ßµŠÅ Ä MµTµ Littafi Na Biyu (2) Part A Na Abdulaziz Sani M /Gini Marubucin Yaci Gaba Da Cewa SA'ADDA boka Rufyan ya zo jawabinsa sai hankalin yarima Muraisu ya dugunzuma har kwalla ta zo masa, ya dubi boka Rufyan cikin tsananin takaici ya ce, "Yanzu ke nan kana nufin cewa nima mutuwa zan yi nan ba da dadewa ba kuma idan ban auri gimbiya Husnaila ba shi ke nan babu mai kawar da su azzalumaí Huraisu?". Koda jin wannan tambaya sai boka Rufyan yai shiu ya kasa cewa komai, kawai sai ya mike tsaye ya koma can gefe daya ya zauna yana mai sunkui da kansa kas. Cikin fushi yarima Muraisu ya mike zumbur yaje gabansa ya tsaya ya dubeshi a fusace ya ce, "Saboda me ka ki baní amsar tambayata?" Boka Rufyan ya dago kai ya dubi yarima ba tare da shakka ko tsoro ba ya ce, "Ai ba kowacce tambaya ce ke da amsa ba. Ina so ka sani cewa zamanmnu anan bashi da wani amfani, domin zaman Jaki da kaya ne. Idan kana ganin za ka bi wadannan matakai na samun matar da za ka aura ka tashú mu. bi sawunsu gimbiya Husnaila. Dik da cewą tsakaninmu da su akwai tazarata a kalla tafiyar kwana arba'in, zan iya đaurc mana kasa mu riskesu a cikin kwana shida da yini daya, domin ka yakesu ka rabasu da Husnaila idan ka yi nasara sai mu rakaka izuwa bakin dajin Kirzufa mu -tsaya daga wajensa kai da Husnaila ku shiga cikinsa, ba za ku fito ba sai bayan kwana ukun. Sannan mu rankaya mu tafi izuwa can birnin Lairuf domin a yi shagalin bikinku", Lokacin da boka Rufyan ya zo nán jawabinsa sai jikin yarima Muraisu ya yi sanyi, ya koma can gefe ya zauna kuma ya yi tagumi inda ya fada cikin kogin tunani. Ba wani abu yake tunawa ba face gagarumin aikin da ke gabansa wanda ya i karfin tunaninsa. Abinda ya fara fado masa a rai shi ne, ta ya ya zai iya tarwatsa wadannan dakaru guda dubu dari uku shi kadai alhalin KAIFI DA TSINI baya tasiri a jikinsu? Kuma idan za a kwana uku ana yaki da su ba z4 su gaji ba? Abu na biyu, ta ya ya zai iya shiga dajin Kirzufa ya har ya yi kwana uku a cikinsa alhalin mahaifinsa ma da kyar ya iya yin sa'o'i a cikinsa?" Koda Muraisu ya zo nan a tunaninsa sai ransa . ya baci ya ga cewa boka Rufyan ya raina masa hankali, domin bai ga dalilin da zai sa ya umarceshi yin abinda shi kansa ya san cěwa ba zai yiwu ba. A fusace ya sake mikewa tsaye ya nufi kan boka Rufyan gadan-gadan, kawai sai boka Rufyan ya mike ya tareshi ya ce, "Idan ka so ka zare takobinka ka kasheni yanzu take, amma ka sani cewa zabi daya ne garcka cikin biyu. Walau ka koma gida ka zuana ka įira ranar da makiya za su Z0 Su cimu da yaki, kana ji kana gani, ko kuma ka nemi matar aurenka wacce za ta haifa maka dan da Zai kwatar mana 'yanci anan gaba. Ko ka ki ko ka so baka isa ka sauya kaddara ba. Babu makawa sai an ci mu da yaki kuma ba lallai bane ni ko wadannan abokan tafiya namu dayanmu ya yi nisan kwanan da zai ga ranar da za a karbar mana 'yancin mu ba." Koda jin wannan furuci sai jikin yarima Muraisu ya yi sanyi a karo na biyu, ya koma inda yake ya zauna yai shiru bai ce komai ba, ya shuga sabon tunani. Nan take yaji duniyar gaba đaya tayi masa zali, musamman da ya tuna cewa shi fa yanzu bashi da uwa kuma a ko yaushe ma zai iya rasa mahaifinsa. "To wai shin na akan Wane dalili zai damu da duniya tunda bashi da saran masoyi?" Wata zuciyar kuma ta ce da shı, "To mene ne am fanin kaina ka gushe kamar yadda iyayenka za Su gushe ba. tare ta ka bar. zun ar da za a gania Tinka tunawa da kai ba?" Koda ya zo nan a tunaninsa sai hawaye ya zubo masa. Yana dago kai ya ga kuyanga Sabirat tsaye a gabansa. Sabirat ta zauna kusa da yarima Muraisu ta dubeshi a nutse, sannan ta ce, ""Ya kai jarumin kwarai, ka yi sani cewa namijin baya kuka, kuma bai san tsoro ba. Shi ne wanda baya shakkar shiga ckin kowanne irin bala'i kuma shi nc wanda bai dauki RAI a bakin komai ba, muddin bukata za ta biya." Koda yarima Muraisu yaji wannan batu sai dukkanin tsoro ya kau daga cikin zuciyarsa kawai sai ya dubi Sabirat ya yi murmushi ya ce, "Madallah da kuyanga ta gari wacce ke yiwa ubangidanta tuni bisa abinda ya kamaceshi." Gama fadin hakan ke da wuya sai Muraisu ya mike tsaye ya dubi Boka Rufyan da Badakare Kirzal ya ce, "Ma za ku samu akan hanya wacce za ta kaini inda zan riski gimbiya Husnaila da jama'arta a cikin kankanin lokaci" Kafin Muraisu ya gana rufe bakinsa tuni Kurzan da Rufyan sun mike zumbur sun kama dawakansu sun haye. Saoirat da Muraisu ma suka yi sauri suka hau nasa dawakan. Kurzal ne ya wuce . kan gaba, Boka Kufyan na-biye da shi sannan su yarima. Dukkaninsu suka sukwani dawakansu da gudun tsiya suka nausa cikin daji. Nan fa Yarima, Kurzal da Sabirat suka rinka ganin abin al'ajabi, domin cikin dakiku kadan suka rinka shafe tafiyar sa'o'i. Nan da nan suka ga sun zO wani wuri maj irin yanayi dabam da sauran dazuzzukan da suka wuce. Shi dai wannan wuri da suka zo ya kasance daji ne mai yawan lumshi tamkar rana ba ta taba baiyana ba a cikinsa. Bishiyoyin da ke cikinsa kuwa duk dogaye ne masu fala-falan ganyaye, haka kuma akwai duwatsu manya-manya in-in masu tsawo da fadi. Koda 1SOwar Su yarıma wannan wuri sai Kurzal yai sauri ya sauko daga kan dokinsa ya kifa kunnensa akan kasa yai nazari, sannan ya mike tsayc, ya dubi yarima ya ce, 'Ya shugabana nan gaba kadan tafiyar 'yan dakiku akwai mutanc sama da guda dari biyu a labe cikin duhuwar bishiyoyi". Koda jin haka sai Boka Rulyan ya yi murmushi, sannan shuma ya dubi yarima ya ce, "Sai ka shige ciki ka riskesu ka karbo gimbiya Husnaila ta kowanne hali. Mu kam amu Jiraka ne nan har iZUwa tsawon sa'a bakwaj. Jdan ka fito da nasara sai mu rakaka izuwa bakin dajin KirZula, acan mas mu jira izuwa sa'adda za ku kwana uku a cikinsa ku fito, sannan mu rankaya gaba daya izuwa gida. Idan kuma mu ka ji shiru ba ka fito ba, mun san ccwa ka hallaka sai mu juya mu koma gda". Yarima Muraisu ya gyada kai ya ce, "Haka za a yi". Kawai sai ya juya zai shiga cikin wannan daji mai kwarjini, ai kuwa sai ya hada ido da kuyanga Sabirat. Bisa mamaki sai ya ga hawaye ya zub0 a idanunta. Boka Rufyan da Barde Kurzal kuwa, ko kwalla babu a cikin nasu idanun. Nan take Muraisu yajı zuciyarsa ta sosu kuma ya cika da mamakin dalilin da ya sa Sabirat ta zubar masa da hawayc, alhalin bai kasance komai face ubangidanta. gareta ba Shin tsananin sabon da tayi da shi ne ya sa ta Zubar da wannan hawaye ko kuwa so nc irin wanda ke tsakanin mace da namiji? Nan fa Muraisu ya kasa baiwa kansa amsa, kawai sai ya kau da kai ga barin kallonta, ya kunna kai cikin wannan daji yana mai zare takobinsa. Karar zare takobin tasa ce ta fargar da wadannan dakaru guda dari uku masu gadin gimbiya Husnaila, su ma sai lkowanncnsu ya zare tasa takobin. A wannan lokaci gimbiya Husnaiíla tayi tumbur a cikin wata korama tana wanka, Wasu kuyanginta guda hudu suń rike manyan mayafai sun kare inda take don kada wadannan Dakaru su ga tsiraicinta. Kwatsam! Ba za to ba tsammani sai gimbiya Husnaila da kuyanginta suka ji an barke da azababben yaki banda karar karafa babu sautin da ke cika dodon kunne, har amsa kuwwa yakea cikin dajin. Ko kadan gimbiya Husnaila ba ta tsorata ba, domin ba ta ma san mene ne tsoro ba a rayuwarta, amma su kuyanginta sai suka firgice, jikinsu gaba đaya ya kama kyarma. Nan da nan suka hada gumi sharkaf. Koda gimbiya Husnaila ta ga halin da kuyanginta suka shiga sai ta daka musu tsawa ta ce, "Idan ba za ku iya ci gaba da aikinku ba zan sa takobi duk na sareku". Koda jin haka sai dukkanínsu suka nutsu akan aikinsu. Ita kuwa Husnaila sai ta ci gaba da wankanta tamkar a cikin gidanta take. Cikin tsananin gudu yarima Muraisu ya.ratsa cikin wadannan Samudawan dakau da nufin ya wuce ta tsakiyarsu ya isa inda gimbiya Husnala. take wahka, ámmna sai wadannan Dakaru suka ce wane shi, nan take suka yanyameshi suka haushi da sara da suka. Shi kuwa ya wanzu yana mai karcwa da mai da martani. Shi kansa sai da ya yi matukar mamaki bisa ganin inin tsananih zafin naman da ya samu a yanzu wanda a da can ya tabbatar da cewa bashi da irinsa, in da ya sami matsala shi ne, tunda Dakarun suka kewayeshi a waje daya aka ci gaba da gumurzu sai ya kasa karawa gaba. Domin sun babbake hanya babu ta inda zai iya wucewa. Abinda ya fi daga masa hankali shi ne, duk sa'adda ya sari dakarun ko, kuma ya sokesu da takobinsa sai ya ji kamar karfe ya kaiwa hari, domin tartsatsin wuta ne ke tashi gami da hayaki. Su kuwa duk sa'adda suka sari jikinsa makamin baya tasiri, amna sai jikinsa ya gaya masa, domin ji yake kamar an sa shi a cikin turmi ana yi masa lugude da tabarya. Hakika Muraisu ya yi mamakid a ya ga karfe bai ci jikinsa ba, domin shi dai ya san bashi da wannan sihiri, amma da ya tuna cewa ai ya sami zafin nama irin wanda bashi da shi a da sai ya gane cewa lallai akwai sabon al'amari wanda ya zo masa bako tuntuni. "Mene ne sabon wannan al'amarin ?" Muraisu ya tambayi kansa a cikin zuciya, amma sai ya kasa ftar da amsa. Lokacin da dakarun suka ci gaba da laflawa Muraisu makanansu a dukkan jikinsa, sal ya Zamana cewa ya kasa ci gaba da yaki, har ma ya yarda takobinsa kuma ya fadi kasa. Koda ganin haka, sai suka ci gaba da tattakashi, nan da nan suka yi laga-laga da shi, jini ya rinka tsartuwa daga cikin bakinsa da hancinsa. Kafin cikar 'yan dakiku ya baje wanwar a kasa yana num fashi da kyar ko yatsansa guda ya kasa mnotsawa. A wannan lokaci ne. shugaban dakarun ya yi mnusu inkiya suka ja da baya sannan ya dubesu gaba daya ya ce, "Duk yadda aka yi wannan jarumin ya fito ne daga kasar Lairus, kuma ya zo ne domin ya sace gimbiya Husnaila ya tafi da ita. Tunda dai makami ya ki ya yi tasiri a jikinsa, ma za ku kamashi da karfin tsiya ku murde masa Wuya ku jefa gawarsa cikin wancan ramin". Shugaban dakarun ya yi nuni da hannunsa izuwa ga wani rami mai zurfin gaske wanda ya kai kamu dari da tamanin. Kamar a cikin kunnen yarima Muraisu shugaban dakarun' ya yi wannan bayani, domin ba za to ba tsammani, sai suka ga Muraisu ya mike Zumbur! ya daka tsalle sama ya dira a kan kafadar daya daga cikinsu, Cikin bakin zafin nama Muraisu ya kama kan Badakkaren da ya dira a kafadarsa ya mrde masa wuya. Take Badakaren ya sulale kasa matacce, ji ka ke dam! kamar giwa ta fadi. Zan dakata anan saikuma wani lokaci ßµŠÅ Ä MµTµ Littafi Na Biyu (2) Part B Na Abdulaziz Sani M /Gini KAICO! Ashe tsuliyar dodo Muraisu ya tabo, domin suna ganin ya kashe daya daga cikinsu sai suka yì kukan kura suka afka masa gaba dayansu aka sake kacamewa da azababben yaki. Wannan karon dayansu bai samį damar koda taba jikinsa ba, domin wata iriyar zulliya ya rinka yi a tsakankaninsu ya inka kama hannaycnsu da kafafunsu yana kakkaryawa tamkar yana karya sillen kara. Gumbiya Husnaila da ke can cikin korama tana ta wanka, sai ta fara jiyo ihun Dakarun tsaronta. Al'amarin da ya matukar ba ta mamaki ke Cikin hanzari ta karbi mayafi daga hannun kuyanginta ta daura iya kirjinta, sannan ta fito daga cikin koramar. Ko tufafinta ba ta tsaya sawa ba ta durfai inda ake wannan gumurzu. Su kuwa wadannan kuyangi na ta sai suka ruga izuwa cikin daji a dimauce ba tare da sanin inda suka dosa ba, saboda tsananin razanar da suka yì domin sun san cewar bala'in da ya sa wadannan samudawan dakarun ihu ba Karami bane. Tun daga nesa gaimbiya Husnaila ta hango dakarunta suna zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona. Koda ta kara matsawa kusa sai ta ga ashe wanda yake ragargazar su ma dan mitsitsı ne akansu, bai fi ta kwatantashi da dan tsako ba a cikin tsakiyar dubunnan Muzurai. A iya rayuwar gimbiya Husnaila yau ne ranar farko da ta ga abinda yai matukar ba ta mamaki, amma ba wai burgcta ya yi ba. Koda ta ga yadda Muraisu ke ta kakkarya dakarunta suna zubewa kasa sai ta sunkuya ta dauki mashin daya daga cikinsu ta ike ta tsaya cak! Tana jiran ta ga abinda zai faru. Kafin cikar rabin sa'a Muraisu ya zubar da dukkan dakarun a kas suna ta koke-koke da iface- iface, babu đayansu da ya iya mikewa tsaye. Koda Muraisu ya ga ya gama da dakarun sai ya yi arba da kyakkyawa Husnaila a tsaye a gabansa ike da mashi, fuskarta a murtuke babu annuri, kuma ga ta a tsayc kyam babu wata alamar tsoro a tare da ita, Koda ya ga kyakkyawar surar jikinta da kuma wani kyakkyaw an gashin kanta sar ya rude ya dimauce, bai san sa'adda ya nufeta ba gadan-gadan da nufin ya rungumeta. Koda ya ragc bai fi saura taku daya su hadu ba sai ya kai ma ta raruma, ita kuwa ta goce ta soka masa mashi a gefen kirjinsa. Bisa mamaki sai ya ji mashin ya nutse a cikin kirjin nasa, bai san sa'adda ya kwalla ihu ba. Husnaila ta zare mashi jini yai feshi daga cikin kirjin Muraisu, ya sake rusa ihu a karo na biyu. Jiri ya debeshi ya yi luu!! kamar zai fadi kasa, amma sai yaı ta maza ya tsaya bisa kafafunsa. Husnaila ta sake saitashi da mashin ta tsaya cak! A waje daya suka fara kallon-kallo. Daga can sai ta dubeshi ta kyalkyale da dariya a cikin sautin murya mai zakin gaske, sannan ta hade rai ta ce, "Kai wayc, kuma me ka ke nufi da ni? Saboda mne ka zo ka ragargaza mini dakaruna? Ka san kO ni wace ce kuwa? Ka amsa mini tambayoyina da gaskiya ko kuma na hallaka ka yanzzun nan!" Koda jin wannan batu sai Muraisu ya bushe da dariya sannan ya ce, "Ni ne yarima Muraisu dan Sarki Salmar mai binin Laius, wato babban makiyi ga dan uwanki Sarki Ishmar. Ina mai sanar da ke cewa na baro gida ne domin neman matar da zan'aura, kuna ba wata ba ce wadda zan aura face ke din nan". Koda jin haka sai Husnaila ta tuntsure da dariya, 1lokaci guda kuma ta hade rai ta sunkui da kanta kas tana tunani. Muraisu ya katse ma ta hanzari ya ce, "Ya ke Husnaila Sarauniyar mata, me kike tunani ne?" Husnaila ta dubeshi ta ce, "Mamaki nake bisa daıyar da na yi yanzu, domin kaine mutum na farko da ya ta6a ganin dariyata.. Hatta dan uwana kuwa Sarki Ishmar sai dai ya Ce ya ga murmushina ko hawaye na, amma bai taba ganin dariyatą ba ko kukana'". Da jin haka sai Muraisu ya yi mumushi ya ce, "Al ni mutum ne na musamman a cikin mutane, da sannu za ki gasgata haka". Husnaila ta ce, "Ai kuwa na ga alama tunda ban taba sukar wani abu da makami ba ya rayu sai kai. Shin za ka iya gaya mini sirrin da ke tattare da kai?" Muraisu ya cire wani rawani da ke ikin damararsa ya daure kirjinsa lamau don tsaida jini, sannan ya dubi Husnaila a nutse ya ce, '"Ina zaton dai irin sihirin da ke tare da ke shi ne a tare dani, domin gashi dakarunki sun kasa cutar da ni da makamansu, amma ke gashi kin cutar da ni". Husnaila tayi murmushin mugunta, sannan ta ce, "Ka yi babban kuskure da kake tunanin za ka aureňi, domin abu ne wanda ba zai taba yiwuwa ba Babu wani da namiji da ya isa ya mallakeni, idan kuma kana ganin za ka iya ka jarraba!" Muraisu ya gyara tsayuwarsa sannan ya ce, "Ai babu wani abu wanda ba zai yiyu ba a wannan duniya, sai dai ba a jarraba b. Ina da labari cewa dan uwanki ya tsarcki da dukkan sihirin tsafinsa, amma ni nayi imanı cewa sirin da nake da shi a yanzu ke baki da shi tunda shi kansa dan uwanki har yanzu bai samu ikon shiga dajin Kirzufa ba. Ba shi da wani buri wanda ya fi haka. Ina tabbatar miki da cewa har ya mutu ba zai cika wannan buri na sa ba, ni kuwa mahaifina ya shiga dajin Kirzufa, Đima kuma zan shigeshi yanzu, kuma tarc da ke, kuma dana ma sai ya shigeshi. Ina mai shawartarki da ki bani hadn kai mu tafi cikin salin-alin, idan kuwa kika ki, to fa ko ta tsiya-tsiya sai mun je". Sa'adda Husnaila taji wannan batu sai ta sake bushewa da dariya a karO na biyu, sannan ta hade fuska ta ce, "Ai sai na ga yadda za a raba hanta da jini!" Kafin Muraisu ya budi baki ya ce wani abu luni Husnaila ta dako tsalle a sama daga inda.take kamar an cillota daga cikin baka ta sake kawo masa mummnunan hari da wannan mashi a ciki. Gimbiya Ilusnaila ta ce, "Ta ya ya aka yi ka san cewa ni ce Sarauniyar kyawawa ta duniya?" Muraisu ya ce, "'Saboda mu a wannan nahiya lamu gaba daya babu kamarki". Gimbiya Ilusnaila ta cC, "Ba zan iya gaya maka ba, saboda ba kowacce tambaya ce ke da amsa ba" Muraisu ya ce, "Maganarki dutse ce, amma akwai gyara". Gimbiya Husnaila ta cc, "To mene gyaran?" "Bari na matso kusa na yi miki bayani, domin wani babban siri ne wanda ba kowa ake fadawa ba'". Kai tsaye Muraisu ya tali inda Gimbiya Ilusnaila take tsaye kamar wani abu zai rada ma ta a kunnc. Koda ya iso daf da ita sai ya shammaceta cikin bakin zafin nama ya debo hodar banju daga aljihunsa ya watsa ma ta a fuska. Nan take Gimbiya Husnaila taji jiri ya kwasheta, la tafi luu! za ta fadi kasa, sai ya sunkuya uya sabata a kaladarsa ya juya da baya ya nufi inda ya baro su boka Rufyan suka tsaya suna Jiransa. Barde Kurzal, kuyan ga Sabirat, boka Rufyan na tsayc suna hangen hanyar da Muraisu ya bi cikin zullumi da fargaba. sai kawai suka hangoshi ya nufosu sabe da Gimbiva Jusnaila a kafadarsa, ga raunı a kirjinsa daure cikin shátar jini, yana tafe yana raba kafa kamar wanda ya sha giya ya bugu. Koda ganin haka sai Barde Kurzal da boka Kutyan suka ruga gareshi cikin matu kar farin ciki suka taroshi. AA Misau Barde Kurzal ya karbi Gimbiya Husnaila ya taho da ita inda Sabirat ke tsaye, shi kuma boka Rufyan ya dauko Muraisu suka kawosu bakin wata bishiya suka shimfidesu. Cikin hanzari boka Rufyan ya kwance raunin Muraisu yana matukar mamakin yadda aka yi ya sami raunin alhalin ya san cewa Sarki Salmar ya bashi gashin sihirinsa. Nan da nan yai sauri ya sa ma sa gan magani akan ciwon nasa, sannan suka bashi ruwa ya sha. Ita kuwa Gimbiya Ilusnaila, tunda aka shim fideta ta ci gaba da barcinta ko motsawa ba ta Bayan Muraisu ya dawo cikin haiyacinsa sai boka Rufyan ya dubeshi cikin jınjinawa ya ce, "Ya kai namijin duniya, dodon maza, ya ya aka yi ka Saml Wannan gagarumar nasara har ka daukO gimbiya Husnaila daga cikin tsaron da aka ba ta?". Koda jin wannan tambayar sai yarima Muraisu ya kwashc labarin duk abinda ya faru ya Zalyane musu. Koda jin al'amarin sai duk su ukun suka sake cika da mamaki, musanman boka Rufyan wanda ytai shiru ya shiga tunani mai zurli. Daga can sai ya dago kai ya dubi yarima Muraisu yą ce, "Ya shugabana hakika shirin sarki Ishmar ba na wasa bane, ban taba tsammanin yana da karfin sihiri kamar haka ba. Ina tabbatar maka da cewa duk wannan jarumtaka da Husnaila ta yi ba gaskiya ba ce, tsabar karfin sihirin tsafi ne kawai. Tabbas itama tana da gashin sihiri a jikinta, amma abinda na ke zargi shi ne, ba irin naka bane a Jikinta, shi ya sa mahaifinta ya kasa shiga cikin da in Kirzufa. Hakika ba don kayi wannan hikima ba ta watsa ma ta banju a fuskarta da babu yadda za a yi ka iya kamota har ka zo da ita nan wajenmu. Ina son ka sani cewar dole ne yanzu ka hanzarta zuwa dajin Kirzufa da Husnaila kafin hodar banjun ta saketa nan da tsawon sa'a daya jal. Idan har ta farfado ko duniyar nan za ta taru a kanta ba za a iya taiya da ita ba, kuma idan ma ka shiga da ita cikin dajin Kirzufa sai ka sa ido sosai a kanta don za ta yi iya shammatarka tayi maka irin abinda ka yi ma ta". Koda jin wannan batu sai Muraisu ya mike zumbur! ya dauki gimbiya Husnaila ya đorata akan doknsa, sannan shima ya hau nasa dokin, suma Su Rufyan sai suka yi sauri suka hau nasu. Barde Kurzal ne ya wuce kan gaba suka zaburi dawakansu da gudu suka bishi a baya. Basu tsaya a ko ina ba sai sai a bakin dajin Kirzufa. Lokaci guda su duka suka yi tirjiya, sannan suka sauko daga kan dawakansu. Yarima Muraisu ya sake đaukar gimbiya Husnaila a kafadarsa. Har ya juya zai shigc cikin dajin na Kirzufa, sai ya Waiga ya dubesu su ukun cikin wani iin kallo mai nuna alamun bankwana, wanda ya sa duk su ukun suka ji tsigar jikinsu ta tashi, kuma dukkaninsu sai zuciyoyinsu suka karaya, nan take tausayin yarima ya tumukesu, saboda sanin cewa masifar da zai shiga yanzu ta ninka wacce ya shiga a baya sau dubu. Muraisu ya tsaida hankalinsa a kan boka Rufyan ya ce, "Bani labarin mahaifina, shin hạr yanzu yana raye ko kuwa ya mutu?" Koda jin wannan tambaya sai boka Rufyan- yai shiru ýa kasa cewa komai, kawai ya kurawa Muraisu idanu. Barde Kurzal da kuyanga Sabirat kuwa, sai hankalinsu ya dugunzumna, suka kama raba idanu a tsakanin Muraisu da Rufyan, jira suke kawai su ji amsar da Rufyan zai bayar. Tsawon 'yan dakiku Rufyan bai ce komai ba, kuma bai fasa kurawa Muraisu idanu ba. Koda ganin haka sai idanun Muraisu suka domin ciko da kwalla har hawaye ya subuto masa, ya ji a jikinsa cewa MAZA SUN FADI! Kawai sai ya juya ya durfafi cikin dajin Kirzufa kai tsaye, a lokacin da ya ji dukkan tsoro ya kau daga cikin zuciyarsa, ji yake ina ma mutuwar za ta zo ta daukeshi da ya fis amun nutsuwa. Da shigar su Muraisu dajin Kirzufa sai ya fara arba da dabbobin daji ii-ii, kuma manya-manyan ababan tsoro, domin sun kasance na usamman ba irin wanda ido ya saba gani ba. Tsananin kwarjinin dabbobin ya wuce misali, ko kwatance. Tsakanin Muraisu da dabbobin sai kallon- kallo kawai, dayansu bai yi yunkurin koda zuwa kusa da shi ba, shima Muraisu ko kallonsu bai yi ba, kawai sau ya je karkashin wata bishiya ya shimfide Husnaila, sannan ya koma gefe daya ya tsugunna ya kura ma ta idanu, kuma ya fada kogin tunani. Abinda ya fara fado masa a rai shi ne, yanzu ya zai yi da Husnaila idan ta farka ta tsinci kanta a cikin dajin Kirzufa? "Lallai akwai kazamar rigima a (sakaninmu" Muraisu ya baiwa kansa amsa. "Kuma saí tayi yunkurin guduwa...Amma kuma ai boka Rufyan ya gaya mini cewar ba tưisa ta fice daga cikin dajin ba har sai mun yi kWana uku a cikinsa, saboda haka zan zuba ma ta idanu ne kawai na ga iyakar gudun ruwanta. " Haka dai Muraisu ya yi ta sake-sake a cikin zuciyarsa har ya gaji, shima saí ya kishingida a jikin wata bishiya. Abinka da gajiyayye, bai dađe da kishingida ba sai barci ya kwashe shi. Bayan 'yan dakiku kadan kuma sai Husnaila ta farka. Koda la bude idanu ta tsinci kanta a cikin wani iin daji na musamman sai ta takarkare ta tsandara uban ihu. Muraisu ya farka firgigit! a razane, dabbobin cikin dajin kuwa, hatta sauran Rananan kwari da tsintsaye sai da suka razana, suka kama guje-guje. Duk dabbar da tayi arba da su Muraisu sai ta yıyo kansu: Nan fa aka kasa uban tserc tsakanin su Husnaila da dabbobin dajin gaba daya. Babu abinda zai baiwa mutumn mamaki face Lsananin gudun da Muraisu da Husnaila ke yi tamkar akan iska suke yinsa ba a kan kasa ba. Duk su biyun sun yi matukar mamakin irin gudun nasu, domin tamkar walkiya suke gifta komai, sai dai karfin gudun nasu duk ya zama na banza, domin duk sa'adda suka waiga bayansu sai su ga dabbobi kusan guda dubu daf da su. Duk inda suka dauke dabbobin suke sa nasu. sawayensu anan da Babu abinda ya fi firgita su Muraisu face cafka kawo musu yadda dabbobin ke bakunansu, don su cinyesu, musamman wani katon Zaki wanda idan ya wangame bakinsa sai ka ga kamar ijiya mai zurfi da fadi aka bude. Sai da su Muraisu suka shafe sa'a guda cif! Suna falfala natsanaicin azababben gudu, sannan suka hango wani katon tsauni a gabansu. Basu tsaya jiran komai ba suka hau kan tsaunin a guje, har sai da suka je can. samansa sanann suka waigo baya. Bisa mamaki, sai suka ga gaba dayan dabbobin sun tsaya a kasan tsaunin đayansu bai yì yunkurin hawowa ba. Al'amarin da ya matukar basu mamakia ke nan, Kawai sai suka zube kasa a saman tsaunin suka kama haki, da fitar da numfashi da saurí da sauri. A sannan nc fa kishirwa ta ischsu, kuma gashi babu damar shawagi a kasan tsaunin tamkar an basu gadin abinda ke kan tsaunin. A dai-dai wannan lokaci ne Husnaila ta dubi Muraisu cikin harara da fushi ta ce, "Ya ya aka yi ka kawoni cikin wannan daji?" Koda jin wnanan tambaya sai Muraisu ya yi murmushi ya ce, "Ba wannan tambayar ya kamata ki yí mini ba a yanzu, kamata ya yí ki tambayeni a ina zamu samu ruwan sha?" Husnaila ta sake murtuke fuska ta ce, "Ba ruwa ne a gabana ba. Ka mayar da ni inda ka daukoni, domin ina da bukatar na koma gida kafin magariba tayi". Koda jin wannan batu sai Muraişu ya bushe da dariya har da bingirewa Kasa, sannan ya nutsu ya ce, "Ai idan har kin ga kin fita daga cikin dajin nan sai kin yi kwanaki uku cikakku a cikinsa!" Cikin fushi da mamaki Husnaila ta mike tsaye ta ce, "Ai kuwa idan ka ga na kara koda dakika đari ne a cikin wannan daji sai idan bana numfashi. " Koda gama fadin hakan sai ta mike tsaye ta fara saukowa kasan tsaunin. Muraisu ya bita da kallo kawai ko motsi baiyi ba daga inda yake zaunc. Lokacin da ya rage saura bai fi taku biyar ba ta iso kasan tsaunin, sai kawia ta ga wannan ma ta haikan Zaki ya taso turmusheta. Ba shiri ta juya da baya da gudu ta koma kan tsaunin inda Muraisu yake. Koda ganin abinda ya faru sai Muraisu ya kama yi ma ta dariya. Al'amarin da ya kara tunzurata ke nan, ta kamu da tsananin fushi. Bisa dole taje gefe daya, nesa kadan da inda Muraisu yake zaune itama ta zauna. Babban abinda ya i daurewa Husnaila kai shi ne, ya ya ita da bata da tsoro ko kadan amma taji tana tsoron dabbobin wannan dajı? Kawai sai ta dubi Muraisu ta ce, "Wai shin wannan wane daji ne muka shigo?" Muraisu ya yi ajiyar zuciya sannan ta ya ce, "VWannan shi ne dajin KIRZUFA! Kanar yadda na gaya miki da farko sai mun yi kwana uku a cikinsa ni da ke, a sannan ne na sami Zan sauya miki rayuwarki, kuma soyayyarki, mu tafi izuwa birninmu na Lairuf mu yi aure". Kafin Muraisu ya gama rule bakinsa tuni Musnaila ta tofa masa yawu a fuska, Cikin tsananin fishí ya mike tsaye zumbur! ya zare takobinsa, itama saí ta mikc Zumbur! ta rike mashinta suka fara kallon-kallo, har gaba dayan jikin Muraisu na tsuma saboda fushi, domnin a íva rayuwarsa ba a taba yi masa iin wannan wulakancin ba a matsayinsa na dan Sarki, kuma gawurtaccen jarumi. Husnaila ta dubcshi a wulakance ta ce, "Na tsancka! Kuma na tsani dukkan zuril'arka, Har abada ba zan ta6a sonka ba, kuma ní da dan uwana Sarki Ishmar sai mun baje birninku, mun konc dukiyoyinku, mun kame matanku da 'ya'yanku sun zama bayinmu. Mazajenku kaf sai mun kashesu", Koda jin wannan batu saí Muraisu yaji ya tsani lusnaila kamar yadda yaji ya tsani mutuwarsa. Duk wannan tsananin kyawu nata sai ta rama kamar dodanníya a idanunsa. IHar ya yunkura zai afka ma ta su yi yaki, sai ya tuna cewa ai sihiri ne a jikinta wanda ya sa ba za ta laba son wani da namiji ba face ta ci ta sha daga abubuwan da ke cikin wannan daji na Kirzufa na tsawon kwana uku. Koda tuna wannan al'amari sai jikin Muraisu ya yi sanyí, ya fasa afkawa Husnaila ya koma ya zauna. Koda ganin haka, sai itama ta koma inda take ta zauna. A sannan ne fa kishirwa ta ci gaba da addabarsu. Babu shiri suka mike tsaye suka kama yawo akan tsaunin kowannensu na neman ruwa, amma babu ko alamarsa. Duk sa'adda suka leko kasan tsaunin kuma sai suka ga wadanann dabbobi suna nan suna kewaya tsaunin, jira kawia suke su sauko su afka musu, Bisa dole suka hakura. Lokacin da 'yan sa'oi suka kara shudewaa sai magariba ta doso kai, gari ya fara duhu, a sannan ne tsananin kishirwa tasa suka baje a kasa suka kama num fashi sama-sama kamar za su muti. Sai da kowannensu ya fara suma, kwatsam! ba zato ba tsammani sai hadari ya gangamo aka fara tsawa da walkiya gami da wata irin gagarumar iska mai karfin gaske. Kafin a jima ruwan sama ya tsuge karmar da bakin kwarya. A sannan ne Muraisu da Husnaila suka farfado, sai kowannensu ya wangame bakinsa suka kama shan ruwan, har sai da suka koshi, sannan suka dawo cikin haiyacinsu, sai dai babu inda zå su fakewa wannan ruwan saman, dole suka hakura ruwa yai ta dukansu har izuwa tsawon sa'a guda, sannan ruwan saman ya dauke dif. Nima Kuma Wanga Ruwa Yana Daukewa Nima Na Dauke Daga Typing hhhhh Zan dakata anan sai kuma wani lokaci Zamu cigaba Insha Allah Likes and comments Domin hakan na sa mu cigaba Ga masu shA award whtsp grp https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q BUSA A MUTU Littafi Na Biyu (2) Part C Na Abdulaziz Sani M /Gini AA Misau Ke Magana MURAISU DA LUSNAILA SUKA MIKE TSAYE SUKA kallo juna kowa ya kau da kai. A wannan lokaci ngar jikin Husnaila ta dame sakamakon wan saman da aka laftla, hakan ne yasa surar jikinta ta baiyana karara a ili tamkar tsirara take, Roda Muraisu ya ganta a cikin wannan hali sai ya ude ya dimauce vaji ya kamu da tsananùn sha'awa, amma sai ya danne zuciyarsa ya juya ma ta baya. Lokacin da suka leko Rasan tsaunin sai suka cika da mamaki, domin babu dabbobin dajin a wajen ko guda daya. Da yake suna jin yunwa matuka, sai suka sauko daga kan tsainin. Suna saukowa sai suka tsaya cak! Muraisu ya juya ma ta baya don baya son ya ci gaba da ganin tsiraicinta. Cikin fushì Husnaila ta bude baki ta ce, "Saboda me za ka rinka juya mini baya alhalin kaine ka kawoni cikin wannan masi faffen daji? To ka sani cewa ni yanzu yunwa nake ji, saboda haka sai ka je ka nemo mìni abìnda zan įi"'. Tana gama fadin hakan taje ta zauna akan wani dutse. Cikin matukar harzuka Muraisu ya juya a fusace ya ce, Yadda kike takama ke yar Sarauta ce nima haka nake. Ni da ke kowa ta sa ta fissheshi a cikin wannan dajı. Idan ma za ki iya sai ki yi kokarin fita daga dajin". Koda gama fadin hakan sai Muraisu ya juya ya tafi ya bar Husnaila a zaune tana binsa da kallo gami da harara da tsananin kiyayya, taji kamar ta ruga kansa ta tsircshi da mashin da ke hannunta. Muraisu ya ralsa izuwa cikin dajin Kirzufa, domin neman abinda zai ci, wata irin iska mai karfin gaske ta fara bugawa, bishiyoyi suka kama rangaji kamar za su kakkarye su fadi kasa. Da yake dama an tafka ruwan sama sai dajin gaba daya ya dume da sanyi, gashi kuma magariba ta yi, duhu ya fara. Nan take Husnaila taji ta kamu da tsananin tsoro, kuma gashi saura kiris Muraisu ya bace ma ta da gani, domin ya yi nisa sosai daga inda take hangoshi. Kawai sai ta mike zumbur! ta ruga da gudu izuwa inda yake tana rike da mashinta, ta riskeshi suka jera suna tafiya, amma ko kallon juna ba su yi - ba, kuma kowannensu fuskarsa a murtuke take. Haka dai suka wanzu suna ta ta fiya a cikin dajin suna hange-hange da waige-waige ko za su ga abinda za su iyaci ya magance musu yunwar da ke addabarsu, amma babu. Hatta bishiyoyin dajin babu mai fure a jikinta bare a samnu dan itaciyar da za a iya ci. Sai da Muraisu da Husnaila suka shafe kusan rabin sa'a suna tafiya a dajin basu ga koda tsuntsu ba ko wata karamar dabba wacce za su lya rafkewa su yanka su ci. A dai-dai wannan lokacin ne suka jı sun gaji likis, saboda haka sai suka tsaya suka zauna a kasa dirshan suna haki. Duk sa'adda suka kalli juna sai kowa ya harari dan uWansa su kau da kai. Kwatsam! ba zato ba tsammani sai suka ga wata katuwar jimina mai giman ban mamaki ta sauko daga sama ta dira a cikin wadansu ciyayi ta kama kiwo abinta. Nan fa Husnaila da Muraisu suka dubi juna suka yiwa kansu inkiyar su tashi su afkawa jminar domin su sami abinda za su ci. Lokaci guda suka mike tsaye a tare. Muraisu ya zare takobinsa, ita kuma Husnaila ta mikar da mashinta suka durfafi inda Jiminar takc. A wannan lokaci Jiminar ta juya musu baya tana ta tonon kasa da bakinta. Koda Jiminar taji motsin taiya a bayanta sai ta dago da kanta tå tsaya cak! kamar gunki suma sai suka tsaya cak amma da Jiminar ta ci gaba da tonon kasa sai su ma suka ci gaba da durfafarta. Da suka ga ba ta sake tsayawa ba sai suka ruga da gudu izuwa kanta. Manufarsu ita ce, su- soketa da makaman hannunsu. Koda ya rage bai fi saura taku daya jal a tsakaninsu da Jiminar ba, sai ta waigo cikin bakin zafin nama ta makesu da dogon wuyanta. Saboda karfin makuwar sai da suka yi sama da baya suka fađo kasa a tare a matukar galabaice. Duk su biyun sai suka raina dukkanin jarumtakarsu suka san cewa tabbas sun shiga dajin Kirzufa. Kafin su yunkura su mnikc tsayc sai jiminar la taso musu haikan, nan da nan ta iso garesu ta karwa Husnaila wawar caka da tsinin bakinta. Cikin zalin nama Muraisu ya fisgo Iusnaila daga inda take kwance. Bakin Jiminar ya caki kasa, ya nutsc gaba daya a cikinta. Koda Jiminar ta zarc bakinta sai ga rarmi zururu mai tsawo da fadi wanda za a iya binne jarini a cikin. Nan fa aka fara masifa ffen artabu tsakanin Jinina da su Muraisu, la wanzu tana mai kai musu suka da tsirin bakinta, su kuma suna buge bakin na, lá da makaman hannunsu. Duk sa'adda makaman nasu suka hadu da bakin na la sai ka ji Rara Ral! kamar karfe da karfe ne suka hadu. Sai da suka shafe lokaci mai dan tsawo suna Wannan gumurzu, ya zamana cewa sun kasa taba jikin Jininar domin ta fisu nama, kuma gashi ko kadan ba la gajiya, su kuwa sai suka fara sarewa. Ana cikin haka ne Jiminar ta shammaci Ilusnaila ta kai ma ta wawar suka a cinyarta, duk da cewar IHusnaila ta gocewa harin da dukkan zafin namanta amma sia da kaifin bakin jiminar ya yanketa. Wani inn dogon yanka tamkar da takobi aka yanketa. Take waycn ya dare, jini yai feshi. Ilusnaila ta kurma uban ihu ta sulale kasa sumammiya. Koda ganin abinda ya faru ga IHusnaila sai Muraisu ya fusata ya yi zumbur! ya daukì mashin IIusnaila ya hada da takobinsa ya ci gaba da yakar jiminar. Ya rinka kai ma ta muggan hare-hare da takobi da mashi cikin matukar fushi da zafin nama. Bisa dole jiminar ta rinka ja da baya, amma kuma wani lokacin saì ka ga la taso masa da dukkanta itama ta kuntalashì tana korashi baya. A haka ta sảmu shima ta yankesbi da kaifin bakin na ta, har sau uku. Yankan farko a hannunsa na dama nc, na biyu a kaladarsa ta hagu, na uku kuma a gadon bayansa, sai gashi jinio na zuba a jikinsa har jiri na đibarsa, amma saboda yana da dakakkiyar zuciya irin ta maza bai fadi kasa ba, kuma bai fasa kaiwa jiminar hari ba. Ana cikin haka sai Jiminar ta sami nasarar buge takobi da mashin da ke hannaycnsa suka fadi kasa, kuma ta matseshi ta hanashi daukar makaman. Bisa dolc Muraisu ya fara ja da baya, gashi bayansa wani katon dutse ne, idan har ta kuresgu a jikin dutsen ba makawa sai ta hallakashi tunda ta cika hanya babu ta inda zai iya tserewa. Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa ke nan, zuciyarsa ta karaya domin bashi da sauran wata dabara a zuciyarsa da zai iya kubular da kansa. A dai-dai wannan lokaci ne Husnaila ta farlado daga dogon suman da tayi, ta ga abinda ke shirin faruwa. Koda ta tunkura da nufin la mike tsayc sai taji ta kasa đomin kafarta tayi nauyi tamkar an aza ma ta katon dutsc akai. Kawai sai ta zuba ido tana jiran ta ga iin kisan gillar da jiminar za ta yiwa Muraisu sanann ta Juyo kanta. Ya yin da ya rage bai fí saura taku biyar ba kacal tsakanin jiminar da Muraisu ta kaishi jikin dutsen da ke bayansa, sai kawai ya fusata ainun ya daka wawan tsalle sama izuwa kan jiminar tamkar an harboshi daga cikin baka. A Saman ya kama wuyan jiminar da hannaycnsa biyu ya murdeshi da dukkan karlinsa. Ta ke wuyan jiminar ya karye ya bayar da sauti kararas! Ta ke Jiminar ta yanke jiki ta ladi kasa tim! Tamkar giwa ce ta fadi har sai da kasa tayi girgiza, wala gagarumar kura ta tashi. A sanann ne Muraisu ya yanke jiki ya fadi kasa. Maimakon ya yi kokarin yiwa kansa magani a jikin raunikansa sai ya nufi inda Ilusnaila ke kwancc da jan jiki domin ya kasa mikewa tsayc. Yana isa garcta ya fiddo garin magani a jikinsa ya shafe raunin cinyar Ilusnaila.. Ta ke ta kurma uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogịn da taji ta sake bajewa a kasa sumammiya. Nan take hankalin Muraisu ya dugunzuma ainun,-yaji ya kamu da lsanänin tsoro, domin a zatonsa Ilusnaila ta mutu. Cikin ruđewa ya daure ya míke tsaye da kyar yana tangadi, yaje ya dauko babbar ruwan shansa ya budeta ya zazrAge ruwan akan Husnaíla. Dama sa'adda aka yí ruwan sarma ne ya sarnu ya cika battar ruwan. Ai kuwa yana zuba ma ta ruwan saí ta farfado tana mai dogon ajíyar num fashí. Koda ta bude idanu ta fa Muraisu tsaye a kanta sai ta daka masa tsawa ta ce, "Me yasa ka cecí rayuwata? Ka san cewa na tsaneka fiye da yadda na tsani mutuwata? Da dai a co kaine ka kubular da rayuwata gwara dabbobin dajin nan su yí kaca-kaca da sassan jikina su cnyc". Koda jin wannan batu sai zuciyar Muraisu ta kama tafar fasa, yiji kamar ya sa takobi ya sare kan IHusnaila saboda lakaici. Amma da a tuno da birnin Lairus sai ya danne zuciyarsa, ya mıke tsaye yaje ya koma can gefe daya ya ratIna ya shiga yíwa kansa magani, har sai da ya tsaida dukkan jinin da ke zuba a jikinsa. Bayan ya dz wo cikin haiyacinsa sOsai sai yaje ya samo kirarcn wula ya ncmno kyastu ya kunna wuta sannan ya 1arc wata wuka mai kaifi a ikinsa ya rauna ya fcd: wannan jimina tsaf ya daddatsa naman jikinta. Da kyar ya dauki cinyar jiminar guda ya soketa a jikin ítac mai gwafa ya shiga gasawa. Da naman ya gasu sosaí, sai kawaí ya fara cin abinsa ko kallon Husnaila bai ba. Da yake itama a cikin bakar yunwar take saí ta taho da jan kafa a zaunc don la kasa mikewa tsaye, ta iso har gaban naman ta dinga yanka tana Har duk su biyųn suka ci suka koshi basu kalli juna ba, kuma dayansu bai ce uffan ba. Duk wanda ka dubí fuskarsa sai ka ganta a nurtuke tamkar an aiko masa da sakon mutuwa. Ai kuWa suna gama. cin wannan naman ne hadari ya sake gangamowa, aka fara wata iin bakar guguwa wacce ta firgitasu la firgita dajin gaba daya, domin nan take bishiyoyí suka kama kakkarycwa suna zubewa kasa. Kai duwatsu ma wadanda ba su cika girma ba sai suka kama mirginowa akan kasa da kansu. Ba shiri Muraisu ya mike tsaye ya ciccibi Husnaila tamkar ya dauki dan karamin yaro ya ruga da gudu izuwa cikin dajin yana neman malafa. "Su kansu sauran dabbobin da ke dajin sun firgice suna la gujc-guje suna shigewa cikin ramuka da manyan koguna don su tsira da rayuwarsu. Muraisu dai ba a son ransa ya dauki Husnaila da hannunsa ba, sai don kishin kasarsa, sbaoda lallai nan gaba yana son dansa ya ceto ratyuwar jama'arsa daga sharrin abokan gaba. Ita kuwa Husnaila, koda ta ga Muraisu ya dauketa da hannayensa biyu tana rungume a kirjinsa sai zuciyarta tayi bakikkirin ta kama zancen zuci tana mai cewa, "Saboda me babban makiyina zai taba jikina? Ai kuwa sai na yanke wadannan hannaye nasa duka biyun wadanda suka taba jikina!" Muraisu na cikin wannan gudu ne ya hango wani kogon dutse, kawai sai ya durfafi kogon kai tsaye. lar ya kunna kai zai shiga ciki sai ya dawo da baya ya tsaya cak! ba wani abu banc yasa ya dawo da bayan ba face ganin tsananin duhu a cikin kogon, kuma babu mamaki akwai wata muguwar dabbar a cikin kogon a la6e. Kawai sai Muraisu ya ajiyc Husnaila a kas sannan ya karyO wani icen bishiya kuna ya zura hannu a cikin aljihunsa ya dauko duwasun da ya yi kyastu da su a baya ya shiga kokarin kunna wuta a |ikin wannan ice da ya karyo. Da yake an yi ruwan sama a baya bada dadewa ba da kyar da sidin goshi wular ta kama, sannan Muraisu ya zare takobir sa ya shiga cikin kogon, hannunsa guda na rike da icen mai wuta yana haskawa. Kogon bashi da zuri sosi, haka ma fadi, kuma ko Rwaro daya bai gani ba a ciki. Bayan ya tabbatar da lafiyar kogon sai ya ita ya dauko Husnaila ya shigo da ita ciki, sannan ya ajiycta ya sake lita ya nemo wadansu itatuwan ya kunna wuta mai kari domin su ji dumi. Faruwar hakan ke da wuya sai ruwa ya sake kecewa kamar da bakin kwarya. A dai-dai wannan lokaci nc tsananin gajiya tasa Muraisu ya fara 8yan-gyadi. Yana cikin wannan hali ne lHusnaila ta faki num fashinsa ta suri daya daga cikin itatuwan da ya kunna wular da su ta maka nasa shi a nuka- mukinsa. Ta ke Muraisu ya baje a kasa sumamme har jini ya bul6ulo ta cikin kunnensa ya zamana cewa ko num fashi baya yi tamkar ya zama gawa. Koda IIusnaila la ga la sami wannan nasara sai ta cika da farin ciki, kawai sai ta mike tsaye da kyar tana dingishi ta leka wajcn kogon lana kallon yadda ruwan sama ke kwarara. Ai kuwa bala jima ba a tsaycn sai ruwan saman ya dauke dif! Nan take ta fita itama tajc ta dcbo wadansu itatuwan ta zubasu akan Muraisu. Sai da ta tabbatar da cewa ta lullu6cshi da itatuwan san ann ta debo itatuwa masu cin wuta ta zuba a kansu. Nan da nan kuwa wuta ta sake kama itatuwan da ke kansa. Kawai sai Husnaila ta juya ta fice daga cikin kogon tana mai kyakyata dariy ar mugunta cikin tsananin farin ciki domin ta san cewa ta gama hallaka Muraisu dole ne wuta ta babbakeshi ya konc kurmus! Dama Husnaila ta fita ne ikec da ice mai cin wuta don haska hanya saboda duhun dare. Kawai sai ta ci gaba da tafiya ba tare da sanin inda ta dosa ba a cikin dajin Kirzufa. Koda ta fara nísa a cikin dajin tana Jiyo gurnani da koke- koken dabbobi, kawai sai ta j tsoro ya kamata. Al'amarin da ya matukar ba ta mamaki ke nan, domin ita a saninta bata san wani abu wai shi tsoro ba a rayuwarta, amma tunda ta shigo dajin Kirzufa taji ta zama matsoraciya. Kwatsam! Sai ta hangi wari kogon dutse a gabanta, don hak a sai ta yanke hukuncin ta shiga cikin kogon ta kırasa kwana a ciki, tunda ba zai yiyu ta ci gaba da tafiya a cikin daren ba. Burinta shi ie ta fita daga cikin dajin Kirzufa ta koma can birnin Hutaira. Lokacin da Husnaila la iso bakin kofar wannan kogo sai ta tsaya ta leka cikin kogon tana mai haska cikinsa da wutar icen da ke hannunta, amma sai ta ga babu komai a ciki, duk da haka sai ta kasa shiga ciki, dalili kuwa shi ne, ba ta iya gano karshen kogon. Kogo ne mai zurfin gaske, kuma mai lunguna da sako-sako. Nan take Husnaila taji tsoro ya dada baibayeta har zuciyarta ta kama bugawa da karfi amma da ta tuna cewa babu in da za ta iya kwanciya face a cikin wannan kogo sai kawai ta kunna kai ciki. Maimakon ta shiga can cikin kogon sai ta zauna daga baki-baki. Bisa sa'a sai ta ga tarin wadansu kiraran itatuwa a gefe daya. Al'amarin da ya sa tayi zargi cewa lallai akwai wasu halittu a cikin kogon, ko kuma dai sun shigo sun fita Nan da nan Husnaila ta tara kiraren a gabanta ta hada wuta sannan la kishingida a gaban wutar tana jin dumi. Tsawon kusan rabin sa'a ba ta |l motsin komai ba a cikin kogon, don haka sai ta saki jikinta ta daina jin tsoro. Abinka da gajiyayya, nan da nan sai Huśnaila ta kama gyan-gyadi. Ai kuwa sai bárCi ya saccta bata sani ba. Faruwar hakan ke da wuya sai ga wadansu irin jibga-jibgan Birirrika suna fitowa daga cikin kogon dutsen, Hakika girman wadannan Birirrika ya wuce misali, domin komai jarumtakar mutum idan ya yi arba da su dole ne ya razana saboda kwarjininsu da muninsu. Adadin Birimikan ya kai dari. Takun sawunsu ma kadai ya isa abin tsoro domin yana haddasa karamar girgizar kasa. Amma hakan duk bai sa Husnaila ta farka daga barcin da take yi ba mai nauyin gaske. Lokaci guda Birirrikan suka kewaye Husnaila su duka, suka zuba ma ta idanu kawai. Har sun yunkura za su dasa wawa akanta sai suka jiyo gurnanin Shugabansu. Gaba dayansu sai suka ja da baya suka dare hanya ta samu a tsakiyarsu. Gurnanin da Shugaban asu ya yi ne ya sa Husnaila ta farka daga barcinta a firgice! Koda ta bude idanunta tayi arba da wadannan Biririka zagaye da ita sai ta kwalla uban ihu cikin tsananin razana. A dai-dai wannan lokaci ne Shugaban Birirrikan ya karaso gaban Husnaila. Shugaban Birirrikan ya karewa Husnaila kallo sama da kasa, kawai sai ya sa hannu ya dauko Husnaila da yatsunsa biyu kacal tana ihu da kururuwa ya juya da baya ya nausa cikin kogon, sauran Birimikan suka take masa baya suna ruri da gurnani wanda ya cika dajin gaba daya. Husnaila tayi iya kokarinta akan ta zille daga Cikin yan yatsun Birin nan amrna ta kasa duk da cewa tana ta caka masa mashin da ke hannunta, amma tamkar dutse ta kę cakawa, domin ko kwarzanewa jikin nasa bai yi ba. A wannan lokaci ne hankalin Husnaila ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe, domin ta san cewa rayuwarta ta zo karshe donin babu ta yadda za ta iya kubuta. Bisa mamaki sai taji nadam a ta zo ma ta bisa abinda ta yiwa Muraisu ta hallakashi. Tabbas ta san Inda yana raye, kuma suna tare zai iya tabuka wani abu a yanzu. Duk da cewa Husnaila ta tsani Muraisu kamar yadda ta tsani mutuwarta, amma a wannan karon sai taji tana kaunar ganınsa. A karon farko a rayuwarta sai taji hawaye ya zubo ma ta, kuma tunanin dan uwanta Sarki Ishmar ya fado ma ta a rai. Nan take ta cika da mam akin yadda Sarki Ishmar ya kasa sanin halin da tak e ciki, har ya kasa aiko ma ta da agajin gaggawa a matsayinsa na gagarumin matsafi.... Nima Kuma na cika da mamakin Ganin Masoyiyata yau ta manta dani bata nemeni ba Kuma ta kasa aiko mun da sako hhh Anan zamu dakata sai wani lokaci BUSA A MUTU Littafi Na Biyu (2) Part D. Na Abdulaziz Sani M/Gini AA Misau ke Magana Marubucin yaci gaba da cewa.. AIKO MA TA DA AGAJIN GAGGAWA A MATSAYINSA NA GAGARUMIN MATSAFI. Birimkan suka cì gaba da kutsawa cikin kogon dutsen suna ta tafiya. Sai da suka yì yar doguwar taiya mai tsawo sannan suka iso wanı babban wuri mai cìke da bìshiyoyì da wata korama a tsakiya wacce ruwanta ke gudana ta cikin dutse yana kwarara izuwa cikin wanı kwararo. Bishiyoyin da ke wajen duka sun yì 'ya'yaye nunannu da danyu, kai da gani ka san cewa wadannan Biimka suna jin dadin rayuwarsu a Wannan wu. Da isowar biimkan wannan wun sai aka daure Husnaila a jikin wata bishiya da ke tsakiya da wala inyar danyar jijiyar bishiya aka daureta tamau, tayi ta wutsil-wutsil domin ta kwance kanta ta kasa. Nan fa tayi amfani da dukkan karfin sihirinta domin ta kwance kanta amma sai ta kasa. A sannan ne ta gane cewar babu wanì sihinin tsafi da yake tasiri akan dabbobin da ke cikin wannan dajì na Kirzula, dajin Bala'i da masifa! Nan fa birirrik an suka kama dukan kirjinsu da hannayensu tamkar ganguna- suke dogawa. Karar bugun kirjin nasu ya cika dajin gaba daya A wannan lokacı ne HuSnaila ta gane cewa biririkan kirari suke yiwa shugaban nasu suna zugashi akan ya alka ma ta. Koda fahimtar hakan sai Husnaila ta ci gaba da kwarara uban ihu. Shi kuwa birnin sai ya durfafo kanta Ya yin da ya rage bai fi saura taku uku ba kacal a tsakaninsu sai kawai aka jiyo wani abu ya taho da gudu ta baya. Lokaci guda gaba dayan birirrikan suka juyo har shi kansa shugabansu. Kafin daya daga cikinsu ya yi wani yun kuri sai kawai suka ga mutum ya dako tsalle ya dira a tsakiyarsu ya hausu da SARA DA SUKA. Ba wani bane wannan mutum face yarima Muraisu. Al'amarin da ya matukar daurewa Husnaila kai ke nan, domin a tunaninta tuni Muraisu ya dade da konewa ya zama toka. Abinda ya kara đaure ma ta kai shi ne, ko alamar kuna babu ajikinsa. Muraisu ya Wanzu yana mai sara da sukan wadann an biririka su kuma suna kai masa mangari, yakushi, calksa da cizo yana gocewa. Duk sa'adda suka kai masa yakushi da faratan hannayensu ya, goce ko dutse suka, karta sai ka ga ya dare gida biyu saboda tsananin kailin faratan nasu. Shi kuwa Muraisu duk sa'adda ya sari jikin Birirrikan ko ya sokesu sai ya ji kamar karle yake sara. Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa ke nan, domin ya san cewa idan áka dade a cikin wannan hali zai iya gajiya. Da zarar kuwa ya gaji birirrikan za su sami lagonsa su hallakashi. Nan fa ya fara tunanin dabarar da ya kamala ya yi ya ccci rayuwarsa da ta Husnaila wacce ke daure a jikin bishiya. Haka dai aka ci gaba da wannan gumurzu har tsawon rabin sa'a ba tare da wata dabara ta fadowa Muraisu ba. A sannan ne kuma ya fara gajiya. Ai kuwa sai shugaban biririkan ya shammaci Muraisu ya gabza ma sa naushi a fuska. Saboda karfin naushin sai da Muraisu ya yi katantan wa sau uku a tsaye sannan ya baje kasa jini na yoyo ta hancinsa da bakinsa a cikin matsanaicin hali mai kama da suma da gushewar hankali. Koda Husnaila ta ga halin da Muraisu ya shiga sai ta saduda ta tabbatar da cewa itama ta ta ta kare don haka saí ta sake kwalla ihu ta fashe da matsanaicin kuka. Shí kuwa wannan shugaban birrrikan sai ya zo : kan Muraisu ya tsaya ya raba kafafu akansa ya. surnkuyo kasa da nufin ya cire kansa ya cinye. Ba zato ba tsammaní aka ga Muraisu ya dunkule hannunsa ya gabzawa shugaban biririkan naushi a ido. Take ruwan idon ya fashe jini ya rinka kwararowa daga ciki tamkar an bude IDANIYAR RUWA. Kawai sai birin ya sulale kasa ya fadi rikica ya zama gawa. AI kuwa sai sauran birirrikan suka yi caa! akansa za su yagalgalashi. yaki. Nan fa aka ruguntsume da sabon azababben Cikin zafin nama Muraisu ya ci gaba da naushin birimikan a idanu suka rinka ihu suna zubewa kasa matattu, amma saboda na ci basu fasa kai masa muggan hare-hare ba. A haka ne suma birimikan suka rinka yi masa raunika a sassan jikinsa. Kafin Muraisu ya sami nasarar kashe gaba dayan birirrikan sai da ya sami raunika a jikinsa sama da guda ashirin, ya zamana cewa gaba dayan jikinsa yai fata-fata da jini. Ai kuwa yana gama kashe birirrikan sai shima ya kife kasa a sumamme. Muraisu bai farfado ba sai bayan rabin sa'a, sannan ya mıke zaune da kyar yana numfashi sama-sama, kamar ransa zai fta. Koda ya dago kai Ya hada ido da llusnaila sai ya ga tayi masa guntun murmushi. Kawai sai ya kau da kai ga barin kallonta ya shiga yiwa kansa magani. Bayan ya gana gyara raunikan jikinsa gaba daya sai ya mike tsaye da kyar ya je yasa bakinsa a ciin wannan koram a ya sha ruwa ya koshi. Kawai sai yaj. Husnaila ta ce, "Ya kai wannan jarumi ka taimakeni ka kwanceni nima na zo na sha ruwan nan, domin ishirwa ta addabeni". Koda jin haka sai Muraisu ya dago kai ya dubeta ya Ce, "Ta ya ya kike tsammanin cewa zan sake aminta da ke? Shin kin manta ne cewa sau biyu kika yi yunkurin hallakani, kuma yanzu sau biyu ke nan ina ceton rayuwarki. Na sani cewa kin tsaneni fiye da komai a duniya, don haka babu yadda za a yi na yarda da ke. Ba zan kwancc ki ba daga jikin wannan bishiya har izuwa kwana biyu, amma duk abinda kike bukata zan yi miki". Koda jin war nan batu sai hankalin Husnaila ya dugunzuma ain un, ta ce. "To yanzu kuma idan bukatar bawali ko bayan gida ta kanani fa?" Murajşu yai numushi ya ce, "Ai sai dai kiyi komai anan inda kike'. Kamar yadda Muraisu ya fada haka al'amarin ya kasance, sai da suka kwana biyu a cikin wannan kogon dutse suna rayuwa. Tsawon wadannan kwanaki Husnaila na daure, a jikin bishiyar take kwana, a jikinta take bawali, Muraisu bai yarda ya kwanceta ba. A ranar kwana na biyu ne da yammaci daf da magariba Muraisu ya kwance Husnaila daga cikin wannan itaciya. Saboda tsananin gajiyar da tayi na tsayuwa a tsaye, sai ta fadi kasa ta kasa mikewa zaune. A wannan lokaci ne tausayin Husnaila ya kama Muraisu ya dubeta ya ce, "Ki gafarceni ya ke wannan ma'abociyar kyawu, ki yi sani cewa na ki kwanceki ne daga jikin wannan bishiya saboda tsoron kada ki sake yi mini abinda kika yì mini a baya", Bisa mamaki sai Muraisu ya ga Husnaila ta juyo ta dubeshi tayi murmushi sannan ta ce, "Hakika abinda ka yi min shi ne dai-dai, domin na tabbatar a wancan lokacin ina jin kiyayyarka a cikin zuciyata fiye da komai a duniya, amma a yanzu ka kwantar da hankalinka ka saki jikinka domin na fahimci, cewa bani da wani masoyi a duniya sama da kai. Hatta dan uwana da ya kasance jinina bana jin zai nuna mini irin kaunar da ka nuna mini a cikin wannan daji". Koda jin haką sai Muraisu ya yi murmushi ya ce. "Na san da haka, kuma lallai ni yanzu na tabbatar da cewa ba za ki cutar da ni ba", Koda jin haka sai mamaki ya kama Husnaila ta ce, "Mene ne tabbacinka cewar ba zan ta6a cutar da kai ba?" Muraisu ya ce, "Saboda tun kafin na fito nemanki na san cewar idan har muka kwana uku a cikin wannan daji na Kirzufa sai kin daina tsanata. Haka bokan mahai fina ya tabbatar mini". Da jin haka sai Husnaila ta gyada kai tayi dan tunani sannan ta ce,"Tabbas biri ya yì kama da mutum. Hakika yanzu na gane cewa dan uwana Sarki Ishmar ya tsafanceni ne da irin tsafin da zai sa na tsaneka. Ina fatan yanzu za ka yi mini gafara bisa abubuwan da nayi maka a baya". Koda jn haka sai Muraisu ya yì murmushì ya ce,"Ai duk abinda kika yi mini a baya na manta da su, domin inda abin na raina ba zan biyoki nan cikin kogon birimika ba na ceci rayuwarki." Haka dai Muraisu da Husnaila suka yi ta hira har dareya fara babu alamar jin barci a cikinsu. Da lokacin cin abincinsu ya yi sai Husnaila ta ki cin abincin da hannunta ta ce sai dai Muraisu ya ciyar da ita da hannunsa. Al'amarin da ya matukır baiwa Muraisu mamakí ke nan. Ba tare da gardamar komai ba kuwa Muraisu ya fara ba ta abíncin da hannunsa. Koda fara ba ta abincin sai ya ga ta kura masa idanu tana murmushí tana yi m asa wani irin kallo fnai nuna tsantsar kauna a zuci.. Haka daí Muraisu ya ci gaba da ciyar da Husnaila har saí da ta koshi sarnnan shima yasa hannu don ya ciyar da kansa. Sai tayi caraf! ta rike hannunsa ta fara cíyar da shí da hannunta. Saí da ta tabbatar ya koshí sannan ta bashi ruwa ya sha, ítama ta sha. Maimakon ta tashi daga kusa da shi ta koma can gefe daya ta kwanta, saí ta kwanta daf da shi ta dora kanta a cínyarsa tana kallon fuskarsa tana murmushi irin wanda ke kuantar da hankalin masoyi. Shima sai ya kura ma ta idanu, tsawon 'yan dakiku dayansu bai ce uffan ba. Daga can sai Husnaila ta dubi Muraisu ta ce, "Yanzu me ka tsara mana a rayuwa?" Koda jin wannan' tambaya sai Muraisu ya yi ajíyar zuciya sarnnan ya ce, 'So nake gobe da sassafe mu bar wannan daji mu lafi izuwa birninmu Domin a daura nana aure mu fara sabuwar rayuwa la jin dadi da kwanciyar hankali", Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa llusnaila, al'amarin da ya matukar baiwa Muraisu mamaki ke nan, ya dubeta cikin tsananin damuwa ya ce, "Ina dalilin zubar da wannan hawayc naki?" Husnaila tayi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Ina JI a jikina Cewa abu nc mawuyaci mu yi rayuwa mai tsawo ni da kai. Ka tsaya ka yì tunani, a halin yanzu mutanen birninku suna cikin tashin hankali na shirye-shiryen yaki da za a yi. Shin za su tsaida hankalinsu ne akan shagalin bikinmu ko kuwa akan shirin yaki? Shawarar da zan bamu ita ce, kawai mu daurawa kanmu aure anan cikin dajin Kirzufa tun kalin mu koma can birninku a fara yaki. Ka ga ke nan da mun je sai mu fuskanci yakin a ci gaba da tanadin yadda zaa fuskanci abokan gaba". Lokacin da Muraisu yaji wannan shawara sai ya yi shiru yana tunanı har izuwa tsawon yan dakiku, daga can sai ya yi ajiyar zuciya ya dubi Husnaila ya ce, "Na yarda da shawararki, lallai idan -gari ya waye za mu daurawa kanmu aure". Koda jin wannan batu sai IHusnaila ta kamu da tsananin farin ciki ta mike Zaune ta rungume Muraisu ta kwanta akan kirjinsa, suka ci gaba da hira a haka cikin murna da tsintar kansu a Cikin sabuwar rayuwa wacce basu taba jin ba duk su biyu.A haka barci ya sacesu basu sani ba. Kashe garí kuwa da sassafe Muraisu da lusnaila suka tashí daga barci, Da yake IHusnaila ta fara tashi sai ta kwabe kayanta ta shíga cikin wannan korama tayí wanka. Bayan la fito ne daga wankan Muraisu ya farka. Ba tare da įin kunyar komai ba kuwa IIusnaila ta zauna ta goge danshin jikinta da kyallen mayafi. Koda ganin haka sai shíma Muraisu ya kwabe kayan jikinsa ya fada cikin koramar ya yi wankansa sannan ya fito ya goge danshin ruwan, amma bisa mamaki sai Husnaila ta ga Muraisu yana sunkuyar da kansa kasa cikin alamun kunya, ya kasa dago kaí ya kalleta, Al'amarin da ya malukar bata manaki kc nan, ta dubeshi ta ce, "Ya kai masoyin raina, ina dalilin da ya sa ka ke dukar da kanka kasa baka son ka kalli kyakkyawar surar jikina?", Muraisu yai shíru kamar ba zai ce komai ba, daga can sai ya ce, "Ya ke abar kaunata kiyi sani cewa kunya na dagą cikin alamun karamci da sanin yakamata. Ilusnaila za ta fadi abu ne mai saukin gaske wanda ba zal yi wuyar nemowa ba. Koda llusnaila ta ga alamun camuwa a tare da Muraisu sai ta sake bushewa da dariya sannan la ce, "Kada ka damu ya kai masoyina, ka sani cewa abin kunya ne a ce sadakin aurena abu ne mai sauki a matsayina na kyakkyawar macen da babu kamarta a wannan nahiya lamu, kuma wacce a ta auri sadaukin da babu kamarsa yana da kyau mu barwa dan da zamu haifa abin alfahari, abin tarıhi". Koda IIusnaila tazo nan bayaninta, sai Muraisu yaji dukkan tsoro ya kau daga zuCiyarsa, wani irin gagarumin karfi ya shigeshi, kawai sai ya mike tsaye ya dubi Husnaila ya ce, "Tabbas yanzu zan je na kawo miki wannan sadaki". Husnaila tayi murmushi ta ce, "Ina yi maka fatan nasara da dawowa lafiya". Gama fadin hakan ke da wuy a sai Muraisu ya juya da baya ya fice daga cikin kogon dutsen ya nausa cikin dajin Kirzufa yana farautar tsohon Zaki. Sai da Muraisu ya shafe sa'a biyar yana farautar neman tsohon Zaki amma bai ga koda macen Zaki ba. Al'amarin da ya girgiza hankalinsa ke nan. Abinda ya matukar bashi mamaki shi ne, duk dabbar da ta hangoshi komai girmanta sai ya Ga ta ratse ta bashi hanya, ko kuma ta koma da baya. Wata ma ta tsre da gudu kamar dodo ta gani. Abinda bai sani ba shí ne, duk mutumin da ya kwana uku a cikin dajin Kirzufa, duk halittar da ke cikin dajin tsoronsa take ji. Haka dai Muraisu ya cí gaba da yawo a cikin dajin Kirzufa har ya gaji sosai ainun guiwarsa tayi sanyi kuma hankalinsa ya kara dugaunzuma domin Idan ya koma wajen Husnaila bai san abinda zai ga ya ma ta ba. Cikin sanyin jiki ya juyo da baya domin ya koma can cikín kogo inda ya baro Husnaila. Ba zato ba tsammani sai kawai Muraisu ya ga wanı Jibgegen Zaki a gabansa bisa wani katon dutse. Koda Zakin yai arba da Muraisu sai ya tsaya cak! Suka kurawa juna idanu suna nazari. Shi dai Muraisu murna ce ta kamashi saboda ganin cewar Zakin tsoho ne tukuf, irin wanda yake ncma. Shi kuwa Zakin ya tsoro ne ya kamashi domin yana kallon Muraisu ya ga shima Zakin ne irinsa kuma ya ninkashi biyu a girma. Ashe sirrin dajin shi ne, idan har bil'adama ya kwana uku -a cikinsa to duk dabbar da ke cikin dajin da ta ganshi sai ta ga ya zama irinta kuma ya fita girma da kwarjini. Ya yin da tsohon Zakin ya ga Maraisu ya durfafoshi ya hawo kan wannan dutse da yake bisa sai Zakin ya juya da baya ya soma tafiya da sauri- sauri. Koda ganin haka sai shima Muraisu ya kara sauri. Koda Zakin ya waigo ya ga Muraisu na sauri sai shi kuma ya fita da gudu. Wohoho! Nan fa aka kasa tsere tsakanin Zakin da Muraisu. Duk sa'adda Zakin ya waigo sai ya ga saura kiris Muraisu ya cinimasa. Koda suka iso karshen dutsen sai Zakin ya yi turjiya ya tsaya cak! Saboda gabansa wani rami ne mai tsananin zurlin tsiya. Duk abinda ya fado izuwa kasa sai dai ya zama gawa. Masu iya magana sun ce, "Abinda ya koro Bere daga Rami ya fada wuta, to labbas abin yafi wutar Zafi! Lokacin da Zakin ya leka ksan wannan rami ya ga zurfinsa sai ya juyo da baya ya fuskanci Muraisu ayi duk abinda za a yì. Bayan sun yiwa juna kallo na isawon 'yan dakiku sai kowannensu ya daka tsalle suka rungumi juna a sama suka rikito kasa saka kaima kokawa da birgimą. Muraisu ya shiga kokarin zaro wata wuka a kugunsa domin ya lumawa Zakin, shi kuma Zakin sai ya dinga turmusheshi yana kai masa yakushi da cizo. Nan fa kowanncnsu ya kasa samun nasarar komai. Sai da suka shafe lokaci mnai tsawo suna tumurmusa juna akan dutsen, duk sa'adda Zakin ya karci jikin Muraisu ko ya cijeshi sai yaji kamar dutse ya gatsa, ko kwarzancwa baya yi. Abinda ya dugunzuma hankalin Muraisu shi ne, ya fara jin alamun gajiya amma shi Zakin ko kadan bashi da alamun gajiya. Suna cikin wannan gumurzu ne Zakin ya danne Muraisu kuma ya cafi wuyan Muraisu đa hakoransa yana kokarin gatsawa. Kaifin hakoran Zakin ya kasa huda wuyan Muraisun, amma kuma sai Muraisu yaji ya shaku ainun. Nan da nan idanunsa suka kada suka yi jawur, kuma suka yi luhu-luhu kamar za su fado kasa. Nan fa ya fara kakarin mutuwa, kafin ya ankara ya suma. Koda Zakin yaji gaba daya jikin Muraisu ya sandare baya motsi sai ya yi wurgi da shi domin a zatonsa ya mutu, don haka sai Zakin ya juya da baya domin ya sauka daga kan dutsen. A dai-dai wannan lokaci ne Muraisu ya farfado daga dogon suman da ya yi. Koda ya bude idanunsa ya hango wannan Zaki...... Topah Wannan Zaki Ya Firgitani ta yadda bazan iya cigabaa da typing yanzu ba Sbd haka sai Kuma wani lokaci... BUSA A MUTU Littafi Na Biyu (2) Part E. Takun Karshe Na Abdulaziz Sani M Gini AA Misau ke magana Marubucin yaci gaba da cewa... A DAI-DAI WANNAN LOKACI NE MURAISU YA FARFADO DAGA DOGON SUMAN DA YA YI. KODA YA BUDE IDANUNSA YA HANGO WANNAN ZAKI SAUKA DAGA KAN DUTSEN, SAI YA MIKE ZUMBUR YA RUGA DA GUDUN TSIYA IZUWA KAN ZAKIN. Kafin Zakin ya waigo tuni ya daka tsalle ya dira a gadon bayansa, kawai sai ya shake wuyan Zakin da hannayensa biyu, suka kama mirgin- mirgin akan dutsen. Zakin ya yi iya kokarinsa akan ya kufce daga hannun Muraisu amma ya kasa. Suna cikin mirgi-mirgin akan dutsen nan suka rikito kasa izuwa cikin wannan rami mai tsananin zurfin tslya, Da Zakin da shi Muraisun sai suka hau ihu da kururuwa bisa ganin hallaka muraran. Tun a saman duk su biyun suka sume saboda karfin iskar da ke kadawa wacce ta hanasu yin numfashi. Ba su iso kasan ramin ba sai bayan cikar rabin sa'a. In da Muraisu ya yi sa'a shi ne akan Zakin ya fado. Ta ke gangar jikin zakin ta dagwar gwaje, shi kuwa Muraisu sai ka farsa ta hagu ta karye. Kansa ya bugu da jikin kan Zakin ya tsage jini yai tsartuwa ya baje a kasa sumamme Al'amarin Husnaila kuwa ya yin da taga Muraisu ya shafe sa'oi shida bai dawoba cikin kogon da ya barta sai hankalinta ya dugun zuma ainun ta kasa zaune ko tsaye don haka sai ta fita da gudu daga cikin kogon dutsen ta bazama a cikin dajin na Kirzufa tana gudu da waige-waige tana kwalawa Muraisu kira. Sai da ta shafe sa'a biyu cur! tana yawo a dajin ba ta ga Muraisu ba ba ta ji duriyarsa ba ya z:amana cewa ta gaji ainun da kyar take iya tafiya tana hada kafafu tana tangadi tamkar wadda ta sha giya ta bugu. A haka ta hau kan wannan dutsen wanda Muraisu da Zakin suka yi gumurzu akai. Tana isa kan dutsen ta tsugunna kasa tana haki. Kwatsam! Sai ta yi arba da guntun igar Muraisu. Cikin rarrafe taje ta dauki guntun rigar ta fashe da kuka ta aiyana a ranta cewa lallai Muraisu ya fado kasan wa inan ami ya hallaka. A haka dai ta mike tsaye ta karasa karshen dutsen ta leka kasa sai ta ga ba ta iya gano abinda ke can kasan saboda nisa. A guje ta juyo da baya ta sauko kasan dutsen ta ruga inda wannan rami yake. Husnaila tayi ta gangarawa kasa da gudu har ta iso cikin wannan rami inda tayi arba da gawar Zaki ta ga Muraisu kwance akan Zakin jini na zuba daga kansa ko motsi baya yi. Husnaila ta cuma uban ihu ta ruga izuwa kan Muraisu ta ru:igumeshi ta fashe da sabon matsanaicin kuki domnin à zatonta Muraisu ya mutu. Tana cikin wannan hali ne taji Muraisu ya yi dogon ajiyar num fashi. Cikin tsanar in farin ciki ta ciro salkar ruwa ta sa masa a baki yi kama kwankwada. Husnaila dai ba ta san sa'adda ta bushe da dariyar farin ciki ba. Ai kuwa Muraisu na gama shan ruwan suka sake rungume juna. Husnaila tayi sauri ta janye jikinta daga cikin na Muraisu ta kama gefen rigarta ta yagi kyalle ta daure kansa don tsaida jini. Kawai sai ta dubi Muraisu ta "Idan za ka iya ka cire kan wannan Zaki ka bani yanzu domin an karba ka zamo cikakken mijina". Ba lare da gardamar komai ba Muraisu na daga zaune ya ciro wukar da ke daure a kugunsa ya yanke kan Zakin ya mikawa Husnaila. Tana karba sai ta soke kan Zakin a jikin mashinta sannan ta dubi Muraisu ta ce, "Tashi mu tafi can kogonmu". Maimakon Muraisu ya mike tsaye ko ya ce wani abu sai ya nunawa Husnaila kafarsa. Take ta ga cewar kafar tasa ta hagu ta fara kumbura. don haka sai ta gane cewa ya samu karaya. Husnaila ta mike tsaye ta samo itatuwa sannan ta zo ta gyarawa Muraisu karayarsa ta daure Rafar da itatuwa da tsummokara. Wannan gawar Zaki kuwa sai tà zamo abincinsu, domin wuta ta hada ta gasa naman Zakin wanda tuni ma ya dagargaje. A cikin wannan ramí suka kwana har suka more anarcinsu duk da cewa Muraisu na đauke da karaya a kafarsa. Sai da suka shafe kwana ashírin da daya a cikin wannan rami Husnaila na jinyar Muraisu kuma kullum ita ce take zuwa ta nemo musu abinci da ruwan sha sannan Muraisu ya warke sumul suka yi shiri suka fita daga cikin dajin Kirzufa. Bayan sun yí nisa da baro cikin dajin Kirzufa da kamar tazarar tafiyar zango biyu sai kawaí suka yi kicibus da mutane uku a gabansu. Ba wasu bane wadannan mutane face Barde Kurzal, kuyanga Sabirat da boka Rufyan. Koda suka yi arba da juna sai dukkanínsu suka cika da tsananin mamaki, Sabirat ta ruga da gudu za ta rungume Muraisu sai Husnaila tayi sauri ta sha gabanta ta tsaí da ita ta ce, "Babu wata mace da za ta sake ta6a jikin mijina". Koda jin haka sai Sabirat ta zube kasa ta ce, "Tuba nake ya gimbiya, ki gafarceni". Nan take Muraisu ya baiwa su boka Rufyan labarin duk abinda ya faru tsakanińisa da gimbiya Husnaila a cikin dajin Kirzufa a tsawon kwarakin da suka shude da rabuwarsu da su, sannan ya tambayi boka Rufyan dalilin da ya sa suka ci gaba da zaman jiransu har izuwa wannan lokaci alhalin ka'idar lokacin da aka diba ta wuce? Koda jin haka sai boka Rulyan yai murmushi ya ce, "Ai na yi bincike ne na sm ai nasarar ganowa kuna raye baku mutu ba," Koda jin haka sai boka Ruíyan yaí murmushi ya ce, Yanzu bani labarin gida. A wanne hali mahai fina da jama'arsa ke ciki?" Koda jin wannan tambaya sąi boka Rufyan ya hade fuska ya ce, "Bani da amsar wannan tambaya a yanzu domin ban san komai ba sai dai ka yi hakuri har mu isa can birnin Liruf inda za a yi gagarumin bikin aurenka da gimt iya Husnaila". Muraisu ya ce. "Bani da bukatar wani bikin aure, ni dai kawai burina shi ne na isa gida lafiya na iske mahaifina a raye kuma Ina sami damar yin wannan gagarumin yaki da za ay da abokan gaba". Ba tare da 6ata lokaci ba su Muraisu suka kama hanya suka durfafi birnin Lairus. Bayan sun shafe tafiyar kwana da kwanaki ba tare da fuskantar wata matsala ba gami da taimakon gajarce nisan tafiyar da karfin s hiri sai su yarima Muraisu suka iso birnin Lairus da farkon dare. Tụn daga nesa suka jiyo sautin busa kaho da tambura. AA Misau ke magana Kawai sai yarima Muraisu ya fashe da matsanaicin kuka domin ba a busa Raho da daddare a cikin birninsu face an yi babbar mutuwa. Tabbas yaji ajikinsa cewa Sarki Samral ne ya mutu. Koda ganin Muraisu yana kuka sai su ma su boka Rufyan suka kama kukan. Itama gimbıya Husnaila sai ta rungume Muraisu a lokacin da ta kamu da tausayin sa ta fashe da kuka. Lokacin da su yarima Muraisu suką iso kofar birnin Lairus sai suka iske kofar garin a kulle ruf sai da suka kwan kwasa aka leko kuma aka haska fuskokinsu aka shaida su sannan aka bude musu kofa suka shiga. Suna shiga cikin garin suka iske garin wayam domin gaba dayan jama'ar sun tafi fada. Babu kowa ma a kofar garin daga cikin face Dakarun yaki nasu yawa don tabbatar da tsaro. Su yarima Muraisu suka iso fada inda suka iske ana bikin binne gawar Sarki. Koda jana'a suka hango yarima Muraisu tare da amaryarsa sai aka rugo gareshi gaba daya cikin tsananin farin ciki bisa murnar ganin dawowarsa. A wannan lokaci Muraisu ya daina kuka amma hawaye na sartu akan kumatunsa. Nan dai aka ci gaba da bikin binne Sarki. Bayan an gama binne gawar Sarki Samral ne kowa ya watse sai yarima Muraisu da gimbiya Husnaila suka rungume kabarin Sarki Samral suka ci gaba da zubar da hawaye, basu bar wajen ba saí da dare ya raba sosai sannan suka mike suka tafi izuwa cikin gidan sarautar. Kashe gari da sassafe fada ta sake cika ta batse aka dora Muraisu akan karagar mulki. Nan lake Muraisu ya mike tsaye ya yi dogon jawabi ga jama'ar birnin Lairuf kuma ya tabbatar musu da cewa zai tafiyar da harkokin mulki kamar yadda mahaifinsa ya yi kuma zai ci gaba da shirye-shirye don tunkarar gagarumin yakin da ke gabansu. Haka kuwa al'amarin ya kasance Sarki Muraisu ya sa aka ci gaba da tanadin makaman yaki kuma kullurn ana baiwa Dakaru sabbin dabaru da horo na yakí har tsawon wata bakwai. A wannan lokaci ne gimbiya Husnaila ta sami juna biyu ta shiga laulayi. A ranar da juna biyun ya cika wata takwas ne babban bala'i ya zo birnin Lairuf domin kawai wayar gari aka yi aka ji duwatsun wuta da kibiyoyin wuta na fadowa cikin garin. Nan da nan garin ya hautsine mutane suka firgice aka kama iface-iface da guje-guje. Nan da nan labari ya riski Sarki Muráisu cewar abokan gaba ne suka iso AA Misau ke magana Nan da nan Sarki Muraisu ya yi damara ya kwashi dukkan kayan yakinsa. A dai-dai wannan lokaci ne ciwon nakuda ya kama gimbiya Husnaila al'amarin da ya matukar dugunzuma hankalin Sarki Muraisu ke nan ya rasa abinda zai yi. Kawai sai Sarki Muraisu ya tura aka kirawo wadansu zaratan samari sadaukan gaske su dar bakwai ya hadasu da malarsa gimbiya Husnaila tare da wadansu mata tsofaffi da yara wadanda gaba dayansu adadinsu ya kai dubu uku. Sarki ya dubi wadannan zaratan samari ya ce, "Ga matata da wadannan mata da yara na baku amanarsu. Duk yadda za ayi komai RINTSI DA TSANANI ku fitar da su daga cikin garin nan ta bayan gari. Kada ku ajiye matata a ko ina sai a bakin dajin Kirzufa, na yi imanin cewa matata za ta iya shiga cikin dajin Kirzufa tayi rayuwa a cikinsa koda ita kadai ce. Sauran wadannan mata da yara kuwa ku yi gudun hijira da su izuwa wata kasar dabam. Mu kam zamu je mu fuskanci abokan gaba yanzu. Ko za a karar damu gaba dayanmu ba zamu ja da baya ba, dole ne mu tsaya mu kare mutuncin kasarmu da jama'armu". Koda gama wannan jawabi sai Sarki Muraisu ya sallami wadannan zakwakuran zaratan samari da tawagarsu suka tafi da su gimbiya Husnaila ba tare da Husnaila ta sami damar yin bankwana ba da mijinta Muraisu domin a wannan lokaci ba ta cikin haiyaçinta sakamakon ciwon nakudar da take ciki. Sarki Muraisu da sauran dakarunsa suka yi hawa suka nufi kofar gari har a sannan ba a daina harbo kibiyoyin wuta ba izuwa cikin birnin ba. Koda Sarki Muraisu ya ga yadda gidajen jama'a suka kama da wuta suka AA misau ke magana babbake kuma ya ga gawarwakin jama'ar birjik a ko ina a kasa sai takaici ya kamashi hawaye ya zubo masa. A sannan ne ya tabbatar da cewa maganar boka Rufyan ta tabbata gaskiya. Nan take Muraisu da dakarunsa suka daga garkuwoyin su sama suka rinka kare kibiyoyin da ake harbo musu. A haka aka bude kofar birnin suka zaburi dawakansu suka tasamma abokan gaba. Kaico! Idan mutum ya ga yawan abokan gaba akan yawan su sarki Muraisu dole ne ya tausaya musu domin sun ninkasu sau uku. Koda su Sarki Muraisu suka badu da su Sarki Ishmar sai akakacame da azababben yaki. Ana cikin gumnurzun ne Sarki Muraisu ya ga dan uwansa Huraisu da sarkí Ishmar sun taso masa su biyu a lokaci guda. Ai kuwa sai ya tare su da dakakkíyar zuciyarsa suka ruguntsume da azababben yaki ya wanzu yana mai kai musu SARA DA SUKA cikin tsananin zafin nama suma haka. Shí kansa Sarki Muraisu ya san cewa sarkin yawa ya fi sarkin karfi, amma sai ya jajirce iya karfinsa ya ci gaba da wannan yakin ba tare da tsoron komai ba. Duk da cewa Ishmar da Huraisu sun hada karfi don su hallaka Muraisu sai ya zame musu alakakai har ya sari kowannensu sau biyu. Koda suka ga ya yi musu wannan rauni sai suka kara zage dantse suka afko masa da dukkan karfinsu. Da yake karfin sihirinsu da na sa ya zo đaya sai kowannensu sihirinsa na tsafi ya lalace ya daina aiki don haka sai suka ci gaba da yaki da tsagwaron karfin dantse da kwarewa. Idan mutum ya ga yadda ake ragargazar dakarun birmin Lairuf suna zubewa kasa matattu dole ne lausayi ya kamashi har ya zubar da hawaye. Lokacin da Huraisu da Ishmar suka kara zage dantse alkan Muraisu sai suka samo lagonsa suka yi ta lafta masa sara, suka yi kaca-kaca da sassan Jikinsa Jiri ya kwasheshi ya fado daga dokinsa ya baje a kasa malacce. A wannan lokaci ne aka busa kahon samun nasarar yaki. Yarima Huraisu da Sarki Ishmar suka cika da tsananin farin ciki. Nan take aka 6alle kofar birnin Lairuf da karfin tsiya aka kamo mutanen birnin gaba daya aka tarasu a fada. A sannan ne aka gano cewa wasu daga cikin jama'ar garin sun sulale ta bayan gari sun gudu, domin an ga sawayen dawakansu. Nan take yarima Huraisu ya jagoranci wadansu dakarun yaki su dubu arba'in aka bi sawun su gimbiya Husnaila. Wannan shi ne asalin gudun hijirar da aka yi daga birnin Lairuf. Su yarima Huraisu sun riski wannan runduna ta masu gudun Hijira inda aka kacame da sabon yaki. Da kyar da sidin goshi barde Kurzal ya sami hanya ya gudu da gimbiya Husnaila akan dokinsa a lokacip da take cikin mawuyacin hali na nakuda har jini ya fara zuba a jikinta. Shi kansa barde Kurzal a jikinsa akwai saran takobi sama da guda ashiri. Ko ina a jikinsa jini ne ke zuba amma saboda naci da juriya sai da barde Kurzal ya kai Husnaila bakin dajin Kirzufa sannan ya fado daga kan dokinsa ya mutu, Itama Hsunaila saí ta fado daga kan dokin ta ci gaba da jan ciki har ta saní darmar shiga cikin farkon dajin Kirzufa, A dai-dai wannan lokací ne yarima Suraisu da sarki Ishmar suka karaso bakin dajin suka hango Husnaila a kwance tana nakuda Huraisu ya yunkura zai Sada cikin dajin Kirzula sai sarkí Ishmar yai wuf ya rikeshi ya Ce, "Kana shiga cikín wannan dají shí ke nan sai dai a dauko gawarka," Suna ji suna gani Husnaila ta haihu a gabans ta yanke cibi da hannunta kuma ta gyara jikinta, Nan take bakin ciki ya turnuke Sarki Ishmar ya fashe da kuka ya dubi husnaila ya ce, "Ya ke 'yar uwata hakika kin cuceni. Yanzu kí rasa wanda za ki haihu da shí saí babban dan makiyina," Koda jin haka sai hawaye ya zuhowa husnaila ta daga jaririnta sama ta nuno fuskarsa ga su Ishımar ta ce, "Kwarai kuwa ku je ku mallaki birnin Lairus, amma ku sani cewa komai dadewa wannan yaro sai ya kurbi birninsa, Tabbas an baifi jarumin da zai zamo annoba a dukkan SARAKUNan duniya Wanda zamo MAI kahon BUSA A MUTU" Cikin rudowa da rashin fahimta su Sarki Ishmar da yarima huraisu suka kalli junansu kuna suka kalli husnaila, domin basu gane ko mene ne kahon Busa a mnutu ba, kuma basu gane yadda Wannan jariri zai Zamo annoba ba a dukkan Sarakunan duniya! WACCE IRIN RAYUWA HUSNAILA DA JARIRINTA ZASU YI A CIKIN DAJIN KIRZUFA? IDAN DANTA YA GIRMA YA ZA A YI YA MALLAKI KAHON BUSA A MUTU? YAUSIIE NE DAN HUSNAILA ZAI DAWO BIRNIN LAIRUF YA KARBI MULKI WACCE IRIN ANNODA SARAKUNAN DUINIYA ZASU HADU DA ITA A DALILIN KAHON BUSA A MUTU? Mu hadu a littalin BUSA A MUTU kashi na uku don jin ci gaban wannan kasaitaccen labari Daga mai dcbe nuku kewa a kullum da ko yaushe. ABDUL'AZIZ (Sani Madakin Gini) Nine Dai Naku A ko yaushe AA Misau ke magana Ku danna blue din rubutun nan don kasancewa damu a WhatsApp Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q