ba, ki yi tunanin halin da zaki shiga da kuma wanda ďanki zai shiga, da kuma wanda zaki jefa Dr Hamid, da Jamila balle kuma Mr Bashir da mahaifiyarki, ba fa kudi nake nema a gurinki ba Zahra face amincewarki ki aurene, har na baki dama idan baki son duniya ta sani zamu iya yin abun mu a boye” “Ba zan yi ba, ka je ka yi duk abun da zaka yi, saboda kun maida ni ba ni da kowa sai ku rika juya ni yadda kuke so” Na karasa cikin kuka, sai ya miko min wayarsa. “Duba wannan, ina fatar dai baki fadawa Mama komai ba, kuma baki nemi shawarar kowa ba sai zuciyarki” Ban karbi wayar ba, hakan kuma be hana ni hango takardun gwajin jinin da aka fadada a cikin wayar ba. “Na ki ne da na ďanki, wanda aka saka Dr Zainab ta sauya, sauran na Mr Bashir da matarsa na suna ciki, wadannan original din ne ba fake din da aka bashi ba, ita kanta Dr Zainab bata san na dauki wannan ba domin ita ma zai jefata a matsala idan har Mr Bashir ya san gaskiya” Guiyoyina ne da suka yi sanyi suka kai kasa, idaniya na zubda hawaye na daga kai na kalli Sauban. “Wane irin rashin imani ne wannan Sauban? Me na maka? Miyasa idonka zai rufe ka aikata kwatankwatan zalinci da Deen ya taba aikata min, me na muku? Miyasa ma na sanku?” “Idan har Deen zai kirki komai saboda ya same ki, ya kike tunanin ni da ba kirkira zan yi ba na fashe kwan kawai zan yi? Zahra na boye miki wani abu ne kawai amman tun daga lokacin da na fara saka kafata a cikin gidan nan na saka ran batawa da Abiey domin na san ba zai lamunci min na aureki ba, amman na boye masa har sai da na samu hujojin da zan dogara da su su yi min iso gurin neman aurenki, haka yanzu haka ba ma ga maciji da Abiey saboda ke, yan'uwansa sun dauke ni a matsayin macuci shi kanshi haka yake kallona, amman na zabi na jure komai saboda na same ki, sai a yanzu da kowa ya san da komai har iyayena na sanarwa sai kuma ki ce ba zaki aure ni ba? Ke ki wanke kanki ki fita free ni kuma ki bar ni a kunya da bakinciki da nadama, wai Zahra baki yarda ina sonki ba?” “Mai sonka baka ganin ramarka idan har so na kake zaka so farinciki ka so kwanciyar hankalina, ba zaka nemi daga min hankali ba” “Ba daga miki hankali nake ba, mafita nake nema miki, ko dan saboda Jamila da Mr Bashir, Zahra ko da wani abu ya faru rigar aure zata kareki, domin bana jin Jamila zata kyale ki a haka idan ďanki ya girma, zata yi ta tsammanin wata rana zaki dawo ki aure mijinta ko kuma ki kwace ďanki amman aurena zai kawai da komai Zahra” “Bayan ka fallasa komai sai me zai biyo baya? Karshenta a ce za a rufe ni gidan yari, bayan wannan sai kuma me?” “Zaki barwa iyayenki da ďan naki da kika saida tabo da ba zai taba goguwa a zuciyarsu ba, Zahra wannan ce dama ta karshe da zan baki, kuma ina kara jadadda miki idan har baki son kowa ya san da zancen aurena da ke, ba za a sani ba, zan aure ki kuma na sallame a lokacin da kike so” Na mike tsaye. “Kawai ka fito fili ka ce jikina kake so” Sai yayi saurin kawar da fuska. “Subhanallahi, idan na nace haka ai ban yi laifi ba domin ba zina na aikata ba, kuma ba ita na neme ki ba, zaki iya jurewa maganganun mutane akan aurenmu, amman ba zaki iya jurewa na siyar da cikin da kika yi ba, saboda haka idan kin koma cikin gidan nan kawai ki amsawa Mama da cewar eh kima so na, shikenan sai na sanar da iyayen su sami naki iyayen domin bana son a dauki lokaci” Ya bude motarsa ya shiga yayi mata key yayi reverse ya bar ni a gurin tsaye. Komai ya zo min ta hanyar da ban yi zato ba, na kasa yardar Sauban ne yayi min haka gani nake kamar a mafarki komai yake zuwa min, duk yadda zan yi Mama ta saurari uzurina na yi amman bata yi ba saboda ranta ya bace sosai. Kamar wasu abokan gaba haka muka kwanta muka tashi da safe Mama bata son magana da ni, gaishe ma da na yi bata amsa min ba, cikin damuwa da kufuwa na fito waje na share BQ din na wanke kayan da muka bata, sannan na zauna kusa da wasu fulawoyi na rafka uban tagumi, ina ta tunanin abun da zai fitar da ni. “Ya Allah idan abun da Sauban yake nufina da shi alheri a gareni, Allah ka saukar min da natsuwar amince, ka kawar min duk wani abu da nake gani, idan kuma ba alheri bane sharine ko cutarwa a garemu Allah ka musanya min ka kawo min mafita, shi kuma ka cire masa ni a zuciyarsa” Ashe Mama na jin addu'ar da na yi, bayan na shafa addu'a ta fito ta zauna kusa da ni tana kallona. “Ba wai bana son aurenku da Sauban din ba ne, ina duba abun da zai zame muku mafita ne, amman na lura kina sonki kuma shi ma yana sonki, saboda ki kwantar da hankalinki zan sami dangin mahaifinki zan sanar musu sai su saka masa ranar da zai je ya same su” Na dubeta sai hawaye suka riga kalaman bakina fita, na kasa cewa bana wannan ne kudirina ba, kamar wanda aka yi ma asari haka bakina ya rufe rub na gagara furta komai, har lokacin ban iya labarta wa Mama barazanar da Sauban yayi min ba, domin ban san abun da zai biyo baya ba idan na fada mata. A daren ranar Ummiter ta shigo BQ rike da waya, bayan mun gaisa ta mika min wayar. “Za'a kira ki ku gaisa” “Wa zai kira” “Yaya Bashir shi yace na kawo miki wayar” A take na samu kaina na faduwar gaba, hankalina yayi matukar tashi babu abun da zuciyata take raya min sai kalaman Sauban, kamar marar gaskiya haka na karbi wayar na rike ina ta kallon hoton Amir dake gaban screen din wayar, sai tausayin yaron da mutumen da ake ikirarin mahaifinsa ne ya kamani, ba su kadai ba har da yan'uwansa da suke nunawa Amir kauna a zuwan ďan Mr Bashir ne. Ta dayan bangaren kuma na san ban kyautawa Hajiya ba da Baba domin su ma za su so ganin jikansu ko da kuwa ace Deen yana raye balle kuma ba shi da rai. A lokaci da kiran ya shigo sai na kasa amsawa jikina ya dauki rawa kamar mazari, Mama ma da kanta sai da ta lura da haka. “Ki dauka mana” “Ba zan iya ba Mama” Na amsa cikin kuka, kiran biyu Mr Bashir yayi a wayar Ummiter da nake kyautata zaton Hajiya Jamila ba ta san da kiran ba, amman na gagara amsa kiran, sai da Ummiter ta dawo ta karbi wayar tana dubawa sannan na mike tsaye da sauri na fito daga dakin. “Baki amsa kiran ba?” Shi ne abun da ta biyo ni tana tambaya. “Na amsa” Ban bari ta ga hawayena ba na bata amsa, bayan na tabbatar ta fice daga BQ din na koma cikin dakin na bude gurin tufafina na dauko wayata na fito na kunna sai ga sakwanni kala kala na samu na Sauban wasu kuma na nuna kulawa ne daga Dr Hamid, sai da na kara matsawa sannan na kira wayar Sauban. “Me ka fadawa Mr Bashir?” Shiru na ji yayi kamar ba zai amsa ni ba, can kuma ya yi gyaran murya ya ce. “Me kika tsammanin zan fada masa? Kin yi zaton wasa nake? Haba Zahra ba zan yarda na yi 2-0 ba” “Hakan be dace ba Sauban” “Miyasa ke ba zaki aikata abun da ua dace ba? Ban fada masa ba, na so ma lasa masa zuma ne kawai a baki, amman zan fada masa matukar baki amince da kudirina ba” Wasu hawaye masu zafi sun sauko min. “Dan Allah ka yi hakuri Sauban karka fada masa” “Kin amince?” Na daga kai kamar yana gabana, na runtse ido ina wasu hawayen da ban san ranar tsayarwarsu ba. “Kin amince zaki aure ni?” Ya sake nanata. “Na amince....” Na furta daker, halshewa har wani haldewa yake maganar na rabewa min kamar mai koyon magana... [11/26, 7:15 PM] Oum_Nuwaira🥰: 6️⃣1️⃣ A gurin na gurfana na zauna ina ta rusar kuka, domin na san na saka kaina tsaka mai wuya, ko kadan bana jin kaunar Sauban a raina kauna ce irin wanda za a iya zaman aure tsakaninka da namiji. Na kusan awa biyu a gurin ina abu daya wato kuka sannan na share hawayena duk kuwa na san hawayena ba za su boyewa Mama cewar na yi kuka ba. Kaina a kasa na shiga dakin ban yarda na kalli gefen da Mama take ba na nufi katifa na kwanata, Mama ta lura kamar bana son magana sai ta kyale ni bata ce min komai. Na kwanta ba dan na yi bachi ba bachi kuma be tukari idona yadda na ga rana haka na ga daren, na gagara runtsawa ko kadan sai ciwon kai da raba kusa da ya sauke kayansa a gurina ya hanani ko da juya kan. Akan idona aka yi kiran sallah asubahi, kamin Mama ta yi wani yunkuri har na yi alwala na shigo dakin, sai da na fara sallah nafila raka'a biyu sannan na gabatar da farillah. Karatu kur'ane ne ya biyo bayan azkar din safe da na yi na dauki kusan awa uku ina karanta suratul Yasin idan na gama sai na maimaita har sai da na samo min bachin da na gagara yi jiya yana neman ranko a idona. Sannan na rufe kur'ane na daga hannayena na yi addu'a bayan na jadda salati ga Annabina. “Ga ruwan tea ki sha, na lura ba zaki iya cin wani abu mai nauyi ba yau” Na kalleta lallai uwa uwa ce ta fahimci ina cikin damuwa amman gudun takura min ya saka bata tambaye ni ba, daman ni kuma bana son sanar da ita ba. Matsawa na yi kusa da ita na dora kaina a kan kafadarta. “Mama na yi magana da Sauban, mun daidai ta kanmu ina son idan kin samu dama ki yi magana da su Baba sai na fada masa ya fadawa iyayensa” “Zahra kina ganin haka ya fi miki?” “Inshallah ina fatar haka, ke dai ki cigaba da yi min addu'a kawai” “To Allah yasa alheri ya tabbatar da alherin” “Ameen” Na amsa ina jin addu'ar da ta yi min kamar ta soka min mashi a kirji, domin hakan na kara tabbatar da cewar auren Sauban din zan yi. Yanzu haka za sake rayuwa a gidan wani da yake da kusanci da Abiey, ni kuma na mutu da kaunarsa? Na tambayi kaina tambayar da bata da amsa, wata kila kaddara ce a haka na rayu da ciwon so kuma na mutu da shi.   Yadda Sauban ya matsa a lamarin auren sai da abun ya ba ni tsoro, wani dama ya samu da yake iya ta controlling dina yadda yake so, ya fada min cewar zai zo ya tafi tare da ni ya gaishe da iyayena da yan'uwan da ya kamata su san juna da shi, a haka na amince masa domin bana da wani iko a yanzu, ina jin kaina kamar mai mutattaciyar zuciya da bata iya tabuka komai sai yadda aka juya ta, da toh kawai nake amsa duk wani abu da yake fada min ko kuma ya ba ni umarni, a ranar muka je na gaishe da mahaifiyarsa mace mai far'a da son mutane, yadda ta tarbe ni tana haba haba da ni sai na rantse da Allah ni ce da surukarta ta farko, kanwarsa kamar zata cinye ni dan murna, sai dai kowa ya kalli fuskata ya san bana farinciki da auren saboda na kasa sake jiki na kasa annashuwa murmushi ma da nake na dole ne, ashiri ta arziki suka min daga mahaifiyarsa har kanwarsa da sauran yan matan dake gidan, domin kyautar da suka min tafi karfin a kirata da goma ta arziki. A bakin gate ya tsaya ya rika min ledodin muka shigo da su cikin gidan. A bakin BQ muka tsaya sallama da shi sai na kasa daga ido na kalleshi domin a halin yanzu ina jin kamar ba ni da wani babban makiyi kamar Sauban idan akwai wanda na tsani gani ko jin sunansa ko mu'amala da shi to Sauban ne. “Zahra ki sanar da iyayenki nan da kwana biyu zan turo nawa iyayen, kuma ina son kisan da cewar auren kawai za a daura tarewar kuma sai ranar da kika zaba, sannan bana bukatar komai daga gareki” Wani hawaye mai zafi ya sauko min, na kasa ce masa komai, cikin karfim hali na taka na karasa kofar dakin mu na shige na bar a gurin tsaye. Kamar yadda Sauban ya bukata haka Mama ta sanar da yan'uwanta da yan'uwan Mahaifina, duk da abun da ya faru tsakaninta da Baba wato mahaifin Deen be hana ta sanar da shi ba, ba dan komai ba sai dan da ba shi hakkinsa a matsayinsa na abokin mahaifinmu kuma uban da ke aurar da mu a duk lokacin da za mu yi aure tun daga kan Yaya Maryam har zuwa kaina. Babu irin fadan da Yaya Maryam bata yi min ba saboda na gabatar da Sauban a matsayin mijin da zan aura a gurin magabatana, ba dan be cancanci aurena ba sai dan tana ganin hakan da zamu aikata kamar zai taba Abiey, a tunaninta be kamata na aikata hakan ba saboda Abiey ya nuna min soyayya mai karfi, kuma be guje ni ba sai dan shiga tsakani da aka yi mana, sai dai na gagara fadawa kowa boyayyen sirrin da ya saka zan auri Sauban saboda ina gudun abun da fadin zai haifar, na yardar wani lokacin ba ni hikimar neman shawara idan zan yi abu saboda ina tsoron kar a ba ni shawarar da zata haifar min da matsala, wata kila kuma shawarar da na zabawa kaina ba zata wanke ni ba. Daman kamin iyayen Sauban su tafi gurin nawa iyayen ya fada min cewar jumma'ar da zata zo ta jibi za'a daura auren tarewa kuma sai lokacin da na zaba, shi dai muradinsa a daura auren. Ko ba a fada maka ba kasan auren yayi gaggawa ace an zo neman aurena a yau kuma ana bukatar daure auren a jibi idan da hali, sai dai ba kowa ya kula da haka ba ganin cewar bazawara ce ni a yanzu ba budurwa ba, musamman da ya fada musu cewar tare ba a yanzu za'ayi ba, sai da yayan mahaifina ya kira wayata ya tambaye ni sadakin da nake ganin ua kamata su yanka, sai na ce na bat masa wuka da nama a hannu su yi abun da ya kamata, sannan suka tambayi cewar ko mun amince a daura auren a jumna'ar nan mai zuwa ta jibi kamar yadda iyayen angon da kuma mijin suka bukata. A daren ranar da aka yi tambayar auren, Mama ta tsare ni da tambaya domin ita ma kanta ta fara zargi kamar akwai cilastawa a amincewar da na yi saboda rashin sukunin da nake da yawan kuka musamnan ma cikin dare ga kuma daurin auren da Sauban ya bukata a kusa kusa, ban yarda na nuna mata fuska da zata fahimci akwai wani abu a kasa ba balle har ta cilastani fada mata. “Daga baya na sake shawara, ina ganin a daga auren nan zuwa wani lokaci nan gaba, ko da wata daya ne” Na daga idanuwana da suka kara bayyana ramar da na yi na kalleta. “Mama wata daya yayi nisa, sun ce basa bukatar komai daga gurinmu” “Ko da basa bukatar komai, ai ya kamata ayi komai cikin natsuwa ba a gaggauce kamar haka ba, wasu da ya kamata su sani ba ba kowa ya sani ba” “Idan an daura auren wata kika tarewar zata dauke mu tsawon lokaci, kin ga mu na da wannan damar ta sanarwa duk wanda ya kamata, kuma ina ganin kamar be kamata acs mun daga maganar ba bayan da har mun fadawa su Baba cewar mun amince da haka” “Ke dai kin matsa kina son auren nan a kusa Zahra, ni kuma ina ganin kamar akwai damuwa, kawai dai kin ki fada min ne” Na kirkiri murnushin da ya tsaya min a iya lefe na ce. “Babu komai Mama” “Su ma ai ya kamata ace sun daga ko dan su bincika, ko da auren Abiey ma da na Deen duk ba su saka bincike ba, balle wannan, amman na tabbatar da ace mahaifinki yana raye zai bincika komai, Allah SarKi Allah ya jikan rai” “Ameen” Na amsa ina wasa da yan yatsun hannuna ina jin wani irin ciwon zuciya marar misaltuwa, wata kila ma idan an daure auren ba zan yi wani tsawon kwana ba domin ciwon ya matsa min sosai tun daga lokacin da na amince zuwa yau. Mama ce ta sanar da Hajiya Jamila zancen auren tsabar murna da farinciki sai ta ji kamar ta kama ni ta saka zane ta goya, hankalinta ya kwanta a yanzu ta samu sukunin cewar ba mijinta zan aura ba, a lokacin ne take sanar da Mama cewar ta san Sauban kanwarta yake aure wanda suke uba daya da ita, har take fadar auren na su ma be dade ba. Da yamma lis Dr Hamid ya shigo gidan, sai da ya fara isa bangaren Hajiya Jamila sannan ya sanar min cewar na fito yana son magana da ni, ban yi mamakin zuwansa ba duk da kasancewar ya kwana biyu be shigo gidan ba, wata kila a yanzu ya zo ya taya ni murnar auren da zan yi ne, domin na san Hajiya Jamila zata sanar masa. Hijab na dauka na rufe jikina sannan na saka talkamina na fito waje ina takawa a hankali idanuwa suna gurin masu gadin gidan dake ta haramar daura alwalar sallah Magariba domin an fara kiran sallah a wasu masallatan. “Assalamu Alaikum” Na mika masa sallamar aminci sai ya amsa min girar sama da ta kasa a hade. “Wa'alaikissalam” Sauke kai na na yi kasa ina ta mamakin dalilin bacin ransa domin ni dai ban san na masa wani laifin ba, wata kila kuma zai ce miyasa zan yi aure ina shayar da Amir ne, wata kila kuma zai ce ban sanar da shi da kaina ba sai ta bangaren Hajiya Jamila ya ji, haka dai na yi ta sake sake a raina kamin maganarsa ta tsinke tunanina. “Zahra na ji wani abun farinciki a gareki, ni kuma a gurina abun bakin cikin ne daman hausawa sun ce a bari ya huce shi ke kawo rabon wani, ban yi tsammanin zaki iya bude zuciyarki ki karbi soyayya wani a kusa haka ba, shiyasa ban cusa kai ba” “Ban gane maganarka ba” “Zahra da farko dai zance na miki murna domin aure babban al'amari ne musamman ace wanda zaki aura din nan tsakani da Allah yake sonki, sai dai ban jidadin da ya kasance wani ne zai mallake jikinki da zuciyarki a yanzu ba, domin na yi wani tanadi a zuciyata da ban sanarwa kowa ba sai yar'uwata shi ma kuma a lokacin da kuka samu tsabani da ita hakan ya kwantar mata da hankali, ashe dai kuma hauka ce kawai nake ba ni ne da rabonki ba” Ya gyara tsayuwarsa, wannan karon a maimakon bacin rai fuskarsa damuwawa take bayyanawa. “Zahra na san ina daya daga cikin mutanen da suka haifar da damuwa da bacin rai a zuciyarki, wannan dalilin ya saka na dauki alkawarin kuranye wannan damuwar na share hawayenki na mantar da ke duk wani hali na bakinciki da kuka taba shiga, na yi kudirin abubuwa da yawa akanki Zahra a farko a kyautata miki da kyautata mu'amala da ke da son duk wani abu da kike so, sannan na yi kudurin aurenki duk kuwa da na san ba lallai ne ki karbi soyayyata ko ki amince da ni ba, a duk lokacin da zan yi yunkurin nuna miki soyayya sai zuciyata tace be dace na yi haka a yanzu ba, saboda ina ganin kamar mijinki be dade da mutuwa ba, kuma ga halin da kika shiga a yanzu wata kila ba ki shirya karbar soyayya ba, ta dayan bangaren kuma ina tsoron irin kallon da zaki min, wata kila ma zaki yi zaton ko kanwata ce ta saka ni ko kuma ina son na aureki ne ba dan Allah ba sai dan na kara rufe sirrin dake tsakaninmu, wadannan abubuwa suka zame min wata tsarka data daure ni na saka duk wani motsi da ya kamata akanki, ashe dai rashin rabo ne ke ta tare ni amman Allah ya sani Zahra na so ki, domin kina da siffa da kyaun da duk namiji mai hankali da sanin rayuwa zai so ki kasance a matarsa” Tare da dogon numfashi ya karashe maganar, ni ma numfashin na ja na sauke a yanzu dai ba zan ce ina tausayinsa ba domin idan har akwai wanda zan ji tausayinsa to kaina ne na fi kowa zama abar tausayi a yanzu, tabbas tunaninsa be bashi karya ba ba dan cilastawar Sauban ba, da ban shirya wani aure ba ko da a nan gaba balle kuma a yanzu. “Wani lokacin abubuwa suna faruwa ba a yadda muke so ba, sai a yadda Ubangiji ya tsara za su faru, wata kila ni din ba alheri ba ce a gurinka shiyasa Allah be mallaka maka ni ba, domin Allah yana zabawa bayinsa abun da ya fi dacewa da su ne” A cikin kalamaina babu na kuka, amman hawaye na ke kamar an sanar da ni awanin da suka rage min a duniyar nan, kuka nake sai na rasa dalilinsa ciwon zuciyar dake neman kaine kasa ne ko kuma auren Sauban da ya zame min dole kuma kaddara. “Haka ne, ina miki fatan alheri Allah yasa mutumen da zaki aura ya rike ki amana, gaskiya yayi sa'a shi ne Abiey?” “Abokinsa ne” Ya kada kai. “Na gane shi, daman zuciyata ta raya min son ki yake ashe kuwa haka ne, bari na wuce kar ya tarar da mu a nan ya fara kishi” Da murmushi ya karasa maganar, sai na saka hannu na share hawayena. “Na gode” Na juya ina tafiya cike da nauyin kafa har na shige BQ be tunna motarsa ba balle na yi tunanin ya bar gurin. The following day Sauban ya kira wayata yana tambayar ko akwai abun da nake bukata kamin a daura auren, na amsa masa da babu, sai ya sanar da ni zai balaguro a gobe kuma ba zai samu dawowa ba sai ranar da za'a daura auren, idan ya furta zancen aure sai na ji kamar ya soke ni da mashi a kahon zuciyata, kalmar tana min daci sosai kuma tana sakawa zuciyata bugawa, Jumma'ar da zata zo ma fargabar zuwanta nake domin kuwa jin ta nake kamar jumma'ar mutuwata, ko wane kallo Abiey da yan'uwansa suke min a yanzu oho, wata kila mayaudariya ko yar cin amana, wata kila ma za su ce na bi kudi ne na auri Sauban, haka dai na wuni da tunanin irin kallon da mutane za su min. Ana gobe za a daura aurena na shiga bawa Amir nono kamar yadda na saba na kan ba shi na safe da rana da kuma dare, ina a dakin Hajiya Jamila a zaune na saka masa nonon a baki yana sha idona na kansa sai ruwan hawaye ta taru a ciki har ya zubo akan fuskarsa. “Zan yi aure Amir amman bana jindadi da farinciki ba, zan yi ne saboda na rufa asirinka kuma na rufa nawa domin ban san da wane bakin zan amsa maka ba idan ka tambaye ni miyasa na aikata haka, wata kila a gurinka da gurin wasu mutanen hujjata bata isa ta zama hujja ba, na san na aikata kuskure mafi girma, amman duk haka zan so na ga girmanka, zan so ka kalleni ko da a matsayin wanda ta shayar da kai ne, sai dai bana da tabbacin zan rayu har zuwa lokacin da zaka yi wannan wayon, amman ina son ka sani cewar ina kaunarka fiye da komai a duniyar nan ina son kasance da kai sai dai babu hali” Ina shafa gefen fuskarsa da yatsana sai yayi min murmushi irin na yaran da suka shiga wata na uku da haihuwa. “Amarya Amarya” Shine abun da Hajiya Jamila ta shigo dakin tana fada, sai na yi saurin saka hannu na tare fuskata har sai da na share hawayena cikin hikima sannan na dago ina murmushin karfin hali. “Yau kuma tsokana kike ji ke da kanki?” “Ai na fi kowa murna da farincikin auren nan da zaki yi ne Zahra, Allah dai ya sa gurin zamanki ne” “Ameen” Na amsa sannan na kalli wayarta dake ringing, da sauri ta karasa gurin wayar ta cikin zumudi da far'a ta karba kiran da nake kyautata zaton Mr Bashir ne ya kira. “Hello Hubby, ahhhh i miss you da gaske? Awww i can't wait wannan jumma'ar ta gobe, Okay Allah ya kawo ku lafiya” Ashe kuwa na canka a daidai domin yanayin yadda take amsa masa da kuma sunan da ta kira ya tabbatar da haka har wani tsalle take kamar yar yarinya tana ta zumudi. Ni dai ban ce komai ba na cire Amir daga nonon na kwantar da shi na mike tsaye na fice daga dakin ina jin wani irin kaunar ďana yana fizgata. A ranar na wuni da tunani da kuma damuwa marar misaltuwa na dan samu sukuni ne a lokacin da Hajiya Jamila ta kirani na fara tayata aikin da zata shiryawa mijinta abinci gobe ta nan na fahimci zai dawo a gobe kenan bayan doguwar tafiyar da yayi, wani abun tun a ranar muka kallama shi, sannan na fito na dawo bangarenmu ina shigowa na rufe windows din da Mama ta bude saboda hadarin da ya taso iska na kadawa da karfi, ina kokarin kwantawa wayata ta yi kara bakuwar number ce cikin fargaba na amsa kiran. “Zahra'u kuna lafiya ina Mamanki?” Ina jin muryar na fahimci Inna ce kanwar Mama, sai na mikawa Mama wayar suka yi magana, bayan sun gama Mama take fada min cewar wai zata zo gobe ita da wata kanwarta. “Allah ya kawo su lafiya” Kawai na iya fada na cire tufafin jikina na saka na bachi na yi addu'a na kwanta. [11/26, 10:50 PM] Oum_Nuwaira🥰: 6️⃣2️⃣ Jumma'atu Babbar Rana, sai dai ni zan iya cewa ta zame min ranar tashin hankali domin na farka da kuka kamar yadda na kwana da shi, ina sallah ma kuka nake a boye saboda bana son Mama ta gani zuciyata ta rike gam kamar an daureta dan motsi kadan sai na ji kamar raina zai fita saboda ciwon da take min, Mama ta shirya abun karyawa amman na kasa cin komai sai ruwa na ke ta sha. Misalin karfe tara na safe Inna ta kira wayar tace tana waje na zo na shiga da ita saboda masu gadin sun hana su shiga. Kamar marar lafiya na fito BQ din na fita gate domin shigowa da su a lokacin ne suka budewa Mai gidan Gate direbansa ya shigo da motarsa ni da su Inna muka rabe gefe har sai da ya wuce sannan na yi magana da masu gadin suka bar su suka shigo. Bana tunanin yayi awa daya da shigowa gidan Hajiya Jamila da kanta ta shigo BQ din da kanta kirana. “Allah yasa ba laifi na yi ba” Ta yi dariya. “Babu laifin da kika yi kawai dai yayi maganar Amir ne sai na ce masa zan sanar masa da wani albishir daga Nannyn Amir amman waka a bakin mai ita tafi dadi zan kira ki fada masa da kanki, shi kenan fa ya tashi hankali sai na kira ki ko abinci be karasa ci ba” Hankalina ya dan kwanta da jin haka, na san da ace ba a aurena za a daura ba da bazata fadi haka ba har tana yakar hakora. Haka na bi bayanta muka shiga bangarensa sai dai na same shi a zaune a falon da Ummiter ta taba yi min iso lokacin da ya aikata ta kira ni. Na shiga kaina a kasa na zauna a makamancin gurin da na zauna a wacan lokacin, ita kuma ta karasa kusa da mijinta ta zauna tana murmushi. “Gata nan sai ta maka albishir din” “Toh Madam ai sai kin bamu guri kin san dai ban saba magana da ita a gabanki ba” Kunnuwa suka ji sautin muryarsa zuciya kuma na raya min cewar idonsa yana kaina. “Ahhh ni ai bana da shan kai ga ta ga ka” Ta mike tsaye ta fice tare da jan kofar falon, tsit falon yayi kamar babu kowa baka jin komai sai sanyin ac dake tashi. “Matata tace akwai wani abun alheri da ya same ki, sai dai bata sanar da ni ko minene ba shiyasa na ce ta kira min ke na ji daga bakinki, abu na biyu kuma kin san ba ki karasa min labarinki ba har yanzu ban gama sanin wacece ke ba, tafiyar da na yi a kwanan baya ban yi zaton zata dauke ni wadannan kwanakin ba, sai dai yanayin aikina ko kuma na ce kasuwancin na ya saka dole na dade a turkiya, a jiyan ma ban saka ran dawowa ba sai gashi kuma mun iso nigeria a jiya din cikin amincin Allah, sai dai ban samu karaso gurin iyalina ba sai a yau, saboda mun dawo late sai na tsaya na kwana a Abuja” Na daga kai na kalli yadda yake jero min bayanin tafiyaraa kamar ance masa ina da alaka da hakan. “Allah ya huta gajiya, wanne zan fara daga ciki Yallabai, albishir din zan sanar maka ko kuma labarin zan karasa maka” “Da dai zaki daina kiran Yallabai din nan wata kila da sai kin fi kima a idona, amman kamin nan bari na yi katsalandan ba ki da lafiya ne? Sannan na kira Ummiter kwanan baya na ce ta baki wayar ina son na tambayeki kina son a gyara muku gidan da aka rusa ne ko kuma a siya muku wani amman baki amsa kiran ba why” Sai a lokacin na gane dalilinsa na neman Ummiter ta kawo wayar da na yi zaton ko zai min maganar abun da na aikata ne da matarsa, a yanzu na gane wautata tabbas da akan haka ne da yanzu hankalin matarsa ya tashi, ni kuma da yake tsoro yayi min yawa sai na yi zaton ko Sauban ne ya fada masa wani abu. “Alhamdulillah, lafiyar bata wadace ni ba kamar ba, kuma lokacin da ka kira na aje wayar ne na shiga bandaki shiyasa” Kafa daya ya dora akan dayar yayi wani zama mai kama da kishingida yana kallona. “Ina da zumuncin na karasa jin labarin abun da iyayenki suka yi a lokaci da sojojin suka ce za su shigo, tun ganin farko da na yi miki na kalli idonki na fahimci kina da wauta da kiriniya da kuma kurciya a tare dake, sai dai ban dauka a cikin labarinki kin wahalar da iyayenki har haka ba ban yi zaton labarin zai saka ni nishadin da na kwana biyu ban yi irinsa ba, Wallahi har a gurin aikin da na tafi idan na tuna murmushi nake, yau dai kam so nake ki karkare min komai sannan albishir din da Matata ta ce ya biyo baya” Ashe da sauran murmushi a kumatuna da ba san da zamansa ba sai a yanzu da Mr Bashir yake fadar na saka shi nishadi. Na kara natsuwa a zaunen da nake sannan na cigaba da bashi labarin daga inda na dasa aya. -Ni kadai suka bari tsaye a kofar gidan, da na ga babu sarki sai Allah sai na juya na fada masa cewar Mama ta shige bandaki Baba kuma ya shige daki ya rufe, sai sojan yayi murmushi ya kara matsowa kusa da kofar ya ce. “Daman fa ba wani abun zan musu ba, ni da nake neman su zama surukaina ina ni ina yi musu wani abu, kawai dai na zo ne saboda na yi magana da su na fada musu cewar ina son yarsu kuma ina son yi min izinin rika zuwa ina magana da ke har mu daidaitu da juna, amman tun da ba su yarda sun fito ba zaki iya musu wannan bayanin albashi idan na dawo kin ga ba sai na sha wahala ba” “Toh sai anjima” “Dan jirani ina zuwa” Ya nufi gurin motarsa ya bude ya shiga ya zauna, sannan ya fito ya nufo ni ya miko min sabbin kudin yan dari biyar biyar za su yi dubu goma, na saka hannu na karba daman can ni bana tsandar kudi ko a hannun waye suka fito kuwa. “Ki bawa Baban kuma ki sanar masa zan sake dawowa Inshallah” “Toh” Murmushi ya sakar min sannan ya juya ya nufi motarsa ni kuma na gyara rikon tufafin Yaya Maryam dake hannuna da dan kwanon naman da Deen ya ba ni daman shi kullin ledar da na sato a dakinsa tana can cikin zanena na laketa yadda ba zata fado ba, sannan na dawo cikin gidan har lokacin Mama na bandaki Baba kuma yana daki ya rufe kansa, karasawa na yi kofar dakin na kara bakina jikin kofar na ce. “Baba yace ga dubu goma a baka” “Allah yasa rai yace a kara min Zahra Wallahi ba zan fito dakin nan ba, idan kika ga na fito to safiya ce ta waye a lokacin kam na tabbatar da ya gaji da tsayuwa ya tafi, yaushe kika janyo rigima da mahaukacin nan Fisabilillahi ya zo yayi min tsinannen duka alhalin ban san hawa ba balle sauka, yanzu kuma ki je ki janyo fada da sojoji dungurungun” “Baba mahaukacin dazun ma shi ya fara fada ni fa, ni kuma na kwashe msa kafafuwa ya fadi shi ne ya biyo ni fa” “Mahaukaciyar banza, ai kin ma fishi haukar, ni ba zan ma sake magana ba, waya sani ko kina nan tare da shi yana jina” “Ya tafi fa Baba Wallahi ya tafi” Baba be sake magana ba, har na gaji na nufi shimfidar da ya tashi na aje tufafin Yaya Maryam na juyo na nufi bandaki na leka Mama da ta yi tsugune ta rafka tagumi idonta narau narau alamar akadan take jira ta yi kuka bayan wanda ta yi dazu. “Mama ya tafi fa, kuma ba jansa na yi ba Wallahi ganina yayi ya ce yana Son yace na kawo shi gidanmu, yanzu ma da yace a sallamo masa Baba kawai zai nemi izinin hira da ni ne, kalli ma ya bada kudi yace a bawa Baba” Mama ta dan taso ta leko harabar gidan ganin babu kowa sai ta ce. “Je ki rufe gidan” Na nufi gidan na rufe sannan na dawo na mika mata kudin. “Kin tabbatar da haka ne Zahra karki janyo mana wahala” “Wallahi gaskiya nake fada miki Mama ai kin san bana miki karya, amman Mama kin san da na tafi gidan Hajiya na tarar tana soya naman kaji da yawa, har tace ba zata sammin ba saboda na ce sai na fada maki Ya Deen ne kawai ya ba ni na shi” Daga can cikin dakin da Baba yake rufe muka ji yana fadin. “Ke kam dai Zahra kin shiga uku, yanzu kuma zuwa kika yi ki hada ni da uwarki? Ni Wallahi na san idan na ganki aljanna rahmar Allah ce kawai ta kaiki, amman wannan halin na ki ba zai bari ki shiga aljanna ba, to ba ni na siya mata nama ba ita ta siya da kudinta” Mama ta tabe baki ta girgiza kai ta fito bandakin. “To sai ki iya bakinki, kuma ki daina dauko mana magana Zahra na rasa abun da yake cikin kanki kullum magana ake amman kamar ana kara cewa ki yi, wannan lamari na ki Zahra ya isheni ya kai min intaha, dazu fa aka cire miki marin nan saboda rashin jin maganarki, amman har kin sake dauko wata maganar” Ma dan matsa baya ina kallonta da damuwa a tare da ni, duk na san da cewa mawuyanci abu ne Mama ta saka min hannu da sunan duka sai idan ranta ya bace sosai. “Mama na daina daga yau, kuma Wallahi dukansu ba wai na ja su ba ne, kin ga wannan so na yake shiyasa ya biyo ni har gida, kuma yayi ya saka yaransa su yi ma Yaya Deen duka sosai” Mama ta fito da ido waje tana mamaki. “Saboda me?” “Wai yayi masa fada ne saboda ya tsaya da ni yana magana” Mama bata ji dadi ba ba dan komai ba sai dan ta san da cewar Deen zai ya fitar da dukan da aka yi masa a jikina. A lokacin da ta tambaye ni ina na samo tufafi sai na yi mata karyar cewar Yaya Maryam ce ta bani, abu kamar wasa sai ga Baba ya kwana a dakin sai da safe ya fito, ni da Mama muka kwana a dayan dakin. Saboda na san ni mai laifi ce sai na shirya da wuri na tafi makarantar, a ranar aka raba mana jarabawarmu ta English da uka yi, guda daya na fadi a cikin dari, daman can ba dai kokari ba shiyasa Yara da yawa suke son zama a kusa ni domin ni ban iya rowar ilmi ba, kuma indai gurin kokari ne idan ban zo ta daya ba to zan zo ta biyu a ajin, sai dai ace bana jin magana amman akwai fahimtar karatu da saurin ganewa. Ba mu dawo gida ba da muka tsaya ni da kawata Hafsat muka yi abun da muka saba yi kamin mu dawo gida wato tsintar kayan marmari, ko da na iso gida ni dai nawa cikin ya cika ovar abinci rana ma kadan na ci na shiga bandaki, ina tsaka da wanka na ji sallamar Deen sai na daina motsa ruwan da nake ina ta sauraren gaisawar da yake da Mama. “Mama ina Zahra” Ina jin ya tambaye ni sai gabana ya fadi, Baba ya fara bashi labarin abun da na yi masa na sakawa mahaukaci yayi masa duka sannan kuma na kira masa sojiji har cikin gida. Aiko a ranar jikina ya fada min domin ina fitowa wankan jirana kawai yayi na saka tufafi na dauko jakar islamiya jikina na mazari na fito ina cewa Mama zan tafi islamiya. “Islamiyar jan magana? Ki je can ki sake dauko Magana?” A lokacin da na dube shi sai an fahimci dukan da sojan nan yayi masa ba dan karami ba ne, domin ua raunata masa fuska sosai kafarsa ma kamar gurgu haka yake tafiya. A lokacin da Deen ya rika hannu be yi min da sauki ba kamar wanda Allaj ya aiko haka ya rika dukana da bulalar da yayi tanadinta tun kamin ya shigo cikin gidan, zaneni yayi ras babu inda babu yabon bulala a jikina sannan ua buga min warning cewar idan ya sake ganin na tsaya da wani ina magana sai ya kusa kashe ni. “Deeni da duka na gyara yaro ina kyautata zaton da yanzu Zahra ta daina abun da take, ina ganin addu'a kawai ya kamata a cigaba da yi mata har Allah ya shirya” Cewar Mama daga inda take zaune ina rike da kafarta kuka na bana iya yi saboda wahalar duka. Baba ya nuna ni da baki yana fadin “Ai wannan da kike gani bata jin magana shi ne kawai maganinta da ace ma baya dukanta wata kila ni da ke da yanzu ta kashe mu” Deen dai be ce komai ya jefar da bulalar dokin ya fice daga gidan, ruwan zafi Mama ta dora akan wuta ta rikoni ta dawo da ni ďaki ta dauko ruwan tana gasa min jiki, ina kuka tana hawaye. “Indai ba ki natsu kin yi hankali ba, wata rana sai yayi miki dukan da ya fi karfin jikinki ya kashe ki, kuma na a isa ayi komai ba, a yanzu ma idan na ce zan yi magana laifina za a gani, Allah ya saka miki” Ina kuka da ihu Mama ta gasa min jikin, har sai da makota suka shigo Tambayar ba'asi, domin ko dazun da yayi min dukan nan na yi ta ihu balle kuma yanzu. Ni da Baba sai muka koma majinyata biyu a gidan shi yana jinyar dukan mahaukaci ni kuma ina jinyar dukan Deen. Wata kila yayi nadamar dukan da yayi min ne ko kuma daga baya tausayina ya kama shi idan zai shigo duba ni sai siyo min nama ko ice cream saboda ya san ni sarkin kwadayi. Ranar da aka yi kwana na uku da faruwar lamarin na yi wanka na saka tufafin Yaya Maryam daman tun a lokacin da na sato su nake ta dauko sakawa ban samu dama ba sai yau, wani abu mai kama da hadin baki ban yi minti goma da saka tufafin ba sai gata ta sallamo a gidan ta saka salati tana son ta kai hannu ta dake ni har sai da Mama ta shiga tsakani. “Mama wannan sabon tufafina ne fa, ban taba sakawa ba daman ina dubawa ban gani ba nasan ke kadai zaki iya saka hannu ki dauketa” Mama ta kai min wani rankwashi mai zafi a kai. “Ai wani lokacin duk abu da ake miki ke kike jawa kanki wahala, miye na sato maka kaya? Ba ce min kika yi ta ba ki ba?” Na yi zuru zuru da ido irin na marasa gaskiya. “Mama ki ce ta yi hakuri to” Na roka ina zuboto baki gaba kamar na yi kuka, ranta ya bace sosai daman na saba yi mata haka sai dai na lura kamar wannan ya fi yi mata zafi, muna cikin gidan Deen ya shigo ya gaisa da su Mama ni dai ko gefen da yake ban kalla ba, haka kuma be hana shi aje min ledar hannunsa ba sannan ya juya gurin Baba yace. “Motar tana waje Baba” “To” Baba ya amsa ni da Yaya Maryam da Mama muka yi masa kallon rashin fahimta jin cewar Deen ya bata masa zancen mota, sai a lokacin ya sanar da Mama cewar wai gidan Hajiya zai koma saboda ita ma ya bata hakkinta ba zai yiyu ya zauna a nan kadai yayi jinya ba. “Amman kuma Malam ba zaka sanar da ni ba sai da zaka tafi Fisabilillahi?” “To yanzu ba sanar da ke nake ba? Wai miyasa kika cika fitina ne Fisabilillahi? Wani lokacin ina duba kamar halinki ne Zahra ta dauko Wallahi, sam sam baki tausayina yanzu ina kwance a halin ciwo ai kamata yayi ki dauke min cefane da wasu lalurorin gida amman ina kullum sai kin karbi kudin cefane a hannuna, kuma kina dai kallo mahaukaciyar yar nan taki ta janyo min wannan lalura” “Allah ya kiyaye ya baka lafiya, ni na yafe kwanan ka zauna a can har sai ka samu lafiya” Cewar Mama sai Deen ya karbe. “Baba Zahra tana da Hankali ba mahaukaciya ba ce, kawai dai bata jin magana ne” “Haka dai kuke gani amman daga ganin idon wacan kasan ba na masu hankali ba ne” Kasa kasa na watsa masa harara yadda ba zai gani ba, Deen ya rika shi tare da wani abokinsa suka fita da shi daga gidan. Yaya Maryam dai sai kallon ikon Allah take. “Wai Mama yanzu jinyar ce ba zata yafe masa yayi a nan ba sai ya tafi gidanta?” “Haka dai ya so, daman ba a komai yake iya kwatanta adalci ba sai idan ya shafi bangarenta, kina jin yana zancen na matsa masa da karbar kudin cefa ne, to waye zai ba mu idan ba shi ba? Ita cefanenta yake duk karshen wata ni kuma sai dai ya rika min guntu guntu a hannu, ka yi magana ace kishi kake saboda ita ya saba yi mata tun kamin na shigo” “Kuma yana siyo mata nama be naki ba Mama” Na kara mata da wani, a take ran Yaya Maryam ya bace. “To Mama idan kina son abu ki rika karba cikin kudinki kina siya mana, sai ki zauna a haka ina son abu ke baki siya ba kuma shi ba zai siya miki ba?” “Ai ina masa zancen kudin nan na san laifi zan yi, ni tun da ya karbi kudin sau biyu kawai ya ba ni ribar daga nan ban sake sanin yadda aka juya kudin ba, idan na tambaye shi sai yace kudin marayu ne kara a rika ajewa” Sam ban san da zancen wasu kudi da Mama ta bawa Baba ba sai a lokacin, aiko na mike tsaye na rausayar da kaina, na nufi daki ban ce masu komai ba, ina jin suna da zancen ita da Yaya Maryam, ni kuma na bude jakata ta makaranta na dauko kullin ledar da na sato a dakin Deen ya bude ina dubawa domin sai yau Allah yayo hankalina ya kai na bude ledar, wani abu ne a ciki mai kamar ganyen ko ma dai na ce ganye sai kwayoyi magani farare fes kamar maganin ciwon kai sai dai ya dara maganin ciwon kai girma. [11/27, 9:20 PM] Oum_Nuwaira🥰: 6️⃣3️⃣ Na fito da kullin maganin a waje na nunawa Mama a tunanina ko maganin mallaka ne. “Mama kalli har da wani magani na samu a dakin Deen waya sani ma ko na mallaka ne” Mama ta karba ta shinshina ta mikawa yaya Maryam sai na ji ta saka dariya. “Zahra kin shiga uku dakinsa kika shiga kina masa bincike kuma?” Mama ta yi mata alama da ta yi shiru duk a gabana sannan ta kalleni ta ce. “Ba maganin mallaka ba ne, maganin da maza suke sha a tea ne” “Oh shi ne Deen yake sha kenan?” “Eh bar shi anan zan saka a wuta, karki sake shiga dakinsa kina masa bincike, ban dan lalacewa ba ma miye kaiki dakin namiji Zahra?” “Nama fa naje dauka shi ne na hado da ledar, Mama ba ni zan kona” “Aa barshi a nan idan na tashi zan kona” Bata yarda ta ba ni, suka cigaba da hirarsu ita da Yaya Maryam har Yaya Maryam take bata shawarar ta karbi ragowar kudinta da suke hannun Baba ta fara wani sana'ar da shi, a lokacin da na lura hirar ta yi musu dadi hankalinsu ya dauka akan abun da suke tattaunawa sai na tashi na nufi daki na dauko jakata makaranta na yi musu sallama na kama hanyar zuwa makarantar sai dai ba makaranta na nufa kai tsaye ba, daman can na saba da shiririta abu mai wahala na tafi makarantar islamiya kai tsaye ba tare da na biya ta wani gurin ba. A gurin da na fi samun abun dadi na nufa kamin ina isa kofar gate din gidan motar Abiey na isowa kofar gidan ni da masu gadi har rigen bude masa kofar muke, bayan na shiga ciki sai na saki kofar na karasa gurin motar da ya fito yana murmushi tare da wani sarauyin da ba zai wuce sa'arsa ba, nuna ni saurayin da nake kyautata zaton abokinsa ne ya yi. “Kar dai ita ce wanda kake ba ni labari” “Ita ce fa” Na dan matsa baya ina kallonsu domin ban fahimci abun da suke magana a kai ba. “Amman ba ta yi kama da wadanda za su aikata wani abun shirme ko kiriniya ba” “I'm telling you, Zahra mu shiga ciki ko” Abiey ya karasa yana nuna kofar dakin, sai na yi murmushi na wuce gaba domin gidan ba bakona ba ne, suka biyo bayana ni na fara shiga falon na zauna sannan Abiey ya haura sama abokinsa kuma ya zauna akan kujera yana kallona sai na ji kunya ta kamani. “Ammy amman baki fada min ba ba, ba zan dawo yanzu ba, ga Zahra ma ra zo, Okay” Shi ne abun da Abiey ya sauko yana fada da waya a kunnensa kamin ya kalli abokinsa. “Ammy ta fita kuma yunwa nake ji Wallahi” “Ina mai aikinku” “Ta yi tafiya, kuma ko tana nan kasan bana cin abincin masu aiki” “Ai kai yunwarka ma mai sauki ce da ka sha tea zaka iya cewa ka koshi, amman ni idan ban ci abinci mai nauyi ba ba zan gane kan garin ba” Abiey ya kalli. “Zahra zaki girkawa Abokina Sauban indomie? Kin iya ai ko?” Na yi kuri da ido kamar marar gaskiya, can kuma na daga kai. “Eh na iya” “Ga kitchen can” Ya nuna min hanyar kitchen din, sai na aje jakar hannuna na mike tsaye na nufi kitchen, kusan a tare muka shiga ya dauko min abubuwan da zan yi amfani da su, sannan ya shiga dorawa kansa ruwan tea yana zolayata. “Kyakkyawa ranar kika ja mana zuma kika gudu ko? Na balle ni a baya da kai sosai fa Ammy kuma kin taimaka mata har tana cewa ashe zata iya gudu idan wani abun ya taso” Na yi dariyar da na tabbatar kara min kyau ta yi domin har wani wara ido yayi yana fadin. “Wow Gaskiya Allah yayi hallita a gurin nan” Na rufe fuskata da sauri ina dariya. “Bari na baki damarki kar na rudaki, idan ruwan tea nawa ya tafasa sai ki kirani” “Toh, amman karka dawo kitchen din sai idan na kira ka” “Yes Ma'am” Ya juya ya fice cike da girmamawa, a nan na takarkare na cire hijabina na aje gefe daya na dora pot din da ya nuna min na zuba mai na fara gabatar da aiki, tarugu da albasa da ya nuna min na daka mai uban yawa na zuba a ciki, ina kallon ruwan ya gama tafasa har ya kashe kansa amman na ki yarda ma fada saboda ban gama girkin ba bana son ya shigo ya tararda ni a haka, na zuba gurinshi da magi a tare na zuba komai na saka indomie na ja na tsaya, ban yi minti biyu da rufe tukunyar ba na bude na saka abu na motsa miyar na lasa, wani tsabar azabar yajin da na ji ban san lokacin da na daka tsalle ba na wurgar da spoon din dake hannuna ko ni da nake mayya bana tunanin zan iya cin wannan abinci. Kofar kitchen din ta falon na rufe na dauki hijab dina na saka na bude kofar baya na fice da gudu, kamar aljana haka na isa gida ina haki, Mama da Yaya Maryam suna zaune a inda na barsu zaune suna ta hira har lokacin. “Ke lafiya wani barakar kika yi kuma?” Mama ta tambaya Yaya Maryam kam sai barkewa ta yi da dariya. “Zahra ashe haka kika yi da Baba? Gaskiya dole ki sha duka hannun Deen kam” Ni kam ban bi ta kanta ba domin na san barakar da na tafka a yanzu ta ci uban dariyar da Yaya Maryam take. “Mama wai Antyn su Hafsat tace na tambayeki me ake sakawa a abinci idan yayi yaji sosai” “Anya? Ko dai wani abun kika yi?” “Aa Mama cewa fa ta yi na tambaye ki, Islamiya ma zamu wuce yanzu da Hafsat” “To ni Wallahi ban sani ba” “Ana saka gawayi, ance yana rage yajin amman dai ban taba gwada yi ba” Yaya Maryam na bada amsar na mika hannu na saci dan kullin maganin da Mama tace na maza ne, na fice da sauri, sai da na bi ta gidansu Hafsat na samu gawayi domin na san ba za a samu gawayi a gidan Ammy ba su da suke amfani da gas me zai hada su da hawayi, kamar wanda ta yi sata haka na dawo cikin gidan na samu kofar a bude kamar yadda na barta, ban ko tsaya wanke gawayin ba na jefa shi haka a cikin indomie sannan na dauko soyayen naman da ya bani na saka na sake motsa taliyar yaran. A kokarin ganin na burge Abiey na bude kofin ruwan zafin na kwance maganin na zuba masa maganin na kwayar dai sai da na murje na ganyen kuma a haka na zuba masa shi, na sake kunna hitar ta sake tafasawa da yayi na zube na tace masa na dauki cup biyu na zuba dora a tray na bude kofar na fito kai tsaye na nufi dinning na dauki kalolin lipton na saka na saka suga kadan na zuba kayan kamshin da na gani sannan na nufo inda suke zaune na risina na aje musu. “Oh Zahra sannu da kokari ai da kin bar shi kin kira ni kawai na hada” Abun da baka saba ba, jikina har rawa yake na yi musu hidimar, Sauban ma sai yawa yake da kokarina yana tambayar taliyarsa bata yi ba. “Ta kusa yanzu zan kawo” “Ya naga abun yayi dark green?” Abiey ya tambaya sai na ce. “Na hada kalolin liptons ne maybe shiyasa” “okay thank you duk da dai ba ko wane kalar Lipton nake sha ba” Ina jin lokacin da Sauban din yake ce masa. “Kar dai ka gasale ta ka daure kawai ka sha” Ni dai ban bi ta kansu ba na dawo kitchen din na cigaba da kula da indomie da ruwan cikin ma yayi mata yawa kuma yajin be rage ba sai ma baki da abincin ya dan yi wani bangare, sai na na sauke tukunyar na tsame rabin naman ciki na wanke a ruwa na cinye, sannan na rage ruwan dahuwar indomie na zuba magudanar ruwa da na gani a kitchen din na dauko plate na zuba musu na saka spoon biyu, na bude kofar kitchen din na fito sai na samu Abiey a tsaye yana ta wani abu mai kama da shillo yana kallon sama, Sauban kuma yana zaune a kasa da rabin kofin tea ya dafe kai, Abiey kam gaba daya ya shanye. A gaban Sauban na aje plate din indomie. “Gashi nan” Sauban ya dago daker ya kalleni sai kuma ya kalli indomie. “Me kika saka a shayin nan?” “Ban saka komai ba” Na amsa ina dan natsawa baya cike da tsoro. “Miyasa nake juyawa? Miyasa komai yake juyawa?” “Yunwa ce ka ci abincin gashi nan na dafa maka” Kitchen din na koma na dauko wani plate ina fifita nasa saboda abincib ya sha iska, har lokacin Abiey na tsaye sai gidaya yake da hannu. “Ka ci ta sha iska” Kamar mai jiran umarnina sai ya bude kafafuwa ya fara auna abinci soma daya ya daki kansa ya tande baki. “Wai mutuwa.... Minenen wannan kuma” Ya sake aika cibi na biyu, ni dai ina ta kallonsa ina jinjina kokarinsa har ya cinye rabin plate wata kila dai saboda yana jin yunwa ne, sai dai ina ganin wani abu mai kama da fitar hayyaci a tare da su, musamman Abiey da ya gagara zama sai kallon sama yake kamin na koma kallon cushion din gidan. Tashi na yi na isa gabansa na tsaya ina kallonsa. “Abiey Lafiya?” “Ina fa lafiya? Baki ne duk sun cika mana gida, ga su nan zai shigowa suke” Na juya gabas da yamma kudu da arewa ban ga kowa ba, amman Abiey sai sannu da zuwa yake musu sai kuma ya dafe kansa yana lumshe ido. “Ya salam, wadannan bakin da muke biki ake ne?” Na waiga na kalli Sauban dake ta shan yaji yana son mikewa, amman ya kasa sai juya kai yake yana wani zazzago halshe kamar maye. Zuciyata bata raya min cewar abun da na zuba musu a tea ne ya saka su wannan abun ba, domin Mama ta fada min cewar maganin maza ne, ba na maye ba wata kila dai lokacin na shiga Kitchen wasu aljannu suka shigo cikin gidan suka shafe su, musamnan ma Abiey da baya cikin hayyacinsa gaba daya. A dole na rika shi ina kokarin zaunarwa ya ki ya zauna sai cewa yake wai bana ganin falon ya cika da jama'a, sai ya fara safa da marwa cikin falon kamar mai rafeti. Tsaye na yi cikin falon ina kallon ikon Allah, Sauban ya zama kamar dan maye yana ta aikin shan yaji yana shafa jikinsa da kansa, ban san lokacin da na fashe da kuka ba na nufi jakata na dauka na rumgume. “Ni dai na shiga uku ban san kuma abun da ya faru ba, miyasa suke yin layi?” Na tashi na karasa kusa da Abiey na bude qur'ane na fara binsa ina karanta masa ina tofawa, idan na yi kamar aya goma sai na dawo gurin abokinsa Sauban na karanta masa shi ma na tofa masa, amman ba wani canj, Sauban din sai bin kujeru yake yana son ya tashi tsaye ya kasa. “Wayyo Jama'a a kai ni gida” Jin haka yasa na rufe kur'ane na maida a cikin jakata na aje jakar a gefen kujera na nufi inda suka aje keys din motar wato kan hannun kujera na nufi kofar na bude na fita na nufi motar da suka zo na saka key din ina da murdawa daker na samu kofar ta bude sai na bude ganbu na dawo falon na rika Sauban daya gagara mikewa sai cewa yake a kai shi gida. “Wacece ke?” “Zahra” “Zahra wa?” “Fatima Zahra” “A ina nake?” “A idan Ammy” “Wacece Ammy?” “Mahaifiyar abokinka Abiey?” “Minene kuma Abii?” Yanzu kam ban san kalar amsar da zan bashi ba, sai dai na yi iya kokarina na ganin na mikar da shi tsaye amman na kasa, domin ni babu karfi shi ma kuma sai shan yaji yake yana lasar baki kamar tsohon maye. “Ina Matata?” “Ina zan sani ni, kana da mata ne?” “Na dauka ina da ita, to Ina Mamata ko ita ba ba ni da ita? Kin san gidanmu? Ina ne nan?” “Ban sani ba ni dai dan Allah ka yi shiru” Ya ki yayi shiru sai tambayoyi yake sako min kala kala da ban san amsarsu ba, Abiey kuma ya ki ya zauna sai zagaye falon yake yana ta yi ma bakin da ban san su waye ba maraba da zuwa, cikin iya Allah na rika Sauban na mika mike tsaye sai ya sako min nauyinsa ni da shi mika fadi a kasa, sai na yi saurin tashi ina rika shi. “Dan Allah ki kai ni gida” “To ai shi ne nake son ka shiga motar sai na tuka ka tafi gida, ni ina zan san gidanku” “Ta can ake bi, sai abi nan sai abi can” Ya nuna min kofar kitchen, jin kamar tsayawar mota yasa na sake shi da sauri na nufi inda na aje talkamina na dauka na dauki jakata na nufi kofar kitchen na bude na tsaya a kitchen din har sai da na ji shigowar Ammy, salati ta saka ita da Anty Zainab tana tambayar lafiya, amman babu mai amsa mata a cikinsu Sauban din sai kiran a kai shi gida yake, Abiey kuma yana fadin gidan da baki babu gurin zama. “Allah yasa ba wani sammun aka yi masa ba, matan uban nan sun saka shi gaba ga kuma makiya abokan wasansa” Ina jin haka sai wata zuciyar tace min na fito na fadawa Ammy abun da ya faru, wata kuma tace min na ranta a na kare, sai na bude kofar baya cikin sanda na fice daga kitchen din, kamin na isa gate din na samu na fice jinina ya hau kusan tari biyar ma domin ji nake kamae ma'aikatan gidan tare ni za su yi. Na isa na fadawa Mama da Yaya Maryam aika aikar da na yi sai Mama ta kwashi yan tufafinta da za su wadaceta ta yi kwana biyu ni ma na debi nawa muka bar unguwar, Family house dinsu muka tare babu fadan da ban sha ba a lokacin da Mama ta fada musu dalilin guduwarmu, Ba dama na san da sai Deen ya same ni a can yayi min dukan daya saba domin ya shata min line tsakanina da Abiey amman ban ji gashi na sake komawa gidan har na sake aikata laifi, sai dai ban tsira da dukanba domin Mama ta yi min nata da kanta sai dai nata dukan mai sauki be ne ba irin wanda Deen yake min ba na fitar hankali. Jin shiru ba a zo nemanmu ba Mama ta tambaya a unguwa aka fada mata cewar babu wanda ya zo nemanmu sannan muka dawo gidan, tun daga lokacin sai ya zamana idan zan tafi makarantar Islamiya sai Mama ta raka ni ta tabbatar na shiga sannan ta dawo, idan kuma muka taso bana yarda na bi ta gaban gidansu Abiey ma saboda Mama ta fada min cewar abun da na yi wata kila idan Ammy ta kama ni zata mika ni hannun sojoji yan sanda kuma za su tuhume ni da mu'amala da kayan maye, ba dan wannan tsoron ba da babu abun da zai hana na koma gidan ko dan na bawa Ammy da shi kanshi Abiey hakurin abun da ya faru. A haka na kwashe wata biyu ko kofar gidan bana yarda na bi balle ya mutanen gidan su gan ni. Wata rana ina zaune ina wanke uniform din makarantar Islamiyar mu sai ga Ammy ta sallamo a gidan tana sanye da bakar abaya ta yafa katon mayafi a sama dayan hannunta rike da jakar alfarma, sai kamshin turare take zubawa irin na manyan matan masu kudi, fuskarta a sake tana ta murmushi. Sai dai hakan be hana na tashi na koma bayan Mama na boya ba gabana sai faduwa yake ina ganin kamar ta zo ta yi wata magana ne ko ta saka a kamani kamar yadda Mama take min hasashe. “Kin san kin yi rashin gaskiya shiyasa kike boya ko?” Maganarta ya saka hankalina ya dan kanta domin a cikin wani yanayi mai kama da raha ta yi min maganar, Mama ta tashi da sauri ta dauko mata tabarma ta shimfida mata ta dora carpet din sallah akai jikinta har kyarma yake. “Sannu da zuwa Hajiya Sannu da zuwa, Allah yasa ba wanin laifin Zahra ta sake yi ba?” “Aa ni da na zo na ji dalilin rashin zuwan Zahra a gidana, ko dai ke kika hanata? Tare da Aliyu mike yana waje shi ya matsa min da maganar Zahra ya dame ni na zo na ji dalilin daina zuwanta” A yadda na kura Ammy mace ce mai far'a da son mutane, kuma bata kyamar talaka haka ma ďanta Abiey. Sun dauki lokaci suna hira da Mama sannan ta sanar min cewar Abiey yana waje yana jirana na tafi gunsa mu gaisa. Wanke kafafuwa na yi na saka hijabina na nufi kofar gida, tafiya kadan na hango inda suka faka motarsu, domin kalar motar kadai ya isa ya saka na gane cewar ita ce motar da Ammy ta shigo, tafiya nake ina jin wani abu mai kama da marmarin ganin Abiey yana sallamo min har na isa, bakin gilashin motar ya sauke karaf idonsa cikin nawa wani kalar kwarjinsa da kimarsa suka cika idona, a take na samu kaina da faduwar gaba da kuma jin kunya a lokaci daya. “Ji idonta sarkin kiriniya how are you?” “I'm fine” Na dan kalleshi kadan na dauke ido da sauri, kwana biyun nan da ban saka shi a ido ba na lura har wani kyau da haske ya kara. Mun dade a tsaye muna hira sannan miko min ledar chocolate yana zolayata wai ya san yara chocolate ko ice cream suke sha shiyasa ya siyo min. Daga lokacin sai wani irin shakuwa ta shiga tsakanina da shi, Mama kuma ta sabu da Ammy wani lokacin ma idan Ammy tana son wani abu a gurin Mama zata aiko ta nema mata, ni kuwa sai ya zamana ba ni da wani aboki sai Abiey komai an dauko a duniyar nan Abiey daman can ina son mutumen da zai iya daukar matsalata, kuma ya zamana yana sakar kin fuska yana nuna min kulawa ba duka ba kyara ba kamar Deen, sai dai duk da irin shakuwar da ke tsakaninmu Abiey baya yarsa ya sha abun hannuna ko ya ci sai idan tare muka siya, Ammy ma bata yarda na shigar mata kitchen idan ma zan ci abinci a gidan sai ta zuba min da kanta ko kuma na zuba a kan idonta. Ban taba yarda Deen ya san da alaka ta da Abiey ba Mama ba ban bari ta sani ba, domin na san idan ta sani zata iya hanani yawan fitar da nake da shi a sace da kuma zuwa gidajen yan'uwansa ko na Ammy da muke, kamar idan an aike mu ko kuma ziyarar ta tashi. A duk cikin yan'uwa na lura Abiey ya fi shakuwa da Dr Zainab duk wani sirri nasa ta sani, duk wata shawara da ita yake, yana yawan zuwa gidanta da ni ko ba ni ya wuni, ban san Abiey babban mutum ba ne har sai da ya taba daukata muka shiga gidan Sarauta gurin step Mother dinsa wato Anty Amarya, ita ma tana da yara biyu mata Aisha da Narji, su ma dai babu ruwansu da daukar kai cikin kankanen lokaci muka sabu. Idan Abiey ya shirya tafiya gurin buga wasansa na kwallo sai na ji kamar zai yi tafiyar da babu dawowa ne saboda shakuwar dake tsakaninmu a ranar bana iya cin abinci haka zan wuni kamar marar lafiya, idan Mama ta lura da na daina zuwa gidan kwana biyu sai nace mata Ammy ta yi tafiya bata nan, idan ya kira waya ko video call a gidan Ammy da sunan mu gaisa sai na ji kamar na shige cikin wayar tsabar farinciki. A lokacin da Deen ya lura da hankalina ya dauke daga kan samari da kuma duk wata shiririta da nake bana da gurin zuwa sai gidan Ammy Ammy dai, ko da na zauna a gida Abiey zai aiko kirana da sunan Ammy na tafi a gidan na wuni, wani lokacin mu yi ta game ko wasan tsere tun Ammy na yi mana fada har ta gaji ta saka mana ido, idan muka yi wani abun sai dai ta yi dariya. Idan Abiey na yi arba da wata budurwa da nake ganin ya dace Abiey ya aureta ko ya so ta, sai na tareta na karbo masa numberta amman ba zai ba ni hadin kai ba, ko da ya fara waya da ita kwana biyu sai ya kawo dalilin da zai saka su yi fada. Idan kuma muka fita tare wani ya nuna yana so na sai yace musu ina da miji, idan kuma na kawo masa labarin samarina sai yayi ta fada da Ammy yana cewa ta gani ta gani ko zata ja masa matsala, kalamin Ammy daya a kullum na tsaya na maida hankali akan karatuna musamman da yake ina ajin karshe a makarantar secondary, duk wani tsadadden tufafi da zaka gani a jikin Ammy ko Abiey ya siya min, babu abun da zan je wa Ammy da shi ba zata karba min ba, har Dr Zainab da take yayarsa tana yi min hidima ta nuna min so saboda Abiey. A lokacin da Deen ya kura da abun ya fara yawa sai ya taka min burki... [11/29, 12:49 PM] Oum_Nuwaira🥰: 6️⃣4️⃣ Hana ni zuwa gidan da Deen yayi sai ya yanke min jindadi, shi kansa Abiey sai ya fara damuwa, da kansa ya aiko Ammy ta bincika masa lafiyata, Mama ta sanar da ita lafiyata kalau yayana ya dakatar da ni daga fita ko'ina ne, har ma ta kara da nata cewar bata son yadda nake da rawar kai ina shigewa mutane. “Ai kiriniya ce kawai take damun Zahra amman bata da wani abun dake nuna rashin tarbiya a tare da ita, idan ba Zahra ta manta ba ko zama kusa da namiji bata yi sai dai tana iya mika hannu ta karbi abu ko kuma ta shiga a inda mazan suke bata dauki wannan a bakin komai ba, kin yi wa yarki tarbiya mai kyau, sai dai hali ne ko da yadda Allah ya shimfida masa nasa, kuma ina fahimtar haka na taba da ke, na yaba sosai da yadda kika tarbiyantar da yarki, sauran sai mu barwa Allah” Mama ta jidadin kalaman Ammy sosai, daman burinta a kullum kar na watsar da tarbiyar da tayi mini, ko zuwan da nake a gidansu Abiey tana yawan nanata min na kama kaina na rike mutuncina, a nan Ammy ke sanar da ni cewar za su koma gidansu da aka gama gyara kuma tana fatar idan zata koma ni da Mama da sauran makotan da bata sani ba za su mu rakata kuma zumunci zai daure, sam ban jidadin wannan maganar ta Ammy ba domin ina ganin zata yi nisa da ni. Daga lokacin sai na fara satar kafa ina zuwa gidan, ina ta nunawa Ammy da Abiey zan yi kewarsu idan suka bar unguwar, sai Ammy tace ke da nake son iyayenki su mallaka mana ke ki dawo tare da mu, sai dai ban fahimci abun da take nufi ba, sai dai na ce mata ai Mama ba zata yarda ta ba ni ba, ko ma ta yarda Deen ba zai bari ba. A lokacin da Deen ya gane na sake maida hankali a gidan, sai ya zaunar da ni yana karanta min cewar Abiey ba zai taba aurena ba, domin su yayan manya basa auren yayan talakawa musamman ma shi da yake sanannen mutum da duniya ta shaide shi, sai dai na tabbatar masa da cewar ba soyayya ce tsakanina da Abiey ba, amman ya kasa yarda. Ranar da Ammy suka koma sabon gidanmu na yi kuka sosai kamar zai cire ido, a tunanin ba zan kasance da Ammy kamar da ba, ashe abun ba haka yake domin kuwa bayan tarewarsu a sabon gidan sai wata kalar shakuwa da aminta da shiga tsakanina da Ammy, idan zan tafi islamiya sai na sa ci kafa na tafi unguwar ina isa Ammy zata ba da kudin Napep na biya wanda ya kai ni, idan kuma na tashi komawa sai a kai ni da mota wani lokacin direbanta yake kai ni wani sa'in kuma Abiey zai maida ni gida, idan yayi min siyayya sai na boye ba zan bari Mama ta gani ba saboda kar ta yi min fada. Wata rana bayan na je can Abiey ya dawo da ni ya sauke ni a kusa da Islamiyar mu ashe Deen na gurin daman yana zargin ba makaranta nake zuwa ba. Tun daga gurin makarantar ya fara dukana har cikin gidanmu a ranar Deen yayi min dukan da sai da ya karya ni, Mama ta yi fushi sosai fushin da kawar da kawaicin da take masa ya saka ta gargadeshi cewar kar ya sake saka min hannu a jiki, ranta ya bace sosai domin duka yayi min wanda ya saka yan'unguwa suka yi zargin ya kamani da wani ne, cikin kankanen lokaci sunana ya bace. Da aka kwana biyu Ammy bata gan ni ba sai ta zo da kanta domin duba ni, a lokacin ne Mama ta fada mata ba zan sake zuwa gidan ba, kuma ba jidadin zuwan da nake ba a gidan ba da sunan zuwa makaranta amman Ammy bata taba koroni ba. Ran Ammy ya bace sosai irin bacin da ban yi zaton zata sake zuwa gidan ba. Daga baya Deen ya zo ya bawa Mama da ni hakurin abun da ya faru, sai ya koma yana kula da ni kamar dai, sai dai hakan be saka Mama sake masa fuska kamar yadda ta saba ba, a lokacin da na fara warkewa ina dan fita na taka kafar Dr Zainab yayar Abiey ta zo duba ni, take min albishir da wata maganar da ta kusan ruda tunanina wai Abiey zai aiko a tambaya masa aurena, sai dai tace min sirri ne kar na fadawa kowa. A ranar na wuni a tunani daman Abiey so na yake ko kuma dai abun da ya faru ne ya saka shi yin haka, amman ban iya boye jindadina ba Mama sai da ta fahimci ina cikin farinciki a ranar, sai dai ban fada mata komai ba. Ba tabbatar da gaske Dr Zainab take ba har sai da Baba ya shigo gidan cikin wani yanayi mai kama da farinciki kuma ba farincikin ba, domin a ranar ba girkin Mama ne ba, jikinsa na dan rawa, sai da ya kalleni ya jinjina kai har sau uku sannan ya natsu ya labartawa Mama wai. Wasu mutame masu daraja daga gidan sarauta sun same shi da zancen nemawa ďansu auren Zahra. Mama ta daki kirji tana tambayar wace Zahrar kuma su waye domin bata taba sanin Abiey ďan Mai Martaba ba ne sai a yau, ni ce kawai na sani ni ma kuma sanin da na yi ban dauka ďansa na cikinsa ba ne domin babu wani good relationship a tsakaninsu irin na uba da ďa. “Daman Abiey đan Mai Martaba ne?” Shi ne abun da Mama ta tambaya ni dai kai kawai na iya daga mata farincikin dake raina ya isa ya hana duk wani yaki da za'a gudanar a duniyar nan a nan gaba, ba wai ina son Abiey saboda yana da kudi ko dan yana dan manyan mutane ba, sai dan ra'ayina da nasa da nake ganin kamar ya zo daya, kuma yana biyewa shirme ne idan ma shirmen ne, yana nuna kulawa baya taba gajiya da duk wani abu na bacin rai da zan yi masa, wani lokacin idan na yi ba daidai ba zai nuna min cikin hikima, yace min Zahra ba haka ake ba kaza ya kamata ki yi cikin kwanciyar hankali babu fada, idan kuma ya gan ni da wani ba zai min fada miyasa nake tsayuwa da maza ba sai dai shi ya fadawa mazan cewar ina da miji ba kamar Deen dake dukana ba. “Na fada musu zan tambayi yarinyar idan ta amince sai na mayar musu da amsa ranar irin ta yau” Abun da Baba ya fada kenan sannan ya tambaye ni ko ina son Abiey babu bata lokaci na ce masa ina sonsa, ba dan na tabbatar ina sonsa a lokacin ba sai dan ina son kasance tare da shi kuma ina son hallayarsa da ta Ammy. A ranar Deen ya shigo gidan ya gaisa da Mama idonsa akaina duk wani motsi da zan yi baya dauke ido akaina, da zai fita sai ya bukaci na rakashi zuwa kofar gida, a can ya fara karantar min wadansu labarai da suka sanyaya min guiwa, wai Abiey yayi haka ne kawai saboda ya zamu damar shiga jikina kuma da zarar ya samu abun da yake so zai guje ni, shi dai yana min tsoron ranar da Abiey zai kunyata. Labaransa ba su tasirin hana ni amincewa ba, sai dai na kagagara na ga Abiey domin na tambaye shi ko zai guje min amman samu dama ba saboda ban samu saka Abiey a ido ba sai a ranar da aka yi mana baiko. A ranar unguwar mu ta dauka domin kayan baikon da aka kawo irin masu janyo magana ne da tseguma abu ne da ba kasafai ake ganinsa a gidajen talakawa ba sai yayan manya. Mama ta boyewa kowa wanda zan aura sai dai ko da wanda yake fada har da masu cewar tsoho aka bawa ni saboda an ga kudi a tunaninsa idan ba tsoho ba ne babu abun da zai saka mu boye ko waye. A ranar da aka yi min baikon Deen ya wuni yana bachi kamar matacce tun daga lokacin kuma be saka lafiya ba, daga ni har Mama muka rasa gane abun da yake damunsa, idan muka tambayi Baba sai yace mana ulcer ce. Daga lokacin muka fara cin arzikin Ammy, ta saka aka gyara mana gidanmu inda gini yayi kadan aka kara inda ke bukar gambu aka saka sannan aka yi mana tayis ko'ina a gidan. Idan Abiey zai zo hira zai so a bakar mota saboda kawaice idon mutane wani lokacin kuma sai na tafi gidan Yaya Maryam a can zamu yi hira. Wata rana na shirya da kaina na tafi sabon gidansu Abiey, domin a ganina ba komai ba ne na shiga gidan Ammy a yanzu, ban samu Abiey a gidan ba, Ammy ma na same a cikin wani yanayi dake nuna kuka ta yi, tana ta kawar da fuska kar na kalleta amman hakan be hana ni fahimtar tana cikin damuwa ba, na ritsara a dakinta na tsareta da tambayar damuwarta sai ta ki fada min ni kuma na saka kuka domin ganinta a cikin wannan halin ya daga min hankali sosai ina kallon Ammy kamar uwar da ta haife ni, idan ba uwarka ba a gidan wa zaka je kayi yadda kake so ka hau gado ka kwanta ka ci abun da ranka yake so ba za a ce maka komai ba ko a nuna maka yar fuska. Bayan na sha kuka na koshi Ammy ta kama hannuna tana dariya. “Haba Autana ta zo mana” “To Ammy me ke damunki? Idan baki fada min ba zan daina kuka ba ko da na tafi gida, saboda zan rika tunanin kina da wata matsala ne” Sai ta zaunar da ni kusa da ita wasu hawayen na taruwa a idonta. “Ina da matsala Zahra, matsalar da bata da magani, amman ina jin kamar na samu magani a lokacin da na same ki, saboda hankalin Aliyu yanzu yana gareki, kullum ba shi da magana sai ta ki, Zahra ina son ki zame masa cikakkiyar yar halak karki butulce masa, akwai mata da yawa da suka fi komai ba amman idonsa be sauka akan kowa ba sai ke, kuma zuciyarsa bata natsu da ko wace mace ba sai ke” “Na miki alkawari Ammy ba zan taba cin amanar Abiey ba” “Zahra na aikata wani abu, wanda shi ya saka ni kuka a yau kuma yake saka ni kuka a ko wane dare, zan fada miki wannan ne saboda ina son kamar yadda nake son Aliyu ban taba fadawa kowa wannan sirrin ba, amman abu ne da ya dade yana cina kuma ina fatar ba zaki fadawa kowa ba, ke ma zan sanar da ke ne saboda ki kara natsuwa da đana kuma ki tausayawa masa” A take hankalina ya tashi domin na san duk wani abu da zai saka uba zubar da hawaye a kowane dare ba karamin abu ba ne. “Na miki alkawari babu wanda zai ji Ammy” Sai da ta share hawayenta ta sake kama hannayena ta rike sannan ta ce. “Zahra karki taba yarda ki mu'amalanci wani da aurenki, kara ki yi shi a waje ko kuma bayan mutuwar aure ba a aure ba, maza basa yafe irin wannan kuma basa mantawa, kuma wannan abun yana shafar yayan da mace zata haifa, ni da Momy wato abokiyar zamana a gidan mahaifin Zainab mun sake aure bayan rasuwar mijinmu, sai dai ni na rigata auren saboda na fita kurciya da kyau, kuma ni na yi sa'ar aurene saboda tsohon manemina ne na aura, ya nuna min so irin wanda Aliyu yake kokarin nuna miki a yanzu, har ta kai baya iya adalci a tsakanina da sauran matansa, wannan ya haddasa fitina kuma zazzafan kishin da ya saka sai da aka ware ni dabam, domin ni ina yaki da bakina ne da anyi min sai na yi magana bana shiru, amman Wallahi ban san hanyar zuwa gidan ko wane boka ba, a lokacin kuma sai hankalinsu ya kara tashi suna ganin kamar zan kara dauke masa hankali ne, sanadin haka sai suka shiga bin bokaye suna kokarin raba ni da mijina, sai kuma suka yi nasara Mai Martaba ya juya min baya irin Juyowar da idan na rabe shi sai ya rika jin warina, idan ya taba ni sai yace jin yake kamar ya taba itace, har tambayar yake miya samu jikinki haka ni kuma ban san miye ba, da abun ya fara yawa sai ya daina zuwa gidana sai dai aiko min da duk wani abun bukata da kuma sakon gaisuwa, bayan ya kaurace min sai na fahimci ina da cikin Aliyu, wanda yace min idan na haife shi sunan mahaifinsa za a saka masa duk kuwa da kasancewar ya hana ko wace mace saka sunan Abban sa amman ni soyayya ta saka ya karya wannan alkawarin da ya dauka. Wata rana kamar an turo shi sai ya shigo gidan fuska babu annuri ban masa laifin komai ba,a nan na samu damar sanar masa halin da nake cikin ina ganin kamar samun cikin zai kawar da komai a tsakaninmu ya dawo da zaman lafiyarmu, sai dai a lokacin da na sanar da shi ina dauke da cikin sai ya kasa farinciki a aka danna jindadinsa akan cikin ya gagara nuna min murnarsa, sai Allah ya raba lafiya kawai yace min, a ranar na yi kukan na yi bakinciki sosai, a dayan bangaren kuma na yi farinciki da kyautar da Allah yayi mine. Na yi bakinciki na kaurace min da yayi ya saka na shiga damuwa sosai har ta kai kanensa da suke uba daya wato Galadima wanda shi kadai yake so na a familyn ya fahimci haka, maganinsu ba tsaya a iya farraku tsakanina da Mai Martaba ba ni ma ya taba tafiyata ya shafi kwakwalwata ya kai bana iya tsayawa na natsu akan wasu abubuwa, ga ciwon kafafuwan da na yi ta neman magani har india na je na kasa samun lafiya. A cikin Aliyu na wata na biyar zuciya da sheirin shaidan suka debe ni suka na aikata masha'a tare da kanensa da zan iya cewa cilasta ni yayi domin yayi ta lallashina har na amince, ashe ban sani ba wani karin damuwa ce ta fuskanto ni, domin muna a cikin halin da be kamata ba Mai Martaba ya shigo cikin gidan sai dai be shiga inda muke ba sai ya zauna a falo, bayan mun fito muka same shi. Daga ni har kanensa mutuwa ce kawai ba mu yi ba, amman mun sha kuka na fitar hankali. Ya saka muka yi masa alkawarin babu wanda zai ji wannan maganar daga ni sai shi sai Allah, saboda idan maganar ta fita zai zama abun magana kuma abun kunya. Bayan kanenshi ya fita sai ya tambaye ni tsawon yaushe muke tare, na fada masa gaskiya cewar yau ne kawai, amman be yarda ba. “Cikinki da ke jikinki zai cigaba da zama a matsayin ďana ko da kuwa ba nawa ba ne, domin jinin ďan'uwana jinina ne, kuma babu wanda zai san da wannan maganar, sannan ina son ki sani na sauwake miki ma'ana na sake ki” Cikin tashin hankali na fara bashi hakuri ina kuka ina fada masa cewar cikin dake jikina nasa ne. “Idan har zan iya zaman aure da uwar da ta haife ni, to zan sake zaman aure da ke Umaima!” Furuncin da yayi kenan ya banranta kansa da ni, daga lokacin sai na dawo gida gurin iyeyena na zauna, damuwa ta shiga kaina ga kuma sihirin da suka min har ya zama na ina yin abu kamar marar hankali, ana ta nema min magani ana min addu'a cikin iyawar Allah na samu sauki. Sai Allah ya dauki kaunar Aliyu ya saka min tun yana ciki domin mahaifinsa be taba zuwa duba lafiyata ba bayan ya sake ni, mutane suna ta fadar cewar maganin da suka min ne ya saka ya sake ni kuma ya dauke idona a kaina domin ina fadawa kowa cewar haka nan sidda ya sake ni ba tare da na masa komai ba. Kamin na haifi Aliyu kanen mahaifinsa yayi hatsarin mota ya rasu, sai ya zamana ni kadai na rayu da wannan bakincikin har zuwa yau. Bayan na haifi Aliyu Mai Martaba be taba ganin fuskarsa ba be taba aiko masa da komai ba, be taba yi masa komai ba ďana ya girma hannuna yayi wayo na yi masa komai da uwa take yi ma ďanta, sai dai kowa ya kalli Aliyu ya san ďan Mai Martaba ne domin babu inda ya rago Mai Martaba a kamanin. A lokacin da Momy ta haifi Yasmin sai muka je barka daga gidanta na dauki ďana na kai shi gidan Mai Martaba, yana kallonsa sai hawaye suka zubo masa, domin be taba saka shi a ido ba sai a ranar. Sai dai haka be canja tsanar da yake masa ba, be saka ya kula da shi ba, ni kuma ban fasa nunawa ďana shi ne ubansa ba saboda shi ne ubansa din na gaskiya, a kokarinsa na mantawa da ni ya auro mahaifiyarsu Aisha da Narjis, ita kuma ta zo sai ta zama mace mai sanyin hali da son gaskiya, tana ta kokarin sada Aliyu da mahaifinsa sanadin haka har aurenta ya taba mutuwa daga baya aka dawo da ita, amman bata fasa abun da take ba har ta yi nasarar samawa Aliyu ďaki a bangarenta ya zamana shi ma zai shiga yayi yadda yake so kamar ďan gidan, tun daga lokacin nake matukar kaunar Aliyu kuma nake tausayinsa domin laifina ne ya shafe shi, wata kila har da maganin da abokan zamana suka yi na shiga tsakakaninshi da mahaifinsa amman wannan abun da na aikata shi ma ya shafe shi, ya shafa masa bakin fenti da idan Mai Martaba ya kalleshi yana tuna abin da ya faru. Da iyayena suka rasu aka raba gidan mu sai na dawo a wannan gidan da tsohon mijina ya bar mine wato na ci gado, na cigaba da kula da kaina da yayana. Kuma Allah ya taimake ni yayana suka samu tarbiya da suka gama karatu na suka samu aiki, Aliyu kuma ya karkara a bangaren kwallon kafa domin abun da ya fi so kenan ni kuma na goya masa baya” [11/29, 11:47 PM] Oum_Nuwaira🥰: 6️⃣5️⃣ “Rashin samun kula daga mahaifi yana matukar tayarwa Aliyu hankali yana damunsa sosai, har yan'uwansa suke son yi masa gori da haka, wata rana da kaina na aka shi a mota na shiga dashi har cikin fadar na zaunar da shi a gaban matan Mai Martaba da yayansa na ce ya fadawa Aliyu da duniyar cewar ba shi ya haifi Aliyu ba, sai ya girgiza kai yace Aliyu ďansa ne ko be fada ba kowa ya kalli fuskarsa zai san da haka, yace Aliyu jininsa ne, a gaban matansa yace Zainab ma da ba yata ba ina sonta kamar yata Umaima saboda ta fito daga cikinki balle Abiey da yake jinina. Daga lokacin sai ya samu kwanciyar hankali, nima na dan samu amman na gagara mantawa, sai dai samun ki da Aliyu yayi, na ga farinciki a tare da shi irin wanda ban taba gani ba, kuma kin kawarda tunaninsa kin dauke hankalinsa daga damuwar da mahaifinsa ya saka masa, neman aurenki ma da aka je sai kanensa ne da yan'uwa suka je, amman shi be ce komai ba” A rayuwata ban taba jin tausayin wani mutun kamar yadda zuciyata take tausayin Ammy a yanzu ba, daker na iya takaita kukana na share hawayena na ce. “Ammy babu wanda baya kuskure, kuma abun da kika aikata Allah ya kaddara sai kin aikata haka din saboda haka ba ki isa ki tsallake haka din ba, ki saka a ranki komai be faru ba, kuma na miki alkawari ba zan taba gudun Abiey ba” Rumgume ni ta yi tana dariya tare da kuka a lokaci daya tana saka min albarka. Muna cikin wannan halin Abiey ya shigo dakin ya same mu a lokacin da har mun dauko wata hirar ta duniya, sai dai ina jikin Ammy ne idanuwana da nata sum kumbura. “Me kuke yi ma kuka” Abiey ya tambaya cikin fargaba duk da kasancewar ya ga murmushi a fuskarmu, ni kuma sai na amsa masa da cewar, ina bawa Ammy labarin mahaifina da ya rasu ne shi ne abun ya saka mu kuka, ya fada cikin labarin da muke aka dasa wata sabuwar hira. Na dade a gidan sannan Abiey ya maida ni bayan ya bi da ni ta gida. Hiayatee haka Abiey yake kirana tun daga lokacin da aka yi ana baiko, muka cigaba da rayuwa da nunawa juna soyayyah, Ranar da na gama graduation na Secondary school na ga gata kamar yar wani minister duk wani abu da zan rawa kawaye da kuma wanda na yi amfani da shi Ammy ce ta yi min, sannan ta tara yan'uwanta da Anty Amarya daga bangaren Mai Martaba suka zo. A lokacin ne Abiey yayi min kyauta da wayar hannu daman na dade ina mafarkin samun wayar amman ba dama domin Mama ba zata siya min ba, na san kuma idan na yi ma Ammy ko wani magana za a ce na bari sai nan gaba, ashe gaban a kusa take. Daga lokacin sai shakuwa da soyayya ta karu tsakanina da Abiey wayar safe dabam ta rana dabam haka ma ta dare, ban tabbatar ina Abiey sosai da sosai ba har sai da na fara damuwa da alakar dake tsakaninsa da Safeena, duk kuwa da na san kawarsa ce tun kamin ya hadu da ni, sai dai a yanzu kawance su na cutar da ni, ko dariya yayi mata sai na ji raina ya bace, sanadin haka na shata musu line da ban yi zaton Abiey zai bi ba, sai gashi ya saurareni kuma ya jingine abotarsu a gafe. Bayan kammala bikin makarantar sai aka fara maganar aure a tsakanina da Abiey, a lokacin ne Mama ta tuntubi Baba domin ya fara bata wani abu a cikin kudin gadon mu da ta bashi ta fara siya min wasu abubuwan, sai ya fara kame kame daga karshe ya sanar da ita cewar ya taba kudin kuma sa'ar siyar da Furnitures da ya fara abun be karbu ba, ba Mama kadai ba ni ma kaina na shiga tashin hankali a lokacin, domin na san da kudin Mama ta dogara kamar yadda ta yi ma Yaya Maryam hidima da su. Yaya Maryam da Mama suka rika siyen abubuwa da be fi karfinsu ba suna aje min. Ana sauran wata biyu bikinmu Ammy ta samu Mama ta fada mata cewar ba za su kawo lefe a yanzu ba saboda gujewa idon mutane tace za a aje min komai a dakina sai dai na tararda shi acan, amman za su min tufafin da zan saka na biki, a nan ta yi ma Mama albishir da cewar bata bukatar komai daga garemu apart from kayan daki har zuwa na kitchen ta tanadi komai, idan an daura aure ni kawai za a kai musu, a ranar Mama ta kwana da farinciki domin samun mace irin Ammy abu ne mai matukar wahala. Bayan sati daya da faruwar hakan Ammy ta maida ni gidanta aka fara min gyaran jiki ana ba ni kulawa, kar ka so ganin yadda fatata ta zama, fari na ya kara fitowa kyauna ma ba a magana, hankalina a kwance muna ta zuba soyayya ni da Abiey, sai dai duk tsawon lokaci Deen ya dauke kafa daga zuwa gidanmu sai dai dukanmu mun dora hakan a kan rashin lafiyar da aka ce yana yi, na sha zuwa duba shi kamar yadda Mama ma take zuwa, sai dai daga lokacin da na koma gidan Ammy da zama sai ya zamana bana fita ko'ina daga gida sai gida, Abiey ma sai a waya muke hira, idan kuma yana son ganina sai dai yayi irin shigowar nan da babu sanarwa ko kuma ya ritsamu a falo ko ďaki. Ba ni da wani damuwa ko tashin hankali ina rayuwar kamar wata yar sarki kauna ake nuna min ga ko'ina, har auren mu ya gabato ban ga wani canji a gurin Abiey ko iyayensa ba har sai da ya rage sauran kwana biyu bikimmu, duk wasu shagulgula an gabatar kamin ranar sai dai na lura Ammy da Dr Zainab kamar akwai abun da suke boye min, Abiey ma na fahimci akwai damuwa a tare da shi ta hanyar hirar da muke, Dr Zainab ta zo ta dauki jinina ta fada min cewar ta dauki na Abiey zata je ta gwada, ban kawo komai a raina ba duk da kasancewar an dauki na farko tun kamin a saka mana rana, sai na dogara da abun da ta fada cewar ba zata bari a daura auren ba tare da ta sake yi mana gwaji ba, ba a matsayinta na yayar miji kuma likita, ni kam ban dauki abun da muhimmanci ba, har zuwa ranar da za a daura aure ban samu wata matsala ba, ina wani dakin Ammy ana min kwalliya na kira Abiey na tambaye wane kalar tufafi ya saka sai yace min farare kamar nawa. Bayan na aje wayar ya sake kirana yace yana son magana da ni a kebe, na ji tsoro sosai kuma na samu kaina da faduwar gaba. Shi ya fada min dakin da zan same shi na taka da kafa cikin farin lace da mayafi na isa har gurin na shiga cikin dakin, sai na same shi rai a matukar bace har baya iya kallona. “Zahra.... ” Sai yayi shiru, hakan ya saka na tari gabansa ina kallonsa fuskata da murmushi. “Minene?” Be iya fada min ba ya fice ya bar ni, cikin tunani da sake sake kala kala, dawowa na yi dakin Ammy na zauna cikin damuwa da sanyin jiki, mutane da ke cike da dakin sai tambayar damuwata amman na kasa furta komai domin ni ma ban san damuwar tawa ba, kawai dai na fahimci akwai matsala ne. Babu wanda ya iya fada min komai sai Ammy da kanta ta kori kowa a dakin ta zaunar da ni tana karantamin yadda kaddara take zuwa da yadda ake son bawa ya karbe ta. “Ammy duk ban gane wannan ba, mi ke faruwa ne?” “Zahra ina son ki dauki wannan a cikin kaddararki, ina mai baki hakuri kuma ina mai bakinciki sanar da ke cewar ba za a iya daura aurenki da Abiey ba a yau...” With full confidence Ammy ta fada min haka, da farko ban yarda ba sai na dauka wasa suke min, har sai da ta jaddamin cewar da gaske ne ba za a daura ba, da na nemi hujja sai ta dauko takardar gwajin da Dr Zainab ta yi ta, bana bukatar wani ya karanta min abun da takardar da kunsa domin ni ma na yi karatu kuma ina cikin yan gaba gaban da makaranta take alfahari da su saboda kokarinsu. “Ammy ko dai ba daidai ba ne” Na tambaya bayan hawayen idona sun gama jika takardar jikina yana ta rawa. “Ki yi hakuri Zahra kadarar ku kenan, shi kansa Aliyu yana cikin wani, shiyasa ya kasa sanar da ke” “Ina son na ganshi Ammy, Ammy wannan takardar da gaske ne?” Kai kawai ta daga min ta share hawayen da suka cika idonta ta juya ta fice a daki, kamar makauniya haka na fadi ina lalaben abun da be bata ba, kuka ya hado kayansa yayi masauki a gurina. Abiey na shigo yana ta kallona ya gagara ce min komai, sai na isa gabansa na nuna masa takardar. “Kalli abun da suka ce amman na san ba gaskiya ba ne, kalli Abiey wai ina dauke da kwayar dake karya garkuwar jiki” Be duba takardar ba sai kawai ya dauke kai. “Hakuri zamu Zahra, na so na aureki a haka amman ban isa na taka dokar Ammy ba, saboda bata yarda ba” A ranar na ga rashin imanin Abiey kuma na yi mamaki, domin a irin soyayyar da yake nuna min na yi zaton zai iya aurena a haka amman sai ya juya min baya, har kasa na kai ina rokonsa ina masa magiya kar ya ba wa iyayena kunya, kar ya watsa jama'ar da aka tara mana, amman ina be saurareni ba, da na fahimci ba shi da niyar canja kudinsa sai na roki ya amince a daura auren daga baya sai ya sake ni, nan ma ban samu ba daga gareshi. Ni da Mama da Yaya Maryam muka shiga cikin tashin hankali saboda abun da ya faru, Baba ma ya nuna damuwarsa sosai musamman ganin sa'a daya ta rage a daura auren taya za a sanar da mutane cewar an fasa auren. A nan ya kawo shawarar a daura da Deen albashi idan ma bana son sa sai ya sake ni bayan an fita kunya, a lokacin na yaba da kokarin Baba da kuma na Deen duk da kasancewar ba shi a gidan a lokacin, haka kuwa aka yi sai aka daura auren da Deen a maimakon Abiey. Kamar wanda aka yi ma mutuwa haka nake ta rusar kuka Mama na ba ni hakuri, ita ma kukan take Yaya Maryam ma haka. Washe garin ranar da aka daura auren aka sake yin gwaji har kala uku yana bada results daya cewar bana dauke da cutar daga lokacin sai na gane yaudara ne Abiey yayi, kuma na gasgata maganar Deen. Daga lokacin sai ala ta yanke tsakanin mu da su Ammy. A lokacin sai na zama wata sarauniya a gurin Deen ya fara nuna min kaunar ba shi ba, duk wani abu da yake marar kyau ya daina kuma yayi min alkawarin cewar har a abada ba zai sake kusantar kayan maye ba, ni kuma na yarda da yi zaman aure da shi domin na karbi kaddarar da ta zo Baba ya kama mana haya, Mama da siyar da daya daga cikin gidan da Baba ya bar mana ta yi min kayan daki, aka bar dayan. Na sha wahala kamin na saba da Deen, sai dai na same shi ba a yadda na yi zatonsa ba, a lokacin na fahimci Deen mutum ne mai sauki kai kuma mai kauna ta fiye da Abiey ma wacan lokacin da ban san komai akai ba, ya mayar da ni sarauniya.......” Na numfasa bayan na dire a linen da na yi masa karyar cewar na haifi cikin da Deen ya mutu ya bar ni da shi babu rai, sai dai ban boye masa cewar yana da ciwon hanta ba da kuma zancen aikin da aka yi masa haka ma na gano cewar shi ya shirya duk abun da ya faru tsakanina da Abiey ba da irin tsabanin da muka samu da Hajiya da Baba ta dalilin haka, har zuwa hana Abiey aurena da Ammy da Mai Martaba suka yi. Na saka hannuna na share hawayena, ina jin wani abun kamar a lokacin yake faruwa. Sai ya koma jikin kujera ya zauna yana kallona. “Akwai abun tausayi akwai abun dariya a labarinki, haka ma akwai abun takaici da bakinciki da bacin rai, sai dai kin rage wani abu daga cikin labarinki” Na dago na kalleshi da idanuwan da hawaye suka ki tsaya min. “Kin manta baki fada min cewar kin siyar da ďan da kika haifa saboda ki nemawa Deen kudin magani ba” A razane na koma baya ina kamar wanda ta ga wani abun tsoro. “Ni.... Ban siyar ba....” “Kin siyar Zahra kin siyarwa Jamila da ďanki wanda ta yaudare ni da shi a matsayin ďana” Ban san lokacin da na rufe baki na mike tsaye da sauri ina girgiza masa kai. “Ba haka ba ne...” Sai yayi murmushin da na tabbatar iyakarsa a fatar bakinsa yayi min alama da na zauna, amman na kasa zaman. “Haka ne, Zahra na san gaskiya saboda na saka a yi min bincike akanki kuma jinin da na saka aka dauka na ki, Dr Zainab ta kawo min gwajin na farko wanda shi ne na gaskiya ba wanda Jamila da dan'uwanta suka bukaci a ba ni ba, Dr Zainab ta fada min gaskiyar wacece ke tun kamin ki ba ni wannan labarin, kuma na tabbatar da gaskiyar haka domin babu banbanci da abun da Dr ta fada min cewar kin yi soyayya da kanenta, kuma kin siyar da cikin ne saboda ki biya kudin aikin da za'ayi ma mijinki” Na fadi gurfane a gabansa. “A yanzu na gane dalilin Jamila na kin yarda kowa ya dubata tun tana da cikin har zuwa haihuwar da a nan ba so ayi ta ba, kuma ta ki yarda kowa ya duba yaron nan sai Dr Hamid, ina ta zargin wani abu amman ban zafafa gudun kar na yi zaton abun da ba shi ne ba” Na hade hannayena guri daya na mika masa daga inda nake zauna. “Kana da damar ka hukunta ni, ka dauki duk matakin da ya dace a kaina, ka yi kokari ace ka san gaskiya kuma zuba mana ido, daman Sauban yace zai fada maka gaskiya, yayi min barazana da wannan, a kokarina na rufawa kaina asiri na amince zan aureshi, shi ne albishir din da Hajiya Jamila take maka domin a yau za a daura aurena na uku da mutum da be dace da ni ba, kuma na san da cewar ka san wannan gaskiyar da ban amince masa ba, na amince ne saboda na rufawa kaina asiri saboda kar duniya ta ji kuma kae iyayen Deen su ji, kai ma kuma sani saboda ina tsoron abun da zai biyo baya, ashe ba zan tserewa tambayoyin yan jarida ba, ashe Hajiya zata hukunta ni, ashe kuka be kare min ba zan kunyata a idon duniya, kuma ďana zai yi Allah wadai da abun da na yi, kaico na ni Zahra” Na karasa ina jin wani irin nadama da bakincikin kuskuren da na aikata, wani irin kuka ya ci karfina. Bakinsa ya cika da iska ya busar yana girgiza kai. “Na jidadi da ya kasance ďan sunna ne Amir ba shege ba, hakan zai karfafa min guiwar rainonsa a matsayin ďana, duniya ta sheidi cewar Amir ďana ne, taya zan fito a idon na fadi cewar ďan da Jamila take ikirarin ta haifa min ba ďana ba ne? Ya za'a kalleni? Na san Amir ba jinina ba ne amman ina sonsa a haka saboda ban taba haihuwa ba, ina son na rike shi a matsayin ďana, na miki alkawari Zahra babu wanda zai san da wannan kar barazanar kowa ta daga miki hankali, na saka muku idone saboda na ga iya gudun ruwanku, kuma na kara karantarki, ina da security camera a ko'ina a gidana ba dan na rashin yarda da matata ba, sai dan taimakawa tsoro, hakan kuma ya taimaka min makura gaya wajen fahimtar wasu abubuwan, karki cilastawa kanki auren mutumen da baki ra'ayi saboda neman rufi asirin da ya dade a rufe, idan har akwai wanda ya dace dake a yanzu Zahra to ni, ko dan saboda ki rika ďanki kuma ya tashi a hannunki, kuma ina d yakinin ta dalilin zan iya samun farincikin da na gagara samu a baya, wata kila ke Alheri ce a gareni” Sam sam sam ban fahimci inda kalamansa suka dosa ba, ba dan ban fahimci da yare da yake magana ba, sai dan rikicewar tunani domin abun da ya fi karfin kwakwalwa ya shiga cikinta, mikewa na yi tsaye ina rangaji kamar yar maye. Ya kalli agogon dake falon. “Lokacin Sallah yayi, amman kamin na tafi ina son na tambayeki shin baki son ki zama silar farincikin wani ne Zahra? Ba ki son ta dalilinki ni ma na samu magaji? Shin baki bukatar kasancewa da ďanki ne? Ki kira yan'uwanki sanar musu kar a daura auren saboda zaki yi shi ne akan cilastawa ba dan kina son shi ba” Na saka hannayena na dafe kaina, wani abu nake ji mai kama da juwa kamar mafarki yake daukata, da sauri na juyo na fito daga falon ina takawa kafafuwana suna yin kamar ba za su dauke ni ba. Daker na iya jan kafafuwan na kawo kaina BQ, Mama da bakinta sai kallona suke kamin Mama ta fara tambayar “Lafiya kike?” Bana tunanin ina cikin hayyacin da zan iya amsa mata, sai faduwa na yi kan katifa na runtse ina jin bachi nake a yanzu ne zan farka daga mafarkin da nake. Tunawa da Sauban ya saka na bude na murza idon na tabbatar ba mafarki nake ba, kuma na nemi tsarin Allah daga sherin shedan kana na zabura da dan kuzarin da yayi min saura na nufi wayata na dauka na kwada nasa kira. Be daga ba na sake kiransa nan ma be daga ba sai na fita waje da sauri gurin Mama na mika mata wayar. “Mama ki kira su Baba ki ce a dakatar da daurin auren nan dan Allah?” “Ba lafiya ba, zan miki bayani daga baya, ki yi magana da su yanzu dan Allah” “Ke Lafiyarki? Baki fada min komai ba zan kira waya na ce kar a daura aure?” Ta zaunar da ni ganin yadda nake ta lilo kamar zan fadi sai haki nake irin na wanda ta yi gudun fanfalaki. “Miya faru?” “Bana son shi Mama bana son shi, daman cilasta ni yayi kuma yanzu na gane gaskiyar bana son shi” “Zahra? Ni fa kwana biyun nan ban gane miki ba? Mi ke damunki” Ganin zata bata min lokaci ya saka na kira Baban da kaina, sai dai na yi rashin sa'a shi ma be amsa kirana ba, na sake kiran dayan shi ma the same be daga ba, wata kila suna cikin masallaci. Wata Gwaggota na kira tana dagawa na ce “Gwaggo Baba na kusa? Ki fada musu a fasa daurin auren nan, kar a daura dan Allah” “Lafiya kike?” “Akwai matsala, Gwaggo kar a daura” Sai ta nemi na sadata da mahaifiyata, a take na mika mata wayar ta karba tana amsar mata da cewar ita ma bata san dalilina na fadar haka ba, amman tun da nace kar a daura to a haka kura kawai kar a daura. Gwaggo ta amsa mata da to, kanen mahaifiyata da suka zo suma suka hau buga waya wasu ba su daga ba, wadanda suka daga kuma aka sanar musu cewar a fasa daura auren saboda an samu wata matsala. Sai kashhhhh mun yi latti aikin gama ya gama lokaci ya kure mai afkuwa da afku, domin daya daga cikinsu ya sanar mana cewar an daura. Baya baya na yi na fadi zaune. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un...” Shi ne abun da nake ta fada ina girgiza kai, hawaye na cin karfina. “Miya faru Zahra? Ki yi min magana mana?” Kasa magana na yi sai kuka na ke, na sake daga wayata cikin karfin hali na sake kiran wayar Sauban wannan karon ya amsa muryarsa radau. “Hello Zahra kin kira wayar tana silent lafiya?” “Ina son ganinka yanzu yanzun nan” “Lafiya?” “Ina son ganinka na ce” Na daka masa tsawa da muryar da ban taba sanin ina da irinta ba. “Okay gani nan zuwa” Ina sauke wayar Mama ta rika hannuna ta shiga dani dayan dakin. “Kin fi karfin awa hudu a bangaren Hajiya Jamila, yanzu kuma kin fito a cikin yanayin dake nuna ba ki cikin hayyacinki kina cewa a fasa daura aure miya faru?” “Mama Sauban ya cilasta ni amincewa da aurensa ne, saboda yayi min barazana da siyar da cikin da na yi, zuwan da na yi a yanzu kuma Mr Bashir ya riga ya gane gaskiyar komai” “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un” Mama ta dora hannu akai, ni kuma na zauna domin ina jin idan na kara minti biyar a tsaye zan iya faduwa. Mama kasa cewa komai ta yi tashin hankali ya hana ta kuka, ni kuma ya saka ni zubar hawayen da ban san adadinsu ba. Kamar kyabtawa da Bismillah yan'uwan mahaifina da na mahaifiyata suka kira cewar suna son su shigo an hana su, sai Mama ta fita domin shigowa da su tana ta sake saken karyar da zata yi musu, domin ba zata fada musu gaskiya a yanzu ba sai idan komai ya fito fili su ji. A daidai wannan lokacin Sauban ya kira wayata ina amsawa ya sanar min cewar yana waje yana jirana. Kamar mahaukaciya haka na fito dakin ko talkami ban tsaya sakawa ba na nufi BQ, jikina ma ya samu rufin asiri ne daga hijabin da na saka a dazun da zN tafi gurin Mr Bashir domin da a yanzu ne ina da tabbacin da ba zan saka shi ba. Kamar aljana haka na isa gurin da ya faka motar ina jin kamar na makureshi na huta. “Ka cutar da ni a banza, abun da nake yi ma gudu ban tsira ba, Mr Bashir ya san komai” “Calm down Zahra” Ya fada yana kwantar min da hannayensa. “Ba zan kwantar da hankalin ba, daman sha'awar jikina ya saka ka cilasta ni ko to ga jikin nawa ka yi abun da kake so, saboda kun maida ni bola kowa ya dauko shararsa akai” Ina kware cinyar hannuna na mika masa cikin kuka, sai yayi baya. “Subhanallahi, ni ba Muhamminki ba ne” Wani kallon uku saura kwata na yi masa, sai ya fadada fuskarsa da murmushi. “Ba da ni aka daura auren ba” “Da....wake....” Na bukata bakina a bushe ina motsa shi daker na hada kalmomin. Zagayawa yayi ta dayan side din motarsa mai bakin gilashin da ba a iya ganin abun da ke ciki, ya bude. Komai na duniyata sai ya tsaya cak.....! Ciki har da tunanina da numfashina da kuma hawayena, lallai a yanzu kam na tabbatar duk abun da ya faru a yau mafarki ne ba zahiri ba...! _______________ Ni kam me Zahra ta gani ne? 🤔 Ina Yan Team Team kowa ya dauki nasa 💃 [12/2, 5:18 PM] Oum_Nuwaira🥰: 6️⃣6️⃣ Kamar hoto haka na tsaya a gurin ina kallonsa, har ya karaso kusa da ni fuskarsa da murmushi ya kai hannunsa ya share hawayen da gudunsu ya tsaya a kumatuna. “Cikar burina...” Ya kama hannayena ya murza yatsun a hankali. “Ban... Ban...” Sai na kasa furtawa ganina yayi nisa irin nisan da kafafuwana suka gagara daukar jiki har sai da taimakon Abiey na tsaya tsaye rabin jikina kuma a kirjinsa. Ba bachi na yi ba kuma ba zan kira shi da suma ba, haka kuma ba zan ce ina a cikin hayyacina ba. “Komai ya kare you're mine now” Na ji maganarshi muryarsa saitin kunnena kamar mai rada, ni da shi muka sulale jikin motar sai dai kamin na kai kasa na ji an yi sama da ni, sai hankali yayi kaura daga jikina ban sake sanin inda nake ba. Sauyar iskar da nake shaka da kuma sanyin dakin ya tabbatar min da a gida nake ba, karfin halin da na yi na bude idanuwana ne na sai na yi arba da kyakkyawar fuskar da har yanzu nake ganinta kamar a mafarki, kwance nake shi kuma yana zaune rumgume da rabin jikina, fuskarsa saitin fuskata. Wani irin tarayya idanuwanmu suka yi wanda na kasa ko da kyabta su balle na dauke kai daga barin kallonsa, sakon lallausan murmushin da yake aiko min ya hana ko dan yatsana na daga balle kuma raba jikina da na shi. Bakinsa ya kai ya sumbanci hancina, a nan na yi nasarar rufe idon nawa na ina sauraren yadda yayi sama ya sumbacin goshi hawayen idonshi suka sauka akan fatar idona dake rufe, yana ta shafa fuskata da hannunsa. Firgigit na yi na tashi zaune sai ya matso kusa da ni, hakan ya saka ni sauko daga kan gadon da a yanzu na tabbatar na asibiti ne. “Ina Sauban?” “Ya tafi gida” “Me nake yi a nan?” “Su ma kika yi” Ya sauko daga kan gadon ya karaso inda nake tsaye ya kai hannunsa ya taba fuskata. “Me kake yi haka Abiey” “Ke halalina ce a yanzu Zahra babu wata katanga ko shamaki a tsakanina dake” Na matsa baya ina rausayar da kai hawaye na taruwa a idona. “Ni ban gane ba” “Yanzu zaki gane” Ya matso kusa da ni sosai na yi baya ya sake matsowa har sai da ya kai ni jikin gina, ya dora gaoshinsa saman nawa yana kallon kwayar idona, saurin rufe idon na yi sai ya fara goga min hancinsa a saman nawa, numfashinsa da nawa suma tarayya da juna, sayin halshensa na ji a saman lips dina, kamin ya zira halshen a tsakankanin fatar labbana ya taba hakorana, a hankali ya kama lebena na kasa ya fara tsusa kamin ya hade bakinsa da nawa, yawun bakinsa ya ke turo min idan na hade sai ya karbi nawa ya maida a bakinsa, haka yayi ta cakusa yawunsa cikin nawa har zai da ya zamana bana jin dandalin yawuna sai nasa, halshensa kuma na aikin juya nawa halshen, wata kila dai mun dauki awa a haka ko kuma kasa da minti talati sannan ya cire bakinsa daga nawa ya sumbanci gefen fuskata ya dora bakinsa saitin kunnen hannunsa kuma daidai kwankwasona. “Hiayatee..... Duk son da nake miki haramci ya taba ba ni damar yi miki haka Zahra?” Na kasa cewa komai zuciyata ta cika da tarin tambayoyi. “Amman a yau hallaci ya ba ni wannan damar” Bude idon na yi sai ya dago yana zagaye fuskarta da nasa idanuwan. “Da gaske kai na aura ba Sauban ba?” “Kina ganin zuciyata zata iya dauka ki rayu da wano namjin da ba Aliyu ba? Duk abin da Sauban yake miki da sanina yake aikatawa, ni na bashi umarni saboda na samu wannan damar da na dade ina mafarkin zuwanta” “Miyasa? Miyasa zaka shirya wannan Abiey? Ya zaka yi da Ammy da Mai Martaba?” “Samunki Hiayatee shi ne abun da nake so na yi, a yanzu kuma duk abun da zai biyo bayan wannan mai sauki ne” A cikin abokan tarayyar nan guda biyu wato farinciki da bakinciki sai an rasa wanne zan yi. Murnar na samu Abiey a matsayin mijina ko kuma bakinciki ya aureni ba akan ka'ida ba? “Taya wai aka musanya Sauban da kai” Ya kama hannuna ya kai saitin zuciyarsa ta dora, wani irin bugawa zuciyarsa take fiye da kima. “Tambayi wannan” Na kwantar da kaina a kirjinsa ina kuka. “So be kamata ya saka mu mu aikata haka ba Abiey” Sai ya rumgume ni. “Dole ce ta saka Zahra, babu wanda zai saurare mu babu wanda yake son farincikinmu, kowa kansa ya sani” Kamar an yi min bushara da rahama da gafara haka na ji a lokacin da nake jikin Abiey, muka a dakin manne da juna ni da shi, sai da muka ji motsin taba kofar dakin sannan na raba jikina da nashi, shi kuma ya tashi ya fita bayan ya gaisa da Mama, a nan Mama ta kara fayyace min komai, ashe da aka je daura aure sai aka gabatar da sunan Abiey wato Aliyu a maimakon sunan Sauban na ainahin wato Tahir. Mun wuni a asibitin can bayan sallah Magariba Dr Zainab ya shigo, dubani na yi mamakin ganinta, ina kallonta da faduwar gaba domin ina jin tsoron ranar da za su gane gaskiya, a kusa da ni ta zauna, yana min ya jiki. “Ya jiki Amarya” Na sunkuyar da kao cike da kunya da kuma tsoro a lokaci daya, daman ta sani ne? Mama ma kallonta take da mamaki ita kuma tana ta dariya. “Kuna mamakin yadda aka yi na sani ne?” Mama ta ce “Aikan da mamaki, mun yi zaton daga Abiey sai Sauban ne suka san gaskiya” “Toh da ni aka shirya komai, Ammy da Mai Martaba ne kawai ba su sani ba, amman babu abun da Abiey zai yi da ba zai fada min ko ya nemi shawarata ba, ba dan ni da kanen mahaifin Sauban da aka tura ba su yarda sun je ba” “Amman a matsayin ki na babba be kamata ki aimata wannan abun ba, saboda gudun matsala? Musamman gurin Mai Martaba” “Da ni aka lalata auren Abiey da Zahra na farko, domin Deen yayi garkuwa da mijina ne har cikin gidana, kuma na rasa hujjar da zan gabatar da shi a gaban kotu har sai bayan da komai ya faru, sun shigo a cikin gidan dauke da bindigogi sanye da mask a fukokinsu ta yadda bana iya tantance ko daya a cikinsu, sai dai na gane cewar shi din ne bayan an daura aurenki da shi, tun kamin su bar gidan sun gargade ni cewar kar na karna kuskura na fadawa police domin rayuwar mijina suke so ba tawa kuma ba dukiyar da muka tara ba, kowa yayi magana a cikin mutanen da suka yi magana ban da mutum daya wanda nake kyautata zaton shi ne Deen, tun a ranar suka ba ni umarni na yi duk abun da zan iya a fasa aurenki da Abiey, idan ba haka wanda ya dauke mijina zai kashe shi sannan ya akashe kansa, sun yi min rantsuwar dake nuna ba da wasa suke ba, lokacin idona ya rufe musamman da aka dauki kwana biyu babu kira babu wani bayani daga jami'an tsaro cewar an gano inda mijina yake, gashi lokacin da suka ba ni umarni ya rage kwana uku a daura auren Zahra da Abiey, na rasa yadda zan bullowa lamarin ina ta sauraren ko za su kirani amman ba su kira ba, hankalin Ammy da na yan'uwan mijina ya tashi balle kuma ni da nake matarsa, a lokacin ina ganin kamar ransa yana hannuna ne, domin aikata abun da aka umarce ni zai ceto rayuwarsa, akasin haka kuma zan rasa shi, amman Abiey ya kasa fahimta ta saboda kaunar da yake miki ta rufe masa ido da baya iya hangen komai sai ke, be aminta na aikata ba, bayan mun shirya komai na fada masa sai yace ko da haka ta faru zai aureki, a nan Ammy ta shata masa line ta ce idan har ya zabi auren Zahra akan rasa rayuwar yar'uwarsa, to sai ta masa baki, a dole ya hakura dake sai dai ni yake ta dorawa laifin, bayan mijina ya fito aka daura aurenki da Deen sai muka fahimci shi ya aikata wannan abun, da na tambaye mijina a ina ya aje shi sai yace sun kai shi a ciki daji ne, kuma tabbas da ban aikata abun da suka bukata ba da kashe shi za su yi da gaske, sai dai yace da za a dawo dashi cikin gari bayan an daura aurenki sai da aka rufe masa fuska kamar yadda aka yi masa a lokacin da za a shiga da shi dajin, a tsawon zaman da yayi a dajin be ga fuskokinsu ba kuma be ji muryar wani da zai iya ganewa, haka kuma ba su bar masa wata alama da zai fahimci komai ba, even camera tsaro dake wajen gidanmu ta dauki motarsu ne kawai da bata da number kuma aka gagara gano shi har sai dai mao faruwa ta faru, bayan komai ya laba na ce zan saka shi a kotu sai Abiey ya hana domin ba mu da wata cikakkciyar shaida a lokacin, sai dai muna da kudin da za mu iya sakawa a daureshi ko da shi ne da gaskiyar a haka dai Abiey ya hana saboda kar a tashi hankalinki, tun daga lokacin na gane kaunar dake tsakaninku daga Allah take, yan mata da yawa su kan so namiji saboda kudi ko wani abun da yake da shi, sai dai ke ban ga haka daga gareki ba, shi ma auren da kika yi be saka kaunarki fita daga ransa ba, sai ma karuwa da ta yi, saboda muka samu rashin fahimta da shi, a yanzu kuma na samu hanyar da zan gyara wacan barnan da na yi, me zai hana na yi haka? Idan ban taimaka masa a yanzu ya samu abun da yake so ba? Da wane ido zan kalleshi? Ke ma kuma na san kin dauke kai daga gareshi ne kawai saboda an shata muku layi, ya fada min idan ya fito fili ya nuna yana sonki abu ne mai wahala ki amince masa, saboda kin nuna masa ya bi umarnin Ammy da Mai Martaba, shiyasa muka bullo miko da wannan hanyar” Tun da ta fara maganar bata tsaya ba har sai da ta kai aya, ni kuma na dago na kalleta hawaye wasu na bin wasu. “Amman hakan zai kara lalata alakarsa da Mai Martaba ne kawai, wata kila sanadin haka Ammy ta kara tsanata?” “Ke miye laifinki a ciki Zahra? Ke da aka yaudara aka aura? Idan akwai mai laifi to ni da Abiey da Sauban ne, ki cire wannan a ranki, kuma karki takurawa kanki da neman sai Abiey ya rabu da ke ina da tabbacin idan haka ta faru, to zamu rasa shi ne a lokaci daya, ko a yanzu kadan ya rage mu rasa shi domin damuwar dake ransa ta haifar masa da babbar matsala, wata kila warkewarsa na daga cikin samunki, shiyasa ni ma na jajirce har haka ta faru...” “Dr ki daina yi min wannan fatan, da yardar Allah ba zan sake zama matar takaba, ba zan sake binne mijina ba sai dai shi ya binne ni” Murmushi ta yi ta kwantar da kaina jikin kafadarta. “Ni kaina ban jidadin yadda abubuwa suka faru ba, amman wani lokaci ya kamata mu yarda da kaddara mu bar zukata su yi aikinsu, Allah yasa Ammy ta fahimci haka” “Ameen Mama” Ta daga ni ta mike tsaye. “Zan tafi wata kila ba zan samu dawowa ba, sai dai na same ki a gida” “Na gode sosai Dr mun yi magana da Mr Bashir, ya sassauta min fiye da yadda na yi zato kuma hakan ya faru me ta dalilin bayanin da kika masa kamin na dora masa da nawa” Ta dawo ta zauna tana kallona da mamaki. “Ya miki magana kenan?” Na daga mata kai ina jin tausayinsa a raina. “Yayi kuma ya roki ni abun da da ace ba da Abiey aka daura auren nan ba, da na amince masa ko dan Amir, domin ya fito min a sigar da ban yi zato ba, ya nuna min natsuwarsa da hankali, daga ni har matarsa da Dr Hamid ba mu kyauta ba, amman ya kasa natsu be yanke hukunci a cikin fushi ba, na dade ban ga wani mutum mai hankali da kwantar da kai ya aiwatar da wani abu ba kamar shi” “Daman can na sa ran haka, domin be dauki abun da zafi ba, kuma daman idan har zai yi tunani haka ya fi dacewa domin idan yace zai hukuntaki ko matarsa duniya zata kalleshi a matsayin marar tausayi da tunani, kuma har wanda be san abun da ya faru ba zai sani, hakan kuma ba zai goge komai daga zuciyarsa ba haka ma daga abun da suka aikata, tabbas Mr Bashir mutum ne, na jidadin abin da yayi, Allah ya dubi zuciyarsa ya ba shi haihuwar da yake nema” “Ameen” Ni da Mama muka amsa, bata dade da tafiya ba, yan'uwa Mamata suka shigo duba ni. ABIEY POV. A hanya yayi sallah Magariba sannan ya shigo cikin gidan, kallo daya zaka yi masa ka fahimci yana cikin farinciki, da kuzarinsa ya shiga dakin Ammy ya zauna gefen gadonta har sai da ta sallame sallah sannan ya dawo kusa da ita ya zauna. Ta kalleshi da duba na mamaki “Aliyu ya kake yau kamar wanda aka yi ma bushara...?” Na sumbanci kumatunta yana murmushi. “Na cika wani buri nawa ne da na dade ina zuwan jiransa, Alhamdulillah ko a yanzu na mutu zan tafi cikin farinciki” Ya kwantar da kansa jikin Ammy a shagwabe ya fara magana. “Ammy na miki wani katon laifi da ba lallai ne ki yafe min da wuri ba, kuma be zama lallai zuciyarki ta karbi abun da wuri ba, amman dai ke zaki taya ni yakinsa a gurin Mai Martaba har na yi nasara ko kuma shi yayi nasara a kaina wanda bana fatar haka” Carjin dake hannun Ammy ta aje ta juyo da kyau ta kalleshi cike da fargaba. “Ban fahimta ba, fito fili ka fada min abun da ka aikata” “Sai kin min alkawarin ba za ki yi fushi da ni ba” “Idan har kasan abun da zai saka raina ya bace ne miyasa zaka aikata tun farko?” Ya gyara zamansa ya sauke kai kasa with serious face ya ce. “Ammy kin san yadda nake matukar son Zahra” Ammy ta daga masa hannu. “Dan Allah karka fada min ka aikata wani abu akanta, ba kusa ba ba kuma nesa ba na shata line tsakaninka da yarinyar nan” “Haba Ammy wannan ba halinki ba ne, kuma kin fi kowa son abun da nake so” “Eh amman haka ba zai saka na so abun da zai cutar da kai ba” Ya kwanta saman jikinta. “Ta ina Zahra ta zama cutarwa a gareni Ammy? Yarinyar da ke da kanki kika shiga kika fita wajen ganin an mallaka min ita?” “A da can ko Aliyu? Ba a yanzu ba, da Mai Martaba ya zaba maka matar da zaka aura, kuma yarinyar babu kalar wulakanci da bata yi maka ba bata yi ma yan'uwanka ba” Ta janye jikinta ta matsa baya cikin bacin rai tace. “Tsaya ma wai me ka aikata?” Murmushi yayi ya shafa kansa. “Ammy wani zuwa da Zahra ta yi a nan kika koreta, bayan kin mareta na bi bayanta, ina bata hakuri sai ta ce Abiey ka nuna min kana kaunata tsakani da Allah ta hanyar bin umarnin Ammy da Mai Martaba, so yayi kadan ya saka ka bijirewa umarnin mahaifanka, ina son ka nuna min banbancin naka so da na Deen, karki yi son kai bakan ne kawai zai tabbatar min da kana so na da gaske, tun daga lokacin sai na dauki alkawarin zan nuna mata da duniya ina Sonta so na hakika, a lokacin ne na bullo da shawarar Sauban ya fara nemanta, yana nuna mata kulawa har ta amince da shi, saboda na san duk wata hanya da zan bi ba ku yarda ina son Zahra ba balle har ku tausaya min ku bar ni na mallaketa, ita kuma ba zata aminta da ni ba idan na fito mata a mutum, saboda tana matukar tsoron halin da zan jefa kaina a sanadinta, shiyasa na biyo ta wannan hanyar” “Har yanzu ban fahimci abun da kake nufi ba, da ka biyo ta wannan hanyar sai aka yi yaya?” “Hakarmu ta cinma zuwa da Sauban domin be fito a sigar yana sonta ba, har sai da wata mafitar ta bullo mana ta siyar da cikinta da ta yi ga matar da take zaune a gidanta a yanzu, kamin tafiya ta yi nisa sai da Sauban ya sanar da matarsa ni ma kuma na same shi har gida muka kara yi mata bayani saboda ta gamsu, gudun kar wata matsala ta taso ko kuma wani ya kawo mata wata maganar daga baya, ban aiwatar da komai a karan kaina ni kadai ba har sai da na shawarci Dr” Ammy ta daka masa tsawa. “Kana ta bata min lokaci Aliyu ka fada min abun da ka aikata” Ya hade hannayensa guri daya. “Mun yi nasara, Zahra ta karbi Sauban da hannu biyu, sai muka yi amfani da damar siyar da cikin da ta yi Sauban ya cilasta mata aurensa, mun tafi tare da Dr mun yi magana da mahaifiyar Sauban, ganin mahaifinsa baya raye sai ta samu kannen mahaifinsa ta gabatar musu da abun da muke bukata, kuma muka yi nasara suka amince, Zahra ta gabatar da Sauban a gurin iyayenta, da aka tashi daura aure sai aka ambaci sunana a maimakon na Sauban” Ta mike tsaye da sauri tana kallonsa kamar wanda ta yi arba da wani abun tsoro. [12/2, 11:00 PM] Oum_Nuwaira🥰: 6️⃣7️⃣ “Aliyu kana cikin hankalinka kuwa, da gaske kake wai ko wasa?” Ya saki murmushi. “Taya zan zauna na tsara miki karya mai tsawo a haka? Idan baki yarda da ni ba zaki iya kiran Sauban ko mahaifiyarsa ko Dr kinji” Ammy ta koma kallon sabuwar farar shaddar dake jikinsa ga wani uban kamshi da a yau yake da ya banbanta da na kullum. “Aliyu ka aikata babban kuskure, taya son zuciya zai dauke ka ka aikata wannan abu? Ina tunaninka ya tafi? Ina taya idonka zai rufe ka aikata wannan abun?” Ya mike tsaye yana kallonta fuskarsa cike da damuwa. “Ammy karki kasa fahimtata mana kin fi kowa sanin yadda nake kaunar Zahra” “Na ji kana kaunarta! Idan ma na fahimce ka taya mahaifinka zai fahimce ka? Daman shirin da kake kenan shiyasa ka ce a matso da aurenka da Yasmin?” “Tasa mai sauki ce, idan har ke kin fahimta, a yanzu ne zan gane idan Mai Martaba ne mahaifina ko akasin haka, na san labarin zai fita kuma kamin kowa ya ji shi ni zan fara sanar da shi” Ammy ta girgiza masa kai. “Aa karka aikata wannan kuskuren Aliyu, ba zai fahimce ka ba, kuma tsabanin da zai shiga tsakaminku zai saka yan'uwanka jindadi, akwai makiya a tare da kai be kamata ka aikata wannan abun ba Aliyu” “Na gagara fahimtar irin son da kike min Ammy kina so na amman baki son farinciki na? Mi Zahra ta yi miki ne kika juyar da soyayyar da kike mata zuwa kiyayya?” Ammy ta matso kusa da shi tana kwantar da murya. “Ba son Zahra ne bana yi ba Aliyu, ka fi kowa sanin irin rayuwar da Zahra ta yi a gidan nan, ka fi kowa sanin yadda nake son farincikinka, amman haka ba zai saka na goyi bayan butulcewa mahaifinka ba” “Ba zan butulce masa ba, zan bi umarninsa zan auri Yasmin, amman ba zan rabu da Zahra ba, kuma haka da na yi ta taimaka masa domin an yi auren a sirrance, ba tare da sanin kowa ba, na san abun da Mai Martaba yake gudu yan da jama'ar gari su zage shi ko kuma su zafafa da mugayen kalamai akan auren, kamar yadda suka buga labarin cewar na rusa gidan uban matata saboda ya hana ni ganinta” Ammy ta yi baya ta zauna saman gado ta lumshe ido. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, shekara nawa ina neman hanyar da zata gyara tsakaminka da mahaifinka, sai a yanzu da komai ya zo karshe sai kuma ka bullo min da wannan?” Ya durkusa a gabanta. “Ban yi dan na bata tsakanina da mahaifina, kuma bana fatar haka, kuma na miki alkawari idan har Ke ko Mai Martaba kuka dage akan sai na rabu da ita, tabbas zan hakura da ita, amman ki sani tana ciki raina kuma rabuwa da ita zai iya ajalina” Ammy ta kai hannu ta shafa kansa. “Allah ya sanyaya zuciyar mahaifinka ya fahimce ka, kuma ya karbi Zahra da hannu biyu, ba ni da matsala da haka, ina son abun da kake so ďana, amman ba zan boye maka ba, wannan abun da ka aikata ko a film ba a haka, ita ma dai Zahra ta yi sake ta yi ganganci” Ya kwantar da kansa jikin cinyarta yana jin wani sanyi da kalaman da ta yi masa. “Wallahi ko kadan Zahra bata da laifi Ammy, ba da saninta muka aikata ba, gargadi ta yi min yasa ban yarda na tura Sauban ko kuma ni na tafi mata kai tsaye ba, kuma ina son ki bar ni na fara yin magana da Mai Martaba har sai idan abin ya gagara tukuna sai ki shiga ciki, amman ina son na yi magana irin ta uba da ďa shi, ina son na samu wannan yanci da zan iya tunkarar mahaifina at any time na yi magana da shi” “Allah ya saka ya fahimta” “Ameen” Ya amsa sannan ya saka hannunsa ya ciro wayarsa dake vibration ya mike tsaye. “Sauban ne” Be amsa kiran ba sai kawai ya juyo ya fito daga dakin ya sauko downstairs ya nufi kofa ya bude, sai suka sakarwa juna murmushi Sauban ya shigo cikin falon suka rumgume juna. “Congratulations” “Thank you na samu komai ta dalilinka” “Yeah anything for our friendship, Allah yasa Ammy bata yi maka tsawa ba” “for now dai kamar ta fahimta, sai dai ban san abun da gaba zai haifar ba, kasan Ammy wani lokacin bata da dadi, amman ba samu sauki ta fahimci, kuma ta fada min idan har Mai Martaba zai karbi Zahra bata da matsala” “Alhamdulillah, haka muke so, fatan Allah ya sa Mai Martaba ma ya fahimta” Ammy dake saukowa ta amsa da “Ameen, Sauban kai kake biyewa Abokinka kuna aikata duk abun da ya zo muku ko? Sam sam sam haka be de ba, kuma na tabbatar da ba ni ce ba, da abun da zai faru zai fi wannan” Sauban yayi dariya ya karasa shigowa cikin falon, ya zauna yana fadin. “A gafarce mu Ammy, mun aikata kuskure amman dole ce ta saka, mum aikata hakan ne saboda muna tunanin kamar hakan shi ne mafita” “Amman kuskure Babba Sauban, abu ya zo mana ta inda ba mu yi zato ba, kun saka mu a ciki tashin hankali, kuma na yi mamakin da har Dr ta iya biyewa kudirinku” “Mi zai hana ta yin haka Ammy? Matar dake neman hanyar da zata gyara tsakaninta da kanenta? Kuma ta san abun da Abiey yake so, na tsorata da irin son da Sauban yake yi ma Zahra Ammy, idan ya rasa Zahra ke ma zaki iya rasa shi, sannan ban ga dalilin da zai saka ku tsaya kai da fata ku haramta abun da Allah ya halatta ba, ban san ko dan tana bazawara ne, amman Zahra mace ce kuma tana da hali mai kyau sam ban ga wata matsala a tare da ita ba” “Matsalar ba daga ni ba ne, daman can ni ina kaunar Zahra sai dai hayyalar da ta tsira bayan mutuwar Deen ya shafa mata bakin fenti a fuskata, a yanzu kuma ina kallon yadda Mai Martaba zai dubi abun ne, domin abu ne na bacin rai ace ďanka yayi aure a boye bayan kuma ka zaba masa matar da zai aura, daman can basa jituwa yanzu kuma ban san yadda zai ji ba kuma ban san wani irin hukunci zai yanke ba,” “Wata kila zai fahimta idan aka biyo masa ta siffar da zai fahimta din” Sai a wannan gabar Abiey yayi magana. “Shiyasa na ce zan yi magana da shi da kaina, kuma zan sanar masa tun kamin labarin ya yadu wasu su sanar masa” Ya mike tsaye yana. “Zan je na duba Zahra, tun da na baro gurin ban koma ba dazun” “Miyasa same ta?” Ammy ta tambaya tana kallonshi. “Suma ta yi, lokacin da ta fahimci ni ta aura ba Sauban ba” “Saboda dadi?” “Saboda tashin hankali dai” A tare suka fito da Sauban. Ammy ta sauke ajiyar zuciya, ko kadan bata son ganin laifin ďanta, ta san yadda yake son Zahra, kuma ta san yadda so yake domin ta taba shiga a makamancin wannan halin ba. Number Dr Zainab ta yi dialing sannan ta mike tsaye ta fara safa da marwa a falon. Dr na yin picking Ammy ta hauta da masifa. “Haka ake yi? Sai ki biye masa ku zama marasa tunani? Ke ma kin zama kamar Deen kenan ai” “Na san daman haka zai biyo baya, shiyasa muka boye ba mu sanar da ke ba sai a yau da komai ya riga da ya faru, Ammy da zaki ga Zahra ko ki kalli Abiey da duba na tsanaki da kin tausaya musu, suna son junansu idan a wacan karon kaddara ta raba tsakaninsu a yanzu kuma minene? Ammy Abiey ko be nuna miki ba, be fada miki ba dole zai aje abun a zuciyarsa cewar ke da Mai Martaba ba ku kyauta masa ba, wata kila Allah ya jarraba imaninsa ne shiyasa ya kawo kaddarar ta shiga tsakaninsu, ko ba komai sun kara tabbatar da suna kaunar junansu, kuma haka zai kara aminci a tsakaninsu, shi mutumen da zai iya runtse ido ya kawar da komai ya aikata haka me kike tunani a irin son da yake mata? Ammy ki yi ma Abiey adalci, karki duba yadda Mai Martaba zai kalli abun shi uba ne, hankali da tunani ba zai yana zama daya ba” “Wannan duk ba hujja ba ce ta saka saka ki goya masa baya ya aikata abun da yake so ba tare da sanin iyaye ba, aure ba abun wasa ba ne Dr” “Shikenan Ammy idan baki aminta ba, ko umarce shi da ya sake ta, na san zai ji maganarki domin Abiey mutum ne mai matukar biyayya” Ammy taja tsaki ta yanke wayar. HAJIYA JAMILA POV. Sai da ta gama shirya masa komai na karyawa ta bi ta jera masa sannan ta dauko flask din ruwan zafi ta dire a gabansa ta zauna a kasa kamar yadda shi ma yake zaune a kan carpet, duk wani motsi da take na hada masa tea da zuba kayan soye soye da ta yi idonsa na kanta wani kallo yake mata wanda ya fi kama da kallon tsana, domin a yanzu ne da ya tabbatar da gaskiyar Zahra kuma ya tabbatar ya rasata yake jin zafin abun da Jamila ta yi masa, sai yake jin kamar ka kara dandana masa dacin rashin ďana a yanzu fiye da. “Gashi Hubby” Ya fada bayan ta saka tea spoon a tea cup ta mika masa, ya mika hannu ya karba. “Imaan zata dawo gidan nan wata kila gobe ko jibi” Cikin tashin hankalin da ya dade be ziyarci zuciyarta ba ta kalleshi. “Imaan fa ka ce?” “Eh ita fa” “Ta tuna da gidan nan kuma?” “Daman ai ba mantawa ta yi da shi ba, rashin jituwar da kuke samu ne yasa ta bar gidan ta koma gidan Gwaggo da zama, a yanzu kuma da na kara karantar rayuwa da yau da gobe sai an fahimci babu inda ya dace kanwata ta zauna kamar gida” Jikin wani yanayi mai kama da fargaba ta kalleshi domin bata saba jin bakinsa yana furta irin wadannan kalaman ko makamantansu ba. “Hubby yau sai ka yi min wani dabam kamar ba kai ba” “Ni din dai ne da kika sani, amman dabi'u da hayyala suka sauya domin na fahinci rayuwa a yanzu fiye da da” “Ban fahimce ka” “Yarda ce ta saka na aminta dake, har ki girka min abinci na dauka na ci, wannan yarda ta yi tasiri a jikina da zuciya har nake ganin kamar ba zaki iya cutar da wani ba balle kuma ni” “Ta ya zan iya cutar da mijina abokin rayuwata? Ya kake magana kamar ka manta wani abu” Ya gyara zamansa yana “Haka ne na manta ban tunatar da ke ba, an daura auren Zahra a jiya, kuma an yi kuren daura shi da ni ne, da ace na yi magana da ita kamin jiya wata kila da yanzu ita din amarya ce, wata kila ma ta dalilin na samu cikar burina” Hajiya Jamila ta mike tsaye. “Kam uban nan? Au daman take taken ka kenan? Shiyasa kake ta wani rawar kafa akan Nanny har da zancen a hade girkinta da na mahaifiyarta a cikin mu, har kana zancen nema mata makarantar koyon girki?” “Ina ganin kamar Zahra bata cancanci komai daga gareni ba, sai kyautatawa, kamar yadda bata cancanci komai daga gareki ba sai wannan” “Wannan wane irin rai nin wayo ne, zaka dika tallata min yarinyar da zo a gidan kula da ďanka? Wai ko da kai aka daura auren ne ba ni da labari?” “Irin rainin wayon da kika min kika dauko ďan da ba nawa ba kika kawo a cikin gidan nan a matsayin ďana, sannan kika gayyato mahaifiyarsa ta rika shayar da shi a matsayin Nanny” Yar siririyar dariya Hajiya Jamila ta yi irin na manyan yan bariki masu kokarin samawa kansu mafita a ko wane hali suka shiga. “Wannan wace irin magana ce kuma? Oh daman kebewar da kuke yi da Zahra irin karyar da take Shimfida maka? Idan tana son ta aureka ko kuma kai kana sonta ba sai kun biya ta wannan hanyar ba, daman babu yadda ba aga halin maza ba, ba sai kuntar da ni ko kun shigenta min yaro ba” Ya daga kai yana kallonta fuskarsa da murmushi takaici. “Dan ki ne kuma kika bukaci a canja gwajin jini? Ko kin manta da 50m naira da kika aika dan'uwanki da shi gurin Dr Zainab?” “Ni... Anya dai ba mafarki kake yi ba Hubby?” “Zaki iya wasa da hankalin kowa ba da nawa, domin na zan ki cikinki da waje, sai dai duk da sanin da na yi miki ban yi zaton zaki iya aikata wannan mummunan aiki va Jamila, da ace nan gano gaskiya ba, haka zamu tafi na raini yaron da yake na nawa ba, kuma ban hada komai da shi ba? Karshe na mutu ya gaje ni? Miyasa zaki saka farinciki a zuciyar yan'uwa da tawa zuciyar? Ki saka kowa farinciki da karyarki? Yanzu da wane idon zaki kallesu?” Ta zube kasan guiwoyinta hawaye na safa da marwa a tsakanin idanuwanta da kumatunta, tun da take a rayuwarta bata taba jin tashin hankali da kunyar duniya ba irin wannan, a yanzu ta gane duk wani bacin rai da ta shiga na rashin haihuwa da tsoron tonon asirinta duk shimfada ce yanzu ne yake tafasa. [12/4, 2:34 PM] Oum_Nuwaira🥰: 6️⃣8️⃣ “Na yi tunanin zaki fi kowa sanin zafin da mace take ji idan ta rasa ďa, ban yi zaton zaki iya raba wata uwa da ďanta ba, da kuma irin ciwon da zan ji idan na gano gaskiya, amman sai idonki duk tausayin da nake miki baki gani ba, ina tausayin kaina na rashin haihuwa, amman na fi tausayinki sama da kaina, ashe abun da Zuciyarki take saka miki dabam” Ta matsa kusa da shi ta dafa kafafuwansa. “Ka gafarta min mijina, ka jikaina ka tausaya min, duk abun da na aikata na aikata ne saboda farincikinka, ban aikata haka saboda na cutar da kai ba, ban raba Zahra da ďanta ba saboda na bakanta ranta ba, kuma da na san da cewar dawowarta a gidan nan zai haifa min da wannan matsalar da ban nemi haka ba” “Ba Zahra ce ta fada min ba, matar da kuka bawa miliyan 50 saboda ta boye sirrin ita ta fada min gaskiya, bata karbi kudin ba har sai da na bata umarni, har takardar yarjejeniya da kuka sai da ta nuna min, Zahra ta fada min iya abun da na tambaye ta ne kawai bata fada min komai game da yarjejeniyarku ba, har sai da ni na yi mata magana da kaina, kin ban ba ni mamaki Jamila, miye ban yi miki ba a duniyar nan? Da har dan kason da za ki samu a gadona zai saka zuciyarki bushewa ki aikata wannan mummunan aiki?” “Ka yi hakuri, ka tausaya min” “Da ban yi hakuri da matakin da zan dauka sai ya fi wannan zafi, amman hakurin da na yi da bin komai daki daki shi ya saukaka min zuciyata har Zahra ta samu muhallin a ciki, domin bata da laifi ita din kawai tana nemawa kanta da mijinta mafita ne, da ace na samu abun da zuciyata ta kudirta ta na maye gurbinki da Zahra ta cigaba da rainon ďanta ba tare da kowa ya sani ba, amman ina...! Na makaro ta auri wanda ya fi ni cancantarta” A matukar firgice takr kallonsa. “Ita Zahra zaka aura?” “Kwarai kuwa, amman a haka da bata kasance matata ba, zan cire mata raddadin zafin rashin ďanta zan mallaka mata ďanta a hannunta” Ta girgiza kai ta sauri tana kara rike kafarsa. “Aa dan Allah karka yi haka, ka rufa min asiri ka bar min yaron nan, na yarda ka yanke duk hukunci da kake ganin ya dace da ni amman ban da na raba ni da Amir, Wallahi ina son yaron nan, kuma raba ni da shi kai ma tonuwar asirinka ne, domin duniya zata san halin da muke ciki....” A take ya wanke mata fuska da mari har biyu masu zafi. “ Kin san da wannan kika aikata abun da kika aikata Jamila? Tun daga lokacin da likitoci suka tabbatar mini ni da ke bama dauke da wata matsala da zata hana mu haihuwa, sai na fi tausayinki fiye da kaina, ashe abun da kika ta saka mana dabam, da ace na fadi na mutu haka zaki bar yaron nan ya ci gadona a matsayin ďana? Sau nawa kike min magana akan mu fi wata hanyar samun haihuwa ina fada min ban shirya butulcewa Ubangijina ba, amman a haka kika zabi idona ke da dan'uwanki kuka aikata abun da ranku yake so” “Ban yi hakan dan komai ba sai dan nema mana farinciki mai daurewa.. Ka tsaya ka natsu Bashir karka yanke hukunci cikin fushi” Tasss ya sake wanke mata fuska da mari hawaye na sauko masa. “Ga farincikin nan ai kin sama min Jamila, kalli idona ki gani farincikin da kika sama min shi nake a yanzu zuciyata kuma tana cike da shi, tirrr da ke tirrr da hakinki, ya kike tunanin yan'uwana da abokaina za su ji? Makiyana za su min dariya, shi ne farinciki da kika sama min? Miyasa ba ki bar ni a yadda Allah yake son ganina ba? Da baki aikata abun da kika aikata ba, da ban san yaron nan ba balle har na ji zafin rabuwa da shi, Allah ya waddaranki Jamila” Ya fisge kafarsa domin duk marin da yayi mata bata saki kafarsa ba, ya fice daga karamin falon, faduwa ta yi a gurin tana wani irin kuka na tashin hankali. “Dan Allah karka raba ni da Amir Bashir, ka yafe min dan Allah ban aikata hakan saboda na cutar da kai ba, sherin zuciya ne ni ma ďana ne” Wani irin kuka take mai gunji ta dafe zuciyar da take jin kamar zata fashe mata, kamar wata Sabuwar mahaukaciya haka ta tashi zaune, ba dan tana bil adam ba, da zaka iya rantsewa da Allah kogi ne yake tsastsafa da ruwan sama tsabar zubar da hawaye yake yi a idonta, duk wani tashin hankali data taba shiga a baya a yanzu ta gane shimfida ne da sharar fage ake mata, a yau ne watan kukanta ya kamata, tsoron da ta dade tana yi na rabuwa da mijinta da tsonuwar asirinta sun hade mata a wannan bakar rana sun sallamo mata lokaci daya, firgigit ta mike tsaye ta zuba da gudu zuwa dakinsa sai ta tararda dakin wayam baya ciki, ta fito ta shiga dayan nan ma babu kowa, da sauri ta fito haka ta zagaye part din ta duba ko'ina bata ganshi ba, sannan ta nufo bangarenta tana kuka. A lokacin da ya fito falon bangaren Hajiya Jamila ya nufo yana tafiya hawaye na masa zuba, ba al'adarsa ba ce yin kuka a public place ko da kuwa shi kadai ne a gurin, idan ma zai yi kukan rashin haihuwa ko wata damuwa zai yi a inda Allah kadai ya san yayi kamar bandaki ko kuma dakinsa, amman a yau gashi yana ta zubar da hawaye tun daga bangarensa har ya shigo sashen Jamila, sai a yanzu yake jin bakincikin rabuwa da Amir da zai yi domin be yi zaton abun zai saka shi damuwa duk da kasancewar ya dade da sanin komai tun kamin ranar yau. Kai tsaye ďakin da Amir yake ya nufa, a bakin kofar dakin ya tsaya ya sai da ya share hawayensa sannan tura kofar dakin ya shiga, Ummiter ya samu a dakin tana tsaye rike da wayar a hannu Amir na kafadarta tana jijjigashi, juyowa ta yi fuskarta cike da annashuwa ganin Yayanta ya saka ta nufo shi cikin farinciki. “Yaya yanzu nake magana da Imaan wai tace ka yi magana da Momy Farida zata dawo ta cigaba da zama a gidan nan da gaske ne?” Tausayin kansa da kuma na kanwarsa ya saka hawayen da suka taru a idonsa suka yi nasarar subucewa suka sauko a kumatunsa, ganin Amir a kafadarta daga ita har yayar tata Imaan ya san basa jituwa da matarsa Jamila amman haka be shafi son da suke yi ma ďansa ba saboda suna kallonsa matsayin jikinsu kuma jinin ďan'uwansu. Ummiter na ganin hakan hankalinta yayi matukar tashi domin zata iya shaidar wannan ne karo na biyu da ta ga hawaye a idon dan'uwanta tun bayan mutuwar Mahaifinsu. “Yaya Lafiya miya faru?” Hannu ya mika ya karbi Amir yana kallonsa hawayensa na sauka a fuskar Amir dake ta wasa da kafafuwansa, digar hawayen suka yi masa kama da wasa Mr Bashir yake masa a take ya fara dariya. “A lokacin da Jamila ta sanar da ni ta samu cikin yaron nan, sai na ji kamar dukamin matsala ta da damuwata sun kare, a lokacin da ta haife shi kuma na yafe abubuwa da yawa da aka yi min na bacin rai, saboda ina jin cewar na sami dauwamamen farinciki, na kyautar sa yawa daga dukiyata, ina jin ko zan mutu a yanzu ba ni bakinciki da damuwa domin na samu Magaji har na maye gurbinsa da sunan mahaifina, a yau kin ďanďana min zafin rashin haihuwa Jamila fiye da baya” Tuni hawaye suka wanke fuska Ummiter, cikin wani mai kama da tashin hankali take tambayar yayanta. “Yaya miyasa kake kuka? Kuma miya saka kake wadannan kalaman? Dan Allah ka fada min ban gane ba” Ya zauna a bakin kasa kamar ba shi ba yana kallon Amir. “Mu uku kawai Mahaifiyarmu ta haifa, ba mu san yawan kannen ko yanyaye ba, sai dai na yan'uwa, da kuma yawan ďangi, hakan ya saka na kudirta a raina cewar zan yi ta haihuwa har sak na manta da wasu yayan da na haifa, domin ina son na kalli wannan na kalli wacan ace duk zuri'ata ce, daga lokacin da likitoci suka tabbatar min da babu wata matsala a tare da ni, n auri mace hudu sai dai zaman mu baya dade saboda suna samun matsala da matar da nake ganin ta yardar da kaddarar ta da Allah ya rubuta mana ta zauna da ni, yaron nan ba jinina ba ne, amman ina da tabbacin da ace Allah zai rubutawa wasu zuri'ar fitowa a karkashina ba zan so su kamar Amir ba, Wallahi a yau ina jin kamar ace ina da wata dama da zan rufe idon kowa na sauya jinin yaron nan izuwa nawa” Cikin kuka Ummiter ta ce. “Ni ban gane duk wannan abun da kake ba, dan Allah Yaya ka yi min magana” “Amir ba ďana ba ne! Jamila ta siye shi a gurin Zahra ne a shigo min da shi a ciki gida a matsayin jinina” Da sauri Ummiter ta dora hannu saman kai ta runtse ido. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un Allah yasa wannan ba gaskiya ba ne” Mr Bashir ya mike tsaye ya dora Amir a kafarsa ya isa gurin gadonsa ya kwatar da shi ya kai hannu ya tana fuskarsa, a daidai lokacin ne Hajiya Jamila ta shigo tana wani irin kuka. “Dan Allah karka rabi da yaron nan, Wallahi ina sonsa tsakani da Allah ni ma kuma uwarsa domin na shayar da shi, ka tausaya min Bashir dan Allah, na san ban kyauta maka ba amman karka ce zaka rabu da ni shi ne abun da bana fatan samu daga gareka, amman ka yi min hukunci da duk abun da kake ganin ya dace ban da saki, kuma ban da karbe Amir a hannuna, domin hakan tonuwar asirinka ne kowa zai san abun da muke ciki” Uffan be ce mata ba ya juya ya fice daga dakin, sai ta rika gadon Amir tana kuka, Amir kuma ya sakar mata dariya a kurciyarsa da zatonsa irin na yaro mai irin wataninsa ita din ma tana yi masa wasa ne. “Da na san da zuwan wannan ranar, da ban aikata abun da na aikata ba, da ban rabaka da mahaifiyarka ba, wata kila da ban fuskanci wannan tashin hankalin ba, na san ni din ba mahaifiyarka ba ce amman na shayar da kai, ko da nono baya baka lafiya ya zauna a cikinka wannan farincikin da na ji na shayarda nono a matsayin uwa kadai ya isa ya saka min kaunarka Amir” Ta kurkushe a gurin ta fashe da kuka mai taba zuciya, Ummiter ma kukan tausayin ďan'uwanta take domin ta san zai shiga bakinciki da tashin hankali sanadin abun da Jamila ta aikata, ko bayan shi ita ma kanta ta sabu da Amir irin sabon da ko aiki ta fita yana cikin ranta tana tunawa cewar a yanzu sun samu ďa bayan tsawon shekarun da yayanta ya dauka yana nemansa, sai take ganin farincikinsu ya kammallu a yanzu ashe ba haka ba ne. Mr Bashir ya dawo dauke ta takardu biyu ya karaso har gurin da Hajiya Jamila take zaune tana rusar kuka da na tabbatar idan ya dauke ta zuwa wani lokaci zata iya suma ko ma ta rasa ranta gaba daya. Cak din kudi ya fara mika mata. “Wannan kudin zai isheki ki rike kanki na wani lokaci, akwai kamfanin fulawa zan mallaka miki shi idan komai ya lafa” Sannan ya mika mata dayar takardar da take ganin kamar ajalinta ne a ciki. “Wannan kuma takardar saki ce, na sauwake miki idan kin cika idda kika samu miji ki yi aure, wata kila ma ki samu naki zuri'ar domin likitoci sun tabbatar babu wata matsala a tare da ke, hakan kuma ba zai saka na yi wani abun ba, idan kakanin yaron nan zuka zabi hukuntaki, karki yarda ki sake alakanta sunanki da nawa” Ya sakar mata takardun da ta kasa mika hannu ta karbi ko daya, kuka take na tashin hankali. Ummiter ta mike tsaye tana kallon Mr Bashir “Tun da nake a rayuwata ban ta a ganin wani mutun mai kamanci da sani ya kamata, mayar da sakamakon sherin da alheri ba irinka Yaya, a yanzu duk bayan abun da Jamila ta yi maka ka saka mata da wannan? Da yanzu haka idan duniya ta san abun da ta aikata sai an tsine mata!” “Haka Annabi ya koyar da mu, Jamila ko da zaman wata daya tayi tare da ni ya kamata ta ci arzikina balle ta yi zaman shekaru tare da ni, kowa ya aikata mai kyau zai ga da kyau, akasin haka ma kowa zai gani” Bayan haka be sake cewa komai ba ya dauke kai ya fice daga dakin yana jin zuciyarsa na yin sama kamar zata rufe numfashinsa. Ummiter ta kalli Hajiya Jamila da take ganin tata ta kare ta ce. “Allah ya isa tsakaninmu dake Jamila, kin hana matansa zaman lafiya sai da kika koresu, ni da yar'uwata kika hana mu sakat a gidan dan'uwanmu saboda ke Imaan ta bar gidan nan, bayan duk huduwar da Baban yayi mana cewar ta ni Yaya Bashir kamar mahaifinta amman kullum sai kin hada ta fada da shi, saboda ku samu maslaha ta bar miki gidan ta koma gidan kanwar Mahaifiyarmu da zama, duk wannan be wadatar da ke ba sai da kika sake biyo mana da wannan hanyar ke dai burinki ki wargaza farincikinmu, Allah ya isa” Kai kawai Hajiya Jamila take iya girgizawa bakinta ya kasa furta komai, kamar ambaliyar kogi haka idanuwanta ke zubar da ruwan hawaye. Ummiter ta bi bayan ďan'uwanta a dakinsa na karatu ta same shi yana zaune ya daga kansa sama yana kallon ceiling sai tausayinsa ya kara kamata, ta zauna a kujerar dake kusa da shi sai ya dago ta kalleta cikin karfi irin na babban yaya ya sakar mata murmushi. A nan ta samu kwarin guiwar tambayarsa yadda aka yi ya gane gaskiya, sai ya karanta mata komai ciki har da kudinsa na auren Zahra da yayi. “Tafi ki kirata” “Amman Yaya ai Jamila siyen ďan ta yi, da ka bar mana shi ko dan rufin asirinmu” “Mu da muka tsinceshi daga sama muka jin zafin rabuwa da shi, balle ita da ta dauki cikin wata tara ta yi nakudarsa ta haifi ďanta, karki biye Jamila ki aikata son kai mana Ummiter” Ta share hawayenta ta mike tsaye, ta kofar waje ta fita harabar gidan ta doshi BQ, kamin ta karasa ta hango motar da ta tabbatar few people ne suke da kudin mallakar irinta fake nesa da BQ din kadan, Zahra dake kwance kafadar Abiey ta daga sakamakon hango Ummiter da ta yi, sai ta raba yatsunta da nasa. Abiey ya bude ido ya kalleta. “Miya faru?” “Ummiter ce Maybe magana zata yi da ni” Ya kalli gaban motar, yana ganin Ummiter ya tuna inda ya san ta wato a Masarauta gurin Mama Lami, bude motar yayi ya fita ya zagaya ya budewa Zahra side dinta ya mika mata hannunsa ta rika ta fito. Cak Ummiter ta tsaya domin ba ta yi zaton Abiey ne a cikin motar ba, can kuma ta cira kafa ta karasa inda suke tsaye, ko kadan Abiey be kalleta ba domin kallon da yayi mata a mota ya wadatar da shi, idonsa na kan Matarsa wanda kallonta baya kundirar da shi. Zahra ta taka ta matsa daga inda suke tsaye da Abiey ta tsaya da Ummiter tana kallonta ta san Ummiter ba karamin kuka ta yi ba, kamar yadda Ummiter ma ta karanci damuwa a fuskar Zahra. “Yaya yana son ganinki yanzu” Zahra ta juyo ta dawo gurin Abiey sai dai shi bata fada masa cewar Mr Bashir ne yake son ganinta ba, domin ta san halin angonta. “Hajiya Jamila ce take son magana da ni” Ya mika hannayensa ya rika fuskarta yana shafawa a hankali daman can ba jin zai taba jin kunyar rika hannunta ko taba jikinta a bayyanar jama'a, balle a yanzu da take halak malak dinsa. “Da safen na yi Hiayatee? Bata san kin kwanta asibiti ba ne jiya? Bata ma zo ta duba ki ba ko?” Magana yake mata yana kallon kwayar idonta kamar zai maida su cikin nasa. “Ta zo, bari na je wata kila magana ce mai muhimmanci” “Okay” Ya amsa mata ne kawai dan baya son musa mata, domin baya son rabuwa da ita, shi ya dauko su daga asibiti ya dawo da su gidan jiya da darea, haka kuma be hana shi tarewa a kofar gidan bayan yayi sallah asuba ba har sai da rana ta fito sannan ya shiga cikin gidan ya kira a waya ta fito. Ya Sumbanci goshinta ya rika hannunta ya murza sirara kuma tatausan yastun hannunta. “I love you...” Ita din ce kunya ta lullube ta, ta san duk wani unkuri da zata yi ba zai hanu daga taba jikinta ko rumgumarta ko furta yana sonta a gaban kowa ba, hakan ya saka bata yi unkurin yin haka ba. Tsaye yayi yana kallonta har sai da ta shige sannan ya rufe motar ya zagaya ya shiga side dinsa ya kuna motar. Zahra na rufe kofar falon Ummiter ta juyo tana kallonta. “Yayana mutum ne mai karamci ba dan haka ba, daga ke har Jamila sai ya rufe ku, domin yana da iko da kudin da zai iya yin haka, amman be yi ba duk da bakinciki da kika saka masa, muna kallon ďanki a matsayin jikinmu a yau na ga hawaye a idon yayana yayi kukan da ban taba ganin irinsa ba, kuma ni ma nayi, kuma na zo ya aureki saboda Jamila ta dandani dacin abun da ta aikata mana, ko da yake yaro babu ruwansa ba shi da hakkin kowa, sai dai ki tanadi amsoshin da za ki ba shi idan ya tambayeki” Zahra ta daga idonta ta ya fara safa da marwar hawaye tana kallon Ummiter. “Wata kila hakkinsa ne, zai fara bibiyata a yanzu ya hana ni farinciki a gaba ko ma ya hanani samun kwanciyar hankali a gidan aurena” “Daman mutumen da Yaya ya fada min Jamila tace an daura miki aure da shi a jiya da ba Sauban ba Abiey? Shi ya saka kika suma?” Zahra ta daga mata kai. “Shi ne, an daura auren ne ba tare da sanina ba, kuma ba da sanin iyayensa ba, ina tsoron abun da zai biyo baya wata kila hakkin yayanki ne duk da ban aikata da niya ba” Ummiter ta hade yawun bakinta ta nuna Zahra hanyar da zata bi. “Yana dakinsa” Fitowa ta yi daga bangaren ta dawo bangaren, Hajiya Jamila ta shiga dakin Amir inda ta bar wayarta a dauki wayarta ta shiga contact list dinta ta nemo number kawar mahaifiyarta wato Mama Lami ta kira, cikin ikon da iyawarsa aka amsa wayar. “Hello Mama an tashi lafiya” “Lafiya Kalau Ummiter, ya aikin? Kuma ya yayanki da iyakinsa” “Lafiya kalau Mama” “Maa Shaa Allah, kwana biyu kin daina zuwa mana” “Aiki ne yayi min yawa Mama, Mama Abiey na gani a gidanmu yanzu tare da Zahra Nannyn da Anty Jamila ta dauka ta rika kula mata da Amir” Sai kuma ta yi shiru, a nan Mama Lami ta samu damar tambayar. “Miya kawo Abiey a gidan?” “Cewa ta yi mijinta ne a yanzu wai an daura musu aure a sirrance, ba tare da sani iyayensa shiyasa na kira na tambaya da gaske ne?” “Abiey din aka daurawa aure? Abiey dai na mu?” “Shi fa Mama har kissing dinta yayi gabana” “Aa ba dai aure ba, sai dai idan falkarsa ce, wato duk abun nan da na saka aka yi masa be saka ya rabu da yarinyar nan ba? Ko a yanzu ya bude kofar wata hatsaniyar ce a tsakaninsa da mahaifinsa, ai tun da har ya ki bin zabina sai ya ga abun da baya so, na gode Ummiter” Ta katse wayar, Ummiter ta juya tana kallon gadon Amir. “Ai kara dai ta rike ďanta ko dan rufin asirinmu, da ace matar ďan'uwa ta kawo masa ďan ba nashi ba, kara acw ya aure Nannynta, wata kila ma sanadinta ya samu nashi yayan tun da ita tana haihuwa, shi ma kuma ba shi da wata matsala....” Karasawa ta yi gurin gadon ta leka sai ta ga wayan babu Amir. [12/5, 12:10 AM] Oum_Nuwaira🥰: 6️⃣9️⃣ ABIEY POV Sai da ya fara kallon Ammy sannan ya kalli Dr Zainab ta kanta ke kasa tukuna ya karaso cikin falon. “Lafiya?” Dr ta dago ta kalleshi sai dai bata ce komai ba ya maida kanta kasa. Ya ga damuwa karara a fuskarta, yanayin Ammy ya nuna fada ta yi domin yana karanta kowane irin hali mahaifiyarsa take ciki, damuwa ko bakinciki ko fada da murna da farikciki. A sanyaye ya zauna yana kallon Ammy. “Ammy kar dai kin tsare Dr da fada ne” “Idan ban nata fada ba wa zan yi ma? Da bata biye ka da yanzu komai be faru ba” “Ko ta bi ra'ayina ko ta ki, ba zai sauya kaddarata ta auren Zahra ba, domin na shirya yin haka ko da amincewarta ko babu, sannan kamin komai ya faru sai da na gargadeta cewar kar ta fadawa kowa wannan ya zama tsakanin mu” Ammy ta mike tsaye ta nufi dakinta ba tare da ta sake cewa komai ba. Dr ta dago ta dubi Abeiy idonta cike da kwalla. “Idan ban aikata ba laifi, idan na aikata laifi kun saka ni a tsakiya” Abiey ya bar kujerar da yake zaune ya dawo kusa da Dr ya zauna yana murmushi. “Ammy tana jin tsoron Mai Martaba ne, ba wai tana wannan abun saboda bata son Zahra ko bata son aurena da ita ba, ta san irin tsamin dake tsakanina da mahaifina tana jin tsoron abun da zai biyo baya ne” “Tana da gaskiya Abiey be kamata ka samu matsala da mahaifinki saboda mace ba, dole zai ji ba dadi na abun da ka aikata” “Haka ne, kuma ina fatar ba zai cilasta min zabe tsakanin shi da Zahra ba” Ya fada yana kallon wani bangare na dakin sannan ya mike tsaye ya shafa aljihun wandonsa ya nufi dinning, wayarsa ta yi vibration da sauri ya ciro wayar ganin number Sauban ya saka shi murmushi. “Hello” “Ango ina amaryar taka? Ya jikinta?” “Ta ji sauki, tun jiya aka sallameta tana gidansu yanzu ma ban dade da dawo daga gidansu ba” “Shikenan fa ba zaman lafiya, ka auri Zahra ko?” “Har yanzu gani nake kamar ba gaske ba ne Sauban, kuma har yanzu ina tsoron kaddarar da zata raba tsakaninku” “Mai Martaba?” “Mutuwa idan aka raba ni da Zahra a yanzu ba makawa na san mutuwa zan yi, Sauban na kai stage din da bana iya sauraren kowa a yanzu a game da Zahra sai zuciyata” “Zahra ta riga da ta zama taka a yanzu Abiey, ka aje wannan a gafe ka fuskaci matsalarku so that ka magance abun da wuri tun dare be maka ba” Ya aje cup din da ya dauka da dayan hannunsa yana wani tunanin na dabam. “I will” Ya yanke wayar ya saka aljihunsa sannan ya juyo a zatonsa sai yi arba da kujera kawai babu Dr a kai, upstairs ya kalla sannan ya kalli kofar fita falon, wata zuciyar na raya masa ta shiga ďakin Ammy. Kofar ya nufa yana wani irin taku na kasaifa da tausayin kasar da be san yana yi ba, har ya shiga motarsa ya kunna be daina saka yadda zai fuskanci Mai Martaba ba. Driving yake a hankali har ya isa Masarautar ya bude motarsa ya fito ya nufi bangaren macen da ta zame masa uwa a cikin gidan. Ba ala'adarsa ba ce ya kwankwasa kofar falon da already ya san a bude take, amman a yau yayi kuma ya tsaya jiran a masa izinin shiga wato domin zuciyarsa ta yi nisa da tunani. “Laaa Yaya” Cewar Najis domin ta manta when last ta saka yayan na ta a ido, murmushi ya sakar mata ya shigo cikin falon yana kallon Anty Amarya dake rike da kaskon zamani a turaren wuta. “Abiey yau kuma kai ne a gidan na mu?” Ya kara fadada murmushinsa. “Ni ne Anty barka da safe” Ta nemu guri ta zauna tana bayyana masa damuwarsa. “Na kira wayarka baka dauka ba, na ji abun da ka aikata Ammy ta fada min komai, Abiey miyasa? Na san kana son Zahra amman ya kamata ka yi tunani kamin ka aikata, ina laifin ka yi ta Mai Martaba Magiya har ya amince maka a maimakon ta biyo ta bayan fage?” “Zuwa yaushe zan yi ta magiyar? Kima tunani Mai Martaba zai fahimci halin da nake ciki har yayi min umarnin zama da Zahra, ni da ita duka muna son junanmu amman kowa ya kasa fahimtar haka, idan kaddarar farko ta hana mu kasancewa da juna? A yanzu ma kaddarar ce? Wata kila za su tausaya min idan kuka ga ina gagarin mutuwa akan sonta, amman ina mai tabbatar miki idan har Mai Martaba ya cilasta ni sakin Zahra to kamar ya cilasta mata ni kashe kaina ne” “Karka wakilta ni magana da Mai Martaba akan wannan babban lamarin ina gudun kar hakan ta shafe ni, ko kuma yayi zaton na goya maka baya ne” Yayi murmushi daga zaune da yake a hannun kujerar. “Da kaina zan yi magana da shi” “Aa karka aikata haka, ka fadawa Ammy sai wata kika ya saurareka idan ka je tare da ita” “Ita ma tsoro take ji kamar ke, ku bar ni na yi magana da Mahaifina ba tare da shamaki ba, ina da gaskiya fa” Ya mike tsaye, ya nufi hanyar da zata sada shi da bangare, Anty ta biyo bayansa tana ta bashi shawarar kar yayi magana da Mai Martaba kai tsaye, amman be saurareta ba har ya shiga bangaren Mahaifinsa. Sai da ya natsu sosai sannan ya tura kofar falon ya shiga, sam be yi zaton zai same shi a falon farko ba, sai dai ga mamakinsa yana falon zaune yana shan lipton Abiey ya cire talkamin kafarsa ya karasa cikin katon falon na alfarma mai dauke da kayan alatu na kawata falo. Mai Martaba ya dauke kai daga kallon tv da yake ya kalli Abiey da ya doso inda yake kadan sannan amsa sallamar cikin isa irin ta manya sarakun, sannan ya maida hankalinsa girin Tv ya cigaba da kallo, Abiey ya karasa kusa da shi ga zuba gafensa ya kwashi gaisuwa sannan ya sauke kai kasa be sake cewa komai ba. “Akwai wata matsala ne?” Abiey yayi fuskar tsoro da fargaba da kuma tausayi a lokacin daya, sannan ya fara magana murya can kasa cikin ladabi da tsantsan da kai. “Mai Martaba kai uba a gurin kowa balle kuma a garemu, Ammy tana yawam fada min cewar na yi duk wani abu da zai saka ka kauna ce ni, domin na taso a cikin wata rayuwa da ban san dadinka ba, balle dadin zama da kai, ban isa na matsa a kusa da kai ba, ban iya na nunawa kai ubana ne a gaban jama'a ba, saboda tsanar da kake nuna min wanda ta banbanta ni dabam da sauran yayanka, soyayyar da kake min bata kai ta yayanka ba na sani, kuma ba tare da na maka laifin komai ba, domin Ammy bata fada min wani laifi da na aikata wanda ya saka ka tsane ni ba, ina tunanin tsanar ta darsu a zuciyarka ne, saboda Allah ya rubuta kaddarar kiyayyar mahaifi ba tare da hakki ba, na yadda wannan jarabawa ta ce, kuma ban isa na tsallake ta ba, ban isa na canja ta ba, da ace ina da iko na wanke zuciyarka ko kuma na canja kaina, na zo a matsayin wani yaro da mahaifinsa yake matukar kaunarsa” Mai martaba ya ake cup din hannunsa, cikin wani lafazi mai kama da na izza ya ce “Umaima ta zaunar da kai ta yi ta karanta maka karatukan banza ko? Shiyasa zuciyarka take raya abubuwa marasa kyau” “Alif bata taba karanta min akanka, sai dai tana yawan fada min na yi hakuri da duk halin da zan samu kaina, kuma kar na yarda na butulce maka kar kuma na bata rananka” Mai Martaba ya yi masa alama ada zo da hannu, sai Abiey ya baro inda yake zaune ya dawo kusa da Mai Martaba ya zauna for the first time har jikinsa na gugan na Mai Martaba, Mai Martaba ya kalleshi ya sauke numfashi a hankali. “A cikin yayana babu wanda ya dauko ni a kamanin da siffa irinka, haka kuma ban taba haihuwa ďan na ji bana kaunarsa shi, sai dai son da nake yi ma wani ďan ko yar ya dara na wani, wannan kuma wani abu da Allah yake saka shi a zuciyar bawa, sai kuma yawan kyautatawa da yaya suke yi ta biyo baya dole ne zuciya ta fi kaunar mai kyautata mata, ba ayi wani ďa da zuciya take kauna take son kusanci da shi ba kamar kai Abiey, zancen bana sonka wannan wani abu ne na dabam da zuciyarka ta fahimta, na sha fadar maganar nan babu abun da zai fito a cikin Umaima na gagara sonsa balle kuma jinina, sai dai an haifo ka ka zo duniya a yanayin da ba haka na so ba, sai kuma aka yi min shamaki da yadda zan nuna maka kauna ko soyayya, a duk lokacin da zan yi unkurin haka sai na kasa” Mai Martaba yayi shiru kamar ba zai sake magana ba. “Ina yawan tunani, tun kana karami ko wane hali kake ciki? Me kake bukata? Amman bana iya yunkurawa na yi maka komai, cutar da kai da na yi na tsawon shekarun nan yana daga cikin abun da ya haifar min da hawan jinin da nake ganin zai iya ajalina a ko da yaushe, rayuwa zata dauwwama a guri daya Abiey idan ina raye a yau bana raye gobe, kuma idan ban nuna maka soyayya da kauna a dan wannan lokacin da ya rage mana yaushe zan nuna maka? Ba zan bari na mutu na koma ga Ubangijina ya tambaye kiwonka da ya bani ba na rasa bakin amsa masa, yaya suna da hakki akan iyaye kamar yadda iyaye suke da hakki a kan yayansu” Ya juyo ya kalli Abiey “Na ji dadin yadda Umaima ta tarbiyantar da kai, kuma ta nuna maka bin iyaye da amincewa da duk abin da suke so, wannan ya kwara min gwarin guiwar na shiga cikin rayuwarka na yi maka duk abun da ya dace” Abiey ya sauke ajiyar zuciya hawayen farinciki na sauko a idonsa. “Ranar yau ta zame min wata farar rana mai cike da tarin alheri da ban taba mafarkin zai zo ba, kalaman nan sai na ke jin kamar ba daga bakinka suke fitowa ba Mai Martaba, yau ni Aliyu ni nake zaune a kusa da kai kuma kai da bakinka kake fada min kana kauna ta, Allahu Akbar....!” Abiey ya kama hannayen Mai Martaba ya sumbanta. “Ko a yau na mutu na cika burina, na samu soyayyar mahaifina” Mai Martaba ya shafa kansa. “Allah ya maka albarka, kuma ya sanya albarka a cikin aurenku ya saka abokiyar zamanka ce har aljanna” Da tsoro da mamaki Abiey ya kalli Mahaifinsa dake murmushi. “Mai Martaba....Mai Martaba...Mai Martaba....” Sunansa kawai yake kira rudewa da tsabar farinciki ya kasa barinsa ya furta komai. “Na samu labari, ban jidadin abun da ka aikata ba, amman hakan ba zai saka saka ka aikata abun da shaida zai yi murna da faruwarsa ba, al'arshin Allah kuma ta girgiza saboda shi, ba a biyayye ga iyaye a tsabawa mahallinci, idan ban saka maka albarka ba zan tsine maka ne? Ka aikata boye ne saboda kana tsorona kuma a yanzu ka fuskance ka nemi yafiyata hakan ya faranta min rai sosai, baka fito kai tsaye ka nuna min kai sai ita zaka aura ba, wannan kadai ya isa ya saka na daga maka kafa, na cilasta aje kwallo kuma ka bi umarnin a lokacin da kake tsaka da kaunar sana'arka duniya take yayinka, bayan kuma baka girma a tare da ni ba, amma a haka ka godewa Allah ya ba ni ďa irinka Abeiy wannan ma wani abu ne abun alfahari” “Amman a ina ka samu labarin nan Mai Martaba...? Akan wannan auren Ammy ta daga hankalinta tana ganin kamar zaka yi fushi da ni, tana ganin kamar zan lalata yar ga6ar da na samu zan lalata, ta jaddamin idan har ka zabi na rabu da Zahra to dole na rabu da ita ko kuwa hakan na nufin rasa rayuwata ne, kuma da gaske Mai Martaba da ace ka zabi rabani da yarinyar nan da ka rabani da duniyar nan gaba daya” “Shiyasa na yi saurin fahintarka ďana saboda na taba kasancewa a irin halin da na kasance a wani lokaci can ba, na kaunaci Mahaifiyarka irin kaunar da har yanzu babu wata mace da ta maye gurbinta a gurina, a wacan lokaci mu yayan sarakuna ba ma zaban matan aure, sai dai a zaba mana wannan ce kaddarata ta farko da, rabon a same ka ya kashe mijinta ya mallaka min ita, kamin mai faruwa ta faru mu kasance a haka a yanzu, wannan ya saka a lokacin da Lami ta shigo min da labarin abun da aka ce ka aikata, amaimakon raina ya bace sai na ji tausayi, ka rasa abubuwa da yawa da suke saka ka farinciki, na kudirta a raina idan har da haske ne ka aikata haka, zan maka uzuri domin idan na matsa maka ban san abun da zai biyo baya ba, indai kana son matarka mu masu yi maka marhabun ne, tunanin Babba be taba zama irin an yaro ba, babban dole ne ya kasance ta mai hakuri da kawar da kai kuma yin tunanin kamin yanke hukunci...” Abiey be san lokacin da ya rumgume mahaifinsa ya fashe da kuka kamar mace, lallai a yau ya tabbatar mai hakuri mawadaci ne, kuma kowa yayi hakuri ya ce be ci riba ba to kadan yayi, abubuwa biyu masu matukar tsada a rayuwarsa sun zo masa a lokacin da be yi tsammani ba. [12/6, 12:23 PM] Oum_Nuwaira🥰: 7️⃣0️⃣ Tun da na shiga falon ban yarda na kalli inda yake ba balle har mu hada ido, kaina an kasa har na zauna a kusa da kofar ba tare da na ce komai ba. “Zahra na kira ki ne akan maganar yaronki, ke da Jamila dukanku ba ku yi tunani Mai Kyau ba kamin aikata abun, sai dai za a duba miki domin talauci da rashin mafita ne ya saka kika aikata, a yayinda ita kuma ta yi amfani da damar da take da shi ta aikata wannan laifi, wanda ya haifar mata da bakinciki a yanzu, ni ma kuma ya haifar min zai kuma haifarwa yan'uwana, kuma zai zame min abun magana a gari da dangi, abun da zai saka makiya na su jidadi su yi dariya, amman haka Allah ya kaddara ba mu sa mu zabi abun da zai faru da mu ba, kuma ba a mana ikon kawar da abun da bama so ba sai abunda Allah ya rubuta mana” Yanayin yadda yake magana akwai matukar tawakkali da tausayi, muryarsa har rawa take wata na hawa kan wata. “Ban aikata hakan saboda na cutar da daya daga cikinku ba, ban kuma yi tunanin nima hakan zai cutar da ni ba, idona ya rufe a lokacin da nake neman mafita akan rayuwar Deen, na manta da iyayensa, da kanwarsa da yan'uwansa, na siyar da Amir ba dan bana kaunarsa ba, sai dan ina ganin kamar hakan mafita ce a gareni, ina neman yafiyarki hakika mun cutar da kai na sani, kuma zaka iya daukar ko wane irin mataki amman baka dauka ba saboda hallaci irin naka” “Zan hannata miki ďanki a hannunki, sai ki tanadi bayanin da zaki gabatar ma kakaninsa da zai wanke ki ke a gurinsu” Na dago na kalleshi idanuwana cike da kwalla. “Babu wani bayani da zan tana, abun da ya faru sirrina ne, babu wanda zai san da wannan sirrin har abada” “Ban fahimci ki ba Zahra” “Idan har akwai wanda ya cancanta ya rike Amir a yanzu to kai ne, yan'uwanka sun san Amir a matsayin ďanka, su kuma ba su san shi ba, ba su san dadinsa ba, amman kai kasan dadinsa domin ka rike shi na tsawon watanin a hannunka, duniya tana kallon Amir a matsayin ďanka abun tozarci ne a gareka a yanzu labarin nan ya fita cewar yaron da kake ikirarin naka ne an gano ba ďanka ba ne, nasadin haka labarinka da nawa da kuma na matarka zai fita, wata kila har ya janyo maka wata matsalar, idan har zaka rike Amir tsakani da Allah kamar ďanka da ka haifa, ni kuwa zan bar maka shi kuma ba zan tana siffanta kaina a matsayin uwarsa ba haka ba zai san wani a matsayin ubansa ba sai kai, wannan sirrin zai cigaba da rufuwa har kasa ta rufe idona” Baki sake yake kallona, kamin ya girgiza min kai. “Karki yarda ki sake aikata wani abun ba tare da neman shawara ba, ina tunanin yana daga cikin abun da ya haifar min da matsalar da kike ciki a yanzu, kuma idan mu ka yi haka kamar kin cutar da kakanin yaron nan ne, domin su ma suna da hakki akan dansu, kuma idan ban manta ba a cikin labarin da kika ba ni kin fada min cewar su biyu kawai ta haifa a yanzu kuma ya rasu, na tabbatar da ace ta san da cewar jikanta yana raye ba za ta bar ki da shi ba” “Amman kai kuma fa?” Ajiyar zuciya ya sauke ya kishingida jikin kujerar da yake zaune, yana kokarin magana sai ga Ummiter ta shigo hankali a tashi jikinta har rawa yake. “Yaya ban ga Amir ba, na duba a dakinsa ban ganshi ba” Mr Bashir ne ya riga ni zabura ya mike tsaye. “What...! Kin duba da kyau kuwa?” A lokacin ni ma na mike tsaye ina kallon Ummiter hankalina a tashe. “Wallahi na duba ko'ina a dakin ban ganshi ba!” “Kin duba dakin Jamila” “Aa ban duba ba” A gaba daya muka dugunzuma muka fice zuwa bangaren Jamila, da wani kalar sauri mai kamar gudu na bi bayan Mr Bashir na shiga dakin Jamila, sai muka sameta kwance a kasa rumgume da Amir tana rusar kuka, gaba daya ta hargitsa dakin ta watse tufafinta kamar dakin mahaukaciya. Mr Bashir ya karasa kusa da ita da sauri ya saka hannu ya dauki Amir. “Akan me zaki dauki yaron mutane” Sai ta tashi da sauri ta rumgume kafarsa ta fashe da kuka. “Ka yi hakuri dan Allah, ka yafe min mijina” “Ni ba mijinki ba ne a yanzu, kuma ki yi gaggauwar fice min daga gida tun kamin raina ya kara bace” Martanin da ya maida mata ne na fahimci cewar sakinta yayi, ban san yadda saki yake ba ba a taba domin ba a taba min ba, amman na ji babu dadi musamman yadda take ta kukan nan akwai matukar tausayi, kamar ta san tausayinta ne ya cika min zuciya sai ta juyo gurina tana rokona. “Zahra ki yi hakuri, ki ce yayi hakuri ya yafe min” “Ba zan iya cigaba da zama dake ba Jamila, ko da na zauna da ke zuciyata ba zata sake natsuwa da ke ba, zan yi ta dubanki da wannan abun ne” Mr Bashir ya fada sannan ya miko min Amir. “Ga danki, hakan kuma ba zai hana na kyautata miki kamar yadda na yi alkwari ba” Sai na tara hannu biyu na karba ina hawaye. “Akwai kyautatawar da ta wuce wannan ne? Ni ka gama min komai tun da ka zabi rufa min asiri a lokacin da nake tsoron bayyanarsa” Uffan be sake cewa ba ya dauke kai ya fice daga dakin. Ummiter kuma ta zo gabana ta tsaya tana kallon Amir ta kalleni “Dan ki rufa asiri karki fadawa kowa abun da ya faru, Saboda ba ma son sirrin nan ya fita, babban mutum kamar yayana ace haka ta faru da shi ba zamu jidadi ba” Ta juya hawaye na sauko mata ta fice daga dakin, sai ya rage daga ni sai Hajiya Jamila dake kuka ni kuma ina hawaye. “Saninki be yi min rana ba Zahra, gashi yanzu zamanki a nan ya haifar min da ciwon da na dade ina tsoron ya kamani, da ace na san da zuwanki a gidan nan ba alheri ba ne, da na bar yaron nan a yadda yake ko kuwa idan ya sha nono mutuwa zai yi, da yanzu duk wannan be faru ba, da ban rabu da mijina ba, da yanzu asirina be tono ba, daman can kin ba ni dan ne ba da zuciya daya ba, shiyasa komai yake faruwa” “Kaico yanzu duk abun nan da ya faru be isa ya saka ki nadama ba? Baki fahimci kin aikata kuskure ba balle har ki tuba? Sai neman kakabawa wani laifi kike? Ashe ke din ba abar tausayi ba ce, na yi kuskure da tausayinki ya darsu a zuciyata a yanzu, Wallahi kin cutar da mijinki kin haifar masa da bakinciki da damuwa marar misaltuwa kuma ya kamata ki gane haka” Kamin ta sake ce min komai na juyo na fito ďakin rumgume da Amir, har na iso BQ ban daina kallon ďana ba ina shiga da shi dakin sai ya fara kuka sosai har wani fisga yake. Mama dake karyawa ta dago tana kallonmu. “Yau kuma ta barki kin taho da ďan?” “Mama Amir ya rabu da Jamila da mijinta a yau, ya dawo a matsayin ďana na asali, Mr Bashir ya mallaka min shi” A take Mama ta tsame hannunta a abincin da take ci ta mike tsaye. “Miya faru?” “Ya saki Jamila, saboda ya gane gaskiya tun da dadewa amman ya saka mana ido ya ga iya gudun ruwan mu, ya tambayi labarina na fada masa komai na rayuwata sai ya biyo min da abun da na aikata, shi ya nemi na fasa auren Sauban indai saboda tsoron tonuwar asirina ne har ya bukaci aurena a yanzu kuma da komai ya faru, sai ya mallaka min ďana kuma ya zabi rabuwa da matarsa” Mama ta saka hannu ta karbi Amir idonta na cika da hawaye. “Hukunta ki zai yi kenan?” “Aa yace ba zai yi komai ba, domin abun kunya ne a gurinsa, Mama tausayinsa ya kama ni, ban ga wani mutum mai hakuri da kawaici irinsa ba, wata kila da zai yardar da karbi Amir a matsayin ďansa ina da tabbacin zai rike shi amana” “Su kuma iyayen Deen ki yi yaya da su?” “Ba su da Amir ba, na riga na sanar musu cewar ďan ya mutu, babu san dadinsa amman Mr Bashir ya saba da shi, kuma ya riga ya nunawa duniya Amir a matsayin ďansa, idan Amir ya zauna tare da su zai samu rayuwa mai kyau ya kamu karatu da tarbiya, kuma na tabbatar idan ya girma ya san abun da na aikata ba zai jidadi ba, musamman idan suka nuna masa irin soyayyar da suka nunawa Deen wanda ta saka ya lalace ya zama ba shi da aiki sai shaye shaye da abokanan banza, wanda ya zama silar faruwar komai a yanzu. Mama ki duba tun daga lokacin da abun nan ya faru har ta kai Baba ya sake ki be sake waiwayarmu ba, daga shi har Hajiya sun dauki abun nan da zafi, idan suka san abun da na aikata za su hukunta ni kuma za su sanar da duniya, wata kila ma hakan ya saka kallon da iyayen Abiey suke min ta kara tsami, har wadanda ba su san ni ba wata kila za su ji sun tsane ni, shi kuma Mr Bashir zai shiga damuwa kuma duniya zata san an siyar masa da ďan wata kila ko da iyayen Deen sun hakura hukuta tace zata hukunta ni, amman idan yaron ya zauna a hannun Mr Bashir duk hakan ba zai faru ba” “Amman ke kina jin zaki iya jure rashinsa Zahra?” Na daga mata kai ina kallon Amir din dake ta kuka har da hawaye. “Zan iya, na rayu ba tare da uba ba, na kuma rasa mijina na rayu balle ďan da na san zai kasance a kyakkyawar rayuwa kuma zan iya samun wasu yaya a gaba” Na mika hannu na karbi Amir din dake hannun Mama na cire hijabina na saka hannuna na ciro Nono na saka masa a baki, sai ya ki karba sai kara fashewa da kuka yayi kamar ya san abunuwan da suke faruwa. Sai da na dorashi a kafata na fara yawo da shi a dakin ina jijjigashi wai ko zai yi shiru amman a banza kamar ma na kara masa, Mama ta karbeshi ta goya tana rarrashinsa nan ma a banza, kuka yake sosai har wani shakkuwa yake kamar zai tsude, a take hankalina yayi matukar tashi, cikin fargaba na saka hijab dina Mama ta saka nata muka fito daga BQ din muka nufi gate domin kai shi asibiti, gurin masu gadi na nufa daman can asali su suke bude min gate idan zan fita domin ban iya bude kofar ba saboda nauyinta. “Dan Allah ku bude min gate asibiti zan kai Amir” “Aa Mai gidan yace kar mu bari a fita da yaron nan daga gidan nan yace ko da matar gidan ce” Cike da mamaki nake kallonsu. “Shi ya fada muku haka?” “Eh” “Asibiti zan kai shi ba ku ga yadda yake numfashi ba” “Umarni ne aka ba mu, kuma idan za a kai shi asibiti ai ba ke ya kamata ki kai shi ba iyayensa” Kamar ya san cewa zan yi ya kira Mai gidan ya fada masa sai ganin na yi ya kara waya yana karanta masa abun da ya faru. “Gata nan a bakin gate” Wata kila cewa yayi a bani wayar sai ya miko min, ni kuma ba karba na kara a kunne. “Hello...” “Zahra... Miya samu Amir?” “Kuka yake tun da na karbo shi, na bashi nono ya ki ya karba, ina tunanin kukansa yayi yawa ne shi ne numfashinsa yake yin sama, su kuma sun hana na fita wai ka ce kar a bari kowa ya fita da Amir” “Eh ba fada musu haka ne saboda na yi tunanin ko Jamila zata yi kokarin guduwa da shi ne, zan fito yanzu nan” Na mikawa mutumen wayarsa sannan na juya na kalli Mama na fada mata yadda muka yi sai muka koma gurin kofar bangarensa muna jiran fitowarsa kamin ya fito har na matsu na dauko da Amir a bayana ina kallonsa gani nake kamar mutuwa zai yi domin abun karuwa yake har wani lumshe ido yake kamar mai bankwana da duniya. “Mama kalli mutuwa zai yi” “Wane irin mutuwa kuma, kawo shi a nan” Amaimakon na mika mata shi kamar yadda ta bukata sai na tura kofar shiga falon Mr Bashir na shiga da gudu ina kuka, karo muka kusa yi da shi domin shi ma ya fito da saurinsa ne sanye da sabuwar shadda. “Subhanallahi miya same shi ne” “Tun da na karbo shi yake kuka har yanzu be daina ba, kalli numfashinsa cirewa yake” Ya mika hannu ya karbe shi, Sai Amir ya bude ido ya kalleshi ya sauke ajiyar zuciya a take kukansa ya yanke, har sai da na yi zaton ko an zare numfashinsa ne. “Ko ya mutu ne” “Aa” Ya amsa ni yana kallon Amir din da shi ma kallonsa yake. “Karbe shi zan musu magana, direba zai kai ku asibitin yanzu” Ina mika hannu na karbe shi sai ya sake fashewa da kuka da sauri Mr Bashir ya janye shi ya fara jijjigashi. “Sorry sorry” Sai kuma yayi shiru, ba shi Mr Bashir din ba har ni har ni da Mama mamaki muke, domin jariri mai wata uku zuwa hudu be isa zaben uwa ko uba ba, haka kuma be yi wayon da zai ce da Mr Bashir yake son ya zauna ba balle na ce zaba yayi, idan ma shakuwa ce ina tunanin zai fi shakuwa da ni da nake shayar da shi fiye da Mr Bashir da yake a matsayin ubansa a yanzu, akan kafadarsa ya dorashi ya wuce gaba ni da Mama muka bi bayansa kamin mu isa gurin Motar Ummiter ta fito da shirinta idonta a kumbure kana ganinta ka san kukan da ta yi ba kadan ba ne, kamar ita aka yi ma laifin ba Mr Bashir ba. “Ina zaku je?” “Asibiti Amir za a kai” “Me ya same shi?” “Kuka yake yi yaki yayi shiru numfashina har sama yake kamar zai suma” Yayanta take tambaya amman ni nake amsa mata, tsaye ta yi a gurin har muka shiga motar da Mr Bashir ya nuna mana direba ya nufo motar da sauri ya shiga, Mama ce ta fara shiga sannan na mika hannu na karbe shi sai ya fashe da kuka, ina kokarin shiga motar Mr Bashir ya dakatar da ni. “Zahra kawo shi” Na mika masa shi, a nan ma yana karbar sai yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya, mun dade a tsaye yana rumgume da shi yana shafa kansa, sannan ya sake miko min shi yana fadawa Direban asibitin da zai kai mu, ya juya da sauri ya koma ciki, a take Amir ya sake fashewa da kuka, kukan da be daina ba kenan har muka isa asibitin da take ta kudi ce, wata kila Mr Bashir ya sanar da ma'aikatan gurin tun kamin mu iso, domin mun same su suna jiran isowarmu, a asibitin muka wuni har yamma sun dauki hotonsa an auna jininsa sai dai ba su fada mana komai ba har dare, wata a wannan asbitin ba su sanar da abun da yake damun yaro da wuri ko kuma ba su gama binciken su ba ne, Amir kuma be fasa kuka ba har garin Allah ya waye idan na bashi nono ba zai sha ba sai kukan kawai yake ta yi har sai da likitan safe ya shigo yayi masa allurar bachi sannan muka samu yayi bachi, muna tare da Mama har lokacin domin bata son ta tafi ta bar ni kadai, ni kuma hankali ya kasu gida biyu daya a nan daya kuma a gurin Abiey ina tunanin ko a wane hali yake a yanzu, idan iyayensa suka gane abun da ya aikata ko wane irin hukunci za su yanke masa? Gashi na bar wayata a gida balle na kira shi na tambayi halin da yake ciki. Dawowar likita ne ya yanke min tunanin da nake sai na gyara zamana na kalli Amir dake bachi. “Madam ya mai jiki?” “Gashi nan yana bachi, amman Dr baka fada mana abun da yake damunsa ba” “A iya bincike da muka ji na jiya be nuna akwai wata matsala ko wani ciwon a tare da shi ba, amman za mu sake yin wasu waje wajen a yau Inshallah” “To miya yake kukan?” “Shi muke kokarin mu gano, domin be kamata a rubuta masa maganin komai ba har sai mun gano abun da yake saka shi kuka, kar ya zamana mun yi magani dabam cuta dabam to yaro ne karami ba shi da baki balle ya iya fada mana matsalarsa” Na juya a hankali na kalleshi. “A da can yana ciwon cikin idan ya sha nonon da bawa nawa ba, ban sani ba ko matsalar ce har yanzu, amman shi ma ya daina daga baya domin bayan nono akan hada masa da madara kuma ya sha bata masa komai ba” “Eh Alhaji Bashir yayi mana wannan bayanin tun a jiya da na sanar da shi ba mu ga wata matsala ba, to amman kin bashi wani abun ne?” “Aa madarar dai ko jiya ya shekaranjiya ya shata ban san ko ita ce ta haifa masa da matsala ba a yanzu” “Dole a kawo mana madarar mu gani kuma zamu son gwada ruwan nono na ki so that mu gano idan ta wata matsala, sannan za a sake yi masa wani hoton da wasu manyan gwaje gwaje Inshallah” “Toh” Na amsa jiki a sanyaye ina jin wani yanayi na rashin jindadi, sai da likitan yayi abun da zai yi ya fita sannan na kalli Mama cikin damuwa na ce. “Mama ko dai shi ma mutuwa zai yi?” “Ko kuma dai Allah mai hikima yana nufin shirya wani abu a tsakanin bayin nan nasa” “Ban gane ba” “Tsakanin Alhaji Bashir da Amir din mana, baki lura ba idan ya dauke shi ya kan yi shiru?” Na zaro ido sai kuma na juya da sauri na kalli Amir din. “Amir be yi wayon da zai kulla wannan makircin ba, saboda haka mu barwa Allah komai Zahra, ni ma na gamsu ki bar yaron nan a inda zai samu rayuwa mai kyau da tsabta, shi ma kansa Alhaji Bashir din yaron ya shiga ransa tun da har ya riga mu samin halin da yake ciki” [12/6, 6:08 PM] Oum_Nuwaira🥰: 7️⃣1️⃣ Yana shigo kitchen din gaban Ammy ya fadi, sai ta rage gas din ta kalli Jummai dake juya miyar hantar sake saman wuta ta ce. “Je ki bangarenki idan na gama zan miki magana” “Toh Hajiya” Ta aje cokalin dake hannunta ta gaishe da Amir sannan ta fice daga kitchen din, Ammy ta kalleshi fuskarta dauke da damuwa. “Ina ka je?” “Gurin Mai Martaba” Ya amsa mata yana kokarin boye farincikinsa. “Ka yi magana da shi?” Ya daga mata kai sai ta yi saurin sauke kai kasa gabanta na kara faduwa. “Ya ce ka sake ta ko kuma ya sake yin fushi da kai?” “Be min ko daya ba” Ya tako ya karaso inda take tsaye sai ya fashe da dariyar da ta firgitata ya rumgume. “Ammy Mai Martaba ya saka min albarka” “Ko dai ya tsine maka ba” Ta fada tana jin kamar ta fashe da kuka, Abiey ya dago yana kallonta hawayen farinciki na taruwa a idanuwansa. “Ni ma na yi tsammanin zai yi fushi da ni, wata kila har yace ba zai sake saka hannunsa a lamarina ba, domin na aikata wannan abun ba tare na sanar da shi ba, daman can na yi ma kaina alkawarin idan har ta dake akan sai na rabu da Zahra, to zan rabu da ita sai dai shi na kuma zai rabu da ni, domin bana jin zan sake rayuwa idan muka rabu da Zahra a halin yanzu, duk kuwa da irin raya min da zuciyata take na cewar Mai Martaba ba zai cilasta ni yin haka ba, domin mutum ne da ya san mi yake yi kuma ya san abun da ya kamata da wanda be kamata ba, haka kuma Mai Martaba uba ne ko da ba ni ďansa na aikata haka ba na san shi mai shiga gaba ne ya magance komai a gurin wasu iyayen balle kuma a cikin gidansa” “Ni duk ba gane wannan bayanin zan yi ba, kawai ka fito fili ka fada min abun da ya faru” Abiey ya dafa Ammy yana murmushi. “Kamin na sanar da Mai Martaba laifin da na yi masa, shi ya fara yafe min ya kuma sakawa aurenmu albarka” Ammy ta matsa baya. “What... ” “Yes ni ma abun ya ba ni mamaki, Ammy yau na zauna kusa da Mai Martaba har jikinsa na taba jikina har hannunsa ya kai ya taba kafadata, a yau Mai Martaba ya kira kansa a wani mutun da ya kasa ba ni lokacinsa da hakkinsa da Allah yace ya ba ni, Mai Martaba da bakinsa yake fada min ni na fi soyuwa a ransa fiye da sauran yayansa, kuma mahaifiyata ta fi ko wace mace tsayawa a ransa” Ammy ta dafa kirjinta hawaye na sauko mata, sai ta juya da sauri ta dafa sink. “Ba da gaske ba ne wannan abun ba gaskiya ba ne” Abiey ya karasa kusa da ita ya dafata yana cigaba da murmushin farinciki. “Ni ma kamar na ce haka, sai kuma daga baya abun ya zame min kamar mafarki, har kuka na yi Ammy ban taba tunani rana zata zo da Mai Martaba zai yi min furuci mai dadi kamar wannan ba” “Ya kamata na tabbatar” Ta fice daga kitchen din da sauri, dakinta ta shiga ta dauki wayarta ta kira Anty Amarya yanayin yadda Anty Amarya ta amsa kiran ma kadai ya isa ya bayyana mata cewar Abiey gaskiya ya fada. “Wani labari na ji yanzu daga bakin Aliyu wai Mai Martaba ya yafe masa abun da ya aikata” Anty Amarya ta amsa daga dayan gefen tana dariya. “Ba wai ba ne gaskiya ne, be fada miki har da tukuicin albarka ya biyo baya ba? Gani a nan ni da yara sai murna muke” Ammy ta fadi zaune a kasa gaba daya tana rufe bakinta. “Mai hakuri mawadaci Ammy, ni kaina ba tsorota a lokacin da Abiey yace zai yi magana da mahaifinsa, Wallahi na yi zaton zai iya cewa ya tsine masa albarka ma, ashe Allah ya tsara wani abun dabam da shi kadai ya bar wa kansa sani, Wallahi ba yarda mai gaskiya baya tabewa, kuma gaskiya komai ta dade sai ta bayyana” Ammy ta lumshe ido tana kuka sosai. “Shekara fiye da talatin ina fama kiyayyar Mai Martaba akan ďana, ko da rana daya be taba cewa Umaima Aliyu yana lafiya, ko yana bukatar wani abu, amman ku ce min ya saka masa albarka, a lokacin da nake tunanin albarkar zai cire masa?” Ta girgiza kai ta sauke wayar ba tare da saurari abun da Anty Amarya ke fada ba, Abiey ya karaso kusa da ita ya duka ya rumgume sai ta fashe da kuka. “Da ace na mutu kamin wannan ranar da na mutu da wannan bakincikin, amman a yau Allah ya wanke min zuciyata da dattin da ya dade ina dauke da shi a zuciyata, hakurin da ka yi na halin da ka samu kanka shiyasa Allah yayi maka sakamako da abubuwan da kake matukar kauna a lokaci daya, Allah ya maka albarka Aliyu” “Ameen Sweet Mom” Kuka ta yi sosai kamar ba abun farinciki ne ya faru ba, kamar an tsikareta sai ta zabura ta tashi ta share hawayenta muryarta na rawa ta ce “Je...je...je... ka dauko min Zahra karka fada komai ni zan mata wannan albishir din” Abiey ya sumbanci Mahaifiyarsa ya sake rumgumeta sannan ya sake ta ya fice yana dariya, safa da marwa ta fara yi a dakin tana daga hannunta sama tana yi ma Allah godiya, can kuma ta sake nufar wayarta ta dauka ta lasa number Mai Martaba har zata kira sai kuma ta fasa ta aje wayar, can kuma ta sake dauka ta aika masa kira kamin ya dauka gabanta ya fadi sau ba adadi. “Assalamu Alaikum” “Wa'alaikassalam” Sai kuma ta yi shiru bayan ta amsa sallamar. “Umaima” Ta amsa wasu hawayen na silalo mata “Na'am” “Ko dai kamfanin line sun baki kyauta ne, shiyasa kika kira kuma kika kasa magana, na san dai ba zaki kira saboda ki gaishe ni ba, sai idan na taba ďanki zaki kira ki fara min masifa” “Yau din ma ďana ka taba Mai Martaba, irin tabawar da na dade ina jiran ka yi masa, irin tabawar da nake mafarki a kowane dare, na gode Allah ya saka da alheri” Ta fashe da kuka, jimmm yayi na dan lokaci kana ya ce. “Miye abun godiya ga wanda ya aikata abun da yake wajibi a gurinsa? Abiey ďana ne, kuma yanzu nake da damar nuna masa soyayyar da ban yi ba a can baya, saboda yayi alfahari da ni kamar yadda nake alfahari da shi a zuciyata, sai dai hakan ba zai hana na nuna masa kuskuren abun da yayi ba a nan gaba, saboda ya kiyaye ko da yake ba laifinshi ba ne laifinki da kika goya masa baya ya aikata haka saboda kina ganin kin zame masa uba ko? Ko kuma dai kin yi hakan ne saboda ki kara lalata alakar dake tsakaninmu” “Ko kadan ni ma ban san ya aikata ba, har bayan da komai ya faru, ya hada kai da abokinsa da yayarsa Dr Zainab suka shirya komai, na masa fada sosai kuma har alkawarin na yi masa cewar idan har ka dage sai ya saki Zahra to dole ne ya bi unarninka ko kuma ni ma na cire hannuna a lamarinsa, ya aikata hakan ne saboda yana ganin kamar idan babu yarinyar ba zai rayu ba, ka san halin yara da kuma kurciya” Mai Martaba yayi dariyar da Ammy ta dade bata ji irinta daga gareshi ba. “Yara kenan, ko da yake yana da gaskiya ai, soyayya gaskiya ce domin bata tsufa bata canja muhalli ko da kuwa masoyan sun tsufa matukar akwai wannan soyayyar ta gaskiya t zata zauna a raine har abada, Allah ya musu albarka” “Ameen, Allah ya kara lafiya” “Ameen” Ammy ta sauke wayar tana lumshe ido ta ja dogon numfashi ta sauke a hankali. Abiey ya fita gidan da gudunsa kamar wani karamin yaro har shafa kansa yake yana shiga motarsa ya kure volume da wakar Celine Dion da wakarta ta new day has come. _I was waiting for so long for a miracle to come, everyone told me to be strong...._ haka ya rika bin wakar yana rerawa har da su tafi yana juyawa kamar ba driving yake ba, shi kansa ya manta rabonsa da samun farinciki irin wannan, sai dai be yi sa'ar tararda Zahra ba, saboda suna asibiti ma'aikatan gidan kuma ba su fada masa wace asibiti ce ba domin su ma ba su sani ba, ya dade a waje yana ta jira ko zata dawo ko Mama amman be ga kowa ba, ga wayarta yayi kira har ya gaji bata amsa ba, A nan ya kira Sauban ya labarta masa abun farinciki, Sauban ya kasa hakura har sai da ya same shi a unguwar ya taya shi murna, sun dade suna hira sannan ya wuce ya bar shi a gurin, tafiyarsa da mintuna kadan Dr Zainab ta kira shi tana taya shi murna a nan ta shaida masa cewar ta zo gida tana tare da Ammy. A unguwar yayi sallah magariba da Isha'i sannan ya dawo gida bayan ya sadakar da cewar ba za su dawo a daren ba. A lokacin da ya dawo gida Ammy take kara fada masa cewar Dr ta zo gidan. Agajiya ya zauna yana sauke gajiya ya labartawa Ammy cewar be samu Zahra ba. “Allah yasa da sauki to” “Ameen, ni ma abun da nake fata kenan, domin hankalinta a tashe yake saboda abun nan da ya faru” “Amman da ka kirata ko a waya ne” “Na kirata ya fi a kirga amman bata daga ba, ina tunanin ko ta bar wayar gida ne ko kuma wani abun ya faru da bata iya amsa wayar” “Allah ya sauwake” “Ameen” A daren Abiey ya raya shi da nafila yana ta zuba godiya da yabonsa ga Allah, be kwanta ba sai da yayi sallah asuba. 8 na safe ya farka da sauri ya sauka saman gadon ya zura talkaminsa ba bedroom ya nufi gurin da yake aje tufafin daya cire ya raba jikinsa da jallabiya ya daura tawul ya wuce bathroom, wanka yayi ya fito jikinsa na ta kamshi expensive shower gel, madubi ya nufo yana goge jikinaa da tawul just like that yake jin he just want to dance yana kallon kirjinsa a madubin, rawa ya fara yi yana ba tare da kida ba sai jujjuyawa yake sai kai karshen dakin ya juyo ya dawo gurin madubin, can kuma ya aje tawul din hannunsa ya nufi wayarsa ya dauka ya kunna waka ya aje wayar kan drawer ya dauki fillo ya rike yana ta takawa kiyasi yake ace Zahra ce a gabansa, ya sumbanci fillon ya rumgume shi. “I love You Babe” Ya kusan bata waya biyu a dakin sannan ya shirya ya fito sanye da blue jean sai bakar rigar da ta kara masa kyau da kwarjini da haiba, kitchen ya leka ganin Jummai ya karasa ciki ya dauki tsoka daya a cikin ferfesun data sauki ya fito yana goge hannunsa da tissue bayan ya wanke a sink, be takurawa kansa tsayawa ya karya ba da ma ace Ammy na nan ita zata takura masa da cewar sai ya karya zai fita, motar da ya dade be hau ba ya nufa ya bude ya saka mata key ya kunna motar. 8:30 ta yi masa ne a kofar gidan Alhaji Bashir bayan ya tambaya masu gadin sun fada masa cewar Zahra bata dawo ba, sai ya nemi guri ya faka so that ya jirata maybe zata dawo yin wani abu ko ita ko Mama. Sai kusan karfe goma napep ta sauke Zahra bakin gate din gidan, da sauri Abiey ya fito motarsa ya nufo inda take sai da ta mikawa mai Napep dinsa sannan ta kalli Abiey cike da damuwa. “Hiayatee...” Bata amsa ba sai kallonsa take ta tabe irin yadda yara suke idan suna son a taba su fara kuka, be yarda ya sake ce mata komai ba ya jata jikinsa ya rumgume. “I'm here” “Ance ba a gane abun da yake damunsa ba, yanzu ma sun sake shiga da shi gurin wani gwaje gwaje, Mama tace wai yana son zama a hannun Mr Bashir ne, ni kuma gani nake kamar mutuwa zai yi” Ya dagota daga kirjinsa ya rika fuskarta da hannanyen yana ta yawo da idonsa akan fuskar tata. “Zai ji sauki, kar bakinki ya sake furta haka ba zaki sake fuskantar wani bakinciki ko damuwa ba Inshallah” Ya share mata hawayen da suka zubo mata, bata dama da ganin a bakin gate suke ba ta maida kanta kirjinsa domin tana son kasancewa da shi, kamshin turarensa na daga abun da ke kwantar mata da hankali, ga wata natsuwa da rahma da take ji idan ya rumgume ta. “Ka yi magana da Ammy da Mai Martaba?” “Eh Ammy ma ta aiko ni tun jiya na dauko ki, sai masu gadi suka fada min kun tafi asbiti, kuma ba kira wayarki baki daga ba” Da sauri ta dago daga kirjinsa ta kalli fuskarsa. “Ammy? Ni miye nawa a ciki to? Ai ba da sanina aka yi komai ba, ka ga zata zo ta mana fada a tare ko kuma cewa zata yi ka sake ni” Ta fashe da kuka, sai ya rumgume yana murmushi da be bari ta gani ba. “No ni ma dai ban san abun da yasa ba, amman dai ya kamata muje sai mu ji ko ma minene” “Ni ba zan je ba Wallahi ka je ka ce mata na bata, baka gan ni ba idan kuma ta ce ka sake ni ne ai ba dole sai mun je can ba” “No dole mu tafi mana, ya kamata mu ji dalilin kiranta be kamata ki yanke hukunci ba tun yanzu” “Ni dai ba zan je ba, waya sani ko faffala min mari zata yi ma, kuma ta ci min mutunci ta ce min mayya” Be san lokacin da dariya ya so subuce masa ba, sai yayi saurin kawar da kanshi. “Saboda kin auri ďanta zata ce miki manya ta falla miki mari kuma?” “Eh mana sai tace na nace nace na lake maka, alhalin ba da sanina aka yi ba” “Yanzu dai kamin ki shiga ciki ki fara zuwa gurin Ammy, ko ma dai minene sai mu je” Sai da yayi da gaske sannan ta yarda ta shiga motar, yana hawan titin ya kwantar da ita jikinsa yana driving da hannu daya, ita kuma sai rara kuka take a hankali, sai da ya faka motarsa a harabar gidan sannan ta dago ta kalleshi. “Idan tace ka sake ni sakina zaka yi ko?” “Ba zan iya yanke hukunci a yanzu ba” Ya sumbaci hancinta, sannan ya bude gefensa ya fita. ZAHRA POV. Zagayowa yayi ya bude min na fito wasu hawayen na taruwa a idona, tunanin maganar Mama da kuma kiran da Ammy take min sai ya zame min biyu, daman can ina ta tunanin yadda Ammy zata ji idan ta san gaskiya, side hug yayi min wata kila ya manta a cikin gidan Ammy muke ko kuma dai kunyar tasa ce ta yi karamce oho, muka nufi kofar shiga falon, yana bude kofar falon na ji fitsari ya cika min mara, da sauri na janye jikina daga nashi amman hakan be hana shi miko hannunsaya rika hannuna, muna kokarin shiga falon ina buge masa hannu alamar so nake ya sake ni kar Ammy ta gani. Da sallama ya shiga falon na ina jin muryar Ammy ta amsa masa yan hanjina suka kara kadawa, a zaune muka same ta ni dai ina kallonta na yi saurin rufe ido har sai da Abiey ya zaunar da ni, ido daya na fara bude na kalli saitin inda Ammy take ganin ni take kallo fuska ba yabo ba fallasa ya saka dole na bude idon gaba daya, na kara matsawa kusa da Abiey sosai domin gani nake kamar ma zata iya aiko min da marin daga inda take. “Wallahi Ammy ba ni na ce yayi ba, ba da hadin bakina aka aikata ba, ban san sun shirya hakan ba sai da komai ya faru, dan Allah ki yi hakuri” Na fada tuni na fara kuka, kokari akwai nake na wanke kaina kar Ammy ta dora min laifi. “Yanzu ya kike so ayi? Na bar shi ya cigaba da zama da ke ko kuma na ce ya sake ki” Ammy ta tambaya tana kallona babu wasa a fuskarta. “Idan har baki son aure zaki iya cewa ya sake ni, amman dai ni ina son shi, kuma shi ma yana so na, idan kina ganin akwai maslaha a sakin, ni ba ruwana sai ya sake ni” Plate din dake jikinta ta aje ta mike tsaye ta nufo inda muke zaune a take natsuwata ta bar jikina zuciyata na raya min marina zata yi, na matse Abiey sosai kamar zan shige jikinsa. “Dan Allah ki yi hakuri” Abiey ya dora hannunsa a jikina kamar zai rumgume ni kuma be rumgume ni din ba, zuwa ta yi ta kama hannuna ta dora akan na Abiey. “Zahra fitinanniya, kin fitini zuciyar ďana kin hana shi sukuni har sai da ya auro ki ko? To ga amanar shi nan na baki, karki kuskura ya kawo min kararki cewar kin masa laifi, zan miki hukunci mai tsanani, Allah ya sakawa auren da kuka yi albarka ya ba ku zama lafiya ya albarkacin yaran da zaku haifa da zuri'ar ku, Mai Martaba ma ya sakawa aurenku albarka shiyasa na ce Aliyu ya kawo min ke ni zan miki wannan albishir din” Ta karasa tana murmushi, da sauri na kalli Abiey sai ya sumbaci goshina yana murmushi ko kunyar Ammy ba ya ji, fashewa na yi da kuka na mike tsaye na rumgume Ammy, sai ta saka dariya ya kankame ni. “To Shagwababbiya, mijinki zaki yi ma wannan ba ni ba” Ban yi zaton komai zai zo mana da sauki kamar haka ba, kamar wata Sarauniya haka na zama a gidan Ammy Abiey kam be da madubi sai ni, tare da ita muka koma asibiti ta duba Amir a nan ta sanar da Mama abun da ya faru ni ma na kara shan labari yadda komai ya faru, ni kaina na yi farinciki jin cewar Abiey ya shirya da mahaifinsa. Da dare likitoci suka sake tabbatar mana cewar ba su ga wata matsala a tare da Amir ba, gashi kuma be daina kukan da yake ba, sai dai ya sha nono na kadan sai ya saki ya cigaba da kuka, muna a wannan halin Mr Bashir ya shigo tare da Ummiter da wata da ba zata wuce sa'ar Ummiter ba ko kuma ta dara ta kadan kamannin dake fuskar Ummiter ne suke zube a fuskar Matar da nake kyautata zaton budurwa ce ita ma. Bayan mun gaisa ta sake dubana ta ce. “Ke ce Zahra?” Na amsa mata da kai, sai Mr Bashir ya gabatar min da ita a matsayin kanwarsa da Ummiter ke bin bayanta wato Imaan, kana Mr Bashir ya mika hannu ya karbi Amir dake rusar kuka, kamar wani abun tsafi yana karbarsa sai yayi shiru ya sauke ajiyar zuciya, ba ni kadai ba, Mama da Ummiter da Imaan din duk kallonsu muke, Mr Bashir yayi murmushi. “Tun a jiya na fadawa Zahra akwai abun da yake shirin faruwa tsakaninka da yaron nan, kuka yake babu tsayawa kuma na lura idan ka karbe shi yana kan yi shiru, gashi kuma likitoci sun cd ba shi da wata matsala” Imaan ta kalli Mama da ta yi maganar ta ce. “Abun da ya kawo mu kenan, Yaya ya fada mana komai kuma ya ce Zahra ta yi nufin bar masa Amir amman yaki ya karba saboda yana tsoron abun da zai biyo baya, ni da Ummiter muna ganin kamar karbar shi ne mafita a garemu da kuma ku gaba daya, domin ba ma son labarin nan ya fita, kuma ina kallon wannan abun kamar wata kyauta ce da Allah ya fara yi mana ta bangaren Yaya ba mu san abun da gaba zata haifar ba, domin ba shi ya aikata ba, kuma ba da saninsa aka yi komai ba, wannan kukan da yaron nan yake yi ma kadai ya isa ya saka mu fawwallawa Allah komai, kuma mu masa godiya” Mr Bashir da ya dora Amir a kafadarsa ya sauke ajiyar zuciya, sai tausayinsa ya kara kamani lallai rashin haihuwa wani mugun ciwo ne, musamman a gurin mutum mai son yara da kuma tara iyali, ba dan haka ba wata kila da Mr Bashir da yan'uwansa tsanar Amir za su yi jin cewar ba jininsa ba ne, amman hakan be canja komai daga soyayyar da suke masa ba. “Allah ya baka ikon rike shi amana, kuma ya baka ikon tarbiyantar da shi, amman ina son ka yi min alkawari ko da bana raye ba zaka taba bari hawayen Amir ya zuba a gurin da ka san zaka iya share masa ba, kuma ba zaka taba bari ya san komai akan lamarin nan ba” Na furta hawaye na masu zafi na sauko, ina jin wani irin kaunar yarona da kuma tausayinsa na kama ni fiye da zatona, zuciyata ta yi mugun karaya. “Na miki alkawari Zahra, ko da bana raye Amir ba zai taba kukan maraici ba, soyayyar da zan nuna masa ko dan da na haifa jinina iya ka kenan, daga ni sai yan'uwana muka san wannan gaskiyar, kuma na tabbatar ba zasu fada masa ba za a rufe maganar nan har a bada” “Hajiya Jamila zata iya fada” “Na gargade ta, kuma ita ma kanta ta san abun kunya ne a gareta ta fadi abun da ta aikata shiyasa da tafi gida sai ta fada musu cewar aure zan yi shiyasa na rabu da ita” Na matsa kusa da Mama na kwantar da kaina a kafadarta, ina jin wani abu mai kama da kewa na yi min yawo a zuciya. ___________________________ (Ni ko na ce anya Zahra zata iya hakura idan ta kyautar da Amir 🤔 to zamu dai gani WANI GARI Littafin da zai zo a 2050😁 nan da 28years masu zuwa amman fa a rayuwar littafi) [12/8, 5:19 PM] Oum_Nuwaira🥰: 7️⃣2️⃣ YASMIN POV. Tana gama karanta jaridar ta dauki wayarta da sauri ta kira Abiey gabanta sai faduwa yake, sai da wayar ta kusan yankewa sannan ya amsa kiran. “Hello Yasmin” “Na'am an tashi lafiya” “Lafiya Kalau, ya Momy” “Lafiya kalau take” Sai kuma ta yi shiru, hakan ya saka shi aje wayar a jikin madubin dake dakin ya cigaba da lika batulan rigarsa. “Yasmin” “Na'am” “Kin yi shiru” “Wani abu na gani a jarida yanzu nan, wai an daura aurenka da Zahra a sirrance” Abiey ya dafe kansa da sauri. “Oh abun har ya kai a buga a jarida?” “Da gaske ne kenan?” “Eh gaskiya ne” Yasmin ta mike tsaye da sauri ta dafe zuciyarta tana haki. “Yaushe? Abiey da gaske kake?” “Yau kwana biyu, ina zaton ban taba miki karya ba” “Amman ba ni da hakkin da zan sani ne? Da ba za a fada min ba sai dai na gani a jarida?” Jikin Abiey yayi sanyi domin ya san be kyauta mata ba, ya kamata ya sanar da ita komai ko shi ko Ammy amman be iya yayi ko daya ba saboda murna da farinciki sun dauke masa hankali, zauna yayi a kujerar madubin yana kallon kansa. “Ki yi hakuri Yasmin, ban kyauta miki ba Wallahi na sha'afa ne gaba daya, amman zan zo na same ki anjima zamu yi magana akwai ma labarin da zan baki mai daďi idan na zo” Lumshe ido tana hawaye masu zafi ma sauko mata, har cikin kokon zuciyarta take jin zafin abun da Abiey yayi mata. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un” Ta furta tana jin wani irin azabar sonsa da kishinsa na fisgarta, fashewa ta yi da kuka mai karfi abun da bata taba yi ba, da gudu Momy ta shigo dakin ta zauna kusa da ita ta dafa ta. “Lafiya Yasmin?” “Momy da gaske ne Abiey yayi aure” Momy ta yi murmushi ta kwantar da ita kan kafadarta. “Shi ne kike kuka? Daman can zuciyarki ta raya miki ke kadai zaki zauna a gidan namijin da zaki aura ko da ba Abiey ba?” “Aa Amman Momy ai an saka ranar aurenmu fa” “Auren Zahra zai hana shi aurenki ne? Bayan ke zai iya karo auro wata ma, kuma kin gani a jaridar ance an daura auren ne a sirrance, Allah kadai ya san abun da ke nan” Momy ta dago ta ta share mata hawayenta. “Ni shawara daya zan baki, karki yarda ki nuna masa kishinki a kan Zahra, matukar kina son ki zauna lafiya da shi, to ki koyi sonta, ni a ganina ai wannan abun farinciki ne ya same shi da ya kamata ki taya shi murna ki nuna masa kin fi shi jindadi, kamin na auri Mahaifinki ni da Hajiya Umaima miji daya muke aure, ba za a ce babu kishi ba, domin duk mace tana da kishi amman mai hankali da wayo ita take boye kishin nata, ita kuma wanda miji yafi so idan tana da wayo da hankali sai ta rika dora shi akan hanya ta gari, da ace ba mu yi zaman lafiya da juna ba, da Abiey ba zai yarda ya aureki ba, idan ma ya yarda mahaifiyarsa ba zata yarda ba, amman zaman lafiya ya saka mun zama yan'uwa wani lokacin Abiey da kansa zai kawo min karar mahaifiyarsa ko kuma yayi fushi da ita ya dawo nan ya zauna, mi ya kawo haka ba zaman lafiya ba? Ki yi kishin mijinki kishi abu ne mai kyau amman karki yarda kishin nan ya fi karfinki domin zai cutar da zuciyarki ne ita kuma ta cutar da ke, ki rike Zahra kamar yar'uwarki, idan abun farinciki ko sabanin haka ya same ta ki taya ta murna ko jajantawa ko da kuwa ita din bata miki haka, ki bita irin bin da mijinki zai fahimci babu wata cuta ko kiyayyarta a ranki, musamman Abiey da yake matukar son Zahra, idan kika nuna masa baki kaunarta abu ne mai wahala ya iya zama da ke” “Amman Momy ai yafi sonta” “Dole ya fi sonta ai, daman namiji ba zai iya daidaita soyayyarsa tsakaninsa da matansa ba, Allah be bashi wannan ikon ba, amman mai yawo shi yake boye soyayyar kuma ya kwantanta adalci a tsakani, karki yarda Zahra ta fiki kyautatawa Abiey da yan'uwansa da iyayensa, da wannan zaki karbe soyayyarsa har ya dawo yana sonki fiye da ita” “Toh” Ta amsa wasu hawayen na kuranyo mata, wayarta ce ta dauki kara tana duba mai kiran sai ta yi arba da Abiey. “Shi ne ya kira” Ta fada tana dubi Momy, Momy ta yi matan alama da ta amsa da hannu. “Hello” “My dear ina wajen gidan zan samu ki fito please” For the second time ta ji ba zata iya yi masa abun da ya bukata ba. “Ni aiki nake yi” “Toh ni gani nan shigowa” Ta sauke wayar tana kallon Momy dake hararta domin ta ji abun da ya nema ita kuma ta yi ta yi masa. “Yanzu wannan ba soyayya ce ya nuna miki ba? Ina kara gargadinki Yasmin matukar kika biye zuciyarki to zata kai ki ga halaka ne” Momy ta mike tsaye ta fice daga dakin, tana fitowa falon ta samu Abiey tsaye yana kallon kofar dakin Yasmin kamar mai neman wanda zai aika a kira masa ita, a da can babu kunya tsakaninsa da Momy sai dai a yau yana hada ido ta ita sai ya ji kunyarta ta kama shi irin ta sukuri da ya shigo gidan surukansa, har yake jin ina ma be shigo falon ba har sai da aka yi masa izini. “Momy” “Abiey ne” Ya risina mata abun da be taba ba. “Eh Momy ya gida” “Lafiya Kalau ya Hajiya Umaima” “Lafiya kalau take” Yayi shiru na wani lokaci Momy ta nufi kitchen domin kawo masa abun karyawa kasancewar safiya ce. “Momy zan wuce daman na zo ne kawai na gaishe ki” Momy ta juyo tana murmushi. "Toh a gaida gida, amman ka jira waje Yasmin zata fito yanzu” “Toh Momy thank you” Ya juya ya fice yana shafa kansa kamar ba shi ba, mutumen da ada idan ya shigo gidan har kusa da ita zama yake, kai ta girgiza tana jindadin samun Abiey a matsayin sukukinta domin miji ne da ko wace mace zata yi alfahari da shi, ta sani matukar Yasmin ta kwantar da hankalinta shi kuma ya kwatanta adalci zata jidadin zama da shi. Dakin Yasmin ta shiga ko da ta shiga ta same ta har ta saka hijab dinta tana ganin Momy ta boye fuska tana jin kunya. “Je kitchen ki sama masa abun karyawa ki fitar masa da shi” “Toh” *** *** *** Abiey na zaune cikin motar yana video call da Zahra ya hango Yasmin ta fito dauke da faranti sai yayi saurin gyara zamansa. “Hiayatee i will called you back Okay” “Miya faru?” “Ba komai wani abu zan yi, ina gamawa zan je gurin Mai Martaba idan na dawo sai na zo na dauke ki mu tafi shopping din, i love you” “I love you more” Ya sumbanci wayar sannan ya daga mata hannu ya kashe, hakan yayi daidai da bude front seat da Yasmin ta yi da dayan hannunta ta shiga ta zauna, amman ta ki yarda ta kalli inda Abiey yake zaune kuma ta ki tace masa komai haka ma ta kasa boye fushinta. Abiey yayi murmushi mai sauti ya mika hannu ya karbi tray ya dora a jikinsa. “Na san na yi laifi, amman neman yafiya na zo fa ko karyawa ban yi ba” Ta nade hannayenta ta juya masa fuska. “Kin tana ganin mace ta yi fushi da mijinta? Haba Yasmin ayi hakuri ma, mun shirya abun ne a boye ban yi tunanin abun zai zo mana da sauki har haka ba, Yasmin kin san ya so yake ba ki bukatar na fada miki komai ina jin da ace na rasa Zahra a karo na biyu ke ma da kin rasa ni, amman yanzu Alhamdulillah komai ya wuce” “Sai a jarida na ni fa Abiey” “Ban san an saka a jarida ba, ban kuma san waya saka ba bayan mun gama waya dake Mai Martaba ya kira ni yake fada min abun da yake faruwa kuma yace min yanzu haka ya saka a kawo masa wanda ya buga labarin daga nan gurinsa zan tafi, domin sun buga labarin ne da nufi bata suna, secondly sune wadanda suka wallafa wacan labarin na rushe gidan da aka yi, ban san inda suke samo labarin ba. Yanzu ni dai tuba nake a yafe min” Ta dan saki fuska. “Ina Zahra take?” “Tana gidansu ko na kawo miki ita?” “Aa na sani ni ko bata son gani na” Ya wara ido. “Saboda me?” “Zata ce ina son mijinta mana” “Kina son mijinki dai, babu zance ni mijin Zahra ne ko mijin Yasmin ni mijin mace biyu ne a yanzu da dai ace Zahra kawai nake aure to zan zama mijin Zahra ita kadai, amman Allah yayi min kyauta da kyawawan mata har biyu a lokaci daya” Ta yi murmushin jindadi ta sauke kai kasa domin bata yi zaton jin haka daga gareshi ba. Ya maida hankalinsa gurin abincin ya fara ci. “Uhhhh waya girka wannan?” “Ni ce” “Aa ban yarda Momy ce” “Wallahi ni ce” “Daman haka kika iya girki? I thought Islamiya bata barinki girki ai, i got lucky daman ina son macen da ta iya girki kuma ta iya tsabta” Haka yayi ta zuba santi wani abun da gangan yake yinsa saboda ya saka ta nishadi kuma yayi nasarar yin haka domin ya tafi ya barta zuciyarta fes sai dariya take. Daga gurin Yasmin Abiey ya wuce gurin Mai Martaba kai tsaye bangarensa ya nufa babu tsayawa neman iso a gurin Anty duk kuwa da ya san yau din ba girkinta ba ne girkin Hajiya Kilishi ne. Yana shiga da sallama Mai Martaba ya amsa masa yana murmushi da jindadin ganinsa. “Babana” Hajiya Kilishi ta sake waigawa ta kalli Abiey da kyau domin tabbatarwa idan shi din ne ko waninsa, Abiey ya karasa gaban Mai Martaba ya kwashi gaisuwa sannan ya zauna Mai Martaba ya mika masa mug din tea dake hannunsa, sun tattauna abubuwa kadan a ciki har da abun da Mai Martaba yake son yayi handled, sai da Hajiya Kilishi ta fita sannan Abiey ya tambayi Mai Martaba. “An gano maka shi?” “Eh an gano shi, ai ba boyayyen mutum ba ne, kuma ba shi kadai na saka a kama ba har da wadanda suka buga wacan labarin, dole akwai hannun wani a ciki ko dai daga cikin gidan nan ko kuma daga bangaren abokanka ko kuma bangaren ita yarinyar” “Ni ma na yi wannan tunanin, domin wacan karon ma ba ni na saka a rushe gidan ba amman aka rusa saboda a bata min suna kuma a ja min zagi” “Za mu gane ko waye tsakanin yau da gobe, masara idan ta ji wuta ita ke daďo” Daga haka Mai Martaba ya rufe babin maganar ya dauko zancen nadin sarautar da za ayi masa cikin satin nan. “Mamanka ta kawo shawara wai tana ganin kamar ka tare kamin lokacin zai fi armashi a kafin nadin sarautar, tun da bayan nadin sarautar da wata daya za a daura aurenka da Yasmin, ina ganin mu dai daga bangarenmu babu wata matsala idan ka shirya” Abiey ya sauke kansa kasa sosai ya jidadin shawarar da Anty Amarya ta kawo daman ta yi masa wannan maganar tun shekaranjiya. “Eh to Mai Martaba idan haka yayi muku ni ma ta gurina babu matsala sai dai na tuntubi bangaren ita Zahra na ji” “Allah ya bada iko, idan kana da matsala da ni ka tunkare ni kai tsaye ka fada min ba sai ka laba da wasu ba” “Ameen, na gode Allah ya kara lafiya” Bangaren Anty Amarya ya shiga ya labarta mata yadda suka yi da Mai Martaba, Anty ta numfasa cikin farinciki ta ce. “Ni gani nake kamar Lami ta shirya wannan abun, domin wacan karon na kasan a gaban yarta aka yi ina tunanin ita ta bata labarin sai ta saka aka shirya wannan saboda ta kara bata tsakaninka da Mai Martaba sai gashi Allah be cika mata wannan nufin ba, a yanzun ma ta yi haka ne saboda ta ga Mai Martaba be dauki wani mataki a kanka a madadi hakan na sai Allah ya shirya tsakaninku” “Ko ma dai wanene za mu ji Inshallah asirinsu zai tonu” “Da yardar Allah kuwa, Mai Martaba yayi maka maganar tarewa?” Abiey ya shafa kansa. “Yayi min yace kin masa magana” “Haka na ga ya dace, ace an nada maka sarautar matarka tana gidanka abun zai fi bada kala” “Sai dai ban san ko ita Zahra zata yarda ba” “Ban gane zata yarda ba? Kai ne fa mijin karka zama mijin tace mana kai da zaka bata umarni ta bi” Abiey yayi dariya. “Ai ni tun kan tace ne ma, Zahra haba Anty kamin tace ma na aikata” Haka suka yi ta hira cikin nishadi har suna tunawa da baya Anty tana tsokanarsa. Sai azahar ya fita gidan ya bayan ya sake wanka ya feshe jikinsa da turare wai kar ya jewa amaryarsa yana karni kamar wanda be yi wanka safe ba. Baya ra'ayi shiga gidan a domin haka ya faka a wajen gidan ya kira wayarta ya sanar mata zuwanshi, ta kusan bata rabin awa tana shiryawa sannan ta fito tana taku kamar wata matar sarki, tun kamin ta karaso ya fito ya bude motar ta shiga ta zauna sannan ya zagaya ya zauna kai tsaye ya kai hannunsa ya riko nata sumbata ta biyo baya. “How are you” “Fine” Ta amsa cikin yanayi na damuwa, yana ganin hakan ya san ba lafiya ba, matsawa yayi ya hade bakinsa da nata wani hot kiss ya sakar mata, kasancewar doguwar riga ce sai mayafi a jikinta hakan ya bashi access ya saka hannayensa yana lalabe iya inda ya dade yana sha'awar tabawa a jikinta, tun yana yi saman abayarta har ya kasa hakura ya zira hannunsa ta saman rigarta, sai da ta ga yana kokarin dago ta ta dawo saman jikinsa sannan ta yi saurin cire bakinta ya zare masa hannayensa, ta yi saurin maida fuskarta gefe shi kuma ya kwanta jikin kujerar yana wani tandar baki mean he need more domin be taba jin kansa a irin wannan yanayin da ya samu kansa a yanzu ba har wani ajiyar zuciya yake saukewa yana lumshe ido. “Fada min waya taba min yar autar mata” Ya fada murya kamar mai rada, ya dago ya mika hannunsa ya juyo da fuskarta. “Hiayatee what happen?” “Amir...” “Miya same shi?” “Ba komai, kawai dai ina jin kewarsa ne” Tashi yayi zaune da kyau ta yadda zai fuskance ta da kyau, ya matso da ita ya kwanto da ita jikinsa. “Hiayatee idan kin san zaki cutu ki karbo yaron mana, daman ni na san zai tsaya miki a zuciya kuma ina tsoron kar hakan ya haifa mana da matsala a gaba, kin ga ki daina tunanin abun da iyayen Deen za su yi na sha fada miki indai ina raye babu wanda ya isa ya taba ki” “Bayan na riga da na kyauta da shi, har ya samo masa Nanny fa kuma tun shekaranjiya har yau ba su kawo shi ya sha nono na ba, ina tunanin madara suka bashi, kuma jiya ya kira Mama ya fada mata cewar yau za a kai ta, ta duba wani gida idan ya mata sai mu tare a can, ni daman ba saboda kaina kawai na yi ba saboda Mr Bashir din domin shi ma ya ce baya son duniya ta ji abun da matarsa ta yi masa” “Abun da mataraa ta yi masa be shafe ki ba, matarsa ce rayuwarsa ce ke babu ruwanki a ciki, ke dai yaro suka siya kuma kin sai da yanzu kuma ta gaskiya ta fito an dawo miki da abunki, Zahra kakanin yaron nan ma fa suna da hakki da shi, idan ba ki son ya zauna a gurinsu ne zan dawo da shi gurinmu ya zauna ayi masa duk abun da yake bukata” “Amman shi Mr Bashir ai zai ce ban kyauta ba, kuma duniya zata ji” “Zan masa bayani, kowa ma zan masa bayanin da zai fahimta” “Aa ni dai yaron ma ai baya so na kuka yake min idan na dauke shi” ‘Ai kara haka so that mu zamu rayuwa cikin farinciki da aminci’ Ya fada a ransa daman bayan Mr Bashir Abiey ya fi kowa farinciki da hukunci da Zahra ta yanke not because of baya son Amir din but because of yana dan Deen kuma yana tunanin kamar idan Amir ya fito a matsayin ďan Zahra kai tsaye zai iya haifar musu da matsala a zamantakewarsu, idan har yace yana son Amir yayi karya, sai dai baya tsanarsa kuma zai iya yi masa komai saboda ďan Zahra ne, ba na Deen shi kadai ba, and since da sanin mahaifiyarta ta yanke wannan shawarar ba zai iya hanata ko saka ta ba, da ace dai ita akaran kanta ta yi haka to da zai hanata, gudun kar hakan ya haifar mata da matsala a gaba. “Yanzu Shikenan, tun da haka kika zaba amman ya zama karo na karshe da zan sake ganin hawayenki akan yaron nan” Kamar jira take sai ta fashe masa da kuka. “Ni ba wai bana son shi ba ne, ai ina son shi ai” Uffan be sake ce mata ba, har ta yi kuka ta gama, sannan ya zaro tissue ya goge mata hanci ya share mata hawaye. “Kukan ya isa haka, i promise you muna fara haihuwar yayanmu saki samu sukunin kewar Amir zata rage miki, who's know ko gobe ma mu samu yaya ko kuma yau ma” Ta yi saurin daga jikinsa ta kalli fuskarsa sai ya kashe mata ido daya. “Kin san Anty ta saka mana ranar tarewa?” “Yaushe?” “Cikin satin nan, Mai Martaba ma yayi min magana yace ya kamata na tare kamin a yi nadin sarautar” “Aa ni ban shirya ba” “Haba Hiayatee me zamu jira kuma? So nake Mama ta tare a sabon gidan da aka gina da yake kusa da na Baba, ta koma tsohuwar unguwarku saboda ta saba da can da mutanen ciki, idan Mr Bashir ya baku gidan idan haya zaku saka ko ki aje sai ku yi haka, but for now Mama gidana zata zauna, mu kuma zai mu tare a jibi” Ta lake kafada daya tana masa abun da ya ke kara rikitashi wato shagwaba. “Aa ni ban shirya” Hannunsa ya mika ya janyota. “Ni ban ce a shirya min komai ba, Inda zaki zauna za a zuba komai a ciki, lefe ne kawai zamu hada da kan mu, idan an gama nadin sarautar sai mu tafi siyayyar a kasar da kike so ki hada lefenki da komai a can” “Aa ni dai” “Haba Babe ya kike son na yi ne? Ba ki san ina cikin mawuyacin hali ba? Kuma kin ga Anty zata ce ba ki ji maganarta ba, Mai Martaba ma zai ce ba mu ji shawararsa ba” “Sai na yi magana da Mama” “Shikenan, idan baki ra'ayin tarewar a yanzu ba zan cilastaki ba, amman babu abun zai rage ni da shi ina son ki san wannan” Ta dago ido tana kallonsa “Me kake nufi?” Ya hura mata iska a idon yana murmushi. “Abun da zuciyarki ta raya miki” Cikin rada ya bata amsa yana goga mata hancinsa kamin ya sauke bakinsa a kai ya fara tsotsar hancin nata. [12/9, 5:32 PM] Oum_Nuwaira🥰: 7️⃣3️⃣ Ba dan ya so ba ya barta ta fita motar ta shiga gida, ya dade a cikin motar kwance domin jikinsa ya gama mutuwa gaba daya, sannan ya juya motarsa ya nufi gurin Ammy. A inda ya saba parkin ya faka motar ya fito ya shiga ciki, yana shigowa falon ya samu Dr da Ammy suna lunch, Dr sai zolayarsa take wai ango Ango, murmushi kawai yayi ya shige dakinsa sai da yayi wanka ya shirya sannan ya fito, wannan karon akan sofa Ammy take zaune domin ta gama cin nata abincin, Dr ce kawai zaune a kujerar tana ta ladawa, kujera yaja ya zauna ya dauki plate ya fara zuba ma kanshi. “Dr kullum kika zo gidan nan sai kin ci abinci” Wani kallon uku saura kwata ta yi masa “Hana ni cin abincin ni da gidanmu, kai na ai ka kusa daina cin abinci” “Aa ba wannan ranar” “Idan matarka ta tare ai dole ka dauke mana kafa ko?” Cewar Ammy tana dariya, juyawa yayi ya kalleta. “Ammy ai kin san Matata bata iya girki ba, kuma ni bana son Mai aiki ni zan rika yin wanke wanke da shara, sai ki rika mana girki na zo na dauka ko ki aiko mana” “Hmmm Allah ko? Ashe kana da aiki, to Wallahi ka fada mata ta koya tun yanzu domin ba zan yarda Ammy ta yi muku wannan wahalar ba” Harara ya watsawa yayar ta shi. “Ina ruwanki da shiga tsakanin uwa da ďa” Ammy ta ce. “Da gaske ne fa, in dai ba wai auren nan da ta yi ta koya ba, Zahra bata iya girki ba, amman dai ga Yasmin ai ta isheku da dai ita kam na san mahaifiyarta ba zata yarda ta kai gidan miji bata iya girki ba” “Au wai aurenka da Yasmin yana nan?” Dr ta tambaya yana kallonsa ya daga kafadunsa. “To ya zanyi, tun farko ta dage sai an yi abun nan, gashi nan tana son rusa mana jindadi ni da Zahra” Yana aje numfashi Ammy ta karbe tana fadin. “Aa babu inda ta rusa muku jindadi fa, ita ma kanta take yi ma yaki, kuma ai ta riga ta fadawa Iyayenta cewar tana son a fasa auren amman suka ce hakan ba zai yiyu ba saboda sun riga da sun amincewa Mai Martaba, yanzu haka Anty tana nan tana ta hadin lefe” “Ni kam da dai zaka bi shawarata da ka samu Mai Martaba ka yi masa bayani domin a yanzu yana fahimtarka ai, sai ka nuna masa kai fa baka son Yasmin, saboda ka samu Zahra ne ya saka ka yi kara da ita, saboda kar bayan aurenku ka zo abu yana damunka” Abiey ya kalli Dr yana nazarin maganarta. “Ni ma ina tunanin haka, har ina ganin kamar Yasmin zata fi Zahra zafin kishi ma, kuma na san Zahra ba zata jidadin zama da kishiya ba, amman sai nake ganin kamar Yasmin ba zata jidadi ba idan na yi haka, kuma mahaifiyarta ma ba zata jidadi ba, shi kan shi Mai Martaba zai zama kamar na cilasta shi ne ya aikata hakan, domin da ace yayi ra'ayin janyewa da ya janye ko kuma yayi min maganar da kansa” Ammy ta taso daga inda take zaune ta dawo kusa da ďanta ta zauna. “Aliyu, indai har kana jin kaunar Yasmin ko kadan ne a ranka to ka yi hakuri da ita ka aureta a haka, domin idan har ka janye maganar auren nan bata kyauta mata ba ni da mahaifiyarta kuma ba zamu jidadi ba, sannan baka san tanadin da Mai Martaba yayi ba wannan bikin naka, ka ga ka riga ka daura aurenka da Zahra a sirrance ba kowa ya sani ba, sannan wasu bukukun da ya kamata ni da mahaifinka mu gabatar ba zamu samu wannan damar ba, amman a aurenka da Yasmin zamu samu wannan damar mu yi bikin da zai amsa sunan biki, kuma ina tabbatar maka idan ka auri Yasmin zaka jidadi domin tana da tarbiya ga ilmin addini, sannan zaka rage wani abun kamar ta bangaren girki da ka fada, wata kila ganinta zai saka Zahra ta maida hankali ita ma ta iya, sai dai fa karka yarda son Zahra ya saka ka zalinci Yasmin, kuma karka nuna musu banbanci kyautatawa ce kawai ba zan cilasta ka ka yi ma wata ka hana wata ba, dole wannan wanda ka fi so ko kuma wanda ta fi kyautata maka kai ma ka kyautata mata, kuma ban baka shawarar ka aje su a gida daya ba, domin kazantar da baka gani ba tsabta ce inji hausawa, idan daya bata ganin daya an fi marmarin juna, kuma wata soyayyar da zaka nunawa daya ta banbanta da wata ba lallai ne dayar ta sani ba, sannan karka yarda ka nunawa Zahra ka fi kaunarta akan Yasmin haka ma karka nunawa Yasmin ka fi kaunar Zahra akanta, kuma karka wulakanta ko wace, kar ka daya wata ta zagi wata a gabanka, karka aikata irin kuskuren da mahaifinka ya aikata wanda ya haifar mana da matsala a yanzu” Ya jinjina kai cike da gamsuwa da shawarwarin da Ammy ta ba shi. “In'Shaa Allah, Allah ya ba ni ikon yin haka, amman abun nan ba sauki, ni ban ma taba sammanin zan iya zama da mace sama da daya ba” “Daman haka rayuwa take, kana nata Allah na nashi, dukam mu ba mu yi tsammanin haka ba, kai dai ka yi ta godiya ga Allah na yadda abubuwa suka zo maka da sauki kuma cikin farinciki da jindadi” “Ina ta yi kuma zan kara i love you sweet Mom, Amman ina son na fada miki Zahra ta barwa Allah Mr Bashir Amir” Abiey ya karasa yana kallon Dr dake murmushi domin ta san da labarin, Ammy kuma da take jin labarin wani banbaragwai ta zaro ido ta rufe baki. “Ya sanar yana ra murna, ya fada a yanzu har ya fi jin kaunar Amir fiye da baya, ta yi abu mai kyau domin ta rufa masa asiri kuma shi ma ya cancanci haka, ya kira ni da kansa ya fada har ya nemi na zama mai rike masa sirrinsa” “Amman Zahra ba ta yi tunani ba, anya kuwa da sanin mahaifiyarta ta aikata wannan abun?” Abiey ya kalli Ammy dake tambayar. “Da saninta ta aikata, ita ma ta bata shawarar yin haka wai suna tunanin haka zai fi saboda tana tsoron kar labarin ya fita ace ita ta aikata, kuma tace min yaron ma kuka yake idan ta rabe shi ya fi sha'awar zama a gurin Mr Bashir din, and Ammy kin san indai yaron nan yana hannun kakaninsa ko gurinmu hankalina ba zai kwanta ba, domin Zahra zata tattara hankalinta gaba daya ta maida gurinsa ne, ba dan abun da ubansa yayi ba da yanzu ďana ta haifa ba Amir ba” “Kai dai Abiey kana ta kishin mutumen da bashi raye, ni fa har yanzu ina ganin Deen ya aikata abun da ya aikata ne saboda yana son Zahra, kamar yadda ka aikata abun da ka aikata a yanzu wanda na tabbatar da ace Mai Martaba da Ammy tsine maka albarka za su yi zaka yarda ka sauki wannan” A take ran Abiey ya bace da maganar da Dr ta yi. “Daman ai kina goyon bayan abun da ya aikata shiyasa ba ki ganin laifinsa, and that's why i hate him so much wannan Amir din ma ba dan Zahra ba da babu abun da zai saka na kula shi, domin jinin makiyina ne” Ammy ta ce. “Yanzu ai komai ya wuce tun da shi ya bar duniyar kuma ka mallaki Zahra a yanzu me ya rage, gashi Allah ya kara maka da Yasmin zaka auri budurwa kai ma ayi maka wanka lalle irin yadda ake yi ma kowa” Mikewa yayi tsaye ya fice daga dinning. Mama Lami ce zaune a gaban Mai Martaba yana kallon video da aka turowa Mai Martaba na wasu yan jarida gudu uku sai dai dayan cikin ruwan sanyi ya bada amsar wadanda suka saka shi, sauran kuwa sai da suka sha wahala sannan suka fadi cewar Rilwan ne ya fada musu komai kuma ya bada umarnin su je su dauki rahoton har ya hada musu da tukuicin kudi. Mama Lami dake rike da baki ta girgiza kai jikinta sai tsuma yake idonta sun yi kwayan irin na marasa gaskiya domin tonuwar asirin ďanta kamar nata ne, domin ita ta saka shi yin komai da saninta aka aikata. “Wannan sheri ne kawai” A take Hajiya Kilishi ta karba mata. “Yauwa ni ma ai na fadi haka, domin mutane babu sherin da ba a iya ba ko dan a haka shi da Mai Martaba” Anty Amarya ta tabe ki domin ta san borin kunya suke kuma bakinsu a hade yake. “Wallahi wannan sheri ne aka yi masa Mai Martaba ka fahimci haka, akwai wanda ke son ya hada ka da shi ne, shi kanshi Abiey ai zai iya haka saboda kar sunansa ya bace shi kadai” Mai Martaba ya mika hannu ya karbi wayarsa rai a bace. “Na tara ku a nan na nuna muku wannan saboda na gargade ku, ku cire idonku da hannunku akan ďana, saboda ina fushi da shi, hakan ba yana nufin bana sonsa ba ne, kamin na nuna miki video ne saida na yi magana da Rilwanu kuma ya karbi laifinsa, kuma ya fada min gaskiyar abun da ya faru daman can na saka ran wannan abun a tsakaninku ya fito, domin idan ba nan ba babu ta inda labarin nan zai fita, Abiey ya fada min cewar ba shi ya rusa gidan nan ba, yanzu ma na kara yarda hakan domin Rilwan ya fada min cewar ke kika saka shi, kuma be kara min komai ba sai son Abiey da godiya ga Allah da ya ba ni ďa irin Abiey, ina son na ja kunnenku ne gaba dayanku kar na sake ji ko ganin wani abu makamancin wannan akan kowa balle kuma akan Abiey, inda hakan ta sake faruwa na bincika na gano gaskiya to zan dauki tsastsauran mataki akan haka” “Amman Mai Martaba wannan ba adalci ba ne, daga mutane sun fadi sunan Rilwan sai ka dauka da gaske ne, kuma har ka tara mu kana mana irin wannan gargadi akan wani ďana kamar su sauran ba haihuwar ka yi ba?” Cewar Hajiya Kilishi a kokarinta na tarewa yar'uwarta laifin da dukansu sun san gaskiya ne, har Rilwan dake zaune a can gefe sai gumi yake, ya kasa dago kai ya kalli kowa. “Bana kwai sai da zakara, ba iya wannan abun suka fada ba, har shaida sai da suka nuna ta kudin da ya tura musu da kuma maganar da yayi da su, shi ma ai be amsa min laifinsa kai tsaye ba sai da ya ga hujojin da ba zai iya wanke kanshi da su ba, saboda haka ina gargadinku dukanku ku cire Idonku akan Abiey, ba shi kadai ba har da sauran yayana, idan wani abu ya sake faruwa ko wacce ku ta shiryawa zaman yayanta, domin zan iya zabar yayana akan matana, idan baku taimaka min na hada kan iyalina ba, be kamata a same hannunku a cikin ruguzasu ba” A take Mama Lami ta saka kuka, Hajiya Kilishi na bata hakuri. “Ki yi hakuri, wannan abun duk sherin makiya ne, shi kansa Rilwan din da wahala idan a hayyacinsa ya amsa cewar ya aikata wannan abun ,domin ba halinsa ba ne kuma babu yadda ba a iya ba, shiga tsakanin uba da ďa ko uwa da uba duk ana yi” “Kilishi ki yi zaman yayanki, Zuwaira tashi ki koma bangarenki” Mai Martaba ya fada cikin bacin ran musun da Hajiya Kilishi ke masa, gaba daya kamar bakar kaza yake ganinta a yau. Anty Amarya ya rufe baki da sauri, jin Mai Martaba yayi furucin da bata taba sa ran zai iya ba ga matan da take ganin sune yan lelensa kuma yan gaban goshin da sai abun da suka fada ake yi. Wani irin zabura Hajiya Kilishi ta yi ta daki kirjinta. “Ni kuma? Ni Mai Martaba? Daga bada hakuri sai abu ya dawo kaina, aa ba dai ni ba Wallahi, haba Mai Martaba ni miye nawa a ciki daga ba da hakuri, dan Allah ka yi hakuri, abun da ba ayi da kurciya ba yanzu bayan an yi yaya da jikoki za a ce a rabu ka dubi girman Allah ka yi hakuri” Ta kai kasa tana kuka tana rikon kakafuwansa mikewa yayi tsaye yana kokarin shi na janye kafafuwan na sa yayi ma Anty Amarya alama da ta tashi ta tafi domin mamaki abun da ya faru ya saka ta manta da umarninsa. “To Wallahi ba ki isa ba, Lami idan ma wani kullin ne kika shirya min to wutar ba zata ci ni kadai ba, daman ai kishiya ba yar'uwa ba ce, ba ki yin min da kurciya da zan iya aurowa ba sai yanzu da tsufa ya kama, wato ki zauna ki mulke gida yadda kike so?” Lami ta fara yi mata alama da ido cewar ta yi shiru, amman ina son a yau Hajiya Kilishi bata sauraren maganar Lami saboda an yi mata abun da ba a taba ba, kuma akan abun da ba ita ta aikata ba. “Ba zan yi shiru ba, ai babu kalar shirinki da ban sani ba, haka kika yi sai da kika fitar da Umaima a gidan nan, ke da bakinki kika fada min indai kina raye ita da duk zuri'arta ba za su taba samun muhalli a zucutyar Mai Martaba ba, shi ne a yau ni zaki dawo kaina? To Wallahi sai dai niyarki ta biki, kuma Wallahi ke kika saka aka rusa gidansu Zahra, saboda ki kulla masa sheri kika aika ďanki Rilwan ya saka yan Jarida su kitsa wannan abun saboda ki bata tsakanin ďa da uba” Lami dake tsaye kamar karan dawa ta girgiza kai cikin kwarewa ta iya makirci na mata. “Lallai kin hauka a yau Kilishi ni kike kullawa wannan sheri saboda abincinki ya kare a gidan nan? Kamar ni nace Mai Martaba ya sake ki? Ina kika kai hankali ne? Idan ma kishi ne ai an yi can da da kurciya amman yanzu girma ya kama an watsar da komai, kuma idan magana kike ta asiri ai tare muka aikata domin munduwa daya bata amo, har kara ni na yi na iya wanda mijina zai kauna ce ni ne, ke fa ke da bakinki kika fada min cewar Umaima har ta mutu ba zata sake aure ba, kin riga kin jefeta da mugun kullin, wannan haukar da kike ma amanarta ce ta kamaki Wallahi shiyasa kike fadar abun da kika aikata kina dangantasu da ni, amman ni ban san wannan sherin na ki a ina ya zamo asali ba” Kilishi ta yi cikinta kamar za su daki juna sai ka rantse da Allah ba manya yaya ne da su ba. “Karya kika yi, Wallahi ke kika shirya komai ai daman kin fada cewar babu macen da zata yi mulki bayan ke, Zuwaira ma da aka kawo daga bayan nan mallake kika yi kika saka mata tsoronki kin mallake kowa a gida, ni ma ai banza kika bar ni kuma Wallahi Allah ya isa” Mai Martaba ya nade hannayensa baya yana kallon dramar da ake a gidansa, abun da be taba tsammanin faruwarsa ba, kuma be yi zaton da sa hannun matansa a lamarin Ammy ba. Anty Amarya ta mike tsaye idonta cike da kwalla na tausayin Ammy ta fice daga falon ba tare da tace komai ba tun da Mai Martaba ya tarasu har rikicin ya faru. Da gangan Hajiya Kilishi ke fadar abun da Mama Lami ta yi saboda Mai Martaba ya ji komai domin a tunanin Mama Lami ta shirya mata wani abun ne ta fitar da ita a gidan ta wargaza mata yaya, daman can ana zaune ne kawai amman babu aminci da yarda da juna, ko wace tana yi ma yar'uwarta asiri. Uffan Mai Martaba be sake cewa ba ya fara takawa cikin takun kasaita irin na manya sarakuna ba tare da ya san yana yi ba. Dakinsa na bachi ya shiga sai da ya kai karshen dakin sannan ya daga kansa sama yana jin zuciyarsa babu dadi, be taba jin bakinciki rayuwa da Ammy ba irin yau, ya dade yana tambayar kansa dalilin kauracewa matarsa da yayi wanda hakan ya jefata ga halaka, i duk lokacin da zai waiga ya duba sai ya tarar babu wani laifi da ta yi masa kawai ya kasa zama da ita ne, har abun da ya faru ya saka shi sakinta. ANTY AMARYA POV. shiga bangarenta ke da wuya ta dauki wayarta ta kira Ammy, bugu daya ta yi Ammy ta amsa kiran. “Assalamu Alaikum” Amsa sallamar ma bata Anty bata samu yi ba, ta fara zayyana mata abun da ya faru cikin kuka. “Ki gode, a yanzu komai ya zo karshe, kara ke an sake ki da kurciya ita kuma yanzu da tsufanta ya haramtawa kansa ita domin yace ta yi zaman yayanta kuma na tabbatar bakin ciki ba zai bari ta iya zama a cikin gidan nan ba” “Wani abun a nesa yake na yarda, na sha wahala, na rayu a cikin bakinciki tun bayan fitowa a gidan nan, kuma Allah yayi musu yadda suke so sun raba auren kuma sun yi nasarar yin min aikin kar na auru, tabbas tun bayan fitowa ko kare be sake zuwa yace yana so na ba, amman hakan be dame ni ganin ina da Yaya sai na maida hankali gurin rainon yayana” “Allah ya saka miki Ammy, Allah ya isar miki” Ammy ta share hawayen da suke mata zuba mata ta ce. “Ya isar min ai, sai dai a lahira ayi wannan shari'ar, a cikin yayansu waye na kwarai? Matan ne kawai suka samu gurin zama mai kyau amman mazan daga masu neman bata masa suna sai wadanda ke jiran ya mutu a raba gado a ba su, ni ko ki dubi ni Zuwaira ba fariya ba Allah yayi min komai a cikin yayana babu lalatacce, dukansu suna aiki kuma suna arzikin da za su iya gogawa da masu kudi ko masu mukami, a cikin yayana ina da sojan sama da na kasa ga babbar likita a kuma Aliyu babban dan kwallon da duniya ma tana ji da shi, to me Allah ya rage ni da shi? Alhamdulillah, shiriyar yaya ai ita ce babbar shiriya iya haka ni Allah yayi min komai, balle kuma yanzu da Allah ya bawa ďana matar da yake so kuma ya shirya tsakaninsa da Mahaifinsa” “Haka ne, idan Allah ya hana ka wani abun sai ya baka wani, hanyoyin Allah yawa ne da su, Allah ya karkato da hankalinsa ya dawo dake cikin gidan nan, hankalin Abiey zai kara kwanciya” Ammy ta yi murmushi bakinciki still hawaye na kwaranya a idonta. “Aliyu ai be rasa uwa a gidan ba, ke zaman wa kike ba ďana ba? Wallahi ko mutuwa na yi a yau na san Aliyu ba zai yi maraici ba saboda ke, ke ma kuma lokacin jindadinki ne ya zo a yanzu a da can sun kame gida babu mai iko sai su, yanzu kuma komai ya wuce, ni kam sai aljanna idan Allah ya ba ni ikon zaben abokin rayuwa, amman zaman aure tsakanina da Mai Martaba ya kare har abada, yanzu aure ba ya burge ni ai sai dai mu yi ta bawa yaya shawara” Da tausayin Ammy Anty Amarya ta yi sallama, domin an raba aurensu ne a lokacin da suke matukar kaunar junansu kuma suke da kurciyar zama a tare, a zaton Anty Amarya Mai Martaba yayi ma Ammy saki uku ne da babu gyara shiyasa ba take fadar cewa zamanta da Mai Martaba ya kare a duniya. [12/9, 7:56 PM] Oum_Nuwaira🥰: 7️⃣4️⃣ ONE MONTH LATER... ZAHRA POV. Abubuwa da yawa sun faru a wata nan, a cikin akwai tarewa ta a gidan mijina kuma masoyina wato Abiey, da kuma tarewa Mama a gidan da Abiey ya gina dake fuskantar na mu na da, wanda ya cilasta mata zaunawa a ciki duk da kasancewar Mr Bashir yayi mana kyautar gida na alfarma. An yi bikin nadin sarautar da ya amsa nadin sarautar da aka dade ba ayi irinsa ba. Domin an kashe naira kuma cikin ya samu halarta manyan mutane daga bangaren Ammy da Mai Martaba sai ka rantse sabon Sarkin Kano aka hada ba dansa a matsayin Galadima ba. Hakika na ga kauna da soyayya daga gurin Mai Martaba a ranar da aka shiga da ni Masarautar da sunan gaisuwa kamin ya a kawo ni gidan da zan nake da tabbacin shi ne na zamana har aljanna. Mai Martaba ya tara iyalansa ciki har da yayansa da matan biyu wato Hajiya Lami da Anty Amarya jawabin maraba da ni a cikin zuri'ar bayan ya kira da sunan Mahaifiyarsa, kyautar tsadadiyar Alkyaba yayi min a take aka saka min ita a gurin aka cire yan kunena na zinari aka saka min wasu na zinarin da Mai Martaba yayi min kyauta da su na miliyoyin nairori, ranar yayi mana nasiha ni da Abiey sannan aka yi addu'a tare yi mana fatan zaman lafiya, turaren da aka feshe ni da shi sai ka rantse da Allah a gidan aka kafa kamfanin turare. A lokacin da zamu fita gidan Anty Amarya ta bada sabuwar motar da aka kawata da balon balon da fulawoyi da kuma jan kyale. Ni kadai aka dauka a motar wasu motocin suka shiga gaba wasu a baya masu busa na ta aikinsu har muka isa gidan da aka kawata da kusasasun dawankan Abiey guda Hudu. A ranar na ga taron mutane sosai ashe Ammy ma tana da yan'uwa da yawa domin sun yi ta zuwa gidan ganin Amaryar ďanta a cikin har da matan yayun Abiey Wato Yaya Auwal da Sani, ta bangaren Mai Martaba ma na ga yaya da yawa wanda ya kara tabbatar min da lallai na shiga babban gida mai cike da zuri'a da kuma sarauta, kowa a unguwar sai da ya san matan Abiey aka kawo kuma surukar Mai Martaba saboda busa da aka cika kofar gidan da shi da kuma shigowar manyan motoci. Na ga baki kala kala wasu am har na manta rabon da na ga fuskarsu, wasu tsofin abokaina ne wasu kuma makonta mu yan'uwa har da na nesa, suna ta zuwa bawa idonsu abinci. Sai dai duk wannan cin daka ayi aka cinye Hajiya da Bahijja ba su tako ba, balle na yi zaton samun albarka daga gurin Baba. Walimar da Mama ta shirya a ba su halarta ba kuma ta gayyace su. A daren da aka kai ni, na samu kaina a cikin wani farinciki da ya saka ni hawayen, mun raya daren kamar Annabinmu ya koyar da mu, wato da sallah da kuma abinci da sha, sauran abubuwan da suka biyo bayan wannan kuma ina tunanin kamar bana bukatar bayyana sirrin mijina domin sanannen abu ne da ba sai na fito duniya na fadi abun da ya faru ba. Sai dai na dandana kudata sosai a daren domin na sha gyara irin gyaran da ban yi zaton da gaske bayan macen ta haihu zata iya komawa budurwa ba, tabbar kayan Hajiya Aisha 08032350261 babu algus daman tun kamin lokacin na ji canji a jikina, fitsari ma idan na tafi da wahala nake yinsa, ita da kanta ta hana ni tarewa a lokacin da Abiey ya bukata a haka na cilasta masa daga tarewar har sai bayan an yi nadin sarautar da sati biyu, a gidan ta na karasa satin daya saboda na samu biyan bukata, wanda ke min dilka ma sai dai ta same ni a can ta yi min. Cikin satin uku na zama wata yar shala daman can ni din ba mai jiki bace balle kuma yanzu da jikin ya sha gyara kuma zuciya ta samu kwanciyar sai na kara kyau da haiba, kana kallona zaka san Amaryar babban mutum ce ni. Har yanzu kirjina ciwo yake min domin wahalar ta zo biyu yayen da na yi na Amir da ya daina shan nono tun a ranar da aka sallamo shi daga asibiti, saukina daya na sha kayan gyaran nonon da na siya a gurin Hajiya Aisha wanda ya kara maida nonon nawa a tsaye kamar daman can ban taba shayarwar ba, ciwonsu ya dawo min sabo a lokacin da na yi zaton Abiey zai tausaya min, ashe mugun kansa ne ta wannan bangaren da baya iya tausayina ko da na kwayar zarra, sai dai ba ni kadai na wahala ba har da shi. Har a yanzu ba zan ce na saba ba, duk kuwa da kasancewar ba wannan ne aurena na farko ba, amman wannan ne jarumin maza kuma gyaran da Hajiya Aisha ta yi min ya saka na fi jin azaba a yanzu fiye da can ma, domin Abiey ya zama tamkar karamin yaron da hausawa suke cewa ba a lasawa zuma a dan yatsa, shi yake ta shan rawar kafa baya barin na huta, sai dai ni na yi ta fama da wahalar. Karamin tawul ne a jikina da nake kokarin cirewa bayan na gama shafa mai na saka sabbin tufafin da lefen da Ammy ta hada min su da kanta, domin naki yarda mu tafi honeymoon kamar yadda ya bukata balle na hada lefen a can, ba dan kuma bana bukatar zuwan ba sai dan na san zuciyata ba zata iya jurewa ba idan aka daura aurensa da Yasmin yace zai tafi da ita kamar yadda ni ma ya tafi da ni. Bayan na saka tufafin na tsaya a gaban madubi ina kokarin saka dankunnen, ta cikin madubin na hango ya bude kofar dakin ya shigo, wani sako idanuwansa suke aiko nawa idanuwan ta jikin madubi, kamin murmushi ya samu muhalli a fuskata. Kasancewar dikin atamfar da na saka irin ta matan auren nan ce dake bayyana kafadu waje, sai ya dora bakinsa ya sumbanci kafar tawa ya sake sumbantar wuyana. “Good Morning Hiayatee” Na juyo na ya rika fuskarsa na sumbanci bakinsa. “Morning Love” Sai ya saka hannayensa ya zagaye kumkuruna da su yana shafa bayana zuwa mazauna na da dayan hannunsa, goshin ya hade da nawa cikin siffar da ke nuna daren jiya be wadace shi yake tambayar. “How was your night? Fada min kin yi mafarkina?” Ya sumbanci bakina. “To ai baka bar ni na yi bachi ba ma balle na yi mafarki” “Ah... Hiayatee na ban da sheri fa” Ya saka hannayensa ya dauke ni kamar yar baby ni kuma na saka nawa hannayen na zagaye wuyansa da su ina runtse ido. Falo ya fito da ni ya zarce dinning na yi zaton zai sauke akan kujerar da ya saba dora ni idan zamu karya ko kuma akan ciyarsa amman a yau sai ya dora akan dinning din yaja kujera a gabana ya zauna, ta gefena ya hada komai ya saka hannunsa yana dauka yana saka min baki idan na ci sau biyu sai ya ci sau daya. Hannu na mika zan dauki tissue sai yayi saurin rike hannun nawa. “Hey Princess wait your prince is here” Da kansa ya dauko tissues ya goge min baki, sannan ya bar ni na sauko dinning, da sauri ya mika hannunsa ya janyo ni na fado jikinsa sai ya rumgome. “Come hare fada min me zamu dafa da rana?” Na tabe baki a shagwabe na ce. “Zamu da fa kuma?” Ya ja zirin hancinta. “Yes dole ne mu koyi girki, Ammy tace ta gaji da ciyar da mu, ai ya kamata mu koya ko dan jawabin da ta yi mana ko?” “To waye zai koya mana?” “Mu zamu koya mana, ai akwai waya yanzu ina dawowa zamu fara” Na kara kwanta a kirjin da idan na rabe shi nake jin kamar an gafarta min zunubaina. “Ina zaka je” “Sauban ne yake nema, daman ke nake jiran ki farka mu yi breakfast sannan na fita” A take na yanayi ya canja, ko be fada min ba na san kiran Sauban ba zai wuce shirye shiryen da ake na aurensa da Yasmin da aka kusa daurawa ba. Fuskata ya girgiza min kai sannan ya hade bakina da nasa, sai da ya fara bawa lebena na kasa hakkinsa sannan ya bawa na saman. “Bana son ganin a tamfa a jikinki, har sai idan zaki fita ko kuma za mu baki, ko irin friday, amman bayan wannan na fi sha'awar ganin ko wane bangare na jikinki a waje, that's why na cika miki dayar wardrobe din da kananan kaya, ni ma'abokin sonsu ne, ina ko da yaushe na rika ganin cinyar matata ko kirjinta a waje, sai ban yarda ko bakin kofar falo ki leka ba, kuma mai sharar nan zarar ta gama mopping ki sallame ki rufe kofa i love you” Yana maganar ya sauke min zip din rigar atamfar, sosai ya sumbanci kirjina yayi wasa d shi, sannan ya rika hannuna na raka shi har bakin kofar falon, a nan sai da ya sake sumbatar ya jika min makoshi da yawunsa sannan ya bude kofar ya fita. Jugowa na yi na dawo na rasa abun da ke min dadi ban taba tunanin haka mace take ji idan mijinta yana da wata matar ba sai da na auri Abiey, ko da rana daya be taba waya da Yamin a cikin gidana ba, kuma be taba barin wata alama da zan san suna tare ba, amman hakan be hana ni kishinta ba, musamman a yanzu da na san dadin mijina. Zaunawa na yi ina kallon falon da aka murzawa naira gabas da yamma aka kawata ko'ina da manyan kaya an alfama da ake sakawa yayan manya. Sai dai sam hankali ba gurin kayan yake ba domin ba a yau na fara ganinsu ba, hankalina ya tafi a gurin auren da Mijina zai yi ne. Kamar ya san tunaninsa nake sai gashi ya dawo falon ya nufo inda nake zaune ya zauna kusa da ni yana kallona. “Na kasa tafiya saboda na lura kamar ranki a bace yake, gashi yanzu na tarar kina hawaye” Hannu na kai na taba fuskarka sai kuwa na ji sanyin hawayen da ban san da zubar su ba. Kwantar da ni yayi a kirjinsa yana shafa bayana, “Auren Yasmin ba zai canja komai daga kaunar da nake miki ba, bana son ki daga hankalinki matukar ba so kike ba tsabawa umarnin Mai Martaba ba” Kamar wata jaririya haka na lafe a jikinsa ina ta hawaye, fitar da be samu yi ba kenan sai dai ya kira Sauban a waya ya sanar masa ba zai samu fitowa ba. A tare muka girka jallon din kifi da kwai da kuma soyayyen nama kamar yadda ya fada, ta waya muke kallon yadda suke yi sai mu yi tare, bayan mun gama muka shiga bathroom yayi min wanka ni ma na sama sannan muka fito daure da tawul daya, wato ina cikin jikinsa skin dina na taba domin na juyo masa kirjina ns ya hadu da na shi na rumgume shi, shi kuma ya saka yawul din ya nade mana jikinmu gaba daya, muna tafiya kamar zamu fadi muka isa gaban madubin, a nan na raba jikina da na shi na dauki zane na daura na mika masa kafata da hannayena ya shafa min mai ya dauko kanan kaya mafi soyuwa a ransa ya saka min, wata yar karamar farar riga ce da bata kai cibiyata ba sai wani wando jean na mata mai kwalliya da shi ma be kai guiwata ba. Shi ma kanann kayan ya saka sannan ya riko hannuna muka dawo dinning din falo muka ci abinci. Ashe dai ni ma A ce a bangaren abinci domin jalof din ta yi dadi sosai ko da yake da kwabata ce ni kadai wata kila da ba zata ciwo ba. “Yayi dadi ko?” Ya daga min gira daya yana kai min lemu a baki. “Ai dole ta yi dadi, ni fa na girka, ko baki gane ba” Ya kashe min ido daya, cikin tsananin kunya na boye fuskata a kirjinsa ina dariya, sai ya aje spoon din hannunsa ya fara mitsintsikata wai sai na fada masa idan haka din ne ko aa. Da zamu kwanta na yi waya da Mama sai take fada min cewar Mr Bashir yana shirye shirye komawa Abuja da zama, sam ban jidadin hakan ba duk kuwa da kasancewar ban isa na hana hakan ba, sai dai na jidadin fada ma Mama da yayi a inda zai zauna a Abuja, koda be fada ba ma na san ba zai zamu rasa sani ba domin ba boyayen mutum ba ne. Ina son na tambayi labarin Dr Hamid amman ba dama domin Abiey ya canja min line kuma duk abubuwan nan da suka faru Dr Hamid be kira ni balle ya same ni mu yi magana, haka ma ban sake jin duriyar Jamila ba, ban san a inda take zaune a yanzu ba balle na kuma Dr Hamid, ko a ina yake yanzu a wane hali yake, ko ya samu labarin abun da ya faru Allah masani. [12/11, 4:28 PM] Oum_Nuwaira🥰: 7️⃣5️⃣ Hausawa suka ce an baro kyau tun ranar wanka. Domin wadansu hotunan auren Abiey da Yasmin da kuma shagulgulan da aka yi na tabbatar sun wuce ni, irin wucewar da ban iya na dawo da baya ba balle amaimaita min irinsu. Har aka yi shagulgulan bikin aka gama hankalin mijina yana kaina, nawa kuma yana gurin zaman da zai yi da Yasmin, a dare da aka kawo ta a matsayin abokiyar zamana kamar yadda Ammy take ta nanata min cewar kar na dauke ta a matsayin kishiya, na kasa rike kaina duk wanda zai kalleni ya san bana farinciki da auren, musamman ma mijina da ya kasance a tare da ni kamar ba shi ne angon ba. Duk wani abu da Abiey zai yi ya kwantar min da hankali yayi, ba ni da tabbacin zai iya adalci a tsaninmu har sai zamantakewarmu ta yi nisa, amman a ina ganin ido da nake masa a yanzu da kuma kyakkyawan zaton da zuciyata take masa ina ganin kamar ba zai iya cin amanata ba. Sai da aka fara kawo ta a gidana ta gaishe ni Ammy ta yi mana nasiha sannan aka fita da amarya zuwa gidan angonta, kaina na a kasa har sai da Ammy ta fita sannan na dago na dawo dakina sai na fadi kwance akan gado na fashe da irin kuka na bakinciki da damuwa marar misaltuwa, a ranar na ji kamar zuciyata zata fashe, duk irin soyayyar da nake yi ma Abiey sai ya rika ba ni haushi, wata zuciyar na raya min akan me zai hada soyayyata da ta wata, ban zauna da kishiya a gidan Deen ba, saboda haka ban zan zafin kishi da mace take ji ba, sai a yanzu da na hadu da ita a gidan mutumen da a fi kauna fiye da komai a rayuwata. Kuka sosai nake tun ina yin na hankali har ya fara fita ina ihu kamar zan tashi gida, a lokacin da mijina ya shigo ya same ni a wannan halin sai hankalinsa ya tashi, cikin damuwa ya rumgume ni, yana ta rarrashina da kalamai masu dadi, da kara tabbatar da kaunar da yake min. Har kusan goma na dare ina tare da mijina har sai da Sauban ya shigo ya fara fada a falon sannan Abiey ya sake ni ya fita bayan ya aje min kayan ciye ciye. Wallahi hauka ce kawai ban yi a daren ba domin na shiga damuwa da bakinciki marar misaltuwa, da zarar na motsa zuciyata ta raya min cewar Mijina yana tare da wata a yanzu sai na ji babu natsuwa da kwanciyar hankali a tare da ni, daker na ga safiya, ina sallah asuba zazzabi ya rufe ni, kanwarsa Aisha yar wajen Anty Amarya da ta kwana a gidan ce ta kira shi a waya ta sanar masa, sai gashi ya isa tun kan duhun asuba ya gama wayewa. Ina kwance ya yaye mayafin da na rufe da shi ya dago ni ya rumgume yana tambayar jikin nawa, kamin ya saka hannayensa yana buda idona. “Ba ki yi bachi ba” Ban isa na ce na yi bachin ba, domin idanuwana da suka kumbura saboda kukan da na sha ya nuna haka. “Jikinki da zafi sosai, tashi na dauko miki tufafi ki saka mu je asibiti” “Ba su fito ba yanzu” “Okay then bari na kai ki gurin Dr Zainab ta duba min ke” Ya sumbanci ni cike da kulawa, yadda ya fada haka muka yi, shi ya dauko min tufafi ya taimaka min na saka sannan muka fito ya saka ni a mota ya dauki hanyar gidansu yar'uwarsa. Kusan mu muka tashe su daga bachi ta taba jikin nawa ta rubuta masa maganin da zai siyo min sannan ta shirya mana abun karyawa, ba dan na so ba na ci kadan sannan na sha maganin na kwanta. Ko da na farka Abiey ba shi a gidan, sai wayata ya kira yayi min ya jiki bayan na gama karanta sakonsa. Sai da azahar ya dawo a gidan muka wuni a nan har dare a lokacin da yace zai dauke ni ya maida ni gida sai Labari ya canja domin bana bukatar zama a gidan a yanzu kasancewar ba shi a ciki. A dole ya hakura ya bar na kwana a gidan bayan Dr ta cilasta masa yin haka saboda tsoron kar na je can zazzabin ya sake dawowa. Ba laifi na samu bachi a nan domin mun dade muna hira da Dr ta rage min kewar mijina har sai da na fara jin bachi sannan na shiga daki na kwanta, the following day na koma gidan Ammy da zama bayan Dr ta fada mata abun da yake faruwa, sai dai zama a gidan Ammy sai ya fi min bakinciki fiye da zama a gidana domin sauran bakin da suka rage na biki da ba su tafi ba idan Abiey ya shigo sukan tsokane shi su ce masa ango hakan kuma yana min zafi sai nake ganin kamar da gayya suke min. Duk yadda Abiey ya zo na koma na cigaba da zama a gidan Ammy bata yarje masa ba, nima kuma hakan yayi min dadi domin bayan tafiyar bakin sai ya rage daga ni sai Ammy sai mai aikinta Jummai ne a gidan, idan zata yi girki ta kan kira ni na taya tana nuna min wasu abubuwan, tana fada min abubuwan da Abiey yake so da wandanda baya so, da kuma kalar abincin da mijina ya fi so, a dan zaman da na yi a gidan na kara karantar halin Ammy mace ce mai matukar saukin kai da kuma son zaman lafiya, domin a duk hirar da zamu yi zata ba ni labarin irin zaman lafiyar da suka yi da mahaifiyar Yasmin ne, da kuma yadda zan kwantar da hankalina kuma na nuna wa mijina yadda zai kwatanta adalci ko da ya kasa yin haka. A cikin abubuwan da Ammy take yawan nanata min akwai koyon girki da kuma rage yawan kukan da nake da duk wani abu da zai daga hankalin mijina, ta fada min da iya girki ta kara kwance Mai Martaba a lokacin da ta zauna a gidansa, hakan ya saka na darsa a zuciyata cewar ni ma zan koya ko da na kara samun damar murza kambuna na cikakkiyar mace, sannan ta fada min na rike kamshi daya, wanda zai rika tunawa mijina da ni a duk inda zai ji mai irin kamshi, har ya zamana ba shi dadin kamshi wani turaren mata sai nawa. Sai da Abiey ya cika sati daya cir a gidan Amaryarsa Yasmin sannan Ammy ta maida ni gidana, a ranar na zage damtse na gyara ko'ina na cikin gidana da kaina na cika ko'ina da kamshi na canja wasu abubuwan. Abiey na shigowa na danne duk wani zafin kishi da nake ji na rumgume shi ina masa maraba da zuwa, a falo muka fara shiriricewa sannan muka shiga daki, taya shi cire tufafin jikinsa, daga sunan raka shi bandaki sai ya janye ni muka yi wanka a tare, a can ma sai da muka shiririce sannan muka fito, shiga na yi mai kyau irin ta alfamar shi ma ya saka shadda sannan muka fito makalle da hannun juna, tsaye na yi har sai da ya bude min mota na shiga sannan ya zagaya ya shiga muka dauki hanyar gidan Amaryarsa, kamin mu isa ya bi ta shopping da ni na zaba mata turaruka masu kamshi da kyau sannan muka isa gidan. Na yi mamakin yadda ta tarbe ni a nan na lura ta fini wayo da kuma wayewa domin har ga Allah ni ba zan iya hadeye kishina na sakar mata fuska da jiki kamar yadda ta yi min ba. Amman sai gata tana jana da hira har da su dauko waya ta dauke mu hoto da Abiey sannan ta yi mana ni da ita daga karshe kuma ta dauke mu a tare gaba daya, da gangan na rike hannun Abiey na shiga dakunanta ina dubawa ita ma dai an narka mata dukiya, ko da yake ba abun mamaki ba ne domin yar manyan mutane ce ba kamar ni ba, hakan kuma be kara min komai ba sai kaunar Ammy wanda ta tsaya ta tsara min komai da na zo na tarar da shi a gidana. A falonta Abiey ya tambaye kwana nawa muke ganin zai yi mana a tsakaminmu, a karshe muka zabi kwana biyu biyu domin shi yafi dadi da kuma adalci, da zamu fito ta dauko wasu daga cikin kayanta na lefe ta yi min kyauta da su, Abiey ya rika min jakar muka shiga mota tana daga min hannu har muka fice. Isowarmu gida da kamar minti talatin ta kira number ta tambaye ni ko mun iso lafiya, na yi mamakin a inda ta samu number wayata sai Abiey ya warware min ta hanyar fada min da yayi cewar ta karbi number tun a shekaranjiya, har yake nanata min wai ban fada miki Yasmim bata kishinki ba yarinyar tana da hankali ai, a nan na gane wayayyiyar yarinya ce Abiey ya auro kuma idan ban tashi tsaye ba zata iya kwance min mijina. Daren mun kure junanmu da soyayyar da kuma kewar juna da muka yi na tsawon sati daya ba a tare. Kwana biyu yayi ya koma gurin Yasmin, hakan ya taimaka miki gurin gyara kaina na shiryawa shimfidar mijina kamin girkina ya dawo. Yasmin na cika sati biyu a gidan Abiey na shiga makarantar koyon girki, a nan na hadu da wata kawa mai kirki ashe ba ni kadai ce matar auren dake fama da rashin iya girki ba, wasu kuma yan mata ne da aka kawo su koyi kalolin girki kamin aurensu. A ka'idar koyon girkin wata uku ne, kuma kullum ake zuwa domin ko wace da kalar abun da ake girkawa, idan ka dawo gida zaka kara gwadawa ne, haka nima nake idan na dawo ranar abun da na koyo shi zamu ci domin shi zan girka. A haka kachar aka yi wata biyu da ni saboda laulayin da na fara, da farko na yi zaton ko nauyin jiki ne kawai saboda aikace aikacen da nake fama da shi a yanzu, sai dai ganin ina yawan Amai da kwadayi ya saka na fahimci laulayi ne, daman watan nan gaba daya ban ga al'adata ba, a gidan Deen ma sai da na yi wata uku sannan na samu ciki. Ranar da abun yayi min tsanani har Abiey ya fahimci haka, a asibiti muka wuni domin baya wasa da lafiyata. Daga Asibitin ya dauke ni muka biya a masarauta muka gaishe da Mai Martaba kuma muka duba Mama Lami da aka yi ma aikin ido. Daga ranar Abiey ya dauke min aikin komai, motsi mai karfi ma idan na yi sai yace babynsa, kamar akansa aka fara haibuwa. Yanayin wannan cikin yayi min kama da na farko domin laulayin kusan iri daya nake, hakan ya dawo min da tunanin ďana sosai a raina ina ta jin kewarsa har ta kai ko ruwa na sha sai na tuna da shi na tambaye kaina ko a wane hali yake a yanzu. Cikina na wata shida na yi ma Abiey zancen ina son naje na duba Amir a take na ga yanayin fuskarsa ya canja, kuma ya kasa amsa min da mu tafi din ko kar mu tafi, a madadin haka sai ya dauke ni muka tafi muka gaishe da Baba da Hajiya yayi musu alheri, ba laifi Baba ya dan sauko domin har godiya yayi da abun da Abiey yayi masa kuma ya saka mana albarka sai dai na lura Hajiya ko kallon fuskata bata son yi. A lokacin da cikina ya fara tsufa, sai abun ya zame ma Abiey biyu domin a lokacin ne Yasmin ta fara nata laulayin, gashi nata ya zo da wahala ba kamar nawa ba, domin ita har gida sai da aka maida ita saboda yawan rashin lafiyar da take. Wani gata da ban taba saka ran samu ba, shi ne haihuwa a wata kasar da ba mahaifata ba, domin ina daf da haihuwa aka shirya min komai ciki har da mutanen da za su rakani a England, a can na haihu kyakkyawan Saurayi bayan na yi awa uku ina nakuda, domin fara nakudata a tsaye ne tun a lokacin da na shiga watan haihuwa ta, sai dai a lokacin da haihuwar ta gabata gadan gadan sai na samu sauki taltalo ďana fari tas kyakkyawa. A ranar lashe ni ne kawai Abiey be yi ba, amman tsabar farinciki ni da shi duk sai da muka zubar da kwalla. Kwana na biyu a kasar ran na uku muka dawo Nigeria, a gidan Mama na sauka duk kuwa da kasancewar Ammy da Abiey ba su so haka ba. Na samu kyakkyawar kulawa a gurin mahaifiyata da kuma yan'uwanta ciki har da kanwarta wancce ta dawo da zama a gidan. Cikin rashin lafiyar Yasmin ta zo duba ďana tare da katon akwatin na barka da ta yi masa, a gaskiya na jidadi ko da a munafunce take nuna min sosai hakan ya faranta raina ballantana ma yadda na tabbatar babu wata zuciyata a zuciyarta domin a dan zaman da muka yi na fahimci haka har ina sha'awar a hade mu a tare. Daga ni har yaro mun ga fuskoki kala kala daga dangina har na Abiey, yan'uwana sun yi min kyauta daidai gwagwado hali, na Abiey kam ba a magana har rasa bakin godiya na yi. Ana sauran kwana biyu suna aka tafi da yaron gurin Mai Martaba ya gan shi ya saka masa albarka, da kuma Mama Lami wanda gani yayi wa karanci a yanzu duk kuwa da kasancewar an mata aikin idon kusan sau uku a maimakon ta samu lafiya sai abun ya kara lalacewa. Ranar suna yaro ya ci sunan Mai Martaba aka yi masa alkunya da Malik. Daga ni har shi mun ga gata irin wanda ban taba ayyana samunsa a rayuwata ba, kamin na cika arba jikina yayi kyau saboda kulawar da nake bashi da kuma kayan gyara jiki da gyara gado da na siya a gurin Hajiya Aisha. Arba'in dina da kwana sati daya aka soma shirye shiryen bikin Aisha wato yar Anty Ammy, Ammy da ni ce kirjin biki, domin Ammy ta zama kamar wata uwarta ni kuma na zama matar babban yaya duk da kasancewar ba ni ce kadai matar yayanta ba domin akwai manyan yayan Mai Martaba da matansu sai dai kasancewa da Abiey suke shiri hakan ya maida ni wata babba a gurinsu. Duk wata hidima da aka yi ta bikin da Aisha ba ayi ta da Yasmin ba domin cikin dake jikinta be barta ta samu lafiya ba har ta shiga watan haihuwarta, hankalinmu ya tashi matuka a lokacin da likiton suka tabbatar mana da cewar ba zata iya haihuwa yan biyun dake cikinta da kanta ba, daman can Abiey yayi mata bukin din asibitin da zata haihu a England domin shi ne adalci yayi mata kamar yadda yayi min. Ana sauran sati biyu edd dinta ya cika muka kwasa har da ni da Abiey da mahaifiyarta da wata yayarta da suke uwa daya muka tare a kasar, ashe wanda ba shi da shi ne yake mamakin idan an fada masa wani abun har ya karyata ko yayi mamaki domin na samu labarin yayan manya da kuma matan masu kudin da suke zo wa haihuwa a asibitin da aka yi ma kyakkyawar shaida. A lokacin na tabbatar da Yasmin ta yi gadon kirki a gurin mahaifiyarta ne domin da ita muke ta zancen, a hannunta Malik yake wuni idan na karbe shi sai idan nono zai sha ko kuma yayi bachi. Yasmin ta samu kyakkyawar kulawa daga gurina kuma hakan ya kara mana fahimtar juna da kuma kaunar junanmu, sai dai ashe sayyanar ta mu ba mai dadewa ba ce domin an fasa cikinta aka cire mana yan biyu duka mata masu rai da lafiya ita kuma ta kasa survived sai gawarta aka ba mu. A ranar mun ga tashin hankali domin mun samu rai biyu muka rasa daya, har na kan ina ma yayan muka rasa ita a bar mana ita, sai dai Allah baya barin wani dan wani haka kuma ya tsata abun da zai faru tun ranar gini tun ranar zane. Ni da Abiey aka rasa wanda ya fi sonta da kewarta, na dauki yaran da suka ci sunan Nimra da Namra wato sunan mahaifiyarta da kuma na Ammy na da da Malik ina shayarwa, abun nan is not easy amman a haka na yi ta dawainiya da su ana hada musu da madara har suka isa yaye na yaye su. Wata rana na saka yara a gaba muka tafi gidan Dr a gidan muka wuni, na kwance mata cikina na son sanin halin da ďana Amir yake ciki, domin idan na yi ma Abiey maganar sai ya nuna min bacin ransa, sam baya son maganar Amir har cewa yake baya son ina masa maganar abun da ya shafi Deen. “Ni ma ba ni da labarinsu a yanzu, domin Dr Hamid ya yanke alaka da ni, ya daina aiki a asibitin da nake aiki a yanzu, kwana kin baya ma na ji ance yayi gobara har ya rasa yarsa daya, amman dai zan bincika na ji” Na sauke Nimra daga cinyata ina kallonta. “Amman kina ganin zai fada miki? Bayan Mr Bashir ya rabu da kanwarsa ko kuma ya maida ta ne?” “Be maida ta ba, ai ba gurin Dr Hamid zan bincika ba, zan tuntubi Mr Bashir din ne da kaina domin har yanzu muna da contact din juna, sai dai mun dade ba mu yi magana ba” Tana rufe baki ta dauko wayarta ta duba numbersa. “Allah sarki...” Ta fada sannan ta miko min wayarta, hoton Amir ne a dp Mr Bashir din, rabin kamanin fuskarsa na fuskata ne, a yayinda rabin kuma ya so ya dauko Deen kuma be yi kama da Deen din sosai ba. A take na cire hoton na turawa kaina ina sharce kwalla. A daren na kwana da begen ďana na yi kuka sosai kukan da ban san na me zan kira shi ba, tausayin ďana ko tausayin kaina ko kuma na kaunarsa, ko na rashinsa a kusa da ni, a yanzu na fi jin kaunar Amir fiye da da, duk kuwa da kasancewar a yanzu ina da wasu yayan da za su cire min kewarsa, ina ta kallon hoton da aka yi masa tare da yayan turawa yana sanye da kayan sanyi an rufe masa jiki ruf. Washe gari bayan mun karya nake nunawa Abiey hotonsa ina murmushi hawaye na kwaranya daga idona. Sai ya ki karbar wayar a take yanayinsa ya canja. “Duk damuwar da zaki shiga bata kai wanda iyayensa Deen za su shiga ba, domin su sun rasa ďa kuma ba su da jikan da za su rika kallo a matsayin ďanta” Na share hawayen. “Abban Malik ai su ba su san Amir a matsayin jikansu ba, saboda ba su san zafin rashinsa ba, amman ni na sani domin na zauna da shi na shayar da shi dole na san zafin rashinsa” A lokacin ne Abiey ya kalli kwayar idona yayi min wani kalami marar dadin ji. “Zahra baki da godiyar Allah, duk kyautar nan da yayi miki baki gode ba sai kin daga hankalinki a kan wani abu can dabam? Hakan yana kara tabbatar min da cewar kina son Deen har gobe” Na girgiza kai da sauri. “Ina dai son ďana kuma ina tausayinsa” Mikewa yayi tsaye ya saka hannu ya dauki ďansa Malik ya fice daga falon zuwa harabar gida, share hawayena na yi na mike tsaye na bi bayansa sai na tsame shi tsaye yana rike da hannayen Malik yana sumbata, na risina a hankali na kwantar da kaina a bayansa. “I Love My Son” “I Love You so Much Abban Malik” Na tari numfashinsa a lokacin da yake furtawa ďansa cewar yana kaunarsa, sai ya juyo ya kalleni ya sumbanci goshina. “I love you too, je ki dauko min Twins” Na mike tsaye na dawo falon na janye plate din da suke rigima akansa na goge musu hannayensu na fito da su waje, sai ya hade su su ukun yana wasa da su, ni kam ina tsaye gefe ina kallo kamin na fara shigarwa Twins har muka yi winning shi da ďansa suka fadi. Tun daga ranar sai na tattara lamarin Amir na aje gefe, ba dan bana kaunar ďana ba sai dan na lura kamar maganarsa ko nuna damuwa akansa ya kan haifar da matsala tsakanina da mijina, sai dai a kullum kaunarsa karuwa take a raina, har ta kai wani lokacin idan ina tsaka da tunaninsa na kan kira Malik da sunan Amir, idan Abiey ya ji ranar ba za mu kwana cikin dadin rai ba. Sai dai na kwana ni kaina shi kuma ya kwana da yaransa. Kauna da shakuwa ta shiga tsakaninmu sosai da Twins wato Nimra da Namra, har ta kai wani lokacin idan zan fita sai dai na fita da su na bar Malik a gida, ko na yi musu abu na kyale Malik, idan Abiey ya gani sai yace ai daman ba son ďansa na ke ba, mutane har basa sanin ba ni ce mahaifiyarsu ba sai wanda ya sani. Tun bayan haihuwar Malik sai haihuwar ta yi min shiru sai da Malik yayi wayo sosai sannan na sake haihuwar Mace. Rayuwa ta ci gaba da tafiya kamar yadda na dade ina mafarkin ta kasance a gareni, wato cikin kwanciyar hankali da farinciki, ga yarana sai tasawa suke, soyayya tsakanina da mijina kuma kamar domin mu kawai aka hallicce ta, ba ni da wata matsala ta rayuwa a yanzu, soyayya dama da hagu, ba ta bangaren Ammy ba ba ta gurin Momy ba wato mahaifiyar Yasmin ba kuma ta bangaren Mai Martaba ba, ga kuma Mahaifiyata a gafe. A ranar da Dr ta turo min video da hotunan Amir da Mr Bashir ya turo mata na sha kuka har na gode Allah, sai dai na jidadi sosai sanin cewar ďana yana cikin farinciki da kwanciyar hankali kuma a gurin da zai samu ingantacciyar rayuwa da tarbiya mai kyau. A gurina Baba ya cancanci alheri domin ko ba ya rike mu har girmanmu kuma ya aurarda mu, saboda haka shi ma ya cancanci cin alfarmata, hakan ya saka na biya masa kujerar makka a shekarar da Abiey yayi rabon na sa kujerun ga yan'uwanshi da nawa, mun kusan sati muna fada da juna saboda abin da na yi, a tunaninsa ina kyautatawa Baba ne saboda yana mahaifin Deen, shi kuma a gurinsa ba shi da babba makiyi kamar shi. Baba ya ji dadi sosai yayi ta godiya yana nuna rashin jindadinsa akan abubuwan da suka faru, a sirrance na siya masa wani gidan a makwafin gidansa da aka rusa a wacan lokacin na baya, ta dalilin abun da na yi masa ya dawo yana neman yafiyar Mama har ya share dattin dake tsakaninsu zamansu ya dawo da jindadi fiye da baya. *** *** *** Bayan wadansu shekaru...! A yanzu na gane iyayenmu sun sha wahala na rayuwa da mu, domin tarbiya yara ba abu ne mai sauki ba ko bari bari kawai ya isheka. Ina risine ina sakawa Mahmud safa Abban Malik ya shigo sai da ya fara kaiwa bayana duka sannan ya zauna ina gama saka masa safar ya janyo ni na fado jikinsa. “Hiayatee ki daina zancen bude gidan abincin da kike a nan” Na gyara zamana a jikinsa ina taba hancinsa na ce. “Saboda me?” “Saboda za mu koma Abuja da zama, sai ki bude a can” “Abuja kuma?” “Yes Mai Martaba ya bukaci haka, saboda kula da abubuwansa da suke can, ni kuma i can't say no” Kwantawa na yi jikinsa a shagwabe na ce. “Na saba da nan fa Abiey na” Na mitsike cikina. “Can din ma ai sabawa zaki yi da mutane” “Ni dai gaskiya aa, sai dai ka rika zuwa kana dawowa” “Aa ba wannan maganar sai dai na kwashe yarana na tafi da su, na bar ki a nan ke kadai idan na samu wata yar shala a can na aureta...” A take na saka hannu na cire hular kansa na jefar na kama kan nashi na kasa a murkushe. “Ka ma isa, ai Wallahi daga ni ba kari” “Inji wa? Na yi alkawari da ke?” “Kana auro wata zan maka hauka, na tashi hankalinka” “Ni fa yanzu na gama dake, ba dai kin haifa min carbon copy ba?” Na yi fuska, sai ya fara kyalkyalata har sai da na yi dariya. “Wasa fa nake, ni na isa na hada Zahra da kishiya? Ke da yayan na ki ai ba za ku bar kishiya ta jidadin zama ba, shiyasa idan mata suka min signal na ke ce musu ni fa na auru tace bata son kishiya” Ban san lokacin da dariya ta subuce min ba, na rumgume shi, shi ma dariyar yayi ya shafa bayana. “I love you so much Hiayatee” “I love you more Zauji” Na dago fuskata sai ya hade bakinsa da nawa... _______________________________ THAMMAT BI HAMDILLAH 😍🙏 Na gode Allah da ya ara min lokaci na kawo yanzu, zan yi amfani da wannan damar na nemi yafiyar wadanda na batawa, ayi hakuri a dubi rahmar Allah da jikansa ayi min afuwa. Ina fatar Allah ya yafe mana gaba daya ya hada mu akarkashin inuwar Al'arshensa tare da Manzonsa masoyinmu Annabi Muhammd Sallalahu Alaihi Wassalam Idan kika karanta littafin nan ba tare da kin biya ni ba ki sani kina da hakki akanki pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008. And send the evidence of payment to 08036126660