[10/2, 5:43 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 Luv story😍 By *Salmerh MD* 💫 *DA BAZAR MU* *WRITER'S ASS* 💫 We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all....... *DA BAZAR* *MU MUKE* *TUN'KAHO.* Dedicated to *Safiyya Aliyu wakili* (Masoyiyar asali)... marubuciyar *MASAUQIN SO* da *SHI NAKE JIRAH* ....on point....... Allah ubangiji ya saka miki da mafificin alkhairi (AMEEN SUMMA AMEEN)👏🏻 *Bismillahir* *rahmanir raheem* Littafin Captain Abbas ba na ku'di bane, kuma ni.ban ce asiyar ko asiya ba duk kuwanda yayi kuskuran aikata hakan toh yaci da gumina kuma na bar ahi da fitowar rana da fa'duwansa. 🅿1 'Yan makaranta naga suke ta wucewa da alamar tashin su kenan daga makarantar, daya ke yara qanana ne shiyasa mafi yawancinsu kafin ma su tashi ake zuwa zaman jiran daukan su, wanda inka duba zaka ga motoci ne awurin suka fi yawa sai da tsirarun 'yan adaidaita, wasu kuwa daba nisa ne dasu ba sae suke qarasawa da qafafunsu da alamar sun riga sun gane hanyar gidan dakansu basai anmusu jagora ba, kadan daga cikinsu kuwa musamman ake xuwa dan aqarasa dasu gida koda qafan ne ,hakan yana nuni dacewa ba'a so ne suka mo hanyar gidan su kadai...... Wata yarinya ce nagani atsaye bazata wuce shekara takwas ba,tsaye take da lunching box din ta kalar pink mai kyau ahannu..... Atsayenta ta ke bata da alamar motsawa ko ina ga dukkan alamu itama jira take azo atafi da ita gida, Har yara sun fara watsewa sae kuwa naga wani kyakykyawan yaro matashi ne wanda bazai haura 15 yrs ba yazo tabayanta ahankali ya lalla6o karab yarufe mata idanu, Kokadan banga alamar razana atattare da ita ba sai ma dan dariya data yi irin nasu na yara. sannan tadago hannun daman ta ta saita hannun daya rufe mata idon dashi ta sa ke mar mintsini mai shiga jiki take ya bude mata idanun sannan yafara yarfe hannu Kai , kai, kai "Haba ke kuwa dan Allah yafada kamar zaiyi kuka. Dariya tafara yi masa tana qara kallonshi. "Gaskiya yarinyar nan muguntarki ta shahara Wama ya koya miki irin wannan abin ne dan Allah." Ya fada yana qara kallon cikin idanunta Da alamar mintsinin yashige shi sosai Kamo hannunta yayi daniyar su fara tafiya,zuwa gida don yasan daman bayaga dariyan toh ba magana zata sake yimar ba Al'adarta kenan ita inde tamar mugunta toh sae de tayita dariya amma ko me zai fada bata ta6a bashi amsar maganrsa Mu wuce gida toh" yace da ita Na kusan yin maganinki ae badae ni kike rainawa ba. ah ah yayah Bakai ne karufe min ido ba" sai yanzun ta budi baki tayi magana tana me turo bakin gaba Toh dan na rufe miki ido sae akace kuma ki gutsure min fatata? Kalli fah yanda kika yimin! fuskar tausayi tayi dan ganin gurin yayi jaa sosai Sorry yayah bazan sa ke ba!! Kima sake kiga wanda zai ringa dawo da ke gida. Yitayi kamar zatayi kuka,ta tsaya da tafiyar Miye kuma ya faru? Bakai bane? Toh yi haquri taho abinki daddy's angel kinga yau akwai rana,muyi sauri muje gida kar rana ya dafa mu. Tafiya tafara ahankali ganin hakan yasa shi yah qara kamo hannunta tare da kar6ar lunchbox din dake hannunta Nace kiyi sauri wannan ranar fah tafara damuna. Wae ma ni kekam da ba ke kadai kike dawowa bane? Wato dan nazo sau daya na rakaki gida kuma shikenan kema kika daena tahowa dakanki ko? Zanyi maganinki ae yarinyah kwanan nan....... Bata kula maganar daya ke yi mata ba. Sai ji yayi tafara cewa yauwa yayah yau apple xaka siyamin tana fada tana tsalle irin na farin cikinnan tana kuma nuna mai teburin fruit din dayake junction din shiga unguwar tasu. Ke nifah yau banfitoh da kudi ba...... Take kuwa tafara kuka tana mar ihun ita kam dole sai ya siya mata bai kulata ba suka cigaba da tafiyah. Aikuwa suna zuwa daidai gurin mai kayan fruits din ta kwace hannaunta daga cikin nasa ta qi wuce wa takafe awurin tana kwa6a fuska..... Yasan ko mai zai ce da ita ba yadda zatayi ta bishi batare da ta ga abinda takeso din ahannunta ba. "Maiyah" yace qasa qasa sannan yawuce wurin mai fruits din ya kar6o mata aleda sunkai guda biyar akan anjima zai kawo masa kudin. Dayake sun saba da mai fruits dinma sosai so bashida matsala da yaran yasan kudinsa zasu zo cas ba ragi shiyasa bai damu ba daman kullum idan akazo daidai mai fruits din zakaga ta fara tsalle tana fadin abinda takeso asiya mata Wataran tace pineapple,wataran watermelon,wataran kuma tace babana,ko kuma apple kamar yanda tayi nayau kenan. Lemu ne kadae bata sha ita kwata kwata bata sonshi ma kokadan. Kuma kullum Indai suka zo wucewa sai ya siya mata abinda yake ao din inkuwa bae siyaba toh kuwa zai sha rigima sosai aranar Sallama yayi apalourn kafin yatura qofar yashiga,ganin bakowa apalourn yasashi zama akan two seatern dake cikin palourn. Ita kuwa ciki ta wuce dagudunta uniform kawai tacire ko kaya bata saka ba tasake fitowa da sauri ta nufi ledar da apple dinnata ke ciki. Bai lura da ita ba harse data dau ledar tanufi kitchen kafin ya hango ta "Teemah" Yace da qarfi Na'am ta amsa mai Yayah wankewa zanyi neh a kitchen" Ta tafada mar dan ita azatonta akai ne yake qiran nata. Dawo nan Yafada tare da miqewa xaune" Dawowa tayi da ledar ahannunta tazo gabanshi ta tsaya Hannu yasa ya kar6i ledar ya ajiyeh agefensa sannan yadaga hannu yakamo kunnanta daya "Stubborn girl kike so ki zama ko" Kuka zata fara Ya daka mata tsawa " oyah jeki sa kaya my friend" yafada sannan ya sake mata kunnan nata. Ban hanaki zama da pant ba ne acikin gida? Wuche kije kisa kaya ni inbahaka ba zanga mai baki apple din ai. Yarinya sai rashin jin tsiyah" Dakuka tajuya dakin nata, taje tasako wata riga mara kauri iya gwiwanta tafito Duk ta qagu taganta tanashan apple dinta . Tana shigowa sae kuma ga fanni (house maid) dinsu ce itama tashigo.Kusan sa'ar sa ce itama amma zata dan girme masa kadan "Fanni kunna min AC pls." Yafada da dan guntun tsuka da alama zafi Ya ishesa sosai. Ha 'ah kun iso kenan? Matar dake shigowa ta wata qofah daban ta ke fadi Ehh mundawo mummy tun dazu ma" Matashin yaron ne yabata amsar maganar tata Murmushi tayi Sannan tace ai kuwa najiyo hayaniyar ku dazu ina shirin tada sallah ne shiyasa ban fito ba ehh nida wannan mara jin ne ai yafada yana kallonta. ita kuwa ko ajikinta sai faman kokuwa ta ke yi da apple din dake gabanta. Toh yau din kuma za aji kanku kenan" ceawr mummyn nasu sannan taqara da cewa "Yanaga hannunka kamar ciwo yayi ja. Kallon Teemar yayi yaga ko ajikinta kamar bada ita ake maganar bama. Bugewa nayi mummy Ayyah sannu Abbas" Shiga dakina akan mirror inaga akwai man zafi Kasamu kashafa awurin da wuri. Toh mummy. Yace da ita.... Sannan yamiqe daniyar zuwa dauko maganin Bayan fitarsa ne mummy tadawo da kallonta ga Teeman tace da ita "yau Teemah ko kulani ma bazakiyi bako kinsamu apple ya dauke miki hankali" Dagudu ta taso tazo ga mummyn tana da dariya dan zuwa yanzu taci iya wanda zata iya ci daga ciki kuma ya isheta,daya da rabi ta cinye rabin kuwa sanda mummy ta mata magana ne ta ajiyeshi ta taho gareta Qoqarin hawa jikin mummyn ta ke yi mummyn ta dakatar da ita da fadin "a' a dakata daganan mamana bakiga hannunki bane" Maza jeki fanni ta watsa miki ruwa sae ki zo ina jiranki kinji " Da gudunta tafita ta nufi wurin fannin" Dai dai nan shima ya dawo dakin yana me qarasa shafa maganin ahannunsa Zama yayi a inda yatashi dazu Yarinyan nan akwai rigima mummy...... Wani abin tamaka ko? Mummyn tafada tana me tattaro hankalinta garesa Nan yabata labarin abinda Ya faru dazu awajen me kayan fruits suka danyi dariya dukkansu. Shiyasa ai naga ta nutsu ta bata hankalinta akai Ashe rigima tayi akai sosai. Inka ci abinci sai ka zo ka miqa masa kudin nasa. Uhmm barin ci abinci tukunna. Abbas din yafda sannan ya miqe ya nufi daining side ya dibi abincin dai dai yanda xai iya ci,ko takanta bai bi Dan yasan tunda tasha wannan abin toh ba qara waiwayan abinci zatayi ba. *Wannan kenan* 👌🏻 *Interested* ?🤔 *Pls keep following* *me* ......... Akwai cakwakiyah fah agaba😃 *Salmerh md* 😍 [10/2, 5:48 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 💫 *DA BAZARMU* *WRITER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all........ *DAZARMU* *MUKE TUN 'KAHO* Luv story😍 By *Salmerh md* *Alhamdulillah* !, masoya. *CAPTAIN* *ABBAS* haqiqa naji dadin yanda kuka nuna soyayyar ku ga wannan littafin.hakan yasani matuqar farin ciki marar misaltuwa........kusani in sha Allahu *ana tare* 🤝 *HAPPY JUMMA'AT* *2 ALL MUSLIMS* 👏🏻 *Bismillahirah manir* *raheem* 🅿 *2* Mintina goma ya dauka agurin cin abincin,cak ya miqe tsaye Dakinsa ya shiga ya watso ruwa yayi sallah Sannan yayi zaman shirya jikinsa da kyau. Abbas yaro ne shi amma sam bashi da wauta ko hayaniya irinta yarintan nan anatse yake komansa kamar wani babba. Haka idan yayi gayu har mamaki zai baka don irin yadda ya iyah zama ya gyara jikinsa tsab kamar bashi ba. Fitowa yayi da niyar zuwa gurin mummy,sai kuma yaganta a parlour tana kallon wani hausa movie. Mummy dake zaune acikin parlourn kallon inda taji motsin tafiya tayi,sarai tasan Abbas ne dan jiyo irin qanshin turaren dayake amfani dashi da tayi. murmushi ne ya su6ce mata sanda ya bayyan aidanunta Aranta ta ke jinjina irin tsabta da kula da kai da Abbas din yake dashi. Qaraso wa yayicikin parlourn amma tunkafin yayi magana sai mummyn tariga shi dacewa "harka shirya kenan" Murmushi yayi mata batare dayayi magana ba. 'Karaso wa yayi ya zauna agefenta Sannan yace "barka da hutawa mummy" Amsa masa tayi da "yauwa dan albarka" Sannan tajeho masa tambaya tana qara kallon inda yake zaunen daga gefenta. "Yanzu zaka miqa kudin mai fruits dinne?" Kai Abbas din yadaga mata alamar "ehh" cewa tayi "Bari toh na dauko maka kudin " tana fada ta miqe ta nufi bedroom dinta 2k takawo ta miqa masa.tare da zama a inda ta tashi dazu Abbas. Bai kar6i kudin ba illah dariyah yayi kadan sannan yace "Mummy inaga fah bazai wuce 1k ba kudin, dakyar ma inzai kai. Cewa tayi kar6i de nikam Abbas ka kaimasa,idan kuma kaje da 1k din shikuma yace bai isa bafah, cewa yayi da ita "zai ma isa mummy " Sa ke miqa masa kudin tayi tana fadin "ungo kaje Abbas bana son musu" Kar6a yayi sannan ya juya ya fita yana fadin "sai na dawo mummy" "Uhm" kawai tace dashi sa nnan ta maida idonta taci gaba da kallon data keyi a television. Teemah kuwa nacan bacci ne ma yadauke ta bayan fanni tamata wanka,kafin ta ahafa mata mai sai bacci ya dauke ta,ganin hakan fanni tasa ka mata pant kawai tabarta,adakin tafito taci gaba da ayyukanta. ,3:00 dot tatashi abaccin, dayake ranar alhamis ce, ba islamiyah, shiyasa babu wanda ya damu da baccin datayin. Tana tashi kuwa dakin mummy ta fara zuwa da kwa6a66an fuskarta irin na yarinta da kuma yanayin bacci. Tura qofar tayi tashiga,gani tayi bakowa adakin,amma jin motsin ruwa abayin yasata gane cewa mummyn nata bayi ta shiga,hakan yasa ta nufi bakin gadon mummyn ta dora kanta akai,amma 'kafafunta suna a qasa. Tsawon minti biyar mummyn ta qara sannan ta fito daga bayin,ganin Teemahr ahaka yasa ta taho gareta Mummy Zama tayi abakin gadon itama sannan ta ce "ya akayi ne 'yan mata" Ta fadi tare da dago kan teemar ta tsayar da ita. lumshashshun idanunta ta sau'ke akan na mummyn batare da tayi magana ba. Ganin hakan yasa mummyn ta kama hannunta ta koma da ita bayin ta sake watsa mata ruwa dan ta warware daga baccin da tayin. Tare suka fito da mummyn Amma sai ita mummyn tawuce gaban madubi ta zauna akan dressing stool da niyyan yin shafa. Gani tayi Teemar still tana tsaye, "Ke baki da kunya ne kam da kika tsaya ahakan din" mummyn tace da ita da dan tsawa kadan "Maza jeki fanni tasa miki kayanki sai kidawo"mummyn tasake fada mata amma wannan karon idonta naga shafa man data keyi ne. Pant din data cire shita dauka ta mayar jikinta sannan ta nufo inda mummyn ta ke ahankali, Jikin mummy taje ta dora kanta a bayanta, mummyn bata kulata ba itama ta ci gaba da abinda takeyi,sai bayan tagama ne zata miqe sannan ta sa hannu ta jawo ta gabanta Kallon fuskar ta mummyn tayi da kyau sannan tace "wai ni yau me ke damunki mamana"? Bude baki teeman ta yi tace "Daddy! " Mummyn kallonta tasakeyi tare da fadin "me kuma daddyn yayi"? Kwa6ah fuska Teema tayi tare da turo baki kamar anmata wani abin ne Ganin hakan da mummyn tayi yasa ta fadin "tsaya toh bari idan na shirya sai in qira miki shi. Kai Teeman tadaga alamar toh "Maza kema jeki wajen Fanni kice tasaka miki kayanki, Inyaso sai ki dawo inqira miki shidin kinji mamana" mummy ne yi wannan maganar alokacin data duba kayan dazata dauko. Teema yi tayi kamar bataji abinda mummyn tace da ita ba. Wata super exclusive atampa mummyn tadauko mai kalar ganye da zanen yellow yellow ajiki,baqaramar kar6arta kayan suka yi ba,tana gama shiri takamo hannun Teema tare daukan wayarta suka fito parlour, ahanyan zuwan ta ke cewa "bakijin magana ko Teemah? So kike Abbas yayi fishi yadaina rakaki school ko? sai yanzu Teemah ta 6udi baki tace "a'a mummy zanfara jin magana", "Karki fada mishi kinji mummy" Murmushi kawai mummyn tamata, tunkan su qaraso mummy tafara kwalla qiran fanni,bakinta biyu ana ukun fanni ta amsa tare da nufowa parlourn da hanzarinta. Atare suka iso cikin parlourn da fanni "Gani hajiya" Fannin ta fada tana mai risinar da kanta Mummyn na shirin zama tace da fannin "Don allah taimakeni da kayan yarinyar nan,yau rigima ta ke ji dashi" "Toh hajiya" Fannin tace tare da juyawa dan dauko abinda hajiyar ta umarce ta Mummyn ne taqara fadin "kinga fanni harda man shafar ta ki dauko min pls" "Uhm" fannin tace sannan taci gaba da tafiyah Mummy wayarta tadago tayi dialling number din Daddy Sallama tayi bayan yadauki qiran Shima daddyn ya masa mata "Yah akayi ne uwar gida? Lpy lau" Cewar mummyn sannan ta ciga ba dafadin "Wannan qiran bana wa bane alhaji na angel dinka neh." Cewa daddyn yayi "ahh toh bata mana " "Ina take "? Yasake Fada ! Teemah da tun da taji muryar daddynta ta matso da sauri kamar ba wacce ta ke ta kwa6a fuska dazu ba. Kallonta mummy tayi taga yanda ta warware daga sakalcin data ke yimata dazu. "Ungo mummyn ta ce da ita" Dawuri ta kar6a sannan taja gefe ta zauna akan wata kujerar daban dan nesa da mummyn,sannan ta dago wayar ta qara akunnenta. "Daddy" tace da farin ciki afuskarta cewa yayi "na'am mamana"! " yah school? "tace lafiya daddy " "Yauwa mamana kina karatu ko? Kai ta daga alamar ehh Daddy yaushe zaka dawo ? Cemata yayi "very soon angel zan dawo" "kin ci abinci ko? Ya tambayeta Cemasa tayi " a'a daddy apple naci! Yayah ne ya siyamin ahanyar school dinmu. yace "Gaskiya yayah ya kyauta. Abincin fah ? "Shima zanci" cewa yayi "Toh je kici abincin sai muyi awayar ajima ko " Toh "tace masa Sannan ta tashi ta kawo wa mummy wayar Akunne mummyn tasa ka Anan daddyn yake tambayarta ina Abbas dinfah. Dan dariyah tayi sannan ta bashi labarin abinda ya faru briefly,taqarashe da cewa Abbas yakai kudin mai fruits dinne. Cewa daddyn yayi idan "Abbas din yazo ta qirashi anjima. Daga nan sukayi sallama kowa ya ajiye wayar. Mummy kallon Teema tayi sannan tace iya fitinar dama kenan.? Dariya kadan teemah tayi sannan tace "mummy ina yayah yake " "Ya kai kudin bashin da kika sa yaci....! Amsar kenan da mummy ta bata. Toh dayake bawani fahimta tayi ba hakan yasa tayi shiru bata qara magana ba. mummy Kallon kayan dake ajiye agefenta tayi sannan ta ce "Oyah zoki saka kayanki" Tun dazu takawo lokacin kina waya" Matsowa teema tayi kusa da mummyn. Mai mummy tafara shafa mata sannan tasa mata kayanta pink din riga da wandon jeans mai kyaun gaske,sosai kayan ya kar6i jikinta. Mummy tana gama shiryata ta miqe tace bari taje tayi sallar la'asar. Tafiya tayi tabar Teemah tan game da wayarta awurin,koda mummyn ta idar ma bata sauqo dawuri ba can tayi zamanta adakinta. Abbas ma sai da yayi sallah a masallaci kafin ya shigo gidan,aparlour ya taddata tana ta game abinta,koda yayi sallama ma batasan yayi saboda hankalinta yadauku a game din datakeyi din. Zuwa yayi ta bayanta ahankali ya kwace wayar Sai sannan tadaga kanta da sauri ta juya bayanta Tana gani. Shi ne kuwa ta taso da gudu tazagayo inda yake,kafin ta iso shikuma yafara jada baya- baya ,itama sai ta biyo shi,guje guje suka farayi yanata mata dariya,ita kuma kamar zatayi kuka tanata binshi akan sai ya bata wayar wai,dayagaji da gudun sai ya zauna akan kujera yana dariyah,zuwa tayi itama inda yake din tana cewa " yayah ni kabani " ta ke masa qafa tayi Dayaji zafi yace "wash" Ke tsaya ni kin karyan yatsu" Baya ta matsa kadan tana qare masa kallo "Ungo "ya ce tare da miqa mata wayar " Bata kar6a ba itama sai tsugunan datayi awurin qafar tasa inda hannunsa yake yana shafa qafar,nan itama takai hannunta ta daura akan hannun nasa, "Sorry yayah" Tafada kamar zatayi kuka, shikenan ai yahuche ,ya daina zafin" Haka yace da ita, Don yadda yaga tayi yau din yabasa mamaki,bahaka tasaba yi masa ba musamman idan tasan ta mai mugunta,dariyah take qara binsa dashi,amma yau harda cewa "sorry" datayi hakan sai yaji tabasa tausayi. Abbas akwai sa haquri sosai,bai fiya yin fushi ba akan abu.yakan bi komai ne da murmushi koda na 6acin rai ne,gashi akwai tausayi. Ita kuwa Teema "sorry" data fada mar, tafada ne dan tsorotan datayi ganin yanayin fuskarsa,dukda wayo bai isheta ba amma tafahimci cewa yaji zafi sosai,kuma gashi bada niyyan mugunta ta takasanba.......arashin sani ne.shiyasa ta ce sorry. Shikuma abbas ganin tayi hakan yasa shi daure wa yace mata yadaina jin zafinma,duk da azahiri bawai yadaina ji din bane. Jin yace yadaina yasata danji dadi. "Kinci abinci kuwa? abbas ya tambayeta Jijjiga kai tayi Alamar a'a "Oyah muje kici abinci" Yana fada ya miqe tsaye Teema kuwa niqe kai tayi gefe. Ganin hakan datayi yasan bata da niyyan ci dinne. Shiyasa yace "Tashi kinji haba angel din daddy" Still batah kula shiba. "Tashi muje inbaki abaki" Yafada tareda riqo hannunta, Tashi tayi tabiyo shi suka nufi dinning din. Haka yadinga bata abaki ita kuma tana bashi labarin cewa wai tayi waya da daddy dazu" "Cewa yayi tayi shiru tukunna bakyau surutu in ana cin abinci, insun gama sai ta bashi labarin. Shirun tayi kuwa ,shikuma yaci gaba da bata abaki. Suna zaune awurin mummy tasauqo itama,dayake dama tasan sun saba hakan shiyasa bata kulasu ba.illah tambayar teema datayi wayarta.Don mafi yawancin lokuta teemah bata yadda taci abinci dakanta,musamman in rigimarta ta tashi,sai dai abbas yabata abaki,inkuwa bahaka ba toh sai de tayi zamanta batare da taci abincin ba,randa taga dama kuma dakanta take cin abinta. Abbas ne ya miqawa mummy wayar dayake ahannunsa ta ke. Sannan yace "mummy kinga abinda nafada miki ko? Yafada yana dan darawa, "Meyafaru? Tatambayesa. #800 kawai yakar6a mai fruts din" Yafada yana qoqarin ciro ragowar canjin daga aljihunsa, Juywa tayi tafar tafiya. Cewa yayi" mummy ga canjin" Ka ajiye akwai gobe ai.mummyn tafada batare data juyoba. Murmushi yayi sannan yakoma yazauna.daman yasan sarai mummy ba kar6ar kudin zatayi ba. Ahankali yace "dauko hijab dinki muje mu sayo choculate." Ai tanajin haka ta miqe da gudu ta nufi dakinta. Parlour ya koma dan ya jirata. Bata da de ba tafito da half hijab dinta ahannu Kar6a yayi sannan ya tsuguna dan yasamata. Ahankli yace mata "mummy taganki? Ah ah tace dashi hadi da jijjiga kai. Toh muyi sauri muje mu dawo,kinsan tahan shan za'ki..... *Salmerhmd* 😘 [10/2, 5:48 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh md* Luv story😍 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* Dedicated to.....daukacin masoyan CAPTAIN ABBAS😘........ina tare daku masoyana.💔 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *3* fita suka yi daga 'kofar palour cikin sauri don ma kar mummy tagansu, cikin sa'a kuwa bata gansu dinba har suka je suka siyo choculate din suka dawo gida, tarkace dayawa Abbas ya siya mata,sai dai bai hallaka kudin duka wajen siyan choculate din ba dan yana tunanin gobe idan Allah ya kaimu karta qara mar rigima irin na jiya a hanyar,shikuma be so ya sa ke dauko abu batare da kudi awurinsa ba don gaskiya ya na kunyar sa ke tambayar mummy kudi, Hakan yasa ya rago kusan #500 yabari a aljihunsa. Duk kayan za'ki Abbas ya siya mata bai ma siyah wa kansa komai ba sai wani sweet guda biyu da basufi #50 ba. Adakin Abbas din suka yada zango,anan yasata agaba tana ta cinye cinyen ta,daga 'karshe suka fito suka dawo parlour,suka bar ragowan kayan adakin Abbas din. lokacin ma daf maghrib ta yi,hakan yasa Abbas yace shi kam zai tafi masallaci.Yace itama ta je maza tayi sallah. Toh" tace tare da miqewa ta nufi dakin mummy. Waya ta samu mummyn tanayi,sai kawai ta qaraso wurinta ta zagaya ta bayanta sannan ta kwantar da kanta a kafadun mummyn. Mummyn bata kulata ba har sai da ta kammala da wayar kafin tace "Angel din daddy daga ina haka? Teemar cewa tayi "Yawo mukaje da yayah" "hmmm" Mummyn tace sannan ta qara da fadin "Lalle teemah, wato kin samu Abbas kin mnta da ni ko? Tafada da dan murmushi akan fuskarta "har zaki je yawo ko ki fadamin? Teeman Cewa tayi "sorry mummy munje siyan cho........ Awwwn.......tace da wuri tare da kama bakinta ita adole kuskuren fa'da tayi. Murmushi mummyn tayi sannan ta zagayo da ita ta gabanta "in qarasa miki? Tafa'di tana kallon idon teemah Jijjiga kai Teemahr tayi alamun "a'a" Meyasa ? Mummyn ta tambaya. "Yayah yace kar infada miki" teema tafada da dan fuskar tsoro kadan. kamo hannunta mummyn tayi ta matso da ita daf da ita, sannan tace Kun fi qarfi na ni kam Teemah ,keda Abbas bakwa jin maganata yanzu,shan za'kin nan ban sonshi kokadan amma keda Abbas baku ji ko.? jijjiga mata kai tayi teemar tare dacewa " mummy sorry baza mu sake ba" Bata kula ta ba mummyn kawai ta miqe tsaye dan ji da tayi anfara qiraye qirayen sallah. Bayan anyi sallahr isha suka hadu a dinning dan cin abinci. Abbas yana bawa teemah abakinta tana ci,duk dama kafin ta kar6a sai yayi kusan spoon uku kafin ta kar6i daya. Mummy bata kulasu ba,har sai da suka 'kare cin abincin kafin tafara wa Abbas fada akan shan za'kin nan dasu keyi. mamaki Abbas yayi akan tayaya akayi mummy tasani. kallon idon teemah yayi sai yaga ta sunkuyar da idonta 'kasa hakan ya tabbatar masa da cewa ita ta fada wa mummyn. Aransa yace "zanyi maganinki ai yarinya" Afili kuwa ha'kuri yabawa mummyn tare da cewa insha Allahu bazasu sakeba. Jinsa kawai mummy tayi don tasan abu mai wahalar kenan shi ne su daina din. Musamman ma shi Abbas din. matu'kar Teemah zata nuna masa tana son abu toh kuwa dole na fa sai yaga ya nema mata abun ko ma miye ne shi. "Allah yasa" ta ce sannan ta miqe ta wuce parlour tazauna a akan cough. Abbas kuwa mummy na tashi shima ya ajiye spoon din dake hannunsa kamar dama jiran tashin nata yakeyi,sannan ya kamo kunnen Teemah da 'karfi. Sosai taji zafin wajen "Yayah" Teemah tafada cikin azaba. Kamar zatayi "Ganin dayayi tana shirin yi mai kuka ne yasashi tsare ta da idanu,tare dora dan yatsansa akan bakinsa yaqara da fadin. "shiiiiii.......Don't let that tears out" 'Kasa 'kasa yayi da muryarshi saitin kunnanta sannan yace "Baki jin magana ko"? Dawuri ta jijjiga kai alamar "a'a 'Kayi ha'kuri yayah bazan sake ba" Ta fada tana mai kai wan hannu akan Hannunsa inda ya riqe mata kunnan. Tausayi ta bashi saiya sake ta da wuri. Amma ahankali yace mata "Wlh inbaki daina yawan gulman kinnan ba ko,zanga mai 'kara rakaki makaranta ai." Turo baki tayi gaba don in akwai abinda ta tsana aduniya toh bai wuce Abbas ya ce bazai 'kara rakata makaranta ba. "Nifa yayah ban fada mata ba fah,dakanta ne tasani,"da kuka ta 'karashe maganar. Ganin haka yasa yace "toh naji ni,ya isah haka". "Abincin ya iSheki ne? Ya tambayeta yana mai kallon fuskarta dayake ta sa hannunta akan fuskar so baya ganin idanunta,itama bata kulashi ba. "Ina tambayar kiii? Ya 'kara fada cikin dan dagun murya kadan. Tashi tayi da gudu tayi wajen mummyn tana kuka. "Mummy kinga yayah ba"Tafada tana me dora kanta akan cinyar mummyn. "Kun fi kusa ai mamana" Mummyn tafada batare da damuwa da kukan da teeman keyi ba. Don sarai tasan bai wuce akan case din shan choculate dinnan bane. Shine har Sukayi fada akai. 'Kara powern kuka teema tayi tare bubbuga 'kafan ta akan tiles din dakin. "Haba *TEEMAH* so kike kijiwa kanki ciwo ne ? 'Dagowa teeman tayi sannan ta ce " mummy bashi bane? Me yayi ne wai 'dan nawa." Mummyn ta tambayeta tana mai kallon fuskarta. "Wai ma bazai rakani school gobe ba. Cewa mummyn tayi "Kiyi shiru wasa yake miki " Daganan mummyn takamo ta ta kwantar da ita akan cinyarta sannan tacigaba da lalla6a ta,anan kuwa bacci ya dauke ta. Abbas kuwa tun sanda ta gudo wajen mummy shima ya tashi ya wuce dakin sa. Harya watsa ruwa yayi shirin bacci,sai kuma yaji dai inah, hankalinsa bai kwanta ba. sai ya fito ya dawo parlourn da sallamarsa yashigo.anan ya samesu da mummyn teema harta yi bacci. Mummyn ne tace "yauwa abbas 'kira min fanni man tazo takaita dakinta. kaga hartamin bacci anan tana kan rigima." Cewa yayi "mummy bari kawai na kaita " Owk . "Matso wa yai ya dago ta amma sai da yayi nishi,don ba laifi teemah akwai nawi. Da 'kyar ya 'karasa da ita dakin nata,ya kwantar da ita akan gadon yana haki. Kafin ma ya fito sai ga fanni tashigo itama. Cewa yayi " yauwa saka ma ta kayan baccinta. Sanan ya juya yatafi ko amsar fannin ma bai jira yaji ba. Washe gari da zai kaita makarantar suna fita ya tare mai adai daita Ya 'karasa dasu makarantar. koda aka tashi ma haka ya sa ke tare musu wani adaidaitan suka sake hawa. Teema bata ankara ba har se data gansu a 'kofar gida kafin nan ta lura. Aikuwa kuka tasaka tunkan ma sufito daga cikin adaidaitan. 'Dan adidaitan ne ya juyo tare da fadin "yadai 'yan mata" Abbas kuwa Bai kulata ba illah ciro kudi da yayi ya miqawa 'dan adidaitan,sannan ya fito,itama fitan tayi tana qara kwa6a fuska. "Wuce muje" Yafada a tsare. Yarda abin da ke hannunta tayi ta wuce ciki da gudu,da qarfi bu'de get 'dinta ta shiga,don duk abinta tana tsoronsa wani lokacin,don inya tsare toh baya wasa . Dagudunta tashiga gidan baba maigadi ma yana mata magana amma kota juyo. Dayaga haka sai ya tashi ya leqa wajen shima don zatonshi ko wani abin ne yafaru. Abbas ya hango yana tahowa hannunsa riqe da lunch box dinta data yar awajen. "Aww ashe tare kuke ma" Inji baba maigadi Murmushi kawai abbas din yamasa Sannan yawuce abinsa ciki. Kodaya shigo bai ganta ba,sai yayi zaton ko tana wajen mummy neh. Ai kuwa mummy tasha rigima aranar, data gaji da rigimar ne sai ta aika aka 'kira mata Abbas. Koda yazo tambayarsa mummyn tayi "wai meke faruwa ne? "Cewa yayi mummy yau ba'a siyo fruits ba ! Ya 'karashe da dariyah Tambayarsa mummyn tasake yi " akan me yasa toh be siya mata ba." Cigaba tayi da cewa "mantawa nayi ne ma ,harfa naciro kudi akan zan baka lokacin dazaka tafi dauko tan saboda rigimarta ,amma ban tuna nabaka ba har sai da ka tafi nagani, yanama ajiye akan mirror. Dauko ka bawa habibu (drivern gidan)yaje ya siyo mata . Dariya ya sakeyi kadan sannan cike da mugunta yace "Rabu da ita mummy it's her purnishment". Cewa mummyn tayi "kamata toh kuje can ku 'Karasa ni ta dameni da kuka. Hannu yasa ya 'dagota sama ya fice da ita,bai ajiyeta ko ina ba sai dakinsa. Yana ajiyeta yana fadin yarinya 'karama sai uban nawi. Aikuwa ranar yasha rigima da 'kyar yasamu yaje ya sallaci juma'ah,saboda hayaniyar kukan da ta keyi. Ana sallamewa kuwa ya dawo gidan da sauri,don gaba daya hankalinsa na awajenta neh. zuwa yanzu yafara regreting din 'kin siya matan dayayi. Yayi yayi taci abinci kuma ta'ki. Har kusan la'asar ta 'ki nutsuwa. Daga 'karshe tausayi tabashi sosai,haka yasa ya fita yaje gurin habibu ya bashi kudin sannan ya sanar dashi abinda zai siyo din kafin yadawo ciki. Da 'kyar ta yadda fanni ta mata wanka kafin habibun yadawo. Daya ke ma wurin banisa ne dashiba a 'karshen layinsu ne wajen mai fruits din,so habibun bai dade ba yadawo lokacinma ko wankan ba'a gama mata ba. Da fanni tagama shiryata saita kawota wurin Abbas din,Mummy kuwa duk wannan abin bata san anayi ba,alokacin mummy baccin ta ta ke yi. Shima daya gata dawo din, tashi yayi yaje ya dauko mata ledar gaba daya ya dan'ka mata,kar6a tayi tare da fitowa parlour ta zauna akan kujera cikin sanyin jiki,kuma har alokacin bata daina ajiyan zuciyan kukan datasha ba. Bata dade da zama agun ba bacci ya dauke ta rungume da ledar ahannunta,batare dataci komai daga ciki ba........ Koda Abbas yafito zashi masallaci sallar la'asar ne yagan ta anan tana bacci. Yaso yatashe ta saboda baccin la'asar babu kyau,amma ganin yanayin yanda take baccin sai yaji tabashi tausayi. Hakan yasa ya'kyaleta kawai ya yi tafiyarsa masallacin.amma kafin yatafi sai da yadawo da ita ya kwantar da itaA tsakiyan 'dakin. Sannan yafice ya tafi. Lokacin data tashi abaccin kuwa kamar ba ita ba,tsab ta warware,tamanta rigimar datayi. Washe gari Saturday wuni sukayi suna buga game a 'yar 'karamar laptop dinsa.anan ma zokuga drama awurinsu kamar TOM nd JERRY....... Sai da lokacin islamiya yayi kafin suka tashi.....amma kafinma ace sun gama shiri,sUnyi sallah,sunci abinci har sun dan shiga lokaci. Haka ahanzarce suka fito,dole yau sai habibu yah kaisu saboda kartayi latti,don inyace yauma da kafar zasu toh kuwa ba 'karamin latti zatayi ba. Koda suka sau'keta gida suka dawo abinsu shida habibun batare da ko sau'ka yayi a motar ba.bye bye kawai yamata tashiga ciki. 'Karfe biyar daidai yakama hanya ya koma islamiyar don ya dawo da ita gida yanda suka saba abinsu.Dayake sai 5:30 ake tashinsu. ***** Abbas ba'ko ne agidansu teemah watansa daya kenan da zuwa gidan yanzu. Amma idan aka lissafa a duka duka wannan shine zuwansa gidan na uku kenan akaf din rayuwarsa. kuma tunda yazo Habibu bai sa ke kaiwan Teema makaranta ba,haka ma dauko ta,dan acewar Abbas din ahakan ne zai ga gari da kyau,amma in amota ne wai bazai gani dakyau ba. Teemah kuwa tun ranar farko dasuka zo daidai wajen mai kayan fruits daya siya mata babana, shikenan tasamu abinka da yarinta wai kullum Sai an siyah mata,kullum da kalan data ke za6a,in kuwa aka 'kii siyah toh fah ranar antaro *match*............ ***** The following day kuma takama ranar sunday ne,kuma aranar daddy yayi musu zuwan bazata. Sosai sukayi farin ciki da zuwan nashi ,musamman ma daya cika su da tsarabobi ai sai suka sake rikicewa da farin ciki......haka suka yi ta murna da annashuwa....... Awurin cin abinci ne bayan sun kammala da abincin Daddy yasake yimusu wata bazatar kuma...,,.... Don cewa yayi zuwa ranar laraba Abbas zai tafi makaranta. Dama hutun J.S.C.E. yakeyi,so yanzu shima zai koma SS1,already ma daddy yace an kammala masa komai ,shi kawai yarage ya tafi............. *Yah ne readers,* *kuma nasan daddy* *ya muku* *bazata ko?* ( *Hhhh* 😃) *don't worry just* *keep following* *ME* ........ *YANZU FAH MUKA* *FARA* . *Ur comments is needed* 👌🏻 nd *Share pls* *Salmerh md* 😍 [10/2, 5:49 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 _Wattpad@_ _Serlmerh-md_ 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 ~We are here to~ ~make you~ ~happy,smile,educate~ ~and to~ ~realized~ ~that we are the best~ ~among all~ ..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *4* Shirye-shirye aka farayi na tafiyar abbas 'din makaranta,dayake hankali bai gama isan Teemah ba shiyasa bata wani damu da batun tafiyar ba har se ranar da ze tafin kafinnan, wato ranar laraba. Dawuri yagama shirinsa don shima irin yaran nanne masu jarabar son makaranta.Baya wasa da harkar karatun shi tun asali,wannan halayyarsa ne tun yana yaro qarami. Ballantana Yanzu da ya 'kara wayo sai ya fi jin yin karatun sosai. 11:00am ne flight dinsu,ba sassafe zasu tafi ba,hakan yasa yau 'din ma yace shi ne zai kaita makaranta. Ahanya neh yake sanar da ita cewa shima fah zai tafi makarantarsu anjima,ko ajikinta bata damu ba illah cewa datayi "ai nima zan dinga raka ka kullum inzaka je" Dariya ma tabashi shikam,dan shirman nata abin dariyah ne, wannan shi ne ana ce miki ga gabas kina 'kara tambayar ina al'kibla. Sai da yayi dariyar kuwa sannan yace mata " ke bafa anan bane makarantar,tafiyata zanyi nima,yanzu sai de Habibu ya rin'ka kawoki a mota kullum." Kanta ta lan'kwasa gefe 'dayan kafa'darta tare da fadin "hum um-hum um" harda bubbuga kafafunta a'kasa irin na shagwa6a66un yaran,sannan tace ni banaso. Kallonta yayi sosai dan so yake ta fahimci maganar tasa sosai amma yarinta bazai barta ba sai kawai yace mata "dolenki ai yarinya,inkuma bahaka ba sai de ki rin'ka zuwa ke ka'dai."Kinga habibu ma huta da zirga- zirga. Kuka tafara masa na rashin dalili,ehh mana rashin dalili,daga cewa habibu ne zaina kawota makaranta kuma sai kuka,toh danma bataga yatafi yabarta ba kenan daya zatayi. abin dariyah wai cewa tayi . "sai na fa'da ka da Daddy" Batasan cewa daddyn shi ne jagoran tafiyan ba.kiyi ha'kuri karki fada ni da daddy ya fa'da da sigar yanda itama tayi magananta,ta ke kuwa yabata dariyah."me zan siyo miki idan naje makarantar ya tambayeta."ai nima binka zanyi inzaka tafin,irin yanda kake rakani,a'a nawa nikai zanje bawanda zai rakani kuma idan natafi zandade bandaqo ba.amma wannan karon bata kulashi ba don yafara bata haushi.sai kuma ta tuna fruits 'dinta Kai ta 'daga ta kalleshi,hannunta na ri'ke cikin hannunsa suna tafiyar.sai tace toh yayah idan katafi wazai dinga siyamin Apple da pineapple harda babana ma? Habibu zaina siyamiki kinji? Yabata amsar tambayarta ta cikin sauri. Kuka tafara masa wai ita bata son na habibun nashi take so. suna tafiyah tana kuka,tausayinta yakeji dan yasan dolene daman taji ba da'di,shikansa ma bada'din yakeji ba don sosai sukayi sabo fiye da zaton mai karatu. Da 'kyar ya lalla6eta tayi shiru sai da yace mata dawasa yake mata babu inda zaije.Kuma shine zai na siyamata apple 'dinta kullum. tana jin haka kiwa kuka ya 'dauke cak. Haka ya rakata makarantar dai dai zata shiga ya miqa mata lunchingbox 'dinta yace ta shiga class dinsu banda wasa,harta fara tafiyah sai ya 'dan 'daga 'kafa ka'dan ya iso gareta,dayake bata wani yi nisa da inda yake tsayen ba,hannunta yakamo sannan ya tsuguna dai dai tsayinta. Sake daidaita mata 'dan Hijab 'din uniform 'din dake kanta yayi,wanda dudu-dudu bai wuce iyah kafa'dunta ba. Kallon cikin idonsa tasa keyi itama,sai yayi murmushi ya kamo kumatunta duka biyu ya 'dan jijjiga mata fuskar "Smile mana kin wani 6ata rai kamar an dokeki" Dariyan kuwa tayi masa.Tana sa ke kallonsa. "Silly girl" Yace ahankali yana murmushi Hannunta ta 'dago ta danna saitin dimple 'dinsa. Bawani zafi amma dan kawai ya 'dauke mata hankali yasa shi cewa " kai kai,Allah yarinyan nan kin iyah mugunta" Sai yayi kamar zaiyi kuka tare da kama gurin data danna 'din. "Sorry yayah" Tafada tana turo baki gaba Sake 6ata rai yayi sannan ya ce. "Zan ha'kura amma sai naje anmin allura idan ya daina zafi toh shikenan zan han'kura amma idan bai daina ba toh shikenan bazanma dawo ki ganni ba. Kin yadda? Ya tambayeta. Kai ta 'daga masa alamar ehh tayadda. Tashi yayi tsaye sannan yace toh ki je class," "barinje amin allauran ko? Sa ke 'daga masa kai tayi "ko zaki rakani?ya sake tambayarta yanzunma kai ta kuma jijjigawa alamar a'a. "To kije class anjima habibu zaizo ya 'dauke ki kinji. Duk da kai take bashi amsa. Sannan tajuya tanufi cikin makarantar shima bai tafiba tsaya wa yayi yana kallon bayanta harta isa bakin class din su sai ta juyo kamar tasan bai tafinba. Hannu ta 'dago ta mai bye-bye. Shima 'daga mata hannun yayi. sai da yaga ta shiga class kafin shima yajuya ya kamo hanyar gida.awurin mai kayan fruits ya tsaya,alokacin ma mai kayan bai gama kintsa wurinba,haka Abbas yajirashi tsaye agefe har ya kammala gyara wurin ya kik-kintsa fruits 'din kowanne a muhallinsu kafin abbas ya matso yasiyah matah,wanda tafi ra'ayinsu daganan ya isa gidan. Yana shiga yasamu mummy zaune aparlour tana kallon wani series,binsa tayi da kallo dan ganinsan datayi ri'ke da leda a hannu. Dariya yayi yana kallon mummyn shima saboda irin kallon tuhumar datake binsa dashi. "Mummy kayan Teemah ne na siyo mata don zata dawo yau bana nan" Murmushi mummyn tayi tare da fa'din "lalle Abbas da 'ko'karinka.Kai da zak tafi har se ka biyeta kasiya mata bayan ma kawi agida.a'a mummy cewa tayi nawan tafiso." Ku kuka sani ai mummyn ta qarasa zancen nata tare da komawa ta jinginu da kujerar da take zaune akai. "Toh kaiwa fanni tasaka mata a fridge kafin tadawo karsu lalace dan yauma naga garin adafe yake,ragowar mafa inaga yawa ne dasu a fridge din" Ce mata yayi " a'a mummy wannan yafi da'di.haka yafadawa mummyn yana qoqarin barin parlourn . "Zan gani ai idan ka tafi wa zai rin'ka siya mata mai da'din tunda namun ba da'di. Dariya kawai yayi sannan ya 'karasa Fita daga 'dakin,wurin Fannin ya nufa a inda yasan zai fi samunta cikin sau'ki, daga nan yawuce 'dakin Teemahn,bayan yabata ledar. Guri yasamu ya zauna abakin gadonta ya yi tagumi. Ha'ki'ka sabo ba da'di don yanda Abbas yakeji,jiyake kamar kar yatafi yabarta,amma bazai yiwu ba. Sosai ya 6ata lokaci a'dakin nata amma shikanshi baisan dalili ba,illah kawai kewarta dayake ji tun kan ya tafin. 10:30 suka fita shi da daddy da mummy,Habibu ne ya kaisu airport 'din daganan ya dawo da mummy gida su kuma suka wuche Abuja. Koda lokacin tashin su Teema yayi Habibun ne yaje ya 'dauko ta yadawo da ita gida. Sai data gansu a 'kofar get 'din gidan habibu na danna horn kafin ta turo baki Sannan tace "Nifah bahaka yayah yake min ba" Juyowa yayi ya kalleta daidai anbu'de get 'din gidan. Cewa yayi Bayan yaja motar ciki " me yayan yakeyi wanda ni banyi ba,? ni dama na kawoki a mota" "shi ai yayan kullum se ya siya min fruits ahanya" Kai kuma baka siyamin ba,ai inya dawo daga alluran sai na fa'da masa" kuma 'dazu yace wai zaka dinga siyamin kafin yadawo" Tafa'da masa da turarren baki irin ita adole tayi fishi 'dinnan. "Fishi yana gaba yarinya " habibu yafa'da azuciyarsa don yagane cewa wayo Abbas 'din yamata da sunan allura zashi. Afili kuwa yace mata yayi " ii ha'kuri 'yar Daddy yanzu zanje insiyo miki." "a a ni banaso na yayah nakeso ni,idan ya dawo zai siyo min ai. tafa'di hakanne bayan sun fiffito daga motan. Aransa yace "ashe zaki jima yarinya" afili kuma ya ce mata"kinga ai kin hutar dani" Ciki tashiga da sallamarta 'yar siririyah,bataga kowa a parlourn ba hakan yasa ta wuce 'dakin mummy. Zuwa tayi da gudu ta rungume mummyn nata tabaya dayake atsaye take agaban ma'ajiyan kayan sawanta wata 'kila wani abun zata 'dauka ko ajiyewa dan ba kaya ta ke nema ba. "Oyoyo mummy" Teeman tafa'da Itama mummyn cewa tayi "oyoyo yarinyar mummy" Sannan ta kama hannunta tazauna akan side drawer daga gefen gado tace mata"wato yau yayah bayanan harda oyoyo na samu ko? "Ai mummy allura yaje zai dawo yace min " Hmm " kawai mummyn ta ce Rage mata kayan jikinta tayi sannan tace mata taje fanni ta watsa mata ruwa,sai ta dawo. Fita tayi hannunta ri'ke da kayannata tashiga 'dakin ta watsa su akan gado tayi wajen fannin akitchen tasameta tana wanke wanken kayanda aka gama anfani dasu yanzu. 'Dakin suka koma fanni tamata wanka kafin su gama kuwa tasha surutu kuma duk hirar yayah ake tayi mata. Itama fannin ta biyeta,suka tayi tare. 'Dakin mummyn suka dawo bayan fanni ta shiryata. Mummy naganin sun dawo ta mi'ke tace suje suci lunch dan tana so ne ta'dan fita. Harsun zauna anfara zuba abinci teemah tace ita kam a'a bazataci abinci ba pineapple ta keso. Jin haka yasa mummyn ta fara mata masifa da 'dagun murya akan rashin son cin abincin data koya.fanni ce ta tuna da fruits 'din da Abbas ya kawo 'dazu kafin ya tafi. Bata yiwa mummyn magana ba illah zuwa datayi ta duba,cikin sa'a kuwa tasamu pine apple 'din aciki.shikadai tadauka ta feresa mai kyau sannan ta dauko takawo wa Teemahn. Sai da taka wo sannan mummy ta tuno dashi,Ashe fah Abbas yasiya mata kafin yatafi kamar yasan ma zata musu rigima akai. Haka ta wuni tana shan abinta taqi cin abinci. Da lokacin islamiya yayi habibu ne yakaita ya dawo da ita kuma. Har washe gari bata wani damu da rashin Abbas 'dinba,don ita duk atunaninta alluran yatafi dagaske kamar yanda ya sanar da ita.kuma ai yace mata sai ya warke sannan zai dawo.......... Dataga lokaci yafara jah ne sai tafara takurawa mummyn akan ina yayan yaje?,mai yasa ya'ki dawowa? Tun mummy na ce mata yatafi alluran itama kamar yanda Teemahn ta 'dauka harta gaji ta tafara ce mata ya tafi makaranta ne bazai dawo yanzu ba. *Serlmerh-md* @ *wattpad* Vote nd share pls 👌🏻 [10/2, 5:49 PM] Ummiyo: [3/14, 10:26 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* Dedicated to sister Safiyyah😍Allah yabar zumunchi.🤝 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *5* Tun lokacin da Abbas ya tafi kuwa Teemah bata ta6a mantawa dashi ba,don mafi yawancin lokuta idan ka ta6a ta ko kamata wani abin takance "sai nagaya ka/ki da yayah,koda kuwa amakaranta ne ko gida,harta mummy da Daddy basu tsira ba,suma abu kad'an sai tace sai ta fad'awa yayah dan ita azatonta har yanzu watarana zai dawo. Mummy bata ta6a kuskuren had'a su awaya ba don acewarta daga ta gwada k'ira mata shi sau d'aya tasan Teemah ta ringa damunta kenan kullum,shiyasa bata ma fara ba,duk da basu fasa waya da ummahn Abbas d'in ba suna wayarsu kusan kullum, haka sometimes mummy kan bata labarin irin rigimar da Teemahn keyi akan rashin ji daga Abbas d'in da batayi ba har yanzu,dariyah kawai kowaccen su keyi daga haka su shashantar da zancen. Akwai ranar da ta ta6a saka mummy agaba da kuka wai dole suje gurin yayanta,mummy tarasa yazatayi da ita ta ce mata ai alluran nasa bai k'are ba"kuma in yak'are zai dawo da kansa,amma sam ta'ki yadda.ita wai dan dole suje su kawo shi gida, Haka data dage sai da mummy tayi wayar k'arya ta tambaya awayar ta ce "abbas nake nema? "Aw baya kusa? Alluran haryanxu? Owk toh shikenan inya dawo ace masa Teemahn shi ce ta ke nemansa. Da mummyn tacire wayar akunnenta sai tace mata " ai wai bayanan amma alluran ma yakusa ya k'are kuma idan ya k'are zai dawo. Ai Teemah najin haka tafara dariyah ta fad'a kan cinyar mummyn. Salati mummy tafara kamar gaske , Kai abbas d'in nan bayajin magana ,ashe yawo yatafi abinsa ya kyale angel d'ina agida. D'ago kai Teemah tayi ta kalli mummyn "Mummy ke ba yayanki bane? "A'a Teemah" mummyn tafad'a sannan ta sa hannu ta d'ago Teemah ta tsayar da ita agabanta. "Mummy yah abbas fah sunansa ke kuma kina ce mishi "Abbas" Kumatunta mummyn takama duka 6angare biyun tana mata murmushi. Teemah "Abbas d'ana ne ba yaya na ba.ke kuma kinga ai ke k'arama ce.K'anwarshi ko? Kai TEEMAH tad'aga wa mummyn tana d'an smiling itama. "Yauwa my angel "maza jekiyi home work d'inki ko" mummy is sleepy" Da haka mummy tasamu ta kora ta daga wurinta dan tasan inba hakan tayi ba to hirar bazai ta6a k'arewa ba. Teemah da fara'arta ta fita daga d'akin mummyn ta nufi nata.Yau farin ciki ta keji har aranta don yayah yace zai dawo in allurarsa suka k'are. Ai kuwa daga ranar tafara lissafin ranar da abbas d'in zai dawo.ita kadai tayi ta ware rana amma kullum shiru ba labarinsa. "Mummy gobe yayah zai dawo ko"? Kullun sai tambayi mummyn,amsar mummyn kuwa baya wuce "bansani ba nima Teemah"dan bata so tafiye yi mata k'arya. Inkuwa daddyn ta ne zai fita ce mas take yi idan yaje yadawo mata da yayah! Shima cemata yake toh,inya dawo ta kuma tambayarsa kuma sai yace ai basu had'u bama da Abbas d'in. Itama Teemah tun tana damuwa harta zo tadaina damun kanta akansa,takance "ai ba ruwana da yayah yanzu tunda ya manta dani yah daina sona" haka ahankali harta ha'kura ta manta dashi ma gaba 'daya,abinku da yarinta. Hakan da yafaru kuwa ya matu'kar samawa mummy lafiya,dan acewarta itama ta huta da fitina. Har ta gama primary tashiga Js class amma Abbas bai 'kara dawowa gidan su ba itama kuma ba'a ta'ba zuwa abuja da ita ba.Kuma zuwa wannan lokacin kwata kwata ta manta da tarihin rayuwarta tare Abbas d'in,tadai san tana da 'dan uwa amma ko da a photo taganshi bagane shi zatayi ba. Tana Ss1 wata ranar jumma'ah tadawo gida dayake dawuri ake tashinsu. In ranar Friday neh,motar su na shigowa ta hango wata sabuwar mota a wajen parking bata san me motar ba,dan haka ta shiga parlourn da sallamarta,Daddyn Abuja tagani azaune shi kad'ai a parlourn yana waya.da fara'arta ta k'arasa inda yake zaunen ta zauna kusa da shi,daga inda ta ke zaunan tana iyah jiyo muryar wanda suke magana da daddyn,tana jin irin yanda yake yiwa daddyn nata. Kauda kai tayi tare da ta6e baki. Daya gama da wayar ne ya kalleta ya ce "uwata kin dawo ne" Dariyah tayi kad'an tace "nadawo daddy ya hanya yah 'yan Abuja? "'Y'an abuja gaba d'aya "dadyn ya tambayeta.sannan yacigaba da fad'in mamana fah ashe an girma" Kunya taji da sai tad'an rufe fuskarta da hannunta. Daidai nan kuma daddynta ya fito cikin shirin sa na fararan kaya. Sai da ya iso ya zauna akujerar da take fuskantarsu kafin yace mata "ya akayi ne baga kin dawo da wuri?" "Daddy yau fa friday kamanta ne," Ohh sorry haka ne fah,ashe dawuei kuke tashi," Na zaci ai ganin daddynki kika dawo kiyi dan kinji yazo" ya fad'a mata da sigar zolaya. Toh aini bansan ma yadawo ba daddy waye zai fad'amin nida nake makaranta. Nasani ne angel " Ko daddyn naki ne yasanar da ke. Dariya sukayi gaba d'aya daga nan ta tashi ta d'auki jakarta "daddy ina zuwa " Tafad'a tare da barin d'akin. Parlourn mummy tafara zuwa tana yin sallama taga ummah azaune au da mummy,yada jakar tayi ta tafi da gudu tafad'a kan cinyar ummahn tana dariyah, "ummah na ashe harda ke akazo shine daddy bai gayamin ba? Ai gani kinganni" Ummahn tafad'a tana maijin dad'I har cikin ranta yanda Teemahr take sonta. Gaida ummahn tayi tare da yimata ya hanya amma still bata bar jikinta ba. Mummy ce tace mata "Ai se ki d'aga ko tunda hankalinki ua kwanta,da wanne zataji da gajiyar hanya ko kuma da nauyinki" "Katuwa da ke sai son jikin tsiyah" Ai tana jin haka ta turo baki gaba [3/14, 10:28 AM] 🌸Salmerh🌸: "Ummah wai ni k'atuwa ce inji mummy"! "Kyaleta mamana bawani k'atuwar da kike"Kawai dai tana fad'a ne. "Hakama fah d'azu naji wani ma babba dashi yana yiwa daddyn Abuja shagwa6a awaya"amma ni sai mummy tahana ni tace min wai ni k'atuwa? Tak'arashe da turo baki gaba.Dariya ne yaso kama ummah dan tasan wannan sai aikin Abbas. Amma afili bata cewa Teemahn komai ba illah cigaba datayi da lalla6ata harta hak'ura. mummy kuwa kauda kai tayi sannan tace "rashin aiki dai" "Ai in kika biye ta wannan zaki sha fama" mummyn tafad'a tana mai nuna Teemahr da baki. Murmushi sukayi ummah da Teemah dajin abinda mummy tace, mummyn kuwa ta ta6e baki. Tashi tayi daga kan cinyar ummahn ta zauna sannan tasa hannu ta d'auki d'aya daga cikin abin ta6awan da aka ajiye wa ummahn. "Ummah bari na watsa ruwa in dawo" Da toh ummahn ta amsa mata,ita kuwa tuni ma takusa barin parlourn. Sai da ta cire kaf d'in kayan uniform d'in dake jikinta sannan tafara k'ok'arin neman abinda zata d'aura ajikin nata amma bata samu ba, tana daga tsayen tafara kwalla k'iran Baabah lami mai aikin gidansu na yanzu,bakinta biyu kafin tayi na ukun baabah lami ta amsa mata tare da tahowa d'akin,bata tuna ba kaya ajikin ta ba harse da taji motsin tafiyar Baabah Lami d'in kusa da d'akinta kafin ta tuna,hijab d'in makarantarta ta d'auka tasaka akanta ko gwiwa ma bai rufe mata ba,amma dai yafi babu. Da sallama Baabah Lami ta shigo d'akin Tun kan ma ta gama shigowa Teemah ta jefa mata tambayar "Baabah Lami banga Towel d'ina ko d'aya ba."? "Aw suna baya bakince a wanke miki su ba". "Owk toh anwanke d'in ne ? "Ehh anwanke" Baabah Lami d'in ta amsa mata dashi. Sannan ta k'ara da fad'in barin je inkawo miki.Daga nan tajuya tafita daga d'akin. Dayake fanni tajima dayin aure hakan yasa tabar aiki agidan nasu sai aka samo musu wannan Baabah Lami d'in. Baahbah Lami bawata babba bace don bazata wuce 27/28yrs ba amma dayake bazawara ce,yaranta hud'u kuma sune suke k'iranta da wannan sunan wato Baabah Lami hakan yasa sunan yabita kowa ma haka yake k'iranta da shi yanzu. Koda Baahbah Lami ta kawo towel d'in azaune tasame ta abakin gado tana kallon fuskarta acikin d'an madaidaicin mirrorn dake rik'e a hannunta.Daganin Baaba Lami d'in kuwa ta tashi ta kar6i kayan ta,tsayuwa tayi har sai da taga baabah Lami tafita taja mata k'ofar kafin ta cire hijab d'in kanta ta d'auki towel d'aya ta d'aura ajikinta, sauran kuma ta ajiye su a inda tasaba ajiyewa sannan ta d'auki wani fari k'arami daga ciki ta rik'e ahannunta kafin nan tashiga bayin. Ta 6ata ak'alla kusan 40mins a wanka da yin shirinta kad'ai. Tana fitowa kuwa wajensu daddy tafara zuwa ganin basanan sai ta nufi wajen su mummy,tana shiga da sallamarta tafara tambayar mummy "ina su daddy suka je kuma,? harararta mummy tayi, da me zaki musu? Mummyn ta tambayeta. sai ummah ce ta bawa Teemahn amsa da fad'in "sun tafi masallaci ne zasu sallaci jumma'ah" "Ohh na manta ne ummah ashe fah yau Friday" Daya taga reaction d'in mummy data shigo,mummy da harara tabita kuma tasan ma'anar hararan haka yasa yanzun bata zauna ba ta kuma ficewa daga d'akin,don tasan in bata fitan ba mai zai biyo baya anjima ko gobe,kunnan ta ne zasuji ajikinsu. Mummy bata son wai taringa zama a inda ta ke matuk'ar tana tare da bak'i.Dan yana rushe tsarin tarbiyar yaro.Itama dayake tasan abinta sai kawai tafice can bayan gidan tayi zamanta a inda taga yafi mata da'din zama. Da lokacin sallah yayi ne ta koma ciki dan ta yi sallahr itama. Bayan su daddy sun dawo ne aka had'u agun cin abinci,kowa yana ci amma banda teemah da bai fi spoon biyu taci ba kawai,Daddyn abuja ne ya hankalta da ita hakan yasa ya tambayeta ko bata jin dad'in abincin ne? Murmushi tayi masa batare datayi masa magana ba. Daddynta ne ya bawa daddyn abuja amsa da fad'in "da de kayan itatuwa ne da ba sai ka 6ata bakinka wurin sata ciba ,amma abinci kam ni har na gaji da yi mata magana akai ma" Da kyar ta dage tad'an ci abincin dan yadda taga daddyn abuja yadamu da rashin cin abincin nata, bai san cewa wannan d'in ma daure wa tayi tafara ci ba dan ganin suna nan,amma in su kad'ai ne ita da iyayenta ma ko kula dining d'in batayi musamman in abincin rana neh,su har sun riga da sun saba da wannan halayyar tata. Kwanan su Daddyn Abuja d'aya washegari suka koma Abuja,dayake daman wani abu ne yakawo su garin,shine har suka kwana. Teemah jitayi kamar ta bisu da zasu tafin don ita akwai son mutane sosai. Baifi wata biyu da tafiyarsu ba Daddynta ya shirya wai zasu je passing out d'in Abbas a katsina shida su daddyn Abuja,Allah ya kiyaye kawai Teemah tayi mar tare da fad'in ya gaida mata da su ummah da daddy. Har gun mota suka rakashi "shiga yayi bayan ya amsata driver yaja suka tafi airport. Haka suka je lapiya qalau cikin ikon Allah.acan suka had'u da su daddyn Abujan har sun rigashi isa ma. Abbas yayi murna da zuwan Iyayen nasa,inda suka gama abinda yakawo su cikin sa'a har zasu tafi ma sai kuma Daddn yace su jira Abbas d'in kawai inyaso su taho tare tunda shima washe gari zai tafi. Kud'i sosai su daddy suka kashe kafin Abbas yasamu wannan matsayin,don da farko har daddyn Abuja ma yace wai sai dai Abbas d'in ya hak'ura ya bari ya nemi wani aikin,amma daddyn Teemah yace sam baza'ayi haka ba, don sanin daya yiwa Abbas tun yana k'arami burinsa kenan,Burinsa yazama sojan Nigeria,dan haka ya dage sai da yaga burin Abbas ya cika,don acewarsa rashin bada muhimmanci akan al'amarin yara yana matuk'ar affecting d'in cigaban yaran.don haka ya tsaya tsayin daka ya shiga ya fita har sai da yaga burin abbas d'in ya cika kafin ya samu salama.Dayake daddy yana da manya kuma yabi masa ta sama ne,kuma short service yaje, shima Abbas d'in ya shak'i karatu sosai shiyasa cikin sa'a yafito da babban matsayi, amma kafinnan fa aljihun daddy sai da yayi kuka. A can katsinan aka barshi ba aka kaishi ko'ina ba amma kafinnan sai yayi hutu tukunna zai koma gaba d'aya..... *Salmerh* 😍 share pls👌🏻 [10/2, 5:50 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh md* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* Dedicated 2 _my family_ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Why do we often feel like we can speak with authority on someone’s life? How can we when we’ve not experienced what the other person has; we’ve not walked in their shoes. We have the tendency to stereotype people and think like we know it all. *The* *truth is we don’t!* 🅿 *6* Da zasu dawo su baro katsinan Abbas bai bi su ummahn sa zuwa Abuja ba sai yabiyo daddyn Teemah suka taho tare. Yanda yatarar da gidan ya matuk'ar birgesa,musamman yanda aka canja tsarin gida ya koma na zamani,hakan ya k'ayatar dashi.Aransa yakejin ai hakan yafi da ace ana ta canje canjen muhalli ana bin zamani ai gara ka renovating wanda kake dashi in hakan zai yiwu. Sosai yaji daddyn ya burgesa da irin yadda ya maida gidan "so take away😘 Bakamar daddynsa da kullum cikin canja muhalli suke ba. Lokacin da suka dawo Teemah na school,bayan ta dawo ne ta tarar da daddyn ta ya dawo,murnar kamar tacinye sa d'anye.Inka ganta sanda ta ke murnar zaka zaci tafiyar shekara guda yayi,nan kuwa kwanansa uku kacal da barin gidan.Sai data gama murnar sannan daddy yace toh taje ta gaida yayanta,shima yazo yana d'akinsa,Zaro ido tayi waje sannan tace "daddy wani yayannawa?" "Abbas neh angel ,Abbas na Abuja." Daddy ya bata amsar tambayar data yi. "Owk" Tacewa daddyn Sannan ta k'ara da "amma daddy barinje incire uniform d'innan tukunna" Tafad'a tana kallon fuskar daddyn nata. "Uhm,jeki cire abinki" Daddyn ya bata amsa da haka. Tashi tayi ta sannu ta d'auki school bag d'inta,harta fara tafiya sai kuma tace ''daddy ina mummy fah" "sai yanzu kika ga daman tambayar inda nake ko? "Wato dan kinga daddynki ko? Muryar mummy tajiyo tana fad'in hakan,yayinda daddy yafara dariya k'asa 'kasa. Waigowa Teemah tayi nan ta hango mummyn awajen dinning tana k'ok'arin daukan abu. Karakata kai tayi gefe . Mummyn ko kulata ma batayi ba,data d'auki abinda zata d'auka ficewarta tayi tabarta a inda ta ke tsaye. Daddy ma kauda kai yayi kamar bai san meke faruwa ba. Ganin haka yasa ta fice kawai daga parlourn, d'akin ta ta nufa,kamar yanda tasaba sai da tacire uniform d'in kaf,kafin nan tanemi towel ta d'aura ajikinta. Toilet tashiga ta watso ruwa tare da d'auro alwala,Shiryawa tayi cikin wata gown na material marar nauyi,d'inkin ya mata kyau yayi cifcif dajikinta wani k'ara min gyale ta d'auko wanda bai ma fi ak'ira shi da d'ankwali ba,ta yafa akanta. Parlourn ta koma ,dan ita kwata-kwata tama manta da batun wani yayah,amma haka sai tana jin ranta wani iri sai taji bata da nutsuwa. Daddy tasamu still azaune yana kallon news d'in rana,aranta tace "daddy da news badama." Shiganta keda wuya tun ma kafin ta zauna kamar had'in baki sai ga mummy ta 6ullo ta itama har tayi wanka tacanja sutura. muryar Mummyn tajiyo tana fad'in "yauwa Teemah yiwa yayanki magana kinji,lunch is ready". Dum taji zuciyarta ta amsa,bata san dalili ba,amma tafi kyautata zaton k'ila dan ta jima bata had'u dashi bane shiyasa. Dayake daman bata kaiga zama ba,sai kawai tajuya ahankali ta fara tafiya dan zuwa aiken mummyn. "Ni kinma je kin gaidashi kuwa?" Tasake jin muryar mummyn tafad'I. Kai ta jijjigawa mummyn batare data waigo ba dan duk jitayi jikinta yasaki. "baki san yazo bane? Mummyn tasake tambayarta. Ynzun kam saida ta waigo kafin tace "nasani mummy,d'azu daddy ya fad'amin,daman inada niyyar zuwa" Kai alanga6e tayi maganar kamar zatayi kuka. "Hmm" kawai mummyn tace,daganan bat qara kallon inda Teemahn ta ke ba. Daddy kam k'ala bai ce musu ba. Juyawa tayi taci gana da tafiya,koda taje k'ofar d'akin nasa ma jitayi kamar karta shiga,amma data tuna cewa mummy ce ta aiketa aikawai sai tayi shahada ta tura k'ofar ahankali tashiga sannan ta maida k'ofar ta rufe,gani tayi d'akin duhu bak'i k'irin ba haske,neman inda switch yake tayi ta danna,amma still ba haske. Hakan ya tabbatar mata da cewa bulb d'inne suka lalace,kuma dayake ba'a cika amfani da d'akin ba shiyasa babu wanda yabi takansu,ballantana a canza su. Ahankali ta k'ara cikin tsakiyar d'akin jitayi shiru ba alamar motsi,sai de uban k'anshin turaren da yau ne farkon fara jinta dashi,da kyar ta tattara la66anta ta harhad'a sunansa. "Yah....yah Abbas"! Shiru taji "Yah Abbas"!! Ta sa ke maimaitawa amma still no answer.Juyawa tayi tafita daga d'akin,taje tasanar da mummy akan bayanan Yah Abbas d'in. "Babu inda Abbas yaje Teemah,k'ila ko zuwa bakiyi ba" Cewar mummy Teemahn ne ta kar6e da fad'in..... "Allah naje mummy,kuma fah d'akin duhu ba haske". D'auki wayata ki haska,maza kije ki dubo minshi, inaga ma bacci yake saboda gajiya" Tana d'aukan wayar tace "mummy harfa k'ira nayi amma babu wanda ya kulani" "Shine ai nace ki duboshi in bacci yake karki tasheshi,ki dawo kawai"k'ila ma dakika ga duhun k'in shiga kika yi ko? Kwa6a fuska tayi "Nashiga mana mummy " "Naji toh ni sauri ki dawo" Mummyn tafad'a sannan takawar da kanta gefe. Fita Teemah tayi ta nufi d'akin Abbas d'in,data isa bakin k'ofa zai ta tsaya ta kunna hasken wayar kafin ta tura k'ofa tashiga. Ko sallama batayi ba don ita azatonta babu kowa ad'akin kamar yanda ta tarar dashi d'azu. Saida ta maida k'ofar ta rufe kafin ta d'aga hasken hannunta haska,Hasken ya gama haska ilahirin d'akin ,don wayar mummyn badai haske ba. Mutum ta hango a tsaye dogo mai d'an hasken fata,k'ugunsa d'aure da towel,wuyansa ma wani towel d'inne rataye kuma duka farare,hannunsa d'aya riqe da man shafawan daya d'auko da niyar shafawa, jin an6ud'e masa k'ofah batare da neman izini bane yasa ya tsaya,dan yaga wani gwani ne wannan. Ko tsoro bataji ba tasake daidaita hasken asaitinsa a k'ok'arinta naganin wannan mutumin da akace wai shine yayanta. Hannunsa d'ayan ya d'aga ya kare hasken dashi,dan ta saita masa ne afuska,sannan ya mik'a d'ayan hannun ya ajiye man shafar. Kallon mai haskashin yake da mamaki,so yake yaga waye wannan d'in,amma dayake hasken ahannunta yake sai hakan ya hanashi ganinta dakyau. Takowa yafarayi zuwa inda ta ke tsayen,amma still bai sauk'e hannun daya d'aga dan kare hasken dashi ba. Bata motsa ba,kamar yanda bata kawar da hasken daga saitinsa ba,sai da taga yakusan cimmata kafin tajuya bayan ta yada wayar agurin,ta nufi k'ofa da gudunta. Tsayawa yayi cak,daga inda yake tsayen, sai ya kama kunkumi da dukka hannayensa biyu gefe da gefe,yabi bayanta da kallo,harta k'arasa bakin k'ofar. Jijjiga kansa kawai yayi jin yanda ta ja k'ofar da k'arfin gaske. Idonsa ne yakaiga wayar data jefar d'in garin gudun rashin gaskiya. "Hmm" afili,sannan ya k'arasa ya d'auki wayar ya kashe hasken.Daganan ya koma ya d'auki mansa ya shafa ya shirya ya fito da wayar a hannunsa. Ahankali yake takawa danko k'arar takalmansa ma ba'aji. Abakin k'ofar shiga parlourn yayi sallama,daga ciki daddy ya amsa masa,jin amsawan da akayi ne yasa shi d'aga labilen yashiga fuskarsa cike annuri........ _Share pls_ 👌🏻 *Salmerh* 😍 [10/2, 5:51 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Dedicated* *2* _my family_ 😍 🤙🏻 Masoya ina godiya nima da soyayyar ku ga littafinnan Allah ubangiji ya barni daku.Ameen👏🏻 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🤞🏻🤞🏻🤞🏻 Being quiet and gentle doesn’t mean you’re weak. Such people show deep, inner strength that’s under control. It’s knowing when to speak and when to listen; when to take action and when to wait. Don’t underestimate such people. *They walk* *the earth with the* *greatest strength!* 🅿 *7* Tana fita daga d'akin nasa waje tayi tana haki,taje tasamu k'ark'ashin wata bishiyar mango da ke acan bayan d'akunan gidan tayi zamanta dayake akwai abin zama agurin,aranta take ta tunani wai daman wannan neh yah Abbas d'in,? Wannan ai babba ne,wata zuciyarta tace ta ce mata amma fah yah had'u,mtssew taja tsaki afili ,toh sai a gidanmu zai zauna neh,ni bana sonshi wlh, nafi son yah Abbas d'ina na dah,don mummy tace har makaranta yake rakani da islamiyah harda yawo muke zuwa,amma wannan dagani mugunta zai yi. Haka ta zauna ita d'aya agurin tana ta tunani batare da ta je tafad'awa mummy sakamakon aiken ba. Daddy da mummy neh kad'ai suke zaune a cikin parlourn sanda ya shigo,cikin hikima yad'anyi yawo da idanuwansa acikin ilahirin d'akin ta yanda babu wanda zai lura da abinda ya akaita ko kuma manufar yin hakan,amma bai ganta ba,ya k'araso inda yakamata ya zauna,harya samu wuri ya zauna mummy bata ga Teemah ba, da farko ta zaci abayansa zata shigo tunda basu shigo tare ba,amma sai taga wayam,hakan yasa ta dube shi sannan tace "ina kuma 'yar aiken ta tsaya?" "Tun d'azu fah ta taho mummy" Abbas d'in ya bawa mummyn amsar tambayanta,fuskar sa cike da murmushi. wayar dataje dashi d'in ya miqawa mummyn "Harta manta wannan ma" "Hmm" mummyn tace tare da miqk'a hannu ta kar6i wayar,sannan ta k'ara da fad'in kaga kuwa bata biyo tanan d'in ba,ta fad'a tana me daidaita zamanta, "kode yasar min wayar tayi garin haukarta ko? Mummyn ta tambaya tana kallonsa Jijjiga kansa yayi alamar a'a. Daddy kam bai kulasu a maganar tasu ba,don gaba d'aya ya tattara hankalinsa ne akan kallon labarai. "Yah gajiyar hanya toh? mummyn tasake tambayar Abbas d'in tana kallon labaran itama. Da Alhamdulillah ya amsa mata. Daganan mummyn tamiqe ta isa ga dinning,Bismillah ta musu tana me k'ara shishshirya wajen da kyau. Abbas ne ya fara mik'ewa tsaye,kallon Daddy yayi sai yaga kamar ma bai san dasu awajen ba gaba d'aya,dan bashi da alamar miqewa,gaba d'aya labarun ne suka d'auke masa hankali,murmushi ya saki sannan ya isa gaban TV d'in ya tsaya k'ik'am ya tare komai,Daddy bazata kawai ya gansa tsaye agabansa,waiwaya wa yayi ya kalli gefensa tukunna kafin ya sawo da kallonsa ga Abbas d'in,dan bai san ma sanda ya bar gefensa ba. Hannu ya ware ya dan k'wali 🖐🏻Abbas d'in dashi,tare da fad'in "kaci gidanku" Dariyah Abbas ya k'yalk'yale dashi,yana kallo, daddyn. "Abinci zaiyi sanyi kuma naga alamar baka da niyyan tashi"Abbas d'in ya fad'I bayan ya tsagaita dariyar tasa. Mik'ewa daddy yayi ya isa ga Abbas d'in,hannu yasa ya kamo kunnan Abbas d'in d'aya yana murmushin shima,fara jan sa yayi ahakan ya nufi gurin cin abincin dashi. Yana kama kunnan Abbas d'in take yayi k'asa ya rage tsayi kad'an, dan ba bak'aramin zafi yajiba.Daddy da k'arfi ya kama kunnan nasa. "Awchhh daddy zafi"Abbas d'in yafad'I tare da dafe kan hannun daddyn da duka hannayansa biyu. Ahaka har suka isa gurin dinning d'in bakin Abbas baiyi shiru ba sai cewa yake "afuwan,afuwan daddy wlh bazan k'ara ba". Daddyn sakinsa yayi har se da suka isa daf da wajen cin abincin. Dariyah suka ji an k'yalk'yale dashi daga bayansu. Daddy dayasan wace mai dariyar ko juyawa baiyi ba yasake kunnan Abbas d'in,dan yasan wannan aikin sai Teemah,dama yamasa hakan nema dan ganin bata nan,datanan da ko farawa bazaiyiamba dan sanin halinta dayayi. Waigawa Abbas yayi inda yaji sautin dariyar,four eyes sukayi da ita,take ta zaro ido waje tare da d'ago hannunta ta rufe bakinta dashi,da gudu tajuya tayi hanyar d'akinta,daman shigowarta kenan,sai taga daddy yana jan kunnansa shine ta tsaya dariyar mugunta. Mummy da tunda taji dariyar itama ta waiga tana kallonta da mamaki."Allah ya shirya"mummyn tace bayan Teemahn ta wuce ciki. Cigaba tayi da zuzzuba musu abincin,tana aikin zubawan ne tace wannan yarinyar akwai shakiyanci wallahi,Zo ka zauna Abbas manta da ita zanyi maganinta ai....... Tahowa yayi yaja kujera ya zauna d'in kamar yadda mummyn tafad'a, yana zama mummy ta tura masa nasa abincin danshi daddy kam ma har ya fara aikawa da su. Bismillah yayi shima yafar ci,kamar yanda kowa dake gurin yayi,amma ga mamakinsa har suka kusan gamawa babu Teemah babu alamarta kuma babu wanda ya damu da rashinta awurin. Baisan cewa su sun riga da sun saba da rashin cin abincinsu batare da ita ba. Gyaran murya yayi kad'an sai yaga duk sun kallo sa. Ganin hakan sai ya d'aga hannunsa ya nuna inda tabi d'azun tare da fad'in wancen yarinyar bata cin abincin ne ita? yayi maganar ne batare da kallon kowa ba daga cikinsu.kuma hakan kenan yana alamta cewa daga bakin kowa ma amsa kawai yake da bukata inda hali. Daddy ne ya d'an murmusa sannan yace "kamanta kaika koya mata?, "Wannan yarinyar ai rainonka ce Abbas"sai da yad'an bud'o idansa kadan sannan yasake fad'in "ta kware yanzu kuwa a wannan tafiyar" Abbas kallon daddy yayi da fuskar mamaki. "Ehh" Daddyn yasake tabbatar masa da abinda ya fad'i. "Tun barinka gidannan Teemah bata bar al'adarta ba na k'in cin abinci da rana ba sai ranar data ga dama take ci. K'asa yayi da kansa yaci gaba da cin abicinsa batare da yayi magana ba. Mummy ce taci gaba da fad'in "Aini bakina har kusan tsayi yayi akan cin abincin nan,sai da naga da gaske takeyi sannan na kyaleta nima na hutawa raina." Murmushi kad'an Abbas yayi acikin ransa yace "zakuwa musa k'afar wando d'aya da ita". Babu wanda yasakeyin magana acikinsu har suka k'are cin abincin. Daddy ne yafar tashi awurin ,yabar mummy da Abbas wanda shima tun d'azu ya ajiye spoon d'insa dan already yaji shi full,amma bai bar kan dinning di'nba illah baya da yayi ya jingina da jikin kujeran dayake zaune akai. Har sai da yaga tashin Daddy tukunna kafin ya dawo da jikinsa kan kujerar da kyau,sannan ya fusaknci mummy. K'asa yayi da muryarsa yanda ba kowa zaiji sa ba. "Mummy " Ya ambata ahankali Kallonsa tayi batare da ta amsa ba,ko dan ganin suna kusa ne oho, "Kardai waccan Teemah ceh"yafad'a tare da nuna hanyar databi d'azun kamar yanda yayi da farko da zai tambaye su ita. 'Daga masa kai mummy tayi alamar "ehh"tana d'an murmushi,daganan tacigaba da duban cikin wayarta data keyi tun da farko. Abbas kuwa baya yayi yakoma ya jinginu tare da lumshe idansa yakuma bud'esu atake. Arannasa yake jinjina al'amari irinna ubangiji da ba'a ta6a yimasa gyara. Tsinkayo muryar mummy yayi tana cigaba da bashi labarin irin rigimar da suka sha bayan wancen tafiyar tasa. Mamaki yaringa ji aransa danshi bai ta6a zaton ma zata jima batare data manta dashi ba,saboda bawani jimawa yayi tare da ita ba alokacin, its just 3month l,bud'an baki yayi yace "lallai mummy kinsah rigima. Murmushi mummyn tayi sannan taci gaba da fad'in aikasan halin yaro sai ahankali, yaro yana da saurin saboda kamar yadda yake da saurin mantuwa,dan idan yaro ya riqe abu akansa zaka samu ba fiya mantawa ba,sai dai idan akayi rashin sa'a ya manta d'in toh kuwa da wuyah yasake tunawa. Jinjina kansa yayi alamar gamsauwa da maganar mummyn,dan kuwa shima yasan da hakan dan baya raba d'ayan biyu yanzu Teemah tamanta da ko shi d'in waye ne agurinta. Koda ya koma d'akinsa ma kwanciyah yayi bayan ya cire rigar da ke sanye ajikinsa,rigingine ya kwanta yana tina yarintar Teemahn, Murmushi yasaki daya tino inda mummy tace wai Teemah tace mummy tak'irashi da yah Abbas ba Abbas ba,So ths stubborn girl bata manta dani da wuri ba kenan,take yaji yana ma son yaganta dakyau, dan duk haduwar da suka yi ba haduwar arzik'i bace tunda yazo gidan.so yake ya ganta da kyau yanzu. Juyi yayi zuwa d'ayan b'angaren hannunsa,ya cigaba da tuno rayuwar da suka yi abaya,muguntar yarinyan nan har yanzu bai barta ba. "Hmm" yace afili sanda ya tuno irin dariyar data k'yalk'yale dashi dan kawai taga daddy yana jamasa kunne. Tashi yayi ya zauna ya d'au wayarsa yak'ira wani abokinsa.sukayita surutusu.Daganan ya tashi ya canza kaya sannan yabi jikinsa ya feshe da turarukansa masu dad'in k'anshi,wayoyinsan yasa hannu ya d'auka,ya fice daga cikin d'akin cikin tafiyarsa mai k'ayatarwa. Gurin habibu ya nufah yaje ya anshi key d'in mota,da kansa yayi driving ya fice daga gidan zuwa inda zashi. *ur comment is* *needed* 👌🏻 _Share pls_ ☝🏻 *Serlmerh* 😍 [10/2, 5:53 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* Dedicated 2 _my family_ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Never let the experiences of your past bring harm to your future. Remember, your past can’t be altered and your future just doesn’t deserve the punishment. 🅿 *8* Teemah kuwa tun fitar ta d'azun bat k'ara fitowa ba,bacci ne yad'auketa bayan tagama dariyar muguntar ta,ita adole in anbarta wai taga babba yanan kuka,"kai daddy ya iyah purnishment tafad'a cikin dariyar,nima fah haka mummy take min inna yi mata laifi,gashi nima yau daddy yarama min,Horhh daddy kabiya ni wallahi" Haka tayi ta sumbatu ita kadai,har tafara jin bacci,takuwa kwanta tayi baccinta bayan tacire doguwar rigar dake jikinta. Ba ita ta tashi ba sai kusan la'asar,tashi ta yi ta watsa ruwa tare da d'auro alwala. Sai da tayi sallar kafin tashirya cikin uniform tafito taahiga kitchen neman abinda zata ci,duk ba wani abin kirki taciba,amma ita tana ganin hakan yafi mata akan ta zauna taci abincin. Koda tagama kale kalen nata a kitchen d'in d'akin mummy taje,bata samera a parlourn ta ba,hakan yasa ta wuce bedroom d'in mummyn,sallah tasame ta ta nayi,amma azaman tahiya take,ganin haka yasa tawice gaban mirror tana k'ara gyara fuskarta da kyau. Tacikin mirrorn ta hanago mummy ta yi sallama,ganin hakan sai ta baro wajen datake tsayen ta taho ga mummyn, "Mummy natafi islamiyah" Kallonta mummyn tayi batare data yi magana ba dan bat so ta yanke azkar d'in datakeyi,sai d'an yatsanta data d'aga ta nuno Teemahn dashi tana d'an juya shi kad'an. "Mummy bacci ne fah ya d'auke ni shiyasa na makara'?" Tafad'a da d'an ta6e baki alamr shagwa6a dan tasan ma'anar hakan da mummyn tamata. Jijjiga kai mummyn tayi kawai tare da d'auke idanta daga kan Teemar. Ganin hakan yasa Teema ficewa daga d'akin,dan mummy ta gama sallamarta. Waje tayi tanufi cikin gidan,tana fita kuwa tafara kwalla wa Habibu k'ira,shima yanaji ya taso da d'an saurinsa ya iso inda taken dan wajen da ake parking motocin gidan ta nufah ita. "Y'ar gidan daddy ganinan ya akayi" Cewa tayi "yauwa malam habibu ka kaini makaranta mana, yau na makara wallahi" baki yakama sannan yace "ta6, "kinga kuwa babu key awurina,shiga ki kar6o key saiki zo mutafi dawuri" Kallonsa tayi sannan tace "toh ina na wurin naka"? "Wannan bak'on ne yafita dashi."Ya bata amsa. "Wai yah Abbas kake nufi?"Tasake tambayarsa. "Oho ai bansan sunansa ba."Zaro ido yayi kamar wanda yaga wani abin tsoro "Kar dai wannan shine Abbas d'in gidan nan"ya yi tambayar yana kallonta. "Ehh wai shine inji mummy"itama ta bashi amsa. "Baki habibu ya sake kamawa cikin tsananin mamakin gani wannan murd'ad'd'en ne wai Abbas,ta6d'i" Habibun ne yasake cigaba da fad'in "Abbas ne yayi irin wannan girman h............. Kafin yajai ayar magabar tasa sukaji adanno horn daga wajen gidan,da gudu mai gadi yaje ya lek'a sannan yadawo da kansa ciki ya wangale get d'in. Ahankali motar ta shigo tazo tayi parking gefe dasu kad'an, Habibu ne yace "yauwa gashinan ma yadawo" Teemah kam batayi magana ba illah ido data tsurawa motar. Tsawon mintina biyu da tsayuwar motar sannan taga anbud'e marfin motar,ta 6angaren da suke tsaye,ita da habibun. "Wow" Tace azuciyarta tareda kwalalo ido waje tana kallonsa. Gani tayi yayi kyau da sky blue d'in shaddar dake jikinsa tare da farin glass a idonsa,iyah abinda ta lura dashi kenan ajikinsa amma ba k'aramin kyau yayi mata ba. Abbas kuwa tun tsayu warsa agurin yake kallon su hannunsa nakan stairy,kallonsu yake musamman ma ita, tare da mamakin tsayuwar uwar me take yi awurin,gashi jikinta sanye da uniform. Dayake tinted glass ne da motar shiyasa babu wanda ya hangosa,motar daddy ce dayafi amfani da ita,duhun glass d'inne yahana su ganshi ,duk da lura da yayi duk hankalinsu naga motar dayake d'inne da alama duk ak'age suke suka fitowar tasa. Hakan ne yasa shi fitowa. Yana fitowa bayan ya maida k'ofar ya rufe, gurinsu yanufah direct,hannu yad'aga sama, tana ganin haka ta rintse iso da k'arfi,dan atunaninta sauk'ar mari zataji,murshi yayi dayaga yanda ta tsorata d'in,sai ji tayi yakam kunnanta irin yanda daddy yamasa,harya fara tafiya sai kuma yajuyo,yah wullo wa Habibu key d'in motar,sannan yacigaba da tafiyah. Cafe key d'in Habibu yayi sannan yacigaba da kallon bayansu tunani yake aransa taya akayi wannan yazama Abbas? Abbas ai bay kyashin yiwa mutane magana,amma wannan sai zafin kai,d'azu da kar6ar abu zaiyi awurina ai yamin sallama,amma ganshi yanzu ko kallon arzik'i ma bansamu ba,ballantana sallama. acewarsa fah😏 Teemah kuwa Zafi taji kamar tayi tsallen wahala,harda guntun kwallarta,shikuwa k'in sakinta yayi har se da ya isa d'akinsa yatura k'ofar bayan sun shigo,sake kunnan nata yayi,sannan ya tsaya agabanta yana k'are mata kallo. K'asa tayi da idanunta tare da turo baki gaba,hannunya d'aya kuma na sama kan kunnan tana shafawa ahankali, "Mugu" tace acikin ranta Uniform d'in jikinta yasakr kallo,dayake yamma ne,yasan sai dai na islamiya,. Gyara tsayuwa yayi yan kallon nata sannan yace "Anan ake islamiyar ko? Kanta ta jijjiga batare data d'ago ta kalleshi ba,dan muryarsa har cikin kanta take jinsa,lion voice ne da shi mai ratsa jiki,musamman yanzu da yake maganar da ita ,sosai yanayin muryar tasa ta ratsa ko ina ajikinta.take tsoronsa ya shigeta. "Toh tsayuwar me kike yi agun kuma? Yasake jeho mata wata tambayar. Kasa magana tayi dan wannan tambayar bayyanan niyar amsa take da buk'ata.ita kuma sam bazata iya furta komai ba. Yawan hawayenta taji yaqaru akan d'an guntun dayake mak'ale tun d'azun,ta ke suka fara sintiri akan fuskarta. Kallonta yayi da mamaki aransa yace "lallai yarinyar na bazata canja ba" Juyawa yayi yafara tafiyah sannan yace "jeki" Tanajin haka ta juya da sauri ta fice daga d'ajin. Gurin mummy taje ta sameta a babban parlour, fad'awa jikin mummyn tayi tana kuka mai sauti,hankalin mummyn ba k'ara min tashi yayi ba da jin kukan da Teemahn keyi ba. Dan a zatonta ma tuni Teemahn ta tafi islamiyar. Dakyar ta samu tayi shiru sannan ta tambaye ta dalilin kukan, bud'e baki teemah tayi sannan tace '"bawan nan yayan bane yakama yayita jan kunnena ba,kuma ni babu abinda namasa". Tsaki mummyn taja kad'an sannan ta kauda kanta daga kallon temmahn "Yah kyauta ai,bake rashin ji ba" Shine harda zuwa kisani agaba da irin wannan kukan Teemah"? Ke kinmanta d'azu ba dariyarsa kika yi tayi ba dan iskanci"? Baki teemah ta turo gaba jin mummy bata goyi bayan ta ba. "Toh islamiyar fah? Mummyn tsake tambayarta. Teema ta bud'e baki zatayi magana kenan sai idonta ya hango mata mutum atsaye daga bakin k'ofar shigowa parlourn. Suna had'a idanun da ita sai ya ce "Assalamu alaikum" Mummy ce kawai ta amsa masa sallamar tasa.Teemah kam kyautar harara ta bashi,amma sai yayi kamar bai gani ba,hakan yabata damar cigaba ta hararsa har ya iso gefensu ya zauna. Gaida mummy uayi bayan ya zauna,daganan suka cigaba da hirarsu da mummy babu wanda yasake bi takanta. Haushi kamar ta sa hannu ta buge sa,abinda ya zaunar da ita ma jin da tayi suna hirar su Hannah ne lil sister d'inshi,da badan hakan bama da tuni tabar inda suke d'in, Ji tayi hirar tafar dawowa kanta,abin sai yafara bata haushi,wai ita ai ta tsaya canje canjen makaranta ne shiyasa har yanzu bata yi nisa ba ga Hannah nan tana SS2 yanzu,mummy ne tafad'i hakan jin datayi cewa wai Hannah na SS2 daga bakin bakin Abbas. sannan tak'ara da fad'in ai Daddyn naku ne ma dayake biye ta wlh duk laifinsa nake gani" Ga dukkan alamu dai wannan abin ya sosa ran mummy, dayake daman tun sanda sukeyin abin tana tsananin jin haushi,ganin cewa duk makarantar da aka kaita sai tace wai bai mata ba,ba taso,daddy kuwa yabiye mata ya canja mata wani da kyar akasamu ta zauna awannan d'in da ke yanzun,kusan makarantu hud'u tacanja. Teemah najin haka ta mike ta fice daga d'akin afusace. Dan tasan anta6o mummy kenan indai akan makarantar tace. Binta suka yi da kallo dukkansu kowa da abinda ke ransa har ta 6acewa ganinsu.sannan suka ci gaba hirarsu. Ita kuwa tana shiga d'akin ta fincike hijab d'in da ke kanta tare da rigar sanna ta cire wandon ma duk ta watsar dasu,sai kace sune sukayi mata laifin. *share pls,nd ur* *comment is needed* 👌🏻 *in ba* *haka ba zan d'au* *hutu* . *Salmerh* 😍 [10/2, 5:53 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* Dedicated 2 *Safiyyah Aliyu* *Wakili* . & *Khadija candy* I heart u guys tnx 4 ur luv nd suppoart_ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* A Mistake increases your experience & experience decreases your mistakes. You learn from your *mistakes* and then others learn from your *success* .👌🏻 🅿 *9* Zama tayi abakin gadonta daga ita sai pant da bra ranta amatuk'ar 6ace,asama take jin ran nata,"wai wannan shine yah Abbas d'ina kuwa anyah? "Ayanda mummy take fad'a min ai yah Abbas baya min mugunta,amma shi wannan daga zuwansa gidanmu har ya iyah bayyana nashi salon muguntar,kamar fah yasan abinda nafi tsana kenan arayuwa ta wannan jan kunnan,don ko mummy duk ranar da ta min ma wuni nake bana kulata,shiyasa ma ban fiyah yin abinda nasan zai sa ta min irin hakan ba,sosai nake kiyayewa,Ai kuwa da daddy zan had'a shi ya ramamin abuna. Murmushi ne ya kwace mata dalilin tunowa datayi da sanda daddy ke jan kunnansa, "Allah shi kara" Tace afili.harda cije bakinta irin na muguntan nan. Daga nan ta ta shi ta nemi kaya tasaka sannan ta fito tasamu Mummy da Baabah Lami a kitchen ko kulasu ba tayi ba,ita adole fishi take yi an mata ba daidai ba,mummy ma ko inda take bata kallah ba,Sai Baabah Lami ce ma tayi mata magana,ita ma maganar tata k'ara 6ata ran Teemahn yayi, dan cemata tayi "Fatun daddy ya akayi ne naga kinata shan k'anshi haka? Bata kulata ba sai baki data k'ara turowa,dan ta tsani wannan sunan wai "Fatu," Fuuu......ta juya tafice daga kitchen d'in aikin da batayi ba kenan,daman mummy ce tace matuk'ar tana gida lokacin yin girki yayi toh dole ne tashiga kitchen d'in ayi da itah,shiyasa yanzun ma ta zo,toh amma tun kan ma takama aikin Baabah Lami ta kunnata dayake daman a 90 take,kuma dama tun asali ta tsani "fatun" nan, abakin Baabah Lami kad'ai tafara jinsa kuma suna yawan shan rigima da baabah Lami d'in akan sunan,kwanaki harta da'n daina fad'ar sunan sai gashi kuma shi yau kuma ta tuno dashi,kawai sai ta fake da hakan k'ara gaba abinta,dama ba son yin girkin takeyi ba tsoron mummy yasa tafito. Murmushi mummyn tayiwa Baabah Lami tana kallon fuskar ta tace "kin k'ara rura mana wutar kuma ai inaga" "Aikuwa dai,naga alama"cewar Baabah Lami d'in tana d'an dariyah. Mummyn ce ta k'ara da cewa "fushi takeyi wai yanzun da yayanta,amma inaga abin kowa ma bai tsirah ba." Murmushi sukayi dukkan su,daga nan suka ci gaba da sabgoginsu akitchen d'in suna yi suna d'an ta6a hira jifa-jifa. Basu k'ara had'uwa ba sai bayan isha'i,dasuka zo cin abincin dare,Nan ma mummy tace taje maza tak'ira shi. Tana jin abinda mummy tafa'da ta fara bubbuga k'afafu ak'asa,tana fad'in "haba mummy shi wai bazai zo da kansa ba sai ank'irasa"? Tsawa mummy ta daka mata "bana son rashin kunyah Teemah,aiken nawa ne bazaki ba ko kuwa shid'inne kika fi k'arfin ki k'irashi" Tana jin haka ta juya ta fara tafiyah zuwa d'akin nasa, "mthww" mummy taja tsaki biyan tajuya d'in, ita kuwa haushi kamar ya kasheta sai mita takeyi k'asa-k'asa ahankali "wlh mummy duk so take yi ta zubar min da ajina agun wannan mutumin😅,so take ya raina ni gaba d'aya.(kujimin yarinya fah🤔😏) Bakinta kuwa kamar na 6era tsabar yanda ta turo shi gaba. Duk da ran mummy a6ace yake,amma bata kasa fahimtar yanayin Teemahn ba,kuma duk tasan bazai wuce akan abinda yafaru d'azun bane,take wannan abun. Haka taje k'ofar d'akin ta tsaya daga waje tana knock in d'in k'ofar,jitayi babu wanda yace mata ko cikanki ne,sake bugawa tayi da 'dan k'arfi,amma still shiru taji, babu alamun ma anjita. Hakan yasa ta tura k'ofar azuciye,tashiga cika batare ma da sallama ba. Gani tayi yanzun d'akin da haske ba kamar d'azu da ta zo ba. Ta6e baki tayi tare da rarraba idanu ad'akin dan bata ga alamar mutun ba aciki.Komai nakin tsaf dashi tagani,babu gurin data isa ta kushe ad'akin,sai uban k'anshin turarensa mai dad'in shak'a. Ita kuwa dan iskanci sai ta d'aga hannunta ta toshe hancinta da su,harda ta6a fuska,adole wai turaren bai mata ba ita. Dai dai shima yabud'e k'ofar d'akin ya shigo,ga mamkinsa sai yaga tana toshe hanci,k'arasa shigowa yayi a mamakance idonsa na kanta,so yake yaji menene dalilinta na toshe hanci a muhallinsa,tunda yasan bai bar komai ad'akin da zai sa har aji wani abu makamancin wari ba,dan ko bayin dake cikin d'akin ma atsaftace yake,ko abinci inta kama sai ka iyah ci aciki,balle ma shi bayaga wanka babu abinda ya had'a sa da bayin tunda yazo gidan sai ko alwala. Bin d'akin ya sakeyi da kallo akaro na biyu sannan ya kalleta, wuri-wuri tana rarraba idanu,taku yad'anyi kad'an zuwa inda take,tana ganin haka tayi baya itama da sauri,ganin haka sai ya tsaya a inda yake d'in. "Wani isakanci ne yasaki toshemin hanci ad'aki?" Dan sosai abin yaba shi haushi,ba k'aramin cin fuska bane yin hakan ga wani,babu wanda zai so ace anji wani abu da ya danganci hakan a inda yake rayuwa,balle mutun irin Abbas da tun tashinsa da tsafta aka sanshi,tun yana yaro ya tsani k'azanta..................... "Ba tambayarki nakeyi bane" Ya fad'a atsawace dan jin bata amsa masa tambayar farkon ba. Muryarsa na razana ta amma,dan jikinta har rawa ya fara,amma haka ta dake ta bashi amsa da "d'akin yana wari ne" Ranshi a6ace yake amma baisan sanda ya zaro idanu waje ba tsabar mamaki, "Wari kuma.......? "Warin me toh? Ya tambayeta. " *Turare* " Ta bashi amsa kanta tsaye. Tsabar takaici kasa yin magana yayi,illah kallon daya bita dashi,amma dai yad'an ji nutsuwa datce warin turare ne,abin takaici kuma har yanzu bata bar toshe hancin ba. Gani da yayi still tana rufe da hancin ta ai sai ya yunkura zai kamota,tana ganin ya nufota kuwa ta juya baya,dagudu tabar d'akin,cikin sa'a ma abud'e tasamu k'ofar,dan mamakinta ne yasa daya shigo ko k'ofar bai mayar ya rufeta ba,shiyasa tasamu sauk'in gudu,fit ta fice abinta batare da ta tsaya jan k'ofar ba. Sai da ta tsaya wani lungu ta daidaita numfashinta kafin ta isa wurin mummyn, "Mummy wai yana zuwa" "Uhm" mummyn tace sannan ta k'ara. Da fad'in yakin da'de, "Bansame shi ad'akin bane mummy" tafad'a kamar wata mumina, dan ji take ranta wasai yanzu dalilin wannan abin data yimasan. Shikuwa bayan fitar ta ad'akin sai yaje ya tura k'ofar tare da fad'in "useless kawai" sanin da yayi wa kansa, k'anshi ko wari ko yaya suke kuwa sai ya jiyosu indai wad'annan abubuwan ne,bata isa ta nuna masa jinsu ba. Dawo wa yayi cikin d'akin yatsaya ya sake k'arewa ilahirin d'akin kallo,sai kuma yayi murmushi, "zan had'u da ke ne yarinya" afili ya fad'i hakan sannan ya ka'rasa bakin gado ya ajiye wayarsa. Shima ya zauna ya fara 6alle botiran rigarsa, har ya kusan 6allewa sai kuma ya tuna k'ila aikota akayi, tunda yanzu lokacin cin abincine agidan kamar yadda yasani tun ada, take sai ya mik'e ya fice daga da'kin. Ya nufi main parlour................. Drop ur comment pls readers🤞🏻,inkuna son ku faranta min🙈 *Salmerhn* 😍 ku ce 👌🏻 [10/2, 5:53 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* Dedicated 2 _Friendy like no_ _other_ ....... ( *Mamee Hafsat* *Ndahi) I hrt u baby* *girl* ._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Ego is just like a dust in the eye ….... without clearing the dust you can’t see anything clear........,. *so clear* *the ego* *and see the world.* 🅿 *10* A dinning ya same su gaba d'ayansu har daddy amma basu fara cin abincin ba har yanzu,da alamu jiransa suka tsaya yi. Teemah na ganinsa tafara zare idanu tayi k'asa da kanta sarai tasan tayi masa laifi kuma bata kyauta ba,don babu wanda zai so a kushe masa muhallinsa ballantana ma ita na raini tayi. Ko kallon inda take ma baiyi ba yaja kujera ya zauna tare da yiwa su daddy barka da gida. Amsawa sukayi daganan suka yi bismillah auka fara cin abincin su. Teemah yau kam har mamaki ta bawa iyayenta ganin yanda ta ke cin abincin,ita kuwa cin k'arfin hali ta ke yi,don so take ta riga kowa barin kan table d'in tagudu d'akinta ta kulle kafin yah Abbas ya cafkota. Kusan duk kaiwa spoon d'inta baki toh sai ta kalleshi,amma ko sau d'aya basu ta6a had'a idanu ba. Taci abincin yakai rabin plate sannan ta tashi awurin tsam ko sallama bata musu ba. Babu kuwa wanda yah tankata dan mamakin da ta cika su dashi,Abbas kuwa ko ajikinsa,cin abincinsa yake yi cikin kwanciyar hankali,yi yayi kamar bai san ma da ita awurin ba,koda ta mik'e d'in kuwa k'in d'aga kai yayi ya kalleta, amma tak'asan ido babu abinda ya wuce wa ganinsa,ta k'asan idanu yake ta kallon duk abinda takeyi harta gama ta tashi d'in. Tashin bata wani dad'e ba shima yaji ya k'oshi hakan yasa ya wa su mummy sai da safe ya wuce abinsa. Ita kuwa Teemah ruwa ma sai data bi kitchen ta d'auka sannan tawuce d'akin ta da shi,tana shiga kuwa ta danna key tana Hamdala,murna fal cikinta dan tana ganin ai ta tsira. Ruwan tasha ta ajiye ragowan agefen gadonta,sannan ta d'an rage kayan jikinta,school bag d'inta ta d'auko ta dawo ta hau tsakiyar gadon ta barbaza takardu wai nan karatun Test takeyi,batajima ba ta fara hamma,minute-minute kuwa hamman ke zuwa,tsaki tafar jerawa itama aduk sanda tayi hamman,haushin wannan cin abincin datayi yau sosai d'in nan takeji, "ai duk wannan mutumin nan ne yasani" tayi maganar azuciyar ta tare da biyoshi da wata doguwar tsuka. Takai 1hr tana karatun sannan ta tattare shirgin takardun akan gadon,daga nan tayi addu'a adaddafe ta kwanta. Washegari tana tashi kuwa sai da tayi sallah kafin taje ta yi wanka,zaman shafa mai tayi bayan ta fito daga bayin,sai da ta gama goge jikinta tukunna ta kai hannu ta d'auko man nata datake shafawa kullum. "Awsh namanta ashe ban fad'a wa mummy ba" tafad'i tare da dafe goshi. Da kyar tasamu tashafa man kasancewar babu ya k'are acikin robar,shiri tayi cikin uniform d'inta,tafito ta nufi d'akin daddynta,dayake daman idan daddy yana gari shi take fara zuwa gaisarwa kafin mummy,gani tayi baya nan,hakan yasa ta fito ta nufi d'akin mummy. Daddy kuwa tafiyace tasame shi ta gaggawa,tafiyar bazata dan jiya kusan 10:15pm aka k'ira shi,Allah ma yasa yana da passport d'insa ,so tun adaren ya k'ira yayi booking flight,6:30am yabar gidan,kasancewar 10:00am zasu tashi. Gaishe da mummyn tayi sannan ta tambayeta "ina daddyn ta yake? "Yayi tafiya ne" Mummyn tabata amsa. Sai cewa tayi "aida ya fad'a min ma da da tare zamu" Kallonta mummyn tayi da mamaki sannan tace "Toki bishi mana,ai baki makara ba" Dariyah tayi kad'an "Allah kuwa mummy da binsa zanyi da nasan zaiyi tafiyah,in bahaka inaji ina gani zaman gidannan sai ya gagare ni saboda wannan........,.......sai kuma ta kasa k'arasawa. Mummyn ce takar6e zancen da fad'in " ahh toh in juninki rashin kunya ne da tsokana aikuwa ba ruwana ni,dan ni nawa ido" "Mummy hakama zakice"? "Toh me zance Teemah? "Bake rashin ji kika ce shine halinki ba? Fushi tayi data gama jin abinda mummyn ta ce. Tea kawai tasha shima sama-sama daga nan ta tashi tsaye. "Mekenan" mummyn ta tambayeta tana kallonta. "Ni na k'oshi mummy" D'auke ido mummyn tayi daga kallonta kafin tace "Ke kika sani ai",kije jakata bak'an nan ki d'auki Kud'i aciki" fara tafiya Teemah tayi zuwa d'akin mummyn sai tajiyo muryar mummyn na sake fad'in "Kuma yanda kika saba tafiyah dashi zaki d'auka, bance ad'auki harda na shan kayan zak'i ba,sai wata yayi ki takura min da fitina" Karaf akunnen Abbas da shima ya zo dan ya gaida mummyn. Kuma atake ya fahimci me mummyn take nufi,mamaki yafara yi ashe yarinyar nan har haka ta girma amma shine bata da wayo har yanzu? Da wannan tunanin ya k'arasa inda mummyn take,tana ganinsa kuwa ta sake fuskarta dan mummy ba dai son jama'ah ba,sam bata da wannan al'adar ta k'in dangin mijinta. gaida ta yayi shima,sannan yad'an zauna kamar mai jiran wani abu, nan kuwa zaman jiran fitowar Teemah yakeyi agurin. Koda mummy ta masa maganar break fast d'inma cemata yayi a'a bayanzu ba sai zuwa anjima zai ci. Teemah da batasan da shigowarsa ba,tafito kenan daga d'akin mummyn taganshi zaune, Turus taja ta tsaya dan jitayi zuciyarta ta tsinke daganin nasa,dayake baya ya juya mata,so bai ga fitowar tata ba ,mummy ce dai ta lura da ita,kallonta tayi suka had'a idanu take sai tayi k'asa da kanta kamar mara gaskiya. Dayake kuma daman da rashin gaskiyar,sai ta taho ahankali izuwa inda suke d'in. "Ina kwana yayah " Sai da ya d'an juya kansa sannan ya kalleta, dan bata gama k'arasowa daf dasu ba ta masa gaisuwar, "Lafiya"ya amsa mata dashi,sannan ya dawo da kansa saiti suka ci gaba da maganar su da mummy. Tana ganin haka ita kuwa tafice taje dakinta ta d'auko school bag d'inta sannan ta dawo zata wuce, gani tayi yanzun baya zaune awajen, mummy kad'ai ne azaune, "Na tafi mummy" Tafad'a sanda take gyara zaman jakarta akan kafad'arta. "Adawo lafiyah" kawai mummyn tace mata. Harta fita sai kuma tadawo tasake dawowa ta tsaya daga bakin k'ofa tace "Mummy mai na ya k'are fah" D'aga kai mummyn tayi ta kalleta batare da magana ba. Teemah kuwa ta juya tafita abinta don tasan ai mummyn taji me tace d'in. Tana isa wajen motar da za akaitan aciki taganshi a mazaunin driver. kasancewar Habibu ne yakai daddy maiduguri inda zai hau jirgi, da kyar ma in sun isa yanzu ballantana ayi zancen dawowa. Turus tayi taja ta tsaya tana k'are masa kallo. kusan minti biyu shima dagangan yak'i yi mata magana,sai da yaga bata da niyyan shiga ne sannan yace mata "U ar just wasting ur time,let me tell you,ni inada abinyi" Bai kalli inda take ba yayi maganar hannunsa d'aya kuma na kan stairy. Ahankali ta ta ko tazo jikin motar,tana k'ok'arin bud'ewa tashiga ta tsinkayo muryarsa yana fad'in "Habibu kika gani ne acikin motar? Sarai tasan me yake nufi amma sai tayi kamar bataji sa ba harta bud'e k'ofar tana k'ok'arin shiga sai taji wani uban tsawan da ysa take ta firgita ta,balle daman muryarsa razana ta take. Dawani irin b'acin rai yayi maganar "bana son rainin hankali fateema,sa' anki ne ni? Ai tana jin muryar tasa jiki na rawa ta rufo k'ofar ta dawo gefensa tashiga ta zauna. Wani guntun tsaki ya sake sannan yaja motar,wani uban horn yadan na tun kan su isa bakin get d'in,da gudu mai gadi yaje ya bud'e musu suka fice agidan. Bai sarara da gudun ba har saida ya dangana da babban titi kafin nan,kasantuwar bai san inda makarantar ta ke ba,kallon ta kawai yayi sai yaji tace "NANA AISHA" Aransa yayi murmushi dan yanda yaga tsoro kwance akan fuskarta"ga shegen tsoro ga rashin kunya,afili kuwa ko kad'an babu annuri akan fuskar tasa. Daya ke yasan gurin sai bai k'ara ko kallon inda take ba ballantana magana har suka isa,yana yin parking ta fita da sauri tare da rufe k'ofar da iyah k'arfinta kai kace yau ta fara shiga mota,shigewa tayi ciki abinta batare da tasake ko waiwaye ba,bayanta yabi da kallo yana k'ara mamakin duk ina wannan yarinyar ta koyi rashin ji haka,komai na rashin ji salo-salo ta iya su,inbadan mummy tasani ba ma ke kinsa ne na kawo ki makaranta (Kunji yamanta da shekarun baya😅) Jan motar yayi ya shiga cikin gari,bai dawo ba har sai kusan 12na rana. 12:56pm Mummy ce tsaye ajikin mota abakin makarantarsu Teemah tana jiran tashinsu,dayake cewa Abbas tayi ya kaita idan ta tashi zata bi ta 'akota tunda ita zata yi,shiyasa bai koma d'auko tan ba,hakan ma mummy tana ganin kamar ta takurashi amma bata fad'a masa yaji ba aranta ne take jin hakan. Abbas kuwa baisan dan hakane mummyn tace masa zata bi tad'auko tan ba,daya sani kuwa bazai barta ita taje d'in ba. Bata wani dad'e agurin ba aka tashe su,tana ganin hakan sai ta koma cikin motar ta zauna saboda hayaniyar yara da kuma k'ura,kuma atunaninta ai Teemah tasan motar gidansu inta ganta ai zata ganeta. Teemah ma bata san cewa mummy ce tazo tafiyah da ita da ba,bata fito da wuri ba sai da kusan rabin d'aliban suka wuce kafin ta fito, kuma koda ta fito data fito d'inma sai ta wani d'auke kanta daga ganin motar,dan ta zaci Abbas ne yazo yanzun ma. Bakin titi ta nufa da niyyan taran adaidaita amma cikin rashin sa'a sai bata samu ba,don gaba d'aya d'alibai sun tashi yanzu,kuma a irin wannan lokacin samun abin hawa wahala yakeyi,gashi ana zabga rana. Wasu ne 'yan mata su biyu suka zo inda take tsayen,'yan class d'insu ne,suma napep zasu hau,anan suka tsaya surutu,ranar ne yafara isanta,dan tun tana jurewa harta ji inaah bazata iyah ba,da gefen ido ta kallo motar,ga mamakinta sai ta hango mummyn ta zaune aciki. Take taji wani farin ciki ya lullu6eta........ *Drop ur comment* *nd share pls* 👌🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 5:54 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Wannan page d'in_ _naku ne ku_ _d'ai_ 👌🏻' _yan_ *CAPTAIN* *ABBAS FANS* *2* , _inajin_ _dad'in comment_ _d'inku har_ _6argona......__ 😍 *Bismillahir* *rahmanir raheem* Worry is a total waste of time. It doesn’t change anything. All it does is steal your joy and keep you very busy doing nothing. 🅿 *11* Da saurinta ta isa gurin motar,alokacin ma mummy hankalinta harya fara tashi da rashin ganin Teemahn,tana k'ok'arin fitowa kenan ta duba ta dakyau,sai taji muryarta ta k'ira ta "Mummy" Da sauri mummyn ta d'aga kanta ta kalleta kana tace "Haba Teemah a ina kika tsaya fisabilillahi? Karkata kai Teemahn tayi gefe tayi kalan tausayi, Mummyn kuwa tacigaba da fad'in "Wato dama haka kike wa Habibu idan yazo d'aukarki ko kisashi yayi ta jiranki ko? "Ahh fah mummy ni na _d'auka_ wannan yayan ne shiyasa fah nak'i zuwa" Haushi mummy taji dajin abin nan data fad'a d'in,gata gwanar fad'ar gaskiya bata fiye 6oye al'amarinta ba ita. Cikin jin haushi mummy ta bata amsa da " toh ai sai ki _ajiye_ da kika ga bashi d'in bane kuma" "Sorry my mum" cewar Teemh ta fad'a tana zagawa d'ayan b'angaren ta inda zata shiga motar. "Wato ke bazaki bar raini da mugun halinkin nan ba ko? Mummyn ta ce bayan Teemah ta shiga motar "Shiru tayi bata yi magana ba. "Inda Abbas d'inne kenan haka zaki shanya shi? Waini sa'anki ne shi d'in? "Kalli time fa Teemah kusan 1:30 amma sai yanzu zaki taho,kinsan tun yaushe nake anan d'in inaji ranki? "Allah mummy bansan ke bace kika zo da bazan dad'e ba. "Hmm"Allah ya shiryeki " Kawai mummyn tace tare da yiwa motar key,sun iso daf wad'ancan friends d'in Teemahn sai Teemah tace "mummy sabon pegi" tafad'a tare da nuno su. Tsayawa mummyn tayi,Teemah kuma tayi musu magana suka shigo dan har yanzun basu samu abin hawa ba. Gaida mummyn suka yi ta amsa musu cikin sakin fuska daganan ta d'auki hanyar sabon pegin,ba hanyarsu bace amma haka sai da ta kaisu har k'ofar gidan su da taimakon kwatancen da suke mata,har suka isa,godiya sukayi mata sannan suka shiga ciki dan dukkan su 'yan gida d'aya ne. Daga nan mummy ta juyo ta nufo hanyar gidansu dake Nyanya Quaters gujba road Damaturu. "Allah mummy gwanda da kika zo,d'azu da wannan yayan yamin wani tsawa har sai da naji fitsari. "Wataran ma ai har dukan ki zaiyi inde kika ce juninki rashin jine" "nifah babu abinda namasa mummy" Bata kulata ba,dan tasan koma me zata ce toh 6ata bakinta takeyi abanza kawai dan Teemah baji takeyi ba. Horn mummy tayi aka bud'e mata get d'in tashiga. Da sallama suka shiga parlourn,babu kowa aciki dan haka kowa yanufi d'akinsa. Teemah na shiga ta fara ciccire kayan jikinta,sai da taga tacire komai sannan tafad'a kan gado tare da fad'in "wash wallahi nagaji" takai tsawon mintina biyu akwancen kafin ta mik'e tsaye Towel ta d'auka akan k'ofar bayinta ta d'aura sannan tayi unhooking bra d'in jikinta ta ajiyesa,ta nufi k'ofar fita,harta kusan fita daga d'akin sai ta tuna abinda ke jikinta dawowa tayi sai kuma ta tsaya ta fara kwalla k'iran Baabah Lami,bakinta uku taji shiru babu amsa sai ta d'auki hijab d'inta ta saka sannan ta fito,kitchen ta shiga ta d'auko ruwan goran c'est,garin fita daga kitchen d'in ne ta had'u da Baabah Lami ita kuma tana k'ok'arin shigowa kitchen d'in. "Baabah Lami inata k'iranki kika k'i kulani" "Yi hak'uri fatee,naje wurin hajiya ne, "Owk dama ruwane kuma ma kinga na d'auko abuna" "Babu wani abinda kuma kike buk'ata? Baabah Lami d'inne ta tambayeta da dukkan kulawa. "Ah ah bakomai " Teemahn ta bata amsa. Daganan tawuce d'akinta da ruwan ahannunta,tun kam ta k'arasa cikin d'akin sai ta cire hijab d'in ta rik'e a hannunta, zama tayi akan side drwaer d'inta ta d'aga goran ruwan takafa abakinta,dan ko kofi ma bata d'auko ba,sai data sha kusan rabi kafin ta rufe ta ajiye "Gaskiya yau kam masha Allah akwai zafi" Wanka ta tashi ta shiga kusan 20mins tana bayin sannan ta fito,wajen dressing mirror ta nufah tana goge jikinta,sai yanzu taji d'an dama dama,domin ruwan sanyi tahad'a tayi wankan dashi,shiyasa take so tad'an shafa mai koda ak'afarta da hannunta ne dan kar suyi mata wani iri. Har taje ta tsaya gaban madubin sai kuma ta tuno ashe man nata ya k'are gaba d'aya,ai kawai sai ta fito ta nufi d'akin mummy ahakan datake,shaf ta manta da batun wani Abbas agidan shiyasa take al'amuranta cikin sake wa kamar yanda tasaba. Sallah tasamu mummyn nayi take ta tuna ashe fah batayi azahar ba itama. Zama tayi tajira mummyn harta idar sannan ta tambayeta batun man shafuwan. Mummy cewa tayi "aini mantawa nayi ma gaba d'aya,ki bari da yamma zan aika asiyo miki" "Toh" tace sannan tamik'e da niyyar fita daga d'akin, "Teemah"Mummy tak'irata tana daga zaune akan sallayar datayi sallahr. "Na'am"ta amsa tare da juyowa "Kindai san yanzu bamu kad'ai bane agidan nan ko? "Kai ta d'agawa mummyn alamar "ehh" "Toh ki daina fita da irin wannan shigar dan Allah." "Toh mummy yan zunma mantawa nayi ne kuma dana fito ma ban had'u da kowaba" "Ki dai kiyaye" "Uhm" Teemahn tace sannan ta fito daga d'akin. Bata lura dashi ba har sai da tazo tsakiyar parlourn sannan taganshi,abu yake k'ok'arin d'auka a gefen TV,jitayi kamar tajuya tunda bai ganta ba,amma kafin tayi yunk'urin juyawan har ya d'ago daga inda yake tsayen. Salati tafara acikin zuciyarta dataga yakafeta da idanunsa,ko kyaftawa bai yi,shikenan wannan mutumin yau kan nashiga uku ahannunsa,tun daga k'afarta yafara bi da kallo ahankali har zuwa cinyoyinta,dayake towel d'in k'arami ne sosai sai hakan yabashi damar kallon surar jikinta da kyau. "Masha Allah" yace azuciyarsa,yarinyace amma babu laifi take yaji wani sabon yanayi yana ratsa shi ta ko ina. Ido yad'aga ya kalli fuskarta sai suka had'a idanu,kunyar ganin jikinta da yasan tasan yayi ne yasashi d'aga k'afafu ahankali ya tunkari inda take,itama kuma da tayi ya fara nufo inda take tsayen, sai ta rintse idanunta da k'arfin gaske jikinta har rawa yakeyi."wayyo Allah nah" take ta nanatawa acikin ranta. Daf da ita yazo ya tsaya ya wani k'ank'ance idanu kamar gaske bayan yagama morewa kallonta. Har ya d'aga hannu zai kamo kunnanta sai kuma yafasa ya mai da hannun nasa k'asa,dan yana ganin kamar idan ya mata hakan zai iya sawa d'an guntun Towel d'in dake jikinta ya kunce saboda yanda yaga duk jikinta na rawa abin har yaso bashi dariyah,amma sai yayi murmushi kawai,"shegen tsoro da rashin kunyah duk ta tara". Jin shiru datayi bayan ta riga ta tabbatar da ya iso inda take tsayen,dan tanda tashi alamun mutun agaban,tsammanin sauk'ar mari tayi amma sai taji shiru 6ud'e ido tayi ahankali. Sai taganshi tsaye agabanta yana sake kallon k'asan wuyanta. Baya ta d'anyi da sauri tare da bud'e idanun gaba d'aya. Matsawan datayi sai ya bada gaf mai d'an tsayi atsakaninsu. Kuma sai hakan yasa taji wani k'warin gwiwa ya shigeta. "Ba kijin magana ke ko? "Nan d'in gidan iskanci ne aka gaya miki" Ya fad'a da wani serious tune kamar gaske nan kuwa rasa abin fad'a ne yashi cewa hakan. Batayi magana ba illah kallonsa data keyi itama kamar yadda ya k'ureta da idanu. "Kunnan k'ashine da ke ko" Hannunta ta d'aga ahankali ta sada shi da kunnanta, ta6a kunnan tayi,kamar wanda batasan da zamanshi ajikinta ba sai yau. Jitayi kunnan da laushi.Sai ta sauk'e hannun nata. "Tambayarki nake kin min shiru" Ya sake daka mata tsawah. "Kunnan k'ashi ne dake nace ko"? Yafad'a awani hasale. Jijjiga masa kai tayi tana kallonsa, "Umhm" ya sake fad'i. "Kunnena bana k'ashi bane "! "Toh menene? Ya sake tambayarta shima. "Na nama ne " Ta bashi amsa. Ji yayi dariya takamasa sosai,da kyar ya samu ya tsare,amma saida ya d'an kalli gefe da gefen sa sannan ya samu ya basar ,maida dariyar yayi tazama murmushin gefen baki. "Zan kuwa koya miki hankali yau d'in nan" Yafad'a yana me k'ara nufar inda take, Ai da gudu tayi hanyar d'akinta,tana shiga ta tura k'ofar ta rufe ta jinginu tana maida numfashi. Tsayawa yayi yabi bayanta da kallo,yanda mazaunanta ke juyawa lokacin datake cikin gudun har sai da ta 6acewa ganinsa. Jijjiga kai yayi tare da fad'in " ~astagfirullah~ " Mena keyi ne wai?. Sai da ya isa d'akinsa sannan yaji dariyah ta k'wace masa,ya kuwa yi abinsa son ransa,zuwa yanzu duk lokacin day tuna Teemah jiyake kawai tana bashi dariyah,saboda irin ta'asar data iyah "Yarinyan wallahi tafara bani tsoro" Ficewa ya sakeyi daga gidan ya tafi yawonsa. Teemah kuwa tashi tayi ta d'auro alwala sannan ta zira wata bak'ar abaya ta tada sallar azahar, Bayan ta idar ne tacire abayar,kuma se alokacin tafara tunanin abinda ya faru,"mugu kawai dana tsaya k'ila da sai de mummy ta d'auki gawata,dan nasan jibgata zai yi,babu ruwansa. (Kunjifah🤔 ita damuwarta lpyar jikinta ne bawai kallon bati da ya yiwa jikin nata ba). shiryawa tayi cikin uniform d'in islamiyarta da zindimemen hijab ta fito.yanzun kam a parlour tasami mummy tana zaune,cewa tayi "Ah yau har kin shirya dawuri haka,babu latti kenan",murmushi tayi wa mummyn sannan tace "hadda ta tarumin ne mummy inaso in rage" "Abinci fah" "Kai mummy,may be sai na dawo" Daganan tafitah daga d'akin zuwa cikin gidan. Bata fi 7mins da fita ba ta dawo ciki,sai da tayi sallamah,kafin tace "mummy gidan fah babu mota ko guda d'aya" "Haka akayifah namanta ne,Habibu bai dawo ba har yanzu,Abbas kuma inaga ya fitane,zoki d'auki #200 ajakata inaga de kamar akwai,maza ki hau adaidaita ki tafi,kuma in antashi kar ki tsaya jiran driver ki dawo abinki dan ko Habibu ma yadawo zai hutane babu inda zashi sai dai zuwa gobe in Allah ya tashemu. Da "toh " ta amsawa mummyn tare da shiga d'akin. Fitowa tayi sannan tace "toh na wuce mummy" "Uhm Allah ya tsare" "Ameen" tace sannan tafice daga parlourn. Abbas ma bai dawo gidan ba sai da yamma,koda ya dawo d'inma kuma zamansa yayi a gaban gidan yana duba abu a system d'insa. Dawo wanta kenan daga islamiyah ta ganshi zaune aharaban gidan. Harara ta banka masa kasancewar baya kallonta,tana isowa inda yake kuwa dan dolenta tace masa "ina yini yayah" "Lafiya "ya amsa mata dashi batare da ya d'ago ya kalleta ba,harta d'an gotashi sai kuma taji yace "ke kinga zonan! dawowa tayi baya ta tsaya d'an nesa dashi. "Waye ya kawoki gidan? "Babu" tabashi amsa dan bata san inda tambayar ta dosa ba. "i mean keda wa kika dawo, banji anbud'e get ba sai kawai na ganki"? "Ehh ni kad'ai dawo" tabashi amsa. "Habibun fah ko har yanzu bai dawo bane? "Nima bansani ba" tabashi amsa. "Ok jeki" Juyawa tayi tawuce ciki aranta tace "Mutum sai mugun hali da bak'ar zuciyah" (Toh fa,ni nakasa gane wanda keda mugun halin acikinsu) Baijima ba awurin shima ya taso ya shigo ciki,zuwa yayi ya tambayi mummy akan batun rashin dawowar habibun har yanzu,anan takece masa itama abin na ranta wallahi,amma bari tak'irashi taji. Koda ta k'irashin ma cemata yayi yana hanya yama shigo cikin gari. Sai da taji haka sannan ta tsinke wayar tare da fad'in "toh Allah ya tsare. Ba'a dad'e ba kuwa sai gashi ya iso. Ashe accident yasamu bayan ya sauk'e daddyn ahanyar ta dawowa gida,daya ke ma bai bar cikin maidugurin dawuri ba,sai da yayi sallahr azahar acan,sannan yakamo hanya cikin tsau tsayi kuma sai wani mai golf yamar karo daga bayan motar,toh shine ya tsaya aka d'an daidaita natsuwar motar kafin yasamu ya iso,jimami sukayi gaba d'ayansu,daga nan mummy tace toh yaje gida yad'an huta koda na sati d'aya ne,sannan tashiga ta kawo mar 'yan kud'ad'e tabashi. Godiyah yata zubawa mummyn. "Nagode hajiyah Allah yayi albarka, Allah ya kare zuri'a........Allah ya......... Allah yah..... Hakade ba iyaka,mummy kuwa sai Ameen taketa fad'i dan acewarta ba'a raina addu'ah ko yaya take bakasan bakin wa yafi albarka ba. Kafin yafita sai Abbas ya rigashi barin d'akin Habibu nafitowa sai suka had'u a hanya. Hannu ya mik'awa habibun suka yi musabaha,raba hannun nasu keda wuya habibun yafara zuba wata sabuwar godiyar,shi kuwa bai tsaya ba ya wuce abinsa zuwa d'akinsa. Ashe shima kud'i yabawa habibun,saboda yana tunanin Habibun da kud'in jikinsa yayi gyaran motar kuma karsu shiga hakkinsa arashin sani,amma dayake bai bari kowa yagani ba sai babu wanda yasan nawa ne.Amma de inaga bazai wuce 20k ba. Ranar kam ko agun dinning ma basu had'u ba,dan Abbas bai nemi abinci ba ba ranar, Kuma mummy bata aika ta k'iransa ba. Tade neme shi a waya anan yace mata,bai jin ci ne yau d'in,tace anya lafiyarsa kuwa ? "ehh lafiya mummy kawai de ak'oshe nake ne. "Toshiken Allah ya k'ara lafiya" "Ameen summah Ameen"yace mata daganan sukayi sallama. Teemah ranar farin ciki kamar ya fasa mata k'irji haka taji. _Share nd drop ur_ _comment pls_ 👏🏻 Farin cikina shine comments d'inku🙈 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 5:54 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 dukkan masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs.Nagode da_ _irin kyawawan_ _addu'o'inku_ _gareni.Nima ina_ _sonku sosai_ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Sometimes we must get hurt in order to grow, we must fail in order to know, sometimes our vision clears only after our eyes are washed away with tears. 🅿 *12* Washe gari kuwa Abbas da sassafe ya fice agidan,ko da Teemah tayi shirin makaranta ma sai dai kud'in adaidaita mummy tabata, ranta ma baya son hawan adaidaitan amma babu yanda zatayi tunda Habibu bayanan. Haka taje ta tari adaidaita ya kaita makarantar,koda aka tashima haka tadawo,amma sai bata dawo dawuri kamar yanda tasaba dawowa kullum ba,koda tadawo d'in kuwa zube wa mummy tayi ajiki da fitina wai kanta na ciwo saboda tsayuwan data yi abakin titi dan jiran adaidaita,gakuma gari akwai zafin rana sosai. Haka mummy yau kam tayi ta biye mata,dan gaskiya ta d'an tausaya mata ganin yanda duk tayi sanyi. Ranar ko islamiyah ma batajeba,sai da aka nema mata panadol tasha tayi bacci kafin nan ta warware. Wasegari ma ba taje makarantar ba,k'in zuwa tayi,ganin haka yasa d following day Mummy ta kaita ta kuma d'auko ta,next kuma ta tafi a napep Abbas ne yakawota gida. Kwanan daddy biyar ya dawo,Abbas ne yaje har maiduguri ya d'auko sa zuwa gida,dayake daman tafiyar ba wata qasa bace yaje, lagos ya tafi batun kasuwancin su da suke yi kusan atare shi da yayan mummy,tare ma ake sauk'e musu kaya,yayan mummyn acan yake da zama shida iyalansa. Dawowar daddyn Teemahn ne yake sanar musu cewa ai Mahmud (d'an yayan mummyn) anan zai zo yayi service d'insa kuma nan da two days zai iso,nextweek zasu shiga camp. Mummy dataji wannan batun kawai sai ta fara hawayen farin cikin zata ga jinin d'an uwanta bayan tsawon wasu shekaru,babu wanda ya hana ta kukan dan daddy ne kad'ai yasan dalilin kukan nata,Abbas da Teemah kam babu abinda suka sani dan haka suka zuba mata idanu,Abbas mamaki yake yi akan dalilin kukan nata daga jin zasuyi bak'o..............kodai.......kodai....... Teemah kam dataga mummynta na kuka,da farko itama tsayawa tayi kallon mummyn amma daga baya itama sai ta fara kukan dan bata ta6a kallon mummy tana zubda ruwan hawaye ba tunda tayi wayo. Mumm ganin da tayi y'arta na taya ta kukan sai ta yi k'ok'arin dakatar da nata hawayen,tana murmushi. Janyo Teemah tayi ta rungume ta kiyi shiru,ki daina kuka kinji,kukan farin ciki nakeyi Teemah cikin ikon Allah bayan wasu tsawon shekaru zanga wani daga cikin danginah,Teemah jinin d'an uwana,maganar take tana murmushi amma still hawayenta bai daina zuba ba,kana ganin yanayinta zaka gane tana cikin wani irin yanayi ne marar misaltuwa. Daddy ma ido ya zuba mata yana k'ara jin tausayinta acikin ransa. Sallar la'asar ne ya tada su awurin,Daddy da Abbas suka wuce masallaci,Teemah kuma da mummy kowa ta nufi d'akinta. Kafin isowar Mahmud d'in mummy akullum annurinta k'aruwa yake yi,komai tana yinsa cikin walwala da farin ciki,da ka ganta kasan annurin daya ke kwance asaman fusakrta har cikin zuciyarta yake,musamman yau daya kasance suna saka ran isowarshi agobe. Musamman taje kasuwa tayi siyayyah sosai wai afad'arta duk na taran d'anta ne. D'akin da zai zauna kuwa tun jiyah aka gama gyarasa tsaf,aka sa dukkan wani abin buk'ata aciki. Washe gari asabar mummy dawuri ta tashi ta taso k'eyar Teemah ma,seda suka koma ta sake duba d'akin da zai sauk'a aciki ta tabbatar da babu wata matsala kafin suka fito,Teemah mamakin wannan al'amarin yabi ya cikata. Kitchen sukaje da mummyn anan suka samu Baabah Lami,dukkansu mummy taraba musu ayyuka,yau da kanta tayi girkinta duk wanda take ganin zai burgeta shi tayi kusan kala uku,juice kuwa sun had'a d'aya already ansa afridge,gasu kuma suna kan had'a wani daban,inka ga yadda mummy ta dage agirkin,ka kuma dubi yawa da kalolin abincin zakayi tsammanin family guda ne zasu zo,abin ya d'aurewa Teemah kai,ita de jitayi ance mutun d'aya ne zaizo amma ga mamakinta sunyi girkin da kusan mutane goma ma zasu ci su kuma rage saura. Kallon mummyn nata tayi sannan tace "mummy wai bak'i nawane zasu zo? Mummy cikin murmushi tace "Mahmud ne zaizo Teemah." "Mahmud d'in shi nawa ne mummy? "'D'aya mana Teemah,wai miye matsalarki ne ke kam.? Kauda kai tayi daga kallon mummyn ta cigaba da blending d'in data keyi,amma sai taji zuciyarta ta kasa hak'uri da wannan abin. "mummy amma de kinfi sanshi akaina ko? Dariya sosai tabawa mummyn hakama Baabah Lami,dariyarta sukayi san ransu,Teemah kuwa ta wani basar ko kallon inda suke batayi ba dan ita tambayarta har zuciyarta tayisa,so ta ke taji amsarta amma kuma sai suka maida maganar abin dariyah. Saida suka tsagaita ne Baabah Lami tace "kai Fatu tun yanzu harkin fara kishi ne? Fushi ta k'ara akan nada d'in datayi,dan maganar baabah Lami duk abin haushi ne awurinta. Wai fatu........ Kuma wai tana kishi..........ita aganinta ai gaskiyarta ne,dan yanda taga mummyn na zumud'in isowar Mahmud d'in dole ya sosa mata zuciyah amatsayinta na y'a k'walli d'aya tal agun mummyn,aiko zuwan Yah Abbas ma mummy batayi wannnan azar6a6in ba,koda yake shi zuwan bazata yai musu basu san da zuwan nashi ba,kawai sai de suka ganshi. Turo baki ta k'ara yi gabamummy ce tace mata "ki rabu da Baabah Lami d'innan kinji yayanki ne fah,ana kishi da yayah ne kuma ai ba'a yi, kinga ni kuma ai dole nayi farin ciki da zuwansa shekaru nawa rabo na dasu Teemah." Lalla6anta mummyn ta cigaba dayi da kalaman kwantar da hankali,dan tasan halin Teemahn nata ba dai kishi ba,haka tayi ta binta a hankali har suka gama aikin gaba d'aya. Sai bayan la'asar kafin Mahmud ya iso gidan, lokacin Abbas da mummy ne kad'ai agida. A babban parlourn gidan suka fara sauk'ar dashi, lokacin da mahmud ya iso daddy baya nan,Teemah ma tana islamiya,mummy tayi murna da farin cikin zuwansa sosai,Abbas kuwa sai dai ido,dan mummy murnar tata tanayi ne had'e da hawaye tana tambayarsa labarin iyayensa,shima d'in duk jikinsa yayi sanyi dan anjima ba'a had'u ba amma shi bai wani yi kuka ba,ganin mummy takasa daina hawayen ne yasa Abbas ya fara bata hakuri duk da bai san manufar kukan nata ba. Koda teemah tadawo ma sannu da zuwa kad'ai tamasa,dan ba saninsa daman tayi ba,gara shima yasan da ita,kawai dai rashin zumunchi ne yasa babu shak'uwa atsakaninsu. "Fatima zarah " Ya k'ira sunanta lokacin data mar sannu da zuwa d'in,dayake sunzo sunanta kuma fatima zarah shine sunan da aka ambaceta dashi aranar. Amsawa tayi daganan tawuce ciki abinta batare da ta zauna a inda ta tarar dasu d'inba. Sallar maghrib ne ya tadasu a parlourn,Abbas masallaci suka tafi suna idarwa kuwa suka dawo gida sai a sannan suka tarar da daddy yadawo,gaisawa sukayi da daddyn daganan ya wa mahmud d'in Barka da isowa dan shi ya riga da yasanshi ,dayake suna yawan had'uwa idan yaje Lagos. Ganin sun dawo d'inne sai mummy tafara kwallawa Teemah k'ira,bakinta d'aya ana biyu Teemah ta amsa. Akan dinning tasame su,nufo wurin tayi tana fad'in mummy dawuri haka yau kuma? "Uhmm" Kawai mummyn tace mata. Daddy ne yace "yau mummyn ki ta sauya mana tsarin mu angel saboda taga sabon d'anta yazo" Yana murmushi yayi maganar. Mahmud ne yace "a daddy harda kaima ko ? "Ahh toh mahmud ai munga ana mana wariya ne,dole inyi k'orafi" Sai asannan mummy tayi magana tana murmushi tace "Bafah haka bane,ina gudun hucewar abincin ne kunsan dawuri aka gama shi kuma nasan idan ya huce bandaro zaiyi" Dukkansu sai suka murmusa,sai asannan ne mummy tad'an sake ta rage damuwar data ke ciki,da kanta tayi serving d'insu abinci,kowa yayi bismillah ya fara cin abincinsa,amma banda Teemah da take ta kora ruwan juice tana binsu da kallo d'aya bayan d'aya. Cikin haka suka had'a idanu da Abbas yawani sakar mata harara,murgud'a mai baki tayi sannan ta d'auke kanta gefe,Mahmud kuwa har yanzu haushi yake bata,dan ta lura mummyn ta tafi sonshi akanta,shiyasa shikam ko kallon arzik'i ma bai samu ba,gani yayi tana ta wasa da cokalin bata ci ba, baifi spoon biyu taci acikin abincin ba, "Yah dai" yace mata Bata san ma da ita yake ba amma sai ta d'ago idanu,had'a ido sukayi dashi,sai tawani d'ago baki sama, "Me aka miki ne? Ya sake tambayarta. "Kyaleta mahmud daina 6ata bakinka indai wannan ce" Daddy ne yafad'i hakan.murmushi kawai mahmud da mummy sukayi,Abbas kuwa sai ya kalleta. caraf suka yi 4 eyes dashi sai tayi k'asa da kanta tana gunguni,minti biyu bata k'ara ba agurin sai ta mik'e tsaye,juice d'in tak'ara tsiyayah ta wuce d'akinta dashi kowa bayanta yabi da kallo,amma banda Abbas. Sai da suka gama cin abincin kafin suka mik'e suka fice ad'akin,Mahmud da Abbas ne suka fita harabar gidan suna d'an taba hira atsakaninsu. Sosai suka fahimci junansu dan Mahmud gwani ne a surutu shikam,bakamar Abbas d'in ba. Tun daga lokacin wani shak'uwa ta shiga tsakaninsu sosai dayake kowa yaji d'an uwansa yamasa har aransa. Abbas da mahmud kusan sa'anni ne,Mahmud yasamu delay d'in yin makaranta ne dalilin mahaifiyarsa,shiyasa sai yanzu zaiyi service d'insa. Koda suka dawo daga sallar isha'i ma ad'akin Abbas suka yada zango,kuma sai alokacin mahmud yake d'an bawa Abbas labarin d'an abinda yasani,shima Abbas d'in sai yaji mummyn tabashi tausayi sosai. Anan suka ci kusan 2hrs ,sai 10:15 Abbas ya koresa yace "kaje kai ka kwanta ka huta mana,kamanta nisan tafiyar dakayi ko"? Dariyah mahmud yayi kad'an tare da fad'in "kai de nagano ka so kake in baka wuri ka sake" "Ehh naji ni dai jeka" Tashi yayi yabar d'akin yana fad'in mu kwana lpy. "Allah ya bamu alkairi" Abbas d'in yabashi amsa. Sannan ya mik'e yarage kayan jikinsa yayi shirin bacci. ******** Dangantakar mummy da Mahmud tasamo asali ne daga iyayen su mummyn. Iyayensu asalin 'yan kano ne,dan tun tashinsu a kano suka tsinci kansu,Malam mamman sada shine sunan mahaifinsu,kayan miya yake siyarwa a kasuwa mahaifiyarsu kuma ummah fatsin kusan kowa haka yake k'iranta dashi, iyayensu su biyar suka haifah,amma duk sauran Allah ya kar6i abinsa,su biyu ne kawai suka saura agaban iyayensu har suka girma,suna rayuwarsu cikin rufin asiri da wadatar zuci,yayan mummy mai suna yusuf yana gama secondary mahaifinsa ya dage har seda yaga yasamu gurbin karatu a BUK kafin ya samu nutsuwa,cikin ikon Allah ya fara karatun da sa'a dan bai sami wata matsala ba,shigansu 200level ne suka had'u da kabiru shikuma yazo D.E ne,kuma shine yakasance abokinsa har suka k'are makarantar dan kusan halayyah d'aya garesu....... Tare suke komai a makarantar inka gansu zaka zaci y'an uwan juna ne ma su,dan basu fiyah rabuwa da juna ba. Lpy lau suka gama makarantar su, Cikin ikon ubangiji kuma kamar abinda babansu yake jira kenan yace ga garinku nan,dan kwanan yusuf hud'u da gama makaranta ranar da yamma Baban yana dawowa daga kasuwa mota takad'e shi,garin tsallaka titi hannunsa rik'e da ledar y'ar tsarabar daya saba kawo musu idan zai dawo daga kasuwar,abin ya faru ne akan titin unguwarsu ,hakan yasa ba'a sha wani wahalar ganeshi da gidansa ba. Dawuri labari ya iso musu,duk kansu suka fice bakin titin da gudun gaske su ummah na kukan fitan rai,dasuka ganshi kuwa take mahaifiyarsu ta suma a wurin. khadija kuwa kuka ta zube tanayi dan rasa kan wa zata fara zuwa tayi. Da k'yar aka samu aka tattara su aka kai gida,shikanshi wanda ya kad'e mahaifin nasu kuka yakeyi da hawaye, ba'a wani d'au lokaci ba aka masa sutura, kanshi ne yafashe dan bazama kaso kaga yanda kan yayi ba hatta likkafanin ma sai da yayi ja,dukda an d'an ninka a wajen kai d'in amma sai da ya ratso,Yusuf ne kad'ai mai dauriyah addu'a kawai yakeyi azuciyarsa har suka sada baba da makwancinsa na gaskiyah. Dayake wanda ya kad'e baban ma zuciyarsa mai kyau ne,dashi akayi komai har zuwa sadakan bakwai,kuma aranar ne ya bayyana abinda ke ransa game da batun diyyah. Yusuf ne yace su basu son wani diyyah akan mutuwar baban,koda akaso fahimtar dashi akan musulunci ne yazo da hakan ma cewa yayi ya sani,kawai bazai iya kar6ar komai akan dan babansa yarasu ba,mutuwa ai ta Allah ce. _Drop ur comment_ as u do always🤞🏻 _pls_ , _and i don't need that_ *heart* ❤ or *tnx* / *Thanks*, _even the_ *sticker* 👎🏻 _I don't like it,all i_ _need is ur_ _comments_ .🤙🏻 *Salmern ku ce* 😍 [10/2, 5:54 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* masoyan_ _CAPTAIN ABBAS. Kusani ina yinku irin sosai sosai d'innan,Nagode da_ _irin kyawawan_ _addu'o'inku_ _gareni.Nima ina_ _sonku sosai_ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Free your heart from any hatred. Free your mind from any worries. Live simply. Give more. Expect less. 🅿 *13* Da malaman suka ji ya fad'i haka sai suka ce toh shikenan daman hakkin addini ne kuma dan gudun siga hakki ake son sauk'e shi,amma tunda yace haka shikenan,Allah ya k'ara musu hak'urin rashin dasu kayi,amma duk da haka sai sunji daga bakin manyansa tukunna,wasu daga cikin y'an uwan baban haushi sosai sukaji dan aganinsu Yusuf bak'aramin bak'in ciki yayi musu ba,amma da sukaji za'a tambayi manyansa sai suka d'an ji dama-dama dan sun zaci za'a samu sa6anin harshe ne. Sai dai basu yi sa'a ba,dan da aka tambayi ummahn suma cewa tayi " _a'a yanda idonta yaga jinin Baban ya zuban nan ko da sun kar6i kud'in gani zasuyi kamar jinin baban suka fansar,tsautsayi da k'addara ai abokan tafiyar dukkan wani halitta ne,babu wanda ya isa ya gujewa k'addararsa,Allah ya riga da ya rubuta inda ajalinsa yake kenan dan haka su basu da wani abin fad'a fatansu kawai Allah yah kyautata makwancin Baban" Ummah tana hawaye take wannan maganar,kusan kowa dake zaune agun sai da ya share hawaye,duk da zuwa yanzun abin yad'an bar zuk'atansu,sun riga da sun dangana tsakaninsu da Baban yamzu addu'a ce kawai. "Allahu akbar", "Allahu akbar" "Allahu akbar" Babban malamin dake zaune agun ne yafad'i hakan tare da jijjiga kansa,d'ago wa yayi ya kalle su gaba d'aya sannan yaci gaba da cewa "Hak'ika wannan kad'ai baiwa ce da Allah ya riga ya halicci ahalin wannan gidan dashi,kalamanku su suka bayyana hakan,ga dukkan alamu ba wani k'arfi ne daku ba amma wannan furucin naku yah tabbatar mana da cewa wadatar zuci abokiyar tafiyar ku ne,Allah kad'ai kuka dogara dashi,Hak'ik'a agurin Allah ku masu arzik'i ne da yardarsa,Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairi ya kyautata rayuwarku gaba d'aya daga yanzu har yaumul sa'a. "Ameen-Ameen"! sauran dake gurin suka amsa masa dashi,amma kowa jikinsa ya matuk'ar yin sanyi. Sake kallon Ummah yayi dake faman goge hawaye tun d'azu,sannan yace "Kuyi hak'uri insha Allahu mutuwar malam hutu ce agare shi muna mishi fatan alkhairi insha Allahu,malam mutum ne da kowa yaji wannan mutuwar tashi ta matuk'ar ta6a zuk'ata da yawan gaske,amma dukkan mu yazama mana dolene muyi hak'uri,addu'a itace gatansa ayanzu" Babban malamin ne yasake juyowa ga ragowar ahalin Baba yasake tambayarsu,suma da wuri suka amince sai bakinsu yazama d'aya dukkansu. Da haka taron yawatse amma har aran Alhaji Muhammad ji yayi ya kasa hak'uri da wannan lamari ji yake bazai iyah kyalesu a haka ba amma bai yi magana awurin ba yadai bar abinsa aransa ne kawai. Dangin Baba kuwa haushinsu k'aruwa yayi akan nada, ji suka yi kamar su rufe ummah da duka lokacin da ta ke nata bayanin,koda aka zaga yo kansu da tambayar kuwa suma dan dolensu suka amince badan ransu yasoba,dan de kar aga zak'ewa da zilamar su ne,shiyasa basu canja baki ba,tunda bau wanda yasan meke acin ran su sai kowa ya yabawa wannan zu'ri'a ta mariga yi masu sanin ya kamata da girmama k'addarsu, inka d'auke mutune biyu dasuka kasance su d'in k'anne ne ga Baba,Mal.Hadi da mal.kallah sune kad'ai suka yi maganar datake har cikin zuciyarsu ne badan komai ba sai dan saboda Allah kawai, amma saura daga ciki duk bada son ransu suka amince ba,dansu aganinsu a irin yanayin talaucin da suke ciki kud'in ba k'aramin taimaka musu zaiyi ba,basu sani ba ashe irin kud'in nan baya kawar da buk'atar mutum dan tafiyah yake kamar ana hure shi,daga k'arshe ma karasa ya akayi ne ma yak'are gaba d'aya,inkayi wasa da tunani kawai zai barka,amma bansani ba kodan basuga yadda k'arshen d'an uwan nasu yakasance bane shiyasa tsoron rayuwar bata shigesu ba,domin kafin su iso har an sada baba da makwancinsa na har abada. Mal.kallah kanin marigayi Baba ne da suka kasance uwa d'aya su kad'ai mahaifiyar su ta haifah inda tarasu tun awajen haihuwar Mal.Hadi haka yataso baisan mahaifiyarsa ba da dad'i da wuyah haka de ya girma ahannun kishiyoyin uwa shida wansa,kuma sun kasance y'a'ya k'anana daga cikin y'ay'ayn da mahaifinsu ya haifa,dan mahifiyarsu itace ta k'arshe acikin matan mahaifin nasu while mal.Hadi kuma uba suke d'aya. Mahaifinsu ma masha Allah,dan ya mori duniya sosai,shekarar sa baifi uku da rasuwa ba yanzuh,tsufa yayi jigib cikin ikon _buwayi_ har baya gane mutane,kafin Allah ya kar6i abunsa. ***** Alhaji Muh'd wanda yakad'e baban kenan kayan abinci yaci kasu dashi sosai iya iyawarshi,sannan yaci gaba da zuwa akai akai yana dubasu,kuma bai fasa yin azumin da shari'ah ta d'ora kansa ba. Dangin mahaifin nasu kuwa tun daga ranar suka fita daga harkar su,basu k'ara waiwayarsu ba,kowa gudun d'awainiyah yake yi saboda yanzu sun zama marayu,mahaifiyarsu kuwa dama y'an cirani ne,ba'a san inda danginta suke ba tunda ta auri baba shikenan rabuwarsu da ahalinta.So basu san kowa daga 6angarenata ba. Haka har Lokacin tafiyar Yusuf tayi,yatafi service d'insa,a Taraba state batare da wani fargaba ba,dan yanzu Alhamdulillah basu da matsalar abinci,domin sosai suke samun tallafi daga al'umma dan wani lokaci mutane basa tuna su taimaka maka koda sun san baka da k'arfi har sai sunga ka kwanta dama,alokacin ne zakaga zuciyar taimakon ta motsa, inkayi sa'a zuri'ar ka bazata wahala ba ko bayan baka,sannan ga Alhaji muhammad ma bai ta6a mantawa dasu ba,yanayin iyah k'ok'arinsa akansu wani lokaci har suna tausaya masa,na ganin kaddarar mutuwar baba tasa wani nauyi ya hau kansa batare da ya shiryawa hakan ba sannan sunyi-sunyi dashi akan yad'an huta da d'awainiyar sam yak'i,sai dai yace musu shi saboda Allah yakeyi badan komai ba. Kafin yah gama azuminsa rama yayi sosai kamar wanda yayi wata ka'aramar jinya,Addu'a kawai kawai suke binsa dashi dan itace kad'ai sakayyar da suke ganin zasu iyah masa,hak'kik'a yacika mutum managarci,ba kowa keda irin halinsa ba acikin mutanen mu na yanzu. Sau kusan biyar yusuf yazo ganin gida acikin shekara d'ayan da ya yi a taraban. Yana dawowa kuwa Alhaji muhammad ya bashi jari,akan ya fara kasuwancin kansa da kansa,da kyar ya kar6i kud'in dan gani yake kamar sun d'orawa Alhajin wani nauyi ne na daban akan k'addarar da kowa bai isa ya tsallake ta ba,amma Alhajin yace sam dole sai ya kar6a,da yaga Alhajin yafisa baki sai yace toh yah rage yawan kud'in nan ma Alhajin yace shi abinda yayi niyyar bayarwa kenan so baze rage ko kada'n ba,haka dan dolensa ya kar6a,godiya kuwa shi kansa sai da ya rasa adadin daya ambace su,daga k'arshe ma Alhajin barin d'akin yayi ya barsa shi kad'ai aciki rik'e da kud'i,yana hawaye ya fito daga d'akin shima,karo suka ci. da y'ar Alhajin tana k'ok'arin shigowa itama,binsa tayi da kallo har ya fice agidan,dan take taji ya kwanta mata. Shikenan tun daga ranar ta nace masa mahaifiyar ta ma ta goye mata baya,har se da taga sun sami had'in kansa kafin nan ta sami salama. Ga Alhaji muhammad kuwa bawai ba yason auren bane a'a shima yana matuk'ar farin ciki da kasancewar yusuf d'in sirkinsa dan ya yadda da tarbiyarsa sosai, matsalar kawai maganan mutane yake gudu,kar wasu suce shi ya lik'a masa y'ar sa adole dan yaga basu da k'arfi,ko kuma dan basu da wani akansu yanzu. Amma da malamin daya wakilci auran ya fahimtar da shi cewa shi aure had'i ne na Allah,shiyake tsara abunsa aduk yanayin da yaso a kuma duk inda yaga dama,hakade malamin yata nusar dashi muhimmancin da hakan ke dashi, take kuwa shima yayi na'am da zancen,aka yi bikin lafiya aka kawo amaryar gidansu da suke zaune bayan gidan yasha kwaskwarima sosai. Kuma Alhajin ne ya d'au nawin komai na bikin danma kar yusuf ya ta6a wani abu daga cikin dukiyar da ya bashin sai ya kar6e ya ajiye agunsa sai bayan bikin ya maida masa da abinsa. Ganin yawan k'ud'in ne yasa yusuf yaje ga mahaifiyarsa neman shawarar sana'ar data dace yayi,cemasa tayi yayi kowanne ma inde yaga ta kwanta masa bata da matsala dashi matuk'ar yasan bazai sirka dukiyarsa data haramun ba toh yaje ya za6i duk sana'ar data mishi yayi. Godiyah yayi mata tareda alkawarin insha Allahu zai tsaya akan iyaka halak d'insa ne bazai wuce hakan ba izinin Allahu. Da addu'ar samun sa'a tabishi. Rasa yanda zai yi da kud'in yai kwata kwata daga k'arshe sai ya k'ira abokinsa da suka yi makaranta tare mai suna kabiru dan yaga kamar su d'in ma harkar kasuwanci mahaifinsa yake yi,so aganinsa zai fi samun clue daga bakinsa. Abokin nasa kuwa d'an albarka sai ya had'asa da mahaifinsa ya fara juya masa kud'in,watansu shida tare sai mahaifin kabirun ya ware ma yusuf iya tashi dukiyar tare kuma da ribar da suka samu akai,daganan ya k'ara ha d'asa da manyan y'an kasuwa da suke harka tare yace ya cigaba da harkokinsa shikad'ai dan sha'anin dukiyah wuyah ne da ita. Yin hakan baifi da sati biyu ba Allah ya yiwa mahaifin kabirun rasuwa,Sosai mutuwar ta ta6a su gaba d'aya satin yusuf guda cif a Gombe wurin ta'a ziyar mahaifin kabirun sannan ya dawo gida cike da alhini,dan bazai ta6a manta karamcin mutumin ba,sai fatan Allah ya kai haske kabarinsa. Ana raba musu gado kabiru ya taho kano yasamu yusuf suka yi shawarar yin kasuwanci atare,kabiru yanada k'anne biyu mace da namiji Sunan macen Zahra kuma itace ka'rama sai namijin mai suna Hassan 'yan biyu ne shi amma d'ayan bai rayuba shekara ukune tsakaninsu da Hassan d'in,ko lokacin da aka raba musu gado ma kowa karbar nashi yayi danshi hassan tun shekarar data gabata yayi aurensa,auren gida Hassan d'in yayi shikuma kabiru ya tsaya yin karatu,Zahra ma tana gama secondary Mahaifinta ya aurar da ita rana d'aya da Hassan,alokacin da mahaifinta ya rasu ma ciki ne da ita. Sun fara kasuwanci lafiya lau kuma suna ganin haske aciki,Kwatsam sai suka wayi gari babu mahaifiyarsu Allah ya kar6i abinsa,tun daga lokacin kuma sai khadijan tashiga wani hali dan har alokacin ma bata k'are secondary ba,shekara kusan goma sha d'aya ne tsakaninta da yayanta Yusuf. Matar Hassan kuwa ta haifi d'a namiji Hassan sai ya maida sunan mahaifinsu wa yaron wato _Muhammad_ ,sunyi matuk'ar farin ciki adangin gaba d'aya dan mahaifinsu mutumin kowane bade taimako ba,tun daga lokacin suka fara k'iransa da suna _Abbas_. Zahra kuwa lokacin dazata haihu tarasu daga ita har y'ar data haifa babu wanda yayi rai acikinsu. Hak'ik'a wad'an nan mutane sunga ikon Allah sai dai fatan Allah yajikan magabata . "Ameen" Yusuf shikada'ai wannan karon ma yaje ta'aziyar Zahra a Gombe,dan matarsa cikinta ya tsufah sosai. _Share and comment_ _pls_ 🤞🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 5:54 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _In dedication_ _2 sister Safiyyah Aliyu Wakili. 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* No need for revenge. Just sit back & wait. Those who hurt you will eventually screw up themselves & if you are lucky, God will let you watch. 🅿 *14* Bayan rasuwar Zahra baifi da 3 weeks ba matar Yusuf ta haihu,ta haifi d'a namiji mai kama da ubansa sak,yaro kyakykyawa dashi,tun da Khadija ta ga yaron nan ya shiga ranta sosai dan dama ita kad'ai ke rayuwarta bata abokin hira inde tana gida, dan matar yayanta ba wani sake mata fuska take yi ba asalima shiyasa tun da aka haifi yaron nan farin ciki yacika ta, Atunaninta zata samu abokin yin hira da wasa. Ranar suna yaro yaci suna Mahmud,akayi shagalin suna aka watse, Bayan anyi suna ne kabiru yazo ganin jariri,alokacin kuma yaron yana tare da Khadija ne so da yusuf yashigo da zummar kai wa abokinsa yaron sai ya gansa a hannun khadijan, mahaifiyar yaron kuma tana bacci,kawai sai yace ta kaiwa Kabiru mahmud d'in yana can d'akin bak'i bari zai watsa ruwa yanzu,toh ta ce tare da d'aukan mayafinta tafita daga parlourn. Da sallamarta ta shiga d'akin ba'kin,daga ciki ya amsa mata shiga tayi kanta a'kasa ta isa har inda yake zaune ta mi'ka masa yaron. Kar6ansa yayi amma idonsa nakan fuskarta ganin ta'ki ko ha'da ido dashi. Juyawa tayi da niyyan barin 'dakin sai ya dakatar da ita yace tazo ta wuce da Mahmud d'in shi sauri yake y yanzu zai wuce,dawowa tayi kusa dashi ta tsaya,tsayuwar minti 3 zuwa hu'du tayi sai ya mik'a mata yaron bayan ya masa addu'a a kunnensa. Leda ya sake mik'a mata a nan ne ta d'aga kanta ta kalle shi suka had'a idanu,da k'arfi ta gyara zaman yaron da ke ri'ke a hannunta,dan ji tayi kamar ze su6uce mata. Dawuri tayi 'kasa da idanunta ta maida kallonta ga mahmud da ke 'dan motsawa saboda yanda ta matse shi a jikinta. Sake mik'a mata ledar yayi tare da fad'in "kayan yaro na ne aciki naga kina wani tsorn kar6a" Hannun ta d'aya ta mik'a ta kar6i ledar sannab tajuya,sai data fara tafiya kafin tace "angode" Dan alokacin data kar6an idan akace dole sai tayi magana ma toh kuwa da sai de tasa kuka,dan ji tayi zuciyarta ta tsinke sosai da suka had'a idanun dashi,da zai lura ma da ya fahimci irin yanda jikinta ke rawa sosai. koda ta koma d'aki kuwa rasa mai yake mata da'di tayi,shiru ta zauna tana tunani tunanin da ita kanta bata san na menene ba. Haka tasa Mahmud d'in da kayan agaba ta tsura musu idanu,kukan Mahmud ne ya fargar da ita,dawuri ta tashi ta 'dauke sa tare da ledan da niyyan ta kaiwa Mahaifiyarsa shi. Ha'duwa sukayi a kofar shiga parlournta,tana ganin su sai ta juya ta koma ta zauna,khadijan ma sai ta biyo bayanta Saida ta zauna sannan tafara fad'in "Daman zaman me kike min da yaro bayan kinajin irin kukan da yake yi tun 'dazu dan salon rashin imani bazaki kawon shi ba" Tana kar6ar shi ta 'karasa maganar. Karkata kanta tayi gefe sannan tace "Ayyah Anty yanzu fah ya fara kukan shine na kawo shi" "Dallah ni rufe min baki,wawuya kawai" Antyn ne tayi wannan maganar tana 'ko'karin sawa yaron mama abaki. Ajiye ledar tayi tana shirin juyawa ta fice tajiyo muryar Antyn tana fad'in "wannan fah malama zaki ajiye min abu batare kinmin wani bayani ba." Tsayawa tayi amma bata juyo ba tace "na Mahmud ne yah Kabiru ne ya kawo masa" Tsaki Antyn taja batare data sake magana ba,domin ita asali jininta bai wani ha'du dana kabirun ba,kuma haka shima,shiyasa ko yau d'in ma dayazo bai nemeta dan su gaisa ba. Yusuf dake shirinsa acikin 'daki yanajin duk abinda suke fa'di amma bai kulasu ba. Ita 'dinma bata san yafito daga wankan bane da bazata yi wa khadijan fa'da ba. Sai da ya gama shiryawa sannan ya fito,kallon da ya mata ka'dai yasa tagane yaji abinda ta yiwa Khadijan. Saboda a idonsa bata ta6a nuna wa khadijan tsana sai dai in abayan idonsa,saboda yanda yake nuna mata muhimmancin Khadijan a wurinsa. Sosai tasha jinin jikinta,amma dayake ta riga ta yi nisa kuma tasan halin sa sai ta watsar da batun kawai. Rakiya yayiwa abokinsa wani wuri kuma daga can ma yayi wucewarsa Gombe. Yusuf sai da yamma lis yadawo gidan,dayake bashi da ri'ko sai bai dawo da wani 6acin rai ba,amma still abun yana ransa hakan yasa yamata maganar anutse,daman shi in abu yafaru adaidai lokacin yafi nuna 6acin ransa,amma in aka d'an 'dauki lokaci toh shi kenan 6acin ran nasa ya kau. Kamar de yanda ya kasance yau d'inma,atake kuwa ta nuna masa ai yau 'dinma bada niyyah tayi ba kawai haushin kukan da taji yaron yanayi ne shiyasa tayi mata fad'an. "Ni dai banaso pls ki kiyaye kinji" Sai ta 'daga masa kai alamar taji. Kad'an daga cikin irin rayuwar da Khadija takeyi kenan agidan yayanta tun bayan rasuwar mahaifiyarta,bata da sukuni ko ka'dan agidan dan ma tanada ha'kuri da kau da kai ga abubuwa. Aikin gidan kaf ita ke yinsa,ga rainon Mahmud data riga ta saba da shi,ga masifah da hantara idan abayan idon yayanta ne. Islamiyah kuwa tun haihuwar Mahmud bata 'kara zuwa ba dan babu lokaci,bokon ma da 'kyar take samu taje ahakn ma kusan kullum sai tayi latti. Kuma a kullum sai ta dawo daga makarantar take d'aura abincin rana,dan babu mai yi Antyn bata yi,toshuwar da suke zama tare kuwa ba lafiyar idone da ita ba balle ta ringa yi musu girki,ga wankin kayan yaro duk tara mata akeyi idan ta dawo take wankewa,ga 'daura ruwan zafi,ita zata 'daura idan yayi ita zata ha'da ta kai ban'daki sannan ta dawo ta ha'da na jariri ma ta kai wa tsohuwa. Alhaji muhammad hanata zuwa wankan gida yayi yace tayi zamanta a gidanta yafi,sai ya 'dauko wata babarsa daga kauye yace su yi arba'in d'in tare. Wankan jariri kawai tsohuwar keyi,dan ko wankan mai jegon ma Anty da kanta takeyi. Alhaji muhammad ko mahaifiyar Antyn ma hanata zuwa gidan yayi,acewarsa baya son fitina. Koda tace zata zo bayan da akayi suna ma sai ya ce sai dai zuzo tare da ita,haka ya sako ta agaban mota suka zo,basu wani jima bama ya ce su koma gida. Haushin hakan yasa bata 'kara maramarin cewa zatazo d'in ba. Sosai zaka tausaya wa Khadijan agidan,idan ka ganta. Amma ita hakan bai wani dameta ba dan tasan komai lokaci ne komai yanada 'karshe. Babu irin ha'kurin da batayi ba da matar yayan nata har suka gama kwana arba'in d'in, Akwai ranar da zazza6i ya damu Khadijan harta je makaranta ma sai akace ta dawo ganin yanda jikin nata yayi zafi sai kakkarwa takeyi,Antyn ne da kanta ta 'kira yayan khadijan tasanar dashi cewa Khadijan ta dawo gida da zazza6i,yanajin haka kuwa ya garzayo ya nufoh gida,asibiti ya kaita da gaggawa mafi kusa dasu aka duba ta aka rubuto musu magunguna da allurai,kafin suka dawo gida. Fita yayi bayan ya dawo da ita gidan,yakoma ya siyo mata magani tare da kayan marmari,da kansa yazauna ya bata maganin tasha daganan yace maza ta kwanta tayi huta,tana kwanciyah sai bacci ya 'auke ta,tun a baccin tafara gumi cikin ikon Allah kuwa tana tashi a baccin tajita garau kamar ba ita ba,ganin hakan yasa Anty tace to ta goyi Mahmud tunda ta warke ita sai tayi girkin saboda yau 'din rigima shima yakeji dashi. Aikuwa tana goyashi yafara ihu yana zille-zille dan daman shi basan goyo yake ba. Kamar an jeho yah Yusuf gidan sai gashi ya yi sallama,cikin mamaki ya sake ledar da ke ri'ke a hannunsa ta fad'I ak'asa "Me nake gani haka ? Yafad'a da fuskar mamaki tare da nufowa inda take tsayen. "Sannu da zuwa yayah" tana murmushi tayi maganar. Hannunsa ya 'daga mata "ba wannan na tambayeki ba ni" "Khadija yaushe jikin naki ya sau'ka dahar zakiyi goyo" Baki da hankali ne? Fusata ya sake yi ganin yanda yaron yake zizzille wa abayanta har yana 'ko'karin kada ita. "ina mamar tashin take ? "Tana kitchen ne yayah tana girki shiyasa na goyeshi" Ta fa'da tana me 'kara jijjiga yaron,abinku da me zazza6i,kuma daman zazza6i ya iya yin lamo kamar ya sau'ka nan kuwa yana nan daram, take khadija tafara jin 'karfin ta duk yayi low sai ta fara jin jirijiri,aikuwa caraf yah yusuf yah ri'keta dan ganin ta fara yin alamun fad'uwa,kunce goyon yayi daga bayanta ya zaunar da ita da kyau,tacigaba da maida numfashi. Kitchen d'in ya nufa da yaron ahannu,ranshi duk ya gama 6aci,a ganinsa wannan ai rashin imani ne dazata ha'da yarinya da goyo bayan tasan ba lafiya ne da ita ba ga shi Mahmud 'din ba laifi akwai auki dayake baruwa ake basa ba _baby_ _friendly_ suke masa shiyasa yazama wani 6ukeke dashi. Ranshi a6ace ya isa kitchen d'in,suna ha'da idanu ya sake mata wata muguwar harara take jikinta yayi sanyi "baki da hankali ne Maryam " taya zaki had'a yarinyar nan da goyo bayan kinsan ba lafiya ne da ita ba? idan goyon da dad'i ke ki goyi abinki mana ba d'anki bane,ko ita ta haifa miki shi" "Yanzu badan Allah yasa nazo ba da kinsan me yake shirin faruwa ne,ke kina nan,wannan wani irin rashin imani ne dan Allah yake damunki? Na bar yarinya rai ahannun Allah ina can na gagara sukuni hankalina na gida inata tunanin halin da take ciki ashe ma ke kina nan kin had'a ta da renon d'anki ga jaka ko? "Okay shiyasa na yi ta 'kiran wayarki kika 'ki d'aukan wayar dagangan ko,missed calld nawa na miki amma kika 'ki 'dauka." Da masifah yake ta maganar idansa har ja yayi dan yanda yakejin ransa a6ace. Kokad'an bai bata chance d'in yin magana ba,hakan yasa tayi shiru tana jinsa,zancen wayan da yayi d'inne ma yasa ta d'an d'ago idanu ta kalleshi dan bata san da wannan batun ba,asalima bata san inda wayar take ba ma tun 'dazu data 'kirasa bata sake bi takanta ba. Daga lokacin be sake fita agidan ba har yamma masifah kuwa sai abinda ya 'karu,dan wuni yayi abirkice sosai ya nuna mata kuskurenta,tun tana kar6ar laifin har tagaji ta fara jin haushi kuma,sai ta maida jin haushin akan Khadijan dan rainin wayo, a ganinta itace dalilin komai badan itan ba da haka bazai faruba. Harta samu sauk'i bata 'kara yin komai agidan ba dan sosai yayanta yatsaya mata,kwananta biyar ta warke rass harta koma makaranta Ko abayan warkewarta ta kuwa sai ta'dan samu sauk'in aikin ka'dan dan yanzu Antyn tana 'danyin girki wani lokacin,wankine dai sam batayi sai dai Khadijan tayi. Ahaka har tagama secondary school 'dinta gaba d'aya zuwa wannan lokacin kuwa Mahmud yayi wayo sosai har mamar shi ta yayeshi ma. Ana cukucukun nema mata wata makarantar ne Kabiru ya 6ullo da batun san aurenta dan afad'ar sa wai shiru yayi kawai baiyi magana ba amma ya da'de da burin auranta aransa yayi shiru ne ganin bata kammala makarnatar ta ba. "Yanzu kuwa Alhamdulillah tunda ta gama to yana neman izini" Murmushi yah yusuf 'din yayi sannan yace "lalle ka shammace ni Kabiru" "Toh ya za'ayi ne babban yayah sharrin zuciya ne ba ni ba." Dariyah sukayi gaba d'ayansu. Daga 'karshe Yusuf d'in yace yabari yayi magana da ita tukunna sai su san yanda zasu 6ullowa lamarin" Godiyah Kabirun yayi masa. Yusuf bai wani 6ata lokaci ba da yaji maganar,yana komawa gida ya sami Khadija yafa'da mata cewa Abokinsa Kabiru na sonta da aure,itanma cewa tayi duk abinda yaga ya masa kawai yayi ita batada za6i. Farin ciki yayi duk da yasan daman bazata fad'i wani abinda yake sa6anin hakan ba amma sai da ya nuna mata farin cikinsa afili dayasa ta gane cewa lallai yayi na'am da maganar tun farko. Ba awani d'au lokaci ba,aka fara shirin biki bayan sunje k'auye dukkansu sun sanar dasu maganar,mal.Kallah yafi kowa farin ciki dajin maganar dan sauran kusan kowa bai bada wata muhimmanci a maganar ba,tsoronsu Allah da kuma batun kayan d'aki kar ace su zasuyi. _Comment & share_ _pls_ 🤞🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 5:54 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all........ *DA* *BAZAR MU MUKE* *TUN'KAHO* 😍 Dedicated to all masoyan CAPTAIN ABBAS. *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Words are seeds. They land in our hearts. Be careful what you plant and careful what you say. You might have to eat what you planted one day. 🅿 *15* Anty ne ma ta d'anso ta kawo musu wani mishkila kad'an dan fara cewa tayi wai "ai Kabirun ya girmewa Khadijan sosai ta yaya za'a ce shi zai aureta" aganinta ai bai dace ba hakan. Babu wanda ma yabi takanta a maganar tata duk dama basu san manufar maganar tata ba,Yah yusuf ne ma yad'an nuna mata cewa ai ba haramci aciki,tunda annabi ma yayi hakan kuma ba'a haramta mana ba,so bata da hujjar da zata ce hakan ba dacewa bane tunda bawai Kabirun ya shiga sahun dattawa bane,har yanzun sa amatsayin matashi yake" Taji haushin k'in kar6ar maganar da akayi,amma dolenta ta hak'ura tayi shiru. Ba awani d'au dogon lokaci ba aka yi bikin,sosai yah yusuf yayi k'ok'ari wajen ganin ya siya mata duk abubuwan buk'ata tare da sa hannun Alhaji muhammad amma bai yi da sanin 'yar sa ba daga shine sai yusuf d'in suka sani,ahakan ma saida ya gargad'esa akan kar ya sake yaji labari koda abakin y'arsa ne,sosai yusuf yake yabawa da karamcin wannan bawan Allah,bashi da abin rama amsa illah yayi ta masa fatan alkhairi har karshen rayuwar shi. Bayan angama bikin ne kabiru ya d'auki matarsa yakai ta Gomben gefen iyayensa da 'yan uwansa. Anty kuwa sai bayan bikin Khadijan sannan ta san muhimmancinta da amfaninta agidan,dan sosai tafara shan wahala da aikin gidan,ga kuma yaronta da tun tashin sa Khadija ce ke kula dashi,yanzu kuwa abu ya dawo kanta,sai abin ya taru ya mata yawa ga rashin sabo,ga shi sam bata san k'azanta sai ta rasa yadda zatayi da rayuwarta,wuni take akan k'afarta amma still bata gane kan gidan,sai da aka samo mata mai aiki kafin gidan ya saitu mata. Cikin hakan Allah ya d'aga kasuwancin Yah yusuf shima yazama tsayayye da kansa amma da taimakon Kabiru dansu sun san kan kasuwancin sosai,kan kace me sun zama manyan 'yan kasuwa sosai kud'i ya zauna musu. Tunda Anty taga Khadija na shirin kamota a komai sai tafara jin k'yashi aranta,sosai take jin Kishin khadijan,dama tun farko bata so Khadijan ta auri Kabiru ba aganinta ai ya fi k'arfin aurenta shiyasa takawo suka lokacin bikin amma b samu nasara ba. Taso da wani daban aka samu aka aura mata dan ta samu damar takasu amma sai hakan bai yiwu ba. Son zuciya sai ya kaita ga fara Shige-shige,amma Allah bai bata ikon cutar su ba,taso ne tashiga tsakanin auran kKhadija da mijinta amma sai Allah ya karesu da karewarsa. Shekarar Khadija uku da aure sannan ta haifi,'danta namiji sunyi farin ciki sosai musamman dayake tad'an d'au lokaci bata haihu ba sai wannan karan,amma dayake kana naka ne Allah kuma na nashi,tun kan ayi suna yaron yakoma ga mahallici,Khadija tasha ruwan hawaye dan tana da jarabar son 'ya'ya tana murna tasamu nata kuma sai Allah ya kar6e abinsa,dakyar Kabiru ya taushe ta ta hak'ura ta dangana. Ashekarar kuma Kabirun ya kafa cibiyar kasuwancinsa acikin garin damaturun jihar yobe,zama sai ya so ya gagare shi kullum yana cikin tafiye-tafiye. Amma hakan bai ta6a damun Khadijan ba illah addu'ar sa'a datake binsa dashi akoda yaushe,yana kuwa jin da'din addu'ar tata kuma matuk'ar birgesa hakan yakeyi har baya iyah 6oyewa shima,sai ya bita da albarka mad'aukakiya. Sai da aka shekara kafin khadija tak'ara samun wani cikin,murna kam kamar ance musu harta haihu ne ma kowa yana farin ciki da wannan abin musamman daya kasance Kabirun shine babba a familyn gidan,so kowa so yake yaga ya haihu shima. _Allah buwayi gagara_ _misali_ shine yasan sirrin komai da kuma ma'anarta............ cikin rashin sa'a sai cikin ya 6are a wata shida bayan ciwon da tasha na azaba harta fita a hayyacinta ma. Wannan karon kam cewa tayi zata dawo gida ta huta,dakyar mahaifiyar Kabiru ta barta a cewarta toh ta zauna da ita mana basai taje can kanon ba amma fir tak'i yadda. Data je d'in kuwa sai datayi wata uku kafin tadawo,ran da zata dawo ma Mahmud kuka yayi tayi dan azaman datayi ba k'aramin sabo sukayi ba,ita ke tayashi komai,homework,da sauransu. Kabirun da kanshi yazo yatafi da ita gida.Yana tsokanarta wai tazo gida tazama k'atuwa,kuma azahiri bawani jiki ta k'ara ba kawai de tsokana ce irin tasa. Wai ko dai tafison zaman kanon ne yabarta,cemasa tayi ehh" Duk da bawani jin dad'in zama da antyn takeyi ba amma dai tana jin dad'in ganin ahalin gidan nasu kuma zuwa yanzu ta yi wayon da komai Antyn zata mata ba damunta yake yi ba.tunda kallo ne kawai yanzu tsakanin su sai de ko habaici da Antyn ta tsiri yimata marar dalili. Har k'auye duk taje ta kai musu ziyara kuma sunji dad'i musamman data je musu da tsarabar kayan amfanin yau da kullum, sosai sukayi mata tar6ar mutunci da karramawa. Daworta da kusan shekara kafin tasamu wani cikin kafin nan kuwa har ta d'an fara shiga damuwa,mijnta ne ke tausar tare sake tunatar da ita cewa komai k'addar ne kuma ikon Allah ne. Da tayi hak'uri ta dangana kuwa sai gashi Allah ya bata yanzu. Cikin yaso ya bata wahala da farko amma data kai 3month sai ta ji garau,wannan karon ma kokad'an bata saka ran abinda zata haifa d'in zai zauna ba,sai dai tana addu'ar Allah yaraba su lafiya a kullum. Da ikon Allah kuwa lokacin haihuwar da tayi sai ta gagara haihuwa da kanta,hankalin dangi yaso yafara tashi,amma sai likita yakawo shawarar cewa amata C.S,da wuri Kabiru ya amince dan yasan hakan shine kad'ai mafita agaresu. Cikin sa'a kuwa akayi aikin aka ciro mata 'yarta 'yar mitsitsiya da ita. Kowa ya ganta sai yayi mamakin girman nata dahar ya hana a haifeta sai dai da theatre,Khadija kuwa hamdala kawai take da Allah ya rabasu lafiya da babyn duk dama de theatre ce amma dole ta gode wa mahallici. Mahaifinta ne yayi mata hud'uba da FATIMAH ZAHRA a madadin k'anwarsa data rasu ashekarun baya. Kafin suna kuwa gida ya cika mak'il da jama'ah abin gwanin birgewa,dangi ta ko ina,Anty ma sunzo da ita da Mahmud,ga dangin Kabiru ma kaca-kaca. Iyalan Hassan (mahaifin Abbas) kenan suma kusan kullum suna gidan dasu ake komai. Abbas alokacin suma suna da jinjirar su mai suna Hannah,so bai wani damu da ko ganin jinjira ba harkar gabansa kawai yakeyi,shi kuwa Mahmud har yau bashi da kowa,shiyasa ya nace wa wajen da jinjirar take duk inda akayi da ita toh shima nan zai yi. Anty 'ki tayi ta sake haihuwa tun bayan data haifi mahmud,acewarta d'awainiyar yara wahala ne dasu,yah yusuf bai sani ba ma taje aka juya mata mahaifarta. Koda taga yanda Mahmud yake ji da jinjiran nan kuwa haushi kamar ya kasheta,gashi daman zuwan dole tayi tace ma bazata zo ba da farko amma da yah Yusuf ya dage dolenta ta shirya ta taho. Tunda tazo kuwa take ta shan k'anshi,ta na wani kallon raini a mutane,sukuwa babu wanda yabi ta kanta ma balle tankata suka ci gaba da sabgoginsu. Ko kunya bata jiba ta tawo Mahmud ta jajja masa kunne akan nacin dayake wa yarinyar. "Aranta khadija tak m Sanin halinta da sukayi yasa babu wanda ya tankata,tunda d'anta ne ita ta haifi abinta,kuma ita keda iko da shi. Khadija aranta take mamakin irin halin Antyn dan kwata-kwata batayi irin halin mahaifinta ba,shi ba haka yake ba sam. Duk da haka bai fasa ba dan yaro idan yaso abu da wuya ake raba shi da abin,anjima kad'an ya faki idan mamar tasa ya dawo,lokacin Jinjira na hannun Khadija tana shan mama,hannun jinjirar ya kama,yace "Anty miye sunanta ? Murmushi khadijan tayi sannan tabashi amsa da FATEEMAH sunanta" "Lah Anty akwai wata 'yar class d'inmu ma sunanta haka amma da TEEMAH kowa yake k'iranta,itama babyn Haka zanna ce mata " "ko Anty? Kai ta d'aga masa tana murmushi alamar "ehh" wasu dake zaune acikin d'akin ma murmushin sukayi suna jinjina wayo irinta yaron. Kamar wasa kuwa sunan yabita har girmanta. Haka har taron suna ya watse suka koma kano,kuma tun daga lokacin Antyn bata k'ara waiwayar Gombe ba. Sai ita mummyn Teemah da zuwan yazame mata dole,domin su kad'ai gareta sai kuma mijinta da 'yarta. Watanta hud'u da haihuwa taje Kano d'in, zuwa lokacin kuwa yarinya tayi 6ul6ul kamar ba ita ba. Alokacin kuwa ba k'aramin wulak'anci tasha ba awurin Antyn danko y'ar ma bata ta6a d'auka ba,kuma ta hana d'anta zuwa inda Khadijan take,takaicin hakan na damunta,domin bata san dalilin da yake sa Antyn yin haka ba. Samun sauk'inta d'aya idan yayanta ya dawo gidan,danshi d'aukan y'ar yake yayi ta mata wasa shida Mahmud yarinya kuwa tayita dariyah. Khadija tayi ta murmushi ganin yanda suke son y'arta ta. Koba komai hakan kad'ai ma na sata nishad'i Anty kuwa sai dai ta kauda kai gefe tsabar mugun hali dan babu yadda ta iyah dashi sai dai ido. Da lokacin komawar ta yayi kuwa yayanta yacikata da kayan amfani sosai yayi mata siyayyah,na kayan sawan jinjirar da kuma nata bayan wanda ya aika mata a suna. Siyayyah tsakaninsa da Allah yayi mata bawai dan bata dashi ba a'a kawai sai dan yafaranta mata a matsayinta na y'ar uwarsa kwaya d'aya tal daya mallaka. Hakan da yayi kuwa ba k'aramin cika haushi yayi ba azuciyar Anty,wutar tsanar suce tasake ruruwa azuciyar ta fiye da na baya. Mahmud kuwa kuka yayi tayi kamar zai shid'e, "Teemah na! Teemah na!! Teemah nah.......!!! Haka yayita ambata,yana kuka babansa ne yayi ta rarrashinsa dan uwar kam ko kallo ma bai isheta ba da kyar ya hak'ura kuwa yayi shiru. Wash 😢manage pls👏🏻 nagaji wlh 😅 _Comment & share_ _pls_🤞🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 5:55 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all........ *DA* *BAZAR MU MUKE* *TUN'KAHO* 😍 Dedicated to all masoyan CAPTAIN ABBAS.kuyi hak'urin jina da kuka yi shiru kwana biyu,amin uzuri pls.kunsan jiki da jini...... *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* It’s not the mistake that matters; it’s how you deal with it, what you learn from it, and how you apply that lesson to your life. 🅿 *16* Zuwansu kano na k'arshe shine lokacin da Fatima take da shekaru hud'u da haihuwa. sunje da farin cikin su kuma sun samu tarba agun yah Yusuf da Mahmud kamar yanda yake musu aduk lokacin da suka ziyarce su Alokacin Mahmud ya yi girma sosai ya 'kara wayo,shine ya kama hannun Teemah ya rink'a kaita neighbours 'dinsu yana nuna ta wai suga 'kanwarsa shima Daya ke surutacce ne shi hakan yasa itama Teemahn ta sake jikinta dashi aikuwa sunsha yawo babu ruwansa idan yazo yasa su Khadija agaba da surutu har baya gajiya da yi "Anty kudawo nan mana muzauna tare! "Anty kibar min Teemah anan kinji mun zuwa makaranta da ita"!! "Anty in zaku tafi zan biku nima indai bazaki barmin Teemah ba" !!! Khadija murmushi take binsa dashi kawai dan tasan acikin maganganunsa faruwar d'aya daga ciki zai yi matuk'ar wahalan gaske. Tunda tasan tafiyah da Mahmud bazai ta6a yiwu ba dan Anty bazata bari ba kamar yanda ita kanta bazata iya barin 'yarta a gun Antyn ba,itama daya ta tsira balle 'yar cikinta. Tana iyah hango irin hararar da Anty take binsa dashi idan yana irin wannan maganar, Afili zaka fahimci manufar Antyn dan k'iri-k'iri take nuna bata k'aunar alak'ar Mahmud d'in dasu abinda kuma zaiyi mata wahalar gaske wato yanke alak'ar dake tsakaninsu. Dan Mahmud jininta ne,kamar d'anta yake,ba kama bama Mahmud 'danta ne,me rabata da Mahmud kuwa sai dai Allah. Sau tari takanyi mamakin halin Antyn ace k'arfi da yaji ka nuna baka son jinin mijinka,ada ta d'auka ko abin Antyn da yarinta ne idan tayi girma zata daina,amma sai taga sam bahaka bane,don zuwa yanzun ai Antyn ta manyanta, ya kamata ace tasan dacewa da rashin sa basai an karantar da ita ba. Satinsu d'aya tal suka koma Gombe abinsu,da d'umbin tsaraba daga Yah Yusuf harma da Alhaji muhammad. Dawowar su kuwa baifi da 7months ba Yah yusuf ya tattara iyalansa gaba 'daya suka koma Lagos da zama. Kafin su tafin ma Khadija (mummyn Teemah) taso ta koma suyi sallama amma yah Yusuf ya hanata zuwa yace tayi zamanta kawai babu komai. Bazata kawai tagansu a Gombe shida Mahmud,cikin sa'a kuwa alokacin Daddy yana gari,ranar kam tayi murna sosai dan wannan ne ziyarar farko daya ta6a kawo mata musamman dan ita batare da wani dalili ba. Amma washegari da yamma suka koma Kano dan k'arasa shirye-shiryen tafiyar tasu bayan ya cika mummy da d'umbin alkhairai. The next day sukayi sallama da Kano suka d'aga garin ikko. Toh tun komawarsu Lagos mummy bata k'ara zuwa inda suke ba saboda nisan wuri,haka suma shiru, sai dai suyi gaisuwa awaya ko kuma idan Daddy ya kawo musu labarin su dayake suna d'an had'uwa da Yah yusuf d'in wani lokaci saboda kasuwancinsu. Anty kuwa komawa Lagos 'din sai yazame mata abun farin ciki,dan ji tayi kamar dan ita akayi. Da farko tana d'an d'agun kai da fad'i ma kowa,saboda tanajin kanta cewa ita d'in wata abace daban hakan yasa ta dad'e bata samu ko da wacce zasuyi maganar arziki ba ma balle huld'a. Sai daga baya Allah ya had'a ta da wata jibgegiyar 'kabilar mata. Awajen saloon suka had'u acikin unguwan tasu,dayake Allah ya riga da ya tsara had'uwarsu sai bata yiwa matar irin halinta ba,tun a shagon saloon 'din suka saba har da aka gama musu ma suka fito tare. Ahanya ne suka fahimci cewa ashe ma a kusa suke da juna,shikenan tun daga ranar suka d'inke suka zama aminai na bugawa a jarida. Anty chideh ake 'kiran matar dashi haifaffiyar garin Lagos ce,sosai tasan Lagos fiye da zaton mai karatu,kuma zata d'an girmi Antyn da kusan shekaru hud'u zuwa biyar ahaife. Zakuyi mamakin rayuwarta idan kuka gani bata da matsala da komai,sannan bata da 'da ko guda d'aya rayuwarta take yi daga ita sai mijinta _na zo mu_ _zauna_ wanda ya kasance shine abokin rayuwarta alokacin. Ba aure sukayi ba zamane kawai suke yi najin dad'i idan kaga yadda take ikonta shi abin har zai baka mamaki duk da yake ba 'karamin mutum bane shi amma sharrin mace yasa yazama sokon cikin gida. Anty ne ta shiga gidan ranar wata asabar domin haka suka saba ajunansu kowa yanada ikon zuwa gun d'an uwan sa aduk sanda yake da lokaci basa ta6a wuni basuga juna ba tunda suka san junansu. Aduk lokutan da Anty take zuwa gidan bata ta6a had'uwa da mijin Anty chideh ba sai yau. Mamaki ta tsaya yi bayan tashigo harabar cikin gidan,ganin yanda Anty chidehn tasaka babban mutun agaba yana wanke mata inners d'inta,ita kuma ta kame akujera sai taunan chewing gum takeyi tana bashi orders shikuma jikinsa na rawa yana bin umarni. Duk da masu aikin da ke gidan da kuma loundary machine amma hakan bai hanata sashi yimata aiki ba dan kawai ta muzanta shi. Abin haushi abin dariyah,da sassarfa Anty ta k'araso gareta Anty chidehn na ganinta kuwa ta washe hak'ora tareda mik'ewa tsaye. Hannunta ta kama sukayi ciki,aparlourn Anty chidehn suka yada zango. Gaisawa sukayi sama-sama da Antyn,gama gaisawan nasu keda wuya Anty Chidehn ta fara kwalla k'iran maid d'inta jin datayi bata amsa ba alamar maid bata kusa sai ta mik'e da kanta dan kawo wa Antyn ruwa. Dakatar da ita tayi akan cewa tabari kawai bata jin 'kishi ita. "Why nah, ah' ah" Mum Mamud u don't want to eat anything in this house why nah" da fad'a da d'an 6acin rai. Murmushi Antyn ta mata sannan ta bata amsa da harshen da zata fi fahimtar ta akan cewa bata buk'ata ne kawai shiyasa bazata sha ba. Nan kuwa in kabar Antyn wai tana kyankyami ne ba zata iyah cin abincin daya fito daga hannun su ba. Anty batayi k'auran baki ba kuwa tambayarta tayi ya akayi taga oga yana wankin inners bayan ga maid in ita bazata yi da kanta ba. Nan Anty chidehn tayi dariya sannan tace mata kawai haka ta ga dama dama. Antyn nuna mata tahau yi akan hakan ai bai kamata ba,tana rage masa darajar sa ne agidan kuma ma ai yafi k'arfin yin agareta. Jin hakan yasa Anty chidenhn ta hau bata labari dan ita sosai ta yadda da Anty. Dalilin da yasa ta ke mar hakan wai da farko aure suka so suyi amma danginsa musamman mahaifiyarta suka k'i ta wai bade ita ba sai de ya canja wata. Alokacin kuwa suna son junansu hakan yasa suka gagara rabuwa har suka fara zaman su ba tare da kowa yasani ba. Watarana Maman san sai takawo masa ziyara kawai sai ta ganta agidan,itama tayi mamaki dan atunaninta sun rabu da jimawa amma sai ta ganta agidan. Atake kuwa ta tada musu bori da kyar yajata ya kaita gidanta yanata bata hak'uri harda alk'awarin zai sallameta aranar ma ba sai an kwana ba,don ko kad'an baya son 6acin ran mahaifiyarsa. Itama Anty chideh taji haushin abin sosai zama tayi tafara tunanain mafita na yanda zata 6ullo ma al'amarin. Shikuwa yana dawowa ya hau rarrashinta da bata baki akan tayi hak'uri akan abinda mahaifiyarsa tayi ma ya ciro kud'i masu yawa ya bata yace ta koma gida zuwa wani lokacin kafin yayi settling da 'yan uwansa. Bata yi musu ba ta kar6i kud'in daganan taje ta tattara kayanta ta tafi danbata so ya ga nacewarta. Amma ga mamakinta tunda suka rabu bai sake neman inda take ba har kusan wata biyu sai abin yafara damunta. Sai ta yanke shawarar dawowa taji inda maganar su ta kwana,amma cikin rashin sa'a data zo bata same shi ba wai yana Cotonou,haka takoma gida cikin jin haushin rashin samun nasa da batayi ba. Wata guda ta k'ara kafin ta sake nemansa wannan karon kam ta sameshi agida,mamaki yayi daya ganta danshi har ya fara mantawa ma da al'amarinta. Kusa tasa masa tazo da gudu ta rungume shi tana fad'a masa yanda tayi missing d'insa,shikuwa sai bubbuga bayan ta yake alamar rarrashi. Daga k'arshe sai yasake bata hak'uri tare da jaddada mata haryanzu mum d'insa tak'i yadda kawai su hak'ura da juna yafi. Tana jin hakan ta tashi afirgice tana kallonsa shi d'inma tashin yayi yana k'ok'arin yin magana kawai ta suri jakarta tafice da sauri tana me share hawaye. "Chiddy! "Chiddy!! yafara kwalla mata k'ira amma tak'i waiwayowa tayi tafiyarta. Tun daga lokacin ta fara neman hanyarda zatayi maganinsu gaba d'aya cikin sa'a kuwa ta samu. Domin dakansa yaje har gidansu ya d'aukota ya dawo da ita gidansa. Tace yanzu ko cewa tayi ya mari maman nasa toh kuwa marinta zaiyi da rawar jiki ma,rabonsa kuwa da zuwa inda mamar take har ita kanta ta manta,uwar cema ta ke d'an zuwa da kanta,idan kuwa tazo sai tace masa ya kulata kafin zaiyi mata magana,inkuwa bahaka ba harta tafi bazai kulata ba. Tace yanzu maman ta daina zuwa musu dan kusan kullum idan tazo da kuka take komawa shiyasa ta hak'ura ta daina zuwa inda suke. Anan Anty ta tambayeta "toh shi miye nashi laifin da har zata dinga bautar dashi haka." Anty chidehn cewa tayi wai haka ta ga dama." Har suka rabu mamaki bai bar Anty ba,sosai abin yatsaya mata arai har yasa tafara jin sha'awar aikata irin na Anty chidehn itama saboda guntuwar tunani. Tun daga lokacin kuwa suka k'ara d'inkewa da Antyn sosai kamar wasa tafara bayyana ra'ayinta ga Anty chidehn. Da Antyn chidehn taji tasamu passenger kuwa sai ta tayata k'iyayyar itama,nan tajata sukaje gurin mai mata aikin suka fad'i abinda suke so ayi musu. Takuwa ci nasara don ba k'aramar katanga ta gina atsakanin iyalan gidanta da kuma mummy Khadija ba. Tun daga lokacin zumuncinsu ya yanke kat.danshi yah yusuf har mantawa yakeyi da batun yana da wata 'yar uwa aduniyah. Sau tari zasu had'u da daddy har su rabu amma baya tuna tambayarta ma balle ya bada sak'on gaisuwa akawo mata. Daddy kansa yana mamakin abin,shiyasa idan ya dawo in dai yasan mummy tasan da had'uwar tasu sai yace mata yah yusuf na gaisuwa. Amsawa takeyi ita d'inma kawai bawai danta yarda shid'inne ya bada gaisuwar ba. Dan ko awaya ta k'irashi ma bai fiyah tsaya wa ya saurareta ba,balle ya kaiga gaisuwa. Uzuri ya fiya bata da alk'awarin sake k'iranta daga baya idan yasamu lokaci,ki'randa bazata ta6a gani ba kenan yawuce ta. Sau tari kuka take yawan yi idan hakan yafaru daddy ne mai lallashinta ya kuma bata hak'uri akan abin. Da k'yar ta zo tasaba da hakan dan da kanta ta ta fahimci ehh lallai Yah yusuf dagaske yakeyi yanzu yamanta da ita. Daga baya sai abin yabi jikinta itama ta daina neman nasu koda awayar ma,amma bata ta6a mantawa dasu ba azuciyarta. Watan su Yah yusuf hud'u da komawa Lagos Hassan (baban Abbas) shima ya k'aura yakoma Abuja da iyalansa. Ganin hakan yasa daddyn Teemah yace suma su koma damaturun gaba d'aya tunda harkokinsa sunfi yawa acan. Dasuka koma damaturun kuwa sau biyu Abbas yakawo musu ziyara alokacin daya samu hutu sosai sukaji dad'in zuwan nasa dan Abbas sam baida rigima irinta yaran nan,kuma mummy nason shi dan nutsuwar shi jininsu ya had'u da shi sosai. Mummy taso Mahmud ma ya dinga kawo musu ziyara kamar yanda Abbas yayi sai dai inah haka bazai yiwu ba bata san dalili ba amma abin sosai ya ke damunta naganin har zuwa yanzu babu wata shak'uwa tsakanin 'yarta da jinin yayanta. Zuwan Abbas na 'karshe a damaturun kuma sai alokacin suka fi sabawa da Teemah dan zuwa lokacin tafi da wayo sai dai kuma tunda ya tafi bai sake dawowa ba sai da ya girma yayi passing out d'insa. Wannan dalilin ne yasa da daddy ya kawo mata maganar cewa Mahmud zai zo yayi service d'insa a damaturu kawai sai tafara hawaye dan tunowa datayi da yayan nata da kuma barinta da ya yi k'arfi da yaji batare da wani 'kwa'kw'kwaran dalili ba. _Comment and share_ _pls_ 🤞🏻 *Serlmerhn ku ce* 😍 [10/2, 5:55 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all........ *DA* *BAZAR MU MUKE* *TUN'KAHO* 😍 In dedication 2 my sorority sisters *Ummie* *Maijee* *Zuwairah* *Ameerah* and my lil baby sis *miemie.* Allah ya barmin ku.... *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* God does not create a lock without its key & God does not give you problems without its solutions! *TRUST* *HIM* . 🅿 *17* Da daren ranar da Mahmud ya iso ne mummy takewa daddy k'orafin rashin kammala makarantar Mahmud d'in dawuri tace Mahmud d'in fah sa'an Abbas ne amma dubi yanda Abbas ya jima da kammala karatun degree d'insa amma shi Mahmud sai yanzu" Daddyn cema ta yayi shima abin ya bashi mamaki da Yah yusuf d'in ya ce masa wai Mahmud zai zo dan yin service a damaturu har hakan yasa shi tambayar dalilin dayasa har ya makara haka! Yah yusuf d'in ne ya bashi amsa da cewa "wallahi matsalar daga mahaifiyar sa ne. "Hmm Allah ya kyauta"kawai mummyn tace daga nan tayi kwanciyarta tana mai k'ara godewa mahallici. ***** Mahmud ma ranar kwana yayi batare da ya runtsa ba tunani kawai yakeyi akan halin mahaifiyarsa. Tun lokacin daya kammala secondary school ta dage wai sai dai an kaishi k'asar waje yaci gaba da karatun acan shi kuma Abbansa yace sam d'ansa bazashi wata k'asa dan yin karatu ba tunda ga makarantu nan a Naija sai wanda ya za6a shi ba zai kashe kud'insa dan zuwa wata k'asa karatu ba, shi bai ma amince wa Mahmud d'in yaje ko'ina ba in dai har ba cikin Nigeria bane toh bada yawunsa ba" Wannan dalilin ne yasa Mahmud d'in yajima bai cigaba da karatu ba,domin Mahmud d'in kansa da farko ya yi na'am da batun fita abroad d'in amma daga baya daya ga abin kanshi yake shirin cuta sai ya hak'ura kawai, dan ganin Abbansa bashi da niyyan canja ra'ayinsa kamar yanda Anty ma ta nace akan nata ra'ayin. Ganin hakan yasa ya yanke shawarar cewa shifa zaiyi karatunsa koma a ina ne yafi mishi da wannan zaman banzan daya keyi. Akan wannan maganar Anty har fushi tayi dashi wai dan yak'i amincewa da batun data zo dashi,kuma aganinta wai taimakonsa takeyi. Da kyar ya sha kanta ta hak'ura sai da ya bata baki sosai akan hakan kafin ta hak'ura ta barshi. Cemata yayi ta bari yayi wannan d'in inyaso idan yagama inzai cigaba sai ya nema awajen ai duk d'aya ne. Ran Anty baiso ba ta hak'ura duk da irin aikin datasa akayi mata akan al'amarin amma wannan karan batayi nasara ba. Koda Mahmud yajewa Abbansa da batun zaiyi karatunsa a Naija ba k'aramin dad'i Abban nasa yaji ba har hakan yasa ya bud'i baki yayi ta sanbad'o masa albarkatai gwanin birgewa. UNILAG mahmud ya nema ya fara karatunsa kamar wasa sai gashi kuwa ya kammala lafiya k'alau. Toh gurin cika service ne yayi abinsa batare da shawaran kowa ba,dan abin Antyn shima yafara damunsa gani yayi kokad'an bata son yayi ma zancen Antynsa Khadija balle yayi zancen zuwa wurinta. Hakan yasa ya cika service d'insa da Yobe dan yana da labarin Anty Khadijan nasa a Damaturu jihar Yobe take da zama kuma abakin Antyn yaji hakan. Itace da kanta ta fad'a masa watarana daya tambayeta,da fad'a-fad'a ma tabashi amsar amma shi ko ajikinsa bai damu ba tunda dai yaji. Dama niyyansa ya sand'i jiki watarana ya taho Yoben batare da sanin kowa ba amma kafin hakan ya yiwu sai Allah ya dubi niyyarsa ya aiko masa da batun service alokacin da baiyi zaton hakan ba. Dan har ya isa wurin cikawan ma tunanin cika yobe bai zo kansa ba,wani yaji daga gefensa ya ambato yoben a maganarsa sai kuwa yaji. Take shima sai ya tuno da batun Anty Khadijansa. Murmushi yayi daya tuna wannan ma babban chance ne Allah ya aiko masa tunda iyayensa basu san zumunchi ba,shikam zai yi ne ko ta karfi ma sai yaje yoben nan ko nawa zai kashe kuwa bashi da matsala da hakan matuk'ar zaiga kansa acikin jihar yobe toh he can do anything just to see himself there. Iyayen nasa dukkansu babu wanda yayi tunanin zai cika da nisa shiyasa ma babu wanda yasa al'amarin akansa. Cikin sa'a kuwa list na fara fitowa sunanshi ya fito acikin sunayem y'an tafiya yobe state. Farin ciki yaji kamar yayi fiffike ya tashi sama amma haka ya 6oye murnar tasa acikinsa adole ya sakawa fuskarsa 6acin rai lokacin daya shigo gida. Koda yazo da slip d'in gida ma mik'awa Abbansa yayi tare da fad'awa kan kujera batare da yayi magana ba. "Me nake gani ne haka Mahmud? Abban ya tambaya yana mai sake kallon papern da kyau. "Abbah yobe aka turani fah" Zaro ido Abban yayi waje tare da fad'in yobe kayi mai kuma? "Bautar k'asa Abbah" Mahmud ne yabashi amsa da wani tsarewa alamar shima bayason gurin. "Haba Mahmud shine har can saboda Allah! "Abbah toh ya zanyi an riga an cire list d'in bansan yanda zanyi ba,nima yamin nisa gaskiya, amma dai zan gwada sa'a ta nagani ko za'a dawo dani kusa" "gaskiya kam ka gwada amma ai yobe yayi nisa sosai." Mahmud bai k'ara magana ba illah tsayawa da yayi yana kallon Abban nasa da mamaki,ganin dayayi kokad'an bai kawo batun y'ar uwarsa dake zaune acan d'inba ko kuma irin yayi farin ciki da hakan yaru ba kamar yadda ya saba. Aganin Mahmud ai murna ya kamata Abban nasa yayi dayaji batun zuwansa yoben bawai yayi againsing ba,amma ga mamakinsa sai yaga ko ya nuna alamun irin da wani nashi ma acan d'in baiyi ba balle ace zai k'arfafa tafiyar kodan dalilin Anty khadijan. Lokuta da dama yana mamakin irin girman laifin da Anty khadija tayiwa Abban nasa da har yasa yake kaucewa duk wani al'amari dazai shafeta. Gagara hak'uri yayi har baisan lokacin da ya bud'i baki ya tambayi Abban nasa ba. "Abbah meyasa kamanta da Anty khadija ne? Yah yusuf najin abinda Mahmud d'in yafad'i sai ya d'ago fuskarsa da sauri ya tsurawa fuskar Mahmud d'in ido kamar wanda akace zai ga wani abu akan fuskar Mahmud d'in idanuwansa har tara ruwa suka yi. Gani hakan yasa Mahmud lumshe idanunsa tare da d'auke fuskarsa daga saitin daddyn yamaida shi inda yaji takun tafiyah anan ya k'arasa bud'e idanun nasa ya sauk'e su akan K'afar Anty dake tahowa da takunta na k'asaita. "Ha- ah "yah na ganku jigum-jigum haka? "Meke faruwa ne? Tana maganar ne tare da hanzarto wa izuwa garesu. Abban ma sai da yaji muryarta kafin ya d'auke idanunsa daga kan Mahmud d'in ya maida shi kanta. 'Zuwa tayi ta zauna a gaf d'in dake tsakaninsu,sannan ta maimaita tambayar tata. Mahmud bai kalli inda take ba ya bata amsa da fad'in Anty service d'ina Yobe state yafito" Hannunsa yana yawo akan fuskarsa yayi maganar. Karkuso kuga yanda Anty ta firgita daga jin an ambaci yobe har taso k'ara saka Mahmud cikin tunani amma sai ya waske. "Haba no wonder naganku jigum-jigum ai dole" "Su rasa inda zasu kaika sai wancan garin? Dukkansu kallonta sukeyi yanzu kam,kowa da abinda ke ransa. Abbah so yake yayi maganar 'yar uwarsa Khadija amma azahiri yakasa furtawa,aransa kuwa harhad'a maganar yakeyi tsaf "Yauwa Alhamdulillah fad'uwa tazo dai-dai da zama tunda Khadija nacan ma na tabbata baka da matsala da komai" Maganar dake ran Abbah kenan amma afili ya gagara furtawa,nawi yakejin harshensa yakeyi akullum indai akan Khadija ne. Mahmud kuwa mamaki yakeyi aransa shima naganin ko Anty ma bata kawo batun sauk'in da hakan keda shiba ganin Anty Khadija nacan ko kuma irin yaga ta nuna farin cikinta akan faruwar hakan. Alwashi yaci aransa nasa cewa sai ya tambayi Anty yaji ko me Anty Khadija ta musu suka tsaneta haka,kowa baya son abu agidan indai al'amarin yashafeta ne. Ahakanma gara Anty dan ita idan ya tambayeta abu tana d'an bashi amsa koda kuwa da fad'a-fad'a ne sa6anin Abbansa da ko magana baya masa indai ya had'a da batun Khadija ne toh sai dai kallo da idanu babu magana ko kad'an. Abbansa bai ta6a bashi amsar tambayoyin dayake masa ba akan Anty khadija ko da kuwa sau d'aya. Washe gari kuwa yaje yasamu Anty da tambayar laifin da Anty Khadijan ta musu da har suka d'auki irin zafi haka da ita! Masifa Antyn ta fara masa kamar ta ari baki garin masifar ne ta d'an kuskure ta ce masa "Bana son fitina Mahmud kai komai sai ka bishi da tambaya ne? Meyasa bazaka bar komai ayanda kaganshi ba? Ina zaman zamana kar ka kuskura kaja min fitinar dana kwantar da ita da kyar" "Fitina kuma Anty wace iri? Ya tambayeta da mamaki kwance akan fuskar sa. "Irinta uwarka"🙈 Tabashi amsa kai tsaye. "Ah ah naji ne kince kin kwantar da ita da kyar toh kuma ni bansan fitinar ba Anty laifine dan na tambaya? "Katashi kaban wuri ni banason hauka" Ta fad'i da matukar 6acin rai dan zuwa yanzun sosai ranta ya fara 6aci dan ganin Mahmud d'in nason ya k'ureta. Bud'an baki yayi zai sake magana ta mik'e tsaye kamar andannna mata remote hanyar fita ta nuna masa "I said get out from this room now" Da wata uwar tsawa tayi maganar hakan yasa ya mik'e tsaye yana k'ara gyara zaman rigar dake jikinsa har ya fara tafiyah sai kuma ya juyo ya kalleta sannan yace "Hakan da kuke yi ne yake k'ara samin sha'awar tafiya wancan garin dan na san meke faruwa na tabbata zanji koma menene acan d'in ba kamar yanda kuka barni acikin duhu b......... Bai k'arasa ba ta kar6e maganar "Mahmud kar ka ce min da kanka kacika wannan garin dan ka muzanta ni........tak'ara sa maganar tana nuna kanta da yatsanta. Murmushi yayi sannan ya lumshe mata idanu. ga dukkan mai wayo yasan hakan dayai alamar tabbatarwa yayi mata. Haushi sosai taji sai kuwa tace "Za ko kaci ub........🙈 Juyawa yayi ya fara tafiyah ahankali yana jijjiga kansa yana fad'in "yau kad'ai Anty kin koyi zagi narasa ma'anar hakan fah" cewa tayi "Eh zaka ce haka mana dake ka maidani sa'ar ka,zanga kuwa ubanda zai barka kaje can d'in ai, idiot" Bai kulata ba yanzun kawai ya cigaba da tafiyarsa har yabar cikin d'akin,yana k'ara jin mamakin Antyn yanda ta wani d'au zafi akan wannan simple abun. Ai dole ma naje kodan na tambayi Anty Khadija abinda ta musu suka tsaneta haka. Kwanaki na k'ara ja lokacin tafiyar Mahmud na sake k'aratowa,kamar yanda hankalin Anty ke k'ara tashi akan batun tafiyar,ita aganinta tasamu ta d'an sake babu batun dangin miji ya zai je ya jaji 6o mata jaraba tana ji tana tana gani. _Kuji fah ikon Allah_ Babu irin k'ok'arin da batayi ba akan tafiyar amma abun yaci tura gani take kamar ma himma take k'arawa Mahmud d'in akan tafiyar. Shikuwa dagangan yake komai akan batun tafiyar duk dama har yau Abbansa baice komai akai ba amma yanda Antyn tayi reacting so yake yaji dalilinta nayin hakan kuma tak'i sanar dashi asalin dalilinta dan haka yake abinsa da gangan dan yata tunzura ta ko zata yi zuciya tafad'a masa dalilin amma shiru. Sai dai tayi ta hantarar sa kamar wani yaro d'an goye ga wani zafin rai data d'auka ta d'orawa kanta da ya rasa manufarsa kwata-kwata. Tafiyar saura baifi sati ba ne Daddyn Teemah yazo Lagos anan Abbansa yake fad'a masa cewa ai mahmud d'in zai zo Yoben Bautar k'asa. Daddy dayaji hakan bak'aramin farin ciki yayi ba musamman kodan matarsa Khadija yasan zatafi kowa farin ciki da wannan batun,amma bai nuna zak'ewarsa ba tunda yaga yanayin Yah yusuf d'in asanda yake maganar shima bawani farin ciki ya nuna da faruwar hakan ba. Sai dai duk da haka sai da yatambayi meyasa kuma sai yanzu Mahmud d'in zaiyi service?...... me yasa baiyi karatun da wuri ba?......... Amsa Abbah ya bashi atakaice. Haka suka rabu da Yah Yusuf d'in Daddy nacewa Allah ya kawo shi lafiya ina nan ina jiran isowarsa. Shima dagangan ya daina sako zancen Khadija a tsakaninsu dan ganin kamar yah yusuf d'in baiso. Dan idan ya matsa masa da tambayar ya sanar dashi laifinta kodan ta nemi yafiyarsa ma sai yaga yatsaya jim kamar an dasa shi wani lokaci har k'walla yake sharewa amma still bazai bada amsa ba. Ana washe gari Mahmud zai tafi ma Antyn kamar ba d'anta ne zaiyi tafiya ba,ita adole fushi takeyi dashi har wani lokaci ji yake kamar yafasa tafiyan amma inah sai yaga bazai iya ba yazama dole ne ma yaje shi d'in. Zuwa yayi ya zauna akusa da ita sai tayi kamar bata ganshi ba taci gaba da kallon television d'in data keyi. Shima sai ya maida kallonsa zuwa inda take kallan sannan ya fara magana "Yanzu Anty fisabilillahi kin kyauta min? ace zanyi tafiya amma ko kulani ma sai ki dai nayi bayan kinsan dole ina buk'atar sa hannunki ashirin da zanyi? Ni ne fah Anty ki ganni dakyau fah idan na tafi ba dawuri fa zan dawo ba" Amsa shi tayi da "Sai mai toh Mahmud,idan katafi dan Allah karka dawo Har abada kaga ko zan damu" Ido ya zaro waje tare da fad'in "har abada dai Anty" "Uhm,ka gwada mana kagani" ta bashi amsa. "Niii d'in "ya kara tambayarta Harara tabisa dashi kawai "Toh aini Anty bazan iyaba,ina zan iya rayuwa babu ke akusa dani!" "okay sai yanzu kasan amfani na kenan,daka maida ni tamkar abokiyar wasan kan kamanta ko? "Bahaka bane fah Allah,haba Anty kefah uwace ,kar kifiya son kanki dayawa mana,ki tuna abaya dalilin bin umarninki nayi shekaru ina zaman banza agida batare da na k'ara sa makaranta ta ba,alokacin fah dakin bari nayi na tabbata da yanzu na wuce wannan level d'in da jimawa,amma haka na biyeki daga k'arshe kuma bagashi ba ahakan dole nayi batare da burin naki yacika ba. Toh wannan d'in ma haka kike so na kuma yineh? Bayan inada right d'in yin hakan Anty? "bama wannan ba Nidai dan Allah ki daina fushin nan kisamin albarka awannan tafiyar tawa." Kinji". Haka yayi ta lalla6a ta harta sauk'o daga fushin amma dai har yanzu ranta bai d'auki tafiyar ba. Haka dai ta hak'ura tanaji tana gani washe gari ya kama hanya yayi tafiyarsa dolenta tayi masa fatan Alkhairi badon taso ba sai dan son da take masa a matsayinsa na d'anta k'wallin k'wal a duk fad'in duniya. Juyi mahmud yayi zuwa d'ayan gefen sannan yace wannan tambayar ta dawo kanki mummy dole in tambayeki dan so nakeyi in sami amsa ta kafin nabar garin nan. *Serlmern ku ce* 😍 [10/2, 5:55 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all........ *DA* *BAZAR MU MUKE* *TUN'KAHO* 😍 In dedication 2 my sisters👇🏼 *Ummie* *Maijee* *Zuwairah* *Ameerah* and my lil baby sis *Miemie.* Allah ya barmin ku....(Ameen) Masoya nagode da addu'o'inku I'm safely arrived,nima ina muku fatan alkhairi gaba d'ayanku,duk wacce tamin addu'a Allah ubangiji ya saka mata da mafificin alkhairi,Allah ya kar6i ibadunmu.👏🏻 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Mathematics may not teach us how to add love or how to minus hate. But it gives us every reason to hope that every problem has a solution. 🅿 *18* _Back to labari_ ........ Sam Mahmud baiyi wani baccin kirki ba adaren,sai kusan 3:00 o'clock kafin baccin ya d'auke sa bayan yayi sallahr nafila sannan yayi baccin. Sallar asubah ma da kyar ya yi ta acikin d'akinsa,saboda baccin dake fisgar idansa,yayin da su Abbas suka wuce masallaci dan sunta mar knock amma bai bud'e k'ofar ba a tunaninsu baccin gajiya ce ta d'ebesa basu san cewa kwanan zaune yayi ba shikam. ***** Washe gari ma Mahmud bai fito ba sai kusan 10:16am kafin suka ganshi. Ad'aki ya samu Abbas yashiga da sallamah abakinsa amma bai tsaya jiran umarnin shiga ba ya shiga abinsa. Abbas na zaune akan cough da system a gabansa sai kawai yaga mutum yashigo,danshi sam baiji sallamar da mahmud d'in yayi ba dan gaba d'aya hankalinsa yatafi ga abinda yake kalla. Juyawa yayi suka had'a ido da Mahmud take sai mahmud d'in ya mik'o masa hannu. Shima hannun ya mik'a suka tafa "Ya ne guy u look bored,meke faruwa ne"? Abbas d'in ya tambayeshi. Tsaki kad'an Mahmud d'in yaja sannan yace "kabari kawai gajiya ce wlh" "Hmm jiya danake koranka kaje kayi baccin ai iskanci kaso yimin sai gashi kuma tun ma ba'ayi nisa ba kana complain" Abbas ne yafad'i hakan yana d'age gira sama. Mahmud baiyi magana ba illah tashi da yayi tsaye sannan ya d'anyi mik'a,Abbas d'in sai ya sake binsa da kallo yana murmushi yace "sai wani abu kake fah kamar mace yanzu akan baccin ne kaketa wannan abin"? "Allah baccin bai isheni ba ne" "Sai ka koma ai ka cigaba dayi tunda bai isheka ba" inji Abbas "Mummy nakeso ingani ne shiyasa in badan haka ba ai ko tasowa ma bazanyi yanzu ba." Abbas d'in ma mik'ewan yayi jin Mahmud ya ambaci mummy. Yace "muje toh nima ban shiga ba har yanzu" Atare suka fito suka isa babban parlour,koda suka isa babu kowa acikin d'akin hakan yasa suka zauna akujera suna d'an hira. Zaman sun baifi da 7minutss ba saiga mummy tafito,murmushi ta sake data gansu,sai kuwa ta nufosu fuskarta cike da annuri. Haka tazo ta zauna suka gaisa ta tambayi Abbas ya yanayin garin yace "Alhamdulillah mummy" "Masha Allah" tace Sannan ta juyo ga Mahmud shima tamai ya gajiyan hanya da kuma bak'unta, cewa yayi "wlh mummy jinayi ma kamar yanzu ne nayi tafiyar tsabar gajiya" "hmm" kawai Abbas yace Mummy kuwa murmushi tayi sannan tace "sai a hankali ai", gacan break fast d'inku a dinning Daddynku ma shikam yafita tun d'azu,bari na k'ira Teemah dan itama bataci ba ni tun safe ma banganta ba" Tana fad'a tamik'e tsaye. Amma sai Abbas yadakatar da ita da fad'in "haba mummy dakanki? yi zamanki bari na mata magana." "Toh shikenan tunda ka hutar dani ai." Tayi maganar tana komawa a inda ta tashin. Abbas kuwa wucewa yayi kamar da gaske,ya nufi d'akin Teemah,daya isa bakin k'ofar sai kuma ya tsaya,sai ya rasa ya zaiyi ma,to k'ira zai kwalla mata ne ko kuma sallama zai mata idan tafito sai ya hankad'a keyarta zuwa parlourn. Rasa wanda zaiyi acikinsu yayi,sai kawai yasa hannu ya tura k'ofar ahankali ya shiga ciki. Gani yayi d'akin bakowa,sai ya hau rarraba idanunsa,yaune farkon shigarsa d'akin nata tunda yazo gidan. D'akin tsab ba wani datti sai dai tabar windown baya a bud'e. Takawa yayi a hankali ya isa wurin windown,labilen ya d'aga sai ya hango yanayin wurin ya matuk'ar k'ayatar dashi. Daga inda yake tsayen yana iya hango cikin lambun dake gidan nasu,sai yaji hakan ya matuk'ar k'ayatar dashi hakan yasa ya 6ata lokaci agun yana kallon wajen har ma baisan lokacin data fito ba. Itama bata lura da shi ba dan yunwa na cinta sosai sauri ta ke ta shirya dan taje ta samu abinda zata ci,kuma kokad'an bata zaci wani zai shigo mata d'akin ta ba. Allah sai ya taimaketa bata cire towel yau ba kamar yanda tasaba. Gaban mirror ta wuce tazauna tana k'ok'ari d'auko man shafawan ta ne ta hango sa tacikin mirrorn,firgita tayi sosai take saita mik'e tsaye daidai shikuma ya juyo. Kallonsa ta tsaya yi kamar yanda shima yake kallonta. Tsawon mintina biyu kafin ya kauda kansa gefe. "Astagfirullah" Yace azuciyar sa sannan ya dawo da kallonsa kan fuskarta. "Ya akayi ne kin wani tsaya kallona" Batayi magana ba still illah k'asa da tayi da idanunta. Ganin hakan yasa ya juya ya koma wurin windown. "Meyasa kike bari abu'de?yajeho mata tambayar. "Mantawa nayi" Itama ta fad'a atakaice. Barin wajen yayi yasake dawowa inda taken "kidinga kulawa idan zaki kwanta kinji" kai ta d'aga masa alamar taji Daga nan sai ya nufi hanyar fita harya kusan isa ga k'ofar kafin yace "kiyi sauri ki shirya ki fito mummy na k'iranki" "Uhmn" ta masa masa dashi daga nan sai ya fice abinsa. Sharp-sharp ta shirya tafito tasame su a palourn. Zuwa tayi gefen mummy ta zauna sannan ta gaisheta daga nan tagaida su Abbas ma. Mummy ce tafara mik'ewa tana fad'in "bismillanku" Teeamh ce tafara biyo bayanta sannan su Abbas ma. Bayan sun isa sun zauna ne mummy tace toh teemah tayi serving d'insu. Tashi tayi ta had'awa kowa nasa sannan tahad'a nata ma daga nana ta zauna. Mahmud ne ya lura da yanda take shan tea d'in yau ba bu yanga sai yace "cin abincin daman zuwa-zuwa ne" Mummy ce takar6e zancen dafad'in "ai in kaga haka toh yunwa ne yaci k'aniyarta" "Ai kuwa naga alama"yana murmushi yayi maganar. Abbas kama bai kulasu ba illah kallonta dayayi sun kuwa had'a idanu sai tayi saurin kawar da kanta gefe. Itace tafara tashi a table d'in ta koma d'akinta. Su kuwa suna gamawa Mahmud yace su fita yawo cikin gari. Haka suka fice yayinda Mahmud kejan motar sikuma Abbas na gefensa azaune. Yobe state university(YSU) suka je dan Mahmud yace akwai wani friend d'insa dake lecturing acan. Basu suka dawo gidan ba har saida suka yi sallar azahar. 15minutes to 2 suka shigo gidan,direct kuwa suka nufo parlour dana tun d'azu Mahmud ke mitan yunwa yakeji kuma yayi-yayi da Abbas akan su tsaya wani wuri su d'an ta6a abu sam Abbas yak'i shi wai sai abincin gida zaici. Zubewa sukayi aparlourn yayinda suna d'an ta6a hira. Muryarsu ne yasa mummy fitowa anan ta samesu sun yi d'ad'd'aya akukera,Abbas sai mita yake yi wai Mahmud bashida dauriya ya fiya ragwanci. "Mahmud kuma yace angaya ma yunwa ta tana yi da wasa ne? "Toh cinye ni mana kafin abincin ya iso"inji Abbas kafin Mahmud yayi magana sai sukaji muryar mummy tanace musu duk su taso abincin ai tun d'azu yake jiransu. Sai alokacin suka lura da fitowarta,gaida ta sukayi ta amsa tana zolayarsu daganan suka mik'e suka wuce kan dinning d'in gaba d'aya. Tun kafin su isa mummy taketa kwalla k'iran Teemah, jin Teeman ta amsa ne yasa mummyn yin shiru suka zazzauna. Mahmud ne yace "wai ita mummy kullun wannan yarinyar sai an gayyatota cin abinci ne kafin takeci" Mummyn amsa masa tayi da fad'in "ai inka barta kace sai ta nema da kanta toh kuwa zaka dade baka ganta ba,shiyasa nake sata ci acikin jama'an wai ko zata saba" Mummy nagama fad'in hakan sai ga Teemah ta 6ullo,binta sukayi da kallo harta k'araso. Abbas aransa yace "masha Allah" dan sai yanzu ya lura da kyaun datayi dukda bawai ta canza kaya bane tun na safen ne data saka ajikinta amma kuma sai yanzu ya lura da kyaun datayi dan d'azun bai kula da hakan ba. Jiyayi yana jin zafin kallon da suke mata d'in gaba d'aya. Zuwa tayi itama ta zauna akusa da mummy sai ya kasance tana tsakanin Mahmud ne da mummyn. Mummy ce tace Teeman ta tashi tayi serving d'insu abincin. Zaro ido Teemah tayi waje tare da fad'in"mummy nikuma? Da "ehh mana Teemah" mummyn ta amsa mata. Sai tace "amma mummy idan na saka kowa sai ya cinye nasa gaba d'aya" "Naji ni dai tashi kisa mana abinci yarana duk yunwa suke ji" Tana jin haka sai ta turo baki gaba sannan tace "wlh mummy kullun wareni kikeyi agidan nan tunda kika gansu,nima indai hakane gidan daddyn Abuja zan koma abuna" Dariya tabasu gaba d'aya,amma sai dai mummy da Mahmud ne suka dara Abbas kam murmushi kawai yayi. mahmud ne yana d'an dariya yace "kai mummy ki barmin lil sis d'ina pls adaina 6ata mata rai" "Hmm ni wlh dariya ma kike bani Teemah toh har ina abin fishin yake anan,kede Allah ya rabaki da mugun halin nan Teemah" "Kauda kanta tayi gefe haushi kamar zatayi kuka. Mahmud kuwa ganin bazata saka musu abincin bane yasa shi fad'in "banace zan kaiki da kaina ba maza tashi kisa mana abinci kinji baby sis rabu da mummy" "Ai cemin tayi mai mugun hali" "Sorry 'yanmata wasa take miki fah" ya fad'a yana kallonta. Zata sake magana yace" haba mana Teemah yunwa fah nakeji" Abbas kam sai rarraba idanu yake akansu ya kalli wannan ya kuma kallon wannan. Dayaji mahmud yace yunwa yake ji ne shima yace "Allah dai ya shiryaka mahmud" "Ehh naji haka kurun ai da gaskiyata ko so kake nayi shiru yunwan ta illatani ne" "Kai kasani ai" Abbas d'in ya fad'a dajin haushi Daganan Teemah ta tashi tana turo bakin ta zuba musu abincin harda na mugunta sannan tasaka nata kad'an ta zauna. "Hmm mummyn tace tana k'ara yin murmushi ahankali tace "Teemah ko rigima in ance mugun hali kuma tace ita ba ita ba,inbanda haka ina zasu kai wannan abincin." Bata kula magananar mummyn ba Zama tayi suka fara cin abincin. Wurin shiru bakajin k'aran komai sai na cokula. Kowa yayi nisa dacin abincinsa yayinda Teemah kwata-kwata spoon d'inta uku sai juya cokalin takeyi a hannunta kamar mai k'rga abincin. Mahmud ne ya lura da ita ganin bata cid'in ne yace "Yadai kici mana keda kika ce kowa sai ya cinye nasa gaba d'aya,ahakn ne zaki cinye?" Sarai tasan da ita yakeyi amma sai tak'i kulasa ko d'aga kai ma takalle sa k'inyi tayi. "Barta mana wai ita sarkin wayo ba" cewar mummy Mahmud kuwa barinta yayi ya sake d'iban wani abincin yakai bakinsa,daganan ya d'ebi wani ya nufo ta dashi. "hun haahh" yace yana kallonta,itama da mamaki tabi abincin da kallo sannan ta kallesa. "Open your mouth mana" Yafad'a da seriuos tune Sai da ta kalli mummy tukun sannan ta kalli Abbas sai ta ga dukkansu babu wanda hankalinsa yake wurinsu. Bud'e bakin tayi yasaka mata abincin. Abbas kuwa duk abinda ya faru yana lure da shi,sai da yaga zata kalleahi ne kafin ya maida kansa k'asa tamkar tun zamansa awurin bai kalleta ba........bata san tun d'azu yake lura dasu ba, jiyayi tamkar ransa zai fita ajikinsa data kar6i abincin,jiyayi ya gagara natsuwa sam,"innalillahi yake ta fad'i azuciyarshi bai san dalili ba amma sai yaji ya tsani wannan scene d'in. Take tunanin baya ya fad'o masa arai,irin yadda yake kula da ita shima yake bata abinci abaki,yau ga wani daban ya fanshe shi.......... Haka yaci gaba da bata abincin ita kuwa kamar jira takeyi daman abata sai kar6a takeyi mummyn kam cewa tayi "aikuwa aiki ya sameka Mahmud indai wannan ce" Maganar tata ce ta dawo da Abbas cikin hayyacinsa sai alokacin ya lura ashe Mahmud cigaba da bata abincin yayi ko kunyarsu bayaji. Shikuwa Mahmud zuciyarsa d'aya yake bata,dan yasan is not a crime tunda sistern shi ce. Spoon kusan biyar takar6a a hannun Mahmud sannan tace ya isheta. Wani uban tsakin da Abbas yaja harni ma na tsorata da ita,sai dai sa'an shi d'aya azuciyarsa yayi shiyasa babu wanda yaji. Cak ya mik'e tsaye ransa amatuk'ar jagule amma babu wanda zai fahimci hakan sai wanda ya sanshi sosai,saboda yanayin yariga yazame masa jiki,shiyasa babu wanda yagane halin dayake ciki. Ummansa kad'ai ke fahimtarsa aduk halin dayake ciki sai ko Daddynsa. D'akinsa yawuce direct yana shiga ya hau fincike riga kamar ita ce tamai laifin. Bayi ya shiga ya watso ruwa ya fito dayake yana ta fad'in "la haula wala kuwwata illah billah"acikin zuciyarsa tunda abin yafaru sai hakan yasa yad'anji sassauci. Kwanciya kawai yayi agadon dake d'akin sa cikin sa'a kuwa sai bacci ya d'auke sa. Yayin da Mahmud yake can zaune da mummy Teemah kuma tashiga dan shirin zuwa islamiya. Fitowa tayi da hijab d'inta ahannu tace "toh mummy na shirya yau wazai kaini"? "Je ki d'auko kud'in adaidai ta ajakata"cewar mummyn. Har Teemah ta juya da nufin zuwa d'akin mummy sai Mahmud yace ta dawo zai kaita. "Dauko wanda zaki dawo dashi toh"mummyn tasake fad'i Mahmud d'in ma sake cewa yayi "bari zan d'auko ta mummy idan sun tashi" "Karfa a takura ka Babana"mummyn tafad'a tana kallon sa "Haba mummy akan d'an wannan d'in" Shima yabata amsar maganar tatta yana murmushi Teemah hijab d'inta tasaka ranta fari k'al dan dama ta tsani hawan adaidaitan dan bata samu ma da wuri gashi ana zabga rana. Koda suka fito kuwa Mahmud sai da ya lek'a d'akin Abbas da niyan sanar masa da fitar tasu amma sai yaga ma yana bacci. Hakan yasa ya fito suka tafi abinsu. Kamar yanda yafad'a d'in kuwa ana tashi yawuce ya dawoda da ita gida. _Comment share and_ _vote pls_ 🤞🏻 *Salmern ku ce* 😍 [10/2, 5:55 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 dukkan masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs.Nagode da_ _irin kyawawan_ _addu'o'inku_ _gareni.Nima ina_ _sonku sosai_ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Fake friends are like shadows, always near you at your brightest moments but nowhere to be seen at your darkest hours. 🅿 *19* Mahmud shegen surutu ne dashi, gashi baya da bak'unta sam gashi da iya jan mutun da hira hakan yasa awannan fitar da sukayi da Teemah har sabo ya shiga tsakaninsu na ban mamaki. Tun daga ranar shiyake ajiyeta a school ya kuma d'auko ya dawo da ita gida da yamma ya ajiyeta a islamiya kuma. Tare suke zama suyi hira haka abinci ma bai fasa bata ba kamar yanda ya fara tun farko sai ya mik'e kawai da haka, dan suna zama a kan table zai fara bata sai yaga tace mar tak'oshi kafin yaci shima, wani lokaci har d'akin sa take zuwa dan kawai suyi hira idan taga Mahmud d'in bai zo nemanta ba,idan akayi rashin sa'a kuma ranar yana d'akin Abbas sai fatattako ta tmdawo tana ture-turen baki tana mita,mummy najinta kuwa aja bakin har sai tayi kuka. Koda lokacin shiga CAMP d'in Mahmud yayi ma Abbas ne da Teemah suka rakashi,Teemah harda d'an guntun hawayenta tana ta mar shagwa6an wai zai tafi ya barta shikuwa Mahmud yanata mata dariya. Abbas haushin hakan yaji, sosai abun ya sosa ransa har ya gagara juran ganin abinda Teeman takeyi dan Mahmud zai shiga CAMP ai baisan lokacin daya sa hannu ya finciko ta da k'arfi ba, bai tsaya ko'ina ba sai daya danganta ta da cikin motar ya tura marfin ya rufe sannan ya zagaya ya shiga shima ko takan Mahmud d'in ma bai k'ara bi ba. Idan kagan shi zaka yi zaton ko gajiya yayi da abinda Teeman keyi shiyasa yayi hakan, kamar dai yanda Mahmud ma tunaninsa ya tsaya iya nan.Hakan yasa yabi bayansu da murmushi yana k'ara jinjina hali irin na Abbas d'in sam baisan wargi. Abbas kuwa takaici ne yagama cika mas kwakwalwa, suna shiga cikin motar kuwa ya d'aga hannu ya sake mata wani rankwashii mai azabar zafi dan ya yishi ne a zuciye, amma sai ya waske da fad'in cewa bata da kunya ita kokad'an, wai 'yar k'arama da ita sai fitinan tsiya. Bata fahimci mai yake nufi ba, amma zafin abinda yamatan sai yasata kuka,kukan tafara da d'an sauti dan abin biyu yazame mata ga missing d'in yah Mahmud ga kuma zalinta da akaci abanza. Takuwa k'iyin shiru da gangan ma taketa yin kukan da sauti aranta take cewa aikuwa zaka ga fitina yau d'in nan ganin idonka. Bai k'ara kallon inda takeba balle ya kulata sai da yaga kukan bana k'are bane kafin yayi parking agefen hanya da k'arfinsa sannan ya kalleta yace "Zan 6a66allaki anan wallahi idan bakimin shiru ba idiot" yafad'a yana wani zaro idanu Shiru tayi cak kamar anyi offing switch dayake daman kukan na isaknci shiyasa tayi tsit da wuri dan sosai ta tsorata da yanayinsa na yau d'in acikin ranta tasake fad'in "ashe dai ni zanga fitinar bashi ba." " _Banza jarababbiya_ " Yafad'a lokacin da yake k'ok'arin tada motar aranta ta amsa da "wallahi badai ni ba kam sai dai kai" Tana fad'a tawani kau da kai gefe kamat wata jaruma. Dayake bajinta yayi ba shima sai bai kulata ba. Tuk'in ya cigaba dayi batare da ya d'auki hanyar da zata sada su da gida ba. _Waziri ibrahim_ ya nufa ita kuwa sai ware ido takeyi da mamakin yaushe yasan unguwar kuma mai ya kawo su hanyan nan d'in, kodan ma ai bai san gari ba ba mamaki 6atan kai yayi"duk aranta tayi wannan tunanin. Hakan yasa da gwanintan ta tace "yayah nan fah ba hanyar gida bane" Hannunsa ya d'ago da niyar gwa6eta a baki sai tayi saurin yin k'asa da kanta ta 6oye fuskar atsakanin cinyoyinta. Hakan datayi ne ya kwaceta sai shima ya maida hannun nasa kan stairy tare da fad'in "nonsence". Tafiya kad'an ya k'ara sai ya sa hannu ya d'ago wayarsa yayi dialling wata no. Baiyi magana ba sai kawai "uhm" dayace yana fad'in hakan kuwa ya cire wayar akunnan sa tare da ending call d'in sannan ya ajiye wayar a gefensa. Parking taga yayi a k'ofar wani gida,minti biyar mai kyau basu k'ara ba sai ga wata y'ar kyakykyawar budurwa tafito daga cikin gidan tana zuba murmushi. Shikuwa yana ganinta ta fito sai shima ya bud'e motar ya fita ya tareta suka had'u a tsakiya. _vote & comment pls_ 🤞🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 5:57 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 dukkan masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs.Nagode da_ _irin kyawawan_ _addu'o'inku_ _gareni.Nima ina_ _sonku sosai_ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Fake friends are like shadows, always near you at your brightest moments but nowhere to be seen at your darkest hours. 🅿 *20* Yarinyar kam masha Allah ba dai kyau ba,Teemah k'ura mata ido tayi tana ta kallonta har Abbas d'in ya isa gareta.Sai alokacin nr ta d'auke idonta daga kan yarinyar. Saitin yarinyar Abbas ya tsaya sai ya zamana Teemah bata hangota kok'ad'an dan duk tsawon Abbas ya kare ta,sai dai bakin gyalen yarinyar da iska yake ta kad'awa shi kad'ai Teemah ke iya hangowa game da yarinyar. Amma tun fitowar yarinyar Teemah ta lura yarinyar "A" ce afagen kyau, hak'ik'a kyau kam Allah ya bata ba laifi,taso tayita ganin yarinyar har tasamo abin kushewa amma sai Abbas yayi mata yaawah yayi babakere ya rufe ta gaba d'aya sai bayanshi kad'ai Teemah ke iya hangowa bata san meke gudana a tsakaninsu ba, ba kuma tajin akan abinda suke tattaunawa. Rasa abinda zatayi tayi aranta takejin kamar tafita taje inda suke tsayen taji mai suke fad'a amma tsoro ya hanata dan tsan inta kuskura tamasa badaidai ba tilabta zaiyi shikam baruwansa balle ma yanda taga yau d'in yake 90% tasan babu abinda zai hanasa dukanta. Kalle kalle tafara acikin motar kamar wanda yau ne tafara shiga cikinsa,ita kanta batasan mai take nema ba cikin haka kuwa idanta ya sauk'a akan wayarsa dake ajiye agefen inda ya tashi. Karambani yasata ta d'auko wayar, cikin sa'a kuwa wayar bata shiga security ba tana bud'ewa taga akan k'iran da yayi d'inne wayar take haryanzu "Muhibbat" tagani arubuce, karantawa rasake yi kusan sau uku, jitayi sunan ya tsaya mata aranta, amma daga ganin sunan tagane itace wacce yayi waya da ita d'azu dan tunda sukayi wayar bai kuma yin wata waya ba, kenan wato sunan wannan yarinyar ne Muhibbat d'in tunda da ita kad'ai yayi waya kafin ya fita a motar , ta6e baki tayi sannan tafita daga wurin k'ira ta nemi gallery ta shiga,images tagani sai kawai ta danna kansa ta shiga pictures d'insa ne zallah aciki, sai wanda taga sun d'auka su uku acikin parlour zaune akan kujera da wata yarinya bazama ta wuce sa'arta ba da kuma Ummahn Daddyn Abuja. Yarinyar ma dashi take kama aranta tace k'ila itace wacce ake gulamata akanta d'in kwananki. Canja folder tayi ta shiga camera, anan taci karo da zallan hotunansa masu d'aukar hankali, wasun sanye yake da kayan sojoji wani ma harda bindiga rik'e a hannunsa. Cigaba da dubawa tayi takuwa dinga cin karo da hotunsa wani kuma bashi kad'ai bane,wani suna training ma akayi,cigaba da bi tai tayi harta iso wanda akayi da daddynta da daddyn Abuja da Ummah da kuma wasu daban da bata ma sansu ba,tana k'ara turawa taga wanda yayi shi kad'ai ya d'aga bindiga kamar zaiyi harbi. Jitayi photon ya birgeta sosai,sai ta tsaya akan wannan d'in tana ta kallon shi,gani tayi yayi kyau sosai har bata son wuce wurin dan inta d'anyi gaba sai ta kuma dawowa baya. Afili tace " ai dole kayi mugunta, mtun kullum cikin mugun hali, ashe har bindiga ne dashi shima wannan yanda yake da muguntan nan ai inkayi wasa wataran harbeka ma zaiyi" Tana cikin maganar sai ta d'ago kanta ta kalli inda suke tsayen,ai kuwa sai taga yana k'ok'arin dawowa,da wuri ta mik'a hannu ta ajiye wayar a inda ta d'auka garin sauri ma ko fita a galleryn mantawa dashi tayi, jikinta har rawa yakeyi tsabar tsoro. Sa'anta d'aya bai kalli inda ma wayar take ba, kamar yanda ita kanta bata samu kyakykywan kallo daga wurinsa ba. Tada motar yayi ya nufi hanyar gida, tak'asan ido Teemah take kallonsa, sai yanzu take mamakin yaushe ma yazo garin harda zaiyi budurwa lalle wannan kam akwai aiki agabansa indai hakane, ta6e baki tayi tare da maida idanta ga titi,babu wanda yayiwa d'an uwansa magana har suka iso gida. Cikin sanyi ta shigo d'akin dan sai da suka shigo harabar gidan kafin Mahmud ya fad'o mata arai. Sai yanzu taji sabon missing d'in Mahmud d'in aranta," Allah sarki yayah" Tace afili gurin mummy taje ta zube ajikinta ta kwanta shiru batare da magana ba, sai mummyn ce ta tambayeta ya akayi ? Amsa ta bawa mummyn cikin sanyi " mummy yah Mahmud ya tafi ya barni" "Abinda yakawo shi garin kenan ai Teemah"Mummyn tabata amsa. D'ago kanta tayi sama tana kallon mummyn "Toh kenan bazai sake dawowa ba mummy" Ta sake tambayar mummyn nata. "a a zai dawo mana nan da 3weeks insha Allah" "Allah ya nuna mana" kawai Teemahn tace sannan ta maida kanta kan cinyar mummyn ta kwantar. Mummy har ranta sai taji tana tausaya wa 'yar ta ta, domin tasan illar shak'uwa ba dad'i musamman in aka had'a da kalmar rabuwa toh sai a hankali. Abbas kuwa yana shiga d'aki ya d'aga wayarsa da zummar k'iran daddynsa dan yau basu gaisa ba kwata-kwata yana bud'e wayar sai yaga hotonsa afiskar wayar mamaki ne yacika shi dan shi dai yasan bai san picturensa a wallpaper ba,amma ga mamakinsa daya shiga sai yaga ashe akan gallery ne wayar take "TEEMAH" Ya anbata dan ita tafara fad'o masa kuma yasan inba ita ba babu maiyi masa hakan. Murmushi ne yaji ya kwace masa da ganin hakan sai zuciyarsa ta tabbatar masa da cewa ai photonsa ta tsaya kallo shiyasa har tamanta ta bari akai abinka da marar gaskiya. Sai hakan yad'an sanyayah masa zuciyah. ***** Koda da dare da akaje cin abinci ma cakula ta dingayi M har aka k'are cin abincin ita bata ci komai ba. Duk Abbas na lure da ita, sarai yasan matsalarta, dan shima dauriya kawai yayi yaci abincin, wannan abin nan da Teemah keui jiyake kamar azabtar da zuciyarsa takeyi,ita kuma bata san hakan ba, dan kar aga kamar abu na damunsa ne shiyasa kawai ya daure yaci saboda sanin halin mummy da yayi dan tana ganinsa wani iri zata saka sa agaba da tambaya ne shikuwa bai san amsar da zai bata ba. Kwanan Mahmud biyar kacal agidan kai agarinma gaba d'aya amma zakayi mamakin shakuwar su da Teemah, acikin kwana biyar d'in kwana d'aya ce da wuni d'aya rak ta waru wanda yakasance Mahmud bashine ya ciyar da ita ba amma sauran kwana kin duk shike bata abincin abaki hakan sai yana tuno masa da rayuwar su tabaya. Washegari Habibu ne ya kaita makaranta da yake ya dawo tun last 3days, koda akaxo cin abinci ma da daren ranar haka tayita rarraba idanu,dan rana kam ma bata cikin lissafi ita ba'a maganarta danko waiwayo gun abincin batayi. Har suka gama bata ciba ita, mummy ce tafara mata surutu akan tunjiya ta lura bata wani ci abinci agidanba, amma daddy yace "tabarta ai ita tayi ra'ayi ba wani ne yace karta ci ba, kuma ai intana jin yunwa dakanta zata nema basai ansata ba". Jin haka yasa ta cewa " nama fah ci amakaranta daddy" "Toh ai kinji" daddyn yafad'a yana kallon mummy Tsaki kad'an mummy taja daga nan bata k'ara kallon inda suke ba ma dan takaici. Tun daga ranar Abbas yarage ganinta ma gaba d'aya, dan yanzu mummy ma ta daina damun kanta tunda ta lura daddynta ke goye mata baya. Bak'aramin jin haushin abin nan datake yi d'in yake ba, amma bai ta6a kulata ba, sai dai yana ganin kamar ta raina su ne gaba d'aya. Kuma abin mamaki rainin datake masa na rashin kunyan bata ta6a yiwa Mahmud ba koda sau d'aya a lokacin da yake gidan. Idan ya tuno yanda take sake jikinta suyi ta hira da Mahmud d'in suna wasa da dariya,in baka sani bama sai kace agida d'aya suka taso sa shi. Lokuta da dama idan yana ganinsu a hakan bak'aramin jin haushi da takaici yakeji ba, amma bai ta6a nuna musu hakan ba,nuna musu yakeyi sam bai damu da al'amuransu da shirginsu ba ma. Koda korarta da ya keyi wasu lokuta idan tazo yana yi ne irirn kamar tazo ne zata damesu da surutu bawai dan wani abu ba kuma ko Mahmud d'in ma haka ya d'auka. Sai shima Abbas d'in ya tafi a hakan dukda manufarsa daban shi kam, dan azahiri takaicin ganinsu taren ne yake sashi koranta. Sarai yasan rashin sakin fuskan da baya yi matane ya sa ta ke k'insa da kuma hana tayi sabo da shi, dan shi da Mahmud they are 2 different people halayyarsu ta d'an banbanta kad'an amma tsabar zafin kai sai ya take wannan ya d'au laifin gaba d'aya ya d'ora mata. Kawai sai yasa aransa cewa ai raini ne yake damunta.......... Koda awurin cin abinci lokacin da Mahmud yake nan sosai suke bashi haushi, dan tunda Mahmud ya fahimci bata kula abinci sai an gayyato ta ko kuma an tilasatata, tundaga lokacin sai Mahmud ya d'auki d'amarar sata taci dan dolenta koda bata da ra'ayi. Ko kunyar su mummy baya ji haka zai ta lalla6ata akan ta ci abincin ita kuwa tayi ta yanga da shagwa6a, haushi kamar yakashe Abbas amma adole yake mazgewa. ****** Gani yayi abin nata sai k'ara gaba yakeyi gashi indai aka zauna sai ta sako hirar Mahmud,abinci kuwa sai abinda yayi gaba. Abbas ma daga baya daina zuwa kan dinning d'in yayi gaba d'aya, da farko mummy ta tura Teemah akan tak'ira sa sai yace mata he is full,the following day ma haka sai dai wannan karon da taje ki'ran nasa cemata yayi taje ta kawo masa abincin ad'aki zaici. Zuwa tayi ta had'o takawo masa,tana shirin fita ya tsaida ta kamar wanda zaice ta mik'a masa wani abu amma sai jitayi ya tambayeta wai " taci abincin ne ita" kai ta jijjiga masa alamar a a, ai kuwa ya tsareta yace wai dole sai taci abincin data kawo masa d'in inbata ciba kuwa shida ita ne dan harbeta zaiyi da bindigan sa wai kanta zai fasa babu abinda ya damesa. Vote, share nd comment🤞🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 5:57 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _This page is specially dedicated to my dear fans Mar-yerm Ummu Haidar Meerameen Ummul Abdul maman Husna Ummi Tamama Bintu kabir Nanah Wash........ idan nace zan k'irgo ku yawa ne daku Hak'ik'a ku na daban ne, kamar yadda soyayyar ga littafin nan yake na daban. Allah ya bar k'auna.❤😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* There’s a story behind every person. A reason why they are the way they are. Think about that before you judge someone. 🅿 *21* Aikuwa tazauna ta hau cin abincin adole duk da ranta bayaso amma haka ta ta turawa, shikuwa yana kwance abinsa da wayarsa a hannu yana ta aikin dad-dannawa, data ga ta k'oshi sai kawai tafara hawaye. Allah ya taimake ta adaidai lokacin sai ya d'ago kai ya kalleta da niyar ganin ko tana ci d'in ne ko kuma a a, sai yaga taci ma kusan rabi amma tana kuka, suna had'a idanu kuwa ta sake kukan nata mai sautin sa ya bayyana. Dariya tabashi shikam amma sai ya tsare bai dara ba. Tashi yayi ya zauna kafin ya zubo da k'afafun sa k'asa sannan ya sake kallonta. "Miye kuma na kukan? Ya tambayeta. Batayi magana ba kawai sai ta cigaba da kukan ta abinta. Kyaleta yayi kawai yatsaya kallonta tana kukan kusan mintina biyu sannan yasake magana "idan bazaki fad'a min ba kimin shiru inba haka ba Allah makeki zanyi" Cikin shash-shek'a tabashi amsa da "nah.........nah......k'oshine..........daga k'arshe taja dogon ajiyar zuciya. Sosai maganar ta d'in ya k'aramar dariya amma sai ya jijjiga kansa kawai"yarinyan na bazaki ta6a girma ba" ya fad'a acikin ransa sai yayi murmushi agefen bakinsa. "Tashi kije" Yafad'a yana komawa kwanciyar daya tashin. Ai tana jin haka tayi saurin mik'ewa tsaye ta tattare plates d'in ta fice da sauri, shima bayan ta yabi da kallo aransa yace "mara kunyan banza kawai, nida kene ai a gidannan". Tana fita ta wuce kitchen ta ajiye plate d'in sai ta wuce d'akinta,tana shiga kuwa tafad'a kan gadonta taringa kuka mara dalili amma deep down tana tunawa da Mahmud ne dan tasan da yana nan da hakan bai faru ba, da shikam tayata ci zaiyi ya,a bata abaki amma wannan shi sai bala'in mugunta. Washe gari ma da aka zo cin abincin haka mummy tayi ta kwalla mata k'ira dolenta ta fito tazo tasami mummyn. Mummyn cewa tayi "yiwa yayanki magana maza yazo yaci abinci" Baki ta tura gaba tayi kamar zatayi kuka, mummy kanta ak'asa yake bata ma lura da abinda TEEMAH tayi ba. Ganin haka yasa Teemah juyawa tanufi d'akin nasa ranta amatuk'ar 6ace. Knocking tai tayi daga waje shikuwa yana zaune agaban d'an k'aramin madubin d'akin yana jinta ya k'i kulata dan yasan itace inba ita ba babu mai mar irin wannan iskancin. Ganin ank'i kulata ne yasa ta tura k'ofar ta shiga a hankali, take taja ta tsaya dan ganinsa datayi zaune akan kujera yana gyaran fuskarsa, sai jin haushin ta ya k'aru fiye dana d'azu, a tunanainta barci yakeyi aai kuma taganshi a zaune. Azuciyarta take ayyana "dama yana jina yak'i kulani dan salon wulak'anci kenan, dayake gani k'aramar danga amma daya je wurin waccen yarinyar ai tana fitowa shima ya fice ya tareta ahanya irin ma kar ya 6ata lokaci ranta ya 6aci d'innan" Haushi ne ya k'ara kamata sai ta kalleshi dayake bayansa take iya kallo sai kawai ta banka mar harara. Karaso wa tayi kusa da shi,ta tsaya "Yayah ina yini" tafad'a tana wani kauda kai. "Banganshi ba" yabata batare da ya kalleta ba. Juyowa tayi da mamaki ta kalleahi dan ita tasan ba wani abu ta tambaya ba, giransa d'aya ya d'aga mata sama sai taga ya bala'in yi mata kyau take abinda ke ranta d'in ya kau ta hau wassafa kyaun sa aranta, dan d'an zaman da yayi agidan har fuskarsa tafara tara gashi, kuma ya mar kyau dan sanda yazo gidan babu komai akansa da fuskarsa amma yanzu kam duk sun fara fitowa kuma sosai suka masa kyau.l suka kar6esa. Sosai taji ya birgeta musamman data ga shima hankalinsa nakai alamar shima yanason abin. Ta6e baki tayi ta maida idonta gefen madubin sannan tace "mummy na k'iranka" Juyowa yayi kamar baisan da tsayuwarta agurin ba tun farko. "Baki iya sallama bane? Ya tambayeta idonsa k'ur akanta. Kasa tayi da kanta da wuri batare da ta k'ara yin wata magana ba. Bayyanan niyar murmushi yayi wanda azahiri sautin ya bada "hmm" sannan ya juya yaci gaba da abinda yakeyi "kije in abinci ne ki had'o ki kawo min nan d'aki" Tana jin haka ta juya ta nufi hanyar fita aranta ta ce "Nikam na shiga uku na, yau kam Allah yasa bani zai sa cin abincin ba" Haka taje ta had'o tana ta farga ba jikinta har rawa yakeyi tsabar tsoron kar yasata cinyewa sai tasaka abincin d'an dai-dai. Yaukam cikin sa'a sai yace mata ta zauan tajirasa idan yaci sai ta wuce da plates d'in. Tasabar farin ciki har sai da tayi murmushi duka yana lura da ita. Tun da ya fara ci bai d'ago ya kalleta ba, kansa da hankalinsa ya tattara gaba d'aya ya bayarwa abincin. Kamar wasa ya fara ci sai gashi kuwa yacinye tas. Kuma sai daya cinye d'in kafin ya d'aga daidai ta kalleshi sai suka had'a idanu sai abun yabasu dariya gaba d'aya amma murmushi suka yiwa juna. Yana murmushi yace " kinga ai yau d'in na rowa kika sako min gashi yamin kad'an" Sai kuma yafara yunk'urin mik'ewa yana fad'in "jeki k'aro min" Ai kuwa da rawar jiki tatafi k'aro wan takuwa d'ibo yanzun harda na mugunta ganin d'azu bai sata taci ba shine ta k'aro da farin cikinta. Koda ta dawo sai ta sameshi atsaye yana 6alla botton d'in rigar jikinsa. Shigowa tayi ta ajiye masa tana shirin shirin juyawa ya dakatar da ita akan cewa ta tsaya ta daman wannan nata ne shi ya riga da yaci nasa. So wannan nata ne kuma tayi da wuri dan fita zaiyi yana da gurin zuwa,irin najiya yace maza tacinye tas. Sai ta d'ago da sauri ta kalleshi,da alamar mamaki "uhhhm" yace mata da alamar shima amsar mamakin nata yabata. Sai itama tace "Abincin fah yawane dashi yaya" "Ahakan nan kuma zaki ci 'yan mata" Fuskar tausayi tayi zata fara magana ya dakatar da ita da fad'in "hurry up pls nace miki zan fita ko" Sai tace "Toh kaje abinka yayah Allah zanci" "Gani yaro ko Teemah" Yafad'i yana kallonta Jijjiga masa kai tayi da sauri sannan tafara chin abincin dan taga kamar tafara k'ureshi. Haka tafara tura abincin da kyar data k'oshi sai ta karkata kanta gefe tana kallonsa da ido ruwa-ruwa. Ji yayi ta bashi tausayi gashi kuma shima yana da uzurin fita sai kawai yace "tashi kije" Yauma da sauri ta tattare ta fice daga d'akin nasa amma koda taje kitchen d'in sai ta samu wuri ta zauna tana maida numfashi dan gaba d'aya taji ta wani iri kamar ba ita ba abincin data ta turawa ne suke sata jin numfashinta yana sama-sama. Baabah Lami ce ta tambayeta " wai lafiya kuwa Fatu"? Kallon Baabah Lami d'in tayi batare da tayi magana ba. Illah kauda kanta gefe datayi sannan tace " Baabah Lami keda Yah Abbas ne kad'ai bakwa k'aunata agidannan" Zaro ido Baabah Lami d'in tayi tare da fad'in "haba ke kuwa k'auna gaba d'aya? "Ehh mana kullun sai kin k'irani da sunan da bana so shi kuma duk abinda banso shi yake sani yi kullun" "Toh kiyi hak'uri an daina insha Allahu" Baabah Lami d'in tafad'a tare da ficewa ta k'ofar baya. Da kyar taji ta tayi d'an daidai sai ta tashi ta lalla6a tawuce d'akinta taso taje wurin mummy tace mata tayi masa magana ya daina sakata cin abincin dolennan amma sai ta tuna mummy ma ba goya mata baya zatayi ba. Sai kawai ta wuce d'akinta tana rage kayan jikinta sai taji kawai tana son shiga bayi. Da sauri ta wuce ta shiga bayin aikuwa bayan gida mai taurin tsiya ne ya matsa ta. Da kyar tasamu yafito har sai da idonta ya cicciko da hawayen azaba. Koda tafito sai ta kwanta agado tana maida numfashi. Afili tace "Gab ake da kashe miki y'arki mummy amma nasan kona gaya miki bayansa zaki bi bani ba" Sai data huta kafin taje tawatsa ruwa tazo ta kwanta take kuwa bacci yayi awon gaba da ita. Washe gari ma data tashi sai da tayi kashi kafin anan tayi wanka " nikam Allah zai saka min wallahi, mutun wai in baiga yayi mugunta ba bai jin dad'i" Haka ta shirya tafito dan har ta d'anyi latti ma. Drop ur comment pls mutane na I heart u all🤞🏻 *Serlmerhn ku ce*😍 [10/2, 5:57 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO_* 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *22* Zuwa yanzun satin Abbas uku agidan su Teemah inda adaidai wannan lokacin yaci kimanin rabi da quarter daga cikin hutun da ya samu na aikinsa. Shikansa yanzun ak'age yake ya koma ya fara aikin,har ji yake zaman gidan yafara isansa dan dama bak'aramin so yake yiwa aikin nasa ba dalilin hakan ne yasa yafara k'irga ranar tafiyarsa. ***** Mummy ce zaune akan kujera Teemah kuwa na gefenta sai zun6uro baki takeyi gaba tana guna guni k'asa-kasa, mummy kuwa ko kallon inda take ma batayi ba kanta na gefe. Teemah data ga mummyn bata da alamun sak'k'owa sai ta k'ara risina ta had'iye miyau tare da daidaita bakinta sannan tace " mummy dan Allah kiyi hak'uri ki barni naje mana Allah idan naje bazan dad'e acan d'in ba" tana kawo wa nan sai zamo daga kan kujerar ta zube akan gwiwoyinta tayi kalan tausayi agaban mummyn nata, mummyn ma sai tak'i ko kallon inda take balle ta san tanayi. "mummy please" ta k'ara fad'i kamar zatayi kuka. Sai a sannan mummy ta juyo ta kalleta, suna had'a idanu sai ta k'ara rausayar da kanta gefe alamar rok'o. Sai kuwa taji mummyn tace "zan barki kije Teemah amma kuma cikin 2hours zakije ki kuma dawowa, idan kika kuskura kika wuche hakan wallahi ni da ke ne agidan". Wani tsallen da Teemah ta buga ta fad'a jikin mummyn har sai daya firgita ta. Sai tace " haba Teemah miyeh hakan kuma kin kuwa san yanda kika tsoratar dani? Dariya Teemahn tayi sannan tace "duk murna ce kawai mummy" "Hmm Allah ya shirya minke nikam Teemah" "Ameen mummyna" "Ki zauna kina min iyayi anan yarinya duk cikin lokacin ki ne ai ni babu abinda ya dameni" Dawuri ai ta mik'e dataji abinda mummyn ta fad'a sai tace "Banaje in dubo Habibu in fad'a mar zai kaini unguwa in bayanan kuma sai ki k'iramin shi awaya dan kar yayi nisa yamin cikas" Kai mummyn nata ta d'aga mata alamar taji. Har ta fara tafiya sai mummyn ta dakatar da ita da fad'in ta k'yale habibun kawai dan ita bata yadda Habibun ya kai Teemahn ba , domin tariga da tasan halin Teemahn tsab, acewar mummyn wai Teemah tariga ta raina Habibun kuma koda sun fita ba bin maganarsa zatayi ba sai dai nata. Duk mummy tayi maganar ne Teeemah na tsaye a inda tatsaya tun sanda mummyn ta dakatar da ita. Sai da taji k'arshen maganar mummyn kafin tafara tafiya ta dawo ta zauna a kusa da mummyn. "Toh mummy idan bashi d'in wa zai kaini? ta jefawa mummy tambayar. Amsa mata mummyn tayi da fad'in " zan rok'i Abbas ne ya kaiki kuma zai jira ki idan kin gama zai dawo dake " " kafad'a ta d'aga tana kallon mummyn alamar tak'i ita bata yadda ba. "Then sai kiyi zamanki agida abinki tunda bakya son zuwa ni kinga banda problem". Mummyn ta fad'a tana mai nuna halin ko in kula ga zancen. Da Teemah taga kamar mummyn nata dagaske take sai tace" Mummy kinsan mugun halin yayan kuwa, nidai kibari Habibu ya kaini dan Allah mummy"! "Ai na riga da nagama magana nikam Teemah, inba iskanci ba da Abbas d'in da habibun miye banbancinsu wato dan kinga kin raina Habibun shiyasa kike son shi ya kaiki ko? "a a fah mummy yah Abbas d'in ne ni kawai bana so ya kaini" "Ai shine dai-dai ke Teemah gara yana yin maganin kin ai inkuwa ba haka sai ki zamanki agida ba lallai ba dole" Zatayi magana mummy ta dakakar da ita da fad'in idan fah bazaki ba babu dole nace kuma nasan kinjini, ni bazan canja magana ta ba" Ai tana jin hakan ta mik'e dan bata so tayi missing d'in zuwa wajen. "Bari inje in shirya toh, ai da babu gara ba dad'i . "Daya fi miki kam" mummy tace mata. Daganan ta tashi da gudu ta nufi d'akinta da niyar shiryawa. Tana shiga ta hau cire kayan da ke jikinta sai data ciresu gaba d'aya kafin ta nemi towel ta d'aura. Kayan da ta cire d'inma sai ta tattare su ta ninke ta bud'e ma'ajiyar kayan wankinta ta jefa su aciki. Tana juyowa daga wurin sai taci karo da k'adangare mai jan kai a tsakiyar d'akin. Jikinta take yafara k'yarma tafara rawan baki awurin. Shi kuwa k'adangaren kansa asama yana wani jijjigawa alamar da warginsa ya taho Aikuwa sai ya d'an motsa daga inda yakrn sai akayi rashin sa'a inda ya nufa d'in anan Teemah take tsaye. Wani ihun da Teemah ta saka sai da ya firgita duk ahalin gidan gaba d'aya. Abbas da shigowansa kenan daga masallacin sallar la'asar yana k'ok'arin shiga d'akinsa sai yajiyo ihun ta. Fasa shiga d'akin nasa yayi ya dawo ya isa main parlourn gidan,inda shigowansa yayi dai-dai da 6acewar mummy daga parlourn itama bin bayanta yayi shima ya nufi inda yaga tabi, hanyar da zai sada mutun da d'akin Teemah sukayi. Tana tafiya yana binta abaya batare data sani ba, isowan mummy sai yayi dai-dai da fitowan Teemah daga d'akin nata arikice sai sukayi karo da mummyn takuwa k'ank'ameta jikinta sai rawa yakeyi takasa cewa komai. Ko fad'an damuwarta ma ta kasayi illah rintse idanunta da tayi da k'arfin gaske. mummy duk ta shiga damuwa sai tambayarta take ta faman yi amma ko amsa d'aya bata samu ba daga Teemahn ba.. Abbas na isowa sai ya wuce d'akin nata ya shiga, anan yaga k'adangaren shima anan inda Teemah ta ganshi har yanzu bai motsa ba, sai ya tsaya kallonsa da mamakin ta inda ya shigo d'akin. Har ya fara rarraba idanunsa a d'akin. Ai kuwa take ya tuna da ranar dayaga windown ta a6ud'e harya mata magana akan tana rufewa. Tunowa da yayi da hakan yasa ya d'aga kansa ya kallo 6angaren da windown yake, ga mamakinsa sai kuwa ya gansa a bud'en yauma, hatta net d'in ma ta zuge tabarshi a bud'eko miye fa'idar hakan oho. Zuwa yayi ya bud'e wurin datake ajiye kayanta da niyar d'auko wani abinda zai kama k'adangaren dashi sai kawai ya d'auko wani farin vest d'inta ya je ya d'au k'adangaren dashi . Ta windown data bud'e d'in ya jefa k'adangaren tare da vest d'in gaba dokin yasan ya tsaji a aiki , sannan yaja ya rurrufe glass da net d'in sannan ya sake labile. Koda ya fito su mummy basa inda ya barsun sai kawai ya wuche parlourn mummy, anan yatarar dasu dukkansu Teemah tawani shige jikin mummy kamar me shirin komawa cikinta. Zama yazo yayi shima agefen su sai mummy tajefo masa tambayar" wai miye ad'akin ne Abbas inata tambayar ta tak'i tabani amsa tun d'azu sai rawar jiki takeyi" Amsa ta yayi atakaice da fad'in "K'adangare ne mummy" Baki mummy ta kama sannan tace ikon Allah nikam garin yaya kuma ya shiga har cikin d'akinta?" Baiyi magana ba illah d'aga idanunsa dayayi ya kalleta sai yaji ta matuk'ar bashi tausayi, musamman yanda yaga duk tayi laushi, idanunta a lumshe yake hakan yasa ya k'are mata kallon da kyau sai dai daya lura ba kayan kirki bane ajikinta sai ya kauda kansa gefe tare da korar shaid'an azuciyarsa. Tambayar dayake so yamata ne yasa shi adole badan yaso ba ya sake kallonta ahakan " _Fateemah_ " ya k'ira sunanta asanyaye ta bud'e idanunta batare da ta amsa k'iran daya mata d'inba. Sanin datayi cewa shine yak'iratan yasa ta sauk'e idanunta akansa. "Ban ta6a cewa ki rufe windown d'akin kinnan ba? ya tambayeta K'asa tayi da idanunta dan tasan taurin kantane yasa tak'i rufewa ba komai ba. "Tambayarki nakeyi fah! Da kyar ta bud'i baki tace "ehh kafad'a yayah" " Owk ban isa inyi magana kiji bako " Yafad'a ad'an harzuk'e. Jin hakan yasata jijjiga kanta alamar "a'a". Sai yanzun mummy takar6e maganar da fad'in "ai in juninki taurin kai ne kuwa kina tare da wahala wallahi, ashema dagangan kike barin windown kenan kuma har amiki magana amma bazaki ji ba, yanzu toh wa gari ya waya?! Ran mummy a6ace yau tketa sababi ta inda take shigaa bata nan take sauk'a ba sai da Abbas ya ga kamar ran mummyn k'ara 6aci yake yi kafin ya fara bata hak'uri musamman daya lura akalar fad'an naso ya canja gaba d'aya. Dan mummy duk tana masifar ne akan rashin bin maganar Abbas d'in data k'iyi ne bawai dan shigar k'adangaren d'akin ba. Teemah kuwa tun fara fad'an mummy take zubda ruwan hawaye dan tun d'azun batayi kukan komai ba tun faruwar al'amarin sai yanzu sai hawayen yak'i tsayuwa abin sai ya zame mata biyu. Sosai jikin Abbas yayi sanyi sai yaji ba dad'i,dan kana ganin hawayen zaka san cewa kukan daga zuciyarta yake fitowa. Tausayinta yakeji na k'aruwa masa a zuciya sosai da sosai kuma saboda hakanne yasa yayi wa mummyn magana akan tayi hak'uri. Sai da yaga komai yayi normal ne kafin yace Teemahn tatafi tasa kaya ajikinta aikuwa tak'i taje fir sai ma k'ara shigewa jikin mummy data keyi. Ganin hakan yasa mummyn cewa "aww bazaki partyn bane ko kin fasa" Sai kawai ta jijjiga kanta " mekenan? Mummyn tasake tambayarta dan bata fahimci takamammiyar manufar wannan amsar ba wato jijjiga kai d'in da Teemahn tayi. Sai Teemahn ta bud'i baki tace "zani ban fasa ba mummy " murmushi mummyn tayi kafin tace " ai kuwa dai sarkin yawo babu fashi da yake fita unguwa neai, sai Teemahn ta sake 6oye fuskarta a jikin mummyn ita nan wai taji kunya. "Tashi maza kije ki shirya toh inyaso sai yayankin ya kaiki" Cewar mummy Sai da Teemah ta tashi ta zauna kafin ta ce " mummy toh kiraka ni ". Duk wannan dramar Abbas na zaune yana kallonsu fuskarsa tallafe da hannayensa amma baiyi magana ba. Mummy ce ta kalleshi wannan karon batare data amsa maganar da Teemah tayi mata ba, sai ta dawo da kallonta ga Abbas tace masa " kayi hak'uri dan Allah ka kaita wai zata je birthday partyn k'awarta ne a _Abbah ibrahim_kuma idan na had'ata da Habibu ba dawowa da wuri zatayi ba kasanta da rashin kunya shiyasa na keso kai ka kaita" "Ai bakomai mummy taje ta shirya d'in sai tazo kawai mu wuce" " yauwa d'an albarka ai nasan bazaka k'i ba" Daga nan ta dawo da kallonta ga Teemah sannan tace "tashi muje toh ki shirya" Tashi tayi tafar tagiyah sai mummy ta biyo bayanta suka wuce d'akin nata da mummy sai da aka kusan isa d'akin kafin taja ta tsaya mummyn ce ta wuce gaba tare da yin tsaki dan tasan manufar yin hakan domin duk cikin salon tsorone irin na Teemah. Da d'ari-d'ari ta shirya suka fito daga d'akin, mummy naganin ta sa kaya sai tayi hanyar waje itama sai ta kwaso mayafinta da takalminta tabiyo bayan mummy dagudu sai suka fito atare. Dariya ne wannan karon yaso kwacewa Abbas ganin yanda Teemah take tafiya tana waiwayen bayanta. Aparlourn tak'arasa shirinta sannan taje d'akin mummynta ta d'auko kayan make up d'in ta tazo ta yi kwalliyar aparlourn sannan suka fito atare da Abbas d'in bayan sunyi sallama da mummy akan cewa sai sun dawo. Sosai Teemah tayi kyau acikin shigar datayin sai ta zama tamkar tauraruwa mai haskaka zuciyar............(mamuda)lolz😜 Abbas har satan kallonta yakeyi tsabar yanda yaga tayi shar da ita,sai da suka hau titi taga ya nufi Gashua road sai alokacin tace masa " yayah kawuce fah Abbah ibrahim zamu" Ko kulata baiyi ba yaci gaba da tuk'insa........ _comment and share_ _pls_ *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 5:58 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 dukkan masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs.Nagode da_ _irin k'aunar da kuke min da kuma kyawawan_ _addu'o'inku_ _gareni.Nima ina_ _sonku sosai ni da ku mutu ka raba _ 😍 Sister safiyyah Ina tayaki murnar kammala littafinki *(BA JINSUN MU* *BACE*) hak'ik'a wannan littafin ba k'aramar karantar damu yayi ba Allah ubangiji yasaka miki da mafificin Alkhairi ya kuma biyaki....up up up❤ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* For those da suke rubuta jamb Allah ubangiji ya baku sa'a yasa daga wannan ba k'ari an wuce kenan. 🅿 *23* Cikin gari ya wuce da ita shikanshi da farko baisan inda zashiba,sai da yaga ya shigo cikin garin kafin ya yanke shawarar zuwa bayan tasha. Koda suka isa bayan tashan guri ya samu yayi parking sannan ya bata umarnin fitowa daga motar. Kamar bazata fitoba sai kuma taga ya k'ureta da kallo fuskarsa ba alamun walwala sai kawai ta bud'e motar ta fita bakinta kamar zai fad'i k'asa tsabar yanda ta turo shi gaba, dan ita bata san mai yake nufi da hakan ba, inda akace ya kaita daban inda kuma ya kawo ta daban, haushi ne ya sake cikata data tuno irin rok'on data tayi kafin mummy tabarta zuwa birthday party d'in sai gashi kuma wannan mutumin yakama ya yi wani guri da ita. Tafiya kad'an suka yi sai taga ya shiga cikin wani babban shagon kayan make-up. Dakansa ya dinga nuna abinda za'a mik'o musu While Teemah na zaune a gefe ko kallo bai isheta ba dan ita gaba d'aya zuciyar ta tatafi ne ga tuanain zai 6ata mata lokaci dan bata son ta makara zuwa birthday d'in da'ake yi na k'awartan hartana zooming d'in yanda k'awayenta zasu fara cashewa ba ita, tasan da tana da waya da yau d'innan k'ira sai ya isheta. Haka yayi sayayyansa kaca-kaca sannan ya jagorancesu suka fito daga shagon suka kuma shiga mota. Atunanin Teemah daga nan gurin partyn zasu wuce dan harta fara murna amma sai taga ya d'auki wani hanya daban haka yaita zaga cikin gari kamar me neman wani abu daga k'arshe sai ya nufi hanyar gida. Teemah tayi ta masa magana yafi sau a k'irga amma ko kallon 6angaren da take ma baiyi ba ballantana ya kulata balle har tasamu amsar maganar da ta masa. Sai da taga ya d'auki hanyar gidan kafin tasake masa magana akan batun birthday party d'in, duk da bata da tabbacin zai amsata amma sai da tayi dan tasan ko bai bata amsa ba ai dai ya ji ta. Ga mamakinta kuwa sai taji yanzun ya bata takaitacciyar amsa da " bazaki ba" ya bata amsan ne batare da ko kallon kirki ba. Ai tanajin haka sai ta fara bori da kuka dan harga ba k'aramin haushin fita da shi d'in nan tayi yau ba, data sani dama adaidaitan ta hau.......... data sani dama Habibu driver ne ya kaita....... Data sani tayi shi yafi sau ak'irga. Shikuwa koda yaga tana kukan sai bai kulata ba illah juya kan motar da yayi ya shiga u-turn ya dawo da baya,murna tafara daganin hakan atunaninta zai kai tan ne, dan daman wucewarsu unguwar su Leemah (birthday girl) kenan dataga bayada niyyar shiga shine tamasa magana dajin amasr daya bata kuwa sai tafara wannan iskancin kukan. Ganin yasake wucewa sai kawai ta yi tagumi dan zuwa yanzun tagama sawa ranta tayi missing birthday d'in kenan har ma tanaji aranta cewar ya wuceta already. Hanyar Jerusalem ward ya d'auka dake gefen nursing school, sai kuma tafara tunanin toh me suka zo yi anan kuma? Kar dai wata yarinyar kuma ya kwaso acikin unguwar nan kuma? Kauda kai tayi gefe tare da jan tsaki aranta ta kuma fad'in mutun sai kwashe-kwashen tsiya har arn......ma bai bari ba. YETIM care foundation (gidan marayu) taga yayi parking awurin ya fito sai da tayi kalle-kalle kafin ita ma tafito tabiyo bayansa suka shiga ciki. Sun tarar ma ana wani programme sai basu wani dad'e ba suka fito bayan ya gaiggaisa da mutanen wurin akan sai gobe insha Allahu zai dawo. Mota suka koma yaja ya nufi hanyar gida. Yanzun kam da suka fito bata wani tsaya mamaki ba bud'e bakinta tayi ta tambayeshi muryarta wasai tace" yayah yaushe kasan nan wurin? Sai da ya kalleta kafin yace "Mahmud ne ya kawo ni nima kwanaki" "Sai ta sake cewa " toh shi yah Mahmud d'in wa ya nuna masa ai naga shima bai san nan garin ba akace"? "Toh sai ki jira idan yazo ki masa wannan tambayar? Yayi maganan ne fuskarsa ba yabo ba fallasa sai ta d'an ji dad'in hakan hartaji tasamu k'arfin gwiwar sake yi masa magana, aikuwa ta kuma cewa" yayah toh ni mai yasa kak'i ka kaini inda mummy tace ka kaini d'in?" " Banyi ra'ayi bane" ya bata amsa a takaice. Tura b aki tayi gaba sannan tace " amma yayah k'awata ce fah ita seat mate d'ina kuma" " Kice mata ni na hana ki zuwa" Ya bata amsa lokacin dayake k'ok'arin tada mota. " Dan Allah ni........... Zata sake yin magana ya dakatar da ita da fad'in " ya isheni please kimin shiru" Dan dolenta tayi shiru bawai dan ta gama fad'ar abinda ke ranta ba. Suna zuwa gida kuwa tafice daga motar da gudu tayi ciki. Kamar anjeho ta ta fad'awa mummy ajiki tana k'ananun kuka kamar wata yarinya k'arama. Mummyn ce tace wai nikam ke kullum bakya ganin kin k'ara girma ne Teemah? Cikin shesh-sheka dajan magana tace..." mummy k'in kaini fah yayi ya dinga yawo dani acikin gari kamar nace masa inaso" "dai-dai kenan maganin irinku kenan ai" Mummyn tafad'a tare da murmushi kwance akan fuskarta. " mummy ke kullum-kullum bazaki bi bayana ba sai shi ko?, Allah in Daddy ya dawo sai na fad'a masa nima " tana gama fad'in hakan ta tashi tayi d'akinta da sauri amma sai dai me........ tana zuwa harta shiga tafara zuge zif d'in rigarta ai sai ta tuna da k'adangaren d'azun sai kuwa tafito da gudunta ta dawo parlourn dai-dai Abbas ma ya shigo sai ya ganta aguje "ke lafiyarki kuwa?" ya jefa mata tambaya da mamakin irin yanda ya gantan kamar an koro ta. Bata kulashi ba har sai da taga kanta zaune akusa da mummyn ta kafin ta d'anji dama-dama. Abbas d'inma k'ara sowa yayi ya zauna akan kujera yana ta kallonta so yakr yaji me yakuma korota, yarinya kamar mai ta6in hankali. Mummyn nata ne tasake tambayarta the same abinda Abbas d'in ya tambaya, sai a sannan tace " mummy k'adangare a d'akin fa kin manta?" "Hmm"kawai Abbas yace kuma sai a sannan ya ajiye ledojin dake rik'e a hannunsa. Mummy kuwa masifa tafara yimata inda tace " banason hauka ni kinga Teemah, kadangaren da aka fitar tun d'azun shine kike wannan uban gudun akansa?" "Waye ya fitar dashi toh? Teemah ta sake tambayar mummyn. Mummyn ma amsa ta sake bata da fad'in " yayanki mana" Sai ta zaro idonta waje tare da fad'in " yah mahmud ya dawo ne dama"?. Dank'walinta mummy tayi dan tasan dagangan tayi tambayar sannan tace "bafa nason iskanci ya dawo d'in ne kuma bazaki ganshi ba, koshi kad'ai ne akace yayanki?" 'Kasa tayi da kanta sai ta jiyo muryar Abbas yana fad'in " zo ki kwashe kayan nan anan" yafad'i tare da nuna mata ledojin daya shigo dasu d'azu a hannunsa. Dayake atsare yayi maganar sai bata wani yi iyayi ba taje ta tsugunna ta kwashe ledojin ta mik'e tsaye sannan ta kalli inda yake d'in sai suka had'a idanu, sai da ta kauda kanta kafin tace "ina zan kai kayan" Kallonta ya tsaya yi aransa yana mamakin yanda yarinyar nan ta gama raina shi gaba d'aya ya kuma rasa dalili. Dayake baiyi magana ba sai tayi zaton ko baiji tambayar data masan bane sai ta sake maimaitawa a karo nabiyu. Baiyi niyar bata amsa ba dan gani yake kamar iskanci ne ke damunta baya ga haka ai tasan dai ita yayiwa siyayyar tunda da ita suka je, darajar mummy dake gurin a zaune ne yasa shi bata amsa da " naki ne " (nikuwa nace oga Abbas d'in mar-yerm sai a hankali, in ba haka waya san meke cikin zuciyarka da har kake tunanin Teemah tasan cewa siyayyan ta ne kayi).😅 Tana jin haka sai ta fara tafiya batare da ta kuma cewa k'ala ba. Haushi mummy taji da wautar Teemahn sai kawai ta k'irata amsaw tayi kafin ta dawo da baya " baki da hankali ne Teemah?,bazaki iya bud'an bakinki kiyi godiya ba bayan mutun ya miki kyauta, bakinki ciwo yake yine? ko kuma iskanci da rashin hankalin kinne yayi k'wari" " Kiyi hak'uri mummy daman inada niyyar yi " Teeman tafad'a da kwa6a66an fuska mummy kuwa tsaki kawai taja ta kauda kanta gefe dan halin Teemah gaba d'aya yafara isanta. Ita kuwa sai ta juya ta kallo inda yake kamar baya wurin kansa na k'asa fuskarsa na kallon wayarsa dake rik'e a hannunsa sai tace " nagode yayah" Ko ya nuna yasan ma da shi take bai nuna ba balle tasa ran yajita, sai ta k'ara maimaitawa ai kuwa sai taga ya d'aga waya yasa a kunnensa yafara magana cikin natsuwa kamar bashiba, jitayi ya matuk'ar birgeta ashe daman yana magana haka anatse, tsabar yanda ta tsaya kallonsa har abinda ke rik'e da hannun damanta ya fara zamewa, taroshi tayi da wuri ta daidaita rik'on ledan sannan ta d'an juyo ta kalli mummy da k'asan ido gani tayi mummyn na hararar ta. Sai kawai tace " mummy kinga yak'i ya kulani ko " "Toh tsoronki yake jine Teemah da godiya ma sai an saki kafin kimasa" sai Teemahn tace " "toh ai shine mummy" "Shine me? Mummyn ta sake tambayarta. Amma kafin Teemahn tasake magana sai mummyn ta kuma cewa " jeki ajiye kayan sai ki dawo kima sa godiyan kafin nan yagama wayar ma ". Tanajin haka sai ta juya da farin ciki a zuciyarta har tana ayyana babu wanda zai sake ganin ta ma ayau kam, dan batayi niyyar yiwa mutun godiya ba ita kam tunda bata rok'i kaya agun mutun ba. Amma sai dai me.........tana fara tafiya sai ta tuno da abinda ke d'akinta. Sai ta fasa shiga kawai ta nufi hanyar d'akin mummy " Karki kuskura kishigan min d'aki " Muryar mummy tajiyo tana fad'in haka. Kwafa tayi sannan ta karkata kanta gefe " ayyah mummy toh ina zan kai"? " Baki da d'aki ne ke"?cewar mummyn. Teemah ma sai tasake fad'in " mummy toh kizo ki rakani d'akin nawa " " karkije inhar saina rakaki" Dajin hakan tasan mummy ba rakata zatayi ba tunda tafad'i haka sai kawai ta nufi d'akin nata tsoro fal ranta. Koda taje bakin d'akin ahankali ta tura k'ofar sai ta mimmik'a kayan hannun nata da sauri sannan ta kuma jan k'ofar ta rufe sai ta wuce kitchen tafita ta k'ofar baya tayi zamanta awaje. Tana zaune awurin tanata sake-saken missing birthday da tayi kusan 15mins can sai ta ga Abbas ya fita amma ganin yana d'an sauri sai ta gane cewa masallaci zashi. " Mthceeeeew" taja dogon tsaki tare da banka masa harara dan a duk sanda ta kalli Abbas d'in sake tunowa take da batun birthday d'in daya hanata zuwa "mugu kawai " ta k'ara fad'i afili.. (Ni kuwa nace kanki akeji y'an mata).😜 Bata tashi awurin ba sai da taga gari yad'an fara duhu kafin ta tashi ta zagaya ta shiga ta k'ofar parlour. D'an zaman da tayi awajen sai ta manta da batun tsoron k'adangaren, dan haka tana shigowa sai ta wuce d'akinta saboda tana sauri taga tayi sallahr maghrib dan lokacin yad'an shige kad'an. Hartayo alwala tazo tahau sallaya bata tuna ba tana cikin yin ik'ama kafin ta tuno da batun sai kawai ta daure tayi ta a'uzubillah sannn tacigaba da sallahn. Da ikon Allah kuwa harta idar tsoron bai zo mata ba, sai data idar kafin ta juya ta kakakkali cikin d'akin sai taga babu komai, tunowa tayi da maganar yah Abbas akan window, nan ma sai taje ga windown amma sai ta ganshi arufe dad'i taji har aranta sai taji Abbas d'in ya matuk'ar birgeta. _Comment and share_ _pls_ 🤞🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 5:58 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Don’t engage small-minded, petty people unless you’re able to help them. What you say & do will never be good enough for them. They’ll make your life difficult. Focus on controlling our own actions. We can’t allow ourselves to get sucked into their madness or we’ll end up hurt! 🅿 *24* Dan tasan bazai ta6a barmata k'adangaren a cikin d'akinta ba, tunda har mummy tace ya cire toh ya cire d'in ne. Dawowa tayi cikin d'akin sai caraf idonta ya sauk'a akan kayan ledan data ajiye d'azu. Da saurinta taje ta d'auko kayan ta zauna a bakin gadonta ta cicciro su tafara dubawa. Teemah kam dama badai son kayan make-up ba, d'azun ma da haushin k'in kaita partyn da baiyi bane yasa ta nuna halin ko inkula da kayan kamar irin bata so d'innan ne. Zazzage su tayi gaba d'aya sai farin ciki ya cika mata zu, dan ganin man da take amfani dashi acikin kayan datayi set d'insa kuma gaba d'aya, ga wani had'ad'd'en tarkacen powder daya tafi da imaninta harda hair removal cream(shavingcream) dasu turare da sauran abubuwan amfani. Sosai wannan siyayyan ya birgeta, domin a kayan make-up d'in daya dace amatsayinta na 'yan mata tana amfani dashi abubuwa kad'an ne basu zo a siyayyan ba. Haka tayi ta murna da farin ciki har taso ma ta manta haushin Abbas d'in da ta keji aranta. Agun kayan ta shantake har aka k'ira isha'i, sai da taji ank'ira isha'i d'in kafin ta fara tattare kayan gaba d'aya. Kan mirrorn ta taje ta jajjera su sauran kuma da bana kan mirror ba takaisu bayi ta ajiye su suma, haka ta rink'a jin kanta wata so special irin an girma d'innan. Sai data sallaci sallar isha'i kafin ta fito ad'akin ta koma, parlour tunkan ta zauna ta d'auki remote a hannunta ta fara canja tasha sai da ta samo inda yamata kafin ta zauna ta cigaba da kallo abinta. Anan mummy tazo ta sameta itama ta zauna suka ci gaba da kallon tare ko kuma nace surutu dan Teemah tun zaman mummy agurin data mata sannu da fitowa shikenan ta hau bata labarin kayan da Yah Abbas ya siya mata sai yaba kayan take tana k'arawa daga kaji yanda take yi d'in zaka san cewa kayan sun matuk'ar birgeta, mummy data gaji da sauraran surutun ne sai tace mata " amma d'azu da kike yangan d'aukan kayan fah?" Amsa tabawa mummyn da fad'in ai haushi yabani ne d'azun shiyasa" Ta6e baki kawai mummy tayi tare da fad'in "hmm" ciki-ciki dan bata buk'atan wani bayani akan batun Teemahn saboda tariga da tasan manufar haushin. Sun kusan ak'alla 40mins zaune awurin kafin Teemah ta karkata kai tace " nifah yunwa nake ji mummy" "Je k'ira yayanki toh tun d'azu banji motsinsa bama!"mummyn tafad'i tana me daidai ta zamanta akan kujera. Kuka kawai Teemah ta sanya wa mummyn nata, abin sai ya bawa mummyn mamaki sai kace ba ita keta zuba surutu anan kamar wata parrot ba. Baki mummyn takama dan abin na Teemah ya fara d'aure mata kai sosai. Sai bata takura ta ba kawai ta tashi ta koma d'akin ta ta d'auko wayarta ta dawo wajen dinning d'in tazauna sannan tayi dialling numbern sa. Shikuwa yana can kwance shikansa bai san takamamman me ke damunsa ba har zuciyarsa, sai dai wani lokaci yakanji aduk sanda ya tuno da tafiyarsa (komawarsa wajen aiki) jiyake kamar zaiyi wani abu ne wanda ilahirin gangar jikinsa da zuciyarsa basu son hakan.Amma tunaninsa yagagara tantance masa menene matsalar ko kuma meke damunsa. Yau d'in ma hakane yana kwance ne shiru yana tunani amma idan da tsare shi za'ayi ace tunanin me yake yi da shikanshi bazai ce ga abinda ke sashi tunanin ba. Ringing d'in wayarsa ne ya dawo dashi cikin natsuwarsa, dayake wayar na d'an gaba dashi kad'an so baya ganin sunan me k'iran hakan yasa koda yabar tunanin bai wani motsa ba illah ido daya tsurawa wayar kawai batare da yayi yunk'urin d'auka ba. Haka har k'iran ya yanke wani yasake shigowa amma still bai motsa ba. K'iran na gab da yankewa ne sannan ya mik'a hannu ya d'auko wayar, ganin sunan da ke kai ne yasa shi mik'ewa zaune da sauri sai dai yana shirin d'auka sai wayar ta kuma yankewa atake yabi bayan k'iran amma cikin rashin sa'a sai yaji ance masa ai katinsa yak'are kaf gashi kuma bata sake k'ira ba, sai kawai ya yanke shawaran zuwa can ya sameta duk dama yasan batun bazai wuce na abinci ba, amma yasan tunda har ta masa 2missed call bai d'auka ba zata iya tunanin ko ba lafiya bane shiyasa ya yanke shawara zuwa d'in. Tashi yayi ya shiga bayi tukunna amma kuma koda yashiga sai ya manta da batun k'iran da mummyn ke masa, ya d'an 6ata lokaci kad'an abayi, daya fito kuma sai yayi tunanin kawai gara yayi recharging through VTU awayar tasa inyaso sai ya k'irata kawai. Teemah kuwa wani rigimar ta saka da mummy ta ajiye wayar bayan k'iran nasan datayi, sai ta ce Teemahn ta je ta dubo shi tunda gashi ta k'ira bai d'auka ba. Toh rigiman da Teemahn ta sanya ne yasa mummyn bata wani takurata akan sai taje dubo shin ba sai ta tsaya kallon Teemahn kawai dake ta bubbuga k'afafu tana fad'in "nikam bazani ba, Allah mummy idan naje mugunta yake min kullum idan naje" Kuka takeyi da hawaye take fad'in hakan, da mummy taga haka sai cikin hikima ta tambayeta asalin dalilin da yasa bata son zuwa aikan domin kar arashin sani ta cigaba da tura y'arta inda bai dace da rayuwar ta ba. (wannan haka yakamata iyaye mata su ringa yi domin haka na yawan faruwa azahiri ma, sai kaga yarinya/yaro wani lokaci yakanso yafad'i wa iyayensa damuwarsa ko kuma wani abu dai daban da shi baida ikon d'aukan mataki amma sai kuga rashin goyon bayan iyayen da kuma rashin tsayawa mu fahimci 'ya'yanmu da kyau sai kuga abu yazo ya lalace sai daga baya kuma azo ana dana sani wanda ta kansance k'eyace bata kuma ta6a dawowa gaba, koda abun ba haka yakeba yi k'ok'ari dai ki fahimci y'ay'anki kodan gyaran kuskuren da ba'ason ma ya auku idan kuwa ya aukun matuk'ar wahalan gyara ne dashi.). Teemahn kuwa cewa tayi "Mummy kullun fah cewa yake ni incinye abincin wallahi kokad'an bayaci shi, kuma kona k'oshi sai yace dole sai naci in bahaka ba wai harbeni zaiyi" Mummy dataji haka take ta sauk'e ajiyar zuciya, sai tayi istighfari aranta akan tunanin daya d'arsu azuciyarta d'azun, wani sanyi ne taji azuciyarta tare da wani nutsuwa dan sai yanzu taji dama-dama. Amma sai ta wani had'e rai tace "zoki wuce ki dubo min yarona ni banason shashanci" Wani kukan tasake sanyawa tajuya da nufin zuwa duboshin kenan sai wayar mummyn yafara ringing. Tsayuwa tayi cak dataji mummy na fad'in " au kaine? "Naga sabuwar number ne" Okay ba matsala ai, amma lafiya kuwa? toh shikenan za'a kawo d'in" Abinda mummyn tafad'i kenan daga d'aukar wayar zuwa ajiyeta. Hakan yasa Teemah tagane da Abbas mummy tayi wayar kenan. Bata juyo ta kalli mummyn ba haka kuma bata cigaba da tafiyan ba sai ta sake jiyo muryar mummyn na fad'in " zo Teemah ki had'a abincin ki kai masa kinji" "Dawowa tayi ta wani tura baki kana ganinta kasan aiken ne bata so duba da yanayin data koma gaba d'aya ta wani canja. Sai mummy tace mata " wai ni da kike ta wannan abin so kike ni nakai ne ko yayah" Sai Teemah ta jijjiga kanta ahankali alamar "a'a. " Toh wa kike tunanin zai kai masa idan bake d'in ba?" Sai tace " ga baba mai gadi ko kuma ak'irashi awaya mana mummy ya dinga zuwa yanaci da kansa" " Ai yau d'in baijin dad'i yace shiyasa"cewar mummyn. "Ai kullum haka yake cewa mummy" " nidai kiyi sauri " Teemah kuwa haushi sai ya hanata yin wata magana dan tasan bawani rashin jin dad'i da yake saboda tasan halinsa yanzu tana zuwa zai fara wani bubbud'awa da iyayi dan ya ganta k'arama afad'arta, duk da yau d'in tanajin yunwa sosai amma ita ba agurinsa taso taci ba tafiso taci atare da mummy zata fi ci a nutse amma shi nashi harda na haramun yake sata taci (injita nefah amma)🤣 Had'a abincin tayi ta kai masa d'akin nasa amma yau d'in sai tayi sa'a dan cewa yayi tare zasuci dashi, sai ya bata mamaki daya fad'i hakan har sai da ta d'aga kai ta kalle shi sai ya d'aga mata gira d'aya sama, aranta tace "dama ai nasani bawani rashin jin dad'i kawai so yake yaga nazo ya wulanka tani abanza" Tare suka fara cin abincin dashi sai kawai take jinta wani iri dan abun ban barakwai ya mata saboda tunda ya zo garin nan hakan bai ta6a faruwa atsakaninsu ba. Dayaga ta tsaya bata ci sosai sai ya d'iba yakai mata bakinta ita kuwa batayi wani musu ba kawai ta bud'e baki ta kar6a taci. Daganan yace mata sudinga d'iba atare dan bayaso yaga ta tsaya batare da taci abincin ba. Ahakan kuwa har suka gama ci gaba d'aya sai ta tattaro ta dawo da plates d'in kitchen, yau d'in dai da d'an sauk'i batajita a sama ba dan yau d'in ya tayata cii bakamar na baya dayake sata ci ita kad'ai ba. ***** Wata ranar laraba da azahar tana parlour akwance har aka idar da sallah tanaji gaba d'aya kasantuwar tana fashin sallah yasa bata tashi taje tayi ba, sai ta mik'e kawai tanufi d'akin Abbas dan tasan yana masallaci adai dai wannan lokacin. Ahankali ta tura k'ofar tashiga idonta baikai ga kan doguwar kujeran dake d'akinba gado kawai takalla dataga wayam shikenan dayake tariga da tasa aranta yana masallaci ne shiyasa bata wani damu da ko yana d'akin ko bayanan ba ita dai oho. Zuwa tayi bakin gadon ta zauna can kuma sai ta tashi ta nufi gaban madubin dake d'akin, turarensa tafara d'auka dan dama turaren ba k'aramin birgeta yake yiba musamman idan taji ya fesa ajikinta feffeshe jikinta dashi tayi itama dukka sai data fesa turatukan nasa sannan tajawo stool ta zauna sai ta buga tagumi agaban madubin tunaninta ya tsaya cak dan yanzu jitake kamar Yah Abbas kar ya tafi. Tun shekaran jiya dataji suna maganan komawarshi da Daddynta tarasa meke damunta. Bata so taji wai zata yi missing d'insa irin yanda tayi missing Yah mahmud dan shi Yah Abbas ba sonta yake ba, amma ga mamkinta sai taga tagagara samun natsuwa gaba d'aya. Ko yanxun ma ita kanta bata san me yakawo ta d'akinsa ba jitayi kawai tana sha'awar shigowa d'akin. Shikuwa yana kwance yana ta kallonta da mamakin abinda ya kawota d'akin nasa. Dayaga hankalinta bai zo gareshi ba ne yagane cewa tayi zaton baya d'akin ne shiyasa ta shigo. Akwance yake shima tun d'azu, duk ya rasa sukuni yana ji aka k'ira sallahn har aka idar amma bai motsa ba,for the first time yayi missing jam'i tunda ya girma ya san kansa. Dayaji anyi sallama ne kawai ya yanke shawarar cewa zai bari kawai ya watsa ruwa idan yaso kawai sai ya fita gaba d'aya daganan sai yawuce shagon barbing amar aski da gyaran fuska. Toh yana kwancen ne sai yaga shigowar Teemah cikin d'akin. Ita kuwa tana zaune agaban madubin kusan mintina takwas sai kawai ta mik'e tsaye da nufin ficewa daga d'akin dan kar ya dawo ya sameta yaci k'aniyarta. Fara tafiyan datayi kenan dayake tana rarraba idanu ad'akin sai ta hango shi kwance akan doguwar kujera tsoro yaso ya kamata amma koda taga kamar yana bacci ne sai ta dake ta wani tsaya k'arewa fuskarsa kallo. Gani tayi yayi mata kyau sosai a yanda yake d'in,take sai tunanin waccen yarinyan yazo ranta wato _Muhibbat_ take sai taji ranta ya 6aci atunaninta itama taga kyan nan dayayi sai ta fara d'aga k'afanta ahankali-ahankali harta tsinci kanta tsaye gaban kujerar dayake kwancen. Tsayinta ta rage tayi k'asa ta tsugunna daidai yanda kujerar take. Cigaba tayi da kallonsa sai taji kamar tasashi acikin jaka kar ya tafi yabarta amma tasan inah no way. Har ta d'ago hannu zata kai kan fuskar tasa sai kuma take fuskar muhibbat ya bayyana mata a idanu dai-dai sanda tafito daga gida ranar daska je dashi d'innan, fuskar _Muhibbat_ d'in k'unshe da murmushi har ana hango wushiryarta, tuna hakan ne yasata ta maida hannun nata k'asa dan wani sabon 6acin rai ne taji ya lullu6eta. Take ta mik'e kamar an bata umarni bata kuma tsaya wata-wata ba ta fice daga d'akin ta nufo nata d'akin. Sai da yaga ta fita kafin ya bud'e idonsa yabi k'ofar data fitan da kallo. Mamakinta yaji dan duk abinda ta aikata yana kallonta itace kawai tayi zaton bacci yake, abinda yake zuciyarta ne kawai bai sanda shi ba sai kuma yanda yaga tafita d'akin da zafi-zafi da kuma had'e rai wannan ma bai san manufarsu ba. Idansa kawai ya bud'e bayan ya gama tunanin kuma yasake kulle su baiyi zaton zata dawo ba amma cikin ikon Allah kwata-kwata bai san dalilin daya sa yagagara motsi ba dan koda d'an yatsansa bai motsa ba murmushi kawai yayi sai ya sake maida idanun ya kulle su. Cikin haka ne yaji an sake bud'e d'akin an shigo bai wani damu yasan wanda yashigo d'in ba dan baya raba d'ayan biyu itace tashigo jin babu alamun sallama daga bakin mai shigowar. Ita kuwa kansa tazo ta tsaya hannunta rik'e da robar hair removal cream. K'asa ta maida idanunta daga gefensa ta k'asa.Tunani takeyi a zuciyarta dan gani take wannan abin da take shirin aikatawan kamar ba dai-dai bane. Shikuwa hakan da tayinne yabashi chance d'in ganin abinda ke rik'e ahannunta batare da tasan yana kallont ba. Ahankali ya maida idanunsa ya lumshe bai bari ta lura da bud'e idanun dayayi d'in ba. Muje zuwa fans,Teemah fah zata yo rigima anan☺ _Vote, share and_ _comment pls_ 🤞🏻 *Salmerhn ku ce*😍 [10/2, 5:58 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *25* Tayi tsayuwan mintina yakai hud'u tana tunanin tayi abinda zuciyarta ke raya mata ne ko kuma kartayi. Kawai sai ta yanke shawarar data ga yafi kwanciya mata azuci......musamman idan ta tuno irin muguntar daya ke yimata da masifah ga kuma _Muhibbat_data mata karan tsaye itama azuci. Sai take ganin ai idan bahaka tayi masa ba bazata rama abinda yake mata ba. Dawo da kallonta tayi kan fuskarsa sai taga har yanzu baccinsa yakeyi bai ma san tana tsaye akansa ba. Kamar wata mai hankali haka ta tsugunna agabansa ahankali idonta na kansa tafara matso mai d'in, koda ta matso sai ta tsaya kallon hannun nata, jin wani kuzari tayi yazo mata farat d'aya ai kuwa batare da wani dogon tunani ba tafara shafa masa man afuskarsa gaba d'aya duk gurbin data ga akwai gashi (beard) sai da tabi tashafa shi. Shikuwa mamaki ne yaci kasa dayaji abinda take yi masa a fuskarsa, saboda ko lokacin daya ga abin rik'e a hannunta baiyi tunanin shine target d'inta akan abin ba. Sosai yayi mamakin hali irin na Teemahn da ko da wasa bai ta6a tunanin rigimarta har ta kai haka ba. Sai yanayin rashin tsoro da kuma k'warin gwiwarta akan abu yaji ya birgesa, duk dama ga dukkan alamu kafin ta aikata hakan sai da tayi d'an nazari akai, duba da yadda tayi tsaye akansa batare da wani dalili ba hakan yana nuni ne da cewa tana jin tsoro, amma still tsoron bai hanata aikata abinda zuciyarta tariga ta sak'a mata ba. Teemah kuwa harda cije baki sanda take shafawan dan ita a tunaninta idan ta gama shafawa sai tayi tafiyarta ta barshi so ko ya tashi daga baccin ba zaiyi tunanin ita ce ta aikata masa ba. Sake matso manli d'in kuwa tayi dayawa ahannunta tafara shafawa amma tana cikin shafawan sai taga ya bud'e idanunsa ras akanta, " yah subhanallah" tace ahankali garin janye hannayenta cikin gaggawa kuma sai ta d'an goche hannun ya shafu a goshinsa, dayake bawani gashi mai yawa bane akannasa sai mai d'in yayi saurin ratsawa har k'asan gashin. Sa ke lumshe idanu yayi yace " yah salam" dan ya riga yasan ba k'ara min aika-aika tayi masa yau d'in nan ba. Da sauri ta mik'e tsaye zata gudu shima kuma kamar yasan hakan zai faru sai ya sake bud'e idanunsa sai ko ya ga tana shirin guduwa,sai ya mik'e da sauri ko taku hud'u batayi ba taji anrik'o hannubtaShikuwa mamaki ne yaci kasa dayaji abinda take yi masa a fuskarsa, saboda ko lokacin daya ga abin rik'e a hannunta baiyi tunanin shine target d'inta akan abin ba. Sosai yayi mamaki hali irin na Teemahn da ko da wasa bai ta6a tunanin rigimarta har ta kai haka ba. Sai yanayin rashin tsoro da kuma k'warin gwiwarta akan abu yaji ya birgesa, duk dama ga dukkan alamu kafin ta aikata hakan sai da tayi d'an nazari akai, duba da yadda tayi tsaye akansa batare da wani dalili ba, amma still bata ji tsoron yi masa abinda zuciyarta tariga ta sak'a mata ba. Ita kuwa harda cije baki sanda take shafawan dan ita a tunaninta idan ta gama shafawa sai tayi tafiyarta ta barshi so ko ya tashi daga baccin ba zaiyi tunanin ita ce ta aikata masa ba. Sake matsowa tayi dayawa kuwa tafara shafawa amma tana cikin shafawan sai taga ya bud'e idanunsa ras akanta, " yah subhanallah" tace ahankali garin janye hannayenta cikin gaggawa kuma sai ta d'an goche hannun ya shafu a goshinsa daya bawani gashi mai yawa bane akai d'in sai mai d'in yayi saurin ratsawa har k'asan gashin. Sa ke lumshe idanu yayi yace " yah salam". Da sauri ta mik'e tsaye zata gudu shima kuma kamar yasan hakan zai faru sai ya sake bud'e idanunsa sai ko ya ga tana shirin guduwa, sai ya mik'e da sauri ko taku hud'u batayi ba taji ya rik'o hannunta d'aya, okda ta gwada ja kuwa sai tajita k'yam dan dolenta ta waigo ta kalle shi, suna had'a idanu sai tayi k'asa da kanta. Shikuwa jan hannun tan daya kama yayi batare da yayi magana ba yajata zuwa gaban madubi suka tsaya awurin, kallon kansa yayi acikin mirror d'in sai ya maida idansa kanta, gani yai idanunta na kallon k'asa a hankali ya k'ira sunanta " _Fateemah_". Ciki-ciki ta amsa da " na'am" batare da ta d'ago ta kalleshi ba dan tasan yau d'innan mai raba su sai Allah, ita sam bataso yatashi yanzun ba taso sai bayan tagama abinda zatayi tatafi kafin ya tashi amma sai ya 6ata mata plan yatashi da wuri. " D'ago ki kalleni" Ta sake jiyo muryar shi yafad'i haka. Amma sai ta gagara aikata yanda yake so d'in sai ma ta k'ara yin k'asa da idanunta. Cikin tsawa ya sake cewa " nace ki d'aga kanki ki kalle ni ko!" Take jikinta yafara 6ari cikin idanunta yafara tara hawaye. Tsura mata ido yayi yana kallonta batare da ya sake magana ba itanma a hankali tafara d'ago idanunta yayin da ruwan dake cikin idanun suke k'ara yawaita. Da farko lokacindata fara d'ago kai d'in idonta a bud'e yake amma data ga tana gab da d'agowa gaba d'aya sai tayi saurin rintse idanun take kuwa hawayen daya taru a gurbin idanun ya gangaro zirr ya jik'a kumatun ta.....ahakan ta k'ara sa d'agowa takuma k'i bud'e idanun nata. Tsayawa yai yana kallonta da kyau, a kullum gani yake yarinyar na k'ara yin kyau ne tafiya take da imaninsa da kuma tunaninsa gaba d'aya. Kusan mintina uku babu wanda yayi magana a tsakaninsu illah jikin Teemah dake ta faman 6ari dan yau tasan tashigo hannu sai yanda Allah yai da ita abanza ma yaya balle ta aikata laifin azahiri. Ganin yanda jikinta ke karkarwa ne yasashi murmushi aransa yace " halin yarinyar nan sai ita, ga uban tsoro ga kuma fitina da neman magana". Sai kuma yaji ta bashi tausayi sosai sai ya tsurawa crying face d'in nata idanunsa shima na tsawon sakanni bai d'auke idanun san daga kallon fuskarta ta ba yace " open ur eyes"! Atsare yayi maganar amma bada zafi ba. Duk da tana son bud'ewan amma sai ta gagara bud'ewa saboda tsoron yanayinsa dazata gani takeyi, shikuwa da ya ga bata da alamun bud'ewa sai ya sake maimaita mata " I said open ur eyes Fateemah" Wannan karan ma asanyaye yayi maganar. Ita kuwa jin yana yi mata magana da muryar rahama sa6anin yanda ta zata da farko sai hakan yasa ta jin d'an sanyi-sanyi sai ta bud'e idanun kamar yanda ya buk'ace dayi. Cak idanun nata suka sauk'a a cikin nasa tana niyyar sauk'e nata idan ne yayi saurin dakatar da ita da d'an k'arfi..." don't try it!" Dan dolenta itama ta bar idanun tan akan san duk da yanda take jin bugun zuciyah aduk lokacin data had'a ido dashi, amma haka ta daure batare data so ba. Tambaya taji ya jefa mata amma sam ta kasa bashi amsar tambayar tashi saboda kwata-kwata ita bata ma san me zata ce dashi ba koda ta bud'i bakinta. Sai tayi shiru kawai tana rarraba idanu, ganin tayi shirun shikuwa sai ya sake maimaita mata tambayar kamar yanda ya fad'i da farko batare daya canja ko kalma d'aya ba " me yasa kika shafa min nace"! Wannan karon ma a nutse yayi tambayar sai hakan da yayi yasa taji kusan 40% daga cikin tsoron data ke ji d'in ya kau. In-ina tafara sai yayi saurin dakatar da ita da jijjiga kansa. Hannu ya sa ya kamo fuskarta ya d'ago saitin fuskarsa suna kallon juna " then tell me now" Ya sake fad'i. Ita kuwa sai tak'i magana sai ta sake jin jikinta wani iri tsoronsa ya k'ara kamata ga kuma bugun zuciyarta dake k'ara yawaita, zuwa yanzun koda tace zata yi masa magana toh bata san me zata ce masa ba domin bakinta kansa yayi mata nauyi. Da yaga bazata yi masa magana ba sai ruwan hawayen ta dake matuk'ar ta6a masa zuciya, sai ya sake mata fuskarta ta ya mik'e tsaye singlet d'in dake jikin sa kad'ai ya cire sai ya dawo inda take ya kama hannunta ya fara tafiya da ita. Bata yi turjiya ba tunda tasan itace da laifi sai kawai tabisa. Shikuwa bayi ya nufa da ita,koda taga yana niyyar shigar da ita bayin ne sai ta d'an turje, juyo yayi ya bata wani dirty look take kawai ta d'aga kaf'afu tabishi. Shahada tayi ta bishin duk da bata san mai zai biyo baya ba sai kawai ta rink'a addu'a azuciyarata akan cewa Allah ya ubangiji ya d'ora ta akansa Allah ya ku6utar da ita. Suna shiga bayin yayi zamansa akan wani stool da ke ajiye musamman acikin bayin.Sai yace mata " bismillah k'arasa aikinki". Bata gane mai yake nufi ba amma dana haka sai taja tayi tasaye tana wasa da yatsun hannunta. Tsawon mintina sai yakuma fad'in "banaso idan ina ma mutun magana ana shareni ki kula sannan kuma warning naki na k'arshe kenan" Haryanzu bata fahimci mai yake nufi da bismillan ba amma tsab ta fahimci warning d'in daya mata kawai dai bata san mai zata yi ba ita. Shi da kansa ya fahimci bata gane manufarshi ba sai yace mata " ni nace miki ina buk'atar aski ne ko shaving?" Sai ta jijjiga kanta alamar " a'a" " Ni nace ki shafa min mai jikina?" Nan ma jijjiga kanta tayi. " Ni sa'anki ne agidan nan?" Harta fara jijjiga kai sai taji ya daka mata tsawa inda yace open your mouth and talk to me or are u deaf?" Da sauri tace " umm-umm" Dan gani tayi take ya juye mata tamkar mayak'i idanunsa taga sunyi jajir. " Raini ne kenan yasaki yimin haka ko?" Da rawar murya ta ce " ah....'ahh..... yayah..... dan.....dan girman Allah kayi hak'uri. Bai sake yi mata mata magana ba kawai ya sa hannu ya matso da ita kusa dashi ya d'aga mata fuskar sai da da lumshe idanu kafin ya furta " clear it"......... Dan dolenta tasa hannu ta kunna tap sannan tafara wanke masa fuskar tasa duk inda cream d'in ya ta6a sai da tabi ta wanke tas. _Comment and share_ _pls_ 🤞🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 5:58 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *26* Tana k'arasa wankewa sai ta d'age hannunta daga fuskar tasa shima daidai sai ya bud'e idanunsa ya sauk'e su akan madubi, tacikin mirror d'in suka had'a idanu ai kuwa tana ganin yanda yakoma sai taji dariya yakamata. Hannunta ta d'ago ta rufe bakinta dashi wani shape da goshinsa yacire ne yasa takasa rik'e dariyar tata sai ta juya kawai da gudu tabar bayin. Bata zame ko'ina ba sai a d'akinta tana shiga kuwa ta tura k'ofar ta danna lock. Dariya tayi taci abinta harda rik'e ciki. Abbas kansa shima dariyar taso kamashi amma sai kawai ya maidata murmushi ya k'yale dariyar, haka ya k'urawa mirrorn idanu yana kallon kansa yanda Teemahn ta sauya mar kamanni, ita kawai yake hangowa lokacin da ta ke shafa masa cream d'in gani yake kamar yanzu ta ke yi masa hakan, sai kawai ya lumshe idanunsa bai dad'e ba ya kuma bud'esu. Tunanin yanda zai je agyara masa kan nasa ne yafad'o masa, take sai yaji ba dad'i jiyayi ransa na so ya 6aci akan hakan, amma sai ya danne 6acin ran nasa, taimako d'aya Allah ya mata dan dama he is about to leave kuma dole kafin ya tafin sai yayi aski, amma badan hakan ba yace " hmm" kawai sai da yakai hannu ya na shafa kannasa kafin yace " yayarinyar nan ta gama raina ni wallahi dole inkoya miki hankali". Tashi yayi yafara rage kayan jikinsa dayake daman bai cire su ba d'azun. Sai da yayi wanka kafin ya fito daga bayin d'aure da towel yana tsane ruwan dake jikinsa. Shiri yayi dolensa cikin captan mint green yasa hula ya daidaita ta da kyau ta rufe gurbin kannasa sannan ya fice daga gidan ya nufi barbing saloon d'in dayafi kwanta masa arai domin a gyara masa 6arnar da Teemahn tayi masa. ***** Teemah ce kwance ad'akinta akan gado sai kwasar dariya take harda hawaye, ko tayi niyyan bari amma sai taji sabuwar dariya na k'ara zuwa mata seconds-seconds take sake jin wata dariya na kamata, cikin dariyar take fad'in " kad'anma kagani ai tunda dai ni kace zaka sa agaba kam sai dai mu zuba mu gani". Juyi tayi ta kifu agadon sai tunanin yanda suka kwashe da Leemah yazo mata a washegarin ranar daya hanata zuwa birthday. Har kusan fad'a suka so yi da ita dan tagama saka ran Teemahn zata je sai kuma taga shiru ga shi kuma babu waya a hannun Teemah balle tak'irata sai hak'an ya k'ona ran Leemah sosai. Haushin mitan da Leemah ke wa Teemah ne aranar ya had'u da haushin da yah Abbas ya k'unsa mata sai kawai ta fara yiwa Leemahn masifah toh dayake Leemahn itama ba baya bace wurin magana sai suka dinga yi atsakaninsu da k'yar suka yi shiru sai da Fauzee(class representative d'insu) tace zata had'a su da Uncle d'insu (Uncle Hasheem) kafin sukayi shiru dayake suna jin tsoronsa sosai. Har kuwa kusan kwana uku sukayi basuyin magana da junansu kafin daga baya suka zo siluka shirya kowa ya huce. Shiyasa ko yanzun data masa hakan kokad'an batayi dana sani ba acewarta tunda itama yana had'ata fa'da da mutane gara ta rama. Wunin ranar kuwa kaf d'insa acikin d'akinta tak'arasa shi dan k'in sake fitowa waje tayi dan ma kar su had'u da shi yaci k'aniyarta ko kuma ya had'ata da mummy. Batama san ya fita agidan ba dan hatta islamiyah ma yau k'in kulawa tayi da al'amarinsa, Mummy cema data ga shirun yayi yawa ga kuma lokacin islamiya har ya wuce bata ga gilmawarta ba shine tazo ta bubbuga mata k'ofar, amma sai tak'i bud'ewa tace da mummyn wai kanta naciwo ne sosai shiyasa bata fito ba tanaso tayi bacci ne. Mummyn dataji haka sai tace mata "toh Allah ya sauwak'a" sai kawai ta juya ta koma d'akinta. 8:02 pm Abbas bai dawo gidan ba sai da dare yana shigowa kuwa yawuto parlourn domin ya gaida mummy kasancewar tun gaisuwan safe da yayi wa mummyn basu kuma k'ara had'uwa da ita ba. Yana gab da shiga parlourn sai wayarsa tafara ringing, dakatawa yayi da tafiyar sannan yaciro wayar ya duba mai k'iran nasa Saleem ne abokinsa wanda sukayi course tare dashi sai ya tsaya awurin yayi receiving k'iran. Teemah na daga cikin parlourn suna zaune da Mummy sai taji ringing d'in wayarsa daga waje aikuwa ta wani razana hatta mummy sai data tsorata da yanda tayi d'in, da gudu ta tashi tayi d'aki batare da ko mummy tayiwa magana ba. Abin ya d'aure kan mummy sosai yau Teemahn na yin wani abu kamar marar gaskiya ta kasa gane inda gakan kuma ya dosa, ko d'azaun da k'yar tasamu tafito bayan sallar maghrib sai da mummyn ta kusan 6ata ranta kafin tafito daga d'akin ahkan ma tana wani d'ar-d'ar da kalle-kallen gefe. Shikuwa d'an dakali yasamu aga hanyar shigowan parlourn ya jingina sannan yasamu damar amsa wayar da kyau saboda wata gajiya yake ji sosai. Duk magana ce sukayi da Saleem d'in akan komawarsu wurin aiki dake k 'ara k'aratowa, bayan sun kammala da wayar ne ya dawo ya shiga cikin parlourn da sallama abakinsa. Mummyn ce ta amsa masa sallamar ta sa dan tuni Teemah kam ta ware d'akinta. Sai da suka gaisa kafin mummy take tambayarsa ko akwai abinda ya had'a au da Teema ne dan ta lura da ita kamar tana d'ari-d'ari da shi. Shi kuwa bai 6oye mata ba ya sanar da ita abinda Teemahn tayi masa yau d'in kaf bai 6oye mata komai ba. Salati mummyn tasanya da jin abinda Teemahn tayi fad'a tafara bayan ta kammala da salatin kamar ta ari baki. Daga k'arshe kuma sai fad'an yadawo kan Abbas d'in shima dan acewarta shi yajawo har hakan ya faru ai tana lura da shi bata ta6a ganin ya hukunta Teemahn ba duk da irin iskancin data ke masa". Shiru yayi yan jinta sai da ta dasa aya kafin yafara bata hak'uri dak'yar kuwa ta hak'ura bayan ta hak'uran ne yasake rokon ta akan karta yiwa Teemahn komai dan Allah ta bar shi da ita zaiyi maganinta kafin yawuche. 'Kin kulashi tayi kawai ta kauda kanta gefe hakan ne yasa Abbas yagane ba k'aramin 6aci ran mummy yayi ba da jin maganar nan. Har sai yaji yana dana sanin sanar matan da yayi ma. Hira yafar kawo mata sama kamar yadda ya saba saboda shi daman kalaman bakinsa kad'an ne. Mummy kuwa daga " uhmm ko ehh " Bata k'ara wani abu akai saboda tagama fahimtar shi so yake abin yawuce dan yaga ranta ya 6aci shi adole ya kauda zancen. Haka yayita d'an surutunsa yagama dayaga ba response mai kyau sai ya yi mata sallama ya wuce d'akinsa. Washe gari da safe............... _Vote, comment and_ _share pls_🤞🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 5:59 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._wad'anda nasani da wanda bansani ba. 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *27* Washe gari da safe da ya tashi sai yayi shirinsa da wuri ya fito, har kuwa lokacin daya fito d'in Teemah bata fito ba, gashi lokaci yad'anja dayake bahaka tasaba ba duk da bai fiya yawan fitowa a irin wannan lokacin ba amma dai yasan Teemahn bata fiya makara zuwa makaranta ba. Har zai basar kuma sai ya waske kawai ya wuce d'akinnata da niyyar tada ita, sau uku yana yana buga k'ofar amma shiru ba'a kulasa ba ganin hakan yasa kawai ya tura k'ofar yashiga ko sallamar ma bai yi ba. Kwance ak'asa ya tadda ita tana ciccije baki tare da mammatse cikinta duk ta had'a gumi ga kuma robar ruwa ajiye agefenta. Da sauri ya k'arasa inda take ya tsugunna " lafiya kuwa" ya fad'a yana tatta6a jikinta daga fuskarta zuwa hannunta da niyyar jin temperaturen ta, azatonshi ma zazza6i ne amma sai yaji jikin normal sai dai d'umi babu wani abu. " meke damunki ne wai" yasake tambayarta jin bata amsa masa tambayar farkon ba. Ita kuwa Teemah dukda tana d'anjin ciwon kad'an-kad'an amma sai hakan bai hanata jin dad'in har cikin zuciyarta da jin muryar Abbas d'in cikin rahama akusa da ita duk da tana tsoron hukuncin da zai mata amma tasan tana cikin wannan halin bazai ta6a yi mata mugunta ba dan duk abinsa yana da tausayi, balle yanda taga yake tambayarta cikin kulawa da k'yar ne ma idan bai manta abinda yafaru d'in ba. Yunk'uri tayi kamar zata tashi sai yayi saurin tareta ya zaunar da ita da kyau, " ina......kwana yayah" ta fad'a idanunta na k'asa da d'an in ina saboda cikin yad'an sake murd'a mata ga kuma tsoronsa data keji. Atakaice ya amsa mata da " lafiya " sannan ya k'ara da fad'in " wai me yasame ki ne Fateemah" " cikina ne yake ciwo, amma nasha magani yafara raguwa ma ciwon yanzu"Teemahn ce tafad'i haka Shikuwa tsayawa yayi yana kallonta sanda take kan maganar sai da ta dasa aya kafin ya sake cewa " wani magani kika sha"? " ibuprofen" tabashi amsa. " tun yaushe yafara miki ciwon" " bayan an idar da sallah ne". Yariga yagane meke damunta tunda shi ma atleast yayi zaman class koba komai yasan amfanin shan ibuprofen musamman ma ita da nata period d'in baya mata da wasa amma hakan bai sa ya fasa k'udurinsa akanta ba daya d'aukarwa kansa al'kawari. Kallonta yasakeyi dakyau sai yaga tayi wata fayau da ita tamkar wacce ke jinyar satikai. " me kuke yi a makaranta yanzu." Ya tambayeta. " test " itama tabashi amsa atakaice da irin sigar da ya mata tambayar dashi. " toh yaza'ayi kenan, zaki iya zuwane?" Kai ta d'aga masa alamar " ehh" sai yace "okay hanzarta ki watsa ruwa sai in sauk'e ki inyaso inkin rubuta Test d'in sai mu dawo gida. "Toh" tace tare da fara yunk'urin mik'ewa sai ya sa hannu ya da'agota suka mik'e tare sannan yasaketa. Bayi ta nufah da niyyar yowan wankan, shikuma sai ya tsaya yabita da kallo sai yanzu ma yake ganin yanayin kayan dake jikinta ashe ma na bacci ne shi duk bai kula ba. Juyawa yayi ya fita daga d'akin nata yana mai korar shaid'an azuciyarsa. Yasamu mummy na shirin shiga d'aki itama ganin sa yasa ta dakata suka gaisa anan yake ce mata ai cikin Teemah na ciwo amma wai tasha magani........ Taran bakinsa tayi tunkan ya dasa aya tace " Allah ya sauwak'a mata, makarantar fah ko bazata ba", a yatsine tayi maganar kamar bata so shid'inma yagane tun 6acin ran jiya ne bai barta shiyasa take hakan ga dukkan alamu ranta ya 6aci sosai da Teemahn, sai kawai ya bata amsa yace mata " a'a zataje tana shiryawa ne". Tana jin hakan ta juya abinta ta wuce ciki. Dakansa yau ya had'a mata tea tun kafin ta fito daga wankan,sugar d'an dai-dai yasaka mata aciki saboda condition d'in datake ciki. Itama Teemahn dawuri tayi wankan ganin lokaci yad'an ja sai ta yi shirin nata da gaggawa tafito dayake ma tadaina jin ciwon marar sai dai kad'an-kad'an shiyasa tayi komai da kuzarinta. Bak'aramin dad'i yaji ba dayaga ta fito normal kamar ba ita ba sai kawai yace " zonan ki yi breakfast mu wuce karkiyi latti " Ahankali ta taho ga dinning d'in danji tayi banbarak'wai dayake bahaka Yah Abbas d'in yasabar mata ba, tsakaninsu sai dai kallo, kallonma sai ranar daya ga dama sannan take samu, a kullum miskilanci agurinsa shine gaba da komai, Daddy da mummy ne kad'ai bata ganin yana musu hakan. Haka yasata agaba yace tasha Tea d'in sosai, tana kur6a taji salam sai ta d'aga kai ta kalle shi had'a idanu skuayi dashike shima d'in ita yasa agaba da kallo. "Ba sugar aciki" tafad'a tana kallon gefen fuskarsa. " ahakan zaki sha ai, ke baki san illar sugar agareki ba ko? Tsoron masifarsa yasa tadinga kur6a tana kuma danna bread a bakinta kamar wasa sai gashi tasha mai yawa dan cup d'in daya had'a mata gaba d'aya ta shanye shi. Dire cup d'in tayi bayan tashanye d'in sai ya kalleta yana murmushi yace " iyehhh, irin yau anyi abin kirkin nan". Maganar tasa sai ya sata dariyah shima dayaga tana dariyar sai ya tayata suka yi tare gaba d'aya yau ya canja mata kamar ba yah Abbas d'in data sani ba, zata iya cewa yau ce rana ta farko data ta6a ganin dariyarsa tun zuwansa gidan nan, take sai tata dariyar ta tsaya sanadiyyar tunanin data shiga. Ita data ke tsammanin mummunan hukunci daga wurinsa sai kuma akasin hakan ya faru, bata ta6a zaton yah Abbas zai yafe mata laifin sata masa da wuri haka ba amma ga mamakinta sai ya sauya hakan da wani sabon salon annashuwa da farin cikin da bazata ta6a mantawa dashi ba. Idonta k'ur akansa amma sam hankalinta ba'a kansa yake ba, sau d'aya ya mata magana da yaga bata amsa ba sai kawai shima ya yi shiru ya k'ura mata nasa idanun yasan bai wuci mamakin sauyin data gani tattare dashi take yi ba wanda yasan dole ne daman tayi wannan tunanin,bama ita kad'ai ba duk wanda yasanshi idan yaganshi yanzun sai yayi mamakin sauyawarsa. Sai dai shikuma kokad'an baya so ta samu chance d'in da zata yi tunani akan hakan har sai ya bar garin tukunna dan haka sai ya d'ago hannunsa yaja kumatun ta tare da jijjigawa, ai kuwa sai ta dawo daga tunanin tare d'an firgicin tsoro bayyane a cikin k'wayar idanunta dayake daman bata gama sake jiki dashi ba har yanzu, amma ganinsa da smiling face yana kallonta sai ta saki ajiyan zuciya slowly, " kin manta zakiyi Test a school ko?, tashi kije ki gaida mummy sharp-sharp kizo muwuce". Asanyaye ta tashi tsaye tana duban fuskansa afakaice shikuma alokacin agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa yake dubawa amma duk da haka sai yace " kiyi sauri kije nace kuma kin wani tsaya anan kina kallona! Fuskarsa sake take aduk lokacin da zai kalle ta ko zai furta mata wata magana shikansa jin kansa yake wani iri daya ke bahaka ya saba ba amma wannan d'in aganinsa dolensa ne yayi mata hakan kodan ya yi maganinta saboda rashin jinta. Bata fi 3mins agun mummyn ba ta fito da d'aurarren fuska, tana fitowa kuwa shima ya mik'e tsaye ya iso gareta dan ganin dayayi bata da walwala " ya akayi ne " ya tambayeta bayan ya tsare gabanta wanda dan dolenta hakan ya dakatar da ita daga cigaba a tafiyan datakeyi. " ba mummy bace ta min masifa....... " me kika mata " Ya jeho mata tambaya tunkafin tak'arasa fad'in abinda tayi niyyar fad'a. " Nima bansani ba" Tabashi amsa ashagwa6e sai baiyi magana ba kawai ya juya yafara tafiya sannan yace "oyah hurry up muje kiyi test d'in idan mun dawo sai ki bata hak'uri. Bin bayansa tayi itama batare da ta yi wata magana ba. Shikuwa bai tsaya ko'ina ba sai wajen parking sai da ya bud'e motar ya shiga kafin ma ta k'araso itama ta shiga. Ahanya ne yayi tajan ta da hira yana tsokanarta har sai dayaga ta sake gaba d'aya kafin ya kyaleta. Koda yakaita makarantar ma dakansa yakama hannunta ya isa har office d'in shugaban makarantar yayi masa bayani tare da neman alfarma akan cewa bata jin dad'ine kuma tace zasu yi test shiyasa ya kawo ta so idan sun gama test d'in yana so ya wuce da ita clinic a dubata. Principal d'in ne ya tambayeta sunan malamin da zaiyi musu test d'in tagaya masa, sai kawai yak'ira shi awaya ya tambayeshi lokacin dazai yi test d'in sai yace masa nan da 30mins ne. Bayani yayi wa Abbas d'in daganan suka fito atare gaba d'ayansu sai Abbas yayi musu sallama akan cewa Teeman taje class ta jira lokacin yayi inyaso idan sun gama sai tasame shi amota. Daga k'arshe suka yi musabiha da principal d'in yakoma office Abbas kuma ya tafi ga motar sa yayinda Teemah ta wuce class. Tana zuwa ma bata dad'e ba akazo akayi musu test d'in alokacin kusan 11:00am tayi, ko da suka gama sai class rep d'in su (Fauzee) da wata friend d'insu suka rakota har wajen motar. Abbas kuwa hankalinsa naga wayarsa bai ga tahowarsu ba har sai da Teemah ta k'wank'wasa masa glass kafin ya ankara dasu. Ahankali ya sauk'e glass d'in yana murmushi yace " lil sis yadai ko har kun gama test d'in?" Kai kawai ta d'aga masa alamar "ehh". " Shiga mu wuce " Yace da ita. Su Fauzee kam tun da ya sauk'e glass d'in suka k'ura masa idanu suna k'are masa kallo dan sosai yatafi da imaninsu. Jin da Teemah tayi shiru bataji sun gaishe shi ba gashi har yana cewa tashiga su tafi sai ta d'an waiga ta kallo su gani tayi dukkansu suna kallonsa take sai ta ji ranta ya 6aci da hakan sai ta juya shima ta kalli 6angaren dayake taga nashi yanayin, cikin sa'a sai taga shi d'in bai masan suna yi ba dan hankalin sa ma sam baije ga inda suke ba. Sai da ta bud'e marfin motan kafin takuma kallonsu tace musu "toh Fauzee nikam na wuce sai gobenku". D'agowa fauzeen tayi ta kalli Teemahn sai ta kuma maida kallonta ga Abbas d'in tare da fad'in " ina kwana Yayah" 'Dago kai yayi ya kalle su dan shi harga Allah bai kula dasu awajen ba, sai lokacin da yaji Teemhn na musu sallama kuma ko a sannan bai zaci suna tsaye agurinba atunaninsa wucewa sukayi. "Lafiya ya school " ya amsa mata dashi. Ga mamakin Teemah sai taga ya amsa mata wasai bawani d'aure-d'auren fuska kamar yadda yasaba fitowa a asalin millitary force d'insa ba. Sai d'ayan k'awartasu mai suna Ameena itama ta gaisheshin kamar yadda Fauzee tayi abin mamaki bayan amsa gaisuwar harda tsokanar su yayi akan test d'in da suka yi wai ina de basu yi satan amsa ba" yanda ya sake musu fuska sai suma take suka sake dashi yayinda suka bashi amsa da fad'in " haba dai ai an girma anwuche wurin yanzu mun girmi satan amsa" "Ohh daa anyi kenan" yafad'i da d'an zaro idanu waje. Sai suka d'anyi dariya su Fauzeen Shikuwa cewa yayi " toh Allah yasa dai hakan ne", bari mu wuce kunga lil sis d'ina ba lafiya ina so in kaita clinic yanzu" Har karo muryoyinsu sukeyi wajen fad'in " toh Allah ya kawo sauk'i yayin da d'aya ke fad'in Allah ya sawwak'e . Jinjina kai yayi kawai tare da d'aga musu hannu daga nan yaja motar suka tafi. Sosai su Fauzee suka ji Abbas d'in ya yak'ara birgesu. Sai da ya hau titi kafin ya kallo Teemahn jin tayi shiru tun d'azun, sai yayi gyran murya ita kuwa fuskanta na saitin gabanta amma sai ta fahimci da it hakan dayake yana kallonta yayi. Sai juyo itama ta kalleshi yayin da shi kuma yariga da ya maida hankalinsa ga tuk'I. " wai dama kasansu ne yayah? Ta jefa masa tambayar tana kallonsa. " shi kuwa murmushi yayi mata dan dama abinda yake so kenan, amma sai yace mata " me kuma yafaru?,ko laifi ne dan mun gaisa dasu? " a'a" tace ahankali tare da kawar dakanta gefen hanya. Sarai ya fahimci damuwarta kishin Teemah sam baya iyah 6uya, he can recalled that lokacin daya zo gidansu batason ko gaishe shi ma tayi balle magana ya had'asu, haka ma da Mahmud yazo tai tayin rigima dan dai mahmud d'in ba irin sa bane da yasan har lokacin barinsa gidan bazasu yi wani shirin arzik'i dashi ba, kuma duk hakan yana faruwa ne sanadiyar son kanta sam bata so wani yafita ko kuma afifita wani akanta tafison a kullum ta zama tasha gaban komai akuma ko'ina ta kasance A. Bai sake kulata ba har sai da suka zo daidai wajen mai saida kayan itatuwa harma ya d'an gota shi sai kuma yadawo da baya. Fita yayi bayan yai parking sai yaje ga mai saida fruits d'in yasayo da d'an dama kuma kala-kala sannan yadawo motar aka zo aka sa masa su a boot daga nan yaja yafara tafiya yanzun ahankali yake tuk'in har suka zo gida suna yin parking yace mata "ki bud'e baya ki shigar da kayan can na ciki, "toh tace tana k'ok'arin fita ya kuma cewa " kinsan mai yasa na saya? Da kai ta amsa masa alamar "a'a". " toh tuna baya nayi ko kin manta? Murmushi kawai tayi dan tasan labarin baya d'in kaf abakin mummy, shima sai yafara gaya mata irin abinda take masa abaya d'in lokacin tana k'arama da irin muguntar datake masa da rigimar sai an saya mata fruits kullum. Dukkansu abin sai basu dariya sai ta bud'e motar tafito shima ya fito suka nufi bayan atare shi ya bud'e ita kuma tasa hannu ta d'auko ledar, tana fitarwa tayi saurin dire shi ak'asa tana nishi " miye kuma" ya tambayeta da mamaki. Karkata kai tayi gefe tare dayin k'walk'wal da idanu tana kallonsa. " gara ma ki zage ki d'auka domin ni nayi nawa tun abaya yanzu kuma lokacin kine kema" Yana rufe boot d'in yake maganan. Cikin shagwa6a tace " Allah akwai nauyi sosai yayah" " koma menene fah sai kin d'auka yau d'in nan dan na fahimci ba k'aramar raguwa bace ke d'in kina nan kullum sai surutu amma ba amfani." Baki ta tura sannan azuciye ta cicci6i ledan tayi ciki da shi, shima bayanta yabiyo hannunsa rik'e da wayarsa da kuma key d'in mota. Tafiya kad'an ce ta iso dashi inda take tafita da k'yar kamar zata fad'i, tausayi tabashi da ganin yanda take kokuwa da ledan sai alokacin kuma ya tuna da bata da jin dad'i ma ashe sai yasa hannu ya kar6i ladan ya rik'e ahannunsa " muje intayaki d'auka kafin ki fad'i wa mutane". Yaryarfe hannu ta fara bayan ya kar6a d'in ita adole wai zafi, yana tafiya tana binsa abaya har suka isa kitchen sai da ya ajiye ya juya kafin yace mata " inkin gama ki had'a min fruits salat ki kawo min" "Ayyah yayah kamanta banda lafiya ne " Tafad'a kamar zatayi kuka dan harga ita bacci takeso tayi. " kin warke ai naga." Yana kan tafiyar ya bata amsa atak'aice. Ita kuwa haushi ne ya cikata daman ba barinta zaiyi ta huta ba shine ya hana zama a school? Cewa Baabah Lami tayi ta zuba su acikin fridge ita kuma tafice daga kitchen d'in. Gurin mummy ta koma dan sanar da ita akan sun dawo amma koda taje sai bata tarar da mummyn ba hakan yasa ta wuce d'akinta ta sauya kaya kafin ta dawo kitchen d'in dan had'a masa abinda yasata. ***** Acikin kwana ukun daya rage wa Abbas ya tafi ba k'aramar sakewa da Teemah yayi ba hakan kuma shi ya kawo shak'uwa mai k'arfin gaske atsakaninsu yakan 6ata lokaci yana mata hira da labarai na ban dariya, wani lokaci ya k'ira mata Mahmud awaya suyi ta hira dashi Abbas yana jinsu sai dai yayi ta murmushi in kuma sunyi abin dariya shima sai ya dara, yawo sukanje kusan kullum dashi hakanan yakan kaita islamiyah da boko ya kuma dawo da ita gida hatta muhibbat sai da suka kai mata ziyara tare da Teemah, anan ne ta fahimci ashe ma ba budurwarsa bace wacce abokinsa zai aura ne wato Saleem. Ita kanta wani lokaci takanyi mamakin al'amarin takance ashe dama Yah Abbas ya na da fara'a da sakewa haka?, amma mai yasa bai ta6a gwada min asalin halinsa ba sai ya ari wani hali ya ya6awa kansa, kodan shi soja ne shiyasa yake mugun hali oho. Mummy kanta taji dad'in wannan sauyin domin dama can bata son wancen d'abi'ar tasu ta rashin jituwan nan, kawai dai bata da yadda zatayi ne, kuma ganin hakan ne yasa ta manta da fushin datakeyi da Teemahn akan abinda tayiwa Abbas d'in saboda sosai hakan ya 6ata ran mummy aganinta raini ne kawai ke damun Teeman tunda shi Abbas d'in ai ba abokin wasanta bane. Cikin wannan kwanakin ne kuma Fauzee ta takura Teemah akan al'amarin Abbas d'in yayinda abin yake matuk'ar k'ona ran Teemah fiye da zaton mai karatu, tun daga ranar da Abbas yakai Teemah school har suka gaisa shikenan kullum sai sun rakota in sun tshi zata koma dan kawai su ganshi, wani lokaci har 6uya take yi dan kar su ganta, hakan bazai hana washegari su kuma tambayanta abu akansa ba most especially fauzee tafi damuwa dashi sosai. Bata kula ta haka take danne ranta har sai inta dawo gida sannan ta yi ta masa mita da fitina akan hakan shikuwa da bama sanin kirki yayi musu ba yadai san sun ta6a gaisawa da k'awayenta amma yanzu koya gansu he can not even recognize them amma duk da haka dan ya k'ara bata haushi sai yace " wai har yanzu bata daina damunki ba, jiya fah da mukayi waya nace mata karta na sakoki akan maganar amma bataji, kiyi hak'uri lil sis ki barni da ita zanyi maganinta" Hakan kuma bazai hana washe gari taji sabon salo daga Fauzeen ba sai duk suka bi suka d'aure mata kai gaba d'aya tarasa waye ne mai gaskiya acikinsu. Akullum Fauzeen zancenta ita a had'ata da Abbas tana so ne dan Allah ko phone number d'insa ne Teemah ta bata yayin da shi kuma yake nunawa akan ai suna waya ma da ita kawai fooling d'in Teemah takeyi tana wasa da hankalinta. Dataga inaah so suke su caza mata kai kawai sai watsar da al'amarin gaba d'aya tama daina kulawa koda Fauzeen tamata magana. Lokacin da Abbas yafara shiryen-shiryen komawa da Teemah suke komai duk wani abu daya dangamci tafiyarsa da ita akayi shi kansa yana yabawa da k'ok'arinta akan hakan sai dai deep down yana matuk'ar jin tausayinta har aransa domin shak'uwar da sukayi ba irin shak'uwar da za'ace anyi ta ankuma manta ta bane tana mat'uk'ar tsaywa azuciya, dakansa yafahimci irin yanda take ji da nuna kishinsa wanda yanada tabbacin ita kanta bata san ma'anar hakan data keyi ba. Wani lokaci yakanyi danasanin hakan daya mata yasan zai cutar da zuciyarta ne ba kad'an ba dan yana da tabbacin da bai sake da ita har haka ba da bazata ji zafin rabuwa dashi ba kokad'an koda kuwa yabar garin, duk da yake shi ya shirya hakan a matsayin hukuncin rashin jin data tayi masa da kuma rashin kunya amma shida kansa yanzu yasan bai kyauta mata ba. Ana gobe zai tafin da k'yar ta tafi ta kwanta amma kuma sam bacci yagagara d'aukanta haka ta kwana idanunta biyu tana ta tunanin rabuwa da yayanta. Kusan sallar asubah ne ta tashi ta dauko jakar makarantar ta ta fitar paper ta yagi d'an k'arami da biro tayi rubutu akai, ajiye shi tayi bayan ta gama rubutawa, sannan ta sake yagan wani the same size da wancan takuma yin wani rubutun shima ta ajiye, wasa wasa sai da tayi kusan kala biyar duk ta tarasu agefe ta d'ora kanta akai. Har akayi sallar asuban tana kwance idanunta a rufe gaba d'aya sai takejin babu dad'i, dakyar ta tashi ta d'auro alwala tazo tayi sallar asbah d'in, sai dai tana idarwa bacci ya d'auke ta akan sallayar datayi sallan. Dayake bata yi bacci da dare ba sai wannan baccin yamata nauyi sosai har gari ya waye ma bata sani ba har kusan 7:00 tana bacci. Abbas kuwa dama fitan wuri yake so yayi shiyasa yayi shirinsa da wuri yayi zaman jiranta dan sun rabu ne akan cewa da sassafe zata zo ta tashe shi daga bacci dan kar ya makara ganin lokaci na tafiya ita kuma shiru sai ya fito ya nufi d'akin nata dan ba mamaki ma mantawa tayi da batun tafiyar tasa acewarsa. Ahankali ya tura k'ofar ya shigo bayan bugun da yayi yaji shiru yana shigowa kuwa sai idanunsa ya sauk'a akan gadon ta dayafi zaton tana kwance akai tana bacci amma kuma sai bai ganta akan gadon ba sai yaganta ak'asa akan sallaya, murmushii yayi kana yace " daga sallah sai bacci kenan" . Takardun dayagani agefen gadon ya nufi wajensu aransa yake tunani k'ilan kwanan karatu tayi shiyasa take baccin yanzu. Hannu yasa ya d'auko takardan dayaga k'ananun papers akai sai yaga anyi rubutu kamar haka........ _People are like_ _stained-glass_ _windows_ . _They sparkle and_ _shine when the sun_ _is out_ , _but when the_ _darkness sets in,_ _their true beauty is_ _revealed_ _only if there is a_ _light from within_ . Kauda wannan yayi ya je ga na k'asa shima yaga ta rubuta..... _Hold on to what you_ _must do,_ _even if it’s a long_ _way from here_ . _Hold on to your life_ , _Even if it’s easier to_ _let go_ . _Hold on to my hand,_ _even if someday_ _I’ll be gone away_ _from you. __I'm_ _going to miss u _so_ very much yayah_ Sosai jikinsa yayi sanyi dayaga papers d'in haka yadinga d'aga wa yana gani tare da k'ara maimaitawa har kusan sau uku. Daga k'arshe sai ya zare guda d'aya wanda yafi sanyaya mashi rai ya ninke yasaka abayan condom (cover) d'in wayarsa sauran kuma ya mayar mata abinta ya ajiye mata. Inda take kwancen yaje ya tsaya yana kallonta yanda take baccin ba k'aramin birgesa tayi ba " she's innocent while sleeping. Wayarsa ya ciro ya kashe hasken camera d'in sai ya d'auke ta a photo daganan yajuya ya tafi abinsa. Koda ya fito d'in sai yabiya ta kitchen dayake yasan mummy kullum dasafe in kana son ganinta toh a kitchen zaka same ta har sai taga ta sallami kowa kafin hankalinta yake kwanciya. Da sallama ya shiga kitchen d'in tana juyawa ta amsa sallamar tareda fad'in " bade harka shirya ba"? Murmushi yai mata sannan yace "nagama shiri mummy inaso inje dawuri ne dan akwai abinda nakeso nayi acikin maidugurin kafin nawuce. Jinjina kanta tayi alamar gamsuwa, sai sannan kuma suka gaisa tare dayi mata sallama gaba d'aya, itama mummyn fatan alkhairi tayi masa da kuma d'umbin godiya bisa ga karamcin daya nuna musu wata guda cif na hutun daya samu awajen aikinsa yabar mahaifansa ya taho dominsu saboda zumunci. Sai yau ne zashi Gombe kuma acan ne zasu had'u da daddyn Teemah dayake shima yanacan yaje gaida 'yan uwa da mahaifiyarsu. Amma shi Abbas d'in gobe zai wuce dayake bawani yawane da 'yan uwansu nacan d'inba kusan kowa yanufi inda zashi Daddyn ma goben zai taho watak'ila ma su fito tare da shi gaba d'aya. Dayake saturday ne sai Teemah tayi tashan baccinta tana baza mafarki ba ita tatashi ba sai ba sai kusan 9:am balle yanda baccin yayimata dad'i kwata-kwata sai ta manta da batun tafiyar yayan nata. Tana farkawa kuwa shi fad'o ranta sai kuma idanta ya hango window gani tayi hasken rana gal ya haske ko'ina, wani mik'ewan datayi arazane harta ni sai dana tsorata da hakan. _Vote , comment and_ _share please_ 🤞🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 5:59 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* _Not edited_ 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 Spread love everywhere you go: first of all in your own house. Give love to your children, to your wife or husband, to a next door neighbor... Let no one ever come to you without leaving better and happier. Be the living expression of God's kindness; kindness in your face, kindness in your eyes, kindness in your smile, kindness in your warm greeting. *RAMADAN* *MUBARAKH* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Beginnings are scary. Endings are usually sad, but it's what's in the middle that counts. So, when you find yourself at the beginning, just give hope a chance to float up. *And it will* . 🅿 *28* Da gudu tafito ta nufi d'akinsa tana zuwa, k'ofar d'akin ma a6ud'e yake hakan yasa bata sha wahala mr bugu ba kawai ta fad'a ciki. Yanayin d'akin ne ya tabbatar mata da cewa yatafi d'in ne dagaske domin ko'ina shau tagani babu wani sauran abubuwan amfaninsa a d'akin. Take kawai taji jikinta yayi sanyi har gwiwoyinta na barazanar kasa rik'e ta a tsayen data ke. Sai ta k'arasa kan gadon dake d'akin ta kwanta gaba sai ta rasa mai ke mata dad'i, tasan bazata ta6a iya hana shi tafiya ba amma atleast taso ko sallama ne suyi, taso tamasa kallon k'arshe dan bata tunanin akwai chance d'in sake kallonsa kwana kusa. Ta kai a k'alla kusan mintina talatin ad'akin kafin ta lalla6a tafito. Zuwa lokacin kuma wani zazzafan ciwon kai ne ya ziyarceta sanadiyar bugun da zuciyarta keyi akai-akai. Tana fitowa sai ta had'u da mummy cikin shiri ga dukkan alamu ma fita zatayi. Ai tana ganin mummyn sai ta yafi da sauri ta rungumeta take sai hawaye ya gangaro mata zirrrr. Mummyn ma dayake ta fahimci damuwarta musamman dataganta tafito daga 6angaren d'akinsa sai ta fahimci cewa shi taje dubawa tunda tasan basuyi sallama ba. Hakan yasa tafara bubbuga bayanta cikin tausayin 'yarta ta amma sai bata nuna tasan damuwarta ba illah tambaya data jefa mata nacewa "meyafaru,? meke damunta?". Temah 'kinyin magana tayi sai da mummyn tayi kamar ranta yasoma 6aci ta hasalo tare da maimaita tambayar da d'an tsawa sannan ne Teemahn tace mata " mummy yayah yah yatafi abinsa kuma yak'i yatasheni abaccin yatafi kayansa......... Tsaki mummyn taja tare da fad'in " zamanki yake ne da har sai yatashi kafin yayi tafiya. Shiru Teemah tayi dan zuwa yamzun kalamanta sun fara mata nauyi, tafara gwammace yinshiru fiye da yin maganar ma gaba d'aya. Hakan yasa tabar jikin mummyn tawuce d'akinta yayin da mummy ma tayi tafiyarta tana mai gyara rik'on jakarta batare da ko waiwaye tayi ba. Haka cikin sanyi tayi dukkan abinda zatayi tagama ta shirya tafito sannan ta had'a tea tayi zaman sha kallon kofin tayi sai take Yayanta ya fad'o mata arai ta tuna a d'an zaman sun da sukayi dashi irin abubuwan walwala dayake sada ta dasu, ta tuna ranar daya sata ta masa alk'awarin daidaita kominta yadda kowa keyi, tadaina rashin ji da rashin kunya wa babba kuma taringa cin abincinta akan lokaci yace inhar tayi hakan toh ya mata alk'awarin wani abu amma sai ta gama secondary school kafin ya gaya mata, tayi tayi dashi akan yasanar da ita yak'I sam yace bayanzu ba shi dai fatan shi tayi masa alk'awari, duk da tana son sani koma menene abun amma haka ta hak'ura ta d'auka masa al'kawari. Sake kallon kofin data had'a tea d'in tayi ahanakali sai ta kai hannun ta d'auko kofin takai bakinta, tunda takafa shi akai bata cire ba har sai data shanye shi ras kafin ta dire kofin dai-dai da mik'ewarta dan tana dire kofin ta bara arean dinning d'in takaoma d'akinta. Gidan shiru bakowa bakuma motsin komai dayake ba yara k'anana ne agidan ba ballantana aji hayaniyarsu kuma mummy ma bata nan balle ko k'aran TV ne taji, sai kawai tata shi itama ta fito agidan da niytar fita amma harta kai k'ofar fitan kuma sai taji ranta na 6a ci da fitan kuma ma taka mammiyan inda zataje ma bata sani ba, sai kawai tajuyo ta dawo gida. She feels like tayi kuka amm bata son ta 6ata hawayenta abanza tunda shima yayan bai damu da ita ba so no need ta ta zubda hawayenta akansa duk da tana ganin idan ba kukan tayi ba sam bazata ji ta normal ba, baza ta ji kanta daidai ba. ***** Hak'ik'a sabo baida dad'I kokad'an kuma Abbas bak'aramin nasara yaci ba akan Teemah dan wannan tafiyarsa tasa ta matuk'ar jijjiga ta, sosai yashiga jikinta har tana jin kamar tunda take bata ta6a missing d'in wani abu kamar haka ba. Mummy kanta abin har yaso yafara damunta ganin yanda Teemahn nata ta dawo, kwata-kwata ta canja gaba d'aya kamar ba ita ba, zakayi mamakin inda rashin jin Teemah yatafi wata kalar shiru-shiru tadawo, dayake abin ya had'u mata da girma sai suka had'u da kewar yayanta da kuma girman data yi sai ya haifar mata da wata natsuwa taban mamaki. Duk wanda yasan Teemah ada idan yaganta yanzu tokuwa yasan ta canja gaba d'aya, bata fiya magana ba yanzun takan zauna tayi shiru na fin awa biyu batare da ko kyaky-kyawan motsi tayi ba. Wani lokaci mummy tayi ta mata magana amma bazama tasan tanayi ba, makaranta kuwa tsakaninsu sai dai ido idan kaga tayi doguwar magana toh kuwa sai dai in abin yazama dolene sannan takeyi, ko ma menene akeyi ko akayi her only answer is "ehh ko a'a" wani lokaci kuma tayi anfani da wani sassa na jikinta domin tabbatar da abinda takeso agane. Sabon salon miskilancin nata har classmates d'inta suna mamaki da hakan dan Teemah sune irin class disturbance d'innan amma cikin k'ank'anin lokaci duk wancan halayyar ta kau. Yanzun kam takan zauna taci abinci 3square meal d'innan baya wuceta ,takan ci dai koda babu yawa ma musamman idan ta tuna da alk'awarin data yiwa Yayan nata sai take daurewa tana d'an kiyaye abubuwan daya sa ta alk'awarta masa akan zata nayi, tunda tasan matsayi da kuma girman alk'awari duk da yanzun tanaji kamar ta tsani yayan nata har zuciyanta amma hakan bazai hana ta kasa cika masa alk'awarin data d'aukar masa ba. Abbas kuwa suna waya da mummy ko ranar daya bar damaturu ma bayan ya isa gombe yak'ira ta haka dazai wuce ma saida ya k'irata kusan ma kullum sai sunyi waya da mummyn nata inda mummy a kullum take binsa da addu'ar sa'a da kuma kariya aduk inda yake tana kuma k'ara masa tuni akan addininsa da kuma rk'o da gaskiya da amana tare da kwatanta adalci aduk inda rayuwa tajefashi. Babban dalilin daya sa Abbas ke yawan k'iran mummy kenan saboda baya so akullum yayi missing d'in addu'ar data ke yi masa, sosai hakan ke masa dad'i amma abin mamaki bai ta6a tambayar Teemah ba koda wasa, ita kuwa hakan sai yake k'ara bata haushi, daga baya ma inta ga suna wayar sai ta tashi tayi wucewarta indai tana tare da mummy alokacin inkuwa bata wajen ma shikenan. Koda Daddyn ta yadawo shikansa yayi mamakin canjawarta dayake bai samu yadawo a washegarin ranar da Abbas d'in yaje Gomben ba saboda wani issue daya rik'esa kusan 3days yak'ara bayan sunyi sallama da Abbas d'in. Shi da kansa ya jawo Teemahn jikinsa ahankali da lallami yake tambayarta ko wani abu ke damunta dan yanda yaganta d'in bak'ara min mamaki yayi ba, amma tace masa ba komai yayi tambayar har ya gaji amma bai samu gamsashiyar amsa daga gareta. Daga baya ne bayan sun ke6e da mummy yake sake tambayarta me yasamu Angel d'insa yaganta bakamar yanda yasaba ganinta ba, sai mummy bata 6oye masa ba ta sanar dashi cewa Teemahn tadawo hakane tun bayan komawar Abbas wajen aikinsa. Dariya daddyn yayi sannan yace " ta gaji mamanta kenan" Cike da mamaki mummyn ta d'aga kai ta kalle sa, sai ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa. Yakuma k'ara da fad'in kin manta da k'yar nasamu kika dawo hayyacinki lokacin rabuwarku da Alh.Yusuf?" "Murmushi kawai mummyn tayi masa dan kokad'an bata so ta tuna baya shiyasa bata k'ara furta wata kalmah ba ta basar da maganar kawai. Babu wanda yakuma kulata akan maganar kowa sai ya k'yaleta dan sun san na lokaci k'ank'ani ne zata warware dakanta. Ita kuwa hakan yafi mata tagi so kowa yabarta yanda yaganta bataso ake yawan tambayarta akan hakan dan bata sanin amsar bayarwa sai dai ma taji haushinka kai mai tambayar abinda yasame tan. Kwanan Abbas shida da tafiyah sai ga Mahmud ma ya dawo, aranar dasuka fita daga camp, Teemah kam bazata ce batayi murna da dawowar tashi ba saboda shima tayi kewarsa amma tagagara bayyana murnarta afili. Shikansa yayi mamikn inda rawar kan Teemah yatafi amma sai yabar hakan amatsayin girman data san yasameta ayanzun,duk da yake yasan sun fara shiri da Abbas kafin yatafi amma bai ta6a zaton shak'uwar dake tsakaninsu har takai matsayin da rabuwarsu zai ta6ata har haka ba shiyasa ma sam wannan dalilin bai zo kansa ba. Sai kawai yayi ta tsokananta wai ad'an tafiyan daya yin neh harta yi wayo haka?, ko kuma idan tayi wani abin yace " iyeh irin angirman andaina yarinta" murmushi kawai takeyi masa shikuwa daman dayake akwai wasa atsakaninsu sai baya ta6a gajiya da tsokanan nata koda bazata kulashin ba sai yayi. Mahmud yaso yayi zamansa a damaturun kafin yafara aikin bautar k'asan amma Anty ta rink'a damunsa da k'ira akan wai yadawo gida tana son magana dashi. Dafarko yaso ya share ta yak'i zuwa saboda babu wani anfani zuwan nashin, gani yake gufin yayi nisa sosai kuma idan yaje d'in ko 1week mai kyau bazaiyi ba zai dawo toh ina amfanin zuwan nashi. Data matsa masa sai kawai yace mata shi bashida kud'in transport d'in dazai kaishi lagos manufarsa intaji ta hak'ura da tafiyar amma abin mamaki sai yaji Bank alert tamasa transfer d'in kud'i isassu daza su kaishi su kuma dawo dashi, ko k'ira bai yi yamata godiya ba, sai kuwa k'iranta yabiyo baya inda take cewa yabi flight maza yataho. "Toh" kawai yace mata tare da yanke wayar aransa yake mamakin fitina da kafiya irin na mahaifiyar tasa. Dabara ce ta fad'o masa na k'iran Abbansa yagaya masa amma shima abin mamaki sai yace masa wai yatahi d'in kawai wai ai suma sunyi missing d'insa musamman Antyn nasa acewar Abban wai sosai take damuwa da rashin Mahmud d'in akusa dasu. Tsaki ne yaji na shirin kubce masa yayinda yake shirin yanke k'iran amma sai ya danne yayita acikin ransa. Haka ransa baiso ba ya shirya yayi sallama dasu mummyn yatafi maiduguri daganan yabi jirgi yawuce Lagos d'in. Abin takaici ma ba komai zai mata ba kawai a fahimtarsa fitina ce ke damunta bataso yad'an zauna tare da mummyn in an barta nan wai ita mai dabara. Washegarin zuwansa wata tazo gidan mai suna Munira, mahaifiyarta ce ta aiko wajen Antyn, lokacin data zo kuma Antyn bata nan sai Mahmud tasamu kwance akan kujera. Wani fi'ili da salo tafara yi masa ita adole tana yanga, shikuwa haushi yabi ya cikashi da k'yar ya bata amsar tabayar data yi masa na cewa ina mum d'in sa take? Zata sake magana ya tare ta cikin k'osawa da kasancewarta akusa da shi d'in ga kuma haushin uzura masa da Anty tayi inda azafafe yace mata " contact her mana karki dameni ni dallah" Jan bakinta tai tayi shiru tana k'are masa kallo, shikuwa yana da kwancen yaga ta kasa d'auke idonta akansa da farko yabata chance saboda yanayin kallon na d'an lokaci ne zata 'auke idanun ta amma sai yaga ina bata da niyyar dainawa, sai yatashi ya zauna da sauri yana kallonta idonta acikin nashi yace mata "naci miki bashi ne? Jijjiga masa kai tayi alamar "a'a" " so why the eyes?" Yasake fad'i sai sannan ta kauda idonta gefe cikin jin d'an nauyi. Tsaki yaja kana yakoma ya sake kwanciya amma ko 2mins bai k'araba ya tashi ya bar parlourn yayinda munira ma ta raka shi da idanu. 🔏🔏🔏🔏🔏🔏 our pencil is up!!!! *Anan zamu dakata* _inai mana fatan Alkhairi yah y'an uwa al ummar musulmi ubangiji Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa,haskensa rahamarsa,da falalarsa acikin wannan wata mai alfarma.Allah ka datar damu kabamu ikon yin ibadunmu cikin natsuwa.Allah ubangiji yasa ibadunmi kar6a66u ne Allah yasa yanda muka ga farkonsa lafiya Ubangiji Allah yasa k'arshensa ma yazo mana da falala masu d'aurewa, Allah ubangiji kasadamu da daren lailatul qadr Allah kasa muna cikin bayinka dazaka y'antar acikin wannan wata mai alfarma ( *AMEEN SUMMAH* *AMEEN* ). Sai idan Allah ya nuna bayan sallah lafiya zamu d'ora daga inda muka tsaya, idan kuma Allah bai sa zamu sake ganawa ba zan iya cewa ayi min afuwa akuma gafarce ni hak'ik'a ranmu ba'a bakin komai yake ba zamu iya tsintan kanmu akowani irin halin idan ya Allah ya.gadama karmu manta da wannan. Ban rik'e kowa azuciyata ba kuma dan Allah nima inaso ayafeni kunsan d'an Adam ajizi saida yafiya da kuma uzuri. Labarinmu kusan zan iya cewa ba'ayi komai aciki ba inajin yanzu ma aka fara sauran kuma sai wanda suka bibiye ni abayan sallah in da rai kenan. Fatan alkahiri ga dukkan masoyana nagode sosai da irin addu'o'i da kuma uzururrukan da kuke min Allah ubangiji ya baku dukkan abinda kuke so, Allah ya amsa muku dukkan addu'o'inku ( *Ameen)* *Salmerhn ku ce*😍 [10/2, 5:59 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Hak'ik'a munga k'arshensa kamar yadda muka ga farkonsa, Allah ubangiji yasa mun dace acikin wannan wata mai alfarma daya gabata. Allah yasa muna daga cikin 'yantattun bayi. ' *'YAN UWA BARKA DA SALLAH* . Ku gafarceni dan Allah nasan dayanku sun k'osa kuji daga gareni amma kuka jini shiru wanda hakan yasa wasunku suka bini private sukayita tambayata nasan hakan duk cikin k'auna ce wasu ko harsun gaji da zuba ido sun hak'ura ....... duk da ban samu lokaci nayi muku abinda kuke so akan lokaci ba amma nasan kun min uzuri sosai Allah yabar k'auna.(Ameen) *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Respect people’s feelings. Even if it does not mean anything to you, it could mean everything to them. 🅿 *29* Ajiyar zuciya Munira ta sauk'e lokacin da Mahmud ya6acewa ganinta, take kuma sai murmushi ya d'an k'wace mata data tuno da mahaifiyarta tasan bata da wata matsala matuk'ar ta furta cewa yamata. 5minutes me kyau Munira bata k'ara ad'akin ba ta fito itama, dan ji tayi zaman ya gundureta tun bayan da Mahmud yabar d'akin hakan yasa ta mik'e tafito itama. Azaton ta zata ganshi a harabar gidan ne, amma ga mamakinta ko kalar rigarshi ma bata gani ba ballanatana shi da kansa jitayi datasan inda yayi da babu abinda zai hanata zuwa kodan ta k'ara ganinsa ma kawai koda bazaiyi mata magana ba . Haka ta taka ahankali taje ga motarta ta tayar tayi gaba zuciyarta fal farin ciki da ganin Mahmud d'in da tayi for the first time arayuwarta domin basu ta6a had'uwa ba sai yau d'in gashi kuma akayi sa'a shid'in ya mata 100%. Shikuwa yana fita 6angarensa ya nufa ransa a matuk'ar 6ace dan tun ganinsa da yarinyar yaji yatsaneta sam bata birge shi ba, balle data k'ura masa idanun nan nata ji yayi kamar ya hauta da duka ma sa'anta d'aya shi ba mai saurin hannu bane inbahaka ba yace da mari zata sha d'azun dan yanda tabashi haushi. Tsaki yaja lokacin daya isa d'akin nasa ji yake kamar ta shiga rayuwarsa ne dan yana cikin hutawansa tasa ya tashi ba shiri ya fito sai ya zauna abakin gadonsa yana wani jijjiga k'afa kai kace wani abin 6acin rai irin sosai d'innan akayi masa. Nan kuwa bahaka bane ko tsanan Muniran dayaji yanayi ya samo asali ne daga tsanar daya yiwa duk wani wanda yake huld'a da Antynsa domin acewarsa duk ba alkhairi bane yahad'a su. Munira bata jima da barin gidan ba Anty ta dawo kuma koda da dawo d'in da bataga Mahmud ba bata wani neme shi ba sai tayi zamanta apalournta ta hakimce kamar wata sarauniya. Tunowa datayi da sak'on da sukayi za'a kawo mata saboda abinda yasa tadawo gidan dawuri ma kenan dan kar azo ba'a sameta ba gashi har sun shiga lokacin yanzu, dayake daman sun saka lokaci koda ta dawo d'in kuma sai bata tadda kowa ba agidan da alamun kuma sak'on ma bai iso ba har yanzu . Wayarta ta lalu6o ta nemi numbern me aiko sakon ta kirata dan taji dalilin jinkirin da aka samu d'in. Bayan sun gaisa ne matar take ce mata ai ta aiko ma already 'yarta ta taho zata kawo mata sak'on tad'an jirata kad'an bari ta sake ta6ota awaya taji inda ta tsaya. "Ok" kawai Antyn tace tare da cire wayar daga kunnanta numbern Mahmud tasake k'ira tabashi umarnin zuwa yasameta a palourn sannan ta ajiye wayar a gefenta. Mahmud kamar bazashi k'iran Antyn ba amma dai ya daure yatashi yaje wayar tasan ma ad'akin yabarta domin bayyi zaton zai jima awurin Antyn ba. Da sallamarsa ya shiga d'akin yayinda Antyn ta amsa ciki-ciki kamar bata so ta amsa sallamar ko kuma kamat dole akayi mata ta amsa inba ka lura bama bazaka gane ta amsa d'in ba. Jijjiga kansa yayi cikin takaici, sai da ya isa gefenta ya zauna kafin yace mata " wani lokaci kina abu kamar bada hausawa kika tashi ba Anty" Ido ta zubashi mishi alamar tambaya take mishi batare data furta tambayar tata da bakinta ba. Shikuwa sai yaci gaba da fad'in " yanzu fi sabilillahi tsabar isa sallamar ma sai kin ga dama kike amsata Anty?" Azafafe Antyn ta amshe maganar tasa da fad'in " toh d'an ayi,ubana malam Muhammadu, kadawo kuma ko zaka fara takur min, nagade ni ce na haifeka kuma tun kan ahaifeka nasan ana sallama aduniya ko kai zaka koyamin yanda akeyi yanzu? Murmushi yayi dan ganin yanda Antyn ta hayyak'o masa kwata kwata ya rasa matsalar matannan sam bata son gaskiya ita. daga magana kuma Anty sai ki hau......... Kar6e maganan tayi da fad'in ehh banaso. Kawai sai ya bata hak'uri yana murmushi dan ya shatantar da zancen, sai yace tunatarwa ce fa kawai nayi Anty kinsan ni bakina baya shiru idan naga abu shiyasa. Kauda kanta tayi cike da jin haushi ganin hakan yasa shima yaja bakinsa yayi shiru. Haka sukayi zaman kurame kusan na mintina goma babu wanda yasake yiwa wani magana illah Anty dake d'an jan tsaki time to time wanda yake da harshen damo domin haushin nata biyu yazama, gana mahmud gana Matar da tasata jiran sak'o kuma tasa6a lokaci. Harji takeyi ai badan tana matuk'an buk'atar abinba da cewa zatayi tafasa su bari kawai. Daga k'arshe sai Mahmud ya mik'a hannunsa yajawo remote ya kunna T.V domin katse zaman shirun da sukeyi dashi da Antyn tasa. Jiyake kamar ya bud'i baki ya tambayeta dalilin k'iran datayi masa amma ganin yanda tasha mur sai ya hak'ura da tambayar, yana matuk'ar so kuma ya tafi yabar d'akin domin akwai inda yake son zuwa sai dai ayanda yasan halin Antyn yasan bori zata masa kar kuma tace ta k'ira shi yak'i ya saurareta saboda ya rainata.......wannan dalilin ne yahanashi barin d'akin kawai ya kunna T.V duk da ransa ba son kallon yake ba amma dan dolensa ya kurawa T.V d'in idanu dukda baya wani fahimta sosai, jira yake yaji ta anbatoshi amma shiru. Sun kai 20 minutes zaune agurin sannan yaji anturo k'ofar parlourn tare da fad'in "ex.......cuse me........." Da tura k'ofar da yin maganan da kuma shigowan duk sun faru ne adaidai lokaci d'aya. Da mamaki Mahmud yasake juyawa ya kallo k'ofar dan ganin waye mai wannan rainin hankalin, kawai sai idanunsa suka sauk'a akan yarinyar daya gani d'azu, shi harya manta ma da ita bacin yanzu da ya sake ganinta. Kallon inda Anty take yayi sai yaga yanda take 6are baki tana dariya wa yarinyar kamar ba ita ce mai uban fushi da tsaki ad'an wasu takaitattun lokutan da suka gabata ba, ga dukkan alamu bak'aramin farin ciki tayi da zuwan yarinyar ba. Mahmud sai ya jijjiga kansa kawai yakuma maida dubansa ga T.V d'in tare da fad'in " ALLAH YAH SHIRYAH". Munira kuwa zuwa tayi ta zauna akusa da Antyn tana murmushi suka gaisa da juna bayan sun gaisa d'in ne Munira tace harfa nakusan isa gida ma sai mummyna ta k'irani tace wai kindawo in sake komowa. " kardai kice min kin zo bana nan"? Cewar Antyn ta fad'a da kulawa " ehh nazo mana wannan be sanar miki ba" Munira ce ta fad'a tare da nuna inda Mahmud yake zaune da idanu tana d'an satan kallonsa. "Humm zai fad'a min ne wannan me mugun halin ?" Antyn tafad'a tare da ta6e bakinta gefe. Shikuwa ko kallonsu ma baiyi ba sai yayi kamar irin bai san ma dashi sukeyi d'innan ba.Amma acikin ransa bak'aramin haushin Kalmar mugun hali da Anty ta ambace shi da shi agaban yarinyar nan yajiba. Yana gani Munira ta ciro sak'on Antyn tabata a leda bak'i, bama wani abu me yawa bane amma yaga duk farin ciki da walwalar Anty ya k'aru alokacin datayi arba da sak'on a hannunta. Haka kawae yaji zuciyarsa taraya masa ba abun kirki bane aka kawo mata bana arziki bane abin. Koda Munira ta mik'e da niyyar komawa inda ta fito sai Anty ta mik'e da fara'arta take tambayarta wae da abun hawa tazo ne? Da " ehh" Muniran ta amsa mata. Sai Antyn tace dama wae ko Mahmud zai sauk'e tane amma tunda da mota tazo shikenan. Yana ganin yanayin canjin fuska atake agurin Munira amma sai ta d'an basar tace " bakomai akwai wataran ai" Amma aranta bak'aramin haushi taji ba na missing wannan damar datayi. Acewarta aida tasan abinda Antyn zata ce kenan da bazata ce da mota tazo ba....,,..,,....(nikuwa nace ai danasani k'eyace Munirah)😜. Anty dakanta tarakata har wurin motar tata suna takunsu kamar wasu k'awaye. Lokacin data dawo daga rakiyar kuma bata sami Mahmud a palourn ba shima tafiyarsa yayi dayake daman hanya yake nema shima. Koda ya koma d'akin nasa misscalleds yatarar awayarsa kusan 5 , ciki kuwa harda na Abbas guda d'aya da sauran abokanshi da kuma wanda suka yi dashi akan zasu had'u yau. Saida yasamu yazauna duk ya bisu da k'ira kafin yayi shirin fita inda zashi d'in. Mayafi Anty ta k'ara d'auka ta nufi gidan k'awarta Anty chideh. Lokacin da Anty tashiga gidan shiru taji ba motsin kowa koda tata knoking sai taga ba'a amsa mata ba sai kawai tabata uzurin ko Anty chidehn na wanka ne shiyasa. Saita turo k'ofar tashigo ciki kanta tsaye, amma saidai me........ wani gani da Anty tayi har sai da takusan kwara amai a inda take d'in take tayi fatan kar Allah yasake nuna mata irin wannan abin har abada. tana k'ok'arin juyawa sai Anty chidehn ta hango ta, yunkurawa tayi da niyyar tashi ta zauna sai hakan yabawa abokiyar masha'artata dama tafahimci meke faruwa dalilin d'ago kan datayi. Sai jiyo muryar Anty chidehn tayi tana fad'in " ah' ah mum Mamud why did u stand there"? Hankalinta akwance tayi maganar kamar ba wacce aka ganta ta ke ayyakata babban sa6o ba. Anty kamar bazata juyoba sai ta daure ahankali ta juyo sukayi 4eyes da Anty chidehn, murmushi tayi mata yayinda Anty tasha mur sosai dan kokad'an bata ta6a kawowa aranta Anty chidehn na irin wannan harkar ba. Tashi Anty chiden tayi ta zauna tana 'ko'karin lullu6e jikinta tace " k'araso mana " Daurewa Antyn tayi ta k'araso chiki yayinda takasa d'auke idanunta daga kan house maid d'in Anty chidehn wacce zuwa yanzu tafahimci ba house maid kad'ai yarinyar ta tsaya ba harda........ Koda ta iso ma dakyar tasamu guri ta zauna jikinta duk yayi sanyi. Anty chidehn ne tace mata Wai ita tafiya tsoro dayawa miye ma abin yin shocked anan sai kace yau ne tasan aka fara yin lesbian? Tambayar ta bawa Anty mamaki sosai har hakan yasa ta d'ago idanu ta kalli Anty chidehn sosai. Sam Anty takasa daina mamakinsu dan ganin datayi su kwata kwata abin bai wani damesu ba kamar ba abin jin kunya tasame su sunayi ba. Dariyah kad'an Anty chidehn tasaki ganin yanda Anty ta kasa daina yi mata kallon tuhuma. Sai ta mik'a hannu ta d'an kamo hannun Antyn atake kuwa Anty ta wafce hannunta da k'arfi domin zuwa yanzu in akwai abinda tafi kyama toh itace babbar aminiyar shawaran tata wato Anty chideh. " come on, feel free mana mum mamud bakomai fah" Tafad'i da dukkan gaskiyarta tana kallon Antyn ita adole in anbarta ba abin damuwa vane hakan, ganin Antyn bata kulata ba sai ta k'ara da fad'in " sucking kawai nake sata tamin when I'm in need but nothing else". "hmm" kawai Antyn tace tare da mik'ewa daga kan kujeran datake tace tatafi gida. Magana taso suyi akan maganin da aka kawo mata d'azu amma wannan 6oyayyen halin Antyn chidehn data gani yau yasata fasa yin maganar ma gaba d'aya kawai ta koma gidanta. Anty chidehn ma batawani damu ba dan tasan damuwar na yanzu ne kawai dakanta ma zata dawo kodan wani dalilin na daban. Anty kuwa koda takoma gida tunanin abun yakasa barinta sam bata ta6a kawo hakan ga k'awartanba duk da yake ahlul kitabi ce ita amma sam bata kawo cewa rashin imanin Antyn yakai har haka ba. Wannan dalilin ne yasa tad'an d'aukewa Anty chidehn k'afa na kusan kwana biyu, yayin da Anty chidehn tabata chance itama akan ta huce tukunna tasan cewa akan hakan bazasu rabu ba sai dai akan wani dalili daban domin bak'aramin sanin sirrin juna sukayi ba, ko wannan d'inma Anty Chidehn ta 6oye mata ne dan ganin kamar ita ba ra'ayinta bane yin hakan shiyasa bata ma bayyana mata ba. Shima Mahmud zuwan Munira da kwana biyu yace shikan zai koma ana nemansa Daddynsa ma baya gari amma ya tattara yakoma yobe state d'in abinsa domin jiyayi sam zaman chan d'in yadaina yimasa dad'i. Da farko Anty taso ta hanashi komawa dan ita afad'anta wai sai ya jira Abbansa yadawo tukunna. Mahmud kuwa yak'I amincewa da batun nata don dolenta ta kyaleshi yatafi badan ranta yasoba. A week d'in daya koma ne Munira tasake dawowa gidan amma wannan karon tafiyar kanta ce ba aike ba ne, koda tazo suka gaisa da Anty kamar yanda suka saba suka d'an zauna suna ta tad'i tsawon mintina bataga Mahmud ba bakuma taji Anty ta ambace shi ba a maganar dasukeyi d'in. Kasa hak'uri tayi sai da ta tambaya tace " Anty ina yaronki"? Dariya Antyn tasaki kad'an sannan tace kardai kice min tafiyar batawa bace ta Mahmud ce"? " murmushi Muniran ma tayi tare da fad'in haba shikuma ? " kedai fad'i gaskiya yarinya" Yanda Antyn ta ke sakewa suyi hira da kuma yanda tayi mata magana ayanzun yasata ko shakkun Antyn ma bataji sosai ba dukda yake son d'anta yakama zuciya amma tasan dole sai dasa hannunta sannan zata sameshi inba haka ba kam tasan samunshi zai d'an mata wahala. Sai batayi k'auran baki ba tafara sosa kanta tana sussun kuyar da kai kamar wata mumina, take sai Antyn ta gama ganota aikuwa sai tayi murmushin da kana ganinta kasan farin ciki taji har zuciyarta. Tashin farko sai takamo hannun muniran sannan ta bata assurance akan cewa karta damu indai Mahmud ne kamar tasameshi tagama tadaina ma damun kanta." Wannan albishir d'in ne yasa Munira ta rungume Antyn da k'arfi tana murna da godiya kamar bazata daina ba, tana sake Antyn kuwa ta tashi ta zari key d'in ta da gudu ko kunya bataji tayi waje wai bari takaiwa mummynta albishir mai dad'i. Da murmushi Anty ma tarakata yayinda tana fita itama Anty ta zari mayafi ta tafi gidan aminiyar ta Anty chideh shab ta manta da batun lesbian d'in tsabar farin cikin datake ciki. Kuyi hak'urin rashin jin update da dawuri da bakuyi ba pls abubuwane suka min yawa. Vote, comment and share pls🤞🏻 *Salmern ku ce* 😍 [10/2, 5:59 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* * *MUKE TUNK'AHO* _Dedicated to_👎🏻 😍 *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* When people walk away from you, let them go. Your destiny is never tied to anyone who leaves you, and it doesn’t mean they are bad people. It just means that their part in your story is over. 🅿 *30* Koda Anty chideh taganta murmushi kawai tayi, daman tasan dolene zata dawo kodan yanda sukayi sabo sosai ma. Haka Anty ta kora mata bayanin abinda yafaru tare da nuna tsantsar farin cikinta afili. Dama tun asali tafison ita taza6awa Mahmud matar aure da kanta sai kuma akayi sa'a fad'uwa tazo mata daidai da zama Munira ta nuna tana ra'ayinsa. Munira y'ar k'awar Anty ce dasuka had'u sanadiyyar maganin mata. Domin duk wani nau'i na magani da suke anfani dashi ita da Anty chideh Mahaifiyar Munira ke musu order daga sokoto kuma sunajin dad'in maganin shiyasa suke shiri sosai. Anty tana gani kamar samun Munirah amatsayin matar d'anta wata dama zata samu dazai sa zumuncinsu da mahaifiyar Muniran ya d'ore sosai. Anty chideh ma sai tayata murna tare da k'arfafa mata gwiwa akan hakan. ***** Mahmud kuwa koda yakoma bai wani dad'e agidan ba yawuche inda aka turashi awani d'an k'auye ne zaiyi bautar k'asan. Da farko Teemah murna takeyi sosai data ga yadawo d'in dan azatonta yanzun agida zai zauna amma sai yace mata ai shi tafiya zaiyi take sai murnar tata ta koma ciki. Dayaga haka sai ya mata alk'awarin zuwa duk weekend yana dubata sai da taji haka kafin tad'an sake fuska. Haka sukayi ta dashi aranar daya sauk'a d'in kuma duk hirar bata wuce ta Abbas ba. Shima sai ya ringa biyeta ganin hakan tafi buk'ata. Harda yayi niyyar k'ira mata Abbas d'in su gaisa amma sai ya fasa daya tuno cewa Abbas d'in yanzu yana bakin aiki ne. Haka suka gama hirarsu suka rabu, yana komawa d'akinsa kamar Abbas d'in yasani sai ga k'iran sa ya shigo. D'auka Mahmud yayi yana murmushi yace " d'an halak" "Allah ko"? Cewar Abbas d'in slowly Mahmud ne yaci gaba da fad'in wallahi nake gaya ma yanzu muka gama hirarka da lil sis harfa da zan k'ira layinka in had'a ku sai kuma nayi tunanin ko kana aiki ne" " hmm ai gara ma baka k'ira ba, bayanzu zanyi magana da ita ba tukunna da sauran lokaci" Mahmud na dariya yace "Kai oga Abbas hukunci ne wannan ko kuma ra'ayine? " duka biyun" Abbas ma yafad'a atakaice. Kafin Mahmud yasakeyin wata magana sai Abbas d'in ya k'ara fad'in yaushe ma kadawo ne bansani Mahmud? " Yau-yau d'in nan na iso amma inajin gobe ko jibi ma zan shiga wani k'auye" " owk Allah ya kaimu" da " Ameen" Mahmud ya fufe maganar sannan sukayi sallama da juna. Washegari da yamma Mahmud yawuche yabar Teemah da kewa. Amma wannan karon bata wani damu sosai ba dan zuwa yanzun tafara sabo da irin hakan. Tafar gane cewa dole ne irin hakan sai ya faru tunda suna da 'yan uwa kuma dole a ziyarci juna. Bazai yiwu ace kowa yazo sai ta yi kewarsu ba saboda ba kowane zai zo yakuma zauna mata agida ba dolene atafi tunda kowa nada muhallinsa koma badan hakan ba kowa nada abinyi. Haka tacigaba da zuwa makarantar ta harsun kusa kammala S S 2 d'in sai Daddynta yace waec zata rubuta kawai bazatayi SS3 ba. Itama dataji datayi farin ciki sosai dan dama tagaji da zaryar zuwa makarantar nan. Shikuwa Daddyn ganin girman data ke k'arawa ne yasashi yanke wannan hukuncin, dan Teemahn akullum kamar hurata akeyi haka ta k'ara k'iba dukta cicciko. Yayinda Mummy sam hakan bai mata ba, inda asonta taso Teemahn ta kammala gaba d'aya kafin sai ta rubuta waec d'in, amma koda ta gwada sanar da daddyn Teemah k'i yayi ya amince dan acewarsa bata da hujhan da zai sa dole sai anyi hakan, dolenta ta hak'ura ta zuba musu idanu. Ana cikin hakan ne wani matashi yabi ya uzzura ma rayuwarta yahanata sakat. Akullum inta fita zuwa islamiyah sai ta ganshi yasha gabanta da niyyar yimata magana. Itakuwa kokad'an bata so daya takurata ma sai ta daina zuwa da k'afan datake zuwa dayake dama itace tace zata na zuwa dakanta bama sai ankaita ba, amma dataga matsin yayin yawa sai ta ce Habibun yaci gaba dakaita kawai. Amma me.....gudun gara take ganin kawai tayi domin tana fitowa zata ganshi tsaye ajikin motarsa yana rarraba idanun ta inda zai ganta. Rashin sa'an datasake yi kuma shine wani lokaci Habibu baya isowa da wuri har sai an d'an fara watsewa yayinda wasu lokuta kuma har jiranta yakeyi tatashi kafin su wuce gidan. Aduk ranar da Habibun bai iso dawuri ba haushi sosai Teemah keji kamar tayi fiffike yayinda ga matashin kuma abin farin ciki ne dan yana samun chance d'in zuwa kusa da ita harma yayi mata magana, dukda bawani kulashi takeyi ba amma dai yana jin dad'in hakan sosai. Ranar kuwa da bai samu daman mata magana ba yakan bisu abaya har sai sun shiga kafin yake wuchewa shima. Sai dai bai ta6a gangancin shiga musu gida ba yakanzo ya tsaya na tsawon wasu lokuta a k'ofar gidan daga d'an nesa batare daya nemi kowa ba shidai akullum burinsa yaganta koda sau d'aya ne. Yau ma takama ranar Sunday, koda Habibun ya sauk'eta gida yakoma suka fita da mummy kuma basu dawo dawuri ba har aka tashi a islamiyar dan siyayyar mummy baya k'arewa matuk'ar tashiga kasuwa shiyasa suka 6ata lokaci sosai. Tsaye take ak'ofar makarantar tana ganin duk kowa na tafiya amma ita sam ba Habibu babu alamarsa, zuciyarta nagaya mata cewa tabi ayarin masu wucewan itama suwuce tare sai dai tana tsoron kar kuma waccen mayen yabiyo su abaya abinda ta tsana kenan. Kafin ta ankara sai taga har ankusa watsewa gaba d'aya domin d'ai d'aiku ne kawai suka rage dan dolenta tafara tafiyah da niyyar cimmah way'anda suke gabanta su had'a hanya amma taku biyar me kyau batayi ba sai kawai taga mutun tsaye agabanta yana murmushi, kallonsa ta tsaya yi da mamaki hankalinta kuma yana ga wad'anda takeso su tafi taren daya fahimci haka sai ya d'an k'ara matsowa kusa da ita hakan da yayi sai ya hanata ganinsu ma gaba d'aya sanasiyyar katangan ta yayi musu. " kiyi hak'uri ya kad'ai nakaiki gida" Yafad'a yana kallon fuskarta. Muryarta na rawa tace" awani dalili". " masoyi" yabata amsa atakaice. Da mqmaki ta d'ago kanta ta kalleshi. "Koba haka bane? Yasake tambayar ta. Bata bashi amsa ba illah hanya da fara k'ok'arin nema dan ta myi wucewarta. Amma mutumin ya hanata wucewa domin duk wani motsin da zatayi sai shima ya motsa ya kuma tare gabanta. Dan dole tasake tsayawa ta wurga masa harara tare da fad'in " wai me kake buk'ata ne"? " ki saurareni"! Kauda kai tayi gefe cikin fushi ranta inyayi dubu toh yau jitake ya6aci saboda mutumin nan sam ta tsami hakan dayayi mata ko tace yake kanyi mata. Shikuwa ganin hakan da k'warin gwiwarsa yaci gaba da fad'in............. Kamar yanda na ta6a fad'a miki sunana Imran dan nasan kin manta tunda ba damuwa akayi dani ba. Kuma ni ba a unguwar nan nake da zama ba, nazo ne duba wani fili sai Allah yasa naganki kuma kika kwanta min araina duba da yanayin nutsuwarki. Dafatan zan sami kar6uwa kodan mu k'ara fahimtar juna da kyau dan ni ji nake nasamu matar aure nagama......... Murmushin takaici Teemah tayi wanda ya tsaya mata a kan le6e kawai....aranta tace su matar aure manya! Horn sukaji daga gefensu take dukkansu suka kallo gurin, Teemah naganin motar gidansu ne tatafi da sauri tana hamdala wa mahallici. Bata kula da mummy acikin motar ba sai da ta shiga ta ja marfin motar ta rufe kafin ta lura da mummyn. Innalillahi wa innah ilaihir raji'un tafad'a azuciyarta dan yau kam tasan me rabata da mummy sai Allah. Baki ta bud'e da niyyar yin magana sai mummy ta dakatar da ita da fad'in " waye shi "? " nima fah ban san shi ba mummy" K'ura mata idanu mummyn tayi tana karantar yanayinta afili zaka fahimci rashin sabo da hakan da batayi ba ga dukkan alamu tilasta ta tsayuwan akayi kodan ganin yanda ta taho da sauri daga jin horn d'in mota duk da bata ma san wake cikin motar ba balle tace danta ganta ne, amma hakan bazaisa takasa yi mata fad'a ba ko dan saboda ta k'ara tsare mutuncinta a matsayinta na 'ya mace. Wannan dalilin ne yasa mummyn ta d'ago hannunta tare da ware yatsa d'aya ta nuna Teemahn dashi kana tafara magana. " kinsan Allah Teemah ki shiga hankalinki banason rashin hankali da rashin wayo, baki san mutun ba shine harda tsaywa dashi a k'ofar makaranta? Owk nagane, saboda ki nuna ke kin isa ko me? Hawaye Teemahn tafara tare da jijjiga kanta Allah mummy bansan shi ba yau ne fah yafara.......... Hannu mummyn ta d'aga tare da dakatar da ita daga cigaba da maganan, sai kawai ta sunkuyar da kanta k'asa tana zubda hawaye, bata so kokad'an mummy tayi fushi da ita akan hakan taso ta yi mata bayanin komai amma mummy takasa tsayawa ma ta saurareta ballantana taji abinda ke faruwa. Takaicin ta d'aya shine akan wanda bata ma ta6ajin zata so shiba mummyn ta na shirin yi mata fushi. Motar shiru baka jin k'arar komai sai na shashekan kukan Teemah har suka iso gida. Koda suka iso gidanma mummy ko kulata batayi ba suka fiffita a motan suka barta, kayayyakin data siyo d'inma Habibu ne da ita suka kwashi abinsu kota kan Teemahn batabi ba. Sai da Habibu yafito ne yazo gurin motar ya d'an bata baki akan tayi hak'uri ta shiga ta bata hak'uri zata sauk'o ai. Da jajayen idanu ta kalleshi tace Mummy tana fushi sosai dani ko ? Yace a'a zata hak'ura ki shiga ki bata hak'uri. Da k'yar ta daure ta fito a motar ta shiga ciki lokacin ma har maghrib ya k'arato, ganin haka kawai sai ta wuce bayi ta d'auro alwala ta zo ta tada sallah. Ba ita ta tashi agurin ba har sai da tayi sallahr isha'i. Addu'a sosai tayi kafin ta tashi ta nad'e abin sallahr. Ko hijabin datayi sallan dashi bata cire ba ta nufi d'akin mummyn ahaka. Da sallama ta shiga d'akin sai ta sami mummyn na shirin kwanciya. Zama tayi ak'asa kanta ak'asa tajira har mummyn ta gama shirin baccin kafin taje gareta da muryar kuka take bata hak'uri. Mumnyn yi tayi kamar batasan da ita a d'akin ba domin kwanciyarta tayi ta juya mata baya, sai da taga kukan da Teemahn keyi kamar zaiyi yawa kar kuma yasata ciwon kai. Koda tayi tunanin nan d'inma sai da k'ara minti guda akai kafin ta tashi ta zauna ta fuskanci Teemahn tare da fad'in " inajinki yah akayi? Vote, comment and share pls🤞🏻 *Salmern ku ce* 😍 [10/2, 5:59 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* People say, Find good people & leave bad ones but it should be, Find the good in people & ignore the bad in them. Remember No One Is Perfect in This World. 🅿 *31* Teemah kamar bata ji abinda mummyn ke fad'i ba taci gaba da rera kakanta ahankali kanta akan cinyoyinta. Da mummy taga kamar Teemahn bazata yi magana ba sai ta sakeyin wata maganar da d'an d'agun murya tace " idan zaki bud'i baki kimin bayani toh inkuma bahaka ba ki tashi kiyi tafiyarki" . Daga haka mummy bata k'ara yin wata maganar ba illah ido data zubawa 'yar tata tana kallonta. Ahankali Teemahn ta d'ago kanta suka had'a idanu da mummy, take tausayinta yah kama mummy musamman yanda taga idanun Teemahn sun k'ara girma da jaaa, alamun rashin nutsuwa kaf sun bayyana agareta, sai taji sam bata kyautawa gudan jinin nata ba, bahaka yakamata tayi mata ba tunda bata ta6a samunta da irin laifin ba yakamata tayi mata uzuri, ita kanta sai ta rasa dalilin da yasa ta d'aukewa Teemahn wuta ma, amma yaxatayi, mutunci da darajar y'arta take son karewa bakomai ba. Kauda kai tayi gefe daga kallon Teemahn, yayinda Teemahn ma tak'urawa hannayenta idanu tarasa me zata ce da mummyn, tanaso tayi mata bayani amma sam tarasa abinda zata fad'a. Da 'kyar ta daure ranta tafara magana ahankali cikin natsuwa. " Mum......my kiyi hak'uri dan Allah ki yafemin , kar kiyi fushi dani, ni bansan wayeshi ba, last week na fara ganinsa nima, kuma duk ranar da.......dana fita saina ganshi, shine dakansa yafara zuwa k'ofar makarantarmu amma wallahi mummy ki yadda dani banta6a sauraransa ba yau d'inma bada son raina bane bayadda zanyi ne shiyasa natsaya.............daganan mummy dakatar da ita daga magana inda tace " saurara yah isa". Tsawon mintina biyu kafin mummyn ta mik'a hannunta ta kamo na Teemahn yayinda hakan ya matuk'ar haskaka zuciyar Teemah tare da sanyayawa tasan ko ba komai hakan kad'ai da mummy tayi yana nuni mata ne dacewar mummyn nata ta d'an sauk'o daga fushin data keyi da ita........ Mummy ne taci gaba da fad'in " kina jina ko? Da wuri Teemah ta d'aga kanta alamar " ehhh tanajinta" wa mummyn. " Waye mahaifiyarki? Mummyn ta tambayeta tana kallon fuskarta. " kece". Teemah ta bada amsa a sanyaye " waye ya kamata yasan damuwarki da kuma walwalarki? " kece mummy" " kina ganin zan iya ganin kin hau hanyar da bata dace ba in kuma barki akanta kici gaba dabinta? Kai Teemah ta girgiza tare da fad'in " a 'a ". Toh kin gani ko, ki fahimceni, ba ina nufin k'untata miki ko kuma takuraki bane sam, bani da burin da ya wuce inga kina farin ciki Teemah sannan duk duniya babu wanda zaiso ganin walwalarki sama dani.........amma banda ta wannan hanyar, har yanzu ke yarinya ce, da sauranki, banason tun yanzu ki fara wannan kule-kulen samarin saboda bashi da amfani. kuma ma baki san wani abu ba ayanda kike d'innan duk wani wanda yake ganin sonki yake da gaskiya toh iyayenki zai fara nema ba ya dinga bibiyarki yana tsaidaki a ko ina ba, me sonki bazai ta6a yi miki haka ba ki kiyaye kinji. Kai Teemah ta sake d'agawa alamar toh Sai mummyn tacigaba da fad'in " daga yau karki k'ara kula kowa ki bari ko secondary school d'inma ki k'arasa ta tukunna kinji kafin nan ki,ga awancen lokacin ko auren kikace kina so babu Me hanaki." 'Kasa Teemahn tayi da kanta dan k'arshen maganar mummyn kunya ya bata sosai. Daganan mummyn tasake mata hannu tare da fad'in tashi kije ki kwanta toh. Bata mik'e ba kamar yadda mummyn ta umarceta sai ta jefawa mummyn tambaya kanta ak'asan batare da ta kalli mummyn ba tace " shikenan kin huche mummy" tana murmushi tayi maganar. Mummyn ma murmushin tayi sannan tace mata " zan huce dai idan naga kin kiyaye maganata"! " da sauri ta tashi tana murna har hak'oranta na bayyana afili tace " insha Allahu zan kiyaye mummy" "Allah yasa " kawai mummyn ta'kara fad'i tare da yun'kurin mik'ewa da niyyar shiga bayi. Teemahn ma hanyan fita tayi tana jin ranta fari k'al " Mummy sai da safe " tace wa mummyn tana tafiya ahankali. Mummyn ma na gab da shiga bayin ta amsata da " Allah ya bamu Alkhairi". Koda mummy tagama uzurinta tafitoh ma zama tasakeyi abakin gado tana tunanin hali irin na zamanin yanzu, daga k'arshe addu'a tayiwa 'yarta akan Allah ya kareta ya rabata da sharrin masu sharri yarabata da soyayyar wahala da duk wani al'ummar musulmi. Dan wannan soyayyar wahalan ita tafi lalata al'ummah yanzu, sai kaga matashi ya 6ata lokacinsa da dukiyarsa akan yarinya zai nuna mata so tamkar ya had'iyeta in akayi rashin sa'a itama yarinyar sai ta fara masa mahaukacin so inda wannan son da ta fara yi masan in ba sa'a ba sai ya zame mata abin dana sani agaba. Domin dashi samarin yaudara suke anfani su lalata tarbiyar yara at last kuma su guje su batare da sun aure sun ba. Shiyasa ita tun da idanta yaga 'yarta tsaye da wannan saurayin hankalinta yagagara kwanciyah bawai dan Teemahn bata kai ta tsaya da saurayi, bane a'a kawai dai in so samu ne yazo gida su gana da mahaifinta kafin nan, inda hakan yayi bazata ta6a jin yayi ba dai dai ba ko kuma tayi fargaban ke6ewarsa da y'arta. ( ALLAH YA RABA AL'UMMAR MUSULMAI MUSAMMAN 'YA'YA MATA DA MUGAYEN DAKE CIKIN MAZA,SUMA MASUYIN HAKAN ALLAH UBANGIJI YA SHIRYE SU.). Mummy bata samu tayi bacci da wuri ba aranar dan sai yanzu ta k'ara tunowa da halinda rayuwa take ciki a yanzu, sai ya zamana tana kwance ne amma baccin gaba d'aya ya k'aurace wa idanunta, duk juyin dazata yi kuwa sai ta jefi 'yarta da addu'an kariyar ubangiji haka har kusan k'arfe biyu kafin bacci 6arawo ya saceta. Yayinda Teemah ke can ad'akinta tana ta kwasan bacci cikin kwanciyar hankali, tun lokacin data ga murmushi a fuskar mummynta tajita wasai shiyasa koda ta dawo d'akinta cikin farin ciki tayi addu'a ta kwanta dan bata tare da wata matsala a yanzun tunda mummy ta huce. ***** Tun daga wannan lokacin Teemah ta dinga kiyaye had'uwar su da wancen gayen, bama shiba duk wani wanda ya nemi ya tsaya da ita ko wani abu daban kyakykyawan kallo ma baya samu ballantana kuma lokacinta gaba d'aya. Haka saurayi Imran ya gama iyah biye-biyen da zai yi mata dayaga bata da niyyan sauraransa sai ya hak'ura ya daina kulata dama shima bawai son nata yakamashi sosai bane Imran irin samarin nan ne wad'anda a duk inda auka ga yarinya sai sun kulata musamman ma idan ta birgesu , sai Allah ya taimaki Teemah tak'i sauraransa hakan ne kuwa ya ku6utar a ita daga fad'awa tarkonsa. Tsabar yanda take kiyaye wa ma saboda kar ta ringa had'uwa da kowa ciki kuwa harda imran yanzu kwata-kwata ta daina zuwa ko'ina, duk dayake dama itan ba gwanar yawo bace, daga makaranta sai islamiyah, toh su d'inma yanzu bata fiyah zuwa ba, kasancewar ta gama karatun ta yanzu muraja'ah takeyi da kuma gya-gygyara haddanta, boko kuma tunda aka mata registern weac sai ta daina 6ata lokacin ta wajen zuwa, tana d'an zuwa amma ba kullum ba sai ranar da taga dama tukunna take zuwa, kuma ko zata je d'inma amota ake kaita akuma je adawo da ita gida bata ta6a yadda ta matsa ko'ina batare data hango motar gidansu ba tana fitowa kuwa babu 6ata lokaci sai cikin mota. Wannan dalilin ne yasa ganinta yayiwa imran wahalar gaske shiyasa dan dolensa badan yaso ba ya hak'ura da ita. Mahmud kuwa kusan duk sati sai yazo musu week end inkuwa be samu yazo asati d'aya ba toh satin gaba sai yazo ko kuma alokacin da ya samu dama koda ba week end bane sai yazo, kamar de yadda wannan weekend d'inma ta wuce basu ganshi ba haka nagaba ma. shiru gashi kuma gurin babu network me k'arfi ko sun nemeshi bazasu ta6a samunsa ba. Sai da yayi kusan 3weeks kafin yasamu dakyar yazo shi gida sai kawai suka ganshi tsulum kamar anjeho shi. Mummy da Teemah na zaune Teemah na gyarawa mummy farce kawai sai suka ji sallamarsa. Aikuwa dukkansu bak'aramin farin ciki sukayi da zuwan nashi ba ji sukale kamar sun shekara ne basu ganshiba. Koda mummy tayi masa complaint akan rashin jin nasa dasu ba d'in sai ya bata hak'uri tare dayi mata bayanin rashin network d'in da suk ke fama dashi amma yace yakusan barin wajen ma zai dawo gida inyagama abinda yake yyi acan d'in yanzu zai dawo gida inyaso duk sanda aka buk'ace shi sai ya je shi. " sosai sukaji dad'in hakan dayace d'in musamman ma mummy saboda dama tafison ya zauna agida ko dan saboda insecurityn da ake d'an fama dashi alokacin amm shi Mahmud d'in yak'i yadda da hakan yace shidai yana son zuwa k'auyen. Haka suka cika masa gabansa da kayan ciyeh-ciyeh dan acewar mummyn wai rama yayi sosai kamar bashi ba dan ya bud'e ciki yaci abinci ko zai warware tace idan ma yak'i dawowa wannan karon kam dakamta zata je k'auyen ta dawo dashi gida ta k'araseh da fad'in " hab irin wannan wahala haka. Dariyah sukayi mata shida Teemah mummy kuwa sai ta tashi tana mita ta barsu awurin. Teemah dakanta ta rink'a bashi labarin, imran lokacin da suka fita yawo dashi, shikuwa yayi ta kwasan dariyah yana fad'in village girl toh haka akeyineh ke,? "Gaye ya dage yaga 'yan mata sai kuma kika kwafsa bai san dama da 'yar k'auye ya had'u ba." Turo baki Teemah tayi gaba tace " nice y'ar k'auyen ko yayah" . Shiru yayi yana gumtse dariya batare daya kalle ta ba. Kasa hak'uri tayi sai da ta k'ara cewa " abinda ma naa fishi kyau" Dariya ne sosai yakama Mahmud Teemah kuwa sai ta kauda kanta gefe kamar zatayi kuka ta tsani wannan dariyar har ranta sai da yagama dariyar sannan yace " sorry lil sis wasa nake miki ai shine babban d'an k'auyen ma ". Ko kulashi k'inyi tak'ara yi har suka koma gida sai da mummy tasa baki kafin suka shirya. _Comment, vote and_ _share pls_ 🤞🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 5:59 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ⚠ *NOT EDITED* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Just because you have experienced pain doesn’t mean you won’t feel happiness again. 🅿 *32* Shak'uwa ce sosai tsakanin Mahmud da Teemah fiyeh da zaton me karatu, sai dai compared to shak'uwar dake tsakaninsu ayanzu toh wancen nabayan ba komai bane. Tun da Mahmud ya tattaro yadawo gida shikenan Teemah tasamu d'an uwa, aboki kuma yayah, batada da matsala ta kowani fanni, sosai Mahmud yayi k'ok'ari wajen ganin ya gina zumunchi mai k'arfi a tsakaninsu and he win. Yakan 6ata lokacinsa sosai wajen ganin yah koya mata karatu musamman dayaji labarin zata zana weac ashekaran, sosai shima yaji dad'in wannan labarin dan Teemahn kam masha Allah akwaita da saurin girma. Haka idan suka fita yawo sukan 6ata lokaci sosai suna zaga gari, dan Mahmud ma ba de son yawo ba sai akayi sa'a kuma itama Teemahn gwanar son yawo ce shiyasa bakinsu yake yawan zama d'aya dashi. Ko sabon saurayi Teemah tayi ko kuma irin wani ya nemi yin magana da ita d'innan toh tare suke raina musu hankali da Mahmud d'in. Wani lokaci idan ya tsare ya 6atarai yana masifah har zakayi rantsuwa akan ehh lallai akan gaskiyarsa yake masifahn nan kuwa duk yanayin hakan ne saboda Teemah tu,da ya lura batason hakan shima sai ya biyeta. Axuk lokacin saza'a mata magana toh nuna sukeyi kamar wai ai they are already married, ma'ana matarsa ce, wani idan yaji hakan sai yabshi hak'uri yawuche abinsa, wani ko k'in yadda yakeyi da hakan sai ya k'aryatasu tare da k'ara dagewa akan shifah lallai sonta yakeyi kuma da aure. Idan kaga Mahmud na masifah wa saurayi akan Teemah toh baya rasa nasaba da k'in yadda da saurayin yayi akan cewa Teemahn matarsa ce. Haka zai dage yayi ta bud'e ido yana masifah Teemah kuwa sometimes dariyah ma yake bata amma bazatayi dariyar ba dan kar agano su. Sai idan su, ke6e ko kuma su shiga mota sannan sai tafara dariyah tana kwatanta masa yadda yayi alokacin dayake masifan, shima tayata dariyar yakeyi suyi tayi dayake suda kansu sunsan abin dariyar sukeyi. Akwai ranar da wani yabiyo bayansu har k'ofar shiga gida, da Mahmud yaga kamar binsu akeyi sai yayi parking shima atare suka fito da me binsu d'in sai kowa ya tunkari d'an uwansa da mabanbantan manufah. Mahmud shi damuwarsa yaji dalilin binsun dayakeyi yayin da d'ayan kuma yake burin son magantuwa da yarinyar daya gani d'azu tashiga motar. Fitowan da Teemah tayi ne ya d'auke hankalin mutumin daga kallon Mahmud ya mayar dashi kan Teemahn, ya wani k'ura mata idanu kamar zai cinyeta d'anyah. Lura da inda mutumin ya kai duba da hankalinsan da Mahmud yayi ne yasashi fahimtar manufan binsun dayatayi har zuwa gida. Sun had'u da mutumin amma sam hankalinsa yatafi wani wuri be ma san sun had'un ba may be shi de ya tsaya da tafiyar daya keyi. Ahankali Mahmud yajuya ya kalli inda mutumin yasa hankalinsa sai suka yi four eyes da ita. Da saurinta ta k'araso inda uake ta rink'e masa hannu da dukka hannayenta biyu yayinda take k'ok'arin 6oye fuskarta da rigar dake jikinsa. Dukkansu sai suka tsaya kallonta ganin tana k'ok'arin 6oye fuska ne yasa Mahmud d'ago idanu ya kalli mutumin dai dai shima ya kallo Mahmud d'in suna had'a ido dai Mahmud ya d'age masa gira alamar tambaya. Sannan yah furta " hakalinka ya kwanta ko? " Kana ganin yanda ka tsoratar min da 'yar uwa, meke faruwa ne? In ina mutumin yafara yanaso yayi magana amma yanda Mahmud d'i. Yayi masa magana sai yasa shi fargaban abinda yakeso ya furta d'in. " Dakatar dashi Mahmud yayi tare da d'agamasa hannu " go straight to the point mr. man don't waste my time here". Haka de mutumin ya daure ua furta abinda ke cikin ransa nan kuwa Mahmud yafara masa bori kamar zai ari baki. " can't you see that she is married?, how dare you said you love her? Karkata kai yayi tare da rik'e kunkuminsa sanna, yace " owhh wato kune irin mutanen nan masu lalata tarbiyar al'ummah ko? Mutumin najin hakan ya rik'e baki tare da saurin bawa Mahmud hak'uri, yace shi bahaka bane manufarsa, kuma be masan da aurenta da bazai ma fara binsu ba balle har yayi musu magana, hak'uri sosai yayita bawa Mahmud kafin yajuya yakoma cikin motarsa yaja yayi gaba. Har yaja moitar tasa Mahmud natsaye ayanda yake yana binsa da idanu sai da ya daina hango motar kafin ya juya kad'an ya kalli gefensa inda Teemah ta k'ank'ameshi yace "ke sakeni" Ahankali tad'ago kanta dataga mutumin bayanan kafin ta sakeshi gaba d'aya. Cemata yayi " miye hakan wai kikeyi naga harda su 6uya? " wallaho yayah tsoro yabani ni yafiyeh kallo dayawa" " Daga kallon kuma fah? tace " shikenan" "Hmm,Toh ke nakasa ganewa haka zaki tazama ba saurayi ne? naji fah daddy na cewa aurar dake zaiyi daga kin k'are secondary school ke kuma sai sani kike ina ta kore in- laws d'in nawa." Dariya kad'an tayi tace" kai yayah harda wani in-laws? " ehh mana,musammam ma wannan duk yafi birgeni wallahi da alama zai so ki da gaskiyah gashi ba laifi harya d'an fiki ma kyau ya k'arasa da zolaya. " haba yayah ahakan nidai wallahi be fini kyau ba..... , " toh naji yah isa wasa nake miki ai daman ki, fishi kyau waneshi ya kamo lil d'ina kyau." " amma ai de shid'in yah miki ko" Dawuri ta jijjiga kanta tare da 6ata rai tana tura baki. " mekenan" ya tambayeta " nidai banaso..... "Sauran fah toh ? Yasake tambayarta amsa shi tayi da fad'in " dukkansu"! Ido yah zaro waje yace " babu wanda ya miki? kai ta d'aga alamar "ehh" " ta6 lalle kam". Haka kawai yace tare da jajjiga kansa alamar mamaki sannan yasake kallonta "ki shiga gida barin shigo da motar sai mu k'arasa maganar agida ko? " uhm tace tare da juyawa ta tura k'aramar 'kafar dake jikin gate d'in gidan tashiga ciki. Shima sai yaje ga motar ya tayar tare da danna horn take kua axka bud'e gate d'in yatura motar yashiga yanayin parking yafito yasameta a inda take tsayuwan jiransa. " muje " Yace mata atak'aice tare da nufar k'ofar dazata sada su da babban parlourn gidan. Baifi taku uku yayi ba yaji yo muryarta ta k'ira sunashi a hankali. Tsayawa yayi tare da waiwayowa ya kallota " ya akayi" ya jefa mata tambayar agajarce " fishi kayi danine yayah? yanajin abinda ta fad'a ya juya yafara tafiyarsa sannan yace " ba dole nayi fushi ba, lil sis k'arfi da yaji kin maida ni babban mak'aryaci a gidannan." Daga yadda yayi magana ta fahimci babu wani fushin dayakeyi da ita kawai dai ......... Garin saurin ta taroshi sai k'afanta d'aya yad'an karkace aciki. High hill d'in dake k'afar tata bata ji ciwo, komai ba amma sai tace wash tare da rage tsawo ta kama k'afar kaman dagaske ciwon taji. Aikuwa dawuri Mahmud yadawo yana tambayarta " menene ya faru? " yar k'auye kawai yanzu dan wannan takalmin ne shine harda fad'uwa? Abinda yace kenan bayan ya fahimci dalilin wash da kuma durkuson nata . Hannunta yakama ya mik'ar da it tsaye,sannan yace cire takalman ki rik'e ahannunki tunda mun iso gida, bazanma k'ara siya miki irinsu ba tunda kin kasa iyah koyan tafiya dasu har yanzu." Gaba tayi tafara tafiya tabarshi agun sannan tace " ni ba abinda yasameni dama so nake ka jirani". " kut lalle Yarinyar nan" yace tare da mik'a hannu kamar zai kamota ita kuwa sai ta kwasa da gudu tayi ciki shima sai ya bi ta abaya. Mummy na zane kawai taga mutun tazo kanta da gudu ta ruk'unk'umeta kafin tana k'ok'ari, yin magana kawai sai ga Mahmud ma yashigo kamar yanda Teemahn ta shigo. Salati mummy tasake tare da fad'in " wai meke damunku ne wai? Haka ne sallamar ? " kyaleta mummy Allah yarinyar nan tarena ni sosai." tana daga jikin mummyn tafara fad'in " bawani mummy niban raina shiba kawai dan na........ Kafin taka'arasa mummy ta buge mata baki " kubb" yimiin shiru ni". Sosai taji zafin hakan aikuwa take idanta yai jah kamar zatayi kuka Mahmud kwa mezeyi inba dariyah ba, haka yatashi yafice ad'akin da sauri yana kwasar dariyah. Teemah kuwa gefe tayi tayi zugum tarsa meke mata dad'i. Sai da ta daina jin zafin kafin ta tashi ta wuche d'akinta. Tana shiga tamik'e agadonta tana shan iska bayan ta rarrage kayan jikinta. Waya taji na vibrating ad'akin nata gaba d'aya sai tarasa takamamman inda k'arar ke fitowa har k'iran ya yanke bata samu inda wayar take, vibration d'in ne yasake tashi akaro na biyu kuma sai asannan ta tuna wayar Mahmud dake cikin jakar ta wanda tafita dashi d'azun. Ai da gudu ta tashi taje ga jakar taciro wayar "AUNTY" tagani arubuce akan fuskar wayar, k'iran na gab da yankewa tayi recieving " hello" tace ahankali. Dan tunda ta fahimci me k'iran sai taji gabanta ya fad'i shiyasa ma ta amsa asanyayeh. " shiru taji ta d'ayan 6angaren hakan yasa ta k'ara furta "hello.....d'in akaro biyu tana shirin yin na uku ne taji an amsa mata da " keh dan ubanki kyaleni ni!" " ina mai wayar" " asanyayeh ta amsa mata da " kiyi hak'uri Anty bari in kai masa." " 'duut" Taji wayar ya yanke sai ta dafe k'irji da hannunta d'aya saboda yanda taji bugun zuciyarta na k'aruwa komawa tayi ta kwanta rigingine tana ayyah na hali irin na wannan matar data rasa dalilin tsanar datake yimusu wanda tun ba yau ba ta fahimci hakan. Ahankali tatashi dan ta kaiwa Mahmud wayar sa, cikin sa'a kuwa sai suka had'u da Mahmud d'in yazo ansan wayartasa. Mik'a masa tayi kawai tajuya ciki shikuwa sam be damu ba saboda azatonsa tun fushin d'azu nake bata sauk'o ba. Haka yajuya yayi tafiyarsa zuwa d'akinsa,yana shiga d'akin kuwa yana shirin ajiye wayar sai yaga Anty ta k'irasa. D'auka yayi tare da zama akan side drawer yayi receiving called d'in. " Assalamu Alai..... .... Kafin yak'arasa sallamar sai yaji tace " wacce 'yar iska kabawa wayarka Mahmud? " kai Anty 'yar iska kuma?, " Teemah ce fah,yarinyar Anty....?? " shine ne me? Shiru yayi be sake yin wata magana ba sai itace tacigaba da fad'in " yaushe zaka dawo gida? " ni kam babu rana gaskiya " yafad'i akufule. Itama dataji haushi sai ta fara yi masa masifah akan babu ranar dayace. Wai saboda me ze ce haka, tsabar ya raina ta har tana tambayarsa ranar dawowarsa ko kunya wai baya ji zaice mata barana dan yaje ya tare agurin waccan munafukar, umarni tabashi akan cewa nan da 1week take buk'atan ganinsa a lagos koma ya zeyi ya neni hanya yazo tana buk'atan ganinsa. Cire wayar yayi daga kunnansa kafin yakashe ta gaba d'aya ma ak'asan mak'oshi yake fad'in "baza'a zo bad'in". Mahmud be sanar da kowa yanda sukayi da mahaifiyarsa ba daga mummy har daddy babu wanda yake da labarin domin yadda ya yanke aransan cewa bazashi ba toh sam bai da niytar zuwan ne shiyasa yak'i sanar da kowa dan yasan mummy najin labarin zatayi convincing d'insa akan lalle sai yaje. Hatta Teemah ma bata sani ba. Amma yadda Antyn ke yawan tuntu6arsa awaya akan tafiyar kad'ai yasa mummy fahimtar wani abu game da shi. Dan ayanda ta lura duk sanda zai d'aga wayar indai na mahaifiyarsace tana lura da canjin fuska atattare da shi matuk'ar akusa da ita yake. Kuma ko minti nawa zai kai da wayar akunnansa bazaka ta6a jin yayi magana ba shiru kawai yakeyi yana sauraronta. Hkana kad'ai dayakeyi babbar alama ce dake nuni da wata matsalar azahiri. A kwana na biyar ne ta zaunara dashi ta tambayeshi abinda ke faruwa domin walwalarsa gaba d'aya tayi low. Aranar kama be 6oye mata ba haka ya zayyano mata duk yadda sukayi da Antyn tasa a tunaninsa ko Mummyn zata bashi shawaran da zata taimake sa. Ai kuwa mummyn fad'a tayi masa sosai itama har kamar zata yi kuka, take fad'in me yasa zai yi haka, ai koma me Antyn ta buk'aci ya mata kamata yayi ya mata batare da musu ba kodan darajar ta na uwa agare shi. Tace akan me zai 6oye yak'i yin bayani bayan yasan koma miye zai faru ko yafaru toh kanta abin zai koma tunda ahalin yanzun tare yake da ita. Koma badan hakan ba tace " mahmud mahaifiyar ka ce fah ai tafi k'arfin hakan, tafi k'arfin tace kayi abu kuma kak'i yinsa matuk'ar bai bar kan hanya ba toh dole ne kayishi koda kuwa ranka bayaso." Hak'uri sosai yabawa mummy tare da fad'in shi abinda Antyn keyi ne yafara isansa shi yasa yak'i zuwa amma insha Allahu zai shirya yaje shi d'in kamar yadda ta buk'ata." " Murmushi ne ya kwace wa mummyn take kuwa tasanya masa albarka tare da yi masa addu'a da fata mai kyau daga indallahi kana ta sallameshi dan yaje yafara shirin tafiya acewar ta gobe take so yawuche. Haka Mahmud wannan karon ma ya shirya yatafi bada son ransa ba wani lokaci ji yake kamar yakai k'aranta wurin Abbansa dan yadda take takurawa rayuwarsa amma idan ya tuna cewa aikin banza zaiyi sai kawai yafasa dan ko da yafad'a d'in toh kamar yakai kukansa ne inda bazai samu biyan buk'ata ba koda kuwa kad'an, .ai san dalili ba amma shi wani lokaci ji yake kamar yana jin haushin iyayen nasa musamman Abbansa da sam baya fighting masa komai sai dai ya zuba masa idanu ko ya k'yale sa sai de inshi yana so ya yunk'ura, shi yasa yafi son zama awurin Antynsa Khadija shi aganinsa acan yafi walwala idan yana can sam baya jin cewa yana da matsalar komai. ***** Lafiya lau ya sauk'a ,koda ya sauk'an kuwa be k'ira kowa yasanar da sauk'an tasa ba aidansu, wani friend d'insa yak'ira yazo ya d'auke shi yakawo shi gida, be ma shiga ba yajuya yakoma saboda akwai uzuri agabansa godiya kawai Mahmud yamasa sannan shima ya shiga gida. Ahankali yake tafiyar tamkar bazaiyi ba hannunsa babu komai sai agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa, gefen kafad'arsa kuma 'yar jakar da yake saka kayansan da zai bukata inzaiyi tafiyane. Haka ahankali har yak'araso k'ofar parlournsa, key hondern dake tare dashi yaciro ya lalu6i makullin da zai bud'e masa d'akin yasaka ya bud'e yashiga ciki. Sake tura k'ofan yayi ya rufe abinsa tankar ma ba'a bud'e ba. D'akin ma ashare tsab bawani datti dayake duk bayan kwana biyu Anty take sawa a share masa koda ma bayanan so bashi da matsala da wannan, kawai sai ya ajiye jakar kayansa tare da rage kayan dake jikinsa. Bayi ya shiga ya watso ruwa tare da d'auro alwala yazo ya tada sallah ya rama wanda yawuche shi tare da sallatar wanda tagabato adai dai lokacin. Yana idarwa ya d'auki wayarsa ya k'ira mummy ya sanar da ita isowanshin lafiya harma suka d'anyi hira da Teemah kad'an basu wani d'au lokaci ba yace mata bacci yakeji he need to rest, sallama tayi masa tace idan yatashi yak'ira zata bashi wani labari, " toh kawai yace mata atakaice dan yasan babu wani larin da zata bashi k'aryace kawai da kuma son yak'iratan datakeyi. daganan ya kwantaa bayan ya maida wayar a silent da niyyar kishingid'a, kamar wasa kuwa sai bacci ya d'auke shi suka tafi.😜 Antynsa bata san ya iso ba, kuma duk k'iran data ta yi masa aranar ko guda d'aya bai d'auka ba hakan kuwa bak'aramin 6ata ranta yayi ba amma sai ta kyaleshi da niyyar duk lokacin data sameshi awaya sai taji dalilin hakan inma zigashi ake yi yamata rashin kunya toh duk zataji. Bashi ya tashi ba sai da aka k'ira sallar maghrib,koda yatashi alokacinma sai yaji gaba d'aya kansa yamasa nauyi,hakan ya sa yad'an 6ata lokaci abayi yana cikin ruwa da kyar yasamu yafitoh. Sallar maghrib d'in yagabatar tare da zaman jiran lokacin isha'i yacika itama ya gabatar da ita, baya son yaje masallaci su had'u da Abbansa ne shiyasa baije ba amma da farko harya yi niyyan zuwa sai fasa. K'arfe takwas da rabi daidai tayi masa ne ak'ofar babban parlourn Anty. Hannu yasa yatura ahankali tare da yin sallama ciki ciki. Suna can wajen cin abinci dan haka basu ji sallamar tasa ba amma sunji k'arar k'ofan. Jin k'arar dasukayi yin ne yasa suka maida hankulansu wajen k'ofar shiru sukaji babualamun mutun kuma domin daya shigo tsayuwansa yayi awuri d'aya shiyasa basu kuma jin motsinsa ba. "Waye ne? Abbah ya tambaya batare da ya mik'e ba. Ahankali yah amsa da " nii neh" kamar dole aka saka shi. Suna jin muryarsa suka mi'ke atare suka nufo shi tare da ambatar "MAHMUD" alokaci guda. " Mahmud kani da daren nan? Abbansa ya tambaya cikin mamaki. Kai ya d'agawa Abban alamar ehh Hannunsa yakamo suka koma gurin cin abincin dukkansu nan take Anty ta had'a nasa nasa plate d'in ta tura masa shima. Dayake daman yunwa yakeji sai be wani yi yanga ko gardama ba ya bud'e ciki ya kwashi abincinsa sai da suka gama kafin Abbansa ya tambayeshi meyasa yayi tafiyar dare? " bayanzu na zo ba Abbah" Yabawa Abban nashi amsa . Ido Abban ya ware "bayanzu babana tun yaushe kazo? " Tun da rana". Salati Anty tasaka takama baki sanna tace " yanzu Mahmud tun da rana ka iso amma kak'i zuwa inda muke sai yanzu". Abbane ya d'aga mata hannu yana murmushi yace " pls barshi Maryam may be yagaji ne shiyasa...... " amma me yasa bazai ko sanar akan yana hanya ba..... Anty ne tasake fad'in hakan. Abbah kuwa cewa yayi wannan tsakaninku amma dai kibarshi kwa gama dasafe idan Allah yah tashemu lafiya". Juyawa yayi ya kalli Mahmud yace " abana jeka huta sai da safe koh". Mahmud da tun d'azu yake zaune kamar mutum mutumi kallon Abban sa yakeyi da mamaki, domin yajima baiga Abbansa na irin hakan acikin gidansa ba, sai yau yaga Abbansa na dakatar da Anty akan abu kuma tayishi, sosai hakan yasashi mamaki matuk'a, shiyasa be ma ji abinda Abban ya fad'a da farko ba sai da Abban yasake maimaitawa kafin ya yi firgigi. be san cewa addu'ar da mummy keyi akullum bane yafara tasiri akan Abban. " meke faruwa ne ? Aban ya tambayeshi. "Ahh bakomai Abbah " " toh maza jeka kwanta sai da safe" Tashi yayi tare da sake yi musu sallama ya wuche abinsa. Anty kuwa abin ne yafara yimata yawa domin ga matsalar Mahmud daya d'an d'au lokaci aranta tana tunani ta yadda zai yadda da batun auran Munirat, sai rana tsaka kuma matsalar Abbah ta kunno kanta kusan sati kenan tarasa gane kansa, gashi duk tarasa dalilin hakan. Koda tayiwa Anty chideh magana kuma sai ta rink'a yi mata yanga kamar ma bata son zuwa. Itakuma vagane gurin zatayi ba yanzu kuma bata son canja wa tagi son wancan wurin d'in dasuka yi mata aikin tun farko dan sosai ta yadda da aikin nasu. Washe gari daya zo gaida iyayen nasa sai yace wa Antyn yanso me yakoma dawuri domin akwai aikin dake jiransa acan idan wani abu take so ya mata tafad'a dawuri sai yagama mata shi ayau dan yanaso yakaoma" Antyn kamar bazata fad'a ba dan tsoron abinda zai biyo baya kar kuma tak'i fad'a yace yau yake son komawa tunda babu abinda zai mata, sam bahaka taso ba , taso su ka6e su biyu sannan suyi maganan musamman ma dayanzu yadda yakasance Abbansa na yawan yi mata katsalandan a abu shiyasa take tsoron fad'in abinda ke ranta a gaban idanunsa. Tunanin hakan yasata ta bud'i baki badan ranta yaso ba anan ta yada manufarta nasawa datayi yazo d'in. Haushi Mahmud yaji sosai bayan yaji bayanan Antyn. Dayake cewa tayi yakamata ya tsaida matar da sai aura kodan gudun lalacewar da duniya take ciki dan hakneta mtsa akan yazo gida domin su tsaida magana wuri d'aya. Haushinsa d'aya ne dayaji wai duk wannan masifan data tayi masa d'in wai akan batun aure ne toh ni wama zan aura ? Ya tambayi zuciyarsa. Azahiri kuma murmushi yamata kana yace " kwantar da hankalinki Anty, nibama yanzu na shirya yin aure ba gaskiya, shiyasa ma har yanzu banda kowa da muka yi batun aure da ita kinga kuwa ai da sauran lokaci" Abbah ido kawai ya zubawa wayarsa tamkar baya jinsu amma kuma gaba d'ayan hankalinsu da kunnuwansa na gare su ne. Anty ne h tasake fad'in cewa " ai karka damu Akwai wata 'yar k'awata.......... sai tadakata ta kallo Abban Mahmud d'in.... " mahmud aransa yace dama nasani ai" yayinda afili kuwa kallonta yakeyi kamar wanda tana fad'an maganar zai amince. Gani tayi Abban Mahmud d'in sam hankalinsa baya tare da su sai tayi hamdala azuciyarta. Daganan taci gaba da fad'in...... " yarinyar nada hankali Mahmud shiyasa nayi sha'awan kai ka aureta nasan baza'a samu matsala daga gareta ba bansan dai kai ba" Takarashe maganan da yanayin tausayi. Shi kanshi sai yaji tausayinta amatsayinta na uwa mahaifiya agareshi, idan har tana ganin bata da matsala da yarinyar toh why not shi data haifa kuma? Batare da wani 6ata lokaci ba take yace mata gobe yake so ya koma amma insha Allahu kafin ya tafin zaije yaga yarinyar inyaso sai yabar komai ahannunsu. Farin cikin da Anty taji tamkar ta goya shi haka taji kawai sai fara yi masa godiyah kamar wanda yamata kyautan wani abu. Sai asannan kuma Abbah yayi magana inda yace " ga dukkan alamu yarinyar tatafi da hanakalinki gaba d'aya ko? Murmushi tayi amma bata yi wata magana ba dan karta 6ata plan d'inta tunda tasamu ya amince ai shikenan. Da yamman ranan Anty ta had'a Mahmud da drivernta dayake ahi yasan gidan sai ta masa bayanin abinda zai kaisu gidan atsanake. Fita yayi bayan sun isa ya bar Mahmud d'in zaune acikin mota shikuma yaje yayiwa Mai gadin gidan bayani take kuwa yawuce ciki yah isar da sak'on da aka bashi. Minti goma mai kyau bata cika sai ga Munira tafito cikin shirinta na k'asaitacciya awurin iyayenta. Riga tasa iya gwiwanta yakuwa yi mata kyau sai dai rigarasosai yakama mata jiki dayake roba ce da dogon wando daga ciki kanta kuma wani d'an k'aramin veil me tayane kanata dashi, tana tafiya tana karairaya dayakr dama tasan da zuwansa mahaifiyarsa tariga ta sanara tun kafin ma ya iso shiyada tayi masa shiri na musamman. Tun daga nesa Mahmud ke k'are mata kallo yana karantar yanayinta. Murmushin takaoci yayi lokacin daya fajimci yarinyar ya kuma tuno inda yafara ganinta,sam ba irin matan dayake ao ya aura ba kenan asali ma shi baiga wani abinso tattare da yarinyar ba tun farko dahar Abty take ganin dacewansu dashi. Tsaki ne ya subce masa lokacin daya tsinkayo muryarta tana fad'in " Hi " Bai kulata ba sai ma kauda kai da yayi gefe kome yatuna kuma oho sai ya fito yazo tagabanta ta tsaya tare da folding hannayensa a k'irjinsa. Gaishe shi Munirah takuma yi tare da yi masa iso zuwa cikin gida. Bai amsa mata ba sai ma tambaya daya jefah mata nacewa " wacece ita? Murmushi tayi tare da fad'in " ohh sorry" Sunana Munirah kuma nice wacce Mahaifiyarka ta za6a maka atsayin mata. " oh really " Yafad'a da sigar rainin hankali yana kuma murmushi. Kallonsa ta tsaya yi domin afili zaka fahimci manufarsa koda baka da wayo balle ita. " kinsan wani abu? Idonsa acikin nata yayi maganar sai kawai ta jijjiga kanta dan sosai jikinta yafara yin sanyi. " ko kad'an bakiyi min ba! Sake matsowa yayi kusa da fuskarta yakuma fad'in " kinsan dalili? Da kai ta bashi amsa alamar " a'a". Sai yace mata " saboda ko kad'an baki dace dani ba". " Ki gayawa zuciyarki cewa Mahmud d'innan banaki bane, dan nasan wannan duk munafurcinki neh,ni kuma insha Allahu bazan ta6a auranki ba, mark my word." Yana fad'in haka yajuya ya shiga mota da gudu driver yazo ya shiga shima yatada motar suka fita agidan. Har suka bar haraban gidan Munirah bata iya motsawa ba, mintina yakai uku ta k'ara bayan fitan motar tasu daga gidan kafin ta dawo hayyacinta, gefe da gefenta ta kallah taga babu kowa da gudu tayi cikin gida tana rusa kukan takaici bata zame ko'ina ba sai gurin mahaifiyarta. Da k'yar tasamu Muniran tayi mata bayanin abinda ke faruwa ai kuwa take ta d'aga waya ta k'ira Anty tafad'a mata abinda Mahmud d'in yai wa 'yarta. Ran Anty ya 6aci sosai aganinta ai tozarci yayi mata, inbahaka ba yasan baya so mai yasa tun farko yace mata yaya yadda da batun auran sai da ta riga da ta sanar da su amincewarsa kuma sai yaje yaci musu mutunci har cikin gidansu? Safah da marwa take tayi tana Allah-Allah ya dawo ahima yazo yasameta tunda shi bai san mutunci ba. Mahmud kuwa k'in komawa gida yayi da wuri yace su wuce yawo acikin gari basu suka dawo gidan ba sai kusan 11pm beyi niyyan shiga ciki bama dan yasan had'uwarsu da Anty yau bazaiyi musu dad'i ba. Bai san cewa Antyn tun d'azu gadinsa takeyi ba yayinda Abbah ma duk yake kula da ita batare data sani ba. Tana jin tsayuwar mota kuwa ta fito da gaggawa ta tare shi alokacin yana gab da shiga d'akinsa. Mahmud! Tafad'a ranta a 6ace. A hankali ya tsaya tare da juyowa daidai kuwa yaji sauk'an mari tasssss akan kuncinsa. Ido kawai ya rintse ta re da bud'e wa ya sauk'e su akan Antyn. " baka da hankali ne Mahmud , ni zaka raina ma wayo , so kake ta tozarta ni ko,wallahi akan wannan maganar bari kaji zamu matuk'ar samu matsala ni da kai matuk'ar kace bazaka bi abinda nakeso ba.......... "Uhm-uhm fah Maryam kar muyi haka dake, karki ce zaki takurawa yarona akan abinda bashida ra'ayi domin ni bazan lamunci hakan ba ". Bazata suka jiyo muryar Abbah nafad'in hakan sosai k'irjin Anty ya buga dan bata ta6a zaton idansa biyu ba awannan lokacin. Shi kuwa Mahmud har yanzu kallon Anty yake da mamaki, aransa yake k'ara jinjina hali irin na Antyn tasa yana ganin cewa lalle halinta sai ita, idan dai har zata iya d'aga hannu ta mareshi akan waccen yarinyar tun yanzu toh ashe idan ya aureta ma har zanashi zata ce zatayi idan ya 6ata wa yarinyar rai, toh taya ma za'ayi na auri yarinyar da ake marina akanta, tun yanzu Anty hanyan raina ni ta bud'ewa yarinyar. Abban sa neh ya taho ahankali izuwa inda Mahmud d'in ke tsaye,yana cikin tunanin yaji ankamo hannunsa, firgigi yayi ya kalli hannun sannan ya kalli Abban nasa. " je ka kwanta Mahmud " kaji! Baiyi magana ba still yaci gaba tsayuwa Abban ne yakama hannunsa ya shigar da shi cikin d'akin sannan yafito yaja masa k'ofar. Zuwa yayi yabi ta gefen Antyn yace "wuche muje" Ahankali ta bishi abaya har d'akin baccin nasu. Abbah bai k'ara bi takanta ba yayi kwanciyarsa yayinda abin yaso daya farun yaso hana Anty bacci dan tana tsoron maganar Abban bata so yaji ba amma ya shammace ta, bata sani ba ashe ya biyo bayanta, dole nayi maganin abin tunda wuri tunkan abin yazo yafi k'arfina, dole nayiwa tufkan hanci. Mahmud kuwa wayarsa ya lalub'o ya nemi Abbas a waya.......... Comment,vote and share pls🤞🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 5:59 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Good or Bad, whatever you do will come back in one form or another; that would explain why the earth is ROUND. 🅿 *33* Sau kusan uku wayar nayin ringing amma no response, har yayi shirin sake k'iransa karo na hud'u sai kuma yafasa kawai ya ajiye wayar. Kishingid'a yayi ajikin gado na tsawon mintina shida ransa a hargitse yake jinta wai yau Anty ne ta mareshi akan wata banza, sai daga baya sannan ya tashi ya zauna abakin gadon, hannayensa ya d'ago duk biyun ya cusa su acikin gashin kansa tare da furzar da iska mai zafi daga bakinsa. Halin Antyn sa na matuk'ar damunsa sosai, can you imaging ace mahaifiyarka amma bata k'aunar taganka cikin farin ciki akullum sai dai sa6anin hakan,abinda Anty bata masa tun yana yaro ba wai sai yanzu daya girma ne zata ce zata yi masa saboda me? Idan da wani yake bashi labarin hakan zai iya k'aryatawa amma sai gashi akan kansa abin ke faruwa. Ace Anty tarasa da wacce zata had'a shi maganar aure sai da waccen yarinyar?? Toh shi me zaiyi da ita? Rashin mai bashi amsa yasa dolensa yah hak'ura da tambayar dayake yiwa kan nasa domin yasan idan ya matsa kansa zai jawo wa ciwo abanza and no body cares! Tashi yayi ya cire rigar dake jikin sa sannan ya shiga bayi ruwa ya watsa tare da d'auro alwala yazo ya shimfid'a dadduma. Sallar nafila ya gabatar tare da neman sauk'i daga gurin mahalicci akan dukkan al'amuransa rok'on haske, rahama da kuma kariyar Allah yayiwa iyayensa musamman ma Abbansa duk dama yaga kamar Abban ya d'an canja ba kamar kwanaki ba, amma yasan addu'a bata ta6a yin yawa a bawa kamar yanda bata tafiya abanza saboda Allah shida kansa yace a rok'eshi zai amsa. yadad'e awurin yana Addu'o'i kafin yatashi ya kwanta ko daddumar ma be samu yah nad'e ta ba saboda bacci. Alokacin kusan 1:06am bacci ne sosai a idanunsa shiyasa daga kwanciya sai bacci yah d'auke shi cikin natsuwa kuwa yayita shek'a baccinsa batare da yasake bi takan damuwarsa ba. Washe gari ma da wuri ya farka domin tafiyarsa na nan aransa be fasa ba, dan haka yana dawowa daga masallaci yafara tattara d'an abinda yasan zai buk'ata ako'ina yake, abubuwan basu wuche tarkacen amfaninsa ba irinsu laptop wayoyinsa da sauran k'ananan abubuwa . Dayake sun had'u da Abbansa da asbah a masallaci kuma yariga ya sanar dashi batun tafiyar tasa so bashi da damuwa akan haka yasan Abbahn bazai hanasa tafiya ko kuma wani abu daban ba indai bawani dalili ba kam. K'arfe tara ya fito daga d'akinsa kafad'arsa rataye da jakansa hannunsa d'aya kuma wayarsa ce arik'e yayinda d'ayan hannun ke rik'e da key holder d'insa me tarin keys ajiki. Guda d'aya ya ware yasaka ya rufe k'ofar parlourn nasa sannan yasake zareta. Daga nan ya canja rik'on key d'in izuwa hannun sa na hagu sai ya maida wayar tasa zuwa hannun damansa. password d'in dake kan wayar tasa ya cire sai yafara neman layin Abbas dan sosai yake da buk'atar ganin sa amma is hardly su had'u d'in shiyasa yake so ko samunsa awayar ma yayi. Sai dai ko yanzun daya sake k'iran ma _call waiting_ ya gani sai ya dakatar da nashi k'iran ya d'an bashi time zuwa wani lokaci. Kusan mintina biyar sun shud'e yana nan tsaye a inda yake still sai dai ad'an tsayuwar dayayin har ya samu chance na k'iran mummy suka gaisa yah tambayi lil sis da Daddy mummy tace masa suna nan lafiya qalau. Hira kad'an sukayi sukayi sallama da mummyn sai yace mata shima d'in insha Allahu yau zai shigo , suna gamawa sai ya sake gwada layin Abbas d'in batare da yayi zuciyah ko fushi ba. Amma still _call_ _wating_. Wannan karon kam tsaki yaja tare da fara tafiyah ya tunkari sashin iyayensa da wayar tasa ahannu. Mahmud irin mutanen nan masu son fad'ar abinda ke damunsu ga wani wanda ya kasance makusanci agaresu, yana son akan komai abashi shawara kafin yayi abin, idan ma damuwace tadameshi yafison yayi sharing ga wani sai dai wani lokaci idan ya rasa wanda zai tunkara da damuwarsa sai ya rik'e abinsa azuciyarsa duk da hakan na damunsa amma bazai fad'iwa kowa ba yafison sai wanda ya yadda dashi tukun na,kuma wannan dalilin be sa yazama mai yawan fad'e-fad'e ba, mutun d'ayan nan dai ne ke sanin damuwarsa baya kuma sake fad'i wa wani daban. Yakan yanke hukuncin abinda zaiyi dakansa idan abu zaiyi saiyayi abun kawai ayanda ayanda yake ganin shine dai dai. Adacan baya kafin had'uwarsa da Abbas _Anty_itace abokiyar shawaransa ita yake sanarwa da duk wata matsalar data kunno masa kai arayuwarsa, amma daga baya shikansa be san dalilin dayasa ya daina fad'a mata ba, ko dan irin shawarwarin data ke bashi ne oho, domin akowani abinda Anty zatayi selfishness take fara sawa agaba kafin wani abu, bai sani ba ko wannan dalilin ne yasashi ya janye jiki daga gareta ba, amma haka kawai yaji baya son sanar mata da wasu al'amuran da suka shafi rayuwarsa. Daga baya ne sai yafara sanar da wani abokinsa dasukayi makaranta tare shikuma matsalarsa baya 6oye k'yashi da hassada afili yake bayyana su fahimtar hakan da Mahmud yayi sai yasa yadaina fad'iwa kowa kawai yake rik'e abinsa shi kad'ai . Alokacin Abban sa ba sauraronsa yake ba dan abubuwa shima sun masa yawa sosai kasuwancinsa ya bunk'asa shiyasa kullum baya zama, akullum yana kan tafiye-tafiye banda matsalarsa tacikin gida, gara yan zuma daya d'an daidai ta al'amuran sa waje d'aya sannan yasamu yake d'an natsuwa agida. Tunda suka had'u da Abbas sai yake jin har aransa yasamu aboki jin Abbas yake tamkar d'an uwansa kuma sai akayi sa'a ma jininsu ya had'u da Abbas d'in shiyasa wannan karon yake so yakai damuwarsa gurin Abbas ko zai samu sgawara me kayu daga garesa duk dama yariga ya yanke decision aransa kuma bazai canja ta ba amma dolene yaji ra'ayin Abbas akan hakan. Yana gab da shiga shiga parlourn yaji wayarsa na vibration ahannunsa d'ago wayar yayi sai yaga sunan dake k'iran sa, nima sai na d'an lek'a kad'an dan ganin me k'iran nasa☺ _Oga Abbas_nagani 6aro 6aro akan fuskar wayar. Yana ganin Abbas neh sai yah dakata da tafiyar tasa cak ya tsaya sannan yayi picking call d'in yakai wayar kunnansa. Abbas ne yafara fad'in "yah ne corper kana lafiya? " qalau" Mahmud d'in yace agajarce, sannan ya cigaba da fad'in " tun jiya fah naketa neman layinka amma baka picking me yasa? " ainasan sekayi magana tunda naga missed called d'inka jiya,nagaji ne wallahi ina hutawa shiyasa kuma banma jiba cuz' wayar na silent,inama da niyyan k'iranka fah se kuma k'iranka yashigo" "Ba wannan bama tunda kasameni yanzun then fad'amin abinda ka k'unshe dan nasan wannan duk damuwar k'iran ba'a banza ba."! Abbas ne yafad'i hakan yana murmushi tamkar Mahmud d'in na gabansa. Mahmud d'inma murmushin yayi sannan yace "kana ina ne yanzun inaso mu had'u fah " " tasamu kenan, " a' a kai bakomai babu wani abinda yasamu" Mahmud ya dakatar dashi da fad'in haka. Sai Abbas yace " kuma kaga nad'anyi tafiya yanzu haka ina borno inajin kuma anjima kad'an za mu wuche". "Shikenan toh nima yanzu nake shirin komawa sai dai da k'yar mu had'u may be kafin na iso kunwuce kasan nazo lagos 2days back" " Haba mana 2days kuma har zaka koma?" " ehh kamanta bautar k'asata nakeyi ne?, Kabari insha Allahu idan na sauk'a zamuyi magana." Mahmud ya k'arashe maganar da d'an gaggawa dalilin hango mahifinsa dayayi ya fito da shirin zuwa office dan hannunsa rik'e take da briefcase d'insa, bayan Abban kuma Anty ce itama ga dukkan alamu fitan zatayi. Yana yanke k'iran suka had'u dayake dama ba wani tazarar kirki bace atsakaninsu. Suna had'uwa sai ya gaishe dasu, Anty yafara gaisarwa dayake sun riga da sun gaisa da Abbah tun a hanyar dawowa daga masallaci sai dai ko gaisuwa ta biyu. Antyn ma adak'ile ta amsa masa yayinda Abbansa ya cira hannu yah mik'a masa sukayi gaisuwar muslunci yana murmushi yace "harka shirya kenan" " ehh Abbah inajin daganan ma sai airport" " Abbane yace bakace tafiyar sai 11:30 ba? " ehh zanbi wajen Jabir ne kafin na wuche". " alright ba matsala Allah ya tsare ya bada sa'a" "Ameen- Ameen Abbah". Duk maganar nan da sukayi Anty kauda kanta gefe tayi tamkar bata jinsu, Mahmud kuwa yana gamawa da Abbansa ya dawo gareta yace mata zai wuche . Tunani tafara aranta wai dama dagaske Mahmud ayau d'in zai koma? Kar dai duk akan maganar Munira ne ya yanke wannan hukuncin? Toh idan yakoma ayau ai tamkar ya dakatar da batun auren ne, while itakuma dawuri takeso ayi. Koda ta tambayeshi dalilin tafiyar sai ya ce mata akwai aikin dake jiransa ne acan shiyasa. Sababi tafara ranta a matuk'ar 6ace take fad'in " aikin banza aikin wofi, harni zaka nuna wa wani aiki, ince dai service kajeyi acan d'in ba neman aiki ba da har zaka min iyayi anan. Cewa yayi " shi d'in dai service d'in nake fad'i bakomai ba Anty". Bud'e baki tayi tacigaba da masifanta inda acikin masifar tace ai akwai mutane dayawa da wannan bautar k'asan duk ba yinta suke ba why not shima ya tura musu ko nawane suke buk'ata inyaso yayi zamansa agida basai ya koma ba" Shikuwa yace a'a yafi buk'atar yayi bautan dai kodan saboda ya jaddada kasancewarsa cikakken d'an k'asa. Aikuwa sai tacigaba da fad'in wai Mahmud ya raina ta sam baya bin maganarta dan me zai ringa ja inja da maganarta abinda daa ba haka yake mata ba , kenan ya je yakoyo banzan hali zai zo ya rink'a yi mata sai kace ba ita ta haife shi ba" Kallonta suke yi daga Abbah har Mahmud suna mamakin masifar tata ta dosa da kuma dalilin yinta. " wallahi indai kace ni zaka raina akan wata banza zaka.......... Da k'arfi cikin tsawa Abbah yace " shut up maryam....,stop it,how dare you zaki ringa fad'in hakan infront of me!"... Yatsansa ya d'aga sama yayi nuni da gefensa kana yace " waccen d'in fah da kike so ki zaga 'yar uwata ce!, gudan jinina!!, ita kad'ai nake dashi !!!meyasa baki gane abu ne ke,.......yatsan nasa ya dawo dashi saitin Antyn sannan yace " kinsan Allah, idan nak'ara jin kin fad'i ba dai dai ba akan Kha.....kha....di........... Sai yayi shiru yaja tsaki. Hannun Mahmud ya finciko ya yi gaba dashi har gurin da driver ya ajiye motar da Abban zai fita da ita. Nan yace Mahmud yashiga motar sai dayaga yashiga sannan Abban shima yaxaga yashiga. Mota d'aya suka shiga suka tafi suka bar Antyn tsaye agurin tamkar andasa ta. Mahmud kuwa hamdala yake ta yi azuciyarsa duk dama ba hakan yaso ba, hak'ik'a duk d'ah nagari bazai so ya ringa kallon husuma na tashi acikin gidansu tsakanin mahaifansa kuma yaji dad'in hakan ba. Amma shi kan sai yaji farin ciki kad'an bawai dan Abbah yayiwa Anty masifah ba " a'a " Canjin daya gani azahiri tattare da mahaifin nasa shine yasashi farin ciki. Lalle Allah maji rok'o ne yakan amsa addu'o'in bayinsa aduk lokacin daya so hak'ik'a yau ranar farin ciki ce ga Mahmud domin yau yaga mahaifinsa na acting as Magidanchi cikakke mai fad'a aji acikin gidansa, sa6anin baya da komai in za'a yi baya ta6a tankawa koda kuwa abin ba dai dai bane sai dai yayi shiru yasa ido yana kallo. Abbah office d'insa ya wuche da Mahmud sukayi zamansu aciki suna d'an ta6a hira kamar bashi bane yayi masifah d'azun, ayyukan dake gabansa ma dakatar dasu yayi yah bada hankalinsa ga d'ansa suka fahimci juna sosai anan ne Abban ya nemi jin asalin ra'ayin Mahmud akan waccen yarinyar Mahmud kuwa bai 6oye masa komai ba ya sanar da shi akan sam baya so saboda yarinyar yaga kamar bata da tarbiya kuma ma shi ba yanzu zaiyi aure ba sai zuwa gaba. Kwantar masa da hankali Abbah yayi akan batun auren da baya so d'in kuma yace insha Allahu babu mai yi masa dole matuk'ar yana numfashi, amma batun bayanzu zai yi aure ba yama daina fad'i dan aure lokaci ne idan kuma lokacinka yayi babu makawa sai anyishi koda kuwa ba'a so yana faruwa ne tamkar mutuwa. Godiya sosai Mahmud yata yiwa Abbahn nasa take kuwa sai yaji duk wani damuwarsa ta kau dama dan haka yake so ya had'u da Abbas saboda idan ya yi magana da mutun akan matsalarsa yakanji kwarin gwiwa sosai sa6anin barinta azuciyarsa. Magabar dayayi da Abbansa sai yaji yama fasa sanar da Abbas maganar tunda Abbansa yah bashi assurance mai kyau akai so yanzu baya buk'atar sake ji, komai daga wani. 'Karfe goma daidai Abbah yak'ira drivern office d'insu yace ya kaishi airport d'in saboda hold-up ma yasan kafin su isa lokaci zaiyi yak'ara da fad'in ya k'ira jabir d'in yabashi hak'urin rashin had'uwarsun yace masa Abban ne ya rik'esa a wurinsa. Mahmud Yana dariyah yace " haba Abbah bakomai zanyi masa bayani insha Allahu" Daganan sukayi sallama Abbah yayita masa addu'a har suka rabu. Comment vote and share pls🤞🏻 *Salmerhn ku ce**😍 [10/2, 6:00 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍 HAPPY ANNIVERSARY sis HUSSAINAH B ABUBAKAR (Mrs Abubakar) *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Ya Allah, turn our sadness to happiness,frowns to smiles,hate to love, weaknesses to strengths, and cleanse us of our shortcomings. 🅿 *34* Tun lokacin da Abbah ya fara yiwa Anty tsawa akanta taji duniyar ta tsaya mata cak, wani duhu taji ya mamaye ilahirin kanta har cikin k'wak'walwarta gaba d'aya, wasu abubuwan daya fad'a d'inma bata jisu da kyau ba ido kawai ta tsurawa fuskarsa yayinda yake mata masifar inka ganta alokacin zaka zaci hankalinta da nutsuwarta ta mayar akansa don ta fahimci me yake nufi da kyau, amma azahiri ba haka bane. Anty ta kusan minti goma agurin tsaye tana tunani abin ne takeji wani banbara k'wai it seems different, kamar almara............wai yau ita Abbah ke yiwa tsawa akan abinda be taka kara ya karya ba. Jijjiga kai tayi da k'arfi take sai tunaninta ya dawo daidai, gani tayi ba kowa agabanta ita kad'ai ce tsaye awurin, koda ta kalli gefe da gefenta ma duk haka tagani bakowa,da sauri ta juya takalli inda motar Abban ke ajiyeh sai taga wayam bakomai, alamar sun ma bar mata gidan gaba d'aya batare data sani ba tsabar yanda ta shiga zurfin tunani. Ranta taji ya matuk'ar 6aci,wani 'kullutun daya kullera azuci ji tayi tamkar ta kurma ihu ko zai waraware, ahankali tafara d'aga k'afafunta tajuya da niyyar shiga cikin gida saboda fitar ma jitayi tafice mata arai. Kan kujera taje ta zube sharab tamkar wata majinyaciya, sam takasa yadda cewa wannan ABBAn mahmud ne, ji take kamar an exchanging mata shi ne gaba d'aya, inkuwa wannan mutumin da kuma wannan al'amarin daya farun ya kasance gaskiya to kuwa hakika zama bai ganta ba. Bazata ta6a bari aci nasara akanta ba matuk'ar tana numfashi,kuma nan take tayiwa kanta alk'awarin tarwatsa rayuwar duk wani mai shirin yiwa aikinta _zagon k'asa_ (khadija candy). Tayi alwashin koda waye ke yi mata hakan sai taga bayanshi sannan wannan auren data fara magana akansan bata ga uban daya isa ya hanasa faruwa ba matuk'ar tana numfashi, ada bata d'auki al'amarin da wani girma sosai bama, saboda kawai tana tunanin zata lalla6e shine ahankali ya amince ya auri Muniran tunda ita ta nuna tana sonshi, amma yanzu ji takeyi aranta kodan abinda Abban Mahmud yayi mata ayau d'in sai ta bawa duk wani mai shirin shiga tsakaninsu kunya, sannan kuma daga baya ta kuma tarwatsa shi kamar yadda yafara had'a mata hargitsi acikin gida. (Kunsan shi me yin abu akullum shi tunaninsa kowa ma yanayi ne, gani suke kamar duk abinda yasame su toh yi musu akayi, gaba d'aya mantawa sukeyi da k'addara) Allah ubangiji kasa mufi k'arfin zuk'atanmu _AMEEN_ . Koda Mahmud ya koma damaturun babu wani abinda yakeyi saboda already ya gama abinda zaiyi tun kafin yaje lagos kwanaki. Abinda ANTY tace yayi d'in batasan yayi hakan tun kafin ta furta ba,so yanzu bawani zuwa wurin bautan k'asa daya keyi zamansa yake kurum agida, sai dai suje yawo, ko suyi karatu suje ziyara inda suka sani idan ta kama,wani lokaci kuma daddyn Teemah yajashi suyi tafiyah tare. Yakan d'an ziyarci wajen dayake service d'in amma sai lokacin daya ga dama, kuma zuwan ma yana zuwa ne bawai dan yayi wani abu ba kawai yana zuwa ne dan ya san meke faruwa awurin kar shirun yayi yawa. Wani lokaci acikin ransa sai yaji cewa bai kyautawa Anty ba daya k'i zama awurinta, yasan amatsayinta na mahaifiya dole tana buk'atar sa akusa da ita musamman ma daya kasance shi kad'ai ALLAH YA BATA dole tarink'a jin kewar d'anta. Amma sam bazai iyah zama a Lagos ba yanzu, sosai yagaji da fitinar Anty, bata k'aunar azauna lafiya ita sai k'ak'ale-k'ak'ale. Wannan dalilin ne yasa yaji zamansa a damaturun yafiye masa can tunda mahaifinsa bai hanasa ba. ***** Lokacin da aka fara zana waec kusan tare Mahmud da Teemah suke yi dan baya ta6a barinta tayi karatu ita kad'ai ko exam d'inma zataje tare suke tafiya. Ana tsakiya da waec d'in ANTY tasake hura masa wuta akan yadawo gida haka nan tunda already yagama service d'insa toh zaman me kuma yakeyi, tace masa ya dawo gida wai afara maganan aurensa da Munirah. Tambayar ta yayi cewa "wani maganar aure kuma ?. Dan shi shaf yama manta da batun tun sanda yadawo nan, bai sani ba ashe abin har yanzu yana ran Anty. Koda ya tambayetan haushi taji bata bashi amsa ba sai kawai ta yanke k'iran daga 6angarenta tacigaba da masifah. Acikin kwana biyu tak'ira shi yafi sau a'kirga kuma duk akan maganar ne, daya ga haka sai ya 'kira Abbansa yayi masa bayani. Abban nashi ma cewa yayi ya koma gidan kawai tunda haka mahaifiyarshi keso shi yasan mai zaiyi akan maganar auren. Bai 'ki maganar Abban ba amma yace masa sai an gama weac zaizo, daga lokacin zuwa agama d'in yakama kwana tara kenan ya rage. Dahaka sukayi sallama da Abban nasa kowa ya yanke 'kiran. Mahmud wannan karan kokad'an bai bari Mummy ta san da labarin ba, dan yasan tana sani zata sashi agaba sai taga yatafi itama kafin hankalinta ya kwanta,bawai dan ta gaji da zamansa tare dasu ba " a'a " kawai wai dan kar ashiga hakkin mahaifiyarsa ne. Tun kafin a kammala waec kuwa yafara shirye-shiryen tafiya gida, kwana biyu bayan waec d'in ya shirya yatafi wannan karan kam shirinsa na barin garin ne gaba d'aya, saboda da wuya ya sake dawowa, duk wani abu da yyake nashine na buk'atarsa ya tattare su haka yatafi ya bar kowa da k'ewarsa agidan. ***** Dawowar Mahmud Lagos shiyafi komai faranta ran Anty dan tana ganin kasancewar sa tare da ita shine zai sa burinta yayi saurin cika, musamman ma yanzu da take ganin yin auren nasa shine zai sa ya rabu da son rayuwa awurin Khadija, tunda idan da aure akansa ai bazai yi gigin son tafiya wani gari yabar iyalinsa ba. Adole take sa shi ya shirya ya ziyarci Muniran batare da yaso ba, kuma wannan shine karo na uku kenan dayake zuwa wajen Muniran, sai dai abinda Anty bata sani ba shine zuwan nasa ba anfanan su yake da komai ba saboda a duk sanda zai baya fad'a mata wata magana daban face sake jaddada mata dayake akan baya kaunarta and he can't even marry her saboda bata dace dashi ba.Maganar arzi'ki bata ta6a had'asu ba. Antyn ce da kanta tasa Mahmud ya sanar da Abbansa cewa ya samu matar aure wai aje ayi masa tambaya, afad'ar Antyn wai in itace tayi ma Abbab maganar tasan ba amincewa zaiyi ba kuma zaiga kamar ra'ayinta bana Mahmud d'in ba. Shiyasa take so shi yaje dakansa yayi bayani. Nan ma da 'kyar Mahmud ya yadda ya amince akan zashin d'in har sai da yaga ranta na shirin 6aci kafin nan ya amince da zuwa d'in. Da farko kafewa yayi akan shi bazai iya ba, ita tayi magana wa Abban nasa mana ai ba dole sai shi dakansa ba, kuma dagangan ya ya kafe akan hakan saboda yasan tana tsoro yanzu bakamar da bah, bazata iya fad'an ba shiyasa shima ya kafe akan hakan. Dayaga rantan ya 6aci kafin ya amince akan zaiyi magana wa Abbahn saboda shi wannan mitan ya tsana bakomai ba, itakuwa Anty babu abinda yafi birgeta akan tayita k'ananun maganganu......aganinsa fah. Ranar wata talata da dare around 8:00pm yaje yasamu Abban bayan sallar isha'i, Abban ma na ganinsa ya fahimci akwai abinda ke damunsa, domin jikinsa sanyi k'alau ya shiga gurin Abban, zuciyarsa duk ba dad'i don ya tsani yarinyar can bai san me yasa ba, gashi mahaifiyarsa ta nace akan dole sai ita zai aura, infact shi auran ma ba yanzu ya shirya yi ba gaba d'aya. Zuwa yayi ya zauna akusa da Abban ya gaida shi, shiru ne yabiyo baya bayan Abban ya amsa gaisuwar cike da kulawa. Mahmud rasa ta inda zai fara yayi bai san yanda zai fara fad'ar maganar ba, dayake asali Mahmud shirgin mata bai dameshi ba, shi sam bashi da matsala dasu, aganinsa mata damuwa ne sosai su, ko lokacin da ya ke higher institution d'insa ma inka ganshi da mata toh friends ne ba komai ba, kwatsam sai gashi yanzu mahaifiyarsa ta 6ullo masa da maganar aure alokacin da shi sam bai shiryawa hakan ba, amma babu yanda zai yi dolensa ya kar6i maganar kodan darajar da take dashi na mahaifiya agareshi bazai bada ita ba, yayi alk'awarin cewa da iznin Allah sai ya nuna cewa shid'in d'aah ne, kuma na halak cikakke. Ido Abban ya tsura masa da dukkan kulawa yana kallonsa , sosai ya fahimci d'an nasa na cikin damuwa sai yayi gyaran murya ya fuskanci Mahmud d'in da kyau sannan yace masa " yah akayi ne Babana"!. Ahankali ya d'aga kai ya kalli Abban nasa suka ha'da idanu take sai yayi gefe da kansa kamar mace tare da k'ak'alo murmushin k'arfin hali. Da k'yar ya samu ya tattara bayanan dake bakinsa ya dunk'ula ya furta "Ab...bah wai dama maganan yarinyar da zan aura ne, wai ko za'a je ayi tambaya". Murmushi Abban yayi sannan yace "Mahmud ba dama, wai ko za'a je ayi tambaya ko kuma kana so aje ayi maka tambaya? Murmushin yakuma yi batare da magana ba. " babana yau d'in kai ke yin abu kamar mace!? " hmm toh a ina yarinyar take? Abban ya sake tambayarshi. Ahankali ya kwatantawa Abban nasa,daga yanda yake maganar sai Abban ya fahimci abin sam baya ran Mahmud d'in musamman daya tuno ranar da Antyn ta maresa akan wata yarinya,sannan ranar da Mahmud d'in ya 'kirasa alokacin dayake damaturu akan maganan auren da Anty take yawan yi masa harma ta uzzura masa yadawo gida duk akan maganar ba shakka wannan duk tilastawar Maryam ne, ni kuwa bazan ta6a tilastawa yarona abinda baya so akan wad'anda bama sanin asalinsu yayi ba. Lokacin da Mahmud yasanar da Anty cewa sun gama magana da Abban kuma ga abinda yace ji tayi kamar ta goyashi saboda farin ciki. Tayi zaton ai Mahmud d'in zaiyi mata taurin kai ne yak'i zuwa amma kuma sai yaje, hakan kuwa ba k'aramin farin ciki yasata ba. Abbah binciken yayi kamar yanda ya fad'ad'in yayinda binciken ya d'aukesa kusan sati kafin ya gama gamsuwa da duk wani abinda yake son sani game da wannan family d'in. Bai sanar da Mahmud ba ya k'yaleshi, yana so ne yaga ko Mahmud d'in zai zo dakansa yasake tambayarsa idan yaga shiru ko yayah ,yasani cewa matuk'ar da yaddansa a auren to shi zaifi kowa rawar jiki dan ganin an kammala komai dawuri inkuwa bahaka ba ma'ana bai sakeyin magana ba toh kenan shima be wani damu da maganar ba kenan rashin damuwarsa da maganar kuma na nuni da cewa baya ra'ayin abin har ransa. Hakan ya sanya Abbah yayi gum da magabar shima yana jiran yaji daga Mahmud d'in. Rashin ha'kurin Anty yasanya ta kasa ha'kuri da taji shiru babau wanda yasake bi takan maganar sai ta tuntu6i Abbah da maganar shikuwa yace mata bincike yake yi tukunna har yanzu, ita a ganinta tunda Mahmud yariga yayiwa Abbansa magana ai itama zata iya yi masa maganan irin kamar Mahmud d'in ne itama ya sanar da ita. Bata wani damu ba saboda ita kanta bata san asalin tarihin 'kawartan ba shiyasa koda Abban yace zaiyi binciken bata damu ba. ***** Teemah kuwa tana can sun gama hutun interval d'in dake tsakanin waec da Neco d'in har sun fara Neco yau suke na biyu,tun kafin ayi nisa tafara missing d'in Mahmud domin tasaba karatun dashi sosai yake highlighting d'inta akan wasu abubuwan da bata ganesu, yanzu kuwa babu shi, sai dai tayi ita kad'ai, dayake Daddyn ya sai mata waya a satin daya gabata, arana ta uku tana tsaka da karatun data ji ba sugar sai ta 'daga wayarta ta ta 'kira Mahmud tayi ta masa complain akan ita fah bata ganewa tunda yatafi take shan wahalan karatun gashi kuma ya'ki dawowa. Lalla6anta yayi tayi yana bata ha'kuri a itakuwa tayita masa shagwa6a,ahakan ya tambayeta inda bata gane ba d'in data fad'a masa sai yayi mata bayani ata'kaice yanda zata gane. Shikenan kusan kullum in tana da exam sai sunyi waya dashi a haka har aka kusan kammala Neco d'in . 2 days to candidate d'inta Daddy suka rabu da Abban Mahmud A lagos basu ma gama abinda sukeyi ba amma daddyn Teemah yace zai dawo gida saboda graduation na Teemah yana so ya halatta. Anan Abbah yayi mata fatan alkhairi harma yace badan akwai aiki agabansa ba da shima zai je shi, Daddy ne yace bakomai ai addu'ar ma ta wadatar, sai Abban yace duk da haka ma insha Allahu idan yasamu lokaci ko bayan graduation d'in ne zaije musamman ya ziyarcesu. Farin ciki ne sosai yacika ziciyar Daddy dan yajima baiji irin hakan daga bakin abokin nasa ba, so yana jin hakan yasan ikone kawai na ubangiji dayake kawo 'karshen duk wani al'amari inma me kyau ko akasin haka. Ko da yaje gida kuwa bai sanar da mummy ba saboda yana son koda Abban Mahmud d'in zaizo toh zuwan ya zamewa mummy na bazata, kar kuma ya sanar da ita yanzu cewa Abban zaizo zuwan kuma yak'i yiyuwa duk dama ba'a fatan hakan, amma kuma idan hakan ya faru zai kasance ne kamar shine ma'karyaci a idanunta. _Comment vote and_ _share pls_ 🤞🏻 (4 those that missed Abbas insha Allahu next page zaku jishi )😃 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 6:00 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍 *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Sometimes u have 2 4give & 4get,4give them 4 _hurting_ & 4get that they even _exist_ . 🅿 *35* Lokacin da daddy zai dawo gida sai ya siyo wa Teemah tsarabar set 'din 'dan kunnan gold mai kyaun gaske afad'arsa wai zatayi anfani da shi ne ranar graduation d'insu as his gift, mummy najin haka tace "a'a sam" badai aranar ba kam sai dai ordinary day haka ta saka dan bazai yiwu taje cikin taro da wannan sar'kar ba, yanda duniya ta lalace d'innan duk dama ba'a fatan wani mummunan abu amma ai _maganin kada ayi_ _toh kada afara_ . Daddy ma dayaji bayanan mummyn take yaji ya gamsu sosai tuni ya amince da batun mummyn, Teemah kuwa na tsaka da murna ta tsinkayo muryar mummynta na fad'in haka take sai murnar ta tsaya cak, sai ta tura baki gaba tare da sake matsowa kusa da daddyn ta tana ta wani muzurai. Babu wanda ya kulata sai da yagama da mummyn kafin ya juyo ya fuskanceta yace tayi ha'kuri za'a siya mata wani wanda zata saka ranar inyaso daga baya sai tayi anfani da wannan 'din...... Kafin ma ya 'karasa fad'a mummy tace " ai already ma na siya mata wanda zata saka d'in." "Yauwa shikenan ma kin hutar damu ko my angel " cewar daddy yana murmushi. Teeamah kuwa 'kasa tayi da kanta taci gaba da kallon bangles da zoben dake tare da sar'kar bata 'kara yin magana ba har mummy tabar gurin, sai da mummyn tatafi kafin ta 'dan sake har take tambayarsa labarin yayanta Abbas, dayake tafiyan dayayin sai da yaje Abuja tukun na kafin yawuce lagos sai ta tambayeshi wai ya ga Yah Abbas kuwa dayaje Abuja?. Dariya yayi mata tare da fad'in " wato yayanki kad'ai kika sani ko? Murmushi tayi harda wani sunkuyar da kai ' kasa kamar dagaske. Daddyn ma sai yayi murmushin sannan yace" Abbas ai baya Abuja porthacourt yake aiki" Tana jin haka sai ta 'dan tura baki gaba kana tace " aini ba ruwana ma dashi daddy tunda shima ya manta dani" Ido daddy ya zaro kad'an " ke da yayan naki"? " ehh mana daddy, tunda yatafi fah ya manta dani, kuma inaji ko suna waya da mummy baya tambayata, baya cewa agaishe dani kuma mummy ma bata ta6a cemin in kar6a mu gaisa da shi ba...........shiyasa nima da aka siya min wayata ban saka numbern shi ba, ta yah Mahmud kad'ai na............ shiru tayi ta 'daga kai ta kallo 'kofa sakamakon jiyo muryar mummy datayi tana fa'din " sai kiyi ta tura bakin nan ai har sai ya ta6o 'kasa tunda ke bakijin maganan mutun " Mummy dake 'ko'karin shigowa ne ta kar6e maganar Teemahn da fad'in haka. Shiru Teemahn tayi bata 'kara magana ba,sai kawai ta sunkuyar da kanta 'kasa taci gaba da kallon abinda ke ri'ke a a hannunta, sai da mummyn ta ta iso ta zauna kafin daddy yace tura bakin me kuma tayi ne hajiya? " " Ka 'kyale yarinyyar nan ,wallahi ko kad'an bata jin magana, dubi fah 'karfi da yaji yanda ta maida bakinta kamar tsuntsuwa........ Dai dai nan ta juya ta kallo Teemah sai idonta ya sau'ka akan hannun Teemahn ganin da tayi tana jujjuya d'an kunnan ahannunta take sai ta sake fad'in " bani ni karki 6alla shi abanza daga kawowa" tafad'a tare da mi'ka hannunta saitin Teemahn.. Teemahn ma sai ta mi'ka mata sar'kar batare da wani 6ata lokaci ba. Sai da mummyn ta kar6a kafin ta d'aga kanta caraf sai suka had'a idanu da daddyn, hannu ya 'daga tare da ware yatsa 'daya ya nuno mummyn dashi yana jujjuya kai da kuma yatsan nasa duk atare da murmushi akan fuskarsa alamar " ke bah" dayake kan Teemah na 'kasa duk bata lura ba. Mummyn ma sai ta saki murmushin tana maida sar'kar a gidanta take fad'in " naji ma ana gulmar yaro na laifin me kuma yayi muku?" Daddy fa'da'da fara'ar sa yayi sai ya bata amsa da fa'din " Laifin ai harda ke , ya za'ayi kullum kuna waya da Yayanta tanaji amma baza'a bata waya su gaisa ba,kuma laifin harda naki da kema bakya ce mishi gata nan akusa". "au laifin kenan dama? Mummyn ta tambaya tana 'dan murmushi idanunta na kan Teemah. " 'kwarai kuwa, wannan 'din 'karamin laifi ne aganinki? " hmm" kawai mummyn tace. Sai daddy yace " ba hmm ba, so muke agyara adaina ware min angel 'dina agefe, shima Abbas 'din zan had'u dashi ai" Take sai yah 'daga wayarsa da niyyan 'kiran Abbas 'din sai kuma cikin rashin sa'a 'kiran be shiga ba. " Allah ya taimake shi ai" daddyn yafad'a yana mai ajiye wayar agefensa. Daganan ya cigaba da lallashin Teemahn da bata ha'kuri akan wai duk ranar daya samu Abbas d'in awaya zai yi masa masifan dan me baya son tambayanta idan suna waya da mummy." Bata dad'eba ta sau'ko daga fushin suka cigaba da hirarsu anan daddy yake tambayan ta yanda aka tsara graduation d'in duk ta fad'a masa,tana gama fad'a tace ta tashi tace zata tafi 'dakinta,sai yace ta kunna masa NTA kafin tafita. Tana kunna masa tafice bayan ta mi'ka masa remote 'din TVn. Labarai yaci gaba da kallo abinsa,dama daddy gwani ne a kallon labaran duniyah idan yana watching news hankalinsa gaba d'aya suke tafiya awurin. ***** Ranar Saturday shine ya kasance ranar da za'ayi graduation d'in Teemah, sosai wannan family d'in suka yi shiri na musamman a wannan ranar just to make their one and only daughter happy, ga wanda bai sani ba idan ya shiga gidan aranar ze yi zaton ko wani d'an hidiman biki akeyi agidan, amma ga wanda yasani sai de yace masha Allah. *'Karfe 9:00am* Teemah ce tafito cikin wata ha'da'd'diyar gown d'inta d'inkin tela kalar ja, d'inkin ba 'karamin kar6anta yayi ba, 'dass ya zauna mata kamar ajikinta aka yi 'dinkin rigar, yayinda kanta yake 'daure da head golden colour kamar ba da hannu akayi 'daurin ba, tsabar yanda ya zauna akanta , wata mata data amsa sunan ta ce afagen make-up ita tayi mata 'daurin, wanda mummy musamman ta sa aka nemo mata matar dan kawai tayi wa Teemah kwalliyan graduation d'in, gefen kafad'anta shima golden colour veil ne mai kyan gaske , ba naa ce ga adadin kud'insa ba dan ko nima bansan lokacin da mummy tayi wannan siyayyan ba,ga wani high hill d'inta mai kyau shima duk kalan gyalan nata. Turare kuwa ba laifi 'kanshin na tashi dai-dai ajikinta bata saka daya wa ba dayake Teemah ba son anfani da turare mai 'karfi take ba body spray kawai ta fesa ajikinta tafito. Kallo 'daya zaka yiwa Teemah kayi zaton ko amarya ce dan tsabar yanda tafito tamkar wata tauraruwa. Ahankali take tafiya tana wani basarwa, ita adole irin an girman nan. Kalle-kalle takeyi acikin harabar gidan tana 'dan waiwaya wa, sai kuma tacigaba da tafiya yayinda ta tunkaro inda mummy ke zaune ahankali. Tun daga nesa da mummy ta hango ta fara'arta ya 'karu aranta take fa'din _tubar kallah masha_ _Allah_ Allah yah ya raya minke 'yata. Kafin Teemahn ta iso gurinta ma harta mik'e tsaye tana murmushi Teemah na isowa kuwa ta bud'e mata hannu Teemah kamar jira takeyi tafad'a ciki tana dariya. Dariya mummyn ma tayi dukkansu sai ya zamana ha'koransu kawai zaka gani afili tsabar yanda suke jin dad'i fuskarsu kawai zaka kallah kasan cewa ehh lallai suna cikin farin ciki. Mummy aranta take tayiwa Teemahn addu'an kariya daga kowani irin abun k'i. Koda ta saki Teemahn ma abinda tafara fad'i azahiri shine " Masha Allah, yarinyata anzama 'yanmata, Allah ubangiji yasa wannan level d'in yah 'kare kenan har abada, Allah yasa anyi a sa'a, Allah yasa ba'a yi gaba anbar baya da 'kura ba". " Ameen yah Allah " Teemahn ta fad'a tana d'an dariya. Sannan tace mummy ni nagama shiri yanzu zan wuche,kinsan ance mana kar muyi african time, gashi ma yanzu 9:00 d'in kusan da rabi ma "! Ta 'karashe tana mai duba agogon cikin wayarta.Dayake ance 'karfe goma ake bu'katan su awajen gaba d'aya candidates d'in. " toh kije ki samu Habibu ya sauk'e ki, sai mun iso muma" Juya wa tayi tare da fad'in " toh mummy sai kun iso " " yauwa kar amanta da addu'an barin gida fah" Wannan karan kam da kai ta amsa batare data juyo ba. 10:00am aka fara programme d'in,Teemah na can ita kad'ai daga ita sai 'kawayenta, akai akai take duba hanya ko zata hango mummy amma shiru harta gaji ta ha'kura ta maida hankalinta ga abinda ke gabanta. *10:35am* Mummy na tsaka da aiki sai ta tashi ta je kitchen ta d'auko abu fitowan da zatayi kamar ance ta kalli harabara gidan sai idanunta suka sau'ka akan Abbas daidai ya bud'e mota ya fito. Aikuwa mantawa da abinda ta 'dauko in tayi da ke ri'ke a hannunta,da sauri tafara tafiya ta nufi wajen data hango shi d'in, shima da farko be lura da zuwan nata ba sai da ta kusan isoshi kafin ya ankara da ita, aikuwa sai yafara murmushi kana yace " mummy har kin ganni ne ". " ai dole in hango ka wannan irin suprise haka Abbas"! " wallahi kuwa mummy". Tafiya suka farayi ska nufo cikin gidan atare yayinda mummy take tambayarsa ya wajen aikinsa yace " aiki kam Alhamdulillah sai godiyan Allah kawai". Zuwan nashi ya matu'kar bawa mummy mamaki domin bata ta6a kawo cewa zai halacci taron ba, sai kuwa gashi nan yazo. Sosai taji dad'in zuwan nashi, basu ko gaisa da kyau bama dashi dan hankalinta na wajen aikin data bari anayi acikin gidan, data d'an tako masa tace mishi yaje 6angaren daddyn su yana ciki be fita ba tukun na, bari ta dubo abu tana nan zuwa yanzu itama, tana gama fad'a sai ta juya ta wuce cikin gidan. Shikuma sai ya tsaya awajen, sai da yaga takoma kafin nan yajuya ya koma inda suka yi parking motarsu ya je ya ciro wani kwali me d'an girma amma ba sosai ba,wanda suke taren na jikinsa na rawa yake 'ko'karin 'dauka masa sai Abbas ya dakatar dashi da hannu yace yayi zamansa ba matsala zai 'dauka kawai ga dukkan alamu drivern sane mutumin duba da yanda yake ta ambaton " sir " adukkan maganar dazata had'a shi da Abbas 'din. Lullu6e kwalin yake da wrapping sheet baka gane kami game da kwalin faa ce size 'din kwalin. Sai da ya kai dubansa inda yaga mummy ta nufah 'dazu sai yaga hankalinta gaba d'aya baya wani guri aikin dake gabanta kawai ne tasa agaba ga da alama a'kage take taga aikin ya kammala ganin hakan dayayi yasa ya taho da sauri ya nufi 'k'ofan babban parlour, amma cikin rashin sa'a daf dazai shiga parlourn idanun mummy ya hango shi akaro na biyu, hannunsa ta duba da wuri ganin cewa yana ri'ke da abu ahannun sai dai bata wani gane abun ba sai tayi zaton ko jakar kayansa ne. Da yake yasan kan gidan sosai batare da an jagoran ce shi ba sai ya wuce direct 'dakin Teemah ya ajiye kwalin dake hannunsan kafin ya mi'ke tsaye sai da ya tsaya ya 'karewa 'dakin kallo kaf kafin ya fito ya nufi 6angaren daddyn. Koda yaje 6angaren daddyn kuwa sallama yafarayi sai yaji shiru ba'a amsa masa ba, sai da ya sake yin wata sallamar sau d'aya yaji still ba'a amsa ba sai ya d'an tsaya na 'dan da'ki'ku, 'karan TVn daya jiyo ne yasa shi fahimtar dalilin dayasa daddyn be ji amon muryarsa ba, kuma yana da yak'inin cewa koda zai yi sau ba adadi ne daddyn bazai ji ba matuk'ar TV d'in akunne yake. Sanin cewa daddyn shi d'aya ne acikin 'dakin yasa ya tura k'ofar tare da sake yin wata sallamar ciki-ciki, ahankali ya maida 'kofar ya rufe bayan ya shigo d'in, sai ya tsaya kamar an bashi umarni, daddyn ya tsaya yana 'karewa kallo yanda yasha manyan kaya yawani fito shar dashi tamkar wani sabon matashi. Ahankali yafara takawa yayinda salon tafiyar tashi ya matu'kar amsan zubi da tsarinsa ga duk wanda yasan menene had'uwa toh ba sai na gaya masa yana kallon Abbas yasan cewa ya ha'du sosai, be tsaya ko'ina ba sai dayaje gaban TV d'in kafin ya tsaya, sai dai kuma be bari daddyn yaga fuskarsa ba,baya ya juya wa daddyn da sauri ya maida fuskarsa take fuskantar inda bangon da TVn yake bayansa kuma na kallon daddyn. Daddy da bai san anshigo bama balle yasan waye ya shigo kawai sai yaga mutum tsaye ya tare masa news d'in dayake gani, lumshe idanunsa yayi dayaga hakan tsawon dak'ik'a goma kafin ya bud'e tare da fad'in " _ABBAS_ " . Dariya Abbas d'in ya kwashe dashi sannan ya juyo yafara tahowa zuwa inda daddyn ke zaune. " ya akayi ka gane ni da wuri haka daddy bayan baka kalli fuskata ba " ya tambaya yana kallon daddyn bakinsa d'auke da murmushi. " toh wa nake dashi da zai min haka banda kai" Daddyn ma yabashi amsa yana murmushin shima. Dukka sai suka yi d'an takaitaccen dariya. sai daddyn ne ya kuma cewa " ja'iri daga ina haka kamar an jeho ka?" " wallahi kuwa, escaped nayi daddy yau d'innan za koma ma kafin anemeni, ba shiri nataho kuma akwai ayyuka agabana". " haba kuma sai kace dole ai daka bari zuwa wani lokaci in kasamu isasshen time basai ka zo ba." " ba na so na.....,,. Daidai nan mummy tashigo da sallamarta abakinta. Sai Abbas d'inma ya dakata daga maganar da ya yi niyyan fad'i duk sai sukayi shiru suka jira harta iso ta zauna. Barka da isowa tayi masa tare da fad'in " dazu ina sauri bamu wani gaisa da kyau ba ". Murmushi yayi mata kawai sai ta sake fad'in " gaskiya ka shammace mu Abbas gashi bansan da zuwanka ba ko muhalli ba'a gyara maka ba" . " Ai ba komai mummy ina ma kan hanya ne yanzu zan wuce" " dawuri haka?, ka de bari ka 'dan huta ka'dan de ko,ai nayi zaton ma graduation d'in kazo halatta dana ganka"! Abbas cewa yayi wai " a'a shi yama manta da wancen batun ai tuntuni tun bayan data sanar da shi abin be kuma zuwa kansa ba.". Su kuwa duk sai suka yadda akan ehh dagaske yamanta d'inne ba mamaki ko dan saboda irin aikinsan,wani lokaci abubuwa kansha kan mutun sosai. Abinci aka shishshigo dashi da abin sha aka jejjera sai da aka gama sannan mummy tace toh bismillah ya d'an samu ya ta6a ko kad'anne ma kafin ya wuce d'in. Dukka atare suka mik'e har daddyn suka nufi wajen da aka jera abincin, mummy na zuzzubawa tace " kamar kuwa kasan kullun sai anmin mita agidan nan, harda su kaiwa 'kara na wai bana bata waya kuma kaima baka tambayarta ko ka 'kira wayan ". " daddy ne ya kar6e da fad'in toh dah d'in 'karyane?, ai da gaskiyarta" , daganan sai ya dawo da dubansa wurin Abbas yace " me yasa baka tambayarta awaya idan ka'kira kuma ko sa'kon agaishe ta ma baka ta6a fad'a ba." Dukkansu sai maganar daddyn da yanda yayita kamar titsiye sai ya basu dariya, shima daddyn sai ya taya su dariyar, sai da suka tsagaita kafin yace " toh haka nayi al'kawarin zanyi ku kuma naga kuna min dariya". Abbas baiyi magana ba sai mummy ce tace "ai idan kabiye Teemah kam abinda yafi haka ma zakayi shi". Murmushi sukayi daganan suka fara cin abincin da mummy tagama zuzzuba musu, mummyn kuma tafita abinta ta basu waje tatafi domin ta shirya. Abbas na gamawa yacewa daddyn shi zai wuce dama ya shigo ne brief ya gaishe su, cikin sa'a ma kuma saiya samu daddyn nagida. Albarka da addu'o'i sosai daddy yata yimasa sannan ya rakoshi har wajen parking inda drivernsa yake, tambayar drivern daddy yayi wai anya kuwa yaci abinci yace" ai be san cewa tare suke ba da an masa iso shima", sai ya 'daga hannu ya d'an mari 'keyar Abbas yace " ai duk laifin kane dabaka fa'da cewa dawani kuke ba " Abbas 'kasa ya d'anyi kad'an tare da shafa gurin kamar irin yaji zafin nan, sai yace " Afuwan daddy Allah na manta ne shiyasa". Murmushi sukeyi gaba d'aya har drivern ganin yanda Abbas yake yi agaban daddy kamar bashi ba amma idan awurin aiki ne ko ha'koransa da wuya kake gani. Sai drivern ma yace " yalla6ai aina ci abinci Hajiya ta aiko an kawo min anan" " Ahh toh shikenan sai ya juya ya kalli Abbas d'in ya sake cewa "Allah ya taimakeka da sai ka jira yaci abinci duk da saurin naka". Abbas da daddy kawai yayi sallama ko mummyn be jira sun sake had'uwa ba yayi tafiyarsa. _Comment,vote and_ _share pls_ 🤞🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 6:00 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* ⚠ *NOT EDITED* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍 *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* SMILE ….. It irritates those who wish to destroy you. 🅿 *36* Suna fita ya fad'awa drivern sa inda yake so ya kai shi, koda suka je kuma basu tarar da kowa ba face mai gadi. Zuwa yayi ya mi'kawa mai gadin hannu suka gaisa sannan ya tambaye shi inda 'daliban suke take mai gadin ya sanar dashi. Abbas godiya yayi masa tare da juyawa ya koma cikin mota driver yaja suka nufi wajen. Da kwatance drivern ya gane wurin koda ya isa yayi parking a wurin Abbas kamar bazai fito ba kusan 10:mins kafin ya 'daga hannu ya duba agogon dake hannunsa sai yayi maza ya fito daga motar. Tsaye yake jingine ajikin motar yana ta 'karewa 'dai'dai kun mutanen dake wulgawa kamar me karantar wani abu tattare dasu. Tafiya ya fara cikin 'kasaita in ka ganshi zaka zaci daga wani gidan sarauta yafito, ahankali yake tafiya ya nufi hall 'din daya fi tunanin nan ne ake programme d'in dan anan ya ga anfi taruwa. Daf da zai shiga hall 'din daga gefe ka'dan ya idonsa ya hango masa ita cikin gungun 'dalibai sunata surutu ga dukkan alamu shirin yin pix suke yi ko kuma har sun 'dauka domin dukkansu zagaye suke da photo grapher ne. Tsayuwa yayi kamar andasa shi awurin shi bai shiga ba shi kuma be matsa daga inda yake tsayen ba. Be san mai suke tattaunawa atsakaninsu ba shi dai kawai sai yaga ta fara dariya, yayinda da dariyar tata ta matu'kar birgesa, sosai ya tafi da yanayin tsari da kwalliyar da ta tsantsara ayau d'in. Aransa sai yaji kamar tunda yake da ita be ta6a ganin kwalliyar sata amsheta irin wannan ba. Yanda ya 'kura mata idanu sai ajikinta taji tamkar ana kallonta, tana cikin dariyar sai ta 'dan fara dube-duben gefen ta. Garin dube-duben nata sai idanunta ya hango shi take kuwa idanunsu ya sar'ke cikin na juna, Abbas lumshe idaunsa yayi ita kuwa bata gane shi ba koka'dan saboda akwai 'dan rata atsakanin su kuma bata ta6a zaton ganinsa awannan lokacin ba, hakan yasa kawai tayi masa kallon kamar tasanshi sai ta kauda kanta gefe da sauri. Sai de kuma sam taji zuciyarta takasa nutsuwa da hakan sai ta 'kara juyawa ta kallo wurin, wayam tagani babu kowa abin ya matu'kar bata mamaki hakan kuwa yasa tafara tafiya ahankali ta baro cikin mutanen. Tsoro ta fara ji kardai ace ba mutun tagani ba yanzun, amma ace daga ganin mutun sai kuma tarashi. Allah yasa dai mutun ne inbahaka ba ai nashiga uku! Haka taketa nanatawa azuciyarta,yayinda tsoro yake 'kara cika mata zuciya aduk wani step 'dinta. Caraf taji ancafko hannunta tabaya,wani firgita da tayi shi kanshi sai da yaji wani iri, tana shirin k'walla ihu sai yasake hannun nata dawuri ya rufe mata baki da hannun. Bakinsa ya matsar daidai kunnanta ahankali yace mata " bana son hauka ki juyo ki ganni I'm your b........... Sai kuma yayi shiru ya 'kirasawa, ido ta zazzaro waje dan tana jin amon muryarsa tagane shi, muyrasa ko acikin dubun mutame zata iya ware shi. Bakintan daya rufe yasake mata, yana sakewa kuwa ta juyo da sauri ta fuskance shi, da 'karfi tace " Yah Abbas kaine dagaske"?! Tsaye yake agabanta ya maida hannayensa duka cikin aljihun wandonsa ya 'kurawa fuskarta idanu tamkar yau ne farkon ganinsa da ita. Koda ta tambayeshin ma be ko nuna alamun yaji ta ba sai data 'kara maimaitawa sannan ya 'daga mata kai alamar ehh shi 'dinne. Take sai 'yan shagwa6anta suka motsa mata ta ha'de rai ta tura baki gaba yanda tayin sai ya 'kara mai data 'yar 'karamar yarinya. Murmushi yayi aransa yace " mai hali kenan". Azahiri kuma sai yace mata " me kuma yafaru naga kin 6ata rai ohh aren't u happy 2 see me?". Sai ta 'daga kanta sama. Waje ya fito da idanunsa tare da fa'din " saboda me"? "Bakai bane ka tafi ka manta dani?" " ohh sorry sis who told that na manta dake?, Allah kullun kina raina kinji" Idanunsa akanta yake maganar da dukkan kulawa amma sai ta'ki yarda tawani karya wuya irin ita bata yadda ba 'dinnan. " toh shikenan tunda yanzu nazo bashikenan ya wuche ba"? Sai ta jijjiga kanta alamar "a'a". Daya rasa yadda zaiyi da ita sai 'daga hannayensa duka biyu yakamo kumatun ta dashi, jijjiga kan yayi yana murmushi yace " stubborn head 'dinnan har yanzu yana nan ko?. Yanda yayi 'din ita kanta yabata dariya amma sai ta juya masa baya tana dariyar 'kasa-'kasa. A'dan nesa dasu kad'an ta hango wata 'kawarta dasuka fara 'kawace lokacin da aka fara waec, ta yaba da hankali da nutsuwa irinna yarinyar shiyasa ma bata yi mata mugun hali ba irin yadda tajewa sauran 'kawayenta. Tana ganin yarinyar sai tafara tafiya da nufin 'kiran ta taga yayanta. Takunta biyu kafin tayi na uku taji Abbas ya 'kira sunanta " FATEEMA" cikin wannan lion voice 'dinsan nan me ratsa mata zuciya. Take ta tsaya cak tare da waiwayowa ta kalle shi, ahankali ya tako ya iso inda take tsayen, shima ya tsaya. "Tafiya zakiyi ki barni anan?" Da sauri ta jijjiga kanta. " toh menene"? ya sake tambayarta?. Kasa magana tayi awannan lokacin domin irin kallon da yayan ke mata ya banbanta dana kullum, jikinta duk taji ya mutu sai kawai tayi 'kasa da kanta. Bata zata ba sai taji yasa hannunsa yakamo hannun ta nadama ya bu'de yasa ka mata wata takarda sannan ya maida hannun ya rufe mata. Da ido tabi hannun nata da kallo yayinda ta matse hannun nata gam-gam ta ri'ke takardar da kyau dukda bata san ta menene ba amma tanaji ajikinta tamkar takardan nada wani kyakkyawan muhimmanci arayuwarta. Sai daya sake mata hannun ya maida nashi 'daya cikin aljihu yayinda 'dayan ke sau'ke daga gefensa kafin yace mata " zan tafi Fateemah inada aiki a office banida isheshen time yanzu " Dasauri ta 'daga kai takalleshi sai yayi murmushi yace " sai munyi waya". Yana fa'dar hakan yajuya yakoma mota be ko sake waiyowa ya kalleta ba, yana shiga kuwa driver yaja kamar daman jira yakeyi ashigo. Ita kuwa mamaki hanata motsawa yayi saboda data ganshin ko dawasa bata kawo cewa ze koma dawuri haka ba. Har suka 6ace daga wurin bata sani ba, tana can tana tunani. Lokacin da runanin ya tsaya kuma koda ta kalli inda taga yayin gani tayi babu kowa. Dasauri ta 'daga 'kafa ta taho gudu gudu ko zata ganshi amma ina bata ga kowa ba illah 'kuran wata ba'kar mota data hango awajen gate tana shirin fita. " wai dagaske ne......yah Abbas ............kuma ka sake komawa".?! Kamar ta fasa ihu haka taji amma kuma bazata iya ba. Tana tsaye bata bar wurin ba taji ana mata horn sai tajuya dasauri takalli wajen zatonta shine yadawo amma sai taga motar gidansu ne wannan 'din. Mummy ce ta bu'de motar tafito ta nufo ta dasauri domin yanda taga Teemahn abin ya 'dan bata tsoro. Mummy na isowa inda take kawai tafa'da jikinta tayi lamo, sai da mummy ta 'dan bata 3mins tayi backin up kafin ta 'dagota ta tsayar da ita agabanta sannan ta tambayeta " me yafaru?. " mummy Ya.....yah.. ne " Tayi maganar tana nuna hanyan gate. " wani yayan me kuma yafaru dashi?" Mummyn tafa'da tare da jijjiga ta da 'dan 'karfi. " mummy yah Abbas ne......yatafi..... Tana gama fa'dan hakan sai ta fa'da jikin mummyn tayi shiru. Mummy data fahimci 'yartata sai kawai tabarta ayanda take ajikin nata taringa bubbuga bayanta har tasamu ta d'an dawo daidai kafin tasamu da 'kyar ta lallesheta har se da taga ta warware sannan takama hannunta suka shiga ciki. Tun daga lokacin Fateema bata 'kara yin wani abu da kuzari ba yayinda mummy kuma take jin bada'di tare da tausayin 'yartata. Tana tsoron kar dai ace yarinyar nan soyayya ce takamata domin kallo 'daya zaka mata ka fahimci badaidai take ba, inkuwa hakane ai ta shiga uku!, yaza tayi ta iya sada Fateemah da farin cikin ta, idan yazamana shi'din ba haka bane azuciyarsa?". Domin tasan it's hardly ace mutun kaman Abbas yaso Fateemah, kai Allah ma ya sauwa'ke Alla ya kiyaye ya tsare mu da sharrin zuciya.".( Ameen) Atare suka koma gida koda aka tashi a wurin......ahankali Teemah ke tafiya tamkar mai tsoron taka 'kasa mummy kuma na bayanta itama tana binta ahankali . Jijjiga kai mummy tayi data ga Teemah ta nufi 6angaren da 'dakinta yake daga shigowanta parlourn ko tsayawa bayiba ta wuce abinta. Babu komai atare da ita sai mayafinta da kuma wannan takardan da Abbas ya bata, tun lokacin da yabatan har yanzu bata canja masa ri'ko ba bata kuma bu'de taga miye aciki ba. Tana shiga 'dakin ta tura 'kofar ta datse da makulli sannan tacire head 'din dake kanta tayi jifa dashi akan gadon tare da mayafin baki 'daya tana niytan cire rigar ne taji hannunta da abu, da sauri ta bu'de hannun tare da kallon shi da wuri domin sai alokacin ta tuno da cewa Yah Abbas ne yabata takardar. Amma saboda ri'kon ' karfi datayiwa takardan ga kuma gumin hannunta da yake gimtse tsawon lokaci, su suka had'u suka narkar da takardan a hannunta. Da6as ta zauna abakin gado idanunta nakan hannun nata koda tayi 'ko'karin raba takardar da hannunta sai taga ya 'kara yagewa. Duk iya 'ko'karinta naganin ta fahimci abinda takardar ke 'dauke dashi takasa saboda daidai inda akayi rubun daidai wurin ne yafi samun matsala. Dolenta ta tattara ta cire da me 'dan girma da wanda ya raki6e ahannun nata ta ajiyesu acikin side drawernta. Sannan tacire doguwar rigar dake jikinta yarage daga ita sai pant, underwear da bra, ahakan takoma takwanta rigingine akan gadonta. Ita kanta bata mecece damuwarta ba, haka kawai sai take jin ta wata iri, tamkar bata da ishashshen lafiya. Nocking 'din 'kofa taji anfara yi kawai sai ta mi'ke ta nufi bayi batare da ko cire ragowar kayan dake jikinta ba, towel ma ahannu tashiga dashi bayan ta jashi akan 'kofar bayin. Ba ita fito a bayin ba sai kusan 5:00 hakan ma dalilin tunowa da sallar la'asar 'din da batayi bane shiyasa tafito dasauri. Tana fitowa kuwa idanunta suka sau'ka akan wannan kwalin da Abbas ya ajiye ma da tun shigowanta bata lura dashi ba sai yanzun. Sallar dake gabanta ne ka'dai ya dameta adai dai wannan lokacin, dan haka kallon arziki ma kwalin be samu ta nufi wurin kayayyakinta ta 'dauko wanda take son sakawa ta sakashi sannan ta shimfi'da dadduma tare da zunbula hijab ta tada sallahnta. Comment, vote and share pls🤞🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 6:00 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍 *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi masoyana* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* “Time is free, but it’s priceless. You can’t own it, but you can use it. You can’t keep it, but you can spend it. and once you’ve lost it you can never get it back.” 🅿 *37* Koda ta idar bata bi takan kwalin ba har yanzu, kwanciyarta kawai tayi sai dai tana kwantawan mummy ta fa'do mata arai kawai sai ta mi'ke da hanzari tatafi wurin mummyn dan tasan dole zata damu idan tajita shiru. Murmushin 'karfin hali ta 'ka'kalawa fuskarta yayinda ta tunkari inda mummyn take, koda mummy taganta ahakan kuwa sai ta 'dan ji dama dama. Murmushin tayi itama sannan tace " yanzu kuwa nake so na aika aduba minke sai kuma gashi kin fito"! Batayi magana ba sai da ta 'karasa kusa da mummyn ta zauna kafin tace " kaina ciwo mummy sosai" tayi maganar tana wani yatsine fuska tare da dafa goshinta da hannunta 'daya. " haya niya ai, bari anemo miki magani kisha zaki d'anji daidai". Mummy tayi maganar tata cikin kulawa sai ta 'kara da fad'in " ki koma 'daki ki kwanta ki 'dan huta idan ankawo maganin sai kisha ". Kai Teemah ta 'daga alamar " toh tare da mi'kewa tsaye ta kama hanyar 'dakin nata. Koda takoma 'dakin kuwa kwanciya tasakeyi, so take tayi bacci amma sam sai taji takasa yin baccin ma fuskar Yayanta ka'dai ke yimata gizo tana ganin tamkar bashi 'din bane dagaske tagani. Wayarta da tun safe take ajiye a gefen mirror itace tayi 'kara alaman shigowan sa'ko kuma 'karan ne ya yanke mata tunanin yayantan datakeyi. Kuma sai alokacin ma ta tuna da wayarta saboda tunda tafara shiri bata 'kara bi takan wayar ba sai da tagama shiryawa ne ta 'dauko wayar ahannunta ta kashe selfii bayan tafito da nufin tafiya wurin graduation d'in sai kuma ta ji ri'kon wayar ya dameta shine ta aiko aka ajiye mata ad'aki. Toh shiyasa bata 'kara bi takai ba sai kuma yanzun dataji wayar tayi 'kara. Ahankali ta tashi taje ga wayar bawai dan 'karar sa'kon dataji ba " a'a " kawai jii tayi tana bu'katan ganin cikin wayar tata da ta 'dau tsawon awanni batare da sun gana ba. Dawowa tayi ta kwanta rigingine kanta nakan pillow yayin da 'kafafun ta ke ajiye akan katifa ta wani had'esu guri d'aya. Koda ta bu'de wayar sa'kon Mahmud tafara cin karo dashi a fuskan wayar ga dukkan alamu shine sa'kon da ya shigo 'karshe 'dan mintina 'kalilan dasuka gabata . Bud'e sa'kon tayi domin ganin me aka rubuta mata . " wai nayi laifi ne bansani ba? " Haka taga anrubuta Sai tayi reply da " haba laifin me zakayi kuma yayah"! Daga nan tabar wurin messages 'din ta koma taga tarin missed calls 'din data tara duk daga yayanta Mahmud. Data ta bud'e tashiga whattsap anan ma takuma cin karo da sa'konni da dama na groups dakuma na wasu contact d'inta ciki kuwa harda na Mahmud inda yake mata good wishes na gama makarantar ta, cikin sa'a kuwa sai taga yana online hakan yasa ta rubuta " Yayah" Tayi sending. " Na'am, lil sis yau me nayi ne haka" ? Tasan wannan tambayar duk bazai wuce akan tarin missed calls d'in data gani yayi mata bane hakan yasa ta bashi ha'kuri tare da yi masa bayanin rashin fita da wayar da bata yi ba ne shiyasa. Tace sai yanzu ne dawowarta taga missd calls d'in kuma ciwon kai yasata agaba. " eyyah sorry lil sis zakiji sau'ki kinji, ina kinsha Magani?" " a'a mummy ta aika asiya min yanzu" Yace " wish u quick recovery owk". Itakuma ta rubuta masa " Thanks". Sannan ta 'kara rubuta " Yayah " Shikuma yace " Na'am 'kanwa".! " Yah Abbas yazo yau "! " Haba ai be gaya min zaizo ba, amma gaskiya ya kyauta sosai , ki gaishe min dashi before muyi waya". " Ai ya riga yakoma ma " " Ok ba matsala kinsan yanayin aikinsa ai sai a hankali". Bata 'kara yin wata magana ba bacci ya 'dauke ta da wayar akan cikin ta, koda mummy ta zo kawo mata maganin ma tun a'kofa data hango ta tana bacci sai ta juya kawai batare da ta shigo ba. Shima Mahmud 'din daya ga bata 'kara magana ba sai ya 'kyaleta azaton shi ko ciwon kan ne ya matsa mata, shiyasa ya barta yace ta huta . ***** Washe gari bayan ta idar da sallahn asubah tayi addu'o'inta kamar yadda tasaba yi kullun, sai data karanto adduar safiya da maraice ta shafa sannan sai tasa hannu ta jawo wannan kwalin da nufin ganin abinda ke ciki. Ledan dake jikin ta yage sannan tasa hannu ta bud'e cikin kwalin. Hannu tasa ta ciro jakan dake sama aciki ta ajiye ta 'kara ciro wani tagani. Dogin riguna ne aciki masu kyaun gaske irin 'yan italy 'din nan kusan kala hud'u wanda idan ka saka ajikinka ako'ina kowa yasan sunsha kud'i ba 'karya, sai takalma suma masu tsada guda biyu abinda kad'ai ke cikin kwalin kenan. Ita kanta sun mata kyau sosai yayin da 'daya daga cikinsu yafi 'daukan hankalinta mai kalan coffee. Tashi tayi ta tsaya sai ta d'aga rigar ajikin ta tana kallo kamar mai gwada tsayi nta da rigar. Adaidai lokacin kuma sai ga mummy ta turo 'kofarta tare da yin sallama wanda tazo ne da niyyan ji da ganin jikin Teemahn ko yaya ta kwana. Kafin Teemah ta amsa sallamar sai mummy a firgice tace. " ke wannan fah daga ina kika samu". "Anan na nagani nima " tafa'da tare da nuna gurbin da ta ga kwalin a ajiye. Da mamaki mummyn takalleta tace "anan kuma Fateemah". Sai Teemah ta d'aga kai alamar " ehh" " toh wah ya ajiye"? Inji mummyn Sai Teemah ta jefa mata tambaya inda tace " mummy bake kika siya min bane"?. Tayi maganar tana kallon fuskar mummyn nata. Mummy bata kulata ba sai tasa hannu ta kar6i rigar dake hannun Teeman aranta take wassafa kyau da tsaruwar rigar, sannan kuma ga uban kud'i, idan batayi kuskure ba tace rigar tana kaiwa kusan Eighting thousand Naira (18000) akasuwa, zama tayi abakin gadon Teemahn tare da jawo kwalin ta firfito da ragowar kayan dake ciki. " yah salaam " Tace aranta " toh daga ina haka" Ta sake tambayar kanta. tace kuma ba daddyn Teemah bane ya kawo domin shi tasan yariga yabata gift 'dinta tun lokacin daya dawo daga tafiya and she believe that matu'kar zaiyi abu toh sai ya sanar da ita.! " toh wannan daga ina haka!".? Zuwa Teemah tayi ta zauna akusa da mummyn saboda yanayin dataga mummyn tashiga itama kuma sai alokacin tunani wanda ya kawo kayan ya shige ta musamman data ga duk hankalin mahaifiyarta ya tashi da ganin kayan ,sai ta dafa ta tace " mummy wani abu ne?". " a 'a ina tunanin ta inda kayan nan suka fito ne"! Daga nan mummy n tasake yin shiru tana kallon Teemahn badan tariga tasan halin 'yarta ta ba da sai tace tasan daga inda kayan suke tunda har acikin 'dakinta aka gani, amma kuma ahalayyar Teemah babu 'karya sai dai uban rashin ji da taurin kai sannan bata 6oye gaskiyarta ko kad'an ita. _ABBAS_ shine ya fad'o ran mummy atake wanda hakan yasanya ta sauke sassanyar ajiyar zuciya tare da hamdala acikin zuciyarta. Domin da farko har kanta yafara caji hankalinta ya d'an soma tashi narashin sanin asalin takamamman inda kayan suka fito. Amma tuno cewa Abbas yazo ayau d'in duk sai wad'ancan abubuwan suka kau, mussamman data tuno lokacin data ganshi ze shiga parlour hannunsa rik'e da wani abu wanda tun alokacin bata 'kara tunowa da neman sanin miye abin ba, zaton ta jakar kayansa ne tagani ahannun nasa , sai kuma yanzu tafahimci menene abin tunda shi da be zo zama ba ina yaga ta shigowa da jaka har gida. Murmushi tayi abayyane data tuno halayyar Abbas d'in shi sam baya son inzaiyi abu wani yasani komiye dalili oho, sai dai hakan da yakeyi d'in ita kanta yana birgeta domin halayya ce tagari ga dukkan wani musulmi abin kwaikwayo ga kowa. Kallon Teemah tayi da tun 'dazu ta zuba mata idanu tun sanda tafara murmushin nan tace " inajin Abbas ne yakawo dan naganshi da kaya 'dazu dayazo lokacin hankalina nakan aiki". Sake 'daga rigunan mummy tayi tare da jujjuya takalman ahannunta tace " size 'dinki ne kuwa beyi kuskure ba". Kar6an takalmin Teemah tayi tana 'ko'karin gwadawa a'kafarta. Yayinda mummy taringa sanya masa albarka, fatan alkhairi, da kuma fatan gamawa da duniya lafiya da ganin haske adukkan al'amuransa. Acikin zuciya Teemah taringa amsawa da Ameen. Sai mummy tace " ki ajiye bari anjima anunawa daddynki shima yagani " . Da " toh " Teemah ta amsawa mummyn, kuma sai asannan ne mummyn tace " ya ciwon kan naki " Dariya Teemah tayi tace " sai yanzu kika tuna da ni ko mummy". " 'kaniyarki wannan 'dinma ai duk saboda kene kikaga nashiga tunani."...... Daganan suka kwashe da dariyar dukkansu har mummyn gaba 'daya. ***** Kwana biyar bayan graduation d'in Abbah ya sau'ka a damaturu.............. _Comment,vote_ _and share_ 🤞🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 6:00 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍 *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Don’t be ashamed to be different........ Be proud that Almighty Allah made you like no one else. 🅿 *38* Mummy na can uwar 'dakinta taga daddy ya 'kirata awaya akan wai tafito parlour yanzu yanzun nan. " lafiya kuwa?" Ta tambaye shi Sai yace " lafiyar kenan Khadeeja". yana gama fad'an haka ya yanke 'kiran sai kwai ta tashi ta fito parlourn domin ams a 'kiran Daddyn. Sai dai tun kafin ta 'karaso tafara jin zuciyarta na tsinkewa, bata san dalili ba amma sai dole hakan yasa yanayin saurinta ya ragu ba kamar yadda ta farao tafiyan da farko ba. Koda ta iso parloun ma ciki-ciki tayi sallama bata damu da ko daddyn yaji ko be ji ba domin damuwar luguden da zuciyarta keyi ne ka'dai aganbanta awannan lokacin. Bata ankara da ko mutune nawa bane zaune a d'akin ba har se da ta iso sannan ta 'daga kai a'ko'karinta na neman inda ya yadace tazauna sai kawai idanunta suka hango mata yah yusuf zaune agefen daddy. Yatsa ta 'daga tare da fa'dan sunan shi cikin tsananin mamaki " Yah........... Yusuf.........kaine ko............ko.........i"adanuna ne...? Murmushi yayi mata sannan yace " Nine nan ba idanunki bane Khadija 'Karaso ki zauna". Ya 'karasa maganar tare da nuna mata wajen zama. Bata 'karaso inda yake 'din ba sai zune jagwab a inda take tsayen tama kallon shi yayinda idanunta suka da'de da fara zubda ruwan hawaye..... " Ashe zan sake ganin 'dan uwana aduniya........ashe da rabon in sake ganin ka, Yah Yusuf me yasa ka manta dani, kamanta da koni wacece agareka...ka manta da............ Daidai nan daddy ya dakatar da ita da fad'in " Khadija " ! Da 'karfi yayi maganar wanda yasa dan dolenta tayi shiru sai dai hawayenta dasuka kasa tsayuwa. Teema ce ta taho da niytan zuwa gurin mummyn ta ta sai ta tarar dasu a parlour dukkansu shiru sai mummynta dake zaune a'kasa kamar me neman gafara tana kuma share hawaye. A sukwane ta iso gurin mummyn ta zauna itama kusa da ita tafara tayata goge hawayen batayi magana ba amma ga dukkan alamu kukan take shirinyi itama. Daddy da yaga haka sai ya 'kirata akan tazo wurinshi sai kawai ta kalleshi batare da tayi niyyan tashi daga jikin mummyn ba tace " daddy me yasami mummy"? Rashin sanin abin da zai ce da ita yasa shi yin shiru " toh me ze mata yasaka mahaifiyarta kuka?". Juyawa yayi ya kalli Yah yusuf instead of ya bata amsar tambayar da tayi masa, cikin sa'a kuma daidai nan mummy ta dakatar da kukanta ta kamo Teemah, ta rungumeta ajikinta, tana 'dan bubbuga bayanta. Daddy da yah yusuf ne suka ha'da baki wajen bawa mummy ha'kuri. Sai tace bakomai ai ya wuce tunda taganshi yanzu, tace abinda yasa ma har yaga tana kukan bakonai ba ne face tunawa da tayi da Mahaifansu, ta tuna irin gwagwarmayan da mahaifinsu yasha arayuwa 'karshe kuma Allah ya kar6i abinsa, daga baya kuma mahaifiyarsu, wacce tayi iyah 'ko'karin ta wajen ganin ta kula da rayuwarsu yanda ya kama ta bayan ba ran mahaifinsu amma ita ma Allah ya kar6i ranta tun ba aje ko'ina ba. Tace " Iyayenmu sun barmu mu biyu da tabbacin zamu had'e kanmu mu kala da kan mu da rayuwarmu, amma hakan sai ya kasa faruwa muka kasa yiwa kanmu wannan gatan, nasan da mahaifan mu na raye sai sunyi Allah wadai da faruwar wannan al'amarin".... Daga nan ta 'daga kanta ta kalleshi taci gaba da fad'in " yah yusuf bansan me yasa ka 'ki ni ba ka gwammaci rayuwarka takasance babu ni aciki duk da kasance wata matsayin 'yar uwa agare ka wacce duk iya rayuwata kai ka'dai ne wanda zan yi tutiya dashi amatsayin 'dan uwana, Allah ne kawai ya dubeni ya bani miji nagari badan haka ba da ban san ya rayuwata zata kasance ba, amma Alhamdulillah ko yanzu na godewa Allah na tunda ban nemi komai na rasa na jin dad'in rayuwa ba ". Tana gama fad'in hakan tayi 'kasa da kanta sai Yah yusuf ne ya bud'i baki da kyar fara bata hak'uri yace shi kansa bai san me yasa duk wannan abubuwan suka faru ba amma insha Allahu yayi mata al'kawarin matu'kar yana numfashi kuma yanada lafiya bazai 'kara maimaita irin hakan agareta ba." Bai tsawaita magana ba yayi shiru shima duk tunanin iyayensa ya dawo masa fil aransa . Sallahr maghrib suka fita da daddy suka nufi masallaci, koda suka suka dawo kuma sai suka zauna aharabar gidan suna tattaunawa akan maganar Mummy anan ne Yah yusuf ya ke cewa shi yanzu wata alfarma zai nema awurinsu duka bayan yafiya yana so idan har zai yiwu su basu auran Fateema saboda kar Khadeeja tayi zaton ko nan gaba zai 'kara barinta duk da ahima ba ason ranshi hakan ke faruwa shi kansa be san har yaushe ne ya aikata irin hakan ba amma zaiso Khadeeja tasawa ranta salama da kuma yadda akan cewa shi 'din yana nan amatsayin 'dan uwan ta bazai ta6a gujan ta ba har abada, yace sai dai yana ganin hakan zai kasance ne idan har sun had'a wata kyakykyawan ala'kar da zata 'dore har abada. Daddy kuwa shiru yayi yana sauraransa domin be san manufar maganar Abban ba da kuma inda ta dosa abinda ka'dai ya tsaya matsa shine cewa da Abban yayi " _abasu_ _auran_ _Fateema_ " ................ " toh shi da su waye?". Abbah da yaga daddy yayi shiru batare da ya fa'di ko kalma 'daya ba kuma daya lura sai yaga kamar ma abokin nasa hankalinsa naga wani tunani sai ya sa hannu ya dafa kafa'dar sa anan daddy ya fuskanceshi sai Abban yace " baka ce komai ba kabarni inata surutu". Gyaran murya daddyn yayi tare da fad'in bana fahimceka ba ne yalla6ai " ya 'karasa manmganar yana murmushi. "Manufar magana ta shine inda hali ina nemawa Mahmud auran Fateema awurinka saboda sake 'karfafa dan'kon zumunci ". Kallon Abbah daddy yake yi da kyau sai yanzu ya gama fahimtar me yake nufi tun farko. Shikanshi da hakan zai faru zaiyi matu'kar farin ciki ko dan saboda sanin irin sha'kuwar dake tsakanin Mahmud da Fateemahn, amma bai sani ba ko kowa ma zai so faruwar hakan bataga shi da Abban. Bai bawa Abbah amsar maganar tasaba ba ya dai ce ya bari tukunna zasu 'karasa maganar anjima ko zuwa gobe ne insha Allahu. Duk da Abbah na tunanin komawa agobem amma be tankawa daddy akan maganar daya fad'a d'in ba dan yana ji aransa cewa in dai akan maganar ne he is ready to sacrice everything dan kawai yaga yiwuwar auran. Saboda shi aganinsa idan akace Fateema natare da su toh hankalin Khadeeja zai fi kwanciya da yayan nata dan indai haka ne zai wuya zumunci ya yanke atsakaninsu. Sai da sukayo sallar isha'i kafin suka 'kara komawa cikin gida, suna zuwa yawuce wurin mummy yace 6angaren sa yake so akai musu abincin su acan zasu ci. Da " toh " ta amsa masa shikuma daganan ya juya yakoma 6angaren nasa ya samu Abbah. Teemah aka saka ta kawo abincin gaba 'daya, kuma sai alokacin ne ta samu tagaida Abbahn saboda 'dazu batasamu hankalin gaidashi ba ganin mummynta na kuka. Muryarta da sanyi sanyi tace "ina yini" Yana cewa" lafiya" kan ya 'kara wata magana harta ma'ke tsaye bata 'kara yin wata magana ba, saboda ita sam ji tayi mutumin be kwanta mata arai ba musamman data fahimci adalilinsa mummynta ke kuka 'dazu kuma tun fitar su take ta tambayar mummy akan abinda yasa metan ta'ki gaya mata haka ma data ce mata mutunin 'kin kulata tayi, tana ganin kamar tasan mutumin awuni wuri amma takasa tuno a inda tasan shi 'din hakan yasa tayi fishi ta 'kyale mummyn tayi tafiyarta 'dakinta bata sake dawo wa ba sai yanzun da mummy tasa ta kawo musu abinci. Tana cikin tunanin taji yo muryar Abbah yace mata " angama makaranta lafiya ko Fateema?" " ehh lafiya 'kalau". " Toh Allah yabada sa'a yasa me amfani ne" Ciki-ciki ta amsa da " Ameen ". Shi kuma daddynta da yaga yanda tayi maganar kamar ranta be so cikin sanyi sai ya 'kirata zuwa inda yake zaune yace mata " yah na ganki haka Angel 'din daddy, meke faruwa ne? " bakomai daddy"! Yace " kin gane wannan 'din kuwa "? Ya 'kara sa maganar da nuno Abbah da hannunsa. Jijjiga kanta tayi tare da kallon Abban atake sai ta gano kamar da yake da Mahmud da tunda bata lura ba sai yanzun . Bud'an baki tayi tace. " Lah daddy kamar yana kama Yah Mahmud". Dariya suka sanya dukkansu har Abban Teemah kam sai ta tsaya tana kallon su, hatta da dariyar su ma iri 'daya ce da yah Mahmud ta fa'di aranta. " Allah me iko" . Sai taji daddynta na fa'din " mamanki bata fa'da miki waye shi ba? ". Kai ta 'kara jijjiga wa alamar " ehh". Abbah da daddy duk sunyi mamaki kowa yajinjina al'amarin Khadeejan acikin ransa wanda hakan 'karara ya nuna azahirance cewa ranta ya 6aci da Yayan nata ne duk da 'dazu ta 'dan sau'ko kafin tafiyarsu masallaci. Abbah beyi mamaki ba domin aganinsa sam koma me tayi bata da laifi ta cancanci tayi fiye ma da hakan saboda ita akawa ba dai dai ba. Yayinda Daddy yake tunanin irin 'kunci da damuwan da ta rin'ka shiga abaya duk asanadin rashin 'dan uwanta amma ace yanzu taganshi yana cikin gidanta amma kuma sai ta tsiri shariya! Kai abin da mamaki gaskiya, amma yazama dole Fateemah tasan matsayinsa awurin ta da maman nata gaba 'daya, koma miye yafaru ai be kamata ta'ki sanar da 'yarta koshi waye ba." Azahiri kuma sai ya fuskanci Teemah yace " Kinga wannan dakike gani azaune anan toh yayan mummyn kine, Uncle 'dinki ne, kuma mahaifin yayanki ne wato Mahmud. Ido ta zaro waje tana kallon daddyn alamar mamaki. Sai ya yayi murmushi tare da jinjina nata kai sannan yacigaba da fa'din " musamman fah yazo tun daga Lagos dan ya gaishe mu yakuma tayaki murnar kammala makarantar dakika yi" Yana kawo wa dai dai nan yakamo hannunta yace " Jeki gaida shi da kyau kinji ". Duk abin nan dake faruwa Abbah kallonsu kawai yakeyi, ba 'karamin birgeshi sukeyi ba sai azuciyarsa yake 'kara jin son faruwar wancen al'amarin musamman ma daya lura da cewa Fateemahn akwai nutsuwa, zai so 'dan shi ya aureta su rayu dashi, in har Mahmud ya aureta koba komai yasan shi bazai yi rashin dacen iyali irin nasa ba. Ahankali cikin natsuwa ta mi'ke ta nufi Abban taje ta tsugunna gefe dashi daga 'kasa ta gaida shi ya amsa fuskarsa kamar gonan auduga. Tambayarsa tayi yasu Mahmud fah da An..Anty " Ta tambaya harda Antyn ne saboda sanin sunan Anty datayi a bakin Mummy da kuma Yah Mahmud lokacin data Antyn ke yawan damunsa akan ya koma gida sa'ilin da yana service anan balle data ta6a daka mata wta uwar tsawa wata rana akan ta 'dauki wayar Mahmud toh tun lokacin bata ta6a mantawa da ita ba. Abbah kuwa da 'din hakan yaji sai ya amsa fa'din " suna nan lafiya tare sanba'da mata ruwan albarkatai. Bata tashi akusa da Abban ba mummy ta shigo da sallamarta ,suka amsa gaba 'dayanau har Teemahn Abin mamaki fuskar mummy wasai tana murmushi tacewa Teemahn " ke kuma kin wani nutsu kamar me hankali ya baki zuba musu abincin ba haryanzu ?" Dawo da kallonta tayi gurin Daddy tace " hala bakwa jin yunwa ne shiyasa." " Yah yusuf hu'du ban me kake mata haka har kuka manta da cikin ku." Dariyah suka sanya dukkansu cikin jin da'di, Teemah ce ka'dai tayi murmushi ,kowannensu yaji dad'in sakewan da Mummy tayi musamman daya kasance ita da kanta tazo harma tasa su dariya, ta kuma 'kara da fa'din " dan ku tashi kuci abinci dare na 'karayi ". Da kanta ta zuzzuba musu abincin tace bismillah Teemah kuwa hanyar wahe ta nufah sai Abbah ya hangota sanda take daf da barin 'dakin " tafiya zakiyi ko Fateemah" Tsayawa tayi caka ta juyo tace " ehh Abbah inajin bacci ne sai da safe" " toh Allah ya bamu alkhairi" Abban ya fa'di tare da fara cin abincinsa. Harta kusan fita a'dakin sai mummy tace " ki jirani a'dakina ina zuwa yanzu". " Toh mummy" Tace tare da barin 'dakin. _Comment_ , _Share &_ _Vote_ _Pls_🤞🏻 *Readers adinga* *min uzuri dan Allah kamar yanda nasan ku dashi, nasan ba kullum nake samun* *daman yi muku* *typing ba* *abubuwane suke* *min yawa , ni kaina bajin da'din hakan nake ba amma* *insha Allahu komai* *yakusan* *daidaita* . *Bear with me pls* Ina masoyan Mahmud ku toh duk ku marmatso kuji😜........ *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 6:00 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍 *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Control your _Anger_ , it is one letter away from _Danger_ . 🅿 *39* *BORNO STATE* Motar su Abbas na fita daga wurin graduation 'din hanyan Maiduguri suka 'dauka basu tsaya ko'ina ba sai a wani gidan mai, koda suka sha man kuwa hanya straight suka kama batare da ya sake komawa gida ba. Hakimce yake a seat 'din baya inka ganshi zaka zaci wani basareka ne musamman inkayi duba da yanayin zaman dayayi, yawani hakimce baya fa'din komai sai in lokacin da zai yi magana da driver ne kafin zakaji muryarsa, balle ma ba wata maganar kirki sukayi tsakaninsu ba inya wuci aikin bada umarni. Da ikon Allah kuwa lafiya lau suka isa, Abbas saka drivern yayi ya yi tu'ki a high speed shiyasa suka isa dawuri, kuma cikin kariyar ubangiji babu wani abin da suka ha'du dashi ahanya wanda yake ba daidai bane. Da shigarsu cikin garin Maiduguri sai suka wuche gidan ogansa me suna Oga philip, suna yin horn me gadi ya bu'de musu 'kofa. Ko zama Abbas beyiba ya fara shirin tafiya inda ya fito oga Philip bai so hakan ba amma Abbas yace ana nemansa ne shiyasa, dolen oga Philip ya barshi yagama kintsawa yafito, lokacin 'karfe hu'du kusan da rabi na yamma 4:28pm , sallama yayi musu tare da godiyah sosai saboda Oga philip mutun ne daya cancanci ayi masa godiya, tun farko Allah ya ha'da jininsu da Abbas tun farkon ha'duwarsu awurin wani course dasuka je bada jimawa ba, yana shiyake kula daduk wani abu dayashafi Abbas 'din ko kuma zai taso ta 6angarensa yakan yi 'ko'kari sosai wajen ganin ba'a samu wata matsala ba. Duk sau'kan da Abbas zaiyi a maiduguri toh Oga philip ne ke bashi masau''ki ko a agidansa ko kuma wani gidan daban, shiyasa ko wannan zuwan ma da yayi sai ya sau'ka agidansa, bashi da matsala komai,inkuwa yaji an'kira sallah baya 6ata lokaci yake isa masallacin dayake akwai akusa dasu, kuma daya sanar dashi cewa yana so yaje damaturu amma yace bazai kwana ba aranar zai dawo sai Oga philip 'din yace " toh ba matsala daganan ya ha'dashi da driver suka kama hanya suka zo damaturun atare, yakuma ce da drivern yakula da tu'ki da kyau dan kawai saboda Abbas 'din. Yanzun ma sawa yayi aka 'kara kai Abbas 'din airport yakuma binshi da fatan alkhairi. Bai 'kira kowa ba aranar sai mummy ya mata sallama awaya dayake itan basu ha'du ba lokacin da zai tafi shiyasa ya 'kirata yace mata ya wuche Porthacourt. Sai dai kuma tun lokacin da yatafi ya bar Teemah a tsaye yakejin be kyauta mata ba harma dashi kansa, sai yake jin dama ya tsaya ya kar6i leave awurin aiki kafin ya taho 'din da yasan komin yaya de zai 'dan yi kwana biyu, da zaiyi irin wannan tafiyar ba. Amma yazaiyi hakan ma ba laifi tunda yagama abinda yakawo shi dama burinsa yaganta kuma yagantan, wannan ma satan hanya yayi shiyasa and baya son tun ba'aje ko'ina da fara aikin ba ya fara samun problem dasu shiyasa yatafi aranar batare da ya ko tsaya sun yi gaisuwar kirki da su daddyn ba dan ma kar ya shiga cikin lokacinsa. *DAMATURU, YOBE* *STATE* Koda fitan Teemah a'dakin direct 6angaren mummyn ta nufa dan cika umarninta, mummy kuwa bata bi bayanta ba sai ma kujera dataja tayi zamanta, su Abbah nagama cin dinner suka sha hirar yaushe gamo da kuma tuna baya da yayan nata wannan karon faran-faran batare da wani damuwa ba. Daddy ne yace maza ta tashi ta tafi dan kamar yaji tace Teemah ta jirata a'daki yace tayi sauri taje kar ta hana masa yarinya bacci. " su yarinya manya" Inji mummyn Tana dariya tabar 'dakin tare da yi musu sai da safe. Koda ta isa 'dakin nata kuwa barci tasamu Teemahn nayi abakin gadonta kamar ma zata zame ta fa'do, aranta tace " Allah sarki harta gaji da jira tayi bacci. Taso ta tasheta amma ganin yanda tasake take bacvcn sai ta 'kyaleta kawai anan 'din sai dai ta 'dan bigeta ahankali tace " ta gyara kwanciyar tata da kyau. Daddy har yayi shirin bacci sai kuma yaji kamar akwai kukan sauro ka'dan a'dakin kuma gashi yanada ba'ko sai yace bari ya 'dauko magani dayake shi dama ba so yakeyi ba be fiya anfami dashi ba dama mummy ce dayake ita ko kukan sauro na hanata bacci shiyasa sam bata rabuwa da insecticide a'dakinta. Mummy nagama shiri kenan saura ta kwanciya, sai kuma tajiyo kamar motsi a parlour da farko harta 'dan tsorata sai ta tsaya cak a inda take tsayen, tana cigaba sauraron motsin yayinda yake 'kara tunkaro ta sai kuma tajiyo muryar daddy yana sallama ahankali saboda dare. Sai da ta amsa kafin tace " ai har kaban tsoro ma" " very sorry, maganin sauro za'a bamu naji kamar akwai 'dan kukan sauro a'dakin". " ah ah kaida kece bakaso?". " ehh albarkacin ba'ko za'a bani " "Hmm kai de fa'di gaskiya " Tayi maganar tare da juyawa dan zuwa inda maganin yake ajiye, sai kuma asannan daddy ya lura da Teemah dake kwance, "sai da kika samin yarinya bacci anan ko?" Sai tayi saurin fa'din " kafin nazo ma harta yi baccinta". " badole ba ina zata iya jiranki kinje kin samu Yayanki kina ta'di kin manata da ita, badole tayi baccinta ba itama, aini banga laifinta ba". Batayi magana ba bayaga " hmm" kawai sai mi'ka masa Insecticide 'din shi kuma maimakon ya kar6a a'a, sai ya mi'ka hannunsa ya cafko nata hannun yajata zuwa parlour binsa tayi kamat ra'kuma itama. Zama yaje yayi akan kujera ita kuwa sai takalleshi da mamaki tana daga tsayen tace " yalla6ai ya haka naga ka zauna?". " magana zamuyi Khadija " Ido ta zaro waje tare da fa'din yanzun kuma?, da daren nan." " ahakan tazo Khadeeja, kuma ahakan za'ayi" Ya fa'da in a serious tune ,ganin hakan yasa mummy taje ta zaunan itama ta fuskance shi. " yauwa ki saurareni da kyau kiji, kinsan Yusuf 'din nan abokina ne shi tunma kafin na ha'du da ke right? Sai tace " ehh". " toh amatsayinsa na abokina misali idan akace ya nemi alafarma agurina kina ganin ya kamata na'ki saurarensa"? tace " a'a " " saboda me"? " saboda zumunchi ,kuma ya kamata ka karramashi amatsayinsa na aboki agareka." " idan kuma ya 'kara da zamowa sirki ( in-law) agareni fah "? "Fiye da hakan ma zakayi masa inda hali". "good". Yace da jin da'di sannan yaci gaba da fa'din " Yataso ne musamman all d way from Lagos ya zonan dan kawai yasada zumunci dake tsakani, wanda nake tunanin cewa ada sam babu shi, nasan kinsan da haka ko"? " ehh" Tace asanyaye dan tafara jin tsinkewan zuciya akan wannan irin maganganun daddyn. " Lokacin da zaizo be zo da niyyar neman aure ba face abin da nafa'da miki abaya, saboda ya sanar dani da jimawa akan zezo mana nan amma bai sa rana ba saboda kar ya saka rana yazo tafiyar bata yiwu ba, shiyasa yabari ahaka nima kuma dalilin dayasa na'ki fa'da miki kenan, amma Alhamdulillah sai gashi yazo mana batare da munsan ma yataso ba, sai kawai muka ganshi. "Hakane"? Mummy kai kawai ta 'daga masa domin jikinta yafara yin sanyi da wa'dannan irin maganganun, kardai Yah yusuf ku'di yake bu'kata awurin Daddy, haba no waonder taga ya rame ba kamar da dayake da 'dan 'kibarsa ba, ashe ya'dan shiga damuwa ne shiyasa............... Firgigi tayi tana kallon daddyn domin tana cikin tunanin tajishi yace " kina jina" da 'dan 'karfi, bata sani ba ashe bakinsa na biyu kenan domin na farkon kamma batasan yayi ba. Ran'kwafowa yayi yana dubanta da kyau sannan yace " tunanin me kuma kike yi Khadeeja"? Bakinta har karo yakeyi wajen fa'din " ba komai". Owk Yace sannan yaci gaba " Allah cikin ikonsa tun da yaga Fateemah sai ya yaba da hankalinta harma yace yanason aurenta ma 'danshi Mahmud" Ido mummy tazaro waje tare da mi'kewa tsaye akan daddyn. " Mahmud de" Tafa'di tare da nuni da wani 6angare tamkar Mahmud 'din yana wajen. " shi de bawani ba, be yi bane ko me" Shiru tayi still tana tsayen. Hannu ya mi'ka yakamo nata hannun "Zauna mana sai ki yimin bayani da kyau wala Allah zanfi fahimtarki". Zaman tayi kamar yadda ya bu'kata amma bata iya yin wata magana ba. Daddy kuwa sai yaci gaba da fa'din " Khadija mun kusan kammalawa da maganar ahalin da ake ciki yanzu 'karshen furuci na kawai yake jira yaji". "Toh kace masa baka amince ba kawai" " awani dalili" yaddyn ya tambayeta. " Habah, haba dan Allah Mahmud fah naji kace? " ehh mana, ko kina da wani wanda kike ganin yafi Mahmud 'din" Karka'da kai tayi cikin takaici "Amma inajin ka manta wacece mahaifiy.......... " hold it pls, lets go straight to d point, ok!". Yatari maganan da tayi niyyan fa'din cikin gaggawa harma da 'daga hannunsa 'daya sama , wanda hakan 'karara yake nuni da cewa baya bu'katan jin komai daga gareta. Shiru mummy tayi tare da binsa da idanu, mamaki ma yake bata daman ta da'de da fahimtarsa aganin ta shi sam baya so yaji anfa'di karkatacciyar magana akan Yah yusuf 'din sai yayi 'ko'karin gyarata, shiyasa da datake yawan complain akan sharetan da yakeyi shi daddyn shine me tausarta akullum sai ya nuna kamar wai abubuwa ne suka masa yawa, sai da abin yayi yawane kafin shima ya saduda ya goyi bayanta amma duk da be ta6a nuna mata cewa Yah yusuf 'din badai dai yakeba, sai de yace suci gaba da addua kawai, kuma duk wannan abubuwan dasuke faruwa ita aganinta bakomai kesa daddy yin hakan ba face akan goya masa baya da Yah yusuf 'din yayi lokacin da daddyn ya nemi auranta. Jinsa yayinda shi kuma yaci gaba da fa'din " munyi magana dashi kuma na fahimce shi, ayanzu kuma gab nake da nuna amincewa ta 100% saboda girma dayake dashi a idanuna, bazan iya 'kin nuna amincewata ba kuma ina fatan kema zaki goya min baya with all your support". Ya 'karashe maganan yana kallonta. Itama kallon nasa ta tsayayi daga baya baya kuma ta kauda kanta gefe. " taya za'ayi na goyi bayanka alhali ina da tabbacin Anty bazata ta6a son zuri'armu ba, balle ma har ace 'yar da ni na haifa, 'danta ya aura!" Gashi kai kuma ka kasa fahimta ta" Nasiha sosai daddy ya mata wanda ya matu'kar kashe mata jiki tare da kawo ayoyi da hadisai wanda suke nuni akan halayyar 'dan Adam da kuma bata misalai akan yadda ikon Allah ya buwayi ko'ina yace mutun ba komai ba bane shi compares to mahallici dan haka komai zatayi ta yadda da Allah da kuma 'karfin ikonsa kafin tasa tsoron wani abin halitta. Ya 'karasa da cewa " ina fatan kin fahimceni kuma zaki bani ha'din kai" ahanakali tace" insha Allahu". "Yauwa, sai da safe". Yana mi'kewa ya fa'di hakan yayinda mummy takasa amsa sai da safen dayake mata, ta dai tsaya atsaye duk tunani ya cikata, " ha'ki'ka gaskiya Daddy ya fa'da kuma tasani cewa Allah ne mafi rinjaye akan komai, toh amma abinda takasa ganewa shine kar dai ace wannan dalilin ne ya kawo Yah yusuf inda take?" Sosai abin nan ya dameta, washe gari kuwa bata nuna komai ba suka yi gaisuwa cikin sakin fuska har suka gama karyawa sannan ne da suka ke6e da Abbah ta sake jefah mishi tambayar da ke damunta azuci inda tace " kar dai abin nan daka fa'da jiya shi ya kawo Yah Yusuf garin nan?". " ah, ah, ah, khadeeja, kin manta me na gaya miki ne jiya hala? Ido ta tsura masa tana kallonsa ga dukkan alamu cikakken bayani take bu'kata daga wurinsa. Ganin hakan sai ya ci gaba da fa'din " ba abinda yakawo shi kenan ba, kamar yanda na sanar dake ,yazo ne ya sada zumunchi sai kuma yayi katari da Fateemah sai yaga dacewa da sha'awar aurawa 'dansa ita shine yamin maganan nima kuma na amince, kinga gara namiki gwari-gwari yanda zakifi fahimta." Ya 'karasa da murmushi " amma kai kana ganin bawata matsala ko? nifah gaskiya ina tsoron abinda zaije yadawo, kafa san halin Anty ba 'kaunar mu take ba gaba 'daya". " Kin manta wannan 'dinma kenan ko?" Kauda kai tayi gefe tare da fad'in " ban manta ba" " toh karki damu kanki dan Allah, ita 'din ba Allah bane ya halicceta?, ki ringa sawa ranki yadda da 'kaddara kowacce iri ce, na tabbata 'kaddaran wannan al'amarin ne yakawo shi akwannan, toh kinga kuwa idan har Allah yace za'ayi toh fitinan wani ko wata be isa yasa afasa ba,dan haka ki saki ranki kinji". "Da kai ta amsa masa, dan kasa bu'dan baki tayi ta ce komai. Ko bayan barin sa 'dakin ma bata motsa ayanda ya bartan ba, tun yanzun tausayin 'yarta yafara shiganta. Daddy kuwa da komawarsa wurin Abbah sai suka kammala magana inda daddy sai alokacin ne ya nuna amince warsa akan lamarin, 'karyar da yiwa mummy kuwa akan tunruni ma ya amince yayi hakane saboda ta daina sawa ranta kamar maganar zata fasu. Yayin da Abbah ya nuna tsantsan farin ciki da amincewar daddyn harma ya 'kara da fa'din " bada wani jimawa ba zasu ji daga garesu domin baya so a'dauki dogon lokaci akan lamarin". " bakomai ai, Allah ya nuna mana " inji Daddyn Teemah Zama suka yi suna 'dan ta6a hira tsakaninsu anan mummy ta tadda su, aka cigaba da hiran da ita, ranta ajagule take jinsa ,amma bata so Yah yusuf ya zargi wani abu daga 6angarenta shiyasa ma ta taho inda suke 'din, kuma ma dan kar daddy yace ta'ki jin maganarsa. Da lokacin tafiyar Abbah yayi sosai ya musu alkhairi daga mummyn har Teemah, ya bawa kowa kyautan ku'di daidai yanda yayi ra'ayi saboda acewarsa be taho musu da komai ba wai suyi ha'kuri da wannan sai in ya 'kara dawowa. Teemah da bata san abinda ke faruwa ba taringa bashi 'sakon gaida Yah Mahmud kusan sau hu'du tana maimaitawa jitake kamar tabishi su tafi, shikiwa Abbah sai amsa mata yakeyi yana murmushi da jin da'di, sai da mummy ta banka mata harara kafin tayi shiru ta daina magana. Da daddy suka tafi domin shima akwai abinda zai kashi can arean Lagos 'din harkan kasuwancinsa. *LAGOS* Koda Abbah ya isa gida Mahmud ne ka'dai ya nuna farin ciki da dawowar tashi, dan tun da yaje 'dauko shi a airport yake washe ha'kora, wannan na 'daya daga cikin burikansa dayake son ganin faruwarsu, sai kuma gashi hakan yafaru, ba 'karamin da'di yaji ba da Abbah yace zaije Yobe , da farko ma yace zai bishi suje tare amma da Anty ta azalzale shi a'daki tayi masa masifah tare da fa'din matu'kar ya 'dauki 'kafa yabi Abban nasa toh yasani _babu ita_ _babu shi_ " Dajin hakan sai ya ha'kura da tafiyar saboda duk yanda yakai da rashin ji sam baya son mummunan kalma daga mahaifansa, ha'ki'ka iyaye iyayena kuma duk girmanka da ikonka yazame maka dole kabisu kodan samun rabauta awurin mahallici, amma be sanar da Abbansa abinda yafaru ba sai kawai ya nuna masa cewa akwai abinda yataso masa ne shiyasa ya fasa zuwa, amma insha Allahu zaizo yaje ko daga bayane. Abbah be wani damu ba yace " toh shikenan ba matsala, kai ai daman 'dan can ne ko bakaje yanzun ba matsala, da'ace baka ta6a zuwa ba ne toh da 'kafata 'kafarka amma yanzu kam ka fansheku, Allah ya nuna mana lokacin dazaka sake zuwa 'din " "Ameen" Mahmud ya amsa wa Abbahn dashi, be damu da _yah_ _fanshe sun_ da Abbah yake nufi ba sam ma abin be zo kansa ba, Abbah kuwa nufinsa shi Mahmud 'din da Antyn sa. Sai kawai ya 'kyale Mahmud 'din yayi tafiyarsa shi ka'dai, domin koshima bazai so bakin uwa yakama 'dan sa 'daya tilo da Allah ya mallakawa ba. Abinda Mahmud be sani ba shine duk abinda Anty ta fa'da kaf yaji ta, kuma wannan dalilin ne yasa ya 'kara saka himma wa tafiyar tasa. Koda yatafin kuwa basuyi waya ba har yaje ya dawo gida ko fatan sau'ka lafiya bata yi masa ba ballantana taji yanda ya sauka shine ma ya gwada kiranta sau 'daya dayaga bata 'dauka ba sai be sake 'kiraba yace inhar ba da gangan ta'ki 'dauka ba toh intaga missed call zata kirasa, ilai kuwa yaji shiru, bata 'kirashin ba kamar yadda shima be sake 'kiranta ba har ya dawo sai dai suyi wayarsu shi da Mahmud. Ko yau 'din ma da zai dawo Mahmud kawai ya 'kira ya sanar dashi ,shi kuwa be sanar da Anty ba kawai yaje ya 'dauko shi. Anty bata ma gida lokacin da Abbah ya dawo tatafi yawace-yawacen ta acikin gari ita da 'kawarta Anty chideh. _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh* 😍 [10/2, 6:00 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍 *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Remember the 5 (five) simple rules to be happy, Free your heart from hatred.....Free your mind from worries...... Live simply.......Give more and Expect less. 🅿 *40* Koda ta dawo ta ganshi agida kuwa 'dauke kai tayi tamkar ma bata ganshi ba, shima Abbah sai ya'ki yi mata magana yasan da kanta ma zata kulashi idan nata ya 'debo ta. Kwana biyar bayan dawowarsa sannan ya 'kira Mahmud tare da Anty, yayi musu bayanin abinda ke faruwa, yayin da hankalin Mahmud yakai 'kololuwa wurin tashi rasa yadda zaiyi ma yayi hakama Anty. Ita kam tsaye ta mi'ke da gama jin abinda Abban yagama fa'di tace "banji abinda kake fa'da da kyau ba, 'dan sake maimaita pls". Murmusawa Abbah yayi, yana kallonta har kamanninta sun soma sauyawa atake, be damu ba ya sake mai maita mata akaro na biyu duk da yasan ta ji shi da kyau, kawai sha'kiyanci ne ke damunta shikuwa yana daidai da ita awannan karon. Kwankwaso ta kama da hannunta 'daya jikinta har rawa yakeyi tsabar masifah. "Amma kai ko kunyar fa'da ma bakaji? Kallon ta Abbah yayi wannan karon sai ya koma baya jikin kujera ya zauna ya jinginu yana binta da kallo yana murmushi dama yasan sai ta masa rashin hankali shi kuwa me sashi barin maganan nan se ikon Allah kawai sai yace mata. " abin kunya nayi ne da har zanji kunyar fa'di"? "Dakata dan Allah Alhaji, inaga kamar ka manta da maganar da akayi kwanaki agidannan ko, inace kai da bakinka kace zakayi bincike bayan yaro yasanar dakai ga abinda yakeso shine zakaje ku wani 'kulla 'kulle-'kullenku daga zuwanka, ka zo kace ga abinda za'ayi, kai aganinka kayi adalci kenan,? Toh ya kuma kake so ayi da ita waccen da take s.....da Mahmud 'din yake sonta? Da wuri ta daidaita harshenta dan kar ta kwafsa. " kinje kin tambayo auren ne"? Abban ya tambayeta hankalisa akwance domin shi baya jin yana da damuwa koka'dan saima wani farin ciki dayakeji, yayin da masifar da Antyn keyi yake 'kara masa kwarin gwiwa dan ganin yacika Burinsa. " haushi tambayar tasa ta bata, take kuwa ranta ya 'kara 6aci tafara masifa kamar ta ari baki " taya za'ayi kace ko na tambayo aure dama mace tana tambayar aure ne? "Ni na sani ne ko akanki za'a fara"! yasake fa'da cikin kwanciyar hankali . " Wallahi Alhaji karka ga nayi shiru akan wannan maganar ka zaci ko maganar ta fasu ne, dama na fahimci take-takenka tun farko so kake ka'ki sa baki amaganar shiyasa ka tsiro da wani batun bincike, toh wallahi bari kaji ba rantse da Allah ko zan tafi tsirara ne sai naga Mahmud ya auri Munira, kuma bari in tabbatar maka wani abu da baka sani ni 'dana bazai auri wata 'kazama wai Fatima ba ko da kuwa mata sun 'kare a duniya toh sai sai ya zauna ba mace amma bazai ta6a auranta ba ,akai kasuwa". Tana gama fa'din hakan tayi waje tana ta sababi. Binta da kallo dukkan su sukayi har Mahmud 'din wanda yake zaune akan 'kafafunsa tamkar gunki tun lokacin dauaji bayanan Abban nasa na farko be 'kara jin komai ba, masifan da Anty tafara na 'karshe shine ya dawo shi cikin hayyacinsa saboda da 'karfi tayi maganan. Sai data 6acewa ganin su kafin suka dawo da kallon su ga juna suna ha'da idanu kuwa Mahmud yayi 'kasa da idanunsa. Bayyanan niyar murmushi Abban yayi sai yace " Mahmud kaima baka so ko"? Shiru Mahmud 'din yayi yana rarraba idanu , baya jin ya yiwa Abbah adalci idan yace " ehh bayaso" inkuwa yace yanaso toh tamkar ya siyawa gidan nan tashin hankali ne, tunda yasanAnty bazata ta6a goyon bayan Abbah akan maganar ba, bayaga haka ma shifa kwatata bayaso yayi aure yanzu, bayanzu ya shirya yin aure ba kuma ko zaiyi auren ma ba dai Fatima ba, sai dai kuma ai da yarinyar da Anty ta keso ya aura 'dinnan gara Fatima sau dubu akanta, kai bama ha'di, duk itama Fatiman be ta6a yi mata kallon so ba , be ta6a ko kwatanta wai shi ze so ta ba, shi bai ma da plan 'din yin aure akwana kusa amma be san dalilin Abbah na nema masa auren Fatima ba. Yace da ace Abbah zai bashi za6i da ita Muniran ze za6a saboda wani dalili. Yana cikin tunanin ya tsinkayo muryar Abbah yana sake maimaita tambayar daya yi masa da farko ha'di da cewa " kar ka damu Mahmud ka bu'de zuciyarki kasanar dani abinda ke ranka ,ni mahaifinka ne, bazan ta6a 'kin kar6ar kowacce irin uzuri daga gareka ba, matu'kar kaga za6in dana ma ka be maka ba ka sanar dani" Numfasawa Abban yai jin har yanzu Mahmud be ce komai ba sai ya'kara cewa " sai dai inason kasan wani abu Mahmud har abada ni mahaifinkane, me 'kaunarka ne, bazan ta6a yima za6in da nasan zai cutar da kai ba, idan waccen yarinyar ne da mahaifiyar ka ke magana akai i thought na maka bayani, bincekena be nuna min komai na alkahiri tattare da su ba shiyasa bazan ita barinka ka auri yarinyar ba, amma bansani ba ko kana son abinka ahaka, feel free ka sanar dani ra'ayinka kaji Mahmud"! Da 'kyar Mahmud ya bu'di baki yace. " Abbah.......sai kuma yayi shiru. " Inajinka " "Abbah ban'ki za6in da kayimin ba, na amince kuma nagode sosai, Allah ya 'kara girma". Albarka Abban nasa yata saka masa saboda farin cikin be watsa masa 'kasa a idanu ba, ha'ki'ka wannan ranar ta farin ciki ce agareshi ,daga nan ya sallami Mahmud ya tafi. Koda ya koma 'dakinsa kuwa zama yayi kawai abakin gado ya dafe kansa dake masa sara ba 'ka'kkautawa, kasa aiwatar da komai yayi alokacin jin abin yake kamar amafarki, " _wai shi_ _aure, auren ma_ _kuma_ _Teemah_ " . Yana a zaunen wayarsa tafara ringing se ya 'kyaleta danji yayi ma ta 'kara masa takaici, kusan 'kiran zai tsinke sannan yasa hannu ya 'dauko ha'di da jan tsaki domin da farko beyi niyyar 'dauka ba amma da 'karan yayi yawa ne yasashi bashiri ya janyo ko duba sunan me 'kiran beyiba yayi picking kawai ya kai kunnensa. Shiru yayi ko daya 'dauki 'kiran amma daya jiyo muryar Abbas ne sai ya 'dan saki ransa ka'dan. Bayan sun gaisa sai Abbas 'din ya sanar dashi cewa yana Abuja yau 'din nan ya sau'ka, Take sai shima ya bashi amsa da fa'din nima ina hanya insha Allahu" "Toh se ka iso" Daganan suka yi sallama kowa ya ajiye wayar. Mahmud be fito daga 'dakin nasa ba sai da shirin tafiya Abuja, a harabar gida yasamu Abbah ya sanar dashi cewa zashi Abuja. " ina fatan lafiya" Abban ya tambaye shi Sai Mahmud ya bashi amsa da "ehh lafiya 'lau kawai zashi ne yana da appointment da wani acan" Fatan Allah ya kiyaye Abbah yayi masa sannan yace ko akwai wani problem "? Mahmud yace "a'a Jinjina kai Abbah yayi. Daganan Mahmud yayi tafiyarsa yakama hanyan Abuja. *ABUJA* Abbas bacci yakeyi lokacin da Mahmud ya isa gidan, wanda baccin ya 'dauke shi sa'ilin yana kwance akan kujera a parloun dake 6angarensa, yana tsaka da tunanin Fatimansa baccin yayi awon gaba dashi. Mahmud na shigowa 6angaren nasa sai kuwa shima ya farka daga baccin da yakeyi 'din, dama shi Abbas haka yake sam baya bacci me nauyi, da salati ya farga daga baccin sai idanunsa ya sau'ka akan Mahmud dake tsaye yana kallonsa yana ayyana dama shine a irin wannan yanayin narshin damuwa amma shi kam be san ranar da farin ciki zata 'dore agareshi ba. Da sauri Abbas ya mi'ke zaune yana masa murmushi, " harka iso ne" Abbas 'din ya fa'di. Sai dai ga mamakinsa fuskar Mahmud a 'daure take tamau babu fara'a balle yayi tunanin samun amasar shi, damuwa ce 'karara tattare da fuska da kuma yanayin Mahmud 'din, dama yasan za'a rina domin tun lokacin dasukayi waya da Mahmud ya fahimci ba daidai yake ba sai kuma gashi yanzu daya ganshi da idanunsa sai yafi gasgata zuciyarsa fiye da 'dazun dayaji muryarsa acikin wayan. Be ce da Mahmud 'din komai ba kawai sai ya tashi ya wuce cikin bedroom 'dinsa, bathroom ya fa'da bayan ya cire kayan dake jikinsa ya watso ruwa tare da canja kayan dake jikin sa zuwa dogon wandon jeans da rigarsa fara sa6anin da dayake sanye da 3quatern wando baki da kuma singlet. Kayan daya saka 'din sun matu'kar amsan jikinsa sai suka 'kara fito da ainahin kyaunsa da kwarjininsa afili. Sake fitowa yayi cikin takunsa na 'kasaita ya nufo palourn nasa inda yabar Mahmud, turus shima ya tsaya mamaki ne ya 'kara cikashi ganin ayanda ya bar Mahmud 'din ahaka yadawo yasame shi tsaye hannayensa duka zube acikin aljihun wandonsa. Abbas aransa yajinjina wannan lamari " lalle Mahmud na cikin damuwa sosai" shi kanshi abinda ke damun Mahmud 'din sai ya fara damunsa tun ma kafin yaji menene. Sosai ya tsorata da yanayin Mahmud 'din kasancewarsa mutun me surutu da haba haba da jama'a, da wuya kaganshi a irin wannan yanayin da yake ciki ayanzun in dai bada wani kwakkwaran dalili ba. Hakanne ma fa yasa koda yaje yin shirin sa be 'dau dogon lokaci ba ya kamalla dawuri ya wuri ya fito dan ya yaji me ke faruwa. Abotarsu daga Allah ne, tun lokacin dasuka ha'du a damaturu sai Allah ya sanya musu 'kaunar junansu sannan suna mutunta juna tare da damuwa da damuwar junansu tamkar 'yan uwa na jini. Abbas na kammala tunanin nasa sai ya wuceh wurin fridge ya 'dauko fresh milk tare da glass cup guda biyu ahannunsa. " why are you still standing Mahmud ka zauna mana zaifi ai ko" Yafa'da bayan ya iso ya tsaya daga bayan Mahmud 'din. Ahankali Mahmud ya taka yaje ya zauna akujera me zaman mutun biyu yayin da Abbas yabishi abaya ya joining 'dinsa suka zauna atare. Yana zama sai ya fara tsiyaya fresh milk 'din a ' daya daga cikin kofunan daya kawo 'din bayan ya ajiye su akan centre table dake gabansu. Abbas mi'kawa Mahmud cup 'din yayi batare da yayi magana ba, sai alokacin kuma Mahmud yayi ajiyar zuciya tare da huro zazzafan iska da 'karfi daga bakinsa sannan ya 'daga lumsassun idanunsa ya kalli Abbas da su. Shikuwa Abbas sai ya 'dage masa gira 'daya tare da nuni da abinda ke ri'ke ahannunsa da idanunsa alamar " anshi mana" . Hakan da Abbas yayi ne yasa Mahmud shima ya kallo hannun Abbas 'din sannan a hankali ya cira hannunsa ya kar6i cup 'din daga hannun Abbas. " hmm " Abbas yace tare da jijjiga kansa bayan Mahmud ya kar6i abinda yake bashi 'din ,sake jinjinawa wannan al'amarin yakeyi dahar ya iya meda Mahmud haka a 'dan 'kan'kanin lokaci,because it's hardly kaga Mahmud na fishi arayuwarsa. Shima Abbas tsiyayan fresh milk 'din yayi yasha sannan ya ajiye cup 'din ahankali, sar'kafe hannanyensa yayi cikin junansu bayan ya gyara zamansa da kyau ya fuskanci Mahmud 'din sai yace masa " naganka wani iri, hope all is well with u"? Comment Vote Share *Salmerh* 😍 [10/2, 6:00 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍 *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 👎🏻 *HAPPY JUMMA'AT* *2 ALL* *MUSLIMS* . 🅿 *41* " hmm" kawai Mahmud yace daganan ya kuma yin shiru. Shirun da Abbas yaji ne yasa ya 'dago kansa ya kalli Mahmud da kyau, aransa yake tunanin " wai yau Mahmud ne haka? Abin na bashi mamaki sosae musamman da yaga yanda idanunsa suka koma ja alamar yana tattare da 6acin rai sosai. Sake 'daukan cup 'din dake gabansa yayi ya 'kara kur6an freshmilk 'din, kafin ya cire kofin abakin sa yajiyo muryar Mahmud yana furta " Fatima" irin amamakance 'dinnan, Abbas bewani damu ba koda yaji ya ambaci sunan domin shi ayanzu bashi da burin da ya wuce yaji meke tafe da Mahmud 'din dan haka sai yaci gaba da shan abinsa ahankali batare da ya tankawa Mahmud ba. Kallon Mahmud yaci gaba dayi daya zurawa centre table 'din dake gabansu idanu tambayr Mahmud ya yanke shawaran yi inda yace " wacce Fatima kuma Mahmud" yana gama fa'di ya'kara kaiwan cup a bakinsa. Mahmud kuwa kamar an tsikare shi ya mi'ke tsaye yaci gaba da fa'din " _Teemah fah_ Abbas, _wai_ _Abbah na Teemah zai_ _aura min "_. Abbas be san lokacin da ya furzo freshmilk 'din da ya kur6a ba, wanda ke bakinsa dai dai yasha kenan yaji maganar Mahmud 'din tamkar atsakar kansa yayi ta, hakan yasa ya furzo shi da 'karfin da bai shirya ba sai ya zarce da tari. Sosai tarin ya sar'ke shi tamkar wani me ciwon TB dan har Mahmud dake tsaye cikin 6acin rai ma saida ya taho da sauri kusa da shi yana masa sannu, fridge Mahmud yakoma ya 'dauko masa ordinary ruwa ya bu'de marfin sannan ya mi'ka masa, ka'dan Abbas yasha sai ya ajiye goran kana yaci gaba da kallon Mahmud tamkar wani sabon halitta ya gani. Shiru suka yi dukkan su, na 'dan wani lokaci yayin da Abbas yake ta addu'a aransa cewa " Allah yasa kunnuwansa ba dai dai suka jiyo masa ba, inma dai dai ne Allah yasa ba tashi Fatiman Mahmud yake nufi ba ". Murmushi Mahmud yayi wanda ni kaina bansan ma'anar ta ba domin bata farin ciki bace, sannan yaci gaba da fa'din " kamar de ni, Abbas kaima kayi mamaki ko? Shiru Abbas yayi yana kallon sa bashi da buri ayanzu illah yaji 'karshen zancen Mahmud 'din. Tunawa da maganar Mahmud yayi wanda yayita bada jimawa ba inda yace " wai Abbah _Teemah_ _zai aura_ _min_ . Kauda kansa gefe Abbas yayi da sauri daya tino maganar acikin zuciyarsa in banda innalillahi babu abinda yake iya fa'da. Yana juyowa sai suka ha'da idanu da Mahmud sai yace. " kaima kana tayani mamaki ko Abbas, ni bansan me yasa Abbah na ya yanke wannan hukuncin ba batare da ko yin shawara da ni ba, juyowa yayi da sauri kamar zautacce yayi facing Abbas sannan yaci gaba da maganarsa. "Kasan wani abu Abbas? Ni ban ta6a kawo faruwar hakan ba ko da a wasa, hasashe na be ta6a kawo min yiwuwar aure tsakanina da Fatima ba not even in my dreams". " Fatima fah Abbas, my lovely sis, my lil sis how can I........... Dafe kansa yayi da sauri ya kasa 'karasa maganar da yayi niyyan fad'i. Abbas ma rintse idanunsa yayi da 'karfi yayi baya ya jinginu da jikin kujerar daya ke zaune. Mahmud kansa ya ri'ke da 'karfin gaske dayake mugun sara masa, yanajin da zai iyayin hawaye ayanzu da babu abinda zai hanashi yayi saboda yasan shine ka'dai zaisa ya samu 'dan sassauci amma ina...... Da 'kyar Abbas ya daure ya tashi yakoma kusa dashi ya sa hannunsa ya dafa kafa'dar Mahmud 'din duk da yanajin wani 'kuna azuciyarsa da be ta6a experiancing akwai irinta ba, amma yah ya iya akan son zuciyar shi bazai iya ya bar Mahmud ya bijire wa maganar mahaifinsa ba, duk da ba wani sanin Abbahn yayi sosai ba amma yasan Abbah bazai ta6a yanke hukuncin da yasan akwai cutarwa aciki ba musamman ga 'dansa na cikinsa, kuma ma idan yayi la'akari da yanayin da suke zumunci must especially labarin da Mahmud yabashi farkon ha'duwarsu a Damaturu ya tabbata Abbah ba zai rasa dalilin da ya sa ya za6i hakan ba. " Laifina ne, nasani laifina ne da ban bayyana kudurina akanta tun farko ba, na ri'ke abuna acikin raina, ina can ina tunanin yaushe ya kamata na mallaketa!, yaushe zata zamo tawa!!, bansani ba ashe BURINAH da mafarkina bazasu ta6a tabbata ba. " Amma duk da haka bazan iya barin ka acikin wannan yanayin ba, Mahmud ko ba komai kai abokina ne. Duk acikin zuciyarsa yake wannan tunanin. Dan a yanayin da yaga Mahmud 'din sosai ya tausaya masa alamu sunnuna 'karara shi be yi na'am da wannan ha'din ba. Da 'kyar yasamu ya bud'i bakinsa yafara magana " kayi hakuri Mahmud kasan Abbah yana sonka bazai ta6a ha'da ka da abinda ba dai dai bane agareka, ka daure ka ya'ki zuciyarka kayi masa biyayya na tabbata zaka ga ribarsa wata rana, ko ba komai iyaye abin girmamawa ne nasan kasan wannan, kuma shi aure ba yana nufin tashin hankali bane, Mahmud aure rahama ne, sannan ibada ne, cikon addini ne. Ni agani na Abbah gata yayi maka tunda har yayi maka za6in matar aure da kansa, kuma ma ai kaga Fatima yarinya ce, kasanta, kasan kalar tarbiyyarta ,kasan damuwarta farin cikinta da ba'kin cikinta kaga baka da matsala da wannan kamar yadda nasan bazaka samu problem da ita ba. Idaan kuma batun *so* ne, na tabbata ahankali zaka so ta basai an 'dauki wani dogon lokaci ba,insha Allahu baza 'a samu matsala ba musamman inkayi la'akari da sanayya da kuma shakuwar dake tsakaninku, inkuma kana tunanin ba ita kake so ba wacce kake so daban, Mahmud ai kai namiji ne kana da damar dazaka auri mata daga 'daya zuwa hu'du inkaga zaka iya" Muryar Abbas har rawa takeyi da 'kyar yasamu yah dasa ayar maganar tasa tare da numfasawa duk a'ko'karinsa naganin ya taushi Mahmud 'din. Da 'kyar yasamu Mahmud ya sau'ko ya 'dan kwantar da hankalinsa daga 'karshe bedroom 'din Abbas ya shige shima ya watsa ruwa sannan yazo ya kwanta, cikin sa'a kuwa yana kwanciya bacci ya 'dauke sa. Se bayan shigan Mahmud ciki kafin Abbas yasamu ya mi'ke akan 3seatern shi fuskan shi na kallon ceilling yayin da ya tsurawa ceilling fan 'din dake juyawa asaman idanunsa, hannun sa yasa ya dafe saitin zuciyarsa dayake jin yana harbawa da 'karfin gaske, daga 'karshe lumshe idanunsa yayi ahankali, wani abu yakeji ya tokare masa 'kirji wani abu da besan mene ba ke damunsa ba, ehh mana be sani ba shin nauyin da yake ji azuciyar san na son Fatima ne ko kuma na ba'kin cikin rabuwa da ita neh. Be ta6a tunanin irin wannan abin zai iya zuwa ya yanke masa kyakkyawar ala'kar da zuciyarsa ta 'kulla tsakaninsa da Fatima ba. Jijjiga kansa yayi ahankali kamar da wani yake hira akwancen acikin zuciyarsa yace " ina son...ki..Fati....amma ga dukkan alamu yanzun kinmin nisa". Bu'de idanunsa yayi sanadiyyar sallama da kuma 'karan 'kofa dayaji alamun anbu'de anshigo. Hannah ce yagani tsaye ajikin 'kofan tamkar tana tsoron shigowa, daya ga haka sai ya maida idanunsa ya kuma rufesu kamar yanda suke da farko batare da ya kula. Ko kuma amsa sallamar tata ba. Itan ma data ga haka sai tace masa " Ummah ce tace in zo in duba ka wai tajika shiru". Baifi tsayuwar second biyar tayi ba bayan tayi maganan sai ta juya takoma inda ta fito, domin tasan Yayan nata ba magana zai yi mata ba shiyasa ma ta juya batare da ta jira amsa daga gareshi ba. Kamar be ji me tace dashi ba ,sai can sai ya yun'kura ya tashi tare da saka takalmansa yafita a'dakin. Parlourn Ummah ya nufah inda ya sameta zaune akan kujera me zaman mutum uku Hannah ma na zaune agefenta. Ciki-ciki yayi sallama sai suka amsa dukkansu atare suna masu maida hankulansu gareshi saboda yanayinsa daya canju. Agefe dasu ya zauna sai ya gaida Ummahn nasa tare dayi mata barka da yamma, ita kuwa a gaggauce ta amsa domin damuwa data gani 'karara a fuskan Abbas 'din harma da muryarsa ga idanunsa da suka yi jajir suma. Hannah ce ta tashi ta bar 'dakin Ummah ma bata lura da ita ba sanda ta fitan domin hankalinta nakan Abbas alokacin. " me yafaru ne Abbas ko de kana bacci Hannah ta taso da kai," Be yi magana ba sai ita ce tacigaba da cewa "ka ganka kuwa, meke damunka ne pls?" Lumshe idanunsa yayi ahankali koda ya bu'de kuwa sai ya sau'ke su akan fuskan Ummah. Tasowa yayi ya dawo kujeran da take zaunen inda Hannah ta tashi, koda ya zauna 'din kuwa sai ya zamo ya kwanta tare dayin matashi da cinyar Ummahn, ita kuwa sai binshi takeyi da kallo tana mamakin sa. "Abbas meke damunka ne wai " Tasake maimaita tambayar tata akaro na biyu tare da 'dora hannunta akan sa. Ahankali yace " Ummah Abbahn Mahmud yace wai aure zaiyi masa!". 'Kwafah tayi tana kallonsa kana tace " haba Abbas shine kuma kabi ka 'daga hankalin ka dan Mahmud zaiyi aure"? " Mahmud baya son auren fah Ummah, kuma ma wai kwanan nan za'a yi auren gashi can duk ya bi ya 'daga hankalinsa akan maganar da kyar nasamu ya sau'ko Ummah". Daga nan yayi shiru domin daman da 'kyar yake maganar daurewa kawai yayi, in baka sani ba zaka zaton damuwar da Mahmud yake ciki ce shima ta dame shi amma ga wanda yasani kuma sai de yace.......🤔( me za'ace)? _Ni de nace_ _Allah sarki bawan_ _Allah_ . Comment Vote Share *Salmerh* 😍 [10/2, 6:00 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍 *Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 👎🏻 🅿 *42* *ABUJA* Fa'da Ummah tafara yiwa Abbas atsanake inda take cewa " wato na fahimci dukkanku ra'ayi 'daya gareku ko Abbas? Gaba 'daya sai kuka ha'du kuka 'daga hankulanku akan batun aure kawai,! saboda Allah me hakan ke nufi kenan? abin mamaki ma se kace wasu yara 'kanana, dube ka fah yanda ka koma kaima kenan inaga shi uban gayyar kuma? kaida ya kamata ace ka bashi baki ya amince sai kuma ka tayashi shiga damuwa wannan ai shirme ne Abbas, daga kai har Mahmud 'dinma ni bansan lokacin dazaku girma ba wallahi, ace dan abokinka zaiyi aure kazama haka toh in kaine kuma ai Allah ne ka'dai yasan ya zakayi........ hakan da kuke yi fah bakomai yake 'karawa ba illah 'kara fito da zallar 'kiyayyar da kuke yiwa aure" Baki ta kama tace "anya ma lafiyarku qalau kuwa Babana". Shiru yayi mata be bata amsa ba. aransa yake cewa " lafiyar mu 'kalau Ummah ,bazaki gane bane! kowa na tashi damuwar daga ni har Mahmud 'din, ni ita nakeso ina sonta sosai Ummah fiyeh da kaina, amma yanzu kam dole na ha'kura da ita domin tayi min nisan da bazan iya kamota ba har abada, da ace ba Mahmud bane da wallahi babu wanda ya isa ya shiga tsakanina da Fatima ko ma waye shi sai inda 'karfina ya 'kare, amma Mahmud kam dole na ha'kura inba zuciyata ha'kuri domin shi mutun ne, mutum ne da kowa zaiyi alfaharin kasancewar sa atare dashi, bazanso akan mace ala'kata dashi ta rushe ba, da irin wannan tunanin bacci yayi awon gaba dashi akan cinyar Ummahn daman aikin sa kenan idan yadawo gida sai de yayi ta bacci wani lokaci sallah ce ka'dai ke tada shi yana idarwa kuwa zai koma, amma idan yana bakin aikinsa kuwa kusan mantawa ma yakeyi da batun bacci arayuwarsa koda yake yanzun ma zuwan Mahmud ne ya tada shi abaccin kuma badan zuwan Mahmud 'din ba da zai 'dan 'dauki lokaci yana bacci abinsa. Ita kuwa Ummansa idanu ta zuba mishi kawai tana 'kara mamakin hali irin na sa, shi baya son ace yayi aure sannan kuma ance abokin sa zaiyi nan ma kuma sai duk sauka ha'du suka 'daga hankulansu, " kai yarannan kuna da abin mamaki, Allah dai yakawo muku abokan zama nagari".(Ameen). Washegari Abbas da Mahmud tare suka fita daga gida bayan Ummah ta ha'da su tayi musu nasiha sosai daganan ta sallame su suka tafi kowa ya nufi inda zashi, bayan Abbas ya sake 'karfafa wa Mahmud gwiwa akan maganar daya zo da itan tare da jaddada masa muhimmancin bin maganar iyaye kamar yadda Ummah tayi musu. Haka suka rabu Mahmud na yiwa Abbas 'din godiya da kuma fatan alkhairi domin zuwa yanzun Alhamdulillah ya ji dama-dama a zuciyar sa, he is now ready to face his reality. *DAMATURU* Daddyn Teemah be bari mummy ta sanar da ita ba shine dakansa ya zaunar da ita yayi mata bayani yanda yasan zata fi fahimta, itanma da farko ta 'dan ji tashin hankali amma aranta, dayake bawani zama takeyi ta fahimci me zuciyarta take ciki ba shiyasa takasa gane inda nutsuwarta ta dosa akan maganar daddyn. Ji takeyi tamkar tayi na'am da maganar amma deep down tana jin kamar kuma bata aikata daidai ba. Daddy kuwa kafin su rabu sai da ya tabbatar da cewa ta amince da maganar 100% kafin hankalinsa ya kwanta, daman damuwarsa kenan shine kar Fatiman ta'ki amincewa duk da yana ganin kamar wayo be gama isanta ba kuma hakan bazai barta ta kasa amincewa da maganarsa ba, amma 'dan adam sai Allah, kowa nada nashi kalan burin arayuwarsa. Har Daddy suka gama maganar su da Teemah mummy bata saka musu baki ba, ita abubuwa ne suka taru suka yi mata yawa azuci, tunda ranar da akayi maganar auren nan mummy bata sake yin baccin kirki ba, tausayin 'yarta ta yawa yake yi mata ta fuskoki da dama. Babban damuwarta shine yanda Anty zata kar6i batun nan, tasan da wahala ta yadda da auren, idan ma ta yadda 'din toh wani irin zama zatayi da Fatiman. Sannan secondly alamu da yawa sunnuna cewa tun ba yau ba Teemah ta fara son Abbas, she can proof that Zuciyar Fatima Abbas takeso, amma rashin wayo irin nata yasa takasa bambance abinda takeso harma gashi ta amsawa mahaifinta cewa ta amince da auren Mahmud. Yanzu kam mummy ta saduda ta barwa Allah komai " bani da abin cewa nikam ayanzu sai de nayi ta miki addu'ar Allah ya tabbatar da alkhairi aryuwarki". Teemah sai da ta koma 'daki sannan ta fara fahimtar yanayinta, jin ta tayi wata iri, kaf sai ta nemi nutsuwa azuciyarta ta rasa sai asannan taji tamkar bata yiwa kanta adalci ba. Fa'dawa tayi rigingine akan gadonta abun duniya duk sun taru sun mata yawa, Abbas ne ya fa'do ranta karo guda sai taji zuciyarta ta tsinke da 'karfin gaske, har sai da ta rintse idanunta ta kuma dafe 'kirjinta da hannunta. Daga nan abubuwan da suka faru atsakanin su suka rin'ka dawo mata 'daya bayan 'daya...... Yah Abbas.....Rashin fara'arsa......Muguntarsa....Masifarsa.... Komai ma nashi yaringa dawo mata azuciya, juyi tayi zuwa 'dayan 6angaren yayin da ta tuno lokacin da Mahmud ya zo gidan su, basu wani 'dau lokaci ba suka saba da juna sa6anin Abbas da alokacin ma kullum sai sunyi fa'da dashi. Tashi tayi ta zauna abakin gadon ta cigaba da tunani haka kawai batare da tasan dalili ba taji zuciyarta tana mata comparing halayyar Abbas da Mahmud amma kwata-kwata ta kasa samun laifin Mahmud aranta ko 'daya sai de duk da haka zuciyarta takasa nutsuwa da maganar da suka gama da mahaifinta lokuta 'kalilan da suka gabata, sai take jin ma dama ba Yah Mahmud daddy ya za6a mata da sunan ta aura ba. Tashi tayi da gaggawa kamar wacce aka bawa umarni ta nufi wurin ajiyan kayanta sanadiyyar tuno wani abu da tayi, bincike tafarayi acikin kayan inda ta ringa ciro kayan da 'da'dd'aya tana zubo dasu 'kasa sai da ta ciro kusan rabi daga cikin kayan nata kafin ta samu abinda take nema 'din. Da sauri ta tattara ta dawo 'kasa akan tiles ta zubasu itama ta zauna dirshan agabansu. 'Ko'karin ha'da papers 'din takeyi amma har yanzu ta kasa ha'dasu, haushi hakan ya bata dan ayanzu damuwarta be wuce tasan miye acikin takardan ba da tun ranar daya batan takardan ta lalace da gumi, tun ranar taji ba'kin cikin rashin ganin abinda ta kardan ta 'kunsa ga dai alamun rubutun da akayi da biro tana gani amma gane ko menene sam ya gagare ta. Ko ta 'dan harha'da sai taga beyi yadda take so 'din ba ga dukkan alamu guri me muhimmancin ne ya fi ji'kuwa tun awancen ranar. Haushin bazata ta6a ganewan ba yasata ta dun'kula su tayi jifa dashi kamar zatayi kuka. Tana watsarwan kuwa sai tajiyo muryar mummy ta 'kira sunanta tare da 'karasowa cikin 'dakin nata ahankali. Tana ganin mummyn sai taji hawaye ya gangaro mata da bata san dalilinsa ba, tahowa tayi da sauri ta rungumo mummyn suka zauna abakin gado. Fatima bata sani ba ashe tun fara binciko kayan da Teeman tayi mummy ke tsaye tana kallon ta dama so take taji asalin ra'ayin ta akan maganar, koda tazo tasameta awancan halin kuwa sai ta tsaya karantar yanayinta tayi zaton ko wani abin ne daban yake faruwa , and now she's crying. Sai da ta yi kukanta kusan na mintina biyu kafin nan mummy ta 'dagota daga jikinta, atsare tasa ta tayi shiru kana tace tasanar da ita meke damunta, menene yasata kuka. Ido mummy ta zuba mata tana karantar yanayinta da kyau, yayin da Teemah ta maida kanta 'kasa kamar me jin kunyar ha'da idanu da mummyn sai kawai taci gaba da tsiyayar da hawaye, hawayen ma da sauri suke 6ul6ulowa dan koda mummy tayi 'ko'karin goge mata ma kasa tsayuwa suka yi dolenta ta barta . Sai da tasake maimaita tambayar tata kafin ahankali Teemah ta 'dago tace da ita " kirjina zafi yake min mummy" "Miye dalili" mummyn ta tambayeta. Hannu ta 'dago ta 'dora akan kirjin nata sannan taci gaba da fa'din " mummy dagaske daddy yakeyi wai aure zai min?" " miye saki zafin 'kirjin " mummyn tasake tambayarta maimakon ta bata amsar tambayar da Teemahn tayi mata. Sai tace itama bata sani ba, kawai de tana jin kamar bata son auren ne. " bakya son auren ko kuma Mahmud 'din ne bakyaso"? Mummyn tasake tambayarta idanunta kafe akan Teemah. " Nima fah bansani ba mummy nide kawai zafin nakeji a 'kirjina". Shiru sukayi dukkansu na 'dan wasu da'kiku sai mummyn tace mata ta share hawayenta kukan ya isa haka. Tambayarta mummy tasakeyi wai "meyasa ta amince wa mahaifinnata bayan tasan bataso. Goge hawayen tayi kamar yadda mummy ta bu'kata, amma kuma game da tambayar sai ta rasa amsar dazata bawa mummyn dan haka kawai sai tayi shiru. Ganin hakan da Teemah tayi tasan zaiyi wahala tasamu jin amsarta dan haka sai ta juya ta kallo cikin 'dakin inda Teemah ta zauna 'dazu. " wa'dancan 'kananun papers 'din fah na menene su kuma"? Juyawa Teema tayi ta kallo inda suke itama batare data yi niyyan fa'din komai game dasu ba. Fahimtar da mummy tayi cewa Teemahn bata da niyyan sanar da ita sai kawai ta mi'ke tsaye tace " inkin gama kisame ni apalour ina jiranki." Da kai Teemah ta amsa mata daga nan takama hanyar waje. Binta da idanu Teemah tayi harta 6acewa ganinta, daganan ta tashi sai ta nufi gurin data watsar da pieces 'din takaddun, ta tattare su gaba 'daya ta maida su can 'kar'kashin jerin kayan da suka rage bata wargaza ba. Tana 'kokarin fara gyara kayan sai ga Baabah Lami ta shigo da sallamarta tace "Hajiyarki tace kayanki sun zubo " Kai ta 'daga alamar "ehh" sannan ta matsa daga gurin kayan ta nufi hanyar bayi domin ta watsa ruwa dayake daman bata yi wanka ba lokacin da daddy yakirata. Daga ita sai towel tafito abayin, yayin da tabaro kayan data cire abayin domin wanki suke bu'kata. Fitowarta kuwa keda wuya Baabah Lami ta jefa mata tambayar wai yau kuwa lafiyarta ? "Uum lafiya ta 'kalau me kika gani"? tayi maganar tana 'ko'karin goge fuskarta da wani 'dan 'karamin wiper dake ri'ke ahannunta na dama . Baabah Lami shiru tayi taci gaba da gyaran kayan da takeyi, Teemah kuma sai ta wuce gaban madubi ta sake duba yananyin fuskarta daganan ta dawo inda kayan tan suke zube aciki tasamu wanda zata sanya sai ta koma 'daya 6angaren da tuntuni arufe yake ta bu'de shi ,bakomai aciki illah tarkacen inners 'dinta dasuke kala kala. Zura doguwar rigarta tayi bayan tasaka ta saka bra da pant ko kunyar Baabah Lami ma bata ji ba tayi shirinta abinta, tana gamawa kuwa ta zari mayafi ta fice a'dakin tare da cewa Baabah Lami " ina zuwa" ta nufi gurin mummy. Tana isa gurin mummyn ko gama daidai ta zamanta bata yi ba mummyn tace " yanzun muka gama waya da Abbas yace wai agaisheki" Murmushi ne ya kubce mata har sanda ha'kwaranta suka 'dan bayyana afili. _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh*😍 [10/2, 6:01 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all _cApTaIn_ _AbbAs Fans_ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* To know that you do not know is the best. To pretend to know when you do not know is a disease. 🅿 *43* Har bata san lokacin da tace "Kuma mummy dakansa yace agai sheni? kai mummy ta 'daga mata, sai ta sake cewa " lallai Yah Abbas sai yau yaga dama ya tuna dani kenan" "Da in cemiki akayi ya manta dake ne? " ya manta dani mana mummy "! Teemah ta bawa mummy amsar tambayarta. Mummy bata 'kara kulata ba sai de afakaice take 'kara kula da yanayin ta saboda murmushin da tayi tun 'dazun yakasa barin kan fuskarta harma sai ya 6oye damuwar da take ciki 'dan lokuta ka'dan da suka gabata. Tausayi Teemahn take bawa mummy sosai zuwan yanzu ta gama harbo jirgin 'yartata sai de ga dukkan alamu ita kanta bata san me take ciki ba har yanzu, shiyasa kawai zataci gaba ro'kon Allah akan ya takaita mata yabar abin a lullu6e kamar yadda Teemahn bata gane ba Allah yasa yatafi a hakan har abada, domin matu'kar Teemah ta fara gane bambancin soyayyar 'yan uwan taka da kuma soyayyah me zaman kanta (ta aure) tasan za'a samu matsala ne,fatan ta de Allah yasa har ayi agama lafiya kar asamu problem 'din komai, tunda aure ma zatayi ai shikenan. Domin indai Abbas ne tana ganin da kamar wuya, ko yanzun ma babu wani gaida ta da yace yanayi, ita ce mummyn dakanta tabashi labarin abin da ke faruwa a gidannasu kuma ko da ta fa'da masan ma bata wani ji alamun canji atattare dashi ba ko daga muryarsa har yanayinsa, da suka gama wayanne suna sallama sai yace" agaida mutan gidan " shine ita kuma mummy tace da ita Abbas na gaidata kuma tafa'di hakanne saboda mitan da Teeman keyi wasu lokuta akan cewa Yah Abbas ya manta da ita. Acikin satin aka gama maganar auren Teemah harma aka sa rana sati hu'du masu zuwa. Daddyn Teemah dakansa ya yanke wannan lokacin domin yana ganin adaidai wannan lokacin zai fi dacewa ayi bikin batare da kowa ya takura ba. Mummy bata so hakan ba domin ita aganinta lokacin yayi kusa bata so aka yanke lokacin kwana kusa haka ba, koda ta yiwa Daddy maganar ma sai yace mata "kar ta damu ai komai lokaci ne, ba gaggawa sukayi ba wata 'kila haka Allah ya riga ya tsara lokacin bikin Fatiman yace kinga kuwa mu bamu isa muja da ikon Allah ba". Dolen mummy taja baki tayi shiru, 6angare guda kuwa hankalinta yakasa kwanciya sam da wannan auren.Yayin da daddy shikam ba ruwansa, kusan kullum idan ya zauna sai dai kaji yana waya ya sanar da cewa lokaci kaza ne bikin Fatima 'yar wajensa, acikin lokaci 'kalilan kusan mafi yawa daga 6angarensa sun san da labarin auren kama daga kan abokansa har 'yan uwa da dangi ma duk ya sanar dasu. 'Bangaren Anty kusan hauka taso tayi akan wannan maganar gaba 'daya ta hana kowa sukuni agidan, gajiya Abbah yayi da halintan datakeyi musu akan auren, wani lokaci ya tanka mata ai kuwa kamar jira ta keyi, shi dama mahaukaci yafi so idan yana abinsa yasamu mataimaki, daga nan haukar Anty ya 'karu daddy ma ranshi ya 6aci sosai musamman yanda take ha'da ilahirin zuri'arsa ta zagesu kaf abin na masa ciwo sosai, amma sai ya lallashi zuciyar sa ya samu ya 'dan sassauto domin ji yake a ranar kamar yayiwa Antyn dukan tsiya, amma yasan haka bazai ta6a kawo gyara ba, zagi kuwa har sai da yaji kamar ya toshe kunnuwansa, munafukai takirasu yafi sau a'kirga, shikuwa yariga yayi alwashin ganin faruwar wannan auren yace ko ma miye zai faru sai dai ya faru amma shi kan be ga me hana shi 'daurawa Mahmud aure ba , mahmud dama ba ya gida tun dawowarsa daga wurin Abbas be fiya zama agida ba, wani lokaci arana sau 'daya Abbah ke kallonsa amma hakan ba damunsa yakeba, tunda dai be musa masa cewa bayaso ba ai toh "Alhamdulillah zai sau'ko ne idan ma fushi yayi. Da abin Anty yayi yawa ne sai Abbah ya yanke shawarar sanar da mahaifinta halin da ake ciki, beyi 'kasa agwi wa ba ya shirya yatafi kano musamman ya je domin yakai 'karanta agurin mahaifinta Alhaji Muhammad, abinda be ta6a faruwa ba kenan tun farkon auren su sai awannan lokacin. Yanzun ma yaga abin nata yayi yawa ne shiyasa, dan ko kunya bataji ballantana tsoron Allah take furta maganganu marasa kan gado ciki harda alwashin kisa akan wai inhar suka yadda auren nan yayiwu. Ran Alhaji Muhammad ba 'karamin 6aci yayi ba da yaji abinda Abbahn yagama zayyano masa, tun ma kafin Abbah yabar wurin yafara masifah yana nunawa mahaifiyarta illar rashin hankali da kuma 6ata rayuwa da halayyan yaro tun bai je ko'ina ba, yace wannan rashin hankali har ina, maimakon Abbah da za'a bawa ha'kuri sai ya zamana shine ke bawa Alhaji ha'kuri gashi girma ya kamashi yanzun sosai harma baya fita harkan kasuwancinsa sai de a jagoranceshi,maganar ma da 'kyar yake fizgota yakeyi tsabar ranshi daya 6aci da Antyn. Da 'kyar suka samu ya sau'ko daga dokin fushin da ya hau, mahaifiyar Anty har sai da hawayen ta ya 'diga tsabar yanda taji hankalinta ya tashi domin fa'dan Alhajin kakaf kanta ya tattara ya dawo afa'darsa wai ai duk laifin tane. Koda Alhajin ya sau'ko sai ya bawa Abbah ha'kuri sosai tare da cemishi idan yakoma yaturota tazo yace mata yana nemanta inda hali ma su dawo tare. "Abbah yace bakomai za'ayi kamar yadda ya keso" Alhaji Mahammad yayi yayi da Abbah akan ya 'dan kwana musu biyu amma Abbah ya'ki amincewa yace yana so ne yaje yaga 'yan uwan mahaifinsu" Alhaji Muhammad dayaji haka sai ya washe baki yace " ai babu komai hakanma yayi, yace daman ma yanaso ya tambayeshi ko yajeshi 'din ashe ma abin nacikin ransa, Sai Alhajin ya 'kara jan hankalin Abbah akan kyautata mu'amala da kuma ri'ke zumunchi yace zumunchi ba'abin yarwa bane akula da ita sosai.. Fatan alkhairi yayi masa shi Alhajin daga nan Abbah ma yayi musu sallama yafita agidan yana me 'kara yiwa Alhajin godiya tare da yi musu alkhairi sannan yayi tafiyarsa. A waya sanar da Anty sa'kon mahaifin nata inda ya 'kara da fa'din " nan da kwana biyu tasamu ta je domin yace karta 6ata lokaci" Batayi magana ba illah wani dogon tsaki da ta ja sannan ta kashe wayan, Abbah kuwa be damu da yanda tayin ba dan shi fiye da hakan ma yasan zata aikata, transfern ku'di yayi mata a account 'din ta kafin ya maida wayar cikin aljihunsa wanda yasan zai isheta duk wani shige da ficenta har taje ta dawo. Koda Abbah ya isa gurin 'yan uwan mahaifinsa sun yi farin ciki da zuwansa sosai, 'dai 'dai ku daga cikin su ma sun rasu yayinda ma'danda suke rayen ma duk 'karfin su yakasa ayanzun, wasun da suka rasu Abbah yanada labari wasu kuwa be sani ba sam dan ba wani communication sosai ne atsakaninsu ba, tausayinsu yakeji sosai duk 'kinsu dasukayi abaya be damu ba yasan ko ada 'din ma ba laifinsu bane giyar talauci ce tasa su sukayi yadda suyi rayuwa dasu. Sai ya ha'da yayi musu ta'aziya gaba 'daya yakuma yi wa iyalansu kyaututtuka sosai wanda zata anfane su tareda wa'dan da suka rage arayen daga yayu da 'kannen mahaifin nasa dukka ya ha'da yayi musu alkhairi. Da ya sanar dasu ma batun auren Mahmud ne yatashi sunnuna farin cikin su sosai harma da dama daga cikin su suka rin'ka zubda hawaye suna masu neman yafiya daga gurin Abbah akan abinda suka aikata musu abaya. Shima kusan kukan suka saka shi domin idan yagansu akowani lokaci tunowa yakeyi da mahaifinsa amma dole ya daure ya hana nashi kukan tasiri ya ta basu baki yana nuna musu cewa ai tuntuni komai yawuce shi agurinsa be ri'ke su a zuciya ba komai yafaru ai mu'kaddari ne kuma rubutacce ne awajen mahallici. Kwanan sa uku tare da dangin mahaifin nasu kafin Anty ta iso wai a hakan ma sai da Abbah yayi mata 'karyan a kwana biyu mahaifinnata ke nemanta amma duk da haka sai da ta 'kara akan yanda ya sanar da itan. Be tafi aranar ba sai washe gari sannan yayi sallama da kowa yakama hanya. Alhaji fa'da yayi wa Anty sosai harma ya jajjada mata cewa matu'kar tace bazata kwantar da hankalinta ta zauna lafiya agidan aurenta ba toh kar tayi tunanin tana da mahaifi aduniyan nan. Yace kuma datake wani borin hana auren bata tunanin cewa shi Mahmud 'din da ita 'yar gidan Khadijan sun fi kusa akan wata daban da takeso 'dan tan ya aura, yace wata daban 'din ma girman cikin garin lagos. Shi aure mu'kaddari ne kuma lokaci ne, idan Allah ya riga ya tsara abu toh babu wanda ya isa ya canja shi, sannan ba'a jayayya da qaddarar ubangiji koma ayaya tazo maka u must have to accept it, karta bari shai'dan yayi galaba akanta akan abun da ba ita keda ikon sawa ko hana yiwuwarshi ba, yace da ace son ran mutun ne dashi dakansa bazai barta ta auri Yusuf alokutan baya ba saboda yasan halinsu da bambamci , amma miye dayake Allah yariga ya rubuta sai sunyi auren yace bagashi ba , ni ban isa na hana ba, kamar yadda kema kika yi ka'dan ki hana dan haka tun wuri ki maida hanakalinki ki san me kike ciki, idan har kika kuskura na 'kara jin kinyi irin abu makamanciyar wanda naji ayanzu toh wallahi Maryam kisani zamu raba ala'ka dake ,saboda ni kinga ban aurar dake ga wannan bawan Allahn dan ki ta 'daga masa hankali ba, yace wallahi da yasan abinda zata aikata kenan ma da tun farko ba zai amince da batun auran ba, amma bakomai wannan duk cikin 'kaddara ne kuma babu wanda ya isa ya gujewa tasa 'kaddarar matu'kar tazo. Da nasiha ya kammala maganar tasa ga dukkansu tare da 'kara bawa Abbah ha'kuri yace ya 'kara akan wanda yayi tayi abaya. Godiya Abbah yayi masa daga nan suna idar da sallahr azahar ya kama hanya ya koma lagos. Anty kuwa kusan Satin ta 'daya a kano bayan komawan Abbah, duk da bawani da'din zaman takeji ba amma wani lokaci takanji cewa zama agidan yafi mata wai ko zata hita da taahin hankali, gashi tana ji tana gani abu na nema yafi 'karfinta abanza kuma takasa 'daukan mataki. Kuma ako wacce wayewar gari sai mahaifinta yayi mata nasiha sosai cikin natsuwa akan rayuwar duniya iya yanda yasan zata fahimceshi, ita kanta mahaifiyar tanma yanzu ba kamar da ba, dayake girma yakama ta itama kuma sai tayi sa'a yazo mata da shiriya, wani lokaci takanji tamkar tayi kuka dan ba'kin cikin halin da akace 'yarta nayi, domin tasan komai akace maryam 'din tayi laifinta ne komai da aka 'kirga awurinta ta koya sai dai yanzu tanaji tamkar maryam 'din tafi 'karfinta tama kusan nunka mugun halin data koya agurin mahaifiyarta 'din. Itama sosai take zaunar da Antyn duk dama bata fiya sauraranta ba domin ba 'karamin raina mahaifiyartan tayi ba, gara ma shi Alhaji tana 'dan jin shakkan shi hakan yasa dole take zama ta saurare shi ko bata so ko da ba zata 'dauki abinda yake fa'da 'din ba amma dai zata zauna dolenta, tsawon lokaci tana sauraran karatun nasa batare da ta 'dauki koda abu guda daga ciki ba. Abinda basu sani ba ayanzun shine, Anty bata da burin daya wuche taji ance babu wannan maganar auren. Tsana mafi girma take ji azuciyarta game da auren, tana jin koda me nene ze faru sai ta ga ta hana wannan auran faruwa. Duk da yawan nasihar da Alhaji muhammad ke mata amma dai dai da rana 'daya tak sam 'Kudurin Anty be canja ba daga cikin 'kudurorinta na baya sai ma abinda ya 'karu domin 'karan tan da Abbah ya kawo bai gyara komai ba sai ma lalata wa dayayi. *sharhi nake bu'kata ga duk wanda yakaranta* 🤞🏻 *Salmerh* 😍 [10/2, 6:01 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* There is no any slave of Allahwho commits a sin, then he perfects his ablution, stand b4 Allahu subhanahu wata'ala to pray 2raka'ah of prayer, then seeks Allah's 4giveness, expect that Allah will 4give him. Abu Dawud,2/86, At-tirmizi 2/257. 🅿 *44* Abu 'daya ke cin zuciyar Anty akoda yaushe in ta tuna shi kuma shine yafi sata damuwa fiye ma da batun auren Mahmud 'din haushin hakan kuma shike 'kara sata takae jin haushin kowa,dan tasan batun aure me sau'ki ne matu'kar tasamu ta ziyarchi gidan _'dan_ _Oga_ (boka) tasan matu'kar ta samu ta ha'du da shi to bata da sauran damuwa. Amma prolem 'dine taya zata ha'du dashi? Mtsalar ka'dai dake cinta kenan har azuciyarta, ita aganinta maganar auren nan dasuke ta wani 6ata bakinsu akai arana 'daya zata iya warware shi kaf kuma waru kenan, da ace ta 'dau mataki toh da dolen kowa ya ha'kura da maganar auren amma kuma sai tayi rashin sa'a 'kawarta Anty Chideh ta'ki sam ta taimaka mata akan lamarin, sai ma wasu banzayen sharu'd'da datake faman gindaya akai kafin wai tayi mata jagora zuwa wajen _'dan Ogahn_ itakuwa sam bazata iya abinda Anty chiden take 'ko'karin taga ta aikata ba, akullum tunaninta yanda zata samo mafita ne amma taras,shi 'din nan dai tafi yadda da aikinsa sai dai ta rasa yadda zatayi tunda 'kawarta ta'ki kaita , tambaya kuwa babu irin wanda batayi ba amma tarasa wanda yasan shima balle 'kauyen dayake rayuwa. Idan ta matsa sai akwatanta mata wani wuri daban , da zumu'din ta take zuwa amma kamar ha'din baki kalaman su iri 'daya ne. Akwai wani guri da suka je da wata 'kawarta, bokan ce musu yayi wannan auren babu fashi sai anyi, the same abinda wata matsafiya ta gaya musu da suka je da mahaifiyar Munira harma da ita kanta Muniran. Anty kamar zatayi hauka dataji abinda suke ta faman sanar dasu. Inta matsa wai ko za'a samu wata hanya da za'a awarware maganar takance ita ko nawa ne she is ready to pay it indai auran zai fasu. Akwai wani bokan dayace mata ehh akwai dama za'a iya warware maganar amma ba ku'di zata biya ba zata tattaro ta dawo gurin na tsawon wata guda akwai aikin daza'a yi. Sam sai taji zuciyarta be yi na'am da wannan batun ba, auren da ake 'ko'arin yinsa nanda sati uku masu zuwa taya ya itakuma za'a ce tayi 1month tare dasu da yaushe kenan za'a warware maganar, bayan an 'daura kokuwa? Bata manta labarin da Chide 'kawarta ta bata ba na wani daya ta6a yi mata aiki tace satin ta guda agurinshi yana faman sex da ita ba 'ka'k'kautawa sai cewa yayi wai suna 'diban abinda zasu ha'da jinin tane da mijin nata alokacin, itakuwa dayake ta 'kagu taga ta malleka shi sai bata damu ba ta daure tayi ta jure wahalhalun da bokan ke bata, tace har tacika satin ana abu 'daya, tace data koma gida sai da tayi jinya kusan na. 11days kafin nan ta warware, atlast ma kuma bata ga komai ya canja ba babi wani abinda ya faru sai da ta je gurin wani daban kafin nan tayi sa'a aikin ta yaci. Tace ballantana ita da ba mallaka ko juyo da hankalin wani take bu'kata ba ayanzun burinta ta warware maganar ne toh dan me zata tattaro ta dawo gurin boka har na tsawon wata guda, yana nufin ita ma so yake yayi mata irin na 'kawarta kenan Allah ya kiyaye tace afili, _angudu ba'a_ _tsira ba kenan_ . 'Kin amincewa tayi kawai tayi tafiyarta. Dama agurin Anty chiden take da hope 'din samun ingantaccen wurin da tasan za'a share mata hawaye domin itace tasan gurare da dama acikin garin na lagos, amma kuma shara'din Anty Chidehn tazo mata dashi sai ya girmi tunanin ta, sam bazata iya aikata abinda 'kawartan ta ke son ta aikata ba, how on earth ace tayi irin wannan abin.... Koda ta koma gida (Lagos) ma cigaba tayi da neman mafita amma tarasa ta ina zata fara, kullum hankalinta atashe yake, gaba 'dayan su agidan ma sai suka rasa gane kanta, Abbah kuwa ko kallo ma bata ishe shi ba, kamar yadda itanma bai isheta kallo ba , zaman gidan tamkar wasu abokan gaba aka tara aciki haka suke yinta kowa harkar dake gabansa kawai yakeyi, Anty ta 'debi abin ne da zafi 'karfi dayaji take so taga ta hana abinda Allah bai haramta ba, duk kuwa abinda take yi shiga da fitan ta da wasu abubuwan Abbah kallon ta kawai yakeyi yana mamakin taurin kanta, zai yanzu yake 'kara jaddada wa kansa rashin sa'ar mata yayi, ha'ki'ka shi kan baiyi sa'a ta wannan 6angaren ba, bayaga haka kan be sa me zai ce ba, Alhaji Muhammad mutumin kirki ne dashi kanshi zai iya bada shaida akan haka, sannan yana da tabbacin Alhaji yaja wa Maryam (Anty) kunne akan haka harma ya ha'da da tabbatar mata cewa matu'kar bata kar6i wannan auren ba toh babu ita babu shi, lokacin da Alhaji Muhammad yayi wannan maganar shikanshi Abbah bai ji da'di domin bazai so ace iyalinsa ta samu matsala da mahaifinta ta dalilinsa ba, yaso yayi magana tun awancan lokacin amma sai yayi tunanin wai ko zata yiwa kanta fa'da da wannan kalmar ta saduda ta barwa Allah ikonsa amma sam sa6anin haka yagani wanda be sani bama sai yace acan ta 'karo taurin kan da taje, ha'kika duk wanda yayi nisa da wuya yake jin 'kira koda me 'kiran ya hau kan babban tsauni ne,sai dai kawai Allah ya shiryamu gaba 'daya.(yasa mu gane gaskiya gaskiyace kuma yabamu ikon yin aikin da ita). Shima Abbah babu abinda yasa agaba ayanzu illah yaga anyi auren nan angama shi lafiya ko hankalin kowa zai kwanta. Abbah da kanshi yasa Mahmud agaba suka je gurin wata matar abokinsa suka yi maganar kayan lefe afa'darsa tunda mata suka suka san kayan mata 'yan uwansu, transfern ku'di kawai yayi mata masu yawan gaske yace ta ha'da masa lefe nagani afa'da yace baya san algus ko ka'dan aciki saboda yarinyar ma 'yarsa ce ahaka kawai ma zai iya yi mata ballan tana kuma ace aure ne sanadi kuma auren 'dan cikinsa zata yi. Dariya sukayi masa sannan matar ta bashi tabbacin bashi da matsala da wannan ya kwantar da hankalinsa komai zai yi kamar yanda yake bu'kata, dayake daman tana sarin kaya tace wannan satin zata yi ordern su sauran kuma dole sai anan Nigeria za'a siya. Godiya yayi mata sosai ,sai abokin nasa yace " ban ta6a jin inda mahaifin ango yayi kane-kane akan kayan lefe ba............... "Akaina zaka fara gani Alhaji" Abbah ya karasa maganar yana dariya. "Asalin tuwona mai na 'din kenan Alai yusuf lallai zaka kafa tarihi a 'kasar nan". "Kwarai ma kuwa ". Abbah ya sake bashi amsa still suna dariya. Mahmud kam tunda suka zo daga gaisuwa be sakeyin wata magana ba sai kawai ya ciro wayarsa yana danne-danne dayaga sun gama maganar sun koma hira suna dariya sai kawai yatashi ya basu wuri, binsa sukayi da kallo har ya 'karasa barin 'dakin. Alhajin ne ya tambayi Abbah abinda ke damunsa shikuwa Abbah be '6oye masa ba yabashi labarin yanda batun auren ya kansance ya 'karasa da fa'din fushin Mahmud 'din na rashin son yin aure yanzu ne wai shi ba yanzu zai yi aure ba sai nan gaba , laifina anan shine nace yanzu zaiyi aure shikuma ba haka ya tsara wa rayuwarsa ba shine fushin." "Allah sarki yaro kenan, inbanda abinsa ai aure bashi da lokaci" Inji Alhajin. " rabu dashi bazai gane hakan ba ai, amma nasan wataran dakansa zai gode min idan yafahimci banyi hakan dan na ba'kanta masa face gata da nake 'ko'karin yi masa". Inji matar Alhajin "Hakane kam". Ajiyar zuciya Abbah yayi sannan yace " Allah shi kyauta" Tare da mi'kewa tsaye, Alhajin ma sai ya mike yamasa rakiya har inda sukayi parking motar su . Mahmud na hango su ya tada motar kmar daman jira yake yaga fitowarsun. Ahanya ne Mahmud yake tambayar Abbah wai kayan miye zaa siyo? Abbah ce mishi yayi "kayan auren kane!" "Toh ni Abbah ya baka siya min ba sai ita ka'dai" "Abu mai sau'ki ne ai wannan babana idan kanaso zan siya maka kwantar da hankalinka." Shiru Mahmud yayi yaci gaba da tu'kinsa har suka isa gida bai sake magana ba. Mahmud yanzu bashi da abokin hira sai 'dakinsa da kuma wayar sa, hatta Fatima (wife to be 'din nasa ma daina kulata yayi tunda akayi maganar auren su sau 'daya suka yi waya dashi daga nan be sake 'kiranta ba, haka ita ma bata 'ta6a 'daga wayarta ta 'kira sa ba, ko a chat ma babu me kula 'dan uwan sa yanzu ko wa harkan gabansa yake yi duk wannan sha'kuwan sun manta da ita. Wayewar wa ta safiyah ne wanda idan aka lissafa 13days yarage wa bikin Mahmud, sai Abbah ya'kira shi yake sanar dashi cewa ya kamata ya ziyarci Fatima ko da sau 'daya ne kafin lokaci ya iso, duk dama already sun san junansu kuma akwai fahimta atsakaninsu amma sanayyar dake tsakaninsu ada da na yanzu is totally different, yakamata su'kara fahimtar juna, bai musa wa Abbahn ba take ya amince akan zashi sai Abbahn yace toh yaje duk lokacin da ya shirya tafiya sai yayi masa magana yace ya bashi nan da 3days. " toh Abbah" yacewa Abbahn nasa kawai sannan yatashi yatafi. Bai sake bi takan maganar Abbahn ba kawai ya share yayi zamansa har akayi kwana hu'du babu wani alamar yana da niyyan tafiyar da zaiyi, rana na biyar ne da Abbah yaga shiru sai ya sake yi masa tuni akan maganar tafiyan wanda lokacin yayi dai dai da kwana tara cif yarage wa lokacin da aka saka na 'daurin aure. Mahmud 'kasa yayi da kai tare da shafa gashin kanshi sai yace da Abbahn" ai shi yamanta ma kwata kwata , amma insha Allahu kwanan nan zai shirya yaje shi", " yah kamata kam ". inji Abbahn ya fa'da lokacin yana 'ko'karin 'daukan jaridar dake gabansa yaci gaba da dubawa. Lokaci nata 'karatowa yayin da shirye shiryen biki ya kankama aduka 6angarorin guda biyu, koda yake a6angaren Mahmud Abbah ka'dai ne ke ta faman shirin sa, yayinda Anty kam ko oho bata damu ba kallonsu kawai takeyi. Mummy kuwa busy take ako da yaushe bata samun lokacin kanta 'ko'karinta taga komai yatafi yanda yakamata, duk wani abu datasan hakkin ta ne aiwatar dashi toh bata natsuwa sai taga ta sau'ke shi, sai dai har yau takasa yiwa Teemahn koda abu 'daya ne daya danganci gyara da ake yiwa amare rasa ta ina ma zata fara tayi ,daga 'karshe sai ta yanke shawaran barinta ayadda take kawai ta cire wannan a lissafinta, ta daiyi 'ko'karin tanadar mata duk wasu abu na gyaran fata da gyaran jiki kuma ta tsaya tsayin daka dan ganin komai na tafiya dai dai. Ummah (mahaifiyar Abbas) ce ma tayi mata maganan wai ko ta ha'dawa Teemahn kayan mata dan taga wasun sukan yi wa 'ya'yansu idan lokacin auren su yazo, sai mummy tace "ahh'ahh ita kam bata ba ta komai ba tsoro takeji,abinda kullum yake damunta azuci ma kenan amma dai daga bay ta yanke shawarar gara ta barta hakan kawai. Sai kuma Umman ma tace "yauwa hakan yafi ai gara abarta a yanda take saboda yiwa yara abubuwan da suka shafi wannan 6angaren kafin susan kansu yana da illoli da dama amma tunda ma ba'a matan ba shikenan ,tace dama ta so ma tun wuri suyi maganan amma sai ta sha'afa gaba 'daya abubuwa sun sha kanta itama". ***** 7days to ranar 'daurin auren Ummahn Abbas ta iso ita da Hannah suka zo dan Hanna damunta tarin'ka yi wai tafiso suje dawuri ayi komai da ita ,bata son komai yawuche ta shiyasa dolen Ummahn ta shirya suka taho, dama nufin ta sai nan da kwana biyu zasu taho, Daddyn Abuja ma yabiye wa Hannah yace ai gara su je tun yanzu duk 'daya da jibin da Ummahn tafa'di tunda bawani abu suke jira anan 'din ba ai gara sutafi ayi hidima dasu gaba 'daya, yace shi sai ranar Friday zasu ganshi ( dayake bikin ranar Saturday ne). Teemah bata ta6a ha'duwa da Hannah ba amma zuwan Hannah ya yi mata da'di sosai, saboda tasamu abokiyar hira, sosai Hannah ke 'debe mata kewa surutunta tamkar uwarsu 'daya da Mahmud itama badama gata da saurin sabo bata da ba'kunta. Washegari cikin sa'a sai ga wasu daga cikin 'kawayen Teemah na makaranta kusan su hu'du suka zo, Teemah wani ihu da ta saka ta rungumesu har ma bazaka ce tana da damuwa ba, Hannah ce tace "mata kiyi dai ahankali dan kin kusa ki zama matar gida". Bata kula da maganar Hannah ba tajasu gaba 'daya suka nufi 'dakinta kowa tasamawa kanta matsuguni, wanda kusan dukkansu akan makeken gadon Teemahn suka zuzzube Hannah ce ka'dai ta 'dan 'dosana 'duwawunta saboda sauran duk kwanciya sukayi so ba space sosai, sai kuma Teemah dake zaune akan side drawer tana facing 'dinsu, musamman ta janyo shi zuwa gaban nasu dan taringa kallon su da kyau gaba 'daya. ***** Aranar da su Ummah suka bar Abuja aranar shikuma Abbas yaje shi, dan ma irin zuwan nan na shi da ba da'dewa yakeyi 'din nan bane 'kar'karinta a yayi 'ko'kari shine yakwana 'daya shikenan zai ce zai tafi, shi akoda yaushe yafi son yaganshi a wurin aikinsa baya so yaga yayi nisa da su he so much care about his career. _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh* 😍 [10/2, 6:01 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Don’t confuse your path with your destination. Just because it’s stormy now doesn’t mean that you are not headed for sunshine. 🅿 *45* Daddyn Abuja ne ya sanar da Abbas 'din cewa da safiyar yau suma suka wuche Jihar Yobe, sosai Abbas yaji haushin rashin samun sun da be yi ba, har ma yace wa Daddyn nasa " me yasa toh suka tafitun yau"? Cikin jin haushi yayi maganar. " haba Abbas ka manta bikin waye za'ayi ne"? daddyn ya tambayeshi da mamaki. Kauda kansa yayi gefe sannan yace " ban manta ba Daddy kawai naga sunyi saurin zuwa ne ai dasun bari ranar Wednesday ko Thursday sai su tafi". "Yanzu kam ai shikenan tunda sun tafi komai ya wuce, in ganin su kake son yi ka bi su can 'din." Shiru yayiwa daddyn nasa bai tanka ba,kawai ya tashi ya nufi 6angarensa domin watsawa jikinsa ruwa. Daga lokacin da ya iso zuwa daren ranar tsakin da yayi yafi sau a'kirga, abubuwane suka taru suka mar yawa acunkushe ya ringa jin zuciyarsa , koda yaji yunwa ta dameshi sai ya nemi abinci anan ma Daddyn Abuja yace yajira akawo abincin ya aika asiyo. Ka'dan yarage tsakin da yayi azuciyarsa tafito fili Allah ya taimakeshi azuci yayi ta shiyasa Daddyn nasa be ji ba. Sai kawai ya tashi ya nufi harabar gida amma sam yarasa inda zai samu nutsuwa, tunani yayi ko de ya shiga cikin gari yawone?, Toh inka fitan ma ina zaka nufa? Wani 6angare daga zuciyarsa ta tambayeshi. Safa da marwa ya fara yi agurin yana tunani " wai dagaske ne za'ayi auren kenan?, Dagaske Mahmud ne zai auri Fatima bani ba". " ehh dagaske ne mana tunda gashi su Ummah ma sun tafi domin halartar 'daurin auren". Wani 6arin zuciyarsa ne ya sake bashi amsa. Tambayar kansa da kansa yayi wai " me yasa duk wani abu daya shafi 6angaren Fatima ni nake cutuwa aciki meyasa haka ?,is it because dan ba zan sameta bane ko me,? _First_ ha'duwarsu da Mahmud, lokacin ba 'karamib takaici yajiba na yanda yarinyar nan ta nuna tafison kasancewa da Mahmud fiye dashi da 'kyar ya samu ya lallashi zuciyarsa akan hakan. Then _secondly_ batun aurensu, wannan kam shiyafi komai 'kona masa zuciya saboda yanajin kamar bawai ha'din iyaye bane kamar yanda Mahmud yayi masa bayani gani yake tamkar Fatiman nason auren duk da yasan shi Mahmud 'din baso yake ba amma zuciyarsa takasa amince masa da cewa Auren na ha'di ne kamar yanda zuciyarsan akullun take bashi tabbacin cewa babu wanda zai auri Fatima akaf duniyan nan sai shi, Fateema Zahra ta Abbas ce shi ka'dai. And _now_ yayi missing kirkin Ummahn sa duk adalilin wannan banzan auren. Haushi sosai hakan yasaka shi, yace yanzu da Ummah na nan ai da ba ruwansa da neman abinci, dan ita akoda yaushe idan ka nema toh zaka samu, ya tsani cin abincin hotel shi, yafi son cin abinci agida, shiyasa akoda yaushe yake kan hanyan zuwa gida duk da nisan da gurin ke dashi hakan besa yayi ganda zuwa aduk lokacin dayaso, abu ka'dan ke sa ya kamo hanyar gida baya yin cikakken 2 weeks mai kyau batare da ya le'ko Abuja ba, koda ba zai kwana ba ma amma in ya so sai yazo, wani lokaci dan kawai yaci abincin Ummansa ma yakoma saboda na wajen da wuri suke fita akansa bakamar na mahaifiyarsa ba. Ko yanzun ma da aka kawo abincin da 'kyar yasamu ya'dan tatta6a ka'dan yabari, ba danma yanajin yunwa ba da bazai ko bu'de ba. Washe gari ma Daddynsa ne ya sake aikawa aka kawo musu breakfast, shikan 'kin ci yayi yacewa daddyn nasa shi lipton kawai zaisha, daddy ne kawai yaci abincinsa, Abbas dakansa yaje kitchen ya tafasa ruwan lipton 'din yakawo musu da daddyn dan yasan shima Daddyn gwanin shan ruwan lipton ne. Yana gamawa kuwa yayi wanka ya shirya sai yayi sallama da Daddyn ya kama hanya. Teeemah na cikin 'kawayenta suna ta zuba surutu abinku da student in an ha'du ba dama sai an yada hali, musamman na yanzu da ya kasance 'dayarsu zatayi aure dayake kusan itace ta farko ma bayan gama makarantar tasu kuma classmates 'dinta yanzune suke SS3 basu gama ba so sai suke ta marmarin ganin lokacin bikin ya iso, itace aka fara saka ranar bikinta shi yasa suke ganin kamar wani abu ne na daban, hira suke tayi abinsu, na dariyane, takaici ne, abin tausayi ne duk suna ta tunowa da school life 'dinsu lokacin suna tare da ita, ita kanta Teemah ma warewa tayi suna ta shan hirar su, ga Hannah ma acikin su kamar da ma already sun san juna. Garin yin dariya ne wata acikinsu me suna Naanah ta danne 'kafafun Teemah dayake ta mi'ke 'kafafun nata ne a abakin gadon saboda gajiya datayi da yanda ta tankwasu tun farkon zamanta agun " waashh....... Naanah kin karyan 'kafata". Ta yi maganar tana wani kwa6e fuska tare da janyo 'kafarta ta zuwa gabanta. Duk kan su sai hankalinsu ya dawo kan Teemahn suka zuba mata idanu kowa na mata sannu, sorry, da sauransu. Fauziyya (Fauzee) ce tace " ke Naanah ki riinga kulawa kar kisa ahana mu fita daga gidannan bari kiji "! Sai Hannah ta kar6e da fa'din " gaskiya kam, in ba haka ba ina ke ina jiwa amarya ciwo" "Ai kuwa de " inji Hauwa da ke 'ko'karin ja wa Teemah 'kafar tata". "Kuma dai wallahi, ku kyaleta dallah inta karye banda murakata da sabon wheel chair 'dinta agefenta, kunga ta kafa tarihi a auranta". Dariya dukkansu suka sanya har Teeman, tana cikin dariyar tace " wallahi kin iya wula'kanci yarinyar nan. " ai gaskiya ne, kya tsaya kina wani yi mana raki anan bayan ciwon bawani na kirki bane.......! Fauzee ce ta amshe maganar da fa'din " ke bata son jikin ta ya samu matsala ne ke baki ga yanda ta koma bane ta wani yi fresh da ita". " 'kwafa Teeman tayi kana tace " har ina wani abin fresh 'din anan dan Allah, ahakan ne zaki ce na wani yi fresh dani?, haba Fauzee..... dubeni fa ke baki ganin irin ramar dana yi ne,?Allah mummy da kanta ma cewa take yi wai na rame dayawa sai ta ta sani cin abinci kullum wai ko zan 'dan murmure". "Duk da haka de ke kam ki yadda kin canja, ai rama daban canjawan skin ma daban" Cewar Naanah. Fauzee kuwa tace " muma dai ya kamata mu fara haramar yin auren nan ko ya kuka gani"?Ta 'karasa maganar tana rarraba wa sauran idanu. " toh zakwa'di ai de kya bari ki 'kare secondaryn tukunna ko?" Inji Teemah Baki Fauzee ta rufe "au ashe fah da sauran mu mu 'din bamu gama ba". Dariya suka kwashe mata dashi dukkansu sai Jiddah tace " 'yar rainin sense....da 'din mantawa kika yi kenan." " Tamanta cewa ni ka'daice na girma acikinku" Teemah ce tayi maganan tana musu dariya. " ai ki bari wallahi nima da nasani da nace wa Babana zan rubuta waec alokacin nasan da bazai hana ni zai barni, kunga da ina yin candy nima sai asha biki na irin na Fatima Kb". sai Teemah tace " ke kika sani, yanzu kam ai ya wucheki sai ayi ha'kuri ajira next year " Haka suka ci gaba da hira atsakaninsu, gwanin birgewa Teemah kwata-kwata mantawa tayi ma wani batun aure, ji take kamar suyi ta zama ahaka kar su tafi. Acikin hirar ne Naanah tace da Fatima itafa gaskiya bata san waye angon ba anuna mata shi ko a pix ne, saboda taji ance wai yayanta ne 'dan gidansu, kuma yayun nata kusan mutun biyu tasani bata san kuma wanene shi daga cikin su ba so tana so taganshi. Sai duka sauran ma suka goyi bayanta dan hatta Hannah ba ta gane shi ba, ko lokacin dayaje gidansu ma basu ha'du dashi ba har yatafi shiyasa bata sanshi ba. Teemah wayarta ta tashi ta 'dauko ta nemo photon shi 'daya daga cikin wanda yake tura mata tun lokacin suna chat sosai dashi ta nuna musu kar6ar wayar sukayi suka ringa zuzuta kyanshi dan ba 'karya Mahmud ba baya bane wajen kyau da cikar kamala. Koda wayar tashiga hannun Hannah ma " wow " tafara fa'di tace gaskiya ya ha'du, ni sai na gama kamar kuna 'dan kama ka'dan dashi"? " badole ba ke kuwa abinki da jini 'daya" Cewar 'daya daga cikin su. Mahmud kyakykyawa ne shi, yana da tsayinsa daidai gwargwado, shi ba fari tas bane kuma ba ba'ki ba skin colour 'dinshi me kyau ne kuma ya kar6i yanayi da tsarin sa, gashin kansa irin na asalin fulani ne ananna'de yake kuma akwance luf luf dam ma shi yana yawan aske wa be fiya son tara gashin ba sai dai yabar 'dan daidai, kammanin sa na fulani sak yayi wata 'kila yabi jinin kakarsa ne mahaifiyar Babansa ( Innah Hansatu) sai de shi yana da 'dan kauri ka'dan kamar Antyn sa (mahaifiyarsa ) bashi da sirinta ko ka'dan, abinda kenan ya 'dauko daga wurin mahaifiyarsa." " danma baki ga 'daya yayan nata ba, shi sun ma fi kama da Kb sosai, inji Fauzee tafa'da tana me kallon Hannah Azaton su ita 'dinma wata 'kawar Fatiman ce daga wani 6angare daban duk da akwai 'dan kama na jini tsakaninsu, saboda duk wanda yaga Teemah yakuma ganin Hannah sai yaga wannan kamar da suke dashi, amma su basu ma lura da hakan ba, shirman su kawai suka sa agaba. Daga nan suka cigaba da zuzuta kyawu da tsaruwar yayun Teeman dayake sun sansu gaba 'daya ada lokacin tana zuwa school duk cikin su babu wanda be yi mata rakiyar zuwa makaranta ba daga Mahmud 'din har Abbas. Fitsari ne yadami Hannah sai ta tashi ta shiga bayi to ease her self, ko da tayi fitsarin tagama sai kuma tayanke shawarar yin wanka saboda lokacin da Teemah tayi wanka 'dazu ita daman batayi ba tana kwance tana ta chat abinta har 'kawayen Teeman suka zo. Shi yasa data shiga batin sai tace kawai bari taha'da da wanka gaba 'daya. Shiganta ke da wuya kuwa sai akazo akayi kiran Teemah wai suzo inji Ummah ita da Hannah. Tashi Teemah tayi tace wa 'kawayen nata "bari inje ina zuwa yanzu, idan Hannah tafito ku sanar da ita Ummah tana nemanta dan Allah". "Toh" sukace mata daga nan tayi waje. Koda taje d'in sai Ummah ta tambayeta ina Hannahn kuma bayan nace kuzo tare, yayanku ne yazo kuma zai wuche yanzu shine nache ya tsaya ku gaisa inajin yana 'dakinsa, kinsan shi da gaggawa wai yana da abunyi agabansa". " Ummah bayi Hannahn tashiga bari in dubota toh sai muje tare".Teemah tayi maganar tana 'ko'karin juyawa har muryarta na rawa. " ah ah kyaleta kar a6ata masa lokaci ke kije ku gaisa kawai in tafito dawuri sai ta samoki". Ummah ne tafa'di haka dai dai shigowar Mummy da try ahannunta an shishshirya abinci akai "ingo tafi masa da wannan"inji mummyn tayi maganar tana mi'kawa Teemahn try 'din dake hannunta. Kar6a Teemah tayi tafara tafiya ahankali, tunda Ummah tace _yayanku ne yazo_ take jin zuciyarta na harbawa da 'karfi, bata bu'katar wani dogon 'karin bayani domin tasan Yah Mahmud ne yazo shi tun da tasan shine future husband 'dinta dole shine yazo, dan shi ka'dai ne zai bu'kaci ganinta awannan lokacin dole tasan sai hakan yafaru. Ita duk atunaninta Mahmud ne yazo ,kuma bata san me yasa taji tsoro yashige ta ba, duk da wani tsoron Yah Mahmud 'din take ba amma sai takejin wani iri tamkar karta taje gurin shin haka taji, wai yau zata ga Yah Mahmud 'dinta, her beloved brother, amma ba'a wannan matsayin da ta sanshi akai ba, yau Yah Mahmud amatsayin wanda zai kasance miji ne agareta zata gani. Bata so tasake ganin Yah Mahmud ba, inda son ranta ne har se bayan anyi auren wata 'kila alokacin zataji son ganin shi amma yanzu kam da za'a tambayi ra'ayin ta kafin yazo da ta ce yayi zamansa basai yazo ba, bata san me zata ce da shi ba ko da ta ganshin ma yanzu. Tafiya takeyi ahankali tana tunani har ta isa 'kofar 'dakin da tasan na Mahmud 'dinne wanda iya zaman sa agidan anan yayi rayuwa, hannun ta da abu so babu daman ta tsaya yin nocking a'kofar, thank God ma 'kofar ba'a rufe gam take ba sai kawai tasa 'kafa ta tura sai 'kofar ta bu'du, ciki ciki tayi sallama bata wani jira jin amsa ba ta tura kanta ta shiga ciki. Bugun da zuciyar ta keyi ne ya 'karu fiye da na baya, sai ta kasa 'daga kanta ta kalleshi har taje ta ajiye tire 'din a kan centre table 'din dake cikin 'dakin sannan ta 'dago ta kallo bayan wanda ke tsaye agurin window tamkar andasa shi. Maganar mummy ta tuno da kusan kullum sai ta mata tuni akai inda take cewa " ayanzu baki _da wani makami Fatima face addu'arki da kuma ha'kuri, dan nasan su ka'dai ne zasu jagorance ki ga dukkan al'amuranki, dole ne kiyi ha'kuri da duk wani abu da zai faru ko zaki gani, kawai kisawa ranki daga Allah yake kuma 'kaddararki kenan, kuma shi yaso ganinki awannan matsayin, domin yawan nuna damuwa akan abu bashine zai kawo miki sau'ki ga al'amarin ba face addu'ar ki, damuwar taki bata da amfani koka'dan sai ma yasake 'daga miki hankali, tunda ke kanki kinga alamun Daddyn ki ba barin zancen auren nan zaiyi ba inajin mutuwa ce ka'dai zata sa yafasa 'daura auren nan ayana yin da naga yake ciki, ki daure ki ya'ki zuciyarki kisawa ranki san auren tun yanzu, idan ma kina jin rashin son Mahmud 'din ne to ki dole ne ki daure ki kauda wannan tunani tun yanzu, Mahmud 'din nan dai da kika sani shine zaki aura ki kuma zauna dashi, dan haka kiyi ha'kuri na tabbata Allah yana tare da dukkan bawansa me dogaro dashi, Fatima ni mahaifiyarki ce kuma mai tsananin sonki fiye da zaton ki, wallahi da'ace inada wata dama ko hanyar da zan iya hana faruwar wannan auren da zan hanashi ko dan ganin farin cikinki ka'dai ma, amma na tabbata dai dai da 'kwayar zarra ban kai ubangiji mahalicci sonki ba kuma shine yaga dama ya za6a miki shi Mahmud 'din dan haka kinga mu bamu isa mu ja da lamarin ubangiji ba, sannan mahaifinki ma basai na sanar dake son da yake miki ba Fatima ke kanki kinsani, kuma shi kanshi bazai ta6a yi miki abinda yasan cutarwa ne agareki ba har abada nasan kinsan wannan, ki daure kiyi masa biyayya kinji.... ina da ya'kinin duk daran da'dewa watarana zaki ga haske arayuwarki insha Allahu_ " Hawayen daya zubo mata tasa hannu ta goge shi tas tana yi tana sake bawa kanta 'karfin gwiwa "Mummy bazan yi kuka ba, bazan sake yin kuka dan zan auri yah Mahmud ba, na miki al'kawari insha Allahu mummy" Tana goge hawayen fuskar tata take wannan maganar. Mummy tana nufin insoka ya Mahmud in 'kaunace ka badan komai ba sai dan saboda Allah mahalicci, dama ni ban ta6a jin bana sonka ba Yah Mahmud amma wani lokaci sai inji dama ba kai Daddy ya za6a min ba sai inji dama ya barmu a yanda muke tun farko kaci gaba da zama amatsayinka na yayana nafi feeling compotable akan haka, ban San me yasa ba amma sau da dama sai inji dama Yah Abbas Daddy yace zai aura min ba kai ba". 'Daga kai tasake yi ta dube shi, tun 'dazu data shigo ahakan yake be canja tsayuwarsa ba tsaye yake hannunsa 'daya acikin aljihu ga dukkan alamu tunani yake yi wata'kila shi yasa bata samu amsar sallamar ta data masa lokacin data shigo, Yah Mahmud bai fiya yin hakan ba yakan amsa sallama koda baya cikin yanayi na walwala sannan baya ta6a kyaleta matu'kar ta kusanci inda yake koda kuwa tayi masa abin 6acin rai baya ta6a yin fushi da ita amma ji yanzu yanda ya shareta tamkar ma besan tashigo bayan tana da tabbacin yaji shigowarta tunda da sallama tashigo, gashi ma sai taga ya 'dan rame mata 'ka'dan bakamar yanda yake ada ba, kar dai shima baya son auren ne kamar ni,? kardai maganan auren ne yasaka cikin damuwa ? Ahankali ta 'dago 'kafafunta ta har sai da ta iso kusa dashi kafin ta tsaya daga bayansa " _Yah Mahmud_ "! Ta 'kira sunan shi ahankali kamar bata son yin maganan. Be amsa ba kamar yadda be juyo ya kalleta ba haka kuma babu abinda yacanja daga yanayin tsayuwarshi. Sai ta yi tunanin ko beji ta bane sake bu'de bakinta tayi da niyyar sake 'kiran sunan nashi _" Yah Mahm............_ Da wannan lion voice 'din nasa ya daka mata tsawa _"Shut up da Allah"!_ Ya fa'di maganar tare da juyowa. *Hi every one!* 🙋‍♀ _Naga sakonninku readers da dama wasu a groups nagani yayin da wasu suka yiyyi min magana ta private, duk kanku nagani kuma na yaba da 'ko'karinku kuma ina godiya da dukkan addu'o'in da kuke bina dashi, nima ina muku fatan alkhairi.Ha'ki'ka me son ka shike iya bu'dan bakinsa ya zanzaro_ ma _addu'o'i nagartattu batare da haufi ba, duk da yasan Allah na iya amsawa ako wani lokaci, gaskiya godiya nake 'yan_ _uwana_ . *(ALLAH YA* *BAR 'KAUNA).* *FEELING* *THANKFUL* 👏🏻 _Gareku commenters kuma inajin da'di sosai da yadda kuke bawa littafin nan kulawa harma idan kunga shiru ku tambaya ko lfy, agaskiya hakan ba 'karamin sani farin ciki yake ba, harma yake kuma 'kara min 'karfin gwiwa, as u can see last week akwai ranar da nayi posting 2pages saboda jin_ _da'din_ _ku kawai masoya na._ *( NIMA INA SONKU ADUK INDA* *KUKE).* _Nagaji ne amma badan haka ba da na lissafo suna yenku koda ka'dan ne, sai dai duk da haka bazan manta daku ba insha Allahu nayi al'kawarin jero_ _sunayanku koda ba dukkan ku ba aduk lokacin dana samu_ _chance_ _insha Allahu._ *'KORAFI* 👎🏻 _Sai dai kuma naji wasu daga cikin ku suna ganin kamar wai ni ina team 'din_ _Mahmud_ _ne_ 🤔. *SUGGESTION* !👌🏻 _Azahiri bahaka ba ne kar ku manta fa ni na kowa ne dukkan su ina son su babu wanda bana so aciki, kuma ai ba lallai bane arayuwa ace wanda kafi so kuma shi yafi tara dukkan abubuwa in dai hakane ashe za'a iya cewa 'dan Adam_ _batara yake ba yacika goma cif-cif, ba dole bane ace Star 'din littafi shi yafi iya komai acikin littafin tunda kowa ma mutun ne, kuma kowa nada tashi irin baiwar Allah yayi masa kunga dole sai ansamu similarities da difference sannan asamu best_ *.(hakane)* ❓ _Dan haka karku manta wannan littafin sunan shi_ *CAPTAIN* *ABBAS* _kuma star_ ' _dinku a_ _littafin sunanshi_ *oga* *ABBAS*👈🏻😃 _dan haka_ 👇🏼 🤞🏻 *ACIGABA DA*. *GASHI KAWAI* ................... ❓ _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh* 😍 [10/2, 6:01 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _If you don’t care about what people think about u, you already passed the first step of success._ 🅿 *46* Cikin firgita Teemah ta matsa baya ka'dan tare da furta _" Yah Abbas "_ asaman la66an ta. Ganin yanda idanuwan sa suka koma tare da irin kallon da yake mata ma ka'dai abin tsoro ne ballantana kuma irin ihun da ya daka mata aka. 'Kasa tayi da idanuwanta da har sun fara 'ko'karin tara ruwa shikuwa sai ya tako ahankali zuwa gabanta tamkar wani abin arziki zai mata sai kuma yasa hannu ya 'dago habarta zuwa sama dolenta ta 'dago kannata batare da taso ba dan ita yanzu tsoro ya Abbas yake bata sak ya juya mata wani irin halitta daban mai abin tsoro. Rintse idanuwan nata tayi da 'karfi jikin na rawa saboda lokacin da ya 'dago kannata tayi zaton sau'kar mari zataji amma kuma sai taji shiru. Shikuwa Abbas kallon fuskar tata ya tsaya yi, sosai yaga yarinyar ta rame masa amma be tsaya yabi takan ramar tata ba sai hankalin sa ya tafi ga rintse idanuwan da tayin, haushin hakan yaji, shi tunaninshi tayi hakan ne dan bata so taga ko da fuskar ne while bahaka bane ita ta rufe idanun ne saboda tsoronsa, tsoron ha'da idao takeyi dashi. Sake mata fuskartata yayi sai yacigaba da 'kare mata kallo, be kawar da idanun sa daga kannata ba yace _" lover girl !_, _" kin zaci saurayin ki ne yazo ko"?_ Be jira jin amsarta ba yajuya mata baya ya fara taku ahankali hannunsa 'daya har yanzu na acikin aljihunsa kamar an ce kuma yajuyo, sai ya dawo inda take tsayen ya cira hannunsa yaja hannunta da 'karfi. Be zame ko'ina da ita ba sai a wajen kujera ya wani jefata da 'karfi ya tsaya akanta yana huci, ita kuwa sai ta kudun dune jikinta wuri 'daya yayin da hawayen da ya taru acikin idanunta 'dazun yasamu damar gangarowa abinsa, ci gaba tayi da zubda hawayen helplessly kanta acikin tafin hannunta. Sau'kan duka kawai take jira awurin yah Abbas 'din dan zuwa yanzun gaba 'daya ta saduda da wannan alamarin, bata san laifin data yi masa ba, dan ita bata masa laifin komai ba a iya saninta amma ga dukkan alamu ranshi a6ace yake da ita. Ko kuma cewa da taji akeyi anawa sojoji allura wata'kila gaskiya ne, gashi yau tashiga hannunsa Allah ne ka'dai zai 'kwace ta yau ahannunsa, ahankali cikin kukan ta fara fa'din _" Yah Abbas... dan Allah.....dan Allah kayi ha'kuri, wallahi bazan sake ba, dan Allah karka dake ni, in ka dake ni_ _mutuwa zanyi Yah_ _Abbas........"_ Ahankali take maganar dan in ba akusa da ita kake bama bazaka ta6a fahimtar me take fa'di ba saboda cikin shashsheka tayi maganar. Shi kanshi Abbas yanda tayi sai da ta bashi tausayi amma sam yakasa jin nutsuwa acikin azuciyarsa, yakasa bawa kansa ha'kuri akan abinda yakeji, aganinsa ai shi rani masa hanakali kawai take shirin yi kamar yanda tasaba abaya, azahiri shikanshi be san laifin data yi masa ba she looks innocent, amma shi aransa ji yake tamkar wani babban laifi tayi masa da babu wanda yata6a aikata masa irin laifin akaf fa'din duniya. Da 'kyar yasamu ya 'dan sassauto ya 'daidaita nutsuwar shi, sai ya yun'kura da niyyan zama agefenta akan kujeran daya jefa tan. Teemah kuwa na ganin haka ta zamo da sauri ta dawo 'kasa akan carpet kusa da kujerar taci gaba da rera kukanta. Gira 'daya Abbas ya 'dage da mamakin abin da tayin yana kallonta. _"meke nan wai "?_ Ya tambayi kansa azuciyarsa. Teemah kuwa tana sau'ko wa taci gaba da bashi hak'uri " _Nifa banyi laifin komai ba Yayah dan Allah kabarni na tafi, inbaka yadda ba ka tambayi mummy kaji Allah banyi mata laifi ba "_ Rashin sanin amsar da zai bawa tambayar tasa yasa ya watsar da tambayar kawai ya dawo da dukkan hankalinsa gareta yaci gaba da sauraransa ha'kurin nata tana dasa aya yayi murmushin takaici tare da 'dan rankwafo da kansa daf da ita " _Fatima_ " ya 'kira sunan ta cikin natsuwa. Shiru tayi bata amsa ba duk da tayi mamakin hakan domin ayanda taganshi 'dazun batayi zaton zai sau'ko so soon haka ba, yau de _" Allah kai ka'dai zaka fitar dani_" ta fa'di aranta sai ta 'dan 'dago kanta ka'dan amma bata kaiga duban fuskarsaba. Shima be takurata ba wannan karan dan zuwa yanzun ko ba'a fa'da ba dakansa yafara fahimtar irin tsoratan da tayi dashi, ya gane cewa duk abinda takeyi atsorace take yinsa. _" Waye yace miki bakiyi laifi ba"?_ Shiru tayi masa wannan karan ma dayaga bazata yi magana ba sai yaci gaba da tashi maganar _" anyway,_ _ki bani_ _labari"_. Yayi maganar yana duba agogon dake 'daure da tsintsiyar hannunsa sai kawai ya 'kara da fa'din _" ki ban labarin yanda kike so auren ki yakasance"!._ Ko yanzun ma shiru tayi batayi masa magana ba, kawai sai ta 'kara maida kanta 'kasa kamar yanda yake da farko ko ka'dan bata yi alamar zata bashi amsa ba _" toh_ _me yake so_ _ince masa, har akwai wani yanda nakeso aure na ya kasance ne?. Muryarsa tajiyo yana fa'din _" idan nayi magana banason ashare ni Fatima wata'kila kin manta da wannan ko?"_ Yayi maganar tare da komawa baya ya jinginu da jikin kujerar tamkar wani basarake. Kai tayi niyyan jijjiga masa amma da tuno da warning 'dinsa daya ta6a mata abaya akan hakan shiyasa sai ta bu'di bakinta da 'kyar kamar ma bazata yi maganar ba tace " ban manta ba". Shirun shima yayi idanuwansa nakan la66anta datayi maganar, kukan da tayi gaba 'daya sai yasa suka zama jajir, zuba mata idanu yayi shi ka'dai yasan me yake sa'kawa aranshi. Tsawon mintina biyu suna ahakan, motsi Teemah tafara sanadiyyan gajiya da 'kafafunta suka yi dayake lan'kwashe su tayi ta zauna akansu, zogi taji sun fara yi mata take sai ta sake yamutse fuska tare da daidaita su yanda zata 'dan ji dama-dama. Motsin data yin ne ya'dan ankarar dashi daga zuba mata idanun da yayi, sai da ya 'dauke idanunsa ya kawar gefe kafin daga bisani ya dawo da kallon shi gareta. " kina jina" Ya tambayeta. Sai itama ta bashi amsa daidai da yanayinta a'kasan ma'koshi ta amsa masa da " uumm" tare da 'dagowa a'dan sace ta dube shi. Bata san meyasa ba amma wani 6angare acikin zuciyarta na kwa'daita mata son kallon fuskar sa yayin da 6angare 'dayan kuma tsoro ya rinjayar shi kuma sai tsoron yafi mata tasiri saboda idanun ya Abbas tsoro sosai suke bata ayau 'din aduk lokacin da yake yanayin da ba dai-dai ba ko ada ma da take masa iskanci son ranta dan be ta6a ritsata bane shiyasa, amma duk da haka de sai da ta 'dan saci kallon san wannan karan dan yadda yayi mata maganar cikin natsuwa sai yasata har ta samu 'kwarin gwiwan 'daga kanta ta kalleshi, idanunsa 'kur akanta ita kuwa bazata iya sar'ke idanuwanta acikin nashi ba dan haka sai tayi gaggawan maida idanuwanta ga tafukan hannunta dake kan cinyarta luguden da zuciyarta ke yi mata ma ka'dai ya isheta. _" dagaske ne wai aure zakiyi Angel 'din daddy"?_ Muryarsa asanyaye yayi maganar cikin nutsuwa sai kace bashine ya daka mata uban tsawa 'dazu ba, sai ta 'dago da kanta ka'dan itama amma bata kaiga fuskarsa ba sai ta sau'kar da idanun nata akan hannunsa 'daya dake ajiye akan hannun kujera, a irin yanayin da yayi maganar itama sai tace _" Daddy ne nima ya_ _fa'da min haka"._ _" toh meyasa ni baki 'kirani kin gaya min ba a lokacin"._ Sai tayi saurin bashi amsa da fad'in " _Wallahi Yayah mantawa nayi kayi ha'kuri"._ Ta 'karashe maganar da karkata kanta gefe harma ta daure ta sanya idanunta cikin nashi. Yanda tayin ba'karamin birgeshi tayi ba sai kawai ya tsaya yana kallonta kamar baze sake magana ba. Ita kuwa har godiya takewa Allah dayaga yayi shiru yana kallontan, _"Allah kasa ya ha'kura ya barni na tafi"_ duk zaton ta laifin da tayi masa kenan shiyasa yayi maltreating 'dinta 'dazu har tana tunani aranta " ashe dama akan 'dan wannan abin ne, toh ai in de wannan ne harda kai a laifin, kaima ai baka ta6a 'kirana ba, toh ni meyasa zan 'ki...... Tana cikin tunanin taji ya sake fa'din " _kin_ _manta kika_ _ce_ "? Ga mamakinta wannan karan atsaye yake hannunsa 'daya cikin aljihunsa harma ya juya mata baya kamar me shirin barin 'dakin. Mamakinta be wuche na har yaushe yabar nan 'din ba batare da tasani ba. _" Fatima toh dani kika manta ko kuma da 'kirana a waya?_ Yana gama fa'dan hakan ya juyo ya fuskance ta ga dukkan alamu amsar tambayarsa yake bu'kata gamsashshiya daga bakinta. Ita kuwa rasa abin da zata ce masa yasa tafara in ina domin ta kamamman abinda zata furta wanda bazai zama laifi ba take so dan ta kar ta 'kara yi masa wani tunda tasamu ya sau'ko, kuma sai tarasa, sai da 'kyar tasamu ta furta _" da wayar"_. Murmushin takaici yayi inda murmushin ya tsaya masa a iya saman la66ansa sannan ya juyo ya dawo kusa da ita kanta ya 'dago zuwaga kallonshi wannan karan kam jitayi zata iya kallon idanunsa tunda taji ya 'dan sau'ko daga masifar da 'daina shayin ha'da ido dashi aikuwa takalleshin idanun su suka 'sarke cikin na juna _" ki gaya min gaskiya, ke ma kina son auren nan ko?._ Ita kanta bata san lokacin da har kanta ya motsa ta bashi amsa ba saboda wani bug...bug take jin zuciyarta kamar zata fa'do waje. _" Fatima kina son Mahmud"_? Ya sake tambayarta. Yanzun kam shiru tayi masa sai da ya sake maimaitawa da 'dan 'karfi kafin ta sake 'daga masa kai alamar _"ehh_" Yagane me take nufi amma dan yasake tabbatarwa yace mata be fahimceta ba dolenta ta bu'di baki ta bashi amsa da " _ehhh"._ _" kin tabbatar "?_ kai ta 'daga masa yanzun ma dan ji tayi bakinta yayi mata nauyi koda zai doke tane bazata iya bashi amsa da bakinta ba. Yana gama fahimtar ta take sai yasake mata kanta ya koma ya zauna da kyau akan kujera ya lumshe idanunsa tare da jingina bayansa tsawon mintina biyu. Tashi yayi cak kamar an mintsine shi ya nufi 'kofar fita daga 'dakin, yanda ya buga 'kofar ma ka'dai abin ka juya ka kalleshi ne domin da 'karfinsa ya bugata tamkar tayi masa babban zunubi. Teemah tana inda ya bartan har ya bar 'dakin bata iya 'daga ido ta kalleshi ba, tana zaune tamkar mutun mutumi, bata san me yasa take jin kamar bata kyauta ba haka kawai sai take jin rashin nutsuwa ga kuma damuwa da tausayin kanta da bata san tushensu ba na ratsata ta ko'ina hakan sai ya 'kara kashe mata jiki tare hana ta motsi agurin banda gudun da hawayen ta ke yi babu abinda ke motsi ajikinta. Yana fita daga 'dakin sai su kaci karo da Hannah da ta taho da saurinta itama ta nufo dakin, dan tun 'dazu tun fitan Teemah take cikin bayi bata san da labarin zuwan shi ba koda ta fito kuma 'kawayen Teemah basu tuna sun sanar da ita 'kiran da Ummah take yi musu akan lokaci ba, sai da ta 'bata lokaci awurin yin shirin tagama kafin Naanah ta tuna da cewa an'kirasu tun 'dazu. Koda taje gun Ummah kuwa masifah tafara yimata akan wai ina ta zauna tun 'dazu bata je sun gaisa ba alhalin tasan baya da'dewa akan hanya yake, ha'kuri tabawa Ummahn tare da fa'din ai batasan shine yazo ba" Mummy ce ta tari maganan da fa'din je ki sameshi ku gaisa kafin ya tafi yana can 'dakin. Toh ita da suka zo jiya Teemah duk tabi da ita ta nunnuna mata ko'ina agidan da 'dakunan yayun tan, hakan yasa da mummy tace mata yana 'dakinsa sai ta nufi 'dakin da Teemah ta nuna mata jiya amatsayin 'dakin sa, amma sai bata ga alamar ma anbu'de shi ba ( ashe ita kuma mummy key 'din 'dakin Mahmud ta bayar aka sau'keshi aciki), ita kuma sai Hannah tayi tunanin ko bata gane lissafin bane tace bari ta dubo 'dayan tagani tukunna ( abinda ya sa tayi delay 'din zuwa da wuri kenan). Tana zuwa kuma sai ta ha'du dashi harya fito, _"ah ah_Yayah _har tafiya zakayi_ __ne_ _bayan bamu ha'du ba? _"Sauri nake yi Hannah lokaci zai 'kure min"._ "_Toh yayah kaci abinci ne ?_ " Duk maganannan da sukayi akan tafiya suka yi ta, Abbas be tsaya ba koda ya gantan sai yaci gaba da tafiyarsa, itama tana binsa abaya take ta faman jero masa tambayayoyin, ganin kamar zata takura shi. Sai ya ce _" Hannah naci jeki fito da sauran suna ciki"._ Yasan in ya fa'di haka zata koma tayi abinda yace dan yasan Hannah bata ta6a musanta masa magana kowacce irice. Illai kuwa hakanne, dan yana fa'din haka ta tsaya cak daga binsan da takeyi, ta bi bayansa kawai da kallo daga bisani kuma sai ta juya ta koma 'dakin domin fito da ragowar abincin kamar yadda ya ce da ita. Tana shiga sai ta hango Teemah a zaune tana zubda hawaye, da sauri ta 'karasa inda Teemahn take tayi zaman dirshan a gaban ta arikice take tambayarta abinda yafaru. Teemah kuwa bata san da shigowan Hannah ba sai kawai taganta agabanta lokaci guda. Hawayenta ta fara 'ko'karin gogewa ita adole kar Hannah tagani. Duk 'ko'karin da Hannah tayi dan taji meyasamu Teemah tayi amma takasa samun gamshashshiyar amsa ko guda 'daya ne daga wurin Teemah. Data gaji da tambayar sai tace mata _" nasan me ya faru ai kawai baki san sanar dani ne"_ Shiru Teemah tayi kawai tana kallonta ita kanta so take taji abinda yasame ta so take taji daga bakin HANNAH, dan idan zata tambayi kanta da kanta ma bata san meke damunta ba bata san mezata ce yafaru tsakaninta da Yah Abbas ba. _" wannan sojan ne nasani, nasan shine yasaki kuka domin shi ne ka'dai naga yafita daga 'dakin nan kuma nasan sarai zai iya"_ Hannah tayi maganar tare da mi 'kewa tsaye ta nufi inda taga tray 'din abincin. _" gaskiyarki ne Hannah, Yah Abbas ne !,toh amma me zance yamin har nake kuka"?_ azuciyarta tayi wannan tunanin, sannan itama ta mi'ke tabi bayan Hannah zuwa gurin abincin. Hannah sai da ta zauna kafin tafara bu'de su 'daya bayan 'daya tana gani. _" 'kila ya tsaya yi miki mugunta ne ma shiyasa ko abincin be saurara ba harda wani cewa wai inzo in kwashe_ _sauran ashema ko bu'dewa beyi ba"_ tayi maganar dai dai tana 'ko'karin rufe plate 'din daya kasance na 'karshe data bu'de " _muje sai na tambayeshi ai laifin me kika masa da har yasaki kuka, innayi sa'a shi zai gaya min tunda ke kin'ki sanar da ni, problem 'din ma miskilancin tsiya gareshi da 'kyar ma yakulani idan yaga dama, amma nasan me zanyi ai in ya'ki bani amsa Daddy zan 'kira infa'dawa ince in yazo nan dukanki yake yi kullum kafin yatafi "_ Suna kan tafiya Hannah take ta jero bayananta batare da Teemah ta fa'di ko kalma 'daya ba sai da Hannah ta dasa aya sannan Teemah tace _" ke nifah bance miki ya Abbasa ya doke ni ba"!_ awani tsare tayi maganar tamkar wata jaruma. Turus Hannah taja ta tsaya _"Toh yah akayi? fa'damin_ "! _" ayaya kika sameni"_ ? Sai da Hannah ta 'dage gira tukunna tace _"Azaune mana kina_ _kuka"!_ _"Toh abinda yasame ni kenan, gajiya nayi da zaman kuma kafata ta ri'ke sai zogi takemin nakasa ko motsa ta shiyasa ni kawai nafara kuka"_ _" shikuma yatafi ya 'kyaleki ahakan"_? _"Sai da ya fita sannan na fara jin zafin"_! _" kin ma rainawa kanki hankali yarinya amma da nazo 'din waye yataimaka miki kika mi'ke?" Da sauri Teemah tace _" ai lokacin 'kafar ta daina zafi"_ _" kuma hawayen kasa tsayuwa yayi ko"? ,_ Shiru Teemah tayi ta kauda kanta gefe. Hannah kuwa sai taci gaba da maganarta _" kekika sani wallahi indai juninki wai adake ki 6oye ne kin shiga_ _ukun ki,_ _Yah Abbas fah bashida kara shikan_ _babu_ _ruwansa muguntarsa intazo yinta yakeyi ako ina indai shine, kicigaba da rufa masa asiri wai ke gaki me_ _yayah ko hmm_ , _jiki_ _magayi ai_ _yarinya"__ _"ke kin kasa yadda be min komai ba_ _ko"_ ? _" ai ko bani ba babu me amince miki Teemah"._ _"Allah kuwa Hannah babu abinda ya min idan abu yamin ai zan sanar dake kinsani"!_ " _ke kika sani fah ni babu ruwana_ " Hannah tafa'da 'kasa-'kasa. Teemah kuma acikin zuciyarta tace _"kanki akeji parrot_ _kawai."_ Hannah alwashi tayiwa aranta sai ta bincika ta gano abinda ke faruwa saboda tana ganin kamar Teemah na 6oye mata wani abin ne, kuma batason Teemah ta kullaci Abbas saboda idan ya kasance kullum mugunta yake mata dole zata na jin haushin sa aranta,itakuwa tana son yayan ta batason kuma taji ance anajin haushin wani abu nashi daya dangance shima ballantana shi da kanshi, tafi son taji kowa nason shi, shiyasa ko yanzun ma ta damu dataga Teemah na kuka taso Teemahn tasanar da ita meke faruwa dan tayi maganin abin, amma Teemah ta'ki. Abbas kuwa tun kafin ya isa 6angaren da yasan zai samu Ummahn ya 'daga waya ya 'kira Mummy.............. *ACIGABA DA KAFTAWA MUTANE NAH...........*🤞🏻 *Sa'kon Ta'aziya ga 'yar uwa RAHAMA NALELE da dukkan al'ummar musulmi, Allah ubangiji ya ji 'kan magabata yasa alajanna hutu ce. Allah ubangiji ya musanya abinda* *aka rasa da alkhairi* *mafifici.* _Sorry 4d late condolence._ _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce*😍 [10/2, 6:01 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* We can’t solve problems by using the same kind of thinking we used when we created them. 🅿 *47* Mummy cewa tayi ya shigo tukunna suyi sallama da mahaifiyarsa mana kafin yawuche 'din, yayi 'ko'karin ce da mummyn ta sanar da Ummahn kawai basai ya shigo ba da 'kyar mummy tayi convincing 'dinsa yashigo koda ya shigonma atsatstsaye yayi musu sallamar yawuche abinsa kafin su Hannah su shigo ma har ya wuche dukkansu sun fahimci 'yar 6oyayyiyar damuwan dake kwance asaman fuskarsa amma basu tsaya sun tambayeshi ba saboda sun san basamun amasa zasu yi ayanda suka san halinsa. Hannah da Teemah kuwa koda suka shigo 'din ma sai kowa yabi hanyarsa, Teemah 'dakinta ta wuche wurin friends 'dinta bayan ta daidaita nutsuwa da yanayin fuskarta, Hannah kuwa kitchen ta shiga ta ajiye tray 'din da ta 'dauko sannan ta dawo wurin Ummah tazauna agefenta. _" Ummah wallahi Yayah ko cin abincin ma beyi ba ya fito kayansa"_ tace da Ummahn cikin yanayi na shagwa6a66u. Sai Ummahn tace mata _" 'kila baya tare da yunwa ne shiyasa "._ 'Kasa-'kasa tayi da murya dan kar kowa yajiyo ta tace _" Ummah kinsan wani abu"?_ Kai Ummahn ta girgiza mata alamar _a'a_ sai ta cigaba da fa'din _" kukafa nasamu Teemah nayi a'dakin nasa na tambayeta kuma ta'ki ta sanar da ni_ _abin da yasameta"._ _" nasan za'a rina"_ Mummy tace azuciyarta. dan duk 'kasa-'kasan da Hannah tayi da muryarta sai da Mummy tajiyo ta batasani ba, dah ita a shirmenta wai ba'a jiyo ta Ummah ce ka'dai kejinta, wannan karan Ummah mantawa tayi da sirrin 'karyar da Hannah take so suyin tace _" toh me yasame_ _ta"?_ da 'dan 'karfi tayi maganar. _" oho nima bansani ba, amma inaga itada yayah ne"!_ Hannah ma dolenta ta dawo da muryarta daidai yayin fa'din hakan dan Ummah tariga ta tona ta. Mummy naji amma bata tanka ba sai da taga Ummah taciro waya sannan taso saka baki amaganar duk da bata so haka ba amma sai taga yazama dole ne tayi maganar, tana shirin yin magana sai Hannah ta rigata tambayarta abinda Ummah zatayi da wayar ganin tana shirin nemo wata number, afirgice tace da ita _"wa kuma zaki 'kira Ummah da wayar"?_ _"Abbas mana, tambayarshi zanyi abinda yarinya nan tayi masa ya daketa"_ Hannu Hannah tasa tana 'ko'karin kar6ar wayar tace _"kai Ummah bazaki ci ribar zance ba kekam, daga magana sai ki 'kirashi kalan yazo yaci 'kaniyata yace ni ce nafa'da miki".?_ _" Toh me yasa zai daketa yatafi abinsa, daga zuwa gaishe shi dan_ _neman fitina da rashin ha'kuri sai yakama ya doketa, yarinyar da ake shirin taron bikin ta shine zai daka tsabar shi_ _ishashshe ko me?"_ Sai yanzu mummy tasamu damar saka baki amaganar tasu ganin Ummah ta 'dau zafi tace. _" dama kin hutar da bakinki da zuciyarki akan yaran nan, indai Teemah da Abbas ne toh wallahi_ _gajiya zakiyi da magana har bakin ki yayi tsami, haka suke kullum cikin abu 'daya"._ _" toh ai wannan duk rashin ha'kurin na sa ne, taya zai rin 'ka biyewa yarinya 'karama har haka"?._ _mthewww_ Ta 'karashe da yin tsaki sannan ta da dawo da kallon ta da Hannah tace " _kinga Hannah je 'kiramin ita Fatiman, maza yi_ _sauri"._ Tafa'da tare da 'dago hannayen Hannah sai da taga ta tashi tsaye kafin tasake ta. _" ki sauri mana"_ Ta 'kara cewa da Hannah ganin tana 'daga 'kafa ahankali kamar ba son zuwa take ba. _" hmmm"_ kawai mummy tafa'di a'kasan ma'koshinta, ganin ko'karin Ummahn takeyi ita. Ko bayan fitar Hannah Ummah cigaba tayi da surutu tana mita akan lamarin mummy ce ta dakatar da ita da fa'din _" wannan abinda kike yi fah duk abanza ne inde akan yaran nan ne, kuma nasan babu_ _wani dukanta da Abbas yayi dan tunda muke dashi agidannan banta6a ji ko ganin yasa hannu ya_ _ta6a_ _lafiyarta ba duk kuwa da irin rashin ji da Fateema keyi_ _agidannan, ko yanzun ma nasan iskancin Teemah ne kawai ki rabu dasu."_ ! Kauda kai Ummah tayi gefe kamar bataji ba ga dukkan alamu maganar mummyn be wani shiga kanta ba, sai mummy ma tayi murmushi kawai ta ta tashi ta bata wuri. Da Teemah ta tashi zuwa 'kiran da Ummah keyi matan gaba 'dayan su suka taho da sauran friends 'din nata dan cewa sukayi suma zasu wuche gida ganin lokaci ya 'dan ja. Da fara'ah dukkansu suka shigo 'dakin saboda ragowar dariyar dasukayi duk be bar kan fuskokinsu ba, Naanah ce take kwatanta rawar da zatayi wai agurin bikin Teemah gashi bata iya rawar ba abin dariya kuma wai ita adole sai tayi ,Fauzee kuwa data kare mata kallo sai tace _wai_ _rawar Naanahn_ _tamkar agwagwa na tafiya_ hakanne yasasu dariya gaba 'dayan su shiyasa suka zowa Ummahn da murmushi akan fuskokinsu. Ummah idanunta akan Teemahn yafara sau'ka da har yanzu takasa ri'ke tata dariyar idonta har yana hawaye tsabar dariya, aduk lokacin da ta tuno maganar Fauzee sai kawai taji sabuwar dariya ya kamata. Mamaki Ummah tayi sosai kuma sai alokacin ta yadda da maganar mummyn data gama fa'da yanzun kafin ta tashi, yanda taga idanun Teemahn badan taga tana dariya ba da sai tace kukan dukan da Abbas din yamata ne amma ganinta tana dariya sai ya wanki ranta ta 'danji wasai. Sallamansu kawai tayi batare da ta tambayi Teemahn abinda yafaru ba, haka suka je suka yi musu rakiya awurin gate suka musu sallama tare da godiyan ziyaran dasuka kawo musu daga nan su Fauzee sukayi gaba sukace sai nan da kwana biyu kuma idan sunzo shan shagalin biki. ***** *LAGOS* Mahmud kullun addu'ah yake kar Allah yasa Abbah yasake tunowa da maganar zuwa yoben nan dan shi ba son zuwa yake ba, Allah kuwa ya taimakeshi Abbah be sake bi ta kai ba, sai kawai yaci gaba shiryen shiryen dake gabansa. Anty kuwa zuwa yanzun hankalinta inyayi dubu toh ya gama tashi, dan ganin yanda shirye-shirye ya kankama gashi Anty chideh ta 'ki bata ha'din kai suje gurin neman maganin har yanzu, ta ro'ki Anty Chidehn iya yanda zata iya amma sam ta'ki yadda har Anty ta ha'da da cewa zata iya samo mata 'yan mata duk irin wanda take so wanda suka ri'ka awannan harkar ko guda nawa ne matu'kar zata amince ta kaita wurin 'dan ogah, amma Anty Chideh ta'ki yadda tace ita kanta zata iya nemowa kanta indai tana da bu'katar su wannan ba matsalarta bane ayanzu. Anty kuwa tace ita sam bazata iya aikata lesbian ba, bata ma son ko ka'dan taji ana labarinsa ji take yi kamar zatayi amai tun ranar data ga Anty Chideh nayi ta 'kara tsanar abun bata ma ko san tunowa dashi ballantana ita ta aikata shi da kanta, akan hakan ta gwammaci ganin auren Mahmud da ire-iren 'ya'yan Khadija ko da su nawane aduniyan nan indai har sai ta aikata lesbian zata ga rashin yiwuwar hakan. Akan haka kullun suke dramma da 'kawarta Anty Chideh inda kowa ya kafe akan nashi ra'ayin, duk kuwa da wannan abinda Anty chidehn keyi mata hakan besa daidai da 'kwayar zarra taji haushin Antyn Chideh ba ko ka'dan, ahaukarta ita gani take kamar _so ne_ ai har yasa Anty chidehn taza6e ta akan hakan, sai dai rashin sa'ar da Anty Chidehn tayi shine ita Anty bata da ra'ayi. Maimakon ta 'dan ja baya da Anty chideh a'a sai ma wani sake lalla6a ta data keyi akullum, saboda tsoron kar ta ce zata fita aharkanta ta rabu da ita gaba 'daya wanda take ganin kamar in hakan yafaru ba 'karamin asara tayi ba tana ganain cewa wahala zata sha in Anty Chideh bata tare da ita, gani take zata shiga uku domin Anty Chideh itace idanun ta afa'din garin Lagos, duk wani damuwarta, farin cikinta, ba'kin cikinta samu da rashin ta kafin kowa yasani sai Anty Chideh tasani. Inkuwa matsala ce ta kunno mata kai bata san ta tsaya ta kaiwa Allah kukan ta ba, sai de Anty Chideh, zuciyar Anty gaba 'daya ya lalace da zuwa gurin bokaye da 'yan tsibbu harma tana ganin kamar matu'kar kana da 'yan canji toh baka da matsala da komai arayuwa inhar bokaye na existing toh damuwarta ka'dan ce, bata san tasaka Allah a lamarinta ba sai dai bokaye sosai tayi amanna dasu da ayyukansu. Wata 'kawarta ce ta ziyarce ta asatin bikin tasame ta cikin yanayi na damuwa anan tabata shawaran cewa wai tasaki ranta kawai asha biki agama lafiya duk da baso takeyi ba ta 6oye hakan aranta tunda yanzu tarasa mafita inyaso bayan bikin sai ta shi tsaye ta nemi hanyar 6illewa tayi maganin su gaba 'daya. Aranar da matar ta fa'di haka Anty kamar zata cinyeta 'danye dan masifah, da 'kyar matar tasamu ta fita ta wuce inda ta fito tana mai dana sanin kawo wannan shawaran datayin, Anty cewa take wai dan me matar zata ce haka, tana nufin ta tsaya kenan har sai angama bikin tana kallo, tana nufin idanu zata zuba kenan tana gani 'danta ya auri waccen _banza_ _dangin mayun_ , tajima tana kunfar baki baub wanda ya tankata agidan, dayake ma Abbah baya nan alokacin, house maid ne ka'dai da ita agidan, da 'kyar Anty tasamu ta lallashi zuciyarta tayi shiru. Sai dai wani abu da batasani duk wannan dramar da Anty keyi akunnan Mahmud kaf aka yi su har sai da yaga matar tafita sannan shima yakoma 6angarensa, dama shigowar sa gidan kenan yanufo parlour daniyar duba ta, sai kuma yaji suna wannan maganar. Hawaye yake ta faman sharewa na ba'kin ciki da takaicin halin da mahaifiyarsa ta cusa kanta 'karfi da yaji, har yaushe Anty zata gane ta dawo kan dai dai, har yaushe zakace a kullum sai kayi jayayya da lamarin ubangiji bayan shike da kai ba kai kake dashi ba. Hawaye Mahmud yake sharewa yake wannan tunanin, babban dalilin dayasa tun farko yanuna baya son auren nan kenan, dan bazai iya tsayawa ya juri ganin Fatima awani yanayi ba, dan yasan Anty bazata ta6a saduda taso zuri'arsu ba, wannan wani irin rayuwa ne?, karo na barkatai kenan daya ke jin irin mugun alkaba'in data ke bin danginsa dashi, bayan yasan ako ina zasu tsaya ko suje ita ce abin zagi basu ba ga duk wanda yasan halinsu gaba 'daya. Darajar haihuwa kawai Anty take ci amma wani lokaci Mahmud jiyake tamkar ya sha'keta saboda kawai ya huta da ganin ba'kin ciki awanan gidan. Duk da lokuta da dama yana tanka mata akan abinda takeyi 'din sai de baya jan maganar sosai sai ya 'kyaleta haushi ma baya barin sa ya 'dau dogon lokaci tare da ita, haka kuma be fiya son suna jayayya da ita ba akan abu. Bayan fitan matar ne kuma sai Anty ta zauna tayi tunani da kanta akan maganar matar sai kuma taga hakan kuma fah yafi mata, saboda bata san ta ina zata fara ba yanzu kam amma bayan angama biki hankalin munafukai ya kwanta asannan ne ita kuma zata bayyana nata haukan. Sosai tayi na'am da wannan shawarar da zuciyarta ta batan, takuwa bishi dan Abbah da kansa yayi mamakin yanda farat 'daya Anty ta sau'ko ta zubda dukkan makamanta na ya'ki ta kama shirin biki babu 'ka'k'kautawa, yanda ta nuna tana son auren ma har in baka sani ba zakayi zaton ko tafi Abbah ma burin son ganin anyi auren angama. Mahmud ne ka'dai yasan dalilinta shikuwa akullum addu'ah yake kar Allah yabata sa'an cutar da kowa, dan yasan ha'ki'ka sihiri gaskiya ne, tsafi gaskiyar mai shi. *INAJIRAN GANIN MUHAWARAR KU READERS.........* 🤞🏻 👎🏻 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce*😍 [10/2, 6:01 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _Happiness is not a goal, but a way of life._ 🅿 *48* Anty da kanta ta 'dauki driver suka je da Abbah gidan abokin Abban ta sake duba kayan da aka harha'da 'din, anan ta nuna cewa wasu abubuwan ai sunyi ka'dan ya kamata a'kara gaskiya saboda wannan bikin na _kai_ _da kai ne_ . Speechless Abbah ya zauna yana kallon iyayin da Antyn keyi, take kuwa ta sake tura ku'di wa Hajiya Aisha tace a'karo kayan tanaso bikin 'danta ya kasance fitattace wanda za'a jima ana kwatancensa aduniya. Hajiya Aisha kanta tayi mamakin yanda abin ya dawo, domin ba haka labari ya iso mata ba da farko ganin alokacin Abbahn shine tsaye akan komai, sosai tayi mamakin yanda Mum Mahmud 'din ta canja cikin 'kan'kanin lokaci, dan akwanakin baya ka'dan kafin zuwan yau akullum in suka yi duba da yadda Abbahn yayi ruwa ya kuma yi tsaki akan lamarin auren ba sa cewa komai sai dai suce Allah ya shiryi Mahaifiyar Mahmud 'din, Allah da ikon sa kuwa ashe shiriyar tata na kusa yanzu kam sai dai suce _"ALHAMDULILLAH"_ dan Mum Mahmud tabawa kowa mamaki alokacin da basu zata ba. Aranar Anty bata koma gida ba kasuwa ta wuce tayi siyayyah sosai ma kanta, kaya tsadaddu ta siya ta bada 'dinkin express a inda tasan bazasu bata matsala ba, bata damu da tsadan 'dinkin ba ita damuwar ta tasamu adai dai lokacin da zata bu'kace su. Ta dawo gida da sauran ragowar siyayyan data yi ni'ki-ni'ki a hannu. Tun daga ranar Anty bata 'kara nutsuwa guri 'daya ba akullum tana hanyar fita, kasuwa da sauran abubuwa. Haka duk mutanen data san zata gayyata duk ta gayyace su daga 6angarenta, 'kawayenta ma wasun sunyi mamakin canjuwarta ta amma koda sukayi magana sai tabisu da murmushi kawai batare da ta basu gamsashshiyar amsar da suke son ji ba. Akwana biyu kacal da sa'k'kowar Antyn har gida yafara cika da wasu daga cikin 'yan uwa da abokan arzi'ki, hatta 'yan uwan Abbah da suke 'kauye 'kalilan daga cikin su sun samu sun zo hakama yan uwan Antyn. Abin mamaki Anty duk ha'dasu tayi tai musu sau'kar bangirma, bata nuna mugun hali ba koka'dan bata bari sun samu 'kofara da zasu zageta da ita ba wanda hakan duk yana cikin target 'dinta ne nagaba. Abbah da kansa ya nemawa Mahmud 'din gida flat house mai kyan gaske ya kuma zuba komai na bu'kata dai-dai da zamani sai 'dan abinda ba'a rasa ba, sai dai gidan babu nisa da gidan Abbah yake duk a area 'daya suke, da farko ma Anty takawo shawarar cewa wai ko a side 'din Mahmud za'a kawo amaryar, har Abbah yaso ya amince domin shi be kawo komai aransa ba game da canjawar Antyn zatonsa shiriyah ce kawai tazo mata daga Allah, amma da aka sanar da Mahmud shi kam sai cewa yayi a'a shi ba zai zauna a nan ba gaskiya sai de anemo wani guri daban, jin hakan yasa Abbah ya yarda da batun Mahmud 'din dan shi lalla6a shi yake yasamu yaga de an 'daura auren yasan daga lokacin komai zai wuche yazama tarihi. Hakan yasa ya nema masa gidan da kansa ya biya ku'din lokacin ma Mahmud 'din be sani ba sai daga baya Abbah ya 'dauke shi ya kaishi gidan dan yaga yanayin gidan ko ya masa. Shikanshi Mahmud ya yaba da tsarin gidan, dan shi dama yafison gida flat mutun yafi sakewa aciki sai dai kuma duk da haka sai da yayi wa Abbah complaint cewa wai ai sun yi kusa sosai shi fah bahaka yaso ba yafison yayi nisa dasu. Ido Abbah ya kwalalo yana kallonsa da mamaki " Mahmud wai lafiyarka kuwa"? Abbahn ya tambayeshi. Baiyi magana ba illah 'dago hannunsa dayayi yana duba tsadaddiyar agogon dake 'daure atsintsiyar hannunsa. Cigaba da magana Abbah yayi. " Babana dan zakayi aure shine zaka guje mu gaba 'daya har baka son zama kusa damu?" "Bahaka bane fah Abbah"! Kwafah Abban yayi kana yace "toh menene?" Shiru Mahmud 'din yasake yi ya sunkuyar da kansa 'kasa. "Mahmud karfa laifina ni danasa ka kayi aure alokacin da baka shirya ba yashafi wata daban, inaso kaji tsoron Allah Mahmud adukkan lamuranka , wallahi idan ka kuskura ka cutar da yarinyar nan azaman aurenku da ita bazan ta6a yafe maka ba, sanin kanka ne ni...nine na nemi ha'din auren nan da kaina, kuma kasan inde har hakane kuwa bazai yiwu in zuba ido inga ancutar da ita inakallo ba batare da nayi magana ba, dole zan 'dauki mataki matu'kar hakan yafaru koda kuwa waye ne yata6ata" Mahmud kansa ya 'dago ya kalli Abbahn nasa sannan yace "Abbah nifah bani da burin 'kuntata wa ko cutar da Fatima arayuwata ko ka'dan............"! " toh menene "? Abbahn yatari maganar Mahmud 'din da sauri. " Tausayinta nakeji ni Abbah " " you see......,"Abbahn yafa'di tare da nuna Mahmud da yatsansa yakuma cigaba da fa'din. "Ai shi yasa nake ce maka akullum kaji tsoron Allah, ina son ka sani cewa daga ranar da akace an 'daura maka aure toh nawi ne babba ya hau kanka bana wasa ba, daga ranar amanar Allah ta hau kanka duk abinda ka aikata kai da mahallici ne kar kayi zaton ko babu wanda yaganka, idan tausayin nata kakeji da gaske tun yanzu zakayi 'damar zama da ita idan kuwa tausayin ta dan zata auri wanda baya son aurent ne toh kasanar dani inji...." Shiru Mahmud yayi yana sauraran maganganun Abbahn, shi kanshi yasan gaskiya Abbahn yake fa'da masa amma shi koka'dan abinda ke ransa beyi matching da na Abbahn ba, taya Abbah zaiyi tunanin shi zai cutar da Fatima dan kawai ansashi ya aureta bada son ranshi ba, ai ko da ace yana bacci ne aka tashe shi aka ce ga matarka an aura maka ita bazai cutar da ita ba ballantana kuma Teemah,! yasani daman idan yace be son zama guri 'daya dasu dole daga Abbahn har Anty sai sunyi tinani daban kowa da abinda zai zo cikin ransa,shi kuwa manufarsa tayin hakan daban ce da tasu. Har Abbah ya kammala da nasihar tashi Mahmud bai ce masa komai ba shiru yayi yana sauraransa, sai daga 'karshene da Abbah yace masa kar yaga kamar yamanta da batun zuwa Yobe ne dan yaga yayi shiru, yace kawai ya 'kyaleshi dan yaga alamar bason zuwa yake ba kuma dan kar abun ya masa yawa shiyasa ya 'kyaleshi amma hakan bawai yana nufin ya bashi 'kofa bane da zai ci zarafin yarinya ba ko da bayan auren dan bazai lamunci hakan daga gareshi ba. Aranar akan wannan maganar suka kusan wuni da Abbah dan har suka koma gida Abbah be daina yi masa tuni akan magabar ba haka yake yin ta fa'da-fa'da, nasiha-nasiha, garga'di-garga'di. Tausayintan da Mahmud yace yake jine yafi tsayuwa aransa dan takamamme ya rasa dame zai fassara ma'anar hakan. Koda Anty tasamu labarin gidan da Abbah ya nemawa Mahmud itama sosai tanuna farin cikinta azahiri harma take nuna musu zumu'dinta nason zuwa ganin gidan itama yayinda take jin tamkar wuta ne azuciyarta yake ci dan ba'kin ciki da takaici, taso Mahmud ya zauna acikin gidan da suke saboda zatafi saurin cimmah burikanta akan auren cikin sau'ki amma Mahmud yayi mata yawa, sai de duk da haka ba ta yi 'kasa a gwiwa ba tace de _" su zuba_ _sugani "_ . Ana gobe 'daurin auran dasafe Daddy ya 'kira Daddyn Abuja yake tambayar labarin Abbas sai Daddyn Abuja yace ai a kwana kinnan ma yazo amma kwanansa 'daya yakoma bakin aikinsa yace kasan 'dan naka gwani ne wurin bin doka, baya son wasa da aikinsa. Dariya daddy yayi tare da fa'din ai hakan yana da kyau shine daidai domin sau'ke nauyin daya rataya akansa, ya'kara da fa'din shima yasamu labari agida sunce masa Abbas 'din yazo amma yakoma, yace amma fah dukda haka kar Abbas yace min bazai zo ya halarci wajen 'daurin auren nan ba"? Daddyn Abuja cewa yayi "Ehh toh gaskiya bamuyi maganar nan dashi ba amma bari zan tambayame shi naji ya ake ciki". " yauwa kace masa injini nace auren fah ahannunsa na dan'kata gaba 'daya shine zai bada auren Fatiman ma'ana shi zai kasance _alwali_ agareta. Baki Daddyn Abuja ya washe tare da fa'din "Ahh gaskiya abu yayi kyau bari zan sanar dashi yasamu lokaci ya taho kafin goben, nima anjima da yamma insha Allahu ina hanya" " Toh bakomai Allah ya tsare ya bada sa'a" Daddyn Teemah ya fa'di tare da yanke 'kiran. 👎🏻 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/2, 6:01 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _Trust is like a paper…....Once it's crumpled, it can't be perfect again…......_ 🅿 *49* Koda daddyn Abuja ya sanar da Abbas sa'kon daddyn Teemah Abbas ji yayi tamkar zuciyarsa zata fita daga 'kirjinsa ta yo waje tsabar yanda bugunta ya 'karu, shiru yayi batare da ya bawa daddyn nasa amsa ba, ha'ki'ka badan daga bakin mahaifinsa yaji maganar ba da cewa zaiyi tsantsar rainin hankali ne yasa aka za6eshi domin yayiwa Teemah wakilcin auren ta, amma sanin daga bakin mahaifinsa yaji da kuma sanin wanda yaza6e shin shiyasa yayi saurin kauda wannan tunanin azuciyarsa, Hello!..... Hellloo Abbas kana jina kuwa?.... hel..... Muryarsa asanyaye yace " ina jinka Daddy"! " aww toh naji shirune shiyasa"! Daddyn Abuja sake maimaita abinda ya fa'din yayi zaton shi Abbas 'din be ji yace dashi 'dazun ba sai de tunkan ya 'karasa maganar Abbas ya tari numfashinsa da fa'din " Daddy abubuwane agabana masu yawa wallahi, yanzu ma shirin tafiya nakeyi zuwa Kogi state bani da wannan lokacin"! " toh ya za'ayi kenan"? Dadyn ya sake tambayarsa. "Daddy please ka wakilceni ko kuma kasa wani amadadina in babu matsala, zan 'kira Daddy Babban ma nayi masa bayani " "Toh shikenan ba matsala, Allah ya tsare ya rufa asiri"cewar Daddyn, da "Ameen Ameen "Abbas ya amsa masa sannan sukayi sallama kowa ya ajiye wayar. Abbas da tsaki ya cire wayar a kunnansa dan ma Daddyn Abuja yariga ya yanke 'kiran badan haka ba babu abinda zai hana shi jiyo tsakin da Abbas 'din yabi bayan wayar dashi. Baya yakoma ya kwantar da jikinsa tare da 'daga kansa sama yana jujjuya kujerar dayake kai 'din, wani huci yake fitarwa tamkar wani wanda ya dawo daga gudun kilometre. " kar Allah yasa a 'daura auren in de har sai ni zan bada shi, mthewww" Ya 'karasa da jan tsaki kana ya sake 'daukan wayar yayi dialling no. tsawon mintina biyu ne ya 'daukesa a maganar yana kammalawa kuwa ya mi'ke tsaye da hanzari yafara rage kayan jikinsa. Wanka yashiga sharp-sharp ya watso ruwa ajikinsa ya fito, shiri yayi cikin kakinsa na sojoji gwanin birgewa, dan ba 'karamin kar6arsa uniform 'din keyiba, kamar kar ya rabu dasu har abada idan yasaka su. Zama yayi dan saka socks da takalmi, yana gamawa da shirin yafito ya kulle 'dakin ko wayarsa ma be tuna ya 'dauka ba, hularsa ce kawai ya ri'ko a hannunsa ya tafi. Taku yake cikin ta'kama da 'kasaita duk da cikin hanzari yake tafiyar amma hakan be hana bayyana isarsa afili ba, Abbas 'karshe ne wajen iya tsarawa kansa komai, ciki kuwa harda tafiya be barta abaya ba, musamman idan ya shiryo cikin uniform 'dinsa jiyake tamkar yafi kowa, jin kansa yake kamar bashi ba, alokacin jin kai da miskilancinsa 'karuwa sukeyi sosai. Ballantana yanda yake samun girma aduk lokacin da ya fito hakan ba 'karamin birgesa yake ba, dan dayawa daga cikin sojojinsu na girmama shi, ciki kuwa harda wa'danda suka girme wa shekarunsa suka kuma fishi da'dewa a akan aikin nasu, shiyasa akowani lokaci yake godiya ga Allah da kuma daya ya tsaya tsayin daka ya jajirce dan ganin ya samu wannan matsayin daya kai 'din ayanzu. Ko yau 'dinma daya fito daga block 'dinsa hakanne yafaru, dan duk inda ya ha'du dana 'kasa dashi sai de kaga suna 'kamewa suna mishi gaisuwar ban girma, ko kulasu ma bayyi yake wucewarsa dan abin da ke gabanshi ne damuwarsa awannan lokacin, hakan kuwa bazai hana su cigaba da sara masan ba. Office 'dinsu direct yawuce ya nemi jin batun tafiya Kogi state 'din da aka ce zasu da kuma lokacin da za'a yi tafiyar, aka sanar dashi cewa nan da 2hrs ne tafiyan, da 'kyar ya samu yayi cancelling sunan shi aciki aka maye da wani daban inda da kanshi ya sanar da wancan 'din cewa akwai tafiya nan da 2hrs dan haka ya shirya ya taho kafin lokacin. Uzuri sosai ya basu kafin yasamu suka cire sunan nashi da shara'din cewa ths is d first and d last da zai 'kara yin irin hakan ya kuma amincewa sannan ya 'kara da neman pass na kwana biyu. Da yamman ranar ya baro Porthacourt ya sau'ka a Abuja, gidan babu kowa ya samu sai me gadi kawai dan daddyn sama aranar suka wuche kuma dawuri suka tafi, tafiyar motan da zasuyi daga Maiduguri zuwa Damaturu ne yasasu tafiya dawuri dan basu so dare ya same su ahanya saboda dokar da ke wannan yankin alokacin mai tsanani ce. Kaya kawai Abbas ya canja cikin wani kaftan brown colour bayan yayi wanka tare da gabatar da sallan la'asar dake gabansa daga nan ya fita daga gidan yatafi airport da 'kyar yasamu flight 'din da zashi maiduguri 7:00pm, daga can yashiga gari yarage lokaci tare da ziyartan wani abokinsa. Koda Abbas ya sau'ka a maiduguri hotel ya nema ya yada zango dan bayajin zuwa gidan oga philip wannan karan, duk dama ba'karamin taimakonsa oga philip 'din keyi ba ko ta wajen ha'da shi da driver ma dayake yi, amma wannan karan ya gwammaci ya hau motar haya kawai yafi masa badan komai ba sai dan ji da yakeyi yanajin haushin kowa ma gani yake kowa damuwa ne. Abbahn Mahmud da shi kanshi Mahmud 'din already sun iso da sauran abokan arzikinsu da suka zo musamman domin halartar 'daurin auren, suma ganin suna da 'dan yawa sai suka taso da wuri cikin sa'a kuwa basu samu matsala da komai ba suka iso akan lokaci kuma lafiya 'kalau, dan har sun riga Daddyn Abuja ma isowa. Daddy acan wani guest house 'dinsa dake bayan legislative quaters ya sauke su harma da wasu ba'kinsa na nesa da suka samu damar amsa gayyatar daddyn, 'dakuna isassu ne agidan so babu wanda ya takuru da wanzuwar 'dan uwansa anan kowa ya sau'ke gajiyarsa. Babu wanda yabi ta kan Abbas domin daddy da kansa yayi musu bayanin yanda sukayi da Abbas 'din awanni ka'dan dasuka gabata, zatonsa shi ka'dai ne yasani dan Abbas da zai masa maganan be nuna masa cewa yayiwa Daddynsa bayani ba. Dukkansu basu damu da rashin sa agurin ba dan sunsan yanayin aikinsa bakamar su bane da su suke sarrafa kominsu yanda suka ga dama. Mahmud ne ka'dai ya damu da rashin Abbas 'din dan tun safe yake ta trying layin Abbas 'din amma baya samunsa, da farko yayi ta 'kira ba'a 'dauka daga baya kuma not reachable, ko bayan isowarsu ma yayi ta gwadawa amma baya samunsa. Mahmud bahaka yaso ba, yaso Abbas yakasance tare da shi awannan hidiman dan shike 'kara masa 'karfin gwiwa a kullum. Amma dayaga be same shi ba dole ya ha'kura da nemansa fatansa de Allah yasa lafiya yake. Sai dai yasa aransa cewa matu'kar Abbas be halacci wurin 'daurin auran nan ba yace da kansa zai je har porthacourt 'din yaji dalilinsa nayin hakan bayan shine yasashi ya amince da auren tun farko. ***** Washe gari saturday gari na wayewa kowa yafara shirin 'daurin aure. Abbas da safiyar ranar ya iso around 9:30 am, alokacin kuwa shirye shirye yariga ya kankama kowa harkar gabansa yakeyi, ta 'karamar 'kofan dake bayan gidan yashigo dan baya son kowa ya ganshi shi, gaishe-gaishen damuwan nan ma shi baso yake ba, Allah ya taimake shi babu kowa ta bayan hakan yasa cikin natsuwa ya nufi 'kofar dake kitchen wanda ita zata sada shi da ainahin 'dakunan dake cikin gidan. Koda yashiga ma wasu mata yagani a a palourn kuma ayanda ya lura duk ba'ki ne be wayi ko 'daya daga cikinsu ba dan haka sai yayi wucewarsa ciki ya nufi 6angaren dayayi niyyan zuwa. 👎🏻 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/2, 6:01 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _Treat your parents with loving care. You will only know their value when you see their empty chair._ 🅿 *50* Abu'de yasamu 'kofar dan haka kanshi tsaye ya tura kansa ciki ya shiga, sai de yana shiga ya tsaya daga bakin 'kofar dan ganin mutane biyu ne acikin 'dakin. Dubansa ya kai kan gado domin ya banbancewa idanunsa cikin su biyu amma tunkan tunaninsa yayi nisa yafara jiyo muryar wacce ke kwance akan agadon kunnan ta sa'kale da earpiece tana bin bakin wa'kar Umar m Shareef mai taken ( SAQAR ZUCI) ,hakan yasa yayi saurin fahimtar cewa wannan wata dabance bawacce yasani ba, 'dauke idanunsa yayi yah mayar wajen mirror inda ya hango wata kuma azaune amma kallo 'daya yai mata ya gane ko wacece ita, domin yasanta da san zama gaban dressing mirror, dan haka sai ya 'daga 'kafafunsa cikin nutsuwa ya isa gareta. Zaune take tayi zugum tun 'dazu tana kallon kanta acikin mirror 'din, sai de azahiri ba ganin kan nata take ba, tunani kawai takeyi da bata san inda ya dosa ba. Dukkan su basu lura dashi ba yanzun, dan ita wancen wayar datake sarrafawa ahannunta shiya dauke mata idanu yayin da ita kuma wannan hankalinta yatafi ga tunani, kuma ma a yadda ya shigo 'din ba lallai ne kasani ba koda kuwa kana daidai cikin hankalinka, ne dan tamkar wani marar gaskiya haka ya shigo ballantana su da kowa hankalinsa yana wani wuri ne daban. Da isar sa kusa da itan sai ya tsaya daga bayanta shima yana kallon fuskarta ta cikin madubin gani yayi ta yi kyau sosai fiye da ganinta dayayi na 'karshe, hakama ramarta ta 'dan zarta yanda ya ganta last week. Dubansa yakai ga hannayenta yaga yadda hannayen suka sha kyau cikin zanan flower baki da ja kamar kar su rabu da hannun nata sukasance haka har abada. " is it all because of th...............! " ohh no bahaka bane"! Ya fa'da tare da jijjiga kansa. Be da'de da tsayuwa awurin ba sai ta mi'ke tsaye sanadiyyan tuno maganar Ummah datayi akan ruwan wankan da aka ha'da mata tun 'dazun mai cike da ha'din kayan 'kamshi musamman aka ha'da saboda ita inda Ummahn tace mata karta kuskura ta bari ruwan ya huce batare da tayi wankan ba domin da 'duminsa akeso tayi wanka saboda zaifi kama jikinta yanda akeso idanta gama kuma me shiryata zata zo " tunowa da wannan maganar ne yasata ta mi'ke tsaye da 'dan sauri domin cika umarnin Ummahn. Amma mi'kewanta keda wuya sai ta hango mutun tsaye daga gefenta yana kallon ta, bata waiwaya baya ba sai kawai ta kalli fuskarsa ta cikin madubin tayi murmushi, jikinsa sanye yake cikin kaftan mint green 'dinkin ba 'karamin kar6ar sa yayi ba, rigar tsayinta be wuce gwiwarsa ba, hannun rigar 'daure da links, irin 'dinkin dayafi birgeta kenan acikin 'dinkun maza, yasanya hula wacce ta dace da kalan kayan jikin nasa. Hannu ta 'dago ta nufi madubin dashi daniyar ta'bashi zaton ta idanunta ne ke hasko mata shi domin taganshi ne exactly yanda tayi mafarki dashi adaren jiya, bayyananniyar murmushi tayi aranta tacigaba da fa'din " da wannan daurarriyar fuskar tashi daba ko yaushe ake ganin sakewarta ba sai lokacin da yaga dama sannan kaga murmushinsa sai inko yana tare da Daddy ne wannan kam har zaka gaji da ganin dariyar tasa alokacin" Daf da zata ta6a jikin madubin sai taji an ri'ko hannunta daga baya, hannun ta kalla inda aka ri'ke tan tabi hannun da kallo zaton ta ma Hannah ce sai kuma taga sa6anin hakan domin wannan hannun beyi kala koka'dan dana Hannah ba not even from her friends. A 'dan tsorace ta kuma juyawa takalli cikin madubin sai taga wanda ke bayan tan ne yah ri'ke mata hannun nata, sai alokacin tunaninta yadawo dai-dai sai ta juyo afirgice zuwa inda yake tsaye 'din, gani tayi shi'dinne azahiri ba mafarki ba kamar yadda tasaba ba kuma atunani ba. 'Dayan hannun ta 'dago ta rufe bakinta dashi ta zaro idanu kamar wacce tayi karya tace " _huh_! _Yayaah"!!!_ . Tafa'da ahankali bada bayyanan niyar sauti ba saboda bata manta irin tsawan daka mata ba ranar dayazo last kafin yau, shikuwa be amsa ba duk da yaji me tace saboda tun 'dazun tsayawa yayi yana kallonta sai ma 'kara binta da idanun dayake 'karayi yana wassafa abubuwa acikin ransa ciki harda irin kyan daya ga ta 'karayi, take sai yaji yana kishin duk wanda zai ganta a irin wannan yanayin. Teemah data ga be yimata magana ba kuma be motsa daga tsayuwarshi dayayi ba har yanzun sai tayi tunanin ko irin mafarkan data saba yine, hakan yasa ta 'danji haushi harda turo baki gaba tana 'ko'karin 'kwace hannunta daga nashi sai shi kuma ya 'ki sakinta. Teemah bata tsoron Yayanta na mafarki da tunaninta danshi be ta6a yi mata tsawa ba shiyasa bata wani jin shakkansa, ko yanzun ma dataga ya'ki sakin hannunta sai tace " ka sake min hannuna yayah ni baruwana da kai, kullum idan naganka baka min magana sai de kayi shiru, inaso ma in baka ha'kuri tun ranar da kayi fushi katafi amma bansan yanda zanyi ba, saboda kullum kinmin magana kakeyi idan naganka" Rausayar da kai tayi gefe sai taci gaba da magana " kuma fah ba laifina bane dana 'ki gaya maka, ni bansan me zance bane alokacin koda nace zan fa'da 'din shiyasa ban 'kiraka ba". Sake juyowa tayi ta kalle shi da sanyin murya tace " ka ha'kura yanzu yayaah? Lumshe idanu kawai yayi ya kuma bu'desu akanta duk tana gani, sai de ita hakan be gamsheta ba sosai tagaji da irin hakan daya keyi ita so take ya bu'di baki yayi mata magana kamar yadda suka saba. Data ga bashi da niyyan yin magana sai tace " sake min hannu na toh, Ummah fa'da zata min in tazo taga banyi wankan ba har yanzu " Idanunta akan hannayen nasu tayi maganar. " me yasa? Haka kawai Abbas yace shima yana kallon hannayen nasu inda idanun Teemah yake. " Baka gani ne? yaufa za'a 'daura auren yah Mahmud wai....wai.... danii. Ta'kara fa'da da jan maganar tare da sunkuyae da idanunta zuwa kasa. Duk da tana zaton wannan ma Yah Abbas 'din mafarkin ta ne amma haka kawai take jin nauyin sanar dashi maganar aurenta kai tsaye. Tun ranar daya tafin nan kusan kullum sai tayi mafarkinsa ha kama tunaninsa yasako ta agaba kuma ko amafarkin ma ba magana yake mata ba, wani lokaci sai de tayi ta masa magana shi ya 'ki bu'dan baki yayi magana wani lokaci kuma sai tace tayi fushi itama sai tayi shiru suta kallon juna amafarkin. Abbas da kansa ya gane cewa har nzu bata yadda shi 'din bane dakansa, domin yadda take yadda take yi masa magana ma ka'dai shaida ne. Ga mamakinta sai taji ya mintsine ta ahannun daya ri'ke 'din hakan kuwa yasa ta ta 'dago da sauri ta kalleshi suka hada idanu, rintse idanun tayi da 'karfi ta kuma bu'dewa a 'ko'karinta naganin ta tashi daga baccin da takeyi 'din, amma ko da ta bu'de 'din ma sai ta sake cin karo da fuskarsa agabanta still yana kallonta, baki ta bu'de da niyar yin magana sai ya ja hannun nata da sauri ya janyo ta zuwa jikinsa, ha'da bayanta da jikinsa yayi sai ya juya ga dressing mirror 'din, sai ya zamana dukkansu suna fuskantar madubin, kwantar da kansa yayi agefen kafa'darta yace _"_ _oyah tell me now"!_ Shiru tayi bata yi masa magana ba illah kallonsa data cigaba da yi sai shine yasake fa'din _" bani ha'kurin yanzu inaji"!_ _Comment_ 🖊 _Vote_ *⃣ and _Share_ 🤞🏻 pls _My fellow_ _wattpadians jinjinar_ _bangirma I heart u all._ *Salmern ku ce*😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* A moment of patience in a moment of anger saves a thousand moments of regret. 🅿 *51* 'Kasa Teemah ta maida idanunta batare data yi niyyan yi masa magana ba dan rawar da jikinta keyi ma ka'dai ya isheta ba sai ta 'kara da wata damuwar ba sanadiyyar ganowa datayi cewa Abbas din zahiriyya ne ba mafarki ba, bugu da 'kari ma ita babu wanda ya ta6a ha'da jikinta dashi tunda take hatta da Abbas da Mahmud ada iya kacinta dasu surutu ne na fatar baki, amma sai taga Yah Abbas 'din yau kamar bashi ba tsoro ta keji sosai dan batasan yau kuma da wacce kalar masifar yazo ba, 'kila yau kan zaneta zaiyi tunda ranar ma bata yi magana bama ya daka mata uban tsawa ballantana yau da tayi masa dogon surutu. Agogon hannunsa ya kalla sai yaga lokaci ya 'danja dan haka sai ya raba jikinsa da nata, hannu yasa a aljihu ya ciro wani 'karamin case ya bu'de hannunta ya sanya mata shi ahannun ya kuma rufewa. Sai ya saketa ya juya da sauri ya nufi 'kofah taku 'daya ana biyu sai ya dakata cak ya tsaya amma be juyo ba yana kallon 'kofan yace " _ina miki fatan alkhairi arayuwar auren ki Fateemah"._ Be sake juyowa ya kalleta ba kawai ya sa kai ya fita daga 'dakin ita kuwa tsaye tayi kawai ta bishi da idanu har ya 6acewa ganin ta, kawarta da ke kwance agadon da tun 'dazu ta ke kallon ikon Allah sai ta taso da saurinta ta iso wurin Fatiman," _Fateema wai meke faruwane waye wannan 'din,? shine mijin naki ,? shi zaki aura ?"_ Ta jero mata tambayoyin 'daya bayan 'daya da buri, samun amsarsu daga bakin Teemah. Yayin da ko kallon kirki bata samu daga Teemahn ba ta dai ka'da mata kai alamar kawai alamar _"a'a"._ Kwafah yarinyar tayi yarinyar sannan ta sake fa'din _"meaning"_!!! Shiru Teemah tayi kamar ma bada ita yarinyar keyi ba. Data ga haka itakuwa sai kamo kafa'dar Teemahn da nufin dawo da attention 'din Fateeman zuwa gareta. Teemah dan haushi sai ta dallah mata harara take takuma juya kanta da nufin _kin_ _dameni_ sai taci gaba da kallon 'kofar da ya fita 'din ji take tamkar zata ganshi yasake dawowa. Yarinyar bata damu ba sai ma wasu tambayoyin data sake bin Teemahn da shi. " toh wanene shi naji yana cewa fatan alkhairi ko minene dai namanta, dan Allah ki fa'da min waye shi ? Tafa'da tare da dawowa ta fuskanci Teemah dan ita harga Allah bata san shi ba bata ta6a ganinsa bama ' kawar Fatima ce da suka ha'du lokacin sunje yin wani programme a (Y C A) Yobe Childrens Academy, bata ma san ina yarinyar tasamu labarin bikin ba shine harta wani zo da sassafe ita adole me 'kawa, dan ita Teemah bata gayyaci kowa ba, 'kawayenta na makarantar su ma duk zuwan kansu ne Teemah 'kin yin gayya tayi wai bata son damuwa, mummy tayi-tayi da ita harta gaji gaskiya ba laifi Teemah akwai taurin kai, akan hakan Mummy takan ce mata " mutum fah rahama ne Teemah ko su ka'dan ne ki daure ki kai musu invitation card 'din ai zasuji da'di" Teemah azuciyarta cewa take " sun da'de basuji da'din bai ndai har se naje na gayya toh su ne" dolen mummy ta ha'kura ta 'kyaleta kawai akan ra'ayinta, dama ita Mummyn so takeyi Teemah tasamu masu 'debe mata kewa amma tunda ta'ki sai mummyn ta kyaleta. Haka duk wacce taji labari inta yi ra'ayi sai tazo wacce kuwa taga bazata iya ba sai tayi zamanta. Kafin Teemah tayi magana sai ga Ummah tashigo bayan ta da wasu mata guda biyu mummy kuma na bayansu hannunta ri'ke da kaya da wata jaka. _" kin yi wankan?"_ Abinda Ummah ta fara tambaya kenan data shigo, Teemah sai ta maida idanunta 'kasa dan bata san me zata ce da Ummahn ba ahalin yanzun bayan duk kashedin da ta mata akan ruwan wankan kafin tabar 'dakin 'dazu. Ganin hakan sai Ummah ta fahimci cewa bata samu tayi wankan ba kenan. Hannunta Ummah takawo danta ganta wata iri ma duk ta canja, mummy dake gefe dasu ne ta sake jefo wata tambayar kamar yanda Ummah tayi. 'Kawar Teemahn ce tace " a'a yanzu dama zatayi" Ran mummy 6aci yayi da jin furucin 'kawar Teemahn abin ya bata haushi sai da akace tayi wankan dawuri amma tsabar iskanci ta'kiyi suka tsaya shirme bayan uban ha'din da aka yiwa ruwan mai shegen tsada dan kawai a ga tafita daban. Mummy cewa tayi " tsayuwar me kukeyi toh anan 'din da har yasa ta'kiyin wankan dawuri"Mummy ranta a6ace tayi maganar dan ba 'karamin 'kuluwa tayi ba. 'Kawar Teemahn ce ta bu'di baki zata fara bayani sai Teemah ta 'dago hannunta da sauri ta sau'ke shi akan na Ummah, dukkan su akan idanunsu hakan ya faru dan Teemahn na tsakiyan su ne, dan haka sai yarinyar ta dakata da maganar da tayi niyyan yi 'din dukkansu suka zuba ido dan ganin ko menene manufar hakan da Teemahn tayi. Ummah 'dago hannunta tayi tana jujjuya abin ahannunta, sai take tambayar Teemahn wai " menene wannan 'din kuma ?. Mummy kuma tace " a ina kika samu? dan tuni kwakwalwarta ta canja daga haushi da masifar da ya turni'keta zuwa tambaya tun lokacin da Teemah ta dan'kawa Ummah abin ahannunta. Teemah a hankali ta basu amsa da fa'din. _" Yah Abbas "_ !! " wani Abbas 'din'? Ummah da Mummy suka ha'da baki wahen fa'din haka. _"Yaayah Abbas "_ Tasake maimata musu. Tsaki Mummy tayi dan zuwa yanzun ba'karamin haushi ne ya'kara kamata ba, haushin rashin cikakken bayani daga bakin Teemah. "Tun yaushe yabaki "?mummy tasake tambayarta. _" yanzu"._ "YANZU kuma!! ? Ummah da mummy suka ha'da baki wajen tambaya da mamaki, kai Teemah ta jinjina musu alamar tabbatar wa. Mummy bakin gado tatafi ta zauna ta dafe goshi tare da fa'din " _na shiga uku_ .!!! Ummah tana bu'de case 'din take fa'din " shi da akace bashi da lokacin zuwa ashe kuma zai taho shine harda 'karyar aiki sun masa yawa"? tana murmushi tayi maganar. Yayinda mummy take tunanin yaushe toh har ya zo gidan batare data sani ba. _" WOW!!", "DIAMOND"_!!! Mummy taji yo muryar Ummah na fa'din haka, sai kawai tayi tagumi, sosai take tausayin 'yartata ita, bata ta6a jin 'kin son Abbas ba ko ka'dan arayuwarta amma wannan karan jitayi dama ace be zo ba dan tasan hankalin Teemah zai zama wani irine bayan tasamu ta nutsu ta daina damuwa wata'kila yanzu kuwa sai yanda Allah yayi duk dama tasan Teemahn tana tafiya damuwar ne batare da tasan damuwar tata ba, amma idan ta fiya ha'duwa da Abbas ba mamaki ta iya gano meke damunta shi yasa take tsoron yawan ha'duwarsu dashi, bata son abubuwa suyi wa Teemahn yawa tun tana 'yan 'kananun shekarunta. Da zata iya data mantar da Teemahn nata kowa da komai dan kawai taga ta zauna ta rungumi auran ta hannu biyu tayi facing reality, wata 'kila in hakan yafaru damuwarta zata kasance 'yar ka'dan inyaso sai ta ci gaba da binta da addu'ah Allah ya ha'de kansu da mijinta da kuma Anty yasa Antyn ta 'kaunaci 'yarta 'kauna mafi girma, amma bata da wannan damar sai de ta ha'da dukka tata ro'ka mata ubangiji ya 'kara sassauta mata kamar yanda ya hanata fahimtar takamman abinda zuciyarta ke ciki, bata san me yasa Abbas yake yiwa Teeman haka ba, bata sani ba ko shi'din yariga yagane Teemahn na son shine!!........kai Allah ya kiyaye sam bata fatan hakan ma ya kasance". Kallon Teemahn tayi taga yadda takoma lokaci guda duk da dama yau 'din bata tashi da walwala sosai ba amma gara yanayinta na 'dazu fiye da na yanzun, Ummah ma da ta lura da ita sai tace " hala yau 'din ma sai da kukayi fa'dan kafin yatafi ko dan naganki duk wata iri haka ?....! Dai dai shigowan su Hannah da suka dawo daga kasuwa yanzun, da sallamar su suka shigo Hannah nashigowa ta tsaya turus tace " ya haka kuma dan Allah? wai har yanzu amarya bata shirya ba Ummah meyasa?...... kai !kai !!kai !!! Ummah nawaye wannan gaskiya ya ha'du ta kar6a tana 'ko'karin gwadasu ahannunta ta saka bangles tacire tana 'ko'karin gwada zoben ne tace "dan Allah Ummah nawaye ne? Cikin zumu'di take maganar as if ance mata nata ne. " na amarya ne Yayanta ya kawo mata"? Ummah na murmushi ta bawa Hannah amsar tambayar ta. Sai Hannah tace "wani Yayan kuma Ummah........ kar dai Yah Abbas?" "Shi dai" inji Ummah atakaice. " kut....lalle ma Yayan nan, toh ni ina nawa ?" " kanta Ummah ta dungure tare da fa'din 'kaniyarki. Hannah ance miki na amarya ne toh ke 'din amaryace "? " Ummah toh ainima zanyi kwalliyar naga" "Ki jirashi toh inkin ganshi kwa gama dramar dashi ni kan ki barni na sha iska......... " Yaushe ma yazone Ummah ba ance bazai samu damar m zuwa ba"? " nima jinayi ance yazo amma banganshi ba",.... kinga 'kyaleni in shirya 'yata lokaci nata tafiya har yanzu bata yi dressing ba" Ummah tayi maganar tare da nufar hanyar bayin dake vikin 'dakin Teemah.........tace " Biba yanzu kam sai kin 'kara ha'da mana wani ruwan ko dan inaga wannan yagana yin sanyi." Da " toh" Biban ta amsa tare da ajiye mayafinta itama ta nufi bayin domin ha'da ruwan wankan. Hannah kuwa gurin Mummy ta nufah da set 'din 'dan kunnan tace. " Mummy kinga Yah Abbas abinda yayi ko....... " tunkan ta 'karasa Mummy tace rabu dashi zai zo har gida yasame ni, sai naji dalilin dayasa ya ware ki be siyo miki naki ba ke ma". Daga mummy ta juya gurin Teemah tana kallon ta tace " maza ki hanzarta ki yi shirin wankan toh gashi za'a ha'da wani ruwan. "Gaskiya kam kiyi dawuri danni har na matsu inga anyi angama shirya amarya naga irin kyan da zakiyi da wannan abubuwan". Hannah tayi magaban tasigar zolaya. ***** Babban limamin masallacin Yobe mosque and islamic centre da ke cikin garin damaturu aka gayyato domin 'daurin auren Teemah, guri yacika ma'kil da jama'ah na nesa dana kusa, su daddy suna daga gaba gaba kusa da Limamin, duk hankalinsu yatafi ga sauraron Hu'dubar da akeyi na 'daurin auren yayin da Mahmud ya sunkuyar da kansa 'kasa sam yakasa jin farin ciki da wannan auren yakasa amincewa zuciyarsa kasantuwar Teemah a'kar'kashin ikon sa,yana ji kamar bazai iya ri'keta ba, jiyake kamar nauyin da zau kannashi yafi 'jarfin sa sosai, kamar ya bu'di baki yace adakata da 'daurin auren a 'daura da waninsa, wanda zai iya ri'ke masa amanar Fatima da hannu biyu amma bazai iya ba,bazai iya furta hakan ba gani yake idan yayi hakan tamkar yayi wa mahaifinsa butulci ne da kuma tozarci musamman idan yayi duba da yanda dubban al'ummah suka bar ayyukan dake gabansu suka taho dan kawai su shaida 'daurin auren sai yaji kawai ya saduda ya barwa Allah kawai, fatan shi de Allah ya zama gatansa yaba shi ikon kulawa da amanar dazata hau kansa, Allah yabashi ikon yin ri'ko da ita da gaskiya. Daddyn Abuja ne da kansa ya kar6i wakilcin Fateema saboda rashin zuwan Abbas 'din. Daf da za'a 'daura auren Mahmud yaji mutun ya zauna daga gefensa na hagu da farko ya share dan sanin yawan mutanen dake zaune agurin wata 'kila saboda yawansu ne yasa dole sai sun ha'da jiki, amma sai yaji zuciyar sa takasa ha'kura da sharewan dayake so yayi 'din 'dagowa yayi ya kalli gefen nasa sai kuwa yaga Abbas zaune akusa dashi yana kallonsa. Take yaji wani sanyi azuciyarsa kasancewar Abbas 'din awurin sai yaji wani sabon 'karfin gwiwa ya shige shi, murmushi yayiwa Abbas 'din tare da bashi hannu shima Abbas sai ya mayar masa da martani daga nan sai suka maida hankalinsu wurin da ake hu'dubar. 11:50am awannan ranar dubban jama'a suka shaida 'daurin auren FATEEMAH ZAHRA KABIR da Angonta..................!!!!!🤞🏻 *Keep following me*👌🏻 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmern ku ce* 😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs _ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _People_ *change* , _love *hurts* , friends *leave* , things *go wrong* but just remember that life still_ *goes* *on* . 🅿 *52* ..............,Abbas lumshe idanu yayi jiyayi da 'ace shi ka'dai ne awurin da babu abinda zai hana hawayen shi zuba a dai-dai wannan lokacin amma yanzu kam daya kasance acikin mutane, mutanen da bazai ta6a iya sanin yawan su ba sai kawai yace _" Allah_ _kaine gatana, Allah_ _ka ji6anci_ _lamura na"_. 'Daurin auren ba 'karamin al'ummar annabi ya tara ba kama daga kan manyan 'yan kasuwa da manyan 'kusoshin gwamnati da sauran jama'ar musulmai baki 'daya. Mahmud da kansa sai da yaji fa'duwar gaba, zuciyarsa tsinkewa tayi da 'karfin gaske _innalillahi wa innah_ _ilaihirraji'un_ dukkansu suke faman ambata azu'katan su. Abbas ne ya daure ya 'ka'kalo murmushi na dole ya azawa fuskarsa sannan ya ciri hannunsa ya mi'ka wa Mahmud suka yi musabiha " _Inai muku fatan Alkhairi 'dan uwa, Allah ubangiji ya baka ikon yin ri'ko da gaskiya da amana ya sanya fahimtar juna a tsakaninku"_ Shima Mahmud murmushin ya 'ka'kalo yayi wanda ta tsaya masa a iya saman la66ansa ko ka'dan ba wannan bane azuciyarsa amma dan kawai ya nuna wa Abbas 'din yabawa da godiyarsa sai ya 'kir'kiri murshima shima sai yace " _Ameen-Ameen Yayan mu godiya marar iyaka"._ Kasa sake hannun Abbas 'din yayi suka tsaya ahakan, Abbas gefe ya maida idanunsa yana jinjina al'amarin ubangiji acikin ransa, in just a month gashi an raba shi da farin cikinsa, wannan aikin kam sai de a'kira da _'kaddara_ saboda shi koda wasa be ta6a tunanin faruwar hakan ba yariga ya barwa zuciyarsa cewa Teemah tashi ce shi yasa be ta6a damuwa ya kauda irin hakan ba, sai gashi rana tsaka ta inda bai ta6a zata ba, aka datse masa mafarkinsa batare da kai ga idda shi ba, sai gashi Teemah ta barshi, bari kuma na har abada. Tunda suka gama maganganun su kowa sai murmushinsa ya kau. Abbas na so ya cire hannunsa daga cikin na Mahmud amma sai Mahmud ya sakin masa hannun, dole tasa ya dawo da kallonsa ga Mahmud 'din gaba 'daya. Idanun Mahmud na cikin na Abbas 'din yace _" Abbas_ _nagode, nagode_ _sosai da irin 'kokarin 'da kai ta faman yi akaina dan ganin na cika BURIN mahaifina_ , _nasani cewa mai sonka shine wanda akullum yake 'ko'karin ganin baka_ _kauce hanya_ _ba, wannan itake tabbatar da son gaskiya da aminci!, Abbas yau gashi BURIN_ _ABBAH NA yacika, amma ni na kasa jin farin ciki azuciyata, inajin tamkar bazan iya ba, inajin tamkar_ _wani gagarumin nawi ne ya hau kaina, Abbas taya kake ganin zan_ _iya ri'ke wannan babbar amanar bayan ban shirya amsar ta ba?"_ Abbas 'din sai yace mishi _" Daure wa zakayi Mahmud, nasani cewa nauyi ne, nauyi ne ya hau kanka Mahmud sai de ba irin wanda kai kake zato ba, kai dai kawai ka mi'kawa Allah komai nasan zai maka jagora"_ Ahankali ya janye hannunsa daga cikin na Mahmud da ya tsaya shiru kamar me tunani dafa kafa'darsa Abbas yayi sai ya 'dago ya kalli Abbas 'din Abbas sai ya daga girarsa sama batare da yayi magana ba, ya kuma 'dan juya jajayen idanunsa yayi wa Mahmud nuni ga mutanen dake gurin. Atare suka mi'ke tsaye ganin yanda guri ya har'de da jama'ah ana faman gaisuwa yayin da dayawa daga cikin mutanen ma tuni sun kama gabansu zuwa gidajensu da masana'antun su saboda an riga an kammala komai, aure yariga ya 'dauru. Kamar jira ake su mi'ke kuwa sai aka fara mi'ko wa ango gaisuwa da fatan zaman lafiya mai 'dorewa. Yanda Abbas yasaki ransa yake amsa gaisuwa agurin har inbaka sani ba zakayi zaton ko shine ma angon domin azahiri annurin da ke kan fuskarsa ta nunka ta Mahmud 'din banbancin kawai shine kasantuwar Mahmud 'din a matsayin ango ya riga ya bayyana domin shike sanye da fararan kaya harma da babbar riga, Abbas kuwa be sa babbar riga ba shi kam. Dukkansu suka ha'du suke amsa gaisuwar da duk aka mi'ko musu sai de kowa abinda ke ransa daban, kowa damuwar shi kala dabance, da haka har suka isa wurin da su daddy ke tsaye da sauran abokan Mahmud 'din dake tare dashi suna binsu abaya, suma su daddy sai faman gaisuwa suke yi da jama'ah suna kuma mi'ka 'dumbin godiyarsu marar iyaka. Daddyn Abuja ne yafara ganin tahowarsu take sai ya fa'da'da fara'arsa fiye da ta baya. Hararan Abbas yayi yana murmushi irin ka shammace mu 'din nan sa'annan ya mi'kawa Mahmud hannu da sauri, Mahmud sai da ya 'dan rissina tare da 'ka'kalo murmushi ya ya6awa fuskarsa kafin ya mi'kawa Daddyn hannun nasa suka gaisa Daddy nata yi masa addu'ah da sanya alkhairi cikin zolaya ya'kara da fa'din _" saura abokin ka ko Mahmud tunda kai 'din ansamu kayi da 'kyar saura kuma shi dan na_ _lura ra'ayoyin kusan_ _iri 'dayace "._ Murmushi kawai Mahmud yayi tare da sosa 'keyarsa yana wani sukuyar da kai. Abbas kuwa gurin Abbah ya nufa ya fara gaidashi sannan yadawo kan Daddy babbah ( daddyn Teemah). Daddy bai amsa gaisuwar da Abbas ya mi'ka masa ba sai ya mi'ka masa hannu kamar zasu gaisa sai kawai ya zarce da hannun ya kamo kunnan Abbas dashi yaja " _Awshhhh daddy_ _zafi"_ Sake ja daddy yayi sai kuma ya sake atake yana murmushi. Abbas yasan dalilin yimasa hakan da daddy yayi ba zai wuche baki biyun dayayi bane akan zuwan shi shiyasa daddy yake purnishing 'dinsa da haka dan haka sai yace da daddyn " _ango nake fah yau 'din daddy"_ Dariya suka sanya dukkansu dake wurin inka 'dauke Mahmud da 'yar murmusawa kawai yayi sai shi Abbas 'din da haryanzu hannunsa ke kan kunnansa yana shafawa su ka'dai ne basuyi dariyarba. Sai da suka gama dariyar sannan daddy ya juyo da kallonsa gurin Mahmud suka sake gaisuwa akaro na biyu shima daddy yasa masa albarka a auren nasa. Daddy gurin Abbas ya juyo ya kamo hannunsa suka fara tafiya ahankali kamar masu yin wata shawara sai daddy yace masa " _ya akayi kuma na ganka bayan kace babu dama?_ " _Da 'kyar na taho daddy sai da nayi roko tare da cancelling wata tafiya da zamuyi tun aji yan kafin nasamu dama"_ _" amma ba wata matsala_ _ko ?_ Daddyn ya sake tambayarshi Da _" insha Allah babu komai Daddy"_ Abbas ya amsa mishi tare da fa'din anjima ka'dan ma zan koma. _"Toh Allah ya tsare ya bada_ _sa'a_ " daddyn yafa'da dai dai isowarsu su daddyn inda suke. Sallama Abbas yafara yi musu dan afa'darsa cewa yayi zai koma dama wai 'daurin auren ne ya kawo shi. Abbah ne yace da Abbas 'din wai ko dan bikin ba da'di ne shiyasa zai tafin ,Abbah yace abokin ka ne yace ba zaiyi kowani event ba da 'kyar ya yadda mahaifiyarsa ta shirya yin dinner inajin shi ka'dai za'ayi " Sai da Abbas ya juya ya kalli Mahmud sai ya dawo da kallonsa gurin Abbahn kafin yace _" ai mu Abbah_ _albarkar auren kawai muke bu'kata"_ Abbahn ma cewa yayi _"Hakane, hakan ma yayi Allah ubangiji ya sanya alkhairi ya albarkace ku gaba 'daya"_ _"Ameen Ameen_ _Abbah"_ Abbas ya amsa masa dashi. ***** Yanda aka tsara wa Teemah kwalliya ba 'karamin fito da ita yayi ba, tayi kyau cikin wani code-less 'din ta blue-green mai kyan gaske da ratsin golden ajiki,'dinkin dai dai jikinta akayi shi, Head, net, bridal shoe and purse 'dinta ma duk golden colour ne sai wani set 'din 'dan kunnan ta na gold da daddy ya sai mata kwanaki, ba'karamin kyau tayi ba, light make-up akayi mata daya 'kara fito da asalin kyaunta afili. 'Kawayenta nata rawar kai amma ita banda ita, ko ajikinta kamar ma ba bikinta akeyi ba, photuna suka yita 'dauka da 'kawayen nata har sai taji tagaji, da ta ga kamar sun dame ta sai ta ce da Hannah su tafi 'dakin Mummy hayaniyar ta isheta haka. 'Dakin mummyn suka tafi suka yi zaman su acan suka bar 'kawayen nasu. Teemah cewa tayi " _wallahi ba dan ina tsoron masifar mummy ba da cire kayan nan zanyi Allah insha iska, duk sun bi sun_ _dameni"._ _" ke kika sani ni dai baruwana idan ta kamaki dan kina cire kayan tafiya zanyi inbarki kinga_ _bata ganni tare da ke bama balle abin ya shafe ni"_ Tsaki Teemahn tayi kawai ta cire takalman dake 'kafarta tana wani yatsina fuska duk da haka sai data 'daga net 'din da aka rufe mata kai dashi zuwa sama. Hannah tace yauwa bari na 'dauke ki a pic. Su mummy da Ummah nacan hararabar gidan ta baya inda ake shirya abinci suna ta 'ko'karin ganin komai ya kammala saboda ba'kin daddy da suka zo kuma an riga an gama 'daurin aure shiyasa suke ta hanzari dan suga sun ha'da musu abinda zasu bu'kata. Lokacin da Abbas ya shigo domin ya gaisa da su Mummyn ya kuma yi musu sallama dan daga nan wucewa yake so yayi be gansu ba shikuma ba son ratsa cikin taron matan nan yake ba takaici yake ji idan ya gansu ayanzu bashi da burin daya wuce yaga ya bar garin Damaturu, yana ganin zai fi jin sassauci. Koda yashigo bai gansu mummyn ba sai ya ciri wayarsa ya 'kira layinta sai kuma bata 'dauka ba, haka ma na Ummahn sa itama bata 'daga ba. Hakan yasa da ya shigo kawai sai ya wuche 'dakin Mummyn direct dan zatan shi acan suke tunda bai gansu a babban palourn ba. Da sallamar sa ya shiga 'dakin Hannah ce kawai ta amsa sallamar yayin da Teemah taji ta wata mummnar fa'duwar gaba ta zubawa 'kofar idanu har ya shigo, shima yana shigowa idanunsa akanta ya fara sau'ka. Kallon kallo suka tsaya yi wa junansu, Abbas kyan da Teemahn tayi ne ya tafi da imanisa sai yaji wani 'daci azuciyarsa na takaicin dakilin kwalliyar tata. Tunowa da yayi cewa yanzu fah Fateema matar mutun ce bashi da damar yi mata irin wannan kallon, take sai ya kauda kansa gefe tare da yin istigfari acikin ransa. Dubansa ya mayar gun Hannah data tsaya tana 'kare musu kallo da mamaki inda ta kasa tsaida idanunta kan mutun 'aya sai juya idanunta take idan ta kalli wannan sai ta dawo ta kalli wannan. _"Hannah ina Ummah na 'kira layinta bata 'daga ba?"_ Cikin sanyi yai maganar. 'Ko'karin fita daga 'dakin Hannah take yi tare da fa'din " _bari_ _indubo ta"_ Dakatar da jta yayi da fa'din _" a'a '_ _kyaleta ki sanar da ita na wuche kawai "_ _"Bata yi nisa bafa Yayah kuma ma dama tana so ta ganka injita"._ _"Toh sauri ki dabata karki 6ata lokaci "_ Inji Abbas 'din tare nufar wajen window ya tsaya yana kallon waje. Teemah ma bayansa ta kalla ahankali ta tashi tare da saka takalmanta ta bar masa 'dakin dan bata san me zata ce dashi ba, wani lokaci sai ta ji tarasa 'kwarin gwiwar da har zata iya yimasa magana , ballantana yanzu da taganshi duk yayi sanyi sai taji ya cika mata idanu bazata iya ce da shi komai ba shiyasa ta yanke shawarar barin 'dakin. Sallama yayi da su bayan Teemah ta'kira Mummyn saboda Ummah abubuwan dake gabanta dayawa, dama Hannah tace ya tsayan ne saboda ta tunawa Ummah fa'da mishi batun sar'kar ta data ke so ya siyan mata itama sai kuma Ummah bata samu daman zuwa sai dai Mummy duk da haka sai da ta tuna wa Mummyn. Murmushi mummy tayi sannan tace. _" ki bari bayanzu ba bayan kwana biyu idan ya koma da kaina zan sanar dashi kin ga lokacin_ _taro duk ya 'kare kowa hankalinsa ya dawo jikinsa zai fi_ _fahimta amma yanzu kinga al'amuran jama'ah_ _ko"_ . _"Hakane mummy amma pls karki manta fah"_ " _Bazan manta ba insha Allahu"_ Duka akan tafiya sukayi wannan maganar daga nan suka yi shiru suka 'karasa 'dakin mummyn inda Abbas yake, Ummah ma ana tasame su bayan tagama abinda ke gabanta. Abbas yau ko hanyar maiduguri be kalla bakawai ya shiga Tasha ya hau motar Kaduna dan takaici bai ko tsaya ya wuni agidan ba. Ana idar da sallar azahar alace za'a tafi da amarya saboda yanayin nisa n da gurin ke da shi. Tun lokacin da Teemah taji labarin tafiyar tafara kuka, hatta sabo shirin da ake sake yimata ma acikin kuka aka yishi har aka gama sai de ba'ayi mata make-up ba saboda hawayenta ya'ki tsayawa. Daddy da kansaya ratso cikin matan yazo har 'dakin Mummy yakama hannunta izuwa sashen sa. Shi kanshi dadyn dauriya kawai yakeyi amma zuciyarsa ba da'di sam sai dai bazai iya barin hakan ya baiyana afili ba dan baya son Fateemah taga kasawarshi koka'dan, dan haka sai ya zaunar da ita agefensa akan kujera ganin su Daddyn Abuja na 'dakin sai ta zamo ta dawo 'kasa ta zauna tana maici gaba da kukanta. Mahmud ne yasgigo shima da sallamarshi dan Abbah ne ya'kira shi awaya yace yazo nan'din yanzun nan shiyasa ya taho. Dukkansu aka ha'da si aka yi musu fa'da sosai akan rayuwa Abbah ne yafara nasa akan kyautata mu'amala sai Daddyn Abuja yayi nasa akan tsoron Allah da bin dokokin sa azaman takewarsu, Daddy ne yayi daga 'karshe inda yaja hankalinsu akan ha'kuri da kaiwa zuciya nesa, Sosai nasihohin nasu suka ratsa su Teemah sai kuka takeyi harda shashshe'ka. Dasuka gama ne Abbah, Daddyn Abuja harma da Mahmud 'din suka tafi suka bar 'dakin domin zuwa fara arranging yadda tafiya da amaryan zai kasance aka bar Daddy da Fateemansa ka'dai. Dawowa tayi da kanta akan cinyar Daddyn ta kwantar dashi tana mai cigaba da kukanta. Daddy sai ya fara bubbuga mata kai 'din ahankali alamar rarrashi tare da fa'din _" Haba_ _Daddy's Angel stop crying mana"!_ Cikin kukan tace _"Dad...dy ni bana son in....tafi inbarku, bana son......auren Da...ddy "_ " _Kiyi ha'kuri Fateema!, aure dole ne zakiyishi, ko bakiyi yanzu ba dole watarana sai kinyishi ko dan cika sunnar ma'aiki sallallahu alaihi wa sallam (S.A.W), balle ma yanzu ke da kike tare da yayanki Mahmud, ga Antyn ki, ga Abbahn ki ma duk akusa dake, ai can 'dinma kamar gidane, karki damu kinji"_ Cikin shagwa6a tace _" a' a ni Daddy nan nakeso"_ _"Toh shikenan kiyi shiru, zanje kwanan nan inkun tafi sai dai bazan gaya miki ranar ba, zanje amma idan naga kina kuka da rashin ji kullum toh bazan dawo dake gida ba, idan kuwa bakyayin ko 'daya daga ciki kika kwantar da hankalinki kika zauna da mijinki lafiya kika yi masa biyayya toh zan 'dauko ki in kawo ki gida kiga mummyn_ _ki kinji"._ Da kai ta amsa masa alamar taji. Sai yace _" yauwa_ _my Angel share hawayen ki toh karki sake yin kuka"_ Share hawayen ta tayi harama da murmushi sai Daddy ya'kira mummy awaya yace zuso su tafi da ita. Suma su mummy nasiha suka mata sosai sai dai Mummy kasa ri'ke nata hawayen tayi daga 'karshe ma kasa magana tayi dan yanda kuka yaci 'karfin ta. Kusan duk wa'danda suke wurin sai da suka share hawaye dan ganin yanda Mummyn ke kuka. Baranma Teemah data ji mahaifiyarta na kuka ai shikenan, da sauri tatafi jikin mummyn ta rungumeta tace " _Mummy ni bana so intafi inbarki.......mummy tunda ba...kyaso nima ba zanje ba"_ Kuka take tana maganar yayainda tausayinta ke 'kara cika zuciyar mummyn kamar tace Teemah bazata ko'ina ba, kamar tace babu inda yarta zata, karo na farko kenan da Teemahn zatayi doguwar tafiya batare da ita ba , she can't bear the pain, bazata iya jurewa ba , tayaya bazata tausayawa yarinyar da tsawon rayuwarta bata yishi batare da iyayenta ba,dai dai da rana daya bata ta6a kwana a inda ba mahaifiyarta ba sai gashi kwatsam zata tafi inda zai dauke ta tsawon lokaci kafin sugana. Kai Mummy ta dagata sama tace _" Allahu ga amanar ka nan Allah ka kula min da ita ka kareta daga sharrin masu sharri ka kareta daga dukkan abin kii!"_ Dai-dai nan Daddy ya shigo da niyyar sanar da su cewa angama komai lokacin tafiya tayi, sallamarsa ma bai 'karasheta ba ganin irin abinda ke faruwa a'dakin. Cikin tsawa yace " _menene kuma haka Khadija_? _Yazakisa yarinya agaba kina aikin kuka inabaso kike ki karya mata gwiwa ba ?"_ Bai jira ji, cewar kowa ba ya 'karaso yaja hannun Teemahn yatada ita tsaye, _" tashi_ _mamana kyalesu ba mun gama magana ni da ke ba, meyasa zaki zo nana kuma_ _kina_ _kuka ?_ _"Daddy kuka_ _mummy takeyi_" Baiyi magana ba kawai yaja hannunta suka bara 'dakin daf da 'kofa yatsaya yace _" mai_ _niyyan tafiya ta fito motoci na ready"_ Yayi maganar batare da ya juyo ya kalle su ba yana gama fa'da kuwa yasa kai yafice hannunsa ri'ke dana Teemahn. Da kansa yahe yasanta amota,Ummah ne tazauna agefenta 'daya yayinda wata 'kanwarsu daddy da suke cousins tazauna 'daya gefen, Hannu da waus 'kawayen Teemahn su biyu suka zauna awata motar daban . Mummy ko gurin tafitar ba ta fito ba ita kam tana ciki kawai tana jimamin rabuwa da 'yartata tana so ta tashi ta ko leke su ta window ma takasa ji tayi ga6o6in ta duk sun mata nauyi aranta sai take jin tamkar ta rabu da Teemahn nata ne rabuwa ta har abada, tana jin dirin tashin motocin kawai sai ta rintse idanun ta. Basu tsaya ko'ina ba sai a Airport na Maiduguri inda daga nan suka hau jirgi sai garin ikko (LAGOS). ***** Zaune acikin mota shiru ko wanda ke gefensa be kalla ba tunda ya shiga motar tunani ya sako shi agaba, tunanin yadda kunnan sa suka jiyo masa 'daurin aure tsakanin " MAHMUD YUSUF MUH'D da Fateemah, yanaji yana gani aka 'daure sunan Fateema da waninsa, bashi ba. Har suka isa kaduna babu wanda yako samu kallon arzi'ki acikin motar daga gurin Abbas, yana sau'ka ya tari adaidai ta yayi drop zuwa _Barrack 44_ dake cikin kadunan inda Saleem abokinsa yake. *Wash........* *Naso yafi haka amma wallahi ansamu akasi, Please ayi ha'kuri da wannan* *insha Allahu zuwa gobe zakujini* _Ina Team Mahmud ina jira daga gareku , idan naga sharhi ruwa-ruwan ta insha Allahu I_ _ll not fail_ _you agoben_ _zakujini idan muntashi cikin rayayyu._ _Team *ABBAS* ina kuke kuma 'din ku matso domin Abbas yace ayi muku albishir da new_ _catch 'din da_ _zai muku._ 😅 *Much luv MUTANE NAH😍 da sauran drama fah agaba* .👌🏻 *Keep following me* 👌🏻 👎🏻 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _This page is specially dedicated_ _to CAPTAIN ABBAS FANS 1&2 your comments always drive me crazy Allah ya barmin ku._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _Dreams are like stars…....you may never touch them, but if you follow them they will lead you to your destiny._ 🅿 *53* Agidan Anty akayi musu masau'ki inda Anty ta matu'kar bawa kowa mamaki, sau'ka tayi musu na mutunci da karramawa tamkar ba ita ba. Anty da wasu 'kawayenta 'yan bani na iya da suka yi ruwa suka kuma yi tsaki abikin sune zazzaune a palour suka tari amaryar Mahmud 'din. Bayan gaishe-gaishe da ban gajiya sai su Ummah suka mi'ka amanar amarya Teemah ahannun Anty inda Anty ta matu'kar nuna vajinta wurin kar6ar amanar harma ta nuna musu ai bakomai duk 'daya suke tace ai itama amaryar 'ya ta ke agurina, mu'karraban Antyn kuwa cewa suka yi wai su Ummah su kwantar da hankalinsu domin amanar su ta kar6u sai fatan Allah ya bada zaman lafiya mai 'dorewa, mutane nata amsawa da Ameen,Ameen Anty kuwa acikin ranta ta ce _" ba Ameen ba, can da su gada gayyar tsiya Allah ya tarwatsa"_!!! Har su Ummah sun mi'ke zasu tafi masau'kin su sai wasu daga cikin mutanen Antyn suka ha'da bakin cewa su basu ga fuskar amarya ba gaskiya abu'de mata fuska su ganta. Murmushi Ummah tayi tare da umartan Hannah data bu'de mayafin Teemahn. Ahankali Hannah ta matsa jikin Teemahn dan ita iyayin wa'dannan matan yafara isanta. 'Daga lullu6in tayi ahankali kamar mai tsoron ta6awa sai data dangana shi da saman kan Fateeman kafin ta barshi. Dukkan su sun yaba da kyaun amaryar hatta Anty sai da ta yaba da amaryar Mahmud 'din dan ta jima bata ga yarinyar ba tun tana 'yar 'karama, tace ashe Khadija harta haifi 'yah kamar wannan?! Sosai suka yabi kyau da tsariwar amaryarta su dan duk munafurcin ka baka isa ka kushe kyaun Teemah ba ballantana kuma an ha'da da kwallliya da 'kyalkyalin amarci. Dai-dai nan Anty Chiddy ta shigo dayake taje gida bada jimawa da niyyar daman zata dawo sai kuma aka samu akasi kafin ta dawo har amarya ta iso, tana shigowa kuwa idanunta ya sau'ka akan fuskar amaryar. Anty Chiddy kam baki ta sake tana kallon inda tsagwaron kyawun halitta yake, sosai tayaba da Teemah har aranta, tace kamar daga indiya tazo yanayin shiga da kwalliyarta shigen taau ce, banbancin ta au ka'dan ne sai dai su nuna mata hasken fata ita kuwa 'daurin kai zata nuna musu domin 'daurin da akayi mata ba'karamin zanuwa yayi ba, indiawa kuwa basu 'daure kai irin namu na Naija . Take taji masifar son yarinyar yashige ta karaf 'daya, a hankali ta tako ta iso ta samu gurin zama ta zauna itama tare a zubawa yarinyar idanu. Hannah rarraba musu idanu taringa yi jin yadda kowa ke fa'din albarkcin bakinsa akan Teemah, haka taringa binsu da idanu tana kallon su itama, garin 'kare musu kallon ne idanunta ya kai ga Anty Chiddy data zubawa Fateemah idanu kamar zata cinyeta 'danya, kallon kallo tayi atsakanin Fateema da Anty Chiddyn sai data 'kara tabbatar wa idanunta inda Anty Chiddyn ke kallo sannan ta buga uban tsaki tare da ha'de rai kamar anzagi wani nata ne, jan mayafin tayi ta maida shi ta rufe fuskar Teemahn sannan tasake 'dagowa karaf sai suka ha'da idanu harara Hannah ta banka mata tare da murgu'da bakinta aranta tace _" aniyar_ _ki ta biki inma maita ce dake dan mu jinin mu tamkar acid yake sai gani sai hange sai ta Allah bade ta mutun ba, mutun 'dinma irinku, daga ganin tama arniya ce wannan, tawani baza attachments kamar mahaukaciya....mthewwww "_ ta 'karashe da jan tsaki. Anty Chiddy kam gurin Anty ta nufa ganin an rufe fuskar data ke kallo 'din, sai data kai kanta kusa da kunnen Anty kafin ta furta _" your_ _daughter in-law is so beautiful"._ ('Kalubale na farko) Anty murmushi kawai tayi mata dan hankalinta naga matar da taga ta mi'ke tana 'ko'karin tada amarya, Ummah ce tace mata zasu wuche masau'kin su saboda suna da uzirirrika ciki kuwa harda sallah da basuyi ba, lokacin anyi suna kan hanya. Kamar gaske gmsu Anty suka bisu da godiya da kuma fatan alkhairi sannnan Anty tasa aka kaisu 6angaren Mahmud tare da sawa aka wadatasu da dukkan wani abin bu'kata domin anan aka shirya tar6ar amarya ayau 'din har se an'kare hidiman gobe kafin asada ta da gidan mijinta na ainahi. Bayan fitar su Ummah ne Anty da mu'karrabanta suka zauna maida zance akan amaryar da danginta inda suka yabi na yaba tare da kushe abinda suka ga be musu ba, Anty kanta aranta cewa tayi " ha'ki'ka Mahmud yayi dacen mace kyakyawa da kyakykyawan asali, sai de hakan bazai hanani cin uban yarinyar ba, har se da kanta ta nemi saki daga gurin mijin dan neman sassauci, dama tajima da yin wannan al'kawarin tace sam babu zancen zaman aminchi tsakaninta da dangin miji, afa'darta wai duk munafukai ne, auren ma na 'daya daga cikin munafurcin nasu saboda sama taka taji wai za'a yi aure tsakanin Mahmud da 'yar Kabiru (Daddy) batare da anyi shawara da ita ba ko kuma a tambayi ra'ayinta ba, dan anga yaronta mai hankali son kowa 'kin wanda yarasa shine aka li'ka masa ita daga zuwa bautar 'kasa agarin dan haka itama sai inda 'karfinta ya 'kare bazata ta6a amincewa dasu ba itama _shege ka_ _fasa._ Washe gari ma tun kafin wasunsu su gama tashi a bacci har breakfast ya iso su mai rai da lafiya, inda akaiyshi kala daban daban kusan kala uku sai wanda yayi maka zaka za6a kaci. Ta wannan fannin sosai Anty tayi 'ko'kari dan tun zuwan su basu nemi komai sun rasa ba agidan, sau da dama ma tun kafin su nemi abu ake bayyanar dashi agabansu, su Ummah sun matu'kar yabawa da karamcin Antyn hankalin su sam be tashi ba Ummah bata damu ba koka'dan tatafi tabar Teemah da tunanin zata samu farin ciki da yardar ubangiji, tunda ita bataga wani abu na daban daga mahaifiyar Mahmud ba har ma sai taga kamar tsoron da Mummy kullun take anbata wata kila hasashen ta ne kawai dan ita ko ka'dan bata ga haka daga Antyn ba, bataga alamar komai ba. Ummah da sauran manyan matan ne suka wuche aka bar Teemah da 'kawayen domin yin shirin dinner, inda already Anty tariga ta shirya komai hatta 'yan mata sai data kawo wasu daga 6angarenta inda suka ha'du da sauran 'kawayen Teemah sai suka bada ma'ana instead of su hu'dun da suke dukda amaryar. Kaya da zasu saka duk Anty ta tanadar musu gaba 'daya hakama amarya dan wani kaya ta 'dinka mata mai kyau da tsada pitch colour da Teemah tasa kuwa ba'karamin fito da ita yayi ba, Hannah ce tace sai dai Teemah tasa wannan set 'din earings da Abbas ya kawo mata 'dazu acewarta zaifi fito da ita. Ammah sun nema acikin kayan sa suka zo dashi basu samu ba ashe mummy ce ta6oye bata bari yabiyo kayansu ba tace daga zata bawa Daddyn ta ya kaimata. Dole tasa wanda Anty ta ha'do dashi shi'dinma mai kyau ne yafi 'karfin kushe. Ummah na isa gida Abuja ta nemi layin Mummy tasanar da ita irin kar6ar mutuncin da Mahaifiyar angon tayi musu tace gaskiya sai de su godewa Allah domin ita sam bata ga wata matsala atattare dasu ba tace may be Allah ne yashiryeta tun ma kafin Teemahn tazo, mummy ba'karamin da'din hakan taji ba, sosai canjawar Antyn yabata mamaki matu'ka, dama burinta kenan, burinta taga 'yarta tasamu farin ciki agidan auren ta, dama ita ba Mahmud take gudu ba halin mahaifiyarsa ne yake yawan sata damuwa, yanzu kam sai de tace " _ALHAMDULILLAH_" tunda Antyn ta sau'ko. Tun daga lokacin da Mummy tasamu labarin meke faruwa sai ta warawre walwalarta ta dawo dukkan damuwarta ta kau , dama abinda ya dame ta kenan kuma yanzu taji good news akai so no more worried....... Zakayi mamakin yanda event centern ya 'dinke da jama'ah kuma duk Anty ce ta gayyato su musamman dan suzo su kwashi shokky. Ai kuwa ba 'karamin cashewa akayi ba awurin dinner 'din, Mahmud kuwa 'kin zuwa yayi ballantana abokansa, sai gurin yakasance mata zallah ne agurin babu maza sai 'dai'daiku hakan sai ya maida dinner 'din ya riki'de ya juya izuwa mother's night. Teemah duk inda ta juya walwali takeyi kuma idanun Anty Chiddy 'kur akanta har mantawa takeyi da abinda akeyi agurin idan ta tsaya kallon Teemah. Idan kuwa akace Teemah na tsakiyar fili itama bata iya zama, fitowa takeyi ta bu'de bakin jaka tayi zazzaga mata li'ki wanda hakan sai yazama na tamkar gasa kowa yafara 'ko'karin ganin ya nuna tasa bajintar, hatta Munira ma ba'a barta abaya ba dan itama da ita akayi komai agurin taron haka kuma tayi ta zuwa tana watsa wa amarya li'ki wanda garin yin li'kin ne ta samu ta ha'da ku'din da wani hatsabibin maganin dake hannunta ta watsa asaman kan amarya Fateemah, duk kuwa maitar mutn bazai ta6a fahimtar abinda yafaru agurin ba, tana gamawa kuwa ta koma tayi zamanta tana dariyar mugunta tun daga nan bata 'kara tashi ba har taron ya watse domin tariga tagama abinda ya kawota. _('Kalubale na biyu)_ Fateemah na tsakiyan jama'ah tafara jin kanta na matsanan cin sarawa sai ta dafe kan nata jiri na neman kadata, Hannah ce ta lura da hakan sai tayi saurin ri'keta ta maida ita mazauninta tana tayi mata aikin sannu sannan tatafi wurin Anty ta sanar da ita abinda ke faruwa. Anty waya ta lalubo ta'kira Mahmud akan cewa yazo yatafi da Fateema gida saboda bata jin da'di, da " okay" Mahmud ya amsa tare da yanke 'kiran tsawon mintina ashirin ya 'dauke su isowa wurin daya ke daman ba da nisa suke ba already sun riga sun shirya zuwa 'dauko sun. Ba'a maida su gidan Anty ba sai aka kaisu asalin gidan da Fatima zata zauna, Hannah ce ta yi 'ko'karin ganin ta aikata komai da Ummah ta tsara mata kafin tatafi dan haka dazasu shiga gidan sai tace da Teemahn tayi bismillah kuma 'kafar dama zata fara sawa agidan, hakan tayi niyyah dama domin already tu, a Damaturu Mummy ta karantar da ita hakan takuma 'kara da nata addu'o'in na neman kariya daga dukkan ma sharranta daga 'karshe ta rufe addu'ar tata adaidai 'kafar shiga palour da fa'din (A uzubillahi minash shai'danir rajeem, Bismillahi tawakkaltu alal lah wala haula wala kuwwata illah billah) tana gama fa'din hakan tasa kanta tashiga parloun gida. Cikin sa'a ma data 'dan watsa ruwa ajikinta sai taji dama-dama aranar kam basuyi da'de ba sukayi bacvi dan duk sun gama gajiya. Da safe da Teemah tatashi ji tayi kanta yayi mata nauyi sosai sai data nemi panadol tasha bayan sunyi breakfast kafin tajita 'dan dai dai. 12:00pm nayi abincin rana ya iso musu daga gidan Anty lokacin ma duk basu fara jin yunwa ba kasancewar basu ci break fast 'din da wuri ba gashi Anty tasake lodo musu wani abincin. Sai da suka yi sallar la'asar kafin suka fito dan tafiya gida, Mahmud da kansa yagama musu komai na tafiya inda sukkansu zasu sau'kane a Abuja zasu kwana agidan Ummah inyaso washe gari sauran 'kawayen Teemah sai su bi mota su wuche gida. Dazasu tafi Teemah kuwa sosai takeyi ji tayi kamar ta bisu amma badama, haka ta 'karaci kukan ta tayi shiru danko mai lallashi bata samu ba,Mahmud daga wajen gate ya tsaya ya turo aka ce su fito dan haka ko ganin sa bata samu daman yi ba balle har tasamu ban baki daga gareshi. Bai dawo gidan ba sai 'karde tara na dare 9:00pm wanda alokacin idanun Teemah tsuru tsuru duk tsoro yagama cika mata zuciyata na rashin jin motsin kowa acikin gidan sai ta samu guri 'daya ta takure akan kujera tunda suka tafi bata tashi awurin ba ko sallah bata je tayi ba dan tsoro, motsin kirki intayi jitaje tamkar za' a cafkota ne, anan maghrib da isha duk suka sameta batayi su ba, kuka kuwa tayi shi har sai da idanun ta suka daina fitar da ruwa ta komayi azuciyarta. Tana zaune agurin taji an mata knocking tare da sallama duk alokaci 'daya, sanin muryarsa ne yasa tatashi da sauri taje tabu'de masa 'kofar dan dama a'kage take taji motsi sai kuwa taji yazo ai ba 6ata lokaci. Mahmud shi ka'dai yazo gidan nasa batare da neman rakiyar kowa daga cikin abokansa ba. *Keep following me da sauran chakwakiya fa agaba.👌🏻.* 👎🏻 *Kunsan wani abu?.... yau an 6atan raina ka'dan amma bakomai !* ~Tambayace~ ❓🤔 *|-* Shin mu ba musulmai bane kam? *||_* Ko munfi 'karfin jarabtar Ubangiji ne? *|||*_Ko kuwa akwai wanda ya isa yace Allah be ta6a jarabtarsa da wani abu bane wanda yakasance abun 'ki agare shi? _Ni aganina bakomai_ _bane dan hakan ya faru ga bawa tunda daga_ _daga ne,_ _kuma kafin kai million dubunka sunyi experiancing makamancinsa_ _sannan abayanka ma fiye da dubu na jiran jarrabawa daga mahallici_ . _Sai de fatan Allah yasa kyakykyawa ce kuma yabamu_ _ikon amsarta da_ _hannu bibbiyu_ . 👎🏻 _So wanda suke ganin kamar *SALMERH* tayi babban laifi ko kuma ta canja_ _salon labarinta data_ _ha'da auren_ _Teemah da Mahmud harma suke ganin kamar labarin yabar kan hanya ko kuma suke_ _jin daga yanzu labarin yabar kansu ma'ana sun daina bibiyarshi_ *pls* ' _kofa abu'de_ _take ba' ayi muku dole ba, dan labarin CAPTAIN ahaka yazo kuma_ _babu canji ahaka zamu_ _tafi wa'dan da suka fahimta ne ka'dai zasu gane manufar_ _labarin da kuma abinda yake nufi._ _Jinjina ga wa'dan da suka fahimceni suka kuma 'daura 'damarar bin bayana domin jin 'karshen labarin *CAPTAIN ABBAS* ina godiya sosai ina kuma fatan zaku cigaba da bibiyata dan jin 'karshen labarin.........Much luv mutane nah soyayyata daku ta musamman ce Allah yabar 'kauna._ _Masu tausayin Abbas kuma kuyi ha'kuri ni kaina yabani tausayi sai dai kuma kunsan_ _wani abu.......... yace kwananan zai mana new catch muyi ha'kuri inajin_ _sunanta...........ohh so sorry namanta ashe yace kar na fa'da yanzu shida kansa zai zo ya sanar damu.........._ Wattpadians, Facebook followers and most af all Masoyan CAPTAIN na whattsapp jinjinar bangirma sosai nake yabawa da kokarinku......kuma ina yinku iriin trillions 'dinnan.❤ *ACIGABA DA GASHI* ..........🤞🏻 _Comment_ _Vote_ _Share_👌🏻 *Salmerhn ku ce*😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ⚠ ~NOT EDITED~ _In dedication_ _2 my Famliy_ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _Nobody wants to hear this but it's true that sometimes the person you want_ _most is the person you are best_ _without._ 🅿 *54* Mahmud shika'dai yazo gidan nasa batare da neman rakiyar kowa daga cikin abokansa ba, fuskarsa ba yabo ba fallasa lokacin daya ganta ,be yi mata magana ba kawai yasa kansa zuwa ciki itama sai ta bishi abaya ahankali bayan ta tura 'kofar. Babbar rigarsa yacire ya ajiye sannan yakoma ya kukkule 'kofofin gidam gaba 'daya ya daqo yasameta zaune akan kujera. Umartan ta yayi da tayi alwala taje tayi ta dawo sai ya mata nuni da dadduma ma'ana ita yake jira. Ahankali tace masa " _banyi maghrib ba_" dan ita zaton ta sallar isha'i zasuyi. Kallon ta yayi da mamaki ya ce " _meyasa bakiyi ba tun 'dazun"_? " _Ni tsoro nakeji Yayah tun 'dazu fah nika'dai ce agidan kuma su Hannah tafiyar su sukayi suka barni"._! Cikin shagwa6a tayi maganar tamkar zatayi kuka. Shi kuwa sai ya samu ya zauna yace mata ta hanzarta tayi toh dan lokaci na tafiya yace kuma kiyi harda isha'i ma. Sai data jero sallolinta duka biyu sannan ya tshi ya jasu suka yi wata raka'ah biyu ,sosai yajero musu addu'o'i kusan na mintina ashirin sannan suka shafah zuwa lokacin kuwa Teemah tayi hamma yafi sau a 'kirga idanunta duk sunyi luhu-luhu. Cemata yayi taje kitchen ta 'dauko plate da cups takawo. Batayi musu ba kuwa ta tashi taje har wani jiri jiri takeji tsabar baccin daya ci idanunta, babu ma inda tasani acikin gidan ita dan tunda tashigo gidan bata je ko ina ba su Hannah keta shige da ficen su tana kallonsu batare data nemi sanin ko'ina agidan ba. Ko yanzun ma da ta tashin bata da'de ba ta dawo ta e masa ita bataga kitchen 'din ba. Sai kawai ya 'mi'ke yakama hanyar zuwa itama sai ta bishi abaya, dakamsa yashiga ya 'dauko plate 'din suka dawo parlourn. Yayi-yayi da ita taci abinci ta'ki ci sai kawai tayi kwanciyarta akan kujerar dake gefensa tare da yin pillow da 'dan 'karamin throw pillows 'din dake kan kujerun, take sai bacci ya 'dauke ta awurin bada jimawa ba, shima be wani ci abincin ba dan shi'din ma ba ra'ayin cin abincin yake ba dama dan ita ne kuma ta'ki ci dan haka sai ya ture daga gabansa. 'Debe tarkacen yayi gaba 'daya ya mai da su kitchen sannan ya dawo ya tsaya akanta kamar ya tasheta dan ta koma 'daki amma sai ya barta ganin yanda ta saki ranta take baccin cikin kwanciyar hankali ga dukkan alamu akwana kin bata samu wani baccin kirki ba. Sai de duk da haka yana ganin kamar kayan dake jikintan zasu mata nauyi, anyways bari na barta in sun dameta ai dakanta ma zata tashi ta nemi rabuwa dasu. Komawa bedroom yayi yawo shirin baccinsa sannan ya 'dauko pillow yazo ya jefa akan carpet for d first time arayuwarsa ya kwanta bacci ba akan gado ba. Duk da sanyin da tiles 'din ke badawa amma haka ya daure ya kwanta awurin dan kawai ya kasance kusa da ita, domin cika amanar aya kar6a baya so hakkinta yafara hawa kanshi tun daga ranar farkon auren su. Da zai iya kwantawa akan kujerar shima amma kuma 2seater yayi masa ka'dan bazaiji da'din kwanciya akai ba, Teemah kuwa baccin ta ya riga yayi nisa akan 3seatern shiyasa kawai ya yanke shawarar kwanciya a'kasan. 'Karfe biyu da mintina sha takwas 2:18am tafarka garin yin juyi sai idanunta ya sau'ka akansa taga yanda yatakuru ga dukkan alamu sanyi sosai yakeji, sai data ta tashi ta zauna ta fahimci manufar kwanciyarsu aparlourn tunowa datayi cewa tariga shi yin bacci dan ta barshi ne yana 'ko'karin cin abinci. Sake kallonsa tayi sai taji tausayinsa ya kamata "Allah sarki Yah Mahmud" tafa'di aranta. 'Dakin da duhu amma ta daure ranta ta tashi dayake ma akwai hasken farin wata kuma ya 'dan ratso ka'dan ta jikin windown glass 'din dake parlourn dan haka batayi wahalar gane mashigar bedroom ba, sai data shiga kafin ta kunna bulb 'din bedroom 'din sannan haske ya gauraye ko'ina a'dakin, abin rufa ta 'dauko ta dawo ta lullu6a masa ahankali sannan ta koma ta sake yin kwanciyarta ko kayan jikinta ma bata tuna cirewa ba haka ta dawo ta kwanta. Kusan 22mins ta 'dauka idanunta biyu kafin wani baccin yakuma 'daukanta. Washe gari Mahmud ya rigata tashi, koda ya tashin kuwa mamaki yayi daya ga jikinsa lullu6e da abin rufa domin a iya saninsa shi be 'dauko wani abin rufa ba jiyan amma sai gashi ya tashi yagansa dashi, kallon inda take yayi sai yaga tana ta baccin ta kamar dae jiyan be ga wani canji atattare da ita ba. Ture abin ruafar yayi ya tashi yaje yayo alwala dan gabatar da sallar asuba sai da ya idar da nashi salkahn yayi azkar kafin yatashe ta dan itama tayi tata sallar. Koda ta idar sai ta hau gado tasake bu'de wani sabon babin bacci. 'Karfe shida da kwata 6:15am Mahmud ya shiga bedrrom 'din da kayan da yayi amfani dasu wurin bacci sai yaganta na'de agado, dama yayi tunanin haka tun daya ga shiru bata fito ba kuma tun 'dazu baiji motsin ta ba. Ajiye su yayi sannan yashiga yayo wanka ya dawo ya shirya cikin 'kananun kaya ya fita parlour ya zauana tare da bu'de system 'din sa. Teemah kuwa bata tashi ba sai takwas saura 7:46am ta tashi wanda ba 'karamin baccin safen datayin taji ba dan in har batayi baccin ba da wannan farkawan daren datayin ba'karamin ciwon kai zai sata ba kuma bacci zai dameta darana sosai amma yanzun kam tasan kozai dameta da sau'ki. Sai da tayi wanka ta shirya cikin atamparta suoer holland mai kyaun gaske 'dinkin dai dai jikinta, powder kawai ta shafa afuskarta sai kwalli data saka acikin idanunta ta, simple'dauri tayiwa kanta amma duk da haka sai gata tayi fess da ita, fitowa tayi parloun tasame shi zaune yana aikin duba system 'dinsa. Sai data zauna agefensa kafin tace _" ina kwana Yayah"_! Tafa'da tana kallonsa, shima sai ya 'dago ya kalleta sannan ahankali ya amsa da "lafiya 'kalau Fateemah kin tashi lafiya?" Da kai ta amsa yanzun kam tare da kauda kanta gefe dan ganin irin kallin dayake binta dashi. Tunani yake aransa wai dama haka auren yake ne?, shi be ta6a zaton haka ba, ba yau ya fara kallon Fateema ba, ba yau yafara kallonta cikin kwalliya ba amma yanayin dayake ji azuciyarsa yau 'din ya bambanta da kullum, ko 'kanshinta na yau 'din ma daban yake. Maida idanunsa yayi wurin da system 'din daniyar vmcigaba da abinda yakeyi sai ya tsinkayo muryarta tana fa'din " Yayah nifa yunwa nakeji sosai". Kallonta yayi shima sai suka ha'da idanu take yagane cewa asalin gaskiyarta kenan tafa'da masa dan yadda yaga tawani marairaice ta lan'kwasa kai gefe. Tashi yayi bayan ya rufe system 'din yace tashi muje kitchen mu samu abinda zamuyi " yayi maganar tare da juyawa ya nufa kitchen 'din Teemah ma sai ta biyo shi abaya. Tambayarta yayi me takeso taci ita kuwa tace Tea kawai takeso, Mahmud kuma yace "alright nikuma inaso da irish chips dan haka araba aikin, ki 'debo irish ki fara fere shi nikuma zan 'dora Tea 'din idan nagama sai inzo intayaki mu fere tare dan yayi sauri ko? Kai ta 'daga masa alamar "ehh" Da haka suka gama duk abinda zasuyi suka dawo kan dinning domin karyawa. Da rana ma tare dashi sukayi girkin abincin su suka ci, dan ranar Mahmud beje ko'ina ba agida ya wuni abinsa. Sai da dare ne yafita yace mata bazai da'de ba zai dawo, koda ya fitan kuwa gida yaje ya gaida iyayensa Abbah nata saka mai albarka yayinda Anty keta ta6e baki daga gefe amma bata bari kowa yaganta ba. Sai da zai tafine tace ya gaida amarya. Sai daya biya ya siyo mata kayan za'ki dangin su choculates kafin yadawo gidan dan yasan halinta bacin abinci zatayi ba musmman da dare, da ranan ma da 'kyar ta 'danci dayawa sai dayayi ta bata abaki kafin na 'dan kar6a, dan cewa takeyi wai ita bawani yunwan datakeji ai basu da'de da yin breakfast ba, shikuwa yace dole sai ta jar6a tunda har shima yaji yunwa ai yasan itama zataji saboda tare suka ci abincin. Yana komawa gida ya Teemah tafara yimasa rigimar son yin waya da Mummyn ta Mahmud kuwa yace bayanzu sai zuwa safiya dan yanzu dare ya 'danyi yace dasafe zasu 'kirata, 'kin amincewa tayi har fushi tayi dashi wai dan yace se da safe, sai da yayi mata cakulkuli kafin yasamu ta sau'ko bayan tasha dariya. Kamar yanda yafa'din kuwa washegari ya 'kira mummyn suka gaisa sannan ya ha'data da Mummyn yayi tafiyarsa cikin gida dan yasan tsakanin 'da da uwa dole akwai wani sirri. Mummy kuwa ba'karamin da'di taji ba yanda taji muryarsu ka'dai ma ya wadace ta, domin dama tana 'dan jin tsoro dan sarai tasan Mahmud ma bason auren yake ba duba da yanda ya nuna halin ko inkula da Teemah kafin ayi bikin, amma yanzu dataji muryarsu wasai batare da wata damuwa ba sai ta 'kara godewa mahallici daya sau'ka'kawa Teemahn abubuwa. Duk da haka sai data 'kara tambayarta cewa ko akwai wani damuwa, Teemah ta bata amsa da " a'a bakomai mummy ni dai inaso in ganku ne, daddy yace min zai so shi idan muka taho kuma har yanzu banganshi ba ya'ki yazo" Ashagwa6e tayi maganar, mummy kuwa sariya abin yabata ma, tace " haba Teemah dududu yaushe ma kuka tafin , kiyi ha'kuri ai kinsan yana yawan zuwa lagos 'din akan lokaci kuma duk ranar dayaje zaki ganshi tunda shi yayi al'kawari, yanzun yana da wata tafiya ne agabansa Dubai zashi kuma inajin zai 'dau lokaci kafin ya dawo" _"Toh mummy ke yaushe zaki zo"?_ _" zanzo insha Allahu, amma ba yanzu ba sai naga kin nutsu kin kwantar da_ _hankalinki_ _tukunna"._ Zata sake magana mummy ta dakatar da ita da fa'din " ina Yayan naki,? "Bari inkai maa mummy baya kusa " Da " toh mummyn ta amsa mata sannan tacigaba da jan kunnan Teemahn akan tayi wa Yayah Mahmud 'din biyayya, banda taurin kai tace komai yace kiyi masa kiyi kinji inde bana sa6on Allah bane, dan dah da tanzu ba 'daya bane komai yanzu inkika masa Allah zai rubuta miki lada kuma banda rashin kunya kinji" "Toh mummy" Yauwa 'yar albarka kuma banda 'kazanta, nama sanki da kwalliya kidingayi kullum, kuma banda taron 'kawaye barkatai, ki ringa ri'ke sirrinki kinji ko"? "Uhmm" Teemah ta amsawa mummy. Sai mummyn tace " Yauwa ina yayan "? " bari inkai masa da sauri" Koda ta kaiwa Mahmud 'dinma Mummy ce masa tayi kar fa yace zai biye mata dan tana 'yar uwarshi yace komai tayi daidai ne, tace dan nasan halin Teemah da rawar kai, idan tayi badaidai ba ka hukuntata dan ta kiyaye gaba kaji" Murmushi yayi tare da amsawa mummyn sannan yayi mata godiya sosai daganan suka yi sallama tana me sanya musu albarka. Yana gamawa Teemah tace " saura Hannah " "Me kuma ya sami Hannahn"? Ya tambayeta dagan gan batare da ya kalli inda take ba yariga yasan manufarta na fa'din hakan. Teemah kuwa sai ta wani turo baki gaba cikin shagwa6a tace _" zamu gaisa ne harda sauran friends 'dina dasuka tafi tare"_ _"Duk da wacce wayar za'ayi wannan gaisuwar, wai nikam ina taki wayar take ne ?_ Mahmud ya tambayeta yana 'ko'karin mi'kewa. _" Banda credit ko ka'dan aciki Hannah duk ta gama dashi "_ ! Cewa yayi _"jeki_ ' _dauko ingani "_ Zuwa tayi ta lalubo wayar da kyar tasamota cikin drawer dan tun tafiyar su Hannah bata 'kara bi takai ba. Gani tayi ma anmata har 12misssedcall dayake wayar na silent shiyasa bata ji. Atsaye tasame shi lokacin da ta kawo mishi wayar, sai ta mi'ka mishi tare da fa'din _" har ma ta'kirani ashe duk_ _banji ba"_ Mi'ka hannu yayi ya kar6a yana dubawa yace _" taya zakiji bayan ke da kanki baki san inda kika cusa wayar ba"!_ Yana gama maganar ya mi'ka mata yace _" sata a_ _caji naga ma 1percent yarage dab yake da 'daukewa, inya 'danyi cajin sai_ _kiyi 'kiran bari_ _na miki VTU kona bari sai na dawo_ ? " _a a yanzu_ " Tabashi amsa da sauri. Har ya juya zai fita sai ta dakatar dashi da fa'din " _Yayah pls_ _karka da'de"!_ Murmushi yayi sannan ya dawo baya ahankali zuwa inda take yace " _karna da'de kika_ _ce?_ Da kai ta bashi amsa, sai yace mata _"saboda_ _meyasa?"_ " _Tsoro nakeji ni agidan idan ni ka'daice"_ " _idan nafara_ _fita office_ _fah"_ _"Rakaka zan nayi_ _ai kullum"._ Murmushi ya sakeyi tare da kaiwa nannunsa yaja kumatunta ka'dan sannan ya juya ya nufi 'kofar fita, har ya kusan fita daga parlourn sai yace mata " _me zan kawo_ _miki?"_ _" Berries da pineapple"._ Tabada amsa da sauri. Da kai ya amsa mata kawai daga nan sai yasa kai yafice zuwa harabar gidan hannunsa ri'ke da makullin motarsa. Koda ya shiga cikin motar be tada ta ba sai da ya tabbatar yayi mata VTU 'din kafin ya tada motar tare da dannah horn, wani 'dan guntun bayaraben me gadinsa yazo da gudu ya bude masa gate yafice daga gidan. ~AFUWAN~ 👎🏻 _Kuyi ha'kuri da typing errors pls wallahi bansami lokacin yin editing_ _bane shiyasa_, _And jina shiru da kukayi ma 2days amin afuwa please ,banji da'di ba ne amma yanzu kam Alhamdulillah komai zam zam._ _Comment_ _Vote_ _Share_👌🏻 *Salmerh ce*😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _In dedication 2 my_ _lovely Family._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* *_Friends,* *Health* & *Love* ......... _These_ 3 _things_ _don’t come with a_ _price tags, but when we lose then we realize the *COST* ._ 🅿 *55* A kwana na hu'du da auren nasu, da dare suna cikin bacci Teemah taji tamkar ana tashin ta abaccin, ahankali tabu'de idanunta sai kuma taji tsoro ya shige ta karab 'daya, zaune ta tashi afirgice tana rarraba idanu tare da yin salati acikin zuciyarta. Matsawa tayi jikin Mahmud ta sake kwantawa tare da shigewa cikin jikin sa kamar wata 'yar baby tayi luf amma still sai taji hakan be yi mata ba, jitayi zuciyarta na fisgarta zuwa wani abu daban daya girmi tunanin ta, hakan kuma sai yasa tsoron ta yasake 'karuwa, danne fuskarta ta 'kara yi sosai ajikin katifar haka zalika kafafunta da hannayenta duk ta baibaye su ajikin Mahumd 'din. Dole tasa Mahmud sai da ya farka daga baccin daya ke yi, yana farkawa kuwa idanunsa ya sau'ka akanta mamakin abinda yasata yin hakan yayi, sai kuma yaji jikinta da 'dan 'dumi ka'dan, tunani yayi ko bata jin da'di ne, 'kila ko zazza6i ke damunta. Yun'kuri yayi da niyyar tashi sai yaji ta 'kara 'kan'kame shi kamar me tsoron kar ya gudu ya barta, _" Fateemah"!,_ Ya 'kira sunan ta ahankali adaidai kunnuwanta yanda ya tabbatar zata jishi. Teemah kuwa bata amsa ba sai ma 'kara yin luf datayi tana mai 'ko'karin cusa kanta a'kirjinsa. _" meke damunki ne_ _Fateemah?"_ Shiru ba amsa. " _Zazza6i kike jine_ ?" Yasake tambayarta. Yanzun ma shiru be samu amsar tambayarsa ba. Mahmud binta yayi da idanu mamakinsa na 'kara yawaita, ganin bazata yi masa magana ba sai ya koma ya kwantar da kansa akan pillow ya barta ayanda ta ke so 'din, yace 'kila sanyi take ji ne shiyasa, dan in bahaka ba yasan Fateemah baza tayi haka ba, tunda ba yau ne farkon ranar da suka kwanta tare ita ba, be wani da'de da kwantar da kansa ba yaji hannunta akan a'kirjinsa tana shafawa ahankali. Rintse ido yayi tare da fa'din " _innalillahi_ _wa_ _inna ilaihiraji'un, wai meke faruwa_ _ne?,meke damun Fateemah? , kardai ina shiga hakkin Fateemah azaman mu da ita batare da na sani ba?, amma har yaushe Fateemah tayi wayon da zata san haka?, this is unbelie..........."._ Tunanin sa ya yanke ne lokacin daya ji numfashin ta awajen kunnansa, ga dukkan alamu tayi nisa acikin yanayin da take 'din, dan ko daya 'dan matsar dakansa ma sake biyo shi tayi da nata kan da azama. Afirgice ya mi'ke da 'karfinsa sanadiyyar wani sabon salon daya ji take 'ko'karin yi masa. Dafe kai yayi tare da zuba mata idanu yaga yadda hannunta ke yawo akan gadon a inda ya 'daga jikinsa ga dukkan alamu shi take lalu6awa " _Fateemah!,_ " _Fateemah_ !!........ _Tashi kiji...._ _tashi_ _ki gaya min_ _meya faru, meke damunki?_ Yayi maganar yana me kusanta kansa da kunnuwanta yanda ya tabbatar zata jishi da kyau koda kuwa bancin me take yi dole zata jishi. Amma ga mamakinsa kota nuna alamun taji anyi magana da ita ma bata yi ba balle yasa ran zata bi umarnin daya bata, ganin haka sai yasa hannayensa ya tada ta zaune, tana tashi ta zauna 'din sai ta yi luuu tadawo kan jikinsa ta kwantar da kanta akan kafa'dar sa tare sar'ko shi izuwa jikinta da hannayenta. Kai ya dafe duk abin Fateeman yabi ya 'daure masa kai gaba 'daya yama rasa me ze yi mata, jiyake tamkar ba Fateema bace kamar ba Fateemansa ba, tamkar an canja masa ita haka yake gani, asanin da yayiwa Fateemah ma sam bata da gigin bacci balle yace ko mafarki ne ko kuma gigin baccin ne yasata yin hakan. Shima kawai sai yasa nasa hannun ya rungume ta izuwa jikinsa ya jinginu da jikin fuskar gadon yana shafa bayan ta ahankali, ahaka bacci ya 'dauke su gaba 'daya har zuwa asubah. Da asubah da ya tashi sai ya gyara mata kwanciya ahankali yanda baze farkar da ita ba, sannan yaje yayo alwala ya tada sallah, bayan ya idar addu'o'i yadinga jerowa yana ro'kon Allah ya sanya zaman lafiya da fahimtar juna atsakaninsu, Allah ya tabbatar da alkhairin dake cikin wannan auren yakuma kawar musu da Sharrin dake 'kunshe dashi, kuma ya shirya masa mahaifiyarsa shiriya na gaskiya. Sai daya idar da sallahn kafin yaje yatashe ta dan itama tayi nata sallahn, yana tashinta kuwa ta tashi ta zauna tare da rero salati tana kallonsa. Kanta taji yayi mata nauyi sosai sai tasa hannu ta dafe kan tayi shiru tare da sunkuyar da kanta. _"Ya dai"_ Ya tambayeta bayan ya zauna daga gefenta. _" kaina ciwo Yayah_"! " _Ohh very sorry, ki watsa_ _ruwa kafin kiyi alwalar zakiji sassauci bi'iznillah_ _inyaso ingari yawaye sai mu je_ _clinic abaki magani_ _ko"?_ Kai ta 'daga masa alamar "toh". Sai yasa hannunsa ya tayata ta mi'ke tsayen ya rakata har bakin toilet sannan yace mata ta shiga. Nuni tayi masa da towel sai ya 'dauko ya mi'ko mata da sauri dan yanda yaga idanunta yanda take bu'de su ma da 'kyar sosai yaji tausayinta ya kamashi. 8:00am ya kaita wani 'karamin private hospital aka dubata aka rubuta musu magani kawai suka taho gida, amota ya ce ta jira shi yashiga wani babban chemist dake kan hanya ya sissiyo magungunan da aka rubuta musun sannan yazo suka koma gida. Ranar Mahmud beje ko'ina ba ya zauna ya dinga kula da ita, sosai yake bata kulawa ita har yana bata dariya ma dan ta da'de da sanar dashi cewa ciwon kan ya daina amma sam ya 'ki yadda motsi ka'dan intayi sai ya tambayeta ko menene. Ranar da kansa ya tafasa musu indomie da rana suka ci da dare kuwa yace ta shirya suje eatry suci acan dan ba ze iya girkin komai ba yanzu duk ma be fi exercise ba, Teemah tace yaje yaci ya dawo ita kam bata jin cin komai yanzu, Mahmud kuwa yace dole sai taje, tayi-tayi dashi ya'ki barin ta har tace toh yaje in yaso yazo mata da nata still ya'ki amincewa saima ya 'kara da fa'din wai idan ya fita bazai dawo gidan ba sai 11:pm yace in dai zata iya zama agidan ita 'daya toh shikenan sai yatafi karkuma ta kuskura tayi masa complain idan yadawo, dagangan Mahmud yafa'di haka dan yasanta gwanar tsoro ce ita, aikuwa yaci nasara dan yana fa'din haka tami'ke taje ta 'dauko zunbulelen hijab tasa akan kayan dake jikinta suka fita tare. Mahmud nata cin abincinsa yayinda Teemah tari'ke spoon 'ahannunta tana ta juyawa tare da kallon abincin, murmushine ya kubce mata sai ta 'dago kai ta kalli Mahmud sai kuwa suka ha'da idanu " ' _yanmatan Daddy ya_ _dai_ yace mata. Sai itama tace bakomai. " Yah Abbas na tuna wallahi, shifa sam be son cin abincin waje ko yunwa zata masa illlah ne baya ta6a ci har se yadawo gida" Murmushin shima yayi tare da fa'din " _Abbas zakin fama ba, haka halinsa shikam ai kominsa yana da nasa tsarin."_ Hirar Abbas suka tayi har suka 'kare cin abincin inda Mahmud ne kawai yaci Teemah 'dan cakula tai tayi kawai daga nan kuma sai suka wuce shopping store suka 'dan siyi wasu abubuwan anfani. Mahmud gidan mahaifinsa yawuce dasu basu sami Abbah agida bama sai dai Anty na nan sun same ta tana waya ne sai suka yi zaman jiran ta, jisuka yi tana fa'din "ehh lafiyan ta gasu nanma yamzu suka zo, ok ta'kqre maganar dashi tare da mi'kawa Teemah wayar kar6a tayi tare da fa'din "Hello" atakaice duk da bata san waye akan layin ba amma sai ta tsinci zuciyarta da rashin son yin magana alokacin. Daga cikin wayar taji wata murya da bata san ta tana fa'din _"Baby how are_ u?. Da 'yar muryarta da haushi yafara cikawa ta furta _" Fateemah ce !"_ atakaice _" i know naa, don't_ _worry u ll_ _soon........._ Bata bari ta 'karasa jin mai matar zata fa'da ba tacire wayar akunnanta tare da mi'kawa Anty wayar, afakaice Anty ta doka mata harara batare data bari sub lura ba sannan ta kar6i wayar dan ayanayin response 'din Fateeman Anty ta fahimci ba gaisuwar kirki suka yi ba hakan kuwa sai yasata 'kara jin haushi amma bata bari yanuna akan fuskarta da yanayinta ba sai ta tsare ta daidai ta nutsuwarta atake. Tana kar6ar wayar ta yanke 'kiran tare da 'ka'kalo murmushi tace " ga dukkan alamu dai amarya tayi uwar 'daki, kinga kuwa yanda ta damu kullum sai ta tambayeki idan ta'kira awaya ,ai dan tayi tafiya ne ma inbahaka ba nasan da yanzu har kun saba ma da ita tun ranar da kuka sau'ka agidannan taji kin manta................. Teemah baki ta ta 6e lokacin da idanun Anty yabar kanta, aranta tace " _su uwar 'daki manya, shine har da wani cemin baby, ce_ _mata akayi ni inason uwar 'daki ne?, mummy na_ _ma ta isheni nikam_ " Mahmud kuwa shiru yayi kawai yana nazari dan kuwa yasan wannan uwar dakin bana gaskiya bane, bazai so ya tankawa mahaifiyarsa magana a gaban Teemah bane dan gudun watarana kar kuma yazamana shine da kansa yabada kofar raini ga mahaifiyarsa, inba dan haka ba daya ce baya son wannan ala'kar saboda yasan duk wani abu dazai tunkaro su ta 6angaren Anty toh ba alkhairi bane shiyasa yake tsoro, amma azuciyarsa sai yayi alwashin cewa ze tsaya tsayin daka dan ganin ya ruguza wannan ala'kar tun kafin tayi 'karfi. 'Bangaren Anty kuwa kar6an su tayi ba yabo ba fallasa suka gaisa, tare da gabatar musu da abinsha agabansu sai dai suna gama gaisuwan ta tashi ta shige ciki tace dasu tana zuwa, zaman kusan 1hr sukayi ba Anty ba labarinta, Mahmud daya gaji sai yace mata ta tashi su wuche be ko sake neman Antyn ba sukayi tafiyarsu dan yasani sarai Anty dagangan tayi musu hakan. ***** Tun ranar da Abbas yabar garin damaturu bayan 'dauri auren Mahmud be 'kara samun lokacin kansa na kirki ba, harma hakan sai ya zamana kamar taimako ne agareshi da zuciyrsa harma da rayuwarsa dan sam be samu lokacin da zai zauna har yayi tunani akan rayuwarsa da rabuwarsa da Fateema ba sai dai duk da haka 'yar walwalar dayake da ita yanzu babu shi koka'dan, yanayin komai ne ayanda sabuwar rayuwarsa ta zo masa da shi. Saleema kansa tunda Abbas 'din ya sau'ka a wurin shi be gane kansa ba, kuma sam ya'ki ya bu'di baki yayi masa bayanin meke faruwa dashi, ya dai ce masa daga damaturu yake yaje 'daurin auren sister 'din shi, tun daga nan be 'kara yi masa wani bayani akai ba, dayake Saleem yasan halin kayanshi sai ya 'kyale shi dan yasan matu'kar Abbas be yi niyyan yin magana ba toh babu wanda ya isa yasashi dole, dan haka sai shima yabarsa kawai yaci gaba da abinda ke gabansa, toh dama ma yaya lafiyar kura...... Washe garin ranar daya bar Barrack 44 Kaduna, aranar ko zama beyi ba ogansa ya wakiltashi zuwa wani taro acikin garin porthacourt 'din. Ranar lahadi ne ka'dai ya 'dan samu ya huta washegari kuwa rakiya yayiwa ogansa zuwa Biu Borno state domin halartar wani taron bu'de wata makaranta acan cikin garin Biu Nigerian Army Institute of Technology & Environmental Studies (NAITES). Sosai hakan ya'kara taimakon Abbas dan kuwa taron sosai ya me dashi busy man harma sai ya 'dan manta da damuwarsa ya ajiyeta agefe guda ganin cewa saka damuwa aransa ayanzu tamkar yana kashe kansa tabaya ne dan kuwa cutar kansa kawai zaiyi batare da yasami dan taimako ba idan har yace sai ya zauna yayi tunaninta, yarinyar datariga ta tafi ta barshi, bari na har abada toh miye abin 6atawa kansa lokaci shi kuma akanta. *LAGOS* Mahmud duk wani 'ko'kari dayasan ze wanzar da zaman lafiya da fahimtar juna atsakanin sa da matar shi yayi 'ko'karin ganin ya aikata shi duk dama har yanzu beji cewan shima magidanci me iyali bane shi gani yake kamar wata 'kaddara ce tasasu kasancewa atare, amma hakan bai hana yabata dukkan kulawan daya dace ba, ko dan kasancewarta matsayin matar sa da jama'ah da dama suka shaida, sannan kuma 'kanwa ce mafi soyuwa azuciyarsa, abu 'daya ke 'daure masa kai yanda akowani dare sai yanayin Fateema ya canja yakasa fahimtar inda matsalar take tasowa yama rasa gane meke yawo akanta da har yake sata lalu6ansa akowani dare bayanshi hakan kokadan baya gabansa. Ranar da suka cika 16days da aure aranar anyi ruwan sama sosai kuma duk ruwan akansu ya 'kare dan Fateema duk ranar dataga za'ayi tunkan ruwan ya sakko take fara shirin shiga ruwan , shiri zatayi cikin riga da wando marasa nauwi ko bra bata sawa idan zata yi shirin wasan ruwan sai ta rufe kanta da shower cap. Da farko Mahmud 'kin barinta yayi amma data rin'ka rokonsa dolensa sai daya amince ya barta, daga baya kuma sai ya fara tayata shiga ruwan, tun daga lokacin be 'kara hanata ba kodan lura da yayi hakan na 'daya daga cikin abubawan dake matu'kar sata farin cikima, sai ma su shirya dukkansu sushiga ruwan sunata juyi suna dariya wataran kuma sukama hannaye suyi ta juyi aruwan suna tsalle-tsalle kamar 'kananan yara. Mahmud da kansa yafara mamakin kansa dan irin kayan da take sawa su fita wasan ruwan dashi shika'dai ma abin kallo ne, sau da dama yana mamakin kansa yanda yake ganin Fateemah akowani irin yanayi amma be ta6a jin wani sauyi tattare da shi ba, sau da dama yakan tsaya ya ta kallon yanda kayan jikinta suka manne mata suka bayyana dukkan surorin jikinta sanadiyyar ruwan saman da ya ji'ka su, awannan lokacin kowani irin 'da namiji yaganta sai yaji wani abu aransa da jikinsa koda kuwa ya yake amma ga mamakinsa shi be ta6a jin wani canji ajinkinsa game da hakan ba, da farko abin baya damunsa dan ya 'dauka ko rashin 'daukar auren nasu amatsayin aure ne yakawo hakan amma daga baya abin sai ya fara damunsa, shikansa yaji yana so yaji wani sauyi tattare da shi amma sam yarasa dalilin hakan, tsakaninsa da ita sai de kallo da ido and nothing more. Exactly that day kamar yanda Fateemah tasaba yi masa hakan tayi, zuwa yanzun ma yafara sabawa da yanayin nata ya fahimci kawai hakan take bawai rigima bane kawai ko wani abu daban, saboda tun ranar data fara yi masa irin wannan 'din dai-dai da rana 'daya bata ta6a fashi ba akullum sai ta lalu6e shi, tun baya kulata har ya fara taimaka mata, wasu lokutan yakanyi romancing 'dinta duk dan yataimaka wa yanayin nata dake ciki bawai dan yana jin da'din hakan ba, cikin sa'a kuwa sai yaga bacci ya 'dauketa bayan hakan wataran kuwa idan abin yafaskara baya sanin lokacin dayake fara jero mata addu'o'i ma da ikon Allah kuwa sai yaga tayi la'kwas tayi bacci tare da jero ajiyar zuviya acikin baccin. Idan darana ne kuma kamar ba ita ba sam bazama kace ita ce ke neman sa arikice da dare ba. Na yau 'din kam yasha bam-bam dana kullum, dan kukanta ne yatashe shi abacci, kukan take sosai tana danne cikinta tare da takura kanta guri 'daya tana shiga jikinsa, koda ya nemi yi mata kamar yanda yasaba 'din sai ta nuna masa alamun bahaka take so ba ita. Rasa yanda zaiyi da ita yayi gashi sosai take bashi tausayi, mamakin kansa sai ya hana shi taimaka mata illah tsayuwa dayayi saroro yana kallonta, so yake ya lalu6o dalilin amma yarasa dan ayanda yasani da ba haka yake ba, be san me ya maida shi mara anfami yanzu ba, gashi yanzu taimakonsa ka'dai Fateemah take nema awannan yanayin while shikuma badama. Dayaga kukan data keyi yana so yayi yawa sai ya koma yajawota jikinsa ya rungumeta da 'kyar, tausayinta ya da'da karya masa zuciya ganin da kanta take neman raba jikinta da kayan baccin data ke sanye dashi, zafi rau yaji jikintan kamar wacce take tsaka da zazza6i, hawayene yaji ya gangaro masa sai ya lumshe idanu ahankali yafurta _" ki yafe min Fateemah, bansan haka ne zaizo yafaru dani ba_ _kamar yanda bansan haka yanayin ki yake ba tun farko, wallahi_ _dana san haka ne da bazan amince da auran ki ba ko dan gudun kar nashiga hakkin_ _ki, da ha'kuri zan bawa Abbah na da Daddy akan afasa 'daura mana aure, amma nasan 'kaddara ce ta ha'da auren mu kuma ni ban isa na dakatar da ita zuwa garemu ba, ki yafe min kinji......_ _ki yafe min Fateemah insha Allahu zan nema miki mafita.........."_ _Comment vote and_ _share pls_ 🤞🏻 *Salmerh ce*😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _A rumor goes in one ear and out of many mouths._ 🅿 *56* Washe gari Mahmud asibiti ya je aka duba shi aka bashi magani hadda allurai daga nan sai ya wuce office 'dinsu amma ko 2hrs mai kyau beyi ba awurin yadawo gida kafin haka kuwa yayita 'kiranta yafi sau biyar yanajin ya take. Yana komawa gidan kuwa Fateemah tafara yi masa rigima akan wai dole sai sunje sun yi wasan basket ball dashi, Mahmud duk da yana cikin damuwa amma haka ya daure ransa ya amince mata suka fita wurin wasan dan kawai ya faranta mata, daya ke akwai wurin yi 'din acikin gidan nasu daga 'dan nesa ka'dan da bakin get, wurin 'dan daidai ne bawani babba ba musamman aka tsara shi saboda masu gidan. Bomshort ne ajikin Teemah wanda yakama jikinta sosai sai wata 'yar 6ingilar ba'kar riga da bata ko rufe cibiyanta ba kanta kuwa wani bakin shararan hula ne da aka sa'ka shi da zaren lilo, ba 'karamin kyau tayi acikin shirin nata ba, Mahmud kansa gani yayi tayi masa kyau sosai ba 'karamin birgeshi tayi ahakan ba, yakan juyo ya kalleta lokaci zuwa lokaci dan yasan iya abinda Allah yabashi iko kenan akanta tunda ga halin daya tsinci kansa aciki, duk dama yana saka ran samun sau'ki akowani lokaci tunda likita yayi masa bayani mai kyau kuma ya gamsu, ya sa hope 'din sa akan magungunan da aka bashi tare da taimakon Allah da kuma izninsa zai sami sau'ki. Isar su filin keda wuya suka fara buga wasa, Fateemah daman bawani iyawa tayi ba tsabar rigima ce, garin shige shigen ta acikin gidan ne idonta yaci karo da wurin wasan shine fah ta dage sai anyi, 3:0 Mahmud yamata tana ganin haka kuwa tafara tsalle tana fa'din a'a bata yadda ba gaskiya wai itama yajefa mata ko sau 'daya tunda ita ta kasa. Dariya ma abin yabashi, yakuwa dara, acikin dariyar yace " _a ina kika ta6a ganin anyi haka, nine kuma zan jefa miki?_ _Hhhhh_ ya 'karasa maganar tasa da dariya." _U ar so funny Fateema "_ tare da nunata da yatsa. Baki ta turo tayi fushi har zata juya yasa hannu ya cafko hannunta 'daya yace mata " toh shikenan amma sau 'daya zai jefa mata tana jin haka tace ehh ta amince. Jefawan yayi da sunan nata ne, ai kuwa take tafara tsalle da murnan taci 'daya, da ya 'kara yi kuma take sai yabata 4:1 daga nan kuma tace ya 'dagata itama tasaka da kanta, yazaro idanu tare da fa'din _" kai....... ke 'katuwan nan ne zan 'daga ?_ Yafa'da da sigar zolaya, _"gaskiya kina cutata haka ake wasan ne?_ Bubbuga 'kafafu tafara yi a'kasa cikin shagwa6a tace _" ni de sai ka 'daga ni bayan sai shana kake yi kawai dan ka ga ka fini tsawo, ai da yah Abbas na nan nasan da zai tayani nima"_ Kwa6a fuska tayi kamar zatayi kuka ganin haka sai yace toh tazo ya'daga ta, tana jefawa tasake sakin murna tana dariya kamar wanda yin kanta ne bada taimakonsa ba, tsalle take tana fa'din " _yeehhhh naci_ _biyu"._ Shima sai ya yatsaya kallon ta yana dariya yace. _" kinmanta 4:2 muke, ratar biyu fah nabaki"!_ _"Ehh ai biyu ne kacal kuma nima yanzu zan taro ka"_ Tana fa'din haka sai taci gaba da murnarta abinta. Horn sukaji an danno daga waje, mai gadi yaje da gudu yale'ka sannan yadawo ya tura gate 'din batare da yayi magana ba dan ganin wanda ke cikin motar. Teemah kam jin horn 'din koka'dan be dakatar da ita daga murnar data keyi ba dan bata ko damu da waye yazo acikin motar ba. Mahmud kuwa bin motar yayi da kallo ganin dayayi cewa motar ta gidan sune ta shigo sai dai bai gane wacce ke cikin motar ba dan sun 'dan yi nesa dasu ka'dan, motar na tsayawa su Anty suka fito atare ita da 'kawarta daga cikin motar idanunsu gaba 'daya nakan su Teemah, dan tun shigowansu suka hango su a filin wasan. Wani tuku'kin takaici ne yacika zuciyar Anty ganin cewa wai har lokacin yin wasa suka ke6e acikin gidan domin kawai su sha'kata, lalle nayi sake, shirun nawa yayi yawa, shiyasa har yarinyar dana so na wargaza auren ta tun ranar farko tasami saken da har zata buga basket ball agidan da na tsani ganinta aciki har ma da 'dana 'daya tilo dana mallaka aduniyan nan kuma na tsani ganinsu atare. Zagayawa tayi da sauri 'daya 6angaren da 'kawarta take tsaye dan ita tun fitowanta daga motar bata 'kara ko motsin kirki ba awajen, ta tsaya saroro tana kallon Teemah kamar zata cinyeta 'danya. Dafa kafa'dar ta Anty tayi sai ta juya da hanzari, akufule Anty tafara magana " _kin gani ko, kinga abinda nake ta faman gaya miki amma kika 'ki_ _taimakona saboda wani dalili bayan kinsan sai da kene nasara take zuwar min, yanzu gashi_ _shirun danayi na zuba ido yasa har sha'kuwar su tayi nisa, dubesu kiga........"_ Ta 'karashe da nuna su. " _Come down mana mum Mamud,_ _everything ll be alright since am here komai zai zo da sau'ki in dai har kika goya min baya_ _zan taimake ki kirabasu kamar yanda kike so amma sai kin tayani cika_ _*BURINAH* "_ Kallon Anty Chideh kawai Anty keyi dan koka'dan bata fahimci manufarta ba, karta ce har yanzu tana kan bakanta na wancen maganar ne, in de kuwa har hakane toh sai de kowa ya ha'kura da 'kudirinsa dan bazata iya aikata wancan aikin ba da girmanta ba yarinya , infact tunda ma har ta iya bari akayi auren akan ta'ki amince mata toh kuwa bayan auren bataga dalilin da zai sata ta aikata ba. Anty Chideh kuwa murmushi tayi ganin Anty ta tsaya shiru tana tunani, tasan cewa maganar su nabaya take tunawa dan haka sai ta dago hannu tashafi fuskar Anty ,baya Anty taja da sauri, Anty Chideh kuwa sai ta sake murmusawa tare da fa'di. " _feel free mum Mamud this time around daughter in-lawn ki nakeso not_ _u, tunda ke kin'ki bani ha'din kai na ha'kura dan nasan bazaki amince ba, amma yanzu kam matu'kar kika tayani fighting_ _nasameta toh na miki al'kawarin raba auren nan rabuwa_ _na har abada, zan kaiki duk inda kike so kika kuma za6a_ _dan kawai ki cika naki burin._ " Sosai maganar Antyn Chideh ya suprising Anty, bata ta6a zaton iskancin nata har zai koma kan 'yar cikinta ba, no wonder shiyasa tun ranar da aka kawo yarinyar ta yabeta dan ma tayi wata 'yar tafiya ne inbahaka ba tasan da tunda wuri tagama ya'da manufarta, tunowa tayi lokacin da Anty Chidehn bata nan kullum sai ta 'kirata awaya takuma tambayi lafiyar amarya ashe akwai 'kunshin abu aranta, harma ranar tace abawa Fateeman waya dan kawai taji cewa sunzo suna kusa, amma Anty bata wani damu ba jin cewa abin ya bar kanta ya koma kan makiyarta ai ita hakan yafi komai yi mata da'di tunda kuwa hakane dole in goya mata baya. Daga nan ta tabbatarwa Anty Chidehn cewa duk yadda take so haka za'ayi dai dai nan Mahmud ya iso wurin da suke tsayen cikin ya'ke yace " _ahh barkanku da zuwa Anty ya kuka tsaya anan kuma?, mu_ _'karasa daga ciki pls"!_ ya 'karasa maganar tare da juyawa. Anty batayi magana ba illah kallon bayanshi datake yi sai kuma bata ga Teemahn ba. Kasa ha'kuri tayi sai da ta tambaya inda tace " _ina amaryar taka kuma Mahmud batare_ _naganku bane_ _'dazu",_ kai Mahmud ya sosa tare da fa'din _" ta_ _wuche ciki yanzu?_ Sababi Anty ta fara akan wai " _tsabar ta raina ta ne shiyasa tana ganinta ta wani yi wucewarta_ _inbahaka ba me yasa bazata zo ta tar6eta anan 'din ba kamar yanda Mahmud 'din yayi, kodan tana ganin ba nice na haifeta ba, na tabbata da Khadija tagani anan da sai ta riga ka ma zuwa inda isowa"._ Mahmud be yi magana ba da be san me zai ce da Antyn tasa ba, toh yace mata kunyar kayan jikinta yasa tayi 'dakin ko kuwa yace mata tatafi suturta jikinta ne. Murmushi ne ya kubce masa daya tuna lokacin da zai taho inda su Anty suke Teemah ma fara biyo shi tayi ahakan dan ko damuwa batayi da kayan da yake jikinta ba kota manta ne oho, sai da yace " _kiyi sauri ki wuce ciki ki saka gown akai kar su ganki ahaka ko bakya jin kunya ne_ _su ganki ahakan.......?_ Yana fa'din haka ta juya da gudu ta koma ciki, may be lokacin data wuche 'din hankalin su Anty baya kansu shiyasa ma basu lura ba. Anty Chideh ce tace da Anty tayi shiru mana bata son yawan fa'da bayan tasan cewa yanzu Teemahn propertyn tace, tace mata kayan jikinta 'kanana ne may be tana jin kunyane shi yasa bata zo nan 'din ba. 'Kasa-'kasa tayi maganar yanda Anty ka'daice zatajita. Duk da Anty Chideh cikakkiyar bayerabiya ce amma yawacen yawacen data tayi a wurare da dama yasa tasan dayawa daga cikin al'adun hausawa shiyasa tayi saurin kare Teemah da wancen maganar. Anty kuwa ta6e baki tayi, 'kasa-'kasa tace _" iskancin banza da 'din me yasa ta saka kayan tunda tasan tana jin_ _kunya aganta dasu"_ Mahmud ne agaba lokacin da suka shiga cikin parlourn, bayansa Anty ce sai Anty Chideh daga 'karshe, a'kofa ma suka ha'du da Teemah tana 'ko'karin fita ganin su yasa ta basu hanya suka shishshigo, hijab tasako babba akan doguwar rigar data saka 'din sosai tayi kyau acikin hijab 'din dan ya 'kara fito mata da hasken ta da kuma 'dan madaidaicin fuskarta tayi 'das aciki. Abinsha tawuce ta 'dauko musu sannan ta zo ta zauna ta gaidasu Anty Chideh ce kawai ta amsa da fara'ah tana wani kallon cikin idanun Teemah, Anty kuwa ayatsine ta amsa mata, bata wani damu da yanayin da Anty ta amsa gaisuwar ba, illah kallon da Anty Chideh ke binta dashi ne ya 'dan so ya 'daure mata kai dan haka sai tayi 'kasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta. Tashi Mahmud yayi ya shiga ciki da niyyar saka ko jallabiya ma akan wandon three quatern dake jikinsa, da wannan lokacin Anty tayi anfami tayiwa Teemah bayanin wacece Anty Chideh awurin ta, tace saboda watarana ko bani zata iya zuwa duba ki ita 'daya ina so ki san cewa matsayina danata tamkar guda ne awajenki karki kuskura ki yi mata badai dai ba, kinji ko baki jiba, da _" Naji "_ Teemah ta amsa mata ahankali. Mahmud na sako rigar ya fito yadawo parlourn. Su Antyn ma basu wani da'de ba dan ko 10mins basu yi ba suka ce zasu tafi dama Anty Chideh ce ta matsa sai sun zo wai tanaso taga daughter in-law 'din nasu ne, Anty bata so zuwan ba dan haka tace bari kawai ta 'kirasu suzo sai Anty Chideh ta'ki amincewa da hakan, dolen ta ta shirya suka taho, alokacin ma Anty bata san meke ran Anty Chideh ba sai bayan isowarsu ne da ta mata bayani. Har gurin mota su Mahmud suka musu rakiya, Teemah nata ra6ewa ajikin Mahmud dan avoiding ha'da idanu da Anty Chideh datakeyi, Mahmud kansa ya lura da haka amma ya basar dan be san dalilinta na yawan kallon Teemahn ba, sam ta tatsani ganin matar ita, ganin cewa 'katuwar babbar mace da ita amma tana mata abu kamar mara hankali ,inbahaka ba miye abin yawan kallo awurina, sai kace bata ta6a kallon mutum kamar ni ba". Acikin ranta taketa wannan masifar, azahiri kuwa kanta na gefe bata ma kallon inda suke. Sai da suka ja motar sannan ta sau'ke ajiyan zuciya tare da dokawa bayan motar harara, ta kalli Mahmud sai suka ha'da idanu take sai yayi sama da girarsa, ga dukkan alamu yaga abinda tayiwa bayan motar su Antyn, da sauri tace _" wallahi Yayah banason matar nan ni koka'dan"_ hannunta yakamo suka fara tafiya sannan anutse yace _" wacce daga ciki?_ _"Wannan inyamuran matar mana, sai ta ta wani kallona tana smiling bayan ni banma_ _santa ba, ban ta6a ganin ta ba ma ni, haushi tabani sosai yau 'din nan"!_ Murmushi yayi sannan yace mata " _'kawar sirikar ki ce kinga kuwa dole ki_ _sota ai "_ _" ehh ai Anty ta fa'da min 'dazu."_ da wannan hirara suka koma parlour suka zuzzube , Teemah na shiga ta fincike hijab 'din tare da rigar data saka wai zafi yadameta, dama garin sauri ko na cikin bata tsaya ta cire ba ta 'dora doguwar rigar akai. ***** Mahmud har 10:00pm ya kai a parlour yana kallon News a NTA, yayinda Teemah tayi kwanciyarta tai bacci dan dama ita ba gwanar zama tayi kallo bace, sam kallo be dameta ba arayuwarta. 10pm cif Mahmud yatashi tare da kakkashe switch 'din sannan ya shige ciki, sai da yaje ya watso ruwa kafin yazo ya kwanta, yana sa jikinsa akan gadon kuwa ko addu'ar bacci be gama ba yaji wani bacci me shegen nauyi from no where yana firgarsa har idonsa ma baya iya bu'dewa, be masan lokacin da baccin ya 'daukesa ba danko addu'ar yin baccin be gama karantowa ba, be tashi sanin kansa ba har se lokacin sallar asubah, har alokacin kuwa baccin be bar idanunsa gaba 'daya ba still yanajin idanunsa na masa nauyi, da 'kyar ya ya'ki zuciyarsa ya samu ya tashi, koda yatashi sai be ga Fateema akan gadon ba, sai yayi zaton ko tana bayi, zaman kusan minti biyar yayi amma beji motsinta aciki ba kamar yadda bega alamun ta a bayin ba, tunowa yayi yau ko motsinta beji ajikinsa ba _"where_ _is she_ _toh_ ? dan har yanzu wutar 'dakin akashe yake, in kuwa Fateemah ta tashi ne yasan dole sai ta kunna wuta saboda tsoron da ya san tana dashi. Sai da ya duba cikin toilet yaga bata nan kafin ya wuche parlour 'a'dan rikice dan zuwa yanzu ya 'dan fara shiga ru'du da rashin ganin Fateeman, switch ya kunna na parlourn sai ya hangota kwance a'kasa ta kwanta akan ruwan cikinta tana baccinta cikin kwanciyar hankali, ajiyar zuciya ya sau'ke daya gantan sai ya sake kashe mata wuta ya wuche ya yo alwala, sai da ya idar da sallah ya 'daga hannu ya jero addu'o'i sosai kamar yanda yasabayi kullum, sannan ya tashi ya koma parlourn domin yatashe ta. Lokacin data tashin ita kanta taso tayi mamakin inda ta ga kanta saboda kalle-kalle tafari da mamakin meyasata kwana ana 'din, sai daga baya da ta'dan yi recalling abin da yafaru sannan ta tuna ashe da 'kafafunta tazo parlourn. Koda ta ganshi agefenta kuwa take sai ta tura baki gaba tare da kau da kanta gefe tana wani yatsina fuska _" meya faru ne Fateema, meyasa kika dawo nan kika kwanta ke 'daya"?_ Mahmud yayi maganar cike da kulawa. Yana kaiwa ayar tambayar tasa kamar jira take yayi shiru sai kawai ta mi'ke tsaye bata ko 'kara kallon inda yake ba, binta yayi da idanu harta 6acewa ganinsa yana mamakin 'kin kula shin data yi, wanka tayi tafito , lokacin ma gari har gari yafara haske, gurin dressing mirror ta nufa tana goge jikinta da towel , Mahmud kuwa yana zaune agefen gado yana kallon bayan ta, sai da tazo ta bu'de closet 'din kayanta kafin tace _" ina_ _kwana yayah"_ tayi maganar kanta akan kayan batare data ko kalli inda yake ba, shima be amsa mata ba illah hannunta da ya jawo ta dawo gefe dashi ya zaunar da ita, tana 'ko'karin sake tashi ya dakatar da ita da fa'din " _inajinki me kika ce_ " yafa'da yana kallonta, " _ina_ _kwana_ " tasake fa'di atakaice kanta na 'kasa. Murmushi yayi batare da ya amsa gaisuwar ba yasake fa'din _" sallar fah sai yaushe zakiyi?"_ _" Nayi"_ Yace _"Yaushe?_ _'"Dazu"!_ Tabashi amsa tana yun'kurin tashi. _" a ina kenan?"_ Yasake tambayarta. Sai ta bashi amsa da fa'din _"a parlour._ " Jijjiga kansa yayi dan yasan 'karya take bawani sallar datayi. _" wai laifin menayi ne haka lil sis please tell me kinji_ _banson kin......_ Be 'karasa maganar ba ta tare shi da fa'din _" bakai bane,_ _jiya ciki na ciwo yatayi dadare_ _nakasa bacci, ina ta tashinka kai kuma ka'ki ka kulani, bayan nasan kana_ _jina "_ Kansa yadafe tare da fa'din _" innalillahi, ya akai duk bansan anyi haka ba, pls_ _Fateemah kiyi ha'kuri kinji aikinsa bahaka nake yi miki ba ko, wallahi jiyan_ _ne baccin ya min nauyi ni kaina nayi mamaki, amma insha Allahu hakan_ _bazai sake faruwa ba kinji"_ Shiru tai masa batayi magana ba, _" bazaki ha'kura ba_ _ko Fateemah?_ Tashi yai kamar zai tafi irin yayi fushi 'din nan shima, take sai Teema ta kamo hannunsa koda ya juyo kuwa sai suka ha'da idanu, kai ta jijjiga masa sai yace mata _"kin_ _ha'kura"_ da kai ta amsa masa alamar _"ehh",_ yana ganin hakan sai yadawo gefenta ya zauna yace toh tayi dariya yagani, murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta 'kasa shima murmushin yayi yace cikin zolaya yace _" wato dan na 'ki kulaki shine kika yi fushi kika koma parlour kika barni ni 'daya a 'daya a'daki ko?._ Dariya sukayi atare daga nan maganar ta wuche suka shiga harkokinsu kamar kullum. 'Karfe takwas 8:am na safe Mahmud ya wuche offfice tare da rakiyar Teemah har wajen da zai shiga motar sa, tana 'kara jaddada masa wai ya dawo fah da wuri dan ita tsoro take ji, kullum dama inzai fita sa'kon ta kenan, sai kuma tace ya siyo mata tarkacen fruits da har yau tafi sansu akan abinci, takan sha ko ci aduk lokacin da Mahmud ya matsa mata akan taci abinci, wani lokaci kuma sai taci abincin musamman ranar da ya 'ki siyo mata fruits 'din, yauma daya tambayeta abinda zai kawo mata sai tace masa Apple kawai takeso yau, murmushi kawai yayi ya juya ya shige mota dan baya so ta sake yin fushi dashi akaro na biyu badan haka ba da bazai siyo mata ba, dan yasan idan tana ganin fruits 'din bata ta6a waiwayar abinci akan lokaci sai ta ga dama. Bye-bye ta masa daga nan yaja mota ya fita agidan shima yana me 'daga mata hannu. ***** Duk wani abu daya rage na tafiyarsu Daddy yayi ya kammala komai harma yarage saura kwana biyu kacal su tafi, Mummy taso taga 'yarta kafin su tafi amma Daddy ya hana ko awaya ma yahana ta sanar da ita saboda baya so ta 'daga hankalinta, yafi son tayi zamanta hankali kwance agidan mijinta batare da sa damuwar komai aranta ba, Mummyn ma damuwarta ayanzun bai wuce tasan irin zaman da Teemahn keyi da Anty ba abinda yafi damunta kenan, dan tasan 6angaren Mahmud da sauki duk dama tana zargin bason auren yake ba, amma koda ta 'kira Teemah awaya bata samun labarin komai, Teemah bata sanar da ita matsalar dake damunta, akullun cikin farin ciki take jinta, tun tana zargin ko Teemah na 6oye mata ne har tazo ta yarda cewa Teemahn bata tare da damuwa, fatanta dai Allah yasa hakanne, Allah ya wanzar da farin ciki da zaman lafiya a tsakaninsu gaba'daya. Wata'kila shiriyace tazo wa Antyn shiyasa ta yada makan ya'kinta ta ri'ki Teemahn amatsayin matar 'danta Mahmud. Mummy takanyi murmushi ita ka'dai idan hakan yazo ranta domin babu abinda ya fimata da'di da farin ciki ayanzu irin taga Teemah na rayuwa cikin walwala ga dukkan alamu kuma burin ta ya cika. Hatta Ummah da su Hannah basu sanar da ita tafiyar da iyayentan zasu yi ba, dan gaba 'daya Daddy ya hana kowa sanar da ita, bayan kwana biyu ranar wata litinin da 'karfe biyar na yamma jirgin su yatashi zuwa dubai tare da rakiyar Abbas daya baro bakin aikinsa anan cikin maidugurin dan yakusan sati anan 'din da aka kawo su, domin kwantar da tarzoma da irin matsalolin 'yan ta'adda dake addabar yankin na arewacin Nigeria musamman ma jihar Borno, koda zasu rabu ma su Daddy na ta sa masa albarka da zuba masa ruwan addu'o'i na kariya daga dukkan munafukai da mahassada dama dukkan wani abin 'ki musamman ma yanzu daya taho nan domin yin ya'ki da 'yan addacin 'kasar tamu ta Nigeria, da Ameen kawai Abbas ke amsawa dan shi kanshi yasani zuwa yin aiki a Borno a wannan zamanin shi yafi komai risk ga rayuwar duk wani ma'aikaci irin sa, zuwa borno awannan lokacin tamkar sai da rai ne, 'kalilan daga cikin ma'aikatan nasu kan ajiye aikinsu dazarar sunji cewa zasu jihar borno, masu 'karfin imani, zuciya da tawakkali sune ke aimincewa zuwan sa6anin Abbas da dakansa ya sa aka sanya sunanshi acikin jerin list 'din amatsayin jagoran batallion nasu, domin yana ganin zamansa a borno shi yafi masa dan yasan akoda yaushe zai kasance ne cikin shirin kota kwana tunaninsa zai kasance ne akan aikinsa akowani lokaci bazai samu lokacin tuna past dinsa ba yafi son yamanta da komai. Daga 'karshe Daddy yace masa _"Nabar Fateemah agidan mijinta bai san awani hali take ciki ba, yace Abbas_ _duk lokacin daka samu lokacin zuwa Abuja ka daure ka 'karasa ka dubo_ _min ita amma bawai nace dole sai kaje bane karka takura kanka sai in_ _kaga kana da lokaci sannan,"_ _" bakomai daddy insha Allahu zan 'ko'karta inje da iznin Allah."_ " _Yauwa Babana Allah ya ma albarka yabaka sa'a_ _adukkan al'amuranka "_ _"Ameen Daddy_ _nagode sosai"_ Kallon daddy yayi da kyau sannan yace " _Inason zuwan farko da zan sakeyi awannan 'kasar yakasance taron daurin auran_ _Babana nazo"_ Mummy najin haka ta dawo da kallonta ga Abbas din sai kuwa taga yayi shiru ya tsurawa Daddy idanu amma ga dukkan alamu hankalinsa da tunanainsa ba akan daddyn yake ba, sai daddyn ya dafa shi kafin ya dawo dai dai. _"Tunanin me kakeyi kuma ?,ina fatan dai kaji abinda_ _nafa'da"._ _" ehh naji daddy insha Allahu zan_ _'kokarta."_ Jinjina kai daddy yayi cikin farin jin kyakykyawar amsa daga bakin Abbas . Abbas sai da yaga tashin jirginsu kafin yajuya ya tafi yakoma bakin aikinsa yana me alhinin rabuwa dasu tare da tunanin dalilin dayasa su irin wannan tafiyar _.(safe trip mummy and Daddy)._ Daddy ya yanke wannan shawarar ne sanadiyyar tashe-tashen hankula da suka yi yawa a jihar yobe, har ya kasance akullum ba'a kwana atashi cikin kwanciyar hankali harin kullun da kalan yanayin sa, so 'yan uwa da dangi duk sun masa cha akan yabar garin ko dan yawan hare-haren da ake yawan kaiwa, da farko ya yi biris da maganar amma daga baya da yaga abin na neman yin yawa kawai da kansa sai ya aminche. Daddy ya shirya musu komawa Dubai 'din ne tun kafin ayi zancen auren Teemah, da maganar auren yataso ne kuma sai ya danne nashi 'kudurin azuciyarsa har sai da aka kammala komai ya mi'ka Teemah gidan mijinta kafin nan. *Ur comment is getting low, I feel like nima in 'dan huta, saboda gaskiya banjin dadi'n hakan da* *kukeyi* 😭. _Agyara pls_ 🤞🏻 _Nasan ana yi but_ _anunka_ 👌🏻 *inason ganin sharhinku kalakala ne dan idan ina karantawa ji nake kamar kar in daina wlh, INAYINKU IRIN......,,,,,,,,,,,,'Din nan .* 👎🏻 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _Never argue with a fool because People might not know the difference....._ 🅿 *57* Ciwon cikin Teemah da yamma ya 'kara dawo mata sabo fil, gashi ita ka'dai ce agida kuma har alokacin bata sha magani ba, data rasa yanda zatayi sai kawai ta fara kuka tana mirgine-mirgine dan tayi iya 'ko'karin ta dan ganin ta danne ciwon amma sai da ya fi 'karfinta tafara kuka. Acikin wannan halin Mahmud ya dawo gida ya sameta, ai kuwa jifa yayi da jakar dake hannunsa arikice ya kinkimeta yayi waje da ita be ma tsaya tambayarta dalilin kukan ba saboda yaga tana ta ri'ke cikinta tana mur'kususu, be manta ciwon datace cikinta yamata jiya cikin dare ba, shiyasa yana ganin ta awannan halin kawai ya nufi asibiti da ita. Allah ma ya taimaka ba wani nisa sosai ne tsakaninsu da asbitin ba, dan haka be 6ata lokaci akan hanyar ba, duk dama zuwa lokacin hold-up yafara taruwa amma dai yasamu ya isa akan lokaci, kanta ko mayafi babu lokacin da suka isa asbitin, amma duk wannan be zo kan Mahmud ba shi dai damuwarsa aduba masa lafiyarta a kuma bata magani. Cikin sa'a ma sai yasamu wani likita ya duba masa ita akan lokaci tare da yimata allurai guda biyu, cikin ikon Allah kuwa daga nan tasamu bacci ya 'dauke ta. Bayani likitan yamasa game da abinda ke damunta, da kuma yadda za'a magance shi cikin sau'ki, sosai Mahmud ya fahimce shi, dan shi da farko hakan ma be zo ransa ba sam, yama manta da cewar mata na irin wannan abin lokaci zuwa lokaci, dan ko data fa'da masa cewa jiya cikinta yayi ciwo ma shi zaton shi wata matsala ce daban be kawo hakan aransa, ko data masa 'karyar tayi sallah ma yau da safe be yi wani dogon nazari akai ba dukda yana da tabbacin bata yi sallar ba. Ya 'dauka ko abinda tasaba yi ne kullun cikin dare shiyasa ma yau daya fita ya 'kara zuwa wani 'kwararren asbitin daban domin asake duba masa lafiyarsa da kyau, yafi so yaji gamsashshiyar amsa game da matsalar dake damunsa, amma ako ina baya samun amsa mai kyau su kan tabbatar masa da cewa lafiyar sa 'qalau baya tare da wata damuwar da har zata hana shi amfanuwa, sai dai ko 'dan abinda ba'a rasa ba, ko yau 'din ma wasu magungunan daban aka sake rubuta masa tare da tabbatar masa abinda likitan daya ganshi da farko ya fa'da masa inda yabaro asbitin da zummar bada himma ga shan maganin ko dan matsalar da matarsa ke ciki domin kar ya kaita ma'kura, shikan shi yana so yaji kansa amatsayin cikakakken namiji yanaso mazantakar sa ta dawo kamar da, dukda ma acikin jikinsa baya ji kamar yana tare da wata matsala ajikinsa, jinsa yake garau, amma me yasa ba ze iya biya wa matarsa bu'katar ta ba bayan likitoci ma sun shaida cewa lafiyarsa 'kalau? Wannan abin na 'daure masa kai ba 'dan ka'dan ba. Baccin kimanin mintina talatin Teemah tayi sai ta farka, Mahmud tagani zaune agefen gadon da take kwance ya 'kura wa 'karfen gadon idanu, sai da ta juya ta kalli 'karfen sannan ta dawo da kallonta gareshi, _"Yayah "_! tace da dasashshiyar siririyar muryarta da bata gama warwarewa daga baccin da tashi yanzun ba. Mahmud be ji ta ba domin be amsa sunansa data ambata ba kamar yadda be kawar da idanunsa daga inda yake kalla tun 'dazun ba. Ganin haka yasa Teemah ta yun'kura ta tashi ahankali ta kai hannunta ta dafa kafa'darsa tare da sake 'kiran sunansa, juyowa yayi ya kalle ta take sai ya 'ka'kalo murmushi tare da dawo da dukkan hankalinsa gareta _" kin_ _tashi?_ Ya tambayeta yana 'ko'karin kamo hannunta dake kan kafa'darsa. Da kai ta amsa masa alamar " _ehh_ " " _Ya jikin naki_ ? Ya sake tambayarta da kulawa. Sai ta bashi amsa da fa'din " _na daina jin komai_ _yanzu"_ Fa'da'da murmushinsa yayi tare sa fa'din " _Masha Allah, ubangiji Allah ya 'kara sau'ki, zaki iya tafiya kuwa ko de na 'dauke ki?_ yayi maganar yana kallon cikin idanunta. _" a'a zan iya tafiya_ _ma da kaina_ " Teemah tabashi amsa tare da yun'kurin sau'kowa daga gadon, sai de bata kaiga ajiye 'kafafunta a'kasan ba taga gurin wayam ba alamar takalmin ta, sai ta juyo ta kalleshi tace. " _Yayah takalmi_ ! Mahmud kai ya dafe tare da fa'din " _oups, ni ai duk ma na manta, ko tunawa banyi da batamun takalmanba garin_ _sauri, kin rikitani sosai Fateemah har ma bansan inda_ _hankalina ya tafi_ _ba"_ Murmushi tayi masa kawai dan bata san mezatace dashi ba alokacin. Tambayarta ya sakeyi da fa'din _" yanzu ya za'ayi ne_ _toh ?_ sai tace yakoma gida ya 'dauko mata kawai sai yazo su tafi. Ido yazaro waje yace " _kina nufin wai har gida zan koma in kuma sake dawowa nan?_ Da kai tabashi amsa alamar _ehh_ , jijjiga kai Mahmud yayi tare da fa'din se kace bani da hannaye, yana maganaar yana 'ko'karin cicci6anta, be zame ko'ina ba, sai inda ya faka motarsa, daya ke already likita yariga yagama dasu yagama sallamarsu ,dama Mahmud zaman jiran farkawanta kawai yake su wuche gida. Dakansa yasata acikin motan sannan yazaga 'dayan 6angaren yashiga. Tun kan ya 'karasa daidai ta zamansa tafara fa'din _"alluran da wannan likin yamin fah akwai zafi sosai "_ tayi maganar tana kaiwa hannuta wurin da aka mata alluran tare da langa6ar da kanta . _"Eyyah sorry , very soon zaki daina jin zafin ai"._ _"Ni de karka 'kara_ _kawoni gurin nan Yayah ..........!_ _"Bana ma fatan 'ki 'kara yin ciwon har_ _abada"!_ Ya tari bakin ta da fa'din haka. Sai itama tace _"Ameen Yayah, Allah mutumin mugune, ai har nayi niyyan cizon shi danaga ya 'dauko allura kawai de_ _nabarshi ne yamin dan yanda cikina kemin zafi sosai, amma fah har guda biyu yamin dan mugunta"_ Murmushi yayi mata kawai tare da shafo fuskanta sannan yace " _Alluran ai shine daidai baki ga acikin 'kan'kanin lokaci kin samu lafiya ba"_ . Dai-dai wani babban store Teemah tace ya tsaya tana son ta siyi abu, kallonta Mahmud yayi da sauri yace _" ina fatan de ba dangin su choculates bane, dan doctor yace ki rage shan su saboda ciwon cikin nan naki"._ _" ah ah Yayah basu bane wani abu daban nake so"_ Sai da yayi parking agefe kafin yace ta fa'da toh yaje yakawo mata yanzu sai su wuce gida dawuri ko dan tasamu ma ta'dan huta gashi maghrib takusa. Teemah kuwa cikin shagwa6a tace masa. _"Ni fa zan sayo dakaina "_ Kwafa yai yana kallon ta da mamaki, ganin ta'ki ta fa'da masa abinda take so 'din sai yace mata _" ba_ _takalmi ba mayafin zakije "_ Jijjiga masa kai tayi tare da fa'din masa yanda za'ayi. Tana gama masa bayanin yafice amotar batare da yayi magana ba. Minti goma me kyau be yi ba yadawo da leda ya mi'ka mata, kar6a tayi ta ciro takalmin ta sanya a'kafarta dayake ya san size 'din 'kafar ma sai ba 'a samu wani kuskure ba, 'dan 'karamin mayafin dake cikin ledar takuma cirowa ta yafa shi akanta. " _Muje toh_" tafa'da tare da bu'de bangaren data ke zaune, shima fita yayi ya bi bayanta bayan ya dannawa motar lock. Dakanta ta 'debi duk abinda takeso Mahmud na gefe yana kallonta sai da aka zo wajen biyan ku'di kafin ya ga abubuwan da ta kwaso, harara ya doka mata sai ta kauda kai tare da yin fi'ki-fi'ki da idanu, tasan daman ai hakan sai yafaru shiyasa ma tace da kanta zata shigo dan tasan inshi 'din ka'dai ne yazo 'kin siya mata zaiyi. Be kulata ba yabiya ku'din tare da 'daukan ledan itama sai bishi abaya suka fito suka koma mota, har suka isa gida be 'kara yi mata magana ba. Data ga haka sai ta dawo kusa dashi lokacin yana zaune akan cough a palourn su, _" Yayah_ _inkawo maka ruwa kasha_ ? Be yi magana ba sai ya jawo ta zuwa gabanshi ya nuna ta yatsa yace _"wato_ _ke ba kya ji_ _ko?,_ _ciwon cikin be ishe ki ba ko"_ Hannayenta ta 'da go tarufe gefe da gefen fuskarta dan zaton ta marin ta zaiyi yanda taga yake maganar sosai yaso ya firgita ta. Ledar ya sa hannu ya janyo ya ajiye agabanta yace _" oyah fara ciro su 'daya bayan 'daya kina min bayanin su"_ Haka ta yi kamar yanda ya bu'kata amma sai da ta ciro su pads 'din data siya da farko ta ajiye ta ciro wani turare ma ta ajiye sannan ahankali tana kallon fuskarsa tafara ciro dangin choculate 'din data ta jida kusan kala hu'du. Harara ya doka mata yakai hannu zai kamo kunnanta take tayi saurin matsawa baya tace _" Allah Yayah sunmin kyau ne shiyasa fah na 'dauko, kuma fah sabon product_ _ne baka ta6a kawo min irinsu ba shiyasa ne 'debo, bama yanzu_ _zan sha ba sai na sami sau'ki"_ _"Waye yace miki sabo ne "_ ? Yafa'da atsawace Sai Teemah tace " _ni ai ban ta6a gani_ _bane"_ Mahmud 'kyaleta kawai yayi ya tashi ya wuche ciki domin ya watsa ruwa ajikinsa dan yasan inya biye wa Fateemah har ciwon kai sai ta sashi abanza. *Bayan kwana biyu* Mahmud sosai ya dage yana kula da shan magungunan sa akan lokaci saboda shi kansa ya 'kagu yaji shi cikin 'koshin lafiya, hakan yasa sam baya wasa da lokutan shan maganinsa ko agida ko a office baya ta6a sa6a lokaci. Acikin kwanakin kuma Anty Chideh ta ziyarci Teemah inda tasameta ita ka'dai agida saboda Mahmud na office ita ka'daice gida. Alokacin ma Teemah na kwance tana ta trying layin su Mummy taji baya shiga abin sosai yadameta ya 'daure mata kai, dan ko no. 'din Daddyn ta ma baya shiga a'yan kwanakin, kuma kullum haka takeji in ta 'kira su Hannah da Ummah kuma sai suce mata wai sede in matsalar network ne amma su kam wai suna 'dan yawan gaisawa da mummyn ko basu kira ba ita tana 'kiran Ummah su gaisa. Mamaki yakan cika wa Teemah zuciya, tarasa meyasa se da ita hakan zai faru, takan yawaita tambayar kanta _"toh me yasa Mummy zata 'kira kowa amma ni ta manta dani, ko dama in akayiwa mutun aure shikenan kowa agidansu mantawa yake da shi?........_ Tana cikin wannan halin taji door bell na kara, tsaki taja ta share kawai, sai da akayi tayi kusan sau uku kafin azuciye ta tashi taje ta bu'de sai taga wannan 'kawar Antyn ce tsaye ita ka'dai, dariyar ya'ke ta 'dan saki tare yi mata maraba da zuwa sannan ta bata hanya ta shigo ciki. Anty Chideh na gaba Teemah na biye da ita abaya, sai ta ta6e baki tare da 'karewa shigar Anty Chidehn kallo. Sanye take da wani ba'kin mini skirt wanda be ko rufe gwiwarta ba hakan ma da 'dan tsago ka'dan daga baya wanda hakan ya taimaka wurin ganin fararen cinyoyinta afili, sai wata riga wanda ta wadaci jikinta domin bata kamata sosai ba, yadin rigar kamar yadin material ne da zanen 'kananun flowers ja, kanta kuwa yasha fixing na ba'kin attachment irin wanda kana gani kasan hula ne ba gashinta bane ba. Duk cikin 'yan da'ki'ku tayi wannan lissafin sai ta ta6e baki tare da 'fa'din _" arnanci de beyi ba, har yaushe zaka rin'ka yawo da_ _irin wannan 'dan iskan kayan acikin gari kamar baka da mafa'di."_ Afili kuwa sai ta saki fuskarta tare da yiwa Antyn barka da zuwa, bata zauna ba sai data kawo mata abinsha Kafin nan ta zauna nesa da Anty Chidehn ta gaidata. Cikin fara'ah ta amsa mata sannan ta tambayeta ya zaman gida Teemah ta amsa da " _lafiya_ ' _kalau"_ Sake tambayarta tayi wai ina Mahmud sai *Teemah* tace " _ya_ _tafi office"_ Jinjina kai tayi tana murmushi, 'yar hira ka'dan taja Teemah dashi ganin Teemah bata saki jiki sosai da ita ba yasa bata da'de ba ta mi'ke da niyar zata tafi Teemah ma mi'kewa tayi tsaye kamar yanda Anty Chidehn tayi. Sai alokacin data mi'ke sannan ta lura da irin she'danin kallon da Anty Chideh ke binta dashi musamman ma 'kirjinta daya kasance ana 'dan ganin kusan rabinsa awaje dan wata armless red top ne ajikin ta mai bu'dadden round neck wanda ya 'kara bayyanar da haske fatarta afili, ba karamin kar6an jikinta rigar tayi ba, ta sanya shi da wani jeans trouser daya kama jikinta sosai, gashi kanta ko 'dan kwali babu gashin kawai takama da wani 'karamin jan ribbom ba mayafi balle tacire ta lullu 6a dashi. Afakaice ta samu taja rigar sama yarufe mata 'kirjin sannan tama ta rakiya iya bakin parlourn tadawo ciki tare da jan wani uban tsaki. Wayarta ta 'daga ta buga shi akan kujera kamar shine Anty Chiddyn afili tace " _Duk sharrin wayar nanne, in bahaka da nasan bazan manta 'dauko mayafi ba balle har matar nan ta ganni ahaka ba, kamar mayya sai ta ta kallon mutum tana_ _murmushi_ ." _Your Comments always encourage me, pls kar ana manta wa........I heart u all_ *CAPTAIN ABBAS* *COMMENTERs* , _Allah yabar 'kauna._ _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmern ku ce* 😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _NO matter how talented you are, not everybody is going to like you, but that’s life, just_ _stay strong and always be your self_ . 🅿 *58* Washe gari ma haka Anty Chideh tazo wurin Teemah bayan Mahmud yatafi office. Yau ma daurewa Teemah tayi ta kar6eta hannu bibbiyu ba yabo ba fallasa ta 'dan saki fuskarta, sai de yau 'din Anty Chiddy cewa tayi da Teemah wai zata na zuwa kullum tana tayata hira tunda ita ka'dai take wuni agida, Teemah murmushi kawai tamata batare da ta bata kykakkyawar amsa ba, dazata tafi yauma Teemah iya 'kofar parlour tayi mata rakiya amma duk da haka Anty Chiddy kasa ha'kuri tayi har se data 'dago hannu ta shafi fuskar Teemah tare da fa'din _" I really love u"_ 'kasa-'kasa tayi maganar, Teemah kuwa rintse idanu tayi cikin takaici, sannan ta 6ata ranta afili hatta Anty Chiddy ta lura da hakan amma itan kuma sai tayi murmushi ta 'kara 'dago hannu da niyyar shafo la66an Teemahn daya ke matu'kar 'dauke mata hankali a kowani lokaci sai Teemah tayi baya da sauri, Anty Chiddy ganin hakan yasa kawai tajuya ta tafi aranta tana kissima ranar da aka ce tasamu wannan yarinyar ahannu, ga dukkan alamu she is hot, tace ha'kurinta yakusan 'karewa akan yarinyar bazata iya jira har se lokacin da sukayi sabo da ita sosai ba sannan tasameta kamar yadda mum Mahmud ta ce da ita, afa'dar ta in har tace hakan zatayi zuciyarta ze kusan bugawa ne abanza, tace gara taje tasamu mum Mahmud su sake shawara dan she is in need of her, she so much love the girl yadda ita kanta batasan yaushe hakan yafaru ba, bata da buri ayanzu daya wuce taga ta samu yarinyar a hannu. Teemah kan takaicinta na yau na musamman ne dan ita ka'dai tasan yadda takeji azuciyarta , dama akwai damuwar rashin samun iyayenta da bata yi awaya daya matu'kar tsaya mata azuci, ko da ta yiwa Mahmud maganar kuma shima sai ya nuna mata rashin damuwarsa akan hakan, sai ma ya tabbatar mata da matsalar network ne kawai bakomai ba, tana cikin wannan takaicin kuma Anty Chiddy tazo tasake jagula mata lissafi, ita ka'dai sai zuba tsaki takeyi, haushin Anty Chideh da haushin abinda tamata duk yabi yacika mata zuciyarta, wani mugun 'daci takeji aranta, taci alwashin sanar da Mahmud damunta da matar nan takeyi dan ita baso takeyi ba gara ayi mata magana ta daina zuwa gidannan tunda ita bata san girma da arzi'ki ba. Sai akayi rashin sa'a kuma ranar Mahmud be samu yadawo gida da wuri ba, sanadiyar aiki da ya musu yawa a office, hakan yasa be shigo gidan nasa ba sai kusan 9:01pm ya dawo, alokacin ma Teemah harta fara yin bacci. Koda yadawo a parlour yasameta kwance tana bacci, da shigowarsa kuwa ta ta shi ta zauna ta na mar barka da isowa. Zama yayi agefenta tare da sakin ajiyan zuciya ga dukkan alamu amatu'kar gakiye yake, Teemah ma bata bu'katan wani 'karin bayani saboda tun da yamma ya 'kirata yayi mata bayanin abinda ya ri'ke shi a office 'din, awa biyu da suka wuce ma ya 'kara 'kiranta yaji lafiyarta hakan yasa bata wani damu ba yin daren nasa, duk dama tana 'dan jin tsoro amma zuwa yanzu dolenta ta'dan fara sabawa da zama ita ka'dai agida. Ruwa Mahmud yaje ya watso ya dawo parlourn da niyyar yi mata magana akan ta tashi ta koma bedroom ta kwanta, sai yasameta ma harta koma bacci abinta, kyaleta yayi dan shi be fiya son tada mutun ba idan yana bacci dan haka sai yaje shima yakwanta aparlourn akan doguwar kujera bayan yagyara mata nata kwanciyar tare da gabatar da duk wani al'adunsa daya saba yi kafin yayi bacci. Kamar kullun yauma yana kwanciya bacci me shegen nauyi ya 'dauke shi da be san inda yasamota ba, badan ma ya kasance yana da iyali ba, da bazai ta6a sanin cewa yana irin wannan baccin ba saboda ada idan yariga yayi bacci toh yatafi kenan domin shi bashi da irin al'dun tashi cikin daren nan, ko nafila zaiyi yakanyi ne kafin ya kwanta bacci sai de hakan.baya hana shi sanin duk lokacin da ze juya cikin baccin ko kuma yaji motsi ya farka, amma yanzu sam baya 'kara sanin ina kansa yake da zarar ya 'dora jikinsa a makwanci, kasancewar yana da Teemah akusa dashi ne tasa yagane mummunar lalurar daya ke tare da ita da be san tsawon yaushe yafara ta ba, abakinta yake fahimtar wannan sabuwar lalurar data sameshi, mamaki yake yi idan gari ya waye yaga ta canja wurin kwanciya ko kuma yaga ta bar 'dakin ma gaba 'daya. Sau tari yakan ji kunyar kansa da kansa idan tafara yi masa mitan ya'ki yi mata abu kaza da dare ko ya'ki yi mata kaza sai yasaki baki kawai yana kallonta, akullum so yake ya nemo mafitar wannan abu amma ya rasa, bayan yasan sarai shi bahaka yake ba. Da gari yawaye yau kam da sauri-sauri yayi kominsa yagama, ya fita daga gidan tun 7:o clock dan baya son Teemah ta samu chance 'din yi masa complain akan wani abu daya faru cikin dare domin hakan na matu'kar sanyaya masa jiki da zuciya, be san wani irin ha'kuri ze jero mata ba, shiyasa yafice da wur wuri batare da ya bata wani 6ari daga cikin lokacinsa dazata yi anfani dashi wurin kawo 'kararsa wa kansa ba, toh wani irin hukunci yakamata inyiwa kaina tunda kullum nine me yin laifin kuma ni ake kawo wa 'kara, Mahmud tun yanzu su fara 'yar hakan ba, tun ba'a je ko'ina ba su fara wasan 'yar 6uya da ita ba amma gani yake yi inbahakan yayi mata toh akullum kunyarsa gareta 'kara 'karfi zai rin'ka yi, saboda bashida wata mafita, sai de akullun yana ro'kon Allah ya ye masa wannan matsalolin da suka kunnowa rayuwarsa wuta suke son su hanashi sakewa da walwala shida iyalinsa, dan zuwa yanzu abubuwan sun fara zarce tunaninsa dole ne ya nemi mafita, mafitar dazata 6ille musu gaba 'daya batare da an shiga hakkin juna ba, aransa ya ayyanacewa idan yadawo gida ayau duk zai zauna su fahimci juna da ita, ze yi mata bayanin matsalolin daya fuskanci yana tare dasu in yaso ita tasani, saboda ta daina zarginsa da yawan shareta dayakeyi cikin dare wata'kilha ma inta fara saka shi acikin addu'arta sai yaga yasamu sassauci. Da burin hakan ya'kara office 'din su, yana zuwa kuwa yaga aiyuka sun taru masa dayawa saboda rashin kula dasu sosai da baya yi acikin 'yan kwanakin. Rarrabasu yayi wa'danda ze sa hannu da wa'dan da ze tura su ne zuwa wani guri da kuma wa'dan da zai 'dora a Internet. Signing 'din yafara sai de be yi nisa da yi ba wauarsa tafara 'kara , ajiye biron dake hannunsa yayi sannan ya 'dauki 'kiran, Abbas ne ya 'kira shi suka gaisa atakaice dashi ya tambayi lafiyar kowa, sannan ya 'kara da fa'din suk lokacin da yasamu lokaci da iznin Allah ze ziyarce su. Sosai Mahmud yaji da'din furucin Abbas 'din har ma yakasa 6oye murnarsa sai da bayyana ta har Abbas yagane. Mahmud yaso yayiwa Abbas maganar abinda ke damunsa amma daya tuna cewa sirrinsa ne, sirrin auren sa kuma Abbas tamkar wa yake agurin Fateemah so da kunya ace yasana sirrin zaman aurenat irin wanann dan haka sai yayi shiru kawai yayi tagumin yana tunanai bayana sun gama waya da Abbas. Fitar Mahmud daga gida agag gaucen ne ya dakatar da Teemah ga fa'da masa abinda tayi niyyan sanar da shi, amma duk da haka bata ha'kura ba dan har ga Allah ita bata son damuwa, matar nan kuwa tafara shiga rayuwarta ta inda bata so, so take ayi musu tsakani kowa yayi rayuwarsa yadda yakeso. Wani abokin Mahmud a office 'dinsu ne wanda yakasance mataimaki ne ga Mahmud 'din mai suna Umar yashigo yasame shi da tarin files agabanshi amma yayi zugum yana aikin tunani. Umar ' dan asalin garin katsina ne aiki yakawo shi nan garin Lagos har suka ha'du da Mahmud kuma sukayi sabo da juna dai-dai gwargwado, domin har damaturu akaje dashi wurin 'daurin auren Mahmud. Umar yanada mata har da 'yaransa guda biyu mace da namiji inda yake tare su anan garin Lagos 'din. Ya nemi jin asalin meke damun Mahmud ne saboda yawan samunsa cikin damuwa da yakeyi a office musamman ma dayake shine mataimaki agare shi so yakan sha ganinsa cikin halin tunani da damuwa. Bayan 'dan nazari da Mahmud yayi sai yaga dacewar sanar dashi matsalar daya ke ciki wala Allah ko ze samu kyakkyawan shawaran da zata anfane shi. Umar kansa dayaji matsalar dake damun Mahmud 'din kansa sai da ya 'daure domin hakan be fiya faruwa ga mutane ba, sai dai ko in da akwai wata matsalar ta daban wanda takasance sirri ne 6oyayyiya. Jin dayayi Mahmud yace masa ya ziyarci likitoci a'kalla kusan guda uku amma duk furucin bakinsu iri 'dayace kamar sun ha'da baki sukance azahiri baya tare da matsalar komai, sai yace da Mahmud toh inkuwa hakane sai ko aljanu ke son hana ka sakewa, sai de insune ke son shiga rayuwarka inbahaka ba kuwa samo dalilin ze yi matu'kar wahala tun da shikanshi Mahmud 'din ya shaida akan cewa bahaka yake ba ada, yasan kansa da yawan bu'katar mace amma yanzu rabonshi da ya tsinci kansa a irin wancen halin ma har ya manta, sosai Umar yake jinjina lamarin tare da tausaya wa abokin nasa. Daga 'karshe shawara Umar yabashi akan cewa matu'kar yanason zama da matarshi toh dolene ya nemi mafita, mafita wacce zata 6ille musu. Mafita a garesu kuwa za6i biyu ne acikinsu kuwa dole sai anyi 'daya domin zama haka ba zai ta6a haifar musu 'da mai ido ba babu anfani sam, dan haka ya za6a ko ya saki matarsa taje ta auri wani namijin lafiyayye wanda ze iya da bu'katun ta, ko kuma yatashi tsaye ya shiga neman magani, ma'ana magani ingantacce wanda musulunci ya yarje mana muyi anfani dashi, Umar yace " _a dun'kule dole ne ka nemi sanannun malamai abokina, kuma ashawarce inaga yakamata iyayenka su san halin da kake ciki tun yanzun ko dan gudun abinda zai je yadawo duk dama ba'a fatan komai marar kyau amma dai ka sanar dasu wata'kila za'a sami wata mafita daga 'bangarensu"_ Sosai Mahmud ya gamsu da bayanan da Umar ya masa daga 'karshe godiya yai binsa dashi domin Umar ya tunasar dashi abinda yakasa tunawa da kansa, kalaman Umar 'din sosai sukayi tasiri azuciyar Mahmud, domin shi hankalinsa be je ga neman magani ta wannan 6angaren ba face da Umar ya farkar dashi hakan, yace zasu sake zama da Umar 'din insha Allahu. ***** Aranar da Teemah tacika kwana hu'du tana fashin sallah kuma aranar tayi wankan tsarki tacigaba da ibadar ta kamar kowa. Allah cikin ikonsa kuwa adaren ranar kusan 'karfe biyu kamar an tsikareta ta tashi cikin wani matsanancin sha'awa idanunta har basu iya bu'du wa gaba 'daya ga marar da take jinsa a dunkule guri guda. 'Yar rigar baccin dake jikinta ta fincike shi tayi jifa dashi sannan ta cigaba da juye-juyenta cikin matsancin damuwa, ahankali ta jawo jikinta ta dawo kusa da Mahmud tashige cikin jikinsa amma tamkar gawa be san tanayi ba, haka tayi ta lalu6an jikinsa, amma Mahmud kam ko motsin kirki beyi ba, daga kuka tafara abin tausayi tun tana yi na zallan hawaye har tadawo yi da sheshsheka, da kukan ta kwana ajikin sa har zuwa sallar asubah. Mahmud yarigata farkawa dan haka yana tashi sai ya ganta ta cusu acikin jikinsa kuma har alokacin bata daina ajiyan zuciyan kukan da tayi cikin dare ba, Mahmud dafe kai yayi yana jin ba bu da'di aransa, dan sosai yarinyar take bashi tausayi musamman idan yaga tashiga irin wannan halin, danma yaga ta 'dan kwana biyu bata yi ba, acikin kwanakin ko ya tashi baya ganin alamun sauyi atattare da ita, har yana jin da'di sai kuma kwatsam yau abin yasake tashi mata. Ashe muguwar sha'awar da ke damun Teemah yana bin yanayinta, domin lokacin data ke cikin rashin tsarki ko ka'dan sha'awar bata tashi mata ba, ko dan lokacin ko tayi bazata samu biyan bu'kata bane oho, sai yanzu cikin ikon Allah gashi tana yin tsarki sai ya tashi mata. Ahankali Mahmud ya janye jikinsa daga nata sannan ya janyo mayafi ya lullu6a mata ganin jikinta bakaya. Zuciyarsa cike da tausayinta har ya gabatar da sallarsa, bayan yayi addu'o'i da dama yashafa ne sai ya tasheta ahankali cikin sanyin jiki. Ahankali ta tashi tare da jero salati azuciyarta kana addu'ar tashi daga bacci ya biyo baya. Kwata-kwata ta manta da cewa babu kaya ajikinta har sai data mi'ke zaune, ganin irin kallon da Mahmud yake binta dashi ne yasata ta kalli jikin nata itama. Da sauri ta kai hannu ta janyo mayafin ta kare jikinta dashi Mahmud kuwa sai ya yi 'kasa da kansa cikin kunya. Ehh kunya mana tunda shi be yi mata anfani alokacin data ke bu'kata ba yanzu kuma yazo yana bin jikinta da kallo. Teemah sai da ta rufe jikin kafin tafara recalling abinda yafaru jiya da da dare, tsaki taja acikin ranta, zuwa yanzun abin Yah Mahmud 'din yafara bata haushi, dan me yasa yake share ta kullum bayan cikinta sai ya tadata da ciwo acikin daren meyasa sai 'kyaleta tayi ta fama bazai ko kawo mata magani ba, gashi har garin ciwon cikin ta cire rigarta daga jikinta bata sani ba. Duk wannan abinda da takeyi 'din ita aganinta ciwon ciki ne kawai da 'kullewar mara ke damunta, domin ita bata san wani abu wai shi sha'awah ba, ko lalu6an jikinsa datakeyi tana yine ayanda zuciyarta ta raya mata kuma take jin tana matu'kar son haka koma fiye, har ma takejin kamar zata samu sassauci idan Mahmud ma yamata irin yadda takeji tanaso 'din, bazata iya fa'dan asalin meke damunta ba alokacin domin wanda takeji azahiri shine yafi damunta, sai de da ace zata samu kamar yadda jikin nata ke so bazata ta6a 'ki ba sai ma ta'kara kaimi wajen ganin bu'katar tata ta biya. Da mayafin ta tashi ta wuche taje ta 'dauko rigarta sannan sai da ta sa shi ajikinta kafin tacire mayafin ta na'de shi ta ajiye, ko magana.bata masa tayi wuche warta toilet domin yanzu haushin Yah Mahmud take ji aranta. Shima Mahmud shawara yayi da zuciyarsa ganin kamar yafara kaita ma'kura tunda gashi tafara canja masa fuska dan harta zo ta idar da sallahn ta bata yi masa magana ba, sai da ta idar tagama addu'o'inta kafin ta ce masa " _ina kwana_ " atakaice, shima.da " _lafiya_" kawai ya masa mata yana fargabar sake yi mata magana domin be san meke cikin zuciyarta ba, yana nan azaune agurin yaga ta wuce parlour tabarshi a'dakin shika 'dai. Dafe kai yayi yana.tausaya wa halin da rayuwa take shirin jefa su aciki, take agurin ya yanke shawarar zama su da ita su fahimci, domin tasan halin da yake ciki tasan cewa ba laifinsa bane duk abninda ke faruwa wala Allah ko zata rage haushin sa data ke ji ta fuskoki da dama, inyaso sai su cigaba da addu'ah tare ko Allah zai tausaya wa rayuwarsu ya kawo masa sau'ki, amma sai ya dawo daga office sannan suyi maganar yamzu kam binta zai yi ayanda take so har yasamu yatafi. 11:30am su Anty su ka shigo gidan lokacin tana kan waya da Ummah tana sake yi mata complain na rashin samun wayar Mummy da Daddyn ta da batayi kamar zatayi kuka take maganar, Ummah kuwa sai ha'kuri take ta bata tare da fa'din ta bari idan Daddyn su yadawo zata fa'da sai yaje har damaturun yagani ko lafiya..... Suna cikin yin wayar taji 'karar door bell, 'kin kulawa tayi aranta ta ayyana cewa wannan jara babbiyar matar ne yau kam bazan bu'de ba. Ci gaba tayi da sauraran Ummah har suka gama wayar sannan taci gaba da buga game 'din Candy crush da wayar. Can taji shiru door bell ya daina ya 'kara afili ta furta " _yafi miki._ " Befi 2hrs ba taji ana sake danna bell 'din sai taja uban tsaki tare da tashi ta le'ka tajikin 'kofar,Anty ta hango tsaye ta qajen da gudu takoma 'daki ta burmo hijab akan kayan jikinta sannan ta tazo ta bu'de 'kofar. _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmern ku ce* 😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _Success means having the courage, the determination, and the will to become the person you believe you were meant to be._ 🅿 *59* Anty (mahaifiyar Mahmud) ce agaba dan haka ita ta far kutso kanta ciki, bayanta kuwa Anty Chiddy ce data bi tagama rikice wa da tunanin abinda yasamu Teemah , dan dataga ba'a bu'de mata 'kofar ba 'dazu tana barin nan gidan Anty direct ta nufa tayi mata bayanin abinda ke faruwa arikice don ita zatonta ma ko wani abu ne yasamu yarinyar shiyasa, amma Anty sai bata wani damu ba tace iskanci ne kawai ke damunta ba wani abu ba duk da haka Anty Chiddy sai da ta tattago ta suka zo tare. Anty na shigowa tafara bin Teemah da wata muguwar harara tare da ta6e baki gefe, Teemahn na musu barka da zuwa ma amma Anty ko kulawa batayi ba tace da Teemahn" _hamsha'kiya amaryar Mahmud....., ashe kina ciki?_ da wani dirty look ta ha'da tayi maganar tata. Jikin Teemah sosai yayi sanyi da yanayin Antyn amma duk da haka sai ta daure ranta ta 'daga mata kai cikin sanyi tace " _ehh Anty, ina_ _nan"_ Muryarta har crashing yake lokacin datayi maganar . Anty sai ta ta6e baki ta juya ta kalli 'kawarta tare da nuna wa Teemahn ita tace _" wace_ _wannan awajena_ ? _" she is your friend "_ Teemah ta bata amsa da rawar baki. " _me na fa'da miki game da ita_ ? Anty tasake dokawa Teemah wata tambayar tare da kure ta da idanu. Teemah kuwa yanzun sai tayi shiru ta sunkuyar da kanta 'kasa hannayenta sar'ke cikin junansu batayi magana ba. Anty kuwa haushi hakan yabata dan haka sai ta daka mata wani uban tsawa akanta daya matu'kar firgita Teemah sannan ta sake maimata tambayar tata ga Teenma cikin masifa. Take idanun Teemah suka fara tara 'kwalla jikinta yafara rawa. Anty kuwa sai ta fara kewayata tana 'kara nazarin Teemahn sannan ta wuce taje ta zauna akan cushion ta 'dora 'kafa 'daya kan 'daya kamar wata me fa'da aji.. _" Zo nan ke !_ Tasake dakawa Teemahn tsawa hatta 'kawarta se data juya ta kalleta, Teemah kuwa se ta juya tatafi ahankali ta zube akan gwiwoyinta ta zauna, ta sake yin 'kasa da kanta, tsoron Antyn yagama cika mata zuciya ayau 'din dan bata ta'ba sanin cewa 'dayan side 'din Anty haka yake ba, sosai takejin wani iri gameda hakan duk da ma bata san taka mamman abinda ta mata ba ko kuma abinda ke faruwa ba bata san wani laifi tayiwa Antyn ba, sai de tana kyautata zaton wannan arniyar ce takai 'karanta gurinta. Anty Chiddu ma takowa tayi tazo ta zauna gefe da Anty tana idanunta akan Teemah. Tana cikin tunanin ta tsinkayo muryar Anty na fa'din " _har ke kin isa kinyi girman da zaki ja da maganata ko?, toh bari kiji uwar data haife ki ma bata isa tamin gadara ba domin ba'a bakin komai take wurina ba balle kuma ke......... kuma kisani baki isa kice zaki hana duk wanda yayi ra'ayin shiga gidan nan shigansa ba saboda baki da wannan damar, kinyi ka'dan, wannan da kike gani tamkar nice.......tamkar mahaifiyar Mahmud take......inajin da kaina na tako musamman nazo nayi miki bayani_ _akanta shine kuma zaki ce zaki hanata shiga gidan_ _nan?.......,_ 'Kwafah tayi tare da jijjiga kanta sannan tacigaba da fa'din " _daga yau baki da wannan ikon Fateeema, banyarda ba_ _kuma ban amince ba ma daga yanzu a'kara saka lock a'kofar nan saboda akowani_ _lokaci zaki iya ganin ba'ki wa'danda zasu zo musamman saboda ke, sannan kisan wani abu guda karki ga tun_ _zuwanki ban nuna miki asalin ko wacece ni ba ki saki ranki cewar kinsanu wurin zama harma_ _hakan yasaki za'kewa ki zarce huruminki, tace bakomai ne yasani yin sanyi ba face wani gagarumin_ _tanadi da na miki me ban mamaki kuma inafatan kin shirya tar6arsa_ _kamar yanda kika shiryawa zama amatsayin matar Mahmud"_ Ta 'karashe da wata muguwar murmushi tare da mi'kawa Anty Chiddy hannunta 'daya alamun kar6ar abu. Teemah kam kanta na 'kasa inbanda kuka babu abinda takeyi, ita duk ma ba wannan surutan Antyn bane suka dameta, tunaninta nacan wurin iyayenta data rasa samun ji daga garesu ta kowani kafa. Anty Chiddy tablet 'din dake hannunta ta mi'ka wa Anty. Fuskar Anty cike da murmushi ta ke duban cikin tablet 'din, wasu 'yan shige-shigen ta 'danyi sannan ta 'dago ta mi'kawa Teemah tablet 'din tare da fa'din. " _kalli kigani amaryar Mahmud............. wannan shine_ _babban tukuicinki na amincewa auran 'dana 'daya tal danake_ _dashi................wato_ _Mahmud"_ Hannun Teemah na rawa ta'dago ta Kar6i Tablet 'din, bata san menene ba, bata san me zata gani ba amma kawai sai ta tsinci zuciyarta da harbawa da 'karfin gaske. Ahankali ta sau'ke idanunta akan wayar abinda idanunta ya sau'ka akai ne ya matu'kar gigita numfashi da tunaninta, take sai ta rintse idanu wasu zafafan hawaye na rashin gata suka gangaro mata take sai ta fara jero istighfari azuciyarta na kallon abinda bata ta6a tunanin wanzuwarsa ba. Dukkansu suka dawo saitin kanta suka tsaye dan mugunta Anty ta daka mata wata uwar tsawa akan wai dole ta bu'de idanunta ta kalla da kyau saboda so ake ta koya, daga yau akai zata fara practice akai." Teemah hawaye kawai take fitarwa jikinta na mugun rawa tsoron Anty na 'kara 'karfafa azuciyarta badan haka ba da babu abinda zai sa ta bu'de idanun nata akaro na biyu, ahakan ta bu'de idanun ta sau'ke su akan Fuskar tablet 'din, ganin yanda wata baturiyar mata ta kwanta tsirara ta bu'de 'kafafunta wa wata wacce itan ma takasance irin ta domin dukkansu babu komai a jikinsu tana sucking mata hq ita kuma sai nishi takeyi tare da shafa kan lespartner 'din nata ga dukkan alamu ba 'karamin enjoying take yi ba, abin ba kyan gani ko ka'dan. Duk cikin 3 to 4 seconds tayi wannan nazarin tana gamawa kuwa ta kife tablet 'din tare da sakin wasu sabbin zafafan hawaye helplessly idanunta a rintse. Bazata iya kallon wannan abin 'kya mar ba koka'dan koda kuwa Anty kasheta zatayi bazata ta6a iya 'kara gani ba, abin har tashin zuciya yake sata ayanzun jitake yi kamar zatayi amai. Da rawar murya tace _"Anty dan Allah... kiyi ha'kuri....... wal..lahi bazan iya kallon wannan abin....ba kuma babu kyau ma mu....tun yaga tsiraicin wani Allah ya haramta mana kuma ya tanadar da azaba mai ra'da'di ga me aikatawa"._ Dariya Anty tasake na ban maki tana tafa hannaye tace _" Sannu Alshekiya uztaziya Fateemah......toh ki sani wa'azinki be samu shiga ba, and wannan abin da kike gudun ganin ina tabbatar miki da cewa yariga ya kusanto ki, is better ki fara shirin tararsa kamar yanda na gaya miki cewa tukuicin kine_ _hakan kinga kuwa dole na baki"_ Kuka Fateemah ta rushe dashi mai sauti cikin kukan take ce da Anty ita wallahi ta yafe bata son wani tukuici ita a kaita wurin Mummynta kawai dan Allah". Dariya Anty tayi cikin mugunta tace " _ki kwantar da hankalinki 'yan mata....dole ai zaki koma gidanku_ _amma kafinnan sai na sabauta rayuwarki na_ _wula'kantaki nasa kin zama abin gudu da 'kyama acikin mutane yanda duk_ _wanda yasanki abaya inya ganki sai yayi ko kwanto......... "_ Da sauri ta matso da kanta kusa da Teemah tana kallon fuskarta tace _"Kin san dalili?_ Teemah bata iya bata amsa ba illah baki data sake tana kallon Anty da mamakin irin muguwar nufin data ke dashi akanta. " _anya Anty kece_ _kuwa_ ? Ta yi tambayar asaman la66anta badan tana neman jin amsa ba sai don yanda kanta ya daure. Amma Anty sai data jiyota dan haka sai ta mi'ke tsaye tace " _idanunki ne ko zuciyarki ke son sanin asalin ko ni wacece?_ _" hmmm"_ ta murmusa daga gefen bakinta sannan taci gaba da magana in a serious tune inda tace " _baki gama tabbatar da ko wacece mother-inlaw 'dinki ba ko?, toh let me clear up_ _your doubt"_ kirjinta ta nuna tare fa'din _" sunana Maryam matar kawunki Yusuf kuma mahaifiyar mijinki Mahmud, sannan wannan da kike gani itace lespartner 'dinki as from now kuma banson taurin kai and you must obey my rules in bahaka ba..........kasheki zanyi Fateemah in kuma binne gawarki_ _yadda babu wanda zai 'kara sanin labarinki da abinda yasameki_ ." Kukan Teemah sosai ya tsananan ta ta ha'da hannaye tana ro'kon ta tana bata ha'kuri akan bazata iya ba pls karta kasheta ta barta ta tafi wurin Mahaifiyarta. Anty ko kulata bata 'karayi ba ta juya abinta ta koma ta zauna. Anty Chiddy ne ta iso wurin Teemahn da sauri tafara 'ko'karin share mata hawaye tana fa'din " _it's ok babe.... stop crying huh........please just trust me i only_ _love u I ll not going to harm u ok...."_ Teemah duk da hankalinta yagama tashi amma hakan be hanata kau da kanta gefe ba tare da yiwa Anty Chiddyn wata muguwar harara. Ashe Anty na kallonta sai kuwa tace " _gara ma ki saki jiki yarinya ki fara 'daukan darasi domin bagudu babu ja da baya wannan tamkar cikar_ *BURINA NEH!!* ". Tana gama fa'din hakan ta tashi ta nufi 'kofar fita, harta kusa barin 'dakin sai kuma ta juyo ta dawo baya, tsayuwa tayi ta fuskanci Teemahn sannan tace _" ban baki izinin sanar da kowa abinda yafaru ba da ma wanda zai cigaba da faruwa,_ _ciki kuwa harda Mahmud da duk wani wanda kika sani, idan kika sake wani yasanda_ _labarin nan wallahi Fateemah yanka wuyanki zanyi da_ _wu'ka inkuma farka cikinki inba karnuka hanjinki,_ _kuma kar ki kuskura kiyi mata gardama like I told_ _u before nasan ai baki_ _manta ba"._ Idanunta ta mayar kan Anty Chiddy tace _" in 'taki baki ha'din kai ko tayi miki gardama pls let me know"_ Tana gama fa'din haka ta wuce ta tafi abinta. Teemah kam kuka takeyi tunda Anty ta tafi kusan mintina ashirin tana ta kuka abin tausayi sai yanzu tafi jin ba'kin cikin rashin samun mummy awaya, inba dan haka ba da babu abinda zai hana ta sanar da mummy sai de in kashetan zasuyi su kashe, amma yanzu wa take dashi , waye yarage mata?........Tasan idan tasanar da Mahmud toh dole ne Anty tasani domin ayanda tasan halinsa ba shiru zai yi ba shikam zuwa zai yi yasamu Antyn wanda hakan dai-dai yake da tsayuwar numfashinta. Tun tana kukan da sauti harta komayi azuci Anty Chiddeh kuwa tagumi kawai tayi ta zauna jigum tana kallonta, acikin ranta takejin babu da'di, saboda kukan Teemahn ba 'karamin 'daga hankalinta yake ba, ita haka kawai ta tsinci kanta da son yarinyar kuma bata jin zata iya janye ra'ayinta koka'dan akanta tariga tasanyawa ranta sha'awar kasancewa da ita amma ga dukkan alamu hakan ba ze faru ayau ba, dole ne tayi mata uzuri zuwa wani lokaci kafinnan ta warware, in hakan ya'ki yiyuwa kuwa zata yimata na dole ne koda ranta be so she can do anything just to have her as her lover. Taso ta rarrasheta akaro na biyu amma Teemah ta nuna mata 'kyama da tsana azihiri dan haka kawai sai ta tashi tafice ri'ke da tablet 'dinta ahannu. *Toh fah readers* ~Yah kuke ganin~ ~abin zai kasance ne.....?~ ~Shin Teemah zata amince da 'kudurin Anty ko kuwa akasin haka?~ ~Menene ma'kasudin~ ~na'kashewar Mahmud~ ? ~Zai sami magani~ ~~ko a 'a?~ Wai shin ina labarin~ *Captain* ne ? ~Shin akwai yiyuwar aure atsakaninsa da Fateemah ko~ ~a'a?~ ~Ku dai kuci gaba da~ ~biyoni domin~ ~jin 'karashen labarin~ *CAPTAIN ABBAS* _Ga duk mai bu'katan farkon labarin zai iya garzayawa shafina na wattpad @_ *Serlmerh-md* . 🤞🏻 _Sai kuma idan Allah ya kaimu bayan sallah da rai da lafiya zamu 'dora daga inda muka tsaya._ ~MASOYANA ACIGABA DA GASHI SUYA SAI RANAR~ ........... *ohh namanta ashe ma lokacin Gashi da suyan yazo* 🤣 _kar_ _dai amanta_ _da nawa kason_ . 👎🏻 ~HAPPY EID' EL KABIR ( SALLAR CIN NAMA) IN ADVANCE.~ 😃 👇🏼 *ouww na manta ban sanar daku ba..... kowa yarage min nawa share 'din zan kaifa ha'kwarana sosai na kuma zauna da babban daro na domin nasan* *nama sai ya isheni.* hhhh🙈 *SALMERH NAYI MUKU FATAN ALKHAIRI* 🤞🏻 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmern ku ce*😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Indedication to all muslim Ummah..... brothers and sisters in islam_ *HAPPY EID'EL* *KABEEER* 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _Ability is what u’re capable of doing, motivation determines what u do, and attitude_ _determines how well_ _u do it._ 🅿 *60* Da yamma Mahmud yadawo gidan kamar yanda yasaba dawowa a mafi yawan lokuta, kallo 'daya yamata ya fahimci bata cikin hayyacinta duba da yadda idanunta suka 'kan'kance suka kuma yi ja tare da yin luhu-luhu, ga kuma fuskarta ma data nuna alamun kumburi 6aro-6aro musamman saman idanunta. Da ta bu'di baki kuwa tayi masa barka da dawowa sai gaba 'daya yanayin nata yasake rikita hankalinshi, domin muryarta ma adashe take da 'kyar ta harha'do maganan ta furta masa. Tambayarta yayi abinda ke damunta cikin kulawa tare da ri'ko hannayenta zuwa kusa dashi. 'Kasa tayi da idanunta ta kasa furta masa komai, sai ma wani sabon kuka daya kubce mata. Arikice yajata ya ha'de ta da jikinsa ya rungumeta tare bubbuga bayanta ahankali, shikanshi ji yayi hankalinsa ya tashi tsoronsa 'daya kar Fateemah tafara gajiya da zama da shi ayanayin da yake ciki ne, abinda kawai tunaninsa yabasa kenan dan haka sai yabarta ajikinsa tayi ta kukanta son ranta harta gaji tayi shiru tafara sau'ke ajiyan zuciya. Sai a lokacin Mahmud ya 'dagota daga jikinsa ya zuba mata idanu yana sake karantar yanayinta. " _me yasami Fateemah na ?,pls sanar dani me aka miki, waye ya ta6a minke ?_ 'daya bayan 'daya ya jero tambayar ta sa cikin natsuwa wanda hakan yasamo asali daga karyewar da zuciyarsa tayi shikanshi jinsa yayi gaba'daya yayi laushi ganinta awannan yanayin, baya so hasashensa ya kasance gaskiya, domin in har hakanne yasan tashin hankalinsa yazo kenan. Kanta ta komar kan 'kirjinsa tayi shiru domin aha'ki'kanin gaskiya ita bata san me zata ce dashi yasa meta ba. _" please Fateemah ki sanar dani damuwarki kinji I'm always here 4u, nima hankalina_ _yakasa kwanciya, zargin kaina nakeyi akan duk wani abinda ya sameki_ _nakan rasa sukuni nima pls daure ki sanar dani kinji"_ Yanzun ma shiru tayi masa sam bata da niyyan bashi amsa ko labari dangane da abinda yafaru tsakaninta da Anty. Ko dan kasheta data ci alwashin yi akan hakan, ita kuwa ba mutuwar take tsoro ba ayanzun dan akan wannan 'kazamin aikin da suke son tayi tanaji gara mutuwan yafiye mata sai de ahalin yanzu bata so mutuwa ta risketa batare data san ainihin meke faruwa da iyayenta ba, tanaso taji daga garesu taji meyasa ta daina samunsu awaya kuma suma suka daina nemanta suka manta da ita, abinda ke gabanta kenan awannan lokacin. Ahankali cikin sanyin murya ta furta " _Yayah_ !" Sai ya amsa mata da irin yanayin data ambace san da fa'din _" Na'am matar_ _Yayah"!_ Murmushi maganar tasa yasata jin ya kwaikwayi kalar muryarta sai ta 'kara yin luf akan 'kirjin nasa ta lumshe idanunta sannan taci gaba da fa'din " _Mummy da Daddy na sun manta dani ko_ _Yayah_ ? 'Dagota yayi daga kan 'kirjinsan da sauri sai yace mata _" waya gaya miki Mummy sun manta dake,? Mummy kullun idan muka yi waya sai tace in gaisheki hakama_ Daddy shima yake fa'damin kullum" Idanu ta waro akansa alamar " _dagaske?_ Sai ya jinjina mata kai tare da medata ya sake kwantar da ita akan 'kirjin san shima ya lumshe idanunsa shiru yayi yana jin bugawar da zuciyarta keyi da 'dan sauri-sauri ,sannan yaciga ba da fa'din _"Daddy yace zaizo yaganki da kansa amma sai inyaga kin kwantar da_ _hankalinki tukun na, mummy kuwa bata son ku ringa yawan waya ne saboda ita aganinta_ _kamar inkuna waya da ita akai-akai tunanin gida bazai barki da wuri har ki_ _kyautatawa auranki ba, itama tafiso sai kin saba da gidan mijinki tukunna."_ Wannan duk shirin Mahmud ne ya ha'da ya irga mata ayanda zuciyarsa ta lissafa masa sai ya gaya mata da sunan abinda iyayenta suka fa'da masa kenan akanta, kuma yayi hakane domin ya kwantar mata da hankali badan komai ba, saboda yasan da zaran Fateemah tasan iyayenta basa 'kasar nan rigimarta ba zai ta6a 'karewa ba. Aikuwa yana gama fa'din haka ta 'dago ta kalleshi _" kuna waya da mummy kullum ko Yayah?_ Yace " _ah 'ah fah Fateema ni bance ba, ba kullum muke waya ba lokaci_ _zuwa lokaci ne yawancin 'kiran ma sai na fita office muke wayar"_ " _meyasa kuma bakuyi idan kana gida?, Yayah_ _Mummy bata sona yanzu saboda anmin aure ko?, ko to gaya mata idan_ _kunyi waya kace mata ni na fasa auren zan dawo_ _gida muyi zaman mu tare da ita"_ cikin dasash shiyar shagwa6a6-6iyar muryarta ta yi masa maganan. " _waye ya gaya miki auran nan zai rabu Fateemah?.....wannan auren babu wanda ya isa yaraba shi sai mahalicci wanda yayi dalilin faruwarsa.....ke ba kya tunanin halin da zan shiga ne idan kika barni?, pls karki sake cewa zaki tafi ki barni kinji"_ Jin yace auren nasu ba me rabuwa bane take sai ta turo 'dan 'karamin bakinta dake zagaye da pink lips 'dinta gaba alaman ta ji haushin hakan kenan. Sai daya kai ayar maganar tasa kafin ta 'daga masa kai alamar taji amma still bakin ature. Mahmud kam Sosai yanda tayin ya matu'kar birgeshi, idanunsa ya sau'kar akan la66anta da sukayi jajir dasu dayake tayi kuka sosai, take sai ya 'dago hannunsa ya wari yatsa 'daya yashafa su ahankali. Teemah kuwa 'dan jan jikinta tayi daga na Mahmud da niyyar tafiya tabar inda yake, amma Mahmud be bari tayi nisa ba yasa hannu yadawo da ita jikinsa, duk da jikinsa be nuna alamun son kasancewarta ra6e ajikinsan ba amma zuciyarsa na matu'kar son hakan shiyasa ya dawo da ita. " _kin gaji da zama da niko Fateemah_ ? Idanuta ta 'dago da sauri ta sau'ke su akansa. " _pls tell me kinji, banaso hakkin ki yamin yawa akaina dan nasan Allah sai_ _ya tuhumeni akan zama na da k......."_ Da hannunta tayi saurin rufe masa baki wanda hakan ya tilasta masa yin shiru da maganar da keyi . _" Kinsan wani abu?_ Ya tambayeta da nutsatstsiyar muryarsa. Da kai ta bashi amsa yadda zai fahimceta. Sai kuwa yaci gaba da fa'din " _kinason yin waya da Daddy_ ? Da sauri ta 'daga masa kai alamar " _ehh_ " Sai yace " _alright...., zan 'kira miki shi amma da shara'din sai kin_ _sanar dani_ _abinda yasaki kuka_ _da bana_ _nan........"._ Tunkan ya 'karasa rufe bakinsa tabashi amsa da fa'din _" cikinta ne yadameni da ciwo shiyasa tayi kuka"_ _" toh me yasa baki 'kirani awaya ba ki ka zauna da ciwo har haka, kuka yana magani_ _ne Fateemah...?, kin ga kuwa yadda kika dawo , Allah_ _dana ganki hankalina yatashi sosai"_ Shiru tayi tana jinsa sai da taji yayi shiru kafin ta ce " _Yayah kira min Daddyn toh mana yanzu !_ Murmushi yayi ganin yanda ta 'kagu dajin muryar Mahaifinta, hannunta yaja suka koma kan cushion suka zauna sannan ya lalu6o phone number 'din daddy ta Nigeria dagangan yayi dialling dan yasan sarai bashiga zaiyi ba. A speaker yasaka wayar dan haka ba sai ya bu'di baki yayi mata dogon bayani ba akan wayar daddyn, saboda da kunnuwanta taji ance numbern is switch up. Langa6ar da kai tayi gefe kamar zatayi kuka ganin haka sai Mahmud ya hau bata baki akan wai tayi ha'kuri may be Daddyn ya 'danyi wata tafiya ne, yace nikuma kinga bani da numbers 'dinsa na waje ko'daya balle muyi trying, amma bari zan tambayi Abbah I'm sure bazai rasa agunsa ba. " _Toh yayah 'kira ka tambayeshi mana tun yanzu kar ajima kuma ka manta_ " Ajiyan zuciya ya sau'ke tare da ajiye wayar agefensa bayan ya dannata tashiga security dan kar ma Teemah ta 'dago 'karyar da ya shirga mata, sai yace da ita _"Nagaji kinji yanzun lil sis ki bari idan na 'dan huta anjima sai naje gidan ma gaba 'daya da kaina inkar6o inajin_ _hakan zaifi ko?"_ Yana maganar ne tare zamowa ya kwantar da kansa akan cinyarta. Teemah kuwa zuciyarta tsinkewa yayi dajin ya ambaci zuwa can gidan ita ayanzu in akwai abinda ta fi tsana aduniya toh be wuce Anty ba ta tsani ko ganin tama , amma bata yi masa magana ba sai kawai ta 'daga hannunta 'daya ta cusa acikin kwantaccen ba'kin gashin kansa tana shafawa ahankali. Mahmud kuwa lumshe idanunsa yayi tausayinta na 'kara ratsa shi, akullum yanajin kamar baya mata adalci a zaman su, balle yau 'din dayaga yanda ta dawo duk sai komai nasa ya tsaya cak, in ba tunanin mafita ba baya komai. Kusan minti sha biyar suna ahaka kafin Mahmud ya yun'kura yatashi yace zai watsa ruwa. Fita yayi bayan yagama shiryawa be zame ko'ina ba sai gidan Umar abokin aikinsa yayi masa bayanin meke tafe dashi yace yana so in zai yiwu su tafi gobe, daya ke dama Umar yace masa akowani lokaci idan ya shirya zasu iya tafiya shi ba shi da matsala. Hakan kuwa akayi domin Umar take yabashi tabbacin samun rakiyarsa aduk lokacin daya bu'kata yanzun ma cewa yayi babu komai Allah ya tashemu lafiya". Da farin cikin sa yabaro Umar din yana me jin 'kwarin gwiwa da fatan samun nasara ji yake ajikinsa kamar matsalarsa ta kusan zuwa 'karshe, da yardar Allah komai zai daidai su shida matarsa kamar yadda kowa su irin ma aurata ke rayuwa agidajensu. Daga wurin Umar Mahmud gidan mahaifinsa ya nufa amma be samu Abbah agida ba sai de Anty da ya samesu tare da Munnirah suna tattaunawa be san akan miye bane amma yanda yaga fuskarsu kamar gonar auduga yasa yagane anin farin ciki ne agare su, saboda musamman Anty tayi 'kiranta tazo domin tayi mata albishir 'din abinda take shirin aikatawa daughter inlawn ta, takuma 'kara lallashinta akan sun kusan rabuwa ai tunda Anty Chiddy yanzu matar Mahmud 'din take hari, kuma da zaran burinta yacika zata sada ta da gidan bokan dake mata aiki,shikuwa aikinsa kamar ayi yanka da sabuwar rezor blade yana yi maka aiki toh labari ze canja shiyasa nafi gane zuwa wurinsa, shegiya itakuma dan iskanci sai take ta min yanga da 'kyar nasamu ta amince zata kaini amma sai ta samu abinda take so. Dariya Munnirah tayi tace " _kice nafara shiri na kusa zama amarya"_ Anty ma dariyar tayi tace _" ai ki kwantar da_ _hankalinki ina gaya_ _miki aure tsakaninki da_ _Mahmud tamkar_ _anyi shi angama ne!_ Sunan cikin wannan yanayin Mahmud ya shigo yasame su sai de be ji abinda suke fa'di illah dariyar ya tarar. Mahmud ganin Munnira na gurin yasa be ko kula da su ba yayi wucewarsa ciki bayan sun amsa masa sallamar da yai musu. Munnira bin bayansa tayi da kallo tana murmushi musamman dataga yanda yawani basar yai shigewansa ciki aranta tace " _ohh boy.....ka gama fa'din ranka da girman kanka yanzu..... domin very soon ka kusan dawowa hannuna, kuma nawa ni ka'dai injuya ka yanda nakeso babu me takurani"_ Anty ne tabi bayansa zuwa 'dakin daya shigan bayan ta gama sallamar Munnirah ta tafi gida dan tasan ganin Munnirah ne yasa shi shigewa cikin. Gaishe da ita yayi tare da sanar da ita batun tafiyar da ta taso masa amma be gaya mata ainahin tushen tafiyar ba sai kawai yace da ita zashi katsina gobe in Allah ya kai rai domin akwai wani urgent meeting 'din da ze je yi acan. Fatan alkhairi tamishi daga nan be zame ko ina ba ya koma gida wurin matarsa. Yana zuwa kuwa ta tare shi da batun numbern Daddy sai yace mata ashe Abbah ya tafi cotonou shi be ma sani ba, amma de yana kyautata zaton dawowarshi cikin satin. Dolen ta ta ha'kura sai kuma tabawa zuciyarta tabbacin Abbah na dawowa zataje dakanta ta kar6o no. ~Barka da Sallah 'yan uwa nah,~ *ALLAH UBANGIJI YA NUNA MANA SALLAR NEXT* *YEAR LAFIYA MUNA MASU KUSANCI DA* *UBANGIJINMU.* 👇🏼 ~GAREKU DUKKAN CAPTAIN~ ~ABBAS~ ~FANS DAKE KOWANI GROUP NA WHATSAPP, FACEBOOK HARMA DA WATTPAD~ _ha'ki'ka Ur comments always drive me crazy ina_ _matu'kar jin da'di, kuma yana sani nisha'di, bansan me zance da ku ba_ _masu samba'da min addu'o'in nan wallahi idan nagani_ _ji nake tamkar banda masoyi sama da me_ _min addu'ar, fatana akullum shine Allah ubangiji yabiya muku_ _bu'katunku na Alkhairi yaji'kan_ _mahaifa._ 🤞🏻 _Godiya ta ragaggiya ce compared to soyayyar da ku ke wa Littafin nan Allah ubangiji_ _ya_ _bar min ku._ *KUSANI ANA* *MUGUN* *TARE* 🤝 👎🏻 *ACIGABA DA GASHI* *MASOYAN* *ASALI...........* _wai_ _akace suya sai_ _ranar_ *SALLAH* 🥰( ~aww ashe fah yau~ ~ce ranar~ ~suyan kardai amanata da nawa kason~ )🙈 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmern ku ce* 😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _Life is so confusing, sometime what we want we don’t get it, what we get we are_ _not satisfied with it, what we expect never happens & what we hate generally_ _repeats......._ 🅿 *61* Sai da dare Bayan sallahr isha'i Mahmud ya sanar da Teemah batun tafiyan nasa, take kuwa tafara mai daru akan ita wallahi sai de sutafi tare ita bazata zauna ita ka'dai agidan ba, yace toh zai kaita wurin Anty su zauna kafin ya dawo. Ai tana jin haka sai kawai tafara yi masa kuka tana cewa ita bata so dashi zata tafi, wai dan Allah yatafi da ita, da 'kyar yasamu ya shawo kanta tayi shiru bayan ya amince cewar bazai kaita wurin Antyn ba kamar yadda baze barta ita ka'dai agida ba. Washe gari da sassafe bayan kowa ya shirya suka tafi tare zuwa gidan Umar, sai da suka tashi tafiya kafin ya sanar da su cewa Teemah zata zauna da iyalan abokinsa Umar 'din kafin su dawo, saboda tace tana tsoron zama agida ita ka'dai. Matar Umar murna tayi sosai da zuwan Teemah dan dama ba 'karamin kewar 'yan uwanta hausawa take yi ba. Bayan tafiyar su Mahmud matar Umar ta ringa jan Teemah da hira ganin ta zauna shiru kamar me tunanin wani abu. Tun Teemah bata sakewa da su har tazo tasaki jiki gaba 'daya ta saki ranta suka rin'ka surutu da yaran Umar 'din. Tare da matar Umar suka shiga kitchen suka yi girkin abincin rana (lunch) suka ci bayan sun yi sallar azahar. Sai de duk yadda Teemah ta so ta 6oye damuwarta abin ya faskara, takan zauna tayi shiru wani sa'in har se matar Umar ta ta6ata kafin take dawo da hankalinta garesu. Hakan yasa matar Umar ta fahimci akwai wani abinda ke damun Teemah. Sai de bata tsawaita tunanin ko mene ba ta de barshi akan wata'kila tafiyar da Mahmud 'din yayi ne ke damunta dayake amarya ce ita batawani da'de da yin auran ba, bayaga haka ma kuma Teemah yarinya ce dole zata damu tunda da shi tafi sabawa agarin. Bayan sallar la'asar ne Mahmud ya'kira Teemah awayarta dan yaji ya walwalarta take agidan. Cikin sa'a kuwa lokacin Teemah na tsakiyar yaran Umar suna ta hayaniya, kuma koda ta 'dan matsa gefe da su ma kafin ta ankara sun 'kara biyota dan haka kawai sai ta zauna tayi maganar acikinsu hakan yasa be wani fahimci komai daga wajenta ba har suka 'kare wayar , se ma yaji da'di ganin tasaki jikinta agidan Umar 'din. Matar Umar nada mutunci sosai kuma tana da son jama'a gata da kula da duk wani abu da ya shafi mutuncin auranta hakan yasa take da son taga duk wata 'ya mace na da babbar fada awurin mijinta bata son taga mace na wulan'kanta sanadin aure. Awayar da Teemah tayi da Mahmud sau uku a wunin ranar sai ta fahimci rayuwar auren sun kamar ba daidai yake tafiya ba, domin bata ga wani kula ko nuna damuwa da rashin junan sun da sukeyi ba awayar da sukayin face jin lafiyarta da kuma ko wata matsala na damunta abin da ka'dai Mahmud yadamu yaji kenan daga gareta duk da suna matsayin sabbin ma aurata, sa6anin ita data ke da 'ya'ya har biyu ma amma sam bazata iya yin waya da mijinta agaban kowa ba saboda bako wani irin magana zata iya fa'da agaban mutane ba idan suna waya da mijinta. Zatonta zataga fiye da natan awajen Fateema da mijinta saboda ita 'din har yanzu amarya ce amma sai taga yanayin sha'kuwa da kulawarsu yayi 'kasa da nata ne ma sosai, ko irin missing 'din junansun nan bataga alama acikin kalaman su ba. Hakan yasa taci 'damarar ankar da Fateemah babban matsayi da muhimmancin mijinta agareta. Da dare bayan anyi sallar Mahgrib suka ci abinci inda duk cin abincin Fateemahn ya kasance kamar kullum sai de ta 'dan caccakula tabari wanda matar Umar ta fahimci ko darana ma hakan ne ya kasance. Abin na bata mamaki yanda damuwar Fateemah na rashin mijinta ya bayyana kansa afili amma kuma cikin kalamanta sam babu hakan. Sai da sukayi sallar isha'i sannan suka yi zaman su apalour suna 'dan ta6a hira inda ba awani da'de ba yaran duk sukayi bacci sai su biyun suka rage. Da wannan damar matar Umar tayi amfani ta dinga jan Teemah da magana da kuma shan cikinta akan rayuwar aurensu, anan ta 'dan fahimci wani abu ka'dan, sai de bata gama fahimta ba sai washegari data bata wani magani sinadarin mata tayi mata bayanin yadda ake amfani dashi da kuma irin tasirin dayake dashi harma ta nuna mata cewar zata ji da'din mu'amala da mijinta matu'kar tayi anfani da maganain, anan ne Teemah ta nuna mata cewar ita bata san me take nufi ba kwata kwata. Matar Umar batayi 'kasa agwiwa ba ta bayyana mata komai a yanda zata fahimta. Nan kuwa Teemah ta to na ma kanta asiri dan atake ta nuna jin kunya da maganar da matar Umar 'din ta mata ta kuma nuna bata san komai akan hakan ba, sai tace da ita ai su ba irin wannan zaman sukeyi da Mahmud ba, ta ce ai yayah Mahmud ba irin mutanen nan bane shi baze yi mata haka ba. Mamakin matar Umar 'karuwa yayi akan nada da jin maganar da Teemah tayi mata ayanzun. Take sai ta saki ranta ahankali ta ringa yiwa Teemahn bayanin menene aure da kuma abinda ya 'kunsa, ita matar Umar duk akan Mahmud ta 'dora laifin tunaninta ko shima yana 'daya daga cikin irin mutanen da ke raina mace idann an aura musu ita da sauran 'kuruciyarta, amma ai zuwa yanzun Teemah tayi girman dazata iya 'daukan bu'katun mijinta duk kuwa yanda yake tunda a'kalla zata kai 18yrs da haihuwa ayanzun, dayake bata san da batun matsalar dayake damunsu ba shiyasa ta ke gani kamar laifinsa ne da har yanzu be fahimtar da Teemah ma'anar zamansu aguri 'daya ba, amma duk da haka tayi 'ko'kari wajen jawo hankalin Teemah inda ta bayyana mata asalin manufar aure a addinance. Teemah ta 'dan fahimce ta harma hakan yasa ta 'dan saki jiki ta baza kunnuwa tana 'daukan darasi domin ita sam bata san da wannan batun ba. Daga nan matar Umar ta bata wani ha'din magani me zuma aciki, maganin yamata da'di dan haka ta ringa sha abinta tana lasan baki dama ta nan tafi kauri gurin kananun ciye-ciye da kayan zaki. Daga nan suka zarce hiran rayuwa acikin hiran ne Teemah ta tuna da mahaifiyarta, take kuwa sai jikinta yayi sanyi tafara bawa Matar Umar labarin rashin jin iyayen nata da batayi ba gashi tarasa yazata yi ta same su tace kota 'kira gidan 'kanin mahaifinta ma (Daddyn Abuja) bata samun gamsashshiyar amsa daga wurin su. Ta tausaya wa Teemah har ranta da jin cewa tun bayan aurenta da kwanaki ka'dan bata 'kara jin iyayenta ba, gashi guri da nisa ba kusa ba balle ta je ta ganosu, bayan hakama garin ba zaman lafiya ake yi ba dole hankalin Teemah yatashi. 'Dan tunani ka'dan matar Umar tayi sai tace da Teemahn ta 'dauko wayarta suyi wani abu. Tashi tayi taje ta 'dauko wayar sai matar Umar tace ta gwada 'kiran Mahmud su gaisa tunda basuyi waya da safiyar yau ba sai ta tambaye shi ko yanada layin Umman Abujan kode wani haka acan tace yatura mata domin tayi loosing wasu contact 'din ta kuma tana son ta 'kira su ne. Koda ta 'kira shin kuwa sai yace bashi da numbern kowa sai na Abbas, amma zai tambaye shi sai ya tura masa idan yaturo zai mata sending. Da " _toh_ " ta amsa masa daga nan sai ta kashe 'kiran. Shiru matar Umar tayi tana tunanin wata mafita dan kuwa tana ganin kamar idan Mahmud ya turo numbers 'din shirinta ya wargaje, taso ne kowa ya zamana bashi da contact 'din tsakaninsu. Teemah kuwa tsayawa tayi tana kallon ta domin jin manufar hakan daga bakinta. Tsawon mintina biyar suna ahaka sai ga 'kiran Mahmud yadawo wayar Teemah, bin wayar tayi da kallo kafin daga bisani ta 'daga wayar ta sada shi da kunnan ta. Daga 'daya 6angaren Mahmud jikinsa da sanyi yake ce mata " _Tayi ha'kuri zuwa wani lokaci dan Abbas_ ' _din yanzu_ yana cikin maiduguri yana kan aiki kuma anyanke gaba 'daya network 'din Borno harma da wasu garuruwan dake makwabta ka dasu, so ba zai same shi ayanzun ba sai de ko inya 'kira shi ko kuma idan yadawo sai suje gurin Abbah yabasu numbern Daddyn Abujan inyaso sai ya ha'da ta da su Hannah. Daga 'karshe yace taringa yiwa Abbas 'din addu'a pls, yanzu shima ake fa'da masa cewar maidugurin ba lafiya ahalin yanzu an kai musu harin bazata. Teemah ji tayi hankalinta yatashi da batun Mahmud 'din na 'karshe. Tana sau'ke wayar tafara dialling numbern Abbas amma baya tafiya, tayi harta gaji ta ha'kura. Yanda abin ya tsaye mata kuwa har yasa tafara hawaye, yanzun hankalinta yafi kullum tashi saboda damuwarta sun kara yawaita ne musamman data ji cewa Yah Abbas na cikin maiduguri kuma ankai hari ga kuma iyayenta a damaturu kuma bata samunsu awaya ga kuma sarka'kiyar Anty to me ke faruwa ne ? Abin nan na matu'kar damunta sosai. Da 'kyar Matar Umar ta lallashe ta ta samu ta 'dan nutsu sai ta ringa kwantar mata da hankali ta ce mata bari suyi wani game wata'kila zata samu jin labarin iyayen nata idan tayi sa'a. Tace Teemah ta 'kira Hannah tace mata tana hanya yau zataje dubo iyayenta. Hakan kuwa akayi Teemah ta 'kira Hannah ta gaya mata abinda matar Umar 'din ta ce ta fa'da sai taji Hannah ta rikice tana mata masifar waye yace mata ta hau hanya, tasan kuwa irin abinda ke faruwa awancen yankin, tace tun wuri ki nemi damar da zaki koma gida inba so kike kiyi tafiyar banza ba" Cikin sanyin murya Teemah tace " _tafiyar banza kuma Hannah, nida zanje inga mummy da Daddy nah_ ? " _angaya miki mummy tana can ne? Me yasa baki_ _fa'dawa Ummah ba kafin ki fara shirin tafiyar?_ arikice Hannah take duk wannan maganar. Matar umar najin haka aranta tace " _anzo gurin_ " Domin wayar a handsfree take duk atare suke jin komai. Suna jinta ta cikin wayar tana ta kwallah 'kiran _Ummah_ arikice, _Ummah_ !...... _Ummah_ !!......... _Ummah kinji abinda Teemah ta ke shirin_ _yi kuwa? Wai fah takama hanyar zuwa_ _damaturu ayau 'din nan._ Kar6ar wayar Ummah tayi tana kar6a itama tafara fa'din " _Fateemah meyasa kika yanke wannan shawaran batare da kin sanar_ _dani ba!_ shiru Teemah tayi Ummah kuwa sai taci gaba da magana tace " _ina Mahmud 'din yake?_ Sai alokacin Teemah tace " _Nabarshi agida yasani a mota ne shi ya koma gida_ " Azabure Ummah tace " _kina nufin amota zakiyi duk wannan doguwar tafiyar_ _Fateeemah kuma ke_ _ka'dai?_ " _a ina kuke yanzun?_ Ummah tasake tambayarta. Kame-kame Teemah tafara kamar irin zata fa'di wurin 'din nan sai Ummah ta tare ta da fa'din " _koma a ina ne ki maza ki dakatar da tafiyar nan ki koma gida dan kuwa Khadeeja basu_ ' _kasar nan a halin_ _yanzu suna Dubai"_ Wani sanyin da'di Teemah taji ya ratsata take farin ciki ya bayyana akan fuskarta tana murmushi tace " _har Dubai mummy ta tafi shine bata sanar dani ba_ _Ummah.....toh ki tura min numbernta idan na koma sai_ _in' kirata."!_ Da sauri Ummah ta tare ta da fadin " _Ehh zan tura miki amma ki kula da zarar kun shigo cikin gari ki ce da su su sau'ke_ _ki ki nemi mota ki koma gida indai bakuyi nisa ba, in kuma_ _kunyi nisa ki iso_ _nan Abuja"_ " ah ah bamuyi nisa ba Ummah" Teemah ta da ita. " _toh maza ki koma gida zansa Hannah ta tura miki layin Mummyn naki_ _yanzu"_ Ummah ta 'karasa da mita inda take cewa " _amma ni wallahi wannan karan Mahmud be birge ni ba, taya zai biye shirmenki yasaki_ _amota ke ka'dai kuma ya kwantar da hankalinsa agida_ _da sunan kinyi tafiya, wannan ai rashin hankali ne, inkin koma gida ki_ _ha'da ni dashi dan_ _Allah"_ ! Da " _toh_ " Teemah ta amsa mata sannan ta yanke 'kiran tana me farin ciki da wannan al'amarin har tsalle ta buga ta rungume matar Umar da 'karfi tana me zuba mata ruwan godiya da wannan babban kyautan datayi mata, itama dariyar takeyi tana me nuna farin cikinta afili ganin yau Teemah tasaki ranta sosai. Mintina biyu basu cika ba taji wayar ta tayi 'karan shigowan text, da sauri ta 'daga ta duba sai kuwa taga international number aka turo mata harda 'karamin plus a afarkon numbers 'din. Godiya ta 'kara yiwa Allah tare da fa'din " _Yah mahmud ka gafarceni na maka sharri nasan yanzun zuciyar_ _Ummah acike take taf da jin haushinka amma_ _zan warware komai_ _daga baya_ ". Take ta gwada 'kiran layin da aka turo matan sai kuwa taji yashiga. " _Assalamu alaikum_ " Tajiyo muryar Mummy na fa'din haka. Lumshe idanu tayi sai taji zuciyarta ta karye take hawaye ya ratso tacikin lumsassun idanun ya gangaro kan kumatunta, Ahankali tace " _mummy ke ce_ ? Ita kanta mummy jikinta rawa yafara da jin muryar 'yar tata bayan tsawon wasu kwanaki, sai tace " _nice mamana ya kike"_ " _Mummy shine kika manta dani keda daddy kuka yi tafiyarku wata 'kasa kuka barni anan ko_ _nemana baku 'kara yi ba, mummy daman idan anyiwa mutun aure_ _mantawa ake yi dashi?,mummy ina daddy na yake inji muryarsa"_ Shiru mummy tayi tausayin 'yartata na ratsa zuciya da gangan jikinta ita ma ba 'karamin dauriya tayi ba harta kai tsawon wannan lokacin bata nemeta ba, takan yawaita jero numbers 'din Teemah kamar zata 'kira amma sai ta fasa saboda bin dokar da Daddyn yakafa mata bata son ta karya masa dokarsa har ransa ya 6aci shiyasa takasa 'kiran Teemah koda sau 'daya ne. ahankali tafurta " _hoo Teemah irin wannan tambayoyin wanne daga ciki zan fara amsa miki?_ " _Duk kansu mummy_ " Teemah tabata amsa cikin za'kuwa. Murmushi kawai mummy tayi sai ta fara bata ha'kuri tana mai tambayarta yanayin zamanta da Anty da kuma mijinta. Teemah tace komai normal babu matsalar komai. Teemah taso ta sanar da Mummy matsalar dake tsakaninta da Anty amma tana tsoron abinda ze biyo baya dan tasan mummy ba shiru zatayi ba idan taji maganar dole sai ta nemi fitar da ita daga al'amarin wanda hakan ke dai dai da tsayawar numfashinta akowani lokaci. Suna cikin yin wayar daddy ya shigo sai kuwa mummy ta mi'ka masa wayar batare da tayi masa magana ba " _waye_" ya tambayi mummyn 'kasa 'kasa yanda mummyn ka'dai zataji shi. Sai dai Teemah ta jiyo shi itama sai ta ce dashi " _daddy_ _nice fah_ " cikin shagwa6a tayi maganar. " _ahh ah Angel 'dina kece yau akan layi?_ " _daddy shine kaima ka manta dani ko?_ " _Waye ya gaya miki haka? bana so mu ringa damunki ne shiyasa kika jimu shiru amma yanzu_ _ma haka ina planning zan shiga lagos 'din next_ _week"._ Take tace " _Allah daddy dagaske?_ Murmushi kawai yai mata batare da ya yi magana ba. Sai itace tasake fa'din " _daddy dan Allah idan kazo karka tafi bamu ha'du ba akwai maganar danake_ _so ingaya maka!"_ Sai yanzun yace " _Toh shikenan insha Allahu zan zo har gida karki damu ki kwantar da hankalinki muma_ _bamu ta6a_ _mantawa da ke ba_ _kinji_ " ***** Yau ba 'karamin da'di take ji ba, tana gama waya dasu ta 'kira Mahmud tasanar dashi cewa yau sunyi waya da Mummy harda daddy ma" Tambayarta yayi taya hakan yafaru kode sune suka kirata, sai tace ah ahh ita ta 'kirasu daga nan tabashi labarin yanda akayi harma da maganar da Ummah tafa'da akansa, yana dariya yace " _lallai yarinyar nan wuyanki yayi 'karfi wato harda ni acikin shirin 'karyan_ _naki_ _ko_ ? Dariya itama tayi tare da yanke wayar. Ba'a jima ba sai ga 'kiran Ummah tana me sake tambayarta kota koma gidan, sai Teemah tayi mata 'karyar yanzu ta sauka za'a sata motane yanzun, sai tace idan ta koma gida zata 'kirata " _yauwa Fateemah maza ki koma gida kinji, Allah ya tsare ya kare ya kuma_ _bada sa'a_ " cewar Ummah " _ameen Ummah_ , _nagode a_ ". Farin cikin Teemah yau baya 6oyuwa yanda taji muryar iyayen nata ita ka'dai sai tana sakin murmushi musamman idan ta tuna cewa daddy zai zo nextweek sai take ganin kamar matsalarta ta kusan zuwa karshe, dan tagama sawa ranta cewar daddy na zuwa zata ma'kale masa sai ya tafi da ita ko dan ta huta da fitinar su Anty ma. Sosai take jin farin ciki wanda hakan yagama bayyana kansa azahiri kowa ya kalleta take zai gane hakan, sai de deepdown her heart tana jin zuciyarta ajagule kamar bata da nutsuwa, da 'kyar tasamu ta lalu6o damuwar tata da dare bayan ta kwanta bacci alokacin ta zurfafa tunanin ta sai data gano 6oyayyiyar damuwar tata. Lumshe idanu tayi take tausayin sa ya tsarga mata azuci ta ringa tuno rayuwar su dashi abaya abu na 'karshe data tuno shine ranar da za'a 'daura auren ta da Mahmud daya zo yabata gift har cikin 'dakinta. Tsintar kanta tayi da tausaya wa rayuwarsu shida ita take ta tashi tayo alwala tazo ta tada sallah bayan ta sallame ta ringa jero addu'o'i na nema musu kariya wurin mahallici, musamman ma shi da yake fama da 'yan ta addah. Mahmud kuwa sosai ya samu tarba wurin shehin malami kakan Umar abokinsa, yayi masa tambayoyi akan abubuwan da ke faruwa dashi, Mahmud duk yayi masa bayani. Sosai ya jinajina wa al'amarin tare da sanar da Mahmud 'din cewa matsalarsa ba abin damuwa bace matu'kar za'a yi anfani da abinda 'qur'ani ya karantar, yace matsalar sa bakomai bace face matsalar aljanu amma da iznin Allah komai zai daidaita. Atake yabashi wani ruwan addu'a ha'de da ganyen magarya yace yayi bismillah yasha ya kuma wanke fuskarsa. Hakan Mahmud yayi kamar yanda malamin ya umarce sa da yi daga nan yabashi wasu addu'o'i yace ya ringa yi akoda yaushe sannan ya yaiwata yin istighfari, sadaka da neman yardar Allah akowani lokaci. Washegari malamin ya ha'dawa Mahmud magunguna na islamic medicine tare da bashi wata jarka da ke chike da ruwan rubutu yayi masa bayanin yanda zai na anfani dasu. Sosai Mahmud yaji da'din al'amarin harma yarasa da me zai sakawa malamin, banki ya tafi yaje ya chiro ku'di kusan 200 thousand naira ya kawo yabashi, amma fir ya'ki kar6a, sunyi-sunyi ya kar6a ya'ki Mahmud kamar ze yi kuka domin gani yayi kamar in be kar6a ba tamkar wani nauyi ne akansa. Dayaga sun dage ne shine ya kar6i twenty thousand yace ya isa Allah ya sa adace yakuma bada sa'a, yace da Mahmud 'din shi bashi da matsala da ku'di amma ze iya ya bayar da sadakan ku'din ga koma wanene inyaga me shi nada bu'kata. Godiyar Mahmud kamar su yi wa malamin rumfah suka masa sallama suka fito da niyyar tafiya. Taxi suka tara suka hau tun acikin unguwa suka samu, dayake cikin unguwa ne sai suke tafiyar ahankali. Wani gida suka wuce daf da zasu fita a unguwar ginin 'kasa duk ya lalace ma katangar gidan ruwa duk ya wanketa ta dawo yar guntuwa har kana hango abinda ke faruwa acikin gidan, 'kofar gidan ma da wani tsohon buhu aka tare shi daga shi kuwa babu komai. Acikin 'yan sakanni Mahmud ya gama karanto fasalin gidan, take kuwa zuciyarsa ta karye, tausayin wahalar da al'ummah suke ciki duk yabi ya cika masa zuciya. Gaba ka'dan sai yaga wata yarinya da bazata wuche 10-11yrs ba, kayan jikinta kuwa ko goge takalmansa aka ce za'a yi dasu sai ya hana ayi balle har su kasance ajikin mutun, tsabar yanda ko'diya da datti suka cikasu ko gane zanen zanin da kyau ma ba'a yi. Dur'kushe take tana kwasan wani farin abu a'kasa hankalinta duk yabi ya tashi tana yi tana waiwaye ga dukkan alamu bada sanin ta ba ya kuskure ya zube. Mahmud dakatar da drivern taxi 'din yayi bayan sun wuce yarinyar ka'dan, amma kafin Mahmud ya yi yun'kurin fitowa har wata mata ta fito ta iso inda yarinyar take tsugunne tana masifa itama ta tsugunna tana tayata kwasan abun. Ahankali ya tako ya iso kusa dasu basu ma lura dashi ba hakan yasa wannan matar bata dakata da masifar datake yi ba amma ba da hayaniya takeyi ba tanayi ne yanda yarinyar ka'dai zata jita sai ko Mahmud daya musu la6e. Jiyayi matar na fa'din " _yanzu fisabilillahi meram bazaki dinga kulawa ba, akullum_ _magana 'daya kike son inyita maimaita miki?, ke ko duba yanayin da aka samu 'dan_ _ku'din nan bakiyi kika zo kika zubar da alabon nan yanzu dan Allah a_ _ina kike so mu shiga mu samu ku'din da za'a siyi wani ga yara duk yunwa tabi ta ishesu,_ _badan albarkacin surfen nan da matar yakubu takawo_ _bama da yau Allah ne ka'dai yasan yanda zamu kasance, kuma muna murna zamu_ _samu abin ta6awa sai kizo kuma ki zubar?_ Ahankali Mahmud ya 'karaso kusa da su tsabar yanda yaji tausayinsu har idanunsa na tsatstsafo da ruwan hawaye amma be bari sun sau'ko ba kawai ya dinga fa'din _Alhamdulillah_ azuciyarsa da rufin asirin da Allah yayi musu, ha'ki'ka rayuwar bin Adama ma aya ce babba, yanda damuwoyin junanmu suka bambanta kowa da kalar tashi damuwar, kamar shi yanzu yanda Allah ya rufa masa asiri takowani 6angare bashida matsala da komai sai kawai ya jarabce shi da dakushewar wani sassa na jikinsa wanda hakan ya matu'kar 'daga masa hankali, balle wa'dannan, ya zasuji da damuwar su takasance akan rayuwa ce gaba 'dayanta, ha'ki'ka Allah buwayi ne gagara misali domin shine yayi al'kawrin jarabtar kowa daga cikin mutane harma da ajannu da kowani irin al'amari, sai de fatan Allah ya sassauta mana ya kuma bamu ikon cin jarabawar. Adaidai lokacin ya iso kansu ya tsaya sai yaga sun ma gama kwashewa sauran wanda ya gaurayu da 'kasan ne suke sake kwasa. _Comments Vote and share_ *Salmerhn ku ce*😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir rahmanir raheem* _Before you go pointing your fingers at someone else, you may want to make sure your own hands are_ _clean............_ 🅿 *62* Da sauri yace " _ah ah Innah wannan ai 'kasa ce ta rage_ " Bata 'dago taga me yi mata maganan ta bashi amsa da fa'din " ' _kyaleni yaro, inban kwashe duka ba 'dan waken ba isan yaran zaiyi ba hakan ma daya za'a ci ballantana kuma ya gaza haka_ " Mahmud cikin tsananin mamaki yace " _wai kina nufin wannan abin abinci za'ayi da shi Innah_ ? Sai wannan karan matar ta dakata da kwasan abin da takeyi ta 'dago jin tambayar yayi matan kamar ta rainin hankali. Tana mi'kewa taganshi tsaye kusa da ita ga wasu su biyu ma tsaye abayansa, ita tsoro ma ya bata dan yanda taganshin take tsoro ya tsarga mata azuci. Hannun 'yarta takama tayi baya ka'dan sannan tajuya suka nufi gidansu da saurin gaske. Wannan gidan da Mahmud yagani 'dazu nan yaga suka shiga shima sai ya biyo su abaya amma kafinma ya iso su har sun shige ciki abinsu. Tsayawa sukayi suna 'dan dube-dube can suka hango wani matashin saurayi da bazai wuce shekara 20 ba yana kallon su daga 'dan nesa ka'dan. Hannu Mahmud ya masa sai kuwa ya taho da sauri kamar dama jira yake su 'kira shi. Yana iso wa ya gaida su suka amsa sannan Mahmud ya tambayi sunansa . Matashin yace sunan sa _Rabi'u_ . Mahmud ne yace " _yauwa Rabi'u dan Allah ko zaka mana magana da mai gidan nan_ " Matashin mai suna Rabi'u yace " _Allah sarki ai maigidan ya kwan biyu da rasuwa, matarsa da 'ya'yansa ne ka'dai_ _suka rayuwa_ _agidan_ " Tausayin mutanen ne ya sake shiga dukkanin azuciyoyin su har drivern taxi 'din. Bayani Mahmud yayi wa Rabi'u akan abinda ke tafe dasu, nan take kuwa farin ciki ya baibaye ilahirin fuskar Rabi'u yafara yi musu godiya tunma be tabbatar da gaskiyar lamarin ba, shiga gidan Rabi'u yayi yai wa matar gidan bayani wanda da 'kyar ta amince da batun da Rabi'un yazo mata dashi, domin ita rayuwar yanzu tsoro yake bata, mutane sam babu tsoron Allah azu'katansu, dayawansu basa taimako saboda Allah sai dan su cuceka ko dan wani abu daban, ita kuwa da take ta fama tana lalla6a rayuwarta da 'yan yaranta guda hu'du sam bata son wata sabuwar fitina ta 6ullo musu. Da 'kyar Rabi'u ya shawo kanta ta yadda ta amince da su Mahmud 'din sannan Rabi'u yakoma yayi musu iso. Su Mahmud basu tsinke da al'amarin matar ba har sai da suka sanya kawunansu acikin gidan, inda suka ga komai kamar ba inda 'dan adam ke rayuwa ba, babu komai da zai birge mutun acikin gidan face tarkace da tsummokara, Mahmud sosai ya tausaya musu jikinsa yayi sanyi 'kalau. Rabi'u ne da kansa ya je ya janyo wata ru6a66iyar tabarma ya shinfi'da musu suka zauna akai, ganin yanayin matar ne yasa Umar yayi mata bayani abayyane cewa ta saki jikinta karta ji tsoro sadaka suka kawo musu ba cutar da su zasu yi ba, amma intaga kamar bata yadda dasu ba har yanzun tana iya yi musu bayani sai sukoma inda suka fito. Rabi'u ne yayi saurin taran maganar da fa'din " _ah ah ai baza 'ayi haka ba nariga nayi mata bayani 'dazun ai kuma ta fahimta_ " Mahmud kam shiru yayi yana sauraransu yariga da yasawa ransa cewa ze taimaka musu cikin abinda Allah ya hore masa, so ko matar nan zata na dukansa tana koransa ne ba ze fasa ba. Ku'di masu yawa Mahmud yaciro ya mi'kawa Umar shikuma ya bawa Rabi'u yace ya nemo masu gyara su 'dan 'kara tsayin katangar gidan saboda rufin asirin masu gidan, sannan yaciro wannan ku'din da malam ya'ki kar6a ya mi'kawa matar yace wannan sadaka ce taringa siyawa yaran abinci me kyau suna ci ba irin wannan ba, sannan kuma ta na siya musu omo da sabulu sunayin wanki akan lokaci, yace karta damu da 'karewar ku'din insha Allahu ze dawo ba da'dewa ba ya sake dubasu. Kuka matar tasaki tare da godiya ta 'dago kudin ta ri'ke ahannunta hawayenta na sau'ka akansu yayinda yaranta duk suka matso sukayi jigum agefenta suna kallonta. Tun bayan rasuwar maigidanta yauce rana ta biyu da wasu suka dube su da fuskar rahama, inka 'dauke masu basu zakkar abinci na kowacce shekara idan lokacin sallar azumi yayi Rabi'u ne mutun na farko daya taimakesu kuma yake kan taimaka musu aduk lokacin daya samu dama, domin har yau be ta6a fasa taimaka musu ba, aduk lokacin daya samu canji yakan kawo musu ku'di wataran har ledan taliya yakan siyo yakawo musu yace su dafa suci, randa hakan be samu ba kuwa yakan basu har naira 'dari yace su sayi wani abin dashi. Atarihin rayuwarsu bazasu ta6a mantawa da Rabi'u ba, na biyunsa shine yau da wa'dannan bayin Allah suka zo suka taimaka musu, cikin kukan taketa jero musu addu'ah, " _Allah ubangiji ya saka muku da alkhairi ya haskaka rayuwarku, Allah yasa ku gama_ _da duniya lafiya, kamar yanda kuka ji 'kanmu kuka taimake mu_ _Allah ubangiji ya ji 'kanku kuma ya.........._ Da " _Ameen_ " kawai suke ta amsawa. Sai da suka mi'ke sazu tafi ne sannan Mahmud ya kalli yarinyar dayaji 'dazu mahaifiyarta ta 'kira ta da suna meram yace " _mamana ana zuwa makaranta kuwa?_ Sai data juya ta kalli bayanta dan ganin koda wa yake maganar ganin saitin ta yake kallo sai taga babu kowa agurin illah ita ka'dai, da kai ta amsa masa alamar " _ah'ah_ " " _islamiya fah_ ? Yasake tambayarta Nanma ta'kara jijjiga masa kanta wanda manufar amsar duk ya bada ma'anah daya. " _meyasa haka toh_ " Yayi maganar tare da ya hannu. Kafin meram tayi magana se mahaifiyarta tariga ta yin maganar da fa'din " _kayyah 'dannan abincin daza'a ci ma daya aka samu, gagararmu yakeyi ballantana har_ _asamu ku'din biyan makaranta, wannan dakake gani......._ Ta nuna Rabi'u sannan tacigaba da fadin " _shi ka'dai yasan damuwarmu yasan halin damuke_ _ciki, shine akullun yake da burin yagama makaranta domin yasamu abinyi_ _nima kuma shi 'din nakewa addu'ah yasamu yagama koda baze taimaka mana agaba bama_ _bazanji haushi ba kokadan, domin wanda yayi abaya ma ka'dai ya isa, hakanma ya isa_ _yasa nayi ta masa fatan alkhairi har 'karshen rayuwarsa, domin Rabi'u mutun_ _ne yaro ne shi amma me zuciyar manya, burina inga Rabi'u yasamu abinda_ _yake so, amma inbashi ba mukan ai tamu rayuwar daban take, ba wai dan bandamu da_ _rashin karatun yaran bane ah' ah kawai dai inaga kamar mu'din haka Allah yaso ganinmu shiyasa ya yomu daban, kaga kuwa ai bazamu yi shishshigi wa lamarin ubangiji ba_ " " _hakane kam Innah amma ai ba a yanke kauna da rahamar ubangiji domin idan yaso_ _akowani lokaci ya kan iya sauya ma rayuwa, kuma kinga zama hakan ba ilimi ai babu da'di_ , _duk da Allah ne dakansa ya halicci mutane iri daban daban amma kinga ta 6angaren_ _neman ilimi be bambanta mu ba yace ne kowa ya nemi ilimi.......... amma bakomai_ _nafahimci sosai.......yanzun muna kan hanya ne, da iznin Allah zan sake dawowa_ _kwana kusa insaka mamana amakaranta_ " Ya dubeta yace " _ko_ _bakyaso_ ? da murnarta ta bu'di baki tace " _inaso_ ". " _Yauwa Mamana sai dawo ko_ " Yafa'da tare da juyawa suka nufi hanyar fita matar nasake zuba musu ruwan albarka da godiya har suka 6acewa ganinta. Rabi'u ne ya rakasu har gurin motarsu, wanda anan Mahmud ya ciro card 'dinsa yabashi yace ze iya nemansa idan ana da bu'katar wani abu kafin yadawo 'din ko kuma idan ku'din daya bashin suka gaza yin aikin yace ya'kirashi. Sannan ya 'kara ciro 10 thousand yabawa Rabi'un yace wannan nashine ya ri'ke agurinsa. Rabi'un ma godiya yayi yana 'daga musu hannu har motar tayi nisa ya daina hangosu. Katin ya tsaya yana kallo aransa yake tunanin dama ashe har yanzu akwai irin mutanen nan ne aduniya, lallai kuwa Allah yayi gaskiya ha'kuri nada riba watarana, gashi yau ha'kurin innah yayi mata rana. Allah ubangiji yasaka musu da gidan Aljannah ya biya musu bu'katunsu na alkhairi ya 'karashe da fa'din haka. Mahmud tasha suka zarce suka nemi motan zuwa kano shi Umar, gidan kakansa Alhaji muhammad ya nema. Alhaji muhammad ba 'karamin farinciki yayi da zuwan jikan nasa ba hakama matarsa, sosai suka rin'ka nan nan dashi, kamar su goyashi, Mahmud kansa yaji da'din hakan harma yakeji aransa dama tun farko agurin kakan nasa yatashi dayafi masa yanzun ma jiyake kamar karya tafi badan yabaro aikinsa da kuma matarsa ba da babu abinda zai sa shi komawa lagos. Gidan 'yan uwan Anty kaf sai da ya zaga ya gaidasu kowa na farin ciki da ganinsa, musamman ma dashi 'din suka ga sam beyi halin 'yar uwar tasu ba hakan yasa suka 'kara sonshi fiye ma da mahaifiyar tasa. Kwanansu biyu suka wuce 'kauye gurin danginsu na can, wato 'yan uwan mahaifinsa, nan ma haka suka ta hidima dashi kowa na tambayarsa iyalinshi da iyayensa, kafin yatafi sai da yabi yaraba musu ku'di 100k ma dukkansu mazan dayake lokacin damina ne sai yace suyi aikin gona dashi. Hakan dayayin ba 'karamin farin ciki ya sanya azu'katansu ba, nan kam be kwana ba aranar suka wuche kuma ko tsaraba 'kin kar6a yayi yace bagida suka yi ba tukunna kuma kayan zai zama musu damuwa ne tunda motar haya suke hawa. 'Karfe hu'du na yamma suka baro 'kauyen suka dawo kano. Da 'kyar suka sami flight 'din da zai sau'ka a Lagos da daren ranar, dan haka suka je suka gabatar da salllolinsu kafin nan. 'Karfe 11pm suka sau'ka acikin garin Lagos ganin dare yariga yayi yasa suka wuche gidan Mahmud suka kwana acan sai washe gari da safe suka shirya suka fita atare inda Mahmud ke jan motar Umar na gefensa. Dayake ma already Teemah tasan da dawowar shin so tun dawuri tagama ha'da kayanta suna zuwa bawani 6ata lokaci tabi mijinta suka wuche gidansu amma zuciyarta cike da kewan matar Umar da 'yaranta musamman ma little Amal. Aranar Mahmud beje shi ko'ina ba acikin gidansa ya wuni dayake ma ranar takama ranar asabar ce shiyasa ma be fitan ba, sai da akayi sallar azahar kafin yafita yaje masallaci yayi sallah daga nan yawuche gidan mahaifinsa. ***** Washegari kuwa tunda sassafe suka tattaro inner wears 'dinsu gaba 'daya wa'danda basu sawa a loundry machine suka wanke atare, Teemah natayi masa dariya wai be iya wanki ba, itanma bawani iyawa tayi ba amma yanda taga Mahmud 'din keyi sai yana bata dariya shiyasa take ganin kamar tafishi iyawa. Kasuwa suka shirya suka tafi bayan sungama wankin, sukayo siyayya ni'ki-ni'ki tarkacen kayan abinci. Dangin su stock fish, ice fish, naman kaza dana 'karamar dabba, cry fish, ganyen su oghou, tarkacen fruits da sauransu kaya de dayawa suka siyo. Atare suka shiga kitchen suka adana komai a inda yadace nasawa a fridge suka saka na , ajiyewa haka duk suka adana abinsu. Fruits salad Teemah ta ha'da musu mai da'di suka sha aranar wanda shi ka'dai dasuka sha basu 'kara neman abinci ba har sukayi bacci. Washe gari tunkan yagama shirinsa Teemah ta shirya ta yi zaman jiransa yagama nasa shirin, suna gama yin breakfast yatashi da niyyar tafiya anan Teemah ma ta ce itafa bazata iya zama agidan ba gaskiya tsoro takeji sai de sutafi tare, bayason ta 6ata masa lokaci dan haka yace toh sutafi . Gidan Umar yakaita daga nan yawuche wurin aikinsa. Matar Umar ta'danyi mamakin zuwan Teemahn amma bata tambayeta dalili ba haka suka wuni abinsu dan yanzu kam Teemah tariga da tasaba dasu sosai. Da yamma Mahmud yabiya ya 'dauko ta suka dawo gida. Mahmud kansa yanzu yana mamaki yanda yake samun damar yin baccinsa cikin natsuwa da kwanciyar hankali tun bayan da ya fara amfani da magungunan da aka ha'da mai, yanzu kam Alhamdulillah, dan ko jiya da Teemah ta tashi cikin dare ma dakansa ya farka dayaji motsinta, gashi yauma har ya kwanta suna hira da Fateemahn sa6anin da da yana 'dora jikinsa akan gadon zaiji wani bacci me shegen nauyi harma baya sanin lokacin da baccin yake 'daukansa. Labarin duk abinda yafaru wajen tafiyar sa yake bata, na yanda yaga wannan matar da 'yarta dama duk abinda yafaru agidan yace tausayin matar da yaranta yakasa barin zuciyarsa, duk lokacin dayasamu chance zai koma yasake duba su, Teemah najin haka tace itama zata bishi tana so tagansu itama. Be musa taba ya amince, dan yasan ko yace baza bishi bama ba yadda zatayi ta zauna agidan ita ka'dai ba dan haka gara yatafi da abinsa yafi masa. haka suka ci rabin satin yana fama da ita, sam ta'ki zama agida kuma ya kaita gurin Anty ta'ki, sai de ko su tafi office 'din tare ko kuma ya kaita gidan Umar. Sosai abin yafara isansa yarasa takamamman dalilin dayake sata wannan abin while ada da bata saba bama bata yi masa haka, ya tambayeta kuma sai de tace bakomai kawai tana tsoro ne. Toh tsoron na menene sam yarasa. Anty Chiddy kuwa zuwa yanzun hankalinta sam ya daina kwanciya da rashin samun Fateemah, domin tagama saka rai da samun yarinyar sai gashi kuma bata samunta agida, kullum bata nan tarasa ina take zuwa, gaba 'daya ta 'dora ranta akan yarinyar har hakan yasa ta sallami yaran datake hul'da dasu ganin tasamu sabuwa. Tayiwa Anty maganar ma kuma duk abanza dan da kunnanta taji ranar da Mahmud yake fa'din wai ai islamiya take zuwa shiyasa bata zama agida. Da yamma kuma ai Mahmud nagida babu damar taje. Daga baya sai tayi wani tunani wanda take ganin shine dai-dai, ta yanke shawarar kawai gara tasa ayi mata kidnapping yarinyar taje ta 6oyeta sai ta gama abinda zatayi da ita sannan tadawo musu da ita gida. Wannan shawaran ita ka'dai tayishi azuciyarta ko Anty bata sanar mawa ba, domin dama kawai tana yaudarar Anty ne akan zata kaita inda za'a warware auren bawai dan tana da tabbacin hakan ba, dafarko taso ta samu kan Anty ne sai kuma ta'ki amincewa da ita suna cikin haka kuma saita yi arba da amaryar Mahmud yarinyar sai ta gama tafiya da imaninta taji kaf duniyan nan ita ka'dai take da burin kasancewa da ita shiyasa plan 'din yadawo kan Teemahn madadin Anty, sai gashi kuma itama Teema tana neman fin 'karfinta ita kuwa bazata iya ha'kura da ita ba sam. ***** Haka yauma Mahmud suka fito daga gida shida Fateemah ya sau'keta agidan Umar yatafi wurin aikinsa. Abin nabawa matar Umar mamaki na yanda Teemah take 'kin zama agidan mijinta ta gwammaci zama agidan mutane domin tariga tasani Teemah bata son zama agida, matu'kar bata gidanta toh Mahmud yawuche office da ita, dan haka yau ta yi 'damar sanin dalilin hakan bawai dan ta gaji da zama da ita ba, sai dan kawai ta gyara mata kuskurenta domin tasan Mahmud bazai ta6a jin da'din hakan ba sai de yabiye mata kawai saboda jin da'di da farin cikinta, sam babu namijin da za'a ce matarsa bata son zama agidanta kuma yayi farin ciki da haka. Koka'dan bata ta6a canjawa Teemahn fuska ba aduk zuwan datakeyi saima ta'kara jawo ta ajiki tare da bayyana mata wasu sabbin abubuwan da suka shafi zamantakewar aure, wanda zuwa wannan lokacin sosai Teemah tayi nisa da sanin menene shi auren kansa takuma gane irin zaman da sukeyi da Mahmud 'din daban yake da kowa. Gata da jarabar son yara musamman ma yarinyar Umar 'yar karamar da bata wuce 1yr da haihuwa ba ( Amal), kullun idan tazo yarinyar najikinta, ita take mata kitso kullun watarana jitake yi kamar tatafi da ita gidansu. Matar Umar nayi mata dariya amafi yawancin lokuta idan taga tana 'ko'karin goya yarinyar amma kamar wata me wasan yara sam bata iya ba. Takance da ita " _zanga ranar da zaki goya naki' dan ai Fateemah gaskiya zansha dariya in 'koshi_ " Sai Fateemah cikin za'kuwa tace mata " _da gaske nima maman Amal zan haihu na sami 'dana da 'yata watarana_ ? " _Zaki haihu mana lokacine ai, in Allah ya yarda kamar yau_ _ne_ " Fateemah na matu'kar jin da'di idan taji ance zata haihun nan har ta 'kagu taganta da babyn ta itama. Matar tana so tayiwa Teemah magana amma kwata kwata tarasa ta ina ma yakamata tafara dan tasan ko ayaya tayi maganar zai iya bada cewa tagaji ne da zuwan Teemah gidanta itakuwa bahaka bane manufar ta burinta Fateemah ta kasance mace ta gari abin alfahari agidan aurenta. Duk wani motsinta tanayi ne da tunanin yanda zata fara tunkarar Teemah batare data jahilci niyyarta da manufarta ba. Bayan sunyi sallar azahar sunci abincine da suka gama matar Umar take ce da Fateemah " _yanzu idan Mahmud yadawo gurin aiki_ _me zaici_ " " _bakomai_ " Fateemah tabata amsar tambayarta atakaice. Sai tasake fa'din " _kode shima irin kinne duka bakusan cin abinci hala_ " " _Ah'ah maman Amal muna ci mana harma shi yafini!_ " _Toh meyasa bazakiyi zauna agida kiyi masa girki ba"_ Fateema Sai cewa tayi " _shima yasani bana gida ne da ina nan zanyi masa ai_ " " _Me yasa toh bazaki zauna agida kiyi masa ba, Fateema kinsan kuwa 'dimbin ladan da_ _mace ke samu idan tayiwa mijinta hidima yaji da'di?" inji matar Umar_ . Narai-narai Fateemah tayi da idanu tace " _Allah ni Maman Amal tsoron zama agidan nakeyi ni ka'dai shiyasa_ " " _daurewa zakiyi kinji ahaka sai kiga kinsaba, amma idan kika ce bazaki na zama ba toh yaushe_ _zaki saba Fateemah_ " Shiru Fateemah tayi tana tunanin taya za'ayi ta zauna agida bayan Anty da 'kawarta so suke su maida ita 'yar ma'digo tace gara tayi ta yawo agurare data zauna agida su tarar da ita har zuwa ranar da daddynta zaizo sai su tafi abinsu yafi mata. Ji datayi matar Umar nasake lalla6a ta akan taringa zama agida yasa ta fayyace mata duk abinda ke faruwa, wanda ya matu'kar 'dagawa matar Umar hankali fiye da zaton mutun , abin ya kulle mata kai dataji cewar mother in-law 'din ta ce ke jagorantar abin, wannan wani irin al'amari ne haka. Fateemah dataga hankalinta yatashi tana ta maganganu sai tace mata tayi shiru dan Allah kar kowa yaji tasake tunatar da ita cewar Anty tace kashe ta zatayi idan tafa'di maganar wa wani tace dan Allah karta fa'dawa kowa. Jinta kawai matar Umar tayi domin bazata iya yin shiru akan maganar ba sam dole ne Mahmud yaji domin ya 'dau matakin daya dace tunda kam mahaifiyarsa ce, ze iya dakatar da ita. Koda Mahmud yazo 'daukan Fateemah kuwa cikin sa'a sai be shigo ba horn kawai ya danna mata daga waje dayake tunkan ya 'karaso yake 'kiranta ya sanar da ita. Fita tayi ta sameshi suka tafi. Matar Umar kuwa yanda maganar ya tsaye mata arai yasa takasa ri'keshi har sai da ta sanar da Umar komai. Umar kansa yayi mamaki, ya de san Anty bata son auren Mahmud da Fateemah amma be ta6a zaton 'kiyayyar Anty har yakai haka ba, domin be ta6a zaton Anty zata nemi lalata rayuwar yarinya 'karama irin Fateema ba. Umar har gani yayi dare yayi masa tsayi dan kawai yanda ya 'kagu gari ya waye ya ha'du da Mahmud. Mahmud kuwa tunda ya 'dauko Teemah sai yaga kamar ba'a daidai take ba haka dai ya 'kyaleta yana karantar duk yanayinta, har kusan 'karfe 8 na dare bata dawo daidai ba, tana kwance akan 2 seater yayinda shi kuma yake zaune daga gefenta ta 'dora kanta akan 'kafarsa tayi shiru, sai alokacin ya tambayeta meke damunta. Shiru tayi masa kamar bata ji abinda yace da ita ba, sai ma tayi yun'kuri ta tashi ta wuche bedroom, bayanta yabi da kallo har ta shige ciki, jijjiga kansa yayi tare da dawo da hankalinsa kan labaran da yake kalla. Minti shabiyar be 'kara ba yatashi yabi bayanta bayan yakashe dukkan swich 'din, domin gaba 'daya daina fahimtar labaran yayi zuwa wannan lokacin hankalinsa gaba 'daya ya tashi da ganin Fateemahn ahaka, ya tabbata akwai abinda ke damunta. Koda ya shiga 'dakin akwance yasameta dan haka sai ya wuce bathroom tsawon mintina biyar kafin ya fito yadawo kusa da ita ya zauna wanda tana ganin hakan tawani lumshe idanu kamar me bacci. Duk ya kula da hakan dan haka sai yayi murmushi kawai tare da 'kiran sunanta ahankali, sai da ya 'kira ta kusan sau uku kafin ta amsa kamar me yin baccin gaskiya. " _Tashi maza ki zauna tambayarki_ _zanyi_ " In a serious tune yayi maganar dan haka dolenta tami'ke zaune badan ranta naso ba. " _meke damunki ne wai yau 'dinnan please Fateemah banason ganinki a_ _irin wannan yanayin koka'dan, gaya min_ _kinji_ " ahankali tace " _bakomai fah yayah ni babu abinda ke damuna_ " " _me 'karya_ " ya fa'da da sigar zolaya. murmushi kawai Teemah tayi masa . " _Haba akwai mana, nasani akwai abinda ke damunki_ ........" Yana fa'da yana murmushin shima. " _Allah yayah babu komai_ "! Fateema ta tareshi da fa'din haka. Shiru yayi ya zuba mata idanu ita kuwa sai tayi 'kasa da idanunta tana wasa da yatsunta. Mahmud kwata-kwata kansa ya kulle ma yarasa ya zaiyi da ita. Hannunsa ya mi'ka yakamo nata hannun datake wasa da shi 'din yace mata " _me kike so toh gaya min kinji, i promise ko menene zanbaki shi_ " Jikinsa ta dawo ta kwantar da kanta akan kafa'darsa tayi shiru tana tunanin _toh me ma zatace dashi_ ? Ganin tayi shirun ne yasa Mahmud yasake ce mata " _gaya min mana Fateemah karkiji tsoro kinji_ " Murmushi tayi data tuno hirarsu da matar Umar 'dazun sai ta 'daga kanta ta kai bakinta kusa da kunnansa ahankali tace " _Yayah kasan me nake so_ ? Jijjiga kansa yayi alamar " _ah'ah_ ". " _Ni baby nakeso_ ". Tafa'da tana murmushi tare da komawa daga bayansa ta 6uya. Mahmud kam mamaki ma hanasa magana yayi kawai ya bude baki tare da zaro idanu. _Comment Vote and Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir rahmanir raheem* _Beauty catches the attention but character catches the heart........_ 🅿 *63* Tausayin ta ne yakama shi dan yasan kamar yanda bakinta ya furta hakan toh ko cikin zuciyarta ma hakan ne, kuma duk wanda yace ma yanasan 'da toh yana so 'dinne da dukkan zuciyarsa, saboda soyayyar 'ya'ya 'ka'k'karfar soyayya ce dake wanzuwa azu'kanta dukkan iyaye. Juyawa yayi gaba 'daya ya fuskance ta sai ta fara 'ko'karin guduwa daga inda yake. Hannu Mahmud yasa ya dawo da ita inda take zaunen sai tayi maza ta me da kanta 'kasa yanda baze ga fuskarta ba, 'kafafunsa dake tan'kwashe ta kifa kanta akai tana murmushi, hannunta kuwa ri'ke acikin nasa. Hakan kuwa datayi sai yasa Mahmud baya ganin komai sai bayanta. Shima murmushin ne ya kubce masa yana murza yatsunta dake hannunsa yace mata " _kinsan cewa abin kunya ne meyasa dama kika fa'da_ ? Luf tayi ta'kiyin ko motsi kamar ma bada ita yake maganar ba illah murmushin data keyi 'kasa-'kasa. Kunyan iyayin nata ba karamin birge shi yake yi ba, aransa ya yanke shawaran gara kawai ya gaya mata gaskiyan abinda ke faruwa dashi tunkan shirun nashi ya 'kurewa ha'kurinta. Mahmud jan jikinsa yayi ya jinginu da jikin gadon ya lan 'kwashe hannunsa akan 'kirjinsa tare da mi'kar da 'kafafunsa wanda hakan yabawa Fateemah daman kwantar da kanta da kyau akan 'kafafun nasa tana kallon gefe, har yanzu ta'ki ta kalli inda yake ma balle har su ha'da idanu dashi ita adole kunya takeji. Mahmud ne yafara magana da fa'din " _Fateemah kinsan kwanan nan nayi tafiya ko_ ? Shiru tayi masa taki yin magana, shima yasan bazata tanka sa ba dan haka sai yaci gaba da maganarsa. " _Daga Umar abokina babu wanda yasan dalilin tafiyar danayi wacce nayi ta ne dan neman magani wa matsalar data same ni da ni kaina bansan_ _takamamman lokacin da hakan ya faru ba, daga zuciyata sai Umar sai kuma ke da zan sanar dake ayanzun bayaga haka babu wanda yasan abinda ke damuna. Fateemah ada na kasance mutun ne ni lafiyayye ta ko wani 6angare wanda ni kaina na shaidi hakan bana bu'katar sai nayi_ _wani dogon nazari akan haka, dai-dai da rana 'daya ban ta6a tsintar kaina cikin wata matsala_ _acikin jikina ba, wanda badan nasan hakan ba da babu abinda zai sa in amince da batun auranki, bama ke ba koda kuwa wata_ _macece daban bazan taba yadda in aureta ba ko dan gudun kar na shiga hakkinta_ _ma_ . _Kwatsam bayan aure na dake sai na tsinci kaina cikin wani hali, halin da baze ta6a barina in rayu da iyalina cikin kwanciyar hankali ba, nakan gode Allah amafi yawancin lokuta daya sanya kece kika kasance mata agareni ba wata daban ba, wanda na tabbata da wata daban ce da yanzu mun da'de da samun matsala da ita ko ma mun_ _rabu, saboda ba kowacce mace bace zata iya zama dani ahaka yanayin da nake mu zauna cikin rufin asiri ba sai ko in nayi sa'a_ , _kinga ke kuwa kin zauna dani ahakan baki ta6a nuna min damuwarki akan haka ba baki ta6a_ _nuna min_ _gazawarki ko canjin fuska akan zama dani ba duk da nasan ba asan ranki bane, ni da kaina_ _nasan kina da bukatar kasancewa da mijinki alokuta da dama ba sai an_ _sanar dani ba ni ni shaida ne akan wannan.Fateema_ _kinga ko awannan 6angaren ma ka'dai dole in godewa Allah na tare da yabawa da za6in_ _Abbah na, domin shi yayi ruwa yayi tsaki wajen ganin kin kasance mata agareni. Ko_ _yanzun ma banyi mamaki ba dan kince kinada bu'katun baby_ _domin nasan wannan shine burin dukkan ma'aurata, ni kaina Fateemah inason baby amma_ _ayanayin dana tsinci kaina kinga dole ne na ha'kura na sanyawa_ _zuciyata salama har zuwa lokacin da Allah ya bani lafiya inda rabona sai kiga yabani"_ Hannuntan yasake kamawa ya rike cikin nashi tare da ran'kwafo da kansa kusa da nata kan sannan yaci gaba da maganarsa. " _Fateemah kema ina so kiyi ha'kuri kinji kitayani ro'kon Allah ya bani lafiya cikin gaggawa_ _wala Allah ko zamu dace dasamun farin_ _cikinmu_ " Yana kaiwa nan yasa hannunsa yadafa kanta sai ta juyo ahankali ta kalleshi, take kuma sai ta kauda kanta da barin kallon shi, ita bazatace ga yanayin datake ciki ayanzun ba domin maganganun Yah Mahmud gaba 'daya sun karya mata zuciya tama rasa tunanin me zatayi kwata-kwata, data san hakane ma da bazata kawo maganar babyn ba, ashe ita bata sani ba ashe matsala ce dashi har da take ganin kamar wai shi daban yake harda cewa matar Umar cewa su ba irin zaman dasukeyi ba kenan dashi, batasani ba ashe sirrin aurenta ta fitar. Mahmud kuwa hannunta dake acikin nasa ya kallah tare da 'dora 'dayan hannun nasa ya lullu6e natan dashi sannan ya 'kira sunanta ahankali. Kallonsa tajuyo tayi batare datayi magana ba jin yanayin da ya ambace tan cikin slow voice da sanyi, shima Mahmud be saurari jiran amsawarta ba ko hankalinta data bashi ma ka'dai ya wadace shi sai yace. " _Fateemah......ki yafe min_ _kinji......kiya femin dan Allah nasan ban kyauta miki_ _ba koka'dan ban miki adalci ba dana zauna dake ahalin danake ciki, amma inaso kisani banyi_ _haka dan na 'kuntata wa rayuwarki ba koka'dan face_ _dan rufin asirinmu dana mu, kuma insha Allahu inasa saran samun sau'ki acikin kwanakin_ _nan.......ki daure dan Allah ki taushi zuciyarki ki yafe min hakkinki dana kasa sauke miki a iya zamanmu_ _dake kinji........._ Da sauri ta 'kwaci hannunta ta tashi ta toshe mai baki da hannun nata sai suka tsaya kallon kallo dashi, kanta ta jijjiga masa ahankali tare da fa'din " _Ni baka min komai ba yayah kuma nasan har abada bazaka_ _ta6a yin wani abu dan ka cutar dani ko rayuwata ba, don Allah ka daina_ _neman gafara ta kaji Yayah_ ! _Kaifa kace ka godewa Allah da ya sanya nice matarka_ , _toh ni me yasa bazaka bani dama ingode masa ba da ya Yah Mahmud yakasance_ _shine miji ba agareni, dan kawai Allah ya jarabcemu da wata kaddara sai hakan_ _ya sanya ka neman yafiyata?, toh in hakane Yayah ni agurin nemo_ _yafiyar_ ? Hawaye ne yaji suke shirin gangaro masa saboda yanda kalaman nata suka ratsa shi, da sauri ya janyo ta ya rungume ta acikin jikinsa sannan ya lumshe idanu take hawayen nasa suka 'karasa gangarowa suka sau'ka akan wuyan Teemah. Akan la66ansa ya furta " _Allah ya miki albarka matata Allah ya albarkaci rayuwarki duniya da lahira_ " Yana gama fa'din haka sai ya rintse idanunsa da 'karfi tare da sake matse ta ajikinsa tamkar wani na shirin 'kwatarta. Damshin dataji asaman wuyanta ne yasa ta yunkuri ta 'kwaci jikinta daga nashi ta kalli fuskarsa sai taga still yana hawaye. Da rawar murya ta furta " _kuka kakeyi_ _Yayah_ ? Yatsansa yasa ya rufe mata baki alamar tayi shiru sai yasake janyota ya rungume ta akan kirjinsa tare da gyara zaman nasa zuwa kwanciya yayinda idanunsa ke kallon ceilling fan 'din dake saman 'dakin, Fateemah kuwa kanta akan kirjinsa ta kwanta tayi shiru itama gaba 'daya jikinta yayi sanyi. Hannu Mahmud yasa yana bubbuga bayanta ahankali tamkar wata yarinya 'karama yayinda yakejin wani sabon yanayi tattare dashi da be ta6a tsintan kansa aciki game da ita ba sai yanzun, ahankali bakinsa ya furta " _I love u Fateemah, i really love u with all my_ _heart, ha'ki'ka ke daban ce acikin mata, Allah ubangiji yabani lafiya da tsawon rai_ _dan kawai inkula dake da rayuwarki, in cika rayuwarki da soyayya ta yadda bazaki ta6a dana sanin kasancewa tare dani ba_ " Rasa takamamman yanayin da take ciki tayi alokacin farin ciki ne ko akasin haka kasa ganewa tayi, aru'de ta bu'di baki da niyyar magana "Ya....... da sauri Mahmud ya dakatar da ita da fa'din " _shiiiii_ " Take kuwa tayi shiru kamar yadda ya bu'kata 'din bata 'kara yin magana ba, shima kuma shirun yayi yana cigaba da kar6an duk wani sa'kon da zuciyarsa ke bashi game da Fateemahn, ahaka bacci yayi awon gaba dasu gaba daya. 'Karfe ukun dare yaji Fateemah na mutsu-mutsu ajikinsa sai kuwa ya bu'de idanu akanta gani yayi tana sake cusuwa masa ajiki tare da yamutse jikinta guri guda. Sunanta yafara 'kira ahankali yana 'ko'karin tada ita, bata amsa masa ba sai ma kuka data sanya tare da 'ko'karin janye rigarta tamkar rigar na mintsinin jikinta ne fincika take yi da 'karfinta kamar rigar nayi mata 'kai'kayi. Ganin haka yasa Mahmud ya ri'ke hannun nata sannan ahankali yajanye mata rigar yacire kamar yadda yaga take da burin yi. Mahmud idanunsa ya 'kura 'kur akan 'kirjinta wanda suka matu'kar tafiya da imaninsa. Tun aurensa da ita be ta6a tsayawa ya 'kare musu kallo har haka ba sai yanzun, ha'ki'ka Allah yayi halittarsa awannan gurin. Hannu yakai da niyyar ta6a wa sai yaji sau'kan numfashinta ahankali, dubansa ya mayar kan fuskanta sai ya ga ma har tayi bacci. Ajiyar numfashi ya sau'ke tare da hamdala azuciyarsa daya kasance abin nata be ja tsayin lokaci ba yau 'din. Fasa ta6awan yayi kawai sai yaja mayafi ya lullu6a mata. Yana rufa mata mayafin ya mi'ke ya wuce bathroom alokacin 'karfe uku da mintina ashirin (3:20am) dan haka alwalarsa ya 'dauro yazo ya tada sallah raka'ah hu'du yayi ha'de da sallamarsa guda biyu sannan ya 'daga hannu ya dinga zuba musu addu'o'i na kariya da zaman lafiya harma da nemawa aurensu albarkar mahalicci, yana shafawa ya janyo Al qur'ani yafara karantawa kafin lokacin sallah yayi saida ya karance suratul Ankabut sannan ya rufe karatun nasa da suratul Ikhlas, Nasi da Falaq ya shafa da salatin Annabinmu Muhammad ( S.A.W). Saida yayi raka'atanil fajri kafin ya kawo sallar asubarsa abayanta. Be tashi agurin ba sai da yayi azkar 'dinsa na safiya kafin yatashi yaje ga Teemah domin yatashe ta itama tayi tata sallar, alokacinma gari har ya 'dan fara haske. Koda yatashe tan ma da 'kyar ta bu'de idanunta saboda nawin dataji kanta yamata ga kuma bacci da har alokacin be bar idanunta ba, tana daga kwancen ta bu'de idanunta sai kuwa ta hango windo gani tayi gari har ya fara haske. Da wuri ta mi'ke arazane ganin lokaci yatafi, sai kuwa takoma da sauri sanadiyyan ganin jikinta bakaya. Mayafin data yaye ajikin tan ta kuma janyo wa ta 'kara rufe jikinta dashi. Mahmud yi yayi kamar be ganta ba ya wani fuske ya kauda kansa gefe. Teemah kuwa baki ta turo gaba tana gunaguni 'kasa baya ma gane mai take fa'di. Mahmud kuwa murmushi yayi mata kawai tare da fa'din " _Gara ma ki bu'di baki ki fa'di abinda ke ranki yafiye miki dan kukkuni ba ze kaiki ko'ina ba_ " Baki ta 'kara turawa gaba tana kalle kalle shikuwa sai ya rin'ka binta da kallo kawai murmushinsa na 'kara yawaita. Data ga bata samu abinda take neman bane sai ta bu'di baki cikin shagwa6a tace " _Ni kam wallahi Yayah ka daina ciremin rigata idan ina bacci_ " Ido ya 'dan zaro waje yace " _waye yagaya miki ni ne_ _na cire miki_ ? Kamar zatayi kuka tace " _Ehh mana kaine idan ba kaiba wayene naga ni dakai ne kawai acikin gidan_ " cewa yayi " _Dan ke da ni ne kawai agidan kuma sai aka ce miki ni ne na cire ko_ ? " _Toh waye ne yacire min_ ? Da muryar kuka ta tambayeshi tana kallonshi. " kai ya kaudar gefe cikin ko inkula yace " _toh idan ma ni 'din ne ai ke kika sani, kece kika ce incire miki saboda tana_ _damunki_ " Yanzun kam kukan tafara yi masa acikin kukan kuwa tace " _bawani ni kam wallahi ban fa'di haka ba, kawai dan kaga ina bacci na sai kakama kayi_ _min sharri_ " Ta 'karashe da kukkuni 'kasa-'kasa tace " _kawai ka kama ka wani ganewa mutun jiki abanza_ " Tsayawa yayi yana kallon ta domin ayanda yasan Fateemah sarai yasan da iya gaskiyarta take wannan fitinan babu zancen wasa aciki. Ita kuwa tana cikin fa'dar hakan ta hango rigar tata daga 'kar'kashin pillown dake gefenta sai ta sa hannu ta janyo ta still bakinta ature. Tana 'ko'karin sawan ta 'dan saci kallonsa sai kuwa taga ita yake kallo. Kwa6a fuska ta'karayi tare da tura 'kafafu kamar wata karamar yarinya cikin sakalcin kuka da takaici tace " _toh Yayah ka daina kallona mana nii dan Allah_ " Shima cikin halin ko inkula yace " _Idona yana cizonki_ _ne_ ? Ya tambayeta batare da ya kauda idanun nasa akanta ba. " _Toh ka juya zan saka riga ne fah_ " Cewa yayi " _me kuma za'a 6oye min, kin manta ne nagama ganin komai_ ? Kukan shagwa6a ta fara tare da dukansa da rigar hannun nata tana 'kara 'ri'ke mayafin data kare kirjintan dashi da hannunta daya. Mahmud kam yana dariya yatashi yabar mata 'dakin ya koma parlour. 'Karfe shidan safiyar ranar Hannah ta danno mata 'kira alokacin ma ko tashi akan sallaya batayi ba jin 'karan wayan ne yasata ta tashi ta 'dauko ta. Ganin Hannah ce ke 'kiran yasa ta zauna abakin gado tare da amsawa. Gaisawa suka yi Teemah ta tambayeta Ummah da lafiyarta. Hannah kuwa tace da Teenahn " _Ai itace ma tasa na 'kiraki tun jiya ta damu akan na 'kiraki wallahi, wai bata ce idan kin dawo gida ki ha'data da Mahmud_ _bane shine taga shiru har yanzu baki 'kira ba shiyasa ta damu_ " Teemah Cewa tayi da Hannah " _ke nifa babu inda naje dama shirin 'karya nayi dan nasan idan akaji hakan za'a sanar dani abinda ke faruwa dasu Mummy, kuma baga shi ba 'karyata tayi min rana nayi waya dasu mummy harda daddy ba, amma fah dan Allah Hannah karki fa'dawa Ummah haka kawai kice mata wayata bata shiga ne kinji_ " Dariyar mugunta Hannah tayi tare fadin " _Na yaushe kuma yarinya kin makara ai Umnah kan gata nan agefena_ . " Ido Fateemah ta zaro waje tace da Hannahn " _dan Allah dagaske_ ? " _ko de inbata wayar ne 'kilan zaki fi yadda....._ 'Kit Fateema takashe 'kiran tare da kashe wayar ma gaba 'daya tana rufe baki kamar Ummahn na gefenta. Aranar ma da Mahmud zai tafi aiki binsa tayi ya sau'ke ta agidan Umar, shikansa yana 'dan jin kunya yanzun da yawan zuwan Teemahn gidan be san da me zasu fassara hakanba, kuma kar yazamana yawan zuwan Teemah gidan ya kasance yana cutar da matar Umar, shikansa bayason hakan amma be san yadda zeyi ya dakatar da ita ba. Domin koda yace zai kaita gidan Anty ma ba yadda take ba har intaji hakanma sai yaga tafi rikicewa fiye da idan yana ro'kon ta akan ta zauna agida, kuma shi aganinsa ai gidan Anty yafi tunda ko ba komai gidan mahaifinsa nan ne gadaransa . Wannan sabon salon Teemahn na 'daure masa kai matu'ka yanda fir ta tsani zama agida yanzun be san dalilin ba amma shi bayajin da'din hakan ko ka'dan. Haka ya isa office zuciyarsa cike da tunani. Yana zuwa ko zama beyi ba Umar yatare shi da wani sabon batun daya kusan juya mai 'kwa'kwalwa, jiyayi badan abakin Umar abokinsa maganar ke fitowa ba da babu abinda zai hana yayi wa wanda yafa'da 'din mugun dukan da sai yaga stars a idanunsa. Amma dayake Umar ne sai kawai yayi shiru yana sauraransa ransa kuwa gaba 'daya a6ace yake jinsa, daga 'karshen ma daina fahimtar komai yayi yade yi shiru ya zuba wa bakin Umar 'din idanu motsin da bakin yakeyi ka'dai yake iya gani. Har Umar yayi yagama maganar be tankasa ba sai da ya matso ya dafa kafa'dunsa yace " Ban fa'da maka maganar nan dan in tozarta ka ba Mahmud face dan kawo gyara wa lamarin, kai da kanka ka zauna kayi nazari akan haka inajin dakanka zaka fahimci gaskiya, ni kaina naso nayi jayayya kan maganar amma idan kaduba yarinyar nan ka kula da tsanar zama agida datakeyi ita ka'dai shika'dai ma ya isa yasa ka yadda cewa akwai wani abin a'kasa, inaso kabi ahankali harka gano asalin meke faruwa kuma suwaye ne suke shirin yi mata hakan" Umar nagama fa'din haka ya juya ya fita ya bar Mahmud zaune saroro yana tunani. Jiyayi komai ma ya tsaya masa cak, waye.....waye da wannan mugun nufi akan Fateemah,Tunaninsa yakasa bashi ko waye ne. Haka ranar ya wuni a office be tsinana abin kirki ba, koda ya biya 'daukan Teemah ma jikinsa duk da sanyi ita kanta Teemahn sai taji wani iri babu da'di sanadiyyar ganin Mahmud 'din ahaka. Zaton ta ko abinda tamasa da safe ne ya6ata masa rai shiyasa har yanzun be sau'ko ba, amma ai da zasu fita gida ba haka yake ba alokacin har tsokananta yake yi ma. Shiru tayi tana satan kallon shi lokaci zuwa lokaci shikuwa gaba 'daya hankalinsa akan tu'kin dayake yi ya mai dashi wanda hakan yasake rikita zuciyar Fateemah sam takasa samun natsuwa. Koda suka koma gida ma harkokin dake gabansa kawai yayi yayin da Teemah kuwa hankalinta duk yana wajensa sam bata jin da'din yanayin Yayan nata ayau. Har se da akayi sallar maghrib bayan ya dawo gida daga masallaci ya zauna a parlour wanda jin motsinsa yasa ta fitowa tazo gefensa ta zauna tsabar yanda hankalinta yakasa kwanciya ma ko hijabin datayi sallar bata cire ba Fuskar tausayi tace " _Yayah nayi maka wani laifine_ ? Shiru yayi beko kalleta ba. Sai tasake fa'din " _Pls Yayah kayi ha'kuri toh ka yafe min bazan sake 6ata ma rai ba_ " " _Kaji_ ! Be yi magana ba illah juyowa da yayi ya kureta da idanu, itakuwa kasa tayi da nata idanun ganin yana kallonta, kamar ba zeyi magana sai can shima yajefa mata tambaya yace " _Fateemah idan na miki tambaya kinyi al'kawarin zaki_ _sanar dani gaskiya_ ? Zuciyarta taji ya tsinke duk da bata san tambayar da ze matan ba amma gaba 'daya sai taji bata son yayi tambayar. 'Daga idanu tayi sai kuwa caraf suka ha'da ido da Mahmud shikuwa be jira jin amsarta ba yaci gaba da maganarsa. _Comment, Share and Vote @_ ~Serlmerh-md~ *Salmerh ce* 😍 [10/2, 6:02 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir rahmanir raheem* _Laugh when you can, apologize when you should and let go of what you can’t change........_ 🅿 *64* "Fateemah kigaya min meyasa baki son zama agidannan idan ke ka'dai ce? Da rawar murya tabashi amsa da fa'din" banace maka tsoro nakeji ba" " Tsoron me kike ji inason yau ki gaya min" Mahmud ya fa'da da sauri. Kame kame tafara tarasa ma me zata ce dashi sai ni.......ni....tsoron....... ts Ganin batada niyyan fa'da masa sai yasake jefa mata tambayar su waye suke zuwa gidan nan idan baya nan. Da sauri tace "Bakowa " Tana rarraba idanu. Shima ce mata yayi " 'karya kikeyi Fateema nasan akwai, ki fa'da min zansa ayi maganinsu kinji, bazan ta6a bari su cutar min dake ba muddin ina numfashi, ko kinfiso kullum ki dinga zama agidan mutane yafi miki akan gidan mijinki? Shiru tayi tana sauraransa sai ya kamo hannayenta yari'ke acikin nasa da sigar lallashi yace " _Fateema nifa mijinki ne,me burin ganin farin ciki da walwalarki akowani lokaci, meyasa kika_ _za6i ki 6oyemin damuwarki bayan ni yakamata in fara sanin me_ _kike ciki amma sai de naje naji awani guri Fateema kinajin hakan kinmin adalci_ _kenan_ ? _nine fah me hakkin kula da duk wani hakkinki da_ _damuwarki ayanzun meyasa bazaki bani wannan matsayin ba_ " Fateemah kam haushin kanta take ji ayanzun dan tasan da bata nemi jin damuwarsa ba da baze tuhumeta da wannan maganar a dai-dai wannan lokacin har haka ba, ita kuwa ayanzun da jiran zuwan Daddy kawai takeyi me zesa tafa'da masa abinda ke faruwa, kalan aje akasheta kafin Daddy yazo. Shirun da Mahmud yaga tayi masa ne yasa shi bu'dan baki yana 'karfafa mata zuciya da fa'din " _kar kiji tsoro Fateemah karkiyi kokwanto ko shakka dan Allah ki gaya min kinji_ _am always here 4u_ " Kalmar nan dayafi tsana tasake maimaita, masa wato " _bakomai fah Yayah in akwai ai zan gaya maka_ .... Kallonta yayi cikin idanu domin zuwa yanzun haushi tafara bashi " _Fateemah kina ganin kamar 6oye min damuwarki shine zai kawo miki masalaha acikin_ _al'amuranki ko_ ? _Shikenan idan hakan kike ganin yafimiki so be it nima bazan damu_ _ba, bazan 'kara damuwa da irin hakan ba tunda baki san ina shiga_ _lamuranki_ !" 'Kasa tayi da idanunta da suka cicciko da hawaye tsawon mintina biyu bata 'dago tasake kallonshi ba, hakan yasa Mahmud ya fahimci cewa bazata sanar da shi 'din ba kenan. Tashi yayi da sauri ya tsaya tare da sa hannunsa 'daya ya naushi cikin 'dayan da 'karfi. Kansa yadafe zuciyarsa na masa suya sam yarasa ya zaiyi da ita, 4d first time arayuwarsa da taurin kan Fateemah ya 6ata ransa, daya san bazata sanar dashi ba da be bari Umar yatafi batare da ya sanar dashi ko suwaye suke neman lalata masa rayuwar mata ba. Damuwarsa be wuce yasan kosuye ba, domin yana mamaki, tsawon watanni biyu kenan da zuwan Fateema garin Lagos amma be ta6a jin tamasa hiran wasu da tasani anan 'din ba, kamar yadda yasan bata ta6a fita da sunan ziyartar wani gida ba haka itama bayaga Anty mahaifiyarsa babu wanda ya ta6a zuwa gidan nasu hatta abokansa tun bayan aurensa basu 'kara zuwa ba, mamakinsa shine ya akayi masu neman nata suka santa, da wani lokaci kuma a ina da har zasu nemi maida masa ita jinsin 'yan ma'digo. Toh in dagaske ne meyasa kuma bata sanar dani ba tunda har bata so wanda dalilin hakan nema yasa bata son zama agida, kenan har cikin gidanta suka sameta wannan ai rainin hankali ne. Tunowa yayi da maganar Umar inda yace wai anmata barazana da kisa ne idan har tashigo da wani cikin lamarin, kenan hakan ne dalilin daya sanya ta'ki ta sanar dani, in hakane kuwa lallai mutanen nan basu da hankali, har yaushe zaka sa yarinya 'karama irin Fateemah agaba, meyasa bazasu je su cigaba da yin sha'aninsu a iya junansu da suka saba ba har se sun shigar da innocent soul irin wannan a haukansu. Fita yayi haraban gidan ya ringa gwada 'kiran wayar Umar amma baya 'dagawa haushin haka ya 'kara sa shi jin suya acikin azuciyarsa, jiyake badan dare bane yanzun da babu abinda zai hana shi zuwa wajen Umar 'din ya tuhume shi sai ya sanar dashi kosuwaye ne, dan yanada ya'kinin Umar ze san wani abu akai tunda har labarin ya iso kunnansa, sai de ayanzun shikanshi baya so ya rin'ka garajen barinta agida saboda rashin sanin me ze iya biyo bayan hakan. Haushin kansa ma yake ji da shi da kansan be tsanantawa ransa tunanin dalilin dake hana Fateema zama agida ba, ya tabbata daya nutsu ya bincika da kansa wata'kila da tuni ya san meke faruwa, amma bakomai ko yanzun ma lokaci be 'kure masa ba, da iznin Allah zai bincika 'din kuma zai samo su dakansa koda Umar be fa'da masa ba. Wannan karan kam ba ze yi shiru ba Abbah zai samu yafa'da masa abinda ke faruwa inyaso sai yayi magana a division sukawo masa security ana yi masa gadin gidan a 6oye, kodan ayi saurin kama wa'danda ke da hannu akan lamarin cikin sau'ki. Umar kuwa ya 6oye wa Mahmud sunan dayaji ne akan lamarin badan komai ba sai dan saboda gudun kuskure, kar yaje kuma bayan yafa'a masa bincike yazo ya nuna bahakan bane yaji kunya daga baya shiyasa ya 6oye masa sunan yafi so idan ma su'din ne toh binciken sa ya nuna masa base yaji daga bakinsa ba, kuma idan ya bincika dakansa yaganecgaskiya zefi yadda da batun sa6anin idan aka sanar dashi baze yadda ba sai kaida ka fa'dan idan kayi wasa kanka fushin zai dawo. ***** *MAIDUGURI BORNO* *STATE* Rayuwa yanzu tayiwa Abbas zafi, sam baya ta6a jin da'din duk wani abu dayakeyi, wanda tun farkon auren Mahmud da Fateemah ya tsinci kansa a wannan yanayin, dalilin ma daya sanya shi neman hanya ya taho Barno kenan amma still ya kasa saita al'amuransa, wanda ada yake ganin kamar yin hakan ze 'dabe masa kaso mafi yawa daga cikin damuwarsa amma sai yaga hakan ya kasa yiwuwa agareshi, be tashi fahimtar Fateemah ce rayuwarsa ba har se da ya tabbatar da cewa yarasa ta, shikanshi be san iya adadin soyayyar da yake mata ba sai da yaji labarin za'abawa Mahmud auren ta sannan ya farga da hakan. Rayuwarsa bayan auren Fateemah ta kasance ne gaba 'daya ajuye alokacin komai yakeyi Fateemah ce kawai ke zuwa tunaninsa da idanunsa akowani lokaci, ganinta yakeyi tare da wani da sunan mijinta ne wanda shida kansa shaida ne akan haka. Ya kan 6ata lokaci yana tunaninta ko kuma yayita kallon pictures 'dinta dake cikin wayarsa wanda ita kanta ma bata san da zamansu ba, musamman yake yawan zama da wayarsa agefensa saboda yawan 'dagowa yaga hotonta daya keyi akan lokaci sam baya gajiya, wani write up data ta6a rubutawa ranar da hutunsa ya'kare a Damaturu wannan ma baya ta6a gajiya da karantashi idan yana karantawan kuwa harji yake kamar muryan ta ne ke karatun azuciyarsa tsaban yanda yasata aransa, idan kuwa yazauna yana tuno childish behaviourn ta shi ka 'dai se de kaga yana murmushi duk kuwa da 'kuncin da zuciyarsa take ciki amma baya ta6a denying murmushi akan tunaninta, yagama bawa ransa tabbacin cewa Fateema daban take agurinsa, bayaga mahaifiyarsa da Hannah arayuwarsa be ta6a bawa wata mace muhimmanci ba kamar Fateema shikansa ya yadda cewa irin soyayyar dayake matan nan ba me yankewa bace har abada domin ko bayan auren nata ma be ta6a jin soyayyar ta taragu acikin zuciyarsa ba koda da 'digo 'daya ne. Ganin kamar abin na neman illata masa future 'dinsa ne yasa yanemi hanyar zuwa Borno alokacin har angama cire list ma amma ya nemi asaka shi, wanda kusan kowa idan yaji yana mamaki domin dayawan mutane basu so koka'dan ace sunan su yafito ajerin masu zuwa borno sai gashi shikuma dakansa ma ya nemi asakaya shi, ogansa yaso ya'ki amincewa amma Abbas 'din yadage ya kwantar da kansa yace ko na 5months ne pls akaishi yagaji da zama anan 'dinne kuma shima yanaso adama dashi cikin masu karawa da 'yan ta'addan. Da hakan yasamu aka sanya sunanshi aciki. Bayan bikin Fateemah da sati uku Abbas ya gudu Maiduguri, tunda yazo kuwa abubuwa suka so shan kanshi domin har alokacin dai-dai da kwayar zarra zuciyarsa bata sarara masa daga tunanin Fateemah ba, inda yasami sau'ki ma yanzun baya waya da Mahmud saboda rashin network dan Mahmud baya kwana hu'du me kyau batare da ya 'kira sa ba, wani lokacin sai yaga kamar da gangan Mahmud 'din keyi masa hakan, domin he can't deny it, ba'karamin kishin Mahmud yakeji ba har zuciyarsa ya tsani ganin 'kiran Mahmud awayarsa amma ahakan yake daurewa wani lokacin har shima yake 'kiransa kafin yadawo Maidugurin kenan. Rashin hanyoyin sadarwan dake Jihar Borno yasa ya'danji dama dama yanzun yarage masa ne tsakaninsa da zuciyarsa kawai tunda ba zaiji labarin komai daga wurin kowa ba. Yakan yiwa wayarsa caji duk da batada anfani saboda ba 'kira yakeyi da ita ba kuma shima babu damar a'kirashi amma dan kawai ya ringa kallonta aciki yasa sam wayar bata rabo da caji, duk da idan ya farga da abinda yakeyi 'din yakan yi gaggawan bari tare da neman yafiyar ubangijinsa saboda ayanzu amatsayin matar waninsa take, amma he can't help it baya sanin lokacin da yake zurfafawa atunanin nata ko kuma duba hotunanta da har yau yakasa maye gurbinta azuciyarsa da wa ta. Yanaji tamkar yagama da al'amarin mata arayuwarsa, tun rabuwarsa da Fateemah be 'kara kallon wata mace sau biyu bama balle har yamata kallon mata. Bayaga mahaifinsa dake ta matsa masa akan aure shi kan baya jin kamar ze iya zama da wata mace amatsayin matarsa, ita ka'dai yaso ta ya 'kaunace ta ita ka'dai yabawa muhimmanci arayuwarsa, ita ka'dai take da gurbi da matsayi babba azuciyarsa kuma baya jin akwai wacce zata maye wannan gurbin har abada. Wani sa'in yakanyi mamaki domin kafin rabuwarsa da ita yasan already Fateemah nada feelings akansa, amma be san meyasa ta ta amince da auren Mahmud ba, ko dayake wasu soyayyarsu ba guda bace takan rarraba kanta zuwa wani 6angaren daban. Da yawan lokuta Fateemah yake 'daurawa laifi dan shi aganinsa da amincewarta ne komai ya wakana badan ta amince ba da yasan daddy bazai ta6a 'daura mata aure da Mahmud ba, wani lokaci sai yaga kamar da gangan ne taza6i Mahmud akansa danta muzant shi. Bayan zuwan sa Maiduguri da 'yan kwanaki ne ya 'dan fara jin dama-dama azuciyarsa game da Fateemahn badan komai ba sai dan yariga yasawa ransa cewar tabarshi kenan har abada, kuma sai yake ga dama haka 'kaddarar rayuwarsu tazo kaddara kuwa dolen kowani musulmi ne ko ya so ko ya'ki sannan aikin daya kawo shi maiduguri ma sai ya 'kara 'dauke hankalinsa gaba 'daya daga kan mafi yawan abubuwan rayuwarsa, abubuwa duk suka rinca6e masa, komai na rayuwarsa yaja baya, be fiya samun lokacin da ze zauna yayi tunanin rayuwarsa ba ko wani abu daban, abinda kawai yasa agaba shine ta'addacin dake bawa jahar borno kashi yake kuma sasu rayuwa cikin 'kunci da tashin hankali akowani lokaci. Wannan dalilin ne yasanya komai ma yabar kansa hatta Fateeman yakan wuni ya kwana bata shigo cikin tunaninsa ba, sai yake jin ma hakan yafi masa gara ya fuskanci rayuwarsa ya manta da duk wani abinda ya wuce tunda bashi da ikon canja komai, sai de dukda haka al'kawarin daya yiwa daddy kullun yana cikin ransa so yake abubuwa su 'dan tsagaita masa yasamu damar cikawa daddyn al'kwarinsa kamar yadda ya 'dauka, lokaci ne basamu ba amma be ta6a mantawa da hakan ba, yariga yasawa ransa zuwan duk da zuciyarsa bataso amma dole ne yaje Lagos saboda Daddy yafi 'karfin wasa arayuwarsa. ***** *LAGOS STATE NIGERIA* _8:21am_ Munnira ce zaune agefen a kan dinning table Anty yayinda ke siffing tea ka'dan-ka'dan at d same time kuma Anty ke bata ha'kuri tare da sake jaddada mata cewa takusan samun Mahmud a hannu domin Chiddy nasamun abinda takeso komai zai zama tarihi. Dariya Munniran tayi tace " _ai na dena damuwa Anty, tunda naje ni aka_ ' _kara duba min cewa har yanzu aikina na jikinsu hankalina yakwanta_, _dan nasan kowan nan ka'dai na dogara dashi ma makami_ _ne babba balle kuma ke da kanki kinsa min hannu_ " Anty ma murmushi tayi tace " _ke kuwa 'yar nan wani irin aiki kikayi haka_ ?. Munnira kwashe komai tayi ta sanar da Anty. Tace " _ai tun ranar dinner 'din auren su_ _nayi_ _maganinsu, kinsan yanda nake son Mahmud haka nake kishin sa, toh taya zan bari inagani ya_ _ra6i wata mace daban ni ina nan........._ Kaita ta juya ka'dan tace " _zuciyata bazata iya 'dauka ba Anty, shiyasa nasaka akayi musu_ _katanga wanda bazai ta6a bari su anfani juna ba , ita nasa akasawa_ ' _karfin sha'awa wanda idan ya 'debe ta dole sai ta nemi atallafa mata....._ _amma fah Anty da 'kyar nasamu aikin yayiwu......._ " _Mtheww wai su adole masu rotson Allah, kinsan kuwa wanda nayi mata ranar dinnern_ _ma ko kamata beyi ba, sai da na koma shine bokan yace min wai sede atura mata aljani wanda zai ri'ka sata jin_ _sha'awar ammafa bakowani lokaci ba, sai in lokacin daya samu kanta_ _tukunna sannan se sakata, shi 'dinma Anty da 'kyar yasamu yashigeta_ _inji bokan, amma jiya dana koma yace min komai_ _normal, shirina yana tafiya akan_ _tsari banda_ _matsalar komai_ ". Kallon Anty tayi wacce tabaza kunnuwa take jin tsaban shu'umanci irin na Munniran sai ma taji ta 'kara birgeta data yi maganinsu, ai ita da farko ma tunaninta beje ga hakan ba tazauna sa'ka'ka kawai tana jiran rabuwarsu ashe hauka tayi, inbadan Munniran ta yun'kura bama ai tanajin abun nasu sai yafi haka. Sai de kuma ai yiwa Fateeman haka bashine mafita ba, domin koda abun yatashi mata mijinta ze iya yin maganin matsalar ai tunda shi ba 'a yi masa komai ba. Sai de duk da haka ta wani guri batun Munniran ze iya samun kason maki mafi girma idan aka gangara 6angaren yawan bu'katuwa da kuma sashin gazawa. Ta iya yiwuwa hakan ya ta6a zaman lafiyarsu idan mijin yaga ji da yawan bu'katan Fateeman ze iya nuna gazawarsa wanda ta nan babban matsalan zai iya bayyana harma ya illata farin cikin dake cikin zamankewarsu....... lallai Munnira tayi tunani me kyau. Anty na cikin wannan tunanin se Munnira ta katse ta da fa'din " _Anty kinsan iskancin dana sa akayi musu kuwa_ ? Da kai Anty ta bata amsa alamar " _a'a_ ". Murmushi Munnira tayi sannan tace " _Mahmud bashi da daman taimakon Fateemah koda jarabarta ta tashi_ _saboda shi bashida anfani, tsakaninsa da ita sai de kallo Anty, kinga idan_ _abun ya isheta dole zata nemi mafita mafitar danasan bazai wuce tace_ _araba auren sun ba, kinga dazarar auren yarabu sai inkoma insa adawo wa_ _Mahmud da lafiyar mazantakarsa sai muyi aurenmu dashi, ko kuma ince ya aureni ni zan iya_ _zama dashi ahakan tunda ita ta'ki kinga bayan an 'daura auren sai lafiyarsa ta dawo ni_ _kuwa zama daram Anty sai ke sai jikoki"_ Ta 'karashe maganar da dariya. Anty ma murmushi tayi da farko dataji batun Munniran akan Mahmud hankalinta ba 'karamin tashi yayi ba amma 'karshen labarin sai ya wanki wancen 'din tunda taji komai zai dawo normal daga baya sai taji ranta wasai. " _lallai kanki naja 'yan mata shiyasa nake 'kara sonki ai, dan nasan ki akwai kishin kai, sai dai kuma fah karki kuskura wannan abin yata6a min lafiyar yarona dan kinsan mutuncinsa kenan_ _ako'ina_ " Wani dariyar 'keta Munniran tasaki kamar wanda Anty sa'ar ta ce, Sannan tace " _Haba Anty,ni da nake farautarsa dan anfanin kaina taya kuma zan bari gangancina ya illata sa, komai da kike gani akan tsari nake yinsa kuma kafin ayi aikin sai dana tabbatar da cewa za'a iya rabashi da hakan_ _aduk lokacin dana bu'kata kinga kuwa ai ba abin damuwa_ _anan_ ". Anty kuwa tamkar wawuya haka take binta da idanu domin gaba 'daya ta tsinke da lamarin yarinyar gani takeyi tamkar wannan tamafi uwarta shu'umanci, amma tsabar haukan Anty bata ji ko 'diris aranta cewa wannan ba kalan auren 'danta Mahmud bane sai ma taji 'karin 'kwarin gwiwa akan Munniran. Ita kuwa Munnira tana gama fa'din maganar ta mi'ke tsaye tare da gyara zaman rolling 'din dake kanta tace " _Yauma ni kinga son ganinshi nakeyi wallahi shiyasa ma kika ga na fito_ _da sassafen nan office 'dinsa zani gara tun wuri mu fara_ _fahimtar juna tunda gab muke da zama_ _abu 'daya_ " " _Aikuwa da gaskiyarki_ " Anty tabata amsa gami da fa'din, " _inkinje ki dawo dan Allah kafin ki wuce gida akwai sa'kona_ " " _Toh Anty bazan_ _ma da'de ba_ _zandawo_ " Munnira tayi maganar tana nufan 'kofar fita daga parlourn. ***** Mahmud kam lokacin daya shirya fita aiki exactly be sa6a lokaci ba yakan yawaita barin gida 7:30 dayake sai 9:00 ake bu'de kamfanin nasu so yana samun time yayi komai atsanake. Ko yau 'din ma haka yayi shirinsa cikin wata arniyar shadda gezna milk colour, Fateemah nata binsa da idanu domin ita yau 'din gaba 'daya bata jin da'di, fargaba ne yacika mata zuciya da batasan kona menene ba, hatta ga6o6inta asake take jinsu, duk abinda Mahmud yakeyi da idanu kawai take binsa. Break fast ma yau tea ka'dai taha'da masa ita kam tasha ma sam ta gagara shine dai yasha ka'dan sai ya tashi da niyyar tafiya, itama mi'kewa tayi dama already mayafinta yana ajiye agefenta sai kawai tafara warware shi. Ganin hakan yasashi tsayuwa saroro yana kallonta sai data gama warwarewan kafin yace mata " _yau fah ba inda zakije, agida zaki zauna tunda kin'ki ki sanar dani_ _dodon dake hanaki zama, kuma ma kinga yau friday ne bazan da'de ba zandawo 12:00_ _za'a rufe office ki_ _zauna agida kijirani_ " Fateemah najin hakan tafara masa kuka dayake daman acike take da damuwa so kamar jira take yayi maganar kawai tafara masa kuka tana fa'din "wallahi ita bazata zauna ba. Yayi -yayi ta sanar dashi matsalan amma ta'ki, sai kawai taci gaba da kukanta, haka Mahmud ya6ata tsawon lokaci yana bata baki da lallami akan ta ha'kura ta zauna agida amma ta'ki. Daga 'karshe kawai ya ha'kura yasata agaba yace toh suje a lokacin ma har 8:01am tayi. Haka suka kulle 'kofan suka nufi inda motarsa take. Har yayiwa motar key sai ya tuna ashe ya baro jakansa aciki wanda ke 'dauke da dukkan muhimman abubuwansa na wajen aikin. Fita yayi yakoma ya 'dauko jakar wanda ya barta anan kan cough inda ya zauna dan rarrashin Fateemah. Gurin motar ya koma ya bu'de baya ya ajiye jakar duk da idanu kawai take binsa. Be shiga motar ba taga yasake komawa cikin gidan can bayan mintina biyar sai gashi yafito da 'dan saurinsa yashiga yace " _kin wani ha'da min Tea me sa fitsari sai da na koma na yi kafin naji dama dama_ . Kauda kai kawai tayi dan batasan me zata ce dashi ba damuwar ta ma ka'dai ya isheta. Horn ya dannawa Gate man 'dinsu dake daga can baya yana duba flowers 'din gidan. Da gudu yazo yafara 'ko'karin bu'de gidan, kafin ya 'karasa tura gate 'din ne sai Mahmud yasake ce mata " _inajin kamar nayi mantuwa aciki wallahi, kuma fah bakomai bane tsaban yanda kika_ _rikitani ne da rigimarki yasa nake ganin haka_ ." Shiru tayi masa yanzun ma shima kuwa sai ya shareta yaja motar yayi gaba dai-dai inda gateman 'din yake ya tsaya kamar yanda suka saba kullum suka gaisa sai de yau Mahmud yaciro ku'di ya dan'ka masa ko jiran godiya be yiba yaja motar suka fita. Sai da suka hau kan titi kafin ya 'dan kalleta yace " _inajin nextweek fah zan koma katsinan nan, se ki shirya tafita bakince_ _zaki_ _rakani ba_ ? " _Umm_ " Tace a'kasan ma'koshi. " _toh sai ki fara shiri domin da mota zamu_ " 'Dan sake fuska tayi ka'dan tace " _zamu har Abuja ko_ _Yayah_ " " _Insha Allahu, ko ni banje ba ke zaki je_ " ya bata amsa atakaice. _Toh fah readers sai ku mammatso kusa domin jin yanda ha'duwar Mahmud, Munnira da kuma_ _Teemah_ _zai_ _kasance_ ........za'a kafta🤞🏻 ~Taku akullum Salmerhmd.I heart u all masoyana.~ 🥰 _Comment, follow, Share and Vote@_ ~Serlmerh-md~ *Salmerh ce* 😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* Dedicated 2my lovely fans da ke ~whattsapp~ ~facebook~ & ~Wattpad~ Inayinku sosai nima, Allahu ya bar 'kauna. 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir rahmanir raheem* _True friends are not the ones who are there when it’s convenient. True friends are there when it’s not._ 🅿 *65* Sa'kon gaggawa ne ya iso musu cewar kayan da za'a kawo musu a Lagos za'a sau'ke su so sai aka wakilta Abbas akan zuwa kar6o kayan, dama da farko maiduguri za'a taho da kayan direct sai kuma aka samu wani matsala inda dole sai de a sau'ke a Lagos sai suje su 'dauko. Ko ka'dan Abbas be kwana da niyyan tafiya ba amma da asubar fari aka sanar dashi lokacin ma yana zaune dafe da kansa bayan farkawar da yayi daga bacci da mafarkin Fateemah sosai mafarkin ya tsaya masa aransa, wai tana ta kuka saboda tarasa hanyar zuwa ko'ina ne oho, duk inda tabi de sai taga gurin yah mata duhu gashi wai tana ganinsu agabanta sun kewaye ta, a wurin akwai Mahmud, yaga Hannah, Antyn Mahmud yaga Daddy ma da kuma wasu mutane kimanin biyar da be sansu ba, amma inda akwai hanyan 6angaren Mahmud ne, Antyn Mahmud, wata da be santa ba da kuma shi kanshi, so take ta wuce amma tarasa ta ina zatabi, cikin wa'yancan ukun duk inta bi 6angarensu duhu ke mamaye gabanta, dalilin haka sai ta sake sakin kuka tana yarfe hannu, shi ka'dai ne kawai 6angarensa be yi mata duhu ba, amma ko data biyoshi 'din sai hanyan yayi mata nisa sosai yanda zai yi mata wahalar cimmasa shi kansa ma nisan yayi mata tana hangoshi yayinda har hannunsa yake mi'ka mata dan ta kama amma bata iya kamawa, hakan sai yasa taci gaba da kuka tana fa'din " _Yah Abbas_ ! _Ya...... Abbas_ !! Yana san taimaka mata shima amma sai ya kasa, Mahmud kuwa daganin tana bin inda Abbas 'din yake tana 'kiran sunan shi sai shi kuma ya juya bayansa yana murmushi, taku 'daya biyu zuwa uku yayi sai ya 6ace 6at suka daina hangoshi sai haske ya mamaye gurin gaba 'daya tare da wani lumshi me 'kayatarwa. Dai dai 6acewar Mahmud 'dinne Abbas ya farka daga baccin yatashi ya zauna dafe da kansa yana sake bitan mafarkin dayayin tare da juya al'amarin acikin ransa, yarasa ma'anar mafarkin gaba 'daya, abu 'daya ya iya fahimta shine Fateemah na bu'katar taimako arayuwarta sai de be san dalilin da ze kawo hakan ba. Yana cikin tunanin mafarkin ne sai ya samu sa'kon tafiya zuwa Lagos, wanda yazo masa a bazata a kuma dai dai lokacin da ze fi bu'katan hakan, haka ya tashi yayi komai cikin hanzari ya gama shirinsa tsaf. Su shida suka tafi , jirgin 'karfe 6:30am na safiyar ranar juma'ah suka bar Maiduguri zuwa Lagos. Sai dai kuma cikin rashin sa'a sai da suka isa Lagos suka sake tarar da sa'kon cewa sai zuwa yamma zasu iso dan haka sai suka nemi gurin da zasu huta kafin yamma amma sam basuji da'din hakan ba. Da wannan damar Abbas yayi amfani ya nufi office 'din Mahmud wanda a'kage yake yaji ya Fateemah take agurin Mahmud 'din, dan shi gani yake kamar rashin son auren da Mahmud yace baya yi ne yasa shi ya kasa kula da ita, be san gidansa ba office 'dinsa yasani dan haka sai ya nufo office 'din, yana da tabbacin adai dai wannan lokacin Mahmud na office. ***** Fateemah da Mahmud kuwa basu suka isa office 'din ba sai 9:13am dayake ansamu ha'duwar holdup sosai ahanyar shiyasa ma suka 'dan 6ata lokaci kafin su isa. Da isarsu office 'din ko zaman 20minutes be yi da ita ba, bayan isowarsun Mahmud ya amsa 'kira through landline 'din dake kan table 'dinsa, yana gama wayar kuwa ya mi'ke tare da sanar da Teemahn cewa yana zuwa bazai da'de ba zai dawo. Tashi tayi da sauri tace zata rakashi itama, saboda sosai yau 'din take jin babu da'di aranta, fa'duwar gabanta kara yawaita yakeyi acikin kowani da'ki'ka. Mahmud kuwa yadakar da ita da fa'din " _ah'ah please wait 4me mana Fateemah u ar safe here karki damu_ , yace mata files 'din da ze kai 'din masu matu'kar muhimmanci ne dole akwai wasu 'karin bayanin daya kamata shi zaiyi kafin aturasu zuwa China shiyasa zashi. Duk tunanin Mahmud tsoron da takeji ne yasa har a office din ma takasa sakewa. Haka ta tsaya 'ki'kam batare da tayi masa magana ba domin haka kawai yau 'din take jin wani sabon yanayi game da Yayah Mahmud 'din har bataso yayi nesa da ita. Da fitarsa kuwa Fateemah ta 'daga hannu ta dafe goshinta, bata san dalili ba amma akowani sa'a takan tsinci kanta cikin tsananin fargaba, wanda tun da safiyar yau data' farka daga bacci ta tsinci kanta cikin wannan yanayin. Bazata ce ga ainahin matsalarta ko damuwarta ba ayanzun ita de kawai tana ji har cikin zuciyarta ba ta da nutsuwa a hargitse take jin kanta gaba 'daya, dan haka kawai sai ta ringa maimaita _inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, lahaula wala quwwata illah_ _billah_ acikin zuciyarta wanda yin hakan ne yake 'dan sama mata sukuni idan taji fargaban ya yawaita. Da rigimarta sai ta wuce kan kujerar da ya ke zama a office 'din ta wani hakimce tana juyi ahankali tare da lumshe idanunta yayinda ta ringa faman sarrafa tunaninta ko zata gano babban damuwarta alokacin. Mahmud be da'de da barin office 'din ba Teemah taji anturo 'kofar ahankali batare da annemi izinin mamallakin office 'din ba. Dubanta takai wurin 'kofar sai ta ga wata matashiyar budurwa ce tsaye da fuskar mamaki wacce zata girme mata ahaife. Sanye take da wata riga doguwa yellow rigar roba ce sosai kuma bawata me fa'di ba, hakan yasa rigar tabi duk jikinta ya kwanta, tare da bayyana duk wata halitta dake jikinta, kanta kuwa da wani jan mayafi ta zagaye shi, ba laifi kam ayanayin zubi da tsarinta tayi kyau sosai sai de atsarin musulunci sam bata da maki ko guda 'daya. Kallon kallo suka tsaya yi da Teemah kowa da abinda yake sa'kawa acikin ransa, tunanin Teemah ko itama 'daya daga cikin ma'aikayar su Mahmud ne, tace wata'kila haka suka saba shigowa gurin Mahmud 'din batare da neman izini ba, sam Teemah bata san Munnira ba tunanin ta ta6a ganin ta wani guri ma sam be zo kanta ba, saboda ko lokacin dinnern auren sun akwai mutane da dama so bazata iya tunawa da kowa da ta gani awurin ba. Yayinda Munnira aranta take jinjina kyaun da ta ga Teemahn ta 'karayi, duk da yake ta ganta alokacin hidiman bikinta kuma kwalliyar biki daban yake dana kullum amma duk da haka bata ga aibin Teemah ba koka 'dan sai ma wani fresh data 'karayi tayi kyau bayaga haka bata ga wani abu daban ba, take kuwa tsantsan kishin datake ji azuciyarta game da Teemah ya motsa, amma duk da haka sai da ta 'dan yi dariyar mugunta wanda ta 'dan cije ta maida shi murmushi yanda Teemah bazata fahimci manufarta ba. Ahankali take takowa izuwa gaban Teemahn yayinda takalmin dake sanye a 'kafafunta yasamu daman bada sauti 'kwas.....'kwas me 'dan 'kara ka'dan saboda yanayinsa. Teemah sam batada niyyan kulata ko yi mata magana ba duk da taga cewa ta tunkaro ne, ita tun ganinta nafarko ma yarinyar bata birge ta ba koka'dan ganin cewa girmanta be sa tasan muhimmancin yiwa mutun sallama ba sai de ta tsaya kallonta. Komawa tayi ta jinginu da kyau da jikin kujerar ta kwantar da kanta tare da 'dora 'kafa 'daya kan 'daya harda lumshe idanu tana juyi da kujerar ahankali tamkar itace mamallakiyar office 'din, sai tayi kamar irin ba matsalarta ba ce zuwan Munniran. Idanunta alumshen ta tsinkayo muryar Munniran akusa da ita tana fa'din " _Amarya me da'din_ _tuwo!!!_ muryarta cike da murmushi tayi maganar. Ahankali ta bu'de idanunta ta sau'ke su akan Munniran daga idanun kuwa bata motsa koda 'yan yatsun ta ba. Kallon a ina kika sanni tayiwa Munniran tare da 'dan zaro idanu ka'dan ta juya su. Murmushi Munniran tayi itama ta zuba wa Teemahn idanu, Idon su cikin na juna Munnira ta'kara fa'din " _soyayyan be 'kare agida ba kenan shine kuka kawo sauran a office ko mrs Mahmud_ ? _Sai de kuma naga ai angon naki ba me amfani bane........ko de akwai wani sirrin ne bayan wannan?_ Teemah bata kulata ba saima mamakinta daya 'karu tambaya ta fara yiwa kanta shin wacece wannan haka sam Teemah ta tsani shishshigi. Munnira tagama fahimtar Teemahn da abinda ke cikin ranta dan tasan dama Teemah da wuya tagane ta dan haka sai ta gyara zama tare da yin murmushi tace " _kina mamakine amaryar mijina?Ki kwantar da hankalinki 'yan_ _mata kinsan fah Mahmud shine rayuwata kinga kuwa dole insan_ _abubuwa da dama game da rayuwarsa, saboda in 'karfafa soyayyata wanda nake tunanin shi_ _kansa ma 'kila be san da su ba, amma inke kina so ki sani zan iya sanar dake bawani_ _abu_ ! " Ganin da tayi Teemahn bata tanka ta ba har yanzun illah idanu data ke binta dashi yasa tayi murmushi, murmushintan da aduk sanda tayi shi tana jin izzah ne aranta irin kamar tagama dasu 'dinnan. Kamar an matsi bakinta ta furta. " _kin san wani abu amarya_ ? Bata jin cewar Teemahn ba taci gaba. " _ni 'din nan da kike gani babbar_ _masoyiyar mijinki ne tun ranar farko dana ganshi naji wani mahaukacin_ ' _kaunarsa yakamani amma cikin rashin sa'a sai Mahmud_ _yayi watsi dani da_ _bu'ka'ata ta duk da kuwa yasan ina matsanancin son shi hakan be sa yayi min duban_ _masoyiya ba koda kuwa sau 'daya ne tak, nayi 'ko'karin ganin na fahimtar dashi 'dimbin_ ' _kaunar danake masa amma sam yakasa bani dama, ana cikin haka_ _sai maganar aurenku ya 6ullo daga bakin mahaifin sa, Anty ne tasanar da_ _Mamina komai, nayi 'ko'karin ganin na hana auren yiyuwa amma hakan ma befaru_ _ba, saboda ance auren Mahmud dake zanannen 'kaddara ce da dole sai ya faru,_ _Malamin mami na ne ya fa'di ne yafa'di haka, badan naso ba na ha'kura har aka 'daura_ _auren ki da Mahmud............ Fateemah kina ganin zan iya ha'kura naga_ _rayuwar farin ciki_ _na wanzuwa atsakaninku ne dukda tarin ba'kin cikin da Mahmud ya 'kunsa min_ ? Kai ta jijjiga tace " _sam bazan iya ba, bazan iya juran ganin wannan ranar_ _ba............._ _"Inajin kamar inasonki ne shiyasa nake gaya miki wannan...."_ Dai dai nan Teemah ta hango Mahmud tsaye abakin 'kofar office 'din ganinsa kawai tayi bata san tun yaushe yake wurin ba, dayake Munnira data shigo ganin Fateemah yasa bata tura 'kofar da kyau ba hakan ne kuwa yabawa Mahmud damar gani da jin kalamanta da kyau ba batare da wani tangar'da ba. Teemah ce ke saitin 'kofa dan haka ita ka'dai ce ta hango shi sai yayi mata ido akan ta 'dauke kanta akansa ta daina kallonsa hakan kuwa tayi sai ta meda hankalinta da idanunta wajen Munniran dan kalaman data gama furtawa yanzun yasa ta ji tausayinta sosai harta fara jin cewa dama Yah Mahmud be mata haka ba tunda tana tsananin son shi daya daure ya aure ta, Munnira bata san da zuwan Mahmud ba, dan haka sai taci gaba da maganarta kanta tsaye, Teemah kuwa taci gaba da sauraro bata 'kara kallon 'kofar ba koda asace. " _Tun kafin auren ku nake ta neman hanyar da zan hana auren ku ya'duwa tunda hana yiyuwar_ _auren ya gagareni, nasha fama sosai da 'kyar nasamu hanya_ _wacce itace ta 'dan sanyaya min zuciya har tasa na rage damuwata domin na yadda da aikin_ _danayi_ " Ido 'daya takashe wa Teemahn tana murmushi taci gaba da fa'din, " _ba sai na tuna miki ba nasan kinsani tunda ke ke fama da matsalar......._ Cikin izgili tace " _ya kike yine idan jarabar ki ta tashi cikin dare? ai an gaya min cewa da dare ne kawai kike da damuwa da rana kina rayuwarki ne kamar kowa_ " Dariya ta yi ita ka'danta sannan taci gaba da fa'din " _ranar dinnern aurenku da nasa Anty ta shirya shi nasamu nasaran_ _aiwatar da niyyata akanki... zaki iya tunawa dani kuwa_ ? Goshi Teeemah ta ha'da tare da kawar da kanta gefe alamar ita ta manta. " _Ai nasan bazaki iya tunawa ba, yanzun ma inajin fah kamar inasonki ne shiyasa na_ _ke fa'da miki wannan maganar dan kinsan sirri ne_ _babba awajena fiye ma sirrin dake_ _tsakaninki da Mahmud.Kuma kinsan wani_ _abin birgewa aciki mother in-law 'din ki ce take 'kara min_ ' _kwarin gwiwa akan komai wanda har hakan yasa tayi kyautar ki gaba daya wa 'kawarta_ _musamman saboda farin cikina.........._ Sau'kar mari kawai Munnira taji akan kuncinta wanda yakusan gigita ta kafin ta gama fahimtar ta inda marin yazo sai ta sake jin wani marin, sai da ya mata mari lafiyayyu guda hu'du wanda yasa har takai 'kasa ta zube tana kuka tare da dafe kuncin nata da hannayen ta duka biyu. Kalle- kalle yafara yana neman abin duka kasancewar ba belt ajikinsa jumpa ya saka shiyasa shi neman abin, haka ya gama kalle-kallen sa be ga komai ba. Tunawa yayi da wani toshon cable 'din daya daina amfani dashi da sauri ya tashi ya bu'de drawern yajanyo wayar ya fara nanna'de ta ransa amatu'kar 6ace kana ganinsa zaka san an ta6o shi yau 'din dan Mahmud ba haka yake ba. Teemah ce taje dagudu ta ri'ke masa hannu dan ita tuni ma harta fara kuka saboda bata ta6a ganin tsantsan 6acin rai azahiri na Mahmud 'din ba irin yau . " _Yayah please karka daketa kaji! dan Allah.... Yayah kayi ha'kuri._ " ta yi maganar da muryar kuka. Mahmud kuwa ko kulata ma be yi ba dan shi ka'dai yasan abinda yakeji azuciyarsa game da kalaman Munniran be ta6a tunanin haukarta har ya ha'da da cin zarafi da shiga hakkin wani ba. Yana isa inda take ya sau'ke mata cable 'din abayanta, yayi niyyan yamata dukan tsiya ne na fitan hankali yanda gaba ko ganinsa tayi ahanya bazata tunkari gabansa ba ballantana hartayi tunanin cutar dashi. Amma yana 'daga cable 'din akaro na biyu Fateema tazo dagudu ta ru'kunkume shi ta baya tana kukan itama, idan baka sani ba zakayi zaton ko dukkan su biyu yake duka. " _Yayah........please kabari, karka daketa dan Allah Yayah kayi_ _ha'kuri.........kaifa musulmi kar kabiye sharrin zuciya_ _Yayah please kabarta ka yafe mata kaji....._ Cikin sanyin jiki ya sau'kar da hannunsa daga barin dukan nata. Munnira kuwa gaba 'daya tabi ta rikice dana sanin zuwan ta office 'dinsa ma takeyi ayanzun, domin tunda take arayuwarta, ba'a ta6a marinta bama balle har takai ga duka da cable. Kuka takeyi kamar ranta zai fita tana so ta fice a office 'din amma babu dama dan Mahmud sai da yarufe da lock kafin ya 'karaso ciki. Dawo da Fateemahn yayi ta gabansa yana bubbuga bayanta alamar rarrashi yace " _yi shiru ya isa haka Fateenah, bakya ganin cutar da rayuwarmu datayi_ _ne, Fateemah wannan da kike gani babbar shai'daniya ce_ _ki bari in koya mata_ _hankali_ " Kai Teemah ta jijjiga masa alamar " _ah ' ah_ " Sai yace " _okay......on one condition, zan barta amma sai ta fa'damin komai_ _data sani game da munafurcin da suka 'kulla gaba 'daya in_ _bahaka ba wallahi ba zan 'kyaleta ba_ " Munnira kam tun kafin ya rufe bakinsa cikin sheshshka tace " _wallahi Mahmud zan gaya maka gaba 'daya nayi al'kawari_ " Idon su gaba 'daya suka maida shi kanta inda taci gaba da basu labari gaba 'daya. Asirin datayiwa Teemah dashi kanshi Mahmud 'din sai da ta fa'da tace " _manufar hakan kuma shine wanzar da fitina da rashin aminta da junansu wanda_ _hakan ne zai iya yin sanadin rabuwarsu cikin sau'ki_ .Tace kuma Anty ma tasan da maganar dan ita ta'kara goya mata baya kuma itace ta ke jagorantar 'kawarta Anty Chiddy domin samun kan Fateema wanda hakan ma wani shirin ne daban a6oye. Kasa jurewa Mahmud yayi saida ya zauna tsaban haushi da takaici. Zaman ma sai ya gagare shi yasake mi'kewa. Yana huci yace " _Ai kuwa kinyi kuskure, Munnira munafurcin ki beyi tasiri ba koka'dan, domin Fateema bata_ _san ma tana da wannan_ _matsalarba balle har ta 'daga min hankali akai, har yaushe......Munnira_ _har yaushe zaki tsaya 6ata lokacinki akan yarinya_ ' _karama irin wannan, ko angaya miki ma ko na rabu da Fateema zan aureki ne?, wallahi_ _ko babu mata aduniya Munnira bazan ta6a auranki ba........._ _Kuma aurena da kike gani ni da Fateema auren zobe ne in bakisani ba ma yau ki sani, Allah_ _ne ya ha'da kuma shika'dai zai iya rabashi ba de ke ba kam Munnira_ ". Yana kaiwa nan yayi Wulli da wayar ya ja hannunta zuwa gabansa wanda hakan ya tilasta mata tashi tsaye tare da fasa wani 'kara, zaton ta ko wani dukan ze kuma mata. Teemah ma da sauri tace " _Yayah please........_ Juyawa yayi ya kalli Teema sai ya sake kallon Munniran, fasa fa'dan abinda yayi niyya yayi sai kawai yaja hannunta suka nufi 'kofar fita. Be damu da takalmanta da mayafinta dasuke jefe a'kasan office 'din ba haka yajata suka ratsa cikin Companyn har zuwa inda yayi parking, yana zuwa yaturata abaya yarufe sannan ya zagayo ya shiga driver seat. Teemah ce cikin sauri ta tattaro sauran tarkacen Munniran ta ri'ko ahannunta da gudu tabiyo bayansa amma kafin ta iso har yaja motar da 'karfi 'kuran bayan motar kawai ta tarar. Zuwa lokacin kuwa hankalin dayawa daga cikin ma'aikatan yadawo kansu dan ko lokacin daya bar cikin companyn ma wasu nata mamakin dalilin daya sashi hakan. Umar ne da shigowansa kenan ya 'dan fita waje yasamo Teemahn tsaye hannunta rike da wasu kaya. Mamakin dalilin hakan yayi sai yanemi ji daga bakinta. Amma bata sanar dashi ba sai ma ro'konsa data fara yi akan ya taimaka yakaita gida wata'kila Mahmud can yanufa da Munnira. Tana cikin ro'kon Umar sai ta hango Abbas na 'kokarin giftasu, gaba 'daya sai hankalinta ya koma gurinsa. Hatta Umar sai da ya juya ya kalloshi dan yanda hankalin Fateemah ya 'dauku izuwa kallonshi dole tasa Umar ma yabi gurin da kallo. Take ya gane shi domin sun ha'du wajen 'daurin auren Mahmud a damaturu duk da be da'de tare da su ba amma hakan be sa Umar ya manta da fuskarsa ba. " _Yah..... Abbas_ ! Ta fa'di sunansa da tunanin shi 'din ne ko kuwa wani ne me kama dashi. Cak kuwa ya tsaya duk da be gama tantance shine ake nufi da 'kiran ba ko waninsa, amma muryarta ba ze ta6a mantawa ba ko a ina yaji ta. Hakan ne kuma yashi waigowa ahankali sai caraf idanunsu ya sar'ke cikin na juna. Teemah kam kasa juran hakan tayi dan haka sai ta meda idanun nata 'kasa ta taho ahankali zuwa inda yake kayan Munnira rungume a 'kirjinta. Mamaki Abbas yakeyi ganin Fateemah a harabar companing su Mahmud kuma batare dashi ba. Tana isa inda yake sai taji idanunta na 'ko'karin tsatstsafo da ruwan hawaye ahankali tasake 'daga idanu takalleshi amma kwarjininsa ya hanata sakewa. " wai ke faruwa ne? Ina Mahmud 'din? Ya tambayeta cikin sauri. Daidai nan Umar ya iso ya mi'ka masa hannu suka gaisa sai ya sanar dashi cewa yana zaton Mahmud 'din be jima da fita ba saboda wata 'yar matsala dake faruwa yace shima yanzu yake so ya sau'ke ta agida. Tare suka koma motan dukkan su inda Teemah tashiga baya sukuma Abbas da Umar na gaba. Rintse idanu yayi yana sake recalling mafarkinsa wato dagaske Fateema na bu'katan taimako, in bahaka ba meyasa yaganta haka tana kuka? Amma ba ze iya bu'dan baki ya tambayeta ba. Ganin da Umar yayi kamar abin ya sar'ke zuxiyar Abbas ne yasa shi sake tambayarta abinda ke faruwa. Zuciyarta na tsananin bugu ga damuwa da suke son suyi wa zuciyarta yawa amma haka ta daure tayi musu bayani atai'kace dan muryarta shaking yakeyi sam bazata iya dogon magana ba ahalin yanzun. Abbas jiyayi tamkar zuciyarsa zata fito waje tsabar haushi ba'kin ciki dan Teemah batun Anty Chiddy ka'dai ta sanar dasu bazata iya fa'da musu 'dayan maganar ba. Jikin Abbas har rawa yake yi saboda yanda ransa ya 6aci amma ko 'kala be ce ba shi de yayi shiru Allah ne ka'dai yasan yanda yakeji azuciyarsa wato Mahmud zuwa yayi ya watsar da ita har wasu banzayen 'yan iska suka samu daman shiga rayuwarta da haukarsu. Jiyake da zaiga mutanen awannan lokacin dashi ka'dai yasan abinda ze musu. Da wannan tunanin suka isa gidan Mahmud amma baya nan, Abbas ne yayita gwada 'kiransa amma kusan missed call uku yamasa be 'daga ba. Hakan kuwa ya 'kara tunzira zuciyar Abbas aciki yake jin ciwo da 'kunan abin. Shiru Umar yayi duk da be gama fahimtar abinda yafaru duka ba amma ayanayin labarin da Fateemah ta basu ya fahimci cewa ran Mahmud yagama 6aci ayau 'din. Tunanin inda zai samu Mahmud yake a dai-dai wannan lokacin, ina yanufa da yarinyar da Fateemah tace yafita da ita. ***** Mahmud kuwa be zame ko'ina da Munnira ba sai gidan Anty, yana shiga kuwa ya hangota tana shirin shiga mota itama ga dukkan alamu fita zata yi. Ko gama parking beyiba ya fita tare da jawo hannun Munniran yakawo ta gaban Anty da tun shigowar motan ta tsaya saroro tana ganin ikon Allah dan ayanayin daya shigo ka'dai ma sai da mamaki ya kamata balle data ga Munnira ahannunsa wujuga wujiga ai shikenan tunaninta ya tsaya cak. Yana isowa yatura Munniran kamar kayan wanki ta fa'di agaban Anty tana kukan fitan rai. Azuciye yace " _saurari yarinyar nan Anty kiji abinda take fa'da, Anty bana fatan abinda_ _naji ya kasance gaskiya domin hankalina baze iya 'dauka ba._ _Anty wai dake za'a ha'du acutar dani da rayuwata, Anty idan ma kina_ _gadaran 'danki ne ni toh ita Fateemah fa?,miye yarinyar nan ta tsare miki_ _aduniyan nan da har zaki nemi sata a mummunan harka irin ma'digo_ , _Anty_ _bakya tunanin alhakin Allah ne_ ?, _Kun hana yarinya rayuwa me kyau agidan aurenta kun hanata sakewa, kun sanya tsoro yazama abokin tafiyarta duk meyasa hakan Anty dan kawai kin tsaneta, wallahi ni cewa kikayi insake ta takoma wurin iyayenta daya fimin da wannan alhakin!!_ _Itan fa jinina_ _ce......Fateema_ _dangina ce da ko ba aure atsakanin mu ni me iya ri'keta ne_ _awajena, banda haka ma Anty_ _me kike so ingayawa mahallici na idan ya tsaida ni akan amanarta_ _dana kar6o a hannun iyayenta ?_ _Anty_ _bakya tunanin ranar da Allah ze tuhume mu gaba 'daya_ ......... " _Ya isa haka ni Mahmud_ ...... Anty ta daka masa tsawa tare da 'dago Munnira ta jingina ta da jikinta. Taci gaba da fa'din " _ai kariga kasan dalili, nasan baka manta ba, lokacin dana yi ta fama_ _daku kaida mahaifinka akan karka auri yarinyar kun saurareni ne?_ _ko kana zaton dama i ll give up so easily ne haka da har kayi saurin manta abinda_ _yafaru? .....Mahmud wannan da kake gani ita ce_ _za6ina agareka kuma har abada bazan canja ra'ayi ba, ko ka 'kyaleta ko ka illata ta_ _Munnira itace uwar 'ya'yanka bawata ba, dan haka kama kama kanka ka_ _nutsu banason hauka, duk abinda na aikata kuma ina yi ne_ _saboda kai, ai nagaya maka bana 'kaunar ganinka da yarinyar nan,_ _banaso, bazan iya juran ganin jinina na rayuwa da dangin matsiyata_ _ba_ . _Kuma da kake batun ancutar da ita ka je ka tambayeta mana, ita tace tanason a tallafa_ _mata dan tana da bu'kata shiyasa na ha'da ta da 'kawata saboda akore mata_ _kishirwar dake damunta, bayaga haka me kuma na aikata agareta_ ? Mahmud hawaye kawai yaji ya zubo masa na ba'kin ciki yanzun kam yasan Anty bazata ta6a canjawa ba yariga yasan tayi nisa tunda har ta iya tsayawa gabansa amatsayin sa na 'dan data haifa ta gaya masa maganganu son ranta gameda aurensa, ha'ki'ka yasan idonta ya rufe da tsanar da take yiwa dangin mahaifinsa wanda kwak'kwaran dalilinta nayin hakan bazata iya fa'da ba. Har ya juya zai tafi sai yakuma dawowa gaban Antyn idonsa taf da hawaye ya furta " _Anty ki yafemin........_ _ni 'danki ne ke kika haifeni, albarkar ki dole in nema_ _adukkan al'amurana, ke da Abbah kun yi fama dani tun ina 'karami_ _har girmana..... kun bani dukkan gatan daya kamata, ban_ _ta6a yin kuka dan rashin wani abu ba, amma Anty ki_ _gafarceni..... wannan karon bazan iya 'dauka ba, bazan iya zuba_ _ido ina gani aci zarafin yarinyar da bataji ba batagani ba..... zuciyan_ _Fateemah awanke yake tas bata da hakkin kowa dan haka bazan bari_ _acutar da ita ba , kicewa Abbah na ya yafemin idan ya_ _dawo Anty_ " Be 'kara magana ba ya juya ya tafi yana share hawayen sa daya kasa controlling 'dinsu. Yariga ya sanyawa ransa cewar zai 'dauke Fateemah su bar Lagos bari na har abada, zai yiwa Anty nisa, nisan da zai sa ta harse ta manta da kalar fuskan Fateemah ma balle rayuwarta, abu 'daya zai iya dawo dashi shine Abbahn sa, yanaso yasake ganin Abbah kafin yatafi sai de hakan baze samu ba dan haka dole watarana ze dawo kawai domin Abbahn sa. Tafiya yake yana share hawaye, damuwarsa gaba 'daya ya tattaro ya taru masa akan idanunsa zuciyarsa kuwa cike take da hanzari jiyake ko awa 'daya ba ze iya 'karawa acikin garin Lagos ba, zai 'dauke matarsa suyi nisa yanda ze nisanta ta da dukkan ma'kiyanta. Kwakwata ma Mahmud mantawa yayi da cewan yana driving ne, ya manta duk wani doka da tsarin tu'ki abinda ya dameshi ne ka'dai yake yawo a 'kwa'kwalwar sa. Be ta shi sanin hakan ba har se da yaji 'karan wani horn ha'de da taka birki me 'karfin gaske take ya rikice yarasa me ma zaiyi dishi dishi idanunsa suke gani hakan ya sa be ma lura sosai da gabansan ba bayan 'karan da ya ji be sake gane komai ba, kafin ya ankara kuwa rabin motarsa tashige 'kar'kashin wata babbar motar da ke gabansa . Mafiya yawan mutanen dake gurin Hannu kawai suka 'dora akawunansu wasunsu na fa'din " _jesus crist_ " yayin da tsirarun su ke maimaita _innalillahi wa inna ilaihi raji'un_ .............. _Comment vote and_ _share pls_ 🤞🏻 *Salmerh ce*😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir rahmanir raheem* _People change, love hurts, friends leave, things go wrong but just remember that life goes_ _on........Love_ is _so strange.......Sometimes it becomes reason to live life and sometimes to leave life._ 🅿 *66* Umar na tsaye jingine da jikin mota, Fateemah kuwa na gefe har yanzu 'kirjinta rungume da kayan Munnira idanunta banda ruwan hawaye babu abinda yakeyi, ita kanta bazata ce ga abinda ke sata kukan ba amma yanayin datake jin zuciyarta ayanzun shi yafi komai 'daga mata hankali, tare da karya mata zuciya. Abbas ma tsaye ya juya musu baya, sam baya son ganin hawayen Fateema koka'dan hakan na matu'kar soya masa zuciya, baya jin cewa ha'duwar su da Mahmud ze yi kyau koka'dan, jiyake kamar babu wanda ya ta6a 6ata masa rai kamar Mahmud 'din aduk fa'din rayuwarsa ,hannunsa 'daya cikin aljihunsa yayinda 'dayan yake ri'ke da wayarsa bayan ya gama 'kiran Mahmud yaga baya 'dagawa, ransa duk a6ace shi tunaninsa yabashi akan Mahmud ya'ki 'daga wayar ne dagangan dan kawai ya wula'kanta Fateemah . ***** Cikin 'kan'kanin lokaci mutane suka zagaye wurin kowa na fa'din albarkacin bakinsa, da 'kyar akasamu aka ciro motar Mahmud 'din daga 'kar'kashin 'dayan motar se da ma suka 'daure motar Mahmud daga baya 'dauri sosai yanda ba ze motsa ba, tare da jan babban motar zuwa baya ka'dan sannan akasamu aka raba tsakaninsu. Da fitowar Motar Mahmud 'din kuwa sai da kowa jikinsa yayi sanyi wasu ma kauda kansu sukayi dan baza su iya kallansa ahaka ba. Sai da ambulance yazo kafin aka ciro shi tare da duk wani abu nashi na amfani dake cikin motar aka me dashi cikin ambulance 'din zuwa asbiti. Tun a cikin ambulance aka fara bashi taimakon gaggawa har zuwa asbitin suna zuwa kuwa aka wuce dashi A&E (Accident & Emergency) likitoci kusan uku ne suka ha'du akansa domin ceto rayuwarsa cikin gaggawa. Da 'kyar suka samu suka daidaita numfashinsa tare da yi masa dressing 'din raunikan daya samu. Bayan hakan ne wani daga cikin wa'danda suka taimaka masa har zuwa asbitin da kuma drivern babban motar da wani likita sune suka fara neman wanda zasu 'kira cikin 'yan uwansa. Misscalled 'din _Oga_ _Abbas_ Suka fara gani da be wani da'de da 'kiran wayar ba dan haka shi suka fara dannawa 'kira. Abbas na tsaye a inda yake tsayen tun 'dazu be motsa ba, ya dai 'kira layin mahaifinsa yasanar dashi cewa yashigo Lagos sannan ya'kira wani abokinsa ma sukayi magana, daganan yaci gaba da tsayuwa jira kawai yake yi yaga zuwan Mahmud gidan tunda kam baya office dole ai idan yagama abinda yakeyi 'din gida ze dawo. Wayarsa ce tafara 'kara alamar shigowan 'kira, yana 'dagota kuwa yaga sunan Mahmud na yawo a fuskar wayar. Da sauri Abbas ya amsa 'kiran tare da yin shiru danjin wace 'karya Mahmud ze shirga masa. Ga mamakinsa kuwa sai yaji ba muryar Mahmud bace ke tashi acikin wayar yake fa'din " _hello_ ! _helloo_ !! Da mamaki da kuma izzah Abbas ya amsa da fa'din " _Yes, who is on the_ _line_ ? Bayani aka yi masa akan abinda yafaru ata'kaice. Sosai Abbas yaji zuciyarsa ta karye da jin al'amarin amma be nuna afili ba yanda zasu gane koda ya juyo ma cewa kawai yayi da Umar su shiga mota suje wani guri. Har se da suka hau titi kafin Abbas ya sanar da shi asbitin da zai kaisu. Teemah kam bata magana sai aikin hawaye bugun zuciyarta ne yasake 'karuwa fiye ma dana baya koda suka isa asbitin ma ita da 'kyar take ciran 'kafa take binsu abaya domin gaba 'daya 'kafafun nata nawi suka yi mata, hakan ma bata ji abinda yafaru gaba 'daya ba dan har suka isan Abbas beyi musu bayani cikakke ba, zuciyarta ce ke gaya mata cewan Mahmud ne ya illata Munnira shine har aka kawota nan shiyasa suka zo. Daga Abbas sai suka 'kira layin Abbah shima sukayi masa bayani. Hankalin Abbah ba 'karamin tashi yayi ba dan shi baya ma 'kasar dan haka ya 'kira Anty ya sanar da ita sunan asbitin yace taje ta duba halin da Mahmud ke ciki kafin ya dawo, yace mata zuwa anjima shima ze dawo insha Allahu. Isan su Abbas keda wuya sai ga Anty ma ta taho itada da Munnira dayake har alokacin basu rabu ba suna tare lokacin da Abbah ya 'kira Anty. A reception suka zauna gaba 'daya suna jiran ji daga likitocin, domin sun ce sai zuwa nan da 30mins zasu ganshi kafin nan an 'dan kintsa shi kuma watakila ze farfa'do ya dawo hankalinsa. Duka abin nan dake faruwa Abbas da Umar ne ka'dai suka sani shima Umar 'din be da'de da samun labarin ba,bayan isowansu ne suka je tare wurin likitan inda shi yayi musu bayanin komai, Teemah kam har yanzu bata san abinda yafaru ba. Shigowarsu Anty ne ma ya 'dan fara bata mamaki ganin ta tare da Munniran ga kuma Antyn hankalinta duk atashe. Da farkawar Mahmud kuwa doctor ya basu damar shiga su ganshi, nan suka shiga gaba 'dayansu zuwa ciki. Anty ne ta wuce gaba da sauri ta isa gaban gadon tana 'kiran sunan shi. Wanda Teemah ma sai alokacin ta farga da wanda ke kwance agadon, ai bata san lokacin da ta zubar da kayan dake hannunta ba ta taho da gudu itama tana fa'din " _Yah Mahmud kaine anan?_ me _yasameka haka,Yayah Mahmud dan Allah ka tashi, ka tashi kaga Yayah Abbas yazo_ ?" Anty na kuka tana 'karawa tare da kamo hannunsa wanda be samu raunin sosai ba, Teemah ce tashiga tsakaninsu dan ita ta na zuwa sai ta shige gaban Antyn tana kukan fitan rai. Abbas da Umar kam tsayuwa sukayi suna 'kara jinjina al'amari na ubangiji, Umar tunani yakeyi awanni 'kalilan da suka wuce rabuwarsu da Mahmud yana cikin 'koshin lafiyarsa, sai gashi yanzu kwance agado cikin yanayin da bama ze iya fasaltashi ba. Ahankali ya bu'de idanunsa ya sau'ke su akan Teemah gefe da ita kuma Anty ce yaga dukkan su suna kuka. Ga Munnira ma daga 'dayan 6angaren itama tana share hawaye, can tsaye kuma Umar ne shida Abbas da rabuwarsu yanzu kusan wata uku kenan. Murmushi yayi tare da motsa hannun nasa da 'kyar ya ri'ke hannun Fateema dake risgar kuka iya son ranta. " _Yah.....Mahmud me yasame ka haka?....._ Teemah tasake fa'da cikin kuka. Anty kam kasa magana tayi banda hawaye babu abinda take sharewa, Abbas kansa dauriya kawai yayi beyi 'kwalla ba amma inkaga yanda jijiyoyin kansa duk suka mimmi'ke, idanuwansa suka yi jajazur take zaka fahimci halin da ke ciki da inda zuciyarsa ta dosa. " _Yayah Mahmud ina hannunka..... guda 'dayan yake......waye ya cire maka_ ? Teemah tasake tambayarsa tana bin jikinsa da kallo har zuwa fuskarsa. Murmushi yayi tare da waro idanunsa akanta nan ta 'kara ganin yanda cikin idanunsa suka koma tamkar jini gaba 'daya sun riki'de sun canza launi. Ahankali takai hannunta saman idanunsa tace " _Yayah......idanunka ma sun koma jini....Yayah......_ " _Allah ne ya min haka Fateemah kiyi min addu'ah kinji_ " Yayi maganar da 'karfin hali domin shi ka'dai yasan abinda yakeji acikin jikinsa, 'kafafuwansa ma gaba 'daya sun sami matsala dama ana shirin shiga dashi 'dakin thearter ne a'karasa cire 'kafafun domin bazasu sake yi masa amfani ba. Kafin hakan ne ya nemi ganin iyalansa bayan farkawarsa daga 'dan gajeran suman daya yi shine aka shigo dasu. Toh yanzun ma likitocin da suka ga kamar hayaniyan zai masa yawa zuwa sukayi suka ce su fita su barshi ya samu hutu. Da kansa yace a'a abarshi yagana da iyalansa bayi son hutun komai. Gurin shiru ko motsin kirki babu me yi acikinsu, kowa yayi tsit hatta su Fateema ba ihun kuka sukeyi ba sai de hawaye kawai suke sharewa. Da 'kyar muryarsa ke fita amma ahakan ya dubi Anty yace " ku daina kuka mana Anty, ku daina min kuka, ba gani nan ba zan warke ai insha Allahu" " Haba Mahmud ka dube ka fa bakaga yanda ka dawo bane? " _Karki damu Anty! haka dama Allah yaso gani na, kuyi min addu'ah kawai kinji Anty, idan kina kuka Fateemah ma bazatayi shiru ba!_ Sai ya juya ya kalli Munnira yace " _Share hawayenki ki daina kuka kinji, na riga na yafe miki tun lokacin dana san gaskiya, kema ki yafe min nasan nayi ta 6ata ranki abaya, dan... Allah_ _kiyafe min kinji Munnira, ban'ki auren ki dan bana sonki ba kawai de bani da burin yin_ _aure da wuri ne alokacin shiyasa, amma kun kowa ya kasa fahimta_ _ta.........._ Kai ta jijjiga masa itama Munniran tare da fa'din " _kabar ro'kona Mahmud ni ya kamata ince kayafeni, har abada ni me laifi ce_ _agareka nasani ni kaina bazan ta6a yafewa kaina ba, domin nasan na_ _cutar da kai, ayanzu kam bani da kalmar da zan ro'ke'ka gafara_ _sai de fatana Allah ya baka lafiya Mahmud ya in ganta rayuwarka_ _kai da zuri'arka gaba 'daya_ " Murmushi yayi mata itama 'kasan ma'koshi yace " _nagode Munnira_ " Hawaye yaji ya sau'ka akan hannunsa, sai ya waigo ahankali ya dawo da kallonsa wurin, ganin Fateemah yayi tana ta na ta 6ul6ulo da hawaye. Suna ha'da idanu hawayenta yasake 6ul6ulowa fiye da na 'dazu. " _Ya...yah Mah........_ Tanaso tayi magana amma sai taji gaba 'daya harshenta yamata nauyi. " _Shiiiiiii_ " ya dakatar da ita yana murmushi yace " _Maza share hawayenki kinji, kin manta nace zamu je Katsina tare_ ? Kai ta 'daga masa alamar ehh idanunta taf da hawaye. " _Har Abuja ko_ ? Ta sake 'daga kanta sama. " _Yauwa toh yi shiru kiji, share hawayenki_ " Hawayen tayita 'ko'karin sharewa amma baya tsayuwa kamar sake turosu akeyi haka taji. " _kinji abinda Munnira tafa'da 'dazu ko_ ? kai ta 'daga masa. Sai yaci gaba da fa'din " _nima ba nagaya miki ba_ _rannan_ " Da kai kawai take bashi amsan dukkan maganarsa. " _Toh ki yafe mana kinji, ni nasan dukkanmu masu laifi ne agareki har Anty, amma Fateemah wani abin sam ni bansan da faruwarsa ba, abakin Umar naji kuma koda na_ _tambayeki ma baki fa'damin ba kika 6oye min, bansan ta yadda zan tunkari_ _al'amarin ba saboda banji daga bakinki, kaina gaba 'daya ya kulle narasa mafita, cikin haka sai Allah_ _ya kawo Munnira ta bayyana miki komai agabanki wanda Allah yasa nima sai ya fa'da kunne na, hankalina yatashi_ _sosai Fateemah dajin sunan Anty aciki, bansan wani mataki zan 'dauka akai ba dan Anty mahaifiya tace_ _ita ta haifeni, daga 'karshe kawai sai na yanke shawaran zamu tafi mu bar_ _musu garinsu, zan 'dauke ki muyi tafiyarmu yafi amma kafin inje inda kike sai gashi yanda Allah ya maida ni, duk da haka nagode wa Allah na dayasa_ _nasan komai tunda ran numfashi na_ " Bu'dan baki Anty tayi zatayi magana Mahmud yayi saurin dakatar da ita da fa'din " _Karki ce komai Anty, ni komai yawuce agurina, sai de ko in Fateemah kuma itama nasan tahakura tuntuni_ " Kan Abbas ya maida idanunsa, suna ha'da idanu sai Abbas 'din ya taho wajensa ya zauna abakin gadon yace " _sannu Mahmud Allah yabaka lafiya cikin_ _gaggawa_ " Ido ya lumshe tare da bu'de su akan Abbas 'din yace " _Abbas idan na baka amanata zaka_ _kar6a min_ ? " _Me ze hana Mahmud zan kar6a_ _mana_ " Abbas ya bashi amsa da kulawa dan gaba 'daya tausayin Mahmud 'din yabi yacika masa ziciya ya maye gurbin haushinsa da yakeji lokuta 'kalilan da suka gabata. " _Amanar Fateema zan bar maka Abbas ka kula min da rayuwarta kaji, dan Allah....... kabata farin ciki dan tunda nake da ita bata ta6a 6ata min ba..... naso Allah ya bani tsawon rai nima in cikata da farin ciki.... amma ban samu wannan damar_ _ba Abbas, dan Allah kacika min burina kaji......_ " _bar fa'din haka Mahmud nasan da yardar Allah zaka warke, ka rayu da matar..... ka cikin farin ciki da walwala....._ " " _Hmm_ " kawai yace da Abbas 'din sannan yakomar da idanunsa kan " _Fateemah yace bazaki bar kuka ba ko?, in kina kuka fah bazanji da'di ba ko ba kyason in_ _warke ne_ ? " _inaso yayah inaso ka warke acire maka duk wannan farin abin_ "! " _Ko anciremin wannan Fateemah ai dole za'a sake sakamin wasu masu yawa ma, amma kiyi shiru kinji share hawayen ki bana son gani, in bahaka ba zan yi tafiyata in barki ke ka'dai.....,Anty kice mata tayi shiru banasan kukan nan_ ! Anty ne ta kamo ta ta share mata hawayen tace " _bar kuka kinji Fateema kukan ya isa haka_ _nan_ " Dayaga tayi shirun ne yace mata " _yauwa Angel 'din Daddy,_ _zakuje da Abbas kinji Umar ma zai rakaku........idan kinje kice da Innah ni yanzu bani da lafiya ne shiyasa banzo_ _ba, kice mata taringa yi min addu'ah, duk ranar da na samu sau'ki zanje in dubo su da kaina."_ Teemah kam wani sabon kukan ne ya 'kwace mata tace " _Yayah.....da kai zamuje, ni da kai zani idan kasamu sau'ki zamuje kaji, kai da kanka zaka sa mamanka_ _amakaranta kamar yanda kayi al'kawari da izinin_ ........ Tun kafin ta 'karasa maganar tari ya sar'keshi ganin haka yasa likitan cewa su 'dan fita su barshi ya huta please surutun yayi masa yawa ne" Anty ce tafara fita sannan Munnira followed by Teemah, Abbas kam be ko yin yun'kurin tashi ba hakama Umar da sai yanzu ma shikam yasamu damar matsowa kusa da shi. Godiya Mahmud yake 'ko'karin yi masa saboda sosai umar yabada babbar gudum mawa arayuwarsa amma karan nan maganan yakasa fita gaba 'daya, da sauri Umar ya dakatar dashi yace karya damu basai ya gode masa ba,yace komai dayayi yayi ne saboda Allah and for d sake of there friendship bakomai ba, yace Allah ya baka lafiya Mahmud" Lumshe idanu kawai yayi tsawon mintina uku kafin ahankali bakinsa ya furta sunan _Abbas_ kasancewar yana kusa dashi ne yasa ma yajishi da wuri sai ya amsa masa da fa'din " _gani nan Mahmud me kake_ _so_ ? " _Abbas..........'kaina.....kir....jina_ _bayana....._ Sai ya kuma yin shiru. " _ciwo ko_ ? Sosai Abbas ke jin tausayin Mahmud, gaba 'daya zuciyarsa ta karye da al'amarin dan yasan Mahmud ba 'karamin dauriya yake yi ba har yake bu'dan baki yayi magana, kana ganinsa zakasan yana jin jiki sosai bayaga haka ma ga wasu munanan raunikan dayaji wanda su ka'dai ma masifa ne amma ahakan yake daurewa yayi magana. Likitocin Abbas ya bawa guri yace su kula dashi suyi masa abinda ya dace. Har sun juya zasu fita a'dakin sai suka ji shi yana wani wahalallan tari, Da sauri suka koma kanshi suna yi masa sannu, idanunsa alumshe gefe da gefen idanun kuwa wasu sirarun hawaye ne yake bi ahankali. Bakinsa duk ya bushe yayi fari fat kamar wanda yayi sati be sha ruwa ba, " _Ab...bass_ ! " _Na'am Mahmud gani nan agefenka_ " " _Abbas_ _inajin....tamkar.....laifina_ _ya girmama.....ka tayani ro'kon Fateemah tayafemin dan Allah"_ " _Haba Mahmud ba anwuce wannan gurin ba, ka daina fa'din haka ka_ _kwantar da hankalinka kaji, batace ta yafemaka_ _ba_ ? Kansa ya 'daga har sau uku alamar ya tuna. Daga nan yayi shiru, still idanunsa alumshe. Matsawa Abbas yayi inda likitoci suka ci gaba da aikinsu, shi da Umar 'dinne suka juya zasu fita, Abbas har ya ze juya sai kuma yaga kamar bakin Mahmud 'din na motsi, sai ya dawo da sauri kusa dashi yayi 'kasa da kansa zuwa wajen bakin Mahmud 'din. " _Rasulullah_ " kawai yaji Sai ya 'karasa da fa'din " _sallallahu alaihi wa sallam_ " amma beji farkon abinda yace ba, sai de yana kyautata zaton kalmar shahada ya jero, daganan kuwa be sake ganin ya motsa ba, duk da yake dama ba yawaita motsin yayi ba amma yanzun daya 'kura masa idanu sai yaga kamar yanayinsa yacanja damma yanayin fuskar cike take da murmushi shiyasa ma yake 'dan jin dama dama. Umar ne yayi saurin ankarar da likitocin abinda ke faruwa, take kuwa ya iso ya dudduba shi, ganin dayayi cewa nunfashin sa baya tare da shi ahalin yanzun yasa shi jan farin mayafin dake jikinsa ya lullu6e shi zuwa sama har kansa. Sannan ya jiyo garesu, yanda yaga Abbas ya 'kuresa da kallo baya ko 'kiftawa yasa shi tsaida idanunsa akansa yace " _i'm_ _sorry_ ......."! Tsam Abbas ya kasa 'dauke idanunsa daga kallon likitan hakan yasa likitan ganin cewa ko be fahimce shi bane sai ya sake cewa " _i mean Allah yayiwa 'dan uwanku rasuwa_ ". Yana gama fa'din hakan ya juya ya fita sauran biyun dake taimaka mishi suma suka bi bayansa. Yayin da Abbas ya 'daga 'kafafun sa da 'kyar ya koma gaban gadon ya 'daga lullu6in da aka yimasa. Gani yayi fuskarsa shar har yanzu da murmushi, sai ma wani 'kara yin fari dayayi kamar yace tashi Mahmud amma wai babu shi. Acikin zuciyarsa yace " _Allah ya ji'kanka Mahmud yayi maka rahama, Allah ya haskaka 'kabarin ka yasa aljanna itace makomarka, Allah yasa mutuwa hutunka ce Mahmud_ " *Masoyan Mahmud ayimin afuwa, tun asali ahaka labarin yazo, ina fatan zaku cigada bina dankin 'karshen labarin.* ~Team Abbas ku kuma muna jiran jin yadda zaku ri'ke mana amanar Teeman mu~ . _Comment_ _Vote and share_ *Salmerh ce* 😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir rahmanir raheem* _Every moment of life is a step towards death......._ 🅿 *67* Ahankali suka fito daga cikin 'dakin tamkar wa'danda basu so suyi tafiyar, kawunan su duk na kallon 'kasa. Anty ne tafara tambayar su " ya jikin nasa ? yasamu yayi bacci ne? Ta jero tambayoyin nata ajere. Abbas ne yayi dauriyar yin magana dan shi kam Umar yana daga bayan Abbas 'din yana faman share hawaye. " _Muje akaiku gida_ " Abbas yafa'da idanuwan sa na kallan gefe, sosai mutuwar Mahmud 'din ya bige shi, acikin idanuwansa ka'dai zaka gane hakan. Anty ne ta hango Umar daga baya ka'dan da Abbas yana faman share hawaye take ta maida hankalinta gurinsa tace. " _Umar me ya samu Mahmud kake kuka?,nunfashinsa ya tsaya ko_ ?. Ganin Umar be tankata ba kuma be 'dago ya kalleta ba yasa ta furta " _Nashiga uku na Mahmud ya rasu Munnira_ " Tayi maganar tare da 'dora hannu akanta, sai luuu ta zube a'kasa sumammiya. Tsawon mintina ashirin kafin ta farfa'do inda ta tsinci kanta kwance agadon asibiti, farko idanuwan ta akan Teemah ya fara sau'ka dake gefenta azaune tayi tagumi ta 'kurawa gadon idanu, yayinda Munnira ke zaune agefen gadon da Antyn take kwance itama tayi shiru. Ita da Munnira ne kawai a'dakin su Abbas kuwa na can suna preparation na tafiya da gawa. Anty na farkawa ta gansu zaune jigum-jigum ai sai kawai tasa kuka wanda kukan nata ya sa suka farga da cewa ta dawo hayyacinta. Cikin kukan take fa'din " _Dagaske ne Mahmud 'dina yarasu ko Munnira_ ? _Dagaske ne yarona_ _ya tafi ya_ _barni_ ? " _Yi ha'kuri Anty dan Allah ki daina kukan nan haka nan, addu'ah zakiyi masa kinji_ " Cewar Munnira dake 'ko'karin tallafota . Teemah kam binsu kawai take da idanu bata san me zata furta ba sam. Sai da aka wuce da Mahmud gida kafin Umar yaturo driver yazo ya koma dasu Anty gida, kafin nan kuwa gidan harya fara cika da mutane. Abbah ne yace a 'dan jinkirta masa ka'dan yazo yaga gawar 'dansa da idanuwansa hakan yasa aka 'daga jana'izar Mahmud 'din sai zuwa bayan sallar juma'ah. Kafin hakan kuwa jama'ah da yawa sun iso daga 6angarori da dama, ciki harda su Daddyn Abuja, Ummah, da su Daddyn Teemah mutanen Dubai, Abbah ma ya iso tuntuni inda ganin gawar 'dansan kwance yasa yakasa ri'ke zuciyarsa sai da ya share hawaye kusan sau uku amma be tsawaita ba dan yasan kukan bashida wani amfani koka'dan ga dukkan mamaci. Amma shi ka'dai yasan me yake ji azuciyarsa , 'dansa 'kwaya 'daya tak daya keso kamar ranshi amma yau gashi kwance agabansa da gawa, wanda yafishi ya amshi abinsa, Allah ka jikan Mahmud ka haskaka masa 'kabarinsa, nasan beyi gaggawa ba muma kuma ba jin kiri mukayi ba. Dayake Ummah tariga su Mummy isowa yasa Teemah tunda taga Ummahn ta tafi ta lafe ajikinta tayi shiru gaba 'daya koman ta ya tsaya mata cak hatta tunani bata iyawa sai de idanuwa da take faman rarrabawa ko rintse idanu bata son yi saboda tana rintse idanun sai taga Yayah Mahmud nayi mata murmushi lokacin dayake kwance a hospital, hakan yasa ta 'kin rintse idanu koka'dan. Sai da Mummy tazo sannan tatafi wajen Mummyn ta rungume ta tare da sanya kuka abin tausayi tace " _Mummy ance wai Yayah Mahmud ya rasu_ "! " _Yi shiru toh ki daina yi masa kuka, addu'ah zakiyi masa ba kuka ba kinji_ " tace " _ai kema kukan kikeyi Mummy_ ! Janta Mummy tayi ta ha'da ta da jikinta sosai ta rungumeta dukkansu na kuka da rashin Mahmud 'din, ga kuma tausayin Teemahn datake ji sosai ahalin yanzun. Sai ganin Anty sukayi tsaye akusa dasu tace " _Khadija kema kuka kike yiwa Mahmud ko_ ? 'Dagowa Mummy tayi ta kalleta idanun ta duk hawaye. Murmushi Antyn tayi me ciwo tare zama daga gefen Mummyn sannan tace " ba ke ya kamata kiyi kuka ba Khadija nice, kuka dani ya dace, inajin kamar da hannayena na kashe shi, ha'ki'ka na cuci rayuwata na cuci rayuwar mutanen da basu ta6a min koda kallon tsana ba balle su cutar dani, bansani ba Khadija ashe sakayyata me girma ce, ban ta6a tunanin mugun halina ze iya sanadin 'dana na cikina ba, banta6a tunanin haka ba, sai gashi Allah ya nuna min iyakata ta yanda ban isa inja da yinsa ba koka'dan koda da wasa" Idanuwa ta lumshe sai ga hawaye sun ziraro mata da gudunsu bata damu ba taci gaba da fa'din " yaune rana ta farko dana ta6a yin dana sanin aikata mummunan laifi arayuwata, Mahmud 'dina yarasu Khadija, Mahmud ya tafi ya barni da tarin laifukana bansani ba ko Allah ze ji'kaina ya yafeni" Wata mata dake zaune daga gefenta ce ta fara bata baki akan tayi shiru ta daina kukan mana tace fa'de-fa'den ma bashi da amfani. Ko kallonta Anty batayi ba kawai ta jijjiga kanta tace " baki san yawan abubuwan dana aikata ba ne, na tabbata da kinsani nasan da kema tsanata zakiyi kamar yanda yarona yatafi da mugun tsanata azuciyarsa, juyawa tayi ta kalli matar tace kinsan abinda yakashe min Mahmud ne ? Kinsan sanadin mutuwarsa? ko kinsan mugun ciwon da ya dasu acikin zuciyarsa kafin ya rasu? Ni naga wannan 'kuncin acikin idanuwansa naga hawayensa dayake fitarwa me ciwo kafin yabar gidan nan, duk naga hakan rintse idanu nayi ban ko ji tausayinsa ba, ni de 'kudurina kawai ke gabana" Mahmud yaro ne me matu'kar biyayya yana kula da dukkan hakkin iyayensa daya rataya akansa be ta6a yin abu dan ya 6ata min rai ko mahaifinsa ba duk kuwa da surutun da Allah ya bashi hakan be sa ya kasance mara kunya ba, nice nafara 'kuntatawa rayuwarsa ta hanyar dasa masa 'kaunar yin makaranta a'kasar waje wanda tun bashi da ra'ayin haka har yazo ya amince saboda yanda yaga na kafe akan hakan , nariga nasan mahaifinsa baso yakeyi ba amma na dage nace sai anyi, sanadiyyar haka har ya 'debi shekaru kusan biyu batare da yayi makarantar ba, daga 'karshe me yazo yafaru ? "anan garin lagos yayi makarantar kuma yagama lafiya, tun anan ya kamata nasan abinda kalmar 'kaddara yake nufi amma sam ban yadda ba sai ma na 'kara jahilta kaina da tunanin sakacina ne yakawo hakan, lokacin da Mahmud yace min zai je service ajahar yobe wallahi hankalina ba 'karamin tashi yayi ba, naso na hana hakan badan komai ba sai dan muguwar 'kiyayyar da na kewa Khadeeja wanda alokacin ajahar yoben take da zama, anan kam Mahmud yace shi fa sai yaje dole na nayi ha'kuri na barshi yatafi duk da raina be so ba amma haka na ha'kura na barshi se de har yayi yagama hankalina be kwanta, nakan yawaita takura masa akan yazo gida duk da bani da wani takamman dalilin yin hakan amma zuciyata tariga da tayimin muguwar sa'kar 'kiyayya da be anfane ni da komai ba sai da nasani da bashi da amfani. Mahaifinsa da kansa ya nema sa auren Fateema musamman dan yabawa da yayi da natsuwarta da tarbiyyarta wanda kafin hakan ni kuma nayi masa maganar auren Munnira duk da ya nuna min baya ra'ayi amma na nace akan sai ya aureta haka abaya so 'din ya amince min sai de mahaifinsa dayake yafini iko dashi, shine ya nemasa auren Fateema alokacin bazan iya misalta yanda naji ba dan haushi da takaici, nayi-nayi iya 'ko'karin dan ganin na hana auren amma hakan ya gagareni, hatta bokaye da malamai duk nabi amma ban iya dakatarwa ba, tsana kuwa 'karara nake nunawa duk wani abu daya danganci auren, sanadin haka mahaifin Mahmud yakai 'karata wajen mahaifina a kano, sosai mahaifina yaja kunnena, yayi min garga'di, yamin wa'azi amma duk abanza koka'dan ban 'dauka ba, ganin haka mahaifina har la'antata yaso yi amma mahaifin Mahmud ya hana shi sai yace matu'kar na aikata wani abu da be kamata ba toh be yafemin ba. Wannan kalmar batasa na yi wa kaina fa'da ba, mahaifiyata matayi 'ko'karin jan hankalina amma na nuna mata bata isa ba dole itama tazuba min idanu ta 'kyale ni. Ko bayan auren nayi ta neman hanyan dazan rabasu amma narasa yadda zanyi, ni kaina bansan me yasa na tsani auren ba, bansani ba ashe shai'dan ke ingizani, dan Fateema bata ta6a 6ata raina ko sau 'daya ba amma duk da haka banji amincewar barinta ta zauna amatsayin matar 'dana ba. Hakan nema yasa da 'kawata ta nemi ha'din kanta izuwa aikata alfasha nice na tsaya tsayin daka wajen ganin faruwar hakan, akan haka Mahmud yazo yau 'din nan dasafe yana kuka Khadija, yana hawaye yake ro'kona akan meyasa nayi haka, meyasa zan bada irin wannan gudummuwar wa rayuwarsa, banji komai araina ba face 'karin haushin matarsa araina hakan yasa nafa'da masa maganganu son raina wanda be kamata ni in fa'da masaba amatsayina na mahaifiyarsa, Kinsan me yace min ? "Cewa yayi zai 'dauke matarsa su bar min garin yace inyafe masa in Abbahn sama yadawo ince ya yafe masa laifukan daya masa daga nan yatafi yana share hawaye, ashe 'karshen Mahmud kenan, 'karshen rayuwarsa kenan, ban masa adalci ba koka'dan amma duk da haka yace ya yafemin yace in yi masa addu'ah kawai Mahmud yatafi ya barni da ba'kin cikin rasashi da muguwar dana sanin da bazata ta6a amfanata da komai ba, kaicona nikam wallahi dana kasance me tsananin son kaina, inama zaka dawo Mahmud mu sake rayuwa dakai da sai na so ka na sada ka da 'yan uwanka na kula da kai yanda se ka zama abin kwatance zan zame maka uwa yanda kowa sai ya yi sha'awar rayuwarka, da kai kanka sai kayi alafahari da kasancewata uwa agareka, amma babu dama, ni da kai na nasan ni ba uwa tagari bace, ban kasance acikinsu ba face masu cika rayuwar 'ya'yansu da 'kunci, wahala da azaba gashi ni da kaina nayi sanadin rayuwarka.. inasonka yarona, inason ka Mahmud bansan me ya 'dauke hankalina na manta cewa kai 'din amana ne agurina ba, amanarka Allah ya bani gashi sanadina kabar duniya da tarin ba'kin ciki azuciyarka, Allah kaji'kan yarona kayi masa rahama, Allah ka hasakaka kabarinsa kasa shi 'din me rabone" Ta 'karashe da kuka me ciwo tana dafe 'kirjinta, kusan dukkan wa'danda ke cikin 'dakin sai da suka zubda hawaye tsaban yanda Anty tacika zuciyoyinsu da tausayi. Cikin kukan tace "Khadija dan Allah ku yafemin, tun da sauran rayuwata, Mahmud ya tafi ya barni batare da yabani damar da zan ro'ki yafiyar sa ba wanda inajin ciwon hakan har azuciyata nasan wannan nawin baze ta6a barina in rayu cikin salama ba, Khadija idan ke ma kika 'ki ki yafeni bansan ya 'karshen rayuwata zata kasance ba, na tabbata nayi babban hasara dana 'dauki tsana mafi girma na shinfi'da atsakaninmu, gashi nan shine sanadin komai nice nayi hasara arayuwata gaba 'daya, Fateemah ki yafemin kinji dan Allah ku yafe min ko Allah ze ji tausayina " Mummy kuka take tayi harda sheshsheka har maganar ma kasayi tayi gaba 'daya jikinta yayi sanyi da al'amarin Anty duk da yake dama ita bata wani ri'keta da haushi azuciya ba, kullum addu'ah take faman yi akan Allah ya shiryata yasa tagane cewa ita 'din bata nufinta da komai, tagane cewa 'dan uwa ba abin yarwa bane, amma hakan be samu ba har se da rai yabi al'amarin kafin nan, yanzu kam se fatan Allah ya jikan Mahmud yasa aljannah itace makomarsa muma Allah yasa mucika da imani Allah yasa kalmar shahada itace 'karshen kalmarmu. (Ameen). Kafin Mummy ta bu'di baki tayi magana sukaji anyi sallama ashe har anfito daga masallaci, anzo fita da gawa, cikin masu shigowan harda Abbas aka shigo. Anan ne kam koke-koke ya 'karu dan Anty da Teemah kukansu nin kuwa yayi fiye dana baya, banda su Ummah ma da sauran mutane suma sai share hawaye sukeyi. Anty kam ri'ke shi tayi tana sake zubda hawaye tare da dana sanin abubuwan duk data aikata abaya. Abbas ne yace su 'dauka su tafi kawai kukan bashi da anfani tunda ba addu'ah zasuyi masa ba. Haka suka 'dauke shi suka fita dashi zuwa waje. Teemah kam cak kukanta ya tsaya tabisu kawai da idanu har ta daina hangosu, babu wanda ya lura da ita sai Ummah, itace tazo ta mi'kar da ita tsaye sannan suka koma gefe suka zauna taringa yimata nasiha tare da bata baki har ta nutsu. Agurin Abbah aka ajiyeshi yayi masa addu'ah sosai hakama Alhaji Muhammad (kakansa mahaifin Anty). Daga nan akayi masa sallah aka sada shi da makwancinsa na gaskiya. Abbas kam suna dawowa daga ma'kabarta be wani da'de ba bayan yasamu ya isar da ta'aziyarsa ga su Abbah kawai ya wuche abinsa, dan baze iya shiga cikin gida gurin matan ba a wannan lokacin, bayaga haka ma shi sam ya tsani ganin fuskar Anty ayanzun. Yana komawa kuwa ya tarar komai ya kammala sai kawai suka 'dau hanya. Niyyarsa idan yakoma 'din ze nemi pass ne sai yasake dawowa gurin rasuwar amma kuma koda suka koma sai suka tarar da wani mummunan hari da aka kawo, an kashe dayawan sojojinsu aranar, ka'dan ne suka samu rauni inda 'kalilan daga cikinsu kuma suka tsira da rayukansu da 'kyar. Washegari sauran 'yan uwan su dake 'kauye suma suka iso da 'yan uwan Anty inda so rin'ka tunawa da alkhairin da Mahmud ya musu kwanaki ka'dan da suka gabata, suna jinjina halin rayuwa ha'ki'ka rai ba'a bakin komai yake ba. ***** Abin ya matu'kar 'kona ransa yanda 'yan ta'addan ke faman wasa da rayukan mutane batare da damuwar komai ba, sun maida rayukan al'ummah tamkar ran kiyashi, son ransu suke 6arna agurare batare da damuwar komai ba, haushin hakan yasa ya manta da batun mutuwar Mahmud kawai yafara tunanin neman mafita. *BAYAN SATI 'DAYA* . Kafin a'karo musu wasu sojoji Abbas da kansa yayi shiri sosai jin inda ma6oyar 'yan ta'addan yake acikin garin daga wani majiyar sirri sai ya yi shirinsa sosai musamman dayake akwai kayan aiki agurinsu sai sukayi amfani dasu tare da taimakon wa'dan da suka rage daga cikin battalion 'dinsa suka tunkari wajen da harin ko ta kwana. Yariga yasawa ransa cewa ze yi ya'ki dasu da dukkan 'karfinsa da zuciyarsa hakan yasa be ji ko 'dar ba ya tunkare su da zuciya 'daya Allah kawai ya mi'kawa dogoransa, abu 'dayane dama abin tsoron shine mutuwa shikuwa be dame sa ba, yasan ko mutuwa yayi awanan halin Allah yasani, bashi da alhakin kowa dan haka no retreat no surrender. Basu fi su goma ba, ha'di da armourtank guda biyu suka tunkari sansanin. Allah cikin ikonsa kuwa gaba 'daya suka tada gurin suka 'kona komai, kafin hakan sai da yayi ko'kari wajen ganin ya kama director 'din su dake gurin araye, sai de kuma shima Abbas 'din an kashe kusan bakwai daga cikin sojojin nasa befi su biyar bane suka tsira da rayukansu. Wannan abin da Abbas yayi ba 'karamin girma ya 'karawa hukumarsu ba, dan kuwa aganinsu yayi abinda bakowa ne ze iya yi ba sosai sukayi farin ciki tare da alfahari dashi, hakan yasa duk su biyar 'din da suka rage aka yi musu albishir na 'karinum girma. Hutu aka basu na tsawon wata 'daya dan su koma ga iyayensu da matayensu. *CONDOLENCE*😭 Sa'kon ta'aziya ga dukkan 'yan uwa musulmai da suka rasa yan uwansu da 'ya'ya yensu, ubangiji Allah yaji'kansu da rahama (Ameen). Kuyi ha'kuri kuma masoyana, ha'ki'ka ni kaina naji mutuwar Mahmud sosai kamar yanda naga wasu dayawan ku ma suke fa'di , amma ya zamuyi , mutuwa dole ce akan kowa, kuma ahaka labarin yazo tun asali, kunga sai de muyi hakuri.... Dafatan zaku ci gaba da bina har akai ga ci........🤞🏻 👇🏼 Fatan zaku cigaba da min uzuri na jinkiri danake yi kafin kuga update musamman Wattpad reader's wlh abubuwa ke min yawa amma kullum kuna raina ban ta6a mantawa daku ba.😍 _Share_ _Vote_ _Comment_ *Salmerh ce*😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated to u my lovely fans.....Allah ya bar min ku_.🥰 *Bismillahir rahmanir raheem* _Failure is only a temporary change in direction to set you straight for your next success. Only_ _those who dare to fail greatly can ever achieve greatly_ . 🅿 *68* Abbas ma porthacourt ya koma ya 'dan huta tukunna sai da yayi kwana biyu kafin yakoma Abuja. Daddyn Abuja yaji labarin abinda sojoji suka aikata a Borno akafan ya'da labarai amma be ta6a zaton 'dansa Abbas bane ya jagoranci abin har se da Abbas ya dawo gida yake sanar dasu 'karin girman da za'a yi masa. Mamaki sosai Daddyn Abuja yayi har yake tambayarsa dama haka akeyine, daga shigan mutun sai 'karin girma yabiyo baya. Anan Abbas yayi masa bayani atakaice akan abinda yafaru, ai kuwa anan Daddyn Abuja yafara masa masifa akan abinda ya aikata 'din yake cewa yanzu badan Allah yarufa asiri ba inda sun kashe shi awurin fa, yace shi sam baya son rigima da tashin hankali yace shiyasa tun farko ni hankalina be wani kwanta da wannan aikin ba in ban dama Yayah Kabiru ya sa baki da wallahi bazaka yi wannan aikin ba ballantana har kaje kana rigima irin wannan, 'karin girman banza da wofi salon cuta, aidan sunga kana bada rayuwarka ne shiyasa inda bakayi hakan ba da bawani girma da sazu 'kara maka" Shiru Abbas yayi yana sauraronsa sai da yaji yayi shiru kafin ya fara bashi ha'kuri amma kamar 'kara zugashi yakeyi sai sake 6allewa yakeyi yana bu'de sabon salon masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, shi tsakaninsa da Allah yaji haushin abinda yafarun. Abbas dayaga haka sai yayi shiru kawai yaci gaba da sauraransa. Allah sai ya taimaki shi ya kawo masa Daddy Babba dayake shi be baro wajen ta'aziyar Mahmud ba sai yau kasancewar Abbah babban abokinsa ne dole ya kasance dashi a kowani irin hali. Yana shigowa kuwa yaji me suke tattaunawa akai sai da yaji Daddyn ya kasa fahimtar Abbas ne kafin ya jefo nashi da fa'din " _haba Hassan, ya zakayi haka kuma? dama ya shiga aikin ne dan ya zauna yaga ana abinda bashine ba_ _ya kuma sar'ke hannuwa yana kallo?_ " _Ai kamata yayi ka 'kara masa 'karfin gwiwa tare da godewa mahallici daya sanya ya tsira da ransa, bawai kasashi agaba da bambami irin haka ba, da wanne zaiji?_ " Shiru Daddyn Abuja yayi ya kauda kai gefe, hakan yasa Daddyn Teemah 'karasowa ya zauna shima. Dan ya fahimci ran 'kanin nasa a matu'kar 6ace yake tunda har ya nuna halin ko in kula da zuwansa. Da 'kyar yasamu yashawo kansa ya sassauto. Amma be wani saki jiki sosai ba, duk lokacin dayaga Abbas 'din sai kawai ya tuna da abubuwan da yayi taji a labarai sai yaji ransa ya 6acida hakan. Kusan kwana uku da dawowar Abbas amma maganar bata wuce ba, su daddy suka koma Dubai da Mummy sai daga baya da ya samu Daddyn nasa yayi wata tafiya kafin yasamu ya 'dan sake a Abujan. Sai da su Mummy sukayi kwana biyar da tafiya kafin yasamu suka zauna da su Ummah har suka 'dan tattauna akan rasuwar Mahmud wanda dukkansu abin ya ta6a rayukansu ciki harda Hannah ma da ita bataje ba kuma ma bawani sabo tayi dashi ba, amma yanda Ummah ta ke basu labarin yasa duk takejin tamkar tana gurin akayi komai, dataji batun saka Teemah ta aikata lesbian da Anty taso yi da wata mata wacce bama musulma ba ce yasa tunanin Hannah yayi saurin kawo mata cewa waccen matar ne data ganta ranar da suka kai Teemah gidan uwar mijinta dan taga yanda matar take kallon Teemah alokacin tamkar zata cinyeta 'danye bata ta6a raba 'dayan biyu itace. Hannah ce ta tambaye Ummahn tace da ita " _toh meyasa kuma aka baro Teemah acan bayan duk faruwar wa'dannan_ _abubuwan, basa jin tsoron abinda ze biyo baya ne_ ? sai Ummah tace " _Antyn yanzu tana bata tausayi ne sosai kuma ita ta ro'ki abar mata Teemahn saboda_ _ka'daici_ " Ummah tace itama bata amince ba da farko 'ki tayi dan taga yanda yanayin Teemahn yake har yanzu bata saki ranta ta sosai ba, taso a 'dan nesantata da garin ko zata samu ta warware da wuri, amma se Mummy tayi saurin amincewa da batun Antyn. Ummah tace " _koda muka ke6e ma naso in tuhumi Khadija akan_ _meyasa tayi haka amma sai ta nuna min bakomai ai yanzu Anty tayi_ _nadama ta gane kuskurenta, mutuwar Mahmud ya kasance aya ne agareta me girma, dan haka abar mata Teemahn kawai wai_ _Antyn tausayi take bata sosai itama yanzun_ " Ta6e baki Hannah tayi ta 'dauki wayarta taci gaba da latsawa tamkar bata damu ba amma Allah ne ka'dai yasan yanda taji haushin hakan azuciyarta, abar yarinya ma da abinda ya dameta za'a wani 'kara barinta agurin muguwar matar nan, itama Teemah ai abin tausayi ce ba wata Anty ka'dai ba, ji take da 'ace tana da iko da sai ta je ta 'dauko 'yar uwarta zuwa gida , yayinda Abbas ya kauda kansa gefe sam yaji nutsuwarsa ta kau, shi ai be ta6a tunanin an baro yarinyar acan ba, taya ma za'ayi ace tana can gurin matar da ta fi tsananta aduniya se kace tarasa 'yan uwa ko kuma tarasa inda zata zauna , wannan ai rashin gata ne akayi mata, sam ya tsani matar nan har zuciyarsa, halinta sam be masa ba, yanzu kuwa dayaji komai kaf sai yakejin ma gaba 'daya itace abu mafi girma dayafi tsana arayuwarsa, tausayin banza tausayin wofi shi be abin tausayi awurinta ba sam. Be ce da Ummah komai ba kawai ya tashi yana wani ha'da goshi yakoma 'dakinsa. Ummah da idanu kawai ta rakashi dan ta fahimci ba'a saiti yake ba. ***** Yanzu komai ya dawowa Anty sabo fil, ibada kawai tasa agaba tana neman gafarar mahallici tare da yiwa marigayi Mahmud addu'an neman dacewa, kusan kullum sai ta zubda hawaye musamman idan ta dubi Teemah sai taji dama ta bari sun yi rayuwarsu cikin kwanciyar hankali sun haifa mata jikoki masu kyau kamar su, da ma bata shigo da su Munnira cikin rayuwarta ba, tasan da yanzu komai be faru ba, lallai gaskiya ne da'ake cewa tsalle 'daya tak zakayi kafa'da rami amma fita daga ciki kuwa sai kayi dagaske, yanzu gashi nan ita gari ya waya dan kowa na zaune da 'ya'yansa cikin so da 'kauna ita kuwa babu nata, tsanan data yiwa Khadija na ba gaira ba dalili gashi ita abin ya cutar, awannan lamarin bata tashi da komai ba face hasara me girma, ko Anty Chiddy da take aminiyar tama gashi tun rasuwar Mahmud 'din har yau sau 'daya tak taganta agidan, bata 'kara zuwa ba, ha'ki'ka masoya nada wahalar samu wani lokacin ma'kiya kuwa ko'ina suna nan birjik akewaye dakai, gashi ita masoyanta ma na kusa da ita amma ta rintse idanu ta ringa hango ma'kiyanta dake nesa da ita 'karfi da yaji ta matso dasu kusa da ita, bata sani ba ashe kanta zata cutar, gashi nan Khadija data nunawa tsana muraran itace ta bar mata 'yar cikinta amatsayin sanyin idaniya dan ta rin'ka 'debe mata kewa batare da ta yi musu ko da ka'dan ba, yau da ace burin Anty Chiddy ya cika akan Fateemah tayi lalata da ita da bata san ya zatayi da abin kunya ba, tasan ita kanta da se ta tsani kanta da rayuwarta, Alhamdulillah ma da abubuwa suka 'dan yi sau'ki Allah ya tsare Fateema ya bata kariya. Abbah kansa yanzu baya kula ta ko da ya shigo sede su gaisa da Fateemah ya 'dan jata da hira da tambayarta damuwarta sannLnan ya yi mata nasiha daga nan ya tafi abinsa ko kallon inda Anty takeyi ma bayayi. Da farko tana damuwa da hakan amma ganin dagaske yakeyi yasa itama ta ha'kura ta daina damuwa tasawa ranta cewa girban sharrinta kawai takeyi adun'kule, tariga kuma ta kar6i duk wani 'kalubale da zai zo mata ko da kuwa Abbah zai ce ne yasake ta bazata damu ba in kuwa yankan naman jikinta zai rin'kayi kullum shima bazata yi musu ba, dan tasan ka'dan kenan daga cikin abinda Allah ze mata dan ba 'karamin amanar amintattun bayinsa taci ba. Abbah kullum idan ze dawo sai ya kawo mata wani abu naci sha kona sawa sannan yayi ta mata hira har se yaga ta 'dan saki jiki kafin ya barta, shi kanshi ma bawai mutuwar bata dameshi bane a'a sosai yake jin kewar 'dansa amma baya nuna damuwarsa afili, sai ko in yana 'dakinsa shi ka'dai kafin nan yake tunani tare da yi masa addu'ah sosai, amma kana ganinsa kasan mutuwar ta bigeshi, musamman idan kayi duba da irin ramar da yayi, tausayin Teemahn yake ji ayanzun ganin cewa wannan lamarin ya sameta ne tun a 'kananun shekarunta, tana yarinya 'karama da ita shiyasa ma kullum yake 'ko'kari wajen ganin ya faranta mata. Anty kuwa kawai dubanta yakeyi baze iya koda maimaita abinda yafaru abaya da ita, be ta6a sanin haukarta takai hakaba, shi dai baze rabu da ita ba saboda darajar mahaifinta amma bayajin ze 'kara yadda da ita har 'karshen rayuwarsa, tsana me girma yake yi mata wanda baya jin akwai ranar da hakan ze bar ransa. Teemah har karatu take 'karawa Anty ka'dan dan gaba 'daya ta mantasu duk da ta yi karatun abaya amma rashin kulawa yasa yanzu ko izu biyu bazata iya kawowa da kanta ba, hakan yasa tace Teemahn tana yi mata ko zatana tunawa dasu. Tanajin da'din hakan kuwa dan kuwa sosai take 'karajin kusancin ta ga mahallici, sai de lokuta da dama sukan bar karatun ne saboda kukan da Anty takeyi musamman idan ta tuna baya ta tuna da 'ko'karin da mahaifinsu yayi tayi akansu amma duk ta watsar, shima yau gashi da fushinta ya yabar Lagos beko tsaya ya saurareta ba, tasan yanzu kusan kowa ya tsaneta tunda gashi iyayenta ma basu saurareta ba, saboda mummunan halayenta. Anan ne Teemah sai tayi ta bata ha'kuri tana mata nasiha hartayi shiru, gaba 'daya damuwar Anty sai ta nunka na Teemah harma wani lokaci manta nata takeyi sai de Anty. Itama yanzu sosai Antyn take bata tausayi ganin yanda gaba 'daya take damun kanta alokuta da dama. Gashi Abbah ma sai ya daina shigowa sai de ya 'kira Teemahn zuwa 'dakinsa suyi hirarsu ya bata duk abinda zai bata sannan ya sallameta, sau tari sai bayan ta fita damuwarsa ke 'kara yawaita addu'arsa kullum agareta shine Allah ubangiji ya bata miji nagari wanda zai so ta ya kuma kula da rayuwarta. Haka rayuwar Abbah ayanzu sam Anty kwatakwata ta daina ganinsa ma. Ganin kamar abin ze mata yawa ne yasa Teemah ta 'dan fara yiwa Abbah magana akan ya yafewa Anty kar damuwan yayi mata yawa tunda yanzu ta tuba tace ya yafe mata shima, Allah ma yafe mana yakeyi idan mukayi masa laifi meyasa mu bazamu yafi junanmu ba. Da 'kyar da su'din goshi Teemah tasamu kyakkyawar kalmah daga gurin Abbahn dan kusan kwana uku sukayi akan maganar kafin yace zai yafe mata amma sai in ya ga cewa tuban gaskiya tayi sannan yace hakan ma darajar Fateemahn zataci in ba dan haka ba da beyi niyyan sake waiwayanta ba. Sosai Teemah taji da'di harma takasa ri'kewa sai da ta gayawa Antyn abinda Abbah ya fa'da, Anty tana jin haka kuwa ta rarumo Teemah ta rungumeta tana mata godiya tare da sanya mata albarka . Duk wani kulawa da ya kamata uwa tayiwa 'yarta Anty nayiwa Teemah shi inka gani sai kayi zaton tun tasowarta tare suke da ita, gata babu irin wanda Anty bata mata shi komai takeyi hankalinta nakan Teemahn motsi ka'dan tayi kuwa sai ta ji dalili ita kanta Fateemah wani lokaci murmushi kawai takeyi da canjuwar Anty. Anty tariga ta yanke shawarar Teemah agidanta zata yi duk watannin takabanta dan haka tasaki jiki sosai ta rungumi rayuwarta dana Teemahn tare da kiyaye duk wani abu da ze sa Abbah ya zargeta daga wani abu. Kwanan Abbas shida agida amma sam zuciyarsa ta gagara saduda da barin Teemah da akayi a Lagos, gani yake kamar 'kara salwantar da rayuwarta ne akeso ayi abanza. Gashi shi ba ze iya 'kara tunkarar Ummah da batun ba kawai abin nacinsa ne azuci, wani lokaci ko dadare kasa bacci yakeyi, sai ya ringa tuno da mafarkin da yayi kwanaki, idan ya fasa mafarkin nasa sai yaga kamar azahiri abin ke faruwa, tunda kam gashi Mahmud yatafi yabarsu, toh in hakane kuwa meyasa za'a bar Teemah wajen Anty data so ta lalata mata rayuwa abanza. Haushin wannan al'amarin yasashi ya kasa zama a Abuja, rana tsaka kawai ya fito da shiri yace zai tafi Porthacourt, dayake ma saura kwana bakwai za'a yi musu 'karin girman su shiyasa ma Ummah bata yi wani tsokaci game da tafiyar ba tunaninta ko wani abin zeje yayi kafin ranar dan haka kawai sai ta bishi da addu'an Allah ya kiyaye ya bada sa'a. Koda ya isa can ma bawani abu yakeyi ba dayake yana hutu bashi da aiki, tunanin nan dai ne yakasa barinsa, kusan kwanansa biyu amma still be samu nutsuwa ba, cikin hakane ya tuno da amanar da Mahmud yabashi kafin rasuwarsa, take kuwa yaji wani 'kwarin gwiwa ya shige shi. Be bari yasake kwana a rivers state ba sai daya ganshi a Lagos. Wani ha'da'd'den hotel ya nema ya sau'ke gajiyarsa dayake shigan yamma yayi washe gari misalin 'karfe sha 'daya yayiwa gidan dirar mikiya. Abbah na shirin fita sai kawai ya ganshi ya shigo daga ba'kin gate, dayake da taxi yazo so tun a wajen gate aka sau'keshi. Fuskarsa ba yabo ba fallasa bazaka ce ga asalin yanayinsa ba, amma shikam zuwansa ayanzun gaba 'daya ya tuno masa da Mahmud komai yadawo masa sabo fil. Abbah kam ba 'karamin farin ciki yayi ba da zuwan Abbas 'din dan yasan albarkacin Mahmud yaci bayaga haka yasan da baze ta6a waiwayar inda suke ba, yana godiya ga Allah sosai daya kasance abokan marigayi 'dansa Mahmud duk mutanen kirki ne hakan ma na 'daya daga cikin alamomin nagartar mutun, dan jiya Umar da iyalansa gaba 'daya suma suka zo gaishe su, daga rasuwar Mahmud zuwa yau yasamu kar6ar ba'ki da dama ta sanadin Mahmud 'din, su jafar, da wasu friends 'din sama sun zo sun gaisheshi sosai hakan yake sashi farin ciki ko bakomai yasan cewa 'dan sa yayi mu'amala ne da mutane masu kyawawanan halaye. Kar6a me kyau aka yiwa Abbas agidan dan Abbah be samu nutsuwa ba sai da yaga an wadata shi da komai da komai, musamman dayaji cewa ya kwana a hotel ne acikin gari so yasan dole zai bu'kaci wani abin zuwa yanzu. Shikuwa Abbas sam duk ba wannan bane agabansa damuwarsa tasha bambam, aikuwa ko ruwa be shaba batare da jan wani dogon lokaci ba ya bayyanawa Abbah abinda yakawo shi. Abbah yayi mamaki sosai amma yace meyasa baze barta anan 'din ba, koda watanninta ne ta 'karasa. Sai yace " _Hankalina yakasa nutsuwa ne Abbah, amanarta Mahmud ya bar min hakan yasa rashin ganin irin rayuwar data keyi yake 'daga min hankali, kayi ha'kuri Abbah ba wai na raina kulan datake samu anan 'din_ _bane kawai de inaga can 'din zaifi kaga bazatana tunani ba tunda ga Hannah nan suna tare kuma zanfi kulawa da amanarta dana kar6a idan tana kusa dani_ " Abbah beyi masa musu ba take ya amince masa, sai de yasan ba wannan dalilin bane yakawo Abbas 'daukan Fateemah ba, ta iya yiyuwa tarbiyar gidan nashi ne be yadda dashi ba ko kuma wani abu daban amma ba de wanda ya fa'da ba, duk da haka bega lafinsa ba, dan yasan koma menene yafaru bakowa bane yaja hakan face matarsa, shiyasa duk abinda zakayi ka kula kayi shi akan dai-dai in kasan farkon abu toh ganin 'karshensa ne damuwa. Fateemah kam bazeyi ba'kin ciki da tafiyarta ba duk da ransa be so hakan ba amma idan zata fi samun farin ciki acan 'din falillahil hamdu, shi bashi da haufi akan hakan, duk da ze so taci gaba da zama awurinshi amma tunda hakan baze samu ba bakomai yasan wannan ka'dan kenan daga halin rayuwa, sede ze yi ta binta da kykykyawar addu'ar dacewa har 'karshen rayuwarta. Atake ya 'daga wayarsa ya 'kirata yace tazo, itama tayi mamaki dan basu jima da rabuwa ba yace mata ze fita sai kuma gashi taji wai akawo masa kayan tarar ba'ko and now kuma wai ita taje. Hijabinta ta nema tasaka akanta, dama kullum ahaka take zuwa gurin Abbahn bata ta6a zuwa inda yake batare da hijabi ba. Amma yanzun kam tunda ta tunkari 'kofar Abbahn ta rin'ka jin zuciyarta na dokawa, haka de ta daure tashiga da sallamarta. Tana shiga kuwa idanunta ya sar'ke cikin na Yayanta Abbas. Ahankali ta 'karasa ta zauna nesa ka'dan da su, tace " _gani Abbah_ " Yana murmushi yace " _baki ga yayanki bane, naji baki gaishe shi ba_ ." 'Daga idanu tayi ta kalleshi sai taga yawani kauda idanu tamkar ma be san da zuwanta 'dakin ba. Sai itama tayi 'kasa da nata idanun tace " _Ina kwana Yayah_ ? Yace " _lafiya 'kalau_ " Kamar ba ze sake magana ba sai can yace " _ya 'karin ha'kuri_ " Can 'kasan ma'koshi yayi maganar albarkacin Abbah ne ma yasa yayi tambayar badan haka ba ze tambayeta ba. Itama ahankali ta amsa da fa'din " _Alhamdulillah_ ". Murtarta na 'dan rawa Kamar zatayi kuka, hakan yasa ya 'dago ya kalleta da kyau jin yanayin muryarta. Aikuwa sai yaga tana share hawaye, tsayawa yayi kallanta da mamaki wato har yanzu bata daina kuka ba kenan da rasuwar shiyasa ma yaga tayi fayau da yawa duk ta rame kamar ba ita ba, aransa yace " _toh ki bishi mana tunda kin fi kowa damuwa da rashinsa._ " Abbah ne yayi mata bayanin abinda yakawo Abbas 'din inda ya 'karashe da lallashi ganin cewa tunkan yafara magana ma harta fara kuka yasan be wuci tambayar da Abbas yayi mata bane yasata kuka, dan kusan kullum haka takeyi indai za'a ambaci abinda ya danganci Mahmud toh sai tayi kuka koda kuwa gaisuwa ce shima Abbahn hakan datakeyi na damunsa shiyasa ma gara ya barta ta koma Abujan ko zata 'dan samu sassauci ta 'dan manta wasu abubuwa. Abbas kam haushin kukan nata yakeyi jiyake kamar ya maketa idan yaga tana share hawayen, dan haka sai yayi 'kasa da kansa yayi shiru yana sauraren yanda Abbahn ke bata baki. Yanzu kimanin kwana ashirin kenan da rasuwar Mahmud amma ace har yanzu yarinyar nan bata bar kuka ba yaushe kenan zata daina? Abbas ne yake wannan tunanin aransa. Abbah kam sallaman ta yayi yace taje ta shirya yanzu zasu wuche dashi. Tashi tayi salaf-salaf ta fita ahaka ta isa har gurin Anty, ita yanzu duk ba wannan bane matsalarta, ko ina ma tana so ta zauna dan zuwa yanzu tayi sabo sosai da Anty yanda bata jin koka'dan zataji da'din rabuwa da ita, sannan zata so zama a Abuja musamman ma tare da Hannah, saboda ita ma tana sonta kuma 'yar uwa ce ita mai damuwa da damuwar waninta, amma duk wannan bashi ze hanata son zama da Mummyn ba, gurin mummy take son zuwa, sai de ga dukkan alamu mummy ta sallamata ne, tun da akayi mata aure da Yah Mahmud Mummy take gudunta, gashi yanzu ma da mijinta ya rasu take bu'katan 'kirjin lallashi mummy ta tsallake ta tatafi ta barta. Anty kawai ganinta tayi tana kuka da sauri ta kamo hannun ta tana tambayarta me akayi mata me ya faru? Kuka tacigaba dayi da 'kyar tasamu ta bu'di baki tafa'di abinda Abbah ya sanar da ita. Anty bata hanata ba, kamar yanda bata nuna damuwa da hakan ba, da kanta ta lallasheta hartayi shiru sannan ta ha'da mata kayanta gaba 'daya da kanta, harma tace ko akwai abinda zata 'dauka acan gidan nasu, Teeemah da wuri tace " _a'a_ " dan ita koka'dan bata son gidan yanzu tsoro yake bata, bata son duk wani abu da zai dangantata da zuwa gidan ayanzu bazama ta iya zuwa ciki ba tanajin ita da wannan gidan har abada. Haka Anty ta gama shirya mata komai kuma tanayi tana bata baki tare da janta da hira, dan kawai taga Teemah tasaki ranta har tace mata bazata da'de ba zata je ta dubo ta dakanta har Abujan. Duk iya dauriyar da Anty taso tayi amma kasawa tayi musamman da suka yi musu rakiya zuwa inda zasu hau mota bayan ansaka kayan Teemah a boot taga Teemah nayi musu sallama tana share hawaye take itama sai hawayenta ya gangaro, dama ri'ke nata kukan taketa faman yi tun 'dazu dan kar ta 'dagawa Fateema hankali amma yanzu kam dataga ehh dagaske Fateemah zata tafi ta barta sai kawai takasa ri'kewa, tasan yanzu ne zatafi jin mutuwar Mahmud, idan Fateema ta barta shine zata san tayi rashi babbah domin ka'daici ne gadan-gadan ya tunkaro ta. Ga wani son yarinyar daya bi yacika mata zuciya jitake tamkar Khadija ma bata kaita son ta ba, sai gashi kuma Abbas na 'ko'karin rabasu, sai dai tasan bakomai yajawo hakan ba face banzan halinta, data kasance me son kanta fiye da komai, da ace ta kasance uwa tagari tasan da babu wanda ze yi shayin rayuwar waninsa tare da ita, kuma tana da tabbacin wannan dalilin ne yasa Abbas zuwa musamman dan ya koma da 'yar uwarsa Abuja. Kuka takeyi Teemah ma nayi haka suka rabu, Abbah kam daure ransa yayi yayi musu bankwana, rayuwa kenan, babu abinda baya faruwa idan kana raye zakaga abubuwa da dama najin da'di da rashinsa, duk akwai sai fatan Allah yasa mu dace [AM££N]. Tun a mota kukan da takeyi ya ishesa sosai kukan ke sosa ransa amma ya 'kyaleta ganin suna tare da driver in badan haka ba da shi ka'dai yasan abinda ze mata. Duk da haka sai da ya ringa sakin tsaki akai-akai kafin su isa kuwa yayi tsakin sau ba adadi har se data fahimci cewa da ita yakeyi tukunna. Suna sau'ka kuwa bayan wucewar drivern ya watsa mata kallo yace " _Idan kika kuskura kika min kuka acikin mutane ni da kene, angaya miki ke ka'dai akayiwa mutuwan ne_ ? Lokacin ma hawaye kawai take sharewa, daya kasa tsayuwa mata, ahaka ta 'daga idanun nata dake cike taf da hawayen ta kalleshi. " _Wipe all those tears kafin in sa6a miki, banson kukan nan ni_ " _Wannan addu'o'in naku na matu'kar sani annashuwa, tare da 'kara min kaimi wajen ganin na faranta muku kuma......._ *GODIYA SOSAI MASOYANA, ALLAH UBANGIJI YA BIYA MUKU BU'KATUN KU NA ALKHAIRI KUMA HASKAKA RAYUWARKU.* _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated 2 my family._ *Bismillahir rahmanir raheem* _God is the best listener and you don’t need to shout, nor cry out loud. B’coz he hears even the very silent prayer of a sincere heart..........._ 🅿 *69* Yanda yayi maganar atsare dole yasa ta goge hawayen nata ta ringa ajiyan zuciya kawai ahankali. Hotel 'din da ya kwana anan suka koma yace tajira shira shi yaje ya nema musu flight 'din zuwa Abuja sannan yadawo. Ummah na zaune a parlour tana kallon wani Hausa Movie kawai taji muryar Abbas nayi mata sallama kamar daga sama. A mamakance ta amsa sallamar tare da maida dukkan hankalinta gareshi. Fuskan nan atamke ya 'karaso ciki Ummah da mamaki take dubansa ganinsa ayau 'din bayan be da'de da tafiya ba, baya ga haka ma tasan yana da uzuri acan, mamakinta ne ya 'karu ganin Teemah ta shigo da sallamar ta itama kanta a'kasa ta 'karaso wajen Ummahn. " _Ah'ah, Teemah kune tafe_ ? _Keda waye haka_ ? Ummahn ta tambaya tana me waro idanu ko zata ga abokin tafiyan Teemahn tare da kamota ta zaunar da ita kusa da jikinta. Abbas kam 'dauke kai yayi tamkar be san da zancen ba dayaga hakan ma be masa ba sai kawai ya mi'ke ya wuce ciki. " _Keda waye kuka zo ne Teemah naga shiru har yanzu banga kowa ba_ ? Ummah ta sake tambayar Teemahn akaro na biyu. " _Ni da Yayah ne muka_ _zo_ ? Teemah ta bata amsa ahankali. Da wuri Ummah tace mata " _wani Yayahn kenan_ ? Sai tace " _Yayah Abbas_ " " _Abbas dai_ ? Ummah ta sake tambaya da mamaki. Kai Teemah ta 'daga mata alamar _ehhh_ . " _Toh garin yayah haka ta faru_ ? _a ina kuka ha'du_ ? _Ko ke kika ce masa zaki zo nan 'din, ina_ _ita Antyn_ _naki_ ? Shiru Teemah tayi dan bata san wanne daga cikin tambayoyin Ummahn zata fara amsawa ba. Ganin haka yasa Ummah kam ta fassara shirun da abinda hasashen ta ya bata. Kafin tayi magana sai ga akwati an shigo da shi wanda kallo 'daya tayi masa ta fahimci cewa na Teemah ne. Jinjina kai tayi tace " _lallai yaron nan wato sai da yaje ya taho dake ko,_ _ai dama tun ranar da_ _yaji labarin kina can_ _naga sai wani huhhura hanci_ _yakeyi yana kauda kai gefe ashe shirin da yayi aransa_ _daban_ . _Zai zo ai yasame ni neh sai naji dalilin_ _hakan_ " Kallonta ta dawo dashi kan Teemah tace " _maza shiga ciki ki watsa ruwa ki huta kinji Fateemah_ " Duk wannan dramar Teemah bata ga Hannah ba tun zuwanta Ummah ce tayi mata kwatancen inda 'dakin Hannah yake tace mata Hannahn na ciki. Koda taje 'dakin ma bata ganta a'dakin ba motsin ruwa data jiyo abayi ne yasa ta gane cewa tana bathroom, cigaba da tsayuwa tayi kamar me jiran abata umarni, bakomai take tunawa ba kuwa sai Mahmud tare da tausayin Anty dayayi matu'kar tasiri a zuciyarta. Tana tsayen har Hannah tafito daga bayin tagama firgita da ganinta dan bata ta6a zaton ganinta awannan lokacin ba, har kuwa tazo ta fahimci cewa itan ce dagaske ita Teemah bata ma san ta fito ba, sai da Hannah ta taho ta dafa kafa'dar ta tare da 'kiran sunanta kafin tayi firgigi ta dawo hankalinta. Ai kuwa tana ganin Hannah ta sanya kuka tare da rungumarta zuwa jikinta sannan tacigaba da kukanta. Hannah kam shiru tayi tama kasa magana dan mamakin zuwan Teemahn tare da farin cikin ganinta duk su suka cika mata zuciya ayanzun. Sai da taga kukan Teemahn bana 'kare bane kafin tafara bata ha'kuri tana bata baki da 'kyar ta sarara da kukan wanda hakanne yabawa Hannah damar tam bayarta tace " _ke dawa kika zo ne Teemah kinsan kuwa yanda naji haushin zamanki acan ai wallahi dama niyyata in je in zuga daddy ko kuma Yayah a'dauko ki haka kawai sai awani barki agurin muguwar matar nan, ni ai kin min dai-dai da kika taho wallahi_ , _Allah yasa bazaki sake_ _komawa ba_ " Cikin rawar murya Teemah tace " _Anty tana bani tausayi sosai_ _Hannah nasan zata shiga damuwa sosai dana barta_ " Fa'din Teemah tana me cigaba da zizaro hawayenta. Hannah kam kwafa tayi tana kallon Teemah sai daga baya tace " _ke wallahi wani lokaci rasa inda wayoki_ _yake tafiya nakeyi, ina ruwanki da ita? tausayinta na banza da wofi, ita ta_ _tausaya miki ne lokacin da take neman cin mutuncin ki duk da kina matsayin_ _matar 'danta kuma 'ya agurin mijinta? Sai yanzu ne data ga babu 'dan shine zata wani kalallame_ _ki dan ki zauna tare da ita tasamu hanyar_ _sake cutar da ke_ _cikin sau'ki ko_ ? Teemah cewa tayi " _Hannah ba haka bane fah, Allah Anty ta canja yanzun ba kamar da take ba_ " Hannah tace " _ni ya isheni haka da_ _Allah bari kiga nayi sallah lokaci na 'kurewa kema jeki yi alwala, ni yau_ _farin ciki ma_ _inajin baze_ _barni na samu bacci_ _ba_ " Agurin cin abinci suka ha'du dukkansu Abbas kam sai wani shan 'kamshi yakeyi kamar besan me ya aikata ba nan kuwa duk yana hakan ne dan kar Ummah ta samu daman yi masa fa'da akan maganar . Hannah ce " _tace Yayah bakaga Teemah bane_ ' _dazunnan fah tazo itama bata jima ba_ " Tunanin ta wai ko Teemah tariga shi isowa ne shiyasa ta fa'di haka dayake bata san lokacin daya zo ba. 'Dago kai yayi ya sauke shi akan Teemah yaga yanda ta ke kallon abincin tana wasa da spoon aciki sai ya maida kansa 'kasa asaman la66ansa yace da Hannah " _na ganta mana!_ " Ummah ce tace " _Hannah ai shi tun kafin ki ganta shi yariga yaganta_ " Hannah kam waro idanu tayi da mamaki tace " _haba dai, Ummah a ina toh suka ha'du tun 'dazu fah muna_ _'daki_ ? Atakaice Ummah tace mata " _shine dakansa ya_ _kawota_ " Hannah kam kallonta ta miyar kan Abbas 'din da fara'arta tace " _wallahi Yayah ka kyauta kamar kasan meke cikin raina, ni dama_ .... " " _Stop talking and eat your food Hannah later then kyayi surutun, okay_ " Cin abincin tafara cikin farin ciki tanayi tana murmushi dan ita yanzu komai normal ne a6angarenta bata da damuwar komai tunda kam ga Teemah agefenta zaune. Cikin hakan ta waiwaya 6angaren Teemah sai taga ba ta cin ma abincin ita kam. Zungurinta tayi da kafarta, data 'dago ta kalle ta sai ta mata nuni da abincin Teemah ma sai ta fara kaiwa kamar gaske. Ummah ma ta lura da hakan amma bata nuna ba dan zatonta ko idanun mutane ne yayi mata yawa shiyasa takasa ci, sai ta bari akan idan sun gama zatace da Hannah ta 'diba mata zuwa 'daki wata'kila can zatafi sakewa. Abbas kam da hanzari yake cin nashi abincin 'ko 'karinsa yayi ya tashi ya bar gurin dan yasan Ummah dole ne sai ta tuhume shi shikuwa be san ma me zece da ita ba. Ummah ma duk tana lura dashi sai ta 'kyaleshi kawai tana jiran su Hannah su tashi dan bata son yimasa surutu agaban 'kanwarshi sam shima kuma yasan hakan shiyasa yake hanzari yayi ya rigasu barin table 'din. Yagama kenan yana niyyan tashi sai yaga Hannah ta rigashi mi'kewa tana shirin yin magana sai Ummah tari bakinta da fa'din " _'Dauka wa Fateemah abincinta naga bata ci ba sam may be a'dakin zata fi sakin jiki taci_ " " _ah' ah nifa nama koshi Ummah basai_ _ta 'diba min_ _ba_ ! Cewar Teemah tana 'ko'karin mi'kewa itama. Wani kallo da Abbas ya watsa mata yasa take tayi kasa da 'kanta 'kirjinta na harbawa. Ummah cewa tayi " _ah'ah Fateemah ni banga wani abin kirki da kika ci_ _anan ba_ , " _Hannah maza 'diba mata ko ka'dan ma tasamu taci zama_ _da yunwa ai bashida da'di koka'dan_ , _dubi fah yanda duk kika 'kare abanza_ " Hannu Hannah tasa ta harha'da mata komai sannan tace da ita " _tashi muje_ " Shima mi'kewa yayi daniyar barin gurin sai kuma Ummah tace masa " _zauna Abbas_ " Dayake yana kusa da ita shiyasa shi ka'dai yaji maganar da Ummahn tayi. A'darare ya koma ya zauna yana me shafo kansa da hannunsa 'daya. Sai da su Hannah suka shige ciki kafin nan Ummah tace masa " _sannu ko_ " Kallon " _me nayi_ " ya yiwa Ummahn yana murmushi " _Haba Muhammad yazakayi haka dan Allah bayan da kai rannan mukayi_ _magana akan yarinyar nan, shine kuma ka san'di jiki ka koma ka taho da_ _ita_ ? " _Kai ko kunya ma bakaji ba, ka duba halin da matar nan take ciki amma sai_ _ka yi wannan rashin mutuncin, itace fah da kanta ta nemi_ _abar mata yarinyar nan_ _agurinta harta gama watannin takabarta kuma aka amince mata_ _sai daga baya kuma_ _haka yafaru kai kana ganin zata_ _ji da'di_ _ne_ ? Ta 'karashe maganar tana kallonsa. " _'kyale ta kawai Ummah yariga ya_ _wuce ai yanzu tunda gashi mun_ _taho_ " Ya bata amsa yana me duba agogon hannunsa. Shi koka'dan bega rashin kyautawar sa ba a wannan lamari dama me yasa za'a barta acan 'din in ba ahanata mantawa da mutuwar ba. Ummah kam kwafa tayi tana dubansa jin irin amsar daya bata sai tace masa " _Toh na barta tunda haka kace, amma shikuwa kawun nata fah, miye laifinsa acikin_ _lamarin ko kuma shi 'din kana ganin zaiji da'dine ace rana tsaka_ _kawai ka dira masa ka wani ce zaka tafi da ita bayan sun saki ransu cewa_ _zata zauna tare dasu, kuma ai baka ji ra'ayin yarinyar ba akan haka baka_ _sani ba ma ko can 'din yafi mata fiye_ _da nan_ ..." " _i don't care Ummah, shi 'din lokacin da_ _abubuwan sukayi ta faruwa yana ina?, da ace an samu_ _nasarar cutar da ita Ummah da ya za'ayi, nifah banga abin damuwa_ _anan ba dan tausayi ina jin tausayinsa mana amma gaskiya_ _bazan sake barin yarinyar nan ta zauna tare da muguwar matar nan ba, domin_ _amanar ta aka barmin, koma menene zatayi tayishi tagama anan babu inda_ _zataje_ " " _Muhammad_ !! Ummah tafa'da tana kallonsa. Juya kai yayi ya tare ta da fa'din " _bazaki gane bane Ummah, wallahi na_ _tsani matar nan, ki fahimce dan_ _Allah Ummah, wani lokaci fah jinake kamar inje_ _in sa akamamin ita nayi ta dukanta har se_ _ta suma......amma bazan iya ba, bazan mata haka ba_ _saboda darajar_ _Mahmud_ , _albarkacin 'dan data haifa take ci_ _awurina da kuma Abbah in badan_ _haka ba da ni ka'dai nasan me zan_ _mata.... kiyi ha'kuri Ummah amma gaskiya yarinyar nan bazata_ _koma ba koda kuwa me ze_ _faru_ " Ummah kam shiru tayi tana kallonsa yanda yasata agaba da masifa, amma bata wani yi mamaki ba dan tasan abinda ke cikin ransa yake fa'da mata and kuma tasan iya gaskiyarsa kenan dan haka tayi shiru tana sauraransa. Yana gama maganar ya tashi ya wuche zuwa 'dakinsa da ido kawai Ummah tarakashi har ya shige ta daina kallonsa sannan ta dawo da idanunta gabanta. Koda ya koma ciki ma tunani ne duk yabi ya ishe shi, sosai yake jin haushin Anty tare da Allah wadai da halinta, at d same time yana tausayawa Fateemah, cikin haka ya tuno da abinda yafaru 'dazu a wajen dinning, yasan halinta sarai tana dai-dai 'dinta ma bata bawa abinci daraja ba balle kuma ance tana cikin damuwa ai se ahankali. Shiyasa ma yaga duk ta rame ta lalace. Wayarsa ya 'dago ya 'kira layin Hannah. Hannah na 'ko'karin shiga wanka taji 'karar wayanta, zuwa tayi ta 'daga tare da yin sallama. Ciki-ciki ya amsa mata tare da fa'din " _Hannah me kikeyi_ _ne pls_ ? Sai da ta 'daga idanu sama ta kuma juya su kafin tace " _wanka zan_ _shiga Yayah_ "! yace " _Okay, akwai abinci_ _agurinku_ _ko_ ? " _Ehh sai na Teemah ne wanda bata ci ba_ " cewa yayi " _Yauwa ki bata ta_ _kawo min_ _yanzu_ " Hannah da mamaki tace " _Toh, amma Yayah baka ci abinci 'dazu_ _ba_ ? Be bata amsar tambayarta ba kawai sai yace da ita " _hope kinji me nace_ _ko_ ? Da sauri ta bashi amsa da fadin " _Umm naji_ " Be sake magana ba ya yanke 'kiran kawai. Bin wayar Hannah tayi da kallo sannan ta 'karaso wurin Teemah tace " _Yayah yace wai ki kai masa abinci inajin tsutsar ciki ke damunsa, 'dazun nan fah yaci abinci_ _amma kiji wai a'kara kai masa wani_ " Teemah tuni tayi kicin-kicin da fuska kamar zatayi kuka tace " _Hannah ni kuma zankai masa dan Allah_ ? " _nima haka yace min ko baki ji ba sanda nace masa_ _wanka zanshiga, ki daure ki kai masa yanzu zaki dawo ai_ " Hannah tana maganar tana 'ko'karin 'dauko mata plate 'din abincin. " _ungo ki kai masa_ " Kar6a Teemah tayi ta kama hanyar fita. " _'Bangaren yamma zakiyi 'kofarsa ce ka'dai zaki fara gani agabanki_ " cewar Hannah dake tsayen abayan Teemah. Teemah kam fita tayi ko waiwayowa batayi ba ta fice daga 'dakin tana jan 'kafa kamar bazata ba, tariga tasan halinsa sarai bawani abincin da ze sake ci tunda baya cin abinci sau biyu lokaci 'daya 'kilan kawai wani abin ne yasa shi cewa takawo masa. Da sallamarta ta shiga 'dakin nasa taje ta ajiye abincin akan 'dan 'karamin dinning 'din dake 'dakin nasa me kujeru biyu kacal. Tana shirin juyawa ta tsinkayi muryarsa yana fa'din " _kawo min_ _nan_ " Komawa tayi ta 'dauko sannan ta kawo masa tana ajiyewa shikuma yana mi'kewa yake fa'din " _zauna kici ina zuwa yanzun_ _nan_ " Hawaye kawai taji ya gangaro mata, kamar tasa hannu aka tayi ihu dan takaici, dama tasan bacin abincin zaiyi ba, da ta san cewa ita ze sa taci ma da bazata zo ba. Kusan mintina biyu tana zaune da abincin agabanta, tana share hawaye, dataga ba yanda zatayi kawai sai ta bu'de tafara ci ahankali sanin halinsa datayi akan hakan, dan tunda yace taci toh matu'kar bataci ba baze ta6a barinta ta tafi ba, dan haka sai ta ringa ci ahankali take turawa bakinta harta jita dam, daga nan ta tsaya da cokalin ahannunta, tana jiran fitowarsa. Ashe watsa ruwa yaje yayi sai da ya shirya kafin ya dawo parlourn cikin kayan baccinsa me birgewa jikinsa na tashin sayayyan 'kamshi. Zuwa yayi ya zauna tare da ha'de hannayensa wuri guda yasata agaba yace mata " _ya dai_ ? " _Na'koshi ne Yayah_ " Muryarta na rawa tayi maganar. Baya yayi ya jinginu da jikin kujera dan yaga ba laifi ta 'danci ka'dan sai yace " _U can leave, amma fah ki kiyaye kina cin abinci akan lokaci dan duk ranar dana_ _dawo na ga baki canja ba wallahi zan sa6a miki ne, bana son yawan_ _kukan nan da damuwa kuma, ko shi Mahmud 'din ce miki yayi ki dinga yi_ _masa kuka idan_ _ya rasu_ ? Da kai ta bashi amsa alamar " _ah'ah_ " Sai kawai yaci gaba da da fa'din " _Ya kamata kisani Mahmud is now no more, baze ta6a dawowa ba, is better ki nutsu ki san_ _abinda ya dace ba ki ringa damun mutane da kuka da damuwa_ _ba, zan bawa Abbah_ _ha'kuri akan tahowarki dan nasan beji da'din hakan ba, sannan_ _idan nadawo naga kin saki jiki ni da kaina zan kaiki Lagos 'din ki dubo_ _su har wurin Mummy ma duk zan kaiki amma sai naga kina jin_ _magana tukunna......_ _clear_ " Ta gya'da kanta tare da furta " _yes_" ahankali. " _Toh gudnight_ " Daga nan be sake kallon inda take ba ya maida idanunsa kan television. Tashi tayi ta fita zuciyarta fal farin ciki, musamman dataji yace zai kaita gurin Mummyn ta, ai gaba 'daya sai ta manta da komai. Hannah ma sai da ta fahimci farin cikin dake kan fuskar Teemahn data tambayeta kuwa take ta sanar da ita yanda sukayi da Abbas 'din. Murmushi kawai Hannah tayi tare da jinjina masa aranta tasan yana yin duk hakan ne dan yaga 'kuncin Teemahn yaragu. Wani lokaci takan ga kamar Teemahn na da sa'ansa domin Yayah yakanyi mata abinda bakowa ke samun hakan daga gareshi ba, bata san dalilin sa ba amma tana jinjinawa dangatar dake tsakaninsu. ***** Washegari 'karfe bakwai ya bar gidan yayi tafiyarsa ya koma Rivers state, Umman ce ka'dai tasan da fitarshi itan ma atsatstsaye yazo yayi mata sallama yafice. Tasan halinsa sarai yanzun yana hakan ne dan kar tasake yi masa magana akan Fateemah shiyasa yayi hakan ita kuwa yanzu ta riga ta saduda barinsa zatayi taga iya gudun ruwansa tunda kam yace Fateemahn amanar sa ce ita, toh nata kallo ne. *Masoya Abin alfahari ina yin ku sosai da sosai wallahi nima, bazance muku komai ba dan bani da bakin gode muku all i know is that kuna sani farin ciki...... addu'o'in ku nasani walwala, Allah ubangiji ya bar minku ya sada ku da dukkan alkhairinsa.* ~WANNAN SALMERHN NAYI MUKU FATAN ALKHAIRI~ _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce*😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated to my sister Khadeeja Usman Allah ya bar min ke._ *Bismillahir rahmanir raheem* _A good heart and a good nature are two different issues, A good heart can win many relationships, But a good nature can win many good hearts._ 🅿 *70* Kwanan Fateemah biyu agidan sannan ta 'dan saki jikinta, Daddyn Abuja ma daya dawo sosai yayi farin ciki da zuwanta dan ko shima bawani da'di yaji da barinta da akayi acan ba kawai de yayi shiru ne saboda al'amarin ahannun matan yake, yanzu kuwa da ya ganta ya kuma ji labarin cewa Abbas ne ya kawo ta ai shikenan gaba 'daya sai ya manta ma da haushin Abbas 'din daya keji ya ringa sa masa albarka. 'Ko'kari sosai Hannah keyi wajen ganin ta mantar da Teemahn damuwar da take ciki, saboda bata barinta zama shiru sai de in tatafi makaranta wanda makarantar ma dan ya zama dole ne shiyasa lokuta takance da ita badan tana zaman 'dakin rasuwar mijinta bama da se ta ringa rakata makarantar ai. Teemah kam baki take ta6ewa ta yi shiru, dama yanzu gaba 'daya ta canja wannan rashin jin duk babu shi ta dawo wata salihar 'karfi da yaji, wani lokaci idan tana abu se kaga kamar ba ita ba. Haka abinci ma yanzu bata ci da wasa 3square meal 'din nan duk basa wuceta takanyi 'ko'kari taci a'kalla kamar spoon goma koma fi akowani lokacin cin abinci, Ummah sosai take jin da'din canjawar tata musamman data ga yanzu tasaki jiki har tana cin abinci batare da an takurata ba. Damuwar ma duk ta rage shi yanzu ta barwa zuciyarta, addu'ah kawai take masa akowani lokaci musamman idan tayi sallah toh sosai take 6ata lokaci waken yi masa addu'ah wanda a lokacin ne tafiya yin kuka sai de ko Hannah bata bari ta fahimci yanayin data ke shiga. Tana waya dasu mummy da Anty akai-akai, inda mummy kanta da taji cewar Teemah ta dawo Abuja sai da ta sau'ke ajiyan zuciya da can 'din ma kawai ta daure ranta ne tare da yiwa Anty kawaici, amma tunda ta koma Dubai sai taji zuciyarta ya kasa nutsuwa sai take ganin kamar Antyn zata iya sake cutar da Fateemah tunda tana gabanta. Anty kuwa bayan tafiyar Teemah da kwana biyu sai taji damuwarta ta dawo mata sabo fil, tunaninta ya yawaita akoda yaushe bata da aiki sai zubda 'kwalla, gashi babu wanda ke zuwa gurinta ayanzun, Abbah ma 'kara nisanta kansa yayi da ita, dan tun tafiyar Teemah sau 'daya kawai ta ganshi, wannan 'dinma ta window ne lokacin shigowar sa gida kenan jin dirin mota yasa ta le'ka sai taganshi. Ganin sa 'din kuma sai ya 'kara kashe mata zuciyar dan gaba 'daya Abbah ya lalace wani rama taga yayi na masifa, tausayinsa har se da ya sata sakin hawaye, tasan koma menene yafaru laifinta ne, mutuwa ba a hannunta yake ba, amma tasan son zuciyarta shine sanadin komai. Komawa tayi ta jinginu da jikin window ta lumshe idanu yayinda hawaye suka ci gaba da gangarowa ta 'kasan idanun suna sau'ka saman kuncinta, samata 'daga kanta tace " _Allah na tuba ka yafe min, ka yafe min kura kuraina, ya ubangiji Allah ka sanyaya zu'katan duk wa'danda na_ ' _kuntatawa, Ya Allah kaji'kan Mahmud ka haskaka masa 'kabarin sa_ " Washe gari da sassafe tayiwa 'dakin Abbah tsinke, sallamrta ka'dai ya amsa saboda darajar da sallama ke da shi ga dukkan wani musulmi, daga nan yaci gaba da shirinsa be ko kalli inda take ba, kallo 'daya Anty tayi masa ta fahimci cewa shirin tafiya yakeyi dan haka sai ta zauna agefen gado ahankali tace " barka da warhaka Alhaji fatan antshi lafiya" Da " lafiya 'kalau" Kawai ya amsa ta atakaice. Anty ma sai tayi shiru bata 'kara magana ba kawai ta rin'ka binsa da idanu. Ganin kamar bashi da niyyar sake kulata sai tace dashi " _Alhaji dan Allah kayi ha'kuri ka yafemin laifukana, ka daina fushi dani,_ _wallahi nayi dana sanin duk abubuwan dana aikata abaya, ni kaina inajin tsanar kaina akan haka_ , _bansan ya zanyi in goge laifina awurin mahallicina ba amma nasan idan kun yafeni wata'kila_ _Allah zaiji tausayina ya min afuwa_ " _Nasan ban yi mana adalci ba koka'dan, ban kyauta wa rayuwar mu ba gaba 'daya tunda_ _gashi son kaina yasa har nayi sanadin da 'dana yarasa_ _rayuwarsa......_ Kuka ne ya kubce mata tayi na kusan mintina biyu sannan taci gaba da fa'din " _Mahmud yace kayafe masa Alhaji, yace in ro'ka masa yafiya awurinka akan duk laifukan_ _daya maka arayuwarsa......_ Sai ta sake sakin kuka gwanin tausayi. Abbah ma dakansa sai da ya share hawaye da jin abinda Anty take fa'di tunanin yaronsa da tausayin kansa ya 'kara kamashi, 'dansa 'kwaya tal da Allah ya bashi gashi be samu damar bashi farin cikin daya dace ba har ya bar duniya, yau gashi babu shi, Mahmud ya tafi, sai de yasan Allahn daya kar6e shi yafishi son shine, yasan kuma Allah baya ta6a barin wani dan wani yaji da'di, sai fatan Allah yayiwa Mahmud Ubangiji ya sada shi da dukkan rahamarsa. Yana goge hawayen fuskarsa ya 'dauki 'yar 'karamar jakar kayansa daya gama shiryawa tare da 'daukan wayoyinsa ya nufi hanyar fita. Ganin Abbah na shirin fita batare da taji kalma 'daya me kyau daga bakinsa ba yasata ta mi'ke da hanzari tace " _Alhaji ko bazaka min magana ba dan Allah kayi min izini in tafi kano_ " " _Allah ya kiyaye_ _hanya_ " ya fa'da tare da ficewa abinsa daga 'dakin. Anty kam kuka tasanya har tana 'dan bubbuga kanta da hannunta, nadama da takaici ne duk suka ha'du sukayi mata yawa, duk da tana farin ciki da barinta da Abbah yayi amma kuma halin dayake cikin ya matu'kar tsaya mata arai, tasan dama ba ze ta6a hanata zuwa kano ba, baze ta6a shiga tsakaninta da ahalinta ba, shi akullum ma burinsa taringa ziyartar su tare da mutunta familynta sa6anin nata halin. Zata je ta nemi gafarar iyayenta ta gyara dukkan kurakuranta na baya, ta faranta musu a matsayinta na 'ya agare su. Ko zata samu su yafe mata laifukanta garesu. ***** Daddy musamman ya baro Dubai yataho domin ya amsa gayyatar Abbas inda suka je shi da Daddyn Abuja suka halacci taron 'karin girmansa inda daga ranar ya amsa matsayinsa na *CAPTAIN* . Tun acan Daddynsa yafara wa Yayan sa magana akan Abbas 'din, complain ya shigar akan cewa wai yayi-yayi dashi ya yi aure amma ya'ki, shi kuma duk wannan abubuwan ba farin ciki suke saka shi ba, dan ko wani irin matsayi mutun yakai aduniya matu'kar bashi da iyali toh darajarsa ragaggiya ce, gara tun wuri kayi wa 'danka magana yafito da mata inbahaka ba wallahi da kaina zan za6a masa mata idan nagaji da magana. Murmushi Daddy yayi sannan yace "Haba Hassan kabarshi mana yasamu nutsuwa, yaushe ma yasamu ya zauna da har za'a fara yi masa maganar aure, shi auren de lokacine idan lokacin yayi kuwa ba se ka tsaya 6ata bakinka ba, da kansa zakaga ya furta, dan Allah ka sarara masa Al-Hassan ka raba masa hankali" Kauda kai Daddyn Abuja yayi wanda Daddy yafahimci cewa maganar tasa bata wani shiga ransa ba amma de yasan Hassan 'din ba ze taka maganar sa ba tunda ya furta, dan Hassan na matu'kar bashi girmansa sosai. Daddy daga can ya wuche ko Abuja be dawo ba, saboda baya son ha'duwa da Teemah a dai-dai wannan lokacin dan uasan rigimarta yawa ne da ita. Abbas kam tare suka dawo gida shida Daddynsa, dan har yanzu acikin hutunsa yake be gama ba. Sai da yazo gida kafin su Ummah suka shirya wata 'kwarya-'kwaryar walimah acikin gida na tayashi murna, yaji da'di sosai da hakan barin ma daya ga Fateemah ta 'dan saki ranta yanzun bakamar da ba, gashi ta 'dan yi kyan gani duk da hijab ta zun6ula har 'kasa amma hakan be hanashi fahimtar canjawarta ba. Ahankali ya 'kara fahimtar rungumar 'kaddara da tayi saboda ko a dinning yaga yanzu tana ' dan sake wa taci abinci harma ayi hira da ita, duk da murmusho yafi yawa anata fuskar amma sometimes takan jefa nata ka'dan. Idan Hannah na makaranta kuwa sau tari da Ummah zaka same ta tmsuna ta'di abinsu, ko kuma ta yi kwanciyarta akan cinyar Ummahn tana shagwa6arta wani lokaci har bacci takeyi agurinta. *Bayan sati 'daya......* Teemah ha'kurin ta yafara gazawa ganin har yanzu Yayah Abbas be sake mata maganar tafiyan ba, kuma xe mata yayi idan yadawo zai kata, tayi 'ko'karin kiyaye duk wani abu da tasan ze sa shi canja ra'ayi amma shiru bata ji yace komai ba. Bata san me zata ce dashi ba dan haka sai ta fara bawa Ummah labari ka'dan-ka'dan, sai tace da Ummahn " _Yayah fah uace zamu je wurin Mummy da Anty in gaishesu amma kuma naji be sake_ _maganan ba_ " " _Antyn naki ba kince tana kano ba_ ? Ummah ta tambaya tana kallonta. Sai tace " _Ehh tatafi kano, ai shi ne yace zamu_ _wajenta_ " "Toh inaga be shirya tafiyan bane tukunna, amma nasan tunda har ya fa'da toh babu shakka zai kaiki 'din, zai fison idan kin warawre gaba 'daya" Cikin shagwa6a tace "Ummah nafa riga warware gaba 'daya" " _Toh ni Fateemah ni miye nawa, ba fa dani kukayi_ _shawaran ku ba_ " Kwa6a fuska tayi kamar zata yi kuka gani hakan yasa Ummah ta janyo ta zuwa jikinta ta kwanatar. " _Haba Fateemah, kiyi ha'kuri mana ki 'dan 'kara bashi lokaci kinji_ " Ummah ma biye ta ringayi da lallami har zancen ya kau. Ita kam ma ai jinta take yi kawai, dan ko Abbas ya 'dago zancen tafiyar toh ita ba yadda zatayi ba. Yawon ai ya isa hakan gara ta zauna wuri 'daya ta iddasa zaman takabarta inyaso daga ko ina ne ma taje. Teemah kam ha'kurinta 'karewa yayi, kwana biyar bayan maganar da sukayi da Ummah sai taje dakanta tasame shi. Duk yanda take ganin ta canja Abbas cewa yayi be ga hakan ba shi har yanzu dan haka tafiya ba yanzu ba. Ranar kam kuka tasha da dare dan haushi, tana cikin kukan ne Anty ta 'kirata awayarta tana 'dauka kuwa tasake mata kuka, take Anty ta rikice ta fara tambayarta abinda ya faru, me aka mata? cikin kukan tayi mata bayanin komai, Anty kam murmushi tayi dan take ta fahimci wayo kawai Abbas yamata dan ta saki ranta ta sake da kowa, amma duk da haka sai tace da ita " _har kin sa na ji wani iri ma, ai inajin Abbas 'din yama fiki gaskiya, amma de kiyi ha'kuri kinji, ki bari idan na koma Lagos 'din nasan zai kawo ki tunda shi yafa'di haka, ai yawo banaki bane yanzu Fateemah, akwai sauran lokaci kinji inna samu lokaci ma zanzo na duba ki a Abujan kinji_ ? Baki ta tura gaba ciki muryar shagwa6arta tace " _Dan Allah Anty kizo toh, ni nagaji da zaman ne Anty, bafah na zuwa ko'ina ko shopping Hannah ce_ _ka'dai take zuwa, ni Ummah bata_ _barina in bita kuma idan ta dawo sai ta ta min dariya_ " Murmushi Anty tayi daga 6angarenta, tana mamakin yarintar Teemah ita kam, ashe yarinya ce ' karama sosai har yanzu, tasan koda tace zata mata bayani ma 'kila ba gane manufarta zatayi ba, dan haka sai ta bar wancan tunanin kawai tace " _Ayyah very sorry kinji, soon kema zaki fita ai yanzun be kamata kina yawo bane shiyasa amma in lokaci yayi nasan babu me hanaki fita_ " Sosai Anty tayi ta rarrashinta har ta ha'kura tayi shiru. Ganin ta nutsu yasa har Anty ta bata labarin kaf yanda suka yi da mahaifanta bata 6oye mata komai ba, yanda tasha gwagwarmaya kafin ya amince da ita, da 'kyar ya furta mata kalmar yafiya dan shi tsakaninsa da Allah ya tsani ganinta arayuwarsa ma. Teemah ta tausaya mata da jin labarin, inda tasake bata 'kwarin gwiwa sosai kamar ba ita bace me zuba shagwa6a ba 'dazu. Anty najin da'din kasancewa da ita dan ko ba komai takan 'de be mata kewa, gashi tana 'ko'karin bata shawarwari masu kyau duk da take yarinya 'karama amma akwai ta da ilimi, bayan sata ahanya data tayi lokacin suna Lagos, Anty tamkar sa'arta ta maida ita dan duk shawaranta da ita takeyi yanzu, in abune ma ya dameta Teemah take sanarwa su jajanta tare sosai take janta ajiki tana jinta tamkar 6arin zuciyarta ce. Sau tari Anty na addu'ar Allah yasa Fateemah nada cikin Mahmud saboda zata so ace tasamu jika daga ita, amma lokaci guda take kauda wannan tunanin idan ta tuno kato6arar da Munnira ta aikata, musu sai dai akullun bata cire rai idan son jikan yacika mata zuciya sai kuma taji kamar batun Munniran 'karyane babu wani barrier da ta yi atsakaninsu ,alokacinn ne take 'karyata Munnira da kuma aikin bokayen sai taji kamar tunanin ta gaskiya ne, Fateemah nada cikin Mahmud ajikinta. Har kwatanta ranar da za'a ce maganar ta tabbata takeyi tana misalta irin farin cikin da zataji, takance da kuwa anga zallar so dazata nunawa jikan nata, bata jin akwai abinda zata so fiye dashi aduk fa'din rayuwarta kuwa. Lokacin da sukayi sallama da Anty Fateemah ma shiru tayi tana tunani, abin na damun ta sosai, yanda akabi aka tsare ta agida kamar munafuka, turare wannan Ummah hanata amfani tayi da shi, duk kuwa da yanda Teemah ke da jarabar turare amma hanata akayi amfani da masu 'karfi, sai da taga Teemah na shirin yi mata kuka kafin da 'kyar ta barta take amfani da wani me sanyin 'kamshi sam bashida 'karfi, wani lokaci idan tasaka shi ajikinta mintina biyar bayayi ajikinta sai taji babu 'kamshin duk ya gushe, sannan bata kwalliya kullum tana nan sai fama da waya a'daki. Islamiya wannan idan suka ce zasuje tare da Hannah Ummah hanata takeyi, akwai ranar dama ta san'di jiki suka fita ta 'kofar kitchen har suna murna amma cikin rashin sa'a sai ga Yayah agabansu take kuwa ya maida ta gida yace maza ta koma babu inda zata je. Ranar kam tasha kuka, wani lokaci gani take kamar ita ka'dai aka tsana agidan shiyasa akeyi mata haka, yayinda kuma taga ake riritata tare da girmama bu'katunta fiye da Hannah sai kuma ta 'karyata zancenta na farko, sam tarasa dalilin hakan gaba 'daya ta gaji. Dai-dai lokacin da tacika sati uku cif da zuwa gidan adai-dai lokacin Yayah Abbas ya koma bakin aikinsa wanda yayi dai-dai da wata biyu da kwana uku da rasuwar Mahmud. Zuwa lokacin kam Teemah ta saduda ta daina damuwa, ri'ke 'kuncinta kawai tayi azuciya. Abbas 'din ma dayake bazama sosai yayi agidan ba, ita dai tasan yaje Gombe inda daganan taji labari abakin Ummah cewa ya wuche Dubai daga can. So rashin zaman nasa yasa bata fiya ganinsa ba, amma duk da haka 'ko'kari sosai ko da bayanan amma yana kula dasu yana yawan turawa Hannah ku'di yace suyi amfani dashi, wai shi duk a'ko'karinsa naganain ya kula da amanar marigayi da ya kar6a, Hannah kam murna ta ke yi aduk lokacin da taga alert awayan ta takance " _albarkacin ki fah nake ci Teemah, da Yayah baya son bani ku'di ko na tambaya baya bani sai yaji 'kwa'kwkwaran dalili kafin nan yabani, kuma Daddy ma baya bani idan na tambaya sai ya wani ce in tambayi_ _Yayah na yabani kuma fah yasan dramar da muke sha dashi, amma duk da haka gurinsa yake turani, shi wai adole_ _be so_ _insaba da kashemanyan ku'da'de sai kuma_ _yanzu naga ba'a tambaya bama bayarwa yake yi_ " Ta6e baki Teemah kwaia tayi dan ita bata da matsala da wannan. Abinda ke damunta ma ya isheta, dan haushi ranar kam har kuka tayi musamman da ta tuno da Mummy, da ance aure toh yanzu kuma fah tunda babu auren memiye kuma dalilin tsareta, bata ja tsawon lokaci ba ta bawa kanta ha'kuri, wani lokaci harda laifin mummy take gani, tasan ai itace ta shareta da bata manta da ita ba da duk haka be faru ba. Daddy kam ba'a ma maganarsa dan shi samun layinsa bata fiye yi ba dayake yana yawan tafiye tafiye shiyasa bashi da takamammiyar number da zata sameshi akai . Ko bayan tafiyar Abbas ma bata damu ba dan zuwa yanzun babu ba'konta cikin duk rayuwarta komai tasaba dashi, zaman gida da sauransu, ita kanta ma yanzu tana jin da'din rayuwarta mafi yawan damuwarta ya kau, Anty ma har yanzu tana kano bata koma Lagos ba kuma cikin sabo da sha 'kuwarsu babu abinda ya ragu sai ma 'karuwa. Ahaka da da'di ba da'di har Mahmud yacika wata hu'du da rasuwa, inda duk mutanen zuwa yanzu alhinin rashin sa ya ragu azu'katansu addu'a kawai suke binsa dashi. Alhaji Muhammad kuma sosai yagaji da zaman Anty agida koda yayi mata magana kuwa sai tace Abbah ne yace tazo gida, tafa'di hakane kuma dan bata so mahaifin nata yaringa damunta da batun komawa. Shikuwa da be san manufarta ba suna rabuwa da ita sai ya tuntu6i Abbah awaya yace masa " _Yusuf wai meke faruwane, naga tsawon wata biyu kenan harda_ _kwanaki Maryam nagida, bamu ta6a tattauna dalilin zaman ba, naga_ _kuma ko ka 'kirani baka kawo maganar ince dai lafiya ko?_ Abbah cewa " _Lafiya 'kalau Alhaji ina nan ma zuwa kwanan nan insha Allahu nima_ " " _Toh Allah ya kawoka lafiya, gara de ayi abinda ya dace ina ganin zai fi_ _ko_ " Cewar Alhaji Muhammad yana me shafa gemunsa. Abbah sai ya tabbatar masa da cewa " _insha Allah komai zai tafi dai dai bisa dacewa_ " _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir rahmanir raheem* _Crushes are more beautiful than affairs because there is no_ _responsibility, no worry_ , _no commitment. Just look at your crush and smile like an_ _idiot_. 🅿 *71* Abbas kam yanzu girma ya 'karu, ta'kama da izzah sai abinda yayi gaba, Daddynsa ne ka'dai yake 'dan kashe masa gwiwa aduk lokacin da yayi masa zancen aure walau awaya ne ko kuma azahiri, sam bayason maganar auren nan amma yarasa yanda ze 6ullo masa, babban damuwarsa kenan ayanzu shiyasa ya tsani maganar ma kwata-kwata. ***** Kamar yanda Abbah ya yiwa Alhaji Muhammad al'kawari hakan ne ya faru domin acikin satin ranar wata laraba ya sau'ka garin Kano, Alhaji Muhammad yaji da'din zuwansa dan kuwa ko ba komai yana ganin yanzu ne ze san matsayin da 'yarsa ta take awurin Abbah, dan haka bayan gaishe-gaishe har Abbahn ya huta ma sannan Alhaji Muhammad ya nemi jin salin abinda ke faruwa daga bakin sa, Abbah kam be sanar da shi komai ba yace masa kawai tace ne zata zo ta duba iyayenta shi kuma yace ta bashi lokaci in yayi settling sai suzo tare, ganin kamar lokacin tmya'ki samuwa ne shi yasa ta taho, batun kuma cewa shine yace ta zo 'din bahaka bane, yace wata'kila bata ahirya komawa yanzu bane shiyasa ta fa'di. Alhaji Muhammad kam shiru yayi masa amma bawai dan ya gamsu ba, duba da yayi da cewar tun tsawon shekarun auren su da ita hakan be ta6a faruwa ba, toh me yasa sai yanzun kuma, yana kyautata zaton matsala suka samu amma Abbah yake 6oye masa, Alhaji be tsawaita tunani ba shima ya basar da zancen dan yasan basu ta6a samun matsala har abin yazo gabansa ba sai de lokacin auren marigayi Mahmud da ya kawo 'karar ta, wannan ma Abbah ya kawo 'karan ne dan kawo gyara wa lamarin, kafin da bayan hakan kuwa be ta6a sanin ya yanayin zamansu ba, yanzu kuwa da babu ran Mahmud be san takamam man menene matsalar su ba kuma ya san de baza'a rasa ba dole akwai wani abu, kawai de Yusuf na 6oye masa ne shikuwa ba haka yaso ba, yaso yaji abinda ke faruwa domin ya 'dan gyara al'amarin idan Allah ya bashi dama, dan shi da kanshi wani lokacin Maryam na bashi tsoro duk kuwa dayake 'yar cikin sa ne amma tun lokacin dayaji asalin 6oyayyen halinta gaba 'daya ya tsinke da lamarinta. Alhaji aikawa yayi akayi masa 'kiran Anty (Maryam), koda tazo kuwa mamaki tayi da ganin Abbah ita kam, domin bata ta6a zaton zuwansa adai-dai wannan lokacin ba. Sai ma taga ya 'dan murmure yanzun ba kamar da ba, fuskarsa se wani 6oyayyan annuri ke haskawa. Alhaji Muhammad ne ya nemi jin abinda ya faru daga bakinta karo.na biyu, sanin da Anty tayi cewa yariga yasan komai yasa bata bata 6oye masa ba ta kwashe duk abinda ta aikata da dalilin da Abban Mahmud ke fushi da ita duk ta sanar dashi. Alhaji Muhammad beyi mamaki ba dan yariga yaji duk abubuwan da yafaru 'din tun a Lagos sai de be san cewa hakan.ne ya kawo sa6ani tsakanin su ba, duk da kuwa cewa yasan ba kowa ne ne zai juri faruwar hakan ba, ko shi kanshi idan hakan yafaru cikin iyalinsa yasan da 'kyar ya iya sake zama da me shi shiyasa sam be ga laifin Abbah ba ko ka'dan sai ma ya jinjina masa da be aikata fiye da wannan ba, sake tambayar Abbah yayi inda ya tambayan ne kawai dan tabbatar wa. Nasiha dukkan su ya ha'da su yayi musu game da zamanta kewar su, sosai yaja hankalinsu game da tsoron Allah cikin al'amuransu, sai da ya gama nasihar kafin ya baiwa Abbah dama yace yana da ikon za6an duk abinda yaga yayi masa wanda ya dace dashi, yace " _karka damu dani Yusuf, ni tamkar mahaifinka nake bazan takuraka akan komai ba, sannan ina so_ _kayiwa kanka adalci karka dube ni kowani abu daya shafeni, Maryam matar kace,_ _kuma_ _kai ke da ikon za6an sake zama da ita ko kuma akasin haka, duk ra'ayinka_ _ne_ _Yusuf_ , _bazan ta6a tilas ta ka dan ka zauna da ita ba dan tana matsayin 'yah agareni, wallahi_ _Yusuf da ace ni ni ke da iko da kai da bazan ta6a barinka kasake zama da Maryam a matsayin_ _mata ba, kuma ko yanzun ma kana da damar za6a ni nawa_ _shawara ne koma me ka aikata ni.kam.ina maraba dashi Yusuf domin kuwa nasan kai 'din'dan halak ne me matu'kar ha'kuri sosai wanda ina zaton da iznin Allah rayuwarka bazata ta6a birkicewa ba Insha Allahu_ ". Tuntuni Anty take zubda hawaye tana 'karawa tasan koma me ya faru duk laifinta ne, laifinta ne da ta saka.son.zuciya ya rinjayi duk kan al'amuranta, yau gashi mahaifinta da kansa yake bada shawarar kar azauna da ita. Godiya Abbah yayi masa sannan ya sanar dashi cewa shi bashi da burin 'kuntata mata koka'dan kuma.duk abinda zaiyi zaiyi shi ne dan gyara duk wata 6araka da ke tsakaninsu, yace ha'kika Maryanlm.ta 6ata raina ta shammace ni alokacin da banyi zaton faruwar hakan ba, Maryam ta ninke ni a baibai da sunan ta kar6i maganar auren Mahmud bansani ba ashe mugun sa'ka tayi a6oye wanda warwareshi ke da matu'kar wahala, ban ta6a zaton Maryam zata aikata haka ga 'dan cikinta ba, wanda ya kamata ace ta so shi fiye da komai arayuwarta, amma kash! Mahmud be yi dacen samun hakan ba sa6anin haka sai ma ya rasa rayuwarsa. Bayan jin hakan na tsani Maryam irin.tsanar da banta 6a zaton zan mata shi ba, naso in hukunta ta ta yadda bazata ta6a ma tunanin sake aikata wani abu makamanciyar wannan ba, sai de banyi hakan ba saboda ganin girma da kake dashi Alhaji a idanu na, bayaga haka ma Fateemah sai ta nutsar dani muhimmancin yafiya da falalar ta, kuma na gamsu sosai sanadin hakan na yafi Maryam azuciyata sai de bakina nawi yamin in furta mata haka nabari har se naga nadama ya ratsata tukunna. Cikin hakan Allah ya nufe ni da neman aure kuma nasamu Alhaji zancen ana danake maka ayanzu kwanaki goma ne suka rage a 'daura aure " Fuskar Alhaji tuni ya cika da murmushi ya ringa sanya masa albarka tare da fatan alkhairi yace yayi matu'kar farin ciki da faruwar hakan kuma yana bayansa 'dari bisa 'dari. Anty kam hawaye masu zafi ne suka zubo mata wanda tun rasuwar Mahmud basu fasa zuba ba, sai de na yau yasha bambam dana kullum, akowani 'digon hawayen ta nadama ke lullu6e ta tare da wanke duk munanan halayenta dake zuciyarta, yanzu kuwa kukanta na godiya ga mahalicci ne da Abbah ya furta mata yafiya, ta tsani kishiya abaya amma yanzu kam ji take matu'kar ze yadda ya amince ya sake zama da ita toh a shirye take ta zauna da kishiyoyi uku ma ba 'daya ba. Komai faru laifin tane, Abbah be ta6a yi mata maganar kishiya ba tunda suke dashi sai yau 'din, yanzu kuwa da duk abubuwa suka yimata yawa ina ita ina 'daga hankali dan zeyi aure, tace Allah ubangiji ya ha'de kawunan mu ya sa hakan shine mafi alkhairi. ***** Abbas tunda ya tafi kusan 3weeks kenan har yanzu be dawo ba, kullum sai dai su gaisa dashi awaya sai ya ta cewa ayyuaka ne suka yi masa shiyasa be le'ko gidan ba, Ummah bata damuwa dan tasan yanayin aikinsa dama fiye da hakan ma zai iya faruwa shiyasa kullum da addu'ar nasara da kariya kawai take binsa. Daddynsa kam ko ajikinsa, sarai yasan matsalar Abbas 'din gudun ha'duwarsu yakeyi saboda batun aure shiyasa ya'kizuwa Abuja shikuwa babu fashi lokacin daya 'dibe masa na cika zaiga abin mamaki dan kuwa ba ze fasa ba. Ranar da Teemah ta gama watannin takabarta ranar har se da tayi mamaki dan yanda Ummah ta fitar da ita tsab, sai dama ta ha'da ta driver suka je saloon suka dawo sannan tabata wasu ha'da'd'dun gown 'yan italy matsu kyau da tsada sai alokacin ne Teemah take jin labari ashe wai Mummy ce ta aiko musu dashi tun zuwan Abbas kwanaki shine Ummah ta 6oye su sai yau ta fitar ta bata nata na Hannah kuma tace sai ta dawo zata ksr6i nata. Data shirya tafito kuwa ita kanta tasan tayi kyau har jin kanta takeyi, ji take yi kamar wata dabance ba Fateemah ba, for about 4months da wasu kwanaki tana ta fama da atampopi yau kam wani iska takeji yana shiganta me da'din gaske, tun ba ma da Ummah ta bata wasu turaruka masu kyau tace nata bane, take ta rungume Ummahn tana dariya tare da godiya. Haka taringa fesawa ajikinta tana 'karawa har se da 'kamshin ya 'dan fara yimata yawa kafin ta sarara. Jin kanta yau 'din takeyi tamkar wata sarauniya gaba 'daya ta dawo daban. 'Daki ta koma ta ringa kashe selfie kala-kala wasu abin dariya wasu kuma abin birgewa ita adole tana farin ciki yau tasamu freedom afa'darta. Ummah da kanta tace idan Hannah ta dawo da wuri ko da da yamma ne sai sunje shopping musamman kawai saboda Teemah. Ai kuwa Teemah taringa 'kiran layin Hannah amma baya shiga kusan 5 missed calls ta mata, data ga bata 'daga ba sai ta tura mata text " _Hii bae, pls ki dawo da wuri today is my day, Ummah tace zamu_ _fita_ " Hannah na can tana rubuta test dan haka bata ma bi takan wayarta ba sai da tagama rubuta test 'din tafito sannan ta ga missed calls 'din Teemah tare da text 'din da tayi mata, ai kuwa tana gani ta hau murnan yau zasu fita da 'yar uwarta , bata 'kara bi takan sauran lectures 'din da zata yi ba batare da jiran komai ba ta kamo hanya ta dawo gida. Tana zuwa suka rungume juna suna murna, Hannah da kanta itama sai da taga canjawar Teemah har ta kasa daurewa sai da ta tambaye ta aka wai yaushe kuma har tayi saloon batare da tasani ba? Murmushi Teemah takeyi ta bata amsa da fa'din " _yau da safe naje nayi lokacin already kina school ai shiyasa_ . 'Bata rai Hannah tay tace " _shine kuma kika 'ki jirana muje tare ba, duk laifin Ummah ne_ _ai da ta gaya min da wuri_ _da sai in fasa makarantar mutafi amma shine aka 'kyaleni harna tafi_ " Teemah tana kan haska selfie tace " _yanzu kam ai ya wuce ki, yi sauri ki shirya muje yawo yarinya yau zanga gari yarinya, kayanki ma na gurin Ummah, ke ko irin kice nayi kyau 'din nan ma baki fa'da ba kintsaya surutu_ " Tashi Hannah tayi taje wurin Ummah ta amsa kayanta tare da shigar da complain 'din bata je saloon ba ita. Ummah lalla6ata tayi har zancen ya wuce sannan ta wuce 'daki domin watsa ruwa. Abbas kam be dawo Abuja ba har sai da ya cika sati hu'du cif-cif kafinnan, ranar daya dawo 'din kuma sai yayi dai-dai da ranar da Teemah ta gama takabanta. Bayan shigan Hannah wanka ne Teemah ta 'kira Anty tana 'dauka tace " _Anty albishirin ki_ ? " _Goro fari 'kal-'kal_ " Anty tabata amsa tana murmushi. " _Anty yau zan fita_ _yawo nida___ _Hannah...._ " _Kai dan allah kice_ _yau sabuwar_ _rayuwa_ ' _yata zata fara_ " Labari Teemah ta bata na irin kayan da ta saka da sauransu. Daga 'karshe Anty tace mata itama insha Allahu gobe tana hanya zata zo Abujan, Teemah murna kamar tafasa wayar da ihu, sai da Anty ta kauda wayar akunnanta tana murmushi da gode wa Allah ga dukkan baiwarsa. Tana gama wa da Anty ta 'kira layin Mummyn ta. Mummyn ma tace ai tana ta 'kiran layinsu be tafiya tun jiya har na Ummah ma, tace Teemah ta ha'da ta da Ummahn pls. Fita tayi dan kaiwa Ummah wayar inda ahanyan ne take bawa Mummy labari akan yau zata fita yawo ita da Hannah tace Mummy kinga kayan da kika aiko manan nan kuwa yanda yamin kyau dan Allah Mummy ki 'kara siya min wani, idan nazo kawai in samu, zan ro'ki daddy ai yabar ni inzo. Mummy cewa tayi " _Nima zanzo ai insha Allahu gobe ko jibi_ " Wani tsalle da ihun da Teemah ta buga da jin furucin Mummy tare da gwalo idanun ta yasa Abbas dakatawa daga tafiyar dayakeyi ya tsaya kallonta. " _Dan Allah Mummy_ _dagaske_ _zaki zo_ ? Ta tambaya da murna kamar zata fasa wayar ta ganta agaban Mummy. Mummyn ma cewa tayi " _zanzo mana Teemah ina miki 'karyane_ ! Tsalle ta buga tace Anty ma zata zo tace min Mummy, dan Allah karku fasa kinji....... Maganar tata yankewa yayi jin an fizgo wayan daga kunnanta daga bayanta, juyi tayi da 'karfi zaton ta ma Hannah ce harta gama shiri ta fito hakan yasa ta fara furta " _banason iskanci_ _Hannah da_ _mum...._ ganinshi tsaye tayi yana kallonta, baki ta rufe da hannunta tare da zaro idanu waje. Wani kyau da kwarjini taga yayi mata, muryarta na rawa tace " _sannu_ _da zuwa Yayah_ " Kallonta yayi kawai batare da ya amsa mata ba, sai ma yace mata " _welcome back Nana_ _parrots_ ! _Ke ihun naki be_ _damunki ne_ , _ke 'daya amma kinbi kin cika gida da hayaniya kamar kasuwa_ ? Anutse yayi mata maganar bada masifa ba ita kanta tayi mamakinsa yau 'din. Amma duk da haka sai tayi shiru tai 'kasa da kanta batare da ta furta komai ba. Dayaga bata da niyyan yin magana sai ya huya kansa tare da fa'din " _Any ways, i heard u said zaki yawo ko?, har zuwa ina kenan haka_ ? " _Shopping zamu_" Ta bashi amsa atakaice. Sake tambayarta yayi " _ke da waye_ ? Tace da " _Hannah_ " " _inji wa_ ? 'Dago idanu tayi ta kalleshi jin yanata jero mata tamabayoyi kamar wani 'dan jarida, da suka ha'da idanu sai ya 'dage nashi idanun zuwa sama. Ta fahimci manufarsa dan haka sai tace " _inji Ummah_ ! Tana fa'din haka tafara ro'kon Allah azuciyarta akan Allah yasa kar ya hanasu fita tasan ka'dan ga aikin sa ne yace bazasu ko'ina ba, ita kuwa tana jin da ya hanata fitan nan gara yayi mata komai ma amma banda shi. Cikin haka wayan ta dake hannunsa yafara ringing 'dagowa yayi sai yaga Mummy ce ta'kira, yana ganin haka sai ya mi'ka mata wayar yana kallon cikin idanunta. Ahankali tasa hannu ta kar6a tare da sada ta da kunnenta tace " _hello, Mummy_ ! " _Ah ah ban kai ba tukunna bari nayi sauri inkai mata_ " Iyah abinda yaji ta fa'da kenan. Tana fa'din haka ta yanke 'kiran tare da juyawa da niyyar tafiya. Muryarshi tajiyo yana fa'din " _In kin kai mata wayan ki kawo min ruwan sha_ " Shima yana gama fa'din haka ya juya yafara tafiya, Teemah kam bayansa ta tsaya tana kallo tana kwa6a baki, mutun kullun kamar ghost be ta6a yin dariya. 'Dan 'karamin tsaki taja da ta tuna cewa duk da hakan da yakeyi bata san meyasa lokuta da dama takanji son ganisa ba duk da kuwa bawani abin kirki ke ha'da su ba amma zuciyarta na yawan janta zuwa tunaninsa ko son ganinsa. Kamar yanda yace 'din kuwa tana kaiwan wayan ta taho domin kawo masa ruwan tasa meshi tsaye yawani zuba hannaye acikin aljihun army green 'din wandon dake jikinsa. Ita kanta da ta shigo tayi mamakin yanda 'dakin yayi 'kura ko dan an kwana biyu ba ayi amfani dashi bane oho. Tana shirin fita daga 'dakin ya dakatar da ita da fa'din " _Zo ki kintsa min 'dakin nan_ _please_ " Waro idanu tayi waje idanunta har ya fara tara hawaye bata san ma lokacin da bakinta ya furta " _Yayah yanzu fah zamu fita mun gama shiryawa_ ! Gira ya 'dage zuwa sama yace " _So_ ? _Come on zo ki kintsa min 'daki, kwaje shopping 'din gobe in Allah ya kaimu_ " _Comment_ _Vote_ _Share_ (Ga duk me son farkon *CAPTAIN* *ABBAS* har zuwa inda aka tsaya should follow me a shafina wattpad @ *Serlmerh-md* *Salmerh ce*😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ~Dedicated 2 my family~ *Bismillahir rahmanir raheem* _*3 C’s of LIFE* : Choice, Chance & Change – You must make a choice to take a chance or your life will never change._ 🅿 *72* 'Bangaren Hannah kuwa harta gama shirinta tafito bata ga Hannah ba sai ta yi gurin Ummah dan ganin ko tana can ne, amma kuma sai ta tarar da Ummah zaune ita ka'dai, tambayar Ummahn tayi tace " _Ummah ina Teemah fa ko de tagaji da jirana ta wuce abinta dan naga_ _yau zumu'di_ _takeji_ _dashi_ " Murmushi Ummah tayi tace kafin ma ta rufe bakinta sai Ummah tace mata " _Ta kaiwa Yayanku abin sha ne bari ta dawo_ " " _Yayah ya zo ne dama Ummah_ ? Hannah ta tambaya lokacin tana shirin zama agefen Ummah. Amsa ta bata da fa'din " _ehh be ma da'de da isowa ba yanzun nan ya shiga ciki, kije mana ku gaisa_ ". 'Dan 'karamin tsaki Hannah tayi tace " _barshi Ummah sai mun dawo kawai naje kafin nan ma kinga ai ya 'dan huta_ " 'Dan hira suka 'dan fara ta6awa da Ummahn kafin Teemah tazo, anan ne Ummah ke sanar da Hannah batun zuwan Mummy harma da Anty da Teemah tafa'da mata. Hannah tayi murna sosai har zuciyarta da jin cewa Mummy zata zo saboda ita kam tana son Mummy ko dan goya mata baya ma datake yi akan komai sa6anin na Anty data kya6e baki tace " _Allah ya kwaota lafiya_ " Teemah kuwa nacan tana aiki tana share hawaye, haushi gaba 'daya ya bi yacikata shima Abbas yana tsaye har yanzu be motsa ba har ta shiga tagama kintsa bedroom 'din ta wanke bathroom ta fito yana nan tsaye ,tasan cewa zefi fara bu'katan can 'din kafin parlour shiyasa tafara gyara cikin. Tana aikin takaici fal zuciyanta tarasa meke damunsa shi akullum yafi son yaga ya 'kuntatawa mutun in bahaka mi ye ruwansa da fitan su harda zai ce wani bazasu fita yau ba sai gobe, salon yanuna halinsa afili kawai, bayan gobe Mummy da Anty zasu zo shine kuma zata fita yawo? tama rasa me ya dawo dashi wallahi, mutum sai fitinan tsiya. Yana nan tsaye, yana tunanin yanda yaga yau duk ta canja tayi wani kyau na musamman da ita, duk da yake dama ita 'din me kyau ce amma na yau 'din na musamman ne, sai de har yanzu tana nan arame bata mai da jikinta nabaya ba. Hawayen da yaga take ta sharewa ne ya 'dan 'dauki hankalin sa sai ya fara bin duk wani moves 'dinta da idanu, gani yayi da gaske kuka takeyi da hawaye, alokacin ma barta kammala shara ta goge ko'ina saura goge center table 'din dake tsakiyan parlourn ne ka'dai yarage take kan yi, sai ya taka ahankali ya isa inda take. Hannunta ya kama ya mi'kar da ita tsaye sai kuma ya tsaya yana 'karewa cikin idanun nata kallo, 'kasa tayi da nata idanun jin gaba 'daya sun mata rauni, sam yanzu bata iya juran kallon tsakiyar idanunsa, intayi hakan kuwa jikinta har rawa yake 'dauka gaba 'daya, Yayah Abbas kwarjini yake yi mata sosai. Ko yanzun ma 'kasa tayi da nata idanun hawayenta na sake gangarowa ahankali. Da yatsan sa 'daya ya shafo hawayen nata sai ya sake nuna mata a saitin idanun ta wanda dolenta ta 'dago ta kalli yatsan daga nan ta 'dan kalle shi ka'dan, suna ha'da idanu sai shi ya sake bu'de nashi tare da 'dage gira sama da sauri tayi 'kasa da kanta ahankali yace " _dan nasaki aiki kike yin kuka_ ? Kai ta jijjiga masa alamar " _ah' ah_ " " _Toh menene_ ? Ya sake tambayarta. " _bakomai_ " Teemah ta bashi amsa ahankali. " _Ohh dan na hana fita yawo ne ko_ ...? Kafin ma ya rufe ba kinsa cikin shagwa6a66iyar siririyar muryarta ta tare shi da fa'din " _Na da'de fah Yayah banje ko'ina ba, kuma kullun ina son siyan abu_ _amma bana fita ko'ina, sai yau Ummah tace zamu ni da_ _Hannah...kuma...kuma_ ... Sai ta 'karashe da in-inah ta kasa 'karasawa illah sabon hawaye hawaye daya gangaro . Abbas ne ya 'karasa mata da fa'din " _Kuma sai na hana_ _ko_ ? Shiru tayi masa bata tanka ba, sai ta sake kwa6a fuska kawai. Abu 'daya ke sanyaya ranta idan ta tuna zata ga Mummynta shiyasa ma take 'danjin dama-dama. Abbas kam tsayawa yayi yana kallonta yarintarta na birge shi, komai nata ma shi birgeshi yake yi sai de kukan da takeyi 'din har zuciyarsa yake jin ciwonsa, tausayinta yaji ya kamashi, hakan yasa shi lowering voice 'dinsa yace mata " _banace gobe zakuje_ _ba_ ? Kai ta 'daga masa alamar " _ehh_ ". " _so why d tears_ ? Yayi maganar tare da 'dage gira 'daya. Cikin wani shagwa6an tace " _gobe fa Mummy zatazo, kuma banaso tazo bana nan_ " Murmushi yayi mata da jin wannan shirmen kuma sai yace mata " _kin fiye kwa6a ke kam,_ _angaya miki idan tazo 'din zata koma kafin ki dawo ne_ ? Jijjiga kai tayi. " _Toh oyah wipe all those tears ban son shirme_ " Fara share hawayen tayi da hannunta 'daya, sai ya 'dago 'dayan hannunsa ya fara tayata gogewa ahankali, yana gogewan yake fa'din, " _kar na 'kara ganin_ _hawayen nan kinji, idan bahaka ba naga kin sake yin wani kuka toh goben ma baza'a je_ _ko'ina ba kuma zance da Mummyn ma karta zo_ ...... Hannah ce ta iso da sallamarta da niyyar duba Teemah ganin lokaci na tafiya kuma tajita shiru. Cak ta tsaya tana mamaki ganin su tsaye daf da daf Kamar ze mai da ta cikinsa yana share mata hawaye. Abbas kam ko ajikinsa sallamar Hannah kawai ya amsa tare da 'dauke hannunsa daga kan fuskar ya yi kamar babu abinda yayi. " _Ina yini Yayah_ " Hannah ta fa'di tare da kawar da kanta gefe. Da " _lafiya_ " kawai ya amsata daga nan ya juya ya shige cikiabinsa, itama Hannah bata damu ba dama tasan iya amsar dazata samu kenan dan haka sai ta nufi gurin da Teemah ke tsaye da sauri ganin ta wata iri. Hannunta takama taja ta suka nufi hanyar fita, sai da suka 'danyi nisa da 'dakin nasa kafin Hannah ta tsaya ta tambaye ta cewa " _me Yayah yake miki afuskarki yau kuma_ ? Bata bata amsar tambayar taba sai tace " _Yayah yace wai ba zamu fita yau ba, sai de gobe_ " Duk da taji haushi sosai da jin abinda ya fa'da 'din amma ita bashi take son ji ba dan haka sai tace " _that a side Teemah bani amsar tambayata_ " Shiru Teemah tayi mata dan bata san me zata ce mata ba,tace da hawayen ta ya goge mata ko kuma tace me? Juyawa Teemah tayi ta nufi hanyar 'dakinsu. Shan gabanta Hannah tayi tace " _to shikenan tsaya,_ _wai dagaske cewa yayi bazamu_ _ba_ ? Cikin sanyin murya tace " _Dagaske ne mana Hannah zan miki karyane_ "! Hannah cewa tayi " _Toh shi dama baya zo ba sai ya damu mutun, sarkin kwafsi ai nasan ze aikata tunda naga kin da'de baki dawo ba sai dana ayyanah, Allah Yayah ya cika bada mutun wallahi, sai dana gama 'daga wa kaina hankali nagama shiri ina murnar zan kaiki kiga gari shine ya hana kuma_ " 'Dakinsu suka koma ko wajen Ummah basu kuma zuwa ba. sai can da Ummah taga shirun yayi yawane shine tafito dubasu. Direct 'dakin Abbas ta nufa dan tayi zaton ko shi yari'kesu. Koda ta isa 'dakin nasa zaune tasame shi akan cujera ya na duba system 'dinsa ganinta yasa shi 'dago kansa zuwa kallonta. Ummah kam ganin ko'ina fes sai tayi mamakin yaushe kuma aka gyara shi, atake ta tuna ashe fa ba'a gyara 'dakin ba shaf ta manta wallahi, wata'kila akan aikin yari'ke min yarinya. Kauda zancen tayi ta jefa masa tamabayar " _ina yaran nawa suke_ ? " _Ummah ai sun da'de da barin nan_ " Mamaki tayi tace masa " kamu su wani abin 'kila dan nasa haka banza bazan ji shiru har haka ba" Murmushi yayi yace mata " _toh ni me zan musu Ummah_ ? Tace " _Ni da kai ne ai idan_ _naji wani abu_ " Be yi magana ba kawai ya sunkuyar da kansa yana murmushi da jin maganar Ummahn. Ahankali Ummah tace " _ya bangansu ba toh, bari dai_ _induba ko suna 'daki_ " Tayi maganar tare da juyawa ta koma zuwa dakinsu. Tana tafiyar take tunanin kardai tafiya sukayi batare da sun mata sallama ba, in kuwa haka ne tasan duk tsirin Hannah ne. Tura 'kofar Ummah tayi ta ri'ke ahannunta batare da ta 'karasa ciki ba ganin kowa na sabganshi a'dakin tamkar sun manta da batun fitan da zasuyin gashi har yamma ta kawo kai basu tafi ba. Sukuwa 'karan bu'de 'kofan ne yasa dukkansu hankalinsu ya kai gurin 'kofar afirgice domin basuyi zaton mutun ba sai suka ga ashe Ummah ce Cewa tayi " _har kunje kun dawo ne_ ? Hannah ce tayi saurin bata amsa da fa'din " _ba Yayah ya hana mu ba, wai sai gobe zamu_ " Murmushi Ummah tayi cikin nuna halin ko'in kula tace " _toh Allah_ _ya kaimu goben_ "! Zaburowa Hannah tayi tace " _haba Ummah kema haka zaki ce kuma?_ " _Toh me kike so in ce Hannah bayan lokacin daya hana ku fitan baku zo kun sameni ba, yanzu da lokaci ya 'kure kuma me zance in banda Allah ya kaimu goben_ "! Kwafa Hannah tayi tace " _Allah Yayah yaban haushi Ummah, kuma fah shi ya ri'ke Teemah da aiki har sai da yaga_ _lokaci ya 'kure tukunna_ " Teemah kam ko 'kala bata ce ba dan kwata-kwata ma bata san me zata furta ba ita. 'Karasowa ciki Ummah tayi ta zauna akan stool 'din dressing mirror sannan ta dubesu tace. " _kuyi ha'kuri ai inda rai gaben ma kamar yau ne karku damu kunji?_ Kallonta ta mayar kan Teemah tace _Fateemah kiyi ha'kuri kinji halin Yayan naku ne_ _sai a hankali_ " Murmushi Teemah tayi itama ta sunkuyar da kai 'kasa yanzun bata jin yin magana ne. ***** Washe gari kuwa dawuri suka gama shirin su tun 11am, saboda su samu su sake sosai sun gama tsara cewa yau 'din sai sun sha yawo sosai kafin su dawo duk da suna tsammanin ayau 'din bazasu fasa ba. Hannah ce ma data tsaya waya da Bilal ita ce ta 'dan 6ata musu lokaci, dan Bilal baya 'kasar shi kuma ba ko da yaushe suke samun damar yin waya ba sai lokaci zuwa lokaci saboda abubuwan dake gabansa hakan yasa duk lokacin da ya 'kirata hirarsu bata yankewa da wuri, Teemah haushi kamar ta 'kwace wayar ta jefar ganin har kwalliyarsu na shirin dusashewa amma basu fita ba, musamman idan taji yanda Hannah ke 'ko'karin lan'kwashe muryarta idan tana waya da Bilal 'din sai haushin Hannah ma ya 'kara kamata tace ai duk da laifinta ma tunda take biyeshi gashi sai 6ata musu lokaci yake abanza. Ba ita ta 'kare wayar ba sai 11:28am wanda tana cire wayar akunnanta Teemah taja tsaki tare da banka mata harara. Hannah murmushi tayi tace mata " _ya haka ne 'yan mata, let me be please ko dan ke baki san so ba ko? yes na_ _tabbata hakane, shiyasa ma naga kike wani banka_ _min harara..._ " Dakatar da ita Teemah tayi cikin jin haushi da fa'din " _ban san so ba kika_ _ce_ ? _Karki manta fah har aure nayi kinga kuwa 'karshen sanin so kenan ko_ " Dariya ka'dan Hannah tayi idanunta akan wayarta tace " _wancan ai is different, aure kikayi amma ba soyayya ba, na tabbata duk ranar da soyayya ta kamaki zaki gane cewa nawa wasa ne, wancen auren kin ai bashi da bambanci da babu,_ _ehh toh kuma, bansani ba kam ko kafin ya rasu ya koya miki soyayyar shi, kuma fah ba mamaki dan yanda naga kika_ _rin'ka kuka kina damuwa da rashin san nan ze yiwu son mijin naki ke damunki......._ Mi'kewa tsaye Teemah tayi tace " _Ya isa dan Allah Hannah kitashi mutafi ni surutun ya ishe ni haka_ " Tayi maganar tana 'ko'karin 'daukar mayafinta. Ganin ko motsi Hannah batayi ba yasa Teemah taja tsaki ka'dan tace " _Haba dan Allah kina gani ko Hannah lokaci na tafiya salan Yayah ya sake hanamu fita ko me_ ? Tana gama fadin haka ta nufi gaban mirror tasake duba jikinta ganin batada matsala yasa ta dauki turare kawai tasake feshe jikinta dashi. Sai lokacin Hannah kuma ta ajiye wayar tata ta sau'ka a agadon tana dariya tare da fa'din " _da kin barni na fa'di gaskiya ai yarinya_ " Juyawa Teemah tayi tace " _Ni dai muje dan_ _Allah, inkin gama ki sameni wajen Ummah._ " Teemah ta fa'di tare da barin 'dakin gaba daya. Hannah kam Teemah na fita ta janyo wayarta tacigaba da chat 'din da takeyi da Bilal. Tana isa parloun ta hango Ummah zaune akan kujera nesa ka'dan da kujerar dake gefenta kuma Yayah Abbas ne zaune suna 'dan hira. Kallo 'daya Teemah tayi masa sai ta 'dauke kanta, sanye yake cikin black trouser da wata longslip ash colour me zanen ba'ki layi-layi ajiki, sosai kayan sukayi masa kyau suka kar6eshi. Kirjinta taji yana bugawa wanda hakan yayi sanadin rage mata speed 'din tafiyarta, ahankali ta 'karaso har inda suke 'din ta zauna gefen Ummah, sai da ta iso ma sannan taji mahaukacin 'kamshin turarensa mai da'di ya bigi hancinta, daya ha'du da nata 'kamshin kuwa sai ya riki'de ya bada wani 'kamshi me 'kayatarwa, Ummah ce ka'dai zatayi iya bayyana hakan saboda ita ce atsakaninsu. Abbas kam yi yayi kamar be ganta ba, amma Allah ne ka'dai yasan yanda zuciyarsa ta yaba da yarinyar, sosai yaga zallan kyaun ta ayau 'din dan purple atamfar data saka ba 'karamin fito da ita yayi ba. " _Har kun gama_ _shiryawa ne_ ? Ummah ta tambayeta bayan ta maida dukkan hankalinta zuwa ga Teemah. Kai Teemah ta 'daga mata alamar " _ehh_ " Kasancewar sun gaisa da Ummahn dasafe Abbas ne kawai basu gaisa ba dan shi ba'a zuwa 'dakinsa haka kawai dan gaisuwa idan ba shine yanemi mutun ba toh sai de inya fito ka gaisheshi, hakan yasa ta 'dan 'dago kanta ka'dan tace " _ina kwana Yayah_ ! Be amsa ba sai da ya 'dago shima ya kalleta kafin ya amsa da fa'din " _lafiya 'kalau_ ." Bata 'kara wata gaisuwar ba dan tasan ko tayi ma ba sake amsata zaiyi ba. Abbas kam yanzu kasa 'dauke idanunsa yayi akanta Allah ma sai ya taimakeshi Ummah ba shi take kallo ba hankalinta nakan Teemah ne, Teemahn kuwa kanta na kasa shiyasa ma yasamu chance 'din kare mata kallo hankalinsa kwance. " _Dan Allah Fateemah inkun je_ _karki biyewa Hannah kinji, nasanta iyayi gareta gashi inta fita shopping tana da'dewa kafin ta dawo kamar zata na'do komai pls_ _karki biyeta Fateemah ku dawo_ _da wuri kinji Antynki ma tana hanya yau zata zo_ ? Ummah ce tayi maganar cikin sigar lallami. Kai Teemah ta 'daga mata alamar " _toh_ " Tana murmushi dajin cewa Anty na hanya sai de gaba 'daya jitake ta takura da zaman, hakan yasata lafewa ajikin Ummah kamar wata 'yar yarinya 'karama. Muryar Abbas suka jiyo yana fa'din " _wai Ummah ina zasu ne ba fah na son yawon nan ni_ " 'Dagowa Teemah tayi da mamaki ta kalleshi suna ha'da idanu kuwa sai ta kauda kanta gefe tare da turo baki aranta tace _lallai ma Yayan nan, bacin shine jiya ya hanamu fita yace sai yau kuma da_ _yau 'din tayi sai_ _yawani ce be san da_ _zancen ba_ . Ummah tariga tasan halinsa na nuna ko'in kula akan abubuwa shiyasa ma bata meda zancen baya ba duk da tasan yasan da batun fitan amma sai kawai tace masa " _Shopping zasu je ko_ _zaka kaimin_ _su_ " " _Ni kuma Ummah? Inada inda zani fah_ " " _Nasani ai Abbas naga akn hanya shiyasa_ " ummah ce ta fa'di hakan tana kallonsa. Yana so yace ina driver amma sai yaji bakinsa yayi masa nawi, kawai sai ya koma baya ya ha'da jikinsa da jikin kujera yayi wa Ummahn shiru, minti 'daya be cika ba sai ga Hannah ta fito cikin 'dan sauri-sauri ta nufo su. Sai da ta gaida Yayan kafin tace da Teemah su tafi. Dayake alraedy Ummah ta sallame su inda ta tura ma Hannah ku'din shopping 'din a account bata basu cash ba. Tashi Teemah tayi suka yiwa Ummah sallama , Ummah nata yi musu addu'ar Allah ya bada sa'a suka amsa da (Ameen) kafin suka nufi 'kofar fita. Abbas ma tashi yayi ya bi bayansu yana wannan 'kasaitacciyar tafiyar nan tasa me birgewa. Ahanya yazo ya wuche su Teemah nayi mata gulmar wai shi ai zai kaisu. Haushin ha'da su da Ummah tayi Hannah taji dan tasan ba barinsu zaiyi su sake ba. Koda suka isa jikin motar ma Hannah 'kin shiga gaba tayi dan har yanzu basu gama da Bilal ba chat sukeyi dashi shiyasa ma bata son shiga gaban don tsoro takeji kar Abbas ya kamata. Muhawara suka tsaya yi dan Teemah ma 'kin shiga gaba tayi sai da ya daka musu tsawa kafin kowa tayi saurin bu'dewa tashiga. Koda ya kai sun kuwa 'kin barin su yayi sai da yaga sun gama yabiya ku'din kafin yasako su agaba suka dawo gida. Shopping sosai sukayi dan suna da ishashshen ku'di a account 'din Hannah shiyasa ma suka saki ransu suka jidi tarkace harda na banza, cikin sa'a kuwa sai Abbas ma ya biya bill 'din. Koda suka isa gida kowa 'diban kayan yayi, Hannah ce tafara 'diba ta wuche ciki, koda Teemah ta 'diba ta fara tafiya kuwa kasawa tayi sai da ta ajiye dan wanda Hannah ta bar mata sunfi yawa. Numfashi take sau'kewa ahankali tana watsa hannu ga dukkan alamu zafi suke mata. Tana 'ko'karin sake 'dauka ta tsinkayo muryarsa yana fa'din " _idan bazaki iya ba dole sai kin 'dauka duka lokaci 'daya ne_ ? Sai lokacin ma tunanin hakan yazo mata dan haka sai ta raba kayan ta 'dauki ka'dan ta nufi ciki inda ta bar sauran awurin akan inta dawo ta 'karasa 'dauka. Tana cikin tafiya taga yazo ya wuche ta hannunsa da ragowar kayan, bin bayansa tayi sai ya kasance kusan tare tafiyar tasu take. Yana shiga parloun kuwa itama ta 6ullo sai ya kasance atare suka shigo. Anty na saitin 'kofa ne dan haka ita tafara ganinsu take kuwa taga dacewar kasancewarsu a inuwa 'daya, zata so Fateemahn tasamu jajirtaccen namiji irin Abbas wanda zai kula da rayuwarta ba kamar yanda ta so cin zarafinta abaya ba. Teemah na shigowa idanunta kan Anty ya sau'ka ai bata san lokacin data sake kayan ta nufe ta da gudu ba ta fa'da jikinta. Abbas bin ta yayi da kallo yana mamakin hakan kuma, wanda sai alokacin shi kuma ya hango abinda yasa Teemahn gudu. Ahankali ya 'karaso bayan yayi 'ko'karin danne ba'kin cikinsa ya yi mata barka da zuwa sannan ya ajiye kayan su Teemah ya shige ciki. Anty bakinta kamar gonar auduga ganin Fateemah ta warware. " _Anty dagaske dama ashe zaki zo_ ? Ta tambaya tana dariya. Antyn ma dariyar tayi tace " _zanzo mana Fateemah bani na fa'da miki ba_ " " _Mummy ma tace zata zo ai itama_ " Cewar Teemah Washe baki Anty tayi tace " _Allah ya kawota lafiya ashe shiyasa naga bakinki ya'ki rufuwa duk murnar za'a ga Mummy ne?_ " Dariya dukkansu suka sanya har Ummah Teemah ce ta 'karasa da fa'din " _harda kema ai Anty_ " Bayan sun gama dariyar ne Ummah tayi mata bayanin cewa ai Mummyn ba yau zata taso ba sai zuwa gobe in Allah ya kaimu. Hannah kam tuntuni ta shige ciki tunda ta gaida Antyn tayi shigewar ta dayake dama ita bason matar takeyi ba. Ranar kam Fateemah murna kamar ta tashi sama dan taga Antyn ta. Awurinta ta wuni tabi tacika ta surutu har yamma suna tare da 'kyar Ummah ta korata dan Antyn ta samu ta 'dan huta. Da daren ranar Daddyn Abuja ya dawo, Abbas kam beji da'din haka ba danshi tsoron ha'duwa dashi yakeyi dama kafin yazo ma sai da ya tabbatar baya gari kafin ya zo ashe ma yakusan dawowa. Daya san haka kuwa da ya koma abinsa tun da safe. Ai kuwa da daren ya gama shirinsa da sassafe ya fito yaje ya gaida daddyn yayi masa sallama. Daddy yariga ya fahimce shi ayanzu be 6oye ba kuwa yace masa " _wato kana guduna ne ko Abbas_ ? 'kasa yayi da kansa yace " _ah ah Daddy bahaka bane dama yau 'din na shirya komawa_ " Daddyn ma ce masa yayi " _Toh ba komai, Allah ya bada sa'a amma karka manta kadawo da wuri domin nextweek za'a 'daura auren ka nariga nagama shirya komai ranar kawai ake jira tazo, sai ka fara shiri_ ". _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce*😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ~Dedicated to my~ ❤ *Bismillahir rahmanir raheem* _Do not think about the past..... Accept the Present..... Think for the Future....nd face tomorrow with a sweet and beautiful smile._ 🅿 *73* Abbas a firgice ya 'dago idanunsa ya sau'ke su akan Daddy, Daddy kam ko ajikinsa dan yana gama fa'din abinda ze fa'da ya shige ciki. Motsi me kyau Abbas kasawa yayi sai de yabi bayan Daddy da kallo da idanunsa da suka gama riki'de wa zuwa ja, har ya shige cikin kuwa Abbas be daina kallon 'kofar ba tsawon mintina biyar kafin ya tashi ahankali 'kafafunsa ma nauyi suka masa da 'kyar yake 'daga su ya nufi 6angaren Ummah. Zuciyarsa ce kawai ke beating da 'karfi ajikinsa bayaga haka kuwa gaba 'daya jikinsa yayi sanyi 'kalau. Fasa zuwa wurin Ummah dan yi mata sallamar yayi kawai sai ya wuce 'dakin sa ya zauna a kujera tare da dafe kansa. Tsawon mintina yana a haka shi ka'dai yasan me yake ji azuciyarsa baya fatan abinda Daddy ya fa'da ya kasance gaskiya, aure!......aure kuma da waye haka toh? Yana jin wannan karan kam ba ze sake yin saken da zata ta kubce masa ba, ba ze 'ki yiwa Daddy biyayya ba amma shima zai auri za6insa koda daga baya ne. Su Teemah ne yau a kitchen suna aikin breakfast ita da Hannah, sunayi suna 'dan ta6a hira inda duk hirar tasu Hannah ce 'kwa'kulo ta wani lokaci har fa'da sukeyi in maganar Hannah ya bawa Teemah haushi garin haka ruwan zafin jikin marfin tukunya ya zuba wa Hannah a 'kafarta. Tare da su Ummah da Anty suka ci breakfast 'din, bayan gamawar su ne Ummah ta 'dauki na Daddy tace zata kai masa, Anty ne tace da su Hannah sukai na Yayansu ma tun da be fito an karya dashi ba, take Ummah ta hana tace abarshi yanzu akaran banza zai koro min yara na tace abari sai yazo dakan sa dan baya son ana damunsa idan yana 'dakinsa, dayake bata san da batun tafiyar sa ba. Koda takai na Daddyn kuwa ta same shi ne yana amsa waya hakan yasa ta gama harha'da masa kafin ya kare wayar ta kawo center table ta ajiye masa agabansa, dan tasan shi be fiya cin brekfast akan dinning ba. Yana sau'ke wayar kuwa yace mata " ' _danki ya wuche ko?_ Da mamaki tace masa " _wani 'dan kuma Alhaji?_ Tea cup 'din dake gaban sa ya 'dauka ya 'dan kur6a ka'dan sannan ya cire daga bakin sa ya kalle ta da kyau ya ce " _Abbas nake nufi!"_ Mamakinta kasa 6oyuwa yayi har sai da ta bu'di baki ta tambaye shi dalili dan kuwa daya zo be cemata zai koma so soon haka ba, bayaga haka ma ko sallama be je yayi mata ba haka kawai sai take jin bata yarda ya tafin ba. Anan daddy yayi mata bayanin komai dake faruwa yace " ' _kilan haushi na da yake ji ne ya shafeki kema shiyasa har ya wuche be sanar da ke ba, amma ni kam yazo yayi min sallama da sunan zai koma bakin aikinsa ni kuwa ban dakatar dashi ba"_ Ummah kam gaba 'daya kanta sai ya kulle da maganar Daddyn bata fahimci komai ba dan haka sai tace " _Alhaji haushin ka na me Abbas zaiji kuma, ko de akwai wani 6oyayyan_ _abinda yafaru ne da_ _bansani ba_ " Juya kai Daddy yayi tare da fa'din " _Ehh toh kusan zance hakane gaskiya, sai de wannan al'amarin daban ne, kinsan dama ina shan yawan yi masa batun aure while shi kuma baya so, toh ina ganin dalilin kenan da ya sa ko ha'duwa dani be son yi shiyasa daya ga na dawo jiya sai shi kuma ya shirya komawa ayau, lokacin daya zo min sallama ni kuma nasanar dashi hukuncin dana riga na yanke, wanda dama ko da be zo Abuja ba ni zansa shi yazo saboda dole ana bu'katarsa_ _domin auren sa za'a 'daura a sati me zuwa in Allah ya kaimu_ " Ummah kam wani banbara'kwai taji maganar tamkar amafarki cewa tayi " _haba, haba Alhaji aure kuma da gaggawa haka ba wani shiri kamar_ _wani abin sirri, gaskiya be kamata ba, meyasa baza kayi hakuri ka 'kara masa lokaci ba_ ? " _Nagaji da jiran lokacin nasa ne shiyasa nayi haka, ke kanki kin san mun dad'e muna fama dashi a kan maganar nan, ba sai na gaya miki ba, amma yaron nan baya ma saka zance na acikin al'amuransa ballantana ya bata muhimmanci, sanadin haka ma kina gani wasan 6uya ya fara dani, duba fa kigani jiya-jiya na zo gidan ga_ _amma dan ya nuna min halinsa yau da sassafe sai ya zo min da batun komawa, duk nasan manufar sa ai tunda ni ne na haife shi, har yaushe zan ta maimaita masa abu iri 'daya kullum?_ Kwantar da murya Ummah tayi ta ringa bashi ha'kuri dan taga kamar beji da'din abinda Abbas 'din ya masa ba amma sai Daddy ya dakatar da ita da fa'din " _ni ai banda matsala dashi yanzu, na riga na yanke decision 'din dana ga yayi min and bazan fasa ba, munyi magana da Yah Kabiru akan haka kuma Alhamdulillah nasamu ya amince amma fah da 'kyar dan kin san shima 'dan partyn Abbas ne, wai taya zance ya auri bazarawa bayan shi be ta6a zama da mace ba"_ Zaro idanu Ummah tayi akansa tace " _Yah subhanallah, me kakae shirin fa'da ne Alhaji? dan Allah Alhaji ka daina wannan maganar ai ko ni nan ba yadda zanyi ba inde har bazawara kake nufin zai fara aura, wallahi bazan ta6a goyon bayan hakan ba, kayiwa Allah Alhaji ka dakatar da wannan zancen, zanyi magana dashi insha Allahu cikin 'kan'kanin lokaci zai zo maka da_ _magana mai kyau_ ............" Kafa'da Daddy ya 'dage alamar wannan ba damuwar sa bace shi, sannan yace " _ai da zaiyi hakan da ya da'de dayi tun ma ba azo wannan_ _matakin ba daya da'de dayi tun abaya, kuma da_ _kike cewa wai bazawara menene....ki gaya min auren bazawaran haramun ne_ ? Dolenta ta jijjiga kanta domin tasan bata da hujjan haramtashi tunda annabin mu haka yayi. Duk da haka sai tace " _Amma dai Alhaji ka duba lamarin kaima dan Allah, dududu nawa Muhammad 'din yake ne har ayanzun fa be gama cika shekara talatin ba, amma kake ta faman damun kanka da batun yayi aure har yanzu fa yana da sauran lokaci......._ Taran ta yayi da fa'din " _Bazaki gane bane ke, nifa da kike gani zaman sa hakan nan 'din ne sam banso, musamman da ya kasance aikinsa na yawo ne, sosai na yadda da tarbiyar yarona kuma na bana zarginsa ,dalili ma kenan da ya sanya na ke so naga yana da iyalin kansa dan gudun_ _kar wata 6araka ta 6ullo daga baya shiyasa nake son taran ta da wuri_ , _dan Adam duk 'dan Adam ne, hankali na zaifi kwanciya sosai idan ya_ _kasance yana_ _da iyali_ " Kauda kai Ummah tayi gefe dan ta lura Daddyn ba canja ra'ayi zaiyi ba sai tace " _Toh Alhaji in kuma iyalin ne dole sai ya kasance bazawara_ ? 'Dan 6ata rai Daddy yayi ka'dan yace mata " _Kinsan banason musu ko_ ? Sai tace " _Kayi hakuri Alhaji_ " " _bana so na sake jin kin fa'di haka, inada iko akan yarana shiyasa na yanke hukunci, kuma nasan dukkansu zasu min biyayya, kuma babu fashi auren nan da iznin Allah sai anyishi, iin kuwa_ _har kikaga ba'a 'daura auren yaron nan da Fateemah ba to ikon Allah ne ka'dai_ _ya hana hakan faruwa_ " Shiru Ummah tayi tana juya zancen a 'kwa'kwalwarta dake cushe tab da tashin hankali, bata sake furta masa komai ganin kamar maganganun nata basu da wani amfani dan ga dukkan alamu wannan mutumin bashi da niyyan sauya ra'ayi, tsawon da'kiku tana ahaka yayin da da Daddy ke ta shan tea 'dinsa cikin kwanciyar hankali, can Ummah ta mi'ke tsaye jikinta sanyi 'kalau ta nufi hanyar barin 'dakin tare da fa'din " _Allah ya kyauta_ " Daf da zata fita ta tsinkayo muryarsa yana fa'din " _baki tambayi wacece yarinyar ba kike shirin tafiya kuma_ ? Juyowa tayi ta kalleshi sannan tace " _babu amfani ai tunda ba saninta nayi ba, sunan ta danaji ma ka'dai ya_ _isheni_ ........" Da sauri ya tare ta da fa'din " _who told u that jin sunan ta ka'dai ya ishe ki?, Fateemah ce fah , Fateemahn gidan_ _nan_ !" Ummah najin haka ta washe baki tace " _haba dan Allah Alhaji , gaskiya baka kyauta min ba Fateemah ce shine_ _kuma ka barni nake ta 6ata bakina abanza_ ? Murmushi Daddy ya mata yace " _yanzu kam ai kinji sai kuje ku fara shirye-shirye dan nasan ba'a rabaku da shi_ " Yana gama fa'din haka yaci gaba da cin abincin sa. Ummah ce ma ta 'kara fa'din " _Shirye- shirye sosai ma_ _kuwa_ " tare da barin 'dakin. Daga wurin Daddy Ummah direct 6angaren Abbas ta wuce, bata same shi a palournsa ba dan haka sai ta nufi ciki da sallamar ta inda tasame shi zaune abakin gado sanye da dogon wandon jeans da farin singlet , bazaka ta6a gane yanayin da yake ciki ba in ba kasani ba, sa6anin Ummah da suna ha'da idanu dashi ta fahimci ba dai-dai yake ba. Da sauri ta 'karasa kusa dashi ta 'kira sunanshi. Jin yanda tayi maganar ne ya sashi 'ka'kalo murmushin dole ya sanyawa fuskar sa tare da 'dagowa ya kalleta amma be tsawaita ba ya kauda kansa gefe dan ba ya son ta fahimci halin dayake ciki. Da 'kyar ya bu'di baki yace " _ina kwana Ummah_ ? Da " _lafiya 'kalau_ " ta amsa masa, kafin ta sake yin wata magana kuwa ya tareta da fa'din " _Ummah baki bari naje ba sai kika zo da kanki kuma_ ? Cewa tayi " _bakomai ai duk 'dayane_" sannan ta 'kara da fa'din " _u look tensed Abbas meke faruwa ne_ ? Abbas kansa ya shafa yace " _ba komai fah Ummah kawai na tashi da ciwon kai ne yau_ _'din_ " Tace " _Ahakan kuma da kace zaka hau hanya_ ? Shiru yayi mata beyi magana ba. Ummahn ma sai ta zauna a gefen sa tare da fa'din " _look Abbas, mahaifinka yagaya min cewa nextweek za'a 'daura aurenka, hakane ko_ ? Cemata yayi " _Haka nima haka yagaya min 'dazu_ " Tace " _good, kasan me nake so da kai_ ? 'Dagowa yayi kawai ya kalleta sai taci gaba da fa'din " _banson ka sanyawa raka damuwa da wannan batun balle har yayi affecting al'amuranka dan Allah, ni nan inada_ _tabbacin auren ka alkhairi ne Abbas kuma ha'din Allah ne, da izninsa kuwa bazaka ta6a yin kuka da Fateemah ba, zakaji da'din auranka insha Allahu domin na yadda da tarbiyar Fateemah 'dari bisa 'dari kuma kaima kanka shaida ne akan haka......."_ Tun anan kan Abbas ya fara yi masa nauyi be san wace Fateemah bace amma yanaji ajikinsa kamar ya santa. Har Ummah tagama surutunta ma be jiba hankalinsa duk ya 'dauku ga tunanin ko wacece yarinyar sai ya ji Ummah na sake fa'din "......... _please ka cire damuwar nan aranka kaji_ ? Ahankali bakinsa ya furta " _insha Allahu_ " Dan be san me ze ce da Ummah ba bayaga haka. Ummah kam tashi tayi tsaye tana fa'din " _yauwa babana Allah ubangiji ya albarkakaci rayuwarku gaba 'daya ya sanya haske cikin al'amuranku"_ Da " _Ameen-Ameen_ " ya amsa mata. Daga nan tayi hanyar fita tana fa'din " _yaran nan zasu kawo maka breakfast 'dinka yanzu sai ka samu ka 'dan ta6a please ko ka'danne_ " Shikam yanzu ba breakfast bane damuwar sa maganganun Ummah ne ke masa yawo a 'kwa'kwalwa, so yake yasan wacce Fateemah ce haka da har mahaifiyarsa ma da kanta ta yadda da ita har kuma take ikirarin shima shaida ne akan halinta haka?. Wani sanyi yaji ya lullu6eshi tare da ratsawa har cikin zuciyarsa wanda hakan ya sashi lumshe idanu. Be san wacce yarinya bace amma ji yayi zuciyar sa tayi na'am da batun auren nata, azahiri kuwa sam bahaka bane domin 'kwakwalwar sa bata daidaita ba har yanzu yakasa tantance yanayin da ya shiga, yafi so ya san yarinyar kafin komai yabiyo baya, Ummah yakamata ya tambaya amma yakasa aikata hakan yana gani harta tayi tafiyarta. Tunda Ummah tafa'di sunan yarinyar ya 'danji dai-dai damuwar sa kaso hamsin duk ya kau, natsuwa yaji ya 'dan shige shi ka'dan da be san dalili ba, shi kansa yana so yaji da'din auransa kamar yadda Ummah tayi masa fata sai de kafin hakan ya kamata yasan yarinyar tukunna. ***** ' Bangaren Mummy kuwa yau ta gama duk wani shirin ta na shigowa Naija, dama tun jiya taso ta taho amma wani sabon al'amari data ji daga bakin Daddyn Teemah sai yasa ta fasawa a jiyan kawai ta shiga kasuwa ta bugo siyayya na fitan hankali sai yau ne take shirin tahowa da 6oyayyen farin cikinta azuci da Daddy ne ka'dai yasan tana ciki. Sun rabu da Daddy akan shima yana bayanta nan da 'yan kwanaki, da kansa shine ma ya rakata airport har se dayaga tashin su kafin ya koma gida. Abbas na zaune har yanzu abakin gadon motsin kirki ma bayayi kamar an dasashi, ringing 'din wayarsa da yajiyo a parlour ne ya fargar dashi amma be ko motsa ba balle ya je ga wayar tasa. Sai da yasake jin ringing karo na biyu kafin ya tashi tare da yin tsaki ka'dan dan shi ayanzu besan damuwa wanda yake ciki ma ka'dai yana jin ya isheshi. Ganin sunan B-Daddy da yayi akan fuskar wayar ne yasashi 'dagawa da sauri amma kafin yayi receive har 'kiran ya yanke dan haka sai yabi bayan 'kiran tare da zama akan 'daya daga cikin kujerun 'dakin, ringing 'daya na biyu Daddy ya 'dauka Abbas ne yayi saurin yi masa sallama. Daddy ma amsawa yayi daga 'dayan 6angaren tare da fa'din " _na 'kira baka 'daga ba_ ? " _Afuwan Daddy bana kusa ne wallahi_ " Ya 'kara da fa'din " _Daddy kana can ana shirin yimin aure ba shiri_ ? Murmushi Daddy yayi jin ya maida abin kamar wasa bayan acikin muryarsa ma zaka fahimci 'kuncin dake tattare da shi. Yace masa " _Nima haka sama ta ka labarin yazo min, Hassan ne ya 'ka'kabo mana_ , _nayi 'ko'karin hana dan ban goyi bayan al'amarin ba amma Hassan ya dage 'karshe dole sai da na amince, amma karka damu amince wata ba yana nufin tauye maka hakki_ _bane ni nan ina tare da kai, ya ake ciki gaya min yanzu, ra'ayinka dama na 'kira inji idan kayi na'am toh shikenan sai in kar6a maka in kuwa kaga baka so toh feel free ka sanar dani babu wanda ya isa yayi_ _maka dole matu'kar ina numfashi, karka damu da cewa Fateemah jinina ce ita bandamu ba_ _dan nima ha'din be birge ni ba, dan kaga ita ta ta6a yin aure sa6anin kai, ni sam banga dacewa_ _anan ba..........."_ Dai-dai nan Abbas ya dakatar da shi da fa'din " _Daddy_ .....!" " _Ya akayi, sanar dani karka damu_ " Daddyn ya sake fa'da masa. Be san me ze ce ba dan haka sai ya yanke 'kiran kawai yana murmushi, komawa yayi da baya bayan ya sar'ka hannayen sa biyu cikin junan su tare da maida su 'kar'kashin kansa yayi pillow dasu, idanunsa na kallon cielling 'din 'dakin kamar me karanta wani abu ajiki, daga bayane ya lumshe idanun sa maganar Ummah ce ta dawo kansa " _.....da izninsa kuwa bazaka yi kuka da Fateemah ba, zakaji da'din auranka insha Allahu_ " Wani farin ciki yakeji yana lullu6e shi, kamar a mafarki wai yau auransa da Fateemah saura 1week, jiyake kamar bashi ba, finally burin sa na gab da cika cikin sau'ki batare da ya wahal da ransa ba. ***** A can parlour kuwa har yanzu Ummah nata dramma da yaranta akan kawowa Abbas breakfast. Farko Hannah akace ta kai masa take kuwa tace " _Ummah nafa 'kone da ruwan zafi a'kafata 'dazu da muna kitchen kuma zafi yake min,_ _Teemah ta kai masa please_ " Hannah na maganar ne tana satan kallon Teemah afakaice. Juyawa Ummah tayi ta kallo Teemah ta tambayeta wai dagaske ne Hannah ta 'kona 'kafarta akitchen 'dazu? " _Dagaske ne Ummah amma ai ka'dan ne fah kawai bata son zuwa ne_ "! Ummah cewa tayi Hannah ta nuna mata gurin ta gani tukun na. Sai Hannah ta nuna wani guri daya 'danyi ja ka'dan. Ummah ma cewa tayi ai wannan ba ze hana ta tafiya ba dan haka maza ta tashi ta ha'da ta kai masa yana can har yanzu bakomai acikinsa. Rigima Hannah tafara irin na shagwa6a66u kamar gaske wai ita zafi waye-waye. Anty na murmushi ta 'dan juyo ta kalli Teemah tace " _yi ha'kuri kinji mamana daure ki kai masa ki dawo tunda yau 'din_ _'kafarta na ciwo_ " Turo baki Teemah tayi tace " _Allah Anty ruwan fah 'diga kawai yayi...."_ Tare ta Anty tayi da fa'din " _bana ce kiyi ha'kuri ba! maza tashi kije kinji_ " Tsaye Teemah ta mi'kewa tana bankawa Hannah harara da har yanzu dramar su da Ummah be kare ba, afakaice ta yiwa Teemah gwalo ganin ita zata kai. Teemahn ce ka'dai tagani takuwa 'kara sha'ka har wuyanta tare da jin matsanancin haushi . Aranta tace " _zan rama ai_ " Da Ummah taga ta ha'da masa kuwa ta ringa saka mata albarka tana 'karawa, duk da haushin da take ciki amma bakinta be kasa amsawa da _AMEEN_ ba. Tana tafiyar take tuna iskancin interview 'din da Hannah taringa yimata 'dazu a kitchen ita adole sai taji abinda yafaru jiya tsakanin ta da Yayah, tasan yanzun ma iya shege ne kawai bawani ciwo daya dameta. Abbas kam jiyake kamar idan yaci gaba da zama agarin nan toh kowa ma zai iya fahimtar yanayin farin cikin dayake ciki, dan haka take ya yanke shawaran gara ya tafi kawai tunda yanzu yanada tabbacin mallakarta inyaso sai ya dawo lokacin auren. Dama already kominsa a ha'de yake dan dama da niyyar tafiyan ya kwana,maganar daddy ne ya dakatar dashi, yanzu kuwa da ya san cewa za6in Daddyn cikar farin cikinsa ne ai shikenan, da yake dama shi ba ya yin tafiya da kayan sawa in dai tsakanin Abuja da Rivers ne sai de kayan da yasan zasu masa amfani, dangin su wayoyi, system da sauransu. Acikin wata jaka kalar Army green ya ha'da komai, Rigarsa daya cire 'dazu bayan ya dawo daga gurin Daddyn sa ita ya maida jikinsa tare da 'daukan jakan ya rataya akafa'dan sa ya nufo palour. Teemah na isa 'dakin ta tarar dashi tsaye agurin switch yana 'ko'karin kashewa, kafa'dar sa rataye da jaka sallamarta ne ya dakatar dashi sai ya juyo ya zuba mata idanu bayan ya amsa sallamar tata. Itama bata ajiye abin hannunta ba sai ta ri'ke tare da yin 'kasa da kanta tace " _ina kwana_ _Yayah_ ! Be amsa ba sai ya tako ahankali zuwa inda take tsayen ya jefa mata tambayar " _Yau kuma fushin me kike yi? Me ya sameki_ ? _Ya tambayeta tare da tsare ta_ _idanunsa masu rikitata gaba 'daya_ . Jikinta har na rawa saboda irin kallon daya ke binta dashi. 'Kasa-'kasa ta amsa da " _bakomai_ " Juyawa yayi ya koma gurin switch 'din da be kashe ba 'dazun, yana kashewa kuwa take 'dakin ya dawo duhu ba'ki'kirin. Sannan ya mi'ka hannu ya kakkashe conditioners ma gaba 'daya daga nan ya sake dawowa inda take tsaye. Yanzun kam da hasken 'dakin ya ragu har 'daga kanta tayi ka'dan ta kalleshi sannan ta kauda idanunta gefe. " _Kunyi magana da Daddy ne_ ? Jijjiga kai tayi sannan ta furta " _ah' ah_ " " _Okay ba matsala, amma make sure that baki tsallake duk wani umarninsa_ _ba koda bana nan, and ki daina fushin nan haka abincin ne bakyaso ki kawo_ _min ko kuma menene_ ? Afirgice ta 'daga idanu ta kalleshi, hakan kuwa datayi sai yasa shi saurin fahimtar ya harbo jirgin ta, zuwa inda yake ne bata so. Murmushi yayi sai yace " _Yes, ai nasan halinki baki ta6a appreciating yin wata hidima agareni ba, nima ban son abincin ki koma da abinki am ok na hutar dake_ " Cikin shagwa6a tace " _bahaka bane fa Yayah!_ Jakar dake kafa'dansa ya gyara Sannan yace " _toh menene gaya min naji_ " " _Ni....ni...nifah_ .... Kame-kame ta hauyi ta rasa takamamman abin fa'da. Murmushi Abbas yayi yace mata _"maganata gaskiya ce kenan_ ? Yana gama fa'din haka ya juya zuwa 'kofa a hankali. Teemah kam baki ta tura tabi bayansa da kallo. Har ya kusan rabin 'dakin sai kuma yajuyo ya sake kallanta yace " _ki saki ranki ki daina fushin nan kin manta yau Mummy na hanya_ _ko_ ? Da kai ta bashi amsa sai yaci gaba da fa'din " _kinga nima yau ina cikin farin ciki kema ki tayani kinji_ "? " _Uhmm_ " Tace masa Shi kuma yasake fa'din " _natafi_ " " _Allah ya tsare_ " Tace ahankali shima asaman la66ansa ya amsa da " _Ameen_ ". Daga nan yafice abinsa be sake juyowa ba. Teemah ma tsayuwa taci gaba da yi agurin tama rasa mai ke damunta, jitake kamar tafiyar tasa ne bata so amma sam tarasa dalilin hakan, yau ka'dai sai taji tamkar zatayi missing 'dinsa idan ya tafi. Komawa tayi kitchen ta ajiye kayan kafin ta wuche 'dakinsu ta kwanta agado tayi luf abinta. Hannah ma a 'dakin ta sameta wanda barinta gun su Ummah kenan bayan wuchewar Abbas. Tana barin gurin su, Ummah ta bawa Anty labarin abinda ke faruwa. _Comment_ _Vote_ _Share_ *Ur comments are gating very low gaskiya kuma banajin da'din hakan harga Allah.* ~Mabiya Labarin *CAPTAIN ABBAS* kuyi min uzuri najina da kukayi shiru kwana biyu abubuwa ne sukayi yi min yawa amma yanzu kam insha Allahu nadawo da 'kafafuna, insha Allahu zaku rin'ka jina akan lokaci.~ *Salmerh ce*😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated 2 my_ ❤ *Bismillahir rahmanir raheem* _Silence is the best answer of all questions nd Smile is the best reaction in all situations............ Unfortunately both never help in VIVA & INTERVIEW_ . 🅿 *74* Anty taji da'din hakan sosai tace kamar an shiga ranta anga ni, dama ita ta jima da ganin dacewar hakan, tace ai kuwa zama be kama ta ba, shiri ne gagarumi ya kusanto ta dan ma abin yazo a 'kurarren lokaci ne in ba dan haka ba ai da bikin sai ya zama bikin 'yar gata wanda aka da'de ba'ayi irinsa ba, duk da haka de tace bazatayi 'kasa agwiba dole ne tafitar da 'yarta yanda zata zama abin kwatance. Ummah ce ta dakatar mata da tunaninta ta hanyar shigo da 'korafi akan rashin sanar da Fateemah da Daddy be yi ba inda tace da Anty " Sai de ina ganin kamar fa ba'a kyautawa yarinyar ba, saboda bada yaddan ta mahaifinsu ya yanke wannan hukuncin ba, ina tsoron kar a shiga hakkinta sosai dan kinsan yanzu tana da daman da zata za6i miji da kanta ba sai an za6a mata ba musulunci ne dakansa ya bata wannan damar, duk da cewa za6a matan ma ba haramun bane amma naso da an nemi yardan ta tukunna" Murmushi Anty tayi tace " karki damu da wannan dan Allah, ni nan nasan halin Fateemah bazata ta6a yin musu ba, shima mahaifin nasu yana da tabbaci akanta ne shiyasa kika ga ya yanke hukuncinsa kai tsaye batare da wata fargaba ba saboda yasan dukkan su zasu yi masa biyayya shiyasa be damu ba, kuma yawanci idan kinga mace tayi jayayya da iyatenta akan maganar aure toh already zaki samu tana da wani me daban, Fateemah kuwa ai nasan bata da wani manemi daban ko akwai? Anty ta ta'karasa maganar tata da tambaya. Jijjiga kawai Ummah tayi tace " Bana tunanain haka gaskiya" "Toh kin gani, insha Allahu bazata damu koda ta damun ma zata sakko da yaddar ubangiji" Shiru Ummah tayi tana tunani aranta, ita aganinta duk da haka ya kamata Teemah tasan me ake ciki, kafin lokaci yazo ya 'kure yakamata aji nata ra'ayin, ita Ummah 'daukan alhaki ne take tsoro shiyasa ma ta damu sosai, wanda tunanin nan yayi mata karan tsaye a zuci ya hanata sakat dan haka sai ta yanke shawarar samun mahaifin nasu da batun. Anty kuwa baruwanta da'di taji dajin wannan labarin sai de kuma wani 6angaren tana tunawa da marigayi Mahmud, amma bata bari hakan ya nuna afili ba sai kawai ta takaita tunanin da ro'ka masa addu'ar dacewa wurin mahalicci. Sai da ta koma 'daki sannan tasha kuka har ta godewa Allahn ta, babu wanda yasani, dan haka da kanta ta ha'kura tayi shiru. Ayanda akasa ranar bikin Abbas 'din zai kasance kwana 'daya tsakaninsa da na Abban Mahmud domin shi nashi ranar Saturday ne sa6anin na Abbas daya kasance ranar Friday. Da yamman ranar Mummy ta iso su Hannah murna kamar zasu ha'diye ta baran ma Teemah da tayi matu'kar missing 'dinta sosai kuka ta sanya ta rungume ta da 'kyar Anty ta lallashe ta tayi shiru. Mummy kam dataji labarin bata wani damu ba dan ta riga da taji abakin Daddy tun a Dubai, sai de tana tunanin ko shi Abbas 'din baze amince ba tunda yanzu Teemah matsayin ta daban, bazawara ce ayanzu. Abinda kenan ya tsayawa Mummy ama'koshi ya kuma hanata jin da'di. Amma ganin yanda kowa ke farin ciki da al'amarin musamman Anty dan kane-kane tayi ta hana Fateemah zuwa ko'ina bayan ta nemo matar da zata ringa yimata komai, hakan ne yasa Mummy ta saki jiki tabi ayari aka cigaba da hidima da ita. Ummah tasamu Daddy da abinda ya dameta amma shima nuna mata yayi ba komai shikansa yanaso yayi mata maganan amma yafi son idan Yah Kabiru ya iso, dan shi ka'dai bazai iya ba yarinyar na matukar bashi tausayi ganin bataje ko'ina ba amma rayuwa ya gwara kanta, kuma yana tsoron kar jin labarin ya dawo mata da past 'dinta baya. Babu wanda ya sanar da Fateemah cewa auranta za'ayi kowa kawai harkar gabansa yakeyi, su Mummy tunanin su wai kar atuna mata da baya kuma ta 'daga hankalin. Ummah cema ke yawan yawan damun Daddy akan asanar da ita saboda kar garin neman gira kuma a rasa ido, ita kullun damuwarta gudun shiga hakkin yarinyar, ganin ba'a bata daman daya kamata abata ba aka hau shirin 'daura mata aure. Daddyn kansa abin na damunsa amma jiran Yayah Kabiru yakeyi idan yazo sayi maganar tare, yanada tabbacin cewa Fateema bazata ta6a gujewa umarninsa ba, dama Abbas ne matsalan dan kuwa har yanzu be san inda al'kiblarsa take ba akan auren, duba da yanda ya tattara yayi tafiyarsa duk da kuwa yasan cewa auren ya iso, hakan kuwa dayayi sai Daddy ya bari akan rashin son auren ne yasa, shi kuwa bayajin akwai abinda zai hana auren nan yiyuwa koda ma Fateemahn tace bata so toh dole sai tayi ha'kuri tunda ita da Abbas 'din 'yan uwan junane, saje can su 'karata. Idan yaga akwai cutarwa ne sannan zai 'dau matakin daya dace akan Abbas 'din. Tuntuni su Teemah sun can cewa Yayansu zaiyi aure amma kuma hakan ba dalili bane da zai sa har a tsare ta a'daki da gyaran jiki ,wata rana kuma harda Hannah akeyi musu, hakan da aka mata kuwa sai ya dinga tuna mata da lokacin aurenta da Mahmud wancan ma kusan hakane yafaru. Bata san dalilin daya sa za'a ringa yi mata gyaran jiki ba, dan wani zaiyi aure amma dayake gwanar son kwalliya ce ita sai kawai ta basar da zancen ta saki jiki aka cigaba da gyara ta. Duk kuwa da yanda aka kai da yimusu abubuwa tare amma cikin lokaci 'kan'kani Teemah ta yiwa Hannah zarra ta fita haskawa, wani lokaci dukkan su suna mamaki wai duk akan auren Yah Abbas ne ake musu wannan shirin? Lallai Anty na bala'in sonmu sosai. Hannah ce ma me 'dan 'ko'karin tambayar Mummy wai a ina Yayah ya samo matar auren da ake wani uban shiri haka? Gaba 'daya gida ya 'dau 'dumi, ga ba'ki sai zuwa suke tako ina, duk da maganar bata fito da wuri ba amma fah yadda dangi ke 'ko'karin zuwa abin na basu mamaki sosai. Tace " gaskiya ni Mummy abin na bani mamaki sosai, kamar wani 'yar gidan minista ko shugaban 'kasa zai auro? Murmushi Mummy tayi tace mata " _Za6in Daddyn ku ne shine ya za6a masa matar_ " Zaro idanu Hannah tayi cikin mamaki tace " Mummy kuma Yayah ya yarda? Mummy amsa ta bata da fa'din "Abinda nima bansani ba kenan har yanzu" Ta6e baki Hannah tayi tace " _ta6 gaskiya ina jin tausayin yarinyar nan, kinsan fa halin Yayah sai a_ _hankali, da wuya ake fahimtar sa_ " Teemah kam banda bugu babu abinda zuciyarta keyi alokacin dan kuwa fargaba ne taji ya kamata na fitan hankali da batasan dalili ba, bata sani ba ko itama tausayin amaryar Yayan takeji. Bata sa musu baki a maganar ba amma tsuru-tsuru tayi kamar wata marar gaskiya. Kanta na 'kara kullewa ne aduk lokacin da ta ga yanda Anty ke sata a gaba da abubuwa , shafa wannan, sha wannan, yi kaza, abin sai ya fara bata tsoro mafi yawa ita da Hannah ake yiwa amma idan abin sha ne ita ka'dai ake bawa tasha, idan kuwa ta tambayi Anty dalili sai tace shima 'din na gyaran jikin ne ko bata ganin cewa Hannah tafita haske, Anty sai ta dulmiyar da ita da fa'din haske kawai zai 'kara mata itama, tace ai kinga Hannah tafiki haske ka'dan shiyasa ita ba'a bata. Hannah kam kullun jimanta wa wannan amaryar Yayan takeyi, tasan shi bashi da yawan fa'da amma tasan halinsa shi bau'da'd'den mutun ne, da gane al'kiblarsa nada matu'kar wahala, magana wannan sai yaga dama yake yinta koda kuwa babu abinda ya damesa, idan ransa na 6ace kuwa wannan 'kasaita da miskilancin na musamman ne, ita kuwa a tsarin ta bata son mutun haka, tana ganin kamar ita bazata iya auren mutun irin sa ba, dan wani lokaci magana da baki ma na sanyaya al'amura akan mutun ya 'kyale ka, shi kuwa wannan yazama jinin jikinsa, tana ganin miskilancin Yayah ya shahara sosai da ita kanta abin na damunta balle matar da zai aura su rayu tare. Idan fannin kyau ne, ita kanta tasan Yayah 'karshe ne a wannan fagen dan ko ita ma bazata nuna masa komai ba duk kuwa da tana matsayin mace amma Yayah ya mata fintinkau, yana da kyau da kwarjini na musamman wanda ba kowa ke dacen samun irin sa ba. Sannan ya nada sanyi hali aduk lokacin da dayaga dama baka gane hakan har sai rayuwa ta ha'daka wauri guda dashi. Ranar da Hannah taji cewa Teemah Yayanta zai aura........ 🤞🏻 *Karku raina please kunsan wannan kyauta ce kawai nayi muku, sai mun ha'du gobe idan* *Allah ya kaimu kuma* . 👎🏻 ~Muna gaiyatar ku zuwa bikin mu fah, mun tanadar da masauki me girma sai kun zo....~ 🤠🤠 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ~Dedicated to my fans.~ *Bismillahir rahmanir raheem* _If you treat her the same way you treat others, how is she supposed to know that she is special to you....?_ 🅿 *75* Ranar da Hannah taji labarin cewa Teemah ne Yayah Abbas zai aura ba 'karamin farin ciki tayi ba, sai de kuma tana jin tausayin Teemah ka'dan saboda halinsa, amma damuwar ta be yi yawa ba danta fahimci cewa tsakanin Teemah da Yayahn akwai wani 6oyayyen sirri da har yau takasa gane ko menene shi. ***** Sai da bikin ya rage saura kwana biyu kafin Daddy yazo, hakan ma Mummy ce ta matsa masa akan yayi saurin zuwa saboda Teemah, amma da shi niyyan sa sai ranan Thursday zai taho inyaso friday sai a'daura aure aranar kuma sai ya wuce lagos saboda auren Abbahn Mahmud da za'a 'daura ranar saturday. Amma da Mummy ta matsa kawai sai ya taho, ganin sa kuwa har sai da ya sanya Teemah kuka taje da gudu tafa'da jikinsa tana ta rungume shi tana kuka, Daddy kam murmushi yayi ya dinga bubbuga bayanta ahankali yana bata ha'kuri harta yi shiru sannan sukayi gaisuwa me kyau da ita ha kama Hannah da suka zo gaida Daddyn tare. Hannah kam mamaki ba 'karamin cika ta yayi ba na ganin shagwa6ar da Teemah ke yiwa Daddy dan ko ita da take auta ma wani abin idan Teemah tayi sai dai ta tsaya kalonta dan ita bayi take ba duk kuwa da take autar gida ce ita, kuma Yayah Abbas ne ya hanata, dan baya barinta aduk lokacin daya ga tana yiwa Ummah shagwa6a taka mata birki yake yi 'karfi dayaji sai da ya hanata. Tun shigowan su ta kama guri ta zauna tayi shiru tana jiran Teemah ta gama kukan dan gani da tayi hankalin Daddy gaba 'daya ya koma kanta da rarrashin ta kamar wata yarinya 'karama. Dasuka gaida shi kuwa suka fito ahanyar koma wan su Hannah ke tsokanan Teemah cewa " _taji kunya ai da shagwa6a kamar wanda Daddyn goya ta zai nayi dan ta da'de bata ganshi ba shine harda irin wannan kukan?_ " Tayi maganar tana ta6e baki. Amsa Teemah ta bata da fa'din " _Anyi 'din ina ruwanki_ " Kai Hannah ta ka'da taci gaba da tafiya take fa'din " _hmm, kiyi dai a hankali dan ina jiyake miki watarana, wannan_ _irin shagwa6an sai kace wata 'yar shekar uku? ke da_ _aure ke gabanki_ " Azafafe Teemah tace " _ai kema auren ne ke a gabanki tunda kema macece_ " " _Nasani ai shiyasa ma nake gaya miki, shi aure ai duk sunansa aure, amma kuma mazan kala-kala_ _ne_ !" fa'din Hannah Teemah kuwa cewa tayi " _shiyasa ai naga kina wa Bilal shagwa6an kuma yana kar6a miki tun_ _ma kafin yazama mijin naki_ " Dariya Hannah ta saka sannan ta juyo ta kalli Teemah tace tace " _aini nawa daban ne dan indai Bilal ne ze kar6a min fiye da haka ma shiyasa ma ai nace miki mazan_ _kala-kala ne_ " Tafiya Teemah ta fara tare da fa'din " _nima indai mijin irin Yah Mahmud ne toh bana fargaba koka'dan_ " Da gudu Hannah tasha gabanta tace " _Waye ya gaya miki irin marigayin mijinki ne_ ? _naki tamkar dodo yake inkin ce zakiyi ta masa haka wahala zaki sha_ " Haushi ne yacika Teemah sai ta ja ta tsaya tayi kwafah sannan tace " _Hannah bana son wula'kanci da mugunta_ "! Gaba tayi tana mita, Hannah ma sai ta bita abaya tana murmushin mugunta, ita kam tana son 'yar uwarta kuma tausayin Teemahn takeji sosai. Teemah kam sai mita takeyi 'kasa-'kasa take fa'din. " _akan me zaki rin'ka yimin mugun fata ? angaya miki dodo zan aura ne da har zansha_ _wahala a wurinsa? Wama yace miki zan sake yin auren ?_ _Ni babu wani aure da zanyi bari kiji yanzu, ko da zanyi ma ba yanzu zan_ _sake auren ba kuma ma sai na za6a na tace wanda nasan bazai kawo_ _min matsala ba sannan zan yadda na aure shi_ " Dariya sosai ne ya kama Hannah dan duk taji abinda Teemahn ta fa'da amma sai ta mazge ta maida shi murmushi tace " _kice kafin nan ma har na haifi 'yata ko 'dana sannan muzo musha biki mu kwashi shoki a bikin babbar uwa mama Fatee!"_ Teemah kam ko kulata bata yi ba ta wuce hanyar bayi direct tana tsaki asaman la66a tace " _ke kika sani ai mara kunya kawai_ " Hannah zubewa tayi akan gado tana murmushi aranta tace " wai yaushe za'a sanar da Teemah cewa auren ta ne ya kusanto? ya kamata asanar da ita gaskiya hakanan, ai lokaci na tafiya ni sam banga anfanin 6oyewan ba, ni kam idan bazasu fa'da ba wallahi anjima zan gaya mata meke faruwa inyaso sai ince karta fa'di cewa abaki na taji" " _Yes!, hakan ma za'ayi_ ! Ta karashe da murna ita ka'dai kamar me ta6in hankali. Da daren ranar kuwa sai Daddy ya 'kira Teemah yafara da bata ha'kuri akan tafiyarsu Dubai batare da ta sani ba, da kuma lokacin rasuwar Mahmud da be tsaya ya tausheta ba be wani ke6e da ita a matsayin sa na uba ya bata baki ba wanda shi kanshi yasan be kyauta ba, sai de alokacin tsananin tausayin ta da yakeji ne yasa hakan, ya kara da fa'din mata batun gadon ta wanda aka bata cewa komai a hannun Abbas sai yanda sukayi, yana cikin maganar ya shigar da batun auren da ake kai ayanzu, inda yaringa 'ko'karin fahimtar da ita cewa bawai rashin gata ko so bane yasa duk hakan ke faruwa face tsananin son da ake mata. yace " _duk abinda zanyi ina yi ne Fateemah saboda ke da farin cikin ki, abaya ni na za6a miki mijin aure wanda Alhamdulillah kin cika 'ya ta gari Fateemah da_ _kika yi min biyayya wanda har shi Marigayin_ _ya koma ga mahallici banji wata sa6ani a tsakanin ku ba, naji da'din haka_ _sosai da kika amince da za6ina Fateemah yau ga ni na sake dawowa da_ _wani 'ko'kon barata, kuma mai girman gaske ban sani_ _ba ko zaki iya tayani cika shi!, a karo na biyu Fateemah na sake za6a miki mijin aure wanda na yadda da nagartar sa, nasan yanzu 'yancin kine ke keda wannan damar kuma addini ne yabaki, amma na shiga gabanki_ _na tauye ki, kiyi ha'kuri Fateemah ki ya femin sannan_ _kimin uzuri ki kar6i za6ina, duk abinda zanyi ina 'ko'karine inga na baki abinda nasan ya dace_ _dake domin na tabbata ba zakiyi kuka dashi ba ba zakiyi dana sanin amincewa da za6ina ba insha Allahu_ " Fateemah kuka takeyi sosai amma na zallan hawaye, hawayen ta ya kasa tsayuwa, kuma ta kasa bu'dan baki tayi magana aranta take fa'din " _na amince Daddy na amince da za6inka, ni 'yarka ce kaine ka haifeni kabani dukkan gata insha Allahu bazan ta6a_ _baka kunya ba, bazan ta6a bijirewa umarnin ka ba, bazan ta6a cewa_ _me yasa ka aikata hakan agareni ba_ " Hakan takeso ta furta amma bakinta yayi mata nauyi ga kuka daya ci 'karfinta sosai har sai da Daddyn Abuja ya sanya baki shima yayi ta rarrashinta kafin tayi shiru ta tsagaita kukan amma dayake daga zuciyarta kukan ke tasowa sai hawayen ta ya kasa tsayuwa gaba 'daya, dole cikin kukan ta tabbatar wa Daddy amincewar ta. A tare suka ha'da baki wajen sanya mata albarka da kuma haske mai 'dorewa har 'karshen rayuwarta sannan suka sallameta. Tana jin 'kunci, takaici da ba'kin ciki ga memories 'din Mahmud da ya dawo mata sabo yabi ya cika mata zuciya tab amma ko dan irin yadda taga farin ciki kan fuskar iyayen nata ma dole zatayi musu biyayya dan kawai ta faranta rayukansu kuma taci gaba da ganin hakan har abada hakan ma ka'dai ya isheta. Kwance take akan gado amma hawayen ta duk yabi ya ji'ka pillown jagab kamar wanda ruwa ne ya zuba akai, ita kanta tana so ta daina kukan amma hawayen ta yakasa tsayuwa. A wannan halin Hannah ta shigo ta same ta tana kan kukan, tana jin motsin Hannah kuwa ta taso ta taho gurinta ta rungume ta sai yanzu ne sheshshe'kan ta ya bayyana, Hannah ma duk jikinta yayi sanyi sai de bata raba 'dayan biyu cewa maganar aurenta taji shiyasa take kuka, dan haka sai ta bata chance sai da tayi kukan ta isheshshe sannan ta fara bata ha'kuri wanda da 'kyar tayi shiru har sai da Hannah tace zata je ta sanar da su Mummy cewa tana kuka kafin ta 'dan sarara ta sanar a Hannah meke faruwa. Hannan bata yi mamaki ba danta riga ta sani dan haka sai ta ringa lallashinta tana bata ha'kuri har ta samu tayi shiru. Abakin Hannah taji labarin cewa Yayah Abbas shine mijin da za'a aura mata nan da kwana biyu, zuwa lokacin kuwa zuciyarta da idanunta sun riga sun bushe ta fawwalawa Allah komai, ta fahimci cewa duniya dama kowa da kalar 'kaddarar sa da Allah yake jarabtarsa dashi wata'kila nata kalan 'kaddarar kenan na fannin aure, shine *auren za6in iyaye* , hakan ma ta gode Allah tunda nata iyayen na raye kuma tasan son da suke yi mata ne duk yasa haka, tasan dayawan mutane na son su kasance tare da iyayensu ko dan su ri'ka yi musu biyayya ma amma babu su basu samu wannan damar ba kuma sunyi ha'kuri, balle ita da nata iyayen na raye toh me ze hana ta yin biyayya agare su ko dan gudun dana sani agaba ma dole zata basu farin ciki koda kuwa wani iri ne indai har tana da daman yin hakan zatayi shi koda menene kuwa. Yanzu ne ta fahimci manufar komai, yanzu ne tagane cewa gyaran amare akeyi mata wanda wasu lokuta ake ha'da ta da Hannah ayi mata a fahimtar ta dan kar tunaninta ya yi tsayi ne shiyasa ake yin hakan. Ke nan kowa ma na farin ciki da wannan auren, kowa murna yake yi akan zatayi aure shiyasa tun ranar da taga aka fara yi mata gyaran farin ciki ya sa'k'ko cikin gidan nasu, zuwan Mummy ne ma ta 'dan ga canji daga gareta dan ita Mummy bakace ga damuwar ta amma tana yawaita tunani wanda ita kanta Teemah abin na damunta. Yanzu ne ta fahimci manufar maganan Hannah da tace *nata mijin dodone* ! Tare da tunowa da kalaman Yayan ranar da zai tafi inda yake cewa ta tabbatar tayiwa maganar Daddy biyayya koda baya nan. Tarasa ina tunaninta ya tafi tun farko da batayi noticing komai akan lamarin ba. Aranar kasa bacci tayi tunanain Mahmud duk ya dameta gaba 'daya baccin da ya kamata tayi ma kasawa tayi, har kusan 2:00 am idanunta biyu. Tunowa tayi da wayarsa dake cikin kayanta tayi sai kuwa ta tashi da sauri taje ta lalu6o wayar. Tayi 'ko'karin kunnawa amma wayar akashe dan haka sai ta jona a charge ta zauna tayi tagumi agabanta. Shawara ta yanke dan haka sai ta mi'ke ta nufi bayi ta 'dauro alwala tazo ta tada sallar nafilfili bayan ta idar ta ringa jero addu'o'i sannan ta shafa. Tana idarwa kuwa sai ta fara jin bacci dan haka akan sallayar bacci yayi awon gaba da ita. Ba ita ta farka ba kuwa sai da Hannah ta tasheta cewa ta tashi tayi sallah lokaci ya 'dan ja. Hannah na idar da sallah ta tafi gurin Mummy ta sanar da ita abinda ya faru na cewa Teemah tasan da batun auren ta yanzu, Mummy cewa tayi " _dama mahaifinku yace idan yazo shi zai sanar a ita da kansa ai_ " Mummy taji da'din haka dama ita tafison asanar da ita barinta cikin duhun bashi da amfani sam. Teemah kuwa Tunda ta idar da sallah ta gama addu'o'in ta shafa sai ta 'dauko wayar Mahmud ta kunna tare da kwanciya akan gado, Gallery ta shiga ta dinga bi 'daya bayan 'daya tana kallon pictures kala-kala nashi dana wasu da bata sansu ba, sai nasu da suka 'daka tare ita da shi tare wani suna dariya wani kuma ma ba'a gida sukayi ba. Sosai pictures 'din suka tuna mata da baya ta ringa gani tana 'kara maimaitawa, sabo fil Mahmud ya dawo mata, haka mutuwar sa ma sai ta ke jin tamkar yau ne suka rabu..... Takai 1hr da wayar a hannnunta sosai ta shagala da kallon pictures 'din dama tun rasuwar sa bata 'kara bi takan wayar ba sai yanzun shiyasa duk hankalin ta ya 'dauku ga kallon hotunan kawai sai taji wayar ta 'dauki 'kara. Firgita tayi har sai da ta tashi ta zauna tarasa yanda zatayi har 'kiran ya yanke bata 'daga ba wanda atake wani 'kiran ya sake shigowa a karo na biyu duk numbern 'daya ne da na farkon kuma babu suna yafito. Daurewa tayi ta 'dauka da niyar sanar da me 'kiran cewa me wayar ya rasu 'kilan bashi da masaniya ne shiyasa. Receive ta danna tare da bu'de speaker, bata 'kai wayar kunnan ba sai ta ri'ke ahannu. Tanajin yanda me 'kiran ya furta _Alhamdulillah_ daga 'daya 6angaren ga dukkan alamu 'daukan da akayi ne yasa shi jin da'di. " Assalamu alaikum, Yalla6ai Rabi'u ne daga Katsina, kullun munata neman layinka bama samu sai yau 'dinnan, wallahi duk na damu akan baka zo kaga aikin da aka yi agidan ba, gashi da sauran ku'din ma har na sa Meram a makaranta tafara zuwa ga..... Ko sallamar be bari ta amsa ba yaci gaba da koro bayani. Cikin rawar murya Teemah ta tare shi da fa'din " _bashi bane, shi 'din ya rasu tun wata hu'du da suka wuce_ ...... Kuka ne ya kubce mata tana jin yanda me 'kiran yafara jero salati sai tayi saurin kashe 'kiran tare da kashe wayar ma gaba 'daya. Sai yanzu tunanin waye Rabi'u yazo kanta, yanzu ne ta tuna da labarinsu. Ranar 'karshe ranar da Mahmud zai rasu ma sunyi magana da shi akan komawa katsina kamar yanda yayi al'kawari. 'Kiran da Rabi'u yayi mata ne yasa kukan ta ya kasa tsayuwa ta ringa zubda hawaye tana tuna baya, dama tana tunanin Maman Amal (matar Umar) kullum, yanzu da abubuwa sukayi mata yawa kuwa jitake bau wanda tafi bu'katan ha'duwa dashi sama da ita gashi bata da contact 'din ta batada na Umar ma, cikin haka Hannah tazo tayi 'kiran ta akan cewa wai Anty ne 'kiran ta, dayake yanzu kullum da safe ne ake yi mata wankan turaren sauran duk abinda za'a mata already an gama shi tun jiya sai de abin da Anty ke bata kullun tana sha ne har yanzu bata daina bata ba. Tashi Teemah tayi tana wani kauda kanta wai dan kar Hannah ta ga hawayenta, amma tuntuni Hannah tasan kuka takeyi amma bata kulata ba, dan ita kanta tana jin tausayin ta ahalin yanzu. ***** Ana gobe 'daurin auren ne Abbas ya iso da 'karfe bakwai na dare, sai da yayi alwala ya sallaci sallar maghrib kafin ya shiga cikin gida domin gaida iyayensa da burin ganin ta azuciyarsa. Ummah kuwa sai da ta ganshi hankalinta ya kwanta saboda kafin yanzun hatta layukansa ma basa shiga, hankalinta duk ya bi ya tashi da rashin zuwan nasa tsoronta 'daya kar Abbas ya 'ki zuwa ne tasan mahaifinsa bazai ji da'din hakan ba, kuma idan har hakan ya faru kenan 'kiyayyar sa ga auren ya nuna 'karara wanda ita sam bahaka take bu'kata daga gareshi ba. Gaida su yayi gaba 'daya fuskar sa normal ba yabo ba fallasa yana yi yana rarraba idanu afakaice ko zai ganta amma be ganta ba ko Hannah ma be gani ba. Ko da ya tashi zai tafi sai Ummah ta tashi tabi bayansa awani corridor suka tsaya ta tambaye shi dalilin daya sa be taso da wuri ba tace " _harka 'daga min hankali wallahi_ _sosai na 'dauka bazaka zoba, bansan har sau nawa na gwada 'kiranka ba ayau amma duk ban same ka ba_ " Murmushi Abbas yayi mata yace " _haba Ummah zanzo mana ai Daddy ne da kansa yace in dawo_ . " _Yauwa Babana kayi ha'kuri dan Allah ka kar6i_ _auren nan da hannu bibbiyu, dama ai kace Fateemah amanarka ce, kai kace an baka amanarta tun abaya so kaga sai kaci gaba da kulawa da_ _amanarka cikin sau'ki tunda ta dawo 'kar'kashin ikon ka, dan Allah Muhammad karka bani kunya, karka_ _cutar min da yarinya kaji_ ? Tabbaci ya bata da fa'din " _Insha Allahu Ummah karki damu_ "! Albarka tasa masa tare da yi masa zancen abinci yace akwo masa coffee ma ka'dai ya isa. Ummah da kanta ta ha'da masa sannan aka fara cigiyar Hannah akan tazo ta kai masa coffee 'din da 'kyar aka samo ta a 6angaren Daddy yasa ta gyaran wasu kaya daga. Hakan yasa dole sai de Teemah ce za ta kai masa tunda kam Hannah na aiki. Tana kwance akan gado rufe ruf da blanket kanta ciwo yakeyi mata ga jikinta zafi rau amma ahakan ta aure ta mi'ke lokacin da sa'kon ana 'kiran ta ya risketa. Hijab ta zun6ula har 'kasa kan shararar rigar da ke jikinta sai ya kasance fuskar ta ne ka'dai ake gani. Ahaka ta kar6i coffee 'din ta taho zuwa 'dakin nasa. Tunani takeyi na yadda Yah Abbas zai kar6e ta amatsayin mata, sannan ga Zazza6i ciwon kai da mara da yasa ta agaba tun 'dazu tarasa yadda zatayi, Hannah taso sanar mawa ko zata samo mata magani amma tun lokacin data fara jin ciwon marar bata sanya Hannah a idanunta ba. Ahankali take tafiyar kamar bazata yi ba har ta isa 'kofar 'dakin inda tun kan ta shiga zuciyarta ya fara harbawa, ahankali ta tura 'kofar tare da yin sallama ta shiga. Abbas kam be amsa ba sai ma ya lumshe idanu aransa yace " _Alhamdulillah_ " Da ganinta, dama idanunsa da zuciyarsa ba 'karamin son ganinta suke ba. Teemah kam rashin amsawan nasa sai ya sa ta shiga ru'dani tunda tasan sarai yaji ta duk kuwa da cewa ahankali tayi sallamar amma ta tabbar yajita sai de ko in beyi niyyan amsawan bane kawai. Shi kuwa Abbas tsayawa yayi kallonta duk da ba wani wadataccen haske bane a'dakin amma kallo 'daya yayi mata yaga canjawar da tayi afili tayi wani kyau na musamman ga haske data 'kara na gyaran data sha ya kuma sake ha'duwa dana menstrual period, daya ke idan tanayi haske yake 'kara sata ka'dan. Gaban sa tazo ta ajiye 'karamin tray 'din bata mi'ke ba sai da ta gaida shi tukun na. Abbas amsawa yayi yana kallonta dan tuni ya shagala da sha'kan da'd'da'dan kamshin dake tashi ajikin ta, 'dakin bawani haske sosai illah hasken television da ke aiki kawai a palourn shi 'din ma be wani wadaci 'dakin ba dan wani guri idan aka nuno yakan yi duhu ne gaba 'daya hakan kuwa sai ya sa 'dakin ya kasance ba shida maraba da wanda babu hasken ma gaba 'daya. Lokuta da dama tana mamakin sa yanda yake son kasance wa a cikin duhu shi, kamar wani marar gaskiya. Tana 'ko'karin mi'kewa sai kamar an matsi bakinsa yace " _tafiya zakiyi kuma_ ? Fasa mi'kewan tayi sai ta koma kamar yadda take tsugunne da farko. Zazza6i takeji sosai ga ciwon kai sanadin haka kuwa har yanasa idanun ta tara ruwa. Data rasa me zatayi sai kawai ta 'dauki cup ta tsiyaya masa coffee 'din tare da mi'ka masa. Hannu ya sa ya kar6a tare da fa'din " _I thought kin manta ne ai_ " Maganar tasa bata bu'katar amsarta dan haka sai ta yi shiru. " _Wai meke damunki ne_ ? Yasake tambayar ta yana kallon ta. Tambayar kuwa sai ya sa ta sakin hawaye, da sauri ta kai hannu ta share hawayen wai dan kar ya gani amma ina yariga yagani. Zaro idanu yayi yace " _me aka miki_ ? _Ko yau 'din ma ba'a son ranki kika zo ba, nifa bance dole sai ke zaki kawo_ _min abu ba!_ _Ko wani abu na miki yanzun_ ? Girgiza masa kai tayi alamar " _ah ah_ " Hawayenta naci gaba da zuba. " _So kukan fah na_ _menene_ ? yasake tambayarta. Cikin in i nan kuka tace " _Kai...kaina ke min.. ciwo_ " Abbas be yi mamaki ba dan lokacin data mi'ka masa coffe 'din yaji 'dumin da jikinta ya 'dauka dama yasan za'a rina. Ajiye coffee 'din yayi yakai hannu ya ta6o fuskarta sai yaji zafi gau take yace " _Sabhanallah tun yaushe yafara miki?_ " _D'azu_ " tabashi amsa atakaice. " _Kinsha magani ne_ ? Ya sake tambayarta. " _ah 'ah_ " tabashi amsa tare da jijjiga kanta. Mi'kewa yayi yace mata " _tashi muje_ " Yayi maganar yana fita daga 'dakin, itama Teemah sai ta bishi abaya a hankali dan har jiri takeji yana 'dibanta, hatta haske bata son gani dan sai taji idanunta na mata zogi sosai. Wurin driver ya wuce ya kar6o key sannan ya nufi gurin motar har ya bu'de zai shiga kuma sai ya tuna wani abu. Jiranta yayi sai data iso sannan yace mata " _zonan wato dana tafi bakya cin abinci sosai ko_ ? Shiru tayi masa tana rarraba idanu. Tsaki ka'dan yaja sannan ya juya ya shiga motar tare da tada ta. Teemah ma shiga tayi yaja suka fita daga gidan. Sai da yabi da ita wani eatry yasata dole sai da ta 'dan ta6a abinci tukunna kafin suka wuce inda zasu. Wani 'karamin private clinic dake kusa dasu ka'dan ya kaita. Suna zuwa kuwa suka samu wata nurse ce a duty dan haka itace ta duba Teemah. Abbas kam kamewa yayi akan kujera yace Teemah tafa'di abinda ke damunta wa nurse 'din. Nurse 'din itama murmushi tayi tace " _meke damunki ne_ _'yan mata_ ? Ahankali Teemah ta bu'di baki tace " _Zazza6i nakeji da ciwon kai da....da kuma...._ Kasa 'karasawa tayi sai ta 'dan saci kallon Abbas sai taga shikan idanunsa nakan wayar sa ne. Muryar Nurse 'din tasake ji tana fa'din " _inajinki, da me kuma?_ Sai da sake kallonsa kafin ta fisgi maganar tace ".... _da...Menstrual_ _pain_ " Tana gama fa'di sai ta wani rintse idanu da 'karfi. Abbas kam murmushi yayi ganin akan wannan abin take wani jan magana. Nurse 'din ma murmushi tayi mata tace " _kina jin kunyar_ _Yayah ko_ ? Bata kulata ba sai ta kauda kanta gefe. Tashi Nurse tayi taha'da mata magungunan da suka dace, taso tayi mata allura amma Teemah tace bata so, harta fara lalla6ata sai Abbas yace abar alluran kawai tunda bata so. Koda suka koma gida kuwa be barta ba sai da ya tabbatar tasha maganin ta tukunna , tana shiga 'dakin su kuwa ta tarar da Hannah tsaye da waya a hannunta Anty ma na zaune a gefen gado ta zubawa Hannah idanu. Sallamar ta ce ta dawo da hankulansu gareta Hannah harda ajiyan zuciya Anty kuwa da sauri ta zo ta tareta. Hannah ce ta jefa tambaya tace " _Teemah ina kika shiga dan Allah duk kinbi kin 'daga mana hankali_ _gashi mun ta 'kiran wayarki bakya 'dagawa har 'dakin_ _Yayah naje fah ban same ki ba?_ Teemah da dafe kai tace. " _Wayar na nan 'ka'kashin pillow ne kuma tana silent_ " Anty ne ta taho da sauri ta ri'ke ta tare da fa'din " _Fateemah meya faru kuma naji jikinki da zafi_ _sosai_ ? Ledan magungunan ta 'dago ta bawa Anty a hannunta tare da fa'din " _Anty clinic mukaje_ _da Yayah_ " daga nan ta basu labarin zazza6in daya dameta 'dazu. Anty kar6a tayi da mamaki tace " _Ya akayi baki sanar da_ _kowa ba toh_ ? Tana shirin yin magana Anty ta dakatar da ita da fa'da akan shirun da tayi bata sanar musu halin da take ciki ba, tace karta sake yin irin haka yanzu ba dan shi Abbas 'din ya lura ya tari abin ba da tasan meze faru ne? Su suna can suna shirin biki while ita wacce akeyi domin tan kuma tana nan tana fama da jinya ina anfanin haka? Ha'kuri Teemah tayita bawa Anty tace bazata sake maimaita irin haka ba. Anty bata bar 'dakin nasu ba sai da ta tabbatar da sassaucin zazza6in kafin nan taje ta kwanta itama. Abbas kam da kansa yazo ya duba ta lokacin 'karfe 11:48pm su suna ma bacci basu san yazo ba, ganin tana bacci yasashi jan 'kofar ya rufe ahankali tare da hamdala dan yasan zazza6in ya sau'ka kenan tunda har tasamu tayi bacci, yaso ya shiga ya ta6a yaji lafiyar jikin amma saboda kasancewar Hannah na 'dakin yasa kawai ya juya batare da ya shigan ba. ***** Washegari yakama ranar Friday wanda ya kasance aranar jama'ah da dama suka shaida 'daurin auren Muhammad Abbas Al'hassan tare da amaryar sa Fateema Kabeer inda yasamu hallatar alummar musulmai da dama dayake a masallaci aka 'daura auren bayan an idar da sallah juma'ah. Abbas kam farin cikinsa ba ze ta6a misaltuwa ba domin shi ka'dai ne zai iya fassara irin yanayin daya shiga alokacin daya ji an sar'ke sunansu waje guda, godiya kawai ya ringa zubawa mahalicci dan bashi da abin da zai iya furtawa bayan haka. *Wash Allah na nagaji sosai............Dan Allah readers ku taimaka inga ruwan comments in ba haka ba ni daku sai jibi ko ma monday wallahi.* _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce*😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir rahmanir raheem* _No man succeeds without a good woman behind him......either Wife or mother, if it is both, he is twice blessed indeed_🤞🏻 🅿 *76* Haka a gida ma da yawan mutane na farin ciki da wannan aure sai faman sanya albarka akeyi. An shirya Teemah cikin wata doguwar riga mai kyan gaske kalar touqoise blue da ratsin golden, rigar ta kama ta sosai daga 'kirji 'kasan rigar kuwa abu'de yake ba 'karamin fito da kyaunta rigar tayi ba. Hannah kam yau ba ta jin gari, tunda aka 'daura auren ta fara 'kiran Teemah da suna _amaryar_ _Yayah_ , Teemah tun tana mitar bata so har ta ha'kura tayi shiru balle da taji kanta yafara sara mata ai tuni sai ta nemi 'dakin da aka sau'kar da Mummy ta shiga da niyyan hutawa. Mummy kam korota tayi tace maza taje cikin 'yan uwanta ta zauna bata son zama shirun nan. Fuskar shagwa6a tayi tace " _Allah Mummy kaina ke ciwo ne shi yasa_ " Mummy tace taje yanzu ta 'dau maganinta tasha ba jiya an siya miki magunguna ba, hayaniya ne ke saki ciwon kan ba komai ba. Fita tayi taje 'dakin su nan ta samu Hannah da 'kawayenta sai ihu sukeyi, haka ta zauna agefensu tayi shiru bata kula su amma duk yadda Hannah tasan zata takalo ta tasata magana sai tayi. 'Karfe uku nayi duk suka wuce gidajensu da sunan zasu je kowa ta yo shirin walima su dawo. Hannah ma kasuwa ta shiga aka bar Teemah ita ka'dai. Taji da'din raguwar hayaniyan amma kuma sai ta ringa jin zazza6i na son taso mata. Zama tayi a'dakin nasu ta'ki zuwa ko'ina kuma ta'ki shan maganin ma . Kafin yamma kuwa zazza6in Teemah sabo fil ya dawo ga jiri dake faman 'diban ta har bata iya tsayuwa da kanta sai ta kama abu, gaba 'daya ta fita a hayyacinta. Anty ne tazo neman ta dan afara shirin yi mata kwalliyar yamma ta zuwa walima, gagarumin walima ne da Daddy da kansa ya shirya shi. Sosai Anty ma tayi 'ko'kari dan kuwa duk wasu kaya da Fateemah tayi anfani dasu da ma wa'dan da zata sa agaba duk Anty ne ta 'dau nauyin yinsu tare da 'dauko wata shahararriyar mata wacce ta 'kware a fannin kwalliya na zamani domin ta ringa yiwa Teemah make'up har biki ya 'kare. Ko yanzun ma da kanta ta shiga duba Teemah sai ta tarar da ita kwance ta du'kun'kunu a cikin blanket. Da sauri ta 'karaso tazo gareta tana tambayar ta "me ya faru? Tayi saurin fahimtar abinda ke faruwa ne sanadin zafin da taji jikinta yayi ga kuma ha'duwan da ha'koranta keyi. Fita tayi da sauri da niyyan 'kiran Mummy sai kuma tariga ha'duwa da Ummah tun kafin ta kai ga Mummyn. Ummah kam ganin hankalin Anty atashe yasa tayi saurin barin maganar da takeyi ta taho ta tareta da tambayar meke faruwa ne? Bayani Anty tayi mata atakaice tun kafin tadasa aya kuwa Ummah ta furta " _subhanallah_ " sai tayi gaba, tare suka 'dunguma zuwa 'dakin su Teemahn da Anty da wasu mata guda biyu. Ganin yanayin Teemah yasa Ummah fa'din " Fateemah sannu ko, sannu Allah ya sauwa 'ka! Juyawa tayi ta kalli 'dakin tace "wai ni har yanzu Hannah bata dawo bane? Wata Antyn su da suka zo daga Gombe ce ta bata amsa da fa'din " inaga de bata dawon bane 'kila" Ummah dialling no. tayi ta 'kira shiru tsawon seconds bakwai sannan ta furta "Ameen wa alaikassalam" "Jama'ah Alhamdulillah" "Fateemah ba ta jin da'di ne nace ko zaka aiko doctor adubata " "Ok, toh shikenan" tafa'da tare da yanke wayar. Iya abinda kowa yaji kenan kuma babu wanda yasan da waye tayi magana. Sai da ta cire wayar a kunnanta kafin tayi musu bayanin cewa " Abbas zaizo yanzu 'kila ya taho da likita ko kuma ya kaita asibiti ban san wanne zaiyi ba" Fita tayi tace "bari tana zuwa yanzu kafin ya iso" 15mins be cika ba sai gashi ya bayyana a'dakin cikin wata arniyar shadda sky blue mai kyan gaske wanda ya dace da yanayin jikinsa. Da sallamar sa ya shigo tare da gaida wa'danda yagani a'dakin. Sake tambayar Anty yayi abinda ke damun Teemah Antyn sai tace dashi " _inajin zazza6in ne ya dawo dan jikinta ya dau zafi gaskiya sosai_ " Tayi maganar tare da kaiwa hannunta zuwa jikin Teemah. Abbas kam tana gama bayani sai ya kallo inda yaga maganin ta jiya, aikuwa sai yagansa still agurin, zuwa yayi a hankali ya isa inda yake ajiyen ya duba sai ya ga tun wanda ya 6alla mata jiya ne bata 'kara shan wani ba. Sai yanzun yakai dubansa kan Fateemah da tun safiyar yau yake mararin ganinta amma be ganta ba sai yanzun. Jikinta arufe ruf illah kanta ne yake iya kallo dan fuskarta yana 'daya bangaren ne ta juya musu baya. Tuni 'daurin da aka mata ya zame ya koma gefe ya bar iya gashinta dake kwance gwanin sha'awah awaje yana ta she'ki. Takawa yayi a hankali zuwa bakin gadon yasa hannu ya ta6o fuskar tata sai yaji zafi gau be 'dauke hannun ba sai da ya shafi gashin kanta da ya 'dau hankalinsa yanda babu wanda zai lura cewa dagan gan yayi. Juyawa yayi ya fara tafiya yace da su akaita motansa zai same su acan, yace gara muje hospital adubata yafi" Yana gama fa'din haka ya bar 'dakin. Wasu su biyu ne suka kama kafa 'dunta zuwa inda ya fa'da 'din Anty na binsu abaya. Anan ya same su ri'ke da ita an lullu6a mata mayafi akanta wanda yarufe jikinta da kyau, hakan kuwa ba 'karamin da'di yaji aransa ba, sai daya iso ya bu'de motan kafin ta shiga da taimakon Anty sannan shima yashiga tare da furta _bismillah_ don zatonsa ko da 'dayansu za'a. "Sai kun dawo, Allah ya tsare ya bada lafiya in gantacciya" Anty ne tafa'di haka kafin ya amsa kuwa har sun juya masa baya. Ganin sun juya kuwa yasashi sakin hamdala azuciyarsa dama shi ba son rakiyar yake ba dan sai ya cire babbar rigar dake jikinsa ya wulla ta baya dama duk ta takurasa ha'kuri kawai yakeyi da ita na yau ka'dai. Jan motar yayi suka bar haraban gidan, sai da ya hau titi kafin ya juya ya kalleta sai yaga ta kwantar da kanta ajikin cinyoyinta ta takura guri guda ga dukkan alamu sanyi takeji sosai. Be yi mata magana ba hannu yasa kawai ya kashe AC gaba 'daya sannan yaci gaba da tu'kinsa. Koda aka gwada ta ma ba komai ke damunta ba zazza6in ne kawai sai stress daya mata yawa amma bakomai, kuma ciwon na 'kara 'karfi ne sanadin rashin cin ishshen abinci da batayi. Yau kam cewa yayi ayi mata allura dan bata son shan magani ma yace ko najiya ma 'kin sha tayi. Kuka tafara tare da ro'konsa akan dan Allah yayi ha'kuri bazata sake 'kin shan magani ba. Kau da kai yayi yace da nurse 'din ta ha'da injections 'din yace kuma bata son cin abinci ma doctor. " _Yayah plz kace ta bari Allah zan rin'ka shan magani kullun_ "! Yi yayi kamar beji ta ba sai ma yace da doctor ta hanzarta please. " _Wallahi ni bana son alluran nan, kuma sai na gayawa Ummah da Anty da Daddy ma_ ". Murmushi doctor tayi aranta take mamakin irin dramar wa'dannan Yayah da 'kan wan suna matu'kar birgeta ita kam. Dakansa ya ri'ke ta tana fiffisgewa amma sai da aka mata har biyu sannan ya saketa. Zamewa tayi ta 'dora kanta ajikin 'kafafunsa taci gaba da kukanta daya ga haka sai yace ta koma kan sofa 'din dake office 'din ta kwanta, itama sai tayi kamar bata jishi ba, murmushi yayi ka'dan yasan haushinsa takeji yanzu dagangan sai yace da nurse 'din " _doctor inajin fah alluran be isheta_ _ba_ " Tana jin haka ta mi'ke ta koma inda ya fa'din ta kwanta shiru tana sau'ke ajiyan zuciya, dayaga kamar zatayi bacci ne sai yace su tafi gara taje ta huta gaba 'daya a gida. ***** Can gida kuwa already shirye-shiryen walima ya kankama kowa nata faman shiri, lokacin da suka iso gidan ma 'dakinsu yayi niyyan kaita amma jin hayaniyar Hannah da 'kawayenta a 'dakin dole sai ya maida ta 6angarensa dan so ya ke ta huta sosai zuwa lokacin kuwa bacci yariga yaci 'karfinta gaba daya. Suna isa tazame ta ta 'dora jikinta akan gadonsa sai kuwa bacci ya 'dauke ta ahakan sai sakin ajiyar zuciya take yi na kukan da tayi 'dazu. Abbas kam tsayuwa yayi akanta yana 'kare mata kallo ba 'karamin kyau ta masa ayadda take 'din ba, ahankali yadawo da idanunsa saman la66anta da suka 'karayin ja sosai. Da sauri ya kawar da mugun tunanin da yazo ransa tare da fa'din " a _uzubillah_ " Gani yayi kamar kayan da ke jikinta sun mata nauyi dan haka sai ya 'dauki wayarsa yakoma parlour, layin Hannah ya'kira amma bata 'daga ba, daya sake 'kira kuwa sai ta 'daga amma bata jin sa tsaban hayaniyan daya yi yawa agurin da take. Take yayi tsaki ka'dan tare da yanke 'kiran. Dama so yake ya sanar da ita ta kawo wa Fateema kaya marasa nauyi amma hakan be samu ba ganin bajinsa zatayi ba, sai kawai yafara tunanin wata mafitar daban. Baifi 5mins a parlour ba sai ya tashi ya koma bedroom 'din tare da 'daukan stool yakoma gaban gadon ya zauna ya zuba mata idanu. Ahankali yakai hannunsa zuwa bayanta ya zuge zip 'din doguwar rigan da ke jikinta wanda yakamata 'dam ya zauna sosai. Ahankali ya zare rigar zuwa 'kasa har ya cire ta gaba 'daya. Abbas kam suman zaune ne yaso kama shi dan be ta6a tsintan kansa acikin irin wannan yanayin ba, be ta6a kallon surar mace azahiri irin hakan ba, macen ma kuma Fateema, idanunsa be ta6a cin karo da abu makamancin hakan ba, 'kirjin ta ya kura wa idanu dake sanye cikin jan bra mai kyan gaske, ajiyan zuciya ya sauke tare da kawar da idanunsa gefe itama Teemah adai -dai lokacin sai ta motsa ka'dan dan sosai taji alamun sauyi atattare da jikinta iska taji na hura ta amma saboda 'karfin alluran dake yawo ajininta yasa bata wani yi motsin na kirki ba ta cigaba da baccinta. Tashi yayi yaje cikin kayan sa ya 'dauko rigar polo ba'ka na aikinsa ya dawo inda take, yanzun kam hawowa gadon yayi gaba 'daya yafara 'ko'karin saka mata rigar, a hankali, idan yaga kamar zata motsa sai ya dakata da abinda yakeyi sai ta kuma yin luf sannan yake cigaba da sawa kamar me dressing wa jinjirin da ba'a so ya tashi a bacci da haka har yagama mata, shi kansa mamakin kansa yakeyi yanda har ya iya tsayawa ya 6ata lokacinsa wurin sanya mata kaya duk kuwa da cewa hakan ba'kon lamari ne agurinsa amma a hakan sai da ya sa mata. Shida kansa ya san Fateemah dabance a rayuwarsa, bata da me kama koka'dan azuciyarsa. Yana gamawa kuwa aransa ya furta " _tubarkallah-masha_ _Allah_ " tare da shafa gashin kanta ahankali, Dan yadda rigar ta matu'kar amsan jikinta ya kuma 'kara fito mata da asalin kyaunta da haskenta kamar ace nata ne, baran ma da ya ha'du da ba'kin skinny trouser 'din dake jikinta ai ba magana, sosai Abbas yaga 'karin hasken ta ya zarce na baya. Abbas kam shashancewa da kallon ta yayi ya mori wanda suka wuce shi ma abaya, shi kansa yasan Fateemah mace ce, mace ce da kowa ni 'da namiji zaiyi sha'awar kasance wa da ita. Ya godewa Allah aransa yafi sau a 'kirga saboda kawai mallaka masa ita da yayi amatsayin mata. Abbas 'dinku kam kasa jurewa yayi lokacin da idanunsa suka sau'ka akan bakinta, sai ji yayi kamar an fizgeshi ya ran'kwafo da kansa zuwa dai-dai fuskarta, bakinsa ya ha'da da nata ya bata light kiss asaman la66an ta. Yana cire bakinsa kuwa yaga ta turo bakinta gaba tare da juyi zuwa 'dayan 6angaren. Sai da ya lullu6eta kafin ya tashi yana murmushi ya koma kan stool 'dinsa ya zauna. Tsawon mintina talatin yana zaune wurin agabanta kamar mai gadin ta, sannan ya koma parlour anan ya tarar da tarin missed calls awayarsa har da na Daddy, Ummah da sauran abokansa. Abokansa kam dama yasan dole zasu neme shi dan be yi sallama da su ba ya taho abinsa, amma be bi ta kansu ba, sai yabi bayan 'kiran Daddy, shima na Daddyn be shiga ba wanda hakan yasa ya gane cewa tafiyar su zuwa Lagos tayi nisa kenan. Sai da ya 'kira Ummah yace da ita yana bu'katar ruwan tea ta amsa masa da toh sannan ta tambaye shi jikin Fateemah yace da sau'ki yasanar da ita cewa sun dawo ma already suna gida. Godiya wa Allah Ummah tayi tare da fa'din tana zuwa anjima toh tadibo ta. A silent ya saka wayar bayan sun gama magana da Ummah tare da ajiyeta agefensa, sam be yi niyyan zuwa ko'ina ba dan haka yayi zamansa a parlourn yana gadin farkawar ta. Daga shi Abbas har ita babu wanda ya halacci taron walimar, inda kuwa babu laifi walima ta 'kayatar fiye da zaton mai karatu, gurin ma ka'dai abin kallo ne dan idan kaga yanda aka tsara gurin dole sai ya birgeka komai fari akayi decoration 'din wajen gwanin birgewa, ga wasu shahararrun malaman musulunci da aka gayyato maza da mata inda suka ja hankalin mutane akan ha'kuri da zaman takewar aure, ga 'dumbin jama'ar al'ummar musulmai da suka halatta suma ba 'a cewa komai, Ga Hannah ma da tawagar ta agefe guda suma ba laifi yawa ne da su, zakayi mamaki idan ka kalli ayarin 'yan CAPTAIN ABBAS FANS 1&2 suma agurin suna ta rawar kai abin su afa'dar su wai bikin nasu ne,'dai-'dai kun cikin su ne ke zaune aguri 'daya, wasu ko fuskar nan babu walwala, musamman ma masoyan CAPATIN na ha'ki'ka da suke jin cewa za'a musu kishiya, su kam har banson ganin fuskar su dan ko ka'dan babu walwala, sunzo ne da niyyar ganin kalar amaryar Abbas 'din amma basu samu dama ba dan Cpt. abbas ya 6oye amaryarsa ya hana su ganinta, basu sami ganinta ba kuwa har taro ya watse gaba 'daya. Ummah da kanta ta kawo masa Tea 'din inda tasame shi zaune a parlour, taso ganin Teemah amma Abbas yace bacci takeyi dan haka sai kawai ta tambayi yanayin jikin ya sanar da ita cewa ba laifi jikin da sauki, tace "toh Allah ya sauwa'ka" daga nan ta tafi da zummar sake dawowa ta dubata idan ta tashi. Mummy naso taga 'yarta taga halin datake ciki dan rabon su da ganin juna tun da rana data hanata 6uya a'daki, zazzabin nata ma labarin sa tazo taji bayan sun wuce asibiti ta kira layin Teemahn kuma ba'a 'daga ba, tana so taganta amma nauyin ganinta tare da Abbas 'din sai ya rinjayi 'kudurinta dole ta sanyawa ranta ha'kuri zuwa gobe idan Allah ya kaimu. Bayan sallar maghrib Hannah tazo da sallamar ta ta gaida shi tare da fa'din " 'dazu ka kirani Yayah? Yana kishingi'de cikin kujera be ko kalleta ba yace " meyasa toh sai yanzu zaki zo? "Ayyah Yayah muna wajen walima ne fah alokacin shiyasa" Sarai yasan 'karyane dan haka sai ya jijjiga kansa ya kauda kan daga barin kallon ta yace ki 'dauko wa yarinyar nan kayan baccinta inajin zata bu'kace su" Taso ta tambaye shi wacce yarinyar amma tsoron yanayin dayake ciki ya sanya ta ta ja bakinta kawai tayi shiru ta fita. ***** Teemah kam bata tashi ba sai 'karfe tara kusan da quarter ma sannan ta farka, ahankali ta bu'de idanunta sai kuwa taga duhu, bata tashi ba sai ta fara lalu6en Hannah a gadon hannu da 'kafa amma bata jita ba, " Hannah! " Hannah!! ta kira sunan ta har sau biyu, jin shiru yasata ta janye bargon dake jikinta ta sau'ko daga gadon tamkar zatayi kuka, tana shirin barin 'dakin sai taga haske ya gauraye ilahirin 'dakin gaba 'daya. Juyawa tayi sai caraf suka ha'da idanu dashi, zaro ido tayi waje tare da rufe bakinta da hannayenta duka biyu wanda sai alokacin kuma ta fahimci a inda take. Be kulata ba sai ya kawar da kansa gefe duk kuwa da cewa yaji da'din yanda yaga ta tashi garau da ita, amma be nuna hakan afili ba, sai ya wuce ta ya nufi bayi ya dan watso ruwa sai alokacin ne yaji nutsuwar yin wankan ya shige shi, tun 'dazu yake so yayi amma ya kasa sallah ka'dai ke sashi barin inda take yana idarwa kuwa baya 6ata lokaci ako'ina yake dawowa yaci gaba da gadinta, dama burinsa be wuce ya ganta ta warware ba. Yana shiga bathroom 'din kuwa sai itama ta wuce parlour da hanzarin ta da niyyar barin 'dakin, amma sai ta tarar da 'kofan arufe da lock, mamakinta kuwa be wuce na yanda akayi tazo nan 'din ba ga kuma wata riga ajikin ta dabata san daga ina ta sameta ba. Kan stool 'din dake wajen dressing mirror ta koma.ta zauna tana jiran fitowarsa domin ya bu'de mata 'kofa ta tafi. Abbas ma yaso ya 6ata lokaci a gurin wankan amma daya tuna cewa bataci komai ba sai kawai ya hanzarta ya fito in less than 15mins. Shima yana fitowa direct gaban dressing mirror ya nufa dan ganin yanayin jikinsa yi yayi tamkar be ganta ba sai ma murmushin mugunta daya sake yi tare da kwar da kansa. Dama yasan zata nemi hanyar fita shiyasa ya sakawa 'kofan lock kafin ya baro parlourn tun da wuri. Towel 'dinsa 'daure a 'kugun sa ya fito, da farko Teemah rintse idanu tayi data ga ya nufo inda take ahaka, amma daga baya data gaji da rufe idanun sai ta bu'de su ahankali ta sau'ke su akansa. Abbas duk yana lura da ita amma be tanka ta ba. Ita kuwa akan cikinsa ta sau'ke idanun ta, ta kuwa 'kurawa jikin nasa idanu ta na kallo har zuwa 'kirjin sa. Tasaba ganin Yaya Mahmud ahaka amma yau da taga Abbas sai ta ga tsarin halittarsa ba iri daya 'daya data Mahmud ba, sosai yanayin jikinsa ya birgeta yanda jikin ya wani mummur'de ga wasu parks da ya ajiye sai take jin sha'awar ta6awa, amma bazata iya ba dan tasan halinsa idan ta ta6a shi 6a66allata zai yi wannan Yayan kam, kan ta 'daga zuwa fusakarsa, suna hada idanu sai ya 'dage mata gira tare da fa'din " _ya dai_? Kau da kai tayi gefe da sauri tace " _ni ina so in tafi ne"_ " _Zuwa ina kenan_ ? Ya tambaya batare da ya kalle ta ba. Amsa ta bashi da fa'din " _D'akin mu, gurin Hannah..._ " Taranta yayi da fa'din " _can 'din yafi nan ne_ ? Bata bashi amsa ba sai kawai ta tura baki gaba tayi fuskar kuka. Ko kallan inda take Abbas bai sake yi ba yaci gaba da sha'anin gabansa. Teemah kan kukan shagwa6a tafara yimasa ka'dan-ka'dan, Abbas still 'kin kulata yayi sai daya ga kukan na shirin yin yawa ne sannan ya waigo azafafe ya dubeta yace " _for god sake ni na hana ki tafiya ne? Kije abinki mana ko na 'daure ki ne.._ ? Da turarren baki cikin shagwa6a ta furta " ' _kofan fa arufe da lock ai na duba 'dazu_ " Goshi ya dafe kamar ehh dagaske ya manta ne sai yace " _muje in bu'de miki_ " Gaba yayi aransa ya furta " _zanyi maganinki ai_ " Itama sai ta bishi abaya har zuwa parlourn, yana budewa kuwa ko magana bata sake yi ba ta fice abinta. Tura 'kofan kawai yayi da gangan ya barta abu'de dan ya san zata dawo. Ai kuwa ko bedroom 'din be gama shiga ba yaji ta dawo da saurin ta har tana shirin wuce shi. Murmushin gefen baki yayi yana tafiya yace " _ya kin dawo kuma_ ? Tana ha'ki ta bashi amsa da fa'din " _Ni...ni tsoro nakeji, Yayah gidan fah shiru kamar ba kowa ga shi_ _hasken...ma ya ragu sosai bazan iya tafiya a...haka ba_ " Cigaba da tafiyar sa yayi, itama take tabi bayansa tana fa'din " _please Yayah toh ka rakani mana!!_ Bai waigo ba yace da ita. " _Saboda me kenan_ ? " _Ayyah plz Yayah, wanka.... nake so naje nayi kuma inajin....tsoro_ " Ta sake ro'konsa cikin jan magana sanadin ha'kin da ke damunta har yanzu. Sai cewa yayi da ita" _toh ni ina ruwana da wankan ki_ " Abayan sa ta tsaya lokacin yana cuming kansa, sai tayi fuskar tausayi tare da ran 'kwafar da kai gefe gashi dama 'dan gudun datayi yafara sata jin jiri daya ke ya ha'du da yunwa ga rashin 'karfin jiki ga maganan da takeyi yanzun sai yasa zuciyarta ya riga harbawa faster than d normal duk gaba 'daya sai suka ha'du suka canja reaction 'din ta atake sai ta fara ganin dishi-dishi, tuni hawaye ya gangaro mata asaman kuncin ta. Abbas sam be lura da yanayin da ta shiga ba dan ya riga ya juya mata baya, har ya isa wurin mirror ya 'dauko man dayake shafawa a'kafar sa ya zauna akan stool tare da fa'din " _zo nan inkina son in rakaki zo kimin wani aiki_ " Duk da yanayin da ta shiga amma tana jin ya fa'di haka ta taho a hankali zuwa inda yaken kamar yanda ya bu'kata. Shi kuwa 'kafar sa 'daya ya 'dago mata sannan ya mi'ka mata mai 'din tare da furta " _take this_ "! Teemah bata yi wani musu ba kanta a 'kasa tasa hannu ta kar6a dan ta riga ta fahimci manufarsa dan haka sai ta tsugunna tafara shafawa a hankali. Aranta take fa'din dole zatayi masa a yanzun kodan ya rakata ma, dan bata da wani bu'katan da ya wuce ta fita daga 'dakin nasa abubuwa dayawa take so taje tayi . Abbas kam yanda take shafawan slowly ba 'karamin birgeshi yayi ba, hakan kuwa yasa shi 'kura mata idanu yana kallon fuskarta, anan ya hango hawayen datake fitarwa, take kuwa ya janye 'kafar sa da sauri. Faruwar hakan kuwa ke da wuya sai ta 'daga kanta ta kalleshi, ha'da ido sukayi dashi kafin ta 'dauke nata idanun sai ya jefa mata tambayar " _me ya faru kuma ? Ba nace zan raka ki ba_ ?. Bata bashi amsa ba sai ta kauda kanta gefe tare da yun'kurin mi'kewa tsaye. Jiri ne ya 'debeta tana 'ko'karin fa'duwa sai yayi saurin tarota ta dawo jikinsa. Kan gado ya maida ita ya kwantar inda hawayen ta yaci gaba da gangara ta gefen idanuwan ta. Abbas be yi mamakin hakan ba dan yasan jirin nata harda yunwa ma musamman daya san cewa da kansa yasa an mata alluarar cin abinci. Dan haka da hanzari yafara 'ko'karin rabata da kayan dake jikinta da nufin idan ta watsa ruwa sai ya bata abinci zatafi jin ta normal sosai. Amma sai Teemah ta ri'ke masa hannu tana hanashi aiwatar da abinda yayi niyya tana mai 'kara sautin kukan ta. Hannun yabi da kallo ba tare da ya kulata ba sai ya cire hannunsa daga cikin nata ahankali tare da kamo hannayen nata duka biyu ya ri'ke cikin hannunsa guda 'daya, yasan idan yabiyeta zata ta 6ata masa lokaci ne abanza shiyasa gara yayi mata hakan. Skinny 'din dake jikinta ya janye shi gaba 'daya zuwa 'kasa tana mutsu-mutsu amma be 'kyale ta ba sai daya ga ya raba sa da jikinta sannan ya sake mata hannuwan ta. Take kuwa tafara 'ko'karin kare jikin ta dasu wanda hakan sai ya bashi dama ya cire rigar ma cikin sau'ki. Tana ganin haka kuwa ta juya ta kifu da cikinta a 'ko'karinta na ganin takare jikinta tana gunjin wani wahalallan kuka. Abbas ko 'kala be ce da ita ba sai da yaga ta kifun sai ya 'kara samun daman kai wa hannu yayi unhooking bra 'din dake jikinta sannan ya mi'ke tsaye. Wani 'dan 'karamin sabon towel ya 'dauko mata ya lallu6a mata daga bayanta. Tana jin haka kuwa ta kai hannu takama shi tare da 'ko'karin cusa shi a'kar'kashin ta sai da taga tarufe jikinta sannan ta tashi ta zauna tana 'ku'k'kuni. Abbas kam ko kula 'kala be ce da ita ba sai ma ya wuce bathroom ya ha'da mata ruwan wanka da kansa, wanda itama Teemah sai alokacin ta zare bra 'din ganin baya 'dakin sai tayi saurin cusa shi a 'kar'kashin pillow ta 6oyeshi. Tana ganin ya fito kuwa sai tayi saurin mi'kewa tsaye tana rarraba idanu tamkar mara gaskiya, wani sabon jiri taji na 'diban ta sanadin tashi da tayi a fizge sai ta kai hannu ta dafe goshin ta dashi tare da komawa ta zauna abakin gadon. Abbas ma da sauri ya 'karaso gabanta ya sa hannu da niyyan 'daukan ta amma sai tafara yi masa rigima, hakan kuwa yasa ya barta yace toh maza taje tayi wanka tafito yanzun nan. Teemah kamar gaske ta tashi tafara tafiya dan ji take data bar shi ya 'daga ta gara taje da kanta koma a yaya ne, taku biyar mai kyau batayi ba sai taji idanuwanta sunyi luuu, take taga duhu ya cika mata idanun. 'Kasa tayi da sauri ta zauna dirshan akan tiles tana maida numfashin wahala har yun'kurin amai tafara ji sai kuwa ta saki kuka tare da 'kiran sunan Mummy.. Da hanzari Abbas ya taho gareta shikan sa a'kage yake yaga tasa wani abu acikinta dan haka haka be yi wata-wata ba kawai ya cicci6e ta, take kuwa tafara yi mai rigiman bataso ya kaita gurin Antyn ta amma shi ko bi ta kanta ma bai yi ba, be direta ako ina ba sai cikin bathroom. Yana shirin sata a bathtub tayi saurin 'kan'kame shi da 'karfi sai ya kalleta ganin ta'kiyin magana yasa dole sai da ya sau'ke ta batare da ya saka ta acikin ba. Sai daya ajiyeta kafin ya tambayeta " _me ya faru_ ? " _Ni...da kaina zanyi_ " Ta bashi amsa da fa'din haka cikin wata shagwa6a66iyar muryarta. Da 'dan tsawa yace " _ba fah nason taurin kai ni, Allah sassa6a miki zanyi idan kika dameni_ ! Tana so ta bubbuga 'kafafu amma motsin kirki ma yanzu tsoron yinsa take yi saboda tsoron jiri ko ha'ki dan ha ka sai ta juya masa baya tana 'ku'k'kuni. 'Kwafa Abbas yayi yana kallon ta tsawon da'ki'ku, kawai sai ya juya ya fita daga bayin bata sani ba sai ji tayi ya rufo mata 'kofan da 'karfi. Sanadin haka kuwa yasa ta juyowa sai taga baya nan, gurin 'kofan ta isa tasaka lock sannan tazo tayi wankan ta anatse, sosai kuwa taji da'din ruwan daya ha'da mata data gama wankan nata sai ta sake ha'da wani me 'dumin tayi tsarkin ta dashi mai kyau sannan tayi niyyan fitowa tare da 'daura towel 'dinta. Rarraba idanu ta hau yi a bayin ko zata samu abinda zata rufa wa jikinta amma bata ga komai ba, tsaki taja ka'dan sannan ta 'dan le'ko da kanta tare da fa'din "Yayah! Yana bedroom 'din lokacin data 'kira shin yana 'ko'karin saka pyjamas. Hankali kwance kuwa ya amsa ta da fa'din " _uhmm_ " haka kawai yace da ita Sai ta kuma fa'din _Yayah na gama wankan_ " Yace " _toh me kike jira da ba zaki fito ba?_ Cewa tayi " _Ayyah Yayah towel ne fah kawai ajikina dashi zan fito ahaka_ ? Tsayawa yayi da abinda yakeyi yace " _da 'din aya ya kika shiga bathroom 'din_ ? Rage murya tayi 'kasa-'kasa tace " _ni gaskiya kunya nakeji_ !" Sai ji tayi yace " _kunyar wa kenan_ ? Shiru tayi ta'kiyin magana sai hararo hanyar 'dakin da tayi tana tura baki. Abbas kam jin tayi shiru yasa shi fa'din " _Look, Allah 30seconds kika 'kara abayin nan ni da ke ne yau agidan nan zakiga abinda zan miki, ba 'dazu an miki allura biyu ba, toh yanzu hu'du zan sa a miki try me kiga abin_ _mamaki_ "! Zaro idanu tayi waje tare da rufe bakinta kamar wacce tayi 'karya jin abinda ya ce 'din. Sarai ta tuna muguntar da yayi mata 'dazu har yanzu ma zafin allurar be daina ba ballan tana har guda kam ai mutuwa zata yi. Tunowa tayi da 30 seconds 'din da ya ce mata, wuf ta bu'de bathrum 'din ta fito tana wani sunkuyar da kai 'kasa. Abbas ma yi yayi tamkar be ganta ba kawai ya wuce parlour yabarta a'dakin. Kayan ta ta gani na bacci riga da wando da kuma packet 'din pad akan gado sai dai babu pant ita kuma ta wanke na jikinta. Bata tsaya mamaki ba kawai ta 'diba kayan ta koma bayi ta saka su ajikinta, dama yau bata da bu'katan pad sai de ko gobe dan period 'din ta yana bata hutun kwana da wuni 'daya akowani wata, so ko yanzun ma rashin pant 'din be dame ta sosai ba tun da kam tasamu kaya. Kayan kuwa light pink ne mai laushi , gaban rigar kuma bottles dark pink ne ajere da wani 'dan 'karamin flower daga gefen 'kirjin rigar, wandon kuwa yana da 'dan fa'di ka'dan, kayan basu da nawi, dama tana son kayan sosai musamman ma saboda laushinsu. Harta fito sai kuma taga rigar na fidda mata shape 'din 'kirjin ta sosai, haka ta saba sawa amma yanzun sai taga bazata iya fita gurinsa ahaka ba tunda ko mayafi bata da shi. Bra 'din ta ta 'dauko ta sake komawa bayin ta saka. Rashin kaurin kayan ma yaso ya hana ta sakewa, amma bata wani 6ata lokaci ba dan cikin ta har 'kugi yake yi mata saboda yunwa, tunanin ta ma inda zata samo abincin dazata ci a wannan daren. Yanke shawara tayi akan zata ro'ki Yayah ya rakata kitchen tasamu abinda zataci in yaso ko daga nan ma ya barta zata iya komawa 'dakinsu ita ka'dai. Tana fitowa kuwa sai ta ganshi tsaye ransa duk a6ace, a hankali ta 'karasa ta 'karasa bakin gado zata zauna, kafin ma ta zauna sai taji ya kama hannun ta kafin ta yun'kura kuwa taji yaja hannun dole tabi bayansa. A parlour kan dinning 'dinsa na marowatan nan in jita ya ajiyeta, ganin warmers da plates harma da spoons akan table 'din sai ta 'daga kanta ta ta dube shi , " Oyah eat" yayi maganan tare da nuna mata warmers. Abinci ne kala biyu tagani harda pepper soup 'din kayan ciki, ita kuwa duk basu mata ba sai ta bu'de ledan data gani a ajiye shima, fruits ne a ledan tana ganin haka kuwa ta kauda warmers 'din ta janyo fruits 'din ta tafara sha, dama bata jin da'din bakin ta sosai hakan yasa abu me mai ' ko sam bata sha'awar sa. Fruits 'din taringa ci tana za6an masu 'dan tsami tana sha, haka duk ta bi ta lalata kusan rabinsu dan in dai ta ta6a taji ba tsami toh ajiyewa take yi ta 'dauki wani. Tana cikin hakan sai ta ganshi tsaye akantsa hannun sa ri'ke da tea cup. Sosai ta tsorata dan ta zaci ze yi mata masifan 6arnar da tayi ne amma ga mamakin ta sai ta ga ya mi'ka mata 'daya hannunsa, kar6a tayi sai taga magunguna ya 6allo mata kafin tayi wani yun'kuri sai ya mi'ka mata tea cup 'din. 'Kamshin da tea 'din keyi ne yasa ta sha'awar shan sa, aikuwa taringa sha a hankali tare da maganin da 'da'd'aya har ta shanye su. Abbas kam beyi mamaki ba dan yasan halin ta dama da jarabar son fruits shiyasa ma ya sa aka kawo, yazaci ma zata 'danyi sha'awar peper soup 'din amma sai yaga bata ko kula shi ba. Yana ganin ta gama da maganin ya juya ya abinsa koma bedroom. Data ga ya juya ne sai tayi saurin dakatar dashi da fa'din " _Yayah toh tsaya ka rakani mana, na gama fah_ ! Ko kulata Abbas beyi ba yayi shigewar sa ciki. Teemah kam bata tashi ba sai da ta gama da shayin ta dire cup 'din, tayi zaman jiran sa na mintina, 5, 10 zuwa 16 mins zaton ta ko zai fito ne, ganin shiru har yanzu sai kawai ta mi'ke itama. 'Kofan taje ta duba sai taga ya kuma sake saka lock, inda taga ya 'dau key 'dazu nan taje ta duba amma bata ga komai ba dan haka itama sai ta koma bedroom 'din ta same shi. Ganin sa tayi kwance yayi 'da'd'daya agado, haushi yasa ta isa gabansa da sauri kamar wacce zata 'dau wani mataki amma tana isa kansa sai taja ta tsaya tace " _Yayah_ ! _Yayah dan Allah ka tashi ka rakani mana, su Ummah fah zasu_ ta _nema na, haka ma Hannah"!_ Shiru yayi tamkar beji ta ba sai tafara bubbuga 'kafafu a'kasa. Tashi yayi ya zauna, da taga haka sai ta sake fa'din " _Nifah Yayah bacci nakeji kuma ka'ki ka rakani ni atsaye zan kwana_ _ne toh_ ? " _in zaki iya kwana atsayen bismillah ai ban hanaki ba_ " Hawaye tafara tana 'ku'k'kuni 'kasa-'kasa. " _banji ba_ " yace da ita yana kallon ta. Kauda kai tayi gefe tace " _Allah Ummah fah da su Anty zasuyi ta nemana_ " 'Dan 'karamin tsaki yaja dan harga Allah rigimartan yafara isan shi sai ya fara 'Ko'karin sake kwanciya tare da fa'din " _Idan bazaki kwanta ba ki kama hanya kiyi tafiyar ki dan ni babu inda zani_ " Yana gama fa'din haka ya koma yayi kwanciyar sa tare da juya mata baya. Tsayuwan mintina sun kai ishirin tayi ahaka sannan a hankali ta shiga bayi, wani sabon brush data gani ba'a bu'de ba ta 'dauka tayi amfani dashi sannan ta fito. 'Dayan 6angaren gadon ta kwanta nesa dashi sosai tawani 'dosa na jikin ta kamar ace fita ta zura da gudu. Abbas kuwa be kula ta ba ko da yaga ta kwanta 'din ma sai da ya bata tazarar kusan rabin hour kafin ya tashi bayan yaji ta sauke ajiyan zuciya . Kakkashe dukkan hasken yayi sannan ya dawo gaban gadon, ganin har ta fara birgima yasa shi fa'din " _fitinanniya kawai_ " Space sosai yabada atsakanin su sannan ya kwanta. 👎🏻 *HA'KURIN NAN DAI DANA SANKU DASHI SHI NAKE SO KU 'KARA YIMIN, NASAN KUN SHA JIRAN GANIN POSTING AMMA KUKA GA SHIRU, NI KAINA KUNA RAINA....BA NUFI NA IN BA'KANTA MUKU BA KOKA'DAN, PLZ AYIMIN UZURI SABODA ALLAH* _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerhn ku ce* 😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir rahmanir raheem* _If couples who ar in love ar called *LOVE BIRDS,* then couples who always argue should be called *ANGRY BIRDS*..........._ 🅿 *77* Abbas kam ko daya kwanta 'din ma bacci kasa 'daukan sa yayi har kusan 'karfe 12:00 na dare. Tashi yai yayi alwala ya dinga jero nafilfili tare da addu'o'i sosai sannan ya kwanta. 'Bangaren Teemah kuwa bacci ya mata da'di sosai har bata san lokacin da ta gangaro jikin captain ta shige jikinsa ba. Har alokacin kuwa baccin be 'dauke shi ba, ganin ta dawo jikinsa ne yasa shi sakin ajiyan zuciya, kanta akan hannun sa ta 'dora, sai hakan ya bashi dama yake sha'kan dadda'dan 'kamshin da jikin ta ke fitarwa da kuma gashinta, a haka bacci yayi awon gaba dasu gaba 'daya. Da asuba Abbas ne ya rigata farkawa ganin bata motsa ba sai ya sau'kar da kanta dake kan hannun sa ahankali ya mayar mata kan 'karamin sweet design pillow dake kan gadon madadin hannun nasa sannan ya tashi. Alwala yayi ya wuche masallaci domin gabatar da sallar asubah. 'Karfe biyar da rabi ( 5:30am) Teemah ma ta farka. A hankali ta bude idanun ta sai taga ita 'daya ce a 'dakin, tashi tayi da sauri ta nufi bayi ta 'dan kintsa kanta a gaggauce sannan ta fito da sauri ko mayafi bata tsaya nema ba ta fice abinta. Allah ya taimake ta kuwa daya fita abu'de ya bar 'kofan hakan sai ya bata daman fita cikin sau'ki. Har a lokacin gari be gama yin haske ba amma a hakan da duru-duru ta nufi 'dakin su. Hannah na kan sallaya bayan ta idar da sallan asubah sai taji an turo kofa an shigo, waigawa tayi sai taci karo da ita kamar an koro ta ta shigo kanta ko 'dan kwali ma babu. Tashi Hannah tayi da sauri ta tareta tana murmushi tare da zaro idanu tace " _Ah'ah amaryar Yayah ya haka da sassafen nan kuma kamar an koro ki_? Teemah ko kula Hannah batayi ba ta wuce kan gado ta kwanta tare da jan blanket ta rufe jikin ta dashi, tana shirin juya wa Hannah baya sai Hannah ta dakatar da ita da fa'din " _Haba Amarya har da nine a fa'dan amarcin_ ? Sai yanzu Teemah ta bu'di baki tace " _Hannah plz ni ki 'kyale ni, Allah bansan damuwa ki barni nayi bacci na, ina kam jiya 'kin_ _zuwa nema na kika yi dagangan kika barni na kwana acan bayan sarai kin san halin Yayah da masifa ba rakoni zaiyi ba_ "! " _Yanzu dana barki kika kwana acan din me yasame ki? Baga shi kin 'debo lada ba, ke dama zaku tafi tare da shi toh miye abin fushi dan kin kwana 'daya awurin sa_ ? Hannah tace tana kallon ta. "Bazaki gane ba ne ai Hannah dan ba ke bace" " _oh o o'oh barni da Bilalu na ni kam kuje can ku 'karata keda wannan dodon mijin naki_ "! Hannah tayi maganar tana kokarin tashi tsaye. " _ai naje amma Yayah ya hana ni ganinki sai ma ya wani ce dani bacci kike yi irin ke ga me mijin nan.....nima ai barina kika_ _yi anan 'din na kwana ni ka'dai bayan kinsan su Rauda ba kwana zasu yi anan ba_ _amma kika tafi, in hakane nima nayi fushin mana_ " 'Kasa-'kasa tace " _Sai kije ai ki gaya masa wannan kuma, dan nima tsintar kaina kawai_ _nayi acan_ " Juyawa Hannah tayi tana wa Teemahn murmushi irin na tura haushi tace " _may be sace ki yayi babu wanda ya sani_ !" " _Mtheww_ " Teemah taja tsaki tare da gyara kwanciyar ta da kyau. 'Karfe shida cif Abbas ya dawo sai ya tarar bata nan, amma be wani damu ba dan dama yasan matu'kar tasan cewa 'kofa abu'de yake toh bazata zauna a dakin ba. Kai ya jijjiga kawai lokacin da ya ga yanda ta tafi ta bar gadon batare da ko gyara shi tayi ba, yasan duk cikin saurin barin 'dakin ne yasa ko tsayawa ta gyaran batayi ba. " _Allah ya shirya_ " Yace a zuciyar sa, da kansa ya kintsa akin sannan ya koma parlour ya 'dau ko wayar sa da tun jiya ya barta anan. Ogansa ya 'kira suka gaisa inda yayi masa murna tare da sanya masa albarka acikin auren da yayi. Ya 'kara da fa'din be samu ya halacci bikin ba lokacin yaje duba yaron sa ba lafiya ne shiyasa amma yayi ha'kuri. Godiya Abbas yayi masa dan ya tura masa sa'ko musamman yasa aka kawo mishi. bayan haka ne suka yanke 'kiran. Daddy ya kuma 'kira suka gaisa shima yayi musu ban gajiya tare da fatan alkhairi wa auren da suka je 'daurawa. Yana shirin ajiye wayar sai ga 'kiran Saleem kamar yasan yana kusa waya a dai dai lokacin, domin tun jiya yake 'kira amma Abbas 'din be 'dagawa. Yanzun kuwa 'dauka yayi ya kai kunnan sa tare da yin shiru dan yasan meze biyo baya, ai kuwa Saleem 'din cewa yayi " _Girman ka ne yalla6ai ,gaskiya najinjinawa zumuncin ka_ " Shi kansa Abbas yasan be kyauta ba amma sai ya basar yace dashi " _Ya akayi ne Saleem ka 6uya fah?_ Ya fa'da a wani tsare. " _Kai ka bari kawai maza sai a hankali wallahi, amma gaskiya ni banji da'din abinda kamin ba, ya za'a yi auran ka amma kawai sai de inji anyi ba wani labari_ !" Shafo kansa yayi tare da fa'din " _ohh sorry Saleem abin ne yazo unexpected in just 1 week Daddy ya yanke lokacin shiyasa, amma agafarce ni"_ Saleem cemasa yayi " _Bakomai Cpt. yawuce girman kane ai, me ake shirya mana ne ina fatan za'a yi Sword_ _crossing kasan mu ta nan muka fi 'karfi_ " Juya kai Abbas yayi yace " _gaskiya bawani COS da za'a yi nima yaushe na nutsu Saleem, an shirya a Rivers amma inajin ba zai yiwu ba dan bazan samu zuwa ba. Amma may be ayi dinner yau in ya yiwu a nan Abuja inaga shi ka'dai ma ya isa nagaji da hayaniyan nan Allah gaba 'daya Saleem_ " " _Haba mana Captain......ko da yake bari sai na iso kawai nima da yaddar Allah yau_ _zan shigo_ " Cewar Saleem. Abbasa ma sai yace masa " _okay, ba matsala, sai ka iso_ " Yana cire wayar a kunnen sa yaja tsaki aransa yace " _bawani crossing na sword da za'a yi, haka kawai gardawa daku_ _ku saka yarinya atsakiya kuna faman 'karewa halittar jikin ta kallo_ _a banza_ " ***** Ba Teemah ta tashi daga baccin ba sai 'karfe tara na safiya ta gota, tana tashi kuwa Anty kamar jira take tazo ta ha'da mata ruwan wanka na ha'din turare tace tayi dashi. Zama tayi bayan shigan Teemah wurin wankan ta tallafi kanta da hannayen ta duk biyu tana tunani. Anty na jin 'kunci azuciyar ta fiye da zaton mutun musamman da tasan cewa yau Abbah zai yi aure abinda be ta6a ko kwatan ta zancen shi ba tun farkon rayuwar su har Allah ya kar6i ran Mahmud sai gashi Allah cikin ikon sa rana tsaka kamar wasa ana shirin 'daura auren sa da wata daban. Bazata ta6a fasa yi musu fatan alkhairi da zaman lafiya ba, dan koma menene yafaru laifin tane, she caused everything, dan haka ita a yanzu bata da wani buri illah taga 'karshen rayuwar ta tayi kyau kawai fatan ta Allah ya fe mata kurakuran ta na baya. Tana zaune tana tunani har Teemah ta fito daga wanka bata sani ba. Teemah tayi mamaki sosai da taga ta 'kira ta har sau biyu amma bata amsa ba hakan kuwa yasa ta matso dab da ita ta furta " _Anty_ "! Da 'dan 'karfi. Firgigi tayi tare da sakin ajiyar zuciya kana tace " _har kin gama wankan ne? Kinyi da kyau kuwa?_ Tayi maganar tare da 'kwa'kulo murmushi ta sanyawa fuskar ta. Cikin sanyin jiki Teemah ta amsa mata da fa'din "eh _h nayi mei kyau, Anty me yafaru ne naga kinyi shiru kina tunani?_ " _Hmm, bakomai Fatee na kawai ina tuna halin rayuwa ne yanda duniya ke juyawa damu, yau gashi Fateemah na ta sake zama matar wani karo na biyu"_ Anty ta tayi maganar tana mai sunkuyar da kanta kasa bata so Fateemah taga rauninta koka'dan musanman da yanzu ta tuna da marigayi gudan jininta Mahmud. Teemah kam tsayawa kallon ta tayi kawai dan sam bata yarda hakan shine a zuciyan Anty ba, domin 'karara damuwar ta ta nuna a fili kan fuskar ta. Ganin da Anty tayi Teemah tayi shiru sai ta kamo hannun ta dawo da ita gaban mirror ta zaunar da ita kan stool tare da fa'din " _Zo zauna in gyara miki gashin kin nan kafin mai kwalliyar ki tazo_ " Teemah yanzun ma shiru tayi ba ta furta komai ba damuwar ta be wuci ganin sauyin yanayin Anty datayi ba, tana so tasan ainihin dalilin hakan amma tasan Anty idan ba tayi niyyah ba bazata ta6a sanar da ita ba, inda tayi niyya ne da tun ma kafin ta tambaya da da kanta zata sanar da ita. Tsinkayar muryar Antyn ta tayi tana fa'din " _Yarinta ta girma 4d second time, nauyin auren ya sake hawa kanki, amma kin san me nake so dake Mamana_ ? Kai Teemah ta jijjiga mata ahankali alamar " _ah ah_ " Rage murya Anty tayi yanda bakowa ne zaiji su ba sai in kana kusa cikin natsuwa tace " _Kinsan Yayanki Abbas shine mijinki ko?_ Ahankali Teemah ta bata amsa da fa'din " _ehh nasani Anty_ " Anty cewa tayi " _Yauwa uwata, ina fatan zuciyarki ta kar6i hakan baki ji cewa an takuraki_ _ko shiga hakkin ki ba ko_ ? " _Ah ah banajin hakan koka'dan Anty_ " Da sanyin muryarta ta bata amsa. " _Alhamdulillah_ " Anty ta fada harda lumshe idanu dan yanda taji da'di da kar6an auran da Fateemah tayi. Afili kuwa Antyn cewa tayi. " _naji dadi Fateemah, nayi farin ciki sosai, ni kaina na rigaki kar6an auren nan tun ma kafin a ha'da shi, da kaina Fateemah na hangi 'kauna_ _da kishin ki tattare da Abbas kuma nasan da iznin Allah_ _rayuwar auren ku sai ta bada sha'awah watarana!, inaso koda kin koma gidan auren ki dan Allah Fateemah ki ri'ki_ _ibadar ki kinji, ki ro'ki Allah akan komai zai miki maganin koma menene, karki yadda ki kai kukan ki wurin kowa koda kuwa meze faru dake domin kuwa Allah kadai_ _ne mai taimakon da babu wanda ya isa ya miki makamancinsa_ _sai shi din nan dai Allah mabuwayi, Fateema rayuwa ta aya ce awurin_ _ki ai nasan kinsan duk abinda yafaru dani, 'karshe wa gari ya_ _waya?_ _Niice da kaina nayi dana sani nayi Allah wadai da halina!Mijin ki mijinki ne Fateema kuma_ _sirrin kine, 'yan uwan sa kema nakine dan ma kinga ai duk dangin_ _mijinki jininki ne dole ne ma ki so su koda babu aure a tsakanin ki da Abbas ballantana_ _kuma aure ya 'kara ha'da ku, ki so su ki kauna ce su sosai, ki girmama 'karfin_ _zumuncin dake tsakanin ku kar kiyi watsi da shi"._ " _Nasan auren ku auren ha'di ne na iyaye wanda za'a ce dukkan ku ba shiri yasame ku, amma dukkan ku kunyi_ _biyayya kuma na matukar jinjina muku, amma ki sani dole ne sai kinyi ha'kuri dan auren ha'di na tafe ne da wasu irin rikitattun abubuwa_ _wa'danda sai wanda ya ta6a faruwa dashi ne ka'dai zai gane su, ba zance bakwa son junanku_ _ba dan ban shiga zu'katan ku nagani ba amma nasan dole ne sai kin fuskanci wani 'kalubale daga mijinki wanda ha'kuri ne ka'dai_ _zai iya magance miki su, Fateema kiyiwa mijinki biyayya, bansan taurin kai da rashin kunya banda_ _musu da jayayya dashi kinji? na tabbata idan kika ya'ki zuciyar ki kika kuma dogara ga_ _Allah komai zai zo miki da sau'ki amma sai kin daure sosai kinji?_ Ahankali ta 'dagawa Anty kanta dan duk kalaman Antyn sun sa jikinta yayi sanyi matu'ka, duk abinda Anty ta fa'da gaskiya ne sai dai ita can 'kasan zuciyarta take jin ta shiryawa zama da shi a kowani irin hali. Anty cewa ta sakeyi " _Yauwa uwata Allah ya miki albarka, yasa haske arayuwarku har illah masha Allah_ " A saman la66a Teemah ta amsa da fa'din " _Ameen_ " " _Bansan me yasa nake jin da'din wannan auren naku ba har azuciya ta ba, inaji ajikina da iznin Allah auren ku akhairi ne,dan haka_ _ki bawa mijin ki kulawar data dace kinji_ ? Kai ta 'dagawa Antyn tana me sake sunkuyar da kanta. Anty data fahimci taji kunya sai ta yi murmushi kafin tasake yin wata magana kuwa sai ga mai shirya Teemah ta iso da sallamar ta abakinta tare da wata mata abayan ta. Amsawa sukayi dukkan su Anty sai ta mi'ke tare da gabatar musu da kayan da Teemah zatayi amfani dashi a yanzun sannan ta bar 'dakin. Abbas wanka yayi, ya shirya cikin wani shadda golden brown, ajikin babbar rigan kawai akayi aiki da coffee 'din zare wanda ya 'kara haska kayan sosai hakama a jikinsa sai annuri yake yi da sheki sosai kayan ya kar6i jikinsa, yana shirin fita kenan sai ga abokansa sun shigo, take kuwa suka fara yi masa tsiya akan tun jiya ya tafi ya 'kyalesu ko dai amarya ce ta ri'ke shi. Shiru yayi musu kawai har suka gama be kula su ba, dan shi be iya irin wasan nan ba be ma san me ze ce dasu ba. Sai da sukayi suka gaji har sukayi shiru, daga baya suka fara hira normal sannan ne yasaka bakin sa aka 'dan ta6a hirar da shi. Anan aka kawo musu kayan break fast sukaci gaba 'daya still suna masa tsiyan na gaba sai agidan amarya. Wannan karan kam murmushi Abbas yayi dan indai akan girki ne bazata bashi kunya ba saboda yasan Mummy bata barta haka nan ba. 'Daya daga cikin su ne mai suna Auwal ya tashi ya shiga ciki dan yana so yayi using bathroom, ai kuwa anan yaci karo da pant 'din Teemah da ke shanye a bathroom 'din, har Allah-Allah yake kuwa ya fito dan ya baza kanu, aikuwa yana fitowa yaje gurin Abbas ya bashi hannu tare da fa'din " _mazaah!!, ashe angon cewa kayi yau din shiyasa naga kana ta shan 'kamshi!_ " Kallon _me kake nufi_ yayi masa ha'de da harara yace " _ban son iskanci Auwal toh haramun nayi? Me ma kaje yi min acikin 'daki?_ Dariya duk sauran suka kwashe dashi suna nuna Abbas 'din, sosai yaji haushin hakan duk dama abinda suke zato 'din be faru ba amma ai wannan sirrin sa ne damuwar sa ma shine ya akayi har wannan tunanin yazo ran Auwal har haka, yariga yasan kayan ta data cire jiya ba'a fili yake ba sannan shi be ga wani abu a'dakin da zai sanya har mutun yayi masa wannan tunanin ba. Basu wani da'de bama suka tafi, Abbas be bisu ba. Suna tafiya kuwa yayi hanzarin shiga bedroom 'din yafara investigating 'dakin, still shi be ga komai ba dan hatta su bangles da earings 'dinta da sauran su ma ba'a fili suke ba balle yace ko dan sune tunanin sa ya bashi cewa wani abu yafaru, sai dai ko in Auwal bincike yayi masa har yaga wani abin mace shiyasa yayi masa wancan tonon sililin... Tunaninsa ya tsaya ne lokacin da ya bu'de 'kofan bathrum idanunsa suka sau'ka cak akan jan pant 'din ta dake shanye tun jiya abayin. Wani 'kululun ba'kin ciki, haushi da takaici hade da kishi ne ya tokare sa, sai yanzu ne ya fahimci asalin abinda Auwal ya gani da har tunanin can yazo masa. Tsaki yaja tare da jan 'kofan bayin ya koma parlour. Waya ya 'dauka ya 'kira layinta ta kuwa 'dauka dan lokacin already an gama yi mata kwalliya tana zaune da wayar a hannun ta. " _Hello_ " tace ahankali. " _Me kike yi_ ? Yace da ita a kausashe. itama tace " _Ba komai_ " " _maza ki zo yanzun nan karki 6ata min lokaci_ " Be jira jin amsarta ba ya ending call din. Teemah baki ta tura gaba ta kalli inda Hannah take tsaye tana rage kayan jikinta sai kuwa suka ha'da idanu, Hannah da bata gani tayi shiru sai tace " _Ya daga amsa waya kuma kin fara fushi ince dai lafiya?_ Amsa ta bata da fa'din " _Ba Yayah bane yace wai inje_ "! Hannah sai cewa tayi " _Dodo yayi kira kenan, sai ki tashi ki tafi ai kinsan angon naki sai ahankali inajin be gaji da ganin ki bane kika gudo"_ Kalan tausayi tayi tace " _Dan Allah Hannah kije ko kuma 'kira shi kice masa 'kafata na ciwo....._ Tare ta Hannah tayi da fa'din " _Ah ah sai de ince masa 'kin zuwa kikayi..._ Sake marairaicewa Teemah tayi tace " _Haba dan Allah Hannah_ " " _ni baruwana kinga tsakanin ku ne, yanzu fah mijinki ne kun fi kusa, daina sani a shirgin ku please_ " Tana maganar ta nufi bathrum. " _Hannah toh dan Allah tsaya ki raka ni mana_ " " _Daya 'kira 'din yace miki kije ke da Hannah ne, i thought amarya_ _ka'dai ya nema_ ! Tana gama fa'din haka tashige abinta tana dariyar mugun ta. Teemah sharewa tayi kawai ta tashi ta wuce wurin Mummy dayake dama tun safe basu ha'du ba, Mummy da bata san me ake ciki ba sai ta zaunar da ita ta ringa yi mata nasiha kawai akan biyayyar aure. Anan Hannah tazo ta same ta dan tana gama wankan ta taho 'dakin da Mummy take anan take shiryawa tunda aka fara biki, sai kuwa taga Teemah tawani bararraje tana hira. Hannah cewa tayi " _har kinje 'kiran Yayan kin dawo ne_ " Da gangan ta tambaya dan tasan it's hardly ace Teemah taje batare da tayi taurin kan nan nata ba. Harara Teemah ta banka mata tare da ha'de ranta. Muryar Mummy tajiyo tana fa din " _na me kenan_ ? 'Kasa Teemah tayi da kanta ta rasa me zatace dan tuni ta hango 6acin rai a fuska da muryar Mummy, gashi ita ba kowani lokaci ta iya shirya 'karya ba ballan tana ta fidda kanta. Mummy ne tasake fa'din " _Teemah karki kuskura kice min Ya 'kiraki ne baki je ba kika yo nan"_ "' _Karyan Hannah ne fah...Mummy naje ni... tun 'dazu"!_ Tayi maganar kamar zatayi kuka. Mummy juyawa tayi ta kalli Hannah ta ce " _da gaske ne wai Hannah abinda ta fa'da_? Hannah sai da ta kalle ta suka ha'da ido sai ta kawar da nata idanun tace " _Bawani nan Mummy yanzun nan ne fa dazan shiga wanka ya 'kiratan_ " Mummy dawo da kallon ta tayi wurin Teemah tace " _na 'kirashi na tambaye shi kin yarda_ ? Da sauri ta jijjiga kanta alamar " ah ah"ta 'kara da fa'din " _Allah Mummy Yayah allura yake sawa ayimin fah_ " " _Bana son maganar banza Fateemah alluran saboda lafiyar waye akeyin ta?_ Shiru Teemah tayi ta sunkuyar da kanta 'kasa tana ta juya hannayen ta cikin juna. " _Ina tambayarki_ "! Mummy ta daka mata tsawa. Afirgice tace " _saboda... nii....ne_ " " _Toh 6ace min a'daki na tunda ke kullum kunnen ki bana jin magana bane kije kiyi tayi, kuma saura inji cewa baki jeba_ " Tashi tayi sum-sum ta kama hanya tana bankawa Hannah uban harara kamar idanun ta zasu fito. Hannah kam sai gwalo take yimata tana 'karawa har suka daina ganin juna. Aranta tace " _kiyi ha'kuri 'yar uwata ina sonki sosai kuma inason ganin kina farin ciki, amma nasan matu'kar kika ci gaba akan haka toh bazaku shirya da Yayah ba ni kuwa *BURINAH* inga kun gyara auran ku kun rayu kamar kowa"_. Fitan Teemah kenan sai ta ha'du da Anty, take ta jefa mata tambayar ina zata kuma haka? " _ba Yayah bane yace wai inje kuma fah Anty allura yake sawa ayi min_ " Cikin shagwa6a tayi maganar tana turo baki. Murmushi Anty tayi tace da ita " _Habah kuma yarinyata da akeyi miki alluran bakiga kin fi samun sau'ki bane, maza kiyi_ _sauri kije kar ki 6ata masa lokaci_ " Haka ta juya ta tafi tana 'kun'kuni har ta isa. Ciki-ciki tayi sallama haka kuma shima ya amsa mata ahankali. 'Karasowa ciki tayi sai ta tarar dashi hakimce a kujera tamkar wani sarki, ba 'karamin kyau yayi mata ba amma sai ta ta6e baki tare da kawar da kanta gefe. Inda yake ta'karaso ta ce " _ina kwana Yayah?_ Abbas kam wani yanayi na 'kauna da shauki ne yayi nisan tafiya da shi hakan yasa be ma ji lokacin da ta gaishe shin ba, ita kuwa bata 'kara ba sai ta ci gaba da tsayuwan ta. Tunaninsa na dawowa sai ya kauda da kansa batare da ya sake kallon ta ba yace " _kinyi breakfast ko_ ? " _Uhmm_ " tace dashi. " _Me kika ci_ ? " _Chips da...._ Kafin ta 'karasa ma yatare ta da fa'din " _D'auko maganin ki ki kawo ingani_ " Wucewa tayi cikin bedroom 'din nasa ta 'dauko maganin saman drawer ta kawo masa. Maganin ya 6alla ya bata ta kar6a tasha, har zata tafi ma ganin cewa dan maganin ne ya kirata kawai sai taji yace da ita ta wuce bathrum ta 'dauke wannan abin nata da bari kuma karta kuskura ta sake amfani dashi, in kuwa ta 'kijin magana shi da ita ne. Zuwa tayi ta dudduba dan shaf ita ta manta da pant 'din ta nan, tana gani kuwa ta hau gungunin " _ina ruwansa da abuna toh, dama me yakai idonsa wurin da har ya gani._ ? Haka tazo ta wuce shi tana tura baki. Shima binta yayi da kallo harta fita, sai ya jijjiga kansa. ***** 'Karfe 11:07am na ranar aka 'daura auren Abbah da amaryar sa Halimatus Sadiya, 'kanwa ga Hajiya Aisha matar abokin sa da tayi siyayyan kayan auren Mahmud. Anty Sadiya 'yar kimanin shekaru 31,kuma bazawara ce da mijin ta ya rasu ya barta da yaranta maza biyu, bayan rasuwar sa kuwa dangin sa sai suka kar6i yaran a hannun ta suka ri'ke agurin su. Sam bata da matsala koka'dan, tana da hankali da nutsuwa, uwa uba ilimi ingantacce ya wadace ta boko da arabi, ga ta da son mutane da kuma yawan kyautata musu, wanda wannan dalilin ne yasa Abbah da kansa yayi sha'awan auren ta domin ya sa6unta rayuwar gidan shi da ya kafu shekaru da dama da suka shu'de. Ahalin yanzu kuwa burin Abbah yariga yacika domin an 'daura auren da Haleeman sa, bawai dan baya son Anty ba ah'ah sai dan kawai yana so shima rayuwar gidan shi ta canja. ***** 'Kayataccen Dinner aka shirya wanda tsirarun mutane ne suka halatta saboda ba gaiya sosai akayi ba, shima 'din Abbas be wani 6ata lokacin sa ya gaiyaci abokansa ba wa'dan da suke kusa dashi ne suka sani su 'din ma yawanci friends 'din sa na secondary school ne. Daga wurin dinnern aka wuce da amarya zuwa sabon gidanta da ke....... _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated to my fans all over media_ 😍 *Bismillahir rahmanir raheem* _Failure is neccessary 4 any learning curve......_ _Failure makes u stronger, bolder and_ _less scared of taking risks......._ 🅿 *78* Daga wurin dinner sai aka wuce da Teemah zuwa sabon gidan ta dake Maitama. Duk kushen mai kushe be isa ya kushe gidan Teemah ba, dolen sa sai ya bawa wannan gidan yabo ta musamman domin kuwa ko acikin ayari ba ze baka wahalar warewa ba, iya ha'duwa gidan ya ha'du matu'ka da duk wani abu da 'dan Adam yasani na more rayuwa, Ba stairs bane gidan plat house ne dan'karere, sai dai 'dakuna uku ne kacal agidan da kuma babban parlour 'daya dake tsakiya, sai babban kitchen dake daga can hanyar wani corridor da zai fitar da mutun har bayan gidan inda wani 'kayataccen lambu yake gwanin birgewa.... I can't even describ ths house 4u clearly, but u urself should imagine it, koma yaya tunanin ku ya baku just take it as if daku aka shirya komai na gidan. Abbas da kansa ya rakata har 'dakin ta lokacin 'karfe 7:30pm ne, ko tsayawa be ba ya barta ya fito ya shiga nashi 'dakin dake nesa ka'dan da ita. Itama binsa tayi da idanu har ya shige ciki. Teemah kam Abbas na shigewa sai ta tura 'kofar ta ta fara cire 'kayatacciyar shigan da akayi mata na fitan dinner party 'dazu. Sosai irin wannan dressing 'din auren suka isheta, dan kayan na takurata da nauyi, sai da ta cire gaba 'daya kayan kafin ta nutsu kuma sai alokacin ne hankalin ta yadawo jikin ta, kawai sai ta saki baki tana 'karewa ha'duwa, kyau da tsaruwan 'dakin da Yayah Abbas ya ambace shi da suna nata ne. Tashi tayi tana juyi tare da murmushi " _wow_ " tace tare da daka tsalle dan ganin dream bed design 'din ta a'dakin kamar an shiga zuciyarta an gani, most especially colour 'din bed 'din fari ne tas sai akayi masa kwalliya da orange colour daya 'kara haska shi, colourn paint 'din entrance door dana bayi ma duk farare ne, hakama tiles 'din dake 'kasan 'dakin shima fari tas, wani shegen ha'da'd'den labile aka sanya a'dakin orange colour mai matu'kar birgewa. Sosai 'dakin ya tafi da imanin ta haka tayi tsalle ta fa'da kan gadon tana murmushin farin ciki, ta zubawa farin ceiling fan 'din dake saman 'dakin idanu. Mummy da Daddyn ta ne ka'dai suka san best colour 'dinta akaf fa'din duniya sai ko Yayah Abbas dan ta ta6a fa'da masa da jimawa tun suna damaturu lokacin daya je hutun aikinsa acan, bayaga su ukun nan kuwa babu wanda yasan favourite colour 'din ta har yau, hatta Hannah ma bata sani ba, amma acikin su ukun bata san waye ya yi mata wannan kyautar ba koma waye ita kam yasata farin ciki mara iyaka. Shab tama manta da cewa ba kaya ajikin ta duk ta cire su, tana kwancen tana ci gaba da 'karewa 'dakin kallo kawai sai ta ji 'karan sau'kan ruwan sama lokaci guda tamkar da bakin 'kwarya. Afirgice ta tashi ta zauna tana rarraba idanu sam bata san da akwai hadari har haka agarin m bama ita, sai sau'kan ruwan kawai taji. Tashi tayi tafara duba abinda zata saka ajikin ta amma ta kasa samu sai masu nauyi ita kuma basu take so ba, da 'kyar hannun ta ya jawo wata figigiyar riga ja mai sharara bata ma ko wuce mata gwiwa ba amma ahaka cikin hanzari ta saka shi ajikinta. Tana gamawa saka wa sai ta fara duba wani 'dan viel da zata rufe kanta dashi sai kawai taji 'karan thunder mai 'karfin gaske irin mai razanar wan nan ha'de da wal'kiya mai haske. A 360 ta fito a'dakin tana toshe kunne ta nufi 'dakin da taga ya shiga 'dazu, duk taku 'daya da takeyi tsoro ne yake sake kamata da haka har ta isa 'dakin. Tana zuwa kuwa dai-dai shima ya bu'de 'kofan nasa sai sukaci karo dashi, jikin shi ta shige tana kakkarwan tsoro shima dayaga haka sai yasa hannun sa ya rungume ta ajikinsa sosai. Tsawon mintina 8 tana faman sau'ke ajiyan zuciya sannan ya 'dago ta ganin kamar ta 'dan nutsu. " _Me yafaru ne wai? Me yasa meki_ ? Tambayar daya jefe mata kenan tare da jijjiga ta. Cikin in in ta bashi amsa da fa'din " _Yayah ni tsoro nake ji sosai_! " " _Tsoron miye kuma? ke bazaki bar shirme ki girma ba ko_ ? _Ba gani nan agidan ba babu wani abin tsoro agidan nan da ze kamaki, ko kinga_ _wani abu ne_ ? Kai ta jijjiga masa sai tace " _thunder nake tsoro_ ! " _Toh ai baya kama mutun shi, oyah jeki 'dakinki ki kwanta ki huta ko zaki ci abinci?_ " _Ah ah_ " Tace dashi sai yace " _toh jeki ki huta kinga yau akwai sanyi kar ya shiga jikin ki!_ . Teemah kam kuka ta sanya mishi tana bubbuga 'kafafu a'kasa tace " _ni wallahi tsoro nake ji ni ka'dai!_ " _Wai ya kike so in miki ne toh, umm_ ? Ya fa'da yana kallon ta. Shiru tayi bata ce komai ba, ganin haka yasa ya juya ya koma ciki dama dubota zeje yi dayaji 'karan yasan sai ta tsorata sai kuma suka ha'du ashe be yi 'karya ba. Binshi itama tayi abaya tana tafiya tana waiwaye kamar irin wani abu na binta abaya 'din nan. Duk da tana cikin firgici amma hakan be hana ta ganin kyaun 'dakin sa ba, compared to nata ma ai nata bakomai bane, hakama bed size 'dinsa ba irin nata bane, ya zarce nata da girma, nashi komai fari tas aka sanya mishi, curtain ne ka'dai mint green da zanen fulawowi su kuma dark green ajiki. Abbas yana zuwa ya wuce bathroom ya 'dauro alwala, koda ya fito ma kallo 'daya yayi mata ya kauda kansa ya wuce ga dadduma, sallah ya gabatar kusan raka'ah shida sannan ya 'daga hannunsa ya dinga jero addu'o'i wa'dan da bata san iyakar su ba. Teemah tun tana kallon sa har ta gaji ta lalla6a ahankali zuwa bakin gadon ta kwantar da kanta amma 'kafafun ta na a'kasa ahaka bacci yayi awon gaba sa ita. Abbas ne daya idar da sallahn yazo inda take ya tsaya akanta sai yanzu yaga tsantsan kyau da tayi cikin rigar dake jikinta, ahankali yakai hannu ya shafi gashin kanta har ya fara yawo da hannun nasa akan nata sai kuma wani abu ya 'dar su aransa, da sauri ya cire hannun yana kallon hannunsa kamar wani sabon abu ne. Tashi yayi ya tsaya akanta ya 'kura mata idanu yana so ya kauda sa'kar haukan da zuciyarsa ke haska mishi amma ya kasa, ahankali ya gyara mata kwanciyan da kyau ya lullu6e ta sannan ya koma 'dayan gefen ya kwanta shima. Bacci kasa 'daukan sa yayi ya zubawa fuskar ta ido yana ta sa'kar zuci, sam baya son hakan ya dinga zuwa ransa amma bazai iya ba, gashi yakasa kauda tunanin nan aransa. Kishi ne ko shai'dan koma miye ke sarrafa zuciyarsa yakasa ganewa. Ranar Abbas har makara yayi na zuwa masallaci, lokacin da ya tashin kuwa Teemah na jikinsa kamar de jiya haka yau ma tayi, sai ya 'dan bata glance ka'dan dai-dai kuma itama ta bu'de idanun ta caraf sai sukayi 4eyes dashi, wanda motsin da yayi ne ya farkar da ita daga baccin da take yi. Take ta diririce ta fara kalle-kalle ganin yanayin kusancin dake tsakanin su dashi yasa da sauri ta tashi zaune tana sussunkuyar da idanun ta 'kasa dan ta fahimci itace, laifinta ne. " _Mage ce ke ko_ ? Taji ya ce da ita Yayi maganar bayan ya tsareta da kallo. Kai ta jijjiga masa tana 'kif-'kif da idanu, maganar tasa it's clear that ita mai son jiki ce, haka yake nufi kuma ta fahimta amma sai ta'ki bawa kanta laifin ita ka'dai, asace take duba 6angaren daya kwanta itama ko zata ga space 'din daya bari abaya ya matso amma sai bata ga komai ba. Abbas be sake kulata ba dayake ma be fahimci me take yi ba gudun kar ya makara yasa ya mi'ke ya nufi bayi yana tunanin irin shegen son jikin datake da shi ga uban birgima kamar wata yarinya 'karama. Har ya shiga bayin ya gamo abinda zai yi ya fito tana nan zaune awurin kamar yanda ya barta 'dazu. I'kama ya tayar ya gabatar da Sallar sa cikin nutsuwa tare da yin addu'o'in azkar 'din sa cikakke. Al-qur'ani ya mi'ka hannu ya 'dauko saman drwaer ya bu'de suratul A'araf ya fara karatun sa cikin sauti mai da'din sauraro tamkar bashi ne Abbas ba mai jin kai da rashin son maganan nan ba, qur'ani kenan, zancen Allah mai abin mamaki, duk wani girman kan ka ,miskilanci da 'kafafan ka duk rashin iya hausan ka da 'karfin da harshen ka keda shi akan yaren ka but when it's comes to it (QUR'ANIL KAREEM) dole harshen mu ya dawo iri 'daya. Karatun nasa ba 'karamin shigan ta yake yi ba, hakan yasa ta koma ta maida kanta akan pillow tana sauaraon sa tare da zuba masa idanu, wani 'ka'k'karfan ala'ka take jin zuciyarta na 'kulla mata game da Abbas 'din sai take jin tamkar he is the only man in d entire universe take wani sabon babin 'kaunar Yayan nata ya shige ta take jin shi 'din na daban ne, kamar kar ya 'kare karatun haka take ji. Ko da ya 'kare karatun kuwa sai ya sake bu'de wani page daga cikin 'karshen Al'qur'anin yafara karanto addu'ar da ke rubuce a ciki wanda akeyi bayan an gama karanta Al'qur'ani mai girma ( Du'ah 'u Khatmil Qur'an). Yana shirin ajiye wa bayan ya kammala karatun sai suka ha'da idanu dashi kauda kanta tayi da sauri yayin da shi kuma ya kasa 'dauke nasa idanun daga kanta, fuskar ta yake 'karewa kallo har zuwa la66an ta, wani sabon salon 'kaunar ta ke 'kara nin kuwa masa a zuci, wanda har be san lokacin da ya mi'ke ya isa gaban gadon ahankali ba, ita kuwa tuni ta rintse idanun ta ganin ya nufo ta dan bata san me yake shirin aikata wa ba. Abbas kam shai'dan mai masa muguwar sa'kan nan be zo masa ayanzun wata'kila sanadin karatun da yayi ne shiyasa, wannan karan shai'dan 'din be yi masa mummunan sa'kar daya saba yi masa akanta ba, jiyayi kamar ana fizgansa zuwa gareta idanun sa na 'kara haska masa asalin kyaun surar datake dashi......da 'kyar ya dawo da tunanin sa dai-dai tare da jijjiga kansa ahankali. Wani 6ari na zuciyarsa ne ya wurga masa tambayar " _me kake shirin yi ne Abbas_? Lumshe ido yayi yakuma bu'de su atake sai ya sau'ke su akan fuskarta dake 'dauke da rintsetsten idanu har yanzun bata bu'de ba, 'karfin gaske yake jin zuciyarsa na fizgarsa zuwa gare ta. Dakewa yayi a tsayen sai dage ya harha'do wasu 'kabilun kalaman da sam basu ne acikin ransa a wannan lokacin ba " _yau ma bazaki... yi sallar ba...ne?_ " Yayi maganar yana wani gyara tsayuwa. Jin yanda yayi tambayar yasa Teema ta bu'de idanunta ta 'dan waigo a karkace ta kalleshi dayake dama ta bayan ta yazo ya tsaya, goshi ta ha'da dan ji tayi tarasa me ma zata ce dashi, aranta tace " _ina ruwansa toh da sallan ta_ ? Jitayi yasake jefa mata wata tambayar inda yace " _Ko har kinyine bansani ba_ ? Kai ta jijjiga masa amamar ah ah tare da sau'ke idanun ta zuwa 'kasa. Abbas taran ta yayi da fa'din " _amsani da baki i thought mun gama da wannan 6angaren tun ba yau ba_ ? Ahankali ta bu'di baki tace " _a'a banyi ba_ " " _Sai yaushe kenan_ ?Ya sake tambayarta. Cewa tayi " _May be gobe_ "! Tayi maganar kaman an matsi bakin ta ne an sata dole. " _Okay_ " Kawai yace da ita tare da juyawa ya koma parlour dan kallon news 'din safiya. Teemah kam da idanu ta bishi har ya bar 'dakin gaba 'daya, sai kuma taji ta kasa ko da motsin kirki ma, haushin ta 'daya yanda ya wani tsare ta da tambaya shi sam be san yaji kunyar abu ba, hakama ranar yawani cire mata kaya dan bata da lafiya ko kunya bayaji shi bayan yasan ita baso take ba, jiya ma haka yasa ta wai ta 'dauke pant 'din ta a bayin sa bayan ko be fa'da bama idan ta tuna zata 'dauke abin ta da kanta, toh period 'din da takeyi ma sai yaji dalili ne ko kuma ranar gamawar ta ? Duk cikin ranta take wannan tunanin. 'Dan karamin tsaki ta ja bayan ta 'mare tunanin tace " _mutum sai sa idon tsiya gashi kamar mumini amma san bahaka bane_" Tare da juyawa ta gyara kwanciyar ta da kyau. Caraf idanun ta suka sau'ka akan photo enlargement 'din sa dake manne a bangon 'dakin saitin ta, tun shigowan ta 'dakin bata lura dashi ba sai yanzun sai taga kamar ita yake kallo shima. Sanye yake da full dress na Uniform Karky 'dinsa na sojoji, kansa babu hula ya ri'ke ta a hannun sa wanda ya 'dago hannun sa dake ri'ke da hulan ya 'dora akan 'kirjinsa yana murmushi aka haska pix 'din ba 'karamin kyau yai ba ita kanta ya birgeta, daga dungun 'kasan photon kuma wani 'dan 'karamine shima aka ha'da su, shima nasa ne kuma still da karky ajikinsa, ya 'dan 'daga hular dake kansa ka'dan kamar me shirin sarawa wani, bambamcin kawai wannan 'din ya 'dan sunkuyar da kai ne sa6anin sarawa da shi kai asama ake yinsa, wannan ma sai yafi yi mata kyau fiye da waccen babban dan shi 'din yafi sake fuska aciki kuma yayi salo me birge duk wanda yagani yakuma fa'da'da fara'ar sa afili har ana ganin hasken hakoran sa. Daga 'kasa taga an rubuta *Cpt. M A AL-HASSAN* . Sunan ta sake maimaitawa abakin ta sosai taji da'din fa'darsa abaki. Ahankali ta sau'ka daga gadon ta koma gaban pix 'din ta rin'ka shafawa tana kallon sa, ta6e baki tayi aranta tace a photo ka'dai ake ganin fara'a da murmushinsa shi, shiyasa ma yafi kyau anan 'din fiye da ganin sa zahiri" Tayi maganar tana wani shashshafa photon ahankali. Ta shashance tana kallon sa har bata san cewa ta 'dau tsawon lokaci ahakan ba. Har Abbas ya shigo ma bata sani ba gyaran muryarsa kawai taji daga bayan ta sai kuwa tajiya da sauri. Suna hada idanu yace da ita " _Bana son rigima fah, idan kika kuskira kika yi min 6arna ni da ke ne_!" Yana gama fa'din haka ya wuche bayi. Ita ma binsa tayi da kallo tare da hararan bayan sa batare da tace uffan ba har ya shige cikin bathroom 'din. Teemah bata wani 'kara 'daukan dogon lokaci awurin ba ba ta wuce 'dakin ta da rabon ta dashi tun jiya da dare. Wanka tayi tafito ta sami wata atampa cikin jerin kayan data gani jere a ma'ajiyar kayan dake 'dakin nata. Riga ne da skirt kayan 'din kin zamani, ko da tasa kuwa sai taga kamar kayan daga cikin kayan ta ne aka 'dauko shi, domin ganin yanda ya zauna mata ajiki. 'Bata lokaci tayi ta kashe 'dauri bayan ta zizaro kwalliyar ta ta yayi gwanin birgewa sai dai bata cika fiskar ta da tarkace ba light make-up tayi kawai yau 'din. Maman Amal Teemah ta tuna da kalaman ta na baya da kuma Anty da nata maganganun basu da'de ba da ta fade su, wa'dan nan bayin Allahn sun bada 'kyakykyawar gudum mawa arayuwarta ita kanta tasan hakan, sune suke cewa da ita taringa yin kwalliya sosai agidan mijin ta, Allah sarki Maman Amal 'yar uwa mai 'kauna saboda Allah kenan, lokacin auren ta na baya da Mahmud ba 'karamin 'ko'kari tayi ba na ganin ta gyara zaman takewar su, amma bai nifi tsawon rayuwa tsakanin ta da Yah Mahmud ba, Teemah da kanta tasan Maman Amal mai son tsakani da Allah ce kuma har yanzu darussan ta na nan bata manta ba, sosai Teemah tayi missing wannan baiwar Allahn. Tana kammalawa da 'daurin ta tashi tana 'karewa jikinta kallo acikin dressing mirror, 'karan door bell ne ya dakatar da ita sai ta tsaya shiru tana tunanin ko Yayan ta zai je ya bi'de , amma sai taji 'karan ya kasa karewa kusan mintina uku ba'a daina ba hakan yasa ta fahimci cewa babu wanda ya bu'de 'kofar, sai tayi tunanin ko har yanzu yana bathroom ne. Saurin fita daga 'dakin tayi ta nufi palour da niyyar bu'dewa sai kuma taci karo da shi wanda suka bu'de kofa atare suka fito, shima 'din door bell 'din ne yafito shi. Sau 'daya ya kalle ta sai ya 'dauke kansa yaci gaba da tafiyar sa, Teemah daga inda ta ganshi bata 'kara motsawa ba ganin ya fito kawai sai taja ta tsaya. Hannah ce ta shigo hannun ta ri'ke da wasu ha'da'd'dun warmers guda biyu. Tana ganin Teemah tasaki murmushi amma bata kula ta ba, sai da ta rissina cikin natsuwa ta gaida Abbas tukunna wanda yana amsawan yakoma ciki dan be gama shiryawa ba yafi to. Yana shigewa Hannah ta danno da gudu ta rungume ta tana dariya ta ce " _mrs Dodo kinyi kyau fah irin wanna show haka gaskiya kin yi wuta amarya, banzo da waya ba Allah da na miki photon mrs Yayah first day in her husband's house_ "! Ahankali take maganar dan kar Abbas ya jiyo ta. Duka ta kai mata sai ta goce tana dariya. Dariya sukayi dukkan su, hannun ta Teemah ta kamo tace " _zo mu shiga ciki kiga wani abu_ " Hannah da sauri ta 'kwaci hannun ta tare da fact din ke barni ba yau ba, zan dawo watakila gobe yau din nana Ummah da babban warning ta ha'dani tace kar na yarda na wuce time din data bani wai in koma da wuri" " _Ke de Hannah Allah ya shiryeki, idan baki son zama ai bazan tilastaki ba amma miye na buga wa Ummah_ _sharri har haka_ ?. Teemah ta fa'da fuska ba yabo ba fallasa. Tuni kuwa Hannah ta fahimci bata ji da'din hakan ba domin ta tabbatar mata sai tace " _wai ke kina tunanin sharri ne" "ehh mana toh da menene? "Allah Teemah ba sharri nayi mata ba, can't u see hannu na ko waya fah babu!_ Ta dago hannayen ta tare da waresu sannan taci gaba " _Tasan i'm addicted 2 my phone shiyasa ma ta 'karbe bayan ta ha'da ni da warning, dan tana tunanin ko dan wayar ma dole zan koma gida da wuri, ban gama kawo abincin bama fah bari in 'dauko sauran_ ". Hannah tana maganar tana nufan 'kofa, Teemah ma sai ta bita abaya suka fita tare. Sai da suka fitan ne Hannah tana murmushi tace da sigar tsokana " _kin san yanzu ke amarya ce Ummah bata so a dame ku ne shiyasa...._ 'Kasa-kasa tayi da murya tace " _ke inaga fa Ummah jika take so da wuri....._ " Duka Teemah ta kai mata tana dariya itama da sauri Hannah ta goce itama tana dariyar da haka suka isa wurin motan batare da ta 'karasa fa'dan abinda tayi niyyan fa'di ba. Kar6an coolern Teemah tayi a hannun ta itama sai tace da Hannah " _Bani zan tafi dashi ki je abin ki karki 6ata ran Ummah tun da bata so a dame mata ya'yah gara kiyi sauri ki_ _tafi_ " Dariya sosai Teemah ta bawa Hannah takuwa dara tare da fa'din " _yarinya kenan!_ " matsowa tayi daf da kunnan Teemah tace " _Darasin ki na gaba mrs dodo zaki gane kuren ki ai_ "! Hannah na gama maganar ta shige cikin mota tana dariya, sai alokacin kuma Teemah ta gaida driver tare da 'dagawa Hannah hannu. Ashe har da driver Ummah ta ha'do ta ya kuwa jirata dan ma kar ta zauna 'din dagaske. Sai da taga sun bar gidan sannan takoma ciki, tana shiga sai ga Abbas ma ya sake fitowa cikin shigar suits ash colour, yana ganin ta yaja ya tsaya turus, take ya wani ha'de goshi tare da 'kan'kance idanu yace " _what nonsense!.... daga ina kike.._ ? 👎🏻 _Comment_ _Vote_ _Share_ *_Salmerhn ku ce_* 😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _My 'kungiya on top_ 🤞🏻 _This page is specially goes to u *DBWA* i heart u mutane na._ 🥰 *Bismillahir rahmanir raheem* _Whenever you ar *STRESSED* , eat chocolates, sweets nd everything.... because when_ _stressed is spelled backwards it becomes ‘_ _*DESSERTS* ’_ 👌🏻 🅿 *79* Hankalin ta kwance ta bashi amsa da fa'din " _wannan na kar6o "_ Tayi maganar tare da 'dago coolern ta nuna masa dan bata zaci laifi ta aikata ba. Tsawa Abbas ya daka mata har sai da ta tsorata, yace " _Shut up da Allah ni, ke aka aika ki kawo ne_ ? _ko ita wacce aka aikon bata da hannu shigowa da shi sai ke? Wama yace miki ki rin'ka fita a haka da irin wannan shigan?_ Har yanayin fuskar ta ya canja zuwa yanayin kuka kamar yanda na shi ma canja ya koma yanayin 6acin rai, cewa tafara yi. " _Yayah ni...._ Dakatar da ita yayi da fa'din " _Yaya what_ ? _did i send u_ ? Shiru tayi ta sunkuyar da kanta 'kasa ita masifar tasa mamaki yake bata ma. Shi kuwa tsawa ya sake daka mata inda da 'karfi yace " _tamabayar ki nake_ _yi na aike kine_ ? Sosai ta tsorata da tsawan nasa dan ita har ga Allah bata san irin hakan sam. Kai ta jijjiga masa da sauri alamar " _ah ah_ " Kwafah yayi yana kallon ta yace " _so_ ...! tare da 'dage gira 'daya. Baki tura gaba ta juya kai gefe a ranta tace " _kai ka sani ai masifaffe mai hali biyu kawai_ " Afili kuwa 'kun'kuni tafara tana wani ha'de rai itama. Gani tayi ya fara tahowa inda take ai da sauri ta ajiye coolern ta yi 'dakin ta da gudu, tana shiga kuwa ta datse 'kofan ta tsaya maida nunmfashi. Abbas kam binta yayi da kallo har ta shige 'din sai ya saki guntun tsaki, har zuciyarsa yaji haushin fitan da tayi ahakan bayan yasan akwai maza a harabara gidan, batyan mai gadi yasan dole Hannah da driver zata zo amma shine an ta rai,a shi sai ta fita ahaka tana juya musu jiki, wama yasan irin yanda shigar tan ya birge su. Wani tsakin ya 'kara ja ya koma 'dakin sa ya 'dauko keyn mota ko ta kan abincin bai bi ba ya yi waje abinsa. Teemah kam jikin 'kofan ta mannu ta ringa sau'ke ajiyan zuciya, shab ta manta ma akan cewa ya tsani 'kun'kuni shiyasa tayi, da badan haka ba da ba za tayi masa ba acikin irin yanayin da ta ganshi 'dazun...... Afili ta ce " _kai_ _wannan_ _mutumin ba dai mugun hali ba"_ Bata fito ba sai da ta 'dau kusan 40 mins a'dakin sannan ta bu'de 'kofan ahankali ta le'ko, sam bataga alamun mutum ba kamar yadda bata ji motsin kowa ba dan haka sai ta fito gaba 'daya tana san'da ahankali. Jin shiru a ko'ina ne yasa ta 'dan saki jikin ta ganin kamar baya gidan. Coolern data bari a hanya 'dazu taje ta 'dauke sannan tafara bubbu'de su tana ganin abincin. Wainar shinkafan data gani ce ka'dai ya birge ta dan haka sai ta 'diba tafara ci a hankali. Sai da ta gama sannan ta koma 'dakinsa ta gyara shi da kyau babu wani datti amma sanda ta share shi tas ta kunna burner sai ta ja 'kofan ta rufe tare da komawa nata 'dakin duk sai data bisu ta kintsa su inda cikin 'kan'kanin lokaci 'kamshin gidan ya canja, lungu da sa'ko sassanyan 'kamshin turaren wuta ne kawai ke fitarwa. Sai da ta gama da wannan sannan taji ta shiru, saboda babu wayar ta tare da ita, gashi kuma tana so tayi 'kira amma bata san yadda zatayi ba, ta manta 'dazu kuma bata ce da Hannah ta kawo mata ba. Yana fita ko 1hr be kai ba yadawo sai gani tayi ana shigowa da drinks da snacks kala-kala ana ajiyewa. Abinda kawai ya ha'da su cewa da yayi ta saka drnks 'din a fridge da yawa, ya kuma tsaya sai da yaga ta sa 'din ragowar kuma ta adana su kafin ya sake fita batare da yace da ita komai ba. Zuwa 11am sai ba'ki suka rin'ka zuwa daga gida, 'yan uwa da dangi kaca-kaca sun kuwa matu'kar 'debe mata kewa dan kuwa hira auka rin'ka yi da su Hannah gashi da isheshshen abincin su suka taho wanda suka ci ya ishe su har da saura ma. Abbas ma da yake yasan da zuwan ba'kin so bai ko le'ko gidan ba har sai bayan sallar maghrib, a lokacin kuwa dukkan ba'kin sun tafi saura ita 'daya. Gudun hayaniyar su nema yasa be zo dawuri ba sai da ya tabbatar duk sun tafi dan yasan mata duk inda suka ha'du akwai surutu. Yana shigowa gidan 'kamshi ya yi masa maraba, sosai da'din 'kamshin ya ratsa masa zuciya, a parlour ya zauna ya wani lumshe idanu yana sha'kan dadda'dan 'kamshin da ke tashi a parlourn. Tsawon mintina goma sha yana zaune a parlourn, sai daga baya ne ya tashi ya kama hanyar 'dakin sa, yaso ya duba ta kafin ya wuce amma kawai sai ya barta ya shige dan agajiye yake gaba 'daya. Teemah kam bata ma san ya dawo ba tana can kwance tayi zuru-zuru tsoro duk yabi ya cika mata zuciya, motsin kirki bata iya yi banda 'dan 'karan da fanka keyi babu abinda ke tashi a'dakin. Tsoronta sake ninkuwa yakeyi aduk lokacin da idanunta ya kai ga kan agogon dake manne a bangon 'dakin, ganin lokaci na 'kara tafiya amma har yanzu shiru, tunanin inda Yayan ya tafi wannan lokacin ka'dai takeyi taso da ace wayarta na hannun ta da ta 'kira shi ko kuma ta 'kira Hannah ta sake ro'kon ta ko zata tausaya mata ta dawo dan taya ta zama. Abbas kam yana shiga 'dakin sa yatar da shi tsab a gyare ga wani sassanyan 'kamshi na musamman daya ke fitarwa shima, duk dama ba'a birkice ya bar 'dakin ba amma yanayin daya samo shi a yanzun ya matu'kar birgeshi. Wanka yashiga inda ya kwashi kimanin mintina 20 kafin ya fito, shiryawa yayi cikin kayan baccinsa masu birgewa sannan yafito yaje ba'kin 'kofar ta yayi mata knock, Teemah naji ta 'dan firgita amma dataji an sake bugawa sai ta taso a 'darare, da rawar murya tace " _waye ne_ ? Da 'dan hanzari yace da ita " _Open up pls, wa kike tunanin zaizo_ ? Tana jin muryarsa ta yi saurin sa hannu ta bu'de 'kofan, shima Abbas juyawa yayi ya koma parlour, itama Teemah sai ta fito ta biyo shi abaya tare da fa'din " _sannu da zuwa Yayah_ " " _Yauwa matsoraciya_ " Yace da ita batare da ya waigo ba. Dai-dai lokacin da ze zauna yace " _me kike yi a 'dakin dama_ " Da " *bakomai* " tabashi amsa atakaice. " _Tsoro ko_ ? Yasake tambayar ta bayan ya daidai ta zamansa da kyau akan kujerar. Tana tsaye bata zauna ba tace dashi " _Ni ka'dai ce fah agidan tun 'dazu, kuma nace Hannah ta zauna kar ta tafi amma_ _ta'ki yarda sai tayi tafiyarta kuma ni kuma tsoro nakeji_ " " _Kin fiya tsoro daya ne ke, bagashi na dawo ba idan ta zauna ma me zata kare miki_ " Yayi maganar yana 'ko'karin canja chanja channel 'din T.V dake faman aiki. " _Ai zamuyi hira da ita_ " " _Hmm_ " Kawai yace batare da ya sake furta komai ba. Shiru suka yi dukkan su na 'dan wani lokaci banda 'karan T.V babu komai. Abbas ne ya yanke shirun da fa'din " _bani ruwa plz_ " Tashi Teemah tayi a hankali ta nufi hanyar kitchen cikin cikin tafiyar ta me 'daukan hankali wanda ita kanta bata ma san tana yi ba, Abbas binta da idanu yayi yana 'kare mata kallo rigar dake jikinta roba ce, amma tabi duk jikinta ta kamata ta ko'ina, ilahirin shape 'din jikinta babu wanda be bayyana ba, harta shige ya daina kallon ta amma be 'dauke idanun sa daga wurin ba sai daya ga ta fito daga kitchen 'din ne yayi saurin juyar da 'kwayan 'idanun sa ka'dai batare da ya motsa kansa ba, gudun karta kama shi yana kallon ta. Ruwan ta zuba masa cikin wani farin glass cup ta mi'ka masa, Abbas kar6a yayi yana kallon fuskar ta ita kuwa idanunta nakan cup 'din ne so bata san ma yana kallon ta ba, yana kar6a sai ya kai baki ya shanye ya sake mi'ka mata cup 'din. Tana zubawa yasake shayewa sai ya dire cup 'din. Teemah kai ta 'daga ganin irin yawan ruwan da ya sha suna ha'de idanu sai ya 'dage mata gira 'daya. Ita kam kauda kanta tayi gefe tare da 'daukan cup 'din ta mi'ke tsaye domin mai dasu muhallin su, Abbas kam harda kishin gi'da ya sake bin ta da wani sabon kallon har taje ta dawo. Sai data dawo sannan ya sake maida ta 'dakinsa ta 'dauko magungunan ta, data kawo ya sake sata ta dauko ruwa, zuwa yanzun kam tafara gajiya da aikan nasa, meyasa dama ya barata ta maida ruwan bayan yasan ze ce tasha magani, sai ta fara ha'de ranta tana kwa6a fuska. Abbas da ya lura da ita sai yayi murmushin gefen baki kawai ya jijjiga kansa, ri'ke take da ruwan ahannun ta, yayin da shi kuma yake 6allan maganin amma ya tsareta da idanu har se da ta maida nata idanun 'kasa sannan shima ya kalli maganin dake hannunsa yace " _Ni kam ina fatan Allah ya nuna min ranar da matata zatayi farin ciki da kasancewar mu, ranar da zan ce tayi min abu ta aikata min batare da ta 6ata ranta ba_ " Kanta ta 'dago ta kalleshi dan bata san inda kalaman nashi suka dosa ba sai kuwa suka ha'da idanu dashi, ko a fuskar sa da cikin idanunsa Teemah bata fahimci yanayin sa ba dan shi kullun ahakan yake da wuya ka fassara ainahin yanayin da ka ganshi aciki. Jitayi ya cigaba da magana inda yace " _Ban sani ba ko sai ranar dana mallaki Zahra ta, may be ita zatafi faranta min bazata dinga gajiya_ _da min hidima ba_ " Shiru tayi tana tunanin _wacece kuma Zahra dayake magana akai haka_ ? Maganin Abbas ya mika mata tare da fadin " _Kar6i kisha_ !" Ita tunanin Zahra ne ya tsaye mata arai koda ya mika mata maganin ma kar6a tayi kawai ta rike a hannu ta zuba ma hannun idanu, sai daya sake cewa da ita tasha sannan ahankali taringa sha da 'dad'daya har ta shanye lokaci-lokaci takan 'daga ido ta kalleshi zuciyarta cike taf da tambaya amma takasa furtawa. Koma wa yayi jikin kujera ya jingina sannan yace da ita " _ki ringa shan maganin ko bana gida kinga yau ma tun safe baki sha_ _ba_ " Ahankali tace da shi " _ai na riga na warke yanzu ni lafiyata 'kalau_ "! " _Ban yarda ba, ban yarda da half treatment 'din nan ba ki rin'ka sha_ _akan lokaci kinji_ ? Kai ta 'daga masa alamar taji, daga nan ta mike ta maida cup 'din ruwan inda ta dauko. Abbas lumshe idanu yayi yanajin zuciyarsa na harbawa sosai yake jin wani sabon yanayi yana ratsa shi. Koda ta dawo kuwa sai bata zauna ba ta wuce 'dakin ta inda ta watsa ruwa tare da canja shiga zuwa kayan bacci. Zama tayi a bakin gadon ta tana tunanin wayarta sosai tayi missing wayarta a kwana biyun nan dan zama shirun yafara isan ta sosai, gashi ita ba gwanar zama ta kalli T.V ba da kuwa tasan zai 'debe mata kewa. Hisnul Muslim ta 'dauka cikin takardun data gani a drawern 'dakin tafara karanta azkar 'din safiya da maraice bayan shi sai ta 'kara dana kwanciya bacci kafin ta kammala ma sai bacci yaso yaci 'karfin ta, a hankali ta mi'ke agadon ta kwanta take kuwa bacci ya dauke ta. Lokacin da Abbas ya tashi ze daga parlourn har ya le'kata sai yaga baccin ta takeyi, hasken 'dakin ya kashe mata ya bar dim light kawai tare da ja mata 'kofar ya wuce nasa 'dakin. *10:30pm* Ta farka daga baccin kamar an tsikare ta ta tashi ta zauna tabi ilahirin 'dakin da idanu, tana gama fahimtar inda take wato a'dakinta kuma ita ka'dai ai sai ta tashi tafice da sauri ta bar da'kin, Allah sai ya taimake ta hasken parlour na nan be kashe ba. Amma Teemah bata tsaya nan ba ta wuce 'dakinsa, 'kofan abu'de yake dan haka kawai sai ta tura ta shiga da 'yar siriryar sallamar ta. Zaune yake a bakin gado farar singlet ce ka'dai ajikinsa da dogon wando, system 'dinsa na agabansa inda ya bada dukkan hankalin sa akai yana dubawa, 'kafarsa 'daya na tsaye yayin da 'dayar kuma take tankwashe ya zauna akai. Sallamarta ce ta sa shi 'dagowa ya kalle ta da mamaki dan kuwa yasan tayi bacci tun tuni kawai sai ya ganta yanzun kamar an koro ta. 👎🏻 *Duk wacce taji aranta kamar cewa wannan SALMERHn* *bata kyautawa... pls badan niba tayi min afuwa saboda Allah, ni kaina nasan bana kyautawa amma* *abubuwa ne dayawa suka sha kaina, koda banyi typing* *ba amma wallahi kullum kuna raina ba'a son raina kuma nake muku jinkiri ba* , *ba yadda zanyi ne kawai* ......... ~FATAN ZAKU CIGABA DA MIN UZURI DA HA'KURI HAR MU KAI GA CI.~ _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _My 'kungiya on top_ 🤞🏻 _This page goes to u *DBWA* i heart u mutane na._ 🥰 *Bismillahir rahmanir raheem* _Anyone can make u happy by doing something special, but only someone special can make u happy without doing anything._ 🅿 *80* Hankalinsa da idanunsa ya mayar kanta ya tsaya 'kare mata kallo, yau riga da wando ta sanya ajikin ta, yariga yasan zancen daya kawota amma duk da haka sai ya jefa mata tambayar " _ya akayi_ ? " _Babu komai_ " itama tace masa atakaice. Cewa yayi " _Toh me ya hana ki bacci har yanzu? ko rigimar da saura ne bata 'kare ba_ ? Yasake jefa mata wata tambayar. Goshi ta ha'de tawani yi kicin-kicin da fuska tace dashi " Ni bana wani yin rigima.....kuma ma ai baccin nake ji ne yanzun shiyasa nazo dan inajin tsoron 'dakin can 'din" Ido ya zaro waje akanta yace " _Kullun ne wai ke kike jin tsoron_ ? _Come on... go back to ur room kiyi addu'ah ki kwanta_ " 'Kafa ta fara bubbuga masa cikin shagwa6a take cewa " _ni wlh tsoro nake ji ni ka'dai_ .... Yatsan sa 'daya ya 'dago ya nuna ta dashi yace " _bafa na son iskanci ...da 'din da wa kk kwana da zaki tsiro min da wannan iyayin yanzu_ ? Kuka ta sanya mishi yanzun tana 'kara maimaita " _ni wallahi tsoro nake ji kuma ai ko da ma bani ka'dai nake kwana ba_ _da Hannah ne_ ! Kwafa yayi yana kallon ta kamar an matsi bakin sa sai ya sake fa'din " _kafin itan kuma fah_ ? Shi adole tsare ta zaiyi da fa'din hakan. Teemah kuwa cikin kwanciyar hankali ta bashi amsa da fa'din " _ni da Yayah Mahmud_ "! Take Abbas yaji wani mugun bugu azuciyarsa, ransa gaba 'daya yaji ya 6aci atake sai ya rintse idanun sa, wani mugun kishine yataso masa a zuciyarsa ga wani tunani na daban daya 'dar su aransa, sai ma yake ganin kamar da gangan ta ambaci sunan Mahmud 'din dan ta 6ata ransa. Sam shi beyi tunanin zata ambaci Mahmud alamarin ba, he thought da can baya zata yi magana akai dan shima tunanin sa yatafi ne a lokacin datake gida a Damaturu, wancan lokacin kam yasan ita 'dayan ta take kwana kuma dashi yaso kama ta. Be iya jura ba sai da ya dafe kansa tsabar yanda yake sara masa, 'kasa yayi da kansa ya sauke idanun sa akan system 'din dake gaban sa, tamkar wanda yaga abin tsoro aciki ko kuma system 'din ne yayi masa laifin sai ya rufe ta da 'karfi. Kamar an tsikare shi kuma sai ya mi'ke tsaye bai ko sake kallon inda Teemah take tsaye ba ya shige bathroom. Teemah kam binsa tayi da idanu domin bata san me yasa shi canjin mood cikin 'kan'kanin lokaci haka ba, amma ganin har ya shige be kula ta yasa ta tafi a hankali tayi kwanciyar ta. Abbas haka da kayan jikin nasa bai ko rage ba yaje ya kunna shower akansa, zuciyarsa, nutsuwarsa da tunaninsa duk suka caku'de suka dagula masa lissafin sa gaba 'daya. Banda emergining rayuwarta da Mahmud babu abinda ke zuwa ransa alokacin, rayuwarta na baya agidan Mahmud yake tariyo wa har sai da ya kasance shine babban damuwar sa alokacin, shi kansa yasan ba dai-dai yake aikata wa ba amma zuciyarsa ta kasa yadda da cewa 'kaddarar su kenan bayan yariga yasan hakan ne nd he can't change it, he cant even erase d fact that ta ta6a zama gidan wani da sunan aure, kishin hakan ne ya hana zuciyarsa sakewa, shai'dan yariga ya yi masa mugun hu'dubar da ba za ta amfane shi da komai ba. Shi kansa Abbas yasan kuskure ne hakan saboda babu amfani tuna irin wannan passed 'din musamman ma daya kasance yanzu Mahmud is no more but ya kasa goge hakan azuciyar sa, muguwar sa'kan nan ta ri'ke mashi zuciya sosai tana kuma sake haifar masa da zazzafan kishin Fateemah aduk lokacin da hakan yazo ransa. Shi kansa ya'ki yake da zuciyarsa akan hakan mafi yawancin lokuta yana burin ganin ya dai-dai ya tunanin sa, rayuwar auren su ta 'dau hanya, amma kafin faruwar hakan sai gashi da bakin ta ta sake tuna mishi cewa wani ya mallake ta kafin shi, kenan wannan passed 'din ba zai ta6a barin rayuwar su cikin sau'ki ba, rayuwar ta da Mahmud yasan azuciyar ta ne ba zai ta6a iya kankare mata ba amma me yasa sai ta furta masa da bakin ta? Haka ya bar shower nata zuba akansa kusan 1hr yana tsaye guri guda batare da ya motsa ko da 'dan yatsan sa ba, da 'kyar ya samu ya saita tunanin sa da taimakon kalmar innalillahi wa innah ilaihi raji'un dayake maimaitawa ya samu har ya watso ruwa tare da 'dauro alwala ya fito. Lokacin da ya fito ma har tayi baccin ta Teemah kam cikin natsuwa batare da damuwar komai ba. Kallo 'daya yayi mata ya 'dauke kansa, sai daya sa kaya kafin ya shimfi'da dadduma ya tada sallar nafila kamar yanda ya sabayi kullun, shafa'i da wuturi ya 'kara a kai sannan yayi zaman ro'kon mahallici haka ya dinga jero addu'o'i akan Allah ya kawo masa sauki cikin al'amuransa ya daidai ta tsakanin zaman sa da iyalinsa in har hakan shine alkahirin dake cikin rayuwarsu gaba 'daya, kuma ya jikan Mahmud yasa mutuwa hutunsa ce. Bayan da ya idar ma be tashi akan dadduman da wuri ba, sai da yaji ya dan nutsu kafin ya tashi a awurin. Ji yayi kamar yakoma parlour yayi baccinsa a acan, amma sai yaga rashin dacewar hakan kuma daga yanzun baya son yadinga bawa shai'dan 'kofar da zai ringa gina musu katanga tsakaninsu dan haka sai ya tako zuwa gaban gadon ya tsaye nesa ka'dan da ita yana me sake koran shai'dan azuciyarsa. Su hajiya Teemah sarkin birgima har ta juya tafara bararraje wa, jiyayi yana son ganinta sosai be yiwa idanunsa rowa ba kuwa ya 'karaso 'bangaren da taken tare da zama agefen ta yana me kusan ta kansa izuwa gareta, gashin ta dake tsefe ne duk ya baje mata afuska saboda fitan da ribbom 'din dake kan wanda ta 'daure dashi yayi. Tunawa yayi da rigimar ta tun tana 'yar karamar ta bata son kitso sam, yasan hakan ne sanadiyyan zuwa hutu daya keyi acan Damaturu, wasu lokutan idan yana can shine zai zauna ya tsefe mata kan da lallami wataran kuma har sai ya siyo mata tarin choculates kafin take zama, tun be iya tsifan ba har ya zo ya koya da kyau yana mata a weekend. Idan za'a yi kitson ma sai an kai ruwa rana kafin asamu ayi, bayan haka kuwa idan taga kitson akanta sai tafi kowa iyayi da yanga dashi. Har ta girma bata son kitso, kullum kanta atsefe, Mummy kanta tayi tagaji 'karshen ta haka ta ha'kura ta 'kyale ta har abin yabi jikinta. Hakan kuwa be sa gashin ya lalace ba, domin yana nan ne kamar mara zuciya tana dai yin saloon akan lokaci amma babu kitso, gashi ba'ki kullum yana shai'ki ban sani ba ko dan kasancewar ta tsakiyan fulani ne ko kuma nata halittan ne haka oho. Hannu yasa a hankali ya tattara mata gashin gaba 'daya zuwa tsakiyar kanta kusa da goshin ta anan yasa ribbom 'din ya 'daure mata gashin, dan yasan anan kam kowani irin bacci zatayi bazai ta6a takura ta ba. Idanunsa ya tsayar akan fuskar ta ya tsaya 'kare mata kallo musamman 'dan 'karamin bakinta na rashin kunyan nan. Da yatsan sa ya shafo bakin a hankali sannan ya maida hannun nasa gaban goshin ta yana 'dan shafa 'kananun gashin dake gaban goshin a hankali ta yadda bazama tasan ana ta6a jikin ta. Abbas ya kai kusan 15mins agaban ta sannan ya tashi ya koma 'dayan gefen ya kwanta shima yasata agaba yana kallon ta a haka bacci yayi awon gaba dashi. Washe gari da asubah daya tashi yau kam dabaibaye shi tayi, yajima da farkawa sai yajita ajikin sa amma beyi ko motsin kirki ba gudun karya tashe ta, 'kiraye-'kirayen sallah ne yasa shi motsawa tare da yun'kurin tashi wanda hakan yasa ta bu'de idanu. Jin kamar tana jikin mutun yasa ta 'dago idanu da sauri ta kalleshi sai ta kuma komar da kanta 'kasa saboda ta 'dan ji nauyin hakan dayafaru, shikuwa ganin alamar kamar bata da niyyan barin jikinsa sai ya ce da ita " _Madam 'dagani zanyi sallah ne, ko tashin ma sai na 'daga ki kafin ki tashi dan na_ _ga alama naki son jikin na musamman ne_ " Jan jikin ta tayi ahankali ta bar jikinsa tare da juya masa baya tana 'ku'kk'uni. Sarai yajita amma be kulata ba saboda hanzarin karya makara yin sallah ,sai da ya mi'ke kafin yace " _shine azhkar 'dinki na tashi daga shimfi'da ko?_ Shiru tayi masa aranta tayi tsuka sai ayyana irin yanda ya takurata takeyi, kullum baya barinta tayi bacci mai kyau in badan ma tana jin tsoro ba da ina zai ganta ma balle ya dame ta. 'Dan 'karamin tsaki tasake ja tare da gyara kwanciyar ta da kyau dan taji da'din yin wani baccin. Ita kanta tasan tana da birgima dan ko Hannah nayi mata complaint akan hakan watarana wasu lokuta idan suka tashi daga bacci amma ita baya damun ta kamar yadda bata kula Hannah koda tayi mata mitan dan kuwa ita bata san ta yadda zata daina ba. Ko da datake gida ma gadon ta babban size daddy ya sai mata da mummy tagaya masa cewa tana da birgima, bata son taji ta takura idan zata kwanta shiyasa ma take birgimar ta son ranta, duk kuwa wanda yace zai kwanta gado daya da ita sai ya dasawa zuciyar sa ha'kuri sa6anin hakan kuwa sai de kai kayi ta annabawa ka bar mata gadon. Tunanin ta tsayawa yayi cak lokacin data jiyo muryar sa yana rero karatun littafi mai tsarki cikin dadda'dan sautin sa me sa nutsuwa ga fidda dukkan 'kal'kala da dokokin karatu, tana jin fitsari amma ta'ki tashi taje tayi dan kawai kar ta yanke jin karatun. Har ya 'kare karatun tana nan kwance, tana ji har ya gama gaba 'daya ya mi'ke tsaye. Tana ganin ya mi'ke agurin itama sai tayi hanzarin mi'kewa da saurin gaske ta shige bayi ko tura 'kofan ma batayi ba dan yanda fitsarin ya matsata ta ke saurin sau'ke shi. Abbas da idanu ya rakata har ta shige bayin sannan ya jijjiga kansa afili yace " _Allah ya shirya_ " sannan ya dawo da hankalin sa ga abinda ke gaban sa. Yau 'din bacci yakeji saboda baccin sa na daren jiya ka'dan ya samu yayi dan haka yau ko news 'din safe ma be tsaya gani ba kishingi'da. Teemah brush kawai tayo tafito dan tafi son tayi wanka a'dakin ta saboda zatafi sakewa acan kuma ma ko dan saboda kayan dazata saka ma. Inda yake tazo ta tsaya har bacci ma ya 'dan fara 'daukan sa, sai yaji alamun ta akusa dashi, share ta yayi ya cigaba da baccin sa sama-sama sai ya jiyo ta tana 'kiran sunan shi a hankali. Idanun sa ya 'dan bu'de sai ya sau'ke su akanta, suna ha'da idanu sai tayi saurin fa'din " _ina_ _kwana Yayah_ " " _Lafiya lau_ " Yace da ita sai ya sake maida idanun sa ya rufe zaton sa ko dama gaisuwar ce. Ganin haka sai tayi saurin sake furta " _Yayah_ ! " _wai me zan miki ne_ ? Yayi maganr a'dan tsawace. Teemah sai ta nutsar da muryarta cikin natsuwa tace " _Yayah wayar ka zaka 'dan ban aro in 'kira su Mummy tun fa dana zo nan gidan ban 'kara_ _waya dasu ba_ "! idanun sa still arufe yace " _Ina taki wayar_ ? Ya sake tambayarta sai tace " _ni bangani ba bansan ko tana gida ba_ " Baya son dogon surutu dan haka sai ya nuna mata wayar tasa inda take. Teemah 'dauka tayi ta koma parlour ta 'kira layin Mummy kamar yanda taga an rubuta awayar, bayan sun gaisa da ita sai ta ha'da ta da su Anty har ma da Ummah. Inda duk suke 'kara yi mata tuni akan biyayyar aure da bin dokar sa, Ummah ce ka'dai data kar6i wayar taringa ce da ita tayi ha'kurin zama da mijin ta. Cikin farin ciki suka 'kare wayar, bata maida masa wayar ba sai ma zaman ta data gyara zuwa kwanciya tayi pillow da hannun kujera. Galleryn sa ta shige ta ringa bi tana kallon pictures 'dinsa dama wa'danda ba nasa ba. Cikin haka taci karo da pic 'din wata mai kama da ita tana bacci, ganin kamar su da ita ne yasa ta tsaya 'karewa pic 'din kallo sai kuma tafara ganin kamar ita ce bawata daban ba, amma ta kasa tantance asalin gaskiyan waye ce a photon dan haka sai ta tashi tanufi wurinsa tana me 'kara kallon fuskan wayar domin tabbatar wa. Data kasa fahimta sai kawai ta bari akan wata daban 'din ce ba ita ba, domin kuwa ita bata san lokacin da akayi pic 'din ba, amma bari ta tambaye shi. Tun kan ta 'karasa cikin 'dakin tafara 'kiran sunan shi dolen sa ya yanke baccin ya sake bu'de idanun sa tare da fa'din " _ya akayi_ ? Kamar an korota tace dashi " _Yayah kalli pic 'din wata awayar ka me kama dani_ ? Tayi maganar tana me sake kallon cikin wayar. Beyi mamaki ba dan yasan yana da pix 'dinta daya dauka da hannun sa wanda ita kanta bata ma san da zaman su ba. Amma duk da haka Abbas sai yace da ita " _ingani_ "! Dayake yana kusan tsakiyan gadon ne shiyasa sai da ta hau saman gadon ta zauna kafin ta nuna masa. Abbas be kar6i wayar ba sai ya 'dago kansa ya maida kan cinyar ta sannan ya kalli wayar sau 'daya sai ya maida idanun sa ya sake lumshe wa sannan yace " _kinsan ta ne_ ? Amsa ta bashi da fa'din " _ah'ah naga tana kama dani ne shiyasa....! a ina take Yayah?_ Tana maganar tana sake kallon cikin wayar ita dai abin na bata mamaki matuka. Ce mata yayi " _a_ _zuciya ta take_ "! Teemah da mamaki ta kalleshi harda kwalalo idanu waje tace " _Zuciya dai Yayah_ _saboda me kuma_ ? " _Saboda ita Zahra ta ce, farin cikina kuma burin raina ina matu'kar sonta sosai........inda kinsan yawan 'kaunar da nake mata nasan har zaki tausaya wannan mijin naki, kusan hauka nayi abaya da_ ' _kaddara ya shiga tsakanina da ita ya sanya narasa ta sai daga baya kuma tadawo min alokacin da bana zato bayan har na yanke 'kauna_ _da samun ta_ " " _Ni kan ina so inganta Yayah plz ka kaini inganta even once_ " Kai ya jijjiga mata alamar " _ah ah_ " Sai t asake fa'din " _pls Yayah mana nice fa_ "! Yace " _Ke wa_ ? Itama sai bashi amsa da " _Fateema Kabeer_ " Cewa yayi " _Yes ai nasani_ " sai tace " _Toh ka kaini in ganta mana kaji Yayah, Allah bazan 'kara yima birgima ba daga yau 'din nan_ " Murmushi yayi dan kuwa maganar tata dariya taso sashi sai yace da ita " _bazan kaiki ba ai yanzu ma damuna kikayi kika hana ni bacci dan haka nima sai ranar dana ga dama zan kaiki_ " " _i'm sorry toh bazan sake ba Allah na daina daga yau_ " Tayi maganar harda kama kunnuwan ta duka biyu. Abbaskuwa ya jijjiga kansa. Da sauri sai tace " _Yayah toh sai yaushe kenan_ ? " _Bayanzu ba akwai steps b4 aganta kinsan Zahra ta ta da bance_ "! Teemah shiru tayi tana kallon fuskar sa dake kan cinyar ta yana murmushi har dimple 'dinsa na lotsawa. Ita kam abin na birgeta har ma bata san lokacin da ta kai hannu wurin ba. Tuna waye ne yasa tayi saurin 'dauke hannun ta tana sake kallon shi. Ganin be motsa ba kuma be kulata ba yasa ta sake maida yatsan ahankali tana latsawa. Abbas sai ya kai hannun sa ya ri'ke nata hannun dake masa yawo a fuska. Yana cire hannun sai ya sake gyara kwanciyar sa akan cinyar tata. Teemah sai ta tura bakin haushin ya hana ta ta6a dimple 'dinsa bayan ya'ki amincewa ya kaita wurin Zahran sa. Zuba masa idanu tayi cike da takaici, da ta rasa abin yi sai ta fara jan 'kafar ta tare da fa'din " _''daga min kafata nima tagaji Yayah_ " Be ce da ita ko 'kala ba sai ya maida kan nasa yayi matashi da pillow kamar yanda yake da farko tare da juya mata baya. Teemah ma tashi tayi ta ajiye masa wayar a kan drawer sannan tafice zuwa 'dakin ta fuska babu walwala, wanka tayi cikin sanyin jiki. Yau ko kwalliya ma batayi ba powder kawai ta shafawa fuskarta, cikin rashin kuzari take yin komai dan tun barowar ta 'dakin sa take jin 6acin rai nataso mata, ga tunanin Zahran sa daya tsaye mata a zuci, bata san me yasa take jin haushin ta ba, sai taji bata 'kaunar ta ma sam, tasan wata'kila da Zahran ce ai da bazai hanata ta6a mai fuska ba. Yau kam bata fita ba zaman ta tayi a 'daki ko lokacin da door bell yayi 'kara ma tanaji amma ta'ki fita, Abbas ne yaje ya bud'e 'kofar wanda tun da ga jin yanayin gaisuwar su ma ka'dai yasa tagane ba Hannah bace yau takawo musu breakfast 'din. Sai lokacin ma ta tuna ashe yau monday ne Hannah nada lectures a makaranta. Ashe kuwa ya taho mata da tarkacen wayoyin ta da sauran kayan ta na anfani ciki kuwa harda wayar Mahmud aka ha'do. Dama ta sanar da Mummy cewa wayar ta na gida Hannah ta taho mata da wayar idan zata zo. Abbas da kansa ya kawo mata har 'dakin ta ko daya ga tana wani shan 'Kamshi ma sai ya share ta shima ya fice abinsa dan yasan mecece matsalar ta. Zuwan wayar ne ya 'dan sanyaya mata rai ta 'danji dama-dama sai duk ta bi ta sanya su a chaji gaba 'daya. *10:12am* Abbas ya buga mata 'kofa amma be jira ta bude ba kawai sai ya juya zuwa dinning. Tana kwance tana faman chatn jin an buga mata 'kofa yasa ta ajiye wayar ta fito sai ta hango shi zaune yawani hakimce yana amsa waya. Tasan shine ya buga 'kofar dan haka sai ta isa dinning 'din itama. Bata zauna ba sai ta koma kitchen ta 'dauko su plates da cups ta dawo tayi serving nasu kana ta zauna bayan ta tura masa nashi gabansa. Abbas na lura da ita amma be kulata ba dan yasan halinta sam magana be sata cin abin sai in har tayi niyyah sa6anin haka kuma sai de in kai ne zaka'dauki nauyin bata da hannunka dan haka be ma 6ata bakinsa ba, yasan idan taji yunwa zataci ne dolen ta ai tunda ita yunwa ba sabo ne da ita ba. Har suka 'kare cin abincin be ce da ita komai ba haka itama. Ranar kam Abbas be fita ko'ina ba har aka 'kira sallar azahar yana gida, sai de duk da agidan yake amma kowa na 6angaren sa babu wanda yaje wurin kowa. Kafin azahar 'din Teemah tayi wankan tsarki ganin cewa period 'din ta ya 'dauke, dama 4days takeyi. Shi kuma lokacin da yayi alwala zai fita sai yabi ta wurin ta inda yazo dan sanar da ita fitar sa sai kuma ya tarar da ita tana sallah, be jira ta idar ba ya wuce kawai abinsa dan ba yaso jam'i ya wuce shi. Bayan sun fito ne ya 'kira ta awaya dayake yasan wayar natare da ita yace mata shi yafita kuma ba zai dawo yanzu ba, yace m za'a kawo mata abinci sai ta kula idan taji door bell taje ta anso kuma ta tabbatar ta rufe jikin ta da mayafi kafin ta fitan kuma bece ta fita ko da harabar gida bane. Daga 'karshe dan ya sake tunzura ta sai yace " _zanje in dubo Zahra ta ne kwana biyu bana samun ta_ "! Teemah ta6e baki tayi tare da fa'din " _uhumm sai ka dawo_ " Koda ya yanke 'kiran kuwa abin yaso ya dameta dan sosai ya tsaya mata azuci amma sai ta tambayi kanta dalilin damuwar sai ma taga laifin tane na shishshigin damuwar, miye ruwan ta toh da al'amarin sa ai yace itace farin cikinsa toh ita miye nata. Tilastawa kanta tayi 'karfi da yaji ta ya'ki zuciyar ta dole ta kawar da tunanin Zahran Yayah aranta sai de duk da haka lokaci zuwa lokaci tana sake tunawa. Kamar yanda ya fa'da mata haka tayi domin tana jin 'karan door bell tafita bayan ta zun6ula hijabin ta wadatacce babbah da take sallah dashi. Driver ne yakawo sai ta kar6a bayan ta gaida shi tare da kawo masa coolers 'din safe sannan tace da shi kar ya kuma kawo wa anjima wannan ma ya isa. Ciki ta koma tana me jinjinawa 'ko'karin Ummah sosai gashi kullun abincin yawa yake yi musu idan sunci ne ma sai Abbas yayiwa mai gadi magana yazo ya tafi da sauran gaba 'daya ko ya yake yi dashi ma oho, ita dai nata kawai wanke warmers 'din ne. Zama tayi a parlour kawai tare da 'kiran layin Ummah tayi mata godiya da kuma bayanin abincin sannan ta yanke 'kiran. Bata ko sake bi takan abincin ba taci gaba da duba wayar ta. Abbas kuwa har se da yamma ya dawo gidan ya kuwa zo mata da fruits masu yawan gaske. Daya duba abincin shima sai yaga ko ci batayi ba, yariga yasan hakan amma na yau 'din sai yayi tunanin ko harda fushin Zahra ne, dan gudun kar ya shiga ha'k'kin ta da yawa daya watso ruwa bayan ya shirya sai ya fito yace tazo tayi serving nashi abinci. Sai da ta wuche kitchen ta 'dauko plates 'daya da table spoon 'daya sannan ta dawo ta zuba masa abincin dai-dai shi tare da 'dauko masa lemonjuice da ruwa harda fruits 'din da ta gama yanyan kawa tasa afridge ya 'danyi sanyi domin kanta duk ta kawo masa ganin fried rice yau aka kawo kuma nada mai'ko sosai. Tana shirin mi'kewa yadakar da ita inda yayi mata nuni da kujera. Sam batada ra'ayin cin abincin musamman data ga ma cewa shinkafa ce wannan kuma bata cikin ra'ayin ta shiyasa koda zauna 'din ma sai ta na'de hannu kawai tayi shiru tana tunanin 'kila so yake ta taya shi zama. Spoon 'daya, biyu yakai bakin sa na ukun da ya 'debo sai ya nufo bakinta dashi. Teemah cikin idanunsa ta kallah sai yayi kamar be ganta ba hakan yasa ta dawo da idanun ta kan hannun sa dake ri'ke da spoon 'din tare da bu'de bakinta ta kar6a. Sai da yaga ta ha'diye sannan yace " _bakya son cin abinci ko? Idan Zahra ta tazo raina ki zatayi dan kuwa ita_ ' _katuwa ce nikuma babu ruwa na_ " Take tayi fushi ta tura baki harda 'dan hararan sa ka'dan. Murmushi Abbas yayi kawai amma na gefen baki be kulata ba yanzun dan so yake ta 'dan ci abincin koma ka'dan ne shiyasa kawai ya shareta. ***** Washegari da asubah da ya tashi sallah sai itama ya tashe ta ganin tafara yi, amma Teemah ta'ki ta tashi sai ta ringa juye-juye. Har yaje yayo alwala ya fito bata tashi ba da yaga zata 6ata masa lokaci sai ya sa hannu ya 'dago kafa'dun ta ya ta data zaune wanda hakan yasa dolen ta tashi tare da bu'de idon ta. Sai yace " _ki wuce kiyo alwala idan kika 6ata min lokaci Allah zan 6ata ranki kema_ " Tanajin haka dolen ta ta mi'ke tana gunguni bata da'de abayin ba tafito bayan ta 'dauro alwalan. Abbas ne ya mi'ka mata hijab babbah daya 'dauko a'dakin ta ta kar6a ta sanya tare da bin bayan sa yajasu sallar asubah tare da 'daukan dogon lokaci yana addu'o'i tun kan su shafa Teemah take layin bacci suna shafewa kuwa ta koma gado ta du'kun'kuna cikin hijabin ko cire shi batayi ba sanadiyyan sanyin da ke tashi ka'dan-ka'dan da safiyar. Abbas kam Al-qur'ani ya 'dauko ya 'dora da karatu tsawon lokaci sannan ya kammala. Zuwa lokacin kuwa ruwan sama ya sa'k'ko sosai ganin hakan shima sai ya kishingi'da ya lumshe idanu yana me tasbihi ga mahallici. 'Karfe takwas da 'yan mintina Teemah ta farka daga bacci, jin ruwa na sau'ka yasa ta yin luf sosai take jin sha'awar shiga ruwan amma tarasa yanda zatayi dan tasan Abbas ba barinta zaiyi ba, juyawa tayi ta kalleshi sai taga kamar yana bacci ganin haka yasa da sauri ta fincike hijab 'din dake kanta ta ajiye. Cikin san'da ta ta kama hanyar barin 'dakin dama Teemah gwana ce wurin son wasan ruwa Allah-Allah take tagan ta cikin ruwan nan musamman ma da yanzu ya 'dan tsagai ta ka'dan. Abbas idanunsa biyu babu baccin dayake yi duk kuma abinda take yi yana kallon ta sai da yaga ta kama hanyar barin 'dakin ne yayi tunanin ko wani rashin ji zatayi dan haka sai ya dakatar da ita da fa'din " *ZAHRA* ! Cak ta tsaya a inda take amma bata juyo ba shima kuma be sake magana ba idanunsa yasake lumshewa tamkar wanda ba shine yayi maganar ba. Teemah kam jin be sake magana ba yasa ta waigowa sai taga still baccin sa yake yi sai tayi tunanin 'kila ko cikin baccin ne yake 'kiran Zahran sa amafarki murgu'da baki tayi. Taso ta koma ta tashe shi a baccin kodan ya daina mafarkin Zahran ma dan ta 'dan ji wani iri sanadin hakan amma jarabar son ta shiga ruwan sai ya fi rinjayar ta kawai ta juya. Abbas ma sai ya 'kyaleta kawai tatafi. Cigaba tayi da tafiyar ta ta isa har kofan parlourn ganin a kule da security lock yasa ta koma tabi ta baya tafita ta 'kofar kitchen. Da farko hannayen ta tasa tana taran wanda ke sakkowa daga bakin roofing tana tara tana watsa shi afuskan ta tana murmushi, data ga hakan baze mata ba sai kawai tafara 'ko'karin shiga gaba 'daya. Caraf taji an ri'ke mata hannu daga baya wanda ya matu'kar firgita ta domin bata ji zuwan mutun ba ita. Arazane ta juyo sai taganshi take kuwa ya janyo ta zuwa jikin sa yana kallon cikin idanun ta yace " _Kinyi ajiya aruwan ne_ ? " _Umm- umm_ " Tace da shi tana 'kif-kif da idanu. " _Toh me zakiyi_ ? Yasake tambayarta. In ina tafara tarasa me ma zata ce dashi sai yace " _ina jinki_ " Ahankali tace " _wanka... zan..yi ne fah....Yayah_ "! " _Shower ya lalace_ _ne_ ? Ya tambayeta Jijjiga mai kai Teemah tayi ranta har yasoma 6aci dan tasan ba barin ta zaiyi ta shiga ruwan ba tunda ya fito. Sai ya sake fa'din. " _bathtub fah_ ? Da muryar shagwa6a tace " _Yana nan_ " " _Bazakiyi ba toh, wuce muje bana son rashin ji_ " Kalar tausayi tayi tace " _Ayyah Yayah ka'dan fah zanyi.........._ " Kafin ta rufe baki ma ya tare ta da fa'din " _i said bazakiyi ba ko?.....ko ni sa'an ki ne dazan na magana kina jayayya dani_ ? _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/13, 1:56 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 👎🏻 Wannan page 'din naku ne 'yan group *CAPTAIN ABBAS FANS 2* Allah sosai nake jin da'din Comment da conversation 'dinku ina matu'kar jin da'di, koda ace my ka'dai nake dashi nasan labarin CAPATIN ya isar, wannan page 'din naku ne kuyi yanda kuke so dashi.. 🥰 *Bismillahir rahmanir raheem* _Never expect things to happen. It’s better to feel surprised than to feel_ _disappointed_ . 🅿 *81* Rausayar da kanta tayi gefe tana kallon shi, Abbas baya son taga kamar yana matsa mata ne dan haka sai yace " _owk, zan barki kiyi amma make sure that mura na kamaki ba sassauci Anty nurse zan'kira ta ringa yi miki_ _injections har sai muran ya tafi...kin yarda_ ? Tana jin haka ta karya mai kafa'da alamar bata yadda ba. Abbas sakin ta yayi tare da nuna mata hanya yace " _Toh oyah go inside!_ " Dolen ta ta shigo ciki tana 'kun'kuni 'kasa-'kasa, shima Abbas take mata baya yayi bayan ya rufe 'kofar. Teemah 'dakin ta ta wuce cikin fushin an hanata wanka inda tana komawa 'dakin ta hau cire kayan dake jikinta dan sun ji'ke sosai. Sai da ta cire su gaba 'daya kafin ta nemi towel ta 'daura ajikin ta sai ta shiga bathroom 'din ta ta cika bathtub da ruwa ta shige ciki afili ta furta " _in ka hana wancen ai baka isa ka hanani shiga wannan ba, mutun_ _kullum sai de ya hanaka rawan gaban hantsi.....abu ka'dan sai ya wani ce injection! Wannan da ace shine yake yin alluran ai da anshiga uku nasan da kullun sai ya min goma ko.biyar dan mugunta! "_ Ta 'karshe da jan tsaki daga 'karshe. Abbas ma a parlour ya zauna inda ya 'dau lokaci yana amsa waya sai da ya gama kafin ya wuce ciki dan watsa ruwa be ko sake bi ta kanta ba. Teemah kuwa ta jima cikin ruwan hankalinta kwance sai da ta fara jin hanjin ta na motsi ne sannan ta fita aruwan tayi wanka mai kyau tafito. Koda ta fito sai ta tsaya kuma ta 'debi wayarta dana Mahmud ta zauna bakin gado, layin Umar ta nema cikin wayar marigayin ta'kira shi lokacin 'karfe sha 'daya ta wuce sosai 11:42am. Umar yayi mamaki sosai data 'kirashin ya kuma ji da'di musamman dayake shima Maman Amal na yawan damunsa akan batun Teemah. Nan yayi mata al'kawarin zai ha'da su da zaran ya koma gida. Cikin hanzari ta shirya tare da kwaso wayoyin harma dana Mahmud saboda sauri ta fito dan nemawa cikin ta dake 'kugin neman agaji mafita. Turus taja ta tsaya ganin babu komai akan dinning, bata 6ata lokaci ba sai ta wuce 'dakin sa ta same shi yana sa kaya shima. Bata damu da yanayin dayake ba ta isa wurinsa ta ha'de goshi ta ita adole tana fushi dashi tace " _Yayah nifa yunwa nake ji kuma banga komai a dinning ba_ "! Be kalleta ba yace " _Ya za'ayi kenan_ ? _dama nace a daina kawowa ne saboda bakya ci....._ "! Da sauri ta tare shi da fa'din " _inaci mana bagashi yanzu ma ina jin yunwa ba_ " Kwafa yayi yana kallon da ta gira a'dage jin yanda tayi maganar, cikin salo yace da ita " _Harda fa'da ne kuma_ ? Baki ta tura gaba ta kauda kanta tace " _Ni ba fa'da nayi ba ai yunwa nake ji ne shiyasa_ "! Cigaba yayi da 6alle bottuns 'din longslip 'din daya sanya ajikinsa yace " _Sai kije kitchen ki samu abinda zakici ko noodles ma ki tafasa kici zaifi sauri_ " Dan haushi ma Teemah ko jira ya gama maganar batayi ba tafice abin ta, jitayi badan yunwa na damun ta ba da babu abinda zai sata shiga kitchen yanzu. A parlour ta ziba wayoyin dake hannun ta sannan ta wuce. Koda ta shiga kitchen 'din kuwa sai ta wuce fridge ta 'dauko fruits ta gyarashi ta hau sha har da zaman ta kan stool 'din dake cikin kitchen 'din. Sai da ta 'danji dama-dama acikin ta kafin nan ta kunna gas ta dafa indomien ta dai-dai cikin ta tajuye a plate tarufe da wani plate 'din harda 'dora forkspoon 'din ta akai, sannan tayi mixing fruits tayi juice 'din ta 'dan dai-dai a 'kasan glass jug da extra cup 'daya batare da wani 6ata lokaci ba kuwa ta kammala duka tafito. Kan dinning taje ta ajiye su sannan takoma kitchen 'din domin kimtsa shi dan bata son idan tafita tasake dawowa dan kim tsawa ba. Batafi 9mins a kitchen 'din ba ta kammala tafito da ruwan ta mai sanyi a hannunta kawai sai idanun ta ya sau'ka akan Abbas yana siffing mata drink 'din data ha'da cikin kwanciyar hankali kamar ance shi aka ajiyewa abincin. Ga plate 'din abincin ta ma bu'de a gabansa da ga dukkan alamu yana kan ci ne. Turus taja ta tsaya dan haushi ma sai tarasa me zata ce dashi, shima sai yayi tamkar beganta ba yaci gaba da cin abincin cikin natsuwa. Data ga haka ne sai ta taho da sauri har idanun ta na tara ruwa dan takaici sai ta tsaya agaban sa tace " _Yaya abinci na ne fah_ ! Gira 'daya ya 'dage ya kalle ta sai ya kuma kallon abincin yace " _really!_ ? _Ai ban sani ba ne i thought nawane kika ajiye min ai_ " " _Ai baka ce min zaka ci ba_ "! 'Da, zaro idanu yayi yace " _Au sai ma na fa'di zanci kafin adafa dani_ ? Shiru tayi masa bata yi magana ba sai hawayen ta da suka gangaro, harga Allah yau 'din yunwa takeji sosai kuma tayi niyyan cin abincin ta sosai take son jin wani abu acikin ta. Ganin tafara kukane yasa yayi murmushi tare da janyo hannun ta ya zaunar da ita kan kujerar kusa dashi, be yi magana ba sai kawai ya 'debo abincin ya nufo bakin ta dashi. Babu musu Teemah ta bu'de bakin ta ta kar6a. Sai yayi mata murmushi aransa yace da din waya gaya miki Borno gabas take? ai yunwa maganin kowani fitinanne ne yasan badan taji yunwa ba da yau 'din yanda tayi fushi dashi 'din nan dako kulashi ma bazatayi ba sai gashi kuma har abinci yabata abaki kuma ta kar6a, afili kuwa sai yace da ita" _ni ban ta6a ganin inda mata ta hana mijin ta abinci ba sai_ _yau awurin ki! wato cikin ki ka'dai kika sani ko?_ " Shiru taui kamar bada ita yake ba sai ma kauda kanta da tayi gefe, Abbas sai ya sake 'dibowa ya mi'ka mata itama sai ta bu'de baki ta kar6a. Sai daya bata kusan spoon biyar batare da yaci ko 'daya ba data kar6i na biyar 'din ne sannan cike da tsokana yace da ita " _cinye abinki tunda bakya so inci nima zanje wurin Zahra ta ta dafa_ _min_ " Tsayawa tayi tana kallonsa shima kuma haka dan kawai ta tabbatar da abinda yace 'din, ganin hakan shima ya tsare ta da idanu sai ta kauda nata idon ta maida shi gefe, duk iskancin ta da rashin jinta bazata ta6a iya kallon kallo da shi na tsawon lokaci ba, sosai kwarjinin sa ke karya mata zuciya, tsawon mintina kusan biyu babu wanda ya furta komai acikin sannan Teemah ta ha'diye abincin dake bakinta ahankali. Yana shirin 'kara 'debowa sai ta yi sairin rike mai hannu, bata kalle shi ba koda yabi ta da kallon mamaki ma bata san yayi ba, dan ita plate 'din abincin take kallo. Kar6i spoon 'din tayi ta 'dibo abincin tayi dauriyan kai masa bakin sa batare da ta sa idanun ta cikin nasa ba, Abbas kuwa sai ya'ki bu'de bakin sai ma kauda kansa gefe da yayi. Hakan ne yasa ta kalli idanunsa sai ya'ki bata hankalinsa. Cak ya mi'ke tsaye ya koma cikin 'dakin sa domin tsabtace bakinsa. Teemah tamkar statue haka ta zauna ri'ke da spoon a hannu sai ta rasa me yake mata da'di, Abbas be da'de da shiga 'dakin ba ya fito hannunsa ri'ke da makulli ko kallon inda take be sake yi ba ya kama hanyar barin 'dakin. Ganin haka yasa Teemah ta mi'ke da hanzari cikin sassanyan murya ta ce da shi " _Yayah wurin Zahran zaka tafi_ ? Da " _umm_ " kawai yabata amsa batare da waigo ba, yana me cigaba da tafiyar sa ahankali. " _Nima zan bika_ " Ta sake cewa da shi wanda jin hakan ne yasa shi waigowa ya kalle ta dai-dai lokacin kuma sai waya ta 'dau 'kara daga cikin parlourn dukkan su sai hankalin su ya koma wurin. Teemah ce taje da sauri dan tasan ita ta ajiye waya a parlourn, hannu tasa ta 'dauki wayar hannun ta har na rawa dan yanda zuciyar ta ta tsinke tun daga jin 'karan ringing 'din dan tasan ba wayar ta bace ta kuma riga tasan kalan ringing 'dinsa tun yana raye, gani tayi number ce ba suna. Aduk lokacin data ga wani abu daya danganci Mahmud sai ta tuna da shi balle wannan daya kasance 'karan wayar sa ne da ta saba ji atare dashi tuni sai ya sa zuciyar ta bugu cikin sauri. Kafin tayi wani yun'kuri har wayar ta tsinke. Abbas ma ganin wayar da kuma yanayin data shiga yasa hankalin sa ya dawo kanta shima ahankali ya dawo baya ya tsaya nesa da ita ka'dan yana sake karantar yanayin ta, be san wayar waye ba ce kuma yasan ba tata bace dan yariga yasan nata dayake shine da kansa ya canja musu bada jimawa ba ita da Hannah iri 'daya. Take wayar tasake 'daukan wani 'kara wanda yasa Teemah sai da ta danganta jikinta da kujera kafin ta iya amsa 'kiran tana me danne hawayen ta ta kai wayar kunnan ta da rawan jiki. Shiru tayi tana sauraran me ake fa'da mata wanda tuni hawayen tan suka kasa tsayuwa suka gangaro kan kuncin ta. Ganin haka yasa Abbas ya 'karaso kusa da ita ya kai hannu ya cire wayar akunnan ta ya ha'da ta da kunnansa. Yin hakan keda wuya sai Teemah ta fa'da jikin 'kafafunsa ta rungume 'kafafun tana mai cigaba da kukan ta. Yana sada wayar da kunnan sa yaci gaba da saurara batare da ya furta komai ba. Sai yaji ana fa'din"............ _kullum na'kira bana samunka yalla6ai_ _sai yau dan Allah kazo ka duba aikin daka bani, inaso in gaya maka cewar Innah_ _na cikin farin ciki yanzu ha kama yaranta kuma tanaso ta gode maka bisa_ _taimakon dakayi mata amma bama samun ka shiyasa ta damu, ni ma_ _kuma ina so kazo kaga aikin daka bani jagoranci bansani ba kona yi_ ' _ko'kari"_ __ ! Abbas be san kan maganar ba be kuma san inda ta dosa ba, tunda baiji farkon ba kuma ko yajin ma be san waye akan layin ba amma duk da haka sai yace dashi " _Allah yayi wa mai wayar rasuwa tun ba yau ba, amma karka damuni dan uwansa ne kuma insha Allahu zanzo kwanan nan idan nasamu lokaci... yama sunanka_ ? Jikin Rabi'u sosai yayi sanyi ya rinka maimaita innalillahi wa inna ilaihiraji'un....Daga 'karshe ne ya sanar da Abbas sunansa tare da jero adduoi wa marigayin. Da " _Ameen-Ameen_ " Abbas ya amsa masa tare da ajiye wayar, daganan kuwa rabata jikinsa ya zauna gefen tare da fa'din " _who is he_ ? Cikin kuka tace masa " _Nima bansan shi ba Yayah, amma yace sunan shi Rabi'u wai daga Katsina yake kuma_ _Yayah Mahmud yake nema_ " " _Toh ke me kika ce_ _da shi?_ Ya sake jefa mata wata tambayar Amsa ta bashi da fa'din " _Nace masa ya rasu amma ina ga ba yadda bane, dan naji alokacin har ya fara salati amma may be dayaji wayar na tafiya har yanzu ne shiyasa be yadda ba, lastweek ne ya'kira....._ .(daga nan tabashi labarin duk abinda yafaru tun farko kamar yanda Mahmud ya labarta mata. Fa'da sosai Abbas yayi mata akan amfani da takeyi da wayar Mahmud 'din bayan tasan babu shi, ai dama baza'a rasa wa'dan da basu san da labarin rasuwar sa ba kuma ba mamaki su neme shi. Shiru tayi kawai tana share hawaye, tana son sanar dashi cewa ba amfani take yi da wayar ba amma bakinta sai ya mata nauyi ta kar6i laifin kawai. Wayar ya sake 'dauka ya 'dauki layin da Rabi'un ya 'kira dashi awayar sa tare da 'daukan numbern Umar abokin Mahmud duk yayi saving a wayarsa sannan ya cire Sim cards na Mahmud ya tashi ya koma cikin 'dakinsa harda wayar ya ajiyesu a drawer. Ranar haka ta wuni wata iri da ita dan ma Allah ya taimake ta ya fasa fita shima 'din agida ya zauna. Ummah kuwa ta aiko musu abincin rana dan ranta yakasa yadda ta daina kawowan kamar yanda Abbas ya bu'kata dan tariga tayi niyyan yin na sati guda kuwa bazata fasa ba tunanin ta ma ko mugun halinsa ne yasa yace kar akawo da safen. Babu ma wanda yabi takan abincin har la'asar tayi, Abbas masallaci kawai yaje yadawo. Ganin kamar bazata saki ranta bane bayan sallar la'asar 'din sai yace ta shirya su fita. Taji da'din hakan kuwa sosai musamman daya kaita gidan wani abokinsa a Asokoro, matar kyakkywa da ita da yarinyar ta 'daya me suna Nasreen 'yar kimanin shekaru biyu. Yarinyar ce tasa Teemah tasaki ranta gaba 'daya dan yarinyar badai 'kiriniya ba shekarar ta biyu kacal amma akwai wayo ga ta da son mutane. Abbas yaji da'din ganin ta saki ranta tana wasa sosai ma yarinyar balle data biyeta tana tayata surutu tamkar 'karamar yarinyar ita ma ta koma sai hakan ya 'kara birge shi. Da suka fito zasu tafine har Abbas ya kunna mota ma sai Teemah tace dashi " _Yayah plz ka ce su bamu aron Nasreen mana ko na sati 'daya ne mutafi da ita ni kam ina son_ _ta_ "! Be kalle ta ba yace " _suma ai suna son abin su, kema ki haifi naki mana_ "! Dayake son yaran yariga ya cika mata zuciya sai ta ce dashi "ai _nima 'din inaso in haifa, kuma idan nasami baby na bazan_ _bawa kowa ba, Maman Amal ma tace insha Allahu zan haifi baby na in rin'ka goya kayana_ " Kallon ta yayi da mamaki dan yanda yaga son yara 'karara a kalaman ta da kuma yanayin ta yasan bada wasa bane. Da suka ha'da idanu sai tace " _kaima ai kanason Baby ko?_ _Toh ka haifi naka dan ni bazan ta6a baka nawa ba_ " Dariya taso sashi amma sai yayi murmushi kawai yace " _zamu gani ai_ " tare da jan motar suka tafi. Yana mamakin ta shikam lokuta da dama intayi abu kamar wata babba wani lokaci kuwa sai kaga tafi kowa kwa6a. Da suka hau titi ne Teemah tafara ro'kon sa akan ya kaita gida amma ko ci kanki bece da ita ba, haka tayi ta ro'kon sa har ta ha'kura tayi shiru. Sai da ya biya dasu shopping store suka 'danyi siyayya kafin ya sake 'daukan hanyan gida, Teemah kam duk wannan abin ba birge ta suka yi ba tunda be amince da bukatar ta ba. Gidan sa ya wuce da ita inda Teemah ta sau'ka tayi ciki abinta ko kallo ma be ishe ta ba. Kayan ma da suka siya shine ya shigo dasu ita Teemah a dole wai tana fushi. Fruits salat tasha da daren ranar shi kuma Abbas coffee ya ha'da da kansa ya sha. Duk da haka fushin nata be hana ta tahowa 'dakin sa yin bacci ba da lokaci yayi. Yau kam Abbas ko kulata beyi ba har ta zo tayi kwanciyar ta shima ficewa yayi parlour ya tsaya kallon wani Hollywood movie da ake haskawa wanda ya 'dauke shi har kusan 11:00pm na dare. Lokacin daya shigo 'dakin baccin Teemah yayi nisa sosai har ta fara baje birgima da yake gwana ce ta wanan fannin. Jijjiga kai kawai yayi ya shige bayi, sai da yazo yayi sallar nafila yayi addu'o'i kafin ya kwanta agefen ta dan tuni har ta dawo tsakiyan gadon. Fuskar ta ya kallah zuwa 'dan 'kara min bakin ta daga nan ya maida kallon sa zuwa jikinta, 'yar guntuwar sleeping dress 'din data sanya har ya 'dago zuwa sama inda ya bar duk cinyoyin ta afili hatta da pant 'din dake jikin ta ma yana gani. Tsayawa kallon fresh santala-santalan cinyoyin ta yayi yana jin wani yanayi na daban na ratsa shi game da ita. Wani abu yake jin yana fizgansa zuwa gareta tare da ra'da masa ai halalin ka ce kana da damar ra6ar ta aduk lokacin daka so. Rintse ido yayi da sauri ya tashi zaune ya dafe kansa harda ambatan innalillahi wa innah ilaihi raji'un afili kamar wanda yaga wani abin tsoro. Kwanciya ya koma yayi harda juya mata baya amma sai hakan yakasa yiwuwa agare shi, sha'awar ta daya hadu zafin son ta dake zuciyar sa ya yi tasiri a kansa matu'ka. Dolen sa sai da ya sake juyawa ya dawo da kallan sa gefen da taken yaci gaba da kissima abubuwa a ransa. Data dawo jikin sa kuwa kamar jira yake sai yasa hannu ya rungume abinsa hadda ajiyan zuciya yana sha'kan 'kamshin jikin ta tsawon lokaci, bahaka yake bu'kata ba amma sam sai yake ganin kamar ita bata shiryawa kar6an bu'katar sa ba awannan lokacin shiyasa ya ha'kura. ***** Acikin satin sai ya kasance kusan kullun sai anyi ruwa da safe, dama wani lokaci haka yanayin damina yake yakan juya ne aduk lokacin daya ga dama, inda wani lokaci zakaga koda yaushe da yamma ake fiye yin ruwa wani lokaci kuma da rana tsaka inda wani lokaci kuma ruwan yakan ri'ki safiya ne na wasu lokaci. Ko yau 'din ma da hadari agarin suka tashi amma ruwa be sakko ba har kusan 'karfe bakwai na safiya. Teemah luf tayi a gadon tana jin sau'kan ruwan ga wani iska me ha'de da sanyi dake hurawa yana ratsa ta, tana so ta tashi amma ganin sa zaune da system agaban sa yasa ta ki tashi tayi shiru. Juyawa yayi ya kallo 6angaren da take wanda yasa take Teemah ta maida idanun ta ta kulle kamar me bacci, ganin 'dakin babu wadataccen haske sai tayi tunanin ko be ganta ba ne. Abinda bata sani ba kuwa shine tuntuni Abbas yasan ta tashi musamman data zuba masa idanu 'dazu kawai shima ya shareta ne dan yaga gudun ruwan ta. Tashi yayi ya shiga bayi hankalinsa akwnce dan beyi zaton zata sake yin rigimar fita ruwa ba. Teemah kam kamar jira take yi yana shigewa itama ta yun'kura tafito tabar 'dakin. Bata wani tsaya taran ruwan da hannun ta ba yau kawai ta shige ciki gaba 'daya tana juyi tana dariya da tsefaffen gashin ta da ko shower cap bata nema dan rufe shi ba. Gaba 'daya jikinta da gashin ta suka ji'ke dayake ruwan da 'karfinsa yake sau'ka shi yasa komai na jikinta sai da ya ji'ke amma bata bar juyi aruwan tana tsalle ba. Sosai ta shagala da wasan ruwan har tana watsa gashin ta a iska, unexpected kawai taga hasken wal'kiya kafin ta ankara kuwa sai ta ji 'karan tsawa me 'karfin gaske ya biyo baya, shaf ta manta ma da cewa thunder na 'kara idan ana ruwan sama tsabar yanda hankalinta ya 'dauku ga wasan ruwan. Arazane tayi ciki da gudun gaske har ji take tamkar yana biyo bayan ta, da 'karfi ta maida 'kofar ta buga sannan ta wuce da gudunta. Abbas kansa sai da ya tsaya da abinda yakeyi lokacin da 'karan ya sau'ka shi be ma san bata 'dakin ba fitowar sa kenan daga wanka kukumin sa 'daure da towel, so be kai hankalin sa wurin ta ba tukunna. Teemah kuwa bata zame ko'ina ba sai 'dakinsa tana ganinsa sai ta nufe shi dagudu ta je ta ru'kun'kume shi tare da rintse idanunta har sai daya firgita ya 'daga kalle ta da sauri sannan ya juya ya kalli gadon da kyau sai yaga bata gadon, yayi mamakin lokacin fitar ta ma. Jin jikinta ajike kuwa sai yayi saurin fahimtar daga inda tafito, beyi mamakin firgicin nata ba dan shima yaji 'karan thunder 'din. Jikin ta yaji yana kakkarwa sosai gashi ta'ki bu'de idanunta, 'ko'karin raba ta da jikinsa yafara amma babu dama saima sake 'kan'kame shi da takeyi hawaye na sakko mata sirara, gashi shima 'din so yake ya shirya yasa wadatattun kaya amma dole ya danne nashi uzurin ya hugging nata back. Yaso ya barta ahakan amma ganin kamar sanyi ze shiga jikin ta yasa shi 'dan yun'kuri ka'dan take kuwa tasake 'kan'kame shi. Sunan ta yafara 'kira ahankali da niyyar sata ta cire kayan amma ko amsashi batayi ba tsawon mintina uku suna ahaka. Daya ga cewa ta riga ta rikice sosai bazata kula shi ba sai ya kai hannu bayanta yafara 6alle 'kananun bottuns 'din dake jikin rigar ahankali har ya 6alle su gaba 'daya. Hannunta dake zagaye dashi ya yi 'kasa dasu wanda hakan yabawa rigar daman sau'ka 'kasa itama. Take kuwa Teemah tasake maida hannun ta sake ri'ke shi tana mai sau'ke numfashi. Shima 'din Abbas canjin yanayi ne ya ziyarce shi na bazata tun daga cikin jikinsa har zuwa 'kwakwalwarsa gaba 'daya sanadiyyan ha'duwar fatan jikin su. Bra ne ka'dai yarage mata sai kuma pant yanzun dayake da bra take kwana indai zata zo 'dakinsa wai dan bata so yagane mata shape 'din jikinta shiyasa take daure kwana da bra 'din duk kuwa da bata saba hakan ba. Abbas 'dagata yayi ya maida ta kan gado ya kwantar da ita tare da 6alle hook 'din bra 'din dan shima yaji'ke sosai har 'digan ruwa yakeyi. Yana 'ko'karin raba jikinsa da nata amma sai Teemah ta'ki bashi wannan damar sai ma ta 'kara ri'ke shi. Ahakan ya 'kyaleta sai ya 'dan 'dagota ka'dan yazare bra 'din wanda hakan sai da yasashi rintse idanu tare da bu'dewa atake ya sau'ke su akan 'kirjinta. Musamman dayaga yanda boobs 'din ta suka tsaya tsam dasu tamkar zasu tsone masa idanu. Sanyin daya shigeta da kuma tsoratan datayi sai ya 'kara bada gudummuwa wurin sashi yin 'dim yana shai'ki gwanin sha'awah dashi. Abbas kam tasbihi kawai yake ga mahalicci me kowa me komai. Teemah kuwa sai 'ko'karin sake shiga jikinsa takeyi saboda sanyin dayake sake ratsata. Ruwane yasake sau'kowa tamkar da bakin 'kwarya fiye ma da wanda ya sau'ka da farko dai-dai lokacin kuma Abbas yakai hannunsa kan boobs 'dinta ya shafa ahankali, laushinsu da kuma yanda suka cika masa hannu yasa yanayin sa sake birkicewa kwata-kwata natsuawar tabarsa. Kasa sakinsu yayi ya ringa shafawa har zuwa wuyanta saima yafara 'ko'karin sada su da bakinsa. Be yi hakan ba sai kawai ya zarce da romancing 'dinta azafafe, kissing 'dinta yakeyi ta ko'ina, lokacin da ya 'dora bakinsa saman boobs 'din ne Teemah ta sanya masa kuka tafara 'ko'karin tureshi sai yayi saurin ha'de musu baki wanda hakan shiya tilasta mata yin shiru tana mutsu mutsu. Abbas kam yariga yayi nisa cikin yanayin da bazai ji 'kira ba koda kuwa ace an'kira shin, shiyasa ma kukan Teemah be dakatar dashi ga abinda yake yi ba. Pant 'din dake jikinta ya zare ya wullar dashi a'kasa. Ranar kam Teemah taji maza sosai tagane kurenta ahannun captain dan koka'dan beyi mata dawasa ba, beyi mata ahankali ba sanin dayayi cewar hanyar sa abu'de take. Sai da ya riga ya shige ta kafin ya fahimci cewa sa'ar tashi ce, sosai ya girbe ta son ranshi be 'kyale ba kuwa sai daya tabbatar ya maidata cikakkiyar mace aranar. Teemah tasha kuka harda na banza, masifa ro'ko da yakushi babu wanda be samu ba amma be saurare ta ba. ".... _Zan ha'da ka da Daddy.. yaja kunnanka... yacire maka shi........ dan Allah yayah_ _zan mutu......zan ha'da ka da Ummah da Anty...waiyo Hannah_ _ta kuzo ku ceceni_ _plz....Mummmyyyy_ ! _Yayah kasheni zaiyi....dama baya sona! Waiyo Yayah_ _wallahi na daina ma rashin kunya Allah bazan sake rashin ji ba.....!_ Duk da haka Abbas be barta ba harsai da ya gama da duk abinda ya tara tsawon lokaci sannan ya koma gefe yana sau'ke numfashi tare da tunanin halin daya tsinci Fateemah, be ta6a zaton hakan ba bayan zaman datayi gidan wani namijin har na tsawon wata uku koma fi. Janyo ta yayi ya rungumeta hawayenta na cigaba da sau'ka akan 'kirjinsa, jiyake tamkar ya maida ta cikinsa dan so, wani sabon salon babin 'kaunarta ne yake sake nin kuwa masa fiye da na baya, Teemah kam jikinta duk ya saki dan azaba, motsin kirki wannan bata iya yinsa illah hawaye. Abbas kam tunanin wautar daya so tafkawa yayi lokacin da shai'dan ke yawan kawo masa rayuwar ta da Mahmud azuciyar sa ashe duk sharrin shai'dan ne, Zahran sa ajiyar sa ne shi ka'dai cikin nufin ubangiji da kariyar sa sai gashi yasame ta fiye ma da yanda yake zato. Godiya ya ringa zubawa mahalicci, lalle ya yarda komai 'kaddara ne, 'kaddarar aure ne kawai ya ha'da su da Mahmud bakomai ba tunda kam gashi tadawo masa batare da ko kwarzane ba. Ha'ki'ka Fateemah tashi ce, Allah ne ya tsara cewa shine mijinta shiyasa ya adana masa ita da kyakkyawar kulawarsa. Teemah ce tafara 'karfin halin tureshi daga jikinta, Abbas be hanata ba sai ma yatsaya kallon idanun ta da suka kumbura sukayi luhu-luhu, tausayin ta ne yaji ya kamashi, yasan be kyauta mata ba yanda yayi mata da 'karfi. Duk dama yaga 'ko'karin ta da 'karfin halin ta sosai yaji da'din hakan dama baya son raguwar mace. Tashi yayi ya wuce bayi ya ha'da mata ruwan 'dumi mai yawa a bathtub sannan yadawo 'dakin. Teemah kam tana ganinsa sai ta sanya wani sabon kukan tana yun'kurin tashi amma sai taji duk jikinta tamkar an 'daure mata shi. Abbas yana daga tsaye yake kallon duk 'ko'karin nata baya son takurata shiyasa ya barta dan ganin gudun ruwanta. Data kasa tashin kawai sai ta sanya kuka tafara ambatan sunan Anty. Abbas da sauri ya matso kusa da ita beyi wata-wata ba kawai yasa hannu ya 'dagata tana fa'din ka ajiye ni ni bana so, ba ruwana dakai daga yau" Muryar ta ma duk ta dishe ba sosai yake fita ba maganar tsaban kukan da tasha. Abbas be ajiyeta ko'ina ba sai cikin bathtub da sauri Teemah ta taso tare da sakin wani wahalallan kukan dan sosai taji zafin ruwan daya ta6a ta. Abbas kuwa be barta ta 'dago 'din ba sai ya ri'ke kafa'dun ta tana kuka tana mitan bata so kuma duk muguntan daya yi mata sai ta ha'da shi da Ummah ta rama mata. Murmushi yai yace da ita " _naji amma kibari idan nagama yin duk muguntan sai ki fa'da mata kinga sai ki ji da'din cemata girma ne ya kamaki_ " " _Naki bazan fa'da_ _ba'din_ " tafa'da afusace. Abbas daya fahimci cewa maganar sa ne bata so sai yayi shiru ya 'kyaleta taci gaba da mitan ta, be barta ba har se daya tabbatar 'dumin ya ratsa ta sannan yasake canja mata wani ruwan wanda be kai na farkon zafi ba. Yanzun kam da 'kyar da lallami da ban baki tashiga, amma data shiga sai tayi shiru dan ita kanta taji da'din ruwan dayake ta rage jin zafin. Fita yayi ya barta bayan yace da ita tayi wankan tsarki da niyyan janaba. Tura baki tayi tabi bayansa da harara. Koda ya fitan kuwa sai taci gaba da zamanta aruwan harse da taji yayi sanyi sannan ta fito daga cikin bathtub 'din da dabara dan har yanzu tana jin zafin kuma 'kafafunta na ciwo da cinyoyinta. Ahankali tayi wanka sannan ta 'dora da wankan tsarkin sai data gama sai kuma ta duba bataga komai ba da zata suturta jikinta dashi. Kukan shagwa6a ta sanya daga cikin tare da fa'din " _toh ni haka zan fito ne_ ? Da sauri Abbas ya tashi ya matso yace " _me ya faru_ ? " _banga towel ba ne_ " Tace dashi cikin muryar kuka. Murmushi yayi acikin ransa yace " _zakiyi abinda yafi haka ma indai kece_ "! Pls reader's 'din *CAPTAIN* ku rin'ka turawa wa'dan da suke tambayan page 'din da aka tura plz in kuna dashi bawai sai ni ba, nasan kuna 'ko'karin hakan sosai amma wani lokaci Allah sai ayi ta tambaya amma har mutun yagaji yayi shiru kuma ba da'di hakan nima kuma banjin da'di gaskiya. Kunsan ni ka'dai bazan iya handling dukkan groups 'din dana ke ciki ba wani sa'in sai de ahankali kawai. *KEEP FOWARDING TO D ONES THAT ASK PLZ DON'T LET THEM FEEL DISAPOINTED* . _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/13, 1:58 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ~Dedicated 2 all *CAPTAIN ABBAS COMMENTER'S* na nesa dana kusa, ha'ki'ka kuna sani nisha'di marar iyaka~. 🥰 *Bismillahir rahmanir raheem* _it takes just 3 seconds 2 say i luv u, 3hrs trying to explain it, nd it takes a whole life time to prove it_ . 🅿 *82* Wani sabon towel ya 'dauko ya shiga bayin dashi a hannunsa, Teemah naganin sa sai ta juya da sauri tana gunguni 'kasa-'kasa. Kan kafa'dar ta Abbas ya ajiye towel 'din yana murmushi ya juya shima yafita a hankali aransa yake ayyana " _banda shirmen ta miye kuma yarage harda wani 6oye jiki_ ? A hankali tafito bayan ta 'daura towel 'din, kamar wata me tsoron taka 'kasa take tafiyar, sosai takejin zafi aduk lokacin data motsa jikin ta musamman yanzu da take 'daga 'kafafu tana tafiya sai take jin wani sabon azaba na ratsata, kasa jurewa tayi sai tasaka kuka tana tafiyar tana kuka, Abbas ma sai ya tsaya kallon ta domin ya nemi tallafa mata amma ta'ki sanadin haka ma sai ta 'kara volume 'din kukan nata. Bata tsaya ba ahakan ta nufi hanyar barin 'dakin, sau 'daya ta kalli gadon sai taga ya janye bedsheet amma bai sa wani akai ba, ta6e baki tayi ta nufi hanyar 'dakin ta, Abbas kam still da idanu ya rakata dan a wannan halin yasan ko yace zai dakatar da ita ma ba sauraran sa zatayi ba nd shima dakansan ji yayi baida guts 'din tsareta a wannan lokacin ban dama sabon so da 'kaunar ta gami da tausayin ta da suka sake cika masa zuciya bayajin komai shiyasa ma ya 'kyale ta kawai. Bayi ya kai bed sheet 'din daya cire da niyyar wankewa amma tun kafin ya kai ga wankewan yajiyo muryar ta. Tafiyan ce ta gagare ta bayan har ta isa parlour ma sai ta zauna tare da sakin sabon kuka tana 'kiran sunan Mummy. Da sauri ya 'karaso inda take shima ya zauna agefen ta yana tambayar ta meke faruwa. Cikin kuka ta bashi amsa da fa'din tagaji ne kuma 'kafanta ma ciwo yake yi mata. Koda ya nemi ganin inda ke ciwo a 'kafan nata kuma sai ta'ki ta nuna masa sai ma fa'dawa jikinsa datayi tare da sakin wani kukan. Da kansa ya fahimci inda keyi mata ciwon musamman da yaga ta'ki nuna masa wurin sai yaji tausayin ta sosai, hannu yasa yana bubbuga bayan ta ahankali kamar yarinya 'karama yace " _daina kukan haka kinji, laifin Yayah ne ko_ ? Kukan ta taci gaba dayi amma tana 'dan 'kara rage masa 'karfi da haka har yasamu tayi shiru sai yasa hannu ya 'dauke ta da niyyar maida ta 'dakinta, Teeemah kam cike da rigima take fa'din " _bana so ni ka barni ba ruwana dakai......._ " Be kula ta ba har se daya dangan tata da 'dakinta kasancewar nasa gadon ba'a gyare yake ba. Koda ya kwantar da ita kuwa zama yayi agefen ta tare da ran'kwafo da kansa kusa da fuskar ta, fuskar sa na kallon nata yasa hannun sa cikin nata ya sarke su wuri guda nata, 'dayan kuma yasa kan fuskar ta yana 'kara goge mata hawayen dake gangarowa ka'dan-ka'dan tare da tallafan kuncin ta yace " _Stop crying owk...... ko kin fiso ki ringa 'daga min hankali_ ? Shiru tayi bata bashi amsa ba illah hawaye. Rintse ido yayi ya bu'de akanta, shi be san me ze ce da ita ba, lallashi ba layinsa bane be iya ba sam, shiyasa ko yanzun ma ya rasa ya zaiyi da ita, duk kalaman daya tattaro ya dage ya furta amma still she's crying, what can i do now? Ya tambayi kansa. Lallashin ta yaci gaba da yi cikin natsuwa ra'da-ra'da kamar be san yin maganar amma shi ka'dai yasan yanda yake ji azuciyar sa game da ita jiyake tamkar ya maida ta cikin sa dan so, yafi so ta nutsu tukunna kafin ya san taimakon da ze iya bata amma hakan yakasa yiwuwa shi kuma sam be 'kaunar ganin hawayen tan har ransa, da 'kyar ya samu tayi shiru gaba 'daya da ya sake cewa zai gani kuwa ta'ki yarda sam. Sai yace " _Ki bari inga yanda ciwon yake sai in shafa miki magani awurin_ _ya daina zafin ko kinfi son in'kira Anty nurse tazo da_ _injection_ ? Kai ta jijjiga masa a hankali tare da fa'din " _ni banaso_ " "Toh ki bari ingani ko? maganar yana raba jikinsa da hannayen su dake sar'ke. Ganin kamar ta amince sai yace "Yauwa 'yan matan Yayah! A hankali yake bu'de towel 'din dan har yanzu tana ri'ke da shi da hannunta, bata iya ha'da kafafun ta amma ta ri'ke towel 'din da hannu. " _Bari ingani da wuri kafin ciwon yayi tsami kar ya 'kara wani zafin ko_ ? Hannun ta cire ta kawar gefe. 'Kafar ta 'daya Abbas ya 'daga a hankali ya 'dora kan kafa'dar sa sannan ya gani, ba zai iya cewa ga yanayin data ke ciki ba dan shi ba likita bane amma sosai yake jin tausayin ta. Towel 'din ya rufa mata sannan ya fita kitchen sharp-sharp yasa ruwa a kettle ya jira yayi zafi sannan ya ha'do mata lafiyayyan tea be ko sa lipton ba illah milo da ovaltine daya zabga mata aciki. Teemah na nan har yanzu akwancen tayi luf da ita sai ma rufe ilahirin jikinta datayi da blanket tana fidda siraran hawaye da. Stool ya janyo zuwa gaban gadon yasata agaba sannan ya ajiye cup 'din akan side drawer tare da janye mayafin a hankali. Yana janyewa ta sake jan abinta ta shige ciki gaba 'daya tace " _ni ka 'kyaleni ba ruwana da kai...._ Taran ta yayi da fa'din " _naji ai nima baruwana da ke tafiya ma zanyi_ _amma yanzun kitashi kisha tea sai in tafi in barki in_ _ba haka ba in 'kira Anty nurse 'din tazo da allura uku tayi_ _miki_ " Tana jin haka ta bu'de kanta tana 'kwaba fuska, Abbas ne ya sa hannu ya talla fota zuwa jikinsa ta jinginu, anan yaji jikin ta ya 'dau zafi rau yasan zazza6i ke shirin kamata, baya son kukan nata ko ka'dan dan tana karya masa zuciya ne sai yaga tamkar be aikata daidai ba laifin kansa yake kamawa tsaban tausayin ta daya ke ji yake tamkar ya cire mata ciwon da ana yin hakan be san wani irin lallashi zai mata tayi shiru ba. Kanta ya 'dago ya ritsa ta idanu yace " _bar kukan haka nan mana ko so kike in 'kara miki_ ? Jijjiga kai tayi da sauri alamar "ah ah" sai yace " _toh shikenan share hawayen ki bazan sake ba ai wancan 'dinma laifin ki ne bana hana ki wasan ruwan nan ba amma ki ka 'ki jina shiyasa nayi miki amma in kina jin_ _magana ta bazamu sake yin fa'da ba ko kina so muna fa'da_ ? Da kai tabashi amsa alamar "ah ah". Abbas sai yace " _yauwa 'yan matan Yayah, Allah yayi miki albarka ya haskaka rayuwar ki fiye da yanda kika hasakaka min zuciya ya saka_ _maki da aljannar sa ma'daukakiya ......_ Hannu yasa ya 'dauko tea cup 'din a hannunsa yana juyawa fuskar sa da murmushi yace "...... _ya kuma baki baby mai kama da waye ma.......?_ Ya ritsa ta da idanu. Murmushi maganar tasa ta tasa ta sai ta tarasa mai ma zata ce dashi kuma sai kawai ta ya mutsa fuska tare da rike cikin ta alamar yunwa takeji. Abbas ma murmushin yayi mai sauti sai ya bata cup 'din a hannun ta ta ringa sha a hankali bata shanye ba ta mi'ka masa cup 'din tace ya isheta dan bata jin da'din bakin ta sosai. Abbas be matsa mata ba sai ya kar6a ya ajiye tare da tambayar ta zafin ciwon muryarta ciki ciki ta bashi da fa'din yana mata zafi ka'dan-ka'dan amma idan ta motsa 'kafarta sosai takejin zafin. Abbas cewa yayi da ita " _sorry... zai daina very soon da iznin Allah kinji_ " Shiru tayi masa tafara 'ko'karin kwanciya, Abbas sai ya gyara mata kwanciyar tare da lullu6e ta da kyau yace bari yana zuwa daga nan yafita a'dakin. Yana komawa 'dakin sa ya'kira layin nurse sukayi magana inda ya roketa cewa kar ta 6ata lokaci bayan haka sai ya tura mata address 'din gidan nasu sannan ya ajiye wayar. Bayi ya koma ya wanke bedsheet 'din daya cire a gadon harda kayanta da suka jike 'dazun gaba 'daya ya hada ya wanke ya fita corridon baya ya shanya su. Yana kammalawa ya shiga bathroom yayi wanka na biyu sannan yafito ya shirya cikin wani ba'kin long trouser da jan T-shirt kamar bashi ba, yana shirin fitowa sai yaji 'karan door bell, yasan Anty nurse ce ko kuma driver cikin su 'dayane ya iso. *Toh ga al'kawarina na sauke read more biyu ne bayawa nayi muku, amma nima sai a daure a faranta min dan naji da'di* .🥰 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerhn ku ce* 😍 [10/13, 1:58 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* I _dedicated this page to my fellow *Wattpadians* , Ha'ki'ka *SALMERH*_ _najin da'din kasancewa daku ,wannan page 'din kyautar kune_ .🥰 *Bismillahir rahmanir raheem* _A mistake is only a mistake when u don't learn from it. Otherwise it is a *LESSON* ._ 🅿 *83* Zuwa yayi ya bu'de 'kofan sai yaci arba da driver a tsaye kar6an abincin yayi bayan sun gaisa harma drivern na bashi ha'kurin jinkirin da aka samu yace ruwane yasa ba'a kawo dawuri ba. Abbas kuwa yace masa bakomai ai sannan ya wuce dinning. A gate motar driver da Anty nurse suka yi clash yana fita itama ta shigo, Abbas na ajiye abin hannunsa sai ya kama hanyar 'dakin ta domin duba yanayin datake ciki kafin ya isa sai yasake jin door bell karo na biyu, be 'karasa 'dakin ba sai ya juya izuwa 'kofan dan a 'kage yake Nurse ta iso dan ta duba masa ita. Anty nurse ce tsaye tana murmushi shima murmushin yayi tare da matsawa yabata daman shigowa yana fa'din " _har ina shirin sake 'kiranki ai_ " Nurse tace " _na hutar da kai ai tunda gani na iso"_ ! Zama take 'ko'karin yi a kujera Abbas ya dakatar da ita da fa'din " _muje dai tana ciki ai ba batun zama kuma_ "! Dariya nurse tayi itama tace " _toh bakomai yalla6ai ai dama ba zaman nazo yi ba_ " Gaba yayi ta bishi abaya har zuwa 'dakin Teemah inda suka same ta har tafara bacci, motsin shigowar su ne ya farkar da ita sai ta sau'ke idanu a kansu. Tana ganin nurse sai ta maida kallon ta kan Abbas tana kwa6a fuska. Nurse 'din ne tana dariya tace mata " _Ashe 'yar shagwa6an Yayah me tsoron allura ce ma! Ya jikin naki_ ? Ahankali tace " _na warke tun 'dazu!, ina kwana Anty_ " " _Lafiya lau Alhamdulillah_ " Anty nurse tace tare da zama agefen ta, Abbas kuma yana tsaye ya kama kunkumi da duka hannayensa biyu yana kallon ta. " _Meke damunki_ ? Anty nurse 'din ta sake tambayar Teemah tare da ta6a wuyanta. Take idanun ta suka tara ruwa sai ta 'daga kai ta kalli Abbas 'din suna ha'da idanu ya taho kusa da ita ya zauna tare da tallafan ta zuwa jikinsa sai ta 6oye fuskanta a'kirjinsa a hankali tace " _Ni bana son allura Yayah_ " Jinjina kai yayi tare da fa'din " _Alright ki nutsu bazata miki ba magani kawai zata baki idan ta dubaki, kinji"_ Dayake yariga yayiwa nurse 'din bayani tun a waya so bawani sabon bayani datake bu'kata daga wurin su illah ha'din kan Teemah. Hanglove take sawa a hannun ta take fa'din " _ina jin guri zaka bamu fah yalla6ai dan naga alama in kana kusa ba zamuyi abinda ya dace ba da wannan shagwa6a66iyar_ ". Raba ta da jikinsa yayi yari'ke kafa'dun ta yace " _ki nutsu ta duba ki kinji in har kika yi mata rashin ji_ _kinsan tana da allura ko, ni kuwa bazan hanata yimiki ba, zan dawo yanzu bari in 'dauko_ _wayata_ ". Fita yayi ya bar su inda Anty nurse 'din tace mata ta gyara da kyau ta dubata, hawaye tafara yi ka'dan-ka'dan tare da fa'din " _Anty dan Allah kar kimin allura in kika yimin mutuwa zanyi, Yayah ma mugunta yamin 'dazu........._ " " _Shiii...! yi shiru bazan miki allura ba karki damu kinji_ " Kai ta 'daga mata sannan ta bata chance ta duba ta. Bama wani ciwo taji ba kawai dai 'kan'kanta da rashin 'karfi da jikintan ke dashi ne ha'di da rashin sabo yasa take jin bada'di, ga kuma shigan 'karfin da akayi mata shiyasa take jin zafi sosai. Da farko nurse 'din tayi tunanin ko ciwo sosai Teemahn taji amma sai kuma taga abin da sau'ki musamman dayake ta yi anfani da ruwan zafi so ba wata matsala sosai. Data ga haka sai tace da Teemahn " _Dama shi mijin kine_ ? Da " _Ummm_ " Teemah ta bata amsa tana mai jin kunyar ta ga jikinta. Nurse na cire hanglove 'din hannun take fadin shine kike cewa yayi miki mugunta ko? Waye ya gaya miki ana fa'din haka?ko bakya son shine akayi muku auren ? Teemah kam shiru tayi tana tunanin me zata ce da Anty nurse 'din, ita kuwa nurse tana har ha'da magunguna taci gaba da fa'din " _kar kinayin taurin kai in bahaka ba kullum ciwo zaki rin'ka ji kinji_ ? Kai ta 'daga mata alamar " _toh_ " " _Yauwa Fateemah, ko kinfi son mijinki yana neman wasu matan awaje_ ? Yanzun ma da kai ta bata amsa daidai Abbas ya turo 'kofan ya shigo dan hankalin sa yakasa kwanciya. Dukkan su sai hankalinsu yakoma kansa. Gefen Teemah yazo ya zauna sai nurse tayi masa bayanin babu ma matsala sosai idan taci gaba da amfani da ruwan 'dumi ma komai zai dai-dai ta. Sai ta bashi wasu magunguna kala biyu tace ta sha wannan zazza6in nata zai sau'ka kuma zai 'kara taimakawa wajen healing ciwon da wuri. Godiya Abbas yayi mata inda a take yabawa Teemah maganin ta sha sai suka fita tare da nurse suka bar Teemah ita ka'dai inda ta koma ta sake kwantawa. Suna fita parlourn nurse tace dashi " _yalla6ai kafa so kayi 6arna gaskiya_ " Kai Abbas ya sosa yace " _Allah ya takaita ai na kuma gode masa_ "! Sai tace " _hakane amma dai a kiyaye gaba saboda gudun matsala duk dama farkon shine_ _me wahala amma gaskiya a'dan sarara mata na kwana biyu_ " " _Bakomai wannan ba matsala bane dr. nagode sosai_ " Daga nan sukayi sallama ta tafi. Teemah kam fitsari ne ya matsata ta tashi ta shiga bayi, tana tsugun nawa sai ta mi'ke dan azaba zafi take ji sosai amma sai ta daure ta sake tsugunnawan sama-sama tayi fitsarin idanun ta harna hawaye amma haka ta daure dan bata so Yayah yasan da ciwon balle yayi mata batun allura. Abbas ma 'dakin nata ya koma sai ya be ganta ba motsin ruwa da yajiyo a bayi ne yasa ya fahimci tana ciki, tsayuwa Abbas yayi yana jiran fitowar ta. Teemah na share hawaye ta fito, tana ganinsa sai tayi turus ta sunkuyar da kanta ahankali ta isa gefen sa kanta a'kasa. Hannunta ya kamo yajawo ta zuwa jikinsa yace " _me yasame ki kike kuka, what's wrong kuma ba kince kin warke ba_ " Kai ta 'daga masa. Abbas shiru yayi yana kallon ta ya san tana jin zafin kawai de tace ta warke ne dan kar yace allura. A hankali ya sake fa'din " _Toh meyafaru_ ? Tace _"ni ka kaini wurin Mummy_ !" " _Ba yau ba sai kin warke zan kaiki owk!_ Shiru tayi bata masa magana ba sai shine ya sake fa'din " _Baki gaji da zama da towel 'din bane har yanzu_ ? " _Yanzun ma kaya zan saka_ " tace da shi a hankali. Sakin ta yayi taje ta dubo kayan sai kuma ta tsaya ta rungume su a'kirjin ta tana kallon shi. " _Ya akayi in zo insa miki ne_ ? Da sauri ta jijjiga kanta " _ko sai na fita_ ? Yayi maganar tare da 'dage gira. " _Umm_ " tace dashi. Sai yayi murmushi tare da barin 'dakin yace " _ina jiranki a parlour yanzu kar ki sake kwanciya fah kinji._ " Kayan tasaka cikin natsuwa sannan ta fita ta same shi akan dinning yana break fast, wurin sa ta isa ta zauna tayi shiru daya nemi taci dai tace ahh sai anjima zata ci,sai daya gama sannan suka koma 'dakin sa dukkan su Teemah bacci take ji dan haka sai da ta kwanta Abbas kuwa system 'dinsa yasa a gaba yana operating zaune kusa da ita seconds-seconds yake juyawa ya ganta. Ranar haka ya wuni agida babu inda yaje illah masallaci, da azahar Teemah ta tashi ta koma 'dakin ta sallah itama, dayake data yi baccin sai taji jikinta yayi mata wani iri zazza6in babu yanzu amma kuma still bata koma normal gaba 'daya ba, ruwa ta watsa ajikin ta ta reda sake zama cikin ruwan 'dumi dan ta fahimci shine ya 'dan sanyaya mata zafin 'dazu dasafe. Wata ba'kar doguwar riga ta sanya ajikin ta me adon golden colour stones manya, sai data idar da sallah sannan ta 'dauki veil shima golden ta yane kanta dashi, parlour ta dawo dan yanzun kam ba laifi ta 'dan ji dama-dama, anan Abbas yazo yasame ta ya kuwa ji da'din hakan shima cikin shigar 'kananun kaya yake bai so fitan ba amma daya tuna cewa gobe ne tafiyar su Mummy sai yaga dacewar kaita dan suyi sallama ma kuma ko dan ya faranta mata tunda dakan ta ma ta nemi zuwa 'dazun, shaf ya manta da batun tafiyar sai yanzu daya fita Daddy ya 'kira shi dan ya isar masa da wani sa'ko shiyasa ma ya tuna sai kawai ya ce da ita tatashi ya kaita gurin Mummy. Yana tafiya zuwa 'dakin sa domin 'dauko key yayi maganar so be kula da yanayin da ta shiga ba abinda ka'dai yasani shine zataji da'din hakan. Teemah kam farin ciki ne yacika sosai har da tashi da 'karfinta dan murna alokacin ne ta tuna da taji zafi a'kasanta amma ahakan ta daure dan kar yace yafasa. Abbas sam hankalin sa be je kan yanayin tafiyar ta ba saboda yaga ta warware shiyasa ma be damu ba be sani ba ashe idan an kula sosai za'a ga chanji tattare da ita. Suna shiga parlourn suka tarar da su Ummah ga6a 'dayan su zaune a cikin parlourn, Teemah taso ta isa da gudu amma sai taji tsoron kar taji zafi sai ta 'karasa a hankali, hakan ma dan tana daure wa ne shiyasa sosai take 'karfin hali wurin ganin ta 6oye ciwon ko dan gudun allura ma. Tana isa ta fa'da jikin Mummy sai kuma ta saki kuka, wanda ya jawo hankalin dukkan su zuwa gare ta, Abbas kam mamaki ne yacika shi ganin lafiya 'kalau suka taho toh menene kuma na kuka yanzu anan. Anty murmushi take yi dan tana ganin Teemah ta fahimci yanayin ta data ke ciki, Ummah kuma mamaki ne ya ziyarce ta yayin da tausayin Teemah ya cika zuciyar Mummy nan take. Abbas zama yayi daga 'dan nesa da su ya zuba mata idanu. Mummy bata tam baye ta me yafaru ba illah kawai rungumar ta da ta yi itama tana babbuga bayan ta alamar rarrashi. Ummah kam Abbas take kallo ganin duk ya zama kamar a birkice da ganin kukan Fateemahn. Anty ne tace da ita " _zo nan Fateema wai me ya sameki kike kuka haka nan ko duk missing 'din namu ne_ ? Taso wa tayi a nutse ta dawo wurin Antyn tana me cigaba da zubda hawaye. Anty mi'kewa tayi tare da kama hannunta suka shige ciki inda sika bar parlourn batare da ko gaisuwa sunyi da Abbas ba. Fitan sun ne yabawa Abbas daman gaida su Ummah, gama gaisuwar keda wuya kuwa Mummy ma ta bar 'dakin dan sosai yau 'din taji nauyin sirikin nata ya kamata. Ummah kuwa ganin anbar su su biyu take sai ta 6ata rai ta kalle shi tace dashi " _Muhammad wace mugun ta kake yiwa yarinyar nan da har_ _take irin wannan kukan_ ? Ido Abbas ya 'dan zaro waje yace " _mugunta dai Ummah ni 'din_ ? _Ai kinsan halin yaron ki ba mugu bane, Allah shagwa6a ce ke kawai damun_ _ta wai dan kanta na ciwo_ " Ya 'karashe maganar da sosa kansa. Ummah cewa tayi " _Ni dai kasan banason zalinci koka'dan ballantana rashin imani da tausayi, komai zakayi ka rin'ka tuna cewa shekarun ku ba 'daya da ita ba da kuma raunin ta na 'ya mace_ "! " _Toh Ummah insha Allahu zan kiyaye_ " Yasan halin Ummahn sa adun'kule yanzun tayi masa fa'dan, yasan ba mamaki tagano matsalar su ne shiyasa tafa'di hakan dan ta gama gano abinda yafaru. Yanzune ma yake jin dama be kawo ta ba yazo abinsa shi ka'dai, bayan yasan su Ummah sun girmi tunanin sa, sai dai kuma a wannan yanayin ba ze iya fita yabar ta ita ka'dai ba hankalinsa ba zai kwanta ba sam, dama beyi niyyan zuwa ko'ina ba sai kuma Daddy ya aike shi. " _Tasha maganin ciwon kan ne_ ? Ummah ta tambaye shi. Da " _ehh Ummah tasha magani tun 'dazu ma_ " yabata amsar tambayar tata. " _Allah ya sauwa'ka toh"_ Toh Ummahn ta sake fa'di atakaice. Anty kam suna shiga ciki ta zaunar da Teemah a bakin gado tare da tsare ta da tambayar me yafaru. Da in-inah Teemah tafara magana cewa " _Ya....yah ne...!_ Da sauri Anty ta tare ta da fa'din " _dukan ki yayi_ ? Sai ta jijjiga kanta alamar " _ah ah_ " Anty kuwa bata sake tambayar ta sai tace " _Toh shikenan kiyi shiru ki daina kuka, jikinki na ciwo sosai ne?_ Cikin shagwa6a Teemah ta bata amsa da fa'din " _K'afata na min ciwo idan...zauna da tafiya... ma_ " " _Toh yi ha'kuri a hankali zai daina kinji, ina kinyi amfani da ruwan zafi_ ? Kai Teemah ta 'daga mata. Anty ma sai ta jinjina kai kawai batare da furta wata kalma ba. Wani abu ta ha'da mata a cup da madara tabata ta ce ta shanye zafin zai daina da iznin Allah. Teemah da bata san ko menene ba kar6a kawai tayi ta shanye abinta dan so takeyi zafin datake ji ya daina gaba 'daya ko dan tana yin fitsari ba fargaba ma. Yanzune Anty ta fahimci cewa barrier 'din da Munnira tayiwa Mahmud da Fateemah yayi tasiri akan su, yanzu ne ta sake tabbatar da gaskiya cewa Mahmud be 'dorawa Fateemah iddar komai ba har yakoma ga mahallicin sa. Ha'kika ta cutar da rayuwar 'danta ta fuskoki da dama, addu'ah tayi masa cikin ranta tare da nema masa gafarar mahalicci. Lallai da gudummuwar ta rayuwar gidan 'dan ta na cikinta ya ta6ar6are, ha'ki'ka bata kasance uwa tagari ba, bata fatan irin hakan yasake faruwa ga rayuwar wanin ta har abada. 'Ko'kari tayi ta maida hawayen ta tace yah Allahu kayafemin, ka kai haske cikin 'kabarin Mahmud. *2:20pm* Hannah ta dawo da mugun gajiyar ta inda tasami Ummah da Abbas zaune a parlour suna 'dan ta6a hira, zama tayi a kusa da Ummah tare da fa'din " _wash Allah na, Ummah na gaji sosai yau 'din nan,_ _Allah gudowa ma nayi_ ". Abbas kallon ta yayi da mamaki yace " _saboda me kenan_ ? Hannah juya idanu tayi sai suka ha'da ido da Ummah afakaice, sai tace " _Yayah lecture 'daya ne yarage mana kuma ance lecturer 'din baya gari shiyasa na taho_ " Abbas shiru yayi ya dai ji tane kawai ba wai dan ya yarda ba, amma be kulata dan shi yanzu damuwar da ta dami ransa dabance, so yake yasan halin da matar sa ke ciki kafin ya wuce. Hannah gaishe shi tayi sai ta tambaye shi " _Yayah ya Teemah fah_ ? Kafin yayi magana sai Ummah ta bata amsa da fa'din " _tana ciki tare suka zo, ba mamaki tana wajen Antyn ta_ " Hannah najin haka ta tashi da sauri jakar ta ma anan tabari ta nufi ciki. Teemah har yanzu tana wurin Anty inda take 'kara jan hankalin ta akan ri'ke mutuncin aurenta sanin girma da kuma darajan da mijin ta ke dashi tare da ri'ke sirrin dake tsakanin su. Da sallama Hannah ta shiga 'dakin ta samu Anty na 'daure wa Teemah gashin kanta. Da gudu taje ta rungume ta tana fa'din " _i so much miss u matar Yayah!tun yaushe kuka zo_ ? " _Zaki karyani Hannah dan Allah_ ! Inji teemah Hannah kuwa sai tace " _Ba laifi ai kona karyakin be wuci ace 'kiyayyar dangin miji ba_ " Murmushi Anty tayi tace musu maza su koma 'dakin su suje su huta wannan hayaniyar ta isa haka. Suna shiga 'dakin Hannah ta sake tambayar ta wai tun yaushe suka zo? Da " _Bamu da'de ba_ " Teemah ta bata amsa tana yatsina fuska. Abbas har zai tafi sai yace da Ummah bari yaga Mummy kafin ya wuce. Yana shiga 6angaren da zai kaishi 'dakin da Mummyn take sai yajiyo hayaniyar Hannah yasan may be suna tare ne tunda yaji hayani ya har haka. Canja hanya yayi ya isa 'dakin Hannah be tsaya bugawa ba kawai ya tura 'kofar sai ya tsaya batare da ya shigo ba. Shiru sukayi da ganin san dama ita Teemah ba wani dogon magana takeyi ba Hannah ce me surutun. Shi kanshi be san me yakawo shi ba, zuciyar sa ke bu'katan hakan, dama ganin ta yaso yi kuma daya gantan sai ya rasa abin fa'da kawai sai ya 'karaso cikin 'dakin a hankali, yazo gabanta ya tsaya yana kallon ta a hankali ya furta " _ya jikin naki_ ? Da sauri tace dashi " _da sau'ki_ " Yace " _toh zan tafi amma anjima zan dawo mu koma gida kinji_ " Teemah shiru tayi masa shima sai kawai ya juya ga Hannah yace " _Hannah plz ki tabbatar taci abinci_ " Yana gama fa'din haka ya fice a 'dakin cikin takunsa na 'kasaita, shi kansa yana mamakin kansa a yau 'din yanda yake ji game da matar tasa, Hannah na wurin ne ma shiyasa be son jan magana sosai. Yana fita Hannah ta tashi da sauri ta le'ka bayan sa ganin yatafin yasa ta sake dawowa wurin Teemah ta dafa kafa'dar ta da mamaki tace " _matar Yayah nifa bangane ba, me ya sameki naji Yayah yana tamabayar jikinki harma da bani kwangilar saki cin abinci_ ? " _banda lafiya ne_ " Teemah ta bata amsa a takaice. Karkata kai Hannah tayi da zararran ido take kallon Teemah da sigar tsokana tace " _Ciwon amarci ko?_ " _Wata'kila_ "! Teemah tace tare da gyara zamanta. " _Kede fa'di gaskiya matar captain ai nima naganki badai ba_ " Da 'dan 'karfi Teemah tace " _Bansani ba Hannah plz ki 'kyaleni ke dama ba mutun ya ha'du dake ba duk_ _yadda yakai ga kewar ki sai kin 6ata ran mutun kike jinda'di_ " Dariya Hannah tayi tace " _Come down mana amarya! 6ata ran me kuma nayi miki amaryar Yayah fisabilillahi? ke de kice bakya so in san cewa Yayah ya fa'da_ _ne, amma ai tun 'dazu ma bangane kanki ba duk kin canja Allah kinyi wata iri_ _ashe ashe yarinya taji da bambanci ne_ !" Saukar da murya Teemah tayi tace " _Hannah Allah banaso bambancin me kuma naji?_ Da murmushi Hannah tace " _Kin fini sani ai yarinya keda kika san komai kuma ni zaki tambaya, jifa yanda yazo shima 'daya ko kunya_ _bai ji wai ya jikin naki.? Bayan yana gani na wurin ko kunyata fa be ji ba"_ Baki ta kama tace " _kai Allah ya shiryi Yayah wallahi_ ". " _Kema Allah ya shirye ki ai kema ba kunyar ne dake ba da kike waya da Bilal a inda nake kina jin kunyata ne? kuma kamar a kunnan sa hakan da kika ce"_ " _Bazan yi mamaki ba ai nasan yanzu amarya kike kuma ba kya laifi, so ko kin kareshi ma nasan ba laifin ki bane, ballantana_ _yanzu da kika san da'din miji nasan fiye da haka ma zakiyi, sai dai plz kiji 'kaina karki fa'dawa Yayah_ _abinda nace nayi al'kawarin indai da raina zan tayaki zaman jego da rainon baby_ " Duka Teemah ta kai mata tare da fa'din "' _yar rainin sense_ _kawai_ " sai ta goce tana dariya tace " _Toh ina laifi da zan miki zaman jego tunda wannan 'din ba a gayya ceni ba wancen kam_ _ai kinga ko babu gayyata sai naje may be ma sanadin haka na samu namesake_ " " Allah ya kiyaye 'yata tazama takwararki" Hannah kwafa tayi tace " _Harma_ ....."? Da " _ehh_ " " _aw ashe ma zaki haihun kinga kuwa zuwana tabbas_ " Teemah ta amsa mata tayi da fa'din " _bismillah sai ki je ai mugani_ " " _Dai na gagagwa kamar yau ne insha Allahu matar Yayah ai anyi me wuyan.... kai amma fa nasan kin ji jiki da ganin_ _yanda kika koma har kina bani tausayi wallahi_ " Juya wa Teemah tayi ta kwanta kawai tana mita wai Hannah ta tattare surutun duk 'yan gidan nan akanta, she is so talkative ita bazata iya da surutun Hannah ba. Hannah ma tashi tayi tana rage kayan jikin ta take sake fa'din " _dan Allah matar Yayah in zaki haihu ki haifo min baby girl me kama dani_ _kinji_ ? Teemah 'kin kulata tayi da Hannah taga haka sai tace bari ta je ta kawo musu abinci......tana fitan tasake fa'din " _ko baki kulani bama de sai kin haifa_ " Abbas daga wurin Mummy ya wuce bai sake dawowa ba. Ko gurin cin abincin Hannah bata bar Teemah da tsokana ba har suka 'kare. Sai daga baya suka koma wajen su Mummy anan ta sake suka ta hira abinsu kamar ba ita ba. Sai bayan sallar isha'i Abbas ya dawo gidan dan su tafi, lokacin kuwa hajiya Fateemah an saki jiki a gida kawai sai taji labarin wai yazo. Ummah ce tace ko za'a barta agida kawai zuwa gobe sai ta koma saboda ganin kamar Teemah batason tafiyar. Teemah kam da murnar ta ta amsa da " _ehh Ummah...._ " Da sauri Mummy da Anty suka ce " _ah ah tafiya zatayi, zaman me zatayi musu kuma anan, gara ta koma gidan_ _mijinta yafi_ " Dole Ummah tayi shiru dan bakin su yafi nata. Da fushi kuwa ta tafi suka bar su Hannah da kewa. Bayan tafiyar su ne Anty tayi wa su Ummah bayanin cewa dama ba iddar Mahmud akan Fateemah, Mahmud be 'dora mata iddah ba, tabasu labarin duk abinda ya faru game da hakan da yake a baya lokacin rasuwar Mahmud bata bayyana wannan 'din ga kowa ba saboda aganin ta sirri ne. Dukkan su sunyi mamaki sosai sai abin yaso ya dawo musu sabo aransu kowa na tunanin ashe har haka Teemah tayi zaman 'kunci tare da Mahmud lalle duniya abin tsorone, tunda gashi wanda akayi domin san ma babu shi yatafi ya bar kowa da tarin nadama. *Allah Ubangiji ya sa mufi 'karfin zu'katan mu ya kyautata mana 'karshen mu.* ( ~Ameen~ ) Mummy ce ke wannan addu'ar acikin ranta, Anty kam hawaye take sharewa a hankali dan ta tuna da 'danta marigayi, Ummah kuwa har taje bacci tana tunanin wannan abin aranta. Suna komawa gida direct 'dakin Abbas suka wuce amma bai bari ta kwanta ba sai da ya bata magani tasha sannan ya bari ta kwanta yaraka 'dakin ta canjo kaya ma 'ki yayi dole sai da ta saka wata t-shirt 'dinsa mai 'dan girma sai kuwa rigar ta rufe mata jiki ka'dan domin ya'dan sau'ko mata, shi kanshi Abbas rigar tana bashi balance bai fiya sakata ba sai in yanada bu'katar shan iska., wanka ya shiga koda ya fito ya shirya ma sai da yayi sallah sannan ya hawo gadon, jikinta yazo ya matso ya rungumo ta Teemah take ta fara 'ko'karin barin jikinsa da sauri dama 'dari-'dari takeyi dashi shiyasa tun 'dazu bacci yakasa 'daukan ta, Abbas sai ya ra'da mata " _come on... ki nutsu ban son rigima i thought rage miki wahala zanyi, naga anjima dakan ki ma zaki shige min jiki_ _ko da banaso_ " Shiru tayi kawai ta zubawa 'kirjinsa idanu tana jin tsoron sa har ranta amma data ga bai yi mata komai ba sai ta saki ranta ajikin nasa har bacci ya 'dauke ta. Abbas ma dagangan ya 'kyaleta be mata komai ba dan ya fahimci tsoronsa dake cikin 'kwayar idanun ta, kuma baya so tsoron yayi tasiri azuciyar ta shiyasa. Washe gari da safe bayan sunyi sallah Abbas wanka ya shiga yafito da hanzari yake yin komai yayin da Teemah ke bin sa da idanu, yana gaban mirror yana gogec ruwan kansa ta cikin mirror ya hango yanda take kallon sa. Juywa yayi yace da ita " _kallon fah_ " Tare da 'dage gira. Take ta tura baki ta tayi sama da idanun ta zuwa kan photon sa dake sama tace " _ni kai nake kallo ne_ ? " _Toh wa kike kallo gaya min_ ? Ya sake tambayar ta. Sai ta nuna masa photon da hannu. Murmushi yayi yace " _photon ki ne toh wannan 'din_ ? " _Umm-umm_ " Tace a hankali. Sai ya sake fa'din " _Photon mijin ki kike gani ko_ ? Shiru tayi masa tana 'kun'kuni Abbas kam 'dauke idanun sa yayi a kanta yaci gaba da abinda yake yi. Shine yaje ya raja su Mummy da Anty ranar duk suka wuce kano gaba 'daya, Mummy ma naso ta gaida dangi wa'dan da ba su ha'du da su ba dan basu samu halattan bikin ba. Kafin ya dawo kuwa Teemah ta tashi dayake taji 'karfin jikin ta yanzun bata jin zafin komai, aiki tayi agidan sosai inda ya dawo tsab da shi sannan tayi wanka ta shirya cikin 'kananun kayan ta riga da ta kai mata ko gwiwa ba da dogon wandon skinny tayi kyau kamar asace ta, gashin ta ta kama ta 'daure a tsakiyar kanta da 'karamin ribbom. Abbas kansa daya dawo yaji da'din hakan sai ma yaji wani sabon san kasancewa da ita a lokacin. Zama yayi a kujera yana kallon ta da lumsassun idanu yace " _nagaji yau 'din nan zo ki tayani rage kaya na plz_ ! 'Kasa-'kasa tace " _kai baka da hannu_ _ne_ ? Sarai yaji ta amma sai yayi kamar be ji ba sai ma cewa da yayi " _quickly plz yunwa nake ji fah_ ! A hankali ta 'kara so inda yake ta fara 6alle masa bottuns 'din rigar batare da ta kalli idanun sa ba. Abbas hannu yasa daga bayan ta ya tura ta ta fa'do jikin sa tana 'ko'karin mi'kewa Abbas ya 'ki bata dama sai ya matso da fuskar sa kusa da tata, rintse idanu tayi da 'karfi hannun kan 'kirkinsa tana so ta ture shi amma hakan ya gagare ta dan ko motsi be yi ba, bakin su ya ha'de ya fara bata lafiyayyan kiss me tsayawa azuciyar masoyi. Teeemah kam tsintan kanta tayi awani irin yanayi bazata ce ga yanayin data tsinci kanta ba amma duk da haka sai take mutsu-mutsu dan ta 'kwaci kanta, Abbas be bar ta ba sai da ya tabbatar cewa sa'kon sa ya isa sannan ya 'kyaleta. Muryar sa ciki-ciki yace " _tashi ki bani abinci_ "! Shiru tayi kamar bata ji ba tana maida numfashi a hankali kanta akan 'kirjin sa " _kina son 'kari ne?_ Ya tambaye ta sai ta mi'ke a hankali ta isa dinning shima Abbas a baya yabita yana 'ko'karin daidaita nutsuwar sa. Haka Abbas yaci gaba da kulawa da ita be 'kara ra6an ta ba duk kuwa da cewa yana tsananin bu'katan hakan amma ya danne saboda tausayin halin da zata shiga. Sai de yakanyi 'ko'kari wajen koyar da ita karatun sa mai wuyar fassaruwa musamman idan suka zo bacci, sosai yake 'daura ta akan alayi mai wuyan mantawa, dan baya barin ta kwanciya haka batare da yayi wasa da albarkatun jikin ta ba koda kuwa da wani lokaci ne yakan ritsata da hakan. Wani lokaci idan zatayi masa gardama yakan yawaita tsorata ta da Anty nurse abu ka'dan sai yace zai 'kirata tayi mata allura tun Teemah tana masa taurin kai har tazo ta daina balle data ga baya mata irin na rannan me zafi sai kawai itama ta rin'ka barin shi koda wani lokaci ne kuwa. ***** Kwance take ajikin sa wani dare, idanun Abbas na lumshe lokacin har ya fara bacci ma sai ta rin'ka 'kiran sunan shi ahankali, bai bu'de idanun sa ba ya amsa mata da fa'din " _inajinki_ " Muryarta a sanyaye tace dashi " _Yayah yaushe zaka kaini inga Zahra_ ? " _Sai ranar da kika zama cikakkiyar doctor_ ? Ya bata amsa da lumsassun idanu. Teemah ta 6ata rai tace " _Hum-umm ni nace ma inason zama likita ne_ ? " _Zaki zama ai da iznin Allah ki rin'ka yiwa wasu allura kema harda Zahra ta sai kin mata_ _dan bataji kullum rashin kunya take min.... irin alluran Anty nurse zaki nayi mata mai zafi_ " Yatsina fuska Teemah tayi harda karya wuya tace " _Ni kam banaso_ ! " _Toh kuwa babu ke babu ganin Zahra ta_ "! Shiru tayi kawai tana tunanin wannan Zahran. ***** Kwana biyu bayan hakan da wata safiya fitowan ta daga wanka kenan ta tsaya gaban mirror tana goge ruwan dake jikinta, al'adar ta ce wannan, kusan ma za'ace tasaba da hakan tuntuni idan ta fito daga wanka bata damuwa da komai take raba jikin ta da towel 'din wani lokaci ma dashi take goge jikin ta sannan idan tagama sai ta shanya shi, sanadin haka yasa har yau bata son yin wanka a 'dakin Abbas saboda gudun masifar sa. Turo 'kofa kawai taji anyi batare da ko sallama ba sai ma " _excuse me_ " daya fa'di dai-dai da tura 'kofan. Firgita tayi daga inda take tsayen take kuwa ta fara lalu6en towel 'din da sauri. Koda ta 'daukan kuma garin sauri sai ta kama ba daidai ba bakin sama dana 'kasa ta kamo sai ya kasance a mur'de kamar ta kama, kamar ta tsala ihu haka taji dan takaici gashi ya 'kura mata idanu kamar zai cinyeta. Sai data samu ta daidai ta towel 'din kafin ta juya baya, 'kasa-'kasa tace " _sai kace ba musulmi ba zaka wani shigowa mutun 'daki babu ko neman izini_ " Caraf taji an kama hannun ta tare da juyo da ita, Teemah bata san lokacin daya iso kusa da ita ba sai hakan ya 'kara tsora tata. Cikin idanun ta yake kallo ita kuwa sai tayi 'kasa da nata idanun ta sau'ke su akan 'kirjinsa, bata juran irin wannan kallon daga gareshi, kwarjininsa rauni yake sata. Abbas idanun sa ya mayar kan wuyan ta sai ya 'kara matso da ita zuwa jikinsa sosai daf da juna yace " _zagina kike yi ko_ ? Kai ta jijjiga masa da sauri " _toh menene_ ? Ya sake tambayar ta tare da sake rage 'yar 'karamar tazarar dake tsakanin su. Yayinda Teemah tayi shiru sosai ta ke tsorata da wannan yanayin. " _Me kika ce fa'da min naji_ " A hankali yayi maganar yanda ita ka'dai ce zata ji. Itama a irin yanayin tace " _da kaina nake yi fah!_ Tun kam ma ta 'karasa yace " _shiyasa nake so in sani ai_ " Baki ta tura gaba dan bata san me zata ce dashi ba a wannan halin gashi ya takurata banda numfashin sa bata sha'kan komai. Murmushi yayi tare da 'dage idanu sama ka'dan yace " _kinji haushi ne dana kalli jikin ki?_ Shiru tayi dan takaici sai ma idanun ta suka fara tara hawaye. Abbas kam sai yasake fa'din " _an gaya miki haramun nagani ne toh ko kin manta jiya da da_ ...... Da sauri Teemah ta toshe masa baki da hannunta 'daya dan kar ya 'karasa fa'da, ita kanta ta manta cewar yagama ganin dukkan ilahirin jikin ta musamman jiya da yi mata wani mahaukacin romance 'din da be ta6a yimata irin sa ba, ita kanta sai da taji cewa ta isa, yanzun daya tuna mata kuwa bata so tasake ji ya furta da bakinsa, kunyarsa zataji sosai. Idanun ta cikin nashi suna kallon kallo, take kuwa hawayen ta suka gangaro wanda yasa dole sai data lumshe idanunta. Abbas kam hannun ta ya cire daga bakin nasa sai ya samu daman ha'de musu baki, bai barta ba kuwa har se da ya tabbatar ya danganta ta da gadon dake cikin 'dakin. Sosai ranar ya sake maimaita wa, gara ya kwasa son ranshi sannan ya 'kyale ta. Teemah kam yau bata ji zafi ba amma kuma hakan be hana ta kuka ba inda taringa ha'dawa har dana shagwa6a ma. Tare sukayi wanka a bathroom 'din ta Abbas nata tsokanan ta wai ai ranan tace zata ha'dashi dasu Daddy da Ummah su cire masa kunne, meyasa yau kuma bata fa'di hakan ba sai ma ita ke 'ko'karin cire masa kunnan nasa saboda santi. Dayake yau 'din da 'dan karfin ta ba kamar rannan ba, duk dama Abbas din bana wasa bane sosai ya galabaitar da ita amma hakan be sa bakin ta ya mutu ba, sai ta bu'di baki a hankali ta maida masa martani da fa'din " _bawani santi ita kam dataji banda azaba....... kuma ai sai ta gaya shi da Daddyn tunda baze_ _daina yi mata muguntan ba_ " Abbas kam cemata yayi " _bari na 'kara toh sai ki ji da'din fa'da musu mai dalili_ " Tana jin haka ta tashi ta fito ta barshi abayin da sauri. Dariya yabi bayan ta dashi kawai, daman ma tsokanan ta kawai yakeyi. Sai da yafito kafin ta koma tayi wankan tsarki Abbas na sake cewa da ita wai " _matsoraciya_ ". *SORRY 4 THE LATE UPDATE PLZ.* 👏🏻 ~Kai ur comment always make me felt like am d best wlh, godiya nake 'yan uwa na.~ *KEEP IT UP MASOYANA* 🤞🏻 👎🏻 *Ummu haidar* da *Sis Mar-yerm* _sako daga Teemah tace wai ita bata son kishiya abin mamakin kuma_ _shine Abbas ma ya amince wai redcard zai baku amma gaskiya Ummah bata goyi bayan hakan ba tace wai tana son ku_ _saboda bakwa fa'da da junanku_ 🤠. 😍@ *TAMAMA* _Hhhhhhh_ _wa'kar ki fah nasani rawa da juyi har ana min dariya wai_ _na zauce gaskiya ngd 'yar uwa jinjinar ban_ _girma_ .👍 ~MOST READ~ 👇🏼 *KUNGA DA YAWA NAYI MUKU KO?TOH HARDA NA GOBE NAYI , IN DA RAI KUMA SAI SATURDAY MU HADU IDAN ALLAHU YA KAIMU, IN KUMA NASAMU* *DAMA BA MAMAKI KUGA UPDATE* . _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerhn ku ce* 😍 [10/13, 1:58 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* I _dedicated this page to my fellow *Wattpadians and Whatsapp fans* , Ha'ki'ka *SALMERH*_ _najin da'din kasancewa tare daku comment 'din ku addu'o'in ku, tare da conversation 'dinku na matu'kar 'karamin karsashi, wannan page 'din kyautar kune👌🏻_ .🥰 *Bismillahir rahmanir raheem* _I learn that life is a book, every day is a new page, every month is a new chapter and every year is a new series._ 🅿 *84* Kwana biyu bayan hakan Abbas ya koma Rivers dan dama hutun 1week aka bashi, kafin hakan kuwa sun sha drama da Daddyn Abuja akan tafiyar, Abbas ya so su koma tare da matar sa amma Daddyn Abuja ya hana shi, dan cewa yayi baza'a tafi masa can wata uwa duniya da yarinya ba, salon aji da'din cutar da ita acan ba, shi be yadda da zaman sun ba har yanzu yana ganin kamar Abbas mugun hali zai yi tayi mata, amma idan tana kusa da su toh abin zai zo da sau'ki kuma dole ne ya rin'ka kulawa da ita ko dan ganin idanun su ma. Daddy gani yake kamar a bayan idanun su Abbas zai na zalintar ta ne kawai, shiyasa yace tukunna sai yaga yanayin zaman nasu kafin ta bishi. Shi kansa daddyn cewa yayi bazai bar Abbas 'din yaringa daukan tsawon lokaci ba dole zai na zuwa duba ta. Abbas be iya musu ko jan magana ba dan haka sai ya yi shiru kawai amma ba wai dan ransa ya so hakan ba, ya so ya sanar da Daddy babbah saboda yasan shi ka'dai ne zai sa Daddy amincewa amma kuma nauyin sa yake 'dan ji yanzun kuma ma dan kar Daddyn nasa yaga kamar yana jayayya ne da maganar sa shiyasa kawai ya fasa. Ya dai 'dora hope 'din sa akan Teemah da tunanin ko zata yadda itan tace zata bishi, amma ko daya zo ya same ta da batun sai ta nuna 'kin amincewar ta sai ma tace zata koma gidan Ummah kawai idan ya tafi. Bai san dalilin ta na 'kin amincewan ba, amma ba 'karamin haushi yaji ba yasan da ita ta amince toh da Daddy ma zai yi shiru akan lamarin. Ai kuwa shima Abbas yace babu inda za taje agida zata yi ta zama ita ka'dai tunda bazata bishi ba. Sosai ta tsorata da zaman da zata yi a gida ita ka'dai 'din saboda tuna baya da tayi, amma sai take ganin da ta bishi 'din gara ta zauna agidan in yaso idan ya tafi sai ta koma abinta ai baze sani ba. Sosai Teemah ta 'dauki abin wasa. Haka har Abbas ya tafi da haushin ta ha'di da kewar ta da zaiyi azuciyar sa. ***** Anty ma a cikin week 'din ta bar kano ta koma Lagos, yanzu kam zuciyar ta fes ba wani damuwa, bata da burin cutar da kowa aranta illah taga ta gyara tsakanin ta da ubangijin ta ta kuma gyara lahirar ta, gidan ta ma ba 'daya da kishiyar ta ba amma bayan ta koma Abbah ya kawo amaryar sa har gida suka wuni tare dan Abbah kansa zuwa yanzun ya yadda da cewa Anty ta yi nadama ta gaskiya ta gyara halin ta gaba 'daya ta canja su daga munana zuwa kyawawa musamman daya ga yanda taje har Abuja musamman saboda Fateemah shiyasa ma batare da fargaban komai ba ya bar amaryar sa tare da ita. Anty ma a'dan zaman nasu ne ta fahimci cewa kishiyar ta irin alkahiri ce mai sanyin hali, dangin albarka, tariga ta 'dauri aniyar kar6an kaddarar ta aduk yanda tazo mata, ta yarda cewa zata zauna zaman amana da kishiyar ta, cikin aminci da salama shiyasa ma bata damu ba ta budewa Anty Sadiya zuciyar ta gaba 'daya. Haka kishiyar ta ma bata nuna mata komai ba suka ha'de kansu tamkar 'yan uwan juna, kowa ya ri'ke matsayin dayake kai. Raba kwanakin su sukayi kamar yadda dukkan ilahirin masu kishiya keyi wato kwanaki bibbiyu. ***** Ummah ma taso Abbas ya koma Porthacourt da matar sa sai Daddy ya hana, tayi ko'kari sosai wajen ganin ta gyara abin amma be yiwu ba, bayan haka kuma sai tayi tunanin ko Teemahn zata dawo gida ne kafin ya dawo, sai kuma Abbas shima ya yi nasa ikon ya hana. Mamaki Ummah tayi sosai akan hakan kuma sai ta tambayi Teemahn ko tayi masa wani laifi ne tace ah ah wai dan ta'ki binsa ne shiyasa, Ummah batayi mamaki ba dama tasan sai da dalili kafin zaiyi hakan dan tasan baze yi purnishing 'din ta akan laifin Daddy ba, tasan yayi hakan ne dan yayi purnishing 'dinta akan 'kin amincewa binsa da tayi, Ummah sam hakan beyi mata da'di ba, aganin ta tunda abaya nema ake yayi auren amma ya'ki har sai da akayi masa za6i, Alhamdulillah kuma sai ya kar6i za6in nasu da hannu bibbiyu toh me yasa kuma ba za'a bar shi ya nutsar da hankalin sa wuri guda ba, me yasa baza'a barshi ya tafi da iyalinsa ba ko dan ma sha'kuwar su ta 'mara 'karfi. Aranan da ya tafi Ummah ta 'kira Abbas akan zaman Teemah ita ka'dai agida 'din tace masa ai be yiba tace yayi ha'kuri Teemah ai yarinya ce kar yana biye ta akan wasu abububuwan tunda yasan bazata iya ba, shi kam rufe ido yayi yace da Ummah abar ta kawai, akwai security aciki da wajen gate babu komai insha Allahu, yace Ummah ai kowa ma haka take zama agidan auren ta so ba wani sabon abu bane, Ummah taso tayi convincing 'dinsa amma Abbas yakasa fahimtar ta dolen ta tabar shi akan ra'ayin sa kawai sai ta tura Hannah akan su zauna tare. ***** Teemah yanzu hankalin ta a kwance yake bata da damuwar komai, duk kuwa da cewa Abbas ya hana ta zuwa ko'ina amma hakan be dame ta ba, yace ta zauna a gidan ta bai yadda taje ko wajen gate ba, suna zaman su da Hannah lafiya domin Hannah na taya ta surutu sosai ta 'dauke mata tunanin komai dan Hannah ba dai surutu ba, lokacin zuwa makaranta sai ta tafi, in sun gama lectures sai ta dawo gida. Suyi fa'da suyi da'di dan Hannah akwai tsokana na fitan hankali. Abbas tunda yatafi yau kwanan sa biyu amma sau 'daya tak ya 'kira ta shi' din ma da tunanin ta ya ishe shine ya 'kira ta dan kawai yaji muryar ta, Teemah kuwa gaishe shi tayi tare da tambayar sa ya ya isa. Jiya yai muryar ta ras hankalinta akwance lokacin datake tambayar tasa bata tare da wata damuwar komai. Bai amsa maganar ta ta ba sai ma ya tambaye ta yace " _wato ke bakya missing 'dina ko_ ? Dan ransa yakasa yin ha'kurin bata damu da rashin sa ba. Shiru tayi masa bata yi magana ba, sai dariya datakeyi 'kasa-'kasa, sosai Abbas yaji haushin hakan sai ma yaga kamar farin ciki take yi daya bar ta a Abujan dan haka shima sai ya kashe 'kiran kawai ya dafe kansa. Teemah kam bata damu ba taci gaba da walwalar ta bata 'kara bi ta kansa ba haka shima. Tana waya da su Anty da Mummy harma da Daddyn ta ha kama maman Amal itama suna waya akai-akai musamman dataji cewa Teemahn tasake yin aure ma sai ta ke yawan bata shawar wari wa'dan da bazasu cutar da rayuwar kowa ba, Anty ma kullun maganar ta kenan guda 'daya shine ta kula da mijinta ta kula da hakkin da ke kanta, kuma ta daina rashin ji da taurin kai. Sosai maganganun sun yake tasiri azuciyar ta musammman sai dai bata san ta yanda zata yi handling wasu abubuwan ba dan ta fahimci Yayahn 6au'da'd'de ne. Amma data ga ya 'kara kwana da wuni be 'kira ta ba sai abin sai ya fara damun ta, da kanta ta fahimci bata kyauta masa ba. Wasa-wasa kusan kwana biyar bai 'kirata ba sai dai Hannah ce ke yawan sanar da ita cewa ai Yayah ya 'kirata data na school kusan kullun hakan Hannah ke sanar da ita, amma idan tana gida bata ganin yana 'kiran Hannah, kuma Hannah bata ta6a cewa da ita ya neme ta ba ko yace a gaida ta ba abin na 'daure mata kai sosai. Hannah kuwa bata san cewa basa waya ba da yake ba'a gida take wuni ba, sai dai itama daga baya tafara yiwa Teemah mitar bata ta6a ganin suna waya da Yayah ba shin basa missing juna ne ko kuma sai abayan idon ta akeyi. Teemah "hmm" kawai ta ce da ita, dan ita kanta zuwa yanzun tafara shiga ru'du, missing 'din sa takeyi sosai shi kansa, muryar sa, fitinar shi, touches 'din sa da komai nasa. So ma take ta ganshi gaba 'daya dan ba 'karamin missing 'din sa takeyi ba, tunanin sa kullum na damun ta musamman ma idan taje bacci da dare. Sau tari idan ta tuna da Zahran sa takanji ba da'di har zuciyarta, inda take sai taji hankalin ta yakasa kwanciya wani sabon tsanar yarinyar take ji na tsarga mata. Hannah ma da kanta ta fahimci Teemah ba daidai take ba a kwanakin nan dan tafiya ganin ta cikin tunani amma data ga bata sanar da ita meke faruwa ba sai itama bata tambaye ta ba. Ranar daya cika kwana bakwai da tafiya ranar Teemah na kwance da dare takasa bacci sai juyi take yi, Hannah har ta gama waya da Bilal ta kwanta har ta 'dan yi bacci ta farka garin yin juyi sai ta ga Teemah zaune idanun ta biyu lokacin kuwa sha 'daya da kusan rabi na dare, batayi mamaki ba sai ma tausayin Teemahn daya kama ta. Tashi tayi ta zauna tare da dafa Teemah tace " _Me yafaru ne naga har yanzu idanun ki biyu, bakya jin da'di ne_ ? Kai Teemah ta jijjiga mata tare da fa'din " _bakomai Hannah ki kwanta abinki nima yanzu zan kwanta_ ". Tana gama maganar sai ta juya ta kwanta ita bata so Hannah tasan matsalar data ke ciki. Hannah kam da kallo ta bita ganin 'karfi da yaji take 'ko'karin 6oye damuwar ta bayan fuska da yanayin ta sun riga sun bayyana komai. Teemah kam baya ta juya mata da tunanin zata kwanta itama, yayin da Hannah ta bi bayan nata da kallo tsawon da 'ki'ku biyar tausayi Teemahn take bata ita musamman daya kasance auren ta biyu amma har yanzu batayi dace da samun farin cikin daya kama ta ba duk da yanzun tana mata kwa'dayin samun farin ciki da Yayahn amma tana ga hakan bazai yiwu ba dole sai ta yi nata yun'kurin kafinnan, dan duk wacce Allah ya jarabce ta da auren miji irin Yayah Abbas toh dole sai ha'kurin ta yazarce nakowa sai tayi nin kin wanda kowacce mace keyi agidan mijin ta sannan ta'kara da du'a'i saboda neman agajin mahalicci. Duk mijin da ze nuna maka abu bai damesa ba ya nuna maka bashida matsala da komai bacin ba hakan bane aransa toh kuwa dole mace sai ta tsaya tsayin daka wurin ganin ta sai ta hankalin sa wuri guda, bako wani namiji bane wanda soyayya ke sashi bin duk abinda kike so, wanin shi ba damuwar sa bane koda kuwa yana yi miki irin son da ya zarce nakowa ne a duniyan nan. A hankali kamar ba zatayi maganar ba tace da Teemah " _matsalar Yayah ne ke damun ki ko_ ? Zaro idanu Teemah tayi tana daga kwancen sannan ta juya a hankali ta kalli Hannah bata so Hannah tasan abinda ke faruwa tsakanin su dan haka sai ta jijjiga wa Hannah kai tare da fa'din " _ni fa bance miki haka ba Hannah plz mukwan ta dare yayi fah!_ Kwafah Hannah tayi ganin yanda Teemah keso ta bin ne ta abaibai bayan kowa yagan ta a wannan yanayin yasan tana tarexda damuwa, ita kanta Hannah bataso yin shidshigi wa lamarinsu ba musamman ma daya kasance mijin Teemah 'din wanta uwa 'daya amma wani lokacin idan abu ya so barin hanyar da ta dace inkana da dama taro shi zai yi matu'kar amfani ko dan saboda gaba ma. A hankali ta kuma fa'din " _Karki maida ni shashasha mana Teemah, kin 'dauka bansan meke tafiya bane har yanzu_ ? _na jima da fahimtar kina tare da damuwa a gidan nan kawai 6oye_ _min kike yi shiyasa nima na 'kyale ki, kuma nasan ba zai wuce matsalar Yayah ba hakane_ ?. "Ah ah" Teemah tace da sauri. Hannah kuwa cewa tayi " _Allah idan baki gayamin ba ina fita gobe Ummah zan samu in fa'dawa_ _nasan zata sanar da daddy kamar yanda nasan cewa Daddy ba zai yi shiru hakanan ba dole sai ya tambayi Yayah_ _kinga ai lokacin dole ki bu'di baki kiyi magana ko_ ? Teemah da hanzari ta kamo hannun Hannah tace " _dan Allah Hannah kiyi ha'kuri karki fa'dawa Ummah, Hannah yaushe_ _ma akayi auren da har irin haka zai fara faruwa ki taimake ni karki fa'da ma kowa plz_ "! Goshi Hannah ta ha'de irin boss din nan tace " _sanar dani toh if dont want me to tell Ummah about it_ " Baki Teemah ta tura gaba " _tace ai nagaya miki bakomai tun 'da zu_ " "Kin tabbatar? Hannah ta tambaye ta. Kai ta daga kamar yarinya 'karama. Hannah kuwa tace " shikenan toh, ni bazan musa ki ba amma kisani babu abinda zai hanani sanar da Ummah gobe sai dai in ban tashi cikin rayayyu ba"! Tana maganar ta juya ta kwanta. Teemah ri'ko ta tayi tace " _Haba Hannah nice fah_ ! Da jin haushi Hannah tace " _ai nima nice!!_ Shiru Teemah Teemah tayi na 'dan lokaci sannan bayan har Hannah ta cire rai da cewa zatayi nagana ma sai taji a hankali tace " _Hannah laifi ne dan ina yawan tunanin Yayah?Inajin kewar sa sosai Hannah kuma gashi kinga baya ko 'kirana nima_ _kuma tsoron 'kiran sa nakeji dan bansan me zance da shi ba_ " Hannah muguwa duk da haushin dataji 'dazu amma hakan be hana ta darawa ba dataji abinda Teemah tafa'da. Teemah kam tsayawa tayi kallon ta idanun ta na tare hawaye dan bata san dalilin dariyar ba, HANNAH sosai ta dara son ranta ganin Teemah na zubo da hawaye ne yasa ta 'dan tsagai ta da dariyar tace " _ashe lokacin da sauri zai zo haka_ ? _Kin manta nace miki naki son idan kika fara sai kin fini amma kika 'ki yadda gashi nan tun ba'aje ko'ina ba abu ya bayyana kansa_ , _yanzu kam ai kin yadda cewa banyi 'karya ba ko_ ? Teemah shiru tayi mata sai ma tafara 'ko'karin kwanciya dan taga alama abin dariya tazama harta regretting fa'da matan da tayi ji take badan ance magana zarar bunu bace da babu abinda sai hanata mai da maganar ta cikin ta ta rike damuwar ta ita ka'dai. Hannah naganin ta kwanta sai ta ha'diye dariyar tata tace " _yi ha'kuri matar Yayah tashi muyi magana plz na daina dariyar_ " Teemah 'kin kulata tayi sai Hannah ta dawo ta gabanta ta fuskanceta tare da fa'din " _I'm serious Allah tashi kiji, nayi al'kawarin bazan sake yimiki dariya ba yanzu"_ A hankali Teemah ta yun 'kura ta tashi ta zauna. Hannah ma zamanta ta gyara da kyau sannan tace "Kin san Allah ko tun ranar da naga Yayah yayi 'kirana awaya nayi tunanin ko dai be same ki bane shiyasa amma daga baya sai naga ya zage da 'kirana ba gaira ba 'dan dalili sai na fahimci akwai dalilin hakan dan ba haka muka saba da shi ba, Yayah be fiya 'kiran layin na ba sai dai in akwai wani dalili, na fahimci bakwa waya ne kuma saboda ban ta6a ganin kunyi ba, nasan halin Yayah da zuciya akan abu koda kuwa yana son abin zai iya basarwa idan ransa ya 6aci wannan kadan ne cikin halayyar sa. Ni kaina banso kika 'ki binsa ba tunda yanason hakan bazai ta6a cutar dake ba, wallahi Teemah Yayah na matu'kar son ki tun ba yau ba na fahimci hakan, ya na 'kaunar ki da dukkan zuciyar sa irin son da be ta6a yiwa wata 'ya mace irin sa ba a dunitan nan bama na tunanin ko agaba akwai wacce zata taro ki a zuciyar sa bansani ba ko in wani ikon Allahn ya sanya, Yayah na miki son da kowacce mace take burin mijin ta yayi mata irin wannan son, Teemah ki lura mana yanda kike yiwa Yayah abu son ranki wanda na tabbata ba ze 'dau hakan daga wurin kowa ba koda kuwa nice danake autar 'kanwar sa Yayah ba ze sarara min ba shiyasa ma kika ga bana farawa, sau tari ina mamakin yanda kuke rayuwar ku dashi kamar abokan gaba wani lokaci kuma na kanji kuna birge ni sosai, a hankali sai na fahimci 6oyayyan soyayyar dake tsakanin ku wanda bakowa ne yasan da shi ba, daga zuciyoyin ku sai de ko Mummy"! Da sauri Teemah ta 'dan bu'de idon ta akan Hannah da Mamaki, sai Hannah ta jinjina kanta tace " _Yes... Mummy ce ka'dai tasani, lokacin auren ku ta sanar dani yanda tayi farin ciki da ha'din auren_ _naku take ce min ta jima da fahimtar son Yayah Abbas dake 6oye a zuciyar_ _ki, wanda tana ganin kamar ke kanki ma baki san dashi ba, tace damuwar ta Abbas_ _ne bata sani ba ko zai kar6i auren ko ah h, nice nan take_ _na bata tabbacin Yayah baze 'ki ba danshi ma yana tsananin sonki_ _fiye da zaton mutun_ . _Bazan 6oye miki ba Teemah duk da nasan kin fini sanin menene aure tunda kinyi shi har sau_ _biyu, amma har ga Allah kina sakaci da kulawa da mijin ki, lokuta da dama_ _nakan ji wani iri idan naga kina nuna halin ko in kula da shi, mijinki ne fah, naki ne_ _Teemah me yasa zaki 'ki binsa bayan kinsan yana da bu'katar hakan zaman me zakiyi_ _anan 'din tunda wanda kike zama domin sa baya nan, ba 'da ba ba komai_ _ba me yasa kika za6i raba muhalli dashi?_ _idan baki kila dashi yanzu ba yaushe kike son rayuwar auren ki tayi saiti_ ? _kin fi son sai ranar da wata ta shigo tsakanin ku ko kuma yaushe_ _Teemah_ ? _Ki duba fah duk da ransa a 6ace amma bai fasa 'kirana dan yaji lafiyarki ba_ _ke da kanki ki duba wannan lamarin dan Allah_ " A hankali Teemah tace " _Ni kaina Hannah naga kuskure na kuma Allah yayah fushi yake yi dani ban san yanda zanyi ba banson fushin san_ _koka'dan_ " Hannah cewa tayi " _Nima banaso Teemah, dukkan ku 'yan uwa nane kuma mafi soyuwa abin 'kaunata, lokacin danaji auren ku bazan iya misalta miki_ _irin farin cikin dana shiga ba, inson ku sosai bazan ta6a son 'daya na bar 'daya ba har abada kamar yanda bazan so ganin ba'kin_ _cikin 'dayan ku ba ballan tana na dukkan ku biyu_ " _Wannan laifin kinsan naki ne ko_ ? Kai Teemah ta 'daga mata, sai ta cigaba da fa'din " _so kinga ke ya kamata ki gyara laifin, nasan Yayah ma be kyauta ba daya share ki amma kema da naki laifin me yasa da kika ga baya ko 'kiran_ ki _baki 'kira shi ba......._ _kinsan wani abu ne matar Yayah_ ? Kai Teemah ta jijjiga wa Hannah alamar " _ah ah_ " sai Hannah tace " _wannan taurin kan dake kan kin nan shine ya haifar miki da girman kai, zaman aure_ _da hakan kuwa baya ta6a yiwuwa, ki sau'kar da wannan shirmen ki nutsu ki gyara auren ki ki jawo mijin ki ajiki ki kula dashi da hakkin sa, sannan_ _ki dinga ro'ka muku haske wurin mahallici, Allah_ _Teemah banaso ko da wasa inga wata ta ra6i rayuwar ku, ke kanki kinsan hanyoyin kulawa_ _da mijin ki dan nasan Anty da Mummy suna_ ' _ko'kari sosai akan haka ni shaida ce......._ " _..........Harda maman Amal ma Hannah itama tana bani shawara sosai_ " Teemah ta tare da fadin hakan. Hannah jinjina kai tayi tace " _toh kin gani ma ashe suna da yawa masu sin ganin rayuwarki cikin farin cikin_ , _amma abinda ke kanki ne yah hana ki fahimtar cewa Abbas 'din nan_ _dai yanzu shine rayuwar ki kuma aljannar ki, dole_ _ne ki sauke naki dan biyu bata ha'duwa kinga kece 'karama akanshi, kafin yazama miji agare ki Yayan ki ne, kinga dole biyayya naki ne kuma ke ka'dai_ _banda shi, sai kin dage dan maza yanzu babu ruwan su tun kafin_ _yaje yayi miki kishiya awaje ba fata ba amma ki dage gaskiya"_ " _Hannah plz ni yanzu ya zanyi toh ki gaya min"_ Teemah ta fa'da tare da kamo hannun Hannah. Agogo Hannah ta kalla tace " _yanzu dare yayi may be yana bacci, amma ki daure ki 'kira shi gobe, in kinyi sa'a zai sau'ko, sai kisan me zaki ce dashi wanda zai sanyaya_ _masa rai tunda ke ce da laifi sai ki bashi ha'kuri ki kuma kiyaye gaba"_ " _Bakomai insha Allahu gobe zan gwada 'kiran sa naji"_ Hannah tace " _Toh Allah ya kaimu ya kuma daura ki akansa_ " Da haka suka rufe maganar zuwa safiya. Washe gari Hannah na da lectures a makaranta ita ka'dai tayi break fast 'din ta daya ke Teemah babu inda take zuwa so ba da wuri take yi ba ita, tare sukayi aiyukan da zasuyi dukka 'dakin Abbas ne ka'dai Hannah bata taya ta gyarawa ba ita ka'dai take yin abinta, 'karfe bakwai da rabi Hannah ta bar gidan dan 8:00 zata shiga lecture. Teemah data gama komai tayi wanka tayi shirin ta tsab kamar me zuwa unguwa, sai ta dawo 'dakin sa tayi dialling number 'din sa, sai de har ta gama ringing bai 'daga ba, sake 'kira tayi shima still har yayi miss called be 'daga ba. Take ta rintse idanun ta da 'karfi sai ga hawaye ya gangaro mata baya tayi ta kwanta, fuskarta na kallon cielling 'din 'dakin afili tace " _plz Yayah na ka yafemin, ka 'dauki wayata"!_ Abbas na bayi lokacin data 'kira 'din shiyasa be 'daga ba ko daya fito yaga miss called 'din kuwa sosai yayi mamaki amma sai ya ajiye wayar batare da ya 'kirata ba. Shi kansa yana rayuwa ne amma kewar matar shi na damunsa sosai, tunanin ta na matu'kar hana shi sukuni da walwala yayin da soyayyar ta ya tsaye masa azuciya koda yaushe tana cikin ransa. Abinda kullun yake fama da shi kenan tare da jin haushin rashin ta a kusa dashi, duk kuwa abin nan dayake yi mata yanayi ne dagangan duk da cewa shi kansa hakan na cutar dashi amma ya nuna mata cewa bai ji da'din 'kin biyo shin data yi ba yasa ya daure ransa, dan yana tunanin idan hakan ya ishe ta next idan yace su taho bazata masa gardama ba koda Daddy ya nuna bai so, dan yasan ita bata fiye 6oye 'kudurin ta ba. Teemah bata tashi a kwancen ba sai ta sake gwada 'kiran sa da niyyan daga wannan bazata sake ba in har be 'daga ba. Cikin sa'a kuwa sai ya 'daga Teemah har sai data toshe bakin ta dan farin cikin data tsinci kanta aciki. Abbas shiru yayi yanajin yanda ta sauke ajiyan zuciya, shima sai ya lumshe ido ya kuma bu'dewa atake. Teemah a hankali tace " _Yayah_ ! " _Na'am_ " shima ya amsa ta da shi kamar wanda akayi masa dole. Kuka kawai Teemah ta sanya mai me tsuma zuciyan ma'abocin sauraro. Cikin kukan ta furta " _Yayah shine ka manta dani ka daina 'ki rana ko_ ? Yace " _Ni ban manta dake ba abubuwa ne sukayi min yawa ma shiyasa_ " Da sauri tace " _Amma Yayah ai kana 'kiran Hannah nice ka'dai baka 'kirana_ !" Dan ya takaita zancen sai yace " _Shikenan toh zan na kiranki... owk_ ? Shiru tayi masa tana share hawaye. Da yar ka'dan 'din muryar tace " _Yayah fushi kake yi dani ko?_ Sosai yanayin data yi maganar ya ratsa shi har 'kwa'kwalwar shi amma ya basar. Sai ma yace " _i ll hang d call now office zan je.....see u later ummm_ " Bata yi magana ba har ya yanke 'kiran sai kawai tabi wayar da kallo da mamaki, lalle ta 6ata ran Yayah sosai acikin muryar sa ta fahimci hakan dan duk wasu abubuwan shi dayake yi abaya bata ta6a jin muryar sa a irin wannan yanayin ba, sai dai abinda takasa ganewa shine haka 'din da yake yi soyayyar da Hannah tace yana yi mata ne yasa ko kuma haushin kawai ta'ki binsa? Share hawayen ta tayi tare da tabbatar wa kanta cewa zata bishi aduk yanda yake so 'din harta gano asalin matsayin ta awurin sa. Abbas ma daya yanke 'kiran sai daya jinginu da jikin kujera ya lumshe idanu baya son irin wannan na faruwa tsakanin su koka'dan amma tunda hakan take so, so be it!, shi zai daure rashin ta na tsawon lokaci ko dan ya koya mata yanda ake kewar masoyi da yanda tasirin soyayya yake a zu'kata. Tun daga ranar Abbas yafara 'kiran ta safe da kuma dare, amma kullum daga gaisuwa baya sake fa'da mata komai, duk da hakan Teemah najin da'di domin yafi ace baya 'kiran gaba 'daya, sau tari har 'kaguwa takeyi ya 'kirata dan kawai taji muryar sa ita hakan ma ya isheta. Baya yi mata magana mai tsayi sai in har bu'katan hakan ya taso, farkon dogon maganar su shine ranar da ya ta6a tambayar ta cewa bai ga debit alert ko sau 'daya har yanzu ko bata da bu'katan komai ne? Sai tace masa Hannah na zuwa musu shopping every week. Ya sake tambayar ta cewa ku'din fa sai ta bashi amsa da fa'din " _Ummah ce ke bada ku'din idan Hannah zata_ " Shine ranar da maganar tsakanin su tayi tsayi, na biyun sa kuma ranar da Hannah zata je saloon kuma itama Teemah tanaso tayi dan kanta cunkus take jinsa. 'Kiran safiya da yayi mata sai ta tambaye shi zuwa saloon 'din, ai kuwa hana ta Abbas yayi sai ma yace in har yazama dolene sai tayi 'din toh Hannah taje ta siyo komai zai turo ayi mata agida, Teemah sosai taji haushi dan kuwa ba 'karamin gajiya tayi da zaman gidan ba. Sosai take so ta'dan fita amma Yayah fir ya hana ta. Hakan kuwa akayi dan da yamman ranar wata mata tazo gidan Teemah bata san ta ba, Hannah ce dai ta gane ta dan ta ta6a zuwa gyaran gashi wurinta sau 'daya, sunan ta madam Mansoora, agida tayi musu komai harda Hannah ma, hatta da gyaran farce sai da tayi musu mai kyau ta kuwa yi 'ko'kari dan su kansu sai da suka yaba da aikin nata. Sai daga bayane ma da Hannah taje gida n Ummah sai suka ji labarin ashe Ummah yasa ta turo ta. Duk abin nan dake faruwa bai sa Teemah taji haushin sa ba sai ma 'kara ganin shi data ke sonyi ga begen sa dake yawan damun ta. Ita kanta wani lokaci mamakin kanta takeyi, yanda ta damu sosai da rashin sa kusa da ita yanzun bata san dalilin wannan canjin ba, sosai take kewar mijin ta a yanzun sai dai bata bari ko Hannah tasan hakan ba saboda Anty tace mata komai dake tsakanin ta da mijin ta sirrine mai girma, kar ta yarda ta ringa bari wani na sani, shiyasa ta ri'ke sirrin ta aranta. Kullum take shiga 'dakin sa ta share koda babu dattin komai amma bata gajiya da share shi, ta tsaftace bayi kullum ta kunna burner, anan take wuni da rana har in bacci yakama tayi abinta da dare kuwa tare da Hannah suke kwana a'dakin ta, idan gari ya waye suka kammala ayyukan su gaba 'daya sai Hannah ta shirya ta wuce makaranta. Teemah kuwa nan 'dakin san take komawa tayi baccin ta kwanta tana kallon photon sa tare da rungumar pillow a 'kirjin ta. Tana fitowa sai ta kulle 'dakin ta kai key 'din cikin drawer 'dakin ta ta ajiye shi. Duk weekend Hannah ke zuwa shopping idan ta dawo kuma sai ta gudu gidan Ummah ta 'karasa yinin both saturday & sunday acan haka takeyi, amma bata kwana sai ta dawo, hakan ma Ummah bata barin taringa mitan ta baro Fateemah agida ita ka'dai. In kuwa zata dawo Ummah sai ta ha 'data da wani abin ta6awa na zamani ko na gargajiya tace ta kawo wa Teemah. Su hajiya Teemah kam najin da'din hakan har sai ya zamana ma duk ranar da Hannah taje gida bata cin komai jiran ta kawai takeyi ta dawo sannan taci abinda Ummah ta ha'do ta dashi, tasan Ummah na 'ko'kari sosai dan kamar tasan abinda ranta ke 'dan iya bi takan rin'ka yiwa Hannah santi musamman ranar da aka kawo mata pepper soup 'din hanta ko dambu mai ha'din isassun kayan lambu, ranar kam har rowa take yiwa Hannah ma. Haka rayuwar ta ya kasance agidan auren ta batare da mijin ta agida ba, satinsa uku yanzu da tafiya, zuwa wannan lokacin kuwa har ma Teemah ta riga ta saba da rashin san azahiri amma sai dai damuwar datake ji aranta koka'dan be ragu ba sai ma abinda ya 'karu musamman data ga cewa dagaske yakeyi bazai dawo Abuja dawuri ba, sau tari idan ya 'kirata takanji kamar tayi masa mitan hakan amma sai ta danne ranta dan tafi son idan suna tare burinta ma be wuci tasan matsayin ta ba, amma a yanda tasan halin sa ma tasan idan yaga dama baze ma tsaya ya saurare ta da kyau ba dan shi bai fiya son jan magana ba. Dramar su da Hannah kuwa sai ma abinda yayi gaba musamman da har yanzu Hannahn bata fasa 'kiran ta da suna mrs dodo ba, yanzu kuwa sunan na 6ata ranta, sosai yake jin haushi idan Hannah ta 'kirashi da dodo. Ranar da Hannah ta ishe ta kuwa ce mata tayi " _kar ta 'kara 'kira mata miji da suna dodo, tace ita mijin ta ba dodo bane koma miye ne ita a hakan yafi birgeta_ " Hannah ido ta zaro da zolaya tasake fa'din " _iyeeh, kice abin yafi najiya bansani ba, yi ha'kuri toh matar Yayah bazan sake ba"_ Teemah a tsare tace da Hannah " _Daya fi miki_ _in bahaka ba kuwa in tona miki asiri awurin Ummah ince kina da 6oyayyan saurayi bata sani_ _ba_ " Cikin ko in kula Hannah tace " _Toh miye aciki ban kai nayi saurayin bane?_ " _kin kai harma kinfi, karki damu yarinya zaki gani zan baki mamaki ai_ "! Da sauri Hannah ta dakatar da itada fa'din " _Ah'Ah baiwar Allah abin be kai haka ba, wasa fah nake yi miki, indai mijinki ne ai nace na bar zancen sa ko, da Allah rufe wannan_ _chapter 'din bana so Yayah yasan ina da wani saurayi dan da kaina nace masa makaranta zanyi kinga kuwa ai_ _idan yasani na 6allo ruwa_ " Teemah cewa tayi " _Sai ki kiyaye bakin ki in kina so nima na rufa miki asiri_ " Hannah ma da sauri tace " _Kwantar da hankalin ki matar Yayah wannan shi yafi komai sau'ki_ " " _Dayafi miki_ " Fa'din Teemah daga 'karshe. Murmushi kawai Hannah tayi tace " _ni kaina ya kulle fah Allah, wai yaushe yafara yi miki ne_ ? Atakaice Teemah tace " _Jiya da safe_ ! Hannah ma sai tace " _Ai kuwa ba mamaki gaskiya, amma fah kin ban tausayi wallahi, abin yakama ki da 'karfi sosai_ ? Ringing 'din da wayar ta ta 'dauka ne ya katse musu hiran, Hannah kam naganin me 'kiran sai tayi murmushi tare da 'dagawa. ***** Tun ranar da Abbas ya cika sati hu'du da tafiya be 'kiran ta ba tun daga ranan, itama kuwa bata damu ba dan halin san yanzun tafara sabawa dashi, itama batayi tunanin 'kiran sa ba kamar yadda bata sanar da Hannah meke faruwa ba, wasa-wasa har suka kwana biyu amma shiru ba labarin sa, ranan na ukun ne abin yafara damun ta sosai, tanaso ta 'kira shi taji me ya faru amma sai zuciyar ta ta rabu kashi biyu, inda 'daya ke bata 'karfin gwiwan ta'kira shi yayin da 'dayan ke bata shawaran ta 'kyale shi itama, kamar yanda yayi 'din wata'kila tana damun sa ne shiyasa. Wannan 6angaren tunanin ne yayu tasiri azuciyar ta har ma sai ya rinjaye ta gaba 'daya. Bata 'kira shin ba amma kuma sam nutsuwa ya'ki zuwa mata, haka ta wuni wata iri da ita, hatta wayar ma yau ko bi ta kanta batayi ba tsaban yanda tunani ya yawaita a brain 'din ta, 'dakin nasa ma yau ko bu'de shi batayi ba acikin nata 'dakin ta wuni. *1:13pm* Ta tashi tafara rage kayan jikin ta a hankali dan so takeyi ta watsa ruwa ko zata 'dan ji dai-dai, ga mararta ma dake 'dan mur'da mata ka'dan-ka'dan wannan karan period 'din ta yayi mata jinkirin kwanaki dan kuwa wata har yawuce da kwanaki amma bai zo ba, jin mur'dawan da yake yi mata sama-sama ne yasa ta saka ran zuwan sa daga yanzun zuwa kowani lokaci, ga tsoron ciwon maran dayake tasan baya yi mata da wasa, sosai yake damun ta. Tana tsayen sai taji 'karan door bell tasan Hannah ce dan haka sai ta 'daura hijab kawai akan skirt 'din dake jikinta, dayake tariga ta cire riga sai bra ne ka'dai yarage asaman ta shiyasa ma tasa hijabin, a haka ta nufi 'kofan ta bu'de batare da tunanin komai ba dan tasan bayaga Hannah bata tsammanin kowa. Turus tayi ha'di da wani bugu da zuciyan ta yayi har sai da yasata 'dauke wuta na 'yan seconds kafin ta dawo dai-dai, kallon-kallo suka tsaya yiwa juna na 'dan lokaci kowa na ayyana irin yanda yaga 'dan uwansa ya canja, kowa ji yayi aransa babu da'di ganin duk da irin 'kuncin da zu'katansu ke ciki amma be hana 'dan uwansa yin wani sihirtaccen kyau da 'kiba azahiri ba. Teemah kam harda mamakin ganin sa ma duk suka cikata. Abbas ne yayi gyaran murya sannan Teemah ta bashi hanya ya shigo, bata sake kallon shi ba ta tura 'kofan ta rufe sannan ta dawo ciki itama, haka tawani 'dauke kanta gefe tana tafiya tace dashi " _sannu da_ _zuwa_ " bata ko jira taji ya amsa ba balle tayi tunanin kar6an jakan sa talkless of welcoming nasa da abin sha ko kuma wani abu daban ba ta wuce ciki abinta. Abbas ma be amsa ba sai ya bita da idanu kawai, tana shigewa 'dakin ta sai ya jijjiga kansa tare da nufan hanyar nasa 'dakin, amma sai ya jita akulle, beyi mamaki ba dan haka sai ya koma nata 'dakin har yanzu da jakarsa akan kafa'dan sa. Ga mamakin sa kuwa yana shigowa tana fa'dawa bathroom ga dukkan alamu wanka zatayi. Jakar tasa ya sau'ke ya ajiye sannan ya zauna abakin gadon nata, he wish yasan inda ta ajiye keys 'din da bazai tsaya jiranta ba 'daukan abinsa zai yi ya. Zaman sa keda wuya sai kuma yakoma ya kwanta rigingine akan gadon yayiwa kansa matashi da hannayen sa biyu dake bu'de kuma sarke da juna, 'kafar sa 'daya na lan'kwashe akan 'dayar yayin da 'dayan 'kafar ke tsaye yana faman jijjiga su. Teemah tana bayi tayi zaman ta sarai tasan yana cikin 'dakin nata amma haushin irin wannan zuwan dayayi matan yasa ta share shi duk kuwa da tasan cewa 'dakin sa a kulle amma hakan be sa tayi tunanin tayi hanzarin fitowa ba. 11mins ya 'dauke ta a bayin kafin ta fito d'aure da towel ajikinta, koda ta fito 'din ma idanun ta kansa suka fara sau'ka amma sai ta 'dauke kanta tamkar bata ganshi ba, shirin ta ta hau yi a tsanake tayi light make up tare da zura wata doguwar riga da hijabin sallahn ta. Sam Teemah 'dauke hankalin ta tayi daga kansa tamkar bata san cewa akwai wani abu mai rai dangin halittar mutun acikin 'dakin ba. Dadduma ta 'dauko ta shimfida ta tada sallah abinta. Duk abin nan dake faruwa Abbas na kallon ta shima be tanka ta ba, iya gudun ruwan ta yake so yagani, ganin ta fara sallah batare da ta ko kalli inda yake ba yasa yatashi a hankali ya zauna yana kallon bayan ta dayake yana daga bayan ta ne, kamar an tsikare shi kuma sai ya mi'ke, daukan jakarsa yayi ya juya yafice agidan ma gaba 'daya. Sai da ya tsaya a masallaci ya sallaci azuhur kafin 'dan adaidaita ya sau'ke shi a 'kofar gidan mahaifinsa. Teemah koda tayi sallamah bata juyo da wuri ba sai data 'dan 'dauki lokaci tana ro'kon ubangijin ta bu'katun dake gabanta sannan ta shafa ta tashi, taji motsin fitar shi tana sallahn amma batayi zaton gidan yabari ba, tayi zaton ko parlour ya koma ne. Tana na'de daddumar taji aranta cewa bata kyau ta ba dan haka bata 6ata lokaci ba tafito parlourn sai kuma taga empty babu kowa, da mamaki tajuya zuwa 'dakinsa nan ma adatse yake tun rufewar ta na safe, 'dakunan gidan duk tabi ta dudduba amma bayanan arikice ta dawo 'dakin ta da tunanin inda ya shiga. Wayar ta ta 'dauka ta ta 'kiran layin sa amma baya 'dagawa. Take taji komai ya tsaya mata cak. Abbas kam ga mamakinsa gani yayi kowa dake gidan su na farin ciki da zuwan sa tun daga kan ma'aikatan gidan har mahaifiyar sa gaba 'daya, sa6anin ita waccen yarinyar da ko kallon arzi'ki ma bai samu daga wurinta ba. " _Toh me ya faru ne_ ? _Me ke damunta?_ ya tambayi kansa. Wani 6arin zuciyarsa ne yabashi amsa da fa'din " _babu komai iskancin ta ne kawai yau 'din ya motsa mata_ ". Firgigi yayi lokacin daya tsinkayi muryar Ummah ya daki dodon kunnan sa da 'dan 'karfi, ga dukkan alamu ba farkon maganar ta kenan ba " _Muhammad meke faruwa ne wai_ ? Yaji ta fa'da da kulawa ganin ya shiga 'dan guntun tunanin daya yi saurin tafiya da hankalinsa gaba 'daya, sosai hankalin Ummah ya tashi da ganin hakan, mussamman ma da yake yanzu isowar sa bata san kuma da me yazo mata ba. Abbas bai bata amsar tambayar ta na farko ba sai data 'kara maimaitawa kafin ya kauda kai tare da fa'din " _bakomai Ummah_ " Kafin Ummah tasake yin wata magana sai taji 'karan wayar ta, dayake ma wayar na gefen ta shiyasa tayi hanzarin 'dauka ta sada shi da kunnan ta. Abbas baya yayi ya jinginu da kujera tare da 'daga kansa sama ya lumshe idanu kamar mai tunani. Gaisuwar da ake yi mata daga 'dayan 6angaren ta amsa tare da fa'da'da fara'ar ta, afili zaka fahimci matsayin me 'kiran awurin ta musamman idan kayi duba da yanda ta bada hankalinta sosai tare da 6acewan damuwar dake kan fuskar ta tashi guda. Bayan gaisuwar sai Teemah ta tambayeta a 'dan kunyace inda tace " _Ummah Yayah yazo ne_ ? Sai da Ummah ta juya ta kalleshi kafin tayi dariya ka'dan tace da ita " _ehh yazo, gashi nan ma agefe na, inaga anan yafara sau'ka dan na ganshi da jaka!, bakuyi waya bane_ ? Da sauri Teemah tace " _Ah 'ah Ummah na 'kira layin sa fa baya 'dauka bansan dalilin ba_ " Jin hakan yasa Ummah ta kauda wayar a kunnan ta sannan ta juya ta kalle shi tace " _ina wayar ka Abbas_ ? Yace " _Tana nan Ummah_ ! " _Meyasa baka daukan 'kira toh_ ? Dagangan ya'ki 'daga 'kiran nata duk da yagani amma sai yace da Ummah " _wayar na silent ne banji ba_ " Murmushi Ummah tayi domin ta fahimci kamar wani abin ne ke faruwa a tsakanin su. Maida wayar tayi a kunnan ta inda ta tsinkayi muryar Teemah nata fa'din " _hello_ ! _Helloo_ !! " _Ina jinki Fateemah_ " Ummah ta bata amsa da kulawa. Teemah cigaba tayi da fa'din " _Ummah sai dafa yazo nan dan yaga ina sallah shine yayi tafiyar sa ko ganin sa bai_ _tsaya nayi ba_ "! Cikin shagwa6a ta kare maganar tamkar da Mummyn ta take wayar. Sai data gama fa'din maganan kuma sai taji kunya harda rufe baki. Ummah da mamaki ta juyo ta kalle shi jin abinda yayi, shi kuwa Abbas sai ya 'dauke kansa ya mayar gefe tamkar baiji abinda Teemah tace ba. 'Karasa maganar Ummah tayi da fa'din " _yi ha'kuri toh kinji zai dawo yanzun nan insha Allahu......._ Ko jira taji 'karshen maganar ma bata yi ba ta yanke 'kiran sanadiyyan wani nauyi da kunyan Ummah dataji ya kamata. *Hhhh* *DO NOT UNDERESTIMATE TEEMAH PLZ nasan wasu zasu ce tayi rashin kunya........*👌🏻 👇🏼🙈 *Toh fah na shiga magana kwana uku ba update nasan babban laifi nayi, amma ayi min afuwa dai har kullum ina 'kara baku ha'kuri haddata na gyara dan kar nasha bulala🙈.........kar ayi fushi dani plz* 👏🏻 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce*😍 [10/13, 1:58 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* I _dedicated this page to my fellow *FANS* all over media, Ha'ki'ka *SALMERH*_ _najin da'din kasancewa tare daku, wannan page 'din kyautar kune_ 🥰 *Bismillahir rahmanir raheem* _Don’t let anyone’s ignorance, hate, drama or negativity stop you from being_ _the best person you can be_ . 🅿 *85* Ko da Ummah ta yi masa magana akan hakan sai yace mata ai yana sauri ne zai wuce Ekiti state shiyasa bai tsaya ba. Ummah kam dalilin nasa be gamsar da ita ba koka'dan sai ma sake cewa dashi tayi " _Tashi dai ka koma gidan ka bana Abbas bafa nasan son kai da rashin adalci, ni ban san ranar da zaka daina wannan miskilancin ba wallahi, ace kabar yarinya_ _tsawon wata guda hakanan amma kuma ka zo ma bazaka tsaya ka ko duba lafiyar_ _ta ba sai ka wani ce kana sauri_ ? _Ko uzurin ta idara da sallah ma bazaka iya yi mata ba Muhammad? To ni 'din daka zo gaishe ni har da zama min a'daki 'din bamu a saurin ne?_ Ummah tana sababin tasa shi agaba har gaban mota jakar shi na hannun ta haka ta tisa 'keyar sa tare da driver dan ya sau'ke shi sannan ta koma ciki. A hankali yake tafiyar kansa a 'kasa kamar bazai yi ba har ya isa kofar dazata shigar dashi parlourn gidan nasa, yanzun kam shigan sa kawai yayi dan 'kofar babu lock. Ciki-ciki yayi sallamar dan daga shi kansa babu wanda yasan yayi sallama agidan balle Teemah da can cikin bedroom take. Teemah tana bedroom tana 'dan murzawa fuskar ta powder a hankali, kunyar tambayar Ummah da tayi akansa gaba 'daya yasa ga6o6in ta yin sanyi saboda jin nauyi, atamfah tasa ajikin ta mai fulawa ja riga da skirt ne sun kuwa amshi jikinta sosai. Har ya shigo 'dakin bata sani ba dan hankalin ta gaba 'daya ya tafi ga tunani, duk da tasan cewa zai zo shi kamar yanda Ummah ta fa'da 'din zai dawo amma duk da haka sai ta tsinci kanta cikin matsanciyar damuwa. Tana gama shafa powder 'din ta 'dauko jambaki kenan ya shigo cikin 'dakin bata ji shigowarsa ba 'karan ajiye jaka kawai taji daya ajiye yana daga tsaye hakan yasa ta waigowa a 'dan firgice tare da mi'kewa tsaye. Kallon juna suka tsaya yi na 'dan lokaci tsawon mintina biyu batare da kowa ya furta komai ba. Abbas kam gani yayi ta masa mugun kyau na fitan hankali tayi 6ul-6ul da ita he wish data ganshin ace farin ciki tayi da kuwa yau sai ya nuna mata yanda nasa farin cikin ya zarta nata, amma sa6anin hakan daya samu daga gare ta yasa sam baiji da'din hakan ba. Yaso da bata 'kira Ummah ba da kuwa yau 'din nana da taga halinsa na asali, dan tafiyar sa zaiyi Ekiti ba zai dawo ba har sai ya kammala abinda ya kaishi, dan kuwa sai ta 'kara lafiyayyan 1month koma fin hakan kafin tagan shi. A hankali yafara takawa zuwa inda take batare da ya 'dauke idanun sa daga kanta ba. Teemah kam tsayawa tayi tana kallon ikon Allah sai da taga ya kusan iso ta kafin tafara ja da baya itama ganin hakan sai Abbas ya fara magana inda yace " _wato ke duk duniya ni kadai kika raina_ _ko_ ? Teemah da sauri ta jijjiga masa kai alamar " _ah ah_ " dan yanda ta ganshin sosai yabata tsoro, ko 'yar fara'an da take 'dan gani akan fuskar tasa ma yau babu ita. " _Me yasa kika 'kira_ _Ummah_ "? Ba ta bashi amsa ba sai kawai ta tura baki gaba tana 'dan kallon shi da fuskar shagwa6a66u. A 'dan hassale yace " _tambayar ki nake yi why did u called Ummah_ ? Jin kamar ransa yafara 6aci ya sa ta fa'din " _To ba kai bane?_ Tayi maganar tamkar zata yi kuka. Shima da sauri ya sake furta " _ni ne me? I think har gidan nan nazo kika 'ki kulani kuma bayan na tafi ki wani ce nine da na yi me ? Tell me!_ Ya 'karashe da 'dan tsawa. Teemah bata bashi amsa ba sai hawaye daya gangaro mata sirara. Abbas kuwa 'kura mata idanu yayi ka'dan sai ya 'dago hannun sa yana kallon agogon dake 'daure a tsintsiyar hannun. Tahowa yafara yi zuwa inda take tsaye, Teemah kam naganin haka sai ta fara ja da baya again. Amma da ya 'daga 'kafa taku biyu yayi ya cimmata, tana ganin ya iso ta sai ta juya tare da yun'kurin guje masa, sai hakan ya bashi daman cafko hannun ta 'daya wanda yasa dolen ta sai da ta tsaya tare da waigowa cikin firgici da rawan murya tafara bashi ha'kuri akan bazata sake ba. Shi kuwa Abbas fuskar ta ma ya tsaya 'karewa kallo tare da sauran sassan jikin ta ganin gaba 'daya ta canza masa a wata 'daya kacal da barinta. Hannayen ta ya ha'da duka biyu ya maida su ta bayan ta ya ri'ke dan mugunta batare da damuwar komai ba yasa hannu ya zuge zip 'din rigar ta sannan ya sake hannun. Yana sake ta tafa'da ga'do dan shi ne a kusa da ita taci gaba da maida numfashin azaba dan sosai ri'kon daya yi mata 'din nan ya shigeta. Biyota gadon yayi a hankali yana 'ko'karin 6alle mata bra, hakan yasa ta kalle shi da sauri sai ya 'dauke kansa yayi kamar be san tana kallon sa ba yaci gaba da abinda yakeyi. Yana 6alle mata ta kifu da cikin ta dan tasan hakan ne ka'dai zai sitirta mata jikinta. Ba 'karamin tsoro ya bata ba yanzun dan gaba 'daya ya juye mata ne zuwa Abbas 'din da ta sani tun farko. Duk kuwa da cewa a nutse yake yi mata dukkan abubuwan amma yanda fuskar sa ke a'daure ne take ji yana bata tsoro. " _Bashi kike so ba_ " Taji ya fa'da yana 6alle botilan rigar sa daga tsaye. " _Nifa bance ba Yayah_ " Da sauri ta bashi amsa da fa'din hakan. " _Ki min shiru ni_ " Ya tare ta fa'din haka. Koda ya cire rigar san ma dawo wa yayi sannan ya juyo da ita dan dolen ta saboda 'karfin su ba 'daya ba ne, sai kawai tasa hannu ta rufe 'kirjin ta duka biyu. Shima bai kula ta ba sai yabi hannun nata 'daya a hankali ya 'dora nashi akai yana shafawa slowly sannan ya ha'de musu baki. Good 5minutes kiss ya bata sannan yafara 'ko'karin saka hannun sa cikin nata dan sosai yake so yaji lafiyan su, abu na farko kenan dayafi 'dauke masa hankali ajikin ta sosai yanayin boobs 'din ta ke birgeshi balle yanzu daya ga sun wani canja masa gaba 'daya, sosai yake jin son ta6a abinda ta rife da hannun nata, zuwa lokacin kuwa Teemah tafara yin laushi ga mamakin sa sai yaga hannunsa ya maye gurbin nata hannun cikin sau'ki batare da ta bashi wahala ba. Cigaba yayi da murzawa a hankali yana feeling cikowan da suka yi a hannun sa sannan ya cire bakin sa a nata yabita da kallo still hannun sa nakan boobs 'din yana murzawa, wanda har lokacin idanun ta arufe suke ba bata bu'de ba sai numfashi datake sau'kewa a hankali amma da sauri-sauri. Wuyanta ya maida kansa ya ringa kissing ko ina yaci karo da shi har zuwa 'kirjinta. Idanunsa ya mayar kan boobs 'din tare da saita bakin sa akai ya 'dan ciza ka'dan, idanunsa akan fuskar ta sai yaga taja dogon numfashi, bakin san ya sanya ya ringa sucking mata boobs 'din tamkar zai rabata dasu. Teemah kam kuka tafara yi masa tana jan jiki sai yacire kansa a hankali ya dubeta yace " _in bar ki ko?_ Da sauri ta 'daga kanta sama alamar " _ehh_ " Sai ya juya a hankali ya kwanta a gefenta yana kallon yanda take sau'ke numfashi. Tsawon mintina sannan da yaga ta nutsu tana yun'kurin tashi taji yace " _ha'da min ruwan wanka kinsan bansan kan bathroom 'din ki ba_ " Yi tayi tamkar bata jishi ba dan bata nuna alamun tajin ba. Ganin hakan yasa Abbas ya kamo ta dayayi wani juyi sai ta koma 'kasan sa nan take yayi mata rumfa. " _Allah...ya...yah naji zanje in ha'da ne fa yanzu, plz ka 'kyale ni......_ " "Shiiii" yatare ta dashi data yi shiru sai ya ce da ita " _kina so ne ai shiyasa kika ha'da ni da Ummah ta dawo dani bayan natafi yanzu kuma kina min pretend_ _as if nii ne na dame ki ko?"_ Da sauri ta jijjiga kanta alamar "ah ah " _to menene_ ?" yasake tambayar ta Sai tace " _nifah ganin kawai nake so nayi dama_ " Bai bi ta kan maganar tata ba sai ya maida idanun sa da hankalin sa wani wurin daban yace " _me ya kumbura wannan_ ?" tare da nuna boobs 'din nata da baki. Sai lokacin ma ta tuna ashe bata rufe ba, da sauri ta kai hannun ta ta rufe kafin ta harha'do magana da in ina tace masa " _wannan?....zanyi...lokacin period 'dina ne yayi shiyasa_ " " _D'auke hannun ki ingani_ " Ya fa'da idanun sa nakai. A tsare yayi maganar dan haka babu wani musu ta janye hannun ta a hankali. Sai da ta 'dauke hannun sannan ya sake fa'din " _dama haka yake miki ne_ ?" Tace " _ehh amma ba koda yaushe ba_ " Bai sake magana ba sai kawai ya tsaya yana kallo tsawon mintina biyu sannan ya barta ya koma gefe. Teemah kam da sauri ta mi'ke bata tsaya neman abin rufe jiki ba kawai ta fa'da bathroom 'din dan kar ya'kara tsaida ta. Tana shiga ta cire kayan dake jikin ta 'dan 'karamin towel ne a bayin so sai ta 'daura shi ajikinta, sannan ta ha'da masa ruwan wankan da turaruka masu 'kamshi. Tun ma kafin ta fito a bayin taga ya shigo da boxer ajikinsa, hakan yasa ta nemi hanyar barin 'dakin da sauri tare da tunani aranta inda tace " _kai Yayah zai yi abu dayawa shi bazai 'daura ko towel ba ko kunya ta baiji haka?_ mtheww taja 'karamin tsaki. Tunanin ko bai gani bane yasa ta 'dauki nata 'daya duk da dai tasan zaiyi masa ka'dan amma ai yafi ace babun gaba 'daya. 'Kofar ta tura batare da ta shiga ba ta mi'ka hannun ta ciki fuskanta ta waje tace masa " _Yayah ga towel_ " Kallo yabi hannun nata dashi sannan ya saki murmushi yasan manufarta nayin hakan kenan bata so yasake fito mata daga bathroom a irin yanayin daya shiga. Hankalinsa a kwance ya bu'di baki yace da ita " _shigo ki mi'ko min to"_ 'Kafa ta buga a'kasa ta ha'de rai kamar zatayi kuka, amma dayake tanaso ya 'daura 'din sai ta daure ta shiga kanta a'kasa ta je kusa dashi ta ajiye batare da tayi masa kallo 'daya mai kyau ba tana shirin juyowa yasa hannu ya jawo ta cikin abin wankan. Teemah agigice ta 'dago ta kalle shi tana shirin yin magana sai yayi mata ra'da a kunnan ta yace " _Ke de Allah 'yar 'kauye ce, ni bansan lokacin da zakiyi wayo ba, Zahra tafa kullum ita ke_ _tayani wanka amma ke kin wani ha'da ruwa kin barni kinyi tafiyar ki a hakan ne kike_ _so ki ganta_ ? Da 'karfi tayi yun'kuri zata fita daga ruwan dan haushi har idanun ta na tara hawaye, sai yayi saurin maida ta yace " _relax babe, na yau ka'dai kinji_ ? Yanayin rungumar dayayi mata a ruwan bazai barta ta samu daman fita ba dan haka dole ta ha'kura sukayo wankan suka fito. Amma bata daina hawaye ba, shi kuwa yana ganin ta amma bai hana ta ba sai ma murmushi daya ke yi ciki-ciki na mugunta. Ganin ba kayan sa a nan yasa shi 'kara neman ta da fa'din " _bagashi ba kayan ma baki cira min ba a hakan ne kuma harda 'kiran Ummah da mitan_ _natafi baki ganni ba bayan ba abinda nake so kike min ba_ ". Hawayen tane ya 'kara gudu fiye da na 'dazu sai ta koma bakin gado ta zauna ta kauda kai gefe tana mai cigaba da sauraran sa. Abbas kam tsayuwa ya gyara ya fuskance ta da kyau sannan yace " _dama da kike so inzo 'din me kika tanadar min tunda gashi inga jikinki ma hana wa kika yi sai ma kika hau kuka inajin dan_ _haka yasa kika sani na dawo ko_ ? Shashshe'ka tafara tana murza idanu batare da tace dashi komai ba, ganin dagaske takeyi yasa shi matsowa kusa da ita ya 'dan sassauta muryar sa ahankali yace " _me ya faru kuma, kuka ya isheni plz ?_ Yayi maganar as if bai san kukan kishi da maganganun sa take yi ba. Bata kula shi ba sai shine ya 'dan sauko da muryar sa da sigar lallashi ya sake fa'din " _shikenan to daina kukan haka nan, 'dauko key 'dina muje ki nema min kayan dazan saka kinga kema sai in fara cewa kina nema min kaya ko?_ Ya 'karashe maganar tare da 'dago ta tsaye, bata daina kukan ba sai dai ta daina sheshshekan illah hawaye ne yanzun, amma a hakan ta wuce ta 'dauko key 'din sai ya mi'ke tabishi a baya a hankali suka fita. Koda suka isa ma guri ya bata ta bu'de 'kofan sannan suka shiga ciki a tare wanda suna shiga Abbas ya tura 'kofan tare da ha'da ta jikin 'kofan yace " _bazaki daina kukan ba_ ? _Owk gaya min to kukan na menene, na son Yayah ne_ ?" Sai ta jijjiga kanta gefe da gefe. " _Ohh na missing 'dina ne_ ? Sai tayi shiru ta sunkuyar da idanun ta 'kasa bataso tayi 'karya yanzun domin ita kanta tasan tayi missing mijinta kafin yazo tsoron kuma kar tace "ehh" ya tsokane ta tuna hakan yasa ta tayi shiru da tunanin idan tace ah ah ma duk bata tsira awajen sa ba. Hannun sa 'daya yasa ya 'dago fuskar ta zuwa sama idanun ta arufe yasa ta bu'de ta sau'ke shi acikin nasa. Sukayi kallon kallo na 'dan lokaci yayin da Abbas yake sake rage 'dan tazarar dake tsakanin fuskokin nasu har suna jin tiririn numfashin juna, a hankali sai ya ce da ita " _did u missed me?_ Yayi maganar ne ta yanda baya ga su biyun babu wanda zai ji abinda yafa'da cikin wani salo na daban. Ru'du, fargaba gami da da rikicewar datayi yasa batasan lokacin data bu'di baki ta furta " _ye...ss_ " a hankali ba, bakin ta ne ka'dai ya bu'du shima 'din yagane me tace ne sanadin kusancin dake tsakanin su. " _kina son Zahra ta ?_ ya sake tambayar ta. Sai ta jijjiga kanta ahankali alamar " _ah ah"_ " _kina son ni kuma in fi sonta_ ? yasake tambayar ta. Nanma da kai tabashi amsa sai yace " _to inbaki so in so ta zaki nayi min fiye da abinda take min kin yarda_ ? Sai ta 'daga kanta sama alamar "ehh ta yadda. 'Dan tazarar dake tsakanin su ya 6atar tare da ha'de bakin su wuri guda, sosai yake kissing 'din ta yana 'karawa duk da bata mayar masa da martani amma yanda ta nutsu ma ka'dai ya wadatar dashi, yawo hannayen sa suke yi ajikin ta tako ina har ya dawo da bakinsa zuwa wuyan ta yana chigaba da bata lafiyayyan sa'ko mai shiga jiki, bata yi yun'kurin hanashi ba duk da tana tsoro amma yanayin da ta shigan sosai ya dilmiyar da tunanin ta, sau'kan bakin sa kan boobs 'dinta ne yadawo da hankalinta jikinta take sai tayi baya da kanta tana sau'ke numfashi. Abbas be barta ba sai daya samu yanda yake so sannan ya 'kyale ta ganin lokaci yaja kuma gaban sa da tafiya, aranan ne kuma Teemah ta fahimci cewa ita 'din ce dai Zahran Yayah bawata ba duk da bata cikin nutsuwar ta amma hakan be hana ta fahimtar kalaman sa ba daya ke ta sa mata albarka na yabawa da jin da'di. Anan ta fahimci 'dumbin son da yake mata da jimawa wanda duk hakan yafaru ne ta sanadin ha'din kan da tabashi ya biya bu'katar sa da kyau ita kanta sai data gane bambancin dake tsakanin ha'duwar su na yau da na baya musamman ma data ga bata samu matsalar komai ba, bataji zafi kamar na kwanaki ba. Wani wankan suka shiga kowa ransa wasai babu wata damuwa sannan suka dawo suka shirya cikin kyakkyawan shiga. Yunwa yace mata yakeji wanda ko itama yau 'din wani mur'dan yunwa ke damunta na fitan hankali duk da 'dazu kafin yazo taci abinci amma sai take jin tamkar bata ci komai ba zuwa yanzun. Abincin Hannah daya rage wanda idan ta dawo zataci shine ta 'dauko musu suka ci, Abbas har yana mamakin ta yanda yaga ta zage tana cin abincin batare da wani iskanci ba kamar yadda ta sabayi kullum, bai ta6a kallon ta cikin wannan yanayin ba sai a yau 'din. Agaba yasa ta da mamaki ya zuba mata idanu harma ya daina ci yatsaya kallon ta. Ganin hakan yasa ta fara bashi tana murmushi dan tasan kallon na menene yake yi mata, ita kanta jiya zuwa yau abin na bata mamaki yanda yunwa ke saurin kamata wanda yasa dole sai taci abinci. Kasa ha'kura yayi sai da yace da ita " _shi kuma wannan canjin fah ko duk missing 'din Yayah ne ya kawo shi shima? Dan_ _nasan wasu idan suna cikin damuwa in suka rasa abinyi sai su sa abinci agaba suyi ta 'durawa inaga ma shiyasa_ _naga kin zama 'katuwa har kika fini......next idan na dawo oyoyo na goyo ne dan ke 'din_ _nan naga alama zuwa gaba sai de in zama 'dan baby a wajenki"_ Dariya ma yabata sosai ta kuwa dara har fararen ha'koran ta na fitowa fili. Abbas kam murmushi yayi yace " _bawasa fa nakeyi ba, ke baki san kin fini 'kiba yanzu ba ko"_ Idanunta da suka cika da hawayen dariya ta waro akanshi sannan tace " _ka ganka ne Yayah? Allah kamar ba kai ba inajin ko tunawa dani ma bakayi shiyasa kazama kamar ba kai ba"_ Cewa yayi " _Me yasa bazan tuna dake ba ke fa matata ce dole ai na yi tunanin ki, wataran ma sai inji kamar inzo in miki bulala da kika 'ki bina_ " Baki ta ta6e sannan tace " _Ca6! da na ha'da ka da daddy kuwa ya ramamin nima_ " " _Nima Zahra ta zata rama min ai akanki kuma_ " Ranta fari 'kal tace " _wacce kenan, Zahra matar ka ko kuma Zahran 'karya_ ?" 'Dan bu'de ido yayi yace " _karya niii_ ?" Tashi tayi tsaye da sauri dan yanda ya matso fuskar sa sanda zai yi tambayar sai ta 'dan ji tsoro. Tana tsayen tace " _ai naji ka fa'da 'dazu_ " Da mamaki yace mata " _Me nace 'dazun kuma_ ?" Ido ta 'daga sama kamar wata mai tunani tace " _Ka....ce.....kace...._ In ina ta tsaya yi ta kasa fa'din abinda ke ranta sai ta tsaya tana murmushi. " _Fa'da min mana inji_ ?" Yayi maganar yana kallon ta. Bazata iya maimaita masa ba saboda kunya takeji dan haka sai ta matsa zuwa bayan sa da sauri ta sa'kalo da hannayen ta a wuyan sa ta sar'ke su tare da kwantar da kanta akan kafa'dan sa tana cigaba da murmushin ta a kunne tara'da masa " _kunya nakeji ni_ " Murmushin kunyan iyayin nata yayi sai yace " _rufe idon ki to zaki daina jin kunyan sai ki fa'damin naji_ " Kai ta juya a kafa'dan sa alamar "ah ah" "Hmm" yace sannan ya tambaye ta " _Kunyan wa kike ji anan 'din ni ka'dai ne fa bawani ko ni 'din kike jin kunya_ ? " _Ummm_ " Tace atakaice Sai yace " _naji to, ni bari in fa'da miki tunda banjin kunyar ki, nace Allah Allah yayi wa matata_ _Zahra albarka ya haskaka rayuwar ta ya faranta mata kamar yanda ta_ _faranta min ko haka nace ba_ ?" ya 'karashe da tambaya. Teemah kuwa tace " _Hakane amma ai dayawa ka fa'da 'dazun_ " Dagangan yace mata " _d'azun dawani lokaci kenan ni na manta wannan ka'dai nasani......._ _oww na tuna 'dazu lokacin da......_ " Da sauri Teemah ta 'dage gira sannan ta 'daga hannu ta kai bakin sa ta rufe dan kar ya fa'da. Ahankali bakin ta dai-dai kunnan sa tace " _Yayah kai baka jin kunya ko_ ? Kai ya jijjiga mata tare da fa'din " _inaji mana amma banda na matata_ " Hannu yasa ya dawo da ita ta gaban sa idon su cikin na juna yace " _wato ke ana baki sa'ko ma kina tsayawa 'diban gulma ko_ "? Zara ido tayi tace " _Ni kuma gulma Yayah ni banyi gulma ba_ " Sai yace " _Wanda kikayi yanzun fah, inba jin gulma ba ya akayi kika san abinda na fa'da duka_ ?" Rintse ido tayi da 'karfi tana dariya tafa'da jikinsa ta rungume shi. Murmushi yayi shima tare da fa'din " _silly girl_ " sannan shima ya saka hannayen sa ya rungume ta, a kunne ya ra'da mata " *i luv u Zahraty* " Batayi magana ba sai ta 'kara yin luf ajikinsa ji take tamkar su kasance a haka har abada, wani tsuma take jin zuciyar ta nayi game da shi, sabon yanayi ke shigan ta wanda bata bata ta6a jin irin hakan ba sai yau 'din nan, ita da kanta tasan cewa tana so da 'kaunar mijinta sosai fiye da yanda mafarkin ta yake bata. Kalmar 'daya fa'da 'din kuwa ji take shine mafi soyuwan kalmar da tafi mararin son ji daga gare shi koda kuwa zasu dawwama ahaka ne bazata damu ba. Abbas ma kansa wannan moment 'din yatafi dashi he wish da ace Rivers zai koma da babu abinda zai hana shi 'dauke matar sa su tafi, shi ka'dai yasan yanda yayi kewar ta a wata 'dayan nan, bai ta6a zaton zaiyi missing komai nata har haka ba sai daya tsinci kansa acikin damuwa sosai da rashin ta, yarinyar ta, rashin jinta, 'kun'kunin ta, 'dan 'karamin bakin ta na rashin kunyan nan, jikinta da komai nata kafin ya ya gama amincewa zuciyar sa cewa itace farin cikinsa, haushin 'kin binsa datayi kuwa har yaso ya ninka haushin daya shiga lokacin da aka bawa marigayi ita suka tafi. Yanzu kuwa da yake da ita a gidan sa take kuma kwance akan 'kirjin sa sai yake jin kaf duniyan nan bayaga ahalin sa baya jin akwai abinda yakai girman matsayin ta a zuciyar sa. *4:30pm* Yabar gidan domin flight 'dinsa na zuwa Ekiti 'karfe 5:00 ne inda suka rabu da matsananciyar kewar junan su afili da kuma zu'katan su. 5:28pm Hannah ta dawo gidan sai taga Teemah cikin annashuwa ko bata bu'di baki ta fa'da ba amma farat 'daya zaka gane cewa yau walwalar ta na daban ne, musamman idan ta tuna kalmar I LUV U daya fizgo daga bakin sa 'dazun hakan ka'dai ke sata sakin murmushi, jin kanta take sosai tana jin tamkar tafi kowa she feel very exiting, wai Yayah na son ta. Hannah kam dayake bakin ta baya gani ya 'kyale sai tace da ita " _albishir 'din menene ya iso ki haka da kike irin wannan walwalar_ ?" Da sauri tace da ita " _uwar sa 'ido kawai........to Yayah ne yazo yau_ " Tayi maganar da cikakkiyar murmushi kwance akan fuskanta. Hannah 'dan gwalo idanu tayi tace " _dan Allah?_ _Kice intattara in koma kunkumin uwata_ " Hannah tayi maganar tare da mi'kewa tsaye dayake dama a parlour suka zauna. Dariya ka'dan Teemah tayi tace " _sai ki je 'din kuma ai, abinda har ya tafi ma_ " " _Haba dan Allah dagaske, shi kuma kamar ana koran sa haka?_ Hannah tayi maganar da mamaki. Teemah kam hankalin ta kwance ta bata amsa da fa'din " _Ekiti state ya nufa dama yana kan hanya ne shine fa yabiyo ta nan 'din"_ Hannah komawa tayi ta zauna da jin abinda Teemah tace, sai data zauna sannan da sigar zolaya tace " _Yayah yazo duba amarya kenan_ " Teemah cewa tayi " _To ko laifi ne yin hakan_ ?" " _Haba! wace ni ince haka? Ai ban isa ince laifi bane dan ban san sirrin dake 6oye bayan wannan gagarumar fara'ar_ _ba, abinda kawai nasani shine rai yasamu abinda yake so that's all_ " Fa'din Hannah kenan tana watsa hannu sai Teemah ma tace " _toh ya za'ayi ne Hannah abinda yafi haka ma inajin idan_ _nayi ai ba laifi bane, mijina ne fah Hannah tsawon wata guda bangan shi ba..._ " _hmmm bazaki gane yanda nayi kewar sa bane yarinya_ " Ta 'karashe da murmushin tsokana. Hannah ma murmushin tayi tace " _ke kika so hakan ai, amma yanzu da kika ganshin fah_ ? Da sauri Teemah ta tare ta fa'din " _sai naji tamkar kar yatafi wallahi_ " Baki Hannah ta ta6e tace " _ehh lallai yarinya kin hau layi Yayah ya koya miki halin sa ni dai ba ruwana_ " Dariya ma tabawa Teemah wanda cikin dariyar ta furta " _dai-dai kenan, ai baki san wani abu ba Hannah? har fa da kyautar I LUV U na samu yau daga wurin sa_ " Ido Hannah ta zaro tana dariya tace " _kice dara taci gida kenan_ ?" Dariyan sukayi dukkan su, suka sha hannu cikin so da 'kaunar junansu. (TeemHan) ***** Yanzu kam sau 'daya yake 'kiran ta a duk lokacin da ya samu dama wata rana kuma ma ko 'kiran nata baya yi. Haka kuma salon 'kiran nashi bai canja ba sai ma abinda ya ragu dan yanzun baya fin 2-3mins kullun idan ya 'kirata saboda abin da yake gabansa, daga gaisuwa baya jan magana ahakan ma yafi yin 'kiran da dare wani lokaci ma har sai tayi bacci kafin ya 'kira da safe ne kawai take ganin missed call. Tana kuwa jin haushi sosai idan hakan yafaru kuma ko ta 'kira shi baya 'dagawa har sai lokacin da ya ga dama sannan sai yayi calling nata back, daga baya ma sai ta ha'kura ta daina 'kiran nasa gaba 'daya. Shikuwa Abbas rashin sakewa da ita a wayan ya samo asali ne da kasancewar Hannah na tare da ita, sam baya iya tambayar ta komai daga yaji lafiyar ta da damuwar ta shikenan dan baya so yayi wani abinda zai sa Hannah ta ringa yi masa kallon wani abu daban. Satin sa shida (6weeks) A Ekiti yanzun amma sau 'daya tak yabata daman zuwa gaida Ummah tun farkon tafiyar sa daga nan bai 'kara barin taba, takan yawai ta mamakin hakan aran ta sau da dama Hannah ce ke 'dan wayar mata da kai akan wasu abubuwan da suka shige mata duhu. Damuwar ta 'daya yanzun shine yanda 'karfi da yaji ta zama chop-chop daga wayewar safiya zuwa dare tana cin abinci a'kallah kusan sau shida ko ma fi, wani lokaci har cikin dare ma yunwa na damun ta wani lokaci dole sai ta tashi ta nemi abinda zata saka abakin ta koma wani iri ne kafin take jin dai-dai. Abin na damun ta sosai musamman ma da taga sai 'kara huruwa takeyi tasan bakomai ne yake sata yin 'kiban ba sai lodin data ke yawan yi acikin kwanakin nan, bata so amma dole zuciyar ta ke tilastata yawan cin abincin. Gashi wani sa'in sai ta kasa bacci da dare sai dai tayi ta gadin Hannah har sai ta kusan raba dare kafin bacci ke 'daukan ta. Takan yawaita blaming sabon salon cin abincin datake yi yanzun game da komai dan aganin ta duk shine yake sata yawan baccin dama shiyasa ta tsani cin abu mai nauyi ita tun asali, Hannah na tafiya school itama take yin bacci dayake sai sun kammala dukkan ayyukan su kafin Hannah take wucewa shiyasa take iya yin baccin ganin babu wani aiki a gabanta, dan ma baccin nata baya tsayi dududu in tayi dayawa shine takai 30mins tana baccin. Lokacin data lura da yanda ta 'kara haske boobs 'din ta ma ya 'kara huruwa shima yawani cicciko bakin yayi ja sai abin yafara bata tsoro ma data yiwa Hannah mitan hakan sai Hannah tace " _ki bari idan Yayah ya dawo sai ki sanar dashi in ciwo ne zai nema miki magani ai, in kuma kiwona ke da kyau kinga sai in samu kyauta da lambar yabo daga wurin sa_ " Hannah na maida abin wasa kullum while Teemah kam abin har ranta yake damun ta. Ranar da zai dawo ya sanar da ita da safiyar ranar bayan har Hannah ta wuce makaranta. Ranar kuwa Teemah sam bata jin da'din jikinta sai dai bata ko sanar da Hannah ba dan kar tace bazata je school ba saboda hakan, jitake kamar anyi mata dukan tsiya a ga6o6in ta duk nayi mata ciwo. Da 'kyar ta samu ta shiga 'dakin sa dan yau 'din ko le 'kawa batayi ba, babu ma wani 'kura da yake kullun tana gyara shi yau ne kawai bata yi ba, amma duk da haka sai ta daure ta fara da tsabtace bathroom sannan ta dawo 'dakin ta share ta kunna burner tare da canja bedsheet 'din dake kan gadon ta fito ta jawo 'dakin yana tashin dadda'dan 'ka mshi. Kitchen ta shiga inda sai data samu wuri ta zauna tukunna ta 'dan huta harda maida numfashi, zazza6i ne take jin kamar zai kamata. Adaddadfe ta ha'da masa lafiyayyan abinci irin na hausawa wanda yaji kayan lambu dan ita yanzu sune cimar ta bata son ganin abinci batare da veggies ba. Juice 'din zo6o ta ha'da masa mai 'dan karan santi ta sashi a fridge abincin kuma ta kai su dinning, tana dafe kai dan sosai take jin ba da'di a duk ilahirin jikinta, gajiya take jin na damunta. Koda ta koma 'daki ma da 'kyar ta samu ta watsa ruwa tana yi tana hutawa yau ka'dai sai data fita a hayyacin ta, shirin ta tayi cikin wata doguwar rigar atampa data kama ta sosai daga 'kirji, ganin rigar zai takurata ne yasa ta cire ta canja da wata mai 'dan fa'di marar nauyi maroon colour sai ya 'kara fito da hasken ta afili. Duk yanda take jin jikinta kuwa hakan bai hana ta neman abincin ba saboda mur'dan yunwan da cikin ta keyi mata. Sosai ayyukan suka ja mata lokaci, tana idar da sallar la'asar tajiyo 'karan door bell, zuwa tayi ta bu'de 'kofan da fatan Allah yasa shine kowani wanda zai iya taimaka mata dan tasan Hannah kam da sauran lokaci tace ma zata bi gidan Ummah kafin ta dawo so zuwan ta yanzun da 'kyar ne. Cikin sa'a kuwa shi'din ne, tana bu'de wa taganshi tsaye kafa'darsa rataye da jakar sa, fuskarsa ba yabo ba fallasa koda ya gantan beyi wani reaction ba sai ma ya tsaya yana mamakin canjywar ta na yanzun. Teemah kam gaba 'daya sai tayi loosing control tasaki murmushi sai sannan ya maida mata martanin murmushin nata, dan farin ciki ma har bata san lokacin data fa'da jikinsa ba sai kuma tafara hawaye a tun safen da take jin ta wani iri 'din batayi kuka ba sai yanzu da ta ganshi, a hankali ta furta " _sannu da zuwa Yayah_ " Abbas kam fuskar sa ba yabo ba fallasa sa6anin zuciyar sa dake cike tab da farin cikin ganin ta. Bai amsa mata sannun data masa ba sai hannun sa 'daya dayasa shima ya rungume ta, jikin ta babu zafi illah 'dumi da yayi shiyasa ko'ka'dan Abbas be fahimci yanayin datake ciki ba. Dayaji sau'kan hawayen ta a'kirjin sa ne ma sai ya 'kara sakin murmushi, zaton shi duk kukan na ganinsa ne. A kunnan ta ya ra'da mata " _kin koyi rashin kunya ke ma ko? Shine harda kukan farin cikin gani Yayah_ " Duk da yanayin datake ciki amma sai datayi murmushi ta 'dan motsa ka 'dan sai ya sake fa'din " _jakata zaki kar6a nagaji sosai fah_ " Da sauri ta tashi a 'kirjin san tana mai sau'kar da idanun ta 'kasa dan kar yayi saurin fahimtar halin datake ciki. Kar6ar jakan tayi batare da ta kalli fuskar sa ba tana jin ta cikin wani yanayin farin ciki marar misaltuwa. Sanyin da ga6o6in ta sukayi ma duk sai taji ya ragu batasan dalili ba. Abbas kam 'kura mata ido yayi da mamakin yanda take avoiding ha'da idanu dashi yau 'din bai san dalilin ta ba amma sai yaji hakan ya birgeshi ganin kamar tafara yin wayo ne tunda har take kunyar shi. Cikin hakan sai kuma ya fahimci kamar akwai abinda ke damunta. Bayan ta yabi da kallo har ta shige 'dakin sa da jakar sannan ya 'karaso cikin parlourn inda ya yada zango akan kujera tare da 'daga kansa sama ya lumshe idanu, yana tunanin damuwar tata ko ta mecece oho. Wani zazzafan iska ya huro daga bakin sa take sai ajiyan zuciya ya biyo baya. Teemah bata fito ba sai da ta ha'da masa ruwan wanka sannan ta fito inda ta same shi zaune ya jingina da jikin kujera, afili ta fahimci tsantsan gajiyan daya kwaso sai taji tausayin sa sosai dan tasan irin aikin su babu sau'ki sam. Fridge ta wuce ta 'dauko masa ruwa mai sanyi da cup ta zo gefen sa ta zauna wanda hakan yasa shi ya 'dan bu'de idanu yabi jikinta da kallo. Sai data tsiyayi ruwan sannan ta mi'ka masa, ya kuwa kar6a ya shanye, koda tayi yun'kurin 'kara masa sai ya girgiza mata kai tare da mi'ka mata cup 'din. Komai cikin 'karfin hali take yinsa dan bata so tabawa 'dan 'karamin zazza6in data ke ji 'din 'kofar da zai sanya har ya dawo mata babba balle ayi mata zancen injection, she hate it at all. Cup 'din ta ajiye agefe sai ta sau'ka ta tsugunna dai-dai 'kafafun sa tafara warware igiyar boot 'din dake 'kafar sa tare da socks 'din gaba 'daya ta cire su ta matsar gefe. Tana jin 'dan nauyin sa amma haka ta daure ta kama 'kafar tasa ta dinga mammatsawa ahankali tana mi'kar da yatsun 'daya bayan 'daya. Sosai Abbas yaji da'din hakan sai ma yasake lumshe idanu yana jin tamkar karta daina yi masa. Bata wani da'de a hakan ba ta tatashi ganin agajiye yake dole zai bu'kaci freshing up saboda ya'dan warware sai ta dawo ta zauna inda ta tashi 'dazu daga gefen kujera a hankali ta fara 6alle masa botilan rigar tana 'kara sau'kar da idanun ta 'kasa. Abbas kam yana jin hannun ta a'kirjin sa ya bu'de idanu yana kallon kan fuskar ta zuwa idanun ta amma ta'ki bari su ha'da idanu. Bai hana ta ba dan yanda yake jin gajiya bai 'ki wan kan ma ta taimaka masa ba saima yake 'kara mamakin wannan sabon sauyin dayake gani daga gareta komai ma canja masa yayi, daga ita har rayuwar ta gaba 'daya. Idanun sa ya lumshe ya sake yin baya da kansa Teemah kam har ta ji da'di taci gaba da 6allewan cikin natsuwa bata sani ba ashe a hakan yake 'karewa halittar ta kallo. Gani yayi ta ko'de sosai farin ta ya 'karu, ga wani 'dan 'kiba datayi hips 'dinta ma suka 'kara fitowa sosai, aransa yace " _sam bata damuwa da rashina ji yanda tayi kyau ta 'kara 'kiba abinta ta manta dani da rayuwata."_ Har ta gama 6alle bottles 'din yana karantar yanayin ta, sai data gama kafin tayi 'karfin halin 'dago idanu ta sau'ke su akan nasa sannan tace " _Yayah saura kayi wanka ko sai kaci abinci tukunna_ ?" Bakin ta kawai ya tsaya kallo harta gama maganar bai ko yi yun'kurin nuna alamun yaji bama balle tasaka ran samun amsar ta, aransa yake tunanin.....how on earth zai gaji da kallon wannan yarin yar? Angel 'dinsa, kyautar Allah, amanar sa, matar sa, kuma 'kanwar sa, his first and last lover wacce yake fatan ta kasance uwar 'ya'yan sa gaba 'daya kuma 'kar'kashin ikon sa har abada. Acikin muryar ta ya 'dan fahimci damuwar dake tare da ita inda ya gaskata zarginsa saboda muryar ta kansa fizo shi takeyi ta harha'da kalaman data furta masa. Tana shirin mi'kewa yasa hannun sa ya janyo ta sai ta fa'do jikinsa, zafi taji acikin ta dan yanda ta tafi ba shiri da sauri ta yamutsa fuska sannan tace " _awwshhh....Ya...._ " _.......Tell me! Me ke damunki_ ?" ya tare ta da fa'din hakan. Take sai ta tura baki dan bata san me zata ce dashi yake damun ta ba. Turo bakin datayi ne yasa shi ya kai yatsan sa 'daya kan bakin ya shafa slowly tare da 'kara rage 'dan tazaran dake tsakanin su sannan ya sake fa'din " _gaya min mana inji me yake damunki ko ciwon rashin Yayah ne ya shige ki sosai haka_ ?" Goshi ta ha'de tare da niyyan fara gunguni sai yayi saurin 'daura bakin sa akan nata wanda hakan ya tilasta mata nutsuwa. Passionate kiss ya bata wanda ya matu'kar ratsa ta har cikin jikinta tare da sake matso ta zuwa jikin sa sosai. Door bell ne ya fara 'kara wanda yasa ta tafara mutsu-mutsun 'kwace jikin ta, ganin hakan sai Abbas ya sake mata bakin amma be raba jikin sa da nata ba, taga kamar baida niyyan 'kyaleta ga door bell nata bada sauti sai ta juya ta kallo 6angaren 'kofan tare da da dawo da kallon ta gareshi duk yana kallon ta. Bu'dan baki tayi zatayi wata maganar sai yasa 'dan yatsan sa akan bakin nata hakan sai yasa tayi shiru tabi hannun da kallo sannan ta kuma maida kallon nata kan fuskar sa. Sake matso da kansa yayi yabata wani peck a tsakiyan goshin ta wanda yasa ta har sai data lumshe idanu sannan yaraba jikinsa da nata sai ta mi'ke tsaye ahankali ganin ya sake ta shima take ya mi'ke tsayen kamar yanda tayi ya nufi 'dakinsa. Teemah binsa tayi da kallo har ya shige sannan tasa hannu ta 'dauki mayafin ta ta rufe kanta dashi ta tafi ta bu'de 'kofan. Tana bu'dewa Hannah tace " _hala bacci kike yi da la'asar 'din na ko, tun 'dazu fah nake ta faman aikin danna bell amma shiru_ "? _Comment Vote and Share_ *Salmerhn ku ce* 😍 [10/13, 1:58 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ~Dedicated to my family~ 🥰 *Bismillahir rahmanir raheem* _Never be afraid to help others in their time of need. You never know when you may need that_ _shoulder to lean on_ . 🅿 *86* Muryar ta ciki-ciki tace da Hannah " _har kin dawo_ "? Hannah dake 'ko'karin shigowa tace " _ehh na dawo ai ban bi gida ba kawai na taho nan, bana ma sam inje ni ta rin'ka kora 'din_ _nan wai ita a dole ina barin ki ke ka'dai a gida_" Teemah cewa tayi " _Hmm, gaskiyar ta ne ai Hannah ba 'karya bane....._ " Hannah da sauri ta tare ta da fa'din " _Ba wani nan naga kona zauna 'din ma baccinki kike sha ki barni ina gadinki, kuma Allah ki daina_ _baccin la'asar 'din nan kin ganki ne yanzun yanda kika zama tamkar mara lafiya fa"_ Hannah ce tayi gaba sai Teemah tabiyo bayan tana me fa'din " _ai ba lafiyar ce dani ba Hannah ko dan ban fa'da miki bane shiyasa, Allah yau ban jin da'di........._ " Maganar tata tsayawa tayi dalilin cafko hannun ta da taji Hannah tayi sai ta nuno takalman data gani a parlourn a mamakance 'kasa-'kasa tace " _ya dawo ne_ ? Da kai Teemah ta bata amsa alamar " _ehh_ " Hararar ta Hannah tayi tare da sakin hannun ta, Teemah kuwa sai tayi murmushi. " _ina yake to_ ?" Hannah ta tambaya. Teemah ma sai ta bata amsa da fa'din " _d'akinsa_ " A takaice Hannah sai tace " _Ki sanar dani cewa mijin ki ya dawo ne mana kika wani barni nake ta zabgawa bacci sharri_ " " _Ke kika sani ai_ " Teemah tace tare da wucewa cikin parlourn ta kwashi takalman nasa tayi gaba dasu zuwa d'akin sa. Hannah ma d'akin Teemah ta shige da niyyan tattara kayanta ta koma gida tunda ya dawo. Shigan Teemah d'akin nasa sai ta tarar dashi har yashiga bathroom, kayan daya cire 'din ta kwashe ta fitar masa da wasu marasa nauyi riga arm less da 3quarter trouser dan taga idan yana gida da ire-iren su yafiya amfani. Fita tayi ta koma wurin Hannah anan ta same ta tana kan ha'da kayan ta. Turus taja ta tsaya tana kallon ikon Allah, data ga cewa dagaske take yi kaya take ha'dawa sai ta 'dan matso tare da fa'din " _Hannah wai miye hakan kike yi ne dan Allah_ ?" Hannah bata 'dago ba tace da ita " _inda nafi wayo zan koma ko so kike in zauna har sai mijin ki ya_ _korani kafin in tafi_ ?" Amsa Teemah tabata da fa'din " _Ce miki akayi zai koreki? Ko kin ta6a jin ya kori wani ma agidan sa ballantana kuma ke_ ?" " _ke nifah 'kyaleni Teemah gara na ware yafi, ya za'ayi gandamemiya dani kuma in zauna agidan amare_ ?" Hannah na maganar tana zuge zip 'din akwatin kayanta. Teemah kam tsaki tayi cike da haushi ta koma parlour Hannah ta rakata da murmushi tana murnar yau sai kwana a gida wurin Ummah. Teemah zama tayi a parlourn ranta duk ajagule, Bata da'de da zama a wurin ba sai gashi shima yafito cikin shigar kayan data fitar masa yana amsa waya. Sosai taji da'din hakan domin yau ne karo na farko data ta6a aikata masa irin hakan kuma tayi sa'a bai gwale ta ba. Dinning ya nufa da wayar a kunnan sa itama sai ta tashi ta bishi abaya. Koda ya isa wurin ma bai zauna ba har sai daya kammala da wayar kafin yaja kujera ya zauna. Teemah kam bata zauna ba abincin tafara zuba masa dai-dai nan Hannah ta fito. A hankali ta 'karaso wurin tayi masa barka da zuwa, Suna ha'da idanu da Teemah sai ta banka mata harara, sannan taci gaba da abinda takeyi. Hannah kam dariya ma Teemah ke bata . Abbas gaisuwar datayi masa yayi tare da tambayar ta ya makaranta. Inda ta amsa da " _Alhamdulillah_ ". " _Allah ya taimaka_ " Yace 'kasa-'kasa. Zama sukayi dukkan su bayan Teemah tagama serving nasu kafin su fara ci sai tace " _Yayah kaga Hannah ba! wai tafiya zatayi dan ka dawo har ta_ _gama ha'da kayan ta ma_ " " _Ah ah ba yau ba_ " Yace atakaice tare da saka abinci abakin sa. Teemah kam murmushi tayi itama tayi bismillah tare da fara cin abincin. Tana murmushin ta kallo Hannah da suka ha'da ido sai Hannah ma ta harareta ita kuwa Teemah tayi mata gwaliyo. Hannah bata wani ci na kirki ba ta tashi ta koma 'dakin Teemah ta turo 'kofar. Shiru sukayi kowa nacin abincin a hankali, Abbas kam ma daina cin nashi yazo yayi ya tsaya kallon ta ganin yanda take cin abincin, duk da bata ci ko rabin plate ba amma sosai yake 'kara ganin sauyi ta wannan 6angaren tattare da ita. Saboda kwanaki ba haka take yi ba. Yana ganin ta gama sai ya mi'ke tsaye ya koma parlour ya zauna, Teemah kam sai da ta tattare komai kafin ta bar wurin taje tana shirin wucewa 'dakin ta wurin Hannah sai yace da ita ta dubo masa 'dayan wayar sa a 'dakinsa. D'akin ta wuce ta fara dubawa amma bata gani ba, shima 'din yasan bazata gani ba saboda bai ajiye inda zata yi saurin ganin ba dama dagangan ya turatan dan so yake yaji 'dumin matar sa, dan haka sai ya tashi ya bi bayan ta. Ko yanzun ma waya yake amsawa wanda take kyautata zaton da abokin aikin sa ne saboda yanayin maganar dataji yakeyi, aranta tace " _wannan dai yau inajin cutar amsa wayace takama shi_ " Tsayawa tayi tana kallo da jin yanda yake maganar da ta'kama tamkar wani sarki sai kace dole aka saka shi, tana ganin ya gama sai ta kauda kanta gefe da sauri. Yana cire wayar a kunnan sa yace da ita " _come on, zo nan ki gaya min how u missed me_ " A hankali ta taho sai ta zauna agefen sa 'dan nesa ka'dan dashi. " _What is ths kuma?, bayan kin gama min rashin kunyar ki 'dazu shine zaki zo kimin wani fi'ili anan ko? Zo matso nan ki gaya min_ _wama ya koya miki......_ Tun kafin ya rufe bakinsa tace " _ni babu kowa_ " Gira ya 'dage sama yana kallon ta yace " _Really_ ? Shiru tayi ta kauda kanta gefe. Sai yace " _to naji shikenan, zo in koya miki wani da bakiyi 'dazun ba ko baki so ki koya?_ Kai ta 'daga masa alamar " _ehhh_ " Bata ankara ba taji ta ajikinsa inda yazo ya rungume ta bayan ta hannun sa daga cikinta ya sa'kalo su yayin da ya kwantar da kansa kan kafa'dar ta a hankali kamar ra'da yace " _guduna kike yi ko_ ? Kamar zatayi kuka tace " _umm-ummm_ " tambaya ya sake jefa mata da fa'din " _To meyasa baki son zuwa kusa dani?_ " _Ni....ni... bani da lafiya ne fa shiyasa....._ " " _Shiyasa kike gudun mijinki_ ? Sai tayi shiru. " _what's wrong with u then, meke damunki_ ? Sai yanzu ne tabashi amsa da fa'din " _Nima bansani ba 'dazu ne naji kamar banda lafiya amma yanzu yayi sau'ki_ " Sai yace " _muje wurin Anty nurse ta dubaki ko?_ Kafa'da ta 'daga da sauri ta kwa6e fuska sannan tace " _ai na warke yanzu_ " Hannun ta dake cikin nashi ya kamo ya 'dago shi sama ya 'kara kalla da kyau sannan yace " _Kuna sayan lightning cream kuna amfani dashi da bana nan ko_ ? " _Ah'ah_ " Tace dashi dashi. Da mamaki yace " _ya akayi haka to ke baki ga kin canza sosai ba, miye dalilin_ ?" Cewa tayi " _Nima fa bansani ba Allah Yayah_ "? Shiru yayi yana feeling 'dumin jikinta kawai sannan ya cusa kanshi 'kar'kashin wuyan ta ya sumbace ta sai ya 'dago kansa a hankali yace " _Zaki fara zuwa makaranta kema, gaya min wanne kike so kiyi_ ? Tace " _bana son ko wanne_ " " _Kamar Yayah_ ? Ya tambaya da mamaki. Sai tayi shiru bata bashi amsa ba. Cigaba yayi da fa'din " _kin fi son kiyi ta zaman ki a gida haka kawai kenan_ " kai ta 'daga masa up&down. Sai yace " _saboda me to, baki ga Hannah na zuwa tana karatun ta ba......_ Taran sa tayi da fa'din " _Ni fa banaso ne kawai Yayah_ " Juyo da ita yayi ta fuskance shi sai yaci gaba da lalla6an ta dan ta yarda yace " _baki son ki zama doctor ne irin na Anty nurse?.......ba wahala fah idan kika gama kinga_ _sai ki haifi babyn ki dayawa ko ba haka ba?_ Teemah najin zancen baby tasaki fuska tana murmushi amma duk da haka sai tace dashi " _to ni Yayah shikenan bani da daman in zauna agida batare da yin wani makaranta ba_ ? Idanun sa cikin nata yace " _Yes kinada shi mana, Fatima nada wannan daman a ko'ina sai dai akasin da aka samu shine ita wannan 'din Zahra_ _ce!, Zahran Abbas kuma,_ _Zahran Abbas kuwa batada wannan damar ita_ " Baki ta turo gaba tayi fushi sai ya kamo chicks 'din ta duka biyu da hannun sa yace " _Angel 'din Yayah a daure a cikawa Yayah wannan burin plz kinji_ " Batayi magana ba illah bugan 'kirjin sa da tayi a hankali da hannun ta 'daya tana 'kif-'kif da idanu. Shikuwa kamar gaske sai yayi baya akan gadon ya 'dora kansa cikin hannayen sa ya wani lumshe idanu. Da sauri tabishi tanaq 'kiran sunan shi " _Yayah_ ! _Yayah_ !! Tare da jijjiga shi. Abbas 'kin tashi yayi ya kuma 'kin motsawa ko ka'dan, sai daya ga ta rikice sosai sai ya 'dan bu'de idonsa 'daya ya kalleta caraf sai akan idanun ta. Da sauri ya maida idon ya kuma rufe shi. Ita kuwa dan mugunta harda cije baki ta kai kanta a hankali zuwa saitin fuskar sa kamar zatayi abin kirki sai kawai ta cije mai hancin sa. Zafin dayaji ne yasa shi bu'de idanun da sauri tare da fa'din " _awwshh_ " yana shafa hancin. Tana 'ko'karin guduwa ya cafkota take ya maida ta 'kasan sa, suka fara kokuwa tana dariya take fa'din " _Allah Yayah bazan sake ba please kayi ha'kuri_ " Shima yace " _Babu ruwana ramawa zanyi, in ada kin min mugunta na barki yanzu kam ba'a cutata na 'kyale mutun_ " Kokuwa suke ta faman yi kowa na 'ko'karin ida nufinsa, Teemah so take ta 'kwaci kanta dan ta riga ta gano inda ya dosa ita kuwa a yanzun bata shiryawa hakan ba musamman ma data ke 'dan jin marar ta na 'dan mata ciwo sai take jin bata son damuwa sosai yanzun, kuma tasan muddin ya raba ta da rigar ta to ba 'kyale ta zaiyi ba, bazai barta ba uwar wuya zata sha a wurinsa. 'Karfin su koka'dan ba 'daya bane dan haka tana ji tana gani ya raba ta da kayan jikin ta sai suka tsaya kallon kallo dashi, hannu takai ta rufe 'kirjin ta tana ci gaba da kallon sa. Ganin tana rurrufe jikinta hakan yasa shi yasa hannun sa duka biyu ya bu'de hannayen ta zuwa gefe da gefen ta sai ya zuba mata idanu yana kallon canjin da jikin ta yayi. Kwa6e fuska tayi a hankali cikin muryar shagwa6a tace " _Yayah ba nace sorry ba_ ? Shiru yayi be kulata ba ganin haka sai ta sake ce dashi " _Plz kayi ha'kuri ka kaji Yayah?, ina ciwon ciki fa_ " Dawo da idanun sa yayi kan fuskarta ya kalleta, sai ta lumshe masa idanu a hankali ta kuma bu'de su alamar yayi ha'kuri. Murmushi yayi mata dan ya gama fahimtar ta, Teemah tafiya tsoro dayawa shi kuwa baya son hakan sam. Kansa yakai a hankali yayi kissing 'din ta a wurin wanda yasa dukkan su lumshe idanu dan dukkan su sai da kowa yaji a jikinsa. Yana bu'de idanun sai ya sake mata hannun ta ya koma gefen ta ya kwanta, shima yana kallon ceilling kamar yadda take. Sai yace " _wa ya fa'da miki Abbas na ha'kuri idan akayi masa laifi_ ? " _Zuciyata_ " ta bashi amsa a hankali. sai yace " _to tayi 'karya_ " Juyowa tayi ta kalle shi sai tace " _to karama_ " " _Kin amince_ ? Ya tambaye ta yana murmushi. Da " _umm_ " ta amsa shi tana kallon shi. " _Are u sure_ ? Ya sake tambayar ta. Kai ta 'daga masa ha'de da lumshe idanu ta kuma bu'dewa. Sai yasaki wata munafukar murmushi wanda shi ka'dai ne yasan ma'anar ta. Juyo da kansa yayi ya fuskance ta yana daga inda yake 'din yake kallon cikin idanun ta da nasa lumsassun idanun. Teemah ma bata kawar da kanta ba sai suka tsaya kallon juna. Tunowa datayi har yanzu jikin ta abu'de yake yasa ta fara 'ko'karin janyo bedsheet domin rufe jikin nata dashi. " _Ban ce ba_ " Yace da ita wanda still yana a yanda yake 'din bai motsa ba tamkar ba shine yayi maganar ba. Dolen ta ta bari kamar yanda ya bu'kata 'din itama ta maida kallon ta gareshi. Dai-dai sanda taji ya dawo kusa da ita sai ta rintse ido aranta take fa'din _innalillahi_ dan tasan yau kam mai 'kwatan ta sai Allahu, bata gama tunanin ba kawai sai taji bakin sa akan nata. Babu abinda ya mata amma sosai ya galabaitar da ita sannan ya 'kyale ta, bakin ta har nayi mata zogi da boobs 'dinta. Hannah bata 'kara ganin Teemah ba sai da maghrib lokacin ma masallaci ya fita sai ta samu tafito. Already ma har Hannah tayi musu abinci tagama komai shigan ta 'daki kenan sai ga Teemah ma ta shigo a bayanta da idanun ta wuri-wuri na rashin gaskiya, ita kanta tasan bata kyau ta wa Hannah ba bayan ita ce tayi 'ko'karin ganin an hanata komawa gida, amma ai itama ba laifin ta bane laifin Yayah ne daya hanata sakat. Murmushi Hannah tayi tace " _Amarya bakya laifi, barka da fitowa kinji_ " Shiru Teemah kawai tayi ta wuce ta zauna sannan tace " _naga abinci a dinning wai har kin gama kirki ne bansani_ "? " _Ehh nagama da 'din jiranki zanyi ne ko me?_ cewar Hannah, Teemah shiru tayi bata bata amsa ba. Hannah ce tasake fa'din " _a irin hakan ne zaki wani ha'dani dashi ya hana ni tafiya dan gani banda wurin zuwa ko_ ?" Sai yanzun Teemah ta bu'di baki tace " _kai Hannah yau 'din nan fa ya dawo dan naje wurin sa kuma shine laifi_ ? Hannah cewa tayi " _Laifi nace miki kinyi ne?, ni ba damuwa ta kenan ba so nake in koma_ _nima kusa da uwata tunda kema mijin ki yadawo_ " " _Hannah wai meke damunki ne dan Allah_ ?" Temmah tayi maganar cike da haushi dan ta tsani Hannah tana maganar komawan nan sam ita. Hannah amsa ta bata da fa'din " _Bakomai dake damuna kawai so nake na baku space a gidan ku ba in zama mai gadi ba_ " " _Hannah plz ki bar maganan nan in dai wurin Yayah ne ai kema ba'a hanaki zuwa ba_ " Ido Hannah ta zaro sannan tace " _ni rufa min asiri ban shirya ganin abinda ya girmi tunani ba_ " Teemah k'asa ta sau'kar da kanta tace " _naji ni dai kiyi ha'kuri karki tafi dan Allah"_ Hannah bata 'kara yi mata magana ba kawai tayi shiru tafara 'ko'karin shgia bayi. Bawai zaman gidan nasu ne bata so ba, a ah, ita zama a gidan idan Yayah na nan ne sam ta tsana, tafi so takoma gida in yaso bayan ya tafi sai ta dawo amma duk sun ha'de mata baki sun kasa fahimtar ta, su bata damar tafiya, shiyasa take nunawa Teemah kamar taji haushin barin tan datayi ne duk da kuwa ba haka bane a zuciyar ta, in akwai wanda zaiso ganin kusancin su to be wuci iyayen su da suka ha'da auren ba na biyun su kuwa itace. Basu 'kara ha'duwa da shi ba sai 8:00pm na dare wajen cin abinci, nan kowa ya 'dan tattaba yabari da yake bawani yunwa sosai sukeji ba. Teemah bata 'kara komawa 'dakin sa ba shima 'din bai damu ba dan yasan dama bazuwan zatayi ba tunda Hannah na nan. Hannah ce ma taso sata zuwa ita kuwa ta'ki tace bazata ba a haka suka kwana. Washegari da safe data je gaidashi sai ya tsare ta da tambayar " _me yasa bata dawo jiya ba ko gudnyt kiss bata zo tayi masa ba_ ? Sai tace " _Hannah na nan fa Yayah_ " " _Shine me_ ? _Ba gidanki tazo ba, ina ruwan ki da ita?, kawai kice kin fakecda ita kika gujeni_ " " _Yayah.....!_ Sai kuma tayi shiru tambayoyin nasa gaba 'daya sai suka mata kama dana son kai dan tasan shi babu ruwan shi ba kunya ne dashi ba. " _Uhmm ina jinki_ " Yace da ita. A hankali tace masa " _ni dai kunya nakeji gaskiya_ " Take yace da ita " _me 'karya, bayan kin gama enjoying mijinki shine kuma daga baya kike jin kunya_ ? " _Ni ba wani enjoying 'din danayi_ ? tafa'da tana ha'de rai. Sai yace " _dagaske_ ? " _Umm_ " tasake fa'da, sai yace " _to bari a gwada yanzu dan in sake tabbatar da gaskiyar ki_ " Kanta ta 6oye ajikin sa tana murmushi shima 'din haka, sai yayi kissing kanta sannan ya sake rumgumar ta ajikinsa yana me cigaba da sha'kan 'kamshin jikinta a haka wani sabon bacci ya 'dauke su gaba 'daya. Har Hannah ta wuce makaranta basu sani ba, sai da suka tashi a baccin ne kafin Teemah ta tuna da Hannah koda taje ta duba kuwa bata same ta hakan kuwa ya sanya ta taji babu da'di har aranta. Hannah kuwa bata dawo ba koda suka tashi 'din ma gida ta wuce abinta, suka 'dai suka wuni agidan babu inda Abbas yaje sai masallaci yana idarwa kuwa yake dawowa gida. Sai da yamma tayi lis Teemah taga Hannah bata dawo ba sannan sai hankalin ta yafara tashi dan bata saba yin irin hakan ba. A waya tayi 'kiran ta sai Hannah tace ita kam tana gida, sai lokacin hankalin Teemah ya kwanta da taji inda Hannah take sai dai ta jinjinawa nacin Hannahn. Da dare kuwa a 'dakinsa suka kwanta kanta akan 'kirjin sa yana ta mata mitan tazama 'katuwa wai zata 6alla masa 'kirji, ita kuwa tace dole sai anan zata 'dora kanta. A haka suka yi baccin kuwa sai dai bai barta ba sai da ya yamutsa ta tukunna. Sha biyun dare ta farka daga baccin shi kuwa lokacin yana kan baccin sa, amma sai da ta tashe shi dan rigimar ta, bayan ta gama 'kare masa kallo sai ta saka yatsanta acikin kunnan sa ta ringa juya wa a hankali wanda dole hakan sai da ya sashi ya farka shima. Kallon kallo suka tsaya yi sai ya tashi ya zauna ya tambaye ta "me kuma ya hanata bacci" Tace ita ma bata sani ba kawai takasa yin baccin ne, kuma tana jin yunwa" Da mamaki ya kalle ta yace " _yunwa dai_ ? _Wai anya ke 'din nan lafiyar ki kuwa?_ " _Ni lafiya ta 'kalau_ " tace masa da sauri tun ma kafin abin ya kama ransa. sai yace " _Me kike so kici to da wannan daren dan Allah? Ki bari mana sai gari ya_ _waye inyaso sai ki nemi abincin_ " Tace masa " _ah'ah ita dai yanzu takeso, kawai ya rakata ta ha'do tea shi ka'dai ma ya isheta_ " Kai ya girgiza sannan ya mi'ke tabiyo bayan sa suka fita da kansa ya ha'da mata tea 'din sannan suka dawo 'dakin nasa. Bai kwanta ba ya zauna yasa ta agaba yana tunain shikuma wannan salon daga ina tasame shi, sai kace 'karamar yarinya neman abinci da dare, sai da ta shanye tea 'din kafin yasata agaba sukayo alwala yarakata ta 'dauko doguwar riga da hijab suka tada sallah. Addu'o'i ya dinga jerowa bayan sun idar da sallahn sannan suka koma suka kwanta. Anan kam Abbas be barta ba har sai daya biya bashin sa na tsawon wata gudan da yayi bayanan kafin ya sarara mata, Teemah har sai da tayi dana sanin tada shi a baccin dan sosai ta galabaita a wurin sa, shikuwa banda albarka babu abinda yake sama ta. Washe gari kuwa da wuri suka yi shiri suka tafi gida, Teemah jitake yi kamar tayi tsuntsuwa dan murna, tun bayan zuwan ta gidan sau 'daya tak ya barta ta fita kafin hakan ma kuma bata ta6a fita yawo acikin garin Abuja ba dan tana kammala iddar ta aka sake 'daura mata aure. Sosai garin yayi mata ya birge ta taringa kallon hanya har suka isa, Ummah ma tayi farin ciki sosai da ganin su musamman dataga yanda Teemah tayi kyau ga dukkan alamu hankalin ta akwance yake yanzu, sai ma ta'kara fahimtar amincin dake tsakanin su daga yanayin su. Hidima ta ringayi dasu kamar ta maida su cikin ta, Abbas har da tsokanan ta wai yasan badan shi take yi ba dan 'yarta ne dan haka shi babu ruwan sa baze ci komai ba. Dariya tayi tace masa " _ai kai ka girma yanzu na yaye ka tuntuni kuma ma gara ka zage kaci tunda bana waje ka iya ci ba dan ya'ta bayan zu zata koma gidan ba balle kasa ran zata sama maka wani abin kaci_ " " _Yace ni dai na'ki_ " Teemah kam murmushi takeyi kawai tana kallon su suna birgeta musamman data ga yanda Yayahn yake wa Ummah sakalci son ranshi yama manta da cewa ta na wurin. Haka suka ringa hira tsakanin su, Teemah kam bata fiya saka musu baki ba domin nauyin Ummah take 'dan ji yanzu ka'dan-ka'dan ba kamar da ba da har kwanciya take yi akan cinyar ta, hakan kuwa yasa ta kasa sakin jiki sosai, Ummah ce ma me yawan janta da hira dan kar ta zama shiru a gefe. Daga baya Abbas ya tafi ya bar ta anan da Ummah, Allah ya taimake ta ma Hannah da wuri ta dawo. Da suka ke6e ne sai Teemah take tsokanan ta wai " _sarkin fushi mai yaji_ " Hannah tace " _ba fushi bane tsare mutuncina nayi kan a koroni, haka kawai sai ku ringa_ _shige wa kuna barina tamkar marainiya bayan nima inada uwata akusa, lalala kinga gara dana nemi_ _hanyata yafi min_ " Dariya Teemah tayi tace " _ai kin taimaki kanki yarinya_ " Hannah tace " _aww ashe kingane_ " " _Ehh mana ai nima ba laifina bane kinsan idan ina tare da Yayah mantawa nake da kowa a_ _duniyan nan shiyasa kema nake mantawa dake_ " Hannah dariya tayi tana nuna Teemah tace " _ai dama na ta6a gaya miki idan kika fara naki soyayyar sai kin ninkani kika 'ki yadda gashi tun ma ba'aje ko'ina ba kina confessing_ , _shine ranar har da 'kin zuwa dan wai karki barni ni 'daya ko? salon ki sa Yayah yazo ya tsaneni abanza_ _yace na ri'ke masa matarsa_ " " _Haba kema kinsan ai yayah baze yi haka ba_ " Cewar Teemah. Sai Hannah tace " _ke de gama bakin ki anan wannan dodon mijin naki miye ma bazai aikata ba_ " Teemah ha'de rai tayi tace " _Ah ah Hannah ya haka kuma kike zagar min shi agabana dan Allah_ ? _Wanann ai cin mutuncine....ke kika san wani dodo amma ni bansan shi ba mijina ka'dai_ _nasani_ " Dariya Hannah tayi tace " _Lallai!...... gaba-gaba dai amaryar Yayah.... kice abin ya zarce_ _tunani na, da'din abin ma dai inada Bilalu na nima_ " Teemah ma dan ta tsokane ta sai tace " _may be shine dodon naki_ " Da sauri Hannah tace " _Allah ya kiyaye wallahi Bilal ba haka yake ba_ " Baki Teemah ta ta6e ta kauda kai gefe. Sai Hannah tace " _ke ai baki sani ba, dana dawo fa Ummah ta tsare ni wai sai dai na koma ta ya zan taho nan da yamman Allahn nan na barki agida_ _ke ka'dai.....,dayake ban tsara fa'dan komai ba sai na rasa mai zan ce_ _mata ma sai dana ga zata fara masifa shine nace mata ai Yayah ya dawo ne shiyasa na taho_, _Ummah najin haka kuwa kinsan shiru tayi bata 'kara yimin fa'dan ba_ " Teemah cewa tayi " _To dan taji ya dawo ne shiyasa tayi shirun ba dan wani abu ba dai hajiya parrot_ " " _Ke de.... fa'di gaskiya...... malama_ " Hannah ta yi maganar tana dariya. Murmushi Teemah tayi tace " _Allah kin raina ni Hannah, nifa yanzu Yayar ki ce kin sani ko?...Anty_ _ma ya kamata ki fara 'kira na?_ " _Kuma gaskiyar ki ne fa Anty Fateeman Yayah_ " Teemah sai cewa tayi " _Yauwa ya kika ji sunan abakin ki dan Allah?_ Tashi Hannah tayi tsaye sannan tace " _Hmmm, Allah ya shirye ki da son girma ke kam......ba nayo wanka in zo in baki labari, Bilal ya_ _kusan dawowa_ " Tana gama fa'din haka ta shige bathroom. Teemah kam baya tayi ta kwanta take sai fuskar Abbas ya zo ranta. Tashi tayi ta lalu6o wayar ta ta 'kira layinsa yana 'dagawa sai yace " _y'an matan Yayah ya akayi_ ?" Ita kanta bata san dalilin 'kiran nasa da tayi ba dan haka sai tayi shiru tana murmudhi daga 'dayan 6angaren sai ya sake fa'din " har kin fara missing 'dina ko?" "Ah ah " tace da shi. Sai yace " to me kikeyi yanzun?" Da "bakomai" ta bashi amsa. Sai yace " in zo in dawo dake gida wurin mijin ko? , ai nasan dama ba iya zaman zakiyi ba " Tace " _Nifa bahaka bane Yayah_ " Tana turo baki. Abbas cewa yayi " _Oww murya ta kike son ji kawai_ ?" Teemah kam kashe wayar tayi da hanzari tana murmushi, shima 'din murmushin yayi jin ta yanke 'kiran. _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/13, 1:58 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated to my family_ .🥰 *Bismillahir rahmanir raheem* _The greatest thing in life is finding someone who knows all ur mistakes nd weaknesses nd still loves u nd thinks u ar d best thing in there life!_ 🅿 *87* A haka Hannah ta fito daga bathroom 'din ta same ta tana murmushi ita ka'dai. Batayi mamaki ba dan hakan sai tace " luv thing-thing" "Ke kika sani ai amoebo" Dariya Hannah tayi tace "na canka dai-dai kenan? Teemah batayi magana ba sai tayi murmushi kawai ta sake d'ago wayar ta. " _murmushin fa na menene ko duk na soyayyar Yayah ne_ ? Hannah ta tambayeta. Teemah sai tace " _ke ni 'kyaleni Mummy zan 'kira_ " " _Zama ki fa'di gaskiya ai_ " Hannah tace tana mai goge jikinta. Teemah Mummy ta 'kira da Anty duk suka gaisa da yake tana cikin farin ciki tayi 'kiran shiyasa ta sanya zu'katan su suma cikin farin cikin sosai ganin ta saki jiki agidan ta. Da Mummy ta tambaye ta lafiyar ta sai tace " _lafiyata 'kalau Mummy, amma yanzu kullun bana iya bacci mai kyau da dare kuma sai in tajin yunwa sosai kuma fah bana son hakan ni Mummy_ " Murmushi Mummy tayi dan tashin farko ta fahimci meke damun Teemahn amma ganin bata sani ba itan sai Mummy ma ta bita a hakan tace da ita "bakomai ai is normal watarana bazatayi hakan ba" Kafin tayi maganar Hannah tazo ta 'kwace wayar ta kai kunnan sannan tace da Mummy " _Allah Mummy Teemah chop-chop ta zama sai kinga yanda tazama, har ta nin kani sau biyu_ " Hannah kam harda kari tayi dan bawani jikin kirki har na azo agani Teemah tayi ba kawai dai ta d'an canza ne kuma bai 6ata ba sai kyau da wani fresh ta sake yi abinta. Teemah na daga inda take tace " _Allah Mummy 'karyan Hannah ne dama ita ai tsililiyace kawai tana kishi dan taga na fita kyau ne_ " " _Hmmm, Toh Allah dai yasa lafiya ne_ " Fa'din Mummy kenan tana murmushi. Da haka suka gama wayar kowa na farin ciki haka kawai suka tsinci kawunansu cikin annashuwa da farin ciki mara misaltuwa. Bayan sun gama da wayar ne Hannah ta bawa Teemah labarin zuwan Bilal, akan yace zai dawo ayi maganar auren su sai ya koma. Teemah najin haka tace " _kice nima dai na kusa in huta da rainon ki kenan_ " Hannah da wuri ta tare ta da fa'din " _kut amma kin gama dani wallah, ni dake waye me rainon wani fisabillahi, duk_ _wahalan da kike bani ki hana ni baccin dare ki hanani sakewa a gado shine zaki ce wani kina raino na, ni Allah ma yasa_ _Yayah ya tafi dake can garin na huta da rigimar ki_ _wallahi_ " Musu suka hau yi a tsakanin su kowa na depending kansa kamar wasu 'kananun yara har sai da Ummah tazo sannan sukayi shiru. Hannah da Teemah ne sukayi girki da dare, Ummah tayi-tayi su bari ko dan saboda Teemah ma amma suka 'ki, bayan sun gama suka sake yin wanka sukayi sallar maghrib da isha'i sannan suka ci abinci. 'Daki suka koma, Teemah kam ganin har 8:00 ta gota bai dawo ba sai tayi shirin bacci gashi dama duk jikinta ciwo yakei mata kamar wacce akaiwa dukan tsiya haka take ji, rigar bacci mai kyau ta 'dauka a cikin kayan Hannah tasa ka, riga da wando wanda bai gama kaiwa 'kasan 'kafarta ba, dan ita tafi son nighty mai wando dan tafi sakewa dashi. Hannah na mata mitan an gaya mata anan zata kwana ne da har take wani saka nighty? Da " _ehh mana baki ga dare yayi sosai bane_ " ta amsa mata tana mai cigaba da shirinta. " _Hmm Allah yasa Yayah ya barki toh_ " kawai Hannah tace daga nan bata 'kara magana ba. Teemah na kwanciya bacci yayi gaba da ita Hannah ce ma ta 'dan ja lokaci saboda tana duba wani handbook 'din ta. Abbas be zo gidan ba sai kusan 9:30pm Ummah sai tace ya dubo su itama taji shiru tun 'dazu tana kyautata zaton sun riga sunyi bacci, tace dashi amma idan sunyi baccin ya 'kyale su yayi tafiyar sa. Da " _uhumm_ " ya amsa mata bawai dan zai iya barin nata ba. Ahankali ya tura 'kofar sai ya fara cin karo da fuskarta ta da yake basu offing switch ba wuta a kunne suka kwanta, mamaki yayi ganin yadda tayi 'da'd'daya akan gado kamar sunyi da ita akan zata kwana anan 'din. 'Karasawa yayi 6angaren da take ya tsaya, Hannah na daga can 'dayan gefen bakin gadon ta juyawa Teemah baya. Hakan yasa shi zama daga wajen kanta ganin Hannah bazata ganshi ba, a hankali yafara shafa gashin kanta har zuwa wuyan ta, Teemah kam har da gyara kwanciya ta 'kara gyara wa kanta matsuguni duk zaton ta mafarki takeyi, sai da ta ji abin na neman yin yawa ne sannan tafarka daga baccin, da idanuwan ta tafara motsi daga nan sai ta tashi a firgice ta zauna, ganin 'dakin da take ga kuma mutun azaune sai taji tsoro ya kamata, har ma hakan sai ya sata bu'dan baki da niyyan k'wala ihu sai yayi saurin toshe mata bakin da hannun sa 'daya sannan ya tsare ta da idanu. Hawaye ne yafara gangaro mata a hankali idanuwan ta cikin nasa. Tsawon mintina biyu suna a haka sannan sai ya bu'di baki in a whisper yace da ita " _let's go to our house_ " Yana gama fa'din haka ya sakin mara bakin, sannan ya matsa ya bata daman tashi. Teemah tana jin bakin ta ya bu'du sai tace a shi " _dare fah yayi sosai Yayah ni dan Allah ka barni anan zan kwana_ " " _Ni kuma ban amince ba, in kuma kince ba haka ba to sai dai ki matsa min mu kwana_ _anan 'din dukan mu_ " Ido Teemah ta ware a kansa sannan tace " _gidan Ummah ne fah Yayah_ " Sai yace " _Yes nasani, kinga tunda bazaki bini ba sai kawai ki matsa min in kwanta a gefenki in yaso da safe sai mu wuce idan Allah ya tashe mu_ " Juyawa tayi ta kallo 6angaren da Hannah ke kwance sai kawai ta mi'ke tsaye tana hawayen ba'kin ciki tana 'kun'kuni. Shima da murmushin ya bita dama yasan intji haka zata tashi da kanta ma ba sai ya sake 6ata bakin sa ba balle ro'kon ta. Wurin kaya ta nufa da niyyar sauyawa, sai ya wuce gaban ta ya rigata isa wurin kayan, hijab kawai ya duba babba ya mi'ka mata, sai da yi ta6e baki kafin ta kar6a ta sanya, har 'kasa ya sau'ka mata kuwa taje ta dau wayarta tana huhhura hanci suka bar 'dakin, ta so ta tashi Hannah suyi sallama amma ya hanata yasata agaba suka fito. Zaune a parlour suka tarar da Ummah, tana ganin Teemah ta fahimci ranta bai so tafiyan ba, sai ta 'daga kai ta kallo Abbas ta harare sa, kai ya sosa ya mayar mata da martanin murmushi. Yana murmushin yace " _Ummah mun wuce sai da safe_ " Kai ta dan juya kana tace " _yanzu sai da ka hana yarinyar nan bacci ko Muhammad_ ? Da sauri Abbas yace " _babu fah wani baccin da tayi Ummah ido biyu na same ta_ " Ya 'karasa maganar da kallo Teemah dan kar ta 'karyata shi sai ma yaga kanta a 'kasa tana wasa da yatsun ta. Ummah duk ta kula da shi amma ta basar sai kawai tace " _Hmm, kai dai kasani_ " Kan Teemah ta mai da kallon ta tace " _Fateemah wannan mijin naki sai ha'kuri kinji, Allah ya 'kara miki_ _ha'kurin zama dashi_ " Kai Teemah ta 'daga sama tana mai 'ka'kalo murmushi a fuskar ta a hankali ta amsa da Ameeen ta yadda babu wanda zaiji a cikin su. Ummah na shirin sake yin magana sai Abbas yayi gaggawan taran ta da fa'din " _Ummah zaki sa yarinyar nan ta raina ni Allah_ " Da fillanci yayi maganar wanda hakan yasa Teeemah bata fahimci me yace ba saboda ita ba iyawa tayi ba, shima 'din ba sosai ya iya ba amma dai zai iya defending kansa ako'ina when it comes to his tribe. Ummah da 'kuwa tayi masa tare da fa'din " _kayi min shiru ai gara in fa'di_ _gaskiya_ " " _Y'ata Allah ya bamu alkhairi ko_ ? Cikin sanyin murya Teemah tace " _toh Ummah sai da safe_ " Fita sukayi Abbas na gaba Teemah biye a bayan sa yayin da Ummah ta rakasu da idanu har suka fice. Sai da ta daina hangosu sannan ta jijjiga kanta tare da fa'din Allah ka ha'de min kansu ka dai-dai ta tsakanin su ka sanya fahimta sosai a tsakanin su. Teemah bata kulashi ba tayi shiru har suka isa gida, duk kuwa da cewa Abbas na driven amma hannun sa na cikin nata ya ri'ke yana murzawa amma 'kala ba tace dashi ba. Ranta a 6ace yake dashi amma ita kanta bata san dalilin daya sa ta kasa janye hannun ba har suka isa gida. 'Dakin sa suka wuce direct wanda tana shiga ta fincike hijabin ta ninke sa ta sama masa matsuguni sannan ta hau gado ta kwanta. Abbas da idanu yabita kawai ganin yanda kayan baccin suka bi jikinta suka kwanta da yake mai santsi ne kuma kalar haske sai ya bayyana surar ta gaba 'daya. Abbas bai tashi sanin fushi take da shi ba har sai daya gama duk wasu al'adun sa daya saba yi na bacci ya hawo gadon, hannu ya kai ya janyo ta da niyyar rungume ta suyi bacci sai yaga ta janye jikin ta da sauri. Da kallon mamaki ya bita, dan bai fahimci manufar ta ba sai ya sake kaiwa hannu jikin ta, matsawa tayi da sauri, take sai yace " _miye hakan kuma wai? ke kullum rigimar ki bata 'karewa ko?_ _Miye aka miki_ ? Shiru tayi masa bata ce uffan ba, bama ta da niyyan amsa shi, Abbas kam ranshi yaji ya fara 6aci dan haka sai ya daka mata tsawa yace " _ba dake nake magana bane_ ? Kuka ta sanya tana daga inda take kwancen kamar wanda dukan ta yayi harda shashshe'ka. Sai yaji ba da'di kuma, calming kansa yayi sannan ya 'dan sake matsowa kusa da ita, bai ta6a jikinta ba sai yace " _is owk shikenan, tashi ki gaya min me ya same ki_ ? 'Kin tashi tayi ta cigaba da rairo kukan ta, shima kallon bayan ta ya tsaya yi tare da sauraron kukan nata, daya ga bazata sarara ba sai yace " _kinsan ban son kukan nan ko?_ _Mute it right now nd tell me ur problem_ " Tashi tayi ta zauna tana murza idanu tace " _ba kai bane_ " da shagw6a sosai tayi maganar kamar 'yar yarinya 'karama. Shima fuskar sa ba yabo ba fallasa yace da ita " _me nayi toh fa'da min inji_ " " _Ba ka'ki barina in kwana a gida ba kuma kazo ka yiwa Ummah gulmata da yare ba_ " Dariya sosai ta bashi dan sosai yaga 'danyar yarinyar ta ta wannan 6angaren, musamman daya kasance har yanzu bata bar murza idanu ba. Murmushi yayi mai sauti yace " _who told u that gulmar ki nayi? Naga kema yaren ki ne miyesa baki ji abinda nace_ _ba...._ Hannu ta cire a idanun ta turo baki tare da 'kan'kance idanu tace " _Ai ni ban iya bane shiyasa_ " Dariyar da bai shirya yi bane ta 'kwace masa, Teemah kam sai ta tsaya tana kallon shi amma bata daina tsiyayar da hawaye ba, sosai ya canja mata a yanayin da yake dariyar sai taga ya canja mata zuwa wani abu daban tamkar kar ya 'kara rufe ha'koran sa. Sai daya gama dariyar kafin yace " _shine duk wannan masifar dan ke ba kya ji_ ? Sabon hawaye ne ya sakko mata. Abbas sai ya daure ya fara lallashin ta ganin kukan nata na 'karuwa fiye dana 'dazu. Kumatun ta ya kamo da duka da duka hannun sa biyu ya 'dan jijjiga mata kai, idanun su cikin na juna yace " _my crying baby shikenan daina kukan hakan nan ko? I'm here for u in kina son kiji gulmar_ _da nayi mata ai sai in sanar dake bawani abu_, _Kina son kiji ko_ ?" Sai ta 'daga masa kai sama. " _owk kawo kunnan ki kiji_ " Da shirmen ta sai ta mi'ka masa kunnan nata shima kansa ya matsar kusa da kunnan, a hankali yace " _kawai fa cewa nayi matata is so hot bazan iya barinta acan ta kwana batare danaji 'dimin jikinta ba, haka fah kawai nace shine_ _kuma kike min bori_ " Baki ta 6are ta sanya kuka, tana hahhar ba 'kafafu. Abbas sai yace " _toh 'karya nayi ne? Ai gaskiya na 'fada_ ? Teemah kuwa cikin rigima tace " _Ni wallahi ban yadda ba shine zaka gayawa Ummah haka salon tagane kana ta6ani_ , _tagane abinda kake min kullum ajikina_ " " _To idan ta gane 'din kuma fa, haramun kika yi ne?_ Ya yi maganar kamar dagaske abinda ya sanar wa Ummahn kenan. Teemah kam cikin kuka sai tace " _ai ni kunya nakeji....._ Abbas bazai iya da rigimar tata ba dan haka sai ya ha'de bakin su wuri guda, wanda yasa dolen ta tayi shiru da maganar, bai bar ta ba har sai daya tabbatar da nutsuwar ta kafin ya 'kyaleta dan da farko taso tayi kokuwan 'kwace kanta amma dataga bazata iya ba sai ta ha'kura daga 'karshe kuma sa'kon ya shige ta sosai, dan yana sake mata bakin ta fa'da kan 'kirjinsa tayi luf da lumsassun idanu, sai yayi murmushi a kunnan ta yara'da mata " _I'm starving fah, me zan samu?_ " Yun'kuri tayi tabar kan 'kirjin nasa sai tayi 'kasa da idanun ta tana kif-kif dasu kamar mara gaskiya ganin hakan sai yace " _yanzun ma zaki ce laifina ne ko? ai kingani da kanki kike son shiga jikina_ " Baya ta juya masa da sauri ta sau'kar da 'kafafun ta 'kasa daga 6angaren da take hannayen ta kuwa dafe da gadon gefe da gefe. Abbas matsowa yayi jikinta ta bayan nata, unexpected kawai tajishi ajikin ta ya kwantar da kansa akan kafa'dun ta, tare da sar'ko hannayen sa ta 'kar'kashin nata hannun zuwa cikinta. Yawo da hannun nasa yafara acikin ta yace " _an gaya miki anayin bacci ba tare da an bawa miji abinci bane_ ?" Muryar ta na rawa tace " Yayah...ai bana gida.... ne shiyasa, kuma ai dakaje..... gidan Ummah bansan cewa kanajin yunwa bane shiyasa..... ban baka abinci ba" Shiru yayi ya maida idanunsa kawai ya lumshe, ahankali ya cigaba da yawo da hannun sa har yakai ga boobs 'dinta, Teemah lumshe ido tayi itama jin yanda yake shafawa a hankali har zuwa saman yana mata kamar tafiyar tsutsa har bata so ya bari, dama zogi suke mata da batasan dalili ba. Squeezing 'dinsu dayayi ne ya sata sakin 'dan 'kara ta kai hannun ta kan nasa ta 'dan ri'ke. Daya sakeyi kuwa sai hawaye tar ya gangaro mata sai ta 'kan'kame hannun sa har da fa'din " _washh_ " Jin sau'kan abu kamar ruwa a hannun sa yasa ya bu'de idanu da sauri sai yaga da gudu hawayen ke sau'ka banda ma ajiyan numfashi datake yi akai-akai. " _Me yafaru kuma_ ? Ya tambaye ta cikin nutsuwa da kulawa. Sai tace " _zafi nakeji_ " " _Zafi kuma?miye dalili toh_ ? ya sake tambayarta. Sai tace " _nima fah bansani ba, haka yake min wani lokaci, yau 'din ma tun d'azu yake min zafin har jikina_ _gaba d'aya_ " Abbas najin haka sai ya zare hannun sa daga cikin rigar tan tare da 'dan matsawa baya ka'dan, hakan sai yabashi daman kwanto da ita kan 'kafar sa tana kallon sama. " _Bari in gani_ " Yace a hankali Teemah bata hana shi ba tanaji ya 'dage rigar ta har zuwa sama ya cire ta gaba 'daya ma, rintse ido tayi da 'karfi jin ya rabata da rigar ya barta da dogon wandon ka'dai. Yana kallo sai yaga sunyi 'dim-'dim suna shai'ki, hannun sa yakai yata6a a hankali sai yaga bata motsa ba, cigaba yayi da shafawa yana murza bakin ahankali yana kallon idanun ta, Teemah kam sosai take jin da'din hakan shiyasa tayi luf sai ma ta cusa kanta ta 6oye agefen 'kafarsa. Shima daya fahimci tana jin da'din hakan sai ya cigaba da lelaya mata a hankali bai matsa da karfi ba sai yaga har ta fara sau'kar da ajiyan zuciya sannan ya bar ta ya gyara mata kwanciya ganin tayi bacci ya lullu6a mata abin rufa iya wuyanta. Kitchen yaje ya ha'da coffee dan sosai yake jin yunwa yanzun rabon sa da abinci tun safe. Koda ya gama da coffee 'din ma zama yayi tukunna yana tunanin dalilin ciwon 'kirjin nata amma yarasa, sai daga baya ya tuno zancen period 'din da tamasa amma har yanzu be ga tayi fashin sallah ba. Da asuba bayan sunyi sallah ne ya tambaye ta batun period 'din. Tana jin haka sai ta ta6e baki aranta tace " _zai fara tambayar rashin kunyar tashi ai, bayan gashi ma yasa na kwana_ _a jikinsa ba riga_ " sai ta murgu'da masa baki dayake ba fuskantar ta yake ba shiyasa bai gani ba. " _Baki ji abinda nace bane?_ " " Naa.......ji" tabashi amsa da jan maganar. " _Uhumm...._ ?" kawai ya sake cewa da ita, tasan manufar hakan, dan haka sai tace masa " _Nima fa bansan me ya hanashi zuwa ba, tun last month ma banyi ba_ " " _Dama yana miki hakan ne_ ?" Shiru tayi tana tunani, can sai ta ce " _ehh ya ta6a yin 3month bai zo ba, amma a lokacin dana sanar da Mummy sai tace min is normal daman yana_ _yin irin hakan cycle ne kawai dakan sa ma_ _zai dawo_ " Sai yace " _Kuma haka yake saki ciwon jiki alokacin_ ?" Shiru tayi dan ita har ga Allah ta manta. Ganin tayi shiru sai yace " _idan bazaki fa'da min ba da kaina zan tambayi Mummy ai nasan_ _ita zata fa'da min_ " Azabure ta mi'ke zaune tace dashi " _Mummy kuma dan Allah Yayah me zaka ce da ita kuma?_ " " _Sai ince mata breast 'din ki kullum ciwo yake miki sai ni kike sawa aikin 'kai'kaya miki kullum bana hutawa in tasan_ _dalilin sai ta fa'da min kinga shikenan ta hutar da ke_ " atsare yayi maganar kamar he means it 'din nan. Sai tace " _ni ai naga toh ba kullum yake min ciwon ba_ " Cewa yayi " _toh shikenan ai sai in ce mata jiya ne ka'dai_ " Zaro oily eyes 'din ta tayi tace " _wai Yayah wa Mummyn zaka fa'di haka_ ? Sai yace " _Ehh mana tunda kin 'ki gaya min ba, kuma ai kema ai naga kina gaya mata idan ya dameki toh miye_ _laifi dan na fa'da_ " Tace " _Toh ai ni ce_ " Shima cewa yayi " _ai nima ni ne_ " Tura 'kafa tayi tare da mik'ewa zaune ta fuskance shi sannan tace " _Ni fa ba'ki nayi ba Yayah Allah na manta ne shiyasa_ " Shima 'din sai yace " _Mummy zata tuna miki kar ki damu bari in 'kira ta_ " yayi maganar da 'dauko wayar sa kamar dagaske 'kiran zaiyi. Sai tayi saurin ri'ko hannun sa mai wayar tace " _please Yayah don't call her, Allah inajin kunyar ta fa, in kace mata kana ta6a min jikina ni kam mutuwa zanyi_ " Baiyi mamakin kunyan datace tanaji ba, dan shi kansa ya san cewa abin kunya ne sai yace " _kin tabbatar mantawan kika yi ba?_ " Da sauri ta 'daga masa kai alamar " _ehh_ " Tana tunani aranta cewa tsab zai iya aikatawa tunda har ya iya sanar da Ummah cewa bazai iya barci ba sai da ita toh ko Mummyn ma aganin ta ba kunyar ta zaiji ba, nima ai baya kunyata tace aranta, shiyasa take ganin cewa duk abinda yace yayi 'din dama wanda yake shirin yi 'din duk zai iya aikatawa. Abbas kam cewa yayi " _shikenan toh na yadda kwanta kiyi baccinki_ " Yana maganar yana 'dan shafa mata face da lallausan tafin hannunsa. Yaso ya tambayi Anty nurse dan yaji ehh dagaske ne ana hakan ko kuwa wani ciwo ne daban, amma daya tuno cewa Mummy tace da ita ba matsala bane sai shima ya basar da zancen ya cigaba da harkokin sa. _Comment_ _Vote and Share_ *Salmerh ce*😍 [10/13, 1:58 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* Dedicated to all Naija's PEOPLE. *HAPPY INDEPENDENCE NIGERIA* (59th anniversary)🇳🇬. My nation my proud....Nigeria d promise land, the great nation..👍 *Bismillahir rahmanir raheem* _Time passes, memories fade, feelings change, people leave but hearts never forget_ . 🅿 *88* Bayan sallar azahar yace da ita ta shirya su fita yawo, Teemah kam take tafara murna da farin ciki ta wuce 'dakin ta, cikin 'kan'kanin lokaci tayi shirin ta cikin wata Arab gown baki mai 'dan fa'di musamman daga 'kasa dan daga saman ya dan kamata, sosai rigar ta kar6i jikin ta. Light make-up kawai tayi inda ta shafa powder kawai sai ta sanya wa idanun ta kwalli sannan ta shafa lipstick ja. Veil 'in ta ta 'dauko tayi rolling da shi ta sanya flat shoe a 'kafar ta tare da 'daukan wani 'dan 'karamin side bag mai kyau da tsada, har zata fita sai kuma ta koma ta 'dan fesa perfumes kala biyu sama-sama kasancewar ta mai masifar son 'kamshi. Cikin natsuwa ta isa 'dakin sa ta tura tare da yin sallama ahankali. Abbas ma a hankalin ya amsa tare da yi mata kallo 'daya sannan ya juya yaci gaba da abinda yake yi. Teemah kam baki ta ta6e aranta tace " _mutun kullum sai fama da longslip shirt kamar abin ibada_ " Bakin gado ta isa da niyyan zama amma kafin ta zauna sai taji yace da ita " _zo nan Zahra"_ Fasa zaman tayi sai ta cire jakar tan ta ajiye abakin gadon sannan ta 'karasa inda yake tsayen, tana 'karasa wa ya juyo gareta tare da 'dauke hannun sa daga kan 'kirjin nasa yace " _help me plz"_ Bata sha wahala wurin gane abinda yake nufi ba ganin gaban rigar sa abu'de, abin mamaki ma duk kokuwar dayake ta faman yi 'din guda biyu kawai ya sanya. Badan farin singlet 'din dake jikinsa ba da dukkan 'kirjinsa afili zata gani dayake daga 'kasa yafara 6allewa sai itama takama daga wurin tacigaba har zuwa sama. Yana son amfani da irin kayan amma har yanzu yakasa sabawa da 6alla bottles 'din riga cikin sauri. Abbas kam shiru yayi yana bin fuskar ta tare da sha'kan dad'd'an 'kamshin da jikin ta ke fitarwa. Within a minute Teemah har ta gama 6alle masa bottles 'din tana 'ko'karin sau'ke hannun ta daga 'kirjinsa kawai sai ya ri'ko hannun yana kallan cikin idanun ta da murmushi yace " _kinyi kyau fa amma ka'dan_ " Murmushin tayi itama dan tasan tsokanan ta kawai yake yayi kuwa bata son 6ata lokaci yanzun ta 'kagu tagan ta a mall shine babban burin ta ayanzun shiyasa bata ja maganar ba. Dan haka itama sai tace dashi " _amma ai na fika kyau duk da haka tunda nayi make-up kuma kaga kai bakayi ba_ " " _Really_ " Ya fa'di tare da 'dage gira sama yana murmushi yace " _let see_ " Tare da matso da kansa kusa da nata tana 'ko'karin jan baya sai yayi saurin 'dora bakin sa saman nata yafara bata wani passionate kiss mai shiga jiki. Teemah tun tana 'ko'karin 'kwace kanta har ta zo ta ha'kura kasancewar gwiwoyin ta da suka yi mata nauyi, daga 'karshe kuma sai tafara jin zafi sosai abakin nata, hawaye tafara sau'kar wa sirara na azaba wanda ganin hakan yasa Abbas sakin mata bakin sai ta koma ta rungume shi tana mai ci gaba da tsiyayar da hawayen a hankali. " _Mufasa fitan ne_ ? Ya tambaye ta dagangan tare da kallon bakin ta yana murmushi ganin babu jan lipstick 'din gaba 'daya. Sai tayi saurin jijjiga masa kanta tare da barin jikinsa ta koma bakin gadon ta zauna tana mai cigaba da maida numfashi. Juyawa yayi yana kallon mirror dan gyara dressing 'din sa sannan yace da ita " _kinsa yayi yawa ne shiyasa na cire miki, i feel like perfumes 'din ma incire shi gaba 'daya......who told u ki rin'ka irin wannan_ _abin while going out_ ? Shiru tayi bata ce uffan ba sai yanzun tagane dalilin abinda yayi mata, yanzu ne ta tuno da lipstick 'din ta ashe abinda yayi targetting kenan dan mugunta yarabata da kwalliyar ta, shi yayi kwalliyar sa shine ita zai hanata, tana gani ya dinga fesa turare kusan kala hu'du ajikinsa amma shine nata ya zama laifi? Be 'kara kulata ba sai daya gama komai ya 'dauki key kafin yayi gaba yace " _muje ko_ " Tashi tayi tabi bayansa tare da bankawa bayan nasa harara ji take badan ita ke son zuwa yawon ba da babu abinda zai sata binsa. Bin bayansa tayi suka fita daga parlourn, da kansa yaja motar ya haura titi. Teemah ranar da'di da farin cikine sosai ya cika zuciyarta, daga yawan parks 'din suka wuce shopping mall. Inda anan ta ring baza rigima son ranta, abubuwa kala- kala ta ringa 'diba inda da dama kyan package 'din ne kawai ke sa ta 'dauka koda bata san ya yake ba wasun kuwa 'kamshin su idan ta tuna sai taji ai shima tanaso, da yawan su ma ba sanin su tayi ba, in Abbas yayi mata magana kuwa sai ta fara bubbuga 'kafafu tana rigima tace " _ai inaso ne shiyasa_ " dole sai ya 'kyaleta ta 'dibi duk abinda yayi mata, duk dangin kayan cinye-cinye ya takwasa. Shi kam Abbas sai ya dawo binta da ido kawai ya daina kulata bawai dan zai bar ta taci wasu abubuwan ba sai dai dan kar ta tara masa mutane aka, dan kuwa yasan lokacin period 'din ta idan yayi tana shan wahala sosai aganin sa ita mantawa take da hakan. Idan ta hango wani abin asama sai tace Yayah wancan, dan tana son ya cira mata, shikuwa sai ya harare ta kafin yaciro 'din, Teemah kuwa sai ta tura baki tana 'kun'kuni. Duk dramar da sukeyi 'din nan kuwa kaf a idon wata matashiyar budurwa ce da tun 'dazu take bibiyar su batare da sun sani ba, tun ganin da tayi musu farkon shigowan su taji ya birgeta, da ta bibiye su ne da wayo yanda bazasu gane ba sai ta 'dan karanci kalan shagwa6anTeemah irin na yara 'yan autan nan ne, bata tsawaita tunani ba ta yanke cewa lil sis 'dinsa ce ita, dan haka batayi 'kasa a gwiba ta cigaba da bibiyan su ta ma bar abinda ya kawota. Sai da suka canja hanya zuwa wajen perfumes ne sannan ta zaga itama tasha gaban su, dai-dai kwana sai ta fito suka ci karo da shi, yana amsa waya ne alokacin shiyasa sam bai lura da ita ba, take kuwa wayar tasa tayi 'da'd'daya a'kasa. Baki ta dafe dan sam bata zaci faruwar hakan ba, Bin wayar yayi da kallo kafin ya 'dago ya kalle ta take sai tayi 'kasa cikin hanzari tafara tattaro masa wayar tasa. Abbas kam da kallo yabita har ta 'dauko wayar ta 'dago sannan tace " _afuwan pls yalla6ai Allah ban lura da ku bane shiyasa_ " Kar6an wayar yayi yace mata " _ba komai karta damu_ " Batayi mamakin jin yace bakomai ba dan kana ganinsa kasan yafi 'karfin nuna damuwa akan faruwar irin hakan sai dai dan wani abu daban, amma duk da haka sai tace " _Yalla6ai ko zamu duba maka wata wayar anan_ ? "No no....never mind dear" cigaba yayi da tafiyar sa Teemah ma sai ta bishi abaya a hankali. 'Karasa shopping 'din sukayi Abbas yabiya bill 'din sannan suka fito. Boot ya je ya bu'de akasa saka kayan aciki, yana zagowa domin shiga motar sai ta sake bayyana agaban su tana zuba murmushi hannunta ri'ke da wata jaka mai kyau tace " _zaku wuce kenan_ ?" " _uhmmm_ " kawai yace da ita a ta'kaice juyawa tayi 6angaren da Teemah take ta bata jakar hannun nata tace da ita " gashi ko baby sis naki ne" Saroro Teemah ta tsaya kallon ta sai ta kalli Abbas ma, da ido yayi mata alaman ta kar6a kawai su wuce sai ta kar6a tare da yin godiya. Wani takalmi ne ta siya mata new design brown colour mai kyau. Rungume hannun tayi saman 'kirjinta ta kalle shi da kyau sannan tace " _gaskiya na yaba da karamcin ka yalla6ai duba da irin 6arnar danayi maka amma ka yafeni cikin sau'ki, harga Allah ka matu'kar_ _birgeni dan ba kowa zai iya yafe irin 6arnar ba iphone8 a wannan zamanin gaskiya nagode sosai_ " Kai ya 'dan juya harda 'dan lumshe ido, baya so yayi ta repeating magana 'daya amma ita kuma ta dameshi, bai san mai take so ta'kara ji daga bakinsa bayan wanda ya fa'da 'dazun ba. Sai yace " _i told u karki damu ko, 'kaddara ce ai so ba matsala komai ya wuce_ " yayi maganar tare da bu'de gaban motar yasa 'kafan sa 'daya. " _i need ur contact plz, saboda in 'kara gode maka kuma muna gaisawa in babu wata matsala_ " Yana jin haka sai ya 'daga kai ya kallo Teemah dake tsaye saroro hannun ta ri'ke da jakar da ta bata tana kuma kallon ta, murmushin da beyi niyyan yi bane ta kubce masa ganin irin kallon da Teemah ke mata , hannu yasa ya dauko card 'dinsa ya bata, da farko beyi niyyan bata ba amma saboda tsokana sai ya 'dauko ya mi'ka mata yana wani killer smile. Washe baki tayi saboda farin ciki a hankali tace " _Thank u_ " Sai a sannan kuma tasa hannu ta kamo Teemah tace " _Baby sis ya kikayi shiru ne? in kinje gida ki gaida min mummy_ _kinji_ " Bata jira jin amsar tata ba sai ta 'dago ta kalleshi tace " _lil sis 'dinka is so beatiful yalla6ai, i really like her_ " Murmushin yayi shima kawai tare da yiwa motar key sannan yace da Teemah " _shiga mu wuce ko?_ Ahankali Teemah ta zagaya ta shiga 'dayan 6angaren, saida Teemah ta shiga kafin yarinyar ta mi'ko masa hannu tace " _i'm Haleesah Ibraheem Yaqoob, but people used to call me Leesah_ " Hannun ya mi'ka mata shima sannan ya jinjina kansa, tare da fa'din " _nice name_ " Itama " _Thank u_ " tace da shi tana murmushin jin da'di. Teemah kam hannun nasu ta kafawa idanu har suka raba hannun, wani 'daci ta ringa ji yana taso mata ga ba'kin ciki da haushin su duk ka biyu daya tsarga mata lokaci guda. Shi kansa Abbas sai daya ja motar sannan kuma yafara jin bai yi dai-dai ba daya bata hannun sa back saboda ko a musulunci ma haramun ne, amma be san wani shai'dan 'din bane yasa shi biyeta, istigfari yafara acikin ransa har suka iso gida. Sam bayi tunanin abin zai ri'ke zuciyar Teemah ba. Teemah kam bata kulashi ba har suka isa gida, tana sauka tayi jifa da jakan hannun ta wanda yarinyar ta bata ta shige ciki abin ta. Shine da kansa ya kwaso dukkan bags na shopping 'din ya shigar mata ciki dan bai san matsalar ta ba. Bai ta6a zaton batun yarinyar ne zai sata yin hakan ba dan shi bai ma sata aka ba. Da yake dab maghrib suka dawo sai bai bi ta kanta ba kawai yayi alwala ya wuce masallaci, sai da yayi isha'i kafin ya dawo gidan anan yatarar da ita zaune a parlour tayi tagumi, yana shirin zuwa ya ji dalilin tagumin sai yajiyo 'karan 'dayan wayar sa a 'daki, wucewa yayi kawai ya 'dauki wayar sai yaga new no. dayake yasan hakan na iya faruwa akowani lokaci saboda yanayin aikinsa shi yasa bai tsaya wani tunani ba ya 'daga wayar. Muryar mace yaji tana fa'din " _yalla6ai Leesah ce, da fatan kun isa lafiya yasu Mummy da baby_ ?" Ajiyan numfashi ya sau'ke a hankali sannan ya furta " _Kowa lafiya_ " yace da ita a takaice. Sai ta sake yi masa godiya once again, ta kuma requesting yardar sa akan su rin'ka gaisawa time to time yace " _ba matsala_ " Daga nan sukayi sallama tare da sa'kon gaida mata baby sis yace " _owk zataji_ " daga nan ya fito da wayar a hannun sa yadawo kusa da ita ya zauna. Remote ya 'dauka yana canza channel yace da ita " _Leesah na gaida ki_ " Kamar jira takeyi kawai sai ta sanya masa kuka da ita kanta bazata fa'di dalilin yinsa ba abu 'daya ne ya tsaye mata rai shine yanda taga sun sha hannu da yarinyar abin ya kasa barin ranta, toh tayaya ma zata iya manta sunan ta, bayan k'unci da takaicin data haddasa mata azuciya shine harda k'iransa. Abbas kam jin ta sanya kuka yasa shi juyowa da mamaki ya kalle ta yace " _me kuma akayi miki_ ? Ya tambaye ta cike da mamaki, Teemah kam bata ce da shi uffan ba sai taci gaba da rera kukan ta, koda yayi 'ko'karin zuwa kusa da ita sai ta matsa da sauri tana fa'din "ni _bana amsawa karta sake cewa tana gaishe ni, kuma sai na fa'da ka da Ummh tunda kam kowa ma ta6a jikin su kake yi har wanda baka sani_ _ba ma shaking hands kakeyi dasu_ ? Sai yanzu ya gano asalin manufar fushin tan tun na 'dazun da bai ma kawo ha'kan aransa ba duk da yafa saurin fu wurinta amma bai zaci har haka zata ja abin ba. Murmushi ne yaji ya k'wace masa aransa yace " _jealousy_ " Murmushin da yayin sai ya 'kara tunzirata ta 'kara sautin kukan ta akan nada. Abbas ma sai ya matso kusa da ita ya fara lallashin ta amma sam ta'ki sauraron sa sai sake cewa takeyi ita sai ta ha'da shi da Ummah. Abbas kam sai yace " _toh shikenan na yadda kije ki fa'da mata amma fah karki manta ki fa'da harda naki duk abinda nake yi miki ai basu ka'dai_ _nake ta6awa ba har da ke_ " Tana jin haka ta kwanto jikinsa ta ri'ke hannun rigar sa da kyau tamkar yace mata zai gudu ne, abin tausayi taci gaba da rero kukan ta ajikinsa, " _cikin kukan take fa'din aini matarka ce kuma ita wancen_ _din ai ban san taba_ " Kafin kace kwabo har ta ji'ka masa gefen rigar jagab da ruwan hawaye. A hankali ya kai hannayen sa ya rungumo ta da kyau ajikinsa yana fa'din " _sorry.....i'm so sorry kinji bazan sake ba tunda bakyaso kinji_ " Sosai ya jinjina wa kishin nata, sai da yaga tafara rage kukan sannan yaci gaba da lallashin nata a hankali har ta nutsu amma bata daina ajiyan zuciya ba. Shima sai ya sake rungumo ta sosai har bacci ya 'dauke ta. Ganin da yayi baccin ta yayi nisa ne yasa shi maida ta 'daki ya kwantar da ita. Washe gari da safe ma da ta tashi sai take jin babu da'di har aranta, amma sai ta daure tayi duk wasu abubuwan da ke gabanta ta gama, tare suka yi break fast kuma awurin ma babu wata maganar kirki data shiga tsakanin su har suka tashi awurin. Har zuwa yamma maganar tsakanin su bata yi yawa ba, dan tsakanin ta da Allah take jin haushin sa ita shikuwa sai ya rin'ka binta ayanda take so 'din bai takurata akan komai ba, dama abinci ne damuwan kuma da kanta ma tana ci basai yayi magana ba. Dare kuwa data zo bacci a'dakin sa sai ta juya masa baya ta tafi can 'karshen gadon ta du'kun'kune wuri guda. Yana kallon ta amma bai kulata ba sai daya ga ma abinda yakeyi gaba d'aya sannan ya hauro gadon ya janyota jikinsa. Kokuwan k'watan kanta tafara sai ya sar'keta da 'kafafunsa takasa motsa wa. Kansa ya cusa cikin gashin ta yana sha'kan 'kamshin da gashin keyi a hankali yace da ita " _fushi kike yi dani ko kuma kishi_ ? Sai tace " _ni kan ka barni Yayah banaso_ " Tace da nishi. " _Ni ai inaso, kuma kema k'arya kike yi kina so........kin manta ranar da kika wuni agidan Ummah da kika 'kirani harda cewa yaushe zan zo in dauke ki mu dawo gidan mu...ai nasan kewata kikeyi_ _alokacin kuma abinda kenan kikeso_ " ya 'karasa maganar tare da maida kansa 'kar'kashin wuyanta yana hura mata numfashin sa. Teemah kam kukan shagwa6a ta sanya inda cikin kukan tace " _ni bawani bahaka bane_ " "Naji toh bahakan bane, amma ai naji abinda kika ce da Hannah jiya da safe ko sai na maimaita kafin ki yarda?" Rintse idanu tayi da 'karfi tana tunano yanda sukayi da Hannah ajiyan, hakan ma yana bathroom ne lokacin da Hannahn ta 'kira take mata tsiyar wai ta tashi bata ganta ba ina ta shiga ? Sai tace inaga gida mana irin atsare 'din nan Hannah kuwa tace wani gidan kenan bayan banganki ba. " _Toh ina gida wurin mijina abinda kike so kiji kenan ina kam_ " Haka tace da Hannah a 'dan hasale. Hannah kuwa take sai ta wani kwashe da dariya tace " _ai dama na gaya miki Yayah ba zai barki ki kwana ba kika'ki yadda yanzu waye ma'karyaci tsakanin mu_ ?" Teemah sai tace " _ke de kika sani ni ai banga laifinsa ba 'kauna ce ke sa hakan kin sani kuma ma ai kinga ladan nan 'din yafi nacan so abarmu_ _mu huta please 'kiran naki yayi sassafe madam_ " Hannah tana dariya tace " _ehh aikuwa naga 'kauna anan ba 'karya_ " Iya abin da sukayi da Hannah kenan kuma wannan 'dinma duk batayi zaton yajita ba ashe yaji. Shiru tayi bata sake yi masa magana ba. Shikuwa daya ga haka sai ya sake fa'din " _Wato kina min bu'kula ne dan nayi kasuwa nasami wacce zata so ni ko?, ke bakiga bani da kowa mai sona bane bakya tausayina ko_ ? Hawayen ta ta goge dake sau'kowa ka'dan-ka'dan sannan ta 'dora hannunta kan nashi. Sai ya cigaba da fa'din " _Nima ai inaso asoni ko laifi ne dan na samu wacce zata soni_ ?" Kamar an matsi bakinta tace " _Ai kana dashi ba sai ita bace zata so ka "_ Shima sai yace " _Ni ai bansan kowa ba to in ke kin sani gaya min naji su waye"_ Teemah sai tace " _Ga su daddy ga Hannah da su Ummah, ga...ga... ga..Nii...ma_ " Ta 'karashe da in ina. Cewa yayi " _Oww dagaske kema kina sona? amma ai banta6a ji kin gaya min ba, wannan kuwa nasan kullum sai tace min I LUV U SWTHRT kuma_ _bazata na min rashin ji ba_ " Da sauri tace " _ai nima zan na fa'da maka kuma zan daina rashin jin ni dai bana so tana 'kiranka awaya_ " " _In_ _baki so to fara fa'da tun yanzu inji ko kin iya, ranar dai naji da ina miki wannan_ _abin nan kamar kince min Yayah i luv u amma bansan ko dagaske bane ko kuma kawai_ _kunnuwa na ne"_ Batayi tunanin wani abu daban yake nufi ba dan haka ranta wasai tace masa " _dakana yi min miye_ ? Bai yi magana sai kawai yakai hannu 'kasanta cikin panties d'in ta ya shafo da sauri takai hannu ta ri'ke hannunsan da kyau tare da 'kiran sunan shi cikin shagwa6a. Kiss yabata agefen wuyanta tare da fa'din " _let me Zahra...plz_ " Kai ta jijjiga masa tace " _tsoro nake ji ni Yayah_ " Yace mata " _Ba zafi ai_ " Yana maganar yana shafa mata mara. Batayi magana ba illah jijjiga kai. Sai shine ya sake fa'din " _Bari in gwada toh mu gani ko da zafin, idan yamiki zafi zan bari amma fah karki min rashin ji gwadawa kawai zanyi kinji_ " Da wautar ta sai ta 'dage kai sama alamar ta amince. Abbas be maida hannun ba sai yaci gaba da sunsunan wuyanta har zuwa kirjinta yana bata lafiyayyun kisses a hakan har ya rabata da kayan ta gaba 'daya. Sosai ya kashe mata jiki da salon wasannin sa masu wuyar bayyanawa yana yi yana tambayar ta akwai zafin? kai kawai take juyawa tako'ina bata magana tsabar yanda ta hau network. Gaba d'aya ta manta da damuwar kishin datake ciki illah masifaffaen so da kaunar mijinta dake yawo aduk ilahirin jikinta. Washe gari data tashi sai ta nemi fushin tarasa gaba ya. Yau kam bayan sun idar da sallar asubah bai barta tayi bacci ba yasa ta agaba sukayi karatun al-qur'ani mai girma sannan yayi musu addu'o'i. Sai da suka gama komai kafin ta sake komawa ta kwanta idanunta akan photon sa tana kallo tana murmushi tace " _Yayah wai dan Allah yaushe zamu sake komawa inje inga Nasreeen ne_ ?" " _babu rana_ " yace da ita kawai a takaice. Sai ta mi'ke zaune azabure tace " _haba Yayah dan Allah nifah ina son in ganta ne kawai_ " " _ba za dai aje 'din ba koma menene_ " Yace da ita yana shirin shiga bayi. Kun'kuni tayi 'kasa-'kasa tace " _mutun sai rowa dan ma ba 'yar ka bane_ " Sai ta murgu'da baki. Afili kuwa tace masa " _ai nima na ro'ki Allah ya bani nawa in huta da rowa_ "! Da 'dan 'dagun murya tayi maganar dan ya kusan shigewa ciki. Sai shima yasake fa'din " _Dayafi miki ai_ " yana fa'din haka ya shige bayi. Teemah sai ta dawo da kallon ta kan photon sa dake sama tana murmushi kuma, wani sabon so da 'kaunar sa ke ratsa dukkan ga6o6i, zuciya da gangan jikinta, tuno abinda yafaru tsakaninsu jiya sai tayi saurin rintse idanu ta juya baya, yanzu kam tana jin bazata iya bari wata banza ta zo ta 'kwace mata miji tana ji tana gani ba, ai in dai biyayyan ne itama ta iya shi babu abinda bata sani ba daya danganci zaman aure kawai dai halin Yayahn ne yake sata yi masa wasu abubuwan kuma wani lokaci sai taji bazata iya daina masa rashin jin ba, amma yanzu dole zata tashi tsaye domin ganin ta katange tsakanin mijinta da dukkan wasu mata musamman masu sharri marasa alkhairi atare dasu, ji takeyi bama zata iya rintse ido ta bu'de ta juri ganin Yayah da wata macen ba, ko ma badan su ba ko dan ta gyara rayuwar auren ta da kyau ta kuma nemi aljannar ta. Duk rayuwar datakeyi a har yanzun rayuwa ce kalan wadda tayi shi agidan Mahmud bata canja ba, bambancin kawai shi Mahmud baya tilasta ta yin abu, sannan komai tace tana so baya hanata yi baya 'kin sayo mata duk abinda tace tanaso baya mata tsawa ko ihu amma duk tasan hakan dama tun can asali ba halayyarsa bace bashi da fitina shi tun asali, hakan nema yasata tasaki jiki dashi sosai har sukeyin wasu abubuwa tare suyi wanka cin abinci kwana tare da komai ma, tun auren ta da Mahmud basu taba raba makwanci ba, sai dai shi bai ta6a kusantan ta ba har ya koma ga mahallicinsa wani lokaci ne dai ya kan 'dan romancing 'din ta amma ba sosai ba shima dan zata iya irga sau nawa hakan yafaru, iya abinda ke tsakaninsu da shi kenan now that Mahmud yarasu ta dawo mallakin wani daban kuwa wanin ma irin Yayan ta Muhammad Abbas so dole ne sai ta sauya dan ko wani tsuntsu da kalan kukan sa, tana son mijinta kuma tana son zama dashi tana son ta rayu dashi har 'karshen rayuwarta tana so ta haifi babyn ta masu kama dashi da kwarjininsa dayawa, musamman ma data fahimci cewa yana son ta shima so take sai ta 'daura aniyar canza salon ta tabar duk rashin kunya da rashin jin nan a gefe ta runguni mijinta ta dawwama faranta masa. Da irin wannan tunanin har wani baccin ya sake daukan ta kafin fitowar sa daga bayin. ***** Acikin kwanakin sosai natsuwa ya shige ta dan Abbas yayi proving kansa akan ba bu wani ala'ka dake tsakanin su da Leesah illah zumunci sai ya zamana ma har awaya yana ha'da su su gaisa, da kansa ya sanar da Leesan cewa Ai Teemahn matar shi ce ta sunnah ba wai sistern sa ka'dai ba. Leesah tayi matukar mamaki sosai dan koka'dan data gansu bata ji ajikinta cewa matarsa bace dukkuwa da cewa sosai taga dacewar su ganin yanda ta ke zuba masa shagwa6a son ranta kuma yana biyeta kamar yarinya 'karama sai ta bari akan sister take awurinsa. Yanzun kuwa dataji cewa matarsa ce Fateemahn sai ma taji ya 'kara birgeta sosai musamman idan ta tuno yanda Teemah ke yi masa sakalci da shagwa6a kuma ya kar6a mata, bakowa ke iya kar6an hakan daga wurin mace ba face cikakken namiji wanda ya san kansa yasan darajar matarsa. Amma bata nuna hakan ya dame ta ba sai ma ta sanya musu albarka tare da basu tabbacin kawo musu ziyara idan ta samu lokaci kuma in sun bata damar yin hakan. Tana yawan k'iran Abbas su gaisa daga baya ma har da numbern Teemah take 'kira, dan ranar da kanta tace Teemah ta k'irata da numbern ta. Acikin kwanakin da basufi biyar ba sukayi sabo da juna dan Teemah yanzun tafahimci abota ce kawai bakomai ba a tsakanin su, duk da shi'din na yawan tsokananta game da Leesah amma sam bata wani reaction sai dai tayi murmushi. Leesah ta 'dan girmi Teemah ka'dan dan ita 25-6yrs take yayin da Teemah har yanzu take da 19yrs. Amma duk da haka bai sa Leesah 'kiranta da sunan ta ba dan soyayyar da tafara yi masan sai ya juye ya dawo ta abota da 'yan uwantaka, jin Abbas take yi tamkar d'an wanta na jini. Takance dashi *bross* Teemah kuwa *sister* take k'iranta. yayin da Teemah ke k'iranta da *Anty Leesah*, har labarin Hannah take bata idan suna waya itama Leesah na bata labarin wanta da yanzu ma baya k'asar yana waje. *Duk naji za6in ku yanda kowa yafa'di ra'ayinsa game da ranar da za'ana update kuma na fahimce ku gaba 'daya, duk da cewa ra'ayoyi bai zo 'daya ba amma ni na* *yanke cewa zamu rin'ka posting CAPTAIN ABBAS 2-2 days saboda ganin hakan yafi ni awurina, kuma ma zan fiyi anutse, sannan kuma zakufi* *samu dayawa* . *Wa'danda suka ce aringa yi kullun 'din nan kuyi ha'kuri dan Allah ba wai na'ki taku bane amma kunsan komai cikin natsuwa yafi.* 🤞🏻 👎🏻😰 *Sannan kuyi ha'kuri babu wuta ne a garinmu shiyasa kk jini shiru kwana 2....... kuma jiya nayi rubutu na dayawa har saura nayi editing ma kawai sai whattsap 'dina yayi clearing komai narasa chats gaba 'daya, wa'danda suka min magana basu ga amsa ta ba suyi min ha'kuri dan Allah domin bangani bane shiyasa* _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce*😍 [10/13, 1:58 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _This page is specially dedicated_ _to my hard&die fans 👇🏼 *Mar-yerm, Mum Haidar, 🌹Tamama🌹, Mom inteesar(mai ku6ewa), Ummin Diga, Faateemaah🥰, Ummy Aliyuu, Nanerh, Hassan Adam Kagadama ('dan Nigeria* 🇳🇬 *)Fatee Duguri, Nusaibateey, Maamah love, Khadija Hussain,i Fiddausi, Bebin soo, 💅🏻Zulaihart💅🏻,Ayshah🍃 Humaira,* *mj, mom Ansar, A.S, Mum Khady, Maman Muhammad, Mumyn Minal, Aneesa, Zb, Teemah baby, Fatima2(, AMINA, Maman Arfat, Maman* *Nawwara, 💋Sheerdert💋, Khadeja Abdulhameed, Baby on top, Ummu Zahra, AbdullahiZainab, Maman Zahra, Oum Farhan, Hauwa Gulumbe, HafsatJabyr, Asma'u Usman, Maryam Wakili, Mommy F's, Zainab Bala Abubakar..........anya zan iya kuwa?🤔Allah yawa ne da ku sosai, ha'ki'ka 'kauna ta da ku ta musamman ce, daku* *dama wa'danda ban fa'de su anan ba inaso kusani cewa ur COMMENTS nd* *DU'AHS na matu'kar faranta raina, Allahu ya bar* ' *kauna ya kareku ya haskaka rayuwar ku a ko'ina kufi 'karfin ma'kiyanku......INA MATU'KAR YIN KU MUTANE NAH...........IRIN UN LIMITED 'DIN* *NAN🤞🏻.* 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _We are all here for some special reason......Stop being a prisoner of ur past..... Become d architect of ur future_ . 🅿 *89* Anty Leesah nada mutunci sosai dan ko ka'dan bata sanyawa ranta 'kiyayyar Teemah ba sai ma 'kara janta a jiki da tayi tana kula da dukkan al'amuran ta tamkar sistern ta na jini, Abbas kansa najin da'din yanda take bi da Teemahn sosai hakan ya 'kara mata fada awajen sa kuma dalilin kenan daya sanya shima yake girmama zumuncin dake tsakanin nasu. ***** Satin sa biyu da dawowa Abuja sai ya 'kira layin Umar sukayi magana akan zuwa katsina da ke gabansu, har suka shirya batun tafiyar ma bai sanar da Teemah ba Coz da farko be yi niyyan tafiya da ita ba amma da kansa kuma daga baya sai yaga dacewar zuwa da itan ko dan cika niyyar marigayi Mahmud ma tunda da ita uayi planning zuwa kafin rasuwar sa. Duk da haka sai ana jibi tafiyar sannan ya sanar da ita, Kwana biyu kacal yace zasu yi acan dan haka bata sha wani wahalar shirya musu kaya ba da kanta ta za6a musu harda shi ma kayan da zai yi amfani dasu har su dawo gida. Washe gari gidan Ummah suka wuce inda suka yi mata sallamar tafiyar ta su da yamman ramar Umar kuma ya iso Abuja inda yazo wa Teemah da tsarabar sirri daga Maman Amal, Abbas binta da idanu ya rin'ka yi Teemah kam idan sun ha'da ido sai ta murgu'da baki ta yi kamar bada shi take ba, duk yana kula da ita, kuma itan ma tasan kallon na menene shiyasa take ta kakkauda kanta gefe. Kamar jira suke Umar ya wuce sai Abbas yace dole sai ta nuna masa abin yagani dan bai yadda da wannan sabon salon 'kawancen ba, haka ya dage akan shi bai yadda ba sai yaga menene abin da aka kawo mata. Teemah kam tashi tayi da sauri ta koma daga bayan kujera tare da yin baya da hannun ta ta 6oye laidan sai 2seatern dake parlourn yazama atsakanin su, tana tsayen itama tace ai kuwa ba zai gani ba ai sirri ne aka kawo mata kuma babu kyau gulma da sa ido" Abbas najin tace gulma da sa idon nan sai ya zabura da sauri zai kamo ta ai kuwa tayi 'dakin ta da gudun gaske tana dariya ta shike dayake shine akusa da ita bai kamata ba kuwa, tana shiga sai ta datse 'kofan harda murd'a lock sanna tafara maida numfashi sama-sama. Sai data gama sau'ke numfashin kafin ta tashi taje ta 6oye shi inda ba zai ma gani ba koda kuwa ta bashi garin nemowa. Soasai taji 'kishin ruwa na damunta dan haka bata 6ata lokqci ba ta sake bu'de 'kofan ta fito tazo tasame shi zaune akan kujera ya na'de 'kafafu. Jikinsa ta fa'da tare da furta "ruwa"! Baiyi wani musu ba ya tashi da kansa bayan ya gyara da kyau yaje fridge ya 'dauko mata ruwan da kofi. Koda tasha 'din ma sai data 'dan huta kafin taji ta dawo normal dan tsokana sai ta kalli idanunsa tayi murmushi, shims sai yace "ina kika 6oye min wato kin yadda da wasu fiye da ni ko Zahra?" Sai tace "Ayyah Yayah bafa haka bane kawai dai tace ne fah kar kowa yagani" Gira 'daya ya 'dage yace "Shine harda ni? Kuma kika yadda? "Ai bakomai idan nagani ai kamar ka gani ne ko? Cewa yayi " ni fah kin san ba na son shirgin 'yan Lagos 'din nan kin manta abinda sukayi miki ko? Ahankali tace "ah ah ban manta ba ai wannan 'din daban ne" "Nine dai ban yadda nuna min inga ko menene" Rungumarshi tayi ajikinta tana murmushi ta 'dage masa kafa'da tare da fa'din bazai gani ba tunda ya koyi gulma shima" Yanda yaga ta dage akan bazai gani 'din ba yasa dole ya ha'kura da ganin. Amma da shara'din idan tayi amfani da wani abin dake ciki har ya samu nasaran cutar da ita toh yayi mata al'kawarin har ita kanta bazata tsallake wa hukuncin sa ba" Teeemah tace " ehh ta amince" akan haka maganar ta 'kare. The next day suka 'dunguma garin Katsina bisa jagorancin Umar dayake shine ka'dai yasan asalin inda suka dosa. Umar sosai yaji da'din yanda Abbas ya cire lokaci musamman dan ganin ya cika wa marigayi Mahmud burin sa da kafin cikarta Allah ubangiji ya kar6i ransa, yasan ko ba komai hakan ma na 'daya daga cikin halin girma, sosai Abbas ya birge Umar, baran ma daya ga yanda ya ri'ke Fateemah da kyau yake kula da ita sai yaji ya 'kara birgeshi, saboda yasan banda wahala da rashin kwanciyar hankali babu abinda ta tsinta agidan auren ta da Mahmud amma Allah cikin ikon sa sai ya musanya mata da wani mai so da tausayin ta wanda duk a yanayin su ya fahimci haka. Koda suka isa Katsinan kuwa Umar mamaki yayi na yanda ska tarar da gidan Innah gaba 'daya ya canza dan yasan shi ada, sa6anin su Abbas kuwa da basu san komai ba nasu sai dai ido ne kawai. Duk kuwa da cewa gyaran ba wani na kirki bane amma cikin rufin asiri akayi komai kuma bu'kata ta biya, gidan Innah ya canza sosai haka ma yaran ta dan wannan dattin nasu ya 'dan ragu ba kamar da ba, duk dama zuwa yanzun sun 'dan fara shiga wani hali saboda 'karewar ku'din da Marigayi Mahmud ya bar musu danma sunan da kayan abinci dai-dai gwargwado shiyasa ma abin yazo musu da 'dan sau'ki sai wahalar ta 'dan 6oye kanta. Umar ne yayi musu bayanin rasuwar Mahmud 'din gaba 'daya a takaice inda Innah ta ringa kuka da hawaye tana binsa da kyakykyawar addu'ah. Hatta Rabi'u sai da ya zubda hawaye duk dama ba wai yau ne ya fara jin labarin ba amma irin karamcin Mahmud 'din yasa sam bai mantawa dashi yake kuma jin alhinin rashin sa sosai. Teeemah ma sai da ta tuna da shi itama ta taya su hawayen rashin nasa da suke yi. Kunyar matar ka'dai ya hana Abbas rungumo matar sa ya share mata hawayen amma duk da haka bai iya jura ba sai da ya maida hankalinsa gaba 'daya kanta suna ha'da ido sai ya yi mata alamar bai son kukan ta daina. A hankali ta yi 'kasa da idanu batare da ta daina hawayen ba dan ko tace hawayen ya tsaya ma hakan ba zai samu ba. Dukkan su sun yaba da 'ko'karin Rabi'u akan a halin Innah dan sun fahimci cewa yaro ne shi mai zuciya da amana, Teemah kam da farko ta sha shima 'din 'dan Innahn ne sai daga baya cikin maganganuns u ta fahimci basu da wata ala'ka sam. Nan take Abbas ya ce da shi kafin gobe ya samu ya bu'de account kafin su koma. Kafin su tafi zuwa masau'kin su kuwa sai da suka je gidan mahaifin Rabi'u suka gaida shi tare da yimasa alkhairi na ban mamaki wanda sam bai yi zaton samun sa aranar ba amma sai gashi dalilin 'dansa ya samu hakan, shima dan farin ciki rasa mai ma zai ce dasu yayi illah albarka da ya ringa sa ka musu tare da fatan alkhairi. Daga nan masau'kin su suka koma bayan sun sau'ke musu tulin tsarabobin da suka taho musu dashi, gasassun kaji da kayan itatuwa masu yawan gaske sun kuwa ji da'din hakan sosai. Innah bata bar yaranta sun 6ata tsarabar duka ba sai da ta ware na Rabi'u da kuma wanda zai kai gidan mahaifin sa kafin suma yaranta ta basu sauran. Teemah kam har suka isa masau'kin su bata daina share hawaye ba, Abbas sai ya share ta duk da abin na damunsa amma dan kar ta sashi yin abinda bai dace ba acikin jama'ah yasa ya 'kyaleta taci gaba da kukan, coz yasan fa'da da baki bazai sata tayi shiru ba, yasan ba komai zai sata kukan ba face memories 'din Mahmud wanda shi kansa ma ji yake duk yayi laushi sosai. Suna shiga room 'din da suka sau'ka kuwa yajawo ta jikinsa ya fara share mata hawayen yace kukan ya isa hakan nan ta daina" Da 'kyar ya samu kukab nata ya tsaya sannan shima ya 'danji natsuwa ta shige shi. Wanka suka shiga a tare wanda kafin su fito daga bayin sai da ya tabbatar ta bar kukan nata gaba 'daya ta sanywa fuskar ta murmushi tukunna ya sarara mata. Tana shafa mai a 'kafarta ta 'kira sunan sa yayin da shi har ya fara saka kaya ma itan ce dai ta tsaya sai yanzu dayake ma bata 'dan jin da'di sosai duk jikinta bata jin da'din sa ga marar ta dake 'dan mata ciwo. Yana jin ta 'kira sunan shi sai ya waigo ya dube ta batare da ya amsa ba. Tambayar sa tayi cewa "Yayah ina wancen ku'din nan da aka ce wai na gado na ne" Sai yace mata "yana nan kina so kiyi amfani da shi ne? Teemah tace "ehh" Inda ta ro'ke shi akan tana so duk abinda za'a yi wa su Innah ayi musu da wannan ku'din" Abbas kai ya girgiza mata yace "ah ah wannan ai burin Mahmud ne komai za'ayi da sunan shi ne, yace shima 'din da sunan Mahmud yazo kuma duk abinda yakama ayi zai yi shi koma menene amma duk bada sunan shi ba, su 'din kamar 'yan aike ne domin wannan tafiyar ta Mahmud ce, da sunan ne akayi ta, yace in taimako zatayi tabari idan sun koma gida sai suyi planning wani abin daban yace ko makaranta ma zata iya ginawa da ku'din shima ba laifi bane kuma akwai sosai shima. Shiru tayi ta sunkuyar da kanta 'kasa bawai dan bata yadda da abinda yace 'din ba ah ah, sai dan yanda take jin yanayin da take ji ajikinta na 'kara tsananta. Abbas barin abinda yake yi yayi da sauri ya 'karaso inda take ya zauna, inda yana zama sai ta kwantar da kanta ajikinsa hawayen ta na 'kara sau'ka a hankali, sosai yaji hankalin sa ya tashi sai yafara tambayar ta mai ke faruwa meke damunta. Kamar bazatayi magana ba sai can ta 'kira sunan shi a hankali ta ce " _Yayah_ ! " _Na'am_ " Ya amsa ta dashi yana me bada dukkan hankalin sa izuwa gareta, sai ta kamo hannun sa ta kai kan marar ta tace "Yayah zafi yake min sosai ka danna min a hankali dan Allah" Kamar yanda ta bu'kata haka yayi mata sai dai instead ya danna matan sai ya rin'ka shafawa a hankali yana sake kallon cikin nata ganin ya 'dan taso ka'dan. Yana shafawan yake 'kara lallashin ta da kalamai masu sanyi tare da tambayar ta ko zasu je hospital a duba ta, girgiza masa kai tayi tace " ah ah gajiya kawai tayi shiyasa kuma zai daina ma anjima ka'dan" Shiru yayi mata kawai ya ci gaba da shafa marar har bacci ya 'dauke ta, ganin haka sai ya saki ajiyar zuciya tare da gyara mata kwanciya ya rufe ta da kyau. Kafin ta tashi har an kawo abinci da yake dama da yunwar ta tashi so bata tsaya 6ata lokaci ba ta lodi abincin ta, Abbas na ta kallon ta dan shi coffee kawai yasha tun zuwan sa sai ko kayan itatuwa, sai da ta gama kafin tayi sallah inda daga nan suka fita yawo cikin gari ganin ta warware sosai, Abbas ba haka yaso ba dan shi clinic yaso kaita amma Teemah ta'ki amincewa da hakan tace dashi ai ta riga ta warware. Washe gari da yamma Rabi'u ya tabbatar wa Abbas cewa ya gama komai na bu'de account inda ATM ne ka'dai ya rage masa. Tare dashi suka je store amma Abbas bai bari Teemah ta bisu ba yace babu inda zata, siyayya suka yo na kayan abinci masu yawan gaske inda duk suka sau'ke shi gidan Innah. Sannan Abbas yayi transfern ku'di cikin sabon account 'din Rabi'u yace ya tabbatar da cewa yaran Innah basu nemi wani abu sun rasa ba kuma duk suna zuwa makaranta, shi kansa Rabi'un ma Abbasa ya bashi daman ya rin'ka yin bu'katun makarantar sa da ku'din kar yaji tsoron ta6awa tare da yimasa al'kawarin 'daukan nawin makarantar tasa in har yana raye har inda ya ga daman tsayawa da karatun. Abbas yayi al'kawarin cewa da izinin Allah zai yi 'ko'karin ganin ya kula da hakan. Kuka da godiya ranar kam yasha su sosai kamar su goyashi, Umar kansa sai da ya ga karamcin Abbas sosai inda shima ba'a barshi abaya ba ya ciri ku'di kimanin 20k ya dam'ka a hannun Innah. Shi kuwa Abbas duk abinda yayi 'din ko 'daya bai yishi da sunan kansa ba yayishi ne da niyyar cikar burin marigayi Mahmud coz niyyar sa ce hakan shine yafaro abin tun farko dan haka duk da cewa da dukiyarsa yayi amfani amma niyyarsa daban ce. The following day suka koma Abuja inda suka bar Umar acan saboda mahaifar sa ce zai tsaya ya duba 'yan uwa da dangi kafin ya wuce Lagos. Da komawar su kuwa Abbas yaji zaman Abujan kwata-kwata ya isheshi gaba 'daya, da isarsu ko hutawa bai yi ba ya wuce ya dubo gininsa da yake yi acikin unguwar tasu, washegari kuwa gidan Ummah suka dira, suna can ma sai kuma wani abokin sa ya 'kira shi cewar suna hanya zasu kawo musu ziyara. Wannan dalilin ne yasa suka dawo gidan nasu suka tari ba'kin da suka zo, Teemah naganin Nasreen ai sai ta washe baki tana murna ta rungume ta tare da fa'din " oyoyo my baby girl", Nasreeen kam harta manta ma da ita, amma dayake asali bata 'kin mutane sai suka sake yin wani sabon kuma, yanda Teemah takeyi da yarinyar tamkar wata yarinya 'karama itama ta koma, Maman Nasreeen kam sai de tayi ta musu dariya. Da zasu har wajen mota suka yi musu Rakiya inda Teeemah tacikawa Nasreen haka da kayan ciye-ciye irin nata. Abbas yaso ya koma da matar sa Rivers su 'karasa hutun acan amma ganin Daddy nagari sai ya sashi ha'kura dan jin tsoron abinda daddyn zai ce coz sam shi bai son haniya akansa ballantana har ransa yasake 6aci karo na biyu akan zancen tafiyar. Sai ya cire batun tafiya da ita aransa ma gaba 'daya kawai ya yanke cewa gara tafara zuwa makaranta tunda babu abinda takeyi yanzun illa zaman gida wanda yake ganin kamar hakan ma zai 'kara sata ta warware in tana shiga cikin 'dalibai 'yan uwanta 'kila ko lokacin yin tunani ma bazata samu ba. S.S.C.E result 'dinta ya nemi gani dan ya san ta ina zai fara nema mata admission kafin ya wuce. Nan kuwa yasha mamaki dan Teemah kam da taji yace " Result 'dinta " Sai ta zaro idanu kamar da mamaki tace " Ni.... ni kuma nawa Yayah? Abbas yace " da 'din wa kike ganin zan tambaya anan?" Teemah da iskanci, juyawa tayi kamar dagaske ta 'dan kakkalli cikin 'dakin wai ko zata ga wani daban a ba ita ba sai kuma ta tura baki tace " Nima fa Yayah bansan inda yake ba" Waro idanu yayi akanta da mamaki yace "kamar yayah bangane ba?" Sai tace " Ni....nifa agida na barshi can damaturu kuma bansan inda yake ba yanzu sai dai a tambayi Mummy" Abbas tsaki yaja ka'dan yace " Yanzu fisabilillahi result 'din makarantar ki ne kike cemin baki san inda yake ba, to ke da kanki baki adana ba waye kike tunanin zai adana miki?" Allah zanga ranar da zakiyi wayo kekam, a hakan ne kuma kike wani son baby, salon ki ta koya musu shirmen ki ko?" Kauda kai tayi gefe ta 'kasa-'kasa tace " Ni kam inada wayo na" Muryarshi data jiyo yace mata" _meaning_ " neya sata gane cewa yajita. A'dan firgice tajiyo sai ta cikaro da shi tsaye kusa da ita da gira 'daya a'dage sama ya kama kunkumi da dukkan hannyensa kamar mai shirin fa'da da sa'an sa. 'Kasa tayi da kanta tana muzurai. Sai taji ya sake fa'din "tambayarki nakeyi ko?" Teemah 'dan matsawa baya tayi ka'dan ta kauda kai tana 'kun'kuni sai taji ya 'dalli bakinta da yatsun sa biyu. Kuka ta fara tana ri'ke bakin tana kallon shi sai ya daka mata tsawa inda yace " Shut up da Allah, dama ni sa'anki ne da zaki rin'ka yimin hakan? Kuma karki min shiru kiga abinda zan miki right now, cry-cry kawai" Hanyar barin 'dakin takama sai ya sake fa'din " kuma ki 'kira Mummyn ki tambaye ta yanzun nan ina jiranki kizo ki sanar dani feedback" Fita tayi da sauri kamar an kunnata da switch shima sai bita da idanu tare da sakin tsaki, haka kawai yau 'din ya tsinci kansa cikin 6acin rai. Koda ta koma 'dakin ma sai data sha kukan ta na shagwa6a son ranta dan ba kukan ciwo bane kawai shagwa6ar ce yau ta motsa da kuma haushin ya 'dalli bakin ta, kafin daga baya ta tashi ta koma gaban mirror ta duba fuskar ta da kyau, gani tayi ma bakin bai ko tashi ba amma duk da haka sai ta janyo stool ta zauna taci gaba da 'karewa fuskar tata kallo. Bata san meke damun sa ba yau 'din amma kallo 'daya zaka masa ka hango 6acin rai tattare da shi, ita kanta tasan bahaka ya kamata tayi masa magana ba musamman dayake neman hanyar da zata janyo mijinta ajiki takeyi yanzun take sai kuma taga rashin kyautawarta. Wani 6arin zuciyarta ne yashigar mata da tunanin "ai shima bai kamata ya 'dalli bakinta ba bata mar komai ba haka kawai dan ranshi ya 6aci kuma ai tasan ba ita bace ta 6ata masa rai 'din meyasa zai zo ya huce akanta?" Kalaman Anty ne suka bijiro ranta inda tace da ita " auren ha'di na tafe da wasu irin 'kalubale wanda sai kai da kake cikin sa ne zaka san hakan in kayi sa'a kuwa bazaka fuskanci irin wa'dan nan matsalolin ba sai kaga ka dawwama cikin farin ciki, amma dukkan su ba'a cin galaba akan su har sai in an ha'da da ha'kuri" Teemah ido ta lumshe tana tunanin abinda Yayah zai yi da result 'dinta tasan dai duk ba zai wuci batun makaranta ba ita kuwa sam bata so, wanda tayi abaya ma Allah yasa albarka amma tunda yace yanaso 'din bari ta 'kira Mummyn taji ko ta san inda yake. 'Daukan wayar ta tayi ta 'kira layin Mummy, bata 'daga ba sai da ya yanke kafin tana sake 'kokarin gwadawa sai ga 'kiran Mummyn ya shigo, gaisheta tayi cikin natsuwa tare da tambayar ta Daddy daga nan ta 'kara da tambayar result 'din sai Mummy tace da ita duk suna nan Dubai ta taho dasu tama manta ne dama taso ta taho mata da shi amma sai ta sha'a fah. Teemah aranta ta ringa godewa Allah sam bata son damuwar makaranta ita aganin ta ai ba dole bane tunda wasu ma bayi suke yi ba gaba 'daya. Sallama sukayi da Mummyn ta ajiye wayar sannan ta tashi a hankali take tafiya kamar mai jin tsoron 'kasa tafito daga 'dakin nata. A parlour ta same shi sai ta 'karasa gefen sa ta zauna tace " Yayah! Tun fitowar ta ya ji motsin ta amma bai nuna alamun ya ji ta ba sai ma ya rintse idanun sa yayi sama da kansa. Jin ta ambaci sunan shine yasa ya bu'de idanu tare da juyowa ya kalleta inda take ya hango rauni tattare da ita. Suna ha'da idanu sai ta ce " Mummy tace wai tatafi dashi Dubai" A nutse tayi maganar wanda shi kanshi sai da yaji natsuwa ta shige shi, sai yayi murmushi ka'dan wanda ya tsaya masa iya gefen baki yace " kin kyauta ai yanzu kam, it seems like kinfi so ki cigaba da zama agida fiya da zuwa makaranta ko?" Teemah kam kanta ta 'daga sama alamar " ehh" Da mamaki ya kalleta yace " wai ke dagaske kike yi ne dama? Degree 'din ne baki so ko kuma me? Baki so ki rin'ka zuwa makaranta irin na Hannah? Da kanta ta sake bashi amsa tana wasa da yatsun hannun ta. "Wonders shall never end" Yace aransa yayin da mamakinsa ya 'karu fiye dana da. Bai 'kara kulata ba kawai ya shareta aransa yake tunanin may be bata da lafiya ne coz bai fiya ganin wanda ya nuna zallar 'kiyayyar sa da karatu har haka ba, shi ada datake cewa bata so 'din nan duk ya zaci wasa ne sai yanzu ta suprising 'dinsa amma duk da haka bai fasa ba yasan idan ta tsinci kanta cikin makarantar dole ne zata waraware ai tayi abinda ke gabanta. Abbas be 'kara kulata da maganar ba har akayi kwana uku, kafin hakan kuwa zama mai kyau ma basu yi da ita ba dan saboda abubuwan da ke gabansa. Ran kwana na ukun ne shine yace da ita nextweek zata fara registration dan already an yi nisa da bada admission shima da 'kyar yasamo mata admission 'din tunda batayi jamb ba zata fara ne tun daga remedial kawai sai ta fara preparation na zamowa student. Tana jin haka sai ta yatsine fuska tace " Allah nifa banson wata makaranta Yayah" Abbas be kulata ba kawai ya 'kyale ta coz ya riga ya yanke decision cewa matu'kar bazai tafi da ita Rivers ba kuwa makaranta dole ne agareta. Kafin lokacin registration ne 'din ma shi ya koma ports bakin aikin sa, aranar ne kuma ya 'kira ta da sassafe cewa su tafi tare da Hannah ta rakata NILE, inda yace ta duba drawern 'dakin sa zata ga komai da zata bukata aciki. Ko 'kala Teemah bata ce da shi ba har ya yanke 'kiran shima bai damu ba tunda yana da tabbacin tajishi. Tana cire wayar a kunnan ta sai ta dannawa Ummah 'kira cikin siririyar muryarta da shagwa6a tace " Ummah kinga Yayah ko? Wai sai na je Nile ni kuma banaso! Cike da kulawa Ummah ta tambayeta "to wanne take so?" Teemah kuwa tace " ni fah Ummah banason ko 'daya kuma ai na gaya mishi tun ranan ma" Ta 'karashe tamkar zatayi kuka. Ummah kam lalla6a ta ta hauyi tana bata baki da ha'kuri wai ko zata amince. Amma Teemah ta kafe akan ra'ayin ta, Ummah ganin haka sai ta ha'kura ta 'kyaleta kawai tare da sanar mata cewan zata yi masa magana daga nan ta sallame ta. Take Ummah ta sake 'kiran Abbas ta sanar dashi yanda sukayi da Teemah tare da bashi ha'kurin ya 'daga mata 'kafa zuwa wani lokacin 'kila da kanta ma ra'ayin karatun zai shige ta Ummah tace yabita a hankali aga iya gudun ruwanta. Abbas kam zuwa yanzun haushi tafara bashi yarasa sam ita wace iriyar yarinya ce da komai ra'ayin ta sai ya bambamta da mutane ga shegen taurin kai, in haka ne kuwa tsab zaiyi maganin ta shima akan zuwa University 'din nan sai ya bata mamaki. 'Kin amincewa yayi da batun Ummah duk kuwa da da'da'dan kalaman da ta ringa yimasa saboda sanin halin sa amma duk da haka maganar bata wani shiga kansa ba sai ma yake ganin kamar iskancin Teeemah ne kawai yayi yawa ba komai ba, kuma ai karatun dan kanta ne zata yishi bawai shi zata yiwa ba toh ma miye abin gudu a makaranta in banda shirmen ta. Ummah data ga bazai saurare ta ba sai ta sanar da Daddyn Abuja abinda ke faruwa. Shima yayi mamakin hakan inda da kansa yasa suka zo da Hannah yaringa lalla6ata da bata baki akan ta amince da makarantar, saboda shima Abbas ya sanar da shi komai ya sanar dashi babban dalilin sa na son tashiga makarantar musamman ko dan ta rage zaman gida ita 'dayan ma da takeyi shiru kullum tunda Hannah ma ba yini take ba kwana ne kawai, Daddyn ma da kansa yayi supporting Abbas 'din 100% ya goyi bayan hakan dayake yasan shine ya hana Abbas 'din tafiya da ita. Dalilin kenan daya sanya ya ringa nuna mata muhimmanci da amfanin ilimi musamman ga 'ya'ya mata, harda manyan misalai ya ringa kawo mata amma yarinya ta 'ki canja ra'ayi duk kuwa da cewa ta fahimce shi. Amma hakan bai yi mata tasiri ba sam dan ita aganin ta tunda ba ilimin addini bane toh babu ruwanta. Daddy kam dayaga ita da Abbas 'din duk sun kafe akan ra'ayin su sai ya sanar da Daddy babbah ( mahaifin Teeemah). Daddy murmushi yayi daya ji labarin abinda ya farun sam bai yi mamaki ba coz sarai yasan halinta da kafiyar ta kuma indai akan karatu ne haka Allah yayita tun tana yarinya 'karama sam bata so har garama na islamiya ta kan bashi muhimman ci. Daddy ma awaya ya 'kirata cike da farin ciki ta gaida shi tare da tambayar sa Mummyn ta, Daddy yace tana nan lafiya sai ya 'kara da fa'din " Angel 'din Daddy sarkin rigima, ba nace ban son taurin kai ba shine kuma kike yiwa yayanki ko?" Shagwa6e murya tayi tace " banayi masa fa Daddy " "Toh ya akayi naji wai ance baki son karatu har kina 'karan Yayanki akan hakan?" Hawaye tafara inda cikin hawayen tace dashi " Allah ni Daddy ban son wani makaranta shi kuma Yayah yace sai nayi ni kam banaso Allah" Sai yace " gaya min to ni inji meyasa baki so Angel?" Tace "ni haka kawai ne Daddy" "Bakya tunanin gaba zai miki amfani ko? karfa watarana kizo kiyi regretting akan hakan?" "Insha Allahu bazanyi ba Daddy karka min fatan hakan, kuma ko nazo nayi ma bazan yi blaming kowa ba tunda nasan babu wanda ya hanani" Daddy cewa yayi "shikenan to Angel 'din Daddy amma fa banda rashin ji kinji " Da murnar ta tace "toh Daddy ai na ma daina" "Yauwa uwata Allah yayi miki albarka yasa haske cikin rayuwarki" Da "Ameen" ta amsa masa sannan sukayi sallama. Daddy yasan kowani irin mutun nada kalan nashi burin da Allah ya halicce sa da shi hakama ra'ayoyin mu suke mabambanta ne. Yasan halin Fateemah da taurin kai akan abu musamman idan batayi ra'ayi akai ba toh da wuya ka iya tan'kwarata, ha kama karatun yasan koda ansata bayi zatayi ba tunda bata yi niyya ba ba abin kirki zatayi ba kuwa ko da ta fara, shiyasa ma ya rin'ka biyeta lokacin da takeyin secondary school, makarantu sun kai hu'du ya ringa canza mata duk dan ta nutsu, duk wanda tace tana so baya gardama yake canza mata da 'kyar ta tsaya tagama aguda 'daya. Shi karatu ra'ayine kuma ba'a ta6a yiwa mutun dole, domin kuwa ko ka tilasta wa mutun ya fara to in bashi da ra'ayi bazai ta6a yin karatun ba ballantana har asamu abinda akeso. Tunda an lallasheta ta'ki ji kawai sai abarta, dayawan mutane ma ai sunyi surviving batare da sunyi karatun ba, so ba matsala bane dan ta 'kiyi rayuwa duk tacgaji haka, wani zaka yasamu amma yana 'kinyi yayin da zakaga wani yana fafutuka da 'karfin sa da komai dan kawai yaga yasamu, wani kuwa duk ma sai kaga babu damar, domin bai samucgatan ayi masan ba kuma shima sai kaga Allah bai bashi hanyar da zai nema da kansa ma ba sanadin haka dole sai kaga mutun ya ha'kura gaba 'daya, amma duk hakan ba laifi bane face salo na rayuwa kawai domin kowa da kalar tashi 'kaddarar. Balle ga ita data ke matsayin 'ya mace ai zaman auren shine gaba ayanzu, matu'kar zata zauna a hakan cikin kwanciyar hankali ta bautawa ubangijinta ta kuma yiwa mijinta biyayya to shi bashi da matsala da ita burinsa dama tayi farin ciki. Abbas Daddy ya 'kira yayi masa bayani tare da bashi ha'kuri akan maganar yace ya 'kyaleta kawai tunda bata yi ra'ayi ba, wata 'kila watan wata rana ta nemi yi dakanta lokacin da ra'ayin hakan ya shigeta. Abbas bai so hakan ba amma ya ha'kura shima ya bar zancen kawai, amma sosai ya jinjina wa kafiya irin tata, ace mutun karasa abokin gaba sai karatu.....gaskiya abin da mamaki, yasha jin labarin irin dramar da ake sha da mata akan karatu amma nata salon daban ne, maimakon tayi fitinar an hanata yi ah ah sai ma fitinar ita bataso.......ha'ki'ka duniya kowa da kalan halin sa, abinda kake ganin dai-dai ne awajen ka sa6anin hakan kuwa ga wani sai ya zama abin gudu da 'kyama na musamman, sosai yake 'kara jinjina mata a duk lokacin daya tuno duk lamarin hakan yafi matu'kar ri'ke ransa. Shima kuwa Abbas sai yace in dai hakane kuwa ba ita ba zaman Abuja dole tabishi Porthacourt, wannan karan Daddyn Abuja bai hana shi ba dan yasan shi ke da iko akan iyalinsa, ko wancan lokacin ma ya hana ne dan gudun kar ya cutar da ita, amma zuwa yanzun ya fahimci akwai 'yar fahimta a tsakanin su, kuma ma idan yacigaba da shiga tsakanin zaman nasu to bazasu ta6a sabawa da juna ba musamman idan akayi la'akari da yanayin aikinsa ba ya basu damar da zasu sake da iyalansu kamar kowa, kuma kusancin da ke tsakanin su shi yafi komai muhimmanci, abinda Ummah tayi ta 'ko'karin fahimtar da shi kenan tun a wancen lokacin amma yakasa fahimtar ta son 'yar sa da gudun kar a cutar da ita yayi wa zuciyarsa 'kawanya a lokacin ya hana shi ganin gaskiya. Teemah bata damu ba sai ma da'di da taji coz ko itama yanzun baso takeyi take yin nisa da mijinta ba ko dan ma ta cigaba da faranta masa, saboda ita ka'dai tasan halin da ta shiga wancan lokacin daya tafi ya barta. Ko ta je Rivers 'din kuwa bai nuna mata 6acin ransa ba koka'dan akan abinda yafarun duk ya fitar aransa dama dan ita ne to ita wacce za'a yi domin tan kuma tace bata so to shi miye na shi. Itace ma take 'dan jin fargaban ha'duwar su saboda tasan bata kyauta masa ba dole ransa zai 6aci da ita amma da suka ha'du ta gansa wasai sai itama ta saki ranta. Abbas rungumar matar sa yayi cikin walwala da farin ciki suka cigaba da rayuwar su. Amma Teemah kasa daurewa tayi sai data bashi ha'kuri daga baya domin guilty conscious ya kasa barin ta sai take ganin tamkar kawai yana kallon ta ne da abin aransa batare da ya furta ba, ga mamakinta kuwa sai yace mata ai bakomai karta damu komai ya wuche shi awaken sa. Sosai Teemah taji da'din hakan har cikin zuciyarta. Cikin cinye-cinyen Teemah kuwa babu abinda ya ragu aciki Abbas har ma ya saba da komai yanzu kuma ko damuwa ba yayi da canzawar ta balle yayi wani tunani akai, kawai ya bari akan lokacin cin abincin nata ne yayi shiyasa abinda kawai yasa aransa kenan duk kuwa da yasan cewa sam ba halinta bane hakan amma baya damuwa, ga wani shegen son sex daya shigeta yanzun, wannan ne ka'dai ya tsaya aransa, shi kansa yanajin da'din kasance wa da ita sosai fiye da baya har ma hakan yasa baya ta6a gajiya da kasancewar ta su be it shi ke so ko ita ta nema sam baya ta6a 'kin amincewa da hakan, sai dai wani lokaci takanyi ciwon mara, akan hakan ne yaso suje ganin likita amma tsoron kar ayi mata allura yasa ta'ki bashi ha'din kai. Abbas hankalin sa sai yakasa kwanciya da hakan sai ya shirya mata wani shiri batare da ta sani ba akan tunda bata san clinic ba anan garin da wayo zai kaita asbitin yasan in sun riga sun isa dole ne ta tsaya a dubata dan gudun kar ya cigaba da biyeta yana bin ra'ayin ta kuma abubuwa su zo su girmama su fi 'karfin tunaninsa a 'kurarren lokaci duk dama ba'a fatan faruwar wani mummunan abu amma wai akace maganin kada ayi toh fa kada asoma shi yafi. ***** Kwance take......... 👎🏻 _Ina gaida mutane na makarantan wannan littafi ina kuma yi muku albishir 'din cewa just some few pages ne suka rage mana mu kammala wannan labarin sai dai alal ha'ki'ka ni kaina bansan zuwa kwana nawa hakan zai 'dauke mu ba gaskiya, fatan dai zaku cigaba da samba'do madaran comment wanda zasu rin'ka sani yi muku typing akan lokaci koda kuwa ban shiryawa hakan_ _ba......lolz_ 🤪..... *A KAFTAH* 🤞🏻 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce*😍 [10/13, 1:58 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 👇🏼 Assalama Alaiki warahamatullahi wa bara katuhu. Gaskiya salma na yaba maki da wannan novel naki mai suna *captain Abbas* Allah ya kara basira ameen summa Ameen. *From* _Abubakar Saleh Al~Quyraemey_ *Ngd 'dan uwa, i really appreciate....nd i dash ths page specially 4u where ever u ar*👍 😍 *Dr.Khausar* Allah ubangiji ya baki lafiya ya kuma albarkaci baby ya sa ta cikin bayinsa salihai.( *AMEEEN* ) *Bismillahir rahmanir raheem* _Every heart has a pain......only d way of expression is different.....some hide it in eyes while some hide it in their smile_ 🤞🏻 🅿 *90* Kwance take akan kujera mai zaman mutun uku jikin ta da wata rigar bacci sharara mara nauyi, rigar 'yar 'karama ce dan ko cikin ta bai gama rufe wa ba sai 'dan wandon rigar mai d'an fad'i da ka'dan ya wuce mata gwiwa shima, sosai take jin da'din kayan dan rashin nauyin su da kuma yanda take sakewa cikin sa idan ta sanya su. Yayin da Abbas ke zaune facing nata akan wata kujerar daban yana kallon CNN gaba 'daya hankalinsa na kai ganin an kai hari ma wani 'kauye inda aka yi musu kisan gillah manyan su da yaransu kuma gwamnati takasa yin komai akan hakan, abin haushi yake bashi na yanda ake 'daukan rayukan al'umma batare da wani 'kwa'k'kwaran dalili ba tamkar baza'a mutu watarana aje fadar Allah domin kar6an ayyuka ba, mutane mantawa sukeyi da hakan...... time to time yana sipping mango juice da Teemah tayi masa 'dazun nan. Hannun ta 'daya na kan cikin ta sai aikin shafawa takeyi a hankali tana lumshe idanu tana feeling yanda cikin nata ya 'dan d'ago ka'dan wanda tun ba yau ba ta fahimci hakan, hatta Yayah ma sai da ya tsokane ta akai last three days wai Fatee bombom mai tummy, ta kuwa ji haushi sosai dan ranar kuka ta ringa yi masa kafin da 'kyar ya daina tsokanan nata amma sai ya cigaba da yi mata dariya. Ita kanta ma ba so take yi ba abin na bata haushi sosai, musamman da yake tasan cewa ba komai ne ya jawo mata hakan ba face yawan cin abincin nan da take yi. Murmushi tayi lokacin da ta tuno yanda kwa'dayin awaran 'kwai ya sa ta a gaba 'dazu da rana lokacin ita 'daya ce a gida Abbas na office, sai ta tashi taje ta ha'da komai ta yanyan ka 'kwan bayan ta dafa shi sannan ta sake ka'da wani 'kwan ta wadata shi da albasa da da 'dan maggi dan yanzu bata fiya son taji 'dan'danon gishiri abakin ta ba, tafiya son tajishi da nisa sama-sama, in abinci ya kasance hakan kuwa har wani santi yake sata tana jin da'din sa sosai. Dududu da 'kwai biyar tayi amfani har ta gama. Sauce tayi na zallan attaruhu da shima yaji albasa na fitan hankali da spices ta harhad'a abinta a plate tazo ta ajiye, bata ma tsaya a parlour ba sai ta wuce 'dakin ta da abincin, bata bu'katan wani juice a lokacin ruwa kawai take jin ya isheta dan haka sai ta 'dauko mai 'dan sanyi ta shige ciki. Har Allah-Allah take yi taji shi cikin bakin ta dan yanda take jin kwa'dayin nasa abin har na bata mamaki. Bata 6ata lokaci ba ta fara aikawa dasu bakin ta inda da'din sa ke ratsa mata har cikin zuciyar ta tare da sauk'ar mata wani nutsuwa na bam mamaki irin rai ya samu abinda ke so d'in nan kuma at d right time. Ci takeyi a hankali tana korawa da ruwan sanyin ta, in kaga yanda ta nutsu take cin abincin har zakayi zaton ko shine abu na farko da yafara shiga bakin ta a yau 'din. Sai dai bata ko ci rabin sa ba taji lokaci d'aya amai ya yun'kuro mata, ido ta zaro ta tare da gumse bakinta da k'arfi tana mamakin silar faruwan hakan sai taji ya sake yun'kuro mata da karo 'daya ai bata san lokacin da ta ajiye plate 'din agefe ba tayi cikin bathroom, amai ta ringa kwarawa har sai da ta amayar da duk abinda ke cikin ta a lokacin sannan ta fara sau'ke numfashi. Sosai taji ta galabaita sai ta jingina bayanta da jikin sink 'din tana maida numfashi bayan ta tsabtace wurin. A hankali ta fito daga bathroom 'din tazo ta zauna a parlour kan kujera tana sauke numfashi har da 'dan tattaba wuyan ta zuwa jikin ta wai ko zataji tashin zazza6i amma bata ji komai ba banda d'umi da jikintan ke dashi, wannan kuma tasan ba sabon abu bane awurin ta, kusan kullum haka jikinta yake...." _to me ya kawo hakan kuma_ ? Ta tambayi kanta. Bata raba d'ayan biyu wannan cinye-cinyen da takeyi ne ya kawo mata hakan. D'an k'aramin tsaki taja a hankali tana yawo da kanta gefe da gefe tana sau'ke hawaye tare da tuno yanda tun farko ta tsinci kanta tsundum cikin son cin abinci na fitan hankali, ita kanta bata son hakan amma tarasa ta yanda zata daina shi, ko tace zata 'ki ci ma bata iyawa, coz wani lokaci har bata tunawa da batun bari 'din har sai ta gama ci, sosai ta gaji da wannan rayuwar, gashi yau abinda hakan ya jawo mata har da she'ka amai, tasan Yayah na jin wannan labarin to ko ta'ki ko taso sai ya kaita clinic ita kuwa tsoron kar ace za'a yi mata allura ya sanya ta ja bakin ta tayi gum. Kafin ma ya dawo ta warware ras kamar ba ita ba shiyasa sam Abbas bai fahimci komai tattare da ita ba, balle da ya samu ta tanadar masa 'kayataccen girki ai sai ya ringa sanya mata albarka kawai yana cin abincin sa. Teemah tana ta murmushi, abinda yasa yake birgeta kenan, ko da kuwa bata jin da'di ko kuma wani abu makamancin hakan takan daure ranta tayi masa abinda yake so, sam bata samun natsuwa har sai taga ta tanadar masa abinci kafin nan, ba dan komai ba kuwa sai dan yanda yake yabawa da hakan a kowani lokaci baya raina girkin ta idan tayi masa koda kuwa wani iri ne, yana matu'kar nuna mata jin da'din sa idan tayi masa abu musamman girki. Sai itama ta zauna ta sashi a gaba tana zuba 'kayataccen murmushi har suka bar table 'din cin abincin. Har zuwa dare bata sanar da Abbas batun aman da tayi ba, yanzu kuwa da take ta faman shafa cikin ta sai take 'kara jin haushin yanayin saboda yanda duk take ganin ya sauya mata abubuwa da dama na jikinta da kuma tsarin rayuwar ta ma gaba 'daya. Hannun ta nakan cikin nata har yanzu, tana kan shafawa har zuwa marar ta da taji ya 'dan yi mata tauri ya dunkule wuri guda, kawai sai hawaye ya sau'ko mata sirara masu 'dumi da bata san asalin silan sau'kan su ba. Take kuma sai taji wani matsancin son Fresh milk na asalin fulani ba na company ba ya taso mata sai ta rintse idanu da 'karfi. Ta so ta basar amma ina zuciyar ta wani irin son nonon yake yi mata da bazata iya hawa kai ta zauna ba sosai take jin son sha har a bakinta. A hankali ta d'ago kai ta kallo shi daga inda yake ya zaune, sai ta tashi ta zauna ta fuskance shi. Abbas bai 'dauke idanun sa daga abinda yake yi ba duk kuwa da yaga ta tashi ta zauna tana kallon shin dayake facing juna suke yi so yana kallon ta, zaton shima already tayi bacci dan babu wadataccen haske a 'dakin. A hankali ta 'kira sunan shi sai ya amsa da " _Inajin ki 'yan matan Yayah ya akayi_ ?" Yayi maganar batare da ya juyar da kansa ya kalleta ba. Sai tace " _Yayah dan Allah fresh milk irin na fulanin nan nake so_ " Abbas cewa yayi " _ki bari gobe idan Allah ya kaimu za'a nemo miki"_ K'afa ta shura tare da zun6ura baki cike da sakalci tace " _sai gobe kuma Yayah? ni fa yau 'din nan nake so... tun fa 'dazu banci komai_ _ba kuma yanzun yunwa nake ji shi nake son sha_ " Sosai ta marairaice tayi kalan tausayi ha'de da shagwa6a, Abbas yanzun kam ido kawai ya zuba mata har ta kawo k'arshen maganar tata, yanda tayi 'din sai ta bashi tausayi har ransa amma daya ke yana ganin kamar iskancin nata yayi yawa sosai ne da har zata ambaci abinda tasan sai an nemo shi da wannan daren.... sai shima ya ha'de rai a cikin ransa ya tambayi zuciyar sa. A ina zai samu? Yaso ya balbale ta amma daya tuna halin rigimar ta sai ya saki wancen layin dan baya so abin yayi tsayi. Cikin natsuwa yace da ita " _Zahra da wannan daren ina zan samo miki wannan abin plz....ina ce ni dake ne a gidan tun 'dazu me yasa baki fa'da min tun 'dazun ba an nemo miki_ _kika bari har sai da daren nan ya kike so inyi ne ke kam? Ki duba fa almost 9mins to 10 ki ringa abu da lissafi plz_ ? Sai cewa tayi " _ai d'azun bana so ne, yanzu ne na fara son sha_ " " _Hmm_ " kawai Abbas yace yana kallon ta tsawon da'ki'ku yana tunanin halinta, yarinyar nan is so rude sosai abin yake bashi haushi........sai da ya gama karantar yanayin ta sannan yace " _owk...naji aike ka'dai ce kika isa da haka amma ki bari idan Allah ya_ _kaimu gobe insha Allahu zan kawo miki har sai ya_ _ishe ki_ " Yayi maganar da sigar lallashi dan har ga Allah shi ba son fita yakeyi ba a wannan lokacin. Teemah kam da jin ya ambaci goben sai ta sanya masa kuka ta taso ta dawo gefen sa ta zauna ta kama 'dayan hannun sa ta rungume shi ajikin ta tana squeezing 'dinsa tana fa'din ita yau take so dan Allah ya nema mata" Hayaniyan kukan ta da kuma na TV sai ya sanya shi cikin wani hali sosai ya nemi nutuwar sa ya rasa. Allahn da take ta ambata cikin maganar ne yasa shi fahimtar dagaske takeyi, sai ya kai 'dayan hannun sa ya 'dauko remote ya rage volume 'din TV sannan ya samu 'dan nutsuwan rarrashin ta yace " shikenan.....ba fresh milk kike so? Sai ta 'daga kai Yace "Ai akwai a fridge kin manta akwai wanda nakawo jiya?" Sam shima ya manta ne har ya bar ta tana ta masa rigima. Ga mamakin sa sai yaji tace "ai nasan da shi ni ba irinsa nake so ba" Abbas kwafa yayi yana kallon ta sai yace "Yanzu dan ba kya sona sai ki yadda na fita da daren nan? Shiru tayi masa kawai tarasa mai zata ce, ganin haka sai ya fara 'ko'karin mi'kewa yace "bari inje to, amma idan kika ji shiru ban dawo ba babu ruwana nikam kinji" Zuciyanta ne ya tsinke da k'arfi wanda take Mahmud ya zo ranta sai ta rintse hawaye ya sau'ko mata sirara take kuma sai ta sake bu'dewa ta sau'ke su akansa lokacin ma har ya kusan barin dakin ba dan ma girman da parlourn ke dashi ba da tuni ya 6acewa ganinta. "Yayah! ta ambata sai cak ya tsaya tare da waigowa a hankali ya dubeta hasken TVn dake haskawa ne yasa yake ganin ta da hawayen ta. Sai ta tashi da gudu taje ta rungume shi shima take ya sar'ke hannun sa ajikin ta. Teemah a hankali ta furta " don't leave me please Yayah kaji, na fasa shan milk 'din just stay with me" Abba bai yi magana ba sai ya sake hugging nata tied. Shiru ne ya 'dan ratsa wajen na tsawon mintina sannan Abbas ya fara 'ko'karin rabata da jikin sa Teemah kam ta zaci tafiyan zaiyi dan haka sai ta'ki sakin sa cikin muryar kuka tace "....Yayah...plz...dnt go" "I ll not Zahra i'm here with u kinji? Jin haka ne yasa ta sakin sa sai ya kama hannun ta suka koma suka zauna hawayen ta share mata batare da magana ba while takasa daina kukan wanda tunanin rasa shi yasa hawayen kasa tsayuwa mata. Fuskarsa ya matsar kusa da nata sai ta lumshe idanu a hankali sai ya ha'de bakin su. Tsawon mintina biyu yana bata passionate kiss sannan ya saki bakinta sai ta komar da kanta ta kwantar jikin hannun sa. Abbas murmushi yayi yace " kukan fa na menene bayan kin requesting abu kuma zan miki nd why all dis? "Nafasa" tace a hankali. Sai yace "dalili" Cewa tayi "Saboda bana so ka tafi ka barni" "Karki damu zan dawo ai bazan da'de ba kinji" "Nidai ah ah" tace tare da tashi ta zauna ta fuskance shi. ".....i insist" Baki ta dano gaba tana kallon fuskar shi tare da 'kif-'kif da idanuwa. Sai yayi murmushi Yace " wai me kike tsoro ne tell me?" Cike da shagwa6a tace "ai kaine kace in katafi bazaka dawo ba" "Hmmm.... matsoraciya kawai...ni ai wasa nakeyi miki, kuma ma in kina tsorn hakanne an gaya miki akwai abinda yake shiga tsakin rai da mutuwa ne?....abu 'daya ne shine lokaci bayaga haka kuwa...."sa ya juya kansa left& right yace " babu wani abu...ki bari yanzu zan dawo kinji insha Allahu zan kawo miki" Yana fa'din haka sai ya mi'ke Teemah da sauri ta kamo hannun sa ta ri'ke tare da sau'ke hawaye tana jijjiga mai kai idanun su cikin na juna. Abbas sai ya koma ya zauna gefen ta sannan ta saki hannun sa, sai ya kalli hannun sannan ya kalle ta hawayen ta har yanzu hawayen ta na cigaba da gudu. Sai ya sa hannun sa yayi knocking goshin ta kad'an yace " ur sturbborness is always increasing....oyah stop crying nd tell me how u ll miss me when i'm not around" 'Kirjinsa ta fada tare da kai masa bugu a hankali cikin shagwa6a tace " ni dai ba ruwana" Murmushi Abbas yayi wanda har ha'koron sa suka bayyana. A saman la66ansa yace "silly girl" Sannan ya kai hannun sa akan batanta yace "kin san wani abu? sam bana son kukan nan nd seriously bana son ki haifi baby mai irin kukan ki, i need a little soldier just like me a hero nd my little princess" Murmushin yasata itama dan jin dadin wai duk ita zata haifi wannan harma bata san lokacin da bakin ta ya furta "Yayah to yaushe zan haihu? Abbas cewa yayi "Tashi in gaya miki" yana maganar yana 'dago ta daga jikin sa. Dariya tafara a hankali tare da k'ank'ame shi sosai. Shima Abbas dariyar yayi sannan shiru ya dan ratsa wajen. Abbas ne ya yanke shirun da fa'din " "tashi ki mi'ka min phone 'dina" Tashi tayi ta 'dauko wayar ta bashi sannan ta koma gefensa ta zauna tayi shiri tana kallon sa ganin ya maida hankalin sa ga wayar. Numbern wani friend dinsa ya 'kira wanda shima yake nan cikin barikin, sun rabu dazu da yamma akan zaije night party 'din wata babe 'dinsa dake birthday yau a hotel. Christian ne shi kuma bashi da aure sunan sa Samuel amma da Sam ake 'kiran sa. Koda Abbas ya 'kira shin kuwa tambayar shi yayi ko ya dawo sai ace "ah ah but he is about to" Abbas bayani yayi masa na abinda yake so 'din da sunan shi tare da sanar dashi inda zai mu nan kan hanyar da zai 'dauko zuwa gida ba sai yayi yawo ba. Take Sam ya yi masa al'kawarin siyowa sannan sukayi sallama. Abbas nada tabbacin matu'kar samuel ya samu dama zai cika al'kawarin sa musamman da yake cewa ya san baya shan hiya so cikin hankalin sa zai dawo. Bai wuci 40mins da yin wayar ba kuwa sai wayar sa ta 'dauki 'kara, ganin Sam ne sai ya tashi tare da 'daukan wayar ya fita harabar block 'din nasu wanda anan ya hadu da Sam, hannu suka sha sannan ya bashi sa'kon. Abbas sosai yaji da'di, koda ya ciro kudi ya bashi kuwa Sam 'kin kar6a yayi kawai yayi gaba abinsa. Abbas ma sai ya koma ciki yana 'kara maimaita tunanin abin a ransa, murmushi yayi 'dan ta k'aitacce yace " _Zahra rigima_ "! Teemah kuwa duk da haka sai taso ta kawo masa rigimar ita ba na company take so ba ai ta gaya mishi, sai yace "yanzu kam sai kizo ki tsotse ni Zahra k'ila hankalin ki zaifi kwanciya tunda ke ba'a miki gwanin ta, banyi kokari bane ko da da daren nan a ina zan samo miki wancen?" Ita kanta tasan hakan amma daya ke tasa ba rigimar ne shiyasa. Ciki-ciki take mita akan maganar daya gama yi yanzun wanda ita ka'dai tasan abinda take cewa Abbas kam share ta yayi yaci gaba da al'amuran sa. Dan haka sai ta sa hannu ta 'dauki wanda ta ciro da farko 'din ta bu'de a hankali ta 'danyi tasting. Sosai taji ya ratsa mata zuciyar ta, baran ma sassanyan k'amshin da yake yi gashi da kauri sosai ai sai taji yama fi na asalin da'di. "Nagode Yayah" tace masa tana murmushi sai ya kauda kai yace "yi ki gama ni dai kiji dani" Bata tanka ba sai ta cigaba da shan abinta kamar wasa sai gashi ta tada roba guda ta kuma ciro wani wanda ko rabin sa ma bata shaba sai bacci yayi gaba da ita. Abbas duk na lura da ita, harta yi baccin, kai ya jijjiga kawai daya kalle ta aransa yace "sarkin rigima, bayan tace tafasa kuma da taga an kawo kuma harda mita" Sai da ya gama kallon abinda yake yi sannan ya juyo gareta, tana daga zaune ta kishingi'da a hakan kuma tayi baccin. Kiss ya bata a bakin ta yana 'dan murmushi. Teemah sai ta 'dan motsa ka'dan. Shima sai ya 'dan ja baya dan kar ya takura ta, sauran fresh milk 'din ya 'dauka ya je ya sassaka mata su cikin fridge sannan ya 'dauke ta ya maida ta bedroom ya kwantar da ita sai kuma ya sake dawowa parlourn ya kakkashe komai sannan ya koma shima ya hau shirin bacci. ***** Har kwana biyu bayan haka Teemah bata 'kara neman wani abu ba, sai dai ta kanyi da kanta idan taji tana so. Duk ranar da tayi wani abin kwa'dayin to dole shima yake ci dan bata sake yin wani abincin kuma, wasa-wasa har Abbas ya saba da irin cimar tata dan in dai tayi sai ta ajiye masa, tun yana 'kinci har dai ya saba shima dan ma da rana ne tafiya yi masa hakan da dare kam zagewa takeyi tai tayi masa girki mai rai da lafiya wanda tasan ba zai ci da takaici ba. Girki salo-salo.kuwa duka ta iya su, kuma ko a TV tgaa anyi kalan girki bata wasa sai ta gwada shi tagani in tgaa yayi kyau sai ta ta jin da'di shikenan daga lokacin kuwa ko a wani akace ta koya toh zata iya. ***** Ranar ya kasance saturday ne tun bayan da sukayi sallar asubah suka yi karatun al-kur'ani sai ta koma gado da niyyan koma wa bacci, Abbas ne ya hana ta baccin dan shima dawo wa yayi kusa da ita ya fara aika mata sa'konni, tun qcikin idanun sa ta fahimci sauyi tatare da shi, daya ke kusan kwana uku kenan yau bai samu kanta ba, ita kanta tana jin kewar sa amma kawai take basarwa. Sosai Abbas yau 'din ya rikitata da salo da tsarin sa na zallar 'kauna da soyayya wanda ke tafiyar gangan jiki da zuciyan duk ma'abota soyayya, ita kanta sai da tasan cewa mijin ta cikakke ne, gwani ta kowani 6angare domin sosai ya tafiyar da 'kananun matsaloli da damuwar dake cikin zuciyar ta, Abbas bai barta ba har sai da ya tabbatar da cewa ta 'dauki darasin sa kuma irin 'daukan nan ma mai wuyan mantawa. Sai bayan da komai ya lafa kafin suka koma bacci baya sun tsarkake jikin su. Shine ya riga ta tashi in da ya tashin a hankali dan kar ya tashe ta, A gadon ya zauna daga gefen ta 'kafar sa 'daya na 'kasa yayin da 'dayar ke lan'kwashe daga saman gadon ya zubawa system idanun sa. Around 10:04am itama ta farka daga baccin ganin shi zaune a gefen ta yasa tayi luf daga kwancen tana kallon sa. Jikinta da wata riga ce pink mai dogon igiya daga gaba wanda aka saka igiyoyin ya zama tamkar bottle, sai ya kasance shine ya tare gaban rigar ya hana aga jikin ta, daga rigar kuwa babu komai ciki dan ko bra bata sanya ba, wandon skinny ne daga 'kasan ta shima pink mai zanen flowers a jiki sosai kayan suka yi mata masifar kyau ta koma tamkar 'yar yarinya. Abbas ne da kansa ya za6a mata kayan yace shi zata sanya ajikin ta kuma shine ya siya mata dan ganin kamar zai mata kyau wani ranar da suka je shopping tare da shi. Gashin kanta har yanzu babu kitso sai ta kama shi ta 'daure da ribbom kanta babu 'dan kwali. Kallon sa take yi tana sakin 'kayataccen murmushi, daga zuciya har ga6o6in ta take jin masifaffan son mijin ta na ratsa mata, tana jin kamar duk duniya ita tafi kowa son shi, bata kuma 'kaunar ganin ranar da za'a ce yau ya kasance da wata matar wacce ba ita ba bata ko 'kaunar wannan irin hasashen. A hankali ta bu'di baki tace "Yayah ina kwana?" Sai da 'dago ya kalle ta sai ya sau'ke ajiyan zuciya kafin ya amsa mata da " lafiya Fatan komai normal?" Ya 'karasa da murmushi, itan ma murmushin tayi tare da 'daga masa kai. Sai da ya gyara zaman 'kafafun sa da kyau inda duk biyu ya hawo da su gadon ya mi'ke straight tare da 'dora system 'din akai sannan ya cigaba da dubawa. A hakan suke 'dan ta6a hira sama-sama idanun sa na kan system 'dinsa. Cikin hirar ne yake mata mitan rashin kitson nata har ma yace zai nemo inda za'a samu musulmai masu kitso suyi mata. Shiru ne ya biyo bayan maganar tasa, saboda ita abinda yake ranta daban ne a dai-dai wannan lokacin, tunanin pepper soup 'din da Ummah take kawo mata sa'ilin da baya nan ne yazo ranta take kuwa taji matsanan cin kwa'dayin cinsa ya bijiro mata. A hankali sai ta d'aga kanta ta dawo dashi kan 'kafar sa ta lafe luf, ta 'kira sunan shi a hankali har sa jan sunan tamkar bata so tayi maganar. Abbas yaji ta amma sai yayi shiru bai amsa ta ba dan so yake ta 'kara saboda yanda yanayin maganar tata ya ratsa masa kwanya sosai tsigar jikinsa ta ta shi. "........Yayah! Ta sake fa'di a hankali cike da shagwa6a. Sai ya amsa ta da " Uhumm ya akayi ne?" Yayi maganar batare da ya kalleta ba. Teemah kam bata damu ba sai ta cigaba da fa'din "Lokacin da baka nan katafi course ko kullum Ummah na aiko min pepper soup mai da'di na hanta" Abbas sai cewa yayi " Ummah ta kyauta sosai, Allah ya biyata" Itama Teemah da "Ameen" ta amsa sannan taci gaba da fa'din " kasan wani abu?" Yace " ah ah, sai kin fa'da min" Teemah sai tace "Shi fa nake son in ci yanzu" Tayi maganar cikin marairaita. Abbas kwafa yayi yana duban bayan kanta da mamaki, zaton sa ko tsaban ta tsokane shi ko kuma taji bakin sa ya sa ta 'kirkiro wannan maganar, in ba haka ba miye ala'kar wancan lokacin da wannan ko de ta manta garin da suke ne a yanzun...... Wannan tunanin ne yasa shi fa'din "Sai ki ci mana to Zahra tunda shi kike so ko na hana kine?" Da gangan ya fa'di hakan ba dan komai ba sai dan cewa da akayi "silly magana or tambaya need silly answer" Daga nan ya maida idanun sa kan system 'din yana tunanin yau kuma da wannan zata hana shi natsuwa, sarai yasan halin ta idan ta riga ta furta abu to matu'kar ba samu tayi ba bata ta6a natsuwa balle shi ma ta bar shi ya rintsa, sosai abin nata ya fara isan sa, sai a ciki- ciki ya 'karasa da fa'din " ni kam wannan abin idan cuta ce hakan Allah ya yaye miki?" Sam baya son hayaniya a kansa amma 'karfi da yaji sai da ya saba da nata, balle ma ita da ta ha'da hayaniyar harda tsirfa da fitina. Kuma yasa a ransa cewa dole ne suje ganin likita domin a san mekecdamun ta har yake sata hakan, bawai dan ya gaji da kashe ku'din sa ko kuma ya gaji da halintan ba ah'ah sai dan kawai yaji musabbabin hakan tunda yasan ba halinta bane wannan tsirfe-tsirfen, sam bai san inda ta aro hakan ya ya6a shi cikin rayuwar ta ba. Teemah kuwa data ga yayi shiru ya shareta bayan abinda ya gama furtawan sai kawai ta sanya masa kuka tana fa'din "Allah Yayah ni fa yunwa nake ji kuma pepper soup 'din Ummah nake son ci......" Tana mai cigaba da sheshshe'ka tayi maganar cike da sakalci da shagwa6a. Kallon "kin isheni" yayi mata tare da ha'de ransa amma hakan bai wani yi tasiri ba dan tana ganin hakan ma sai ta 'kara sautin kukan ta fiye da na baya kuma still kanta na jikinsa. Abbas system 'din ya rufe da 'karfi dan takaici sannan ya kalle ta, sosai ya tsani kukan nata baya so ko ka'dan amma bai san meyasa rigimar Fateeemah ya kasa barin ta ba har yanzu sam ita bata sanin girman ta. Wani lokaci idan tayi masa wani abin ji yake as if tafi kowa wayo a duniya amma kar kaso kaga wurin rigimar ta har sai ta hana shi natsuwa da sukuni idan ta fara domin kuwa 'daga masa hankali take yi ta kuma hana kanta samun natsuwa itama. Ganin bata da niyyan sararawa sai ya kai hannu da niyyan kamo hannun ta dan ya lallashe ta, Teemah kam sai ta fisge hannun nata da 'karfi ta kawar gefe tana jin in dai ba cewa zai yi zai kawo mata ba to ita babu ruwan ta. Yanda tayin sai ya bawa Abbas haushi take sai yaji wani iri a ransa, gashi har yanzu bata daina kukan ba sai ma 'kara volume ta keyi duk ta cukuikuye shi sai ya rasa yanda zaiyi da itama gaba 'daya he had no choice than ya bu'de mata idanu dan haka da 'dan 'karfi yace " Wai ni kam ni na saki jin yunwan kika dameni haka? ba fa na son iyayi ina gaya miki" Itama Teemah kamar an fizge ta sai tace "kaine mana kaine kasani jin yunwa.....kuma sai nacgaya ka da Daddy tunda kullum masifa kake min" Shiru yayai yana kallon ta tana ci gaba da kukan ta wanda maimakon ya ragu "ah ah sai ma 'karuwa da yake yi akan nada. Wata uwar tsawa ya daka mata wanda har sai da ta firgita in da yace " Shut up da Allah! Haba ths is too much, abincin da ba yau akayi ba not even yesterday shine zaki wani ce shi kike son ci? A ina zan samo miki bacin kinsan Ummahn ma kanta ba nan take ba? For God sake Zahra ki barni na huta ki sarara min dan Allah......in ba haka ba zaneki zanyi idan kika isheni.......baga can kitchen ba kije kiyi duk abinda kike so mana ko tsabar kin raina ni ne yasa kike yi min hakan.......?" Teemah kam cak kukan ta ya tsaya tun lokacin daya fara masifar, sanadiyyan wani motsi da taji a cikin ta na ban mamaki da bata ta6a jin irin sa ba tun da tasan rayuwar ta. Taso ta share amma da taji wani motsin na biyu tamkar an harbe ta a cikin ai bata san lokacin data tashi ta zauna ba dafe da cikin nata ta furta " Yah ilahi...Yayah cikina motsi yake yi...., na shiga uku mutuwa zanyi inaga ni kam" Sai ta 'kara sanya wani sabon kukan. Wannan dalilin ne ya sanya shi yanke masifar da yakeyi shima ya dawo da hankalin sa gareta da mamaki ya 'dage gira 'daya sama take kuwa salon maganar tasa ta canza da tambayar " Motsi kuma kamar yaya? Yana 'ko'karin dafo cikin ta nata shima yayi maganar. Cikin kukan tace dashi "Allah ni...ma bansani ba Yayah.... ji naimyi cikin na harbi na ni kam mutuwa zanyi Yayah pkease ka taimake ni" Abbas take jikin sa yayi sanyi dajin irin kalaman nata wanda daga ji ma kasan iya gaskiyar ta take fa'di ba'a baki bane kawai, domin yanayin 'karyar ta ma daban ne. Dan duk wanda yasan Teemah toh yasan cewa bata fiya 'karya ba ita balle wannan da yasan cewa babu mamaki in dai cikin Teemah ne abinda yafi haka ma zai yi ko dan abubuwan data ke yawan 'dirka masa. Tsaban yanda ta tsorata da abin kallo 'daya zaka yi mata ka fahimci a firgice take motsin kirki ma 'kinyi tayi hannun ta dafe da cikin ta har yanzun tana kuma sau'kar da hawaye. Tashi yayi ya tsaya yana kallon ta ita kuwa kanta a 'kasa. Yana gwada kaiwan hannu jikin ta sai tayi saurin fa'dawa jikin sa ya rungume ta, itama ma kuma haka. Chance ya bata ta sha kukan ta shi kuma ya sa hannu acikin yana shafawa a hankali take wani tunani yazo ransa jin taurin dake marar ta ya 'karu fiye sa wanda ya taba ji kwanaki. Yin tunanin keda wuya sai ya cire ta a jikinsa ya ri'ke gefe da gefen kafa'dun ta yace "let's go to d hospital Zahra we need to see........" "Yayah.... Zatayi magana ya tare ta fa'din " shiiii.... Sai tayi shiru dan dole "Oyah hurry up canza dressing ina jiran ki now" *~_UR COMMENT IS GETTING LOW KO HUTU KUKE SO_~* ❓ _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/13, 8:01 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ _2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍 *Allah ya raya mana Princess Fatima, Allah ubangiji ya haskaka rayuwar ta da hasken sa yasa cikon addini ce.(Ameeen)👏🏻 @ Dr. khausar* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _A *true friend* sees d 1st tear, catches d 2nd one nd stops d 3rd.....they ar not d ones who ar there when it’s convenient only...... *True friends* ar also there when it’s not...Hold a true friend nd don't ever let them go coz *True friend* comes just once in a lifetime._ 🤞🏻 🅿 *92* Abbas ma bai fiya barin ta tana shan za'ki ba saboda an gaya masa cewa hakan nada illah musamman ga mai ciki irin ta. Koda ya koma office kuwa baya yin cikakken 1hr ba tare da ya 'kira yaji lafiyar ta ba. Matan blocks 'din su ma na nan-nan da ita musamman saboda karamcin Abbas a wurin su. Bata aikin komai sai yi masa girki, duk kuwa da cewa tana son yi 'din amma Abbas hana ta yin komai yake yi sai dai wani lokacin ta saci jiki tayi idan taga baya nan. Amma da kansa yake yin komai a gidan. Matan block 'din su ma da yake yawancin su manyan mata ne so sai suke tausayin ta da ganin 'kan'kantar ta, su kansu duk ranar da sukayi katari da ita ta 'dauki tsintsiya hana ta suke yi. Cikin ta na da wata bakwai sannan ta sanar da Hannah a chat dan sosai zuciyar ta ta kasa daure rashin sanar da Hannah labarin cikin, duk iya 'ko'karin da ya kamata tayi amma ranta yakasa sakewa, inda suna cikin chat tace da ita " Hajiya ki fara shirin raino fa dan Matar Yayah nada ciki har na tsawon wata bakwai" Hannah kam wasa ta 'dauki abin dan haka sai itama tace " wacce matar Yayahn kenan kike magana? Kinsan ai ni bansan ya 'kara yin aure ba". Teemah bata ba ta amsa ba sai kawai ta 'kirata video call tana murmushi ta nuna mata cikin. Hannah mamaki, murna da farin ciki gaba 'daya sai suka hanata magana ta bu'de baki kawai tana kallon ta. Teemah ma kallon t take yi sai dai ita murmushi ne akan fuskar ta mai sanyi. Hannah nuna ta tayi tace wai dagaske ciki ne a jikin ki?" Teemah cikin ta k'ara nuna mata tace " ga zahiri kuwa kina gani Hajiya" Hannah ihun murna ta sanya tare da tashi ta nufi wurin Ummah tana 'kwala mata 'kira. Da sauri Teemah ta yanke 'kiran tare da kashe wayar ma gaba 'daya tana dariya. Taso ta 'kyale Hannah kawai sai dai taga suprise 'din baby kamar yanda take ganin take-taken Yayah, amma sai ta kasa jurewa saboda sam bata ga dacewan ace har tana da cikin daya kai ciki amma Hannah bata da labari ba. B'angaren Hannah kuwa tana isa wurin Ummah ta dago wayar tana fa'din " Ummah kalla kiga abin mamaki, Fateemah na da babban ciki tace min har ya kai 7months....." Gani tayi Teemah bata kan layi sai ta sake gwadawa amma baya tafiya, ta kira voice call shima akace mata switch up. Ummah kuwa gaba 'daya hankalin ta ta tattara ta mayar kan Hannah jin ta kusan samun jika, ganin Hannah na jan tsaki ne yasa ta tambayar ta " meya faru?" Sai Hannah tace " Wallahi Ummah kinga tayi disconnecting call 'din kuma na 'kira baya tafiya" Ranta duk a jagule tayi maganar ga dukkan alamu bataji da'din hakan ba. Ummah cewa tayi " amma kin tabbatar cewa cikin na ajikin ta?" Sai tace " Allah dagaske ciki ne Ummah ai ta nuna min kuma tace har 7month......" Taranta Ummah tayi da fa'din shikenan naji 'kira min mijin nata, tunda isheshshe ne shi wato har yayi wayon 6oye min abu irin wannan ko? 'Kira min shi da sauri zai zo yasame ni ne" Hannah ba tayi magana ba sai ta hau 'kiran nashi wayar amma cikin rashin sa'a sai na shin ma bai tafi ba. 'Dago wa tayita kalli Ummahn sannan tace " ba fa na samun sa Ummah shima 'din" "K'yale shi zuwa anjima may be za'a same shi" Hannah kam kasa hak'ura tayi ta ringa gwadawa nashi da na Teemah amma gaba d'aya ya 'ki shiga, abin ya 'kona ran Hannah sosai jitake tamkar tayi tsuntsuwa ta taho Ports a lokacin kawai dan taga Teemah. Teemah kuwa bata sani ba ashe da gangan Abbas ya'ki sanar mawa Ummah gudun kar ta uzzura masa akan ya maida ita gida dan yasan Ummah najin wannan labarin ba barin sa zata yi ya runtsa cikin kwanciyar hankali ba. Shikuwa yanzun sam baya so yaga yayi nisa da iyalin sa ba ma ya 'kaunar abinda zai kawo rabuwar koda kuwa menene shi. Sosai yake so ya cika rayuwar ta da zallan 'kauna da soyayya. Hatta hakkin sa da ke kanta daya zama dole ma daina kar6a yayi dan gani yake tamkar abin zai yi mata yawa ne, musamman ma da yake ya san kansa yanda yake galabaitar da ita a duk lokacin daya kusanceta shiyasa ma ya sau'ke mata wannan nauyin, sosai yayi 'ko'kari wajen ganin ya danne nashi bu'katan, in dai ba ita ta nema ba da kansa kam baya ta6a kusantar ta kuma itama Teemah yanzu da sau'ki ba sosai abin ke motsa mata ba sai tayi sati biyu zuwa uku ma bataji wani abu ya dame ta ba game da hakan, itama kuma bata sanyawa ranta damuwa ba musammn data ga cewa shima baya ra'ayin hakan sai itama take 'ko'karin binsa akan yadda yake so 'din duk da bai fito fili ya gaya mata dalilin daya sashi yin hakan ba amma tasan dai ba zai ta6a yin abu dan ya cutar da ita ba. Har kusan 2hrs Hannah bata gaji da 'kiran layin sa ba dan yanda ta 'kagu ta tabbatar da labarin, ga Ummah ma da nata masifan a gefe, da 'kyar suka same shi a nashi wayan har sai data sau'ke ajiyan zuciya data ji ya shiga, da murnar ta ta mi'kawa Ummah wayan tare da fa'din "yesss ya shiga Ummah". Ummah kar6a tayi da sauri ta sada wayar da kunnan ta da fatan Allah yasa abinda taji daga bakin Hannah ya kasance gaskiya ne. Abbas na office yaga 'kiran Hannah, bai san dalili ba amma haka kawai sai yaji zuciyar sa ta tsinke bawai dan basa waya ko bata 'kiran sa ba ah'ah, dan ko jiya ma sun gaisa da ita a waya amma haka kawai yau 'din ya tsinci kansa da fa'duwan gaba ganin 'kiran ta. 'Dauka yayi sannan ya kai kunnan sa, ba halin sa bane fara yin magana idan zaiyi waya matu'kar bada iyayen sa bane amma yau 'din sai yaji bakin sa ya furta sallama. Muryar Ummah yaji ta amsa sallamar tare da fa'din " Muhammad kaji kunya kai kam" Kai Abbas ya sosa duk da bai san laifin sa wurin Ummahn ba da har ta fa'di hakan amma sai yaji shi wani iri sai yace. " Afuwan Ummah, barka da war haka" Ummah bata bi ta kan gaisuwar tasa ba sai cewa tayi "Ina 'yata take?" Amsa ya bata da fa'din " tana gida Ummah ni na fita aiki ne". Ummah sake cewa tayi "Ina fatan dai lafiya take?" Sai yace "Ehh Ummah lafiyar ta 'kalau" " to masha Allah, yaushe zaka dawo min da ita gida dan gaskiya banaso ta haihu cikin inyamuran nan?" Cike da mamaki ya zaro idanu tare fa'din " haihuwa kuma Ummah? waye ya sanar da ke ciki gare ta?" D'an 6ata rai Ummah tayi tace da shi " Ni bana son shashanci Abbas tambayar ka nayi answer me kawai". Abbas sai ya lumshe idanu tare da shafo kansa sannan yace " Ummah ki bari watan haihuwar yayi mana sai in kawo ta...". Tun ma kafin ya idasa rufe bakin sa Ummah ta tareshi da fa'din " ban amince sam kama canza shawara" Shiru yayi yana jin wani iri a zuciyar sa tare sa tunanin yadda zai 6ullo mata, Ummah kam ganin yayi shirun ne yasa ta fa'din " ni dai ina jira nan da 2weeks in ga 'yata a gefe na, in ba haka ba kuwa zaka sha mamaki na Muhammad, domin da kaina zanzo har Rivers 'din in 'dauko ta". Ummah na gama fa'din haka ta yanke wayar ba tare da ta jira jin na bakin sa ba, dan ma abin ya ha'du mata da farin cikin jin labarin cikin shiyasa ma masifar batayi tsayi ba. Abbas kam da kallo ya bi wayar tare da mamakin inda Ummah tajiyo wannan labarin, yasan in ba Teemah ba babu wanda zai sanar da ita tunda kam shi babu wanda ya fa'din mawa. Lokacin daya koma gida sai ya tarar da ita har tayi masa abinci mai 'dan sau'ki, tuwon semo tayi da miyar egussi, sosai yake ya bawa 'ko'karin ta ta wannan fannin, domin shi ka'dai yasan yanda yake ji a duk lokacin daya tarar ta tanadar masa abinci koda kuwa wani iri ne sosai yake appreciating, dan ya fahimci bata wasa da abincin sa musamman data san cewa ba ya cin komai a waje so bata ta6a barin sa ya nemi abinci ya rasa ba, ko da kuwa mai sau'ki tana matu'kar 'ko'karin yi masa kuma yana yabawa da hakan. Haka idan ya dawo a kullum tana 'ko'karin ganin ta tayashi rage kayan jikin sa, a yana hana ta ma amma dole kullum bata barin sa, hatta wanka da wasu abubuwan idan ya kama duk tana taya shi, shima kuma ba laifi lokaci-lokaci ya kan yi mata massaging 'kafafuwan ta dan wani sa'in yana 'dan yin kumburi ka'dan. Sai da ya kammala da cin abincin kafin ya dube ta yace da ita " Ummah ta 'kirani". Teemah na jin haka sai ta zaro idanu waje tana kallansa, take sai ya gane rashin gaskiyar ta sai kuma tace " me tace maka kuma?" Shiru yayi shima ya zuba mata idanu. Duk da bawai yau ne karo na farko da Ummah ke 'kiran sa ba, kusan kullum sai sunyi waya da Ummah hatta ita Fateemah ma suna waya dukkan su da ita amma yanzun kallo 'daya zakayi mata ka fahimci ta shiga wani yanayi da jin 'kiran Ummah. Maimakon ya bata amsar tambayar ta ah ah sai yace da ita " mara kunya....ai na lura tunda kika samu cikin nan kika zama mara kunya kuma shine har da sanar da Ummah cewa kinyi ciki ko?" Kai ta kawar gefe tace " Ni fa bance mata ina da ciki ba". Sai yace " To a ina ta samu labari?" Shiru tayi masa tana 'kara ha'de goshin ta. Sai shine yaci gaba da fa'din " Ni dai let me tell u...idan kika kuskura kika haifamin baby mara kunya ko kuma mara son makaranta ni da kene". Hawaye ta fara tare da mi'kewa ta shige cikin bedroom taje ta zauna dirshan a 'kasan tiles tana zubda hawaye, ji take ranta babu da'di a duk lokacin da Yayah ya ambaci makaranta ko kuma yayi mata gugar zana da hakan, ta so ta yi 'din kamar yanda ya bu'kata amma sam takasa shigar da shi cikin ranta domin koka'dan babu niyyan a zuciyar ta, shiyasa ma ta ha'kura, amma a kullun addu'ah takeyi Allah ubangiji ya cire masa abin a ransa shima ko zata huta da mitar sa akan hakan. Abbas ma tashi yayi biyo bayan ta a 'dakin yazo ya zauna daga gaban ta ya fuskance ta, bai bi ta kan kukan nata ba illah tambaya da ya jefa mata inda ya sake fa'din " waye ya sanar da Ummah cewa da ciki a jikinki ai nasan kece kika fa'din mata". Ya 'karasa maganar tare da 'dage gira 'daya sama. Teemah kam da muryar kuka tace dashi " Ni dai bani bace sai ko in Hannah". Sai yace " ita Hannah a ina taji labarin ?" Teemah shiru tayi kawai tayi 'kasa da kanta wani hawayen na gangarowa, sai shine yaci gaba da fa'din " ai kema kin san tsakanin Hannah da Ummah dole ne idan taji sai ta gaya mata, gashi yanzu tace wai dole sai dai in maida ki Abuja wai bata son ki haihu a nan" Yanayin da ya 'karasa maganar ma kanaji kasan ransa baya son tafiyar koka'dan, amma sai tayi 'ko'kari wajen ganin ta ri'ke kukan da take yi tace dashi " duk 'daya ne ai Yayah da can da nan 'din ba wata matsala". Muryar sa da sanyi yace " kenan kema kinfi son can 'din ko?" Itama a hankali tace " ah'ah fa Yayah ba haka bane....". Sai ya tare ta da fadin " .......haka ne mana, kin fi son ki tafi ki barni ko tausayina bakiji ko?, yanzu fa idan ba kyanan komai ma ni zan rin'ka yi hatta abinci ma babu wanda zai na dafamin......". Bai ma 'karasa maganar ba ta sanya kuka inda cikin kukan tace " Yayah to ya zanyi ni kam, Allah inajin tausayin ka amma ai kaga Ummah ce da kanta ta nemi hakan ba yadda zamu yi ne shiyasa". Hannun ta ya kamo cikin nasa hannun yana murza 'yan yatsun ta cikin natsuwa yace " kawai kice mata ke ba yanzu zaki koma ba in taji daga bakin ki i'm sure zata ha'kura". Kai Teemah ta jijjiga masa tare da fa'din " Allah ni kam bazan iya ba Yayah, Ummah ce fa". Shiru yayi yana kallon ta ko da wasa bai son abin da zai raba su, sam baya son tayi nesa da shi amma kwatsam rana tsaka Ummah ke 'ko'karin shiga tsakanin su, bai san yadda zai yi ba amma gaskiya yana jin tamkar hakkinsa za'a shiga akana hakan, gashi ma tun kafin ranar tazo ya fara shiga wani hali na damuwa. Janyo ta yayi jikin sa ya share mata hawayen tare da rungumar ta a jikinsa sannan yace " kukan fa na menene haka Zahra?, ba kince ba kya son barina ba?". Da kai ta bashi amsa akamar "ehh" sai yaci gaba da fa'din " Kar ki damu kinji, ni duk abinda kike so shi zan miki, so ki kwantar da hankalin ki bana son kukan nan, ko kina son baby yayi miki dariya yace Momcyn shi cry-cry ce?" Kai ta jijjiga tana murmushi sai yace " to oyah wipe all da tears ur husby ll always be by ur side ok..." Da haka ya rarrashe ta har tayi shiru maganar ta wuce batare da sun tsayar da magana 'daya ba. ***** *Bayan sati 'daya* Zaune yake akan dadduma yana karatun al'qur'ani mai girma cikin sautin sa mai dad'i inda yake karanto suratul Anbiya'i. Abbas kenan da hakan ya riga ya zama jinin jikinsa a duk bayan kowacce sallar asubah ya kan zauna yayi karatun sa cikin natsuwa in da watarana suke yi da Fateema wataran kuwa shikad'ai yake abin sa musamman ma yanzu da baccin asubah ke yawan damun ta sanadin cikin. Wajaje 5:30am ne na safe, yayin da Teemah ta tashi ta shiga bathroom dan watso ruwa a jikin ta, domin wani yanayi da take jin kanta tunanin ta ko ruwan sanyin zai 'dan sanyaya mata, da 'dan 'karamin towel 'dinta ta fito 'daure a jikin ta bayan ta watso ruwan ta fito, a hankali take tafiya, da 'dan madaidaicin cikin ta a gaba ya 'dan 'dago daga cikin towel 'din, sai hips 'din ta da ya 'dan 'kara bu'duwa shima da mazaunan ta ta yadda bata isa tayi tafiya ba sai sun motsa. Duk kuwa da ta watsa ruwan amma koka'dan bata nasaran jin wani sauyi tattare da ita ba na daga cikin yanayin ta data keji sai ma abinda ya k'aru, ta rasa mai yasa hakan yanzun bata sani ba ko dan shi baya neman ta ne yake sata itan oho. Zuwa tayi ta zauna a gaban mirror tayi shiru tana kallon sa ta cikin madubin. Abbas dake faman karatun sa tamkar ance ya 'dago sai kuwa suka ha'da idanu ta cikin mirror 'din, Teemah sai ta lumshe ido ta yi 'kasa da kanta a hankali. Abbas kam tuni ya fahimci yanayin da take ciki da suka ha'de idanu, don tuni ya gama karantar ta zuwa yanzun ba sai ta bu'di baki ta sanar da shi yanayin da take ciki ba da kansa ma yake fahimta. Takaita karatun yayi tare da rufe Qur'anin ya dawo inda take ya tsugunna daga gabanta tare da kamo hannun ta ya ri'ke cikin nashi yana wasa da shi. Da idanu tabi hannun nasu sannan ta 'dago da kanta ta kalli fuskar shi. " Akwai matsala ne?". Ya tambayeta idanun su cikin na juna. Sai tayi saurin kawar da nata idanun tare da jijjiga mai kai alamar "ah ah" nufin ta ta 6oye masa damuwar da take ciki. Abbas kam murmushi yayi mata tare da maida hannun sa kan cikin ta ya dora sannan yace " Baby na na son gaidani fa naga yana ta waving min hands". Yanzun kam itama murmushin tayi jin shirgin 'karyan daya shirga wa abinda ke cikin cikin ta da be san mecece rayuwa ba balle ya nemi mahaifin sa. Abbas kam cikin towel 'din ya maida hannun sa wanda har sai da ya sata lumshe idanu dan yanda taji wani irin abu ya ziyar ce ta sakamakon hannun sa da taji kan cikin nata. A hankali ya ringa shafa cikin yayin da Teemah ma tabi kan hannun san da nata hannun suka cigaba da shafa cikin tare suna zuba murmushi, shi kam har 'kasan marar ta yayi da hannun sa a hankali yana mai cigaba da shafawa yana fa'din " Baby na Boss ne da alama tun da har yana yana da wayon son gaidani da sassafen nan" Teenah kam zuwa yanzun shiru tayi tana jin yadda yakeyi matan tasan ba wai dan baby bane kawai. Da haka a hankali ya dawo da hannun sa saman 'kirjin ta sai ma ya janye towel 'din tare da ha'de musu baki, sosai ya warware mata jiki da salon sa kafin ya d'auke ta zuwa kan bed. Abbas sai daya tabbatar ta gama satisfying sannan ya raba jikin sa da nata ya 'kyale ta dan be damu da kansa ba a yanzun, domin yasan ada ba 'karamin 'ko'kari tayi ba wajen 'daukan nashi bu'katun duk kuwa da cewa 'karama ce amma bata ta6a nuna gajiyawa da bu'katar sa ba, dan haka shima yanzun a cewar sa turn 'din sa ne dole zai 'daga mata 'kafa ba zai takurata ba har zuwa lokacin da zata sau'ke nauyin dake jikin ta. Kwance yake a gefenta yana 'ko'karin dai-dai ta nutsuwar sa wanda da 'kyar yake samun hakan domin matu'kar ya kusance ta hankalin sa sosai yake tashi, Teemah kanta tasan hakan har ma ta ta6a yi masa magana sai yayi mata musu ita kuwa ta san ba gaskiya yake fa'da mata ba dan ko be fa'da ba tasan me yake ciki, shiyasa ma cikin kwana kinnan take danne damuwar ta in dai ba abin yafi 'karfin ta bane sam bata bayyana wa cuz bata ga anfanin ya biya mata nata bu'katun shi kuma ya hana kansa ba, bacin ita ba wani ciwo ko wani abu take ji ba da zai hana shi sakewa da ita, amma ta rasa ta yanda za'a yi ya fahimce ta. Ko yanzun ma tana iya feeling yanda gurbin zuciyar sa ke beating so fast, daya ke kwance take bisa 'kirjin sa sai take jin tausayin sa sosai yake kama ta. Sai da ya dai-dai ta kansa ne kafin ya sau'kar da idanun sa kan fuskar ta ya kalle ta. Muryar shi kawai ta jiyo yana fa'din " idan kin tafi Abuja kika barni zaki iya jure rashi na?". Hannun ta na yawo akan fuskar sa dana faman shafa fuskar tashi zuwa gurbin dimple 'dinsa, jin yayai maganar ne yasa ta saukar da hannun ta daga kan fuskar tasa ta dawo dashi k'irjin sa sannan a hankali tamkar bata son yin maganan ta bashi amsa da fa'din " kai ma ai ka juri rashi na Yayah duk da ma ina tare da kai, balle ni ai kaga dole zan iya jurewa tunda na 'dan lokaci ne". Ta karasa maganar hannun ta na yawo akan 'kirjin sa. Zai sake magana yin magana sai Teemah ta jijjiga masa kai, shirun yayi kamar yanda ta bu'kata yana kallon kitson dake kanta. Bazata kawai yaji ta sau'ke hannun ta ajikin sa wanda yasa shi sau'ke ajiyan zuciya ba tare da ya shirya ba. Sosai Teemah tayi 'ko'kari wajen ganin ta faranta masa tare da rage masa abinda yake ji 'din batare da jin kunya ko 'kyan'kyamin sa ba, dan tasan ko da ta bashi dama da jikin ta bayi zaiyi ba, ada kullun inzai kusanceta sai yayi kusan salo a 'kalla kala uku da ita, koda tagaji kuwa sai yayi son ranshi sannan ya barta, sa6anin yanzu da kullun 'daya kawai ya keyi kuma duk tasan saboda condition 'din ta ne yasa. Shima Abbas yau 'din ba 'karamin mamaki ta bashi ba, sosai ta birgeshi ta sanya masa nisha'di a zuciyar sa. Bai ta6a zaton zata iya yi masa irin hakan ba domin bata ta6a ko kwatanta yi mai ba sai yau da tayi surprising 'dinsa, wani gurbi na musamman ta samu ke6antacce a zuciyar sa wanda yake jin babu mai iya ratsa wajen illah ita ka'dai, sosai yaji da'din yanda ta tafiyan tar da shi da bu'katun sa a wannan lokacin. Albarka kawai ya rin'ka sanya mata da har sai da ta rufe mai baki da nata kafin yayi shiru. Haka rayuwar su taci gaba da tafiya kowa na 'ko'karin ganin ya farantawa 'dan uwansa da duk wani abinda zai iya na kyautatawa, zaman su gwanin sha'awa inda suke shimfi'da zallar salon so da 'kauna tare da mutuntaka a tsakanin su. Har watan ramadan yazo ya wuce Teemah bata koma Abuja ba, duk kuwa da cewa kusan kullun Ummah bata gajiya da yi masa tuni akan dawowar tata amma ya kasa kaita sai dai kullun ya ringa bata tabbacin insha Allahu suna hanya. Da haka yayi ta jan Ummah har cikin Teemah ya kai 8months da kwanaki kusan ashirin, wanda a lokacin ne Ummah ta nuna masa 6acin ranta sosai barin ma da Hannah ke 'kara zuga ta a gefe dan itama sosai ta matsu taga Teemah a kusa da ita tana mamaki ita kam wai Teemah ne da ciki abin na bata dariya sosai. B'acin ran Ummahn ne yasa shi fara tunanin kawai gara ya maida ta Abujan, ita kanta Teemah ma ta kan yawaita yi masa magana akan tafiyar amma sai yayi kamar be ji taba, da farko idan tayi maganar yana bata amsa da fa'din " zaki je ai amma sai na shirya tukunna" ko kuma yace " Ina sane da batun karki damu" amma daga baya ma sai ya zamana ko 'kala baya furta mata, ya daina tankata indai akan maganar ne, hatta Anty Leesah na yawan tambayar sa wai " yaushe zata dawo gida? ko can ports 'din zasu je sunan ?" sai dai yace mata " ah ah " kawai a takaice, dayake yanzu Leesah ma ta zama 'yar gida tun lokacin da suka fahimci cewa ita 'din sister 'din Bilal ce shikenan sai zumuncin su ya 'kara 'karfi, ko da akayi tambayar auren Hannah kuwa sai ya zamana date 'din auren su rana 'daya a kasa sanya Leesah da Hannah duk a watan December. Itama Teemah da ta gaji da maganar sai ta kyale shi ganin cewa kullum abu 'daya suke ta maimaitawa. Sai yanzun ne yafara yi musu shirye-shiryen tafiya ganin ya gama tunzira ran Ummah, cikin kwana biyu kuwa har sun gama komai inda a kwana na biyar da yin wayar Ummahn suka dira garin Abuja babban birnin tarayyar Nigeria. Sau'kan su keda wuya kuwa Ummah ta ringa sau'ke masa buhun masifa da 'kyar ya samu tayi shiru, dayake dama fa'dan ba wai na zafi bane kawai na haushin rik'e Teemah da yayi ne acan da kuma wasa da hankalin ta da yayi tayi a banza. Hannah kuwa abin nema ya samu ganin ga ta ga Teemah ga kuma tu'ke'ken cikin ta a gaba. sai da ta gama dariya son ranta da kwatan ta irin tafiyar Teemah sannan tafara gwad'ata wai wlh cikin kyau ya 'kara yi mata tayi fresh skin 'din ta ya 'kara yellow da shai'ki, tace " sai dai kinyi bombom gaskiya da boobs sosai, har da kama baki tace "kai wannan babyn akwai wayo wallahi yana son Dad 'dinsa ya shana" ta 'karashe da dariya. Teemah kam bata damu ba sai ce mata tayi " soon kema ai kina hanya zan rama ne Hannah" Hannah tace " Allah kuwa ba batun wasa anan, inaga ma shiyasa Yayah ya kasa dawo dake gida tuntuni 'din irin wannan kaya haka?, kai tubar kallah!" Murmushi Teemah tayi tace " Hannah ke kam bazaki ta6a canza wa ba, inajin sai ranar da Bilal ya koya miki hankali tukun" Hannah Tace " kamar yanda Yayah ya koyar dake ba, ai naga kin wani nutsu ne duk kin canza ko dai kawai dan ana shirin zama uwa ne?". Teemah sai tace "Bansani ba Hannah kijira naki idan yazo kawai sai ki bani labari" Dariya Hannah tayi tace " ai nawa daban ne da naki kema kin sani...., yauwa ni ya batun birgiman ki? Allah yasa de kin daina dan in ba haka ba yanzu kam sai dai ki koma 'dakin Yayah kiyi ta bajewar ki ke ka'dai da wannan 'katon cikin" Teemah cewa tayi "Zamu gani ai Hannah sai ki kore ni" Murmushi kawai Hannah tayi ta tashi ta fita jin Ummah na 'kwalla 'kiran ta. Washe gari Leesah tazo ta yi musu barka da zuwa, su Hannah sai sunkuyar da kai take yi ita a dole kunya, sai a bayan tafiyar Leesah ne sai Teemah tayi ta tsokanar ta wai mai kunyar iskanci bayan tana ganin yanda take satan kallon ta idan ta juya kai. Hannah tana dariya tace " ai dan tana 'dan kama da Bilal ne shiyasa" Teemah ma dariya tayi tana nuno ta tace " mara kunyar yarinya kawai, wato dan tana kama da Bilal ne shiyasa kike satan kallon ta". Hannah murmushi tayi mai sauti tace " bazaki gane bane matar nan, Allah ina tsananin son Bilal fiye da yanda Yayah ke son ki ". Ta k'arashe da zolaya. Teemah kuwa take ta tare ta da fa'din " kar ma ki fara yaudaran kanki da wannan 'karyan, an gaya miki soyayyan Yayahn irin naku ne?" Hannah 'kin yin magana tayi sandiyyan ganin Abbas tsaye a bakin 'kofa sai kawai ta fara 'kif-'kif da idanuwa Teemah bata san me ake ciki ba ita kam har sai da ta gama fa'din me zata fa'da ta mi'ke sannan ta ci karo da shi a tsaye. Hannah tasowa tayi ta nufi 'kofar fita daf da shi sai tace " Ina yini Yayah?" Da " lafiya" kawai ya amsa ta kamar yadda ya saba. Teemah da idanu ta bi bayan Hannah har ta bar 'dakin sannan ne ta dawo da kallon kan Abbas, sanye yake da dogon wandon jeans da armless shirt, sosai kayi suka amshi jikin sa. A hankali ya tako zuwa inda take ya zo ya tsaya a kanta batare da yayi magana ba. Teemah 'daga kai tayi ta kalle shi suna ha'da idanu sai yayi sama da girar shi tan 'ko'karin sau'kar da idanun ta sai ya sa hannun 'daya ya 'dago ta tsaye ran'kwafowa yayi ya rungume ta baya hannun sa ya kai kan cikin ta yayin da kansa ke a wuyan ta saitin kunnan ta a hankali ya furta " na ji ana gulma ta!, laifin me na aikata kuma?" "Ba komai" Ta ce da shi itama cikin sanyin murya. Kiss ya sau'ke mata a kunnan tare da fa'din " ban yarda ba " Sai tace "Da gaske Yayah ba komai......" Maganar tata yankewa yayi sanadiyyan cizon dataji ya sake mata a kunnan sai ta 'karasa da fa'din " awshh......Yayah ka cinye min kunne na". Murmushi yayi yace " da zafi ne?" Kai ta 'daga masa masa tana shafa kunnan tamkar zata yi hawaye. Sai yace " tell your sister that dafin son Yayah ya zarce na kowa, bai ma da makamanci kinji?" Shiru tayi masa kawai tana jin yadda yake 'ko'karin kai hannun sa har zuwa 'kasan ta. Ri'ke mai hannun tayi tayi kalar tausayi tare da ro'kon sa akan " please yayi ha'kuri" "Dalili?" Ya ce da ita. Sai tace " Ayyah Yayah gidan Ummah ne fah kuma kaga Hannah na iya shigowa ako wani lokaci" Shima 'din ya san abinda ta fa'dan gaskiya amma duk da haka sai ya'ki sakin ta har sai da ya gama kashe mata jikin kafin nan ya bar 'dakin, Allah ma ya taimake ta har ta gama kintsa kanta Hannah bata dawo ba. Satin Abbas 'daya a Abuja sannan ya koma Rivers, ranar daya koma kuwa a ranar Teemah ta bar 'dakin sa ta koma na Hannah bisa umarnin Ummah. Sosai Teemah ke jin kewar sa musamman lokacin da tazo bacci, dan ta saba bacci ajikin sa yanzun kuwa sai take jin ta wani iri, in bama maganar da Hannah tayi mata akan birgima ba ai ita tuni ta mance da cewar tana yi, dan kullun yanda ta kwanta ajikin sa a hakan take tashi bata ganin ta canza wuri saboda baya raba jikinsa da nata har gari ya waye, so ta ina zata samu damar yin birgima a hakan, yau da gobe kuwa yasa har ta saba da bacci a nutsen especially ma idan tana jikinsa dan ko fa'da sukayi da shi kuwa wannan yanayin baccin nasu baya ta6a canzawa ko ta'ki ma dole sai ta ha'kura saboda ba barin ta zai yi ba. Aranar da 'kyar bacci ya 'dauke ta da tunanin sa a ranta har kuwa cikin mafarki sai da ta ganshi. Washe gari da suka tashi Hannah da yake bakin ta baya shiru sai tace " gaskiya Yayah ya iya displine kin koyi bacci mai kyau, da ai har ina fargaban ki danne ni da wannan 'katon cikin naki". Teemah cewa tayi " ke de kika sani Aku uwar magana, ina nan in da raina watarana sai na rama insha Allahu". Hannah murmushi kawai tayi bata yi magana ba tana tuno cewa wai itama watan watarana sai gata ga ciki. " hmm" kawai ta furta a fili with smile on her face. Zaman Abuja yayi wa Teemah da'di, dan sosai Ummah ke bata kulawa tare da bata wasu addu'o'i tana karantawa kullum, bata da damuwar komai yanzu face tunanin mijin ta da kuma fatan Allah ya sau'ke ta lafiya. Shima Abbas 'din suna waya akai-akai dashi dan a'kalla suna waya a rana kusan sau biyar in dai yana da lokaci baya gajiya da 'kiran ta. Tun lokacin da watan haihuwar ta ya kama sai ya kasa jin kwanciyar hankali, kullum baya bacci mai kyau da dare haka zai 'dau lokaci yana yin sallah yana ro'ka mata ubangiji sau'kin na'kuda, haka ma Mummy ba'a bar ta a baya ba tana iya 'ko'karin ta. Da yamma kullum sai sun fita cikin compound 'din gidan ita da Hannah su 'dan zaga tana warware ga6o6in ta, ko ina kuwa zata da ruwan ta a hannu take tafiya, dan yawan shan ruwane da ita akai-akai yanzun. According to her EDD an ce haihuwar ta zai kama ne zuwa kwanaki takwas masu zuwa ko kuma 'kasa da haka, sannan kuma zai iya haura hakan it's depends basu da tabbaci, kuma duk ba matsala bane. Dalilin haka ne yasa yanzun Ummah sam bata nutsuwa kullum hankalin ta na kan Teemah, hatta baccin dare ma bata yin shi gaba 'daya, ta ringa zarya kenan a 'dakin su, haka ta hana Hannah ma dogon bacci duk wai dan kar wani abin ya taso kuma basu sani ba. ***** Ranar wata lahadi ne wanda ya kasance kwana na biyar cikin kwanakin da aka gindaya mata, kenan idan aka bi lissafin da aka tana da sauran kwanaki har uku kafin cikin EDD 'din ta, shiyasa ma bata damu ba koda taji marar ta na 'dan haura mata da ciwo ka'dan-ka'dan, zaton ta ko zai daina kamar yanda ya saba yi mata dan haka sai bata sanar da Hannah halin da take ciki ba ganin tana baccin ta, shiyasa ma ko motsin kirki ta 'kiyi dan kar ta ta she ta. Zirga-zirgan zuwa bathroom ta fara dan yawan fitsarin dake matsata, in ta je 'din kuwa ba wani abin kirki take yi ba sai dai ta dawo tana cije baki tana tafiya da 'kyar kuma a hankali saboda azaba. Gajiya tayi da yawon zuwa bayin ga ciwon marar nata na k'ara tsanani kawai sai ta sanya kuka a hankali ta dur'kushe daga bakin gado dai-dai farkawan Hannah ha'de da turo 'kofan Ummah a lokaci guda. Da hanzari suka yo kanta Ummah kam sai ta daka wa Hannah tsawan rashin hankalin datayi inji Ummah da yake ta mata warning akan kar ta yadda ta ringa yin dogon bacci saboda irin hakan. Take sai Hannah taja gefe tana rarraba idanu tayi kicin-kicin da fuska. Ciwon Teemah kam kamar jira yake yi yaga idanuwa sai kawai ya tashi gadan-gadan, Hannah ma kuka ta sanya ganin halin da y'ar uwar ta ke ciki kafin kace kwabo har hawaye ya wanke mata fuska gaba 'daya. Ummah fita tayi da sauri taje ta d'auko wayar ta da mayafin ta bata dawo 'dakin ba sai da ta fita waje ta yiwa driver magana, Allah ma cikin ikon sa yasa yau 'din agidan su drivern ya kwana saboda daren da yayi bai koma gida da wuri ba shiyasa kawai ya kwana be tafi ba. Hannah kam sai aikin sannu take ta yiwa Fateemahn gwanin ban tausayi idan ka gansu. Ummah na dawowa sai ta umarci Hannah data ta 'daukowa Teemah mayafi su wuce asibiti. Gefe da gefe suka kama Teemah a hankali har suka fice waje wurin mota inda suna shiga driver yaja suka fice daga gidan. Yayin da Fateemah ke jin ranta kamar zai bar jikinta dan azaba, ha'ki'ka haihuwa ko ka'dan ko yake bashi da sau'ki, babu kuwa wanda zai gane hakan har sai abin ya same shi. Tun da suka je asbiti ake abu 'daya tun 'karfe uku na'kuda yasa ta a gaba da azaba sai ya tashi sai kuma ya kwanta har tazo tayi bacci ma kusan na mintina arba'in sannan ta farka da wani matsanancin ciwon, gaba 'daya Teemah ta fice a hayyacin ta ta gama saduda da rayuwar ta ya 'kare dan bata ta6a zaton akwai irin wannan ciwon a duniya ba, duk jarabar ta da son yara sai da taji bata 'kaunar haihuwa muddin ranta, fa'di take yi kawai " ku cire min wannan cikin wallahi banaso, ku raba ni dashi dan Allah mutuwa zanyi......waiyo kuyafe min dan Allah.....Yayah na waiyo zan mutu..." Tun tana kukan da hawaye har tazo hawayen ya daina fita mata ta koma salati, duk wanda yazo mata yi take yi ko da bata kai 'karshe ba sai ta kamo wani, abin dariya abin kuma tausayi. Hannah kam kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita haka takeji, a ranta take tunanin ashe haka haihuwa take sosai ta tsorata da haihuwa ita kam, lalle uwate abin girmamawa ne dole kabisu, tausayin Teemah gaba 'daya ya cika mata 'kirjin ta har ji take da zata iya data rage mata ciwon. Ummah bata sanar da kowa halin da ake ciki ba hatta Abbas kansa, cuz gaba 'daya hankalin ta na kan Teemah ne yanzun ganin yanda take shan wahala gaba 'daya ta karya mata zuciya ganin na'kudan yayi tsayi. Dai-dai an fara 'kiran sallahn shiga masallacin Asubah abu yataso mata gadan-gadan, bayan ta take jin tamkar zai 6alle biyu, Allah kuwa cikin ikon sa mintina biyu basu cika ba sai ga kukan jariri domin da kukan sa ya taho kamar an doke shi. Yana fita daga jikin ta kuwa Teemah ta fara sau'ke ajiyan zuciya a hankali take furta "Alhamdulillah" har bacci ya 'dauke ta. Sai hamdala kawai su Ummah keyi yayin da Hannah ke farin ciki da guntun hawayen ta a idanu. Abbas na alwala yaji tsinkewar zuciya da bai san dalili ba, dan haka sai ya ringa maimaita _innalillahi wa inna ilaihi raji'un_ har ya kammala alwalar tasa har kuwa ya idar da sallar bai ji zuciyar sa tayi dai-dai ba, kuma ya rasa dalilin da ya kawo hakan, Qur'ani ya 'dauka kawai ya yi ta karantawa har gari yayi haske. Baby lafiyar sa 'kalau, Teemah ce dai ta 'dan samu matsala sai da aka mata aiki amma ba sosai ba 'dan ka'danne daga nan aka yi discharging nasu. Ummah bata 'kira shi ba sai 'karfe 8:00am bayan har sun koma gida ta gama gyaran mai jego da baby inda aka shirya shi cikin kayan sa sky blue sun fito ras abinsu sannan Ummah ta 'kirashi da duk wa'dan da suka dace ta sanar mawa. Abbas ne 'karshe da Ummah ta 'kira, shi kam godiya kawai ya ringa sake wa mahalicci yana tasbihi musamman dayaji cewa lafiyar su 'kalau ita da babyn har ma sun koma gida ai farin cikin sa da'duwa yayi akan nada. B'angaren Teemah kuwa zama tayi gefen yaron ta tana kallon shi tana sau'ke murmushi, wai yau gata ga babyn ta wanda ita ta haifa da kanta, baiwar Allah kenan yawa ne da ita yakan kuma baka ta inda baka zato ko kuma akasin haka, sosai ta ringa gode Allah a zuciyar ta, bazata iya misalta yanayin farin cikin data ke ciki ba a wannan lokacin. Babyn ta tsurawa idanu tana so ta gano kamar sa amma takasa, sam bazata iya iya ce ga kamar yaron ba ayanzu domin kuwa ita bagane kamar jinjiri takeyi ba, shiyasa dole ta ha'kura ta barshi, yatsun 'kafar shi ka'dai ta iya gane kamar su irin ta Abbas ne sak sai dai hasken sa da kamar kam takasa ganewa. Baby baccin sa yake yi cikin kwamciyar hankali, tunda akayi masa wanka yake bacci, itan ma garin kallon shi har bacci ya 'dauke ta a gaban sa, ba ita ta tashi ba sai da azahar. Hannah ce ke gaya mata wai ai Yayah ya yi ta 'kira abata wayar tana bacci kuma Ummah ta hana a tashe ta. Shiru kawai tayi dan wani azaban zafi da take ji tun daga 'kasan ta har zuwa cinyoyin ta. Da 'kyar ta daure ta tashi ta zauna tana cije baki, koda zata tashi tsaye kuwa zafin datajin har sai daya sata sau'kar da hawaye. Matar da ta gani zaune a gefe ne tana bawa jinjirin zam-zam tace da ita " yi a hankali Fateemah, sai kin daure kinji" Wa Hannah matar ta mi'ka yaron sannan da kanta ta tashi taje ta ha'da mata ruwa mai 'dumi a bathtub tace idan ta shiga zauna aciki. Kafin ta mi'ke sai ga Ummah ma ta shigo, tana ganin ta zaune kuwa sai ta washe baki tare da yi mata sannu, Teemah ta amsa sannan ta tashi a hankali kamar mai koyon tafiya ta wuce bayin. Da hawaye ta samu da 'kyar da azaba ta iya yin fitsari, da farko ma tsoron shiga ruwan tayi amma sai ta daure musamnan data tuna first night 'din ta irin yadda ruwan zafin ya taimake ta shiyasa yanzun ma ta daure ta shiga. Sai data yi brush kafin ta fito daga bayin tana 'danjin da'din gabo6in ta ba kamar lokacin data tashi a baccin ba. Tana fitowa kuwa aka gabatar mata da abinci, inda ta 'dan tatta6a ka'dan ta bari domin ba da'din bakin ta takeji ba yunwar ma bata ji tun safe da Ummah ta bata wani ha'd'den tea mai kauri tasha har yanzu bata ji yunwa ba, sai 'kirjin ta dake 'dan yi mata zogi saboda cikar da sukayi. Matar ne tace ko zata bashi yasha da yake tun safe daga zam-zam babu abinda ke cikin sa, take Teemah sai ta jijjiga kai alamar "ah ah" matar ma bata matsa mata ba cuz tayi zaton ko zuwa an jima zata bashi. Kamar wasa kuwa har yamma Teemah bata bawa baby mama yasha ba wai tana tsoro yana mata zafi. Ummah bata so ta matsa mata itama dan haka kawai sai ta bar ta, amma abin na damun ta azuci. Da yamman aka sake yiwa baby wanka yana ta faman kaiwan hannun sa baki yana 'ko'karin tsotsa, tausayin shi sosai yake kama Ummah amma bata san yanda zata yi da Teemah ba sam, ko da aka gama shirya shi sai aka bashi ruwa yasha, yana sha kuwa tale sai ya koma bacci abin sa. Itama Teemah wankan ta sake yi bisa jagorancin wata dattijuwar mata tayi shirin ta cikin riga da zani na atampa tayi simple 'dauri ba na 'daga hankali ba daya ke ma ba wani da'di sosai take ji ba shiyasa powder kawai ta murza a idanun ta tare da sanya kwalli, sai uban turaruka data ringa fesawa ajikin ta kamar baza su 'kare ba. Fita sukayi dukkan su suka bar Hannah da Teemah a 'dakin yayin da ta sa Babyn agaba ta zuba uban tagumi, so da tausayin sa na ratsa ta, sai ta kamo hannun sa ta ri'ke cikin nata tare da kwantar da kanta agafen sa tana kallon fuskar sa, ita kanta tausayin sa take ji sosai amma tana tsoron sa mishi maman abakin shi dan yanda take jin yake yi mata zogi, koda za'a wanke ma da yamman nan har kuka tayi saboda zafi da zogi gashi sai 'kara cika yake yi base k'aramin takura ta yake yi ba. Yayi baccin a'kalla mintina kusan hamsin kafin ya farka, sai kuma ya tashi da kuka, wanda ya rikita Teemah ta rasa ma ko ta yanda zata 'dauke shi dan haka kawai itama sai ta sanya kukan. Hannah ce dake bayi tayi saurin fitowa ta 'dauke shi ta fara jijjiga shi amma kamar ziga shi take 'kara yi kukan nasa sai 'kara 'karfi yake yi ga dukkan alamu an 'kure ha'kurin sa ne. Hannah tayi-tayi da ita ta bashi yasha amma ta'ki sai kuka kawai takeyi. A haka Ummah ta shigo ta same su, sai tace " wai ya akayi ne? Ya tashi ko?" Hannah ce dake hautsine ta bata amsa da fa'din " ehh ya tashi Ummah". Kar6an sa Ummah tayi itama ta 'dan jijjiga shi da kukan ya 'dan ragu sai ta kifa shi akan 'kafafun ta tace da Teemah " Yunwa fah yaron nan yake ji kar ashi ga hakkin sa dayawa ki daure ki bashi yasha kinji". Kai Teemah ta 'daga wa Ummah kamar da gaske. Ummah sai ta 'dago shi ai kuwa kamar yana jira sai ya saki wani sabon kukan kuma, mi'kawa Teemah shi tayi tace " yauwa Fateemah maza bashi 'kilan zai yi shiru" Ummah da kanta ta dai-dai ta mata zaman yaron a cinyar ta sannan ta koma gefe. Teemah kam a hakan ta rungume shi tana bin bakin sa da kallo yanda yake kukan hawayen ta na cigaba da sau'ka. Ganin hakan ne yasa Ummah ta fice tunanin ta wai ko kunyar ta ne yasa Teemahn ta'ki bashi a lokacin dan haka sai ta fita ta bar su da Hannah a 'dakin. Hannah kam gaba 'daya taji zuciyar ta ya karye da kukan yaron ita kanta ji take tamkar ta taya shi kukan amma sai ta daure batayi ba. Zama tayi agefen Teemah ta ringa bata baki akan ta taimaka ta daure ta bashi kar kukan yayi masa yawa daga zuwan shi duniya ya yi sabo da kuka. Rashin kautawar ta tagani ga tausayin yaron ta daya cika ta dan haka sai ta daure ta ciro maman a hankali kamar tana tsoron ta6awa dan yanda yake yi mata zafi, wanda hakan shine babban dalilin daya sanya tun 'dazun take tsoron bashi. Da dabara ta gwada saita masa a baki wanda har ya kama sai kuma tayi saurin cirewa ta maida abinta ta rufe, take wani sabon hawayen ya sau'ko mata sai ta kalli Hannah tace " Allah Hannah da zafi bazan iya ba" 'Bata rai Hannah tayi tace " Haba-haba ke kuwa, ki daure ki bashi dan Allah, ke baki ganin irin kukan daya ke yi ne? Tun fa a safe baki bashi yasha ba, kina ganin kyauta kenan? Ko irin tausayin shin nan bakijji ne ke?" Teemah kam sai cewa tayi " d'auke shi Hannah please ki bashi ko zam-zan 'din ma yasha may be zai yi shiru" Ta fa'da cikin hawaye. Tsaki Hannah ta ja tare da sa hannu ta 'dauke shi a zuciye tayi waje da shi. Gani take yi kamar rashin imani Teemahn ya zarce misali ne da har bata iya tausayin 'dan jinjirin dako kwanaki bai ma fara irgawa ba a duniya. Da idanu Teemah ta bisu har suka fice, inda suna fita ta kifa jikin ta a kan gadon tana kuka da hawaye, ita da kanta haushin kanta takeji akan abinda tayi. B'angaren Hannah kuwa koda ta fita da babyn jijjiga shi taci gaba dayi tana tafiya, sai sukayi kici6us da shi a corridor, shogowar kenan yajiyo kukan baby ya cika ko'ina agidan hakan yasa ya 'karaso nan 'din da gaggawa. Da 'dan hanzarin sa ya iso kusa da Hannah. Hannah ja tayi ta tsaya sai ya sa hannu ya kar6i babyn tare da fa'din " me ya same shi ne haka yake ta faman kuka?" Amsa Hannah ta bashi da fa'din " tun safe bai sha komai ba sai zam-zam da ruwa inajin yunwa ce ke damun sa" Yana jijjiga babyn yace mata " ina Fateemahn kuma take me yasa ta barshi haka?" Hannah sai tace " tsoro takeji wai maman na mata zafi". "Where is she now?" ya tambaye ta sai ta bashi amsa da fa'din " tana dak'i na" Tafiya ya fara yi da Babyn a hannun sa ba tare da ya sake fa'din komai ba ya nufi hanyar 'dakin Hannah 'din. Hannah ma 'karasawa tayi 'bangaren Ummah ta dubo ta jin bata fito ba duk wannan uban ihun sai ta tarar ma ashe sallah take yi shiyasa. Tambayar ta Ummah tayi wai " tabashi ne?" Sai Hannah tace " ina kuwa ta bashi, har fa ta ciro kamar zata bashin kuma sai tace wai zafi yake yi mata" Ummah cewa tayi " To ai da kin taho min da shi nan d'in...." Taranta Hannah tayi da fa'din " Yayah ne ya kar6e shi ai, yanzun nan inajin isowar shi ma" " ai kuwa ba mamaki dan ko ni ma bansan da zuwan nashi ba". Ummah tayi maganar tana mai cire hijab 'din data yi sallah dashi a kanta. Teemah kam kasa zama tayi a 'dakin dan yanda take iya jiyo tashin kukan babyn gaba 'daya ya kara'de gidan nasu, ga shi maghrib tayi sam hankalin ta sai ya kasa kwanciya, dan haka sai ta yun'kura ta taso da niyyar bin bayan Hannah, tana 'ko'karin bu'de 'kofa sai kuma taji kukan babyn na sake tunkaro 'kofan daga waje. Kafin ma ta bu'de sai ya riga ta bu'de wa sai suka tsaya kallon kallo. Ita kallon mamakin ganin sa takeyi musamman da ta gansa rungume da Babyn, yayin da shi kuma yake yi mata kallon " kin kyauta ai" Amma fuskar sa wasai babu wani alamun 6acin rai akai sai ma wani 6oyayyen sihirtacce kuma 'kayataccen murmushi. *Only one☝🏻 page to go insha Allah.......* 👌🏻 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce*😍 [10/13, 8:01 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated 2_ *Maman Ahmad &* *Anty Maimounath o.g ( Mahnoor).* *Mungode da 'kaunar da kuke nuna mana Allah Ubangiji ya bar mana ku (Ameeen)* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _U can’t change what happened in ur past, so b4 u let it destroy ur future, learn to live with it...._ 🅿 *91* Ganin kamar zata 6ata mai lokaci ne sai yayi hanzarin wucewa da kansa ya za6o mata doguwar riga da hijab. Da taimakon sa ta sanya kayan a jikin ta tare da rufawa kanta hijab 'din still tana zubda hawaye suka fita zuwa clinic dake cikin barrack 'din nasu. Daya ke ma koda wani lokaci kaje suna aiki basa yankewa so ba tare da wata damuwa ba suka isa ga babban Doctor 'din dake kan aiki a lokacin. Abbas da kansa ya yiwa Doctor bayanin abinda ya kawo su Teemah kam sai hawaye take tana faman rarraba musu idanu daga gefe. Wata nurse likitan ya 'kira yayi mata bayanin abinda zatayi sannan ya ha'da su da Teemah suka je ta 'dibi jinin ta sannan ta bata wani 'dan k'aramin abu tasa ta yin fitsari a ciki. Teemah kam duk da tana cikin wani yanayi na tsananin damuwa amma hakan bai hanata ta6e baki da " mitar wai banda 'kazanta to me ze sa ta haka, a hakan ne wai Yayah zai ce itama ta zama likita" sake kallon robar tayi tana sake jinjina rashin kunya da 'kazanta irin ta likita. Zuwa tayi ta mi'ka ma Nurse 'din tana sake kallon 'kwayar idanun ta amma sai taga bata wani nuna komai ba ta kar6a ta wuce laboratory da shi, bin bayan ta Teemah tayi da idanu har ta 6acewa ganin ta, ita kam wurin tap taje ta ringa dirzan hannun ta kamar zata sille shi sai da ta tabbatar ya wanku tas sannan ta bari ta koma office inda ta baro shi. Zaune ta same shi shika'dai yana amsa waya ga dukkan alamu Doctor 'din ma ya fita ne. A hankali ta 'karasa jikin sa ta zauna tayi luf, sai da ya kammala da wayar kafin ya tambaye ta har an gama ne kai ta 'daga masa tare da fa'din " Yayah wurin ma zafi yake min sosai" Tayi maganar tare da nuna masa gurbin da aka ja jinin. Hannu Abbas ya kai yana shafa mata a hankali yace " Vry sorry...zai daina zafin ai kinji" Cikin sakalci da marairaita ta d'age kanta sama tare da fa'din " har da fitsarina fa ta kar6a Yayah". Abbas duban fuskar ta yayi sannan ya ce mata " ba komai ai test za'a yi da shi". Sai ya kai hannu jikin ta ya ta6a yanayin zafin jikin sannan ya 'kara da fa'din " har yanzu cikin na miki motsin ne?" Teemah sai tace " Ah'ah.......ya daina amma Yayah ni tsoro nake ji" Taran ta yayi da fa'din " Nima inajin hakan Zahra.. but Doctor yace min 'kila abin alkhairi ne zai same mu, amma bari dai mu jira ganin result 'din ko sai muga ko menene?" Teemah sai ta 'daga kai alamar "to" tayi luf a jikin sa amma abin sai yana bata mamaki, kasa jurewa tayi sai 'dago tare da sake fa'din " Yayah dama akwai alkhairi a cuta ne?" Abbas sai yayi murmushi sannana yace " akwai mana Zahra komai ai da irin 'kaddarar da yake zuwa dashi wani mai kyau wani kuwa akasin haka, inajin tamkar wani gagarumin farin ciki ne zai same ni, i feeel ths in my heart kuma ina fatan hakan ya kasance ki kwanatar da hankalin ki kinji ko insha Allahu ba abin damuwa bane". Mai da kanta tayi ta kwantar a jikin san sannan a hankali tace " Allah yasa hakan ne to amma.... ni tsoro...nake ji Yayah bana son in.......". Sai tayi shiru. Abbas ne ya 'karasa mata maganar da fa'din " bakya so ki rasa ni ko?" Murmushi tayi ta 6oye kanta a 'kirjinsa tare da tukuikuye hijab d'inta. Shima Abbas murmushin yayi A saman la66an sa ya furta " silly girl". sannan ya kai hannun sa ya sau'ke shi a bayan ta a kunne ya ra'da mata " babu abinda zai raba mu kinji, sai dai mutuwa insha Allahu". Shigowan likita ne yasa Teemah ta bar jikin sa ta zauna amma still kanta na jingine da gefen hannun sa tana wasa da hannayen ta, Doctor ha'kuri ya bawa Abbas na barin sa da yayi shi ka'dai inda Abbas yace dashi ba komai kar ya damu daganan suka 'dan fara ta6a hira da Doctor 'din sama-sama. Sunyi jiran a 'kalla 30mins kafin result ya fito, a hannun Doctor aka mi'ka result 'din wanda hakan yasa Abbas zuba masa idanu danjin me ke faruwa, Doctor kuwa yana saka idanun sa kan result 'din take sai fuskar sa ta fa'da'da da fara'a Abbas kam binsa da idanu kawai yake binsa wanda fara'ar data sau'ka kan fuskar tasa yasa Abbas 'kaguwa yaji sakamakon dake ciki. Tsaye likitan ya mi'ke tare da mi'kawa Abbas hannu, Abbas ma mi'kewan yayi sannan ya bashi hannun shima Doctor yana murmushi yace "Congratulations sir" Abbas bu'de idanu yayi a kansa shima da alamar tambaya tare da fatan Allah ya tabbatar masa da zaton sa. Juyawa yayi ya kallo Teemah da ke ta binsu da nata idanun ganin kalar game 'din da suke yi akan result 'din test 'din da akayi mata. Abinda dukkan su kunnuwan su ya jiyo musu shine ".......ur madam is pregnant...." Daga bakin likitan. Ba Abbas ba hatta Teemah sai da ta bu'de idanu a kansa tana sake kallon bakin sa daya furta hakan sannan ta dawo da kallon ta kan Abbas cike da mamaki, Abbas kam ido kawai ya waro a kansa da alamar wata tambayar Doctor sai ya lumshe idanu ya kuma bu'dewa alamar tabbatar masa da gaskiyar sa sannan ya 'dago 'dayan hannun sa ya mi'kawa Abbas papern result 'din ya kar6a ya duba. *Fateema Kabir* ya fara gani a sama daga shi sai *Positive* idanun sa ya 'kara sau'ka a kai bayan sunan ta dake saman. Kan sa ya 'daga ya kalli likitan yana murmushi duk da yanzu yagama tabbatar da hakan musamman daya tuno 'dan 'dagowa da cikin nata yai ga kuma motsin da ta ji wannan kadai ma ansawer ne amma duk da haka sai ya sake tambayar likitan cewa dagaske ne Fateemahn sa ne 'dauke da ciki? Tambayar bai yita dan neman amsa ba face tsaban farin cikin daya cika zuciyar sa. Bai jira jin amsar likitan ba ya juya inda take ya ha'da da Teemahn da papern duk ya rungume su yana juyi da ita yake fa'din " Zahra ta zaki haifi baby very soon, i'm going to be a father...." Teemah kam kukan farin ciki takeyi wai yau itace da ciki itama zata goyi babyn ta wanda za'a 'kira da suna nata. Abbas cigaba yayi da godewa mahalicci kawai a zuciyar sa da wannan babban kyauta da yayi masa, a fili kuwa banda mahaukatan kisses babu abinda yake aika mata. Doctor kam tuni ya fice daga office 'din ya basu wuri ganin yanda Abbas ya 'dimauce da jin labarin. A kunne ya ra'da mata " u ar carrying my baby, my little angel, little me ....Zahra am about to become a father...." Teemah kam kuka take yi da hawaye bata iya cewa komai ba kawai sai ta 'kara rungume shi a jikin ta ganin har ya fita farin ciki da jin tana 'dauke da ciki. Abbas raba ta da jikin sa yayi ya cupping face 'din ta da hannayen sa idanun sa cikin nata ya matso da kan sa dai-dai nata sannan yace " Zahra zaki haifa mana baby ko? ashe motsin babyn mu kike ji a cikin ki....baby ne ke yi miki hello a cikin ki" Teemah ma murmushi take yi hawaye na gangara mata. Hijab 'din ta Abbas ya fara 'dagewa yana fa'din " let me say hi to my little angel". Teemah da sauri tari'ke mai hannun sa tare da jijjiga masa kai tace " plz Yayah ba anan ba". Abbas na jin haka yace " to let's go to our house " yayi maganar tare da ri'ko hannun ta. Fita sukayi hannun ta ri'ke a cikin nashi yayin da result 'din ke ri'ke a 'dayan hannun ta. A hanya suka ha'du da doctor sai ya tsaya inda yayiwa Abbas bayanin idan suna so suyi scanning cikin dan sanin sex 'din baby zasu iya zuwa ranar monday, sannan akwai Anti-natal wanda ya kamata tafara zuwa in d next 3 days. Godiya sosai Abbas ya yi masa tare da 'daukan masa al'kawarin kyautar tukuici ta mussaman dan yanzu bai fito da komai ba, doctor kam cewa yayi bakomai ai aikin sa ne, daga nan suka rabu kowa da murmushi akan fuskar sa. Kallo 'daya zaka yi masa ka gane yanayin farin cikin da suke ciki, har ya 'dauki hanyar gida ya ma manta da cewar sunzo ne da mota Teemah ce ta tuna masa sannan suka koma wurin motar suka shiga yaja su zuwa gida. Suna shiga parlour Abbas ya janyo ta zuwa jikin sa ya cire hijab 'din dake kanta tare da shafo cikin nata har zuwa 'kasan marar ta yana sake jin tudun da cikin yayi. Gajiyan data ce masa tayi ne yasa yaja ta zuwa kan kujera mai zaman mutun biyu suka zauna sannan yaci gaba da shafa cikin a hankali ba tare da ya furta komai ba. Teemah kam murmushin jin da'di take yi tana tunanin wai yau itace da ciki itama zatayi babyn kanta. Abbas duk ya gama susucewa a wurin yana ta shafa cikin nata ji yake wani zazzafan 'kaunar abin da ke cikin nata na ratsa shi jijiya har 6argo da gangar jikin sa sai ya lumshe idanu kawai yayi shiru sai yanzu ne yake ganin wautar sa ji yake tamkar ya yi ta marin kansa na wautar da yayi, ace tsawon lokaci ya kasa gane cewa ajiyar sa na jikin ta, ya kasa gane gagarumar kyautar da Allah yayi masa ne ya canja ta ya kuma canza mata rayuwa gaba 'daya, ya sanya ta zama chop-chop, sam tunanin sa bai bashi hakan ba da farko. Duk kuwa da yasan cewa ba halin ta ba ne yawan cin abinci amma ya rasa mai yasa tunanin sa bai ta6a basa cewa zata 'dau ciki a wannan 'dan 'kan'kanin lokacin ba da auren su, shi bai ta6a kawo hakan ba, bai ma ta6a saka hakan a cikin tunanin sa ba ya rasa mai dauke hankalin sa da har ya kasa gane cewa cikin sa ne ya hana ta ganin period 'din ta ma gaba 'daya duk da kuwa alamomi da suka bayyana kansu amma shi sam tunanin sa da hankalin sa sai ya karakata izuwa wani abu daban, har ya tsaya yana yi mata ihun tana damunsa da neman abin da tasan bazai samu ba, da yasan hakane da ko da wasa ba zai ta6a yi mata masifa ba akai, daya san hakane da ko a ina abin yake zai je ya nemo mata shi da kansa, ashe bai sani ba already Allah yayi masa kyauta gagaruma sanyin idaniya mai sanya farin ciki a zu'kata, haushin kansa ma yake ji yanzun musamman daya sake tuna janta da yayi har zuwa katsina inda tun acan ya kamata ya gano hakan amma ya kasa ganewa, gaba 'daya sai ya tattara laifin komai ya aza shi a kansa yanajin kansa tamkar wani mai laifi. Kan fuskar ta ya dawo da hannun sa 'daya yana shafa lallausan fuskar ta da hannun sa a hankali suna kallon juna, yayin da ya kamo hannun ta a 'daya hannun sa in a slow but romantic voice yace " ki yafe min kinji, kiyafe min duk abubuwan da nayi miki a baya, ban ta6a tunanin ciki bane ke saki wasu abubuwan, ban ta6a kawo cewar zaki iya 'daukan ciki bane a wannan lokacin shiyasa ma hankalina sam bai ta6a zuwa wajen ba, Zahra inajin kamar nafi kowa laifi a duniya na yadda na kasa gane cewa Allah ya bani kyauta ta musamman 6oye a jikin ki, bansan mai zan fa'da ki gane ba amma plz ki yafe min kinji........." Bakin sa Teemah ta rufe da nata bakin, abinda bata ta6a yi masa da kanta ba kenan iya zaman su da shi. A hankali ta ringa kissing 'din shi slowly Abbas kam mutuwar zaune yayi yama kasa mai da mata martani tsabar yanda ta tafi da imani da tunanin sa, tsawon mintina uku kafin ta saki bakin nasa ta koma kallon idanun shi lumshe ido tayi sannan ta jijjiga masa kai. Abbas rungume ta yayi sosai a jikin sa take kuma ya k'ara cire ta ya kama kafa'dun ta tare da matso da fuskar sa saitin nata hancin su na gugan na juna ya furta " i luv u, i luv u Zahra with all my heart, i luv u my baby mama" Itama a hankali ta furta " i luv u more Yayah plz don't ever leave me" Abbas jiyake tamkar ya ha'diye ta dan so, jiyake duk duniya tamkar yafi kowa sa'a da samun ta a rayuwar sa, duk da irin shirmen ta amma dai-dai da rana 'daya bai ta6a jin son ta ya ragu masa ba ko kuma wani abu makamancin hakan, bai ta6a 'kosawa ko dama sanin kasancewa da ita ba, yau gashi zata haifa masa baby, jiyake babu abinda ya kai masa hakan farin ciki. Bai bata amsa ba sai kawai ya ha'de bakin su tare da kaiwa hannu ya bu'de zif 'din doguwar rigar dake jikin ta ya sa6ule zuwa 'kasa. Sai da ya gama rikitata da mahaukatan kisses masu zafi sannan ya gangara har zuwa wuyan ta yana 'ko'karin sau'kar da bakin sa zuwa 'kirjin ta ta 'dan saki kukan shagwa6a tare da furta " Yayah plz....." "Shhiiiiii" ya ce da ita tare da 'daukan ta zuwa cikin bedroom. ***** *Bayan kwana uku* Abbas da kansa ya raka ta Anti-natal a clinic 'din, inda anan ne aka gano cewa cikin nata har yakai tsawon wata hu'du da 'yan kwanaki akai. Wannan labarin har sai da ya zame masa tamkar shine karo na farko daya ta6a jin labari mai kyau na farin ciki a rayuwar sa, musamman da ya fahimci cewa cikin ya samu ne tun a farkon satin auren su sosai hakan ya faranta ransa, lallai babu wanda ya kai mahalicci iya kyauta ta farin ciki, in bashi ba waye zai iya yi maka irin wannan kyautar ace tsawon lokaci yana tare da abin farin ciki amma bai sani ba, ina ma, ina ma, jiyake tamkar abin ya koma baya ko dan ya nuna mata kulawar da har sai taji kanta tamkar tafi kowacce mace a duniyan nan, kulan da sai taji cewa sosai tayi sa'an samun miji mai son ta da kaunar ta, 'kaunar da shi kansa bai san da yaushe ya fara shi ba, tsintan kansa kawai yayi dumu-dumu cikin soyayyar ta tun ma kafin yasan miye so 'din shikan sa balle ita da a lokacin banda shirme da tsokana babu abinda ta iya. Yanzu kam yasan cewa 'kaunar su daga Allah ne, tunda gashi Allah da kansa ya adana masa ita duk kuwa da cewa ta auri wani miji amma sai ya killace masa komai nata ya kuma bashi ita a lokacin da baya zato batare da ya 'daga hankalin sa ba, 'karshe gashi yanzu ya azurta shi da samun kyautar d'a sukutum, ha'ki'ka Allah ne ka'dai abin bauta domin bashi da tamka koda wasa. Abbas bai damu yaji sex 'din babyn ba dan cewa yayi koma menene Allah ya bashi ya gode koma menene yana son abinshi, so ba shi da matsala da wannan Teemah ma bata 'daga hankalin ta ba tabi ra'ayin sa har suka gama suka dawo gida wani lokaci ita kanta tana mamaki yanda yake yi 'din tamkar wanda ya shekara ashirin da aure bai haihu ba, irin yanda yake treating 'din ta abin har yana 'daure mata kai, yanzu ne ta gane ashe son babyn da take yi nata shirme akan nasa, kawai ya 6oye a zuciyar sa ne tsakanin sa da Allahn sa, idan ta bayyana nata kuma ko ta nuna soyayyar ta ga wasu 'ya'yan sai yace da ita ta haifi nata mana sam a lokacin bata san cewa har da kansa yake wa baran babyn ba. She is totally speechless lokacin da yazo ya sanar da ita cewa ya kar6i hutu har na tsawon 2wks kawai dan ya kula da ita da baby, sosai ta girmama wannan soyayyar dan acewar sa sai yayi har da wanda suka wuce shi a baya da be yi ba ba. Murmushi kawai tayi masa sannan ta ce "Yayah ai rayuwa baya koma wa baya abinda ya wuce ya riga ya wuce kuma ma ai a rashin sani ne yasa har ya wuce 'din ba tare da mun lura ba so ba kawai sai mu godewa Allah ba daya bayyana mana a yanzu kuma muna cikin rayayyu duk kan mu" Abbas sai yace " Na sani Zahra nasan hakan kuma nagode wa Allah ina kan yi kuma har kullum, amma idan ba ba'kin ciki zaki min dan kar na bawa family na kulawa ba plz leave me, i'm just trying naga na yi dukkan duties 'din dake kaina" Murmushi tayi ka'dan tace "me yasa zanyi ba'kin ciki Yayah, kawai dai naga ne kamar hutun da ka kar6a 'din bashi da wani amfani" "Ke kike ganin haka ai, amma ni na san akwai amfani sosai" Yayi maganar yana cire rigar dake jikin sa. Tasowa tayi ta fara taya shi rage rage kayan, sannan ta budi baki da niyyar sake yin magana ya tare ta da fa'din " ya isa plz Zahra babu ruwan ki" Sannan ya matsa daga gabanta ya ja gefe yaci gaba da rage kayan sa, tamkar wani 'karamin yaro ya 'kara sa da fa'din " ke dama ai ba'a yi miki gwanin ta" 'Kasa-kasa yayi maganar amma da yake suna kusa da juna sai taji shi, sosai ya bata dariya amma sai ta gumtse ta dafe baki with smile on her face tace " Yayah ni d'in" 'Dan karamin tsaki yaja yace " Zahra let me be plz, i'm here 4 my baby tunda ke bakya bu'katata baki son ki ringa gani na kusa da ke i know my little me want to, so leave me alone plz" Yana gama maganar ya lumshe idanu. Shiru Teemah tayi kawai tana kallon sa ganin kamar ya d'an d'au zafi kan maganar sai taji babu da'di har a ranta. Ta kowa tayi a hankali zuwa inda yake ta kai Hannun ta cikin hannun rigar dake jikinsa da yake har yanzu yana kan 6alla bottles ne bai gama ba, a hankali ta tafara bin hannun a hankali tana masa tafiyar tsutsa tare da kwantar da kanta gefen kafad'ar sa sa tace "am really sorry Yayah i didn't mean to..." Abbas kasa jure fushin yayi shima yakai hannun sa kan cikin ta ya shafo cikin yace " Little me ur Mummy is so sturbborn na kusan in zane ta a gidan nan" Sosai yanda yayin ya sata dariya domin idan ka ganshi zakayi zaton ko dagaske da mutun yake maganar, amma bata yi dariyar ba sai tayi murmushi kawai tace " Yayah ai nace sorry ko? kuma in ka zane ni nima akan babyn zan rama". Itama tayi maganar cikin tsantsar shagwa6a, sai yanzun ya kalleta sai ta turo baki baki, he just knocked her head a hankali yana murmushi yace " silly mummy...kina ta6a min baby zaki biyani abuna right there" Murmushi tayi itama tare da sunkuyar da kanta 'kasa. Rigar ta Abbas ya fara 'dagewa kawai ba tare da shima ya sake magana ba. Teemah bata hana shi ba har ya cire rigar duka ya saura mata sauran bra kawai, hannu Abbas ya kai ya shafo boobs 'din ta dake cike fam cikin bra 'din kamar zasu fashe. Sai da ya kai hannu bayan ta kafin yace " ki daina saka wannan abin plz ke bakya jin yana damunki ne?" Shiru tayi masa kawai ta lafe a jikinsa, sai ya 6alle bra 'din daga bayan ta sannan ya dawo da hannun sa ta gaba da niyyan zarewa sai ta ri'ke mai hannun " Zaki fara ko?" Ya fa'da yana kallon cikin idanun ta sai ta 'dana baki gaba ta fara k'if-'kif da idanu. Share ta yayi kawai ya zame bra 'din daga jikin ta sai ya tsaya kallon boobs 'din nata sosai suke matu'kar tafiya da imanin sa. A hankali ya kai hannun sa ya shafo su take Teemah sai ta lumshe idanu jin yanda torches 'din hannun nasa ya bata wani electric sparks har 'kwa'kwalwan ta. Bakinsu ya ha'de ya bata lafiyayyan kiss tsawon mintina yana sake shafo ta, daga bakin ta ya sau'kar da kansa zuwa wuyan ta yana cigaba da kissing 'din ko'ina ya ci karo da shi har zuwa wuyanta daga nan ya sau'kar da kansa a 'kirjinta. Ajiyan zuciya ta sau'ke tare da rintse idanun ta da k'arfi tana feeling yanda yake sucking boobs 'din tan cikin gwanancewa. Sosai ya tafiyar da ita a wannan lokacin har sai da ya tabbatar cewa ya cika rayuwa da zuciyar ta fam ta yanda babu wanda zai 'kara samun space acikin zuciyar ta daga shi babu kowa a sannan ya bar ta batare da ya kusance ta ba amma, wanda shi kansa hakan da yayi ba 'karamin samawa kansa sukuni yayi ba. Yanda Abbas yake yi mata a kwanakin abin har mamaki yake bata na yanda yake kula da ita da dukkan damuwar ta, har sai daya sanya wani sha'kuwa na fitan hankali ya shiga tsakanin su fiye da zaton mai karatu. Teemah yanzu bata ko jin nauyin sa balle mitan zai ga jikin ta domin shine ke yi mata komai da kansa ciki kuwa har da wanka, shafa mai, drying na gashin ta da sauran su, wani lokaci kuma haka zata zauna susa hannayen su kan cikin suna jin motsin shi, wani sa'in ma ba motsin yake ba amma basa gajiya da shafa cikin koda wani lokaci wai suna jin lafiyar babyn. Abbas idan yakai hannu yaji babyn na motsi rintse idanu kawai ya keyi ya ringa yiwa mahalicci tasbihi yana jin wani sabon connection tsakanin sa da cikin a koda yaushe. Wai yau shine da baby wanda zai yi bearing sunan sa a ko ina. Sosai Abbas ke yin hidima da su cikin hutun daya kar6a 'din Teemah kanta sai da ta jinjina masa ta kuma jinjinawa irin na shi salon, yanda yake son haihuwa ashe ma har ya fita son baby dan tasan duk wannan abin yanayi ne dan babyn sa ba wai dan ita ba. Girki ne dai ta'ki barin sa yanayi domin itama dagewa tayi tace bazai tayata wannan ba, amma a haka zasu shiga kitchen 'din tare duk da 'kin da ta keyi amma Abbas dole sai ya tayata wani abin kafin girkin ya kammala. Ko yau ma hakane tare suka shiga kitchen sukayi tomato sauce da farin doya tace ita shi take so taci shine sukayi sai ya ha'da mata fruits salad suka kai dinning, da suka kammala komai suka zo wurin cin abincin kuwa sai da ya sha drama da ita daya ce shi zai yi feeding 'din ta sai tace babu ruwan ta ita da kanta zataci, dan yanda take matu'kar sha'awan abincin bata jin in shi zai bata kamar zai gamshe ta, Abbas ma 'kin yadda yayi yace shima bai yadda ba dole shi zai yi feeding 'din su, Teemah sai tace " Allah ni fah Yayah da kaina zanci" Rage murya tayi 'kasa-'kasa tace " abinda ma ba dan ni kake yin hakan ba ai na san da baby ne" Sai ta kauda kanta gefe. Abbas kam dariya ma ta bashi ganin yanda ta ha'de ranta sai yayi murmushin gefen baki yace " jealousy mummy.....ke dai kinji kunya, a duk fa'din duniya naki salon yasha bambam dana kowa " Sai ya saki murmushi mai sauti sannan ya ce " yau ga Mummy na kishi da unborn a gidan nan abin mamaki" Ganin ta juyar da kanta gefe ne yasa shi sake 'debo abincin ya nufo ta dashi sai tayi saurin matsar da kanta baya. "Allah idan kika haifa min baby as stubborn as u ko....hmm...zaki sha mamakin abinda zan miki...., bansan me yasa bakya ji ba sam, inajin sai na fara zane ki tukunna kafin ki daina" Bata kula shi ba kawai sai ta sa hannu tafara cin abincin ta hankali tana satan kallon shi. Abbas kam baya yayi ya jinginu da jikin kujera yana kallon yanda take cin abincin a nutse. Sosai yarinyar ke bashi dariya bai san ranar da yarinta zata barta ba wani 6arin zuciyar sa ne yace masa " may be idan ta haihu" Murmushi kawai yake saki a fili yana tunanin wai nan da 1yr shima gidan shi ya 'karu ya zama mai familyn kansa. A cikin ransa yace "Hmm... i can't wait to see that day, Allah ka nuna min wannan ranar ina cikin masu numfashi" Sai ya lumshe idanu ya bu'de su tare da sau'kewa a kan ta suna ha'da ido da ita sai yace " Baby mama"! Da sigar zolaya kuma cike da fara'a yayi maganar sai tayi saurin 'dauke kanta batare da ta tanka sa ba. A cikin ranta tace " ni ba ruwanka da ni" Abbas ma be kulata ba kawai ya zuba mata idanu. Teemah kamar da wasa tayi maganar kuma sai shai'dan ya ingiza mata maganar har a zuciyar ta yayi tasiri gani take wai dagaske dan babyn sa ne kawai yake kula da ita ba komai ba. Tana gama cin abincin sai ta d'auki fruits salad 'din ta mi'ke tsaye da nufin barin wajen tana wani huhhura hanci, sai yanzu Abbas ya fahimci fushin nata na gaske ne bana wasa ba. Da sauri yabi bayan ta da idanu tsinkayan muryar shi tayi yana fa'din " stop there Zahra" Cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba sai ta kalli glass bowl na fruits salad 'din dake hannun ta sannan ta maida idanun ta gaban ta kawai tayi shiru, tsawon mintina biyu tana a haka, bataji yasake magana ba, kamar yadda bai taso yazo inda take ba balle taji dalilin 'kiran haka itama kuma bata waiga taje ta same shi ba, ganin kamar zai 6ata mata lokaci ne yasa ta 'dan yi 'ko'karin 'daga 'kafa da niyyar shigewa abinta sai taji yace " one step nd i ll slap u" Cak ta tsaya sannan ta juyo ta kalle shi jin yanda yayi maganar kamar da 6acin rai, sam bata 'kaunar 6acin ransa ita balle har ta iya juran hukuncin sa, tun lokacin da yayi mata na farko bata fatab ganin ta sake 6ata ransa koka'dan. Da idanu yayi mata nuni da kujerar data tashin nufin sa ta dawo. Teemah kam tuni har ta fara sau'ke hawaye haka ba dan taso ba ta dawo ta zauna tana mai share hawaye. Kanta a 'kasa hawayen nata na ci gaba da sau'ka tana aikin sharewa Abbas kam ko 'kala bece da ita ba kawai ya zuba mata idanu ya kasa tuno abin da ya sata fushin ma gaba 'daya. Teemah kuwa jin be kulata ba ya sanya ta 'daga kai ta kalleshi fuskarta cike da hawayen sai suka ha'da idanu take sai ta tashi da sauri ta dawo 6angaren daya ke 'din ta rungume shi ta baya sannan ta saki kukan mai sauti. Sosai ta bawa Abbas tausayi musamman yanda tayi abin tamkar 'yar yarinya 'karama wacce tayiwa mahaifiyar ta laifi. Badan kuka takeyi ba da babu abinda zai hana shi yi mata dariya amma sai ya basar kawai ya yi 'ko'karin dawo da ita ta gaban sa sai ta no'ke kanta a arms 'din sa tana sake yin kukan. Lallashin ta yafara cikin hankali amma sai ta 'ki daina kukan har se da ya daka mata tsawan "nace ya isa ko?" Kafin tayi shiru. Bai sake magana ba sai da yaga ta nutsu tana sau'ke numfashi sannan ya 'dago kanta yace " me ya faru ne wai ?" Cikin shagwa6a tace " ba kai bane" Abbas da mamaki yace " Ni kuma Zahra yau kuma me nayi?" Sai ta tura baki tace " ai baka so na kullum sai baby kake so" "Shine kike kishi da babyn ?" Shiru tayi kawai ta kalleshi cikin idanu sannan ta kawar da kanta. Abbas sai yaja kumatun ta da duka hannayen sa biyu sannan yace " 'yar 'kauye da babyn naki kike kishi? Ke da zaki rin'ka goya babyn kullum kina bashi mama kina yi masa wanka miye abin kishi kuma?" Wasa kawai takeyi da hannayen ta kanta na kallon 'kasa. Sai yake fa'din "...owk..nagane...nima kina so idan lokacin yayi nayi kishin ko?" Sai ta jijjiga masa kanta alamar ah ah. Yace " zanyi mana, ai ni ya kamata ma nayi kishi dan baby zai kar6e min abuna dayawa dake wajen ki, kinga zai 'dauke min hankalin ki ki nasan da 'kyar ne ma idan baki daina kulawa dani ba, zaki iya daina tayani wanka, zai kar6e min abinda nafi so ma a jikinki kinga ai dole zanyi kishi" 'Daga kai tayi ta kalleshi da zararren ido alamar tambaya sai yayi mata nuni da boobs 'din ta da idanun sa itama sai tabi wurin da kallo take sai ta gane mai yake nufi sai yaci gaba da fa'din " abin tausayi zan zama may be ma ki daina bani abinci kin ga ai ni ya kamata nayi kishi ko? sai dai kinsan wani abu?" Kai ta jijjiga masa sai yaci gaba da fa'din "amma kuma ni bazan yi kishin ba saboda nasan lokacin sa ne kuma zai wuce idan yayi wayo ma shikenan ni 'din ne kuma za'a dawo ma wa domin ni 'din special ne kuma na har abada......kamar yadda kike a cikin rayuwata, in banda shirmen ki ma a ina kika taba jin anso baby an 'ki uwar da babyn ke jikin ta ke baki san albarkacin ki babyn yaci bane ma har nake kula dashi......." Da irin wa'dan nan kalaman yayi ta lalla6a ta har ta ha'kura inda yace mata gobe zasu fita saloon. Kafin dare ta gama sakewa ta bar fushin gaba 'daya Abbas kuwa koda suka je bacci sai da yayi ta faman tsokanan ta wai " Jealousy Mummy towards unborn" Da 'kyar ta samu ya bar ta tayi bacci har sai data zaune shi gaba 'daya ta hau jikinsa ta 'dane tare da ha'de bakin su kafin ta samu ya yi shiru a haka har bacci ya 'dauke ta da hannnun ta kan dimples 'dinsa, daga baya ne ya gyara mata kwanciyar ta. ***** Washe gari ya kama ranar monday, Abbas da azumi ya tashi ranar dayake yana na nafila monday da thursday, 11:00am suka isa wajen saloon 'din inda suka samu ma ba wasu mutane sosai, kitso yace ayi mata koma wani iri ne amma yace banda 'kari yace ayi mata haka da gashin ta kawai. Teemah kam shiru kawai tashi amma tasan zata sha azaba domin rabon kanta da kitso tun kafin auren ta da Abbas tun da ta aure shi kuwa bata sake yin kitso ba har yau. Abbas a waje ya koma cikin mota yana jiran a gama mata su wuce. Minti sha biyar bai cika ba a wurin wata yarinya dake aiki a wurin madam 'din tazo tayi 'kiran sa. Fita yayi da mamaki yabi bayan ta inda suka koma cikin shop 'din, yana sa kai ciki sai kuwa idanun sa ya sau'ka kan Teemah dake kuka da hawaye hannun ta 'daya akan tana bin hannun mai kitson, tun fitar shi basuyi ko 'daya ba tsagu kawai akayi Teemah ta tsaya rigima wanda hakan ne yasa madam ta aika a 'kirashi. Cikin sassarfa ya 'karaso gaban ta ya tsugunna ya 'dan ha'de rai yace " kuka kuma Zahra kitson da zafi ne?" Sai tayi saurin 'dage kai wani sabon hawayen na sake sau'ko mata. Da rawar murya tace " Kace....mata ta dai....na yi min mai zafi.... to". " Naji shikenan to share hawayen ki wani iri kike so ayi miki?" Ya tambaya yana share mata hawayen. "Chukwun ibra zata yi min amma zafi yake min sosai ni bana so". Da kansa ya sake za6a mata wani kitson kalba yace ayi mata shi 'din 'kila ba zaiyi mata zafi ba daga nan yafita ya bar su. Sun kai 1hr suna kitson kafin suka kammala ta fito idon ta jajur da 'dan kwalin ta a hannu ta fito veil ne kawai ta bari akan nata ko kunya bata ji tasha kukan kitso da girman ta. Abbas ne ya koma ya biya balance sannan ya dawo cikin motan ya so suje yawo amma ganin ta kamar ba'a nitse ba yasa kawai ya maida ta gida. Suna isa barrack gaban block 'din su yayi parking Teemah fita tayi ta shige ciki da sauri. Abbas kuwa ganin Sam abokin sa ne yasa shi tsayuwa a wurin sa dan su gaisa. Tana shiga ciki ta zame veil 'din tare da cire pencil skirt 'din dake jikinta ya rage mata 'dan guntun wandon skinny wanda yake iya gwiwa da rigar 'dinkin 3quarter atamfar ta bari kawai ajikin ta. Bedroom ta shige domin ajiye kayan sannan ta wuce wurin mirror ta na kallon kitson. Duk da bawani style mai kyau bane amma ita kanta tasan ta canja sosai goshin ta ya fito har iska takeji yana shigan ta. Tana tsaye gaban madubin tajiyo muryar sa yana 'kiran ta sai ta fito a hankali tamkar bata son yin tafiyar ta nufo shi. "Zo inga kitson naki mana kuma". Yace da ita yana murmushi sosai ya shirya tsokanan ta a yau 'din. Itama kamar ta sani sai ta shirya dakewa a zuciyar ta dan tasan sai yayi mata dariyar tayi kukan kitso. Kusa dashi tazo ta zauna tana wani shan kunu ita a dole zata tsare. Abbas murmushi yayi yace " kitson fa nace zan gani kika wani ci magani a can " Matsowa tayi tare da 'dora kanta akan cinyar sa ta kwanta sannan tace " gashi nan ka gani". Murmushi yayi ya shafo kitson yace "gaskiya matar nan ta taimakeki, jibi fah yanda kan naki yayi kyau shine ko kunya baki ji baby na kallon ki kika ringa rusa kukan kitso ko?" Baki ta tura gaba sannan tace " ai wanan 'din da zafi ne shiyasa". Hannun na kan nata yana ta shafa kitson yace " Ke de kice baki so kawai amma miye abin kuka a kitso". "Allah Yayah da zafi ne rabona da kitso fah tun kafin auren ka". Da mamaki ya tambayeta "Aure na kika ce ? to ke kuma fa banda ke ko? 'Kasa-'kasa tace " har da ni mana" Abbas sai yace " to tun kafin auren mu zakice not me alone.......kinje kina ta kukan fisabilillahi yanzu idan kika haifi baby girl kuma zakiyi mata kitson ko ?....ni kam idan kika dukar min baby akan kitso ni da kene a gidannan....ai na riga naga sirrin" Shiru tayi masa itama tana tunani bata yi magana ba har bacci ya yi gaba da ita. Da yamma ta shirya masa 'kyataccen girki na gaban kwatance sosai kuwa yaji da'din hakan inda ya ringa saka mata albarka yanaci yana yaba mata. Teemah bata tashi sanin tsananin son kitso da Abbas keyi ba sai da sukaje bacci yanda yarin ga yabon kitson yana shafo wa abin har mamaki yaso bata, dan tunda suke dashi bai ta6a nuna mata yana son kitso ba ko yanzun ma tasan ya kaita kitson ne dan yawan 'kai'kayin da kan ke mata kuma wai dan kar tsefaffen gashin ya ringa damun ta. Amma ba wai dan ra'ayin kansa ba. Sosai take jinjina wa miskilancin sa a hakan ma ita bai fiya yi mata ba sosai yake sake mata fuska har take sanin wasu abubuwan sa, in kana son ganin asalin halin sa to ka tsince shi cikin uniform kaki a lokacin ne zaka tabbatar da ko shi waye amma banda cikin gidan sa. Duk kuwa wannan abinda ke faruwa Abbas be sanar da kowa ba, ko su Ummah be iya 'kira ya sanar dasu ba, ya dai sanar da Leesah inda tayi matu'kar farin ciki ta taya shi murna, Teemah kuwa wa Maman Amal ka'dai ta sanar mawa. Tanas o ta bawa wani daga cikin dangin ta labarin abin farin cikin daya same ta amma ta kasa gaba 'daya kunya ya ishe ta ganin shi da yake namiji ma bai fa'da ba sai ita toh ta ina ma zata fara. Watarana da suna waya da Anty sai tayi tunanin sanar da ita don tasan yanzun Anty ta canza ba kamar da bane, bayan sun gama gaisuwa da 'kyar Teemah ta harha'da kalaman tace "Anty ba.... da cikina na motsi ba sai mukaje wurin Doctor Yace mana...wai....wai...." Sai ta kasa cigaba da maganar nauyin kalmar take ji. Antyn ne ta 'karasa mata da fa'din " wai Fateemah na is about to become a mother ko?" Kunya taji sosai sai kawai ta kashe wayar tana murmushi jin Anty ta 'dago ta da wuri. Tun daga ranar kuwa Anty kullum sai ta 'kirata taji lafiyar su ita da babyn, Anty ma ba ta sanar da kowa ba illah Abbah shima sosai yayi farin ciki zaton Anty duk sauran ma na da labari shiyasa tayi shiru kawai batayi maganar da su ba. Hannah Teemah take so ta sanar mawa saboda itace 'yar uwa kuma 'kawar shawara da amana amma tsoron tsokanan Hannah take yi kuma tana jin kunya dan tasan Hannah zata iya sanar da Ummah, ita kuwa bata son hakan. Har watan ramadan yazo suka azumci watan a Ports ba suje Rivers ba, bayan sallah ne yaso suje gida amma sai ya fasa kawai suka yi zaman su, bai ma yiwa Teemah maganan ba dan yasan halin rigiman ta idan taji 'kila tace masa dole sai sunje 'din shi kuwa be so ta bar shi shi ka'dai anan. A haka har zancen ya wuce bata da labari, suna waya da kowa da kowa ciki kuwa har da Mummy itan ce ma some time take tambayan ta wai babu wata matsala ko, ko kuma tace ya jikin ta, Teemah kam sai ta ce " ni lafiya ta 'kalau Mummy" Murmushi kawai Mummyn keyi bata 'kara wata magana. Sai dai su canja hirar tasu. Sosai Teemah tayi sa'a dan cikin ta ba mai yawan laulayi bane, amai ma ba kullum takeyi ba sai lokaci-lokaci, wani sa'in ma tana kaiwa sati guda ma batare da tayi aman ba, haka bata yawu sam-sam bata ma san mai ciki nada wannan problem 'din ba, some times sai sunje wurin Anti-natal sannan take ganin wasu abubuwan agun mata masu cikin, bata komai sai dai tana yawan yin fitsari da kuma ciwon kai ka'dan-ka'dan. Kitso kuwa tunda ta fahimci yana birge Abbas sai take 'ko'karin daurewa tana zuwa ayi mata duk bayan 2wks kuma ba laifi domin kwalliya tana biyan ku'din sabulu dan kuwa Abbas na 'ko'karin yaba mata a fili kuma tana jin da'din hakan. Wasa-wasa har cikin Teemah ya kai 6months su Hannah basu da labari, zuwa lokacin kuwa cikin ya fito 6ul abinsa inda kallo 'daya zaka mata ka fahimci cewa ta shiga sahun masu ciki, sai ta 'kara yin kyau abinta, hancin ta ne ka'dai ya 'dan kara girma ka d'an a fuskarta baya ga haka babu komai sai ma wani fresh da tayi, kuma yanzu tarage yawan cin abinci ba kamar da ba yanzu tafi cin kayan itatuwa ne kawai. 👇🏼 ~_*Kuyi ha'kuri da typing errors plz wlh banjin da'di ne shiyasa ban nutsu na duba da kyau ba.*_~ _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/13, 8:01 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated_ my family😍 ~*2nd 2d LAST PAGE*~ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _Wishes are always granted but you just have to wait for the perfect time._ 🅿 *93* Da sassarfa ta k'arasa inda yake tsayen ta rungume shi daga 'daya gefen sa ta saki wani kuka. Shiru Abbas yayi kawai duk da kukan da take yi 'din amma bai bi takai ba sai ya dawo da idanun sa kan fuskar Babyn yana kallo tsawon da'ki'ku fuskarsa ba yabo ba fallasa sannan ya 'dan juyo da kansa 6angaren da take a kunne ya ra'da mata " what's wrong kuma?, why ar u crying ko kina taya yaron ki kukan ne?" Teemah 'dagowa tayi ta jijjiga mai kai, sai ya 'dage gira 'daya yana kallon ta yace " to shi'din kuma kukan me yake yi? Me yasa me shi?" Kwa6a baki tayi tace " Wai fa yunwa yake ji...ni..ni kuma..maman tun 'dazu zafi yake min tsoro nake ji". Abbas cewa yayi " Haba! haba!!, tsoro kuma kike ji?, kika iya haifan shima balle wannan, come on zo muje ki gwada bashi in gani yanzu" Yayi maganar tare da 'karasawa cikin 'dakin, itama Teemah a hankali ta biyo bayan sa tana fa'din " Allah Yayah da zafi fah, ni gaskiya bazan iya ba". Sai yace " ka'dan zaki bashi ba da yawa ba kinji?" Da haka ya 'karasa bakin gado ya tsaya yana jiran isowar ta, daya ke a 'darare take bin bayan san so sai bata 'karaso da wuri ba. Tana isowa sai yayi mata nuni da bakin gadon, Teemah kam a tsorace ta zauna tana matse 'kwalla. Shi da kansa yasa mata yaron a cinyar ta tare da dai-dai ta mata shi inda yanayi yake fa'din " ke ko tausayin sa bakiji ne?, kuma ma idan ke da kika haife sa baki bashi ba to waye zai bashi? in kuma kin daina son shi ne sai ki gaya min inje in kyautar shi wa wata wacce zata kula dashi da kyau, hakan yafi ko? Ya 'karashe yana kallon cikin idanun ta dake cike taf da 'kwalla. Wani hawayen ne ya sake gangaro mata jin abinda ya fa'da sai ta share da 'dayan hannun ta tana sake rungumar yaron zuwa 'kirjin ta. Abbas hannun sa ya kai bayan ta yana bu'de mata Zif yace " Ni ina can kin barni da tunanin zaki iya haihuwa ko kuma akasin haka, ban sani ba ashe ke kam kina nan kina ta yiwa Baby na rowa ko?" Sai yanzun ta bu'di baki cikin shagwa6a tace " Ni fa ba rowa nayi masa ba" Abbas jinjina kai yayi yace " to naji bashi in gani in dagaske ne...kin gama ai har ya gaji da kukan ya ha'kura dan haushi". Kallon sa tayi itama fuskar sa har ta dawo ja saboda rikicin kukan da yayi yanzun, a hankali ta 'daga rigar ta sama Abbas ya taya ta ri'kewa sai ta ciro maman dake saitin babyn, ya cika sosai ita kanta tana jin nauyin sa har tsoron ta6awa take yi ma. Juyowa tayi ta kalli Abbas tare da marairaice fuska zatayi magana ya tare ta da fa'din " Zahra please......." Tace " ni fa Allah zafi yake min" Abbas shima sai yace " ai zafin sai janye miki in ba haka ba fashewa zaiyi kin fi son haka ko?" Jijjiga kai tayi sai yasake fa'din ".....ka'dan zaki bashi to kinji y'an matan Yayah?" Sai ta 'daga kai sama a hankali. Sai da ta sake 'dago babyn tare da ran'kwafawa saboda saman da maman nata yayi, da taimakon sa ta samu ta sanyawa babyn a baki, yana kamawa kuwa sai ta cije baki ta jinginu da jikin Abbas dake ta gefenta, 'ko'karin cirewa ta farayi dan zafin sosai yake ratsa ta har kan ta, Abbas na ganin haka sai yayi saurin zira hannun sa yana shafa mata saman a hankali yana jero mata "sorry sorry.. sorry babe, so sorry momma...." Da haka ya yaudare ta har babyn ya 'koshi yayi bacci abinsa, sannan ta cire maman har da zufa tayi. Kar6an sa Abbas yayi tare da fa'din " Thank u" Yana murmushi yace " koke fah? Murmushin 'karfin hali tayi itama, ita kanta da ta bashi yasha 'din sai ta 'dan ji ta dai-dai sa6anin 'dazu da bata bashin ba kuma hankalinta bai kwanta da hakan ba gashi kuma ciwon bai ragu ba, yanzun kuwa hatta cikan ma sai ya 'dan ragu da zafin. Hu'duba Abbas yayi masa a duka kunnuwan sa biyu bayan ya gama sai ya rungume 'dan sa a jikin sa yana jin sau'kan numfashin sa yayin da ya zuba mata idanu yana murmushi ba tare ya furta komai ba. Teemah ma murmushin tayi ta sunkuyar da kanta tana wasa da 'yan ya tsunta. Dai-dai nan Ummah ta shigo, bayan ta kuma Hannah ce. Ummah na shigowa bayan ya amsa mata sallamar ta sai ta tambaye shi cewa " ta bashi yasha ne?" Da " ehh Ummah yasha" Abbas ya amsa mata tare da gaida ta, kar6an yaron Ummah tayi a hannun sa bayan ta amsa gaisuwar tana gyara masa kayan dake jikin sa tace " Maman ka matsoraciya ce sosai gaskiya" Tana murmushi ta 'dago ta kalli Abbas tace " da ba ka zo ba da bansan yanda zanyi da ita ba yau 'din nan" Ta 'karashe maganar tare da 'dan sakin dariya. Abbas sai yayi murmushin shima yace " Ummah ai ke kika 'kyale ta da zane ta kika yi tun farko da baza ma akai wannan matakin ba" Murmushi sukayi dukkan su har Teemah da jin abinda ya fa'da 'din wai Ummah ta zane ta. Daga lokacin kuwa bata sake jin fargaban bashi ba duk da zafin bai daina ba amma da sau'ki yana 'dan raguwa mata musamman idan ya sha. Washe gari Anty ta iso, ba'ki dayawa daga 6angaren Ummah ma sunzo, kama daga kan 'kawayen ta da matan abokan Daddy har ma dana Abbas da wasu 'kawayen Hannah duk sun sukayi ta sam barka wa yaron, duk dacTeemah bata san kowa agarin ba in ya wuci Maman Nasreen amma duk da haka gidan baya ta6a rabo da jama'ah kullum, Mummy ce dai sai ana jibi suna kafin ta iso. Jinjirin ma sai tayi sa'a bai fiya yin kuka ba sai dai idan yaji yunwa sannan shiyasa baya ma wuni a tare da ita. Sau tari dan shayar dashi kawai ake kawo shi wurin ta inda tana gama bashi kuwa za'a kuma tafiya dashi. Wani sa'in har ji take yi tamkar ta ri'ke abinta ta rungume shi a 'kirjin ta amma kunyar jama'ah yasa take basarwa, bata ma hakan aka ba kuma saboda tasan na'dan lokaci ne watarana ma su ka'dan su zasu yini batare da kowa ba. Abbas kansa idan ya zauna yasa su a gaba banda godewa Allah babu abinda yakeyi musamman idan ya gansu wai ace iyalan sa ne su 'din familyn sa ne na kansa abin na matu'kar ratsa shi kalar yanayin farin cikin dayake tsintan kanshi aciki kuwa abin ba'a cewa komai. Matan abokansa duk sunzo da mazajen su suka gaida Teemah wasun su tasan su yayin da wasun kuwa bata ta6a ganin su ba sanadin haihuwar ne ha'duwar su. Maman Amal ma ta zo tun daga Lagos inda Teemah tayi matu'kar farin ciki, musamman da taga yanda baby Amal 'dinta ta 'kara girma tayi wayo tana gudun ta ko'ina. Leesah ma babu ranar da gari zai waye bata zo gidan ba, wani zobe na gold ta siyo ta sawa yaron a hannu mai kyau da tsada itama kullum son Babyn na 'kara ratsa ta barin ma da taga ya na kama da baban sa ai shikenan idan tazo kuwa bata barin kowa ya ri'ke shi sai ita ka'dai. Tun kafin ayi suna ma Leesah tafara 'kiran sa da Annoor ta kuma ce sunan da za'a 'kirashi dashi kenan kenan. Hannah kam bataso hakan ba dan ita da niyyar ta a k'irashi Irfan sai kuma Haleesah ta riga ta sanya masa suna dole badan taso ba ta ha'kura da nata sunan tana jin badan wani abu ba da Leesah bata isa ce zata saka wa jinjirin suna ba amma sai Hannah tayi mata kara ta bari saboda darajar abu 'daya. Ranar suna yaro yaci sunan *Mahmud*, babu wanda bai mamakin sunan da Abbas ya sanyawa jinjirin ba, inda jama'ah da dama suka yaba masa tare da yaba irin karamcin daya yi, especially wa'danda suka ji abin a sama cewa kawai sunan marigayi mijin matar sa na baya ne, sai suke ganin kamar shi 'din halin sa daban ne dan bakowa zai iya irin hakan ba. Wa'dan da kuwa suka san asalin zumuncin dake tsakani sai sam barka kawai suke yi, wannan dalilin kuwa ba 'karamin farin jini ya jawo wa babyn ba. Anty kuwa har kuka tayi dan farin ciki take ta 'kira Abbah tayi masa albishir cewa an yiwa marigayi takwara, ta 'kira mahaifin ta ma ta gaya masa tana hawaye, shima Alhaji Muhammad albarka ya ta sanyawa Babyn masu yawa tare da yiwa mahaifin little Mahmud 'din fatan alkhairi mai d'orewa. Irin 6arnar ku'din da Abbas yayi a wannan ranar abin ba'a cewa komai, dan wurin event 'din da akayi sunan idan kagani zaka saci ko wani 'kayataccen biki za'ayi a wurin, jakunkuna aka rin'ka rabawa mai 'dauke da turmin atampa mai kyan gaske, sannan ga wani jakan kuma shima mai photon baby shima ciki kayan ciye-ciye ne fal duk akayi ta rabawa mutane. Duk wanda ya halacci taron sunan da farin ciki akan fuskarsa ya tafi domin kuwa ko ka'dan ba'a yi wani abu da zai sosa ran wani ko wata ba a wurin har taro ya watse. Kyaututtuka kuwa da Teemah ta samu suma ba'a magana, cikin masu bada kyautar kuwa hadda Anty inda ta yiwa Baby da maman sa kaya masu yawan gaske kowa da nashi akwatin, Daddy ma ya aiko nashi kyautan da yake bai samu yazo ganin baby ba. Ana kammala suna Abbas ya koma Rivers, haka ma su maman Amal da wasu mutanen na nesa duk kowa ya kama gaban sa suna masu farin cikin samun 'karuwar da Abbas 'din ya samu, inda aka bar Ummah da Anty har ma da Mummy suka cigaba da kulawa da mai jego har tsawon sati biyu sannan Anty ta koma Lagos da yake itama a halin yanzun abokiyar zaman ta nada tsohon ciki ne haihuwa yau ko gobe. Mummy kam sai da ta kai 1month cif kafin ta koma Dubai, bayan tafiyar ta ne kuma Abbas yazo ya duba iyalan sa inda ya same su cikin 'koshin lafiya da kwanciyar hankali baby yayi 6ul-6ul a binshi, dan ma kullum sai sun tura masa photon shi a duk wankan da aka mishi su Hannah sai sunyi masa photo sun turawa Abbas wataran dukkan su sukeyi wataran kuwa Baby da mamar sa wataran kuma shi ka'dai. Haka ma yana yawan 'kiran su video call a haska mishi babyn wataran ya ganshi yana bacci, wataran kuwa zai ganshi idanun sa biyu yana wasa da hannun sa abaki. Abbas idan yaga hakan kuwa sai yace mata wato har yanzu tana masa rowan ko?" Teemah sai tace " ah ah" "Toh meyasa yake kai hannu baki?" Ha'de goshi takeyi tace " Wasan shi fah kawai yake yi Yayah, kai dan baka ga yanda yake tsotseni bane shiyasa ai zaka ce wani ina masa rowa" Sai cewa yayi " rama min yake yi ai kema kin tsotseni" Teemah da sauri tace " wallahi ba wani nan, to in dai haka ne ma bazan 'kara nuna maka shi ba" Abbas ha'kuri ya bata yana dariya yace " to shikenan ya wuce, ni wasa nake miki maman Baby" Lokacin da Abbas yazo ya gansu ba 'karamin farin ciki yayi ba har ji yake duk fa'din duniyan nan babu abinda ya kai masa farin ciki sama da su. Wani kyau yaga Teemahn tayi masa da yake already Anty ta aiko an fara yi mata gyara ga haske datayi kamar ba mai jego ba, ko irin 'karnin nan da wasu masu jegon keyi sam bai ji a wurin ta ba illah 'kamshi daga ita har lil Mahmud 'din, da yake ma dama Teemah gwanar son 'kamshi ce kuma Anty tasa an kawo mata wasu ha'din su humra da sauran su masu bala'in 'kamshi shiyasa bata wasa da amfani dasu, dayake kuwa bata wasa da kayan 'kamshi ciki da waje tana 'ko'karin kulawa sosai. Aranar da yazo 'din kuwa Teemah da kayar ta sha, duk da tana yi masa tuni da cewa gidan Ummah ne ya bari fah kar tazo amma Abbas bai saurare ta ba yaci gaba da abinda yakeyi har sai daya gama rikita mata lissafi da salon wasannin sa cuz he really missed her a lot ji yake kamar ba zai sake iya 'daukan lokaci ba tare da ita ba, Teemah kuwa duk da ranta ba'a sake ba amma yanda yake sarrafatan yasa har ta fara 'daukan layi itama. Kukan da Annur ya saka lokaci guda ne ya ceceta domin kuwa da sauri ta 'kwaci jikin ta tafi ta 'dauki 'danta ta rungume tana jijjiga shi. Abbas kam tana barin jikin sa yayi baya ya kwanta tare da lumshe idanu a fili ya furta " Uwa! Uwa kenan!" Wannan shine step na farko dake raba soyayyar mace ga mijinta domin matu'kar ta samu Baby to dole ne soyayyan babyn sai ya rinjayi na kowa ciki kuwa har da mijinta duk da dai baza'a ta bar son shi ta komawa danta ba amma na 'dan sai yayi rinjaye fiye da komai. Abbas tashi yayi ya zauna yana kallon yanda take faman jijjiga shi da dukkan kulawa sai yaui mirmushi a hankali yace da ita " ki kaishi wurin Ummah mana please sai ki dawo " Sai cewa tayi " ah ah Yayah barshi kawai ai zai yi shiru, Ummah ta gaji dayawa yau 'din duk a wurin ta ya wuni tun da rana" "Hmm" kawai yace tare da 'ko'karin sau'kowa daga gadon, sai daya sau'ko da 'kafar sa 'kasa sannan yace " wato dai kince Annur ya fini ko?" Da sauri ta furta " ah ah fa Yayah ai kaga d'azun kuka yake yi ne shiyasa" Tana maganar tana tahowa inda yake ta zauna daga gefen sa tare da raba Annur 'din daga kafa'dar ta sai ta ri'ke shi a cinyar ta, Abbas ne ya 'dauke sa ya 'dagashi sama yana jijjiga shi yana murmushi, yaron ma kallon fuskarsa yake yi kamar an ce masa mahaifin sa ne. Abbas yana murmushi yace " Ai dama na gaya miki, idan kin haihu nasan guduna zakiyi ki tattare duk ki komawa 'dan ki, kika 'ki yadda, ni kuwa nasan hakan dama sai ya faru gashi tun ba'aje ko'ina ba zance na ya tabbata gaskiya" Murmushi tayi ta koma daga bayan sa ta rungume shi tare da fa'din " afuwan Yayah ba haka bane fa, banaso yayi kuka sosai ne har Ummah taji kuma tazo kaga da kunya sosai hakan ai" Yana kallon babyn yace " to ni sai yaushe kenan za'a kulani... kin san fa gobe zan koma akwai aiki a gaba na, ko zamu je can 'daki na mu kwana?" Kanta ta kawo gefen fuskar shi tace " da sauran lokaci fa Yayah,kuma ma ni gaskiya ina jin kunya ace daga zuwan ka har na bika 'dakin ka?" 'Dan b'ata rai Abbas yayi yace " bana son fi'ili ni, yau kika fara kwana acan 'din ne ko kuma yau ne kawai kunyar tazo miki?, ke 'din nan naga alama kin gama gaji dani ko? shikenan bakomai i know what to do kar ki damu" Ya 'karashe maganar cikin basarwa kamar wani da gaske. Ita kuwa jin yanayin da yayi maganar ne yasa ta sanyaya murya dan sai taji ba da'di cikin sanyin jiki tace " me zakayi Yayah?" A tsare yace " amarya zanyi wacce bazata gaji dani ba" Cike da firgici ta saki wuyan sa tare da juyawa ta koma ta jingina bayan ta da nashi tana kuka tace " an gaya maka ni 'din gajiya nayi da kai ne?" Sai yace "ah to nima na sani ne? In kina son in yarda baki gaji dani ba then tashi mu tafi " Kuka ta sanya mishi tana hahharba 'kafa tace " Ni dai kagaya min in kaine ka gaji dani...ai ni ban fa'da ba. "Ban yi tunani akan hakan ba tukunna" Ya fa'da cikin halin ko in kula. Shiru tayi mata yi magana ba, sai ta cigaba da kukan ta, shi kam tashi yayi ya nufi 'kofa da babyn a hannun sa ba tare da ya sake kallon inda take ba. Bai damu ba yasan ko badan bayn bama dole zata biyo shin idan ya tafi ko dan rigimar ta ma dan haka hankalinsa kwance ya fice a 'dakin. Dan haushi ma ita yana fita sai ta ta shi kamar an tsikare ta ta shige bayi, bata san me ya kawo ta bayin ba dan haka sai ta watsa ruwa kawai ta fito, tana fitowa sai suka ci karo da Hannah da shigowan ta 'dakin kenan itama. Kau da kai Teemah tayi tamkar Hannah ce tayi mata laifin sai ta nufi gaban mirror tana goge jikinta dake ji'ke da ruwa. Hannah ta6e baki ganin bata ko kula ta ba itama bata damu ba dan tasan bazai wuci fushin Yayah bane take yi da har itama ta samu rabon ta. Duba gadon Annur tayi bata ganshi ba haka ma nasu gadon ma baya kai wannan dalilin ne yasa ta juya ta kalli Teemah tace da ita " ina yaro na yake in mai gudnyt rabo na da shi tun da maghrib gashi bacci nake ji yanzun" Teemah bata juyo ba ta bata amsa da fa'din " ki je ki kar6o shi a wurin Yayah" Hannah sai cewa tayi "Ta6'di ke de shirya ki kar6o shi ina jiranki kun fi kusa ai". Shiru Teemah tayi ta cigaba da goge jikinta, bata shafa mai ba sai kawai ta 'dauki turaren humrar ta tabi jikinta da shi sannan ta nemi kayan bacci riga da dogon wando ta sanya dan ita tafi son irin su dama. Tana gama shirin ta 'dauki hijab 'din ta babba ta sanya da silifas ta bar 'dakin ba tare da ko kallon inda Hannah take ta sake yi ba. Zuwa lokacin kuwa tuni hankalin Hannah ya riga ya 'dauku ga wayar data keyi bama tasan lokacin da Teemah ta bar 'dakin ba. A hankali ta tura 'kofar tare da yin sallama 'kasa-'kasa sai amsa mata shima ba tare da ya 'dago ya kalle ta ba fuskar sa na kan ta Annur yana yi mai wasa. Shigowa tayi tare da tura 'kofan sai ta ja ta tsaya ta na kallon su, ita haushin ta 'daya warning 'din da Anty tayi mata akan sa, sam bata son ya wargaza mata gyaran da aka soma yi mata tun ba aje ko'ina ba dan ko itama tana so ta tsumu ba yanzu ta so ha'duwar su ba, amma ga dukkan alamu ba fahimtar ta zaiyi ba har da cewa wani amarya zaiyi. Tsaki taja a ranta ta dan ta tsani wannan kalmar sam.. A hankali ta 'karasa inda yake ta tsaye nesa ka'dan dashi sannan tace " Yayah kawo shi mu tafi kaga dare na 'kara yi kuma Hannah ma na so ta ganshi " Sai yace "Ni kuma so nake mu kwana da shi ya za'ayi?" Shiru tayi ta tura baki gaba tare da 'kura masa idanu, bata san yaushe Yayah ya koyi irin hakan ba bata san me ya canza shi ba dan Yayan ta data sani ada ha'kurarre ne akan komai, kallon kallo suka tsaya yi kiwa abinda ke ransa daban, shikam ransa fes babu komai illah so da 'kaunar ta bayaga haka babu komai, shine ya yanke shirun nasu da fa'din " Zo ki zauna ki bashi abincin sa naga yana shan yatsu" Zaman tayi kamar yanda ya fa'da 'din ta mi'ka masa hannu akan ya bata babyn sai bai bata ba sai yayi mata nuni da hijab 'din dake kanta. Ja tayi ta cire shi ta ajiye a gefe. Abbas sai ya mi'ka mata Annur 'din sannan ya taya ta 6alla botiran saman rigar guda uku yace to ta bashi. Shi kam zuba musu ido yayi yana kallon yanda babyn ke sha cikin nutsuwa, babban abinda yafi tafiya da imanin sa ajikin ta bai wuce boobs 'din ta ba, yanzun kuwa ganin yanda suka sake cika suka tsaya sai yake jinsa cikin wani yanayi, dan basuyi komai ba illah da 'da cika da sukayi sosai yake kewar su yake kuma jin son sarrafa su. Har Annur yayi bacci Abbas na gefe yana kallon su, Teemah sai ta cire shi tana rufe bottles 'din ta Abbas ya 'dauke babyn cak ya kwantar da shi sannan ya rungumo ta ta baya tare da ri'ke hannun ta a hankali yace " saura ni ko". Shiru tayi sai ya juyo da ita ta fuskance shi ya sake fa'din " aji dani nima" Tana 'ko'karin yin magana ya 'dora yatsan shi saman la66an ta alamun tayi shiru dan yasan bai wuci complain zata yi ba, matso da fuskar sa yayi kusa da nata ya ha'de musu hanci suna jin 'dumin numfashin juna tare da sau'ke hannun san dake saman bakin nata ya jone bakin nasu wuri guda ya fara shan harshen ta, tsawon da'ki'ku kuma sai ya tsaya tamkar ya manta me yakeyi yayi jim, Teemah kuwa da ta ga haka sai ta cigaba da kissing 'din nashi kamar dama can ita ta fara. Ita kanta tasan tayi kewar shi kawai dai bata son ta watsar da maganar Anty ne shiyasa take 'dan denying 'dinsa, kuma gashi tana jin nauyin Ummah bazata iya sakewa da shi a gidan ba. Tana cikin tunanin sai taji hannun sa a cikin rigar ta yana mata tafiyar tsutsa har zuwa saman 'kirjin ta. Ajiyan zuciya kawai ta sau'ke duk dama bai fito fili ba amma yanda yaga yake samun response 'din ta ma sai bai yi tunanin kusantar ta ba ya tsaya a iya romance ne kawai ba komai da ya mata. Inda ya 'dau tsawon lokaci yana juya ta son ran shi haka kuma itama dan sai da ta tabbatar tayi easing abinda ke damun sa kafin sukayi bacci manne da juna tuni ta manta da fushin amarya. Hannah kam har ta gama waya tayi zaman jiran Teemah amma shiru har kusan 11pm kawai sai itama ta kwanta tayi baccin ta ganin basu da niyyan dawowa. Da asussuba Teemah ko ta gudo daga 'dakin sa wai dan kar Ummah tazo ta ga basa nan. Sallah ta samu Hannah nayi dan haka sai ta kwantar da Annur ta tafi bayi itama sai da tayi wanka kafin ta 'dauro alwala ta fito. Da ta idar da sallar ne Hannah ta jefa mata tambayar " Yayah ne ya ri'ke ku ko" Da'din tambayar Teemah taji dama bata so Hannah taga kamar itace ta 'ki dawowa dan haka da wuri ta bata amsa da fa'din " ai wallahi kamar kinsani...Yayah cewa yayi wai shi sai da 'dan sa zai kwana, ni kuma wallahi kunyan Ummah nake ji kar ta gane a wurin sa muka kwana shiayasa ma kika ganni sassafen nan" Hannah kuwa sai tace " Hmm, kin makara ai Ummah da dare tazo duba Annur wai ko yau ma ya'ki yin bacci irin na jiya? sai nace mata ai kun tafi wurin Yayah" Zaro idanu Teemah tayi tace " dan Allah Hannah dagaske?, na shiga uku ni kam yanzu ya zanyi duk fa laifin Yayah ne Allah" Hannah murmushi tayi tace " Firgici haka sai kace dagaske bayan kinje kin 'din kuma miye abin damuwa?" Teemah sai tace "Ba zaki gane bane Hannah ke kam, ai da kunya irin wannan abin, ni dan Allah ki gaya min ya zanyi?" Murmushi Hannah tayi yanzun ganin yanda duk Teemah tabi ta rikice sai tace da ita "Wasa ni nake miki dan Allah ki nutsu, bata zo ba kuma yanzu kam ai bazata sani ba tunda kun dawo, amma shine kuma kuka barni na raba dare ina zaman jiran ku bayan kin san bazaku dawo ba...Allah naji haushi?" Ajiyan zuciya Teemah ta sau'ke tare da fa'din "Very sorry lil sis baza'a sake ba" Ai ma baki san wani abu ba? Yaron nan in gaya miki yau ko damuna baiyi ba yayi ta baccin sa...." Hannah sai tace "Ah to yaga innar sa taje neman lada ba dole ya risina ba" Fa'din Hannah tana murmushi. Teemah sai tayi murmushi kawai batare da tayi magana ba. Aranar kuwa Abbas ya koma kamar yanda ya fa'da mata, ita kam da fatan alkhairi ta bisa dan bazata iya ce ga takamamman yanayin data ke ji game da shi ba, fama take da zuciyar ta tana ta 'ko'karin 'karya ta kewar shin data ke ji 'karfi da yaji ta sanyawa ranta 'karfin hali da nuna halin ko in kula game da tafiyar sa tasa. Teemah tun bayan sati da haihuwar ta tafara yin sallah, gyaran da ake yi matan kuwa ba 'karamin fitar da ita yayi ba, idan ka ganta tashin farko bazaka ta6a cewa itace ta haifi Annur ba, dan yanda tayi 'das abinta abin ba'a cewa komai. Kullum matar take zuwa daga 10:00am zuwa 12:00pm tayi mata duk abinda zata yi ta tafi so gyaran bai wani takura ta ko shiga lokutan wasu al'amuran ta ba. Shi da Abbas a nufin sa wai suna gama 40days 'din nasu zasu koma amma Ummah ta tayi babakere tace sam bata ji zancen ta haka ba sai sun 'kara hutawa. Abbas har ransa ya 'dan 6aci da hakan amma sai ya 6oye bai nunawa Ummah ba, sai dai Teemah da suka ke6e da ita ya bayyana mata halin daya ke ciki inda ta matu'kar tausaya masa tana jin ba dan Ummah mahaifiya ba ce da babu abinda zai hana ta bin mijinta, domin ita kanta tasan yayi ha'kuri sosai sai dai bazata iya ja da batun Ummah ba dan haka kawai sai tai ta bashi baki har ya ha'kura ya koma Ports. Wasa-wasa har sai da suka haura 2months da 'yan kwanaki kafin Ummah ta bashi matar sa, hakan ma sai data ga ya shiga wani yanayi kafin nan ta sallame su domin a wani zuwa da yayi ya ri'kewa Teemah wuta Annur nata faman ihu amma bai ko kula da hakan ba, Teemah ce ma hankalin ta ya kasu biyu amma shikam yayi nisa cikin son kasancewa da ita, k'aran bugun 'kofa ne yasa shi 'kyaleta ba wai dan yaso ba yayi saurin kintsawa tare da zuwa ya bu'de 'kofan, ganin Ummah yasa shi jin kunya take yayi 'kasa da kansa yabi ta gefen ta ya fice daga 'dakin batare da ya ha'da ido da ita ba, Ummah kam da kallo ta bishi cikin ranta tace " kaji kunya ai fitinanne kawai". Duban ta ta mayar kan Teemah dake faman jijjiga Annur tana sussunne kai itama Ummah sai tace " ki bashi ko ruwa ma yasha zaiyi shiru" Da kai Teemah ta amsa mata batare da ta 'dago kai ta kalli Ummahn ba. "Hmm" Kawai Ummah tace a zuciyar ta kana tayi waje da tunanin yanda Fateemahn zata iya kulawa da iyalan ta Annur dacwannan fitinannen ita ka'dai, ita Ummah tausayin tane yasa ta kasa barin ta koma masa har yanzu, dan gani take Teemahn bazata iya kulawa da babyn ita ka'dai ba, a hakan ma cikin kwanakin nan tana barin ta tana yiwa Babyn abubuwa da kanta wai dan ta koya ta saba kama daga kan wanka, shirya shi, goyo rarrashin sa idan yana kuka harma da canza masa pampers duk ita ke yi da kanta, Alhamdulillah kuwa ba laifi tana 'ko'kari sosai dan haka washe gari Ummah ta sallame su suka koma gidan su, da yake ma already ya kammala ginin sa dan haka babu 6ata lokaci suka dira a can. Sosai tsarin gidan ya bambanta da gidansu na farko dan wannan mansion ne guda ga kyau ga girma, kallo 'daya zaka yi masa ka tabbatar yaci ku'di na gaban kwatance. Sosai gidan ya birge Teemah, ga 'dakuna wadatattu wanda mutane kusan goma ko ma sama da haka zasu iya rayuwa aciki batare da wani ya takura 'dan uwan sa ba. A ranar kuwa Teemah har sai data gane ashe dama shayi da zallar ruwa ake yinsa, sosai ta daku a wurin sa ta sha uwar wuya dan kac-kaca yayi mata, 'dinkin da akayi mata ne ha'de da gyaran da tasha sai ya suka ha'du suka matse ta. Shi kam Abbas baya jin gari sai yi yake yana 'karawa har da bashin sa na baya sai da yayi, shikan sa yayi mamakin yanayin daya same ta domin bai yi zaton haka ba duba da haihuwa da tayi amma sai ya same ta ba yanda ya zata ba hakan ne kuwa ya kusan zautar dashi. Sai da komai ya lafa bayan har sunyi wanka ma sun koma sun kwanta dayake abin na ransa sai bai yi 'kauron baki ba hannun sa cikin gashin ta a hankali yace da ita " ban fa gane ba wai dama haka ake sake canzawa idan an haihu, gaskiya in dai haka ne next year ma zaki 'kara haifa min little princess 'di ta, kinji yanda kika koma kuwa har nayi zaton ma ai ko da amarya ta nake tare fa?" Ya 'karashe maganar da murmushin tsokana. Teemah kam bata 'dago ba sai hannu da ta kai ta kamo kunnan sa taja da 'karfi sai ya ce " awshhh zaki ciremin kunnn fa?" 'Dan sassautawa tayi tare da fa'din "can't u see yanda ka ci zalina ko ?" Abbas sai yace " Sorry babe ba laifina bane ai duk laifin kine da kika rikitani...ban ma gaji ba fa na barki ne ki 'dan huta kawai kafin nan". Cikin shagwa6a tace " ni dai ba ruwana ai baka jin tausayina shine har kake cewa next year in sake haihuwa kama san wahalar dana sha kuwa kafin na haifi Annur?" Yace " ina tausayin ki mana kinfi son sai na fa'da da baki ne?" Sai tace " ai cewa kayi wai in 'kara haifan baby" "Ehh mana zaki haifa min Doctor mana daga ita shikenan sauran kuma ganin damar kine?" Teemah kam kafa'da ta no'ke tace " Ni dai ah ah baga Annur nan ba?" Abbas amsa ya bata da fa'din " shi ai zai gaje ni ne, burina uku ne kacal a duniya a yanzu nasamu biyu, kinga na farko na sameki wannan ya wuce, sauran kuma shine inga na samu yara na sun kuma cika min burina na zama doctor da kuma airforce ko bana raye ki cika min wannan Burin kinji.....insha Allahu Annur 'dina Major Mahmud Muhammad Al-hassan ne kinga insha Allahu in da raina Burina na biyu zai cika da yardar Allah is just d matter of time, kinga saura na ukun sai ki sake haifamin wata babyn wanda ko su biyu ka'dai Allah ya bani bazan yi takaici ba zan gode masa dan sune cikar BURINAH, idan ma suka fi hakan duk ina so bazan 'kiba sai dai fatan Allah ya bamu masu albarka" Teemah a ranta ta amsa da Ameen a zahiri kuwa kawai sai tayi shiru. Yace " kinyi shiru baki ce komai ba me yafaru?" A hankali tace " ba komai" Murmushi yayi tare da fa'din " matsoraciya an gaya miki ana surrender ne addu'ah akeyi sai kiga Allah ya kawo da sau'ki ko har kin daina son yaran ?" Teemah cewa tayi "Ah ah baga Annur ba ai shima ya isa " Sai yace " ni bai ishe ni ba to" "Allah ya kawo masu albarka to" ta fa'da da 'kosawa. Abbas kuwa cikin farin ciki ya ce " yauwa 'yan mata na abinda ya kamata ki fa'da tun 'dazu kenan ai" Da haka bacci ya 'dauke su kanta akan dantsen hannun sa tayi pillow dashi. ***** *Wai ina labarin Munnira ne?* Munnira na can yanzu rayuwa tai mata ba da'di domin bata samun ku'di kamar baya, hatta kasuwancin da mahaifiyar ta ke yi ma sai da ya ja baya saboda 'karancin ku'di, ita kam Munnira hakan bai wani dame ta sosai ba, babban abinda ya dame ta a yanzun shine neman gafarar mahalicci bisa ga abubuwan data aikata a baya, tun daga yawace-yawacen bin maza, zuwa wurin boka rashin cika ibadar ta ga kuma hakkin bayin Allahn data 'dauka wanda duk da da kunnan taji Mahmud yace ya yafe ta amma sai ta kasa sakin ranta gani take yi kamar alhakin bazai ta6a barin ta ba. Bata da abin yi a yanzun daya wuci ibada da istighfari tare da ro'kon ubangiji neman samun kyakkyawar 'karshe, bata damu da komai na duniya ba a yanzun, tuntuni ma ta yanke cewar zata koma sokkoto gidan kakannin ta gaba 'daya da zama ko dan ta samu islamiya mai kyau ma ta shiga ta nemi ilimin addinta. Allah cikin ikon sa kuma kafin tafiyar sai Allah ya ha'da ta da wani bahaushen ba kano, babban mutun ne domin matan sa har guda biyu da yara kusan bakwai, kasuwanci ya kawo shi garin ikko da nufin ubangiji kuma sai ya ha'da su inda ba'a wani 'dau lokaci ba aka saka ranar auren su wanda a kayi kafin bikin su Hannah aka kaita kano cikin matan sa, da da'di ba da'di haka dai rayuwar tayi ta gungurawa. Kishiyar Anty ma ta haihu inda Allah ya nufi Abbah da samun kyautar 'yan biyu mace da namiji tsaban murna Abbah har sai da yayi hawaye haka duk wanda yaji ma farin ciki sosai yake tayashi. Ranar suna yara suka ci sunan Mahmud da Khadija (takwaran Mummy. inda Abbah ya hana acanza wa namijin suna yace a 'kirashi da Mahmud 'dinsa macen ce dai ne ake 'kiran ta da Nanah. *Naso na kammala a page 'daya amma hakan bai samu dan haka ayi min ha'kuri plz.....insha Allahu next page zamu kammala labarin da iznin ubangiji wata 'kila ma zuwa gobe kuji ni.* _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [10/13, 12:50 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕 By *Salmerh MD* Luv story😍 *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Wannan shafin naku ne masoyan_ *_cApTaIn_ _AbbAs* _wanda na sani da wa'danda bansani ba, a duk inda kuke *SALMERH*_ _na jinjina muku_ .😍 ~*LAST PAGE*~💯 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* _U ll never find luv if what u ar seeking is perfection.....cuz d best qualities we have ar d ones we never see.....d worst qualities we have ar d ones we always see_ . 🅿 *94* Sati 'daya da komawar su suka nufi Dubai inda suka yiwa Mummy diran mikiya, bazata kawai ta gansu da mamaki dan batayi zaton haka ba. Yanayin yanda ta saki baki da ganin sun yasa suka kwashe da dariya Teemah har da ri'ke ciki taje ta rungume ta gudu tana fa'din " mu 'din ne de Mummy ba mafarki kike yi ba". Murmushi Mummy tayi tace " kun shammace ni ne ai shiyasa" Daddy kam daya gansu kar6an lil Mahmud yayi a hannun Mummy yana fa'din " Masha Allah yaro har yayi wayo yace da Mummy ta bashi abokinsa su gaisa yasan cewa yana da babban aboki. Kusa da Abbas yaje ya zauna da babyn a hannun sa ya kamo kunnan Abbas yana ja tare da fa'din wai dan yayi familyn kansa shine ya manta da shi ko a wayar ma bai fiya 'kiran sa ba sai sa'in da yaga dama....." yana yin yanda Abbas ke neman agajine ya saka Teemah murmushi Daddy kuwa ya'ki sakin shi sai ji sukayi yace " Daddy Annur fa na kallo kuma zai min dariya". Sakin kunnan nashi Daddy yayi suka 'dan dara gaba 'daya, sai Daddy ya 'daga Annur sama yana 'dan jujjuya shi yana murmushi, shima Annur idanun sa na kan Daddyn kamar wanda yana gane kamar sa ne, Daddy albarka ya ta sanyawa yaron tare da yiwa mai sunan sa addu'ah kana yace daga yau ya samu aboki tunda Abbas ya 'kisa. Su Teemah kam na ganin Mummy ai sai shagwa6a ta dawo sabuwa fil, kacokam 'dawainiyar Annur ta tattara ta barwa Mummy, ita kam sai dai zuwa yawo da Abbas suje can suje nan har mantawa take yi da tana da yaro ma a gida, kwanaki ka'dan ne kawai suka fita dashi da yake ma bashi da rigima sosai indai a 'koshe yake baya kuka shiyasa ma take barin sa hankalin ta a kwance. Satin su biyu a Dubai sai suka dawo inda suka sau'ka a Lagos gidan Anty ya barsu shi kam ya tafi hotel, duk da Abbah ya nuna rashin jin da'din sa akan hakan amma Abbas bai ce da shi komai ba dan shi haka kawai yake jin nauyin Abbah fiye da yanda yake jin na Daddy ma, har gani yake tamkar Abbah shine Father in-law 'din nasa ma, Anty ce de har yanzun ya kasa sabawa da ita da ma halayyar ta, kallon ta yake yi a komai yana ganin tamkar gaskiyar ta ka'dan ce a kullum. Sun ziyarci gidan Umar ma inda iyalan sa suka yi matu'kar farin ciki da hakan tarba mai kyau suka samu daga wurin Maman Amal inda suka rin'ka yabon kyan Baby Annur da yaran ta, har ji suke tamkar Fateemahn kar ta tafi. Abakin Anty suke jin labarin irin muguwar cutar infection 'din da ya ci 'karfin Anty chiddy ya ri'ke harda 'kafafun ta hatta tafiya ma bata iyawa a yanzun, mijin ta ma wai ya koreta daga gidan sa saboda asirin da ta tayi masa duk sun samu matsala hankalin sa ya dawo jikin sa kamar kowa, basu ma san inda take ba a halin yanzun. Teemah kam yanzu ko sunan matar ma bata 'kaunar tunawa gode wa Allah kawai take yi da bai bawa Anty Chiddy nasara akan ta ba ta cimma burin ta, tasan ba dan ikon Allah ba da yanzu itama ta zama wani abu daban " Alhamdulillah" kawai take ta nanatawa tare da tuno rayuwar ta na baya, sai hawaye ya gangaro mata, fakan idanun su Anty tayi ta goge shi Abbas ne ka'dai ya lura da ita amma bai hana ta ba kawai ya 'kura mata idanu.(Allah ubangiji kayi katanga da sharrin shai'dan kasa mufi 'karfin zu'katan mu AMEEEN). Har gidan amaryar Abbah suka je inda taga 'yan biyun Abbah gwanin sha'awa sosai suka birgeta, ga Nanah name sake d'in Mummyn ta itama kyakkyawa da ita. Photo ta ringa 'daukan su a wayar ta gwanin birgewa, sosai twins 'din suka shiga ranta sai taji tana sin su amma da ta tuna wahalar da ake sha kafin a haihu sai kawai ta basar ji take badan haka ba da babu abinda zai hana ta ta ringa ro'kon ubangiji ya bata itama. Amma wahalar da ta sha kafin ta haifi Annur yasa take jin shika'dai ma ya isheta rayuwa. Kwanan su uku a Lagos suka koma gida bayan Abbah yayi musu kyauta ta musamman wanda da 'kyar Teemah ta kar6a da yake ku'dine cash ya bata sai taji nauyin kar6a har sai da Anty ta sa baki kafin ta kar6a, suna isa gida kuwa ta ha'da Abbas da su. Bayan komawar su ne Teemah ta bawa Hannah labarin abinda ya sami Anty chiddy, Hannah ita kam " Allah shi 'kara" tace cuz ta tsani matar dama sosai tun asali. Daga baya sai suka hau hirar Dubai inda Hannah ke jin haushin rashin zuwan da bata yi ba da yake tun bayan bikin Teemah da Mummy zata koma Hannah ta so binta amma makaranta ya hana ta amma still burin hakan na nan acikin ranta. Hannah bata koma ba sai da yamma bayan sun gama hirar ta su kafin Hannah ta koma gida cike da tsarabobi. A kullum Teemah nazarin kalar rayuwar yanzu take yi musamman lokacin da sukayi waya da Anty ta sanar da ita cewa ashe Anty Chiddy Momcyn ta ma koran ta tayi saboda dama tana kawo ku'di ne shiyasa ta ke jan ta ajiki yanzu kuwa da baubu ku'din sai cuta sai taga cewa ai tatsanta kawai zatayi daga cikin 'dan abinda take dashi tunda ita yanzun bata da wani amfani, dan haka sai ta korata ta'ki zama da ita, koda tabar gidan kuwa cikin rashin sa'a da wani dare 'yan iskan gari suka zo 'dan inda suke fakewa da wasu 'kawayen ta da basu guje ta ba anan suka yi raping 'din su inda suka yi musu kaca-kaca sa'annan suka cire mata mama duka biyu da ranta da komai azaban hakan ne ya kashe ta inda aka tshinci gawansu su biyu a wula'kance. (Rayuwar dama kenan, shuka alkhairi ne ka girbi khairi sa6anin haka kuwa kaima kasan makomarka, dama duk wani mutun a duniya sarai yasan abinda yake aikata wa, wallahi kowa yasani inma sharri kake yi kasani haka ma khairi, sai dai idan shai'dan yayi galaba akan kane shine sai kaga ka kasa fuskantar gaskiyan balle har ka bita). ALLAH UBANGIJI KA SHIRYAR DAMU BISA HANYA MADAIDAICIYA KASA 'KARSHEN MU YAYI KYAU AMEEEN. Labarin mutuwar Anty Chiddy sosai ya ta6a zuciyar Teemah sai yanzun take jin tausayinta amma kuma hakan baida amfani saboda a kurarren lokaci ne, kuma gashi bata kasance cikin musulunci ba balle tayi al'kawarin tunawa da ita cikin addu'ar ta. Abbas kam data sanar dashi shiru yayi ba furta komai akai ba sai ma ya fara 'ko'karin mantar da ita damuwar data ke ciki da salon sa. Teemah na kula da Annur 'din ta kamar yadda kowacce uwa kake yi dan a kullum ta kalle ahi jin kanta takeyi tamkar wata babba ga wani son Annur 'din dake ratsa ta kullum ta dube ahi, har bata so taji muryar shi yana kuka, idan ka ga yanda take lalla6a abinta har zakayi mamakin ta, har ayanUn ta kuwa idan Annur ya rikice da kuka ta kasa rarrashin sa itama kukan take sanyawa cuz idan yafar irin kukan baya sauraren komai ko me zata bashi ba shiru yake yi ba. Akwai ranar da Abbas ya same ta a irin halin sosai sai ta bashi dariya amma bai kulata ba sai ya 'dauki Annur daga cinyar ta yayi ya lalla6ashi har ya tsagaita kukan, kafin ya dawo da kallon sa gareta a lokacin Annur na kwance akan ruwan cikin sa yana sau'ke numfashin kukan da yayi. Suna ha'da idanu sa ita sai ya saki murmushi yace " wai dama haka kuke yini kuka idan bana nan?" Share hawayen tayi da hannun tana 'kif'kif da idanu tace " Shine ai baya jin magana kullun sai ya ringa kuka" ta fa'da cikin shagwa6a66iyar muryar ta, abin sosai ya bawa Abbas dariya sai yace da ita " har kin daina son shi dan yana kuka ko?" Da sauri ta jijjiga kanta alamar ah ah, sai ta 'kara da fa'din " ai idan yayi shiru shikenan" Murmushi yayi mata kawai ya ya kai hannun sa bayan ta sai ta taho itama ta kwantar da kanta a jikin sa Abbas sai ya cusa hannun sa cikin gashin kanta. A hankali yace da ita " idan kina kuka haka ai shima bazai daina ba, ko kina son ya raina ki yace kema kina kuka irin nashi?" Jijjiga kai taui sai yace " toh kar kina yi masa kuka idan yana shi sai ki rarra she shi kawai har yayai shiru kinji?" Yayah ai shi'din ne ba yaji idan ya fara kuka" Sai ya tareta da fa'din "...karki damu zane shi zanyi ai ince ya daina yiwa 'yan matana kuka" Murmushi yai kawai dan ta fahimci da gangan kawai yake yi mata in ba haka ba miye abin duka ajikin Annur. Kwanaki sun 'dan ja har lokacin bikin su Hannah yayi inda ranar wata juma'ah aka 'daura auren Hannah da Bilal bayan sallar juma'ah haka ma Leesah wacce aka kaita gidan mijin ta dake Kaduna. Hannah kama tana nan cikin gari aka bar ta a wuse 2 dan Bilal bada ita zai tafi ba saboda makarantar ta sai aka barta a Abuja kafin ta kammala gaba 'daya. Ana kammala bikin su Hannah Abbas ya tattara iyalan sa suka koma Rivers, dayake dama hutun kwanaki ya kar6a kuma ya koma shi ka'dai ya bar su su 'dan kwana biyu ma ya'ki amincewa. Hatta Ummah tasa baki amma ya'ki yadda Ummah kam sai cewa tayi " fitinanne kawai ni dai Allah yasa kar yaron nan ya biyo wannan halin naka da ba'a gane kanka sam". Duk kissa da marairaita tayi dan ya barta amma ya'ki dole badan taso ba ta tattar suka koma a taren. Zuwa yanzun Annur yayi wayo sosai har yana gane mamar sa dan watan sa shida da haihuwa yayi 6ul-6ul abinsa, yayin da yana girma kamar sa da Abbas na sake bayyana ajikinsa da fuskar sa ma gaba d'aya. Watarana da dare lokacin tana yi masa shirin bacci diaper take sanya masa yana ta irin surutan su na yaran nan da hannunsa abaki, Abbas ma na gaban mirror fitowan sa kenan daga bathroom yana tsane jikinsa da towel a hannun sa Teemah sai tace " nifa Yayah bangane wannan abin ba, yaron nan na lura ko kalar farce na bai 'dauko ba kawai ya biyo ka gaba 'daya dube shi dan Allah da wani idanu ko ina zai kaisu oho" Abbas na jin abinda ta fa'da 'din sai ya taho a hankali zuwa inda suke 'din yana murmushi yace " kina ba'kin ciki ne dan yaro na ya biyoni? so yake ya gaji babansa shiyasa amma ai wannan 'kananun surutun da yake yi kam ba nawa bane sai de in ke kike koya masa irin nakin nan..., ni kuwa bana son ya 'dauko irin surutun kin da 'kin makaranta kinnan..... in kika kuskura kika koya masa kuwa nida kene" Teemah murmushi tayi kanta na 'kasa tana cigaba da shirya Annur tace " ai ba haramun bane dan nace bazan yi makaranta ba" Juyawa yayi yana komawa gaban mirron yace " ke de fa'di gaskiya 'yan mata" Itama sai tace " gaskiyar kenan ai" Murmushi yayi mai sauti bayan ya isa gaban madubin yace " kinsan me yasa ya yi kama da ni?" Waigowa tayi tace "ah ah " tare da juya kanta ta kalle shi. Cigaba yayi da fa'din saboda jarumtar da na nuna ne gurin 'daukan cikin sa kema in kina son mai kama da ke sai kiyi 'ko'kari ki nuna taki kalar jarumtar" Bata ma san lokacin da ta banka masa harara ba tana murmushi. Sai yace " ni kike yiwa haka ko, zaki ha'du dani ne yarinya zaki gane da waye kika yi" Ya 'karashe maganar yana 'dan dariya. ***** *Bayan shekara 'daya* Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da haihuwar Anty Leesah inda ta haifi baby girl 'din ta mai suna Aisha amma suna 'kiran ta da Nihal, Hannah kuwa yanzu ne ma take da cikin da bai fi 2-3month ba ga uban wahalar laulayi da take sha duk ta fita hayyacin ta gaba d'aya, har mamaki takeyi irin cikin Teemah yanda har cikin ya zama mutun ajikin ta ba tare da sun san da shi ba, ita kuwa tun baa je ko'ina ba ma ya bayyan kansa, cuz tun yana 1month ya fara wujijjiga ta da su amai ga za6an abinci kamar masifa, Teemah kanta tausayin ta takeji yanzun. Domin taso rana tsokanan ta amma yanda yanayin Hannah ake sai ta ma manta da waccen batun tausayin ta duk ya cika ta. Munnira kuwa babu labarin ciki agareta dan ta ziyarci asibitoci kusan uku ma amma duk ce mata suke yi mahaifarta ta riga ta lalace ikon Allah ne ka'dai zai sa ta haihu ko da gaba ne. Munnira tayi kuka sosai da jin sakamakon ta amma daga 'karshe sai ta ha'kura ta fawwalawa Allah komai dan tasan shine ka'dai mai bayarwa da hanawa in da rabon ta samu ko min daran da'de wa wataran zata haihu. Anty ma kullum mutuwar Mahmud sabo yake dawo mata musamman idan taga yanda Abbah ke nan-nan da twins 'din sa gashi kullum cikin farin ciki zaka ganshi saboda bashi da damuwar komai, koda kuwa ranar da yake gidan ta ne Abbah dole sai yayi waya da yaransa duk da dama ba maganar suka iya sosai ba amma a hakan wai shi muryar yaran sa yake son yaji, cikin dokar kwanan su ma sai da ya ro'ki Anty akan ta yi ha'kuri koda lokutan girkin tane yana so yana zuwa dubo yaran sa dan bazai iya har kwana biyu kuma suna gari 'daya amma bai gansu ba tare da 'daukan mata al'kawarin babu cin amanar ta koka'dan da zaiyi bayaga ganin gudan jininsa. Dolen Anty ta amince batare da ta nuna masa damuwar komai ba a fili, duk da bata ba'kin ciki da yaran nasa amma ita ka'dai ta san yanda take ji idan taga Abbah na zumu'di akan 'yan biyun yaran sosai ta ke 'kara neman gafarar mahalicci akan banzatar da rayuwar nata 'dan da tayi sanadin haka ma yasa kullum sai Mahmud ya samu kyakkyawar addu'ah daga wurin ta bata ta6a shagala da hakan ba. Gashi itama Allah sai ya jarabce ta da masifar son twins 'din, ji take kamar ta 'kwato su a wurin ta, amma babu dama lura da hakan da Anty Sadiya tayi yasa ta yanke aranta cewa idan ta yaye su zata bata little Mahmud kyauta ya zama 'dan gidan ta in yaso ita sai ta ri'ke Nanah in Allah yasake bata wani kuma sai ta hada ta ri'ke su, kuma tana da ya'kinin Abbah ma bazai 'ki amincewa ba, inyaso sai suyi yarjejeniya koda a rubuce ne akan bazata ta6a goran ta mata ko kuma kar6an sa ko da kuwa menene zai faru yariga ya zama 'dan ta, ta dan itama Anty Sadiyan tausayin Anty take ji sosai. Tana yaye su kuwa ta sanar da Abbah ku'durin ta sai dai Abbah ya so ya nuna 'kin amincewar sa sai da ta ta fahimtar dashi kafin nan ya yarda, amma ba wai har ransa ba dan shi yaso yaransa su taso a tare kamar yanda aka haife su kuma a hannun mahaifiyar su saboda ya yaba da hankali tarbiya da nutsuwar ta k'warai da gaske shiyasa bashi da haufi akan tarbiyar da zata bawa yaransa. Da Anty ta sami labarin hakan kuwa har sai da tayi kuka dan farin ciki, tun da aka yaye su aka kawo mata shi sai ta sa aka nemo mata mai kula dashi tun daga kano tazo tana tayata rainon sa da kukawa dashi Anty kam sosai taji da'din wannan karamcin kawai sai take ta godewa mahalicci bisa ga chance 'din daya sake bata akaro ba biyu matsayin mahaifiya wannan karon kam tana jin rayuwar 'danta zai kasance ne kishiyar rayuwar da ta bawa Marigayi bazata sake yin haukan da tayi a wancan lokacin ba zata ja 'dan ta ajiki ta bashi tarbiyar data dace ta kuma cika rayuwar sa da farin ciki har sai yaji cewa yafi kowa sa'an mahaifiya. Wannan abin da amaryar Abbah tayi ba 'karamin daraja ya 'kara mata a idanun Anty ba, sai take jinta tamkar 'yar uwarta ta jini domin tayi abinda ba kowa ne zai iya ba a wannan zamanin da kishi ya zame wa mata tamkar ibada a zu'katan su. ***** Teemah ma tuni ta yaye Annur 'din ta tun yana da 15months da haihuwa ganin yanda yake girma, tsayi da wayo duk lokaci guda, yana da 7 month yafara takawa, da kansa ma sai bai damu da yasha maman ba, dan wataran a yini bai fi sau biyu yake sha ba kuma ko bata bashi ba baya rikici, ganin hakan yasa Abbas yace da ita kawai ta daina bashi ma gaba 'daya ita kama ai dama gaba ta kaita dama bata son ta jima da shi abakin mama har ranta take jin tsoron kar su lalace ganin cewa Abbas nan yafi so a ilahirin jikinta shiyasa take nan nan da shi itama. Ginin makarantar ta da Abbas yace za'a yi mata ma an kammala shi tuntuni amma a Abuja aka yi, wanda makarntar ta tsaru iya tsaruwa, sosai Abbas ya kashe maku'dan ku'da'de dan ganin makarantar ta ginu bisa tsari da daraja har an luncher shi, inda ake bayar da karatu arabi da boko daga 8am to 5pm ha'de da babban masallaci aciki 6angaren mata da maza, inda suke ajiye fannin boko 'karfe 'daya bayan sun yi sallah sun 'dan huta kuma 2:30 sai su siha fannin islamiya sosai ake horara da yara kan dukkan 6angarorin biyu. Abbas ne ya sanyawa makarantar suna A-Z international School, kuma ba laifi makarantar ta samu kar6uwa sosai musamman da yake suna da fannoni da dama tun daga 6angaren Nursery, primary har secondary duk aciki. Haka kuma Abbas bai manta da su Innah ba, bai sake komawa ba kam amma a duk 'karshen wata yake transfer 'din ku'di wa Rabi'u wanda yasan zai ishe su hidimar makaranta da kuma gida, kuma Rabi'u na 'ko'karin 'kiran sa akai-akai yana ha'da su da Innah ma su gaisa da ita. Yanayin yanda yake jin ta ka'dai ma ya ishe sa sanin cewa Rabi'u bai ci amanar su ba daga abinda yake tura masa. ***** Wata ranar Alhamis da 'karfe biyu na rana 2:09pm, Abbas ne ya shigo gidan jikin sa uniform kaki ne da hular sa da wayar sa duk ri'ke a hannu. A gajiye yake gaba 'daya dan haka sai ya zube a parlour kan kujera yana 'kwala 'kiran sunan ta. Teemah iska ta hura a bakin ta ta furzar da jin muryar tashi bata so ta amsa da 'karfi har baccin da Annur ya fara yanzun ya yanke gashi daga jin tashin muryar Abbas 'din har ya bu'de idanu dayake baccin ya 'dan fara cin idanunsa sai take ya kuma mai da wa ya rufe su tasan badan baccin ba da ko ita bata isa ta riga shi isa wurin Abbas 'din ba, dan wata muguwar sha'kuwa ce a tsakanin su, itan ma shiru tayi bata amsa ba dan kar ta tashe sa tun safe be yi bacci ba sai rigimar tsiya yau 'din yake ji dashi, hatta bathroom bai barta ta shiga ba sai da ya bita sukayi wankan tare, inda da dabara ta samu da tayi masa nasa sai ta ha'da shi da abin wasa cikin bathtub daya 'dauki hankalin sa sannan ta samu ta faki idanun sa tayi wankan 'kar'kashin shower tana yi ma tana kallon sa dan kar ya lura da ita bata wanke fuska ba ma sai bayan ta d'aura towel jikin ta sannan ta wanke fuskar tata daga nan sai ta 'dauko shi suka fito. Tsawon mintina biyar tana lalla6a shi tare da mai wasa cikin kunnan sa da hannun ta sannan ta samu baccin ya 'danyi nauyi, sai ta sau'ko daga gadon a hankali ta baro mishi 'dakun bayan ta daidaita masa 'karfin fan yanda iskan baze yi masa yawa ba....jikinta bomshot ne na blue jeans da wata 'yar 6ingilar riga mai bu'da'd'den gaba sky blue sosai tayi kyau cikin kayan kamar 'yar turawa. A parlour ta hango shi zaune idanunsa a lumshe ya kishingi'da ga dukkan alamu agajiye ya dawo domin yanayin sa ne ya fallasa asirin zuciyar sa, 'kafafunsa kawai ya iya sa6ewa daga cikin boot 'din dake 'kafar sa baya ga haka babu abinda ya sauya daga yanayin shigar sa. Isa tayi ta zauna daga gefen sa taja hancin sa a hankali tana murmushi, shima 'din murmushin yayi batare da ya bu'de idanu ba. Sai da ta zauna da kyau kafin tace " Saura 'kiris ka hana min yaro na bacci da wannan ihun naka fa, da bai yi ba kuwa yau 'din zaka koyi goyo babu ruwana" Bu'de idanun yayi ya sau'ke su a kan fuskar ta a hankali ya kuma sau'kar da idanun yabi jikinta yana murmushi yace " really?" Itama murmushin tayi tare da jinjina mai kai sannan ta mi'ke ta 'dauko mai ruwa mai sanyi da cup dayake tasan halinsa matu'kar ya dawo gidan ruwa yake fara nema kafin sauran hidimomin su biyo baya. Shi kam a fakaice yabita da idanu har taje ta dawo in baka sani ba zakaui zaton ko idanun a rufe suke saboda yanda ya 'kan'kansu. Da isowanta sai ta cika mai glass cup 'din da ruwan ta mi'ka mai sai yasa hannu ya kar6a. Ganin ya riga ya cire takalman dake 'kafan sa ne yasa sai ta zauna daga gefen sa tare da 'dago hannun ta tana shirin 6alla mai bottles 'din gabar rigar sai ya cire cup 'din daga bakin sa ya kalle ta suna ha'da idanu sai tace " a kara ne?" bai yi magana ba kawai ya dire cup 'dib tare da janyo hannun nata ta fa'do jikin sa, baki ta tura gaba tana 'ko'karin tashi daga jikin nasa sai ya 'daga kanta ya sau'ke mata kiss a samna lips din ta kad'an yana raba bakin su sai idanunsu ya sar'ke cikin na juna tuni ma har gannunta ya keawaya bayan wuyan sa, ganin hakn kuwa yasa shi mi'kewa tsaye da ita ya nufi bedroom 'din su yana fa'din " wariyar da ake min ya isa haka nima yau dole ki kar6i ajiyar princess 'dita na san ita ba zata na ware ni ba" Bai dire ta ko'ina ba sai a tsakiyar gado sai ya kuma sau'ke wani kisa 'din gefen wuyan ta sannan ya 'dago ya kalle ta bai yi magana ba illah gira 'daya da ya 'dage mata yana murmushi, Teemah ma sai ta maida masa martani tare da fa'din " nifa ban ware ka ba Allah Yayah, ai kasan duk yanda zan so Annur ba zai ta6a kamo 'kafar Yayah na ba cuz shine farin cikina kuma haske na " Tayi maganar ne a hankali cikin sanyi da shagwa6an ta kamar yanda ta saba yi masa a kullum. Fuskar sa ya kawo kusa da nata hancin su na gugan na juna, idanun su ma sar'ke da na juna sannan shima a hankali yace da ita " ban yadda ba ni, sai kin nuna min zahiri na gani" Yayi maganar yanda ita ka'dai ce za taji tare da kai hannun sa zuwa marar ta yana shafowa a hankali still idanun su sar'ke da juna. Itama hannayen ta kai ta dafa kafa'dun sa da shi batare da tayi magana a zahiri ba illah murmushi a cikin ranta take aytana irin yanda take jin son shi a zuciyar ta wanda yariga yayiwa dukkan ga6o6inta dabaibaiyi ta maimaita kalmar " i love cikin ranta har sau biyu na ukun ne bata san cewa har ya fito fili ba tsaban yanda shau'ki yake 'diban ta. Shi kam yana jin abinda ta furta 'din sai ya lumshe idanu domin har tsakar kansa yaji sau'kan kalmar. Bai amsa ba sai da ya sau'ke bakinsa kan nata ya ya sumbaci lips 'dinta daya furta maganan kafin yace " Love u more habibty" Hakan da ya fa'da ne yasa ta fahimci cewa maganar tata ta fito fili domin amsa shi'din ya bata. Yana fa'din hakan sai ya bar jikin ta ya koma gefen ta ya kwanta duk idanun su na kallon saman ceiling, hannun ta dake gefen sa ya kamo ya sau'ke shi saman 'kirjin sa saitin zuciyar sa sai ya lumshe idanu yace " bansan asalin lokacin dana fara son ki ba i just found my heart cike da 'kaunar ki, sometimes har mamakin kaina nake yi cuz bana iya controlling feelings 'dina akan ki matu'kar zuciya ta ta bu'kaci ganin ki ban iya jurewa har sai na gankin sannan nake nutsuwa, tun ada na tsani inga kin fifita wani akaina duk da kuwa nasan rashin sha'kuwa ta dake ne zai sa hakan amma duk da haka ban tantance meke damuna ba a lokacin nayi ta dulmiya cikin 'kunci da takaici, ban tabbatar da girman son da nake miki ba sai lokacin da Mahmud yazo min da labarin auren ku, a lokacin jinayi tamkar 'karshen farin cikina kenan a duniya, ji nayi tamkar nayi hauka... idan na tuna za'a yi auren ki, wallahi Zahra a lokacin tafiya kawai nake yi amma komai idan inayi sai inji tamkar bani bane har sai dana 'kwammaci mutuwa ta fiye da rayuwa duk da kuwa nasan hakan zunubi ne but i cant help it, saboda irin suyar da zuciyata keyi min a duk lokacin da na tuna kin zama mallakin wani ba ni ba sanadin haka na tafi Borno duk da nasan suna shan fama da 'yan ta'adda saboda ina ganin shine hanya mafi sau'ki da zan iya rabuwa da soyayyarki idan na daina numfashi, ban ta6a zama na fa'dawa wani damuwa ta ba balle na samu shawara saboda ban saba hakan ba, sa'a 'daya nayi kawai saboda wani 6angare daga zuciya ta na bani shawara akan na sanya dangana cikin al'amurana, wannan shawarar nabi na mida damuwa ta wurin ubangijina sai dai ban ta6a accepting d fact that wai kin bar ni kenan har abada ba, shiyasa salon addu'ah ta bata canza ba akanki amma ban ta6a tunanin mutuwa ce zata dawo da ke hannu na ba hakan bai ma shigo cikin tunani ba sam kuma ban fatan Allah ya rabaki da mijinki ba, ni dai fatana a kullum shine Allah ya bani Zahra musamman da nake da yak'inin cewa u too had feelings d same as i had 4u is just that babu wanda ya bayyana shi ga 'dan uwansa shine ka'dai damuwa ta da kaina na fahimci son da kike min tun kafin auren ki da marigayi. Sai gashi a lokacin da dangana ya fara zama a raina, na sanyawa raina cewa 'kaddarata kenan, shine soyayyar da babu ranar cikar ta sai kuma Allah ya nuna ikon sa akan hakan ya dawo min dake hannuna.... Zahra our love is like an eternal flame that no one can touch or break it, it can't be blown out, it carries many colors, until the end of time....our love is like d wind....i can't see it, but i can feel it all over me....idan nace miki zan misalta miki girman farin cikin dana tsinci kaina a ciki lokacin da akayi min albishir 'din auren ki bazaki ta6a fahimta ba...all i knew ws u ar my woman, my life, my everything....may be 2 d whole world u may be only one, but to me u ar my world, my happiness my weakness also d strong part of me.....banajin akwai kalaman da zan iya furtawa Zahra to tell u all d love i have 4u within my heart....i wan't u to always remember that i do love u, i'm with u, still with u, nd always be with u 4ever.... ko yau Allah ya 'dauki raina nasan na cika BURINAH a kanki tunda na mallake kuma muka so juna wannan ka'dai ma ya isheni alfahari". Juyo da kansa yayi ya kalle ta tare da bu'de idanu ya sau'ke shi a kan fuskar ta da suka ji'ku da ruwan hawaye bakin ta sai rawa yake yi kamar tana so furta wani abu amma takasa still kuma hannun ta kan 'kirjin sa da ji'ka'k'un idanun ta sanya 'kwayar idanun ta cikin nashi tana jin wani sonshi mai ha'de tarin kwarjinin 'kaunarsa na ratsa dukkan gangan jiki da zuciyar ta hawayen tane kawai suke 'kara 'karfin speed suna sake sau'kowa batare da ta janye daga kallon nasa ba. Idanun su sar'ke da juna yace " I so much luv u 'yan matan Yayah, ke na fara so a rayuwata kuma insha Allahu dake zan ru'fe murfin zuciya ta, ha'ki'ka ke ta dabance a rayuwa ta gaba 'daya......" Rintse ido tayi da 'karfi tana jin yanda zuciyar sa ke bugawa da sauri, ko haka ya bar ta ko da bai furta komai ba ita kanta tasan Yayah na matu'kar 'kaunar ta ko daga bugun da zuciyar sa ke yi bazata 'karyata kalaman sa ba. She is totally speechless, bata san mai zata ce da shi ba da har zata iya kamo kwatankwacin irin son da shi yake yi mata ba, tana jin nata son ba komai bane compare to nashi duk kuwa da cewa tana jine a yanzun tamkar idan babu shi rayuwar ta bashi da da anfani, tana jin bazata iya rayuwa batare da shi ba bama ta fatan wani abu da zai zo ya shiga tsakanin su koda kuwa menene shi, hatta mutuwa in so samu ne zata fison ya 'dauke ta kafin shi. Bata bu'de idanun ba taji shi a saman ta yana faman shinshinan wuyan ta tare da share mata hawayen dake fuskart kamar ba shine ya gama zayyano mata kalaman 'kauna cikin sanyin hali da nutsuwa ba, dai-dai kunnan ta taji ya ra'da mata " kin shirya kar6an ajiyan belove baby nurse 'din nawa?" Shiru tayi bata yi magana ba shima bai damu ba kawai yaci gaba da abinda ya keyi inda kamar wani ba'a son ran shi ba yake shafo ta very slow but so romantic tare da 'ko'karin kaiwan hannun sa can 'kasan marar ta, ita kanta yanda yake yi 'din yafara 'daukan hankalin sa har ta fara tunanin irin abin birgewan dazata yi masa a yau 'din in return to his tadaddun love words 'din da taji daga bakin sa yanzun, wanda ta tabbatar zai faranta ransa shima. Shikam har ya fara 'daukan layi inda ya gama bu'de gaban rigar dake jikin ta yana yamutsa ta yayin da hannun sa 'daya ke kan mararta 'ko'karin 6alle hook 'din bomshort 'din dake jikinta yakeyi caraf kunnuwan su suka jiyo muryar Annur yana fa'din " Daddy! "Subhanallah"!! yace acikin zuciyar sa tare da barin abinda yake yi cikin sauri, amma bai juya ya kalli Annur 'din ba sai ya tsaya kallon cikin idanunta kawai a hautsine. Itama Teemah sai yanzun ta bu'de idanun ta da jin muryar Annur 'din tafara 'ko'karin jan rigar ta rufe jikin ta da kyau, suna ha'da idanu a hankali sai yace "shine dagangan kika 'ki rufe 'kofan ko?" Tasan ba laifin ta bane cuz shine ya kawo ta 'dakin kuma shima 'din tasan yasan hakan kawai dai rasa abin fa'da yayi ko kuma ya mance a yanayin da suka shigo shiyasa, dan haka sai ta saki murmushin mugun ta da guntun hawayen ta tayi masa fari da ido tare da fa'din " Ai kaine ka bar 'kofan bani ba kuma kaga Annur ma yace ka 'kyaleni baya so shima" Lakatan hancin ta yayi da hannun sa yace " zan kamaki ai" sannan ya bar jikin ta ya sau'ka daga gadon ya nufi wajen Annur dake 'ko'karin tahowa inda suke, Abbas 'daga shi yayi sama yace " Oyoyo my boy na dawo bangan ka ba" Dariya Annur yayi masa yana jan hancin sa duk da kuwa bai warware daga baccin daya tashi ba amma yanda yake son Abbas 'din ya sanya shi 'dan warwarewa dan sosai Abbas ke yi masa wasa idan yana gida shiyasa suka sha'ku hatta Teemah 'yar kallo take zama idan Abbas na gida wa'kan da yake yi masa ma yanzu har Annur 'din ya iyata dan sama zai idaga shi yana dariya yana cewa " wah...wah...waladin...Muhammad Nury waladin...., yaron Daddy waladin, yaron Mummy waladin, mai sunan Daddy waladin" Annur ya rin'ka dariya kenan idan yaji wataran kuwa hannayen sa yake kamawa kamar sa'ani suyi ta wa'kar su a tare. Haka hatta wanka shike yi masa idan yana gida ya kuma bashi abinci sannan ya kaishi 'dakin dayake kwana yayi masa addu'ah yana lalla6asa har sai yayi bacci. Sau tari Teemah sai dai ta ta binsu da idanu ko kuma tana rakashi musamman idan zai kaishi bacci sai ta bisu abaya ita kanta tana jinjina wannan sha'kuwar cuz idan kaga Annur ya manne mata to Abbas baya gida ne in kuwa yana nan kallo ma bata ishesa ba. Sha'kuwa ce mai mugun 'karfi a tsakanin su hatta yawo wataran fita suke yi su biyu su barta agida wani sa'in ne idan zasu fita Annur sai ya je ya janyo mayafin da duk yagani a fili ya kawo mata yace " mummy let's go" Abbas idan ranar baiyi niyyan fita da ita ba sai yace "ah ah banda mummy, ita ta ta zauna a gida zamu kawo mata abin da'di". Cuz wataran office suke zuwa wataran kuma yawo kawai zai kaishi, wani gyaran kai da Abbas ya kaishi akayi masa wai wanda yagani, Annur yaro ne amma ba laifi yana da suman kai sosai, hakan yasa Abbas yake kulawa da kan nasa kamar wani babba yasa akai masa low cut aka gyara gashin kamar ba 'dan hausawa ba, kafin Abbas ya zama ma aikacin soja ba irin gyaran kan da baya yi, amma tunda ya shiga aikin sai ya zamana gashin ma ba bari yake ba shikuwa yana da masifar son tara gashi shiyasa ma daga ya 'dan 'dauki hutu zaka ga har ya tara suma ya kuma gyara shi gwanin birgewa kafin cikar hutun Teemah kanta yana bata sha'awah da zarar hutunsa ya 'kare kuma shikenan zai je ya cire su, wannan dalilin ne yasa yake yiwa Annur dan shi bai da damar yin hakan, shi mutun ne mai son cika BURIKAN SA, sai dai baya binsu a gaggauce cikin natsuwa take binsu shiyasa idan bai samu daman yin abu ba sai ya 'dorawa wani nashi burin, kamar yanzun burinsa na son Teemah ta zama doctor wanda ta'ki bai yi fushi ba sai ya 'dauke burin daga kanta abin na nan a cikin ransa amma sai ya bari akan 'yarsa idan har Allah ya bashi....ita zata cika masa wannan burin. Yanzun kuwa da Annur yake ri'ke a hannunsa sai yake ta faman jan hancin Abbas yana dariya, Abbas kuma yana kaucewa tare da mai wasa acikin sa da bakin sa da yake jikinsa babu riga illah pant ne kawai so idan ya hura cikin sai yayi 'kara wanda yake matu'kar sa ka Annur dariya idan yayi masa hakan. Gurin da Teemah take ya koma da shi yana fa'din " Annur baya son zama da kaya agida da alama halin ki yayo" Teemah kam murmushi mai sauti kawai tayi batare da ta tanka masa ba sosai take jin da'din yanda Abbas yake kulawa da Annur duk kuwa da abubuwan dake gaban sa amma sam bai sa sun rinjayi tattalin iyalinsa ba, sosai yake 'ko'kari akan hakan har tausayi yake bawa Teemah wani lokacin idan taga Annur na ma'kal'kale masa, ita kanta tana so suna 'dan barinsa yana samun natsuwa, sau tari sai dai in tana son ya barshi sai ta yi masa wayo tace "bamboo Annur, come on zo in goya ka kayiwa Daddy dariya" Annur idan yaji goyon ne kafin yake zuwa ya bar Abbas 'din, wataran ma har datse 'kofa take yi da key dan ya samu yayi bacci, tun Annur bai gano ba har ya gane so idan baiga Daddyn nasa ba kuma yaga 'kofa arufe sai yaje yayi ta bugawa yana 'kananun kuka tare da 'kiran "Daddy"! A gefenta Abbas ya zauna inda ya maida idanunsa kan fuskar Annur batare da ya kalle ta ba ya fara yiwa Annur wa'kansa ta waladin " wah...wah...waladin.... Annur kam sai dariya yake yi Teemah kuwa binsu take da kallon 'kauna tana murmushi, tasan idan kowa irin Abbas ne to da babu macen da zatayi 'korafi akan raino amma ina tasan bakowa ke sa'an samun hakan ba dan hgaka sai ta furta " Alhamdulillah" da dacen samun miji nagari da tayi mai son ta mai kula da dukkan al'amuranta, mai baiwa bu'katun muhimmanci uwa uba kulawa da ahalin gidan sa. Sai da ya gama wa'kar tasa kafin yace da Annur " Yaron Daddy... you need a baby sis to play with right?" Annur sai ya 'dage kai sama tare da fa'din " yes Daddy just like Anty Ummah's baby" yana washe fafaren 'kananun ha'koran sa waje. (Anty Ummah wata mata ce a block 'dinsu data haihu sati biyu yanzu da suka je da Teemah ta 'dauki babyn shine ya 'kare mata kallo harda wasa da 'kafafuwan ta ). Abbas kam kamar Annur ya ziga shi sai ya ya sake fa'din " Oyah tell ur mum that u want ur baby sis from her like Anty Ummah's baby.." Annur kallon ya dawo da shi kan Teemah data zuba musu idanu tana murmushi cikin maganar sa da bata gama mi'kewa ba yace " yesh Mummy ...i wan my lil prinshesh right away" Teemah zaro idanu tayi tace " see u, right away 'din 'kaniyar ka a ina zan samo maka yanzun?" Abbas kam murmushi yayi ya bashi hannu tare da kama chicks 'din sa yace " That's my boy, we need our princess right now ko ?" Kai Annur ya 'daga masa yana washe baki, Abbas kam yana murmushi yayi pecking 'dinsa a goshi. Teemah kuwa tashi tayi da sauri ta fita taje 'dayan 'dakin ta 'dauko teddy bear 'din sa da yake wasa dashi ta kawo masa tace " ga lil princess 'din taka....bana son damuwa ni" Tana maganar tana cusawa a tsakanin sa da Abbas. Annur yana ansa sai yayi jifa dashi gefe tare da fa'din " Not ths mummy i want d yeal one" Dariya dukkan su suka sanya ilah Annur, Teemah kam harda zama Abbas yana cikin dariyar yace " yaro na na son d real princess ba fake ba sai ki shirya kar6an lil sis 'din Prince 'dina an jima " Kafa'da ta no'ke tace " ni dai ah ah...Allah Yayah duk kai kake koyawa yaron nan iyayi.....har da wani now sai kace an gaya masa haihuwan sau'ki ne dashi, nawa ma yake shi'din 19months ne fa yake har yanzu dan Allah, ni dai gaskiya ba yanzu ba....kuma ya dameni da zancen babyn nan zane shi zan fara ni kam" Abbas sai yace " Kina ta6a min yaro to kuwa sai kin haifi triplet ba ruwana " Sai tayi saurin no'ke kafa'da kamar 'yar yarinya 'karama tana tunzura baki gaba. Abbas ma sai yace " do ur worst 'yan mata zaki kuwa sha mamaki...yaron da nake planning kai shi school kwanan-nan 'din ne zaki ce min bai kai ya samu sister ba? Kin ma yaudari kanki yarinya is better ki fara shiri ma cuz next year like ths insha Allhu i'm with my 2 kids". Jikin sa ta fa'da tana kukan shagwa6a tare da kaimar bugu a 'kirjin sa shikam dariya ma ta bashi da shegen tsoron nata Annur ma ganin yana dariyar shima sai ya bu'de bakin sa da 'kananun ha'koran sa guda 12 yana taya Abbas 'din dariya. _They live happily ever._ *ALHAMDULILLAH WASSALATU WASSALAMU ALA NABIYUL KAREEM*. Anan na kawo 'karshen littafin *CAPTAIN ABBAS* Wanda na 'dauki tsawon lokaci ina rubuta shi amma bazan iya fa'da muku tsawon lokacin ba gaskiya dan kar kumin dariya🙈.....lolz *Yabo da godiya sun tabbata ga Allah ma'daukin sarki mai kowa mai komai wanda* *ya kawo mu har wannan lokacin muna cikin rayayyu.* Fatan darasin dake cikin labarin ya isar, wanda suka ha'da da tsoron Allah, ha'kuri, da kuma tawakkali...ha'kurin ma dai shine kusan mafi rinjaye cikin labarin so ina fatan zaku fahimci manufata duk da nasan bakowa ne zai fahimci hakan ba amma ko da tsirarune daga cikin makaranta labarin idan suka fahimta toh Alhamdulillah *BURIN SALMERH* ya cika...... rayuwar d'an Adam de dukkanin ta aya ce mai girman gaske... nasan munsan hakan, sai dai still bamu fasa aikata son zuciyar mu ba, musamman idan mukayi duba da yanda rayuwa take tafiya a wannan zamanin, mafi yawancin mu mu muna aikata abinda ran mu yake so ne koda kuwa munsan ba akan dai-dai muke ba amma sai zuciyoyin mu su rinjaye mu sai muna ganin kamar dai-dai muke aikatawa azahirance, wanda bazamu tashi yin Allah wadai da hakan ba har sai ranar da Allah ya nuna ikon sa akan mu alokacin ne dayawan mutane ke gane kuskuren da suke aikatawa. Son zuciya, son kai, buri da kaiwa kanmu inda Allah bai kaimu ba shima babu amfani tunda kunga yanda rayuwar Anty, Munnira da kuma Anty Chiddy ya kasance saboda son zuciyoyin su daga 'karshe kowa sai da ya yi nadaman halin sa wanda tun farko rashin ha'kuri ne ya haifar da shi....Yayin da ha'kurin Mahmud yasa ya amsa 'kiran mahaliccin sa ayan yardajje cikin natsuwa. ALLAH UBANGIJI KA KASA MU GANE GASKIYA GASKIYA CE KUMA KABAMU IKON YIN AIKI DA SHI. ....fatan zaku fahimce ni....kuraren dake cikin labarin kuma ku yafemin dan Allah kar ku tuhumeni akan hakan ayi min uzuri saboda littafina na farko kenan duk dama bashi na fara rubutawa ba amma dai kusan zance shine farko tunda al'kalamin sa ya kai 'karshe. *MY MENTOR* Kullum kina raina, 'yar uwa abar alfahari *SAFIYYA ALIYU WAKILI* jagorata, kuma hasken idanuna....ha'ki'ka ina alfahari dake cuz irin ki ka'dan akaf 'din rayuwa, ke ta dabance, alkhairin ki gareni mai girma ne, bani da bakin godiya, dan nasan duk matsayin dana kai a duniyar gizo to sanadin kine...nasan da bazar ki nake taka rawa ta. Fatana Allah ubangiji ya raya mana Khairy da Haidar da ma mabiyan su bisa tafarkin gaskiya. *JINJINAR BAN GIRMA GA* 👍 Anty na (Anty maimunat O.G MAHNOOR) KIN FI 'KARFIN GODIYA SAI DAI FATAN ALLAH UBANGIJI YA SAKA MIKI DA MAFIFICIN ALKHAIRI ALLAH YA RAYA MANA ZURI'A YASA KIFI HAKA YA BAKI HA'KURIN KULAWA DA MU. *BAN MANTA DAKU BA MUTANE NAH* . Anty Rahama Maman Ahmad Mrs Abubakar Rukyn mama Safiyya A W Mama Queen Maryam Abdul Queen Ameena dama wa'danda ban ambata duk Salmerh na gaisuwa.🍭 *SA'KON MASOYA* Fans 'dina na 'kwarai wa'danda sukayi ha'kuri dani da rashin typing 'dina akan lokaci, kurakuraina, da sauransu, suka kuma bada lokuta, si suna faranta min da da'da'dan sharhin su ha'ki'ka bazan ta6a mantawa da ku da addu'o inku ba🤞🏻. Groups 'din duk dana ke ciki nagode sosai da ha'din kan da kuka bani da kuma 'kwarin gwiwar ku gami da sharhin ku Allah ubangiji ya bar 'kauna Ameen.👏🏻 🤙🏻 Umm Haibat, Aisha Aliyu (Zumunta novel ina godiya sosai). *AysherudAhmad*(wattpad)...... yau dai burin ki ya cika Captain ya kammala sai godiya. *JINJINA TA MUSAMMAN GA* 👎🏻 Readers 'din Captain Abbas dake facebook da wattpad duk ina godiya sa'konnin ku duk na iso ni da addu'o'i...kuma ina muku fatan Alkhairi Allah ya bar 'kauna. Bazan iya lissafo sunayen ku anan ba amma kusani kuna zane cikin zuciyata kuma nima ina sonku sosai.😍 *MUST READ* 🤞🏻 Sai mun ha'du a sabon littafina✍🏻 mai suna 💕 *NOORUL 💕 (Haske nah)* Ta'kaitaccen labarine mai matu'kar 'daukan hankali, amma wanda ya bibiyeni ne ka'dai zai fahimci hakan.👌🏻 👇🏼 Daga 🖊al'kalamin👉🏻 *SALMERH MD* follow *Serlmerh-md* @ wattpad and instagram.🤝